*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* *Mallakin* ⬇️ *OUMMU IMAM* *Da Sunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Kai* *Ya Rabbi ina rok'on ka da sunayenka kyawawa masu tsarki yadda ka bani ikon fara rubuta littafin nan,ka bani ikon rubuta abunda zai amfaneni duniya da lahira da al'umma baki daya,ka tsare man hannuwa na daga rubuta abunda zai cutar da ni da al'ummar Annabi(S.A.W).Yadda na fara rubutun nan lafia cike da farinciki ya Allah ka bani ikon kammala shi cikin farinciki da koshin lafia,Amin Ya Mujib.* *Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na wato MUNHIZAFA FAM,Allah ubangiji ya kara hada kawunanmu ya kuma kara rufa mana Asiri fiddunya wal akhira da sauran Al'umma baki daya,Amin.* *Labarin wannan littafin kirkirarran labari ne,idan suna,hali ko yanayi sunyi kamanceceniya arashi ne bada nufi ba.* *Gaisuwar Ban Girma* *Ga mahaifiyata,Allah ya kara girma da nisan kwana,MY FIRST LUV❤️.* *TUKUICI NE* *Ga Hafsat Bature Muhd(Boss Lady) Allah ya kara mana basira da hazaka baki daya Amin.*🤝 Sabuwar Marubuciya wadda ta dade tana yi maku tanadin tsararrun labaran da zasu Ilimantar da fadakar daku,uwa uba kuma nishadantar daku, Littafin *A SANADIN MAKWABTAKA* Na dauke da labari mai cike da barkwanci,tausayi,da kuma tsabtatacciyar soyayya mai ta6a zuciya,kada ka/ki bari ayi tafiyar ba ki/ka. Littafin nan na kudi ne,da zarar nagama sakin free pages sai wanda ya biya ne kawai za'ai tafiyar dashi🤝 *Free Page1️⃣&2️⃣* KATSINA STATE Unguwa ce mai dauke da Manya manya had'i da K'ananun Gidaje,sai dai kana kallon yanayin gidajen zaka fahimci cewa ba tsohuwar unguwa bace,don sam gidajen basu ji jiki ba,wasu gidajen Sababbi ne yayin da wasu kuma baza'a kira su da sabbi ba,ba kuma tsofaffi bane,akwae Manyan gidaje masu kyau wad'anda da ka kalla zaka fahimci masu gidajen nada arziki,yayin da wad'ansu kuma ke nuni da masu su,masu rufin asiri ne.Yanayin layin ba hayaniya sosai akwae mutane jefi-jefi,kallo daya zakae ma layin ka fahimci akwae masu arziki had'i da masu rufin asiri a wurin. Wata mota ce k'irar Corolla S Navy blue ta shigo layin da matsakaicin gudu, K'irrrrrrr! Motar taci burki batare da shiri ba sakamakon wasu yara mata da basu wuce shekara 13 zuwa 14 ba, da suka shigo hanyar da gudu daga Lungun dake a bangaren dama,d'aya cikinsu na dauke da farin matsakaicin Bokiti mai d'auke da wani abu ciki hakan na nuni da tallah take yayin da dayar da ta biyo ta ita bata dauke da komae,lungun da ke opposite da wanda suka fito suka shiga a daidai nan kuma d'ayar yarinyar ta samu nasarar kamo hijab din yarinyar dake dauke da bokitin talla,tura ta tayi jikin bango tana kokarin 6arar mata da abunda take sayarwa, ita kuma ta rik'e bokitin gam, Shi kuwa na cikin Motar still yayi da alamun bacin rai a fuskarsa yadda yaran suka fad'o masa all of a sudden,ba don Allah yasa bai gudu sosai ba da horrible accident ya faru a wurin don gaba dayan su zai dauke su da motar watakil ma ya take su,dan tsaki yaja"Mtsww"A hankali ya waiwaya yana kallon lungun da yaran suka shiga,hango su yayi sai faman kici kici suke alamar dai fad'a suke ga d'ayar yarinyar mai sanye da riga da skirt na atampa kanta d'aure da kallabi wanda daga bayan kallabin yayi tudu sosai alamun dai tana da gashi mai yawa ga gyalenta kuma daure a k'ugunta sai faman kokarin ganin ta 6aro da bokitin dake kan dayar yarinyar da ta matse a bango take, Ganin yadda ta dage bilhakki sai ta 6arar ma d'ayar abunda ke cikin bokitin yasa shi sauke gilashin motar a hankali,"ke,ke" Ya fara k'okarin yima yarinyar magana sai dae ko waiwayo inda yake batayi ba,tunani yayi kilan bata ji shi ba hakan yasa ya k'ara dan daga murya duk da bai so hakan b "Kee sake ta!" ya kara fada,tana jinsa tayi burus da shi,yarinyar mai talla ce tace"ke Fatuu baki ji wancan mai motar na cewa ki kyale ni bane"kara k'ankame bokitin tayi ita kuwa wadda aka kira da Fatun ganin ta kasa 6aro da bokitin yasa ta fara dukan yarinyar don tasan in tayi hakan dole ta saki bokitin ai, Ganin hakan yasa mutumin cikin motar fitowa,Wow! Masha Allah, Wani Kyakkyawan Mutum ne mai dan tsayi sai dae ba irin tsawon nn sosae b, sai dai kana kallonsa zaka shaida dogo ne,kalar fatar sa kuwa fara ce irin farin nan mai kyau mai tafia bai d'aya ba wai irin wanda zaka ga wani wuri yayi dan ja-ja ko yalo-yalo ba,gaba daya fatar shi sumul take,yana da matukar kyawun Fuska wadda da idanu sun kalli fuskar zasu shaida hakan,sumar kansa nada dan tsawo wadda take a nad'e yayin da daga tsakiya ta dan fi gefe da gefen tudu,sam bai tara kasumba ba sai dai akwae sumar kad'an zagaye da fuskar har zuwa saman dan madaidaicin bakinsa wanda labban sa suke kalar peach mai duhu,sanye yake cikin Suit Navy Blue yayin da yar cikin take Black color,Wuyansa na sanye da Necktie kalar suit din wato navy blue wanda yake kwance ak'asan bakar collar din yar cikin,k'asan necktie din kuma an rufe shi data saman ta hanyar sa Ma6allan rigar wad'anda suke bakake masu kyan gaske,hannunsa na sanye da Wrist watch silver mai d'an duhu kai da gani kasan zai yi kudi Agogon, yayin da K'afafunsa kuwa ke sanye cikin wasu dakakkun Takalma cover shoe bak'ak'e, ba k'aramin haduwa yayi ba,ba kamar da kalar fatar sa take fara sai yayi kaman ba irin mutanenmu ba na nan,yadda suit din suka amshi jikinsa cib ya bayyana sam ba ramamme bane yana da cikar kira ba kaman Kafadunsa da suke da fadi,da ka kalli kayan jikinsa da kuma motarsa zaka fahimci yayi shigan da ake kira too match, Ya mayar da Kofar motar ya rufe da hannunsa daya tafiya ya fara yi majestically,da ganin yadda yake tafiyar za kai tunanin irin mutanen nan ne masu ji da isa,gefen su ya tsaya fuskar nan a tamke cikin dan daga murya ya fara yima yarinyar magana"Sake ta!"burus tayi sai ma k'eya da ta kara juyo masa,cikin 6acin rai da daga murya yace"Am i not talking to u, idiot." ya fada a dan harzuke,jin yace mata idiot yasata juyowa a fusace ta fara magana cikin masifa"Ni ba idio......sam ta kasa k'arasa maganar sakamakon hada ido da mutumin dake a tsaye fuska a d'aure,kwarjini yayi mata sosai, "Get your hands off her"ya fada fuska a daure,a hankali ta saki Yarinyar mai talla da alama ta ji abunda ya fada da turanci,d'an ja da baya tayi kad'an,kasa-kasa tace "Don kana da kyau zaka wani daure ma mutane fuska ni ba ruwana da kyaun ka ehe" Still yayi yana kallon yarinyar don yaji duk abunda tace,lallai yarinyar bata da kunya ya ayyana a ransa,"Wuce kibar wurin nan before I slap ur face"ya fada tare da nuna mata hanya da hannu,A hankali ta fara tafia cikin lungun tana turo baki tana waiwayen su,kallon yarinyar da ke dauke da bokitin talla yayi"Wuce ki tafi" ya fada yana nuna mata hanyar da suka fito "To",ta fada tana gyara Yellow din hijabinta da ta cukwikwiye ta fara tafiya,shima juyawa yayi ya nufi inda motarsa take, "Wayyo Allahna! ta 6arar man da Awara...!" Yarinyar ta fasa kuka tana fadi da sauri mutumin ya juyo,da wani irin expression yake kallon yarinyar da ta 6arar da awarar,Ashe ba tafiya tayi ba tana ganin ya nufi motarsa ta fito da sauri tasa hannu ta ture bokitin Awarar,ganin yadda yake mata wani irin kallo yasata jin tsoron shi rugawa tayi a guje cikin lungun ita kuwa mai awarar muryar ta kawai ake ji sai faman ihu take tana fadin"Wllh bazan yarda ba sai an biyani gidanku zan biyo ki,Muguwa,Azzaluma kawae"d'aukko bokitin tayi wanda ya rigada ya fashe ganin haka yasa ta sakin wani sabon kukan, A hankali ya juya ya koma inda take tsugunne tana d'ibar awarar tana zubawa cikin bokitin sai faman kuka take,tsayawa yayi a kanta,d'ago kanta tayi cikin kuka tace"kagani sai da ta 6arar mn da awarar ko,kuma wllh bashin waken soyan da mai Innarmu ta amso sai na sayar za'a kai kudin gashi ma har bokitin ya fashe wllh gidansu zani sai an biya ni" ta k'arasa maganar da matsanancin kuka. "Is okey,just leave the rest" Ya fada,dagowa tayi tana kallon shi da alama bata fahimci mi yace ba,"tashi kibar sauran, baki ga yayi k'asa b" Ya fad'a gently, mik'ewa tayi tana ta sheshsheka cigaba da magana yayi a hankali"Miya hada ki da ita? "Wllh ba abunda nayi mata kanwata ta tare rannan wai sai ta bata alakoro ita kuma tace bazata bata b,shine ta buge ta,kuma ta d'ebi awarar,da Innarmu taji shine taje gidansu da kanta don ayi mana tsakani don ba lokacinne na farko ba da take taremu tace mu batan,to shine aka bugeta yau tana ganina tace tunda Innarmu tasa aka bugeta sai taja mata asara sai dai in tasa a kasheta,ba yad........"its okey"ya katse ta, da alama ya gaji da sauraronta,"Ina ne gidan ku? ya tambayeta a takaice,"Acan layin baya muke gidan Alhaji Sani karofi anan babanmu yake gadi cikin gidan muke acan baya"takae maganar tana goge kwallan idonta. "Shi abun naki na nawa ne? ya tambaya."Awarar dubu da dari biyar ce gashi ta zubar da ita duka yar kadan ce bata baci da k'asa ba,inaga ma ko ta d'ari biyu bata wuce ba,wllh gidansu zanje sai anbiya mu ta k'ara fashewa da kuka,da alama taji zafin abun sosai, Sigh yayi kafin yace"You know what,ku kyaleta kawae tunda bata jin mgn in kun k'ara zuwa kun kai karanta zata k'ara zubar maki da abu,calmly yayi maganar,Hannu yasa a cikin aljihun wandon suit din jikinsa bak'ar Wallet ya fiddo mai kyaun gaske ya bude,Kudi ya kirgo sababbi fil kamar lokacin aka buga su,mik'ama yarinyar yayi wadda ke tsaye ta kafe sa da idanu tasa hannu da sauri ta kar6a,aje fasassan bokitin tayi a kasa ta fara kirga kudin dubu ukku ta gani da tsananin mamaki ta d'ago lokacin har ya juya da sauri tace"Yallabai kudin sunyi yawa ai" Hannu yad'an daga ba tare da ya juyo ba yace"ku siya sabon bucket da sauran" ya cigaba da tafia wurin da motarsa take, Mai tallan kuwa har lokacin juya kudin take da mamaki hakanan bai santa ba ya bata har dubu ukku da sauri tabi bayansa tana fadin "Yalla6ai,yalla6ai..." lokacin har ya kama k'ofar motar zai bude jin yadda take ta faman kiransa da yallabai yasa shi juyowa"What again? Ya tambaya da kosawa,"umm dama².... ta kama inda-inda sakamakon kafeta da ido da yayi,ya lura da yadda ta dabarbarce,dan sakin fuska yayi yace"Uhum ina jinki dama me? Dama so nike in tambayeka in innarmu ta tambayi wanda ya ban kudin wa zance mata? ta k'arasa maganar tana sunnar da kai k'asa"just tell her wh....ki fada mata abunda ya faru kawai"ya juya zai shege cikin motar, da sauri tace "ai tana iya cewa k'arya nike ni na tsara hakan kullum tana ce mana kar wani ya bamu kud'i bamu san shi b,ko yace zai siye mana yayi mana abunda bai dace ba"ta gama maganar kanta a kasa, d'an murmushi yayi na gefen fuska wurin ya lotsa alamar yana da dimple,yaji dadin maganar da tayi ko ba komai hakan ya nuna rashi ne yasa suke tallan ba wai ra'ayi ko son kudi na wasu iyayen, Juyawa yayi yabude motar ya shige ya jawo kofar ya rufe,tana dai ta kallonsa don gaba daya komae yayi burgeta yake sai da yayi ma motar key kafin ya bude Glove box din gaban motar kudi ya kirgo dubu biyu juyawa yayi ya mik'a mata da d'an murmushi a fuskarsa yace "ki hada da wannan ki kai ma Mom din naki" Maida hannunsa yayi ya murza key din jikin motar tana dai ta kallonsa da tsananin mamaki sai da motar ta tashi sannan glass din murfin motar ya fara rufewa sama a hankali juyawa yayi ya kalli yarinyar da har lokacin take tsaye tana ta faman binsa da idanu "Ki ce ma Mom din naki dan gidan HAJIYAR SENATOR ne ya baki" daga haka ya ja motar fuuuu, "Hajiar Sanata! Yarinyar ta maimaita da mamaki had'i da rike ha6arta da hannunta daya,sai kuma ta saki wata irin dariar farinciki da sauri ta juya komawa tayi inda sauran Awarar ke a zube k'asa tace "bari in kara dan kwashe wadda batayi k'asa sosae ba da ansa cikin mai k'asar zata fita ko mu sai muci" a saman marfin bokitin ta zuba mai kasar,mikewa tayi da dan gudu-gudu ta koma cikin lungun da suka fito tun da farko. Yarinyar data 6arar da Awarar ce ta lek'o da kanta daga cikin zauren gidan da ta 6uya,round face gare ta mai dauke da madaidaicin hanci mai dan tsawo tana da dan kumatu,idanuwanta kuwa suna da dan girma sam baza'a kira su da k'ananu ba,tana da gashin gira wanda yake kwance lub haka kuma gashin idonta nada tsawo gazar-gazar bakinta madaidaici ne le6anta na k'asa nada dan fad'i sosae,kalar fatar ta kuwa fara ce sai dai ba sol ba,Amman kana kallonta zaka kirata da fara, sai da ta waiwaya hagu da dama ta tabbatar ba kowa kana ta fito,cikin sand'a take tafiya tana yi tana waiwaye har ta iso bakin lungun daidai inda ta 6arar da awarar,tsayawa tayi tana kallon sauran awarar dake a k'asa, Kafarta tasa tana tattake awarar tana cewa"Gobe ma ta kara sawa a doke ni" ta fada a fili tana mummurguda bakinta gefen kumatun ta na lotsawa sosae alamar tana da dimples, jin k'arar mota ta taho a bayanta yasa tayi saurin juyawa hadi da d'an tattare Skirt dinta da hannayenta biyu tana shirin rugawa ganin ba motar mutumin d'azun bace yasa ta saki skirt dinta tace "In ma shine yazo banjin tsoron sa koda kuwa Aljani ne ehee" ta fad'a lokacin da ta fara tafia ta miki hanya tana yi tana waiwayen bayanta tana watsa hannuwa gami da turo baki, Yar tafiya tayi kafin ta iso bakin wani Gida wanda keda shafen plaster ba fenti a jikin bangon gidan daga gaban gidan akwae k'atuwar kwata wadda ke zagaye da gaban gidajen layin saidai a rufe take da slabs daga d'an gefen kofar shiga gidan akwae Kiosk a saman rufaffiyar kwatan gaban gidan,shiga cikin zauren gidan tayi wanda keda K'ofa da kuma Window a cikinsa da alama irin d'akin zauren nan ne, A bakin kofar shiga cikin gidan ta tsaya,dan leka cikin tsakar gidan tayi wanda yake wayam ba kowa,dawo da kanta tayi cikin zauren ta rik'e habarta da hannunta na dama tunani ta shiga yi "Ba'a kawo karar tawa bane?kodai sun zo har sun tafi" jinjina kai tayi a fili tace"Inma an kawo k'arar tawa nasan abunda zance,cewa zan yi tsokanata tayi,ta kuma yiman daria harda gwalo wai sun sa an bige ni" ta k'arasa maganar tana faman mummurguda baki dimples dinta na lotsawa, A hankali tasa k'afa cikin gidan mai dan matsakaicin girma wanda kasan shi ke malale da siminti gaba daya,d'akuna biyu ne a cikin gidan wanda kofofin su na kallon juna,dakin da ke a bangaren dama babban daki ne yayin da na bangaren hagun k'arami ne a jikinsa kuma kicin yake wanda shine a farko in ka shigo gidan daga bangaren hagun,sai dan fili wanda da gani wurin yin Wanke-wanke ne a gefe daga tsakiyar filin akwae yar Bishiya,daga nan kuma sai Band'aki da ke a can gefe bangaren da kofar shigowa take, Shiga tayi cikin gidan a hankali tana yin sand'a "Daga ina kike? Aka jefo mata tambaya daga bayanta,cikin yar razana ta juya,wata farar dattijuwar mata ce mai dan tsayi,sam bata da jiki sai dai ba siririya bace sosae tana da tsagun yan baka a bakinta,tsaye matar take da buta a hannunta da alama daga band'aki ta fito "dake nake Fatuu" ta k'ara fada da muryarta irin ta fulanin da suka ji hausa sosae,in'ina fatun ta fara yi,ta rasa mi zata ce don tunani take ko an kawo karar abunda tayi ma mai tallar Awarar nan,"Halan kina can wurin jawo man fitinar da kika saba ko" ta k'ara jefo mata tambaya,da sauri fatun tace "A'a gwaggo.." tana ta faman zare ido "to ki fadan ina kika je don na lek'a neman ki da kaina baki a waje" Goggon ta fada ta kafe ta da idanu,"Umm... gidan Hajiyar Sanata naje gaishe ta" taba gwaggon amsa da alamun rashin gaskia a fuskar ta,"Allah yasa da gaske kike don banga ranar da garin Allah zai waye har rana ya fadi baki jawo mun fitina ba" jin hakan yasa fatun gane ba'a kawo k'arar abunda tayi ba" da karfin gwiwa tace "Allah gwaggo daga can nake fa" gwaggon tace"to wannan d'amarar da kika ci da gyalen ki ta mene?" "ba komai kawai gyalen ne ya ishe ni yana ta fad'uwa shine na kulle shi anan" tayi maganar tana kokarin kwance gyalen daga kugunta, gwaggon taci gaba da magana"Ai in ance kisa hijabi sai ki k'iya sam bakya son sa hijab ke kinfi son gyale gashi ko yafawar ma baki iya ba kullum yana ruke a hannu ko daure a k'ugu,to ina amfanin hakan in anyi magana kice ke baki saba sa hijab a kauye ba" ta karasa maganar tana shiga cikin gidan, "Allah gwaggo hijab din shak'e ni yake fa, ni ban saba sawa ba,acan ruga fa wani lokacin ko gyalen ma ba sawa muke ba" ta karasa maganar da sigar shagwa6a tana bin bayan gwaggon "Ai sai ki tayi tunda anfad'a maki nan ma kauyen ne, da kina son sa hijab din ai da yanzu kin saba dashi yaushe rabon ki da kauyen kusan shekara ta ukku kenan fa, kawae dai kin fi son kisa gyalen yadda zaki ji dadin nemo man fitina,Kullum cikin daukko man magana kike nikam na fara gajiya wllh kuma zan yi maganin ki indai baki bari ba tunda na lura sam duka bai maki" ta k'arasa maganar lokacin da ta iso bakin kofar dakin da ke a bangaren dama, d'aga labulan kofar tayi ta shige harda butar da ke a hannunta,ita kuwa fatun labulan kofar da ke kallon wadda gwaggon ta shiga ita ma ta daga ta shige,dakin baida girma sosae, akwae Gado irin na karfe mai spring yana da bakin fenti da katifa wadda aka rufe da tsohon zanin gado,A bangon dake kallon gadon kuwa wardrobe ce mai gida biyu da kananun gidaje a kasa suma guda biyu,ta dan ji jiki sannan yar madaidaiciya ce ba mai tsawo ba,a samanta akwae jakunkuna,daga gefen ta kuma dressing mirror ne kalar ta shima karami ne wanda hannuwan drawers din jikin shi wasu duk sun balle haka mirror din jiki dan guntu ya rage,akwai leda shimfide a dakin wadda ta ji jiki don duk wasu wurare sun farfashe,Saman gadon ta fada hadi da fadin "Washh" sai kace wadda tayi wani uban aiki banda neman rigima,tunani taci gaba da yi "ko sai yaushe zasu kawo kara tan..." k'wafa tayi a fili tace"Allah yasa su kara sawa a doke ni wllh nasan abunda zan yi masu...."Muryar gwaggon tace ta katse ta"fatuu fito ki tankade man garin can na cikin kicin yamma tayi in samu in daura girki......,Fatuu ko bakya jina ne wai? cikin d'aga murya tace "Ina ji fa,gani nan fitowa.." mik'ewa tayi ta nufi k'ofa sai faman k'unkuni take tana jujjuya kai alamar bata son yin abunda aka sata yi. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* *STORY* & *WRITTEN* BY *OUMMU IMAM* *Free page3️⃣&4️⃣* Da d'an gudu gudu ta shiga gate din gidan wanda Babban gidane irin na masu hali wata yar hanya dake a gefen tank'amemen Flat din ta bi sai gashi ta 6ullo bayan gidan,gini ne dan dogo mai dauke da dakuna biyu a jere sai kuma kofofi biyu dake opposite da juna k'ananu,akwae baranda da ta lullu6e d'akunan kana kallon yanayin ginin zaka fahimci BQ ne da ake yi a gidajen masu kudi,BQ din yadan ji jiki saman Ceiling din barandar duk yadan farfashe haka fentin ginin duk ya k'oke,ga damsa kuka duk tayi baki-baki a k'asan bangon ginin, Yara ne bi da bi a tsakar wurin suna ta wasa,yayin da wata mata ke can gefe ak'ark'ashin ginin da ake daura tankin ruwa tana ta faman hura wuta wurin duk yayi baki da gani a nan suke yin girki,yarinyar na isowa wurin wani Yaro ya buda murya yana cewa "Lah inna ga Jamila har ta dawo daga tallan" da sauri uwar ta su ta waiwayo daga cikin inda take ganin jamilar rungume da bokiti ga awara a saman shi da gani 6arin ta tayi,yasa uwar fitowa ba shiri tana fad'in "Jamila mi zan gani haka badae 6arar da awarar kika yi ba..."Salati ta shiga yi lokacin da ta k'araso taga awarar saman marfin duk k'asa cikin tsananin tashin hankali tace"yanxu jamila abunda kika yi man kenan kina sane da cewa ko kudin kayan da akayi awarar nan ba'a biya ba shine kika........" Jamilar ce ta katse ta da cewa "Wllh innarmu bani na zubar da awarar ba" "to ubanwa ya zubar da ita kuma kina aikin mi" ta tambaya a hasale "Fatuu ce ta 6arar man da ita wai don kin kai k'ararta an buge ta" nan ta bata labarin yadda ta bita har ta zubar da awarar, Kwafa Innar tayi a hasale tace "to wllh bazata sa6u ba bindiga a ruwa,dole a biyani awara ta,yarinya ta bi ta addabi kowa to wllh bazan d'auki asara ba dole a biya ni" ta karasa maganar tana shirin juyawa ta daukko Hijabi bata karasa juyawan ba sakamakon kudin da jamilar ta miko mata sabbi fil,zaro ido uwar tayi lokacin da tasa hannu ta kar6i kudin tana jujjuya su "Wannan kuma na miye?"ta tambaya da mamaki a fuskarta "kudin awarar ne inna" jamilar ta bata amsa, "kudin awara kuma,da mamaki innar tasu ta tambaya lokaci guda kuma ta fara kirga kudin,da sauri ta d'ago ido a waje tace "na shiga ukku ni Saratu,jamila ina kika samu kudi haka da yawa? Jamilar tace "Mutumin da abun ya faru agaban sa ne yabani ya....."bata k'arasa maganar ba innar ta katse ta"ya baki kamar ya ya? hakanan bai sanki ba kawai don an 6arar maki da awara ya dauki kudi har dubu biyar ya baki a wannan halin rashin da kowa ke fama,ke jamila ki gayan gaskia kodae wani ya miki wayo ya baki,shine kika tsara man karyar Fatuu ta zubar maki!"ta karasa maganar idanu a waje tana cikin tsananin fargaba,hannu tasa ta fizgo yarinyar har awarar dake a saman marfin bokitin na zubowa tace "gaya man ina kika samu kudin nan ko in yanka ki a wurin nan" jin ance za'a yanka jamilar yasa sauran yaran tasowa suka yi cirko cirko suna kallonsu,da sauri jamilar tace"a'a inna wllh ba wanda yayi man wayo mutumin dana gaya maki anyi a gabansa ne ya bani kuma ma sai da na tambaye shi wa zance maki ya bani in kin tambaya....da sauri uwar ta katseta ta hanyar tambayar"to waye shi yace maki? Har lokaci tana rike gam da hannun yarinyar "cewa yayi ince maki dan gidan HAJIYAR SANATA"yarinyar ta fada cike da kwarin gwiwa don tasan gaskia take fada, "Hajiyar Sanata! Innar ta maimaita lokaci guda kuma ta saki hannun jamilar da mamaki a fuskarta sai maimaita sunan hajiyar sanatan take "to ke kinsan shine dama" ta tambayi Jamilar "a'a Innarmu ni yau ma na fara ganin shi wllh"nan ta shiga fadi mata yadda sukayi dashi bayan an 6arar da awarar,innar tace "To waye wannan mutumin mai kirki haka,lokaci guda ta rike ha6arta da alamar tunani take...... taci gaba"Ni dai a tunani na Hajiyar sanata bata da wani d'a ko d'iya a gabanta gaskia,sai dai danginta da ke yawan kawo mata ziyara da kuma mutanen gari tunda gidanta gida ne na al'umma ko don taimakon da take ma mutane tunda mace ce mai kirki ga taimako gashi kuma d'anta babban dan siyasa ne shiyasa gidan bai rabuwa da mutane kala kala,Oh to shi wannan ko waye?"ta k'arasa maganar da sigar tunani, Jamila ce ta katse ta da cewa"gaskia nidai ce man yayi dan gidan ne shi,kuma da gani haka ne,don baki ganshi ba innarmu Kyakkyawa ne sosae wllh wani irin fari mai kyau gare shi,ga gashin kanshi kaman na yan kasan waje ni wllh innarmu banyi zaton ma ya iya hausa sosae ba sai da yana man magana nayi ta kallon shi,kuma kin san mi inna? "A'a" innar ta bata amsa a inda take tsaye Sototo "Kalar kayanshi irin kalar motar da ya hawo ne,ina irin kayan nan na turawa masu igiya a wuya...tasa hannu tana kwatanta ma innar,ita kuma ta gyad'a kai alamar ta gane kayan"to sune a jikinshi kinga takalmanshi irin rufaffun nan ne masu kyaun gaske kai wllh Mutumin mugun dan gayu ne innah" ta k'arasa maganar tana yarfa hannu, Ajiyar zuciya uwar tayi tace"to kam ina tunanin daya daga cikin jikokin hajiyar ne,don jikokinta tubarkallah akwae kyau sosae wllh don kwanaki can da dadewa munje kar6ar tallafi a gidan naga wani Matashin Saurayi mai kyaun gaske har muka gaida shi ya amsa mana kamar baison amsawar..."inna wllh kilan ma shine,shima wannan fa kamar dan dole yake maganar baki gani ba yana wani haka,ta d'an yamutsa fuska ita ala dole yadda yake magana take kwaikwaya gaba daya suka sa Daria harda Kannenta,Innar ce tace"hakan duk cikin gayu ne ai,kinsan su yan gayu komae nasu na daban ne wllh,kai Allah muma yayi mana arziki mai Amfani" ta d'an daga hannayenta sama, "Amman anya shine kuwa wannan fa anyi shekara biyu koma fi dana ganshi kilan dai dan uwan shi ne,kai koma dai waye nagode kwarai wllh Allah ya taimakeni ta silar shi,da bansan ya zanyi in biya kudin Waken nan da Mai ba dama sai da aka ja man rai aka bani,kai Allah ya taimake ni wllh",hannu ta daga tana k'ara gode ma Allah cikin tsananin farinciki,gaba daya yaran suma suka dauka"Allah mungode ma² suna yi suna tsalle ganin Mahaifiyarsu na farin ciki,kar6ar bokitin awarar tayi tana dubawa"Kai yarinyar nan anyi yar....ko da yake inma na zage ta kanmu abun zai k'are,don ba'a son mutum yana abu ana aibata shi da mugayen kalami,to kara lalacewa yake kuma mutanen da ke tare da shi su abun ke shafa,Allah ya shiryata dai damu baki daya" "Amin"yaran suka amsa da karfi" amman duk da haka ji nake kaman inje in fadi ma gwaggon tata don abun Yarinyar yayi yawa wllh" jamila tace"innarmu ki kyale ta kawae shima Mutumin daya bada kudin cewa yayi kar in bita gidansu don in an kara dukanta zata kara 6arar mani tunda bata jin Magana" hakane gara mu kyaleta tunda ma sanadin abunda tayi mana ji bi abun arzikin da muka samu" ta kara sa maganar tana k'ara kirga kudin, wani yaro ne cikin yaran yace "Inna muzo mu karbi sauran mu cinye tunda an samu kudi" yayi maganar yana d'an noke kai gami da yar daria da sauri Innar tace"ehh maza kuzo ku kar6a" tsalle yaran suka fara yi suna murna,marar k'asar ta babbasu Jamila ce tace "Inna don Allah tunda ansamu kudi zaki ban in siyo hoda mai madubin da na tambaye ki kwanaki kika ce sai kin samu kudi" ta karasa maganar tana sussunna kai kasa,da fara'a a fuskar innar tace "Kwarai kam zan ba ki tunda Allah yasa ansamu kudin,ko dama can abunda yasa ban baki ba kudin ne ba isa suke ba sam kina dai ganin yadda ake ta fama,kinga da kika yi hakuri ba gashi Allah ya kawo ba, shiyasa in aka ce ma Mutum yayi Hakuri to yayi din don mataki ne na nasara rashin yin hakurin kuma ba abunda yake ja ma Mutum face asara da dana sani" cikin washe baki jamila tace"Eh hakane Inna" "to sakamakon hakurin da kika yi harda na siyan jan baki zan baki sai kije ki siyo harda sabon bokitin tallan" tsallen murna jamila ta fara yi tana ta faman daria tana shima dan gayu mai mota daya bata kudi Albarka,itama Innar tasu Albarkar take sa ma mai motar yayin da ta nufi daki don adana Kudin. * * * * * * * * * * * * * * * * * Wani irin Katafaren Gida ne mai tsananin kyau wanda da ka kalla zaka gasgata kyawun gidan,Fentin gidan ya matukar kayatuwa wanda Peach colour ne mai dan duhu had'i da milk colour,Katangar gidan na dauke da peach din fenti yayin da Pillars din dake a jikin katangar ke dauke da Milk din fenti,gaba daya katangar na zagaye da hadaddan Fence wanda ke dauke da farin fenti,daga saman fence din yadan yi tsini kamar mashi anyi mashi adon fenti Golden mai salk'i,cikin fence din kuwa shukan Flowers ne masu kyau da gani suna samun kulawa sosae,gasu a tsare mai tsawo sai ta gabanta gajera haka suke jere gwanin sha'awa,can saman katangar ma zagaye yake da Electric fence bak'i,A k'arshen katangar gidan gaba daya kuwa Masallaci ne mai kyau da girma komai nasa kalan na gidan ne ga Tankunan ruwa manya har biyu a sama da kan Famfuna a jikin ginin da aka d'aura su Yara nata dibar ruwa. Gate din gidan kuwa ya d'an shiga lungu ta yadda in mota ta taho daga bangaren katangar gidan ta dama ko hagu zata shiga gidan sai andan karya kwana, A daidai gidan mutumin ya juya kan motan ya tunkari Dank'areren Gate din gidan wanda shima yake da farin fenti daga saman shi anyi design irin na fence din,ajikin bangon da ke kallon hagu in an shigo kwanar gate din kuwa wata dakakkiyar Kofa ce a rufe itama da farin fenti mai salk'i da kwalliyar irin design din fence din wanda akayi ratsi da golden paint mai daukan ido. Wasu Jami'an tsaro ne guda biyu dake zauna a saman bencin karfe shima da farin fenti suka mike ganin motar ta tunkaro gate din kowannansu na sanye da Uniform,daya uniform din yansanda ne jikinsa dayan kuma na civil defence had'i da Bindigu rataye a kafadunsu,daya ne ya kama gate din yana Sliding din shi right yayin da dayan ya matso kusa da motar yana washe baki,a hankali gilashin motar ya dan bude "Welcome sir" jami'in ya fada baki washe. Mutumin ya juyo fuska adan sake yace"Thanks Officer,how work" cikin sauri officer din yace"Aiki Alhamdulillah gamu a cikinsa,har lokacin bakin shi a washe yake,"Ok,Allah ya taimaka" mutumin ya fadi a lokacin kuma yaja motar fuuu don angama bude masa gate din,da sauri dayan Jami'in ya daga masa hannu alamar sannu da zuwa lokacin da motar tazo saitin da yake a tsaye,Horn na cikin motar ya latsa alamar ya amsa,Parking Spot ya shiga wanda ke dauke da karafa masu farin fenti anyi masu design mai kyau yayin da saman wurin ke rufe da Alminium roofing sheet yana da girma don yana da wurin parker mota shidda,akwae motoci guda hudu a ciki akwai Hilux mai dauke da tambarin NGO,sai Vibe,peugeot 406,da kuma wata Had'addiya wadda na kasa gane sunanta,a kusa da ita ya parker motar a can karshe kuma wani hadaddan k'aton bak'in Bike ne ajiye, daga gaban parking space din wani dan daki ne wanda ba'a sa kofa ba,daga saman wurin shiga an rubuta GENERATOR ROOM,a gefen ginin wata kofa ce ta k'arafa wadda zata kaika cikin masallacin dake jikin gidan. Wani matashin saurayi ne rik'e da tiyo yana ba Flowers ruwa yana sanye da wani kodaddan Crazy Jeans da bakan T-shirt itama dai ba sabuwa b,kanshi anyi mashi aski irin na gayu,yana ganin motar ta tsaya ya saki tiyon ruwan ya nufo ta da yar sassarfa ya tsaya a gefe yana ta faman washe baki sai da aka dauki wasu seconds kafin na cikin motar ya bude yana kokarin fitowa,da sauri saurayin dake a tsaye ya kama k'opar ya idasa bude ma Mutumin,fitowa yayi a hankali yasa hannu yana gyara necktie din dake wuyansa,saurayin ne yace "Barka da zuwa yalla6ai "yana ta faman washe baki, fuska adan sake ya kalli saurayin daga sama zuwa kasa da alama shigar da yayi yake kallo kafin ya tsaida fuskarsa akan tasa yace " Yauwa T.K Babban Yaro,yayi maganar ta sigar tsokana, Cikin dan jin kunya T.k din ya sunkuyar da kansa yana murmushi yace "Ah haba yalla6ai wane mu Almajirai".Murmushi mutumin yadan yi kafin ya bude back door din motar yadan zura hannu ya fiddo da Briefcase din sa,da sauri T.K ya mik'o hannu ya karbi jakan shi kuma yayi gaba,T.k yasa hannunsa daya ya rufe duka kofofin motar ta gaba da ta bayan kafin yabi bayan mutumin. Wata corner suka shiga wadda ke a bangaren dama inda gate din gidan yake, tafiya Mutumin yake cikin corridorn a nutse, yayin da T.k ke binsa a baya rungume da jakar har suka iso wata kofa ta karafa wato Fence door daga can gaba kuma akwae bayan wata kofa wadda ke a rufe tana kallon bangaren da fence door din da suke k'okarin budewa take da alama bayan hadaddiyar kofan nan ne dake a waje kusa da gate,hakan na nufin in kabi ta kofan zaka fito wajen gidan kwanar da gate yake. T.k ne ya dawo gaban Mutumin da sauri yasa hannu ya zare kubar da ke rufe jikin Fence door din yasa hannu ya tura kofan ciki ya dawo gefe ya tsaya saida mutumin ya shiga sannan ya bi bayansa,dan Flat ne mai kyaun gaske wanda kasan ke malale da Interlocks ga Flowers jere masu kyaun gaske girman su daya,gaban flat din na rufe da fence mai dauke da glass wanda ke dauke da zanen flowers ajikinsa hakan ya bada area din da ake kira da Bolcany. Sai da Mutumin ya wuce saman wurin kafin T.k ya bi bayansa da sauri T.k ya murd'a handle din Dakakkiyar kofar shiga flat din ta bude ya dan ja gefe guda yaba mutumin wuri ya shiga kafin yabi bayansa,Ya Allah!ba karamin had'uwa Parlorn yayi ba wanda gaba daya Fentin cikinsa fari ne mai salk'i,haka Tiles din da ke malale a kasa ma fari ne kar da ratsin baki,kujerun ciki kuwa Leather chairs ne L-Shape bakake wanda ke kewaye a tsakiyan parlorn a samansu akwae Throw pillows Red color masu kyau a jere,daga gefen dama kuwa in ka shigo akwae Armchairs guda biyu suma leathers ne amman red color saman kowacce akwai T-pillow bak'i,daga bayansu kuma wani Had'addan Desk ne manne da bango wanda ke dauke da Drawers gefe da gefe fari ne kal sai faman salk'i yake a samansa akwai Table Lamps (fitilu) guda biyu jajaye kowacce a k'arshen desk din,a tsakiya kuma bakin telephone ne ajiye daga dan gaban desk din tangamemiyar Window ce wadda ke rufe da farin Blinds (irin labulen nan mai yanka yanka,wanda aka fi yawan amfani dashi a office),A tsakiyan kujerun parlon dakakken Carpet ne mai laushin gaske baki dauke da ratsin kwalliya ja da fari a samansa kuwa wani hadaddan Center Table ne na glass fari mai kaurin gaske,daga can bangon dake kallon inda jajayen kujerun suke wata Window dince itama rufe da bak'in blinds,a bangon dake kallon duka kujerun parlor din kuwa wani irin PoP Casting ne manne da bangon mai dauke da Manyan gidaje anan kuma madaidaiciyar Plasma T.V ke manne a gidan tsakiya daga kasanta kuma gidan da Sound systems suke ne da DVD player da reciever,a gidajen dake a gafe da gefen bangon da saman inda T.V din take kuwa,Hotuna ne dasu Agogo da Frames na zane wato Artworks ba karamin kyau wurin yayi ba.A gefe kuma d'an corridorn da bedrooms suke ne,a kofan corridor din flower vases ne bakake dauke da Red flowers masu ratsi da farin kananun flowers,a Angles (sako) din dake a bangon kuwa 6arin hagu Standing A.C ce babba a angle din dama kuwa madaidaiciyar Freezer ce a wurin,a tsakiyan pop ceiling din parlon akwae chandelier babba (irin fitilar nan mai adon sarkoki) kwan fari sol yayin da sarkokin jikinta bakake ne,ba k'aramin haduwa parlorn yayi ba ga sanyin A.C hadi da kamshi mai sanyaya rai da ya gauraye ko ina,da ka shigo parlorn zaka ji gaba daya yanayin ka ya canja koda kuwa kunci kake to tabbas ranka zai yi sanyiii. Mutumin na shiga ya nufi inda bakar kujerar take ya dan fada samanta hadi da aje wayarsa wadda take slim mai dan tsawo bayanta sai shining yake a gefensa,ya kwantar da kansa jikin saman kujerar don bayanta baida tsawo sosae,T.k kuwa yana shigowa yad'an lumshe ido hadi da jan dan dogon numfashi alamar sanyayyan kamshin ya kai masa karo,shiyasa a koda yaushe yake son abunda zai kawo sa part din Mutumin koba komae ka samu natsuwa.Wucewa yayi bayan Red Armchairs din parlorn ya daura jakar saman farin desk din dake wurin kafin ya zagayo tsakiyar parlorn ya tsaya saitin Mutumin yace"Yallabai akwae wani abu? A nutse yayi maganar,Mutumin bai dago ba yana a yadda yake yadan daga mashi hannu hadi da fadin "Thanks T.k,u can go" t.k yace "To a huta lpy" ya kama hanyar fita batare da ya jira amsar Mutumin b,don yasan ma b lalle ya kara cewa komae ba, Yana fitowa yaji wani zafi ya bugi fuskar sa a fili T.k yace " Kai masu kudi dai sun ji dadin su,da ace part din nan yazama nawa ai wllh fitowa sai dole"Ya k'arasa maganar hadi da wurga kafa yace "qur'an kau" a daidai lokacin ya fita daga Part din Mutumin. Ya dau tsawon mintuna a haka da alama dai ya gaji ne sosae kafin ya mike ya tunkari hanyar da zata kai shi Bedroom dinsa har zai shiga cikin koridon ya tsaya cak sakamakon karar da Telephone ke yi,a hankali ya juyo gami da kai idonsa saman desk din da telephone din yake yanata faman kara alamar ana kira,tafiya ya fara yi a hankali saida ya zauna saman daya daga cikin Armchairs din dake gaban teburin sannan ya mikar da hannunsa ya dauko kan telephone din,da murmushi a fuskarsa ya kara shi a kunnansa da alama yasan mai kiran nasa cikin murya mai tattare da gajiya ya fara magana"Hello sweetheart" dan saurarawa yayi kafin yaci gaba da magana "Ok ganinan zuwa yanzu" daria yayi har Hakoransa masu kyau da tsari suka bayyana cikin jaddada abun da ya fada ya k'ara cewa "Don't worry, I'm coming right away" yana fadin hakan ya maida telephone din ya mike har lokacin fuskansa da dan murmushi,Corridorn ya shiga kofa biyu ce a ciki daya tana kallon mutum in ya shiga wurin,dayan kuma na a bangaren bangon dake dama,sai da ya tsaya ya cire takalmin kafansa ya daura sa saman Shoe rag din dake ajiye a wurin anyi mashi design mai kyau da daukan hankali yabar safar dake a kafarsa bai cire ba kafin ya tura kofan dake a bangaren dama ya shiga,masha Allah Bedroom ne mai kyau da tsari bai da hayaniya Italian Bed ne da Bedside drawers din shi sai Dressing mirror wanda ke dauke da yan kwalaben turare da yan mayukan shafawa saidai da gani masu tsada ne don jikinsu kadai abun kallo ne,a bangon dake kallon gadon kuwa Wardrobe ce gaba daya bangon wadda ke rufe ruf a iya hangena nakasa gane yadda ake budata don banga hannun da za'a kama a bude ta ba, gaba daya Furniture din Coffee brown ne masu duhu sosai don inba ka shigo sosae ba zaka yi tunanin kayan bakake ne,haka Labulen dake a jikin katuwar Window din d'akin ma coffe ne mai kyaun gaske ga kauri wanda tsakiyan sa ke a tsage anyi hanging din bari daya,a Angles (sako) din bangon da gadon yake kuwa Floor lamps (dogayen fitilun kasa) ne dogaye ko ina an aje daya. Gaban dressing mirror din ya tsaya ya cire agogon hannunsa ya daura a saman wurin kana yasa hannu cikin Aljihun wandon sa ya fiddo da wallet dinsa itama ya daura ta a wurin ya juya ya tunkari wata kofa dake a rufe da alama kofan Bandaki ce,kofan na budewa na tsaya kallon Ikon Allah don kuwa ba toilet bane wani dan daki ne mai tsawo sai dai bai cika fadi ba akwai Wall Cabinet (durowar bango) a jikin dogon bangon dakin wadda ke a bude ga kaya nan iri iri wasu a sagale a jikin hangers wasu kuma a ninke daga gafen cabinet din kuma madaidaicin injin wanki ne wato Washing Machine a jiye.a bangon dake kallon inda cabinet din take katon Madubi ne manne da bango daga kasan shi kuma wurin d'aura mayuka ne dasu Shampoo da sabulai kala kala da alama wurin laundry ne,wato wurin wanki dasu kayan dauda,tsayawa yayi gaban tangamemen madubin wurin yana kallon fuskarsa kafin yasa hannu ya ciro wipe daga cikin wani kwali mai kyau a hankali ya fara goge Fuskansa da ita,nikam zuru nayi ina kallon ikon Allah,ya gama goge ko ina ya jefa ta cikin dustbin sannan ya tunkari Wall Cabinet din ya fara cire kayan da ke jikinsa tun daga kan rigan saman zuwa ta cikin da safar dake a kafafunsa yayi hanging dinsu jikin hangers din Cabinet din ya rage daga shi sai Vest da Short acan sama cikin wani gida ya mika hannunsa ya dauko wani abu dake a linke fari sol cikin kayan da ke wurin da alama Bathrobe ce wato rigan wanka wadda duk jikinta gashi gashi ne mai laushin gaske daga haka ya tura kopan Toilet din dake cikin wurin ya shige. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *By Oummu Imam📲* *Free Page5️⃣&6️⃣* Sanye da Bathrobe din da ya d'auka ya fito,sai da ya cire Slippers din dake k'afar sa a bakin kofan toilet din yasa wasu flip-flops dake a waje cikin laundry din,K'arasowa yayi gaban Mirror din dake a Laundry room d'in ruwa na dripping daga cikin sumar kansa da alama wanke kan yayi,Juyawa yayi ya d'aukko d'an farin towel a cikin Cabinet din bangon ya dawo gaban mirror din yana tsane ruwan cikin sumar kafin ya jawo Stool ya zauna ya rataya towel din a wuyansa a can gefen mirror din ya mika hannunsa ya d'aukko Hair dryer wadda dama a jone take ya fara busar da sumar tasa yana dan jujjuya ta da d'ayan hannun yan mintuna ya dauka yana busar da sumar kafin ya maida dryer din inda ya d'aukko ta,Hair Oil ya matsa a tafin hannunsa ya shafa ma sumar sannan ya bude robar da Cotton buds suke ya zaro daya yana kwalkwale Kunnansa ya gama goge duka kunnuwan ya jefa abubuwan wadanda ba wani dirty a jikin su cikin Wastebin. Daga haka ya mike ya nufi kofar shiga Bedroom din har lokacin Bathrobe din na a jikinsa,gaban dressing mirror ya tsaya ya fara matso mayuka yana shafe jikinsa bayan ya gama wardrobe d'in dakin ya tunkara wadda na k'osa inga ta yadda ake buda ta gefenta na dama ya tsaya,sak'a hannunsa gefenta yayi ya latsa sai ga shi ta fara zugewa da kanta,Iko sai Allah ashe Sliding ce,a tsakiyan murfin ta akwae tsaga wadda ta raba marfin biyu daidai,in ta daman aka bud'e sai ta zugo ta rufe ta hagun haka ma in ta hagun aka bud'e,komai dai na masu arziki na daban ne,Allah kai mana Arziki mai Amfani,Amin. Kayan sawa ne birjik a cikin ta wasu a rataye jikin hangers,wasu a ninninke gasu nan a tsare abun gwanin burgewa. Kowane kaya da wurinsu,Jeans,Shirts,Suits,Shaddoji,Yadiddika,wasu ma kayan a cikin leda suke alamar sabbi ne,ga Underwears suma wurin su daban tsarin kayan dai kaman Boutique,fiddo kayan da zai sa yayi had'i da underwears sannan ya latsa jikin marfin daga ciki ta fara rufewa ya juya ya nufi gefen gadon ya d'aura kayan....... Bayan ya gama sa kayan wanda T-Shirt ce coffe brown da bakin wando tracksuit wanda yad'an tsuke daga k'asa gafe da gefensa akwai zip wanda sai ka k'ura idanu zaka gani,rigan kuwa ta zauna cib ajikinsa hannun rigan ya kama cinyar hannunsa wadda take a murd'e da gani yana Bodybuilding,gaban Dressing mirror ya koma ya matso wani hadaddan mai ya shiga mutsitsika ma tafin hannuwansa,bayan ya gama ya dauko Hair Spray ya fesa ma gashin kansa sannan ya daukko turaren jiki wanda kwalbar shi kanta abun kallo ce ya faffesa ma jikinsa maida kwalbar yayi ya daukko wata itama mai matukar kyau ya fesa.....saida ya fesa turare kala ukku kafin ya dau Comb yana sharce kanshi wanda yake nad'e ko ba'a sharce ba bai yamutsewa,Drawer chest ya jawo ya fiddo da wani kwali mai kyau da k'yalli ya d'aura shi gaban mirrorn sannan ya bude,wasu irin agoguna ne masu kyaun gaske designers kala daban daban kowacce a dan gidanta ya fiddo mai fata kalan rigarsa ya daura sannan ya dauki wadda ya cire d'azun ya maida ta ciki ya mayar da kwalin hadi da rufe drawer. A corridorn ya tsaya ya ciro takalma Slide Sandals bak'ake daga cikin Shoe rag kafin ya fito parlor a daidai nan kuma telephone din ya sake fara ringing,dan girgiza kai yayi yana murmushi bai kalli inda yake ba yasa hannu ya dauki wayarsa da ya aje dazun ya fice. Ta Corridorn daya bi dazun ya fito cikin farfajiyar gidan mai girman gaske cikin natsuwa yake tafiya ya tunkari k'aton flat din dake a cikin farfajiyar wanda sak fentin shi kalar na gidan ne,Wani farin d'awisu ne ya fito daga bayan flat din ya bude jikin shi yana kuka gwanin burgewa,bansan lokacin da ni mai rubuto maku labarin na furta"lah kuga wani hadaddan dawisu,abun ka da ba'a saba gani ba,shi kau yalla6an ko kallon shi bai yi ba ya shige Entrance din,a wani dan corridor ya tsaya ya cire takalmansa da alama nan ake aje takalma kafin ashiga main Parlour din don akwai wasu takalman jere a gefe,shiga yayi cikin parlon wanda yake mai girman gaske fentinsa milk colour yana dauke da Royal Sofas masu kyau yadin su Maroon design din kwalliyarsu golden mai kyau ga Table dinsu aje a tsakiya daga can bayan kujerun kuwa dining area ce mai dauke da dinning table da kujerun shi irin design din kujerun parlorn, gaba kad'an da dining din kofa ce ke kallon su wadda corridor ne anan kuma kofofin bedrooms suke,Pop Casting din dake a bangaren da kayan kallo suke irin na d'akin mutumin da ya shigo ne sai dae hotunan dake wurin sunfi yawa har a sauran bangarorin bangon parlourn duk an kafe hotuna manya manya,hotunan wata dattijuwa sunfi yawa wasu tayi da family dinta wad'anda suke kyawawan gaske,wani kuma tayi da turawa akwai wanda tayi da Governor yana bata Award,da kuma wanda tayi da mutananmu na nan da alama a wurin aiki ne,akwae wanda take ita kadai ta nad'a lifaya fuskanta sanye da glasses tayi daria har hak'orin makkan ta ya bayyana daga kasa an rubuta sunanta,HAJIA HAUWA ADAMU ZAKEE,Akwae hotunan wani babban mutum wanda yayi suna gaisawa da shugaban k'asa,wani kuma tare da dattijuwar matar ya riketa fuskarsu d'auke da fara'a,akwae wanda kuma yake zaune a majalissar tarayya wato National Assembly k'asan hoton an rubuta sunan shi,SENATOR ALI ADAMU ZAKEE. Akwae flowers a Angles din parlorn da A.C manne a jikin bango,Labulayen cikin parlorn kuwa maroon ne da ratsin golden masu shegen kyau. Zaune saman kujera 2 seater dattijuwar matar dake jikin hotunan parlon ce gafenta telephone ne ajiye hannunta rike da magazine yayin da idanunta ke cikin glasses da alama Medical glass ne,da ka kalleta zaka fahimci ta manyanta sosae sai dae yanayin hutu yasa ba lalle ka iya kiyasta ainihin shekarunta ba,tana da haske don ba baka bace,ba kaman kuma da jikin ke samun hutu sosai, Tsaye mutumin yayi a bakin kofar shigowa ya dafa bango da hannunsa d'aya yana kallon matar da murmushi a fuskarsa. Sarai taji shigowar shi amman ta share taki d'agowa ta kalle sa idanunta na kan jaridar hannunta. Dan gyaran murya yayi,still tak'i dagowa ta kalle sa hakan yasa ya dan d'aga kafadarsa cikin ransa yace"Mun saba aii..." cikin parlon ya shiga ya tunkari inda take zaune yasa hannu ya dauke Telephone din dake gefenta ya maidashi adan sak'on da table dinshi yake, Zaunawa yayi gefenta ya d'an kwantar da kanshi a saman kafad'arta yace "Sweetheart fuskan shanun na miye ne? "What happen?" Ya kara tambaya,banza tayi dashi hakan yasa ya juya yana kallon fuskarta hannu yasa yana gyara mata bakin da ta turo alamun fushi,ya cigaba da magana, "Haba Beb fushin na miye ne..? kin wani turo baki,baki gan yanda kika yi muni ba,Smile plss..." ya fad'a har lokacin hannun shi na a gemun ta yana dan jan shi.Hannu tasa ta buge hannun shi kafin tace"Wato don kaga na damu da kai shiyasa nazama abun wulakanta wa ko? "Oh no Sweethrt ya zaki ce haka..,Am not hoping to see that day,dani zan wulakanta ki,ai ko wani nagan zai wulakanta man ke sai inda karfi na ya k'are" ya k'arasa maganar yana kara kwantar da kansa a kafad'an ta. "To amman miya sa na kira ka kace man kana zuwa harda wani cewa right away,Amman shiru ka k'i zuwa tsawon lokaci,akarshe na sake kira kak'i yin picking" tayi maganar tana dan harararsa. D'agowa yayi daga kan kafad'arta ya rik'e hannunta guda yace "Lokacin da kika kira I just came back and I was so tired shiyasa na bari in dan rage kayan jikina in watsa ruwa don insamu karfi" ya kai maganar da d'an murmushi, "To miyasa na sake kira baka dauka ba?" har lokacin bata saki fuska ba, "I was about to come here,lokacin da kiran ya shiga shiyasa naga no need in daukan"ya karasa maganar yana wani lumshe ido, "Yanxu dama duk saboda wannan ne kike ta faman daure fuska,to Am sorr.....bai karasa ba ta katse shi da cewa "bashi kadai bane" "To,what else? Ya tambaya. Gyara zama ta d'an yi shima ya gyara zama yana kallonta alamar ita yake jira tayi magana..."yanzu tsakani da Allah kana kyauta ma kanka,ace kullum sai nayi fama da kai kafin kazo kaci abinci,sam baka son cin Abinci..."katse ta yayi da cewa "Ni kuma,duk abincin da nike ci" Yana maganar da d'an murmushi a fuskarsa "karya kake baka wani cin abinci yadda ya kamata" ta fada tana harararsa,da mamaki yake kallonta with his eyes wide open yace "Yanzu ni da girmana kike cewa karya nike" d'an ta6e baki yayi yace "nidai nasan ina ci kawai dai rigimar kice,ko kuma so kike in rinka yin cin da ya fita Musulunci,Me I don't know" ya dan buga hannunsa guda kan kujera, "baka wani ci,d'an wanda kake cin ma ai sai kaga dama,kullum ka dawo aiki sai ka shige part din ka kadau uban lokaci wai kana wanka sai kaga dama kazo ka tsakuri abinci ka kuma fucewa,wani lokacin ma I have to called u,just like now dai" Yar ajiyar zuciya yayi kafin yace "Nidai nasan ina cin Abinci da banci ai bama za'a ganni haka ba,ji fa uban naman dake hannu na" yayi maganar hadi da d'aga hannunsa sama yana daria, ta6e baki tayi tace"Naman daga k'arfe ko,wllh kabi a hankali inba haka ba wataran k'arfen zai d'aga ka,ace mutum ya wuni yana zurga zurga baka nan baka can amman wai sai an matsa maka kaci abinci, da daddare ma ba wani na kirki kake ci ba da anyi magana kace wani Light food kake bukata". "Fata kike man karfen ya daga ni kenan"ya tambaya,"Ni ba fata nike ba kadama Allah ya nuna man ranar kawai dai ina so ka rik'a cin abinci sosae don kana bukatar hakan,ka daina yaudarar kanka da wannan murd'ewar don bogi ce,kullum kana dawowa direct ka wuto nan ka cika cikinka sai kaje kayi ta bauta ma jiki uwa wata mace,ni wllh ma na dade banji ko ganin mace da take ma jiki wahala irin ka ba abun naka yayi yawa", "Haka dai kika ce ni bana ganinsa a wahala duk abunda ya dace mutum yayi don tsaftar kansa nike nothing's too much" Yaci gaba, "Toh why not a rik'a kaiman abincin can part dina kinga in nagama wahalar jikin kaman yadda kikace sai inci ko? "Kaji dad'in kin cin kenan,a gaban nawa ma ba ci kake sosae ba, balle ba idona". Dariya yake sosae yace "sai kinsa man ido kenan,sai kace wani karamin yaro,You know what,in kingan nadawo na dade ban nemi abinci ba bana jin yunwa ne,kinsan bai yiwuwa in dauki wannan hours din wurin aiki ba tare da naci komai ba" Yamutsa fuska tayi tace "Abinci! Kai dinne zaka ci abinci a waje,wanda ma aka yi cikin gidan sai kaga dama zaka ci balle wanda aka yi a waje,nasan dai kasha wannan bak'in lemun d'an gado sai ko snacks kilan,suma in kagadama kenan"jingina bayansa yayi da kujerar yace"Yanzu dai zaki sa akawo man abincin ko kuwa,don am running out of time fa,ya fada yana duba Wrist watch dinsa,yaci gaba"In kuma inyi tafiya ta to" yayi maganar da sigar tsokana, "Ka tafi mana,cikin wani ba naka ba". "Uhm ai kam da baki bar ni nayi exercise dina ba yadda ya kamata kiran wayarki kadai ya isa ya hana ni yin komae" Yayi maganar yana yar daria."Allahu,yanzu ni har nazama abun tsokana ko,don kawai kaga na damu da kai,don nasan inka cutu tamkar ni na cutu ne shiyasa amman in sha Allahu na daina takura maka,continue doing as u like"ta karasa maganar tana kokarin tashi,da sauri ya jawota jikinshi sai faman daria yake yace "Just kidding u beb" ture sa ta fara yi tana ce mashi "Ni ka kyale ni abun da ke ranka game dani ne ka fada ai" Daria yake sosae don sun saba sai ta tak'alo magana karshe kuma tayi fushi kan abunda bai kai ya kawo ba, Mutsu mutsu ta shiga yi tana son kwace kanta sai dai ya rike ta gam ba yadda za'ai ta iya kwacewa,a kusa da kunnanta ya kai bakinsa yace"Haba Hajiyan Senator nine fa na wajenki,your heartbeat" "Naji sake ni to" yace"sai kince kin hakura my sweethrt, "na hakura amman zan dau mataki a kanka..." wane irin mataki kuma? Tace "to ka sake ni sai in fada ma" sakin ta yayi tace "Matakin share ka zan d'auka ba ruwana da kai duk abunda kaga ya dace da kai kayi tunda ni gani kake ina takura ma" ta karasa maganar tana turo baki. "Oh ya Allah,ba kince kin hakura ba miye kuma na repeating same magana,ba kyau fa ruk'o kinsani,kuma ni na gaya maki wasa nike,ina jin dadin yadda kike so na kina nuna mun kauna nima kuma ina kaunarki and am telling u this deep from my hrt" Ya k'arasa yana nuna mata bangaren zuciyarsa,Murmushin jin dad'i tayi don ba karya yayi ba tana matuk'ar jin shi a ranta, Shima wani hadaddan murmushi yake yace" That's my beb" da sauri tace "kaga ka daina ceman beb din nan tsofai tsofai dani kayi tace man wani beb kamar wata tsohuwar yar dunia ta k'arasa maganar tana ta daria,"No ba wani yar dunia,ni ke beb dina ce,pls kisa akawo man Abincin" "toh" tace ta fara kiran mai aikin ta,"Saude,saude...,"daga ciki Sauden ta fara amsawa ta fito parlorn ta kofar Kitchen dake a gefen dining area tana kokarin k'arasowa inda suke Hajiyan tace "Je ki kawo masa abinci,"toh sauden ta amsa ta kalli inda yake ya kwantar da kansa a jikin kujerar da suke zauna,tace "Ina wuni...." lpy" ya amsa ba tare da ya d'ago ba, Yan mintuna ta d'auka ta dawo dauke da Tray saman shi wata irin Warmer ce mai kyau a gefen warmer din Bowl ne an d'aura Plates kalar bowl din, samansu kuma Cokulla ne da Serving spoon da gani na kulan ne duk anyi Wrapping dinsu,dining table din ta nufa...."Bring it here"ya dakatar da ita daga daurawa saman table din ta nufo inda suke saida ta fara daura tray din saman kujera one seater ta kinkimo sofa table din da kyar hajia na fadin"bi sannu dae kar ki bige kafa," To" tace lokacin ta karaso da table din gaban shi ta maido tray din saman shi ta fara Serving din shi,wata hadaddiyar fried rice ce tasha Vegetables don ba abunda babu na kayan hadinta sai kamshi ke tashi ta warware papern jikin serving spoon din ta fara zuba mashi,ta kusa zuba rabin plate din yace "Is okey.." wani kallo hajiya tayi mashi kana tace da Sauden k'ara masa,"To sauden tace, ta k'ara zuba one spoon tana kokarin karawa..."Ya isa! Yace da dan hanzari waigawa yayi ya kalli hajiar yace "In ta cika man karshe barinshi zanyi ne" ta6e baki hajia tayi tace "kai dai ka sani" d'an murmushi yayi ya juya ga abincin lokacin saude ta rufe warmer din ta bud'e bowl din wanda yake dauke da pepper chicken kamshin sa ba'a magana ta debo wata katuwar cinya ta daura masa a gefe tana kokarin kara masa ya dan d'aga mata hannu alamar ya isa,hajia dai na kallon shi ya d'ago suka had'a ido "Uhm" tace ta juya mashi k'eya, d'ayan plate din da ta rufo wanda ta zuba mashi abinci ta rufe bowl din da shi ta warware cokullan wanda Spoon ne da Fork ta sa mashi cikin abincin,mik'ewa tayi tace "Wane lemu zan kawo" yad'an daga hannu yace"Just water" Hajia tace" Ai mu bamu da lemun da ya saba sha" tayi maganar tana ta6e baki" Zan d'auka in zan fita" yace lokacin kuma ya fara cin abincin sa, "Coleslow din ya kare ne?" Hajia ta tambaya,Saude tace "A'a yanzu zan kawo masa da ruwan" "Just bring the water" yace,hajia tace "kawo masa ruwan kawai,"Toh" Saude tace ta juya don daukko ruwan,Bottled water ne da Acrylic cup ta kawo masa d'ora su tayi gefen tray din ta d'ago,"Thanks" yace,da alama halinsa ne duk akai masa abu yace thanks,"A ci lpy" Saude tace ta juya ciki, Cikin natsuwa yake cin abincin,hajia ce ta fara magana"Wai yanzu har ka fita d'aga karfen? Yar daria yayi yace "Nifa ba daga karfe kawai nike ba duk wani abu na motsa jiki wanda naga ina ra'ayi ina yi,wani lokacin ma ball nike bugawa," "Ball? ai nayi zaton ka daina ta tuntuni" yace "Eh na daina football amman inayin Basket ko Volleyball Har Badminton ma in ina ra'ayi" ya karasa maganar lokacin ya kai abinci bakinsa, Ajiyar zuciya tayi,tad'an tur6une fuska tace, "To kad'an huta yau mana tunda yamma tayi sosae" ta fada tana kallonsa,sai da ya cinye abincin dake a bakinsa yace "So kike in kasa bacci yau,kinsan fa I'm addicted to it" shiru tadan yi kafin taci gaba, "Turawan nan duk sun lalata ka,da duk baka wadannan abubuwan inaga kwallon kafa ce kawae ka ke yi itama kace wai ka bari" Murmushi yayi yace "Sun dai gyara ni,Exercise ai is very² important.....har lafia ma mutum yafi in yana yi,yanxu kinga zan iya d'aukanki a hannuwana bama goyo ba inta yawo dake ko'ina batare dana gaji ba,Wani irin kallo tayi masa tace "Tunda ga jaririya ba" yar dariya yayi taci gaba, "To mi zai hana ka rika yi nan cikin gida tunda akwai wadataccan fili dama kuma naga ai akwae kayan motsa jikin a can G.R.A ko? Kaga kasamu lokacin kanka," yace" No!a Gymnasium yafi dadi cikin sauran players anan dawa zan rika yi,ko ke? dan ta6e baki tayi kafin taci gaba, "Amman dai bada wancan gingimemen mashin din zaka fita ba ko? Ya fahimci bike dinsa take nufi,"Saboda me kika tambaya"yayi maganar yana dan yagar cinyar kazar da ya d'aukko da fork,tace "hakanan nidai bani son mashin din wllh,baida wani Amfani," dariya ya d'an yi yace "Da baida amfani ayi shi sweethrt...." "to ai nidae had'arin shi kawae na sani, Shifa ya kusa kashe dan gidan tsohon shugaban k'asa da kyar ya rayu,an ma ce sai da akasa masa k'arafa a cikin kai fa" Tana maganar fuskarta dauke da damuwa, taci gaba "ga yaron nan dan gidan Honorable Dalhatu Mande wanda ya mutu can kwanaki shima fa bike dinne ya kadashi kwanya waje haka aka tattaro shi nasan duk da lokacin baka k'asar bazaka rasa jin labarin ba a social media ko? Gyara zama yayi ya aje sauran naman yace "Ai nama san shi munyi junior secondary tare duk da dai mu muna a gaban su,nasan lokacin da ya fad'i da bike din....." da sauri Hajia ta rik'e ha6a tana salati "Yanzu duk da haka shine ka zuba uban kudi naira na gugan naira,har naira million biyar ka jajibo mana masifa!" Shi dai kallon ta kawae yake "To gaskia ni bana son mashin din nan wllh don aduk lokacin da ka fita dashi hankali na mugun tashi yake har sai naga kadawo nike samun natsuwa to wllh asan yadda za'ai dashi gaskia,hakanan mutum ya zuba mak'udan kudi ya siyo ajalinshi ina dalili" ta k'arasa maganar tana watsa hannuwa. "Yanzu ya kike son ayi dashi? da sauri tace"A sayar dashi kawae don bana ce aba wani ba tunda ba mashin din arziki bane inma kai baka da abunda zakai da kudin ni kaban ina da abunda zanyi dasu" Ajiyar zuciya yayi kafin yace " ke mi zaki yi da kudi? da sauri tace"Yo in zuba a Organization din mu mana kudi na yawa ne a wannan wurin ai kullum buk'atar su ake ba kaman yanzu da mutane ke fama kaga kaima ka samu lada kuma an kawo karshen wancan dirkeken mashin din maras Amfani. D'an ta6e baki yayi yace"In dai kina bukatar kudi ne ki gaya man na baki,Amman maganar saida bike din can bata taso ba,kinsani bana siyan abu in kuma saida,In har na mallaki abu to fa sai dai na bayar badai saidawa ba" ya karasa hadi da d'an girgiza kai,yaci gaba, "kuma ma ni inason abuna that was why I bought it all the way from US" yayi maganar on serious note,Hajiya tace "Nima ba don had'arin shi ba bazance ka sayar ba,kawai dai ina gudun wani mummunan abu ya faru da kai ne ba fata nike ba" Maida jikinta tayi ta jingina da kujerar,fuskarta har lokacin da damuwa, Tissue ya yago daga saman table din da telephone yake ya fara goge hannu,kallonshi hajiya tayi sai kuma takai dubanta cikin Plate din abincin da ya ci,ya cinye saidai yabar d'an saura kaman yadda dai yan gayu ke yi,naman dai ne yaci rabi yabar saura. "Yanxu cinyar kazar ma bazaka iya cinyewa ba? "Na k'oshi ne" ya bata amsa "To da ka barta waye zai ci sauranka" "Ke mana" ya bata amsa a takaice. ta6e baki tayi,tadan d'ago daga jikin kujerar "Ni kam bazan ci ba kai zaka ci......."bata samu damar karasa maganar ba saboda sauran naman daya dauka ya tura mata a baki ya rike kanta da hannu daya sai kace ya rike karamar yarinya,bugun hannunshi ta fara yi tana kiran"HAISAM! HAISAM!,mi kake yi hakane" baki cunkushe da nama take maganar,bai kyale taba har saida ya tura mata ita duka ya mik'e yana daria "Ba gashi ansamu wanda ya cinye saura na d'in ba" baki cunkushe da nama tana taunawa take harararsa,duk'awa yayi a gabanta ya kama dukkan hannuwanta sai kace wasu Saurayi da Budurwa,koda yake a hak'ikanin gaskia suma cikakkun masoyan juna ne suna kaunar junansu sosai,suna sa junansu yin abu,haka suna hana junansu,ya fara magana cikin nutsuwa"Nasan don kin damu da ni ne that was why kike zullumin kada bike nima ya kasheni..."dan murmushi yayi kafin yaci gaba "Itafa mutuwar nan d'aya ce sweethrt sabubbanta kuma da yawa,so don ina hawa bike ba yana nufin dole shine zai kashe ni ba ko ya lahanta ni kaman yadda yayi ma wasu,Kowa akwai silar Ajalinsa wasu ma hakanan suna a kwance ko a zaune suke mutuwa,kamar dai yadda kike zaune din nan sai kiga na hau bike din naje na dawo lapia ke kuma kin mutu a zaunen...." da sauri ta tsaya da taunar naman da take tana mashi wani kallo,Daria yake sosai ganin yadda ta yi, lokacin ya mike ya nufi dining area gaban Handbasin ya tara hannuwansa yana wankewa kafin ya bude k'atowar Deep Freezer din dake jikin bangon kitchen ya d'aukko Canned Coke ya rufe,"I know why u look all worried,saboda wancan tsohon ne" ya fad'a yana nuna k'aton hoton wani mutum da Coke din hannunsa dake a gidan saman da Plasma t.v take,sanye yake da kakin Sojoji babban mutum ne sosai kayan sun kar6i jikinsa yana da kyau ba laifi ga dogon hanci,kalar fatar shi kuwa za'a iya kiranshi da wankan tarwada wato shi ba bak'i ba,ba kuma fari ba,daga kasan hoton anyi rubutu kaman haka,GEN. ADAMU ZAKEE,daga k'asan rubutun kuma shekarun daya dauka a raye ne zuwa shekarar daya mutu,kallon hoton hajia take da wani irin yanayi kafin ta juyo da kallonta kan Haisam wanda yake kokarin fita,d'an murmushi tayi sam ba walwala a tare da ita tace,"Take good care of ur self for me,pls banda tuk'in gangancii". "Don't worry beb zan dawo lapia,ba yanxu zan mutu ba...tare ma zamu mutun amman sai nayi aure,nayi ya'ya harda jikoki kaman ke,da nayi Achieving all my goals,then sai mu mutun" Ya karasa maganar yanata faman daria adaidai lokacin kuma ya kai bakin kofan fita...da dan d'aga murya hajiyan tace kace sai nazama leda kenan" Daria sukai su duka,a lokacin kuma ya fice,ita kuma hajia ta maida dubanta kan hoton sojan mutumin nan tana girgiza kai, A yanayin Haisam bazaka ta6a tunanin za'ai wannan dogon hiran dashi ba don kallo daya zakai mashi ka yanke cewa irin miskilan mazan nan ne, masu ji da kai,kuma hakan ne don ba kowa yake sake mawa ba yayi fira haka,sai mutanen da ya shak'u dasu sosae suma d'in sai yana jin yin firan,Amman tsakaninsa da hajiyansa wannan ko yaushe yana da lokacinta kaman yadda itama hakan yake a wurinta. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *BY OUMMU IMAM📲* *Free Page7️⃣* Da d'an hanzari ya nufi Part dinsa bayan ya fito daga part din hajiar,hango T.k yayi cikin Parking spot yana ta faman goge motar daya dawo da ita,hakan yasa ya juya shima ya nufi Parking space din ya d'aga ma T.k hannu alamar yazo,da sauri T.k ya daura dan towel d'in saman motar ya nufo sa tun kafin ya k'araso wurin shi ya d'an daga murya yace "My bag" hadi da yi masa alama da hannunsa wato ya d'aukko masa jaka. Juyawa T.k yayi da dan gudu gudu ya nufi part d'insa,shikuma ya shiga cikin Parking space din yana kokarin fiddo da Bike din,daidai lokacin da ya fito dashi cikin harabar T.k ya dawo d'auke da jakar,wata katuwar jakar goyo ce sandar racket ta leko ta cikin jakar ya rataya hannunta daya a bayansa,saukko da jakar yayi yana kok'arin mika masa ya tsaida shi,alama yayi masa da hannu ya bud'a jakar hakan yasa T.k ya aje jakar kasa sannan ya bud'e. Umarni yayi mashi da ya fiddo masa takalman ciki,T.k yasa hannu ya fiddo da wasu kambos masu kyau ya mika masa kana ya zuge zip d'in jakar, D'an jujjuya su yayi da alama basu yake son sawa ba,sai kuma ya juya hannunsa ya duba agogo,ganin lokaci yaja yasa ya duk'a don yasa takalman cire na kafarsa yayi sannan yasa kambas din,ya mike lokacin da ya gama daura igiyoyin takalmin ya haye saman Bike din ya zauna sosae,shi kam T.k sai faman kallon mashin d'in yake ko kyaftawa bai yi, Hannu Haisam ya mik'a ya ciro helmet (hular kwano) daga saman kan bike din yana kokarin sawa a kansa,juyawa yayi ya kalli T.k wanda ke tsaye k'ikam da jaka a hannu ya k'ura masa idanu. Yace"Yadae T.k,ko zaka d'ana ne? da sauri T.k yace "Ah yalla6ai wannan ai sai ku,yafi karfina" yayi maganar yana daria,d'an murmushi Haisam yayi yace"Saboda me yafi karfin ka baka iya mashin ba? Da sauri T.k yace "Na iya yalla6ai irin dai namu wanda aka saba hawa,banda wannan ni tsoronsa ma nike wllh ko goge sa nike sai inta ganin kaman zai fad'o ya danne ni, shiyasa duk in ina goge shi ban yarda na duk'a k'asa" ya karasa maganar yana ta faman daria,shima Haisam din yar daria yayi,ya mik'a masa hannu lokacin da ya gama sa hular alamar ya bashi jakar,da sauri T.k ya mik'a masa,ya amsa ya goya ta a bayansa sosae,d'an juyowa yayi ta cikin hular yace, "Ka shirya soon zaka d'ana don bai yiwuwa kana masa wahala amman baka ta6a hawa ba" yayi maganar da sigar tsokana hakan kuma na nuni da yana shiri da T.k din har suke magana haka, Zaro ido T.k yayi sosae yace "Nidai yalla6ai wallahi na yafe" ya d'an daga hannunsa, shikam Haisam daria yake ta cikin hulan ganin yadda T.k ya zaro ido yana mamakin yadda kowa ke tsoron bike din wanda shi kam sarrafa sa yake tamkar ya hau keke,don sun saba yin gasar tsere dashi a U.S,A daidai lokacin ya kunna bike d'in yana murza shi, kararsa ta karad'e cikin gidan ji kake wani "BHUUMMM²...." da sauri T.k yaja baya,yayin da d'aya daga cikin Officers din bakin gate ya mik'e da sauri ya kama gate din yana sliding din sa,dayan kuma yace"Bari mutum ya matsa kar a d'ebi kwanyarsa yanzun nan" gaba d'aya suka sa daria,A daidai nan kuma Haisam ya taho da gudu,da sauri Officer din daya bude Gate yayi tsalle sai gashi a gefe guda,gaba d'aya ya basu daria sosae harda Haisam din wanda ya fice. Hajiya dake zaune a Parlour tana jin k'arar Bike din tasa hannu ta rufe kunnuwanta har saida ya fice kana ta bud'e,girgiza kai tayi a fili tace "Allah Ya Tsare". ________________________________ Fitowa daga cikin dakin Fatuu tayi,kofar d'akin gwaggo ta nufa sarai fa taji abunda gwaggon tace tayi amman saboda jan magana taje kofar d'akin tana cewa "gwaggo gani" daga cikin d'akin gwaggon tace "baki ji mi nace kije kiyi bane? "Eh" taba gwaggon amsa, "Kije cikin kitchen nace garin tuwo na nan cikin roba kiyi sauri ki tankad'e" Juyawa tayi ta nufi kicin d'in wanda ke a gaban dakinta tana ta faman zum6ura baki tana k'unkuni da gani bata son yin tankad'an. Daukko garin tayi ta fito kofar kicin din ta aje robar da karfi duk don jan magana,ta koma ta daukko tray din silver da rariya shima ta sake shi k'asan yayi k'ara sosae,daga cikin daki gwaggo tace"A'ah Fatuu lafian ki kuwa? Cikin turo baki tace"fad'uwa yayi" gwaggo tace "Yi maza ki gama to", Zaunawa tayi k'asa dirshan ta fara yin tankad'an fuska daure,fitowa gwaggo tayi don ta fara had'a wutar yin tuwon a bakin k'ofa ta tsaya cak tana karema Fatuu kallo wadda duk tayi dama dama da gari har a kumatun ta,gashi duk ta zuzzubar a k'asa,karasowa inda take gwaggo tayi tace "Yanzu don Allah garin ne kika yima haka,kuma miya kai gari har a fuska?Shiru Fatun tayi sai faman d'aure fuska take,"ba da ke nike bane? Sannan tace"Ni fa bamma san ya zuba ba" "To mi akai miki kike ta faman d'aure fuska,hala tankad'en ne baki son yi? "A'ah" tace sannan taci gaba da magana tana turo baki "kema ce gwaggo wllh....sai kuma tayi shiru, "Nima ce mi? Gwaggo ta tambaya tana kallon ta da mamakin jin tace itace to ita mi tayi kuma. "Sai kiyi ta faman yi mana tuwo,sai kin kashe mu dashi" hannu gwaggo tasa ta rike baki alamar mamaki tace"Ni din ce zan kashe ku da tuwo,har da yaushe yaushe nake yin tuwon da zai kashe ku, Amman wllh fatuu baki da godiar Allah sam,ko yau da rana ba shinkafa da wake nayi maku ba?" "To ai baki yin shinkafar ne muci ta har dare sai ki tayin tuwo da daren,kuma wani lokacin ma har da safe sai kice wai shi za'a ci" tayi maganar tana ta turo baki. "To bazan yi shinkafar har daren ba tunda bake ke nemo man kudin shinkafar ba,iya fitina kawai da asara kika iya siyo man,inma baya ga sharrinki ba sai ina nan da yamman nike samun yin tuwon ba,Kuma in bama samun wuri ba acan k'auyen naku ba tuwon kuke ci ba rana da dare wani lokacin har a d'umama da safen gwarama ni,in anci da safe ana had'awa da wani abun,ko ke ai sai kin gadama kike ci da safen ko" tana ta magana har ta shiga cikin kicin ta fito da murhu ta nufi can bangaren d'akinta wani dan fili ne anyi rabin katanga ba'a ida ba akwae keji da yan kaji a ciki ta aje murhun ta fara d'aukko itace daga gefen cage din tana sawa acikin murhun, "Wallahi mu bama yin tuwo rana da dare,wannan ai sai su Yaaya dasu Altine,mu fa kinsan yan gayu ne a gidan,don mu har shayi da biredi muke sha,kuma ana mana shinkafa da miya har da naman zabbi ehe" Ta karasa maganar tana murgud'a baki don tasan gwaggon ba ganinta take ba, Daga inda gwaggo take tana kok'arin daura tukunya saman murhu tace "Ai sai ki tattara ki koma can din kici gaba da shan shayi da shinkafar tunda ni nan kashe ki zan da tuwo" da d'an fada fada tayi maganar,itakam fatuu sai ta kyalkyace da daria tace "Ai ko na tafi sai kinje kin dawo dani,don nasan baki iya zama ba tare dani ba" Girgiza kai kawai gwaggo tayi,don tasan inta biye mata haka zatai ta mata surutan banza da wofi "In kin gama kije ki wanke man tsakin kuma ki sauri", "To" fatun tace tana kokarin mik'ewa,don taga kaman ran gwaggon ya 6aci ta kuma sani sarai mi zai iya biyo baya,Wanke tsakin take yi a wurin da ake wanke wanke ta fara magana"Gwaggo fushi kika yi? ta6e baki tayi tace"Uhm,inyi fushi dake ince nayi fushi da wa,ai da mai cikakken hankali ake fushi...."da sauri Fatuu tace "Wayyo gwaggo ni d'in ce banda cikakken hankali,wllh inada hankali na" ta k'arasa maganar tana ta turo baki, Wai nikam ina Amadu ya shige ne,tun d'azun banji d'uriyarsa ba ko da na lek'a nemanki naga kes dinsa a rufe" fatuu tace"Nima dana fita a rufe yake kuma har na dawo yana rufen", "To ko ina ya shige,Allah yasa l..." gwaggo bata k'arasa maganar ba suka ji ana bud'e d'akin da ke cikin zaure,da sauri fatuu tace"To gama shi nan ya dawo,"KAWU AMADU,KAWU AMADU..." ta fara kwala masa kira,Wani matashin saurayi ne mai d'an tsawo fari kaman gwaggon sai dai yanayin rashin hutu yasa farin nasa yin kala kala,Shigowa yayi yana amsa kiran da fatu ke masa shima da karfi "Na'aaamm" yace "wannan kira haka Hajia fatuu..."da sauri tace "Maman ka keta neman ka bani ba" tayi maganar tana nuna masa gwaggo wadda ta fito daga inda take yin girkin tuwon tana girgiza kai jin maganar da fatuu tayi,kallon sa tayi da murmushi tace"Ina ka shige ne wai Amadu? Yace "Wllh naje wani wuri ne daga nan na biya kasuwa don akwae abubuwan da suka k'are ana ta nema,lafia dai ko?" ya tambaya,"Eh lafia lau,dama maggi nike so namu na nan ya kare," yace"To" ita kuwa fatuu cewa tayi"Kashh dama baka dawo ba" da sauri suka juya su duka suna kallonta da mamaki ya tambaye ta"Saboda me? tace "Inda baka dawo ba har aka gama tuwon dole abar ni ai inyi kwad'o da mai da yaji tunda ba magin miya" ta k'arasa maganar tana gyad'a kai,Gwaggo ce tace"kar ka biye mata,kaje ka bud'e shagon,tun dazun take shashancin da ta saba,tuwon ne bata so,kuma sai nayi,sai dai mutum kar yaci,ta juya ta koma wurin girkin. Amadu ya kad'a kai zai fita a hanya yake fad'in"Lallai yarinya tuwo ai saiti ne,sai da shi mutum zai ji shi gam gam,adaidai nan ya fice,ta6e baki Fatuu tayi kasa kasa tace"dama ai bakin ku d'aya uwa da d'a,kun daukko ni zaku kashe ni" Gwaggo ce ta katseta"Wai nikam har yau tsakin bai wanku bane? "Ya wankuuu" fatuu ta fad'i da karfi,"To ki kawo man mana da ruwan, kije ki kar6o magin kuma" tace "to, Magin taje ta amso sai da ta rabo shi da biscuit wai yunwa take ji kafin ta kawo magin tace "Gwaggo wai miyasa baki yin tuwon a kan d'an gas dinmu,kinfi son kiyi ta wahalar hura icce ne? "Gas d'in ne yayi kasa,kuma dai ni nafi son yin tuwo kan murhu yafi dahuwa" gwaggo ta bata amsa,"To ki kawo ni inyi miyar asaman gas din" fatuu ta fad'a, "Niba in baki yin miyar ba,k'arshe kije kiyi ma mutane shirme" "Wallahi bazanyi ba" Fatuu ta fad'a,gwaggon tace"aifa dayake ke kike son yi dole ki fad'i hakan,da hakanan ne nace kiyi man abu sai kin gama 6ata man rai sannan, Taci gaba"sau nawa na baki kikai man ba daidai ba,kawae don inason ki iya girkin ne nike sake baki,don kar inyi maki aure baki iya ba..."Wata irin juyowa Fatuu tayi tana ma gwaggo dake talga tuwo wani irin kallo tace"Aure! Wa za'ai ma auren? "ke mana,nan da d'an lokaci kadan mi za'a jira" gwaggo ta bata amsa,da sauri tace"Wallahi ba wanda zai man aure har sai nazama Doctor ehee" Gwaggo ta juyo tana kallonta tace"Likitoci ai nutsattsu ne,a hakan ne zaki zama wata doctor,kece kullum rigima da yaran unguwa ga rashin nutsuwa wurin wauta kuwa kece lamba ta d'aya" "Amman dai ai inada kokari a Makaranta,kuma Malaminmu yace in kana da kokari komae kake son zama zaka zama," gwaggo tace"to nidai ina gaya maki muddin kina son ki zama likita sai kin daina rashin jin magana ki natsu don nidai duk likitocin da nike gani masu natsuwa ne,kije ki daukko kayan miyan in nuna maki wanda zaki jajjagan in kinga dama",Juyawa tayi ta nufi kicin da k'arfi tace"To Kakus zan natsu,amman duk wanda ya raina min wayo bazan yarda ba eheee"daga haka ta shige cikin kitchen din. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *BY OUMMU IMAM📱* *Paid Book* *Free Page8️⃣* Officer Civil D,ne ya dawo saman benci ya zauna bayan ya rufe gate d'in har lokacin suna dariyar abunda ya faru lokacin da Haisam ya fice,ya kalli Abokin aikin nasa yace "kasan mi? Officer P yace "A'a" Officer CD yace "Wallahi tunda nike ban ta6a ganin mutumin da ke burgeni sosai ba irin mutumin can Haisam,"Mike burgeka a tattare dashi ne? ya tambaya, "gaba d'aya lifestyle din shi,kai wallahi ba don ance mutum tara ne bai cika goma ba da nace shi din ya cika goma cib,ga kyau,ga ilimi,uwa uba kuma ga kud'i,ga iya daukar wanka malam ko a mata sai anyi dogon bincike za'a samu kamarsa he's a very handsome and classy guy, da kuwa za'a bada kyautar wanda yafi kowa tsafta a Nigeria to wllh ba wanda ya dace sai shi,Daria Officer P,ke yi sosae ganin yadda Abokin nasa ya dage sai faman bayani yake,yace "Kai dai shi ka sani ne shiyasa kake ganin hakan, duk da dai duk abunda ka fad'a game dashi ba k'arya kayi ba gaskia,Amman ni kasan mi ma ya burgeni da shi sosae? Da sauri d'ayan yace "Sai ka fad'a..." yaci gaba "Rashin girman kansa,a fuska idan ka ganshi lokaci guda zaka yanke mashi hukuncin yana da girman kai,sai kayi mu'amala dashi zaka fahimci yana da saukin kai,ji fa ranar nan yadda yazo ya zauna nan muna yin fira har d'an sa baki ya rink'a yi,duk da ba wani dad'ewa yayi ba wallahi nayi mugun mamakin hakan don ban ta6a zaton hakan b,su kam dai sunji dad'i wllh,itama hajia badai kirki ba, Officer CD, yace"Wallahi kam ai wasu mutanen are very lucky,kaga kaman su suka tsarawa kansu rayuwa"cikin tsananin daria d'ayan yace "kai baka cikin su ne? "Uhm inda ina cikinsu ai baka ganni nan kullum tsugunna bakin gate ba,in za'a shiga in bud'e,in aka fito in rufe....d'ayan yace "A dai rik'a gode ma Allah,don shi gwanin hikima ne daga haka sai kaga ka kai inda baka ta6a mafarkin kaiwa ba,duk rayuwar da ya za6a ma bawa ita ta dace dashi,in ka kasance mai gode masa sai ya kara inganta maka...da sauri Officer CD ya katse shi da cewa "Wannan gaskia ne,Alhamdulillahi ala kulli halin,ya cigaba"yauwa nikam inata son intambaye ka..."Officer P yace "game da me fa?" yace "wai mike tsakaninka da Saude ne? Wani irin kallo yayi masa yace"Wace Saude? d'an harararsa yayi yace "ni zaka ma duniyanci kace baka san wace Saude nike magana akai ba" daria Officer P yayi yace "Oh wai ko Saude ta nan gidan kake nufi,to ni mike tsakanina da ita banda alakar wurin Aiki daya da muka hada" ya k'arasa maganar yanata daria,Officer CD yace"don kun had'a wurin Aiki d'aya shiyasa take baka kulawa ta musamman kenan" daria sosae yake yace "ni banga wata kulawa ta musamman da take bani ba kawae dai Sharri zaka man,in don Abinci da take kawowa wannan ai mu duka take kawo mawa,kuma da izinin masu gidan" ta6e baki yayi yace "Uhm kaji nayi maganar Abinci,kuma ko a Abincin ma ai akwae ayar tambaya don ba iya Abinci take kawo ma ba duk wani kayan kwalam da makwalashe da akaci aciki sai ta kawo maka,rannan fa ina ji tana tambayarka wae mi kake so a dafa,ni mamaki ma yasa na kasa yima magana a lokacin" daria sosae Officer P yake yace "nidai ba abunda ke tsakanina da ita,ka rufa man Asiri kada Matata taji kasa a hanamun kwanciyar hankali" ta6e baki yayi yace "in tayi wari maji ai" Yace "ba abunda zai yi wari bare har kaji. Daukar takalman da Haisam ya cire T.k yayi ya koma cikin parking space din ya k'arasa goge motar,sannan ya nufi part d'in sa don kai takalmin ya kuma gyara masa dakin,a ka'ida dama indai Haisam din ya shiga part din bayan ya fita sai an shiga an gyara masa,kuma t.k ne mai gyarawa.Yana shiga ya aje takalman a gefen kofa ya nufi saman kujera L-shape ya zauna ya d'aura kafa daya kan daya ya wani sha murr,can ya kece da dariya a fili yace "yasin dole ake ganin masu kudi kaman suna da girman kai,yo mutum na kwana yana tashi cikin wannan daular ai dole aga yana fad'in rai koda shi ba haka bane a wurinshi....haka t.k yayi ta sokana dama ya saba duk yazo gyaran sai yagama shiririta kafin yayi abunda ya kawo shi,don yana da tabbacin ba CCTV a cikin parlon sai a waje. Mikewa yayi yana fadin"to mima zan gyara anan,ba abunda parlon yayi" Bedroom ya nufa nan ma dai tsaf yake,kwalaben turaren da Haisam yayi amfani dasu ya maida ya jera su,ya dau Bathrobe din daya aje gefen gado ya maida ita cikin laundry ya shanya,ya shiga cikin toilet din wanda yake Had'addan gaske ne mai matsakaicin girma,irin toilet din daya amsa sunan Toilet din yan gayu,komae na cikinsa fari ne tun daga kan,bathtub,toiletseat,washbasin,shower curtains,bathroom cabinet,soap dispenser,hatta tiles d'in dake a k'asa da kuma bangon toilet din fari ne kal sai yan abubuwa k'alilan ne Silver kaman su Mixer tap,detachable shelves,abun saka tissue wato Toilet roll holder,da Towel rack wanda ke dauke da fararen towels k'arami da babba rataye a saman shi,sai salk'i kewayen yake yi yana daukan ido,tamkar ba'a amfani dashi,tsaye t.k yayi yana tunanin to mima zai ma toilet din? d'igo-digon ruwan da Haisam yayi wanka ne kawae a k'asa shima ba wani mai yawa ba don akwae bath mat a gaban bathtub din wadda ke absorbing ruwa in an fito daga cikin kwamin, itama fara ce sol,ka'ida ya fito daga kwamin wankan sai ya fara taka ta kafin ya taka tiles d'in kasan don bayan tsane ruwa tana preventing zamewa. Detachable shelves t.k ya nufa wadda ke like a sama d'auke da toilet cleaning items,ya ciro safar roba yasa kafin ya daukko liquid cleaner da scrub sponge komawa yayi gaban bathtub ya d'iddiga liquid cleaner din ya wanke,bayan ya gama ya maida robar cleaner din ya daukko disinfectant spray ya fesa a saman tiles din kasa yasa mop ya goge fess,ya ciro karamin towel dake sagale a jikin rack ya goge bathtub din da ya wanke,ya dawo ba ko digon ruwa jikinsa,ya juya ya bud'e seat shima dai fess yake ba wani dirty illa ruwan cikinsa da kalarsu take blue kaman ruwan swimming pool hakan kuma ya faru ne sakamakon cleaner tablet da t.k ya saka ciki lokacin daya gyara part din da safe,hakan na nufin ba'ai amfani da seat din bama,flushing yayi har saida ruwan suka koma fari kal sannan ya rufe,ya yago wipe daga cikin wipe dispenser dake manne a gefen seat din ya goge jikin seat din dan damshin jikin wipe din yasa nan da nan seat din ya rinka wani irin sheki gwanin burgewa,ya jefa wipe din da safar hannunsa a cikin farin wastebin dake a bayan kofan toilet din,har zai fita sai kuma ya hango cabinet a bude,komawa yayi ya duba ciki ko akwae abunda ke bukatan gyara,su toothpaste brushes,sabulai,da turarurrukan wanka ne shake a cikinta,ganin komae a jere lpy lau yasa ya rufe ta ya juya ya fice hannunsa rike Mop da yai amfani ya maido ta cikin laundry ya aje. Washing machine ya nufa ya bude,ba wasu kaya aciki sai underwears din da Haisam ya cire dazun,juyawa yayi ya duba cikin cabinet din laundryn ko akwae wasu kayan daudan pajamas kala daya ne da Haisam ya cire da safe,ya daukko su ya saka cikin machine din,a ranshi yace "bari da safe in ya cire wasu sai in hada in wanke"ya rufe,dan karamin farin towel mai laushin gaske ya dauka ya koma bedroom din ya goge furniture din ciki wadanda dama suke ta kyalli,bayan ya gama ya fita parlour desk kawae ya goge sai ya dan tattara bakin kofan shigowa ya dau takalman daya aje na Haisam da floor wiper da dan towel din da yayi Amfani ya maida kowanne wurin da ake aje shi,ya dawo parlon hannunshi rike da Air freshner ya feshe parlon wanda dama yake ta sakin k'amshi mai sanyin dadi,maida freshner d'in yayi ya dawo cikin parlon sai da ya bud'e fridge ya dau lemo Fanta ya bud'e yana sha daga haka ya fice bayan ya jawo kopan ta rufe. T.k,yaron gidan Hajia ne,tun yana d'an karami,Almajiranci aka kawo sa daga wani kauye dake a k'aramar hukumar birnin magaji jahar Zamfara,ta sanadiyar wani dan garinsu Isiyaku wanda ada shine ke Aiki a gidan,to sukan je tare da t.k yana kama masa suna yin shara,da goge gogen motoci sai Aike in Hajia na bukatan wani abu,daga baya isiyaku ya sanarma Hajia cewa zai koma gida don zasu tafi da yayansa neman kudi lagos,Hajia ta bashi shawaran ya tsaya zata sa shi a makaranta yafi tafiya neman kudin nan,amman yaki tsayawa don ba son karatun yake ba,to a lokacin ne t.k ya ce ma Hajia shi ya rika zuwa yana yi mata Aikin? Hajia na Murmushi tace "d'an malam ai harabar gidan nan tayi maka girma baka iya share ta...da sauri t.k yace "da kwarankwatsa zan iya,a gonar babanmu kunya goma nake nomewa kuma wani lokacin har in kara" Hajia taita yin daria jin zancen shi tace "ya sunanka? Yace"Tukur Halliru,ta amince ya cigaba da yin Aikin amman tana shakkun in zai iya don lokacin baifi shekara 11 ba. Aikuwa t.k yaba hajia mamaki don sosae yake yin aikin ba wani kuskure,gashi akwae ladabi,daya ci ya koshi to fa ba zama Aiki kawae ko ba'ace yayi abu ba yaga ya dace yi yake,a lokacin hankalinsa da karfinsa sun girmi shekarunsa,nan da nan ya shiga ran Hajia tasa shi makaranta ya fara daga primary 4 don ya fad'a mata a garinsu ya fara karatun kafin aka kawo sa karatun Allo,sosae t.k yake fahimtar karatu don lokacin ya dawo gaba daya gidan Hajia da zama tasa shi a wata makarantar Allo dake nan cikin unguwa amman kafin ta aikata hakan sai da taje da kanta har makarantarsu ta sanar da Malaminsu niyyarta ta bukaci ya bata number din baban t.k,aka kuma ci sa'a baban nada waya lokacin ta kira babanshi sosae ta fahimtar dashi tace in yana son karin bayani game da ita ya tambayi Isiyaku,ta ba t.k wayan ya k'ara yimasa bayanin Isiyakun da take nufi,Sosae baban t.k yaji dadi don kafin ta kira sa malaminsu t.k din ya kirasa yayi masa bayanin abun Arzikin data kaima makarantarsu,na kayan abinci,omo da sabulai,da takalma silifas,harda kudi masu yawa tace a rarrabawa Almajirai. Cike da zumud'i malam halliru ke sanarma matansa guda ukku abun Arzikin daya samu t.k,mahaifiyar t.k wadda itace ta karshe cikin matan tayi tsananin farinciki yayin da sauran kuma bakin ciki ne ya turnike zuciyoyinsu,dama sun takura ma mahaifiyar t.k don suna ganin mijin yafi ji da ita,don uban gidansa ya bashi auran ta,kullum suyi tayi mata gori suna cemata yar sadaka,ladan noma,ita dae bata biye su don hakuri ne da ita. Malam halliru yaso barin t.k yayi karatun boko don wani malaminsu t.k d'in lokacin har gida yazo ya roki uban daya bar yaron yayi karatu mai zurfi don yana da kokari,amman sauran matan suka tada balae wai sam basu yarda ba yadda aka tura yaransu sukaje suka yi karatun Allo,to dole shima t.k din yaje,ba yadda bai ba ya fahimtar dasu hakan k'aruwarsu ce gaba daya,amman firr suka ki amincewa don bakin ciki,ba k'aramin tashin hankali ya fuskanta ba,ba yadda ya iya haka ya turasa,mahaifiyarsa Hasiya nata kuka,don ta so yayi karatun,dayake Allah hakimun ne sai gashi tafiyar tasa ta zame masu Alkhairi,rabo kuma ya rantse,Malam halliru ba k'aramin girgiza yayi ba lokacin daya kaima t.k ziyara,ganin cikin daular da d'an nashi yake,bada niyyar kwana yaje ba,amman hajia ta matsa ya kwana,da zai tafi ta hada masa sha tara ta Arziki harda Atamfofi ya kaima matansa. Zaune malam halliru yayi a tsakan gida yana basu labarin irin Arzikin da t.k yake ciki,ya sanar masu mahaifiyar sanata ce yake wurinta kuma matar tsohon ministan tsaro Gen.Adamu zakee,kaman yadda t.k ya fad'a masa,murna wurin Hasiya kam ba'a magana,sai ma da t.k din yazo da Sallah,har gida aka rinka zuwa ganin tukur dan gidan sanata,haka mutanen gari ke fada. Private school hajiya tasa shi yayi secondary,bayan ya gama kuma ya tafi Polytechnic dake nan katsina inda yanzu ya shiga ND2 yana karantar SLT,ba faman da Hajia bata yi dashi ba akan aikin da yake ba kaman wankinta da ya hana kaiwar da ake dry cleaning shike wanke mata su fess ya goge a cewarsa baiga abun wahala ba abunda da injin ake yin wankin,Manyan abubuwa irinsu barguna,labulaye da carpet kawae ake kaiwa wurin wanki. Lokacin da Haisam ya dawo hajiya tace ma tk ya samo wanda zai rink'a gyara masa part dinsa acikin abokansa yan makarantar allon su dake kawo masa ziyara akai akai,nan ma cewa yayi shi duk zaiyi ai ba wani aiki ne mai wahala ba,kuma dama yana bala'en son Haisam,ba k'aramin burgesa yake ba,shiyasa in yana gyara masa part din nasa cike da himma yake aikin,ba algus don dama shi tun yana k'arami aikinsa ba ha'inci,shiyasa in ya dage shi zaiyi abu sai hajia ta kyalesa don tasan zai iya din,kuma ba'a ganin ba daidai ba wani lokacin takan tsokane shi tace "na manta jikan nawa fa kakkarfa ne don tun yana karami kunya goma yake nomewa" sukan yi dariya atare, Shikam t.k duk yana yin hakanne don hud'ubar da mahaifiyarsa ke masa duk in yaje ganin gida,takan ce ba abunda zamu iya saka masu dashi,haka zakaga ana zuwa gaida t.k in yaje tamkar shine Senator din,iyaye har tura yaransu yanmata suke wae ko zai taya,basu san t.k ya wuce ajinsu ba sai yar birni,in ya tashi dawowa haka mahaifiyarsa zata bashi,su kuka,kubewa,daudawa,barkono da sauran su ya kawo ma hajiyar,mahaifinsa da har hatsi yake bashi ya kawo,Hajiar ta hana tace iya su kayan miyan ya isa ta gode. Wannan kenan game da Tukur Halliru Birnin magaji,wanda tuni yazama dan gida a gidan Hajiyar sanata don har Senator Ali Adamu zakee yasan da zamansa. A next page zamu fara nitsawa cikin labarin In shaa Allah,aci gaba da share pls. Thanks as u do so🤝🥰 *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *BY OUMMU IMAM📱* *Paid Book* *Free Page9️⃣&🔟* Washe gari juma'a,daga cikin d'aki gwaggo ke magana"Wai fatuu bazaki fito ki tafi ba sai kin makara,kuma a buge ki kizo kina cewa malami kaza ya tsaneki ko" fitowa fatuu tayi sanye da uniform din makaranta hannun ta d'aya dauke da jaka School Bag dayan kuma takalma ne Sandals na roba,a k'arkashin hammatarta ta sak'a jakar ta duk'a tana kokarin sa sandals din saidai igiyan tak'i sawuwa sai faman kici kici take yi dashi a fili tace"Wannan shegen takalmin ni wallahi na gaji dashi" haushi taji ta buga shi da k'arfi a k'asa tace banzan takalmi yaki sanyuwa. Duk maganganun da take a kunnan gwaggo,fitowa tayi ta tsaya a bakin k'ofa hannunta d'aya dafe jikin bango tana kallon Fatun sai kiciniya take. "To taya zai sanyu kin kasa natsuwa kisa shi sosae,ji bi yadda kika wani takure kin cusa jaka a hammata,d'agowa tayi tace"to yaya zanyi" fuska a tur6une da alama takalmin ya k'ule ta, "Ki aje jakar mana a gefe,ki zauna sosai kisa" Aje jakar tayi ta dan zauna a bakin k'ofa kamar yadda gwaggon tace,aikuwa sai gashi takalmin ya sanyu ba wani 6ata lokaci,da sauri fatuu ta d'ago ta kalli gwaggo tana daria tace "Kinga d'an banza ya sanyu kuwa" gwaggo ta dan ta6e baki"Uhm ba wani d'an banza,dama ba ki yadda ya kamata ya sanyun bane,ace komi mutum zai yi bazai sa natsuwa ba, Mik'ewa fatuu tayi tana kokarin goya yar jakar goyon a bayanta tace"zan tafi" gwaggo tace"To adawo lpy,Allah ya tsare" wani irin kallo fatuu tayi mata tace adawo lafia kuma? Gwaggo tace"Eh mana ko baki son Addu'ar ne?, "A'a ina so mana amman ai banji bayani ba" tayi maganar tana yi ma gwaggo alamar kud'i da hannuwanta,gwaggo tace"wai don Allah ba ranar da zaki ce yau dai gwaggo kibar kudin ki ne? Da sauri fatuu tace "iyeee,to kuma dami zan hau mota kuma inyi break,in baki bani ba? Gwaggo tace "to acici baki da magana dama sai ta abinci,a duk satin duniya sai kin cinye mani naira d'ari biyar wani satin ma sai sun fi haka tunda sai ki dawo kice man baki samu bus ba kin ranci kudi kinyi ciko kin hau Napep ko mashin", Fatuu da ke tsaye ta k'agara gwaggo ta sallameta ko ta tafi tace"Don Allah gwaggo kiban,taya karatun zai yiwu da yunwa to ko mota dai ai sai an zuba mata mai take aiki ko" yar daria gwaggo tayi, fatun tace "yau baki zuwa aikin ne? "Zanje,amman sai da rana", Fatuu tace"kenan zan dawo in iske ki? Gwaggo tace "Anya kuwa kinsan yau juma'a,da wuri zan tafi,wurin k'arfe d'aya haka", "to ammn dai zaki yi mana abinci ko ba sai na dawo ba inyi"tayi maganar da sigar shagwa6a" gwaggo ta rike baki tace"Ah kajita ko da yaushe-da yaushe nike tafiya in bar mata wani yin abinci,ai sai dai in ina aikin safe ne kuma shima kusan tare muke dawowa,kamar wadda ta iya wani abincin arziki", Fatuu tace "ai dai ina yi kuma ki ci har kice yayi dad'i" daria gwaggo take tace"Mai karya.....fatu tace"d'an Aljanna,tana daria,"gwaggo kiban don Allah" mik'o mata naira d'ari tayi wadda ke cikin hannun da ta dafa bango dashi,da sauri fatuu ta amsa tace"daman kudin na a hannun ki,amman sai kinja man rai,juyawa tayi ta fara tafia,sannan tace "Kar ki damu kakus,zan biya ki duka kud'aden da kika kashe man in nazama Doctor" har lokacin gwaggo daria take ta girgiza kai tace"nadai fad'a maki ai natsattsu ne ke zama likitoci,in baki natsu ba,ba wata Doctorn da zaki zama" da d'an karfi tace"Insha Allahu zan zama harna rik'a yima ki Allura ma,na tafi" ta karasa fada yayin da ta kusa isa zaure. Gwaggo tace" To Allah ya tsare adawo lafia ban.......,Fatuu dake cikin zaure ta k'arasa abunda gwaggon zata fadi da karfi"BANDA RIGIMA DON ALLAH FATUU" daga haka ta fice daga gidan,girgiza kai gwaggo tayi tana ta daria tace" Shiryayya,a haka ko nace d'in wani lokacin kafin ta shigo gidan an kawo man k'ararta,Allah dai ya shirya"daga haka ta koma cikin d'aki. Tafiya fatuu take ta raba hanya biyu,sam ba natsuwa a tafiyar,hanyar shiru dayake safiya ce sai yara jefi jefi yan tafiya makaranta kamar dai ita,sai wani cilla k'afa take kamar zata tashi wai ita nan sauri take,Horn d'in da akai da k'arfi ne a bayanta yasa tayi saurin komawa gefe,sannan ta juyo tana kallon motar da ta taho,Peugeot ce 406,Maroon color,cikin ranta tace"dama mai motar nan ya rage man han....bata k'arasa ba sakamakon mutumin data ga ya wuce fuuu a cikin motar bai ko kalleta ba,da sauri fatuu ta zaro ido had'i da rike ha6arta tace"Kai! Wancan ai mutumin nan ne na jiya mai kama da Aljani,ba dai a layin nan yake ba? ta karasa maganar da sigar tunani harda d'an waigawa baya,tace"Uhm inma nan din yake,shi dai ya sani" taci gaba da tafiya har tazo wata kwana d'an nesa da gidansu,tana karya kwanar ta tsaya da alamun mamaki a fili tace"lallai ma wannan haulatun,har yanzu bata fito ba,tana nufin in bita har cikin gida kenan" kwafa tayi sannan taci gaba da tafia,ad'an gaba kadan daidai wani gida inda yaro ya fito dauke da d'an bokitin plastic ta tsaya tace ma yaron "Kai haulatu na nan ciki" yaron yace "Eh naganta tazo ta karbi koko a rumfar da Innarsu ke saidawa" ya wuce,ita kuma fatuu ta kad'a kai ta shige cikin gidan wanda gaba daya k'asan gidan kasa ce,sai daga can gaban dakuna ne akai ma k'asan shafen siminti shima duk ya farfashe,a gefe guda wata mata ce cikin wata yar baranda da yara tsaitsaye tana zuba masu koko,matsawa fatuu tayi bakin barandar tace "Innarsu Haulatu ina kwana" da washe baki ta amsa"lafia lau fatee yan makaranta,haulatun na ciki" kad'a kai fatu tayi ciki,tana hawa saman simintin wata yarinya ta lek'o tana daria,wankan tarwad'a ce tana da kyau ba laifi,hannunta d'aya rike da hijabin Uniform dinta dayan kuma kofi ne tana shan koko,tsayawa fatuu tayi tana harararta,fuska daure tace"Ashe ma baki shirya ba don wulakanci kika sa inata sauri" haulatun wadda keta faman daria tace"wallahi markad'e innarmu ta aikan kuma sai na iske layi,amman ai na shirya hijab kawai zansa da Sandals",da yar tsawa fatuu tace "Da Allah to kisa mu tafi,salon sai mun makara wannan banzan displine d'in ya bugi mutane, daman ya tsane ni" ta k'arasa tana murgud'a baki, Haulatu tace"bafa kyau zagin malami fat...." ta katseta"naji,wayace ya tsane ni"fatuu ta haulatu tace"bafa tsanarki yayi ba,kece kike ja ai yana dukan ki,ni kinga yana duka na?" ta kai maganar tana kurbar koko,"dalla ki fito mutafi ko inyi tafiya ta wallahi,daman ke ai baki ganin laifin kowa sai nawa"da alamar ranta ya 6aci, Haulat tace"Haba kawata daga fad'ar gaskia...." "to ki rik'e gaskiyar banso" inji fatuu,mik'o ma fatuu kofin kokon haulat tayi tace ida shanye wa",harararta Fatuu tayi da sauri tace "Wa!Ni zan sha wani koko,kokon ma sauran ki,Allah ya kiyaye,ta tofar da miyau gefe" girgiza kai haulat tayi da d'an murmushi ta idasa fitowa,aje kofin tayi a k'asa ta sanya hijab din da Sandals din dake aje bakin kofar d'akin,ta d'auki jakar ta,ta leda irin ta biki tace"Mu tafi" atare suka nufi hanyar fita,haulat ta shiga rumfar da innarta take,ta ajiye kofin data sha koko tace ma Innar "zan tafi" kud'i innar ta miko mata naira sittin tace"A dawo lpy" Allah yasa" haulat tace ta nufi hanyar k'ofar gida,don ita fatuu tuni ta fuce. A kan hanyarsu ta zuwa bakin titi inda zasu hau Bus fatuu sai faman masifa take ma haulat tana cewa ai in suka rasa Bus itace a matsala don tasan bata da isassun kud'in da zata hau Napep ko mashin,baiwar Allah haulatun ita dai tayi shiru tana sauraranta da alama tana da hakuri,gashi da gani ta girmi fatun ko a yanayin jiki tafi fatuu tsawo a sanyaye tace"Insha Allahu ma zamu samu,in kuma ba'a samun ba sai in dawo ba wani abu,in Allah ya kaimu Monday naje"daga haka ba wanda ya kara cewa wani abu. Suna isowa bakin hanyar kuwa sai ga Bus din da yar fara'a haulat tace "Alhamdulillah",juyowa fatuu tayi tai mata wani kallo fuska a d'aure. Haulatu kawar fatuu ce,tun lokacin da tazo garin,lokacin da gwaggo tasa ta a makaranta har gida taje ta had'a su suyi kawance,don tasan halin haulat yarinya ce mai hakuri da natsuwa,ita kadai ce zata iya jure halin fatun a yaran unguwar,gwaggo ta roki haulat da ta d'auki fatuu a matsayin kanwarta ta rik'a nuna mata abubuwa masu kyau,ta kuma rika hanata maras kyau,gwaggo bata 6oye ma haulat komai ba game da halin fatuu, a gabanta kuma tayi ma fatu fad'a sosai akan ta zauna lpy da haulat ta rik'a jin maganarta,intaji sun yi fad'a tasan itace ta ja,kuma sai ta sa6a mata,Innarsu haulat ta tabbatar ma gwaggo cewa haulat bata da matsala karta damu,dama kuma ana ganin mutuncin Gwaggo a unguwar,Ita kuwa haulat tunda taga fatu taji tayi mata,jininta ya had'u da ita,tace ma gwaggo zata kula da ita insha Allahu,A haka kawancen su ya k'ullu,duk da ance wai sai hali yazo d'aya ake abota,to nan dai halin sam bai zo daya ba,dama kuma sai ansamu bambanci abota ke lasting,misali,daya mai wayo daya mara wayo ko daya mara hakuri daya kuma mai hakuri kaman su kenan,Amman duk da hakurin Haulat wani lokacin sai fatu ta k'ule ta har tayi fushi,sai kuma ta dawo taita bata hakuri har sai taga ta hakura,dama ko gwaggonta haka take mata. K'arfe sha biyu da rabi na rana daidai aka tashe su kasantuwar ranar juma'a ce,Haulatu ce tsaye tana ta faman kwala ma Fatuu kira "fatuu ki taho mu tafi kar acika bus d'in kinsan yau Juma'a fa gaba daya ake tashi harda seniors" ita kuwa fatun tana can sai faman bin students take da gudu tana bugun su,wai na bankwana daga yau sai Monday,girgiza kai Haulat take tayi don ta gaji da tsayuwar,sai da ta gama buge bugen ta taho da d'an gudu sai faman nishi take tana daria, jakarta a hannu d'aya, Dafa kafad'ar Haulat tayi da dayan hannun tace muje k'awalliya,juyawa kawai haulat tayi bata ce mata komae ba suka tafi. Abunda haulat ke gudu shi ya faru don kuwa School Bus d'in ta cika dam sai dai su tsaya a tsaye ko su zauna a k'asa,Haulat ta kalli Fatu tace"Kinga abun da kika ja mana ko,da ana tashi muka taho ai da mun samu seat kika tsaya shiririta,yanzu ai sai mu zauna a k'asan" ta k'arasa maganar da dan 6acin rai,fatuu tace"tabb nikam bazan zauna a k'asa ba duk a tattake ni,ga k'asan ma duk k'asar sandals din mutane,"To ya zamuyi,nidai ban iya tsayuwa gaskia da anzo tudu ko wurin yin kwana mutum yayi ta bugewa" inji Haulat, "ki tsaya kika ga ni,sai na samu seat d'in zama" fatuu tayi maganar yayin da take kutsawa cikin Bus d'in,hango wata yar senior section tayi wadda unguwar su d'aya don tare suke hawa Bus a bakin titi,su biyu ne a zaune,a daidai wurin su ta tsaya tace "D'an matsa man in zauna, "Kamarya? Yarinyar ta tambaya,fatuu tace "Ai ku biyu ne kuma har mutum ukku ana zama ko" tayi maganar tana turo baki,"To in mu biyu ne mu tsaranki ne? Fatuu tace "Yo ina ruwan mota da wani tsara ai dai duk makaranta d'aya muke ko" da sauri yarinyar ta nunata da yatsa tace"Ke karki yi man rashin kunya yanzun nan in mari wannan kumatun naki,dama naji ance baki da kunya to ni in kika yiman zane ki zanyi wallahi" da alama itama yarinyar masifaffa ce, cikin harzuka fatuu tace "Ki zane wa,ai ni wallahi nafi k'arfin ki zane ni sai dai mu zane juna,don ba fina k'arfi kikai ba ehee" ta murgud'a mata baki,da sauri yarinyar ta yunk'uro zata mari Fatuu,ita kuma fatun tayi saurin kaucewa....Sauran Students din cikin motar ne suka had'a baki wurin cewa"Kwandasta ana fad'a" da sauri Haulat ta nufi inda fatuu take bata san mike faruwa ba,amman tana jin ance ana fad'a tasan da Fatuu ne,shima kwandastan ya nufo ciki yana fadin"suwa ke mana fad'an? "gasu nan" students suka ce, daidai inda suke ya tsaya yarinyar ta rik'e wuyan hijabin Fatuu itama fatun haka sunyi cirko cirko,cikin daka tsawa Kwandastan yace"ku saki juna!! Kowa ya saki kowa,yaci gaba"miya had'a ku" da sauri yarinyar tace"Wannan yar rainin wayon ce,wai sai mun matsa mata ta zauna,kuma na gaya mata ba wuri amman zata yima mutane rashin kunya sai kace wani ya hanata tazo da wuri..." ta k'arasa maganar tana ta huci ita kuwa Fatuu ta cika famm kaman zata fashe sai hararar yarinyar take,kwandastan ya juya wurin ta yace "Ah kece baki da gaskia,tunda an riga ki sai ki hakura ki zauna a k'asa ko ki tsaya ki rike karfe,In kuma baki iyawa sai ki hakura ki fita kawai,Amman kar wanda ya kara yimana fad'a,in ba haka ba zan kori mutun ne" ya juya ya nufi gaban motar yana jaddada masu abunda yace. Haulat ce ta kama hannun fatuu wadda ta cika fam,tana yima yarinyar wani irin kallo,"Zo mu zauna a k'asan kawai fatuu don Allah ki kyale ta kar a kore mu kin...."da karfi Fatuu ta fuzge hannunta,ita kuwa yarinyar sai faman cika take tana batsewa tana wani yamutsa fuska. Wata student ce yar junior section acan dayan 6angaren motar tace"Fatuu zo ki zauna ga wuri na matsa maki" k'wafa fatun tayi ta duk'a ta dauki jakarta wadda ta yarda lokacin da zata rike hijabin yarinyar da suke fada,ta nufi inda aka matsa mata ta zauna,ita kuwa haulat baiwar Allah wuri ta samu a k'asa ta zauna sam bata iya tsayuwar. Adaidai kan kwanar da aka saba aje yan unguwar Bus din ta tsaya students d'in unguwar suka fara fitowa harda su Fatuu,sannan yarinyar da sukai fad'an itama ta fito tana ta suratai da kawayenta yan senior guda biyu"Yan section d'insu ke tsoronta shiyasa take masu iskanci,ni in yarinya tace zata yi man wallahi maganinta zanyi yadda gobe ko ance taja wani fad'a bazata yi ba,hakanan azo garin mu ana cin arzikin mu kuma ace za'a rik'a yimana iya shegeee" wata cikin kawayen tace"Wai daman ba yar nan garin bace? "Eh yar jahar Adamawa ce,da gani ma acan d'in yar k'auye ce irin yan rugar nan,kinsan dan k'auye daya samu wuri sai iya shege iri iri" k'awayen suka tuntsire da daria,d'aya tace"kai Murja" wadda aka kira da murja tace "Allah kuwa,duk tabi ta Addabi mutane,duk da ba a layin gidansu nike ba,a layin bayansu muke inajin labarin iskancinta,shiyasa a cikin Bus din nan naso in saita mata hankali da kwandastan nan bai zo ba,tasan ni ban tsoronta" duk maganganun da suke a kunnan Fatuu don a bayansu suke kuma da karfi yarinyar ke maganar don Fatun taji, A farkon kwanar gidansu kawayen nata yake,Murja tace "bari in biyo ku inyi fitsari" suka shige tare,tsayawa fatuu tayi wadda kiris ya rage ta fashe don fushi tana kallon gidan da suka shiga,Haulat tayi saurin cewa"Don Allah,mu tafi Fatuu,karki biye mata" tana kokarin janta" k'in tafiya fatun tayi ta cije a wurin haulat taci gaba "In kika tsaya yin fad'a yanzun nan kinsan za'aje a fad'i ma gwaggo gara ki rabu da ita kawai" A hankali Fatun ta juya suka fara tafiya amman ba haka taso b..,can ta tuna ai gwaggon ma ta tafi aiki tunda ta tabbatar mata bazata dawo ta iske ta ba,da sauri Fatuu ta mika ma haulat jakarta tace"Ki tafi man da ita gidan ku,da safe sai kitaho man da ita Islamiyya", "Ina zaki kuma?" haulat ta tambaya fatun tace"Na manta ne gwaggo ta aike ni..." Haulat tace "to mutafi tare man....da sauri Fatu tace"A'a kije kawai ni kad'ai zanje" Haulat ta girgiza kai tace "ba wani aiken ki da akai fad'an dai zaki tsaya ko...?da tsiwa Fatuu tace "Eh d'in fadan zan tsaya ina ruwanki" haulat tace"Don Allah fatuu kiyi hakuri mana" "Inyi hakuri? Kinajin yadda take gaya man maganganun banza zaki wani ce inyi hakuri, to wallahi bazan yi ba" Haulat tace "haba fatuu,Allah fa yana tare da masu hakuri..." "To ni banda hakurinn ehe" Fatuu tace,hannu haulat tasa ta rufe baki, jin abunda Fatun tace. Ganin haka yasa fatuu ci gaba da magana"Ai ba haramun bane in anyi ma mutum abu yaji bai iya yafewa ya rama,ke komai akai sai kice ma mutum yayi wai hakuri shikenan so kike a raina ni,inzama sakarya kamar ki ko" cikin sanyin murya Haulat tace"Ni babu wanda ya raina ni,kinga wani na tsokanata ne? Kuma yin hakuri ba sakarci bane,wani lokacin rashin hakuri ba abunda yake ja ma mutum sai dana sani mara Amfani,gara ma kayi hakurin tunda Allah da kansa yace yana tare da masu hakuri,in kayi hakurin sai kiga ya saka maka ta inda bakai zato ba"daga haka ta mik'a ma Fatu hannu,ta bata jakar,ita kuma ta juya don tasan ba lalle ta iya hanata yin fad'an ba, cikin d'aga murya Fatuu tace "In ma k'ara ta zaki ki kai to gwaggon bata nan tana wajen Aiki" girgiza kai kawai Haulat tayi batare da tace mata komai ba bare ma ta juyo. Wani gida dake kallon jikin gidan da Murja ta shiga nan Fatuu ta shiga ta 6oye a bayan k'aure tana lek'o waje ta tsagar jikin kofar jira kawai take taga fitowarta,Aikuwa bata fi minti biyar ba sai ga murja ta fito tana yarfe hannunta da alama ruwa ne a hannun,da sauri fatuu ta cire hijabinta ta d'aure ta tamau a k'ugu ta k'ara gyara d'aurin kallabinta,sai da ta bari murjar ta wuce kofar gidan data 6uyan ta fito cikin sand'a tamkar mage na shirin kama k'adangare da gudu ta shak'o murja ta baya cikin sa'a ta kada ita k'asa ta fara bugu dama Fatuu badai karfi ba gashi takai mata hari ta baya sai faman bugunta take,tana fad'in "kafin kiyi magani na ni zanyi naki" cikin wahala murja tace "Don Allah kiyi hak.....bugu Fatuu takai mata a baki nan take bakin ya fashe tace "hak'urin uwarki zanyi,badai ni kike ce ma yar kauye ba, aikam zaki ga yar k'auye, Lokaci guda yara suka kewaye su suna kallon fada,yawanci duk d'alibai ne masu dawowa daga makaranta had'i da Almajirai ba wanda yayi yunk'urin raba su don yaran sun san halin Fatuu. Wata mota ce 406 maroon ta shigo cikin lungun,ba kowa bane cikinta face Haisam,a hankali motar ke shigowa har yazo gab da yaran,dole ya tsayar da motar ba tare da ya kashe ta ba,don ba hanyar da zai wuce yara duk sun rufe hanyar,shiru yayi yana tunanin lafia,don bai hangen su fatuu dake fad'an,Horn ya latsa amman sam hankalin yaran na akan fad'an basu ma ji ba bare su bashi hanya,Wani magidanci ne ke k'okarin fito da wani tsohon mashin daga zauren wani gida acan gaban inda ake fad'an,adaidai lokacin da ya fito waje yace"Bismillahi,mun fito da sunan ka ya Allah,ka matso mana da rabon mu na alkhairi kusa Albarkacin wannan rana,bud'e tankin mashin d'in yayi ya d'an girgiza yace "tabb ashe ma ba man,Allah gamu gareka yan canjin da suka rage man su kenan na bada cikin gidan a samu a harhad'a,yanzu kuma anfito za'a neman gashi ba isashshen mai ma a mashin d'in ,kai rayuwar nan tayi tsanani Allah ka dafa mana",daga haka ya maida murfin tankin yana rufewa, A daidai nan kuma Haisam ya k'ara yin Horn mai karar gaske nan da nan yaran suka shiga darewa ya rage sauran su fatuu dake ta faman tumurmusa a k'asa,da sauri mutumin nan ya juyo jin Horn d'in,sai a lokacin ya lura da meke faruwa a hanyar da sauri ya jingine mashin d'in ya nufi wurin masu fad'an da dan gudu gudu don ya samawa mai motan hanya,k'okarin rabasu ya shiga yi saidai sam fatuu tak'i ta rabu da yarinyar,duk abunda ke faruwa kan idon Haisam,yana kallon yadda mutumin keta kokarin 6am6are fatuu daga jikin d'ayar yarinyar amman ya kasa,saboda ta kafe,tak'i ta saki yarinyar,nan take ran Haisam ya 6aci,bud'e motar yayi,da karfi ya maida kofar ya rufe har lokacin motar na akunne,ya tunkari inda suke fad'an,yau ba suit ne a jikinsa ba,riga ce longsleeve shirt maroon color sai wando jeans bak'i ma6allan rigar ma bak'ake ne,takalmansa kuwa daga saman su maroon din fata ce,shimfid'ar takalmin zuwa kasan shi kuma baki ne,sumar sa tasha gyara sai salk'i take ba k'aramin kyau yayi ba, yauma dai da alama Too match din yayi da motarsa wadda take maroon. Yana isa wurin yasa hannu guda ya fizgo Fatuu ya turata gefe guda sai gata a k'asa wanwar,sauran yara suka sa dariya ganin yadda ta wani wuntsila,juyawa yayi ya kalleta,da dogon dan yatsansa ya nunata yace"You Again..!" da ganin yadda yayi maganar ya ganeta ne,da sauri Fatun ta mik'e tana mashi wani irin kallo ta turo baki cike da tsiwa tace "To ina ruwank....bata k'arasa ba ya wanka mata mari ji kake tasss,da tsananin firgici Fatuu ta dafe inda ya mare tan sai faman zare ido take........, *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *BY OUMMU IMAM📲* *Paid Book* *Free Page1️⃣1️⃣* Su kam yara mi zasuyi in ba daria ba suna fad'in yau anyi maganin masifaffa,hakan ba karamin fusata fatuu yayi ba,Tsawa Haisam ya daka masu yace"kowa ya bar nan!" nan da nan kuwa suka kama gabansu banda Fatuu wadda har lokacin tana dafe da kuncinta sai faman hura hanci take tana mashi wani irin kallo mai kama da harara, cikin yar tsawa yace mata"C'mon leave this place kafin in k'ara maki wani" ya nuna mata hanya da yatsansa,daga jin yadda yake magana zaka fahimci ba mai hayaniya bane,A hankali ta fara tafiya tana yi tana waiwayensa har Lokacin kuma bata cire hannunta daga kan kumatun da aka maran ba,da alama taji zafin marin. Juyowa Haisam yayi cike da takaici bayan Fatuu tasha kwana,kallon murja yayi wadda jini ke ta zuba daga hancinta da bakinta tasa hannu ta dafe hancin,jinin har ya 6ata mata brown hijab din ta,ya ma kasa cewa komae sai mutumin nan ne keta faman girgiza kai yace "kai jama'a yanzu ina Amfanin haka,kuna ya'ya mata kunzo tsakiyan hanya kuna fad'a ji yadda aka raunata ki,ina amfanin haka,cikin sheshshekar kuka murja tace "Wallahi ba abunda nayi mata,ni bama bangare d'aya muke ba a makaranta kawai don tace in....bata k'arasa bayanin ba Haisam ya katseta ta hanyar yima mutumin magana don a tunaninsa komai yarinyar zata fad'a game da Fatun gaskia ne, "Don Allah ko za'a samu chemist nan kusa?" ya tambaya fuskarsa sam ba walwala,da