💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 143877094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 0913691331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page1 ......." Katanfarin company ne da tsayawa fadar iyakarsa bata  lokacin ne domin mutun bai Isa ya fadi adadin girmansa ba , hatta shi Karan kanshi mamallakin company bazai ce ga iya adadin  girmansa ba adalilin kullum sake siyan wasu bangaren yake yana hadewa da company . "mutane kimanin million biyu da wani abu ne ke aiki a karkashin wannan maikatar daake sarrafa karafuna sanye da kayan aiki ." mamallakin wannan company ya mallaki companies masu yawa sai dai akwai guda daya  wanda ya  kasance  hadin  gwiwa ne tun mahaifinsa  na  raye  suke kula dashi  tare da ya'yan  'yanuwa  ."haka  ma  bayan  babu ran mahaifinsa bai wuftar da al'amarin wannan company ba  ya cigaba da kula dashi  saboda  yana matukar qaunar company a cikin zuciyarsa dan ba qaramin wahala mahaifinsa ya sha akansa ba kafin ya samu daukaka da kar'buwa a duniya gabadaya ba  ." A.G.C"wato  Abdullahi group's  company,company ne daya amsa sunansa, company né da suke  da duk wani nau'in kayan sakawa ajiki  ,kama daga na sarakuna ,manya attajirai ,shuwagabanin na  duniya  , kayanmu na gargajiya har ma dana turawa wato suit da kowani irin design's na tsarkoki ,daga ko wacce kasa ka bukaci kayansu zaka samu cikin sauki  sannan kuma  suna  zana  duk irin  design's   din  kaya da tsarkokin da kake so har ma da zanen kanfanunnuka  ,zanen hotuna  kai  duk  wani  nau'in na  zane suna da kwararun  masu zanawa wuyarta ka zaba desing's zasu yi maka ." daya daga cikin maaikatan gurin ya dago yana kallon shugaban da aka d'aurawa halakin kula da ma'aikatar karafuna wanda isowarsa kenan "barka yallabai "barka dai malam mashkur fatan komai dai yana tafiya kamar yadda aka tsara ? dan sam bana son a samu wata matsala sannan bana son a samu sa'banin akan karafen can ka tabbatar an cigaba da samun irin wadan can, sannan wadan can kayan Ina son akawo su da wuri dan mai gida zai .... "bai kai ga karasa maganarsa ba sautin qarar jet din mai gidansa ya katseshi hakan yasa a hankali manager malik ya d'aga idanunshi dake manne da bakin glass zuwa sararin samaniyya cikin sauri yace "shikenan kaje ka cigaba da kula da duk masu aiki ga mai gida nan ya iso ." ADAM TARIQ ABDULLAH kenan, shugaban kafanunnunka ATA  companies ......  matashin dan kasuwan da yafi kowani dan kasuwan bahaushe kudi a Duniya kallo  daya zaka masa ka fahimci matakin shekarunsa, bazaka kirashi da yaro ba haka zalika bazaka kirashi da dattijo ba shi din matashi ne me kimanin shekaru talatin da bakwai   a duniya fuskar shi babu yabo babu fallasa kasancewar haka yanayinsa yake, kullum haka zaka ganshi fuskar nan tashi a hade tamkar hadari sai dai na wannan lokacin ya zarta na sauran lokutan baya wanda hakan ya faru ne akan abinda ke dawainiyya da rayuwarsa." .Adam Tariq abdullahi wanda ake kira da (mr ATA) a duk fadin duniya   kyakkyawa ne ajin farko mai tsantsar kamala da kamewa tattare da haiba sai dai sam bai da faraa komai cikin zafin rai da zuciya yake aiwatar wa , " rayuwarsa rayuwa ce dake da bambamci data sauran mutane  , shi din mutun ne miskili mara saukin Kai dan idan kayi Kuskuren shiga track dinsa  zaka gane baka da wayo  dan ya iya duk wani nau'i na tozarci da rashin mutunci tare da disga mutun   sabanin  mahaifinsa da mahaifiyarsa da sauran yanuwnasa da suka kasance masu tsanani saukin kai  tausayin mutane tare da tallafawa bayi mabukata ,fari ne sol dan babu digo tabo ko daya ajikinsa hatta bakin kwayar idanunshi  gauraye yake da fari  ,dogo ne sosai mai matsakaicin jiki , da kyakkyawar fuska da idanuwa , fatar jikinsa na ya'yan masu kudi sai sheiki yake daga samansa har kasansa babu makusa sannan babu alamun babu a tattare dashi yana da matakin karatu na Phd  akan kasuwanci kuma har lokacin yana kan karatu bai ajiye ba ,shine ya tattara gabadaya kyawun mahaifiyarsa hajiya zulaiheart da mahaifinsa marigayi barrister Kuma shararen dan kasuwa Alhaji Tariq Abdullah ." "duk wani ma'aikacin dake aiki agurin tsayawa yayi cak ya kasa cigaba da aikinsa kamar yadda aka umarcesa saboda kwadayin ganin wannan kyakkyawar fuska har sanda jirginsa mai saukar ungulu ya sauka idanunsu na kanshi , sai da jirgin yayi kamar minti biyu da tsayawa sannan a hankali kofar jirgin ya bude Inda ya matso a hankali shi bai fito daga cikin jirgin ba haka zalika shi bai zauna sosai ba yana kada kafarsa daya cikin nuna Isa da izzar shi din wani ne .a zahirin ake iya ganin gangar jikinsa wanda hakan yasa kayan dake sanye dashi suka bayyana, Suit ne wando da riga ruwan madara yayinda yar cikinsa ya sakance baki kafafunsa sanye da black shoe's haka idanunshi na manne da farin glass yana qarewa haraban gurin kallo tare da kallon ma'aikatan dake aiki ." a natse ya fito hannunsa daya na cikin aljihun wandonsa yana taku daya bayan daya cikin Isa da izza yayinda escort dinsa ke gefen hagu da damansa kowannensu sanye da suit iri daya da makaman tsaronsa wato bindigu ."daya daga cikin escort dinsa na rike da wata karamar brief case kalar suit din jikin  Mr ATA ." manager malik ya karaso da sauri cike da ladabi ya tsaya a gabansa "ranka shi dade mr ATA  barka da zuwa? shiru ne ya biyo baya na kamar second biyar sannan a hankali ya motsa labbansa da kyar "barka m . malik ya kokari ?." alhamdulillah sir " m.malik ya fada yana mika masa hannu   Mr ATA ya mika masa dayan hannunsa dake waje yayinda har lokacin dayan hannunsa ke cikin aljihun wandonsa " gaskiya naji dadin yadda na iske kamfani kowa na kan aiki Wanda nasan duk cikin kokarinka ne dan ga dukkanin alamun aiki na tafiya yadda ya kamata ya karasa maganar yana zare hannunsa cikin na malik ya tsotsa bayan keyarsa sannan ya cigaba da magana yana tafiya a natse "kana yin yadda ya dace daman ba daidai bane tsuntsu ya cinye tsaba batare da yayi aiki ba "ai yallabai dole ayi aiki yadda ya kamata dan kai din na dabam ne sannan bakayi abinda tsuntsun zai cinye tsaba batare da yayi mata aiki ba "ka ajiye wannan maganar na gama daita yanzu, ma cigaba daga baya " m.malik ya gyada masa Kai alamun yaji cike da ladabi yace "sir mu karasa zuwa office mana ? runtse idanunshi yayi kawai batare da yayi kokarin aikata hakan ba ." bayan kamar mintuna talatin ya numfasa "Petir da sinadarin gas tsawon shekara bakwai kenan nayi Ina nema a wani yakin a cikin apapa ban samu ba sai gashi kwatsam na sameshi bayan na kashe billiyoyin kudade , sai dai ka taki sa'a dan Kai na zaba a matsayin wanda zai kular min da gurin ..." duk wannan maganar da yake har lokacin bai zauna ba tafiya yake ahankali a haraban ma'aikatar "Kai amman gaskiya naji matukar dadi ranka shi dade sai dai da za'a barni anan na cigaba da kula da bangaren karafai zai fi min , dan ba lallai ka samu Wanda zai kular maka da gurin nan yadda ya kamata ba ." "karka damu m. malik already y ma nazo da wanda zai cigaba da kulawa da nan din ,adaidai karshen wannan maganar tasa ya samu guri ya zauna akan wata hadaddiyar kujera mai runfa zagaye da kujeru na alfarma dama Kuma duk sanda bai ra'ayin shiga office dinsa ba idan yazo anan yake zama ya d'aura hannunsa daya akan table , Shima m. malik ya samu guri ya zauna yana fuskantar me gidansa da sauraronsa "na zabeka ne saboda baka da wasa akan aikinka gashi kana da rikon amana da mazantakan kula da komai fatana ka cigaba a yadda na sanka ." Ya Kai hannunsa na hagu bangaren hagunsa , nan take escort dinsa me rike da brief case ya daura brief case din hannunsa akan table ya bude ya ciro wasu manyan  freme  mai dauke da zane day day har  guda goma Kuma duk abu daya ne zane acikinsu . Mr ATA   ya dauka ya tsurawa zanen lumtsamtsun Idanunsa masu fitar da zaiban haske tsabar hasken dake cikinsu, second biyar ya dauka yana kallon zanen sannan ya numfasa ya ajiye akan tablet din gabansa yana cigaba da kallo "ko ka samota m. malik ? ko samun labarin wanda ya santa ? "Ina har yanzu dai tukun nan yallabai amman Ina iyakar kokarina kuma zan cigaba wai shin wa...."babu ruwanka da wannan hurumin m.malik dan ....." qarar daya daga cikin wayoyinsa ne ya katse shi yayi shiru batare daya ci gaba da magana ba yana jiran a miko masa wayar escort din dake rike da wayoyinsa ne ya miko masa "my sweetheart " .ya fada tare da rusunawa mr ATA . da sauri mr ATA  ya amshi wayar a hannunsa ya manna a kunnenshi ya mike tsaye cikin tsananin tashin hankali da girmamawa ya fara tafiya yana magana a natse "inna lillahi dan girman Allah sweetheart ki  qara hakuri dani , ki Kara bani lokaci zan yi qokari ,okay  I know nasan kin yi hakuri dani amman Ina da tabbacin wata rana zakiyi farinciki sosai, ina kan neman matar da zan aura ni dai ki tayani da addua murmushin gefen baki ne ya bayyana akan fuskarsa adalilin uzurin da tayi masa nan take ya  samun natsuwar zuciya ya cigaba da abinda yake ." ******* LAGOS Da misalin karfe biyar na yammacin ranar laraba "Yammata ne su hud'u zaune a cikin wata hadaddiyar mota kirar land cruiser prador ,mutun biyu zaune a gidan bayan ,yayinda biyu ke zaune a gaba akan titi masha dake surelere , humaira dake kusa da mubina ta Ciro wayarta iPhone 12 Pro max acikin jakarta ta soma d'aukarsu snap tana ta'ba kafad'ar mubina dake driving dan ta shigo cikinsu ,mubina tayi murmushi ta dan shigar da fuskarta tare da d'aga yatsunta biyu kana ta maida hankalinta kan tuki ." tafiyar mintuna ce ta kawosu Apapa  gra suka tsaya a gaban wani makeken get da aka rubuta ABDULLAHI ESTATE  tare da yin hon ,daya daga cikin masu gadin estate din  ya leko adaidai lokacin da mubina tayi  kasa da glass din motar ganin yaran estate din ne ya koma da sauri ya bude .mubina ta danna hancin motarta ta shiga Katafaren  estate din nansu mai d'auke da gidaje  fiye da ashirin  sama da kasa    sai dai acikin gidajen akwai guda daya wanda ya bambamta dana saura wato gidan hjy zulaiheart ." yanayin gidanta ya bambamta dana saura ne sakamakon marigayin mijinta yafi sauran yanuwansa tarin dukiya kuma ko bayan mutuwarsa yaranta sun cigaba da qawata mata gidanta kullum cikin gyara yake da canza kayan ado na zamani , 'yan aiki  ma sun bambamta dana saura ,yan aiki guda goma sha biyar ne ke  zariyar kula da kowoni bangare na gidanta ,sannan kowannensu sanye da fararen kaya masu ratsin baki . babu mutun ko daya na cikin ahlin estate din dake tsaye akan kafafunsa domin yin aiki sai dai dan aiwatar da ibada , kowa acikin gidan dan gata ne hatta bakin dake zuwa gidan jin kansu suke tamkar ya'yan wasu saboda mutuntaka na mutanen gida, tsarin gidan hjy zulaiheart   kuwa  kace a gidan turawa ne kowani bangare shirye yaki da kayan alatun na more rayuwar duniya ,haka ma kofar da zata shigar da mutun bangaren hjy zulaiheart  tsare yake da securities guda biyu masu duba jikin mutane koda zaa shigo da wani abun cutarwa . mubina ta dauki hanyar inda aka tanada domin paka motocin bangaren gidan hjy zulai nan take sauran yanuwanta kuma kawayenta suka hada baki gurin cewa "ya haka kuma ?"Sai data dan marairace fuska sannan tace "dan allah mun dan shiga muga su marsi   kwana biyu bamuga juna ba daga nan ma  sai mu tsaya muyi  sallar magrib da ishai sai kowace ta kama gabanta dake duk suna shiri da juna yasa babu wacce tayi mata mutsu har tayi parking tare suka firfito daga cikin motar suka nufi  hanyar gidan hjy zulaiheart  ,babu wacce ta jira ayi checking  din jikinta ko mata iso shiga ciki kasancewar nan din ma gida ne a wurinsu tunda bangaren danuwan mahaifansu  ne . sallamarsu maryam da nana hauwa'u suka ji suka mike cike da farinciki suka rungume juna suna wa juna barka da zuwa sannan suka zube akan royal chair's suna tambayar hajiya zulaiheart  "mami tana ciki tana amsa  waya maryam   ta basu amsa zamansu ko cikakken minti biyar basu yi ba sai ga mutun uku cikin masu aikin gidan kowacce sanye da farin kaya da ratsin baki hannunsu rike da tire , tiren na farko lemu da ruwa ne ,sauran biyu din kuwa duk kayan motsa baki danginsu snacks da dambu naman rago , suka gaishesu cike da girma mawa ,suna gama ajiyewa baki abin motsa baki suka Kara gaba suka koma bakin aikinsu .." "Daga ina haka dan naga alamun kamar fita kukayi ? "eh ! fita mukai muje birthday din wata abokiyarmu da muka qare karatu tare ne , dawowar mu kenan nace mu shigo kwana biyu bamu ga juna ba inji cewar mubina "ai kuwa mun gode muma kuna ranmu ,wallahi kullum sai nayi maganarku inji cewar maryam , nuzla taí saurin cewa "babu wani maganrmu da Kikeyi ga baki ga hanci amman zuwa ya gagreku kullum kuna gida kunshe kuna faman posting a social media ." "wannan kuma da sister kike ba dani ba nana hauwa'u ta fada tana murmushi tana kallon maryam , maryam ta kai mata duka ta kauce da sauri tana sake murmushi tana cewa "ai sister daana daura kashi to wallahi data daura nata nifa idan tanayin wani abu har takaici take bani ahankali suke hirar yaushe gamo duk da suna cikin wuri daya amman sukan dauki lokaci basu hadu ba kowa yana nashi wuri ." Suna cikin hira idanun mubina ya sauka akan tangamemen hoton  mr ATA dake manne da bangon falon yana sanye cikin suit bakake fuskar nan tashi kmr Koda yaushe babu faraa amman hakan bai hana kyawunsa fitowa ba ." ta d'auki sama da mintuna  talatin tana kallonsa Yayinda sauran yan'uwanta suka cigaba da hirarsu, murmushi ne ya subuce akan fuskar mubina wanda bata san sanda tayisa ba , nana hauwa'u ta Kai hannu ta dafa kafadanta tana cewa "ya'akayi mubina kika tsare mana yaya da Ido ko dai ko dai ? a matukar firgice wacce aka kira da mubina ta waigo ta sauke idanunta akan nana hauwa'u tana sakar mata murmushi tare da sauke ajiyar zuciya "wallahi kamar kin sani yar'uwata tunda na taso babu abinda nake so kamar ya adam "inna lillahi kice dai saboda kiga hotonsa yasa kika matsa lallai sai mun fara shigowa nan?inji cewar diyana "kuyi hakuri wallahi yana cikin dalilin saboda na kwana biyu bangansa ba ko wulgarwasa fa ina jin ma kamar baya kasar ko ...."? wannan furucin da tayi yasa gbdy yan'uwanta suka maida hankalinsu kanta cike da tausayawa  , nana hauwa'u ta dinga kallonta cike da matsanacin mamaki dan tasan mubina da tsatsanin kunya uwa Uba aji dan ta sha ganin yadda takewa samari wulakanci, samari ma yayan masu arziki amman bata da lokacinsu "wallahi nana hauwa'u da gaske Ina son ya adam so Kuma me tsanani da Ina da tabbacin zai aureni da zan ajiye komai na furta masa Ina son shi saboda son da nake masa bana wasa bane, maryam dake zaune kusa da nana hauwa'u tayi murnushi kana tace "zai soki mana amman sai kinyi kmr kina kiyi gsky ,dan wallahi kallon fuskar shi ma abar tsoro ce kullum fuska a hade ga babu mgn mai dadi komai daga nonsense,rubbish, stupid girl ,crazy  girl ,Ke ni gbdy tsoro yake bani bana ko iya kallonsa. suka kwashe da wata  mahaukaciyar dariya suna cewa "shegiyar matsoraciya ,shine  dan iskanci kike bata kwarin gwaiwa taje yaci ubanta ? "suka sake kwashe da wata dariyar " Nan hirarsu ta koma ta mr ATA wasu na bawa mubina goyon baya ta fada masa zai amince tunda bai tsaida matar aure ba ,yayinda wasu na nuna mata illar hakan amman ita mubina ko uffan bata furta ba illa dai tana ji Kuma tana sauraronsu daya bayan daya, a natse maryam ta tsurawa mubina Ido "mubina idan kin tabbatar kina son shi shawarata ki cire tsoro dan nasan shi kike ji , ki furta masa in sha allahu zai amince Kuma zai soki tunda duk kin hada abubuwan da zaki sace zuciyar kowani nmj "Kai yar'uwata kina gani zai Soni kuwa ?why not ya Adam zai amince da sauri ma a wannan zamanin namiji ya samu macen dake sonsa kmr yadda kike son ya AD ai babu jiran da zai tsaya yi ,kefa sauraniya ce acikinmu karki ji komai na baki goyon baya dari bisa dari ki ........" Kiran hjy zulaiheart ne ya katse maryam ta mike da sauri ta nufi d'akin mami ta barsu suna cigaba da tautaunawa byn wasu mintuna hjy zulai ta fito tana sakar musu murnushin jin dadi tana aiyana Ina ma Adam dinta zai daure ya zabi mata a cikinsu kamar yadda sauran yanuwasa sukayi gasu nan masha Allah dan kusan auren zumunci ake yi a family din amman dai zata gwada yi masa magana taga ko za'a yi sa'a ya amince ,suka hada baki suka gaisheta a mutunce ta amsa tana tambayarsu lafiyar iyayensu , anan suka qarasa yini  suna Hira daga wannan hirar zuwa wata hira sai dare suka kama gabansu ." ****** Bayan wata daya  aka wayi gari akaga gawar mubina agdan qanwar mahafiyarta zainba an kasheta ta hanyar tsoka mata wuka a daidai saitin zuciyarta Kuma aka bar wukar ajikinta ba'a cire ba hankalin family's din abdullahi ya tashi matuka mahaifiyarta kuwa kuka da sambatu take tana cewa daga ziyara shikenan an kashe min 'ya daga ziyara fa ,daga ziyara fa!!  haka ta dinga furtawa har abun yaso zame mata kmr ta zautu saboda ita kadai gareta mace sauran ya'yanta duk maza ne ,sauran yanuwanta sunyi kuka kamar zasu bita lahira maryam kamkame da hannun mubina tana wani irin kuka me ban tausayi saboda akwai sabo me tsanani a tsakaninsu "waye yayi mana haka ?waye ya kashe mana yar'uwa ?an kasheta batare da burinta ya cika na auren ya AD ba sai lokacin mutanen gidan suka San da batun soyayyar da mubina ke yiwa AD batare da bata lokaci ba jamian tsoro suka shiga lamarin suka shiga d'aukar gawarta hoto yayinda daya daga cikin police Ke rike da farar takarda yana rubuce rubuce akan gawar byn sun gama sannan aka cire wukar aka soma kokarin shiryata zuwa makwancinta Inda har lokacin jini bai daina tsiyayya ba." Mr ATA na gidansa dake banana estate yana kallon zanensa  dan wani lokacin idan yana son hutawa can yake zuwa yayi kwana biyu idan ya gaji ya dawo gida wurin mahaifiyarsa dan bazai iya yin nisa daita ba , Kiran sweetheart dinsa ya samesa inda cikin kuka take sheida masa halin daake ciki a zaune yake amman bai san sanda ya mike tsaye rike da zanensa gam yana furta kalmar innalillahi "yaushe kenan ? ya furta cikin tashin hankali " okay ganin nan zuwa nan da wasu yan mintuna  bai tsaya katse Kiran ba ya mike ya leko zuwa falonsa na uku Inda ya bawa masu tsaronsa umarnin fita  yana gama fadar haka ya koma ya shirya dan daman yyi wanka cikin kankanin lokaci ya fito ya karasa Inda motarsa  yake aka bude masa gidan baya ya shiga ya zauna zuciayrsa na tsinkewa hankalinsa na sake tashe sai dai ba'a iya hango bacin ransa a fili sai dai daga ciki yake iya  bayyanashi ai kuwa da yana nunawa da duk ahlinsa sai sun fahimci yadda yaji mutuwar mubina .Kyawawan idanunshi wadan da suka wadatu da gashin idanu ya zubawa gawarta dake kwance a parlour dan har an fito daita domin tafiya daita makwancinta .duk da kasancewarsa mutumin da baya sakewa da 'yanuwansa amman yaji zafin mutuwar mubina sannan ya tausayawa iyayenta kasa furta komai yayi  duk da maganar yake son yi amman maganar taki fitowa hankalinsa sai sake tashi yake yana mamakin yadda aka kashe mubina yana wannan tunanin  aka fito da gawar mubina da jini duk ya bata likkafani aka nufi gidanta na gaskiya ." Bayan an dawo daga kaita duk yan'uwa suka yi tsuru tsuru kowa ka gani yana cikin tsananin tashin hankali me tsananin ,Sosai mr ATA yaji mutuwar yar'uwarsa duk da ba wani sabo ne a tsakaninsu ba, batun tana son shi kuwa sai lokacin yaji abun ya mugun tsaya masa rai duk da yasan babu digon sonta a zuciyarsa kawai dai tausayi ne da jimami , yan'uwa sun jajantawa juna "yarinyar da bata da hayaniya yaushe take fad'a bare a samu abokin gabarta da har zai yi sanadin mutuwarta ,bata shiga harkar mutane kullum cikin faraa take inji cewar hjy zulaiheart kowa mamakin da yake yi kenan a tsakaninsu .muryar mr ATA a sanyaye ya dube police officer din dake tsaye kusa da mahaifiyarta yana mata tambayoyi "kuyi iya bincike da zakuyi Ina son a gano wanda yayiwa mubina kissan gilla dan sam bazan barshi ba koda kuwa danuwana ne ," ya karasa maganar cikin tsananin fushi "karka damu ranka shi dade tabbas zamuji da komai bai ce komai ba ya k'arasa kusa da mahaifin mubina dake rike da wukar da'a aka kashe masa tilon diyarsa ya dafa kafad'arsa sannan ya karbi wukar daga hannunsa yana kallon wukar mai dauke da kan sarauniyya ya dinga kallon wukar da akayi kisan sabuwa ce fil da alamun ma akan mubina aka fara amfani dashi ya furzar da numfashi kana ya soma mgn "karka damu uncle jay dake haka yake kiransa inshallahu za'a gano ko waye yake da saka hannu gurin kashe mubina ka kwantar da hankalinka muddin Ina raye sai nasa an gano wannan mashekin ."ya karasa maganar jijiyo kansa na mikewa, hawaye ya zubo a idanun mahaifin mubina ya daura hannunsa daya akan hannun Mr ATA  dake kafadarsa "na gode ADTA dake shima hk yake kiransa  Allah ya jikan mahai ...."kasa karasawa yayi saboda kukan daya ci karfinsa dan sai lokacin ya samu damar zubar da hawaye mr ATA  ya rungumeshi ajikinsa tsam yana rarashinsa ." bincike sosai akayi akan mutuwar mubina sai dai har wannan lokacin da ta cika wata biyar da mutuwa ba'a samu nasarar gano hannun wanda yayi kisan ba a karshe mahaifinta yace abar case din ya barwa Allah komai amman mr ATA yace sam a cigaba da bincike da kyar uncle jay ya shawo Kansa ya hakura , maryam ta dade tana Jin mutuwar mubina a zuciyarta dan ko runtsawa bata yi duk sanda ta tuna maganarsu na karshe kafin akasheta sai ta rushe da kuka Mai tsanani "ki tayani da addua marsi ina Kara Jin qaunar ya ad a cikin zuciyarta gashi bani da yadda zanyi ya fahimceni tsoronsa ya hanani fuskantarshi da maganar amman zanyi qoqarin fad'a masa acikin satin nan Allah yasa idan na furta masa ya amince ya aurenni ,ni ko baya sona zan zauna dashi haka bare ma wuyarta mu kasance miji da mata tuni zan mantar dashi wani kiyyaya Allah sarki rayuwa kenan mubina Allah yayi Miki rahma .." ******* Bayan shekara daya Yana zaune akan gadon hjy Zulaihat sanye cikin kananan kaya wondo da riga ash colour idanunshi sanye da farin glass yana fama tura sakonni ta shigo dakin ta nufi inda beside dinta yake "sweetheart! ya kira sunan da yake kiranta dashi sabani Kowa dake kiranta da mami "Yaakayi my love ta amsa tare da kallonsa   "ko zan samu black tea ?yayi mgnr yana cigaba da aiki "me zai hana shalelena bari nasa maryam ta kawo maka nayi baki ne . "No abarshi kawai sweetheart idan itace zata kawo min yaran da babu abinda suka iya sai shirmen banza da wofi .tayi shiru shima yayi shiru ,shi dai bai san dalili ba amman baya son maryam a kusa dashi Kullum qara jin tsanarta yake wanda da zaa tsaresa da bindiga bazai ce ga dalili ba, shi dai hk kawai yake jin baya sonta a duk cikin family's dinsa na bangaren uwa da uba ." ta juya ta bude beside tana duba abinda ya shigo daita "yauwa ko zaki  bawa auta ta kawo min idan tana nan  "still bai dago ya kalli inda take ba ?dagowa tayi a natse tana sauke numfashi sannan ta d'an matso kusa dashi ta daura hannunta akan sumar kanshi tana lumshe ido  kana tace" ai duk abu daya ne da auta da maryam dukkaninsu shirmen banza da wofi suka iya zai fi kyau ka kawo wacce bazata dinga maka shirmen banza da wofi ba ta dinga maka abinda kake so " . "ta fad'a tana dauke hannunta akan sumar kanshi ."ya dan dago a hankali ya kalleta suka hada ido yaga yadda fuskarta ya canza sosai alamun bata ji dadin abinda ya fada ba, ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yace  "am very very sorry ma "shikenan yanzu auta zata kawo maka ta dauki abinda ya shigo daita ta fice daga dakin ". Byn  minti  goma auta ta shigo a hankali tmkr kazar da Kwai ya fashewa aciki bakinta dauke da sallama hannunsa kawai ya mika mata tana mika masa cup din tea  ta fice da sauri ta bar dakin, yana cikin aiki ya samu kira daga danuwansa hisham  ya dauki wayar "hello hisham ! "Okay just give me ten minutes I will meet you there ya fad'a yana kokarin kashe system dinsa  byn ya kashe ya dauki system dinsa ya rungume a qirjinsa ya nufi kofar fita  ." yana qoqarin fita  maryam  na qoqarin shigowa dakin hannunta rike da akwatin sarkokin hjy Zulai da wayarta on exepecting taji tayi  karo da gangar jikin mutun nan take  system dinsa yayi tsalle daga qirjinsa yayi kasa ...,"da wani irin mugun sauri tayi watse da kayan hannunta har ma  da wayarta tayi kasa  ta tarô system din da hannuwanta duka tun bai kai kasa ba ta shiga uku ,shi kuwa ATA tsaye yayi batare da wata alamun damuwa a tattare dashi ba yana dubanta sai dai kallo daya zaka masa ka fahimci ransa ya baci da abinda tayi ,shi bama system din yafi damunsa ba kamar haduwar da jikinsu yayi ." jikinta na rawa ta miko masa system tana cewa "am ... am very sorry kayi hakuri dan allah ban ....."ai batasan sanda tayi shiru ba sakamakon wani kwallo da yayi daita  da system din nasa gbdy kamar ball sai gata a waje bisa gwiwowinta  ta dunkule guri daya , bata bi ta kanta ba ta maida hankalinta ga system dinsa ,nan ta hango system ya wargaje a kasa kallo daya tayiwa  system din ya fahimci ya tashi aiki nan fa hankalinta ya sake tashi "stupid girl kawai ." ya furta da karfi yana qarasa fitowa daga cikin dakin sosai ya daga kafarsa daya zai daki gefen cikinta yaji sautin muryar hjy Zulai "karka soma adam ". Numfashi ya sauke yana waigowa zuwa inda take tsaye ranta a matukar bace tace  "me yayi zafi adam zaka kashe yar mutane ne ?laifin me tayi maka ?tayi masa tmbyr ajere ransa a matukar bace yace "ask this nonsense girl ." ya fad'a yana nuna maryam da dan yatsansa hjy zulai ta qaraso tana kokarin daga maryam "me kikayi masa yake kokarin kasheki "? ranta a matukar bace ta soma magana, ahankali ta zayyanewa hjy zulai komai tana sheshekan kuka tmkr ranta zai fita .."naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana dubansa " shine zaka mata irin wannan hukunci ko da gangan tayi bai dace ba bare babu daya "ya kada kai zai wuce "adam ! ta tsaidashi ta hanyar kira sunansa Ya juyo a matukar fusace yana dubanta " daga yau kar na kara ganin ka ta'ba lafiyar jikinta bama ita ba kowani yaro a gidan nan  ban amince ba ban lamunta ba kaji na fada maka........" iska ya shaka ta cikin bakinsa daman kuma duk sanda ransa ya baci baya fesar da iska a fili sai dai acikinsa juyawa yayi ya kama gabansa ."hjy Zulai ta kamo maryam suka shiga cikin dakinta tana bata hakuri "ki dinga kula kinji  maryam wannan yayan naki hakurinsa mai yawa ne ta zaunar da maryam   akan gado  itama ta zauna tare da daura kan maryam akan ciyarta ta daura hannunta akan sumar kanta tana shafawa"  ki tayani da yi masa addua allah ya yaye masa wannan nukufurcin da zafin rai da yake fama dashi ".Allah kiyaye  na rasa wanda zan wa addua sai mutumin daya tsaneni kamar ya kasheni ta fad'a acikin  ranta  mami tace  ,"zaki tayani yi masa addua maryam ?."cikin muryar  kuka ta gyada mata kai kawai ba dan zatai ba "Yauwa na gode Kwarai diyata allah yayi miki albarka ." Da daddare  ATA   na zaune akan makeken gadonsa yana operating  din wayarsa  hjy zulai  ta shigo bakinta dauke da sallama lumshe lumtsatsun  idanunsa yayi saboda ganinta duk halin damuwar da yake ciki da zarar ya ga mahaifiyarsa yake jin sanyi aranshi "fatan kina  Lfy sweetheart "?ya tambayeta yana riko yatsun hannunta daya cikin nashi "alhamdulillah ta fada fuskata babu yabo babu fallasa   ."ga coffe ta mika masa sannan ta zauna kusa dashi ya saki yatsun hannunta ya karbi cup din coffee ya kai bakinsa "me zakayi breakfast dashi da safe ? yayi shiru yana tunani can yace "komai sweetheart dina zata ci nima zanci ." Adam!!!  ta kira sunansa har sau uku ya sake rike hannunta gam cikin nashi yana kurban coffe yana lumshe ido har dimple dinsa na lotsawa ," ina son nayi wata magana mai mahimanci da kai,nan  take ya bar abinda yake ya tattara dukkanin natsuwarsa zuwa gareta "abinda kayi dazu sam banji dadi ba dan allah na roki arziki ba dan ni ba karka sake maimaitawa ."tai shiru tana jiran taji me zai ce "ya lumshe mata idanunshi "naji amman itama ki mata mgn ta daina shiga hanyata "wannan kuskure aka samu domin kuwa maryam na qoqarin gani bata shiga harkarka ba ". "kai  ba ita ba  kowa acikin family's din nan yana takatsntsan ba yara ba ,ba manya ba  sai kace wani azara ilu "yayi murmushin ciki wanda ita kadai take iya fahimtar haka ,"wallahi ka canza kai gaka nan kullum cikin bakin rai da miskilanci yanzu kai ko shaawa rayuwar gidan nan  bakayi kowa na son kowa kalli su hisham dasu tariq sweetie nah kenan ya dauko mai sunanshi tsab ,kai hatta muhd bello da ba dan gidan nan ba yana jan yaran gidan nan ajiki amman kai kowa tsoronka yake ji Kmr wani dodo wallahi ka dinga son mutane dan mutane rahma ne." "to ni nace bana son wani ne acikinsu ?ya fad'a a shagwabe yana daura kanshi saman cinyarta " girgiza kai kawai tayi  tana daura hannunta a sumar kanshi tana shafawa tana kallon kyakkyawar fuskarsa  mai cike da haiba ga kwantaccen gashin fuskarsa  dake  mugu mugun qara masa kyau  sosai ya kwanta luf luf  saboda gyaran da yake sha . "ni sweetheart kin kasa ganewa ne nifa raini ne banason su kuma yan renin sense ne kinga gara na dinga kama kaina "yyi mgnr Kmr bashi yayi mgnr ba ,girgiza kai ta sake yi kana ta cigaba  da mgn "sai abu na gaba "ya batun aure ko har yanzu baka samu true love din ba ? ."Yes of course ban samu ba sweetheart  ,"yanzu kai baka tausayawa wannan mamartaka da shekarunta  yaja ?  " "Adam at any time zan iya amsa kiran allah ko sai bayan mutuwata zakayi aure ? tayi mgnr tamkar zatai kuka nan fa hankalinsa yayi mugun tashi ya mike zaune tare da riko  hannuwanta gabadaya cikin nashi yana kallonta cike da matsanancin soyayyarta gbdy yanayinsa ya sauya kamar zai yi kuka dan baya qaunar abinda zai nisan tashi da mahaifiyarsa bare rabuwa ta har abada ,muryarsa a kasalance ya soma mgn "haba sweetheart me yasa zaki fadi haka ?" Me yasa bazan fadi haka ba ?ai  gaskiya na fad'a kaki kayi aure  kai dai  kullum aiki  kawai kasa gaba baka ma  duba lamarina  bare ka  tausaya min Adam , bana son na koma ga allah banga aurenka da ya'yan ka ba ta qarasa mgnr cikin raunanniyar murya wannan karon kam hawaye ne taf acikin kwayar idanunta "karki min hk sweetheart Kinsan illar zubar da hawayenki akaina, kuma Kinsan babu abinda na tsana kamar na ganki cikin damuwa "idan har da gaske  baka son ganina cikin damuwa to ka dan duba ko a cikin yammatan  estate din nan ai bazaka rasa masu sonka da aure  ba sai ka zabi biyu ko daya acikinsu  ". Ya ware mata lumtsatsun idanuwanshi sosai yana mamakin jin abinda tace  "har mata biyu sweetheart ina zan kai su ? "bansani ba ta fad'a tana zabga masa harara sannan ta cigaba da mgn "wallahi shine burina ka auri mata biyu kuma duk arana daya saboda kasancewarka  namiji kwaya daya tilo da allah ya mallamin "girgiza kai kawai yayi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa  batare da yayi yunkurin sake cewa wani abu ba ya sake jin sautin muryarta "zakayi abinda nace ko nasa araina sai bayan na mutu zakayi aure ?" ya shafa goshinsa yana cewa "okay  zanyi kokarin yin haka sweetheart." Ya fadi hk ne dan ya kawo karshen mgnrsu ."ko kai fa yaron albarka allah ya zaba maka mata na gari , runtse idanuwanshi yayi sosai tare da yin shiru yaki cewa komai dan har kanshi ya fara ciwo ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na  kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page2 ....Da misalin karfe goma na safiyar ranar asabar mr ATA ya sauko daga saman dakinsa jikinsa sanye da bakin riga da wondo baki yayinda kafafunsa ke sanye cikin wasu hadaddun silifas masu matukar kyau suma black kana gani kasan masu tsada ne haka idanunshi suna makale da farin glass wanda ya zame masa tamkar na gado, ko bacci wani lokacin dashi yake sai idan Mahaifiyarsa ta shigo ta gansa dashi ta cire masa ,yayi kyau sosai acikin shigar kasancewarsa fari ."ya qaraso ya dauki jarida daily trust da'aka ajiye masa ya samu wuri ya zauna akan doguwar kujera mai zaman mutun uku ya daura kafarsa daya a kan daya ya shiga duba jarida " yana zaune nana da maryam suka fito suna magana akan inda mai decoration zatai decorate din birthday din maryam dana hanan diyar Aunty zabiba kanwar mr ATA da zaa gabatar a ranar ." suna gama qarasowa parlour'n suka gansa zaune Kmr an dasashi a gurin ."suka bishi da kallo suna jin faduwar gaba babu yadda zaka ga mr ATA gabanka bai fadi ba ko kai waye kuwa saboda tsananin tsare gida , ya gansu amman yayi tamkar bai san da wasu halitta tsaye a wurin ba ,nan take kowacce ta shiga taitayinta jiki a sanyaye suka hada baki wurin gaishesa "good morning ya adam" ? sai daya dauki second goma batare daya amsa ba har sun cire rai da zai amsa suka jiyo sautin muryarsa daga can kasan makoshi "morning ! ya amsa batare daya dago ya dubesu ba ." Naunayen ajiyar zuciya maryam ta sauke dan tasan darajar sister taci yasa har ya amsa gaisuwar dan da ita kadai ta gaisheshi bazai ta'ba amsawa ba Kai tsaye hanyar kitchen suka nufa domin bawa masu aiki umarnin abinda zasuyi na birthday duk da sauran abubuwa masu wuya tun jiya a kammala ,duk abinda suke hankalin maryam na kan mr ATA bini bini ta kallesa taja tsaki acikin ranta dan hakan nan kwanaki take jin matsanancin tsanarsa a ranta dan tasha alwashin tunda bai qaunarta itama bazata qaunacesa ba mai qaunarsa ma baso ." Sai dai duk da wannan tsanar da tayi masa ta kasa dauke kwayar danunta akanshi har sanda ya mike ya isa dining table ya dauki cup din coffee dinsa baki mai shegen kyau da gani daga wata kasar yazo dashi , a natse ya sake dawowa mazauninsa ya zauna fuskar nan tashi a hade tamkar wanda ake masa wahayi da bacin rai." "tunda aka haifeta ta bude idanunta akansa bata ta'ba ganin dariyarsa ba ,kuma haka kowa yake fad'a acikin family's ,komai zaayi na dariya sai dai ya bata rai yaja tsaki tare da cewa nonsense ko rubbish ga shegen miskilanci wani lokaci halinsa na dan burgeta Irin mijin da take so kenan mai matukar kamewa da sanin ciwon kai, dan gsky ita dai nmj mai yawon surutu ko shiga abinda bai shafesa ba yawon fara'a matsala ne agurinta bata so sai dai nashi yayi yawa ko dan murmushin nan ba yayi matukar kaga fuskarsa a d'an sake to yana tare da mami ne shima wani lokacin bata gane kansa kome zatayi bazai sakar mata fuska ba ." byn ya sha kad'an ya ajiye cup ya cigaba da abinda yake har sanda hjy Zulaihat ta fito itama ta shiga kitchen yana nan zaune ya tsurawa jarida idanunshi , al'ameen daya daga cikin securities na bakin get ya shigo bakinsa dauke da sallama sannan cike da girmamawa hannunsa rike da white lailon da box blue and white ,mr ATA ya amsa sallamar aciki yana mai d'ago kansa ahankali ya zubawa al'ameen lumtsatsun idanunshi "Alameen ya qaraso gabansa kad'an ya rusuna "barka da safiya yalla'bai "mr ATA ya gyada masa kai kawai batare daya amsa ba . " amm ga sako wai inji Ana's" mr ATA ya d'an kankace lumtsatsun idanushi yana bukatar qarin bayani daga bakin al'ameen,alameen yayi sauri yace "sakon hjy maryam ne ita yace abawa "shiru mr ATA yayi yana kallonsa da sakon hannunsa kamar bazai ce komai ba sai kuma ya nuna masa kan table din dake gabansa yana jan tsaki a fili al'ameen ya ajiye ya juya ya fice da sauri ya kama gabansa." Maryam dake kitchen wacce daman idanunta da hankalinta yana parlour ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, da sauri ta qarasa inda nana take tsaye "sister na shiga uku nah" ta fada tana riko hannun nana cikin nata "me kuma ya faru allah ya rabamu da shiga uku sister ?"kalli can ki gani sister ta nuna mata parlour'n "me ya faru ? "sakon Ana's ne daman ya turo min text message zai zo ya kawo min gift gsky al'ameen bai kyauta min ba maimakon ya kirani ya bani a hannuna tana magana idanunta na cikowa da ruwan hawaye hjy zulaiheart ta juyo a natse ta dubesu "ku kuma lafiya kuka tsaya kuka hade kai wa ya mutu ? a matukar firgice suka juyo suna dubanta maryam na 'kokarin dauke hawayenta a d'an rikice suka girgiza mata kai alamun "babu kowa " to meke faruwa daku ?babu komai suka sake hada baki "to allah yasa babu komai din amman ni dai na fahimce da komai tsayawa sukai suka qasa cigaba da aiki ." shi kuwa Mr ATA naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske yana shan yaji kamar yadda ya saba sosai ya tsurawa box din dake dauke da sunan maryam da kallamar happy birthday yana lissafa abubuwa dayawa acikin ransa "wai gashi inji Ana's sakon hjy maryam "ya maimaita abinda al'ameen ya fad'a , kafin daga baya ya kwabe baki tare da kai hannu ya bude box din ,da wani hadadden freme idanunshi ya soma cin karo mai matukar kyau da d'aukar hankali an rubuta sunanta da larabci da kuma hausa ." "shiru yayi yana jin wani iri a gabadaya ilahirin jikinsa na tsantsar bakinciki ,a hankali ya dinga kallon abubuwan dake cikin box din mug, pray mate ,Casbaha alqurani da wani qaramin greating card na sokon taya murnar birthday sai kuma qaramin yellow takarda mai dauke da kalaman soyayya "ya dauka yana tabe baki kamar yaga wani mugun abu ya soma karantawa ." hjy Zulaihat ta fito daga kitchen tare da masu aiki mutun biyu zuwa dining maryam da auta suka biyo bayanta jikinsu duk a sanyaye dan basu san abinda zai faru ba "na shiga ukuna sister ki taimakeni karanta sakon fa yake " maryam ta sake fadan hk cikin tsananin tsoro "to sai me idan ya karanta ? " wallahi kin cika abun ban haushi kamarki dan an aiko miki da sako zai zama abun tashin hankali? Ke yarinya ce karki manta master's gareki kuma dole zakiyi aure "ni sister rabani da wani master's na yarda kowa ya karanta sakon amman ban dashi "bangane banda shi ba ? shi waye naki da zakice ban dashi ? tayi mata tmbyr tana kallonta "haba sister ya kike yi kamar baki san abinda nake nufi ba kema kinsan ba haka nake ba ni ba matsoraciya bace amman wallahi shi mugun tsoronsa nake ji ,sannan kinsan halinsa da disgi ." "Dana san halinsa fa ? shi zai auremu?Ko kuwa munyita zama haka kenan bazamuyi aure ba ?"Kinga idan zaki cire tsoro ki cire dan ni wallahi ina samun miji aurena zanyi na barki bazan zauna ba aiki ba aure ba dole zanyi daya ta qarasa mgnr tana jan tsaki maryam tace "banza kamar kema ba tsoronsa kike ba "ina jin tsoronsa amman ban kai ki ba dan dani anas da abbas suke mutuwar só da son aure da tunin ina gidan daya daga cikinsu "ta fad'a tare da qarasawa wurin Hjy Zulai ta rabe a gefenta." daga can inda hjy zulai take tsaye ta hangosa ya baje kayan sannan yayi zurfin cikin karata yellow takarda "Lafiya adam !? ta furta tana cigaba da dubansa ,a tsanake ya mike tsaye fuskarsa a yatsine ya nufo wurinta yana cewa "wani haukan shirme nake karantawa ".maryam tayi wuf ta koma kitchen da sauri tana daura hannuwnta duka bisa kanta itama auta tayi nesa da hjy zulaihat "haukan shirme kuma adam ? hjy Zulaihat ta maimaita abinda ya fad'a "yes sweetheart wannan bashi da maraba da haukan shirme ,wai nmj né zai zauna yana wannan haukan abun kunya kawai "yayi maganar yana yatsuna face dinsa kamar yaga wani mummunar abu "wannan ai iskanci ne ba soyayya ba ya sake mgn yana jan dogon tsaki  ." hjy Zulaihat tayi shiru tana duban mr ATA cikin tsananin tausayawa kanta dashi kanshi ,"bata san ranar da zai canza wannan mummunar halin nasa ba ,bata san ranar da zai bude baki yace ga matar da yake so ya aura ba ko fad'awa soyayya "duba ki gani sweetheart ya mika mata letter yana sake jan tsaki kamar wanda akayiwa dole sai ya karanta." Jiki a matukar sanyaye mami ta karbi letter daga hannunsa tana dubawa gabadaya bata ga inda zantuttukan dake rubuce sukai kama da haukan soyayya ba ,illa ma maganar soyayyar mai sanyaya zuciya da kwantar da hankalin abokin rayuwa , byn ta gama karantawa ta kalli nana hauwa'u fuskarta dauke da tmby, kai ta gyada mata "mami sakon maryam ne "wani mugun kallo ya wurga mata wanda ya hargitsa hantar cikinta da mugun sauri ta bace masa da gani ." sai lokacin Hjy Zulaiheart ta fahimce abinda yasa taga hankalinsu a tashe a kitchen ,numfashi ta fesar tana kallon bayansa dan tuni ya juya ya koma inda kayan suke tare da rike kugunsa ,qarara ake iya ganin bacin ransa bancin alqur'ani dake cikin kayan daya banka masu wuta gabadaya ya kona dan takaici ." wannan shine soyayya ta gsky da gsky yaji sautin muryar mahaifiyarsa tana magana tana tahowa zuwa in da yake "duk abinda ka gani anan kyautatawa ce ta soyayya tare da nuna kulawa "okay yanzu ta haka ne zai nuna emotiona dinsa ?kai gsky dai wasu mazan jakai ne, ya fad'a yana jan tsaki tare da nufar hanyar step har yayi taku biyu yaji mahaifiyarsa ta kira sunansa "adam !." cak ya tsaya tare da juyowa ya tsura mata kwayar idanunshi da suke cike da bakinciki" zaka iya kin yarda da wannan kalaman amman at least kayi respect din emotion din wani ,karka wulakanta soyayyar wani domin bakasan yadda taka soyayyar zata kasance ba ,idan kai baka raayin soyayya karka ji haushin masuyin soyayya domin soyayya maganar Allah ce ."shiru yayi lokaci daya emotion din mafarkinsa ya shiga kai kawo a gabadaya ilahirin jikinsa ,mafarkin ma ya daukesa da mahimanci fiyye da komai arayuwarsa  wannan tunanin yasa ya bude bakinsa da kyar "alright sweetheart amman yana da kyau idan har soyayyar gskiya ce ya turo magabatansa "ya fadi haka ne saboda ya gaji da ganin fuskar maryam din acikin gidan  dan bai san dalilin dayasa ta tare masu a gida ba ,a natse ya juya ya cigaba da taka step fuskar yarinyar mafarkinsa na yawo acikin kwayar idanunshi yayinda mami tabi shi da kallon tausayi  tana girgiza kai ." Sallamar abida né yasa mami ta dauke idanunta daga kallon hanyar da mr ATA ya bi ta maida bakin kofa tsaye take hannunta rike da hannun yesmin sanye cikin doguwar riga yar saudiya mai tsansi sosai cike da sakin fuska mami ta amsa sallamarta tana mata sannu da zuwa "yauwa mami fatan kin tashi lfy ?" ta fada tana zama cikin daya daga cikin kujerun falon .mami ta qaraso ta zauna kusa daita tana kamo hannun yesmin a lokacin mrym da nana hauwa'u sun gama tattara kayan ." a mutunce suka gaishe da aunty abida sannan suka bar wurin zuwa dakinsu nana hauwa'u na cewa "ai kin dai ji abinda ya Adam yace ?me yace sister ? ban gane me yace ba yanzu ke bakiji yace idan soyayyar gaskiya anas yake miki ba ya turo magabantasa ba ?"oh ! abinda ya fad'a kenan ai gabadaya rudewar da nayi bai sa naji komai ba?ta numfasa sannan ta cigaba da magana "wannan ai ba matsalarsa bace idan naga dama na zauna har karshen rayuwata babu aure bai shafesa ba ,yadda bai son ana shiga lamarin rayuwarsa bai dace shima yana shiga rayuwar mutun ba ". oh! ai bansan wuyanki ya isa yanka haka ba amman zo muje ki fad'a masa kar ya sake shiga rayuwarki" nana hauwa'u ta riko tsintsiyar hannunta ta nufi step din da zai kai mutun samansa ,nan take maryam ta zaro idanuwa waje "haba sister kar muyi haka dake mana wannan ai maganarmu ce " a'a babu wani maganarmu ce Ke dai muje kinga daga yau zai kiyaye ,maryam ta fixge hannunta da karfi sauran kadan kwalin hannunta ya subuce "haba sister ! haba sister Ko gskiya? shegiyar masoraciya kawai iskancinki baya qarewa akan kowa sai akanmu yake qarewa dasu anas."maryam ta kwashe da dariya "ai kema Kinsan oga nada ogansa, ina ni ina tarar aradu da fad'in kai ai sai ya tarwatsani , barni na tsira da raina da lafiyata kar ya rage min sadaki suna tafiya suna magana kuma duk akan mr ATA ne ." shiru aunty abida tana zaune har kusan mintuna shabiyar sannan ta dubi mami da kyau "wai ina ATA ne nasan yau asabar yana gida dan duk kwanakin nan bana ganin shigarsa da fitarsa ?"kullum sai yesmin ta tmbyeni shi shiyasa ma yau nace bari na kawota ta gaishesa tunda weekend ce ta fad'a tana murmushi ,mami ta gyara zamanta tana kallon fuskar yesmin "Adam yana nan galau yanzu nan ma ya hau sama ,kwana biyu da bakya ganin shigarsa da fitarsa yanayin aiki ne kwanakin nan duk bai dawo wa gida da wuri haka zalika da wuri yake fita amman yau kam yana gida bana tunanin ma zai fita dan ma ya dauko rigima ai da kin samesa a kasa . "Rigima kuma mami kamar wani qaramin yaro ?ta fad'a tana murmushin farinciki". "wallahi fa nan mami ta zayyane mata abinda ya faru, dariya aunty abida tayi sosai "lallai kam rigima amman ai wani lokacin akan gsky yake abubuwansa ni wallahi yana matukar burgeni yadda yake gudanar da rayuwarsa babu ruwansa da kowa sannan baya daukar raini kamar su abban yesmin koda yaushe hakoransu a bude Kmr masu tallar close up ." "ikon allah banda abunki abida me zaayi da miskilili? ai gara masu farar nan akan masu nunkufurci da miskilanci sun dan jima suna hira sannan ta mike "to mami ni zan wuce daman abinda ya shigo dani kenan sai anjima . "shikenan abida na gode sosai da kulawa amman ki bar yesmin ki aiko mata da sabbin kayanta zuwa anjima zaa kawo hanan domin gabatar da birthday dinta "aunty abida tai murmushi "to ai shikenan  mami zan aiko mata da...." shiru tayi sakamakon jiyo sautin muryarsa yana saukowa daga matattakala cike da izza da shan kamshi hannunwansa duka zube cikin aljihunsa wandonsa, yayinda iPod Ke manne da kunnensa yana amsa waya yesmin na ganinsa ta kwasa da gudu tana kiran sunansa "uncle AD! Hannunwansa duka yayi saurin zare wa daga cikin aljihun wondonsa ya dauketa yayi sama daita na second biyu sannan ya riketa a gefen jikinsa yana shafa fuskarta sai dai ko kadan babu alamun annuri akan a fuskarsa." qarasa saukowa yayi ya wuce aunty abida da mami ya daurata akan wani dogon stood mai tsawo yana cigaba da wayarsa murmushi abida tayi najin dadi domin duk cikin jikiokin gidan baya daukar kowa sai yesmin kuma ta fahimci yana matukar qaunar yarinyar sosai hakan yasa itama take mugun qaunarsa fiyye da qaunar burinsu akansa." a hankali ta qarasa inda yake tsaye "AD ..! ta kira sunansa " baki ga abinda nake yi bane ?ya fad'a a matukar hassale yana wasa da gashin yesmin."Taja bakinta tai shiru na second biyu sannan ta sake yunkurin sake yi masa magana ganin bakinsa bai motsi " uhm daman zan wuce ne ma nace mu gai..." bata kai ga qarasa abinda zata fad'a ba cak taga ya dauki yesmin ya sabata a kafad'arsa ya haura samansa a hankali ta juyo tana duban bayansa Yadda yake tafiya ma kawai duniya ne gabadayansa shi din mafarkin kowace mace dake numfashi a duniya ne shiyasa duk runtsi duk wuya sai burinsu ya cika akansa ." Yesmin ta sakar wa mamanta murmushi tare dago mata hannu tana mata bye bye "abida Kiyi hakuri dan allah nasan Kinsan halin danuwanki ba tun yau ba "no mami ki daina bani hakuri ai idan da sabo na saba da halinsa ya zanyi  da  halin danuwana ?ni gabadaya abubuwansa basa damuna burgeni ma yake ."Masha allah haka ake so duk wani mutumin kirki ya kasance allah ya qara mana hakuri da zaman lafiya da junanmu "Ameen ta amsa ta juya ta fice daga part din hjy zulai ." "Adam na bani matukar kunya mami ta fad'a a matukar fusace adaidai lokacin da mrym da nana hauwa'u suka dawo parlour'n sosai suna tmbyr ta "kunya kuma mami ?eh mana ku duba kuga yadda abida ta damu da shi amman shi bashi da abun wulakantawa kamarta ,ni na lura ma duk yafi tsanar ta akan kowa acikin family's din nan amman dan iskanci ya iya dauke mata diya ya wuce daita sama ." ta fad'a cike da takaici. "ta nan bangaren ya Adam fa yana da gaskiya itama banda abunta taya tana matar aure zata dinga wani shishige masa ".?"Uhm auta ai ita ba da wata manufa take yin haka ba tana yi saboda yanuwantaka ne "kai mami kefa bakya fahimta ,wallahi munafuci ce da bakinciki ne taf acikin zuciyar wannan matar da kike kallo amman kin kasa ganewa yanzu da kin qare mata kallo murmushin yake tayi, waya san abinda ke zuciyarta "babu komai sai alkhairi ku dinga yiwa mutane fatan alkhairi ". ******* Bayan kamar awa biyu da wasu mintuna ya fito sanye cikin wasu kananan kaya riga Orenge da white jeans kana ganin shigar kasan fita zai yi ,lokacin parlour'n Hjy Zulai ya soma cika da kawayen su maryam da yan'uwa sai dai parlour'n babu wani hayaniya a hankali suke komai sanin boss na gida da zarar zasu daga murya, sai maryam ta tsaidasu suna ganinsa kowannensu ya shiga hankalinsa tamkar basa da numfashi ." yaja tsaki yana janye jikinsa dan kar jikinsa ya ta'ba na wata acikinsu ,ya nufi kofar fita nana hauwa'u da mrym suka hada ido tare da dagawa juna gira alamun jin dadi "nuzla tayi tsalle" yeeee ya Adam ya fita zamu sakata mu wala "tayi mgnr tmkr wata qaramar yarinya "ke dai bari nuzla wallahi tun dazu a firgice muke nida maryam ,wallahi gbdy bama cikin natsuwar mu tun dazu addua nake acikin zuciyata allah ya kawo dalilin da zaisa ya fita ya bar gidan gbdy ko ma sakata mu wala sai gashi allah ya amsa adduata, gashi ma ya fito ya ganmu dayawa bai ce komai ba wallahi baqaramin dadi naji ba inji cewar nana hauwa'u ." Maryam tai juyi cikin doguwar rigar dake sanye ajikinta sannan ta tsaida kananun danunta akan nana hauwa'u "sister wannan yayan naki mai sufar zaki akwai shi da mugun iyayin tsiya sai dai fa yayi kyau sosai exactly irin mijin da nake muradin aure kenan amman samun irinsu da matukar wahala , Ina ma zan samu yadda yayi kyau din nan ace Ana's ne da yau mu dauki hotuna masu yawa mu daura a social media nasan da ba qaramin comments da like's zan samu ba." tunda ta fara magana ya dawo bata sani ba yana tsaye a bakin kofa sai faman zuba take "burin kowace mace a duniya ta samu miji kamarsa amman samun irinsu da wahala amman babu komai mayi hidima wa Allah mu samu a aljanna idan muna da rabo " "Kun san wani abu dake bani driya dashi ? duk sukai shiru babu wacce tayi tari "abu kadan zai hade fuska ya kalli mutun ya disga mutun da kalmar nonsense , crazy girl " ta fad'a tana karairaya cak ta tsaya tana duban wadan da ke tsaye a gabanta ga mamakinta taga dukkaninsu babu wanda yayi dry Kmr yadda suka saba a duk sanda wani yayi irin maganarsa ." a hankali ta juya bayanta cike da tsananin faduwar gaba aiko idanunta suka sauka akanshi yana mata wani irin kallo mai dauke da yawon tsanar da yayi mata ,da sauri ta zaro idanuwa waje tana kallonsa kmr a mafarki, ta lumshe idanunta na second daya ta bude taga dai tabbas shi din ne tsaye agabanta ,ta dan juya bayanta tana kallonsu Kmr zatai kuka." Gbdy jikinta ya kama rawa a hankali ta sakê juyowa ta fuskancesa ta hade hannuwanta duka wuri daya tare da yin kasa har ta kai kasa muryarta na rawa "am very very so.." sorry " . shiru yayi yana qare mata kallo tsab sanye take ckin doguwar rigar wanda hannunta daya long sleeve ne dayan kuma hamless gabday an canza mata kamani ta hanyar yi mata make up ga gashin kai tayi fix ya sauko har gadon bayanta abinda yafi tsana kenan daga mace too much of kwaliya da qarin gashi da farce ita kuma duk ta kware wurin yinsu "ita fa a ganinta tayi kyau da wannan shigar da kwaliyar da tai ?ya tmbayi kansa yana jan tsaki dan a idanunshi muni tayi masa barin ma rashin tsawon da Allah yayi mata ,shi kam yayi imani banci farin fatan da allah yayi mata da babu shegen nmj da zata dauki hankalinsa har ma ya tsaya bata lokacinsa wajen haukan shirme akanta ". "kusan second goma ya dauka yana kallonta yana hukuntata da idanunshi kafin daga baya ya bude bakinsa Kmr baya son yin mgn " maid your business duk abinda zaki yi karki sake kuskure ambaton sunana cikin shirmenki me nace ? ya fad'a yana zaro mata ido "Kar...kar !! na sake ambaton sunanka kayi hakuri wannan ma kusku.....you're very stupid dake da kuskuren , daman kin saba this is not your first time koni sa,an wasanki ne ? da sauri ta girgiza masa kai ya gyara tsayuwarsa " ki dinga abu kamar wata mental sam sam baki da natsuwa crazy girl kawai ki godewa allah akwai abinda zanyi mai mahimanci dana tsaya naci ubanki guntuwar banza kawai ." ya fad'a yana sa kai ya hau sama ta sauke wani naunayen ajiyar zuciya aranta tace "oh my god you save me for the first time ,byn kmr second biyar ya sauko ya fice gbdy daga gidan . Bayan fitarsa cikin bacin rai tace "ko kun tayani jin abinda ya fad'a? suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya "wai kece mental crazy girl mara natsuwa a karshe wai guntuwar banza wallahi ni duk shi yafi bani dariya wai guntuwar banza cewar nuzla ta fad'a tana tafa hannu tana dariya "see me see trouble shi fa idan ba zagi ba babu abinda ya iya arayuwarsa dan wulakanci ma har da zagin halittar Allah cewar diyana "kunga karku qara mata bakinciki byn kunsan yau ranar farinciki ne gareta nana hauwa'u tayi mgnr tana mikar da maryam tsaye dan tunda ta durkushe kasa bata iya ta mike ba tsabar tsoro ." Byn ta mike tsaye bisa kafafunta ta kallesu daya byn daya tana maka masu harara mai kunshe da bakinciki "gsky gbdy baku kyauta min ba, kuka barni ina ta faman zuba aka rasa wanda zai min alamar nayi shiru acikinku daman burinku yaci min mutunci kuyi dariya ko? Kema idan zakiyi magana next time ki dinga kallon kofar shigowa ba baya zaki bawa kofa ba in case inji cewar nuzla ,asra tace "au ke nan yanzu haushi kika ji da ba ki godewa allah ba kamar yadda yace dan da yanzu ba wannan labarin kike ba "na so oooo I thank god for saving me." Bayan wani lokaci gidan mami ya cika da ya'yanta da jikokinta da wasu daga cikin jama'ar estate din parlour'n ya hargitse da hayaniyar mutane anci an sha anyi rawa hanan ta yanka cake haka ma maryam tare da daukar hotuna da vedios mutun biyu ne kawai acikin yammatan family's da basa cikin hotunan marigayiya mubina da sultana wacce Ke matakin karshe a jamiar cairo ." su maryam abun nema ya samu domin kuwa duk hotuna da sukai babu bata lokaci take daurawa a social media "nuzla ta samu wuri ta zauna shiru idanunta na cikowa da ruwan hawaye sakamakon tuno marigayiya mubina ,maryam ce ta lura da yanayinta ya sauya dan haka ta qaraso gareta ta zauna akan hannun kujerar da take zaune tana tmbyrta "Lafiya nuzla kika zauna shiru haka ?numfashi ta sauke tana  furta sunan "mubina...!" tun kafin ta rufe baki sai hawaye sharrr sharr!! sun zubo Kan kuncinta dan haka ta kasa qarasa maganarta , maryam ta tsuke baki tana riko hannunta cikin nata " nuzla ki daina kuka haka addua ya kamata kiyi mata alokacin da kika tunota ,wallahi koni sai data fado min arai kuma nasan gabadayanmu babu wanda bai tunata ba domin mubina ta shiga ranmu fiyye da komai ta fad'a tana goge mata hawaye "ki bar kuka haka kada sauran su fahimta kisa hankalinsu ya tashi ,wanda ya mutu babu abinda yafi bukata kamar addua kuma muna mata babu ranar da zatazo ta wuce banyiwa mubina addua ba allah ya jaddada rahma gareta ta fad'a tana mikar da nuzla tsaye suka shigo cikin sauran yan'uwa nuzla kam baa qarasa gudanar da birthday party daita ba ta wuce ." ****** Byn wata shida Sanye yake cikin kananun kaya jeans da riga t shirt tsadaddu product din American yana tsaye a haraban katanfarin estate dinsu tare da hisham hannuwansa duka zube cikin aljihun wandonsa , kallo daya zaka masa ka fahimci ransa a 'bace yake dan fuskar nan tashi babu alamun rahma sakamakon abinda ke dawainiyya da rayuwarsa , uwa Uba sweetheart dinsa dake sake hargitsa masa lissafi da batun auren data bijiro masa da yarinyar daya tsani gani a rayuwarsa dan idan yana qaunar mutuwarsa to yana qaunar yarinyar ."Suna nan tsaye hisham nayi masa magana akan sakonnin daya samu akan kasuwancinsu amman shi sam hankalinsa da natsuwar basa garesa , yana nazarin yadda rayuwa ke tangaliliya dashi da Inda zai ajiye akalar rayuwarsa, da rayuwar da mahaifiyarsa da yan'uwansa suke son yayi a yanzu ." a hankali hisham ya matsa kadan daga gefensa domin amsa kira dan yasan halinsa baya son qarar waya , ringing din wayar hisham daya fara ne ya dawo dashi haiyacinsa ya fesar da iska mai zafi daga bakinsa tare da kai Kyawawan idanunshi saitin gidansu ,maryam da muhd bello babban amininsa ya gani suna 'kokarin fitowa daga cikin gidansu wani irin mugun haushi ya kamashi zuciyarsa ta dinga zafi da tuttukin bakinciki bangaren maryam ganin in da yake tsaye suka nufa yasa bugawar da qirjinta yake ya qaru fiyye da kaida ." Mmm sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO WATTPAD @HAUESH bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page3 ......da wani irin sauri mr ATA yayi saurin d'auke kwayar idanunshi akansu yana juya baya tare da jin wani zafi mai tattare da bakin ciki, gabadaya ya rasa me Ke masa dadi arayuwarsa a halin yanzu babu fuskar daya tsani gani kamar fuskarta ."daga Inda maryam take bata sake yunkurin qara taku daya ba ta cigaba da tsayuwa a waje daya qirjinta na bugawa da matsanancin karfin gaske sbd tsananin tsoronsa ."wannan dalili yasa dole shima muhd bello ya tsaya anan suka qarasa maganarsu ta juya da sauri ta koma ciki ranta duk babu dadi kallonta nana hauwa'u tayi tace " ba dai har kin dawo ba ? ta fad'a haka ne sanin da tayi duk lokacin da suka ke'be da ya muhd bello suna daukar lokaci suna tautaunawa dan jininsu ya had'u sosai dashi ." maryam bata ce mata uffan ba tsabar bakinciki dake kunshe acikin zuciyarta nana hauwa'u ta cigaba da magana tana dubanta a tsanake "halan ya adam na waje ne naga kin shigo fuskarki wani iri ? ta'be lip's dinta tayi tana cewa " ai kema kinsani idan ba ganinsa ba me zai sa fuskata tayi haka ta sauke naunayen ajiyar zuciya " sister na rasa dalilin wannan tsana da ya adam yayi min ,wannan abu na matukar ci min rai ina jin kamar na tattara na bar gidan nan na huta da ganin irin kallon tsanar da yake min kamar ni kadai ce acikin gidan nan ? " tsana kamar ya kashe ni." "haba haba !! sister dan me zaki fadi haka?" ai ba ke kadai yakewa haka ba , ki daukeni misali ma kawai ya isa ki kwantar da hankalinki , ba ke kadai ya adam yakewa haka ba shifa tsanarsa kowa yake wa "maryam ta sake tabe lip's dinta "kowa yake wa amman wallahi nawa yafi na kowa nifa ko kallona baya qaunar yayi na rasa me na tsare masa arayuwa kamar fa ya kasheni haka nake gani acikin kwayar idanunshi nana hauwa'u tai murmushi kawai "kisan ma abinda ya qara kona min rai ne ?nana hauwa ta girgiza mata kai "alamun a'a " wai yana hangomu nida ya muhd bello mutumin nan ya juya mana baya da sauri kamar yaga wani mugun abu ,wallahi bakiji yadda na muzanta ba gabadaya kasa cigaba da tafiya nayi " nana hauwa'u ta kamota zuwa Kan kujerar da take zaune ta zaunar daita tana murmushi a hankali ta shiga kwantar mata da hankali tana kawo mata misalai iri iri dan bata son abinda zai sa maryam ta bar gidan dan ko babu komai abubuwanta na social media na sakata nishadi shiru kawai maryam tayi tana sauraronta ." muhd bello ya k'araso Inda Mr ATA yake tsaye ya Kai hannunsa d'aya ya dafa kafad'arsa ya juyo dashi a hankali ya tsura masa idanunshi fuskarsa kwance da murnushi yace "why ATA ? "me yasa kake quntatawa rayuwarka ?"me maryam ta rasa ? "me yasa bazaka bi zabin mahaifiyarka da yan'uwanka ba ? ya lumshe lumtsatsun idanunshi yana furzar da iska me zafi daga bakinsa "kasan komai akaina m.b tun daga farkon rayuwata har zuwa yanzu da nake tsaye a gabanka babu abinda baka sani ba ..." Na sani ATA ! ya fad'a yana sake matsoshi sosai " Amman at least ka duba lamarin mahaifiyarka da yan'uwanka sun dauki tsawon lokaci da baka dama amman shiru babu wani bayani amman yanzu tunda suna sonka da maryam ka amince masu ka sota ." shiru mr ATA yayi yana masa wani irin kallon up and down "ka amince masu ka sota " kwalkwa luwarsa ta maimaita masa abinda ya fad'a yanzu kafin a hankali ya kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa da yaji bugawarsa yana qaruwa sakamakon furucin muhd bello ,bai an kara ba yaji sautin muryar muhd bello ya cigaba da magana " itama maryam din bata san da maganar ba a yanayin yadda mami ke maganar zaka fahimci hukuncinta ne ta yanke akanka kuma ina da tabbacin ko tasani bazata ki ba, biyyawa kawai zatayi ta aureka koda ranta bai so "shawarata ka amince da aurenta yarinyar nan tana da natsuwa da hankali sosai bazata baka matsala ba ,sannan tana da ilimi tana da kirki daidai nata uwa Uba jininku daya daita abinda yayi ka shi yayita, shi abinda kake gani acikin rayuwarka ba lallai ya zamo gaskiya ba dan ba kowani mafar......" "Stop! "Mb don't don't !! talk anything rubbish okay ya fada a fusace yana sake fuskantarshi sosai ya rungume duka hannuwansa a faffadan qirjinsa ido cikin Ido suke kallon juna tmkr ranar suka fara ganin juna zuciyar mr ATA na wani irin tuttukin bakinciki da zafi muryarsa a zafafe ya cigaba da magana "ko kai ne Allah da zaka fad'a min haka ?" well I don't care about all what you said dan nasan da Allah na dogara ba da kai ba kuma nayi Imani bazai wuftar da lamarina ba zai cika min burina." "Na sani Allah ba zai wuftar da lamarinka ba amman dole sai kabi umarnin mahaifiyarka tukun allah zai duba lamarinka domin Allah ( swa) yace waqada rabuka alla tahbudu ila iyahu wabil walidaini ihsan sannan manzon allah (saw )sai daya ambaci abi uwa har sau uku kafin uba kaga tunda har kasan allah keyin komai to ya kamata kasa aranka kamar anyi wannan auren an gama da izinin Allah har ma na fara tsinkayo sautin muryoyinku cikin farinciki kai har ma ka durka mata ciki yan shida tana takawa da kyar kana rike da jakarta kana mata sannu ya karasa maganar cike da zolaya yana murnushin mugunta tare da dukan kafad'arsa wanda hakan yasa mr ATA sake d'aure fuskarsa sosai yana zabga masa katuwar harara ." suna cikin wannan halin hisham dake tsaye gefensu yana waya ya gama ya tura wayarsa cikin aljihunsa ya qaraso yana mikawa muhd bello hannu shima ya mika masa nasa hannun yana cewa tun dazu nake allah allah ka gama wayar kazo mu taru mu taya mami yakin karshe "akan wa kenan ?"akan wannan stupid din d'an nata mana mai shegen taurin kai kamar dutse "nan ya shiga zayyane masa halin da'ake ciki hisham ya gyada kai yana cewa "gsky mami ta yanke hukunci mai kyau sai dai muce allah ya tayaka rikon amanar maryam , dan allah friend ka amince karka zubawa mami kasa a idanunta bugu da kari aure shine cikar kimar mutun duk inda zaka shiga matsawar baka da aure wallahi kimar ka raguwa take , nima nan da kagani kokarin shawo kan nuzla nake kaga idan allah ya taimakeni ta amince kawai sai a hada bikinmu tare." Mr ATA yaja dogon tsaki ya zabga masa harara Kmr kwayar idanunshi zasuyo waje "naga alamar kai ma baka da hankali kamar wannan "ya fada tare da juya yana kiran all you of are very stupid ." Ahankali mr ATA yake daga kafafunsa batare da ya sake yin wata magana ba dan idan yace zai cigaba da magana sai dai d'ura masu zagi , yana tafiya yana sake jin bacin rai duk wanda ya gansa yasan yana cikin damuwa ,dan haka masu kula da lafiyarsa duk suka shiga hankalinsu kowa na taka tsantsa ,da sauri escort dinsa suka biyosa cikin kamewa da taka tsantsan  kiyaye aikinsu , dan duk lokacin da ransa yake a bace yafi dakatar da mutun daga aiki ." muhd bello ya biyosa suka jero tare zuwa Inda akayi parking din motocinsa escort suna kokarin bude musu murfin mota yayinda hisham ya juya ya nufi gidansu ."mr ATA na qoqrin shiga mota Kira ya shigo wayarsa ya tsaya cak hade da tura hannunsa cikin aljihunsa ya ciro wayar yana dubawa sunan aunty shahida ya gani yana yawo akan screen din wayar ya furzar da iska me zafi sannan ya danna koren maddanin ya manna wayar a kunnensa yayi shiru yana sauraronta " can bangaren aunty shahida ta fara magana saboda tasan ba magana zai yi ba "kana Ina yanzu ? shiru ya cigaba da yi yana ciza lips dinsa na kasa sai data sake maimatawa sannan ya bude bakinsa da kyar "Ina shirin barin gida yanzu "to karka kuskura ka bar gida batare da kabawa mami hakuri ba "naji zan dawo anjima da daddare dan tayi fushi sosai yanzu yayi maganar yana runtse idanunshi zuciyarsa na suya "no kaje yanzu saboda nasan ranta yayi mugun 'baci shiyasa kaji nace haka Kuma bana son tayi fushi da kai adam kasan mami na matukar hakuri damu most especially kai tana hakuri da kawaici akan komai, wannan ma ka kaita makura ne "to ni yaya kuke son nayi da rayuwata ne ? "hakuri sannan kabi umarninta ta fada atakaice "shikenan haka ni rayuwata zata qare cikin kunci Kunki ku tsaya ku fahimceni ? "Wani fahimtarka Kuma zamu tsaya yi tunda an baka lokaci Kaki kayi komai akai ?"fatanmu kayiwa mahaifiyarmu biyayya ka rike mana amanar maryam karka cutar daita sannan na tabbatar maka zakaji dadin maryam dan .."Kinga shahida karki dameni da wani amana ko zan ji dadinta kar in cutar daita "yayi saurin katseta ta hanyar fadar haka " kanku kawai kuke dubawa baka duba halin da zan shiga akan auren nan haka kawai zaku cutar dani akan wani auren baza "shahida kai tsaye ko adam ? "ta tambayesa numfashi ya sauke bai ce komai ba " kiran sunana yau babu ladabi ba komai ba ?"share wannan maganar raina ne ya baci zan zo office din na sameki idan na gama da sweetheart mu tautauna wasu abubuwa daya shafeni ," "karka sake Adam kazo min da wani tsari ko rashin kunya dan ba zan tsaya naji raayinka ba sannan kasani bazan dauki raini ba ,dan iskanci tun yaushe ake fama da kai ? shekara biyar kenan ana fama da kai ka fito da mata Kaki kullum ka zaunar da mutane kana masu karyar baka samu tru love ba ,haka kawai kanata batawa kanka lokaci abanza,tukun nama kana wannna iskanci na ji da kai da fadin rai yaushe zaka samu tru love ."?" kai wace shegiyar ce ma zata dauki wannan wulakanci da ji da Kan da kake fama dashi ? ai daman karshenka kenan ayi maka auren dole kaje can ka karata kowa ya huta dan .."bai tsaya Jin abinda zata sake cewa ba ya sauke naunayen ajiyar zuciyar yay disconnecting din Kiran Yana adduar samu sausauci daga gurin mahaifiyarsa ." ya maida wayar aljihunsa ya koma cikin gidansu a Inda ya bar sweetheart dinsa anan ya isketa zaune gefenta maryam ce ke matsa mata kafafu suna hira cike da tsantsar biyyaya kyakkyawar datjijuwa me tsananin kyau da nagarta da sanin ya kamata da son zaman lafiya da lumana ta d'ago a natse idanunta sanye da farin glass wanda da gani na Kara lafiyar idanu ne ta zuba masa Ido tana mai tsananin qaunar d'anta ."kamshin dadd'adan turarensa (Reed ) mai sanyi da sanyaya zuciya tare da Kashi jiki da sace zuciyar duk wanda sautsayi yasa ya shaka yasa maryam ta fahimci ya sake dawowa falon ,a hankali ta bar abinda take ta dago idanunta dan tabbatarwa kanta shi din ne ko kuwa , ai ganinsa tsaye kikam kamar wani jami'in tsaro ba dan kasuwa ba yasa nan take qirjinta ya shiga dokawar daya Saba a duk sanda zata d'aura idanunta akanshi sannan ta dinga kokuwa da numfashinta kenan har sanda zai bar gurin ." Ahankali idanunsu ya tsarke cikin juna wani irin kallon banza me hade da harara ya sakar mata babu shiri ta zare hannunta daga kafafun Mami ta mike tayi dakinsu ,Koda ta shiga dakin ma kasa samun natsuwar zuciya tayi ta rasa dalilin da yasa take tsatsanin Jin tsoronsa haka da Jin faduwar gaba akansa sannan ta rasa dalilin dayasa ya tsaneta haka koda bai fada mata ba tasan baya qaunarta dan tana ganin tsanarta acikin kwayar idanunshi ." bayi ta bud'e ta shiga qirjinta na dokawa ta kulle kanta dan ganinta shine Inda yafi mata saukin zama ta rarrashi zuciyarta shiru tana tunanin ta nesanta kanta dashi zai samammata kwancinyar hankali, sai dai ina hakan ma ba mai yuwa bane domin mami bazata yarda ba wani sabon tashin hankali ya caki zuciyarta nan take faduwar da gabanta ke yi ya qaru ya wuce misali hattar cikinta sai kadawa take tayi Imani a lokacin da tana da ciki tsab zai fice ya barta ." cike da ladabi da biyayya ya dan saki rashin kadan ya k'araso ya durkusa a gaban mahaifiyarsa kmr zai mata sujjada "Sweetheart! ya kira sunanta bata amsa ba ta cigaba da kallonsa "kiyiwa Allah kiyi hakuri ki bar maganar nan a tsakankanimu karki bayyanata bare kowa ya sani ita kanta yarinyar idan ta sani sannan taji rashin amincewata zataji babu dadi a ranta ," shiru hjy zulaiheart tayi taki cewa uffun har sanda ya dasa Aya " Allah ya huci zuciayrki hjy sweetheart dan nasan zuciyarki na tattare da fushina amman kiyi hakuri ki yafe min abinda nayi " yana gama fadar haka yaja bakinsa ya sake yin shiru yana sauke numfashi ,hjy zulaiheart ta kafeshi da idanunta sosai ta cigaba da kallonsa taso ya fadi fiyye da abinda ya fad'a idan ma da hali yace "ya amince da umarninta amman sai sa'banin haka yake furtawa ,ya tsaya a iya hakuri kawai da kin amincewa ."ta rasa wace irin zuciya ga Adam sam idan ya kafe akan abu ya kafe kenan is very hard ya canza ra'ayinsa wannan halin kawai tafi tsana a rayuwarsa tun yana yaro tayi iyakar kokarinta akan wannan hali abun ya cutura sai dai akan wannan lamarin ta rantse ko zai rasa ransa sai ta canzasa Kuma sai yayi abinda take bukata .. ya d'auki tsawon minti goma yana durkushe yana bawa mahaifiyarsa hakuri wanda ita ba hakuri tafi bukata daga tillon dan nata ba amincewarsa tafi bukata ,naunayen ajiyar zuciya ta sauke da karfi sannan tace "shikenan komai ya wuce na yafe maka amman ka San da sanin bazan taba janye maganata ba tunda na baka lokaci mai tsawo ka kawo min wacce kake so Kaki kullum da dramar da kake bullowa daita ayi mgn kace tru love kake jira ,dan haka bazan zuba maka Ido ba kayita zama babu iyali ba "Kai yanzu sbd Allah baka jin kunya ?duk sa'aninka sunyi aure har da yayansu abun sha'awa ? amman Kai baka wannan kasar baka wancan kasar , Neman kudi kawai kasa a gaba to meye amfanin kudin da Babu magada ? Kai da mahaifinka bai haifeka ba ka gaji tarin dukiyar daya bari ?yayi shiru yana riko tafukan hannuwanta cikin nashi dan bashi da amsar bata " ni dai gaskiya na gaji da zaman ka haka babu iyali Ina bukatar ganin ya'yanka idan Kuma kafi bukatar sai na mutu kayi auren shikenan sai na hakura na daina maka maganar amman fa kasani muddin nayi shiru yana nufi babu ni babu kai har abada ko mutuwa nayi zan bar wasiha kar abarka ka ta'ba ga....." "Dan Allah Dan girman Allah kiyi hakuri Sweetheart ki daina ambato mutuwar Nan ki rufa min asiri idan kika mutu duniyar fa bazata min dadi ba , kece duniyata, ke kike sakani farinciki idan nayi cikakken awa daya banji muryarki ba Ina rasa gane kaina inaga baki duniyar ...?"kiyi hakuri inshallahu zaki ga aurena nida auta kmr yadda kika ga na saura yanuwanmu amman ki dan bani lokaci zan kawo miki wacce nake so nan kusa ,sai byn da yayi maganar ya fahimci maganarsa ta fito ne ba a yadda ya dace ta fito ba dan ta Ina zai fara ...? "Wannan lokacin ya Kure Maka Adam har abada Babu wani sauran lokaci da zan sake baka kaje ka fara shirin aurenka da maryam kawai , tana gama fadar haka ta kawar da fuskarta gefe dan idan ba haka tayi ba zuciyarta zatayi sanyi akan tillon danta har ta fasa aiwatar da nufinta akanshi tsam ya Mike ya soma kokarin barin falon zuciyarsa na tafarfasa da tuttukin bakinciki dan yasan tunda ta kafe ta nace Babu wani sausauci baya ga amincewa kudirinta ." Kai tsaye mota ya shiga muhd bello na ganin haka Shima ya shiga bangaren daya shiga ya zauna suka bar gidan har suka hau kan titi nasiha m b ke masa me kwantar da hankalinli da ratsa zuciya sai dai ko Daya Adam bai jin zai iya saduda da auren maryam gabadaya ya maida idanunshi yana kallon motocin dake gudu akan titi yayinda kwakwaluwarsa ke tunanin neman mafuta dan dole yasan abun yi kafin ayi masa auren dole da yarinyar nan " "Adam ......"! M.b ya kira sunansa ko gezau bai yi ba bare ya nuna alamun mutun na kusa dashi bai tsaya jiran jin amsarsa sa ko akasin hk ba ya cigaba da magana "ka kasa fahimtata amman kayi hakuri kasanyawa zuciyarka sallama ,na fahimci yadda kake ji amman me kake son nayi daya wuce na tayaka yiwa mahaifiyarka biyayya ? yayi maganar kmr zai yi kuka dan ya tsani yaga damuwar amininnasa ya dafe kanshi da hannunsa daya yana dukar da kanshi tausayinsa ya kama Adam ya furzar da iska me zafi daga bakinsa sannan ya soma magana . "MB nima ka kasa fahimtata ne amman Ina da ra'ayina akan mace da nake son na ajiye agidna , muddin na auri Maryam ya zama dole na qara aure abinda bazan so faruwarsa kenan ba bama haka ba ni bani da ra'ayin ajiye mace sama da daya a gidana ."to meye dan ka ajiye sama da daya ? ka Kara mana tunda kana da abinda zaka iya rike mata ko sama da goma ne ba biyu ba ." tsaki Mr ATA yaja a lokacin da direbansa ya karya kwana yana cigaba da tukinsa ,motar tayi shiru can ya sake motsa bakinsa "mb kasan komai akaina sai dai abinda bakasani ba ni bana son auren farar mace, nafi son mace chocolate colour ita ba fara ba ita ba baqa ba sannan mara kiba wace matakin karatunta iya diploma ne sannan doguwa daidai kafad'ana ba guntuwar mace ba "Kai yanzu me zakayi da doguwa har kafad'arka sbd Allah? " yar daidai fara kmr maryam ai ta isheka rayuwa sannan a matsayinka me zaka yi da mai iya karatun diploma ga mai digree har biyu " "Zanci master's ne ? yayi masa tambayar a matukar fusace "yariyar nan babu abinda ta iya common ruwan zafi sai an daura mata ga balain son social media ,Kai ni duk bama wannan ba na tsani farar mace arayuwata ni dai chocolate itace type dina kasan Allah dana yi rayuwa da farar mace sol irin yarinyar nan gara na mutu ban yi aure ba saboda na tsaneta "subhanallah ATA ka daina fadar haka dan allah , dukkaninsu halittar Allah ne , da baki da fari duk Allah ne ya haliccesu ya tabe baki kawai yana furzar da hucin numfashi mai zafi haka suka cigaba da tafiya m.b na nusarsheshi ." Maryam yan'uwa ne da adam, da mahaifin maryam da mahaifiyar adam uwa daya uba daya maryam ce babbar diya agurin iyayenta sai kanwarta Faiza ,islaha manir , Abusufyan , Salman sai auta izzatu wacce suke kira da izza suna zaune a Abuja yayinda adam suka kasance su biyar agurin mahaifiyarsu aunty shahida itace babba Kuma ma'aikaciyar likitanci ce a babban asibitn gwanaty dake jahar lagos a ikeja ,sai aunty khadeja wacce ta kasance maaikaciyar zenith ,sai adam wanda ya kasance dan boko Kuma rikakken dan kasuwar da duniya ke ji dashi,sai aunty zabiba wacce ta kasance lactura ce a lagos state university, sai auta nana hauwa'u wacce tuni itama ta gama karatunta a London tare da maryam akan harkar compurte science , a london akwai tsananin shakuwa atsakanin nana hauwa'u da maryam Hakan yasa sanda suka kare karatu maryam ta kasa zama tare da iyayenta ta dawo suka cigaba da rayuwa gabadaya dangin mahaifiyarsu da mahaifinsa babu baki duk wanda kagani fari ne sol babu mixed ." Direban mr ATA bai tsaya akoina ba sai a haraban asibinti da aunty shahida ke aiki yana parking ya fito da sauri ya Bude masa murfin mota mr ATA ya yunkura da kyar ya fito yana gyara zaman rigarsa "friend ka bani minti ashiri yanzu zan dawo "na baka awa daya ma har ya juya m.b yace " , dan Allah friend karkayi wata ja inja da aunty kawai kace mata ka amince wani banzar kallo mr ATA ya juyo ya banka masa sannan ya juya cigaba da tafiya ." m.b yayi murnushi dan daman yasan sai ya samu tsaraban wannan kallon daga gurinsa kai tsaye office dinta ya nufa cikin takun nan nasa mutane sai kallonsa suke saboda hotunansa sun qarade koina na matsayinsa na dan kasuwar da duniya Ke ji dashi wasu kuwa tsananin kamaninsa da yaruwarasa yasa suka dinga kawo masa gaisuwa wasu ya amsa Wasu ya share barin ma idan ya fahimci yanmata ne , ya tsaya a bakin office dinta yayi knowking ta bashi izini ya shiga yana taku da kyar yana furzar da iska ." ta dago da sauri ta kallesa tana nuna masa gurin zama Dan tasan Halinsa ba karamin aikinsa bane zuciya tasa ya juya ya kama gabansa "zauna na Dan karasa abinda nake zama yayi ya daura kafarsa Daya akan Daya Yana ciza gefen lips dinsa daya zame masa jiki .byn kmr minti biyu ta tsaida abinda take ta sake dagowa ta zuba masa idanunta "Ina sauraronka wani taimako zan maka ?"kisa a fasa auren nan kawai shine babban taimako da zakiyi min ". "me yasa kake kin auren marym? shin kana da wacce kake so ne data fi Maryam komai ?ya gyada mata Kai alamun "eh ! Yana lumshe idanunsa "a Ina take Kuma su waye iyayenta ?wani mataki iyayenta suke dashi a kasar nan ko ....."? Ki tsaya iya haka ma ya isa dan ban San komai daya shafeta ba sbd ban San komai nata ba , Ina take a ina zan ganta duk bansani ba ina dai kan nemanta sai ki tayani da addua Allah yasa na ganta nan kusa kuyi min auren soyayya idan ma soyayyar zanyi kenan ." "aunty shahida na San idan na fada miki komai zaki fahimceni sbd akwai fahimta a tsakankanimu shiyasa kika ji Ina maganata Kai tsaye dake , a zahirin gsky matar da nake so na aura ni kaina na dade Ina nemanta sai dai har yanzu ban ganta ba ......"nifa ban gane nufinka ba Adam , " I mean matar da nake so ban San Inda take ba ya sake maimaita mata abinda yace "Amman dai ku bani lokaci zan cigaba da nemanta idan na ganta zan kawo muku ita ya karasa maganar tare da fito da pendat din sarka dake makale da wuyansa wanda ke hade da hoton zannen yarinyar ya nuna mata ." Shiru tayi tana kallonsa da kallon zanen yarinyar kyakkyawa ce chocolate colour " kinganta aunty ita ce rayuwata , ni dai kaina na zanata akanta na koyi Zane , ta miki kyau ko ?yayi mata tmyr yana sakar mata tsadaddaden murmushinsa wanda ba ko yaushe yake yi ba "subhanallah Adam kana hauka ne ko me ?" Taya zaka kamu da soyayyar macen da baka San Inda take ba hasalima baka taba ganinta ba ....?"Haka ne aunty Amman ta shiga zuciyata ta samu kyakkyawa mazauni acikinta shekara goma sha biyar kenan nake nemanta aunty babu Inda ban nemi yarinyar nan ba acikin garin Nan har ma da kasashe da garuruwan da nake zuwa Amman ban sameta ba ,Kai ko me kama daita Bangani ba "shine Kuma Dan hauka ka cigaba da Sonta? "ya lumshe idanunshi tare da cewa "ya zanyi haka tawa qaddarar ta kasance itama ba wai ina sonta bane amman muddin zanyi aure ita zan aura". "ka manta wannan shirmen dan har abada bazaka ganta ba dan dayawa mafarki ba gsky bane "wallahi aunty jikina na bani tana Nan a duniyar Nan shiyasa kika ga bana son na karbi auren yarinyar Nan mrym gbdy aunty shahida ta dauke maganarsa a matsayin shirme ta cigaba da kallonsa kmr wani sauna ,Taya zai ce yayi mafarki da mace Kuma Yana Saka ran tana Nan acikin duniya Kuma zai aureta sai Kuma tayi tunanin ko aljanu sun shafesa ne a take agurin tace "Adam ka sausarareni da kyau mafarki baya zama gsky ..."no aunty wannan zai zama gsky yayi mgr a fusace .... " jikinta yayi mugun mugun sanyi ta ajiye nata damuwar ta fara lallabashi dan taga alamun idan ta cigaba da mgn komai zai iya faruwa dan ya zurfafa soyayyar yarinyar sosai ya mike tsaye "ki taimakeni ki fahimtar da sweetheart ku tayani da adduar samota "aikuwa zan fada mata, a ranta tace babu adduar da zamu tayaka tunda mun san abinda muke yi har ya bar office din bata dauke idanunta akansa ba ...." Washegari aunty shahida ta shirya ta samu hjy zulai "ta Koro mata duk halin da adam yake ciki" mu tashi da addua mami saboda Adam yayi nesa cikin wata duniya ,hjy zulai ta gyada Kai cike da matsanacin fargaban tace "Allah kyauta inshallahu zan tashi tsaye da addua da Kuma sadaka lallai da alamun aljana ta auresa idan ba haka ba ga lafiyyayar yarinya me zai Yi da wata a mafarki "shine abinda nayita kokarin na fahimtar dashi yaki yarinyar Nan tunda ta taso bata da matsala ke din mahaifiyarta ce zamu shiga gidansa a duk sanda ranmu yaso, Kuma zamuyi abinda muka ga dama tunda ta muce ita ." "Allah yasa ya gane alkhairi ake binsa dashi "Ameen aunty shahida ta fada tare yiwa mami sallama har wannan lokacin Babu Wanda ya sanarwa Maryam batun aurenta da adam ana jiran sai ya amince sannan a tunkareta da batun cikin saa da jajicewar mahaifiyarsa da yayarsa mr ATA ya amince a wanni yammaci sun dade a dakin suna tautaunawa ya numfasa idanunshi a runtse ya cigaba da magana "Amman fa duk sanda na samu yarinyar da nake nema zan Kara da daita "ai wannan ba wata damuwa bane inji cewar aunty shahida ta fadi haka ne sbd tasan da wahala ya samu yarinyar mafarkinsa ita kuwa mami shiru tayi tana kallonsa a karshe ta girgiza Kai tana masa addua acikin ranta ." aunty shahida ta fito daga dakin mami tare da Mr ATA dake faman cika Yana batsewa da cicci magani bai tsaya ba ya nufi kofar fita aunty shahida tace "adam Dan Allah bari na fito ku saukeni a gurin aiki Bai ce mata uffan ba ya wuce sannan ta Kalli Inda maryam dake zaune tare da nana hauwa'u suna kallo da wayar maryam tace "Maza Maryam dauko mayafinki kizo muje kiyi min rakiya zuwa asibiti Nan take ta mike daman a shiryenta take mayafi kawai ta dauka suka fito tare , Kai tsaye Inda motar mr ATA yake suka nufa limoxin ta bude gidan baya ta shiga maryam ma tayi kokarin bude dayan bangare ,aunty shahida tayi saurin cewa "zauna a tsakiya kusa da adam maryam taji maganar wani iri ta dan saci kallon aunty shahida tana mamakin jin furucinta" zauna a tsakiya kusa da adam to me hakan yake nufi?Tana son tai tmby babu hali dan haka  jikin a sanyaye ta bude ta shiga ta zauna nesa dashi kamar wata tsuntsuwa ta kame Kanta tana jin mummunar faduwar gaba from no where " . Direban mr ATA ya ta-da motar suka soma kokarin fitowa daga cikin gidansu "Ina muka nufa ma kika ce ? ita Kuma wannan ina zaki daita nifa bana son kwashe kwashe a motata? asibiti ta bashi amsa duk da tasan yaji abinda tace , bai sake cewa komai ba har suka iso asibiti ,yaki fitowa Yana jiran aunty shahida ta karasa fitowa dan maryam tuni ta fito "adam muje akwai sakon da zan baka yayi shiru yana maimata maganarta yaji Kmr yace ta bawa mrym ta kawo masa Amman Kuma baya son abinda zai hadashi da yarinyar "a hankali ya fito ransa a bace Kai tsaye office dinta suka nufa aunty shahida ta bude office dinta dukkaninsu suka shiga Yayinda mr ATA ya tsaya daga bakin kofa yana jiran ta bashi sakon da tace aunty shahida tace "bismilla mana ranka shi dade mr ATA shigo ka zauna  ga guri nan yayi mata wani irin kallo yana bukatar qarin bayani akan abinda ta keyi "ta gyada masa kai "shigo mana ." da kyar mr ATA ya shigo office din ya zauna yana hura hanci sannan itama maryam ta samu guri ta zauna tana satar kallon fuskarsa kwata kwata babu digon annuri ," " Maryam tashi ki bude fridge ki dauko masa ruwa dan nasan bai fiyye shan lemo ba ,ta mike a hankali ta karasa ta dauko masa ta ajiye a gabansa ta koma ta zauna gabanta na faduwa "ka bani minti goma kawai zan duba wani fayal ne yanzu zan gama sannan ta soma aiki tsaki yaja a ransa dan dai tana da matsayin aunty shi ce if not bai ga dalilin da zai yita batawa kanshi lokaci ba akaron banza ba ."baka sha ruwan ba ?ta dago ta tambayesa cike da kulawa "no need !ya bata amsa ataikaice byn kmr minti biyu ta mike ta fita tace "kanina ina zuwa "zuciya ta sake kawo masa wuya sakamakon barinsa da zatai yi shi da wannan guntuwar yarinyar mai siffar aljanu yaja tsaki yana dafe goshinsa da hannunsa ." Zamansu daga ita sai shi acikin office din baqaramin tashin hankali maryam ta shiga ba ,gbdy duk ta rude sai zufa take fitarwa da zarar tayi kamar zata dago ta kalleshi sai  ta kasa dan gbdy ta nemi natsuwarta ta rasa ji take kamar zuciyarta zata buga allah allah take Aunty shahida ta shigo domin bazata iya cigaba da irin wannan zaman ba ,minti biyar kawai Aunty shahida tayi  da fita amman ganin take Kmr awa biyar tayi da barin office din ,shi kuwa  mr ATA banda tsaki babu abinda yake yana qarawa domin ya fara gajiya da zamansa tare da abinda yafi tsana arayuwarsa ." Aunty shahida na fita ko cikakken minti goma batai yi ba sai ga nuzla ta shigo office din bakinta dauke da sunan Aunty shahida,turus tayi sakamakon ganin maryam zaune gefe guda kuma mr ATA ne zaune kallon tsoro tayi masa ta dauke kanta tana gaishesa bai amsa mata ba kamar sauran lukuta ta qarasa ta dafa maryam "marsi ina Aunty shahida ."? "ta dan fita amman tace bazata jima ba ki jirata , "okay da ido tayi mata tmby me ya Adam yake yi ? itama da kwayar idanunta ta bata amsa da bata sani ba dan babu damar ayi magana mai sauti kasamcewar sun san baya son hayaniyar komai saurin ciro wayarta tayi ta maida silet ." sadiya wacce ta kasance me koyon aiki ce a asibiti ta shigo bakinta dauke da sallama "Assalamu alai...... kasa karasa sallamar tayi sakamakon gani mr ATA zaune idanunshi na kallon screen din wayarsa sanye cikin kanan kaya ,gbdy ta rikice akansa madadin ta karasa ta ajiye file din dake hannunta ta kasa ko daga dan yatsan kafarta garin kallonsa ma har file din hannunta ya subuce daga hannunta ya fadi kasa da sauri ta tsugunna ta dauka jikinta na rawa ta karasa ta ajiye fayal din akan table ,tana faman kallonsa  sai lokacin ta lura da maryam dake zaune  tana kallon yatsun hannunta yayinda nuzla ke tsaye a gefenta "sannuku da hutawa ta furta a hankali ." maryam ta dago tana murnushi tace "yauwa ya kokari ? alhamdulillah sadear ta bata amsa tana kallon nuzla sannan ta fita tana waiwayen Mr ATA tana yaba kyawunsa acikin ranta shi kuwa Mr ATA ko ajikinsa dan iskar ma data debota bai gani ba idan da sabo ya rigada ya saba  da irin kallon da suke masa haka ma kallon da mrym da nuzla Ke masa bai sa ya dago daga duban wayarsa da yake ba . Nurse sadiya na fita daga office suka ci Karo da husaina itama maakaciya ce "ke lafiyarki kika fito a hargitse Kmr wacce aka koro ?"uhm ke dai bari husseina wani matashi na gani a office din doctor shahida mutumin yayi min kyau matuka ya dauki hankalina wallahi irin mijin da nake nema kenan mijin duniya Mijin novel ya hadu sosai da gani yana da kudi yana da tarin ilimin boko da Arabic uwa Uba kyau "ke sadear raba kanki da wahala, kina diyar talaka dake naci ma da kyar kuke samu kullum Kuna yawo a gidan haya , yayanki ma da kyar yake daukar dawiniyarki Amman kin kashe kanki da mugun buri  , ki roki Allah idan yaga dama zai Baki ki Daina zafafa burin akan auren me kudi ." sadear ta Dan turo mata karamin Bakinta tana yatsina fuskar ,jikin Sadia yayi sanyi sosai husaina taja tsaki ta wuce ta barta Nan tsaye tana maganar a fili ." Wayar hannunsa da yake ta faman daddanawa ce ta dauki qara ya manna a kunnensa tare da zamowa kad'an daga Kan kujerar da yake zaune yana lumshe idanunshi "na barota a gida ne ,okay suna bukatar  new design's da kaya ?shikenan ki  bawa kwararrun wadan da suka iya domin  bana son a samu matsalar komai aikinsu  dan last time sunyi complain okay may be tomorrow  yana magana yana lumshe idanuwa yana lasar lip's dinsa  na kasa ." uzla,maryam duk suka zuba masa idanunsu suna kallonsa kowacce da abinda zuciyarta take saqawa jikinsa ya bashi  kallonsa  suke dan haka ya tsaida  lumtsatsun idanunshi akansu  yana masu wani irin kaskantacce kallo  sannan ya dauke kansa ya cigaba da waya a daidai lokacin da husseina da sadiya suka shigo tare ita kanta husseina ta jinjinawa kyawunsa dan sai da tabawa idanunta abinci suka dauki abinda ya shigo dasu suka juya ." Ya sake tsaida idanunshi akansu ganin still shi din suke kallo har lokacin Kmr basu san shi ba wani irin taikaci ya kamashi dan baya son yawon kallo arayuwarsa wani abu ya hadiye mai daci a makoshinsa kafin ahankali yaja tsaki yana cigaba da kallonsu yayinda su kuwa a matukar firgice suke kallonsa cikin tsananin tsoro da firgici sam basuyi tsamanin zai sake  kamasu suna kallonsa ba irin kallon da yake masu yasa suka sake shiga rudani dan basu san abinda zai biyo bayan kallon da yake masu ba sannan basu abinda zasu fad'a dan kare kansu ba nuzla ta kalli maryam itama ta kalleta gabadaya jikinsu ya kama rawa nuzla tayi saurin durkushewa kasa bisa gwiwowinta dan tasan na lahira zai fisu jin dadi idan bata hanzarta bashi hakuri ba dan taga maryam bata da alamar bada hakuri "ka..! kayi hakuri ya Adam magana yake son yi amma ina  jin isa acikin ransa yasa ya gagara furta komai illa kafarsa daya daya shiga jijigawa yana takaici ." ganin har kusan minti talatin aunty shahida bata dawo ba yasa mr ATA ya Mike a fusace ya tura hannunsa daya cikin aljihunsa ya bar office din dan jikinsa ya fara bashi so take ta hadasu da Maryam ta fayyace mata komai a gabansa,yana fita nuzla  ta nufi kofa cikin sand'a itama mrym ta biyo bayanta, nuzla  na gama bude kofar turus  sukai yi sakamakon ganin sadiya da husseina tsaye rungume  da file suna kallon byn mrs ATA suna magana can kasa kasa sakamakon mutanen dake kai kawo " ai wannan ba bakon fuska bane sadiya matashin dan kasuwan nan ne  da duniya Ke ji dashi  sannan kani ne ga sister shahida  yana zuwa lokaci zuwa lokaci ke baki ga kamarsu ba "?lallai kam sai yanzu na ganesa ko dan na rikice ne amman yafi kyau a fili km suna matukar kama sosai da Sister shahida sai dai har ya fita kyau ,wallahi husseina mutumin nan ya shiga raina sosai ban ta'ba ganin halittar daya dauki hankalina ba  kamarsa komai nashi irin mafarkina "uhm uhm sadiya na sha gaya miki ki daina irin wannan hange  ki tsaya matsayinki kin kasa fahimtata ."kisani babu abinda allah bayayi bansan dalili  ba gani daya nayi masa amman na kamu da matsanancin soyayyarsa  " wallahi wannan yafi karfinki Ke ko yaronsa yafi karfinki bareshi  idan zaki dawo haiyacinki ki dawo taja hannunta sukai wuce  sadiya na juya bayanta ." Naunayen ajiyar zuciya nuzla da maryam suka sauke atare suna dafe qirji "marsi wallahi ba qaramin tsorata nayi ba ,koni kusan nafiki tsorata wallahi kadan ya rage ban saki fitsari ajiki ba qaramin saa muka ci ba da yau mun sha maruka suka kwashe da dariya "kinga bari na wuce bazan iya jiran Aunty shahida ba daman nazo karban test din hjyrmu ne nace nazo mu gaisa kinga wucewata sai mun hadu a gida ta zame hannunta dake cikin na maryam ta wuce tana daga mata hannu , maryam ta koma cikin office zaman jiran Aunty shahida ." Bai Dade da wucewa ba doctor shahida ta dawo ta ga wayam bashi Babu alamunsa "sarkin zuciya halan ya gaji ya wuce "eh Maryam ta fada muryarta a sanyaye "okay ta shiga tattara kayayyankinta muje kou daman akwai maganar dana so muyi mu uku Amman zanzo gobe inshallahu idan na tashi daga aiki muyi a gida "magana kuma aunty.?"ta tmbyeta a tsaro ce . "Eh! " wacce magana ce haka Kuma har da ya adam zaayi ?aunty shahida tace ",magana ce me mahimmam ci , dan girman Allah aunty shahida wallahi bana son duk abinda zai hadani dashi nifa tsoro yake bani culmdown my sister ki cire wannan tsoro ba wani Abu bane face alkhairi shiru mrym tayi tana nazarin maganar aunty da tunanin wacce magana ce wannan da har sai anyita da ya Adam Kuma tace alkhairi ne ...? suna fitowa haraban asibinti suga direbansa na jiransu "a ruwa Ina mai gidanka ? sai daya rusuna mata sannan yace "ya kira anzo an daukesa da wata motar aunty shahida ta girgiza Kai ta shiga mota ita da maryam inda take fad'a mata zuwan nuzla "Ayya kanwata ai kuwa na gode sosai itama kuwa ina son ganinta nan hankalin maryam ya dan kwanta jin har da nuzla sai dai har sanda a ruwa ya sauke aunty shahida a kofar gidanta zuciyar mrym bata bar Saka da warwara ba Allah Allah take gobe tayi taji ko meye .." washegari da misalin karfe goma na safe sakon mutuwar sadiya ne ya riski doctor shahida, tayi matukar firgita da Jin wannan mummunar labari saboda cewar da akayi yankar rago akayi mata ta zabura ta mike daga zaunen da take jikinta na rawa ......." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH Arewabooks username Ayshabagudo bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page4 "Wani  irin   gumi  ke tsatsafowa   ajikin  aunty  shahida   yayinda zuciyarta  ta  dinga bugawa da  karfi  fiyye  da  kaida ,nan  take ta mike tsaye ta shiga zariya  a office   ta kasa  zaune ta kasa tsaye  tana  sake jin wani sabon tashin hankali   tana cikin wannan halin sai ga doctor  sa'a   ta shigo  a  rud'e  ta tsaya  suna  kallon  juna  yanayin  doctor  shahida  ya  tabbatar  mata taji abinda  ya  shigo daita office  din  dan  duk ta fita  haiyacinta ,a matukar  tsorace  aunty  shahida  take kallonta qirjinta  na  dokawa  "nasan  kinji  abinda  ya  shigo dani ? wai  an yiwa  sadear  yankan rago a gidansu." har  lokacin  fargaba da  tashin hankali bai bar gangar  jikin  aunty  shahida  ba ,da kyar  ta iya motsa labbanta  "yanzu   doctor zinnira  ta kirani   take  fad'a min wannan mummunar tashin hankali alamarin nan ya  d'aure  min Kai  matuka , hakika  mutuwar  sadear  ya gigitani  jiya  fa  iwar haka muna  tare  daita  har  tana  cewa  zatayi magana mai mahimmanci  dani yau idan mun had'u ko me  zata  fada  min ? ta   k'arasa  maganar idanunta na ciccikowa da ruwan  hawaye "gbdy  mutuwar  mubina ce ta dawo  min , Allah sarki rayuwa , Allah  ya  jikansu ya  tona asirin duk wanda yayi  sanadiyyar  barinsu duniya  , "duniyar  nan ma guda nawa take da zaka kashe dan'uwanka ?cewar  doctor sa'a  "ya  kamata  muje gidansu   yanzu ko ? "Eh ! wannan  gaskiya  ne ya kamata muje " da sauri aunty  shahida ta tattara abubuwanta dan bata   Jin  zata dawo asibiti  daga can gidan hajiya  zata  wuce doctor sa'a  ta  nufi  kofar  fita itama  aunty  shahida ta biyo bayanta da s auri ta rufa mata baya suka jera tana kokarin neman number doctor  zinnira  suje tare ." "Kai  tsaye gidansu sadear    dake  ijora olopa suka  nufa   a kofar  gidan  suka  iske 'yansanda   suna tambayar  aminu   yayan   sadear  yadda  abun ya kasance  "to ni dai bazan qarar da komai  ba , kawai  dai na  tashi da asuba  na shiga d'akinta  Inda take kwana tare da yarana guda  biyu  domin suyi sallah kawai   naga gawarta   cikin   jini  amman  babban yarona  sadi  yace  yaga  bayan matar Kuma ya ganeta   duk  da   jikinta lullube yake da  bakin  kaya  ba'a iya  ganin  komai   nata ".ya qarasa maganar Idanunshi  na  sauya kala." yauwa haka muke so yanzu    Ina  yaron yake ?  police  officer ya tambayi aminu yana gyara tsayuwarsa "  kan aminu  na kasa  hawaye  na tsiyaya daga idanunshi  cikin rawar murya  yace "yana  ciki   gida  " girgiza Kai  aunty  shahida  tayi  cike da  tausayawa masa   ,." a tsanake  suka   gaisa   sannan     gbdy   suka had'a  baki  da doctor sa'a  da  dr   zinnira sukai masa gaisuwa   "aminu  ya  qarin  hakurinmu  Allah  ya  jikan sadear Allah  yayi  mata  rahma halinta na gari ya bita  "Ameen  ya   Allah , na gode  Allah  ya  bada  lada  "Allah  ya  tona  asiri duk wanda keda  sa  hannu  a kisan sadear  ya sake amsawa da" amen na gode Kwarai da gaske yana kukan an cucesa an rabashi da yar'uwarsa tilo ,  a  lisafinsa  yanzu   tayi  awa hud'u  a  kabarinta   shiru yayi yana juya girman  alamrin zuciyarsa na zafin da bai san ranar dainawa ba ." "Nan su aunty shahida   suka  barsu tsaye suka  shiga  cikin  gidan suka nufi  bangaren   yayan  sadear Inda  suka tadda  tsirarun  mutane zaune  a  cikin d'akin ana karba gaisuwa  ,a natse  suka  gaisa  da mutane tare da yi musu  gaisuwa   suka  zauna  Inda  ake  ta jimamin mutuwar kowa  na fad'ar  albarkacin bakinsa  ,wasu  na cewa ai  hadiza ce ta kasheta tunda  daman  ta furta cewar itace zataga bayanta a bayyanan  nasi    ,yayinda wasu na cewa  ba  lallai  bane ya kasance itace ta kasheta ." Suna  zaune  police officers suka shigo tare da aminu da yaronsa  sadi dan kimani shekaru goma shabiyu yana musu bayanin wacce ya gani ." 'yansanda na  sauraron  yaron   daki daki gefe  guda kuma  suna  dudduba   gidan  a karshe suka tsaya a kofar   d'akinsu  hadiza   tare   da   tambayar   wacce   ake   zargi da aikata kisan ." batare da 'bata lokaci ba akayi sallama a bakin kofar  d'akinsu, hadiza  kam  tunda taji sallama police  cikinta ya duri ruwa ta soma juya Kai zuciyarta  na  tsinkewa    dan tunda  akayi mutuwar take  cikin  tsoro da matsanacin  firgici mara iyaka gabadaya komai nata ya tsaya cak ."mahaifiyarta  ce  ta amsa   sallamar  tana fitowa daga  cikin  d'akin "muna son ganin hadiza ko  tana  ciki ?"."eh  ! tana ciki   ta fad'a muryarta na d'an rawa  "hadiza  ki fito ana son  ganinki  da  kyar hadiza  ta  fito kamar wacce  kwai ya fashewa aciki   ta tsaya a bakin kofar  d'akinsu , kana kallonta  zaka fahimci  a tsorace take , sai da suka mata duban tsanake sannan daya daga cikin police  din yace "kece  hadiza  ko ? ta  gyada masa Kai alamun "eh! gabanta na faduwa da sauri da sauri suka ce "muje akwai wasu tambayoyi da zamu miki a office dinmu ." "akan wani laifi kenan?   mahaifiyarta  tayi  karfin halin tambayarsu".  idan  muje office dinmu   kwaji   akan wani laifi ne " suka  tasa  keyarta gaba mahaifiyarta   ta biyosu  da sauri  tana cewa "bazan bari  ku tafi min da yarinya ba ku zubar mata da  mutunci  ba ." jin maganar  mahaifiyarta yasa  hadiza ta tsaya cak  taki  cigaba da tafiya police suka ce "muje ko!" "shiru  tayi  jikinta  na rawa  taki motsawa daga Inda  take   aiko daya daga cikin  yar sanda mace ta rike tsintsiyar hannunta "zaki   da girma da arziki ko kuwa mu tafi dake ta karfin tsiya  ? "cike da tashin hankali hadiza ta  fixge hannunta daga hannun yarsanda  tare da marairaice  fuska  kamar zatayi kuka "ni bazani koina ba har sai na san dalilin da yasa zaku tafi dani office dinku ". zata sake magana suka daura bakin bindiga keyarta "idan kika sake furta wata Kalma zamu sakar miki  wuta  mu tasheki aiki," oya  muje  "tsimi tsimi  hadiza ta soma tafiya  mutane  gidan na kallonta  cikin tsananin farinciki dan daman taadabi kowa acikin gidan  kowa tsoronta  yake ." "wani mummunar tashin hankali   ya   shigi mahaifiyar  hadiza  da hadizan  karon kanta, ana  k'okarin turata cikin motar  'yansanda su aunty  shahida  suka  fito suka   kama   gabansu zuciyoyinsu   cike  da tsoro  da  fargaba ,direban  aunty shahida ya  sauketa a kofar gidansu  sannan  ta bashi   umarnin   ya kai  doctor   sa'a  da zinnira ya dawo, suka yi sallama da abokan aikinta  da  zumar  sai  sun had'u gobe , Jiki  a sanyaye  aunty shahida  ta  shiga  cikin tangamemen  falon mahaifiyarta  parlour'n   shiru babu   alamun  akwai wani  bil adama   acikinsa  hatta    'yan aikin  gidan bata  ji motsinsu  ba ." Ta samu  guri  ta  zauna  jagwab  akan d'aya  daga cikin kujerun Parlour'n   tana sauke ajiyar zuciya har lokacin wani iri take ji ajikinta , shiru parlour'n   baka Jin motsin komai sai na AC  dake aiki a falon  . ko cikakken    minti   biyar batayi ba ta fara Jin motsin mutane , ta d'ago a hankali  masu aiki ta gani cikin shigarsu ta kullum  dukkaninsu rike da farantin silver suka rusuna tare da had'a baki "barka da zuwa hajiya "barka sannuku  ya aiki ?" "alhamdulillah !   suka amsa tare da ajiye tire suna tambayar abinda za'a kawo mata  " me za'a  kawo miki hjy  akwai rice and stew akwai tuwon shekafa akwai dabmu  shimkafa akwai ......? "duk  babu wanda zanci aciki ta fada tana runtse idanunta dan kanta wani irin sarawa yake kmr ana buga mata guduma  ,tana nan zaune hajiya zulaiheart ta shigo cikin shigar alfarma doguwar rigar lace  har kasa wanda kimanin kudinsa ya Kai 500k ta zauna akan kujera mai zaman mutun d'aya  tayi shiru  tana duban fuskar babbar diyarta "lafiya  shahida duk na ganki haka ?a hankali ta bud'e idanunta ta saukesu  akan  hajiya zulaiheart   "wallahi  mami wata mutuwa akayi mana agurin aiki mai shiga jiki ko ince an kashe yarinyar  ......" "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun oh ni zulai me mutane suka d'auki rayukan mutane ne yanzu kashe mutun bai musu wahala ?"wallahi mami sai ma Kinga yayan yarinyar abun tausayi marayu ne babu uwa babu uba sai Allah abun daya fi d'aga min hankali yankar rago akawa yarinyar abun tausayi sam babu Imani a zukatan  wasu  mutane taya zan iya kashe mutun da hannuna ?ta karasa maganar hawaye na zubo mata."uhm  duniya  kenan  Allah dai ya tona asiri ko suwaye  suke bin ya'yan mutane  har gida suna kashesu to Kalli mutuwar mubina kigani abu kamar wasa har an kusan shekara biyu amman har yanzu babu labarin wanda yayi kisan." Allah dai ya kyauta sam kasar nan babu tsaro shiyasa  nasa aka qara  tsaro mai karfi a gidan nan." "hajiya ai ita sadear ana zargin makwafciyarsu ce tabi dare ta  kasheta yanzu haka maganar da nake miki tana hannu jami'an tsaro zasu fara bincike akanta  "alhamdulillah ai gara kam ita kuwa me yayi zafi haka ko akan me zata kasheta  ?mutumin  duniya   hjy ai  ba'a  iya mutumin  duniya sai Allah daya haliccesa, Allah dai ya sawaka kawai zamuce ." "Ameen inji cewar hjy "wai  Ina maryam  da  auta suka shige ne ? sunje gidan zabiba amman dai nasan zuwa la'asar idan anci sa'a babu traffic zaki gansu sun dawo " Anya kuwa zan jira har wannan lokacin ? bari kawai nazo na wuce  gida ." "kin kuwa fada ma maryam   batun wannan sarkin zuciya ?"wallahi a'a jiya dai  nayi kokarin had'asu  gbdy a office dina  sai Kuma hakan bai yiwu ba ga yau ma ,Ina ganin sai dai weekend  zanzo  dan gbdy  jina nake wani iri, wallahi  mutuwar nan  ta shigeni  yarinya mai kirki da biyyaya  da sanin ya kamata  sam sadear bata da matsala a rayuwarta  sannan bata da abokin fada kowa nata ne agurin aiki  ga wasa  da  dariya ga ..."kira ne ya shigo wayar aunty shahida wanda yayi sanadiyyar katse mata magana  ta d'auka tana duba screen din wayar  direbanta  ne mlm garba  dan  haka ta mike  ta d'auki jakarta tayi wa hjy zulaiheart sallama ko a gidanta  ma kasa tabuka komai tayi babbar  yarinyarta madina duk  ta damu sai  faman tambayarta take ta fada abinda ke damunta bata ,boye mata komai ba ta fada mata mutuwar , mutuwar tsaye madina tayi dafe da qirji dan tasan sadear sosai tana janta ajiki idan taje gurin mamanta ,addua tayi mata hawaye na zubawa aunty shahida lokacin da take tuna moment dinsu da yarinya babu abinda yafi daga mata hankali kamar maganar da tace zasuyi a yau din gashi ta mutu batare da san ko akan me zata mata magana ba kwarai  taso tasan ko akan meye , Allah sarki rayuwa  kenan ta dade zaune tana jimamin mutuwar sadear   kafin daga baya ta mike ta shiga dakinta ta kwanta zuciya da gangar jikinta na mata ciwo    .." Har  yansanda  suka karasa office dinsu  kuka hadiza take , aka  nufi d'akin  bincike daita aka nuna mata gurin zama sannan  bayan kamar awa daya wasu qararrun 'yan sanda suka shigo nan suka fara Aiko mata da tambayoyi d'aya daga cikinsu tace  "ko zamu iya sanin dalilin da yasa kika kashe  makwafciyarki sadear ? hadiza taji tambayar tamkar saukar aradu take idanun  sukayo waje  tare da dafe qirjinta "wallahi  bani na kasheta ba nima tashi nayi naji labarin mutuwarta ,"karki wahalar da hukuma zai fiyye miki sauki ki fito ki fada mana gskiya kunyi fad'a da sadear ko ba haka ? cikin tsananin firgici da tsinkewar zuciya tattare da tsoro ta  gyada Kai  alamun "Eh!"can km  ta girgiza musu  Kai alamun "a'a!   police ta gyada Kai sannan ta cigaba "kenan kina nufin babu wata matsala ko fada wacce tasa kukayi sa'insa daita ? nan ma ta gyada Kai alamun babu cikin kankanin lokaci ta fita haiyacinta saboda  tambayoyin  da suka dinga mata tana  kare  kanta   a karshe daya daga cikin police mace tace ' kinyi furucin zaki kasheta Kuma kinyi nasara ko ba haka ba ?ta girgiza kanta alamun a'a juyin duniya akayi da hadiza amman  ta tsaya akan ba itace ta kashe sadear ba  suka  barta tare da turata  wani d'aki tana shiga taji an rufeta da duka cikin kankanin lokaci kamanin   hadiza ya sauya tayi laushi  sosai tana ihu tana Komai aka shiga daita wani daki aka garkame . tayi kuka sosai idan ka ganta sai ta baka tausayi gabadaya ta tabbatarwa kanta tata takare Ina ma batayi fad'a da sadear ba ,a she da me kararen kwana tayi fada ? wayyo Allah ni hadiza kaicona me ya kaini fada da gawa  ....?yau dai ga Inda karshen wahalana ya kawoni ni hadiza nayi nadama   ,nayi danasani ban bar yara ba ,ban bar  manya ba ,ban bar matan aure ba, ban bar tsofafi  ba , ga dai karshena ban san me gobe zata haifar ba  ta karasa maganar tana matso ruwan hawaye mai zafi daga idanunta ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗    MAR'ADAMS    💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH Arewabooks username Ayshabagudo bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page5 " da  misalin karfe   tara  na daren ranar Juma'a mr ATA ya fito daga bathroom jikinsa sanye da  rigar wanka iya gwiwarsa yayinda hannunsa  d'aya ke rike da white towel yana goge kanshi  zuwa  wuyansa ,ahankali ya  qarasa  gaban mirrow ya tsaya  yana kallon  kyakkyawar  fuskarsa  yana qoqarin zare  rigar jikinsa ."shiru yayi yana kallon faffad'an qirjinsa dake  kwance da  laulausan suma tamkar na jariri sabuwar  haihuwa ga Kan nipple's dinsa a tsaye makale da  qirjinsa sai sheki suke, babu lafiyayyar macen da zata gansa a haka bataji sha'awarta ta motsa ba  saboda kyawun cikar halittar da allah yayi masa ." kusan minti goma ya dauka tsaye  yana qarewa kansa kallo kafin  daga bisani ya juya  a natse ya koma  bathroom ." ko  cikakken  second  uku bai yi ba ya fito  ya  d'auki  kwalbar bodyspry ya feshe ilahirin  jikinsa ya saka white singlet boxer's sannan ya shirya cikin wasu hadaddun kananan kaya t shirt fari sol da dogon  wando  baki , ya kai hannu inda tsadadden   Turarensa  (Reed ) yake ya d'auka ya feshe kayan jikinsa , ta  koina a sansar jikinsa kamshi yake tashi mai sanyi da tada tsumin shaawa."  