GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 1 Posted by ANaM Dorayi on 07:51 PM, 29-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura GANGAR JIKINSA NA AURA JAMILA UMAR TANKO {JUT} ⃣Wata kwarababbiyar mota kirar bus mai kararfatattakekkiyar salansa ce ta tsaya a bakin get dinmakarantar 'yan mata ta gwamnatin tarayya dakegarin Kazaure, wato F.G.G.C. Kazaure. Tana tsayawakondastan motar ya ja kofar ya bude "Barararaa"saboda kwankwatsewar da kofar motar ta yi sakamakon cin ruwa da gafje-gafje da tsabar tsufa.Wani dattijo mai kimanin shekaru saba'in da doriyane ya fito, da wata *yar yarinya tana biye dashiwacce shekarunta basu wuce shekaru goma shadaya ba, Bayan sun furfito kondastan motar yazagaya baya wato but ya dauko wata katuwar akwatin karfe irin ta *yan makarantar wacce akadafka sunan mai akwatin garza-garza da fenti bakiHANNE HABU IMAMU. Ya ajiye gefe ya sake janyowata karamar katifa wacce take daure ya doraakan akwatin, sannan ya dauko wani bokitin karfesabo dal yana sheki shima an fenteshi da sunan mai bokitin wato HANNE HABU IMAMU. Daga karsheya mayar da kofar but din ya rufe ya juyo ya kallidattijon wato Malam Habu ya ce "Baba baka fa cikamana kudin motarmu bafa, gashi har kun sauka"Malam Habu ya sake marairaicewa ya ce "Dana daAllah fa nake hadaka kuyi hakuri kudin da yayi saura a aljihuna ko gida bazai mayar dani ba, sai nanemi ciko kayi hakuri dan Allah, dan haka nemanace ta zauna a maleji yanzu baza ka tausayawatsoho ba, karbi arba'in din?" Kondasta ya sakefusata ya ce "Dalla Baba kana bata mana lokaci gafasinjoji har sun fara tsaki sun kagu suma a kaisu inda zasu. Ka zauna kana mana magiya tun dazumuma fa ba'a bati muke shan man motar da mukejigilar nan bafa, da kasan kudin motar taka bai cikaba me yasa ka hau? Har zaka ce wai yarinyar amaleji ta zauna, maleji ba cikin mota bane? Bakasan har a sittin muke daukar na maleji ba daga inda muka dauko ku zuwa nan nayi maka ragi nace kakawo hamsin dinma gashi kaki biya sai wataarba'in ka bani, kai wallahi Baba saika ciko managomarmu kaji ko? Direban motar dake zaune awajen tuki wanda yake jin duk abinda suke yi, saiyanzu ya waigo inda suke yayi magana ya ce "K.b wai yane? K.b ya ce "Har yanzu wannan tsohon baidaina magiya ba wai shi ayi masa ragin goma kudinyarinyar nan data zauna a maleji, Hamsin nace yabiya, ya wani bani arba'in. Kuma ma dan raininhankali harda cewa kudin aljihunsa bazai mayardashi gida ba, wato yana da kudin, cikawa ne bazai yi ba.din aljihunsa bazai mayar dashi gida ba, watoyana da kudin, cikawa ne bazai yi ba. Malam Habuya danji dadi ganin direban yayi magana ko zaice abar masa amma sai yaji kalamansa sabanintunaninsa gara ma abinda kondastan ya fada masa,cewa yayi in har bazai biya ta dadin rai ba to zasu farka aljihunsa su dauki gomarsu, Malam Habu yarike baki don mamakin irin wannan rashinmutunci, can ya nisa ya ce "Allah Ya kyauta, bari nabaku kudinku abin duk bai kai ga haka ba, yasahannu a alhihunsa na dama ya dauko watacukurkudaddiyar naira biyar ya sake saka hannu a aljihunsa na bangaren hagu ya dauko gudar nairaashirin da kwandaloli guda biyar, ya hadakwandalolin nan guda biyar da cukurkudaddiyarnaira biyar din nan ya mikawa kondosta ya ce"Gashi dana Allah Ya kiyaye. Ba kunya ba tausayintsohon nan yasa hannu ya karbe yana gunani "Daman kana dashi ka tsaya kana bata mana lokaciduk fasinjoji sun kagu, direba ya juyo ya ce "YayaK.b ya baka, sun cika? K.b ya ce "Eh sun cika jamujeJ.J.C. Malam Habu da *yarsa Hanne suka bi motar dakallo har ta hau titi ta kure sannan hankalinsu yadawo kan kayansu. Malam Habu ya kalli *yarsa Hanne wacce hawaye ya gauraye idanuwanta dakumatunta, abin ya bashi mamaki ganin Hanne nakuka alhali kuma ita take son karatu take murna dazasu taho, ya sake juyowa sosai ya kalleta yagahawaye ne ke zubowa daga idanuwanta dayanabin daya, ya ce "*Yar Baba, kukan me kike yi? Karki cemin yanzu bakya son makaranta bayan keaka kira fadar mai gari aka tambayeki kika ce kinaso. Ba'a son raina ba nima na kawo ki makarantarnan ke kika amsa musu. Shine kuma yanzu kikekuka? Idan kinsan bakya so to ni a wajena tafinono fari sai mu juya kafin mu shiga ciki. Kansila da mai gari su suka tilastamin in kawo ki amma badanhaka ba nima bazan rabu dake ba na kawo ki nanuwa duniya, babu wanda kika sani. Hanne tagirgiza kai cikin shesshekar kuka ta ce "Baba bamakarantar bace bana so, rashin kunyar da masumotar can suke yi maka shine ya sani kuka. Malam Habu yaji hawaye ya cika masa ido amma sai yajure yayi murmushin karfin hali ya ce "Allah Sarki*yar Baba, babu komai duniya ce. Duk wanda yagagirman tsohon wani, za'a ga girman nasa. Hakakuma duk wanda ya raina tsohon wani sai an rainanasa, zamani ne ya canja babu sanin girman Allah, ko an hada mutum da Allah kamar an hadashi dasa'ansa, wani cewa zaiyi daina hadani da Allahkarka cuceni Wa'iyazubillah. Ya ci gaba da cewa"goge hawayenki 'yar Baba kizo in dora mikiakwatin mu shiga ciki kada dare yayi min kinga harla'asar tayi. Tasa gefen gyalen da taci damara dashi ta goge idanuwanta kana ta matso ya ciccibiakwatin karfen nan ya dora mata a kai shi kuma yadauki bokiti da katifa a daya hannun sa'annansuka juya suka doshi cikin babbar kofar shigamakarantar, yaci gaba da yi mata nasihohi masuratsa jiki yana nuna mata wannan abin da aka yi masa a gabanta ya zama darasi a wajenta duklalacewar tsoho koma ba tsoho bane na gaba da itakada tayi masa fitsara. Ta zamana ko a ina takekuma kome ta zama ta girmama na gaba da ita.Ta zama mai taimakawa mabukata, kasancewartasan talauci ta kuma dandanashi tana kandandanashi. Masu gadi uku suka iske a bakin kofarshiga cikin makarantar, suna zazzaune, MalamHabu yayi musu sallama gami da mimmika musuhannu, Hanne ma ta duka ta gaishesu, bayan sun amsa, Malam Habu ya ce "Yarinya na kawomakarantar nan, ta ina zanbi mu shiga ciki? Dayadaga cikinsu ya ce "Mikewa zakuyi sosai zaku tararda ofishin Malamai dana shugaban makarantar.Malam Habu yayi godiya suka wuce, har sun danyonisa suka ji masu gadin nan sun kwalla musu kira bayan sun dawo, sai daya daga cikinsu ya kallesusama da kasa ya ce "Dan Allah Malam muna datambaya sai bayan da ku ka wuce tambayar ta fadomana. Malam Habu ya gyara kayan dake hannunsagami da yin murmushi ya ce "To Allah Yasa na sani.Ya ce "Wai shin me kake tambaya ne? *Yar makaranta ka kawo daliba ko kuma mai aiki kakawo gidan Malamai a nuna maka gidan Malamai(staff quaters)? Malam Habu ya ce "A'a daliba nakawo 'yar makaranta ce. Su duka suka kyalkyaleda dariya suna tafawa wani harda buga kafa akasa. Abun ya daurewa Hanne da Mahaifinta kai. Menene abun dariya?Konan ba ita bacemakarantar 'yan mata ta gwamnatin tarayya dakeKazaure? Malam Habu ya tambaya suka ce "Nan cemakarantar daka ambata amma watakila kayibatan kai ko baka ji dai-daiba. Malam Habu ya ce"Batan kai kamar yaya? Daya ya ce "Nan makaranta ce ta 'ya'yan masu hannu da shuni,'yan birnimasu kokari, ba haka kawai dan ance 'yarka tacimakaranta ba kaje ka suyo akwati da katifa kazoka zabi makarantar da ranka yake so ka shiga kacega daliba. Daya ya ce "Ko dai waccan makarantar ceta gwamnatin jiha suka rasa suka shigo nan. Koda yake ko can dinma dakyar su kwashi wannan.Sannan na karshe ya ce "Ku dai ku tsaya babumamaki nan din taci abun ai na Allah ne, Malam inatakardar shaidar taci nan makarantar? Malam Habuya ce "Mu babu wata takardar shaidar cinmakaranta a tare damu, ni dai kansilan garinmu yazo har gida ya ce jarabawar da *yata tayi a birnita fito kuma duk karkararmu ita kadai taci, maigarinmu ma ya turo inje ya shaida min ya ce lallai-lallai nan taci in kawota, ya ce min makarantun'yan mata a Kazaure guda biyu ne data gwamnatintarayya data gwamnatin jiha, ta gwamnatin tarayya taci in kawota. Amma ni babu wanda yayi minzancen takarda. Suka sake kecewa da dariya. Dayaya ce "Malam sai kuyi waje don baza ku shiga bababu takardar shaida, ku koma ku sami kansila komaigarin naku su baku takardar shaida sai kuzo kununa sannan mu barku ku wuce. Yau gashi kusan wata daya ke nan da aka riga aka gamakawo yara har sunyi nisa da fara karatu, kai saiyanzu kake kawo 'yarka. Malam Habu ya ja 'yarsaa sanyaye suka yi waje, zuciyarsu cike damummunar damuwa.Hakika Nigeria muna cikin wani hali lokacin da yake ajiye kayan dake hannunsa a waje,yakamawa 'yarsa akwatin dake kanta suka saukekasa. Suka tsaya suka yi cirko- cirko suna kallon masu gadinnan,wadanda har yanzu basu daina yabo musubakakenmaganganu ba. Malam Habu ya nisa ya ce "AllahSarki rayuwa, Allah Ka fimu sanin halin da muke ciki kaizaka fitardamu, 'yar Baba zauna a gefen akwatinki kinjikafin mugayadda Allah zai yi damu. Isa kansila da maigarisuka ja mana wannan wulakancin. Ni nasan a rina, shi yasa dafarko nakifur da akace za'a kaiki birni daukar jarabawa,kuma kema daakayi kiranki me yasa ki amsa musu? Kika ce kinason karatun, ga irinta nan ai. Hanne ta zauna a hankali jikintayayi sanyi,wanda ko yatsanta wuyar dagawa yake yi mata.Zuciyarta cikeda damuwa, babu abin da take tunawa illakomawarta gida haduwarta da iya Abu kishiyar uwarta da'ya'yanta.Irin tsananin azabar da suke gallaza mata dabautar ta din daake tamkar baiwa alokacin cinikin bayi. Ta ce aranta "Da inamurna zanzo makaranta nabar gidan da banahutawa kuma ban taba hutawa ba sai yanzu. Gashi yanzumakarantar masun koro mu dole mu koma gida. Taci gaba da tunairintataburzar da aka sha da Mahaifinta kafin Iya Abutabar su suka fito daga gida zuwa makarantar nan. Wai itaidan Hanneta tafi babu mai yi mata aikace-aikace su sharawanke- wanke,debo ruwa a rafi ko tuka-tuka. Saboda haka nemataki fur wai baza a kawo Hanne makaranta ba. 'Ya'yantakuma garda-garda maza da mata suna zaune ko tsinke basadaukewa saiHanne wacce bata da uwa a gidan. Allah Sarkihawaye ne ya kecewa Hanne yayi ta zuba daga idanuwanta.Maganar dadaya daga cikin masu gadin keyi ita ta katse tadaga tunanindata dulmiya tana yi. Taji kamar daga sama yanacewa "Kai kauyawa ma da rashin tunani suke dan kawai ance'yarka tacimakaranta sai ka taho ka zabi makarantar data yimaka kawaika sako kai, dubi yarinyar daya kawo sai kace maizuwa tallar kalwa riga a cukurkude, zanin daga kasa ya nadekamar annade tabarma. Takalmin kafarta harda leda tadaure waye zaice daliba ce. Daya ya ce "Danmarar data ci kai kacedandali zata, ta daure kugu tamau. Ina jin ma basu san anadinkakayan makaranta ba (Uniform) balle takalmikambas da safa.Hanne tayi ajiyar zuciya ta hadiye yawun da ya cikamata bakinta tayi shiru, kanta a sunkuye a kasa.Tace a ranta "Lallai ko nafi maye kwakwa dole nahakura damakarantar nan harda kayan makaranta akedinkawa. Wayezai dinka min? Ta sake kallon kayan jikinta tace aranta "Kayan sallar tawa shine suke cewa duk a cukurkude? Niina ganinnayi ado kowa a garinmu da muka zo wucewayana cewaHanne yau kuma ina zaki kika ci ado haka? Su anankazan- kazan suke ganina ashe, dole mu koma gida asheban rabu dawahalar Iya Abu ba. Kuka ya sake kece mata hardashessheka. Malam Habu ya kalleta fuskarsa cike dadamuwa ya ce "Yi shiru 'yar Baba bari zamu san yadda zamuyi mukoma gida. Ni yanzu ke nake ji gashi kudin da yarage mun aaljihuna saura Naira ashirin kacal. Da niyyatainnakai ki makarantar in zan koma gida sai in hau mota daganan zuwatashar Kazaure daga can kuma sai in kama hanyada kafa harBabban- mutum (garinsu) idan dare yayi mun insami waje in kwanta washe gari na tashi naci gaba. Har dai inkarasa kokwana nawa zanyi a hanya. To yanzu ba zai yuwuba tundagaki, sai dai kawai mu shiga mota muje tasharKazauren, ko a bakin tashar sai in siyar da akwatin nan ko katifarkoma dukamu samu muyi kudin motar komawa gida. Hanne tazabura tace "Ka siyar da akwati da katifa fa kace? Kansila aisai yasa a kamaka, cewa yayi fa gwamnati ce ta siya ta bani.MalamHabu yayi kasake yana tunani na wani lokaci maitsawo can yace "To laifin waye? Shi kansila da maigari basu sanda kudi za'a zo makarantar ba, babu wanda ya bamu kosisinsa,kansila kullum yana min alkawarin zai je ya karbokudin da zaayi miki siyayya da kayan makaranta da komai dakomai, har cewa yayi motar gwamnati ce zata zo ta kawoki..Daga karshe ya zo ya fara hanya tun dagagwangwarmarakwatin nan da katifa da bokiti babu abunda yakara kawowa.Bansan wacce shawara suka yi da maigari ba kumadaga karshe suka ce inzo in kawoki haka za'a aiko mikikayayyakindaga baya. To yanzu gashi takardar makarantar cebabu aka yimana korar kare ina ga idan muka shiga ciki aka cemu kawo kudi, muka ce babu ai sai a rakomu da duka. CikinsauriHanne ta ce "Lah Baba na tuna jiya maigari ya aikoda watatakarda da yamma ya ce ta makaranta tace, bakanan. Na karba nasa a akwatina ko itace suke tambaya?Malam Habucike da mamaki da zumudin dauko takardar ya ce"Haba 'yarBaba kina 'yar karamarki kike mantuwa, tun dazufa ake maganar takardar duk baki tuna ba. Yi maza kidaukotakardar in nuna musu ko itace takardar. Hanne tadagaakwatin da sauri ta bude, babu komai a ciki saikayan sawarta kala biyu a cukurkude suke kamar anyi sukuwardoki a kansu.Ta binciko can kasan akwatin ta dauko watadoguwar takardafara ta mikawa Babanta. Malam Habu ya karba dasauri ya doshi wajen masu gadin nan yana cewa "Ga daiwata takarda a cikinakwatinta saiyanzu ta tuna ashe mai gari ya aiko da ita jiya kudai ku duba ku gani ko ita ce. A yatsune daya daga cikinsu yakarba yaduba yana dubawa kuwa yaga takardar shaidar andaukiHanne Habu Imamu a F.G.G.C Kazaure ce wato(Admission letter) Sun sha mamaki kwarai da ganin nanmakarantar kuwataci ba batan kai suka yi ba. Cikin sakin fuska sukayi musuizinin su kwaso kayansu suzo su wuce. Cikinmurna Hanne da Mahaifinta suka kwashi kayansu suka wuce izuwacikinmakaranta. Basu tsaya a ko'ina ba sai a bakin wanibabbangini wanda ya kunshi doguwar baranda da ofishinMalamai.Babu kowa a wajen hatta leburori masu share-share da goge-goge duk basa nan, wajen tsit kamar babubil'adama. Sukasami gindin wata bishiya suka sauke kayansu.Hanne ta hau kan akwatinta ta zauna Malam Habu ya ce "To fawannanshine ko in kula, yanzu kuma ina zamu dosa kokuma wazamu tambaya? Ni wallahi abun nan na makarantarbokon nan ya ishe ni daga nan sai can ana tsattsare ka datambayakamar a lahira mun gama da masu gadi yanzukuma Allah nekadai Ya san wa zamu hadu dashi, kai Allah Yakyauta, wannan shine ake cewa ba shiga ba fita wai anbawamahaukaci gadin kofa. Shigowar wata dalleliyarmota ce Jeeplaunin koriya (dark green) wacce ta tunkaro indasuke, ita ta katsewa Malam Habu surutun da yake yi. Ta zo dafda su tatsaya babu abinda yake tashi a cikinta sai sautinkida dasanyin A.C maza ne samari guda biyu suka fitodaga gani wa ne da kaninsa, kanin yana sanye da kayan bautarkasa ajikinsa wato (N.Y.S.C) Yayan kuwa wata tsadaddiyarshadda cefara sol a jikinsa sai kamshin wani tsadadden turarene yake tashi. Abunka da kauyawa sai kallo suke dukkauba da *yar,kanin ya bude but din baya ya dauko wata Jakarkaya, yamayar ya rufe ya ce da wansa "Yaya Habib, na godesai dai nace maka Allah Ya kiyaye hanya. Yaya Habib yayimurmushiya ce "To madalla. Allah Ya bada sa'a sai yaushekuma zaka zomana weekend? Ina fatan dai wannan karan zakayi kamar wata baka zo ba ko?Su duka biyun suka tuntsire da dariya, kanin yace "Ai Yayaranar juma'ar nan zaka ganni a gida ko ba'azodaukana ba mazanzo Kano, haba ai sai jini na ya hau zama a kauyein ba dole ba wa zai iya? Yayan yana dariya ya mikawakanin hannusuka gaisa ya ce "To Allah Ya taimaka, ina ganinranar juma'arda zaka zo may be baza mu hadu ba saboda dasassafe zan tashi zuwa america kai kuma nasan sai da yammazaka tahosai an tashi *yan makaranta ko? Kanin ya ce "Ehkuwa bazamu hadu ba Allah Ya kiyaye hanya Ya dawomana da kai lafiya, Yaya akwatinan auren da nawa da naka yazamo iridaya. Yaya Habib ya ce "Insha Allahu, Yaya Habibya shigamota har zai ja kofar motar ya rufe sai ya juyo yakalli Hanne da Babanta ya ce "Salamu alaikum" Malam Habu yaamsagami da daga hannu, Yaya Habib yaja motarsa yajuya ya nufikofar fita kanin na tsaye yana daga masa hannu.ayan da motar Yaya Habib ta kure, idanuwansuduka na kantasannan hankalin kowa ya dawo jikinsa. TunaninHanne yakoma ga kallon kyakkyawan ginin makarantarginin bulo da bulo,yaune rana ta farko da take tunanin take saran zatakwanta a dakin ginin bulo ba gidan kasa ba rufinazara. Ta cea ranta "Cafdijan yau kuwa zan iya bacci? Anyabazan ringa jin sanyi ba a wannan dogayen gininnikan. Bata sansanda tayimurmushi ba har hakoranta suka fito, sai tawayence ta kifakanta akan cinyarta kada Babanta ya ganemurmushin dadi take. Kyakkyawan saurayin nan ya tunkaro indasuke yanarataye da jakarsa a kafadarsa, ya yiwa Malam Habusallamagami da dan dukawa kadan, kana ya wuce su yajegindin wata bishiyar dake kusa da tasu ya daga wani benci yazauna yaajiye jakar kayansa a kusa dashi yaci gaba dakallon Hanne daMahaifinta. Can Malam Habu yaje ya same shi a indayake zaune ya ce "Dan Allah *yan samari kai maka'aikacine ananko kaima bako ne? Yayi murmushi ya ce "Yaya akayi Baba?Malam Habu ya ce "Yarinya na kawo makaranta tundazu banga kowa ba balle in tambayeshi hannun wa yakamata indankata? Saurayin nan ya gyara zama gami da cirehular dakekansa ya ce "Daliba, daliba ce wannan? Malam Habuya ce "Eh nan aka ce na kawota kuma gama takardar canbari ta mikogama korarmu akayi dazu da babu takardar, yakwalla kira yace "Hanne kawo takardar nan ta dazu.Cikin sauri Hanne tasa hannu a cikin bokiti dakegabanta tadauko takarda tazo ta mikawa Babanta da hannubiyu ta dukahar kasa. Babu abinda wannan saurayi yake saikallon Hanne sama da kasa kayan jikinta yake kallo da takalmindakekafarta wanda ta daure da leda saboda ya tsinkekudin naninma aiki ne, wata uwar danmara kai kace dambentsiya za'a kwasa, wuyan, hannu da kafa tsakiyoyi. Saurayinnan ya kulada lallai Hanne ita kanta tana jin kunyar shigar nantata ganinkallon da yake yi mata, sai yayi sauri ya fara dubatakardar da Malam Habu ya mika masa. Ya karance tsaf, sannanya dagoya ce "Hanne Habu Imamu ko? Tace "Eh, ya ce "ToBaba saikun dan jira don nima nan Malamin nake jira gashitakamaimai ma ni bansani ba ko yana makarantar kobayanan don nima shigowata kenan. Malam HabuyayiHamma gami da yin dan siririn tsaki ya ce "Yaroyanzu bayadda za'ayi ka karbi yarinyar nan, dole sai waccan din ya zo? Saurayin ya ce "Ni Malami ne amma kuma bapermanentteacher ba bautar kasa (service) nazo yi, a ka'idarwannanmakarantar kuma senior master ne ya kamata ya karbetamusamman ma kasancewarta sabuwar daliba ce.Gashi yau lahadi, dama litinin ce ko sauranranakun aiki lokacin principal tana nan, da sauranpamanent teachers duk sai su karbeta koda seniormaster baya nan, amma yanzu ku jira kadan idannan da minti talatin bai dawo ba, zan tashi nima nashiga staff quaters din na gani ko yana ma cikin makarantar dan nima shi nake so na gani zan karbimukullan gidana. Malam Habu ya ce "To Allah Yakawoshi lafiya bari nayi sallar la'asar, nasan biyartayi ko sallar la'asar bamu yi ba. Yaro ina buta? Yanuna masa wani fanfo can kusa dashi kuma dazagayeyyen waje nan ne Masallaci. Malam Habu ya ce "To madalla. Ya kalli Hanne wacce ke tsaye agefe har yanzu ya ce "*Yar Baba koma kanakwatinki ki zauna zanje nayi sallah kinji. Cikinsanyin murya ta ce "To, ta juya ta doshi wajenakwatin. Malam Habu ya bita da kallo zuciyarta cikeda tausayinta ganin yininsu guda babu abun da suka ci tun dan kokon safe da suka dan kukkurbaa tsattsaye bala'in Iya Abu ya hanasu su zauna susha sosai. Malam Habu ya girgiza kai alamartausayawa kansu da kansu ya ce "Allah Sarki *yarBaba hakuri dai za ki yi, ki kuma ci gaba dayi.Sannan ya juya ya nufi wajen fanfo. Kyakkyawan saurayin nan na zaune yana kallonsu zuciyarsacike da alamomin tambaya da tsananin tausayi. Canya nisa yayi ajiyar zuciya ya zaro gilashin dakealjihunsa ya saka a idonsa gami da cusa hular dakehannunsa a cikin aljihunsa na wando yasahannunsa ya dafe habarsa yaci gaba da kallon Hanne dake zaune kan akwatinta tayi lamo tanatunani ba tare da tasan wani na nan gefenta ta cikingilas yana kallonta ba. Ya ce a ransa "Wadannandaga wanne kauye suke?Sun kuwa karanta takardar dake hannunsusunsan me ya kamata su tanada suzo dashi? Kaibasu san dokar da aka rubuta ba a jikin joininginstruction din nan ba. Lallai kuwa da sun san meaka rubuta da baza taci uwar danmarar nan ba tashigo makarantar nan haka ba. Bayan kamar tafiyar Malam Habu da minti ashirin sai gashi yadawo. Ya zo ya wuce ta gaban saurayin ya ce"Sannun ka da hutawa, ya katse tunanin da yakeya ce "Yauwa Baba. Malam Habu ya kara da cewa"Har yanzu dai kaga shiru baizo ba ga rana nan nashirin faduwa yau kuwa anya mai karbar yaran nan zai dawo? Yayi murmushi ya ce "Ina ganin kakawo duk abubuwan da aka ce ta siya da kudinmakaranta zan yi kasada na karbeta yanzu in yasoranar litinin wato gobe idan mutum yazo ya rubutarisitai yanzu sai nayi magana da masu gadin get dinHostel su kirawo prefect din.... Malam Habu ya matso kusa dashi ya ce "Yaro fadamin da Hausasosai na gane me kake cewa? Har da wani abu dazan kawo nan gaba? Ya ce "Eh Baba, ai a rubuce ajikin takardar aka rubuta za'a dinka mata kayanmakaranta har kala hudu, wanda zata sa idan zasuaji da wanda zata saka a dakunansu, dana wasanni (sport) duk an rubuta kuma lallai-lallai sai da kayanmakaranta za'a karbeta ba zata ta saka kayan gidaba, sannan daga karshe aka rubuta zata zo dakudin makaranta (school fees) shi kuma dakesabuwar zuwace sai kun biya sama da dubu.....Malam Habu ya katse shi da sauri ya ce "Tsaya yaro karma ka kirawomin wadannan dubunnai. Ta faruta kare wai anyiwa mai dami daya sata, yaro nagode madallah, sai anjima. Malam Habu ya juya batare da ya jira amsa daga bakin saurayin nan ba yadoshi inda Hanne ke zaune da saurinsa kamar zaikifa cikin gaggawa, ya ce "*Yar Baba tashi maza mu tafi ga magariba ta kawo kai. Cikin sauri ta mike yaciccibi akwati ya dora mata akai ya sungumi bokitida katifa suka kama hanyar get din fita. Sunyi takudaya biyu sai sai suka ji magana kamar daga samaance "A'a Baba ina zaku kuma? Su duka suka juyadan ganin mai maganar sai suka ga wannan kyakkyawan saurayin ne ya taso yazo wajensu.Malam Habu ya ce "To yaro me zamu yi in ba tafiyaba, dubunnan kudi fa naji kana kira, kuma ka tsayacak ka kalleni dani da dubu daya ma waye ya ajiyewani? Daman kansilan garinmu ne da maigari sukasani dole na kawo *yar nan makaranta, suka ce za'a aiko da kudin, na tabbata har ga Allah basusan kudin yakai dubunnai ba da suma basu tankaba. Kuma kudin gwamnati ba'a bashi babu yaddaza'ayi nazo na ajiye yarinya a makaranta babukudin makaranta babu kayan makaranta na ce abimu bashi zamu kawo ba. "Wannan ba zai yiwuba, inji saurayin. Malam Habu ya ce "To ka gani cewasuka yi na zo na kawo ta za'a aiko da kudin kumayadda naji kalamansa shi kansilan a tunaninsakudin makarantar bai wuce dari uku ba, bai sandubunnai bane kuma koda shine yazo ya kawotaaka kira dubunnan nan cewa zaiyi ta fasa karatun. Don karamar hukuma baza ta biya wadannanmakudan kudin ba.Saurayin nan yayi murmushi ya girgiza kaiya ce "Amma Baba bai kamata daga kirandubunnan nan ka kwasheta haka da sauri kacezaku tafi ba. Malam Habu ya fara jin haushinsaurayin nan, ya ce a ransa "Wai shin wannan dukzancen nan da ake bai gane ba ne? Makaranta sai da kudi kuma babu kudin jiran me zanyi, ko shi baisan babu ba ne? Saurayin nan yaci gaba da cewa"Baba kuzo ku ajiye kayan nan bai kamata ka juyada yarinyar nan ba, ai bai kamata ba. Ta cimakaranta har kun shigo cikin makarantar sannanku kwasa ku tafi ka ce ka fasa, babu fa abin da Uba zai yiwa *yarsa a duniya in ba ya bata ilimi ba,yarinya kamar wannan ai kamata yayi tanamakaranta tunda bata isa aure ba, me zata yi agidan? Malam Habu ya sake jin haushin saurayinnan kamar ya doke bakin da yake masa wadannankalamai ya ajiye bokiti dake hannunsa ya ce "Yaro, wai shin a harshen Hausa idan akace babu me akenufi? Yayi murmushi ya ce "Baba kenan, na gameduk dalilan da kake nuna min yanzu, ni kuma abinda nake so na rokeka shine ka fasa tafiya da itatunda ka kawota har cikin makarantar ka kyaletatayi karatu. Abun da ya kamata ka tambayeni shine tayaya zata yi karatu tunda babu kayan makarantababu kudin makaranta? Malam Habu ya ce "toyanzu nasan ka gane babu,ta yaya zata yi karatubabu kudin makaranta babu kayan makaranta?Kyakkyawan saurayin nan ya ce "Yauwa Baba kayitambaya mai kyau, amsar tambayar ita ce in Allah Yaso Ya yarda Hanne zata yi karatu in har kaamince ka yarda zaka ringa turo ta makaranta dazarar hutu ya kare ba sai ta fara ba kace baza tadawo ba ka cire ta.Idan kayimin alkawarin haka kuzo ku ajiyekayan nan ka tafi ka barta. Malam Habu yayi jigumyana tunani, a ransa ya ce "Wannan yaron me yakenufi? Hanya zaiyi mana a dauki Hanne babu kudinmakaranta babu kayan makaranta ko kuma yayaza'ayi? Bana tunanin dai shi zai biya mata kudin makaranta harda dubunnan da ko karamarhukumar mu baza ta iya biya mata ba yaddazamanin nan ya canja masu kudi basa taimako,babu yadda za'ayi yaron nan ya zare makudankudi ya baiwa yarinyar da bai santa ba bai tabaganin ta ba bazan bar *yar Baba a makarantar nan ba in tafi ta wulakanta ba, wacce bata san hanyarda zata bi ta koma gida ba idan an korota. Yanzuakan Naira goma masu mota suke kokarin sudanneni su dauka ina ga dubunnan kudade gakayan makaranta har kala hudu waye zai dinkomata? Saurayin nan ya katse Malam Habu daga tunanin da yake yi ya ce "Baba tunanin me kake yine? Karka yi kokonto ba zaka yi dana sanin barinHanne a makarantar nan ba in Allah Ya yarda babuabin da zai sami Hanne sai alheri da kwanciyarhankali ka tsarkake zuciyarka ka danka Hanne gaAllah wanda a koda yaushe Yana kallon halin da bayinsa suke ciki na kunci kona farin ciki, sannanka danka Hanne amana ce a wajena. Ni kuma namaka alkawarin zan karbi amana na rike. Cikinsanyin zuciya da gamsuwa da kalaman saurayinnan Malam Habu ya juya ya kalle shi ya ce "AllahSarki duniya wani ya munana maka wani kuma ya dadada maka. Yaro tunda ka ce Allah na yadda kakuma ambaci amana, amana kalmace mai girmamai wuyar rikewa kace zaka rike tsakaninka daAllah, na gode yaro, Allah Yayi maka albarka Yabiya maka bukatunka. Abin da kayi min UbangijiAllah Yayi maka fiye da haka, *yar Baba muje mu ajiye kayan. Suka juya harda saurayin wajen bencinda yake, Malam Habu ya kama akwatin dake kanHanne ya sauke mata ya juyo ya kalli saurayin nandake zaune akan benci ya ce "Yaro bazan gaji da yimaka godiya ba.Madalla Allah Ya yi maka albarka zan tafi nabarku lafiya, af kaga ko sunanka ban