sauri mutumin yace"Eh akwae,sai dai yana ad'an can gaba in an fita bakin titi" duba agogon hannunsa yayi kafin ya kalli yarinyar "Muje" yace mata fuska ad'aure, juyawa tayi zata nufi inda motarshi take,da sauri mutumin yace "Yalla6ai in sauri kake ka kawo sai in kaita" d'an dakatawa Haisam yayi yana duban girman mutumin,d'an murmushi mutumin yayi don ya fahimci kallon da yake masa yace "kar kaji komai yalla6ai zan kaita,tunda ga mashin d'ina can ajiye,dama hanyar zan bi,kaga ba sai kasha wahalan komawa ba", Sigh yayi"Ok,nawa ne kake ganin zai isa a duba ta? ya tambaya, Mutumin yace "ai ina ganin dressing ne zasu yi mata,k'ilan su had'a mata da maganin kashe rad'ad'i duka dai nasan bai wuce naira d'ari biyar haka,da Alama mutumin yana da kyan hali duk da halin rashin da yake ciki bai fad'i fin abunda yake tunanin za'a kashe ba,hannu Haisam yasa cikin aljihun jeans dinsa ya ciro wallet maroon mai kyau,kudi ya k'irgo dubu biyu yau ma sabbi fil dasu,ya mika ma mutumin gently yace"Ayi abunda ya dace" da sauri mutumin yasa hannu ya kar6a yana fad'in"to,to.." yana shirin juyawa Haisam ya sake mik'a masa wasu dubu biyun,da d'an zare ido mutumin yake kallon kud'in yace"Yalla6ai su kuma mi za'ai dasu? Cikin girmamawa yake maganar duk da kuwa ya girme masa nesa ba kusa ba,amman girman ya koma kan Haisam tunda shi mai kud'i ne,Allah kai mana Arziki mai Amfani,Amin, "kasa fuel" haisam yace daga haka kuma ya juya,godiya mutumin ya shiga yi yana fad'in"Allah yasa kagama da duniya lafia,Allah ya jikan magabata,Allah yasa kafi haka,ya Albarkaci iyali...." ko a ina iyalin suke. Hannu kawae haisam ya d'aga masa bayan ya nufi inda motarsa take,acikin zuciyarsa kuwa yanata amsa Addu'oin da mutumin yake masa, bud'e motar yayi ya shiga dama a kunne take a hankali ya fara tafiya mutumin nata d'aga masa hannu,horn yayi mashi lokacin da zai wuce shi, juyawa mutumin yayi ya nufi wurin mashin d'in don ya saukko dashi bisa hanya don yana da tabbacin zai kaisu bakin hanyar,sai faman washe baki yake yana godema Allah yanzu yanzu ya gama rok'on Allah da ya matso masa da rabon sa na Alkhairi kusa sai gashi ya samesa a kofar gida Allah kenan,ita kuwa Murja mutumin taso ya kaita don Yan kwanakin nan suna yawan ganinsa ita da kawayenta da safe in zai tafi Aiki,su kuma zasu makaranta,suyi ta santin kyawunshi har Addu'a suke Allah yasa watarana ya rage masu hanya,yau dai ga dama ta samu sai kuma rashin rabo ya gifta. Juya kan motar yayi lokacin da yazo karshen lungun ya hau mik'akkiyar hanyar da zata kaisa har gida,Wata irin k'ara ce ta ziyarci kunnuwansa,A hankali ya d'aga idanuwansa ya kalli Rear view mirror din motar don daga bayansa yaji k'arar,lokaci guda yanayin fuskarsa ya canza zuwa tsananin mamakin abunda idanuwansa ke gani a bayan motar,nan take kuma ya tsaida motar ya bud'e kofar ya fito cikin tsananin mamaki,bayan motar ya nufa ya tsaya yana kallon Glass din bayan wanda yai tartsatsa duk ya tsatstsage wani wurin ma ya 6ule alamun wani abu aka jefo ma glass din,juyawa yayi ya kalli d'an can gefe dashi gaban wani gida,Fatuu ce atsaye ta rik'e kugu ta turo baki tana huci har lokacin hijabinta na d'aure a k'ugunta, kallonta yake ba ko kyaftawa ya had'e girar sama data k'asa,ganin irin kallon da yake mata ne yasata juyawa ta ruga da gudu cikin lungun dake opposite da wanda Haisam din ya fito. Wani bak'in matashin saurayi ne da tunda ya taho daga d'an nesa yaga lokacin da fatun ta jefi bayan motar da dutsi ya karaso wurin,sam ba natsuwa tattare dashi gashin kansa duk yayi cibir cibir yana sanye da kod'addun kaya t-shirt da wando 3-qurter wanda duk ya farfashe,ya d'an sa6ulo ana hangen boxer din ciki la66ansa sun yi baki sosae alamun dai yana shaye shaye,tafa hannuwa ya shiga yi yana salati ganin yadda glass din yayi"La'ilaha illallahu,Muhammadu d'an Abdullahi,tayi tsiyar da ta saba,wannan yarinya anyi yar Akuya wallahi" yayi maganar yana wani ciccije baki irin yadda yan shaye shaye keyi,shidai Haisam still yayi yana ta kallon ikon Allah,matashin ya cigaba"Wallahi Oga haka take bata jin magana ko kad'an eeh duk tabi ta hayyaci mutane tamkar Aljana haka take,toh wallahi Oga ko ni duk iskanci na bazan yi kwatankwacin wannan aika-aikar ba don nasan mizai je ya dawo eehh" ganin yadda Haisam d'in ke masa wani kallo yasa yace "koda yake Oga ba wani iskanci ma nike ba fa,kawai ina nufin yar k'iriniyar mu ta samari" yana maganar yana wani janta, "Amma Oga sam bai kamata ka kyale yarinyar nan ba,inba haka ba zata ci gaba da wannan Akuyancin ne ya kamata kadau k'wakkawaran mataki" nodding kai Haisam yayi alamar to,kawae ya juya don ya gaji da saurararshi, cigaba da magana matashin yayi yana bin bayan Haisam d'in lokacin har ya kama k'ofar motar zai bud'e "Oga in maka kwatancen gidansu ne?" juyowa haisam yayi hannunshi d'aya rike da kofar ya bisa da ido sai da yadau yan seconds yace"Ina jinka" da sauri matashin ya fara magana harda gyara tsayuwa za'ai zuga"Yauwa Oga idan ka mik'e wannan hanyar da zaka bi,ka shiga ciki ina kasan gidan Hajiyar Sanata? Kai Haisam ya d'aga masa alamar "Ehh" ya cigaba"Yauwa to kafin ka kai gidanta ai kasan akwai wata yar kwana da ta raba gidanta da sauran gidajen 6arin tunda ita gidanta kaga tangameme ne yad'an shigo ciki kuma katangar gidanta akwai tsawo....,kowa ya tambaye shi wannan bayanin oho,ya cigaba "to ai gidansu ita waccan Aljanar yarinyar na nan daga shi sai wani sai ita kwanar akwae ma d'an kiyos a gaban gidan,In ma baka gane ba Oga da ka tambayi gidan DIJE ATTENDER,za'a nuna ma da yake awurin kakarta take kuma ita kakar aiki take a asibiti irin masu.....bai k'arasa ba Haisam ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu yace "na gane" yana k'okarin juyawa matashin yace "ko nazo na raka ka ne Oga?" "No Thanks" Haisam yace lokacin kuma ya shige cikin motar,da sauri matashin ya rufe masa kofar yana fad'in "Allah ya tsare Maigida,Sauka lapia maigida" yana d'aga masa hannu kai da gani kud'i yake son ya bashi,shi kam Haisam jan motar yayi yai gaba abunsa don ya fahimci d'an shaye shaye ne, Rik'e kugu saurayin yayi a fili yace"Hakanan a banza na wahalar da kaina ma ashe wurin yi masa kwatance,ko yar asi bazai ban ba,mtsww.." yaja tsaki,kafin ya cigaba"ni har nasa ran zan samu na kayan harka,wasu mutanen dai sun cika mak'o wllh" daga haka ya juya saida ya harbi k'asa irin yaji haushin nan kana yai gaba yana ta wuwwurga k'afa shiga niga,Allah ya shirya. Ko ta kan kwatancan da akai masa bai bi ba,straight gida ya nufa yana karya kwana Officer ya tashi don bud'e masa gate Haisam ya dakatar dashi ta hanyar yi masa horn,juyowa yayi ya nufo wurin motar a hankali ya d'an sauke glass d'in yace ma Officer d'in "I will park it here" daga haka ya maida glass din ya rufe sai daya dan d'auki mintuna kafin ya bud'e kofan ya fito hannunsa d'auke da laptop da charger dinta,Officer yace "You're Welcome Sir" "thanks" Haisam yace kafin ya shige ta k'aramar kofa direct part d'insa ya nufa. Yana shiga palor ya cire takalmansa a gefe saman desk ya nufa ya aje laptop da charger din,ya wuce saman kujera L-shape ya zauna ya jinginar da bayansa had'i da d'age kansa yana facing sama da gani abunda ya faru yake tunani,don makamancin hakan had never happened to him,hasali shi yara ma tsoron sa suke ba abunda ke hadashi da su,shiyasa da yaga fatuu zata yi masa rashin kunya ya mare ta don tun a jiya ya fahimci bata da kunya,shi da har manya ma shakkarsa suke sai gashi yau Fatuu ta aikata masa wannan d'anyen aiki. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* BY OUMMU IMAM *Free Page 12 &13 D'agowa yayi after some minutes yasa hannu gefensa ya d'auki wayarsa wadda ya aje lokacin da zai zauna Contacts ya shiga yayi searching wani suna Iro Mechanic yai dialing kira,bugu biyu aka d'aga speaker ya kunna ya aje wayar a hannun kujeran ya koma ya jingina daga d'ayan bangaren aka fara magana"Assalamu Alaikum" kafin Haisam ya amsa aka cigaba da magana "Allah ya taimaki babban Engineer" amsawa Haisam yayi da fad'in"Malam Iro ya aiki" on the other hand aka amsa "lafia lau wallahi ranka ya dad'e,barka da juma'a" haisam ya amsa"Barka dai,mota ce zaka zo ka d'auka tana nan na parker ta a waje", Iro yace"toh yalla6ai badai matsala ta samu ba ko? d'an murmushin gefe yayi yace "Malam Iro ku da an nemeku ai kasan matsala ce ko" Iron yace"Hakane yalla6ai,to Allah yasa ba babban matsala bace," hannu haisam yasa ya dan shafi fuskan shi kafin yace"Eh,Widescreen din baya ne yayi damage,so it needs to be changed" Salati Iro ya saka yace"yalla6ai garin yaya,wacce ciki ta samu matsalan? Haisam daya fara k'osawa da maganar amsar k'arshen kawai ya bashi "406,in ka lissafa komae let me know" yana niyyar latse kiran da sauri Iro yace "to yalla6ai sai a sanar ma da Jami'an nan zanzo d'auka tunda kace tana a waje duk da sun san mutum sai....." Haisam ya katse shi da fadin"zan fad'a masu" daga haka ya katse wayan. Mik'ewa yayi walking slowly ya nufi gaban desk ya dauki telephone yai dialing numbers sannan ya kara a kunne daga can bangaren daya kira aka d'auka"Security" shine abunda aka ce,shi kuma yace"Somebody will come and take the car I parked out there" daga can bangaren akace "His name sir?" "Iro Mechanic" Haisam ya fad'a daga haka kuma ya kife kan Telephone d'in ya nufi bedroom d'insa,da alama bautar jikin zashi yi inji dai hajia. Bai dade sosai ba ya fito, sanye da wani lallausan farin Voile ana hangen farar vest d'in ciki sai dai ba sosae ba anyi mashi dinkin Senator style,irin style d'innan wanda rigar ke tsayawa a rabin cinya sai dogon hannu wanda ake matse k'asanshi da link yasa links d'in silver da ratsin bak'i,kafafunsa na sanye da takalma plain half cover bak'ak'e masu kyaun gaske kai da gani kasan zasu yi tsada ga wata Hadaddiyar agogo silver,sai hula da ya sa itama bak'a sai dai bata rufe duka kan ba ana ganin gashin kansa daga gefe gefe haka ma na k'eyarsa ya turo,tana da d'an karamin kulu a tsakiyar ta,irin hular nan ce da ake cema Igbo cap amman da ganin jikin wannan mai tsada ce. Part d'in hajia ya nufa tana zaune saman kujera one seater jikinta sanye da jalbab fara sol ga glasses mak'ale a idanuwanta ta d'an duk'a tana karatun Qur'ani wanda ke a saman table,da sallama ya shiga a kujerar kusa da ita ya zauna yad'an kwantar da kanshi yana sauraren k'ira'ar ta a cikin suratul kahf,bai jima da shiga ba ta kammala,d'aga hannuwa tayi tana Addu'a lokaci guda suka shafa ita da Haisam wanda ya d'ago yana kallon ta da murmushi a fuskarsa bud'e baki tayi zatayi magana... ya rigata da cewa "Na karanta a Office" gaba d'aya sukai daria tace "wato har kasan abunda zan tambaya kenan" yace "yeah" d'an ta6e baki tayi tace "ai kwadayin falalar nike maka shiyasa nike tambayar ko ka karantan" "I knew" yace, hajiya taci gaba"To ya wurin aikin,Amman kad'an jima baka dawo ba don har nayi tunanin ko acan zakai sallan juma'ar" shiru yayi ya koma ya d'an jingina yana tuna abunda Fatuu tayi mashi,hajiya ta lura da yadda yanayinsa ya canja da sauri tace"lafia dai ko?? d'agowa yayi ya kalleta yace "Yes,kawai motan ce ta samu matsala", "Wace irin matsala kuma" Hajia ta tambaya da yar damuwa a fuskarta,shiru Haisam yayi baima san mizai ce mata ba,don shi kunya ma yake ji yace wai wata yarinya ta jefar masa mota har ta fasa glass,kuma yasan in har ya fad'i mata abunda ya faru tabbas bazata bari ba sai taje gidan su yarinyar ko ta aika a taho mata da iyayen yarinyar ma don Hajia tana da kirki amman akwae fad'a ba kamar kuma kan abunda ya shafi d'an lelenta Haisam tabbas bazata bari ba,duk da bawai don a biya ba,so bai ma son abun yazama wani big issue,don shi a tunaninsa yarinyar is Abnormal don abubuwan nata sun wuce hankali "Kayi shiru" hajia ta katse shi,d'agowa yayi da d'an murmushi yace"bafa wata babban matsala bace kawai it was faulty lokacin da zan dawo,amman nasamu na k'araso tana waje and I called Iro zai zo ya tafi da ita" sauke numfashi mai karfi hajia tayi don tayi tunanin ko had'ari yayi duk da ta ganshi lafia lau,tace"K'arfen nasara ba tabbas,duka yaushe Iron yazo yayi masu service da ka dawo" d'an ta6e baki Haisam yayi yace "ko kuma ba'a so na ara ba" wani irin kallo hajia tayi masa tace "Eh din,ai kaima kana da taka bama daya ba,karka k'ara daukar man tawa" gaba d'aya sukai daria a daidai lokacin kuma aka fara hud'ubar hausa bayan angama ta larabci a Masallacin gidan,da sauri Hajia ta mik'e tana fad'in kai yau dai mun taushe hannu wallahi,na dawo a gajiye bacci yai awon gaba dani....."ba kince yau ba zaki Aiki ba?" Haisam ya tambaya,"Eh wani abu ne ya taso dole naje, amman ba wani dad'ewa nayi ba don ko tafiya ban bar T.k yayi ba 11:30 muka dawo" ta k'arasa maganar lokacin har yayi gaba ita kuma ta fara kwala ma saude kira"Saude,Saude" fitowa Sauden tayi tana amsawa jikin ta sanye da dogowar hijab brown,hajia tace"Yauwa to mutafi" Saude ta juya tana gaida Haisam wanda ke k'okarin fucewa ya amsa ba tare daya juyo ba suma suka rufa masa baya. Jin an tada sallar juma'a yasa Fatuu lek'owa daga inda ta 6uya,wani gini ne wanda ba'a ida ba,cikin sauri take tafiya tana yi tana waiwayen bayanta kaman zata tashi sama har Lokacin hijabinta na d'aure a k'ugu ga kanta da yayi wani tum da gani kan a tsefe yake duk tayi bud'u bud'u saboda tumurmusar da suka yi a k'asa ita da murja,ta cikin lungun dake tsakanin gidan hajia da nasu ta 6ullo,tsayawa tayi bakin lungun tana lek'en kofar gidansu wanda yake wayam ba kowa shagon kawu Amadu ma a rufe yake don shima yaje makaranta kuma bai dawo ba dama gashi yau juma'a daga can kasuwa yake wucewa ko lokacin da su Fatuu ke yin fad'a sai da wasu yara suka zo kawo sheda suka tarar gidan a rufe. Ganin ba kowa yasata fitowa daga cikin lungun da sauri ta shige gidan farko wanda daga shi sai nasu har tana yin tuntu6e wurin shiga,a cikin zauren gidan taci karo da wani yaro ya fito da sauri da sallaya a hannunsa,tace "kai Umar je ka amso man makulli" yaron yace "kije ki kar6a man nifa sauri nike masallaci zani kuma har an fara...." tsawa ta daka mashi tace" dalla je ka amso man ba yanzu aka fara sallar ba ta d'aure fuska tana harararsa" juyawa yaron yayi rai 6ace yaje ya amso mata makullin don yasan mi zai biyo baya in bai amso ba, Da sauri ta bud'e gidansu ta shige ta maida kofar ta rufe had'i da sa sakata. Ita kuwa Murja bayan Mutumin ya kaita Chemist,aka duba ta ba wani rauni mai yawa bane ha6o ne tayi a hanci saboda bugun hancin da Fatuu tayi sai le6enta na k'asa daya fashe aka yi mata dressing sannan aka bata magani pain reliever,duka ko d'ari biyar dinma ba'a kashe ba,bayan sun fito daga Chemist din Mutumin ya bata naira dubu yace gashi itama ta rik'e,sannan yayi mata nasiha sosai kan rashin dacewar suna ya'ya mata su rink'a yin fad'a haka, ya kuma roketa da tayi hakuri kar tace zata d'auki fansa,kuma ko taje gida kar ta fad'i don ita fitina a kwance take Allah kuma ya La'anci mai tado ta,Murja ta tabbatar mashi da tayi hakuri bazata k'ara yin fad'a da ita ba,Ya k'ara mata naira d'ari yace ta hau mashin ya k'arasa da ita shi kuma ya tura nashi ya tafi yasha mai,bayan ya tafi ta kama hanya k'asa bata hau mashin d'in ba tana ta farin ciki ta samu Naira dubu harda d'ari daya a fili tace"Ko ba komae na rage zafi,wannan mahaukaciyar yarinyar wama zai k'ara fad'a da ita". Bayan angama Sallah Hajiya suka fito daga 6angaren da mata ke yin sallah nan da nan mutane suka kewayeta ana ta kwasar gaisuwa,har d'an rankwafawa wasu keyi in zasu gaidatan,Saude na tsaye a gefe,Haisam ne ya k'araso wurin, ganin yadda hajiyan keta gaisawa da mutane yaji bazai iya jiranta ba ya wuce,Part d'inta ya koma ya kishingid'a saman 3-seater bayan ya cire hular kansa dama duk ta damesa don in yasa dinki irin wannan bai cika sa hula ba,yau ma don yana friday inma baisa ba,hajiya zata matsa masa ne dole sai ya sa, Sai bayan wani dan lokaci su Hajiyan suka shigo,tana shigowa Parlon ta fara kokarin cire jalbabar jikinta tana fad'in "Alhamdulillah,Allah ka nuna mana wata juma'ar cikin k'oshin lpy" Saude ta ce "Amin" ta mik'a ma Saude jalbabar, jikinta na sanye da doguwar riga cotton mai gajeren hannu gaban rigan anmashi wata irin sak'a mai kyau har zuwa k'asa kanta daure da kallabin rigar,ta idasa shigewa cikin parlorn ta zauna kujerar dake kallon wadda Haisam yake kwance yasa pillow a bayansa ya d'an d'ago yana kallon T.V tace "Shine ka k'i jira na mu dawo tare kaman yadda muka tafi a tare" tayi maganar tana cire glass din fuskarta ta aje a saman hannun kujera,d'an murmushi yayi ba tare da ya juyo ba yace"Ina zan iya tsayawa ki gama da wannan mutanen da sukai circling d'inki sai kace kece Senator din" ya karasa maganar da sigar tsokana,daria sosae hajia tayi tace ai ni nafi Senatorn tunda ni na haife sa..." Saude ce ta k'araso ta cire hijab d'in jikinta sanye da riga da zani na atampa tsaf tsaf da ita ta d'an dafa kujera tace"Hajia na gama jera Abincin" hajiya tace "to sannu" daga haka Sauden ta juya,Hajia ta kalli Haisam tace "Oya Food is ready,tashi muje" sai lokacin ya kalleta yace "kije zanzo" harararsa tayi tace "Zaka tashi ko kuwa" hannu ya mik'o mata,tace"mi kenan? Yace "ki dauke ni tunda dole sai tare zamu" kama hannun tayi tana k'okarin kado shi k'asa da iya karfinta,ganin haka yasa haisam janyo hannun da karfi sai gata ta fad'o saman shi gaba d'aya suka sa daria a tare suka mik'e yana fad'in "tsohuwa ba k'arfi". Dining area d'in suka nufa a tare suka zauna bayan kowannansu ya wanke hannunsa a Handbasin d'in da ke gefe,Saude dake tsaye bakin k'ofan kitchen tana dariyar yadda Haisam yaja hajiyar dama kuma sun saba,ta k'araso don yin serving d'insu,wasu Luxury warmers ne guda ukku kai da gani kasan zasu yi kudi ba sai an fad'a ba,Milk color ne,yayin da handle d'insu da kasan su da saman marfin inda za'a juya a bud'e akayi masu wani irin design mai kyau golden,K'atuwar ta fara bud'ewa wadda cikinta ke d'auke da tuwan shinkafa da kuma sakwara kowanne a gefe guda sunyi fari tas an nad'e su da faran leda gwanin burgewa, Plate ta janyo zata fara zuba ma hajia ta dakatar da ita da fad'in "Zuba mashi" "to" Saude ta amsa,wani plate din ta ciro ta warware tuwo guda ta d'aura,ta d'aukko sakwara zata bud'e Haisam yace"Wannan ya isa..." Hajia dake kallonshi tace "Pounded yam ce fa,kuma nasan kana sonta" Shiru yad'an yi yana tunanin anya zai iya cinye su,gashi yana d'an son abinci swallow,ganin haka yasa hajia cewa saka mashi "To" Saude tace,ta saka masa sakwarar sannan ta bud'e warmer ta biyu wadda ke d'auke da had'addiyar miyar Egusi wadda taji ganda da kifi tarwad'a tayi kauri kitif ta d'aukko plate mai gida biyu ta zuba miyar a gidan farko sannan ta bude warmer ta ukku wadda ke dauke da Liver pate wato miyar hanta wadda itace ta sakwarar duk da za'a iya ci da ta agushin ma,ta zuba mashi a dayan 6arin plate din ta turo plate d'in gaban shi tace "gashi" Alamu yayi mata da taba shi cokali da hanzari ta ciro cokalin had'i da fork don in zai d'auko nama ta saka masa a plate d'in tuwon,ta janyo wani Glass jug mai kyau cikinsa d'auke da Kunun Aya fari k'al mai kauri tana k'okarin zuba masa a glass cup ya dakatar da ita da fad'in "Let me finish" hajia tace ni zubo man,tayi maganar bakinta cike da Abinci don tuni tayi serving kanta bata jira Sauden ba,"to,saude tace ta cika mata cup da kunun ayar ta tura a gabanta,juyawa saude tayi ta nufi freezer wani d'an babban Acryclic bowl ta fiddo mai marfi d'auke da fruit salad ta aje masu ta koma ta daukko bottled water shima ta kawo masu tace"Aci lpy" hajia ce ta amsa da"Allah yasa" har Saude ta juya zata tafi hajia ta tsaida ta da fad'in "Kin dai zuba naki ko,nasan ki da duminiya" murmushi Saude tayi tace "na zuba hajia, "to kin zuba nasu Officer?" Saude tace"Eh yanzu zan kai masu" d'aga kai hajia tayi sai kuma ta cigaba"Wai ni ina T.k ne ko a masallaci fa ban ganshi ba,ban kuma ga yazo ya d'auki Abinci ba...kafin Saude tace wani abu T.k d'in ya shigo da sallama sanye da dogayen kayan yadi ya nufi dining d'in ya tsaya daga gefe yana gaida hajia,tace "Ina ka shige ne wai tunda muka dawo ban k'ara saka a ido na ba ko a masallaci ma ban ganka ba" T.k yace "nad'an lek'a makaranta ne acan nayi sallah", "Au dama zaka makarantar baka gaya mun ba muka fita?" d'an murmushi T.k yayi yace "Ai dama duka lectures biyu gare ni yau,kuma Lecturer d'in safen yace bazai samu zuwa ba,ta biyun ce naje" cikin girmamawa yake maganar,hajia tace "Amman duk da haka dai ka makara gaskia,sai fa 11:30 muka dawo,kuma har kayi wanka sannan ka tafi, wace lecture kasamu,ka je dai yawo kawai" ta tura ganda a bakinta, T.k yace "dama dai attendance nike son inje insamu kuma na samu nayi" tace"duk da haka daga yau in kasan zaka makaranta na bukaci mu fita ka gaya man sai insa Officer ya kaini,amman banso kana wasa da karatu sam" T.k yace "In sha Allah" sannan ya maida kallon shi kan Haisam wanda duk maganganun da suke ko kallon su baiyi ba,yace "Yaya Haisam barka da juma'a" hannu haisam d'in ya d'aga masa saboda akwae abinci a bakinsa daga haka ya wuce kitchen don amsar Abincinsa. Ajiyar zuciya Haisam yayi wanda ya kusa cinye abincin saura tuwo d'an kadan a cikin plate din,ya yago tissue acikin kwalinta dake saman table din yana k'okarin goge bakinsa, d'an tura kujerar yayi baya yad'an kwantar da kansa Hajia ta d'ago tana kallonsa tace "Sai kace wanda yake wani uban aiki,to wannan guntun da ka rage fa? ai dai ba wani ya matsa maka cin biyun ba kai ka ga zaka iya don haka sai ka idasa cinyewa" d'an ta6e baki yayi yace "dama nasan sai kin tanka..."da sauri hajia tace "eh d'in,inma bayaga abun ka wannan guntun ai shine Albarkar" d'agowa yayi ya kalleta da d'an murmushi yace "kika sani ko yau ma wani zan samu ya idasa man shi...."da sauri Hajia ta d'aukko wuk'ar yanka bread daga cikin cutlery set din dake saman table din tace "Bismillah" daria sosae haisam yake yi yace "Wannan abun fa da kika rik'e? tace "na kare kai ne" gaba d'aya suka sa daria,Hajia tace "don Allah idasa mana",dan lumshe ido yayi yace "Owk tunda kince Allah,amman fa na koshi in cikina ya fashe you will see the consequences" yayi maganar yana jaddada mata da spoon d'in da ya d'auka,tace "Eh naji" ta jawo Jug din kunun ayar ta cika mashi cup ta tura gaban shi. Mik'ewa yayi bayan ya idasa cinyewa ya d'au cup d'in kunun ayar ya nufi cikin parlon hajia na fadin "Fruit salad d'in fa? Hannun da ba komai ya d'ago mata ba tare da ya juyo ba yace "bansan ina zan sa shi ba" ya idasa shiga cikin parlon ya kishingid'a saman kujera 2 seater yana d'an kurbar kunun ayar yana kallon T.V,bayan wani dan lokaci itama hajia ta mik'e bayan ta zuba fruit salad din acikin d'an bowl tasa cokali ta nufo cikin parlon tana kwala ma Saude kira,da hanzari sauden ta fito tace "gani hajia" hajia ta juya tace mata"Je ki clearing dining din mungama" "to" Saude tace ta nufi Dining area din ta kwashe duk abubuwan da sukayi amfani ta kai Kitchen banda Warmers d'in Abincin don gidan hajia bai rabuwa da bak'i manyan mutane,ba kamar yau da yake Friday ta tabbatar wasu zasu zo a buk'aci ta basu Abincin,tasa towel ta goge wurin yayi fess kaman ba'a zauna anci Abinci ba. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* *Mallakin* ⬇️ *ZAINAB LALUH*🌹 *(Oummu imam)* *Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp banda phone call,Thanks🤝* *Free page1️⃣4️⃣&1️⃣5️⃣* Saman kujerar dake opposite da wadda Haisam ke kishingid'e hajia ta zauna tana shan fruit salad d'in da ta d'ebo tana yi tana kallon American film din da Haisam d'in ke kallo, "Dad called me when I was in office" Haisam yace ba tare da ya kalli Hajiyar ba,d'an ta6e baki tayi tace"Ai nima dai ya kira ni tunda safe,yayi man barka da juma'a" yar daria Haisam yayi yace "Jealous Old Woman" itama dariyar tayi tace "ai don kasan yafi ji dani" gyad'a kai yayi yace "I knew,shiyasa ma koda ya kira ni maganar ki yayi man" da sauri Hajiya tace "Maganata kuma? Kai ya d'aga alamar Ehh,tace "to wace magana ce da ni bai man ba da ya kirani sai kai zai yi mawa,ko dai gulmata ku ka yi?" ta dakata da shan fruit salad d'in tana kallon shi alamar shi take jira ya bata amsa, sai lokacin ya juyo da kanshi yana facing d'inta yace "gulma kuma,No kema kinsan baza muyi hakan ba" ya d'an dakata,sai kuma yaci gaba "Ya tambayi yaushe zan kai mashi ke ne" wani irin kallo tayi mashi tace "Ka kaini kuma,da can da nike zuwa lokacin baka k'asar kai ke kaini? Yar daria yayi yace "to ai yaga kin dade baki je bane shi kuma yana son ganin ki" d'an ta6e baki tayi tace "to tunda yana son ganina sai yazo ya ganni,haka itama waccan ta lagos d'in last week ta kira ni tana ce man wai don Allah inje ta na son ta ganni na...." Haisam ya katse ta "Aikine yayi masu yawa they're always busy" hajia tace "To ni ban aikin ne?" murmushi yayi yace "Kina yi amman ai ba kaman su ba,ke You are less busy kuma Aikin naki is voluntary ke kika sa kanki...."katse shi tayi da cewa "Ai dai duk aiki aiki ne" tayi maganar a harzuk'e daria yake yace"ni daman ai baki ji nace aikin ki ba aiki bane Celebrity" da d'an murmushi tace "Ni ce celebrityn? Yace " Yeah,anata son ganinki kina wulakanci" yayi maganar cikin wasa,dariya Hajiya tayi tace "Miye abun wulak'anci don nace duk mai son ganina yazo inda nike" dan ta6e baki yayi yace "I think suna son kije kid'an kwana biyu ne" tace "Ai ina zuwan ko,kawai ni haye-hayen jirgin ne ba so nike ba wllh" ta k'arasa maganar fuskarta dauke da damuwa,ta aje bowl din saman sofa table kusa da cup din kunun ayar da Haisam ya sha ya rage kad'an,Sannan ta maida Kallonta kan hoton Sojan mutumin nan ko kyaftawa ba tayi. Ganin yadda ta k'ura ma hoton ido yasa Haisam d'an juyar da kanshi shima ya kalli hoton,girgiza kai ya d'an yi ya juyo da duban sa kan Hajiyar yace "Ba lalle silar ajalin ya zama d'aya ba Sweethrt" "I know" hajiya tace,ta kauda kanta gefe har lokacin da damuwa a fuskarta, "In bakya son hawan jirgin ne ki fad'a ma Dad sai asamo k'wararran Driver da zai rink'a kai ki", Uhmm tace batare da ta waigo ba,ya cigaba"Ita kuma lagos d'in in zakije sai ki rink'a hawa luxurious Bus...." da sauri ta juyo tace"Waye zaije lagos a Bus?" Yace "Ke mana tunda bakya son hawa jirgin ko" yayi maganar yana dariya,itama Hajia dariyar tayi tace "tabb inje lagos a mota,aikam in na isa saidai k'ilan a kwashe ni a Wheelbarrow" gaba d'aya suka sa dariya "Saboda me? ba bakya son hawa jirgin ba" tace "Eah amman hakan ba yana nufin zan daina hawa jirgin ba in koma hawa wata Bus can" gyad'a kai yayi ya maida duban shi kan TV, "Yanzu yaushe zance mashi zaki je? ya tambaya ba tare da ya kalleta ba,da sauri tace "Ina wai? yace "ABJ" ajiyar zuciya tayi tace "zanje amman fa ba yanzu ba,dana samu isasshen lokaci Lagos zani don har ta turo man da kudin jirgi,duk da ma wannan kud'in sunfi karfin kudin zuwa lagos ta dai turo man ne kawai", "Har nawa ta turo maki kud'in flight? Ya tambaya,tace "1 million" nodding kai yayi yace"kice bribe aka baki kawai,shiyasa zaki ce lagos zaki,to ki maida mata kud'inta ni zan baki 3m ki tafi Abujan..."da sauri hajiya tace "ban mayarwa,wato ka maida ni ma uwar son kud'i kenan" tayi maganar tana ta dariya,shima dariar yake yace "Aikam zanyi reporting d'inki ICPC,ince ga wata Mom din Senator kuma matar Former Minister of Defence ta kar6i cin hanci..." Hajia tace"Yi sauri kar k'uda ya riga ka"gaba daya suka kwashe da dariya. Hajiya ta ci gaba da magana "ni ina zan iya da jarabar Momynku ta lagos,yanzu abun ince mata bazan samu zuwa wurinta ba,kuma taji na tafi Abuja kaji masifa" Haisam yace "Ai ke ta biyo" da d'an zare ido tace"Masifar?" yace"Eah mana" ta6e baki tayi "tunda fa ka raina ni ai komai kace man" murmushi yayi yaci gaba da kallon American film din da ake, "Wai ni ya FANAN take kwana biyu bamuyi magana ba nasan dai hakanan bata k'in kirana sai dai ko yanayin karatun ne ya hana,ni kuma ban kira naji ya take ba" d'an lumshe idanu Haisam yayi kafin yace "baki damu da ita bane" hajia tace "Aikuwa ni na damu da ita tunda na damu da kai,tunda duk abu d'aya ne ko" murmushi kawai yayi batare da ya waiwayo ba, "Ina son yarinyar saboda akwai hankali ga sauk'in kai sam bata d'auki duniya da zafi ba,ba kamar yar'uwarta ba" haisam yace"wa kenan? tace "FARHA mana,kai wannan yarinya sam halinta ba irin na yar'uwarta bane,ta cika girman kai,ta d'au kanta wata tsiya,ni ina ganin acan dangin Babanta Turawa tayo gadon halinta" dariya haisam yake yace"ko kuma danginku ko..."da sauri Hajia tace "Haram,wallahi mu bamu da wannan halin kaima sai dai in ka k'i gaskiya ko akaina ai kaga misali ba ruwana sauk'in kaine dani ba kuma yabon kai ba atoh,yarinyar nan fa ko kirana bata iya yi ina matsayin kakarta sai dai in muna waya da uwar in na tambayi yasu Farha,shine fa in tana kusa tace man gata hajiya,in kuma bata nan ne inta dawo sai ta kira ni tace Hajia ga Farha d'in ku gaisa", Ajiyar zuciya Haisam yayi sai lokacin ya juyo yana kallon hajiyar,ta ci gaba "ko gidan fa naje yarinyar nan bata iya zama muyi fira,bare kuma tazo d'akina don ta gaida ni, ko da safe wani lokacin in mun hadu a dining don yin Breakfast sai ni ce zance Hajia farha antashi lafiya,sannan za kaga ta wani yamutsa baki tace "Good morning granny" hajia tayi maganar tana kwaikwayon yadda Farhan ke yi da baki,shi dai Haisam sai daria yake yace "Ni kuma kinga in muka had'u lafia muke gaisawa though dai bama wani magana ma sosae,tace "Yo kaida ita ai duk kanwar ja ce,kawai dai kai sai mutum ya zauna da kai zai fahimci saukin kanka amman kaima wani lokacin ai ba son magana kake ba,amman Farhaaa huu badai girman kai ba wllh" ta6e baki ya yi yaci gaba da kallon shi. "Ai wallahi Allah ya yabawa aya zakinta,da bai sa Farha ce ke da kyau da sura irin ta Fanan ba,Wai! da bansan a ya zata rik'a duban mutane ba a hakan ma ya aka cika,ita kuwa Fanan dayake Allah yasan kyakkyawar zuciya ce da ita sai ya had'a mata harda kyaun sura" juyowa yayi yana duban hajia yace "Kina nufin Farha bata da kyau? da sauri tace "ina taga wani kyau da wani hancinta kamar ansammata,idanuwan ma ba wasu masu girma ba,sai uban kumatu,sak uwarta ta biyo hasken ne kawai na uban sai d'an gashin kuma" haisam yace"You see,if to say wani ya fad'a maki baki da kyau da kinji haushi,amman yanzu da bakin ki kin fad'a". Hararar shi tayi "Ni d'in ce banda kyau?" yace "yeah,kince Farha bata da kyau...." da sauri ta katse shi "to ni uwarta ce,ko baka ji nace da mamarta take kama ba? "To miye marabar ki da Mommyn Lagos d'in?" Jimm hajia tayi tana tunani,dariya Haisam yayi yace" I know you won't deny cewa kuna kama dama,don sak fuskan Mommyn Lagos taki ce,she's your duplicate" ya k'arasa maganar yana ta daria ganin yadda Hajiya ta kasa magana,can tace "naji to,amman duk da haka nafi ta kyau" tayi maganar tana daria itama,girgiza kai Haisam yayi "yanzu kina nufin kinfi Farha kyau kenan? tace "Eah hasken fata ne kawai tafi ni sai d'an gashi kuma" nodding kai yayi "Lalle,nan gaba ma har Fanan d'in cewa zaki kinfi ta kyau da alama..." da sauri Hajia tace "nan fa d'aya ai ko giyar wake nasha bana ce nafi Fanan kyau ba yarinyar da har uban nata tafi shi kyau,inaga itama acan cikin danginshi turawa ta samo kyaun nata,kaga kenan ita Farha ta d'aukko hali maras kyau,Fanan kuma sai ta d'aukko kyawun sura" gaba daya suka kwashe da dariya,cikin fahimta suke firar tasu da gani kasan akwai kauna mai tsanani a tsakaninsu. Telephone ne ya fara ringing alamar ana kira,Haisam ya yunk'ura don ya d'auka hajia ta tsaida shi "Yi kwanciyarka bari na d'auka dama na gaji da zaman" ta nufi inda telephone d'in yake ta kara a kunne tace "Hello,Salamu Alaikum" daga d'ayan bangaren akace "W/salam Hajia you have visitors" tace"Okey,hold on" ta rik'e kan telephone din ta fara waige-waige alamar tana neman wani abu,haisam ya d'an kalleta"lafia? Ya tambaya,tace "Eah nayi bak'i ne ina son inga su waye,na rasa ina na aje ma wayan tawa" yace "I don't think tana parlon nan don tunda na shigo banga wayan ba" tace "Oh! namanta tana bedroom kuwa da zan kwanta na aje ta,bari Saude ta d'aukko ma....." Haisam ya katse ta "Let me change it to CCTV" ya k'arasa maganar yana k'okarin canza kallon da ya ke zuwa cctv,nan da nan sai ga vedios din 6angarorin gidan sun bayyana a kan TV d'in,kan vedion farko mai dauke da rubutun CAM01 daga k'asan rubutun ansa Gate ya shiga vedion wajen gate din gidan ya bayyana,wata mota ce a gaban gate d'in mutanen da suka zo kuma suna cikin motar hakan yasa hajia fad'in"to ni bamma gane su waye ba,sai mota kawai nike gani ko sai nasa glass...."Officer da yake jiran umarnin hajia jin abunda take fad'a ta cikin telephone d'in yasa shi lek'o da kanshi ta d'an karamin windon d'akin da suke zama irin na masu gadi wanda window d'in ta fito waje yayi ma wanda ke a mazaunin driver magana,mutumin ya leko da kanshi,hajiya ta k'ura ma mutumin ido tana k'okarin gano ko waye....can ta buga salati tace ma Officer dake jiran umarninta "Officer let them in" yace "Ok", Kallon Haisam tayi tace "Kawunku ne fa" ba tare da ya kalleta ba yace"Wane Uncle? tace"kawun ku Mani,na daura" "Ok" yace ya fara k'okarin mik'ewa hajia tace "Ina zaka kuma? Yace "Zan baku space ne", "to amman ai yakamata ka tsaya ku gaisa ko" komawa yai ya zauna ya ciro wayarshi daga cikin aljihun rigarsa yafara daddanawa. Wasu Dattawa ne su ukku suka shigo na farkon daya fara shigowa yafi sauran jiki da tsawo,bak'i ne yana sanye da manyan kaya farar shadda had'i da babban riga da hula,sai na bayansa shima shadda ce jikinsa saidai ta d'an ji jiki kuma kalar babban rigar daban ta yan cikin ma daban,sai na ukkun wanda shi yadi ne jikinsa riga da wando da hula kuma duk bai kai girman sauran ba. Hajiya na ganin mutumin na farko ya shigo ta mik'e fuskarta d'auke da fara'a da alama shine Kawu Manin,shima yana ganinta ya washe baki yana fadin"Hajjaju makkatun wa madinatun,Hajiyar Minister,Hajiyar Senator " cikin dariya Hajia tace "duk ni kadai" yace"Eh mana ai duk sunanki ne" ya karasa maganar yana k'okarin zama a kujerar dake kusa da ta ta,ta kalli wad'anda suka zo tare tace "Bismillah,ku zauna" suka amsa da "to" suka zauna,sannan suka fara gaidata cikin girmamawa,da fara'a ta amsa masu,ta maida duban ta kan Kawu Mani tana fad'in "kuyi hak'uri fa an barku waje kuna ta faman jira,su ba ruwansu ko da mutum yana zuwa indai ba akai akai ba sai suce sai sun tambayi izini zasu barshi ya shigo", Da sauri Kawu Mani yace "Ah ba komai wllh,ai hakan is part of their work,ba kamar yanzu da ake fama da matsalar Insecurity hakan shine daidai,don shi mugu zai iya zuwa da kowacce suffa ya cutar da mutum" Sauran suka jinjina kai sukace "gaskiya ne" Kawu Mani yaci gaba "Allah dai ya k'ara tsaremu da tsarewarsa,don Al'amarin sai dai Addu'a kawai itace zatai mana magani" Gaba d'aya suka amsa da "Amin" harda Hajia, Haisam ne ya d'ago da kansa ya kalli kawu Mani yace "ina yini Uncle" sannan ya juya ya gaida sauran cikin muryarsa mai cike da natsuwa,a tare harda kawun suka amsa mashi da "Lafiya lau", "Haisam ne d'an gidan Hajiya" kawun ya tambaya da fara'a "Eah" haisam yace a tak'aice, kawu yaci gaba da magana "Masha Allah,Haisam ya karatun? Kafin ya bashi amsa Hajiya tace"Ai ya gama,yanzu haka yaci gaba da aiki a nan garin yana