ya ajiye kwalbar turaren a mazauninsa yasa  hannun ya kwashe wayoyin  business  dinsa guda biyu ya juya  ya fito daga cikin dakin tare da janyo  kofa ." a natse  yake saukowa daga Kan matattakala bene  hannunsa daya soke  cikin aljihun wondonsa  kai  tsaye  yana  gama saukowa ya  qarasa  dining  area ya  zauna akan d'aya daga cikin kujerun  dining yana sauke numfashi kana ya ajiye wayoyinsa akan table ."ahankali sanyin ac dake aiki a parlour'n ya dinga ratsa sansar jikinsa ,lumshe lumtsatsun idanunshi yayi yana ciza gefen lip's dinsa , cikin haka mami ta fito daga kitchen ta soma hidimar  zuba  masa abinci  ,dan shi baya son masu aiki na shiga  huruminsa saboda  Allah yayi shi  mai tsananin tsabta da kyakyami , shiyasa ba koina yake cin abinci ba, ko fuskar abinci ya kalla yaga yayi wani iri to komai za'a yi  bazai ci ba shiyasa duk sanda zai ci wani abu mahaifiyarsa ce kadai ke masa hidima  abinci wannan halin kuwa ya samo ne daga gurin kankansa alhaji abdallah dan shima ba abincin kowa yake ci ba sai wanda yayi masa  ." bayan ta zuba masa jollof din shikafa yar waje wacce taji pepper chicken  ta hada masa coffee dinsa na gado ta ajiye masa a gabansa sannan  ta koma ta zauna a kujerar dake fuskantarsa tana dubansa a tsanake tace  "kasan wani abu my love ? ta tambayesa idanunta na kanshi ya d'an girgiza mata kansa batare da yace komai ba sai ma lumshe lumtsatsun idanunshi  da yayi yana jiran yaji me zatace .Allah  Allah !!nake  kayi  aure  na huta da yi maka hidima "shiru yayi bai yi magana ba yana jiran yaji spoon din abinci bakinsa amman  yaji shiru har tsawon second goma sai ma maganar aure da yaji ta cigaba dayi masa wanda hakan Ke mugun bata masa rai tare da dagula masa lissafi dan a halin yanzu idan akwai abinda yafi tsana bai wuce maganar auren da take bukatar yayi ba gashi burinta ba abu bane dake cikin lissafinsa ." shiru yay har wata second biyar tazo ta wuce bai ga alamun tana da niyyar bashi abinci ba dan haka ya bud'e lumtsatsun idanuwanshi a hankali ya tsura mata yana kallonta fuskarsa a shagwabe kamar koda yaushe idan yana gabanta  "kana wani kallona da wad'an nan idanuwan naka masu firgita mutane ai gsky na fad'a ina bukatar na huta da maka hidima ." muryarsa a kasalance ta fito tamkar mai koyon  magana  "haba my sweetheart ki daina fadar haka mana yanzu baki jin tsoron wani yaji kina cewa kin gaji dani ?ni bance na gaji da kai ba karka canza min magana hidima nace ta fad'a tana hararasa wanda da gani na soyayya ce." ya sauke naunayen ajiyar zuciya still kwayar idanunshi na kanta sai daya numfasa sannan ya sake motsa lip's dinsa "sweetheart ! ya kira sunanta a shagwabe ta kalleshi kawai tana jiran taji abinda zai ce " ai ko na yi aure bazan daina cin abinci  daga hannunki ba domin dashi na saba ." "Ina bazan yarda da wannan tsarin ba dan bazan shiga hurumi da ba nawa ba ,wannan hurumin matarka ce yana da kyau idan mutun yayi aure ya samarwa matarsa farinciki , hurumin mahaifiya dabam haka zalika na mata da  dabam , dan haka kasa wannan a ranka da zarar kayi aure babu  Kai babu cin abinci daga hannuna ." ta karasa maganar tana murmushin jin dadi jin bai ki maganar data fad'a ba ga dukkanin alamun dai yayi amanna da zabinta dan haka ta dauki spoon ta soma bashi abinci a baki tana kallonsa cike da tsantsar kulawa "kinsan  wani abu sweetheart  ? ta tsura masa Ido kawai batare data ce Komai ba dan ta lura yana cikin farinciki shima ita yake kallo cike da matsanacin soyayyarta , anan duniya bashi da kamarta ita kadai yake kallo yaji duk tarin damuwarsa ta Kau." "wallahi idan Ina cin abinda  kika sarrafa wani farinciki nake tsintar kaina ciki , nifa ganin nake ko Allah ya qaddaro nayi aure to kece zaki dinga girka min abinci , dan  abincin my sweetheart  babu sauki akwai dadin  dandano dan zai iya sa mutun ya cire kansa ya bayar kyauta ."ta sake yin murnushin jin dadi  tana zabga masa harara "Kai ko Allah naki wayon." ahankali yake cin abinci suna hira cike da so da qauna dake tsakanin uwa da d'a suna cikin haka auta  ta shigo bakinta d'auke da sallama ta zauna a kusa da mami  tana Kiran "washhhhhh Allah nah na gaji sannan ta maida hankalinta gurin mr ATA "Ina yini  yaya ? "Lafiya ! ya fad'a atakaice yana sake tamke fuska sosai ,  ta maida hankalinta kan wayarta tana chart "wai ke auta idan kina gida baki da wani aiki ne sai rike waya baki istergram baki facebook baki what's app ? Ko karfe daya na dare na hau online sai na ganki ."yayi maganar a can kasan makoshi sam bazakace shi yay maganar ba tsabar miskilanci ." "wallahi kamar kasani son ita da maryam sam basa gajiya da rike waya da daukar hotuna kamar masu aljanu , wad'an nan duk randa aka daina amfani da waya a kasar nan ban san yadda zasu dawo ba " wallahi kuwa mami akwai matsala nana hauwa'u ta fada tana cewa "shekaranjiya fa muna zaune wayar maryam ta d'auke wuta kamar almara kinsan a daren sai da taje aka gyara mata, ai wallahi garani sau dubu akan maryam tunda ta sako sunan maryam ya d'auke wuta dip kamar anyi ruwa an dauke ya maida hankalinsa kacokan a kan wayarsa dake qara ya d'auka ya manna a kunne yana maganar million kudade da zasu fita da wadan da zasu shigo ." "babu gara auta  dake daita duk d'aya ne ,ku dai rage son duniya dan gidan wasu zaku ba kowani namiji ke son irin wannan rayuwar ba , sannan lokacinku kuke ci bamu San sanda mutuwa zata zo ba , suna cikin mgn maryam ta shigo da sallama  sanye da riga da wando na bacci ash colour masu yanayi dana sanye sai dai su anyisu ne dan bacci , nan gabanta ya fadi saboda ganin mr ATA ta tsura masa  Ido tana kallon yadda yake motsa lips dinsa gashi dai magana yake sai dai sam bazakace magana yake ba tsabar jin kai da Isa da miskilanci yana ji da kanshi kamar yadda yanuwansa suke ji dashi a family ,shine babban alfaharinsu bata taba jin ance ya aikata aikin asha ba ya kame Kansa ya rike mutuncinsa kowa yana sonsa ta kowani bangare ko ita zata so ta samu miji kamarsa  sosai  tayi nesa a kallonsa .." "yauwa gara da kika zo zauna kiji wa'azi dan kin fini quanar social media kinganta mami  Kashi ne kawai maryam bazata d'aura a media ba kinsan d'azu da safe da maryam ta rasa abun d'aurawa kwayar tsintsiya shara ta d'auko tayi hoto dashi  ."Mami ta zaro Ido waje tana mamaki sannan ta murmusa ita kanta nana hauwa'u dariyar take kmr a lokacin abun ya faru "shi kam mr ATA tsayawa yayi cak yana cigaba da wayarsa kuma yana sauraron nana hauwa "a she da mahaukaciya ake k'okarin son hadashi aure ?ai duk yadda zai yakice wannan auren zai yi bazai yi rayuwa da mental ba ." "Kai auta banason sharri fa Maryam din ce ke yin wannan shirmen ",wallahi gata nan da ranta ba karya nayi mata ba bari ma na shiga na nuna miki maryam wacce ta dawo haiyacinta adalilin katuwar hararar da mr ATA ya bamka mata tayi wuf ta fixge wayar a hannun nana hauwa'u tana harararta "Kai sister bama yar haka dake fa "nana hauwa'u tayi murmushi "wai gskiya zan nuna ma mami tasan Inda kika Kai a son social media."maryam ta zauna idanunta na kan nana hauwa'u amman kacokan hankalinta na kan mr ATA tana mamakin wannan tsana da yayi mata sam baya qaunar ya ganta a wuri aunty shahida ce ta fado mata arai ko maganar me zatai mata jiya akanshi ? sosai kwakwaluwarta ta shiga thinking ." yana  gama wayar d'ayar wayarsa ta d'auki qara ya d'aga wayar dake ringing yana dubawa sannan ya manna a kunne "okay Ahmed shikenan ayi musu guri na mussaman ,su Kuma wad'an can kwantaina's  din inshallahu zuwa monday zan shigo sai na saka hannu ya karasa maganar yana lumshe idanunshi yana k'okarin sauke wayar Kai tsaye idanunshi ya sauka akan maryam , ya d'auke kanshi tsawon minti biyu ya sake d'agowa adalilin wani Kiran daya shigo ,cikin natsuwa zai d'auka karaf idanunsu ya tsarke cikin juna  idanunta kyam akanshi kamar wata mayya "ke........"kallon uban me kike wa mutane haka na canza miki ne ko yau kika fara ganina ? ya fad'a a matukar tsawace bata San sanda ta sunkuyar da kanta kasa ba  jikinta na d'aukar rawa can muryarta ta fito a hankali"ka..kayi hakuri dan Allah it's mistake "you're very stupid with that mistake ya sake magana a fusace yana furzar da iska mai zafi ."yadda ya kura mata Ido ya tabbatar mata da kallon tsana da kyama yake mata acikin ransa." "me ya kai ki kallonsa alhalin kinsan halinsa? "why why !!maryam me yasa zaki kallesa ? nan take taí blemimg kanta dan haka ta  sake dukar da kanta kasa sosai ganin bai dauke idanunshi akanta ba dan tana jin yadda suke yawo a gabadaya ilahirin jikinta ta soma kokarin mikewa tsaye dan barin gurin mami ta tsaidaita tana zabga masa harara ya maida idanunshi kan nana hauwa da tsawar daya bugawa maryam yasa ta dawo da hankalinta Kansa , da idanunsa  yayi mata alamar ta bar gurin tsam ta mike ta soma k'okarin bawa kafarta iska tun bai sauke zuciya akanta ba ta shiga uku " kema koma ki zauna babu inda zasu  "Kai ba fa na son takura karka takura min yara da bakin rai da miskilanci , idan babu hali zo ka tattara ka wuce gidanka mu sakata mu wala  Ina dalili  wannan maseefa? "Idan dai kana guri shikenan yara basu da natsuwa da kwancinyar hankali ? wani irin daci rai mai mugun tsanani ya rufesa amman idan ba wanda yasan shi sosai ba ba zai gane ba  muryarsa a kasalance yace  "haba sweetheart wai mai yasa kike min haka ne ki dinga min fad'a a gaban wad'an nan premure din ? anyi maka fadan ai Kai ne premature din basu ba , kai  ma ka daina hantarar yaran mutane, babu gaira babu dalili kasawa yarinyar mutane karan  tsana "ni ne kuma pre mature ? yayi maganar zuciyarsa na tuttukin bakinciki tare da banka masu harara ai babu shiri suka  nufi hanyar d'akinsu  da sauri ." "eh mana meye marabunka da premature ? shekararka day day har talatin da takwas a duniya zaka da tara koma nace arbain amman har yanzu ka kasa ajiye iyali akarka shinka shiyasa kullum gaka nan  baka san menene rayuwar muamula da mutane ba sai ta kasuwanci , da kayi aure ne zaka gane meye bambamci rayuwar muamula da mutane amman yanzu Kai da dan shekara shabiyar duk abu daya ne tunda bazaka qarar da abinda wanda yayi aure zai qarar ba." shiru kawai yayi yana kallon mami maganarta taso bashi dariya amman ya maze ya cigaba da kallonta ."Ka daina yiwa yarinyar nan maryam haka banaso wallahi bana Jin dadi ,"ai shiyasa nake ganin hadani daita babbar matsala ne dan ban san ta ina zan fara rayuwa da ..."ba wannan labarin na tmbyeka ba ka daina nuna mata wannan tsanar shine abinda nafi bukata ta katseshi ta hanyar fadar haka "ok  to kice ta daina kallona haka bana son yawon kallo wallahi yana hassalani ita Kuma ta iya kallo kmr renon kauye " kai da wani idon ka kalleta da kasan tana kallonka ?ya dan kashe mata idonaa daya yana ciza gefen lips dinsa na kasa ." girgiza Kai mami tayi "Kai ko Allah yasa ka gane wallahi maryam zata sha aiki ,"sosai kuwa my sweetheart shiyasa naga gara abar hadin nan kar ta hadu da ciwon hawan jini da.."baka isa ba wannan auren fa ko mutuwa zakayi sai an daura shi  kai wallahi idan kasa wasa ma mata biyu zan maka arana daya tayi mgnr tana danne dariyar ta ". nan take ya canza fuska sosai kallo daya zaka masa ka fahimci ransa ya gama baci "duk ranar da aka d'aura aurenka da maryam mussaman zan tasata gaba nayi ta bata hakurin zama da Kai dan Kai mai katoton hakuri irinta  ce zata iya zama da Kai ." ya runtse idanuwanshi saboda bakincikin hadashi da maryam datake yi "bama ni zaki bawa hakuri ba nida za'a wa auren dole sai wata banza can ? ya karasa maganar a shagwabe kamar wani karamin yaro murmushi mami tayi sannan ta mike tsaye "kaga tafiyata tunda ka korar min yarana Kai ma ka zauna Kai kadai bazan zauna ba byn ta wuce ya mike daga kan kujera yana ciza gefen baki ya kwashe wayoyinsa ya nufi hanyar waje ." Ahankali yake tafiya cikin hasken daya haskaka haraban gidan ga securities na kai kawo acikin haraban gidan motsin mutun yaji a bayansa ya juyo a hankali kanin mahaifinsa alhj idres ya gani cikin farar jallabiyya hannunsa rike da jaridarsa ta gado a hannunsa dan sau dari zaka gansa to dole kagansa daita da alamun gurin shakatawa zashi dan gurin an kawatashi idan ka shiga Sam bazaka bambamce dare ne ko rana ba.dole mr ATA yaja ya tsaya domin rashin tsayuwarsa zai iya janyo masa tashin hankali dashi kasancewarsa shi din mutun ne mai zafi zuciya da son fad'a sannan baya daukar raini sai dai duk da wannan hali nasa yana dan shakkun mr ATA dan yadda yake saukewa mutane ruwan bala'i na babu gaira babu dalili baya masa haka." "baba qarami brka da dare ?" dake haka suke kiransa dashi haka zalika akwai baba babba wanda shi Ke bin mahaifin mr ATA " sannu Adam dan albarka barka ya fama da business da jama'a? "alhamdulillahi mun godewa allah " to Allah ya taimaka "Ameen ya fad'a ataikaice yana cigaba da tafiya "amm Adam ya batun sakon dan har yanzu ..? "na tura maka sakonka tun safe "to to shikenan Allah yayi wa rayuwa albarka Allah ya jikan mahaifinka ai kana kokarin ka kula da business dinka sannan ka kula da AGC ya fad'a yana qarasowa daf dashi suka jera tare yana masa magana kasa kasa "yauwa Adam daman akwai maganar da nake son muyi da Kai idan babu abinda zakayi yanzu muje gurin shakatawa muyi mgn ?" Yayi shiru na second biyar sannan ya motsa labbansa da kyar "babu abinda zanyi daman na fito na dan sha iska ne  amman babu damuwa muje suka nufi gurin shakatawa suka shiga suka zauna a lokaci daya baba qarami ya numfasa kana ya kira sunan mr ATA "Adam bakaga  zuwa yanzu ya dace ka ajiye iyali ba ?Mr ATA yayi shiru kawai yana kallonsa daman kuma yayi tunanin maganar aure zai masa , baba qarami ya gyara zamansa sannan ya cigaba da mgn ",ga yara nan acikin dangi me zai hana ka zaba a daura maka aure ?"still shiru mr ATA yayi kawai yana jinsa saboda bai san me zai ce masa ba  ." can part din mami kuwa duk Maryam ta damu kanta akan abinda mr ATA yayi mata hawaye ne Shane shabe kwance a fuskarta ta rasa dalilin da yasa mr ATA ya tsaneta ita har a zuciyarta bata Kinsa ganin yadda yake nuna mata tsana ne wani lokacin take jin haushinsa amman tunda abun ya wuce duk yadda take tunani bazata cigaba da d'aukar wulakanci ba  gara tasan abun yi zata tattara ta koma gidan iyayenta ta huta." ta dauko akwatinta ta soma hada kayanta ",wai meye haka Maryam ? "ke matsalata dake kenan komai damuwa menene abinda zai sa ki damu kanki byn ba tun yau kika San halinsa ba har da zaki damu kanki ?tayi saurin tarar numfashin nana hauwa'u "Haba sister koma menene bai kamata ba Kiri Kiri fa yake nuna min tsana kmr ba jininsa ba ni dai gaskiya na gaji Ina ganin lokacin yayi da zan tattara na koma Abuja "karki yi haka sister mami bazataji dadi ba ki rabu dashi shi da ba mazauni ba gobe ma tafiya zata iya kama sa" wallahi idan kika wuce nima bazan ji dadi ba sister mun Saba sosai idan kika tafi kika barni zan shiga wani hali "to ke me yasa baya Miki haka sai ni? ",waya ce miki? ba gashi  tare ya koro mu  ba nima da nake jininsa ya hada dani ,Allah ba ke kadai yakewa haka ba kowa ne sai dai idan bata hadoku ba ina ma tafiya ta kamashi ya tattara da wahalarsa ya wuce ya barmu mu shakata "da kyar nana hauwa'u ta rarrasheta ta fasa tafiya amman da tace gobe gobe zata wuce ." Mr ATA da kawunsa sun dauki lokaci suna tautaunawa sai dai bai sanar dashi hukunci mami  akansa ba har  sukayi sallama da sharadin nan kusa zai kawo masa matar da zai aura yana shiga d'akin ya ajiye wayoyinsa akan wani karamin stood ya cire kayan jikinsa ya saura daga shi sai farar vest da boxce suma ya ciresu yana shafa qirjinsa zuwa kasan mararsa har ya shiga bathroom ya sakarwa Kansa ruwa byn wasu mintuna ya fito yana goge jikinsa da towel byn ya gama ya tsaya gaban morrow  ya d'auki turare ya feshe ilahirin jikinsa wannan wanka na kaida ne duk daren duniya kafin ya kwanta sai yayi tare da pest haka turare shiyasa idan ya tashi bacci zaka dauka yayi wanka ne dan tsab zaka gansa  ,ya sauya wasu kayan zuwa na bacci farare sol masu taushi ya zauna a bakin gado ya d'auki remut ya qara karfin ac sannan ya ajiye ya d'auki na tv ya danna tashar aljazeera ya dawo ya zauna rigingine  tare da  lumshe  idanunshi hoton princess dinsa ne yashiga yawo acikin idanunshi  , bai san a wani duniyar take ba ."a hankali ya janyo bargo ya shiga ya lullu'be rabin jikinsa ya canza wutar d'akin zuwa dum light idanunshi na kan tv ko cikakken minti ashirin bai yi ba bacci mai nauyi ya daukeshi cike da mafarkin sarauniyar zuciyarsa , kmr Koda yaushe idan ya kwanta dole sai yayi tunaninta, yadda  tunaninta ya zamemasa  dole haka mafarkinta ya zame masa abincin ruhinsa kafin ya kwanta . yana kwance sai gata ta hau kan gadon cikin kayan bacci wanda shi da babu duk d'aya dan a fili ake ganin tsayayyayun nipples dinta  ta yaye bargon daya lulluba ta tsura masa Ido a hankali ya bud'e lumtsatsun idanunshi  akanta yana kallon fuskarta bai tsaya iya nan ba yayi kasa da idanuwansa sai kan nipples dinta dake tsaye cak ,wani irin yanayi ya tsinci kanshi me wuyar misaltuwa , runtse idanuwanshi yayi da suka sauya alokaci daya yana control din kanshi kafin ya bud'e idanunshi yaji tafin hannunta a fuskarshi zuwa chest dinsa tana shafawa tana lumshe masa Ido , yarinya ce karama da bata wuce shekara shabakwai zuwa shatakwas ba a yanzu sai dai Allah yayi mata baiwa da ba kowace mace yayiwa ba , qirjinta a cike suke bammmm da dukiyar Fulani ga shape wanda ya bayyana figure either dinta ga dara daran idanu masu dauke da wadatattun gashi Ido da gira , jin saukar hannunta a girjinsa tana murza kan nipples dinsa yasa gbdy ya susuce bai tsaya wata wata ba ya fixgota zuwa jikinsa ya rungumeta tsam yana sauke wani wahalallen numfashi da ajiyar zuciya yana shinshina wuyanta zuwa qirjinta "Ina sonki my princess kullum da tunaninki nake kwana nake tashi a ina zan ganki .?" Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗      MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 6. shiru tayi tana  kallonsa tana sakar masa  murmushinta wanda ke bayyana ainihin   sahihin  kyawunta  da wushiryarta " am serious my  princess  Ina sonki da yawa ki fad'a min  Inda zan ganki  ? ya  fad'a yana busa mata iskar bakinsa  mai  dumi  tare da  had'e fuskarsu guri d'aya suna shakar numfashin juna   "kice min wani abu mana zuciyata  na  kwad'ayin Jin sautin  muryarki  Ina sonki  dayawa Ina muradinki Ina qauarki Ina sha'awarki  princess". shigewa  jikinsa  tayi sosai   kmr  zata raba jikinsa gida biyu   suna  shakar numfashin  juna suna nan makale  da juna sai ga saukar ruwan sama  "it's  raining princess   lamme  go inside you in this rain I really need you."  nan take ya shiga romancing dinta  cikin zafin nama  yana   kissing  din  wuyanta  kafin daga bisani  ya birkitota ta  dawo kasansa ya koma samanta  yana kallonta itama shi take kallo  bakinsa ya Kai cikin kunnenta yana tsotsa  yana zira harshensa ciki wani irin yanayi ." mika tayi ta sake  shigewa jikinsa ,ta lumshe masa  nata sumammun  idanun  tana  sake shigewa  jikinsa "sonki ya hau min kaina da yawa  habibaty you're the best princess in this world  ya zare rigar jikinta yayi filinging dashi  ta saura babu komai  ya had'eta da jikinsa tare had'e bakinmu  guri d'aya har  yayi nasarar  cafko laulausan  harshenta  nan ya shiga tsotsa  nishi yake fitarwa da iyakacin karfinsa kmr wanda yaci yaji sannan ya zare  bakinsa yayi zaman dirshsn a gabanta ya kamo hannunta ya d'aura  akan jijiyarsa bata d'auke hannunta ba haka zalika bata d'auke idanunta akanshi ba sautin muryarsa ya doki kunnenta "ki shafamin ta lumshe masa idanunta ya sake damke hannunta da joystick dinsa sosai "a hankali ta dinga shafa joystick dinsa tana laulaya kan tana had'owa da dick dinsa matsota yayi sosai ya  sauke bakinsa akan nipples dinta yana tsotsa   yana lasar wuyanta ita Kuma tana cigaba da shafa joystick dinsa dake sake mikewa tana fitar da ruwa  ,hanyarsa yake k'okarin  nema  ta takure jikinta guri daya   "a hankali  ta Kai bakinta   daidai  saitin kunnensa ta soma rad'a masa magana  cikin sanyayyiyar muryarta mai tsananin dadi da tsuma zuciya "banason abinda kake min  ganika naxo yi  kawai ba dan kayi wani dani ba  ,da kyar ya cire bakinsa akan nipples dinta  yana furta "wowww my princess  sautin murya mai dadi amman karki ganni kawai  ki kasance dani na har abada shine abinda nafi bukata  yayi maganar yana sauke ajiyar zuciya ya sake rungumeta tsam tsam  ajikinsa ya matseta har ta bud'e baki zatayi magana ya sake had'e bakinsu ya lullubesu da bargo tsawon lokaci suna tare a cikin bargo  babu kaya ajikinsu yana romancing dinta  sai juyata  yake yadda yake  so yana tambayarta sunanta ." "ki fada min sunanki  my princess Ina son sani  da Inda kike ki taimakeni ki fad'a min  yana mgn yana kokarin shigarta sam taki yarda ya cigaba da kokarin shigarta yana cewa "plz  my princess kiji tausayina yau kibani kanki Ina muradinki sake hade ka'fafunta tayi,ya sake manneta yana kokarin bude leg's dinta cikin kuka tace "ni ka sakeni ba dai zaka auri wata ka barni ba shine ni kake son na mallaka maka kaina ? cikin tashin hankali yace "no no it's not like that my princess Ina sonki kuma zan aureki babu wata mace da zan aura sai ke ,ke kadai ce mace agurina  sauran matan duniya tamkar maza nake ganinsu babu macen da zan samu natsuwa daita sai ke Ina sonki Ina sha'awarki ki taimakeni ki barni nayi  ya k'arasa mgn yana hade bakinsu ya kamo lip's dinta itama  ta cafki nashi. sosai Adam yake juyata yana Kiran my princess  ......." qarar wayarsa ce  ta  farka dashi daga mafarkinsa  a firgice ya bud'e idanunshi yana  fidda numfashi ya zauna a tsakiyar gadonsa yana kallon  jikinsa gbdy ya hada gumi sharkaf tmkr wanda akayiwa wanka  jiyayyarsa  kuwa ta mike sambal tana haniniya duk ruwan sha'awa ya gama bata masa wando numfashi ya sauke yana dafe goshinsa da hannu daya  "ya rabbi har yaushe zan daina ganinta a mafarkina ?ya Allah idan yarinyar nan mutun ce kuma  tana raye Allah ka bayyana min ita a duk Inda take na samu natsuwar zuciya , jiki a sanyaye ya mike ya shiga bayi yayi  wankar sarki  dan ya samu natsuwar zuciya ya d'auro alwala ya  fito ya sanya jallabiyya fara sol ya kashe tv sannan ya karasa Inda   abun sallarsa yake ya tadda ikama yana sallah qirjinsa na dokawa ... Ya dade yana nafilfili da rokon Allah ya kawo masa sauki ,bai koma bacci ba sai da yayi sallah asuba har karfe goma  bai tashi ba shigowar hjy zulaiheart uku  duba shi yana bacci na hudu ne ta iskeshi kwance idanunshi biyu amman bai tashi ba ta k'araso ta zauna a bakin gado tana shafa gefen fuskarshi "lafiyarka adam  baccinka yayi tsawo yau  ko baka jin dadi ne ?motsawa yayi ya  daura kanshi akan cinyar mahaifiyarsa  zuciyarsa cike da rauni yana  fatan haka ya zamo Silar samun sausauci ,  "sweetheart ..."! ya kira sunanta a raunane  "menene adam? " fada min meke damunka ?duk ta rude tana son sani halin da danta yake ciki "zuciya ta na cikin rudani sweetheart soyayya na  kikiniya dani ina son yarinyar Nan  sosai sai dai ban san Ina zan ganta ba , ta shiga zuciyata zata iya sawa ki rasani "naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana riko tafin hannunsa cikin nata ta rike gam "Allah  bazai sa ba sai naga aurenka da ya'yanka  " yaushe zan ganta sweetheart  kullum sai nayi mafarkinta  ?har tsoron runtse idanuna nake saboda dole sai tazo .tausayinsa ya kamata ita dai Allah yasa ba aljana bace ta aure mata da "wata rana zanganta ko Sweetheart ?yayi maganar yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa. "Adam ba dukkanin mafarki ke zama gaskiya ba "Ina ji ajikina gaskiya ne sweetheart  Kuma lokacin haduwarmu  daita ya kusa tunda har tayi  min magana a daren jiya abinda bata taba min ba ,naji sautin muryarta , tana da sauti mai zaki da rikitarwa "shikenan ya Isa ni mahaifiyarka ce zan tayaka da  addua idan mutun ce Allah ya bayyanata idan aljana ce Allah nesantata da Kai  amman ka kwantar  da hankalinka ka aure maryam zata Saka zuciyarka natsuwa zata mantar da kai komai,zakayi alfahari daita  "ya runtse  idanuwanshi gam yana Jin zafin furucin mahaifiyarsa  "Ina jin kunyar auren maryam sweetheart wallahi bansan dalili ba gani nake kmr  abun kunya ne na aureta "Babu wani abun kunya yarinya ce mai sauki hali "Kuma bazata damu  ko ka  aureta sai ka  qara da  princess dinka ta fad'a tana shafa sumar kanshi   "wannan ai  ya zama dole shiru tayi tana jinjina girman alamarin ta fad'a masa haka ne ba dan ranta yaso ba domin ita dai maryam ce cikar burinta ,kuma koda zai hadata kishi da wata ya zamanto ita ce gaba da kowa  a zuciyarsa naunayen ajiyar zuciya ta sauke muryarta a sanyaye tace "shikenan tashi ka shiga wanka  ga break can na jiranka  Allah  ya jishemu alkhairi "ya mike da kyar rike da kugunsa ya shiga bathroom ita Kuma ta fito zuwa parlour. Karfe  daya daidai ya shirya sai dai ya kasa fitowa zuwa falon mahaifiyarsa saboda baya son haduwa da maryam  shi Kansa Yana mamakin zazzafan soyayyar da yakewa princess wanda ma'abota so da shauki ne kawai suka San zakinta yana son yarinyar kamar ranshi, soyayyar da yake mata mai tafiyar da ruhi ne Ina ma ya ganta a duniyarsa ta zahiri  da shi kadai yasan irin so da tattali da zai mata."sauke numfashi yayi da karfi "anya kuwa zaka iya ?zaka iya nuna mata soyayya a fili ?ban yarda zaka iya nuna mata tarin qaunar da kake mata ba  saboda kai din mutun ne mai jin kai zuciyarsa ta fad'a masa haka ya furzar da iska mai zafi yana shafa goshinsa yana girgiza kai ." a natse ya mike ya goya hannuwansa duka a bayansa  yana zagaya dakin numfashi kawai yake saukewa ya dan tsotsa keyarsa "Ina da tarin kudi Ina  da tarin yan'uwa Ina da fada aji a kasar nan Amman duk na banza tunda duk sun  kasa samammin   abinda zai bawa zuciyata natsuwa da zaman Lafiya . karfe daya daidai na washegarin ranar ya bar  lagos zuwa kasar togo sai dai a can din ma kasa tabuka komai yayi   haka ya wuni ya kwana yana tunaninta yana son zuciyarsa ta bar tunaninta amman abun ya cutura  duk saukar numfashinsa  tafe yake da tunaninta yana son  ya samawar kanshi natsuwa amman hakan yaki samuwa yayi shiru kawai yana kallon saman dakin da yake kwance yana tunanin abinda ya kamata yayi  babu abinda ya zoma zuciyarsa a wannnan lokacin kamar kwadayin sigari abinda ya dade bai sha ba hassalima baya sha sai yana cikin damuwa irin wannan shiyasa bazaka ta'ba cewa yana sha ba dan bai nuna a skin dinsa ba ." "a hankali ya qarasa inda  akwatin kayansa yake  har zai bude ya tuna baya yawo dashi  dan haka yaja dogon tsaki yana mai dafe goshinsa  ya koma da baya da baya ya zauna akan kujera jagwba yana murza goshinsa wayarsa dake gefensa ya soma ringing ya kai hannunsa ya lalubo ya dauka ya d'an bude idanunshi kadan ya duba trucaller ne yasa ya gane ko wacce ke kira direct call ya dan ja saki  yaki dauka munubiya ce diyar alhaji  madu tsohon shugabansa nigeria school  mate dinsa ce tare sukayi karatu a chaina ."  ta dade tana son shi Amman shi Sam baya tata gbdy duk hanyar da zata hadasu ya kulleta yanzu ma bai San Ina ta samu wanna number nashi ba ." Byn second biyar wani Kiran  ya shigo ganin me Kiran  ya dauka yayi shiru har sai da yaji yace  " hello sir ! sannan yace "Ahmed ykk ?  ya  fada a kasalance "okay shikenan zan turo maka  zuwa anjima  Jin yanayinsa ahmed ya fahimci yana cikin damuwa  dan haka  ya dinga  jansa da hira ,Ahmed yana cikin wad'an da Mr ATA  ya taimaki rayuwarsu  ya hadu dashi a bakin titi  Antoni  mota ta bugeshi Mai motar ya gudu ya barshi shine ya  taimaki rayuwarsa daga rana ya Maida shi tamkar danuwansa har ya samammansa aiki akarkashinsa saboda ya gama karatu aiki ne ya zama matsala  Kuma shine babban a d'akinsu ga  kannen da iyaye , agarin  nema  aikin ya hadu da wannan accident din Mr ATA  na qaunar ahmed sosai babu abinda baxai iya masa ba dan jinsa yake  tamkar ciki daya suka fito  zuciyarsa a  cunkushe yake da damuwa  amman sai da Ahmed yayi sanadiyyar dawo dashi daidai dan shi mutun ne me abun dariya da barkwanci  haka nan ya tsinci Kansa da Jin dadi Kuma yasan Hakan nada nasaba da wayarsa da ahmed   ya  sauke wayar yana  farinciki ." ****** Tun  daga  ranar  da'aka tsare hadiza  police basu  sake tuntubarta akan komai ba, illa bincike da jami'an  tsaro suke babu dare babu rana har suka samo wani abu daya  dan  danganci fadan  hadiza da sadear ,macen police ce ta taso hadiza gaba zuwa d'akin bincike ta zauna cike da tsoro "inspector  abbas  kunna mata  voice  dinta taji da kunnenta  nan take aka kunna "shegiya karuwa muguwa mai fitsarin kwance Ina dalili da duk saurayin da zanyi sai ya dawo yana sonki da zarar Kinga nayi saurayi shige da fecenki bai karewa har sai kin d'auke masa hankali, abinda zan bari ki gani da idanunki sai kinyi mamaki , wallahi wannan  yayan naki sai ya tausaya miki sai yace bai sanki ba, ke kadai kike da kan maza wallahi idan baki shiga hankalinki  akan  Umar  ba zan siyawa yan iskan unguwar  nan kayan maye su cire miki abinda yake ciki idanunki , ke wannan yarinyar  anyi tsinanniyar me nayi miki  ? shegiya mai ruwan Ido muje neman aiki  tare  dake  ke aka d'auka  yanzu kuma  Umar dake sona kin shiga kin fita kin d'auke masa hankali sadear ki shiga hankalinki dani dan  wallahi zan iya kasheki zan kasheki  na kashe banza  danuwanki  zayi  kukan rashinki ki shiga hankalinki bani fada kune kuke son maidani mahaukaciya Kinga wannan Umar wallahi muddin kika ce zaki kwace sai dai kije lahira idan baki tsaya matsayaki ba zan kasheki , idan ban kasheki ba kuwa abinda zan miki zaki sha  mamaki , idan zakiyi bacci karki saki jiki dan zan iya zuwa na  tsoka miki wuka tunda voice ya  fara babu  sautin  muryar sadear   yansanda suka zuba  mata Ido a zaune dake  tana kuka tare da danasani "ko  akwai abinda zaki kare kanki dashi ?tabbas muryarta ce Kuma munyi haka daita amman har ga Allah bani na kasheta ba kawai dai na fada mata haka ne dan na bata tsoro "daya daga cikin police yace "a'a hadiza daman haka halinki yake kowa Kuma ya sheidake da son fada , ko kinsan wannan wukar da kika yi kisan daita an ta'ba kashe wata yarinya dashi a gra diyar alhaji jamilu ?nan hadiza ta sake rikicewa ta gigice hawaye na zubo mata , "wallahi ban san komai ba gara ma ki fada gsky dan bawa hukuma saukin bincike abu na karshe ki shirya daukar lawyer da zai kareki nan aka sake tasa keyarta zuwa cikin cell ..yadda take kuka sai ta baka tausayi ." da  yammacin ranar asabar   zaune  maryam take a kusa da aunty shahida da aunty   khadeja   tana sauraronta  aunty  shahida ta kalleta  a natse tayi  murmushi  ya naga duk kin firgice ki natsu   please  "kinsan abinda  yasa nake ta son muyi  magana dake tun last week ?maryam ta girgiza  mata Kai kawai tana tattara dukkanin natsuwarta  da hankalinta gareta "mun yanke shawarar  za'a had'a  aurenku da Adam "take gaban maryam yayi wani  irin dokawa ya fad'i ta waro idanunta sosai zuciyarta na tsinkewa  cike da  matsanacin tsoro take duban  duban aunty shahida  da aunty khadeja  tana jin kamar ba abinda ya fito  daga bakinta ba kenan  ,maimaitawar da aunty khadeja  tayi ya tabbatar mata da lallai gsky taji  "wani Adam din Kuma aunty khadeja ? tayi tambayar jikinta na rawa hantar cikinta na kadawa "a'a Adam dai na gidan nan  da kika sani dashi za'a had'aku aure tunda yaki fito da mata mu Kuma mun gaji da zamansa haka  " aunty shahida aunty  khadeja  kuyi hakuri ni gaskiya bana sonsa da aure ........" Mmm sudais 💗💗💗💗💗💗    MAR'ADAMS     💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page7 ........" Cikin mugun firgici da tashin hankali aunty khadeja da aunty shahida suka yi shiru gabad'aya suna kallonta cike da sansar fargaba da tashin hankali "me zasu fad'awa mami data d'auki soyayyar duniya ta d'aurawa aurensu ? " ita kam Maryam kasa kallon cikin kwayar Idanunsu tayi ta takure jikinta guri daya tayi kasa da kanta idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye gbdy ta kasa kwakwaran motsi a zaunen da take , wani iri take ji a gabadaya ilahirin jikinta ,sai lokacin taji wani irin kunyarsu tayi mata diran makiya . ji tayi kamar ta tashi ta bar gurin sai Kuma taga hakan ba daidai bane ,basu cancanci haka daga gareta ba ,zasu d'auka raini ne dan haka ta cigaba da zama zuciyarta na tsalle da bugawa wasu hawaye masu zafi suka samu nasarar zubowa akan kuncinta tasa hannu ta goge wasu na sake zubawa ." Sanyayyaye numfashi aunty shahida ta sauke tana gyara zamanta tare da janyo maryam zuwa jikinta tasa tafin hannunta tana share mata hawaye "kukan ya isa haka tunda baki son shi shikenan zamu san yadda zamu fahimtar da mani amman da zakiyi hakuri kiso AD hakika maryam da kin san kin dace miji na gani na fad'a ba dan AD ya kasance dan'uwana ba ,duk mace zata yi alfahari ya kasance miji agareta kuma uban ya'yanta ki tsaya kiyi tunani maryam karki yanke hukunci cikin tsoro da tashin hankali ". Cikin tsananin kuka da tashin hankali maryam tace "a'a aunty shahida babu wani tunani da zanyi akan ya Adam dan yafi qarfina ta kowani bangare ban Isa na tsaya Inda yake ba bare na kasance mata agaresa ta Ina zan soma rayuwar aure dashi aunty shahida ? "Ta Ina zan fuskanci mutumin da bai qaunar ya bud'e idanunshi ya gani ? "duk duniya idan akwai macen da ya Adam ya tsana to nice "Ina zan kai tsoron da nake masa har nayi rayuwar aure dashi ? uwa uba baya Sona ta yaya kuke tunanin nima zan soshi har naso zaman aure dashi ?" wallahi aunty shahida ni tsoro ma yake bani ban ma san ta ya zan fara rayuwar aure dashi ba , da zarar nagansa bana samun natsuwar zuciya har sai na nisanta kaina dashi to ta yaya kuke tunanin zan iya zaman aure dashi Koda Ina son shi bare bana masa soyayya irin ta aure sai ta yan'uwantaka ?" " ni yanzu tashin hankalina mami wallahi bazan so taji wa......."kuka yaci karfinta ta kasa qarasa maganarta "dan wannan karki damu Ina da tabbacin da zarar kunyi aure shikenan maryam ,bazai nuna miki komai ba sannan zaki daina jin tsoronsa inshallahu zakiyi farinciki a gidansa. "maryam ta zumburo baki "Allah aunty shahida bazan iya ba shine miskilanci shine girman kai , uwa Uba zuciya idan na auri ya Adam bazai barni na rabi Inda yake ba kullum zan tabbata cikin gallazawarsa wa zai ceceni a hannunsa ? ta Kalli aunty khadeja hawaye na gangarowa akan quncinta "yan'uwana ku taimakeni karku bari a had'a auren nan , ban rainaku ba sannan ban ki shawararku ba amman abar wannan maganar yanzu baku ji yadda nake jin zuciyata ba ,ji nake kamar zata fashe tsabar tashin hankalin jin maganarku , Kalli yadda jikina ke rawa aunty khadeja Allah bazan iya ba ta k'arasa maganar tana sake rushewa da wani sabon kuka." Aunty khadeja wacce tayi shiru tana sauraronsu tace " duk na fahimceki Maryam amman yana da kyau mutun yayi dogon nazari akan duk abinda ya kunno kai cikin rayuwarsa zamu baki lokaci kiyi tunani sannan kiyi istahara ..?maganganu masu sanyi da kwantar da hankali aunty khadeja tayi amfani dasu gurin son janyo hankalin maryam duk da a rikice take amman tana fahimtar komai dake fita daga bakinta ,naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana mai kallon aunty khadeja sannan taja gindi zuwa Inda take ta riko hannunta d'aya cikin nata ta damke gam jikinta na sake d'aukar kyarma muryarta a raunane tace "aunty khadeja bazan iya aurensa ba bari ma na fada muku gaskiya akwai wadan da suke  sona sosai ku bari ya nemo matarsa a waje zai fi zame mana alkairi ......" duk yadda sukayi daita ta fahimcesu taki sai faman kuka take tana basu hakuri ganin yadda ta rikice sai kuka take tana rokonsu tana juya Kai yasa suka hakura da batun tare da sallamarta da kyar ta mike tsaye tana layi saboda juwar dake dibarta ta bar parlour, a tare aunty shahida da aunty khadeja suka Kalli juna suna sauke ajiyar zuciya " ban ta'ba tunanin maryam zataki amincewa da wannan had'in ba ,na d'auka zata fi kowa farinciki da murna zata kasance matar AD duba ga yadda naga 'yammata na maseefar son shi da son aurensa inji cewar aunty shahida "ai abun ba daga nan take ba aunty abincin wani gubar wani kuma ma ni banga laifinta ba shi kasan AD matsala ne bare a kai ga halin miskilancinsa aunty khadeja ta fad'a tana jan tsaki " bayan wannan miskilanci nashi bashi da wani aibun da zaa ki aurensa gaskiya kawai dan bata son shi ne abar zance zuwa wani lokaci sai mu fahimtar da mami . "Haka ne amman  ya kamata ki kirasa ki fad'a masa ba'a son shi ko ya dan rage jijji da kai da mislinci da nuna fad'i da Isan da yake  "yanzu kuwa zan sheida masa aunty shahida ta fad'a tana ciro wayarta daga cikin handbag dinta kira d'aya ya katse ya biyo byn Kiranta "kazo yanzu muna parlour'n mami  na uku , tana gama fad'ar haka ta katse Kiran tana jan tsaki dan tasan bancin halaiyan da yake nunawa maryam da babu yadda za'a yi takisa ". maryam kuwa tana fita d'akinsu ta shiga ta zube kan gado tana kuka sosai har da shesheka tana jin rashin dadin kin amincewa yan'uwanta da tayi , ko babu komai yaci darajansu agurinta ta amincewa aurensa "mai yasa na ma su aunty shahida haka ?mai yasa bazan so zabin su ba kuma jininsu da suka fi qauna akan komai ?" hakika ban kyauta ba na yiwa yayar mahaifina butulci da yan'uwana sam basu canci haka daga gareni ba "why why maryam why do  you do this to them ?tana cikin wannan halin nana hauwa'u ta fito da sauri daga bayi dan sheshekar kukanta ne ya hankaltar daita ganin yadda take kuka kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa yasa  ta k'araso da sauri ta hau sama gadon tana mata magana cikin tsananin tashin hankali "menene  marsi ? dan wani loakcin da haka take kiranta mrym ta sake fashewa da wani sabon  kuka zuciyarta na zafi da qunci banci tsakaninta da nana hauwa'u basa boyewa juna komai tabbas da bazata fad'a mata  ba zata boye wannan maganar ta barwa kanta ita kad'ai tunda tasan su aunty shahida ma bazasu  fito da maganar ba . sheshekar kukanta ya qara dagawa nana hauwa'u hankali jiki a mace ta kamota ta rungumeta tsam  ajikinta itama ta fara hawayen tausayin yar'uwata duk da bata san dalilin kukanta ba a hankali ta soma jin sautin muryarta cikin kuka "na shiga uku nana hauwa'u na kasa yiwa yan'uwana abinda ya kamata na kasa bin umarninsu nasan zasu ji babu dadi a ransu tayi mgnr hawaye na gangaro mata ...." "menene abinda kika kasa sannan su wani yan'uwa kenan ? ta fad'a tana sake rungumota jikinata' kiyi hakuri ki natsu marsi ki fahimtar dani abinda ke faruwa "naunayen ajiyar zuciya ta sauke sannan tayi mata bayani komai cikin muryar kuka  tana mai zare jikinta daga nata ta cusa cikin tsakankanin qa'fafunta tana sheshekar kuka tare da kamkame jikinta . Shiru nana hauwa'u tayi  a matukar tsorace tana kallonta tana maimaita maganarta  kafin daga bisani ta motsa bakinta ta soma magana a zafafe "hakika babu aibu a maganarki sister tunda  shima bai sonki kema bai dace ki so shi ba amman wani hanzari ba gudu ba maryam nayi noticing ba ya Adam Kawai ne bakya so kowa ne bakyau qaunar yace yana sonki dan duk wanda ya nuna yana sonki gocewa kike".ta d'ago a hankali ta Kalli nana hauwa'u da take magana "kin tsareni da idanu ai gaskiya na fada aure fa rahma ne yana d'aya daga cikin dokokin Allah da manzonsa cewar aso aure Kuma a girmama shi me yasa ke bakya so ? Kalli yadda abbas  da anás suke haukan sonki kmr zasu  mutu byn su ma akwai wasu amman kullum wulakanci da tozarci ke shiga tsakaninku ,ki duba lamarina maryam kad'ai ya isheki ishara mutun nawa suka ce suna sona a rayuwa ? ." Shiru maryam tayi tana kallonta hawaye na tsiyayowa daga kwarnin Idanunta "me na rasa ajikina ko a tare dani amman har yanzu shiru babu wanda yace yana sona ko acikin family's bare maganar aure ? bamu da wani lokaci maryam a shekarunmu na talatin a duniya ,idan akace babu lokaci ba komai ake nufi da hakan ba illa mutuwa ake magana domin zata iya zuwawa mutun a kowani lokaci ,ni dai shawarata anan kiyi addua abinda yafi zama alkhairi a tsakaninku da ya Adam Allah ya zaba miki ba kuka ba dan duk yadda zaki ki aurensa idan Allah ya qaddaro mijinki ne dole sai anyi  ta qarasa mgnr tare da  riko hannuwanta duka cikin nata tana kallonta a sanyaye  kana ta cigaba da magana "kina da sa'a marsi arayuwarki da har akayi tunanin a had'aki aure da yaya adam byn akwai tarin yammata acikin danginmu wad'an da nake da tabbacin da sune aka nemi a hadasu  dashi da tuni an wuce gurin." " hakika mami  ba qaramin qauna take miki ba , ba dan ya Adam yana dan'uwana ba yana da kirki daidai nashi  marsi ,nagarta ga kyawawan halaiya da kyakkyawar zuciya illarsa dai rashin son magana da mislinci da km tsanar da yake nuna miki byn wannan bashi da wata aibu da za'a kishi , idan kika auresa zaki zamo matar da babu kamarta acikin matan duniya ,kema kuma haka ne kina da halaiyan da baza'a ta'ba barin kije ki auri wani ki barshi ba ." "hankali nana hauwa'u ta dinga kwantar mata da hankali har kukanta ya tsaya ta qura mata Ido tana sauke ajiyar zuciya "ki saki ranki please idan ba kina son nima na shiga cikin damuwa ba "murmushi maryam  ta sakar mata tare da goge hawayenta "yauwa ko ke fa matar yayana inshallahu ta fad'a tana mikewa ta bar d'akin mrym ta kwanta lamo akan katifa tana sauke numfashi sama sama tana tunanin mafuta zata amince ko kuwa zata tsaya akan ra'ayinta ne ?" A parlour hajiya zulaiheart ya samesu zaune sunyi shiru kowannensu da abinda yake sakawa a cikin ransa , yayi sallama a ciki kmr baya so ,suma aciki suka amsa masa kamar yadda yayi dan gbdy haushinsa  aunty khadeja take ji dan gaisuwar da yayi masu aciki ma bata amsa ba  shima bai damu daya sake gaishesu ba dan ba kasafai yake son gaisuwa ba hasalima yawon gaisuwa na cikin abinda ke motsa zuciyarsa "ya k'araso cikin sanyin jikin nan nasa ya zauna akan kujera mai zaman mutun d'aya ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya ya fuskancesu batare daya yi magana ba ." gyaran murya aunty shahida tayi kana ta soma mgn "burinka ya cika AD domin kuwa maryam taki amincewa da aurenka juyin duniya munyi daita tace bata sonka bata ga abinda zatayi da aurenka ba shikenan sai hankalinka ya kwanta ka zuba ruwa a kasa kasha tunda kai ma alal lalurati zaka aureta ba dan kana sonta ba , amman kasan da sani bazaka cigaba da zama haka ba dole ka fito da mata Kuma cikin wannan lokacin kayi aure dan kwancinyar hankalin mahaifiyarmu .." ban san dalilin da yasa kake kin yarinyar nan ba  batare da wani huja ba wallahi sam banji haushinta ba kaso mai sonka haka zalika Kaki mai kinka inji cewar aunty khadeja wacce ta k'arasa maganar cikin tsananin fushi tana jan tsaki a fili wani mugun kallo ya watsa mata mai had'e da harara yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa , ta kawar da kanta gefe tana zuba tagumi ." Shiru kowannensu yayi bayan sun gama zayyane abinda ke ransu shi kuwa yafi minti ashirin yana zaune zuciyarsa na wani irin bugawa batare da yace uffan ba kafin daga baya ya motsa lip's dinsa a hankali "sweetheart tasan da wannan maganar ?ya tambaya yana kafesu da Kyawawan idanunshi masu matukar kyau da bugar da zuciya sai dai a yanzu kallosu kawai zai sa ka fahimci tashin hankali da balain dake cikinsu "bata sani ba amman dole zata sani Kuma a yanzu "A hankali ya dinga girgiza kafarsa d'aya yana cizan lip's dinsa na kasa yana maimata Kalmar da aka fada masa mrym tace " bata sona ? wannan karon a fili ya fad'a yana kallon aunty shahida zuciyarsa na zafi da quna da tuttukin bakinciki mara misaltuwa ,kai tsaye tace "tabbas abinda ta fad'a mana kenan kai daga gani ma tana da wanda take  so....."stop aunty shahida karki fad'a min haka mana taya zatace bata Sona?" wacece ita dan ubanta da har zata ce bata son Adam Tariq Abdullah ?"mace mai daraja da zuciya mai kin wanda yake kinta" ta bashi amsa da haka tana zabga masa katuwar  harara." murmushin gefen baki yayi wanda yafi kuka ciwo yana girgiza Kai "impossible babu wannan macen a fad'in duniya da zata ce bata son ni Adam wallahi ta raina muku hankali ne sannan tayi balain rainaku ni ko giyar wake ta sha bazata ta'ba fada min haka ba , numfashi ya sauke a maganarsa ta karshe sannan ya mike tsaye ya zuba hannuwansa duka cikin ajihun wandonsa ya soma taku kamar baya son taka kasa yana k'okarin barin parlour'n a matukar fusace har ya Kai bakin kofar fita ya tsaya cak batare da juyo ba "abar maganar nan a tsakankanimu banason sweetheart tasan komai zan san abunyi .." "Da dai ya fiyye maka ka ajiye wannan shegen girman kan naka ka fuskanceta da kanka wata Killa zata yarda "inji cewar aunty shahida " ai ni idan na fuskanceta umarnin kawai zan bata Kuma dolenta tabi umarnina koda kuwa mutuwa zatayi yana gama fad'ar haka ya k'arasa ficewa  daga parlour'n bai tsaya jin abinda zata ce ba . girgiza Kai sukayi a tare "kinji ba aunty , kinji abinda yake cewa ko ?"wato shi bazai rusunar da kai ba, Komai ta karfi zai yi byn ita mace yar rarrrashi ce ." Allah dai ya shirya AD yasa ya gane kuma ya wanke masa wannan zuciyar tasa aunty shahida ta fad'a . bedroom din hajiya zulaiheart suka shiga suna qoqarin danne damuwarsu dan karta fahimci komai a hankali suka dinga nuna mata babu wata matsala sunyi mgn da maryam kuma ta amince "masha Allah "Kai alhamdulillah amman naji dadi Allah yayiwa rayuwarsu albarka wannan aure Ina son shi Ina qaunarsa Ina farinciki dashi yanzu sai a sanar da baba babba  shi kuma ya nemi sauran yanuwansa aje neman aurenta gurin saidu ko ? "wannan haka ne amman ki dan tsaya tukun kinsan halin 'yan kayanki muna son ya dan saki jiki da mrym din su samu fahimtar juna sai ayi maganar aure hjy zulaiheart ta gyada Kai tana murmushin jin dadi  "wannan ma shawara ce  mai kyau Allah ya daidata tsakaninsu dan mrym bani da matsalata daita , nan sukayita biyewa hjy zulaiheart dan basa son tasan abinda ke faruwa ta shiga damuwa , domin kuwa muddin tasani akwai gagarumin tashin hankali a gidan ." "Yana shiga d'akinsa zariya ya soma yi daga farkon d'akin zuwa karshe ya kasa zama kamar wanda yayiwa sarki karya can ya tsaya cak yana jan tsaki har lokacin mamakinta yake dan yasan aunty shahida baza ta'ba fad'a masa qarya ba daya qaryatata cikin zafin nama ya soma balballe botiran gaban farar rigar dake sanye ajikinsa ya cire sannan ya zame ash three quarter din da yake sanye dashi ya shiga toilet yana sake jan tsaki ya kunnawa Kansa ruwa yana jan numfashi da rarrashin zuciyarsa tare da son karyata zuciyarsa akan jin haushin maganar yarinyar shiru yayi ruwan na sauka ajikinsa " dole yana bukatar saita kanshi dan ya samu damar tarwatsa zuciyarta cikin ruwan sanyi ban da ma hauka da jakanci irin nata Ina ita Ina shi Adam ai sai dai darajan iyaye ? shi da yake da mace kamar  princess yarinyar da ta samu kyakkyawan mazauni a zuciyarsa me zai yi da mai jiki kamar na turkey, abinda batasani ba da abashi mace irinta gara ya kare rayuwarsa babu aure yana cikin toilet ya dinga jin sautin qarar wayarsa bai fito ba sai daya samu natsuwa sannan ya fito d'aure da white towel iya gwiwarsa ya tsaya gaban mirrow yana karewa kanshi kallon tsab sannan ya sauya kaya riga armygreen da wando baki kafafunsa sanye da takalmi fari sol ya zauna shiru akan kujera duk yadda yaso ya cire damuwar rashin son shi da'akace mrym batayi abun ya cutura wani irin zabura yayi ya mike  ya kwashi wayoyinsa ya fito zuwa haraban gidan Inda security da escort dinsa ke faman safa da marwa suna ganinsa suka hau kikiniyar bud'e masa bayan mota suna furta" barka da fitowa ranka ya dade ya shiga ya zauna fuskarsa a hade batare daya amsa ba direbansa yayi saurin shiga mazaunin direba "aka bude makeken get din gidan ,motor daya da direba da wasu escort sukayi gaba sannan motar da Mr ATA ke cikin sai daya a bayansu suka bar gidan suna hawa kan titi kira ya shigo wayar direba sai daya nemi izini agurin A Mr ATA sannan ya d'auka mgn daya ya katse kiran Tare da tmbyr mr ATA"ranka ya dade Ina muka nufa ne ? "gdn mb ya fada ataikace yana kallon gefe titi zuciyarsa na zafi ,tafiya mintuna kadan sukayi suka k'araso ikeja gra a kofar gidan suka ja suka faka suka yi saurin firfitowa suka zagaye motar da Mr ATA yake ciki ,daya daga cikinsu ya bude masa murfin mota , masu gadin gidan muhd bello na ganinsa suka fara rawar jikin da kokarin kawo gaisuwa. " Kai tsaye ya shiga gidan batare da neman iso ba waje ya samu a rumfar dake ajiye da kujera na alfarma dake haraban gidan ya zauna ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya wannan ya rigada ya zame masa jiki no matter how ya zauna sai ya d'aura kafa daya a kan d'aya , hannunsa daya ya d'aura a kan table yayinda wayarsa ke manne da kunneshi yana neman layin MB cikin kankanin lokaci ya bayyana a gabansa ."sai da gabansa yayi mugun bugawa hankalinsa ya tashi da ganin yanayin Mr ATA , ya zauna kusa dashi yana kallonsa "Lafiya friend na ganka haka kmr kana cikin damuwa ?" shiru yayi masa zuciyarsa na zafi da tafarfasa kmr zata kama da wuta "please talk to me friend what's wrong with you ?"yin duniya mr ATA yaki magana shiru Shima yayi yana kallonsa zuwa sanda mai aikinsa ta k'araso rike da tire dake d'auke da ruwa da lemuka masu sanyi tun kafin ta k'araso ya amsa a hannunta dan yasan yadda mr ATA ya tsani ganin fuskokin masu aiki ya ajiye akan table ita Kuma ta juya da sauri .ta kasan idanunshi yake kallon yadda take daga ka'fafunta haka nan ya tsinci kanshi da kallon every step of her  zuciyarsa na quna ." MB ya tsiyaya masa ruwan ya mika masa "Kar'ba ka sha ka dan ji sanyi ATA ya numfashi ya sauke numfashi kana ya nuna masa kan table "ba ruwa nazo sha ba MB wai har ni wanan stupid monkey din zata ce bata so ......?"yayi maganar yana nuna qirjinsa da d'an yatsansa . a matukar firgice MB yace "who's she ?"wannan monkey revenble person din mana har ni zata ce bata so? " is a lie she just say it "ka natsu plz nifa ban ma fahimceka ba amman duk da haka nasan babu macen da zata ce bata sonka "wannnan yar iskar yarinyar diyar kanin sweetheart dake fama da danyen jiki kmar daga alhalin china aka samota yayi maganar a tsawace yana dukan table din gabansa nan take tire da glass cup suka tarwatse MB bai tsaya bi ta kansu ba ya riko hannuwansa duka cikin nashi dan gbdy zuwa yanzu ya fahimci ko wa yake nufi  "calm down ATA ba fushi yakamata kayi ba soyayya haka take kayi hakuri ka natsu musan abunyi tunda kaji kana sonta yanzu shawo kanta bazai yi mana wa......" MB yayi saurin katse maganarsa sakamakon wani mugun kallon da ATA ya  watsa masa yana zare hannuwansa dake cikin nashi "nace maka Ina sonta ne ? MB yayi saurin girgiza masa kai alamun a'a "to me yasa kace Ina Sonta ?wai naga kamar ka damu ne" "to bana Sonta kuma har abada bazan sota ba Koda kuwa tazamo mata agareni wallahi bazan sota ba kai bancin darajan sweetheart bazan ta'ba iya aurenta ba, bugu da kari ni mallakin princess ne ba kowace mace ba ,Ina son yarinyar  nan MB Ina zaka nemo minta ?na saka 50 billion ga duk wanda ya nemo min ita ka taimakeni abokina ka tayani nemota wallahi muddin na auri yarinyar nan zan cutar da zuciyata sannan zan cutar da yarinyar mutane dan bana son mace irinta bazan yi mata adalci ba bazan iya italic ba  ." "Is okay ATA Ina iyakar kokarina wallahi amman zan qara ya kife kanshi akan table kmr wani karamin yaro zuciyarsa na zugi da rad'adin bakinciki "kayi hakuri friend ka sanyaya zuciyarka maryam bazata kika ba sai dai ta furta hakan ne adalilin yadda kake mata amman ni zan sameta muyi magana kune da kune da fahimta nasa zata fahimceni km zata yarda da au.. ."karka yi MB ka barta kawai kar Allah yasa ta amince  "no no !! baza'a yi haka ba ai ba saboda ita ba darajan sweetheart zata ci, kasan yadda ta damu kayi aure , hakuri kawai zakayi  a shawo kanta " ai bana sonta  MB , ta'ba kaji yadda qirjina yake bugawa ,km  yana bugawa ne duk akan yarinyar mafarkina tunda na fara mafarkinta ban sake samun natsuwar zuciyata ba burina na ganta na mallaketa " yayi mgnr yana furzar da iska tare da kamo hannun MB ya kai daidai saitin zuciyarsa dake beating very fast . " ban taba jin soyayya ba irin wanda kake wa yarinyar nan " "wallahi ni kaina nakan zauna Ina wannan tunani MB ban taba gajiya da tunaninta ba daidai da second daya soyayyarta bata raguwa sai ma karuwa ya karasa maganar tare da yin shiru qirjinsa na dokawa da matsanacin karfin gaske". maganganu masu sanyi MB ya dinga rarashinsa dashi har zuciyarsa ta dan yi sanyi a karshe yace "ka rage tsanar yarinyar nan ATA saboda baka da hujja tsanarta kabi umarnin mahaifiyarka kawai ku rabu Lafiya ita irin wannan tsanar idan ta juyi zuwa soyayya abun ba'a magana please aboki kabar komai a hannuna zan san abun yi ". shiru ATA yayi kawai yana jinsa amman sam baya jin zai sota a rayuwarsa ko neman soyayyarta tare suka je matsalaci basu dawo ba sai da suka gabatar da sallahar ishai sannan suka dawo MB yayi dashi ya shigo suci abincin dare amman sam ATA yaki sai ma cewa yayi ya gaishe masa da madam da yaransa sadiq da hanif ya shiga mota suka d'auki hanyar gida ."hancin motar da yake ciki na shiga haraban gidan idanun maryam ya sauka akansa hakince a byn mota kanshi na sunkuye da alamun Idanunsa na kallon screen din waya ne , motacinsa na kokarin daidaita tsayuwa ita Kuwa tana zaune a baradan dake zagaye da kofar shiga ainin babban falon gidan akan fararen kujerunsa tare da lawan d'an PA din gwana kano,da kyar da balai ta fito gurinsa har sai da hjy zulaiheart tasa baki tace "taje su rabu lfy wulakanta dan adam bashi da amfani ,Jin motor  ya tsaya ya dago idanunshi a hankali karaf ya sauka akansu Aiko ya balain had'e rai har sanda aka bud'e masa murfin mota ya fito yana taku kamar baya son taka kasa ta kasan idanunshi yake kare musu kallon tsaf acikin hasken daya haskaka gurin sai dai idan ba kwakwaran sani kayi masa ba bazaka gane su yake kallo ba .." Gabanta sai luguden bugawa da ganinsa yake sai dai hakan bai sa ta tsaida maganar da ta fara ba "Lawan ka daina zuwa gurina saboda banason abinda zai sa na dinga maka wulakanci, "idan har kina ganin daidai ne abinda kike min ki cigaba mrym , numfashi ta janyo da kyar ta sauke" ni dai lalla'baka nake amman ka gagara ganewa ,"to meye dalilin da bazaki amshi soyayyata ba ? yayi mata tambayar adaidai lokacin da AAT ya k'araso gurin. tayi shiru saboda buguwar zuciyarta daya qaru Shima lawan shiru yayi yana kokarin mikewa domin gaisawa da ATA Amman Ina bai tsaya bin ta kanshi ba tuni ya shige ciki . ya koma ya zauna yana kallonta "Uhm ki bani amsar tambayata Ina jinki me yasa baki Sona me na rasa mrym? yayi mgnr yana kallon jikinsa a ranta tace "many things lawan hatta sunanka bai min ba bare akai ga surar jiki sai data hadiye abinda ya tsaya mata a makoshi kana ta cigaba "Ina son namiji fari sol dogo sannan intelligent abinda zai kara kashe ni ya zamanto yana da tsoron Allah shikenan ya gama da rayuwata zan iya mutuwa akanshi " kasancewar mu bakake yasa ba'a sonmu kenan ? a'a bance bakin mutun bai yi ba amman ni dai a gurina mutun fari sol nake so Irina wallahi ni ko nmj baki zai bani rabin duniya akan sadakina bazan amsa ba na fison kalata dan banason black .."sake baki yayi yana kallonta gbdy yaji ya munzata aguri dan shi baki ne sitik kuma ba wani mai tsawo bane can sai dai baza'a Saka shi cikin sawun gajeru ba tun bai kai ga magana ba ta mike tsaye  "to malam lawan ni zan shiga ciki ta nufi hanyar part dinsu bayanta yabi da kallo yana aiyana abubuwa dayawa akanta sai dai baya jin zai iya hakura daita dan yana son farar mace koda kuwa mayya ce . Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 8 "Ahankali  take tafiya cikin sand'a  tamkar   wata  'barauniya  yana   hankalce  daita  duk da idanunshi a runtse  suke amman bazaka ta'ba gane hakan ba  sai wanda yayi masa cikakken sani , da d'an sauri   ta nufi  hanyar d'akinsu  tana sauke numfashi  Tare da ajiyar zuciya ,ta cire mayafinta ta wula saman katifa sannan ta samu waje ta zauna tare da rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafa zuciyarta a matukar tsorace take  duk da tasan ba wani laifi tayi ba amman tasan tsoronta baya rasa nasaba da muguwar kiyayya da tsana mai tsananin  da ya adam yayi mata  tayi shiru tana sake zurfafa tunaninta sam  bata hango ta inda zata iya amincewa aurensa ba gara kowa yaje ya nemo abokin rayuwarsa a waje domin rayuwar aure dashi daidai yake da kamuwa da cuttutuka kala dabam dabam ."        "mr ATA ya cigaba da zama a parlour'n yana karkada kafarsa daya har sanda  hajiya  zulaiheart ta shigo parlour'n fuskarta a sake amman ganin  yanayinsa yasa ta d'an shiga damuwa muryarta a raunane ta soma mgn "Adamcy nah  har ka dawo ? ya had'e rai sosai  tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa  tare da gyada mata Kai kawai batare da yayi magana ba "Lafiya naga duk kayi wani iri ?fuskarshi a murtuke ya soma magana cikin tsananin fushi "wa yace waccen yarinyar tayiwa saurayinta masauki  akan  kujerun zamana ?mami ta numfasa irin nasu na manya kana tace " ban da abunka Adamcy wa zai sa tayi haka ?" ta dai yi haka né dan tayi ra'ayi  tô ma  menene aciki dan ta zauna da bakonta  akan kujerarka kwana nawa ne ma ya saura ?"ni  dai babu ruwana da wani kwana nawa ne   ya saura ni dai banaso  dan  ba ra'ayi bane kawai  raini  ne  idan ba haka ba kujerun da  nake zama akai shine ya zama na zancenta?yayi maganar yana shan kamshi ." "Kai dai wallahi anyi rigimamme wannan zuciya wannan zuciya !! Allah ya sausauta maka, bakaken magana ya dinga fad'a akan maryam batare da yayi la'akari da matsayinta a gurin mahaifiyarsa ba  mami batace komai ba har sanda ya dasa aya sannan ta kira sunansa a tsanake  "Adam !bai amsa ba illa ya tsura mata kwayar idanunshi dake cike da bakinciki yana kallonta ta sake kiran sunansa "adam ! "a karo na biyu  shiru yayi still yaki amsawa tunda yayi haka tasan bazai amsa ba yasa ta soma magana cikin kaukausan murya "zaka iya yin komai da kake so  amman at least kayi respect din emotion din wani idan kai baka  son maryam ka girmama masu sonta  kuma naji dadi da hakan ya faru domin kasan diyata  ba rasa masoya tayi ba yasa zan  hadaku aure." wani kallo yayi wa mami yana mai rausayar mata da kwayar idanunshi cikin nata muryarsa can kasa yace  "alright  sweetheart amman da me zai hana ku  bar masa ita  ya aureta dan zata fi bukatarsa   da duk wani abinda kuke bukata daga gurina "tabbas nasa zata samu, zata samu duk wata kulawa a wajen duk wanda ta aura acikin masoyanta domin kuwa suna mata   tru love  most especially lawan kalli kaga irin abubuwan daya zo mata dashi ."ta fad'a dan qara masa haushi dan babu abinda ya tsana sama da wannan arayuwarsa ,ai kuwa tayi nasarar takalosa."      " He most be a fool  da har yake bayyanawa common mace emotiona dinsa  ta wannan hanyar , Kinsan allah sweetheart  ko mafarkina na hadu daita a zahiri bazan iya mata  irin wannan haukan ba ta zabga masa harara alokacin da yake kokarin yunkura wa  zai mike  ta dakatar dashi "adam !koma  ka zauna ya koma ya  zauna a kufule yana dubanta "kowani dan adam da yadda yake irin tashi soyayyar idan kai abubuwan bai maka ba watakilla su samarinta  ya masu ,dan  kyauta yana da matukar kyau ga masoya domin yana qara damkon soyayya  dan haka kar na sake jin  ka fadi haka ,kai kullum kana yin kuskure amman kai gani kake daidai kake aikatawa ,kowani dan adam yana kuskure amman wannan bana tunanin akwai wani kuskure acikisa sai ma kyautatawa soyayya sam  sam bana jin dadin abinda kakeyi ...." "to ku aura mata shi dan allah kunga ni  na huta daman ni wallahi bana sonta dan wannan auren babu abinda zai jawo sai damuwa I really has to tell you the truth before everything could mess up ya fad'a a matukar zuciye ."murmushi hjy zulai tayi dan gbdy ta fahimci dan nata haushi yaji koma tace kishi yake yaga maryam da wani ,ta  girgiza kai "ai kasan bana magana biyu tunda muka tsaida  magana  da mahaifinta idan kaga baayi auren nan ba to mutuwa nayi ,idan ba mutuwa nayi ba kuwa na rantse da girman allah  adamcy sai ka aureta kai ko yau na mutu a daura maka aure daita zan bar wannan wasiya  maryam takace ta har abada haka zalika kaima nata né mutuwa ce kawai zata rabaku sannan kai ma muna jiran naka gift din soyayyar tunda ka kamu  idanushi ya ware sosai akanta  yana kallonta a rude tare da furta kalmar "what ? " your gift ! ta fad'a tana tsare shi da idanunta "Allah ya tsareni da wannan shirmen hau..."shut up Adamcy ai baka da wannan bakin dan ka rigada ka haukace tunda kake son abinda babu shi a duniya kuma lallai ka tabbatar da ka kawo naka gift din soyayya ranka shi dade a matukar zuciye ya juya ,da sauri sauri ya dinga taka step zuciyarsa kamar ta kama da wuta ta sake saida shi "adamcy nah !wannan karon a fusace ya juyo kamar zai yi kuka  yace "what again ?  "kaje kayi wanka ga dinner dinka ya kammala "bana bukata ya fad'a a kufule  ."this is totally nonsense my love ta furta tana sakar masa murmushi dan tasan bancin itace da abinda zai fad'a kenan a fusace ya sake  juyawa  yana girgiza kai ." Hjy zulai zaune  tana sake duba  kayan da lawan ya kawo  ta kiran maryam ta fito da sauri tana amsawa cike da girmamawa "maza tattara kayanki ki kai daki  shi kuma Lawan din kin fad'a masa an tsaida miki miji dan ya daina wahalar da kanshi ? ta sauke numfashi sannan  ta girgiza mata kai alamun" a'a ! "okay kice masa yazo gobe ina son ganinsa ta gyada mata kai kawai ta tattara kayanta ta shige dakinsu cike da zullumi ta bar Hjy zulai cikin zullumin wannan auren da take kokarin hadawa sam sam bata jin maryam domin ita din yarinya ce mai tsananin biyayya da hakuri akan komai adam take ji tasan shi tasan halinsa shine matsalarta tunda yace bai só tô har cikin ranshi bai só né sai ta tashi tsaye da rarrashi da addua ,zata bari adduarta yayi karfi da sadaka , sosai tayi zurfi cikin tunani ." Bayan kamar  wasu mintuna ya fito sanye  da wasu kayan wondo da riga farare sol kana ganin shigar  kasan fita zai yi ,lokacin daya sauko parlour'n babu kowa zuciyarsa nayi masa wani irin zafi kamar zai fito waje ,sai dai ya  kasa fita koina Kmr yadda yayi niyya ya bude bayan motarsa  ya shiga ya zauna yana sake jin bacin rai mara iyaka yana marmarin shan sigari domin shansa na rage masa bacin rai sai dai tunanin illarta yasa baya son yawo daita domin yana bukatar ya bar shanta na har abada ." mr ATA  bai shiga  gidan ba sai karfe shabiyu  na dare yana daf da  wucesu ya haye step  yaji sautin muryar mami  "adamcy  !cak ya tsaya yana ciccin magani "zakazo ne ranka dade koni na taso nazo ?"tayi mgnr cike da tsokana." jin ta fadi haka ya soma qokarin qarasowa inda take su maryam naganin hk duk suka mike suka kama gabansu  byn sun masa sannu da zuwa bai amsa masu ba ya cigaba da tsayuwa "zauna ta nuna masa wuri kusa daita "laifin me mahaifiyarka tayi maka da ka dauki  fushi mai tsanani daita ? "what ?! "Yes fushi kake daita mana tunda gashi kaki cin girkin data sha wahala ta girka maka da kanta sannan ka tsallake ka bar gidan nan  tun 9:00  sai yanzu batare da kai mata sallama da zaka fita ba wanda hakan ba dabiarka bace muddin kana kasar nan duk inda zaka sai ka sanar min  sannan ka dawo km kana kallona zaka wuce baka da niyyar ce min komai ya dan kalleta ta kasan idanunshi yana cewa "Wannan  yake nufi ina fushi dake ? yayi mgnr a shagwabe Kmr zaiyi kuka ?shine mana idan ba fushi kayi ba fad'a min abinda kayi ?shiru yayi kawai dan bai san me zai ce ba dan fushi fushin yayi dan bai ga dalilin da yasa zata dinga tura masa yarinyar da tasan yafi tsana arayuwarsa wanda shi kansa bai san dalili ba ." maryam ta lallabo ta fito daga dakinsu ta rabe a gefen step "uhm ina sauraronka shiru ne dai ya sake biyowa baya "ina gift din din  soyayyar maryam "? ya zaro ido sosai  yana kallonta  "haba sweetheart wai me yasa kike min haka ne ?"what did I do to you? yayi shiru yana kallonta Kmr zai yi kuka ta sake bude baki zatai magana yayi saurin dakatar daita .    "Dan girman allah  sweetheart ki daina hadani da yarinyar nan kin ce na aureta naji na amince yanzu kuma zaki sake hadani da wani sabon aiki kina son na mutu ne tun kwanana bai qare ba ?tai mur mushi irin nasu na manya "mafarkinka bai kasheka ba sai mutun a zahiri ne zai kasheka?" " adamcy wallahi ka canza rayuwa  ina guje maka hakin mata akanka." yay shiru kawai yana kallonta "yanzu sweetheart fatan da kike min kenan ?me nace maka nace ka canza sai kace zaka canza ko ba shikenan ba ,ni ai kasan bazan ta'ba maka mummunar fata ba amman dan allah ka canza kaji masoyi ta riko hannunsa   cikin nata shima ya daura hannunsa akan nata " naji zan canza Kiyi hakuri da duk abubuwan da nake yi wanda bakya jin dadinsa maryam ta kasa kunne sosai ko zataji abinda suke tautaunawa amman babu abinda taji dan can kasa kasa suke mgnr zai mike  Hjy Zulai tace "abinci fa ?akoshe nake "me kaci dan nasan baka cin abinci a waje ? Kawai dai bana felling cin komai  amman da zan samu tea mai dan kauri zan sha ya fad'a a yatsine ta girgiza masa kai alamun taji  tare da kwallawa maryam kira "ya salam! ya furta yana dukar da kanshi kasa dan bai so haka ba sam baya son abinda zai shi kallon fuskarta ".a natse ta qaraso tana cewa "mami gani ." "Dan Allah maryam hadowa wannan sarkin zuciya tea mai kauri "to mami ! ta juya a hankali ta nufi inda kayan tea yake ta hado ta dawo a natse dan tasan halinsa abu kadan Ke hassalashi bare ita data kasance makiyayiyarsa ko batayi kuskure ba zai iya maidashi tashin hankali "mami gashi ,Yauwa maryam sannu da kokari kinji mika masa" tayi Jim tana jin faduwar gaba da tsoron mai tsanani numfashi ta sauke a boye na samun sausauci tunda mami na gurin komai zai zo da sauki bazata bari wani mummunar abu ya same ba ,bazata bari ya tozartata ba no matter how zata tsawatar idan taga zai yi wani abu jiki a sanyaye ta mika masa tana cewa "yaya ga..."Banza yayi tamkar bai ji ba nan kuwa yaji haushi ne yasa bazai karba ba " maza  ka karba ka shanye ka miko min cup still kin karba yayi ko kaukauran motsi dainawa ya yi a zaunen da yake ma idan ka kallesa ma zaka dauka baya numfashi ne "ka kar'ba mana "sweetheart bana sha ya fad'a yana fusrzar da iska mai zafi ran mami ya soso tasan yayi haka ne dan maryam ce ta hada "amamn kace zaka sha "yanzu na fasa babu yadda mami bata yi dashi amamn yaki  ya karba ya shan akarshe ma ya mike ya mata  sallama  ya nufi saman dakinsa bata amsa masa ba tabi bayansa da kallo har ya bacewa ganinta gbdy mami ta rasa meke mata dadi shiru tayi tana jin bacin rai har sai datayi datasanin kiran maryam amamn ita tayi haka ne dan su dinga samun kusanci da juna, ganin yadda mami ta shiga damuwa yasa maryam ta zauna inda ya tashi ta fara shan tea tana cewa "mami tunda baya sha bari ni na sha daman cikina empty ne shiru mami tayi tana kallonta ita dai bata fushi akan komai "mami dan allah karki damu kanki akan dan wananan abun da bai ya kawo ba "dole na damu maryam mutun Kmr mai zuciyar dutse ?dan Allah kar wannan abu ya dameki nima da yayi dani ban damu ba wallahi ahankali ta dinga kwantar wa mami hankali ." Cike da  natsuwa ya tura kofar dakin ya shiga ahankali ya zauna akan daya daga cikin kujerar cushion dake dakin  dafe da goshinsa yana furta oh my goodness god wai me yasa sweetheart bazata bar zuciyata ta huta da wannan yarinyar ba ?me yasa abubuwa suke faruwa dani ne komai ya zama worst a gareni ?daman har yanzu anayin auren dole ne bare shi daya kasance nmj "me yasa bazaa barshi har zuwa lokacin da yayi raayin ba ?shine tambayoyin da ya dingawa zuciyarsa ya dauki wasu mintuna zaune sannan ya fara cire kayan jikinsa ya shiga bathroom ya watsawa jikinsa ruwa ya fito ya sauya kaya zuwa na bacci ya hau gado ya kwanta shiru yana tunanin wannan auren da mahaifiyarsa ke bukatar yayi bai wani jima ba bacci ya daukesa  hannuwansa duka  a saman  qirjinsa ." Washegari "10am ya sauko daga bed dinsa yana mika bakinsa dauke da addua kai tsaye bathroom ya shiga yayi refreshing kansa tukuna sannan ya saka wasu hadaddun kaya wando da Riga suit  duk brown colour shiru yayi lokacin dayazo saka takalminsa domin kusan lokuta dayawa adaidai wannan lokacin mami ke shigowa dakin akarshe ita Ke saka masa ya numfasa ya shan iska komai nashi tô mach yayi har glass din dake manne da idanunshi ya kwashe wayoyinsa ya sauko cikin takun isan nan nashi ya soke hannunsa daya cikin aljihun wondonsa tare da jin kai yana neman inda mami take "sweetheart ! ya kira sunanta bai ji ta  amsa ba ita kuwa tajishi Sarai tayi masa banza dan haka ya nufi hanyar kitchen  dan nan yafi tunanin take idanunshi suka sauka akan hjy zulaiheart cikin shiga na alfarma ."         a natse ya shiga kitchen din inda masu tayata aiki suka soma kokarin gaishesa sai dai babu wacce ya amsawa acikinsu wanda daman idan da sabo sun saba da yanayinsa ,ya qarasa ya tsaya bayan mami ya daura kanshi a kafardarta yana mai lumshe lumtsatsun idanunshi "my sweetheart good morning? "Morning! ta fad'a atakaice tana hade rai "Hope you had a great night? bansani ba kamar yayi murmushi amman ya maze yana cewa "sweetheart kamshin girkinki  so nice tare da kai hannu zai bude kular gabanta "don't open! shiru yayi tsaye shi bai ajiye murfin ba  shi bai rufe ba ya sake kokarin budewa "I said don't open "kullum aikin  kenan yabon girki amman ..." bai san sanda ya tamke fuska ba ya katseta da sauri "you're worst sweetheart ! naji muje parlour'n tunda ka hanani magana dan ban san abinda ya shigo da kai kitchen ba sai ka gama batawa mutun rai kazo kana salo" ya sake hade rai  sosai tamkar an aiko masa da sakon mutuwa "me nayi km ?"Bansani ba wallahi adamcy idan baka kiyayeni ba to tayi kwafa kawai bai sake cewa komai ba ya juya ya fita daga kitchen din ransa a matukar bace dan yasan akan abinda yayi jiya ne yasa tayi masa haka dining ya qarasa ya dauki cup din tea dinsa da chocolate cake yaci duk da shi din ba mai son zaki bane sosai bai jima ba mami ta shirya masa breakfast "your breakfast is ready "am okay ya fad'a ransa a hade  sannan  ya mike tsaye tun kafin tace wani abu ya fita zuwa haraban gidan ya nufi motar daya bada umarni yana son shiga Range Rover black color driver yajashi suka fita zuwa babban  office dinsa kai tsaye ." ******* Yauma kamar jiya  maryam tana zaune akan kujerar mr ATA  tare da  saurayinta abbas ta tsura masa idanunta tana kallonsa tana kallon yadda yake  sauke numfashinsa ,muryarsa cike da kasala ya soma fadin "ina matukar  sonki maryam da'ace mutun ya Kan iya  shiga zuciyar mutun ya gani hakika da kin shiga tawa kinga irin zallar soyayyar da nake miki  amman ni nasan bakya sona maryam  kamar yadda nake miki wahalar da kaina kawai nakeyi ."      "yaushe na furta maka  bana sonka abbas ?Ko na taba furta maka haka ?ta fad'a tana hade hannuwanta wuri daya tana kallonsa" tabbas da zata tsaida mijin aure cikin masu sonta da aure to data tsaida abbas domin kuwa yafi sauran dama dama kuma ya dan kwanta mata arai "yadda tayi shiru tana kallonsa haka shima yayi shiru yana kallonta yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa akanta "me yasa kayi  tunanin bana sonka abbas ?ta katse shirun dake tsakaninsu ta hanyar fadar haka ."abbas !ta kira sunansa ya tsura mata ido kawai "kamar yadda kake sona nima ina jin wani abu akan..." "Shiiii !"shima ya katseta "sam ban yarda da abinda zaki fad'a ba maryam zuciyar dake son mutun bata banza dashi dan haka karki fad'a min cewar kina jin wani abu akaina dan bakyasona maryam , ban  ma ta'ba ganin soyayyata acikin kwayar idonki ba sau nawa zan kiraki sai kinga dama Kike dauka ?baki ta'ba tunanin ki kirani a duk tsawon lokacin da muka dauka koda kuwa zan shekara ban kiraki ba  , duk wata alama ta soyayya da mutun maryam bakya nuna min hakan kawai ya ishi ne hujja amman ni nasan tabbas ina sonki dan allah karki boye min abinda Ke ran..." Wayarsa ta soma ringing wanda sanadiyyar hakan ya katseshi ahankali ya dan zame hannu shi ya ciro ya duba dan zabura yayi ganin mai kiransa maryam ta dago ido tana dubansa ya dauki wayar ,bata ji yace komai ba sai "to gani nan ya riko hannun maryam cikin nashi adaidai lokacin da mr ATA Ke qoqarin qarasowa gurin wanda wannan ne karo na farko da hakan ya faru "ki kulamin da kanki na samu wani kiran gaugawa ne amman zanzo dawo zuwa gobe mu qarasa maganarmu ina sonki mar..."giftawar mr ATA ya katseshi tayi saurin zare hannunta dake cikin nashi jikinta na daukar rawa ,abbas ya dan bi bayan mr ATA  da kallo sannan yayi mata sallama ya wuce ya bar zuciyarta cikin tashin hankali." jiki a matukar sanyaye ta shige ciki yana zaune akan kujera kusa da mami sai dai kana kallon fuskarsa kasan yanayinsa babu alamun rahma bata tsaya ba ta nufi hanyar dakinsu mr ATA ya dago lumtsatsun idanunshi da suka canza kala wanda suka nuna tsantsar bacin ran da yake ciki ya zubawa mami sannan ya fara magana a natse sai dai mgnr tattare yake da 'bacin rai byn kmr mintuna goma  sai ga maryam tare da nana hauwa'u sun shigo daskarewa tayi agun zuciyarta na rawa ,kamar ta juya saboda rawar da jikinta yake sai Kuma ta sanyawa jikinta jarumta ta cigaba da tsayuwa tana sauraronsu , "wallahi da tasan yana parlour'n har lokacin bai tashi ba bazata dawo ba batare da bata lokaci ba ta fahimci maganae da  mami keyi akanta ne ." cikin sanyi jiki ya mike tsaye ya soma taku da kyar fuskarsa har lokacin a murtuke take  ya jingina jikinsa da bangon parlour'n yayinda idanunshi ke kallon screen din wayarsa "wa yace ki sake zama min akan kujera da wani gardin banza  har kuna taba juna dan ku din tattun yan iska ne ?tayi tsuru tsuru tana kallonsa  hantar cikinta na kad'awa da jin kalmar daya jefesu dashi "wannan shine first and last karki yarda ki sake zama min akan kujeru dan ba dan ke na tanadaisu ba koni sa'anki ne ?"tayi saurin girgiza masa Kai kamar ta durkusa ta bashi hakuri dan ya bar zuciyarta ta hutu sai ta daure taki aikata hakan "ban tanadi kujeruna dan wata gardiya da garden banza su zauna suyi iskanci akai  ba "adamcy ! no sweetheart bari na fad'a mata taji ko auta tayi min wannan ganganci sai na ballata wallahi bare wannan useless din ya fad'a yana nunata da babban d'an yatsa hannunsa" idan mutun ya sake min ganganci nima zan masa ganganci aikin banza kawai zuba masa ido kawai tayi tana jin wani zallar bacin rai na ratsata yayinda tuni hawaye ya soma bin kuncinta "yanzu irin mutumin daake son tayi rayuwa ta har abada kenan ? mutumin da  duk duniya babu abinda ya tsana  kamar ita  burinsa bai wuce ya wulakantata ya tozartata ba  lallai duk yadda zata gujewa wannan hadin zatayi koda kuwa zai zama sanadin rasa rayuwarta ne tun yanzu ma ya kamata tasan abun yi bazata iya ba ,zuciyarta bazata iya   daukar wannan wulakancin ba ta bud'e baki  da niyyar kare kanta kar mami ta dauka maganarsa gsky ce taga tuni har ya  wucewarsa yana jan dogon  tsaki ." idanuwanta suka ciko da hawaye  cikin rawar murya ta soma "ma..mami wallahi abinda ya fad'a ba gsky ba.."kukan da take ya hanata qarasa maganar nana hauwa'u ta matso kusa daita tare da rike kafadunta "da Allah meye abun kuka bayan kowa ya San halinsa muje please nana hauwa'u ta janyota suka koma cikin d'akinsu tana rarrashinta "Ina ganin lokacin barina gidan nan yayi zan koma Abuja da zama duk sanda yake gidan nan  bana samun sukuni"wallahi babu Inda zaki idan yayi miki ki daina nuna kina jin tsoro dan hkn da kike nunawa  power kike Qara masa idan yayi miki ki rama duka shekara nawa ya bawa mutune duka fa 9 ne ..?" "naunayen ajiyar zuciya ta sauke "bazan iya daukar shawararki ba sister "manta da wannan maganar yanzu dai ya kuka kare da abbas  ?wallahi ya bani tausayi gbdy na kasa fad'a  masa gskiya sbd ina dan jin wani abu akansa "kenan kina son shi  ? Ta girgiza mata kai alamun a'a "ina jin wani abu akansa baya nufin ina son shi bane "tunda bakya son ya Adam shi me yasa bazaki bashi dama ba ?" shiru tayi taki cewa komai "heeeee maryam kiyiwa kanki karatun ta natsu yanzu maza wahala suke karki ga wai iyayenmu nada arzki irinmu wahalar auruwa muke amman Kya kare a auren ya Adam din tunda baki da wanda kike so tana gama fad'ar haka ta d'auki wayarta ta shiga yanar gizo "kisa akawo mana abinci yunwa nake ji sosai ,abincin na fita ci wannan mai dacin zuciyar ya bata min rai " da idanu Maryam ta bita tana jinjina Kai ta d'auki waya ta kira layin kitchen ta bada umarni . ko cikakken minti biyar ba'a yi ba mutun biyu suka shigo cike da girmamawa suka ajiye tiren abinci da lemun irin wanda suke sha suka juya nana hauwa'u ta bud'e kula ta zuba abinci ta soma cin mrym tana dubanta ."kici abinci mana kin tsaya tunani "jiki a sanyaye mrym ta soma tsukura tana ci tana fargaban sake haduwa da ATA  gara tayi ta gudu tun sakon rashin amincewa aurensa ya Isa kunnensa ya sake  damarar cin kaniyarta koma asani ne tsanar ya qaru"? Bayan kwana biyu Mr ATA na kwance akan kujera mai zaman mutun uku a parlour'n hjy zulaiheart ta samesa ta zauna a kusa dashi ta soma magana cikin sanyin murya "kana son ginawa kanka rayuwa na gari dole sai kayi hakuri shiyasa kullum nake bukatar naga kayi aure domin ka zama magindaci saboda hakan zai sa ka canza , mata da ya'ya zasu canzaka saboda qaunar dake tsakanin iyaye da yayansu , Adamcy ka canza Sam bana jin dadin yadda kakewa Maryam acikin gidan nan ko babu komai Maryam yar'uwaka ce Kai yanzu kana ganin da wannan zuciyar zaka samu macen da zata iya zama da Kai ?bari kaji Maryam ce kawai zata iya zama da Kai saboda tana da zurfinn hakuri sosai ,zata yi hakuri da halinka da wannan zuciyartaka ko dokin zuciya ka hau nayi Imani zata san yadda zata faranta maka ka sauko , ka tausaya min Adamcy Kai kadai Allah ya bani namiji acikin ya'yana banason na mutu na barka da wannan zuciyar ta k'arasa maganar kmr zatayi kuka yayi saurin ya mike zaune daga kwance da yake ya  kamo hannuwanta cikin nashi "kiyi hakuri sweetheart karki min haka karki zubar da hawayenki akan wannan matsalar shikenan komai ya wuce ai farincikinki shine nawa inshallahu zan canza Kuma zanyi duk abinda kike so ya karasa maganar yana zamewa ya d'aura Kansa akan saman cinyarta . Sanyayyayen ajiyar zuciya ta sauke na farinciki ta d'aura hannunta akanshi tana shafa sumar kanshi "Allah yayi maka albarka ,Allah yaye maka damuwarka Allah ya sausauta maka zuciyarka Allah ya baka zuria masu albarka kuma ya nuna min wannan lokacin, nifa a son raina ma mata biyu naso aura maka a rana d'aya, d'aya diyar talaka d'aya diyar shararran hamshakin mai arziki ." yayi murnushin gefen baki wanda ita kadai Ke iya ganin hakan ya lumshe lumtsatsun idanunshi yana cewa "lallai sweetheart kina ji dani "sosai kuwa Adamcy nah ai shiyasa kake min salo saboda kasan Kaine zuciyata "Nima kece zuciyata rayuwata sanyin idaniyata Ina sonki fiyye da komai  " a hankali suka dinga hira mai kwantar da hankali daga karshe ta d'auke kanshi ta daura masa akan pillow kujera "thank you my sweetheart "you're welcome my happiness ta fad'a tana mikewa ". Ko cikakken minti ashirin bata yi ba ta had'o masa abincinsa yana ganin dawowarta ya mike yana murmushi "sannu da hidima dani sweetheart ",yanzu kam sauran kwana nawa na huta ta fad'a ta janyo karamin stood gabansa ta ajiye "bismillah kaci ya narke mata fuska "yau daya kaci da kanka ya lumshe mata  lumtsatsun idanunshi kana ya soma ci a hankali "kalli cin abinci so nice my dear komai naka dabam ne bai ce komai ba ya cigaba da kai abinci bakinsa tayi gyaran murya ya dan kalleta domin jin abinda zatace tayi shiru dan haka ya d'auke kanshi ya sake Kai abinci bakinsa ."baka ga ya kamata ka fara jan yarinyar nan maryam ajikinka ba"? " ka dinga janta kana kiranta hira ta haka ne zaka...."wani irin tsarkewa yayi ya fara tari  babu kaukautawa "sorry !! ta fad'a tana bud'e rabon ruwa .." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗     MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Free page *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page9 "Cike da kulawa mami ta tsiyaya masa ruwa a glass cup ta Kai bakinsa "sorry dear kabi ahankali ya kur'bi kad'an yana furzar da numfashi mai zafi ya dafe goshinsa kusan minti goma yana dafe da goshinsa yana jin wani zallar 'bacin rai ,da zai iya daya saka mata kuka a yadda yake jin zuciyarsa dame take son yaji ? mami kuwa zuba masa idanuwanta tayi tana faman jero masa sannu har sai dataga ya dawo daidai sai dai bai iya cigaba da cin abinci ba ya d'an zame jikinsa kad'an akan kujera yayi rigingine ya runtse lumtsatsun idanunshi gam yana jin radadi." muryarta a sanyaye tace "ka qarasa cin abinci "am okay sweetheart ! ya fad'a atakaice batare daya bude idanunshi ba . "Numfasawa tayi ta kira daya daga cikin masu aiki ta tattara kayan abinci sannan ta mike ta shiga bedroom dinta tana tunanin yadda zata bullowa ATA sosai kwakwaluwarta tashiga neman mafuta dan dole tasan abun yi matukar ya nemi ya zuba mata kasa a ido zai ga bacin ranta ." Mr ATA ya cigaba da zama yana kallon tashar CNN ".Kusan awa daya da wasu mintuna yana zaune yana nazarin maganar mami "shine zai kira yarinyar da sunan zance ?"no no !! it can be possible koda zai iya hakan sai dai ba daita ba domin bata kai wannan matsayin ba ."a natse ya mike ya shiga bedroom dinsa yayi taku cikin falon wanda babu motsin komai sai na'urori sanyaya wuri kai tsaye bedroom dinsa ya nufa yana furzar da hucin iska mai zafi daga bakinsa wai kamar shi ne zai kira yarinyar zance wannan lamari na sake bata masa rai da daga masa hankali amman ya tabbatarwa kanshi bazai ta'ba iyawa ba yana da raayin shi sannan ga karfin iko da yake dashi dan haka bai ga abinda zai sa shi kiranta da sunan zance ba koda kuwa zasu shekara dubu ne hakazalika ko auren sukai a haka zata qare rayuwarta batare da samun farinciki ba ." ahankali tamkar mara lafiya ya qarasa bakin gado ya soma cire kayan jikinsa yana mamakin mami "hakika tana qaunar yarinyar dayawa wanda hakan yasa tsanar yarinyar yake sake ninkuwa a zuciyars a hankali ya shiga wanka ya fito ya sanya wasu hadaddun kayan bacci wando da riga farare sol ya feshe ilahirin jikinsa da turaruka masu sanyin kamshi ya kashe wayoyinsa guda biyu ya bar na business dinsa sannan ya kashe tv ya haye gadonsa ya lullu'be rabin jikinsa da bargo mai taushi yana runtse idanuwanshi  da princess dinsa ya soma cin karo sanye cikin fararen kaya sol tana sakar masa murmushinta mai rikitarwa ya tsura mata Ido." duk da idanunshi a runtse suke amman shi ganinsu yake abude " ya za'a yi na gaki ? ya furta yana tsareta da lumtsatsun idanunshi sai daya fesar da iska ya sake motsa lip's dinsa "da zanganki da kin fahimci Ina sonki fiyye da komai , me kike so nayi ki yarda Ina sonki ki bayyana min kanki , ina son ki fada min inda zangaki please, zanyi komai akanki ko cewa kikayi na mutu a yanzu zanyi ya Kai hannunsa yana shafa beautiful face dinta ." idanunta na kallonsa ta sauko  ta jingina da bangon daki ya mike ya tsaya a gabanta suna fuskantar juna tana kokarin juya masa baya da sauri ya rikota   ya matsota sosai kmr zai shige jikinta har dukiyar fulaninta na gogan qirjinsa " ina son ki kasance tare dani ki bari na ganki azahiri Koda sau daya ne ya karasa maganar  suna fuskanta juna " idan Ina kallonki sai naga kin fi kowace mace kyau a duniya idanunki , lip's dinki you look so beautiful....." ya ware hannuwansa duka yana k'okarin rungumeta jin ya rungumi iska ya bude idanunshi fesss yana kallon d'akin kamekame da jikinsa, baya felling din kowace mace sai ita ,baya son kowace mace sai ita, da zai mallaketa tabbas da shi kadai yasan irin rikon da zai mata, zai yi mata riko mai karfi ta yadda babu abinda zai rabasu." a hankali ya mike ya sauko ya fito parlour'nsa ya shiga dayan d'akin da kayan zanensa yake ya shiga firfito dasu daya bayan daya ya dawo falo ya zauna ya shimfida black cavenperpa ya soma zanata cikin shigar da tayi masa gizo ,tayi kyau sosai kamar 'indiya "wooow ya furta tare da furta a fili " gbdy gani yayi ta kara kyau sosai ga tsayayyun dukiyar fulaninta masu girma , shiru yayi yana tunanin anya kuwa yarinyar ba aljanna bace Ke neman yi masa wasa da hankali ba ?yana wannan tunanin shaawarta na sake lulluesa ." ahankali joystick dinsa ya mike tsaye har Kan na harbawa murmushin gefen baki yayi yana sake tsura mata Ido" na rantse da Allah ko aljana ce ke idona idonki baki Isa ki hanani kanki ba wallahi sai na ciki ci mai azaba sai na fanshe wahalata ta shekara da shekaru , sannan kowa kika aura a duniyar nan Ina da tabbacin sai ya bar min ke saboda akwai rabona ajikinki , kin sa min sha'awarki a raina fiyye da kowace mace a duniya, ji nake idan bake na aura ba bazan iya aurar kowace mace ba, dan Allah princess ki bari mu hadu ko brest din nan naki na d'an tsotsa  please .." " dan girman Allah princess ki bari mu hadu Koda na kwana daya ne mu kwana akan gado daya cikin blanket guda   muji dumin juna shiru yayi yana kallon surar jikinta mai daukar hankali ," wallahi princess da kinsan irin son da nake miki da tun tuni kin bayyana min kanki , nasan da zarar mun hadu zaki kamu da matsanacin Sona sannan zaki bani kulawa kamar yadda zan baki a yadda nake jinki idan ban mallakeki ba kin cuceni har abada ,wallahi bana kallon mata a matsayin mata , ki bayyana gareni ki tsotse min baki ,ki tsotse min joystick dina, ki tsotse min nono kinji princess dina yayi kasa da muryarsa sosai kmr zai mata kuka "dan Allah Princess ki bayyana min kanki a zahirin Ina son ganinki yana magana yana shafa fuskarta da gashinta,ya d'auki lokaci yana kallonta yana jin soyayyarta na bin jinin jikinsa hannunsa ya Kai yana cigaba da shafa kwantaccen sumar kanta sannan ya mike ya shafa superglue a bayan cavenperpa din  ya manna ajeren zanenta ya dawo ya kwanta akan kujerar kushin  dake ajiye a d'akin yana kallonta. a hankali ya yaye rigar jikinsa sama kad'an ya d'aura hannunsa a daidai saman mararsa yana shafawa a hankali yana furzar da iska mai zafi yayinda sha'awarsa ke sake motsawa wani irin yanayi ya dinga ji a sansar jikinsa ya kamo lip's dinsa na kasa yana cizawa a haka bacci ya daukeshi cike da mafarkinta, cikin mafarkinsa ya ganta tana gudu sosai tana haki tayi gudu sosai sannan ta tsaya ta dafe gwiwowinta da hannuwanta can sai ga wani hayaki ya llubeta ta koina a jikinta can sai kasa ta dinga budewa ta soma yin kasa tana ihu tana daga hannuwanta sama domin neman d'auki  a daidai wannan lokacin wasu mutane su uku mata biyu maza biyu suka k'araso gurin a lokacin da kasa ta rufeta mutun biyu acikin wadan mutane kuka suke sosai suna  kokarin taimaka mata ." shi kuwa dayan wanda ya kasance babban mutun Tare da mace suka   cigaba da tsayuwa rungume da hannunwa a qirji suna dariyar mugunta "a matukar firgice ya farka yana dafe grjinsa gumi ya rufesa kmr babu ac a d'akin zuciyarsa cike da mamaki mafarkinsa na yau "Anya kuwa mutun ce wannan yarinya ?Anya maganar yan'uwa da abokan arziki bazai tabbata ba kuwa ?ba mutun bace aljana ce yarinyar nan ya furta a fili "da sauri ya girgiza kanshi "Allah bazai sa haka ba inshallahu a mutun zata kasance ,idan km mutunce hakika a duk Inda take tana cikin damuwa da tashin hankali nan take shima ya shiga damuwa da jin tsoro , ranar dai bai iya komawa bacci ba dakinsa ya koma ya dinga juyi cikin tsananin damuwa ." washegari sukusuku ya tashi jikinsa babu kwari kana kallonsa kasan bashi da natsuwar zuciya shirun nasa ya qaru fiyye da sauran lokutan baya, mami duk ta damu da ganin yanayinsa sai dai tambayar duniya yace babu komai ya boye mata saboda muddin taji abinda ke damunsa sai ta fishi shiga damuwa yau kwana biyu kenan bai sake d'aura  maryam a cikin kwayar Idanunsa ba bai damu ba dan damuwarsa tafi rashin qaunar data nunawa yan'uwansa tana yi masa  ." yana zaune a part dinsa yayi shiru yayinda MB ke zaune a gefensa "ka daina damun kanka da tunani kada wani ciwo ya kamaka kasa mu shiga uku meye ma matsalarka?sai daya furzar da iska yace  "ka kasa fahimtata ne kawai  amman matsaloli gasu nan takoina kuma ace mutun bazai ji babu dadi ba. "friend abinda zaka dinga dubawa Allah ya baka Lafiya ya baka tarin dukiya bila'adadin wanda Kai kanka baka san adadin kudadenka da gadarorinka ba ,Allah ya baka komai da komai me yakamata kayi sai ka gode masa  ?komai mai wucewa ne inji cewar MB  "to alhamdulillah na gode masa amman bangaren damuwata ba mai karewa bace. "kaga duk wannan mai sauki ne ni sai nake ganin kamar har da rashin amincewa da aurenka da mrym yasa damuwar tayi maka yawa koma nace   yana cikin abinda ke damunka karka ji komai zanji dashi. "Me zai sa damun tunda ba sonta nake yi ba kawai zan auri maryam ne saboda darajan mahaifiyata kuma zata kare rayuwarta a gidana sbd darajanta "Kai yanzu kana ganin zaka aureta?" zan aureta saboda sweetheart "angama zan san abun yi sun dade suna tautaunawa kafin daga baya ya mike ya fito a parlour ya iskesu har hjy zulaiheart yayi mata sallama "har zaka wuce muhammadu bello bazaka tsaya Kaci abinci ba ? a'a mami a koshe nake da zai fice daga falon yace "Maryam muje na dan ganki tace "to ! tare da d'aukar mayafinta ta yafa ta fito a haraban gidan suka tsaya ." "wato maryam kinsan abinda yasa na kiraki ?ta girgiza masa Kai "ba'a kan komai bane sai akan maganarki da ATA me yasa bazaki amince da aurensa ba ?"banason ki rufe min komai idan kin boyewa su aunty nasan ni zaki fada min gasky menene dalili ? Numfashi ta sauke tana lumshe ido"ina jinki ? a natse ta fara mgn cikin raunanniyar murya "abu na farko ya Adam bai sona sannan abinda na fahimta kamar dole akayi masa ya aureni , ni km bazan iya auren mijin da baya sona ba gsky . "da zai fada miki da kanshi zaki yarda ki auresa ?"a'a bazan auresa ba saboda bana son shi shima km baya sona "shiru yayi yana kallonta "ki dai yi tunani ba yabon Kai ba abokina yana da nagarta da za'a auresa ke ya'yan manyan kasar nan fa binsa suke suna rokonsa ya auresu babu wacce ya amincewa zai aura sai ke "gsky sunyi kokari da son aurensa   ni Kuma kaga banason shi zaka iya fada masa gara ya zabi daya acikinsu ya aura "bazaki duba darajan mami ba dan itace me son had'in ko shi baya so sbd mami ne ?ya fada cike da Jin haushin furcinta ."gaskiya da wahala duk ta Inda MB ya bullo mata sai ta kawo masa hujja haka ya gaji yayi mata sallama sai dai yasan ko giyar wake ya sha bai Isa ya fadawa ATA cewar mrym bata bashi had'in Kai ba ." washegari ranar mr ATA yayi tafiya zuwa hollond Kan harkokin kasuwancinsa gbdy   ya manta wata aba maryam a rayuwarsa harkokin gabansa kawai yake da tunanin princess dinsa ."Kwana biyu da tafiyar ATA maryam ta soma hada kayanta da abubuwa amfaninta ta fad'awa hjy zulaiheart da nana hauwa'u cewar ranar juma'a inda Allah ya kaimu zata Abuja zatayi sati biyu ta dawo "Kinsan sati biyu zakiyi shine baki bari mun tafi tare ba ?inji cewar nana "kiyi hakuri sister nayi kuskure nest time inshallahu iya haka kawai ta fad'a saboda taikaita maganar . Ranar juma'a jirgin karfe goma tabi zuwa Abuja tana sauka ta tarar da kannenta da mahaifiyarta sunzo tarbarta dake sun san da zuwanta daya byn daya ta rungumesu ajikinta suna murnar ganin juna "nayi kewarku sosai "muma mun yi kewarki inji cewar izza ta k'arasa ta rungume mumynta dake tsaye tana sakar mata murmushi "mumy na sa meku lafiya ? Lafiya qalau maryam ya mutanen lagos ?tayi mata tambayar tana shafa bayanta da gani kasan akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu, Ta zareta ajikinta ta rike hannunta suka d'auki hanyar gida tun akan hanya mumy ta fara mata magana akan ATA tayi matukar mamaki da Jin tasan komai "eh haka naji sai dai gaskiya ni bana son shi dan bazai yi caring din mace ba shi kenan kullum cikin dacin rai no yayi gaba ya nemi mata nima Allah zai bani nawa mijin ." "karki soma wannan maganar ke Ina ruwanki da dacin ransa tunda yana da kudinsa ,shi fa mai kudi sai a hankali har suka karasa gida mgn daya suke yi Koda mahaifinta ya dawo yayi murna da ganinta nan ya shiga zolayarta "Hjy mrym ko ace maryamu damtso ko amaidashi irin na turawan nan ace mary duk ke kadai gilashina a she babban kamu kikayi alagos ? Kin tashi daga diyata kin zamo surukata matar d'ana da nake ji dashi gskiya naji dadin wannan had'in, kwarya tabi kwayar kenan kinyi sa'a da dace miji na gari .mrym ta zumburo masa baki "Allah dady ka daina cewa hk ni yarkace ba wata suruka ba km ni babu wani dacen miji danayi tsokanarta sukayita yi har dasu izza..." "zamanta a Abuja taji dadinsa tana zaune cikin yan'uwanta cikin kwanciyar hankali da annasuwa babu tsana babu tsamgwama Kuma kullum suna waya da nana hauwa'u da hjy zulaiheart sati daya sati biyu mrym shiru taki komawa lagos tun abun bai damun hjy zulaiheart har ya fara damunta wani tunani tayi tasan halin d'anta Allah yasa ba wani abun yayiwa maryam ba kafin ya tafi hollond yasa tayi musu wayo ta koma gurin iyayenta ". da yammacin ranar asabar hjy zulaiheart ta kirasa yana dauka tasa masa kuka "wallahi muddin baka auri mrym ba babu ni babu Kai Adamcy "subhanallah sweetheart ki kwantar da hankalinki menene ya faru kike kuka da fad'ar haka ? ni dai ka auri maryam shine kawai abinda nake bukata ,Idan km kana son kwancinyar hankalina Kuma tabbas ni ce rayuwa agareka kmr yadda kake fada lallai kayi wani Abu mrym ta dawo gidan nan sannan ka hanzarta aurenta acikin kankanin lokaci na ganta acikin gidan a matsayin surukata ". Sai daya sauke numfashi sannan yace "shikenan naji ki daina kuka zanyi yadda kike so nayi miki wannan alkwari zan aureta sai da yayita rarrrashita sannan ta sake , suna gama waya Kiran MB ya shigo wayarsa byn sun gaisa mgnr minti biyar sukayi sukayi sallama . kullum abu daya ke damunta har yasa gidan ya fita ran mrym kullum sai mahaifiyarta ta dameta da batun ATA cikin zafin rai tace "mumy nifa inada Wanda nake so jira lokacin nake zan bashi dama ya turo" ke ban son zance banza da wofi ni na haifeki ko yar riko ce ke arzikin rikon danayi miki nace ki auri Adam zaki min alfarma ballanata ni na haifeki acikin cikina har nace ga abinda nake so kiyi min gardama to ki d'auke soyayyar wancan ki maye na adam agurin dan dashi za'a yi babu fashi munafukar Allah butulu kawai , shiyasa kika wani tattaro kika dawo nan? " to dan ubanki sai kin koma tana gama fad'ar haka taja tsaki tana zuba fada ." mrym ta fashe da kuka mai tsananin har ana iya jiyo kukanta "zance banza zance wofi ba kuka ba idan idanunki zai fado tsakiyar d'akin nan aure babu fashi sai anyisa saboda haka garama ki daina kuka karki je kisawa kanki bacin rai hawan jini ya kamaki dan ko hawan jini zai kamaki sai na zama surukar adam, wannan aure babu fashi tana magana mrym na sharba kuka kmr wacce aka aikowa da sakon mutuwa ".Iskanci banza har da cewa Ina da Wanda nake so to ni wannnan nake so Kuma shi zaki so wancan kisa masa kiyayya daga yau na gaya miki ki dauko soyayyar wancan ki d'aurawa Adam ki dauko kiyayyar Adam ki d'aurawa wancan shashar banza shashar wofi munafuka kawai mai yiwa kanta bakinciki ta k'arasa maganar tana sake jan tsaki , Yayan zamani Allah ya shirya wannan maganar fa tun asalin iyaye da kankani uwa ko Uba suna da iKon da zai d'auki duk wanda yake so ya bawa yarsa batare da yar taí yi gardama ba dan yanzu zamani ya rigada ya canza nan ta mike ta barta tana surutai da zaginta ." Tana kwance a d'akinta tana kuka faiza ta turo kofar dakin ta shigo ta hau har kan gadon ta rungumeta tana rarrashinta nan kukanta ya qaru "aunty mrym ki daina kuka dan Allah sheshekar kawai take "wai me yake faruwa ne kike kuka haka?, Kin cewa komai tayi tana cigaba da kukanta nan Faiza ta fashe da kuka tana cewa "Dan Allah ki fad'a min ki Daina kuka cikin muryar kuka tace "wallahi bazan auri ya Adam ba sbd banason shi "Amman aunty mrym yakamata ki duba daranja mami tunda tana sonki sosai "wallahi bazan iya ba bazan iya ba tunda ba da ita zanyi rayuwa aure ba ta k'arasa maganar tana sake rushewa da wani sabon kuka ...." Da daddare ta iske mahaifinta akan batun auren "mrym naji duk bayaninki sai dai banji dadi ba Amman Ina son ki rike abinda zan fada miki mrym karkice zaki yiwa yar'uwata haka karki bari wannan abu yayi silar rugujewar zumuncinmu mrym , idan har kika ki wannan auren zakiyi danasanin a rayuwarki dan bazan yafe miki ba a matsayina na mahaufinki bazan so kiyi nadama a rayuwarki ba, duk d'a na halak so yake ya rabu da iyayensa lfiya ki d'aure kiyi ta addua da sannu soyayyarsa zai shiga zuciyarki idan wannan auren alkhairi ne arayuwarki allah ya tabbatar dashi idan ba alkhairi bane mrym Allah ya canza miki da wanda yafi shi zama alkhairi bare Ina ji ajikina wannan auren alkhairi ne ni kaina bazan so Adam yaje ya auri wata ya barki ba, ni kaina na dade Ina wannan mafarkin duk da na gari zai so ya rabu da iyayensa lfiya Ina sonki mrym hk zalika Ina son aurenki da Adam kuka take a tun sanda ya fara magana har ya dasa Aya yana gamawa ya mike ya shige bedroom dinsa ya barta tana kuka ..." ******* Barrister hayat ne zaune a gaban hadiza lawyer da suka dauka domin kareta "Ina son ki fad'a min gaskiya menene gaskiyar abinda case din yake ciki domin mu san yadda zamu kareki "menene gaskiyar halakarki da wadan wukaken da ake tuhumarki da kisan Kai dasu karki boye min komai yadda zan fuskanci shara'a na kareki "barrister zan fada maka gaskiya yadda alamarin nan yake bazan boye maka ba saboda Ina bukatar na fita acikin wannan matsalar tayi shiru tana numfasawa tare da fargaba fadar abinda ke zuciyarta ...." Bayan wasu mintuna ta cigaba da magana "Wallahi  barister  bani  da  halaka da  wad'an  nan  wukaken  ban san  komai   akansu ba , yadda ka gansu  haka  nima na  gansu  kawai dai  na shiga  track ne  a sanadiyyar furucina.   shiru  barister hayat   yayi  yana  kallonta   tare da nazarinta  "ka yarda  barister  bani  na kashesu  ba  ta sake  fad'a   tana  rushewa da wani  kuka  mai  ta'ba zuciya  "mai   zai sa na kashesu  bani da wani halaka da kisansu   gara ma  ita sadear  mun samu  matsalata daita  har  nayi furucin zan  kasheta  amman ita wannan  yarinyar da naji ana  fad'ar  sunanta  sam  ban santa  ba   hasalima ban  ta'ba  ganinta a rayuwata  ba   tayi maganar  tana  sheshekar  kuka. Ganin yadda barister hayat ke  kallonta  yasa ta  shiga  furta kalmar    "na shiga ukuna ni hadiza  na jawowa  kaina  rashin kwanciyar hankali, ni kaina a daren ranar da sadear   zata   mutu  naga shigowar  mutun cikin bakaken  kaya  an shiga d'akinsu  amman sam ban  kawowa zuciyata cewar  kashe sadear za'ayi  ba ,  Ina da  tabbacin  da  police  zasuyi  aikinsu  yadda ya kamata  zasu  gano ko waye  yake  da saka hannu  cikin mutuwar wad'an nan  mutane guda  biyu  da'ake tuhumata  akansu ta k'arasa maganar cikin tsananin tashin hankali ."       kuka  take sosai  kamar  ranta  zai  fita  "naunayen  ajiyar  zuciya  barister  hayat  ya sauke "tabbas  na   yarda dake  Kuma  inshallahu  zanyi iya  qoqarina  naga kinsamu   ku'buta  duk da mahaifiyar  mubina ta tubure  lallai sai an kar'bawar  diyarta hakinta    shi  dai mahaifinta  alhj   jamilu   ne yace  ya  barwa allah amman   kiyi addua sosai    dan  idan mahaifiyar   yarinyar  ta rinjayi  mahaifinta gsky   sai  dai wata bake ba , bangaren  su  sadear   wannan  mai   sauki  ne   da kansu zasu gaji da zuwa kotu  kar'ban  kwana  wata su hakura , amman su  alhj jamilu suna da baki a kasar nan suna da fad'a aji akoina  dan haka  ki dage  da   addua  sosai  .  "na  gode  sosai barister da  k'okarin, "karki damu  Allah  ya bamu sa'a inji cewar  barister hayat   "Ameen   ta  furta tana kuka   sukayi  sallama da zumar  zai sake waiwayota  kafin a zauna kotu ." ****** Zaune   mahaifiyar  mubina   hajiya  sha'awanatu   take a had'ad'd'en kujera  a parlour'nta kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana cikin tsananin damuwa domin kuwa idanunta sun kod'e  saboda  kuka dan tunda jami'an tsaro suka zo musu da bayanin anyi kisan Kai da irin wukar da aka kashe mubina har anyi nasarar   kama mashekiyar  take cikin damuwa  da kuka , duk yadda    mijinta alhj jamilu ke  k'okarin shawo kanta taki  yarda burinta  bai  wuce a gurfanar  daita a yanke  mata hukunci  daidai da abinda ta aikata ba .a yanzu ma zaune yake   a gabanta yana  fuskantarta domin son kawowa zuciyata natsuwa "dan  Allah ki bar maganar  kisan  mubina  da ma duk wanda yake da saka hannu cikin kasheta mubarwa  Allah ,haka Allah yaso bazamuyi rayuwa mai tsawo tare daita ba , yanzu  karshe  wad'an  da basu ji ba basu gani ba sune  zasu zo suna cin wahala  bana jin wannan yarinyar zata iya shigowa har cikin gidan zainab ta kashe  mubina , dan haka ki natsu dan Allah ki samawa zuciyarki salama da hakuri  ". "uncle jay ........."  da  yake haka itama take  kiransa  kamar yadda ATA ke kiransa " kace na hakura na bar maganar alhalin an kama wacce tayi kisan  ?ya gyada mata Kai  al'amun haka  yake  nufi"  nifa  say  Inda karfina  ya  tsaya, wallalhi  sai nayi shari'a  daita  Koda duk zan qarar da abinda na mallaka  , Kai  bari  ma na takaice maka sai na rakata har  zuwa gidan yari  sannan ruhina zai samu salama , ai tunda asirinta ya tono bazan yarda ba sai itama an sha jininta  kamar yadda tasha jinin di........." Nace   kiyi  hakuri mu barwa Allah ya katse mata numfashi ta hanyar fad'ar haka " duk  wani  matakin da zaki d'auka bafa zai dawo mana da diyarmu da muka rasa  ba ,ta kwa'be.  masa  baki  da fuska  dan sam maganarsa  basa  shigarta   ya mike tsaye yana  dubanta "muddin Ina da iko akanki  ki  bar maganar  nan  mubarwa  Allah  Komai  yana  gama fad'ar   haka ya shige bedroom  dinsa ya barta tana  girgiza Kai  hawayen bakinciki rasa tilon diyarta na zubowa akan kuncinta bata Jin zata iya yafewa wannan yarinyar ." ******** "Adam  zaune  a makaken  office   dinsa  dake  cikin kasar hollond   zagaye da  makeken  table  wanda ke d'auke da file  files  dabam  dabam  sai qaramin  frem din  hoton  mahaifiyarsa da mahaifinsa  , sanye   yake   cikin  riga fara  sol da  wondo  baki  sai  yar  saman suit  dake  sanye a saman farar rigar  .  ya  d'auki  wayarsa  dake  qara tun mintuna   ashirin da suka gaba  har zuwa  lokacin daya d'auka  yana dubawa  miss call's ne rututu  bama zai iya  kirgawa ba , wasu yasan number's  wasu  kuma bai sani ba . ya sauke numfashi   sannan ya fara  da  kiran  MB  kasancewar shine wanda  ya kirasa karshe MB  ya  d'auka  yana  cewa " hello  friend  ykk ?  Lafiya  alhamdulillah  okay  ai Ina ganin  zan  shigo  cikin  satin nan   dan  sweetheart  ta matsa lallai nazo ayi  mgnr  aurena  da wannan yarinya gashi  ni wallahi har yanzu  bana Jin son yarinyar  Ina  jin qinta sosai  abinda  ke Kona min rai yadda sweetheart  ta nace  akan  lallai sai anyi auren nan kusa .   "kasan har cewa tayi  bata yafe ba muddin ban aureta ba ."Kai  gskiya Ina ganin ya kamata  kayi wani Abu tunda kaji abinda tace maganar MB  ta  doki  kunnensa   ",amman ni  aganina da an  bari zuwa wani lokaci sai ayi auren tunda ba neman kai akayi dani ba  " waya fada maka ?ai kuwa muna neman kai da kai mun gaji da ganinka haka dan haka   karka fara  cewar ba yanzu ba domin kuwa zaka samu matsala da mami   kawai  kabi umarni ka  tunkari yarinyar  da kanka."nace mata me MB   ? yayi masa tambayar yana ciza lips dinsa na kasa , shiru shima MB yayi yana sauke numfashi "ya  kake wata mgn haka ?ya sake tambayarsa a kufule  "darajan  da tsinuwar mami shine  abun lura shiru ATA   yayi  can  yace "Anya kuwa zan iya MB  gara  kawai a d'aura  auren zai fiyye min sauki akan na tunkareta  da batu na soyayya dan har abada bazan iya ba ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 Book one Last free page *AYSHA A BAGUDO* AREWABOOKS AYSHAABAGUDO WATTPAD @HAUESH bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 10 "ai Kuma shine babban matsalar abokina domin yarinyar  itama ta kafe akan bata sonka amman nasan da zaka mata magana  da kanka zata iya amincewa kayi k'okarin  ka shawo kanta da kanka dan Allah ,ka kwantar da kai  ka shawo kanta  yarinya nan yar'uwarka ce jininka ce  sannan ita din mace  ce ,mace Kuma 'yar rarra..." "ban son iskanci MB  ya katseshi a matukar  tsawace yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa " sbd me zaka  fad'a min hk ?" how dare you talk to me like that   ? “ shiru mb yayi  yana mamakin yadda abokin  nashi  ke saurin  daukar   zafi  akan abinda bai kai ya kawo ba "to me ma ya fad'a da zai dauki zafi haka ?mr ATA ya mike zumbur  daga Kan kujerar da yake  zaune tare da tura  kujerar baya tamkar ita tayi masa laifi ya soke hannunsa daya cikin aljihun wondonsa "Ita din  makiyata ce ita din ba jini bace karka sake fad'a min cewar yaruwata ce ko jinina ce Ka dinga sanin irin maganar da zaka fad'a min taya da girmana da mutuncina zakace na tunkareta common mace daita yarinyar da umarni kawai zan  bata  kuma dan dolenta tabi ,ta Inda yake shiga bata nan yake fita ba  " Shikenan kayi  hakuri abun ne yazo  hk amman  dai  ka  k'okarta ka....."dan Allah malam ka maida   hankalinka  jikinka sai  wani  qoqarin son saka min magana abaki kake wannan ai  mgnr banza  ce   "ka tsaya ka saueareni mana nifa hankalina  yana  jikina kai dai.... "dan Allah malam  kayi min shiru  babu wani saurararka da zanyi a yanzu  ".yana gama  fad'ar hk  yay disconnecting din   Kiran yana huci  ..."     "Nonsense girl kawai ai bata Isa ba ,bata ma kai wannan matsayin ba shi da mata ke bi suna kuka suna rokonsa  ko gaisawa su dingayi bai kaskantar da kanshi ya amince  ba bare har ya ajiye girmansa matsayinsa komai nashi yace yana son mace macen ma irinta  ko cikakken minti biyar bai yi da katse kiran    ba kiran hjy zulaiheart ya  shigo  sai   da gabansa yayi wani irin mummu nar fad'uwa kusan yanzu duk sanda zai ga kiranta sai hankalinsa ya tashi saboda yasan Kiran baya wuce akan  wannan banzar yarinyar  bane ." ilai  kuwa yana d'auka  da  maganar ta fara "Adamcy  kana  son ganin 'bacin raina  yayi saurin girgiza mata Kai kmr yana gabanta  "wallahi zan cire hannuna acikin lamarinka idan haka kake so "kiyi hakuri sweetheart inshallahu zanyi yadda kike so "kullum abinda kake fad'a kenan ka kasa aiwatarwa dan hk ka  shirya shigowa nigeria dan  cikin satin nan  maryam  zata dawo Kuma tana dawowa zaayi mgnr aurenku  da baba babba  har ta gama maganarta  bai sake  cewa qala ba ganin tayi shiru shima yayi shiru yaki cewa komai duk da yaso komai yaya ya bata hakuri  amman zafin da zuciyarsa keyi ta hanashi aiwatar da hakan har kusan minti goma tana jin yadda numfashinsa Ke sauka  da karfi kamar wanda yayi gudun tsare da kyar ya iya fezgo magana "sweetheart akwai abubuwan da nake son na kammala bazan samu damar dawowa nan kusa ba zaku iya yin  .."   "No babu  wani uzuri  da zanyi maka kayi duk abinda zakayi ka gama ka shigo cikin satin nan shiru ya sake yi yana sauraronta  tana gama fad'ar haka ta katse  Kiran bayan wayar ta katse ya bita da kallo zuciyarsa na rawa ."ajiye wayar yayi  akan makeken table din dake office din ya buga wani uban tagumi wanda dagani na takaici ne."    ya sake had'e fuskar nan  tashi  sosai wani irin bakinciki yake  ji acikin zuciyarsa, ji yayi kamar zuciyarsa  zata kama da wuta yana matukar  jin  bakinciki  abinda mahaifiyarsa  take  bukatar yayi ,shi da yake adduar komai ya watse a manta komai  amman ita kullum burinta  bai wuce taga faruwar wannan auren ba . banda 'bacin rai mai Kona zuciya babu abinda yake ji mikewa yayi ya shiga zariya a office din  yana zagaya koina  yana zurfafa tunaninsa kafin ya soma magana shi kadai  "ya zanyi ?me zanyi ?taya zan soma  rayuwa da yarinyar  da kake qoqarin amincewa aurenta ? sosai kwakwaluwarsa ta shiga tunani neman mafuta  dan dole yasan abun yi kafin mahaifiyarsa tayi masa  wannan auren  mr ATA ranar  kwana yayi  yana tunani  ." ****** Bayan  kwana  biyu  maryam  ta dawo  daga  Abuja murna gurin  nana hauwa'u hjy zulaiheart  da sauran 'yammatan   gidan babu  magana  dan  sunyi  matukar  kewarta sosai  hira  ce  ta yaushe gamo ta barke a tsakaninsu sai yamma suka bar gidan haka ma washegari  suka cika gidan har da rukkaya makociyarsu anan grã gidansu yake asalinsu nufawa né suna cikin hira rukkaya ta Kalli  maryam sannan ta Kalli  diyana  da nuzla tace   "nafi  kowa  Jin dadin dawowar  marsi  bari na  baku labari    nayi wa marsi    saurayi  kyakkyawa   ajin   farko ."      maryam   ta  kalleta   tana  kwa'be  fuska cike da takaicin Jin  maganarta   yayinda  itama rukkaya ta kalleta tana  sakar mata murmushin  jin dadi  . Sai dai a matukar  wulakance  maryam ta cigaba da  kallonta  kamar ta rufeta da dukan mutuwa   sannan ta  fara  magana cikin fushi da 'bacin rai  "bangane  kinyi min  saurayi ba ance Miki  bani  da  saurayi ne  ko ya    ? ke da duk fuskarki ta dame da   bille  kota  Ina an watsa  miki shi ba'a ce anyi miki saurayi  ba  sai ni  da fuskata take  lafiya lau  babu zane ko daya    ,Kalli  bakinki duk a warwatse  kamar  lefen sakarya shine zakice  kinyi  min saurayi , karki qara min  irin  haka wallahi  banaso ai kinfini bukatar saurayi ." Gabad'aya  suka kwashe da dariya rukayya kuwa tsayawa tayi tana kallon maryam da mamaki nana hauwa'u kam har da zubewa kasa  tare da rike ciki dan dry  ."Ina ganin dai  baki san    aljanu sun  shigi     marsi  ba ko ?  ai  babu damar  ayi mata  maganar maza sai hankalinta   ya tashi ." nifa  ba  haka bane  Ina da zabi  acikin  zuciyata  Ina da ra'ayin irin mijin da nake son aure ba kowani shasha ba  amman dai  na  barwa zuciya  irin mijin da nake so Ke mai bille sai ki rike saurayin dan kinfini bukata ." rukayya  ta Kalli nuzla nuzla ta kalleta  sannan a matukar fusace rukayya tace  "karki qara cewa fuskata anyi  min bille "to karya ne ba'a yi miki ba ? "idan bakya so nace miki hk  nima ki barni da batun wani saurayi can   tun da bance miki  nayi ina son ba wadan da nake dasu ma sun Isheni bana neman qari sun  dade  a d'akin  suna hira  akarshe duk suka watse  suka kama gabansu." ****** Karfe   shabiyu   daidai jirgin   Mr ATA ya sauka  a lagos  a haraban  gidansu tun   kafin   jirgin ya k'arasa sauka  security's  dinsa  ke zagaye da gurin har sanda ya sauka , a hankali   ya  mike yana  gyara zaman rigarsa Sannan   ya fara  takowa  daga matattakalar bene yana taku da  kyar cikin  tafiyarsa nan nashi na Koda yaushe wato tafiya cike da alfarma da izza  yana d'aga  kafafunsa yana shakar iska  da kyar  tare  da hura hanci  escort  dinsa already sun fito suna  nan tsaye  suna  jiransa duk Inda ka duba acikin haraban  gida masu aiki ne ke Kai kawo suna aiwatar da aikinsu." yana qarasa saukowa escort dinsa da security's  sukayi masa caaaa har zuwa Inda yake tsaye Inda ya fara taku suna biye dashi har zuwa bakin kofar  shiga cikin   parlour'n mahaifiyarsa  na d'aya ,  yana isowa gurin yaja ya tsaya  d'aya daga cikinsu mai suna muzammil  ya  bud'e masa kofar  ya shiga yabi bayansa shi kad'ai rike da bakar jaka  ATA   bai tsaya akoina ba  sai  a babban falon  mahaifiyarsa   ya  shiga ya zauna ya kame akan  d'aya  daga cikin kujerun falon  ya d'aura hannunsa d'aya  akan gwiwarsa  yana d'an  jijigawa yaronsa  muzammil  ya rankwafo  ya ajiye  masa  jakarsa  ya  bashi  izinin tafiya ya  juya da sauri  ..."  A hankali  mami  tayi sallama cikin  had'ad'd'en falon a zaune ta samesa akan kujera ya lumshe lumtsatsun idanuwanshi ,da kyar  ya bude baki ya amsa sallamarta  batare daya bud'e idanunshi ko matsowa ba har sanda ta zauna akan kujerar dake kallonsa tana jin sanyi da farinciki mara misaltuwa  da ganin kamilallen  danta mai nagarta da haiba illarsa dai rashin ajiye  iyali da miskilanci da zafin rai duk wannan farinciki daga ciki take jinsa dan bata bayyana shi ba . a hankali ya bud'e lumtsatsun idanunshi ya mike ya k'araso gabanta ya rusuna  har  kasa  "mun sameku lafiya  sweetheart? Wani sanyin dadi Ya ratsata  ta kai hannunta kanshi "alhamdulillah ka sauka  lafiya   ya aiki Ya  fama da jama'a ? ta fad'a fuskarta  babu yabo babu fallasa "alhamdulillah sweetheart  yayi magana yana matukar tausayin Kansa dan yasan tunda ya zo ya  dinga cin karo da matsaloli kenan dole sai yayi hakuri dan magana daya ce za'a yita ana mai maitawa ,." A natse  ya mike ya koma mazauninsa ya zauna  yana neman layin M.B  da sauran friend's dinsa   kafin kace me hjy zulaiheart tasa an  cika masa gabansa da kayan itatuwa dabam dabam sai dai babu wanda ya d'auka yaci illa amsa waya da yake ta bangare damba dabam , nana hauwa'u ta shigo ta gaishesa cike da ladabi  "yayanmu Ina yini ka dawo lafiya .?" "Lafiya auta  ykk ya fad'a  atakaice"  lfiya ta bashi amsa da haka sannan  ta  mike ta koma ciki dan yadda fuskarsa take a  murtuke  nan   komai  zai iya faruwa , haka  rashida   da muna   yaran baba qarami   sun shigo  gaishesa a mutunce ,  babu yabo  babu  fallasa ya amsa  haka akayita shigowa yi masa sannu da zuwa sai dai ya amsa atakaice ba tare daya bi ta kansu ba maryam ce kawai bata shigo kawo gaisuwa ba har  sanda MB ya k'araso sai daya yi sallama a bakin kofar falon aka bashi izini  shigowa sannan  ya shiga . ATA  bai motsa daga Inda yake ba har MB ya shigo ya zauna cike da tausayin abokinsa dan kallo d'aya zaka masa kasan baya tare da walwala da farinciki  har wata siririyar rama yayi "ATA..!" ya kira sunansa  anatse ATA  bai amsa ba illa zuba masa kwayar idanunshi   da yayi yana sauraronsa "yana  ga duk ka rame ? shiru yayi bai ce uhm ba bare uhm uhm sai dai ga dukkanin alamun hankalinsa na kanshi "dan Allah ka kwantar da hankalinka komai na duniya mai wucewa ne idan kabi komai a sannu da sannu komai zai zama normal ." wani huci numfashi ya saki yana sake tsaida idanunshi da gbdy  suke cikin damuwa akan mb sai da yayiwa MB kallon wasu mintuna sannan ya furzar da abinda ya tsaya masa a makoshi mai mugun daci cikin son danne duk wata damuwarsa yace "na rasa yadda zan cire wannan damuwar MB "kallonsa MB yayi yayinda ATA ya Maida idanunshi ya lumshe "Ina zanganta ?ya furta a saman labbansa cikin tsananin damuwa  "wa kenan ..?Idanunsa dake lumshe ya d'an bud'esu  da   kamar  bazai yi magana ba sai Kuma ya furta ", princess.."   murmushi MB yayi "ka iya fad'ar sunan nan tamkar kai ka fara tsarashi a duniya "zaka ganta inshallahu Ina maka adduar ta zamo mutun ce ba aljana ba , sai abu na gaba  ka fara da abinda mami   take so "bana jin zan iya MB zan dai ta bin sweetheart  a hankali  har  sanda zan samo yarinyar ko  kuma na samo wata dabam  amman wannan guntuwar yarinyar  bazata zamo mata a gareni ba  sun dade suna tautaunawa kafin daga baya sukayi sallama duk Kuma maganar da suke akunne mami   sukayita , dan  haka ta shaka sosai  tun a lokacin ta fara  shirya abinda zata masa ." Tunda  masu aikin gidan suka  san  ATA  ya sauka kowan nensu ya shiga hankalinsa hatta shigowarsu part din hjy zulaiheart ya taikaita sannan komai cikin sauri suke yi kasancewar sun san  shi dan Oya  oya ne duk da ba  abincinsu yake ci ba sai na mahaifiyarsa  kuma  bata zauna ba har washegari  tana kan  yi masa hidimar abincin da zai ci tare da abokansa Amar, shawul, shamsu MB  sun baje  a falonsa sai kwasar abinci suke Amar yace "friend duk fa matar da ka aura muddin bata iya girki irin na mami  ba zaku samu matsala daita  ",Sosai kuwa dan ni dai Ina ganin zan kawo fedy gurin mami  a sake  bata class na mussaman dan wanan girki yayi inji cewar  MB " suka sa dariya banda ATA  dake rike da waya yana duba mahimmam bayanai masu shigowa  . Sai  daya  rage  mahimmam abubuwansa  sannan  ahankali ya motsa  lip's dinsa "gaskiya ne Ina son macen da ta iya girki kuma qala dabam dabam  shiyasa kuka ga Ina dojewa auren yarinyar  nan dan nasan  babu abinda ta iya sai salo da  rike waya da shiga social  media ,ni Kuma ta Inda za'a samu matsala dani  kenan  dan  bazan yarda da rashin kamun Kai ba.    gbdy suka  gyda  Kai  batare  da  sunce komai  ba  sai can  shawul yace  "ai idan princess dinka  ka aura ko bata iya  girki ba zaka  zauna daita haka  har karshen rayuwarka ATA ya sauke numfashi kawai   batare da yace uffan ba "kayi  shiru ko ba haka bane ? Inji cewar MB "ka'ajiye wannan magana bama zata  zo a haka ba  am very sure ta iya komai  ." Shawul yayi sigili yace " mai kmr mrym me zaiyi da wannan princess din taka ya watsa masa wani mugun kallo  "ra'ayina kenan princess  bana son mace  irin wannan yarinyar da ake kokarin lika min  yayi mgnr yana furzar da iska mai  zafi  daga bakinsa. "Wai  Kai wayace  maka ana auren mace mara kiba a yanzu Kai gaka ba jiki ba , Kai    Kashi  ita kashi kuzo Kuna haihuwar kasusuwa Kai da zaka samu mai nama irin Marym chubi daita komai zamzam inji cewar Amar  gbdynsu babu Wanda bai dara ba MB kam har da fadowa yayi kasa  daga kan kujera dan dariya "ko jini  zamu dinga   haifa   ba kasusuwa ba. nafi  sonta  akan wannan  mai  siffar aljanu guntuwa  gata nan  dai  fari ne kawai ya taimaki rayuwarta.   nana  hauwa'u  da  mryam  dake tsaye a bakin kofar falon hannu nana hauwa'u rike da tiren silver mai d'auke da gasashen kifi anyi raping dinsa  ita kuma mryam na rike da tire na harish   suka  Kalli  juna dan sunji abinda suke tautaunawa daga ciki , naunayen ajiyar zuciya nana  ta sauke tace "mu shiga sister ta fad'a tana  rike tiren hannun maryam  dake  k'okarin  subucewa qirjinta na dokawa tace  "a'a sister  ke dai ki shiga ke kad'ai  bari na tsaya anan  har  ki fito banason na shiga Ina jin tsoron kar ya disgani agaban abokansa ta k'arasa maganar tare da  d'aura  tire  dake hannunata akan tiren hannun nana hauwa . suna  tsaka da hira suka jiyo sallama a bakin kofar falon MB ya bada izinin shigowa tare da komawa mazauninsa    ta shiga a natse ta  gaishesu  cike da ladabi  sai dai kallo d'aya zaka mata kasan ranta a 'bace  yake ta tsani taji yayanta yace bai son mrym ko aibantata  bare yau a gaban abokansa ." Amar ya washe baki yana dubanta kana ya  soma  mata wasa kasance warsu abokan wasa   "a'a gasu cubi   hauwa  fa  ,farar mace alkyalbar  mata Ina ganin nida  madam  zamu  lalla'bo muzo  ki sammana man da kike shafawa kullum ke da maryam kmr bakwa fita rana,  gaku na nan  dau  kmr yanzu kuka sauko daga sama."   tayi masa banza   tana jan tsaki a ranta "Ina kika baro mrym dan nasan ke daita 5&6 ne?  ta sake sharesa   tana kokarin   ajiye  tiren hannunta wayarta dake rike a hannunta tayi kasa zata fadi madadin ta bar wayar sai tayi k'okarin rikota  Aiko tiren  gbdy suka  sullube a hannunta sukayi kasa tiren  kifi ya kife nan take mai  ya fara malala  gabanta ya buga da karfi  nan take jikinta ya kama rawa   ta d'ago da sauri ta Kalli Inda ATA yake zaune gabanta na cigaba da fad'uwa ." wani dogon tsaki ATA  yaja kana ya soma magana cikin fushi da zafin rai   "  kunga irin haukan nasu ba koina zaaje da waya kamar wasu  yan kauye "haba ATA  me yasa zaka dangantata da  Kalmar hauka tsautsayi ne ko babu waya a hannunta hakan zata  kasance "shawul karka goyi  bayan wad'an yaran sam babu abinda suka iya sai hauka komai na mata basu iya ba basu iya girki ba basu iya gyaran daki ba sam basu iya komai na mata ba yan iskan banza kawai  sai aikin rike waya  da surutun banza da wofi da  maza  kije ki dauko abinda zaki  gyara min guri kafin na soma kwallo dake, sai naci ubanku daya byn daya kafin na koma idan Kuma baki dawo kin gyara ba kika turo min masu aiki  sai na canza miki kamanni stupid kawai ." fuuuuu ta fita tana zunburo baki   a bakin kofar  nana hauwa'u ta samu  mrym  tsaye duk ilahirin jikinta rawa yake gbdy  duk ta Kara firgicewa Ta kalleta tana hawaye bata tsaya yi mata bayani ba ta wuce dan tasan taji komai  daya faru." Kai tsaye   kitchen Inda hjy zulaiheart take  ta shiga  ita Kuma maryam ta gudu tayi dakinsu , nana hauwa'u  na gama shiga kitchen ta   soma zuba balai "wai mami  dole ne sai ya Adam   ya  auri mrym ne ." "Dan girman allah me zai hana abar maganar kowa yaje ya auri wanda yayi masa  ? mami ta dubeta a natse  "me yasa kika fadi hk  hauwa wani abu ne ya faru  ?"to  gashi can sai faman fad'awa su ya amar yake wai bai sonta guntuwa ce  fari ne kawai ya  ceceta  mene mene  ko ance masa itama tana son shi ne ? gsky kiyi masa mgn ya daina  nima yanzu kafin na fito sai daya tozartani a gaban abokansa shiyasa wallahi ban so zuwa ba ,wallahi duk matar data auresa ta shiga uku da matsalolinsa  wallahi ni dai a fasa had'in nan da marsi  tana gama fad'ar haka ta juya fuuuu  ta fita  mami  tayi murmushin  takaici  kawai tana girgiza Kai ,nana  bata so komawa bangarensa ba amman babu yadda ta iya haka ta d'auki abun gyara ta koma kafin yaci ubanta  ". ****** Washegari  da misalin Karfe biyu   daidai  Kiran aunty shahida  ya shigo wayar mrym  tana    d'auka tace ki samemu a parlour'n mami  na biyu bata tsaya ji abinda  zatace ba ta katse Kiran ,shiru tayi tana sauke wayar daga kunnenta jiki a sanyaye ta mike ta d'auki mayafin abayar dake sanye ajikinta tayi rolling din kanta ta fito ta nufi parlour'n gabanta na dukan uku uku.      zaune ta iskesu gbdy ya'yan  hjy zulaiheart  banda  nana hauwa'u ATA zaune yana rike da waya yana daddanawa  sau dari zaka gansa to  da waya ne ko system yana operate "samu guri ki zauna aunty zabiba ta fad'a tana nuna mata kan kujera  kasa zama tayi a Inda ta nuna mata . a hankali ta samu guri ta zauna nesa kadan dasu a qasa dan gudun balain ATA  ta kasan idanunta take qare masa kallo  sanye yake da dogon wando da riga mai gajeren hannu blue   da ratsin fari kayan sun yi masa kyau sosai ga gashin Kan nan nasa sai sheki yake wanda da alama yana shafa man gashi ne yasa yake fitar da sheki  ko yaushe ." "Adam ga mryam  nan "inji cewar aunty shahida "naga  tantiriya mara kunya mara mutunci , uhm Ina jinki ki  maimaita abinda kika fad'awa aunty  a gabana ".  