tambaya ba.Saurayin nan yayi murmushi ya ce "Sunana Haisam,Baba. Malam Habu ya ce "To madalla. Ya juya yakalli Hanne wacce ke tsaye idonta ya ciko da kwallaya ce "*Yar Baba zan tafi na barki ga Allah na barki ga wannan bawan Allah. Sai ta rushe da kuka takoma kan akwatinta ta zauna ta kifa kai a gwiwatana kuka. Hawaye ya kecewa Malam Habu ya ce"Nima ba'a san raina zan tafi na barki ba Allah Yakaddara saduwarmu. Ya juya ya kalli Haisam ya ce"Yaro mai wuyar suna har na manta sunan(fatan Yayarmu ma Zee zata iya rike sunan, kodayake ita 'yar birnice, loz) na tafi, sai wata rana. Haisam ya ce "To Baba Allah Yakiyaye. Malam Habu ya juya ya fara tafiya yana facemajina yana goge hawaye da gefen babbar rigarsa,sai yaji muryar Hanne ta ce "Baba ya juyo ya ce"*Yar Baba. Ta taso da gudu ta karaso inda yake takama gefen zaninta ta kwance sai ta dauko wasu cukurkudaddun *yan Naira ashirin guda hudu tace "Baba karka tafi da kafa gashi ka hau mota.Haisam dake zaune har yanzu akan benci yanakallonsu sai da yaji kwalla ta cika masa ido dontausayin Uba da *yarsa. Malam Habu ya ce "AllahuAkbar, *yar Baba Allah Yayi miki albarka. Allah Ya baki ilimi mai amfani, kinji? Waye ya baki harmurtala hudu? Hanne ta ce "Dana shiga makwabtanayi musu sallama suka babbani wasu, saurankuma kudina ne da nake tarawa tun na yawonsalla. Malam Habu ya ce "Kya bani duka ingomurtala biyu ni na dauki murtala biyu, kema ki rika siyan *yar gyada kya zauna haka kina ganin yarasuna siye-siye ke bakya siyan komai? Hanne ta ce"A'a Baba murtala biyu baza ta kai ka gida ba, banaso ka shiga mota kudinka bai cika ba, kana rokonayi maka ragi irin na dazu. Malam Habu ya sakekecewa da kuka ya ce "To *yar Baba na gode na tafi na barki ga Allah baki da kowa, baki da komai,ba ki san kowa ba, Ya juya ya tafi. Hanne na tsayehawaye yana zuba daga idanuwanta tana kallonMahaifinta yana tafiya yana waiwayenta.Taji wani kululun bakin ciki marar misali akirjinta da mummunan tashin hankalin rabuwa daMahaifinta, yaune ranar da ta taba rabuwa daMahaifinta daidai da rana daya basu taba rabuwaba. Gashi a yau ya kawota inda bata san kowa baya juya ya tafi ya barta. Hawaye ne mai radadi yake zubo mata har sai da ta daina hango fararenkayansa ya kure, sannan ta yi ajiyar zuciya tasagefen mayafinta ta goge idanuwanta ta juya tadawo kan akwatinta ta zauna. Haisam na zauneakan benci yana kallonsu zuciyarsa cike datsananin tausayi ji yake wani abu yana yawo a cikin kansa, saboda wani abu guda daya daya bashimamaki ya bashi al'ajabi, shine ganin yadda Hannetake da Mahaifinta suna cikin tsananin talauci ammasuna da wadatar zuci. Haisam yaci gaba da kallonHanne wacce take zaune akan akwati a gabansa tasunkuyar da kanta kasa tayi shiru kamar mai tunani, amma hawaye na digowa daga ganintahankalinta a tashe yake tana cikin damuwa. Yagyara zama gami da zare farin gilashin da yakefuskarsa. Ya ce "Hanne, kukan mai kike yi ne?Bakya so ki zauna a makaranta kiyi karatu kamarsauran yara, kin fi so ki koma gida ki zauna da Baba? Hanne ta girgiza kai alamar a'a, ya ce "Tomeye kike kuka? In kinsan bakya son makarantarnan yanzu nayi sauri na tsayar da Babanki kafinyayi nisa sai ku koma gida. Hanne tayi sauri ta ce"A'a bana so na koma gida, ya ce "To ai kuka kikemeyasa kike kukan tunda kina son makarantar? Bakya son ki koma gida inda zaki yi wasa kuyiwake-wake da kawayenki a dandali? Hanne tayidan murmushi ta sunkuyar da kai. Haisam ya cigaba da cewa "Ni kuwa na dauka danmarar nan dakika ci ta zuwa wake dandali ce. Hanne tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka ta ce "Ni ba'a barina naje dandali wasa. Kullum aiki nake yi sai daiinzo in wuce su in zani debo ruwa. Haisam ya sakegyara zama ya ce "Ban gane ba sai dai ki zo ki wucesu in zaki debo ruwa? Ke kullum a debo ruwa kikebakya zuwa wasa? Hanne ta ce "Eh, sai dai suSaude Yayyena da kanne na ne suke fita wasa.Haisam ya ce "Ina Mahaifiyarki take? Hanne tasake saka gefen gyalenta ta share hawaye ta ce"Tun ina shekara biyu ta rasu. Yaji gabansa yayanke ya fadi ras, saboda yanzu ya gane Hanne agidansu tana cikin halin wahala kasancewarMahaifiyarta ta rasu da alama kishiyar Uwa tana wahalar da ita. Allah Sarki Hanne ya fada a ransayayin daya kura mata ido. Hanne ta bashi tausayida, a yanzu kuma ta sake kara bashi tausayi akantausayi wanda badan ya daure ba da zai iyarushewa da kuka. Can bayan sun dauki wani lokacimai dan tsawo babu wanda ya sake cewa komai. Dukkaninsu kansu a sunkuye a kasa suna tunani,Haisam ya rike kai da hannuwansa guda biyu canya dago ya kalli Hanne ya ce "Yanzu dai a gidankuke kadai Babarki ta haifa kenan baki da Yayye ko?Hanne ta ce "Eh. Ya ce "Shine kuma ake saki deboruwa kullum. Hanne ta ce "Ba debo ruwa kawai ba kullum ni nake wanke-wanke, shara, wankinsu, dakai dabbobi kiwo daga can nayo musu ciyawa.Haisam ya buga kafa a kasa ya ce "Kai wannanwanne rashin imani ne haka? To ya akai kike zuwamakaranta? Hanne ta ce "Sai wajen sha dayan ranakoma wataran bana zuwa, tun ana min dukan makaranta har suka daina su Malamai. Shine waniMalami ya je ya sami mai gari ya ce a yiwa Babanamagana a dinga turoni makaranta da wuri tundaina da kokari, Haisam ya ce "Sai da maigari ya kiraBabanki ya fada masa sannan ake turakimakarantar da wuri? Hanne ta ce "Cafdijan shima Baban ya isa? Ya ce "Kamar yaya bai isa ba.Ta ce "Shima tsoron Iya Abu yake, matar tasazaginsa take,*ya*yanta suyi masa, sai dai in ana dukana inakuka shima yadinga yi. Hawaye ya sake kece mata, shima ya jikwalla ta cika masa ido, ya dauko wani hankici fari kal a aljihunsaya gogeidanunsa ya mika mata, ya ce "Yi shiru Hanne dainakukagoge hawayenki. Ta karba ta goge. Haisam ya ce"Bari na danyi miki tambayoyi naji kina kokari? What is yourname?Hanne ta ce "My name is Hanne Habu,Ya ce "Howold areyou? Ta ce "I'm eleben years old. Wich school areyou? Ta ce "I'm in Babban-mutum special primary school.Haisam yayidariya ya ce "Hanne Habu haka kike da kokari? Toke da bakyazuwa makarantar sosai ya aka yi kika koyi dukwannan? Hanne tayi murmushi ta ce "Ai daga baya maigariyasa akakirawo ita iya Abu da kanta taje fada ya sakashaidu ya ce"Duk ranar data hanani zuwa makaranta ko namakara sai ya kaita kara local goverment. Sannan take barina natafimakaranta da wuri sai dai idan na dawo tayi tadukana tanacewa ga wanke-wankenta nan harya bushe natsaya a hanya ina wasa. Haisam yayi tsaki ya girgiza kai alamartausayawa.Yayi gyaran murya ya ce "Hanne ina so kiyi minalkawarin zakidage kiyi karatu duk rintsi duk wuya. Kar ki zo kifara ayi hutu ki koma gida kiga kawayenki da yayyanki sunagida basa zuwamakaranta kema kiki dawowa. Hanne ta ce"Kwarankwatsazan dawo.(hahah. Inkikayimata dariya bazancigabarmikiba,'Eh' dake nake Zee ) Haisam ya kece da dariya (subhanallahi, tinda shima yayi to kema danyi amma kadan),ya ce"Kwarankwatsabarantsuwa bace wallahi Allah za ki ce. Hanne tayidariya ta ce"Mantawa nayi Malamin makarantar Islamiyya yahana mu cewa kwarankwatsa. Haisam ya ce "Kina zuwaIslamiyyakenan? Ta ce "Eh, ada makarantar allo muke zuwadaga bayaaka bude makarantar Islamiyya da yamma dakuma dare duka ina zuwa. Haisam ya ce dakyau Hanne yanzuidan anyihutu kin koma gida sai kici gaba da zuwa taIslamiyya karkifasa zuwafa kinji? Hanne ta ce "To. Haisam ya cigaba da kallonta har sai da Hanne ta fara jin kunyar kallonda yakemata sannan yayi murmushi ya ce "Hanne dukwannankwalliya ce kika yi a fuskarki, ta zuwa makarantace? Hanne tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa tana rurrufefuska dahannu ta ce "A'a ba kwalliya bace. Ya ce "Gashi nankinrambada kwalli kinja wata doguwar jagira kinyifashin goshi da kwalli kinyi digo-digo duk fuskarki kice bakwalliya bace. Gawannan tsakiyoyi da kika jifga a wuya da hannuhar kafarkima kin daura, Yana dubanta yana dariya. Hannan tace "Eh sarkar salla tace Baba ya siya mun. Ya ce "Kingananmakarantar an hana sawa idan Malamai suka ganizasu kwacesu tsittsinka miki, ciro su ki bani in ajiye miki saianyi hutu in zaki tafi gida na baki. Cikin sauri taji zancentsittsinkawa taciro ta bashi, yadda take bala'in kaunar sarkokinnan natabata son abun da zaisa ta rasa su. Haisam ya karbayana jujjuyasu yaga wasu irin tsohon wuri ne aka jera sucikin liloaka daura ya ce a ransa "*Yan kauye suna gayu.Yayi murmushi ya jawo jakar kayansa ya budewanikaramin zip ya zuba ya mayar ya rufe. Ya juya yakalli Hanneya ce "Kuma a cikin akwatin naki bude in gani kokinzo da wani abunda dokar makaranta ta hana. Hanne tatashi dagakan akwatin ta bude ya karkato ya leka akwatinbabu abundaya hango sai tsummokarai, cikin sauri ya ce "Hanneme wancan nake hangowa kamar miciji a cikinakwatinki? Hannetasa hannu ta zaro wani dan siririn gyale baki yakanannadeya kudindine ta ce "Gyale ne ba miciji bane. Haisamya kyalkyale da dariya ya ce "Na dauka kofi kika yiminna miciji.Hanne ma tayi dariya ta ce "Gyale na ne dan bansaruwa bana kadeshi shiyasa ya cukuykuye, ya sake lekaakwatin sai ya hango wani dan dogon karfe mai huda huda ajikinsa, jikinsakamar farar azurfa yana kyalli ya ce "Hannewannan fa, karfenmenene? Dauko muga. Hanne ta yi murmushi tadauko karfen ta mika masa ya karba ya jujjuya bai san ko meyeba ya ce"Wannan kuma na maye. Hanne ta ce "Idan najekiwo nakeyiwa dabbobi busa dashi, abun busa ne. Haisam yace abun busa kuma? Hanne ta ce "Eh kawo ka gani. Ta karbikarfen tamayar da akwatin ta rufe ta koma kan akwatinta tazauna takaikaice ta fara busawa Haisam wannan karfen kaikace Sarkin busar Sarki ne yake yi, karin busar mai dadi daalama daiwaka ce, Haisam ya buda kunnuwa yana sauraroya baza idoyana kallon yadda take yi.Can ta kyalkyale da dariya ta ce "Haka nake yi.Haisam yayimurmushi ya gyara zama ya ce "To ni abunda bangane ba,kamar yaya sai kinje kiwo kike yi? Daman a wajenkiwo ake yin busa? Waye ya koya miki kuma? Nan da nanHanne tacanja daga yanayin farin cikin da fara'a da sakinjikin da takejikinta yayi sanyi ranta ya baci. Haisam ya ce "Yakika canja nan da nan daga tambayarki? Hanne ta rushe dakuka ta kifakai da gwiwa, Haisam yayi matukar mamaki daganin wannanhali da Hanne ta fada yanzu- yanzun nan ya ce"Yaya kina dariya ki koma kuka, Hanne dago kanki. Ta dagoya ce "Gogehawayenki. Ta goge. Ya ce "Fada min meye nakukan? Hanneta ce "Wani abu na tuna shine ya sani kuka. Haisamya ce "Meye abun da kika tuna? Hanne ta sa hannu tasake gogehawayen da ke idonta ta dauko abun busar dakekan cinyartata rike a hannunta tana jujjuya shi.Tace kullum dasafe nake fita kiwo da raguna da akuyoyin iya abucan dawa. Bana dawowa sai da yamma musammanrabar asabar da lahadi. To awajan kiwo ne nakehaduwa da wani tsoho mai suna malam saleh. Wani lokaci sai yazo ya wuce ni ina kuka idan yunwa tadameni don yini nake anan kuma ba.a kawominabinci. Har dai rannan ya zo ya sameni a gingininuwa ina kuka. Yayi ta tambayata dakyar dai nagaya masa yunwa nake ji. yace '' ba.a kawo minabinci daga gida ?nace ba.a kawomun kuma bana zuwa dashi. Ya ce '' ina babata? Nace ta rasu'' shineya ce min kullum zai rinka bani abinci ina ci dakekullum da rana daga gidansa ake kawo masaabinci nan wajen kiwon rigarsu tana nan kusakusa da garinmu , shine kullum muke haduwadashi yana waka harya koyamin nima nakoya. Sai ya ce ya barmin abun busar tunda na iya, ko bayanransa dansa zai ringa kawo shanunsa datumakinsa kiwo na dinga yi musu busa. Bayan nannaga kwana biyu naya zuwa kiwo bana ganinshanunsa kuma. Hankalina ya tashi naji duk banajin dadin kiwon ni kadai babu wanda muke zama muyi hira muyi busa muyi waka tare. Sai da akadade naga shanunsa da tumakansa an kawosuwajen kiwo amma ba malam saleh bane wanisaurayi ne. Naji gabana yana ta faduwa ko lafiyaina malam saleh yake? Naje na tambayi yaron sai yace shi dansa ne kuma babansa malam saleh satinsa biyu da rasuwa shine a duk sanda naje kiwo nagadabbobinsa sai suyi ta bani tausayi ina kuka''hanne ta goge hawayen da yake zubo mata haisamyayi ajiyar zuciya. Zuciyarsa cike da tausayin hanneya ce a ransa'' hanne yarinya karama tasan bacinrai, tasan tashin hankali ta rasa kowa da zai tarairayeta wanda zata gani taji dadi baya gamahaifinta. Allah sarki , na yiwa allah alkawaribazan kyale yarinyarnan taci gaba d tagaiyara ba''ya juyo ya kalli hanne wacce har yanzu take rike daabun busarta a hannunta tana jujjuyawa.Yacekawo abun busar shima na ajiye miki, idan ba haka shima malamai zasu kwace'' hanne tayi murmushita mika masa ya karba ya jujjuya ya bude zip dinjakarsa inda ya saka tsakiyoyin nan nata ya saka yamayar da zip din ya zuge ya ce'' yanzu abunda za.ayi kije kicin gashi can ya nuna mata da hannunsaya ce kice uwar biyu, tazo inji malam haisam kinji ku taho tare'' hanne ta mike cikin ladabi tana maiamsawa cikin ladabi ta nufi inda ya nuna mata tanatafe tana kara tsuke damarar data ci da gyale akugunta.Haisam ya bita da kallo har ta kure yayimurmushi ya girgiza kai'' bayan tafiyarta da kamarminti biyar sai ga hanne da uwar biyu sun taho tare bayan uwar biyu ta gaishe da haisam durkuso harkasa duk da ta haifeshi tama yi jika dashi amma aidurkusama wada ba gajiyawa bace irin abunalherin da haisam yake yi musu ita da abokanaikinta na kicin sune masu dafawa yan makarantaabinci. Duk ranar da yake duty idan yazo kicin duk sai ya bisu da kudi dukkaninsu don haka allahallah suke malam haisam yazo kicin bayan sungaisa ya ce'' uwar biyu wata alfarma nake si kiyimin idan baza ki takura ba '' uwar biyu ta sakegyara gwiwoyinta da ta durkusa tace'' haba malamhaisam menene ni kuwa a duniya zaka nema ina dashi na takura ai babu sai dai ma nayi murna yauharka nemi wani abu a wajena , mai yi maka kansada kafarsa. Kana yi mana alheri allah ne zai sakamaka da alherinsa'' haisam yace '' amin na gode .Ba wani abu bane daman wannan yarinyar da kikagani kanwatace amma daga kauyenmu taci makarantar nan babanta ya kawota dazu. Tokasancewar acan basu iya karatuba basu san ancea diko kayan makaranta ba da sauran saye saye .To shine naga dasu koma gida gashi garinbakusaba shine nace zan baki ita ki tafi da itagidanki kamar kwana biyu haka kafin na diko mata kayan makaranta( uniform) da sauransiyayya sai tazo ta koma hostel. Uwar biyu tace''allah sarki malam haisam ai wannan ba wani aikibane babu komai ai sai mu tafi daman na gamadaure ledata tafiya kawai zamu yi'' haisam ya ce'' tona gode '' yasa hannu a aljihu ya dauko kudi ba tare daya kirda ba ya mikawa uwar biyu yace '' toga wannan don ku samu ku saisayi dan abundababu'' uwar biyu ta karba zuciyarta cike da farinciki da mamaki irin wannan yawan kudin da koalbashinta na wata baikai wannan haka ba, gashidaman wata yayi nisa. Tayi ta godiya da da shi albarka har ya gaji da amsawa. Ya kalli hanne yace'' hanne inaga yau duk a wunin nan baki ci abinciba ko? Hanne ta sunkuyar da kai tayi murmushitace'' na karya da safe'' uwar biyu tayi caraf tacea.a.a tin karin kumallon safe kuna ta tafiya ko?Haisam yace nisa , don haka uwar niyu kuje ki bata abinci taci ta koshi.Haisam yace ki siya mata tsiren nan na bakintasha dan alla '' uwar biyu tace to in allah ya yardayanzu kuwa'' haisam yaci gaba da cewa'' sannan kisai sabulun wanka da mai me kamshi ki bata tayiwanka , karki barta ta sharba yanxu duk fuskartata kwabe da kwalli. Hanne ki daina yin wannan dige digen kinji ? Hanne tace to uwar biyu tayidariya tace'' ai da haka suma zasu zamo 'yan matasu koyi yadda ake kwalliya me kyau irin na yanboko ko hanne? Haisam yace'' ina ganin har kantasai an wanke , anyi mata sabon kitso, ko kinyi kitsomuga kan? Hanne ta zame dankwalinta ta durkuso da kanta ta nuna musu wayyo allah kowa ya kallikan hanne zai san bata da uwa a gidan ko wanitsayayyen mafadi ko kuma kazamar uwa allah yabata gashi ne irin kanannadaddennan na fulani kobuzaye ko larabawa mai laushi mai santsin gaskebaki wullik mai tsawo sosai wanda yake taba doron bayanta. Amma me ? Yayi datti. Kura, amosalikai kace dambe tayi aka tumurmusa kan a cikinyashi . Sai wani kitso tuma tuma guda biyu dagagani ita tayi da kanta. Uwar biyu tace'' la la hannehaka kanki yake ? Amma kinyi wasa a yashi ko ?Gaki da gashi tubar kalla baki san yan mata yanzu ido rufe suke neman gashi ba. Da kudinsu ma siyasuke su kara yaya kika bar kanki haka babugyara ? Hanne tayi shiru kanta a sunkuye a kasatana kokarin daura dan kwalinta. Haisam wandayake zaune yayi shiru sai girgiza kai alamantausayi. Can ya nisa yace'' uwar biyu yanzu dai abunda za.a yi ga wannan wasu kudi ne ya sakecunkusowa daga aljihunsa ya mika mata tace'' nameye wannan kuma? Ya ce'' ina ganin hanne nabukatar abubuwa da yawa a kwana biyu da zatayigidanki . Ki tsaya a aishalle super market kitattambayi masu wajen irin man wanke gashi, dana kitso da sabulun wanka, wanki, abun goge kafa kisiya mata silifas. Ki duba kan idan akwaikwarkwata ki sayi shaltos duk a fesa su mutu. Kozaki taho aiki gobe to ki sami wata ki biya ta waccezata gyara mata kannan tayi mata kitso. Kai harmawanka kuyi mata da kanku ai bata wuce ayi mata wankan bama'' uwar biyu tace'' in allah yaso yaudin nan kafin mu kwanta da kaina zan gyaratagobe kuma ko zan taho aiki da diyata halima tananan auren ya mutu tana gida sai in barta da ita.Kuma ta iya kitso kala kala sana'arta kenan ki agarin da tayi aure'' haisam yace to nima gobe wajen karfe biyu idan an tashi a makaranta akwai tela dazamu je dashi can gidan naki ya auno ta zai dinkamata kayan makaranta(uniform)sai ki kwatantamin gidanki don naje. A kanti kike ko cikin gari ?Uwar biyu tace'' ah a cikin gari nake. Idan kajefada, kofar gidan sarki daga hannunkan a dama zaka ga titi ya mike to kabi shi kace a nuna makagidan dalhatun kazaure alhaji hamisu to lyngun mudaya ko a gidan kace gidan uwar biyu kake nemayaro karami zai nuna maka dan mu muke yi mususurfe, katangar gidanmu daya'' haisam yace'' toshike nan yanzu k dauki wannan kayan ku kai store din kicin ki ajiye su sai nan da kwana biyuidan anyo siyayya sai a dauko a zuba, sannankuma abinda nake so dake bana son ki gayawasauran abokan aikin ki ga dalilin da yasa zata jegidanki da sauransu. Ko a cikin gari ma kiyi gum dabakinki kinsan jama.a da surutu za.a yi ta cewa an kawo yar kauye makaranta babu komai sai dauwar biyu takai gidanta wani malami ne yayi matasiyayya da dai sauransu. Ba wai nace kin cikasurutu ba ko gulma a'a ko mutum daya yaji saidubu sunji. Kuma ai akwai matan kicin da yawa damuke gaisawa amma dana ga alamun suna da yawan magana ai ban kira su na basu amana bako ? To yadda tasa nace ta kira uwar biyu'' uwarbiyu ta kyalkyale da dariya dadi ya lullubeta '' tacehakane malam haisam ni dana ke cikinsu yangulma ko sun tambayeni ni nasan me zn fadamusu'' haisam yace'' yauwa ku dauki akwati da bokiti da katifar kamar yadda nace akai store aajiye, sai da safe'' suka ce allah ya kaimu''uwar biyuta kama akwati ta dora akan hanne ta dauki bokiti,da katifa a daya hannun suka doshi store din kicininda suma suke boye shirginsu . Malam haisamkuma ya rataya jakarsa ya nufi gidajen malamai (staff qurters). Zuciyarsa cike da tausayin yaddarayuwar hanne take. Kuma da burin canza matanan gaba* * * * HAISAM ABDULHAMID ZAKAR Sunanmahaifinsa ne abdulhamid zakar. Mahaifiyarsakuma sunanta NANA HAUWA'U Wacce a yanzu akafi saninta da hajiya nana ko kuma barista nana kasancewarta kwararriyar lauya ce. Mahaifinhaisam haifaffun unguwar kwalli ne a kano. Kumasun fito daga tushe daya yar kanwace aka hadasuaure a lokacin alhaji abdulhamid ya gama karatumdigiri dinsa a london yana da shekaru ashirin dabakwai ita kuma hajiya nana ta gama karatun sakandire tana da shekara goma sha shida.Dukkaninsu iyayensu suna da matukar arziki. Donhaka an sakar musu kudi yadda ya kamata antafka musu kerarren gida, motoci an kuma bawaalhaji abdulhamid jari mai tsoka yana juyawa itakuma hajiya nana ta fara karatunta na law a jami'a bayero ta kano. Allah ya albarkacesu da ya'yahudu, uku maza mace daya itace autar. Wacce ahalin yanxu ko yaye ta ba ayi ba karama ce.Babban shine yaya habib yanzu yana da shekaratalatin , mai binsa shine abdulhamid ake kiransa dahaisam yanzu yana shekararsa ashirin da shida mai binsa iziddeen shekarunsa ashirin da uku. Sai daiziddeen ya gama sakandire ya shiga jama'asannan aka yi masa kanwa mai shekara daya anakiranta da amratu.Girma yazowa alhaji abdulhamid da matarsaamma kumakarfi ya tasamma ya'yansa zasu iya kula da dimbindukiyarsada kamfanoninsa yaya habib ya kammala digirinsaa jamia'ar a.b.u ya karanta business admin a yanzu yana aikia kamfaninbabansa shine kuma mai zurga zurga zuwakasashe dabandaban na shige da fice da kayan kamfanonin.Haisam wanda a shekarar nan ya kammala karatun jami'a yakaranta bscgeography yanzu yana bautar kasa a f.g.g.ckazaure da zararya gama kujerarsa ta aiki nanan na jiransa a dayadaga cikin kamfanonin mahaifinsa. Na uku wato izziddenyana shekara tauku (level 3)a jami'ar bayero ta kano yana karatunlaw don yagaji mahaifiyarsa wato barista nana wacce itacebabbar lauyar kamfanonin . Tana kuma farin cikin ganin dayadaga cikin'ya'yanta ya taso gadan gadan da karatun lawwanda a cikin'yan shekaru kalilan zai gama ya zama cikakkenlauya ya canjeta alhaji abdulhamid ya dankawa yaya habibragamaraiki ya koma gida ya zauna yana hutawa sai daiyajekamfanonin fisha yaga yadda aiki yake tafiya yakoma gida.Dan lelen abba da umma wato haisam shine yafikowashagwaba a gidansu ko kuma nace shi akafishagwabawa tunyana kankani. Amma ai izidden ne yakamata yayishagwaba kasancewarsa ya dade yana auta kafin ayi masakanwa ammashi yana gefe tun suna yara haisam ne a kancinyarsabodatsananin biyayya, ladabi , tausayi da jinkai irin nahaisam shine ya kara masa fada a wajen mahaifansa sunfisha'awarsu zauna suyi hira da haisam sau dubu da suyi fayayansahabib tun suna yara saboda haisam yake magana acikin nutsuwa yake kalamansa masu muhimmanci akoda yaushefuskarsa cike da annuri(fara'a),wasa da dariya damanya dayara. Bashi da raini ga hakuri , baya ga zunzurutunkokari da allah ya bashi a bangaren karatunsa dukka akur'ani da bokonyasan alkur'ani kamar me a kansa duk gidansubabu maiiliminsa. Hatta mahaifinsa yakan yi masa tambayoyiakan duk wata matsalarsu ta addini ko ta zamani, yana datsananinhakuri sau tari ana masa abu da yawa yayi hakuri.Ammakuma duk gidansu babu mai zuciya kamarsa idanaka kureshi, idan yayi fushi abin babu kyau mai hakuri bai iyabacin rai ba.Da farko a enugu state aka turashi bautar kasa(n.y.s.c) kasancewar shakuwa da sabon da mahaifinsasuka yi dashi basa so yayi musu nisa don haka alhaji abdulhamidyasa adawo dashi kurkusa saboda yasan manya manyakasar nandaga yan boko har rukakkun yan kasuwa. Ammaduk da haka haisam yana korafi shifa kazaure yayi nisa da kanoa dawodashi cikin kano inda kullum zaina kwana gida, dakyar dai akalallasheshi yayi hakuri duka duka bazai yi shekaradaya ba zai gama ya dawo gida gaba daya. Don haka dukjuma'a yaketafiya gida wani lokaci ma a kanon yake yin sallarjuma'a sailahadi da yamma ake dawo wa dashi. Gashi yanzuma baifi saura wata uku ba ya kare bautar kasa kwatakwata ma yakoma daya ke muradi.Bayan tafiyar hanne gidan uwar biyu da kwanauku wato ranar laraba da sassafe sai ga wata mota an kawo hannemakarantahaisam ya roki wani abokinsa safiyanu yaje cangidan uwarbiyu ya dauko hanne da kayanta ya kawotamakaranta. Haisam ya gama mata siyayyarta kakaf ko yaranattajiranmakarantar baza su fita kaya ba(provision)kayanmakarantarta (uniform)suma har kala kala bibiyuyayi matatakalma kuwa kala kala akwai kito, sandal , kambos fari dabaki tsadaddu, silifas dan madina har biyu, ya suyomata dawasu yan kanti riga da siket suma kala biyu. Yasuyo matajakar zuba kaya mai kyan gaske yar madaidaiciya wato (travelling bag)a ciki aka zubawa hanne kayansawarta, nata nada kuwa yana gidan uwar biyu, kayan tande tandedamakulashe kuwa abun baya lissafuwa kama daga biskit kalakala, alewa (chocolate)indomie, madara, milo,sugar ,complakes da dai sauransu ko gari babuballe wanikanzo irin na yan makaranta makilin da brushhadaddu, mayukan shafawa da sabulansu masu kamshi gamayukangashi cike a akwatin hanne hankar da kaya allahya taimaketasa kansilansu ya tashi kawo maya akwatin yakawo mata randimemiya, mai cin kaya da yawa.Hanne sanye take da kayan makaranta(uniform)kafar ta kumafarin kambos ne da farar safa an tufke kitson kantada waniribom mai kyau mai fulawa, duk wanda yaga hanne kwanakibiyu da suka wuce a yau dai bazai gane taba tayifari kyalkamar yar larabawa, ashe mai dangwali ya ba neda bakinkwalli suka cabe mata fuska tayi baki kirin. Safiyanu yazobakin offishin malamai ya tsaya da motarsa sannanya fitodaga ciki ya juya ya kalli hanne wacce ke zaune abaya tanakokawa da murfin kofa ta kasa budewa abunka fa bakauyiiya.Wannan ne karo na farko da hanne ta taba hawadon hakabata san ina zata ja kofa ta bude ba. Safiyanu yazagayo dasauri ya bude mata, ta fito yace'' to dauko jakar litattafan nakimana'' hanne tasa hannu ta jawo wata bakar jaka(schoolbag)tsadadda mai kyan gaske, yar madaidaiciyadaidaibayanta cike take da kitattafan rubutu da litattafan karatu(textbook)duk dai kamar yadda aka zano ajikintakardar babuwanda haisam bai siya mata ba ga biruka da fensirdamathematical set din su ya suya mata . Safiyanu ya nunawahanne yadda zaya rinka ratayawa a bayanta tarataya sukanufi cikin ofishin. Suna shiga suka iske wani malamibayansafiyanu ya mika masa hannu sun gaisa sai yayi masa bayaninabunda ke tafe dasu yace daliba ya kawo, sai yanuna masaofishin vice principal yace nan zasu shiga.sukayi sallama suka shiga suka iske viceprincipal yanaharhada wasu takardu a gabansa, bayan syn gaisasafiyanu yashaida masa cewa yarinya ya kawo yar aji daya cesabuwar zuwa sai ya nemi daya bashi takardar shaidar cewaita dalibarnan makarantar ce wato (joining instruction)daman haisam yabashi ya dauko ya mika masa ya duba yace''sunanta hanne habu imamu daga babban mutum ko ? Safiyanuyace ''eh,''vice principal din nan ya kurawa hanne ido yanakallozuciyarsa cike da mamaki ga yarinya kyakykyawakamar baturiya gashin kanta har baya amma duk dama antufkemata da ribon amma kuma sunnan kauyawagareta gata kumadaa kauye. Ya ce a ransa'' wata kila dai asalin garinsune babban mutum din amma daga birni take, can yanisa yace''babu komai,'' ya jawo wani littafin rasitai ya budeyace dasafiyanu'' sai ku bibbiya kudaden in baku rasitai dasauri don yanxu lokaacin assembly ne, don taje ta shiga cikindalibai ayida ita. Vice principal ya lissafawa safiyanu yawankudade dazai kawo safiyanu ya dauko ya bashi, shi kumayana