nan AIRPORT" da mamaki yace "Wai yanzu har ya gama karatun? Kinsan kafin ya tafi nazo nan muka had'u lokacin kike ceman zai tafi yin Master's Degree a U.S" tace"Aikuwa dai gashi har angama" jinjina kai kawu yayi yace"Time really flies,Allah yasa mudace" hajia tace "Aikam lokaci fa na gudu,Amin ya Allah",sauran ma suka amsa da"Amin", Kallon Haisam yayi yace "Haisam yanzu sai Aure ko,nasan yanzu ai ka kai 30yrs ko?"yayi maganar yana yar daria,d'an guntun murmushi haisam yayi kafin yace wani abu wayarsa ta fara ringing ya mik'e yace masu"Excuse me.." daga haka ya fice, Hajiya dake ta fara'a tace "bai ida shekara talatin ba yanzu ya shiga 29yrs yanayin jikin ne sai ka ce yama wuce 30,dama kuma ga daga karfe yana yi,Auren kuma tukunna dai sai nan gaba in zai koma" Kawu yace "karatun zai k'ara komawa ne? tace"Eh zai koma U.S d'in amman ba karatu zashi yi ba duk dama yace zai kara karatun in ya koman,akwai wani babban Company ne daya danganci karatun da yayi na Computer Engineering suna k'era kwamfutoci da sauran abubuwan su na fasaha dai,shine suke son yin aiki dashi,duk da yanzu haka matsayin Agent d'insu yake anan k'asar,to kasan Uban nashi akwai kishin k'asa,da k'in yarda yayi,sai da Haisam d'in yayi mashi bayanin dalilin daya sa yake son yaje can yayi aiki dasu sannan fa ya aminci amman yace sai ya k'ara yima k'asar shi koda na shekara biyu ne,don gani yake suna iya rik'e shi...." a d'an harzuk'e Kawu Mani yace"Very thougthful of him,wallahi Senator yayi man daidai,don ma bansan dalilin daya sa Haisam d'in ke son zuwa ba,da nace dama gaba d'aya ya hana shi,haba! for how long zamuyi tayin shuka su suna girbe amfaninta,sam wallahi mutanen nan basu son cigaban mu,shiyasa da sunga mutumin mu mai hazak'a sai su bukaci yayi aiki dasu,su kuma mutanen mu sam basu kishin k'asar su,what they're after is the money,su dai kud'i kawai,basu tunanin suma su gina tasu k'asar,koda bazamu iya kamo su ba,mu ha6aka tamu kasar ta yadda zamu daina relying kansu,d'an abunda bai kai ya kawo ba ace sai anfita waje" ya d'an tsaya ya sauke numfashi,sannan ya juya kan mutanen da ya zo dasu ya ci gaba"Wallahi Alhaji Sa'idu karka so kaga yadda mutanen nan ke cin moriyar mutanenmu sai ma kaje asibitocin su zaka sha mamaki yawanci sai kaga manyan likitocin da suke masu aiki duk mutanenmu ne....." Hajiya ta katse shi da fad'in "tabbas,don akwai lokacin da muka kai marigayi Minister da yayi wani ciwo kasar Germany,wallahi likitan dake duba shi mutuminmu ne,kuma ma d'an nan Katsina don bayan mun dawo har zuwa yayi duba lafiyar tasa..."Kawu Mani yace "You see...shine maganan da nike,suna can wasu na amfanuwa dasu sun bar mu nan munata fama da rashin k'wararrun likitoci". Ya juya kan hajia"Wallahi hajjaju mostly likitocinmu yanzu ain't qualified,yan kad'an ne suka san aikin su,wai sai kaje asibiti ko ka kai wani naka,abun haushi kana ma likita bayanin matsalarka sai kiga ya fiddo waya yana googling...wai sai ya tura ma google duk abunda aka bashi shi zai jibga maka kuji fa don Allah wanda ada sam ba haka likitocinmu suke ba k'wazo ne dasu" gaba d'aya suka jinjina kai cike da takaici, Wanda kawu ya kira da Alhaji sa'idu ya fara magana "A haka kuma wasun nasu sai d'an karan wulakanci,haka zakai ta jin Labaru maras dad'i da suka faru a dalilin wulakanci da kuma sakacin da bai kamata ace ma'aikacin lafiya ne yayi hakan ba,wanda na tabbatar in a k'asar wajen suke yin aikin kwatankwacin hakan basu isa suyi ba,ba tare da an d'au kwakkwaran hukunci akai ba" gaba d'aya suka jinjina kai hadi da fad'in "Sosai kuwa", Na karshen ne wanda bai kai su girman jiki ba,shima ya fara magana"Wato Alhaji Mani duk matsalolin nan sun fara ne tun daga tushen fara karatun,yadda yakamata ace ana koyawan ba haka ake koyawar ba ayanzu karatun duk ya ta6ar6are shiyasa masu halin sai su d'auke yaransu su tura su kasar waje karatu,su kuma da sun ga mutum nada basira sai su rik'e shi suna biyan shi kud'i masu yawa,wanda yasan baza'a iya biyansa kwatankwacin su ba a k'asar shi dama kuma ba itace a gaban shi ba,taci gaba ko karta ci gaba shi ba ruwanshi,su kuma maras halin da basu da wani zabi da ya wuce dole su tsaya nan suyi karatun a wahale gashi yawancin malaman sun maida karatun kasuwanci,da abunda d'alibi yakamata ya kashe kudi da wanda bai kamatan ba duka kashe kudin yake,gaba d'aya yanzu karatun d'an talaka ya zama wahala yan kadan ne ke iya jurewa su gama,shiyasa in suka fara aikin sai kaga kaman suna ramuwar gayya ne,ba malaman asibitin ba,ba malaman makarantar ba da dai sauransu,kowa bai tunanin duk abunda yayi ma wani zai iya juyewa kan nasa...., "To Al'amarin kasar tamu dai sai Addu'a kawai amman muna bukatar mu canza halayenmu inba haka ba,haka zamuyi ta zama jiya iyau abubuwa duk suna ta ta6ar6arewa,kowa damuwarsa taya zai samu kudi ba ruwanshi da kasar ta gyaru ko akasin hakan kuma dai ko mun k'i ko mun so k'asarmu ce ba yadda zamu yi,in ta gyaru mu zamu ji dadi akasin hakan ma mune a ciki" lokaci guda su duka sukayi ajiyar zuciya, Hajiya tace"Allah ya bamu ikon gyarawa gaba d'ayanmu harda shuwagabannin mu,yasa mana tausayin junanmu,Amin" suma suka amsa da "Amin", taci gaba da magana "Shi Haisam ma ba kudi ne zasu kaishi ba,sam ba sune damuwarsa ba wllh,dama yana da burin gina katafaren Company wanda ya danganci technology d'in anan k'asar,to shiyasa yake son yaje yayi aiki dasu don ya k'ara samun Experiences,don bama shine Company na farko da suka yi mashi tayin aiki ba,ko lokacin da yayi Degree d'insa na farko a can k'asar Singapore,akwai wani Company daga k'asar China da suka so yayi aiki dasu Uban nasa ya hana yace ya dawo nan gida yayi aiki,to lokacin ya fara a matsayin Engineer mai zaman kansa daga baya ya fara aiki ak'arkashin Ministry of Communication Technology, Kawu Mani yace "haba ni daman nasan badai kud'i ne zasu sa Haisam din son yin aikin ba,ashema babban dalili ne,aikuwa gara yaje kinga sai ayi abunda ake cema ban gishiri inbaka manda" ya d'an dakata kafin yaci gaba"Ai sanata akwai kishin k'asa,wallahi nike gaya maki hajiya da Allah zaisa ya zama shugaban k'asa da munji dadi" dariya hajiyar tayi, ya juya wurinsu Alhaji Sa'idu yace "Allah daba k'aramin adalin shugaban k'asa za'ai ba mai kishin cigaban kasarsa,ga dai misali nan kan Iyalinshi" suka jinjina kai had'i da fadin "gaskiya ne" ita kam hajiya dariya kawai take tace "tau da kamar wuya dai ya fito takarar shugaban k'asa,don takarar Senator d'in ma da yaya ya fito sai da mutane suka taso shi gaba da kyar ya aminci,haka da tenure d'insu ta kare ma so yayi yaki ci gaba,a cewarshi yafi son ya cigaba da aikin shi da kuma kasuwancinsa". Kawu yace "Ai shugaban k'asan ma sai a matsa masa ya fito in Allah yasa da rabo sai kiga ya zama,ni ba don komai bama wallahi sai don fatan samun sauk'in matsalolin nan da suka yima k'asarmu katutu..." ajiyar zuciya Hajia tayi tace "Allah dai ya za6a mana dukkan abunda yafi zama alkhairi" gaba d'aya suka amsa da "Amin ya Allah". "Oh munata tattauna matsalolin da in shekara zamu yi ba lalle mu gama ba,an barku ko ruwa ba'a kawo maku ba" hajiya tace tana kallon su Alhaji Sa'idu da murmushi,suma murmushin suka yi,ta kalli Kawu mani tace "ga Abinci can saman table,dama bamu dad'e da saukkowa ba nida Haisam,don da ana gama sallan juma'a ku ka zo ma a tare zamu ci" Kawu yace"Wallahi nan naso muyi sallar juma'an,to bamu gama abunda muka je yi ba da wuri,dole acan dai mukayi" hajiya tace"Wani wuri kuka je ne? Yace "Eh,Ministry of Agriculture muka je" tace "Allah sarki,ya noman ana tayi ko? Yace "Eh,Alhamdulillah muna ta k'okartawa" "To Allah ya k'ara taimakawa,wasu yankunan ma naga noman ya gagaresu saboda matsalar rashin tsaron nan,gona ta ma da ke hannun baban tukur bara ai noman bai samu ba,Allah ya kawo masu d'auki da mu gaba daya" suka amsa da "Amin" "Jama'a ku tashi kuci abinci don Allah" ta fad'a tana kallon su Alhaji sa'idu,Kawu Mani ne yace "ai inaga Hajiya kaman a sakko mana dashi nan zai fi" tace to,ta fara kiran Saude,daga cikin corridorn da bedrooms suke Saude ta fito tana yafa kallabinta,hajiya ta bata umarnin ta kawo masu Abinci cikin parlor,ta juya ta fara kawo masu,kafin ta gama jerawa Kawu Mani ya juya yana tambayar hajiya"hajjaju ya wajen mutanen Lagos,hajiya Maryam da k'waran mijinta kwana biyu bamu gaisa ba? Daria hajiya tayi tace "suna nan lafiya lau",a lokacin Saude ta gama serving abincin saman lallausan Carpet d'in parlon bayan ta gaishe su tace masu"Bismillah" suka amsa da "to" had'i da yi mata godia,ta juya ta koma ciki Hajiya ma tace masu zata d'an shiga ciki kafin su gama. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* *Mallakin* ⬇️ *ZAINAB LALUH*🌹 *(Oummu imam)* *Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp banda phone call,Thanks🤝* *Free page1️⃣6️⃣&1️⃣7️⃣* Haisam na fitowa daga part d'in Hajiya ya nufi Part d'insa yana amsa wayan da aka kira shi,a daidai stairs din balcony ya gama wayan,tura kofa yayi ya shiga cikin parlon ya zauna kan kujera hadi da daukar Remote yayi powering tv On,ya d'an kishingida yaci gaba da kallon American film d'in da yake kallo a MBCMAX, bayan wani d'an lokaci ya dau wayarsa ya duba time,sake d'aukan remote yayi yai Offing tv sannan ya mik'e ya nufi bedroom. Sanye cikin Sportswear ya fito,red t-shirt da wandonta black daga gefen hagu na rigan na dauke da tambarin ADIDAS wanda akayi da bakar sak'a haka wandon ma adai dai gefen da akayi rubutun rigan shima akayi da jar sak'a daga k'asa yad'an matse,ba k'aramin kyau yayi cikin shigan kayan ba,kuma da ganin laushin kayan tabbas zasu yi kudi,saida ya tsaya yasa takalma a corridor kafin ya iso cikin parlon ya dau wayansa ya fice zuwa masallaci wanda liman ke ta kwalla kiran sallah, Tare da su Uncle Mani ya fito bayan angama sallan la'asar d'in ya nufi cikin parking space don fiddo da Bike d'insa bayan yayi ma T.k da ya fito daga masallaci bayan sun fito umarnin ya daukko masa jakarsa kaman jiya, Uncle Mani ya nufi part d'in Hajia don yi mata sallama su kuma su Alhaji Sa'idu suka tsaya gefen motar da suka zo da ita suna jiran ya dawo gaba daya hankalinsu na kan Haisam daya fiddo bike d'in cikin harabar ya haye yana kokarin sa helmet,adai dai lokacin da t.k ya kusa k'arasowa da jakar, Hajiya da Kawu Mani suka fito suka nufo parking space din,Kawu Mani dake ta kallon Haisam tunda suka fito ya fara magana"Yanzu Hajjaju shima Haisam na hawa irin mashin d'in nan? Hajia ta ta6e baki tace " Unn" adaidai lokacin da suka k'araso wurin su Alhaji Sa'idu ya kunna mashin d'in gaba daya suka toshe kunnuwansu da hannayensu da sauri,haisam ya d'an juyo ya d'aga ma Uncle Mani hannu alamar yana masa sallama bai jira ya maido masa ba yaja mashin din da gudu ya tunkari gate d'in da tuni an wangale masa shi. Uncle Mani ya sauke ajiyar zuciya bayan Haisam ya fice yace"I don't know what's wrong with our Youths,abu mai had'ari shi suke mayarwa abun adon su,and what really baffle me with them shine duk irin mummunan had'arin da mashin d'innan ke haddasawa hakan bai serving dinsu misali su daina hawan...Alhaji Sa'idu ya kar6e"Sam basu bi dashi yadda yadace ne,haka zaka ga suna ta falla uban gudu kai kace zasu kiyama..."Mutumin na karshe ya katse shi da cewa"Ai wasu kam kiyaman suke tafiya wllh sam basu la'akari da irin titinan mu ba kaman na waje bane,su yi ta tuk'in ganganci,gashi naji ance mashin d'in tsada ne dashi sosae..."Hajiya dake tsaye hannuwanta goye a bayanta ta amsa "tsada kam! Miliyan biyar ya zuba kafin ya mallaki wannan nasan..."gaba daya suka zaro ido a tare suka maimaita kudin da hajiyan ta fad'a,ita kam kai ta jinjina masu Uncle Mani yace "to Allah ya kyauta,Allah ya k'ara tsarewa,gaba d'aya suka amsa da Amin" daga haka ya kalli hajia da d'an murmushi yace "to hajjaju mu zamu wuce sai wani lokaci kuma in Allah yasa rayuwarmu ta kai" hajia tayi murmushi tace"To Allah yasa rayuwar tamu ta kai" ta fiddo hannayenta dake goye a bayanta ta mik'a ma Alhaji Sa'idu kud'i dake cikin hannunta na dama da fara'a tace"gashi ayi ma iyali tsaraba nagode da ziyara,Allah yabar zumunci" hannu biyu yasa ya kar6a harda d'an russunawa suna ta godiya shida dayan,Uncle Mani yace"To ni hajjaju ba'a sallame ni ba" dariya tayi tace banda kai ai sune bak'i na, kai na gida ne" shima dariyar yake ya bud'e mota yace"ba wani abu nasan tawa sallamar babba ce tafi karfin hannu k'ilan,zan turo Account details" daga haka ya shige Abokan tafiyarma suka shiga suna ta kara godiar rafar 50k da hajia ta basu cike da farinciki hannu ta d'aga masu bayan sun fita daga cikin parking space din tace"Agaida Iyali",daga haka ta juya ta koma ciki. Tunda ta shige gida take kunshe a daki,bayan tayi sallar Azahar bacci yayi awon gaba da ita,ko Uniform d'in bata cire ba,bugun kofar da ake tayi ne ya farkar da ita a tsorace ta fito daga d'akin tana tafiya cikin sand'a har Lokacin kuma ana ta buga kofar da k'arfi,tsayawa tayi cikin zauren tana tunanin waye ke buga kofan haka? kodai mai Motar ne ya kawo k'ara,ji tayi gabanta yayi mugun fad'uwa nan take tsoro ya kama ta tace a ranta "to ya akai yasan gidanmu bayan lokacin da na jefi motan ba kowa wurin..." wani bugu aka yima k'ofar wanda daji mai buga kofan ya k'ule yasa ta tunkari kofar da sauri ta d'an leka idonta d'aya ta ramin makulli nan take ta gane waye da sauri takai hannu sama ta cire sakatan sannan ta d'an ja baya,aikam da karfi aka bugo kofan don da bata matsa ba daba k'aramin buguwa zatai ba,rai a6ace yake kallonta Kawu Amadu ne hannunshi daya rungume da kwali d'ayan kuma katuwar leda ce,Fatuu dake ta faman zare ido tace "sannu da zuwa Kawu Amadu...."da sauri ya katseta da fad'in "sannu da zuwan uwarwa,don iskanci daman kina cikin gidan kika barni inata bugun k'ofa tsawon lokaci,to waima uban me kike a cikin gidan daba zaki zo ki budan ba? d'an turo baki tayi tace "ba komai,bacci ne ya d'auke ni fa" a harzuk'e yace"to miye na kulle kofa don zaki yi bacci" da sauri tace "ina gudun kar a shigo ayi sata ne ina baccin...." "k'arya kike" yace yana k'are mata kallo kafin yaci gaba "fad'a kika jawo ko? Da sauri ta girgiza kai alamar a'a,kwafa yayi yace "ai na dawo gidan inma rigima ki ka jawo zan gani,kuma uban miye na zama da Uniform har yanxu a jiki da alama ma ko wanka baki yi ba,bare kiyi sallah" ya k'arasa maganar yana kokarin aje kayan hannunsa a bakin kofa,d'agowa yayi ya daka mata tsawa"wuce kije ki wanka kafin na buge ki a wurin" juyawa tayi ta nufi cikin gida tana d'an k'unk'uni har ta nufi d'aki taji yace"bakiji mi nace kiyi bane? Da sauri tace "naji.." yace"to wuce ki dau bokiti ki d'ibi ruwa" ta wuce ta xuba ruwan ta shige band'aki,shima yana shiga wankan yayi a d'an band'akin cikin d'akin nasa ya shirya ya kwashi kayan da ya siyo ya nufi shago don jera su. Sai can bayan Issha gwaggo ta dawo,fatuu dai na k'unk'ume a d'aki cike da zullumin kar akawo k'ararta, koda ta fito tayi ma gwaggon sannu da zuwa dakin ta koma ita kam gwaggo a gajiye take hakan yasa ko ta kan Fatuu bata bi ba balle har ta fahimci wani abu,sai can dare gwaggo tayi bacci sannan ta fito taci abinci tayi sallah ta koma ta kwanta tare da yankewa ranta cewa baza'a kawo k'arar tata ba tunda har aka kai wannan lokacin. Washe gari asabar da safe Fatuu ce da Haulat zaune cikin ajin su na islamiyya,Haulat ta kalli Fatuu da murmushi tace"sannu hajiyar fad'a" wata yar dariyar iskanci fatuu tayi tace "waya ce maki nayi fada" d'an ta6e baki Haulat tayi tace "har gida akazo aka fad'a mana irin fadan da kuka yi, wai har kin fasa ma Murja baki da hanci" murmura idanu Fatuu tayi tace"Yessss,gobe ma ta k'ara gaya man banzan maganganu harta kirani da yar kauye" girgiza kai haulat tayi tace"ni wllh don kince Gwaggo bata nan amman a lokacin da sai na kai k'arar ki tunda ke dai baki da hakuri" harararta Fatuu tayi tace "aida da ta dawo kinzo kin kawo k'arartawa sarkin masu hakurin duniya" haulat tace "tunda ya rigada ya wuce miye na inzo,Amman ai naji ance wani mutum ne yayi maganinki da ki ka k'i barin fadan ya wanka maki mari" ta kai maganar tana tik'ar daria,wata yar iskar dariya Fatuu ta sake yi tace"hehehe ashe yai maganina,muka dai yi maganin juna don shima yayi asara ehe" haulat ta dakata da dariyar da take tace "what do you mean da ku kai maganin juna?wace irin asara kuma? Fatuu ta gyad'a kai da turancin ta na yar sakandire tace "what u hear" Still haulat tayi tana ta kallonta can tace "don Allah Fatuu fad'a man abunda kika yi masa" fatun na shirin yin magana Malaminsu ya shigo hakan yasata yin shiru daga nan kuma basu sake samun daman yin magana ba don yana fita wani ma ya shigo a haka har aka tashi,akan hanyar su ta komawa gida Haulat tace "d'azun na tambaye ki mi kika yiwa Mutumin baki gaya man ba" banza fatuu tayi mata,haulat ta sake cewa "kinji,mi kika yi masa ne" ba tare data kalleta ba tace"ke dalla bafa komai,wasa nike,ba abunda nayi masa kawai don kar kiyi tunanin yayi nasara akaina ne" haulat tace "kawai dai bazaki fadan bane Amman ko nayi rantsuwa ba zanyi kaffara ba tunda kika ce yayi asara da akwai abunda kika yi masa...." cikin tsiwa tace "ehh d'in nayi, tunda ba ki yarda ba abunda nayi masa ba" shiru haulat tayi amman ba don ta yardan ba,can tace "to ki kar6i jakar ki ko,kince in taho maki da ita kuma kin barni inata kayanta" juyowa Fatuu tayi ta figi jakar ba ko nagode tayi gaba abunta sai wurga kafa take da alama dai ta saba da yin tafiya haka,girgiza kai haulat tayi tace daga abun arziki,tabi bayanta har suka zo bakin lungun da suke rabuwa,haulat ta d'an daga murya tace "sai munhade Anjima hajia Fatuu ikon Allah" Fatuu ta juyo tayi mata kallon up and down ta k'ara gaba,Haulat dai dariya tayi a fili tace"Allah ya shirye ki" daga haka ta nufi hanyar gidansu, adai dai kofar shiga gida fatuu ta waiga tana kallon hanyar da haulat ta bi a fili tace "don ina sakarya Allah ya rufa man asiri in tona ma kaina,don na tabbata na fad'i mata sai ta fad'a ma gwaggo ko kuma tayi ta ma mutane nasihar banza ita ga mai hakuri yen-yen-yen" ta d'age baki daga haka ta shige gida. Haulat ce keta faman sauri da yamma zata islamiyya don ta makara sakamakon aikenta siyen gero da Innarsu tayi,tana k'okarin shiga lungun da zai kaita har islamiyyar taji daga gefenta ana magana "Ke,ke yar liman wait" da sauri ta juya tana kallon mai maganan,ya nufota yana wata irin tafiya irin ta nigas,da mamaki haulat ke kallonsa tana tunanin ita miye had'inta da Gaye da zai tsaida ta,yana k'arasowa yace"Ke dalla tambayanki zanyi kike ta faman zare ido uwa mujiya" ita dai haulat shiru tayi tana jiran jin abunda zai ce,ya ci gaba "dama tambayanki zanyi k'awarnan taki an kamata tana can cikin cell ne ko har anyi gaba da ita? cikin rashin fahimtar zancen shi haulat tace "wace kawar tawa kuma? Wata yar iskar daria yayi yace "kina da wata k'awa ne bayan Aljanar yarinyar nan mara jin magana, kullum ba tare nike ganinku ba" nan take ta gane Fatuu yake nufi don duk in suna tare suka had'u dashi Aljana yake cema fatun,da sauri haulat tace "to mitayi da za'a kai ta cell kuma? tayi maganar cike da fargaba tana ta zare ido, rik'e ha6a gaye yayi yace "wai kina nufin baki san aika-aikar da aljanar nan ta aikata ba...? da sauri haulat ta girgiza masa kai alamar a'a, jinjina kai yayi yace"tabb,to wllh ruwa ta 6allo ma kanta don ina tabbatar maki sai taje gidan yari..." da sauri haulat ta dafe k'irji tana salati tace"don Allah Gaye ka gaya man abunda tayi,ni sam wllh bansani ba" sai da ya gyara tsayuwa ya karkace baki yace "to bari kiji wani mutum ne jiya hakanan Aljanar nan ta jefar masa glass d'in bayan mota,gaba daya ta dagargaza glass din don wannan glass din yayi konden..." cikin tsananin tashin hankali haulat tasa hannuwanta duka biyu ta rufe bakinta ya ci gaba "atoh kima fad'a mata ta shirya don comfat (confirm) in ba'a biya shi ba har yakai k'ara na rantse da Assamadu sai taje fursun,yo motar fa ba k'aramar mota bace,to tsaya ma kiji,mai motar dan gidan Hajiyar Sanata ne kinsan kuwa ba'a k'aramar harka a gidan nan......" daga haka ya kad'a kai yayi gaba abunshi, kasa motsawa haulat tayi na tsawon lokaci da k'yar ta juya taci gaba da tafiya a hankali gabanta sai fad'uwa yake tamkar itace akace zata gidan yarin,cikin zuciyarta kam mamaki kawai take na abunda fatun ta aikata,ashe asarar da take nufin mutumin yayi kenan,"tabb lallai Fatuu bata da hankali!" ta fad'a a fili tana jinjina kai. A daidai bakin ajinsu ta tsaya tana tunanin shiga don tasan ta makara gashi akwae malami cikin ajin,can dai tayi shahada ta kutsa kai tare da yin yar sallama,d'an kallonta malamin yayi yaci gaba da bayanin da yake hakan yasa haulat yin saurin shigewa ta nufi wurin zamansu sai dai ga mamakinta Fatuu bata a wurin,tunani ta fara yi a ranta bayan ta zauna"to Fatuu bata zo bane? Kodai anje an kamata...wani irin bugu gabanta yayi da sauri ta d'ago da kanta a lokacin kuma ta hango fatun acan dayan bangaren,tunda haulat ta shigo ta wuce Fatuu ta ganta a ranta tace "da nice na makara da ya buge ni,ni da kowa ya tsana"ta saci kallon malamin ta d'an hararesa kafin ta juya inda haulat take nan take suka had'a ido don tunda ta hango fatuu take ta kallonta cike da al'ajabin abunda gaye yace zai sameta,murgude fatuu tayi mata ta juya,haulat ta girgiza kai cike da tausayinta,ta kuma fahimci dalilin da yasa fatun ta canja wurin zama don ta saba hakan da d'an abu ya hada su wanda bai kai ya kawo ba sai ta canja wurin zama sai tagadama ta dawo ko haulat taje ta bata hakuri sannan ta dawo,haulat ce kad'ai ke iya jure halin fatuu don ta karanci halayenta tsab shiyasa ma bata biye ta. Haulat ce keta sauri ta isko Fatuu don da aka tashi ta tsaya copying rubutun da malam yayi bata nan daga littafin wata kawarta da suke zama tare,ita kuwa Fatuu ana tashi tayi gaba abunta don guje ma haulat din take karta k'ara tambayarta game da asaran da tace Mutumin daya raba su fad'a yayi don tasan halinta wani lokacin nacin tambaya ne da ita kuma karshe inta gano tana iya zuwa ta fadi ma gwaggo "Fatuu!fatuu ki tsaya" haulat dake biye da ita a baya tace,ganin bata da niyyar tsayawa yasa haulat yin dan gudu tasha gabanta,cak fatuu ta tsaya fuska ad'aure tace "miye haka zaki wani shage gaba na" kasa magana haulat tayi don k'arfin halin fatun mugun mamaki yake bata ta aikata irin wannan babbar ta'asar amman hankalinta akwance,tsoki fatuu taja tana kokarin bin ta gefen haulat din,taji tace "To ai yanzu nasan abunda kike 6oyewa hajia" da sauri fatuu ta kalleta sama da k'asa tace "ni mi nike 6oyewa? Haulat ta jinjina kai cike da takaici tace "asarar da kika ce mutumin nan yayi na tambayeki wace asara ce kika k'i fad'a man to yanzu nasan komai,ke yanzu fatuu abunda kika yi kin kyauta?hakanan ki jefar ma mutum mota har ki lalata masa glass....."katse ta Fatuu tayi da fad'in "naje na fasa d'in,dama nasan ai sai kin bi diddigi don kin saba sa man ido,to na fasan kuma ko gobe ya k'ara shiga harkata har ya d'aga hannu ya mareni sai na kara ja masa asara don ni ba ai man na kyale ehe" daga haka ta kad'a kai tayi gaba,cikin d'aga murya haulat tace "to kinsan wanene kika fasa ma gilashin mota.....? a fusace ta juyo tace"ina ruwana da ko waye,Allah yasa d'an sarkin makkah ne" ta juya taci gaba da tafiya abunta don ita tayi tunanin tambayarta haulat d'in tayi,cike da takaici haulat tai tsaye tana kallon bayanta a fili tace "lallai Fatuu bata da hankali wllh bata san bala'en da ta jawo ma kanta bane,tama k'i ta tsaya ta saurare ni...." girgiza kai tayi ta fara tafiya tana ta sak'e sak'e a ranta "ko dai inje in sanarma gwaggo don tasan halin da ake aciki..." girgiza kai ta sake yi da sauri a fili tace "kai a'a,bai kamata ta fara jin wannan mummunan labarin daga baki na ba gaskia" can kuma tace "to wai ma ni ina ruwana da zan damu,ita wadda ta aikata laifin ma ko a jikinta,kawai dai ba dad'i ne kana tare da mutum wani mummunan abu ya same shi,to amman tunda ita taja ma kanta ai ita ta sani" ta watsa hannuwa,daina bin bayan fatun tayi,ta canza hanya,lokacin da fatuu zata sha kwana ta juya bata ga haulat d'in ba ta6e baki tayi a ranta tace gwara da nayi mata haka inba haka ba sai tace zata zo ta gaya ma gwaggo,a fili tace "inma tazo ta fadan sai in k'aryata ta tunda dai ba a gabanta akayi ba kuma bata da shaida" tayi k'wafa tace "ta sake ta gaya ma gwaggo wllh 6atawa zamu yi ba ruwana da ita" tayi maganar tana mummurgud'a baki,To hajia Fatuu ba dai yau kika fara fadin haka ba,kuma ko kun 6ata da kanku dai kuke shiryawa don keda haulat sai Allah. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* *Mallakin* ⬇️ *ZAINAB LALUH*🌹 *(Oummu imam)* Free Page1️⃣8️⃣ Gwaggo ce ta fito daga cikin kitchen lokacin ba'a dade da gama sallar isha ba,hannunta d'auke da d'an kwanon silver madaidaici rufe da murfinsa asaman shi kuma bakar leda ce dauke da wani abu an kulle, tsayawa tayi ta fara kwala ma fatuu kira "Fatuu,fatuu,Worei mi lilma", leko kanta tayi ta jikin labule tace" ina zaki aike ni?" hajia zaki kaima tuwon nan nasanta da son tuwon dawa" da sauri ta fito jin za'a aiketa wurin Hajiyar Sanata,hannunta rik'e da k'aramin bak'in gyale ta fara k'okarin cire hijab d'in islamiyya dake jikinta tana fad'in "dama kwana biyu banje ba wllh...." Gwaggo tace"to miye na cire hijab d'in kuma,kibarta mana" turo baki tayi tace"ni nafi son in sa gyalen kinga na fi shan iska ma", gwaggo tace "A daren nan zaki sa wannan figaggen gyalen da iyakarsa kafad'a,to bar aiken ni bari in mik'a mata da kaina..." da sauri tace "a'a to yi hakuri nabar hijab din" tayi maganar tana d'aga hannu alamar ban hakuri, gwaggo ta mik'a mata kwanon tace "kiyi maza ki kai mata kidawo,sauran kuma ki tsaya shiririta sai tsakan dare ki dawo" dariya tayi ta amshi kwanon ta rungume tana fad'in yanzun nan zan dawo kakus, Gwaggo tace "to ki d'aura akai mana salon miyan ta zubo ta 6ata maki hijab din", fatuu tace "bazata zubo ba zan kula" abunda gwaggo bata lura ba fatun ta 6oye gyalen da ta hanata sawa a kasan hammata shiyasa tak'i daura kwanon aka don kar ya fad'o ta gani, A zaure ta aje kwanon k'asa ta cire hijab din ta sagale ta jikin windon d'akin kawu Amadu tasa gyalen kana ta nufi gidan Hajia. A daidai gate ta tsaya wurin Officer dake zaune shi kad'ai tace"Sannu da gadin gate Officer" ya d'ago ya kalleta yana daria,don maganar tata ta bashi dariya yace "Yauwa kema sannunki yar fillo" tace "kai kad'ai a zaune ina d'ayan Officern yake? Rausayar da kai yayi yace ya tafi yin wani uzuri ne" ta ta6e baki tace "ba wani uzuri wayo yayi maka yanzun haka zance ya tafi wurin Budurwarshi ya barka kai d'aya kana ta aikin tsaro,wllh kada ka yarda ya maida kai sakarai kaima ka rama atoh" jinjina kai yayi yana d'an murmushi jin abunda tace,sam baiji komae ba don yasan ta sam ba datsar k'umba gareta ba duk abunda yazo bakinta fad'i take yace"to yar fillo ya zanyi in rama d'in? turo baki tayi tace "nifa ka daina ceman yar fillo" kyalkyacewa da dariya yayi don dama yasan bata son sunan yace "to ke ba yar fillon bace? tace "to nidai banso ka kira ni da Fatuu na kawae" yace "to shikenan hajia fatuu na bari,sai a fad'i man yadda zan rink'a ramawa nima" tace "yo kaima budurwar zakayi sai ka rink'a tafiya tadi....." katseta yayi yace "to ni ina zan samu budurwa nida kullum ina nan zaune ina tsaron gate" tace "Yo yadda yayi shima ya samu zaka yi" ta juya tana k'okarin shiga gidan yace "to ko ke kizama budurwar tawa kawai ma...", A fusace ta juyo bayan ta tsaya ta bishi da wani kallo,shi kam sai daria yake,tace" God forbid! ni bazan zama budurwar kowa ba yanzu sai na zama likita,kuma lokacin ni nafi karfin mai gadin gate,tana gama fad'in hakan ta shige sai kuma ta sake lek'owa ta cikin gate din tace "in budurwa ka ke so kaje wurin kawata Haulatu don ita ban ji tana da burin zama koda malamar makaranta ba,kuma nasan zata so ka don sakarya ce" daga haka ta shige tana ta tik'ar daria,shima Officer dariyar yake yana girgiza kai. A corridor ta tsaya ta cire takalmanta sannan ta d'an lek'a cikin parlon a hankali ta hango hajia dake zaune saman 2-seater ta d'aura takardu saman sofa table tana rubuce rubuce idanuwanta sanye cikin gilashi,cikin d'aga murya Fatuu tace"Assalamu alaikum ga bak'uwa,ga bakuwa daga makkah" hajiya ta d'ago ta kalli entrance tana daria,fatuu ta k'ara maimaita abunda tace,Hajia ta girgiza kai tasan in ba amsa mata tayi ba,haka zatai tayi tace"Maraba da bakuwa mutan makkah shigo" shigowa fatun tayi tana ta kyalkyalar dariya itama hajiyar dariyar take tace "ja'ira", kusa da ita fatuu taje ta zauna tace"Hajiyar Sanata ina wuni" Hajia tace "lafia lou yar gidan hajiar sanata,kwana biyu baki zo kika gaida hajiyar taki ba, jiya juma'a inata zuba ido banga kinzo yiman barka da juma'a ba" Fatuu ta d'age kai ta kwanta jikin kujerar tace "Ai jiya ban je ko ina ba a d'aki na wuni kamar maijego" ta kai maganar tana ta daria,hajiya dake kallonta tace "hala rigima kika janyo?", "a'a" Fatuu tace tana kunshe daria, Hajia ta girgiza kai tace"habawa,nida nasan hali,hakanan ba ciwo ba mi zai sa ki wuni a d'aka,har yanzu dai kin k'i daina yin rigima da mutane ko Fatima? dago kanta tayi daga jikin kujerar ta d'an turo baki tace"wllh hajiya mutane ne ke tono na..." hajiya dake kallonta ta katseta"ke kuma ba hakuri ko" dariya kawai fatuu tayi,hajiya tace "gaya man abunda yasa kika wuni a daki" sosae gaban fatuu ya fadi a ranta tace "tabb wllh bazan fadi mata na fasa ma wani glass ba" a fili tace "wata yarinya ce muka yi fad'a na fasa mata hanci da baki" ta kai maganar tana nok'e kai,hajia dake kallonta ta girgiza kai tace "kai jama'a! Yanzu ina amfanin haka fatima,aita gaya maki magana baki ji,ke sam baki da hakuri to kuwa kwanan nan zamu 6ata wllh,6atawa kuma ta har abada kar ma kiyi tunanin zaki ban hakuri in hakura...."da sauri Fatuu ta saukko daga kan kujerar ta duk'a gabanta tace "Don Allah Hajiar Sanata kiyi hakuri wallahi tallahi ita taja ni kinji na rantse,daga nace ta matsa man wuri a Bus din makaranta in zauna bayan an tashi,ta fara gaya man maganganu nai shiru na kyaleta,hakan bai isa ba da muka sauka taci gaba har tana fad'a ma abokanta wai ni daga k'auye aka kawoni..." tayi narai narai da idanu kaman zata yi kuka, Ajiyar zuciya hajiya ta sauke tana ta kallon fatuu da har kwalla sun cika idanunta, tasan dama hakan sai ya faru don bata son taji tace zasu 6ata,tace"shikenan tashi ki zauna,amman don Allah Fatima ki rika hakuri kinji,yawan fad'an da kike da mutane shiyasa suke tsokanarki ai,ki koyi kauda kai akan abunda bai kai ya kawo ba kinji yar gidan Hajiya" ta k'arasa maganar ta sigar lallashi, Gyad'a kai Fatuu tayi ta koma kan kujera ta zauna tana murmushin jin dadi,hajiya ta kalli kanta da gyalen ya d'an zame tace "wai har yanzu baki je an kitse kan nan ba? ko rannan ba saida nayi maki magana akan kije ayi maki kitso bane?" Ta marairaice fuska tace "wllh Balarabar ce zafin hannu ne da ita hajia,in tayi man kitso kaman kan zai tuge gaba d'aya,ni shiyasa banson zuwa" hajiya tace"ba wani zafin hannu,nima ai tana man kitson ko,kawai dai baki son kitson ne,don ma Allah ya taimakeki gashin mai kyau ne ai da tuni ya lalace yadda baki kula dashi d'in nan,bari in Balarabar tazo yiman kitson ai nasa tayi maki shi a gabana kuwa", ta juya ta kalli kwanon da fatuu ta aje saman carpet da ta shigo tace"mina samu da daren nan haka" Fatuu ta d'ago tace "tuwon dawa ne,Gwaggo tace na kawo maki" fuskar hajiya d'auke da murmushi tace"Aikam nagode wllh,dama kwana biyu banci tuwon dawa ba,gashi Dije badai iya tuwo ba....." Fatuu tace"nikam dai ai ta kusa ta kashe ni da shi" Hajiya tayi daria tace "A ina ki ka ta6a ganin tuwo ya kashe mutum fatima?" Shiru tayi tana ta turo baki,hajia dake ta daria tace"to kinga tashi kidau kwanon miyan nan kije kitchen kisamu bowl mai kyau ki juyo man miyan sai ki daukko man plate in saka tuwon inci abuna yanzu yabi jiki kafin in kwanta,sai ki wanke kwanon ki zubo abinci na nan a kicin d'in kije kici tunda ni dai bazanso tuwon ya kashe ki ba" ta k'arasa maganar tana ta tik'ar daria, Mik'ewa fatuu tayi ta dau kwanon miyan da ledan tuwon ta nufi kitchen,Hajia tace"ki fara zubo man ruwa a roba in wanke hannuwa", juyo miyan tayi ta warware tuwon a plate ta kawo ma hajia,har ta juya zata koma kicin don zubo abincin ta waiwayo tace"Hajia ina Aunty Saude ne? Hajiya da har ta fara cin tuwon tace "tana a backyard taje ba su d'awisu abinci" fatuu tace "aikuwa bari inje bayan,dama kwana biyu ban gaisa da mutumina Aku ba...." hajia ta katse ta "A'a kar kije bayan nan,kije ki d'ibo abincin kizo ki tafi kinga dare yayi,na tabbata kika je wurin Aku kuma ai sai an biyo sawunki,ki bari gobe in Allah ya kaimu,ana tasowa islamiyyar safe sai kizo kusha fira dashi,yanzu je ki zubo abincin ki ciko kwanon" Fatuu ta gyad'a kai taje ta zubo abincin wanda dafa dukan couscous ne yaji uban kifi sai k'amshi ke tashi,ta dawo parlon ta aje kwanon akan carpet ta nufi kujerar dake kusa da telephone ta zauna lokacin Hajia har ta kusa cinye tuwon,Fatuu tasa hannu ta dau kan telephone din ta kara a kunnanta ta d'aura kafa d'aya kan daya tana murmura idanu,tace"Hajia" hajiya da ta tura tuwo a baki tace "Uwun" tace "wllh in nazama likita sai na sayi irin wannan telephone d'in kuma har a Office dina na wurin aiki zansa" hajia tace "to Allah ubangiji ya bada ikon zama likitan,amman a Office dinma gwamnati zata sa maki ba sai kinsha wahalan siya ba.....", Saude ce ta shigo cikin parlon ta kofar baya hannuwanta rik'e da wata roba mai d'an fadi,tana hango fatuu ta aje roban a bakin kofar kicin ta nufo cikin parlon da fara'arta tace "Ah Fatuu yar gidan hajia yaushe ki ka shigo" Fatuu tace "tun d'an dazun,ai naso inzo bayan hajiya ta hana" ta d'an saci kallon hajia tana turo baki,ita dai Saude Murmushi kawae take, Hajia ta girgiza kai ta kalli saude tace "to wai wurin Aku fa zata da daren nan" Saude ta jinjina kai tace"lallai kam gara ki bari sai gobe don in ki ka je yanzu har sai an biyo ki nasan" Hajia ta gyad'a kai alamar atoh, tace"Saude kije bedroom a bedside din hagu da kin jawo drawer d'in farko akwae kudi ki daukko yan ashirin guda biyar ki kawo man" Saude ta amsa da "to" ta juya don cika umarnin hajiyan. Hannunta ruk'e da kudin ta dawo dan russunawa tayi ta mika ma ta,hajia tace tsaya ina zuwa,ta juya kan fatuu da ta yi mitsi mitsi da idanu ta d'age baki tana kallo tace "to taso ki tafi kinga har tara saura,yau dai banda wani abun ci,amman gashi kije ki siya ko biscuit ne" Fatuu ta mik'e tana fadin"to ki bashshi mana" Hajia tace "a'a,ai yaba kyauta tukwuici,na yaba da tuwon naji dadin shi kwarae,kice mata nagode Allah yabar zumunci,ya kara zakin hannu" takai maganar tana murmushi, Saude ta mik'a mata kudin,ta duk'a ta dau kwanon tace "Sai da safe Hajia" ta juya kan Saude tace "zanzo gobe da safe in antaso islamiyya Aunty Saude", Saude da fara'a tace "to Allah ya kaimu" daga haka ta rungume kwanon a 6arin hannunta na dama ta nufi hanyar fita....... *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* *Mallakin* ⬇️ *ZAINAB LALUH*🌹 *(Oummu imam)* _GARGADI!