sai da gabanta yayi wani irin  mugun fad'uwa taji wani abu ya tsarga mata tun daga qirjinta har zuwa kasan mararta  take taji  marata ta soma murd'awa  taji wani abu mai d'umi ya zubo mata wanda bata raba d'ayan biyu na tsananin tsoronsa ne."   ta d'ago kanta a hankali taga har lokacin kanshi na sunkuye yana danna wayar hannunsa  "ke har kin Isa kice wai bazaki aureni  ba ?tayi saurin   sunkuyar da kanta kasa tana sake jin digar wani abu mai zafi na diga a pent dinta wanda babu tantana jini ne yazo mata a dalilin tashin hankalin daya risketa ne ya cigaba da magana fuskarsa a d'aure tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa  "daraja kika ci bancin haka har duniya ta nade baki Isa ba , km baki Kai matsayin da zaki zamo mata agareni ba ." ta  d'an dago kad'an  ta saci kallonsa adaidai lokacin daya dago idanunshi suka tsarke cikin nata wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki wanda babu tantama na tsoro ne  wani irin mugun kallo yake mata mai firgitarwa "Ina  jinki  fad'a  min abinda kika fad'a masu ?"kaga AD  ba dan ka tutsiye yarinyar mutane muka taro anan ba mufi bukatar amincewarta akan komai "no aunty shahida bari ta fad'a  taga yadda zanci ubanta  ". "nace abar wannan mgn  ta wuce ke  mrym kin amince zaki  auresa ko kuwa  har yanzu baki so dan yau shine final decision domin zamu sanar da mami  komai ? "muryarta na rawa tace "na ...na amince .." "kin amince da me ya fad'a a tsawace yana zaro mata Idanunshi  "na amince zan..zan  aureka " you are very  stupid ,useless kawai tashi ki 'bace min da ganin  kafin na miki dukan mutuwa ,bana sonki kuma bazan aureki ba daman nasan baki Isa  ki kalleni ki fad'a min abinda kika fada musu ba ,  maza tashi ki bar nan bana son  kallon wannan banzar  fuskartaki ya k'arasa maganar  yana jan tsaki tare  da runtse idanunshi ." har ta mike zata  tashi  aunty shahida tace  "koma ki zauna tayi saurin  girgiza mata Kai tana duban Inda yake zaune tare da jujjuya hannuwanta cike da tsoro  "nace  ki koma ki zauna a d'ard'ar  ta zauna tana kallon kasa a ranta tace "masefaffe banza kar Allah yasa ka aureni nima ai banasonka . muryarsa  a kasalance yace "muddin kuna  bukatar na cigaba da zama na saurareku sai wannan yarinyar ta bar falon nan  " shiru falon yayi babu wanda yace uffan gashi babu wanda ya Isa yayi mgn sai aunty shahida ko khadija da yake bi bata isa ba bare zabiba da  kanwa ce ,aunty shahida  ta Kalli maryam tace  "mrym  kin  amince zaki auresa ?tayi saurin gyada mata Kai alamun "eh .! "Okay tashi ki wuce abunki ta mike da sauri  kmr iska ta bar parlour'n "a gsky Adamcy ban ji dadin abinda kayi ba ,a hankali ake bin komai Kai komai zuciya da zafin rai Allah ya sausauta mk zuciyar nan karta sa wata rana kayi nadama  iska ya furzar "yanzu tunda ta amince shikenan sai mu sanar da mami  aunty shahida ta fad'a tana kallon kannenta mata "eh hk ne suka hada baki gbdy . "Da izinin wa kenan zaku sanarwa sweetheart .? "Da fari na amince maku  zan aureta  amman wannan iskancin da tayi yasa na fasa aurenta har abada km  komai zai faru sai dai ya faru amman na fasa "haba yayanmu dan Allah kayi hakuri karkayi haka  tunda ta amince ka aureta kawai a wuce wajen   tsoronka take ji shiyasa kaji ta fadi hk, cewar zabiba "ka taimakemu karka fasa auren nan  kodan mami  kabi komai a sannu please "ai bai ma Isa ba tunda ta yarda dole ya  aureta  ka godewa Allah da kasamu salahar mace mai kamewa kmrta  ." "bafa zan aureta ba I repeat it I can't marry her ,na aureta na kaita Ina da wannan rashin tarbiyar nata ?"yanzu ku baku ga rashin dacewarmu ba ?A tare suka girgiza masa Kai "mu bamu gani ba sai sam barka .Ya girgiza Kai " matar data Kalli tsabar idanunku tace bata son jininku har abar so ce agurinku  ?yayi musu tmbyr a matukar fusace"    dukkaninsu kallonsa sukayi yadda jikinsa ke rawa kmr anjonasa masa shocking ."Ku bar ganinta shiru shiru irin wadan nan  mutanen abun tsoro ne wallahi gara a  bani masefaffiya daita  juyin duniya sukayi dashi yace bai sonta km bazai aureta ba  "na yarda ku nemo wasu mata  ku aura min ko guda hudu ne  km a rana daya na amince amman ban da wannan jakar yarinyar mara tarbiya  yana gama fad'ar hk  ya mike ya kama gabansa kallon junansu sukayi na second  goma sannan suka numfasa "yanzu me kuka ga  zamuyi ?inji cewar aunty khadeja "mu fad'awa mami  kawai tasan komai dan boye boye bashi da wani amfani zan fada amnan mu bari zuwa jibi zan san yadda zan fad'a mata  . atare suka mike suka nufi d'akin hjy zulaiheart tana zaune akan kujera tana duba abubuwan da suka kawo mata  suka shigo jikinsu a sanyaye tana ganinsu ta fad'ad'a fuskarta da murmushin jin dadi  duk suka yiwa kansu mazauni ta kallesu daya byn daya "Allah  dai  ya taimakeku gbdy  yayi muku albarka yadda kuke tsaye akaina da abinda kuke min dukkaninku Kuna min k'okarin gurin yin abubuwa ." "da wanda ya bani million daya da wanda ya bani dubu dari da wanda ya bani  dubu hamsim dukkaninku abu d'aya ne agurina Kuma inshallahu ladanku daya ne saboda dukkaninku abu d'aya ne ni dai fatana Allah yayi muku albarka ,kowa yayi abinda zai iya ban da takura kai , Allah ya raya muku zuriarku yadda kuke hidima dani Allah yasa yayanku suyi muku fiyye da haka "Ameen suka had'a baki gurin fad'ar hk. shiru sukayi babu wanda  ya sake  kokarin fad'a  mata halin da'ake ciki ta d'ago daga duban kayan da suka  kawo mata, shiru tayi tare da tsura musu Ido"ya na ga  kmar bakwa  cikin farinciki alhalin ba haka fuskokinku yake ba a d'azu da kuka zo  ? naunayen ajiyar zuciya suka sauke "ku fad'a  min  idan wani abu ne  ? shiru sukayi kowannensu najin tsoron mgnr ta fito daga bakinsa "Kun min shiru ku fad'a min mana Kun tasani gaba Kuna kallona da kyar  aunty khadeja ta soma bayani "kiyi hakuri aunty shahida zata fada miki komai amman ba yanzu ba ." "akan Adamcy ne ko ?ta tmby tana dubansu a tare suka girgiza mata Kai  alamun "eh  suka tsinci kansu da bata amsa da haka "yanzu har akwai matsalar da zaku boye min bayan bani da kowa daga Allah sai ku duk abinda ya kunno Kai cikin rayuwarmu tare muke had'uwa muke magance matsalar shine yau zaku barni cikin duhu, shikenan na gode karku fad'a dan ko Kun fada min daga baya bazan gode ba Kuna iya tashi ku kama gabanku ." zubewa sukayi a gabanta kamar zasuyi kuka "kiyi hakuri mami  zamu fad'a miki a natse aunty shahida ta zayyane mata  komai tun daga ranar da suka fara magana da mrym har zuwa yau din nan "shiru hjy zulaiheart tayi tana sauraron  aunty  shahida  da sauran  yaranta mata  byn ta gama Jin komai ta numfasa  kafin daga  bisani tace "shikenan ku barni dashi zan nuna masa ni na haifesa bashi ya haifeni ba  daman na dade da sanin  baya son farincikina." nan  suka cigaba da tautaunawa  "Allah  mami   ki bud'e  masa wuta idan yaga kin haukace masa zai yi abinda kike so "ku  barni  dashi a yau din nan zai amince ko kuma ya canza uwa  aunty shahida tace "duk abun bai kai haka ba ki dai bisa a hankali kar komai ya jagule  "babu wani binsa da zanyi ahankali ai shi zuma ne sai ancisa da wuta ake samun kansa daman Ina lallabasa ne na d'auka abun nasa na girma da arziki ne  a she wulakanci ne  tana gama fad'ar  haka ta mike ta nufi d'akinta   .." tana shiga  aunty khadeja ta mike  ta d'auki jakarta ta rataya "ni zan wuce baza'a yi wannan dramar Ina gidan nan ba ,itama zabiba  ta mike jirani mu wuce tare gbdy suka mike suka fito tare  ." ******* A bangare  mrym kuwa tana shiga d'akinsu  ta fashe da matsanacin kuka nana hauwa'u dake zaune ta zabura ta k'araso Inda take ta rungumeta tsam tana tambayarta sai dai taki bata amsa kuka take sosai zuciyarta na zafi da qunci "me yasa ya Adam bai sona ?me yasa nana hauwa'u fada min aibuna  da yasa baya Sona  ? tayi mgnr hawaye na tsiyayowa daga cikin idanunta ,nan nana hauwa'u ta fahimci dalilin kukanta "Kiyi hakuri marsi baki da wani aibu illa rashin sa'a irin nasa domin sai ya aureki zai san yayi Sa'ar samu mata  mai kyakkyawar zuciya."        qaruwa kukan marsi yayi ",yadda bai sona nima bana son shi amman nayiwa kaina alkwarin zan auresa zan rayu dashi muddin rai "  wani murmushin farinciki nana hauwa'u ta saki tare da sake rungumeta ajikinta tana Shirin magana qarar  wayar   yasa tayi shiru sannan  suka saki juna a hankali ta k'arasa ta d'auka tana kokarin fita daga d'akin  mrym ta shige bayi ta kulle ta jingina bayanta da kofar ta sulale  zuwa kasa tare da sakin wani  kuka tana toshe bakinta da sauri nana hauwa'u ta fito zuwa haraban gidan Inda ta iske yayyunta mata da mamaki take kallonsu ",ya haka har zaku wuce ?tafiyar dole ce auta  dan yau bom zai tashi a gidan nan Kuma tashin babba ne gara mu san Inda dare yayi mana "daman na kiraki ne dan kisan yadda zaki kwantarwa mrym hankali tare da bata kwarin gwaiwa ." "Ga ta can kuwa sai kuka take amman ai ta amince zata auri yaya ? " eh ta amince amnan ai shi uban gayyar yace bai yi inji cewar zabiba "Kai! ta fad'a tare da dafe goshinta "kiyi kokari ta dawo normal inshallahu zuwa jibi zamu shigo idan munji yarda suka kare da mami   juya sukayi a tare kowace ta nufi motarta tana tsaye direbobinsu suka jasu sannan ta juya da sauri ta koma ciki. koda ta koma d'akin bata ga mrym ba tana toilet ta kunnawa kanta ruwa tana kokarin daidaita natsuwarta da rarrashin zuciyarta, dole tana bukatar ta  rarrashi kanta sannan ta sanyawa zuciyarta hakurin zama dashi ta kowani hali , guri nana hauwa'u ta samu ta zauna abakin gado tana jiran fitowarta ." Rai  a matukar bace hjy zulaiheart ta shiga bangaren  ATA   tana gama shiga ta fara zuba masa fad'a " tur da haihuwarka Adam  " ya  waigo a matukar firgice yana zaro Idanu lokaci guda yay fillinging da wayar dake rike a hannunsa ya zube kan gwiwowinsa kasan  a gabanta cikin tsananin tashin hankali muryarsa a shake yace "sweetheart  me nayi ?"dan Allah ki yafe min ,kiyi min afuwa bazan sake ba." hjy zulaiheart ta nuna sa da yatsa "Kai Adamcy ban ta'ba  sanin baka da hankali da tunani ba sai yau , yau  tsawon shekaru Ina binka akan magana daya amman babu komai na rantse da girman Allah bazan sake maka magana akan batun aurenka ba ka cigaba da rayuwarka  haka har mutuwa ta riskeka  tunda baka san mutuncin kanka ba, ga yarinya yar mutunci yar'uwarka amman dai..."sai tayi shiru tana huci ta kasa cigaba da mgn  sai lokacin ya fahimci laifinsa ."         ya sunkuyar da kansa kasa yayinda mami  ta cigaba da magana cikin zafin rai "idan baka so maryam ba   wa yakamata kaso?" ba dan maryam na diyar dan'uwana ba tana da nagarta da kamun kan da  kowani nmj zai sota Kuma mahaifinta nada nagarta da zai zama surukinka  "ai ka nuna min ban Isa da Kai ba ko ? to  na gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya biya ." "a'a sweetheart wallahi kin Isa dani sai dai zuciyata ta kasa  ..."mami  tayi saurin  tareshi da cewa ",aikin banza daga yau in nice na haifeka to ka fara shirin aurenka da maryam Koda yin hakan yana nufin rasa komai naka  ATA  ya kalleta da sauri sannan yace "to sweetheart zanyi duk yadda kike so sai dai naso ki dan saueareni kiji ita kanta yarinyar bata ..." Mami  ta juya a matukar fusace tana cewa  "bazan saurari komai daga bakinka ba ni dai na fad'a maka muddin nice uwarka ka shirya rayuwar aure da mrym idan baka zo ka sameni da maganar aurenta a daren yau ba   na rantse maka da girman Allah sai dai ka nemi wata uwar bani zulaiheart ba kayi abinda nake so shine zaman lafiyarka dani  ta karasa fita tana magana  cikin tsananin fushi da bata ta'ba yin irinsa ba ." ATA ya rike kanshi tare da furta "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun"shikenan zuciyarsa ta sake shiga rud'ani   kasa ya zame ya zauna  akan capet tare da zabga tagumi tunani yake yi yanxu ya zai yi kenan?"shin ya cigaba da kafewa akan ra'ayinsa ne ko Kuma ya hakura ya aureta  a wuce gurin ?cike da sanyin jikin ya mike ya nufi bangarenta   Yana kokarin shiga part dinta sukayi karo da maryam  itama d'akin hjy zulaiheart zata sakmakon kiranta datayi ." wani irin gigitacen mari ya ɗauketa dashi Sanna ya rufeta da duka "kina hauka ne da zaki hada jikinki danawa ? kasa tayi dafe da kuncinta tana kallon zara zaran yatsun ka'fafunsa dake jere kowannensu dauke   da kwantaccen gashi ,koina ajikinta rawa yake "mahaukaciya kawai ko ni sa'anki ne ?ta d'ago tana dubansa sai faman huci yake "Maza ki d'auke wad'an nan banzayen idanun naki akaina wallahi ban taba jin na tsani wani halitta ba kamarki har kece zaki bude baki ki fuskanci 'yan'uwana da Kalmar baki sona saboda ke din dakikya ce da bata san hallici ba yasa kafarsa d'aya ya take mata kafa yana watsa mata kallon banza ."    "ki sani bana sonki kuma har abada bazan soki ba wani abu taji ya caki zuciyarta tare da kafeshi da idanunta da suka canza kala zuwa na bacin rai  yayinda wani bakinciki ya tokare mata kahon zuciya wanda yasa hawayen ya cika  idanunta amman ta danne taki barin su zuba  tunda  take baa ta'ba mata wulakanci irin na yau ba wannan shine karo na biyu da ya daura hannunsa ajikinta ranta yayi matukar baci  tana son ta bar wajen amman bazata iya ba bazata iya ba dan batasan me zai sake biyowa baya ba ,dan haka ta kife kanta akasa kuka take son tayi amman bata son tayi akan wani banza da bai san darajarta ba ..." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗    MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS AYSHABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 11 "  har tsawon wannan lokacin yana tsaye yana mata kallon kaskanci kafin daga bisani ya d'an motsa labbansa " biyayya   Kawai zan  yiwa  mahaifiyata na aureki   sai  dai  zakiji  jiki  sai   kinyi  da kin sanin  kalmarki  gareni,  zakin san kin  ta'boni   yana  gama   fad'ar   haka ya d'auke   kafarsa  tare da   shure   mata  kafa  ya nufi  cikin part  din  mahaifiyarsa ransa a dagule .  girgiza  kai  mryam ta  shiga  yi  kafin  daga baya  ta  rarrafa  ta shige  parlour'nsu     ta  ra'be a bakin   kofar d'akin tana  kukan zuci , cikin   yanayi  na tashin   hankali  take  furta    "me  na  tsare maka  ya  adam  ? "me yasa   baka   sona  ? "me yasa   ka   tsaneni hk ? haka tayita  jerowa kanta   tambayoyin da bata da mai bata amsa  sai shi shi din kuma bata isa ta tuknkaresa ba   gbdy  Idanunta   sun canza qala tsabar tashin hankalin data tsinci kanta ." kuka   take  son yi sai  dai   zafin da zuciyarta    ke yi  yasa  hawayenta yaki diga sai idanuwanta gbdy sun burkice    " baka sona   amman  ya zama   dole  na  jurewa  komai  muddin  ina  son rabuwa da iyayena   lafiya , bazata  manta kalman mahaifinta   ba alokacin da zata dawo daga  abuja   domin sun samu kyakkyawan  mazauni  acikin kwalkwaluwarta "maryam  muddin  ni  ne  wanda   nayi  sanadiyyar zuwanki  duniya  Kuma kina  son  gamawa da duniya  lafiya  ki auri adam  bisa umarnina Kuma ki zauna dashi  zama na amana bisa umarnina , yau ace ba yar'uwata ce  ta nemi wannan hadin ba sam bazan takura miki ba zan barki har sanda zaki kawo min irin mijin da kike so   .." A  bakin  gado  ya iske hjy zulaiheart   ta  cika tayi bam   ,cikin   sanyi  jikin nan nashi  ya k'araso   ya  zauna  a gabanta   yana  neman gafararta  ,   ko  kallon Inda   yake   bata yi  ba daga   karshe  ma ta  kawar   da   fuskarta  gefe  al'amun  bata  son ganinsa   ya   runtse idanuwanshi  sosai yana sauke  numfashi ,byn  kmr  second biyar ya bud'e  idanunshi  ya fara  Kame  kame  "uhm ammm   kiyi hakuri   sweetheart   , afuwa sweetheart   I will not  do  it  again , inshallahu  I promise  you  zan aureta ." "hjy zulaiheart taji  dadin jin    furucinsa     har  cikin   ranta  sai  dai ta share  tana  jan tsaki a fili. "ki yarda  sweetheart duk  duniya   babu  wanda  zai  soki  da son farincikinki   kmr ni  ,kiyi  hakuri  bazan  juri  ganin  'bacin   ranki ba   ya fad'a yana riko hannunta ,  naunayen ajiyar zuciya ta  sauke batare  data  fuskancesa ba  ,duk  da  zuciyarta ta d'an  yi sanyi  dan daman fushin na dole ne yanxu kuwa ta   hakura . damuwarta  daman yayi   aure  tana  son  taga aurensa  taga  ya'yansa  kamar  yadda  taga na sauran  yaranta   amman  duk  da  haka  bazata sakar  masa fuska  ba dan tasan halinsa kamar yunwar cikinta canzawarsa  bai da wuya  ya  d'auki  mintuna masu tsawo  agabanta bata  daga  Kai ta  kallesa ba sai ma  ta mike zata  bar masa  d'akin , ya mike da sauri  jikinsa na kyarma  ya  tareta  dan sosai ya hango  damuwa qarara akan  fuskarta  ya sake kamo hannuwanta  duka cikin nashi  , ta  fizge  a fusace tana watsa masa harara   "sweetheart  kiyi hakuri  dan girman Allah  wallahi  zan  aureta  trust Adamcy  zai  aureta tunda  yace  zaiyi wallahi wallahi zan aureta Koda kuwa  zan rasa rayuwata....." hannunta d'aya  tasa ta zare  hannunta daga cikin  nashi   ta tsura masa  idanunta  "wallahi  ban  san  Inda ka d'auko halinka  ba ,  sam mahaifinka   ba haka yake  ba  mutumin kirki  ne, mahaifinka baya  uhm  baya  uhm bare miskilanci ,  kullum cikin neman   yadda  zai kyautata  mana daku ya'yansa da  'yan'uwansa yake ,  a kullum mahaifinku  so  yake   ku  zama na gari a rayuwa  sannan  masu  jin  kan iyaye  da tausayi  Allah ya  duba  bayan mahaifinku  cikin kaf  ya'yan  mahaifinka   Kai ne  kawai  ka  fita dabam acikinsu  da wasu halaiya Kai ma  Kuma wannan  halin miskilancin da zafin zuciyar  ne  illarka tun kafin ya  rasu ya fad'a  yace bashi  ka d'auko ba .bari na  fad'a maka gsky  wannan halin naka sam ba  nashi  bane  Kai ka san  Inda ka samo  abunka dan shi ba haka yake yi  ba,  dan ta mahaifinka    duniya  bazai  tashi ba  ,ga rikon addinin  ga  tsananin zumunci da sanyi hali ." ga lokaci   yazo daya kamata  ka tattara biyayyar  Uba  da  uwa ka had'a   kayi  min amman kullum cikin musguna min  kake akan zance aure  auren da kai ne kaji dadinsa ,  wallahi duk macen  data  samu  miji   irin mai  halin mahaifinka  ta gama dace  a duniya da lahira ni kaina  kullum kukan da nake  yi  kenan mahaifinka  ya bauta mana  ya sangartani   sannan ya bautawa  zumunci  Allah   ya  jikansa yasa aljanna ce makomarsa  ka canja  idan  zaka  canza tana gama  fad'ar  haka ta  fita ta barshi cike da zafin zuciya." Jiki  a  sanyaye  ya bar d'akin  zuwa nashi  yana shiga   d'akinsa  ya shiga zariya   kwalkwaluwarsa ta  shiga tunani , sai dai  Kansa ya  toshe  ya  cunkushe guri d'aya  ya kasa tunanin  komai ya  zauna a bakin gado ya  had'e  hannunwansa duka  a  ha'barsa  yana  tunanin  can  byn wasu mintuna   ya  mike ya koma  kan  bedside ya zauna  yayi shiru yana kallon  d'akin  ,sake  mikewa  yayi  ya  d'aura Kashi  akan  katifa  yana Jin   quna a ransa. zuciyarsa  na  dokawa  da matsanacin karfin  gaske ya  tashi ya nufi falonsa ya  bud'e  fridge  ya d'auki kwalin   stute superior cranberry   me sanyi ya d'auki  glass  cup ya d'aura  drink akan  center  table  ya  juya jiki a mace ya  koma  zuwa  d'akinsa ya  d'auko kwalin sigari  rotimax   ya  dawo    ya    koma  kan  kujera ya zauna  ya  tsiyaya ruwan lemun   ya d'aura kafafuwansa  akan table tare  da hard'esu guri d'aya  ya Kai  Karan sigari bakinsa  ya  kunna ya fara  zuka a hankali yana fitar  da  hayaki "yaushe rabonsa da sha ? sam bazai tuna yaushe rabonsa dasha ba  cike da izza itama sigarin yake zuka idan ba  an fad'a  maka ba bazaka  ta'ba  sanin  shi din mashayin    shigari  bane koda yake  baya sha  sai idan ya tsinci Kansa cikin ' bacin   rai mai tsanani  " . yayi  shiru  yana zuka sigari  yana  tunani   mahaifinsa   yasan  da yana raye duk runtsi  da hkn  bata faru  dashi ba , shiyasa yake son mahaifinsa  Sosai wasu hawaye  masu zafi suka zubo  masa  wanda  rabonsa  daya zubar da hawaye  har  ya manta a tsawon rayuwarsa amman  yau  ya tuna qalbinsa masoyinsa  , ana  cewa mutun  yafi  son mahaifiyarsa  akan mahaifinsa  shi  dai sai dai sonsu  yazo d'aya  a ransa , yasan soyayyarsu suyi  kanka  da juna  ,mahaifinsa ya  soshi  har  cikin  ransa  idan  yana  cikin damuwa  sai ya  fishi shiga  damuwa ,   haka idan yana cikin farinciki  ,daf  da zai  rasu  da zarar ya kyalesa sai  ya  fashe  da kuka alokacin  hjy zulaiheart  ke tmbyrsa  dalilin  kuka  sai  yace  "ba kowa nake wa kuka  ba  sai  Adam ,Ina jin  tausayin  rayuwar Adam  bashi da  dan'uwa kamar sauran mutane naso sun kasance su biyu ya samu abokin shawara  "a  she tabbas shi  din  abun  tausayi ne bai  ta'ba  sani ba sai a  tsakanin   wannan lokacin da abubuwa  suka  kwa'be masa  yan'uwansa mata sun had'e kai da mahaifiyarsa yasan da yana da dan'uwa nmj zai iya bin bayansa Koda kuwa zaa fi  karfinsa  ne hawaye ke gangaro  masa  kamar  karamin yaro  yana  cigaba da  busawa  cikinsa hayaki  ." ranar  a zaune ya kwana cikin   tsananin   tashin  hankali  Kash da Kashi  damuwar auren dole da za'a masa da  tunanin  Nurul qalbinsa   dan   da  zarar  ya  runtse  idanuwanshi dan bacci  sai  yaga hoton princess dinsa  tana  gargadinsa  akan  auren da zai yi  tana gudu tana binsa  tana furta kar yayi aure ya  barta  .tsawon sati  guda  tunda daya amince  da  batun auren mryam  bai sake zuwa Inda  mami   take  ba yana  d'akinsa  yaki barin ya  had'u  da kowa   dan gbdy  fita  ya fita ransa gbdy  soyayyar princess ya  dawo  masa sabo fil  ganin  tunanin  bazai bar kanshi  ba yasashi  mikewa daga kwance da yake  tare  da  zura  takalmi  silifas   ya  fito ya  shiga d'akin  zanensa ya tsaya a gaban hotonta  shiru yana  kallonta kmr yayi mata  mgn  ta amsa fuskarta  d'auke da murmushin  da shine ya zanata  ." Hannu  ya  kai  ya  ja hoton  a zuciye   ya  yaga  yana  furzar da iska mai zafi daga  bakinsa"A ina kike  tsawon shekaru  ?"a Ina  zan  ganki ?"kin hanani  ganinki,kin hanani sukuni   daga yau kin zamo tarihi  gareni  bazan sake damuwa  dake ba ,bazan sake tunaninki ba zan manta dake arayuwata ,zan cire soyayyarki a zuciyata tunda baki da imani baki da tausayi ya fad'a yana wani irin ihu tare da daga hannuwansa duka sama "haaaaaaaa!!!   "Hauka  yake  sosai yana  wargaza  komai  dake  cikin  d'akin tare da cigaba da yaga hotunan zanenta  yana  filinging  dasu  har  da  system  dinsa da tsarkar wuyansa wanda zanen hotonta ne aciki , gbdy  ya  hargitsa d'akin  yana  watsi  da komai   har  sanda  mahaifiyarsa  ta shigo  hannunta  rike  da cup wanda  yake d'auke  da ruwan coffee,  bedroom dinsa  ta shiga bata gansa ba dan ita kanta ta kasa jurewa rashinsa na tsawon   kwanaki , ganin baya ciki ta fito har zata fita   ta jiyo sautinsa  a hargitse dan haka ta shigo d'akin ." ta tsay a bayansa  ta cigaba da kallonsa cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa  bai sani ba  yayi  zurfi  cikin tsananin  damuwa  cikin haka  ya  sake d'aukar hoton  zanen princess  yay  sama dashi sai akan fuskar hjy zulaiheart ta runtse   idanunta da sauri   jikinta na  rawa kamar   ance  ya juyo  ya ganta  tsaye  tana kallonsa  cikin tsananin tashin  hankali  sanye da doguwar  rigar shadda  milk  colour mai  dogon hannu    kyam   idanunta a  kanshi  ta kasa daukewa  ." cikin  sauri  dunkule hannunsa ya naushi iska tare da durkushewa   kasa  ya  soma tattara kayan  daya  hargitsa yana  cewa "so..sorry  sweetheart am really  sorry    cikin  in Ina, numfashi  ta sauke da ajiyar  zuciya  sannan ta zauna  a  bakin  gado batare  da  ta ajiye  cup din hannunta ba sai dai har lokacin idanunta na Kansa tana jin ciwo da zafin halin da yake ciki   ,kusan minti biyar tana zaune tana kallonsa yana faman tattara d'akin yana mata  sannu  sannan ta fara magana a tsanake  ." kayi hakuri   Adamcy  karka  damu  da  wannan"   ya  k'arasa  kwashe  kayan  da  yayi waste dasu  zuciyarsa  na zafi  da quna  "kana jina  Adamcy   ita  rayuwa  babu  takurawa  idan baka sameta  anan ba wata  Killa  zaka sameta a aljanna  ,yakamata  ka gane   hakan , karka  shiga rud'ani  idan an  fad'a maka  gasky  illa  ka dinga  yarda   dashi , komai na duniya  babu  sauki  kmr yadda  ka d'aukeshi sai   an   jajirce  be a man Adamcy  karka lalata rayuwarka  akan yarinyar  mafarkinka ." "kamar  yadda  na  sha fad'a  maka ba kowani mafarki  ke  zama gaskiya ba , ta mike a hankali   ta k'araso  gurinsa ta riko hannunsa  tayi  taku  biyu ta  zaunar dashi akan kujera  kwaya d'aya  dake d'akin , madadin ta bashi coffee  din hannunta sai  ta  fita  gabanta na dokawa da matsanacin karfi dan nan duniya idan akwai abinda ta tsana to bai wuce  damuwar tilon d'anta ba , sam  bata son ganinsa  cikin damuwa ko  wannan auren ma zata yi masa ne dan dole  saboda tasan  muddin batayi masa ba zai iya kare rayuwarsa haka  batare da yayi ba  ." ko  cikakken minti  biyar  batayi ba ta  dawo  da gorar   ruwa  mai  sanyi  ta mika  masa , babu  mutsu ya kar'ba  ya  kafa a bakinsa bai  cire ba sai daya shanye  tasssss sannan ajiye  yana sauke numfashi taja hannunsa zuwa bedroom dinsa yana biye daita  yana zance  zuci .ya yarda  tabbas  mahaifiyarsa na sonshi kuma gsky take fad'a masa akan yarinyar  mafarkinsa  sai dai ya rasa dalilin da  har wannan lokacin ya kasa yarda iya mafarki  ne  kawai  soyayyarsa  zata tsaya ..." Tana shiga d'akinsa ta  zauna akan gado  ya kwanta  ya  d'aura kanshi akan   cinyarta  yana mai Jin   damuwarsa tana raguwa ,  a hankali ta Kai hannunta  saman  sumar kanshi ta fara  shafawa   tana mai sake jin  tsananin  son  d'anta  Ina ma  zata ga wannan yarinyar a zahiri da babu abinda  zai  hana bata  mallaka masa  ita  ta kowani  hali  ba ." ta  dade  zaune har bacci yayi  awon gaba dashi Sannan ta d'auke kanshi ta  maida kan pillow ta lullu'be  masa rabin jiki ta sauko  ta  qara  masa karfin  ac ta kashe masa wuta   ta  duka tayi  kissing  din foring head dinsa tana sake shafa  sumarsa sannan ta  nufi  kofar fita  tana  rufo  masa kofar ."   Koda ta koma d'akinta  kasa  runtsawa tayi   tana tsaye akan ka'fafunta tana Kai wa Allah  kukanta akan lamarin  tilon d'anta  sai da  tayi  sallah asuba sannan  ta d'an  kwanta Shima  bata  wani dade ba  ta farka ta  shiga wanka ta fito  ta shirya cikin  doguwar  riga   ta sanya  awarwaro da zobin   ziniri ta feshe ilahirin jikinta da turaren humura  mai sanyi kamshi hjy zulaiheart  kenna  Allah yayita  da son kwaliyya da son kamshi  tun tana matashiyarta  har zuwa wannan lokacin da tsufa yazo mata  ta  fito zuwa  babban  parlour'nta  tare da  danna bell din bangaren   masu aiki kafin  kace me  gbdy sun  hallara   sun   zube  a gabanta  suna gaisheta cike da girmamawa. ta  dubesu  tare da amsawa cikin tsananin farinciki dan tana da sakewa da masu aikinta bata zalintarsu sannan bata son su zalinceta yadda take jin dadin zama dasu haka suma suke yabonta da yi mata fatan alkhairi a rayuwarta . Fuskarta a sake ta bawa 'yan aikinta  umarni abinda  take bukata su dafa a ranar wanda zai zamo  na sadaka ne  kasancewarsa juma'a  "yau  za'a yi  abincin sadakan   da aka saba yi amman ina son  a qara  hannu  sannan a had'a da  wake  da shinkafa Ina son a rabawa  yara kanana  suka  amsa  da "to"  sannan kowace ta soma k'okarin  mikewa "ke tabawa ..." wacce aka kira da tabawa ta tsaya sauran  suka kama gabansu dan fara aiwatar da aiki "ki shirya breakfast  wa sauran jamar gida idan kin gama ki hanzarta sanar dani  ." "shikenan hajiya itama ta fad'a  tare da juyawa da sauri ." Hjy zulaiheart tana zaune mrym da nana hauwa'u suka  shigo  duk suka zauna suka sanyata a tsakiya  kowacce hannunta empty   babu Komai kamar Koda yaushe  sun baro wayoyinsu    na  gado  a d'akinsu  d'aya byn daya suka  gaisheta   ta amsa cike da sakin fuska a fili  tace   "yau  dai babu danne danne waya ko Kuma an  gaji  da rike wayar ne ? sukayi murmushi  nana hauwa'u tace " ai tun wuri nayiwa marsi kashedi muddin yaya adam zata aura ta saukakawa kanta akan shiga yanar gizo "wannan haka ne domin zai iya kawo rashin jituwa a tsakaninsu abinda bazan so  faruwarsa ba kenan  nafi bukatarta zaman lfy atsakaninsu.  ta Kalli bangaren da  nana hauwa'u take zaune  tace " ya batun shari'a da ake da yarinyar da ake zargi ta kashe mubina ne har yanzu na kasa fahimtar gskyr magana gashi Adamcy nata k'okarin shiga cikin maganar  uncle jay ya hana ?"ai gsky gara da  uncle jay ya hana  wani shari'a za'a yi mami  Abar ko waye da Allah kawai mubina dai ta rigada ta mutu bazata dawo ba komai za'ayi ,haka Allah ya qaddaro mata nata mutuwar zata  rataya a wuyan wani inshallahu ruhinta na aljanna suka had'a baki gurin cewa" Ameen " " mrym tashi ki shiga  ki d'auko min wayata a daki na kira naji yadda ake ciki  ta  mike  tsam ta shiga cikin  bedroom din hajiya zulaiheart ta iske wayar akan katifarta ta d'auka tana duba fuskar wayar nan take gabanta yayi wani mummunar fad'uwa  sakamakon idanunta daya sauka akan hoton ATA  tayi shiru tana kallonsa cikin suit bakake  idanunshi manne da farin  glass yayinda  fuskarsa ke  d'auke da murmushin gefen baki wanda bai gama bayyana ba hakan km qara masa kyau  yake , ta lumshe idanunta tana Jin wani iri a gbdy ilahirin jikinta ,ada sam bata jinsa aranta amman  tun sanda  yasa  akayi kiranta akan batun soyayyarsa ta soma Jin wani Abu akansa komai nashi mai kyau tamkar shi ya hallici kansa ." jiki a sanyaye ta Kai mata wayar  ta amsa tana kokarin neman layin uncle jay byn sun gaisa take tmbyrsa halin da'ake ciki "mgn dai daya ce nace  abarwa Allah abar ruhin diyata ya samu salama  ". "uncle jay taya zaka fadi haka  byn kasan zuciyar  sha'awanatu  bazataji dadi ba   ? "nasani   amman  yarinyar nan da ake tuhunma  ba itace tayi kisan ba , tabbas makashin mutun d'aya ne da wanda ya kashe mubina da wanda ya kashe sadear mutun d'aya ne  amman ba wannan yarinyar bace, ita dai ta taka tsawun barawo ne gbdy bincike ya nuna makashin da hannun hagu yayi kisan  ita  Kuma hadiza  hannun dama take amfani dashi  sam gbdy babu alamun sheidar hannunta  ,yanzu  haka an gama duk wani bincike  ranar monday kotu zata wanke  yarinyar Allah dai ya jikan  mubina yasa ta huta  "Ameen Hjy zulaiheart ta furta a fili tana mai tausaya masa "ko me suka yiwa wannan makashi da yake musu kisan gilla?   "Allah masani  "sun dan jima suna waya sannan sukayi sallama . "Maryam ...!" mami  ta kira sunanta gbdy ta tattara duk wani attention dinta zuwa gareta tana kallonta "Ina saka rai zuwa  karshen satin  nan za'a yi mgnr bikinku  da  Adamcy  " gabanta ne ya sake fad'uwa kmr zai fasa qirjinta yayo  waje "ya kamata ki sake kwarewa agurin girki da sauran abubuwan da yake da bukata  dan haka daga yau kice zaki cigaba da kulawa da komai na bangaren abincinsa  kinji ko ". ta gyada mata Kai  kawai tare da amsawa da "to !" hawaye na ciccikowa acikin kwarnin  idanunta tayi saurin dennewa  ta rasa dalilin da take tsananin Jin  tsoronsa da tsoro  aurensa." "  ki  samu natsuwar zuciya ki tashi kije yanzu ki tmbayesa abinda yake bukatar ci a hankali ta mike jikinta na rawa kamar mazari  ta nufi part dinsa akan hanyarta ta tsaya tana  daidaita natsuwarta sannan ta k'arasa kofar shiga falonsa tayi sallama ba'a amsa ba har ta juya taji sautin muryarsa yana cewa ",waye ne ? ta juyo da sauri "ni ...nice ta fad'a da sauri jikinta da bakinta na rawa "ke wa kenan ? ya sake tmby tayi shiru jikinta na cigaba da rawa hawaye na sake cikowa a idanunta  ta rasa dalilin  hawayen  nata  Jin shiru yasa ya taso da kyar yana mika  daga shi sai gajeren wando  army  green  iya cinyarsa da farar singlet wanda suka bayyana  surar  jikinsa a fili ake iya ganin  kwantaccen sumar dake kwance  a cinyarsa  da  qirjinsa haka kan nipples dinsa  sai farin silifas dake sanye da kafafunsa da farin agogo da alamun aiki yake ." A tsaye ya ganta a bakin kofar gbdy bata cikin  haiyacinta a hankali ta d'ago ta  kare masa kallo saboda kusancin da suka samu muryarsa a kasalance yace  "ke lafiyarki  tsayuwar me kike yi anan  ya fad'a fuskarsa a murtuke"kayi hakuri please mami  ce tace nazo na tambayeka abinda zaka ci a girka maka "  ya tsuru mata Ido  a zahiri yake iya hango yadda qirjinta ke  bugawa wani dogon tsaki yaja a fili ya juya ya koma ciki ya barta tsaye . juyawa tayi tana daga kafafuwanta da kyar ta dawo parlour'n ta tsaya hjy zulaiheart ta dubeta "yaakayi me yace zai ci ?hannuwanta ta tsarke cikin juna sannan ta bud'e baki da kyar "wai a dafa masa komai." mami  ta fad'ad'a fuskarta da murmushin jin dadi , ita Kuwa nana hauwa'u sarai ta fahimci wani abu a tattare da marsi tasan sarai ba abinda yace mata  kenan ba   "to shikenan maza ki shiga ki dafa  masa  abinda  yazo cikin tunaninki amman ki natsu sosai kinji. "ta gyada mata tana cewa "sister muje ki tayani "me .....?dan girman Allah ki rufa min asiri na tsira da mutuncina ke dai kije Allah ya bada sa'a kiyi kokari yayi dadi  sosai ta k'arasa maganar tana kakkabe hannunta. "haba sister ki taimaka mana kin san fa  komai tare mukeyi ,nasani amman ban da wannan wallahi bazan Saka hannu ba abinci yazo bai yi dadi ba ya had'amu yaci ubanmu"  hjy zulaiheart tayi murmushi "Kai Adamcy hukuma kowa tsoronsa yake ji amman Kuma fa yana da sauki Kai Kinga mryam  yi tafiyarki kinji  duk abinda baki gane ba kizo ki tambayeni Simi Simi ta juya ta shiga kitchen kmr ta daura hannunta  tayita kuka dan tasan muddin tayi kuskure sai yaci ubanta duk iya k'okarinta na dafa  masa rice and stew bai ci ba ya wuce juma'a ." ***** Da  misalin  karfe  biyu  na  rana  bayan  an  sauko  daga massalaci  hajiya   zulaiheart  da  kanta  ta fito  zuwa  haraban  gidan ta fara  rabawa yaran dake shigowa haraban estate din sadaka  wake da shimfa  acikin takeaway fari tare  naira dari  biyar biyar sababbin yayinda  ATA  ke tsaye daga can nesa kadan da inda take kunnensa manne da waya yana tafiya a hankali irin na jinin saurarata dan sauranta  yaki   barin jininsa komai nashi  irin nasu ne sanye yake cikin farin yadi voil  kafafunsa sanye da takalmi fari haka ma Kansa sanye da hula fari mai ratsin  baki  yayinda tsintsiyar hannunsa ke d'aure da  agogon silver rolex   yayi  kyau sosai kamar ka sacesa ka gudu  sai dai kallo d'aya zaka masa kasan   zuciyarsa dakushe take  da tsananin damuwa ." tsayawa yayi cak yana cigaba  da kallon mahaifiyarsa  cikin haka ta  juyo  nan take  suka had'a  Ido daita ya sakar mata  taadaddaden murmushinsa dake sake bayyanar da ainihin bawar kyawun da Allah yayi masa wanda wannan murmushin babu mai ganinsa sai ita , murmushi ta sakar masa cike da farinciki ganin murmushinsa  da ba kowa yake gani ba tana tsananin son kyakkyawan tilon  d'anta shi  din dabam ne acikin zuciyarta  ,uwa Uba nagarta   tana   masa so mai  tafiyar da ruhi shine karfin  gwiwarta ." a hankali  ya soma takowa zuwa Inda take har ya k'araso gareta ya tsaya kusa daita yana tayata rabawa yaran kudi duk wanda ta bawa takeway sai ya mika masa kudi  ,tana raba abinci  tana dubansa tana murmushin jin dadi "thank you my beloving prince  " you're welcome my  queen ya fad'a yana kallonta  bayan sun gama  tare suka koma ciki  suna tautaunawa a falonta  sukayi  masauki ya zauna yana runtse idanuwanshi."Adamcy nah...." ! ya amsa  can kasan makoshi" inshallahu wannan satin zanyiwa su  baba babba maganar aurenku ayi a wuce gurin muryarsa a raunane yace "to sweetheart kuyi duk abinda ya dace na sallama miki komai ." "bangane ka  sallama min komai ba kana nufin bazaka tabuka komai ba ?"me kike son nayi sweetheart idan akwai abinda kike bukatar nayi ki sanar min zanyi ganin  idan  ya  cigaba da biye mata  maganar auren zasuyitayi yasa yay  saurin  runtse idanuwanshi yana cewa "wayyohhhly sweetheart cikin kwantar da murya tace "ya'akayi Adamcy ? "sweetheart  yunwa nake ji cikina har ya fara zafi murmushi tayi   "ko kunya baka ji ba kmr wani jinjiri ka dai rage wannan shagwabar ka bar wa yaranka  "a'a sweetheart ki barni nayiwa uwata  suma idan sunzo ga guri nan kowa yayiwa mamansa "to ai shikenan bari nasa maryam ta samarmaka abinda zakaci "wace mrym kuma dan Allah kiyi min da kanki karki rage min Jin dadi wannan yarinyar babu abinda ta iya Kuma ma nafi son Ina cin abinci daga hannunki  ni dai gsky banason abincinta "ya Isa sarkin naci amman dole kaci daga hannun matar da zaka aura wata rana ." "naji amman  ayi sauri ayi min please dariya ya bata sosai  wai ayi sauri ayi mishi  ATA  kenan ko  yaushe idan yana tare da mahaifiyarsa daukar kanshi yake kamar karamin yaro hjy zulaiheart ta d'auki wayarta ta soma Neman layin maryam  sai dai bai shiga ba ta ajiye wayar tana Kiran daya daga cikin masu aiki ." Tana zaune a d'akinsu  hjy zulaiheart ta  Aiko mai  aiki akirata da hanzarinta ta Isa parlour'n tace "kije ki kawowa Adamcy wani Abu yaci yunwa yake ji ta Dan saci kallon Inda yake tana Jin mummunar fad'uwa gaba  sannan ta gaishesa  sai dai bai Kalli Inda take ba bare ya amsa gaisuwarta  ,Kai tsaye kitchen ta nufa sai dai ta rasa me zata dafa masa shap shap yaci ,kawai tayi tunanin daura masa indomi da kwai ta kawo masa a lokacin data  fito  bata  tarar da  hjy zulaiheart ba sai aunty khadeja  zaune agurin suna magana da ATA ta ajiye akan table din dake gabansa tare da gaishe da aunty khadeja kamshin  indomin da yaji ya ziyarci hancinsa ya balain ta'ba zuciyarsa na take ransa ya baci . a hankali ta juya zata wuce dan Sam bata jurar tsayuwa a duk Inda yake muryarsa a kasalance yace"ke meye wannan kika kawo ? ta dawo a hankali ta tsaya  tare da cewa  "indomi da ......"a fusace ya dan gyara zamansa ya tsaidaita  "shine abinda kika iya dafawa?  jikinta na rawa ta dubi aunty khadeja dake zaune  tana juya masa Kai "nace shine abinda kika iya dafawa ?ta girgiza  masa kai jikinta na rawa gbdy a tsorace take a tsaye,shi kuwa  kallonta kawai yake da seyx eye's dinsa wanda hakan yasa hantar cikinta cigaba da kadawa  lumshe idanunshi yayi tare da yin shiru  ya  koma ya jingina  jikinsa  da kujerar da yake zaune ya soma motsa labbansa   "wai  irin wannan matar ake min  sha'awar  ajiyewa a gidana  ?yayi mgnr a fili  yana sake jan tsaki a fili "wacce irin  sakariya mata ce wannan khadeja saboda rashin tarbiya indomi fa me zanyi da ita ? "tuni idanunta suka kawo kwalla bakinta na rawa tace " kayi hakuri bari naje na sake dafa maka wani abu bude idanunshi yayi fesss akanta Yana cewa "shut up me yasa baki dafa ba  tun farko ? ya karasa maganar yana buga mata  wata hadaddiyar tsawa nan take jikinta ya kama rawa  da hannu aunty khadeja tayi mata alamar ta wuce kmr jira take tayi gaba da sauri tana haki ." "kayi hakuri adamcy   da sannu zata iya komai "har sai yaushe khadeja ? nifa akan wannan matsalar   zamu tabbata muna samun matsala daita bazan juri zama da macen da bata iya komai ba?" shekara ashirin da biyar da wani abu amman ace  mace bata iya girka komai ba  sai yaushe ? "gsky gsky ni dai an  ....... " sai Kuma yayi shiru ya kasa cigaba da mgn "yanzu dai kayi hakuri me zaka ci ni sai na shiga na girka maka da kaina  a fusace  yace "barshi kawai  juyin duniya  yaki yace bai ci haka ta hakura ta barshi  ."tsaki ya dinga ja bai san me ma ya jashi cewar zai ci abinci ba  mikewa yayi ya bar gidan gbdy Aunty khadija tabi da kallo gsky akwai kuskure atattare da maryam dan rashin iya girki babban matsala ne a gidan miji ba wai shekara ashirin da biyar da yan kai ba a tunaninta maryam zata kai talatin dan tsirarau da auta babu yawa .." ****** Maryama na zaune da yammacin ranar monday tana wanke kayan Aunty salma da kayan kanwarta sakina wacce ta kasance diya ga Aunty salma duk da lokacin makarantar islamiyya ne amman ita bata samu damar zuwa ba saboda aikin da matar yayan mahaifinta ta sata , wanke take da iyakar karfinta har ya zamo bata iya wankewa da karfinta sakamakon gajiyar data tsarketa domin ta jima batayi irin wannan aikin ba tun karfe biyu lokacin data taso daga makarantar boko gashi har yanzu biyar ta wuce sallace kawai ta tasheta daga tsugunno datayi tana faman dikar wanki ." Sakina ta shigo cikin haraban gidan da sallama babu sukuni a fuskarta dan kallo daya tayi mata ta fahimci haka ganin halin data ganta yasa ta sake shiga cikin damuwa ta matso kusa daita ta tsaya cikin bacin rai " maryama daman wanki kika tsaya shine dalilin da yasa baki zo makaranta ba yau .?" ta fad'a ranta a bace tana kallon cikin falon Aunty salma." da kyar maryama ta kirkiro murmushin dole wanda yafi kuka ciwo dan komai ya wuce a zuciyarta dan bata qaunar sa'insar sakina da mahaifiyarta akanta muryarta a sake tace "kayan makarantar nawa ne basu bushe ba shine nace Aunty salma ta kawo wankinta na wanke da naki dan zaman bazai min dadi ba tunda bazan samu zuwa makaranta ba ta fad'a mata haka cikin zaro wani kaya daga cikin tarin kayan dake ajiye a gefe guda tana qoqarin dannashi cikin ruwan wanki sakina ta fixge cikin fushi tana cewa "wallahi karya ne nafa san halin mama itace ta hadaki da wannan aikin aikin daya yafi karfin ace mutun daya ne zai yi ni ban san me yasa mama take yin haka ba ..." Aunty salma ta fito daga cikin dakinta sakamakon jin maganar diyarta "sakinata har kin dawo sannu da dawowa sakinata ta fad'a tana qarasowa ta dafa kafadarta cike da kulawa da tsantsar soyayya sakina ta zumburo baki "haba mama yanzu abinda kikayi ya dace dan meye zaki lodawa maryama uban wanki haka alhalin kina sane da cewa ko mu duka muka hadu bazai qare acikin kwana biyu ba haba ni wallahi wallahi bana só abinda kikeyi wa yaruwata sautari umma tana sanar dake illar haka karfa ki manta maryama ba baiwa bace a gidan nan ' ya ce kamar kowani d'a acikin gidan nan ko bakya kaunarta ita da mahaifiyarta bai kamata ace kina daukar abubuwan wahala kina sakata ba tunda ko babu komai yaruwata ce ko dan ni ya kamata kina son maryama saboda ina sonta ina qaunarta in har soyayyar da kike min ta gskiya ce ." Aunty salma ta kwabe baki "sannu sarkin yan iyayi ta fad'a a zuciyarta amman a zahiri cewa tayi "meye acikin dan wannan aikin yanzu dan na saka maryama dan wannan aikin zai sa Kiyi zargin bana sonta ne ko wani abu ? tô idan baki sani ba bari na fad'a miki ina mata kwadayin samun lada ne shiyasa nake sakata aiki yanzu Ke kin san irin ladan da zata samu har idan ta gama min ."? "To ni me yasa baki sani ba tunda aikin lada ne in har idan kwadayin lada Kike mata ?" Ki dinga hadawa dani daita gsky ni banaso ." maryama na durkushe hawaye suna son zubo mata daga cikin kwarnin idanunta amman ta dannesu dan kawai bata son sakina ta fuskanci damuwarta dan tasan dole sai ta qarawa yiwa mahaifiyarta bori ita km abinda bata só kenan taga suna samun sabani akanta da mahaifiyarta domin ita kam tarasa gane maanar hakan rashin kunya ce ko gaskiya take fadawa mahaifiyarta da ta kasance damuwa atattare daita da tata mahaifiyar " "shikenan sakina daga yau na daina Kiyi hakuri ina sata ne dan tafiki kuzari yanzu muje kici abinci ai kuwa sakina taki binta "wani irin muje naci abinci ki dai zo mu hadu har dake mu qarasa wanke sauran kayan Aunty salma tabi wanki da maryama ta wanke sama da rabi ta waigo ta dubi sakina "a'a ki bari ta qarasa tunda sauran ka.." A'a wallahi ki tsaya dai mu qarasa tas ita ba mutun bace tun rana take ta faman aiki kamar wata inji." Aunty salma tayi shiru tana duban yarta ta ja tsaki ta nufi hanyar dakinta tana cewa "ai sai dai idan ke zaki iya ni dai babu abinda zanyi taka nas naje na arota wajen uwarta shine dan tsabar iyayi irin naki zaki ce ga zance ga magana da yanzu Ke na saka bazakiyi ba dan yanzu kinga na saka maryama shine zaki zo da shegen iyayi shikenan ki tayata ku qarasa tare ta wuce tana bala'i maryama na tsaye batare da tace uhm ba bare uhm uhm dan bata son tayi laifi dan a yanzu ma tana hankalce da Aunty salma harararta take sakina ta gyara botiki ta cire hijab dinta ta sunkuya ta tura mayafinta da maryama Ke qoqarin turawa cikin ruwan wanki ta fara wankewa da sabulu data tsinta acikin ruwa ." "Why sakina ? mai haka ki barni na qarasa mana bana son naga kina sai sa da mahaifiyarki akaina ki daina babu kyau tunda kinga ni bana yiwa Aunty haka "itama ai abinda take miki babu kyau ko dan ba itace ta haifeki ba kullum sai ta dinga zuwa tana aroki dan taga Aunty shiru shiru bata son magana aikin yau da dabam na gobe dabam ta hanaki zuwa makaranta malam mustaphata sau uku yana shigowa tambyarki nace bakizo ba kina gida bakya jin dadi "ai ba ita kadai Ke sakani aiki ba umma ma ina yi mata "eh kina yiwa umma amman ita tasan daidai dan bazata barki kina aiki har wannan lokacin bakije islamiyya ba kar ma ki hada mama da umma dan ba abu daya bane ." maryama tayi shiru Tare da sunkuyar da kanta kasa tabbas akwai bambamci tana son aikin umma fiyye dana kowa ko babu komai tana qaunar mahaifiyarta kum tana tausayawa rayuwarsu tun kafin mahaifinsu ya bar duniya ta kalli sakina tana son hanata wanki amman tasan bazata yarda ba kawai ta cigaba da kallonta ita yanzu abinda yafi damunta yunwa take ji sosai domin Aunty salma bata bata ko ruwa ba wai sai ta gama sallah ma da kyar tayi ." Sakina ta cire hannunta ta shiga kitchen ta dauko plet din abinci ta fito ta daura mata akan cinyarta "kici !ta tsurawa abincin ido tana kallona batasani ba itama sakina ita take kallo ta matsota da sauri tana son sani abinda yasa tayi shiru bata fara cin abinci ba maryama tayi tsuru itama haka ta kalli abinci ta kalli maryama "ko abinci yayi kadan ne?ta fad'a girgiza kai maryama tayi "ya ma yi min yawa "to me yasa kikayi shiru kina tunani ?" Kai sakina kina son damun kanki akaina ta fad'a tana soma cin abinci jikinta babu kwari ga rawar da yake saboda yunwar da take ji maryama bata bar bangaren su sakina ba sai daf da magariba shima da taimakon sakina ne ." A matukar gajiye ta shigo part dinsu ta zauna akan kujera jikinta tattare da tsananin gajiya Aunty ta qaraso ta tsaya akanta "ya naga duk kinyi wani iri ko kin aikin da yawa ne ? numfashi ta fesar tare da waskewa dan bata son nunawa mahaifiyar ta damuwarta domin duk hakurinta taji irin aikin datayi yau sai taji ciwo aranta dan haka ta dubi mahaifiyarta tace "babu komai ai aikin ma bashi da yawa kuma har munyi mun gama tare da sakina sai lokaci ta saki jikinta ta zauna kusa daita "sannu princess dina shiyasa nake qara jin sonki araina ta fad'a Tare da shafa kanta da yake sunan datake kiranta dashi kenan atare sukayi shiru Aunty na matukar tausaya mata ita da danuwanta habib kasancewar sun taso cikin maraicin uba gashi dangin ubansu ba qaunarsu suke ba idan aka cire mahaifiyar babansu da yayan babansu da matarsa to babu mutun daya da zata cire." Mmm sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS AYSHABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 12 Aunty tayi shiru tana duban maryama yanayinta kamar kazar da'aka tsamo cikin ruwa gaba daya alamu sun nuna gajiya a tattare daita amman dan karfin halin irin nata take boye mata damuwarta , hawayen da suka cicciko acikin kwarnin idanunta tayi qoqarin maidawa tana danne damuwarta saboda farinciki diyarta ." ahankali ta dauke kwayar idanunta aKan tilon diyarta zuwa wani bangare dabam tana tunanin rayuwa da abubuwan da sukai ta faruwa daita ta sha wahala arayuwarta shiyasa batason maryama ta sha wahala irin wanda ta sha ,wannan aikin da aunty salma kesata yana matukar ta'ba zuciyarta domin ko ita da tayi sanadiyyar zuwanta duniya bata sakata aiki haka koda tace zatayi ma bata yarda ta bar mata tayi ita kadai sai dai suyi a tare amman bata da yadda zatayi da rayuwata dan bazata iya hanawa ba "tabbas bata da yadda zatayi kuma bata isa ta hanata ba tunda zaman gidan ya zame mata dole dan bata son rasa yaranta kuma bata son ta koma ga danginta ." tayi maganar a kasan ranta . maryama ta kalli mahaifiyarta duk da bata san me ya canza yanayinta ba amman tasan meke yawo acikin kwakwaluwarta ta matsota sosai tana jijiga Aunty wacce tayi nisa cikin tunanin rayuwa "meke damunki Aunty ?firgigib ta dawo haiyacinta tana dubanta duba mai tattare da damuwa tana cewa " babu abinda Ke damuna princess " ta fad'a tana mai jin tausayinta domin dai duk halin da suka tsinci kansu aciki itace sila, itace silar janyowa ya'yanta rayuwar wahala wacce bata kamacesu ba duk wani abu daya faru da ya'yanta itace ta janyo masu adalilin zunzurutun Kaunar data nunawa mahaifinsu ya janyo mata rasa komai domin ta zabi Mahaifinsu ta bar danginta wanda yasa kowa acikin danginta yaji babu dadi akanta." "me yasa kowa ya tsanemu acikin gidan nan ?" bayan mahaifinmu da granny da umma da abba babu mai qaunarmu acikin gidan nan gashi abba ya rasu ya barmu kamar yadda mahaifinmu ya barmu why Aunty ?me yasa basa qaunarmu ? "Me yasa suka tsanemu ko kin yi masu wani laifi ne ?ina son nasan abinda ya kawo wannan kiyayyar ?shiru kawai Aunty tayi tana dubanta dan bata da abinda zata fad'a mata domin kare kanta maryama yarinya ce da bata wuce shekara ashirin a duniya ba but she's smart in ance smart ana nufin mutun wanda ya kasance mai tsananin hankalin da kwakwaluwa tare da kaifin baseera sannan yarinya ce mai fadar gsky komai d'acinta zata fad'a she's very shap akan komai dan wani lokaci har mamaki take bata idan tayi wani abu kanta naja sosai fiyye da yadda take tunanin tasan muddin taji ta zabi mahaifinta ne akan iyayenta yasa dangita suka juya mata baya tabbas zata fad'a mata gskyr data kasa amsa daga ahlinta "Ina danginki suke Aunty ?ta jeho mata tambayar data nemi bugar mata da zuciya tana mai d'aura kanta a saman cinyarta ." tsura mata ido tayi tana kallonta kafin daga bisani tace "suna nan ! "suna nan amman me yasa bakya zuwa inda suke kamar yadda Aunty salma keyi ?"babu komai "ta bata amsa atakaice tana jin wani tuttukin bakinciki acikin ranta mai tattare da damuwa "Aunty karki ce babu komai lallai akwai dalili akwai abinda yasa bakya son zuwa inda suke har yasa bamu sansu ba ,mahaifiya mahaifi yan'uwa duk ba abun wasa bane domin suna da matukar mahimanci arayuwar mutun ." Naunayen ajiyar zuciya aunty ta sauke tana sake tsura mata ido "dan baki san abinda suka aikata gareni bane maryama shiyasa zaki fadi haka ta fad'a hk a zuciyarta " ahlinki suna da matukar mahimanci sannan suna da hakki akanki most especially iyaye yana da kyau a dinga basu hakinsu domin hakan zai samarwa mai yi kwanciyar hankali ,meye acikin duniyar da babu albarka iyaye acikinta ?yadda kike iya hakurin rashin zuwa ga iyayenki bazan iya barinki daidai da second daya batare dana daura kwayar idanuna akanki ba saboda qaunar da nake miki ina sonki aunty fiyye da komai dake cikin duniyar nan dan haka Kiyi qoqarin kije garesu nasan suma zuciyoyinsu na cike da kewarki da qaunarki tunda kika haifeni na girma na kai wannan shekarun ban ta'ba ganin ranar da kika shirya kika ce zakije ga ahlinki ba , kullum muna cikin dangin dady cikin kaskanci da wulakanci ya kamata ko sau daya ne muje domin nima ina son ganinsu ina son ganin danginki zaki je ga ahlinki ? tayi mata tmbyr tana mai tsura mata kyawawan idanunta masu matukar kyau ." Kusan minti goma aunty bata amsa mata ba har sai data sake maimaita abinda ta fad'a sannan tace "to maryama zanyi qoqarin zuwa." ta fadi hakan ne ba dan zata aikata hakan ba sai dan abar maganar ta wuce "da gaske kike Aunty zaki ga ahlinki ? murmushi tayi mata domin bata son damuwarta dan ta fahimci yau din nan tana cikin damuwa ." maryama ta rungumeta tsam tsam ajikinta tana mai jin dadi "naji matukar dadi Aunty ina son ganin ahlinki nasan habib ma zai ji dadi yaushe zamu je ? ta fad'a tana zare jikinta daga na Aunty yayinda idanunta Ke kallonta aunty tai shiru tana dubanta hakan nan ta tsinci kanta cikin farinciki wanda tasan maryama ce sila tana matukar son farincikin yaranta murmushinsu murmushinta ne haka zalika damuwarsu damuwarta ce tana matukar qaunarsu fiyye da komai dake cikin duniyar nan dan sune iyayenta yayyaenta kannenta komai nata daman tasha yin addua ko a can baya Allah ya bata ya'ya masu albarka wadan da zasu maye mata gurbin yan'uwa." "aunty ! Ta kira sunanta cikin sanyayyar muryarta mai tsananin kashe jiki a duk sanda tayi mata magana da wannan muryar tana tuno mata da mahaifinta ko habib da ya kasance nmj bai dauko sanyin muryar mahaifinsu ba sai ita "na'am my princess ta amsa tana dubanta tana saurararta "a ina danginki suke zaune ?"tayi mata tmbyr fuskarta na nuna farinciki." "suna zaune acikin garin nan" "cikin garin nan ? maryama ta maimaita abinda mahaifiyarta ta fad'a cike da mamaki Aunty ta gyada mata kai alamun" Eh!wani sabon mamaki ya sake cunkushe zuciyar maryama "suna zaune a gari daya amman duk tsawon wannan shekaru bata taba zuwa dasu inda suke ba bare su sansu gashi ta zauna tana rayuwa cikin kunci da babu tamkar wacce bata da kowa acikin duniyar nan ,numfashi ta janyo da kyar ta fesar a hankali kafin ta bude bakinta da kyar "yaushe zamu je wurinsu ?". "karki damu sarauniyata in sha allahu zamu " cike da farinciki maryama ta kai hannunta ta dauki remut tana mai kunna tv tare da maida hankalinta Kan program din daake yi a tashar galaxy tv tana mai jin farinciki da natsuwar zuciya "Aunty zan so naji ranar da zamu na soma lissafa kwanaki "canza fuska tayi batare datai auni ba kafin daga bisani ta kawar da kanta gefe dan karta fahimci damuwarta dan gbdy ta soma neman natsuwarta ta rasa bazata iya zuwa garesu ba ,haka zalika ya'yanta ma bazasuje ga danginta ba most especially mahaifiyarta ta barsu har abada kamar yadda suka barta zata karasa rayuwarta a haka cikin kunci ." a qalla sun dauki mintuna goma zaune suna duban tv babu wanda ya sake yunkurin cewa komai Kafin ahankali cikin sanyi jiki maryama ta mike daga kwanciyar da tai akan cinyar mahaifiyarta ."Aunty lokacin sallah yayi bari naje nayi sallah gashi ina son na danyi zane kafin na kwanata ga bacci da nake jin yana fixgata tamkar zan fadi ni zan shiga ciki sai da safe dan gabadaya yau ko gurin umma bazan shiga ba idan sakina ta shigo kice mata na shiga bacci dan bazan sake fitowa ba allah ya bamu alkhairi ."tana gama fadar haka ta juya ." har tayi taku biyu Aunty ta dakatar daita ta hanyar kiran sunanta "princess! Ta dan tsaya tare da waigowa "abinci fa ? maryama ta dan yatsina face dinta tana ciza gefen lips dinta sannan ta girgiza mata kai alamun "a'a ! "to amman karatun jarabawa ya kamata kiyi ba zane ba ko gobe baku da exam ne ? muna da shi zanyi karatu sannan na d'an yi zanen sai na kwanta " "kiyi karatu da kyau maryama Kinsan a final year kike, ni da son samuna ne da kin bar zanen nan har sai kin gama karatu " karki ji komai Aunty duk zan iya Kiyi min addua da fatan samun nasara ." Aunty ta sauke numfashi tana cewa "allah ya bada saa yayiwa rayuwarki albarka "Ameen sai da safe " "okay to shikenan allah ya bamu alkhairi "Ameen ! ta sake juyawa tana rausaya tamkar zata karye dan rashin jikin da Allah ya bata , har sai da Aunty taga ta shiga cikin d'akinta sannan ta dauke idanunta daga kallon bayanta ." Tana shiga dakin bayi ta shiga tayi wanka hade da dauro alwala ta fito cikin sanyi jiki tana goge gashin kanta da towel tana goge jiki tana mamakin abinda yasa mahaifiyarta bata son zuwa ga danginta alhalin suna gari daya ,"me yasa haka? " zata so tasan dalilin dayasa bata son zuwa garesu da wannan tunanin ta saka doguwar rigar bacci fara sol har kasa ta qarasa inda take ajiye sallaya ta dauka ta shimfida ta kai hannunta ta dauki zumbulelen hijab dinta ta saka ta kalli gabas a natse ta tada sallah ." byn ta idar ta mike ta cire hijab ta ajiye a gefen gadonta ta zauna akan kujera kwaya daya dake dakin wanda gabansa dan qaramin table ne mai dauke da tarin textbook da fararen takardu na zanenta ta janyo textbok daya daga ciki sannan ta zaro farar takarda kwaya daya ta ajiye a gabanta ta soma karatu tana joting kusan mintuna talatin sannan ta rufe ta maidashi inda yake ta sake zaro wata takarda ta ciro pencil da kayan aikinta ta fara zane wanda ya kasance abinci ruhinta a duk lokacin da zaka ga maryama a natse zaka ganta kuma akan aiki idan bata makaranta boko tana islamiyya idan bata islamiyya tana Kan aikinta na Architect wanda dashi take samu take taimakawa mahaifiyarta batayi karatu akanshi ba kawai baiwa ce daga allah ya bata babu abinda bata iya zanawa tun tana qarama take Zane dashi ta girma ." cikin kankanin lokaci ta fara zana wasu hadaddun mutane sanye da kaya na maaurata guda biyu macen sanye da wedding gwan yayinda nmj kuma ke sanye da suit sunyi matukar kyau kamar a kirasu su amsa tayi shiru tare da tura pencil cikin bakinta tana taunawa tana kallon zanen ahankali ahankali tana lumshe idanunta alamun bacci "bari na bar aikin nan haka tunda ba urgent bane zuwa gobe na qarasa idan na dawo daga school ta tattara ta bude durowar table dinta ta tura ta mike tsaye ta sake daukar hijab ta sanya ta tada sallah ishai tayi addua ga mahaifinta da alummar muslimai ta mike ta nade dadduma ta maida inda yake ta hau gado ta kwanta ko cikakken minti uku batayi ba bacci ya dauketa ." A can falo kuwa Aunty zaune kawai take duk hirar da habib da sakina ke zubawa da idanu kawai take binsu hankalinta na wani waje karfe goma daidai sakina tayi masu sallama ta wuce tana fita Aunty ta mike tsaye tana cewa habib "ka rufe koina ni zan shiga ciki allah ya tashemu lfy ta nufi hanyar dakinta har zata shiga ta hango haske a dakin maryama dan haka ta dawo ahankali ta shiga dakin ." tana kwance ta dungule waje daya a tsakiyar katifa ta cusa kanta cikin jikinta kwanciya mai tattare da damuwa duk wanda kaga yayi irin wannan kwanciya tabbas yana cikin damuwa ko maraici kuma a duk sanda taga tayi irin wannan kwanciyar ba komai take tunawa ba illa kanta take tunawa alokacin baya irin kwanciyarta kenan wanda damuwa ne silar nata kuma tasan damuwar ce ta janyo mata itama ta qarasa shigowa d'akin har inda take kwance ta kai hannu ta gyara mata kwanciya ta janyo abun rufa ta lullube mata jiki ta shafa gefen fuskarta tana sake jin soyayyarta acikin ranta ya'ya sune farinciki iyaye amman ita ta rasa wannan gatan daga nata most especially mahaifiyarta ." "abinda mahaifiyarta tayi mata abu ne da mutun zai iya yafewa amman bazai ta'ba iya mantawa ba kuma abu ne da bazata ta'ba yiwa ya'yanta ba zata so ya'yanta tamkar rayuwarta bazata iya kuntata masu ba bazata iya azabtar dasu ba sannan bazata iya hanasu cikar burinsu ba zata basu farinciki duk abinda suke so zata basu matukar bai sabawa shari'a ba, fatanta dai allah ya raya matasu cikin aminci "ta mike tsam har lokacin idanunta na Kan maryama dake qoqarin sake dunkulewa waje daya ta kashe mata hasken d'akin sannan ta fito tana mai janyo mata kofar dakin ta shiga dakinta " Ahankali ta zauna a bakin gado zuciyarta cike da zullumi har kusan shabiyu na dare tana zaune sai dai zuwa wannan lokaci tayi rigingine tana kallon saman dakin daya byn daya maganar maryama Ke dawo mata "me yasa bakya son zuwa inda danginki suke ?" mahaifi mahaifiya yan'uwa suna da matukar mahimanci arayuwar mutun ahlinki suna da hakki akanki most especially iyaye yana da kyau a dinga basu hakinsu domin hakan zai samarwa mai yi kwanciyar hankali,meye acikin duniyar da babu albarka iyaye acikinta ?nan take taji wasu hawaye masu zafi ya ganganro gefen idanunta." "tabbas gaskiy diyar cikinta ta fad'a mata amamn ai sune sukace babu ita babusu har abada me zataje tayi masu a yanzu da take cikin damuwa da bata da komai tasan ko taje garesu wulakanci ne zai biyo baya gara ta cigaba da zamanta hk babu dangi har karshen rayuwarta ,maryama da habib sun isheta komai , sheshekar kuka take sosai wanda batasan tanayi ba maraici sosai take ji alhalin ita din ba marainiya bace ta daura hannunta daya a saman kanta ko zataji saukin zafin da zuciyarta take mata ." tana cikin wannan halin taji an turo kofar dakinta da sauri ta dago tare dawowa haiyacinta tana mai goge hawayen idanunta da hannuwanta duka habib ne ya shigo wanda sakamakon sheshekan kukanta ya shigo dashi sai daya mata kallon tsanake sannan yace "me ye damuwarki male? dake shi kuma haka yake kiranta dashi ta sake sanyawa jikinta jarumta tana girgiza masa kai " alamun babu komai." "karki fad'a min haka byn kukanki ne ya shigo dani ya fad'a yana kafeta da fararen idanunshi qara maimaita tmbyrta yayi tayi kasa da kanta sakamakon hawayen daya sake cika mata ido domin kwalkwaluwarta ta toshe ta kasa fad'a masa dalili "ya sake matsota sosai male ki fad'a min damuwarki domin bazan bar dakin nan ba muddin baki fad'a min ba domin dai damuwa Ke saka mutun kuka irin wannna kuma tunda nake ban ta'ba ganin kukanki irin haka ba kuka mai fitowa daga kasan zuciya ." Ya kai hannu ya dago habarta yana kallon hawayenta dake zuba yabi hawayen da kallon hankalinsa na sake tashi cikin tsananin tashin hankali yace "wanene ya bata miki ranki haka? ta girgiza masa kai kawai "wai meye haka ne male kina son zuciyata ta kasa sukuni ne ko me ?ta sake girgiza masa kai ya juya a fusace zai bar dakin "bari naje na taso heartbeat.." ta riko hannusa da sauri "karka tashe ta bacci dan baccinta yayi nisa gashi gobe tana da exam's "to ki fad'a min damuwarki kamoshi tayi ta zaunar dashi a gefenta ya zauna yana sauraronta kusan second goma sannan ta zayyane masa komai sai daya numfasa kana ya soma mgn "male duk abinda heartbeat ta fad'a is right and it good dan daman nima ina neman hanyar da zan miki wannan tmbyr domin abu ne daya dade cikin kwakwaluwata har ya Kan hanani kwanciyar hankali Kiyi tunani male gsky heartbeat ta fad'a miki ya kamata kije ga danginki ko mu ki fad'a mana inda suke muje domin muna bukatarsu " Jin haka yasa ta barke da wani sabon kuka "baku san me suka min ba baku san irin wahalar dana sha a hannunsu ba ,na sha wahala kuma duk akan mahaifinku ne bana tunanin zasu qaunaceku shiru yayi yana dubanta cike da mamaki "me dady yayi masu haka ?sannan wani irin wahala kika sha a hannunsu ?yayi mata tmbyr a jere cikin tsananin tashin hankali kafin a hankali ya kai hannu yana goge mata hawaye shiru tayi ita kanta tana son ta basu labarinta amman bata san yadda zata dauki abun ba "tana son mahaifiyarta tana tausaya mata tana gudun bacin ranta ,bata son ganinta cikin damuwa amman a karshe itace abar kyama itace abar wulakantawa, itace mara mutunci a idanunta har tana cewa allah yasa mijinta ya wulakantata Allah ya hanata haihuwa Allah yasa ya saketa mijin da take tsananin so duk akan ta zabeshi a matsayin jikin aurenta ." Kuka sosai take tmkr ranta zai fita tana furta "na yafesu har abada zan zauna na qarasa rayuwata ni kadai "yayinda habib Ke share mata hawaye yana kuka yana bata hakuri domin yasa duk abinda yasata kuka irin haka mai girma ne muryarsa a sanyaye yace "kiyi hakuri male ki daina kuka kukanki na balain daga min hankali na hakura da son jin komai domin jinsa bazai zame min alkhairi ba amman kema kiyi qoqarin ki manta abinda ya rigada ya wuce amman iyaye da yanuwa duk abinda sukayi baa yafesu ."yana gama fadar haka ya juya har ya fita ya rufe mata kofar dakin hawaye ne yake fita dga idanunta "yaya suke son tayi da rayuwarta duk abinda suka fad'a mata tasan gsky ne amamn har yanzu zuciyarta ta saka mantuwa akwai wani abu da yake tsaye acikin zuciyarta ta rufe idanunta ta sake jingina jikinta da pillow daya saka mata a bayanta tana jujjuya maganganun yaranta tana yin filla filla dasu tana son kawar da bukatarsu amman tasan gsky suka fad'a mata bata taba daukar ya'yanta zasu girma da son danginta irin haka ba kasancewar suna cikin dangin mahaifinsu." ***** mrym zaune a d'akin hjy zulaiheart tana shirya mata  kayanta  da mai gugansu  ya kawo  tana tsaka da aikin aunty shahida  ta shigo bakinta d'auke da sallama ta amsa tana gaisheta fuskarta d'auke da murmushi  "aiki kike yi ne haka  amaryar  ATA tayi mgnr cike da zolaya " sannu da zuwa auntynmu me kika zo mana dashi ta fadi haka dan kawar da maganarta ,cikin dariya aunty shahida ta zauna akan sofa tana cewa "kayan dadi da bazasu fad'u ba maryam tayi murmushi yasu madina kwana biyu shiru  kmr anyi ruwa an dauke "ke dai bari madina exam ne ya sakata gaba Amman Ina ganin ma zuwa wani sati zasu kammala ". "okay to Allah Bada sa'a "Ameen ta amsa tana cewa "wata shawara nazo miki dashi a tsakaninki da ATA jin haka yasa ta dan tsaya ta kasa cigaba da abinda take hankalinta gbdy ta tattara shi kan aunty shahida " Ina sauraron shawara daga bakin aunty nah maganin kukana " Marym please ki sanya kunnen baseera akan abinda zan fada miki "ta sake mika mata hankalinta sosai " kin dai san halin wanda zaki aura  yana da kyau ki dan rage wasu abubuwa sannan ki koyi wasu abubuwa nasan kin fahimci abinda nake nufi ki zamo mai kwantar da kai da iya girke girke dan bazance girki ba ,daga ke har nana na fuskanci Kuna da matsala ta wannan bangaren dan haka ki dage ki koyi kowani irin girki da tsafta duk Inda zaki kasance acikin gidanki  the next thing shine kamshi domin shi din ma'aboci son dadd'adan girki ne da son kamshi ki zamo mai hakuri da lallabashi domin ta haka zaki yi saurin dakusar da duk wani taurin Kansa abubuwan social media Shima ki rage "dan kinsan bazai yarda dashi ba wasu daukar hoto kullum ana d'aurawa a duniya Shima bazai yarda ba  ". "shikenan naji aunty inshallahu Kuma duk zan d'auki shawararki ki dai tayani da addua biyyaya zanyi a aurena da ya Adam Allah yasa ya zamemin alkhairi "Ameen byn biyyaya har da soyayya sai kunyi aure zaki fahimci hk "Kai aunty babu wata soyayya "  ki rubuta ki ajiye a Inda bazai goge ba ko na mutu sai kin fada "Kai aunty shahida bana tunanin yaya zai soni a yadda yake nunawa ni dai zanyi iya yina kawai "karki tsaya iya yinki kiyi kokari ki canzasa gbdy ta yadda zai manta  da mafar.." "wannan Kuma  impossible aunty bazata iya ba  " suka ji sautin muryarsa acikin dodon kunnensu a tare suka juyo a firgice  suka  Kalli Inda yake tsaye sanye da farar jallabiyya mai gajeren hannu ajikinsa gashi kan nan nashi sai sheki yake zubawa  tamkar balarabe kallon second biyar mrym  tayi masa tayi saurin  d'auke kanta sakamakon mugun kallo da yake jifanta dashi  .matsowa kusa da aunty shahida yayi sosai  fuskarsa a hade babu alamun murmushi "babu abinda za'a ta iyayi wanda zai dakusa wannan soyayyar dake dawainiyya da zuciyata da gangar jikina   Ina son princess so mai girma sannan gara ki fad'a mata babu iskanci da sakarci a gidana  dan bazan dauka ba ." Take kwakwaluwar  mrym  ya shiga ceculating abinda mgnrsa take nufi  kenan akwai  wacce yake so  aka takura masa aurenta ?take jikinta ya kama kyarma ya ware hannuwansa duka cikin jin dadi  "okay a she fa bata san da wannan zance ba fa ?"gsky ya kama ta san cewar  akwai wata acikin zuciyar Adamcy Kuma ko ba dade ko bajima muddin na ganta zata kasance cikin rayuwata bukatata na ganta domin nafi bukatarta fiyye da komai  ." gbdy mrym dake zaune taji babu dadi acikin ranta "tabbas wannan shine dalilin dayasa bai maraba da aurenta  wani bakinci ya ziyarci qirjinta ta mike tsam zuciyarta cunkushe ta nufi kofar fita tana fita aunty shahida ta soma magana cikin fushi "wai me yasa kake yin hk ne sam bai dace ba?  "me Kuma nayi byn gskyr dake cikin Raina na fada gara tasani ?  ''idan kana yiwa mrym hakan bazamu ji dadi ba , rainmu  zai dinga  baci fiye da bacin ran daka gani yanzu acikin kwayar idanuna ,dan bazamu  yarda ka fifita wata banza can akanta ba banzar ma da ba gskiya bace  . "duk son da nake   maka zan   iya ajjiyeshi gefe   na hukuntaka hukunci mai tsanani akan mryam ,kada  ka sake makamancin wannan maganar a gabanta  wannan ya zamo Karo na karshe  ya jiyo sautin mahaifiyarsa wacce ta shigo byn fitar mrym nunfashi ya fesar yana cewa ''relax  sweetheart  insha Allahu  an gama ya fice ya barsu   "Allah ka shirya Adamcy na rasa meke damunsa "  meke damunsa kuwa ban da iskanci aunty shahida ta katse hjy zulaiheart , nifa wani lokacin sai naji kmr Abar had'in nan kar yazo ya bata zumunci   ."babu wani zumunci da zai bata wannan auren Allah ya rigada ya hadashi tunda gashi har ya amince ayi ,da yarda Allah rayuwar gaba zatai dadi "Allah yasa inji cewar aunty shahida. Da fari  baba qarami hjy zulaiheart taso ta kira ta sanarwa hukuncin data yanke kasancewar shi yana bangaren baya inda mallakinsa yake sai dai tayi tunanin ta fara sanarwa baba Babba kasancewarsa babba a tsakaninsu a yanzu   saji  daga bakinsa tayi murmushin Jin dadi dan tasan baba qarami zai ji dadi sosai  idan labarin auren adamcy dan kusan kullum sai yayi mata maganar ." ***** a natse ta fara  neman   layin qanwarta    hjy nuriyya   wacce ta kasance abokiyar wasanta iyayensu uwa d'aya Uba d'aya Kuma akwai shakuwa  sosai a tsakaninsu tana  zaune  a kasar  london  tun aurenta har zuwa wannan lokacin acan ta haifi yaranta duka iyakarta da naija ziyara ko wani sha'ani mai mahimmam. suka gaisa cike da farinciki  Inda hjy zulaiheart take sanar mata batun hada Adamcy aure da maryam  " Kai  alhamdulillah masha Allah gsky abu yayi kyau  sosai Allah ya sanya alkhairi ya  nuna mana lokaci ,wannan karon zanyi k'okari na shigo kasar  kafin lokacin  domin ayi biki dani ". Hjy zulaiheart tace "gsky kam anyi  bukukuwa duk baki  samu  damar shigowa  naija ba "haka ne kam  amman inshallahu  zan shigo wannan bikin nayi ne no any excuse ta k'arasa maganar tana murmushi suna cikin hirar hjy zulaiheart  tace "nuriyya wai kuwa  kina jin  labarin bilkisu  ?dip hjy nuriyya  tai tmkr an d'auke wuta nepa tana jin  wani irin daci acikin ranta sai data yi kusan minti biyar sannan tace  "bana Jin labarinta Kuma bana son na  ji labarin Inda take ,  kuma  Ina son ku shareta ku cireta acikin zuciyarku har abada  Kmr yadda mukayi yarinyar data nuna mana bamu Isa daita  ba ,sannan  bata  sonmu  ta zabi rayuwa ko babu mu me yasa zamu damu daita ? "ni dai duk wanda zai nemata acikinku yaje amman  ni nuriyya bana ciki kuma babu hannuna  babu kafa ta ciki  "naunayen ajiyar zuciya hjy  zulaiheart  ta sauke tana cewa " dan Allah nuriyya kiyi hakuri ko babu komai rayuwarta qaddara ce Allah ne ya d'aura mata wannan rayuwar babu yadda zata gujewa qaddararta ,wallahi  duk sanda ta fado min sai na zubar da hawayen tausayinta , da nasan Inda zanganta  wallahi zan nemota  . "Kune fa kuka damu daita ko nace ke dan duk  cikinmu babu me zanceta wallahi sai ke ,bata ga wuya bane shiyasa bata dawo ba, wallahi nafi son rayuwa ta juya mata baya ta dawo tana kuka  tana  rokonmu  kullum mummunar adduar da nake mata kenan sannan Ina adduar duk tsanani karta dawo mana da zuria Kmr yadda hhyrmu take addua ." "wannan addua ta rashin haihuwa a tsakaninsu batayi ba ku daina mata mummunar addua gskiya "ai babu abinda ya kamaceta da wuce mummanar addua " yanzu dai kiyi hakuri  muyita mata addua da fatan alkhairi a duk Inda take lokaci nata tafiya a lisafinsa shekaru ashirin kenan rabonmu  daita , kiyi hakuri dan mu barwa Allah komai sannan muyi mata adduar Allah yasa ta waiwayo mu cikin koshin lafiya naunayen  ajiyar  zuciya hjy nuriyya tayi  sannan tace  "shikenan big sister ai abinda  kikace shi zamuyi  cike da qauna yar'uwarta hjy zulaiheart sukayi  sallama da yaruwanta suna gama wayar uncle Umar ta kira ta sheida masa tana son ganinsa  ." Ranar asabar   da misalin karfe hud'u na yammaci  baba bAbba   yazo   bisa Kiran da hjy zulaiheart tayi masa , byn sun  gaisa   hjy  zulaiheart ta karanto  masa hukumcinta   akan ATA cike  da farinciki uncle Umar yace "masha Allah wannan hukuncin yayi  Kuma mun gamsu dari bisa dari dan burin mu bai wuce muga adam ya ajiye iyali ba  ,bugu da Qari zaa sake  karfafa zumunci a tsakanin   inshallahu  zan sheidawa sauran yan'uwana sai mu saka ranar da zamu ga alhj saidu  dan  zamu so a daura auren nan  kusa". "wannan  maganar tayi Kuma naji  dadinta  sosai dan  haka a fara sheidawa  baba qarami dan  nasan murnarsa sai tafi  ta kowa domin duk yafi  mu d'auki son ganin  Adamcy  yayi aure ta k'arasa maganar tana murmushin jin dadi  "ai kuwa daga nan ma bangarensa zan shiga na fara sheida masa  Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokaci "Ameen ya Allah,Allah  kadai yasan murnar da zaiyi  idan yaji  ya sha lemu da kayan snaks din da'aka jera masa suka zarce da  tautaunawa  kafin daga bisani sukayi  sallama ." Baba qarami   na zaune akan  kujera me zaman mutun uku  sai ga baba Babba   wanda ya kasance yaya  garesa Kuma Kani ga   mahaifin ATA yana ganinsa ya saki fuska tare da farincikin ganinsa  ya d'an  mike tsaye cike da girmamawa ya bashi hannu  suka gaisa sannan ya nuna masa mazauni atare suka zauna "sannu da zuwa yaya ! "ya gida da iyalin  fatan  suna lfy?"alhamdulillah kowa Lafiya yake ya naka iyalin  ?"Suna lfy ya bashi amsa yana murmshi ya mike ya  dauko masa abun sha "bazan sha komai ba daga bangaren hjy zulaiheart nake na sha "  . suka yi shiru na second biyu sannan baba babba ya fara magana a tsanake " kamar yadda na fad'a mk  daga bangaren hjy zulaiheart nake tayi decide ta had'a Adam aure da diyar kaninta abdulrauf " what ?"when ?ya fada a matukar rude yana Jin wani  irin abu ya  caki kahon zuciyarsa , yayi saurin runtse idanuwanshi "zulaiheart na bukatar wannan labarin ya zamo Kaine ka fara jinsa   bisa kokarinka na son ganin adam ya ajiye iyali dan haka nan da sati me zuwa zamu gana da yayan mahaifin yarinya alhj  saidu  ." shiru  baba qarami yayi har sanda yayansa ya dasa aya  ya mike tsaye"to ni zan wuce duk abinda ake ciki zan kiraka a waya a fusace baba qarami   ya mike Shima  yana cewa "yaya wannan wace irin maganar banza ce kazo min dashi  sannan kana k'okarin sa kai ka wuce ka barni  ? yayi mgnr  a fusace yana sa hannu ya daki center table din dake tsakiyar falonsa wanda ke d'auki da ruwan lemu kala dabam  dabam ,nan take wasu glas cup  suka  tarwatse yana huci yake kallonsu "yanzu ni dana cin burin ya zabi daya daga cikin ya'yana ya aura shine dan munafurci zata hadashi da diyar kaninta saboda son Kai irin nata ? "ya'yana  yafi  dacewa Adam  ya aura ba wannan yarinyar ba ya sake dukan table wanda hakan yasa gbdy ahlin da ke numfashi a part din suka bayyana" burina bai wuce ya'yana ko jikokina su had'a  iri da dashi ba yayi mgnr yana kallon cikin kwayar Idanu dan uwansa  ."me yasa zaka fadi haka idris?  "eh na fad'a yayi mgnr yana cakunar wuyan dan'uwansa da iyakacin karfinsa  yana maxurai  abinda bai taba faruwa ba a tsakankanisu ,hindatu wacce suke kira da hindu     ta samu guri ta zauna tana kallonsu zuciyarta na rawa dan ta dade a tafkin qaunar ATA mahaifinta ne ya hana a fito da soyayyar a cewarsa yana jiran lokaci yau ga lokaci ya zo masu a wani iri . sauran kuwa hankalinsu ne yayi kololuwar tashi ganin yadda mahaifinsu ke rike da wuyan dan'uwansa uwa d'aya Uba d'aya .Wallahi yaya Kai kare ne  da bai san ciwon kanshi ba ! "shin ya'yana basu dace dashi bane ka  bani answer ?uncle Umar yayi shiru kawai yana kallon hannun uncle idris dake rike da wuyansa batare daya ce uffan ba. "me yasa kazo min da  wannan banzar labarin mara dadin ji ?ya k'arasa maganar yana sakar masa wuya yana dubansa yana huci "saboda mu bamu Isa ta hada jini damu ba shiyasa ta za'ba masa acikin dangi ta ?"to me zai faru idan na hana auren ?"zan hana wannan auren ta karfin tsiya yayi mgnr yana d'aga hannunsa sama  sannan  ya dungule ya  naushi bangon  falon sai da gurin ya tsage  ya tsaya yana huci da kallon wani bangare ." Baba babba ya tsaya abayansa hankalinsa a matukar tashe  " maganarka gaskiya yayanmu suka fi dacewa da aurensa   sai dai kayi hakuri dan'uwana bana tunanin da wata manufa zulaiheart ta had'a  wannan auren   ,idan baka manta ba  shekara nawa ana fama da yaron nan akan ya fitar da mata yayi aure  bana  tunanin zata ki had'a  zuria da daya daga cikinmu  sannan da kasan kana da wannan burin me yasa baka fito dashi ba ? Baba qarami bai ce uffan ba illa numfashi da yake sauke da sauri sauri gumi na karyo masa  "dan   haka kayi hakuri karka bari wannan matsalar ta zamo Silar da za'a samu matsala ka bar  wannan burin  bayan anyi wannan auren sai ayi maganar a had'ashi da daya daga cikin yaran". "Kai kare idan ka sake yin min  wannan maganar  banzar sai  na datseka gbdy Komai naka   banga ta yadda nawa burin zai zama daga baya ba muddin d'aya daga cikin yarana basu yi nasarar shiga sawun farko ba babu wacce ta Isa ...." "kayi hakuri ka yafe min ban  fad'i  haka dan quntata  maka ba ya fadi hk kasancewarsa me saukin Kai sannan marason tashin hankali  yafi son yayi rayuwarsa cikin  salama  duk maganar da baba babba yake sam baba qarami bai juyo ba  ",shi wannan  Karen  zai  wuce sai kaji daga garesa sai dai  ya kamata ka sakin ranka dan wata rana ....saurin d'aga masa  hannu baba qarami   yayi still bai juyo ba sai dai  qirjinsa sai faman bugawa yake  Uncle Umar  ya juya cike da matsanacin firgici da  yanayin dan'uwan nasa ." sai lokacin  baba qarami ya juyo yabi bayansa da wani  irin  mugun Kallo   Idanunsa a waje  har sanda takunsa ya kai uku bai juyo ba haka  shima baba qarami   bai daina kallonsa  ba .a sanyaye  fahad dansa   yabi bayan baba babba zuciyarsa na rawa dan shi kansa ya koka da  abinda mahaifinsa yayi  ya raka uncle Umar  sai dai bai Kai shi har bakin get ba a tsakiyar hanya ya barshi yana bashi hakuri "karka damu fahad na gode allah yayi maku albarka ya amsa da Ameen ya dawo part dinsu da sauri  . falon ya d'auki shiru na tsawon lokaci yana tsaye yana  tunanin  bayanin daya samu daga bakin dan'uwansa  a yanzu   wanda  yake jinsa tamkar dalma acikin zuciyarsa , "uhmmmm yanzu dai ta  nuna mana cewa itace  uwar  Adam  Kuma ita  kadai ke da iko akan shi ?sai mugani  idan shi din d'an mace ne  Baba qarami yay  maganar yana jan tsaki a fili tare da watsa katuwar harara da mugun kallo kamar  tana gabansa fahad     ya  d'auki farin  glass cup ya tsiyaya masa   tattacen  ruwan inibi  ya mika masa "kasha baba kaji sanyi a ranka  yasa hannu ya Kar'ba ya  rike shi gam a hannunsa  sai dai bai sha  ba haka zalika bai ajiye ba." "zan iya kasheki akan wannan haukan da kika yi zulaiheart  domin Ina da tanadi da buri akan adam ya karasa maganar yana filinging da  cup din hannunsa a fusace Wanda yasa take  yaransa maza da mata tare da matarsa suka sake  shiga rud'ani   cike da matsanacin firgici suna kallonsa gabansu na faduwa ban da   Hindu    data samu  guri ta kame akan kujerar da mahaifinta ya tashi  zuciyarta tafi ta kowa zafi da tuttukin bakinciki tare da shiga tashin hankali" Fahad ...." !   ya kira sunan dansa Wanda aka kira da hkn   ya d'ago ya kallesa a matukar  tsorace batare da yace komai ba "abinda na fada Ina nufi har cikin zuciyata gara ta bar duniya ko ita yarinyar ta bar duniya akan rasa burina yayi maganar yana nuna sa da d'an yatsansa "wannan shine Karo na sau babu adadi da take kawo mana tashin hankali tun dan'uwanmu na raye dan haka Ina son kasheta na huta da ganinta a doron duniya  muddin ba daya daga cikin ya'yana  adam zai aura ba ." daya bayan daya suka shiga kallon junansu cike da mamakin jin furunci mahaifinsu hatta hindu wannan karon atsorace take kallon mahaifinta  ta gigita kwarai  da gaske "a kullum kokarina naga na kawar daita a duniya darajan halakar da nake son qullawa adam yasa na barta  ya karasa maganar a kausashe .yayi taku daya biyu ya tsaya gaban hindu   yana kallonta "kece ya kamata ace kin auri adam ba wannan yarinyar ba kije kiyi rayuwa tamkar sauraniya   a gidansa ki taka kowa yadda kike so sannan ki juya duk Wanda kika ga dama  wannan hannun nawa babu abinda yasani a halin yanzu kamar ya wahalar da zulaiheart  ya gigita ta hanyar azabtuwa mai muni  ,ya matso kusa da hindu   Sosai suna fuskantar juna "wannan karon fuskarsa da murmushin mugunta akanta  "ke hindu ko zakiyi iya karfin halin kashe min zulaiheart? Wani sanyayyayen murmushi ne ya bayyana akan fuskarta wanda mahaifinta ne kawai ya fahimci manufarsa ganin yadda ahlinta suke kallonta a tsorace yasa tayi saurin waskewa  tace "baba me yasa kake mgn fiyye da kaida ?gsky sam sam hakan bai dace ba tayi maganar tana kawar da idanunta gefe al'amun bata ji dadi ba  gumin da ya tsatsafowa   sauran yanuwanta suka shiga  gogewa suna sauke numfashi da ajiyar zuciya atare  Jin abinda tace daman km ita kad'ai ke iya fadawa mahaifisu mgn kai tsaye batare da shayi komai ba , a hankali ya juya yana taku cikin tsananin damuwa da tashin hankali   suka juya gbdy  suna kallon bayansa har ya shige bedroom dinsa yana shirya yadda zai kawar da hjy zulaiheart ko mrym daga doron duniya   .." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗      MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.                               Page 13 "Baba   qarami  na  kwance har  kusan   tsakiyar  dare  ya kasa runtsawa  dan  sam bacci yaki  zuwan  masa sai  faman  juyi  yake  akan  makeken  katifarsa  ,yayinda matarsa   hjy  aljannatu  ke d'akinta  kwance   tana  sharar  bacci  amman  shi  kuwa  baba  qarami sai  tufka  yake  yana  warwara ya d'an  zabura  ya  mike  zaune  daga kwanciyar  da  yay, ya  had'e hannunwansa  duka  waje  d'aya "babu  tantama  hjy zulai tana da manufar  had'a  wannan  auren  yasan  tayi  haka  ne dan  kar wani acikinsu  yaci arzikin   d'anta , kunga   idan  ta had'asu  aure  da  diyar   d'anuwanta dole dai  arzikinsa yana tare  daita , dan da  zarar mrym  ta  haihu dashi   komai  na adam zai  dawo  nata  gbdy  zuwa yanzu dai  bai san abinda ya kamata  yayi  ba  ko hanyar  da   zai  bullo  masu   a maida auren  Kan  diyarsa ." Sosai  kwakwaluwarsa  tayi  zurfi cikin  tunani  neman  mafuta har bai  san  sanda  hindu ta shigo d'akin  ba ,  ta  matso  kusa dashi ta tsaya tana  jijjiga baba  qarami  wanda  yayi  nisa cikin  duniyar  tunani "baba  baba !! " ta  kira  sunansa  har  sau biyu  ajere   sannan  yayi  firgigib  ya dawo haiyacinsa " wai meye haka  baba?" me yasa  zaka  damu  kanka akan   wannan 'yar qanqanuwar matsalar ?"  baba qarami  bai  iya amsa wa  ba sai  zuba  mata rinannun  idanunshi  da yayi yana dubanta   har  lokacin yana maimaita  abinda  ta  fad'a " ai a wajensa  wannan  ya wuce gagarumin  matsala  ba qanqanuwa ba  ko ita  kanta  tasan da zaman  haka  ta  dai  fad'a ne  dan  kwantar  masa da hankali  shi  kuwa  hankalinsa  bazai  ta'ba  kwanciya ba  matukar  ba  ganinta  yayi a matsayin matar adamu ba ." "Dan   girman  Allah baba ka kwantar da hankalinka  mubi  komai a hankali  idan  muka  bari suka fahimci wani  abu  attare damu bazamu iya  nasara  akansu  ba "  cikin wani irin murya  mai  gyaraye da tashin hankali  had'e  da rud'ani  yake furta  "bazan  iya  ba hindatu , bazan  iya kwantar da hankalina  ba muddin  ba  ganinki  a gidan  adamu  nayi a matsayin  matarsa  ba  ,maganar  aurensa  da  mrym    ta dokeni  fiyye da tunaninki  ,Allah Allah nake gari ya   waye  naje  ga  zulai ayita ta qare  domin   kece kika fi dacewa da  Adam  ba wannan yarinyar ba dan  wannan  tsantsar muguta ne  kawai  take  son  nunawa"kai dai  baba ka  dan  boye damuwarka baba" .     D'akin  ya  d'auki  shiru  tamkar  babu  wasu halitta  acikinsa   sai  na  qara  ac  dake  aiki  da kuma saukar  numfashinsu  haka  zalika baka  jin  motsin  komai  daga  sai  na  tsuntsaye   dake  shawagi  kasancewar  a  gra suke  hindu ta sauke numfashi tana mai kamo  hannunta  mahaifinta  cikin  nata "idan  kaje  me  zaka  cewa  mami  akaina ? " zan so nasan   abinda  zakace  baba  idan  ma  hali  kaje tare dani  ayi  komai  akan  idanuna  shekaru  sha biyar kenan ,  tun   inada  shekaru  sha  shida  nake  dakon soyayyarsa  bazan  iya  jurar  rasashi  ba, bazan zuba idanu  wata ta mallakesa ba "zan fad'a mata komai akan  soyayyarki  ni   ko  ta  biyu ce kizo  bazan damu   ba  burina  ki  kasance matsayin   mata  acikin  gidansa , ki zama tmkr sauraniya, ki yi yadda kike so  nima  nayi  yadda  nake só da  kamfanunuwansa  ."" nan  take ta  had'e  fuska  tamkar  dariya ba  muryarta  a  kausashe  ta  cigaba da mgn "muddin  a ta  biyu  zanzo  nasan   bazai ta'ba aurena ba , ya  adam  fa yana da tsari  acikin  rayuwarsa  shi  din ba mutun bane  kamar sauran mutane bashi da raayin tara mata "wa yace  miki  bashi  da  raayin haka ? zai yi raayi   dan uwarsa  Allah dai ya kai mu gobe tare zamu wajen  uwarsa  kafata  kafarki ." Baba  qarami ya   mike  tsaye ya goya  hannunwansa abaya  yana  girgiza  kai yana duban hindu kafin daga  bisani  ya matso kusa daita sosai  ya  soma mgn   can  kasa kasa  kusan mintuna goma yana mata  mgn murmushin  jin dadi  né ya  bayyana akan fuskarta " idan bata  yarda ni na zama  matarsa  ba  I will  killed mrym  idan ni ban samesa  ba  to babu wacce  zata mallakesa anan  gidan  duniya yadda take  mgnr zaka fahimci da gaske  take  kuma  har cikin ranta abinda  take nufi  kenan ganin byn maryam ." Washegari  da   misalin  karfe  goma na   safiya  a kofar  shiga  bangaren  hjy  zulaiheart  tayi masu  kai tsaye a babban  falon  gidan suka  iske  mami zaune  yayinda  d'aya  daga  cikin  masu aikinta ke zaune   tana  mammatsa  mata  yatsun  kafafunta sallamarsu baba  qarami tasa mami  dauke idanunta  daga  Kan tv ta maida kansu  tana  sakin fuska  sai  dai kallo d'aya tayi  masa  ta  fahimci  akwai damuwa  atattare  dashi  ,aranta tayi addua  allah yasa ba wata matsalar  bace  ta taso , ta amsa sallamarsu  tana cewa "sannuku  da zuwa !" baba  qarami  ya samu waje ya  zauna akan kujerar  dake  fuskantarta yayinda  hindatu  ta zauna a kasa kan kafet  a gaban mami ta  sunkuyar da kanta  kasa  tmkr mai neman  gafara  tare da gaishe da mami cike da ladabi  ta amsa  tana  mami  ta maida hankalinta ga baba qarami   tana   nazarin fuskarsa sannan ta kalli yarinyar  dake zaune a gabanta tace "salaha tashi kije   Ki  bamu  guri  cikin  sauri  yarinyar  ta mike tare da fadin  "tô !"        Mami  ta sake maida hankalinta sosai  garesu sannan ta fara magana a natse "baba qarami fatan dai lafiya  dan naga yanayinka  ba kamar yadda na saba ganinka ba  yace "lafiyar dai da sauki "ta gyara zamanta cikin tsananin damuwa "daman dai na lura da hakan dan ba haka yanayinka yake ba kai din mutun ne mai faram faram duk sanda za'a ga fuskarka cikin murmushi take tô ina jinka fad'a abinda ke  tafe da kai ." Naunayen ajiyar  zuciya ya sauke yana sake gyara zama  yace "zulai  jiya baba babba yazo min da wata magana akan hukuncinki akan Adam"  ta gyada kai tana  sauke  numfashi "haka ne nasan zaka fi kowa jin dadi "tabbas  naji  dadi  sai  dai   wani  hanzari ba gudu  ba nima na dade ina son had'asu  aure da hindatu   "mami tayi shiru tana dubansa da hindu dake   zaune  tana  nazarinta tana son gano wani abu atattare  da hindu domin dai ita din macece mai tsananin  baseera tare da saurin karantar mutun sai data  numfasa sannan tace "ita hindatu tana son shi ne ? "tabbas  tana tsananin sonshi na tsawon shekaru tunda tashi da soyayyarsa ta tashi ni ne mutun na farko data fara sheidawa da fari na nuna mata illar rayuwar data jefa kanta na afkawa soyayya da qarancin shekarunta  alokacin na tmbyeta meye dalilinta  na son shi  ? me  ya  dauki hankalinta akanshi  ? tace ba dan yana dukiya  da kyau ba ,yau da  zai  wayi  gari  bashi da  komai  bashi da hannu bashi da kafa  koda akan titi zasu rayu zatai  rayuwa dashi kawai son shi ta keyi dan  Allah alokacin shekarunta shashida né  kawai  wanda ni nake ganin bata san  ma me take ba bama tasan meye soyayyar ba yasa take fadin haka ahankali baba qarami ya fayyacewa  mami komai akan soyayyar da hindu ke ma ATA  babu abinda ya rage numfashi mami tayi ta saukewa tana girgiza kai cikin tausayawa tana kallon hindu data sake dukar da kanta kasa sosai ." "Masha allah naji dadin wannan abu sosai soyayya mai hade da zumunci allah ya bamu ikon sada zumunci dan allah ba dan kwadayin ko neman wata biyan bukata ba ". ta sake numfasawa ta cigaba da magana  "nima daman tun farko burina kenan adamcy  yayi aure biyu"  ahankali baba qarami ya kalli inda hindu take wacce mgnr mami yasa ta dan dago kanta mami ta cigaba da magana "zan yi iya  kokarina hindu na kawo karshen damuwarki duk da adamcy baya da raayin ajiye mata biyu amman zanyi convincing   dinsa  domin  kawo farinciki arayuwarki da  yarda  allah ."     da  sauri  hindu ta kalli mahaifinta shima din ita yake  kallo domin dai yasan diyarsa da tsananin kishi zata fi bukatar ganin ita kadai ta mallakesa Kmr yadda ta sheida masa kallon da takewa mahaifinta só take yace a fasa auren da mrym gbdy ya aureta  shi kuwa baba qarami a hakan ma maganar tayi  masa dadi "fatana  mu hadu muyi addua akan lamari sannan mu nemi zabin allah allah kuma yasa  gogan naka ya yarda ya amince ya  hadasu su biyu din , ku bani lokaci kadan zan yi magana dashi duk abinda mukayi dashi zan nemeka da  wannan maganar suka kawo karshen zance sukayi  mata sallama ."    Suna shiga  dakin baba qarami   hindu ta fara zubar da hawaye acikin slow voice tace " baba ina ji ajikina ya adam bazai aureni ba dan dai idan amincewarsa zaa tsaya nema wallahi bazai ta'ba amincewa ba bugu da qari ni banason sharing dinsa da kowa nafi son ni kadai dan sam ban dace da zama da  wata aba kishiya ba zan só mu rayu dagani sai shi  ta karashe mgnr tana shesheka murmushi baba qarami yayi tare da fadin "hindu kalleni nan " ta tsura masa  idanunta Kmr yadda ya bukata "ki kwantar da hankali babu wani abu acikin ya haduku biyu din amincewarsa shine abinda muka fi bukata a yanzu dan zaki iya kawar daita byn auren ki zauna ke kadai keda kike da baiwa iri iri nasan zaki bawa babanki mamaki haka dai baba qarami ya tasa hindu a gaba yana kwantar mata da hankali babu laifi hindu ta saki jikinta  tare da  karfafa zuciyarta sai dai ta rantse muddin bata samesa babu wata mace da zata mallakesa tana raye ." **** Sanye  ATA  yake  cikin  farin yadin vol  mai shegen haske da tsada  a hankali yake  taku yana gyara  zaman  hullarsa  baki  haka zali takalmin dake sanye da kafafunsa black cover shoes ne tsintsiyar hannunsa daure  da  agogon rolex   yana dumfaro falon kamshi turarensa ya mamaye koina Kmr  shagon turare yana gama qarasowa yace wa hisham "muje ko ".kai me yasa bakasan ka bawa mutun rai ka bashi hakuri ba duk lokacin dana bata ina zaman jiranka da muje ko  zai qare  " ina laifin kace hisham Afuwa kayi hakuri muje abokina km danuwana." Dogon tsaki yaja kawai batare dayace uffan ba . "matsalata da kai kenan ka gama bata lokaci amman zaka wani jawa mutane tsaki still bai ce komai ba  ya nufi hanyar dakin mami tana zaune ya shigo ta  dago a natse tana duban kofar ganin shine cikin shigar da tafi qauna ta saki fuska cikin tsananin farinciki  tace "Masha allah adamcy nah kayi kyau sosai allah yayi maka albarka  ,sai dai wannan uban wanka  da kashi haka kmr yau  daurin aurenka,  ai ko yau né daurin aurenka sai  iyakarka hk kai  ni kamar ma har da hoda ka shafa ko? Tsuke bakinsa yayi  dan tsokanar sweetheart dinsa na yau yazo da wani salo ana zaman lfy me zai yi da wani hoda shi ba mace ba  ." "sweetheart ni zan fita amman zan dan jima ban dawo ba dan yau zaa bude kamfanin tace mai petir da sinadarin gas "Alhamdulillah masha ,allah allah yasa albarka  arayuwarka data kasuwancinka allah ya  tsare  min  kai  ,yadda zaka fita lafiya allah ya dawo da kai lafiya  sharrin mutun da aljani Allah rabaka  dashi  yace "Ameen !atakaice  ya juya a natse yana taku  tmkr wani jinin saurata "sai na dawo sweetheart  ." a dawo lafiya adamcy nah ta fad'a tana cigaba da kallon bayansa "yau  tsawon  kwana uku kenan tana   son sheida masa bukatar baba qarami amman ta kasa, ita  kanta tana jin tsoron tunkararsa , tayi  dukkanin tunaninta ta rasa ta ina zata fara  shigo  masa da maganar , auren mrym ma  da yaya ya amince yanzu  kuma ta sake kawo masa mgnr wata tasan tattara wa  kawai zai yi ya gudu ya barta dasu  ." har ya kai bakin kofa yana shirin d'aura hannunsa akan handling din kofar ya  tsaya cak  ya waigo bayansa adaidai lokacin  da mami ta sauke numfashi  da  girasa ya tambayeta  ,ta girgiza masa kai kawai tamkr   wata   marainiya "ko akwai damuwa ne ?ta sake numfasa wa kana tace " babu  komai  adamcy nah  ina dai kallonka ne kayi min kyau sosai shigar ta amshi jikinka "me  yasa  bazanyi amfani da wannan damar  na fad'a masa  bukatar kanin mahaifinsa ba ? tayi mgnr acikin ranta  da sauri zuciyarta ta gargadeta "karki soma yace ya fasa auren  gbdy gashi goben  nan zaa je neman masa auren mrym  numfashi ya fesar "saboda Ke nayi shigar dan nasan zaki ji dadi gaahi yau  juma'at  "ai kuwa naji dadi kwarai da gaske na kuma  gode sosai allah ya baka zuria masu  albarka yadda kake ji dani kake min biyayya Allah baka masu yi maka bai amsa ba ya sa kai ya fice daga dakin  zama ta cigaba da yi tana tunanin  mafuta zata jajurce da tsayuwar dare domin neman zabin allah  dan shine kawai mafuta agareta." Aunty  abinda  na gama  jin bayanin  ibrahim  taji kafafunta suna  barazanar kasa daukarta lokaci  daya  zuciyarta na barazanar  tarwatsewa Ibraheem ya matso yana girgiza Aunty abinda wacce ta dawo tmkr mutun mutumi "abida abida!! lafiyarki what's wrong abida?abida tayi shiru kawai tana sauke numfashi batare data amsa ba " baba babba zasuje nemawa ATA auren maryam  gobe goben nan idan dai ba karya kunnuwanta suka jiye  mata ba haka taji ya fito daga bakinsa  " ibrahim me naji kace ? tana bukatar ya sake maimaitawa babu bata lokaci ya sake maimaita mata " wai tukunna wace maryam zai aura ?"maryam dai wacce Ke zaune a gidan mami diyar  kaninta  ita zai aura  "da gaske ka tabbatar mrym zai aura ? ya gyda mata kai kawai  yana maida hankalin Kan wayarsa dake qara " "ina sam sam wannan aure bazai taba yuwa ba ta runtse idanunta da karfi  ATA jarumin nmj né uwa uba kyau da natsuwa da Kamala ga tarin dukiya dasanin yakamata ai babu macen data dace dashi sai sultana gani yana mata wani irin kallo tayi saurin dawowa haiyacinta  sunanta ya sake kira tare da jawo hannunta ya zaunar daita akan kujerar daya tashi cike da rauni tare da yin kasa da murya yace "abida meke damunki ?babu abinda ke damuna nidai dan Allah kar aje neman auren nan wai ma waye ya hada wannan auren ?shi ATA din da kasan  ne ya zabi auren mrym din ?"ta karasa maganar cikin tsananin tashin hankali da bacin rai akan fuskarta ."     "me yasa ?saboda me kar aje neman auren  ?" Meye  damuwarki da aurensu ? kanta ta rike da duka hannuwanta ta fuskancesa cikin sanyin murya tace "sbd sultana né bazan só ATA ya auri wata ya bar sultana ba "ita sultana tana son shi ne ?eh ammm daman umma ce ke ...."sai km tayi shiru ta kasa qarasa mgnr. "auren nan fa kamar anyi shi an gama domin babu wani abu ko mahalukin daya isa ya hana wannan auren mami da kanta ta hadata wannan auren ,ATA nason yarinyar ko baya sonta wannan shine bansani ba amman zuwa neman aure wannan dole ne gara ma ki binne duk abinda ke ranki karki shigo da wata magana da zata janyo matsala cikin jin haushi tace "idan kuma rabon sultana né fa ?har ya bude baki zai bata amsar tmbyrta  wayarsa ta sake daukar  qara ya dauka yana duba screen din wayar sunan ATA yaga yana yawo cikin sauri ya mike ya dauka ya soma mgn yana juyawa zuwa kofar fita tana ganin fitarsa ta  mike tsaye ta soma zagaye falon tana maimaita abinda  ya  fada mata ashe kuwa zaayi wulakanci acikin gidan nan ko ta wani hali koda tsiya koda tsiya tsiya sai tayi duk abinda zatayi sultana ta shiga gidansa koda ata biyu ce ." *****   "Maryama kyakkyawar budurwa ce mai   kyan  gaske  doguwa ce sambal dan tsawonta bai sa  ta  rankwafa ba sai dai ita din ba fara  bace haka zalika baza'a  kirata  da baka kirin ba  chocolate colour ce  tsayinta ya fito  sosai  domin irin matan nan ne masu  shape din cocakola  tana da siririn  hanci  da manya  idanuwa masu  matukar d'aukar hankali  dan duk wanda tsautsayi yasa ya kalli  cikin kwayar idanunta sai ya kusan  suma saboda wasu sirrika da Allah ya hallita acikinsu masu kallon cikinsu  ne kawai zasu iya karar da yanayin da suke tsintar kansu ." idan tayi murmushi kuwa zaka ga siraran wushiriyarta sama da kasa sun bayyana wanda  sune suke  qara  haskaka  kyawunta  ,ga gaban  goshinta kwance suke  da suma  luf luf !! duk  da kanta a daure  yake a koda yaushe da d'ankwali  amman kallo  daya  zaka  mata  ka  gano irin matan  nan  ne  masu  yalwan  gashi  sannan tana  da  kafa  mai kyau haka ma   yatsun  kafafunta zara zara ne  lullube  da farata masu matukar haske haka zalika muryarta idan tana  magana dan dole ka tsaya ka saurareta  kuma dole ka kalleta ." Maryama ta  samu tarbiya mai kyau  daga  gurin  mahaifiyarta tayi  karatunta na   primary  har zuwa  matakin  jami'an  acikin jahar lagos  kuma   duk  akarkashin kulawar  gwanaty  , haka bangaren karatun  alqurni  baa  barta abaya ba  domin tun tana primary ta sauke alqurni  km hakan bai sa ta daina zuwa islamiyya ba idan kaga bataje ba sai dai wani aiki ne ya sha kanta ."     kyawun maryama mai  tsayawa ne arai sai dai duk da wannan kyawu  nata bata da wani  tsayayyen saurayi  duk wanda yazo  neman aurenta dayazo sau d'aya zuwa sau biyu zai daina zuwa  batare da wani dalili ba  koma  karshe  taga  ya koma gurin kaulat diyar  kanwar   babanta  Aunty  hassana  gata   da kyau sosai na bugawa a jarida amman  mutane  na  mata  kallon  mai bakin  jini  abun yana d'an  damunta  sai dai bata nunawa dan ba samari bane a gabanta karatunta  ya fiyye mata  komai mahimanci  koda yaushe ka kalli fuskar maryama  zaka ganta a daure sakamakon rashin farinciki shiyasa  mutane  suke mata kallon mai  tsananin girman  kai   ." Sannu  ahankali  maryama take tafiya tamkar tana  jin tausayin qasa  ko  macijiya dan babu wani karfi  a tattare daita cikin shiga ta Kamala  riga da sket dinki zamani da  kuma  dogon  hijab  mai  hannu  har  qasa  fuskarta  manne yake da bakin  nikaf  kalar hijab din jikinta wanda ya zame mata jiki a duk sanda zaka ganta a waje ko a makaranta   da wannan nikaf din zaka  ganta  sam bata yarda ta fita koina   batare dashi  ba  a cikin gidansu ne kawai zaka iya ganinta sadaka  yayinda  kafad'arta Ke makale da  jaka baka mai dogon igiya ,a zahiri kana kallonta kasan a matukar gajiye take dan yanayin tafiyarta ma ya qara yin slow sa'banin na sauran lokuta  sakamakon ranar data kwaso  gefe da gefenta  qawayenta ne  subai'a  da sumaiya ne suka sakata a tsakiyarsu ."    Tafiya  suke  a natse  suna hirar  yadda  jarabawar su ta qarshe  ta kasance adaidai jeaction din ummahani street   suka rabu da kawarta  sumaiya tayi hanyar hagu da zai kaita unguwar daji suka cigaba da takawa da subai'a itama dai tafiya kadan sukai tayi dama wato markaz ya saura ita kadai ta cigaba takawa zuwa  unguwarsu market street batayi  wani  doguwar tafiya ba ta  qaraso  unguwarsu bata tsaya akoina ba sai   kofar  qaramin  get din gidansu  wanda  kallo daya zaka masa  kasan na masu rufin asiri  ne  dan bazaa kira gidan da gidan mai kudi ba haka zalika bazaa kiran gidan  da gidan  talaka fútik ba daidai misali  gidansu   ginin  da ne kuma ginin kasa ne  filasta  ne ya rufawa ginin gidansu asiri da kuma jamar dake rayuwa  acikin  gidan ." a natse ta  shigo  haraban gidan nasu idanunta ya sauka akan kaulat  wacce  ta sha kwaliya cikin atamfar  chiganvy gold black touch of milk  ,kallo daya tayi masu  ita da wanda ta gani tsaye ta dauke   idanuwanta  zuwa wani bangaren  tana cigaba da tafiya dan wanda suke tsaye  da kaulat din ba bako  bane a wajenta tasha ganinsu tare  ."duk da   bilal  baya ganin faukarta amman  duk  sanda ya ganta yana rasa natsuwarsa a kullum burinsa yaga fuskarta yaga yaya take ,kasa cigaba da motsi yayi  daga inda yake tsaye  yabi tafiyar maryama da wani irin  kallo  komai nata a natse  most especially tafiyarta abun burgewa shi kam ina ma zata yarda ko sau d'aya ta bude nikaf din  yaga fuskarta yasan zatai kyau duk da  bai  ta'ba ganin  fuskarta ba." Kaulat  na ganin irin kallon da yake mata  taja  dogon  tsaki yayinda maryama bata sake  duban inda suke tsaye ba ta cigaba da tafiya zuciyarta na matukar jin tausayi kaulat dan babu abinda tasa gaba sai  aikin tara masu samari  marasa inganci  a gida  maimakon tai concentrate akan  karatunta da kullum yake yin baya   sai ta maida hankalinta ga tara  samari  marasa amfani , tare suka  shiga  jss one  ,sukai  jss1 tare, sukai  jss 2 tare  sukai exam na zuwa  jss3  ta barta suka  wuce ss 1  ita  da sakina itama sakina lokacin  da zasu shiga ss2 tayi fail ta  wuceta  sai dataje ss3  sannan  kaulat   taje  ss1 sakina taje ss2   gashi  ita  yanzu daga rubuta jarabawar karshe ta fito  amman  ita  kuma har kullm cikin repeating take a qalla a tunaninta tayi repeating  ya kai sau hudu   allah yayi  mata jarabawa ta rashin ilimin  dan  babu  abinda tasani  daga bokon  har islamiyyar zero ce amman  ita da mahaifiyarta kullum cikin cin zarafin mutane suke barin ma ita  da tarasa dalilin dayasa suka  tsaneta suka tsani ganin wani  tare daita  duk wanda zasu gani tare daita wala mace wala nmj sai  sunyi qoqarin rabasu " "Wai bilal meye haka ne ? ka wani karkace  kai kana kallon maryama gbdy ma ka manta ina tare da kai idan kasan ba wajena kazo ba na qara gaba dan na fahimci duk sanda kaga wucewarta sai ka maida attention dinka wajenta ko zuciyarka na kanta ne sai kayi min bayani  nasani ba wai ka raba hankalinka gida biyu ba alhalin ina tare da kai  "? "wallahi da tun  asali ita na fara gani  to da babu abinda zai kawoni wajenki  yayi mgnr  acikin zuciyarsa  amman a zahiri cewa yayi  "meye laifi dan kalli halitta mai  natsuwa  ?  ta zaro idanuwata waje  tana masa wani irin kallo kafin  daga baya cikin d'aga murya cike  da  maseefa tace "ko zaka koma  wajenta ne ko me kake nufi da wannan maganar ?da zan samu haka  wallahi da naji dadi sosai "ya sake  fad'a acikin ransa "ai daman haka halinku maza yake da zara kunga mata sai kama 'bare 'bare  to du ka gama 'bare 'barenka ka hakura dan ita wannnan dai ko ka  koma wajenta ma dole ka gudu da kafarka dan idan kasan akanta matsalar  duniya ta qare, kana fara soyayya  daita  komai  daka mallaka  zai  qare idan kayi sa'a ma wani  mummunar bala'i bai sameka ba  tayi samari day day sun kai guda hud'u kuma duk da aure suke sonta amman da zarar sun fara zuwa zance wani mummunar bala'i Ke samunsu ganin ta inda take shiga ba nan take fita ba yasa ya matsota sosai ya rage murya ya soma magana  ." "Haba kaulat banda sharri fa dan kawai mutun yace yana sonta sai wani mummunar bala'i ya samesa sai kace wata annoba ,wannan ai tafi annoba "to  ko zaki hadani daita kawai ina son naga tasirin bala'in dake tattare daita ?tayi shiru kawai tana nazarin maganarsa idan zata kintata daidai son maryama yake cikin karayar da murya kaulat tace "me kake nufi da wannan mgnr ?ya tsura mata idanunshi kawai "kaga bilal banason wannan maganar karka qara min  hk da kuka ta qarasa maganar dan duk cikin samarinta tafi qaunar bilal "ya salam !meye kuma abun kuka anan daga wasa ?kuka kaulat take sosai ganin haka hankalinsa ya tashi sosai "kinga wallahi ni wasa nake ya ciro hankacip ya mika mata "wip your tears karki min asarar hawayenki da kyar ya samu ya rarrasheta ta daina kuka ." Da sallama  maryama ta shiga part dinsu inda ta iske habib na  zaune akan wata tsohuwar kujera mai zaman mutun uku  yana ganinta ya saki fuska yayinda aunty ke zaune akan daddumar sallah  , " heartbeat sannu da zuwa "yauwa after dad  ta fad'a tana  cire  nikaf din fuskarta da hijab din jikinta " yau baka fita bane na ganka a gida ?"wallahi na fita ban dai  jima  bane  saboda  ranar  daake  yau  tayi zafi da  yawa "gsky  kam  yau  an zuba   rana ga doguwar tafiyar  mun   kwaso  wallahi a matukar gajiye   nake  da kyar na  qaraso  gida , kasan tun daga dopemu da kafa  muka  shigo agege ya zaro ido yana cewa "halan matsalar mota ?ta gyada masa kai tana rausayar da kwayar idanunta ." Ya mike  tsaye   ya  qarasa inda  d'an  qaramin fridge dinsu  thermocool yake wanda ya gaji dan murfin ma ya balle idan an bud'e da kyar ake maidashi a rufe ya ciro pure watar mai sanyi ya ajiye akan hannun kujera ya maida murfin  fridge  din da kyar ya qaraso inda take "heartbeat ga ruwa ki sha  "yauwa after dad  na gode  sosai  ya koma Kan kujera daya tashi yana cewa "ya exam din fatan yazo da sauki ?sai data zuke ruwan sannan tace "babu wani sauki amman muna fatan samun nasara daga Allah bata sake cewa komai ba sannan bata zauna ba ta qaraso bayi ta dauro alwala ta fito ta d'auki wani dadduma sallah daga inda suke ajiyewa ta shimfida kusa da mahaifiyarta dake zaune har lokacin tana kaiwa allah kukata akan yaranta most especially maryama wacce ta fita jarabawar karshe ta tada sallah a natse ." Bayan ta idar da sallah  ta mike tsaye  tana  ninke sallayar ta samu waje ta zauna kusa da habib tana sauke numfashi "kai wallahi ban ta'ba gajiya irin na  yau ba wannan hanyar ta yanoba akwai matukar wahala alhamdulillah  daga yau dai mun huta bata gama  rufe  bakinta   ba taji an bako kofar shigowa falon nasu  da  karfi atare suka kallo kofar kaulat ce tare  da mahaifiyarta tsaye suna huci Aunty hassana tace "yauwa gara da Allah yasa na sameku  gbdy uwa da ya marasa  mutunci  to wallahi na gaji  ki jawa wannan tantariyar yartaki mai  suffar  manufukai kunne ta shiga  hankalinta  bata tashi dawowa  gidan nan daga yawon karywancinta  sai yamma tayi lokacin  da manema  auren yarana suke zuwa ta dinga wannan yar iskar tafiyar tata  simi simi kmr macijiya dan kawai ta dauki hankalin samarin  ya'yanmu to wallahi kinyi kadan  bake  ba hatta uwar  data kawoki  duniya ga tanan tayi kad'an bare Ke karan  kada miya ,ko su sukayi koba dinki? " ko su sukace maza su dinga gudunki  ?ko Kuma su suka sanya mugun balai ajikinki da maza ke gudunki ? babu daya da sukayi aciki dan haka daga yau banason sake ganin gyallinki idan bilal yazo gidan nan  aikin banza  kawai kyau  har kyau amman bashi da amfani , ana  fakewa da karatu ana  yawon karuwanci "tana kawo nan habib ya zabura ya mike jikinsa na rawa  tare da daga hannu zai zabga ma Aunty hassana mari...." aunty  wacce ta mike tsaye tun fara maganr Aunty hasana tayi  saurin rike masa hannu tana cewa " qul  habib  karka fara ko ka manta wacece ita da matsayinta agurinka?  "amman male  bakiji kalmar da take fad'awa heartbeat ? "an fada Kuma an sake fada dan uwarka da ubanka kayi duk abinda zakayi karya na fada ba yawon karuwanci take ba ?" idan bashi take ba me yasa samarinta suke gudu su barta ?idan baka sani ba kasani daga yau ai raba masu kanta take kmr MTN shiyasa suke gudu suna barinta  jairi kawai da wani katon kanka can shegu marasa mutunci jinin marasa mutunci ai da bakayi haka ba bazansa kayi gadon dangin uwarka ba masu arziki amamn matsiyatan mutane  ." Tunda ta fara magana hanakalin maryama yay  kolowar tashi sosai ta firgita da kalaman aunty hassana  ba idanuwanta suka cika da ruwan hawaye ta kalli inda kaulat take da kyar ta bude baki cikin sanyayyar muryarta mai tsananin kashe jiki "mama Ke kanki sheida ce akaina Kinsan bazan ta'ba aikata wani abu da zai 'bata sunan ahlina ba ,walalhi bana aikata komai karatu kawai nake zuwa  sannan mama ko babu komai ni din diyar d'anuwanki ce kuma abar tausayi a irin wannan rayuwar da muke wacce babu wani yanci acikinsa sai tsabar kaskanci kece mutun ta farko da daya kamata ki cetomu amamn sai gashi kece mutun ta farko dake bibiyarmu da mugun alkaba'i  ta sake kallon inda kaulat take tsaye tana zabga mata harara." "ga kaulat nan idan zata fadi gsky babu wani abu danayi hassalima ko magana banyi ba ta gefensu na raba zan .." dakata dan Allah malama  banson manufarci bangane atambayeni ba ta fad'a cikin zafi rai kafin daga baya  ta dawo gabanta ta tsaya "duk abinda mama ta fad'a gsky ne kisa kunnen baseera ki  ji abinda aka fad'a miki ,ki tsaya iya matsayinki ki kiyaye shigowa alokacin da bilal yake zuwa tana magan tana nuna maryama da yatsan hannunta "idan karuwanci zakiyi sai ki san inda zakiyi ba ..." tas tas !! habib ya dauketa da gigitaccen mari "da uban wa kike wannan maganar ?da ubanka nake banza kawai mara kunya  ta fad'a tana dafe kuncinta .   "idan kika sake zagina ko zagin yaruwata wallahi sai nayi miki jina jina anan shegiya yar iskar banza kakar  ubanki ce karuwa..."ai bai gama rufe baki  ba Aunty hassana ta sauke masa nashi mari ji kake tas tas !! sau biyu ajere "dan uwarka a gabana zaka mari yata ?" jakar gidan uwarka ce da zaka mareta ?" habib ya bude baki zai sake yin  magana aunty ta sake dakatar dashi" karka Kara cewa komai wannan idan da sabo tuni princess ta saba  dan haka komai hassana zata fada akanta  banason ka  sake cewa  uhm bare uhm uhm dan yarta ce halak malak idan karuwa ce ita tayi silar zuwanta duniya ." aikuwa ransa yayi massefar bacci ya dinga Jin wani tuttukin bakinciki na taso masa "ke ai da kin kuskura ya sake ta'ba min lafiya 'ya wallahi da yaga aika aika da yau mun kwashi Yan kallo dake dan kece saar yina basu ba habib bai daddara ba  yace "allah Aunty  ki kama girmanki Kafin na miki abinda bakya tunani koda yake ai ba girma atare dake mahaifiyarmu tafi karfinki sai dai Kiyi damu ba arabi ba boko shiyasa baki san haramcin abinda kikeyi ba "da uwarka da dangin uwarka kake ba dani ba tana gama fadar haka taja hannun kaulat suka nufi kofa tana cewa"dan kutumar uba kawai ." Kuka  maryama  take  sosai  a wajen  tamkar ranta zai fita  aunty  ta qaraso  wajen da take tsaye  tare da dafa maryama  me ye kuma na kuka  bayan wannan ba sabon abu bane ? Kuka taci gaba dayi  habib ya matso "dan allah heartbeat ki daina kuka idan ba haka ba nima zanyi kuka tana kuka habib na kuka nan da nan aunty ta samu waje ta zauna ta d'aura kanta a hannun kujera itama kukan take da karfi A hankali suka qaraso suka durkushe kasa kusa da kafafun Aunty tare da daura kansu a saman cinyarta  suna  cigaba da rera Kuka    wanda har  umma ta shigo   basu saniba" umma  ta qarasa shigowa da sauri  tare da dafe qirji  bilkisu  me ya faru Kika tasa yara gaba kuka ? Kuka  suka  ci gaba dayi ba tare da sun bata amsa   ba..."Ke maryama taso muje ki gayamun me yafaru da ke  da mamanki da kaninka haka  kuke kuka ? ." hannunta umma  ta riqo suka nufi bangarenta Aunty salma  dake tsaye taga wucewarsu maryama na goge kwalla tasan ba lafiya ba  ta biyo bayansu da sauri umma   ta zaunar da ita  a Kan kujera ,a lokacin kukan nata ya fara raguwa"me ya sameku  haka kuke wannan uban kuka haka maryama ? Jin shirun da tayi ne yasa aunty  Salma   ta tunzura "wani mahaukacin tsawa ta sakar mata wanda sai  da ta burkice  "wai  ba magana ake miki ba ne?sai lokacin umma tasan da shigowarta ta dago tana kallon tana mamakin hali munafurci irin nata ko wa ya kirata data shigo ? umma ta hade rai tana cewa    "a'a salma   ba haka akeyi ba ki barni daita kawai karki hargitsa mata lissafi ki barta zatai magna." "uhm ina jinki maryama fad'a min damuwarki cikin sheshekar kuka ta zayyanewa umma komai da ya faru naunayen ajiyar zuciya ta sauke "gsky bata kyau ba , amman  Kiyi  hakuri ita rayuwa ta gaji haka komai da  kika gani  kafin a samu nasara sai anyi  hakuri   in sha allahu wata rana zai zama labari ,ku ya kamata ku dinga kwantar wa da mahaifiyarku hankali ba wai ku dinga tayata kuka ba yi hakuri kinji maryama   Ki bar komai a wajen Allah in sha allahu sai kin zama madubi abar dubawa acikin gidan nan masu takaki wata rana sai  sun zama fadawanki "wallahy aunty aseeya  har da laifinki wajen iskanci yarinyar nan kawai daga yar wannan mgnr zasu zauna suna kuka Kmr mutuwa akayi ke km   sai  ki zauna kina  bata lokacinki ." " babu ruwanki dole na rarrashi diyata  mikewa tayi ta fice cikin fushi umma tabi bayanta da kallo karki qara damuwa da sharrinsu idan kina kuka suna ganin rauninki to kin shiga matsala dan kullum da abinda zasu dinga miki amman idan kika jajurce kece zaki ga rauninsa ta fad'a hk tana goge mata fuska da gefen zaninta  "kin ci abinci ma kuwa ?ta girgiza kai alamun a'a to maza jeki ki rarrashin mahaifiyarki da danuwanki ki dawo ga abinci kizo kici ta mikar daita ta rakata har bakin kofar fita  da kyar ta fito zuwa bangarensu wanda lokacin tuni aunty ta daina kuka suna zaune da habib  tana gama shigowa taji  saurin muryar Aunty  "my princess taho kici abinci nasan kina tattare da yunwa." Babu yadda ta iya ta sakar mata murmushin gefe baki  tana dubanta tace  "kamar kin sani Aunty gbdy suka qarasa  zuwa Kan kujerun roba dake zagaye da qaramin table wanda shima din na roba ne aunty na zaune tare da yaranta suna cin abinci amamn ita  tayi shiru tana tunani  ta kasa cin abinci "male kici abinci mana ta dago ta kalli habib maryama ta ajiye spoon din hannunta ta soma magana a tsanake kamar ba yanzu ta gama kuka ba." "kiyi hakuri aunty akan duk abinda Ke faruwa a gidan nan wani lokacin  Allah yana gwada mutane ya gwada imanin bawa kinsan al'imanu yazidu wa yankus imani na raguwa yana qaruwa to Ke aunty a mizanin da kike allah yana son ya gwada imaninki ne Kan wasu abubuwa dake faruwa damu  duk duniya bani da abar yabo da koyi da hali mai kyau sama danaki sannan kowa yasan ke din mutuniyar kirkice hatta makiyanki suna fadan hk a bayanki to me yasa abubuwanki sukaki  daidaita duk wannan hakuri naki da juriyar amman ba komai bane  kawai Allah yana son ya gwada imaninki da jin tsoronsa ne dan duk allah yana sane ya tsara  haka  hk ." "Mu  qara hakuri hakuri ne kawai zai kawo mana sauki kuma Allah yace annan nasara maasabarin duk wani nasara na rayuwa yana tare da hakuri , hakuri da kike dashi yana cikin tsani da zai kai  mutun zuwa aljanna, hakuri halin manzon allah ne  wal hilmi wal sabri duk kina dashi aunty kina da dauriya kina da juriya kina da tawakkali kina da imani kina da ibada so duk wani abu da kike ganin yana samunki mara kyau ko yana shirin faruwa dake to wallahi jarabawa ce km kina ta cinye jarabawar sai kiga allah ya tsara bazakaji dadi anan duniya ba sai a lahira ,wallahi aunty da ace kana da rabo a duniya baka dashi a lahira wallahi gara ace kana dashi a lahira  baka dashi a duniya ." "sai abu daya  da nake   son ki fad'a mana" ta dago da rinannun  idanunta ahankali tana duba kyakkyawar  diyarta son kowa kin wanda ya rasa  abar tinkaho  kuma yar baiwa domin samun irinta sai an tona "aunty idan bazan takuraki ba  ina son ki fad'a mana inda danginki suke muna son musani domin na fara tunanin akwai wani mummunar abu daya faru a baya dake ,dan idan babu komai bazai yuwa kana  da dangi kuma kuna gari daya amman bakwa ziyar juna"tunda maryama ta fara magana idanun aunty  suka sake  cika da hawaye basu samu nasarar zuba ba sai data kawo karshen mgnrta "ki fad'a mana mu yaranki ne  bazamu taba juya miki baya ba duk runtsi duk wuya muna tare dake koda kuwa kice kika batawa yan'uwanki zamu kasance dake  domin kece karfin gwiwarmu  ta qarasa mgnr tana riko hannun mahaifiyarta ." Mmm sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 14 "Shiru aunty tayi tana jin fad'uwar gaba mai tsanani tafi mintuna ashirin bata ce qala ba habib ya kai hannu ya d'ago ha'barta yana kallon cikin kwayar idanunta dake kwance da ruwan hawaye "male kece karfin gwiwar dake tafiyar da rayuwarmu Kinyi mana komai arayuwar mu ,kin nuna mana tsantsar soyayya ,kin nuna mana daidai da ba daidai ba kin bamu gatan da ba kowa yake samun irinsa ba wato ilimin addini dana boko , kin inganta rayuwarmu mun yaba miki kuma mun jinjinawa qoqarinki garemu da taimakon Allah da taimakon heartbeat gashi har heartbeat ta kammala karatunta kalamai soyayya iri iri dana sanyaya zuciya yake furtawa gareta wanda yake sake tsuma zuciyarta da soyayyarsu "wannan alfarma ce ki fad'a mana ." Duk   yadda   habib  ya  d'auki lokaci   yana magana sai dai har zuwa wannan lokacin aunty  ta Kasa furta komai garesu   illa numfashin da take  janyowa ahankali tana fitarwa da kyar sun sake d'aukar tsawon awa d'aya a wannan yanayin batare da ta fitar da abinda ke cikin zuciyarta ba ."sosai idanunta suka canza kala kallonta suka cigaba da yi suna jiran ta fara basu labarinta, yadda suke kallonta haka itama take kallonsu zuciyarta cike da wasi wasi tana son magana amman hakan ya faskara tana tsananin son yaranta ba zataso suji abinda zai d'aga masu hankali har da zai yi silar shigarsu damuwa ba haka zalika bazataso suji irin rayuwar da sukai da mahaifinsu kafin aure ba da irin tozarcin da mahaifinsu ya sha a wajen yan'uwanta ba ,ganinta fad'a masu wannan labarin babban kuskure ne zata aikata ko bama haka ba bata tunanin zuciyarsu zata iya d'auka , zuciyarsu ma bazata iya dauka ba , bazasu iya wannan juriyar ba." Ahankali ta lumshe idanunta adaidai lokacin da habib ya d'auke hannunsa daga ha'barta har yau tana jin soyayyar mahaifinsu acikin ranta duk da bai duniya amman kullum ta kalli ya'yan da Allah albarkacesu da samu soyayyarsa na qara hauhawa acikin zuciyarta kuma bata jin Kuskure tayi dan ta auresa ".tana kallonsu suka mike atare suka nufi kofar fita kowannensu da abinda zuciyarsa ke tunani akanta dan daman sun san da matukar wahala mahaifiyarsu ta fad'a masu labarinta kasancewarta mace mai tsananin zurfin ciki da rashin son magana ." bayansu tabi da kallo har suka 'bacewa ganinta bata iya d'auke kwayar idanunta akansu ba byan fitarsu ta gyara zamanta sosai tare da rafka tagumi gabad'aya kuma sai taji babu dadi aranta ji tayi kamar bata kyauta masu ba hakan yasa taji zuciyarta kmr zata kama da wuta ahankali ta mike tsaye cikin sanyin jiki ta isa bakin window falonta ta kai hannunta ta zuge labule tana kallon haraban gidan yaranta ta hango suna tafiya a natse kafad'a da kafad'a wanda kusan kansu d'aya basu tsaya akoina ba sai bakin part din umma "heartbeat  ban san  me yasa haka ke faruwa damu ba  ? bana son ganin kanmu  haka  ina  jin Kmr na kashe  kaina  na  huta  da  wannan rayuwa ". ya fad'a yana dafe  goshinsa   cikin  tsananin damuwa . "Subhanallah  after  dad  ka  daina  fadar  haka  karka sake  fad'ar  wannan  kalmar  Allah bazai sa naga  wannan  ranar  ba ,"ka  dinga  addua a duk lokacin  daka  tsinci kanka  cikin tashin hankali ambaton  sunan  allah  zakayi  karka  bari  zuciyarka tafi  karfinka  muryarsa  cike da tashin hankali "amman  me  yasa anayi  mana  abubuwa  rashin  mutunci  aunty  ta hanani d'aukar   mataki ? "daidai kenan  habib  ,abinda aunty  tayi shine daidai shine abinda kowace uwa ta gari ya dace tayi  idan suna yi muma muna  yi to meye bambamci a tsakanin mai ilimi da  wanda bai dashi ? kowani irin  abu zaka  gani a gidan  nan  ka   d'aure ka  cije ni yanzu damuwata  ba matsalar Aunty hassana bace sanin  inda dangin  mahaifiyarmu  suke  shine babban damuwata ."        Ya riko hannunta  cikin  nashi   yana  dubanta "ki ciresu  aranki  abinda muka fi  bukata sune  dangin mahaifi , ace yau bamu da dangin mahaifi ko  ba acikinsu muke rayuwa ba shine  babban tashin hankalinmu  "suma  dangin  mahaifiya suna da mahimanci  domin  zuciyarsu  tafi ta  dangin uba tausayi  ,  jikina  na bani akwai abinda yasa suka nisanci  juna  dole  ina  bukatar  nasan haka  har lokacin  aunty tana kallonsu har sanda maryama ta nufi kofar shiga bangaren umma shi kuma habib ya nufi get din gidan da alamun fita zai yi ta saki labulen tana sauke naunayen ajiyar zuciya ta koma ta zauna cikin zullumi tana tuno rayuwarta ta baya " Maryama bata iske umma a falo ba dan haka ta samu waje ta zauna akan d'aya daga cikin kujerun falon ta runtse idanunta tana tunani "anya ba wani mummunar abu mahaifiyata ta shuka ba wanda yasa yan'uwanta suka gujeta ita kuma take jin tsoron komawa garesu ba ?"anya ma yan'uwanta su suka d'aura aurenta da mahaifinmu ? anya ma akwai gasky a zamanta da mahaifinmu ? "wad'an nan tambayoyin tayita jerowa kanta wanda bata da mai bata amsa sai mahaifiyarta ko umma ." shiru ta sake yi tana qoqarin kawar da zarginta akan iyayenta bata san shigowar umma ba sai dai taji an girgizata sannan tayi sauri ta juyo cikin tsoro taga tana kallonta tace "maryama mai kike tunani haka ?na shiga uku ni aseeya kar dai abinda ya faru Kika zauna kina tunani ?" nan da nan ta soma girgiza mata kai alamun "a'a! tana in in nah  "amm uhm Allah umma bashi bane ."umma ta girgiza ka fadanta cikin sanyin murya "kin kuwa san lokacin dana dauka ina miki magana baki sani ba ?na jima anan ina kallonki maryama kina tunanin abinda ya faru d'azu still maryama kai ta girgiza mata alamun" a'a! Cike da nuna kulawa umma ta juya ta qarasa kitchen inda fridge yake ta isa ta bud'e ta dauko kwalin hollandia ta rufe fridge ta matsa kad'an inda d'an qaramin tray da glass cup's Ke kansa ta d'auki d'aya ta dawo inda take zaune ta janyo kujera gaban maryama ta zauna tana kallonta ta zuba mata hollandia ta mika mata tare da cewa "gashi ki sha dan nasan har yanzu baki sakawa cikinki komai ba ta kai cup bakinta tana kallon umma kad'an ta sha ta kawar da bakinta alamun ya isheta." "karki sake tunanin abinda ya faru d'azu abinda ya rigada ya faru ya faru karki sakashi aranki yazo ya dameki wani ciwo yaje ya kamaki mu shiga uku dan sai nafi kowa shiga damuwa "Allah umma bashi bane wannan ai idan da sabo na rígada na saba " "Wani kallo umma tabita dashi tare da sanyaya muryarta tace "idan bashi bane maryama sanar dani matsalarki dan bayan mahaifiyarki baki da wanda ya fini ina jinki tmkr ni na haifeki bancin ke kadai uwarki ta haifa da tuni na kwaceki gbdy daga hannunta , wannan soyayyar da nake miki yasa na janyoki jikina sosai karki ji komai sanar dani damuwarki ta fad'a tana kallonta ." sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yatsun hannunta kusan second goma sannan ta motsa labbanta "daman ba komai bane kawai ina son nasan inda dangin aunty suke, ko sanin labarinta "me yasa bata zuwa wajen yan'uwanta suma kuma me yasa basa zuwa wajenta?" laifin me tayi masu? " me ya faru daita tunda na taso nake ganinta cikin damuwa da raunin zuciya wanda har yasa nima nake jin haka atare dani ."? Wani dogon ajiyar zuciya umma ta sauke cikin fargaba ta tashi zata wuce har ta juya maryama tayi saurin riko hannunta cikin nata "umma ! ta kira sunanta muryarta na rawa cak umma ta tsaya tare da juyowa fuskarta da tausayawa itama maryama mikewa tayi cikin tsananin tashi hanakali ta rusuna kasa ta daura hannuwanta a saman kafafun umma cikin raunin murya ta fara mgn Kmr zatayi kuka "umma nasan Kinsan komai daya faru da iyayena dan allah karki boye min gskyr dana sanki daita " umma ta zare hannuta ta sake juyawa "umma Kodai mu din bata hanyar sunah aka haifemu bane ?" Umma ta juyo da sauri tana dubanta qirjinta na dokawa da karfin gaske "maryama ta gyada mata kai kana ta cigaba da mgn "duk yadda muke da aunty duk shakuwarmu da soyyyar da take nuna mana ta kasa fad'a mana haka kema gashi umma zaki wuce ki barni byn kece kika bukaci kisan damuwata . "Nasan kinsan komai daya faru ki fada min mu san matsayinmu wata killa ma shine dalilin da yasa muke ganin tasko acikin gidan nan dan girman allah umma karki boye min abinda yafi komai mahimmanci arayuwarmu ki fad'a min na rabu da nauyin dake daskare da qirjina ta qarasa mgnr cike da sheshekar kuka ." Girgiza kai umma ta shiga yi ta dawo inda take tsaye ta kamota ta zaunar daita akan kujera tana kallonta cike da tausayawa kusan mintuna ashirin sannna ta numfasa tana cewa "ku din ba shegu bane ku din yan halak ne" naunayen ajiyar zuciya maryama ta sauke tana kamo hannu umma cikin nata "kinsan kowani d'an adam da yadda yake kar'bar gaddararsa . wasu mutane basa gane rayuwa duk yadda allah ya rubutawa bawa babu wanda ya isa ya canza maka ita,ita qaddara kuma tana fadawa bawa daidai da yadda allah ya hukunto masa qaddara bata san talaka ba bata san mai kudi ba ,qaddara ce da rabonku ta nisanta mahaifiyarku da yan'uwanta yan'uwanta sun kasa kar'ban qaddarar data fad'a mata amatsayin su na muslimai amman mgn ta gsky ku din yan halak ne sai dai akwai yan'uwanki da'aka samesu bata hanyar aure ba .." nan take jikin maryama ya kama rawa tmkr mazari ta tsaya tana kallonta tana assessing maganarta umma ta damke mata hannu gam cikin nata tana kallonta tana jin yadda jikinta Ke rawa tamkr mazari , maryama tayi imani bancin a zaune take da ta tabbatarwa kanta kafafuwanta bazasu iya d'aukar ba, da zuwa yanzu ta zube kasa."cikin kyarrrma wasu hawaye masu zafi suka shiga turereniyar zubo mata tana jin wani zafi a qirjinta mara misaltuwa cikin ikon allah allah ya bata ikon furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi tayita furtawa tana maimaitawa still jikinta da zuciyarta na rawa ." Umma ta kalleta cikin sarewa ta cigaba da magana "wannan qaddara ce maryama km kowani bawa da tashi irin kalar qaddarar bata wuce Kan kowa ba , ki godewa  allah  da yasa  ta hanyar aure aka sameku bilkisu na bani tausayi matuka kullum idan na kalleta sai na zubar mata da hawaye , da gatanta da komai tana rayuwa tmkr bata da kowa ,tana rayuwa cikin kaskanci alhalin bata cancanci haka ba tunda taji an samu wasu babu aure taji komai ya tsaya mata cak hatta shi karan kanshi labarin taji ya fita kanta ." Mahaifiyarki haifaffiyar wannan gari ce anan aka haifeta aka haifi iyayenta ke hatta kakaninta ana aka haifesu sune asalin yan kasa "Idan mutun ya shigo jahar lagos din nan ya tmbyi family's din alhj rafi'u giwa to babu wanda bai san mahaifinta ba ."mahaifinta ko nace dangin mahaifiyarki gbdy masu arziki ne ."mahaifinta alhj rafi'u giwa yana da mata hud'u kinga kenan suna da yan uba a qalla guda talatin sai dai  bazan iya kawo miki sunansu ba ina dai jin Aisha , hauwa wacce suke kira da jiddah abakinta gbdy a gidansu bilkisu ce auta a mata sai kannenta biyu maza dake binta daga kanta mahaifiyarta bata sake haihuwar mace ba haka ma sauran bangaren matan sun daina haihuwa wanda hakan yayi sanadiyar da soyayya mai karfi ya shiga tsakaninta da mahaifinta da yan'uwanta gbdy kowa yana sonta kasancewarta auta a mata " gabadaya yan'uwan bilkisu masu kudi suka aura daga wanda yake london sai wanda yake Canadá ko American ,mafi yawa daga cikin yan'uwanta suna wata kasa daga maza har mata idan kuma anan ne zaki iske su cikin VI ita kadai ce ta auri talaka marashi ,dan gbdy asalin mahaifinki talakawa ne idan aka cire abban sadam wanda yake da d'an rufin asiri  dan  yana  da  gidan bread da kowa ya dogara dashi amman basu da komai ." "bilkisu ta taso cikin gata da soyayya da kulawar iyaye tun daga tasowarta har zuwa girmanta duk abinda take so shi takeyi ta taso cikin soyayyar iyaye dana yan'uwa kowa yana sonta sannan ta taso da farinjin samari acikin family's dinsu kasancewarta kyakkyawa hasalima  kyawun  jikinta kika d'auko fuskarki  ce ta mahaifinki  amman km shi din ma baki dauko farinsa  ba dan shi fari ne sol tmkr bature   kmr  yadda  kike  ganinsa a hoto  ." kowa na sonta da nuna mata soyayya ,acikin masoyanta akwai mubarak dake mutuwar sonta, mubarak cousing dinta ne da ubansa da uwarta uwa daya uba daya kuma shima  mahaifinsa  mai  kudin  gaske ne  km shi  kadai   suka  haifa ,bilkisu  na da shekara shabiyar a duniya alokacin tana ss 1 a secondary school  alokacin mahaifiyarta da mahaifin mubarak sukai alkwarin aure a tsakanin  yaransu dan mubarak din zai yi tafiya zuwa american qaro karatu , sun bar mgnr atsakaninsu idan ta gama karatunta na secondary sai ayi musu aure ."   mahaifinki ussein adam  shima asalin haifaffen garin nan ne haka iyayensa sun kasance su takwas ne a wajen iyayensu mata hud'u maza hud'u umar ,fatima ,gali saadatu ,nazifi fadeela Kmr yadda kikasani , hassana da ussein ne auta ." yana da shekara ashirin da takwas  a duniya ya fara aiki a gidansu bilkisu  ta sanadiyyar abokin   abban sadam  abdulwahab wanda shi gadi yake a makotansu ." mahaifinki ussein ya kasance direban ne gidansu bilkisu wanda Ke kaita school , idan lokacin tashi yayi ya koma ya d'aukota duk inda zata shike kaita hussein ya kasance mutun ne mai tsananin kirki gashi kyakkyawa aji farko illarsa dai shi din ya kasance talaka ne mai son  jin dadi  arayuwarsa km yana harka da yammata da shaye shaye  sai dai bai ta'ba barin gidansu bilkisu sun san da zaman wannan halin nashi ba a boye yake yi saboda tsira da   aikinsa ." Maryama  ta  runtse  idanunta tana jin wani tuttukin bakinciki   a zuciyarta. ta d'aura kanta  akan cinyar  umma  ko  zata  samu  sausaucin zugin da zuciyarta take  ,dan tun  baaje  koina ba   ta   fara datasanin  jin  labarin   iyayenta  , mahaifinta manemin mata ne ga shaye shaye a iyan nan  ma kad'ai  ta raina kanta ta sake yarda su   din  marasa gata ne ." " tun farkon ganin bilkisu da ussein taji  ya  burgeta     daman   shi  Allah   yayi masa  farinjin  mata  dan  atarihinsa  bai  ta'ba  cewa yana  son  mace  ba   dan  har  prouding  yake , wannan yasa ya qara samun kusanci daita sosai , duk abinda taci sai ta rage masa idan zai kaita school ta bashi tun abun yana bashi mamaki har yazo ya daina bashi mamaki ya ajiye  abun amatsayin ita din mai alkhairi ce , shima kma yana kulawa daita sosai dan hatta murfin mota kafin ta fito ya fito ya bude mata sannan  idan   sun  iske an gama assembly  zai tabbatar  da ta  shiga  class  akan  idanunshi  sannan zai  juya ya koma  gida ,ga iya  bada  labari,  ussein ya iya bada  labarin da zai saka mutun nishadi  amman fa ga wanda  yake da mahimanci  a wajensa duk wannan yana cikin abinda yasa bilkisu ta sake sakewa dashi , shiyasa kullum bata da magana sai na fadar kirkinsa a wajen iyayenta wanda har hakan yasa iyayenta suke son batunsa tana sa ayi masa alkhairi na mussaman kullum da irin kyautar da take sa  ayi masa ." haka rayuwa tai ta tafiya mubarak na kiranta a waya amman sam  bata  bashi  lokacinta  yayinda wata irin shakuwa mai karfin gaske ta shiga tsakanin ussein da bilkisu lokacin da ta kai shekaru sha bakwai ta fahimci ba shakuwa bace kawai a tsakaninsu soyayya ce mai karfi wanda shima zuwa lokacin ya kamu da matsanancin soyayyarta ta yadda ya kasa hakuri sai daya zaunar dani ya fad'a min ciwon dake zuciyarsa yace zai yi qoqarin ya boye nashi domin itama bilkisu ya fahimci irin son da take masa bazai ta'ba barin wannan soyayya ya tabbata a tsananinsu ba domin dai yasan tafi karfinsa tafi  karfin aurensa ita din ba sa'ar aurensa bace babu ta yadda zai sameta arayuwarsa ." "Nima na karfafa masa gwiwa ya  danne abinda yake  ji akan  bilkisu na nuna masa bambamci dake tsakaninsu  daita  samun auren irinsu akwai wahala duk  da babu yadda allah baya al'amarinsa shi yayi talaka kum shi yay mai kudi nace yayi addua sai allah ya kawo masa sauki da mafuta , amman alokacin ya sheida min zai ajiye aiki ya nemi wani still dai nice na hana na bashi kwarin gwiwa ya cigaba da aikinsa ya dai rage sakar mata fuska da kusanci daita ." yana cikin wannan halin kwatsam bilkisu ta bayyana masa soyayyata da fari yaki amincewa hakan yasa ta shiga damuwa mai tsanani har rashin lfy ta kwanta batare da iyayena sun san akanshi take ciwon ba wanda ta kai har dakin daaka bashi a gidan take biyosa tana kukan ya amshi soyayyarta "ya zaunar daita ya fad'a mata gsky soyayya atsakaninsu ba abu ne mai yuwu wa ba duba da matsayinta da nashi , kuka take tana nuna masa babu wani bambamci a tsakaninsu dashi duk abu daya ne a wajen Allah da kalamai masu sanyaya zuciya da soyayya tasa ussein ya amince tunda daman shima yana sonta ranar daya amince aranar yan gidansu suka ga ikon allah domin dai bilkisu ta warke daga rashin lfy da take suka fara gudanar da soyayya ." " tun tana boyewa har tazo ta fara bayyanawa zuwa lokacin a family's duk wanda yasan bilkisu yasan ussein idan har kana son kaga kyautar bilkisu ko yalwataccen fararta to kayi mata mgnr ussein family's dinta babu wanda bai san ussein direba ba idan ya dauko ta daga school zasu samu waje su parka su sha soyayyarsu ussein yana da yammata masu son shi amman soyayyar bilkisu tayi karfin da bazai iya cigaba da soyayya dasu ba ,wata irin soyayyar ussein Ke nuna mata mai karfi wanda har ta kai yana iya ta 'bata batare data hanashi ba nasan wannan ne saboda ussein na kawota gidan nan wajen mahaifiyarsa akwai lokacin dana shiga bangaren hajiya bata nan na iske su a dakin tana kwance ajikinsa sanye da kayan makaranta ajikinta suna romance ."hajiya mahaifiyar ussein ba ƙaramin jin daɗin haɗuwar bilkisu da ussein tayi ba ganin yadda yaron nata ya fara natsuwa ba kamar daba ba yanzu duk wani harkar mata ya jinginar da ita, haka zalika shaye shayensa yayi sauki sai wanda ba'a rasa ba." Bayan bilkisu ta kammala karatunta na secondary akace ta fito da miji saboda masoya sunyi mata yawa kowa na sonta da aure km mafi yawansu cikin yanuwa ne sai kawai ta gabatar da ussein amatsayin mijin da zata aura hajiya rahma na gama jin abinda bilkisu ta fad'a ta mike tsaye tana dubanta abun ya mugun girgizata a matukar firgice tace "bilkisu banji abinda kika fad'a da kyau ba ina son ki sake maimaita min ,fad'a min naji da kyau tayi magana a tsawace batare da wata fargaba ba ta sake maimaita abinda ke ranta ai nan take mahaifiyarta da yan'uwanta da suka fito ciki d'aya suka nuna rashin amincewarsu mamakinta ne ya kamasu daman shakuwarsu ba iya nan ta tsaya ba ,har ta kai matakin soyayya juyin duniya akayi daita tace ussein take so har da ikirarin muddin zatayi aure to shi zata aura ,nan fa suka fara raba jaha da mahaifiyarta yan'uwanta kowa zaginta ya shiga yi me zatayi dashi ta rasa wanda zatayi soyayya sai direba common direba zata aura ? ita dai jinsu kawai take amman ita aranta ta kudurta komai zai faru sai dai ya faru amman ita ussein take so km har lokacin mahaifinki na shaye shayensa sai dai ba kowa ke iya fahimtar hk ba km nasan yawon tsaftansa da amfani da turaruka masu kamshi yasa baa ganewa amman mu dake rayuwa a gidan nan mun sani tunda idan yana gida yana shan kayansa a bayan dakin salma lokacin baa gina ba ." Tashin farko mahaifiyarta tasa akayi kiransa cike da matsanancin fargaba da tashin hankali ya nufi part dinta bakinsa dauke da sallama ya shiga falon tana zaune akan kujera na alfarma bata amsa sallamar da yayi ba haka zalika bata dubeshi ba tun kafin ayi masa gurin zama yayiwa kanshi yana mai yi sunkuyar da kanshi a kasa agabanta tmkr mai neman gafara ahankali ya furta" hjy barka da dare ta dago kai daga Kan tv ta maida kanshi tana qare masa kallon tsab tana nazarinsa ko kayan kirki ma babu ajikinsa kana kallonsa kasan mataiyaci ne mai yaci bare ya bawa bilkisu shi kuwa kallo daya zaka masa ka tabbatar da cewar ba cikin natsuwa da kwanciyar hankali yake ba tunda ya samu kiran gaugauwa daga hajiya rahma bai sake samun kwanciyar hankali ba har zuwa yanzu da yake durkushe agabanta sai data gama qare masa kallo sannan ta numfasa ta fara magana a kausashe "meke tsakaninka da bilkisu ?da sauri ya girgiza mata kanshi alamun babu komai ." Shiru tayi tana cigaba da kallonsa kafin daga bisani ta cigaba da magana cikin bacin rai "kace babu komai ?da sauri ya girgiza mata kai alamun Eh ! "ni nasan akwai komai amman tunda kai da kanka kace babu komai to ya tsaya a babu komai din domin idan ya zamo akwai komai zaka hadu da mummunar bacin raina zan maka abinda har ka matu bazaka manta dani ba sannan daga wannan lokacin aikinka ya qare acikin gidan nan ya dago da sauri yana kallonta a tsorace "haka nake nufi ko kana bin mu bashi ne da ka wani tsareni da ido .?" ya sake girgiza mata kai alamun a'a ! "to maza ka tashi yanzu yanzu ka tattara komai naka ka bar mana gidan matsiyaci banza kawai ,kaga yarinya qarama shine kake son kayi mata wayo,  guda nawa bilkisun take da zata auri me shekarunka ? Idan km kwadayin  kudin  ubanta  kake  kayi  kad'an kaci . matsayinka  bai kai nan ba, ka  bari ya'yan manya ya'yan  masu  arziki  irinta  su more ba kai matsiyaci ba , matsiyacin  ma wanda ko rigar kirki baka dashi tana zuba ruwan bala'i ya zabura ya mike da sauri zai wuce tace " ba estate din nan ba ko a bakin get din estate din nan aka gaya min anganka wallahi wallahi sai nasa an daure min kai ko nasa a 'batar min da kai idan ma ba son abun duniya da son zuciya irin naka ba ina kai ina bilkisu? kai yanzu kaga dacewarku daita ?da sauri ya girgiza kai "a she kasan gsky maza tashi ka bani guri matsiyaci banza kawai ko maza sun qare a duniya mai bilkisu zatayi da kai da sauri ya qarasa barin  falon bai tsaya jin sauran karashen zancen ba yana fita daga falon bilkisu ta fito daga d'akinta  daman km hayaniyar mahaifiyarta ce ta fito da daita ta tmbyeta ita da wa ye ." "Nida wannan matsiyacin ne dake neman cutar da rayuwarki "ta bata amsa atakaice tana dauke kanta bilkisu tayi shiru tana nazarinta idan har ta fahimceta da ussein take ? da sauri ta nufi kofar fita ta dakatar daita "idan kika sake kika bar falon nan sai na tsine miki albarka cak ta tsaya tana kallon mahaifiyarta " shasha shar banza da bata san ciwon kanta ba duk cikin yanuwanki wani dan iskan kika ga ya kawo miji Kmr wannan tsukakken da ko kayan kirki babu ajikinsa kullum yana yawo cikin kodaddun kaya ,kisani ko zaki mutu bazaki auresa ba na haramta miki aurensa ke intakaice miki baki da miji sai mubarak dan albarka in sha allahu a ranar useein ya tattara ya bar gidan ya dawo dakinsa dake nan byn makaranta faidiyya ." Tun daga ranar lamari ya sake lalacewa domin tunda bilkisu tasan ya bar gidan hankalinta ya tashi ta shiga damuwa sosai ta kauracewa kowa numfashi kawai take acikin gidansu amman rayuwarta da komai nata yana wajen ussein  ta kirasa yafi sau babu adadi bai daukar kiranta da kyar da ban hakuri da turo sakonin ya sauko sannan ta dawo daidai, acikin satin tasan yadda tayi  suka  hadu da ussein maganar gsky ussein na sonta shima bazai iya rayuwa babu ita ba ,sai  dai wulakancin da mahaifiyar  bilkisu tayi masa  da kiransa matsiyaci da tayi  shi  yafi  komai  tunzurashi   ,domin  duk gargadinta a banza ya daukesu babu abinda yasa aransa  kamar cima burin  sake kwace mata yarinya ta kowani hali   sannan bai boye ma mahaifiyarsa komai da irin wulakanci daakayi masa itama kwarin gwiwa ta bashi tunda yarinyar tana son shi a matsiyaninsa talaka  kar ya kuskura ya rabu  daita ai su suke da mace sune a wahala ,  ina son nayi mgn  alokacin  amman  babu halin yi a gabanta domin ussein shine auta km soyayyarsa dabam ce  acikin yayanta  amman dana fad'a masa gsky ya janye kudinrinsa ya rabunmusu da  yarinya " "nasan duk wannan ne sbd ni abokiyar hirarsa ce dan duk  gidan nan da yan'uwansa mata bai yarda da kowa ba sai ni domin yace ina da sirri  wasu abubuwan ma a gabana suka faru ,ussein ya sha kawo min bilkisu bangarena ta yini anan bilkisu na da matukar kirki da son mutane sannan bata da rowa idan zata zo wajena tana kawo min abubuwan amfani ga aiki da take min sam bazakice diyar mai kudi bace bata da son jikinta tana son aiki sosai da son mutane sadam kam ya sha gata a wajenta dan komai ta gani na yara zata siyo ta kawo masa wanda hakan yasa naji ina matukar qaunarta har cikin raina nake jin tausayinta domin tana sakewa ta fada min damuwarta da duk halin da take ciki a gidansu da yawon mgnr aurenta da mubarak da mahaifiyarta ke mata tana nuna mata mubarak yafi ussein sam bata dace da ussein ba ." "ni kaina nazo na gano bata dace da ussein ba a wani zuwa datai na zaunar daita nace ina son nayi magana daita a matsayinta na kanwata da muka fito ciki daya baa matsayin matar da kanin mijina keso ba ta bani hankalinta ni kuma na fara magana bilkisu ko kinsan ussein yana shaye shaye ? ."tace min "eh !tasani km tayi masa mgn yace da zarar ya auret zai daina ,na numfasa nace "ke kin yarda zai daina ?tace min "eh ! Ko kinsan yana da yammata byn ke ?ta sake ce min eh ai ya rabu dasu Ina son na bata shawara ta auri mubarak ta bar ussein amman ina jin tsoro kar taje ta kwashe ta fada masa tunda idanunta sun rufe shi kuma ya fadawa mahaifiyarsa na samu matsala na kama bakina amman duk wanda ya kalli bilkisu km yasan family's dinta gsky yasan basu dace da juna ba ." Soyayya ta sake yin karfi a tsakanin ussein da bilkisu dan babu abinda barinsa gidansu bilkisu ya janyo sai tabarbarewar rayuwar bilkisu dan a tunanina ussein ya fara saduwa da bilkisu batare da aure ba ni kaina alokacin naso ace iyayenta sun barta ta aureshi tunda ita taji kuma tagani amman mutanen nan suka ki saboda kyamar talaka , dan da irin rayuwar da suke gara ace aure sukayi, bazan ta'ba mantawa ba wata rana bilkisu ta sameni tana kuka na tmbyeta bata boye min ba ta fada min ciki gareta nan take na shiga damuwa mai tsanani nace "haba bilkisu me yasa zaki sakewa nmj jiki haka ?bakya jin tausayin iyayenki da yan'uwanki bakya gudun ranar da ussein zai juya miki baya ?ina ta mata fad'a Kmr kanwata ta jini ita km tana kuka tace ."na taimaketa acire mata cikin nace babu ruwana bazan saka hannu a kashe rai ba ,muna cikin wannan halin hjy ta shigo ashe taji duk mgnr mu itama cewa tayi abarshi kar acire taje gida zata samu iyayenta sai ayi mgnr aure kawai abu ya bani mamaki kamar wasu yoroba tunda sune ake irin wannan rayuwar dasu sai kayi ciki zaa yi aure km su yin ciki ba wani aibu bane a wajensu murna ma zaayi da samunsa tun daga nan na fahimci duk abinda ussein yake da saka hannun hjy ciki ." Tô tun daga ranar ban sake saka bilkisu acikin idanuna ba a she byn ta bar wajena ussein ya bata maganin zubar da ciki ta sha koda ta koma gida sai ciwon ciki kwana tayi tana murkususu ciwo har garin allah ya waye ,cikin yaki fita ga ciki yaki daina ciwo iyayenta dai suka gaji suka kira doctor ya dubata byn ya gama dubata ya rubuta mata scan tô a wajen scan ne likita yaga ciki a mahaifarta tunda likita ya soma bayani mahaifiyarta ta rikice ta dimauce ta kasa gane takamaiman abinda yake fada ganin ta rude yace mata wani abu ya gani me kama da gas a mahaifarta amman ta kira wani daga gida yazo nan ta kira Aisha yayar bilkisu hankalinta a tashe  tazo ta samu hjy rahma a reception zaune tayi  tagumi bilkisu zaune a gefenta cikin tsoro da fargaba scan taso cikin ya fita cikin sauki batare da kowa yasani ba hjy rahma  tace Aisha tashiga taji me doctor yake nufi da gas din da ya gani a mahaifar bilkisu ta shiga nan likita ya fad'a mata komai itama tashin hankali tashiga mai tsanani amman sai ta boye ta fito tana cewa uwar ulcer ke damunta nan hankalin mahaifiyarsu ya dan kwanta suka koma gida ." Aisha ta kira bilkisu zuwa gidanta tana qarasowa bata tsaya wata wata ba ta rufeta da duka sai datayi mata mai isarta kamar zata kasheta sannan ta barta byn ta gama dukanta ta kira kaf yan dakinsu ta sheida  masu sannan  tasa akayi mata wankin ciki aka cire cikin lokacin da hjytr ussein taji babu cikin Kmr ta mutu dan bakinciki har da kuka tayi an cire mata jikanta dan karfin halin irin nata har da tmbyr bilkisu tayi  wa ya cire  mata jikanta  ita km kuruciya  ta fad'a mata tun daga lokacin hjy ta tsani Aisha da yan gidansu bilkisu amman km tana son bilkisu ace warta bazata tsaneta ba dan tana son danta." Hajiya rahma ta lura tun da bilkisu ta dawo daga gidan Aisha ta  warke sumul babu kwana ciwon ciki ta cigaba  da abubuwanta sai dai Aisha ta kira hjy rahma tace  kar a sake barin bilkisu fito koina  har sanda mubarak zai dawo a daura masu aure abinda bilkisu ta tsani ji kenan dan ta tsani mubarak tsana mai girma bata ma son ana yi mata maganarsa karki ce shima mubarak din mummuna ne dogo ne sosai Kmr ussein sai dai shi baki ne kyakkyawan gaske dan sai dana sa ta nuna min hotonsa a istagram an kafa wa  bilkisu  takunkunmi rashin fita koina hatta islamiyya ta daina zuwa alokacin sai datayi wata uku babu shiga babu fita kawai tana gida zaune km babu  waya a hannunta an kwace da  wayar hjy rahma take mgn da mubarak ." Ganin Kmr ta kwantar da kai suna soyayya da mubarak  Kmr gske yasa mahaifiyarta ta dauka ta cire komai aranta  kuma taji dadin hk kulawa da soyayyarta ya qaru ta  zaunar daita tayita nuna mata illar ussein tana qawata mata mubarak zataji dadin rayuwa agidan mubarak alokacin ta tmbayeta ta yarda zata auri mubarak tace eh ta amince wanda ba haka bane acikin ranta  wata rana yan'uwanta gbdy suka zo gidan suna zaune a falon mahaifiyarsu  yayanta abubakar wanda ya kasance first born  a dakinsu yace a barta ta cigaba da rayuwata ta koma islamiyya Kmr kowa dan lokacin saukar alqurninsu ya kusa duk da bata   zuwa baa cire sunanta acikin yan walima ba ba dan me ma zaa hanata rayuwa sbd wani matsiyacin banza  Aisha da sauran yanuwata mata sukace  a'a basu  yarda da fitarta  koina ba shi  km yace abashi dalili gbdy suka kasa sheida masa dalili su dan haka yace dole ta koma islamiyya nasan kuna tunani ko zata hadu da wannan yaron ne yace su barta dashi   idan ta isa tayi Kuskuren haduwa da ussein nan  take uwar  tace "ai bilkisunta ta canza bama zata kunyatata ba yanzu mubarak ne agabanta ." Cikin satin aka dinka mata sabon uniform ta fara zuwa  islamiyya  Kmr  abun  arziki  sai dai aranar ta samu waya ta kirasa bai shiga ba sai ta kirani nan na tmbyeta kwana biyu da halin da take ciki ,bata boye min komai ba a karshe tace na fadawa ussein ya kunna wayarsa nace mata  "to! na qara da yi mata fad'a kar ta sake yarda dashi  tace taji nan fa suka sake din kewa da ussein soyayya  ta  sake karfi   har tafi nada da zara ta fito daga gida  suke haduwa dashi  km ni na tabbatarwa kaina  bazasu ga junansu su bar junansu  hk ba  tunda sun dandani juna dole sai sunyi wani abu duk da  shiedar zina tana da wahala  "to ! bazan manta ba ranar wata asabar da safe ta fito daga gidansu da nufin zuwa islamiyya kai tsaye dakin ussein ta zarto ashe ana biye daita abaya batasani ba har ta shiga dakinsa  tana shiga suka fara abinda suka saba suna cikin wannan halin sai shigowar mutanen gidansu  sukaji  tana rungume ajikinsa  aiko ranar munga tashin hankalin da bamu ta'ba gani ba ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗      MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number  din 1438775094 Aishat abdullahi access idan  an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.                       Page 18 "wato  afa  akan dai  yarinyar nan ce  da  nazo  akanta  yar  kanin mijina  daya  mutu ya barmana amatsayin  riko  to malam  kamar yadda kasani  banason  yarinyar nan na  tsani  na  ganta  dan  ina ji ajikina  akwai  nasarori  da  anan  gaba  zata  iya  samu  domin soyayyar  da  mutane  suke  nuna mata  kamar  ma aikinka  na  farko bai  ci  ba, yanzu  haka samari  sunfi  biyar  da  suka  nuna suna sonta  sai  dai  dadin  abun  da zarar  sun  zo  lokaci  kad'an   sai su  gudu ."     "to  ga  aikin  nan  yaci  zaki  ce kamar  aiki  bai ci ba , ai  haka  zasu dinga  zuwa  suna  'bata  mata lokaci  suna  wucewa  batare  da tasamu  wanda  zai  aureta  ba babu  fa  wanda  zai  like  mata acikinsu  sai  matsiyaci da  zarar masu  arziki  sunzo  zasu  gudu ." "Ai  ni  ba  abinda nake só kenan ba ,ai  bana  son  ko  matsiyaci  ma yazo  wajenta   nafi  son  ta  qare  rayuwarta  a kaskance  a bauta  da  wahala , sai  tawa  yar  saurayin da  yake  sonta  mutun d'aya  ne kuma  ba  wani mai abun  kirki bane  gashi  kace  yarinyata  zata  samu   farinjin  samari  masu  kyau  da kudi sai gashi  sa'banin  haka  nake  gani  madadin  maryama  tayi  bakin jini  acikin  mutane  da samari  duk  banga haka ba ." "kullum  farinjinta  sake  qaruwa yake  jamaa  suna  matukar  qaunarta  basa  son  kula ya'yana koina  akaje  sai  dai  ace a  gaishe da  maryama  amman  banda ya'yana , wani  abun  bakinciki afa  har  yaran  nawa  suma kullum maryama , suna  matukar  sonta  sunki  su  gane ita din  matsalarsu ce,  ko  wani  abu  nayi  mata  sai dai  kaji  suna  min  fad'a  suna nuna  min  rashin  daidai  nan  ta tsaya  ta  sauke  numfashi da ajiyar zuciya  ,afa  yace  "to  yanzu ki takaita  matsalarki  me  kike son ayi ? Aunty  salma  ta  gyara  zama  tace "ina  son  a fara  rabata  da ya'yana ina  son  naji  sun  tsaneta  fiyye  da  yadda  nake  jin  tsanarta  acikin  raina  wannan  shine  kawai muradina  kafin  nazo  neman wani bukatar  ."afa  yayi  murmushi yace "ai  wannan  shi  yafi  komai  sauki ki  tafi  gida  kawai  zaki  ga aiki da cikawa  cikin  sati  biyu  masu zuwa , amman  ina  son  ki  dawo kafin  kwanakin su cika  akwai abinda  zan  baki  indai  har  na baki  ki  kai   amfani  dashi  magana  ta  qare  amman  yanzu zan  fara  jaraba  'yan  abinda bazaa  rasa ba ." aunty  salma  tayi  godiya  ta  ajiye masa  kudi  ta  fice  tana  faman zuba  godiya  tana  cigaba da zagi da  maseefar  kiyayyarta  da maryama  har  ta  fice  daga  gidan afa  ta  dawo  gida  tana saka da warwara  dan ita ko kashe maryama afa  zai  yi  tana só saboda  tsanar  datai  mata  yarinya sai kace lu'u lu'u ai muddin tana  cikin  gidan  sai  ya'yanta  sun  rigata  samun  gidan  aure kafin  tayi  ,idan  kuma  har  zata yi auren  zata sa afa  yayi  mata aikin  da zata  auri  matsiyacin  daya fi ubanta  talauci ." ***** Bayan  kwana  biyu  da  faruwar wannan  alamarin  maryama  tana tafiya  cikin  kayan  islamiyya ta Ardus-salam   yayinda  hannunta ke rungume  alqurani , yammaci ne duk  mazan  unguwarsu  sun  dawo  daga   aiki  duk  inda  ta  wulga  sai an  kalleta da  shaawar  tafiyarta   tmkr  bata  son  taka qasa tana   cikin  tafiya  taji  tafiya  abayanta  bata  juya ba dan  hakan  baya  daga  cikin d'abiarta ,  sai  ma   qara  saurin da tayi  ta cigaba da  tafiyarta saboda tasan  kowaye  ita yake  bi  zarginta  ma  cikin  samarin  unguwarsu  ne   dan  akwai  masu  nuna  suna  sonta  acikinsu ." "maryama  wannan  uban sauri haka  da  kike  zabgawa ko dan gudun  kar  na  biyoki ne ?ta  tsaya cak  lokacin  data  fahimci  muryar malamin  islamiyyarsu ne  na Ardus-salam  mlm  yahuza  ta juyo a natse  ta  dubeshi  cikin nikaf dinta  tare  da  girmamawa ta gaishesa  ."ya  gyara  tsayuwarsa  yana kallonta , kunyarta  ita  tafi  komai tsoratashi  ,duk  iya  takun  saurayi  in  har  ya  had'u  da  mace  mai kunya  yana  samun  karaya matuka  a zuciyarsa ." yayi  dan  murmushi  irin nasu  na ustaz "maryama  har  kullum zuciyata  bata  da  sukuni  jiddan wala  khairan  ,na  kasa mantawa dake  ,bani  da wani  sukuni  face na  samu  amsarki  game  da bukatata  dana  kawo  miki  ."yayi  shiru  tare  da tsayawa  yana sauraron  yaji  me  zatace  nan take  tayi  kicin  kicin  tamkar wacce  aka  tsare  da wuka  zaa yankata sai da ta  dauki  second  goma  sannan  tace "uhm  !sai   kuma  tayi  shiru  ta  qasa  qarasa  abinda zata fad'a  maganar ta makale acikin zuciyarta  shi  kanshi ganin motsa  lip's  dinta  bai  sawa ranshi cewar zatace  uffan ba  bayan  abinda ta furta  ba ." ba  yau  bane farko haka  zalika  yasan  ba  yau  bane zai  zama   karshe ya  saba tareta a hanya  ta kasa ko  ambaton  sunan shi  bama shi  kadai  ba  kusan  mutane  suna  yawon  fad'ar  haka akanta   bata  da  yawon  surutu  da  saurin  sabo  da  mutun  duk wanda  ka  ganta dashi  tana d'ar d'ar  alamun  tsoro  shima dan matsayin  da  yake  dashi  na malaminta ne  yasa  har  ta tsaya akan  hanya  babu wanda ya kai ta tsaya  dashi  akan  hanya ". "Maryama  idan  na lura  da yanayin  fuskarki  ba soyayyata bace  baki  amsa ba  amman kuma bazan  tabbatar akan cewar kin amsa  ba  ,tunda a kwayar idanunki kawai  nake  iya  karantawa shine kunya  ce ta  hanaki  ki  fad'ar   abinda  Ke  cikin  zuciyarki maryama  ki  daure  ki sanar dani menenê  acikin  zuciyarki  akaina  ko  zuciyata  zata  samu  sukuni da natsuwa  ?". shirun  dai  da  baya  só  shi  tayi dan  bata  da  abinda  zatace  masa  ,bazata  iya  wata  soyayya ba  da'ace  ta d'aurawa  kanta  soyayyar  samari  da  lokacin da suke  guduwa  suna  barinta da ba qaramin  tashin  hankali  zata  shiga ba  gara  ta qarasa rayuwarta  haka  tunda  soyayya  ba  dole bane  arayuwar   mutun  haka  ma  aure   sunah ne matukar  mutun  zai  iya  rike   kanshi   domin  acikin Sahbbai  ma  akwai  wad'an da  suka mutu basuyi aure  ba  dan  haka  mutun  zai  iya zamansa  haka   kuma   aure   da  haihuwa  bashi  bane   karshen   duniya  a ganinta  ko  babu  shi  mutun zai iya  rayuwarsa ." "hakika   maryama   duk   cikin  unguwar  nan  kai  garin  nan  ma  gbdy  har  cikin  islamiyyarmu banga  diya  macen  da  take  burgeni   kuma   zuciyata  take dawainiya   da tarin  soyayyata  kamar ki ba ki samar  da  amsar  soyayyata a cikin  zuciyarki   ko zan samu farinciki da  sukuni  koda  ta  wata  sigace  da  zan fahimta ."sosai  hankalinta  ya  kai  kololuwar tashi  tama  qasa  tsayuwa  bisa kafafunta , kafafunta suka   shiga karkarwa  ,yana  son  ya  bata dama  ta  wuce  gida  saboda  halin  daya  karanta  atattare  daita amman  kuma  bai  gaji  da  kallonta  ba  kuma shi yasani ko zai kwana  tsaye  atare  daita  bazai gaji  ba , sakina  da kanwata ne suka  zo  zasu  giftasu malam yahuza  yayi  sauri yace "sakina ku tsaya  ga  maryama  tsaye  ku wuce  gida  tare ." Shukura  ta  kallesa  tana  jin  wani  irin  tuttukin  bakinciki   acikin   zuciyarta   abun  yayi matukar  bata  mamaki  maryama  tare da mlm yahuza malamin da  take  matukar  só  amman  tsoro da  shakkansa   ya   hanata   fito  da  soyayyarsa "malam ! kawai  tace  tayi  gaba  tana  jan  tsaki  acikin  ranta  dan tasan muddin  tayi a fili ta kad'e  har  ganyenta  dan  mlm  yahuza  babu wasa  wajen  disfila  d'alibai  da  iya  karatu  da  d'aukar  wanka  ga  tsantsar  kyau  shiyasa  kowani  d'alibi  ke  matukar  jin   tsoronsa  a kaf  ardus-salam  babu  malamin  da'ake   shakka  da só kamarsa  da yawa yammata  na   qaunarsa ."sakina  kam   jikinta  a matukar sanyaye  ta  wuce  batare  datayi  mgn  ba  maryama  ta  bita da  idanuwanta  wani  abu ya soki zuciyarta  domin tun safiyar yau ta lura  sakina  ta  canza  mata abun ya  matukar d'aure  mata  kai amman  tayi  mata  uzuri  da cewa yanayin  rayuwa  ne ." Mlm  yahuza  bai  sake  magana ba sai  tunanin  kunyar  shi da sakina taji  dan  ganinsa  da maryama  yasa  ta  kasa  tsayawa dan haka  yace "maryama  sai  gobe  idan  mun  had'u  a makaranta amman  fa  kisani  bazan  ta'ba  daina  tsaidake  anan  ba har sai ranar  dana  samu  na  cire  kunyar nan  kika  amince min  "Kanta  kawai  ta  gyada  masa muryata  a  matukar sanyaye tace "sai  da  safe  ta  juya  ta  cigaba da  tafiya  a natse  bai  bar wajen ba  sai  da  tayi  nisa  sosai  ta 'bacewa  ganinsa  ." yana  juyawa  sukai   ido   biyu   da  mlm  umar mai hausa  atare   sukai  murmushi "wato  kai  har  kullum bazaka daina  wahalar da kanka akan maryama ba  ko ?"Mlm yahuza ya qarasa  inda mlm umar yake ya tsaya  yana cewa "ya  zanyi  umar  allah  ya  jarabeni  da  soyayyar  maryama  bazan  iya hakura  daita  ba "kai   kuma  allah  ya  jarabi mata dayawa  da  sonka  ba ?"wannan kuma  damuwarsu  ce ,ai  dama  haka  zaka  fad'a  duk  kuna  son  maso  wani  ,kai  ma ka tausayawa masu  sonka  sai  allah  ya duba lamarinka  ". "Allah  ma  ya sani  babu  wacce nasan  tana  sona  bare na tausayawa  ya fad'a yana wani  sham kamshi  "Uhm uhm  mutumina  banda  fad'ar son  rai   duk  wanda  ka  fadawa  haka  zai  d'auka  bakasan  abinda kakeyi  ba ,"kaga  umar rabani da wannan  zance  mu  barta  matsawar  bata  sarauniyar  mata zaka  min  ba "karka  duba yanayin  gidansu  maryama  amman  dai  kai  kanka  kasan  tafi  karfin  aurenka , maryama  macece  daya  kamata wani  hamshakin mai kudi  yayi wuf daita ." dan  murmushi  mlm  yahuza  yayi yace "haka  ne  amman  ai  duk  mace   bata  fi  karfin  auren  nmj ba kuma  kowani   mutun  yana da nashi  matsayin  da  zai  iya  burge mace , kuma  ina  dashi  ina da quality da  mace  zata  soni  koda kuwa   bani   da  kosisi  bugu  da  qari  ita  mace  ba  kudi  take  bukata a soyayya  da  kulawa  take so ni  nan  kuma  zan  kula da maryama   ." "da  me  zaka  kula  daita ?karka  manta  ita  din  cikakkiyar 'yar boko ce , yarinyar  da  idan  ta  fara aiki  yanzu  sai  ta  d'auki  nauyin ciyar da  mutanen  gidanku  gbdy  dan haka  banga abinda zai sa ka dinga wahalar  da  kanka  kana 'batawa kanka  lokaci  akanta  ba , kayi hakuri ka rabu daita  domin dai babban goro sai  magogin karfe ." Mlm yahuza  ya  dan ji  zafin maganar  malam  umar dan haka ya  rage  farar  fuskashi "wai me kake  nufi ? kana nufin dan  ita din yar boko ce  tana da  kyau na bugawa a jarida  kana tunanin zata samu aiki  nan  gaba  zai sa ta  iya fin karfin  halittar  ubangiji "? yahuza  abinda  nake  son ka fahimta duk  wad'an nan  abubuwa da  kake  gani  fifiko ne a tsakaninka  da maryama  kawai  abinda  nake so  kaji  aranka  tafi  karfinka tafi  karfin  aurenka  ." "kaga  dan  allah  mlm ka  barni ka zuba  min  ido ba wahalar banza nake  yi  ba ina cikin zuciyarta kunyar da take yawon nunawa akaina ta wadatar dani cewar nayi mata , nan  gaba kad'an zata fahimtar  dani  ."Ka  dai  bi a sannu kar  wata  rana  kana zaune wani hamshakin  mai  kudi ya shigo har cikin  unguwar  nan  ya  aureta .". "bari  kaji  babu  wani  mai  kudin da  zai  aureta  domin  suma  masu kudin  sunfi  son ya'yan masu kudi yanuwansu , ita  maryamar da ba  galihu ne  daita  ba ,ai  ba uban da  zai  shigo  cikin  wannan  rubabbiyar  unguwar   ya   kwashta ai  duk wannan  kyawun  nata akan  irinmu  zai  qare "yana  gama fadar haka ya  juya  dan  baya  son  ya  sake 'bata  masa  rai ." Tafiya  kawai  maryama  take zuciyarta  cike  da  kunci  da  tunani  barkatai  ba  kuma  akan mlm  yahuza  ba   sai  sabon  sauyin  data  gani  akan  fuskar  sakina  dan  na  shukura   mai  sauki ne idan  da  sabo  ta  saba  ita  da yaran  aunty  hassana  haka  suke mata  amman  sakina  fa  basu saba  haka  ba  suna  matukar  qaunar  junansu  tun  suna  yara su din  masoya  ne  na  hakika ." da  wannan   tunani  ta  qarasa  cikin   gidansu   kai   tsaye   ta  nufi  bangaren su  sakina   domin  tambayarta  dalilin  sauyawarta  ashe  wahala ce  ta  shigo  daita  tana sallama  aunty  salma  tace " Yauwa maryama  d'auki   tsintsiyar  ki   share  min  d'akuna  tas   shine  amsar  sallamar  da aunty salma tayi  mata  kamar  tace  bazatai ba amman  ta  kasa  ta  ajiye alquranin  dake  hannunta  ta  d'auko  tsintsiya  ta  fara  shara  batare  da wata  damuwa  ba ." tana  shara  aunty  salma  na  zaginta  ita  da  shukura   amman  sakina  na  zaune  batace  komai  ba  sa'banin da da bata  yarda a  zageta  ko  sakata aiki  akan  idanunta  ,tana  shara wani  gurin  da  simiti  wani gurin babu  ga  kuma  sakina  na   zaune ta  d'ago  idanunta  a  natse ta  kalleta  taga  kurar sharar  na zuwa inda  take  muryata a sanyaye tace "sakinata   ina  ganin  sai  kin  d'an  tashi  kinga  kurar  tana  zuwa  inda  kike  ta  wani  watso  mata harara  "ai  gudun  ruwanki  nake  kallo  naga zaki shareni  ko  kuwa   ."? maryama  tayi  shiru  tsaye  tana karantarta  akwai  wulakanci  acikin   maganarta  "ke  kika  kyaleta  aunty  sakina  amman  banda  jakanta  irin  nata tana   kallon  mutane  suna  zaune zatace  su  matsa , banza  shasha  kawai   mai  siffar  mayu ." inji  cewar  shukara  dake  zaune  kusa  da  aunty  salma  abun  bai  yiwa  aunty salma  dadi  sosai  ba  domin  kuwa  sakina taso ta furta ma  maryama  haka  ba shukura ba  ,sakina  kam  tun maganar  farko  datai  bata  qara ba  ta  tashi  cikin  bacin  rai  ta  shige  daki tana jin  wani  zazzafan  kiyayyar  maryama  ." Maryama  tayi  shiru  kawai  tana bin    shukura  da  kallo "me  kuma  hakan  yake  nufi  dani ? me na yiwa  sakina  ni  kuwa  daga  jiya zuwa  yau  take  fushi  daita  hk ."tayi wa  kanta  tambayar  da  bata  da mai  bata  amsa  sai  sakina  ita  zagin  shukura  bai  dameta  ba kamar  sauyawar  sakina  ta gyada kanta  ta  cigaba  da  shara  tana tunanin  laifin  da taiwa  sakina  har ta  qarasa  ta  wanke  hannunta  da kafafunta  ta d'auki  quraninta ta shiga  d'aki  inda  sakina  take  zaune  akan  gado  tana  cika  tana batsewa  tana  ganin  maryama ta  sake  had'e rai Kmr  taga  mugun  abu  maryama bata damu ba ta zauna  kusa  daita  ta  soma  janta  da mgn taso  tmbyrta  laifin  da  tayi  mata  amman  ganin  yadda  take barsarwa  yasa  tayi  shiru  daga  karshe ta wuce  zuciyarta  cike  da  matsanancin damuwa ." ******* Da  misalin   karfe  d'aya   na  ranar  laraba  wanda  yayi  daidai  da sauran  kwana uku  jirgin  mr ata  ya tashi   zuwa   france   amman  har  lokacin  jikinsa   sai  a hankali  daga  matsanancin  ciwon  kai  ya dawo  masa  ciwon  gabobin  jiki  dan  ko  miyo  baya iya  had'eyewa  sosai  mami  ta  sauko  daga  saman   d'akin    mr  ata  tare da  likitansa  byn  mami  ta sallame  doctor  rafeeq  ta  dubi  maryam  da  nana  hauwa'u tace   "yayanku  fa  yau   tsawon  kwana   biyu bashi  da  lafiya  ku  shiga  ku  gaishesa  keda maryama  ,jiki  sanyaye  suka  ce" to!  suka  mike atare  suka   hau sama ." A natse   sukai  knocking  wanda  nana   hauwa'u  ce  tayi   mryam  na  bayanta  ara'be  kusan  second  goma   suka  d'auka  tsaye sannan  ya  basu   damar  shigowa  d,akin  ,da  sallama  suka  shiga  parlour  suka   gansa  kwance   akan  doguwar  kujerar kushin ya   runtse  idanuwanshi  yana   sanye  da  riga  fari  sol  da  gajeren   wondo  iya  gwiwarsa  yayinda   hannunsa  d'aya  Ke  daidai  saitin  zuciyarsa  ya  d'an  bud'e  idanuwanshi  kad'an  ganinsu  yasa  ya    maida  idanuwanshi  ya  runtse  gam." nana  hauwa'u  tace "sannu  yayanmu  ya jikin  naka kayi  hakuri  walllahi  bamu  san  baka  da  lafiya ba sai  yanzu  da  mami ta sauko  take  fad'a  mana  " shiru  yayi   bai  amsa  mata ba  nan  da nan  maryam ta  shiga  hankalinta  dan tasan  ita  kam  sai ya  had'a   mata  da  tsaki  muddin  tayi  masa  sannu   suna  zaune  shiru  nana  hauwa'u  ta d'an ta'ba maryam  tana  mai  mata  alamar  ta  gaishesa wani abu mai  d'aci  daya  tsaya  mata a  wuya ta had'iye  ta  bud'e  baki  muryarta na  rawa "yaya  sannu "ta fad'a  atakaice  ilai  kuwa  tunaninta ya tabbata  dan kuwa  bai  amsa  ba  sai  ma  tsakin  daya  ja yana  cewa "auta  ya  bani   abun  na  sha a fridge da  saurinta  ta mike ta isa  inda  qaramin  fridge  dinsa   yake  ta  bud'e  donsimo ta  d'auko  masa ta had'a masa  da  ruwa  ta ajiye  masa  akan  table din  dake  gabansa  ." "gashi  yaya Allah ya  baka  lafiya  ya  d'an  motsa lip's  dinsa  alamun ya amsa ya mike  zaune  da  kyar  batare  daya  kalli  inda  mrym  take  ba  itama bata sake  kallon  inda  yake  ba sai ma fuskarta  dake  kallon  wani   katon hotonsa  dake manne  da bangon falon   sanye  cikin  kananan  kaya  riga  da  wondo  milk  colour  touch  of  black  ya  zura  hannuwansa  duka  cikin  aljihun  wondonsa idanuwanshi manne da  farin  glass  fuskar  nan  tashi  a had'e  Kmr koda  yaushe  "auta  ! Ya  kira  sunan  nana  hauwa'u  ta amsa da "na'am yaya! "shiga  bedroom  ki d'auko  min wayoyina da sauri  ta shiga wayoyin na kan katifarsa ta  d'auko tana  danna  gefen  wayar  inda  nan take wayar ta kawo  haske  screen ta  duba  fusakar  wayar wata kyakkyawar  fuska ta  gani  kanta  babu  d'ankwali gashin  kanta  ya  zubo kad'an ya rufe mata gefen  idanunta ." ta tsurawa hoton ido sosai nan ta gane zane ne ba asalin  hoto ba ahankali take tafiya tana  kallon  fuskar  wayar  duk  da  zane  ne  ,amman  yarinyar  tayi  matukar  yi  mata  kyau ta kai  masa  tana cewa "yaya  zanen dake  kan screen din wayarka yayi min kyau  sosai wacece ?"tayi  masa tmbyr  tana duban mrym  da  hankalinta baya kansu yana can kallon mr ata , tana kallon kyaun da allah yayi masa ba abinda yafi  burgeta dashi kamar sheidar sallarsa daya fito masa a saman goshinsa yayi baki tmkr tawadar Allah ." ahankali zuciyar mr ata  ta soma bugawa da karfin gaske  yana jin tmkr ta kunno masa emotion's din da yake ta qoqarin dannewa acikin zuciyarsa nan da nan idanunshi suka canza kala cikin tunanin da maryam take taji yana  cewa "yarinyar mafarkina ce dana  zanata da hannuna, itace  cikar  burina  ce farincikina ina matukar sonta itace mace ta farko da zuciyata take so  .." jin haka yasa gaban maryam  yayi wani mummunar  faduwa sakamakon jin abinda  ya fad'a ta juyo ahankali ta tsura masa idanunta duk da ba karon farko  kenan ya ta'ba fadar haka agabanta ba amman na yau din yasa taji wani iri a gbdy  ilahirin  jikinta  ta lura baya iya boye fellings dinsa  akan  zanen  ." ina ma zata ga fuskar yarinyar taga dame tafita da har zuciyarsa ta zabeta alhalin ita din ba gsky bace ?tuna zane ce   yasa ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya mai  had'e da  zallar  kishi "ina  matukar  sonta  auta amamn na rasata a yanzu haka ina son raba rayuwata da tunaninta da duk abinda ya shafeta yana  magana yana  kallon  screen din  wayarsa wanda  Ke  dauke   fuskarta "mun dace da juna ko ?ya tambayi  nana  hauwa'u  yana  lumshe tsumammun  idanuwanshi   dake  cike  da  azaban ciwo ." Nana  hauwa'u  bata  bashi  amsa  tmyr  da   yayi mata  ba  ta kalli  maryam  dake  tsaye  tana  dubansu   idanuwanta  cike  da  kishi  ajiyar  zuciya ta  sauke  tace "yaya  zamu ce allah ya  baka lafiya "na  tambayeki  baki  bani  amsa  ba ya fad'a a mutukar fusace  yana  watsa  mata  harara "me kace ?" shiru  kawai  yayi  tare  da  tsura  mata idanuwanshi   itama  kallonsa  take  tasan   abinda  ya  tsana  kenan  dan  hk  muryarta na rawa tace "kun..." kun  dace  sosai  kawai  dai  matsalar ita din ba   genuine  bace  wani  dogon  tsaki  yaja  yana  cewa "nonsense !"you  and   this  stupid  girl  should  leave  this  room  right  now "ya fad'a  yana furzar da iska mai   zafi  daga  bakinsa  da sauri ta kamo hannun maryama suka  fice  daga  d'akin ." Bayan  fitarsu  kwanciya  yayi  yana cigaba da kallon hoton screen  din  wayarsa  dayawa daga cikin hotunta ya  konasu  hatta  tsarka  zanenta dake wuyansa always  yayi  flushing  dinsa  ,kadan ne daga cikin zanenta  suke cikin  d'akinsa   sai  na kan screen  din  wayarsa  suma nan kusa yana sa rai zai rabu  dasu  ya  huta  da  tunaninta  sosai  yake kallonta "muguwa "ya  furta a wahalacce   "kin addabi  rayuwata  kin  hanani  zaman  lafiya  ke  wace  irin  muguwa ce  da  zaki  damun  rayuwata ?ya  tambayi  kanshi  yana  mai  kawar da kansa daga kallonta  yana   tunani "anya  bazan  dinga  zagawa cikin  anguwane  anguwani  ba ko allah zai sa na ganta "? wannan ai hauka ne mr ata  kake  shirin yi ,me  yasa  bazaka  yarda  cewar  yarinyar nan ba  gsky  bace  Kmr  yadda  aka  Ke  fad'a  maka ? shiru yayi  yana  jin  wani  irin  buguwa  da  zuciyarsa ke  yi  akanta  sosai  yake son raba kanshi da tunaninta  ." Bangaren  maryam  kuwa   suna  taka  step  tana  maseefa "nifa  shiyasa  bana  son  zuwa  inda yake bashi  da  aiki  sai  maseefa  da  disga  mutun sannan wulakancinsa  baya  qarewa akan kowa sai akaina ko ban shiga  tsabgarsa ba sai ya hada dani ni wallahi bana  son  auren  zan dai  yi  ne kawai dan kun dameni , dan  allah  ku raba ni da aurensa na huta tunda ba'ayin  aure  mutun daya  ." murmushi nana hauwa'u tayi  "na lura kishi kike da zane fa  "babu wani  kishi  sister  amman ka auri mutun zuciyarsa na mafarkin wata aljana can wannan ai sai su shafi  mutun  azo arasa meke damuna "hhhhhhh nana hauwa tayi dariya "yarinya kina da aiki kam dan fasa wannan auren sai dai idan daya daga cikinku ne ya mutu  maryam  taja  tsaki ta  d'auki  hanyar  da  zata kai  ta  d'aki  ta  shige  tayi kwanciyarta dan kar mami  tayi amfani da zamanta  a parlour tayita aikenta  d'akinsa  shi  kuma ya samun damar ci mata  mutunci ." Mr ata  na kwance akai  knocking kofar falon yana daga kwance ya bawa mai yi knocking din izinin shigowa hisam ne ya shigo cike da kulawa ya qaraso ya zauan yana cewa "a she bakaji dadi ba ? ya amsa da  kai kawai "oh my god  amman dai ba matsalar nan  bace ? "no ! wannan muguwar yarinyar ce " maganar ta daki kunnuwan hisham ya dan tsaya yana kallonsa  yana nazarin maganarsa "yes  muguwa ce  taki  barin na ganta a zahiri  taki barin zuciyata  ta  zauna  yanzu  ko mafarkinta nayi bata min  magana , bata min murmushi this love is so hurt  wallahi  muguwa ce amman har yanzu ina jin sonta hisham na qasa  cireta  araina  ." ya sake kallonsa ya girgiza kai cike da tausaya masa ya mike da kyar ya shiga bayin dake ciki ya zubar da yawu ya dawo ya zauna ya sake kallon hisham yaga shi yake kallo fuskarsa da mamaki ya sake  girgiza kai dan gbdy ya fahimci wa yake nufi "gsky wannan yarinyar tana baka wahala " ya langwabar da kanshi gbdy  ya koma kalar tausayi "wallahi yau shekara nawa ina faman da soyayyarta amman sam sam yarinyar nan bata tausayina yayi mgnr duk jikinsa ya sake kana kallonsa kasan bashi da lafiya ." "da  ba dan baka da lafiya  ba  ai da mun dan dinga zagawaya  cikin unguwani ko zamu ganta ko wanda yasanya  nima  nayi  wannan  tunanina  hisham   amman  bazan  iya  ba  ya  fad'a  yana  lumshe  ido yana  jin  wani  d'aci  a bakinsa wanda ya rasa na meye ,"karka ce haka ata  ka bari  idan  ka samu sauki  kaje  france  ka  dawo  lafiya  sai  mu  fara nemanta " nace bazan  iya  ba  wannan  muguwar yarinyar  kona  ganta  damuwa  zata zame min a  zuciyata ." Zuciyarsa  na zafi yace tashi muje ka  d'a zaga gari ko jikinta  zai  rage  nauyin  da  yake "ya fad'a yana jin tsantsar soayyarta na  ratsashi  koina  ajikinsa ya mike da kyar "ata  kayi  zauna  gida  wallahi  jikinka babu  kwari   "karka  damu  muje  kawai tunda kana tare  dani  bani  da  wata  matsala ahankali suka sauko falon  qasa   babu kowa a  falonta   farko da alamun mami  tana  falonta  na  uku yaso sheidawa mami  amman  yasan  zata  hanashi  fita  koina  dan  haka   ta  kofar  baya  suka  fice  dan baya son escourt dinsa su  bishi  ya zauna shiru a gefen hisham dake  tuki  yana ciza lip's  dinsa "ina muka dosa "?cewar hisham ". muje    gra   dan   ina  ji  ajikina a irin  wuraren  nan zamu  samu muguwar yarinyar nan   "hisham  ya kwashe da  dariya  har da  dukan stearing mota shi  kuwa gogan ya hade rai a she a fili   yayi mgn ba "wai muguwar yarinyar nan wallahi ata baka  da dama ,yanzu  dai  wani gra ne  a kusa damu  ?mr ata yayi  masa  banza  ya maida kallonsa  gefen  titi yana kallon mutane da motocin dake kai  kawo "duk  da kaki kayi mgn bari muje ikeja gra nan ma shiru  yayi  yaki  cewa  komai  "gskiy ata ka iya  bada suna pricess ta tashi da  sarauniya  ta  dawo  muguwa"dan  allah  malam  ban son isknaci ka maida hankalinka ga tuki " ya fad'a  yana nuna masa gaban mota da hannunsa  "naji  amman  yanzu ace taki sa'a   ka ganta  a  zahiri zaka ganeta "wallahi  zan  ganeta ". daga haka bai sake yin magana ba  shiru motar tayi babu wanda ya sake cewa komai  har suka d'auki titin  ikeja ." Ahankali   Ummah  da  aunty  da maryama  suke  tafiya a hanyar   fitowarsu  titin unguwarsu domin su dauki  hanya zuwa marcaz  duba jikin hafsat diyar aunty  fati , maryamah  ta  hango mlm yahuza ya nufo  hnayar  da  suke  da littafi a hannunsa  da alamar islamiyya zashi  tun daga nesa ya fara raragefen  alamun Kamala ya durkusa har kasa ya gaishe da aunty da Ummah tare da cewa "unguwa zaku né ? maryama ta d'an kallesa ta  d'an  basar dan kar aunty da umma su  fahimci akwai wani  abu atsakaninsu tace" rakiya zanyiwa aunty  tare da umma  zuwa bakin titi ." " allah sarki ya sake durkusawa har kasa ya  gaidai  umma da aunty duk da yasan tahirin rayuwarta amamn  bai  ta'ba  sanya mahaifiyarta  acikin  kwayar idanunshi  ba  amman ya gane aunty ce mahaifiyarta  dan  ko dan yanayin tsawonsu iri  daya ne , mlm yahuza yayi murmushi yace "dan allah ku dan jirani  minti uku kafin ku isa titi ma na dawo amman dan allah karku tafi a kafa  Ummah  ta d'an yi murmushi tace "kada ka damu dan allah , kada ka wahalar da kanka ba  wani  nisa da inda zamu ba mu gode Kwarai da gaske ." " a dai min Afuwa ina zuwa  yanzu  Ummah  tace tô shikenan mlm yahuza yayi murmushi ita dai maryama ta bisa da kallon mamaki dan bata san me yake nufi da kafin suje titi ya qaraso ba ummah ta dubeta cikin mamaki "wannan kuma wanene ? wallahi malamin mu né na makaranta islamiyya ummah  tayi shiru domin ta danyi zargin son maryama din yake itama dai marayam taso ta fada mata kasancewar bata boye mata komai amman ganin fadar bashi da wani amfani tunda da zarar ta amincewa mutun ya fara zuwa kwana biyu sai ya gudu batare da laifin komai ba ." suna tafiya suna hira  har suka karaso bakin titin gwagulori wanda ya dawo sabon titi  a yanzu sakamakon gyaran daaka masa suna tsaye kawai sai ga mota ta nufo inda suke maryama tasha jinin jikinta domin dai tasan bashi da mota amman babu mamaki ko ta abokinsa ce yayi burki agabansu ya fito daga cikin motar "umma  ku shigo na kaiku har inda zaku "maryama shiru tayi mamaki ne ya damu zuciyarta tunda take bata ta'ba jin mlm yahuza ya dan burgeta ba sai yau sosai tayi farinciki da abinda yayiwa mahaifiyarta da ummanta ido kawai ta tsura masa ta cikin nikaf dinta tana kallonsa cikin farinciki shi kanshi ya fuskanci  hakan ." ya zagaya ya bude masu  mota suka  shiga kafin ya zagaya bangaren direba ya jefa mata wani kallo mai nuna tsantsar so kawai itama ta tsinci kanta da mayar masa da murmushi suka wuce ita kuma ta koma gida duk da  abinda yayi mahaifiyata da ummah  a yanzu bata ji ta  fara jin mlm yahuza acikin zuciyarta ba amman  ta kudirce zata danne zuciyarta ta fara sauraronsa ." Hud'u  daidai  ta shirya zuwa islamiyya bata tsaya jiran sakina ba  ta  kama  gabanta acikin aji sune na farkon zuwa ita da kawarta subai'a wacce suka qare karatu tare ahankali suke hira fitowar result dinsu kafin malamin da zai daukesu darasin qurani ya shigo sosai taso tayi mata hirar mlm yahuza amman ta kasa har aka cika a ajin mlm abbas ne ya shigo nan da nan suka fara karatu ita dai karatun yau dai tazo makaranta tayisa amman zuciyarta fal da walwala da irin farantawar da mlm yahuza yayi mata dan tana matukar qaunar mahaifiyarta da umma duk wanda yaga girmansu kuma ya mutunta matasu tô lallai zai samu wani babban matsayi acikin zuciyarta most especially mahaifiyarta tana tausayin halin data tsinci kanta ciki yana daya daga cikin abinda yasa ta d'auki komai nata da mahimmanci ." "ta godewa allah ta kuma ta godewa mahaifiyarta da umman tare da  abban sadam domin sun tsaya akan ganin sun ingata rayuwarta da karatun boko da Arabic tun alokacin da take secondary babu wanda yasa rai zata cigaba da karatunta zuwa jamia sai gashi kwatsam allah ya taimakesu ita da subai'a sun samu scholarship daf da zaa tashi ta shigowar mlm yahuza makaranta  ,taso Kwarai ta gansa tayi masa  Godiya ta fito tana duddubawa ko zata gansa amman bata ganshi ba zuciyarta taso ta gansa farincikin da yasa  iyayenta  take son tayi masa godiya dan tasan dole zai ji dadi acikin ranshi ." Bayan an tashi daga makaranta bai biyota ba kamar yadda ya saba sai dai kafin ta isa gida kanwarsa nafisa tayi saurin isa inda take daman kuma tasanta sai dai ba aji daya suke ba tana gaba daita sosai suka gaisa tare daita suka cikin gidansu inda suka iske aunty salma a tsakar gida  tana zaune tana waya ganinta tare da nafisa yasa aunty salma kashe wayar suka gaisheta suka wuceta suka shiga bangarensu maryama." suna shiga ta nuna mata wajen zama "nafisa ki zauna ga waje tayi murmushi ta zauna akan kujera ita kuma ta shiga dakin aunty ta duba inda aunty tasaba ajiyar kudi taci saa ta samu naira dari ta dauka ta fito tana cewa nafisa "ina zuwa ." "nafisa ta mike ta biyota ina zaki bari muje tare maryama tayi dan Jim dan taso ta zauna taje ta siyo mata lamurje ta kawo mata amman bata da choice dole ta barta suka sake fitowa tare kai tsaye bangaren aunty hassana suka shiga tayi sallama ta isketa zaune tare da yaranta babu wanda ya amsa sallamarta bare ya kalli inda take bata damu ba dan ta saba "aunty hassana ina yini akwai lamurje? "Akwai na nawa zaki tsiya "?amm.. na naira dari ne wani dogon tsaki taja "ai nasan bazaki canza zani ba daga na naira darin babu qari kullum ana waje daya baa cigaba ni  bani kudin ki shiga ki dauka ki bace min da gani ." Zuciyar  nafisa ta cika da mamakin aunty hassana maryama ta mika mata kudin ta shiga ciki ta dauka suka fito ta mikawa nafisa gashi nafisa babu yawa "kai  haba ai babu komai ai danasan ma kashe kudinki zakiyi da tun farko na hanaki " karki damu ai ba wani abu bane maryama ta fada tare suka shiga bangaren Ummah duk inda maryama tasa kafarta nan nafisa take ajiyewa ta share wa umma gida ta gyara mata koina tare da nafisa suka fito zasu wuce aunty salma ta kirata cike da isa ta isa inda take "kije kiyi min shara " "Shara !" Maryama ta furta a hankali?eh ko bazakiyi bane kika tsaya kina maimata min abinda na fada ?zanyi ta fada a taikaice tare suka shiga bangaren aunty salma ta fara shara "aunty maryama kawo na share miki da sauri dan akwai abinda ya kawoni "? itama tashi jinin jikinta dan tunda suke da nafisa  bata taba zuwa inda take ba sai yau "no ki barni na share nima yanzu zan gama ta zauna akan kujera sakina da shukura suka shigo shukura  na ganinta ta washe mata hakora "nafisa yau kece agidanmu ?ta tambayeta murmushi ya sake bayyana akan fuskarta "eh nazo wajen aunty maryama ne "aunty kuma ?ta fada a rude "eh mana aunty ce ai maryama tunda zuciyar babban yayanmu ta kamu da matsanancin sonta dan har wani kirki ya kirkirawa kanshi dan kawai ya aikoni wajenta ta fada batare da wani shakka ba ." shukura  batace komai ba ta zauna kusa da nafisa " inata son nazo gidanku amman ban samu damar zuwa ba saboda makaranta nafisa tayi murmushi "ai kuwa sai ki arawa kanki lokacin ki dinga zuwa gidanmu tunda yayana ya kamu da soyayyar maryama nasan naki  matsayin sai yafi nawa zance bai yiwa shukura  dadi ba dan haka kawai taji bata son wata halaka a tsakanin maryama da mlm yahuza haka kawai take jin rashin jin dadi aranta ." Maryama tana gama shara ta fara kokarin wucewa yayinda nafisa take qoqarin mikewa shukura  kuma tana janta  da hira "kinga bari na isar da sakon da aka aikoni gobe ma hadu a islamiyya ta tashi tabi bayansa maryama suka jera har cikin falonsu atare suka zauna akan kujera nafisa na cewa "aunty nah "maryama tayi murmushi "kai nafisa da ki daina ce min aunty kullum fa da sunana kike kirana "ai yanzu komai ya canza baki ji yan karin magana ba sunce idan kidi Ya canza dole ma rawa ta canza nafisa ta fada tana dariya "ya karatu yanzu uzukin nawa ?maryama ta sauya magana dan bata son wata maganar soyayya mlm yahuza yayi mata mutunci Kwarai kuma ta yaba masa amman batu na soyayya bata jin zata iya yayana ne yace na fad'a miki zai zo zuwa anjima maryama tayi murmushi amman shine tun dazu baki fad'a ba  kika zaunar da kanki "ai ina sane na zauna ina qarewa zabin yayana kallo naga shin haukan da yake akanta ya dace abun mamakin sai naga tafi gaban tunanina ashe da kawai kallonki nake ta fad'a tana dariya "kai nafisa a she haka kike kema?maryama ta fad'a tana murmushi santi nake yi yayana ya iya zabe wallahi maryama nayi matukar farinciki da yaya ya sanar dani Ke yake so kuma har kin amince nan fa yanayin maryama ya sauya daga murmushi da take zuwa mamaki "ita a ina ta amince masa da zai qarar .? "kun dace da yayana sosai ni daman ina tunani wa yahuza zai dauko mana acikin yammatan dake mutuwar sonshi saboda tsananin kyawunsa da kyawun halinsa uwa uba ilimi kema kuma munyi saa a komai kina dashi taso kwarai ta tsaida nafisa akan yayanta amman kuma sai ta kasa har zuwa lokacin data ciro wata karamar takarda ta bata tace gashi inji yaya in baki hanuna da naki ta fad'a tana shirin tashi daga kan kujerar da take zaune  itama maryama ta tashi ganin tana alamar fita domin rakiyarta da hannunta ta dakatar da maryama "zauna abunki ba sai na wahalar dake ba ki zauna ki karanta sakon yayana cikin tsigar wasa maryama tace "ban son iskanci nafisa naga alamun raini ya fara shiga tsakaninmu ta bude baki "ni kuma  asuwa na raina aunty  amman dai Kiyi zamanki wallahi na gode ?" Ta koma ta zauna ganin idan ta biye mata sai su kai dare bata gama iskancin ba ta fice ita kuma ta samu waje ta zauna ta bude takarda da nafisa ta bata ." _Ina son ki takaita kanki  da abinda kikasan zai war gaza farinciki dana gani akan fuskarki ina bukatar ganinki cikin farincikin dana ganinki dashi yau my maryama ina son jin muryarki cikin kunnuwana ina son jin hirarki zanzo yau byn sallah ishai_ Ta sake karantawa ta sauke naunayen ajiyar zuciya ita sam bata jin wata soyayyarsa wata killa da a shekaru biyu da suka gabata yazo lokacin tana shekara shatakwas kuma alokacin maza basu zama abun tsoro a wajenta ba da babu mamaki taji tana sonshi har ma ta iya aurensa amman zatayi kokari ko yaya ta fahimtar dashi illa soyayya gareta ." ahankali ta jingina jikinta akan kujera tana jin bakinciki abubuwan da suke faruwa daita allah ya bata kyau ya bata ilimi tana da nagarta amman bata san dalilin da maza suke gutunta bayan sun kawo kansu wajenta ba , tana zaune tana tunanin taji sautin muryar aunty salma"maryama !maryama!!ke dan uwarki wannan wani irin rashin mutunci né kalmarta ta katse mata tunaninta ta dawo haiyacinta tana magana cikin bacin rai "au zama ma kikayi dan iskanci ni nawa mijin bai kwanta ya huta ba yana can neman abinda zaku ci shine ke zaki zauna saboda sakarci banza da tunanin banza daga yarinya tazo tana sakarci da munafurci sai ki nemi waje ki zauna kina tunanin iska dana banza da wofi allah dai yasa komai zai faru abanza né tunda bashi da wani amfani ana da kyau amman ya zama na banza ." "tô ai dole ya zama na banza  tunda mugun hali yayi yawa " tarasa me ta tsarewa aunty salma  acikin gidan nan zuwa yanzu bata tunanin iya kiyayya ce kawai ta fara tunani har da hassada take mata akan halittar da allah ya bata idan ba haka ba tana mata komai iya bakin gwargwado tayi mata shara tayi mata wanki idan ta kama wanke wanke duk tana yi dan dai a zauna lafiya da kuma kar ayi masu gorin ciyar dasu daake acikin gidan shiyasa sau tari bata son fita tsakar gidansu tafi son tayi zamanta a daki dan da zarar ta fita ko ita ko aunty hassana sai an samu wanda yasata aiki ko ya zageta ko mata gori ." muryarta a sanyaye tace "yanzu ni aunty salma me nayi miki ?akwai abinda kike bukata da banyi miki ba ?ta rike baki au tambayata ma kike yi  saboda yanzu kin kawo karfi an balaga an balallage an zama iyayen mata ? " "allah yasa ba ita kadai ta balaga ta zama iyayen mata ba wadan da suka balaga suka zama iyayen mata suna da yawa " suka tsinkayi muryar habib abayansu  yana harararta ta juya tana kallonsa "zo ki fitar mana daga daki kafin na miki dukan mutuwa "uwarka da ubanka basu isa ba bare kai qaramin dan iska  bazan fita ba idan kana iyawa zo ka fitar dani tattaccen d'an  iska ." Jin haka yasa cikin fusata ya nufota gadan gadan maryama ta mike da sauri  ta shiga tsakani tana cewa "Uhm uhm after dad babu ruwanka daita "tô wallahi kice mata ta fita ta bar mana dakinmu "au har wani takama kake da dakin aro? "dakin aro ne a aka bawa uwarka  byn kai a kusa da dakin kashi aka haifeka idan bakasani ba kasani ga dakin daaka yi cikinka ga masai Shege ma shegen girman tsiya anyi mugun gado a wajen uwa ". Ya daga hannu zai kai mata mari maryama ta rike hannunsa a rikice cikin muryar kuka tace "haba habib ka barta mana ta fadi duk abinda take son fad'a ai bakinta ne tunda mu din ba shegu bane meye abinda zai dameka arziki kuma  na allah né "kinga makira banason iskanci da munafurci ki barshi yayi min abinda ya ga dama amman gamawarsa ke da wuya zanci uwarsa da shi kansa dan wallahi duk iskanci da yayi akan uwarsa zan rama dan ita ce daidai ni ba shi qaramin dan tasha  ba ,yana yawo suki suki duk yunwa ta gama cinyesa tayi maganar cikin daga murya ". "Dan allah   kiyi  hakuri  karki saka aunty cikin fadan nan habib yayi Kuskure amman kiyi hakuri bazai sake ba habib ka bata hakuri ". "What!" "Allah ya tsareni na bawa wannan matar hakuri kar allah yasa tayi hakuri ko ki fitar mana da wannan mahaukaciyar matar koni yanzu najata na fitar daita sha shar mata mara sallah mai dotti kawai hannu aunty salma ta daga zata wanke masa mari taji ya rike mata hannu sannan ya tsura mata idanunshi cikin sarkewar murya yace "kin gama ta'ba lafiyar kowa acikin gidan nan yanzu ke har yanzu a tunaninki kin kai matsayin da zaki cigaba da marena na kyaleki ? tô  idan kina wannan tunanin ki daina yanzu dan zaki ya girma ya wuce wannan tozarcin dan bake ba hatta wanda ya ajiyeki acikin gidan nan  kanin mahaifina kenan ba bai isa ba bare ke banza jaka dabba mai hali irin na dabbobi mara hankali ." a fusace ta fixge hannunta tare da cewa "da uwarka kakeyi itace jaka dabba  ai ,dan marasa mutunci irin tsiya irin jaraba tana fada yana maida mata ita kuwa maryama sai faman kuka take tana bawa aunty salma hakuri data gaji ma sai tayi shiru kawai tana kuka tana kallon fuskar habib dake tsine mata yana hadawa da yaranta da kaf dangin mahaifinsu da yasan basa qaunarsu  a maganganunsa ta fahimci babu wanda ya tsana kamarsu aunty salma ta fice cikin fushi ta bar dakin cike da tsananin damuwa ." Maryama ta zauna jagwaba akan kujera tana mai runtse idanunta habib ya lumshe idanunshi "shiyasa kullum suke takura miki wannan sanyin naki yayi yawa ki zama mutun ki nuna masu zamani ki nuna ma kema yar zamani ce sai ku dawo daidai dasu ba kullum ki zauna kina asarar hawayenki a banza ba .""haba after dad mutunci aunty zamu duba yanzu kasan halin matar nan sai taje tayi mana wata kullaliyar a wajen baba gali ". "taje dan kutumar ubanta shima dan kutumar ubansa yazo daidai nake  da kowa allah ya taimakesa yazo  idan ban raba masa kanshi gida hudu ba kice Shege ne , anan zan jira zuwansa ya fad'a yana huci tmkr zaki ta mike ta kamo hannunsa ta zaunar dashi ta zauna kusa dashi tana shafa masa baya dan ta fahimci ya dauki zafi dayawa "kayi hakuri komai me wucewa ne wata rana sai labari abinda ya baka dariya wata shi zai saka kuka ka bar aunty salma da duk wanda zai fad'a son rashi acikin gidan nan akanmu." ita fa aunty salma bata da laifi gani tayi yanuwan mahaifinmu suna yi mana yau da sun  ga kima da darajanmu wallahi bata isa ba amman nasan wata rana idan ance tayi bazatayi ba kayi hakuri kaji danuwana rarrashinsa tayita har ya sauko tace "kaje kayi sallah nima zanje nayi kafin aunty su dawo ni na godewa allah ma da bata nan bare taga abun bakinciki  kuma allah yasa kar aunty salma ta fad'a wa baba gali "ta fad'a masa mana Ke kike tsoronsa yazo ni yau a gida ma zanyi sallah ina jiran duk abinda zasu dashi bari ma naje na nemo atakobina wacce zan fellewa mutun kai dashi ." "Dan girma Allah kayi hakuri meye hadinka da takobi kai ba dan daba ba "na zama yau "allah ya tsareni allah kiyaye bazaka zama haka ba Kiyi adduar karsu zo da hauka ya fad'a tare da shigewa dakin aunty kofar  tabi da kallo kafin daga baya ta mike taje tayi alwala ta fita ta tada sallah tana cikin sallah tajiyo sallamar   aunty tana kiran sunanta  tana jin habib ya fita yana cewa "sallah take aunty sannu da zuwa " "Yauwa habib a she kana gida ?nima ban jima da shigowa ba ina kika je ne ?kai habib zaka fara tambayoyinka kenan babu  damar kaga na fita murmushi  yay yana sake cewa "aunty ina kike je ?munje duba jikin  hafsat ne ta haihu amman cs aka mata ".bai sake cewa komai ba saboda ya fahimci  kowace hafsa take nufi diyar aunty fatima yayar mahaifinsu aunty ta mike ta shige dakinta domin yin sallah ." Byn mintuna goma maryama ta fito daga dakinta  zuwan dakin aunty  duk jikinta a sanyaye lokacin aunty tana kan dadduma ta idar da sallah tana dai zaune  "aunty sannu da zuwa "yauwa my princess ya zaman gida ?ta gyada mata kai alamun Lfy!"ya na ganki wani iri ko akwai abinda me damunki ne ?tayi shiru kawai tana jin faduwar gaba "kin dan daura mana wani abu kuwa ?ta bude bakinta ahankali tana shirin bawa aunty amsa suka jiyo hayaniya shiru tayi tare da kasa kunne muryar baba gali ne ta mike da sauri jikinta har rawa yake ta nufi kofar fita itama aunty ta biyo bayanta a tsakiyar falon suka gansa tsaye tare da aunty salma da aunty  hassana sai hargagi suke tamkar wasu karnuka yayinda habib ya shiga kitchen ya dauko zabgegiyar takobinsa mai tsine ya koma bakin dakalin kofar fita  ya zauna  yana wasa  takobinsa ,aunty hasana ta nufo inda yake shi kuwa habib kanshi na kasa yana cigaba da wasa takobinsa  jira kawai yake suyi masa wata maganar banza ." Aunty ta kalli maryama ta kalli habib tana bukatar qarin bayani cikin fusata aunty salma tace babu irin qare maku zagin da wannan tantirin yaron bai yi ba ta uwa ta uba har da ce mana dabbobi jakuna aunty hasana tace "da ubansa yake Shege dan Shegiya "da sauri ya mike yana zagayesu da takobi  kiiiii kake jin tsinin bakin takobi asimintin falon basu ba hatta aunty da maryama sun tsorata "kai ko ka fara shaye shaye ne ko meye ?"da sauri ya juyo kan baba gali da yayi mgn fuskarsa a tsuke alamun bai son ya kawo masa raini "dan ubanka da kake zare masa idanu ka dauka zamu ji tsoronka ne ?" "a'a nasan bakwa jin tsorona kamar yadda nima yanzu babu wannan tsoron duk wanda ya nemi zaman lafiya ayi wanda yace sabanin haka yake bukata bismillah ni bazan bata bakina ba sassara mutun kawai zanyi na aika sa lahira ."ya fad'a yana tsoka takobi daidai kafar baba gali ." Da wani saurin gabadayansu suka ja baya suna kallonsa da mamaki kamar yadda aunty Ke kallonsa "tunda ku kun zama ahlin sheidan bakwa jin wani yare sai na dabbobi bismillah  nima zan nuna muku akwai digon wannan dabbar ajikina  ,tunaninku me zakuyi da kuka wani kwaso jiki gbdynku kuka zo ? "To wallahi  yau koni ko ku duk wanda ya zagi uwata da yaruwata sai na yanke masa harshe byn na raba kanshi gida hudu ." zaro idanuwa sukayi suna sake ja  baya dan ya daga takobin hannunsa daga aunty hassana har aunty salma suka koma bayan baba gali suka boye cikin  karfin halin yace " bamu bane dabbobi da uwarka kake aiko jin haka Ke da wuya habib yayi kansa gadan gadan  zai sara mata takobi  aunty ta rike masa hannu tana zabga masa mari cikin muryar kuka tace "meke damunka habib ta fad'a tana kwace takobin tayi jifa dashi  "zaka kasheni ne  ? "Ai da zai kashe dabba irinki da mun samu kwanciyar hankali "inji cewar aunty salma . aunty kina jinsu ko bani takobina na sassara shegu yan kutumar uba .."inna lillahi wa inna ilaihi rajiun allahumma ajirni fi musibatihi   Waklifli khairan minha tana gama fadar haka ta durkushe kasa tana cewa "yanzu habib irin tarbiyar dana baka kenan ?maryama ta durkusa kusa daita tana mai rike hannunta tana ma habib wani irin kallo mai cike da tashin hankali ". "Me  yasa bazaka koyi danne fushinka ba ?me yasa zaka min haka habib ? me nayi maka dana cancanci haka habib ? "Kuji makira ina allonki allonki yana jahannama ,makira  mata kin gama koya masa yadda zai ci mutunci mutune shine  yanzu kizo kina kukan munafurci yau zamanku ya qare acikin gidan nan ku hada ina ku ina ku ku bar mana gidan nan mun gaji da ganinku daga Ke har wadan nan mataiyatan yayan naki bama bukatarku."inji cewar baba gali ." nan da nan habib yayi kan baba gali duk da yaso ya rabu dashi ganin mahaifiyarsa tana kuka dan a duniya babu abinda ya tsana sama yaga ana cin mutunci mahaifiyarsa da yar uwarsa baya son ana zagar masa su bare a zagi qaddararta da binta da muyagun kalamai ko zubar hawayenta  ,wuyan baba gali yake shirin damka ya jiyo sautin muryar aunty cikin kuka tana cewa "wallahi habib idan ka ta'ba shi sai na tsine maka albarka "cak ya tsaya yana kallon baba gali ido cikin ido jikinsa na wani irin rawa tamkar mazari ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗      MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access  idan an tura sai a turawa wannan  09136918331  alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.              Page 16 Ahankali   maryama   ta  mike  daga  cinyar  umma   hawaye  ne  sha'be sha'be  akan   kuncinta ta tsurawa umma  manyan    idanunta  wad'an da   suka   canza   kala  tana kallonta   batare  da   tace  uffan  ba  ,duk  yadda  taso  ta daure  ta  tsaida  hawayenta  kasawa   tayi  hawaye  take   zubarwa  sosai  cikin  tashin  hankali  mai  tsanani ita  kad'ai  tasan  halin  bakinciki  data  tsinci   kanta   ciki   adalilin   jin  labarin   iyayenta ."labarinsu  yayi  matukar  d'aga  mata  hankali "a  she  wahaalarsu  da  tsanar  da'aka yi  musu   acikin  family's  ta  samo  asali  ne  daga  soyayyar  iyayensu ?  haka nan  taji   tausayin  kansu  na   sake  shigarta   . "      Koina   ajikinta   yayi  sanyi  yayinda   falon  ya  d'auki  shiru  ,yadda  maryama  tayi  shiru tana zubar da  ruwan hawaye  tana sake tariyo  halin  da  iyayenta  suka tsinci  kansu  adalilin  soyayya haka ma  umma  bata  sake  cewa  komai  ba  " ahankali  wani  irin  so  da  qaunar   mahaifiyarta da qaninta  habib   ya  qara  shigarta"  allah  sarki  aunty  "hakika  kinga   rayuwa,  hakika   ahlinki  sun  d'auki  zafi  dayawa  akanki  ." "hukuncinsu  yayi tsanani  dayawa  domin  allah Ke had'a  soyayya  alokacin  daya so ba  dabarar  mutun  ba  ,ba  son ran mutun  bane  ,domin  kuwa  idan da  dabarar  mutun  ne  ko  son ran mutu da  mutanen  duniya  dayawa  basu  tsinci  kansu  cikn ta ba ." a qalla  sun  d'auki  minti  goma a haka  suna  kallon  juna   sannan  maryama ta  lumshe  idanunta da sukai   jajur  alamun  tarin  quna da bakinciki ahankali  umma  ta  numfasa  "maryama !  ta  kira sunanta  a  natse , ahankali  ta motsa  lip's  dinta  alamun ta amsa dan  zafin  da  zuciyarta  keyi  ya danne  fitowar  muryarta "ki  godewa  allah  ba  kuka ya  kamata kiyi   ba  maryama."     "ki  godewa  allah  daya  qaddara  aure  a tsakanin  iyayenki  da  har  aka sameku  ta  hanyar  sunanh "  "Alhmd!ta  furta  a can kasan   makoshinta   tana  dafe  kanta  dake  sara da mugun karfi "ya  kai  ki godewa  allah  ki  sake  gode  masa  ko  bai  kai ba ? kanta  ta  gyada  mata  alamun "eh!. "To  ki  manta  da  duk  abinda na  fad'a  miki  muje  Kiyi  sallah  kici  abinci  ki kwanta ki huta "  da  karfi  maryama  ta  fizgo  magana  "bazan  iya manta komai  ba ,a halin  yanzu  ma   ganin  komai   nake kamar   a yanzu  ya  faru  har  nayi  danasani  umma nayi  danasani   jin  wannan  mummunar   labarin  rayuwa  irin  rayuwar   da  iyayena  sukayi  rayuwar kaskanci  ne a wajena."     "why  umma? "me  yasa  komai yake  faruwa  damu haka ?ahankali  ummah  ta  shafa  kanta zuwa gadon bayanta  tare da cewa "kiyi  hakuri  maryama kowa da  kalar  irin  tasa  qaddara a yanzu  jajurcewa  zaki qara  akan  wanda  kikayi  har kika samu  cikar  burinki  na  zamowa  cikakkiyar  mai  ilimin  lissafi  ,kiyi  qoqari  ki tsaya  bisa  kafafunki  domin  tallafawa  rayuwar   mahaifiyarki   daya  qaninka   domin  ina  hango  tarin nasara  da  kwanciyar  hankali  atattare  dake , bilkisu  na  bukatar  farinciki  ,maryama  nasan  da sannu  zaki  zamewa  bilkisu  sanyin  idaniya  amman  fa  sai kin manta  komai  maryama  kin rungumi  qaddarar  rayuwarku ." "Na  yarda  da  qaddara  ummah  domin  yana  daga  cikin cikar  imani  mutun , na yarda da qaddara  amman  umma  aunty  tayi  kuskure  arayuwarta  bance  laifi   bane  dan  taso mahaifina  amatsayin  da  yake amamn  iyaye  fa  umma ? "manzon   sallahu  alaihi  wa salam  yace "ridal  lahi  fi ridal walidaini , wa sakad'ul  lahi fi sakad'il  walidai ."yarda  allah  yana  tare  da  yarda  iyaye, haka zalika fushin  allah yana  tare  da  fushin  iyaye  allah  ya  fifita  iyaye  akan  komai most  especially  uwa ummah ,babu  uwar da  taza ji  dadin irin rayuwar da  aunty  tayi ." umma  tayi  shiru  kawai  tana sauraronta "misali  na kwatantawa  aunty  irin  abinda  tayiwa iyayenta ya  zataji ? na  kawo  mata  in responsible  man  nace  naji  nagani  sai  shi  duk  tarbiyar da tayi  tsawon  shekaru  tana  bani nasa  kafa na  rugujeta ya zataji ?" magana  ta   gaskiya   iyeyenta  da yan' uwanta   sun d'auki  zafi  dayawa  amman  aunty  ta fisu  laifi  kuma  lallai  ya  kamata  taje  ga  iyayenta  ta  roki  gafararsu sannan  ta  koma  cikin  danginta zuciyarta ta  samu  salama ."    "wallahi  yadda  nake  jin  habib araina  bazan  iya  barinsa  saboda  wani  ba  bare  iyayena  da suka kawoni duniya ba ,abun  da ciwo  ummah  ba  kamar  yadda  kuka  d'auka  bane  kema  uwa ce ummah , aunty  ta  kona  zuciyar mahaifiyarta   dayawa,  yanzu na gano duk  aunty  ce  silar  shigarmu   cikin   matsala , iyayenta  na  can  suna  fushi daita  har  yau  ta  yaya   kike tunanin zataji  dadi ?"ta  yaya  kike  tunani  zan  iya  bata  farinciki  byn  ga  inda  zata samu  fiyye  da  nawa  ."? maryama  ta  kalli  umma  cikin  sarewa  ta cigaba  da  magana " umma  abun na  da matukar  ciwo  irin  ciwon  dake  cin  zuciya da  bargo  ,ciwo  ne da  bashi da  magani  da   mafuta  har  sai  ka  had'u  da  mahad'inka , shiyasa a kullum  idan  na  kalli  aunty  sai naji  tamkar  tana  boye  mana  wani  abu  mai  mahimanci  ga  rayuwarta , ashe  gsky  né  hakika bakinta  bazai  iya  furta  mana komai  akan  rayuwarta  ba  matsawar  ita  din  uwa  ta  gari  ce , dan   allah  umma  Kiyi   min  rai ki  raba  zuciyarta  da  wannnan rayuwar  idan  kuma  baki  yi  ba ni  zanyi  ,zan  rabata da  nauyin  dake   daskare  a  qirjinta ." Tana  gama  fadar  haka ta  mike  a hankali  tana  share hawayen idanunta  da  suka  gagara tsayawa  tana  jin  wani  zafi a qirjinta , bazata  cigaba da d'aukar  wannna  nauyin  ba , koda  aunty bata  amince  ta  koma  ga yan'uwanta  ba ,lallai  ita   zata nemosu  a duk  inda  suke  acikin garin  nan  ."muryarta  a sanyaye  tace "umma ni   zan  wuce  sai   da  safe  " kai  kawai  ummah   ta   gyada  mata  sannan   maryama   ta  fara  tafiya  umma   tayi   shiru   tabi   bayanta da  kallo  tana  kallon  yadda  take d'aga  zara  zaran yatsun kafafunta da  kyar  tamkar  wacce  bata  da laka ."   " A inda  ta  bar  mahaifiyarta anan  ta  sameta  tare  da  habib suna  hira  da  alamun shi  baya cikin  damuwa   kamar  ita." bata   tsaya  ba  byn  tayi  sallama tace  "aunty  sai  da  safe  tana gama  fadar  haka  ta  wuce  ta  nufi   d'akin   baccinta  bayanta suka   bita  da  kallo , yanayinta  kad'ai  ya  fahimtar  da  aunty  akwai  tarin  damuwa  atattare daita  shiru  kawai  tayi  tana  tunani "har  yaushe  maryama zata yi  farinciki  arayuwarta  ?". A natse  aunty  ta  mike tabi  bayan maryama  tana  jin  tsinkewar zuciya  haka  shima  habib  akan kujerar  da  take  zama  idan  zatai zane  suka  isketa  ta  dafe  kanta  tana  sheshekar  kuka  atare  suka qaraso  suka  zauna  abakin  gado  suna   fuskantarta  shigowarsu  yasa  ta   tsaida  kukanta   wanda taso tayisa  sosai  har  taji natsuwar zuciyar."     dogon  numfashi  aunty  taja tare  da  cewa "na  shiga  uku ni bilkisu   " ta furta cikin tsananin tashin hankali dan  bata  qaunar  abinda  zai d'agawa  yaranta  hankali  shi  kuwa  habib  hannun  maryama  ya  kamo  cikin  nashi  ya  damke da  karfi  cikin   tsananin  tashin hankali " heartbeat  meke damunki ?." muryarta  a  raunane tace  "babu  komai after dad "ya  babu  komai  zaki  shigo cikin damuwa  , yanzu  mun shigo mun ganiki  kina  kuka  amman  kice  babu  komai  ki fad'a min idan akwai  abinda  ke  damunki  ." shiru  tayi  tana  cigaba  da  shesheka "ki  sani  bamu saba  boyewa  juna  komai  ba  idan kika  min  haka  baki  min  adalci  ba  ,ko  km damuwar  dazu ce  ? still  dai  shiru tayi  ,sosai  suka  d'aga  hankalinsu  ita  kuma  taki  cewa  komai  sai faman  ajiyar  zuciya  ta  saukewa ." damke  hannunta  ya sake  yi  sosai  yana  rokonta "dan allah   heartbeat  karki  daga  mana hankali  ki fad'a min kukan me  kike yi  ?kallonsa  kawai  tayi  tana lumshe idanuwanta ganin yadda  hankalinsa yay matukar  tashi da yadda ya  d'aga  hankalinsa  ya matukar bata  tausayi  daman kuma haka ne idan daya yana cikin damuwa dole ne daya shima ya tsinci kanshi cikin damuwa."   "Yanzu princess bazaki koyi dauriya akan kowacce irin damuwa bace domin ki tsira da rayuwarki da rayuwarmu gabadaya ,Ke kenan kullum cikin zubar da hawaye akan damuwa me yasa zaki dinga asarar hawayenki  tare da qoqarin kashe kanki abanza ."? "Gara dai ki fada mata gsky aunty domin ita rayuwar nan da take ganinta wani lokacin idan abubuwa suka wa mutun tsanani dole mutu ya rage wasu abubuwa domin tsira da rayuwarsa da lafiyarsa." hawayen da take qoqarin maidawa ne suka samu nasarar gangarowa bisa kuncinta cikin sauri tashiga gogewa wasu na sake gangarowa duk  yadda  suka dinga kwantar da kai da murya dan  suji  damuwarta amman   taki  fad'a masu komai domin da zarar ta bude baki hawaye da sheshekan kuka Ke hanata magana dole tasa suka daga mata kafa suka  fice  d'aya  bayan  d'aya daga dakin  da zumar  zasu  lalla'bata  gobe ta fad'a  masu dalilin kukan  ." tafi  mintuna  goma  byn fitar aunty  da  habib   zaune  sannan  ta  yunkura  ta  tashi  tana  sauke naunayen  ajiyar  zuciya ta shiga bayi  ta d'auro  alwala ta  fito ta gabatar  da  sallahr magariba da isha'i  tare  da  shafa'i  da  wutiri byn  ta  idar  ta  koma  kan  katifa ta  zauna  tare  da  jingina bayanta da  pillow  ta  rungume hannuwanta  duka  a qirjinta ." ahankali  ta  runtse  idanunta  tana tariyo  komai  daya  faru  dasu tun suna  yara  "Kenan  adalili  rasa  mahaifi  da  kaka  yasa  rikonsu  ya dawo  hannun  abban  sadam  ."tun  tana   qarama yar shekara hud'u a  duniya ta  taso cikin so daga  bangaren  abban sadam da umma  da  mahaifiyarta   amman  daga   bangaren  aunty  hassana  da  sauran  'yan'uwan  mahaifinta   kuwa  saboda  haushin  da kiyayyar  mahaifiyata  yasa  suka dinga   nuna  masu  tsana  da tsamgwama ,  sun ci wuyarsu  sosai  most  especially  Ita   ganin kiyayyar  dangin  mahaifinsu  da irin  tsanar  da  baba  gali  yayi masu  ya  bawa  aunty  salma  damar  cin kashi  akansu  da mahaifiyarta ." tun  daga  lokacin  kuruciya har zuwa  girmanta  abinda  yake  rage mata  zafin  gidan  shine soyayyar umma  bancin  ita  kowa a gidan baya   sonsu amman kuma  wani lokaci   shi   kanshi  baba gali  ya kan  tausaya masu  in dai ba fad'a sukai  da  sakina  ba ko  yarshi qarama  ba , idan  tayi  mata  laifi ta  d'an  daketa  shine   zai  fito da 'bacin  ransa  har  ya  fito  da  zallar  kiyayyarsa  ,kuma  tun da ta lura  son ya'ya ne  dashi domin ba ita ba  ko uwar  data  tsugunna ta haifesu  baya  raga  mata  akan ya'yansa  ." "yayan  baba  gali  uku  ne aliyu sakina  wacce sa'artace  sai mai bi mata  salamatu  wacce  taci  sunan hajiya  kakarsu  ana  kiranta da shukura  bata  fi  shekara sha bakwai  ba a yanzu ,itama babu yabo  babu  fallasa  suna  d'an  shiri  daita  sai  dai  idan  taga uwarta  na  fushi  da  zagina bata hanata  sai  ma  dai  ta zugata domin  itama  tana  nuna kishinta akainta  idan  taga  umma tana tarairayata ko wani ." Baba  gali  dinki  yake  ada  rasuwar abban  sadam  yasa   gidan  buredi da  rikonsu  ya  koma  hannunsa  alhamdulillah  babu  laifi  ita  din mai  qokari  ce  ta  kowani fanni boko da arabic ga baiwar zane da Allah  ya  bata ." Alokacin  baya  kullum  ta  allah  sai  aunty  tayi  masu  special  lesson  ita  da  habib  kusan kokarinta ta samu ne a wajen mahaifiyarta  ,duk  unguwar da makarantarsu  ana  maganarsu akan  ilimi  bokon  da suke dashi haka  duk  gidan  ba masu  jin   turanci  kamar  ita  da  habib ko wani  abu  za'a  tambaya  ita ko habib  ake  tambaya mahaifiyarsu ta  tsaya  masu  akan  karatunsu shiyasa  ma  education  dinsu  yayi  very  fast  kuma à sanadiyar qoqarinta ita da kawarta subai'a yasa gwanati ta dauki nauyin karatunsu zuwa lagos state university ".    bangaren sakina da  sauran  yaran  gidan  matsalar  iyayensu ne dan  basa  maida hankali  akan karatun  yaransu  gashi  sam  basu da  isashen  ilimin  boko ko Arabic barin  ma  aunty  salma  karta ji labari  ba  arabi ba boko sai  uban girman  kai  ,sau  tari  idan shukura tazo   koyon  wani  abu a wajenta bata  só  sai  ta  nuna  ai  itama tasani  dan  me  zatazo  wajenta akarshe  idan  tayi  mata  zero take samu  a makaranta shiyasa da  yarinyar  ta gane ta daina  bata  idan tace ta kawo kai  tsaye  take ce  mata  bataso   zero  zataci ." hatta  alwala  ba  daidai aunty salma  take yi ba  kuma sallah ma bata  dameta  ba  ,tun  suna yara baba  gali Ke  mata   fad'a  akan tarukun  sallah din  da take yi amman  taki  ta  daina  shi  kansa daya  gaji  sai ya  rabu  daita ya dinga  Kwa'bar  yaransa da yin sallah  sanin  in  har  dan uwarsu ne sai  dai kar su yi  babu abinda ya  dameta dan  idan ma  koyi zasu yi  daita  sai  dai su  koyi taruku sallah." Su  kuwa  aunty  bata yarda tana gama  dauro  alwala  zata  tura habib  zuwa  masalaci  ita km ta umarceta taje  tayi  alwala sannan  a  kullum  dare auty  ta kan fito  tsakar  gidan  tare dasu  har  sakina  kasancewar  tana  qaunarta  ta  koya  masu  darasin lissafi , tana  daukar  lokaci akansu  har sai  taga sun gane sannan ta bukaci  wanda yake da damuwa a bangaren  karatunshi ko baka da matsala  zatai  'yan  tambayoyi  ana  bata amsa  idan bata gamsu da  amsar  ba ta qara yi masu  bayani , bangaren  karatun alqurni kafin  suyi  bacci  sai  aunty tasa sun  karanta izawaka  da tabaraka kafin  su  kwanta  da  safe kuma sai  sunyi murajaa  alqurni sannan su shirya su wuce  school  ko islamiyya ." A ranar batayi  isashen  bacci ba  ga tsananin  tunani  ga  kwadayin son  ganin  yan'uwan  mahaifiyarta  gargadin  kanta  ta shigayi   akan fad'awa  soyayya  da ma ko waye idan  kuma  soyayyar ta zama dole sai  dai  tayi a gidan aurenta  ga duk wanda ta aura har  asuba  tayi maryama batai   wani  yi  baccin  kirki  ba shiyasa  kiran  sallahr  farko  acikin kunnenta  akayi   ta  gyara kwanciyar  ta koma  ta  kwanta bacci   kad'an  tayi ta  lalubo wayarta  ta  duba  taga biyar da  rabi   saura  lokacin  sallah yayi dan har an  tada sallah a matsalacin unguwarsu ." a hankali ta  mike  zuciyarta cike da damuwa bakinta dauke da  adduar   tashi  daga  bacci ta kai tafukan hannunta tana shafa fuskarta sannan a natse ta zuro kafafunta ta sauko ta  shiga  bayi ta dauro alwala ta fito cike da sanyin jiki ta  gabatar da sallah asuba  byn ta idar  ta d'auko  alqurni ta soma karatu  cikin suratul  baqara anatse ta  kai idanunta  ga  window d'akin taga gari ya  fara sha tayi azkar  din safe tana nan zaune tana lazimi har shida  saura sannan ta koma ta kwanta akan sallaya nan da nan  bacci mai nauyi ya dauketa ba ita ta tashi ba sai goma saura ." Ta  mike da  kyar  bakinta  dauke da  salati  sakamakon qirjinta dake wani irin bugawa ta  gyara gadonta ta fita ta dauko tsintsiyar  shara ta  share d'akin  ta fito har falo ta shiga d'akin  mahaifiyarta  bata  ganta ba   tasan may be ko tana byn gida wajen yin wanki ,dan wannan kaida ne  kullum safiya sai  tayi  wanki  kayanta wani   lokacin  da nasu  ta  share d'akin  tasss ta fito da  sharan zuwa falo ta  shiga  kitchen ta hada kayan wanke wanke ta wanke atake  ta goge koina ta sharo sannan ta hada da share falo tayi mopping ta koma daki ta cire kayan jikinta ta shiga wanka bata wani jima ba tayi alwala ta fito kai tsaye ta shimfida daddumar sallah ta sallacci salatul duhu byn ta idar ta shirya kanta ta kwanta lamo cikin zullumi ta kamkame jikinta waje daya wani iri take ji a duk gbdy ilahirin jikinta soyayya irin wacce iyayenta sukayi bazata ta'ba yarda ta jefa kanta cikinta ba". Ta godewa allah  daya bata kyakkyawar zuciyar da bata da lokacin maza ,bata jin soyayyar ko wani  nmj ta ratsa koina ajikinta ,duk wanda yazo da sunan sonta ya dawo ya gudu bata taba  jin haushi ko kewarsa bare ta damu kanta akansa ita fa gsky tafi ganin laifin mahaifiyarta akan abinda iyayenta sukai  mata kuma taji dadin mutuwar mahaifinta akan rayuwarsa domin daa kalleta ace ita din diyar dan shaye shaye da neman mata ne wallahi gara mutuwarsa akan rayuwarsa, data dangwama tana masa adduar shiruya allah gara ta qare rayuwarta wajen yi masa addua samun rahmar Allah ." Da misalin karfe goma sha d'aya da rabi daidai na safe aunty duk ta damu tun jiya rabon tasa maryama a cikin kwayar idanunta ga dai alamun ta tashi dan har tayi ayyukanta na yau da kullum data saba  dan ga parlour nan a gyare tsab sai zuba kamshi yake koina tsab daga ita har habib sun kasa samun kwanciyar hankali bare su karya ,sai ma wata faduwar gaban data ziyarci zuciyarsu ." mikewa aunty tai ta  nufi dakinta shima habib ya biyota kusan atare suka shiga dakin  har suka shigo maryama batasani ba tana can duniyar tunani tare da rafka uban  tagumi  da sauke numfashi a hankali ahankali, da sauri suka qarasa gareta dan yadda suka ganta ya matsifar daga masu hankali  fiyye da jiya dan har wani doguwar rama tayi atare suka kira sunanta suna tmbyrta "wai  maryama menene  damuwarki ne ?"   "heartbeat   banason  ganinki cikin damuwa  saboda duk duniya babu wanda  nake  so  byn  Allah  da aunty  sai  ke  karki   bari  tunani yasa  mu   rasaki  ya fad'a idanuwanshi na kanta "bansan me yasa kike son kashe kanki akan damuwa ba wanda ni a tunani kowace irin damuwa ce zaki iya hadiyeta". aunty ta qarasa maganar tana furzar da iska me zafi daga bakinta  a hankali ta mike ta koma kan kujerar aikinta ta dauko farar takardar daya  ta ajiye akan table domin samun damar cigaba da aikinta ta zaro pencil har kala uku ta fara zane sai dai zuciyarta rawa take nan da nan idanunta suka cika da ruwan hawaye tarasa dalili daga jiya zuwa yau ta sake rasa sukuni da farincikinta, bata jin shaawar komai babu abinda take so da bukata kamar ta kadaice kanta ." Aunty ta dakatar daita daga abinda take tana dubanta zuciyarta na mata wani irin suya a game da halin da take ganin maryama din ciki wanda bata san silar faruwar haka ba maryama bata dago ta kalleta ba ta cigaba da abinda take gbdy kamaninta ya canza ,ahankali habib ya shiga  rarrashinta da nasiha mai kashe jiki  gbdy fuskarsa ta canza Kmr zai yi kuka , Ita  kam  aunty  kasa  furta  komai tayi  ta  zuba  masu  idanunta tana jin tarin damuwa ganin  hk yasa maryama ta soma magana kamar bata son yi "abinda muka bukaci Auny ta fada mana taki jiya umma  ta fada min babu abinda ta boye min sai wanda batasani ba." ta karasa mgnr tana dago kanta Tare da sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta sakin wani sabon kuka lokaci daya shima kwayar idanunshi suka kada suka canza nan take yaji tsanar dangin aunty ya shigesa kasamcewarsa nmj kuma duk nmj dole yayi kishin mahaifinsa nan take ya yanke cewar a zuciyarsa bazai furtawa aunty komai akan yanuwanta ba  koda kuwa ita kanta uwar gayya ta amince zata koma garesu amman shi babu shi babu su har abada ." "Tô  princes kinji kadan daga cikin tarihin rayuwata kuma ina fatan kin gamsu ?shiru kawai maryama tayi tana kallonta tare gyada mata kai "good my princess kinga rana ya fara ki tashi  kici abinci ki kwanta ki dan huta kafin lokacin sallah yayi ta fada tare da mikewa tsaye "yanzu aunty haka rayuwa zata cigaba da tafiya ?tayi maganr cikin raunin murya aunty taja ta tsaya tana dubanta tare da nazarin maganarta "ina nufin haka zamu cigaba da rayuwa batare da kin san  matsayinki a wajen iyayenki ba ? "karki damu dan ni har yanzu bana bukatarsu arayuwata ina ganin kuma ku ciresu acikin zuciyarku "ni daman a yanzu dana gama jin komai na ciresu araina dan basu da wani amfani a wajenmu gara mu qarasa rayuwarmu haka batare dasu ba "haba habib me yasa zaka fadi haka shikenan ita aunty haka zata qare rayuwarta ? kai yanzu zaka iya rayuwa babu ita da kake goya mata baya ?"tayi maganr cikin tsananin fushi "kai daya kamata mu taru mu shawo kanta shine zaka ce haka .?" guntun numfashi ya sauke yana cewa "lallai heartbeat kina da aiki mutanen da suka wulaqanta mana mahaifi dan kawai talaka ne shine zamu tashi muje wajensu alhalin bamu da komai muna nan dai a yadda suka san mahaifinmu babu wani cigaba da muka samu gsky ni bazanje inda suke ba kuma har abada "gsky habib ya  kamata ka tsaya kayi tunani da kyau abinda ubanka yayi bai kyauta ma iyayen aunty ba, ni nan naji dadin dana girma baya raye wallahi da cigaba da ganin rayuwarsa gara mutuwarsa a wajena ."kallonta habib yayi yadda ta zuba masa idanunta cikin bacin rai tana fidda numfashi da kyar "ni babu wani tunani da zanyi akan wannan matsalar ke ma kuma ki bar magana a iya nan dan banga abinda zai sa naje gurin makiyanmu ba kuma ni banga abinda mahaifinmu yayi ba daya cancanci tozarci irin wanda akayi masa ba tun kafin ya qarasa maganar qirjin aunty yayi wani irin bugawa da karfi duk da bata bukatar iyayenta arayuwarta amman bataji dadin kalmar habib din ba ." "wallahi wallahi habib idan ka sake furta wannna kalmar zan balain baka mamaki "kinga ni tafiyata ya nufi kofar fita yana cewa "allah dai ya baki hakuri amman babu abinda zai kai mu gurin makiyanmu ya qarasa fita ,jikin aunty yayi sanyi ta bude baki zata yi magana sai kuma ta kasa cewa komai  "aunty !. maryama ta kira suannata ,a hankali aunty ta motsa lip's dinta "naam !"karki dauki maganar habib da mahimmanci domin shi yaro ne ke uwa ce da muke kallo muke koyi daita kuma kece malamammu dake nuna mana daidai da ba daidai ba ,ki natsu aunty da kyau ke mai ilimi ce allah subuhanahu wata ala yace acikin suratul ahkhaf aya ta arabin da biyar وَوَصَّيْنَا الْإِنْسَانَ بِوَالِدَيْهِ إِحْسَانًا ۖ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ كُرْهًا وَوَضَعَتْهُ كُرْهًا ۖ وَحَمْلُهُ وَفِصَالُهُ ثَلَاثُونَ شَهْرًا ۚ حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُ وَبَلَغَ أَرْبَعِينَ سَنَةً قَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِي أَنْ أَشْكُرَ نِعْمَتَكَ الَّتِي أَنْعَمْتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَالِدَيَّ وَأَنْ أَعْمَلَ صَالِحًا تَرْضَاهُ وَأَصْلِحْ لِي فِي ذُرِّيَّتِي ۖ إِنِّي تُبْتُ إِلَيْكَ وَإِنِّي مِنَ الْمُسْلِمِينَ Allah yana yiwa mutane wasiha ne akan su kyautatawa iyayensu ,  mahaifiya ta d'auki cikin mutun ,tana mai shan wahala ,kuma ta sauke  shi   cikin  wahala ,da daukar cikin  da  yaye  d'a  na  tsawon wata talatin  har  lokacin da karfin mutun  zai  kai  girma yasan ciwon kansa har zuwa karshen ayar  ,cikin girmamawa ta cigaba da magana "kiyi min wannnan alfarmar aunty , wallahi dan kinje garesu a halin yanzu ba kasawa bane bugu da qari iyayenki  suna da hakki akanki babu ruwan allah da abinda sukai miki ". "maryama mu bar maganar nan ta wuce  dan allah sannan ki fito ki karya kar abincinki yayi sanyi tana gama fad'ar hk ta juya ta fice daga dakin shiru tayi  kawai tare da bin kofar dakin da kallo idanunta na  kawo ruwan hawayen tana tausayin mahaifiyarta  bata san meke damun mahaifiyarta ba akan iyayenta sam sam bata son ana mata maganarsu tamkar wanda akayiwa farra'u amman tasan abinda zatai zata janye jikinta tare da tsananta addua akan lamarin allah ya daidaita da iyayenta  da yanuwanta ,yinin ranar a daki ta yini taki fitowa taci komai ." ***** Tun karfe takwas na safe maryam da mami da masu aikinta ke faman kai kawo a kitchen suna qoqarin had'awa mr ATA breakfast sosai mami take lura da yadda maryam take gudanar da aikinta , babu laifi tafi da kokari sosai sannan ta rage son jikin da take dashi wajen girki suna girki suna hira mami ta cigaba da nuna mata wasu abubuwa suna cikin aiki sai ga sallamar hindu ta shigo maryam ta amsa tare da lekawa tace "hindu ce ki  shigo muna kitchen muna aiki ne." wani irin kallon tayi mata wanda yasa maryam taji wani iri ajikinta ,hindu ta tsaya bata shiga kitchen din ba kamar yadda maryam tace ta samu waje ta kame akan daya daga cikin kujerun falon ,mami ta dawo inda maryam take tsaye tana kallonta "sannuki maryam gsky kinyi kokari sosai yau kin aikatu da kyau haka ake so, maryam tayi murmushi kawai tana jin dadin yabon da mami tayi mata "na gode sosai ai nan gaba zan kware na zama professional ta bangaren girki bazan ta'ba baki kunya ba ." mami tayi murmushi tace "da alama zaki wanke zuciyar mamnki ta gyada mata kai alamun "eh !" "To ni zan hau sama na dubo adamcy Idan kin kammala komai ki shirya dinnig kije kiyi sauri Kiyi wanka ki shirya ki dawo Kiyi saving din sarkin zuciyar Kiyi komai a natse  kin dai san halinsa dan oya oya ne yafi son komai cikin sauri sauri bare yau  din nan sai ahankali ."mami dan allah ki zuba masa da kanki mana"idan kunyi aure nice zan dinga zuwa gidanku ina zuba masa ?"dakewa zakiyi  maryam ai ya kamata ace kin saba da halinsa "wallahi mani babu mai iya sabawa da halinsa sai ke nifa mugun tsoro yake bani idan na gansa hatta kayan cikina karkarwa suke mami tayi murmushi tana cewa ni na wuce "To mami sai kin fito ta fad'a cikin murmushi mami ta fito zuwa parlour'n." hindu na ganinta ta saki fuskarta sosai tare da gaishe da mami cike da sakin fuska mami ta masa tana tmbyrta mutanen gidansu ta amsa da lafiya lau kowa yake "mami ina ya adam ne ko har yanzu bai tashi ba ?"eh!hindatu ina tunanin bai tashi ba amman yanzu haka ma samansa zani na taso shi dan yace idan ya wuce tara bai tashi ba na tashesa rausayar da kwayar idanunta tayi tana jin wani zazzafan sonshi ." Mami ta nufi saman dakinsa tana mamakin hindu su dai yaran zamani basu da ta ido akan nmj so na mugun rufe masu ido shiyasa har kullum take ganin girma da kimar maryam, a dai barta da son social media dinta amman rawan kai akan maza sam bata dashi dan tasan bancin itace ta hadata da adam to har abada bazata iya bude baki tace tana son shi ba ." Maryam ta kammala komai a natse ta fito a yatsine hindu ke binta da kallo tana shirya dining ,ita kuma tana tunanin yadda zasu buga kishi daita idan tai nasara shigar gidan ya adam dinta dan dole ta fita ta bar mata gidan ta zauan ita kadai ,dan idan bata kaita lahira ba lallai zata raunatata dan irin son da takewa ya adam ba na wasa ba so ne wanda bazata iya sharing dinsa da kowa ba ." Marayam ta sha jinin jikinta da irin kallon wulakancin da hindu Ke mata dan duk lokacin data kallo bangarenta sai taga kamar hararata take wanda ta rasa dalilin faruwar hakan ,sai da maryam ta tabbatar da komai yayi neat babu abinda mr ATA zai gani yayi complain sannan ta wuce ta nufi dakinsu cikin sauri still tana mamakin hindu ." tana shiga dakin bathroom ta shiga ta fara wanka sai dai matsalarta bata iya wanka cikin sauri ba idan ta shiga wanka a qalla tana daukar awa daya a bayi amman kasamcewar zatayi saving din mr ATA yasa ta tsakaita tayi wanka ta fito ta dauki man shafa warta wanda shima shafa man kanshi aiki ne domin tana daukar a qalla mintuna talati bare aje ga make up ta shirya cikin doguwar rigar shadda bazin har kasa bata gama kammala shiri ba taji sautin muryar mami na kiranta da d'an sauri ta fito zuciyarta na rawa kuma har lokacin hindu na zaune a parlour'n tayi shiru tana yi masa kallon tsab komai nashi yayi mata irin wanda take so nmj ne sai kallonsa take yayinda mami ke qoqarin jawa mr ATA kujera baya" Wani abu mai mugun daci ya hadiye tare da zama yana mai runtse idanunshi ganin mami na son bawa maryam umarnin saving din mr ATA hindu tayi sauri ta mike tsaye tana cewa "mami bari nayi saving din yayana ta fad'a tana mai sunkuyar da kanta alamun kunya "amm...! "Sweetheart bari tayi kawai ya fad'a atakaice mami ta kallesa na second biyu dan sam bataji dadin hukuncinsa ba dan tasan da wata manufa hindu ta fadi hk shi kuma gudun karyaci daga hannun maryam ya fadi haka dan tasan shi tasan halinsa baayi masa gwaninta ranta ya baci sai dai danne damuwarta ." Madadin mami ta zauna kusa dashi kamar yadda ta saba sai ta koma kan kujera ta hankince ta nunawa maryam kusa daita"maryam zauna anan kinji  yar albarka ta maida hankalinta kan tv mr ATA yaji babu dadin yadda mami taja jikinta amman sanin dan maryam tayi haka yasa ya share ya dauki wayarsa yana duba sakonin dake shigowa yayinda hindu ke zuba masa abinci acikin wani haddaden plet ta matso daf dashi Sannan ta ajiye plet din a gabansa." cike da girmamawa ta kira sunansa"ya adamccccyy...!yadda ta kira sunan cikin slow voice yasa daga maryam har mami suka waigo suna dubanta murmushi ta sakar masu wanda ke nuna tana cikin farinciki sannan ta dauke kanta ta maida kanshi wanda shi gogan har lokacin bai daina abinda yake ba bare ya dago ya kalleta sai faman ciza lips din yake yana kallon screen din waya ." kira ne ya shigo wayarsa ya dauka a natse "ok but I think kasan nan da 1week zan wuce france ya aikin gunka ina fatan akwai nasara ya hade rai sosai haba hisham you should know me by now ka ta'ba ganin inda akayi haka ?kawai dan na tattara hankalina zuwa wani waje kawai su kamawa yiwa mutane barna ,ka kuwa san adadin kudaden da mukayi asara kuwa ?kowa acikinsu kanshi kawai yasani ba cigaba AGC bane agabansu well sai na shigo dai hindu ta marairaice murya sosai tace "ya adamcy ga abincin ka dan ajiye waya kaci abinci ". Banza yayi mata ya cigaba da wayarsa "a lokacin zuwa office muke gashi naji ya sultan yace yau kuna da zama na mussaman "bai kalli inda take ba bare ma ta samu matsayin ya bata amsa hakan kuwa yayi wa maryam dadi sosai ,sauran kadan ta fashe da dariya amman ta danne ,ta kalli mami wacce itama ita take kallo suka sakarwa juna murmushin jin dadi sai daya gama wayarsa ya ajiye sannan ya fara cin abinci babu irin kwarkwasan da batayi masa ba da jansa da magana amman bai ce uhmm ba bare uhmm uhm ba illa ma mikewa da yayi tsaye yana gyara yar saman suit dinsa ya dan qarasa kusa da mami muryarsa a dake yace "ni zan wuce kuma kai tsaye daga nan AGC zani "to Allah ya tsaye sai ka dawo yace" Ameen! "har ya juya ta kirasa "adamcy ! ya dan tsaya yana saurareta "kabi komai a hankali dan Allah karka dauki zafi dayawa ahankali ake bin komai ka tsaya ku fahimci juna da yanunwaka". Kai kawai ya gyada mata ba dan zai yi abinda tace din ba dan yau kusan sai ya tashi rabin mutanen kamfanin kuma daga aiki wanda dayawa yanuwa ne a natse ya juya ya fice yana fita hindu tabi bayansa har tayi taku biyu mami tace "amm...hindu yau yayanku baya cikin moon mai kyau ba kin kuma san halinsa bare idan yana jin miskilancinsa idan kika nemi ki tsaida shi komai zai iya faruwa ko kina son wani abu ya faru ne ?" Hindu ta girgiza mata kai alamun a'a daman ba tsaida shi zanyi ba gida zan wuce "to shikenan sai anjima sai data fice mami ta dawo da kallonta kan maryam "mami me kika karanta akan hindu ni yau gani nayi tana wasu abubuwa kamar son ya adam take mami ta tabe baki "wai son shi take amman shi har yanzu bai sani ba dan dayasani bazai bari tayi saving dinsa ba" maryam ta dan ware kananun idanunta sanna tasa dariya tana cikin dariya sai ga nana hauwa'u "sister yi sauri kizo kije wani sabon rigima da sauri ta qaraso tana cewa "bani na sha matar yayana "wai hindu Ke son ya adam wace hindu kuma ?" Wacce hindu mike dashi a gidan nan data wuce ta gidan baba qarami wallahi har na tausaya mata dan idan ya kirani guntuwa ita km fa me zai kirata ?" gabdaya suka sa dariya har mami "wanna kam gsky ne ina zai kaita ? ga wani cream na organic tasha duk ya canza skin dinta ta dawo farar karfi da yaji ,shi daaka bashi farar mace sol yace bai so ina ga mai shafa cream? ni wallahi da zai karbeta ma ya barni da naji dadi anan ne mami tasa baki "kar na qara jin kin fadi haka ai babu wacce zaki barwa shi da sannu zai koyi sonki dan nasan you are so different daga sauran mata ai shiyasa nace a saka sati uku ayita ta qare burina ki rage media ki janyo hankalinsa cikin kankanin lokaci ku zo juna ." "mami kina ganin komai zanyi ya adam zai soni ?" Mai zai hana maryam zai soki mana aure nawa akayi irin naku km a karshe ya zama soyayya mai karfi ,ni dai ina ji ajikina aurensa zai sa ku rasani da wuri tun lokacina bai yi ba." maryam ta fad'a idanuwanta na kan Mami "ki daina irin wannan tunani babu abinda zai faru sai alkhairi zai soki ki so shi babu abinda zai rabaku sai mutuwa shiru maryam tayi tana jin mami ." Motocinsa na tsayawa a haraban AGC escout dinsa suka firfito daga cikin motocinsu mutun biyu na qoqarin bude masa murfin mota ya bud'e ya fito fuskar nan tashi sam babu annuri yana miqawa na hannun hangunsa wayoyinsa ya nufi cikin kamfanin kallo daya zaka yi masa zaka qara jin tsoronsa fiyye da yadda kake ji ." tunda ya samu information barnar daake yi a kamfanin walwalarsa ta ragu sosai babu inda zaka kalla a fuskarsa kaga rahma ganinsa yasa kowa ya shiga hankalinsa domin a irin wannan ziyarar da yake kawowa yake korar mutun daga aiki yana tafiya ana gaishesa cike da girmamawa yayinda sectary dinsa some na biye dashi abaya hannunta rike da files wanda ake bukatar saka hannunsa duk cikin wad'an da suke gaishesa babu wanda ya masawa daya daga cikin escout dinsa yayi saurin bude masa kofar office dinsa ya shiga a natse yana duba agogon rolex din dake daure a tsintsiyar hannunsa ." ya qarasa mazauninsa ya zauan ransa a matukar bace, cike da girmamawa some tace "good morning sir ?kanshi kawai ya gyada mata batare daya amsa ba "sir ana bukatar saka hnnunka acikin wadan nan file's din ta fad'a muryarta na rawa dan ta tsorata da yanayinsa na yau gabansa ya nuna mata alamun ta ajiye cike da girmamawa ta ajiye tana rusuna masa "ya tsurawa file's din ido kawai yana kallo kafin a hankali ya dauki daya ya rabashi gida biyu a matukar tsorace ta dinga binsa da kallo har ya gama yagasu gabdaya ya watsasu sama suka tarwatse yana hura hanci sannan yace "are you crazy some ? Mmm sudais 💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 17 " are you crazy some "?ya furta a zafafe yana hura hancinsa har zata girgiza masa kanta alamun "a'a ! sai kuma tayi sauri ta gyada masa kanta alamun "Eh! dan ko giya ta sha bata isa tace masa "no ! ba bare tana cikin hankalinta "what's wrong with mr ata I did not do anything wrong ? tayi maganr acikin ranta tana mai sake kama kanta dan karta yi wani kuskuren da zai dakatar daita na wasu satittuka koma ya dakatar daita aiki gabadaya ." " ahankali ya mike tsaye ya kamo lip's dinsa na kasa yana cizawa ahankali ahankali !! magana yake son yi amman ko ya bud'e bakinsa maganar bazata fito ba , daga can bakin kofa akayi knowking tare da cewa "may I coming sir ?". shiru yayi yaki cewa komai sannan yaki kallon kofar , some dake tsaye cikin tsananin tsoro da fargaba ta kalli glass din kofar taga prosper ne tsaye hannunsa rike da file mai cover green wani yawu ta hadiye sannan ta saci kallon inda mr ata yake tsaye taga baya kallonta ta sake juyawa tayi wa prosper alama da hannunta ya koma da sauri ya juya ya bar bakin kofar ." Mr ata yasa hannu ya d'auki wani file mai white cover dake ajiye akan makeken table dinsa yana dubawa , lokaci me tsawo ya d'auka yana dubawa yana shawagi acikin makeken office din nasa zuciyarsa na tafarfasa yayinda wata irin zufa ke tsatsafo wa some akan goshinta kamar an watsa mata ruwa .duk lokacin da taga mai gidan nata cikin damuwa itama sai ta tsinci kanta ciki dan kusan duk abinda yaje ya dawo akanta zai qare tunda itace sectary dinsa duk abinda zai shiga ya fita ta sani ." Ya sake kamo gefen lip's dinsa. na qasa yana cizawa hannunsa dake rike da file ta zubawa ido tana tausayawa duk matar datai ganganci aurensa , tana goge zufan goshinta dake ta tsatsafo mata duk da karfin sanyin ac dake ratsa office din ."Cikin kulawa da girmamawa tace "sir !" ko zan iya kiran metting a yanzu ?" "ahankali ya lumshe lumtsatsun idanuwanshi da suka d'an canza kala alamun tarin 'bacin rai yake ji acikin ransa "sir !ta sake kiransa a karo na biyu ahankali ya motsa lip's dinsa "go !" ya fad'a atakaice batare daya kalleta ba da sauri ta juya ta fice daga cikin office din tana sauke naunayen ajiyar zuciya ." Cikin kankanin lokaci ta dawo ta tsaya a gefe cike da kamewa da girmamawa tace "sir komai ya Kamala kai kawai ake jira." a natse ya goya hannuwansa duka abayansa ya soma daga kafafunsa dake cikin hadadden black canvers tana biye dashi abaya hannunta rike da wata takarda mai bango ja , tafiya kad'an sukai sai ga hisham da yaya Ibrahim tare da wasu manyan maikata guda biyar suka marasa baya suna takawa ahankali har zuwa qasan kamfanin madadin yabi hanyar da zai kai shi comference room sai suka ga ya karya yabi wata doguwar hanya , nan take some tayi gaba da sauri domin ta fahimci inda yake son zuwa kafin ya shiga conference room yayinda sauran suke take masa baya, bai tsaya akoina ba sai abakin wani makeken kofar glas wanda ya kasance anan ake ajiye duk wasu ayyukansu masu mahimanci ya zura duka hannuwansa acikin aljihun wondonsa yana kallon wajen yana bukatar a bude masa ya shiga tare da qarin bayani ." Ahankali ta danna madan nan bude waje suka shiga gabadaya a natse ta shiga yi masa bayani tana nuna masa kayayyakin dake ciki da kuma wanda aka fitar kudinsu basu shigo ba duk abinda take fad'a yana jinta kuma yana fahimtarta , amman ko tari bai yi bai yi ba ." runtse idanuwanshi yayi sosai domin ransa ya gama kololuwar 'baci , daga nan wani bangaren suka nufa inda suka dinga wuce maikata da masu zuwa sarin kaya ,ba qaramin barna akayi masu ba ,yaya Ibrahim "yanzu kuna kallo akayiwa kamfani barna mai girma haka ? ya fad'a yana sake runtse idanushi dan baya ganin komai sai wani irin azababen duhu na 'bacin rai ." Yayi shiru na kusan second goma sannan ya sake motsa lip's dinsa "yanzu har kunnuwanka sun manta abinda dady ya fad'a mana kafin rasuwarsa .?" Ka manta umarninsa akan wannsn kamfani ?" duk wannan maganr da yayi Idanunshi na runtse sannan cikin tsadadden turancinsa yayita " ban manta komai ba adam "ban manta umarnin dady ba amman bani da yadda zanyi ne kai kasan halin sultan da sauran yanuwansa kowa abinda yaga dama zaiyi yanzu dai tunda kazo Komi dawo daidai amman kuma kabi komai a hankali kar asamu damuwar da zata haifar da matsala a tsakaninmu wani irin azaban ciwo yaji yana saukar masa har cikin kahon zuciyarsa yana sukarsa zuciya tazo masa wuya , baya jin zai d'agawa duk wanda yake da saka hannu acikin 'barnar dakayiwa kamfanin kafa ba ,bai sake cewa komai ba ya juya da sauri suka rufa masa baya ." conference room ."d'akin ne da'aka tanada domin tautauna mahiman abubuwa masu matukar mahimanci , dogon table ne zagaye da kujeru bakake na alfarma yayinda jikin bangon d'akin ke manne da hoton mr president na lokacin da gwanar jahar lagos ,sai hotonsa dake tsakiyar hotonsu da certificate dinsa na kasuwancinsa ."mafi yawan mutanen dake zaune aciki room din yan'uwansa ne dake aiki akarkashin kamfanin ,a natse ya shiga d'akin taron ya yana shan kamshi tsit baka jin motsin kowa sai ac dake aiki da kuma na mutane dake fita a hankali , bai kalli inda suke zaune ba ya qarasa kujerarsa wanda ya kasance mallakin mahaifinsa ne ada ya zauna cikin nuna isa." ido sultun ya runtse da karfi saboda bakinciki ganin yadda mr ata yayi wani irin zauna akan kujera na nuna isa da jarumta da kamala duk da cikin yanayi na bacin rai yake amman hakan bai hana ainihin sahihin kyawunsa fitowa ba daman kuma shi haka yake fushi ko damuwa baya hana aga kyawunsa hasalima kyau yake qara masa." wani dogon tsaki sultan yaja wanda bai san a fili yayisa ba sai daya ga gabdaya mutanen dake gurin sun juya suna kallonsa banda uban gayya mr ata wanda ya sake daure fuska alamun babu wasa ,sai dai zuciyarsa banda tafasa babu abinda take ahankali ya runtse tsumammun idanuwanshi domin saisaita kanshi daga aikata abinda ke taso masa ahankali ya motsa lip's dinsa ya soma magan a natse tamkar baya son magana sai dai jin maganar kasan magana ce ta masu hankali ce ." "The journey of thousands miles begings with a step as you all know ,ya numfasa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya cigaba d'an lokacin da muka dauka bamu ziyarci wannan kamfanin ba yasa kowa yayi abinda ya ga dama "hakika anyi mana barna mai girman da bazamu iya bari ba , bayan acikinmu kowa yasan adadin wahalar daaka sha kafin wannan kamfanin ya samu kar'buwa a idanun duniya gabadaya ,but what's more important is that duk wanda yasan yana da hannun acikinku wajen danne kwandala acikin dukiyarmu ya gaugauta dawo dashi a yanzu kafin na dauki mataki akan kowa ye acikinmu dan bazan ragawa kowa ba ,bayanin mr ata yayiwa wasu daga cikin yanuwa dadi most especially mukhtar wanda Ke rike da wayarsa yana daukar vedio tautaunawa da'ake wanda kusan duk lokacin da zaa gudanar taro haka ana yi wani lokaci a daurashi a social media wani lokaci kuma baa daurawa ." "Ina jiranku wad'an da sukayi taadanci da fashiwa kamfani domin su san kansa ba sai na fadesu ba sannan sun san number asusun kawasuwancinmu mintuna shabiyar kacal na bayar a maida kudaden daaka hamdame cikin asusu "malam ka dinga sanin yadda zakayi ma mutum magana yaji dadi (Al kalimatu dayyibat sadaqat)kazo kana wa mutane magana cike da isa da izza wa kaajie anan ? sannan su waye suka yiwa kamfani taadanci da fashi da hamdame kudin kamfani ?"sun san kansu !mr ata yayi mgnr tmkr ba daga bakinsa mgnr ta fito ba ,ya cigaba da sauraron some ." D'akin taron ya sake yin shiru babu wanda ya sake magana hatta yaya Ibrahim bai tofa albarkacin bakinsa ba illa ya zuba tagumi yana ji kuma kallonsa kuma hukuncin adam yayi masa daidai muryarsa a dake mr ata yace " ina jiranku rashin dawo da kudad'an nan fa daidai yake da bari aiki acikin wannan ma'aikatan ya fad'a yana kallon gefensa inda some Ke zaune tana qara masa bayanin wasu a abubuwa" idan haka ake son mutun yasan kuskurensa har gyara da mutane dayawa basu gyara kuskurensu ba sannan dan haka malamanmu suke koyar damu wallahi da babu wanda ze juri zaman islamiyya ba kafi fili ka fad'a mana su waye masu laifi musani ba ka tsaya jin kai da girman kai ba ,dan anan babu wanda ka ajiye , yadda kake iko da wannan kamfanin haka muke..." "Enough ! ya fad'a a matukar fusace yana dukan table "ka shiga hankalinka ,su waye mahamdama macuta yan fashi daya wuce ku " sam gaku nan tamkar. mutane amman baku da bambamci da dabbobi ,sam babu jin tsoron allah acikin zuciyarku , sultan ,fahad , hamid a wani goma sha biyu kawai na baku ku dawo da komai idan ba haka ba..... "me zakayi ?sultan ya katseshi cikin zafin rai "me ka isa kayi ?babu abinda ka isa kayi " "kunsan su dabbobi basu gane yaren biladam sai na dabbobi yan'uwansu dan Allah karku dawo da kudaden nan alokacin da nace "yana gama fadar haka ya mike tsaye ya tura kujerar daya tashi baya ya fice ."nan hayaniya ta kaure kowa na fad'ar albarkacin bakinsa kai tsaye mr ata office dinsa ya koma ." Karfe biyu daidai na rana mami na zaune a parlour tare da yaranta maryam da nana hauwa'u suka jiyo sallamar baba qarami sai da gaban mami yayi wata irin mummunar faduwa ya qarasa shigowa yayi wa kanshi mazaunin nana hauwa'u ta gaishesa haka ma maryam ya amsa fuskarshi babu yabo babu fallasa mami ta kallesu alamun su basu waje ,bayan sun tashi sun wuce mami ta fuskancesa alokacin da shima ita yake kallo "zulai naji shiru akan maganarmu banji kin neme ni ba har gashi an saka ranar auren adamu da wacan yarinyar yana da kyau nasan inda maganarmu ta kwana abun nan zai yuwa ko kuwa ?". mami ta numfasa gabanta na faduwa domin dai ita kam bazata iya sake kuno wa danta wata damuwar ba maryam ma da yaya ya karbeta ?gara kawai ta ari bakin adamcy tace masa a'a tunda tasan ko ta tunkaresa da batun bazai ta'ba amincewa ba cikin shakkakiyar murya tace "nayi masa magana ammm..."sai tayi shiru tana jin nauyin fitowar maganar "amman me ki fada min abinda yace "Uhm daman cewa yayi wai mace daya ta .." shiru tayi ta qasa qarasa maganar ganin wani irin kallon da baba qarami ke mata ido cikin ido furzar da iska yayi ya lashi lebansa na kasa sannan ya hade hannunwansa still idanunshi na kan fuskarta cikin danne fushinsa dan baya son ta gane fushinsa a fili saboda abinda kan iya zuwa yazo bare su suyi zargin da hannunsu ,cikin dakewa yace "yanzu dai kin nuna min bazan iya zuwa neman alfama wajenki kiyi min ba ko ?sam sam ba haka bane kai ma kasan halin adamcy idan kuma zaka iya masa magana da kanka to kayi kamar ma haka zai fi "no ba sai nayi masa kema uwarsa da kika haifesa bai ji maganarki ba maganar ubanwa zai ji ? " iya abinda ya iya fada kenan ya tashi ya kama gabansa ya barta cikin zullumi." Mr ata a matukar gabalaice ya qaraso gida zuciyarsa tamkar zata kama da wuta , sai dai cike da qasaita ya shigo parlour'n Mami babu kowa parlour'n sai qarar tv da motsin masu aiki a kitchen ya zauna akan doguwar kujera ya d'ora kafarsa d'aya akan d'aya yana ciza gefen lips dinsa ,ko cikakken second goma bai yi da shigowa ba sai ga hindu ta shigo dan akan danunta ya shigo tunda mahaifinta ya fad'a mata yadda sukai da Mami ta kasa tsaye ta kasa zaune , zama tayi a kujerar dake fuskartashi ta tsura masa idanunta tana kallonsa tamkar ranar ta fara ganinsa tana qoqarin bude baki tayi masa magana ya mike tsam ya kwashe wayoyinsa ya haye samansa yana jan tsaki dan shi ya tsani yawon kallo , kamar ta dakatar dashi amman ta kasa ta cigaba da zama zuciyarta na mata wani irin bugawa akanshi ." tana nan zaune har mami ta fito sanye cikin doguwar rigar na atamfar super exclusive sabuwar bugu ,mami bata tsufa saboda tsanani tsafta da gyaran jiki fuskarta a sake tace "a'a hindu yaushe kika shigo ?ban wani jima ba mami nazo wajen yaya ne "to ai bai shigo gidan ba tukun . ya shigo yanzu ya hau sama "to shikenan bari naje dakin nasa nazo har ta juya hindu ta kirata sunanta cike da rauni "mami !" Cak mami ta tsaya tare da juyowa ta tsurawa hindu ido "mami da gaske kin yiwa yaya adam maganata yace miki a'a ?"shiru mami tayi shiru ta rasa me zatace mata kafin mami tayi wata magana hindu ta cigaba da mgn cikin rawar murya "dan girman allah mami karki yi min tsakani da ya adam kullum zuciyata tafasa take akan sonshi Ke kad'aice zaki iya taimakawa zuciyata idan ba haka ba zan mutu cikin rawar murya mami tace "mutuwa kuma ?"kanta ta gyada mata tare da cewa "da gaske zan kashe kaina shine fansa akan soyayyar ya adam "na shiga uku ni zulai "mami ta furta acikin zuciyarta "kiyi addua hindu ni kaina zan só adamcy ya auri mata fiyye da biyu amman raayinsa ne auren mace daya macen dayan ma da kyar ya amince amman Kiyi addua nan gaba idan rabo sai ya qara dake da sauri ta runtse idanunta kana ta koma ta jingina bayanta da kujerar da take zaune tana jin wai irin faduwar gaba mai tsanani ahankali take zubar da hawaye ganin da gaske tarasa farincikin rayuwarta "anya kuwa mami nada tausayi da imani ."Anya mami bata da son zuciya ?"Tayi wa kanta tambayar tana jin radadi acikin zuciyarta bazata iya jurar rashinsa ba ,bazata iya ganin da wata a matsayin matarsa ba, yadda bazata zama matarsa a farko ba to babu wacce zata zama "hindu bari naje naga yayanku nazo hindu ta bude idanunta da kyau tana kallon bayan mami dake taku ahankali." Kai tsaye kitchen ta shiga ta bud'e firdge kwalin dynsimo mai sanyi ta ciro ta rufe ta qarasa inda cup's suke ta dauki daya ta daura akan qaramin tray ta fito ta wuce a parlour ta samesa zaune akan kujera yana sanye da singlet da gajeren wondo ta bude kwalin juist din ta tsiyaya a glass cup taja qaramin table din glass din dake tsakiyar dakin ta dora tray ta mika masa cup ya girgiza mata kai tace "na kawo maka ruwan sanyi ?ya sake girgiza mata kai "coffee fa ? still dai kai ya girgiza aranta tace yau dai akwai damuwa ta d'an zauna gefensa "ka daina barin damuwa na hana zuciyarka sukuni "naji sweetheart amman ba wani damuwa bane zazzabi nake ji kawai "sannu bari naje na kawo maka magani ka sha "no need sweetheart thank you "kai har yanzu bakasan ka girma bane meye abun gudu a magani ?ni dai kawai bana só né da zarar na kwanta nayi bacci zanji daidai ,tô karka kwanta yanzu magariba ta kusa ya gyada mata kai yana mai runtse idanuwanshi ta mike tana cewa "me zaka ci dan tuwon shimkafa kayi yau idanunshi ya dan bude kadan "karki damu sweetheart yau bazan ci komai ba amman zuwa anjima I need coffee tasan haka tsarinsa yake wani lokaci sai ya kwana ya yini bai ba ." ***** Tsawon kwana Uku kenan rabon maryama ta shiga harka mahaifiyarta har ma da habibi hakan kuwa ba qaramin taga masu hankali yayi ba gabadaya gidan yayi wani iri saboda rashin walwalar maryama ,ta kuma san duk akan abinda take son tayi ne domin tasan halinta tasan abinda take so da abinda bata só tana da tsananin hakuri amman idan kaga ta kafe akan abu to dole abun zai zama gaskiya ne ko alkhairi ga rayuwar mutun ,ta sani gsky take fad'a mata amman bazata iya abinda take bukata ba bazata ta'ba komawa garesu ba duk runtsi duk wahala zata daure ta cigaba da rayuwarta a yadda take yi , maryama fa ta dauki zafi sosai akan aunty da habibi duk lokacin da ta fito parlour'n tagansu sai ta koma daki ko taje bangaren umma bata dawowa sai dare da zarar tashigo kuma zata shige daki tayi kwanciyarta ko ta dauko kayan zanenta ta fara aiki ." Da misalin karfe tara na daren ranar litini maryama tana zaune akan kujera ta cilla pencil a bakinta tana taunawa a hankali idanunta na kallon celling dakin tana nazarin abinda zata zana taji an turo kofar d'aki ahankali ta kai dubanta ga kallon kofar dakin ,aunty ta gani tsaye ,ta dauke kanta daga kallonta, aunty ta maida murfin kofar ta rufe ta soma takowa zuwa inda maryama take tana ganin haka ta mike tsam ta haye saman gado tayi kwanciyata tare da kamkame jikinta tana jin tausayin kansu na sake ratsa ko ina ajikinta musamman  take jin kewar yanuwan mahaifiyarta da bata taba daura kwayar idanunta akansu ba amman tana jin ajikinta zasu samu kulawarsu da soyayya a duk sanda suka had'u kamar kowani dangin uwa tana kallo aunty ta zauna daidai inda fuskarta take dan hk da sauri ta runtse idanunta tana son tayi bacci ." bacci bai samu nasarar d'aukarta ba ta juya dayan bangaren sakamakon kukan da Ke shirin kufce mata dan ita kanta dauriya kawai take akan sabon canjin data kawo a tsakaninsu hakan bai hana aunty ganin abinda take ba ,daidai inda  fuskarta ke kallo ta dawo ta zauna tana dubanta hade da kamo hannuta cikin nata "me nayi miki my princess kike qoqarin Kaurace min byn Kinsan bani da kowa bani komai sai ku ? Kafin maryama tayi yunkurin cewa wani abu aunty ta sake jiho mata wata tmbyr "yanzu na cancaci haka a wajenki ,"?"Na lura kina bukatar rayuwata princess "idan kika bari damuwarki ta kasheni shikenan sau ki huta ai .... " a d'an zabure maryama ta mike zaune daga kwance da take suna fuskatar juna da aunty yayinda hawayen idanunta suka shiga xubowa sharrrrrrrrr....."   " meye kuma abun kuka daga magana "kiyi hakuri aunty nasan damuwata na damunki ina kukan ne saboda an cuceki an rabaki da yanuwanki da iyayenki alhalin suna sonki , bansan yadda zan misalta miki yadda nakeji ba, aunty ki taba zuciyata kiji yadda take bugawa tayi mgnr tare da  kai hannuta ta kamo hannu aunty ta d'aura daidai saitin zuciyarta dake wani irin bugawa tamkar ana buga mata guduma, tabbas aunty taji kokawar da zuciyar keyi amman bata yadda zatayi gurin raba zuciyar da damuwa addua dai ce kuma tana kanyita babu dare babu rana kuma tasan  ubangijinta baxai barta haka ba batare daya duba lamarinta ba. cikin murya me cike rudanin rayuwa maryama ta cigaba da mgn "bansa me zanyi abubuwa su dawo mana daidai ba har ki cigaba da rayuwarki kamar da? " aunty ki daina daukar iyayenki da yanuwanki a matsayin makiyanki ,iyayenki suna sonki fiyye da tinaninki ,sun nuna miki so da kauna tattare da kulawa da gata alokacin da kike zaman lafiya dasu aunty kema kanki Kinsan irin soyayyarsu garenki "aunty !!! ki daina ganin laifinsu sannan ki dai jin zafinsu dan su dauki fushi dake ?" Su iyaye ne zasu iya yin komai suci lafiya a yanayin yadda rayuwa tazo miki cike da rudanin  yaci ace zuwa yanzu kin samu y'anci ki tsinci kanki cikin  farinciki da jin dad'in rayuwa kwana uku kawai da baki ga walwalata ba kin daga hankalinki inga bana cikin gidan nan ?"ina ga nabi wani na barki ya zakiji ? wallahi iyayenki suna can cikin tsananin kewarki kwatankwacin yadda kike jin namu da zaki koma garesu zasu karbeki su kuma yafe miki " kiyi hakuri aunty ki daina ganin laifinsu ta karasa fadar haka tana xubda wasu zafafan hawaye hade da rike hannun aunty gam tana me tausayawa rayuwarta ." "Idan abubuwan dake faruwa suka cigaba da faruwa bana tinanin zuciyar dake kirjina zata cigaba da baguwa ni dai ki koma cikin yanuwanki dan Allah ki roki gafarar iyayenki su yafe miki mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba . ahankali aunty tashiga bubbuga bayanta "kukan ya isa haka Inshaallahu zan .. zan.. koma garesu da izinin Allah sosai aunty ta dinga rarrashinta da gaya mata maganganu masu dadi da sanyaya rai har  ta soma bacci ajikita cike da samun kwanciyar hankali . Washegari kowa yasan maryama na cikin kwanciyar hankali wanda hakan ya kwantar da hankalin babib da aunty tare suka ci abinci kamar yadda suka saba ,maryama tana zaune a falo byn tayi wanka ta shirya tana kitsa gashinta gida hud'u sakina ta shigo suka sha hirarsu duk aunty na jinsu sosai taji dadi aranta ganin maryama ta saki ranta ,har sakina ta fita ta dawo "maryama amman yau zaki islamiyya?"eh!zani idan na gama zan biyo miki sakina ta qarasa fita ita kuma ta mike ta shiga daki tai sallah ta qara shiryawa ta dauki alqurani ta fito ta tsaya a bakin part dinsu sakina tana jiranta byn ta gaishe da aunty salma sakina ta fito ta tsaya kusa da maryama tana mata magana kasa kasa aunty salma ta bisu da harara har suka fice ,ta nemi guri ta zauna zuciyarta na tafasa ." ta rasa yadda zata kawo karshen shakuwar sakina da maryama duk duniya bata da abinda ta tsana tamkar maryama tayi shiru cikin tsanani tunani abubuwa da dama take sakawa in dai da rai da lafiya sai ta rabasu domin itace kadai hanyar da zata nunawa maryama tsangwama da tsanar datayi mata shegiyar yarinya kamar mayya ko aljanna zatace banda abun sakina ai maryama matsala ce arayuwarta, yanzu ko saurayi idan sakina tayi yayi ido biyu da maryama ai tuni zaice shi ga wacce yake so yarinyar ta cika kyau haka kamar ita tayi kanta ta fad'a acikin ranta ta mike tsaye cikin takaici to ko afa zata kaiwa kukanta , zuciyarta ta kawo mata dauki da wannan tunani aikuwa hakan shine mafuta afa shine zai kawo mata karshen komai da karshen wannan shakuwartasu mayafinta ta dauka ta yafa ta fice daga gidan tana surutai ita kadai kamar yadda na shiga na fita na rabaki da duk wanda yazo da sunan yana sonki da aure yanzu ma sai na rabaki da sakina takowani hali ki cigaba da rayuwarki Ke kadai Kmr mayya acikin gidan nan ." Tayi sallama aka amsa mata daga ciki dan haka ta shiga ta tsaya afa da yake ciki bai amsa ba yayi gyaran murya hakan ya tabbatar mata akwai wani aciki ta dan jira na rabin awa sannan wacce take ciki ta fito suka gaisa ta fice a karo na biyu tayi sallama ta shiga cikin dakin ta durkusa ta gaishe shi yana zaune akan daddumar sallah wani katon tray mai cike da katon kasa da wuri na duba ya amsa mata cike da kulawa "meye ma sunanki yaushe rabon na sakaki a idona ?"Aunty salma tayi murmushi tace afa kenan abine sai ahankali idan ka ganmu tamu ce ta kawo mu yayi murmushi ya dan shafa gemunshi yana lashe lebensa "to ina jinki fara bayanin abinda Ke tafe dake kafin na duba naga gskyar lamari ". Mmm sudais 💗💗💗💗💗💗      MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura wa wannan 0913691 8331  alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.         Page 15 "Aisha ,  saber, da   mahamud ,  ta  gani   tsaye  akansu  suna   huci   kamar   zakuna  cikin  matsanamcin  tashin  hankali   mara misaltuwa  suna   kallonta   kamar   zasu  cinyeta  ai  babu  shiri  daga  bilkisu  har  ussein   suka   mike   daga   jikin   juna  hankalinsu yayi  mugu  mugun   tashi   ."     bilkisu  ta  tsaya  tana  kalle  kallen   inda  zata  boye  acikin d'akin  tare  da  cure  hannayenta  waje   d'aya  jikinta  na sake d'aukar  rawa  bata  ta'ba   shiga  tashin  hankali  da  nadama  irin  na  ranar  ba domin  har  ga  Allah  bata  ta'ba  tunanin   zasu   bibiyi takunta  ba ." Nan da  nan  idanunta  ya   kawo ruwan  hawaye ba  tace  komai  ba, ta    durkusa qasa  bisa  gwiwo winta   dan  tasan  sai   na  lahira  ya  fita  jin  dadi  mahamud  ya  rike  kungunsa  yana  cigaba  da  kallonta  ,mamakinta  kawai   yake  dawainiya   dashi  idan  aka  fad'a   masa  cewar   zata  biyo  nmj   har  d'akinsa   bazai  ta'ba yarda  ba,  watakilla   ma  da  sai  ya  wankawa   wanda  ya  fad'a  masa  hakan   mari  "dan   girman  Allah  kuyi   hakuri   ku  yafe   min  ku rufa  min  asiri   kar  mumy   tasani  ta  karashe   mgnr   tana   kuka  cikin  tashin  hankali mahamud   ya  buga  mata  wata  razananniyar  tsawa  data  hargitsa  mata  lissafi "yi  min  shiru  makira  bana  son   jin  komai  daga  bakinki ." nan   take   tayi   shiru  kukanta ya  qaru ta   kalli  inda  ussein  yake  tsaye    shima   kana  kallonsa  kasan  baya  cikin natsuwarsa  "mahamud   tsayawa  kayi  kallonta  bazaka   fara cin  ubanta  tun  anan  ba ?  Aisha  ta  fad'a  tana  mata  wani   irin kallo  shi kuwa wanda aka kira  da  mahamud  tunanin yake  idan  yace  zai  ta'bata to  babu  shakka  zata  mutu  idan kuwa bata  mutu  ba  zata  jikata ." "dan  girman  allah  Aunty ai.."ai  bata  kai  ga  fad'ar  abinda  take  son fad'a  ba  taji  wani   gigitaccen mari   hagu  da dama akan  kuncinta "you  are  very  stupid   bilkisu  , akanki  aka  fara  soyayya?"  kin  haukace  kin  makance  akan  wannan  banzar  ,me  yasa zaki  mance  ko  ke  wacece ?  wato soyayya  tasa  kin  manta  matsayinki ? cikin  muryar  kuka tace " a'a   Aunty  aisha   ban   mance   ba  amman  kuyi  hakuri  wallahi  bazan   sake  ba  "hayaniyar  yan   yan'uwanta  ya sake   d'aga  mata  hankali   shi kuwa   ussein  sunkuyar  da  kanshi. kasa  yayi   yana  tunanin  ficewa ya  bar  d'akin  dan  yasan Allah ne kawai  zai   kwacesa  a  hannunsu ."   Kai   tsaye   bilkisu   ta  nufi   bayan kofa  ta   boye  jikinta  na  wani  irin rawa  sakamakon   jiyo  muryar hajiya  rahma  tana  cewa "ina bilkisu  take  naga kun  tsaya  jugun   jugun  ko  ta  gudu ne ?  kafin  kace  me  an  samu  wanda   yazo ya  fad'a  mana   halin   da'ake  ciki a guje  na  bazamo  na   bar  hajiya  dan   bazan  iya   jiranta   ba kasancewar  tana  fama da  lalurar  ciwon kafa ." " ina  tafiya  ina  neman layin  yan' uwansashi   da  kyar  na  samu ta  abban  sadam  yana  gama  jin bayanina  cewa  yayi  babu  ruwansa  dan  yasan  halinsa da tara  yammata , babu  yadda banyi dashi  ba yace  bai  zuwa  koina  ya kashe  wayarsa  jin abinda  ya fad'a yasa  na  kira  yayyensa   mata ." Ina   shiga   unguwar  naga   jamaa  sun   yi   cirko   cirko!!  ga   manya  manyan   motoci  na  gidansu  bilkisu  jere a  kofar  gidan ,haka  ina  shiga   cikin  gidan  mutane  na gani  makil   kowa  na   fadar  albarkaci   bakinsa ,yayinda  muryar   mahaifiyarta  ya  karad'e  koina   acikin   gidan   "da  gaske  ne  bilkisu   tana  cikin wannna  ru'babben  d'akin ? Aisha ta  nuna  mata   bayan   kofar d'akin  "tana  ciki   kuwa  ga  makira  nan a bayan  kofa   ta  fad'a  tana   zubar  da  hawayen  takaici  ." "inna  lillahi !  hjy  rahma ta furta  a fili  cikin  tsananin  tashin hankali "kunji   abinda  naji  kuwa  wallahi  ji  nayi   zuciyata  kamar ta  buga ?hankalin  bilkisu  ya bar duniyar da  muke  alokacin  dan  sai  wuri  wuri  da  idanu  take  shi  kansa  ussein kana  kallonsa  kasan  nadama  ne  acikin   ransa  nadama  irin  wacce bata  da  wani rana ." " amman  bilkisu  bakince  min kin rabu  dashi  ba  ?jikinta  na  rawa ta  shiga  gyada  mata kai  alamun Eh! tana   bawa mahaifiyarta  hakuri  da  wani  irin  fushi  ta  juya  inda  ussein  yake   cike  da  nadama ta shiga  zabzabga  masa  mari  ta koina "bana  ce maka  ka rabu  mun  da  yarinya ba  ? ba  banace karka  sake   shiga   rayuwarta  ba?"Ko kaga  yarinyata   tayi  kalar  wacce  zaka ce  kana so ? ta  juya  zuwa  ga  bilkisu  " Ke yanzu  har  wannan  qazamin  ne  abun  so  a wajenki  ? ta  fad'a tana sake   juyowa ta  d'aga hannu  zata  sake  tsinkawa  ussein  mari  nayi saurin   rike   mata  hannu  ina bata hakuri  "kiyi   hakuri  hjy sam  ussein  bai  kyauta  ba  daya  bawa  yarinyarki damar  zuwa  inda  yake  ,ya  karbi laifinsa  ayi  masa  afuwa   in sha allahu  hakan  bazai  sake   faruwa ba   Kinsan   kowa da irin jarabawarsa  dukkanin  rayuwa  rubutaccen   lamari ne daga  Allah ,kuma   kowani  dan  Adam yasan  da  haka  ,yanzu  tunda  abun  ya  zama  haka ku bamu  dama  sai  mu  turo ayi maganar  aure "." Wani  irin  kallo  gabadayansu suka  bini  dashi  ,hjy  rahma  tace  "Allah ya  tsareni  na   had'a  zuria da wannan  ta  nuna  ussein  da  yatsanta  tana  hararsa "wallahi   bilkisuna  tafi  karfen  aurensa  ki kalleta  sama da qasa  ki  kallesa ta  ina   hadin yayi daidai  ?  duk  nasan  da  haka  hjy  amman  a wajenta  shine daidai    bugu da qari   rayuwar  yarinyar ku  zaku duba  domin  ita  diya  mace ce zata  iya fad'awa  kowani hali ." "Ba kowani  hali  zata  fad'a ba ko  mutuwa  zatai  sai dai ta mutu na yarda  na   rasata   gbdy  akan na bawa wannan   matsiyacin aurenta ta  numfasa  tare  da sa  tafin hannunta ta  share hawayen idanunta  "hjy  ki  daina furta  haka  shi  soyayya   allah ne  yake had'awa  , kuma  babu  ruwan soyayya  da  tsiya ko arziki  yarinyar  nan tana  qaunarsa  shima kuma  yana  sonta dan  girman  allah  ki  barsu  suyi  aurensu  kowa ya huta  sannna  babu  wanda  yasan matsiyaci ko  mai arziki  sai Allah  sannan babu wanda  yasan mai gobe  zata  haifar  ku barsu  su  aure juna   domin   samun  kwanciyar hankali ." bata   kulani  ba  har  na  dasa aya ta fuskanci  bilkisu  yayinda  gabadaya  yanuwanta   kacokan  suka  maida  hankalinsu Kan  ussein  duk  sun qagu  suga hukunci  mahamud  akan  ussein kasancewarsa  soja ,  hjy  rahma  ta  matso  sosai  kusa da  bilkisu tana cewa  "ba  dai  ni  zaki  wulakanta   akan namiji  ba ? ."babu  irin  rarrashin da ban miki ba ,babu  irin  hakurin da ban baki ba ,me  kike  son  dani  ? "wallahi  zanyi  dake  bilkisu , yau  zaki ga tozarci  ganin  idanunki  tunda kika nemi ki  wulakantani akan wani banza  can  wanda  ba kowan kowa  bane  shi  ,ba kowa bane  iyayensa   a  duk  fadin  garin nan hasalima rayuwarsa  a  banza take ." "zaki  wulakantani  akan  wani nmj banza da  wofi  wallahi  zanyi  dake muddin  kika  ce  shi  zaki aura sai na  tsine  miki  na  tsinewa  auren ,wallahi auren  bazai  ta'ba  yin albarka tana  mgn  tana   zabga mata  mari a fuskarta da bayan hannunta  , yayinda  azaba tasa bilkisu ta shiga  karewa  dan kar marin yayi mata illa amman matar nan sai zabga mata maruka take kuma a fuska na rantse miki da girman allah maryama tayi mata mari yafi guda tara ajere ana goma ne bilkisu ta rike mata hannu kuma nasan azaba ce tasa tayi haka ,aiko matar nan ta  danneta da iyakacin karfinta ta dinga dukanta  tana cewa ni zaki rikewa hannu in sha allahu kema sai ya'yanki sun miki abinda kika min ,sai sun hanaki kwanciyar hankali kamar yadda kika hanani kwanciyar hankali a karshe  kafa mata hakori a  damtsen  hannunta." "wani irin  gigitaccen  qara  bilkisu ta saki mai ban  tausayi  tana  kuka  tana neman  d'auki  gashi  babu wanda ya  kwaceta  daga  hannun mahaifiyarta sai dukanta  take tana hadawa  da  zagi  ganin  haka yasa ussein  ya  nufi   hjy rahma cikin tsananin  fushi  kamar mayunwanci zaki  idanunshi  sun kad'a sunyi jajur   yasa  duka hannunsa zai d'agata  daga  Kan  bilkisu ai  ganin ya  ta'ba  mahaifiyarsu  gbdy yan'uwanta  suka yo Kanshi shi da  bilkisu  cike  da  jin haushi suka dinga dukan su  kamar zasu kashesu suna furta mahaifiyarmu zaka  duka ? azahiri gaskiya ba wai dukanta yayi  ba  kawai ceton bilkisu zai yi  daga dukanta, ina kuka ina basu  hakuri ina qoqarin kwatarsa daga hannunsu amman ina sarkin yawo yafi sarkin karfi dan sai suka daina dukan bilkisu suka cigaba da dukansa  shi kad'ai har sanda hjy  ta shigo zubewa tayi kasa tana kuka tana cewa "zaku kashemun d'a ne to wallahi idan kuka kasheshi hukuma ce zata rabamu  daku dan wallahil azim  bazan ta'ba  yarda ba ". "kar Allah yasa ki yarda daman kece uwar matsiyaci ?  "nice  uwarsa  kuma  gatansa kuma ni d'ana ba matsiyaci bane dan me zaku masa haka ? "ai yarku zaku jawa kunne ta daina zuwa inda yake shi meye laifinsa ? "laifinsa kulata da yake yi idan baya  kulata bazata zo inda yake ba ,idan yace baya sonta karta sake zuwa inda yake ni nasan bilkisu bazata zo inda yake  ba ki fad'a masa da babban murya ya rabu da kanwarmu  ya zauna lafiya idan ba haka ba zamu 'batar dashi agarin nan ,kina ji kina gani zaki rasa d'anki har abada  "hjy  na fad'a 'yanuwan bilkisu na maida mata martani kuma basu daina dukansa ba ." "neman layin 'yanuwasa mata na sake yi saadatu na d'auka na saka mata kuka ina cewa "bazaku zo ba sai an kashe maku da'nuwa ?dan girman allah kuzo ku hanzarta karku bari su illatashi "bilkisu cikin kuka ta rarrafa ta rike kafafun mahamud domin duk yafi dukan ussein cikin kuka tace "yaya dan girman allah kayi hakuri ka barshi karku kashe min rayuwata sannna karku rabani da dashi wallahi bashi da laifi nice mai laifi" . "ya salam! ya furta a matukar fusace "wai bilkisu me ke damunki ne  "?ta girgiza masa kai idanunta na zubar da ruwan hawaye  kuyi hakuri nayi maku alkwarin bazan sake zuwa inda yake ba "muryar hjy rahma ta sake karade d'akin Aisha riko hannun makaryaciya  karta gudu shi kuma sheidani ku fito min dashi yau zan nuna masa koni wacece agarin  nan zanga uban da ya isa ya kwaceka Aisha ta riko hannun bilkisu  gam bisa umarnin mahaifiyarsu sai dai bilkisu ta dinga turjewa nan ma wani marin aisha ta kai mata tuni daman fuskarta ta canza jini ya kwanta a duka idanunta ." Mahamud kuwa qarasawa  yayi inda ussein yake yace ya kama kunnensa ussein ya kama kunensa cikin kaduwa dan gbdy bai fahimci abinda yake nufi ba mahamud yace "you're very stupid I mean kayi frog jump Aishat ashe ma illiterate ne wallahi ko da wasa naji ka qara shiga harkar bilkisu zan mugun baka mamaki  "mugun ma illiterate katon jahili liability kawai a haka zamu bashi aurenta sai kace kwakwaluwarmu ta juye  ai har abada ,ka wuce dashi kaci ubansa ta yadda ko mai kama daita ya gani da mugun mugu zai arce ." bilkisu na kuka ussein na frog jump nima ina biye dasu ina basu hakuri haka hjy hakuri take basu hankalinta a tashe muna fitowa kofar gida sai ga saadatu da fatima a rude basu tsaya  neman baasi ba dan na rigada na fad'a masu komai  sausauci suke neman masa amman mutanen nan  suka ki banda cin mutunci babu abinda suke zubawa  unguwa kuwa ya cika makil da jama'a yan kallo kowa na fadin albakacin bakinsu wasu suna ganin daidai ne matakin da suka dauka dayawa kuma laifin bilkisu suke gani  ." wani abu mai daci yan'uwansa suka hadiye  tare da matsowa  inda mahamud yake yana laftawa ussein belt a gadon bayansa "yanzu ina zaku dashi ?In ji cewar fatima  tayi maganar cikin tsananin fushi "zamu tafi dashi inda zamu sake koya masa hankali,"  ya fad'a cike da gadara da isa "amman yana  da kyau mu san inda zaku da d'anuwanmu kafin ku wuce dashi?  Eh ! yana da kyau sai dai  bani da wannan lokacin  'batawa idan aka koya masa hankali zaa iya sanar  daku kuzo ku d'auki abinda ya saura ajikinsa " Hjy kuka saadatu kuka haka ma fatima muna cikin wannan halin sai ga gali yace shine yayansa suyi hakuri su bar komai a hannunsa zai sa ya rabu daita rabuwa ta har abada ,mahamud yace "da dai ya fiyye masa  kwanciyar hankali dan wallahi na sake dawowa akan case din nan sai dai ku dauki gawarsa" gali yace "to mun gode komai yazo karshe bilkisu ta bude idanunta da  suka mata nauyi  wani marayan kuka ta fashe dashi tana shesheka tana kallon kowa wanda ni nasan kukan da take alokacin bai wuce na rabuwa da ussein ba ." fatima ta watsa mata harara hade da kallon banza tana cewa  "kukan uwar me zakiyi wa mutane duk bake kika jawo masa matsala ba  yana zaman zamansa muguwa  azzaluma kin janyo yanuwanki sun wulakanta mana d'anuwan an tozarshi, tunda muke anan unguwar aka haifemu muka girma mukayi aure baa ta'ba wulakantamu ba sai yau kuma duk akanki ,kinsa ana dukansa kamar an samu ganga na rantse da girman allah  matukar ussein..." saurin toshe mata baki nayi ina cewa  fatima karki rantse  ,cikin fushi ta cire min hannu "ki barni  aunty nayi magana kalli yadda fuskarsa tayi duk jini saboda Allah yau ayita ta qare ta kama kanta ta daina zuwa inda yake ,yanzu da suka zo suna hargagin banza da wofi da wulakanci shi meye laifinsa? yarinyarsu ya dace suyi wa magana ta daina zuwa inda yake dan muddin ta sake zuwa inda yake kafin ku dauki mataki mu zamu dauka dan ba daga sama ya fado ba azzaluman banza kawai kuma allah ya isa tsakaninmu daku tana fad'a aisha na fad'a."dan girman allah fatima  karki sake cewa komai zo muyi magana na janyo hannunta " babu inda zani aunty ayita ta qare gwama su san muma bama son wannan diyar tasu kuma komai zai faru ..." na sake toshe mata baki "dan Allah ki bar mgnr nan  sulhu ake nema ." Cikin ko in kula hjy rahma tace  da wa zakuyi sulhu ?"kema  Kinsan ruwa ba sa,an kwado bane baku kai wannan matsayin ba yanzu ma wannan maganar da nake duk sai na fashesa akan wannan matsiyacin "nayi tsuru tsuru ina dubanta "tsayuwar  me kukeyi ku taho min  dashi da sauri  gali ya qaraso inda take hjy ai mun gama magana da yaronki, dan allah hjy kiyi hakuri ,in sha allahu tunda muka shiga cikin zance komai yazo karshe zanyi magana dashi  "babu irin hakurin da baa bawa hajiya rahma ba amman  tace sam sai an tafi dashi haka muna ji muna gani aka watsa useein abayan boot din mota aka wuce da ussein ." Kuka sosai maryama take kamar alokacin komai ya faru Kwantar da kanta umma tayi akan cinyarta tana rarrashinta "tabbas Aunty masoyiya ce ta gaskiya ,ta so mahaifinmu a halin babu ,ta zauna dashi har karshen rayuwarsa wallahi ba kowani d'an mai kudi bane mutumin kirki kamarta ,ta tsaya ta dubi mahaifinmu da kalmar so ta gaskiya sai dai akwai illa umma Aunty ta jefa rayuwarta cikin matsala wanda a yanzu take shan wahala ". " tabbas shine gskiyar dana dade ina nuna mata "baa jayayya da iyaye data yi hakuri tabi umarnin iyayenta tabbas zasu sauko dan kansu kasancewar akwai rabo a tsakaninta da mahaifinku ,cikin muryar kuka tace "mune silar jefa rayuwar mahaifiyarmu cikin wahala ko ? ta fad'a tana sheshekar kuka "karki ce haka maryama haka tata qaddarar take ,ita qaddara gata ko arziki ko nasaba bai isa ya canza maka ba ."umma ta numfasa sannan ta cigaba da magana ". Bangaren su  bilkisu kuwa tunda suka dauki hanya  yan'uwanta suke magana suna zagin ussein cikin kuka bilkisu Ke rikon su "ku sani ussein bai muku laifin komai ba dan allah karku hukuntashi akan abinda bai yi ba"  mari mahaifiyarta ta kifa mata haka ma aisha dan ubanki ki kama mana baki har suka kai gida zaginta suke direba na ajiyesu ya wuce da mahamud da ussein ." a matukar gigice bilkisu tabi byn  motar da kallo cikin tsananin firgici, keyarta suka tasa sai cikin bangaren hjy rahma ."Suna shiga part din hjy rahma suka turata daki  suka daureta da igiya tamau sukasa saber  ya dinga dukanta  adaure  tun tana ihu har tazo ta kasa a yadda ta fad'a min cewa tayi har da barkono  mahaifiyarta ta nika tasa mata a gabanta da cikin idanunta wanda yasa tayi suman wuncin gadi ." Bangaren mu rana  babu wanda ya samu sukuni  acikinmu gali yafi kowa  shiga damuwa safa da marwa yake yana cewa "ban  ta'ba kawowa araina duk hakurin dana  basu ba zasu hakura ba , na dauka maganata zai sa su hakura amman ina kamar sake fusata mahaifiyarta nayi wadan nan mutane sam basu da imani ."wallahi basu da imani gali inji cewar hjy ka kalli irin duka da sukayi yarinyar nan bilkisu ko rikonta suke bai dace suyi mata irin wannan dukan ba ." "wallahi ku sheida bilkisu bazata sha wannan wahalar a banza ba komai zai faru sai useein ya aureta ba dai bakinciki su kenan ba saboda suna takama da kudi ,ni bana da kudi amman ina da Allah alfarma annabi da alqurni sai wannan auren ya tabbata ko ina  raye ko byn na mutu mutane sam babu imani aransu bazai hakura da aurenta ba sai dai su mutu fatima zatayi magana ta dakatar daita "banason jin komai daga bakinku sai fatan wannan auren ya tabbata ." abban sadam ya fito daga bayi daman zagayawa yayi yace "har yanzu bazaku hakura da wannan maganar ba ? hjy tace "taya zaa hakura?" da sukutun fa suka wuce min dashi ?naga diyarsu ce tunda sunce basaso tarayyarsu a hakura mana "bazaa  hakura ba bilkisu bazata  sha wahala akan ussein ya tafi a banza ba ina sonta tunda tana son jinina ta gama min komai ni yanzu ta'bo min abokika Abdul zanyi magana dashi babu irin kiran da baayiwa Abdul  ba amman wayar bata shiga ranar hjy bata runtsa ba kwana tayi tana kaiwa allah kukanta ." Washegari ana idar da  sallahr asuba tasa aka cigaba da trying dinsa amman shiru baya shiga sai karfe uku na rana  ta shiga ya dauka da sallama byn sun gaisa hjy  tace "Abdul ko kasamu labarin abinda Ke faruwa da useein ?bansan me yake cewa hjy  ba amman naji tace "meye rashin kyautarwasa haramun ne dan  soyayya tashiga tsakaninsu ?saboda shi talaka ne yasa basu dace ba to shikenan nan in sha allahu gamu nan zuwa  ." Tana gama waya tace muje gidansu  bilkisu mu samu mahaifinta   nace" a'a ta bari ni da gali da fatima  muje da kyar hjy  ta yarda  ta barmu muje babu ita sai dai fatima tace bata zuwa koina nace saboda me kai tsaye tace min ta tsani bilkisu da yan gidansu sai da saadatu da gali mukaje da taimakon Abdul muka shiga estate dinsu sai dai  baa bari mun shiga cikin  gidansu  ba a bakin get din gidan aka tsaidamu yayanta  abubakar muka samu gani muka gaisa dashi  babu laifi fuskarsa da dan rahma dan yafi mahaifiyarsa byn mun gaisa gali ya fad'a masa ko mu su waye  da  dalilin zuwanmu "ayi hakuri ranka ya dade ,hakika danuwanmu bai kyauta  maku ba domin ya shiga hurumin da banashi ba soyayya da diya irin taku shima yasan  bai dace ba , dan allah kasa baki ranka ya dade abamu ussein tun jiya da suka  wuce dashi baa dawo dashi ba ,dan  allah a maido mana dashi ." shiru yayi ya kasa cewa komai ganin hk yasa gbdy muka kwantar da murya "ka taimaka kasa a sako mana ussein cikin ko in kula yace kuje zai dawo gida zuwa anjima amman kuja masa kunne ya fita a rayuwar bilkisu "in sha allahu komai yazo karshe cike da farinciki muka juya zuwa gida zaman jiran dawowar ussein ."bini bini sai mu leka waje ko zamu hangosa amman shiru har kusan karfe shadaya na dare har mun fidda rai dashi sai gashi an  shigo mana dashi bangaren hjy yana dingisa  kafa da kyar ." da sauri muka taresa  dan gbdy muna tare har hassana wacce tafi kowa shan kuka hjy kam  cikin yanayi na tashin hankali ta isa garesa tana  kuka "yanzu haka suka maka ussein ,kawai dan kana soyayya da diyarsu allah ya saka maka ,allah ya bi maka hakinka alfarma annabi muhammadu sai bilkisu ta zama mallakinka "wai meye hk hjy ana kokarin ya rabu da yarinyar mutane ya huta da wahala  amman kina sake dagula masa lisaafi . Gali ya fad'a yana kallon ussein "  kai ka rabu musu da yarinya idan ba haka ba wallahi komai ya sake faruwa babu ruwanmu  ,babu hannu babu kafarmu sai dai ka karata kai kadai dan bazamu iya wahala ba wadan nan mutanen marasa mutunci ne "wannan gsky ne  gali babu ruwanmu dan bazamu iya dasu ba inji cewar saadatu ,to ku yanzu laifinsa kuke gani bakwa ganin na yarinyar ?ai yarinyar tafi shi laifi domin ita Ke zuwa inda yake wallahi na tsani yarinyar nan ." "koni  wallahi na tsaneta maryama  wannan shima mafarin tsanar yanuwan mahaifinki ga mahaifiyarki alokacin ina kallon ussein wani irin numfashi mai zafi ya fesar kana ya samu waje ya zauna da kyar ya daura kanshi akan  hannun kujera ya kwantar tare da lumshe idanun shi  yana jin duk abinda kowa yake fad'a daya byn daya bayan wasu mintuna  ya kuma budewa  yana kallon kowa cikin sanyayyar murya yace "in sha allahu na rabu daita har abada dan  kwana ne kawai a gaba da na mutu "ka kwantar da hankalinka muddin ina raye baka da mata sai bilkisu ka daina cewa ka rabu daita dan na nasan kana sonta har yanzu ." "haba hjy wai me yasa kike fadar haka Kmr baki tausaya masa ? "yanzu ku yarinyar nan bata baku tausayi  ?ita ma ba laifinta bane soyayya ce da qaddara ke tangaliliya da rayuwarta dacen iyaye ne batayi ba shiyasa take shan wahala amman itama abar a tausaya mata ce "gsky mu dai bamu yarda ba kuma ta ina zasu bada aurenta byn kina kallon haukan da suke akanta ? kusa ido kuga ikon allah muna zaune zasu nemo mu da maganarta da izinin allah "babu wanda  yace uffan kowa ya mike ya kama gabansa ." **** Bayan wata  biyu da faruwar komai  mahaifiyarta ta shiga neman taimako akan  bilkisu dan kawai ta rabu da ussein , yau akarbo taimako daga wannan malamin gobe akarbo daga wancan malami , akwai inda aka kaita sai data  d'auki alqurni ta rantse  akan zata rabu da ussein , hankalinta  ya tashi matuka taki amsa  ta firgita kwarai da lamarin mahaifiyarta  ." fito da duka idanunta tayi tana furta tashi uku bataso ba amman mahaifiyarta na kallo mutumin yasa ta dauki alqurni tayi rantsuwa ta rabu da ussein har abada alhalin ita a zuciyarta ba haka bane " babu laifi  bilkisu ta  zauna lafiya kamar sauran  lokutan baya ta cigaba da rayuwarta gudun kar qurani ya cita ,yanuwanta suka dan sake mata kadan haka mahaifiyarta  tun tana gudun abinda zai je ya dawo har ta hakura ta sake janyota jikinta kullum da irin nasihar da take mata  "bilkisu ki  zama mutuniyar kirki ba wai baa sonki bane yasa kika ga anayi miki duk abinda aka  miki ana sonki ne yasa ake gudar miki wahala ,auren wannan yaron wahala zai zame miki arayuwarki , bakya ganin sauran yanuwanki ?kowa na cikin jin dadi me yasa sai ke kadai ce zaki zabar wa kanki wahala?  " tace "kiyi hakuri mumy ina tsananin son ussein amman zanyi  iya kokarin na cire sonshi araina "ko kunyi imole ne ?hjy rahma ta tmbyeta ."tayi shiru tana kallonta" baku ta'ba shan jinin juna ba ?ta girgiza mata kai  alamun a'a to ko ya ta'ba kwanciya dake ne ina nufin sex ?shiru tayi kawai ta kasa bata amsa tmbyrta "idan ya ta'ba kwanciya dake ne ki fad'a min nan ma shiru tayi kawai "karki manta Kiyi rantsuwa da alqurni akan zaki rabu dashi ta gyada mata kai "idan baki son mubarak naji na hakura amman ki kawo min wani banda wannan yaron dan banason shi  daga nan ta zarce da nasiha na kwantar da hankali  tana nuna mata rabuwa da ussein  shine alkhairi arayuwarta wanda alokacin mgnrta na shiga ta kunne na hagunta ne yana bin ta  dama ." wannan  sakewar yasa ta samu damar  turawa ussein sako da duk wayar data  shigo hannunta byn ta tura text  sai ta goge haka haka dai har ta shirya barin gidan da yammacin ranar laraba ta fice daga gidan babu wanda ya sani sai lalubo wa sukayi bata gidan" abun bakinciki tana zuwa gidan nan da hassana ta soma cin karo lokacin ta dawo gida aurenta ya mutu "Ke tsaya ta daka mata tsawa me ya kawoki gidan matsiyata ?tace dan Allah Kiyi hakuri nazo neman ussein ne "ussein din kanin ubanki ne da kikazo nemansa ? yanzu har kin manta irin azabar daaka gana masa akanki ?" "na sani amman Kiyi hakuri ta marairaice mata ta raba ta gefenta zata shigo tace "kina hauka ne ta kara buga mata tsawa wallahi kika shiga gidan nan da kaina zan fito dake na miki dukan mutuwa kuma bazan bari kiga ussein din ba har sai na danganaki da matsiyatan iyayenki masu kiran wasu matsiyata alhalin sune matsiyata , dan masu arziki basa yin abinda sukayi duk yadda akayi arzikin ma daga sama aka samu zaazo a ishe mutune "pata pata tayi mata batare da sanin hjy ba sannan ta korarta ." bangaren hjy rahma taji shiru shiru bilkisu bata fito ba ta nufi dakinta sai dai wayam tagani babu kowa ta duba bayi nan ma still the same nan da nan duk ta rude sai zufa take fitarwa nan fa ta soma kiran yaranta tana tsaye sai ga aisha da mijinta haka ma sajida cikin tashin hankali aka kira abubakar da mahamud har sulaiman har khadija  jugun jugun sukai kafin daga bisani suka fito zuwa nemanta har 12 :00 na dare ba labarinta babansu yace kowa ya tafi kawai makwancinsa har zuwa gobe aga abinda allah zai yi ." daga gidan nan bilkisu ta rasa inda zata domin dai tasan idan ta koma gida azaba zata sha duk yadda zata fad'a cewar bata hadu da ussein ba bazasu yarda ba dan haka ta wuce gidan kawarta farida daman su basa tare da mahaifiyarsu , mahaifinsu ne kuma bai cika zaman gida ba kasancewarsa  jamin tsaro in takaice miki kwana da kwanaki ana neman bilkisu baa ganta ba yayinda ussein yake gida abunsa idan kinga ya fita to zashi area ne kuma bini bini ya dawo gida  ". muna zaune aka zo nemanta basu ganta ba suka wuce intakaice miki kullum sai sun shigo unguwr nan sai dai basa ganinta sai dai su ganshi shi kadai  duk inda suka je nemanta  bataje ba duk ahalinta sun rude mazan kuwa sun bazu nemanta abu kamar wasa har sati baa ganta ba abubakar ya kai report police station duk hankalinsu ya tashi haka zalika ussein shima bai zauna ba duk inda yasan zataje yaje bai ganta ba kullum wayarsa tana hannunsa km a kunne koda zata nemesa duk ya rude ya rasa inda zai sa kansa ." kowa a gidansu bilkisu kuka yake daga bangaren yan dakinsu har sauran bangarorin dan kansu a hade yake kuma suna qaunar juna  ,duk sun rikice sun baza cigiyarta koina kafofin sadarwa amman babu wanda yace ya ganta dan haka suka sa akayi arresting din ussein a tunaninsu ya boyeta sati daya yana tsare ana gana masa azaba har a underground aka saka shi , ranar daya cika sati biyu akabari muka gansa ,koda aka zube magana sune basu da gsky amman kudi yasa aka bamu rashin gsky muka dauka muna bada hakuri akazo dashi unguwar nan sarka hannu da kafa Kmr wani barawo aka bincika gidanmu daki daki lungu lungu baa ganta ba haka dakunan abokansa da dakinsa duk inda aka san yana zuwa sai da akaje dashi amman baa ganta ba aka sake dawo dashi station dokoki aka kafa mana . daya daga cikin police tace tasan koina bilkisu take zata nemeshi dan haka da zarar ta kirasa ya tabbatar sun hadu ya kawota a haka aka bar maganar muka dawo gida wanda tsanar bilkisu ya sake girma a zukanta yan'uwansa hatta gali alokacin ya fadi maganganu marasa dadi akanta wanda shine har yau baya qaunrku da mahaifiyarku amman ita hjy tana sonta dan tayi kuka rashin ganinta da baayi ba ." Kullum hjy tana cikin zullumi da addauar allah ya bayyana bilkisu wallahi hjy tana matukar qaunar bilkisu sam bata ganin laifinta komai zaa fad'a akanta bata gani , cikin ikon allah sai gashi ta nemi useein  da number farida ya tmbyrta inda take ta fad'a masa bai bata lokaci ba ya nufi inda take yana isa sai da yayi mata mari masu kyau har biyu cikin tashin hankali yaja hannunta daga can gidan nan  ya zarceto daita muna zaune sai gashi  ya shigo daita ." hjy  duk tafi kowa jin dadi ta rungumeta ajikinta tana kuka mikewa tayi tace muje   police station Muna   fitowa  ta nemi limamin masalacin unguwar nan tai masa bayanin komai shima kuma ya fahimci akwai matsala duba da yawon zuwan da yanuwanta suke muna isa aka kira yan'uwanta  ai a haukace  suka shigo sabeer yayi kan ussein "kace bakasan inda take ba ?  sukayar da  kansa yayi dan rasa me zaice ."   liman da police suka  tsaidasu suna kwantar masu da hankali amman  suka kasa aiwatar da hakan suka rufeshi da duka hjy ta shiga tsakaninsu tana karesa tana kiran sai dai ku hada dani allah ya isa bata yafe ba ,ita kuwa bilkisu kuka take sosai tana fad'a masu bashi da laifi hasalima tunda ta bar gida bata hadu dashi ba sai yau  cikin fushi aisha tace "ya lalata miki ingantacciyar rayuwar da iyayenmu suka baki ya maidake yar yawo kororo "yayi miki ciki nasa aka cire miki amman duk  ba laifi bane ? "ko dan kinga an rufa miki asiri sai lokacin hjy rahma tasan da wannan maganar wanda hakan ya sake tunzurata da kyar dai da nasiha suka amshi diyarsu nasiha sosai liman yayi masu yace su jajurce da addua sannan  muka wuce da ussein ."        "ai ranar ashe ruwan zafin uwar ta tafasa ta kwarawa bilkisu a gabanta wanda yasa sai data suma a qalla sai da tayi kwana ta yini bata cikin haiyacinta sosai mahaifinta ya nuna bacin ransa akan abinda aka mata ,sai da tayi sati biyu tana jinya sannan ta dawo daidai   mahaifinta abun yafi karfinsa addua kawai yake allah yaye mata wannan masifa data daurawa kanta , amman uwar  izaya  da maseefa kawai tasa gaba ." "yadda ake mata azaba haka zuciyarta take sake tunzura , dan zuciyarta da idanunta sun bushe basa ji kuma basa gani ,ta manta matsayinta babu ruwanta da kowa acikin gidansu ko ince miki ta tsani kowa km har lokacin bata cire ussein aranta ba duk lokacin datayi raayin ganinsa kawai fitowa take taje su hadu ta koma gida randa dare yayi mata kuma ta kwana a wajensa shima dai mutane suna cewa baya jin mgn wanda ni nasan so ne da tausayin bilkisu ke hanashi juya mata baya ." Kwatsam sai ga bilkisu da wani cikin wata biyu cikin na uku ta fahimci ciki gareta alokacin shekararta shakwas cikin ta shatara hankalinsu ya tashi suka zo min da maganar ranar har da kuka nayi dan bakinciki nayi kuka kamar me cikin kuka tace zasu zubar nace a'a ta haifa sai ta bani tunda ni tun haihuwar sadam ban sake samun wani cikin ba shima sadam din da kyar na samesa kuka take tana cewa na taimaketa a zubar da cikin naki yarda ranar tana komawa gida akasa sabeer yayi mata dukan fitar da tayi wanda yayi sanadiyyar fitar cikin alokacin na bawa ussein shawarar ya tura neman aurenta, hakan ta kasance abban sadam da kanin hjy suka je sai akace masu makaranta zatayi ba yanzu zaa aurar daita ba suka dawo suka fadawa ussein ya sameni da mgnr nace kar ya hakura ya sake turawa haka dai byn wani lokaci suka sake zuwa sai mahaifinta yace zai yi mgn da yan'uwansa duk abinda ake ciki zasuji daya samesu suka ce basu yarda ba daman shima bawai yana son aurenta da ussein din bane ." Bayan sun koma akaro na uku ya turasu wajen yan'uwansa nan suka iske wani sabon tashin hankali domin cewa sukayi muddin yana son aurenta a wannan lokacin zai biya duk abinda aka kashe mata tun daga primary har secondary idan sun amince bisimillah ga list nan aka mika masu duk wani abu da suka kashe akanta jiki a sanyaye suka dawo suka miko min a tsorace na gama karantawa domin ko gidan nan da gidan bread muka saka a kasuwa bazai kai kudin da suka rubuta ba abban sadam ya numfasa yace "ki fadawa ussein ya hakura da yarinyar nan mutanen nan basu da mutunci km ko ya auri yarinyar nan wahala zai sha dan tafi karfin aurensa ni kaina na yarda da hakan kawai dai ayi auren ne dan kar suyita saduwa da juna suna ciki shima ussein koda ya samu labari yace ya hakura dan ina yaga million ashirin da biyar ."? Haka dai suka cigaba da rayuwa duk sanda ta fita idan ta koma sai anyi mata duka tare da zagin tana warin maz gbdy kamanita ya canza ta fita haiyacinta tayi firi firi ta zuke ta rame  babbar yayarsu a gabdaya gidan wacce uwar gidan rafi'u giwa ta haifa hjy rabi ta samu yanuwan babansu har ma da baban akan abar bilkisu hakan nan kar rabo yaje ya kashe mutane gabadaya yanuwan mahaifinsu suka ki yarda  kuka ta saka masu ta zayyane masu abubuwan da basu sani ba akan bilkisu da ussein tunda sukaji ussein har ciki ya ta'ba mata suka zubar da makamansu , suka ce tunda taji ta gani abarta ta auresa tunda basu zasu zauna mata  dashi ba  shi dai mahaifinta bai uffan ba ." tun daga wannan lokacin  da yan'uwanta da suke daki daya da mahaifiyarta suka ji hukuncin daaka yanke akan bilkisu suka shiga gana mata azaba iri iri batare da sanin kowa ba  aka dawo rikonta tamkar yar aikin gidansu yadda zakiga yan aikin gidansu na yawo haka ta dawo tana yawo babu shiga mai kyau babu komai amman hakan bai sa qaunar mahaifinku ta ragu acikin zuciyarta ba ." aka saka ranar sati biyu kacal ana sauran sati daurin aure hjy rahma da ya'yanta kaf suka saka bilkisu a tsakiyarsu "duk ranar datasa kafa ta bar gidan zuwa gidan ussein amatsayin matarsa tasan cewar ta fita kenan har abada karta dawo gidan garesu ta nemi wani gidan ,ta nemi wata uwar ta nemi wani uban ,ta nemi wasu yanuwan ,fasa auren daidai yake da bin umarninsu ,amman zuciyar bilkisu bata girgiza ba ta cigaba da shirin aurenta dan Allaha allah take ta bar gidan ta huta acikin satin muka kai dan abinda muka hada na lefe wanda kusan hjy ce tayi komai wallahi in takaice miki maryama wulakanci har da wankan ruwan sanyi akayi mana byn an watsa mana abinda muka mai ." Ranar  daurin aure babu mutun daya daya zo daga cikin ahlinta da wanda suke uwa daya uba daya da wadan da suke yan uba haka zalika mahaifinta bai je ba dan hjy rahma tace muddin yaje ita kuma zata bar masa gidansa kannen mahaifinta mutun uku ne suka je alhj saidu ,Alhaji umar ,Alhaji kaberu ana gama daurin aure aka nemesu aka rasa ,bayan an daura auren hjy rahma ta kira bilkisu ta tsinewa aure babu irin mummunar adduar da bayi ba, allah ya hadata da damuwa allah yasa ussein ya gallaza mata ya korota ,kar allah ya bata haihuwa dashi idan km ta haihu allah ya bata ya'yan da zasu dameta, idan basu dameta ba allah yasa suyi ta mutuwa a duk sanda ta haifesu , bilkisu tayita kuka tana jin Kmr ba hjy rahma bace ta haifeta dan lokacin da take fad'a min cewa tayi ita da uwarta har abada ta yafeta sai dai na fada mata baa yafe iyaye komai abinda suka aikata gareka." lokacin da zaa kawo  bilkisu gidan mahaifinku babu wanda ya rakota saboda ta auri talaka daga ita sai mahaifinku suka  baro gidansu zuwa rubabben dakinsa  inji cewar hjy rahma dan wulakancin da sukai mana yasa babu wanda je dauko amarya . babu abinda iyayenta sukai mata na kayan dakin kuma har yau yan'uwanta na jini babu wanda yasan inda  take sun dai san tana zaune acikin lagos din nan amman a ina take basu sani ba babu wanda ya ta'ba zuwa ." Kusan bakin hjy rahma yayi tasiri akan bilkisu dan sai datayi shekara uku tare da ussein batare da tasamu ciki ba har aka auro salma bata samu ciki ba ussein bai bawa mara d'a kunya ba dan sosai ya dawo da shaye shayensa lokacin data masa mgn akan alkwarin da yayi mata na dainawa yace" yaushe sukayi haka ?sai byn da salma ta haifi ali sannan kwatsam sai ga ciki bilkisu ta samu har lokacin da tayi haihuwar fari tace  abarta  a gidan mijinta  ni  nasan da wani mai arziki ta  aura ko bata je ba dole zaazo a dauketa  ,babu wanda yazo dan lokacin mahaifinku da kanshi yaje ya sheida masu ta haihu intakaice miki korar kare aka masa wai yazo rokon kudi shiyasa duk lokacin da mahaifinku ya bata mata  rai sai dai ni naji   mata haushi ita kuma  tayi kuka ta hakura dan bata san inda zata dosa ba mutane gidan nan gbdy sun daukenta  sha sha wai  ta tare a gindin miji to idan tace ma ta gaji ina zata ? yau da'ace tayi saar uwa da tun tuni ta koma gareta domin tana  neman taimakonta amman no way domin zamanta a gidan ussein  shine gatanta kinga ta rasa gatanta shiyasa a kullum take ganin bata  da gatan daya wuce ussein daku yayanta komai yayi mata  take hakuri wanda kusan hakan yake cikin dalilin da yasa salma da hassana suke cin kashi akanta ta sha wahala sosai acikin yanuwan ussein bayan an haifi habib rashin Lfy ya kama  hjy haka ta dauko hannun bilkisu tasa a tafin hannuna tace na rike mata amanar bilkisu kar na bari tayi kuka idan ussein yasata kuka na tabbatar na wanke mata zuciya sannan ta qara da cewa byn ta mutu bilkisu ta dawo bangarenta ta cigaba da rayuwa acikisa  nace ta tara yayanta ta fad'a agabansu hakan kuwa akayi abun bai masu dadi ba amman haka suka yi hakuri kwana uku tsakani  tace ga garinku ." Bilkisu tayi kuka kamar zata bita domin a gasky ita akayiwa mutuwa dan kusan nauyinta akan hjy yake itace komai nata bare Ke da kika ci sunan mahaifiyarta komai tasamu kece da bilkisu ne shekarar hajiya daya da rasuwa rashin lafiya ya kama mahaifinki  koda aka dubashi ciwon sigari ne ya kamashi har yayi masa illa bilkisu bata gujesa ba itace komai nashi  ,ita Ke kaisa asibiti gwanati ga ciwonsa na bukatar kudi amman babu ke babu irin wahalar da batayi ba har wankau tayi dan  ta rufawa kanta asiri cikin wannan halin rashin lafiya aka samu cikin habib har aka haifesa mahaifinku bashi da lafiya ranar da habib ya cika shekara daya a duniya  Allah ya dauki ran mahaifinku  ,yanzu shekaru ashirin da uku kenan rabonta da yan'uwanta da iyayenta kuma har zuwa wannan lokacin babu mutun daya daya nemi  inda take  to me  zai sa ku ku damu da   inda suke ? Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗      MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.         Page 19 A  matukar  zuciye  ya  sauke duka hannuwansa   yana  huci  sai dai har  lokacin  kwayar  idanunshi na kan  fuskar   baban   gali   yana masa  wani  irin  mugun  kallo  mai tattare  da  bakinciki  lokaci  d'aya kuma  yana  ta  qoqarin  danne  fushinsa  dan  baya  son  'bacin  ran  mahaifiyarsa  ." baba   gali  ya  sakar   masa  murmushin  mugunta  sannan  ya kalli   aunty  hassana  da  aunty  salma  "kuga  wannan  tantirin  mara   mutuncin  yaron    wai  ni   zai  kai  hannunsa   jikinata  saboda   nace  zasu   bar  gidan  nan  kamar  da   kudin  ubansa  ko  da  kudin  uwarsa   aka  gina  gidan  nan  da zai  wani   d'aga  hankalinsa dan  Allah   ku kalli   Irin  kallon  da  yake  min  nasan  yana   jin  kamar  ya  kasheni  ne ."ya  qarasa  maganar  yana  dariya ," Murmushin  jin  dadi  aunty  hassana  tayi  itama  "ai  kuwa  bai  isa  ya  kasheka  ba  sai   dai  ya   kashe  uwarsa  ko  yaje  ya  kashe   wad'an  can  marasa  mutuncin  dangin  uwarsa  ba  amman  mu  nan  munfi  karfin  d'an  kutumar  uba,  shegen  gora  mai  falla  fallan  kunnawa , an  nace  mana  an  zo  an  haifa   mana   irin  jaraba  kuma  wallahi  sai  Kun  bar  gidan  nan  matsawar  bazaku   daina   mana   rashin  mutunci  ba  ." cike  da   raunin   zuciya  habib  yace  "mahaukatan   banza   kawai  da  basu  san   ciwon  kansu  ba " "mu   kake   cewa  mahaukata ?eh !lallai   yaron   nan  wuyanka  ya  isa yanka  ,amman  ka  sani  bamu ne mahaukata  ba  ga  mahaukaciya  nan a  gabanka  kana   kallo wannan  wannan  itace  mental  itace  mahaukaciya da ka  kiramu  dashi  aunty   hassana  ta  fad'a  tana  nuna  gefen  kanta ." "Hassana !" ya  kira sunanta  a matukar  hassale Aunty   hassana   tayi  saurin  zaro  idanuwanta  waje  tana  duban d'anuwanta   cike  da  mamakin  habib "yes  abinda  kunnuwanki  suka  ji  na  fad'a  kenan   dan haka ki  ma  daina  mamaki  zan ma iya fad'ar  abinda  yafi  haka " mutun takin  me  zan  tsaya  yi tunda  kin  kasa  mutunta  kanki ?" ta  maida  hankalinta  da  idanunta  kanshi   sosai  tana  nazarin mgrsa sa  sai  daya   samawar  jikinsa   natsuwa sannan  ya  cigaba  da  zaro  magana  "Ki  kalli   aunty  tsab  ki  gani   Kinsan  dasu wa maganata  ta  dace ,ku  din  dai  kune  mahaukata  kuma  bazan  ta'ba   sauya  maganata ba."   Hawaye  ne  yake  zubowa  daga  idanun   aunty   gashi  magana take  son  yi  dan  ta  basu  hakuri  sannan  ta  tsawatarwa  habib amman  ta  qasa  bud'e  bakinta  bare  ta  sarrafa  harshenta a wannan  lokacin  ita  kanta  taga ya dace  ta  koma  cikin  'yanuwa  cikin  asalin ta  amman kuma idan ta tuna  irin  rayuwar  datayi  har ta kawo  wannan  matsayin  sai  taga komawar   nata  bashi  da  wata  amfani  me  zata  cewa  alhj rafi'u  giwa  da mahaifiyarta  wacce  tafi  kowa  d'aukar  zafi  akan  kowa  wacce  ta  gindaya  mata sharadin  cewar  ta  manta daita ta manta da  kowa  nata  tunda ta zabi auren  ussein  ?".   "gidan  nan  kowa  yasan  gidan  kakanmu  ne  wanda  ya  haifi mahaifinmu   yadda  kuke  taqamar  kuna  da  iko  akan   gidan  nan  haka  muma  ya'yan  ussein  muke da  iko  da   gidan  nan  matsawar  zamu  zauna  acikin   gidan   nan  dan  dole   mahaifiyarmu  ta zauna acikinsa   ." " Ke  ! hassana   da  kike  cewa a dole  mu  bar  gidan  nan  kisani  bamu ya  kamata  mu  bar  gidan nan  ba  ke  da  ya'yanki  yafi  dace wa  ku  bar  gidan nan  dan   da   gidan  miji  mace  take  taqama  ba da  gidan  uba ba  , aunty  a gidan  mijinta  take   zaune  Ke  fa  ? da  har  yanzu  Ke da  ya'yanki  baku  san  garin   ubansu  ba  bare  su  san  dangin  ubansu  ,ki  fara zuwa ki  kai  ya'yanki  su  san dangin  ubansu  tukun  kizo  ki  kori  wad'an  da  su  muhalinsu  suke  ." Cike  da  sanyin   jiki  maryama  ta  dinga  jan gwiwowinta  har  ta qarasa  gabansu  aunty  hassana jikinta  na  wani  irin  rawa   Kafin  tai  kai  ga yin mgn  taji  aunty  hassana  ta hau surfa  mata maseefa  "dan  ubanki  yau  dai  karki  kuskura ki bamu hakuri , shegiya  yarinyar  munafukar Allah taala kin wani  marairaice  fuska  kamar  ta  kirki  zaki bawa mutane  hakurin  gulma  wallahi   yau   shine  zamanku  na  karshe  acikin  gidan nan   sai  kun bar  mana  gidanmu  ,gara  ma  tunda  wuri   Ki  san yadda  zaki  d'auke wnn  uwar  taki  da wannan shegen  kannin naki mai falla  fallan kunnuwa Kmr na fir'una ku  bar  mana  gidanmu  mu  huta da jaraba  sanda  ussein  yana  raye  bai  barmu  mun huta ba sannan  bai  tsinana mana  komai  ba  sai  ruwan shaye shaye da d'auko  mana  magana  wanda sanadiyyar  haka  ya  kwaso  mana  wannan munafukar  uwar  taku  gashi  ya  mutu  ya  barmu da  mugun  iri ."    "Kuka  maryama  ta  fashe  dashi  hade da  sake durkusawa a wajen  batare da tasan abinda zata fada ba,  tana  mai   bakincikin  irin   kalar   rayuwar  da  mahaifinta  yayi a  sanda yake  raye, gashi ya  bar duniyar  amma  basu  huta  ba , wannan wace  irin rayuwa  ce ? me yasa wasu yanuwa suke yin haka ? "tasani da ubansu mai  arziki  ne da  duk abinda yayi babu mai tuna masu  bare  har a zagesu   dashi  ." tsaki   baba   gali  yaja  yana cewa  " Munafukar  banxa  sai  anyi  magana  kisa  mutane a gaba kina kuka,  da  ubannaku  bai shaye shaye  ba  zaa fada? daya  zauna da mutane lpy  zaa ki  fada ?kullum yana cikin d'auko  mana  magana  gashi ya mutu ya bar iri  an  iya  tujara iya tujara  sauran  shaye shaye .." "Allah  bazai sa  ba  ,baba  ka daina masa mugun fata "me ya saura yaro ya zama dan daba ai sauran shaye shaye, habib zai yi  magana   maryama  tayi saurin dakatar  dashi  tana cewa "walalhi karka sake cewa komai ai ga  irin abinda ka haifar ko ?"ni dai na fada maku  maza ku san ynd zaku  yi  ku bar mana  gidanmu tunda  gdn bana ubanku bane,"   maryama da  tarin  qunar  zuciya  da qunar  rai take zubar da hawaye  tafi  karfin minti  goma a durkushe  sai daga baya ta koma  inda  tabar aunty ta durkusa  kusa daita  hawaye na  zuba a idanunta Itama aunty  hawayene take zubarwa a  nata  idanun  tana  jin ciwon abinda  habib  yake  duk da tasan  gsky  yake  fad'a  masu  amman  bata só  yana  fadar duk  abinda yazo   bakinsu  dan  kome  zai faru bazasu  ta'ba  sonta ba  har   yau   tarasa  me  tayi   masu  mai  zafi  a duniya  da  suka  kasa  yafe  mata  sannan suka  kasa   danne  tsanarsu akanta  da  yaranta ." Habib  ya  kalli  aunty  ya  kalli  maryama  itama  duk   kuka  suke  maryama  kam har  da  shesheka  tana  rarrashin  aunty " ku  sani  ku  daina wulakantamu na  kyale  ,  kusani  nadamarku  ta  kusan  zuwa  a nan  kusa  kuma  munafurcinku  ya  kusan  qarewa domin  bazan   sake  yarda  da  iskancinku  dan   kuwa  kun  bari  d'an  zaki  ya  girma yayi  girman  da  zai  iya  kasheku  d'aya byn  d'aya  ,gidan  nan kuma babu mai  korarmu  acikinsa  sai dai a d'aga sa  d'ungurungun  dinsa  a sakashi  a  kasuwa  a  siyar a bawa kowa  hakinsa  kowa  ya  kama gabansa" "Ai  kuwa  baka  isa  ba  wannan  gidan  ubanmu  ne kai   har ubanka  ya  gama  iskancinsa  ya koma  ga  Allah  cima  kwance ne bai  da  gidan  da  zaka yi wannan taqamar  da   kake  yi  "kai  da ba cima  kwance  bane  sannan  bakayi    iskancin    ba  ina naka  gidan  daka  gida  yake  ? "sannan .." "habib  dan   girman    Allah  .." saurin  d'aga wa  maryama  hannu  yayi   ta hanyar  dakatar  daita " ki  barni  dasu  heartbeat  wallahi  kowa  sai  na  bashi  size dinsa   yau  idan sunce basu da mutunci   zan  nuna  masu   ni  d'an  zamani  ne , ya  d'an  tsaya yana  kallonsu  d'aya  byn  d'aya ,nan  take   ya   hango   tsananin  tsoronsa   da shakkarsa   acikin   kwayar   idanunsu "oya   kuna  iya   wucewa   ku  bar  mu  cigaba  da  rayuwarmu  ko  sai  na   fitar  daku d'aya  byn  d'aya?". A yadda  suke  kallonsa  sun  fahimci   zai  iya jansu ya  fitar  dasu  kmr  yadda  ya fad'a  dan  haka  aunty  hassana ta kalli aunty "sai  ki  daina kukan munafurci  tunda  burinki  ya  cika kin  haifa  mana  maseefa  amman in sha allahu  maseefar  akanki zai qare   tunda  ya  fara  zama  d'an daba    tana   gama   fadar  haka ta fice  daga   d'akin  tana zage zage  aunty  tayi saurin  runtse  idanunta  tana  jin  zafin  kalmar  data  danganta  mata  d'a  dashi , itama  aunty  salma  tace   "shegu  a  haka  zaku  qare  jiya  iya  yau  babu   cigaba ta  nufi    hanyar  fita " da sauri  habib  yace "Ke  ina  naki  cigaban  da  kika  samu yake  ? "Ke  da  ko  sallah  bakya  yi ,  qazama  mara  sallah  mai   dotti  kawai  kije ki  gyara  tsakaninki  da  ubangijinki  zai  fiyye  miki  sauki  akan  shiga  rayuwar wasu  ." shi  kam  baba  gali  cewa  yayi  "bilkisu  Ina  tarbiyar  taki ?yau a gaban  idanunki  d'anki  yake nuna min  iyakata "to  sai  me dan na nuna  maka  iyakarka  a gaban  idanunta ?  "kai  da  bakaji tsoron gaban  idanunmu kake  nuna rashin qaunar  mahaifiyarta ba   kiri kiri  kake  zaginta  agaban   idanunmu akwai  abinda  yafi  wannan ciwo ?  wallahi  idan bakasani ba kasani  yanzu  abinda  kukayi  mata a da  tayi hakuri  ta shanye yanzu  ta  haifi d'an da zai kwatar mata  'yanci  zan goge wannan tarihin  idan  ka  cigaba da tsayuwa zafin jinina  zai iya sa na d'auki takobin  can na file  maka kai  dashi ko na  raba  katon kan nan  naka   gida  hud'u  idan yaso  nima  akasheni  salin alin baba  gali ya fice batare da  ya sake  cewa   uffan ba." Yana  fita habib  ya  qaraso inda  aunty da  maryama  suke  durkushe  suna kuka "cike da  girmamawa yace "ku daina kuka  in sha allahu ku daina kuka acikin gidan nan  , kun  daina  damuwa matsawar  ina  raye  zan tsaya maku , zan  kula daku da zarar na gama  karatu  zan ...."bana  son jin komai  daga  bakinka  habib na   fahimci  kana  bukatar  na bar muku  gidan  nan  shiyasa ka kirkiro  abinda za'a koreni daga cikinsa  tana gama fad'ar haka bata  tsaya  jin  abinda  zai  ce ba ta  mike  ta  shiga  d'akinta  ta d'auko  mayafinta  kawai  ta fito zata  fice  ta  bar masu gidan ." Atare  maryamah  da  habib  suka sha  gabanta  cikin  tsananin tashin hankali  "haba  aunty  ya  zaki mana  haka  ?kiyi  hakuri  aunty hakika  habib  bai  kyauta ba amman  karki  tafi  ki  barmu ."maryama  dan'uwanki   baya  bukatata  acikin  gidan nan  yana bukatar  na  tafi  na bar  masa filin gidan  nan  ya cigaba da rayuwa  ta qarasa maganar  tana  zubar da hawaye  ta  tabi  gefen maryama zata raba  ta  wuce  ." habib  ya  riko  mata hannu "kiyi hakuri  aunty  ki fad'a min abinda kike  bukata nayi miki  alkwarin  wallahi  zanyi  kisani  idan  kika bar gidan  nan  bashi  da  wani amfani a  wajenmu "yana da amfani mana tunda gashi  kayi  son  ranka  kasa an zageni  anci  mutuncina  anci na iyayena  ai gara na kama  gabana  tunda zamana acikinsa  babu abinda yake haifa min  sai  damuwa da bacin rai ". Kuka ya  kufce  ma  maryama  ta  d'an  rufe  fuskarta da  tafukan  hannuwanta  saboda  tuttukin  da zuciyarta  Ke yi "kai  ma  kasan  abinda  kayi  ba daidai   bane  har  ka  iya  cire  hannu  zaka  doki baba  gali   wallahi  baka  kyauta  ba   tunda  kasan halinsu  to  meye  amfani  tsayawa  kana  fad'a yana fad'a "ki  fahimci wani  abu  heartbeat  wad'an nan mutane basa  qaunarmu  ,babu  abinda Ke cikin zukatansu sai tsanar mu " tunda mun san halinsu sai mu  kiyaye  abinda  zai  kawo  sa'bani  dasu  shima kukan   yake yi  "suna  nuna  mana  bambamci akan ya'yansu  ,suna  quntata  mana  suna  da  fuskar  gazawa  garemu  musaman   akan ya'yansu  yanzu laifin  me kikayi ma aunty salma ta shigo tana zaginki ?"maryama  bata  sake  cewa komai ba illa ta cigaba da kukanta haka ma aunty batayi magana ba illa qoqarin zare hannunta da take cikin nashi ." "na  tuba  aunty  bazan sake ba ki fad'a min abinda kike so ,nayi miki alkwarin  bazan  sake  ba ya fad'a yana zubar da hawaye itama ta goge hawayen dake zuba  akan  kuncinta  ta cigaba da mgn "daga yau babu ruwanka da  kowa acikin gidan nan  duk abinda  zasuyi  ko  zasu fad'a akanmu ka kawo ido kasa masu , kai ba zagi  ko dukana zasuyi  babu ruwanka a rashin yace ba dai duka ba amman a zahiri yace "to aunty an gama ."wallahi  abinda kayi yau din nan ba irin tarbiyar daaka  bamu  bace "in sha  allahu  bazan  sake ba heartbeat  ki bata hakuri  bazan sake ba  kamo  hannun aunty maryama  tayi suka koma kan kujera mai  zaman  mutun uku da duk  ashon jiki ya  batattake suka zaunar  daita  tare  da sakata a tsakiyarsu  suna bata hakuri ." Kamar  yadda  mlm  yahuza  ya sanarwa  nafisa  byn sallahr ishai zai  zo  sai ga  yaro yana sallama  da maryama  lokacin  suna zaune a falon aunty  ta dubeta amman ita ko  ajikinta sakon da yaro ya fad'a aunty tace "maryama bakiji  bane ?ta  d'an  dubeta ta share yaron ya tsaya yana jiran abinda zaace   "to sai  ki  tashi kije "ina kenan aunty?"bakaji ana sallama daita bane "gsky   babu  inda zata ban san dalilin da yasa da mutun yazo nemanta ba  sai ki bata damar fita baki  san ko waye ba mazan da duk 'yan  iska ne da zarar sun fara zuwa kamar abun arziki da zance aure ya shigo sai su gudu su barta  ni  gsky babu wanda zai sake zuwa ta fita ." "Maryama  tashi  Kiyi  maza  kije ki dawo  saboda ki samu ki d'an huta   karki  dade  duk da nasan ba  dad'ewar zakiyi ba ,ina dalili da zakace  bazata  ba kai zaka aureta ?ya  marairaice  murya "bani  zan  aureta  ba  amman  at least  aunty  ki duba  lamarin  nan kawai  suzo  suna  'bata  mata  lokaci  da  dagula  mata  lissafi "Babu  wani  dagula  lissafi a haka  allah  zai  kawo  mata  wanda  zai  aureta  ,ina  son  kasan  wani  abu  habib   duk   cikin  masu  zuwa neman   auren  maryama  babu mijinta  acikinsu , duk  lokacin da mijin  yazo  to  babu  makawa  sai  anyi   domin  babu  mai  aurenta  matar  wani  kai  yaro  je  kace gata nan  zuwa  yaron  ya  juya  da sauri dan  daman  amsar da yake jira kenan  zata  fito  ko  kuwa  bazata fito ba  ." maryama  ta  tashi  ta  shiga  d'aki dan  tasan  ko  waye  yazo  ta d'auki  hijab  dinta  ta  fito "amman dai  ni  aunty  a wajena  ba  daidai bane  ,ni  fa  kamar  mahaifinta ne a matsayina na  namiji  acikin  gidan  nan  amman  me yasa  sai a dinga  nuna  min  iyakata  acikin gidan  nan  , na  fiku  sanin halin mazan  wannan  zamani  babu komai  acikinsu  sai  tsabar  yaudara ". Aunty  ta  kallesa  saboda yadda yake  maganar  tamkar  wani babban  mutun  tace "wai  har guda  nawa  kake  habib  ?" duka shabakwai  gare  fa  kawai dan allah  ya  baka  jikin  girma "ni dai gsky  ban  yarda  ta  fita  koina ba  girgiza kai aunty  tayi  tana kallon  yadda yake kamaninsa yake canzawa  a  kullum  yana  komawa na  mahaifinsa  tun ba yau ba kusan  kowa  yana  fad'in  kamanin nasu  "gaskiya  habib  kar  ka  zama  mai   hana   neman   auren ." tsayawa   maryama  tayi   tana kallon  fuskar  habib  daya had'eta tmkr  ance  masa  idan  ta  fita guduwa  zaa  yi  daita ,ahankali ta kira  sunansa  "after dad " "Karki  wani   kirani  da  wannan sunan  dan  dani  din  ina  da wannan  matsayin  da  za'a  dinga bin  umarnina " ta  qaraso ta zauna kusa  dashi  ta  riko  tafin  hannunsa  cikin  nata  tana kallonsa  da  idanuwanta  da  suka canza  kalla "after  dad me kake so dani ?"ta fad'a tana kallon yadda shima  ya  zuba  mata  ido  yana kallonta ." "Abinda  nake  so  duk  wanda  yazo karki  qara  fita  koina idan abinda  ake  miki  acikin  gidan  nan  baya  damunki  ni  yana damuna  ,sau  nawa  kina yi  saurayi  agidan  nan a karshe  ko ya  gudu  ko a kwace  miki shi acikin  gidan  nan ?to  ai  duk ba mijinta acikinsu  ne ,no no aunty akwai cutarwa aciki "to   nufinka  yanzu  haka  zata  zauna  babu   mai  zuwa wajenta ?"allah  aunty dasu  dinga 'bata  mata  lokaci  gara  ta  zauna haka  idan  na  girma  na  qare karatuna  zan  mata  komai zan siya  miki  gida  da  mota  itama heartbeat  zan  siya  mata  zan kai ku  aikin  haji  ,kai  har  sojoji  zan daukar  maku  escort  duk  inda zaku  su  dinga  rakaku  aunty da maryama  basu  san  sanda murmushin  jin  dadi  ya  bayyana akan  fuskarsu  ba "shikenan  after dad  bazanje  koina  ba  domin kai  din tmkr  uba  ne  a gareni "yauwa  heartbeat  sai  yanzu  naji hankalina  ya  kwanta muyi  zamanmu ." aunty  ta  kallesu  ta  girgiza  kai "wallahi  wannan ba rayuwa bace kin  wani  zauna  ya  tasaki  gaba  yana  miki  zakin  baki  ,wallahi ki daina  biye  masa  Ke  macece dole  kina  bukatar  Kiyi  aure shifa nan  gaba  kad'an  zai  ce  zai  yi aurensa  dan  wannan  da  son girman  tsiya  nasan .."no no aunty karki  hadamu da  heartbeat  babu wani  aure  da  zanyi  na  barta  idan  dole  sai  tayi  aure  ni  zan kawo  mata  miji  wanda  zai  dinga kwantar  mata  da  hankali  duk ranar da  yayi  gangancin ' bata mata  rai  na  zage  naci  ubansa ". "Lah  lah  lallai  habib  abun  naka babba  ne  "allah  aunty  sai ma ya cika  qaidodina  sannnan "wannan  ai  gara kuje  kuyi  auren  kotu  ku  huta maryama  tai  murmushi  tana jin dadin  yadda  dan'uwanta  ke tsananin   qaunarta  "babu kotun da  zamu amman dole a kular min  da  heartbeat ko kuwa a tashi mutun aiki "uhm  kaga   tashina  ta  mike  tsaye  "  bari  naje na bawa  baba  gali da hassana  hakuri na dawo ." "haba  aunty  ai  komai  ya  rigada ya wuce  wani  hakuri  kuma  zaki basu   salon  su  samu  damar ci miki  mutunci  "? A'a  sai  naje  zaman  lafiya  yafi  zaman dan sarki  ina  zan  iya  dasu  gara dai naje ."Yauwa  aunty  kije  ki basu hakuri  wannan  ai ba komai bane wata  rana  sai  labari  kai ma ya kamata  ka bita  kabasu hakuri wani  irin kallo ya watsa mata  yana cewa "allah  kiyaye ai ni .."sai  kuma  yayi  shiru  sakamakon tuna alkwarin  da  yayiwa  mahaifiyarsu ." "ai  babu  abinda  zai  sa  naje da habib  sai ya  qara  dagula  lissafi sunan wani police a isokoko ni na wuce sai  na   dawo "to  aunty sai  kin  dawo  tasa kai ta fice daga dakin  ta barsu suka cigaba da hirarsu mai  cike  da  kulawa da soyayya shi kam mlm yahuza tsawon mintuna nan duk yana tsaye  yana jira   Fitowar maryama ya  duba  agogon  dake  daure da  taintsiyar  hannunsa  yaga lokaci  ya  tafi  daman  kuma  yaron daya  aika  ya  sheida  masa komai  dan haka a natse ya juya sai dai ya kudurce aransa  zai  dawo  gobe." Ahankali  aunty  take  tafiya  tana tunane tunane abinda zatace idan ta isa gaban baba gali a natse tayi sallama  cikin  bangaren  nasu  basu amsa  mata sallamar ta  ba  dan haka  taji  gabanta ya shiga faduwa  kafin ta kai ga yin wata  magana taji aunty salma ta hau surfa mata maseefa  kamar kullum "me ya  kawo  bangarenmu  "ba komai bane  hakuri nazo baku akan  abinda  habib  yayi ,ya gama ci mana mutunci a gabanki shine  dan  munafurci  kika kwaso  jiki   bayarwa  , shegiyar  munafuka kin wani marairaice  fuska    bayan kin gama zuga d'anki yayi mata walima ta uwa da uba zaki wani kwaso jiki to yanzu hakurin  me kika zo bamu  ?". Numfashi aunty ta sauke ta samu waje ta zauna kusa da baba gali da ko kallon inda take bai yi ba a tun sanda ta shigo "kuyi hakuri gabadayanku in sha allahu nayi maku alkawarin wannan shine karo na farko da karshe da hakan zai faru ...."dakata  bana son jin komai daga  bakinki  dan duk abinda zai fito daga cikinsa karya ne ni dai abinda nake buqata "ki dauki yayanki ku bar mana gidanmu tunda ussein yake raye bai tsina mana komai ba sai tujara gashi nan ya barwa dansa tsaraba har kamar ni wannan yaron zai dinga gasawa magana kuma a gabanki kina kallo  yaron da ya kamata kiyita dukansa har sai kin kusan auna shi lahira amman kika zauna dan tsabar son ya'ya kina kallonsa yana surfa mana zagi ta uwa da uba  ai wallahi bazai yuwu ba ." Sake durkushewa tayi Kmr zatayi kuka batare da tasan abinda zata sake fad'a ba sai dai ita kanta a halin yanzu tana mai bakincikin hada  zuria dasu tsaki aunty salma  taja tana cewa "munafukar banza  munafukar wofi sai anyi magana ki wani  durkushewa mutane  "ni dai ba wani tashin hankali nazo dominsa ba nazo ne dan na baku hakuri dan nasan danku bai kyauta ba "ni wannan yaron ba d'a bane domin kuwa d'ana bazai min haka ba hakuri aunty  tayita basu da kyar baba gali yace komai ya wuce amman tajawa habib kunne aunty salma dai ce taki  hakura   ta mike tana masu sallama "sai da safenku allah kuma ya huci zuciyarku babu wanda ya kulata acikinsu har ta fice zaginta aunty salma take cikin tsananin tsana  ." Daga bangaren baba gali na aunty hassana ta shiga itama dai  tujara  tayi  mata  ta uwa da uba kaf danginta  babu  wanda ta  bari  bare iyayenta zuciyarta  tayi  nauyi  kamar an d'aura mata dotse da kyar ta yunkura ta mike ta fito tana tafiya zuciyarta na  kokawa. a inda aunty ta fita ta bar yaranta anan ta dawo ta samesu zaune  suna  hira "har  kin  dawo  aunty  ?suka  had'a baki murmushi  tayi  tare da d'aga  mata kai  alamar" eh! my princess na dawo ". "Yaya  kuka  qare fatan sun hakura "Eh to  sun hakura my  princess!ta fad'a zuciyarta cike da raunin kuka dan shi take bukatar yi a halin da take ciki  shi kam habib bai ce uffan  ba  illa  ya  cigaba  da  sauraronsu"my princess Kinga dare yayi  bamu  samu  girka komai  a gidan nan  ba ni yanzu ban san me zamu dan girka muci  ba "wallahi  aunty amman bari naje wajen Ummah watakilla bazamu rasa abinda zamu ci ba maryama  ta fad'a  idanun  habib  yana  kanta "ko  zaka   raka ni ne? ta  fad'a tare da miqewa..."Muje ! kawai abinda ya fad'a kenan maryama tayi murmushi "makalema kawai  "kima  ce  bita zai zai  ki  huta  gbdy muje  suka jera ." Suna  fita suka had'u da yaya sadam  ya  fito  daga side d'in  din baba gali zai shiga side din ummah cike da farinciki habib ya qarasa suka gaisa! "A she rabon mu had'u ne yaya yasa heartbeat tace nayi mata rakiya ."ai ko baka fito ba  yanzu  nake  shirin  zuwa  tambayarka a wajen  aunty !Ya mika masa hannu ya kwana biyu  ina  fata dai komai  lafiya? "Lafiya  lau  habib  kawae aiki ne ya  boye  ni 2days ya karatu ?yace "alhamdulillah.!" maryama ta bude baki da kyar ta gaishesa ya amsa mata cike da sakin fuska "Lafiya  su aunty maryam"ji tayi kunya ya kamata da kirata aunty da yayi ! Ya gida da karatu ?Alhmdllh! ta fad'a  cikin jin kunya"kema dazu   nake tambayarki  wajen Ummah take bani labari mai dadi lallai kin fita zakka acikin matan gidan  nan kin tsaya kinyi karatunki yadda ya kamata allah yasa muji sakamakon mai kyau you're  the  best  maryama  duk nmj daya sameki a matsayin mata baqaramin dacewa yayi  ba Allah yasa sawa karatu albarka dad'i maryama  taji sosai  dan duk cikin yanuwanta sadam ne kawai sai habib Ke mata fatan alkhairi idan wani abun farinciki ya sameta tace "na gode  sosai yaya ." Habib yace "a she dai yaya  ka  gane  shiyasa sai  na zaba mata na durje mata  miji  dan ita din ba kalar kowani nmj bace "kaga yaya karka kulashi  mu je ciki  mu  qara gaisawa "wucewa sadam yayi side d'in Ummah  maryama da  habib  na biye da shi sunata hiran duniya..." Zama sukayi a parlour'n  sadam ya fara kiran  "Ummah  Kina ciki ne? Eh! Ganin nan  zuwa dan albarka har ka dawo ne? sadam yace" eh ! gashi na  kawo  miki maryamarki "ban gane ka kawo min maryama ba maryama da muke yini tare dan gulma zakace ka kawo min ita Bari dai nazo ganin nan fitowa ." Bata  wani bata  lokaci ba ta fito cikin  doguwar riga  qaton  tray ta aje  a gaban sadam  na fruits bismillah  sannu da zuwa yau har da habib  to duk sannuku "Ina yini "Habib  yace " lafiya lau  habib Ummah ta kalli sadam ta kalli maryama  sai taga sun maseefar dacewa ina ma su kasance maaurata suna hirarsu gwanin ban shaaawa  habib ya fahimci  maryama kunyar sadam take ji sosai dan taki fad'ar abinda ya kawo su gashi shi yunwa yake ji ." Maryama  tace after dad  ya kamata mu wuce dare nayi  "a'a  har  zaku  tafi kenan maryama  to ai  bakuci  komai  ba "karki damu Ummah  "ban  gane  karta  damu  ba kinga nifa banason kunyar nan  take wai ma wa Kike jin kunya anan  umma  ko  yaya  sadam ,?maryama tayi shiru tana mai sunkuyar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta "kinga  Ummah  nan ya fad'a  mata abinda ya kawosu "kai maryama  amman shine zaki jashi ku wuce to  kuci me idan kun wuce?  allah ya kyauta wannan kunyar taki  kaga habib bari nazo ta fad'a tana mikewa tsaye ta nufi kitchen ". Bata wani bata lokaci ba ta dawo hannunta d'auke da wani madaidaicin kula cike da abinci sannan da wata leda cike da su cincin  wanda tayiwa sadam ta miqa ma maryama tace gashi  kai km habib ka  rike kula " mungode Ummah !Suka fito maryama nayi masa mitar abinda  yayi  dariya kawai  yayi yana cewa "ina ganin gara  kawai  ayi yar gida mu huta da samari masu  mana patrol  "kai dai kasani  ni nasani ko gaskiya suna tafiya suna jan juna har suka qaraso falonsu  habib ya zauna yana kiran "washhhh allah maryama ta cire hijab dinta ta ajiye  akan kujera  tace "habib bari na kira aunty  kanshi kawai ya gyada mata ." Ahankali ta shiga d'akin sai dai abinda yayi matukar daga mata hankali shine ganin mahaifiyarta kwance rigingine akan katifa hannunta rike da wani hoto tana kallon hoton hawaye na zuba daga idanunta  tana tuna irin rayuwar dadin da tayi ada kafin shigowar ussein rayuwarta ,bata haskowa kanta irin rayuwar da take ba sai data hadu da ussein soyayyarta ta gurba tunaninta ." yayinda maryama ke kallon mahaifiyarta da ita kadai ta rage mata a duniya yanzu a natse ta qara taku biyu domin son ganin hoton waye a hannunta take kallo tana kuka  wasu mutane tagani guda biyu cikin shiga na alfarma suna cikin koshin lafiya da farinciki ko baa fada mata ba tasan hoton iyayenta take kallo cike da nadama lumshe idanunta tayi "iyaye ba abun wasa bane , aunty iyaye suna da kimar da darajan da  bazaa iya mantasu ba ." ahankali taji sautin muryarta tana fita  cikin kuka "nayi  kewarka baba , nayi kewarki mamana yanzu ku har yanzu  bakuyi kewata ba ?yanzu ku baku yafe min ba ko nemeni ba? wallahi ina sonku nayi kewarku ,nayi  kewar  kowa da kowa  ta fad'a tana mai daura hoto a saman  qirjinta tana shafawa tana kuka.." Ahankali maryama ta juya tana zubar da hawaye masu zafi ta koma falo ta zauna kusa da habib tana sheshekan kuka nan take ya birkice ya soma tambayarta "heartbeat me kuma ya fara ?kukan me kike yi ? Ina aunty ?yayi mata tmbyr ajere cikin tsananin tashin hankali tasa gefen rigarta ta goge hawayen "yau aunty ta tuna da iyayenta tana daki tana kallon hotonsu tana kuka ni nasan zuciyarta na cike da qaunarsu shiyasa kaga ina son ta koma garesu ." "habib  soyayyar  iyaye  da  yanuwa  baa  wasa  dasu wallahi a tsakaninsu soyayya ce mai karfi ka misalta hakan akanmu musan da qaddara  amman an cuci aunty an yi sanadiyyar rabata da kowa nata ,ta bar iyayenta akan soyayya gashi ta rasa soyayya taki bin umarnin iyayenta gashi duniyar taki mata dadi maryama tana kuka habib na rarrashinta har kukan nata ya ragu adaidai lokacin da sukaji tahowar aunty tayi saurin share hawayenta tana cewa ". karka nuna mata komai da sanyi jiki ta qaraso "kun samo abinda zaku dan ci ?eh mun samu har da cinci tô maza kuci ku kwanta tayi maganr cike da rauni aunty kizo muci tare "aa ku dai kuci ku koshi aa wallahi tare zamu ci habib ya mike ya kamo hannunta ya zaunar daita ya bude kula abinci yana cewa kai abincin nan zai yi dadi maryama ta dauko spoon ta dibi abinci zata kai bakin aunty habib yayi sauri ya kwace spoon "bani ni zan bata da kaina suka sa da dariya ya soma bata abinci abaki yana fada mata kalamai masu sanyi ." "idan nayi kudi bazan yi nesa dake ba zan kasance tare dake ,dan allah aunty ki daina damuwa akan komai kinji ki dinga tunawa cewa kina damu mu din zamu zame miki farinciki a rayuwarki Wallahi sai mun sa kinyi alfahari damu ki cigaba da addau ga heartbeat nan kwanan nan zata fara bautar qasa yanzu ma ina mata  processing yadda zaa dawo daita lagos né daga adamawa wannan farinciki  ya rage tarin qunar da zuciyar aunty take ciki  tace "allah yayi maku albarka yayiwa rayuwarku albarka in sha allahu bazaku dangwama haka ba allah zai saukaka maku rayuwa ,Allah nake roko ya daukaka min ku na yafe  maku duk abinda kuka min da wanda nasani da wanda ban sani ba suna cin abinci suna debewa juna kewa ." ****** da misalin karfe 9:00 na washegarin ranar lahadi mr ata ya fito  parlour'n  mami  ,duk  jikinsa yayi sanyi har wata  katuwar  rama  yayi  daman ya lafiyar kura ?ba wani jikin kirki bane dashi  kusantowar aurensa da maryam yasashi jin    kmr  ana  fixgar  ransa  ,shiru ne  ya  ziyarci  parlour'n yana tunane  tunane yana jin kamar idan ya tafi france  kar  ya  dawo  domin a lissafinsa sauran kwanaki goma cif a daura masa aure da yarinyar daya tsana fiyye da komai arayuwarsa   byn  kmr  mintina goma mami  ta qaraso  da kanta ta  had'o masa abun kari , chips  da soyayyen kwai  da  ruwan tea mai kauri , ta janyo qaramin table  gabansa ta  ajiye kana ta zauna kusa dashi ta tsura masa ido tana kallonsa batare datace komai ba ." ya dauki cup din tea ya kai bakinsa ya kurbi kadan yana mai runtse  idanunshi  shiru har wasu mintuna suka shude yana zaune itama tana zaune tana kallonsa da kyar ya bude baki "sweetheart! "kaci abinci first before anything adamcy , sannan kar naji  kayi  magana  kaci abinci  kawai yaushe rabon ka sanyawa cikinka  abinci  bare a samu magani yayi aiki ajikinka ? ji yadda ka dawo acikin kwanaki uku kacal  ka taimakeni kaci wani abu  kanshi  kawai ya iya d'aga mata batare da ya kalli inda abinci yake ba, saboda sam  baya jin cikinsa  zai iya amsar komai  shima da zata taimakesa da tasa an fasa auren nan da yarinyar an hadashi da wata zai hakura da princess dinsa ya amshi koma wacece  duk da zuciyarsa princess kawai take so da son gani numfashi ya dinga  saukewa ."sweetheart  dina me yasa  kika  manna min wannan auren  haka? " sweetheart  zaki  kasheni da kanki wallahi at least ki sake gara min dama koda  na  tsawon wata guda ne  ." "to me  zan  maka adamcy nah daya wuce haka ? "me  kake  son  nayi  idan  banyi maka  haka ba ? gani nayi  kana  neman hargitsa min kwakwaluwa da qarar da rayuwarka a banza "me kake tunani mutane zasu ce idan   bakayi aure adaidai wannan lokacin ba ? wallahi zaka shiga zargin mutane ,mutun har mutun kamamme kamar ka ka zauna babu aure ko kana neman mata ne adamcy bansani ba da kake gudun aure ." wani  irin kallo yayi mata mai nuna mata bayayi "to idan bakayi me kake jira ?maryam  yaruwarka ce fa "yanzu kai kafi son ka dauko min suruka daga waje alhalin ga wacce tasan darajata take sona nake sonta diyar danuwana yanzu idan an fasa auren nan  me kake son na cewa mutane da yan'uwana ,dan Allah dan annabi in banda   da rigima irin naka ba me ye laifin maryam ..? "wani far yayi da idanu zuciyarsa na dokawa  da numfashinsa da yayi kokarin d'aukewa yayi saurin dawowa dashi gangar jikinsa sannan yace "sweetheart  ni bance tana da laifi ba amman  ki duba lamarin da  kyau  tunda nace bana sonta ai  sai a  hakura kawai  kowa ya kawo zabinsa . "kai rufe min baki ban son shirme banza, ka daina ganin ka had'a komai kana da kudi  kayi tunani zaka iya  juya ni  ."Wannan  aure sai  anyi shi muddin ina raye ." ya marairace muryarsa  sosai  tmkr  mai shirin zubar da hawaye sannan yace "wai sweetheart me yasa kike ganin kmr  wannan yarinyar ce kawai zata iya kulawa dake  ? Allah  sweetheart ki daina mata kallon haka  saboda irinsu sune masu bawa dangi kunya  wallahi duk lokacin da naji kince min itace zata san darajarki  bakinciki nake ji kmr na kashe kaina saboda ni duk macen dana kawo miki dolenta ta soki tayi miki biyayya bama Ke ba sweetheart hatta yayyuna biyu din nan dolenta ta bisu  lalacewar mace daga miji ne  ni kuma bazan ta'ba bada wannan damar ba .. " "Sauran kwanaki  goma a daura maka aure da maryam  a lissafina gobe  ko jibi jirginka zai cale zuwa qasar  france  fatana allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya shahida ta  gama shirya komai na aure  fatan alkhairi da dawo da niyyar  angeancewa lafiya and if you do anything  stupidty I will del with you kai ma kasani ina sonka fiyye da tunaninka amman hakan baya hana idan kayi ba daidai ba naki hukuntaka tana qoqarin mikewa hisham ya shigo ya gaishe da mami cike da girmamawa sannan ya zauna kusa da ata  daya   runtse tsumammun idanunsa tun byn da mami ta soma magana "yaakayi mutumina ya karfin jikin hope you are getting better?"numfashi kawai ya sauke wanda Ke nuna masa alamun ya amsa hisham ya cigaba da magana "har yanzu sultan da fahad basu dawo da komai ba fa  Kmr ma sun dauki abun matsayin shiririta tsabgogin gabansu kawai suke." "ina sane da komai kai kasan bana canza maganata ina jiran na dawo daga france ne suna zaune suna hira mb ya shigo haka ma yaya Ibrahim ya shigo duba jikin mr ata tare da aunty abida har da yesmin wacce ta dane jikin mr ata haka ma yammatan gidan d'aya byn daya  suka dinga shigowa suna gaisheshi da kyar yake bude bakinsa   yana amsa musu cikin rashin sakin fuska , cikin wasu  mintuna  aka cika gaban mr ata  da kayan motsa baki , amman babu abinda yaci  illa coffee daya dinga  tsiyaya a  cup yana  kurba ahankali ahankali   shima yana  sha ne kawai saboda  sabon da yayi dashi ." Parlour'n ya dan rage mutane  ya saura daga hisham sai ata   nuzla da diyana  har ma da mrym da nana hauwa'u suka  shigo parlour'n bakinsu  d'auke  da sallama hisham na ganin nuzla ya saki fuskar  ganin masoyi yarsa  gbdy suka hada baki wajen yi ma mr ata ya jiki  banda nuzla  Kmr koda yaushe da kyar ya amsa  masu hisham  yana kallon fuskar nuzla yayinda  nuzla taja ta tsaya daga gefe can ta jingina bayanta da bango ta rungume hannuwanta duka bisa kirjinta tare da tsura ma mr ata  fararen idanunta tana kallonsa cike da matsanancin soyayyarsa  yadda ko kallon mrym da zai aura bai yi ba  abun yayi mata dadi sosai yadda bai son mrym abun na mata dadi har yana bata kwarin gwiwa dan tun daga ranar daaka saka ranar aurenau take jin haushinta sannan take cikin damuwa mai tsanani  ." ahankali ta bud'e bakinta tace "yaya  sannu ya jiki banza yayi mata Kmr bai ji ba nan kuwa yaji sarai hisham yayi qasa da murya  yace "ata ana maka sannu da jiki "naji !ya fad'a atakaice  dan ya fahimci wani abu a attare daita ba tun  yau ba  yana hankalce da irin kallon da take masa a duk sanda zasu hadu tun a office din aunty shahida yaso yaci ubanta allah ya taimaketa "take gabanta ya shiga fad'uwa sbd fargaba dan ganin ko kallon inda take tsaye bai ba illa kur'ban ruwan coffee  daya cigaba dayi kuma taji amsar daya bawa hisham kuma tasan sauran ma sunji abinda ya fad'a  ." ahankali ta juya ta nufi kofar fita cikin bacin rai sannan sauran yanuwanta suka biyo bayanta "amman ai ya kamata ka amsawa gimbiyata ya sake yin mgn can qasa"gsky hisham baka da hankali km kana bani kunya yanzu kai da gaske sonta kake "?sosai ma kuwa ina sonta sai dai ita bata sona ..""what ?" Wallahi haka ta fad'a ai naso bikin a hadashi da naka amman ya zanyi tunda tace bata só na hakura amman nasan sonta ne zai kasheni "amman shine ka kyaleta baka ci ubanta ba? aa babu wannan ai kai ma kasan yadda soyayya take ka duba yadda baka son mrym kake son yarinyar mafarkinka "ka daina kawo wannan misalin ni bana son wannan yarinyar ita ma kuma bata sona kaga akwai matsala wajen namu hadin ko ka fahimceni ."? "Misali ina sonta to ya zama dole dan ubanta ta soni sannan misali da'ace tana sona nima bazan dinga jin tsanarta haka ba duk da nasan nawa rashin son ne babban matsala dan ita prentending ne kawai nasan babu macen da zata kalleni tace wai bata sona dama ne kawai bata samu ba ,ya fad'a yana jan tsaki ka kira min auta  "me zata maka  ?Kai dai kira min ita kawai   yau  yarinyar nan zataci ubanta da me  tafika da zata ce  bata sonka ?shiru hisham yayi yana kallonsa a she haka ata yake sonshi jiki a sanyaye ya dauki wayarsa ya kira nana hauwa'u cikin kankanin lokaci ta bayyana a falon "yaya gani "je kizo min da nuzla yanzu yanzu kafarta kafarki "okay yaya ta juya da sauri ."su kuma suka cigaba da tautaunawa ." Bayan mintuna goma sai gasu sun shigo nana hauwa'u ta  kama  gabanta  ta bar nuzla tsaye cike da fargaba  ta dan saci kallon hisham dake zaune taga ya sakar mata murmushi  ta kalli mr ata taga ya hade rai sai kafarsa daya yake girgizawa har  kusan mintuna  shabiyar tana tsaye sannan tace "yaya gani wai ..."da sauri ya dakata daita ta hanyar daga mata "waye wannan ?ya nuna mata hisham dake zaune "yaya hisham ". "Very good meye a tsakaninku ?nothing ta bashi amsa atakaice ba hisham ba hatta mr ata sai daya dago tsumammun idanunshi ya tsura mata yana kallonta "kika ce nothing kenan baki san yana sonki ba ?nasani but na fad'a masa gaskiya ni bana son shi dan ..."enough ! bana  bukatar  jin  maganarki ko wani abu  kije ki fara shirin aurensa nan da kwanaki  goma  ." cikin firgici da tashin hankali ta shiga d'aga kafafunta zuwa inda yake zaune  "me yasa  yaya ?" dan Allah kayi hakuri karka min haka  wallahi ni bana son shi a matukar tsawace yace "nace karki sake fad'ar wata  magana anan , karki   sake kula kowa  acikin masu sonki shima wanda kike so ki kashe  soyayyarsa  acikin zuciyarki ki so wanda yake sonki  .." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗      MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.            Page 20 jikinta  na  wani  irin  rawa  ta k'araso ta  durkushe a gabansa har  bata  san  sanda  ta d'aura hannuwanta  duka bisa cinyoyinsa  tana  kallon  cikin   kwayar  idanunsa da  suka  rikid'e  suka  canza   kala   a wulakance  ya   zame   jikinsa  yana  mai  kawar  da   fuskarsa   gefen  hisham  dake  zaune   tmkr   mutun  mutumi  yana   kallonsu   cike  da  matsanancin  tashin   hankali   ,shi   kuwa  mr  ata  alamun  baya  son  kallon  fuskarta  ne   yasa   shi    maida  idanunshi  kan  hisham  ". "dan  allah   dan  Allah !!  yaya  adam  kayi   hakuri    ta  kai  hanuta  tana  qoqarin   juyo  da  fuskarsa  gareta  domin  su  fuskanci  juna , zuciyarta  na  wani  irin    bugawa  da  karfin  gaske  take  kallonsa haka  ma  hisham  zuciyarsa ce take ta bugawa fiyye da   kaida   ya  soma jin  wani sauyi na   daban  a gabadaya  ilahirin   jikinsa   wanda  ke  gauraye da tsantsar   tashin  hankali,  shi  kuwa  mr  ata  mamakinta   yasa   gbdy   ya qasa   magana   duk da maganar   yake  son  yi . Kwayar   idanunta  suka   cicciko  da  ruwan   hawaye muryarta a sarke  tace "dan   Allah  yaya   kayi   hakuri   karka  bari  wannan  auren  ya  kasance  domin   zuciyata   bazata  iya d'aukar wannan  nauyin  ba,   wata razananniyar  tsawa  ya buga  mata  wanda  ya  kamata  ace ta  tsorata   ta dawo da  hankalinta   jikinta   amman   ina  sai  ma  sake  narkewa  tayi  a wajen  zuciyarta  babu  tsoron  komai  acikinta , muryarsa  a kausashe   yace " tashi   ki   bar  nan  ki   kuma  fara  shirinki   kamar  yadda   na  fad'a  miki   oya  leave ." "dan  Allah  ka  saurareni  yaya  "ya  girgiza  mata  kai   yana   cewa "   I don't  want  to listing anything  from   you  just  leave  now "dan   allah  yaya  adam  kayi   hakuri  ka  saurareni    akwai  maganar  da  idan  na  fad'a  maka   nasan   zaka   fahimceni "ata dan  Allah  ka  barta  ta  fad'i  abinda  ke zuciyarta    Hisham  yayi  maganar   yana  qarewa  jikin nuzla  dake  rawa  tmkr   mazari  da   kallo  , yadda  take  cikin   tashin  hankali  haka  shima  ya  tsinci  kanshi  cikin   tashin  hankali  mai  tsanani  har  yana  jin  ma  kamar  ya  cire   mata  nata  damuwar  ya  qarawa   kanshi " Hisham  yayi  tsuru   tsuru  yana  jira  yaji  abinda zata  fad'a  ,yayinda  mr  ata  bai  ce  uffan  ba  ya yunkura  ya  mike  tsaye  ya  kwashi  wayoyinsa  ya  fara   taka  kafafunsa  da   kyar   zai  bar  wajen kasancewar  bai  son  yawon   magiya  bare irin nata dake   hargitsa   kwakwaluwa  nuzla  tayi   saurin  shan   gabansa  tana   fad'in  "yaya  karka  wuce  ka  bar  zuciyata  cikin   maseefa  tayi  maganar  cike  da  tausayawa  ,bai  yi  mata  magana   ba  ya  cigaba  da tafiya  yana  mata  gargadi  da  hannunsa  alamun ta shiga  hankalinta , bata  daddara  ba ta sake  shan   gabansa  dan   gbdy  zuciyarta  ta  rigada  ta bushe  babu  abinda  take  qoqarin  aikatawa  face  ta  bayyana    masa  ciwon  dake  cikin  zuciyarta ." Ya  tsaya   kawai   yana   mata   wani  mugun   kallo yana  furzar  da  iska   mai   zafi   daga  bakinsa muryarta  cike  da  rauni  da  buqatar  atausaya  mata  ta  fara  magana  "bazan  iya  jure  ciwon  rabuwa  da  wanda  nake  só  na  auri  wanda  kake  só  ba ta  karasa  mgnr   tana   rungumeshi  ajikita   tana  kuka a matukar   zuciye  ya  fixgeta  daga   jikinsa   yana  sake  furzar da  iske  "are you out of  your sense ?ni sa'anki   ne  da  kike  shiga  gabana? "  ko  ina  wasa dake   ne  da  ina   magana  kina   magana ? ya fad'a yana   kawar  da  fuskarsa   akanta  domin  dai zuciyarsa  ta  fara  tausaya  mata  tausayawar  da  bata  da   wani  amfani  dan  bazai  ta'ba  iya  mata taimakon  da  take  nema  daga   garesa  ba ." Hisham  ya  rasa   meke   faruwa   atsakaninsu  babu  abinda  zuciyarsa  bata  kissa  masa  ba  a zaune  da  yake  tmkr an  dasashi  irin  kallon da take  ata  da  rungumar da  tayi  masa  ya  fara  gasgata  zuciyarsa  akan  abinda  bai  niyyar  yarda  dashi  ba  yaso ya  mike  ya  qarasa  zuwa inda  suke  tsaye  yasan ko akan  me  take  masa  magiya   har  da  runguma amman  hakan  nan  yaji  gara  ya  cigaba  da  zama a  inda  yake  zai  fiyye  masa  alkhairi   kuma  bugu da qari    yayi  imani  ata  bazai  ta'ba  aikata  komai  ba face  abinda  yasan  zai  zamewa  rayuwarsa  farinciki   he really  trust  him  mutun  ne  shi  mai  kyakkyawar zuciya   akanshi ." Hawaye  na  gangaro  mata  bisa  kuncinta  yayinda  magana  ya  fara  fitowa   daga  bakinta  "ina qaunar ka  yaya  ? bai  yi  mamakin    jin  fitowar  hakan  daga  bakinta  ba  domin  ya  rigada  ya  gama karantata  tsab  "na sani  sai  akayi  yaya  ?ya  fad'a yana   kallonta  yana  jin  kamar  ya  soma  yar yarfa mata  maruka  ta  dawo haiyacinta  "dan  Allah  yaya karka  ce  min  a'a !   a kowani  hali  zan kasance  tare  da  kai "  ta  maimaita  hkn  a fili   yafi  sau   goma tana  mai kai  hannu ta shafa  kasumbar  dake   kwance a  fuskarsa  ji  yayi  kamar  ta  shafa  masa garwashin  wuta ,shi  fa  duk  duniya  babu  macen da  yake  jin  zata  ta'ba  shi   yaji  wani  abu  ajikinsa sai princess  ita ma  din   yanzu  ya  soma  gogeta a zuciyarsa  da  rayuwarsa ."cikin  fita  haiyacinta   ta riko  fuskarsa  sosai  ta  sanya  kwayar  idanunta  dake  tsiyaya  ruwan  hawaye  acikin nasa " ban  san  hka  soyayyarka  tayi  tasiri  acikin  zuciyata ba  sai  dana  qasa  amsar  soyayyar  kowa ." "Ban  san  tasirin  soyayyarka  ta  kai  mizanin  da  zan  iya  rasa  rayuwata  ba  sai  da  naji   zaka  min  nisa  , yaya   kaine  duniyata ruhina  yana  tare  da  kai  ako   da  yaushe , nayi  yunkurin   bayyana  maka soyayyata a tun  lokacin  da  mubina Ke mutuwar  sonka   amman  na  gaza  aikata  hakan  ina  ganin  cewar   zan  iya   cire   soyayyarka  na cigaba  da  rayuwata  amman   still  na  qasa  domin  kuwa  every  each  second   nake  jin  sonka na  qaruwa a cikin  zuciyata ,  ina  ta  qoqarin  sheida  maka  halin  da  zuciyata  take  ciki  kwatsam  kuma  sai   ga  batun   aurenka  da  marsi  bance  ka bar  marsi  ba  amman dan  allah  ka  had'amu  ka auremu " rokonki bai  kar'bu   ba   bare   wata   alfarmar  ya kamata ku koyi  yadda  ake  iya  control  din  zuciya  "ka taimakeni  ban  san  ya  zanyi  ba  " kar    allah  yasa ki   sani   ya  fad'a  yana  jan   tsaki   ." kuka   take  sosai   tana   kallonsa   tmkr  ranar   ta  fara  ganinsa  shi   kuwa  haushi  ne ya turnikesa  a  wajen  zuciyarsa   banda  tuttukin  bakinciki  babu  abinda  yake , a  ganinsa  ma  ta  balain  rainashi shi  zata  kalla  tace   tana so  alhalin  ga hisham dake  mutuwar  sonta?  "kayi  hakuri  dan  girman Allah  nasan zakayi  tunanin  komai  akaina   wallahi  haka  ne , dan  na rigada na   haukace  akanka  bazan  iya jurar  abinda   nake  ji  akanka   ba  sannan  bazan iya amsar    soyayyar   yaya  hisham  ba  ,dan  kona auresa  gangar  jikina  ya  aura  zuciyata  da  komai nawa  yana  gareka   da  kawai  zan  iya  rayuwa ..." Ta  riko  hannunsa  hawaye  na zuba   daga   idanunta  ta  soma tafiya   dashi  taku  d'aya  biyu  yayi ya  tsaya cak , itama  ta  tsaya  suna fuskantar  hisham naunaye  ajiyar zuciya  ta sauke  tana  goge hawayen  dake  tsiyaya  ,ahankali  ata ya zare hannunsa  dake cikin nata  ya  yarfar   sannna  ya  zura  cikin  aljihun wondonsa  yana  jan  tsaki "ya hisham! ta  kira  sunansa  a kid'eme  "banyi  niyyar  fito  da  sirrin  dake  zuciyata  ba  amamn  ya  zama  dole  na  fad'a  maka  tunda  na  fad'awa  yaya   adam babu  komai  acikin   zuciyata  sai..." karki   kuskura  kiyi  wannan ganganci  dan  kome  zaki  yi  tawa  zuciyar   bazata   amince   ba "to  kuwa  gara    ka  ksheni da hannunka  na  huta   dan  nima  bazan iya  auren  yaya  hisham ba , yana   sona  ni kuma kai nake   so.."you're  very  stupid  Kiyi  maza ki  danna  madannin  gogewa  ki gogeni  arayuwarki  da   zuciyarki  dan ni  mallakin  mafarkina   ce   " yana   gama   fad'ar  haka  ya juya  ya haye  sama  yana  taka  step   yana  magana " hisham  ka manta da shirmen   wannan  yarinyar  ka  soma  naka   shirin   domin   wannan  auren ko   zata  mutu  sai  anyisa  useless  girl  kawai  ga  inda ake  sonku  aka  damu daku   amman ku  dinga  kai  kanku  inda  bazaa  ta'ba  sonku ba nonsense " Hisham  ya  runtse  idanuwanshi "kenan  hasashensa  ya   tabbata ,  zarginsa   ya   zama  gasky   kenan akan ata  yake  shan  wulakanci  da  tsana  da wahala a wajenta ?   ,"ya  kalleta  cike  da  tausayawa yace "daman  ata  Kike so ?jikinta  yayi mugu  mugun sanyi ta rasa  me  zata  cewa  hisham  illa ta  runtse  idanunta  gam  tana  jin  zafi  da  ciwo  mara   iyaka a zuciyarta  ,ta durkushe qasa  tana kuka tana nemawar   kanta  mafuta   dan  dole  tasan  abun  yi  kafin  a had'ata  aure  da  hisham shima  ya durkushe  gabanta  ya  dago  ha'barta  ya  sanya  kwayar  idanunshi  cikin  nata , tai  saurin  buge masa  hannu  tana  kallonsa  cike  da tsantsar  tsana "ka  kyaleni  ni wallahi  bana  sonka  tunda  burinka  kenan  na  soka  , dan  girman   allah  ka  rabu  dani  ka manta  dani,  ka  manta da maganar  ka  ta'ba  sona  arayuwarka , ka  mantani  ta qarasa  fad'ar  haka  tana  fidda huci  mai  zafi ." "Dan  allah  kiyi  hakuri  nasan  irin ciwo da  zafin  da  Kike  ji  acikin zuciyarki  ciwo ne  kwatankwacin wanda  nake ji  acikin  zuciyata  nasan  zafin  ciwo da radadin  kana  son  wani  baya  sonka ,wallahi  na  tausaya  miki  amman  me  yasa nuzla ?"me  yasa  sai  ata  zuciyarki  zata  kamu da so byn ni  ina qaunarki  ya  kai hannunsa  yana  share   mata  hawaye"ata bashi  da  wannan  lokacin   wahalar da kanki da zuciyarki   kawai  zakiyi  babu  wannan  tausayin a zuciyarsa    a karshe  ya  rungumeta  ajikinsa   tsam  yana  shafa  bayanta   ahankali  ahankali  babu yadda ta iya dole ta  kasance  rungume  ajikinsa  domin tana  bukatar  wanda  zai  rarrasheta  kuka  take  sosai   tana  rungume   ajikinsa "ki daina  kuka  nuzla  dan  zuciyata  bazata  iya  ganin  hawayenki  da damuwarki  ina  matukar  sonki  da  zaki  bani  dama da  sannu  zaki  daina  son  ata  ki soni  ya  fad'a  yana  qara rungumeta  gam   ajikinsa   ahankali ya mike tsaye  tare  daita  ya  nufi  kofar  fita  tun kafin mutane su  shigo su  fahimci  halin da suke ciki ." Washegarin  da  misalin  karfe tara na dare   ata ya  shiga d'akin mami  sanye  cikin  fararen kayan bacci wondo da  riga , hannunsa  rike  da black cup dinsa  dake  dauke  da ruwan coffee  ,yayinda  dayan  hannunsa Ke cikin aljihun  wondonsa  ya samu mami  tsaye a gaban wordrobe  dinta tana qoqarin  rufewa  tana ganinsa ta sakar masa murmushi tana cewa "Masha allah   adamcy nan ya karfin jikin ?alhamd sweetheart ya qoqari dani ?kwana  nawa ya saura ai Allah Allah  nike  Kayi tafiyar nan ka dawo mu sha biki  ranar bani da dama zan aurar da d'a daya tilo ya  girgiza  kai kawai yana  ajiye  cup din hannunsa  akan bedside dinta  ya tsura mata tsumammun idanunshi yana kallonta tmkr wani maraya "yaakayi adamcy nan duk sanda kayi haka akwai abinda kake son fad'a  "haka ne sweetheart kin fi kowa sanin halina alfarma nazo nema ." "Alfarmar kuma ?mami ta maimaita abinda ya fad'a "Eh  ina neman wata  alfamar a wajenki   sweetheart "ina sauroronka Allah yasa zan iya ,ya marairaice  murya sosai kafin ya soma mgn  "dan  darajan  Allah sweetheart ki   qara min  lokacin auren nan wallahi wallahi wallahi !!! kinji na rantse   miki zan auri yarinyar nan zabinki , wasu yan kwanakin kawai zaki qara min har naje na dawo dan  zan dauki lokaci a france daga nan ma zan wuce  hollond  yi wasu abubuwa  masu  mahimanci  a  yanzu  na samu sauyin  lokaci amman kuma idan kina ganin zaa iya yin komai ko bana nan  fine na amince a daura auren ayi komai  amman da zaa bari na dawo sai nafi farinciki kasancewar ina son a hada auren dana hisham da nuzla yadda take kallonsa ya fahimci kamar bata yarda dashi ba "na rantse fa duk   wanda  aka rantse wa bai yarda ba shi din bana allah bane nayi miki wannan alqawarin sweetheart zan aureta ". "naji amman  har zuwa wani lokaci ni wallahi zaka sani jin kunya auren sauran kwanaki ace an daga "karki damu sweetheart idan akwai damuwa kawai ayi ko bana nan  amman na fi son ina nan ,sai kace wata tsiyar zaka kulla  ko  kana ?ya dan ciza gefen lips dinsa "bansani ba ko zan iya kulla wani abu a auren da bana só ?kaji  dashi  tunani tayi karta je a daura yaki dawowa ya bar  yar mutane da nauyi akanta  gara kawai ta qara masa lokaci idan ya dawo sai ayi"Kwanaki nawa zan  qara maka ?uhm ko  Kmr wata biyu haka yayi  "what ! kai adamcy ban yarda da kai ba ,wallahi ki yarda dani sweetheart bazan baki kunya ba,  ba kuma zan saba alkwari ba I promise you ,ka cika alqawari  adamcy ,karki damu sweetheart  na ranse fa ,shikenan  na yarda da kai ta fad'a  kafin su fad'a hirar duniya a nan yake bata labarin   nuzla  murmshi mami tayi tana cewa "adamcy  nah mai farinjini ." Zaune  mr  ata yake  agaban hajiya zulaiheart sanye cikin suit wondo da riga bakake   jikinsa na fitar da wani  kamshi  na daga hankali   fuskar nan nashi dake kwance da kasumba tayi fresh tayi kyau tana fitar da wani haske na dabam mai daukar hankali abun ka ga fari mutun  sallama  ya shigo mata dan sauran awa daya jirgnsa ya daga zuwa kasar  france  "Allah   kiyayya ya tsare min kai , ka kular min da kanka sosai banda wasa da abinci aci abinci akan lokaci kamar yadda doctor ya fada  "in sha allahu zan kiyaye sweetheart. Allah ya qara girma,ya qara miki lafiya da nisan kwana mai amfani kema ki kular min da kanki "Ameen summa ameen nayi maka wannan alkwarin Allah yayi muku albarka gabadaya ku "inji mami ,sannan taja musu addu'a suka shafa tana shafa masa na hannunta a fuskarshi ."a tare suka mike suka fito inda tawagarsa Ke jiransa  a haraban gidan shi kadai ne zaune a bayan motarsa   limozin sai driver a mazauninshi, hawaye ya tsiyayowa mami   sanda motocinsa suke qoqarin barin gidan sai take jin kamar kar  ya tafi  amman kamar yau ne  zai dawo gareta wannan karan mami  ta kasa daurewa sai da tayi qwalla, gefe tayi da kanta tana  dauke hawayenta ." ***** Yau  tsawon  kwana uku  kenan   mlm  yahuza yana zariyar  zuwa gidansu  maryama amman kamar  kullum    bai samu  ganinta ba  yau  ma   daga  massalaci  ya  wuto  kofar  gidansu  yana  neman yaron  da  zai  aika  cikin  gidansu  ko cikakken minti goma bai  yi da  tsayuwa ba, sai ga yaya sadam ya fito daga cikin gidan , nan  ya mika masa hannu suka gaisa "ina  fatan dai  lafiya  kwana  biyu nan  kake zuwa  gidan nan ?"Lafiya  lau wajen  maryama  nake zuwa  sai  dai duk zuwan  da  nake  yi  bana samun ganinta ,shine  dan  naci kake ta zuwa ?to ya  zanyi  sadam  tunda  zuciyata ta  kamu da matsanancin sonta  duk  da bani  da  tabbacin  ko  tana  sona amman   nasan  tana  son  fitowa inda  nake  habib  ke  hanata  fitowa  yanzu  dai  taimaka min  ka fito min  daita  dan  nasan muddin  habib na cikin gidan  bazai  barta ta fito ba ,murmushi  sadam yayi  yana cewa "kai habib  hukuma ne wannan yaron  bari ina  zuwa  !ya  juya  ya  koma   cikin  gidan  ya  shiga  side  dinsu maryama ." a  parlour  ya  iskesu  gabadaya   suna  hirar  duniya ya  zauna  yana  fuskantar  maryama  suka  gaisa  da  aunty   sannan   maryama  ta gaishesa haka  ma  habib ya  amsa masu da "lafiya  lau cikin sakin fuska  ,ya gida da aiki sadam  ?Alhamdulillah aunty mun godewa Allah yace yana  duban  maryama "ga malamin ku  yahuza  can a kofar  gida  yana  jiranki  yau  tsawon  kwana  uku  kenan  ina ganinsa  ashe  wai saboda  ke yake zuwa  amman  bakya  fitowa."wata  irin  kunya ta  kama  maryama  ta  sunkuyar  da  kanta  kasa  tana wasa da  zara zaran yatsun hannunta". "ai ga  d'an  albarka dake hanata  fita  nan , ko shi zai aureta bansani  ba ?yaro  qarami dashi sai aikin nuna isa da iko ita kuma shegen son dan'uwa  tana biye  masa  aunty ta  qarashe maganar tana zabgawa habib harara  ,habib  bai ce komai  ba ya tashi ya shige ciki  dan  matsawar  yana zaune  a falon bazai iya barin maryama ta fita  zuwa koina ba km hakan zai sa yaya  sadam  yaji  babu  dadi "ai  yahuza mutumin  kirki ne kuma ga dukkanin  alamun da gaske yake aunty tace "allah  yasa shi wai habib dan matsalar daake ta samu akan masu zuwa suna tafiya né yake jin haushi "nima na fahimci haka  amman in sha allahu komai yazo karshe  dan nasan yahuza bazai  mata haka ba nima gsky na yaba da hankalinsa maza  tashi  kije maryama karki dade  maryama bata ji dadi ba ganin habib ya tashi ya barsu  km tasan duk akan mgnr fita ne  ,amman babu  yadda ta  iya  yaya  sadam da aunty suna da karfin  iko   arayuwarta  ta  mike ta fita ta bar aunty da yaya sadam   suna magana bata san abinda ya cigaba da wakana  atsakaninsu ba ." acikin  duhu ta sheida murmushinsa  ganin hasken hakoransa ta dan saki ranta da kawar da damuwar fuskarta  barkanki  da fitowa  gimbiya  maryama "numfashi  ta fesar "kai  ya kamata a yiwa barka da zuwa da  kuma sannu da  qoqarin  zuwan  da kayita yi  baka  samun ganina da km qoqarin da kayi   da iyayena last week  na  gode sosai  " ya dan kyaleta "iyayenmu dai na gyara miki ."  