rubuta rasitai har ya biya kudin komai ya ce '' sannan yafadi sunandakin da zata je, sannan zata je j.s.s. 1A ajin malamhaisamsunan ajin, yanzu ka kaita hall ayi assembly da ita,kayanta kuma a barsu a nan bakin staff room ana tashi tazozamu samaigadi da prefect din dakin suje ta bata gado.Safiyanu ya ce''to'' yayi godiya suka fito yana sake yiwa hannebayani akan abinda vice principal ya ce, yana kuma karalallashinta ganinyadda nan da nan ta canja hankalinta yayimummunan tashidaga shigar su ofishin vice principal duk kwalla tacika mata ido saura kiris ta fashe da kuka. Yace mata'' kar kiyikuka nanmakaranta ce karatu kawai za.a koya miki babumai zaginkiballe duka kinji. Gashi ajin malam haisam za,a kai kidon haka baki da matsala zai kula dake''suna tsaye a bakin baranda yana yi mata nasihasaiga viceprincipal ya fito daga ofishinsa zai tafi hall wajenassemblyyace'' ah har yanzu bata tafi assembly ba ai gara kuyi sallamata tafi,'' safiyanu yace '' aima shikenan mun gamadaman halldin zan tambaya don bamu ganshi ba,'' viceprincipal t harcikin hall din yashige da hanne a lokacin principal tana bayanihall din yayi tsit kowa yana sauraro. Amma dagashigowarhanne da vice principal sai kowa hankalinsa yakoma ga kallonhanne. Hanne ta zama yarinya ''yar dagwas 'yar karama maikyan gaske akwai dubbunan dalibai a makarantardaga jahohidaban daban amma babu mai kyawun hanne watokamarwata tauraruwa ce mai haske a cikin taurari. Sai sheki take danfarar fatarta hanci har baka, dan karamin baki,gazar gazargashin gira dana ido fatar jikinta luwai luwai irintayan hutuamma ita dai daga innallahi. Ga ido dara dara bata da kibakuma bata cika tsaho sosai ba gata dirarriya duk dadaikarama ce masassakin budurci bai fara sassakataba. Wasukitso ne yiri yiri aka yarfa mata kamar bada hannu aka yisuba. Hanne tayi kyau kwarai da gaske a cikinkayanmakarantar nan ga 'yar jakar litattafanta a baya.Babu wandazai kalli hanne bai sake juyowa ya kalli halittar ubangiji ba.Dalibai manyansu da yaransu babu wacce bata cedama nicewannan ba ko kuma ace 'yata ce a ransu ba. Hattahaisamwanda ke tsaye a bakin kofa bai gane hanne ba. Suka zo sukawuce ta gabansa ya bita da kallo sai dai a zuciyarsayaketambayar kansa da kansa ina nasan wannanyarinyar?Tabbasa na santa a wani waje, sai daga baya zuciya ta bashiamsar cewa wannan itace hanne habu kenan. Yayimatukarmamaki ganin yadda hanne ta koma haka a kwanabiyu,hanne ta tsorata ta kuma rikirkice ganin dubbunnan idanuwacaa a kanta, ta tsaya cak, ta kasa tafiya tana shirinfashewa dakuka.Vice principal yayi kiran wata prefect dake tsaye agefe yace tazo ta kaita layin 'yan j,s,s 1A. Tazo ta kamahannun hanne takaita layin ajinsu ana ci gaba da assembly kamaryadda sukasaba. Bayan principal ta gama jawabinta, viceprincipal ma ya fadi albarkacin bakinsa sai aka nemi sauranmalamai sucewani abu akan dokar makaranta. Bayan sun gamaaka yinatsonal pledge kowa ya kama gabansa, ya nufiajinsu. Hanne ta tsaya cak a inda take tsaye tana kallon dalibaikowa yanatafiya ajinsa ta rasa ina zata nufa. Haisam ya matsokusa da itaya ce'' hanne yaya kika tsaya bakya gani kowa yanufi ajinsu ke kika tsaya idan baki sani ba, ba sai ki tambaya ba.To nanmakaranta ce kowa ta kansa yake, gara ki rinkatambayar dukabinda baki sani ba, muje in nuna miki ajinnaku, hanne tace'' to'' ta bishi suka doshi bangaren da ajujuwa sukeyaci gaba dayi mata nasihohi akan kada ta sake ta zamawawuya, idan bahaka ba sai sauran dalibai su raina mata wayo tazama duk abunda bata sani ba ta tambaya musamman idanmalamiyana darasi idan bata ganeba tayi masa tambaya.Hanne nasauraro da alama kuma nasihohin suna shigarta.Haisam ya kalleta yayi dariya ya ce'' hanne ince kin zamacikakkiyardaliba babu wannan damarar? Hanne ta kyalkyaleda dariyahaisam yace'' to tunda kin zama yar birni 'yar bokomai aji to yanzu komai naki yzai koma na aji, kin san abundanake nufi?Hanne tace ''a'a'' yace to sunanki zai tashi dagaHANNE HABUIMAMU ZAI KOMA HANNAH ABUBAKAR IMAM.kowaya tambayeki sunanki kice..'' kafin ya fada cikin murnada farinciki tace '' hannah abubakar imam'' haisam yatuntsire dadariya yace harma kin rike sunan kenan? Hannetace eh hannah yafi dadi Allah'' a daidai wannan lokacisuka haubarandar ajin haisam ya wuce gaba ya shiga ajinhannah nabiye dashi a bayasuka shiga dukkan daliban ajin suka mike dongirmama malaminsu suka hada baki dukkansu''good morning sir'' haisam yayi murmushi yace''morning how are you ? Suka sake hada bakisuka ce'' we are fine sir'' yace thank you sit down ''kowacce ta zauna akan kujerarta. Haisam ya jawo hannah gaban aji yace'' ga wata sabuwar dalibakun samu'' rauda itace monita ta mike tace'' lah ,what is your name ? Hannah ta daga ido tanakallon haisam'' ya harareta ma'ana ta bada amsa ,hannah tace'' my name is hannah abubakar imam''kama yadda haisam yace ta dinga fada. Nusaiba wacce itace mataimakiyan monita tace'' emh, nicename you are welcome hannah'' haisam yayimurmushi ya ce'' kun fara iyayin naku ko ? To mazaku saka mata kujerarta a tsakiyar taku a gabakuma kunga itama yar kucila ce kamar ku'' cikinsauri rauda taje bayan aji ta dauko kujera ta kawo ta koma ta dauko tebur yazo ta dasa a tsakiyar su ajere. Dake duk ajin su duka ukun sune kanananajin sunfi kowa kankanta kasancewar akwaidingin dingin din yammata a ajin musammankabilun na wata sai ka rantse uwa ce amma yar ajidaya ce farin ciki ya lullube hannah da haisam musamman ma haisam yaga hannah ta samu shigaa wajen nusaiba da rauda wadanda su suka fi dukyan ajin kokari dan rauda a america tayi karatunnusery da primary dinta don haka tana bala'inkokari ga turanci daya kama bakinta hausa matana kokarin ta subuce mata.Kuma auwal abokin haisam ne na kuttan kaibabanta alhaji shitu abokin baban haisam nesannan ramla yayarta ita haisam zai aura don hakanema aka kawo rauda makarantar saboda haisamyana nan tazo akayi mata jarabawa taci shikenanaka dauketa, don haka nema take kiransa da yaya haisam sabanin uncle haisam da sauran dalibaisuke kiransa. Nusaiba ma wata tsadaddiyarmakaranta ta gama a abuja, ita yanzu hakaiyayenta suna abuja karatu ya kawota nan ammasu haifaffun garin gwambe ne fulani, rauda danusaiba sun zama kawaye tun ranan da suka hadu ranar da aka kawosu makaranta, ajinsu daya sukakuma ci sa.a dakinsu daya don haka ga gadonrauda ga na nusaiba kuma sun hada kayanakwatinsu. Haisam yace monita da mataimakiyartaku biyoni waje ina da magana daku rauda danusaiba suka mike suka bi haisam wajen ajin. Hannah na zaune babu abunda take sai kallonginin ajin da dalibai daya bayan daya taga kowaccesanye da uniform dinta tsaf tsaf, fararen takalmakambas da fararen safa kan kowacce kitso ne tar.Hannah tace a ranta ashe da na sha kunya da aceranar da baba ya kawo ni a haka na shigo ajin nan da na fita daban, kai wannan malami ya taimakeniallah yayi masa albarka. Taci gaba da kallon gininajin da irin zane zane da akayi a takarda duk anlillika a jikin bango ga fankoki a jikin silin sunatafitar da sansanyar iska suka , ginin bulo hannah tafada a fili ba tare data san a baiyane ta fada ba, bayan fitarsu haisam a bayan ajin suka tsaya yakalli rauda ya juya ya kalli nusaiba yace raudanusaiba su duka suka amsa yaci gaba da cewa gahannah nan , kamar rauda kike kawar nusaiba tohannah ta zama kawarki itama, sannan kamaryadda ke nusaiba kike kawar kawar rauda to ina son hannah ta zama kawarki duk da ku biyudakinku daya to hannah ma yar dakin kuce dakesafiyanu ya fada masa sunan dakin hannah yacedon haka ku uku dakinku daya ajinku daya. Kamaryadda a ko ina kuna tare a hall ne, a ajine a daki neto hannah ma ta zamana kuna tare itama kanwata ce kunji ko ? Su dukka suka amsa. Nusaiba tace''uncle haisam ko baka ce mu zama kawaye badaman zamu zama tana burgemu'' haisam yayidariya ya juya ya kalli rauda yace'' kanwata ke bakice komai ba ke bata burgeki ? Rauda ta tabe bakitace'' yaya haisam rannan fa kace nice kadai kanwarka a makarantar nan yanzu kuma kace itace'' haisam ya kyalkyale da dariya ya dafa kantayace!! Rauda kenan, ai har yanzu kina nan amatsayinki na kanwata itama hannah yar uwata cekibga dole kanwatace, nusaiba ma kanwata ce donhaka karki damu. Gata nan duk abunda bata sani ba akan karatu ki koya mata. Haka kuma maganada turanci ku rika tunasar da ita koda ta manta tayihausa karku rubuta sunanta a masu yin hausa sai ahankali zata saba itama ta rinka yin turanci sosai.Haka a daki idan bata san yadda zata yi amfani dawani abu ba kamar man gashi in zata shafa a jiki ku nuna mata mata na gashi ne ba ku ringa yi matadariya ba kuna gayawa kawayenku kunji ?Musamman ke rauda kinga rose suna yawan kawomun kararki wai kina yi musu tsawa kar in sakenaji kina yiwa hannah kinji ko ? Rauda tace''yayaya za'ayi ta shafa man gashi a jiki sai kace bakauyiya'' haisam ya ce a,a wai a misalai nakenufi, koda ace zata manta ta dauko man gashin''tafiyar wani malami ce tasa duka hankalinsu yahuya baya don ganin mai tahowa, haisam yace'' toshikenan ku koma aji ga malam shaiya nan zaikaya muku maths an kada firs period,'' suka ruga a guje, malam shaiya ya mikawa haisam hannu sukagaisa sannan ya nufi s.s.3c yana da period yanakoya musu geograpykamar haisam yayi duba da yace idan ta daukoman gashi zata shafa a jiki haka kuwa aka yihannah babu abunda ta sani a kayan akwatintadaga ta dauko man wanke gashi [shamppoo] takwaba a jikinta sai ta dauko man shafawa ta makaa kanta makilin ma wani lokaci a tsagar kitso rauda tazo ta isketa tana sharbawa. Suyi ta dariya har sugodewa allah daga karshe dai suyi mata bayanidalla dalla , wannan ne na kaza wannan kuma awaje kaza ake shafawa. Babu laifi a sati biyuhannah ta waye ta gane duk kayayyakin amfani nazamani sannan ta koyi cin kayan gwangwani dana kwali, don da farko inda suka dama comflask damadara cokali daya zatayi sai ta fita a guje ta kelayaamai bata sanshi ba haka sardine da gesha kifingwangwani sai taki ci tace tsutsace amma dagabaya duk ta waye tana ci. Hannah tana farin cikimatuka da wannan sabuwar rayuwar data tsinci kanta. Abinci lafiyayye a akwatinta na makaranta ,gashi tana cikin yara sa'anninta suyi karatu taresuyi wasa tare musamman nusaiba tana bala'inkaunar hannah tafi rauda kirki don rauda ta cikanuna isa da nuna tafi kowa kuma duk girmanka saita riga daka tsawa.Ta fannin karatu kuwa. Ada hannah dumama kujera take yi kawai saboda tsantsar turanci ake yia makarantar amma sai nusaiba ta lura hannahbata fahimta don haka a koda yaushe bayanmalami ya gama darasinsa sai ta matso da kujerartahar kusa da ta hannah tayi mata bayani dalla dalla. Haka shima malam haisam kullum a prep dinyamma yana zuwa ya kira hannah ya koya mataabubuwa da dama. A wata daya hannah ta faragane turanci fiye da yadda kuke zato. Ranar wataasabar da daddare ranar ne ake warewa dalibai sushakata su hole rayuwarsu kamar a saka musu kidan disko su cashe wasu kuma su kada tebur dakansu suna waka wasu na rawa. Wasu kumatalabijin ake kunnawa da bidiyo suyi kallon kasetduk dai abunda ransu keso shi zasu yi. Daga 'yanj.s.s 1 har manyansu s.s.3 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 2 Posted by ANaM Dorayi on 02:02 PM, 30-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura Wannan rana ita ake kirada '' social night'' uncle haisam kuma shine social master wato shine malamin da yake kula da dalibaiyake kula da c.d din da ake kunna disco da bidiyoda talabijin din da ake kunnawa. A wannan dare anyarjewa dalibai su saka kayansu na gida{persinal}kowane iri ne kama daga leshi ko shadda riga daskit kai har jeans da tea shirt duk zasu iya tsukewa. Rauda sarkin rawa ita har tunanin wannan asabardin wacce irin rawa zanyi don har fili ake batakowa ya koma gefe yana kallonta rawa salo salohar wasu suke kiranta janet jacson wai kanwarmacheal jacson nusaiba kuwa ita da hannaah babuabinda suka fi so irin kallon bidiyo hausa fim masu kyau malam haisam yake samowa ko nigerian fims.Social night din wannan asabar din bata yiwahannah da nusaiba dadi ba saboda bidiyo talalacebabu kallo sai dai c.d aka kunna aka ware kida dukmai bukata yaje ya cashe wasu na rawa wasukuma na gefe suna kallo. Amma wasu suna kan barandar wajen hall din a zazzaune basa sha'awaryin rawa ko kallon masu rawa kungiya kunkiyakowanne da group dinsu suna waje suna zazzaunesuna hirar duniya. Hannah da nusaiba suna dayadaga cikin wadanda basu shiga cikin hall din bawajen kida suna zazzaune a can kan wata barandar ofishin malami suna hirar duniya, hirarma ma jifa jifa suke yi saboda duk rayukansu abace yake yau babu kallo kuma wani hadaddenamerican film mai suna''mr bones''uncle haisamyayi musu alkawarin zai saka musu. Nusaiba tayiajiyar zuciya tace anya kuwa yau zan iya bacci saboda bakin ciki na kudiri niyar danin firm dinnan,wallahi fim din akwai abin dariya muna dashi fa agidanmu. Hannah tace na last week ma yayi kyauga abin dariya osofia in london yaya haisam ya iyazabo man films masu kyau. Wata murya ce abayansu tace na kamaku kuna gulmata'' suka juya da sauri sai suka ga yaya haisam ne su duka sukatuntsire da dariya ya zagayo suka matsa masa yashiga tsakiyarsu ya zauna yayi murmushi ya cekuna gulma ta ko, dan ban kunna muku kallo bako ? Nusaiba cikin shagwaba tace'' yaya haisam harkwalla nayi fa wallahi yau duk ranmu a bace yake. Haisam yayi dariya yace'' kai haba harda kwalla ?Ke fa hannah kema kinyi kukan ? Tayi murmushitace a.a banyi ba uncle haisam. ''yaci gaba da jansuda hira yana zolayarsu kamar yadda ya saba wasada dariya da dukkanin daliban makarantarmusamman da wadannan ukun. Ya ce dasu '' ga rauda can a hall tana cashewa kuje ku tayata manako kuma kuyi mata liki. Suka danyi dariya suka ce ''mu bama rawa'' suka ci gaba da jugum , haisam yalura yau dai nusaiba da hannah babu kanta basason magana balle doguwar hira yace nusaiba,hannah yaya haka kowacce tayi zugum babu nishadi kamar yau ba ranar social night ba. Nusaibatace''yaya haisam tsabar bakin cikin rashin kallonnan ne yake damunmu.'' yace shi yasa baku fara'a?To yanzu daya bayan daya sai kun yimin waka darawa tunda yau social night dole kuyi murna'' cikinshagwaba nusaiba tace''yaya ni bana iya waka ba sai dai hannah ta fara tunda itace karama. Hannahtayi dariya tace to bari inyi muku wakan sarkingarinmu,'' hannah ta fara tafi ta fara rero waka.Haisam yace'' to tsaya tafi akeyi muma mu dingatayaki muna muki amshi ? Tace'' ai da kwarya akekida dan dai babu kwaryar ne. Yasa hannu a aljihunsa ya zaro wannan abun busar daya karba awajenta ya ce zai ajiye mata ya ce'' ga abun busarkima ki busa mana ki rero mana wakar kiwo'' cikinfarin ciki hannah ta karbi abun busarta ta haujujjuyashi tana cewa'' allah sarki abun busata nadade ban busa kaba,'' nusaiba tace '' lah busa muji yadda akeyi'' hannah ta kaikaice ta fara busa abunbusarta tana rera waka kamar haka. muyi kiwosamari. Kuyi kiwo yan mata kiwo baiwa ne. Wakabaiwa ce. Haka busa ma baiwa ce kuyi soyayyasamari. Kuyi soyayya 'yan mata ke 'yar budurwaina naki gwanin ? Ni nawa gwanin baya nan. Yayi tafiya amma koda bana tare da gangar jikinsa.Ruhinsa yana tare dani. Haisam yace '' hannahtsaya meye koda gangar jikinsa bata tare daniruhinsa yana tare dani ''? Tayi shiru can tace ohonima haka ya mun wakar nusaiba tace meye ''ruhi ? Hannah tace '' nima ban sani ba, ina jin larabci ne , haisam yayi dariya ya ce '' yarinta mai dadi. Kwanci tashi yau kwanan hanna arba'in amakaranta har an kafe musu tine table dinjarabawa wato end of 1st teem examinationkasancewar daman dalibai sai da suka yi kimaninwata guda da dawowa makaranta sannan akakawi hannah babu abunda yaya haisam yake yi sai nasihohi da yake yiwa yan ajinsa wato j.s.s 1a dakowacce ta cire wasa tasa littafin karatu a gabantadon suci jarabawa. Haka kuma wasu lokuta ya kankira kannansa rauda, nusaiba da hannah yanakara musu fada dasu dage sufi kowa cin jarabawaya sake xewa'' hannah bana jin fargabar su rauda kamar ke don haka ki dage duk abunda ba ki saniba ki tambayi nusaiba ko rauda idan sun sani sukoya muki, idan kuwa basu sani ba to kuzo kutambayeni. Haisam yayi musu rantsuwa da allah acikin su ukun nan duk wanda ta fadi jarabawartasai yayi mata bulala kuma daga ranar data fadi jarabawa babu ruwansa da ita ya cireta a cikinkannansa gaban hanna ya fadi rasa dajin bayaninyaya haisam tace a ranta tace idan yaya haisa yacebabu ruwansa dani aina shiga uku tunda babu maiyimun siyayyar makaranta karshenta ma karshenkaratuna yazo. Ta kudiri aniyar daga yau babu ita babu cikakken bacci zata dage da karatu don tacijarabawa kada haisam yayi fushi da ita. a sati dayasu hannah suka gama jarabawarsu,jarabawabibiyu suke a rana daya. Don haka babu hutu badare ba rana kowacce ta dukufa da karatu,musamman hannah sallah ce da cin abinci tashinta daga kan littafin karatunta, haka kuma ta zanajarabawar cikin sauki ma'ana da an bata questionpaper sai taga tasan amsoshin gaba daya, hakatake amsasu cikin sauki saboda tsaban ta gamakarance litattafanta, hannah tasan yaya haisamzayyi murna da sakamakon jarabawarta tunda tayi karatu yadda ya kamata. Hutu kuma sai juma.a donhaka dukka wadannan ranakun babu abinda sukeyi sai wasanni da raye raye da wasanninkwaikwayo na kungiyoyi (club)din makarantarkasancewar akwai kungiyoyi daban daban amakarantar kaar english club, hausa club, jet club. Che,ical club, geography club. Yoroba da igbo dadai sauransu, kuma kowacce daliba daga yar ajidaya zuwa shida tana da damar da zata shigakowanne club a makarantar. Su kuwa malamaicikin satin nan suka dukufa da aikin makinjarabawar dalibai, don ganin kafin ranar hutu sun bawa kowacce daliba sakamakon jarabawarta tatafi dashi gida iyayenta su gani. Ranar alhamis anagobe hutu haisam ya tara 'yan ajinsa a bakinbabban dakin taron dake makaranatar wato halldon ya bawa kowacce sakamakon jarabawarta(report card) 'yan ajin malam haisam suna da dimbun yawa don dalibai saba'in da shida ne a ajinhausawa da yarbawa,igbo,musulmai da kiristocisma da talatin ba hausawa bane kuma ba kiristocibane, wata ko zo bata sani ba da hausa, tundadaga kudu suke babu abunda suka sa a gaba saikaratun littafinsu don shine abunda ya kawosu tun daga uwa duniya zuwa nan arewa. Don haka babukoma baya a ciki kowacce tayi iya kokarintamatuka a wannan jarabawa. haisam ya kallifuskokinsu daya bayan daya sannan ya kyalkyaleda dariya. Abun mamaki babu wacce ta taya shidariya kamar yadda suke wasa da dariya a aji yau kowacce fargaban jin sakamakonta takemasamman ma hanna. Tunanin maganar da yayahaisam ya fada yayi musu ranstuwa yace dukwacce ta fadi jarabawa sai yayi mata bulala kumababu ruwansa da ita. Hakika bata fargabar bulalarsosai tafi fargabar babu ruwansa da ita din daya fada, idan haisam ya cire hannunsa akan hannahwaye kuma ya tsaya mata a duniya yadda takekaunar makarantar nan aiko hutu bata so ayi. Watohannah na daya daga cikin yan kwaleji tafi gidadadi, ga uwa uba kwanciyar hankali wasa dadariya da kawayenta sabanin a gidansu sai bauta. Anan makaranta akan sasu aiki ko aike ammabamai wahala ba kasancewarsu kanana 'yan ajidaya dole seniors zasu aikesu. Haisam yace ''oh''yau babu dariya duk kunyi cirko cirko kuna jiransakamako to da yawa daga cikinku kunyi kokariamma wasu basu yi kokari ba don haka wadanda basuyi kokari ba sai sun dage idan ba haka bakarshen shekara za'ayi musu repeating kowa yawuce aji biyu a barku a aji daya ku sake maimaitashekara,. Gaban hannah ya sake fadi ras sai addu'atake sannan taji dan saukin dukan da zuciyartatake yi mata. Haisam yace'' yanxu zan fara kiran sunan wadanda suka yi na daya zuwa uku sai atafa musu zan basu kuma kyaututtuka sannan nakirawo na hudu zuwa goma zuma zasu fito a tafamusu sune suka fi yin kokari sauran kuma sai kudage nan gaba ''hadiyar yawu yake ji mukut mukutdakiban nayi don faduwar gaba dariya ta sake kecewa malam haisam ya girgiza kai , sannan yabude file din dake hannunsa yace'' dalibar datayimatukat kokari ta zo ta daya itace Rauda shitu muktar ta kwalla kara don dadisauran suka sa tafi suka juyo suna mata kallonsha'awa kowacce a ranta tana dama nice raudashitu a ransu haisam ya ce taso'' fuskarta cike dafara'a zuciyarta cikw da farin ciki tazo ta tsaya agefen haisam yaci gaba da cewa, sai kuma wacce tazo na biyu itace nusaiba idris,'' farin ciki ya lullubenusaiba itama tazo kusa da rauda shitu ta tsayadalibai nayi mata tafi raf raf, ta uku kuma itacepamella matin benin,pamella ta daka tsalle danmurna ana tafa mata itama ta fito ta tsaya kusa danusaiba idris'' hannah na lungu ta kankame guiwarta da hannayenta ta zura kanata a matsematsin cinyoyinta yayin da kuka ya kece mata.Taga kawayenta biyu rauda da nusaiba wadandasuke karatu tare sun zo sun fita kokari . Ta gamasaddakarwa yaya haisam ya cire hannunsa dagakanta tinda batayi kokari ba. Haisam ya rufe file din dake hannunsa ya kalli sauran daliban da sukezazzaune a kasa yace'' kunda wadannan ukunsunfi kowa kokari a ajina don haka zan basukyaututtuka da zasu je gida su nunawa iyayensusuji dadi , bawai su daban suke daku ba a.a kumakowacce a cikinku ta dage zata iya zuwa na daya, biyu da uku. Don haka duk wacce take so itamanext term taji sunanta a cikin wadannan ukun to tadage da karatu. Don haka to ku sake tafawarauda,nusaiba da kuma pamella. Tafi raf raf raf yadinga tashi saida haisam yace ya isa tukunna sukadaina. Ya dauko wata katuwar anbulan wacce aka like ta da salataf an yi rubutu da maka dara darakamar haka. FIRST POSITION IN J.S.S 1A RAUDASHITU MUKTAR ya mikawa rauda , daliban suna tafamata raf raf yace taje ta zauna, ya sake dauko watawacce girmanta bai kai girman na rauda va, itamaan like jikinta da salataf an rubuta SECONG POSITION IN J.S.S 1A NUSAIBA IDRIS Ya mikawa nusaiba akatafa mata ta tafi ta zauna itama. Ya dauki ta karshenitama girmanta bai kai ta nusaiba ba, ajikinta anrubuta. THIRD POSITION IN J.S.S 1A PAMELLAMARTINS BENIN Aka tafa ta karba da murna ta tafita zauna, haisam yace''to yanxu san kira na hudu zuwa goma suma su fito nan su tsaya a tafa musudon suma sunyi kokari matuka.'' fargaba ta sakedira a zuciyar hannah. Tace a ranta' idan kumabana cikin mtane goman nan ni kaina nasan banyikokari ba, shi kenan karshen makaranta na yazodon nasan tunda malam haisam ya rantse nasan da gaske yake sai ya zaneni sannan ya korani gida, tarushe da kuka dan ta tsani wannan kalman ta gidasaboda tsananin da ake yi mata da azabtarwa .Baya ga bautuwa ga horon yunwa, babu wankako tayi wankan ma kusan daya ne da batayiba,don wankan babu sabulu, sai wani lokacine idan tayi wanke wanke dan omo yayi saura takeboyewa tayi wankan dashi shima a sati baifi sodaya ba anan kuwa sunkinan sabulu zesr haisamya siya mata, ga mayukan shafawa iri iri ba kalarkitson bane ko tayi kitsin kwana biyu ya farazamewa . Amma yanzu da ta sami mayuka masu sashi yayi laushi sai take wankewa da man wankegashi ta mulke da man gashi tasa ribon ta dauretamkar indiya baki sidik a kwance fatar jikinta tayiluf luf sumul sumul ba ita ba, ita bata ki har shekarashida ba'a yi hutu ba . Malam haisam yaci gaba dakiran daliba ta hudu, ya kira ta biyar, ta shida hannah bata ji sunanta ba, ya kira bakwai da tatakwas. Sai kukan da take ya kara tsananta har nakusa da ita suka fara jiyo sheshshekar kukan datake yi suna juyowa suna kallonta, haisam ya kirata tara sannan ta goma yace '' hannah abubakarimam . Shima sai yayi ajiyar zuciyar jin dadi hannah ta mike ta taho idonta tamkar anyi wasan ruwakaca kaca da hawaye. Haisam ya dafa kanta yacehannah kukan meye kike shashsheka lafiya ? Yishiru goge hawayenki kinzo na goma kinyi kokari''dadi da kwanciyar hankali suka lullube hannahyasa aka dinga tafa wa daliban da suka zo na hudu zuwa na goma. Daga karshe yace su koma suzauna yaci gaba da kiran dalibar data na goma shadaya zuwa saba'in da shida ta karshen kenan watagandamemiyar ajin ce tafi kowacce girma a ajin maisuna eneka eddiward itace tazo musu ta karshe, dayawan dalibai suka rushe da kuka jin malam haisam ya furta repeating suna tunanin shikenanza,ayi musu repeating haisam ya shiga lallashinsuyana cewa kowa tayi kokari babu wacce za.ayiwarepeating kasancewar da damar da zasu iyadagewa nan gaba ba.ayi second term ba balle thirdterm sannan suka ji dan sanyi a ransu suka fara goge hawayen daya jika musu ido. Hannah takoma gefe tana kallon jifgin mutanen data kayaryayin da zuciyarta take jinjina mata ai kinyi matukarkokari tunda kin wuce mutane sittin da shida, farinciki ya lullube zuciyar hannah. Ta sake sa randawowa makaranta idan hutunsu ya kare kasancewar taji haisam ya yaba da sakamakontadon haka zai sake yi mata siyayyar makaranta dabiyan kudin makaranta da aka ce duk term akebiya kuma dubunnan nerori. bayan kowacce tayishiru da kukan da dayawa suke yi sai haisam yace''duk kunyi kokari kasancewar 'yan ajin babu marar kokari yace kowacce tazo ta karshe anan ajin ne ab.c. Ko d ita zata zo musu ta wajen goma sha waniabu, kunga kowacce tayi kokari karku damu. Yadauko wata katuwar leda a gefensa ya ce dai dai suringa tasowa suna karba.Biscuit nemai dadi ya rarraba musu kowacce daliba ta samutun daa kan rauda har eneka eddiward kowacce tafara murnar tayi kokari. Da haisam yaga duk sunware yana musu wasa da dariya sai yace'' ina si na shaida muku daga yau ko kuma ince daga dagagobe ranar hutu idan na tafi hutunnan shikenan natafi kenan. Gaban kowacce ya yanke ya fadi. Bamugane ka tafi ba kenan uncle haisam '' su duka sukatambaya . Haisam yayi murmushi yace ''kun san nicopper ne. Nazo ne yin bautar kasa wannan makarantar(N.Y.S.C)KUMA yanxu lokaci yayi damuka kare don haka idan na tafi hutun nan bazandawo makarantar nan ba. Ina muku fatan alherikuma shawara nake baku akan kowacce ta dagetayi karatu banda wasa '' kowacce jikinta yayi sanyifuskarsu alamar basu ji dadin wannan batu na class master dinsu ba . Suna son haisam saboda kula dasoyayya da yake nuna musu wasa da dariya akoda yaushe sai wasu dayawa daga cikinsu sukarushe da kuka. Babu kamar rauda, nusaiba dahannah, ai kuma gara rauda da nusaiba akanhannah wani sabon tashin hankali ya rufta mata fiye dana dazu. Haisam zai bar makarantar nan itakuma ina zata dosa ?''.Haisam ma wani tsananin bakin ciki ne yamamaye a zuciyarsa yana tsananin son yan ajinsa.Baya so ya tafi ya barsu yana tausayinsukasancewar yan yara babu kuma wani malami komanyan daliban da zasu zauna suna basushawarwari kamar hannah, wa zai kula da hannah? A bar zancen kudin makaranta da siyayya(provision )ita kanta tana bukatar a kula da ita dakara karfafa mata gwiwa wajen idan ta tafi hutugida ta dawo makaranta. Koda a gida an ce baza tadawo ba tasa kuka har sai an dawo da ita. Ga wasuabubuwa da suka yi mata nauyi a aji ma'ana bata ganewa sai shi haisam da kansa yake nunnunamata har sai ta gane. Allah sarki hannah ya fada azuciyarsa ji yake kamar ya rushe da kuka dantsananin bakin cikin rabuwa da dalibansa. Ammaya daure ya dinga lallashinsu, idan wadannnansuka yi shiru sai wadansu su rushe da kuka. Haisam har ya gaji da lallashi yace su tashi su tafidakunansu sai gobe zasu hadu a wajen assemblyhutu, suka nufi dakunansu kowacce na sharbehawaye. Haisam kuma ya nufi gidansa dake staffqurters yana mai matukar jin ba dadi a ransa. Kowayayi shiru ya daina kuka amma banda hannah. Nusaiba da rauda suka dinga lallashinta amma takidainawa taki cin abinci sai tayi kamar tayi shiru tadaina sai ta tuna ta rushe da kuka. Haka ta yini curtana kuka. Rauda tace waini hannah kukan nan dakike yi kinfi kowa son yaya haisam ne ? Ni fa munfikusa da shi babana abokin babansa ne. Kuma yayana auwal abokinsa ne. Haka kuma yata ywadaya uba daya ramla budurwarsa ce koma nacematarsa ce don har ansa musu raba, sanda mukeamerica yan gidansu a gidanmu suke sauka insunje kuma da muka dawo nan kasar saboda yayahaisam ma aka kawoni makarantar nan tunda yana malami yace da abbana makarantar akwai karatu.To harni na hakura na daina kuka ke ba za kihakura ba kamar kinfi kowa sonsa. Ya ce dai kekanwarsa ce kuma ni a sanina 'yan uwansa duk akano suke na sansu kuma amma ni ban sanki ba.Kuma duk yan uwansa babu masu kama dake ke kamar balaraniya kike ko buzuwa ce ni ban saniba'' nusaiba tace'' haba rauda meye haka in ba yaruwarsa bace zai fada ne ? Hannah ta sake rushewada kuka. Daman abunda rauda take yi mata yaisheta. Tunda aka kawo ta malam haisam yacekanwarsa ce taga rauda tana kishi da ita. Wai ya za ayi ace hannah kanwar yaya haisam ce bayan itakadai ce kanwarsa a makarantar. washe gari da sassafe dalibai suka shirya kayansutsaf na tafiya gida suka saka kayan makaranatar(uniform) suka dunguma babban dakin taro (hall)don yin assembly hutu. Hannah nusaiba sukakinkimo jakunkunan kayansu na sakawa sukakuma rarrataya jakar litattafansu a baya. Akwatinsu kuwa da katifu da bokitai a wani daki ake lufgawaa rufe. Ba.a tafiya dasy gida. A bakin hall din sukaajiye jakunkunan sannan suka shiga cikin hall dindan yin assembly. Kallo daya haisam yayi wahannah yasan tasha kuka kuma tana cikin tashinhankali . Principal ta sanarwa dalibai cewa an basu hutun kwana arba'in da biyu. Don haka ranar dakwana arba'in da biyi ta cika kowacce daliba kadata kara ko kwana daya. Idan ta kara to za.a koratagida. Baza a karbeta ba. Sannan tayi musu nasihohiakan idan suka je gida su dinga taya iyayensu aikibanda yawo a gari gidan kawaye balle kuma masu samari. Mataimakin principal ma ya tofa albarkacinbakinsa. Ya jawa daliban kunne akan su zamamasu da.a da ladabi da biyayya a duk inda suke.Saura malamai ma suka yi musu nasihohi akan suyiamfani da abunda principal ta fada musu damataimakinta. Sai kuma daga karshe malami uku da suka zo bautar kasa suka yiwa dalibanmakaranta sallama akan in sun tafi sun tafi kenanba zasu dawo ba. Malaman yan bautar kasar suneuncle haisa, rose iliya da hassan bawa. Dalibaimasamman ma yara sunji ba dadi saboda sun sabada malaman. Musamman haisam saboda kirkinsa da wasa da dariyarsa yasa kowacce daliba tahi tanasonsa. Musamman daliban da take koyarwa sunamatukar bakin ciki da rabuwa da malaminsuwanda ya kware wajen koyar musu da geography.Nanfa dalibai suka rode da surutu wasu na kukawasu na fadin'' we miss you ! We miss you so much!! Uncle haisam, we miss you more, stay don'tgo please. A haka dai principal da sauran malamaisuka fice suka umarci daliban suma su tafi dukwacce aka zo dauka. Hannah da nusaiba a bakinbarandar hall din wajen jakunkunansu suka zauna.Nusaiba tace'' allah yasa dady na tun jiya yaxo kano daga abuja. Ya kwana a kano yau da safennan ya kamo janyar kazaure. Kar ace yau zai tahodaga abuja gaskiya sai yamma zai karaso kazaurewallahi murna nake yi kaman za'a sani a aljannah.Dama ace ina rufe idona na ganni a gida'' hannahtayi murmushin karfin hali don babu walwala a zuciyarta dama ace duk wanda son zuwa gida yadaga hannu sai tafi kowa daga hannu dan ta zaunaa makaranta. Nusaiba ta kallo hannah wacce tunsafe bata murna. Musamman ma yanzu da taji ancehutun kwana arba'in da biyu za'ayi sai ranta yasake baci. Ga kuma babban tashin hankali haisam zai tafi. Nusaiba ta kula hannah ko irin dan dokintafiya gida bata yi. Sai surutu take ita kadai hannahbata sauraron ta sai wani tunani take daban.Nusaiba ta dan zungureta da gefen hanni tace''waike hannah meke damunki ko murna bakya yigida fa yau zamu'' hannah ta nisa sannan ta sake yin murmushin karfin hali tace'' me kika gani ?Wallahi nima ina murna dama na bude ido in gannia gida yanzu'' nusaiba tahi dadi da wannangudunmawar hira da hannah ta fara bata tace'' nikuma ina zuwa gida fruit salad zansa ayi min in ciwallahi shi nake marmari ''Nusaiba ta zabura tace'' meye makani,kwatantamin yadda yake nima idan naje gida incea soyamin'' hannah tace'' ai shi makani dafa shi akeyi. Ba kisan gwaza ba ? Nusaiba tace'' gwaza!gwaza!! Menene ma gwaza ? Oh cocoam zaki cemun. Kai allah ya sawake inci gwaza sai kace wata yar kauye ? Hannah tayi shiru don tasan ita yarkauye ce kuma acan su gwaza abun marmari ne.Nusaiba tace. A ina kuke samun gwaza ni banaganin ta ma ko a kasuwan abuja'' hannah tace mumuna samu'' uncle haisam ne ya tunkaro wajen dasuke zaune , su duka suka mimmike tsaye don girmamawa gami da cewa , good morning sir'' yace'' morning hannah, good morning nusaiba. Yauyammata sai gida naga nusaiba sai murna kike yiko ? Nusaiba tace yaya haisam murna yau nakelamar za'a sakani a aljanna. Haisam yayi dariya yace '' hannah kefa, kema kina murna kaman za a sakaki a aljannah ? Hannah tayi murmushin karfinhali tace'' eh'' ina murna nima, shigowar wata motakirar end of discussion ce ta katse hirar da suketazo ta tsaya. Kafin mutumin da yake ciki ya fitodaga motar nusaiba idris ta daka tsalle mike dagudu ta nufi wajen motar nan tana cewa babama oyoyo. Ya taho shima da saurinsa ya rungume ta suduka murna suke yi. Nusaiba ta ruko hannunmahaifinta ta nufo wajen da malam haisam dahannah suke zaune su duka suka mike dongirmamawa. Nusaiba tace, ga class master mu danake baku labarinsa a wasika nace shi yake kula damu uncle haisam sunansa. Alh idris yayi dariyayace. Oh uncle haisam duk wasikun nusaiba sai tarubuto mana labarinka da kai da kawayentahannah da rauda. Haisam yayi murmushi yace allahsarki ai ga kawarta hannah , hannah ta duka tagaishe shi ya mikawa haisam hannu suka gaisa. Nusaiba tace'' baba daga wannan hutun unclehaisam ba zai dawo ba. Alhaji idris ya ce da haisam''ai dama teaching practice kake yi ananmakarantar ? Haisam yace ''eh bautar kasa(N.Y.S.C)nayi kuma mun gama. Alhaji idris yace badadi yara sun saba da kai gashi zaka tafi, mun gode allah ya saka da alheri. Haisam ya ce '' ba komai aikannena ne.nusaiba ta ciro takarda daga jakarta dabiro ta mikawa haisam tace ya rubuta mata lambarwayar sa. Ya karba ya rubuta mata. Ta karba tamikawa hannah tace '' hannah rubuta min lambarwayar ki a kasan ta uncle haisam'' hannah tayi turus ita bata taba taba wayar bama balle ta sanyadda ake amfani da ita har ta san wata lamba.Haisam yayi sauri ya ce a'a ke rubuta mata taki zatakiraki. Nusaiba ta rubuta lambar wayarta ta mikawahannah, hannah ta karba. Daga karshe hannah takamawa nusaiba jakarta suka nufi wajen mota. Alhaji idris ya bude but haisam ya kama ya saka.Nusaiba ta rungume hannah su duka sunahawaye. Nusaiba tace'' kina zuwa gida ki kirani awaya kuma kullum zamu dinga waya munagaisawa. Alhaji idris ya dafa kansu ya ce '' ku dainakuka hutu za kuje yana karewa zaku dawo ai baku rabu ba gaba daya. Nusaiba da mahaifinta sukashiga mita ya ja suka tafi hannah da haisam sunadaga musu hannu har suka kure sannan sukakoma inda suke zaune da suka zauna. Sai gacincirindon dalibai suka zo suka zagaye haisamkowacce na baiyana rashin jin dadinta game da barin makarantar da zai yi, haisam ya baiyana musucewa in allah ya yarda duk term zai dinga zuwayana ganin su. A haka suka dai suka dinga wasada dariya kamar yadda suka saba rauda ma takaraso wajen ta zauna a hirar da ita basu lura dasanda motar gidan su ta shigo ba, sai kawai suka hango auwal wan rauda ya tinkaro su. Rauda tamike da gudu taje ta rungume yayanta, yanakarasowa ya mikawa haisam hannu suka kashe yace'' malam ,malam haka kake sa daliban naka agaba kuna rera hira ? Haisam yayi murmushi ya ce''bankwana muke yi kasan daga yau shikenan bazan dawo ba'' auwal ya ce wai har kun gamabautar kasar haisam yace ''kwarai kuwa ba famanake da kai ba kazo ka dinga yi mana dan kwanabiyu ma kaki to gashi nima allah yayi min komawagida gaba daya mun zama daya. Ya ce'' lallaishekara kwana ce kamar yaune muka kawoka kamar kayi kuka baka san kauye. Haisam yatuntsire da dariya ya ce'' gashi kuwa na saba yanzuhar bana jin dadi zamu rabu da dalibaina, nan daiauwal ya sami kujera ya zauna shima dake gwaninwasa da dariya ne da mutane ya dinga hira dadaliban nan yana zolayarsu dakyar haisam ya banbaro shi daga wajen daliban nan, auwal dazolaya ya sami yara yana ta zolayarsu musammanhannah, duk da ma baisan yadda take da haisamba yana tayi mata wasa wai ita balarabiya ce takoya masa yarensu yana tambayarta me ake cewayaro da larabci? Tayi dariya tace ban sani va shi a tunaninsa taki fada be kawai baisan ita babalarabiya ba ce. Auwal ya mike ya ce da daliban to ragowar kwakida kanzo na tafi tunda kun zama yan kwantai ba'azo daukar ku ba. Ya kallo hannah ya ce'' ke yaryemen jirgin kasarku baizo ba kema mun tafi munbarki sai kinfi kowa kwantai saboda ke ba yar kasaba ce. Hannah ta kyalkyale da dariya sauran dalibai suka ce'' mu bama cin kwaki bamu san ma yaddakanzo yake ba allahnya sawake kuma mumayanxun nan za'a zo daukar mu. Haka wasa dadariya aka dinga yi da auwal da su hannah haisamna gefe yana kallon yana dariya yace'' da hannahkema dauko jakarki kizo mu tafi na riga na muki signing ke da rauda mu tafi kawai. Auwal ya ce dahannah ''ah ke da nace sai kinfi kowa kwantai ashetare zamu tafi dake ko a filin jirgi zamu ajiyeki ne akano ? hannah tayi dariya tace ''oho ni dai banyikwantai ba'' haisam ya dauki jakar rayda cimaksaboda nauyi ba zata iya dauka va ya kai ya saka a mota.Auwal ya ce da hannah'' kawo kema in taya kitunda vaki da karfi don nasan a garinku bakwa cintuwo sai yar gurasa da zuma ko ? Hannah daimurna take kawai da ba gida za'a kaita ba kanozasu wuce da yaya haisam. Rauda da hannah sukaje suka shiga mota a gidan baya suka zauna, yaya haisam da auwal suma suka shiga motar yayahaisam ne yake yukawa auwal yana zaune a gefe,suka nufi get din fita. Dalibai na daga musu hannuhar suka tafi.rabon rauda da ta yiwa hannah magana tunjiya yau ko magana bata yi mata ba saboda tsabankishi da ita wai saboda yaya haisam yana ji da itaitama yace kanwarsa ce, yanzu taga yan uwantakarta tabbata gata a motarsu yaya haisam zai wuce daita gidansu ma. Ta kalli hannah ta yamutse fuska tace'' kema kano zamu dake kenan, daman a kanokike baki taba gaya mana garinku ba ! Hannah tayishiru ta rasa amsar da zata bata. Haisam ya ce ''ehrauda da ita zamu kano a gidanku ma zata zaunakinga sai ku dinga karatu tare ko ? Rauda tace'' saikace basu da da gida ai a gidansu a nemeta. Cikin rada hannah tace'' babu wanda zai nemeni, ni bazani gida ba. Ta mudubi haisam na kallonta yayimurmushi kawai. Haisam ya nufi cikin garinkazaure auwal ya dubi haisam yace a'a haisam inazamuje mu da zamu kama hanyar kano. Haisam yace'' cikin garin zani akwai wacce zamu dauko. Basu tsaya a ko ina ba sai kofar gidan uwar biyu damana shirye take suna aika yaro yayi sallama ya ce injimalam haisam sai ta fito da gyalanta daman a shiryetake tsaf ta fito. Bayan sun gaisa haisam yace da surauda su matsa mata ta zauna, suka matsa ta shigata zauna a kujera baya sannan suka gaisheta dukkaninsu. Haisam yaja mota suka tafi bai tsaya ako ina ba sai a babbar tashar kazaure ya tsaya yajuya ya kalli uwar biyu da hannah yace'' to ananzaku hau mota ko ? Uwar biyu tace'' eh akwai motahar babban mutum a nan'' uwar biyu ta yunkurazata fita ta juya ta kalli hannah wacce bata da niyyar fita bata ma san da ita za'a fita ba a tunaninta uwarbiyu ce kawai zata sauka ita kuma su kara gaba sutafi kano sai taji uwar biyu tace'' to hannatu fito mutafi ko ? Cikin rudani hannah ta juya ta kalli haisamdon jin abinda zaice sai ya rasa me zai ce matakawai ya sunkuyar da kansa kasa ya kasa magana, ya fito daga motar ya bude but ya dauko jakarhannah. Nan da nan kwandastocin mota suka zosuna cewa'' babura zaku ne. Ko daura ? Uwar biyu''motar babura zamu hau sai mu sauka a babbanmutum. Haisam ya mikawa kwandasata da zasubabbam mutum jakar hannah, uwar biyu tace '' af har yanxu hannah bata fito daga motar bane ?Haisam ya leka cikin motar ya tsaya yana kallonhannah baice mata komai ba, ta sunkuyar da kaicikin sanyi jiki ta jawo jakar litattafanta (schoolbag)ta rataya ta juyo ta kalli rauda ta kalli auwaltace'' na tafi sai anjimanku'' rauda tace au har dake zaku shiga motar haya kin fasa zuwa kanon ne ?Hannah ta gyada kai kawai sannan ta fito. Yayaauwal yana yi mata wasa yana cewa, af ashe yarkauye ce ma, motar babura zaku hau ko? Hannahta fita ba tare da ta bashi amsa ba,. Haisam dahannah suma suka nufi cikin tasha dama uwar biyu da kwandasatan daya dauki jakar sun shiga tasha.Motar bus ce wacce baifi mutane hudu ba ta cikaba. Uwar biyu ta zauna a kujerar baya aka sakajakar hannah a but hannah ma taje kusa da uwarbiyu ta zauna, jikinya sanyi kalau kamar marar lakahankalinta a tashe yake kamar wacce za'a kaita lahira ba gidansu ba. Haisam ya zaga ta wundon dauwar biyu ke zaune ya danko kudi ya mika mata yace' ga wannan kuyi kudin mota dan karku mastu kibiya kudin kujerun bayan a barku ku kadai sannanki fito ki shiga aishalle super market kafin mota tacika ki siyowa hannah sabulun wanka, wanki man shafawa dana gashi. Biskit da alewoyi ta yiwa yangidansu tsaraba.?ya sake deno wasu kudi masuyawa yace wannan kuma ki ajiye da zarar hutu yakare ya rage kwana biyu kije ki taho da ita kikawota gidanki zanzo in kara yi mata siyayya namayar da ita makaranta. A cikin kudin ki bawa mahaifinta dan na kashewa ki gaya masa lallai lallaihutun kwana arba'in da biyu aka basu da zararhutu yana karewa zaki zo ki dauke ta inji ni zakice.Ki san dai kalaman da zaki gaya masa na kwantarda hankali kada ya hanata dawowa kinsantsofaffin nan namu, kice ke uwar dakin tace a wajenki take a makaranta na hadaku, kice inagaisheshi da kyau. Uwar biyu tayi godaya tashialbarka kamar ita aka bawa kudin ko jikarta. Yadauko wasu kudin ya mikawa uwar biyu yace'' kisayawa hannah sarka da dan kunne na jiyal maikyau ki bata'' uwar biyu tace'' kai kudin ai yayi yawa malam haisam duk a cikin wannan ya isa nayimata siyayyar'' ya ce ''ba komai na gode uwar biyuallah ya kiyaye hanya'' tace amin malam mune dagodiya'' ya zagayo jikin wundon da hannah kezaune tayi tagumi ta langwabar da kai a jikinwundon mota jawaye ne yake sulalowa daga idanuwanta daya bayan daya. Haisam ya kalletayayin da yaji kamar zuciyarsa zata fashe dontsananin tausayinta , yayi karfin hali yace'' hannahkukan meye kike don kawai anyi hutu zaki tafigida ? Ai hutu na karewa uwar biyu zata je tadaukoki kinji ko ? Zan zo inyi miki siyayya na mayar dake makaranta, yanxu idan kika je gida kinakuka baba zaice wahala kike sha a makarantar yace ba zaki dawo ba. Amma ki nunawa babamakarantar da dadi ga ladabi da biyayyar da akekoya muku ga karatu da abinci a wadace shi kansazaice ki dawo, kinji ko ? Hannah ta gyada kai ta fara share hawayen idonta. Yace gaba da cewa'' kiyihakuri da abun da iya abu take yi miki hutu nakarewa uwar biyu zata zo ta daukeki ta kawo kimakaranta. Sannan kullum ki rika zuwamakarantar islamiyya kina kuma duba litattafankina makarantar boko don karki manta karatu kinji. Allah ya kiyaye hanya hannah. Ya juya ya tafi,muryarta yaji ta rushe da kuka, ya juyo ya tsaya cakyana kallonta sai ya rasa me ma zai ce mata sai yajuya ya tafi da sauri. Yana mai tsananin damuwa datakaici.kukan zuci kawai yake. Ba tare da ya cewa suauwal komai ba, ya ja mota ya fara tukawa. Canrauda ta nisa tace'' yaya haisam daman hannahfulanin daura ne, ko ba daura zasu ba ? Haisam yayidan murmushi kawai. Auwal yace'' haisam ka cikashige shige ina ka samu wannan buzuwar har da kakarta kuma? Haisam yacce'' wai shige shige ni dakai za'a san me shige shige naga daga zuwa harkasan su naja'at suleman ko banga sanda takebaka adiredhinta ba balle ni dana shekara amakarantar'' auwal yace to ya isa ga wannanzabiyar a baya ta bude kunnuwa tana daukar rahoto'' haka dai har suka isa kano jifa jifa haisamyake magana babu abunda yake tunawa sai halinda hannah zata kasance a gidansu. Zuciyarsa cikeda tausayinta kulle kullen yaya zaiyi yaci gaba dataimakonta yake gashi kuma ya bar makarantar,har suka isa kano . A nasarawa g.r,a suleman cresent gidan su haisam yake, suka shiga cikinkatafaren get din gidan . Bayan auwal da rauda sunshiga sun gaisa da hajiyar haisam sai suka yi mususallama suka nufi suma nasu gidan da yake lamidocresent basu da nisa sosai. Alhaji shitu mukhtar sunan mahaifinsu rauda,mahaifiyarsu kuma hajiya jamila sunanta alh. Shitumuktar haifafen garin kano ne, dan unguwankabara ne tare sukayi firamare da sakandire damahaifin haisam abokaine tun suna yara. Haj.Jamila kuwa mahaifiyar su rauda mutumiyar chadi ce ya aureta. Allah ya albarkacesu da 'ya'ya uku,yaya auwal shine wanda ya kammala karatunlikitansa a america yanzu cikakken likita ne. Sai antiramla wanda ta gama sakandirenta a wannanshekaran tana jiran sakamakon jarabawarta tawuce jami'a bayan an cancara bikinta da angonta haisam, saita fara karatu a gidanta, sai yar autarsurauda wacce yanxu take ajin farko a sakandire.Tsantsar yan boko ne yaya uku sun ishesurayuwar duniya suna basu cikakkiyar kulawa datsantsarso da kauna. Allaha yayi musu arziki maiyawa don haka a daula suke ta ko ina hutu, ba su fi shekara biyu da dawowa nijeriya ba kasancewaralh. Shitu muktar yana aiki a embassy, shinejakadan nigeria a america {ambassador} don hakaduk a can suka yi karatunsu har mahaifiyarsu haj.Jamila acan tayi digirinta.al'amarin hannah da uwar biyu kuwa, bayan tafiyar haisam uwar biyu tayi sauri ta sauka daga motartaje ta yiwa hannah siyayyar kamar yadda malamhaisam ya umarceta da tayi. Ta dawo cikin mota dasauri ta iske motar dai bata cikaba , bayan mota tacika suka kama hanyar tafiya. A hanya uwar biyu taci gaba da lallashin hannah tana bata baki dakyar tayi shiru da kukan da take yi. Ta dade daman tanaso taji labarin hannah da dangantakarta da malamhaisam, saboda tsananin kulawar data ga yana yimata, cikin wayo da dubara irin na manya uwarbiyu ta dinga bugun cikin hannah tana son tajilabarina. Abunka da yarinya kuma mai neman agaji da take yi ta ko ina hannah ta fayya cewa uwarbiyu komai daga biri har wutsiya. Uwar biyu tatausaya hannah ta sake jinjinawa malam haisambisa jihadin da yayi saboda allah na taimakonhannah. A garin babban mutum suka sauka aka saukemusu jakarsu . Tun daga sauka hannah ta farafaduwar gaba tazo garin da bawa ya fita jin dadi.Uwar biyu ta lura da hakan sai tayi ta bata baki tanakwantar mata da hankalinta. Kawayen hannahmaza da mata yan garin suka baibayeta suna kallonta wasu kuma suna shishshige mata harrububin yi mata magana su ke. Masu daukar matajaka suka dauka suka dunguma zuwa gidan suhannah. Samarin garin sai kallon hannah suke ganisuke kamar ba hannar da bace da suka sani. Tayijawur da ita tsaf tsaf. Babban mamakin kambas din da ta dana a kafarta suke kallo wasu na cewatakalmin yan ball tasa, wasu na cewa na faretinsojoji ne. Mamaki ya ishesu yadda akayi hannah tazama haka kamar baturiya a wata guda nan danan, kyau na zuba duka cikar garin da batsewarsababu mai kyawun hanne da gogewarta. Nanfa samari kowa ya hau cewa gaskiya tawace wannan.Wancan na cewa na rigaka. Kawayenta da yawasun kudiri niyyar suma sai sun tuburewa iyayensuan kaisu makarantar kwana irin ta hannah donsuma su goge suyi jawur haka. Kafin hanne takarasa gida labari ya kai cikin gidansu ance ga hanne nan zuwa ta zama fara kal kamar baturiya itada wata tsohuwa. Farin ciki ya rufe mahaifinta yaiwuf ya fito kofar gida ya tsaya yana murna yanajiran isowar hannensa(yar boko). Budar bakin iyaabu kuwa sai cewa tayi watakila ciki aka yi mata amakarantar tayi haske don hanne ba fara ba ce kal. Surutai dai na hassada da bakin ciki barkatai tadinga yi.Hanne na doso kofar gida ta hango mahaifintasai su duka murna ta lullubesu. Hannah ta karisa dasauri taje ta rungumeshi kamar yadda taga sunusaiba suna yima mahaifansu sai hawaye suke itada mahaifinta. Iya abu a tsakar gida ita da yayantababu wanda ya amsawa uwar biyu sallamarta da tayi, sai malam habu yace shigo kawai ai ba zasuamsa muki ba'' ya shiga daki ya dauko tabarma dasauri ya shimafida mata ta zauna a sanyaye cike damamaki irin wannan tsana da ake yiwa wannan yarkaramar yarinya wanda ma yake sonta an tsaneshi.Hannah taje gaban iya abu ta durkusa ta gaisheta ko ta amsa ta juya ta gaishe da yayyenta 'ya'yan iyaabu kenan suma suka kwata abunda mahaifiyarsutayi. uwar biyu ta rike baki tace ''oh ikon allah bayinallah me yayi zafi hannah nawa take ? Don allahkuyi mata yar fara'a mana ko taji dan sanyi yanzuko dokinta bakwa yi kusan wata biyu bata nan, aidarajar sabon idon ni bakuwa kwa raga mata harin tafi'' suka yo ca akan uwar biyu uwar biyu nayi yayan nayi, ta mike tsaye ta juya ta kalli hannahwacce ta kame a jikin katanga tana makyarkyatahawaye ne ke zuba daga idanuwanta tasan yauduka da zagi allah ne kadai yasan iyakarsa da zatasha. Hawaye ya kecewa uwar biyu tace'' hannah yihakuri wuya bata kisa ko anki ko anso gidan ubanki ne duk inda kika je sai kinzo gidan dole,''iya abu tace'' gidan uban nata ya gagareta zamaidan naso ba. Malam habu shima yayi jugum yakasa magana tashin hankali ya isheshi sabodayana tausayin hannah yasan wahala zasu ci gabada linka mata ganin allah ya rufa mata asiri tayi kyau, uwar biyu ta fita malam habu ya bita hannahma ta bisu da sauri, uwar biyu tasa gefen gyale tashare hawaye tace'' allah yana nan, malam ni yaraikece. Malam haisam malamin daya karbeta ahannunka din nan. Malam habu ya katseta yace ''ehna gane kiyi mana godiya da kyau da kyau na gode madalla. Tasa hannu a dan tofi ta dauko kudimai dan afki ta bawa malam habu'' inji malamhaisam ya ce a bashi nasa ne na kashin kansa banamakarantar hannah bane. Da zarar hutu ya kare itada kanta zata zo ta dauketa, malam habu yayi shiruyana sauraron uwar biyu sai girgiza kai yake kawai yana mamakin wannan tara ta arziki da haisamyake yi musu yana fadin ashe akwai masu halinsahabba a duniyar nan masu kyautar da dukiyarsuga mabukata irin malam haisam. Malam habu yadago ya kalli uwar biyu yace'' kema daya aikokikika rike amana allah ya saka miki da gidan aljannah dashi da yake mana hidima allah ya bashida mai yi masa haka munji dadi mun gode. Ni inanan wata rana na gaza barci ina tunanin ko yayayar baba, kome take ci a makarabntar na bartababu abinci? Ashe tana cam ta fini koshi, kalliyadda tayi bul bul ah alhamdulillah. Maigari ya aiko da garin kwaki kwano biyu da suga rabin kwanosai kudin motar zuwa kazaure ya ce in kai matamakaranta wallahi matar nan tawa data ga garinnan da kudin mota sai ta sulalo ina bacci ta sacekudin motar ta tilla ledar garin ya dinga tsiyayewa akasa, da naje na shaidawa mai gari ba kiga cin mutuncin da suka yimin ba wai daman talauci yaisheni na sami kayan gwamnati ina wadaka dashi,su babu ruwansu ya dai ya ta ce in barta yunwar takasheta. Nayi kuka da hawaye nazo na zauna nahakura sai addu'a na dinga aikamata daga na allahya hadata da mai bata. Allah ya amsa addu.ata gashi bamu girbe amfanin gona ba shine yasa kotaro nakan tashi babu a aljihuna. Uwar biyu tace,kaico haka kake rayuwa ta malam ? To ni daishawarar dazan baka dan allah dan annabi(S.A.W)duk runtsi duk wuya ka toshe kunnankakome za'ace game da karatun hannah karka cire ta daga makaranta. Babu sisinka. Ba kai zaka dauketaba. Bakai zaka mayar da ita va nice zan dingakawota ina zuwa ina daukarta sai dai ka bata izinikarka hanata saboda karatu ne kawai zai farfadoda hannah ta sami yancinta da jin dadin rayuwartaanan gaba, amma azabar tayi yawa. Malam habu ya ce da gudu kuwa zan barta, aini badan za'ace nasiyar da yata ba, ko ace na kaita birni tana iskancida ko hutu ma sai ince ta dinga yi a gidanki ammayanzu kowa yaji a rediyo an yiwa 'yan makarantahutu ba aga hannah ba za'a fara titsiyeni datambaya a fada. Uwar biyu tace allah ya kyauta ni zan koma, ga sabulai can a jakanta da mayukanshafawa malama haisam ce don allah a dinga bartatana wanka da wanki da kitso ba kamar yadda akakawota ba, kazan kazan ina amfanin kazanta ?Uwar biyu ta fara tafiya bayan sunyi sallama damalam habu yana ta godiya, hannah ta rushe da kuka ta bi uwar biyu da gudu ta rungumeta suduka kuka suke rusawa hannah tace''uwar biyu karki tafi ki barni wuya bake sha ni zanbiki gidanki in zauna a can. Daya daga cikin 'yayaniya abu musbahu shine ya fito daga cikin gidan aguje uwarsa ta turo shi yazo ya dauko mata hannah aka dake suna labe a zaure suna jin dukmaganganun da suke yi. Ya dauko ta aka ya mikata cikin gida ya rufo kofar zaure sai kukan hannahne yake tashi ya cika unguwar kai kace rai ake zaremata saboda irin karar kukan daga ji ba karaminbudu ake yi mata ba, malam habu nata kokarin bude kofar yana bugun kofar kamar zai balla yanaso yaje ya ceci 'yarsa uwar biyu ta juya ta tafi tanarusa kuka kamar ranta zai fita, tsananin bakin cikida tausayin hannah ne ya cika mata zuciya. Tana jinsamarin dake zazzaune akan benci suna jiyo kukanhannah suke cewa''to baiwar iya abu tazo har an fara nada mata dukar kai wannan yarinya allah daiya rayata kar itama wuya ta kasheta kamar uwarta.Haka hannah tayi ta zama cikin wahala da kuncida azabtarwan iya abu har hutun makaranta yakare. Ana saura kwana biyu a koma sai ga uwarbiyu tazo daukan hanne. Tunda iya abu ta ganka tahau fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,anan ne malam habu yake fada mata , kinsan cewa tayi indai da ranta hanne ta daina karatu tundawata gulma aka hada na kaita gidan yan gayubabu wata