maganarsa ta dan mata dadi wannan yasa ta dan sakin fuskarta kad'an "ya kamata mu samu waje mu zauna ko can ne ya dan nuna mata wani dakali dake makoftansu ." tare  suka  qarasa  amman  shi  yaki  zama ya tsura mata ido ya kamata ace kece kika fara zama sannan ni tayi shiru dan tuni ta gane manufarsa ta dan kallesa da idanunta cikin sauri ta kawar da kai ganin kwayar idanunshi na kanta to shikenan na zauna kema ki zauna ta zauna tana gyara zaman hijab dinta sukai shiru na dan tsawon lokaci daga  bisani ya dago ya dubeta "Maryama zuciyata duk ta gama tattara komai agareki a yanzu bani da wani shakka ko kwankwanto akanki muradina ne na samu damar da zan kawo kaina ga iyayenki domin a samu tsayayyen magana a tsakaninmu ."      Soyayyarki ta jima ajikina maryama nayi dawainiya da soyayyarki tun kafin ki kai wannan lokacin na koyar da zuciyata dabarun da kuma yadda na dauki hakuri dan kawai na samu soyayyarki ban ta'ba gazawa ba , ina sonki maryama da zuciya daya ban qara jin ina sonki ba sai danaji halin da ke da mahaifiyarki da kaninki kuke ciki a gidanku bazan boye miki ba ina jin tausayinku most especially mahaifiyarki domin ta fuskanci abubuwa dayawa akan rayuwa kuma tayi hakuri na tausayawa rayuwar da kuke  ciki ki daure ki samar dani acikin zuciyarki mu daga darajan uwa da kuma danuwa mu tallafi rayuwarta data kanin mu  dukkan wani muradinki zan bi na tabbatar kina da burin kiyi aiki byn kin qare  bautar qasa kamar yadda naji kawayenki suna fad'a,burinki kiyi karatu mai zurfi Kiyi aiki ni nan zan barki Kiyi komai kike só zan barki ya dan saurara yana kallonta hawaye taji akan kuncinta  tasan  su da mahaifiyarsu abun tausayi né suna cikin tsananin kunci da bazai yuwu a boyesa ba ." ahankali  ta dubesa "naji dadin  yadda kace zaka tayani  kula da mahaifiyata da kuma danuwana mlm yahuza ina matukar son Mahaifiyata ina son na gatatan rayuwarta domin ita kadace dani na yarda da soyayyarka kuma na amince duk lokacin da kake da lokaci kofar neman aurena a bude take domin burin mahaifiyata kenan  na tsayar da mijin aure fatana ka rikeni amana tayi shiru saboda kunyarta ta motsa ya sauke ajiyar zuciya a zahiri take fahimtar farincikinsa dan bai boye ba ." Yayi  murmushi  yana  shafa  fuskarshi "maryama amanarki  agareni  bake  zaki bani amanarki daga allah  daya  halicceni ce  domin  shi na dinga roko ya bani ke  amatsayin  mata aurena  allah ya amsa tunda  har kin amince min dan  haka shi ya bani  wannan amanar dan haka nayi alkawarin bazaki taba  ganin  sabanin  haka daga gareni ba ,ba kuma zakiyi  danasani ba , aurena zai zame miki abun alfahari  bazan  ta'ba gudunki  ba bazan ta'ba juya miki baya  ba ."Soyayyar sati uku  da  sukai da  mlm yahuza ta fuskanci  tsantsar  son da yake mata kulawa kuwa  har  da mahaifiyarta abun mamaki kowa a unguwarsu  yasan  da soyayyarsu wasu  nasa albarka wasu  nacewa  ba girin girin  ba  allah  yasa a d'aure  kar ya  gudu ya barta kamar sauran." ****** Cikin   wannan  lokacin  maryama da   kawarta  subai'a  suka  je adamawa  domin   suyi   cam for three  weeks  bayan  sunyi  sati uku  a adamawa  alokacin  mlm yahuza   yayiwa    wani  mutun magana  akayi   masu  change  of  location  ita  da kawarta   daga  adamawa   aka  dawo  dasu lagos inda  zasu  fara  bautar  qasa a   Z &A    comapany   dake  kan  titin  guness  bayan  ciku cikun  da  mlm  yahuza  yayi  masu domin  shine  ya  shiga  ya  fita  ya  kar'bo  masu   letter   suka  kai wa  nysc  aka kar'besu  a kamfanin  bayan sun dawo  lagos  suka  fara savieces  dinsu  wannan taimako da mlm yahuza yayiwa maryama  ya  wanke   zuciyar  habib  yaji ya shiga ransa har ma ya fara kiransa da  otherhaif kuma yake  girmamasa yana mai jin ba qaramin dace yaruwarsa tayi ba domin kuwa samun maza irinsa suna  da matukar wahalar samu ." "gashi shi dai ba wani zurfi yayi  a boko ba dan karatunsa  iya  diploma  ne  amman  yana  da  hanya kuma yasan  mutane  sosai dan shugaban RRS  mai ci alokacin abokinsa ne tare sukayi karatun tun daga primary har zuwa secondary inda anan suka rabu amman har gobe suna mutunci  da abota , fara  bautar qasa yayiwa maryama dadi dan daman  zaman gidan ya isheta dan tun da suka qare karatu babu inda take zuwa bayan  islamiyya  gashi ita daman fita bai dameta ba saboda ita ba maabociya son yawo bace amman wahalar da take sha da yawon sata aiki da mutanen gidansu keyi yasa tayi maraba da da wannan fitar tata kullum fatan allah ya taimaketa tana qare bautar qasa ta samu aiki ." Ranar  wata  asabar  tana  zaune  shiru a side dinsu  tana tunane  tunane  akan  sakina  tana matukar  qaunar sakina  aranta ta kasa jurewa   abubuwan da take mata batare da tasan laifinta  ba ,zuciyarta ta bata  shawarar taje ta tmbyeta  ko  wani laifi tayi  mata wanda yasa ta canza mata ,nan  take  ta amince da  shawarar  zuciyarta , dan hk ta mike tsam ta fito ta nufi side dinsu ta yi sallama a tsakar gida babu wanda ya amsa  mata  dan  haka  ta wuce daki  inda tafi  tunanin sakina take  mintuna sha uku da zamanta  amman  sakina  bata ko kalleta ba ." Ahankali  maryama ta  tunkarareta  da abinda ya shiga  a tsakaninsu "haba "yar uwata  mai na yi miki ki ke fushi  dani  tsawon Lokaci  ko  magana ba kya min  mai  nayi miki  da hukuncina ya cancanci haka.?""Cewa na yi kin min wani abu?sakina  ta tambayeta tana  mai  kallo  cikin   idanuwanta  maryama ta sauke nata  idanun  ganin irin  kallon da Sakina ke mata. Ta ce"tô  Sakina tsawon  lokaci   naga  bakya min  magana, in da nayi miki laifi  ne sai ki sanar dani na nemi yafiyarki bana jin dadin yadda kike nuna ko in kula gareni  tsaki kawai sakina  taja ta fice tana magana cikin ranta wanda sam maryama  bata ji  dadin abinda tai  mata ba  "na shiga uku maryama   ta fada a ranta me  zai sa sakina ta yi min  haka  kawata kanwata kuma yaruwarta masoyiyarta?ya Allah  ka  sanyaya  zuciyar  sakina  akaina  idanunta   cike da hawaye ta baro  side dinsu ." Ranar  wata  laraba  aunty  salma da yaranta biyu suna zaune a tsakar  gida  aunty  salma ta dubi sakina "wai  Ke  kwana  biyu  nan mai yake damunki ne  sai  ki dinga kadaita  kanki  kina wani shiru idan wani  abu   aka miki  bazaki fad'a ba  sakina tace" ko na gaya miki ba iya magance  min zakiyi ba duk da ku  ka jawo halin da muke ciki nida  yaruwata shukura ,maryama dake kokarin shigowa cikin side din nasu  ta  dan. tsaya  ta kasa kunne aranta tace "allah  sarki ashe  yaruwata  laifi akayi mata tayiwa gidan kudin  goro  kowa bata shiri  dashi." aunty  salma tace " koma  me akayi  muku   zurfin cikinku ne ya janyo muku Ke kanki kinsani duk damuwarku  kema  kinsan zanyi qoqarin magance  muku   ita matukar  ina numfashi  acikin duniyar nan  sanar  dani  menene  aka muku  da har  yake saka ki  cikin kunci "kusan rabin yan makarantar islamiyyarmu  sun  san  yadda shukura ke son mlm yahuza  amman  kiri kiri  kuna kallo wannan banzar ta  juya abun ya koma  kanta gashi har ana batun saka  rana  aure ." Da alamun  aunty  salma  taji dadin furucin sakina akan maryama  domin  duk irin kunci  da halin koin kula da suke ciki da sakina bata gani ba bare ta shiga cikin maganar  tayi musu sulhu "aunty salma tace" to meye  keda yaruwarki  ? maryama ta fahimci kalmar  cikin  zolaya tayi  maganar ,ai kuwa nan da nan sakina  da shukura suka bata rai cikin nuna tsantsar  tsana "wannan banzar ce yaruwarmu daace kun  koresu a gidan Kmr  yadda kika ce ai da bata yiwa  shukura  kwacen  saurayi  ba  yanzu  gashi nan muna  ji mun gani  wanda shukura take so  dole zata hakura "a'a waya  gaya maku ai  babu wani  maganar wani  hakuri  ,kuyi  hakuri tunda kun fad'a min ku bani  kwana uku zaku ga abinda zai faru." hankalin maryama  ya tashi  kwarai da gaske har yasa  daga  nan bata  sake  sanin abinda suka cigaba da tautaunawa ba  saboda wani daci da  zuciyarta ta dauka ."jiki a matukar ta sanyaye ta dawo side dinsu "ita bata san shukura tana son mlm yahuza ba da sam  bazata  amince da soyayyarsa ba sai ma ta hadasu  amman yanzu ya zatayi ?ko da  yake ta fahimci wani sabon salon cin zarafi ne ake son bullo mata  mata  dashi  dan arabasu dan  haka zata bari adduarta tayi karfin  da bazasu samu nasara akanta ba  tun daga ranar bata sake runtsa idanuwanta ba wajen kiyamul laili  domin  kiyamullaili  tana  qarawa nauyin mizanin  bawa, tana qarawa mutun hasken  fuska  da  samun kwarjini da d'ga darajan mutun acikin mutane kariya ga dukkan sharri  tare da biyawa bawa bukata." Duk  bayan  kwana  biyu  mlm  yahuza  yana  zuwa wajenta  Kmr yadda ta tsara  masu dan bata  son  yawon  zance ,tun bayan kwana biyu  sunyi da mlm yahuza zai  zo sai dai har  karfe  takwas na dare daya saba  zuwa   bai zo  ba amman ta rasa dalili hakan ta kasa  hakuri  ta  shirya  tsaf ta fito zuwa bangaren Ummah  ta iske  shukura  tana  zance  sai  dan kasancewar  dare  bata lura da wa take zance ba sai dai  kawai  kamshin  turarensa  yayi  mata kama dana  mlm yahuza amman  ko  kadan  bata kawo shi bane ta shiga bangaren umma tana zaune suka gaisa Daga  nan  suka shiga hirar duniya har sanda shadaya ta buga ta mike tayi mata sallam ta  koma side dinsu  cikin  tsinkewar zuciya dan bgabanta banda luguden bugawa babu abinda yake ." Shigowarta  kenan  daga  wani  kamfani  kai  zanenta domin  tallatawa  ,da  baba gali ta soma ci karo "yar gwal  idan kin huta ina son magana dake dam taji gabanta  ya  fadi  tun da take arayuwarta bata jin ranar da baba gali yace yana son magana makamanciyar   haka  ba  km  wai  yar gwal  yana son  magana  daita  tabbas  akwai  mahimmiyar magana , bata kawo komai aranta ba sai tunanin watakilla ko mgnr mlm yahuza ce tayi karfi tunda ya sha fad'a mata yana son manya su shiga ciki ta nufi bangarensu ta kammala komai nata  a natse ganin shima ya fita masaalaci tayi sallah har ishai sannan ta dawo parlour ta zauna zuciyarta na tunanin akan maganar da baba gali zai yi daita duk da bata san abinda zai sanar daita ba amman sai maganar ta tsaya mata arai cike sa  fargaba ." Karfe tara daidai  umma ta aiko  a kirata  ita da aunty   nan fa   gaban  maryama   ya cigaba  da fad'uwar da yake , tare suka  fito  da aunty  alokacin shukura ta shigo daga zance tuni aunty ta wuce dan har ta kusan  isa  bakin side din  umma, haka nan ta kalli shukura dake  zaune  kusa da aunty salma dake cin abinci  atsakar gida ta sake gaishe da aunty salma ta wucesu ta shiga bangaren umma ta gaisheta cike da girmamawa  umma taji dadi sosai ta tmbyi lafiyar habib ." shiru ne ya biyo  baya har na kusan mintuna asirin sai ga aunty salma da aunty  hassana sannan byn an gaisa umma  ta numfasa tace "Maryama wata tmby nake son nayi miki game da yaron nan dan gidan lawan yaro ?"dam  taji bugawar da qirjinta yake ya qaru , tayi shiru domin bata damar tmbyrta ta cigaba da magana "tsakanin keda shukura wa yace yana só né ?" Maryama  tayi shiru lokacin da maganar ta doki dodon kunneta wannan  wace irin magana ce akwai abinda  umma batasani ba a tsakaninta dashi ?amman  dai koma menene  batasan abinda yasa take mata  wannan tmbyr ba, ta bude baki zata bata amsa abinda Ke tsakaninsu sai kunya ta hanata tayi kasa kawai  idanuwanta "Maryama tmbyrki nake baki ce komai ta  sake yin  shiru a karo na biyu tana son jin ba kece wacce kuka fara son juna ba har yake zuwa zance wajenki ba ? ta sake yin shiru tana son bata amsa sai dai bazata iya sanar daita ba tunda gashi ita da kanta tasani   kuma tana da masaniyar wajenta yake zuwa, ita me yasa umma zatayi mata wannan tmbyr akan abinda ta rigada tasani tunda sau tari ita ke cewa taje  idan yazo bata son fita ." "Abinda yasa na kiraki nake tmbyrki shine dazu da yamma byn fitarki kai  zane  yan gidansu sunzo domin auren diya a gidan nan kuma sun bayyana wacce suka zo nema ni da azatona kece yahuza yake zuwa wajenki ashe yaruwarki shukura  yake so ." ba idanuwanta  ba hatta numfashinta da kwakwa luwarta sai da suka daina aiki wani tsayawa tayi na wani lokaci kafin ta sauke naunayen ajiyar zuciya  ta juya idanuwanta kana  tashiga   tunani da kwakwa luwarta batace komai ba saboda tashin hankali daya risketa ta sunkuyar da kanta qasa kawai  tana jin damuwa mai tsanani " "Magana nake maryama kinyi  shiru daman bake yake nema ba yauruwarki yake nema ?ta qara yin mata tmbyr bata san abinda zatace ba ganin zata batawa kanta lokaci da jama'ar dake wajen yasa ta dago kanta tace "tunda shi da kanshi ya sanar da wacce yake nema ai babu laifi umma , umma tayi shiru kawai tana dubata ina son gane abun ne domin ni a tunanina Ke din ce  yake zuwa wajen ki kawai ta dago tace "ba wajena yake zuwa ba wajenta yake zuwa tana gama fadar haka ta mike da sauri dan zamanta a waje zai yasa ta zubar da hawaye ta bayan bangarensu inda aunty Ke aiki ta labe tana kuka mara sauti dan kar wanda ya ganta ta tsaya anan ta rarrashin kanta ne dan karta dagawa  danuwanta hankali." Sai datayi mai isarta sannan  ta fito ta shiga falo kai tsaye  ta wuce habib  dake  zaune yana  kallon ball dakinta ta shiga ta kwanta lamo akan katifa ahankali kalaman mlm yahuza daya dinga furta mata suka dinga dawo mata cikin kwakwaluwarta  da taimakonsa  gareta  hakika  bazata   ta'ba  mantawa dashi  arayuwarta ba ta  dinga  girgiza kai shikenan shima ta rasashi  ,hawaye  suka dinga zuba daga idanunta bata san tana shesheka ba sai dataji muryar  habib  yana cewa "kamar shesheka nake ji heartbeat  tayi  saurin  gyara kwanciyarta tayi shiru tare da lullube kanta tana tunani abinda ya kamata ta fad'a masa  idan ya qaraso gareta domin dai abinda yake gudar mata kenan gashi ya faru daita  ta runtse idanunta sosai alamun ta fara bacci ganin hk habib ya juya ya koma falo ." Bangaren umma kuwa gyara zama aunty  tayi ta kallesu "hakika  bakuyi adalci ba  saboda ni nasan wannan yaron wajen maryama yake zuwa me zai sa shukura zata qaunaci wanda yake son maryama har ku iyayenta kusan hanyar da kuka bi kuka raba maryama dashi ?mgnr  tayiwa ummah dadi ko babu komai yau zata gwada kunjinta akan damuwarta Aunty salma ta gyara zamanta itama tasoma magana Kmr tana jira "kada a kawo maganar rainin hankali acikin maganar nan kina tunanin shukura zatace tana son shi ne ?". "to kisani diyata bazata ta'ba cewa tana son wani ba shine da kanshi yace yana sonta kuskure yayi yace yana son maryama dan kawai ya samu hanyar da zai ce yana son shukura bude kunnuwanki da kyau yahuza ya dade da soyayyar shukura acikin ranshi nauyinta kawai yake ji dan hk ya fara gwada soyayyar daga kan maryama ganin bata da wani matsayi da aji ya dawo hanyar madaidaiciya ba kuma diyata tace tana son shi ba idan kuma har abun ya dameki sai kisa diyarki ta sameshi kice ya daina son shukura ya dawo kanta." "Uhm kawai aunty ta furta a fili  sannan a fili   tace allah kai ne allah kai ka kawo ma maryama yahuza amatsayin wanda yake sonta  byn ta rasa sauran kuma na tabbatar yahuza yana son maryama da gsky Allah kai kasan abinda akayi  aka shiga tsakaninsu ya Allah kayi mata sakayya  nasan zaka kawo mata wani wanda ya fishi   komai   "Wai me maganarki take nufi ?kina nufin an kwacewa maryama saurayi ne ko me ?"wannan ai gskyr da kowa ya rigada yasani ce maryama  yake so kuma dan ita yake zuwa gidan nan ,na rasa wannan maseefar babu damar aga maryama da cigaba duk yadda zaa yi sai anyi an rabata dashi ". "Dakata dakata!!  su waye dasu waye idan zakiyi mgnrki Kiyi mgnrki a inda bazai zame miki damuwa ba , ina maryama take ?me ye tafi sauran mata  da idan ta samu cigaba ake rabata dashi ?ita din gwal ce ko me ? inji cewar aunty hassana "tunda yaro yace ga wacce yake so ai magana ya qare sai ayi shirin aure "a'a hasaana wannan ba magana bace  allah baya son zalinci kuma baya son wani bawan yayi ,hakika idan akayi auren nan an zalici maryama "umma ki rabu dasu hassada ke damunsu akan maryama ,amman maryama din da kuke gani tafi gwal wallahi kuma kaf zuriarku babu macen data kaita allah na tuba idan nayi alfahari  ka yafe min ba alfahari nayi ba gsky na fad'a ."da sannu  hassadar  zata cinyeku  ni natashi  allah ya bamu alkhairi  allah yayi mata zabin abinda yafi zama alkhairi arayuwarta da izinin allah maryama sai ta kawo maku wanda bazaki iya kwacewa ba tana gama fadar haka ta mike ta bar falon ."nan fa hayaniya ta kaure aunty hassana na zaginta aunty salma na qarawa ummah kuma tana basu rashin gsky ." Aunty ta  shigo  parlour'n  tana  kuka  nan da nan hankalin habib ya tashi ta wuce shi ta nufi dakin maryama tana kwance  har lokacin tana zubar da hawaye  tana tuno daddan kalaman mlm yahuza gareta atare suka fad'a  dakin  ta qarasa ta zauna bakin gadon ta kamo hannun  maryama ta damke cikin nata jikinta  har ya  dauki  zafi  ta fashe da wani sabon kuka wanda yasa kukan maryama ya fito fili ta yunkura ta mike zaune  cikin  mawuyacin  hali tana cewa "why aunty ?me yasa kike asarar hawayenki akan dan wannan abun ? "duk fa abinda kaga  allah bai baka ba to ba rabonka bane Kiyi hakuri ki daina kuka  please cikin rawar muryar habib yace "aunty meke faruwa ,abinda kake gudu dai ne ya sake faruwa sun rabata da yaron nan yahuza yaron kirki "what !?" "Wallahi habib sun rabata dashi wai shukura zai aura ba maryama ba amman babu komai  akwai allah  wani  irin ihu yayi yana kurma uwar ashariya  ya juya  maryama tayi saurin durowa ta rike masa hannu  ya juyo ya kalleta "ki sakar min hannu heartbeat  ba shukura ba hatta shi kansa mlm yahuza sai naci ubansa yau koni koshi girgiza masa kayi tayi "bashi da laifi nasan akwai abinda akayi masa domin da kunne naji  komai nan ta zayyana masu hirar aunty salma da yayanta akan  mlm yahuza, dan haka kasani mlm yahuza baya cikin haiyacinsa ,mlm yahuza mutumin kirki ne idan nace banji zafin rabuwa dashi ba nayi karya jikinsa a matukar sanyaye ya zame a zauna qasa ya dafe goshinsa da  hannunsa  daya  yana jin ciwon abinda ya faru" yanzu abinda shukura tayi mana kenan ya fad'a cikin jin haushin ,to ya zamuyi mu mun dogara da allah  aunty ta sake riko hannun maryamu "Allah yayi maku albarka a rayuwarku  ,allah ya baki miji na gari,  idan da rabo Allah ya juyo da hnkln yahuza  ya dawo gareki  ya kula dake ." "Maryam tana kuka aunty tana yi tana goge mata hawaye "Kiyi  hakuri  maryama "kema aunty Kiyi hakuri  bana son ki  daga hnkln ki akan matsalar  nan ,in sha Allah nan  kusa  Allah zai bani wani "In sha Allah bazai  dade ba  Allah karka barmu da iyawarmu ka iya mana dukkanin abinda bazamu iya ba  har kusan karfe dayan dare suna tare kuma duk mgnr mlm yahuza suke aunty bata so tayi nesa da maryama  , tafi son bacci ya zo mata  tana  tare daita don Allah ki daina damuwa kinji ' yata ki kwanta Kiyi bacci Allah yayi miki albarka yayi wa rayuwarki data ' ya'yan da zaki haifa  albarka,  In sha Allah bazaki dangwama a hk ba Allah zai saukaka mk  na yafe miki duka laifukan da kikayi min wnd na sani da wnd bn sani ba daga  hk  tayi shiru tana goge hawayen idanun maryama , amma tamkar sake kara mata su ake . Ba  sosai  damuwa  yake  tasiri  acikin zuciyar maryama ba  bare irin wannan damuwar da idan da sabo ta  saba amman tabbas wannan damuwar ta doketa  sosai  dan duk kwanaki   bata iya bacci adduar nenan zabin allah  kawai takewa kanta zuciyarta chunkushe da bakinciki mara misaltuwa har akayi kiran sallah asuba bata runtsa ba hakan yasa ta mike da kyar ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 21 Duk da ba wani son mlm yahuza take ba amman tunanin rabuwa dashi Kullum yana bibiyar zuciyarta dan duk yadda take qoqarin ta yakicesa daga tunaninta abun ya cutura ba dan komai ba sai dan tsananin kirkinsa da tausayinsa gareta komai na duniya ya fitar mata a rai hatta zaman gidansu ya fita ranta saboda Harare hararen da take sha daga kowace fuskar ta mutan gidan wanda hakan yasa ta kasa samun sukunu ta rasa da me zataji da kwace mata saurayi da suka yi ko kuwa da nemanta da fitina da suke yi ?." Tana kwance shiru akan   katifa  kamar mai barci alhalin ba baccin take ba. aunty ta leko d'akin tana kiran sunanta "princes baki ta shi bane ? tasan dole ta kasan tashi saboda abinda ya faru dole zai hana zuciyarta sukuni ."ahankali maryama ta yunkura ta mike daga kwanciyar da tayi ta ari murmushi da sukuni ta dasa a ranta tana cewa "aunty na tashi , tayi haka  ne dan kada aunty ta gano har yanzu abinda ya faru yana ranta har yasa ta qara mata zancen addu'ar ma data kwana yi cikin dare ya d'an sanyayyar mata da zuciya, kuma har ranta taji ta samun sauki dan har yanzu data mike tana maimaita adduar Allahuma ajirni fi musibatihi wa aklifini khairan minha yafi sau babu adadi dan bata san iyaka adadin data yi ba , aunty ta riko hannunta cikin nata suka fito zuwa parlour ta zaunar  da maryama ta lumshe idanunta cikin sanyayyar muryarta tace "aunty ina after  dad ?" "Tun safe ya fita zuwa  filin  kwallo amman nasan yana kan  hanya dawowa yanzu  numfashi ta sauke  da  karfi   sakamakon  tunawa datai yau asabar ce  daman kuma   ranar asabar da lahadi sune ranakun daya ware domin zuwa filin kwallo , ta mike  tsaye a natse ta  nufi hanyar kitchen domin had'a kan kayan wanke wanke ta jiyo sautin muryar aunty   tana  cewa "ina zaki ?" .           "zan shiga kitchen na had'a kayan wanke wanke na wanke ne ." tayi maganar cike da raunin zuciya Kmr  zatayi  kuka , shiru aunty tayi tana kallonta cike da tausayawa kallo d'aya zaka mata ka fahimci bata cikin natsuwarta da kwanciyar hankali tayi wata muguwar rama " ga abinci akan table ki d'auko kizo ki karya kafin ki fara aiki ." ta sauke numfashi sannan ta rausayar da kwayar idanunta bata jin cin komai amman kuma bazata iya cewa aunty bazata ci ba  dan tasan bazata ji dadi ba dan damuwarta damuwar aunty ce , idan ta runtsa aunty ta runtsa ,idan ta kwana Jin  motsinta to haka itama bazata runtsa ba ,ta dinga kai kawo kenan a tsakanin d'akinta da nata ." Jikinta a matukar sanyaye ta qarasa inda kular abincin yake ta bud'e ,shiru tayi tana kallon   abincin , sai  data  d'auki  second  goma  tana kallon   abincin sannan ta kalli aunty   fuskarta d'auke  da  tambaya "ummah ce ta aiko mana dashi , sanyayyen   ajiyar zuciya maryama  ta sauke   sannan ta d'auko Kula tazo ta zauna kusa  da aunty ta fara ci a  natse , ba wani abincin kirki taci ba ta rufe kular tana qoqarin mikewa tsaye  aunty tace "har kin yi me kenan princess ? " ki koma ki qara cin abinci duk fa kwanakin nan ina  lura  dake  ba wani abinci kirki kike ci ba ,ki taimakeni ki manta da abinda ya faru ga gobe can tana d'aga muna hannu kullum cikin miki addua nake , nayi imani allah bazai barki haka ba zai kawo miki wani mafi alkhairi." "Wallahi aunty na koshi ne sannan idan ban hakura ba ya zanyi aunty ? nasan haka Allah yaga dama dani kuma na kar'bi qaddarata ni kawai mlm yahuza nake tausayawa domin duk ranar da zai dawo haiyacinsa sai yayi kukan bakinciki abinda ya faru , tana gama fadar' haka ta shige kitchen ta ajiye kular abincin da taci ta rage ta fara da had'a kan kayan wanke  wanke ta wanke  sannan ta share d'akunansu ta fito da sharar har tsakar gidansu domin kasancewar weekend ce kuma daman ta saba hakan a duk ranar weekend ." Lokacin data fito duk mutanen gidan suna zaune suna hira ganinta suka hau fad'a fad'ensu da suka saba akanta  musamman aunty salma da aunty hassana da  yaranta   kaulat da  Islam dan ita sakina  shiru tayi tana sauraronsu haka ma shukura sai dai duk lokacin da suka had'a ido da shukura sai ta zabga mata harara ,sai dai allah da ikonshi sam bata ji komai game da abinda tai mata ba illah iyaka tausayin mlm yahuza dana mahaifiyarta dake ranta ,adadin soyayyar aunty gareshi mai  yawa  ce,   domin shine saurayi  na farko  da aunty taji ta gamsu dashi ,shine mutumin da rabuwarsu ta ta'ba zuciyarta ,shine wanda har ta tsaya tayi mgn akan ba'a mata adalci ba duk sanda yazo kuwa sakon gaisuwarta zuwa gareshi kad'ai ta kai ashirin, banda yabo da qara mata kwarin  gwaiwa da take mata akanshi." Bayan ta gama aikinta taje tayi wanka ta shirya kanta cikin Jallabiya maron touch of white ta d'aure gashin   kanta da  rebbon  kasancewar  tana da   yalwan   gashi mai  tsoho  sannan  tasa mayafin jallabiyar ta  daure  kanta  ,tana zaune kusa da aunty yayinda hanuta Ke rike da reza ta d'aura kafarta d'aya akan cinyarta tana yanke kunbunan kafafunta suna hira da aunty inda take fad'awa mahaifiyarta tana son zata  1829 super market siyan abubuwan bukatanta  ,aunty ta amince tace "sai da yamma kenan zaki ?"a'a idan after dad  ya dawo yanzu  zamu je tare dashi "princess me yasa bakya iya zuwa koina sai tare da habib ne ?" wallahi aunty bana jin dadi tafiya ni kadai ne sai naji Kmr zaa saceni bare irin wurare nan da jama'a suke cika Kinsan ni fa yawon mutane na matukar   tsoratani." "ai na  sani princess amman dai ya dace ki saba da yin wasu abubuwa Ke kad'ai saboda kinsan wata rana zakiyi aure gashi kinsa habib aranki dayawa karki manta habib nmj ne shi din d'anuwan wasu ne tunda nan gaba aure zaiyi " " babu wacce ta isa ta shiga tsakanina da 'yaruwata , babu wannan matar a nan gidan duniya wannan shine sallama da habib yayi sannan   ya shigo parlour'n sosai ya furta sallama ." atare maryama da aunty suka amsa masa maryama ta d'ago kwayar idanunta daga abinda take ta zuba masa tana sakar masa murmushin farinciki yana tsaye sanye da wondo da riga na yan kwallo na kamfanin arsenal kayan sun amshi jikinsa sosai  ,suna matukar  kama da habib sosai abu d'aya ne ya bambamtasu shine launin fata shi fari ne sol yayinda ita kuma ta kasance chocolate colour ." Aunty tayi murmushi tana dubansa tana sake maimaita maganarta "to ai gsky ne kai d'anuwan wasu ne  mana ,dan girma Allah aunty ki daina furta cewa ni din d'anuwan wasu ne , wasu suwa kenan ? "yan'uwan matar da zaka aura mana ta bashi amsa da haka tana kunshe  dariyarta "dan girman allah ki daina fad'ar wannan mgnr nifa babu matar data isa ta juyani ,haka zata ganmu ta barmu mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka faro babu wacce ta isa ta raba mu ko shiga tsakaninmu bakiji sunan da nake kiranta dashi ba bugun zuciyata ? bani da kowa sai ke daita , uwa d'aya uba d'aya , jini d'aya ina jinta araina fiyye da komai dake cikin duniyar nan "dan allah kama mana baki zaka cika mutane da dadin baki har ka girma kayi auren muga yanayinka ,amman a yanzu babu abinda zaka fad'a na yarda da kai nawa nawa suka cika baki irin naka a karshe ..." "A'a aunty akwai shakuwa mai karfi atsakanina da habib ai duk wacce tace zata shiga tsakanin mu allah ma bazai barta ba bare bana tunaninta hakan ,shi kansa ma bazai d'auko mana matar da zata rabamu ba , matar da ma ni da kaina zan zaba masa inji cewar maryama ta  fad'a  tana murmushi "yauwa heartbeat fad'awa male taji da kyau, nima koda wasa bazan kawo irin wannan matar ba ,sai ma wacce heartbeat ta za'ba min Kmr yadda zan za'ba mata miji anan gaba yana fad'ar haka yasa kai   zai shiga bayi maryama tace "karka dade zaka rakani 1829 "okay ki shirya kafin na fito ya qarasa shigewa ciki ta mike tsam tana cewa aunty "bari naje na sake shirya na fito ."     ta shirya cikin wata doguwar rigar   atamfa   yellow  touch  of   black atamfar   ba  wata  sabuwa bace  dan  ta  dan  kode  sai  dai  fés  take  agoge  sai takalmi flat  kasancewar maryama mayar saka flat ce cikin kankanin lokacin habib ya fito yana kiranta yana d'aura agogo a tsintsiyar hannunsa na gama ke nake jira fa "ganin nan   fitowa   nima na gama hijab  kawai  zan  saka  da  nikaf ,byn   second   biyar   ta  fito  suka yiwa aunty sallama "sai mun dawo aunty ." " to sai kun dawo Allah ya tsare min ku habib ka kular min da yarinya na baka amanarta yayi murmushi yana cewa "to ni kuma wa zai kular miki dani ? ."kai   wannan yaro   wannan yaro akwai manyamce  ku dai je Allah ya tsare karku dade suka fice suna fitowa suka hango yaya sadam a haraban gidan hannusa  daya  rungume a qirjinsa yana waya da murmushi akan fuskarshi suka gaishesa hannu kawai ya d'aga masu suka wucesa ." Basu suka dawo gidan ba sai daf da magariba habib ya wuce massalaci maryama ta cire nikaf dinta tare da hijab ta fad'a bayi domin yin alwala bayan ta idar da sallah suna zaune sai ga dan sako daga umma cewar tazo babu ' bata lokaci ta mike ta nufi side dinta bakinta d'auke sallama ta shiga a natse kamar koda yaushe umma tana zaune a parlour'n   gefenta yaya  sadam ne zaune ya d'aura kafafuwansa duka a saman table yayi crossing leg's dinsa suka amsa mata sallamar ,cike da girmamawa ta gaishesu sannan ta samu waje ta zauna tana fuskantar ummah " . "yauwa maryama gobe  idan Allah ya kaimu zamuyi baki daga cikin gari zasu zo Ina son dan allah gobe da safe kizo ki tayani aikin kaji dazu na aika kizo aka ce kin fita  tare  da habib har na aka Islam ta siyo  min kayan miya ina ganin gobe ma tare daita  da  sakina zaku tayani aiki ." "To shikenan ummah Allah   ya  kaimu zuwa karfe goma yayi ko karfe nawa kike bukatar nazo"? tayi mgnr cikin jin kunya ,"eh to zuwa tara ma yayi ,maryama ta d'an jima suna hira da umma yayinda sadam Ke waya."ahankali ta mike tai   mata  sallama ta dawo side dinsu tana sheidawa mahaifiyarta bukatar ummah dan haka bata tsaya yin wata doguwar hira ba dan lokaci ma ya fara tafiya kai tsaye taje tayi sallah isha'i ta kwanta bacci dan ta  samu ta  tashi da  wuri ." washegari tun bakwai na safe ta tashi ta fara da gyara d'akunan su karfe takwas da rabi ta kammala da aikinta na yau da kullum sannan ta nufi   side din ummah ta fara kama   mata  aiki sakina da  Islam  na zaune basu da ma alamun saka hannu har sai da yaya  sadam ya buga masu tsawa sannan  Islam  da sakina suka  kama mata aikin kajin, saboda ganin aikin da maryama take yayi mata yawa , wanda ita ko ajikinta dan ko ita kad'ai aka bari da aikin zata kammala komai ta tashi ." d'aya bayan d'aya mutanen gidan ke shigowa hatta baba gali sai daya shigo cikin tsananin murna da zuwa bakin da zasuyi wanda ita maryama aranta take raya irin bakin da umma zatayi hakika ko su waye lallai masu matsayine a gun kowa dake cikin gidan tunda take a gidan bata ta'ba ganin hakan daga garesu ba, baya farincikin da suke ciki har da  hidmar wanda ke nuna wani mai matsayi ne zai zo ." Sosai ta kasa kunnuwanta tana son ko kad'an taji irin bakin da zasu zo amman bataji komai ba sai dai ummah da aunty hasana da aunty salma suna ta hira   akan bakon da alamun sun san wanda zai zo alhji  alqasim maude   kenan yaushe rabon shi da kasar nan?". "Ke ai kudi sunyi wallahi dan baki ta'ba zuwa gidansa ba wannan yar wayewar da kike ganin kina dashi sai kin nemeta kin rasa inji cewar ummah ,aunty hassana tayi murmushi cike  da  jin  dadi "haka naji abakin babansu sakina ya ta'ba zuwa tare da abban sadam allah ya jikinsa da rahma yace aljannar duniya ne gidansa kamar ba qasan nan yake ba su kansu mutanen unguwar da yayi ginin kallon gidan suke ."aunty salma ta  fad'a  tana  tafa  hannuwanta ." Sai yanzu maryama  ta gane waye zai zo abokin abban sadam ne wanda sukayi karatu tare tun daga  primary har zuwa diploma har suka girma sukayi aure dake shi alhji alqasim maude yayan mahaifiyarsa yana siyasa shi ya samammarsa shcolaship zuwa qasar india ya wuce tare da matarsa wannan ya dan yanke zumuncin abban sadam dashi sannan mutuwa ta qarasa gabadaya sai dai jin rasuwarsa ya mugun d'aga masa hankali sosai ." mutuwarsa ya dawo da zumuncinsu ya d'aure sosai shine ma ya d'auki nauyin karatun yaya sadam har ya qare karatu kuma shine mutumin daya samammar masa aikin da yake yi ahalin yanzu a awaf  ,alhj  alqasim maude mutun ne mai kirkin gaske da sanin darajan mutune da taimakawa talakawa a yadda ta samu labari duk ya kwashe ya'yan yan'uwa zuwa kasashen duniya wasu na karatu wasu na kasuwanci shine ma ya bud'ewa abban sadam gidan buredi kuma yana taimaka masa a duk   sanda yazo qasar " Umma ta mike tsaye rike da wayarta sakamakon qarar data d'auka ta nufi hanyar shiga side dinta dake a tsakar gida suke aiki aunty salma na gani ta tashi tace "sakina Islam   ku  cire hannunku haka nan ku huta ku barwa   yar wahala ta cigaba da aiki tunda dama ita ta saba aikin neman suna da  neman  gindin  zama  ,wallahi  ba  ai kin kyauta salma  daman tun   dazu  nake  son  dakatar  dasu su bar   shegiya  yar  wahala  ta cigaba  a  haka rayuwarta  zata  ware  bauta ,maryama ta kallesu batare data ji zafin maganarsu ba, dan aiki kam matukar na umma ne zatayi shi sai inda karfinta ya qare ,tayi nasu ma da basu da aiki sai nacin zarafinta bare na umma ,ta cigaba da aikinta ta dauki wata roba ta qarasa inda  korfot yake ta wanke shikafar dake ciki ta bud'e tukunyar dake kai ta zuba shimkafar cikin ruwan zafi tana cikin aiki shukura ta fito daga side dinsu ta zauna adaidai lokacin umma ta fito ." Aunty hassana da aunty salma  har  ma  da  ya'yansu suna hira ummah ta kalli sakina da shukura da islam  zaune suna tayasu hira ta kalli maryama dake  faman dikar aiki "a'a ya zaku bar maryama da aiki ita kadai Ke shukura sakina islam kusa hannu kuyi tare mana na gayyatoku ne dan kutayani aiki ba dan ku zauna kuyi hira ba ,maryama ta fahimci maganar ba dasu shukura kadai ummah tayi ba har dasu aunt hassana tayi cikin rashin son aiki suka qaraso inda take gyara kaji shukura na kunkuni wanda bazai kai ga kunne ummah ba , maryama tace "kinga shukura idan baza kiyi ba ki koma ki cigaba da zamanki idan ma gbdy bazakuyi ba ku barshi duk zanyi dan kawai an sakaki aiki zaki dinga wa ummah kunkuni ta watso mata harara tare da kallon banza "ke ki kama kanki dan na lura tunda mlm yahuza ya dawo da neman aurensa kaina kike min kallon gani gani nake miki kallon gani gani ko kike min ?" maryama ta fad'a  a dan hassale  tana  hura  hanci . "Ban sani ba banza kawai mai bakin jini sai wani 'bare 'bare kike dan kinga mai kudi zai zo , abinda kome zaayi na banza né tunda babu abinda zai haifar sai cigaba da  zaman gida da yawon  ta  zubar  wai  ana  zuwa  bautar  kasa "Ke ni kike gawa magana "? an gaya  miki me zakiyi ?"ai maryama cikin fushi ta zabga mata mari wani qara ta saki tana dafe  kuncinta wanda yasa aunty salma da duk wanda suke wajen suka juyo zuwa inda suke ita kanta irin qarar da shukura ta saki sai da gabanta ya fadi ta tabbatar yau ta dibowa kanta ruwan dafa kanta "kutumar uban can   me tayi miki kika zabga mata mari haka ?"aunty salma ce akan maryama take neman ba'asi cike da maseefa." Maryama tayi shiru tana datasanin Marin datai mata hakan shi ya fusata aunty salma bata tsaya wata wata ba ta zabgawa maryama nata mari har biyu a kowani kunci "idan dadi né kema kiji ina dalili daga tazo ta tayaki aikin wahala sai mari jakar gidan ubanki ce ? taja hannunta zuwa kofar dakinsu tana share mata ruwan figar kajin data goga mata ." Ummah tace "maryama me ya hadaku har daya kaiki ga marinta ? tayi shiru tana shayen zafin marin dan bazata iya fad'a mata bakaken maganganun data fad'a mata ba kawai ta rufe fuskarta saboda tuttukin bakinciki da zuciyarta Ke mata nan da nan kuka ya kwace mata umma ta qaraso kusa daita "kinsan kema uwarta bazata barki ba me yasa kikasa hannunki ajikin shukura ?sakina kanta ta tausaya mata tana son tayi mgn dan kare maryama da sheidawa ummah cewar ba laifin maryama bane laifin shukura né amman ta kasa ." "kinsan halinta ya kamata ki dinga kiyayye duk abinda zai hadaku daita da yaranta ni wallahi nayi danasani ma sakasu cikin aikina kinga sakina tashi ki bisu kuje kema Islam jeki na gode kema hassana wuce  idan  bakin  sun  qaraso  kwazo  ku  gaisa " kukanta ya fiyye mata maganar ummah , bata cewa ummah komai ba tana tsaye akanta ita kuma tana cigaba da kukanta ta share mata hawaye "kiyi hakuri kinji Allah zai saka  miki  maryama bata ce mata komai ba ta cigaba da aiki datasata domin tana ganin hakan shine zai fiyye mata akan kukan da take ." Karfe tara da minti arba'in  da daya daidai bakin suka shigo cikin unguwarsu cikin wata qatotuwa Jeep mutun uku ne a cikin matarshi da kuma shi kanshi alhj alqasim maude sai mai tuka su inda baba gali da yaya sadam suka fito tuni tsayuwar jiransu da sauri baba gali ya qarasa ya bude kofar da alhj alqasim maude yake da murmushi cike da kulawa suka gaisa sosai." Alhj alqasim maude ya rike hannun baba gali yana cewa "Kai amma an jima ba hadu ba, ya jama'a ya iyali.?"baba ya ce,"duk  lafiyarsu   qalau barkanka da zuwa ya hanya? da irin wannan gaisuwa matarsa Hajiya mustafshir ta fito daga motar suka gaisa da baba gali cikin  kulawa, sannan alhji alqasim ya rungume yaya sadam ajikinsa cike da farinciki dan duk sanda ya gansa yana jin farinciki sakamakon kamaninsa da mahaifinsa "sannu dana fatan kana lafiya ya fad'a yana shafa bayan  yaya sadam ya dan zame kadan ya gaishesa "barkanku da zuwa dady da fatan baku sha wahala ba ?"babu wata wahala sadam sukai masu jagora zuwa cikin gida ." kai tsaye babban falon ummah wanda aka qawatashi babu laifi anan abban sadam yake saukar bakinshi kujeru set guda zagaye a dakin sai dan teble a tsakiya na glass , parlour ya sha gyara har da turaran  wuta kala hudu maryama ta saka a kowace kusarwa na falon ,suka zauna ana qara gaisawa da tambayar mutanen gidan hajiya mustafshira tana dan duba wajen tana murmushi itama tana dan ta'ba hira umma ta fito daga dakinta maryama na zaune gefe daya kuma aunty salma ce da sakina har ma da shukura da islam duk komai an gama shiryashi daidai ta yadda duk wanda ya gani bazai raina ba "maryama ki kawo wa baki abinda muka yi ta yunkura zata tashi islam tayi sauri ta dauka batare da an bata izini ba ta wuce dakin da farantin dake da kayan ." Hakan yasa ta koma ta zauna batace komai ba sai dai ummah tace taje wajen baban yara mai Shgo zai bata sako dan haka ta fasa zaman ta gyara zaman hijab dinta ta fice daga falon roban ruwan faro ne guda shida wanda suka dauki sanyi da kwalbar multina shima guda shida ya saka mata acikin leda baka ta nufo ummah bata shiga dakin da bakin suke ba tana zaune suna hira da aunty data iske zaune kusa daita da jamar gidan tace "yauwa diyar albarka ki kai masu amman kawo mugani islam je dauko wadan can kofunan na glass acikin dakina cikin sauri taje ta dauko ta hada da bakar ledar da maryama ta shigo dashi taje ta kai hakan kuwa yayiwa aunty hassana dadi dan tafi son ace islam ce Ke kai kawo a masaukin bakin." ita kuwa maryama ta rasa me yasa take son shiga dakin har da zalamarta aunty hassana da yayanta biyu kaulat da islam suka shiga suka gaisa sun dan jima aciki sannan suka fito sannnan ummah da aunty suka shiga bayan wasu mintuna aunty ta fito ita kadai zata wuce har maryam ta mike zata bita su koma side dinsu tare , aunty ta dakatar daita " ki tsaya idan ummah ta fito bata ganki ba zata damu ko bama haka ba dole Kinsan zata nemeki ." "to ! kawai ta furta ta koma ta zauna bata shiga dakin ba dan ita a ganinta babu abinda zai kai ta ciki zama gurin bai mata ba dan harare hararen da take samu daga yammanta ta mike ta shiga dakin ummah tayi kwanciyarta duk da tana son ganin bakin amman haka ta hakura tana jin su sakina suna santin bakin fad'ar haduwar hjy mustafshira da irin kayan alfarmar da take sanye dashi ita dai shiru tayi bata damu ba domin ko sun tafi basu ga juna ba ita ba damuwa zatayi ba dan ganinta haduwarsu bazai   wani qareta da komai  ba ." Kusan karfe uku saura suna hira dasu ummah da baba gali har ma da yaya sadam suka fito domin niyyar tafiya suka tsaya a falo inda jamar gidan suke zaune aunty salma da ya'yanta haka ma aunty hassana domin suyi sallama dasu "amman gsky yaranku basu da hayaniya amman dai duk sun yi karatu ko "? Murmushi baba gali yayi "Kai kasani dole suyi karatu domin sanin amfaninshi ita wannan tuni ta gama secondary kuma ina son rai zata cigaba ya nuna sakina ." alhj alqasim yace "Allah sarki gsky karatu kam yana da matukar mahimanci kayi qoqarin da ka bar  yaranka sukayi karatu dan da sun biyoka da rashin son karatu da abun bai yi kyau ba dan wannsn zamanin sai da karatu sukai dariya gbdy sakamakon jin abinda alhj alqasim ya fad'a "ai gsky ne yayanshi yafi sa son karatu sosai allah dai bai yi zai yi karatu mai zurfi bane Allah ya jikansa "Ameen hjy mustafshira ta amsa tare da jamar wajen ." Alhaji alqasim ya nuna shukura "wannan yarinyar ussein ce ko ?"uhm uhm bata ita bace wannan diyata ce ta uku  ita ina ganin tana bangarensu baba gali ya bashi amsa da haka ,allah sarki allah ya jikinsa shima yasa suna aljanna Ameen ai kasan ita maryama bata fiyye son shiga cikin mutane ba mussaman idan bakin fuska ne allah ya zuba mata kunya gashi ita har ta qare karatunta na digree yanzu haka ta fara bautar qasa ta kuma yi saukar alquranin mai girma tana da hadda uzu arbain da wani abu akanta ." "kai masha allah a she dai kuna da zakakura acikin dangi ?"sukayi dariya kawai suna yiwa ussein addau "gsky ussein yayi saa arayuwarsa duk wannan rashin jin maganar daya ta'ba amman allah ya albarkacesa da samun yarinya mai kokari haka "? wallahi abun na allah ne yaransa ma duk masu natsuwa sai ma ka gansu, yabon ummah sam bai yi kowannensu dadi ba amman babu yadda zasu yi tunda umma ce kuma sun san adalilin ta suka zo gidan"ai ina qaunar ussein domin shi din mutun ne mai barkwanci da son mutane ai naso na dawo qasar nan na iske shi a raye maryama tana cikin dakin ummah duk tana jin maganar Alhaji alqasim da ummah tana jin matukar qaunar mahaifinta alokacin da bataji tahirinsu da mahaifiyarta  ba amman daga baya dataji komai sai ta daina kewar  babanta duk da ba wani saninsa tayi ba dan duk lokacin data tunashi  sai damuwarta ta ninku acikin zuciyarta ganinta shine ya  raba aunty da yanuwata ,bugu da qari yadda kowa yasan mahaifinta baya jin magana." kuka taji ya kwace mata "Ke shukura je ki kira min maryama taí Jim dan tasan tana dakin ummah amman dan bakinciki karta gaisa da bakin yasa ta fice Jim kadan ta dawo tace "aunty tace bata nan ,bata nan kuma ?ummah ta furta a fili tana qoqarin neman layin aunty can bayan Kmr second goma maryama tajiyo muryar ummah na kiran sunanta "maryama maryama !! hakan yasa tai saurin mikewa ta share idanunta da gefen hijab dinta ta fito ko hada idanu ta kasa da bakin saboda tsura mata idanun da matarshi da shi kanshi Alhaji alqasim sukayi ." "Haka diyar ussein ta girma lallai dan mutun sai allah ussein din guda nawa yake har da 'ya haka ?ita dai maryama gaisuwa ce kawai nata domin bata da abun cewa hjy mustafshira ta shafa kanta sannunki kinji  ya aiki da fatan yana tafiyar miki yadda ya kamata kyakkyawa dake tubarkalla masha allah shine kika fitowa kizo mu gaisa ko ? Ta dan yi murmushi ta dago kanta tana kallonta amamn still ta kasa cewa komai "me ya sameki kamar kuka naga kinyi bata san hawaye na makale da idanunta ba da sauri tasa gefen hijab dinta tana sharewa hjy mustafshira ta qaraso ta dagata daga tsugunno datayi ta dan rungumeta ajikinta "babu mamakin maganr da mukayi ta mahaifinta ce tasa ta kuka ita kanta ummah ta shiga damuwar ganin hawayenta ,ki daina kuka kinji allah zai kai rahama kabarinsa Kiyi hakuri ki cigaba da yi masa addaua shi kanshi yana can yana alfahari da samu diya kamarki mai riko da addini kai kawai ta daga mata tana qara goge kwallar data taru a idanunta  aunty salma da aunty hassana da yaransu kuwa babu abinda suke aikin yi sai harare harare iri iri da bakinciki ." "Ai mahaifiyar ce ta shigo dazu muka gaisa ko ? alhj alqasim ya tambaya yana duban baba gali "Eh itace baba gali yayi saurin fad'ar haka ai tunda ussein ya mutu taki koma wajen danginta bare tayi wani auren ta cigaba da zama anan ai kasan yadda akayi aure danginta saboda rashin son useein din suka sall.." "Eh nasan komai abban sadam duk ya fad'a min alokacin amman dai nayi tunanin komai ya wuce zuwa yanzu Alhj alqasim ya katse maganar ya zura hannu cikin aljihunsa ya zaro kudi bandir daya na yan dubu dubu ya damka ma maryama taki amsa tare da cewa ya barshi sai ummah ce ta karba ." Gabadaya sai daya bisu da kudi yana cewa" in sha allahu zan sake dawowa nan kusa tare da yarana gbdy asan juna kafin mu tattara mu bar qasar yayi gaba yaya sadam ya bishi da baba gali hajiya mustafshira bata saki hannun maryama har bakin mota ita dai bata ce komai ba binta kawai take da alamun tausayinta ne ya game jikinta sai faman hakuri take bata sukai sallama tayi mata godiya sosai suka shiga mota suka tafi ." Ita da yaya sadam da baba gali suka koma gida kai tsaye dakinsu ta nufa da yamma ummah ta shigo ta mika wa aunty kyautar kudin data samu aunty tace "a'a bazan karba ba ummah saboda me balkisu ? Ki rike kawai domin kece mai yin hidima acikin gidan nan bare ma akanmu wannan ai ba wani abu bane amana ce rike a hannuna, ni dai kawai ki rike ." "to ki cire wani abu aciki aunty tasa hannu ta zari dubu daya ummah ta girgiza kai tana cewa allah baki isa ba kin kuwa san ko nawa ne dubu dari ne fa shine zaki cire dubu daya ta raba kudin biyu ta mika mata rabi allah sunyi yawa ummah bazan karba ba nifa ba butulu bace nasan ya kamata ta cire naira dubu biyar tana cewa wallahi iya su sun isa allah yasa albarka rantsuwar datayi yasa ummah bata qara cewa komai ba ta mike ta koma wajenta ." Da yammacin ranar maryama ta shirya zata wuce makaranta islamiyya "aunty ni na wuce makaranta sai kin dawo princess idan kinga malam yahuza ki gaishe min dashi maryama tayi shiru tana kallonta "Eh haka na fad'a har yanzu zuciyata tana qaunarsa dan haka kice masa ina gaishesa "to ! kawai maryam  ta fad'a tasa kai ta wuce zuciyarta cunkushe da damuwar abinda baba gali yayi shi kansa alhj alqasim din yasan maganar bata dace ba shiyasa ya katsesa ". ta kusan kai bakin get din Ardus salam ta hango mlm yahuza yana tahowa ta hanya mai fitar da mutun afanla ta cigaba da tafiya a natse adaidai lokaci daya suka iso bakin get ta gaishesa ya amsa fuskarshi babu annuri sosai bata damu ba domin sakon aunty kawai take son isarwa "aunty tace tana gaisheka "na gode kawai yace yayi gaba ya barta tsaye abun yaso ya bata haushi amman tunawa datai baya cikin haiyacinsa yasa bata ji komai ba sai dai ta kasa cigaba da daga kafafuwanta tayi shiru kawai bata san a tsaye take ba ashe ta kasa tafiya ne sai da wata kawarta lauratu tazo wucewa . "Ke kuwa tsayuwar me kike anan kamar mai jiran wani nan ta diririce "Ke na hango ai kin kusan qarasowa shi yasa na tsaya ta dai jita ne kawai amman alamunta basu nuna hakan ba suka shiga makaranta tare koda mlm yahuza ya shigo ajinsu domin kara masu karatu ko inda take baya kallo sabanin da in har yana cikin ajin murmushinsa kadai ya isheta bayan an tashi ta dan tsaya hira da kawayenta koda suka rabu ta nufi hanyar inda suke tsayawa dashi anan ta ganshi shi da shukura ko kunya babu tasan kuma duk sharrin shukura ne dan ta gansu sosai ne hakan bai dameta ba tunda idan kayi da kyau zaka ga da kyau idan ma akasin haka kayi zaka girbi abinda ka shuka ta wucesu cikin fushin zuciya har ta isa gida abun na cinta arai wai yanzu duk abinda mlm yahuza yake fad'a mata akan soyayyarsa ya tashi abanza ya koma kan shukura hakika basu yi mata adalci ba amman ta barwa allah komai ." ******* Zaune  mr ata  yake acikin masaukinsa  yana jiran abokinsa bashir sosai yayi kyau sai dai ace  masha allah  dan yanayin gyara tattare da kulawar  da jikinsa yake samu ya hana shekarunsa bayyyana dan idan ba kaji shekarunsa ba bazaka ta'ba cewa ya kai 40 wani abu  ba , zaka dauka shekarunsa basu wuce talatin a duniya ba fatar jikinsa kawai ka kalla kasan kudi suna aiki ba karya haka ma kayan jikinsa tun daga kan wondo rigarsa takalminsa har zuwa agogon dake makale a hannunsa dukansu tsadaddun gaske né ,shine ma ya zana da kansa kaf duniya su uku kawai ke da irinsa shi mb sai bashir abokinsa rolex ne mai shegn kyau ." ya hade rai sosai kana kallonsa kasan yana cikin damuwa mai tsanani maganganun sweetheart dinsa yake tunowa a wayar da sukai daita a wannin data gabata. inda take sake jadda masa alqawarin da yayi mata kafin ya bar  qasar , koda yayi qoqarin sake lallabata cewa tayi "kada kace min komai bana son jin wani kalaman yaudararka gareni ,kasani a wata biyu din da kace zakayi yau sauran sati daya ka dawo ."amman idan bazaka dawo ba ,ka cigaba da zama adamcy kayi son ranka kayi abinda kaga dama kayi abinda kaga yafi maka arayuwa ,amman kuma idan ka san  zaka  dawo  ka dawo kamar yadda mukayi alkwari da kai ,karka  dawo da wani abu a zuciyarka ka bar duk wani mugun nufinka a inda kake ,karka dawo gareni da mugun nufi ka barni na cigaba da rayuwa babu kai domin dawowarka da wani sabon salon yaudara ko mugun nufi  zai sa nayi maka abinda har ka mutu bazaka daina mamakina ba abun bazai mana kyua ba adamcy ta fad'a tana kashe wayarta." zuciyarsa ta sake cika da tashin hankali "ina zai ma iya karya alqawarin da yayi  sweetheart dinsa ? ya shiru kawai yana ciza gefen lips dinsa ,ina bazai iya ba bazai iya karyar mata da zuciya ba ita din jigon rayuwarsa ce  zai iya yin komai domin yaga ya faranta mata kamar yadda yasan zata iya sadaukar  masa da faricinta haka shima a yanzu ma da yaji muryarta tausayinta ya cika zuciyarsa " ahankali ya daga tsumammun idanunshi ya sauke su akan agogon dake daure a hannunsa 11:44 am tsaki yaja "what a heck sannan ya gyara zamansa "kada kace min komai bana son jin wani kalaman yaudarar ka gareni ,kasani a wata biyu din da kace zakayi yau sauran sati daya ka dawo ."amman idan bazaka dawo ba ,ka cigaba da zama adamcy kayi son ranka kayi abinda kaga dama kayi abinda kaga yafi maka arayuwa ,amman kuma idan  ka san  zaka  dawo  ka dawo kamar yadda mukayi alkwari da kai ,karka  dawo  da wani abu a zuciyarka ka bar duk wani mugun nufinka a inda kake ,karka dawo gareni da mugun nufi ka barni na cigaba da rayuwa babu kai domin dawowarka da wani sabon  salon yaudara  ko mugun nufi  zai sa nayi maka abinda har ka mutu bazaka daina mamakina ba abun bazai mana kyua ba adamcy ." "shine kawai abinda yake ta yawo acikin kwa kwaluwarsa "why sweetheart ?me yasa kika kasa fahimtata instead ki barni tunda na nuna bana son auren nan ya allah ka kawo dalilin da zai sa a fasa auren nan na huta tsaki yayi inda fuskar princess keta masa yawo a cikin idanunsa da sauri ya runtse idanunshi dan a halin yanzu baya son ko tunawa daita ahankali akayi   knocking din kofar parlour'n yana daga kwance yayi nisa cikin tunani shiru bashiri yana jiran a bashi izinin shiga amman shiru  daya daga cikin masu tsaronsa ya dan leko dakin yana ringine amman bai bawa mai yin knocking din izinin shiga ba ." Dan haka ya dawo ya bawa bashir izinin ya shiga dan ya rigada yasan ko waye bashir  din a wajensa kuma tun safe ya sheida masu zuwansa,bash ya shigo parlour'n bakinsa dauke da sallama shiru mr ata bai amsa ba ."bashir ya zauna yana fuskantarshi sai dai kusan mintuna goma mr ata bai bude kwayar idanunshi akan bashir ba haka zalika bai ma san da shigowarsa ba  ya yunkura ya tashi ya isa inda mr ata yake ya dafa shi a matukar zuciye ya bude idanunshi da niyyar saukewa wanda ya dafa shi maseefa ganin amininsa yasa ya sauke naunayen ajiyar zuciya "kai mutumina meke damunka ne haka duk kayi wani irin ina lura da kai tunda ka sauka a qasar nan kake yawon tunani ?bashir ya fad'a tare da zama a gefensa kallonsa yayi zuciyarsa na zafi "yaushe ka shigo kuma me yasa ka shigo baka nemi izinina ba ?" Ajiyar zuciya bashir ya sauke sannan yace "kai dai anyi dan iska ina tmbyarka kana tmbyta yanzu dai fara bani amsar tmbyata tukun sai na baka taka numfashi ya sauke mai zafi ,kai dai bari kawai ina cikin rudani auren dole zaa min , bashir ya zaro idanuwa "Ata din dana sani zaawa auren dole ? no no it can be possible ya qarasa mgnr yana dan murmushi,kai ma dai ka fadi haka wai kamata zaayiwa auren dole kamar muna in does day nan ya kwashe komai ya fad'a ma bashir har da alqawarin da yayi wa mami , wallahi bana son yarinyar  nan kiyayyarta  bazata misaltu a zuciyata ba gbdy zuciyata bata bugawa idan na ganta, kaga mutuwa kusa kenan dariya sosai bashir yayi tuni mr ata ya kule kallonsa yayi rai a bace ,kaji min dan iska ina fad'a maka damuwa kana mun dariya to wallahi maza tashi ka bar nan yanzu ." "Sorry my friend hukunci mami ne ya bani dry kai da yanzu bata zatar da wannan hukunci akanka ba haka zaka qare rayuwarka kana yaudarar kanka shin zaka tuna kafin mu rabu da kai last na fad'a maka wannan yarinyar mafarkinka ba mutun bace sannan ka guji ranar da mahaifiyarka zata gaji tayi maka irin wannan auren kace bazatayi ba ?kaso wannan yarinyar marym karkazo hannu kazo kana sonta ta samu dama akanka." " dan Allah bash ka bar wannan maganar ka bar kawo min maganar zan sota ya zaayi na sota ma ?"mr ata ya fad'a cikin tsananin damuwa zan cigaba da rayuwata haka zan bar zuciyata babu kowa cikinta yadda zan cire soyayyar princess a zuciyata bazan bawa kowace mace damar shiga ba sai dai na qare rayuwata haka ,haka dai suka cigaba da tautaunawa bashir na bashi kwarin gwiwar yayiwa mahaifiyarsu biyayya ." Ana sauran kwana hud'u mr ata ya dawo ya kira mami ya sheida mata ai kuwa taji dadi har ta kasa boye murnar ta  , ta tattara kan masu aikinta domin su gyara gida da kuma sauya wasu abubuwa dake gidan sakamakon dawowar dan lelenta jirgin karfe hudu daidai na yammaci ranar lahadi zai sauke su tare da babban yaronsa da masu tsaronsa da sukayi tafiyar tare dan haka mami ta hana kowa sakat acikin gidan daga masu aiki har maryama babu wanda ya zauna suna tsaye bisa kafafunsu duk da tun jiya sun yi redy wasu abubuwa da suka san yafi bukata maryam tana wanke hannunta tana qoqarin fitowa daga kitchen sai ga mami abakin kofar kitchen din suka hadu mami ta kalleta da murmushi kwance a fuskarta ." "tun daga parlour nah na biyu nake ji kamshin girki fatan kice kikayi komai da kanki ?Allah mami ki tambayi tabawa duk ni nayi su kawai wanke wanke sukeyi gsky idan duk wannan kamshi daga hannunki ne naji dadi Kwarai da gaske dan tun banga abincin ba miyona ya tsinke muje kawai na fara da jin dandanon girkin kafin adamcy ya qaraso ,ai mami idan kikaci sai kunnenki yayi rawa ,haka né hajiya duk ita tayi gsky babu abinda muka tayata sai wanke kwanuka ,hakika tayi qaqari sosai ." "ai kam yau zan bada maki mai yawa dan tun daga parlour'na nake jiyo kamshi muje suka koma cikin kitchen din tare mami na bude manya kuloli kula farko alkubus da miyar naman rago kula ta biyu shimkafa bastimatic ce da teaw wanda yaji naman kaza sai kula ta uku wanda sakwara ce da miyar egusi wanda yaji ganye ugu da nama da busashen kifi "masha allah mami ta furta a fili "lallai adamcy nah zai ci dadi ,yau kam nasan har da santi zai yi murmushi mrym tayi tana cewa" allah yasa mami allah yasa ya yaba da girkin tayi maganar cikin sanyin murya ,karkiji komai diyata zai yaba ta fada tare da daukar qaramin spoon ta dibi miyar farko ta kai bakinta ". "Woww miyar nan tayi dadi sosai daya bayan daya ta dinga d'an dana miyar tana lumshe idanunta tana santi da yabawa maryam din ,da gaske mami tayi dadi?sosai tayi kawai abu daya ne zan gyara miki shima idan mutun ya kasance mai son cin maggie dayawa a abinci ne bazai ta'ba miki gyara ba "meye shi mami ?ta tmbyeta cikin tsanani damuwa jikinta har rawa yake ,ki natsu ki kwantar da hankalinki ba wani abu bane maggie zaki rage zubawa miya dayawa ,tun daga tafashe kinsa maggie kuma kinga zakiyi amfani da ruwan miya wajen hada miya dan haka baki bukatar zuba maggie dayawa acikin miyarki yanzu kenan maggie yayi yawa ta fada cikin tashin hankali?bawani yawa bane kawai na gyara miki ne dan gaba idan hannunki yana zarcewa a maggie matsala ne." " wannan ne kawai maggie yayi yawa ko duka miyar né ?Ki kwantar da hankalinki kusan duka ne amman karki damu aa mami dole na damu dan wallahi idan yasan ni nayi na shiga uku gara kawai na sake wani ."What ? "mami ta furta tana dubanta babu abinda zaki sake anan haka zai ci  har yayi santi ta sauke numfashi tana cewa "amman mami karki ce ni nayi kice kece kikayi dan allah idan yasan ni nayi wallahi karshenta bazai ci ba ,mami ta kalli agogon dake hannunta kinga karki damu muje ki shirya dan jirgin adamcy ya kusan sauka nima bari nayi sauri na shirya kafin a dauko shi yazo yana yiwa mutane naci dan tun jiya yace bazai ci komai ba sai ya dawo ." Mami ta bawa masu aikinta dake tsaye umarnin su fito da kulolin zuwa dinning suna shirya dinning suna hira suka jiyo sallamar hindu gabdaya suka amsa mata kallo daya mami tayi mata ta dauke kanta tana sanye cikin wani irin ado tasha tamkar wacce zata turakar miji cikin ratsatsen lace maron colour touch of green dinki yaji stone ta koina dan hasken fatarta ya sake haskawa sam bataji dadin ganinta ba bata qaunar abinda zai kawowa adamcynta matsala arayuwarsa ta fada mata tayi hakuri dashi ta nuna a fuska duk wata hanya da zata nuna mata ta hakura dashi tayi amman sam kamar bata fahimta ." "Mami fatan kin shirya muje tarbo ya adamcy ,dawa kenan zakuje?hindu tayi shiru tana dubanta ,ai wannan sai dai matarsa ni kam na yafe ,tô shikenan ni bari naje AirPort tarbosa "allah ya tsare sai kin dawo tace ameen mami ta fada haka né dan tasan halin kayanta bata són taje ya disgata cikin mutane amman hindu ba irin mutunen nan masu fahimta bane ."Mami tana kallonta ta juya tana rausaya cike da farinciki kamar wacce akayiwa albishiri da zata mallakinsa taso ta tsaidaita amman ta barta sai da hindu ta fice daga falon sannan mami ta dawo da kallonta ga maryam zan shiga dakina na shirya kema idan kin gama kije ki shirya mrym tace "tô! Sai data tabbatar da komai yayi daidai sannan ta wuce dakinsu inda ta iske nana hauwa'u kwance tana karanta wani hausa novel acikin wayarta mai suna cutar da kai ,har yanzu kina kan karatun nan sister?ina kai ko akwai abinda zan miki né ?bazakiyi shirin tarban ya adam ba gashi har ya kusan sauka koma mace ya sauka ?ta qarasa mgnr tana duba makeken agogon dake manne da bangon dakin ,wannan kuma kece zan tmby dan ni tsakanina dashi sannu da zuwa né ke dai kije yi maryam bata sake cewa komai ta shige bayi Wanka tayi ta fito ta goge jikinta ta zauna akan kujerar mirrow ta d'auko mai ta fara shafawa ahankali haka nan take jin faduwar gaba mai tsanani ,kinyi shiru bazaki shirya ba sai ya shigo mami tazo tana daga miki hankali ta tsaida hannunta akan damtsen hannunta tana kallon nana hauwa'u ta cikin mirrow sai data numfasa sannan ta mike wallahi sister haka nan nake jin mummunar faduwar gaba jikina har rawa yake gabadaya bana cikin natsuwata tunda mami tace zai dawo yau na tsinci kaina cikin damuwa bare gashi na kwabsa kadan a girki mami tace Maggie ya dan só yayi yawa tsorona kar ya tambayi wanda yayi tace nice ta qarasa magana tamkar zata zubar da hawaye ." "gsky kina tare da aiki marsi wai shi yaya dodo ne da Kike jin tsoronsa haka ?numfashi ta fitar da karfi ta mike tana cewa "ban san me yasa wani lokacin kike manta kiyayyarsa gareni ba ,ki daina cewa kiyayya yaya baya kinki halinsa né km kowa yakewa amman kema zuwa yanzu ya kamata ki saba dan da nice dana maidashi man shafawana ,uhm baki san halin wannan yayan naki ba idan yana kin mutun halinsa dabam kiyayyarsa dabam ta fada tana taku har ta qarasa in da Kwabar kayanta yake ta ciro doguwar rigar lace mai shege kyau da tsada sabuwa ce bata taba sakawa ba sai a lokacin bata tsaya yin wata doguwar kwaliya ba ta zauna zaman jiran kiran mami ." Tana zaune ta jiyo hayaniyar shigowar motoci haraban estate din ahankali cikin sanyin jiki ta mike ta isa jikin window dakin ta dage labule ahankali idanunta ya sauka akan motocinsa da motocin ss guda shida inda masu kula da lafiyarsa mutun uku suka fito da sauri mutun daya ya bude masa murfin mota ya fito ya tsaya bisa kafafunsa ." A natse ya soma taku mutane suka sakashi a tsakiya wanda dayawan su yan tarbosa ne yayi matukar kyau sanye cikin riga da wondo na black suit mai tsaida da sheki yayinda sumar kansa Ke kwance luf yana zuba sheki alamun yana samun kulawa haka zalika farinsa ya qara fitowa alamun yana cikin koshin lafiya sai wani ipod dake manne da kunnensa na jin mgn gaba daya mutanen dake tare dashi ya zartasu a komai hasken fata da tsawo cike da Kamala tana tsaye suka gama wuce wa ta lumshe idanunta na second biyar sannan ta bude idanunta ahankali suka sauka akan hindu tsaye fuskarta murtuke cikin bacin rai aranta tace ko me ya bata mata rai ita da tayi kamkamba da shishigin zuwa tarbosa?." "Uhm yanzu haka halin nasa yayi mata nan wani murmushi ya bayyana akan lip's dinta haka nan ta tsinci kanta da jin dadin yanayin dataga hindu ai kin iya shishigi kuma karshen masu irin halinki kenan ajiyar zuciya ta sauke tana sakin labule ta juyo idanunta cikin na nana hauwa'u,"kin gama kallonsa ." "Shi wa ?" "Ya adam !ta bata amsa atakaice,kai haba sister kai haba sister ko gsky Ke na gama karantarki fa kema kin fad'a sawun masu son ya adam kar muyi haka dake sister ."allah ba wasa nake ba kina son shi son ..." nan da nan idanun maryam ya cika da hawaye nana hauwa'u ta zaro ido ke fa matsalata dake kenan saurin kuka kamar wata qaramar yarinya daga na fadi gsky ." "Aa sister wannan ba gsky bace taya zaki fada min haka ?me yasa zan so mutumin da bai sona? nana hauwa'u ta sauko daga saman gado ta dafa kafadanta zaku so juna wuyarta ayi aure muamular miji da mata ya sha bambam da rayuwar waje fatanmu allah yasa ya sauko da wuri ." " sister bazai sauko ba kema Kinsan halinsa yana son mutun ma ya ya qare bare ni da yake jin Kmr ya kasheni ,ni ban san ya zanyi da rayuwata ba gashi kowa son shi yake kalli hindu fa har airport taje tarbosa " kinga matsalata dake kishin maseefa ." "allah ba maganar kishi bane sister da me zan ji da rashin son da bai me ko kuma da yammatan dake sonshi "kyale wannan mahaukaciyar kema Kinsan bazai sota ba dan hk ki saki ranki kisawa ranki kece sauraniya a gidansa in sha allahu kece glashin idanunsa naunayen ajiyar zuciya mrym ta sauke sai lokacin taji natsuwa ajikinta tana damke hannun nana hauwa'u cikin nata "na gode da addua Sister Allah yasa hakan ya kasance ." Gyada kai nana hauwa'u tayi ta zare hannunta ta nufi kofar fita "ni na tafi tarban babban yaya sai kin fito mami na tsaye a tsakiyar parlour'n fuskata dauke da murmushin farincikin dawowar tilon danta yana gama shigowa tsumammun idanunshi ya sauka akanta cikin shiga na alfarma fuskarsa kamar koda yaushe babu annuri amman duk da haka yayi farincikin ganin sweetheart dinsa cikin koshin lafiya atare suka soma daga kafafuwansu domin isowa ga juna suna gama qarasowa yana qoqarin durkusawa mami tayi saurin rike kafafunsa ta rungumeshi ajikinta tana shafa bayansa "sweetheart mun samuku lafiya ?lafiya lau adamcy nah da fatan ka dawo lafiya ? ajiyar zuciya kawai ya sauke ta zaresa ajikinta ta qarasa dashi kan kujera mai zaman mutun uku ta zauna a kusa dashi tana rike da hannunsa rayuwarta né adamcy tana matukar qaunarsa shiyasa yake mata abinda yaga dama ." nana hauwa'u tai masa sannu da zuwa ya amsa da kyar yana zaune mutanen gidan suka dinga shigowa daya byn daya suna masa sannu da zuwa ita kam maryam bata fito ba tana daki ta kwanta rigingine jiran mami ta nemeta mami bata nemita ba har akayi sallah magrib da ishai sai data ga babu alamun mutanensa a falo dashi kansa ata ta fito ta zauna tare da nana hauwa'u da mami aka cigaba da hira daita " Karfe tara daidai mr ata ya sauko cikin blak long sleve da farin wando na shan iska sai kamshi turarensa na Reed ke tashi akoina ajikinsa ya samu waje ya zauna a daya daga cikin kujerun falon yana duban mami dake zaune tana waya nana hauwa'u ta sake gaishesa ya amsa aciki, ganin haka yasa maryam ta bud'e bakinta da kyar cikin in ina "ya..ya sannu da zuwa da fatan ka dawo lafiya ?"banza yayi mata tamkr bai ji abinda ta fada ba nan kuwa yajita sarai sai ma ya dauke idanunshi akan mami ya maida kan wayarsa numfashi ta sauke da karfi ta kama bakinta ." Bayan Kmr mintuna shabiyar ya motsa lip's dinsa da kyar" sweetheart yunwa nake ji cikina har zafi yake murmushi mami tayi allah shiryeka adamcy kullum girma kakeyi amman sai ka dinga abubuwa kamar yaro ya yatsina fuska a gaban uwata nama fi yaron goye ,allah ya shiryeka me zakaci akwai alkubus akwai rice and stew akwai sakwara "rice kawai ya isa okay maryam maza zuba masa ki daura a tray ki kawo masa nan "bana bukatar daga gareta kisa wani yayi min " "Bangane  haka ba ? yayi shiru kawai yaki cewa komai duk bakinsa mgnr yake son yi  "zaka fara ko daga dawowarka?yaruwarka kuma matar da zaka aura ce kakewa haka ? Allah adamcy ka fita cikin idanuna  daga zuwanka zaka fara da bata min rai kuma ya mukayi da kai ?bance ka bar duk wani mugun nufinka a inda ka baro  ba ?"yi ...ha ..kuri sweetheart ya fad'a tare da dago kanshi nan take kwayar idanunshi ya shiga cikin na mrym wani mummunar faduwar gaba ya risketa saurin cire nata tayi ilahirin jikinta na daukar rawa "maryam jeki yi abinda na sakaki a tsorace muryarta na rawa tace "to! ta juya ta shige kitchen domin dauko trya Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗    MAR'ADAMS    💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.     Page 22 Saurin mikewa tsaye mr ata yayi ya haura samansa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ransa a dagule yake taka step dan idan akwai yarinyar daya tsana anan duniya to wannan maryam din ce, ji yake kamar ya kasheta ya huta da muguwar tsanar da yayi mata ,mami tabi bayansa da kallo har ya qarasa sauka akan step tana jin zallar bacin rai da bugun zuciya yana shiga d'akin ya cire rigar jikinsa da singlet ya cila kan kujera ya shige bedroom dinsa ." koda maryam ta fito daga kitchen taga wayam babu shi babu alamunsa a inda ta barshi ta kalli nana hauwa'u ta kalli mami fuskarta da alamun tambaya "zuba masa abincin daya buqata ki bishi d'akinsa dashi maryam tai saurin zaro ido waje ,cike da matsanancin tsoro ta shiga girgiza ma mami kai yayinda yanayin bugun da zuciyarta yake ya qaru, yanayin tsoratanta kuwa sai ya baka mamaki idanuwanta ta runtse jin tashin hankalin daya kusantota ." nana hauwa'u ta mike daga inda take zaune ta qaraso inda mrym take tsaye rike da tray mrym bata ankara ba sai jin mutun tayi tsaye kusa daita ta dafa kafad'anta ta bud'e idanuwanta da kyar akan nana hauwa'u "common sister ki sanyawa jikinki natsuwa ki rage wannan tsoron please ".ta fad'a tana riko hannunta ta fara tafiya daita."    "Sister bazaki gane bane wallahi ina matukar jin tsoronsa, na sani yanzu dai kiyi abinda mami tace babu abinda zai iya miki keda kike da mami a hannunki ai sai yadda kikayi dashi, da taimakon nana hauwa'u ta had'a komai a tray ta rakata har samansa adaidai bakin kofar shiga parlour'nsa taja ta tsaya tana cewa "ki shiga da kafar dama sannan ki sanyawa jikinki jarumta daga nan ni zan koma "haba sister mu shiga tare mana Kinsan fa bani da wannan jarumtar "rufa min  asiri sister kar ya sauke fushinsa akaina gara ke idan yayi anything stupidty zai had'u da mami ni kuwa fa ? komai yayi min yaci lafiya ,kafin mrym tayi wani yunkuri yin magana har nan hauwa'u ta juya ta soma tafiya tana waiwayenta tana karfafa mata gwiwa "    Cikin natsuwa ta tura kofar parlour ta shiga bakinta d'auke da sallama taga baya parlour ta had'iye wani yawu daya tsaya mata a makoshi tana qoqarin daidaita numfashinta da natsuwarta ,ahankali ta ajiye tray hannunta akan center table din dake ajiye ta nufi kofar bedroom tayi knocking ahankali saboda tasan baya són hayaniya jin shiru yasa ta sake knocking amman still shiru ". ganin kar abincin yay sanyi ta sake qarawa kanta laifi a wajensa yasa ta murd'a kofar cike da tsananin tsoro da tashin hankali ta shiga idanunta a runtse tare da rufe kofar ta sunkuyar da kanta kasa tana jiran ya balbaleta da ruwan maseefa amman taji shiru .jin shiru yasa ta d'agowa taga baya cikin d'akin wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke , kai tsaye kwakwaluwarta ta bata yana cikin d'ayan d'akinsa ." Ahankali ta juya ta fito daga cikin d'akin har tayi taku uku domin isa bakin kofar d'ayan d'akin sai kofar d'akin ya bud'e ya fito daga shi sai gajeren wondon dake sanye ajikinsa a matukar tsorace take kallonsa da kallon murd'add'en jikinsa  dake sheki tsabar kulawar da yake samu ."wani wulakantaccen kallo yayi mata mai had'e da harara yasa a tsorace ta d'auke kwayar idanunta akan shi tayi saurin juya masa baya tana neman afuwarsa "am really sorry mami tace na kawo maka abinci .." Tsaki yaja a fili yana kallon bayanta daga inda yake tsaye yana iya hango tashin hankalin da take ciki ya rasa me yasa sweetheart take masa hk ?ya guji cin abinci daga hannun yarinyar amman sai da tasa aka biyosa d'akin dashi kmr dole sai yaci abincin hannu ?"yayiwa kanshi tmby yana mai sake jan wani tsakin ." ta gefenta ya raba ya wuceta ya shige d'ayan bedroom dinsa dan  ganinsa tsayawa ma inda take asara né ,kusan mintuna shabiyar ya sake fitowa a tunaninsa ta fita amman abun  mamaki tana nan tsaye  Kmr wata  tsohuwar soja , ya ja tsaki  ya zauna akan kujera  ya kunna computer dinsa ya shiga yanar gizo fannin kasuwancinsa . ta cigaba da tsayuwa sai dai ta rasa yadda zatayi masa magana  yaci abinci sai ta motsa  labbanta  zata  masa magana amman  tsoronsa ya hanata  ." tana  tsaye  aka fara kiran wayoyinsa yana amsa kira ,duk abinda yake ko ajikinsa dan babu ruwansa da tsayuwarta ya cigaba da abinda yake tana kallonsa ta kasan idanunta ya kashe computer ya kwashe wayoyinsa ya d'auki rigarsa ya rataya a kafad'ansa ya fito ya barta tsaye ya sauko kasa har lokacin mami na zaune  ita  kad'ai ." Ya zauna batare da yace komai ba , mrym ba tayi fushi ba dan daman ita ba mai saurin fushi bace , kafin kaga fushinta da wahala sai dai akwai zuciya ,zuciyar ma yana dadewa bai motsa ba amman idan ya motsa babu kyau ,ta d'auki tray data shigo dashi ta fito, a parlour ta iskeshi zaune yana shan kamshi inda kasan wani jinin sarauta yana daddana waya ,har gabansa ta qaraso ta ajiye tray din akan table din dake gabansa ta bud'e masa kular abinci cike da tsoro dan kar tayi laifi ta d'auki ruwan dake kan tray ta juya a natse ta shiga kitchen ta bud'e fridge ta canza masa da wani ruwa mai dan sanyi kad'an tazo ta ajiye masa "ga abincin ! Biyayyarta na matukar burgesa domin shi din mutun ne mai tsananin son ya juya duk wanda yake karkashinsa  most especially mace , yanayin tsoronsa da biyayyarta yayi ,matsalar dai baya  sonta , mami  dake zaune  kuwa kallonta kawai take yadda take komai a natse cike da kulawa da tsoro  da gudun kartayi laifi amman sam adamcy bai damu  da duk abinda take ba hasalima hankalinsa da natsuwarsa basa gareta ." duk yadda mami take són mrym din ta kasance a yanzu tayi babu wani abu d'aya saura ga dukkanin alamun zata kular mata da adamcy yadda ya kamata , daman kuma irin macen data kamacesa kenan mai tsananin biyayya da hakuri  da gudun 'bacin ransa  saboda yanayinsa ,maryam bata tsaya ba ta nufi d'akinsu inda ta iske nana hauwa'u kwance tana chart, ita kam zama  tayi shiru cike da damuwa ita kadai tasan halin damuwar da take ciki duk yadda take son waya a wannan lokacin ya d'an fara fita kanta , dan ko ta d'auki wayarta dan shiga what's app bata 'barkata  komai ,hakan  friend's dinta  zasu yita mata mgn har su gaji su hakura ." Mami ta tashi daga mazauninta ta dawo kusa dashi ta zauna ta riko hannunsa d'aya cikin nata tana dubansa cike da kulawa dan bazata iya fushi dashi ba , kuma tasan muddin ba itace ta tursasa masa ba haka zai kwana da yunwa, kuma ta rigada tasan bai ci komai ba dan muddin yana qasar baya ta'ba cin abincin kowa sai nata"."look at me adamcy ,ya bar abinda yake yi ya kalleta Kmr yadda ta bukata ,look at the time adamcy ta nuna masa makeken agogon dake manne a bangon  parlour'n "lokaci na tafiya tunda ka shigo gidan nan ruwa kawai ka sayanwa cikinka "bai kalli agogon data nuna  masa ba bare yasan lokacin daya d'auka bai sayanwa cikinsa komai ba sai ma d'auke idanunshi da yayi akanta yana hura hanci ." "Tsawon wata biyu bamu had'u ba sai kuma tayi murmushi ganin yadda ya qara had'e girar sama data qasa  kamar wani qaramin yaro , ta d'aura d'ayan hannunta akan hannunsa dake cikin nata "me yasa baza kayi abinda zai faranta ran sweetheart dinka ba ? Ta numfasa irin nasu na manya kana ta cigaba da magana "koda yake ina son wannan fushin naka ban sani ba ko dan yana qara maka kyau ne ?" lumshe tsumammun idanunshi yayi batare da ya juyo ya kalli mami ba yace "nima ina son fushina ina son yadda Allah ya halliceni " murmushi mami ta sake yi "to ai shikenan daman ai mai hali baya gudun halinsa yanzu dai kaci abinci shine abinda nafi buqata "na koshi ".ya fad'a atakaice yana fesar da numfashi . mami ta juyo da fuskasa gareta ta dungure masa kai tana cewa "allah baka isa ba ,duk yadda aka sha wahala akayi girkin nan kace ka koshi ,allah sai kaci idan ba haka zanyi fushi mai tsanani da kai sai da mami ta had'a da marairaicewa sannan ya fara cin abinci daga hannunta " a ranta tace hukuma sai da rarrashi ."mami girkin nan kamar ke kikayi Kmr kuma bake kikayi ba?". "me yasa ka fad'a haka ?yayi shiru yana nazari sannan yace "yayi dadi Kmr naki but ya dan yi maggie kad'an ba kamar abincinki ba dan sam girkinki maggie baya yawa , kamar ta fad'a masa gskyr wacce tayi amman tasan halin yan kayanta sai ya birkice mata yanzu ta rasa gane kanshi dan haka tace" ni nayi kasan yau da gobe sai allah, ni kaina naji maggie ya d'an so yayi yawa amman ai yawan da yayi bazai hana a kasa ci ba ,shiru yayi ya tsura mata tsumammun idanunshi yana dubanta a tsanake  bai san me yasa ba sai yake jin Kmr ba gsky sweetheart ta fad'a masa ba ,dan dai yasan wacece sweet heart dinsa a fannin girki babu karya tana da matukar kwarewa tun yana yaro ya sani suna zaune ma take had'a girkinta ta tashi ." bayan ya gama cin abinci mami ta kallesa a natse kafin daga bisani ta kira sunansa "adamcy nah? ya tsura mata tsumammun idanunshi kawai yana kallonta da sauraronta "ya ake ciki da maganarku dasu sultan naji ko a waya baka sake ce min komai akai ba ?ya lumshe tsumammun  idanunshi na second biyar  sannan ya motsa labbansa yace "magana ta wuce tunda sun dawo da  makudan kadaden da suka sace "ikon allah ! account dinka suka saka kud'ad'en ko kuwa account din agc ?" no  Ibrahim  suka kai wa  cheek amman ya fad'a min fahad ne ya kai masa bayan sultan da salim sun qare masa zagi . "Zagi kuma ?! Ya lumshe mata ido kawai alamun "eh ! "Wannan abu  gsky bai yi dadi ba Allah sarki ibrahim bawan Allah to shi meye nashi da zasu zagesa ? a cewarsu yayi masu munafurci alhalin ni bashi ya fad'a min ba hasalima bai sani ba a bakina yaji ,"allah sarki bawan allah ,allah dai ya kyauta kawai , Allah km ya shirye su shiri na addinin muslinci , bancin company agc ya tsaya da kyau nasan da zuwa yanzu an rufeshi kullum daga anemi  kud'ad'e a rasa sai a nemi kaya arasa kuma duk masu yi suna gindinmu ." "sosai kuwa shiyasa yanzu gbdy zan tattara hankalina zuwa agc kusan ma nan zan fi karfi a sati sau uku zan dinga shiga sauran ranakun kuma zan dinga leka wanda suka samu acikin companies dina , hakan yayi daidai allah yasa mu dace yace "ameen ! ya fad'a tare da d'aukar remut ya canza channel zuwa  aljazera. Mami  tayi  shiru tana kallon tv can ta waigo inda yake zaune idanunshi na kallon tv , kallonta yayi ta gefen ido kafin ya  maida idanunshi sosai  kanta ya dage mata girasa daya alamun tambaya ,numfasawa tayi sannan ta soma magana "nace bakaga  ya kamata ka dinga d'an jan yarinyar nan mrym ajiki ba ? "Janta  ajiki kuma kamar wata yarinya qarama ? ya fad'a cike da jin mamaki " ba maganar kamar wata qaramar yarinya bane yana da kyau ka jata ajiki ta yadda zata sake da kai idan ma ta kama ka dinga kiranta hira domin ku samu fahimtar juna ?"Wani fahimtar juna kuma ya saura sweetheart ? yarinyar nan tasan halina tasan abinda nake so da wanda bana só ." "duk da haka dai ya dace ku dinga zan tawa "gsky sweetheart bana jin zan iya, akan na kirata zance gara a fasa auren kawai dan nasan bazan ta'ba iyawa ba ,taya ma zan fara ?"mami tayi murmushi irin nasu na manya tace ,idan baka san ta inda zaka fara ba ai sai ka tmbyi abokanka masu aure sa koya maka ta inda suka fara , idan kuma kana jin kunyarsu ne sai ni na koya maka ko ba shikenan ba tunda dai ni nasan baka jin kunyata ". tunda mami ta fara magana ata ya sanya hannunsa a tsakanin hancinsa da bakinsa kawai yana kallonta "ko na kira maka ita yanzu ?"mrym ! mami ta kwalla ma mrym kira "oh my godness god , haba sweetheart wai me yasa kike min haka ne ?kai ma me yasa bakasan kayi abinda ya dace ba ?"allah sweetheart bazan iya kira kowace mace da sunan zance ba " Allah ko ?! ya dage mata girasa d'aya alamun "Eh! ai kam dole ka kasa iyawa tunda ka zama tuxuru fuskarsa a had'e yace "sweetheart ai itama yarinyar taki tsohuwa ce wallahi , baki ga duk kashin tsufa ya bayyana ajikinta ba ? mami ta dan ware idanunta sosai "akwai wani kashin tsufa ajikin mutun ne ?ta tmbyesa dry na kufce mata ." Wani sanyi dadi yaji aransa yace "sosai ma kuwa akwai ,to kai taya akayi ka gani ? kodai adamcy ya kamu ne yana so yana kaiwa kasuwa ?bai ce mata uffan ba sai dai a zuciyarsa yace " allah ya tsareni ,ata ya kamo hannun mami cikin nashi yana marairaice murya "sweetheart ! ya kirata sunanta tana dariya tace "ina jinka adamcy nah "dan girman allah laifin me nayi miki da kika zabi ki hadani da yarinyar nan aure ?".   "taurin kanka ne ya jawo had'a zumunci "amman sweetheart baki ga rashin dacewarmu ba ni dogo ita duwaf ? ban son wulakanci adamcy yarinyar tawa ce duwaf ?ta fad'a tana had'e rai ."ai yar daidai kusa da kafad'ata kamar zata fi dacewa dani akan mace guntuwa ?," idan ta kai maka daidai kafadanka cin tsawon zakayi ?ta fad'a tana kunshe dryata yayi shiru kawai yana zare hannunsa cikin nata."abinda bakasani ba dogo nmj da mace mara tsawo sunfi dacewa , karka damu da rashin tsawon maryam nagartata zaka duba ,Kmr yadda na sha gaya maka mrym ce daidai da halinka sannan zata haifa maka ya'ya na gari zuqa zuqa ." "Sweetheart sai da safe yayi ma mami sallama ya mike tsaye da rigarsa  akafad'a dan yasan bazata barsa ya huta da maganar yarinyar ba , kai tsaye ya wuce saman d'akinsa wanka ya fad'a zuciyarsa  cike da tsananin mamakin maganar mami "wai ya kiranta zance idan ya kirata yace mata me ?yaja dogon tsaki ,aikuwa muddin sai ya kirata zance sai dai a hakura da auren ,byn wasu mintuna ya fito yana goge sansar jikinsa , byn ya gama ya qarasa inda turarukansa suke ya dauki bodyspare ya feshe ilahirin jikinsa sannan ya saka gajeren wondo iya cinyarsa da riga fara sol ya kwanta yana mai jin tausayin kansa  ." "ya rasa me ya tsarewa mahaifiyarsa da take son ta had'ashi aure da wannan guntuwar yarinyar mai siffar wada yarinya sam babu fasali  , yasan muddin ya auri maryam rayuwarsa da farincikinsa zasu yi kasa ,kai gbdy komai nashi zai canza kuma yasan har da walwalansa ,ya gyara kwanciyarsa tare da janyo pillow ya d'aura asaman ruwan cikinsa ya rungume tsam tsam yana  jin kamar princess ce duk da yana son mantata amman duk sanda zai yi bacci sai yayi tunaninta sannan bacci mai dadi yake d'aukarsa " a yadda yake jin felling din yarinyar yayi imani zai had'u daita sai dai yaushe ne ? a ina ne ? bai sani ba , ahankali ya dinga juyi akan katifar yana jin felling dinta mai tsanani yana sauka a sansar jikinsa ,ji yayi kamar anyi kissing din lip's dinsa ya d'an bude idanunshi yaga wayam babu kowa sai shi kad'ai a d'akin, ya sake maida idanunshi ya runtse sai dai a haka yake jinta kusa dashi kuma yake imaginetion din komai ." sake janyo pillow yayi ya rungume tsam yana jin tamkr itace ajikinsa , ahankali bacci ya d'aukeshi cike da mafarkinta wai gata ta hau saman qirjinsa ta kwanta tana shafa qirjinsa zuwa kan nipples dinsa wani irin d'auke numfashi yayi da karfi dan alokacin da'ace akwai wani a d'akin dan dole ya fahimci yana cikin wani hali .wani irin juyi tayi har rigar dake sanye a jikinta ya zame wanda daman dashi da babu duk daya ganin abinda yafi so ajikinta wato dukiyar fulaninta ya tashi zaune acikin mafarkinsa ya rike hannunta gam cikin nashi yana murzawa "my princess ina kika shiga two day's baki zo min ba ? banje koina ba ina tare da kai ,tayi masa mgn tana kai harshenta qirjinsa ta fara lasa wani irin abubuwa yake ji suna yi masa yawo a gbdy ilahirin jikinsa ." tsigar jikinsa gbdy suka mike yayinda jijiyarsa ta dinga harbawa da sauri sauri rungumota yayi sosai ya sakata a tsakiyar qirjinsa hancinsa ya cusa cikin suman kanta daya zubo har gadon bayanta ahankali ya dinga shakar kamshin jikinta tare da lumshe ido yana jin wani sanyayyen abu a zuciyarsa". "kina sona ?ta gyada masa kai alamun "eh !,to ki taimaka ki bayyana min kanki tun kafin ayi min auren dole ,wani bayyana maka kaina zanyi byn gashi muna tare ?ni da kai muna tsananin son juna ko ka manta tsawon lokacin da muka kulla soyayya a tsakaninmu ?ya gyada mata kai ," alaka soyayyarmu mai karfi ce domin kai din nawa ne na har abada ,sake matsota yayi sosai ya kai hannunsa kan karan hancinta yayi kasa da hannunsa har zuwa kasan marata , yana jin lokacin data sauke numfashi zuciyarta na bugawa da karfi hakan yasa ta shige masa tun daga wuyanta ya fara shafata itama tana shafashi ,kamkameta yayi ajikinsa ya had'e bakinsu waje daya yana wa bakin wani irin tsotsa na fitar hankali ." Bangaren marym itama kwance take tana faman juyi akan katifa dan ta kasa runtsawa tana saka da warwara kwalkwaluwarta na sake nitso cikin kogin tunani ta yadda  zatai rayuwar aure da mutun irin mr ata ,mutumin da baza tace ga ranar data ga murmushinsa ba ,hasalima fuskarsa koda yaushe a had'e take tmkr hadari juyi kawai take tana tunanin abubuwa dayawa akan aurenta dashi bai sonta ,gashi tunda akace ita zai aura bata sake samun isashen bacci ba kullum da abubuwan da take facing ,sai ta dinga jin  kamar ana farautarta, wani lokacin idan ta runtsa idanunta sai taga mutun akanta ana qoqarin caka mata wuka da zarar ta bud'e idanunta ta kunna wuta sai taga wayam babu ko alamun mutun dan wani lokacin tashi take tayi alwala ta gabatar da sallar nafila. yayinda take nan kwance cikin tsananin tunani da fargaba shi kuma mr ata yana can duniyar  mafarkinsa ."ajiyar zuciya ta sauke ta kalli nana hauwa'u dake sharar baccinta hankalinta  kwance "allah sarki sister kin huta, kina rayuwarki hankali kwance baki da wata damuwa ,ya allah kasa auren yaya adam arayuwata alkhairi ne ta furta hakan a fili ,ganin har kusan karfe biyu da wasu yan mintuna na dare bata runtsa ba ga gari ya dauki shiru sosai baka jin motsin komai ,taji kamar ta tashi taje tayi alwala ta roki Allah alkhairi daga cikin alkhairun dake cikin dare amman sai taji ta kasa tashi domin alokacin idanunta sun fara mata yaji alamun bacci ahankali bacci barawo ya d'auketa ." cikin bacci mrym taji numfashinta baya sauka yadda ya kamata kamar an danneta ta kai hannunta tana qoqarin cire abinda taji ya danne mata fuska wanda take tunani pillow ne akayi amfani dashi amman sai taji an sake danneta da iyakacin karfi ta yadda ko sautin muryar ta bazaa iya ji ba nan fa ta fara mutsu mutsu da kafafunta tana kokarin kwatar kanta cikin ikon allah ta samu nasarar rike hannun mai shi nan fa suka fara kokuwa mrym na qaqarin ta amshi pillow amman ana sake danne fuskarta ita km sai qoqarin ceton ranta take ." inda tayi wata irin zabura ta fixge pillow ta kwalla wata razananniyar qara wanda yasa gidan gbdy ya dauki sauti kuwar qararta ,nan da nan nana hauwa'u ta farka daga naunayen baccinta tana kiran sunan da take kiranta dashi " sister lafiya tare da qoqarin kunna wutan dakin ? mrym bata amsa mata ba sakamakon inuwar mutun data ga yana qoqarin ficewa daga dakin tayi wata irin sufa sai gata ta rike gefen rigar mai shi adaidai lokacin da nana hauwa'u ta samu nasarar kunna wutar d'akin adaidai lokacin mai shi tasa hannuwanta duka ta ingiza mrym da iyakacin karfinta tayi baya luuuuu sai dai ido cikin ido suke kallon kwayar idanun juna sanye take cikin bakaken kaya tun daga samanta har kasanta babu abinda zaka iya gani ajikinta sai kwayar idanunta ." a kallon da mrym take ma yanayinta ya nuna mata mace ce hannunta daya rike da wuka duk da suna kallon lokacin da tayi fillinging da wukar a tsakiyar daki ta fice da sauri tana haki nana hauwa'u ta sauko a rude ta tare bayan mrym tana rungumeta ajikinta "sister ki bita karki bari ta fice wallahi kasheni take qoqarin yi duk suka rude sai zufa suke fitarwa mrym tace "wallahi kasheni zata yi ta sake fad'a tana qoqarin mikewa domin tabi bayanta ." Mrym na qoqarin mikewa tsaye alokacin mami tare da masu aikin gidan suka shigo cikin dakin cikin tsananin tashin hankali a matukar firgice maryam ke matsu bayanin komai mami tace "Inna lillahi !a garin yaya ? ta yaya ma hakan ta faru ?wallahi mami da gaske yau kwanana ne kawai Ke gaba dana bakunci lahira daman kullum ina jin ana yunkurin kasheni ,wallahi mami nafi tsawon wata biyar ina jin ana farautar rayuwata cikin dare maryam ta fad'a cikin matsanancin tashin hankali "to akan wani dalili kenan ?"wallahi bani sani ba ta fad'a cikin muryar kuka har da shesheka nan da nan nana hauwa'u ta fashe da kuka ta kamkame mrym magana take son yi amman muryarta ta kasa fita tana kallon wukar dake yashe kasa ,sabuwa fil da alamun baa ta'ba amfani daita ba ." "Mami kalli wukar datazo daita nasan wallahi kwana ne kawai agaba yasa ta fara amfani da pillow bancin haka tana daba min wukar nan cikin bacci sai dai na farka najini a lahira, mami ta qarasa inda wukar take ta tsura mata ido muryarta a sanyaye tace auta miko min wukar data yar , ta dauki wukar ta mika wa mami " wannan kamar irin wukar daa aka kashe mubina ko ?gbdy suka sake shiga rudani nana hauwa'u ta matso kusa da mami sosai tana cewa "tabbas mami irin tace nima kallon da nake ma wukar kenan dan lokacin rasuwar mubina nima na ga wukar " . "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun daman acikin estate din nan makashin mubina take ? domin babu tantama acikin estate din nan ne domin babu wanda zai tsallake masu tsaro sama da goma sha biyar banda securities ya shigo esatate din nan lallai acikin estate din nan ake qoqarin  kashe  mrym nana hauwa'u  ta gyada mata kai alamun haka maganarta take .""auta taso min adamcy da mugun sauri ta fice daga dakin zuwa nashi bata tsaya neman izini ko sallama ba ta banka dakin baccinsa yana kwance rungume da pillow "yaya !yaya! cikin bacci yaji ana tabashi hade da kiran sunansa ya bude idanunshi cikin tashin hankali yana cewa "Lafiya ?wai kazo inji mami da sauri ya kalli qaramin agogon dake ajiye akan bedside dinsa karfe uku yanzu ta wuce saukowa yayi da sauri dan yasan koma meye ba lafiya ba da wannan tsohon dare tace a kirasa ." Jallabiyarsa ya dauka ya zira ya fito rike da gefen Jallabiyar dan ya samu damar daga kafafunsa da kyau biyu biyu ya dinga taka step yana gama saukowa ya karya zai shiga parlour'nta na biyu nana hauwa'u tace "tana dakin mu kai tsaye ya wuce bai tsaya jin dalilin ba atare suka shiga dakin cikin tashin hankali mami take masa bayanin abinda ya faru ." shiru kawai yayi yana duban mrym dake wani irin kuka bai yi mamaki jin abinda mami ta fad'a ba sannan babu wacce tazo cikin tunaninsa sai nuzla domin ta tura masa da sakon lallai idan bai amincewa aurenta ba zata ga byn mrym sai dai itama idan ta kasheta a kasheta lokacin daya ga sakon shi ko ajikinsa dan kuwa da allah yasa tayi nasara kasheta data taimaka wa rayuwarsa ita taje da Allah shi kuma ya huta da qaya." kiran mutanen estate din mami tasa nana hauwa'u ta dinga yi suna nan tsaye a daren sai ga jama'ar gidan duk suka rude iyayen mubina sunfi kowa shiga tashin hankali yayinda mrym Ke kuka har lokacin mahaifiyar mubina kam ta yarda domin kuwa me wukar tazo yi dakin maryam kuma exactly irin wukar ce babu tantama ,mami ta qaraso ga mrym dake  zubar da hawaye "me yasa zasu kashe min mrym ?ince duk esatate din nan yanuwan juna ne babu bare acikinmu ? "me yasa zaa dauki ran wani ?dan girman allah ku taimaka ku fad'a min cewar duk wannan abun dake faruwa a mafarki ne domin bana tunanin haka daga cikin ahlin nan, bana tunanin wani zai iya aikata min haka kuce min wasa ne ba niyyar kashe min mrym akayi ba ?"mrym ta sake fashewa da sabon kuka tana rungume mami ajikinta gbdy ta tsure ta nemi natsuwarta ta rasa itama mami rungumeta tayi tana shafa bayanta ." "Sweetheart kukan ya isa ki bar kuka ki kwantar da hankali kowaye acikin estate din nan zan fito dashi Ke kuma malama kin cikawa mutane kunne da hayani just keep queit I don't want to hear any sound please ya juya ya kalli wadan da suka hallara a dakin dan ba kowa ya shigo ba, dan wasu na can na bacci bama su san meke faruwa ba na kusa kusa ne suka samu damar shigowa yace "kowa ya tafi ya kwanta zai dauki mataki , ya dauki wukar ya fice . daya byn daya suka dinga fita daga dakin cike da jima min , mrym da nana suka bi mami dakinta kowace ta haye gado sai dai ba da niyyar bacci ba dan mrym kam kuka take sosai  babu abinda take gani sai mubina cikin jini shikenan da yanzu wani labarin ake ba wannan ba ,da yanzu tana cikin jini tana wannan imagenation din tana kuka nana hauwa'u kuwa  zaman dirshan tayi da mami suna tautaunawa dan bacci kam ya kaurace masu ." Washgari baba babba ya tara manya gidan tun daga kan kannensa har zuwa kan yayyansa na sama dasu dana kasa dasu dake esatate din acikin dakin na musamman da suke ganawa a duk sanda abu makamancin hk ya faru ,ya dade yana bayanin abinda ya faru a daren jiya tare da jan kunne da nasiha mai ratsa zuciya a karshe yace zaa yi bincike duk wanda aka samu da sa hannusa zaa mikasa hannun hukuma dan maganar da nake daku yanzu haka nayi report wajen police har na mika masu wukar domin a fara bincike duk hankulansu a tashe mrym kuwa har wanna lokacin kuka take aunty shahida da khadija kaf yayan mami tun safe suka yiwa gidan diran makiya jama'a kuwa sai zuwa jaje suke yi wa mami haka ma iyayen maryam sun kira yafi sau babu adadi  wuni ranar haka mrym tayi shi cikin dakin mami cikin tsananin tashin hankali  ." Bayan kwana biyu da faruwar lamarin da misalin Karfe hud'u sauran wasu mintuna mr ata ya shigo estate dinsu drivenshi na tsayawa batare da bata lokaci ba masu kula da lafiyarsa ta hukumar dss suka fito da sauri kafin ma su bude masa ya bude ya fito yana gyara zaman rigar jikinsa kai tsaye masalacin dake cikin esatate din ya nufa domin gabatar da sallah bayan ya idar da sallah ya nufo gidansu nana hauwa'u da da maryama na zaune idar da sallar su kenan sai ga diyana ta shiga hira suke kadan kadan mrym na bawa diyana labarin abinda ya faru daita "amman Kinsan wani abu diyana duk yadda muke da nuzla bangata ba kuma nasan taji abinda ya faru dani har cikin daki aka biyoni zaa kasheni amman ta kasa zuwa tayi min jaje tunanina ni kuwa laifin me nayi mata? wallahi har da kwalla nayi na rashin zuwanta saboda banyi tunanin hk daga gareta ba ." "gsky da mamaki kuma kinga ai ba haka take ba tana da kulawa da mutane most especially idan abu ya sameka na farinciki ko akasinsa amman Kiyi mata uzuri wata killa tana nan hanyar zuwa tunda duka yau kwana biyu ne da faruwar abun ,wannan gsky ne nuzla bata da haka amman baku lura a tsakankanin lokacin nan ta dan canza ba ?inji cewar nana hauwa'u"eh ta canza kam sosai ko Kinsan damuwarta ?ko daya ban sani ba wallahi na dai kula ta canza ko a yanayin jikinta zaki fahimci akwai abinda ke damunta mrym tace " to koma meye allah yafi mu sani Allah ya yayewa kowa damuwarsa Suna zaune mr ata ya shigo gbdy suka masa sannu da dawowa ya amsa Kmr yadda ya saba aciki sannan ya kalli auta yana tmbyr mami "ke auta ina sweetheart. ? "tana ciki ta shiga tayi sallah yana gama ji ya haye sama suka cigaba da hirarsu ." Bai sauko ba sai bayan awa daya sanye da shirt ajikinsa da wondo ficewa yayi bai tsaya akoina ba sai gidansu nuzla ya tmbyi mahaifiyarta ta sheida masa tana dakinta bata jin dadi a natse ya nufi kofar dakinta ya tura kofar ya shiga tare da sallama akan lip's dinsa tana ganinsa ta mike zaune tana ware fararen idanunta akanshi tayi qoqarin ta sakashi cikin nashi idon sanda yake takowa zuwa inda take tana masa duban mamaki dan bata ta'ba expecting zata ganshi har cikin bedroom dinta ba ." sosai ya dauki hankalinta yayi wani fresh yayi qara kyau kaman zane ta koina ya hadu matsalar dai shi din mugun miskili ne sai dai hakan ma qara masa kyau yake ahankali ya janye idanunshi acikin nata ya maida dakin yana qarewa koina kallo "Lafiya yaya adam da wannan zuwan naka na bazata ?" Shiru yayi yana cizan lips dinsa na kasa kafin daga bisani yace "bai kamata kiyi min wannan tmbyr ba domin kuwa Kinsan dalilin zuwana "ya fad'a alokacin daya jingina jikinsa da mirrow dinta yayi crossing leg's dinsa ya rungume hannuwansa duka a saman faffadan qirjinsa yayi da idanunshi ke kallon zara zaran yatsun kafafunsa." da kyar ta mike daga zaunen da take tana cewa "ni ban san abinda ya kawoka ba idan dai ba kazo da niyyar karbar soyayyata bane amman kafin nan me zan kawo maka ?"yayi mata banza zuciyarsa na zafi jin yayi shiru km ta rigada tasan halinsa tayi  tunanin ta kawo masa ko ruwa ne har tayi taku biyu taji ya fixgota da karfi yana watsa mata wani kallo da idanunshi dake cike taf da bacin rai gbdy taji ta fara muzanta daga kallon da yake mata taji gwiwarta tayi sanyi ."Idanushi ya tsareta dashi yana kallonta yayinda gabanta ya fara faduwa tana adduar allah yasa ba wani laifi tayi masa ba ." Sai daya gama kallonta sannan ya watsata akan katifa ta sauka da karfi sai da hantar cikinta ya kada still bai dauke idanunshi akanta ba ,nan take ta soma sheshekan kuka sannan ta fara mgn "yaya idan wani laifi nayi maka ya dace ka fad'a min amman wannan kallon naka na hargitsa min lissafi .kallonta ya cigaba da yi bai ce uffan ba har sai data gama ,cikin izza ya motsa labbansa "nasan kin san abinda kikayi sannan kuma kinsa shine dalilin zuwana " cikin mamaki da tsoro take kallonsa ya tsareta fes da idanunshi yana mata kallon banza ." ranshi a bace ya daidaita tsayuwarsa yana cigaba da kallonta kallon dake qara kashe mata jiki da tsoratarwa "hakika kin tabbatar min da abinda kika turo min a kwanaki uku da suka gabata na zakiga byn mrym , kinyi yunkurin kasheta Kmr yadda kika kashe mubina dan tace tana sona ko?"Idanuwa ta zaro gabanta na faduwa a fili tace" na shiga uku tana dafe qirjinta tare da nuna kanta "ni din na kashe mubina sannan nayi yunkurin kashe mrym ?wani kallon banza yake mata yana jin Kmr ta raina masa wayo ne babu abinda yafi tsana sama da karya yafi son duk abinda ya tmbyeka ka fad'a masa gsky ta haka zaka samu sausauci daga garesa "ban kashe mubina ba me yasa zan kasheta ?"wallahi ban aikata komai ba sannan banyi yunkurin kashe mrym ba tabbas na tura maka sakon zanga bayanta amman wallahi ban aikata hakan ba ,amman ina da niyya to waye yasan da wannan shiri nawa da har ya rigani aiwatarwa? "Lafiyayyen mari ya zuba mata yana cewa "ni kike wa wannan tmby ?nan take ta rude ta dafe kuncinta inda marin ya sauka abinda yafi damuna kashe mubina da kikayi me tayi miki nuzla ?kuka ta saka mashi tare da durkushewa kasa "wallahi sharri ake son min dan ban san komai akai ba .wani kallo ya watsa mata sannan ya juya mata baya "nasan tabbas kece kika kashe mubina dan hatta wukar da kika kasheta kinyi kuskuren barinta a yunkurin kashe mrym ." "Da mrym kika kashe wallahi bazai ta'ba damuna ba saboda neman kai nake daita ,ni da zaki kashe min ita amatsayinki na yartaada kafin ta zama mallakina lallai ni kuma da nayi akawarin aureki .nuzla ta sake rudewa ta gigice ta soma jan gwiwowinta ta qaraso inda yake tana kuka "na baki kwanaki goma masu zuwa ki kashe min mrym kafin ta zama mallakina batare da an samu wata hujjar cewar kece kika aikata hakan ba , sannan kada asirinki ya tono ni kuma zan aureki idan kuma kika gagara kasheta har lokacin dana baki ya cika  ni kuma nayi miki alkwarin zan damkaki a hannun hukuma a kwatarwa mubina hakinta kin dai sani idan hukuma ta tabbatar da kece kika kasheta karshenki biyu ne, kisa ta hanyar rataya ko kuma zaman gidan yari na har abada muddin rai kenan yana gama fadar haka ya soma qoqarin ficewa daga dakin .." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 23 Ji tayi qasusuwan jikinta suna barazanar kasa riketa , lokaci guda zuciyarta na barazanar tarwatsewa bata san sanda ta kurma ihu da iyakacin karfinta tana d'aura hannuwanta duka bisa kanta mahaifiyarta hajiya salema ta shigo d'akin da sauri tana dubanta cikin tsananin kad'uwa da tashin hankali, zata iya cewa yanayin data ganta ciki bata ta'ba ganinta cikin irin yanayin ba sai yau wanda shine karo na farko da taga wannan yanayin atare daita , yanayi ne mai cike da firgici da tashin hankali." Rawar da jikin nuzla yake ya qaru hjy salema ta matso kusa daita ta soma girgiza nuzla wacce ta koma tamkar mutun mutumi a wajen "nuzla nuzla!! lafiya what's wrong with you ?!me ke faruwa dake ? me adam yayi miki kike kuka haka ko ince laifin me kikayi masa dan nasan ruwa baya tsami banza tunda naganshi nasan akwai abinda kikayi masa ? ta jera mata tmbyoyin a rud'e tana riko hannunta cikin nata. nuzla tayi shiru tana wani irin kuka mai d'aga hankali "ki min magana mana ko hankalina zai kwanta ? ta mike a matukar firgice tana duban hjy salema sai dai bata iya amsa mata tmbyoyinta ba dan bata da amsar da zata bata a halin da take ciki ,dan haka ta cigaba da kallonta da rinannun idanunta dake cike da ruwan hawaye kafin daga baya ta fara kuka wiwi tana safa da marwa acikin d'akin hajiya salema na biye daita cikin tsananin damuwa ." " tabbas idan har hasashe da yarda yaya adam akanta ya tabbata a zuciyarsa to fa tabani ta lalace ta shiga ukunta dan wallahi tasan zai iya aikata fiyye da abinda ya fad'a mata .hankalinta ya sake matukar tashi tabbas tayi niyyar aikata hakan amman daga ita sai Allah'n daya halicceta da zuciyarta da kuma yaya adam ne kawai suka sani ,"ba itace tayi kissan ba to waye yayi ?ta furta hkn a qasan ranta tana furta "wayyo allah na shiga uku ni nuzla ta ina zan fara ? waye yake son jifa rayuwata cikin maseefa ? da wani irin sauri ta nufi kofar fita hjy salema ta biyota tana kiran sunanta amman ina bata tsaya ba tunin ta kai kofar fita daga gidan ta biyo bayan ata ." ya d'an yi nisa amman bai kurewa ganinta ba dan tana hango bayansa daga inda take ta kira sunansa da karfi cikin tsananin tashin hankali , shi kuwa ata yana jinta amman yaki waiwayowa ya cigaba da tafiya kmr baya son taqa qasa ."ta qara sauri sosai kamar zata hantsila , kallo d'aya zaka wa nuzla ka fahimci bata cikin haiyacinta da natsuwarta ."adaidai bakin kofar shiga side din mami ta iske shi tare da shan gabansa gif haka nuzla ta zube qasa bisa gwiwowinta agabansa idanunta na qoqarin sake kawo ruwa cikin wani irin murya mai gauraye da tashin hankali hade da rudani take furta "yaya ka taimakeni ka tsaya ka fahimceni karka yanke wannan hukuncin wallahi ban san komai akan lamarin nan ba." ya tsura mata tsumammun idanunshi kafin ahankali ya soma magana cikin izza "taya zan iya yarda da hakan bayan kece da bakinki kika furta hakan kuma kika aikata ? "wallahi wallahi !! idan ka yarda da rantsuwata bani bace sam sam ban aikata abinda kake zargina akai ba hasalima ni yau tsawon kwanaki goma sha biyar kenan kafafuwana basu taka haraban gidan nan ba ina kwance bani da lafiya ."yadda take maganar zaka fahimci tana cikin rud'ani da tashin hankali kamo kafafuuwansa tayi cikin kuka tace "please yaya try to understand me bazan ta'ba aikata hakan ba kawai dai na fad'a maka haka ne dan ka tausaya min ka aureni amman ka yarda dani ban san komai akai ba ." "Bazan ta'ba yarda dake ba domin nasan zaki iya aikata taadanci makamancinsa koma fiyye dashi a halin yanzu ba wannan magiyar bace ta kamaceki ki fara shirin yadda zaki aiwatar da aikin dana baki idan kuma zaki tonawa kanki asiri né tun yanzu bismillah ." jikinta da muryarta na rawa tace "baxan damu ba koda asiri zai tono dan ban aikata komai ba bare naji tsoron fallasa kuma Allah shine sheidata ban aikata ba amman zaka iya bincike akan wanda ya aikata abinda kake zargina akai amman ni bani bace kuma duk inda zaa kaini zan tsaya ne akan gskyta bazan ta'ba karban laifin da bani na aikata ba ." a natse ya soma daga kafafunsa dan wucewa ya barta dan ya gaji da jin sautin muryarta da kukanta yana shiga kanshi over ,yaga tana qoqarin jan gwiwowinta domin biyosa ya kalli securities din dake tsaye a wajen "karku sake ku barta ta shigo ciki "okay yallabai an gama ya shege ciki ya barta durkushe tana kallonsa tmkr wani sabuwar halittta a wajenta ."mikewa tayi tare da cure hannayenta waje daya tana bugawa da juna bata ta'ba shiga tashin hankali da nadama irin ta yau ba har ga allah bata san haka abun zai rikice ya dawo kanta ba ta dauka idan ta fad'a masa haka zataci bulus ne ashe masefa zai zame mata ashe bazataci bulus ba wahala zata sha ?"me yasa batayi shiru da bakinta ba ?me yasa ta gaza hakuri har sai data fito ta fad'a masa shirinta gashi ta kai kanta ta baro ? kaicona ni nuzla bakina ya janyo min matsefa na tarowa kaina bala'i da kaina ta sauke ajiyar zuciya tare da furzar da zazzafar iska daga bakinta ." "Ai kam wallahi sai dai yayi mata duk abinda zai mata idan ta kama ma ya mikata ga hukuma amman bazata ta'ba aikata abinda yake bukata ba sannan bazata ta'ba karban laifinta ba sai dai idan kasheta zaayi akasheta ta yarda amman bazata cika masa burinsa ba, shi idan har da gaske yake baya qaunar maryam din ya aikata lahira da kashi ba sai ya had'a daita ba da sauri ta juya ta soma tafiya kamar zata tuntsura kasa sai kace mahaukaciya ta shigo gidansu inda ta iske mahaifiyar tsaye cikin zullumi ." Tana ganinta ta qaraso gareta tana tmbyrta nuzla ta zauna akan kujera jagwaba tana fidda numfashi duk tmbyr da mahaifiyarta take mata bata kulata ba illa hawaye dake zubar mata "wani laifi kikayi wa adam ?tayi shiru kawai batare da tace uffan ba hjy salema tace "to da alamun laifin mai girma kikayi masa yasa har ya biyoki "kamar ta bayyanawa mahaifiyarta halin da take ciki kafin ya damkata hannun hukuma a kashe mata ita a banza a wofi amman ta kasa dan gaskiya bazata iya ba domin tasan irin qaunar dake tsakaninsu kasancewarta auta a wajenta ,banda kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun babu abinda take furtawa tare da dafe kanta dake mata wani irin sara Kmr zai rabe gida biyu hjy salema ta barta ta koma dakinta dan ta fahimci laifi tayi masa mai girma wanda yasa ta kasa furta wa ." Nuzla ta rufe idanunta gam tana jin yadda maganarsa ke tashi acikin kunnuwanta da zuciyarta so take ta sakawa gangar jikinta hakuri da jarumta har zuwa waadin daya dibar mata ya cika amman ta kasa bata jin zata iya, a halin yanzu ma ba mgnr aurensa bace a gabanta illa mafuta lallai tana bukatar mafuta ta mike tsaye tana zariya acikin parlour'n "ko na gudu ne na bar gidan ne ?ta tmbyi kanta ,gudunki bashine mafuta ba nuzla hakan ma qara min laifi zai yi idan kuma maganar ta fito shikenan kin tabbata mai laifi a wajen kowa dakinta ta shiga tayi zaman dirshan tana saqa da warwara ni dai wallahi nasan bani na kashe mubina ba haka zalika banyi yunkurin kashe mrym ba ,"shin ta ina zan fara ?ni kaina ina bukatar gano wanda yayi hakan , ta lumshe idanunta tana tunani dan dole tayi bincike dan gani wacce tayi yunkurin kashe mrym kuma ko wacece acikin estate dinsu take km itama tana son adam ne Kmr yadda take son shi jikinta ya dauki zafi sosai ." Zaune mr ata yake akan kujera kushin dake d'akinsa yayi zurfi cikin duniyar tunani yayinda hankalinsa gabadaya ke sake tashi a duk sanda ya tuna da maganar aurensa da mrym sai ya dinga jin hankalinsa na sake tashi , yayinda a kullum ya daura kwayar idanunshi akan yarinyar sai ya dinga jin tsananin tsanarta ,shi da kansa ya kasa sanin takamaimain dalilin dayasa yake jin tsananin tsanarta haka dan bazai ce dan rashin tsawonta bane da kuma kasancewar ta fara bane ya janyo haka yanayinta dai ya taimaka wajen tsanarta ne ,duk yadda yake qoqarin yakice tsanarta da sanyata ko kadan acikin ransa zuciyarsa taki amince da zamanta a tsakaninsa tafe tafe har tunaninsa ya kawo kan zanen wukar dake ajiye akan bedside dinsa wanda aka kashe mubina daita kuma ake qoqarin kashe mrym dashi shine ya zana ya ajiye a wajensa kafin a mika wukar ga hukuma ." ahankali ya sauke naunauyen ajiyar zuciya ya sake gyara zamansa sosai akan kujerar da yake zaune tunanin duniya yayi akan wacce tayi karfin halin shigo masa gida da taadanci , baya da tabbacin ko nuzla ce domin kuwa har ya gama kallon mai shi ta camerar d'akinsa bai iya gane ko wacece ba zargin nuzla kawai yake bisa yanayin jikin wacce ta shigo da kuma furucin bakinta amman bashi da tabbas akanta bincike ne kawai zai tabbatar masa daita ce ko kuwa wata ce dabam ta kashe mubina km tayi yunkurin kashe mrym "idan wata ce dabam meye dalilinta ?meye hujjarta ? me yasa take yunkurin aikata hakan ?iya tunaninsa yanzu ya fara gane wasu abubuwa akan me kisan wala akanshi ake yi kisan kmr yadda kwakwaluwarsa take haska masa wala kuma wani laifin suka aikata mata take masu dauki dayday ,cikin sanyi jikin nan nasa tamkar mara laka ya matso ya kunna CCTV camera . idanunsa kawai ya zubawa camerar yana kallon wacce ta shigo masa gida cikin bakaken kaya wondo da riga gabadaya babu inda ta bari wanda zai kafa hujja akanta amman dai tabbas yanayinta ya nuna macece "to wacece wannan yarinyar ?tunaninsa ma yadda ta iya shigowa securities din bakin kofar shigowa basu ganta ba ? ko da yake ta yuwu wani abun tayi masu amfani dashi domin gusar da hankalinsu dan kuwa duk tashin hankali daaka shiga bacci suke basa ma cikin haiyacinsu har sai da aka taimaka masu ,tunda yake a rayuwarsa bai taba ganin mai kaifin baseera irin na yarinyar ba Sannan tunda yake bai taba samun kansa cikin damuwa irin na lokacin ba ,sam sam ya qasa kwanciya yayi bacci sai wurin karfe biyu saura bacci barawo yayi awon gaba dashi ." bangaren nuzla ma yadda taga safiya haka taga dare ga wani zazzafan zazzabi daya rufeta kafin gari ya waye ta sake yin wata doguwar rama jikinta ya dauki zafi kamar garwashin wuta dan haka dole da gari ya waye aka kira doctor ya dubata nan ya tabbatar masu da damuwa ce dan har jininta ya hau ya wuce kaida yayi ja hankalinta akan yawon tunani sannan ya daura mata drip ya kama gabansa hjy salema ta tsura mata ido kawai tana kallon yadda numfashinta ke fita da kyar ta riko hannunta cikin nata zafin jikinta ya ziyarci tafin hannun hjy salema bata son ganinta cikin damuwa da tashin hankali duk sai taji itama ta shiga damuwa yanzu da tana da dama data cire mata ciwon ta dawo dashi kanta "nuzla !."ta kira sunanta ta bude idanunta dake lumshe ta zubawa mahaifiyarta "meke damunki ko akan hisham ne ?ta gyada mata kai kawai alamun "eh! . "Halan akan maganar adamu yazo jiya ?ta sake gyada mata kai kawai dan bazata iya magana hjy salema ta numfasa kana ta cigaba da magana "me yasa zaki saka maganar aranki har haka ?tunani shine abu na farko dake fara nukurkusa rayuwar dan adam ,kiyi hakuri ki fallawa allah komai shi keyi a lokacin da yaso haka shi Ke hanawa alokacin daya so fatana Ki barwa allah lamarinki Kiyi addua abinda yafi zama alkhairi atsakaninki dashi Allah ya tabbatar mana, amman ina kyautata zaton zaki ji dadi agidansa zaki samu kwanciyar hankali a hannunsa domin hisham yaron kirki ne amman dai mu cigaba da addua mu barwa allah komai nuzla ta runtse idanunta kawai tana ji da abinda ya dameta ." tun safe mami da mrym har ma da nana hauwa'u suka shiga kitchen suna had'awa ata breakfast suna hira ,mami ta fito tana amsa wayar hajiya nuriyya wanda adaidai lokacin ata ya sauko hannunwansa duka acikin aljihun wondonsa, sanye da riga brown colour mai hannun long sleeve da dogon wando baki "eh ke dai nuriyya abinda ya faru kenan wallahi acikin estate din nan ne amman yanzu tunda ya dawo in sha allahu bazai wuce a saka sati uku zuwa hudu ba ba ,eh babu damuwa tunda open ticket zakuyi nan ata ya wuce yayi nufi hanyar dakin jim dinsa domin motsa jiki ." Har yayi taku biyu ya soma jiyo sautin magana kasa kasa kuma abinda yaja hankalinsa shine sunansa da yaji an kira ,ya dan dawo baya kad'an ya tsaya ya kasa kunne yana jin tautaunawarsu "matar yaya adamcy ikon allah miko min kayan ingredient din can na zuba ko ke kadai zaki hadawa mijinki breakfast na cire hannuna na kama gabana?"kai sister kina son kasheni da raina ." "dan nace matar yaya adamcy ikon allah shine zan kasheki da ranki ?mrym ta gyada mata kai alamun Eh ! ai in sha allahu sai anyi wannan auren ko ana so ko baa so kuma muna bayan ki kamar doro ki zuba mulkinki son ranki a gidansa dan kinci dubu sai ceto babu abinda zai faru "Allah yasa sister dan irin mijin da nake so kenan . "gashi kuwa kin samu kin yiwa sauran mata zarra ,na yiwa sauran mata zarra ko na fisu shiga matsala ?kina ganin dadi zanji a gidansa ni tun yanzu na fara tunanin yadda tunani da damuwa zai haukatani a gidansa ga rashin sonshi da bana yi ga matsalar taurin kai da wanne zan ji ? ." kina bani mamaki wani lokacin kamar ba mace ba ai ina gaya miki tsab zai sauke komai mrym ta girgiza mata kai kawai tana cewa "taimaka ki zuba min maggie dai dan ni ban san dalili ba duk yadda zan saka maggie a miyya sai yayi yawa ." "gsky matsalarki kenan sister mman da sannu zaki qara samun gogewa agidan yayana ,wannan yaya dai ana sona dashi shi kuma baya sona,ana son na shiga gidansa shi kuma yace aa wanne zaayi aciki ? "Ke manta dashi wuyarta ayi auren ,ko da yaushe sister haka kike fad'a min wani lokacin sai naji na amince da samu natsuwa ,wani lokacin kuma sai naji hankalina yayi kololuwar tashi ni kaina zan so na ganni a matsayin matarsa dan nasan da sannu zan iya son shi da yana son kenan matsalata a halin yanzu rashin són da ....." saurin datse harshenta tayi da karfi sakamakon ganin mutun tsaye ta bayan nana hauwa'u daman ta juya da niyyar fuskantar nana hauwa'u ne shirunta yasa nana hauwa'u tace "lafiya sister kikayi shiru ? bata iya bata amsa ba illa numfashi data dauke da karfi tana cigaba da kallon bayanta ." ya tako a natse ya shiga cikin kitchen din sosai kamshin daddan turare da takun da nana hauwa'u taji yasa ta dan juyo ,ta dan tsorata da ganinsa nan take gabanta yayi wani irin mummunar fad'uwa amman sai ta dake ta bude baki da sauri tana cewa "san ..sannu ya.. "saurin d'aga mata hannu yayi yana qara had'e fuska , nana hauwa'u tayi taku biyu zata bi gefensa ta wuce domin ta tsira da lafiyarta taji yace "munafukar allah Koma ki tsaya wato kina d'aya daga cikin masu bawa wannan guntuwar mummunar yarinyar kwarin gwiwar aurena ? tayi saurin girgiza masa kai alamun a'a "zan kifa miki mari yanzu idan kika sake girgiza min kai koni saanki ne ? ta sake girgiza masa kai cikin tsananin tsoro ." "Kika ce da zarar anyi aure shikenan?idanuwanta sukayo waje wani gumi ya soma tsatsafo mata akan hanci ,sannan kika ce ta manta dani wuyarta ayi auren ni zaa manta dani ?yayi maganar a matukar tsawace cikin bacin rai ,dan allah yaya kayi hakuri nifa ba wani abu nake nufi da hakan ba ina qoqarin gyara au...."ai wani mugun kallo da yayi mata batasan sanda tayi shiru ta qara shiga hankalinta ba ,kinga nayi miki kamata da irin mazan da zarar anyi aure shikenan ?ko kinga nayi miki kama da bawan mace ?ta girgiza masa kai alamun a'a ki shiga hankalinki wallahi idan ba haka nayi sadaka dake na bawa duk wanda naga dama aurenki mu huta sha sha banza da wani katon bakinki a wajen ." ita kam mrym hannuwanta duka tasa ta rufe fuskarta sakamakon hawayen daya cika mata ido idan akwai abinda ta tsana a kalamansa gareta bai wuce munzantata ta hanyar zagin halittar da Allah yayi mata "Ke kuma na dawo kanki nan da wasu kwanaki zaki zama mata agareni ban isa na hana hakan faruwa ba amman kamar yadda kika furta tunani da damuwa ne zai haukataki a gidana tabbas haka ne domin bakinciki da damuwa zaki aura bani adam ba ,daman tunda kika shiga rayuwata kema kinsan bazakiyi farinciki arayuwarki ba, har karshen rayuwarki a wahala zaki qare a gidana gara ma kije kiyi kuka da Kururuwan a fasa auren nan shine kawai mafuta agareki da kwanciyar hankalinki nonsense kawai da bata san me take yi ba ,yanzu ke kina ganin kin dace dani ?common maggie baki iya sakawa acikin abinci ba sai an taimaka an saka miki stupid girl kawai wallahi gara ki taimaki kanki tun wuri yana gama fadar hk ya juya ya fita daga kitchen din yana jan tsaki ." kuka mrym ta qarasa fashewa dashi ta koma bayan kofar kitchen ta hade kanta da bango tana jin wani irin zafi mai radadi duk da yadda take jin rashin sonshi amman haka ta bawa zuciyarta hakuri ta karbi aurensa amman shi burinsa yaci mutuncinta ya tozarta tasan yadda ya fad'a haka ne zai kasance rayuwar bakinci zatayi a gidansa zai hanata kwanciyar hankali da walwala ,zai hanata sukuni da jin dadi cike da jin haushi nana hauwa'u tace meye kuma abun kuka ? kina jin tsoron yaya fiyye da kaida ,"shiyasa naga kin iya mutsa masa alokacin da yake magana yake ci min mutunci , ko kin iya taka masa burki alokacin da yake cin zarafina ?tayi mgnr cikin bancin rai tana mai juyowa gbdy ta fuskance nana hauwa'u hawaye na zuba akan kuncinta." "Sarai kijin abinda ya fad'a yanzu ,kuma Kinsan zai iya aikata fiyye da abinda ya fad'a ,shikenan nan ni haka rayuwata zata qare , kisa hannu sister ki saurari zuciyata kullum cikin bugawa take da karfi kin kuwa san abinda nake ji ?"gano yanayin tsoronki yasa yake miki haka wallahi ni ace nice zai aura bazan dauki abubuwansa ba ,"ki daina zugani sister yana fad'a min duk maganar daya ga dama, yana tozartani a duk sanda yaso , lallai ya kamata nayi kuka nayi kururuwan ataimakeni a kawo min dauki fasa auren ."nan tana gama fadar haka ta fice fuuuuuuu ta bar kitchen din ." kai tsaye dakinsu ta shige ta fad'a saman gado ta kwanta ruf da ciki sai nana hauwa'u ce ta qarasa hada masa breakfast."wuni ranar babu abinda mrym take sai cika take tana batsewa tana jan tsaki tana tunanin mafutar da zatasa a fasa auren ta huta abinda mami ta kasa ganewa bayan rashin son da yaya adam baya mata har da kasancewarta farar mace sol mara tsawo ne dan tasan yadda bai son farar mace yafi son chocolate colour yar doguwa mara kiba baa siyar da tsawo data siya ,baa siyan baki da ta koma baka Kmr yadda yake só tunda baya sonta kuma babu duk abinda yake bukata daga macen da zai so tô meye amfanin auren ?gara itama ta kawowa kanta mafuta tana kwance ta zabura ta mike tsaye ta fito ta nufi dakin mami lokacin karfe biyar daidai na yammaci" Mami na zaune a dakinta abakin gado kunneta manne da waya maryam ta shigo duk jikinta a sanyaye kallo daya mami tayi mata ta fahimci akwai damuwa dan haka ta katse wayar da take ta hanyar cewa "khadija zan kiraki zuwa anjima sannan ta ajiye wayar a gefenta tace "lafiya maryam naga kin shigo wani iri? duk da wuni yau na lura bakya cikin walwala , hawaye mrym ta share tace "gsky mami na gaji da abinda ya adam yake min ,ina ganin lokaci yayi da komai zai zo karshe ,numfashi mami ta sauke cikin tsigar rarrashi "haba maryam haba diyata ki daina fad'ar haka ,kece fa karfin gwiwana idan baki auresa ba nasan hk zai qare rayuwarsa bai yi ba kiyi hakuri wata rana sai labari ." "Amman mami ni haka zan qare rayuwata yaya baya fahimtar nima biyayya kawai zanyi ?nasani mrym amman ina ji ajikina wata rana Adamcy zai sauya zai zo har gabanki neman afuwan abubuwan da yake miki ido mrym ta zaro waje tace "mami ko kin manta halinsa ne ?"ban manta ba maryam amman na yarda da allah kuma Kinsan lamarin ubangiji ya wuce nan karkiyi mamaki wata rana ya zamo bawa agareki barin ma idan kin haihu dashi kuma gani a tsakanimu muddin ina raye bazaki shiga uku a gidansa ba ,ajiyar zuciya maryam ta sauke haka ne mami lamarin ubangiji ya wuce nan nima ikonsa ne yasa har zan zama mata agaresa ." "Haka mami ta zauna ta dinga tausar maryam tana bata baki har mrym ta saki ranta ta manta da batun wulakanci ata ta cigaba da harkokin gabanta ranta fari kwal washegari aka tsaida ranar dazaa daura auren ata da mrym hisham da nuzla nan da sati hud'u masu zuwa kamar yadda mami ta tsara shima dan alfarma cousing sister dinta nuriyya ne domin tana son yaranta suyi hutu tazo dasu gbdy bugu da qari lokacin zai yi daidai da hutun karshen shekara wanda daman kusan lokacin da yan'uwanta dake kasashen duniya ke zuwa hutu kenan bancin hk ai da kwanaki goma kawai zata saka ayi a wuce wajen shi kam mr ata kam ko ajikinsa dan babu ruwansa da ko sati nawa zaa saka idan ma an ga dama a daura a ranar ba damuwarsa bace ." A hankali yake saukowa daga saman mattakala jikinsa sanye da complete black suit yayinda kafafunsa ke sanye da brown shoe's agogon rolex ke daure da tsintsiyar hannunsa ,idanunshi na manne da wani hadadden farin glass ,a hankali ya cigaba da takowa cikin isa da izza alamun shi din wani ne a fadin nigeria ,yana saukowa sanyayyen kamshin turarensa REED ya soma tashi ta koina kamshin turarensa ne ya kaiwa hancin maryam ziyara da sauran jamma'a wurin sakon fitowarsa . Maryam ta dago idanunta a natse ta tsura masa tana kallonsa tun daga sama há qasa tamkar ranar ta soma ganinsa arayuwarta ji tayi gabanta na wani irin mugun bugawa da karfin gaske, hakan nan yau ta tsinci kanta da kasa dauke kwayar idanunta akansa sister dake zaune a gefenta ta bita da kallo tsab domin dai ta fara fahimtar wani abu akan maryam a din a game da yayanta a tun dawowarsa daga kasar france duk da ita taki yarda da zarginta tana nuna mata alamun bata son danuwanta amman kuma ita kar take kallonta domin kuwa akwai dinbin son shi makale a ranta da kwayar idanunta wanda itama bata san tana yi ba . " "taya zaka samu miji kmrshi kace wai baka so ai sai dai idan abun yafi karfinka nmj da mata suke nema har suke rububi akansa itam saa taci da kuma darajan mahaifiya if not har abada sai dai ta tsaya akansu abbas da anas shi kuwa kallo ne daga nesa dan fin karfi kam yafi karfin aurenta ."daga inda yake yana iya jiyo sautin muryoyin mutanen dake zaune a bangaren dining area, a natse ya tsaya idanunshi karrrr akan sister dinsa da maryam wacce ta zama tamkar doluwa a wurin rike da cup din tea a hannunta tana kallonsa abinda yafi tsana kenan kallon kurulla daga mace ,kallo daya yayi masu ya dauke kwayar idanunshi akansu yana busar da iska daga bakinsa tare da furta "nonsense "! a fili wanda hakan daya furta yasa maryam tayi saurin dawowa haiyacinta tana sauke naunayen ajiyar zuciya sai dai ta qasa dauke idanunta akanshi ta cigaba da kallonsa" bai tsaya akoina ba kai tsaye dinning área ya nufa yana shan kamshi , har ya samu wuri ya tsaya tare da soke hannunsa daya cikin aljihun wondonsa ,Still maryam bata dauke kwayar idanunta akanshi ba ,sister ta zungureta da sauri "ke ki dawo hankalinki mana wannan kallon da kike masa kin dai san halinsa , idan yaga dama sai ya sakaki kinyi bayanin wannan kallon dalla dalla ."numfashi maryam ta sake saukewa da karfi tana waskewa ta shafa gefen fuskarta tace "wani irin kallo kikaga nayi masa "? ni gbdy ma hankalina baya cikin gidan nan ." "yana ina shi hankalin naki ?nana hauwa'u ta tmbyeta tana tsareta da idanunta ,domin dai ita tasan gskyr abinda ta gani kenan kallon yayanta take amman tana kokarin waske mata "ki yarda sister da gaske shi kika ga ina kallo ?maryam ta tmbyeta tana qara shafa gefen fuskarta nana hauwa'u ta gyada mata kai alamun "eh!"zai iya kasancewa haka idanuna na kansa amman kuma hankalina ba akansa yake ba, mai ma zan tsaya kallo ajikin mutumin da ba mutunci garesa ba ?"tayi mgnr a hankali." "me kika ce sister naji kamar kinyi mgn ?"no no bance komai ba ,kinga sister dauko wayarki ki daukar mana abincin nan kar na manta ban daura breakfast din dana ci a social media ba ,ta fadi haka ne saboda ta shashantar da zargin sister akanta "okay ni nayi laifi kenan ?tô wallahi bada ni ba , matsawar bai bar parlour'n nan ba babu hoton wani abinci da zan dauka, idan kin matsu ki dauka da kanki wayarki ce bazan hanaki ba ta janyo wayarta dake ajiye ta mika mata ta tashi ta bar gurin gabadaya karta jaza mata balai da sassafe." A hankali maryam ta shiga daukar abinci gefe guda kuma tana faman satar kallonsa ta kasan idanunta, ba qaramin kyau yayi mata ba cikin shigar suit ,da alamu ma barin garin zai yi ko kasar gbdy karaf kamar ance ya waigo idanunsu ya tsarke cikin juna da mugun sauri ta dauke idanunta zuwa wani gefe tana sauke numfashi sama sama dogon tsaki yaja tare da furta stupid girl sannan ya samu wuri ya zauna batare da ya kalli inda sauran mutanen da suke zaune akan kujerun dake zagaye da dining table ba hakan kuma ya faru ne sakamakon zattukansu dake shiga kunnuwansa suna yi masa kuwa ." kallo daya mami tayi masa ta dauke kanta tare da girgiza kai sannan ta tura masa plet din abinci gabansa tare da black coffe wanda ya zame masa jiki a hankali ya dauki cup ya kai bakinsa ya kurbi tea kadan yana lumshe tsumammun idanunshi yana dan motsa kafarsa daya akan tayis magana baba qarami ya cigaba da yi cikin zafin rai sai dai "on expecting suka ji sautin muryar ATA yana cewa "babu abinda zaa bawa kowa sai abinda naga dama shima a siffar albashi ko kyauta zan bayar kamar yadda na saba .""yayi mgnr tmkr ba daga bakinsa ta fito ba hankali kwance ya cigaba da kurban tea yana lumshe ido ." "mai kake qokarin kace adam ?kana nufin mu babu komai namu acikin dukiyar ko me ? yes of course uncle domin babu shi acikin kundin da dad yake rubuce rubucensa aciki , amman mai yasa tun tuni baka taso da wannan maganar ba sai yanzu ?yanzu né naga ya dace nayi magana tunda naga ita wannan uwartaka batasan abun arziki ba, idan kowa yaja bakinsa yayi shiru saboda jin tsoronta da gudun magana toni bana jin tsoronta kuma bana gudun magana ,zanyi mgn km dole a kasafta abani rabona bazai yuwa kayi mana karfa karfa akan gumin da mahaifinmu yayi wahala ya tara tsawon shekaru ba ." "babu abinda zan bayar..., ."ya sake maimata mgnr daya fada yana sakin spoon din hannunsa hakan yasa hankalinsu yayi matukar tashi gab gab !! baba qarami yaji gabansa na wani irin faduwa gbdy parlour'n ya dauki shiru tmkr babu wasu hálittu a wurin "koda ma akwai dukiyar babu abinda zan cire na bawa kowa tunda babu shi a rubuce idan kuma kayi trying wani non..."shiiiii mami ta furta tana daura dan yatsanta akan lip's dinsa dan dakatar dashi domin tasan halin kayanta karshe kalmar nonsense ne zata fito daga bakinsa "wai meye haka kake yi adamcy ? baba qaramin sa'anka ne"? "Karka manta kanin mahaifi ne me yasa ma sai anan zaa yi discution din wannan matsalar dan kawai a daga min hankali ? ta juya inda baba qarami ke zaune "karki fada min hk sannan abu na gaba ki fada wa d'anki yayi bincike mai kyau akan abinda na fada tabbas akwai dukiyarmu acikin dukiyar ubansa wanda byn mutuwar mahaifinmu muka barshi a hannunsa idan kuma ba hk ba komai zai iya faruwa idan wani abu ya faru ki kuka da kanki karki yi kuka da kowa." yana gama fadar haka ya mike cikin tsananin fushi yaransa maza biyu salim da sultan suka mike suna hararar ata kafin daga baya suka marawa mahaifinsu baya . Hajiya zualai ta mike tsaye cikin tsananin tashin hankali tana binsu da kallo gabanta na faduwa tasan yana son kunno da damuwa ne sbd rashin amincewar auren adamcy da hindu da kuma makudan kudaden da yayansa sukai qoqarin hadamewa adamcy ya hana ,ATA ya kai hannunsa ya riko tsintsiyar hannunta "sweetheart ki zauna "ta zauna cike da sanyin jiki tana duban kyakkyawan tilon dan nata nmj kwaya daya da allah ta mallaka mata "karki damu sweetheart da mgnrsa everything will be fine tunda ni bani da wani business dashi so karki saka wani abu aranki ,ban san meye damuwarsa ba ."