makaranta. Wuf iya abu tayi tayo wajedaga cikin daki tazo ta tsaya a dokin kofa tanagirgiza ta kama kugu tana kallon uwar biyu ayatsune. Babu abunda uwar biyu take sai kallon wuyan iya abu galleliyar sarkar jiyal din da tasiyawa hanne ce a wuyanta. Muhajana 'yarta kuwariga da siket 'yar kanti ta hanne ce a jikinta, saigamusbahu shima yazo ya wuce da jakar hanne arataye a bayansa (school bag)wai daga kasuwayake. Iya abu tace'' bai gaya miki ba na hana karatun hanne ko bai fada miki ba ne ? Iwar biyutace '' shine mahaifinta shine kuma mai iko da'yarsa bake ba. Ni kuma akan kin barin yarinyarnan ta tafi zan iya cin dammara mu daku da kowakuma daga na har gaban mai gari zamu je dakeidan kika kwatanta hakan. Iya abu tayi shiru tasan idan aka kaita kara wajen maigari tasan bazai bibayanta ba kasancewar sun sha gogawa akan zatahana hanne karatu bata ci nasara va. Iya abu tanisa tace to kije dawan da kanki ki kirawo hanne'yata ba zata ba. Taja hannun 'yarta mahajana sukashige cikin gida.malam habu ya leka kofar gida ya kira musa dan makwabtansu ya ce yaje dawa yaceda hanne tazo yanzunnan ta koro kiwan su dawogida. Uwar biyu ta tabe baki gami dayin ajiyarzuciya tace'' rabon gado akayi da kayan hannetunda ranta ba'a jira ta mutu ba. Caraf iya abu ta fitoashe a labe take tace'' an raba kayan hannen ko hannen naga dama zan iya rabata balle kayanta.Duk gulmace gulmacen da kuke hadawa ya kare akanku babu wata makaranta da ake kai hanneyawon bariki kawai ake koyawa yarinya ta samoabin duniya'' uwar biyu tayi dariya shekeke tace''wannan yawon bariki na hanne don ke da yayanki take yi irin wannan bushasha da kayan yarinya. Dayake itama uwar biyu badaganan ba wajen iyamasifa da yaba magana suka yi tayi dakyar malamhabu ya hana uwar biyu magana ya ce ta yi shiru takyaleta, iya abu tayi fada tana shiga da fice bakinciki ya lullube mata zuciya kamar zata fashe ganin anzo za'a dauki hanne a tafi da ita wajen da takehutawa. hannah ta shigo a sanyaye tana fargaba tanatunanin me tayi kuma aka ce ta koro kiwo ta dawogida yanzu. Tana shigowa sai taga uwar biyu damahaifinta a zaure a zaune ta daka tsalle tarungume uwar biyu tana mai tsananin murna dafarin ciki tace. Iya daukata kika zo yi mu tafi'' uwar biyu tace'' yanzu kuwa shiga ki dauko kayanki mutafi. Hannah tayi kasake a tsaye murna ta koma cikitayi kamar zata fashe fa kuka. Uwar biyu ta kalletatace'' hannatu lafiya meya faru kuma kika zamahaka lokaci daya kamar mai shirin rushewa dakuka ? Uban yace da kika ce taje ta dauko kayanta shine jikinta yayi sanyi ai babu kayan duk sunkwashe. Harda litattafan makarantar sun yayyagasun siyarwa da mai kosai wasu'' uwar biyu takwada salati tana cewa'' harda manyan litattafankaratu masu tsada suka yayyaga mata ? Iya abutayi wuf ta fito tace da uwar biyu !! Ki kiyayeni don kin zake dawa, karfa ki kuskura ki cika min cikiba'aja dani an yayyaga littafin kyi abinda zakiyikuje ku saya mata wasu ta kawo na sakeyayyagawa muje duk inda zamu je aikin banza.Uwar biyu ta mike tsaye ta juya ta kalli malam habuwanda yayi tsuru abin duniya ya isheshi ya kasa magana tace '' malam na tafi da hanne allah yanabayan mai gaskiya kuma duk dan hakin da karaina shike tsone maka ido zakaran da allah yanufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi.Hanne mu tafi garin da ake kaunarki. ''iya abu tarako su har kofar gida tana zagi tasa hannu ta fallawa hanne duka a baya gami da angazata ta tafitaga taga zata fadi uwar biyu ta riketa tajahannunta suka tafi. Hanne ta rushe da kuka uwarbiyu fadi dake. Duk abinda zaki yiwa hannah bakiisa ki hanata numfashi a duniya ba tunda bake kikahalicceta ba'' suka kama hanya suka tafi, suna ji iya abu ta koma kan mahaifin hannah tana zazzagamasa masifa yayi shiru kamar bada shi take ba. A tasha uwar biyu ta siyawa hanna sabon silifasdomin na kafanta wari da wari ne, suna zaune amota uwar biyu take tambayar hanne abubuwanda ake yi mata. Hannah ta zaiyana mata tsaf tacekusan kullum sai an lakada mata duka an kwacekayan sawarta da jakunkunanta, sabulan ma da mayukan shafawa ko sau daya ba'a barta tayiwanka da suba. Tana dai barinta taje makarantarislamiyya kullum shima saboda tana tsoron maigarine. Hanne ta sake dagulewa kamar ba itace tayikyau din na ba das da ita gwanin sha'awa, yanzu tadawo furtutunta, yagulallun kaya uwar biyu tace'' yanzu har kayan makarantar taki(uniform)duksakawa suke ? Tace eh ta rarrabawa jikokintawasu, wasu kuwa ta sayarwa 'yan jagorar makafi.Bani da sauran kaya sai wannan na jikina, uwarbiyu ta nisa tace allah ya saka miki, kuma wannanyaro haisam shima an sake ja masa sabon aiki'' zugum suka yi su duka kowacce tana tunani harsuka isa tashr kazaure babu wacce ta sake yinmagana suna isa gida uwar biyu ta shirgowahanna abinci mai yawa da mamakinta hanna tatashi dashi tasha ruwa. Bayan sun huta uwar biyutasa 'yarta halima ta wanke mata cukurkudeden gashinta , hannah ta sallah wanka. Kafin magarubahar an gama rangadawa hannah kitso,Sai suka ji ana rangada sallama uwar biyu tacehanne ta leka zaure taga waye yake sallama . Tanalekawa sai taga safiyanu ne abokin yaya haisam,rike da wata katuwar jakar bacco babbar ta karshea girma. Hannah tayi dariya '' tace lala yaya safiyanusannu da zuwa . Ya ce yauwa har kinzo ,hutu ya kare ko ? Hannah tace'' eh ka shigo mana'' dakyaryake jan buhun a kasa saboda a shake yake damda kaya. Suka iske uwar biyu a tsakar gida. Lalemar haban, uwar biyu take cewa hannah tayi saurita shimfida tabarma ya zauna. Bayan sun gaisa da uwar biyu ya fara zazzagekayan dake cikin wannan katuwar jaka siyayyarhannah ce ta makaranta (provision) kaya ne abunbaya lissafuwa komai akwai kai kace kanti za,abude uwar biyu ta rike baki kawai tana kallon ikonallah, tace '' safiyanu wannan kaya ai ya yiwa hannah yawa. Safiyanu yayi murmushi ya ce aikudin da haisam ya bani ne masu yawa ne ya ceduk ayi mata siyayya a wadace. Nima da kainanaga ya dace na bar siyayyar nan haka ba donkudin sun kare ba . Uwar biyu tace ai gara da karago kudin don sai an sake siyan sababbin uniform da litattafai. Safiyanu ya ce ina nata nada , ko dukterm ake sake wa ? Uwar biyu ta gyara zama ta farabawa safiyanu labari duk abunda ya faru da kayanhannah tun daga biri har wutsiya. Safiyanu yatausayawa rayuwar hannah duk da yake damahaisam ya gaya masa kadab daga ciki. Ya nisa ya ce'' abun babba ne kudin da yawa musamman nasayan litattafan karatun(text book)masu tsada negashi haisam din bama ya kasar. Uwar biyu tacebaya kasar ina yaje ? Nifa tun ranan hutu ban sakesashi a idona ba. Safiyanu ya ce'' ai kuwa bai dadeda tafiya ba shi da mahaifiyarsa suka tafi london kinsan shirye shiryen bikinsa ake yi shi da yayansawatakila nan da wata uku za'ayi don haka damanzaiyi wuya haisam ya sake dawowa kazaure tundabautar kasa daman yazo kuma sun kare. Nima dayake daman a kano na sanshi a can muke haduwa.A can kuma ya ce zai dinga kawo min kudin siyayyar hanna. Yanzu dai abunda za'yi duk abindaya tashi na game da makarantar hannah a gayamin zanyi ko nawa ne zan ranta masa nasan zaibiya ni don haka daga yau zuwa gobe zanyi kokarina saisayo mata uniform din da takalmi da kumalitattafan. Zuwa gibe telan daya dinka mata wancan zai dinka mata da wuri . Jibi dai zasu komamakarantar kafinnan insha allahu komai yakammala. Uwar biyu tayi murna dajin bayanansafiyanu tayi ta godiya. Amma hanna ta fita yinmurna da farin ciki don ita da a tunaninta za'acekarshen karatunta yazo tunda yaya haisam baya nigeria to sai taji safiyanu ya ce zai ranta a dinkamata. Suka yi sallama da safiyanu su duka suna yimasa godiya ya tafi, akan jibi hannah ta kwana dashiri zai kawo mata kayan ya kuma mayar da itamakaranta. Haka kuwa aka yi hannah tana dayadaga cikin wadanda suka fara dawowa makaranta tun karfe sha biyun rana, kafin yamma makarantata cika makil kowacce ta dawo tana tsoro sabodaprincipal tace duk wacce ta kara kwana dayabaza'a karbeta ba. yaya haisam baya nan kishin da rauda take yi dahannah ya kau yanzu suna zaune lafiya wasa dadariya, sai dai su dukkansu basa jin dadinmakarantar sosao saboda babu yayansu. Haka dukyan ajin uncle haisam basa jin dadin sabon classmaster dinsu saboda baya tarairayarsu kamar haisam. Kowacce bata manta da nasihohin da unclehaisam yayi musu ba akan suyi karatu sucijarabawa idan ba haka ba za'ayi musu repeating .Kowacce ta dage da karatu ba dare ba rana donhaka j.s.s 1a is the best class in f.g.g.c kazaureyawanci a wajen assembly malamai suna fadar haka principal tasa a tafa musu, tana kuma alfaharida su tana yabawa tsohon class master dinsuhaisam saboda tasan shi ya gyara ajin haka. Tanakuma nunawa sauran malamai dasuyi koyi dashidon ire iren su haisam a makarantar.Bayandawowar daliban makaranta da kamar wata guda. Ranar wata litinin da safe ana assembly sai kuwaprincipal tayi musu albishir da cewa.kwararrenmalamin nan uncle haisam ya dawo makarantar amatsayin permanent teacher. Tasa wani malami yaleka waje ya shigo da haisam saboda a waje la labekada su ganshi suki tsayawa ayi assembly suyi taife ife don haka ya tsaya daga waje. Malam haisam na shigowa dalibai gaba dayansu yara da manyasuka hau ihu da tafi murna kuwa ba'a cewa komaimusamman a wajen hanna. Wai! Yau da za'a budezucoyar hannah aga irin farin cikin da yake cikinzuciyarta da abun da yawa. Dakyar dai dalibansuka dan tsagaita da ihu aka karasa assembly kowacce ta tafi ajinta. Yan ajin su rauda kuwa hadabaki suka yi suka yi kungiya suka nufi ofishinprincipal dauke da manya manyan takardu sunrubuta kamar haka '' we want our former classmaster uncle haisam back.'' waisu zanga zanganlumana suke yi principal da sauran malamai suka sha dariya sannan ta basu amsat cewa za'a dawoda haisam dinsu, su koma aji. Sannan suka tafi sunamurna. Haisam ya dawo yaci gaba da rike ragamarshugabancin ajinsa j.s.s. 1A. Hutu yana zuwa karshe jarabawa na karatowahaisam naci gaba da yiw dalibai nasiha dasu dageda karatu musamman ma hannah yana ci gaba danunnuna mata duk abunda bata gane ba. Ba laifihannah tana sake kokartawa fiye da waccan termdin. Ta fara gane ayyukan makarantar sosai tana kuma gane turanci tana yi kuma. Wannan termdinma kamar wancan sunyi jarabawa sun gamasannan malamai sun yi kokarin sun kammala fitarda sakamako. Haisam ya tara yan ajinsa ana gobehutu ya bawa kowacce sakamakon jarabawarta.Wannan ma kamar waccan bata sake zani ba rauda shitu muktar itace tazo ta farko. Nusaiba ta biyu,pamella matin benin ta uku. Hannah ce dai ta samici gaba maimakon tazo ta goma data zo wancankaron yanzu sai tazo na takwas.Hannah tayi murnahaisam har ya fita murna ganin ba kudin banzayake kashewa ba, da bata lokacinsa a banza ba. Kamar wancan hutun, ranar hutu principal ta yiwadalibai assembly, hutunne bashi da yawa sosaikwana ashirin da takwas ne kawai zasu yi a gida.Amma wannan karan direban gidansu rauda yazodaukar rauda sai haisam ya ce ta tafi shima dagagidansu za'a aiko da direbansa yazo ya daukeshi. Bayan tafiyar rauda babu dadewa sai ga dalleliyarmotar haisam kirar jeep da mahaifinsa ya bashibayan ya gama bautar kasa, muntari sunan direbanhaisam, yazo ya duka ya gaishe da haisam, haisamya nuna masa jakar hannah ya ce ya dauka ya sakaa but. Bayan ya saka hannah ta shiga baya, haisam na gaba direba mutari yana tukawa suka fita dagamakarantar. Haisam na nunawa mutari hanya hargidan uwar biyu kamar waccan lokacin suka iskeuwar biyu a shirye tsaf. Ta fito daga gida bayan sungaisa, haisam yace da uwar biyu su dauki jakarkayan su shifa cikin gida a ajiye, kaya kala biyu kawai za'a bawa hannah da silifas faya amma duksauran a ajiye da litattafanta. Da yake safiyanu yabashi labarin duk yadda uwat biyu ta gaya masaabunda ya faru da kayan hannah. mutari direba ne ya taya su da shiga da kayan cikingida. Uwar biyu ta zaba ma hannah kayan da zatasaka ta cire uniform da kambas aka bata silifas dawani kala daya a leda wanda zata tafi dashi. Bayansun fito daga gida sai suka shiga mota suka tafi,basu tsaya a ko'ina ba sai a tasha. Wannan karan ma har bakin mota haisam ya raka su hannah yadauki kudi mai yawa ya bawa uwar biyu yacr suyikudin mota na zuwa can tayin na dawowarta,sannan a ciki taba mahaifin hannah na kashewa taajiye wanda zata je ta daukota idan hutu ya kar e.Yayi wa hannah nasihohi ya bata hakuri game da halin da take ciki a gidansu.Daga karshe yayi musu fatan allah ya sauke sulafiya. Ya juya ya tafi uwar biyu na tayi masa godiyadashi masa albarka hannah na rusa kuka Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 3 Posted by ANaM Dorayi on 02:12 PM, 30-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura Haka daiuwar biyu da hannah suka kasance idan hutu yarage yan kwanaki sai uwar biyu taje ta daukohannah. Haisam kuma baya gajiya da yi mata siyayya duk abunda za'a bukata na rayuwarmakaranta. Ko yayan masu hannu da shuni na makarantarbaza su nunawa hannah gata ba. Idan aka yi hutuhaisam yana kaisu tasha ya sasu a mota uwar biyuta kaita gida. Amma kuma kaya kadan uwar biyutake bawa hannah ta tafi dashi garinsu kadandinma bata dawo dasu,iya abu ta kwace tabawa yayanta ga bakar wahala da ake bata, wujigawujiga hannah take dawowa hutu kamar ba ita ba.Saboda wahalar da take sha tayi duk sai tayi duhu.Amma daga ta dawo makaranta kafin hutu ta sakefes da ita. Kwanci tashi wannan ne hutun dasu hannah in sundawo makarantar zasu shiga senior class wato s.s1. Don haka duk uniform dinsu sai an sake musuna seniors daban na junior class daban. Don hakatun kafin uwar biyu taje ta dauketa haisam yakawowa uwar biyu uniform din hannah ta ajiye har ya dinka mata ya canja mata school bag tsaleliyairin ta manyan dalibai, akwati maitaya biyu yasayamata babba da karama. Babbar ta zubaprovision karamar ta kayan sawarta, kamar yaddayaga yayan attajirai ana yi musu idan suka shigaajin manya. Ranar da aka dawo makaranta safiyanu ya dawo da hannah. A duk lokacindasafiyanu ya kawo ta makaranta takan kirawokawayenta su zo su gaisa, yayan ta take cewakamar yadda taga kowacce tana kiran kawayentata gaisa da 'yan gidansu. Duk 'yan makarantar sunayiwa hannah kallon wata 'yar gidan gawurtaccen attajiri ko nusaiba da rauda basu san ba dagagidansu ake yi mta siyayyar nan ba saboda haisamyayi mata gargadi kada tagayawa kowa labarintata rike surrinta. Rauda da nusaiba sun dauka uwarbiyu kakarta ce kuma babban mutum din da suketafiya duk hutu garin kakanninta take zuwa. Ko a hira hannah bata cika bada labarin yan gidansu basai dai tayi ta sauraron na mutane. Masassakin budurci ya fara sassaka hannah ma'anata zama budurwa kyau ya sake fitowa. A gaskiyakyan hannah bazai iya suffantuwa ba, farinta yasake haskawa, gashin kanta ya kara tsawo sabidatayi wayon gyarashi ga mayukan gashi kala kalada haisam yake siya mata. Ranar wata social night da daddare ne haisam ya hango hanna, nusaiba darauda sun sha wandunan jeans da teasirt sun nufikatafaran kantin siyar da kayayyaki kala kala dakecikin makarantar. Suna tsaye suna siyayya saidariya suke suna tafi, cikin sanda ya karasa kantindon yaga me suke siya haka suna dariya. Wai ashe rigar nono zasu fara sawa 'yan kanana. To shine yakawo musu guda dai dai suke jin kunyar siyakyma. Hannah tace'' ni dai ba don kunce a siyobireziyar na dani ba da bazan siya ba, yanzu fa dolebazan dinga sakewa ba zan dinga gani kamar anaganin shatinsa ko hannuna yana fitowa ta riga kowa yana gani'' rauda tace'' caf aini da ganganzan dinga sakin hannun rigata don ta fito'' nusaibabata ce komai ba ashe ta hango uncle haisam abayansu a tsaye tana ta kifta musu ido basu ganiba. hannah tace'' ko da yake mun zama senior har 'yanj.s.s 1 ma naga wasu suna sawa fa, nusaiba zabi.Hannah na daddagawa, nusaiba tayi gyaran muryataga dai basu san uncle haisam na bayansu ba. Saitace '' ba ruwana ga yaa haisam nan yana kinku''.Haisam ya kyalkyale da dariya. Sai su duka suka juyo nan fa hannah ta wurgar data hannunta taruga a guje, nusaiba da rauda kuwa suka cusa tasua riga suma suka arce. Haisam yazo ya dauki waccehannah ta wurgar shi da mai kanti suka dingadariya. Haisam yace su hannah yan mata Haisam ya dada kyau sosai hankalinsa ya kwantaya zama mai kudi baya ga albashinsa accountmahaifinsa ya bude masa yana zuba masa ribar dasuka ci a kamfaninsu duk wata yake warewa'ya'yansa, ga hannah ba laifi ta girma wahalar datake sha a gida ta ragu abubuwa da yawa ta fara takawa iya abu da 'ya'yanta burki tana kwatarkanta dole wasu abubuwan suke raga mata. Donhaka kallo daya zaka yiwa haisam kasan dan gidanwani gawurtaccen mai kudi ne saboda suffarsa ta'ya'yan hutu ce, fari ne sol fatarsa mai haske, yanada dara daran ido da dogon hanci, mai yawan gashin?idon dana gira gazar gazar . Wani dan siriringemu ne ya zagaye dan madaidaicin bakinsa(kautar million)gashi dogo mai dan madaidaiciyarkiba. Haisam yana daya daga cikin irin da kowacce'ya mace take mafarkin samun irinshi. Gashi amakarantar yan mata masu ji da kudi da kyau ga gayu. Don haka kusan kullum haisam sai ya samiwasikun 'yan mata akan teburinsa a ofis dinsa sunjefa masa. Wai suna sonsa soyayya mai tsananikuwa sai kawai yayi dariya ya yaga ya zubr kodakuma ya hadu dasu bazai nuna musu yagasakonsu ba. Yan aji shida ne suka fi yi masa wasikun amma wasu 'yan aji biyar din suna rubutomasa shi gani yake suk suna duk hauka suke zasugaji su daina. Gasu kyawawa dasu amma bayaganin kyawun, 'ya'yan attajirai amma shi baidameshiba, shi dai kawai yazo ya cika burin da yakudira ya tafi. senior juwairiyya itace shugaban dalibai (headgirl) juwairiyya kyakykyawan gaske ce fara solharma akan ce suna kama da hannah. Gatamahaifinta wani babban manager ne a wani bankia lagos tana ji da gata da dukiya ga tsananin kokaritafi kowa kokari a shekararsu. Amma sai allah ya jarrabeta da tsananin son uncle haisam tun ba yauba gashi da yawa daga cikin malaman sun mato a sontaita bata son su ta fi son haisam. Ta aika masa dawasiku sunfi a kirga amma shiru ko alama haisambaya nuna mata na yaga wasikarta . Da ta gaji daaika masa da wasikun saita dinga aika masakawayenta baro baro suke tarar sa su gaya masa amsar daya basu cewa yayi duk yarinyar data saketarar sa da maganan juwairiyya saiya sabar mata.Don haka juwairiyya ta rasa yadda zata yi ta shawokan wanda take so . Ranar litinin da daddare an fitodaga (prep) juwairiyya ta sami kan wata baranda tazauna tana tunani don ita son haisam har ya fara dasa mata wani ciwo da yake damunta a zuciya hartake kasa karatu sosai gashi kuwa tafi duk yanmakarantar kokari, don haka nema aka nada tashugabar dalibai. Zaman da tayi wucewar haisamkawai take son ta gani sannan ta iya bacci. Salahanura itace babbar aminiyar juwairiyya tazi giftawa zata tafi ajinsu taga kawarta a zaune a baranda itakadai, taje wajen ta dade a tsaye a kanta juwairiyyabata sani ba. Ta dafata sannan tayi firgigi ta dago .Salaha nura ta zauna a kusa da juwairiyya tace''juwairiyya tunanin meye kike, ke kadai kowa yanaaji ? Juwairiyya ta nisa tace allah salaha inasan uncle maikayu sosai har kamar zan zautu'' salaha tatuntsire da dariya tace'' uncle haisam wai? Shegusunan da kuka saka masa kuma, to juwairiyya yayazamuyi kin rubuta a rubuce yaki kin aikemu yazazzagemu ko ke kika je da kanki ba zai yadda ba.Kwarjini yake mun ba zan iya tarar saba'' inji juwairiyya salaha tace'' to meye abun yi? Juwairiyyata zunguri salaha ta nuna mata haisam ne yatunkaro inda suke daga staff qurters ya karasoinda suke su duka suka gaisheshi cikin ladabi. Yace ''oh shugabar dalibaice da labour prefect ? Sukace mune si'' yace ''wato kun kora yara aji ku kunzo kun zauna kuna hira ko? Kamata yayi kufi kowakaratu yanzu tunda kune masu shirin yin waec daneco da jamb ko? suka amsa eh ba hira muke bawani muke jira'' juwairiyya ta marairaice muryatace'' amma na ganshi yanzu zamu tafi damanfatana in ganshi kawai ''haisam ya gane abunda take nufi sai kawai yayi sauri ya katseta ya ce'' idanzaku tafi gashi kuje j.s.s. 1a science class ku bawahannah abubakar imam. Ya mika mata wata leda adaure ya juya ya nufi ofishinsa ya shiga sannan yarufo kofar. Juwairiyya tace da salaha''kinga abunda nakegudu ko shariya ce da wannan mutumin ko fuskabaya bani da zan gaya masa abunda yake damuna.Salaha nura tace'' to wai ni na lura meye yaketsakanin uncle haisam da hannah abubakar imamne ? Kamar duk makarantar nan yafi kulata komai hannah zaka ji yana ambata kamar shi ya radamata sunan. Juwairiyya tace'' ance abokin wantane wai, kuma saboda rauda shitu kawar hannah itaai kanwarsa ce. Salaha nura tace'' to kanwarabokinsa ai zai iya sonta. Salaha ta karbi ledar da yabawa juwairiyya ta kwance sai suka ga magunguna na ruwa da kwaya ne , na zazzabidana tari ya saya mata. Salaha ta tabe baki tace.Lallai magunguna ya sayo mata tafi karfin ma tashana clinic din makaranta kenan'' juwairiyya tace'' zomuje nasan abunda zan hadawa yarinyar na''salaha ta taso suna tafe suna zancen suka nufi ajin su hannah. Juwairiyya tace'' ba uncle haisam yacekada wata ta kuskura ta kara kai masa sakona bato ni kuma hannar da yake ji da ita daga yau ita zandinga aike wajensa. Salaha tace'' kwarai kuwahaka za'a yi muga ko itama zai korota din'' tawundo juwairiyya ta leka tace'' ina hannah abubakar ? Yan ajin suka ce'' gata can a sit dinta akwance bata da lafiya'' tace ''ko ciwon ajalo take tataso ta zagayo tazo ina kiranta'' nusaiba ce tatasheta tace '' hannah kije senior juwairiyya nakiranki'' hannah ta daga ido dakyar tace'' bazan iyatashi ba bani da lafiya'' jikinta zafi kyau kamar wuta. Jijiyoyinta kanta sunyi rudu rudu don ciwonda yake yi mata. Juwairiyya ta daka mata tsawatace da hannah ta taso allah yasa asibiti ne a kantaba jinya ba. Nusaiba da rauda suka rirrikota sukatasheta tsaye. Juwairiyya ta daka musu tsawa tacemusu munafukai su saketa tazo da kanta. Haka hannah ta fara tafiya tana rirrike bango ta fita tazagaya bayan aji inda suke. Juwairiyya ta mikamata ledar da haisam ya bayar a bata suka ce''gashi inji saurayinki. Hannah tayi jugum tanamamaki can tace waye'' waye kuma saurayina?Salaha tace'' zaki sashi munafuka. Juwairiyya ta mika mata wata takarda tace'' ki kaiwa unclehaisam kice ina jiran amsa yanzu kice nace mikikarki sake ki dawo min babu amsa'' hannah ta faratafiya jiri yana daukarta ji take kamar ta fadi sabodayini cur a kwance babu ko dan tea a cikinta. Ta isaofishinsa ta kwankwasa yayi mamaki da yaji ana kwankwasa masa kofa yanzu, ya tashi ya bude saiga hannah a tsaye. Mamaki ya kamashi yace''hannah lafiya ? Keda baki da lafiya kika iyatahowa? Hannah ta cije baki gami da rike bangokamar zata fadi tace'' aikoni wajenka aka yi'' yace''aike kuma, waye ya aikoki? Ta mika masa wasika tace ''inji senior juwairiyya da senior salaha suncedole in taho musu da amsa kar inzo babu amsa yabata rai ya karbi wasikar ya bude ya karanta.Wasika ce irin ta kullum daga juwairiyya ya cecirayuwarta tana sonsa.Haisam ya cikuikuye ya wurgar ya ce'' sun bakimagungunanki'' tace''ah ina ji sune anan'' ya karbaya bubbude yana tsiyaya mata a murfi yana mikamata sai ta karba tasha. Sai da ya tabbatar ta shadukka sannan ya daure ledar ya mika mata ya ce tawuce daki ta kwanta gibe idan taga baza ta iya fitowa aji ba tayi kwanciyarta zai sanarwa da dutymaster. Daga karshe ya ce'' sai da safe allah ya bakilafiya hannah. Tace amin '' har ta juya zata tafi sai tatuna ta juyo tace masa'' me zan cewa seniorjuwairiyya ? Ya ce'' kice nace tazo ta karbi amsar dakanta. Hannah ta amsa da to sannan ta tafi. Daman su juwairiyya na zaune a wata baranda suna hangosu. Hannah tazo wucewa suka kirata tace musu takai masa ya ce amsar taje da kanta ta karba. Salahatace'' jeki to'' juwairiyya ta nisa tace'' kinga haisamko wallahi wulakanci yake shirin yimin tunda ya ceinje da kaina ni nasan ba wata maganar amincewa zaiyi min ba. Saboda ai nagani cukuikuye wasikartawa yayi ya yar a kasa, ya buge da bata magani aidole ma son hannah yake'' salaha tace'' ammakuwa sunan yarinyar na gawa don sai taci ubanta amakarantar nan , mu 'yan s.s.3 muce muna sonsayaki ya so junior mu ai bazai yuba. Jeki kiji abinda zai fada muki don muci uwarta da hujja'' juwairiyyata mike ta nufi ofishin haisam tana wani karkaderiga tana gyara fuska. Tayi sallama gami da turakofar zata shiga ya dakatar da ita da hannu yace''tsaya daga nan baranda kiji abunda zan fada miki.Don me kika sake yimin aiken wasika bayan nace kada wanda ya sake zomin da wasikarki. Kumawanne rashin tausayi ne da zaki taso yarinya mararlafiya ki aikota, duk daliban makarantar nan, saihannah ? Me yasa sai ita zaki aiko juwairiyya ?Juwairiyya ta tsuke fuska tace'' amma uncle haisamduk aiken dana keyi baka taba kirawoni kace meya sa nake aiko kawayena ba sai dai kacewayan aiken duk wacce ta sake zuwa zaka sabarmata. Meya sa baka fadawa yar aiken ba a wannankaron sai ni ka kira ? Haisam ya fusata ya dakamata tsawa yace'' ina tambayarki kina tambayata ?To kar kiji yauce rana ta karshe da zaki yimin haka. Ki rike darajarki da mutuncinki a matsayinki na yamace budurwa. Idan sai kinyi soyayya a makarantaba karatu ya kawo kiba to ga sauran malaman dasuke rubibin sonki amma ni bani da ra'ayinsoyayya, this is the last warninng bana son na sakeganin sako daga wajen ki sai anjima kije. Wani jiri jiri juwairiyya take ji ta juya ta tafi tana kwafa.Salaha tazo ta tare ta a hanya tana cewa'' meyenake hangoki a baranda ofishinsa ma ya hanakishiga ? Juwairiyya tace'' ke dai muje in baki labarinyadda muka yi'' daman lokacin tashi daga prepyayi duka dalibai sun dungumo daga ajijuwansu sun doshi dakunansu. Don haka juwairiyya dasalaha nura sai suka nufi hostel a hanya ta zaiyanamata duk yadda suka yi da uncle mai kyau watohaisam. washegari talata da sassafe bakwai da rabia lokacin dalibai suke firfitowa daga dakunansuzuwa ajijuwansu domin daukar darussa. Uncle haisam a tsaye yake kem a bakin get din hostelyana kallon masu fitowa daga ciki, mamaki yakama dalibai ganin sabon al'amari meye unclehaisam yazo ya tsaya anan da sassafe haka bashine da duty ba, ba ranar inspection ba kuma.Kowacce idan ta ganshi sai ta duka ta mika gaisuwa ta wuce'' good morning sir'' can ya hangorauda da nusaiba da pamella suna tahowa daganesa ya dauka hannah ce sai da suka karaso yagababu hannah a cikinsu. Bayan sun gaisheshi ya ce''yau kuma ina hannah ko jikin ne ? Rauda ta waigagaba da baya taga babu kowa sai ta matso kusa dashi tace'' hannah ba lafiya tana clinic a kwanceacan ta kwana'' gabansa ya yanke ya fadi ya ce''zazzabin ne ya rufeta ? Nusaiba tace'' wannan yafizazzabi