? " ban san me yasa yakewa kudi mugun só haka ba ."? duk ribar dake shigowa ta AGC ina iyakar kokarina ana cirewa kowa hakinsa na bashi kuma sweetheart a qokarina na kar company ya ruguje kullum hannun jari nake qarawa batare dasanin kowa ba kuma su waye ke kokarin karya company ? yaransa né kullum cikin sata suke sannna yanzu yazo da wani batu this time around sweetheart sai dai ki yi hakuri I can take it dan bazan dauka ba wallahi baba qarami na mugun son kudi duk ma yafi sauran karbar kudi a kamfani amman yanzu yazo yace ga zance ga magana agc ne dai yanzu na soma zuwa kula dashi bazan yanke zuwa ba bare su samu damar yin babakeri da dukiyarmu ." " adamcy ni nasan baba qarami ba kudin yakewa ba, tunda bai taba mgnr wasu kudade ba sai yau na dai lura tunda aka fito da batun mgnr auren da maryam ya canza , amman nasan ba komai yake damunsa ba so yake ka auri diyarsa hindu ."shiru adam yayi yana sauroronta yana tsakurar abincin gabansa batare da ya furta komai ba dan babu ruwansa da mgnr "ko zaka taimaka adam ka had'asu duka biyu ka auresu"? "What ?" ya furta da mugun karfi yana sakin spoon din hannunsa "mami ta lumshe masa ido "kayi tunani akai kaji adamcy nah "am done am leaving kiyi min addua fatan alkhairi ya fada yana mikewa da d'an hanzarin ya soma tafiya cike da kuzari hannunsa daya cikin aljihun wondonsa." tabi bayansa da kallo tana kiran sunansa cikin tsananin tashin hankalin "adamcy !adamcy !!! Ka tsaya kaji me zance adamcy ."amman ina bai juyo ba bare ya tsaya yaji mai zatace,itama tasan adaidai wannan yanayin da yake ciki bazai tsaya ya saurareta ba domin maganarta ce tasa zuciyarsa ta yunkuro har ya kasa sauraranta shiru tai tana dafe goshinta cike da takaici da kuma mamakin halin biladam ."mutane sam sam babu tsoron allah aransu "shekara da shekaru baka tashi dauko maseefa ba sai yanzu dakaga yaro zai yi aure kazo da wata magana ." Tana cikin wannan halin maryam ta qaraso hannunta rike da glass cup da magani ta mika mata "ki cire damuwa aranki mami ki sha magani lokacin shan maganinki yayi mami ta dago kanta ta kalli mrym yana daya daga cikin abinda yasa ta kwadai tawa danta aurenta domin zai samu natsuwa daita muddin tana raye sai ta zama uwar gidansa km uwar yayansa ".na gode maryam da kulawar da kike bani "haba mami kullum sai kinyi min godiya karki manta ni din fa dolenki ce haka kema dolena ce duk abinda nayi miki tmkr nayiwa mahaifiyata ce "haka né maryam amman duk da hk na gode sosai allah yayi albarka kinci abincinki ko kuwa kin tsaya tallatawa duniya "?mrym taí murmushi tace "kai mami naci !"kina ji ko mrym kiyi kokari ki rage son social media din nan idan ba hk ba bazuku shirya da adamcy ba kasancewar shi mutun ne da yake da raayi dan allah ki daina kmr yadda na sha fada miki "in sha allahu mami zan rage tare suka baro parlour'n ." ****** Karfe 11:00 daidai na safiyar laraba nuzla zaune a parlour'nsu ita kad'ai cikin tunani da zullumin abu biyu aurenta da hisham da kuma aikin da ata ya bata wanda ita sam bata jin zata iya aikatawa ita da kyankyaso ma tsoronsa take ji bare akai ga kissan mutun ai tasan duk runtse duk wuya bazata iya ba kullum tana gida bata fita koina duk da tana buqatar fita yin shopping din abubuwan buqatanta amman haka ta hakura ,tun kwanaki uku da suka wuce waadin da ata ya bata suka cika amman shiru babu wani sammacin daga yansanda haka zalika babu wanda yazo mata da magana makamanciyar zarginsa akanta dan haka ta dan samu natsuwar zuciya ta mike tsam ta shiga dakinta ta shirya cikin kananan kaya ta daura abaya a saman kayan tayi roling kanta da mayafin abaya ta dauki turare ta feshe jikinta ta dauki handbag dinta ta rataya ta fito ta shiga dakin hjy salema tana zaune tana lazimi akan dadduma dan ta idar da sallar wallaha kenan ." "momy zan dan je shooprit na dawo murmushi jin dadi ta sakar mata dan yaushe rabon ta fita kullum tana kunshe a daki cikin damuwa "sai kin dawo nuzla allah ya tsareki ta bata amsa da haka cikin halin farinciki "akwai kudi a hannkin ne ?ta waiwayo tana dubanta "akwai kudin da yaya Ibrahim ya tura min cikin account dina dasu zanyi amfani to shikenan sai kin dawo ta juya ta fita daga dakin tana kiran bolt dan bata jin yin driving ." a hankali take taka qasa har ta fito bakin get din estate dinsu fuskarta a daure kana ganinta zaka fahimci tana cikin damuwa kadan tayi tafiya tana kiran mai bolt taji a inda yake kawai taga motar yansanda a gabanta nan take taji gabanta yayi wani mummunar bugawa da matsanancin karfin gaske ta sauke wayar kunneta batare data kashe ba ta tabi gefe zata wuce cikin tashin hankali tana adduar allah yasa ba wajenta suka zo ba amman ga mamakinta mutun biyar suka fito suka sha gabanta suka tsaya ta kallesu daya byn daya cikin tashin hankali kafin ta kai ga bude bakinta duk suka fito mata da ID card dinsu daga gaban aljihu suka nuna mata daya daga cikinsu yana cewa "sunana inspector Almustapha hasan umar da fatan kece nuzla ? Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗    MAR'ADAMS    💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.        Page 24 Qoqarin cire tsoro da fargaban dake tattare da jikinta tayi ta aro jarumta ta sanyawa jikinta tace "Eh yes nice nuzla fatan dai lafiya kuka tsayar dani ? "Ki adana tambayarki tukunna muna gayatarki zuwa office dinmu yanzu ."akan wani dalili kenan kuke gayyatata ? idan munje zaki ji komai ,kamar tayi musu taurin kai amman  sai taga d'aya daga cikin 'yansanda na qoqarin fito da handcuff daga cikin aljihu yana cewa "zaki wuce muje ta girma da arziki ko kuma sai mu saka miki handcuff mu wuce dake ta karfin tsiya ." ba tayi  mutsu ba dan ta rigada tasan da komai dan tun tuni take jiraye dasu saboda dama tasan hakan na zuwa saboda tun rabuwarsu da yaya adam tasan ya zuba tsaro sosai akanta ta yadda duk wani motsinta arayuwarta yana sane dashi ,haka ma yansanda, dan tayi imani anan din ya bada umarnin aka mata dan da suna son kamata cikin tonon silili da har ciki zasu biyota ,ba tayi ma tunanin zata wuce lokacin daya bata batare da ta shiga hannun hukuma ba." sosai zuciyarta ta shiga rudani  taji wani gagarumin bakinciki ya rufe mata kahon zuciya kuma tayi imani matukar tayi gardama dasu haka zasu da'ba mata handcuff su wuce daita , ta ma godewa Allah da ba har cikin estate dinsu suka shigo suka tafi daita ba ai da kuwa ta shiga ukunta ." Ahankali ta soma daga kafafunta domin isa inda motarsu take jikinta na karkarwa a duniyarta idan akwai abinda ke firgitata shine hukuma tana tsanani tsoron shiga hannun yansanda, duk da tasan ba wani laifi  tayi ba ,dan abinda har yasa suka gayyace din akanshi bata aikata ba ."tafiya take tana tunani da mamakin wanda ya aiko su "me ta yiwa yaya adam da zafi har haka daya kasa yafe mata ? shin laifi ne dan tace tana son shi?dan dai tasan hukuncin zafin furta masa kalmar só ne ya janyo mata wannan tashin hankali, tayi masa runtsuwa da Allah bata aikata abinda yake zarginta akanshi ba amman  ya kasa yarda daita "shin tayi masa kama da wacce zata iya kisan kai ko yunkurin kisa ne ? zuciyarta ta dinga mata zafi tana mai sake tabbatarwa kanta lallai  yaya adam baya sonta, bayan soyayya ta aure har da soyayya ta yanuwantaka ma baya mata gashi ita duk duniya babu wanda take so sai shi ." "anya bazata rushe  wannan wahallalliyar soyayyar ba ta dawo qiyayya da tsana mai tsanani ba "? ji tayi jikinta yayi sanyi matuqa dan bata jin zata iya wannan aika aikan ,jikin nuzla a sanyaye yansanda suka sakata a bayan mota tare da wasu jami'an tsaro mutun biyu inda zuciyarta ke wani irin bugawa da karfin gaske sakamakon bakincikin sakata a tsakiyarsu da sukayi tun anan idanuwanta suka canza kala tana kallon tafkeken get din estate dinsu aka wuce daita ,tafiya kadan sukayi suka iso police station."direban motar yayi parking ya kashe motar sannan suka firfito suka shiga ciki suka karbi duka kayanta sannan aka bude wani daki wanda babu kowa aciki suka sakata ciki suka maida kofar suka rufe kukan bakinciki ne ya kufce mata ,ta soma rera kuka tana jin wani irin zafi acikin ranta saboda ta duba hagu da dama babu inda zata zauna duk inda ta kalla qazanta ne da zarnin fitsari uwa uba duhu ." Aqalla ta kusan awa biyu tsaye tana jiran azo a fara tuhumarta domin a tunaninta da sunzo zasu fara jeho mata tamabayoyi tana basu amsa idan sun gano bata da laifi su saketa ta kama gabanta batare da sanin kowa ba sai taga sun shareta sun ma shiga wata tsabgar dabam har wata awa daya tazo ta wuce basuyi lokacinta ba ,wanda zuwa wannnan lokacin kafafunwanta sun fara sandarewa da tsayuwa ahankali tayi qasa ta tsuguna a cimintig dakin tana hawaye yayinda bakinta ya soma furta adduar neman dauki ." Shi kuwa ATA lokacin da sakon samun nasarar kamata ya isar masa yana zaune a parlour'n mami tare daita dan bai jima da shigowa ba lumshe tsumammun idanunshi yayi sannan ya motsa labbansa da kyar "ina fatan babu wanda yaga lokacin da kuka wuce daita ?okay sai nazo ya fad'a tare da jan boyayyan numfashi ya sauke ,okay zaku iya fara aikinku kafin na shigo amman karku ta'ba lafiyar jikinta ,sun dauki Kmr minti goma suna magana yana gama waya ya ajiye wayar a gefensa yana jijjiga kafarsa daya mami wacce kwayar idanunta Ke kanshi a tun sanda ya fara wayar yace ." "Yaakayi adamcy nah naga kayi wani iri ko akwai damuwa ne ?cikin kwantar da murya yace "no sweetheart yunwa nake ji ,bari nasa aka ..."haba sweetheart karki saka kowa please ni ban san me yasa kike yawon sako wasu cikin lamarina ba" to sarkin korafi ,kai dai da wannan halin naka Allah yasa ka canza ,kullm kai kenan cikin bakin hali naga ranar da zaka canza bazaka barni naji da tsufana ba tun kana yaro nake hidima da kai har gashi ka tsufa ta qarashe mgnr cikin salon tsokona tana hade rai ." Ya dago a sukwane ya tsura mata idanuwanshi "yanzu ni ne na tsufa sweetheart?sosai kuwa kai yanzu tunaninka baka tsufa ba ?haba haba !!sweetheart allah idan ba fad'a akayi ba babu mai cewa na wuce 40,dan ni wallahi jina ma nake Kmr .." "kai dan Allah kama mana baki shima gyara ne ,da babu gyara da kasan kai ba yaro bane "wel ko babu gyara zan zama Kmr yaro dan gadon jikin mai kyau nayi " "A wajen kenan ? Ya sake tsaita idanunshi akanta sosai yace "wajenki mana! shakiyi kawai ya dai kamata ka rage wadan nan abubuwan dan ka kusan zama baba nan da wani lokaci ,nan da nan ya hade rai Kmr wanda aka fadawa sakon mutuwa duk da tsananin son haihuwa da yake amman kwata kwata baya qaunar haihuwa daga mrym ya gwamaci ya qare rayuwarsa babu haihu akan ya haihu daita ". Ahankali ya bude bakinsa zaiyi magana mami ta katseshi dan tasan ba alkhairi zai fad'a ba "ina son zuwa yanzu ka bawa mrym matsayi mai girma acikin zuciyarka ,ya sake kallonta cikin rashin fahimtarta "Eh !nasan abinda nake yau idan ka runtse idanunka da zumar bacci ka matso daita kusa da zuciyarka zaka ga abubuwa masu yawa akanta" ya dage girarsa daya yana dubanta dan ya fara gano rikicin tsufa ya fara kama mahaifiyarsa idan ba hk ba ina shi ina wani kusantota da zuciyarsa yaji me ?bai gama mgnr zuci ba ya sake jiyo sautin muryarta ". "tunda ta zama mahadin rayuwarka dole zuciyarka zata dinga bibiyarta " numfashi ya sauke da karfi dan yasan ba abune mai yuwuwa ba shirunsa ne ya bata amsa mgnrta "ta gyara zama kai dai kayi qoqarin yau kawai ka kusantota da zuciyarka idan Allah ya kaimu gobe zan tmb..."sweetheart yunwa !"Okay bari na tashi sarkin korafi "thank you my sweetheart Kiyi sauri please dan yunwa nake ji sosai har cikina ya fara zafi "dariya ma ya bata a duk sanda taji ya fadi haka sai taganshi tmkr yana yaro ,adamcy kenan ko yaushe zai san ya girma ? kullum idan yana gabanta tmkr qaramin yaro yake dawowa ." Jallof din kuskus wanda yaji hanta da nama da ugu ta kawo masa ta ajiye agabansa tace "bismillah sarkin korafi kallonta kawai yayi yana girgiza kai sannan ya fara ci a natse ta zauna a kujerar dake fuskantarsa tana kallonsa hatta cin abincinsa dabam ne ,yana ci tana yi masa hirar yadda take son bikinsa ya kasance shi dai bai ce uffan ba ya cigaba da kwasar abinsa bayan ya gama cin ya mike ya haura saman d'akinsa wanka yayi ya canza kaya marasa nauyi ya zauna abakin gadonsa ya kunna system ,ahankali sakonnin abokan kasuwancinsa ke shigowa wasu ya amsa wasu kuma ya wuce ." Washegari yana zaune akan daya daga cikin kujerun dinning sanye da wondo da riga long sleeve sai dai ya dan nade hanuna rigar kadan ta yadda zaa iya ganin hadadden agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ,yayinda mami ke tsaye a gefensa tana qoqarin saving dinsa ,ta kallesa zaune shiru ya hade hannunwansa waje daya tace "jiya da nace ka rufe idanunka tare da kusanto mrym da zuciyarka , fad'a min daka rufe idanunka me ka gani ."Kai sweetheart "nasan mrym ka gani alokacin daka rufe idanunka ko ba haka ba ?" ni ba wata mrym dana gani sai princes dina na gani ." " kada kayi min karya dan nasan baka iya karya ba "tunda Kinsan bana karya ya kamata ki yarda dani wallahi ni banganta ba Kinsan wani abu a duk sanda na runtse idanuna princess dina nake gani wata rana cikin farinciki wata rana cikin damuwa nifa jikina yana bani yarinyar nan ba karya bace gsky ce km ba aljana bace tana nan acikin duniyarmu sai dai a ina take? " yaushe ne zan ganta ?shine bansani ba amman nasan zamu hadu shiyasa nake jin Kmr a fasa wannan auren "kai sakarai menene ya kawo batun a fasa aure kuma daga magana ?" Kamar yayi dariya ganin yadda magaarsa ta d'aga mata hankali "wannan auren fa sai an daurashi babu makawa zaku rayu tare har ma wata rana zaka amince daita tare da furta wa mrym kalmar so na tabbatar maka da haka "tunda ya fara cin abinci bai sake cewa uhm ba bare uhm uhm har ya gama ya goge bakinsa da tissue ya mike tsaye yana qoqarin yi mata sallama suka jiyo sallamar baba babba fuska cike da damuwa mami ta bar ATA ta qaraso wajensa a inda yake tsaye dan ko zama bai samu damar yi ba kallo daya mami tayi masa ta fahimci yana cikin damuwa suka gaisa adaidai lokacin da ATA ya qaraso ya gaishesa cike da girmamawa sukai shiru mami ta dubesa tace "baba babba ka zauna mana bari akawo maka breakfast ." Yace " zulai ba sai na zauna ba nazo ne na sheidawa adamu tun jiya baa ga halimatu ba daga zuwa siyaya nan da nan hankali mami ya tashi "baa ganta ba to ina taje ?kuma an kira layinta bata d'auka ba ?wallahi kwana mukayi kiran layukanta guda biyu shiru abinda yafi daga min hankali bata saba irin haka ba ,kuma duk runtsi ka kira wayarta zaka sameta "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun mami ta furta tana cewa "Allah ya cecemu " ATA ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yaga lokaci ya fara tafiya ya bude bakinsa da kyar yace "baba babba muje daga waje yana gama fadar haka ya nufi kofar fita suka bar mami cikin tsananin damuwa ."    tare suka jera har haraban estate din baba babba yana sake masa bayanin tashin hankali da suke ciki "ka kwantar da hankalinka baba nasan inda take "wani irin naunayen ajiyar zuciya baba babba ya sauke yana dubansa a tsanake tare da neman qarin bayani ."wani dan bincike zaayi akanta da zarar an kammala zata dawo gida "shiru baba babba yayi yayinda zuciyar tsohon ya shiga bugawa fiyye da kaida domin kai tsaye kwakwaluwarsa ta hasko masa binciken da zaayi akanta muryar tsohon a sanyaye yace "to allah yasa muji alkhairi" ameen !ATA ya furta atakaice anan suka rabu yayi masa sallama ya nufi inda motacinsa Ke jiransa dan tun fitowarsa aka gyara tsayuwar su , tun kafin ya qaraso escort dinsa dake tsaye tmkr mashi suka yo kanshi cike da girmamawa ya shiga mota suka bar gidan ." Bangaren nuzla kuwa  gaba daya duniyar ce ta cakude mata waje daya bata ta'ba sanin haka tashin hankalin irin wanda take ciki yake da ciwo ba"ta dauka zafi da ciwon rashin son da yaya adam ya nuna mata shine damuwa mafi tsayi arayuwarta a she qaramin abu ne damin kwana daya tal da tayi acikin dakin kurkun da take ciki ya ninkashi sau babu adadi ,tana durkushe bisa gwiwowinta tare da rufe fuskarta da tafukan hannunta taji motsin ana bude qaramin kofa ,bata bude idanunta ba bare taga masu shirin budewa ,wata murya taji ta doki dodon kunnenta cikin tsawa tana bata umarnin ta fito sai lokacin ta bude idanunta da suka kumbura tsabar kukan data kwana tanayi ." Koda ta motsa qafafuwanta dan mikewa sai taji ta kasa yunkurawa dan sun qara sandarewa kamar dotse ,hannunta ta kai ta rike karfen kofar sannan ta kai dayan hannunta ta riko kafarta daya ta yunkura da kyar ta mike tsaye ,ahankali ta fito wani qaramin daki aka nufa daita, babu laifi yafi wanda ta fito tsafta kujeru biyu tagani sai table dake tsakiyarsu ."tun kafin abata umarnin zama ta zauna dan kafafuwanta bazasu iya cigaba da daukarta ba ,mutumin daya shigo daita ya fita byn second biyar wata police mace ta shigo fuskarta a hade har tafi na farko ban tsoro da razanarwa duk da bata aikata komai ba amman zuciyarta ta cika da tsoro mai tsanani ." Idanunta na kan nuzla ta ajiye wukake har guda uku akan table din gabanta sannan ta zauna tana fuskantarta ,nan nuzla ta sake tsurewa hankalinta ya sake tashi wasu hawaye masu zafi suka samu nasarar gangarowa daga kwarnin idanunta ." Bayan mintuna goma police ta soma da tmbyr sunanta ta dago idanunta dake zubar da hawaye ta bata amsa sannan ta cigaba "yanzu dai sheidar da muka samu daga bakin danuwanki ya kore duk wata hujjar da muke nema akan masu amfani da wannan wukar wajen kisa da fari ko zamu san dakilinki nayi kisan ? Nuzla tayi shiru dan bata da amsar da zata bata sai dai ta dago ta zuba mata idanunta tana kallonta hawaye na zuba daga kwarnin idanunta ,ganin yadda matar ta soma huci tana fito da jajayen idanunta yasanya hankalin nuzla qara tashi ba shiri ta soma mgn cikin rawar murya "ni ..ni ban kashe kowa da wannan wukar ba, hasalima ni a yanzu na fara ganinta "amman ai kin ta'ba turawa yayanki adam sakon zaki ga bayan matar da zai aura ko me zaki iya cewa akan haka ?babu abinda zan iya cewa akan haka baya ga qaddara , kuma nasan tana iya fadawa akan kowa ,a garin na tsoratar dashi akan tsananin soyayyar da nake masa wannan matsalar ta faru dani ." "kenan kin tura masa sakon cewar zaki ga bayan matar da zai aura ? ta runtse idanunta wasu ruwan hawaye masu zafi suka zubo mata ta gyada mata kai "Eh! na tura masa amman ban aikata komai ba"karya kike karki wahalar da hukuma domin yin hakan yana qarawa mai laifi laifinsa dan haka ki fad'a mana gsky domin kawowa rayuwarki sauki " Nuzla ta girgiza mata kai jikinta na rawa "Allah ki yarda dani ban san komai ba "da fari kin kashe mubina wacce ta kasance yar uwa agareki kin kashe sadiya dake aiki tare da yayarki shahida yanzu kuma kinyi yunkurin kashe mrym shiru tayi kawai tana tunani wacece sadiya kuma ?ta dai san mubina da maryam amman sadiya kam bata santa ba ." "Kin kashe mubina yaruwarki dan ta furta tana son adam haka zalika kun hadu da sadiya a hospital kafin rasuwarta itama ta furta tana son adam kin yunkuro kan mrym ita kuma dan ta amince zata auresa kin kashe mutun biyu din nan adalilin sun furta suna son abinda kike so ko ba haka ba ? Ji tayi zuciyarta ta tsaya CAk ta daina aiki na wani lokacin kafin daga baya taci gaba da bugawa ji take magaarta ba'a kunneta kadai ya tsaya ba har cikin zuciyar ta take jin komai saboda dacin kalmar ."   "kuka ta saki mai cin rai meke shirin faruwa dani ?ta furta a fili cikin tashin hankali da firgice ,wai ita ake zargi da laifin da ba taji ba bata gani ba kallonta tayi da idanunta da suka koma kmr an diga jini acikinsu , tace "me zakice akan haka ?daga kalmominsa komai ya sauya mata ta gane ita din ba kowa bace sannan ta soma fahimtar bata isa tace zata ma kaddarata wayo ba ,yau din taxo mata da tashin hankalin da rudani ya zatayi da kaddara da ta fada mata " ?duk yadda yarsanda taso ta amsa laifinta amman taki dan haka ta mike ta fice ta bada umarnin a canza mata daki zuwa wani dakin dabam ." Ai tana shiga dakin hawaye nadamar furucinta ya kufce mata domin har gara dakin farko daaka sakata dan wannan bashi da maraba da kabari yayinda zarninsa da warinsa da duhunsa ya zarta duk wani wari da mutun ya ta'ba ji tana kuka tana istigifari" Allah na tuba Allah ni bawar ka ce ya Allah kasani ban aikata laifi mai muni hk ba amman na kudurta yinsa ka gafartamin ban isa na maka wayo na hana faruwar kadarata ba " Allah ka kawomin sauki cikin wannna tashin hankali". kuka tayi sosai ,sai dai duk rintse bazata taba karban laifin da bata aikata ba ."Ahankali kwakwaluwarta ke son tuno mata wacce sadiya dake aiki da aunty shahida da tunanin wanda zai iya aikata wannan taadanci acikin danginsu a daura mata , sai dai duk tunaninta kwakwaluwarta ta kasa gano kowacee sadiya da kuma wanda yayi amfani da damarta yayi mata haka ,hakika bata da makiyi kamar shi kuma ya cutar daita ya zalinceta ba kuma zata ta'ba yafe masa ba ,wajen bazai isheta zama ba dan hk ta gwamaci ta kwana acikin zarni da kazantar waje tana kwance taci kuka ta koshi idonta sunyi lulu dasu ." Qarfe biyu daidai na rana ya fito daga cikin makeken office dinsa kai tsaye hanyar massalacin dake cikin ma'aikatan ya nufa yayi sallar azahar sannan ya bawa direbansa da masu tsaronsa umarnin tafiya police station babu bata lokaci kowannensu ya zama ready yana qarasa isowa aka bude masa mota ya shiga suka dauki hanyar police station yana shiga kai tsaye da cp Amir suka hadu suka tsaya suna magana akan nuzla suna gama magana cp yayi gaba zai masa iso wajen dpo ."tun kafin ya kai ga shiga dpo ya mike ya fito da kanshi cikin girmamawa yau ga matun kamar adam tariq abdullahi acikin station dinsu dan kasuwan daya fi kowani dan kasuwa kudi ya shiga office din suka zauna cp ya basu waje suka gaisa sannan suka soma tattaunawa akan nuzla ". "ranka ya dade mai zai hana awuce kotu kawai ?ciza lip's ATA yayi yana girgiza kai muryarsa a matukar raunane yace "a'a nan ma ya isa banason aje ga kotu fatana ma ya zamanto babu hannunta ciki ,amman yanzu abi mataki na karshe ayi amfani da sheidar hannunta "muma shine last option dinmu domin shi zai warware komai ya runtse idanunshi hankalinsa na sake tashi babu wanda yake tausayi Kmr mahaifinta da mahaifiyarta yayyenta da kuma masoyinta hisham ya tuna halin daya gansa yau din gbdy baya cikin natsuwarsa haka ma yan'uwanta ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana cewa "ko zan iya ganinta ?why not ranka shi dade "inspector runke !ya kwallawa yarsandar dake kan kanta kira cikin girmamawa ta shigo sai data sara masa sannan ta kame waje daya "jeki fito da yarinyar nan wacce akawo jiya "Okay sir ta fad'a tana juyawa cikin sauri ." Tana fita ATA ya kalli dpo "amman babu wanda ya ta'ba lafiyar jikinta kawai gsky nike bukata ?"yallabai babu wanda ya ta'bata yarinyar ma bata da rigima tunda aka kawota take kuka, very gud kar wanda ya ta'ba lfyta in sha allahu yadda kace haka zaayi batayi ma rashin kunyar da zaa ta'ba lafiyarta ba kawai dai taki amsa laifinta ne ya qarasa mgnr adaidai lokacin daaka shigo daita kallonta kawai yayi yana mamakin yadda kamaninta ya canza acikin kwana daya da yinin datayi ga dai shi babu alamun duka ajikinta amman cizon tsoro yayi mata yankan qauna ga dotti ya soma zama ajikinta tana ganinsa ta fashe masa da kuka tana cewa "dan girman allah yaya adam ka ceceni kasa a fitar dani daga nan wallahi idan na cigaba da zama anan mutuwa zanyi wallahi ban aikata komai ba ." ATA dake kallonta ya sake hade fuska babu wata alamun tausayi bata damu da yanayinsa ba dan tasan halin miskilancinsa da zafin zuciyarsa dpo Karan kanshi ya tausaya mata ya nuna mata wajen zama ta zauna ATA ya tsareta da idanunshi yana kallonta yayinda ita km ta cigaba da sheshekar kuka "har yanzu kenan baki shirya fad'ar gsky ba ?ban aikata komai ba me yasa zan amsa laifin da ban aikata ba wallahi kasa a tsananta bincike ni nasan ko waye acikin estate dinmu yake amman ni ban aikata ba ,wani kallo yayi mata sannan ya mike tsaye zaa yi bincike na karshe akanki kiyi adduar babu hannunki dan muddin ya zamoto kece zaki qarasa rayuwarki a inda yafi nan muni yana gama fadar haka ya bada umarnin a fitar daita tana kuka tana kiran sunansa aka fice daita ya kalli dpo yana sake jadda masa kar ta'ba lafiyar jikinta har sai an gama bincike yayi masa kyauta sannan ya wuce ." ***** bayan tafiyarsu alhj alqasim ummah suna hira da maryama tace da zarar kin qare bautar kasa kema zanyiwa alqasim magana ya nema miki aiki mai kyau ta yadda zaki samu damar taimakawa aunty ,dan Allah ummah kiyi masa maganar idan ya dawo kinga yace qasar ma zasu bari kinga idan yasan da maganar wata killa zai barwa wani sallahu". " in sha allahu maryama zanyi masa mgn kuma nasan zai min wannan alfarma bare kuma naga alamun kin kwanta masa arai murmushin jin dadi maryama tayi tace "ai duk saboda ke ne ummah darajanku naci banci haka ai bazan taka matsayin ko daura kwayar idanuna akanshi ba ". hirar sukayi sosai cike da so da kulawa wata ya qare ummah ta saka ran zuwansu alhji alqasim amman shiru har wani wata ya kai goma dan haka ta fidda rai da ganinsa koda ummah tayi hirar da maryama ta rausayar mata da kwayar idanunta domin ita a ganinta haka masu kudi suke da fad'ar abu su fasa mussaman idan bai shefesu ba "ummah karki wani damu da rashin zuwansu tunda daman su suka saka kansu ba wani ne ya sakasu ba ." Satin da suke ciki ya qare babu dalilinsu sai da aka sake shiga wani sati sai ga wayarsa yana sanar da yaya sadam yana nan zuwa ranar lahadi ranar suna jumaa dawowarta kenan daga wajen aiki ta samu labarin zuwansu daga bakin ummah ai kuwa dadi kmr ya kasheta da murna ta shiga side dinsu tana sanar da aunty cewar ranar lahadi zasu zo dan daman ta fad'a mata taimakon da ummah zatai mata sosai taga farinciki a fuskar aunty daman ita kadai take tausayawa a rayuwarta tana son ta taimakawa mahaifiyarta amman bata da hali ,dan zanen da take ba wani manya kudi yake kawo mata ba sakasancewar sai kayita bin office office na masu kudi dan ba kowa ya gama saninta ba bare su nemeta dan kansu, gashi tana son fitar da mahaifiyarta  cikin wahalar da take ciki amman bata da iko sai dai ta mika lamuranta zuwa ga Allah dan ya kawo masu saukin halin da suke ciki. ranar lahadi aka sake maimata irin hidimar daakayi masu a wancan ranar sai dai kuma wannan zuwan nasu akwai qarin abubuwa masu yawa daakayi karfe goma da yan mintuna motarsu ta tsaya a sabon titi market street wannan zuwa babu driver da babban dansa yusif da kuma kanwarsa Kausar sai dady da yake zaune a bayan mota ranar kamar wacan ranar yaya sadam ne ya tarbosu zuwa cikin gida sai dai shi Yusif bai shigo ba ya tsaya a haraban gidan yana amsa waya ."sakina aunty salma da aunty hassana da yayanta da baba gali duk suka fito tarbonsu ita kuwa maryama sai ta koma dakin ummah duk da tana bukatar farinciki wa rayuwarta amman sai ta boye kanta ."Kausar tafi yusif surutu dan ita take ta haba haba da su sakina da Islam da kaulat har ma da shukura da bata ta'ba ganinsu ba umma ta fito suka gaisa ta tmbyesu hanya ." Wannan dalilin yasa ta fito daga dakin umma dan karta kwatanta na kwana baya sai dai ta kasa shiga cikinsu ta rabe can nesa dasu byn ta gaishe da dady ta fito ta zauna a tsakar gidansu hannuwan yusif acikin aljihu ya shigo bakinsa dauke da sallama wacce ta makale a fatar bakinsa ganin maryama ya tsayar masa da sallama ya tsura mata ido jikinta ya bata ana kallonta dan haka ta dago a natse domin ganin mai kallonta nan take ta firgita ta qara gyara zamanta da daidaitawar mayafinta." ya tsura mata ido sosai yana kallonta ahankali yace "sannu !" sautin muryarsa ta doki dodon kunnenta amman ta kasa maida masa da sannun da yayi mata sai sunkuyar da kanta tayi dan bata son yawon kallo shine ma dalilin da yasa take yawo da nikaf duk inda zata dan sai mutane suyita kallonta wai tana da kyau da sauri ta mike ta nufi hanyar side dinsu ya dan lekota adaidai lokacin data waiga suka hada ido jin alamun tafiya yasa ya dawo da natsuwarsa sannan ya shiga cikin parlour'n umma da sallama tana ganin shigarsa ta dawo dan bata son tayi nisa ummah tazo tana nemanta ai kuwa tana zama tajiyo sauti muryar ummah tana kiran sunanta jiki a sanyaye ta shiga parlour'n ta durkusa." Kausar na ganinta ta fadada murmushinta ta riko hannunta "mamana ta bani labarinki ta fad'a hannunta na cikin nata maryama tayi murmushi wanda Ke bayyana kyawunta tace "da fatan tana lafiya? tana lfy tana can tana kewarki tace kin fini kyau da kunya har ma da qoqarin karatu da fari na karyata amman yanzu na gasgata a ganin da nayi miki a karon farko ,alhj alqasim da ummah sukayi murmushi yayinda yusif sai kallon maryama yake bai ce komai ba Islam kam sai wani yatsina fuska take jin yadda kausar ke yabon maryama ,alhj alqasim yace "ku bamu waje kuje kuyi hira "maryama muje wajen mamanki mu gaisheta lumshe idanunta tayi tare da cewa "to ! Hannun kausar na cikin na maryama suka fice Islam na biye dasu a baya maryama ta lura da irin kallon da yusif yake mata dan haka tasha jinin jikinta ,suka shiga side dinsu kausar tabi falon da kallo sannan ta dawo da kallonta kan maryama "tabbas nayi farinciki da ganinki a matsayin wacce mamana ta yaba da halinta har ma naji qaunar yin kawance dake ."maryama tayi murmushi kawai dan ita bata iya doguwar hira ba sai dai acikin ranta taji dadi ,ko bakya sona da Kawa ?ya zaayi naki sonki da qawa ai daman ke qawata ce kuma yaruwata ,ta rike hannuwan maryama da'ace acikin gari kike da yanzu ana nan ana hada gumi akanki maryama bata fahimci maganarta ba sai dai ta fahimci tana yi ne akan kyawunta murmushi tayi tace "akan me zaa hada gumi akaina ." Ta gyara zama "kyawunki yafi karfin zama acikin geto area bakowane acikin geto area hk zai iya cewa yana sonki ba saboda sanin kinfi karfinsa ko kina da samari ?"Sosai ta bawa maryama dariya ta kuma girgiza mata kai alamun bata da dan ganinta shi ya fiye mata sauki akan tace sun gudu sun barta ne ko kuma an kwace mata ,ai dole samari suji tsoron zuwa irin wannan kyau Masha allah wallahi ba wasa nike ba tun kafin na ganki momy ta fad'a min tayi min kyakkyawar qawa jinta kawai nayi domin ina jin babu wata macen da zan iya qawance daita anan amman ganinki na sha mamaki banda qawa zaki iya zarce komai agareni maryama tayi murmushi kawai tace "na gode ." "Kinga yayana yusif? Ta tambayeta tana kallonta "ko da yake ba sai anji a bakina ba maryama ta tsura mata idanu kawai tana kallon kausar cikin rashin fahimta dan ta fuskanci kausar nada yawon magana sosai ita kadai take kidinta take  rawarta,dan ko tmbyr manufar abinda ta fad'a batayi ba ta rabu daita suka cigaba da  hirar geto area ."acan kuma parlour'n umma alhj alqasim da baba gali da yusif da yaya sadam suna zaune bayan sunci abinda aka kawo masu saí alhj alqasim yace "ka gane wannan ?ya nuna masa yusif da hannu baba gali yace "yusif ne mana ya zaayi na kasa ganesa, a'a to yaron yanzu ne kwana kadan idan baka gansu ba sai kaga sun qara girma yusif yayi murmushi ya basar bai sake cewa komai ba ." Bayan tashin ummah dady ya dube baba gali yace "Gali wato zuwan da mukayi wancan karon wani ikon allah mai dakina mustafshira tun ganin maryama sai taji qaunar yarinyar har taji tayiwa danta shaawarta a matsayin matar aurensa dalilin da yasa banzo kenan ba tun wancan watan danayi alqawarin ba yusif baya nan yaje canada wannan dalilin yasa na tsaya har sai ya dawo sannan zamu zo tare ,yaron yaso yaki wai tayaya zai zo geto area neman matar aure amman sai na shawarcesa daya daure yazo ya gansu gbdy wacce tayi masa sai ayi maganarta ." Baba gali yayi murmushi zuciyarsa cike da farinciki yace "gsky abu yayi kyau mutun uku suna nan babu wacce akayi mgnr aurenta Islam da sakina sai maryama wacce take bautar kasa sauran biyu din km tun daga secondary basu cigaba ba amman dai ni ina son sakina ta cigaba alhj alqasim yayi shiru yana kallon Yusif yace kai duk gasu nan wacce ka tarar anan itace Islam din da nafisa ko ?baba gali yace a'a sakina wacce ta shigo karshe itace maryama "to kaji yusif itace sakina sai Islam wacce ta shigo karshe itace wacce mahaifiyarka tayi maka shaawar duk yayana ne babu wacce bazan yi murna idan ka aminta daita ba ,kai ma bazaa takuraka ba idan kaji babu wacce tayi maka sai a hakura ." Yusif yayi shiru yana tsotsa keya yace " zabin momy shine zabin da yayi min dan haka maryama itace ta shiga raina a kallon farko danayi mata alhj alqasim ya washe baki yana murmushi baba gali ba dan ranshi yaso ba yace to shikenan duk da daman akwai maganar wani dake sonta amman dai babu komai sai abashi hakuri alhj alqasim ya tsayar da idanunshi akan baba gali "da kuma kace babu wanda yake nemanta da aure? ya tmbyesa cikin mamaki shi kuwa yusif ido ya ware sosai dan shi wallahi yayi mata ko sama da kasa zasu hade sai dai ya hakura ya bar masa ." Baba gali yayi sauri yace "ai kasan samarin yanzu ba wani serious yayi ba amman sharesa kawai dan sama sama yake ma zuwa yusif ya sauke ajiyar zuciya alhji alqasim yace "shikenan ayi mata magana tayi miji shi wannan babu zuwa sama sama yazo kenan ayi mata magana sai muje mu gaisa da mahaifiyarta koda yaya sadam ya fad'awa umma murna har da sujja tayi ita kuwa Islam cikin kunci ta shige bangaren su byn ta gama ji sakina kam ko ajikinta dan ita tana son maryama bata dai san meke sata jin tsanarta ba ,maryama da kausar suka fito suna hira ganinsu yasa shi ya tsayar da hankalinsa akanta tabbas ta hadu yayi mamakin samun mace kamarta gata yarinya qarama just 20 amman ta hada abubuwa masu yawa dan ya darata da kusan shekaru shatakwas a duniya" Alhj alqasim ya bukaci ganawa da maryama ta shigo a natse ta zauna tare da takwashe kafafunta kanta sunkuye yayinda yusif yake ta kallonta bai ta'ba sanin akwai baki mai kyawun da tafi fari ba sai akanta ko da yake bazaa kirata da baka ba  sai dai chocolate colour" maryama ina son nayi miki wata tmby guda daya kuma ina son ki sanar dani tsakani da Allah ki sanar dani gsky ki daukeni tmkr mahaifi ne yake tmyrki ita dai shiru tayi tana tunanin irin tmyr da zai mata domin bata kawo komai aranta ba ko hasashen abinda zai tmbyeta "maryama ya'ya zamanku yake acikin gidan nan "? Ta tabbatar akwai abinda alhj alqasim ya gani yasa har yayi mata wannan tmyr tabbas bata da tacewa ba zata iya fad'ar irin bambamci da abubuwan da ake mata daga bangaren baba gali da aunty hassna har ma da sauran yanuwansu wadan da suka kasance yanuwa ga mahaifinta tunda daman duk mutumin da bashi ya haifeka ba ,dole sai an gane kuma bai zama lallai ya soka ba ,ya qara mata tmbyr ganin bata da niyyar cewa komai hakan kuwa ya qara sa zuciyar yusif mace wa akanta gbdy ganinta yasa ya manta da husna yarinyar da suka dauki tsawon shekaru daita kawai taimakonsa bai kawota gidansu ba daya san shikenan ya tafka asarar samun maryama ." Ya sake tmbyrta a karo na uku cikin sanyayyar muryarta tace "ban san ta inda zan fara ba amman dai bani da matsala muna zaune da kowa lafiya tayi mgnr tana sunkuyar da kanta shi kuwa yusif ya kasa dauke idanushi akanta alhj alqasim yayi shiru na dan wani lokaci sannan ya shaki iska yace "har mamanki ?ta sake gyada masa kai duk muna lfy bamu da wata matsala da kowa acikin gidan nan ita kam bata ga dalilin da zai sa ta fitar da sirri gidansu ,su din yanuwanta ne duk da basu dauketa a haka ba ." yayi shiru yana nazarinta shi dai ya fuskanci akwai matsala daga hasana har gali amman gashi ta boye masa yayinda zuciyar maryama ta dinga raya mata ta sanar masa gsky zaman da suke wanda naci ma da taimakon umma suke samu amman ina bazata iya ba ." Wannan hali nata yasa yaji lallai ta qara shiga ranshi duk nmj daya sameta yayi saa a duniya domin macen dake iya rike sirrinta itace mace da haka ya gama yace ayi masa iso wajen mahaifiyarta  a natse Umma tayi masu iso zuwa wajen aunty ta tarbi bakinta yadda ya kamata dan katuwar tabarma ta shimfada masu, alhji alqasim ya jima yana kallon aunty cikin tsananin tausayawa sannan ya dubi Yusif muryarsa sanyaye yace "ga mahaifiyar maryama suka qara gaisawa shima yana satar kallonta da alamun ya gano kyawunta maryama ta dauko duk da bata cikin sukuni amman fatar jikinta ta ya'yan masu kudi tana nan lafiya lau kyakkyawar fata mai sheki babu abinda ta rasa wajen auna kyakkyawa , hanci baki mai kyau idanu kausar kam kusa daita ta koma ta cigaba da zuba mata surutu nan da nan hira ta barke sosai atsakaninsu " Alhj alqasim ya gano dansa na bukatar kebewa da maryama dan kallon da yake mata babu sauki yace "maryama fitar da wannan matsoracin yaga cikin geto area daga nan akwai abinda zai fahimtar dake ta dan yi murmushi tare da dago idanuta suka hada ido da yusif wanda yayi zuru da idanunshi akanta aranta tace "bashin me naciwa bawan allah nan yaketa bina da kallo? bai yi tsammanin zata iya fad'ar haka ba dan hk yace mata "bashin gaisuwa mana baki gaisheni ba sai lokacin ta fahimci a fili tayi mgnr ai kuwa da sauri ta mike ta fice daga parlour'n jamar dake zaune a wajen sukai dariya yayinda yusif ya mike ya fito tana tsaye a tsakar gidan rungume da hannunwanta ya qaraso inda take tsaye "ina kwana ta fad'a tana sunkuyar da kanta sakamakon idanunshi dake yawo a sansar jikinta "yanzu ne ina kwana ? to ai bashi ka biyo kuma gashi na baka." Shiru sukai na dan lokaci ta sake sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ko zan iya tmbyarki ?kai kawai ta gyada masa tare da yin shiru tana mai jin tsanani kunya most especially idan ta fahimci sanar daita kalmar só zaayi ko mgnr aure dan ma wayewar karatuta ta rage mata wasu abubuwa ,amman duk da hk a shirye take da irin tmyr da zai mata dan kallon yayanta take masa tunda mahaifinsa yace ta daukesa tmkr mahaifi kunga kuwa dole ta daukesa matsayin yaya agareta muryata a sanyaye tace "nima ina da tmby idan kayi naka ka gama ?ya danyi taku kadan yana shirin barin wajen domin canza waje" muje daga can ta biyosa cike da natsuwa cikin tafiyarta kamar bata son taka qasa ." Ya tsaya tare da tsura mata idanunshi ya gyara tsayuwa hade da rungume hannunwansa a qirji "Kinsan tambayar da nake son nayi miki ?ta girgiza masa kai tana mai sake dukar da kanta "kina da saurayin da kike so ?ta dan dago idanusu suka tsarke cikin juna tayi saurin dauke nata tana cewa "acikin ranta kar dai abinda nake tunani ne zai tabbata ?kamar tace tana da mlm yahuza dan saukakawa kanta sake shiga wata rayuwa amman sai ta tsinci kanta da ce masa "a'a bani da kowa kin san kuwa kina da kyau sosai ?tace ina dai ji mutane na fad'a amman ni dai nasan bani dashi ,kiji tsoron allah yadda yayi maganar yasa tayi murmushi har fararen hakoranta da wushiryarta suka bayyana ." "Kina da matukar kyau ,Ke rayuwarki ce kawai a irin wannan area amman siffar ki da halinki suna manyan unguwa ne kinfi dacewa da zaman acan nasha mamakin dana ganki anan ?tayi murmushi "to saboda me zakayi mamaki dan na kasance a irin wannan unguwar ?",su mutane dake rayuwa acikinsa su ba mutane bane ?ya sake tsareta da idanunsa ganin karfin halinta akan maganarta "har wani dagewa kike da tmby okay ai an kusan daukeki tunda baba ya amince ? Shiru tayi tana nazarin maganarsa ai an kusan daukeki tunda baba ya amince domin kawar da maganar tace "dady yace zaka fahimtar dani wani abu me zaka fahimtar dani ?yayi shiru murmushi akan fuskarsa yace "matsalarki kunya ni kuma tsoro ta dan yi Jim ,a ina na zama matsala ?bai bata amsa ba sai kallon gabansa daya cigaba da yi daga bisani yace "ni baki tmbyeni ko ina da yammata ko bani dashi ba ?ta dan daga kafadanta alamun babu ruwanta da hakan domin wannan babbar maganace tama fi karfinta me ma ya kai ta ga wannan tmbyr ? "kodan saboda baki damu da yayanki ba ? "A'a? "Ya a'a da kin damu dani nasan zaki tmby ko yaya abinda ya shafi rayuwata mussaman Kiyi koyi da irin tmbyr danayi miki akan samari " nan da nan taji wani iri da alamun zai yi rigima da jan magana idan ba haka ita ina ruwanta da wasu yammatansa "karkiji da wai sai kin mun irin tmbyr da na miki zaki bar nan idan ba haka sai dai na tasa keyarki na wuce dake " ta zaro ido tana kallonsa da mamaki wannan shi ake kira karfin hali barawo da sallama "to shikenan bari na tmbyeka sai dai ba tmyr ka zanyi akan kana da yammata ko baka dashi ba dan nasan kana dasu aruru wata killa ma kullum sai kayi budurwa sama da hudu "dariya mai dan sauri yayi yana kallonta "lallai sai kace wani na mamajo yadda ya fadi mgnr ya bata dry dan hk daga dryr bata sake cewa komai ba sai shine ya cigaba da cewa "ni nan da kika gani matsoraci ne tsoron mata ne dani ban ta'ba cewa ina son ko mace daya ba ,ba dan kuma bana ganin wadan da nake so ba sai dan kawai dana tunkaresu da maganar só sai naji gabana yana faduwa ." Murmushi tayi "lallai ka cika matsoraci ta fad'a acikin ranta ya dan kyaleta amman gashi momy ta gaji da zamana haka ta samomin wacce zan aura "gsky kaji kunya kai yanzu mata ma kake jin tsoro a yadda zamani ya samu cigaba,sai kana yiwa mace kallon macen arziki sai kaga ashe ba haka bane ta dan yi jim ,"ina tmbyrka a ina matsalar take kace matsalarka tsoro ni kuma kunya a wani fannin kenan ?shiru ya biyo byn tmyrta har ga allah bata kawo komai ba saboda bata tunanin hadadden saurayi kamarsa zai ji wani abu akanta har ma ta burgesa sam bata kawo akanta ba haka take biyewa zancensa ." Ya katse mata tunani da cewa "daace zuciyar kowa zata fitar da matsalarta dana tabbatar zamu samu fahimtar juna har ki fahimci dady da kuma kin gane zabin da momy ta tay min "tayi shiru a ganinta mgnrsa bata dace daita ba bata san komai akan rayuwarsa ba ya sake katse mata tunani "kin shirya cire kunyar ki ni kuma na cire tsoro dan ki samu amsar tambayoyinki .?ta dan tabe baki " ni wai waya fad'a maka ina da kunya ya zaro ido "Subhallah Au baki da kunya ?tayi murmushi "to ai kaine wallahi ni ne wallahi me ?"wai na cire kunya sai kace kunyar takalmi ce ya danyi murmushi ya tsaida idanunshi akanta ita ma shi take kallo dan tana tunanin zai fadi matsalarsa ne ganin yaki dauke idanunshi akanta yasa tayi qasa da idanunta ta fara shan jinin jikinta domin irin kallon da yake mata mai fassara ne ." "Maryama wacce momy na ta zabar min ita ce daidai da rayuwata kuma tana kusa dani yardarta abbana yake nufin a matsayin na fahimtar daita soyayyata ya dan gyara tsayuwa "kece zabin abbana kece zabin momy sannan kece zabin kanwata ta sauke kanta ta qasa tsayuwar da kafafuwanta wata shuumar kunyarsa ta mamayeta ji take tmkr ta nitse a wajen daman manufarshi kenan agareta amman ta tsayar dashi tana ta dogon zance dashi ya qara fuskantarta "kece kadai naji duk duniya tun a kallon farko soyayyarki ta doki zuciyata da wani shauki ganinki a karon farko kaunarki ta mamaye ni yardarki itace yarda da abba yake nufi ki bani yardar soyayyarki ni kuma zan nuna miki hallacin so zan fayacce miki irin soyayyarki da take cikin raina ." Kamar ruwa ya cinyeta haka ta koma a wajen tmkr ba itace Ke hira ba ita kanta hirar datayi a awaanin abaya datasanin yinta take ,da kyar ta daga idanunta ta kallesa ganin gbdy idanuwanshi suna kanta yasa ta sake gyara mayafinta "ki daure ki sanar dani abinda zanjewa da momy domin ta samu sukuni momy na tana matukar qaunarki kullum tana kewarki da alfahari da halinki domin tace bata ta'ba ganin diyar talakawa da irin jarumtarki ba fannin hali da tarbiya da ina ganin momy ta dauki abun da zafi amman ganinki ya tabbatar min ni kaina zanyi alfahari dake idan kika kasance mata agareni kin dace da rayuwata ." Hakikanin gsky sai dai taki yusif saboda gudun rashin tabbacin samunsa ba dan bai cancanta ba har zuciyarta kalamansa sun dan wanke mata mikin dake daskare a zuciyarta na rashin mlm yahuza da abinda akayi mata amman duk da hk bazatai ganganci amsar wata soyayya a yanzu ba ina ma tana da tabbacin samunsa ? kinyi shiru kice min wani abu "batare dasanin ba kawai taji kalmar allah ya tabbatar mana da alkairi,kenan kin amince zaki auri matsoraci ?kai ma ka yarda zaka auri mai kunya tana gama fadar hk ta bar wajen da d'an saurinta ta boye abayan windowsu tana sauke numfashi ita ba wai tana jin sonshi bane aa ta gaji da rayuwar gidansu km tana son ta dauke mahaifiyarta daga cikin gidan suyi rayuwar farinciki kuma taga alamun zata samu a wajen Yusif ," Da zasu wuce aka shigo da kayan abinci masu uban yawa umma ta kara masu godiya yayinda maryama bata bari sun qara yin wata hira da Yusif ba duk da shi yaso suyi sallama amman taki duk mutanen gidan suka fito har yammatan gidan a tunaninsu zai ce yana só nan kuwa basu san tuni ya gama amayar da abinda ke ransa ba, suna tsaye a tsakar gidansu daga nan maryama bata qara taku daya ba ta koma side dinsu har bakin mota suka rakasu baba gali bai saba boyewa aunty salma komai ba dan ya kwashe abinda ya faru ya fad'a mata sakina na zaune tana jinsu aunty salma tayi shiru hankalinta a matukar tashe tace kai wani irin mutun ne da bai san ciwon kanshi ba ? ga sakina bazakayi mgnrta ba gsky wannan hadin bazai yuwu ba kenan rasa yahuza ma cigaba ya kawo mata ? "to ai kece da baki ruguza mgnrsa ba ai da dole cikin yayanki zaa aura shiyasa naso ki barta dashi Ke kuma kika matsa ." "Tô ai sai ka nuna masu akwai wanda take so idan yaso duk abinda akayi akan mlm yahuza sai a kwance kaga dole nasan zai dauki shukura ko sakina tunda iyayensa anan suke son ya zabi matar aure baba gali yayi shiru aikin gama dai Ya gama shiyasa komai nake gaya miki ki dinga bi ahankali gashi nan da kanki kin rusa rabon yayanki dan da tuni yusif rabon yayanki ne aunty salma tayi shiru tare da cewa "yanzu ma bata baci ba nan da dan wani lokaci kadan zai fasa ya kalleta ai nasan zaki iya amman hakan zai sa iyayensa su gane akwai wata sannan mutane ma zasu zagemu ."tsaki taja kai ka damu da wannan in har kana son yayanka da arziki ya zama dole wannan karon ka bani hadin kai baba gali yayi murmushi to ai ki bada himma da haka suka kawo karshen hirarsu tá tashi ta dauki mayafinta ta nufi gidan alfa Tayi saa bata samu kowa ba duk abinda ya faru ta sanar dashi yayi murmushi yace "kada ki damu Ke ai mutumi yar arziki ce bakya rabuwa damu duk runtsi kuma da yarda allah zan taimaka miki ki tashi kije ko kaffara bazan yi ba wallahi sai yusif ya auri sakina ko shukuran Kike so ,cikin farinciki ta koma gida duk yadda sukai da alfa ta sheidawa baba gali ya kuma yi murna dan shi kanshi da baya son tana zuwa bin malamai dan yasan har dashi takewa amman yaji dadin na wannan karon tunda yar shi guda jininsa zata taimaka ." duk mutanen gidan suna zaune a tsakar gida Maryama na zaune kusa da umma ganin kamar zaa tautauna akan yusif yasa ta yunkura ta mike nan kuwa taji sun fara tautaunawa akanshi tana tafiya tana tsinkayo maganarsu har tayi nisa ta daina jin komai ."da misalin karfe tara na dare sai ga kira daga baba gali bata kawo komai aranta ba sai mgnr yusif zai mata ,tana isa ta gaishesa ya amsa yana gyara zama yace "wai me ya hadaki da mlm yahuza ne ?tambayar tazo mata a bazata domin irin haka bata ta'ba hadata dashi ba, koda suka rabu bai kirata ya tmbyeta ba sai yanzu data manta dashi tace "babu komai dan ban san abinda nayi masa ba daya canza da shukura" to ai ba soyayya bace a tsakaninsu da shukura ita kanta salma rashin fahimta ne ku dawo Kmr yadda kuke dan dazu da kanshi yazo neman ki" "Nemana kuma me kuma zai min ai ni na rigada na yafesa har abada ,aa maryama ban sanki da fushi ba Kiyi hakuri idan ya dawo ki samu ku sasanta kanku kinji bai kamata ba dama shi irin wannan sabanin ai dole yana zuwa a mijin da zaka aura ,ido kawai ta zuba masa kafin daga baya ta sunkuyar da kanta kasa ahankali ta furta to "baba ina kuma alqawarin da kayiwa abban kausar ?yayi shiru yana dan nazari "maryama da na zama qaramin mutun ta bangaren mahaifin mlm yahuza ai gara na zama ta bangaren alqasim maude domin shi zai min uzuri kuma idan na hada yusif da yaruwarki sakina ko shukura nasan komai zai wuce ." Tayi shiru kawai hawayen takaici suka nemi zubo mata daga idanuwanta gbdy ta rasa abun yi kawai ta mike ta koma banger su ta fad'a dakinta ta kwanta ta kudundine kanta ta fara rusa kuka mara sauti dan tasan wannan ma ya zama ba rabonta ba tunda ma baba da kanshi ya furta mata haka yanzu ita hk rayuwarta zata qare cikin kunci da wahala "me ta tsare masu da basa qaunar cin gabanta? duk wani abu da suka san zai zama cigaba arayuwarta basa so ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 25 Allah sarki maryama kwana tayi kuka har sai da garin allah ya waye sakamakon haka fuskarta ta kunbura ita kanta ta rasa dalilin me yasa take kuka rashin yusif da zatayi ne ko kuwa dawowar mlm yahuza ne ?a zahirin gsky duk bbu ko daya aciki dalilin zubar hawayenta ,zubar hawayenta bai wuce na rashin qaunar da baba gali yake nuna mata kiri kiri ba, lamarinsa yana mugun daure mata kai ." Tarasa gane kanshi ,mai hakan yake nufi da aikatawa? anya ma kuwa baba gali yana cikin haiyacinsa dan kwananan abubuwan da yake sun qara shan bambam dana da ? al'amarin ya damu maryama har yasa kwalkwaluwar kanta Ke neman tarwatsewa ,da gaske dai baba gali da sauran dangin mahaifinta basa qaunarsu sai ma a yanzu ta qara gane cewa ba dalilin haduwar iyayenta bane silar qiiyayyarsu garesu daman can basa qaunar mahaifinsu ." Babu kuzari ajikinta haka ta tashi da safe aunty da habib suka damu sosai da ganin sauyi atattare daita idanuwansu na kanta lokaci zuwa lokaci suna lura da damuwar da take baibaye daita sai dai basu ce mata komai ba sanin ko sun tmyeta zata fad'a masu babu komai, amman ita maryama tana lura da yanayinsu nason yi mata magana ." aikinta data saba na safe tayi bayan ta kammala ta shiga wanka wanda zuwa lokacin Auty ta gama girki ta fito cikin doguwar rigar tana zama aunty ta kawo mata nata abincin tasa abincin agaba tana tsakura yayinda zuciyarta ke mata tuni da abubuwan da suka faru jiya atsakaninta da yusif ta jisa dabam akan mlm yahuza ,ko kadan zuciyarta ta kasa daina tunaninsa ba wai dan tana sonshi ba dan gsky daga haduwarsu jiya bata ji cewar tana son shi ba ta dai amincewa aurensa ne saboda ta samu saukin rayuwa ,soyayya kuma tasa aranta bayan sunyi aure zata so shi daman ita kuma ba dabiarta bace saurin zurmawa soyayya ." Tana tsakurar abinci sannu ahankali har taci rabi ta dauki plet din da taci abincin ta kai inda suke yin wanke wanke ta dawo ta nufi hanyar dakinta tana qoqarin shiga aunty ta kira sunanta cikin muryarta mai tsananin tausayawa agareta ta juyo a natse tare da amsawa sannan ta dawo inda take zaune ta durkusa agabanta ,aunty ta dubeta sosai ta sauke numfashi tace "yanzu princess har akwai damuwar da zata dameki ki kasa fad'a min ? Nan da nan ta rikice domin dai bata son fad'a mata komai sannan bata son tasan ma tana cikin damuwa dan ita a ganinta gara ta boye damuwarta muryarta a matukar sanyaye tace "aunty ai bana boye miki komai kuma Kinsan idan akwai abinda Ke damuna kece mutun ta farko da zan fadawa tunda bani da wacce ta fiki ko babu komai adduarki nada matukar mahimanci agareni "yanzu zaki iya rantsewa da Allah babu abinda ke damunki ."? Maryama tayi shiru dan bazata iya rantsewa ba kuma bazata iya sanar daita ba dan zata fita shiga damuwa ita kuma bata qaunar ganin damuwarta wallahi akan taga aunty cikin damuwa gara ita ta qare rayuwarta aciki ,duk maganar da aunty ta keyi ba tace uffan ba illa ta sunkuyar da kai kawai tana sauraronta zuciyarta na karkarwa , duk yadda aunty taso taji wani abu daga bakinta amman taki ita dai ta karbi qaddarata na rashin yusif." Haka ta kasance acikin gidan zuciyarta babu sukuni kwana uku da faruwar abun sai ga mlm yahuza yazo gurinta har da bata hakuri yana mai jinjina abinda yayi mata ,yace shi kanshi yayi mamakin abinda yayi ,wai shine yake kin kulata kuma shine yayi soyayya da shukura ? yana magana Kmr zai yi kuka wanda ita ahalin da take ciki bata jin tausayinsa kuma bata jin zata karbe shi ta barwa duk wata mai so kai auren ma ta hakura dashi har abada ." duk hirar da yake mata baya mata dadi wani irin tsanar shi taji yana shigarta sannan duk nacinsa haka ta wuce ta barsa ta koma cikin tana tunanin yadda alamarin zai kasance shin idan yusif yaji hukuncin baba gali ya zai yi ?."zai amince ne ko kuwa dai shima zaa kawar masa da tunaninsa ne kamar yadda akayiwa mlm yahuza? " bani da gata bani da kowa sai allah da kuma mahaifiyata ta sheidawa kanta haka ." "mai zai hana ki fadawa mahaifiyarki gskyr lamari sannna ki tashi tsaye da addau zuciyar ta ,ta fad'a mata haka? zan dai tashi da addaua amman bazan iya fadawa aunty komai ba dan zata fini shiga damuwa gara idan maganar ta fito taji daga sama ta kwanta shiru tana kallon saman dakin hawayen na gangarowa ta gefen idanunta ." Kuka take har da shesheka wanda bata ma san sautin muryar kukan na fita ba, cikin haka aunty ta turo kofar dakin ta shigo ganinta haka yasa taji wani gagarumin tashin hankali da sauri ta qaraso kusa daita ta zauna tana kiran ainihin sunanta "maryama ! a matukar firgice ta dawo natsuwarta ta mike ta zauna tana goge hawayenta da hannuwanta duka ,aunty ta tsura mata ido kawai tana kallonta dan gbdy rasa abinda ke mata dadi arayuwarta take idan taga maryama cikin damuwa ." A dan fusace tace "kukan me kike yi ?wani irin bugawa qirjin maryam ya shiga yi nan take ta shiga kokuwa da numfashinta dake barazanar daukewa sakamakon kukan da take sannan ahankali ta shiga girgiza wa aunty kai alamun babu komai "babu komai kike kuka haka maryama ?"yanzu bazaki fad'a min damuwarki ba ?"Ke kenan kullum cikin damuwa cikin zubar da hawaye nasan acikin kwanakin nan akwai abinda ya faru wanda kike boye min meye shi sannan waye yazo wajenki ."? hawayen da take kokarin maidawa suka samu nasarar gangarowa bisa kuncinta cikin sauri ta shiga gogewa wasu na sake gangarowa cikin muryar kuka ta soma magana "da fari dai mlm yahuza ne yazo "mlm yahuza kuma ?me yazo yi?tayi mata tmbyr a jere tana dubanta qirjinta na bugawa da karfin gaske "wai ya dawo ! shiru aunty tayi tana nazarinta sannan tace "shine dalilin shigarki damuwa ?maryama ta girgiza mata kai tana cewa "bashi bane! "to menene ni ?" abinda Ke damunki nake bukatar sani "ban san me yasa baba gali baya qaunata ba ta qarasa mgnr tana zubar da wani hawaye "Kawai dan baya qaunarki shine zaki zauna kina kuka kina damun kanki ?ai ba dole sai ya soki ba, rayuwar nan fa da kike ganinta ba kowa bane zai soka, sai ku fito ciki daya da mutun yace bai sonka bare shida dan uwa yake a wajen mahaifinki ." aunty ta kamo hannunta daya cikin nata sannan ta kai dayan hannunta tana goge mata hawaye "ki cire wannan damuwar ki manta da batun bai sonki wata rana sai labari kuma maganar dawowar mlm yahuza karta daga miki hankalinki tunda nan kusa zakuyi aure da yusif naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana sake matso ruwan hawaye idanunta "Allah sarki aunty ai shima ya zama ba rabona ba ta fad'a a kasan ranta zama aunty tayi tana rarrashinta har bacci ya dauketa sannan ta mike ta bar dakin ." ***** A yammacin ranar litini wanda yayi daidai da kwanan nuzla uku a police station labarin halin da take ciki ya samu jama'ar dake rayuwa acikin abdullahi estate kowa ya shiga damuwa matuka amman banda hindu dan ita murna tayi sosai dan ta fahimci itama tana cikin masu son abinda take so , hisham kam yafi kowa shiga damuwa yayinda hjy salema banda kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun babu abinda take furtawa da zubar da hawaye ." "Ya'yan hjy salema suna zaune gbdynsu a cikin parlour'nta cikin jimami har hisham wanda ya fita haiyacinsa ATA ya shigo bakinsa dauke da sallama ,baa kai ga amsa masa sallamar da yayi ba hisham ya tashi a matukar fusace ya soma magana cikin zafin rai "me ya kawo ka ?" me kake takama dashi ?ya tmbyesa .ATA ya zauna yana duban screen wayarsa" laifin me nuzla tayi maka? me ta tsare maka ?komai zata maka ai bata cancanci kayi mata haka ba ? zaka iya yiwa nana hauwa'u haka ko zaka iya yiwa zabiba haka ?" ATA bai kulasa ba dan yasan baya haiyacinsa so ya rigada ya zautar dashi." "Mutumin banza dan rainin hankali kawai da bai san mutuncin na gaba dashi ba ,kace baka son yarinya amman gashi akanta kasa an kama yarinyar mutane ATA bai dago idanushi ba ya cigaba da kallon screen din wayarsa yana cewa "ka shiga hankalinka hisham zaka iya fad'ar komai na barka dan nasan a haukace kake ,amamn idan ka sake hadani da yarinyar nan zan ajiye haukan soyayyar dake damunka a gefe nayi maka wulakanci." "Kai ne dai mahaukaci amman ni lafiyata lau "hisham zamu samu matsala !mun dade bamu samu ba ,nace kana sonta !! baka sonta me yasa zaka sa akama nuzla ?nan zuciyar ATA ya motsa ya somawa hisham wani kallo mai tattare da tashin hankali ganin kar abun ya zama fad'a a tsakaninsu baba babba ya takawa hisham burki ." ahankali ATA ya soma warware komai da sakon da nuzla ta aika masa dashi "nayi wannan bayanin ne saboda hjy da kuma baba Babba sai ku yanuwanta dan kusan dalilin da yasa ta shiga hannun hukuma "ban bada umarnin ayi mata komai ko a ta'ba lafiyar jikinta ba ,abinda yafi zama mai mahimanci shine bincike kuma ana kanyi abinda nake son gbdynmu mu fahimta yana da kyau mun san daga inda matsalar take wacece ta kashe mubina ? "wallahi ni ba akan yunkurin kashe wannan yarinyar yasa na damka nuzla hannun hukuma ba dan ko nana hauwa'u aka kama da laifin kisa ko yunkurin kisa da kaina zan damkata ga hukuma haka zalika nuzla qanwata ce Kmr yadda nana hauwa'u take a wajena ,tayi kuka tayi rantsuwa akan bata aikata ba amman wacce ta aikata tana tare damu kuma nasan muddin ba nuzla bace hakika muna tare da mai yin kissan dan haka da zarar an kammala bincike da kaina zan dawo daita gida mu san abun yi amman ya zama dole mu san wacece ta kashe mubina acikinmu ." parlour'n ya dauki shiru duk suka zuba masa ido kawai suna kallonsa da sauraronsa bayan kamar minti goma ATA ya numfasa sannan ya kalli inda hajiya salema take zaune tana faman kuka "kuyi hakuri hjy km ki kwantar da hankalinki matsawar babu hannun nuzla acikin zakiyi farinciki yana gama fadar haka yayiwa baba babba sallama ya nufi kofar fita yana zabgawa hisham harara ." tsaye hindu take tare da jingina jikinta da bangon dakinta ta hade hannuwanta duka waje daya ,sosai tayi nisa cikin duniyar tunanin yadda zata kawar da maryam a doron duniya tun kafin akai ga daura masu aure da adam ,dan ta gwamaci ta kasheta idan yaso itama akasheta kowa ya rasa adam din gbdy ." ji tayi an dafa kafadarta ta juyo a hankali idanunta ya sauka akan baba qarami ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana runtse idanunta yayinda gabanta Ke dokawa da wani irin karfi "karki illa kanki akan wannan dan iskan yaron da bai san mutuncin mutane ba "kafi kowa sani baba ina mutuwar son shi wannan maratuncin da dukkanin rayuwata kuma kafi kowa sanin bazan iya rayuwa babu shi ba, amman kana ji kuma kana gani kana da ikon da zaka sa umarni kawai zaa bashi ya aure ni amman kaki kayi komai akai wallahi baba ji nake kamar na mutu ta kamo hannun baba qarami ta kai daidai saitin qirjinta yaji yadda qirjinta ke bugawa da sauri sauri ." gbdy ya sake shiga rudani duk tunaninsa ya tsaya ya rasa ta ina zai fara ga matsalarsu ta kamfani da kullum cikin rigima ake ga qaddarar data dade da fadawa diyar daya fi so da qauna "idan bazakayi komai akai ba ni zanyi koma nace na fara zan kuma cigaba daga inda na tsaya dan bazanyi asararsa ba sai dai duk mu taru muyi asararsa ,wallahi idan ban kashe mrym acikin estate din ba zan shirya inda zan kasheta "tsaki yaja yana cewa "ban san me yasa kike son Kiyi kisa akan wannan dan iskan yaron ba baba qarami ya fad'a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ." matsawa tayi kusa dashi ta qarasa bakin gadonta tana jan zanin gadon tana sake shimfidawa "hakika zanyi abinda yafi kissa akanshi idan akwai ,kuma zan mutu amman kafin na mutu duk sai na rabashi da masu sonshi idan kuma nayi nasara asirina bai tono ba zan mallakesa idan kuma ban mallakesa ba shima zan kashesa a karshe na kashe kaina da kaina shikenan na mutu cikin salama ta qarasa mgnr tare da kwanciya tana mai kamkame jikinta waje daya wani son ATA ne Ke sake ratsa koina a sansar jiknta yayinda tsumammiyar soyayyarsa data dauki tsawon shekaru tana yi masa ya dinga taso mata kuka ta fashe dashi dan tana son rage wa kanta radadin dake makale a tsokar dake qirjinta a fusace baba qarami ya fice ya bugo kofar dakin da karfi har sai da qararrawar zuciyarta ta amsa ." Ammi da nana hauwa'u diyana humaira suna zaune a saman kujera,yayinda maryam ke zaune a qasan carfet humaira na yi mata kitso hirar abinda ya faru da nuzla suke kadan kadan suna mamakinta diyana tana cewa "wallah gara da yaya adam yasa aka ka mata ni yanzu nake tunanin ma itace ta kashe mubina "babu mamaki dan mutun abun tsoro ne inji cewar humaira ." "A'a karki ce haka diyana Allah ne kadai yasan wanda ya kashe mubina tunda ita ba anan aka kasheta ba kuyi wa yaruwarku kyakkyawan zato , mami Kiyi tunani da kyau da irin wukar da akayi yunkurin kashe maraym da ita aka kashe mubina , me yasa zakiyi zarginta ?sannna akan wani dalili har zata aikata hakan akan mubinarmu bayan gabadayanmu muna son mubina nana hauwa ta tmyta ? Wannna fa ba zargi bane tunda yaya adam yasa aka kamata kunsan akwai wata a kasa babu rami me ya kawo rami ."? "Ni kuma nafi tunanina akan yaya adam ne inji cewar humaira "akan yaya adam kamar ya ? duk suka kalleta fuskarsu da alamun tambaya "ai ta dade tana son shi kusan ranar da mubina ta furta agabanmu cewar tana mutuwar son yaya adam hankalinta ya tashi . duk suka natsu suna sauraron humaira ta cigaba ai bayan mun rabu ni ta fad'a min amman alaokacin cewa tayi tunda mubina ta rigata furtawa ita ta hakura sai kwatsam sai ga mutuwarta ni tun lokacin naso na fasa maganar amman nayi shiru gudun abinda zai je yazo ."nana hauwa tayi shiru kafin daga baya ta numfasa bata tunanin nuzla zatai haka dan ko byn mutuwar mubina ta dade tana jin mutuwar ,ita kam maryam ta yarda da hakan dan lokacin da akayi yunkurin kasheta kowa yazo amma ita bata zo tayi mata jaje ba ." "Lallai mami danki yayi kasuwa dan ita karon kanta a ynzu ta fara jin son shi aranta amman kuma meye a attare dashi da kowa Ke son shi haka ? tana jinsu suka cigaba da hira batare data tsoma bakinta ba ."suna cikin hirarsu ATA ya sanya hannunshi ya turo qofar falon tare da sallama akan labbansa duk da bai bude muryarshi sosai ba,maryam dake kallon kofar shigowa ta dago fararen idanunta suka sauka cikin nashi sanda yake takowa cikin falon mami na masa duban mamakin dawowarsa adaidai lokacin sosai ya dauki hankalin maryam dan yayi wani fresh ya qara kyau kaman wani sabon matashi amma fa fuskar nan tashi tana nan kamar koda yaushe babu annuri a hade da miskilancin wanda na yanzu ya qaru " Kallo daya yayi mata tai saurin janye idanuta akan shi shima ya maida kallonsa kan mami fuskarshi babu yabo babu fallasa"Lafiya dai ko adamcy Nah naga ka dawo by this time ?"Lafiya qalau sweetheart ..." Ya fadi alokacin da yake qoqarin zama a saman daya daga cikin kujerun falon idanunshi na kallon sama suka hada baki suka gaisa ya amsa da "Lfy ! kawai "Adamcy yanzu me ake ciki akan halimatu ne ? ni kaina yanzu bazance komai ba sai abinda hukuma suka ce " ya fad'a yana furzar da iska yanayin yadda yay mgnr kamar yana cikin damuwa." "Me za'a kawo maka? "coffe " to maza mrym tashi ki kawo masa" badan ranshi yaso ba yayi shiru dan ko yace zai yi mgn damuwa kawai zai qarawa kanshi."ranar da nuzla ta cika kwana biyar aka kira ATA daga police station bayan yaje aka tabbatar masa an kammala duk wani bincike kuma ansamu bambamci a wajen gwajin zanen hannu ,dan nuzla da hannun dama take amfani yayinda mai kisan da hannun hagu, bugu da qari ba zanen hannunsu daya ba dan haka zai iya tafiya daita "to shikenan a fito daita ya fad'a lokacin daaka fito daita shi kansa ya tausaya mata tana ganinsa ta durkushe a gabansa ta kamkame kafafuwansa ajikinta saurin dauke numfashi yayi sai dai tausayinta ya hanashi zareta kafafuwansa ajikinta duk da dottin da jikinta yayi ." Murya cikin kuka ta soma mgn "yaya na fad'a maka ban aikata komai ba wallahi bani bace kasa aka kawo ni nan kalli jikina yaya ni kaina bana son ganin kaina haka dan allah karka barni anan ka tafi dani gida ka tausaya min kafin na mutu da kyar ya samu ya zare kafafuwansa yana sauke numfashi ya mike tsaye yana mikewa dpo hannu "na gode sosai idan na koma gida zan kira akwai maganar da zamuyi "okay yalla'bai sai najika zumbur nuzla ta mike tsaye tana kuka "dan allah yaya karka barni wallahi bani bace dpo yayi murmushi yana cewa "ai ki kwatar da hankalinki yau a gida zaki kwana wani irin naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana masa godiya ATA yayi gaba ta biyosa da sauri ." Suna shiga cikin estate dinsu kai tsaye hanyar gidansu suka nufa sukai parking masu tsaronsa suka firfito shima ya fito suka nufi cikin gidan a parlour'n suka iske hjy salema da wasu yanuwanta mutun biyu da gudu nuzla ta qarasa ta fad'a jikinta tana kuka itama tana kuka ta rungume diyarta tana shafa bayanta ganin irin kukan da suke yasa ATA ya juya ya kama gabansa alkwari ne kuma ya cika ranar kam murna wajen hjy salema da yanuwanta baa magana sai da kira doctor domin lafiyar nuzla tare da allurar." Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah kullum kwanakin bikin ATA da maryam qara matsowa yake har yau ya rage sauran kwana bakwai kuma har lokacin zuciyar ATA bata rusuna ba salim da mb har ma da hisham ango suke yin duk abinda ya dace dan shi dai ATA yace bazai bata kudinsa akan auren maryam ba kuma babu abinda zai yi na event duk kuma wanda ya kashe kudinsa kar yace dan shi yayi ,dan bai aike kowa ba duk sun jisa amman babu wanda ya tankasa mb da hisham sunyi rabon iv sun kai duk inda ya kamata ace sun kai sosai shirye shirye yayi nisa amman babu ruwan ango dan ko tautaunawa baya yarda suyi dashi da zarar sun soma mgn zai bar wajen ." Yau tun safe maryam ta tashi jikinta a sanyaye ji take kamar zata rasa rayuwarta komai take gabanta na faduwa abu na tashin hankali dana farinciki duk sai taji gabanta ya yanke ya fadi har kasan mararta take jin ga zuciyarta dake tsinkewa shiru kawai tayi kwance har zuwa lokacin da mami ta shigo "maryam bacci kike yi ne ?ta tmbyeta tana shigowa dakin sosai ta yunkura ta tashi daga kwanciyar datayi tana cewa "a'a mami ba bacci nake ba na dai dan kwanta ne ."akwai abinda zan miki ne ?mami tayi murmushi tana dubanta dan ta lura tunda aka shiga satin bikinsu take cikin damuwa ." "akwai abinda ke damunki ne ? Ta girgiza mata kai alamun a'a "ki sanar dani idan akwai abinda Ke damunki ni din tmkr mahaifiya ce agareki ? ta sake girgiza mata kai alamun a'a sai dai kallo daya zaka mata ka fahimci akwai damuwar dake damunta ,ki cire damuwa aranki kinji maryam babu abinda zai faru sai alkhairi ta lumshe mata idanunta alamun ta gamsu "maza tashi ga mukulin mota kije gidan shahida yanzu ta kira wai kije tana son ganinki anya kuwa zan iya tuki nan mami ? bana jin zan iya dan bani da kuzari ajikina ,to shikenan bari nayiwa nura direba mgn ya kai ki ." "to mami amman bari naje nayi masa magana da kaina tare suka fito maryam ta fice ta bar mami da nana hauwa'u a parlour'n zuwa haraban gidan akan idanun hindu ta fito dan haka tayi adduar samun nasara da aiwatar da nufinta akanta domin kusan wata guda kenan tunda aka saka lokacin aurensu take neman hanyar da zasu samu kebewa ." bayan maryam ta fad'a masa zai kaita gidan aunty shahida ta juya ta koma ciki domin ta qara shirya kanta a parlour ta tsaya kusa da nana hauwa'u "sister muje ki shirya ki rakani." a'a babu inda zani maganarku ta matan aure zakuyi ina ni ina rakiya kinga je ki kawai sai kin dawo allah ya tsare hanya" ganin mami zaune a wajen yasa maryam bata sake cewa komai ba ta shige ciki .yayinda hindu ta qaraso inda nura yake zaune tana cewa "mlm nura ina son na dan aike ka ko akwai abinda zakayi ne ?tayi masa tmbyr dan tasan me zai yi adaidai lokacin "hajiya mryma zan kai unguwa okay to shikenan karka damu allah ya tsare ta juya zata koma ciki ,kina bukatar wani abu ne ? Ta tsaya cak ta dan juyo fuskarta a sake "daman abu nake son a karbo min anan bakin titi amman tunda fita zakayi karka damu ,aa baa yi haka ba kawo nayi sauri na karbo miki kafin ta fito ta mika masa kudi dan cake zaka amso min amman mai chocolate ya karba kudin ya nufi babban get din estate din da dan saurinta ita kuma ta shiga gidansu domin ta shirya ."akan idanunta still maryam ta fito kafadarta makale da jaka tana neman nura direba tayi sauri ta fito tana cewa "mrym amarya fita zakiyi ne ?ta waigo bayanta a hankali ganin hindu ta saki fuska sai dai mgnr datai mata yau din ya dan bata mamaki dan sam batayi tsammani ba dan ba abokiyar maganarta bace domin dai kusan duk kallon mai girman kai suke mata kasancewar ta girmesu km bata shiga cikinsu " "Eh wallahi fita zanyi nura direba ne zai kai ni gashi na fito ban gansa ba ko ina ya shiga ,Allah sarki okay muje na saukeki mana nima fita zanyi ta fad'a tana qoqarin shiga motarta da kamar bazata shiga ba amman sai tayi tunanin karta ga Kmr tayi mata wulakanci dan haka ta yanke shawarar shiga idan yaso direban aunty shahida ya dawo daita ta bude dayan bangaren ta shiga ta zauna hindu ta tada mota suka fice daga gidan koda nura direba ya dawo kai tsaye gidansu hindu ya nufa ya bada sakonta ya dawo zaman jiran fitowar maryam ." Ahankali suke tafiya hindu na jan mrym da hira "Maryam amarya adamcy kenan gashi yazo amman naga baki fara shirin komai na amare ba, wallahi ban fara ba dan bana cikin natsuwata "to me kuma Ke damun amarya ko fargaban kasancewa da angonki ne ? maryam tayi murmushi kawai "Ke kuwa me zasa kiyi fargaba alhalin auren soyayya zakuyi ?ko auren soyayya ne dole kaji wani iri dan aure ba wasa ba, kenan gskyr labarin danake ji daga bakin mutane daban daban na kina son adamcy gsky ne ? zuciyar maryam a dake tace "eh hk ne muna son juna ." "Na tambayeki ? "Ina jinki ! mu ajiye maganar wasa zaki aure adamcy ne saboda kina son shi ko kuma zaki auresa ne dan biyayya wa mahaifiyarsa ? "zan aureshi ne dan ina son shi "akan wani dalili kenan zaki so shi ? tambayar tabawa maryam mamaki amman sai ta kawar da mamakinta tace "akan dalilai masu yawa ."ko Kinsan akwai wacce ta fiki son shi da son mallakarsa wacce zata iya komai akansa ? "Eh nasani "! "Wacece ?ke mana na samu labarin kina mutuwar sonshi Kmr Kiyi hauka afirgice hindu ta juyo gareta tana cewa "tabbas bakiyi karya ba ina mutuwar son shi irin son da zan iya yin komai akanshi dan haka abinda zan iya ce miki ki rabu dashi ki kuma fasa aurensa saboda adamcy raina ne akanshi babu abinda bazan iya yi ba ". "ni kuma akan na rabudashi na bar miki gara na rasa raina." shine nima abinda na gani kenan, kuma nake tunani akai, kmr mutuwar ce zata fiye miki sauki akan ki cigaba da rayuwa a doron duniya , dan zan kasheki tun wa'adin kwanakin mutuwarki bai cika ba, zanyi sanadin rasa ranki batare da kin shiryawa hakan ba, ta karasa mgnr cike da matsanancin zafin rai tana fitar da hucin kishi. "wai meye haka ne hindu kike kokarin aikatawa ruhin da bai d'aukar miki laifin komai ba? "gsky zan gayawa mami . "ba sai kin rayu ba tukun zaki gaya mata ina tabbatar miki daga nan sai kabarinki, domin kuwa zan miki aika aika ,zakiyi mutuwa mafi muni da rad'ad'in azaba wanda ko makiyinki yaga gawarki sai ya koka miki "aikin banza kawai daman da wata manufa kika daukoni a motarki ? "Yes of course da wata manufa na dauko ki mana ,amman da yake Ke jaka ce kika qasa ganewa tana gama fadar hk taja wani irin wawan birki sannan taja motar aguje ta soma hajijiya da motar akan titi bata tsaya akoina ba sai atsakiyar titi , ta fito da hanzarinta, kafin maryam tayi wani yunkurin fitowa daga cikin motar , tuni har hindu tayi lock din motar gbdy , ta tsaya rike da kugunta tana dubanta tana murmushin mugunta ,"wai meye hk ne hindu ? "mutuwa kenan !" "ki budeni karki kasheni da wasa nake miki wallahi bana son shi nima zan auresa a dole sbd mahaifiyarsa "hhhhhhhhhhhh karyarki yarinya ai wasan ya rigada yazo karshe sai ki jirasa a lahira har zuwa sanda zai iso gareki so that kwa auri juna acan inda wata katuwar tanka mai ta nufo motar gadan gadan a matukar tsorace maryam ta saka wata razananniyar k'ara me sauti "tana toshe kunnuwanta duka tare da runtse idanunwata ....... Mmn sudai 💗💗💗💗💗💗 MAR'ADAMS 💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 26 hankalin maryam ya qara tashi Kuka take sosai da iyakacin karfinta tana furta duk wata adduar data zo bakinta domin neman cikawa da imani dan gabadaya ta sadaukar da rayuwarta akan mutuwa zatayi yayinda hindu ke tsaye rungume da hannuwanta duka a qirji tana sakar mata murmushi farinciki tana kallon yadda motar ke tahowa wajen motarta da maryam ke ciki ." maryam ta kamkame jikinta sosai tana mai sake fashewa da wani gigitaccen kuka jira kawai take taji saukar motar akanta amman sai taji shiru sai ma jiniyar motar ' yansanda ta jiyo dan haka da sauri ta ware idanunta dan tabbatarwa kanta gaske ne ?ganin motar yansanda ta sha gaban motar yasa ta sauke wani naunayen ajiyar zuciya da numfashi atare ,yayinda mutumin dake ciki motar ya soma qoqarin fitowa domin ya tsire amman cike da hanzari yansanda suka samu nasarar damke bala ,cikin tsananin tashin hankali yake masu bayanin komai dan gabadaya ya gama rud'ewa " Yayinda hindu ke tsaye awaje kamar an dasata tsabar firgitar da tayi zufa ce kawai ke karyo mata dan kana kallonta zaka fahimci yadda hankalinta yayi mugu mugun tashi , gashi tana son guduwa kamar yadda bala yayi qoqarin yi amman ta kasa aiwatar da hakan har sanda ' yansanda suka samu nasarar daba masa ankwa a hannuwansa tana tsaye kikam kamar mashi ." Zuciyar hindu ta shiga bugawa da matsanancin karfi nan take ta shiga sake sake hade da jerowa kanta tmby "wa yasan shirinta ?wa ya turo 'yansanda ?"yaakayi suka san inda zata aiwatar da shirinta akan maryam ?ita dai tasan daga Allah sai bala da zasu yi aikin tare suka san komai dan hatta babanta bata bari ya sani ba ." shiru tayi kawai har zuwa lokacin da yansanda suka qaraso zuwa inda take tsaye suka tsaya a gabanta a wulakace ta d'aga kanta tana kallonsu d'aya bayan d'aya tare da bude bakinta zata soma zazzaga masu ruwan bala'in 'bata mata shirinta da sukayi amman sai taga daya daga cikin police din dake tsaye a gabanta ya ciro I'd card daga gaban aljihunsa yana nuna mata kasancewar babu uniform ajikinsu da alamun cid ne ." wani dogon tsaki taja tana cewa "ai ni ba makauniya bace, ko baka fito da I'd card dinka ba nasan ku din yansanda ne "? dan sanda ya gyada mata kai kawai yana kallonta a tsanake kafin daga baya ya soma magana "da fari ki miko mana key motar hannnunki a fito da wacce kikayi yunkurin kashewa " furzar da iska mai zafi tayi daga bakinta kafin daga baya cike da maseefa tace "bazan bayar ba ,dan tunda nayi niyyar kawar da maryam daga duniya a yau din nan sai nayi babu fashi idan yaso nima daga baya akasheni tana qarasa maganar tabi gefensa zata wuce har tayi taku biyu taga wata gajeruwar macen yansanda ta harde mata kafafu sai gata dim a kasa ta zube bisa gwiwowinta inda key'n hannunta ya fadi kasa ." Macen yansanda ta qaraso inda hindu take wargaje a kasa cikin azaba ,kallo daya zaka ma macen yansanda kasan babu rahma a fuskarta ta d'auki keyn daya fadi ta mikawa d'ansandar dake tsaye a kusa daita"ungo naziru maza ka fito da yarinyar" ya karba keyn daga hannunta da sauri ya nufi inda motar take ." Macen yansanda ta fito da ankwa daga cikin aljihunta tana duban hindu a tsanake kafin daga bisani ta soma qoqarin kamo hannunta domin da'ba mata ankwa amman hindu ta fixge tana zabga mata harara "ki miko hannunki na saka miki ankwa ko kuma na harbe kwakwaluwar kanki yanzu ." wani murmushin bakinciki ya bayyana akan fuskar hindu "bazan so faruwar haka ba ,dan bazan so na bar duniyar nan batare dana kawar da mutun biyu din nan a duniya ba,wannan hatsabibiyar yarinyar da kuma wanda zai aureta, duk da na shiga hannu amman ban yi nadama ba ,dan ni kadai nasa me nake ji a zuciyata yadda zan rasashi dole itama ta rasashi ." Ta sake yin murmushi wanda kana gani na takaici da bakinciki né da rashin cimma buri "duk da na shiga hannun amman nasan zan fito dan mahaifina zai yi iya qoqarinsa sannnan zai kashe ko nawa ne akan yaga na fito tana gama fadar haka ta mika mata hannuwanta duka , sai da suka kalli juna da sauran yansanda nan take suka fahimci yanayin cewar hindu bata cikin hayacinta ,ta daba mata ankwa a hannuwanta tana cewa "duk abida kike taqama dashi wanda yasa muka bibiyi rayuwarki har zuwa yau din nan ya fiki kuma yafi mahaifinki komai ." "idan taqamar mahaifinki nada kudi ya zartashi dan haka kisani matsawar bashi ne ya lamunce ki fito ba ubanki bai isa ba ,kuma bashi da kudin da zai fito dake oya muje ."ta qarasa mgnr alokacin da aka qaraso da maryam wacce ke kuka har lokacin ga wata zufa dake tsatsafo mata a dukkanin ilahirin jikinta kallo daya zaka wa maryam ta baka tausayi ." Wani wulakantaccen kallo hindu tayiwa maryam sannan ta yunkura ta mike tsaye cike da d'agawa da isgilanci ta kalli macen yansanda tace "koma waye shi ina mai tabbatar miki mahaifina yana da karfin ikon da zai sa shi ya lamunce a fito dani ta qarasa maganar tana sake watsawa maryam mugun kallo "Ke kuma ki jira fitowata wallahi karon mu bazai yi kyau ba, bazan ta'ba barin kiji dadin rayuwarki ba, baqar makira wallahi nice ajalinki ki rubuta ki ajiye ." wasu hawaye masu zafi suka gangaro acikin idanun maryam hankalinta ya qara tashi fiyye da lokacin da take cikin mota ,yayinda zufa ke sake karyo mata muryarta a raunane. tace "police kunji abinda take fad'a wai zata kasheni itace ajalina "ki kwantar da hankalinki babu abinda zata iya miki daga hannunmu sai kotu zaa kaita daga kotu kuma sai gidan kurku kinga babu wata hanyar data sauran mata "karya kake munafukin Allah bani ce zani kurku ba uwarka ce zata kurku shegu matsiyata kawai tass tasss!! taji saukar mari har sau biyu ajere akan kuncinta nan da nan ta rikice ta dinga zaginsu tana tsine masu albarka mrym tana kallo aka tasa keyar hindu da bala abayan motar yansanda ita kuma aka sakata cikin wata motar aka d'auki hanyar gida daita ." Acikin mota hindu ta kalli macen yansanda taja wani dogon tsaki ta bude baki zatayi magana kenan taji sauka mari tasss!! ta sauke mata wani lafiyayyun mari "kina sake bude mana wannnan rubabben bakin naki zan qara miki wasu marukan dan haka ki kama kanki ki bari salin alim mu kai ki office idan ba haka ba zan sakar miki harsashi yadda taga matar tana mgn tana zazzaro mata idanuwa tana huci tasan da gaske take zata iya aikata fiyye da haka amman bata jin zatayi shiru ." Ta dinga kallon matar zuciyarta na cigaba da yi mata zafi ranta da zuciyarta na wani irin tafasa ta dinga zagin yarsadar can kuma tayi shiru tana son sani waye yyi mata wannnan shishigi da katsalandar cikin rayuwarta ? cure hannuwanta tayi waje daya tana bugawa da juna batayi tsamanin shirinta zai ruguje haka ba ta dauka zatayi komai ta gama babu wanda yasani taci bulus ,wato mutuwar maryam ya tafi a banza bata kawo abun zai zame mata haka ba ." Suna isa police station ta ciro wayarta daga cikin jaka zata kira number babanta amman taji an bata warning tare da kwace komai dake hannunta aka turata cikin wani qaramin daki wanda aka tanada domin masu laifi irin nata sannan suka maida kofar suka rufe garam ."kukan bakinciki bata cima burinta ba gashi kuma ta shiga hannun hukuma ya kufce mata ,dan haka ta soma maganganu cikin zafin rai tana zage zage tana tsine masu amman babu wanda ya kulata har sai data gaji dan kanta tayi shiru ta fara bin d'akin da take ciki da kallo kusuruwa kusuruwa banda duhu da zarni ba abinda ke tashi ciki ,ga kukan tsoro tun yanzu data kasance ranar allah ce ina ga dare yayi ? tsayuwa tayi taki zama dan bata ga wajen zama ba koina ta kalla kazanta né shiru tayi kawai tana tunanin mafuta ." Cikin wani irin tashin hankali maryam ta shiga part din hajiya zulai tana kuka a parlour'n ta iske nana hauwa'u da mami zaune suna ganinta gabadayansu suka mike cikin tsananin damuwa suka isa inda take mrym ta zube jikin mami tana yi mata bayani abinda ya faru gaban mami yayi wata irin faduwa "yanzu d'an rashin imani hindu tayi qoqarin kasheki ? ta qarasa mgnr tana mai sake kamo maryam din zuwa jikinta ta rungume tana cewa " yanzu ina hindu take ? police sun wuce daita ." Mami ta dafe kanta cikin yanayi na tsarkakkiya da shiga tashin hankali ,cikin tsananin' bacin rai mami ta zaunar da maryam ta soma magana "aikuwa wannna karon bazan yarda ba ,bazan zuba ido su kashe min ke ba ,"wannan ma ai rashin sanin darajan d'an adam ne ,wallahi da nasan police station din aka kaita da sai naje naci ubanta inji cewar nana hauwa'u " zagi kam babu wanda hindu bata sha shi a wajen nana hauwa'u ba, ita kuwa mami har da kwallar takaici ta zubar tana mai jin tausayin maryam wacce har lokacin kuka take ." Suna cikin wannan halin na tashin hankali ATA ya turo kafar parlour'n ya shigo tare da sallama duk da bai bude muryarshi sosai ba fuskarshi kamar koda yaushe, cike da ladabi ya gaishe da mami yana mai zama akan kujera idanunshi a runtse ta amsa tana masa bayanin abinda ya faru "yanzu da wani abu ya faru da maryama shikenan taci bulus " "Ina fa taci bulus ". ya fad'a haka acikin ransa amman a filli yace "ai ni data samu nasarar kasheta ma da ta taimakawa rayuwata "ya fad'a yana ciza gefen lip's dinsa da d'an karfi yanayin yadda yayi maganar ya bala'i daurewa hajiya zulai kai ,tayi matukar mamakin jin abinda ya fad'a, ba ita ba hatta nana hauwa'u tayi mamakinsa kuma taji babu dadi aranta "yanzu abinda zaka fada kenan adamcy ? yayi shiru kawai yana lumshe idanuwanshi "rayuwar mutun kake fadar haka kamar rayuwarta baa bakin komai yake ba "?me zan fada sweetheart da wuce haka nifa kasancewarta a raye babbar matsala ce arayuwata ." "Ka kuwa san abinda kake fada adamcy "? "iyakar gskiyata kenan na fada sweetheart kuma kin san bana fadar abinda bashi né acikin zuciyata ba ,wannan kawai ya isa ki fahimci irin rashin son da bana mata ,wallahi da zata mutu da gaske da zanfi kowa jin dadi " ni kake fadawa haka adamcy ?a gabana kake wulakata min 'ya dan baka da mutunci na rantse da girman allah sai na sa'ba maka akan wannan maganar kuma matsawar baka d'auki mataki akan abinda akayiwa maryama ba sai ka had'u da fushina da baka gani ba ." maryam ta sunkuyar da kanta kasa tana sheshekar kuka zuciyarta na wani irin bugawa da karfin gaske wani irin tsoro ne ke ziyartar zuciyarta bata ta'ba sanin qiyayyar da yake mata ta kai haka ba sai yau din nan cike da fushi mami ta cigaba da magana "idan banda rashin mutunci irin naka agabana adamcy ,nice fa da kaina na zaba maka maryam yau ko aljanna ce maryam nace ka aura ai baka mata fatan mutuwa ba bare diyar mutun diyar ma tawa ko ka manta matsayin maryam ne a wajena "? Yana jin mami yayyi shiru dan duk abinda ta fad'a din ya sani "wallahi ban ta'ba sanin rashin mutuncinka ya kai haka ba sai yau ,mutun sukuntu guda kuma jininka da ubanta da ni uwarmu d'aya ubanmu d'aya fa, amman dan rashin mutunci kayi mata wannan fatar ,wallahi yadda zakayi farinciki da mutuwar maryama nima nasan zakayi farinciki idan na fadi na mutu "ya bude baki zai yi magana tayi saurin katseshi ta hanyar cewa "wallahi idan ka sake min wata maganar banza a nan zan iya kafa maka hakora "bai ce uffan ba ya mike tsam ya haye samansa, jiki a matukar sanyaye mami ta mike tana goge kwallar idanunta ta nufi hanyar d'akinta." tashin mami ya bawa maryam damar rushewa da wani kuka "banason na kawo damuwa acikin familes ,sister ya zaa yi a fasa auren nan kowa ya huta ? nana hauwa'u ta rungumeta tsam ajikinta tana rarrashinta"sister ki duba yadda yake nuna tsanata qarara wannan wani irin kiyayya ne haka me na kashe masa ?"."yasan adadin mutane dake bukatar aurena aka daukeni aka bashi ba dan ya cancata ba ?" wallahi gara na mutu tun kafin zuwan auren nan dan nima zanfi bukatar mutuwa ina jin kamar na kashe kaina da kaina kowa ya huta har ma dashi mai tsanartawa dasu masu bukatar ganin rayuwata ta tagayyara dan nasan aurena da yaya Adam babu abinda zan tsinta acikinsa sai bakinciki ?ta qarasa mgnr tana sheshekar kuka ." "maryam ! nana hauwa'u ta kira sunanta "me yasa kike fadar haka ai bashi zaki duba ba "sister wa zan duba ?zan rayu tare dashi ?karki manta tare zamuyi rayuwa dashi kuma acikin gida daya idan ma ta kama a daki d'aya idan damuwa yake kunsa min ni kadai zan shanye ,haka zalika idan farinciki ne ni kadai zan ji duk wani abu da zan tsinta acikin gidansa akaina zai qare kina tunanin zanyi farinciki a gidan mutumin da baya sona ?"bana jin akwai halittar da yaya adam ya tsana kamar ni, a wasu lokutan na Kan zauna nayi tunanin me yasa yake tsanata haka ?ta sauke numfashi mai hade da sheshekan kuka ya Adam yayi mugu mugun tsanata sister ." "Na fada yanzu ma zan sake fad'a aurena dashi babu abinda zai haifar sai damuwa domin kuwa bazai yi yadda kowani magidanci yake a gidansa ba ,bazai dauki duk wani responsibility dina ba,zai watsawa mami qasa a idanunta domin zuciyarsa bata tattare da tsoron kowa ko shakkun kowa na sha jin yadda yake fadawa ya hisham da yaya bello cewar baya sona ,nima idan banki auren ba sister me kike son nayi ?ni da akwai yadda zanyi na tsaida maganar auren nan wallahi da nayi domin nafi bukata hakan ko kuma mutuwata dan wallahi zan so faruwar haka da dai na kasance a gidansa abar wulaqantawa ." nana hauwa'u ta riko hannuwanta duka cikin tsananin damuwa tana cewa "tabbas akwai ciwo sister ciwo kuma mai zafi acikin zuciyarki nasan yaya Adam bai sonki sister amman bazan daina baki shawara akansa ba domin ina ji ajikina zai canza zaki canzasa sister ."maryam ta girgiza mata kanta alamun "a'a ! bazan iya ba sister bazan iya canzasa ba ,yaya adam yafi karfina yafi karfin hada rayuwa dani babu wanda yasan abinda Ke ransa gabadaya acikin halayensa bai gama fitowa dashi fili ba saboda babu wanda Ke rayuwar akarkashinsa ,sister zuciyata zata buga matsawar aurena ya tabbata dashi nasan nan gaba kadan zan mutu dan bazan cigaba da rayuwa mai dadi ba ". "kiyi addua sister dayawa anyi irin aurenku karshe kuma yayi kyau kuma anyi farinciki ki hasasowa kanki haka ki daina tunanin bad things a tsakaninku ."at every step sister ta ina kike hango min jin dadi ki duba irin abubuwan da yake ta yaya kike son nayi scricfied din rayuwata akanshi ?"nasani sister amman ki bari ayi ki gani daga ranar ki fara Kirgawa day by day wata rana soyayya zata kasance a tsakaninku wallahi inada wannan tabbacin kirki zubawa mami kasa acikin idanunta domin kuwa ta yarda dake ta fad'a ta sake jadaddawa cewar zaki mata biyayya bazaki zuba mata kasa a ido ba dan allah karki karyar da yardar data tayi miki ." "mami tayi alkwarin muddin tana raye sai anyi auren nan kuma sai kin samu farinciki a gidan yaya kuma ma shi ya Adam ya amince zai aureki har yau din nan bai ce ya fasa aurenki ba "bisa umarnin mami ba ?cewar maryam tana duban nana hauwa'u hawaye na turereniyar zubowa bisa kuncinta "ina ..!ina jin bazan .."sai kuma tayi shiru ta kasa cigaba da maganar gabanta na wani irin faduwa da karfin gaske." dan allah ki bar maganar nan haka sannan ki bar kuka nan tashi muje d'aki ki kwanta ki huta jiki a matukar sanyaye da taimakon nana hauwa'u ta mike tsaye tana jin wani irin sanyin a gabobinta tana jin kafafuwanta sun gaza daukarta nana hauwa'u ta rikota sosai ta makaleta a gefen jikinta suka nufi daki ." ATA ya sauko tsaf cikin wata dakakkiyar gezner tamkar ranar zaa daura masa aure dinki ya balain yi masa kyau takalmin kafafunsa cover shoes ne yayi matukar dacewa da shigarsa kanshi babu hula sai agogon fata dake daure da tsintsiyar hannunsa ahankali yake taka step yana saukowa yana duba agogon hannunsa har zai fita sai kuma ya dawo baya ya dauki hanyar dakin mami, ya tura kofar dakin a natse ya shiga ya isketa zaune hannunta rike da waya wanda ya nuna masa alamun waya ta gama tana ganinsa ta sake hade fuska tamkar bata ta'ba dariya ba dan kalamansa sun ta'bata sannan sunyi mata ciwo matuka a tunaninta ko mai aikinta bata cancanci adam yyiwa mummunar fata haka ba bare diyar danuwanta wanda su kadai iyayensu suka haifa suka bari a duniya." cikin kankanin alokacin yaga sweetheart dinsa ta canza ganin irin kallon da yake mata yasa ta kawar da fuskarta aranshi yace "har abun ya kai haka ?."shiru yayi kawai yana dubanta a tsanake shi a ganinsa babu wani laifi acikin maganarsa dan so ba karya bane haka zalika rashin so ba karya bane , hakuri yake son ya bata amman daya tuna akan maryam ne sai yaji ya fasa ,yayinda ita mami hakurin tayi tsammanin ya shigo ya bata dan shi take bukata daga garesa amman sai taji sautin muryarsa can kasan makoshi kamar koda yaushe yana cewa "sweetheart ni zan fita amman bazan wani jima ba" bata juyo ta kallesa ba bare tace masa wani abu jiki a sanyaye ya fice daga gidan gbdy can qasan zuciyarsa cike da bakinciki da fargaban shirun sweetheart dinsa dan a duk sanda tayi shiru haka matsaloli ne zasu biyo baya ." Daga shi sai direbansa acikin mota kira ne ya shigo wayarsa yana duba screen din wayar sunan aunty shahida ya gani bai dauka ba dan yasan kararsa mami ta kai wajenta yana kallo har kiran ya katse wani kiran ya sake shigowa sai datayi masa kira biyar bai dauka ba haka aunty khadija kiranta biyar har suka isa station kiransa suke yi amman yaki dauka ya fito daga cikin mota kai tsaye office din dpo ya nufa ya tareshi cikin farinciki ya mika masa hannu suka gaisa yana nuna masa wajen zama da hannunsa a hankali suka fara tautaunawa akan hindu." "ranka shi dade yarinyar nan bata da mutunci ga rashin kunya ga bakinta baya mutuwa an kawo mata abinci ma ta kwafar tana zagin wanda ya kawo mata tun daaka kawota bakinta bai yi shiru ba sai tsinewa mutane take "dubansa ATA yayi yana cewa "baku ladabtar daita bane shiyasa "ai yalla'bai na dauka kamar wancar yarinyar ce da kace kar ataba lafiyar jikinta shiyasa nayi masu gargadi amman dai tasha mari a wajen inspector romoke numfashi ya sauke "abinda ya kawoni yanzu ina son a tsanata bincike akanta fiyye da wanda akayi akan nuzla idan ta kama da duka duk ayi mata domin ta amsa laifinta ." "bare ma wannnan yarinyar cikin sauki zata amsa laifinta dan ta tabbatarwa da jami'an da suka kamota muddin ta fito sai tayi ajalin yarinyar dakasa a bibiyeta ga dukkanin alamun itace mashekiyar da muka dade muna nema ATA ya gyada kai kawai yana saurarensa."dpo ya cigaba da magana "ko akawo maka ita ne ?ya fadi haka ne ko zai bukaci ganinta kamar yadda ya bukaci ganin nuzla." ya girgiza masa kai kawai alamun baya bukata "abinda nake so bana son maganr kamata ta fita zuwa koina har ku gama bincikenku akanta sannnan bana son kowa yasan inda take har sai ta fad'a maku itace ta kashe mubina cikin girmamawa ya amsa masa da to "matsawar ta amsa itace ta kashe mubina ina son tasan girman laifin data aikata ku kaita kotu batare da sanin kowa ba alqali ya yanke mata hukunci daidai da laifinta a turata kurku wannan shine kawai abinda nake bukata "in sha allahu yalla'bai zaayi duk yadda kake so "tare da dpo suka fito yana sake jadaddawa dpo baya son tana tsare ya fito da kudi masu yawa kamar wancan ranar ya damkawa dpo sannan ya wuce ya tafi ." Ahankali yake takawa har ya isa cikin dakin mami ya sameta zaune a saman abun sallah tana jan carbi kana kallon idanunta kasan kuka tayi kuma ba kadan ba ya qarasa ya zauna a gabanta ya riko hannunta daya cikin nashi yana kiran sunanta "sweetheart!"da kyar ta dago kunburarrun idanunta ta tsura masa sannan ta zare hannunta cikin nashi tana cigaba da jan casbaha jikinsa ya sake yin sanyi bai ta'ba ganin wannnan yanayin atattare daita ba sai yau duk abinda zai mata bata taba daukar zafi dashi irin haka hasalima a inda abun ya faru anan take barinsa ." Ahankali ta mike tsaye ta koma bakin gado ta zauna shiru yayi kawai yana kallon yatsun kafafunta kafin daga bisani ya yunkura ya mike tsaye ya isa inda remut din ac yake ya dauka ya kunna saboda zafin da yake ji ya zauna kusa daita ta sake mikewa ta fito daga dakin ta barshi zaune yabi bayanta da kallo sannan ya biyo bayanta ,koda ya fito parlour'n bai ganta ba sai sautin muryarta yajiyo sama sama daga dakinsu nana hauwa'u dan haka ya haye samansa." Tun bayan  fitar hindu hajiya aljannatu Ke kwance tana bacci ,acikin baccinta ne tayi mafarkin wai ga wasu mutane sun zagaye hindu wanda batasan ko su waye ba ,macen dake cikinsu taje ta samu tana tambayarta lafiya suka zagaye ta amman tayi mata shiru tana kallonsu zasu wuce daita tace  "ina zaku wuce min da yarinya ?da wannan kalmar ta farka daga mafarkinta tare da kallon sugura dake zaune akan dadduma da alamun ta idar da sallah né tace "sugura ina hindatu ?"ai tunda ta fita bata dawo gidan nan ba "ta fad'a mata haka sannan ta cigaba da laziminta bandaki umma ta shiga tayi alwala ta fito tayi sallah tana idarwa tace "wallahi duk jikina ciwo yake "sannu Atu " dake haka suke kirata ." "yauwa sugura dauko min wayata na kira naji inda take "sugura ta mike ta dauko mata wayar ta mika mata ta fita atu ta soma neman  layin hindu sai dai abu daya aka fad'a mata a karon farko "switch off ta sake maimaita kiran the same thing tayi shiru rike da wayar tana jin wani iri ajikinta da tunanin inda taje  dan  ita ba mai yawon leke leke bace acikin estate din bare tace a dubota koda yaushe tana gida idan kaga ta fita zata siyan abu ne ko kuma da shiga gidan hjy zulaihat ."wasa wasa har dare babu hindu ba alamunta nan fa hankalin mahaifiyarta dana yayyunta ya tashi nan da nan baba qarami ya fita nemanta tare da sauran yan'uwanta amman duk inda suka je basu ganta ba ,dan haka suka qarasa police station mafi  kusa dasu sukayi report sannan suka dawo gida cikin matsanancin tashin hankali." Har washgari baa ga hindu ba  koda hjy zulai ta samu labarin abinda ya faru batayi sanya a gwiwa ba ta d'auki kafafunta taje gidan baba babba  tayi masa  bayani  komai ,shine ya kira baba qaramin  koda ya  shigo ko kallon inda mami take bai yi ba sai bayan da baba babba ya   sheida masa  aiko cikin tashin hankali da  zafin rai yake tmbyrta police station din daaka wuce daita "ina zan sani tunda daga sama allah ya kawowa maryam dauki "bangane hausar baki sani ba "iyakar abinda nasani kenan na fada sai ka bazama zuwa duk wani  police station dake kusa da nesa domin nemanta idan kuma angata lokacin ni kuma zan shigar da qarar abinda ta aikata ." wani mugun kallo ya watsa mata yana cewa "ki kalleni da kyau  zulai kinga nayi miki kama da irin wadan nan mutane ?kisani ni ba wannan shashan bane da danki ya garkame masa 'ya kwana da kwanaki bai dauki mataki akai ba dan haka wulakancinki da isarki  ta tsaya akansa ke kuma ki tsaya a iyakarki.." idan ba haka ba me zai kayi ?bai yi magana ba illa nunata da babban dan yatsansa da yayi alamun gargadi sannan ya juya kamar zai tashi sama naunayen ajiyar zuciya baba babba ya sauke yana cewa  "kiyi hakuri  kin rigada kinsan halinsa "nasani amman a haka yake son na bawa d'ana umarnin ya auri hindu ?ai wallahi dana bari adamcy Ya auri hindatu gara nuzla bancin hisham dake tsakani nan suka cigaba da tautaunawa akan matsalar ." ATA ya sauko a natse cikin shigar suit a hankali yake takowa yana kallo koina a parlour'n har ya qarasa saukowa , babu kowa parlour'n har sweetheart dinsa bata nan ,wanda adaidai lokacin daya sauko daita yake fara cin karo agabanta zai ci abinci har sai ya bar gidan take tashi ta shiga ciki wani lokacin kuma ta cigaba da zama amman yau babu ita babu alamunta ." kallon dining yayi da alamun an gama shirya masa breakfast numfashi ya sauke ya nufi hanyar dakinta ya shiga bai ganta ad'akin ba ,dan haka ya samu waje ya zauan a bakin gado yana jijiga kafarsa a tunaninsa ko tana ciki bayi kusan minti goma yana zaune amman shiru ,ya mike tsaye ya fito yana neman layinta kiran na shiga amman bata dauka ba, layin nana hauwa'u ya kira tana dauka yace "ina sweetheart ? okay ya fad'a takaice yasa kai ya wuce zuwa office bai tsaya bin takan abinci ba ." Bangaren baba qarami da yayansa duk wani office din police na kusa dasu sunje amman babu labarin hindu duk inda suka je sai ace ba nan aka kawota ba dan haka suka bazama zuwa headquarters sukai report ,da yamma koda ATA ya dawo bai iske mami ba sai dai tasa an a shirya masa dining amman bata tsaya ba tunin ya gano manufar mami akanshi tashin hankali kenan wanda baa saka masa rana idan kowa zai iya barin rayuwarsa ya hakura amman banda sweetheart dinsa bazai iya ba zai iya komai akanta zai iya sadaukar da farincikinsa gareta ." wanka ya shiga byn ya fito ya sauya kaya zuwa na shan iska ya sauko ya shiga dakin mami tana zaune tare da maryam tana shirya mata kaya a kwaba tana ganinsa ta dauke idanunta zuwa kan maryam "Yauwa maryam kwashe wannan kayan ki maida su sama, jiki a sanyaye ta dauki kayan ta ajiye kamar yadda mami ta buqata sannan ta maida murfin kwaban ta rufe ta raba ta gefensa ta fice daga dakin ." Ya sauke numfashi "ammm sweetheart "kada kace min komai please dan banason jin komai daga bakinka yadda na zuba maka ido kaima ka zuba min ido kowa yayi tsabgar gabansa kayi abinda kaga ya fiyye maka arayuwarka mami ta fad'a tana nuna masa kofa .."sweetheart "dan allah adamcy ka bar min daki tunda ba kai ka gina min shi ba fita kafin nayi maka abinda bazai mana kyau ba "sweetheart ." ya fad'a a karo na biyu zuciyarsa cike da matsanan cin tashin hankali "ka fita adamcy ka fita bana son ganinka fita ta fad'a tana kawar da fuskarta ." "Da gaske dai sweetheart dinsa bata son ganinsa me yayi da zafi haka ?a ganinsa shi bai yi laifin komai ba juyawa yayi ya fita yana waiwayenta yana jin kuna acikin rashi tun daga lokacin mami ta fita harkarsa shi kuwa abun ya damesa idan ya sauko yaga bata nan baya tsayawa karya wa zai wuce office washegari ya kasance weekend yana saukowa kai tsaye dakin mami ya shiga ya sameta zaune ya gaisheta cike da ladabi ta amsa tana qoqarin mikewa saboda har lokacin tana jin zafi da radadin abinda yayi mata har tayi taku biyu taji ya riko hannunta "dan girman allah sweetheart kiyi hakuri da abinda nayi ya fad'a cikin rawar murya." wani sanyi dadi taji ya lullubeta daman abinda take bukata kenan daga garesa sai dai taki kallonsa ahankali ya dawo gabanta ya tsugunna bisa gwiwowinsa "ina mai neman afuwarki sweetheart ki yafe min nima ba yin kaina bane ki fahimceni wallahi bana jin son yarinyar nan araina ." "amman sai kayi mata mummunar fata ?ta fad'a abun na ta'ba ranta ayi ganganci da rayuwar yarinya tankar mai fa adamcy wallahi a tunanina ko dabba na ajiye a gidan nan akayi mata haka bazaka fad'a haka ba bare mutun wacce kasan tana da mahimanci arayuwata" ta qarasa maganar adaidai lokacin da aunty shahida da aunty khadija suka turo kofar dakin suka shigo shiru kawai tayi tana dubansu ." A natse suka qarasa shigowa cikin dakin sosai suka samu waje suka zauna mami ma ta zauna tana dubansu daya bayan daya "mami kin tashi Lfy?lafiya lau ya kwanan yaran ?"duk suna lafiya suka amsa mami ta dubi babbar diyarta tana cewa "a yau nake sa ran jama'a zasu fara sauka domin zuwa bikin adamcy da maryam amman sakamakon abinda yayi na janye maganar aurensa da maryam ya d'ago kanshi da sauri ya zuba ma mami idanunshi ." "Ku sheida na yafe masa duniya da lahira yaje ya kawo min wacce yake son ya aura ita kuma mrym in sha allahu zan samo mata wanda zai min biyayya ya aureta" wani sanyi dadi ya lullubesa na farinciki jin maganarta ta farko amman kuma a karshe yaji wani irin tarin damuwa na shiga zuciyarsa matsowa yayi daf daita yana cewa "sweetheart ai na baki hakuri dan allah kiyi hakuri "na hakura adamcy amman da wani abu yaje ya sameta a sanadiyyarka kazo kana murna da jin dadi gara a fasa ." Shiru yayi ya kasa cigaba da magana "mami dan darajan allah kiyi hakuri tunda yayi nadama har ya baki hakuri sannan babu abinda zai samu maryam zata cigaba da rayuwa kamar kowacce yar adam Kiyi hakuri ki yafe masa kin rigada Kinsan halin adam bai iya magana ba duk maganar data fito bakinsa haka yake cabawa inji cewar aunty khadija wani mugun kallo ya wurga ma mai hade da harara ." "Me yasa bazai zama mutun na farko da zai ji ciwon abinda akayi mata ba? maryam fa matar da zai aura ce, matar da zai raba duk wani farinciki da akasin haka ce daita ,kuma yaruwa mafi kusanci da rayuwarsa amman ya dinga nunawa duniya baya sonta , wallahi ina matukar qaunar zamansu tare amamn tunda abun ya kai ga haka nima na hakura sannan bana fushi dashi na yafe masa duniya da lahira ya kawo wacce yake so ta qarasa mgnr kuka na kwance mata .."cikin muryar kuka aunty shahida da khadija suka durkushe agaban mami suna kuka suna bata hakuri "dan allah mami Kiyi hakuri karki bari a fasa auren nan bayn an gama komai ." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗      MAR'ADAMS      💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.              