yaya'' rauda tace'' su senior juwairiyya nesuka yi mata duka da tsakar dare kusan dukkan s.s3 sai da kowacce ta doki hannah jiya ina ji a sume ta fadi da kyar matron suka zo suka hana su. Mumabamu san me tayi musu ba. Kuka mu ma mukakwana muna nan da nan haisam ya canja ido yakada yayi jawur gashin jikinsa ya mimmike kai kacemuku mukun sanyi ake amma duk da sanyin safiyazufa yake yi. . Ba tare daya ce tak ba ya juya ya nufi clinic inda hannah take a kwance ya same ta rikkicifbata sanma inda hayyacinta yake ba. Abinka dafarar fata sai sabun bulalan suka mata jawur a jiki ,har wuyanta da fuskarta shatin bulala ne lambar.Ya dade a tsaye yana kallonta kawai yasa hannu yacire mata wani ganyen maina daya makale mata a wuya a sanadiyar duka sai yaji jikinta zafi kaukamar wuta, yaja mayafin dake kan gadon yalullubeta. Babu kowa a clinic din nurse din ma batanan. Ya juya ya fita a fusace ya nufi ofishin principal.Ya shiga ofishin gami da yin sallama ya sami wajeya zauna bayan sun gaisa ta dubi haisam tace''haisam lafiya yau na ganka ranka a bace dukwannan fara'ar taka ? Ya ce''dole raina ya bacisaboda kusan kashe wata yarinya akayi a daren jiya a makarantar nan 'yan aji shida ne suka dakiwata yar aji hudu da tsakar dare kamar zasukasheta tana clinic a kwance'' principal ta zaburatace'' subhanallah'' ta danna kararrawa masinja yashigo tace maza yaje aji shida ya kira matajuwairiyya. Haisam da principal na zaune sunyi jugun kowa yana tunani a zuciyarsa. Can saigajuwairiyya ta karaso ita da wani malami mai sunasahabi tazo ta dutkusa a kasa ta gaishe daprincipal. Principal ko amsawa bata yiba ta rufejuwairiyya da fada tana cewa'' in har ba zaki iyahana a aikata laifi ba a makarantata banga amfaninki ba a matsayinki na shugabar dalibai''haisam yace'' madam ai itace ta gaiyato sauran yanaji shidan suka hadu sukayi dukan'' principal tace''oh har da ke head girl kuka hadu aka kusa kasheyarinya, kiyi kneel down yau sai kun yabawa ayazakinta'' uncle sahabi yayi carab ya ce'' madam tsaya kiji, juwairiyya ta fadamun duk abunda yafaru daman zamu taho wajenki muka hadu damasinja a hanya a gaskiya yarinyar ce bata dakunya wai cewa tayi zata yi dambe da head girlshine juwairiyya ta danyi mata bulala uku labourprefecr tayi mata biyu. Ga yarinyar can ma a aji tana daukar darasi babu wani zancen kisa'' haisam yafusata yayi kan sahabi da fada yana cewa'' karyazanyi musu? Yarinyar da duk makarantar nan babumai shirunta da ladabi yaushe zata ce zatayi fada dahead girl ? Kawai baza ka tsaya kayi bincike ba donsun gaya maka karya da gaskiya shine zaka yarda, kaje clinic kaga jikinta a farfashe bata san ma indahaiyacinta yake ba . Sahabi ya ce '' madam donallah ki raba mana rigima ki aika clinic a dubo idanakwai wata marar lafiya. Babu kowa ta warke tamike ba'a gabanmu hannah tazo ta wuce ba dazuko ba hannah ba ce wacce kake cewa an kusa kasheta ? Kuma kai duk wannan hakilon da kakecewa akan hannah saboda kai saurayinta ne fa shiyasa kake wannan sauran da ake duka ka tabamagana ? Principal ta lura maganar babba ce saimanya sai tace da juwairiyya ta tashi ta tafi zata aikoayi kiranta. Fuskar juwairiyya cike da murmushi ta fice principal ta kalli haisam tace'' kwarai tun ba yauba ansha fada mun kana soyayya da hannah.Dokar makarantar nan an hana daliba da malamiyin soyayya . Yanxu na gane manufarka don andaki budurwarka shi yasa kayi magana ko? Dagayau zan sa c.i.d kada ka kuskura in sake jin ance kana soyayya'' haisam ya fusata, ransa ya bacizuciyarsa ta hau tafarfasa. Ya dakawa sahabi tsawayaje har gabansa yana nuna shi da hannu ya ce''kai sahabi karya kake yi ni nafi karfin ka yi minsharri kai da juwairiyya zaku gane kuranku amakarabtar nan. Ni kake cewa ina son hannah ko ? Bayan da bakinka kazo ka sameni kana rokona inhadaka da kanwata hannah kana sonta naki nacekabarta tayi karatu ashe kana kullace dani kasaaka yi mata wannan dukkan ko ? Ke kumaprincipak kin goyi bayansu sun daki yar mutabe abanza ko ? To ni sai na daukarwa hannah fansa da kaina'' ya kada kai ya fice. Sahabi ya juya ya kalliprincipal yace'' kinji kuma inda ya lauya maganako ?tace ''kyaleshi bayan kai ma mr.ojo ya fadamun cewa son hannah yake don haka kaci gabada kula dasu. Haisam ya nufi staff qurters ya shigagidansa ya zauna a falon yana huci kamar ya kashe kansa yake ji saboda tsananin bakin ciki yau kodarasi ba zai je yayi ba. Yini yayi cur a gida ya kudiriniyyar zai dauki fansa akan duk mai hannu a cikinwannan al'amari , wai sahabi ne zaiyi masa hakasahabin da ke zuwa har gida yace ya taimakeshi yashawo masa kan hannah wai juwairiyya da kanta take cewa rashin kunya hanna tayi mata zata yidambe da ita wai shine tayi mata bulala uku itakuma principal da kanta take bin bayansu bayantasan hannah tasan halinta tasha yin kwatance daita a wajen assembly akan tafi kowa da'a da ladabishine har ta yarda da kintsin da suka yi mata ko da kyau, haka haisam ta dinga nanatawa a zuciyarsa .Haisam ya dinga nanatawa a zuciyarsa. Haisam baifita daga gida ba sai da yamma misalin karfe biyarya shigo cikin makaranta a lokacin dalibai sunaprep din yamma ya wuce kai tsaye ajinsa don yagajikin hannah, a zaune ya ganta a kan kujerarta ba laifi jikin burdin bulalan ya dan warware zazzabinya sauka sai dai bata iya bude idanuwanta sosai. Yace da ita'' hannah ya jikinki ? Cikin sanyin muryatace'' da sauki'' yace kinsha magungunan naki?Tace eh nasha'' wani masinja ya leko ajin yacemalam haisam kazo inji principal. A fusace haisam yace meye kuma? Dan aiken ya ce'' waya aka bugomaka zaka dauka a ofishinta'' ya ce gani nan zuwahaisam ya juyo ya dubi rauda da nusaiba ya ce'' kudinga kula da hannah ku tabbatar tana cin abincikunji ko ? Suka amsa da'' to zamu kula da ita.Sannan ya fita daga ajin ya nufi ofishin principal yana isa ofishin yayi sallama ya shiga ya gaisheta amurtike. Tace'' yayanka ne habibu yake son yayimagana dakai nace ya kira nan da minti biyar za.akira....'' kafin ta rufe bakinta wayar ta fara karahaisam yasa hannu ya dauka ya gaishe fa yayahabibu yaji da kyar habibu yake amsa wa rai a bace habib yace kai haisam mu fa ba yara bane kananakana ji ko? Saboda me zaka dinga yi mana wasa dahankaki ? Kace shekara uku zakayi a makarantarnan sannan ka bari yanxu shekara uku sun cika,Saboda me zaka dinga yi mana wasa dahankali ? Kace shekara uku zakayi a makarantarnan sannan ka baru yanzu shekara uku sun cika,last week da kazo aka gaya maka cewar ka barteaching dinnan ka dawo gida da kamfanoninbaba aiki yayi mana yawa muna neman ma'aikata, kace da zarar ka koma kafin karshen watannanzaka dawo gida kabar koyarwa gashi munji kashiru. Kujerarka na nan na jiranka ga ramla nan najiranka itama. Har anyi bikina da jidda har ta haihu'yar mutane na zaman jiranka kazo ayi bikinku. Waishin me ka zamar da mune, har nawa kake da zaka dinga juya mu ? Don haka karka sake nazomakarantar nan da kaina ka rubuta takardar barinaiki kabar koyarwa nan ka dawo gida muna nanmuna jiranka. Kai baka kishin dukiyar ubanka saigwamnati zata baka da kake mata wannan wahala,me kake nema ka samu wanda a gidanku baza a baka ba ? Haisam ya fusata yace'' ka gamamaganarka ? To bari in fada maka gaskiya ba zanbar koyarwa ba ina nan bazan dawo gidan ba'' yakifa kan wayar ya fice. Principal ta bishi da kallo harya fice. Wayar ce ta sake yin kara tasa hannu tadauka taji habib ya ce''ina haisam din? Tace ''ya fice'' ranki ya dade kema harda laifinki tun rannanbaba ya kiraki har gida ya ce kiyi murda murda kisaa koreshi daga makarantarki zai biya ki ko nawane. Kika ce bazai yu ba. Wannan yaron ko kasheshiza ayi bazai bar makarantar nan ba. Wanne irinlallashine ba'ayi masa a gida ba yaki ya bar koyarwa'' principal ta nisa tace'' habib tunda kajinace bazan iya sawa a kori haisam ba to babuyadda zanyi saboda wannan makarantar tagwamnatin taraiya ce daga kololuwa aka daukihaisam haka kuma korarsa sai daga can abuja.Dana bincika ma babban director na federal shine ya dauke shi aiki alh.sabi'u auwal abokinbabankune ko? To babu kuwa yadda za'ayi nahada baki dashi a koro haisam daga makarantarnan habib ya ce''zanzo makarantar watakila nan dasati biyu, idan na dawo daga tafiya dole ne ma yabar makarantar donyaga ana yi masa sakwa sakwa ya dauka tsoronsa ake yi don ni banga uwar dayake samu ba a makarantar'' a haka suka yisallama suka ajiye kan wayoyin. BAYAN SATI asheda sahabi ba kadai akwai malamai da yawa dasuke son hannah. Sai yanzu suka dinga baiyana.Ranar talata data zagayo haisam da sauran malamai uncle sahabi da uncle yusuf suna zaune a gindinbishiya da prep din yamma sai uncle yusuf ya aikawata yarinya ya ce taje s.s. 1a ta kira masa hannahabubakar . Haisam na zaune yana tunanin lafiyayake kiran hannah. Hannah ta karaso tazo tasurkusa ta gaishe su uncle yusuf bai amsa ba yace'' hannah yau zan nuna miki karshen taurin kai,girman kai daji da kai. Don haka kije ki karyo bulalakatuwa mai kauri dai dai tsawanki ki kawo min''haisam na zaune yana kallonsu hannah ta tashijikinta a sanyaye ta nufi dawa, can ba dadewa tataho dauke da wata zabgegiyar bulala. Tazo ta durkusa ta mikawa incle yusuf ya ce tayi kneeldown ta daga hannu ya kuwa tashi ya farazabgawa hannah wannan reshen. Haisam ya kauda kai gefe kawai yayi shiru, yusuf yayi mata bulalakamar sau takwas sannan yace ''kin san me kika yimin? Cikin sheshshekar kuka hanne tace'' ban sani ba '' ya sake daddagewa ya sakar mata wanidukkan yace'' kin tuna yanxu? Cikin gigicewahannah tace na tuna''ya ce'' to me kika min? Tacejiya daka aiko kace inzo in sameka a lambu banzoba'' ya ce'' yauwa ashe dai kin gane yau sai nalahira ya fiki jin dadi don kin samu ma ana sonki , ke din me da zaki yi min wulakanci? Sahabi ya tashiya karbi reshen nan ya zazzabga mata sau biyar dakarfi kuwa ya ce'' tashi saura ki ki zuwa nan gabaidan muka aika kiranki prep'' tana tafe tana rusakuka ta nufi ajinsu. Sahabi yana cewa '' bari mugazata zo da prep din daren kuwa? Idan bata zo ba wallahi doble din wannan zamu yi mata. Haisamyayi tsaki ya mike ya nufi ajinsu hannah. Zuciyarsacike da tsananin bakin ciki da tausayin hannah.Yaje ajin ya tambaya aka ce hannah bata shigo ba.Nan da nan hankalinsa ya sake tashi yayi waje dasauri yana dube duben ko daji ta tafi ta zauna tana kuka, yazo wucewa ta ajijuwan yan aji shida yajinishi kamar wata tana tsallen kwado ya leka tawundo da sauri yaga ashe a s.s.3a sun taru kusandukkaninsu suna azabtar da hannah ta jike dagumi sharkab saboda gwale gwale da duka.Juwairiyya ce rike da dorina a hannunta tana biye da hannah tana tsallen kwado tana fyauda mata. Afusace haisam ya daka musu tsawa duk sukawaigo wasu suka ruga ajijuwansu suka zazzauna.Ya hango wani masinja ya kirashi yace yaje daji yakaryo masa manya manyan reshen bishiyar mainaya kawo masa. Ya zagaya cikin ajijuwa ya ce dukkaninsu su firfito waje bai rage kowa ba duks.s.3 din, sun dauka abin wasa ne suna tafe sunarangwada suna tauna cingam, juwairiya kenansuka firfito waje daga ajijuwan ya ce'' su fara tsallenkwado suma, yaje cikin ajin ya tarar hannahsharkab tayi gumi ga sawun bulala nan duk jikinta lambar. Yasa hannu ya tasheta tsaye yace ta daureta tafi daki ta kwanta. Tana tafe tana layi tana rikebango ta nufi hostel.suna tsallen kwadon a duk yadda suka gadama a zatonsu zaice su koma aji su zauna sai sukahango masinja dauke da himilin bulalai kai kacejakuna za'a daka tafka tafka dasu. A fusace haisamya karbi bulala suna tsallen kwadon yana binsu dulwacce ta fadi kota tsaya a baya yana tafka mata wani dogon waje ya nuna ya ce har can zasu kaikuma sai su huyo. Haka suka dinga yi suje su juyohar sai da ya tabbatar kowacce ta jigata hawayenma ya kasa fitowa sannan ya ce su biyo layikowacce ta kwanta flate sannan ya shashsharbamata reshen nan sau gima sha biyu. Bayan jikinsu yayi kaca kaca ya farfashe kuka wiwi dankwalayensu a hannu ga kafa ta sage babu damartafiya. Juwairiyya tafi kowa shan wuya duka yayimata kamar allah ya ne ya aiko shi ko kirgawa mabaya yi daa bulalai suka karkarye yasa kafa yadinga ball da ita daman yana ciki da ita. Kuka wiwi suke suna bashi hakuri daga yau baza su sake ba.Sannan haisam ya gyalesu anan a kwance wasu adurkushe. Tunda haisam yazo makarantar nan baitaba zagin wata ba balle duka yau sai ga haisam yacanja fuskarsa babu digon rahama murtik da itakamar zai kashesu haka yayi musu ligi ligi dukkan da babu malamin daya taba irinsa a makarantar kodispline master baya yin irin wannan dukan. Labariya kai gidan principal , agigice ta fito ta taho a bakinofishinta ta gamu da haisam. Ta dube shi sai taga yacanja gaba daya sai taji ta shiga tsoronsa tayi masamagana. Can tace''haisam wannw irin duka kayiwa s.s.3 yau me suka yi maka haka? Ya juyo a fusaceya ce''ki tambayi kanki da kanki daman n fadarannan tunda baza ki iya daukar mayaki ba akanabunda su juwairiyya suka yiwa hannah to ni nadau fansa , kuma zan iya tin haka akan kowa dukwanda yake marmarin takurawa hannah a makarantar na'' principal ta rike baki kawai tanakallon haisam , ya wuce ya barta anan tsaye ya nufigidansa. Yana jiyo malaman da suke zazzaune awajen suna cewa'' ai kuwa yarinyar nan sai zamanmakarantar nan ya gagareta don sai mun zane ta,itama'' nan dai principal ta hau fadace fadace tana cewa'' dole ne na kira meeting da manyan yanfederal akan abun da haisam yake yi min amakaranta. magaruba tayi uncle yusuf da uncle sahabi sukanufo gidajensu ta jikin gidan haisam suka zowucewa yana jin abunda suke fada wai da prep dindare zasu kira hannah suyi mata dukan tsiya .Shima haisam sin yaji in da dadi. A haka suka rabukowanne ya nufi gidansa. Haisam na idar da sallar magariba yayi shigar wata yar riga mai gajerenhannu damammiya(body hook) ya dora wata suitaka ya fita ya nufi gidan sahabi. Ya kwankwasakofa, sahabi yazo ya bude fuskar haisam ce ya ganimurtik ta bashi tsoro. Yaja da baya da sauri. Haisamyasa hannu biyu da karfi ya angaza shi ya tafi taga taga ya fada kan kujerar dake falon. Haisam yashigo cikin falon ya mayar da kofa ya datse. Sahabiyayi tsuru tsuru a zaune haisam ya karaso indayake zaune yasa kafarsa daya ya taka kujerar dasahabi ke zaune ya duko dai dai fuskar sahabisuna kallon kallo . Sahabi ya yatsune fuska ya ce''meye haka haisam lafiya ko ka zama dan taadda ne kazo har gidana ka angajeni'' ya yunkurazai tashi taji haisam ya turashi karshen kujerawannan karon hannu yasa ya danki wuyan sahabi.Sai ido kuru kuru an shakeshi kai kace mujiya ce tafada rami. Haisam yasa hannu a aljihu ya ciro wata karamar wuka ta bude ta tana walkiya tasansanawa sahabi a hancinsa ya ce '' ka kula daabun fa nake so na fada maka idan ka kiyaye kakubuta idan kuwa kaki to kaiconka kaga wannanwukan zan iya lumata a cikinka ko na yanka ta awuyanka ka fadi ka mutu ko? To ina da niyyar aikata haka in har ka kuskura ka sakw takurawahannah a makarantar nan. Zan iya kashe ko wayeba kai kadai ba don haka ka kiyaye. Sannanhaisam ya sake shi ya mayar da wukarsa aljihu yajuya ya bude kofa ya fita yabar sahabi nan zauneyana tunani kamar a mafarki yau yaji kanshin mutuwa baro baro yana fadin''lallai haisam dagaske yake zai iya kis a kan yarinyar nan fa'' abayyane. haisam na fita gidan uncle yusuf ya shigakasancewat duk yawancin malaman samari nebabu mata a gidan. Daya taba kofar yaji a bude saikawai yasa kai. Kicibus suka yi yusuf ya fito dagawanka daure da dan tawul a jikinsa. Yayi mamakidaya ga haisam a tsakiyar falonsa ko sallama bai ji ba, murtik haisam yake babu walwala. Shima sai jiyayi an tunkudeshi kan kujera yayi masa gargadi,kamar yadda ya yiwa sahabi ya firo ya barshi nanzaune yana mamaki. Saboda tsabagen tsorata suyusuf ko fitowa basu sake yi ba sai da safe . Balle suje su daki hannah da daddare kamar yadda suka shirya yi, haisam ma tunda ya ya shiga gida baisake fitowa ba ba sai kashe gari da misalin shadaya na rana yana da lesson a s.s.2b zai yi musugeography yana doso ofishin principal ya hangomotar yaya habib yana cikin ofishin principal ,kuma yasan yau za'a yi tane ta kawai donshi babu mai rabashi da makarantar nan. Ya karaso da sauriya nufi ofishin principal tun daga kan baranda yakejiyo kukan hannah ya shiga a fusace gami fa yayelabulen kofar bazar ya tarar da hanna a durkushega jakar kayanta nan a gabanta, principal tanarubuta mata takardar kora {dismisal letter} takardar kora daga makarantar kwata kwata ga yaya habiba zaune yana cewa''ai idan yaga tabar makarantarzai bari shima dole ''a gigice haisam ya karaso yakalli yaya habib ya kalli principal yaga da gaskesuke sun sha kunu.Haisam ya wawuro wata adda a bayan kyaurenofishin irinta yankan ciyawa ya dora akan kirjinyaya habib. Wanda mamaki ya hana yaya habib yinmotsi daga kan kujerar da yake zaine, haisamyace''hakika zan iya kashe duk wanda yake dakokarin jefa hannah a cikin tashin hankali da wahala a rayuwarta. Ban dauka zan sameka kanadaya daga cikin irin wadannan mutane ba, ammaduk da haka ba zan karya alkawarina ba. Kaiyayana ne uwa daya uba daya da irin soyayyar damahaifanmu suke yi mana, ka duba kuma irinsoyayyar da muke yiwa junanmu don haka bana son na zama ajalinka . Ba kuma zan bar makarantarnan ba har sai na cika burina dana kudira akanhannah''hannun haisam rike da adda akan kirjinyaya habib karkarwa duk jikinsa yake hawaye neyake shatatowa daga idonsa haisam gaba ki dayansa ya canja, yaya habib ya tabbata haisam ya kai kololuwar bacin rai don shi yasan yadda bacin ranhaisam yake abun babu kyau. Da wuya dai yayifushi abu da yawa bai cika bacin rai ba sai an kaishi bango idan ya hau to kowa sai ya tsorata kumamai lallashinsa ya sauko sai an sha wuya kumaidan ransa ya baci zai iya yin duk abunda ya ce zaiyi. Hanna ta kwala kara tace'' yaya haisam kadaka kashe dan uwanka a kaina na yarda ni zan barmakarantar dan allah yaya haisam, dan allah kayihakuri''wani zazzafan hawaye ne yaci gaba dazubowa daga idanuwan haisam a tsaye yake kawaiya kurawa yaya habib ido rike da wannan adda a wuyan yaya habib. Principal kuwa tuni ta dagatsalle tayi lungu tana jiran taga yadda haisam zaiyida yaa habib sannan ya dawo kanta. A fusace yayahabib ya yinkura zai tashi haisam yasa hannu yaturashi kan kujerar ya koma ya zauna. Haisam ya ce''bani takardar hannunka''yaya habib yace son hannah kake? Ya sake fada cikin tsawa yace''tambayarka nake sonta kake shi yasa ka kasabarin makarantar? Haisam yace''burina ingahannah tana cikin farin ciki a rayuwarta kuma inkwatar mata 'yancinta kamar kowacce yarinyatunda ita ba baiwa bace gatan hannah allah, sai kuma ni a duk duniyar nan. cikin sanyin jiki habib ya mikawa haisam takardar asanyaye sannan haisam ya dauke addar daga kankirjinsa ya wurga bayan kyaure ya dauki jakarkayan hannah ya ja hannunta suka fice. Habib daprincipal suka bisu da kallo suna fita principal tayiajiyar zuciya don da kyar numfashinta yake fita saboda tsabar ta tsorata ta tabbatar yadda haisamya harzuka yau zai iya kashe yayansa balle kymaita. Bayan wani lokaci mai tsawo suna zaune shirubabu wanda ya iya magana suna tunani kawai,yaya habib ya nisa ya kalli principal ya ce'' madamyaron nan da gaske yake don jaka kada a kaishi bango ya zo ya kashe wani a dinga kai kawo akotu, ina ganin a kyalesu kawai don allah a dainadukan yarinyar balle har ya harzuka yayi kisadomin haisam zai iya aikata hakan tunda ya furtayana da zuciya sosai amma fa sai an kaishi bangodan bai taba zai yi kisa ba sai yau akan yarinyar nan, zanje in sanarwa da mahaifanmu'' ya mike yafita, principal kuwa da kyar take iya maganasaboda tsoron haisa tana ganin zai iya binta gidacikin dare ya kasheta. Daga karshe ta yankewakanta shawara gara taje ta sami haisam ta bashihakuri suyi sulhu . Ta kuma yi masa alkawarin baza ta sake yadda kowa ya takurawa hannah ba. Hakakuwa tayi ta sami haisam har gida cikin lumanasuka zauna ta bashi hakuri suka yi sulhu. Tana fitahaisam ya tuntsire da dariya dadi ya lullubeshoi yace HAISAM HANNAH!! Kwanci tashi su hannah sun shiga aji shida {s.s.3}sune manya . Cikin ikon allah da hukuncin allahhannah tazo tafi kusan duk yan makarantar kokarisaboda tun tana zuwa ta takwas ta fara zuwa tabiyar daga nan ta kwacewa pamella matin positiondinta ya zamana rauda ta daya. Nusaiba ta biyu ita take zuwa ta uku. Tafi tafiya saiga hannah tazo tadaya a ajinsu wani lokaci rauda ta kwace kayantaidan nusaiba mata hargistso sai ta kwance itama,haka dai ake ra fafatawa amma yanzu da sukashiga aji shida har malamai ma fada suke hannahtafi su rauda kokartawa don sau da yawa ko tambaya aka yi a aji hannah ce take amsawa sautari. Sannan a class work da assignment tafi kowa ci. An basu mukamai daban daban. Hannahabubakar imam itace shugabar dalibai {head girl}nusaiba mataimakiyarta. Rauda kuwa dake tayikaurin suna a wajen iya rawa da wasanni {games} harma ake mata lakabi da janet jacson sai aka batasocial prefrct da games prefect mukami biyu akahada mata kuma tayi murna da wannan mukaminnata. Duk ranar social night har koyawa yara rawardisco kala kala take yi. Hannah ma ta dace damukamin saboda ana son head girl ta zama mai kokari, wacce ta iya turanci sosai, mai gaskiya,ladabi da biyayya, mai kamun kanta ba ballagazaba, mai aji , da tausayi da kuma adalci to dukwadannan hannah ta hada sun don haka nema daaka tace aka zabeta. Domin a yanzu hannah kohausa bata cika yiba turanci ya kama bakinta sosai haisam har mamakinta yake idan yaji tana zubaturanci. Tana da jan aji hannah ba kasafai ta fiyeshiga cikin yan mate dinta ba suna hayaniya. Gatada tausayi musamman ga yara 'yan kananan aji.Babu ruwanta da cin zali kyma bata yardakawayenta suci zalin yara a gabanta. Tunda itace shugabar dalibai tana da ikon hana sauran prefect . wannan halaye na hannah ya sake fito mata dakyakykyawar surarta hannah ta sake gogewaabun har musaltuwa ta yi kyau kai kace ba yarafrica bace . Yaya haisam yasan irin mayukan dakayan sawar da suka dace da jikin hannah.Haisam yasan irin mayukan da kayan sawar dasuka dace da jikin hnnah . Tsadaddun riga dawando da sket kala kala yaya haisam yake hadawahannah sai dai kawai idan ta dawo hutu ta tarar yaaje mata a gidan uwar biyu, daman tun ba yaubabaya ga mahaifinta babu wani da take ganin girmansa a duniya irin haisam. Amma da yakehaisam mai wasa da dariya ne da dalibai suna wasada dariyarsu a aji kamar yadda ya saba yi musu tuna aji daya. A garin su hannah kuwa hannah hargixo take yi musu. Gani suke kawai baturiya tazotace itace hannah, duk ranar da hannah zata dawo gida hutu samari har tsayawa suke a hanyar dazata wuce suna kallonta mata kuma ta katangasuke lekowa. Ana cewa hannah ce fa yar malamhabu a garin turawa take karatu. Hannah sai tayimurmushi kawai ta wuce. A gidan su kuwa iya abuda yayanta daina magana suka yiwa hannah sunga ci gaba na hannah daga allah yake babu irin asirinda basu yi mata ba dan a korota daga makarantarko kuma ma ta haukace amma baici ba. Hannahtana dawowa da duk kayayyakin amfani wadandazata yi amfani dashi har hutu ya kare, ko ta bawasu iya abu da yayanta sai suce basa so. Sai tayi hutunta kakaf ta bar gidan iya abu bata bataabincin da suke dafawa ba. Ita kuwa hannahdaman tafi sin haka domin ita yanxu ta saba da cinmai maiko a makaranta tuwon dawa miyar kukasai su iya abu. Madara da biskit ne abincinta , alufge a jakarta a dakinta. Sabulan wanki dana wanka masu kamshi take amfani daus ita damahaifinta. Ta bashi yayi wanka ta wanke masakayansa. Malam habu yana jin dadi sosai dawannan abu da hannah take yi masa. Yasan doleidan hannah ta zo zata kawo masa kudi da abunduniya. Ga dinkuna da take kawo masa tace inji yaya haisam. Silifas dan madina dana gayu yanzumalam habu yake sawa. Tsaf tsaf dashi na kashewaya daina gagararsa. hannah ta zama tamkar wata tauraruwa mai haskea cikin taurari a makarantarsy. Akwai kungiyoyi{club} a makarantar da yawa, tun hannah tana ajidaya ta shiga kungiyoyi daban daban. Kuma dukwasannin kwaikwayo da za a yi a kowaccekungiya sai an saka hannah ko tana so ko bata so saboda kyawunta. Tun ana sata a matsayin yarinyahar aka zo ake saka ta a matsayin budurwa. Donhaka hannah ta kware sosai wajen iya wasankwaikwayo suna fita suje makarantu daban dabana fadin kasarnan, kamar su f.g.g.c azare,f.g.g.cbauchi, f.g.g.c. Kano,f,g,g,c, bakori da dai sauransu. Saboda kyawun hannah da iya acting dinta yajawowa.f.g.g. C kazaure suna da farin jini a wajendaliban sauran makarantu. Kowa ya budi baki saiyace kai a f.g.g.c. Kazaure da suka zomakarantarmu akwai wata mai kyau hannahabubakar ta iya wasa. A yau da yamma su hannah ne suke gwaji{rahazal}din wani wasan kwaikwayoda zasu he unity gwaram suyi sati mai zuwa.Kungiyar yan hausa fulani ne suke yi, malamhaisam shine shugaban 'yan hausa club, shinemalamin kungiyar{club master}don kawai yafarfado da al'adun hausawa a makarantar, ya kuma hada kan musulmai yara da manya ya zamana sunhadu a waje daya yare daya sunyi raye raye fawake wake da wasannin kwaikwayo tare. Hannah abubakar itace a mastayin yarinya maisuna talatu cikin wasan kwaikwayo, maryam tijjaniitace a matsayin saurayin ciki mai suna abdul.Haisam ne ya rubuta labarin wasan kwaikwayon. Ayadda wasan kwaikwayon yake maryam tijjani{abdul}saurayin ciki shine ai yi tafiya kasar libiya karatu sai yayi shekaru hudu acan sannan zaidawo. Ga budurwarsa hannah wato talatu a cikinwasan sunyi alkawarin zasu yi aure daman saitafiya ta taso masa yazo zai tafi ya barta. Damanhaisam ya gutsuro takarda ya rubutawa kowacceabinda zata ce a wahen sai ta rike tana karantowa harta rike da ka, kafin ranar da zasu yi ba sai datakarda ba. A yau kusan yan aji shida kakaf sunazaune a hall din nan wajen da ake gwaji{rahazal}din nan da wasu da yawa daga cikin yan aji biyar,hudu da uku yan kungiyar. Maryam tijjani {abdul}itace ta taho da jakar kaya katuwa a rataye a kafadarta tazo wucewa suka hadu da hannah{talatu} dauke da kwarya a kanta zata je kogi deboruwa. Abdul ya sakarwa talatu wani lallausanmurmushi na so da kauna cikin sassanyar muryahannah(talatu) tace''abdul ba dai tafiya ba'' ya ce''tafiya zanyi talatu nazo ne daman inyi miki sallama'' sai kawai kwaryar dake kan talatu ta fado kasa dangigicewa. Ta rushe da kuka. Abdul ya gigice yaajiye jakar dake hannunsa, hannah ta fara karantotakardar da haisam ya rubuta musu tace'' abdulkayi min alkawari ba zaka yi aure ba a cam har saika dawo ka aureni karka je can ka sami yar larabawa ka aura ni ka manta dani'' haisam yasatafi sai duk aka dau tafi a hall din. Haisam yacekunyi kokari wajen yayi kyau kema maryam tijjaniki dage ki bata amsa dan allah banda dariyar nanda kika saba'' maryam tijjani tace to bazan yi dariyaba'' ta daga ido ta kalli hannah(talatu) wani kallom soyayya da hannah take, tayi wani narai narai daidanuwanta kai sai kace a gaban saurayinta nagaske take. Sai dariya ta kwacewa maryam tijjanisai kowa yasa dariya. Haisam yace ''maryamgaskiya kina bata mana lokaci kullum muka zodariya kawai kike yi saura kwana uku fa mu fita excusion idan kinsan ba zaki iya ba nasawata''maryam tace''uncle allah hannah ce take sanidariya baka ga kallon fa take yimin bafa kamar tasami saurayinta da gaske sai kashe idotake''haisam yayi dariya yace''tsabar tafiki iyaacting kenan. Shi daman wasan kwaikwayo ana son duk abunda aka baka kayi kokari ka nunakamar da gaske ne. wajen kuka kayi kuka, wajen murnakayi murna . Kema kiyi mata kallo kamar kecesaurayin kin hadu da budurwar da kika fi so a duniya. Wannan yana nuna kenan hannah ta iyaacting sosai kamar da gaske. Kowa ya hau dariyaana yiwa maryam tsiya ''kema ki yi mata kallonsoyayyar mana ko baki iya bane? Haisam ya tashi yaje ya karbi takardar hannunmaryam ya ce''koma gefe ki dinga kallon yaddazamu yi sosai don ki koya'' ya ce da hannah''tokara karanto naki''babu kunya hannah ta narkarda idanuwanta ta kashe murya lallausa ta dubihaisam kallo ido cikin ido''abdul kayi min alkawarin ba zaka yi aure ba a can har sai ka dawo ka aurenikar kaje can ka sami yar larabawa ka aura ni kamanta dani anan'' haisam ma ya narairaice ido yakurawa hannah ido kawai wannan kallo da haisamyake yiwa hannah ya sosa mata wani waje axuciyarta, ya ce''talatu ba zan yi aure ba, kuma ba zan manta dake ba. Ko a ina nake, ko da gangarjikina bata tare dake ruhina yana tare da ke.,soyayya baiwa ce, hannah kina raina a kodayaushe . Ina sonki hanna'' taji gabanta ya fadi donjin yaune rana ta farko da hannah tasan ma'anarwakar nan da take yi tayi shiru tana tunani tana kallon yaya haisam ta san tabbas wannan wajen acikin wakar nan da take yi masa ya dauko kamardaga sama taji yaya haisam ya ci gaba da cewa''inasonki ina sonki hannah! Ba zan manta dake bakina raina har abada'' wannan karon bakarantowa ya ke a takarda ba kuma ba talati yace ba, hannah sai ta fara ja da baya taba tafiya ahankali tasa hannu ta rufe idanuwanta tanamurmushi. Kunya ta ka mata gaba daya yan kallonsun zubo mata ido suna kallon sarautar allah, domin kowa ya san wannan kallon kadai da sukeyiwa junan su yafi karfin gwaji balle kalaman da yake fita daga bakin haisam ba a jikin takardaryake ba. Sai yaja wani dogon numfashi ya juya yakalli sauran dalibai yace'' kuje ma karasa gwajin dadaddare'' ya fita ya nufi gidansa. Dalibai su ka firfitosuna gulmammaki'' wannan anya hannah da unclehaisam ba soyayya suke yi ba, ke kinga kallon da suke yiwa junansu uncle haisam kamar yarungumeta fa. Haka suka shiga dakunansukowacce ta nufi bangaranta. Rauda ta sami hannah a kwance akan gadonta tadora filo a kanta babu abinda take tunanowa saiidanuwan yaya haisam sai kuma tsananin mamakinyadda ya rike baitukan wakar nan da take yi masatun tana aji daya. Tace a ranta ashe ma'anar wakarkenan banda yarinta nake kai kaicewa nake rera masa ko da gangar jikina bata tare dakai ruhinayana tare da kai. Har nusaiba take cewa hannahmeye ruhi nace ina jin larabcine ashe ni ban sanhausa ba ce tsaba a lokacin . Ruhina , ruhina'' tsakitaji anyi a kanta ta bude ido sai taga raudaamurtuke. Tayi furgigit ta tashi zaune tace'' rauda har kun dawo? Rauda ta kaste ta tace''haka zaki cemana har mun dawo da acan zamu kwana? Komuma son maso wani muke yi da zamu bishigidansa? Yaya haisam dai yana da wacce yake sokuma an gama magana gara kowacce ta komakauyenta ta sami wani bakauyen ta aura amma haisam sai ramla. Hannah tace'' rauda me ya faru ,wani abun akayi ? Nusaiba tace'' ke rauda meyehaka wasan kwaikwayo ne fa kowa yasan gwajine ba gaske bane. Wai ke rauda me yasa bakya sona zauna lafiya ne ? Rauda tayi tsaki ta fice tana cewa'' duk gulmace gulmacen da ake ina sane. Dan iskan kauye yafi na burni iya iskanci da rashinmutunci ai. Hannah ta fashe da kuka, tayi kuka kamar ranta zaifita. Nusaiba na lallashinta da kyar hanna tayi shirusuka je suka yi alwalar magaruba. Bayan sallarisha'i sunci abinci karfe takwas dai dai sai suka jesuka kora dalibai kowacce ta fita ajinsu don yinprep din dare, uncle haisam ya fito daga gidansa takwas da rabi yazo ya kirawo yan hausa club donsuzo su karasa gwajin wasan kwaikwayon da sukeyi. Ta bayan wundo ya hango rauda tsaye akanbencin hannah tana ta gurza mata rashin mutuncihar cewa take da ba'asam asalin balbela ba sai tacemadina ne garinsu. Yaga hanna zaune tayi shiru tana hawaye, ran nusaiba ya baci ta taso tashigarwa hannah kamar zasu daku da rauda. Saihaisam ya leko ta wundo yayi musu tsawa ya ce sufito waje yana son ganinsu. suna zuwa gabansa kallo daya suka yi masa sukasan babu wasa yau a murtike yake kasancewarsunsan bacin ransa babu kyau sai kowacce ta fararawar jiki. Ya daka tsawa yace kowacce tayi kneeldown bayan sun yi ne ya tambayi nusaiba me yafaru. Nusaiba ta zaiyana masa dukkan abunda ya faru tsakanin rauda da hannah tun daga yammahar na yanzu ya juya ya kallo rauda yace'' raudahakane ? Ta gyada kai gami da tabe baki tace''haka ne kuma gaskiya na fada'' haisam ya fusataya kaiwa rauda mari tayi sauri ta kwanta a kasa baisameta ba. Tace' yaya haisam yau ni zaka mara akan hannah? Haisa yayi shiru hannayensa a cikinaljihu kansa a sunkuye a kasa. Can ya dago yace danusaiba ta tashi ta shiga aji. Ya dubi rauda wacce kedurkushe a kan gwiwarta a gabansa rauda tarushe da kuka. Haisam yace'' rauda tun ba yau ba,tun kuna aji daya na lura kin kafawa hanna karan zuka a makarantar nan. Yanzu kece kadai kikarage a cikin masu takurawa hanna zan iya daukankowanne irin mataki a kanki muddin baki fitaharkar hannah ba ki kiyae, idan kuma kin ki ni zanfiki farin ciki don zaki ga abunda zan zartar a kanki.Ko amratu 'yar shekara bakwai zan iya.hukuntata muddin ta nemi takurawa hannawannan alkawari nayi wa allah kuma sai na cika shidon hanna amana ce a wajena'' kamar a mafarkirauda take jin kalaman yaya haisam, tana fada aranta lallai abun nasa babbane da gaske yake'' daga karshe ya ce ta shiga aji tana sharbar kuka tamike a fusace ta shiga aji. Ya shigo shima ajin yakalli hannah wacce ido yayi mata jawur don kukayace hanna ki kira sauran yan hausa club ku tahohall ku sameni mu karasa rahazal din. Cikin ladabihannah ta amsa masa. Ya fita ya nufi hall. Hannah cewa'' rauda muje hall yaya haisam na kira'' tadago ta harari hannah tace'' bazan je ba kuma nafita daga club din ko za'a sani dole ne? Hanna zatace wani abu nusaiba taja hannunta tace ''kyaletamu tafi mu kira sauran. Hutu ya kusa karewa har ana shirye shiryen farafirst term examination. Kowacce karatu takehaikan, sunyi jarabawa an basu sakamako kafinranar hutu. Hannah ce tazo ta daya a ajinsuwannan karon, rauda ta biyu nusaiba ta uku ranarhutu bayan anyi assembly hutu da wur wuri kafin kowa ya fara tafiya haisam yazo ya sami hanna,rauda nusaiba da wasu kawayensu a zazzaune akan barandar hall suna ta hira. Bayan sun gaisheda shi sai ya ce'' hannah taso ga safiyanu yazodaukarki, idan muka saukeki a gidan uwar biyuzamu wuce dashi dan musa can jahar katsina acan yake neman aure zamu kai kayan gaisuwarsurukai'' su duka suka kyalkyale da dariya. Hannahtace ''oh yaya safiyanu daman aure zai yi ko ya fadamana sunanta ranar nida nusaiba muka ga hotontaa motarsa muka ce budurwarsa ce ya ce wai shi babudurwarsa bace'' nusaiba tace'' haka ne kuwa a bayan hoton an rubuta dan musa har nake cewadan musa kuma sunan mace dan musa ya ce ehhaka sunanta. haisam yayi dariya , sannan ya juya ya kallo raudatasha kunu ta kawar da kai gefe daman tundaakayi wannan abun bata cika yiwa hannahmagana musamman idan taga haisam da hannah.Ga uwa uba hannah ta kwace mata position tazo tadaya , sai take jin haushin kamar ta kashe hannah. Haisam ya ce'' rauda ni ba kano zanje ba sai mundawo daga danmusa don gida ma nace kada aturomun da mota auwal zaizo daukarki ko direba?Tace '' sai dai direba yaya auwal yanamaiduguri''yace''oh haka ne fa, to ki gaishe dasuhajiya sai wahen jibi zanzo kanon. Idan muka tafi yau ba damar muyi tafiyar dare dole mu kwanasannan washe gari mu dawo kazaure wata kila inkwana a cikin gari jibi muje kanon da safiyanu .Rauda tace zasu ji . Allah ya kiyaye hanya. Hannahta kira wasu juniors suka dauki jakunkunanta sukazuba mata a mota. Tayi wa kawayenta sallama tana zolayarsu su tana cewa yau itace farkon tafiya dukmakarantarn ta barsu su yan kwantai ne. Rauda tatabe baki tace'' yanxu wata kila har kowa ya isagida ke baki isa gida ba, saboda hanyar garinkukwalta ce sambel ba kasa ba'' hannah da nusaibane kawai suka gane rauda bakar magana ta fada, wato hannah bakauyiya cekenan take nufi saihannah tayi murmushi kawai ta tafi ta shiga motatana dagawa nusaiba hannu har suka fita get . a gidan uwar biyu su haisam suka sauke hanna ,haisam ya shiga cikin gidan bayan ya bawa uwarbiyu kudaden motarsu da wanda zasu kaiwamahaifin hannah suka yi godiya yayi musu sallamaya juya ta tafi har yaje kofar fita ya juyo yace '' koyanzu zaku tafi mu ajiyeku a tashe'' hannah tayi sauri tace yaya haisam da yamma zamu tafi ina soinje gidajen kawayena a nan cikin gari. Yayimurmushi ya ce'' wato akuyar daure ta samu sake,su hannah an iya yawo ko? Su duka suka yi dariyasannan ya fita. Damisalin karfe biyar uwar biyu dahannah suka isa babban mutum , suka je suka iske gida a hargitse anyi tashin hankali. Malam habumahaifin hannah kuka wiwi. Cikin rikice da rudanihannah ta tambaya meya faru babanta yake kuka.Iya abu ta tuntsire da dariya tayi buda da shewatace'' tambayi ubanki. Karshen tuka tiki tik yauallah ya nuna mana gaskiya'' hankalin hannah da uwar biyu ya sake tashi sosai, suna so suji me iyaabu take nufi da wannan habaici nata. Malam habuya sharbe hawaye da babbar riga ya ce''muje zaurein fada muku abunda ya faru'' da yake damantsakar gida suka iske su. Suka je zaure sukazazzauna malamhabu ya nisa gami da langabar dakai yace'' idan ka haifa dole a jawo maka, damanance dan kuka shi ke jawa uwarsa zagi. Uwar biyu dahannah su dai sun kagu suji abunda ke faruwayace'' yanzun nan babu dadewa watakila kunhadu da wata bakar katuwar mota a hanyar shigowa garin nan wata fitsararriyar yarinya cetazo ta cimun mutunci a kofar gidan nan har ta taramun mutane. Hannah tace''wacece baba? Cikinrudani da fargaba ta tanbaya. Ya ce'' farko da tazosai ta tsaya ta karemun kallo a wulakance sannantace naji kunya wallahi yasa naji kunya. Dama yarinyar yar talakawa ce yake bata mun lokaciakanta to baba bari in fada maka ka jawa yarkahanna kunne ta kiyayi mijina idan ba haka ba nizan zamo ajalinta domin zan iya kashe duk yarinyarda zata rabani da haisam abun sona. Kuma ka cireyarka daga makarantar nan domin idan bata bar makarantar va haisam ba zai bar makarantar ba yarabu da ita. Muddin hanna ta sake komawamakarantar to kuwa har makarantar zan bita inzartar da abun da na yi niyya. Ba tana takama itakyakykyawa bace to zan kwara mata wani abuafuskarta {acid}fuskar ta sale ta kwakwkwabe har makarantar zan tarar da ita in yaso sai inga fuskarda zai sota. Don soyayya hannah take yi da mijinava karatu ba. Har sakamakon jarabawar kanwatayake dauka ya bata tazo ta daya a ajinsu. To na gajiwannan shine lokaci na karshe dana bawa hannahidan taki ji ta koma makarantar to wallahi ta kuka da kanta'' malam habu ya sharbe hawaye yaci gabada cewa'' da wata kanwarta yar makaranta tanasanye da kayan makaranta irin naki yar baba itamatana taya ta suka yimin tas, iya abu na ihu tanadariya tana cewa daman ta sani ba tun yau bahanne karuwanci aka kaita tayi ba makaranta ba yanzu gari duk ya dauka maganar ake yi don agaban mutane aka yi haka. Tace hannah taci sa'ada bam sameta ba da sai ta faffalla miki mari sannansuka shiga mota suka tafi. Hannah bata iya cewakomai ba sai ta sunkuyar da kai kasa tana kukamalam habu ma kukan yake uwar biyu ta matse hawaye tace'' kuyi shiru, ku daina kuka wannanduk abune na shirme da karya ita wannan yarinyardata zo ina tunanin matar da malam haisam zai aurace take ganin son hanna yake alhali kowa yasanhaisam a matsayin yaya koma ince uba yake awajen hanna tun tana karama fa inah, ai zancen so ma bai taso ba. Hannah karatu take a makarantababu wata soyayya daga wannan hutun ma bazasu sake dawowa har sai sun gama makarantar makwata kwata saura wata bakwai su gama. malam habu ya zabura yace'' wacce komawa aihanne tazo kenan baza ta koma ba ina wanizancen saura wata bakwai hanne ta gama aikosaura kwana bakwai ne hanne ta gama karatuntabayan a gaban mutane aka ce ba karatu take yi amakarantar soyayya take yi sannan in bar yata ta koma ai sai a dinga cewa tana can tana iskanci harwata bakwai ba ta komo gida hutu ba, ni daiabunda zance muku uwar biyu ke da wannan yarohaisam allah yayi muku albarka amma hanna bazata sake koma wa ba karatun ya isa haka dukkawayenta harma da kannanta duk sunyi aure gara itama in hadata da wani a dangi tayi aurentabaki alaikum kafin a kone mata fuska. Damanabunda muke ji a redio gaskiya ne ace an fesawawani ko wata wani ruwa a fuska ya kwakwkwabogaske ne to ba zai faru akan hanne ba. Karatun datayi na baya ya isa nagode madalla'' cikin rudewa uwar biyu tace'' haba malam habu yaya zaka yimana haka ? Baka kyauta masa ba yarinyar nanduk zance take haisam ba zai barta taje gurinhanna ba balle tayi mata wani abu. Bama a barinkowa yaga dalibai in ba ranar bisitin ba dokarmakarantar ce'' malam habu ya mike ya shiga gida yana cewa'' nifa na gama maganata uwar biyu kiyihakuri ki bar maganan komawar hannemakaranta. Ai ko karan hauka ya cije ni ba zan baryata taje inda za'a halakata ba ina hanne ina kishida wadannan gogaggun yan burnin masu kudi.Tunda tana ganin mijinta son hanne yake ai sai a hakura da taimakon na baya ma allah ya saka'' yashige ya bar hannah tana matse hawayen dakeidanuwanta da wani farin hankici dake hannuntatace uwar biyu'' kyale shi ya tsorata ne kafin hutuya kare zai yadda idan na wayar masa dakai ahankali na lallabashi sai dai idan hutu ya rage sati guda kizo don muji mai zai ce in yaki yadda sai daiyaya haisam yazo ko kuma ya turo principal idankuma yaki yarda na shiga uku karshen karatunaya zo. Hannah ta rushe da kuka, uwar biyu tace ''yadda za'ayi shine haisam zan turo yazo garin nanmahaifinki ya kalli kwayar idonsa ya ce ya hanaki ki koma makaranta, haisam zaizo da kansa. A hakahannah da uwar biyu suka yi sallama. Hanna tayitayi da uwar biyu ta shigo cikin gida ta huta sannanta tafi uwar biyu tace baza ta shigo ba ina zata iyashigowa wajen iya abu masifaffiyar matar da zataiya kashe mutum ma don rashin imani. Hannah ta raka ta har tasha ta shiga mota sannan hanna tadawo gida. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 GANGARJIKINSA NA AURA 1 Part 4 Posted by ANaM Dorayi on 02:25 PM, 30-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura A zaure malam habu ya shimfida tabarmar kaba dawani yagulallen filo da zanin gado irin na da da dadinnan shekara aru aru da suka shude. Nan neshimfidarsa da yake kwana nan ne dakinsa danduk dare duk sanyi da damuna a nan yake sabodaiya abu ta mamaye dakunan gidan. Dakinsa din ya barwa hanna data girma ya dawo zaure don da datana yarinya tare suke kwana a dakin. Ko dayaushe hannah zaka ganta a zaune a gefenbabanta tana lallashinsa tana wayar masa dakaigame da makarantarsu. Tana nuna masamuhimmancin karatu da kuma irin bacin ran da haisam zaiji idan bata koma ba.Ta kwashe labarun abubuwan da suka faru tuntana aji daya har tazo aji shida yadda haisam yakekula da ita da irin tataburzar da aka sha yi akantada dalibai da malamai har ya kwatar mata yancintababu mai dukanta ko zaginta yanzu, kuma yayialkawari zai iya kashe ko waye yake son ya takura mata. Malam habu ya gamsu sosai da bayananhanna ya kuma san haisam ba zai yadda a cuce taba. Hutu ya rage sati guda sai ga uwar biyu ta dira agarin su hanna ta iske hanna da mahaifinta a zaurea zaune zance daya dai suke ta nanatawa kullumshine zancen ya barta ta koma makaranta. Bayansun gaisa da uwarbiyu ta fadi abunda ke tafe da itacewar tazo ne ta tafi da hanna hutu ya kare sai malam habu ya kekashe idanuwansa ya ce shifababu inda hanna zata je. Hanna tayi mamaki da tajiya fadi haka yanzu bayan da ya yarda da tayi masabayani sai kawai hanna ta rushe da kuka, magiyarduniyar nan uwar biyu ta dinga yiwa malam habuamma yaki yarda daga karshe uwar biyu tayi musu sallama ta tafi. Tana isa kazaure ta wuce gidan susafiyanu abokin haisam bata sameshiba ance yanakano sai ta koma gida ta zuba ido ko allah zai jehomata haisam ko safiyanu idan zasu kawo sayayyarhanna ta makaranta tunda sunsan hutu ya karezasu kawo. Har ana gobe a koma makaranta uwar biyu bata ga safiyanu ba balle haisam. A can kuwahanna hankalinta ya gama tashi taji shiru yayahaisam baizo ya taya ta rokar babanta , sai ta daukashima yayi fushi ne yace to a bar masa 'yarsa kartayi karatun mana. Da la'asar likis hanna damahaifinta suna zaune akan lintsimemiyar tabarmar kaba a zauren kasa da rufin ciyawa hanna kukatake yau tun safe. Malam habu lallashin duniyar nantayi shiru ta hakura tama cirewa ranta makarantardon shi ya gama magana bazata koma makarantaba . Taki ci taki sha sai kuka take rafsawa. Kwatsamsuka ji sallama daga idon na da hanna tayi sai tayi ido hudu da yaya haisam , safiyanu da uwar biyusuka yi sallama suka shigo. Da sauri hanna tadauko musu tabarma ta shimfida musu sukazazzauna ta koma ta dauko musu ruwa a randacikin kwanan sha. Ta kawo ta durkusa kasa tagaishe su ta koma gefe ta zauna. Murna ce ta rufe malam habu yama rasa inda zaisa wadannanmanyan baki, yan gayu, ya lalubo kudi a aljihunsaya ce da hannah tayi maza taje bakin kasuwa tasuyo musu fura da nono, su haisam suka ce kaihaba ai su a koshe suke ya barshi kawai. Bayansun gaggaisa malam habu ya gama yi musu sannu da zuwab da tako kare sai safiyanu ya nisayace''baba munzo ne mu ba da hakuri akan dalilinda yasa ka hana hanna zuwa makaranta. Shinemuka zo da kammu mu roke ka baba duka dukasaura wata nawa ne yanzu hanna zata gamakaratunta ta dawo gida'' nan da nan malam habu ya canja fuskar fara'ar dayake ta gushe yace''wai me yasa kuke sani inamuku kin kyautatawa ne ? Bana so ku tambayeniabinda zan kasa baku na gama magana don allahdon annabi ku bar zancen karatun 'yar baba. Nayanke shawara ba zata koma ba. Haisam kokarin da yake yi allah ya saka maka hakan ma ya isa basai ta kara yin wasu watannin ba. Nace uwar biyuta yi maka godiya ka cika min alkawarin da kadauka wallahi ko bata karasa ba ai ka cika alkawariba laifinka bane. Alkawari da amana ai ba karaminaiki bane cika su amma cikin yardar allah ka cika dai dai ubangiji ya saka maka da gidan aljanna.Amma hanna ba zan bari ta koma ba. Haisam yayidan murmushi game da gyaran murya ya ce'' aminbaba, amma idan baka manta ba a ranar dana karbiamanar hanna nayi alkawarin hanna zata yi karatuto kai ma a lokacin kayi min alkawari,kaga alkawari girma ne de dashi baka cika ba, kayi min alkawarinzaka bar hanna tayi karatun don sai dama nasakayi alkawarin zaka dinga turo hanna makarantabaza ka hana ta ba wataran sannan nayi makaalkawarina. Malam habu yayi shiru zuwa wani danlokaci can ya nisa yace'' anyi haka yaro haka akayi nayi maka alkawari to ammma ai abinda yarinyarnan tace gargadi fa tayi min akan kada in kara tura'yata makarantar nan kaga ai kome tayi mata batada laifi nine ban ji ba kenan'' haisam ya katseshiyace'' kare lafiyar hanna da duk wani abinda zaicuce ta yana daga cikin amanar dana dauka in allah yaso babu mai yiwa hanna wani abu. Ramla kuwata fada ne kawai a cikin bacin rai amma babuabinda zata yiwa hanna, a ina ma zata ganta balletayi mata wani abu ? Ta dai fadi son ranta dontatsorataka kaga baba kuma abinda ta fada ba hakabane hanna karatu take haikan a makaranta, kanwa ce hanna a wajena ni ne mai tsawatar matama misali da ace tana soyayya da samari amakarantar . Baba mu canfa akwai doka babuyadda za'ayi malami yayi soyayya da daliba, babukuma yadda za'ayi wata ya shigo cikin makarantardauke da wata guba taje ta cuci dalibai don haka baba ka kwantar da hankalinka ni da kai duk mucika alkawuran da muka daukarwa allah''.Malam habu yace ''to shikenan allah ya taya mucikawa. Hanna dauko kayanki ku tafi allah yakiyaye hanya''suka duka suka ce amin''sai murnata dira a zukatansu. Cikin farin ciki da jin dadihanna ta shiga ta fara hado kayanta ,iya abu tayicaraf ta fito daga bayan kyauren da take labe ta hau malam habu da fada'' au yarda kayi dawannan dadin bakin da suka yi maka. Duk wannangaskiyar data baiyana yarinya iskanci suke amakarantar don yana aiko maka dana goro shinekaki fadar allah saboda abun duniya ? Kallo dayahaisam yayi mata yaga irin wadannan mutane ne masu abun haushi masu kama da aljanu munanamasu bakin hali yaji ya tsani iya abu har baya so yakara kallon fuskar shegiya. Hannah ta ratayajakarta ta fito ko kallon iya abu bata yi ba balle tayimata sallama. Ta duka ta yiwa babanta godiya tayimasa sallama ta wuce cikin mota. Haisam ya danko kudo mai yawa ya ajiye a gaban malam habu.Safiyanu ma haka ya debo kudi ta ajiye masa sukayi masa sallama dukkaninsu yana godiya sunagodiya suka shiga mota suka tafi. Ba safiyanu bahar haisam yaji ya sake tausaya rayuwar hannasaboda ganin yadda gidansu yake. Gidan kasa ne anyi masa katanga da kara rufin azara abin dai abintausayi talauci dai tsagwaransa. Babu abinda zakadaga a gidan ka sayar dashi dari biyar komai ragaraga kaico!hannah na komawa makaranta tasalittafinta a gaba tahau karatu. Sune yanzu masushirin zana s.s.c.e don haka babu wasa sai karatu. kwance tashi su hannah sun fara jarabawarsu takarshe [s.s.c.e} saboda daman tuni sun gamatsarge karatu. Sai suka ga cin tuwo yafi jarabawarwuya sai kawai suka hau fede ta. Geography dinmalam haisam itace wacce suka yi ta karshe damisalin karfe hudu na yamma suka gama daman jakunkunansu su suna baki hall din da sukejarabawar suna fitowa sai kowacce ta dauki jakartasai tafiya daman kowacce ta kagu taje gida taga'yan gidansu basu taba irin wannna dadewa amakarantar ba har watanni bakwai a makaranta.Hatta hanna da bata so ayi hutu itama yanzu so taje gidq taga mahaifinta sai mafarkinsa take kullum takwanta barci. Hanna da kawayenta sun sha kukanrabuwa musamman ita da nusaiba sun saba sosaigashi zasu rabu. Gashi kuma babu waya a garinsuhanna balle su dinga gaisawa a waya. Rauda ma tarungume hanna tana kuka taji duk babu dadi yanzu da zasu rabu kuka wiwi juniors suke yi narabuwa da seniors dinsu zasu tafi su barsumusamman hanna basu ji dadin rabuwa da ita basaboda tayi musu mutunci samun shugabar dalibaiirin hanna sai an bincika. Ta koya musu abubuwana cikin kungiyoyinsu {club}na makarantar. A haka kowacce ta tafi gida kuka wiwi. Safiyanu ne yazo yadauki hanna ya kaita gidan uwar biyu. Yau haisamtun kafin su shiga jarabawa yazo yayi musu sallamaya koma gidansa ya rufe kansa kansa ko wajen daake bankwana bai zo ba saboda tsananin bakincikin rabuwa da yan ajinsa da yake matukar so. Gidan uwar biyu ma sai washe gari yaje ya samuhanna a can. Bayan sun gaisa ya ce da hannah''yau zaki tafi gida ko sai kin sake hutawa kamar satidaya anan sannan ki tafi ? Hannah tayi caraf tace''yaya haisam yau zan tafi na dade banga babanaba'' haisam yayi dariya ya ce'' wato ke yanzu kin bar kazaure kenan zaman kazaure sai mu ? Tayidariya tace'' sai ku ai mun daku wannan hutun harna daina sha'awar garin allah yaya haisam'' haisamya mike ya ce'' to ki shirya zanje nan makwabtasafiyanu yana ciki wajen abokansa ana wankemasa motar ana gamawa sai ku fito zan aiko yaro yayi kiranku sai mu kaiku tasha ku tafi. Da har cangarin zamu kaiku inyiwa baba godiya ince masagaki na dawo masa dake lafiya na cika alkawarishima ya cika to sai safiyanu ya ce kano zai tafi dakakarsa in anjima'' hanna tayi dariya tace'' kai yaahaisam ai babu komai yana gani na yasan lafiya na dawo lallai kuwa ka cika alkawari'' ya juyo yakalleta yace ''ko? Tayi murmushi tace'' E'' sannan yafita yana murmushi. Bayan fitarsa da dadewa sosaiyaro ya shigo ya ce wai uwar biyu da hanna su fitoinji su safiyanu suna kofar gidan dallatu'' daman ashirye suke tsaf sai hannah ta dorawa yaron jifgegiyar jakar kayanta. Jakunkuna uku ne. Yakaiya dawo ya dauki ta biyu sannan yazo ya dauki takarshe sannan suka fito uwar biyu ma da buhuntaa kanta, suka shiga mota sai tashar kazaure.Hannah ta hado kayanta kakaf na gidan uwar biyu.Katifa da bokiti kuwa taba uwar biyu kyauta. Kaya masu kyau atamfofi da shaddoji da yawa. Hanna tabawa uwar biyu kyauta da 'yarta halima. Dake kayatsadaddu leshi ma uku, shadda da atamfofobibbiyu yaya haisam ya yiwa hannah na candy.Bayan takalma da yan kunne, sarka da dan kunneharda gwal ya suyo mata. Suna isa tasha a bakin tasha safiyanu ya tsaya da motar. Ma'aikata nan'yan union su biyi suka zo suka tambaye su inazasu da suka fada sai suka ce babu motar babbanmutum yanzu amma baza a dade ba zata zo. Haisamyace su kwashe jakunkunan su kai cikin tasha,hanna da uwar biyu suka shiga cikin tasha. Safiyanu da haisam suna nan bakin mota a tsaye abakin tasha. Can suna taye suna hira sai safiyanu yakalli agogo ya ce yanzu fa muka yi da hajja kakatazan dawo mu tafi kano tana can tana jira na''haisam tace'' ai ba komai heka kawai nima idannaga tafiyarsu acaba zam hau in koma cikin makaranta.. Suka yi sallama safiyanu ya shiga motaya tafi, haisam kuma ya shiga cikin tasha A cikinwata yar rumfa ya iske hannah a zaune akan jakarkayanta uwar biyu kuma akan wani benci suna'yar hira suna jiran zuwan mota.Haisam ya karasa cikin yar rumfar yanatambayar su''har yanzu motar bata zoo bane? Uwarbiyu tace'' sun dai ce yaznzu zata zo munzo da wurine wai daman motar bata zuwa da wuri'' ta mike dasauri daga kan bencin tace da haisam ya zauna ,yace''lah babu komai yi zamanki mana''' uwar biyu tace'' a'a ka tsaya'' ga kawayena acan suna sayarda zogale bari inje wajensu mu gaisa daman dankar na bar hannah ita kadai shine yasa banje tundazu ba''uwar biyu ta tafi .haisam ya zauna yanakallon matafiya da masu mota ana ta hayaniya. Canya juya ya kalli hanna wacce ke zaune akan jakarta tayi jugum kamar tunanin wani abu take, ya kuramata ido kawai yana tunani a ransa. Babu abundaya fara tunawa sai a ranar da aka fara kawohannah makaranta ta ci dammara ta hau ta zaunaakan akwatinta tayi jugum tayi shiru a lokacin dababanta