Page 27   Cikin muryar kuka mami tace  "har yau na kasa fahimtar me yasa adamcy baya son maryam ?me maryam ta rasa ? me yasa yake jin idan ta mutu zai ji dadi zai  huta?" ta qarasa mgnr tana goge hawayenta "Kiyi hakuri mami  zai sota in sha allahu nan suka dinga  rarrashin mami shi kuwa ATA ya qasa cewa komai sai ma ya mike   cikin yanayi na tashin hankalin ganin mahaifiyarsa na zubar da hawaye akanshi  ya bar  d'akin  zuwa nashi yana furzar da  numfashi  mai zafi ." ko bayan fitarsa hakuri sosai  aunty shahida da aunty khadija sukai  ta bawa mami da kyar suka samu ta sauko ta hakura "kiyi hakuri mami ki yafe masa sannan ki kwantar da hankalinki muddin muna raye adam bashi da wata mata sai maryam kuma bazamu ta'ba barin tasha wahala a gidansa ba sai inda karfinmu ya qare ."sanyayyen numfashi mami ta sauke tana mai sake gyara zamanta  tare da riko hannuwansu cikin nata "na yafe masa dan ko baku nemar masa  yafiya  ba  zan yafe masa domin iyaye ne kadai suke iya yafewa ya'yansu batare da ya'yan  sun nemi yafiya daga garesu ba  ,gaba dayanku allah yayi maku albarka allah kuma ya albarkaci rayuwar ya'yanku kuje ku cigaba da shirye shiryen  biki ina alfahari daku ta qarasa  mgnr tana murmushi ". wani farinciki ne ya mamaye zukansu suka mike  suka  fito daga dakin mami  zuwa  d'akin ATA alokacin yana kwance flat akan  kujera  yana fidda numfashi sama sama ."Jin motsin shigowarsu ya sashi bude idanunshi da kyar sai dai  bai mike  ba har sanda suka samu waje suka zauna  suka tsura masa idanuwansu suna kallonsa, kusan mintuna goma suka d'auka suna kallonsa da nazarinsa sannan   aunty shahida ta kira sunansa "adam !" yana jinta amman yaki  amsawa  sai ma sauke ajiyar zuciya yayi tare da furzar da zazzafar iska daga bakinsa " "kana jina fa  adam ?"eh ina jinki ki fad'a abinda zaki fad'a  ya fad'a a takaice tare da mikewa ya zauna  yana kallon wani bangaren dabam  yana ciza gefen lip's dinsa  yayinda idanuwanshi suka canza kala dan bai ta'ba shiga tashin hankali  irin na yau ba ganin mahaifiyarsa na zubar da hawaye ,"shi kuwa me zaiyi da maryam arayuwarsa ?ai har abada bazai ta'ba sota ba zai dai yi biyayya wa mahaifiyarsa  ." Aunty shahida ta danne abinda taji na haushin abinda yayi mata yanzu ta  soma magana cikin fushi "wallahi adam kabi duniya ahankali da girmanka da komai amamn ka dinga  sa mahaifiyarka kuka a zatonka yadda kake yiwa mami zaka ci bulus ne ?cikin yanayi na tashin hankali ya waigo ya tsura mata tsumammun idanunshi dake cike da matsanamcin tashin hankali duk da magana yake son yi amman ya kasa bude bakinsa dan haka ya runtse idanuwanshi kawai  yana janyo wani irin numfashi mai zafi yana fesarwa ya maida kanshi jikin kujera ya kwantar ." "tsawon shekaru fa take binka akan aure ,ka mance kaine kaki fito da mata har yasa ta yanke wannan hukuncin akanta  ?"iyaye ne kadai suke son  ganin cigaban ya'yansu mami na son ganin gobenka tayi kyau ne yasa  ta hadaka da mrym sannan  karka manta kai ma aure zakayi  yanzu kuma zaka haihu yaya zakaji duk ranar da kacewa d'anka  ko 'yarka ga abinda kake so suka  ce aa ba zasu maka  biyayya ba abinda suke  só shi zasuyi   ? "to ni yanzu me nayi kuma ?ya fad'a a matukar hassale tare da gyara zamansa ya  bude idanuwanshi a hankali ya zuba masu ya cigaba da motsa labbansa "yarinyar nan ce  bana só kuma bana jin zan sota ,sai kuma na kasa fad'ar albarkacin bakina ko ana so dole ne  ? yayi  tambayar  a dan fusace yana kallonsu ,ku tsaya na tmbyeku daga Ke har khadija auren dole mahaifinmu yayi maku ?"sukayi shiru suna kallonsa dan basu da amsar da zasu bashi "gbdynku kuna son mazajenku kuka  auresu  to me yasa sai ni dana kasance nmj  zaa wa auren dole kuma a hanani mgn ?". "amman ai ba dole sai ka fad'a a gaban mami ba ,wannan kalmar da kake fad'a ita Ke sa mami jin wani abu aranta , dannewa ya kamata kayi ka rungume maryam ."har yanzu baku bani amsar tmbyta ba tukun kafin ku shigo da wata ,auren dole akayi maku ?"zuba masa idanu sukayi kowannensu da abinda yake sakawa aransa ,ahankali ya lumshe tsumammun  idanunshi tare da sanya hannunsa daya a saitin qirjinsa yana murza daidai inda zuciyarsa take beating very fast "gbdynku bazaku iya fahimtar quna da radadin da nake ji acikin zuciyata ba  ,so ne dai na fad'a bana sonta kuma wallahi ko yanzu aka fasa auren nan murna zanyi  mutun daya ce kawai ta samu kyakkyawan mazauni anan  itace mafarkina ,me zaayi da wannan guntuwar yarinya yarinyar Kmr agwagwa  kawai fari ne ya taimaketa ya qarasa mgnr yana cigaba da shafa zuciyarsa yana lumshe ido ." "Wani haushinsa ya kama aunty khadija  ranta a matukar bace tace "Idan zaka  manta mafarkinka ka manta ka sanya mrym  a zuciyarka dan wannan auren mutuwa ce kawai zata ra.."Kafin ta qarashe  maganar ya jefa mata wani mugun kallo wanda yasa tayi gaugauwar yanke maganarta babu shiri ,dan girman allah adam kayi qoqari kasanya maryam ko kad'an a zuciyarka "bazan iya ba"ya fad'a atakaice "zaka iya adam kayi qoqarin kwatantawa please."   "bama da ikon waye zamu so waye zamu fad'a soyayya dashi   bazan iya yi maku karya cewar zan sanyata a zuciyata ba   daga baya kuga akasin haka dan bazan iya karya maku zuciya daga baya kuji haushina ba ,kuyi hakuri  kawai  bazan iya ba ,sannan kusan wani abu  a kullum ina fad'a  maku amman kun kasa fahimtata kuskure zaayi a auren  nan yakamata abar maganar auren nan haka mu cigaba da rayuwarmu daita  irin ta yan'uwantaka." "zamuyi rayuwa daita ta har abada shine maanar aure,  akwai abubuwa acikin rayuwar aure,aure   ba abu bane na takaitaccen lokaci idan anyisa anyisa kenan sai fatan mutuwa ce zata raba zata bukaci farinciki ni  km bazan ta'ba bata farinciki ba saboda ni kaina zuciyata bata tare da farinciki komai zuciyata a rufe take da soyayyar wata wato mafarkina kenan ,itama ina neman adduarku allah ya yaye min tunaninta na huta yayi maganr Kmr zai zubda hawaye . yayi shiru tare da rungume hannuwansa duka a qirjinsa yana jin wani irin tuttukin bakinciki." "to Allah  yaye maka tunaninta kai bama tunaninta ba ni zanyi addua allah ya mantar da kai ita gbdy  kaji ka tsaneta  fiyye da komai a duniya inji cewar aunty khadija ,numfashi kawai ya sauke yana kallonta a dage batare da yace komai ba dan shi yasan ba abune mai sauki ba ya mantata.yanzu ga shirye shiryen biki  zaa shiga daga jibi ya kenan ?" "babu ruwana da duk wani abinda zaayi na shirin biki ,ni dai abinda nasani aure ne na amince zan aureta amman batun wani shirye shirye babu ruwana" har maganar rabon iv ?"ya ina fad'a maku bani da wata damuwa da komai  da zaa gudanar kuna qara shigo min  da wani maganar rabon Iv ."yayi mgnr da fushin zuciya . "rabu dashi aunty  shahida duk abinda ya dace salim da hisham  sunyi  ,kai kuma kaje can  ka karata da mugun halinka allah ya ganar da kai mu zamuyi komai kuma aure babu fashi sai an cikawa mami burinta  sai dai idan mutuwa zakayi ka mutu nonsense kawai  "bai sake cewa komai ba har suka mike suka bar d'akin ya koma ya kwanta lamo yana kallon saman d'akin ,ranar yini yayi kwance a d'aki cikin tsananin damuwa ." da misalin karfe takwas na dare ya sauko kamr yadda aka saba an shirya masa dining da kalolin abinci dabam dabam ya zauan akan kujera shiru babu mami haka nan ya kasa ci ya kai hannu ya shafa kanshi zuwa fuskarsa duk tsananin yunwar da yake ji ya kasa sakawa cikinsa komai ya cigaba da zama shiru sai kusan karfe tara mami ta fito daga dakinta sanye ciki riga da zani na atamfa super tana kwallawa auta da maryam kira atare suka fito daga dakinsu suna amsawa mami ta dan yi taku zuwa dining area taja kujera ta  zauna tana cewa "maryam zuba mana abinci jikinta a sanyaye ta bude kular farko tana tmbayarta "mami me zan zuba miki  ?" " bani rice  ma ya isa amman kadan zaki zuba min ta zuba mata ta ajiye agabanta sannna ta zuba abinda tasan ATA yake so rice and stew da miyar kayan ciki da cowslow ,ta zuba shinkafar a plet dabam haka ma miyar daban tayi  masa  ta ajiye a gabansa sannan ta zuba nasu ita da nana hauwa'u ta dauka ta wuce." Ahankali mami take cin abinci amman ATA ko kallon abincin gabansa bai yi ba saboda haushin mami  taki kallonsa ballatana yaga faraarta taki furta komai garesa idan zasu hada ido sai ta dauke kanta sosai ya shiga damuwa hankalinsa ya tashi "to me yayi mata da zafi haka ?shi kam bazai ta'ba boye felling dinsa akan maryam ba yadda zuciyarsa bata sonta haka bakinsa bazai qasa furtawa ba sai dai tayi hakuri dashi ." Ganin yaki ci yasa mami taji babu dadi aranta ta dauki spoon ta sanya cikin abincinsa ta sake tura masa tana tsaresa da idanunta jiki a sanyaye ya sauke numfashi zuciyrasa na sake  karyewa allah sarki sweetheart yasan bazata iya dogon fushi dashi ba ,haka ya dinga cusawa cikinsa abinci tana tsiyaya masa ruwan lemu sai data ga ya koshi sannnan ta mike ta soma tafiya ya dago kanshi yana kallon bayanta zuciyarsa cike da tausayinta ya sani  cewar tana matukar son maryama ,da wani ne yayi abinda yayi mata koda kuwa acikin ya'yanta ne sai ya hadu da fushinta fiyye da yadda ta dauka dashi amman shi allah ya saka mata hakuri dashi komai zai mata tana shanyewa har ma ta kasa daukar dogon fushi dashi." tashi yayi ya haye saman d'akinsa babu laifi   zuciyarsa ta d'an samu  natsuwa." Da misalin karfe hudu na ranar baki  suka fara sauka a gidan mami murna a wajen mami ba'a  magana  ranar a kasalance maryam  tayi komai daga karshe ta shige daki ta kwanta ta huta dan ta samu zuciyarta da gangar jikinta su samu natsuwa da suka rasa tun da taga jama'ar sun fara sauka hankalinta ya tashi jikinta yayi sanyi ."washegari aka fara shirye shirye biki , zaune suke  a falon aunty shahida masu gyara  jiki nata faman shafa masu dilka ajiki  yayinda yanuwa suka zagayesu ana hira daga maryam har nuzla kana kallonsu zaka fahimci suna cikin damuwa da rashin son auren dan fuskarsu kamar zasuyi kuka gidan mami ya sake cika da yan'uwanta  har yau friday da zaayi kamu mutane suna cikin zuwa ." a wani hadadden hall akayi  kamu amare sunyi kyau sosai sai dai ango ATA  bai je koina ba yana kwance a gida ,bangaren maryam ita kadai ce zaune akan kujerar daaka tanada dominsu dan juyin duniya  aunty khadija tayi dashi  amman yaki zuwa aranshi yace "ko bikin da yake so ne zaayi bazai je wani kamu ba bare wanda zaa masa na dole ."mrym kuwa juya  kai kawai take   zuciyarta a jagule bare idan ta kalli hisham da nuzla yadda hisham Ke jefa mata kallon soyayya  da kaffa kaffa daita sai taji kamar ta daura hannuwanta duka  aka ta saka ihu  ko taji saukin zafin da zuciyarta take mata ta sake kallon  hisham taga ya  makale  nuzla sai d'aukarsu hoto ake amman ita nata ango ya wulakantata." aunty shahida tayi  mata duban tsanake nan da nan ta fahimci halin da take ciki ta qaraso inda take zaune tana cewa   "Ki kwantar da hankalinki mrym da rashin zuwan adam kema Kinsan halinsa gara rashin zuwansa daya zo ya kunyata mu ta hanyar wulakanta mu amman muddin muna raye bazakiyi bakinciki a gidansa ba."maryam  tayi narai narai da idanu zatai kuka "qul karki  daga hankalinki bare Kiyi asarar hawayenki da zarar an daura shikenna ya zama naki na har abada  a hankali ta dinga rarrashinta har ta dan samu natsuwar zuciya sai dai taji haushi da bakinciki rashin zuwansa domin  dai so yake lallai sai duniya tasan irin auren da zasuyi ." bayan an gama kamu amarya maryam ita kadai a bayan mota direba yajata suka dauki hanyar zuwa gida  yayinda hisham da nuzla suke zaune abayan tasu motar direbansu na qoqarin kunna mota hisham ya kafeta da ido sosai Kmr zai cinyeta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kamo hannunta  cikin nashi yana  kallo yace "Woow my nuzla gsky lallen yayi kyau my wife waya miki shi ? hade rai tayi sosai  tamkar bata ta'ba yin dariya ba a tsawon rayuwarta tana zame hannunta cikin nashi tace "ka tsaya iya matsayinka karka sake ta'ba min jiki dan wannan jikin ba naka bane "na waye "? ya tambayeta yana matsota sosai Kmr zai shige jikinta "tambayarki nake "jikin waye ?"stil dai shiru tayi  masa " jibi iwar haka kina cikin gidana watakilla ma muna kwance acikin bargo daya makale da juna "wani kuka ta fashe da shi tana qara matsawa ". " to to!!  shikenan na bari  Kiyi hakuri amman dai Kinsan dole zamu kasance tare? tsaki taja ta kawar da fuskarta gefe a haka suka qaraso   gida ."mota bata tsaya a koina sai a kofar gidansu bayan motar ta tsaya   ta fito hisham ya biyota suka jira yana yi mata magana amman taki kulashi tana  qoqarin shiga  gida ya riko hannunta daya cikin nashi ta juyo a matukar fusace tana kallonsa shima kallonta yake with a broad smile a fuskarsa sai itace ta  dauke kanta tana lissafi yadda zata gudu ta bar shi da wahalarsa  ". "anya kuwa zata iya gudu ta bar iyayenta  bayan a yanzu bata iya zuwa koina ta kwana batare dasu ba ?ta tambayi kanta nan take zuciyarta ta bata amsa da" wannan shine mafuta a gareki  idan komai ya natsa sai ki dawo wanda zuwa lokacin dole kowa ya hakura ." ta sake kallonsa taga har lokacin ita yake kallo yana murmushi wanda bata san ko na meye ba ."cike da jin haushi ta  fix hannuta tana mai bakinciki dan  komai ya faru da rayuwarta shine sila shekara da shekaru bata ta'ba tunanin barin iyayenta ba sai a dalilinsa ita kam tsakaninta dashi sai dai allah ya isa  da wannan bakinciki ta shige gida  ta barshi tsaye  yana kallon bayanta ". Sai bayan data shiga  gida sannan ya juya ya wuce  kai tsaye wajen ATA ya wuce koda ya shiga parlour'nsa yana tsaye akan dadduma yana sallar magrib bai zauna ba shima bathroom ya shiga ya dauro alwala ya fito ya bisa sallah ,bayan sun idar ya fara tsokanar ATA "ango ango !!amman gsky kai dai anyi dan iskan ango ,wallahi baka kyautawa maryam ba, ka barta ita kadai allah sarki wallahi na tausaya mata, wallahi abokina kabi a hankali ina guje maka ranar da zaka rufta "wani dogon tsaki yaja yana  watsa masa harara tare da cewa "ka maida hankalinka jikinka da wannan shirmen da kake yi  karka sake min maganar auren nan" hisham  yayi murmushi  yana cewa "ai hankalina yana jikina nan dai yayita jan ATA." Nuzla tsaye a dakinta hawaye na zubo daga kwarnin idanunta alokacin da take daukar abubuwan amfanita masu mahimanci tana tuna rayuwar kuncin da iyayenta zasuyi idan suka laluba basu ganta ba ,bayan kamar awa daya nuzla  ta fito zuwa babban parlour'nsu koina  ta kalla mutane a parlour'n yan'uwan mahaifiyarta gbdy  zaune kai tsaye ta shiga dakin hjy salema bata dade ba ta fito ta rasa yadda zaayi ta sake fita dan haka  ta koma ciki d'akinta  tana tunani hanyar da zata bi ta  kubta  daga wannan wahallen auren ." byn Kmr mintuna goma ta sake fitowa har ta kai bakin kofa aunty maijidda tace "ina zaki kuma adaidai wannan lokacin ? Ta fad'a tana kallon agogon dake manne a falon ,nuzla ta dan diririce sannan tace "yaya hisham ne ya kirani yana waje" tana gama jin abinda ta fad'a  ta juya tayi d'akin da baki suke  ita kuma nuzla  ta samu damar fice wa daga gidan gabadaya ." yan'uwan hjy salema suna ta kikiniyar da hadahadar abincin  gobe diner sam babu wanda ya fahimci nuzla bata gidan  har karfe goma sha biyu na dare ."Hjy salema dake zaune a bakin gadonta haka   nan jikin ta   ya dinga mata wani iri ,ta fito ta shiga dakin nuzla bata ganta ba dan haka ta juya ta fito daga dakin  tana  tmbayr   aunty rabi wacce ta kasance diya kanwarta  ce "umma  bansa inda take ba amman bari na dubata a dakinta "ai  daga dakin nata nike bangata ba shiyasa ma na tambayeki ." to bari naje na tmbyi aunty maijidda ko tasan inda taje da sauri ta wuce hjy salema." A bakin kofar fita daga parlour'n suka hadu  da aunty maijidda "Yauwa aunty maijidda ina nuzla ko ta fad'a miki inda zata "eh d'azu tace min zata wajen hisham amman bari na kirata nan  ta soma qoqarin kiran layin nuzla sai dai numberta na shiga bata dauka  dan haka ta kira layin hisham tana tmyrsa nuzla amsar daya bata yasa ta  shigo d'akin hjy salema da mugun sauri  ta isketa tsaye cikin faduwar gaba ." Aunty maijidda batayi magana ba  ta cigaba da kallon hjy salema "maijidda ko nuzla ta fad'a miki inda zata ?ta bude bakinta kenan zata bata amsa idanunta suka ci karo  da envelop asaman dress mirrow din hjy salema  an rubuta wannan sakon na umma da abba ne kallon da takewa envelop din yasa hankalin hjy salema ya kai kanshi " gabadayansu gabansu ne ya shiga dokawa dan basusan me Ke kunshe a cikinsa ba  tun baa kai ga budewa ba hjy salema ta soma furta kalmar "innalilahi inna ilahi rajiun  azuci  da fili dan ta gama shiga rudani "hannun aunty maijidda na rawa ta dauka  ta bude  envelop ta soma karantawa  a fili hannunta da jikinta na wani irin wara ." _Assalamu alaikum iyayena nasan aloakcin da zaku nemi ni ku rasa zaku ji babu dadi acikin ranku amman ina mai baku hakuri da neman afuwarku akan halin damuwar da zaku shiga a dalilina na tafe ne adalilin bana son aurena da yaya hisham  na fito  maku da manufata  amman kun kasa fahimtata dan haka na yanke shawarar barinku ba dan raina yaso ba ina sonki ummanah ina sonki fiyyr da komai haka kai ma abbanah ina sonka zanyi kewarku sosai_ rabi ta nike takadar ta mayar cikin envelop din tana kallo  hjy salema data zube kasa  jinta ne ya dauke dip  sakamakon abinda wasikar Ke dauke dashi  duk wani kuzari da karfin jiki babu atattare da ita baya ga tashin hankali "ji  take kmr ba ita bace anya nuzlarta ce  kuwa ta ajiye mata wannna sakon  ? Aunty rabbi duk ta rude sai zufa take fitarwa  nan da nan aka kira baba babba da yayyen nuzla maza har ma da hisham da ATA aunty rabi tace baba "kaji wani sabon  tashin hankali  nuzla ta gudu ta mika wa yaya Ibrahim wasikar  ya duba ,hannu  hjy salema  ya kama dan ta kasa motsin kirki binshi takeyi kmr rakumi da akala har  uwar dakanta ya kamota yana qoqarin zauna daita taki zama tana fashewa da wani gigitaccen kuka tana furta sunan "nuzla! "ku nemo yarinyata dan allah ku nemo yarinyata abinda kawai take iya furtawa kenan " "Ki kwantar da hankalinki hajiya zaa nemota yanzu ki zauna ki samu natsuwa ta girgiza masa kai tana mikewa ta fito tana kuka tana kiran sunan nuzla dole ya biyota damuwace karara ajikinsu, dukkan su da abinda suke sakawa cikin sanyi muryarshi wanda koda yaushe a haka take cikin sanyi ATA ya dinga kwantar wa da hjy salema hankali da tabbacin zaa ganta  sai lokacin tadan dawo da ga mummunan mafaarkin da take dan gani take tamkar a dream ne ,, ta dan dawo haiyacinta sai dai kalmr INNALILLAHI INNAILAIHI RAJIUN take maimaitawa " Numbobin yanuwa da abokan arziki aka shiga kira sai dai koina sai ace bata je ba duk suka rude kar ma hisham yaji labari   duk ya rude ya rasa inda zai sa kansa idanunsa suka kada sukayi jajir  gbdy ya nemi natsuwarsa ya rasa ji yake kamar zuciyarsa zata buga."gabadaya yan mazan babu wanda aka bari duk sun bazama nemanta hisham kam  baya fahimtar komai duk maganar da salim yake masa baya shiga kunnuwanshi shiyasa yaji Kmr ya  fita daga cikin motar ya taka da  kafarshi watakilla nashi gudun zai fi na motar duk jikinsa tsuma yake kwakwaluwarsa ta hargitse kamar hauka zai kamashi a haka suka qaraso   babban titin unguwarsu suna gama tsayawa ya fito da sauri yana dube dube amman babu ita babu alamunta ." Numberta ya dinga kiran taki shiga  har karfe  biyun dare basu ganta ba suka dawo gida cikin damuwa baba babba yace kowa ya tafi kawai makwancinsa sai gobe aga abinda zaayi ."ranar kwanan zaune sukayi duk hankularsu a tashe hjy salema kuka kawai take zainab da aunty maijidda ce masu dan dauriya matar salim kuka take hjy salema duk ta rikice masu sai sunan nuzlata take kira ,hisham kwana yayi yana kiran layinta gbdy ya zare sai salim ne ya dinga kwantar masa da hankali ." Washegari duk esatate din ya hargitse da labarin guduwa nuzla fad'ar irin tashin hankali da suka shiga bata baki ne  yan biki sun cika gida babu abinda ake sai jajantawa juna ATA ya  bada cigiyarta a duk kafafen  sadarwa, lokacin da  iyayen hisham suka qaraso daga masaukinsu dan su ba zaune suke a qasar ba hankalinsu  ya tashi matukar most especially mahaifinsa sakamakon jin mummunar labarin abinda ya faru dan kallo daya yayiwa hisham ya fahimce sam hankalinsa bai jikinsa ga wata katuwar rama da yayi acikin kwana daya ." amman ita mahaifiyarsa byn tashin hankali data shiga har 'bacin   rai ta tsinci kanta ciki ranta   ya baci matuka bare da ta samu labarin akan bata son d'anta  ne  ai sai taji soyayyar da takewa nuzla din  ta juye zuwa tsana mai karfi  " Nana hauwa'u na  zaune acikin dakinsu tare da maryam da diyana har ma da humaira , gabdayansu suna cikin jimamin abinda nuzla ta aikata "humaira tace "bansan me zai sa na gudu na bar iyayenta akan zaa aura min wanda banaso ,kowani iskanci mata sune kan gaba ku duba kuga shi nmj komai zaayi masa bazai ta'ba guduwa ya bar iyayensa ba amman sai kaga mace wai ta gudu wallahi nuzla really disappointed me ." "maganarki gsky ai ko maryam ta isheta darasi gashi dai bata son yaya adam amman haka ta daure ta karbi kaddararta cikinsu babu wanda bata  fadi albarakcin bakinta ba suna cikin wannan halin aka turo kofar dakin aka shigo hade da sallama gabdayansu suka waigo bayan suka kalli kofar dakin domin ganin wanda ya shigo ,hajiya zulfa'u suka gani sanye cikin doguwar riga na alfarma hannuwanta da wuyanta da yatsun hannunta duk gwal nd tayi kyau matuka sai dai kana kallon fuskarta zaka fahimce bata cikin natsuwa ." Ta qarasa shigowa sosai yayinda gabadayansu suka maida hankalinsu gareta suka  gaisheta cike da girmamawa ta danyi murmushi wanda kana ganin kasan na karfin hali  sannan ta amsa , ahankali ta samu waje ta zauna agaban nana hauwa tana cewa "ku bani waje zanyi magana da nana hauwa'u gaban nana hauwa'u yayi wani irin faduwa ta hade hannuwanta waje daya tana wasa da yatsun hannunta har zuwa sanda suka fice daga dakin ". "nana hauwa'u!" ta kira sunanta tare da jawo hannunta ta zaunar daita kusa daita bisa kujerar da take zaune akai "meye matsayina a wajenki ? tmbyr ta dan bawa nana hauwa'u mamaki amman dai ta bude baki ta bata amsa da "mahaifiya !" na gode mahaifiya zata iya yanke kowani irin hukunci akan diyar ta sai dai ni bazan yi haka ba sai dai na neman alfarma a wajenki ,nana hauwa'u tayi shiru kawai tana sauronta." hjy zulfa'u ta cigaba da magana "ina neman alfarmar   ki auri dana kuma yayanki hisham " cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da tsoro abinda take shirin aikatawa ta dago da kanta ta tsura mata ido cike da tashin hankali "nasan zaki iya min fiyye da haka ,ki taimkeni kar na kunyata a gobe nazo da tarin jama'a ban san me zance masu ba idan baa daura auren nan a gabe ba ,cikin tsananin tashin hankali da firgici da tsinkewar zuciya da tsoro tare da kyarma nana hauwa'u ta fuskanci kanwar mahaifinta" dan Allah karki bani kunya nana hauwa'u ki amince min zaki samu dukkanin kulawa a gidan hisham cikin zuba mata ido tace "mumy yaya hisham..! karki ji komai kawai amincewarki nake nema " Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗    MAR'ADAMS    💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.        Page 28 ..... Hajiya zulfa'u ta sake riko hannun nana hauwa'u gam cikin nata tana cewa "karki ji komai aranki hisham zai kula dake bazai ta'ba wulaqantaki ba wani yanayi nana hauwa'u ta dinga ji a gbdy ilahirin jikinta, kyarma da jikinta yake ya sake qaruwa ,babu abinda yazo mata alokacin kamar rayuwar maryam da yayanta adam yadda yake nuna rashin qauna garara agaban ko waye ,duk da mami dake tsakaninsu hakan bai sa ya hakura ya rungumeta a matsayin matar da aura ba." ta daure ta cije amman tunaninta na zuwa kan maryam da yayanta ta fara hawaye saboda tasan me zai iya faruwa daita matsawar ta amincewa wannan auren ita kad'ai tasan yadda take jin zuciyarta a halin da take a lokacin wani irin tsananin tsoro ne ya shigeta ." Kukanta ya d'aga hankalin hjy zulfa'u, jikinta ya soma kad'awa kamar mazari tana jin tsoron karta ki amincewa da muradinta amman duk da haka ta sanyawa jikinta jarumta tace "dan allah nana hauwa'u karki ce mun a'a rashin amincewarki zai sa naji kunya.wannan buqatar bawa ni kad'ai zakiyi ba har da martabar danginmu zaki yiwa kuka nana hauwa'u ta cigaba da yi har da shesheka tana mai tausayawa kanta ." " tana son taki amincewa amman kuma bazata iya karya wa mumy zuciya ba tunda tasan ba ita kadai bace budurwa da bata yi aure a family ba ta tsallake kowa ta miki kokon baranta zuwa gareta ahankali ta d'ago idanunta dake cike da ruwan hawaye ta zuba mata "sosai ta tausayawa yanayin da hjy zulfa'u ta shiga dan a shirye take tayi komai akan amincewarta." "Nasan kina tunanin halin da zaki tsinci kanki né a gidan hisham amman kisa aranki duk abinda zai faru na wani lokaci ne da sannu zaki zama tauraruwar agidansa idan kuma kikaji bazaki iya zama dashi ba ki fad'a min idan yayi miki wani abu na rashin kyautatawa just give me a call aurenku bazai qara ko second daya ba zan raba "ta fad'a tana jin d'acin kalmar aranta dan bazata so aurensu ya rabu zataso su kasance da juna har karshen numfashinsu." Still dai shiru nana hauwa'u tayi tana zubar da hawaye "ki tausaya min diyata kar naji kunya ." ire iren sambatun da take mata kenan wanda ya haddasawa nana hauwa'u jin tausayinta mai tsanani bugu da qari ita din mutun ce mai mahimanci arayuwarta sannan taji dadin kalamanta tana ganin abun zai zo mata da sauki ta hanyar mumy muryarta a matukar sanyaye tace "mumy mami fa? "ina ..ina ganin ya kamata muji ta bakinta ?ta qarasa mgnr muryarta na rawa cike da in ina tare da sake sunkuyar da kanta ." Hajiya zulfa'u ta d'aura hannunta daya akan nana hauwa'u tana shafawa tana jin wani irin sonta na shigarta fiyye da soyayyar dataji tana yiwa nuzla, har cikin bargon zuciyarta take jin nana hauwa'u wanda abun ya hade mata ne soyayyar mahaifinta da kuma na d'anta tilo da take dashi wanda a yanzu bata da kamarhi a duniya "nana hauwa'u maminki tasan da komai hasalima gurinta na fara zuwa har ga allah aunty zulai ta amince, tace daman burinta kenan taga kinyi aure kafin allah ya dauki ranta taga yan jikokinta na wajenki kullum adduarta fatan miji na gari take miki ,gashi kin samu domin hisham danuwanki yafi kowa cancata dake nmj né da idan mace ta samesa zataji dadin rayuwa dashi ,domin kuwa miji na gari né allah ya hadaki dashi ta amince dari bisa dari kawai a nemi amincewarki   Ta dago kanta tana kallonta murmushi tayi ga kuma hawaye na gangaro mata tace "shikenan mumy tunda mami ta amince nima na amince kuma nayi miki alkwarin zan zauna lafiya dashi zan kawo miki farinciki arayuwarsa zakiyi farinciki da kasancewarmu ." Nan take hajiya zulfa'u ta rungumeta tsam ajikinta cikin tsananin farinciki tana hamdala a fili "Alhamdulillah diyar albarka na gode nana hauwa'u ,kin tabbatar min da ina da matsayi a wajenki kuma zakiyi farinciki a gidan hisham in sha allahu bazakiyi kuka ba 'allah yayi miki albarka ta riko hannunta Tare da d'agata tsaye ta soma tafiya daita, binta kawai take har lokacin da suka fito zuwa falon gidan wanda a daidai wannan lokacin da karfe shadaya na safiyar ranar ta buga babban falon baba babba ya cika da gabdaya ahalin yaya Alhaji Abdallah." dayawa daga cikinsu zukantasu na cikin da tsananin tashin hankali bangaren baba qarami wanda har lokacin bai san inda diyarsa hindu take ba ,haka baba babba wanda ya rasa diyarsa a daren jiya bangaren mahaifin hisham shima zuciyarsa cike take da damuwar halin daya baro dansa ciki haka hajiya salema tunda ta zauna hawaye kawai take gogewa wasu na sake zubowa haka zalika uban gayya ATA da zaa yiwa auren dole tun daya zauna idanunshi ke kallon sama tunani kawai kwakwaluwarsa keyi ." babban parlour'n ya dauki shiru na kusan mintuna goma sha biyar kowannensu da abinda zuciyarsa take saqawa ,baba babba yayi gyaran muraya sannan ya fara magana a tsanake "zan fara da jajantawa kanmu halin da muka tsinci kanmu a ciki wannan lokacin amman nasan allah yana tare damu ,fatanmu allah ya bamu ikon cin jarabawar data fad'a mana nida dan'uwana" . "ni ai ikon allah da kuma rashin qarar kwana ne kawai yasa har yanzu ban mutu ba akan rashin hindu inji cewar baba qarami jin abinda baba qarami ya fad'a cike da damuwa yasa ATA sauke kanshi ya kallesa kawai yana ta,be baki at the same time zuciyarsa na tsananta bugawa yana jin ina ma shine hisham da nuzla ta gudu ta barshi , ina ma shima wannan guntuwa shegiyar yarinyar ta gudu ya huta tunda itama ba son shi take ba "zaune amman zuciyarsa bata gaji da adduar samun sausauci daga wajen allah ba ". " in sha allahu allah zai bayyana su gabdaya suka hada baki suka ce "Ameen allah ya kawo mana mafuta sun dade suna tautaunawa akarshe baba babba yace "yanzu ya zamuyi ? "dawa zaa maye gurbin nuzla a wajen hisham domin dai bazaa fasa d'aurin aurensa ba ?ya qarasa maganar adaidai lokacin da hajiya zulfa'u ta shigo falon hannunta rike dana nana hauwa'u tana cewa "karku damu ga wacce zata maye gurbin nuzla a wajen hisham nan domin kuwa na nemi alfarma a wajen diyata nana hauwa kuma ta amince da zata auri hisham tsakanin da allah ." Da wani irin saurin hjy salema da kanta ke duke ta d'ago tana kallon fuskar nana hauwa'u zuciyarta cike tashin hankali mara misaltuwa yayinda idanuwanta suka sake cikowa da ruwan hawaye, kallo daya nana hauwa'u tayi mata ta fahimci halin damuwar da take ciki ga dukkanin alamun bata ji dadin hukuncin ba ,ahankali tayi kasa da kanta dan bazata juri kallon cikin kwayar idanunta hjy salema ba dan wani irin tausayinta ne ya lullubeta ,itama bata só haka ba sannan ba yin kanta bane babu yadda zatayi , da ahlinta su kunyata gara ta rungumi qaddarar auren yaya hisham ,kuma ma ai asirinsu zata rufa gabadaya har ita nuzla domin idan basu na gida da suka san ta gudu ba babu wanda zai sani ". Kafin hjy zulfa'u ta sake magan tuni ATA wanda hankalinsa ya tashi matuka da jin maganarta yace "da gaske nana hauwa'u kin amince ko kuwa kina son yiwa mutane wasa da tunani né "?jikin nana hauwa'u a matukar sanyaye ta jinjina masa kai jikinta na kyarma jin yadda jikinta Ke rawa yasa hjy zulfa'u ta rikota sosai ta had'eta da jikinta saboda tsabar farinciki data haifar mata "amman dai nana hauwa'u kin kyauta Allah kuma yayi miki albarka allah yasa ki gama da duniya lafiya lafiya inji cewar baba babba ." "Gsky kin kyauta sam ban yi tsamanin zaki mana haka ba hakika kin fitar da alhalinki jin kunyar duniya ,allah yayi miki albarka yasa ki gama duniya lafiya yadda kika rufa mana asiri kema allah ya rufa miki asiri duniya da lahira hajiya jamila mahaifiya ga aunty abida ta fad'a cike da jinjina mata." gabadaya mutanen dake parlour'n addua suke mata tare da gode mata amman ban hjy salema da mami wacce tayi alkunya ,yayinda ita hjy salema bakinciki né Kmr ya kasheta ,duk da irin qaunarta ga nana hauwa'u sai taji a yau babu ita ta juye zuwa qiyayya mai zafi "me yasa zata amince da wannan auren bayan diyarta ce tafi cancata da auren hisham ?"ko bama haka ba a tunaninta ko auren wasu zaayi dabam ya kamata a d'aga shi sakamakon rashin diyarta da tayi amman hankalin kwance suke bayyana farincikinsu ." wani sanyin dadi ne ya lullube nana hauwa'u jin dadin yadda ahlinta sukai alfahari daita ."muryarta a matukar sanyaye tace "me yasa zakuyita gode min dan Allah ku daina gode min nayi saboda kare martabar gidanmu né ,bazan so ahlina suji kunya ba a idon duniya ba halin yanzu abinda nafi buqata daga gareku shine addua kuma kunyi min "ta qarasa maganar muryarta na rawa hajiya zulfa'u tayi saurin cewa "yar albarka karkiyi kuka idan kikayi kuka nima zanyi ". Cike da zafin zuciya take cigaba da kallon hjy zulfa'u da nana hauwa'u dake drama dan abinda ta d'auka kenan ,ahankali ta mike tsaye ta tsaya a yayinda bakinciki da zafin zuciya ke kutimemeya daita ita kam nana hauwa'u kunyata ce ta kamata da kuma kunyar hada ido da hajiya salema ta sauke ajiyar zuciya sannan ta soma magana cikin fushi "hakika baku min adalci ba ,kowa anan yasan yadda mukayi fama da nuzla akan hisham "yanzu da abinda zaku saka min kenan ?diyata ta gudu saboda bata són auren nan amamn shine zaa dauki wata a maye gurbinta daita ni ko oho kenan shikenan na rasa diyata ?."ta qarasa mgnr tana wani irin kuka" kusani bazan ta'ba manta wannan ranar ba a tarihin rayuwata yadda aka sauya nana hauwa'u da nuzal tana gama fadar haka ta nufi hanyar fita cikin gagarumin tashin hankali." ATA da yayi mutuwar zaune ya mike tsaye zumbur ya soma takowa zuwa inda nana hauwa'u take tsaye, kansa nayi masa wani irin sara ya qaraso ya tsaya gaban nana hauwa dake kallon kasa yasa hannu ya d'ago ha'barta ya zuba kwayar idanunshi cikin nata yana kallon cikin kwayar idanunta da hawaye ke kwance acikinsu sakamakon jin furuncin hajiya salema ." Muryarsa a kasalance ya soma motsa labbansa "daman kina son hisham ne ?ta girgiza masa kai alamun a'a "to me yasa zaki amsa zaki auresa ?ta sake girgiza masa kai "ki bude baki Kiyi min magana yayi maganar a tsawace wani tsoro né yayi ma nana hauwa'u diran makiya taji kmr ta saki fitsari a wajen tsabar tashin hankali da sauri ta bude baki tace "a'a?"!To kiina hauka ne ko kin fara shaye shaye ne ?gabanta ya dinga bugawa gbdy duk wata gaba da allah ya halitta ajikinta rawa take kallo daya zaka mata ka gane hankalinta a matukar tashe yake "kin kuwa san irin hatsarin da zaki jefa rayuwarki ciki ?jikinta na rawa ta girgiza masa kai "kin kuwa san me ake nufi da aure ?aure na nufin mutuwa ce kawai zata raba ko kinsan auren da duk baa ginasa akansa soyayya ba baa samun farinciki acikinsa ,maza maza ki fad'a masu cewar kin fasa wannan auren yana gama maganar ya juya zai fita daga d'akin tayi saurin shan gabansa ta durkushe a gabansa ta rike kafafunsa da hannuwanta "kayi hakuri yaya bazan iya ba na rigada nayiwa mumy alqawari kayi min addua tare da fatan alkhairi , kai ne fa ka hada auren hisham da nuzla ba dan tana sonshi ba sai dan ka faranta masa kuma babu wanda yayi maka mutsu bare jayayya akan hukuncinka me yasa alokacin bakayi tunanin auren da duk baa ginasa akan soyayya ba baa samun farinciki?ni da nuzla duk abu daya ne a wajenka idan har zaka iya yanke hukunci akan nuzla kowa yayi na'am dashi kai ma ka amincewa hukuncin mumy akaina". Numfashi ya janyo da kyar ya fesar yana qoqarin janye kakafusa ta sake rikewa gam tana zubar da hawaye "please yaya karka ki amincewa mumy bata takura min ba ni na amince daga qasan zuciyata kuma zan zauna da yaya hisham tsakanina da Allah." "Auta me yasa bazaki fahimta ba ?"me yasa zakiyi sacrifice din rayuwarki akan farinciki wasu ?idan Ke zaki iya rayuwar kunci ni bazan iya ganin rayuwarki cikin kunci ba ,bazan so rayuwarki ta qare a wahala ba, ciwon zuciya né zai kasheki saboda zai ta kunsa miki bakinciki né tunda ba kece zabinsa ba "kayi min addua kamar yadda kowa yayi min shine kawai abinda nafi buqata ahalin yanzu ta qarasa mgnr tana shesheka kuka runtse idanunshi yayi tare da dafe kanshi dake cigaba da sarawa "akwai damuwa auta ,akwai zafi da radadi ,yau ace nmj ne Ke son mace komai mai sauki ne, na yanke hukunci akan nuzla ne sanin zatayi farinciki tunda hisham na sonta ke fa ?" bai ta'ba kawowa rayuwarsa ke ba, sam sam bai ta'ba tsara rayuwarsa dake ba idan kina kallon mumy na sonki ba shi ya zamanto zakiyi farinciki a gidansa ? "please yaya !ta fad'a tana wani irin kuka mai d'aga hankali kalmamin mumy da ta dinga fad'a a wannin data gabata wanda mami ta fad'a mata ne ya dinga dawo mata daki daki ,tunda har mami ta amince da aurenta da yaya hisham bazata ta'ba kin auren nan ba, domin tayi imani ace yaya hisham ba na gari bane mami bazata yarda da hadin ba hannunsa yasa ya d'agota yana share mata hawaye dake gangaro mata sannan ya rungume ajikinsa yana d'an dukan bayanta" wannan shine karo na farko da yayanta yayi mata haka a tun tasowarsu " daman haka yake tsananin sonta ?daman akwai ranar da zai nuna damuwarsa da kulawarsa gareta "?shiru tayi ajikin yayanta tana sauke numfashi ." Ahankali ya zareta ajikinsa ya zuba mata idanuwanshi itama shi take kallo hawaye na sake cikowa a idanunta "shikenan auta allah yasa albarka yana gama fad'ar haka ya juya Jiki babu kwari ya fice daga d'akin cikin wani irin yanayi na tashin hankali "shi dai har ga allah wannan hadin bai yi masa ba babu yadda zaiyi ne kawai ." Sunkuyar da kanta kasa tayi ta kasa hada idanu da jamar dake falon babu wanda bata burge ba hatta baba qarami ya jinjina mata domin yasan ba kowa bane zai iya yin abinda tayi haka muke fata a kowani lokaci idan mukayi umarni ya kasance kunyi mubaya'a wannan shi zai sake tabbatar mana da irin tarbiyar da muka baku mun gode da biyayya da hukuncin da muka zartar akanki dan haka ina miki albishir da cewar zaki samu farinciki inji cewar hajiya zulfa'u ta kamota zuwa jikinta "my dear dan Allah ki ramin bala direba zai kai wani waje " kai kawai ya gyada mata sannan ya ciro wayarsa ya soma neman layinsa yayinda tayi hanyar waje da nana hauwa'u ta barsu suna cigaba da tautaunawa har d'akinsu inda ta d'aukota ta maidata tana cewa "bani wasu mintuna zan dawo yanzu kai kawai ta gyada mata sannnan hjy zulfa'u ta juya ta fita daga dakin alokacin bala direban ya iso yana tsaye a haraban gidan ya juya kan mota yana jiranta yana ganin fitowarta yayi saurin fitowa ya bude mata gidan baya ta shiga motar ta zauna tana bashi umarnin inda zai kaita ya amsa mata da "tô!."ya rufe mata murfin motar ya shiga mazaunin direba ya tada mota suka fice daga haraban gidan ." Hjy zulfa'u na fita daga dakin nana hauwa'u ta kwanta lamo ranta duk babu dadi tunani ne ya lullubeta ita kanta tasan gsky yayanta ya fata mata aure ana ginasa ne akan soyayya domin samun zaman lafiya kuka nana hauwa'u ta fashe dashi wanda har maryam da diyana suka shigo bata sani ba mrym ce ta isa wajenta tare da dafe qirji tana cewa " Sister lafiya me ya faru ?kuka ta cigaba dayi batare da ta bata amsa ba dan girman allah ki fada min me ya faru ." Diyana ta riko hannunta "me ya sameki hk kike wannan uban kuka haka "nice zan maye gurbin nuzla a wajen yaya hisham "what ?suka had'a baki ta kwanta ajikin mrym da tafi diyana shiga tashin hankali hawayenta take ji ajikinta ta ma rasa me zatace "nima shikenan rayuwata tazo karshe nasan yaya hisham bazai so ni ba tunda nuzla yake matukar só? mrym ta d'agota daga yadda ta kwanta ajikinta "wai wa ya zarta da wannan hukunci ?"shigowar da mumy tayi d'azu nan tayi musu bayanin komai "am very sorry kema da laifinki taya zaki amince mata inji cewar diyana ." "yaya zanyi bazan iya zuba mata qasa a ido ba mumy ta wuce hk awajena bani ba nasan ko ke tayi wa mgn zaki amince mata bugu da gari mami ta amince diyana bata sake cewa komai ba tunda taji mami ma ta amince ,mrym kam rarrashinta take tana karkafa mata gwiwa "tunda mami ta amince ki kwantar da hankalinki kece fa ke bani kwarin gwiwa kina són naji bani da wannan kwarin gwiwar né ."?ta girgiza kai "tô dan girman allah kiyi hakuri kiyi shiru mu barwa allah komai ." bangaren ATA zuciyarsa a cunkushe ya shiga d'akinsa bakinciki abinda nana hauwa'u da auren dole da mahaifiyarsa zata masa na sake ninkuwa ,wani irin zafi zuciyarsa ke masa zuciyarsa na matukar zafi ya bud'e qaramin fridge dinsa ya d'auki gorar ruwa tare da kafawa a bakinsa sai daya shanye tas sannan yayi wurgi da roban." Ahankali ya zame ya zauna akan kujerar kushin "wai me yake faruwa dani né komai ya zama worst agareni shine tambayoyin daya cigaba dayiwa zuciyarsa sam ruwan bai sanyaya masa ransa ba dan damuwarsa na nan bata ragu ba babu abinda yake bukata kamar sigari dan irin sarawar da kanshi yake a yau din nan dole ya had'a da sigari idan ta kama har da giya a hada masa dan yana buqatar ya bugu iya bugawa ya kira daya daga cikin yarasa yace ya kawo masa ta'ba sigari kwali ashirin yana gama wayar ya kwanta yana jiran Peter ." Bai dade da kwanciya ba aka soma knocking kofar falon yana daga kwance runtse idanushi daga shi sai wondo baki da riga hamles ash colour ya bada umarnin shigowa peter ya shigo cikin falon hannunsa rike da leda cike da girmamawa ya rusuna ya gaisa da ogansa ATA ya yunkura ya mike zaune ya amshi ledar had'e da bude wata durowa dake gefensa ya zaro bandir din fararen yan dubu day day ya mika masa sannan ya bude ledar ya zaro kwalin sigari ." karba peter yayi ya cigaba da tsayuwa "kaje ka siyo min giya kwalba biyar mai kyau ka kawo min yanzu yanzu ."ya fad'a yana d'aura sigari abakinsa Kallonsa peter yayi cike da mamaki dan tabar ma ya jima bai aikesa ba ". "amman boss ....." just leave "babu shiri peter ya juya da sauri ya fice daga falon sigari ya soma zuka ko kafin peter ya dawo ya shanye kwali biyu yana kan na uku cike da girmamawa zai ajiye masa yace ya bashi kwalbar giya biyu yasa sauran a fridge ya nuna masa fridge sannan yace d'auko masa glass cup ya d'auko ya mika ya kama gabansa yana janyo masa kofar ." ATA ya kashe wayoyinsa gabadaya sannan ya balle kwalba giya ya tsiyaya a glass cup ya kai bakinsa bai ji komai ba dan babu abinda yafi bukatar alokacin kamar ya bugu ,yana son ya manta komai ciki kuwa har da mafarkinsa ya shanye tass ya sake tsiyaya wani yana sha yana zukar sigari wani irin zuka yayi wa sigarin yana kwantar da kanshi akan kujerar da yake zaune sai daya dauki second biyar sannan ya d'ago ya kalli sigarin hannunsa daya kusan qarewa ya sake kaiwa bakinsa ya zuga da kyau ya d'auki cup din giya ya shanye yana fesar da hayakin sigari ." sosai ya bugu ya fita haiyacinsa can ya mike yana layi ya shiga d'ayan d'akinsa ya d'auko tanga memen hoton zanen princess dinsa ya rungume tsam a qirjinsa yana jin wani tsantsar soyayyarta na ratsashi "ina ...ina sonki princess wai a ina zan ganki ne? " ki fada min inda zangaki mana yana magana yana kallon hoton ya fito falo ya zube akan kujera rungume da zanen a qirjinsa daga nan wani bacci mai nauyi ya daukesa bai sake sanin halin da yake ciki ba ." Hisham yana zaune yana faman kiran layin nuzla mahaifiyarsa hajiya zulfa'u ta amshe wayar hannunsa tana dubansa "zaka kashe kanka ne akan yarinyar data gudu saboda bata sonka ko me ?"haba mumy ko nuzla ta gudu dan bata sona still akwai yan'uwantaka a tsakaninmu" ban son iskanci ba yanuwantaka ba kune ma kashin awaki qarewar yan'uwanta duk yan'uwantakan dake tsakaninku ya kai ta nida mahaifinta ? "karka manta nida mahaifinta uwarmu daya uban daya dan haka wallahi Kayi maza ka cireta aranka ai dana san gantalliyar yarinyar nan bata sonka bazan kashe kaina akanta ba "mumy ki barni naji da damuwa dake damuna please "damuwa ai ta qare kamar yadda aka saka ranar daurin aurenka a gobe tabbas a gobe zaa daurashi "Yauwa mumy har kin sa naji dadi bari na tashi na fita nemanta ko allah zai sa na ganta ." Wani dogon tsaki taja tana dubansa "hisham ka natsu da kyau zaa daura aureka ne amman da wata ba nuzla ba kuma acikin family din nan kamar yadda muka yanke hukunci "what mumy ? haka nake nufi dan allah mumy karki min haka wallahi ni nuzla kawai nike so bazan iya rayuwa da wata ba ,dan allah kar abinda tayi yasa ki yanke wannan hukunci akwai kuruciya a tattare da nuzla wallahi bata da wayon kanta ." " min shiru a nan kuma karka sake min maganar wata nuzla idan ba haka zaka hadu da mummunar baci raina da baka ta'ba gani bata da wayon kanta tasan ta gudu ta bar gida "? tana gama fadar hk ta tashi zata bar falon ya riko hannunta cikin nashi duk ilahirin jikinsa babu inda baya rawa hatta hannunsa dake rike da hannun mahaifiyarsa kirrrma yake yana sake damke hannunta da kyau "ki tausaya min ,ni zaki duba mumy da halin da zan shiga nuzla wata abace mai daraja acikin rayuwata karki maye min gurbinta da wata cike da jin haushi ta fixge hannunta "for the last time karka sake min maganarta sha sha kawai da bai son ciwon kansa ba yarinya ta gudu ana gobe daurin aurenku amman ka tsaya kana fad'a min tana da daraja acikin rayuwarka tunda ta gujeka na tsaneta Ka shirya karka manta karfe hud'u daidai zaa tafi diner "what? ai kasan da zuwa wajen diner dan hk karka bata lokaci tana gama fadar haka ta bar dakin kai tsaye wani haddaden office din gyaran jiki ta nufa ." Nan da nan ya kira salim cikin tsananin tashin hankali bayan sun gaisa ya fad'a masa halin da yake ciki salim din ma kwantar masa da hankali ya dinga yi" kayi hakuri da hukuncinsu hisham ya rude ya rasa abinda Ke masa dadi amman me yasa zaa min haka bayan an bada cigiyarta a kafafen sadarwa to dawa zaa hadani auren "?shiru salim yayi na second goma sannna yace "nana hauwa'u " "Wata irin zabura hisham yayi yana cewa "what !? wace nana hauwa kenna ?ya fad'a a rude idanunshi suna qara canza kala tsabar tashin hankalin da yake ciki ganin irin rudewar da yayi salim yace "ka natsu ka sausautawa kanka, haka rayuwa take hisham kullum tana zuwa da sauyi sauyi bisa izinin allah wanda bawa bai isa ya canzawa kansa qaddararsa ba hisham kayi hakuri nana hauwa dai da kasani kanwa ga ATA ." "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ya shiga furtawa yana maimaitawa rike da waya salim ya dade yana rarrashinsa da yi masa nasiha yanzu dan rashin Imani mai yasa zaa bani nana hauwa'u?me zanyi daita ya qarasa maganar ya hadiye wani abu daya tsaya masa a makoshi "ka taimaka hisham karka kunyata iyayenmu karka manta mutane bilaadadin ne zasu halarci dauren auren nan kuma kowa ya rigada yasan dauri aure biyu zaayi ita kanta nana hauwa'u dan kar kimar gidana ta zube yasa ta amince "shiru yayi kawai ya sauke wayar a kunnensa yana kallon saman dakin ." Yana cikin wannan halin dad dinsa ya shigo da sauri ya kalli mahaifinsa cike da rauni ya mike alokacin da dad dinsa ya zauna kusa dashi hisham ya riko hannunsa yana cewa "abba kaji mumy wai zaa daura aurena da nana hauwa'u dan allah abba kada ka bari a daura auren nan ya qarashe maganr cikin tashin hankali da bacin rai ,cikin zuba masa ido abban shi yace "me yasa zaa bari ?kanshi ya shiga girgiza masa tare da hade hannunwansa waje daya da nashi yace "saboda banasota a bawa wani ita amman banda ni." hisham gsky auren nan fa kamar an daura shi an gama babu wani mahalukin daya isa ya hana wannan daurin auren gara ma ka kwantar da hankalinka tunda ka jurewa auren wacce bata sonka ai sai ka jurewa wacce zata taimakawa rayuwarka sannan wacce zata cire iyayenka cikin shiga kunya "pls abba "kai babu fashi dole sai ka aureta cikin jin haushi ya mike ya shige d'aki ya rufo kofar da karfi ." Hajiya salema ta zube a kasa tana cigaba da hawaye a gaban baba babba dake zaune yana qara karanta wasikar da nuzla ta ajiye musu sannan ya d'ago ya kallesu gbdy "kar ma sake ganin kowanne acikinku ya shiga damuwa akan nuzla tunda ta zabi barin gida tô ina ganin ta ciremu daga cikin mutane masu mahimanci ne arayuwarta dan haka muma yana da kyau muyi saurin cireta daga zuciyarmu a firgice hjy salema ta dago ta kallesa tace "amman alhj kana gani wannnar maganar daka fada babu wani gyara acikinta taya zamu haifi yarinya da cikinmu ace kuma mu manta da ita "?kafin ta qarasa mgnr har baba babba ya mike ya shige d'akinsa dan yaji bakinciki abinda tayi acikin mutane ."hjy salema fashewa tai da kuka suma ya'yanta mata suka fashe da kuka zukatansu nayi musu zafi kamar zata fito." Mmn sudaisi 💗💗💗💗💗💗    MAR'ADAMS    💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi  byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.        Page 29    Ahankali yaya Ibraheem ya shigo parlour'n hankalinsa yayi matukar tashi sakamakon yanayin daya ga mahaifiyarsa da yan'uwansa ciki ,hajiya salema tana kuka aunty amina da aunty zainab suna tayata kuka tamkar ransu zai fita ,sai daya numfasa sannan ya fara magana a natse "amina ,zainab bana son wannan kukan ,idan kuna kuka ya kuke son hajiya tayi ? kune fa ya kamata ku dinga bata kwarin gwiwa da rarrashi amman sai ku tasata gaba da kuka ". "Sam yaya baka ta'ba duba damuwarmu ."koda wani lokaci laifinmu kake kallo idan bamu taya mahaifiyarmu kukan ahalin da take ciki ba me zamuyi ?" Inji cewar amina "shikenan mun rasa nuzla shi kuma hisham an bashi wata amadadinta yarinyar nan fa bata son shi aka takura mata gashi ta gudu an barmu da matsalarmu nasan ko mutuwa tayi basu da asara "zainab ta qarasa mgnr tana zubar da hawaye." Zainab tasa gefen mayafinta ta goge hawayenta kana ta cigaba da magana "kai ma yaya kasan ba'a kyauta mana ba kuma koda wani lokaci baba abayansu yake baka san abinda hajiyarmu take ji acikin zuciyaarta ba , wallahi matsawar baa ga nuzla a rayuwarmu a haka zata qare ,tabbas raywarmu zata qare cikin damuwa amman wallahi kowa sai ya d'and'ani kud'arsa dan wallahi i bazamu yarda ba wannan d'aurin auren bazaa d'aurashi ba sai an nemo mana nuzla zumunci ya dade bai lalace ba kowa yayi ta kansa kawai .." "Kada kuyi haka amina gara mu mika komai zuwa ga allah "yaya Ibrahim ya fad'a yana kamo hannuwansu ya zaunar dasu akan kujera suka zauna suna zubar da ruwan hawaye ,ya kamo hajiya salema itama ya zaunar daita yana dubansu ,kallo daya yayi masu ya gano cewar gabadayansu basa cikin haiyacinsu "sam sam kalmanku basu min dadi ba kuma kun bani mamaki dan banyi tsamanin wadan nan kalaman zasu iya fitowa daga bakunanku ba ,kun kuwa san yadda naji da kuka fadi lalacewar zumunci ? dan allah ku dawo hankalinku sam baba bazai ji dadin duk wani abu da zaku kunno kai dashi cikin ahlinsa ba ." Ya maida hankalinsa sosai ga hajiya salem yace "hajiya Kiyi hakuri ki barwa allah komai ita rayuwar dan adam cike take da qudirin ubangaji kala kala ,dukkan rayuwa rubutacce alamari ne daga Allah duk wani d'an adam ya kamata yasan wannan ,haka Allah ya qaddaro nuzlah ba matar hisham bace duk yadda yake sonta yake muradin aurenta bazai aureta ba wata zai aura ,haka zalika itama nuzla ba abokin rayuwarta bane muyi fatan allah yasa hakan ya zama alkhairi agaresu ,ita kuma nana hauwa'u kuyi mata fatan nasara a rayuwar aurenta ita kuma nuzla allah ya karkato mana da hankalinta ta dawo gida."   hawaye ne ya gangaro daga cikin idanun aunty zainab da aunty amina bakinsu ya kasa furta komai sai kuka ita ma hajiya salema ta qara sautin kukanta sosai ,babu abinda bakinta ke furtawa sai ku nemo min yarinyata sosai jikinta ya dauki zafi rarrashinta kawai suke amman taki yin shiru bakinta ya cigaba da furta ku nemo min yarinyata "hjy ki barwa allah komai sannan ki kwantar da hankalinki ayi komai dake in sha allahu ana gama bikin nan zaa cigaba da neman nuzla ." sanyayyen ajiyar zuciya ta sauke ga kuma hawaye na gangarowa akan kuncinta jin bai biyewa mahaifinsa da yace kowa ya cireta arai ba muryar cike da sautin kuka tace "Allah yayi maka albarka babu abinda yake damuna kamar rashin nuzla yau da diyata tana tare dani aka samu wannnan sauyin bazan ji 'bacin rai haka ba ,dan Allah ka nemo min nuzla zuciyata na cike da kewarta ,nayi nadamar goya masu baya alokacin da zaa hada auren nan ,banci na amince da yanzu yarinyata na kusa dani cikin kwanciyar hankali wallahi nayi nadama ku nemo min nuzla dan bazan iya jurar rashinta ba." yaya Ibraheem ya dafe goshinsa yana jin zafin zubar hawayen mahaifiyarsa tana matukar bashi tausayi ya zai yi ya nemo nuzla ta ina zai fara ?sautin qarar wayarsa ce tasa ya sauke hannunsa ya ciro ya duba a gaban aljihunsa ya duba a hankali ya mike tsaye yana cewa "ku samu wani abu ku bawa hajiya taci sannan ku hada mata da maganin zazzabi tasha jikinta yayi zafi daywa zan dan fita amman bazan dade ba dan Allah ku cire damuwa da kudirinku ayi komai daku sannna kuyi qoqarin kwantarwa hajiya da hankali ".ya qarasa fada tare da ficewa daga parlour'n ya bar hjy salema da ya'yanta." Cikin mintunan da basu wuce talatin ba sai ga hjy zulfa'u ta dawo masaukinta da meera mai lalle da make up ,ta shigo falon bakinta dauke da sallama tana cewa "my dear ina son yake ?"bai dade da shiga daki ba, ban san me ke damun hisham ba kinga yadda ya d'aga hankalinsa ya dinga hadani da allah akan lallai sai an fasa auren nan dan rashin sanin ciwon kai irin nashi ." "rabu dashi zan sauke masa duk wani abinda yake kanshi tana gama fad'ar haka kai tsaye dakin da yake ta nufa ta tura kofar ahankali ta shiga yana kwance idanusnhi a runtse cikin tsnanin tashin hankali ."yaji motsin shigowarta amman yaki bude idanunshi har sai data qarasa shigowa sosai ta tsaya akanshi tana kiran sunansa "hisham !da kyar ya bud'e idanushi ya zuba mata cikin tsananin damuwa "tashi muje kayi min rakiya" "zuwa ina kenan mumy ?kai dai ka tashi muje ta miko masa tafin hannunta ya mike da kyar yana cewa "dan girman allah mumy kiyi hakuri ki bar maganar auren nan nuzla ce rayuwata bazan iya rayuwa babu ita ba wannan yarinyar da zaa hadani aure daita bazata ji dadin rayuwa dani ba saboda ba ita zuciyata take so ba ,"bana son maganar banza hisham yarinyar data rufa min asiri kake fada min haka akanta idan baka kiyayeni ba zan mugun saba maka akanta amman mumy kina ganin ya kamata ki tsani nuzla irin ha .."? "Kada kace komai dan banason jin komai daga bakinka matsawar tozarci né ga nana hauwa'u a halin yanzu bana ji bana gani ita kawai nake só itace rayuwata yanzu tunda zata rayu da kai kuma zan iya yin komai akanta dan ita zan iya sadaukar da farincikina hisham tashi muje ta sake miko masa tafin hannunta zuciyarsa cike da tashin hankalin ya sanya hannunsa cikin nata ." suka fito zuwa parlour'n zasu  wuce dady yana waya tace " my dear sai mun dawo ya d'aga masu hannu suka fito suka shiga gidan baya suka zauna yayinda meera mai lallae ke zaune agida gaba gama zamansu keda wuya direba yaja motar suka fice ahankali motar ke tafiya hajiya zulfa'u na cewa "hisham ka kular min da nana hauwa'u kada ka wulakanta min 'ya dan bazan lamuncewa hakan ba ,daidai satin zuciyarsa ya dafe dan zafin maganarta yake ji "ples mumy ki bar maganr haka zuciya zata tarwatse numfashi ta sauke da karfi bata qara cewa komai ba ." kai tsaye abdullahi estate suka nufa bayan sun firfito daga cikin motar suka shiga gidan hajiya zulai falon gidan cike da mutane ,ana ganinta falon ya hargitse da hayaniya nan aka fara gaishe gaishe ana ga uwar ango da amarya shi kam hisham kanshi na kasa duk yadda abokan wasansa ke jansa bai dago kashi ya kalli kowa ba kusan ya matsu mumynsa ta sallamesa ya kama gabansa ,sai da hjy zulfa'u ta gama taja hanunsa suka nufi dakin nana hauwa'u inda ta iskesu zaune cirko cirko cikin zullumi . suna ganinsu suka tattara hankalinsu ga mumy da hisham , ahankali hisham ya daura idanunshi akan nana hauwa'u sai dai kallo daya yayi mata ya dauke kwayar idanunshi akanta ita kam ta bala'i kafeshi da idanunta tana son gano yayinsa amman kallo dayan data ga yayi mata ya d'aga mata hankali wanda yasa gabanta ya dinga dukan tara tara ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta muryata a matukar sanyaye tace "mumy barka da dawo ."yauwa diyar albarka sannuki da qoqari kinji allah yayi miki alabarka ,allah ya jikan mahaifinki "Ameen!" nana hauwa'u ta amsa tana cigaba da wasa da yatsun  hannunta yayinda gabanta Ke cigaba da faduwa." " meera ga guri ki zauna ki fara aikinki ga wacce zakiyiwa lalle ."ta nuna mata nana hauwa'u "lalle zaayi mata to shi meye na zuwa dashi ?ya d'ago a natse ya kalli hajiya zulfa'u fuskarsa da alamun tambaya , shiru tayi masa tai masa nuni da kujerar dake fuskantar nana hauwa'u kin zama yayi ya cigaba da tsayuwa ,meera ta fara hada lallen da zatayi wa nana hauwa'u "ka zauna mana ka wani tsayawa mutane aka "ni mumy abinda ban fahimta ba me zanyi idan na zauna ?". "ina son ayi mata lallen agabanka "what !? ya fad'a a hargitse ta gyada masa kai cike da mamaki yake kallonta nana hauwa ta sauke numfashi ta d'ago ta d'an saci kallonsa "mumy ki fahimceni ko ina son auren nan bazan zauna acikin mata ba bare bana só shiru mumy tayi zuciyar na rawa kafin ahankali ta motsa labbanta tace "ni zaka fadawa haka hisham ?"Shikenan na gode amman ka zauna  kamar yadda na buqata ."gsky mumy sai dai Kiyi hakuri dan wallahi bazan iya zama ba "yana gama fadar haka ya juya cikin tsnanin damuwa ya nufi kofar fita "hisham! hisham !! hajiya zulfa'u ta dinga kiran sunansa amman ina tunda ya nufi kofar fita bai juyo ba, ta gyada kai kawai tare da samun waje ta zauna zuciyarta na mata wani irin zafi ." "Mumy ! Nana hauwa'u ta kira sunanta muryarta a sanyaye ta d'ago tare da zuba mata idanunta "dan allah karki damu ki kwantar da hankali karki yi fushi dashi dole kowaye ya tsinci kanshi cikin halin da yaya hisham ya tsinci kanshi ya shiga damuwa ,a yanzu rarrashi yafi buqata ba takurawa ba "ta qarasa maganar tana mai sunkuyar da kanta tare da danne kukanta "na gode sosai diyar albarka in sha allahu muddin ina raye sai kinyi farinciki agidan hisham "murmushi nana hauwa'u ta sakar mata ba dan tana cikin farinciki yin murmushi ba sai dan ta kwantar da hankalin mumy ." Ahankali meera ta fara zana mata jan lalle yayinda mumy Ke jan nana hauwa'u ajiki ta hanyar yi mata hira su kansu diyana da humaira har ma da maryam mumy ta burgesu matuqa ,ana zanawa nana hauwa'u lallen mumy na yabawa "Woww gsky lallen nan yayi matukar kyau meera ai kudin lallenki yafi karfin yadda kika caza dole ma na qara miki kudi ."gabadayansu sukai dariya meera tace "na gode hajiya koda meera ta gama mata bata wuce ba dan zata tsaya tayi mata make up din zuwa wajen dinner kowacce ta kama gabanta domin shirya kanta aunty shahida tazo ta d'auki maryam  ta wuce daita domin shiryata ." karfe uku daidai aka fara tsara wa nana hauwa'u kwaliya sosai tayi kyau cikin doguwar rigar less red wanda mumy ce ta kawo mata daman kuma ta tanada ne dan nuzla komai red tayi amfani dashi kasancewarta fara sol tayi kyau sosai abun sai wanda ya gani shima a 'bangaren hisham red din yadi yasa ba qarami had'uwa yayi ba nana hauwa'u gani take ba ya ita amma tana ganin hisham ta raina kanta saboda wani irin kyau da yayi mata ya zarta kyau sosai  ." Tsura masa ido tayi tana kallonsa tsaye shi kuwa ko kallon inda take bai yi ba illa ma cigaba da amsa wayar da'aka kirasa yayi ,wata qawar mumy ce ta riko hannun nana hauwa'u ta kawota kusa da yaya hisham suka jero suka shiga mota zuwa hall koda suka shiga mutane suna ta d'aukansu pic jikin nana hauwa'u yayi sanyi sakamakon kalon baza da yaya hisham yake mata ji tayi kamar ta hana daukar hoton amamn bata damar aikata haka duk tajita a takure kamar ta koma gida ." Bangaren maryam kuwa an tsara mata kwaliya ta ban mamaki tayi kyau iya kyau cikin wani hadadden lace farin anyi mata dinki weeding gwan duk wanda ya daura kwayar idanunshi akanta sai dai yace Masha allah dan kyau kam tayi shi sai daukarta a hoto ake kafin angonta ya bayyana yayinda ango na can a buge mb, salim ,yasir suna tsaye akanshi sun zuba masa idanunsu cikin tsnanin tashin hankali dan sun razana da ganin halin da yake ciki hannunsa ya kai daidai saitin qirjinsa yana murza daidai inda zuciyarsa take bugawa da karfi yayinda gefensa hoton zanen princess dinsa ne yana kallonta yana zukar sigari." Ahankali ya dauke gajiyayyun idanunshi da suka canza kala saboda bugawar da yayi akanta ya dan waresu akansu yaga still shi suke kallo kwalban whisky's guda uku agabansa inda yake dagasu daya bayan daya yana sha yana zukar sigari cikin tashin hankali ,idanunshi sun qara rikidewa sunyi ja sosai ,ganin bashi da niyyar daina shan giyar yasa a matukar zuciye mb ya ture cup din daga gabansa yace "why ATA ?" akanka aka fara irin wannna auren ?wallahi ka sani shan wannan abu bazai amfaneka da komai ba don't forget mami yau tana cikin farinciki kuma ta tara jamaa me kake tunani zataji idan taganka cikin wannan halin ?kana son heart attack ya kamata ne ?." 'Dago jajayen idanunshi yayi ya kalli mb bai ce masa komai ba ya kunna sigari ya kai bakinsa yana zuka yana kallon wani bangaren dabam "wannan wani irin kaskanci ne haka ATA kalli fa ,kalli irin rayuwar da ka jefa kanka daga shan sigari ka dawo giya ni har yaushe ka fara shan giya ?"ban sani ba kuma babu ruwanka da rayuwata haka ya kamata nayi ko na zama wannan ciwona ne ni kad'ai babu ruwan kowa dani ." "why ATA? saboda wata soyayyar banza zaka kashe kanka akan wata yarinyar banza da ba gaskiya bace kana qoqarin 'bata rayuwarka, ka manta da wannan yarinyar ka kama wacce aka baka ka d'aura rayuwarka daita "salim !"ya kira sunansaa tsawace shiru salim yayi yana dubansa ya dauki kwalban giya ya kai bakinsa sai daya shanye tass sannan ya fuskancesu "akan mafarkina nake yi wannan abu ko ba akanta bane ni dai abinda nasani soyayyar da nake mata gaske ce kuma har abada domin Itace duniyata tana cikin nan  a duk inda take nasan itama tana jin yadda nike ji acikin zuciyata." "dan allah princess ki tausaya min bazan iya rayuwa babu Ke ba , idan babu Ke bazan iya cigaba da rayuwa ba ,ya mike da kyar yana layi ya dauki kwalbar giya ya fasa sannan yace "an hadani aure da wata guntuwar yarinya ita kuma nana hauwa'u an hadata da heart attack ,ajiyar zuciya ya sauke sannan yace idan hisham ya cutar da nana hauwa'u zan yanke komai dake tsakanina dashi wallahi wallahi I promise to make his life in to hell he will end his life in prison a firgice suke kallonsa zukatansu na duka tara tara idan kuma ban kaishi prison ba zan kashesa matsawar ya cutar min da yaruwata ." ya nufi kofar bedroom dinsa sauran kadan ya fadi mb yayi saurin kai hannu zai tarosa ya buge masa hannu yana cewa "don't don't touch me just leave my room ya fad'a yana shigewa dakinsa yana shiga ya kwanta flat akan bed tamkar wani matacce ." Dakin suka shigo gbdy suka rufa akanshi kamr zasuyi hauka mb ya hauro har saman gadon ya dagosa ya kwantar dashi ajikinsa ya kai hannu ya kamo fuskarsa yana dan marin kuncinsa tare da kiran sunansa "ATA ka tashi please karka zama haka yayi maganr yana kuka me yasa zaka mana haka ?" salim da Yasir ma sunansa suke kira "wannan fa ya rigada ya bugu babu inda zai iya zuwa kamata yayi a fadawa mami "wa zai iya wannan karfin halin ?wa zai iya tun karar mami da wannan maganar ?bazan so mami ta gansa cikin wannna halin ba inji cewar yasir "to meye mafuta yanzu me zaa bashi ya dawo daidai ?abu daya ne zaa iya bashi shine kokin shi kuma yana fara shanta matsala ne arayuwarsa gara kawai duk mu kwashe duk wani kayan maye dake dakin mu barsa yayi bacci idan ya farfado zai dawo daidai ." Ahankali ya motsa lip's dinsa "I can't marry this stupid girl I can't marry her coz she's not my type shine maganar da yake fitowa daga bakinsa "yanzu me zamu cewa mami ?a gaya mata gsky kawai yasir je kazo da mami ."Okay ya fad'a yana mikewa tsaye ya nufi kofar fita tare da mami suka dawo ai tana ganinsa ta daura duka hannuwanta bisa kanta ta fashe da wani irin kuka tana kallonsa tana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun tana qoqarin zubewa kasa ganin gaba d'aya ATA baya cikin haiyacinsa ,dan tuni bacci yayi awon gaba dashi jikinsu a sanyaye ganin mami na neman zaucewa suka tarota suna cewa "kiyi hakuri mami Kiyi masa addaua " yanzu abinda adamcy zai min kenan ana gabe daurin auresa?" yanzu ka kyauta min adamcy ? "gsky bai kyauta ba mami amman Kiyi hakuri girgiza kai mami tayi sannan ta sauke naunayen ajiyar zuciya ta mike da kyar ta fice daga dakin ."da kyar take jan kafafunta ta sauko ta tashiga 'daki  tana kuka Allah ya taimaketa babu kowa acikin dakin domin mutane duk sun wuce zuwa hall ta kulle dakinta kuka mami take sosai ta kira aunty shahida kiran na shiga amma bata 'dauka ba dan haka ta kira aunty khadija ita kuma wayarta a kashe mami tarasa abinda Ke mata dadi sai da zaa fito da maryam aunty shahida ta lalubo wayarta nan taga missed call din mami yafi goma cike da jin tashin hankali ta soma neman layinta mami ta dauka cikin yanayi na damuwa tace "shahida !". "Naam mami ya naji muryarki haka wani abu na damunki ne ?babu komai shahida ku wuce da maryam hall yau ma dai kamar jiya ita kadai zata zauna "shiru aunty shahida tayi kafin daga baya tace "mami ina adam din yake ?hakan nan mami ta kasa fad'a mata halin da yake ciki tace "yana kwance babu yadda yake bashi da lafiya ina maryam din take "gata nan a kusa dani "bani ita aunty shahida ta mika mata waya ,ta karba tana jin faduwar gaba mai tsanani". "hello mami !" maryam ykk ? lafiya lau mami ya naji muryarki kamar kinyi kuka ? babu komai maryam fatan kinci abinci ? ta gyada mata kai tana cewa "Eh naci numfashi mami ta sauke "kina jina mrym ? tace "eh mami ina jinki "nasan zaki fahimceni zaa wuce dake hall yanzu yau ma kamar jiya Ke kadai zaki kasance bana son kisa damuwa acikin ranki kinji ki dinga tuna kina dani "to mami !" ta fad'a hawaye na cika idanunta aunty shahida ta girgiza mata kai alamun karta yi kuka jiki a sanyaye ta mikewa aunty shahida wayr sukai sallama da mami ." Shiru aunty shahida tayi tana tunanin yadda yau ma maryam zata zauna ita kadai batare da ango ba ,bata ki maganar mami ba domin tasan rashin mafuta yasa ta fadi hakan amman ita dole ta nemo mafuta dan baza bari maryam ta zauna ita kadai ba ko hisham daya tsinci kanshi da auren nana hauwa'u acikin kwana daya ya yarda ya amince har ma sun isa hall bare adamcy da aka dauki sama da watanni ana abu daya ,sosai kwakwaluwarta ta shiga tunanin abunyi zuciyarta ta bata shawarar ta nemi salim ya maye gurbin ango tunda daman jiya babu wanda ya gansa ." da sauri zuciyarta ta amince da haka nan da nan ta shiga neman layin salim kira daya tayi masa ya dauka adaidai lokacin da suke shirin shiga mota dan zuwa hall "yaakayi my aunty ?kana ina salim ?gamu muna shirin zuwa hall ,yauwa salim dan allah kazo ka maye gurbin adamcy babu dadi maryam taje wajen diner ita kadai kafadansa ya daga alamun babu damuwa yace "okay shikenan an gama aunty ya yi discounneting din kiran yana duban sauran abokan tafiyarsa tare da yi masu bayani ,gsky aunty ta kawo shawara wallahi maryam na bani tausayi dan allah ya hadata da wani irin mutun mai shegen taurin kai, bari mu jira a fito daita sai mu mubi bayan motar ku, suna tsaye aka fito da maryam salim ya bude mata bayan mota ta shiga ta zauna shima ya shiga ya zauna aka rufe murfin mota yayinda mb da sauran abokan ango suka shiga motocinsu suka bar gida ." Tamkar ango da amaryarsa salim yayi active suka jera har zuwa mazaunin ango da amarya aunty abida ta kallesu ta kwashe da dariya tana kallon mahaifiyarta ,"mumy kinga abinda nagani kuwa ?na gani abida jiya bai zo ba ga yau ma ,ai halin adam sai ahankali ,shiyasa nake ganin da wahala ki iya shawo kanshi ya auri sultana"kai mami karki hada sultana da wannan yarinya sultana ta kereta a komai duk yadda zamuyi ta shiga gidansa sãi nayi idan allah ma ya taimakemu sai ya sota kinga komai zai zo mana da sauki ato allah yasa ,wannan lamari yayiwa abida dadi dan haka ta dinga jinta cikin tsananin farinciki ." Hall ya cika makil da jama'a ta bangare dabam dabam maryam tayi shiru tana rike da jaka yayinda masu hoto da vedio suka dinga daukarsu hoto har sanda aka kira hisham da amaryarsa zuwa fili ahankali ya mike atare suke daga kafafunsu suka tsaya a fili tamkar wasu gumaka hajiya zulfa'u ta shigo da 'kawayenta da ankonsu iri daya ta dinga likawa nana hauwa'u 1k amma ko kalon hisham bata yi ba MC ne yayi magana wai ya yaga hajiya iya amarya takewa liki ." murmushi tayi tace mishi "ai itace tafi cancata yar albarka yar gidan arziki gaba da baya irin albarka kaga dole ita ta dace da naiwa liki" aikuwa gurin ya 'dau shewa da tafi mutane wasu suce " wannan haka yake hajiyarmu Allah ya 'kara arziki hisham kuwa ya cika makil dan ganinsa tozarci ne abinda mumynsa tayi masa suka koma suka zauna aka kira maryam da angon bugi,maryam dake zaune wasu irin hawaye masu ciwo suka zubo mata ta yunkura ta tashi tsaye salim ya rike hannunta cikin nashi saurin kallonsa tayi sam bai damu ba ya kauda kanshi kawai ya soma tafiya daita ba dan ta soba ta dinga daga kafafuwanta ." da zata taka step ya tsaya ta sauko ahankali yana daga mata rigarta d'an kar ya hardeta abun ya burge mutane mc kuwa ya dauka angon gaske ne nan ya fara zuba "kai wannan ango yana ji da matarsa yana son matarsa see love ai nan hankalin mutane ya sake karkata kansu aunty abida tace "dama shi ya aureta muka huta dan sunfi dacewa dashi sultana kuma da adamcy "ke dai kina qaunar sultana da wannan mai shegen taurin kan tsiya "duk zai daina ne bari dai ya shigo hannun mace ." sosai salim ya kwashi rawa tare da maryam lokacin da aunty abida ta tashi taje liki byn tai liki ta kai bakinta daidai kunne maryam "karshe mai naci kenan da kin nuna baki raayi kamar yadda ATA yayi da yau baki wayi gari da aron ango ba wannan kawai ya isheki misalin irin halin bala'i da zaki shiga a gidansa "har aka gama taron aka watse aunty abida tana mata habaici wanda bata san dalilinta nayi mata hakan ba salim ne ya maida ita gida kai tsaye ta fito ko kallon inda yake batayi ba tashige gida ta rabu dashi dan taji haushin hannunta daya rike shima bai damuba yai tafiyarshi gida mrym tana shiga dakinsu kuka ta saka ranar  yadda maryam taga rana haka taga dare ga kuka datasha kamar ranta zai fita." Karfe daya daidai ata ya farka daga baccinsa ya mike da kyar ya shiga bathroom yayi wanka ya dauro alwala ya fito ya sanya vest da boxer sannan ya daura jallabiya mai garen hannu akai ya qarasa inda daddumarsa yake ya tada sallah bayan ya idar da salolinsa ya zauna yana tunanin awannin daya kwasa yana bacci , can ya mike ya fito zuwa falonsa ya bude fridge bai ga whisky dinsa ba ya kalli inda ya ajiye kwalayen sigari ko karan sigari daya bai samu ba ya maida murfin fridge din ya rufe da karfi yana jan tsaki ." ya koma ya zauna ya zubawa zanen princess dinsa idanu yana kallonta yana zaune mami ta turo kofar dakin ta shigo idanunta ya sauka akanshi idanunshi sunyi wani irin girma ta zauna a kusa dashi bai yi magana ba har sanda ta soma mgn "adamcynah ka tashi ?"eh na tashi! ya fad'a kawai yana duban zanensa yanayin yadda ya amsa kamar yana jin haushinta." ta numfasa kana tace "me yasa baka tashi lalata rayuwarka ba sai alokacin bikinka ?me ya kaika shan giya adamcy ?yanzu ka kyauta min kenan ?ka kunyatani acikin mutane kowa sai tmbyrka yake ka kuwa san adadin karyar da nayiwa mutane ? "ni fa bikin nan bashi da wani mahimanci agareni dan Allah sweetheart ki daina min magana akanshi sake daga min hankali yake "jin haka yasa ta canza magana "me zaa kawo maka? "shiru yayi yaki cewa komai dan idan ya bude bakinsa ba abinda zai ce a kawo masa sai giya da sigari su kawai yake buqata "bari naje na kawo maka abinci ta fad'a tana mikewa ta shafa kanshi sannan tayi gaba ." Tana fita Ya kira yaronsa yace ya siyo masa giya amman wacce tafi duk wanda yake sha karfi da sigari yana ajiye wayar mami ta dawo dakin ta ajiye masa plet din abinci agabansa kaci yanzu da zafinsa ta wuce bai ci abincin ba har sanda yaronsa ya kirasa ya dauka yana cewa "ka shigo mana " mami tana falo okay ina zuwa ya mike tsaye ya sauko lokacin daya sauko mami ta tashi ta shige dakinta ya fita "ya ka dade ?yallabai go slow yafi yawa a shagon siyar da giya fiyye da shagunan siyar da abinci bare adaidai wannan lokacin "okay kaje kawai ya karbi ledar hannunsa kwalba biyar ne aciki sai kwalayen sigari ya dawo dakinsa ya ciro daya ya balle bai tsaya sirkawa ba ya kafa abakinsa bai sauke ba sai daya shanye tass sannan ya daura da sigari haka yayita sha har karfe biyu da rabi ya koma bedroom dinsa wanda alokacin ya shanye kwalba hudu yana kan ta biyar ." ***** Washegari sunday ya kama daurin aure hisham bai tashi ba mumy ta dinga kiransa a waya gajiya yayi da kiranta ya dauka ya mike zaune yaji dalilin takura masa da take yi, yana dauka ta rufeshi da bala'i "wallahi hisham ka kiyayi fushina  idan ba so kake nayi maka baki ba wallahi ka natsu ka shiga hankalinka ka bari ayi komai a gama lafiya "yanzu mumy me nayi ?daurin aure ne a daura mana ai ba lalle sai naje ba "okay ni zaka fadawa haka ?" to dan girman allah karka zo "da taimakon salim hisham ya shirya tsaf cikin wata dakakkiyar shadda gezner fara sol koda suka fito mutane sun cika acikin haraban estate din ." Ahankali mb da sauran abokansu suka shigo falon ATA kowannensu sanye da farin yadi mai shegen tsada ,basu ganshi ba dan haka mb ya tura kofar bedroom dinsa anan ya gansa kwance a kasa shame shame tamkar matace ,da wani irin sauri ya qarasa inda yake kwance ya durkusa a gabansa yana cewa" Kai adam ka tashi mana lokacin zuwa daurin aure yayi fa "ya fad'a yana kallon kofar shigowa dakin "kai yasir kuzo ku ganshi ya qara shan giya ya bugu fiyye da jiya ya sake kallon fuskar ATA yana shafa fuskarsa ," kai wai meye haka ne ?subuhallah ya bugu kuma? inji cewar salim da yasir da suka shigo atare cikin tsananin tashin hankali." " kamo shi mb yayi yana cewa "ku taimaka min mu daga shi gbdy suka kamo shi zuwa kan bed dinsa suka kwantar dashi suka dinga jijiga shi" ka tashi dan girman allah lokacin daurin aurenka  yayi ,amman shiru kake jin ATA dan ko motsi baya yi numfashi ma da kyar yake fitarwa yasir ya kai hannu ya bude idanunshi yana kiran sunansa," kai ku duba fa kugani kwayar idanunshi sun dauke inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kai abokina ka bude idanunka muna tare da kai dan allah karka min haka bana son na rasaka ."mb ya fad'a cikin tsananin tashin hankali mara iyaka . "kana jina abokina ka bude idanunka yana magana yana jijiga shi amman har lokacin ATA bai motsa ba bai ma san a halin da yake ciki ba duk yadda sukayi su tashesa amman abun yaki cikin tashin hankali mb yake kallonsa gabansa na faduwa acikin kwana biyu kacal da soma shirye shiryen biki ya zare ya fita haiyacinsa bai ta'ba tsamanin zai shiga wannan halin ba da shi karon kashi ya shawarci mami a hakura da auren kawai kowa ya huta ." sosai mb yaji babu dadi ganin halin da amininsa yake ciki da sauri mb ya nufi kofar fita daga dakin kunnensa manne da waya yana cewa "hello sadiq kana ina ? "dan girman Allah ka ..ka taimaka min ATA nan ya zayyane masa komai cikin tashin hankali eh kazo da allurar please ya katse kiran ya koma cikin dakin har lokacin kwayar idanunshi bai dawo daidai ba ko dan sambatun nan na bugaggu bai yi ba ." suna tsaye sadiq ya shigo ya fara dubasa "yana da rai numfashinsa ne yayi nisa sakamakon buguwar da yayi amman zan masa allura nan da wasu yan awanni zai dawo daidai ya ciro sirinji daga cikin bakar jakar daya shigo dashi ya hada duk allurar zaiyi masa bayan yayi masa ne suka fito daga cikin dakin dukkaninsu jikinsu a sanyaye inda zuciyar mb Ke bugawa da karfi kamar wasu kurame haka suka sauko babu ango, ganin mami yasa duk suka dan saki fuska dan karta gane akwai abinda yake faruwa sai dai kallo daya tayi masu ta fahimci akwai matsala tun kafin su kai ga fita ta nufi hanyar dakinsa ." Tana shiga dakin yana kwance a buge Kmr jiya ta tsura masa ido bata ko liftawa ga wani tashin hankali data tsinci kanta ciki wanda bata ta'ba jin irinsa ba ,bta ta'ba nadama da danasani ba sai a safiyar yau din nan ,gabadaya jikinta ya dauki rawa kasa dauke idanunta tayi akanshi wadan da tuni sun rikice suna qoqarin zubar da hawaye cikin wani irin salo na yan shaye shaye taji yana kiran sunan "my princess kece rayuwata kece duniyata kinki bayyana min kanki saboda baki sona laifin me nayi miki ?yadda yayi maganar da sunan da yake ta faman kira ba qaramin rudar da mami yayi ba ,da sauri ta fito daga cikin dakin tana goge hawayen nadama da danasani sam sam bata ga laifinsa ko jin haushinsa ba domin itace sila jefa rayuwarsa cikin wannan halin ." mutane masu mahimanci suna zaune acikin massalaci dake cikin estate din abdullahi auren Adam Tariq abdullahi aka fara daurawa tare da maryam abdulra'uf akan sadaki kankani bisa umarnin mami sannan aka daura na hisham Muhammad sani tare da nana hauwa'u tariq abdullahi  duk yadda hisham yake son yayi jarumta amman a karshe sai da kwalla ta zubo masa jin an daura aurensa da wata ba da nuzlarsa ba .wani irin bakinciki ne mara misaltuwa ya lullube zuciyar hisham hannunsa salim ya rike cikin cool voice yace "ka sausautawa kanka sannan ka sanya aranka daman can nuzla ba matarka bace ." Ana gama daurin aure maroka suka fara shela acikin mutane hamdala mami tayi alokacin daakce mata an daura auren sai dai zuciyarta bata cikin jin dadi sannan bakinta bai daina  ambaton sunan Allah ba maryam kam fadawa tayi jikin aunty khadija tana fashewa da kuka mai karfi "aunty khadija ta soma rarrashinta kukan murna da kukan bakinciki maryam take bakincikinta yaya adam baya sonta na farinciki kuma burinta ya cika ta auri abun qaunarta ."hajiya zulfa'u ta kira salim cewar suzo da hisham bangaren hjy zulai suka shigo a tare da abokan ango hisham ko kallon inda nana hauwa'u take bai yi ba nan masu daukar hoto dake biye dasu suka shiga aikinsu anyi hotuna sosai ." Da misalin karfe biyu na rana mami ta shiga dakin ATA tare da mrym yana kwnace adduoi ta dinga yi tana shafa masa a fuskarsa yayinda maryam ta qaraso ta kafeshi da ido tana kallonsa tana jin wutar sonshi na qaruwa acikin zuciyarta qoqarin mikewa yake nan mami ta kama masa ya tashi ta jingina masa pillow a bayansa kallonsu kawai ya tsaya yi kafin ya rufe idanunshi yana sauke ajiyar zuciya "adamcy nah yau ka zama cikakken mutun ina cikin farinciki an daura aurenka da maryam sannna ina cikin bakinciki irin halin daka jefa kanka ciki ta qarasa mgnr tana kuka ". "meye kuma abun kuka bayan burinki ya cika ?ya fad'a yana goge mata hawaye "kukan murna da bakinciki ne , yau ina cikin farinciki da bakinciki ka taimaki rayuwar mahaifiyarka karka canza daga adamcy data sani ,rayuwa qaddara ce sannan kai muslim ne ka yarda da qaddara kayi farinciki da auren nan ka barwa allah komai "numfashi ya sauke baya jin zai yi wani farinciki da wannna auren maryam kam idanunta na kanshi har sai da taji sautin muryar mami ta doki dodon kunneta "maryam jeki hado masa tea ki kawo masa ta fice daga dakin." Bayan fitarta da kyar mami tasa shi ya tashi ya shiga yayi brush da wanka sabbin kayansa ya saka lokacin da mami ke fesa masa turare maryam ta turo kofar dakin ta shigo mami ta karfi cup din hannunta da kanta ta dinga bashi a baki tana masa nasiha ita kam mrym duk hankalinta na kanshi sai faman kallonsa take shi kanshi mamakin irin kallon da take masa yayi wanda kallo ne mai dauke da tsantsar soyayya acikin lokaci kankani...." Mmn sudais 💗💗💗💗💗💗    MAR'ADAMS    💖💖💖💖 💗💗💗💗💗💗 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi  byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.        Page 30 Ahankali ya d'auke kwayar idanunshi zuwa wani bangaren dabam yana jan tsaki dan bazai iya cigaba da kallonta ba "me yasa sweetheart take masa haka ?tasan baya son ganin yarinyar atare dashi amman ita burinta bai wuce taga sun kasance a waje d'aya ba." "dan Allah adamcy ka cire damuwar nan aranka ka kwantar min da hankali ahalin yanzu babu abinda nake buqata kamar natsuwarka da kwanciyar hankalinka ,duk duniya babu wanda zai so maka kwanciyar hankali da farinciki kamar ni mahaifiyar ka saboda nice nafi kowa sanin ciwonka ." "daga ni har kai da duk wani mai qaunarka babu wanda zai so ka qarasa rayuwarka haka batare da ka ajiye iyali ba , sannan zamanka kai kad'ai illa ne ga rayuwarka, idan wasu sun yarda da kai akan baka aikata komai na sa'bo ,wasu bazasu yarda ba, wasu zasu d'aukeka a matsayin mai neman mata ne duba da irin tarin dukiyar da allah yayi maka ,dan haka kayi hakuri ka rungume wannan rayuwar domin itace qaddararka dan adam bai isa ya canzawa kanshi qaddararsa ba." sosai ya fad'a cikin kogin tunani hankalinsa ya bar duniyar da yake wanda hakan ya bawa maryam damar cigaba da kallonsa son ranta tana jin tmkr ta fad'a jikinsa ta rungumeshi ta rarrashi kayanta ,jin saukar hannun mami jikinsa ya sanyashi dawowa cikin natsuwarsa ya d'ago kanshi ya zuba mata idanunshi dake cike da matsanancin damuwa ." "Ina neman alfarmar a wajenka a karo na biyu  " wata irin razana yayi yayinda zuciyarsa ta soma bugawa da karfi kamar zai fasa qirjinsa domin bai san wace irin alfarma zata sake nema a wajensa ba ,bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta da tsumammun idanunshi yana mai allah allah yaji abinda zata fad'a." "na gode maka da alfarmar da kayi min na farko na amincewa auren maryam da kayi alfarmar ta biyu ka taimakeni adamcy kayi min alkwarin bazaka sake kai kwalbar giya bakinka ba bare sigari " tayi maganar Kmr zata zubar da hawaye dan tuni kwayar idanunta sun canza kala ." Wani naunayen ajiyar zuciya da numfashi ya sauke atare dan bai d'auka abinda zai fito daga bakinta ba kenan, ya d'auka zatayi masa magana ne akan tarewar yarinyar "kayi dan Allah dani amadadin giyar da zaka yita sha kana buguwa gara ka rike addua adamcy ,jikinsa yayi sanyi da jin maganarta ya risinar da kanshi kasa batare daya bude bakinsa ba a ransa yace "wannan rayuwarta ce ,ciwona ne ". ta cigaba da kallonsa shi kuwa bai ce mata uffan ba dan baya son yayi mata aqawarin da bazai cika ba ,bugu da qari baya son a shiga rayuwarsa a barshi da damuwarsa kawai sannan abar shi ya sha giyarsa da sigarinsa son ransa domin a halin da yake ciki su kad'ai ne abinda suke rage masa rad'ad'in damuwarsa ." Kallonsa maryam ta cigaba da yi ko kifta idanunta bata són yi akanshi "kallonsa kad'ai ya isa ya harzikawa mutun brain dinsa ,namijin duniya ne ko daga yanayinsa ,wani murmushin farinciki na samun nasara ya subuce mata "duk Kinsa da aureta gashi dai allah ya bata sa'a a karshe ta zama mallakinsa na har abada, domin tasan muddin mami na numfashi a doron duniya bazata barshi ya wulakantata ba bare akai ga maganar saki atsakaninsu zasu rayu tare har karshen numfashinsu dan haka zata  iyawarta da komai ta makallakesa har ma ta zama wani sashin na rayuwarsa ." Duk da ba kulata yake ba bare kallota amman da kyar take iya control din kanta akanshi don kallonsa yana cikin abinda ke sata fita haiyacinta tama rasa a duniyar da take ,a duk lokacin da tayi saa ya kalleta kuwa hakan na matukar sata natsuwa ,ta lumshe idanunta acikin ranta tace "adamcy nah ni kad'ai ,komai naka yayi min ilarka dai baka son rainin da zafin zuciya uwa uba tsanar mutane na babu gaira babu dalili ." Kamar ance ya d'ago kanshi dake risine yaga idanunta akanshi ,a zaunen da yake ransa ya fara 'baci ,zuciyarsa ta dinga tafarfasa sakamakon kallon da take masa na kurrulla irin kallon daya fi tsana arayuwarsa ,numfashi ya sauke ahankali tare da sake kau da kanshi muryarsa a tsarke ya kiran sunan da yake kiran mahaifiyarsa dashi "sweetheart !"ya'akayi adamcy nan? "ta amsa cike da tsananin kulawa "Kece wa yarinyar nan ta bar d'akin nan" a d'an firgice mami tace "wace yarinyar kuma ?" Shiru yayi yana sake 'bata rai mami ta kalli gabadaya parlour'n babu kowa daga ita sai shi da maryam ne acikinsa "kenan dai maryam yake nufi ?"adamcy matarka ce fa ?"oh my god sweetheart ki kalli kiga irin kallon rainin hankalin da take min ." yayi mgnr a d'an tsawa ce mami ta waiga ta kalli maryam wacce tun soma maganarsa tayi saurin d'auke idanunta akanshi ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ." "Ba nasara akayi akaina ba ni naga damar amincewa aurenta dan naga sai wani kallon gani gani take min ,wallahi tun da wuri ki ja mata kunne kar taga an d'aura  min ita ta nemi ta dinga min kallon iskanci idan ma tana tunanin wani abu acikin ranta wallahi tayi maza ta cire  dan hakan ba abu ne mai sauki ba ." "Da me zan ji ?aurenta da aka min dole ,ko da kallon iskanci da take min ? amman barni da zazzafar qaddarar data rufta min shekaru goma sha .." yayi shiru yana sauke zazzafan numfashi ,ya gyara zamansa tare da kai hannuwansa duka ya rufe fuskarsa dashi yana jin kamar yayi kuka kafin daga bisani ya cigaba da sakin bakaken maganganu masu zafi da ta'ba zuciya duk magiyar da mami take masa akan yyi shiru bai yi ba har sai daya samu natsuwa sannan ya saurara inda ya kwanta akan kujera ya juyar  da kanshi gefe yana sauke numfashi ." mami ta kallesa na second biyar sannan ta juya ta kalli maryam dake tsaye gabadaya ta rasa me zata ce ."yayinda maryam Jiki a matukar sanyaye ta matsa daga kusa dasu tare da juya masu baya tana jin faduwar gaba mai tsananin , tsanarsa gareta yana matukar d'aga mata hankali sosai taji bacin rai ,taji kamar ta fice daga d'akin mummansa ganin yadda ya juya baya ko mami yaki kallo ." mami ta qara matsowa kusa dashi tace "Adamcy ka daina zafafa kiyayyar matarka a gaban idanunta saboda ban fidda rai wata rana shakuwa mai qarfi na iya shiga tsakaninku ba dan haka ka dinga qoqarin dannewa ka barwa zuciyarka please " tana gama fadar haka ta mike tsaye ta qarasa inda maryam take tsaye tare da riko hannunta suka fito daga d'akin." Suna fita mami ta soma qoqarin rarrashin maryam ,tayi saurin cewa mami "karki wani damu mami banji komai araina ba," idan da sabo na rigada na saba da halinsa fatana allah yasa aurenmu ya zame mana alkhairi arayuwarmu gabadaya."shiru tayi kafin ta cigaba da magana "mami ni dai ki qara tayamu da addua akan wacce kike mana duk da har yanzu yaya adam bai amince dani ba amman yau kawai naji wani sanyi da samun 'yanci a zuciyata ." Murmushi mami tayi dan tun tuni ta fahimci wani abu akan maryam din hakan kuma yayi mata dadi domin ko babu komai zatayi hakuri da duk wani wulakanci d'anta cike da farinciki tace"na gode sosai maryam in sha allahu zan cigaba da yi maku addua allah yayiwa rayuwar aurenku albarka allah ya azurtaku da samun zuria masu albarka ko ni yau zuciyata ta rage nauyi duk da rayuwar da adamcy ya d'auko ya rage kashi sabain na farincikina amman duk da haka naji zuciyata ta rage nauyi saboda nayi imani ko bayan raina zaki kula da rayuwar dan'uwanki ." "Maryam adamcy rayuwata ne Kiyi hakuri dashi , Kiyi hakuri da halinsa ki kular min dashi "in sha allahu mami zanyi iyakar qoqarina " na gode maryam allah yayi miki albarka "ameen na gode mami allah ya qara miki lafiya da nisan kwana mai amfani "Ameen Ameen mryam shiyasa nake qara sonki akwai ki da hakuri dasanin yakamata ."suka cigaba da takawa ahankali suna magana har suka sauko qasa fuskarsu d'auke da murmushin farinciki ." Bayan saukowar mami ta aika akira mata hisham dan tun safe yana bangaren baba babba tare dasu salim tana zaune a d'akinta yayi sallama sai data bashi izinin shigowa sannan ya turo kofar d'akin ya shiga kanshi a risine a kasa kallo d'aya zaka masa ka fahimci jikinsa a mace yake , hisham ya rusuna ya gaishe da mami cike da girmamawa ,ta amsa masa cike da kulawa tana nuna masa kan kujera amman yaki zama ya zauna akan daddumar daya gani a shimfide akan kafet." "Hisham ya akaji da taro ?kamar bazai amsa ba amman ya kasa ko babu komai mami tana da kima gareshi bazai ta'ba yi mata banza ba,dan haka ya bude bakinsa da kyar yace "alhamdulillah mami ya naku ?to Alhamdulillah hisham allah yayi maku albarka gabadayanku, allah kuma ya baku ikon cinye jarabawa rayuwar, kowani bawa rayuwarsa tattare take tafiya da jarabawa iri iri ." "Kayi hakuri akan sauyin daka samu ka dauki hakan a matsayin jarabawa da kuma qaddara, auren auta yana daga cikin qaddararka wanda baka isa ka goge faruwar hakan ba ,abinda nake son ka fahimta Idan allah bai nufeka da samun wani abu arayuwarka ba sai ka gode masa domin allah sonka yake kuma duk abinda allah ya qaddara shi zaka samu, abinda allah bai qaddara zaka sameshi ba duk yadda abun ya kusantoka at end of the day bazaka sameshi ba duk kuwa son da kake yiwa abun ." "Wannan kuma duk hukuncin ubangaji ne , idan da yau mun sanya hakan acikin zukantamu da zamuyi rayuwa cikin jin dadi cikin annashuwa batare da wata damuwa ba ,idan mun samu allah ne ,idan mun rasa allah ne" wama tasha una illa anyasha allahu rabbul alameen duk yadda kaso idan allah bai so ba bazai ta'ba yuwa ba ." "wannan hukunci ne na allah ,allah yasa hakan shine mafi alkairi wata killan ma idan ka samu auren nuzla arayuwarka ta zame maka maseefa da tashin hankalin da sai kayi nadama ,ta zama bala'i arayuwarka yanzu rashinta sai ya zame maka alkhairi arayuwarka kayi hakuri da sauyin da allah yayi maka da sannu zaka ga irin sakayya da allah zai maka domin duk wanda ya yarda da allah allah zai isar masa ." "idan kuma akwai alkhairi a tsakaninka da nuzla sai kaga anan gaba ka qara daita wannan duk kadan ne daga hukuncin ubangiji fatanmu allah ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi arayuwarmu kar allah ya barmu da zabinmu "duk wannan maganar da mami take kanshi na kasa ya kasa d'ago kanshi har sai data dasa aya ta hanyar saka masa albarka sannan ya d'ago yayi mata godiya ya mike a natse ya fice daga gidan gabadaya." Karfe biyar daidai motoci guda goma na alfarma sukai parking a kofar gidan mami domin d'aukar nana hauwa ,mutanen da suka zo gabadaya sun kasance kawaye ne ga hajiya zulfa'u ,kowacce cikin shiga ta alfarma domin kallo daya zaka masu ka fahimci kudi ya zauna ajikinsu shigar kowace tana wane na wane , sai dai mami tace hisham take son yazo ya d'auke amaryarsa da kanshi lokacin da sakon ya samesa yaji abun wani iri ranshi ya 'baci matuqa ." "duk kawayen mumynsa da abokansa da suka tafi d'aukota basuyi ba sai shi da kanshi yaje kamar wata zinariya ?yayi wa kanshi tmbyr yana jan tsaki bana jin zan iya zuwa dan nasan nauyi kawai mami take són d'aura min ya lalubo wayarsa yana qoqarin kashewa kiran mami ya shigo "ya salam !"ya furta a fili yana mai dafe kanshi kiranta né yayita shigowa har sai daya d'auka ,yana d'auka tace "hisham d'ana kazo ka d'auki matarka " babu yadda ya iya dole ya amsa da "tô mami ganinan zuwa"ransa a matukar 'bace ya tashi ya shirya cikin wani d'anyen voyal fari sol ya shiga d'akin hjy zulfa'u ya fad'a mata inda zashi sannan ya fito ya kamo hanyar zuwa abdullahi estate." zaune nana hauwa'u take agaban mahaifiyarta sanye da fararen kaya tun daga kan takalmi mayafi pos din dake rike a hannunta agogo komai na jikinta fari ne sol jikinta lullube cikin mayafi , shape din fuskarta kawai ake iya gani ,wani irin qamshin jikinta Ke fitarwa mai sanyin dadi da sanya natsuwa tare da kwantar da hanakali yayinda yan'uwata mata ke zaune akan kujera kowace cikin shiga iri d'aya ." nasiha mai matukar ratsa jiki mami take mata tana tunatar daita hakin daya rataya a wuyanta cike da gamsuwa nana hauwa take gyada mata kai tana zubar da hawaye adaidai lokacin ATA ya shigo d'akin sakamakon kiransa da mami tayi bai qarasa inda suke ba ya samu waje ya tsaya ya jingina bayansa da bango d'akin ya rungume hannuwansa duka a qirjinsa yana kallon nana hauwa'u dake zubar da hawaye yayinda aunty shahida ta mike daga mazauninta tana  faman rarrashinta tana goge mata hawaye ." Ahankali hisham ya turo kofar dakin ya shigo ya tsaya yana jin wani iri a gabadaya ilahirin ajikinsa kafafuwansa sukai masa nauyi ya kalli inda ATA yake tsaye rabonshi da ganinsa yau tsawon kwana uku kenan ,numfashi ya sauke yana qoqarin danne abinda yaji yana taso masa kafin ahankali aunty shahida ta qaraso inda yake ta riko hannunsa ta zaunar dashi kusa da nana hauwa'u agaban mami ." "hisham ga amanar nana hauwa'u nan na danqata a hannunka ba dan ina tunanin zaka cutar daita yasa na damka maka amanarta ba sai dan yanayin rayuwa da kuma yadda aurenku ya kasance, aure ne da babu wanda yayi tsamanin faruwarsa amman dake haka allah ya qaddara babu tsimi babu dabara sai ya kasance ,kema nana hauwa'u ga amanar hisham d'ana na damka miki, kisan mahimanci amana ko ban gaya miki ba aure amana ce atsakanin ma'aurata kuma duk wanda yaci amanar dan'uwansa allah bazai barshi ba." " na tabbatar d'ana hisham bashi da matsala idan naga wata matsala daga gurin ne zaki  kuma ki kuka da kanki dan bazan ta'ba d'aga miki kafa ba ko baki uzuri ba dan haka ki kiyaye "aunty shahida dake durkushe kusa dasu tace "hisham ga amanar auta nan allah ya tayaka riko "aunty khadija da zabiba ma dai abinda suka fad'a kenan "shi dai ya shiga ukunsa yanzu mumynsa ta gama damka masa amanarta kafin ya fito tana jadda masa ko rama taga nana hauwa'u tayi sai ya hadu da mummunar fushinta ,yanzu kuma ga mami dasu aunty shahida shi ya suke son yayi da rayuwarsa ?" shifa baya jin zai iya rike wata amana amman babu yadda ya iya muryarsa a sanyaye yace "in sha allahu mami zan kiyaye allah ya qara girma ya qara lafiya" Ameen Ameen hisham allah yayi maku albarka ." Banda kuka babu abinda nana hauwa'u Ke faman yi wanda hakan Ke sake d'aga hankalin ata kwata kwata irin wannan rayuwar bata burgeshi zaa akai mutun gidan miji amman yana kuka irin haka kamar zaa kai shi kabari ,a tunaninsa wannan zalinci ne sam bai kamata a had'a irin wannan auren ba gara idan nmj ke so komai na zuwa da sauki canza rayuwar mace ba abu bane mai wahala ga d'a nmj amamn canza raayin nmj abune mai bala'i wahala ahankali yaga an mikar da nana hauwa'u tsaye shima hisham ya mike suka jero." Kamar ance nana hauwa'u ta d'aga kanta idanunta ya sauka akanshi tsaye cike da sanyin jiki ta soma tahowa zuwa inda yake tsaye yana ganin haka ya kau da kanshi gefe yana sauke numfashi har suka qaraso inda yake bai waigo ba ,nana hauwa'u ta kasa wucesa kowa yayi mata fatan alkhairi tare da damka amanarta a hannun hisham amman banda shi tasan halinsa shirunsa yana nufin abubuwa dayawa a gareta dan haka ahankali ta dawo ta duka agabansa tana masa sallama sautin kukanta na tashi." jikinsa yayi sanyi gayayyun idanunshi ya ware akanta still tana durkushe tana kuka yayinda tafin hannunta ke kife a saman kafarsa wani abu ya had'iye mai d'aci daya tsaya masa a makoshi bai ta'ba sanin cewar yana qaunar qaramar kanwarsa ba sai da aka samu wannan canjin ,babu yadda zai yi daita né domin itace da kanta ta  amince, da tursasata akayi sai dai ayi bala'i da zaayi amman bazai yarda ba ,kukanta ya dinga ta'ba zuciyarsa bai san lokacin da ya kira sunanta ba "nana hauwa'u!" Kanta ta d'ago wanda ke cike da ruwan hawaye ta zubawa yayanta tattausan murmushi ya sakar mata kafin ya mika mata hannunsa alamar ta kama ta mike tsaye ,da wani irin sauri ta kama hannunsa tana ganin kamar a mafarki yake mata murmushi "ina mafarkine ko kuwa ? tayi maganar a fili tana kuka " menene auta ?murmushinka yaya wannan shine karo na farko danaga irin wannan murmushin akan fuskarka" ya qarasa mikar daita tsaye ya kwantar daita akafad'arsa yana shafa bayanta " kiyi hakuri kukan ya isa haka auta "lafewa tayi sosai ajikinsa Kmr wata baby "yaya ka yafe min ban bi umarninka ba "karki damu dani ki kula da kanki ". shi kuwa hisham zuba masu ido yayi yana jin wani zallar 'bacin rai na ratsashi "ki daina kuka auta idan kinga da matsala ki kirani babu wani uzuri da zanwa hisham shima kuma yasan halina bazai yi any thing nonsense ba "wani irin kallo hisham din yayi masa kamar yace masa "me zai yi idan aka samu matsalar sai ya duba idanun mutane dake wajen mami bazata ji dadi ba hka sauran yanuwata da suke da kima a idanunshi ,sannna idan ya fad'a haka mumynsa bazata d'aga masa kafa ba idan taji labari ." ATA ya kamo hannunta ya saka acikin na hisham ya damke waje d'aya "ga amanar auta please ka kular min daita fiyye da yadda zaka kula da kanka" shiru hisham yayi masa yaki cewa komai, Jiki babu kwari suka fice daga d'akin, aunty shahida da aunty Khadeeyja da zabiba na biye dasu suna qarasowa parlour'n hisham ya zare hannunsa cikin nata yayi gaba shiru tayi kawai tana duban bayansa kawayen hajiya zulfa'u mutun uku da suka tsaya suka mike tsaye maryam ta qaraso ta rungume nana hauwa'u tana cewa "shikenan sister zaki tafi ki barni" ta qarasa mgnr tana fashewa da kuka "ai baku rabu ba mrym tunda duk mazajenku 'yan gidan nan ne ,kusan kullum suna nan inji cewar hjy nurriya." Da kyar aka 'bam'bare maryam ajikin nana hauwa'u hjy sumayya ta riko hannunta suka fito zuwa haraban gidan ta bud'e mata bayan mota ta shiga ta zauna ta rufe murfin ,yayinda hisham ke qoqarin qarasawa wajen abokansa hjy summaya ta kwalla masa kira ya dawo ya tsaya gabanta "shiga"mumy kuje kawai daita zan biyoku "aa hisham ba'a yin haka shiga kawai sai wani daga cikin abokanka yajaku "kai !"ya furta a fili sannan ya shiga ya zauna ko kallon inda take bai yi ba ." Su biyu ne zaune abayan motar sai salim a mazaunin direba hawaye yaki tsayawa a idanun nana hauwa'u,wani sabon kuka ne ya kufce mata sanda suka fito daga estate dinsu suka hau titi ,gefe tayi da kanta tana damke hannuwanta cikin juna "salim kasan wani abu ?salim dake tuki yace "aa sai ka fada "wai ATA ke bani amana" salim naji haka ya manna ipod a kunnensa ya cigaba da tuki "aikin banza sai kace shi ya iya rike amanar' yar wasu da yake son shi a rike masa amanar kanwa, mutun sai shegen son kan tsiya sai kazo kasani dole na rike maka amana." kunnuwan nana hauwa'u ya jiyo mata maganarsa acan kasan makoshi kamar ta juyo inda yake sai kuma ta fasa ta cigaba da kallon titi ya sake motsa bakinsa kmar zai yi magan sai kuma yayi shiru ya ciro wayarsa dake ringing yanayin yadda ya amsa ta fahimci yaya amar ne "kaga amar dan allah ku barni da damuwata kowa amana amana !! wai me kuke nufi  dani ne ?" me yasa bakuje kuncewa ATA ya rike amanar maryma ba sai ni zaku dameni da wata amana saboda kun rainani ?"dan girman allah ku barni na huta naji da damuwata no no!! bazan fa gane ba wayar salim ce ta d'auki qara ya danna iPod din dake makale da kunneshi yana cewa "okay mumy an gama har ya gama wayar musayar magana hisham yake akarshe dai ya kashe yana furta aikin banza kawai ." Tafiyar mintuna ta kawosu ikeja gra atare suka qaraso gbdynsu har abokan ango sanda salim yayi parking a haraban gidan hajiya sumayya tayi parking a haraban gidan, hisham ne ya fara fitowa yayi gaba ,jiki a matukar sanyaye nana hauwa'u ta fito hjy sumayya ta qarasa da sauri ta riko hannunta cikin nata suka biyo hisham abaya cikin natsuwa har zuwa bakin kofar shiga parlour'n hajiya zulfa'u tana zaune cikin kawayenta ." wata kawarta marry wacce ta kasance yoroba ta mike da sauri hannunta rike da cup wanda Ke cike da ruwa ta tsaida nana hauwa'u abakin kofar shigowa ta zuba mata ruwan akafafunta tana cewa "barkanki da shigowa gidan d'ana yadda kika shigo cikin koshin lafiya haka zaki qare rayuwarki cikin koshin lafiya ,gidan nan bazai miki zafi ajiki ba ,gidan nan zai zame miki tamkar ruwan sanyi ne yadda muka ga wannan ranar allah ya nuna mana sabuwar shekara munzo suna haka akarshe ta rungumeta ajikinta ." ta shigo daita parlour'n kai tsaye marry gaban hajiya zulfa'u ta nufa da nana hauwa'u ta duka a gabanta hjy zulfa'u ta kai hannunta ta d'agota ta zaunar daita a gefenta kamar yadda hisham ke zaune abokansa gbdy suka shigo nasiha tayi masu mai ratsa jiki abokan ango na jiran abasu amarya su wuce daita gidanta mumy tace su wuce sai tayi sati anan gabadaya sukai mata sallama suka kama gabansu ahankali ta riko hannun nana hauwa'u ta nufi dakin dake kusa da nata suna shiga ta zaunar daita a bakin gado tare da cewa" ina zuwa ."!bata jima ba ta dawo hannunta rike da cup ta mika mata "ki shanye!" babu mutsu ta karba wani abu ta gani kamar zuba ta kafa kanta ta shanye tana yatsina fuska "akwai d'aci né ?"ba sosai ba "!ta bata amsa da hakan "okay  bari akawo miki abinci nasan da wahala idan kinci wani abu ta juya ta fita ." Ahankali ATA ya juya zai bar d'akin mami aunty shahida da aunty khadija suka dawo d'akin "yauwa a she ma ya nan mu koma magana zamuyi da kai "bai ce masu uffan ba ya koma ya tsaya tare da tura duka hannuwansa acikin aljihun wondonsa ,aunty khadija da aunty shahida suka zuba masa ido suna tunanin ta inda zasu fara masa magana ahankali ya lumshe tsumammun idanunshi na second biyu sannan ya budesu fes akansu tare da tsura masu ido alamun yana sauraronsu " . "adam !" aunty shahida ta kira sunansa bai amsa ba illa tsura mata idanunshi da yayi "me yasa ka zabi ka 'bata rayuwarka akan auren nan ?giya fa adam meye hadinka da shan giya saboda allah ? kai babu wanda ya isa da kai kana ganin mahaifiyarmu zata zaba maka abinda zai zame maka matsala né arayuwarka?mami kullum só take taga cigabanmu amman kai da yake mara mutunci né kullum qoqarin kake ka 'ba.""dan allah malama ya isa haka nasan da wannan nasan tana son cigabanmu amman me zanyi  da wuce hkn?yayi shiru yana fesar da iska zata zauna yace  "meye next dan ina son naje na  huta ya katseta ta hanyar fad'ar haka numfashi ta sauke kawai  batayi mamakin abinda ya fad'a ba dan tasan halinsa zai iya ma fadar abinda yafi haka ." Aunty khadija tace "dan allah adam karka qara shan gi..."nifa bazan daina shan giya ba kawai ku barni da rayuwata tunda ni kad'ai damuwarta ta shafa abarni da damuwata kawai ,fuskarsa a daure ya cigaba da magana "wai me yasa kuke manta wani bazai iya ji da ciwon wani ba ?"wannan ciwona ne ni kad'ai abarni kawai naji da ciwona yana gama fadar haka ya juya a fusace ya bar d'akin yana fesar da numfashi."mami ta girgiza kai Kawai cike da taikaci take masa addua. A parlour'n mami na biyu suka kusan cin karo da maryam da sauri taja baya gabanta yayi wani irin mummunar faduwa sannan ta d'ago ta saci kallonsa adaidai lokacin daya d'ago idanunshi suka tsarke cikin nata wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki wanda babu tantama na tsoro da qaunar da take masa ne , wani irin mugun kallo yayi mata mai firgitarwa sannan yaja tsaki yana furta" nonsense"! a fili ya wuceta jiki a sanyaye tabi bayansa da kallo "ya rabbi me zanwa wannan bawa naka ya soni ?rashin qaunarsa gareni yana damuna ya allah ka nuna min hanyar da zanbi ya soni ." Kai tsaye samansa ya hau ranar yau din ata jinsa yake dabam ,jinsa yake kamar an sauyashi daga adam din daya san kanshi zuwa wani adam din dabam ,wani irin bakinciki ke ratsa shi wanda ga duk wanda yasan shi yasan aininhin zahirin fuskarshi zai ga alamun komai ya qara sauyawa agaresa, domin sauyawar yafi na da muni fuskar nan tashi sam babu rahma attare daita ta dawo tamkr ta kumurcin macijin ." Har karfe bakwai sauran wasu mintuna nana hauwa'u na zaune a bakin gado ta zabga tagumi sosai tayi shiru tayi zurfi cikin tunani jefa jefa tana zubar da ruwan hawaye da kallon kular abincin daaka kawo mata da ko bud'esa batayi ba ,tun baaje koina ba ta fara kewar gida wani irin ta dinga ji a ilahirin ajikinta tasan adaidai wannan lokacin da take cikin kad'aici da auren soyayya tayi da dole tasan mijinta yana kusa daita yana rarrashinta bazai barta ta kasance ita kad'ai ba ,amman da yake bai sonta ya bawa banza ajiyarta yayi zamansa a parlour'n ."karfe bakwai da minti goma ta mike tsaye ta shiga bathroom din dake manne da d'akin ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallar magrib tayi adduointa ta sake komawa ta zauan kamar yadda take a d'azu tana cigaba da zubar da hawaye ." hajiya zulfa'u ta turo kofar dakin ta shigo bakinta dauke da sallama yyinda hannunta ke rike da wani cup ba irin na d'azu ba,nana hauwa'u tayi saurin goge hawayenta ta bud'e baki da kyar ta amsa mata sallamar da tayi "har yanzu kina nan a zaune diyata ?"ki rage kayan jikinki mana ki sha iska."nana hauwa'u tayi murmushi kawai d'an bata da wannan kwarin gwiwar bare ta samu karfin zuciyarta aikata haka , burinta a yanzu bai wuce taga yaya hisham ya saki fuskarsa kamar yadda yake mata ada kafin ta zama mata agaresa ba ." tana buqatar sakin fuskarsa ko kadan ne daga garesa ,ahankali ta zare mayafin jikinta ta ajiye cike da jin kunyar hjy zulfa'u,cup din hannunta ta miko mata tana cewa "ungo ki shaye "a natse tasanya hannuta ta karba cike da girmamawa ta kafa kai ta shanye tana yatsina fuska dan kamar irin na d'azu ne kawai kalarsu ne ba iri daya ba ta mika mata cup tana cewa "na gode mumy allah ya qara girma "dan ko bata fad'a mata ba ta fahimci irin maganin da take bata "karki qara yi min godiya dan na baki abu ni fa mahaifiya ce agareki ,ki saki jikinki dani kinji ki cin abinci dana sa akawo miki ?tayi shiru tana tunanin amsar da zata bata kafin tayi mgn har hjy zulfa'u ta qarasa ta bud'e kula abincin yana nan Kmr yadda aka kawo mata "ya baki ci abinci ba ?ki cire komai aranki kice abinci kinji "nana hauwa ta gyad'a mata kai alamun taji " idan kinyi wanka ga kaya can ki canza "tana gm fad'ar hk ta juya ta fice daga dakin ."   Wani abinci hjy zulfa'u tasa aka sake kawo mata wace ta kawo abinci na fita ta dawo dakin wanda kafin ta fita a dakin sai data lallabata dan dole ta fara cin abinci bata wani ci daywa ba ta mike ta shiga bathroom tayi wanka da alwala ta fito ta sauya kaya tayi sallah ishai byn ta idar ta kwanta a gefen gado tana kukan , ita kanta kukan ya isheta haka amman da zarar ta tuna yanayin yaya hisham sai kukan ya sake dawo mata ." hisham daya shigo dakin yaja tsaki karo na farko da yaji ya tsani kukan da take duk da yasanta tun tashinta yasan yadda mami take ji daita ya santa da saurin kuka but ba irin haka ba ,tasan bata són shi me yasa ta amince aka daura masu aure ?dan yasan itama raahin sonahi né yake sata kuka, lalle ko akwai aiki dan wannan na cikin dalilin da zai sa yaji ya qara tsanarta shi kuka idan bana nuzla bane ai aikin banza né a wajensa ,nuzla itace macen da zai iya jurar komai nata tasoshi ko karta só shi he does care wannan alqawarinsa ne ko a wani hali take zai jure matukar akanta ne saboda yana matukar sonta bai zauna ba ya juya ya fice daga dakin daman mumynsa ce ta tursasa masa shigowa ." ****** Da misalin karfe goma na dare ranar lahadi maryama na zaune a d'akinta akan kujerar roba tana zane domin yanzu yana cikin abinda ya fara rage mata damuwa da ta zame mata jiki ,yusif kuwa tuni ta fidda shi aranta da dawowarsa da rashinsa duk daya ne a wajenta ,shi kuwa baba gali tun sanda yayi mata maganar sauyi akan yusif taji duk duniya babu wanda ta tsana kamar shi hatta gaisuwar da take shiga bangaresa ta gaishesa ta daina zuwa ,ko ganinsa tayi a waje gaisuwar sama sama take masa tunda ta rigada ta tabbatarwa kanta baya qaunarta ,ta kuma tabbatarwa kanta baba gali makiyinta ne da keda fuska biyu har ma gara aunty salma dashi ita daman can bata ta'ba nuna tana qaunarsu ba, amman shi baba gali wani lokaci yana nuna yana sonsu ,akan ya'yansa  ne ma wani lokaci suke fuskantar tsana shi kuma wannan daman ta ajiyesa a matsayin uban wani da ya'yan wani akwai bambamci ." Ta numfasa sannan ta dakata da abinda take tare da tura bakin pencil a bakinta tana tunani "life goes on maryama karki qara yarda ko amincewa wani d'a nmj arayuwarki da sunan soyayya, ba lalle sai da aure zaki yi rayuwa ba ,ko da aure ko babu zaki rayu dan haka ki natsu ki qara kwantar da hankalinki ki qare bautar kasa ki samu aiki mai kyau wanda zaki kula da kaninki da mahaifiyarki ki ajiye wani batu na aure dan muddin aunty salma aunty hassana baba gali da sauran yanuwan mahaifinki  na raye bazasu bari kiyi aure ba "na karbi qaddarata allah ka bani ikon cin jarabawa sanyayyen numfashi ta sauke ta cigaba da abinda take." Washegari ya kama monday tun da asuba ta tashi tayi sallah bata koma ba ta shiga ayyukanta data saba ,bayan ta gama tayi wanka tayi shirin na fita aiki ta fito parlour'n alokacin  bakwai da wasu yan mintuna , ta isa inda ta hango mahaifiyarta zaune tana jiran fitowarta ta zauna kusa daita tana gaisheta "aunty ina kwana ?kin tashi lafiya sarauniyata?alhamdullai qaunata ,aunty ta tura mata kofin koko da kosai gabanta ahankali ta soma sha i har ta kammala ta dauki kofi da faranti data ci kosai ta kai shi kitchen zata wanke aunty tace "barshi ki kama hanya ki wuce lokaci ya fara tafiya tayi mata sallama ta fito ta shiga side din umma suka gaisa sama sama tayi mata addua ta fito ." Abakin kofar fita gidan taga baba gali zaune yana sauraron radio ta gaishesa cikin murya mai jin nauyinta ya amsa ta cigaba da tafiya ta jiyo sautin muryarsa yana kiranta ta juyo tare da amsawa ta nufi inda yake zaune yana sauraron radio ta durkusa ta sake gaishesa akaro na biyu ya kalleta sosai sai daya jinjina kai sannan yace "maryama saboda na yanke miki hukunci da abinda yafi dacewa dake shine kike nuna halin damuwa saboda bani na haifeki ba ?". Ta kallesa kawai saboda ita bata san abinda tayi da zai nuna baiyyanar da damuwarta ba maganar bashi ya haifeta ba ai kowa yasan wannan domin da shi ya haifeta bazai mata bakinciki ba amman sai ta kawar da wannan tace "baba ni ba fushi nike da hukuncinka ba sannan banga abinda zai sakani damuwa ba saboda nayi imani rabona bazai taba wuce ni ba matukar yusif mijina ne babu tsumi babu dabara zai aureni idan kuma ba mijina bane nawa mijin zai zo shi kuma ya auri matarsa bare ma ni tuni na manta da babinsa yanzu kai ya kamata kasan abinda zaka fadawa mahaifinsa akan alkwarin da kayi masa ."ya dan gyara zama "wani alkawarin? Tayi shirin domin bazata iya fad'a ba tunda shine yayi alkwarin tuna masa din me zatayi ?duk abinda kike nufi maryama ba abinda zai kawo dakushewar soyayyarki da alhj alqasim abinda ya sanar dake na tabbatar dani ya fara zance amman idan kika duba kunyar mahaifin mlm yahuza babban mutun ne acikin unguwar nan ba qaramin kuskure nayi ba wajen saurin amincewa buqatar alhj alqasim daya zo daita tsakanin ke da sauran yammatan gidan nan kinga shi mlm yahuza Ke yagani yace yana so dan haka Ke din ce wacce yake so ba shukura ba daace zai karbi shukura amadadinki dana bashi ita Ke kuma kin auri yusif ." Shi kuma nasan alhj alqasim zai karbi shukura ko sakina adalilin rashinki tun da daman shi zuria gidan nan yake bukata dan haka ki natsu ki kwantar da hankalinki wannan ba wata matsala bace tunda ni zan tunkaresa da maganar komai ta sunkuyar da kanta kawai tana jinsa tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ita yanzu bata jin mlm yahuza acikin ranta tunda tagansa da shukura har abada babu ita babu shi ko mutuwa zaiyi akanta wallahi bazata auresa ba sannan wannan magana ce kawai baba gali yake batun soyayya tsakanin mlm yahuza da shukura sunyi kawai dai anje an warware aiki ne komai dake faruwa da sanin aunty salma ita Ke shirya komai ." Sarai baba gali ya karanceta dan hk muryar a fusace ya cigaba da mgn "tunda naga kamar kin kamu da soyayyar yusin din allah ya baku zaman lafiya da yusif ita kuma shukura ko sakina allah ya kawo masu nasu rabon "uhm kawai ta furta dan tasan ya fad'a haka ne ba har acikin ranshi ba ,ta dago ta girgiza kai cikin takaici irin rayuwarsu "ni baba bana ja da maganarka a yau ida ka shirya aura da kowacce daga cikinsu ga yusif kayi ." ya sauke ajiyar zuciya yana cewa tô shikenan na gode na tabbatar daman bazaki aikata abinda zai jawo min zagi ba su yusif din zasu zo karshen satin nan dan mun gama magana da mahaifinsa cewar shukura zai aura shima yusif din ya amince da hakan dan haka ko yau mlm yahuza ya kiraki ki amshesa kije ." Nan taji gabanta ya fadi jin wai abba ya amince da kuma amincewar yusif daman yusif ba soyayyar gsky yake mata ba tabbas duk maza mayaudara ne babu nmj dan goyo kalamansu daya haka salon yausararsu daya haka ta mike tsaye jiki babu kwari ga lokacinta daya bata mata ga bakinciki daya kunsa mata abun yayi mata yawa ,bakinta na rawa tace "baba Allah ya tabbatar da alkhairi sai dai ka fadawa mlm yahuza ya nemi matarsa a gaba dan ni a halin yanzu gbdy babu mgnr aure a gabana bazan yi aure ba har karshen rayuwata tana gama fadar haka ta soma daga kafafunta bayanta yabi da kallo yana kwabe baki alamun matsalarta." Yau sunyi very busy a wajen aiki dan daga maakatarsu kwasasur akayi zuwa ma'aikatan man petir  dake apapa saboda kwarewar wasu daga cikinsu ranar haka tayi aiki cikin sanyin jiki da wahala ita ba soyayyar yusif bace damuwarta tunda daman bata fara son shi ba mamakin baba gali ne ya addabeta tmbyr duniya subai'a tayi mata tace babu komai ."bayan an tashi daga aiki ta fito bakin get ta tsaya tana jiran fitowar subai'a su wuce gida ,ta tura hannunta cikin jakarta zata ciro nikaf dinta adaidai lokacin wata mota reven rover ta sanyo kai zata shiga cikin ma'aikatan ,gani tayi motar taja ta tsaya motar bata shiga ciki ba haka zalika bata juya ba mutumin dake zaune a bayan motar taga ya fito jikinsa sanye da suit bakake." da wani irin sauri ta dan matsa gefe ,shi kuwa fuskarta yake kallo daga inda yake tsaye cike da faduwar gaba tabbas wannan fuskar idan ba mafarki yake ba fuskar da mai gidansa yake gani ce acikin duniyar mafarkinsa ."duk da fuskar zane ce  ,amman ya rantse da wanda ke busa masa numfashi itace wace zuciyar mai gidansa take muradi kasancewa tare daita, gbdy idanunwansa sun rufe akanta baya ganin tarin jama'ar dake gurin burinsa ya isa gareta tana qoqarin sanya nikaf taji ya rike mata hannu jikinsa na wani irin kirrrma kafin tayi wani abu taga ya janyo hannunta da sauri zuwa cikin ma'aikatan qoqarin fixge hannunta take cikin tsananin tashin hankali amman yaki sakar mata hannu ." Ana zan dataka sai a book 2 in sha allahu wadan da suke bibiyarmu a arewabooks inshaallahu zasu cigaba da ganin update dinmu kmar yadd muka saba ." Alhamdulillah Mmn sudais