ya tafi ya barta. Amma yanzu maimakon dammarar da taci sai tayi shar da wani tsadaddenbakin leshi mai duwatsu kala kala suna sheki ajikinta. Dinkin fitet tsamammiyar riga da siket ta yafadan yalolon gyale ta dana daurin dan kwali yayinda lallausan gashin nan nata mai santsi baki datsawo ta tufke da bakin ribon a keyarta. Hannah ta dago kai sai taga yaya haisam kallonta yake yikawai a lokaci guda sai kowannensu ya sakarwadayan murmushi. Abunda itama ta fara tunawaranar da babanta ya kawota makaranta ta hau kanakwatinta ta zauna tayi shiru yaya haisam yanazaune akan benci yana kallonta. Mai tallar biredi ne yazo ya ishesu da a sayi buredi ga gardi, zakibiredin tsaraba . Haisam ya kalli hanna yace'' bazaki sayi abun tsaraba ba ne ki kaiwa yara? Hannatace'' kyalesu yaya'' ya ce '' ban gane kyalesu ba,haka zaki yi wata bakwai kije musu hannurabbana, biscuit ko sweat zaki shiga aishalle ki saye, ungo kudin ko ki aiki wani yaron? Ya cirokudi a aljihunsa, hannah tayi dariya tace'' su fasunfi ganewa ayi musu tsarabar biredi'' haisam yace su sha tea da safe dashi ? Hannah tace'' a.a surinka gutsira a haka'' su duka suka yi dariya.Haisam ya ce da mai biredi ya sauke yaje ya siyo jakar bacco ya dawo. Ba dadewa sai ga mai biredidauke da jakar bacco. Haisam ya ce ya juye buredinduka a ciki. Hannah ta rike baki tace'' yaya haisamwadanna manya manyan buredi har wajen takwasai suna da girma sunyi yawa biyu ma sun isa''haisam ya ce a'a basuyi yawa ba kowa yazo yayi miki sannu da zuwa sai ki yago masa gayan birediki bashi kice tsaraba'' su dukkansu suka kyalkyaleda dariya harda mai sayar da biredi dadi yakamashi ana masa ciniki. Mai lemon fata ne yagarzayo da sauri yaga an siye na abokinsa, shimaya bude muryarsa gaba daya yana ''a sayi na tsaraba'' shima haisam yace ya siyo bacco yazo yajiye duka farantin , yayi kololo kuwa dan cika. Nada nan ya garzaya da sauri ya siyo bacco ya juye saikudinsu tumus a hannu. Sika jerawa hannabakkuna a gaba suka tafi suna murna. Hanna tadago kai ta kallo haisam fuskarta cike da murmushi gami da nuna jin dadin kulawar da yake yi matatace'' yaya na gode fa kwarai da gaske'' ya ce''babu komai hanna'' hanna ta dago ta kalle shi sukahada ido tace'' yaya haisam baka bani abin busanaba da tsakiyoyina daka ce in baka zaka boyeminkada malamai su kwace min din nan tun randa aka kawoni aji daya.Haisam ya tuntsire da dariya hanna ma hakayace'' bazan baki ba sai kinyi wannan kwalliyar dakika yi a fuskarki mai digo digo nan da wannandammarar da kike yi sannan zan baki sarkokinki''suka sake tuntsirewa da dariya ya ce'' busa nake yida abun busarki fa. Kusan kullum da daddare kafin in kwanta zaki yi mamaki idan aka ce yanzu na fikiiya busar da wakar. Nafa rike yadda kuke wakarda amratu kanwata zabje in kaiwa a gida ashe bakibani ba, bari inje in dauko muki'' hannah tayi sauritace'' ban san kana so ba na bar maka, hartsakiyoyin ma in so kake? Yace ''eh suma amratu zan bawa ta dinga kwalliya dasu'' hannah tayidariya tace''amratu baza tayi kwalliya dasu ba,komu yan kauye mun daina saka irinsu'' motar dazata je babban mutum ce ta shigo. Doguwar bus cenan da na uwar biyu ta taso tace dasu'' hannah gamota nan tazo daga jakar su zuba kayan a but'' kwandasta yazo ya debi jakunkunan kayanhannah da tsarabar ya zuzzuba a but, hannah dauwar biyu suka shiga kujerar baya su biyu kacalsauran wajen haisam ne yake biya daman hakayake musu in dai ya kawosu tasha to mutane hudubasa zama a baya. Hannah da uwar biyu ne kawai suke zama ya biya kudin sauran kujerun. Matafiyasuna ta shiga mota haisam yazo ta jikin wundonuwar biyu ya mika mata kudaden motarsu dakuma wanda zata bawa mahaifin hannah kamaryadda ya saba aika masa, uwar biyu tana ta godiya.Haisam ya zaga ta wundon hanna wacce jikinta yayi sanyi tana daf da fashewa da kuka, ya mikamata wata ambulam fal da kudi. Ya fara yi matanasihohi masu tsuma zuciya kamar yadda ya sabayi mata amma wannan karon nasihohin sunshabambam da na kullum hade da bankwana yake yiyace'' hanna alhamdulillah allah ya kawo mu ranar da kika gama makaranta kin zana jarabawarkarshe allah ubangiji ya baki sa!a. Hanna ki kula daaddininki sosao daman can ke mai addini ce nasanda haka amma ki kara . Kada ki damu a duk halinda kika tsinci kanki. Na wahala kina jin dadi dukallah yana sane dake kuma yana sonki ba wai ya wareki bane don ya tsaneki yake hadaki da masifuiri iri da bakin ciki. Allah {s.w.a}yana jarababawansa ta duk inda yaso kiyi kokari kicijarabawarki , ki kuma din ga gode masa a dukrintsin da kike ciki. Idan kika gode masa a dukyanayin da kika godewa allah to shi zai canja miki, ina so ki kula cewar babu wani mutum a duniya dazai zama shine matakin gatan kowa don allah kirike wannan allah shiya halicce ki shi yake ba dawakuma shi yake hanawa babu me miki wani abubanda allah kici gaba da yin tawakkali allah yanasane dake. Tsananin kukan da hannah take rusawa shine ya dabartar da haisam ya rasaabunda zai ce shima ji yayi kwalla ta cika masa idotaf sai kawai ya juya ya tafi ya ce'' allah ya kiyayehanya, sai anjima'' wani kululun bakin cikin neyazo ya tokaresu dukkansu a wuya tsananin bakincikin rabuwa da juna. Gagarumin tashin hankali ya mamaye zukatansu kowanne na fidda ran sakeganin dan uwansa kuma. To tayaya hanna zata zokano tace tazo ta gaishe da malaminta bayan ramlana nan na nemanta zata halakata idon ta idon tatace sai taga bayanta. Shi kuma yaya za'ayi haisamyaje garinsu hanna bayan duk gari ya dauka sharrin da ramla tayi, iya abu na yadawa hanna bakaratu take yi ba soyayya take yi da wanimalaminta. Hanna tayi zugum a zaune a mota ji takeduk duniyar babu dadi. Yanzu zaman dindindinzata je suyi da iya abu tasan ba karamin bakin cikizata hadu dashi ba a gidan. Ga tsananin bakin cikin rabuwa da yaya haisam saboda sun saba sosai dontafi jin bakin cikin rabuwa dashi akan nusaibawacce suke kwana tare su tashi komai tare hattabacci baya rabasu. Uwar biyu ma sai duk jikintayayi sanyi shi kenan idan ta kai hanna gida baza tadawo ta dauketa ba kuma. Suka isa gidan su hannah, hannah ta shiga gida da sauri tana murnazata ga babanta. A shimfidarsa a zaure ta ganshikwance sharkab babu lafiya ashe watansa wajenhudu a haka. Ciwo kullum gaba yake sake yi saiakwantar a tayar. Hannah ta gigice har tana nemanrasa hankalinta yayin da taga mahaifinta ya zama kashi a kwance kurket dashi kaninsa ne uwa dayauba daya yazo yana jinyarsa . Dan ta iya abu cewatayi ya mutu mana tace ta gaji da zaman jinya tundayaki warkewa tayi na allah 'yan uwansa kuma suzosuci gaba da kula dashi ita ta huta. Hannah tasakuka taje ta tsugunna a gabansa tace'' sannu baba'' yace'' yauwa sannu 'yar baba ashe da rabonkizo muyi magana ban mutu ba nace aje a kirawomin ke a makarantar kizo kiga gawar mahaifinkibasu je ba'' cikin sheshshekar kuka hanna tace''baza ka mutu ba baba daina fada ma'' uwar biyuma ta matso kusa dashi tace'' sannu malam habu ya jikin ''yace'' jiki dai gashinan uwar biyu sai dai kuyimin addu'a idan na mutu, allah ya saka miki daalheri ke da haisam da gidan aljannah abundakuka yiwa hanne na gode''uwar biyu ma hawayetake yi. Hanna tayi kuka kamar ranta zai fita. Ananuwar biyu ta yini sai da la'asar tace zata tafi suka yi sallama da malam habu dake radai yana maganatashi tsaye ne baya iya yi. Hannah ta rakata hartasha.A hanya Uwar biyutakebawa Hannah shawara ta ce "Tun da ke mai ilimice kiyiamfani da iliminki, ki kai Mahaifinki asibitin Baburatunda kudin da Haisam ya bawa Mahaifinki dawandaya baki mai tsokane zai isheku. Da abarshi a gidaanamasa jike-jike duk wata cuta ake kara masa.Mutum akwance har wata hudu ya kare sai kashi da fata. Atashar Uwar biyu ta sami mai mota aka yi tsadazata jegida a dauko marar lafiya a kaishi asibiti. HannahdaUwar biyu suka shiga mota, dake itama Uwar biyudaman motar Babura zata shiga daga Babura zatahauta Gumel. Sai kawai su duk su tafi tare. Motar tajeharkofar gidan, direban da kwandasta da kanin MalamHabu suka ciccibeshi suka sashi a mota sukashigasuma da *yan kayayyakinsu suka nufi asibitinBabura.Iya Abu nata yiwa Hannah surutu tana cewa gatananUwar iya yi wai har tayi kilin din da zata daukiMahaifinta ta kai asibiti wai har asibitin Babura tazama *yar boko. Sai da Uwar biyu tayi wata gudacur aGumel sannan ta dawo Kazaure tana zuwa tananiyyarta shaidawa Haisam halin da Mahaifin Hannah kecikisai aka ce mata ai bayan tafiyar su Hannah da satibiyushima ya bar koyarwar ya kwashe kayansa yakomaKano. Ta nemi Safiyanu shima aka ce mata ai shitundayayi aure a Kaduna ya tare da sabuwar amaryarsaacan ya sami aiki, sai Uwar biyu ta hakura dasanarwaHaisam don ita bata taba zuwa Kano bama balleta tafinemansa. Su Hannah kuwa sai da suka shafe wataguda da kwana shida sannan aka sallamesu dagaasibiti. Kanin Mahaifinta ne a wajensa amma itamatakan je tayi kwana biyu uku acan har dai sukadawogida gaba daya. Jiki da sauki tunda yana zama dakansa ba sai an tallafo shi ba. Sai dai kudadenhannunHannah sun kare kakat saboda siyan magungunanasibiti.Nan fa balokokon Iya Abu ya tashi akan tagaHannahbata da kudin da zata sayi dan biskit da madarardatake sha idan tazo hutu da, dole ta ci tuwan gidan.Hannah ce shara, wanke-wanke da dafa abincitukatuwan bakar dawa da miyar kuka a murhun kasa.Kwanci tashi su Hannah sunyi wata biyar da gamamakaranta. Hannah har ta fara zuwa makarantarbokongarinsu tana koyarwa. Duk da dai ba'a dauketa amatsayin Malama ba don Jarabawarta bata fitoba.Amma a karshen wata ana bata dan na batarwa.Ranarasabar babu makaranta. Da sassafe bayan Hannahtagama wanke-wanke tana kokarin daura tukunyartuwon burabuskon gero miyar kuka na rana saikawaiIya Abu tazo ta kashe wutar da ruwan tuwon. Tace tacanja ra'ayi yau an fasa yin abincin ranar sabodaunguwa zata ita da jikokinta don haka meyeamfanintuwon. Ta dauke garin tuwon da kukar kadin tasaadaki ta datse ta yafa mayafinta zata fice. RanHannahya baci ta ce "To Baba fa, me zai ci shi da bashidalafiya? Yau jikin nasa a rikice yake tunda sassafeamaiyake. Iya Abu ta ce "Sai yaci hakuri ko ki kwasheamanda yayi ki dumama masa. Cikin fushi Hannah ta ce"Inaraye a duniya Mahaifina ba zaici amai ba inshaAllah"Mari tas Iya Abu ta sakar ma Hannah akanlallasusankuncin nan nata ta ce "Ke kin isa ina fada kinafadalalle wuyanki ya isa yanka. Malam Habu da yakekwance sai jikinsa ya dau kakkarwa tashin hankaliyadira a zuciyarsa yaji marin da aka sakarwa Hannesaiya hau hawaye yana kira "Yar Baba yi hakuri zonanwajena ki zauna. Hannah tana hawaye ta je gefenshinfidarsa ta zauna Iya Abu tana tsaye akansutana tabalokokonta tayi har ta gaji ta kama hannunjikokintasuka fice, da taji ba'a kulata ba. Zuwa can wanilokacimai dan tsawo Hannah da Mahaifinta sunyi zugumsuna tunani sai ta jiyo mai tallar fura da nono tazotazo wucewa, da sauran *ayan canji a jakarta tatashita leka ta kirawota, ta dauko kwanon sha ta saya.Tadama ta tashi Mahaifinta zaune ta bashi yasha yakoshisannan ta gyara masa kwanciyar ya kwanta takomagefensa ta zauna tayi lamo zuciyarta cike datakaici gayunwa tana addabar cikinta. Can Malam Habu yace"Yar Baba, ta ce "Na'am Baba. Ya ce "Allah Yayimikialbarka ya baki miji na gari mai sonki kamarHaisam,sai Hannah tayi shiru tana tunani da mamaki yaakayiMahaifinta yake hada mijinta da Haisam.Malam Habu ya ce "Ya ba ki amsa ba? Ta ce"Babakamar Haisam kuma? Ya ce "Eh kamar yadda yakekuladake yake nuna miki kauna. Tayi murmushi ta ce"Mutunci ne dashi da tausayi amma ba soyayyabace.Malam Habu yayi dan tari ya ce "*yar Baba matsokusadani kiji. Hannah ta matso kusa dashi. Ya ce "YarBabababu mai sonki a duniyar nan kamar Haisam, babumairikeki tsakani da Allah irin Haisam, babu mai rikekiamana ko bayan raina wanda ko dar bana yi saishi*yar Baba. Haisam yana matukar sonki. Hannah tace"Meka gani kake cewa haka? Ba sona yake ba kokadanmutunci ne ai bai taba gaya mun ba. Malam Habuyanisa ya ce "Yanzu tashi kije ki nemi gidansu aKanokice na amince masa ya zo zan bashi ke ya aureki.Hannah ta zabura ta ce "A'a Baba ya za'ayi injekawaiince masa ka yarda yazo ya aure ni bayan bai cezaiaureni ba. Malam Habu ya ce bakya yimun musu,karkifara daga yau bazan ce kiyi abunda zaki cutu bajekikawai ki fada masa. Haisam ne zai rike mun keamana*yar Baba duk duniyar nan shine kadai na yaddayaaureki. Jeki ki shiryo ki tafi yi sauri *yar Baba.Hannahta tashi a sanyaye zuciyarta cike da zuluminwannanal'amari.Ta shiga cikin gida ta sake salla wanka ta sakawanidandatsetsen sabon leshinta kalar brown ta yafagyalenta a kusa da Babanta ta ce "Na shirya zantafi,ya laluba karkashin tabarmarsa ya dauko wasukudi yabata, ya ce tayi kudin mota. Ta ce ya barshi tanadakudin mota, ya ce ta karba shi mai zaiyi da kudininbata karba bama kwashe su za'ayi, kudin da yatattarane na *yan dubiya. Har Hannah takai bakinkofazata fita sai ta tuno ai bata san kwatancen gidansuHaisam ba gashi bata taba zuwa Kano ba sai cantatuna akwai inda ya rubuta mata kwatancengidansu ajikin littafinta (slum book) da ta bashi ya cikemata. Takoma daki da sauri ta binciko cikin littattafanta tadauko sai kawai ta jefa littafin a jaka ta fito.MalamHabu na kwance bacci ya fara daukarsa yajimotsinmutum sai ya bude ido ya ce "Waye? Hannah tace "Nice Baba, ya ce "Baki tafi ba ne, *yar Baba kobakyasonzuwa ne? Ta durkusa a gabansa ta ce "Baba bahakabane mantuwa nayi na dawo amma yanzu zan tafizanbi ta gidan Iya Salma(tsohuwar matarsa ta fari) koitatazo ta taya ka zama kafin in dawo baza a barkakaikadai ba. Malam Habu ya ce "To Allah Yayi mikialbarka. Hannah ta ce "Amin Baba Allah Ya bakalafiyaya ce "Amin *yar Baba, kuma ko bayan raina adauraaurenki da Haisam ina fatan kema kina sonsa?Hannahtayi dariya ta rufe ido, alamar kunya Malam Habuyayidariya shima ya ce "Yar Baba fada min gaskiyamana.Ta ce "Baba saboda tsananin kyautatawa da kuladayake mun sune suka sa nake ganin girman YayaHaisam har naji babu wani mutum da nake so datsananin kauna bayan kai Mahaifina sai kuma shi.Babaina son Yaya Haisam sosai har nakan kasa bacciyanzusaboda tunaninsa da kewar sa musamman yanzudamuka rabu. To amma Baba babu yadda zanyi sainagakamar shi ba haka yake nufi a zuciyarsa ba.MalamHabu ya ce "Tashi kije shima yana sonki fiye dayaddakike ji. Amma muyi addu'a kafin ki tafi mu karanta salati goma gaannabisuka karanta suka shafa. Hanna tadinga kwararo addu'ai sannan daga karshe sukashafa. Hannah ta sake yi masa sallama ta fita. Tanafita gidan iya salmai ta nifa ta shaida mata abundake tafe da ita. Nan da nan iya salmai ya zari gyalenta ta nufi wajen tsohon mijinta dan uwanta abunkaunarta wacce dole ce ta raba su don ta kuladashi kafin hanna ta dawo. Hanna na isa tasha tatarar da mota fijo zata je kano ta cika saura wajenmutum daya tayi sauri ta fada sai tafiya. Babuabunda hannah take ji a ranta yau sai tsananin farin ciki, ji take kamar anyi mata albishir da gidanaljannaj. Tana san yaya haisam har ranta, to shimakuma yadda ta lura yana sonta sosai kuwawadannan dara daran idanuwan nasa ne takehangowa a zuciyarta idan yana kallonta. Da wasufararan hakoransa tasa idan yana mata nasiha wai waya ganni a kano yau a kusa da yayana haisamkuma ma wai yazo muyi aure an bashi ni'' hanna kefada a zuciyartaDadi marar musali ya disu azuciyarta kowa yaga hannah yasan tana farin ciki ayau. Sun isa kano lafiya a tashar yan kura akasassauke su. Hanna ta fito daga mota ta kalli gabas da yamma kudu da arewa. Daga bil'adama neburjik a gaba da bayanta. Tace a ranta''ikon allahkano mai mata da maza, ta dawo tumbin giwa kodame kazo an fika. Yanzu ina zan fara dosa gabas koyamma ? Abunya bata mamaki ganin yadda akekallanta har wasu mazan waiwayenta suke . Da farko ta dauka kowa ya ganta yasan bakauyiya cebata taba zuwa kano ba, ta fita daban da yan garisai da taji wasu samari su biyu sunxo wucewasunce mata'' ke kyakykyawa dan rufe fuskar nantaki kada kisa wasu mazan suyi hatsari a garinkallonki. Sannan ta yarda tsabagen farin da suka gani da kyakykyawan fuskar da kirarta suke kallosai tayi sauri ta dora gyalenta aka ta rufe fuskartaidanuwanta kawai a bude, tace a ranta dukkyawawan matan garin nan daman har wani kyauzaus gani? Kwalelensu yaya haisam ya riga su. Tabude jakarta ta dauko littafin da adireshin gidansu haisam ke rubuce ta karanta sunan unguearsuleman cresent, sai ta sami wani kwandasta motatace malam don allah ina motar suleman cresent ?Yace ''a'a gaskiya babu takamaimai motar da takezuwa irin wadannan manyan inguwanni, ammashawarar da zan baki ki sami tasi ki dau shata ya kaiki har kofar gida. Ga masu tasi nan a tsatstsayebabu kowa a ciki. Ya nuna mata su, tayi godiya takarasa wajensu, babu abunda ta fara hangowa saiwajen waya an rubuta'' make your call here'' takarasa wajen masu wayan tace'' anan ake yinwaya ? Mai waya yace eh nan ne. Ta dauko littafinnan ta dubo lambar nusaiba ta mika masa.Bugu daya wayar ta shiga ta fara ringing. Watamata ce ta dauka sannan ya mikawa hanna kanwayar hanna ta karba tana kallon kan wayar donita baya san yaya zata yiba'' mai waya yace kudinkiyana tafiya an dauka fa kisa a kunnenki kiyi magana. Sannan hanna ta tuna yadda taga ana yibayan ta gaishe da matar sai tace'' hanna kawarnusaiba ce. Nusaiba nake nema'' matar tayi dariyatace'' oh hannah ce ? Nice mami mahaifiyar aiyanusaiba ai tana london har ma an samar mataaddmision tana jiran sakamakon jarabawarta ne ta fara karatu. Hanna tayi bakin cikin rashin samunnusaiba a waya sai suka yi sallama ta mikawa maiwaya kan wayar. Yace''minti uku kika yi. Tace nawane? Ya fada ta dauko ta bashi sannan ta juya ta tafimurna take kawai a zuciyarta yau gata a kano tanawadaka da komai irin na yan burni har kan waya yau ta rike lallai. Wani mai tasi inyamuri baya jinhausa ta samu sai suka fara yarawa da turanci .Tace suleman cresent zai kaita ya fadi kudin ko ragibata nema ba ita a tunaninta komai a burni a kaideyake ba'a neman ragi kuma ita burinta kawaiyakaita taga haisam. Suna shiga unguwar saita dauko littafin ta duba lambar gidan ta gayawadireban ashema a kofar gidan suke sai yace to ai gagidan ta zaro kudinsa ta bashi ta fito daga motar yaja motars ya tafi. Tsantsari, wani tsalelen gida negidan su haisam yafi duka gidajen layin tsaruwahanna tayi matukar mamakin ganin gidan su haisam saboda bata taba zaton haisam dan gidangawurtaccen mai kudi bane irin wannan .wasutsala tsalan motoci tagani a wajen get din gidan sundosho goma. Ta tafi kofar gidan makwabtansu tazauna akan wata kwalbati tana tunanin yaddaza'ayi yau taga haisam,Wani buzu mai gadi ne ya leko ta jikin get yahango hanna a kofar gidan da yake gadi sai yayiwuf ya fito yace'' kai me kana yi anan ? Tace''waninake nema ''yace waye wani, ba zaka tambaya bazaka zo ka zauna anan! Hanna tace''haisam nacangidan. Yace''kace na can gidan me yasa kazo nan ka zauna kuma, kaima bakauye ne ko? Don kayikama da yan garinmu masu yalalo yalalo gashi'' saisu duka suka yi dariya shi da hanna'' mai gadin yaleka kofar gidan su haisam yaji hayaniyar mutanesai ya ce mata'' yauwa ga haisam din can sun fito itada abokanayenta''hannah yace'' dan allah dan garinmu kirawo min shi akwai maza bazan iyazuwa ba. Buzu ya karasa wajen haisam ya shaidamasa wata na kiransa. Haisam cike da mamaki yatunkaro wajen da hanna ke tsaye sai tasa gyale tarufe fuskarta. Ya karaso inda take a tsaye yayi matasallama ta make murya ta amsa. Yace wacece? Hanna ta sake make murya tace bakuwa ce''haisam ya hada girar sama data kasa yace'' wai kewacece in ba zaki fada ba zan koma ina da abunyi''hanna ta yaye mayafin a hankali ta bude fuskarta.Wai, kamar wanii hasken walkiya ne ya haskewahaisam ido da yaga fuskar hanna ,cikin fara'a da mamaki haisam yace hanna! hanna! Kece!! Tayilallausan murmushi tace'' yaya haisam nice'' taduka ta gaisheshi. Taga haisam ya caba ado dawata babbar riga mai aiki a wata tsadaddiyarshadda fara sol yasa bakin takalmi da bakar hulayayi matukar kyau. Tayi dariya tace''yaya haisam yau kaine da babbar riga ? Har kafi kyau haka'.Yace haba? Tace allah'' yace yaya su baba. Dasauran yan gidanku? Tace sunanan lafiya sunce nagaisheku. Yace to zaki shiga cikin gida ku gaisadasu hajiya'' hanna ta dan yatsune fuska tace'' kaisai dai watarab bi kunya nake ji kuma sauri nake sai dai idan na dawo. Yace daman ba nan kikazobane? Hanna tace ''ni kuwa wa gareni a kanoidan ba kai ba? Gurinka nazo baba ya aikonihaisam yace to gani fada min aiken. Zumudin yajiabunda aka aiko ta ya kama haisam. Tayi shiru tahau rufe fuska. Cikin zumudi haisam yace'' haba hanna ki fada mun mana kunyar me kike ji ne?Tace'' baba ne yace inzo in fada maka cewar kazoka nemi aurena ta bakani. Tu kafin ta karasa saitaga haisam ya fara dariya da alama farin ciki yacika zuciyarsa. Ya kurawa hannah ido na wani danlokaci yqce'' abunda kika kasa fada daman? Ya sake yin dariya ya tsaya kallan hanna wacce takerufe idanuwanta saboda kunya ga tsananin farinciki.Haisam ya nisa yace''yanzu baba da kansa yacekizo ki cemun ya bani ke! Hanna ta amsa da''eh''yace yanzu ya bani ke kacokan a matsayinmatata? Yanzu baba ya yarda ki zama uwar yayanamun zama daya dangina sun zama danginki,iyayena sun zama iyayenki? Yanzu baba ya yarda na zama abokin rayuwarki na dindindan har abada? Yanzuhanna kin amince zaki zama abokiyar zamana harabada? Hanna cike da fara.a da murmushi takeamsawa haisam tambayoyinsa da ''eh'' haisam yayimurmushi ya sunkuyar da kai na dan wani lokacican ya dago ya kurawa hanna ido yayin da kowannensu yake sakarwa dan uwansa murmushida wasu masun kauna da suke firfitowa dagaidanuwan kowannensu suna yiwa junansu wanikallo mai kunshe da so, kauna muradi ganin juna.Haisam yayi ajiyar zuciya ya nisa ya ce alhamdulillahhanna na daukarwa allah alkawari ba xika , sannan na cika burina dana kudira akanki na ingakin kammala karatunki. Kuma yanzu na dawo gidazan cika wani tsohon alkawari dana dauka. Nan danan hanna ta kurawa haisam ido ta dainamurmushin da take alamar bata gane abundahaisam yake cewa ba. Haisam ya ce'' hanna na gode madalla , ki yimun godiya a wajen mahaifinki .Good bye, good bye hanna. Ya fara jada baya yanadaga mata hannu yana yi mata murmushi . Bakintaya hau rawa tana so tayi magana ta kasa . Gabadaya jikinta ya hau karkarwa inda jakar dakerataye a kafadrta ta sulmiyo wasu marokane suka wayar mata dakai akan abunda haisam yake nufisuna cewa'' ango haisam kasha kamshi fari maifarar aniya kagaa ango na ramla, yan boko bayinnasara a daura aure lafiya akai maka amarya gidalafiya. Wani abokinsa ne ya taho da sauri yace dahaisam ''ana ta yin waya daga wajen daurin aure ance waje ya cika kai ango kawai ake jira.muje ka shiga nota mu tafi mana. Haisam daabokansa suka shiga tsala tsalan motocinsu sukazo suka wuce hannah anan a tsaye tana karkarwaido da ido suke hadawa da haisam har suka wucesuka tafi. Ta juya tabi motar da kallo har suka hautiti suka kure. Sai hanna ta tsugunna a wajen ta rushe da wana azababben kuka mai radadin fita.Dakyar buzu mai gadin nan ya dinga bata hakuri tadauki jakarta dankwalinta a hannu sai gyalenta tayafa a kai ta tafi. Acaba ta hau har tashar yan kurawannan karon ma taci sa.a tana shiga mota ta cika .Kallo daya zaka yiwa hanna kasan hankalinta a tashe yake matuka don kwandasta sai da yayimagana sau uku yana cewa ta bada kudin motartabata jiba, hankalinta yana can tana tunanin damanhaisam ba sonta take ba. Ramla yake so shine ita damahaifinta suke yaudarar kansu . Yaya haisam meyasa kayi min haka me yasa baka fahimci son dana ke yi maka ba ? Ta nisa tace'' ko da yake bashi dalaifi bai yaudare ni ba, ya taimakkamin ne sabodaallah ni na dorawa rai sonsa. Bai san ina yi bakuma, amma na rabu da farin cikin rayuwa na rasamutum na farko dana taba hi inaso a rayuwata,gashi tun bayan gama makarantarmu ko bacci ma neman gagarata yake na kwallafa raina datunaninsa da tsananin sonsa'' sai da wata mata takusa da ita ta tattabta sannan hannah ta farfadodaga tunaninda take yi. Kwandasta yace kudinmota nake tambayarki kinyi shiru kina tunani''sannan hanna ta zabura ta dauko kudin mota ta mika. Mota ta bar cikin kano ta kama hanya fetal saibabban mutum. suna isa babban mutum tun dagatasha hanna ta dinga jin faduwar gaba kafartakamar bazata iya daukar ta ba dakyar take jefakafar burinta kawai ta isa gida taje ta fada jikinmahaifinta ta sharbi kukanta son ranta tunda duk duniya shine kadai ya rage mata gaba dabaya.kamar yadda data shiga kano taga mutanengarin suna ta kallonta har da waiwaye yanzu ma agarinsu haka ta gani sai kallonta ake tana tafiya harda masu nunata kamar basu santa daba, hanna tayimamakin irin wannan kallo da ake yi mat tace a ranta'' to ko sun san son maso wani nake ? Wandanake so yayi aurensa da wacce yake so'' kallon nandai da ake yi mata ya daure mata kai. Haka daihanna taci gaba da tafiya tana sauri ta karasa wajenmahaifinta shine kadai mai lallashinta, mai gayamata kalaman da zata ji dan sanyi a ranta. Ta kusa kofar gidansu, kwatsam taga wata kungiyar mazadauke da gawa sun yi gabas ana hailala. Tajigabanta ya fadi ta dubi kofar gidansu sai taga taronwadansu maza da yara a zazzaune ana jan carbitace a ranta'' ba dai gawar babana bace waccan?Sai ta zubar da takalmanta da jakarta ta shiga gida da gudu don ta duba zaure shinfidar babanta yananan kuwa. Tana shiga sai taga shimfidar wayambaya na ga silifas dinsa da butarsa a gefe babandaki ya zaga ba. Ga wannan furarsa gefesauran wacce ta dama masa yasha ya rage. Nan danan taga su iya salmai sun fito daga cikin gida suna rusa kuka idonsu yayi jawur suna riketa suna cewasannu hanna wannan ke aka yiwa mutuwa allah yajikan mahaifinki da sunanki a bakinsa har ya mutu.sai wani jiri ta kwashi hanna ta fada kanshimfidarsa ta rirrike filonsa ta kudindine ta runtseido ji take dama kasa ta bude ta fada da ita bakin cikin rayuwa ya isheta. Ta kwalla kara tana karacewa'' innalillahi waina ilaihi raju'un allah kanasane dani, allah ka san halin dana ke ciki. Allahbaka tsaneniba, baka kuma manta dani ba. Bani dakowa a duniya, babu wanda ya ragemin kumaallah kaine gatana kai ka halicceni, ka halicci mahaifina kuma ka halicci haisam. Ka hadani dasumuka saba kuma kai ka raba ni dasu allah. Allahkaine abun godiya. Allah na gode maka. Allahkaine jagorana, allah kar ka barni na dauwama acikin bakin ciki. Allahu akbar sai kowa ya rushe dakuka. Hatta iya abu data tsani hanna yau hanna ta bata tausayi matuka. Sai ta rushe da kuka ta dingarike hanna.....Muhadu 2 dancigaban labarin Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100