_ _Wannan littafin ni na kirkire shi,komae kaji yayi daidai ko shige da rayuwar ka/ki ko wani/wata to arashi ne ba da nufi bane kuma ina mai bada hakuri,Don haka kasantuwar littafin nawa ne,ban yarda wani/wata su canza mun littafi ba ko daukar wani bangare daga cikinsa ba tare da izini na ba,Haka ban amince ba,ban yarda ba,ban lamunce ba a yada man shi ba a wata kafa ba misali,YouTube da makamantansu,ba tare da an tuntube ni ba,ni mai littafin don neman izini,Don haka a kiyaye! kuma idan ka ko kin san ba wani muhimmin abu bane Don Allah kar ayi man magana don bazan kula mutum ba,Don haka mu mutunta kanmu_🤝 *Free Page1️⃣9️⃣&2️⃣0️⃣* Fatuu na fitowa harabar gidan aka bud'e ma Haisam gate ya shigo,parking space ya shige ya parker bike din,ya fito jakar shi rataye a 6arin hannunshi na hagu,hannunshi na dama rike da Bottle water ya d'aga yana d'an sha a hankali ya nufi part dinsa, Fatuu kuwa tsaye tayi a tsakiyan harabar ta rike k'ugunta da d'ayan hannunta da ba komae,a fili tace "Kai! waye wannan kuma da ya shigo a saman waccan dirkeken babur d'in dana gani rannan a ajiye? Ko bak'o akayi bansani ba" yadda tayi maganar kamar irin gidan ubantan nan. Fatuu bata ta6a ganin haisam cikin gidan ba,don bai dade daya dawo ba weekend dinshi na biyu kenan,dama kuma tafi zuwa gidan ranakun da ba islamiyya Alhamis da juma'a saboda Working days ba lokaci da safe taje boko da yamma kuma islamiyya haka Weekends ma Safe da Yamma tana islamiyya sai dai ko da dare in an aikota kaman yanzu da aka aiko tan shima aiken akan kwana biyu ba'a aiko ta ba,Wani lokacin kuma tana cema gwaggon zata zo ta gaida Hajiar in dare bai yi ba sosae,kuma da tazo suka gaisa hajia zata ce ta tafi gida dare yayi.Ranar Alhamis da ta wuce tazo gidan da yamma kaman yadda tace ma Gwaggo bayan ta fito ne ta biyo Jamila suka yi fad'a har ta zubar mata da Awara a lokacin ne kuma ta fara ganin Haisam d'in. Ganin haisam na niyyar shigewa corridor yasa ta bi bayanshi da sauri tana fad'in "Aikuwa sai naga ko waye" daidai lokacin da ta iso bakin fence door d'in shiga part d'inshi,shi kuma yana taka matattakalar hawa balcony,jin kaman motsi a bayansa yasa shi dan juyowa,da sauri Fatuu ta koma gefe ta la6e,a hankali ta lek'o da kanta lokacin ya kama handle din kofa zai bud'e ya sake waiwayowa nan take ta gane fuskarsa don gaba daya hasken fitilu ya haske wurin kaman da rana,da sauri tasa tafin hannunta ta rufe bakinta ta juya da d'an gudu gudu tabar wurin,ko amsa saida safe da Officer ke mata bata yi ba,ta yanki hanyar gida tana yi tana waiwayen bayanta,har tana yin tuntu6e, tana zuwa daidai kiosk din kawu Amadu yace"Ke,daga ina ki ke? Cikin rawar murya tace "d..daga gidan h..hajiya tuwo na kai mata" Yace"miye a cikin kwanon nan" bata bashi amsa ba sai kawai ta bud'e masa kwanon,da yake akwae wuta nan take yaga abunda ke ciki yace "Ah nima kam zanci in kin shiga ki d'an zubo man a plate" tace "toh" daga haka ta shige gidan da sauri,har lokacin hijab d'in da ta d'aura jikin window na nan,tasa hannu ta ciro ta wuce ciki,a bakin kofar kicin ta aje kwanon ta shige d'aki, fad'awa tayi saman Gado ta takure wuri d'aya sai faman zare ido take cike da fargabar Mutumin nan da ta gani,a ranta kuwa sai maimaita abu d'aya take "dama a gidan hajiya yake...!" a fili tace "Innalillahi,to ko ya gaya ma hajia..!!! Can kuma tace "to amman da ya gaya mata ai da tayi man magana" ta rik'e ha6a alamar tunani, Ta ci gaba"to ai bai san ni ko wacece ba,kai kilan ma ya fad'a mata fa" ta shiga yarfa hannuwa tace"Aikuwa in hajia tasani ta kuma gane ni ce...." shiru tayi saboda wani bugu da kirjinta ke yi sai zaro ido take, Gwaggo ce ta fito daga d'aki hannunta rik'e da buta zata band'aki,daidai kitchen ta tsaya tana kallon kwanon da Fatuu ta aje a ranta tace "Ah wannan ba kwanon dana aiki fatuu dashi bane,yaushe ta shigo gidan? hannu tasa ta bud'e kwanon k'amshin couscous din ya bugi hancinta,tace"tabbas fatuu ta aje shi" d'agowa tayi ta kalli bakin kofar d'akin Fatun bata ga takalmanta ba don dasu ta shige d'akin hakan yasa tayi tunanin ficewa ta sake yi kenan,kwafa tayi a fili tace "zata dawo ta same ni,saita fad'an inda taje a daran nan" daga haka ta wuce band'akin. Shiru shiru gwaggo nata jira taji shigowar fatuu,har bayan wani lokaci bata ji ta shigo ba hakan yasa ta fito ta nufi kofar gida ta lek'a ta wawwaiga ko zata hange ta amman bata ganta ba, wani yaro ta hango tsaye a bakin shagon Amadu tace "Kai yiman kiran Amadu don Allah" tunkan yaron yayi magana Amadu yace mashi "naji", bayan ya sallami yaron ya bud'e kofan kiosk din ya fito ya nufi inda Gwaggo take tun kafin yace wani abu gwaggo tace mashi "Fatuu fa? Da mamaki ya maimaita sunan fatu yace "ba tana a cikin gidan ba? tace "a'a bata nan" shiru yayi yana tunani can yace "gaskia nadai ga sanda ta dawo daga gidan Hajiyar Sanata tace ke kika aiketa,harma naganta ta dawo da abinci nace ta d'an zubo man" Gwaggo tace "to ta kawo ma abincin? Yace "a'a,tunda ta shiga banga ta fito ba gaskia,kin duba d'akinta? Tace "ai ko takalmanta babu a kofar d'akin,shiyasa ma ban duba ciki ba,don nasan in tana nan zan gansu a bakin d'akin" Amadu yace"ki dae duba cikin kilan ta shiga dasu don dama kaman a firgice take ta shiga gidan", Gwaggo ta ta6e baki tace " wannan daman ai koda yaushe ma a firgice take,bari in duba d'akin to" har ta nufi ciki ta juyo tace"ka shigo ga abincin can a kofan kicin sai ka d'iba ka rage mata" yace "toh" daga haka ta nufi d'akin Fatuu,tsayawa gwaggo tayi cike da mamakin ganin fatuu kwance saman gado ta duk'unkune wuri guda,ta nufeta ta d'an leka fuskarta sai taga bacci take,gwaggo tace "bacci kuma.." hannu tasa ta d'an bubbuga k'afafunta aikuwa nan da nan ta farka firgigit sai zare ido take tana kallon gwaggon, Gwaggo ta mik'e tana k'are mata kallo tace"yaushe kika shigo gidan? Kuma lafiya kike yin bacci haka? Saukko da k'afafunta tayi k'asa tace "tun d'azun na shigo"tasa hannu tana goge idanunta, "amman ba ke kika zo da abincin da na gani a kofan kitchen ba" tace "ni nazo da shi,hajiya ta bani" Gwaggo tace to "bazaki ci bane kika aje kika zo kina bacci,kuma ma nasan ko salla baki yi ba" ita dai fatuu sai faman zare ido take hakan yasa gwaggo tace"wai mike damunki ne kike ta faman zaro idanu,da gani baki da gaskia,halan wata rigimar kika jawo,don nasan wannan baccin dama ba na Allah bane,da gani na rashin gaskiya ne" gaban fatuu ya fadi rass cike da tsoro take kallon gwaggon, tasan in har gwaggon taji abunda ta aikata kashinta ya bushe balle kuma taji mutumin dan gidan hajia ne tabb......,tsawa taji gwaggo ta daka mata "ba dake nike bane fatuu,mi ya faru ki ka zo kika kwanta haka? A daburce tace "da..dama kare ne ya biyo ni" sam bata san ta ambaci karen ba, Gwaggo ta harareta tace"kece ke tsoron wani kare,sau nawa kike zuwa kina tono karen,ina kwanan nan kika je kika kinkimo d'an karya ta biyo ki har kofar gida,shine zaki wani ce man kare ne ya biyo ki...." da sauri ta katse gwaggon ganin zata gano k'arya take tace "ai ba irin shi bane fa,wannan fa irin mai gashi buzu buzu ne mai kaman zaki" ta kai maganar tana ta zare idanu tana hadiyar yawu, gwaggon tace "to ke miya had'a ki da irin wannan karen, ina ki ka ganshi da zai biyo ki? tace "ina fitowa daga gidan hajia wani mutumi yazo zai wuce dashi shine yaji kamshin abincin hannuna yayo kaina shine na rugo" gwaggo ta girgiza kai don ta yarda da abunda fatun ta fad'a,tace "Allah ya kyauta to" da sauri fatuu tace "Amin,ganin ta yarda da k'aryar da ta gandara, Gwaggo ta juya tana fadin "ki fito kici abincin,kiyi sallah sai kiyi baccin da kyau..."daga haka ta fice,fatuu ta dafe kirjinta alamar tasha,ta mik'e tabi bayan Gwaggon. Amadu na gab da fita hannunshi rik'e da plate din daya d'ibi abinci yaji gwaggo ta fito daga dakin fatuu tana magana,ya juya yana tambayarta fatun na ciki? Gwaggo ta ta6e baki tace "tana nan,wai kare ne ya biyo ta shine ta tsorata,harda su baccin dole" dariya Amadu yayi yace "Ashe akwae karen da zai iya firgita ta haka"ya girgixa kai daga haka ya fice. Washegari Safiyar Lahadi,Fatuu na zaune a ajinsu na islamiyya,tana ta zuba ido taga zuwan Haulat don dama tana riganta zuwa saboda gidansu Fatun yafi kusa da Islamiyyar inta biya ma haulat d'in ta koma baya sosae,sai dai ko in haulat din ta fito da wuri su hade sai in an tashi ne suke tafia tare, Har aka kusa tashi shiru haulat bata shigo ba,hakan yasa fatuu ta fara damuwa a ranta kuwa tunani ta shiga yi tana fadin"To lafia haulat bata zo ba??,sai kace ba fushi fatun take da ita ba,duk tabi ta damu,har aka tashi islamiyyar Haulat bata zo ba,hakan yasa fatuu ta yanke shawarar zuwa gidansu ta gani ko lafia, Tafe ta ke ita kadai a hanya don sam bata da k'awar da take tare da ita inba haulat ba, duk wadda ta fara k'awance da ita ba'a daukan lokaci ake rabuwa ta tsiya tsiya, da fatuu taga mota ta taho sai ta rufe fuskarta wai don kar ace mutumin nan ne na gidan hajia,dama ko da safe da zata zo islamiyyar cikin dar dar ta fito daga gida,karshe ma da gudu ta shige lungun jikin gidan hajiyan duk don kada Haisam ya fito su yi kacibus,a ranta ta ke cewa"Yanzu shikenan sai dai in daina zuwa gidan Hajiar...."ta girgixa kai a fili tace"kam aikam bazan daina zuwa ba tunda ma naga hajiyan bata sani ba ai" "to kuma in ku ka had'e wata rana yace ma hajiyar kece ki ka fasa masa gilashin mota fa?? wani 6angare na zuciyarta yace, sosae gabanta ya fad'i ta kasa cewa komae, Daidai lokacin da ta karya kwanar da zata hau layin gidansu a lokacin kuma Gaye da Abokinshi suma suka shigo kwanar,kai da kagansu sai dai kace Allah ya shirya,tun daga kan askin kansu har zuwa shigar da suka yi,tsayawa yayi yana yin arba da Fatuu,ya rik'e baki da hannunshi guda yace "Kee! Wai har yanzu kina yawo a gari ba'a damk'e ki ba? Wani irin kallo Fatuu tayi mashi tace "A damk'e ni akaini ina? Gaye yace" inda ya cancanta akai ki wato gidan yarii...." Idanu waje Fatuu tace "kaji man gaye da Muguwar fata,yo minayi za'a kaini gidan yari??? Wata yar iskar dariya yayi "Oh baki ma san mi kika yi ba ko,to glass din mota da kika fasa ma wannan mutumin rannan.."sakin baki fatuu tayi tana kallonshi cike da mamakin yadda akai yasan hakan,ya ci gaba "nasan komae yarinya ki ke wani kallo na,don akan ido na kika jefi motar,Oh ke kin d'auka kin jefi banza ko" ya k'ara shek'ewa da dariya "to billahillazi baki ci bulus ba,ruwa kika 6allowa kanki,don kud'in wannan glass din ko wanda ku ka fito ciki d'aya kika fasa mawa na rantse da sarkin da yake busan numfashi bazai kyale ki ba,yo kin kuwa san nawa glass d'in nan yake? Fatuu dake tsaye kaman gunki zufa har ta fara tsatstsafo mata ta girgiza masa kai alamar a'a,gabanta sai fad'uwa yake,Yace "to wannan gilashin yayi naira miliyan d'aya,don ita kanta motar zata yi miliyan 10..." Fatuu ta zaro idanu waje gaba d'aya,sai Maimaita million d'ayan take a cikin ranta,a razane tace "Nawa ne Miliyan d'aya? Gaye da ke kallonta,da mamaki yace "yo ke dama hakanan kike zuwa makaranta kwalwar kifi ce dake,miliyan d'ayan ce baki sani ba? Da sauri tace"nasani, kawae yawan kudin ne a zahiri ban sani ba don ban ta6a ganinsu ba" Gaye ya gyara tsayuwa yace "to kinsan dubu d'ari?" "dubu d'ari..." ta maimaita tana dan tunani,can tace"Eh nasani,Baffa na ya ta6a saida shanuwa dubu dari da talatin kuma har kud'in ma na rike a hannuwana,daya hannu na rike dubu d'arin,dayan kuma dubu talatin d'in" da sauri yace"Yauwa toh,ita dubu d'arin irinta sau goma sune miliyan daya,kudin gilashin kenan,ai mu ma barshi a kudin shanuwar sau goma kawae..." Cikin tsananin tashin hankali Fatuu ta katse shi, "kace kuma dubu d'ari sau goma yanzu kuma kace duka kudin shanuwar...." Gaye ya katse ta"Oh kina nufin baza'a biya kudin gyara ba kenan,ai dole abashi harda na wanda zai yi aikin sa glass din ko Aljana" Idanu waje fatuu ke kallon gaye tama kasa yin kwakkwaran motsi ga zuciyarta dake bugawa ba k'akkautawa lokaci guda taji fitsari na niyyar zubo mata,kana kallonta zaka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki ba kad'an bane, zuciyarta kuwa tana bugawa tana maimata mata "kudin shanu gomaaa!!!" Kamar Gaye yasan abunda take fad'a a zuciyanta yace "kin dai san bazan maki karya ba,don ba inda bama fad'awa a Nigeria,har legas dai tasan da zamana,ba kalar motar da bansan kud'inta ba,ke har kudin jirgi na sani balle wata mota k'aramar Alhaki. Abokin gaye da tunda suka tsaya bai tanka ba kunnansa d'aya mak'ale da earpiece yana sauraron waka yana dan jujjuya kai,yasa hannu ya cire earpiece din yace"Baabah wai yane? mi tayi ne naji sama sama kana ta mata bayani harda uban lissafi?" Gaye yace "ruwa ta 6allo ma kanta baabah....,nan ya bashi labarin abunda fatun ta aikata, yace "na gidan da muka wuto yanzu ka ke tambayata gidan waye,nace ma gidan Uwar Sanata ne kuma Matar tsohon Ministan tsaro? Abokin ya gyad'a kai alamar"Ehh,gaye yace"to mutumin gidan ne ta yi ma wannan aika aikar,don ni farko ma bansan d'an gidan bane ina dai d'an ganinshi kwanan nan yana wucewa a Motoci kala kala,har wani gangamemen Bike yake hawa,ina jin wannan bike din yayi million goma shima ko ma fi, sai shekaranjiya tsoho yaja ni zuwa sallar juma'a a Masallacin gidan,na ganshi tare da Hajiyar sun zo suma,to nan nagane dan gidan ne ashe" Ya cigaba"Kasan masu kudin nan da shegen wayo,in suka gina tangamemen gida sai suyi dan Masallaci wai Allah ga naka,don kar a masu surutun basuyi ba,duk da dai su nasu babba ne" yana maganar yana watsa hannuwa sai kace mai yin debate, Abokin fuskarshi da mamaki yana jinjina kai yace "kai kace master ce ta rashin ji" Gaye yace"ehh mana,wannan da kake gani furofesa ce ba master ba,don inta 6allo wani aikin yasin ko ni jinjina mata nike,dubi dai abunda ta aikata yanzu ni yaushe zan fara haka,ban aje ba,ban ba wani ajiya ba,Iyaye kuwa sai dai ace lahaula saboda talauci" yana maganar yana wani janta, Abokin ya kwashe da daria yace kama aikatan ai kasan inda za'ai da kai,billahillaxi gidan yari straight inbaka biya ba,aje aita cin gabza.."Gaye ya tuntsire da dariya yana rik'e wando, Yace"Allah yai man tsari da cin gabza baabah,shiyasa nike taka tsantsan,nadai je cell inyi kwanaki in fito don wannan yama zama gida,don ina daraja tuwon gyatuma ta,baka sanin dadin shi sai an had'aka da gabza yasinn..." gaba d'aya suka tuntsire da wata yar iskar dariya,ita dai Fatuu sai kallon su take tamkar yau ta fara ganinsu,zufa kuwa tuni ta lullu6e fuskarta,sai had'iyar miyau mai d'aci take. Abokin gaye ya kalleta cikin nuna tausayi yace"Wayyo baiwar Allah na tausayi maki wllh,yanzu zaki bar tuwon gyatumarki ki koma cin gabza,duk wannan hasken fatar naki da kyawun fuskar ki sai ya disashe qur'an,in kuma kina da gashi to duk kwarkwata sai ta cinye shi,sai dai ko in kuna da kud'i sai ku biya shi abunshi kawae...." Gaye ya katse shi da sauri "yo ina suka ga wani kud'i duk kanwar ja ce yasin,itafa kakarta ke ruk'onta kuma in fada maka kakar attendar ce a asibiti irin masu share share da goge gogen nan,ina zata ga miliyan d'aya ai yasin ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba,ko kwatan miliyan bata da" Abokin yace "Kace dai dole sai anje an had'e da gabzar dai...." da sauri Gaye yace "Comfat,don a ranar sai da ya tambayeni nayi masa kwatancen gidansu,shiyasa nayi mamaki dana ganta har yau ba'ai ramm da ita ba, amman nasan kilan sunje basu samu kowa a gidan ba,kuma kaga jiya da yau ba aiki,amman na tabbatar gobe Monday dole azo a damk'e ta", Ya juya kan Fatuu yace "To Aljana,sai ayafi juna,sai Allah kuma ya k'addara za'a sake ganawa,don can d'in ba sauki, wasu ma wuya ke kashe su, nidai na yafe maki" daga haka ya juya kan abokin nashi yana fad'in "hayya,Baabah mu ware ko.." suka yi gaba abunsu suna wata yar iskar tafia. Kasa motsawa Fatuu tayi daga inda take don k'afafunta ba k'aramin nauyi sukai mata ba,Kalaman gaye na k'arshe sun matuk'ar razana ta"Ashe mutumin har yasan gidansu...! Shine abunda ya kara tada mata hankali,kallonsu gaye tai tayi har suka 6ace ma ganinta, irin su Gaye sai su kashe mutum,don halin da Fatuu take ciki tsaff zuciyarta zata iya bugawa don tunda take bata ta6a janyo rigima irin wannan ba,iya ta 6arar ma yara abu gwaggo ta biya ko ta bugi mutum har ta raunata shi gwaggon ta biya kudin zuwa chemist ta tsaya,yau gashi ta janyo rigimar da tabbas tafi karfin gwaggon,duk'awa tayi a wurin don kafafunta rawa kawae suke,ga kwakwalwarta sai tariyo mata da maganganun gaye take,bugun zuciyarta na k'ara tsananta ga zufa da ta wanke mata fuska har wuyan Hijab dinta ya fara jik'ewa,da za'a auna jinin Fatuu a lokacin tabbas daba k'aramin hawa yayi ba. Tsawon mintuna Fatuu na duk'e a wurin kafin tayi k'arfin halin mik'ewa ta fara tafiya a hankali,da kyar ta ke taka k'afafunta da sukai mata wani irin nauyi,a ranta kuwa ba abunda take Maimatawa fa ce "Kud'in Shanu Gomaaa..!!!!" *Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp message banda phone call,Thanks🤝* *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *BY ZAINAB LALUH📲* ~(Oummu Imam)~ *Paid Book* *Free Page 21 Wani mutum ne ya shigo kwanar ta bayan Fatun yana zuwa saitin ta yace "Ke bake ki ka yada jaka bane? sam Fatuu bata lura da ba jakarta a hannunta ba,don bata cikin hayyacinta,d'agowa tayi ta kafe Mutumin da idanu tama kasa bashi amsa,ganin yanayinta,ga fararen idanunta sun rikid'e sunyi ja yasa Mutumin cewa"baki lafia ne? d'aga masa kai kawae Fatuu tayi alamar "eh,juyawa yayi ya d'aukko mata jakar ya dawo inda take tsaye yace "Muje" bata ce komae ba tabi bayanshi a hankali take tafiyar har suka fito suka hau hanya Mutumin yace"ina ne gidanku?" da yatsa Fatuu ta nuna mashi, "to zaki iya k'arasawa?ya tambayeta,Kai ta k'ara dagawa,ya mik'a mata jakar yace "Allah ya sawak'e,ni ta can zan bi ne, ki bi a hankali ki k'arasa kinji" nan ma kan ta d'aga,Mutumin ya juya ya tafi, Ikon Allah wai yau Fatuu ce ta kasa magana,lalle ba karamin tashin hankali kalaman gaye suka jefa ta ba, Lokacin da ta iso gida shagon Amadu a rufe yake,tana shiga zaure taga k'ofar dakinshi a bud'e,shigewa ciki kawai tayi, tana shiga ta wuce band'aki tayi fitsarin da tuni ya d'aure mata mara don har ya d'an zubo ma,tana fitowa ta shige ciki,a bakin k'ofar dakinta ta aje jakarta ta shige,bata bi takan gwaggo ba don tasan bata nan tunda safe ta sanar da ita cewa aikin rana take,amman zata fita da wuri don zasu je Walimar d'iyar abokiyar aikinsu da aka d'aura ma Aure jiya Asabar,daga can zasu wuce Aiki, Can k'arshen d'an gadonta ta haye ta had'e kafafuwanta ta tura kanta ciki,tayi zuru tana ta tuna maganganun Gaye, kwata kwata ta kasa yin tunanin Mafita,don tana ganin ba wata mafita tabbas abunda gaye yace sai ya faru,don kud'in gilashin da yawa ba zai yuwu Mutumin ya yafe ba, tunda gashi harma ya tambayi kwatancen gidansu,sai lokacin wasu kwalla masu zafi suka zubo mata don tun d'azun ta kasa ma yin kukan,wani irin d'aci take ji a bakinta, Ta dau tsawon lokaci a haka, ta kasa ko kwanciya don komae bai yi mata dad'i,tana a haka har aka kira sallar Azahar,tana ji ana yin sallar amman ta kasa saukkowa daga gadon ga yunwa tana ji amman bata jin ma zata iya cin abinci, Amadu ne ya shigo cikin gidan don d'ibar Abinci bayan ya dawo daga salla,ya hango jakar Fatu da takalmanta a bakin k'ofar daki a ranshi yace "Yanzun haka tana can tana baccin tsiya bata tashi tayi Sallah ba" ya nufi dakin Fatun ya d'age labulen,kafin yace wani abu Fatuu tayi zumbur ta d'ago,hawaye duk ya wanke mata fuska,ganin haka yasa Amadu shigowa cikin d'akin yana kallonta yace"Miya faru?" dakyar murya can ciki tace "ban lafia.." Amadu dake ta kallonta har ranshi ya yarda bata lapiyan don da ganin fuskarta ma,yace"mike damunki", Tace"zazzabi da ciwon kai" yace"kinsha magani" girgixa masa kai tayi alamar "a'a" "To ai ba kwanciya zaki yi kita wani kuka ba,ba kinsan inda Gwaggo ke aje magunguna ba sai ki d'auka kisha ko" har ya nufi k'ofa zai fita ya juyo yace "Kinci Abinci" tace "a'a" juyawa yayi ya fice,ba'a jima ba ya dawo,hannunshi rik'e da plate d'in abinci yace"saukko ki ci" aje mata yayi a k'asa ya sake fita,sai gashi ya sake dawowa da Cup d'in ruwa da magani Panadol,tsayawa yayi yana mata wani irin kallo ganin bata saukko ba yace "ba saukkowa nace kiyi bane,in ki ka ban haushi sai in kyale ki kiyi ta zama da ciwon..." A hankali ta saukko cikin zuciyarta tana fad'in"in kayi hakuri ma daga yau ba sake ganina za kai ba" aje mata ruwa da maganin yayi ya nufi k'ofa yana fad'in "kafin in sake dawowa ki tabbatar kin cinye shi kinsha maganin"daga haka ya fice, Tunda ya fita ta kafe abincin da idanu,ta zabga uban tagumi tana ta faman tunanin a ina za'a samu kudin shanu gomaaa a biya mutumin nan,ita dai bata so akaita gidan yarin nan,gashi Gaye yace wasu wahala ke kashesu acan....,Zuciyarta ce ta raya mata "ARD'O" dammm gaban Fatuu ya fad'i,lokaci guda kuma ta fashe da matsanancin kuka,a fili take fad'in "Shi kadai ne zai iya biyan wadannan kudin,amman nasan ko kashe ni za'ai a gabansa da kwarankwatsa ba zai biya ba...." a zuciyarta tace "to ko in fad'ama Kawu Amadu ne..."da sauri ta girgiza kai a fili ta sake cewa"kafin gwaggo ta dawo nasan ya karairaya ni, don dama shi ake sawa yana zaneni"haka dae Fatuu tayi ta tufka da warwara,k'arshe ta maida hankalinta kan Abincin wanda jallof din shinkafa da taliya ne,a hankali tasa hannu ta d'iba ta kai baki ta fara taunawa da kyar take hadiye abincin,tana yin loma ukku ta tsame hannunta,sam bata jin dad'in abincin,shima d'aci yake mata a baki,tayi zuru tana kallon shi don tana jin yunwa sosae,a ranta tace "dama tuwo Gwaggo tayi kilan in fi jin dad'in shi...."Wata zuciyar tace"A ina zaki k'ara ganin tuwon ma,dama kinci Abincin don daga yau shima ba sake ganinshi zaki ba sai dai ki rink'a ganin gabza" da sauri ta jawo Abincin ta shiga turawa a baki ba don dad'i ba. Bayan ta cinye Abincin tana cikin shan Maganin Amadu ya d'aga labulen ganin ta cinye yace" Yauwa,yanxu sai kitashi ki yi sallah inkin gama sai ki kwanta,insha Allahu zaki ji kin wartsake",a hankali tace "toh" ta mik'e don yin sallar, Bayan ta gama sallar ta d'aga hannuwa sai Addu'a take tana fadin,"Allah don Allah na rok'e ka kada kasa a kaini gidan yari,don Allah,don masoyinka Annabi Muhammadu kasa Mutumin ya manta da abunda ya faru kwata kwata,nayi maka Alkawari na daina rashin ji,zan zama kamar Haulatu....." haka tai ta rok'on Allah tana kuka har tagama ta tofe a hannuwanta ta shafa,A saman abun sallan ta kwanta ta takure jikinta tana ta ajiyar zuciya a haka bacci ya kwashe ta. Bayan an kira Sallar la'asar Amadu yazo ya tada ta yace"ki tashi ki watsa ruwa kiyi Sallah,naji ruwan bokitin wurin wanke wanke nada d'umi sai ki d'ibe shi" kai ta daga masa kawae,ya juya ya fice. Bayan ta gama sallar tayi zaune a wurin ta buga uban tagumi,ba laifi ta dan ji dad'in jikinta,tunani ta fara yi ko ta tafi islamiyya taje tagani in Haulat tazo ta fadi mata halin da take ciki...,d'an tsoki tayi a fili tace"koma na fad'a mata,ba abunda zata iya yi,karshe ma ta kama man nasihar banza,baccin lokaci ya rigada ya k'ure" can kuma wata zuciyar ta raya mata"ba gara kije ba,watakil dalilin zuwan Allah ya tausaya maki yasa a k'i zuwa kama ki,amman in kika zauna kina iya ganin anzo yanzu an tafi dake.." zumbur ta mik'e ta nufi yar wardrobe dinta ta ciro wasu kayan Islamiyyar tasa, tunda ta nufo zaure take jin tashin kida a waje,Amadu ne ya kunna wakar india a shagonshi,a hankali take tafiyar don yadda take jin jikinta kaman ta tashi daga ciwo sam ba karfi,lokacin da ta fito waje ta girgiza kanta tace "Shi sam baida matsala,waka ma yake ji" hannu tasa ta share dan siririn hawayen da ya zubo mata a ido daya,tace"in sha Allahu nima indai Allah ya ku6utar dani ba ruwana da kowa" Allah sarki Fatuu har kin bani tausayi,sai dae Allah yasa ba tuban mazuru kike ba. Amadu ya hangota zata wuce ya leko da kansa yace "zaki iya zuwa islamiyyar ne? tace "ehh naji nasamu sauki" yace "dan jira" miko mata biscuit pure bliss yayi da sweet guda biyu yace"Sai kin dawo,kibi a hankali" daga haka ya maida kanshi ciki yana ci gaba da bin wak'ar da yake saurare hadi da dan jujjuya kai,tafiya take tana ta kallon abunda Amadu ya bata tana mamaki wai yau ba tare da ta rok'e shi ba ya bata,ko ya zage ta kaman yadda yake mata inta tambaye shi,wani lokacin har rankwashinta yake kafin ya bata yace ita zata cinye masa jari,dan murmushin takaici tayi a fili tace "tabbas shima yaji a jikinshi ya kusa rabuwa dani" taci gaba da tafiya tana yi tana goge kwallan dake zubo mata da gefen hijab dinta. Tunda ta zauna a aji kanta na k'asa,Haulat sai kallonta take tana nazarin yanayinta gashi akwae malami balle ta tambayeta abunda ke damunta,sam ta kasa natsuwa ganin kwalla na zubo ma Fatun tana sa hijab tana gogewa,tana sauraron bayanin malam dake masu Ahalari tana kuma satar kallon Fatuu, "FATIMA MUHAMMAD ARDO" Malam ya kira sunan fatuu,sai dai sam bata ji shi ba, Haulat ta ta6o ta,lokacin yana k'ara kiran sunan,da sauri ta d'ago Manyan idanunta da su kayi ja ta kalle shi hadi da fad'in "labbaika...." tashi ki k'ara yi mana bayanin da nayi" Malam yace,tsuru tayi ta kafe sa da idanu,don bata san akan mi yayi bayanin ba,gaba daya ajin anyi tsit ana ta kallonta, Haulat ta d'an dukar da kanta murya can k'asa tana fadi mata bayanin da yayi,Fatuu ta saci kallonta sai dai sam bata san mi take cewa ba, A fusace malam yace"ke muke saurare!" Fatuu ta dukar da kanta jin kwalla zata zubo mata,hakan ya kara fusata Malam din yace "fita kiba mutane wuri,tunda ba karatun kika zo dauka ba" ba musu ta nufi hanyar waje har lokacin kanta na k'asa,Malam yaci gaba da magana"don iskanci yara k'anana daku sai kuje kuyi samari,in kuka yi fad'a kuzo kuyi ta tunane-tunanen banza,in baku son karatun kuje kuce Aure kuke so mana" Sauran yan ajin suka sa dariya suna sussunna kai kasa alamun kunya banda Haulat da sam bata ji dad'in maganar da yayi ba,don tasan ba abunda ke damun Fatuu ba kenan,tabb ita da koda wasa akace ana sonta yanzu ta fara masifa da zage zage tana fadin ita bazata yi saurayi ba sai ta zama likita",haulat ta fada a ranta,ita kam Fatuu kallon Malam din tayi da runannun idanuwanta suka hada ido yace"ko zaki zo ki buge ni ne?" batace komae ba ta juya ta fice.... *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *BY ZAINAB LALUH📲* ~(Oummu Imam)~ *Paid Book* *Free Page22⃣* Fatuu na tsaye ta jingina da karfen barandar gaban ajinsu ta tafi duniyar tunani,Malam ya fito,tsaye ya yi a bayanta yana kallonta kafin yace "ke cewa nayi ki fito ki tsaya? Wato kinfi karfin ki rage tsawon ki ko? Juyowa tayi ta kafe shi da idanu batare da tace komae ba,hakan yasa ya k'ule cikin daka tsawa yace " ba dake nike bane! Sunkuyar da kanta tayi k'asa tace"baka ce in rage tsawo na ba ai,cewa kayi in fito waje kawae....." katseta yayi "da yake ke dak'ikiyace komai sai ance ki yi ko?" kallon k'asan ido tayi masa suka hada idanu,a fusace yace "kee! ni kike harara...." daga bayansa yaji ance"abunda yafi harara ma yi maka zatai indae wannan ce" a tare suka juya don ganin mai maganar,wani matashin malami ne ya tunkaro su yana sanye cikin farar shadda jamfa hannunsa na dama rungume da Qur'ani dayan kuma rike da zungureriyar dorina,shine displine a Islamiyyar,ya iso inda suke fuska tamke,wanccan malamin yace"Yauwa Malam Nazifi,gatanan kayi mata hukuncin da ya dace,ina bayani hankalinta na wani wuri,nace ta fito kuma tafi karfin ta rage tsawonta", jinjina kai Malam nazifin yayi daga haka d'ayan malamin ya juya ya tafi, Kallon Fatuu yayi fuska A d'aure yace "bani hannuwanki! ta d'an marairace fuska tace"Malam don Allah ka buge ni a jiki' dama malam nazifi yasan bata son bugu a hannu,hakan yasa ya k'ara tamke fuska yace"ina wasa dake? Girgixa masa kai tayi,ya d'aga bulalan ba tare da yace komae ba,a hankali Fatuu ta mika hannuwan suna dan rawa ta runtse idanunta ya fara bugunta tamkar da gayya,yana yi mata bulala biyar ta janye hannuwan tana dan yamutsa fuska don ba k'aramin zafin bugun take ji ba" yace"nace ki sauke hannuwan ne?" turo baki tayi tamkar zata fashe da kuka tace "don Allah malam kayi hakuri....."ya katse ta "kinsan kina tsoron bugun kike ma mutane iskanci,bulala goma zanyi maki amman wllh kika yi wasa zata koma ishirin", sanin da gaske yake yasa ta sake mik'a masa hannu daya tana yi tana canjawa har ya gama,ta juya tana yayyerfe hannu don sosae ya bugeta hannuwan duk sunyi jawur,malam nazifi ya dakatar da ita daga tafiya ta hanyar fad'in "ban sallame ki ba" ta juyo tana kallonshi cikin ido ta d'aure fuska,"kije Office dinmu ki cika mana bokitinmu na ruwa,sannan kije ki wanke gaba d'aya bandakin ku na mata,basai nace kiyi ba,inkin so kina iya kin yi" daga haka ya juya ya shige Class dinsu don shine Malaminsu na Al'Qurani da tajweed,da sauri Haulat ta koma gun zamansu don dama tana a la6e bakin kofa tana ganin duk abunda ke faruwa. Fatuu ta sauke ajiyar zuciya ta juya don zuwa yin purnishments din da Malam ya bata,a hankali ta ke sa hannu ta na goge kwallar dake zubo mata cikin ranta tana fad'in "Mugu kawae,dama yafi kowa tsanata a makarantar nan,daga yau ba sai ka sake gani na ba zaka bugan..."a fili tace"dama ban zo ba,tunda ba za'a kyale mutum da abunda ya isheshi ba,a daidai nan ta iso bakin staffroom din,Haulat nata faman zuba ido don ganin shigowar fatuu,lokaci bayan lokaci ta ke kai dubanta kan k'opar shigowa amman shiru gashi har an kusa tashi kuma har lokacin malam Naxifi na cikin class d'in saboda abu biyu yake masu,sai lokacin da aka tashi Mlm Nazifi ya fita,da sauri Haulat ta d'auki jakarta had'i da ta Fatuu ta fice da sauri baiwar Allah har tana yin tuntu6e wurin fita,hanyar kewayensu ta nufa don taji Aikin da aka sa fatun,bata k'arasa isa ba ta hangota a hanya tana tahowa,Haulat ta ja ta tsaya tana kallonta itama Fatun kallon haulat d'in take har ta iso wurinta,hannu kawae ta mik'a mata alamar ta bata jakarta haulat ta mik'a mata jakar a hankali fatuu tace "nagode" daga haka tayi gaba, haulat itama ta bi bayanta har suka fita daga cikin Islamiyyar suka mik'i hanya,haulat a ranta tana ta tunanin mike damun fatuu haka,don tunda tazo ta lura da yanayinta tana cikin damuwa ga bugu da kuma aikin da aka bata, A fili tace"ba abun mutum ya tambayeta ba tayi man wulakancin da ta saba,gara ma in kyaleta,da tana son in sani ai da ta sanar dani" can dae haulat ta kasa daurewa ta kira sunanta da yake ba tazara sosae a tsakaninsu don a hankali fatun ke tafiya ba kaman yadda ta saba wuwwurga kafa ba,bata juyo ba haulat ta sake cewa"Fatuu"a hankali ta juyo tace"minene"haulat ta k'arasa gabanta tace "mi yake damunki ne naga kaman kina cikin damuwa tunda kika zo" fatuu tayi yar ajiyar zuciya ta ta6e baki tace"Uhmm,in na gaya maki damuwar zaki man magani ne" d'an murmushi Haulat tayi tace"ai bansan mike damunki ba,balle in san ko zan iya yi maki maganin" girgiza kai Fatuu tayi cikin karewar murya tace "koma kinsani bazaki iya man magani ba,don haka ba sai kin ji ba" ta juya ta ci gaba da tafiya a hankali, Haulat tayi tsaye sototo tana mamakin abunda Fatuu tace ma ta,don tasan bata 6oye mata abu in yana damunta,koma ta 6oye zata dawo ta bayyana mata,a ranta tace" to mike damunta haka da bazata fadi man ba...?cikin d'an d'aga murya haulat tace "Amman ko da bani iya yi maki maganin ai kilan in baki shawarar da zata iya yi maki maganin ko" shiru bata ce mata komae ba kuma bata juyo ba,hakan yasa Haulat juyawa tabi d'ayan 6arin dake kallon wanda fatuu tabi ta fara tafiya,Fatuu nata juya maganar haulat aranta na shawarar da tace zata bata,tabbas Haulat na bata shawara kuma shawarar nayi mata aiki,ta tuna wani laifi da tayi kwanakin baya wanda ta tsorata sosae hakan yasa Haulat ta bata shawarar yadda zata yi ta ku6uta bayan tayi mata fad'a,aikuwa shawarar tayi mata Amfani don ta tabbatar lokacin ba don aiki da abunda haulat din ta fadi mata ba Kawu Amadu sai ya karyata....,da sauri ta juya "Haulat,haulat.." ta k'wala mata kira har sau biyu,sannan haulat taja ta tsaya ta juyo fuska a d'aure da alama tayi fushi ne,ganin haka yasa Fatuu ta nufeta ta tsaya gabanta tace"bari in fad'a maki to,amman shawarar zaki bani kar kice zaki man fada don aikin gama ya rigada ya gama, kuma ko baki man fada ba ma nayi dana sani bazan kara aikata irin hakan ba..."ta sunkuyar da kanta jin kwalla zasu zubo mata,ajiyar zuciya haulat ta sauke ta kai dubanta gaban wani gida dake agefensu,ta kamo hannun fatun tace"muje can to ki fadi man nan akan hanya muke" daga haka suka nufi jikin bangon gidan suka jingina, Haulat tace "ina jinki,mike damunki?" Fatuu dake ta matsar kwalla kamar jira take haulat ta tambaye tan ta rushe da kuka tace "Haulat na bani na lalace,gidan yari za'a kai ni,kuma kilan acan zan mutu ma.." zaro idanu haulat tayi gabanta ya fara faduwa,cikin rashin fahimtar zancen fatuu tace"waye zai kai ki gidan yari?" cikin kuka Fatuu ta zayyana mata duk yadda sukai da Gaye harda aikenta da akai gidan Hajia jiya da daddare harta ga Haisam d'in. Ajiyar zuciya mai karfi Haulat tayi tace "nasan maganar ma" da sauri ta kalleta tace"kinsan za'a kaini gidan yarin dama kuma baki fad'a man ba.." jinjina kae Haulat tayi tace"jiya da yamma nima na hadu da gayen kuma shine ya sanar dani abunda kika yi har da aka tashi nayi maki maganar, kuma naso in sanar dake Mutumin dan gidan Hajiyar Sanata ne amman kika k'i saurarata k'arshe ma sai cewa ki kae wai ko dan sarkin makka ne ke ina ruwanki...." cikin kuka Fatuu tace"ai ni nayi zaton tambayana kike ko nasan mutumin" taci gaba da rusa kuka,Haulat tace "ki daina kuka,ki kwantar da hankalinki..." a fusace Fatuu ta katseta tace"amari hakkilo?ya za kice wai na daina kuka,kuma taya zan kwantar da hankalina bacin nasan tabbas duk abunda gaye ya fad'a gaske ne.." Haulat ta juyar da kanta gefe ta dan gwalo ido cikin ranta tace"tabb lalle abu yayi abu,yau su Fatuu harda yin fullanci,ita da bata son yi,wani lokacin inta fama da ita tayi man ta k'i yi" Fatuu dai sai kuka take tana sambatu "ni wllh bansan haka motan keda tsada ba,da bazan ma fara fasa masa gilashi ba,ace kudin shanu gomaa har sau goma ne kudin motar,ba dole gilashin ma yayi tsada ba" Haulat ta jinjina kae ta kalleta tace "nawa yace motar take ne" da sauri fatuu tace"Miliyan goma faaa" haulat tace "bama tada tsada sosae...",a fusace fuska jage jage da hawaye fatuu tace" miliyan goman ne ba tsada,shiyasa nace baki da hankali,koda yake nasan baki taba sanin yawan miliyan a hannu bane shiyasa zaki ce haka,yo inama zaki gansu" girgiza kae haulat tayi sam bata ji komae ba don dama ta saba datsa mata magana,tace "dama ban ce ai na ta6a ganinsu ba ko,kawae dae nasan akwae motoci masu tsada sosae da yan gayu ke hawa,don na ta6a ji yaya Osman dinmu yace harta miliyan d'ari akwae" da sauri Fatuu ta dafe kai tana fitar da numfashi mai karfi a rude tace "kice Allah yaso ni da ba irinta na fasa ma gilashi ba,yasin nasan wannan sai dae a harbe ni kawae" ta k'ara fashewa da kuka,ita kam haulat dan juyar da kanta tayi tana murmushi don dariya maganar ta bata, Zamewa k'asa Fatuu tayi ta zauna dirshan taci gaba da kuka tana sambatu"mi woni ni fatuu,mi woni..,na bani na,in Gwaggo taji wannan maganar nasan sai tasa kawu Amadu ya kakkarya ni kafin awuce dani kuma gidan yari inje in rink'a cin gabza kwarkwata kuma ta gwaigwaye man gashi,tunda nasan ba yafe man zai yi ba,gaskiyar Gaye wllh nasan ko kawu Amadu nayi ma haka ba zai ta6a kyale ni ba sai ya dau mummunan mataki akaina,balle wannan da ba abunda na had'a dashi,nasan ko hajia taji bazata hanashi ya dau mataki a kaina ba,daman kullum tana man fadan in daina rashin ji,ko jiya ma saida tace zamu 6ata,yanzu kuma taji wannan asaran da na yiwa d'anta ta uban kudi haka,tabb ai nasan ma ba za tace ya yafe ba,to mima muka had'a da ita da zasu yafe,daga makwabtaka....,ga Hajiya dama ta iya masifaa....mi maye ni Fatuu,na mutu kawae" ta d'ora hannuwanta saman kai kafin ta dago tana kallon Haulat wadda tuni dama ita ta ke ta kallo cike da tausayi,tace"dama nasan ba wata shawara da zaki iya bani,wannan babban abu ne ba irin wanda ki ka saba ban shawara bane,nasan dole sai an kaini gidan yarin" ta kai maganar tana ta faman yin sheshsheka. A hankali Haulat ta durk'usa kusa da ita ta kalleta tace"duk da haka ina da shawarar da zan baki,kuma ina tunanin Insha Allahu zata yi aiki..." da sauri fatuu tace"kenan kina ganin in nayi amfani da ita ba za'a kaini gidan yarin ba?mutumin zai hakura?" d'an murmushi haulat tayi"tace ehh,in Allah ya yarda zai hakura nike tunani..." fatuu ta k'ara katseta da sauri"toh don Allah fada man abunda zan yi ko minene zanyi indai za'a kyale ni nidai" Haulat tace "saurin mi kike,zan fad'i maki amman sai kin yi mani Alkawarin in dae aka kyale ki bazaki kara aikata makamancin wannan abun da kika yi ba" wani irin kallo fatuu ta juyo tana mata mai kama da harara,can kuma ta dauke fuskarta ta kalli gefen haulat d'in tace "da yake kare mai bak'in baki ne ya cije ni zan k'ara aikata hakan,ko baki ji tun d'azun nace maki nayi dana sani kuma bazan k'ara ba" ta kai maganar tana turo baki,Haulat tace"nasan halinki ne kin iya tuban mazuru,sau nawa kike cewa baki k'ara yin abu kuma kizo ki karan" Cike da gatse Fatuu tace"to gwaggo kiyi hakuri...,don kawae kinga ina neman taimakonki zaki taman maganganu sai kace ni mahaukaciya ce zan sake,ni in zaki fada man abunda zan yi ki fada man lokaci na k'urewa" ta kai maganar tana dan turo baki tana kallon hanya, Karasa zaunawa a kasa Haulat tayi,ta juyo tana kallon fatuu tace"KI JE KI BASHI HAKURI........ *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *BY ZAINAB LALUH📲* ~(Oummu Imam)~ *Paid Book* *Free Page23⃣* *Haisam* Zaune a cikin parloun sa yana operating laptop wadda take mai kyaun gaske jikinta sai shining yake yayin da bayanta ke dauke da tambarin Apple,jin ana k'okarin shigowa cikin parlon kai tsaye batare da anyi knocking ba yasa ya dan waiga ya kalli kopan, A hankali aka turo kopan ta bud'e,wani matashin mutum ne wanda bazai wuce tsaran Haisam din ba ko ya girme masa da kad'an ya shigo,jikinsa sanye da jeans da longsleeve shirt,kalar fatarsa kuwa za'a iya kiransa da wankan tarwad'a don ba bak'i bane,fuskansa na dauke da k'asumba mai gashi da dan yawa sai dai bai tara a saman kansa ba,gashin fuskan nasa yasha gyara sai kyalli yake da gani yana kashe masa kudi yadda ya kamata. Suna had'a ido da Haisam wanda ya jingina bayansa jikin kujeran da yake zaune ya washe baki yana daria hakan ya bayyana wushiryar dake a bakinsa,shikam haisam murmushi kawae yake yana kallon mutumin,a bakin kofan ya cire takalmansa kafin ya nufo cikin parlon yana fadin"Haisam Alee zakee,yaro dan Senator jikan Minister,na hajiyar sanata sai dubu ta taru,kowa yake son ganin 6acin ran hajia to ya ta6a ka,yaro mai tsananin farin jini,har makiyanka burgesu kake inma akwae su kenan,yadda farin ka yake na daban,haka aniyarka ma take ta daban,kaine uban duk wani mai tsafta.....a 6angaren aiki kuwa,you are the best computer engineer in the whole nation,kai kasan hardware kasan software,a bangaren Networking da robotics kau baka da tsara,ana mutane ruwa biyu kai d'in ruwa ukku ne,kaine hausa,kaine fulani,kaine larabawa.....", Tunda ya fara magana Haisam dake zaune tamkar wani saraki,hannunsa na dama rike da beard dinsa yasa index finger d'insa yana dan bubbuga bakinsa,yanata bin mutumin da ido,ganin baida niyyar tsayawa da kirarin nasa yasa shi cire yatsansa daga bakinsa Calmly yace"Abbasss...." jin kiran sunansa da haisam din yayi yasa Abbas din kyalkyalewa da dariya ya miko masa hannu suka tafa kafin kuma suka gaisa,ya nufi dayan side din kujeran da haisam din yake ya zauna yana fadin"to ya kaji praising din nawa,am i good at it?" dan ta6e baki Haisam yayi hadi da d'age gira"Not bad"yace, still Abbas d'in daria yake"kace inna maida shi sana'a zanci Abinci dashi kenan?"ya fada, Haisam wanda har lokacin fuskansa na dauke da murmushi yace"shi kuma lecturing d'in ka kaishi ina?" zama sosae Abbas yayi ya d'an kwantar da bayanshi jikin kujeran yace"baka ga yadda ya zama ba,duk yana neman komawa shiririta,that's why na fara neman wata sana'ar kaga sai yazama inada alternative in ba wanccan sai inci gaba da bin yaran masu kudi ire-irenka ina masu kirari,nasan ba karamin kudi zan rinka samu ba" Haisam da shima ya dan kwantar da kanshi cike da zolaya yace"wani ke shiriritar da aikin naku baku ba?nan gaba ma in aka biye maku kashe ilimin zaku yi gaba daya,yakamata tun wuri ai taking action akanku" Abbas dake ta daria yace"wani action kuma banda hanamu salary da ake" dage gira haisam yayi"I mean sacking...." da sauri Abbass ya d'ago da kanshi yace"amman kai mugu ne H,zakee,wato kai burinka kenan a kora mu ko" sai lokacin haisam yayi dariyar da hak'oransa suka bayyana, "in an kora mu sai akawo suwa su koyar? ko su ku za'a maido tunda an fada ma lecturing d'in wasa ne", "banyi tunanin zaka yi man wannan tambayar ba,seems like ka manta a wace kasa muke ko,kuma nima kasan dae zan iya ai,miye a ciki,all i need to do is Pgde,tunda ba education nayi ba,kai tsaya kaji ko banyi ba zan iya lecturing din,harma in fi wasu da suka dade a fannin" ya karasa maganar cike da tabbacin abunda ya fada. Abbas yace"aikuwa da kasa mata sun rinka tara c.o" "Why?" haisam ya tambaye shi. "Muddin kazama lecturer ai shikenan kuma zaka janye hankalin mata ya dawo kan ka,ba kamar yan matan jami'a da basu shakkar nuna ma malami suna sonsa komae tsaurinsa,basu damu da zai wulakanta su ba,na tabbatar hakance zata faru da kai,ai gaba d'aya nike gaya maka attention dinsu kanka zai dawo,instead of focusing on their studies,kaga ba karamar barna zakai ba kaima,don kasuwa zakayi sosae abokina" ya karasa yanata faman daria. Shi dae haisam still yayi yana kallon Abbas,tsaf ya fahimci dalilin da yasa abbas din cewa mata zasu maido attention dinsu akansa,don tunda ya taso yana k'arami ake fada masa yana da kyau na musamman har kuma yanxu da ya girma ba'a daina fada masa hakan ba,haka kuma da wuya a kalle shi ba tare da ansake waiwaya wa ba. Abbas smiling broadly ganin haisam din yayi shiru yace"ko ba daidai na fada ba,I lie? Sauke 6oyayyan ajiyar zuciya haisam yayi kafin yace"in tambayeka Abbas...?"abbas yace"I'm all ears zakee" haisam ya cigaba"have u ever talk completely without mentioning women?na rigada na fahimci is hardly a kare magana da kai baka ambaci mata ba,to ni wannan ba matsalana bane,nothing concern me wit dem,kaima da suke kula ka ai don kana kula su ne,ko bansan ka bane" Dariya sosae Abbas keyi harda buga kafa yace"to in ban rink'a ambaton mata ba,maza zan rinka ambato H,zakee,ai mata namu ne,muma kuma nasu ne" d'an ta6e baki haisam yayi yana girgiza kai kafin yace"to ya Abuja?" "sai da ka gama caccaka ta har kana man mummunar fata sannan zaka tambayeni,ashe kaima baka tausayin malamai bayin Allah", Dan ta6e baki haisam yayi"U know I was just funning u dude,ina tausayin malamai mana,especially primary and secondary skul teachers suna matukar kokari sosae,but their Salary structure is still poor,kawae al'amarin kasan namu ne sai Addu'a,may Almighty Allah give us responsible leaders" "Ameeen ya Allah" Abbas ya amsa. "Yaushe ka shigo gari ne?" gyara zama Abbas yayi yace"ban jima da dawowa ba" jinjina kai haisam yayi kafin ya kuma tambayarshi"yasu Nafeesat and my Boy Abdul? Abbas yace"suna nan lafia,ita feenah ma tayi tunanin zuwa kayi ka koma,nace mata kana a gari hajia ta sa an maido mata kai nan,har take cewa shine ko ka leka ku gaisa" dan murmushin gefe yayi"in sha Allah zan je,am not well settled har yanzu" kai Abbas ya daga yace" Allah ya yarda dama ai sai a hankali komae zai warware tunda wurin aiki ka canja" daga haka suka ci gaba da hira. *** *** *** **** Haulat tace"Ina ganin kije ki bashi hakuri tun kafin goben tayi....."cakk fatuu ta tsaya ko kyafta idanunta batayi kamar an dasa mata aya,haulat ta ci gaba"kinga idan ya hakura shikenan waya kawai zai kira yace ya janye inma yakai karar taki", juyowa fatuu tayi tana kallon haulat da alamun mamaki tace"tabb lalle kema haulat din nan wani lokacin kaman baki da tunani wllh,kina nufin in kai kaina ma kenan,kinga daga nan sai hajia tasan ni ce in dama ya gaya mata" "ba kince da aka aikeki gidan,kinga 6angarenshi daban ba?"haulat ta tambaya, Fatuu tace"Eh,amman in naje ya cafke ni ya kaima hajiyar yace ga wadda ta rotsa masa gilashin fa?" girgixa kai haulat tayi"duk da bansan shi ba,nasan da wuya ya aikata haka gaskia,akwae mutumin dana ta6a gani sau biyu kuma ina tunanin shine....."da sauri fatuu tace"wani fari ko?zaki ga kalar farinsa daban" Haulat tace"ni bazan iya ganewa ba don duk a mota nike ganinsa ya wuce kawae dae fari ne" "shine ma,don duk garin nan ba mai irin kalar farinsa.." da sauri haulat ta katseta"ke ya akai kika sani" tace"tabb yo nida na ganshi a kurkusa har sau biyu,ko kafin ya rabamu fad'a da murja har in fasa masa glass ai ran Alhamis ma da yamma sai da ya rabamu da jamila ina kokarin zubar mata da Awar...tsit fatuu tayi lokaci guda kamar ruwa ya cita,sai faman zare ido take. Girgiza kai haulat tayi tace"kin bari yama san halinki kenan,Allah yasa ya hakura" a hankali tace "Amin,ai bazan kara ba"ta6e baki kawae haulat tayi tace"kije ki bashi hakurin,kar kiji wani tsoron wai zai cafke ki yakaima hajia,na tabbatar bazai yi haka ba,don sufa yan gayu aji ne dasu,ba don haka ba yadda Gaye yace yasan gidanku ai da yaso hajiyar ta sa ni da tun ranar ya kaita har gidanku tasan kece amman yadda kika je kaimata abinci bata yi maki maganar ba kinga tabbas bata san kece ba,don haka kije kiyi duk yadda zaki ya hakura,ki nuna masa kinyi nadama kar kuma kice wai don gaye yace za'a kai ki gidan yari in ba'a biyasa ba ki ka je bashi hakurin,inta kama kita kuka ma,in bakije ba har gobe tayi indai har yakai k'arar taki to dole Hajia da gwaggo su sani koda ba'a kai ki gidan yarin ba,kuma kinga shikenan na tabbata hajia 6atawa zatai dake duk kuwa yadda take son ki,ga kawu Amadu hmmm...." Fatuu dai tayi zuru tana saurararta sai zare ido take gabanta na faduwa ta kalli haulat tace"amman kina ganin zai hakuran,ya yafe man haulat,kudin fa da yawa wllh ke baki san yawansu ba ne hmm"ta karasa maganar tana jinjina kai,haulat tace"In sha Allahu ina sa ran zai hakura,tunda na tabbatar yafi karfinsu,kuma ba ita kadaice motarsa ba,ko ni da nace maki na gansa sau biyu duk ba a mota kala daya nake ganinsa ba...."da sauri fatuu ta katseta "nima a mota daban daban nike ganinsa kuma kwalabo yake yi da kayan jikinsa da motar da ya hau" Haulat ta gyada kai"to kingani,kije dai ki bashi hakurin,kinsan wani duk zafin sa idan ka bashi hakuri akan laifin da kayi masa ka nuna kayi nadama bazaka kara ba,yana hakura" Fatuu tace"ni wllh gabana sai faduwa yake kar inje yasa akamani ko tuwon gwoggo na karshe ban ci ba..." wani irin kallon mamaki haulat tayi mata"ke da baki son tuwon kullum kina k'orafin za'a kashe ki da shi" tace"ai na daina,yanzu nagane ba shine mai kashe mutum ba,gabza ce,in kasamu tuwon kawae ka godema Allah kaci"tasa hannu tayi tagumi,ita dai haulat dan girgiza kai kawae tayi tana murmushi don tasan irin nadamar fatuu. Shiru sukayi nadan lokaci can fatuu ta kalli haulat tace"don Allah haulat to kizo ki rakani" da sauri tace"in raka ki ina? Fatuu tace"muje mu bashi hakurin....."girgiza kai haulat tayi da sauri"lokacin da kika yi masa 6arnar ai ba tare muke ba,hasali ma ba yadda banyi dake kiyi hakuri ba ki ka kiya,sai yanxu kice wai in raka ki,salon kija man balae" ta k'arashe maganar tana kallon gefen hanya. Fatuu tace"oh dama kinsan wani abu zai iya faruwa innaje shine kika tura ni don cuta? da sauri haulat ta juyo tana kallonta tace"kindai san ni bazan ta6a cutarki ba ai,kawai ina gudun babana ya ganni tunda kinga limamin masallacin gidanne,kuma kinsan ni ba wani zuwa gidan nike sosae ba sai in na raka ki wani lokacin,dama dai cikin azumi ne shine kullum sai naje kar6ar sadaka da yamma,wani lokacin kuma in raka ki da rana inje insha A.c ko don rage yunwar Azim..." cike da tsiwa fatuu ta katseta"dalla kin cika ni da wani bayani,kawai in zaki raka ni ki rakani,in kuma baki zuwa ki fada man in kama gaba na" Haulat tace "shikenan muje in raka ki amman iyakata wajen gate gaskia" wata irin harara fatuu ta wurga mata tace"to banso kisha zamanki,zanje ni kadai,kuma insha Allahu zai hakura,d'an bakin ciki sai dai ya mutu"daga haka ta mike ta kakka6e jikinta hadi da zura takalmanta ta juya zata tafi,itama haulat ta mike tana fadin"ai da ni yar bakin ciki ce da ban baki shawara ba ko,amman ba komae gobe ma rana ce,ko godiya bazaki man ba sai ma ki kira ni da yar bakin ciki" Juyowa fatuu tayi ta k'ara harararta tace"sai ki jira kiga shawarar taki in tayi aiki,kafin kiyi maganar wata godiya" Haulat tayi dan murmushi tace"insha Allahu ma zatayi kawata kuma kanwata,ba inda za'a kai ki muna tare mutu ka raba" wani kallo tayi mata tana turo baki daga haka ta juya fuu ta tafi. Cike da tsokana Haulat ta dan daga murya tace"kawata bazaki rakani ba,aike na akai in mun dawo sai muje in jira ki a bakin kofan ki shiga ki bashi hakurin" a fusace ta juyo ta kara watsa mata harara had'i da mummurgud'a baki daga haka tayi gaba abunta. Daria sosae haulat tayi ta juya tabi hanyar da tafara bi d'azun a ranta tana fadin"haka kurum kija man yanzu babanmu yaji wannan abun duk da badani aka aikata ba ai sai ya sa6a man wllh,taje dai ina mata fatan nasara,in ma fushi tayi ma shirya daga baya. Tafiya take sam hankalinta baya tare da ita,ta tafi duniyar tunanin shawarar da haulat ta bata,gani take anya kuwa zai hakura don a ganin da tayi mashi sau biyu tana ganin kaman ba zaiyi mutunci ba,ranar farko daya rabasu fada da jamila fuskarshi a murtuke take haka ranar da suka yi fada da murja daga magana bata ma idasa fadin abun da zata fadan ba ya gaura mata mari,tunanin hakan ne ke k'ara mata fargabar zuwa wurinshi,amman ba yadda zatayi dole taje kafin gobe tayi. Daidai shagon kawu Amadu ta tsaya tana jiran ya sallami wani yaro,kallonta yayi bayan yaron ya tafi,fatuu tace"sannu kawu" jinjina mata kai yayi ganinta sukuku yasa yace"har yanzu jikin?" girgiza masa kai tayi"da sauki sosae"ta fada a hankali,d'aura jakar islamiyyarta tayi saman kiosk din tace"kawu jakata zaka aje man,zan dan je gidan Hajia yanzu zan dawo"sanin ba kowa acikin gidansu yasa shi daga mata kai alamar toh,daga haka ta juya ta nufi gidan hajiyar sanata,kirjinta na bugawa damm damm tamkar ana mata luguden ta6are haka ta daure har ta karasa,ta karamar kopa dake a bude ta bi ta shige. _*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp message banda phone call,Thanks🤝* *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *BY ZAINAB LALUH📲* ~(Oummu Imam)~ *page 24⃣* ......Suna cikin fira Abbas ya juya yana kare ma parlour din kallo kafin ya juyo ya kalli haisam"amman dai ya tsaru sosae,order din furnituren kai daga can i guessed" daga yadda haisam din yake ba tare da ya dago ba ya dage masa gira alamar ehh, "da gani ai,sunyi kyau parlourn ma yayi kyau sosae,amman bai kai na gidana ba tunda ba mata a cikinsa,don inda da mace sai yafi kyau" ya karasa zolayar tashi yana ta daria, "na lura dae ba zuwa kai mu gaisa ba,iskancin daka saba kazo yi mun...." da sauri Abbas ya katseshi da fad'in"pulling my best friend's leg,Allah zuwa nayi mu gaisa sosae don nayi missing din ka guy irin sosai din nan,kasan kana zuwa nayi tafiya so bamu wani gaisa sosai ba,and we ave'nt spoken like this for long,ko da yaushe sai dai phone and vid call,shiyasa na tara hira da tsokanan da zan maka sosae,Feenah fa har rigima tasa bazan fito ba,wai daga dawowa na zan wani kama fita,sai da nace mata wurin H,zakee zani sannan..." haisam ya katse shi"ai tana da gaskia dama bata barka ka fito ba,for gud 1 week basu saka ka a idonsu ba,kamata yayi yau througout ka zauna gida kafin gobe ka dasa zuwa aiki kuma" "Hhhh ai ita da kanta take cewa tana da iyaka tsakanina da kai,shiyasa duk abu in ya dangance ka bata jayayya" murmushin jin dadin maganar Haisam yayi,shi kanshi Abbas nada matukar muhimmanci a wurinsa amininsa ne wanda ya zama tamkar dan'uwansa kowa nashi yasan da shi,sun shaku sosae ta yarda zai yi wuya su kwana su wuni ba tare da daya yasa dayan a ido ba indae har suna a gari,in kuwa haisam na Abuja Abbas yaje to a gidansu yake zama koda ma bai a Abujan Abbas din na sauka a gidansu,sai dai ko wani abu da ya danganci aikinsu yaje wanda aka kama masu hotel room shima in yaji bai ra'ayin zama a hotel din sai ya tafi gidan Senator Alee Adamu Zakee, Hannu Abbas yasa a Aljihun gaban rigarsa ya fiddo wayansa wadda tun suna hira yake jin karan notifications,ganin sakonni nata shigowa har lokacin yasa shi fadin"dadi na da zuwa gidan hajiya kenan", "What" haisam ya tambaya ba tare da ya dago ba, "Internet access mana,daga mutum ya kunna wi-fi sai yaita browse and chat for free" dan jinjina kai haisam yayi yace"da alama ma tun kafin kazo kai turning wi-fin on,don tun dazun nike jin notifications tone" kyalkyacewa da daria Abbas yayi"tun a mota kafin in karaso na kunna" dan d'ago kai haisam yayi ya kalli Abbas yace"lalle ka cika son banza Abbas,amman soon zaka fara biya" "ah haba dae,nima fa Senator nan babana ne,ya za'ace mutum da abun babansa sai ya biya, "wannan ba kayan Senator bane na haitham ne" haisam ya bashi amsa, "Amman da kai da kaya naga dae ai duk mallakar wuya ne ko" Abbas dake ta dariya ya fada,girgiza kai haisam yayi daga haka ya juya yaci gaba da abunda yake cikin computer, shi kuma Abbas ya maida hankali kan wayarsa da sakonni keta faman shigowa. Tsaye fatuu tayi a bakin Fence Door din part din haisam tsawon wasu mintuna cike da fargabar karasawa wurin shin don ranta ya bata cewa yana nan ganin mota fake a kwanar gate din gidan,ba komae take ma zullumi ba face karfa yasa a kamata daga nan ayi gidan yarin ko kuma hajia tazo ta ganta asirinta ya tonu,hakan yasa ta kasa shiga tuntuni sai faman wasi-wasi take a cikin ranta,can dae tayi shahada ta shige tana tafiya cikin sanda tana waigen bayanta har tazo bakin balcony a hankali ta tattaka ta haye sai kuma tai tsaye anan ta kasa tunkaran kopan don ba karamin bugu kirjinta ke yi ba,matsawa tayi saitin windown parlourn nashi da niyyar ta hango ciki taga ko yana nan sai dae kuma ta kasa hango komae sai ma kanta da take gani a jikin glass din tamkar tana kallon madubi, Abbas ne ya dago da niyyar yima haisam magana karaf idanunsa suka hango masa fatuu sakamakon blinds din windown dake adan zuge,tayi tsaye ta kasa karasowa sai faman zare ido take tana kallon kanta ta cikin glass din hadi da waige-waigen bayanta tsoronta kar hajia ta shigo sashen, Abbas ne yace"Zakee wacece wannan?ba tare da ya dago ba yace"wa kenan? "Ina nufin waccan yarinyar dake tsaye gaban window" sai lokacin ya dago tare da kai dubansa kan window din,kura mata ido yayi yana kokarin tuna inda yasan face din,lokaci guda ya gane yarinyar,"what d hell is she doing here.. ya fada acikin ransa,shikam Abbas sai ya kalli fatuu sai kuma ya kalli haisam ganin yanayin fuskarsa ya dan canja yasa shi cewa"kasanta ne? girgiza masa kai yayi alamar a'a,kafin yace"may be wurin hajia tazo,inba hakan ba,bama za'a barta ta shigo ba" gyada kai Abbas yayi alamar gamsuwa sai kuma yace"kilan irin yan gudun hijira din nan ne dake yawon neman taimako,to amman miya kawota nan gashi kaman bata da gaskia,kasan fa wasun su da sun samu chance sai suyi ma mutum sata,kwanaki haka akayi wani case a estate dinmu na wata yarinya very young daga shiga neman taimako tayi attempting yin sata,da aka kama ta shine tai confessing wai mom dinta ke tura su gidaje bara daga nan in sun gan abu mai amfani su daukko", Maida idanunsa yayi kan computer kafin yace"Allah ya kyauta" mikewa Abbas yayi yana fadin bari yaje yaga mi take yi a wajen,daidai lokacin kuma fatuu ta bar gaban windown don ta kasa hango ciki kanta kawai take gani,ta nufi kopar shiga falon kirjinta na cigaba da bugawa da karfi, daidai lokacin da ta kai hannu zata kama handle din kopan aka bude,zaro ido tayi cike da razana lokacin da suka hada ido da Abbas,aikuwa da gudun tsiya ta juya saura kadan ta wuntsila wurin sauka,Abbas na fadin"ke,ke,ina ai tuni ta fice daga part din,juyawa yayi ciki yana fadin"dama da ganinta bata da gaskia kaga tana ganina ta tsere,ya kamata ayi ma securityn can magana su bar barin irinsu suna shigowa" ya karasa maganar lokacin da yake kokarin zama,shidae haisam gyada mashi kai kawae yayi alamar toh, Kan kace mi fatuu ta kai gida ko Amadu dake sallamar yara masu siyayya bai ga sanda ta shige gidan ba,can karshen dan gadonta ta haye tana ta faman sauke numfashi hannunta na dama dafe da saitin zuciyarta don ba karamin gudu tayi ba ta tsorata sosae lokacin da Abbas ya bude kopan,dama a d'arare take. Abbas ya dan dago daga jinginar da yayi jikin kujera yana duba agogon wrist dinsa kafin yace"I think i will take my leave now zakee" dagowa haisam yayi ya jingina bayansa da kujera yana kallon Abbas "nayi tunanin za kai magrib anan it's almost time" sigh Abbas ya yi yace"anya kuwa, nayi ma feenah alkawarin ina gida za'ai magrib duk da yanzu ma time ya kure,banso tayi fushi" ya karasa maganar yana murmushi, shikam haisam dan waro idanu yayi cike da mamaki"yaushe kenan ka fara tsoron fushin Nafeesat? tuntsirewa da daria Abbas yayi"A yau din nan,kasan mata sun iya tsiya ba kamar in ka 6ata masu rai sun san ta yadda zasu rama,yadda na dawo daga tafiyar nan ai kaga bazan so in 6ata mata rai ba kar sai anjima in zama kamar d'an maraya tunda nidae ba yan tsallake tsallake nike ba,a iya ta halalin na tsaya...."tun kafin ya karasa Haisam ya d'aure fuska hadi da juyar da kansa gefe guda yana girgiza shi,ganin yadda yayi yasa Abbas kara tuntsirewa da wata yar iskar daria,dama yasan haisam din kunyar irin wadannan maganganun yake,shi kuma gashi bakinshi a sake yake wurin yin irin maganganun ya cigaba da cewa"ko da yake kaifa ba sanin yadda abun yake kai ba balle ka fahim....." da sauri haisam ya rarumi throw pillow ya jefa ma Abbas yana fadin"Go Abbas,Just go pls" sosai Abbas keta daria ya fara kokarin mikewa tsaye yana fadin"komai ka nuna kai mai kunya ne,bari kai auren mugani" shi dai still yayi yana kallonshi ganin ya mike yace"ba zaka shiga ku gaisa da hajia ba?" Abbas yace"next time", gyada kai ya yi"in tace ta ganka baka shiga kun gaisa ba zan fada mata saboda kar matarka tayi fushi ne ka ki zuwa ka gaida ta", "ah ai sai dae in kaine zaka fada mata nazo,tunda bata ganni ba ko ride dina na a wajen gate" dan murmushi haisam yayi yace"I don't have to..da kanta tana zaune zata gan kazo gidan" haisam na fadin hakan Abbas ya fahimci abunda yake nufi hannu yasa ya dafe forehead dinshi"Oh namanta da CCTV fa,tabb dole kam inje in gaidata kar nayi babban laifi,amman fa in na koma gida feenah bata saurare ni ba wllh kiranka zanyi kamata bayanin kai ka rike ni" harararsa kawae haisam yayi ya yunkura ya mike don kiran magrib da aka fara,patting shoulder dinshi Abbas yayi yana ci gaba da tabbatar mashi da zai kirashi indai feenah bata saurareshi ba a haka suka fice zuwa masallacin gidan. Atare suka shigo falon hajia bayan gama sallar magrib,kujera 2 seater haisam ya nufa ya fada samanta ya dan kwanta yayin da Abbas ya zauna saman one seater yana facing din haisam,ganin hajiyan bata a falon yasa Abbas cewa"ina hajiyan ne? watsa hannuwa haisam yayi alamar oho,sai kuma yace"kilan bata gama sallan ba kasan tana dan dadewa" Abbas yace"pls to ka kira ta mana kasan fa ina sauri ne" kura masa ido haisam yayi kaman bazai tanka sa ba sai kuma yace"badai matsalanka feenah bace,to ka kira nin if she denies u..." da sauri Abbas ya katseshi"akwae abunda nike so zan siya a hanya ne" haisam dake ta kallon shi yace"harda bribe kenan zaka bayar,nasan bai wuce chicken karka damu nasan inda zaka samu wannan koda tsakiyan dare ne" ya karasa maganar yana wani irin murmushin rainin wayo,shikam Abbas dan buga kafa yayi a kule yace"pls zakee do call her" hannu haisam yasa yana shafa beard dinsa kafin calmly yace"anya Abbas..." da sauri Abbas ya katseshi"halan ni jarababbe ne zaka ce,mu barshi a hakan idan kayi aure mayi wannan maganar ni dai pls ka kira man ita, Waya haisam ya ciro daga cikin aljihun jeans din jikinsa ya shiga kiran hajiyan tana d'agawa yace"U have a guest" yana fadin hakan ya cire wayan ya ajeta a gefensa, dagowa yayi yaci gaba da kallon Abbas yana wani murmushi hadi da dan girgiza kai,dan guntun tsoki abbas yaja yace"irin ka ne in kukayi aure kunfi kowa jaraba wllh zaka rinka man wani kallon iskanci"cike da rainin wayo haisam ya dage gira yace"haba" kafin Abbas yace wani abu hajiya ta shigo falon tana sanye da dogon hijab har kasa hannunta rike da cazbaha nufo inda suke zaune tayi tana fadin"bako daga ina..."bata karasa ba suka hada ido da Abbas dake kallonta yana murmushi,hannu hajiya tasa ta rike ha6arta"Abbas,dama kaine bakon?aikuwa da nasan kaine ma ba zan fito ba,yanzun ma komawa ta zanyi"ta kai maganar tana kokarin juyawa,da sauri Abbas ya mike yaje yasha gabanta yana daria,ruko hannayenta yayi yana fadin"afuwan hajjaju ta,tuba nike" harararsa tayi tace"ni bawani dadin bakin da zakayi man,yaushe rabon da ka tako kafafunka gidan nan da sunan kazo gaidani?sai yanzu da abokinka ya dawo shine zan ganka wato dai dama saboda shi kadae kake zuwa ko?" da sauri Abbas yace"No hajjaju aikin san dae ina zuwa ko da baya nan,kawae kwana biyu wllh abubuwa ne sukai yawa bansamu na leko ba,amman dama yanzu zuwa nayi don in gaidaki in kuma bada hakuri,dawowa ta gari kenan..."hajiya dake d'an harararsa ta katseshi"dawowarka gari kenan kazo ganin abokinka ko", "a'a ke nazo gaidawa ai shi tun kafin na tafi ma mun hadu,pls tuba nike muje ciki ki zauna sai mu gaisa sosae" uhm tace kafin ta juya suka nufi wurin kujeru,haisam dake ta latsa waya amman yana jin abunda suke cewa ya dago yana kallon Abbas da har lokacin yake rike da hannun hajia guda yace"da girman ka..."da sauri Abbas ya daga masa hannu alamar yayi shiru don Allah,karaf sukaji hajia tace"yake karya ba"gaba daya suka sa dariya, saman 3 seater suka zauna Abbas ya shiga gaida ta,tace"ya iyali,suma dai ka hanamu zumunci kiri kiri Abbas" da sauri yace"ni na isa hajjaju ai in kullum kika ce kina son ganinsu indai ina gari zan kawo maki su", "haka dae kace amman yaushe rabon da ka kawo su tun can kwanaki da kuka zo" "in sha Allahu cikin satin nan zan kawo su hajjaju afuwan nasan nayi laifi", "Shikenan zan hakura amman in baka kawo mun su anyi zumunci ba banga mai sasanta mu ba" da sauri yace"zanma kawo su ai" juyawa hajiya tayi side din da kitchen yake tana fadin"Saude ko ta gama sallan tazo ta kawo maka lemu" tana niyyar kwala ma sauden kira Abbas yace"bari inje in daukko ai ni ba bako bane dama kishi nike ji" ya mike ya nufi hanyar dining yana fadin"ke kin damu dani hajiata,shi wannan gwauron ko tayin ruwanma baiyi munba balle ma ya daukko man" haisam dake a kishingid'e yace"baka san inda ruwan yake bane,ko ni yaron ka ne da zan daukko ma" Bayan Abbas ya daukko lemun bai zauna ba suka yi sallama da hajia,tace ya jira zata bada sako akai ma d'anta,Saude ce ta kawo masa ledar biscuits dasu sweets din da ta siyo ma hajiyar dazun da rana da taje siyayya kasuwa,suka nufi wajen gate inda ya parker motarsa,bayan Abbas ya tafi komawa haisam yayi part din hajiya ya ci gaba da kallo har aka kira sallan isha ya fito ya nufi masallaci. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* *BY ZAINAB LALUH📲* ~(Oummu Imam)~ Free page 25 .......Bayan angama sallan komawa haisam yayi part d'insa ya shiga wanka,bai jima sosae ba ya fito daga cikin bedroom dinsa ashirye cikin riga da wando marasa nauyi rigan sleeveless hoodie ce army green,irin rigan nan mara hannuwa mai dauke da hula mak'ale a wuya igiyoyinta sun zubo saman kirjinshi sannan gaban rigan anyi wani design din rubutu baki mai walwali, wandon kuwa baki ne 3 quarter ya wuce gwiwarsa ya d'an matse,ba karamin kyau yayi cikin shigan ba,kirarsa ta kakkarfa ta bayyana,baisa hulan rigan ba tana kwance a bayansa sai da ya yi shut down laptop din dake ajiye a falon kafin ya fice ya koma part din hajia,don gaba d'aya yau he's busy working on his laptop dama kuma bai zuwa Gym ranar lahadi,tunda rana hajiya keta kiranshi tana korafin yana gida amman bazai zo suyi hira ba,ya sanar da ita yana wani aikine,tace to ya dawo falonta yayi aikin mana yace mata yafi samun network a part dinsa tayi hakuri da dare zai zo suyi firan. *** *** **** Tun bayan da ta shige d'akin bata fito ba saida aka kira magriba ta fito yin alwala anan suka had'e da Amadu yana ganinta yace"ke,yaushe ki ka dawo gidan?ba dazun da ki ka dawo daga islamiyya kince man zaki gidan hajia ba?" fatuu dake ta zare idanu tace"ai..ai hajiyan batanan ne shine na dawo" gyada kai yai ya wuce yayi alwalarsa ya nufi masallaci,itama alwalar tayi ta koma daki tayi salla,gaba daya ranta bai mata dadi sai tufka da warwara take zulluminta kada gobe tayi bataje ta bashi hakuri kaman yadda haulat ta bata shawara ba,gashi ita dae harga Allah tsoron zuwa take don batasan abunda zai biyo baya ba,kuma tana ganin mutumin kaman baida kirki,tana ta zaune har aka kira sallan isha'e,anan ta yanke shawarar komawa bashi hakurin bayan ta gama sallan isha din, tana gama sallan ta shiga yin addu'a tana rok'on Allah da ya taimaketa mutumin yayi hakuri in taje,ta tuba bazata kara ba,tana cikin shafa addu'an ta jiyo sallamar gwaggo ta dawo,gabanta ne ya fadi rass ta shiga tunanin yadda zata fita daga gidan don tasan sai gwaggon ta tambayi abunda zata je yi gidan hajia yanzu, d'aga labulen dakinta da gwaggo tayi yasata juyawa da sauri tana kallonta da yake akwae wutan Nepa,shigowa ciki gwaggo tayi jikinta sanye da uniform din aiki fatuu dake kallonta tace"Dja66ama bé wargo gwaggo", "yauwa,ya gidan? "Lafiya lou" ta bata amsa, "ashe bakiji dadi ba?yanzun nan Amadu ke gaya man a kopar gida" fatuu tace"eh amman nasamu sauki sosai,ya bani magani nasha har islamiyya ma naje" jinjina kai gwaggo tayi"kin kuwa ci abinci?" Girgiza mata kai fatuu tayi alamar a'a,ganinta sukuku gashi idanunta kaman tayi kuka yasa gwaggo cewa"kodae wani abun ke damunki?ince ba fitina kika jawo mana ba dae,dama inata mamaki kwana biyu da ba'a kawo man k'ararki ba,fada man gaskia minene fatuu? gabanta ne ya fadi rasss da sauri ta sunkuyar da kanta kasa tace"a'a gwaggo ba wani abu fa,kawai har yanzu ban dan jin dadi ne"ta karasa gabanta nata faduwa, Jinjina kai gwaggo tayi ta nufi hanyar fita tana fad'in"ki tashi ki ci abincin sai ki k'ara shan magani,Allah ya sawaka,ni bari inje in watsa ruwa insamu na kwanta na kwaso gajiya sosai,kizo ki kar6i abincin gama abun biki can cikin jakata da aka ban in zaki ci su cin-cin ne da dublan" daga haka ta fice,sosai gaban fatuu yaci gaba da faduwa jin maganar da gwaggo ta mata,tabbas dole ta tafi taba mutumin nan hakuri tun gobe batayi ba asirinta ya tonu, *** *** *** *** Hajiya zaune a falo tana kallon sabon shirin kwana cas'in na tashar arewa 24, haisam ya shigo da yar sallamar da ba lalle ma in taji ba ya nufi kujera ya zauna yana facing din hajiyar,juyowa tayi ta kalle shi da d'an murmushi"sannu,yau kasha aiki,yini guda mutum na latse-latse,basu hakuri gobe kaje office din" hannu yasa ya shafo forehead dinsa kafin yace"ba aikin office bane" gyada kai tayi sai kuma tace"halan turawan ne,suda basu ganin mutum mai hazaka su kyale,in sunyi hakuri ba tattarawa za kai duka ka koma wurinsu ba" d'an kwantar da kai yayi baice mata komae ba saima wani lumshe ido da yayi,da sauri ta juya tana kallon t.v jin muryar yawale yana magana,ba karamin cin dariyar acting dinsa take ba yana burgeta,tana ta daria tace"in baya ga ma film,ai ni a zahiri bazan iya d'aukan irin wannan matsayin direba ba,sai kata maimaita mashi magana sannan ya fahimta ina dalili" juyowa tayi tace ma haisam"wai nan direba ne fa ahaka" A hankali haisam ya ware idanunsa kan tv d'in yana kallon abunda hajiyan ke magana akai,dan murmushi yayi ya juya ya dauki wayansa dake aje a hannun kujera yana fadin"in driver dinki ne har marinsa zaki one day", "in naga zai man wasa da rayuwa ba dole na maresa ba,ai wannan kyansa yaron gida ba abu mai mahimmaci kaman tuki ba" shi dai bai ce mata komai ba ya cigaba da latsa wayarsa,ita kuma hajiya taci gaba da kallon su yawale da rayya tana daria,jefi-jefi take waigowa tana ma haisam magana kan shirin don dama haka take bata iya shiru in tana kallo shidai sai dae yayi d'an murmushi ko ya daga mata kai don ba kallon shirin yake ba,so ba abunda yake fahimta. Hajiya ta sake juyowa tace"akawo maka abinci ko?" Kai ya daga mata alamar eh,ta juya tana kwala ma Saude kira,bayan ta fito ta bata umarnin ta kawo ma haisam abinci tace mata basai ta zubo a warmer ba tunda yanzu zai ci ta amsa da to,ta shige kicin don zubo masa abincin,a tray ta d'auro kayan abincin ta nufo inda haisam d'in yake don ta fahimci indai shi kad'ai zaici abinci baison akai masa saman dining table,saman sofa table ta daura tray din tana gaishe shi ya amsa,tana kokarin zuba masa zo6o cikin cup ya dakatar da ita alamar ta barshi zai zuba da kansa,daga haka tace "aci lpy" sannan ta juya, cire plate din da aka rufe abincin yayi ya tsaya yana kallon shi wanda spaghetti ce tasha vegetables da busasshen kifi sai kamshi ke tashi,da sauri ya d'ago yana niyyar tsaida Saude dake k'okarin shigewa cikin corridor"hey...." Hajia ta juya da sauri tace"je ki abunki" kafin ta juyo tana dan harararsa"in ma zaka cinye ka cinye don ba abunda za'a rage,wato dazun don kaga can aka bika dashi shine ka tsakura kace azo a dauke ai dama nace zamu hade da daddare ne" haisam dake ta kallonta yana dan cizon lip d'insa na k'asa had'i da dan murmushi yace "did i say anything?" A tsiwace tace"But u'r about to....haka kurum don ka jaman sharri iyayenka su zo su ga ka rame suce hakanan na matsa ka dawo wurina ashe bana baka abinci" Haisam couldn't help it but laugh,sai kace ta daukko wani k'aramin yaro wanda baisan ciwon kansa ba,itama dariyar take taci gaba da kallonta da har yanzu ake shirin da take kallo,shi kuma ya fara cin abincin. Tunda ta amso abincin ta dawo d'aki ta kasa cin wani na kirki yan lomomi ne tayi taji duk ya fita ranta ba kuma don bata jin yunwar ba,sai don hankalinta daba a kwance ba,tunaninta yadda zata fita yanzu ba tare da gwaggo ta hanata ba don dole fa taje taba mutumin nan hakuri da daren nan,tsam ta mik'e hannunta dauke da plate din abincin ta maida kicin ta rufe a tsakar gida tayi tsaye tana zullumin zuwa tambayar gwaggon daga baya dai ta nufi d'akin gabanta nata faduwa,d'aga labulan d'akin tayi ta shiga da yar sallama gwaggo da har ta kwanta amman bata yi bacci ba ta d'ago da kanta tana k'okarin kunna fitilan wayanta "fatuu,djam? ta tambayeta,Matsawa tayi kusa da gadon tana kallon gwaggon tace"d..dama gidan hajia zanje" cike da mamaki gwaggo tace"gidan hajiya da daren nan,me zaki je yi?", "Un..dama jiya ne dana je tace in koma yau zata bani sako,to dana dawo islamiyyar safe ban lafiya sai d'azun dana dawo ta yamma naje sai na iske bata nan ta fita ita da t.k amman Aunty Saude tace man in koma in ta dawo don kafin ta fitan saida ta aikota tazo ta kira ni ta iske ban dawo daga islamiyyar ba" ta k'arasa maganar sai faman zare ido take gabanta naci gaba da bugawa da k'arfi,ba don ba haske sosai ad'akin ba da tuni gwaggo ta gane k'arya take shirga mata don har yar zufa tayi, sanin dama hajiyar na aikowa kiran fatuu wani lokacin yasa gwaggo cewa"to miyasa tun dazun baki je kinga ko ta dawon ba,kika bari dare yayi har haka tara fa ta kusa inma bata yi ba..." da sauri ta katseta "ai ina niyyar dana gama sallah in koma sai kuma kika dawo" gwaggon tace"to ki maza kije ki dawo karfa ki zauna har Amadu ya tashi" cike da farin ciki tace"ah bazan zauna bama" daga haka ta fice ta nufi hanyar fita ko hijab bata yi tunanin taje tasa ba iya d'an bakin gyalenta na gado ne a saman kanta ga kan yayi wani tum saboda gashinta dake a kwance ba kitso yayin da jikinta ke sanye da riga da skirt na material da alama tana son sa riga da skirt,gidan hajiya ta nufa duk da fargabar da take ji hakan bai hanata tunkarar gidan ba don tasha alwashin a daren nan sai taba mutumin nan hakuri. Sauran kad'an haisam ya k'arasa cinye abincin wayarsa ta hau yin wata kara alamar notification,sanin karar ko ta miye yasa da dan sauri yakai hannu kan hannun kujerar yadau wayan yana dubawa lokaci guda yanayinsa ya canza da wani irin expression mai kaman mamaki kaman bacin rai yake kallon videon fatuu dake sand'a tana tunkarar falonsa,lokaci guda ya furta"Again...! jin haka yasa hajiya juyowa tana kallonsa "ince dai lafiya ko?"ta tambaya,"Yea,nothing" ya bata amsa yana k'okarin mik'ewa don ya yanke a ransa sai yaje yaji mike kawo ta part dinsa,ganin yana kokarin tashi Hajia tace"wai mike faruwa,gashi nan yanayin fuskar ka ya canja kuma ka ki ka sanar dani" d'an murmushi yayi"nace ba komae Sweethrt,just wani sako ne na tura shine aka sanar dani bai shiga ba zanje nai resending" ya fadi mata hakanne don ta kwantar da hankalinta, tace"to baka sha zo6on ba", "kar ki damu zan sha lemu inna koma can" dan 6ata rai tayi ta fara korafi "shikenan baza'a bar mutum ya huta ba,yini guda mutum nata faman latse,latse haba" yar daria yayi yace"to dama mai nema ina yaga hutu sweethrt" yana gab da fita daga falon tace"zaka dawo muyi hira ko? d'aga mata hannu yayi yana juya shi alamar a'a yace"ki ci gaba da kallon ki saida safe tomorrow is Monday and early to bed early to rise.." daga haka ya fice hajiya na fadin"Allah ya tashe mu lpy toh". Da sauri ya nufi part dinsa don baison ta fice kafin ya isa, A hankali fatuu ta kama handle din kopan ta turata kad'an sannan ta turo kanta tana leken cikin falon,a iya hangenta bata hango mutum ciki ba sai computer da ta gani ajiye saman table hakan yasa tayi tunanin ko ya shiga cikin d'aki ne,fiddo kanta tayi waje ta shiga tunanin ko har yayi bacci ne,to yanzu ya zata yi ita?wata zuciyar tace anya kuwa yayi bacci,ai da ya rufe kopa,can kuma tace k'ilan kuma bai rufe kopa tunda akwae jami'an tsaro a bakin gate.....a daidai lokacin haisam ya shigo cikin part din har ya iso bakin balcony din bata ji motsinsa ba,k'ara tura kopan tayi tana sake lek'en cikin falon taga ko ya fito,cike da mamaki haisam ke kallon bayanta yama rasa tunanin da zai yi akanta babban abunda ya d'aure mashi kai shine mike kawo ta part d'insa?miye hadinshi da ita,sannan yama akai tasan inda yake,fuska a matukar d'aure tamkar bai ta6a daria ba ya tattaka stairs din ya haye"Excuse me!"yace mata, a firgice fatuu ta juyo don sam bata ji motsin shi a bayanta ba balle tasan dashi a wurin,a tsananin tsorace take kallonsa ganin ya daure fuska tamau,wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi lokaci guda ta fara ja da baya,atunaninshi rugawa zata yi kaman yadda tayi dazun hakan yasa a kausashe yace"kina guduwa zan sa aje har gidanku a kamo ki,gida mai kiosk right?" hannu fatuu ta shiga yarfawa jin abunda yace,kenan da gaske ne duk abunda Gaye ya fada mata,don dama yace mutumin ya tambayeshi kwatancen gidansu,lokaci guda ta rude ta kid'ime ta shiga fadin"innalillahi....nashiga ukkuna"tana ta faman yarfa hannu kamar wadda wuta ta kona. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *Paid Book* *2️⃣6️⃣* kama handle din kopan yayi ya tura kafin ya juyo fuskan nan ba wasa ko kadan yace"biyo ni! a hankali ta fara jan k'afafunta kaman wadda kwai ya fashe mawa a ciki tabi shi ciki kaman yadda ya bata umarni,haisam na shiga ya wuce saman kujera wurin da ya zauna d'azun da Abbas yazo,ita kuwa fatuu tana shigowa wani ni'imtaccen sanyi had'i da daddad'an kamshi suka kai mata karo,zaro idanu tayi baki bud'e ta shiga bin ko'ina na falon da kallo,ba komai yafi dauke mata hankali ba face chandalier(fitilan sama) yadda take d'auke da sarkoki masu kyau,tunda take bata ta6a ganin irin fitilan a zahiri ba sai acikin film din yan kasashen waje,ita bata ma ta6a tunanin akwae irinta a Nigeria ba,gaba d'aya ta saki baki tana ta kallonta har gyalenta ya zamo ya tsaya kan tudun gashinta dake fake, Ganin bata k'araso cikin falon ba kuma yaji lokacin da ta shigo yasa haisam waigawa ya kalleta,tsayawa yayi yana kallon ikon Allah kaman ba itace ke kerma ba,bai ce mata komai ba ya juya yai powering laptop up ya jingina da kujera ya jira tagama booting kafin ya fara daddanata kuma har lokacin fatuu bata daina kalle kallen da ta ke ba,ganin bata da niyyar shigowa ga dare nayi shi kuma yana son yaji abunda ke kawota part din nasa yasa shi daukan wayarsa ya d'an bubbuga gefenta a saman c-table,aikuwa firgit fatuu tayi ya juya ya dan kalleta ya had'e giran sama da ta kasa,hakan yasa da sauri ta nufo cikin falon can gaban red armchairs ta wuce tana isa gefensu kawai ta zube saman gwiwowinta tayi kneel down, baice mata komai ba yaci gaba da operating laptop d'in hakan yasa ta samu daman cigaba da kallon fitilar da alama ba k'aramin daukan hankalinta tayi ba,a hankali ya d'ago idanunsa ya dan kalleta sai kuma ya mik'e ya nufi bedroom dinsa tabi bayansa da kallo har ya shige kafin ta maida kallonta kan fitilar dai, bai dau lokaci ba ya fito hannunsa dauke da wani k'aramin kwali,daidai bakin corridor ya tsaya ya kai hannu ya latsa wani switch lokaci guda hasken fitilar da fatuu ke kallo ya dauke,sai kuma ya k'ara latsa wani lokaci guda hasken wasu fitilun ya gauraye gidajen dasu T.V suke ko wane gida na pop cast din na d'auke da fitila hakan ba k'aramin kawata wurin yayi ba,ai kuma sai ta maida kallon nan wurin har wani dan dukar da kai take,ita mamakinta daga ina hasken ke fitowa don ba'a ganin fitilun sai dai hasken kawai,komawa yayi ya zauna ya fara kokarin bude kwalin da ya fito dashi hakan yasa fatuu ta maido hankalinta kanshi tana so taga minene a ciki,screen glass ne ya fiddo wanda yake sawa in zaiyi aiki da dare don yai protecting idanunsa daga illar hasken screen,binshi da kallo fatuu tayi lokacin da yasa glass din don ba karamin kyau yayi masa ba tamkar fashioned glass haka yake,kasa d'auke idanuwanta tayi sai kallonshi take tun daga saman kanshi har kasan kafafunsa cikin ranta tana ta mamakin yadda akai hajiya ta haifi mai kama da yan kasan waje ita da take bak'a kuma ba wani kyau ne da ita sosae ba,shikam ji kyau kaman shi yayi kansa ta ayyana a ranta,ga dogon hanci ba kaman na hajiyan ba d'an mai fadi dashi,ji yayi a jikinsa tana kallonsa hakan yasa ya yi mata kallon kasan ido suka had'a idanu,da sauri ta sadda kanta kasa don sai taga kaman harararta yayi,tana ta wasa da yatsun hannunta gabanta na cigaba da faduwa. "mi kike zuwa yi apartment dina? Ta ji ya jefo mata tambaya, Da sauri ta d'ago ta kalle shi tana faman zare ido,ci gaba yayi da magana ba tare da ya kalleta ba"ina sauraranki,ki gaya man abunda ke kawo ki nan don dazun ma naga kinzo" gabanta ne ya cigaba da bugu da sauri da sauri,sai faman motsa baki take ta rasa ma ta ina zata fara,mi zata ce mashi,d'agowa yayi furiously yace"am i not talking to human being? ganin yadda yayi maganar yasa da sauri ta fara magana cikin in'ina tace"d...da...dama..." sam ta kasa magana saboda kafeta da yayi da ido sai faman kerma hannuwanta ke yi,ya fahimci ta tsorata dashi hakan yasa yadan sassauta daure fuskan da yayi yai lowering voice d'inshi yace"uhun dama what?" "dama zuwa nayi na baka hakuri don Allah kayi hakuri ka yafe man laifin da nayi maka,na tuba Allah bazan k'ara ba" ta k'arasa maganar tana dan ta6e baki alamar zata fara kuka sai kace k'aramar yarinya lokaci guda hawaye ya fara sauka daga idanuwanta tasa gefen gyalenta tana gogewa, "wonder shall never end.." abunda haisam ya fada cikin ransa kenan,shi mamakinsa wai hakuri tazo bashi,shi da tunda tayi masa laifin yama manta da ita,to miyasa zata zo bashi hakuri?ya jefa ma kansa tambaya lokaci guda kuma ya tabbatar ma da kanshi dole akwae dalilin yin haka,wannan bayin kanta bane don bai tunanin tana da cikakken hankalin dama zata gane tayi laifi har ta bada hakuri,amman koma miye dalilin he will find out now. Tsayawa yayi yana kallonta kaman mai nazarin wani abun sai kuma ya janye idonsa yaci gaba da abunda yake yi ita kuma sai faman murzar ido take ita ala dole kuka take kaman yadda haulat tace tayi,"wani laifi ne ma kika man? ya jefo mata tambaya ba tare da ya kalleta ba,da sauri ta d'ago tana kallonshi kaman ba itace mai murzar idanu ba,mamaki ne ya cikata aranta tace"kenan ma ya manta abunda nayi masa,dama banzo b...." ya katse da cewa"sai na maimaita maki ne? da sauri tace "a'a,d..dama nice wadda ta rotsa maka gilashin mota,amman na tuba bazan k'ara ba"tayi raurau da idanu alamun zata yi kuka tana ta6e baki, D'agowa haisam yayi ya had'e hannuwanshi ya daura ha6arshi a sama yana kallonta hakan yasa ta sunnar da kai ya lura bata son had'a ido dashi ajiyar zuciya ya sauke yace "miyasa kika zo bani hakuri?" da sauri ta sake d'agowa tana kallonshi sai faman zare ido take sam bata so ta sanar dashi yadda sukai da Gaye don kada yace ashe ba don Allah tazo bashi hakurin ba sai don taji gilashin nada tsada kaman yadda haulat ma ta gargadeta,lokaci guda ta fara tunanin karyar da zata fada masa...kaman haisam yasan abunda take tunani yace"mark u!ba'a man k'arya,da zaran kika fad'a man karya yanzun nan zan gane karya ki ke and I hate people who're telling lie kinga laifinki zai kara yawa kenan" wani irin kuka cikin fatuu yayi ta had'iye miyau da kyar, shikenan ba daman tayi masa karya don ta yarda sosai da abunda yace ta k'ura ma computer din gabanshi ido tana tunanin ko tanan yake ganewa in an masa karyar don taga wasu abubuwa jone ta gefenta. "baki ji mi na tambaye ki bane?bana son maimaita magana" fuska a d'aure yayi maganar hakan yasa fatuu gyara kneeling dinta ta fara motsa baki cike da fargaba tace"d..daman Gaye ne yace wai...wai gilashin motan nada tsada sosae,wai bazaka ta6a yafewa ba sai an biya ka,duk da ni naga kana da kalan masu kirki,am..amma shi yace wai in ba'a biya kaba gidan yari za'a kaini...."ta kwashe duk yadda sukai da gaye ta sanar masa tana ta d'age baki tana langa6ar da kai ita irin yaji tausayinta d'innan", Sigh haisam yayi cikin ransa yace "exactly my thought,cire hannuwansa yayi daga k'asan ha6arsa ya maida kallonshi kan laptop din gabansa "wanene Gaye? Kaman jira take da sauri tace"wani mara jin magana ne anan unguwar d'an shaye-shaye yace wai yaga sanda na jefi gilashin motan ka kuma wai shi ka tambaya kwatancen gidanmu" d'an guntun murmushin gefe yayi jin abunda tace ga kuma k'aryar da gayen yayi masa don ya gane wanda take magana akai,kallon k'asan ido yayi mata"kice mai irin halinki kawai" da sauri tace"ai ni bana shaye-shaye kuma ma ni yanzu na shiryu na bar rashin ji daman shaidanu ne suka yiman fitsari a kai haka kaka na ke cewa" ta k'arasa tana ta6e baki alamar zata cigaba da kuka, Danna wani key haisam yayi da karfi da alamar dot yayi kafin ya d'ago sosai yana kallonta on a serious note yace "While,duk abunda guy din ya fada maki gaskia ne,bcos i see no reason just don na raba ku fada zaki man asara irin wannan,dama abunda yasa ban dau mataki tun ranar ba lawyer na bai gari don bani son ai wasting time dina shiyasa ban reporting wurin police ba,gara muje court kawai a biyani hakkina,but luckily enough ya dawo yau so gobe zamu tafi can don already yasa anyi filing case din" ai ba fatuu ba ni kaina saida gabana ya buga don ba alamar wasa a fuskarsa yayi maganar,ita kam fatuu tsananin tashin hankali ta shiga,kuka na kirki ta fara tana masa magiya, fad'i take"Don Allah,don soyayyar ka da manzon Allah,don hasken goshin manzon Allah kayi hakuri,in kana son ga kabarinka gana manzon Allah,in kana so ka gaisa da manzon Allah(S.A.W) yaya handsome kayi hakuri ka yafe man na tuba Allah bazan k'ara ba...." cike da mamaki haisam ke kallonta ganin yarda duk ta tashi hankalinta tana masa wani rokon da shi tunda yake bai ta6a jin kalarsa ba ga wani suna da ta kira shi dashi wai handsome,jingina bayansa yayi da kujeran yasa hannu daya ya rike ha6arsa had'i da bakinsa yaci gaba da kallonta kaman mai nazarin wani abu,ita kuwa har lokacin kuka take ga majina dake ta zubo mata sai faman sa gefen gyalenta take tana gogewa,hakan da take yasa haisam jin kyankyami don ya tsani majina bama ita kadai ba sam baison abun k'azanta,tsam ya mik'e daga inda yake ya nufi fridge dinsa don tun d'azun yake jin kishi saboda da yaci abinci baisha ruwa ba,ya bude ya d'auko lemun gwangwani tare da wani glass tumbler mai kyau ya rufe fridge din ya dawo cikin falon ya aje su a gefen laptop din sannan ya sake juyawa ya nufi wurin tv cikin wani gida ya dauko silver tissue box mai shegen kyau sai kyalli yake ya dawo ya zauna dashi a hannunsa ita dai fatuu sai binsa take da ido tana murzar idanunta da gyale tana cigaba da yin shesshekar kuka ga wata ajiyar zuciya mai k'arfi da take yi, d'ago kanta tayi suka hada ido yayi mata alamar tazo da hannunshi,mikewa tayi ta nufi inda yake a gefen center table din ta durkushe idanunta sunyi jawur har sun fara kumburi,miko mata d'an akwatin yayi tasa hannu biyu ta amsa tana kare mai kallo don ta rasa mi zata yi dashi duk da tissue din ta leko,ganin haka yasa ya d'an duku ya kar6i abun ya jawo tissue din ya 6allo mata kana ya mika mata ya aje box din a saman c-table ya koma ya jingina yana cigaba da kallonta ahankali ta kai tissue din hancinta tana sunsunawa saboda wani sanyin kamshi da take kaman daga sama taji yace"abunda na baki ki da ita kenan?"cikin sauri ta fara goge fuskar tata sai murzar fuskar take still kallonta yake a hankali ta saci kallonsa suka had'a ido hakan yasa a hankali ta cire tissue daga fuskarta ta rike a hannu gyara kneel down din tayi taci gaba da rok'onsa, cikin marairaicewa tace"don Allah yaya handsome kayi hakuri,kwarankwatsi kaji na rantse bazan k'ara ba,don Allah yadda Allah ya rufa maka asiri kake a aljannar duniya kada kasa akai ni gidan yari,ka barni inci gaba da kwana ad'an gidanmu ina cin abincin gwaggota,don wllh ko munje kotun bani da kudin da zan biya ka Allah kuwa" tana maganar tana d'an jujjuya kai lokaci guda wasu hawayen suka gangaro, Shi abunda yafi daure mashi kai yadda yarinyar ta tashi hankalinta akan maganar biyan kudin,koda su talakawa ne bai yi tunanin zata tashi hankalinta har haka ba,nan take ya fara tunanin ko ana maltreating yarinyar ne,cike da son gano hak'ikanin gaskia cikin cool voice yace"ai bake zaki biya ba,dama duk in yaro ya nemo rigima ai parents dinshi ne a ciki in abun biya ne su zasu biya ke ai nasan bazaki iya biyana ba" kaman jira take ya gama maganan ta kar6e"ai ni a wurin kakata nike kuma bata da kudi talaka ce ita"takai maganar tana sauke ajiyan zuciya, "Amman ai guy din nan yace tana aikin asibiti kuma nasan ana samun kudi a aikin..."da sauri fatuu ta saka salati"Innalillahi... Wallahi gaye bai tsoron Allah,na rantse karya ya fad'a maka", yace"kenan bata aikin? tace "A'a ai kai ba'a yima karya, tana yi amman fa attender ce a asibitin,kasan miye attender din? ta tambayeshi,a hankali ya girgiza mata kai alamar a'a, "masu fa share-share da goge-goge har jinin haihuwa su ke gogewa" ganin ya d'an yamutsa fuska yasa da sauri tace"ai sai sun sa safar hannu suke yin aikin kuma in sun gama suna wanke hannuwansu,kuma ma ita gwaggon tsafta gareta kullum da ta dawo aiki take yin wanka kuma ta wanke kayan aikin" d'an yamutsa baki yayi yace"kyauta take aikin ne" tace"a'a ana bata albashi amman basu da yawa abinci take siya mana bama su isa mu rinka cin shinkafa kullum sai an had'a da tuwo", "Ina Dad dinki?ya tambayeta,tace" ba a garin nan yake ba yana Yola acan jimeta anan kauyenmu yake sunan shi rugar baffa ard'o", "ku fulani ne kenan? daga masa kai tayi alamar eh,yace"kuna da shanu?" batare da ta kawo komai a ranta ba ta k'ara daga masa kai alamar eh,dan guntun murmushi yayi" shikenan sai abani shanun madadin kudin gilashin,ni kuma nan yan kud'adena da nike saving sai in bada a gyara man glass din,tunda na fahimci cash bazasu samu ba" tunda ya ambaci shanu gaba daya ta k'ara rikicewa ta wani zazzaro idanu tana kallonshi lokaci guda tasa tafin hannunta na dama ta rufe bakinta tana girgiza masa kai da sauri,shi dai sai kallon ta yake yana k'ara mamakin yadda ta kara rudewa don yace abashi shanu kuma,dan daure fuska yayi yace"kina nufin shanun ma bazai samu ba duk da akwai? baki na kyerma tace"kwarankwatsi kaji na rantse ard'o bazai ta6a yarda ya bada shanu goma ba akan laifin dana aikata,ai ko baffana ya aikata bazai bayar ba balle ni...."waye shi" ya tambayeta,da sauri tace"kaka na ne wanda ya haifi baba na kuma shine mai garinmu" ta6e baki haisam yayi"ni ai dama bani da case da shi,shi ina ruwanshi Dad d'inki shine zai biya ba grandpa ba" cije le6e fatuu tayi alamar bazaka gane ba,hawaye suka gangaro mata tace"ai shi Baffa na baida shanu goma yan kad'an gare shi ko biyar ma basu kai ba kuma duka ard'o ne ke iko dasu,basu isa suyi wani abu dasu ba batare da ya bada izini ba,nasan wallahi bazai bayar da shanun ba koda harbeni za'ai a gabanshi kuwa..." muryarta ce ta karye ta fashe da kuka, d'an murmushi yayi ba tare da ta gani ba yace"bai ga za'a harbe kin bane" tsayawa tayi da goge kwallan da take, "wallahi ni nasan bazai bada ba,ko fa Akuyan Jibo dana jefa ta mutu da kyar ya yarda aka biya shi..."kawai sai gani Haisam yayi ta kwashe da daria tana fad'in"wllh ranar yakin badar akai..." ganin yadda haisam din ke kallonta yasa ta shiga daidaita natsuwarta tana fadin"kayi hakuri wllh abunne dariya yake sani in na tuno ko banyi niyyar yin dariyar ba" tayi maganar tana turo baki,shi dai kallonta kawai yake can cikin ransa kuwa mamaki yake wai wadda ke cikin wani hali ce haka take daria lokaci guda yai assuring kansa cewa yarinyar is Mental, Hannu ya kai ya d'auki lemun gwangwanin daya daukko ya bud'e hadi da tsiyayawa a cup ya dauka ya kai bakinsa,tunda ya fara tsiyaya lemun ta tsaya cakk cike da mamakin wane irin lemu ne wannan take binsa da kallo har yakai bakinsa ya dan kur6a sau biyu kana ya aje"kice dama kinsaba jifan abun mutane ki kashe masu and the worse of it shine da har abu mai rai kike jifa ki kashe", "Wllh ita kadae ce babban abu mai rai dana ta6a kashewa,sai su 6era,kyankyaso,da kadangare su kuma ai kaga suna cutarwa ko....yauwa na tuna na ta6a karya ma Altine k'afan kazarta amman wannan ramawa nayi, nima take man kafan d'an kaza na tayi kuma ai ba haramun bane in an maka abu kaji baka iya hakuri ka rama ko,ko ita akuyan jibon ba hakanan na kasheta ba laifi tayi man kuma ma wllh bada niyyar kasheta na jefetan ba" ta karasa sai faman nishi take tana daga hannu ita ala dole bata da laifi. "Nima kenan laifi nayi maki don na raba ku fada shiyasa kika fasa man glass din?haisam ya tambayeta yana k'ara kur6ar lemun, "a'a ni badon ka rabamu fada ba,ba gaura mun mari ka yi ba,wllh har saida fa naga wuta" ta turo baki tana sussunar da kai kasa,jinjina kai haisam yayi,da alama dai yana enjoying hiran ko kuma kilan har yanzu akwae sauran abunda yake son sani game da ita ne. "Shi abun da kika jefan ya mutu mi yayi maki shi kuma?ya jefa mata tambaya,kallonshi tayi har lokacin akwae kwalla a fuskarta tace" wai akuyan jibo? dage mata gira yayi alamar eh,durkushewa tayi don ta gaji da kneeling d'in tace"ba a makarantar bokon mu ne aka koya mana yadda ake shuka abinci ba,shine fa na had'a yar gona a gefen gidanmu na shuka gero da masara inason in sun fito in saida insamu kudi saida suka fara fitowa watarana kawai naje gonar naga an tuge su duka wllh ranar naji bakin ciki,kasan mi? ta d'age ido sama,a hankali haisam ya girgiza mata kai alamar a'a,taci gaba"harfa kuka nayi,naita birgima gashi abun haushin ma bansan waye ya tugen shukan ba,Yadikko nace taita bani hakuri da Baffana ya dawo ya sake bani wasu yace inje in shuka yace insamo k'ayoyi na rufe wurin in ta fara fitowa,shine fa na hakuri amman duk da haka na dau alkawarin inna gano ko waye wllh bazan kyale shi ba,bayan wani lokaci da shuka su suka fara fitowa nayi yadda baffana yace inyi sosai nike kula da gonata kowa yasan gonar fatuu masifa ce ba mai zuwa wurinta,abun bak'in ciki...." tasa hannu tayi tagumi cike da damuwa,haisam dai still yayi yana kallon Mental fatuu, taci gaba"wai fa sai da shukan nan suka fara yin tsawo sosai watarana yadikko ta aikeni in debo ruwa a bayan tudu na dawo d'auke da tulu na akai tun daga nesa na hango kaman an bude man gona da sauri na nufi wurin tun kan na isa na hango yar iskan akuyar nan duk ta cinye shukan saura kad'an ta gama,Allah kun bansan lokacin dana saki tulun nan ba na rarumi dutsi na jefa mata bai sameta ba ta fara kokarin guduwa cikin sa'a kayoyi suka tokareta ta rasa yadda zata gudu nikam ina ganin hakan na dau icce na ritsata naita dukanta sosai hardai tasamu ta fice da kyar take gudu saboda kafafunta dana doka sosai,hakan bai ishe ni ba na sake rarumar wani k'atoton dutse na jefa mata aikam basai ya sauka akan cikinta ba kuma dama ciki ne fa da ita nan take ta fad'i a kasa tana birgima idanuwanta na haka...." ta langwa6ar da kai ta kakkafe idanunta tana displaying yadda Akuyan tayi,Haisam couldn't help it but laugh,da farko tausayin akuyan yaji don shi mutum ne mai tsananin tausayi amman yadda tayi yasa shi yin dariya har hak'oransa suka bayyana,yana ganin zata bude idanun ya yi saurin d'aure fuska. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 27⃣ ......Bud'e idanun tayi taci gaba"ina ganin haka na watsa da gudu gida,ashe wani yaro gidado ya gan sanda na jefi akuyan ina jinsa yana fadin sai ya gayo ma jibo,aikuwa d'an banzan yaron nan ya falfala aguje yaje ya gayo ma jibo abunda nayi ma Akuyarsa,ina tsaye gaban yadikko tana ta tambayana ina ruwan,miya faru ta ganni a firgice gashi na shigo a guje,ban kaiga bata amsa ba sai ga yaron yayan baffana sun shigo da Jibo rungume da Akuyar......, kyalkyacewa ta sake yi da daria wannan karon har tafi ta d'azun tace "kai,wllh Jibo baida hankali,kasan wai ko wando fa bai sawo ba don masifa daga shi sai yar riga" d'aure fuska Haisam yayi yana d'an harararta,ganin haka yasa da sauri tace"banfa ganin mashi jiki ba,a'a wllh haram ni ba abunda nagani ai rigan jikinshi ya sauko har gwiwa fa,kama duba a computer ka zaka gan ba k'arya nike ba ni banga komai ba" ta daga hannu, Haisam da yai zugudum yana sauraranta tamkar ya kunna Redio yace"uhum.."alamar taci gaba,tace"masifa da bala'e yazo yayi tayi yana cewa wllh sai an biyasa akuyansa in ya yarda shege ne shi,nan dai duk yan gida suka fito suna tambayan ko lafiya da yake gidanmu babba ne duk yayyu da kannen Baffana anan suke da iyalansu,ganin haka yasa Yadikko ta kira Babana a waya da yake lokacin yana kasuwa,ai yana jin abunda ya faru ya dawo da sauri don yana masifar sona baison wani abu ya same ni su kuwa sauran yan gidan duk sun tsane ni,kowa ya bud'e baki fatuu bata ji,fatuu bata da kunya,fatuu ka za,fatuu yen-yen....,kana ji ko?" daga mata kai yayi kawai da alama al'amarin nata yafi karfin tunaninsa. ta cigaba"gaba daya aka kwasa aka tafi wurin Ardo don yayi shari'a,karshe dai ardo yace za'a bashi wasu yan kudi yayi hakuri,yace bai ganin ni yarinya ce,kuma suma wai fama suke da ni,Jibo kam ya rantse da kwarankwatsi gajimare Akuyarsa za'a biyasa kuma daidai girmanta harda cikin ma,kaji fa don bala'i,shi kuma Ardo yaji haushin jibon yak'i jin maganarsa amatsayinsa na shugaba yace har kudin ma ba'a bashi,aikuwa yace to ko daga nan gari ya nufa yan sanda zaije ya fada mawa,baffana yayi ta ba ardo hakuri yace ya bashshi ya biyasa acikin akuyoyinsu,saboda baison aje wurin polisawan ai man wani abu,da kyar fa aka biya jibo akuyansa,ai yana fita Ardo yace akamo ni da gudu naje na 6uya a karkashin gadon yadikko amman mugun yaron nan Jauro da yake ya tsane ni shima saida ya jawo ni aka zane ni don dama ardo baison abunda zaisa a ta6a masa dabbobi,bayan an doke ni kuma yace a d'aure ni daga ranar ban sake fita ko makaranta ma ban k'ara zuwa,kuma ko aike na ma kada a sake yi wai aure za'a man ya gaji da hali na,na dinga kuka, ni d'aure nin da akayi ma bai dame ni ba don nasaba,jin za'a man aure shi yafi damu na,don ni bana son auren karatu nike son inyi in zama likita,kwana na biyu a d'aure sai dare ake saki na inje in kwanta da rana kuwa ina a daure don karna fita,kaga ni aka maida Akuyan ko,Baffana ba yadda ya iya saidai yayi ta bani hakuri yana man fad'an in daina rashin ji in natsu don Allah,sam baijin dadin yadda ake maganganu akaina,ana cikin hakan rana ta ukku kawai ba sai ga gwaggo ba....." dakatawa tayi ta rike ha6a tana kallonshi tace"kasan wace gwaggon? da farko shiru yayi yanata kallonta kaman bazaice komai ba sai kuma yace "Grandma dinki attender i guess" da sauri tace yauwa ashe kana ganewa, "Aikuwa tana zuwa ta ganni a d'aure ta tambayi dalili aka fad'a mata ai sai tasa kuka,tace yanzu yar jikan tawa mace kwallin kwal ce ake ma wannan horon kaman wata dabba,tace to wllh kafanta kafa na,ina jin haka nima naita kuka nace eh zan bita don ni banson ayi man wani aure,shi Baffana baison rabuwa dani to amman shima baison ayi man aure a lokacin,duka fa ban dade da fita shekara goma ba,shi da gwaggon suka sami Ardo suka roke sa akan ya bada izini gwaggon ta tafi dani zanci gaba da karatu a wurinta,a tunanin ka mi zaice? ta k'ara jefa ma Haisam tambaya, gyara zama yayi yadan bud'e dogayen yatsun hannunshi yace"zaice ki tafi kawae tunda kin dame su...." da sauri ta katse shi "haka fa wllh,cewa yayi Dille,dille Allah yaru on djam...wai kutafi,kutafi Allah ya kiyaye,kwana ukku gwaggo tayi lokacin na tattara komae nawa,muka taho Baffana kaman zaiyi kuka,nima banso rabuwa dashi ba dasu yadikko da yayana Kamalu don su kad'ai ne ke sona,wai kaga yadda aka rako ni kusan duka yan rugan fa kaman an rako wata diyar gwamna amman nasan duk murna suke zan tafi su huta" ta k'arasa sai faman nishi take dama kuma saman skirt dinta ya matse mata ciki saboda ta takure. Sauke ajiyar zuciya yayi"shine da kika dawo nan kika dasa rashin jin instead of ki natsu ko" gyara gyalenta tayi dake ta faman zamewa tace"wllh naso fa in natsu in koma ba ruwana da kowa ko gwaggo ma tayi man fadan haka,to su yan birnin nan sun cika tsokanan fad'a,wai fa don lokacin da nadawo nan banjin hausa sosae duka abu kad'an na iya wani lokacin ma ba daidai nike fadan wanda na iyan ba shine sai suyi ta tsokana na suna ce man yar fillo,ni kuma banso,tun dai ina hakuri har na gaji na fara nuna masu nima yar banza ce" ta k'arasa tana jinjina kai, haisam dake kallonta yace "ya akai kika iya hausa sosai?" "ai nafa kwana biyu anan,shekarana ukku yanzu,kuma acan lokacin dana zo saboda tsokana na da ake shine k'awata wadda gwaggo ta hada mu da ita haulat ta rink'a koya man da kawu na Amadu,gwaggo ma in bata komai tana koya man,ban dade ba na iya,yanzu ma ni mantawa nike da ni fulani ce,duk da gwaggo nayi man wani lokacin wai karna manta gaba daya,kuma ma wani natan ni ba ganewa nike ba" "While,thank u for dat,kinga yanzu kin ban leakage na yadda za'a ban shanun ba wani 6ata lokaci,tunda shi mai akuyan cewa yayi zai kai wurin police,ni yanzu in na tashi sai inje da armies nasan dole za'a bani ko? zaro idanu tayi a firgice tace "Sojoji! dage mata gira yayi"yeah,ko ahakan ma baza'a bani ba?" jiki asanyaye tace"dole ma a baka,amman nasan dole Baffana shi zai biya ardo,kuma ni shikenan zama na anan wllh ya k'are aure za'a man kuma ni wllh likita nike son zama...."kasa k'arasa maganar tayi saboda kukan da yaci karfinta,ganin haka yasa haisam cewa"hey,miye kuma na kuka haka,in kina ganin hakan da matsala sai mu canja wata shawaran ai" jin hakan yasa ta dakata da kukan ta d'ago tana kallon shi, "What about your mom,wannan da kike kiran sunanta a story dinki ita ba sai ta bani ba,kinsan mothers normally sunfi tausayi" cikin muryar kuka tace"wai yadikko? daga mata kai yayi alamar eh,da mamaki take kallonshi tace"kai baka san mi yadikko ke nufi ba? banza ya mata,hakan yasa tace"au yi hakuri na manta kai dan indiyawa ne ba fulani ba,to yadikko ba mamana bace kishiyan mamana ce,kuma ita ina taga wasu shanu goma,ko fa baffana na gaya ma baida shanu goma ballantana ita", "Ita mom din naki fa" ya tambaya,ai kaman jira take ta idasa durkushewa ta langa6ar da kai cikin muryan kuka tace "Mamana ta rasu tun ina yar yarinya,ni marainiya ce wllh,ance tunda ta haife ni bata k'ara lpy ba,har dai bayan wasu shekaru ciwon yaci karfinta sannan fa aka kaita asibiti akace sai anyi mata aiki a cikin cikinta,haka suka dawo da ita gida wai sai an had'a kudin,da kyar Baffana ya samu ya harhada kudin sai da ma ya amshi aron shanayen ardo ana gobe za'a tafi kaita ayi aikin ta rasu...." kuka tasa sosai hakan kuma ba karamin sanyaya ma haisam jiki yayi ba,yayi shiru yana ta kallonta ta kife kai ajikin c-table,can ta dago tana goge kwalla da tissue taci gaba"shiyasa nike son in zama likita don banson in kara rasa wani nawa don wannan dalilin,don Allah kayi hakuri yaya handsome karkasa ayi man aure" Shiru yayi yana cigaba da kallonta kaman yana nazarin wani abu,ita kuma sai sunnar da kai take yi kasa,sigh yayi "kinsan ke marainiya ce,kuma kina da wannan ambition din amman kuma kika kasa natsuwa ko..,while gaskia bazan iya yafewa ba don ba k'aramar asara kika man ba..." ta6e baki ta fara yi zata dasa kukan da sauri yace"karki fara wannan kukan! bake da bakinki naji kince ba haramun bane in an maka laifi kaji baka iya yafewa ka rama ba...." idanu waje take kallonshi ta rasa bakin magana,yaci gaba"kin tuna ko a story dinki da wadda ta 6alla maki kaza ne or what,so is the same da in anyi maka asara kaji baka iya yafewa kace a biya k..." tun kafin ya k'arasa yaga ta mike zumbur,don tun dazun take jin fitsari take rikewa yanzun ko tsabar rudewa tasa bata iya rikesa don gab yake da ya zubo mata,kallonta yayi sama da kasa ganin yadda take ta kerma gashi ta hade kafafunta sai tura hannu take tana dudduk'ewa yasa shi tambayar"lapia..."da sauri tace"fi..fitsari nike ji don Allah,zai zubo" kwalla ne suka fara gangaro mata,da sauri ya daga yatsansa pointing at d door opposite to him,yace"kije ciki akwae kofa by your right ki shiga" da sauri ta juya ta kalli kofan da yake nuna mata kafin ta nufeta da dan gudu-gudu,saboda kafafuwanta da suke a hard'e daidai bakin corridor gyalenta ya silalo kasa ta juyo kaman zata dauka sai kuma ta juya aguje ta tura kopan da alama fitsarin ya fara zubowa ne,sosai taba shi daria yana yi yana girgiza kai a fili yace"Silly Girl, Duk wannan abun gwaggo na can tayi nisa a baccinta,dama tunda ta dawo tace ma fatun ta gaji sosae,ko lokacin da fatun ta tambayeta zuwa gidan hajiyan gab take da fara baccin,shi kuwa kawu Amadu yana shago mutane nata zuwa siyayya kasantuwar gobe Monday akwae aiki ga yan zuwa makaranta kuma,hakan yasa ake ta zuwa siyayyar abun bukata da safe,sam baima san fatuu bata gidan ba. ________________________ Waya Haisam ya dauka ya duba time,karfe 9:30 sauran yan mintuna dama lokacin da ya baro part din hajia tara bata k'arasa yi ba,shiru yayi yana dan tunani sai kuma ya d'an ta6e bakinsa kafin ya Kwantar da kanshi jikin kujeran yasa hannu yana shafa suman shi baya,lokacin ta fito ta duka bakin corridor din ta dau gyalen kafin ta nufo cikin falon tana yafa shi saman kanta,inda ta tashi ta koma tayi kneel down tana kallon shi,dagowa yayi suka hada ido wannan lokacin bata janye idanun nata ba a marairaice take kallon cikin idanunsa sun dan dau lokaci haka kafin calmly yace"hope baki 6ata man toilet ba..." da sauri ta daga masa kai"ai a cikin yar farar tukunyar nayi,a wurin hajiyar nan gidan na koyi yadda ake amfani da ita" dan bude ido yayi"wani hajia?", "Hajiya mamanka,ai ta sanni kuma tana sona sosai har dinki take man,ko kayan nan na jikina ita ta siya man su hadda ma uniform din makaranta ita ke siya man da littattafai....don Allah yaya handsome kayi hakuri ka yafe man,wllh in taji wannan abun da nayi maka 6atawa zatayi dani dama tana tace man nabar rashin ji,wllh daga yau na daina,zan koma kamar haulatu ita ba ruwanta,nima dama don kar a raina ni adauke ni sakara shiyasa in aka man abu ban kyalewa amman tunda kowa haka yake so in koma zan koma Allah kun" "Wa yace maki in baka yin fada raina ka ake ko a dauke ka sakarai? ai yawan fadan kesa ana insulting mutum,kuma shiyasa ma mutane ke tsokanarki,ni bana fada kuma ba wanda ya raini ko kallon banza ba wanda ya ta6a attempting yi man" baki sake take sauraranshi tana kallon bakinshi,jin yayi shiru tace "kai yama za'ai a raina ka,ai da an kalli fuskarka ansan baka wasa da mutane" dan ta6e baki yayi"yanzu ya kike so ayi" da sauri tace"kayi hakuri da abunda nayi maka,kace ka yafe ba sai an biya kaba don Allah yaya handsome" gyara zama yayi sosai ya d'an k'ankance idanunsa"who told u sunana haka?", A hankali ta d'aga yatsanta ta nuna rubutun dake agaban rigarsa,wanda yake baki sai walwali yake,kai dubansa yayi inda ta nuna ya kalli rubutun wanda akayi in italic font an rubuta "*_Call Me Handsome_*, Dagowa yayi ya kalleta cike da mamakin yadda ta iya karanta rubutun duk da style din da akayi ma rubutun bai mata wuyar karantawa ba,hakan ya tabbatar masa da tanada kokari kuma har turanci tana fahimta don in anmata tana ganewa"Ajin ki nawa a school? ya tambayeta,yatsun hannunta ta daga masa guda ukku,hakan yasa ya dan daure fuska da sauri tace"J.s 3 nike" "dama a garinku kin gama primary school ne kafin kizo nan? Tace "a'a aji na hudu zanje biyar na dawo nan da farko ma ba makaranta nike zuwa ba acan gangare wani dan yayan Baffana da yayi karatu yake koya mana kafin yace ma baffana wai ina da kokari akaini makaranta,to lokacin dana dawo nan kawu Amadu nayi man lesson shine yace ma gwaggo basai an maida ni primary ba,akaini secondary kawai" jinjina kai yayi kafin yace"now sit properly zamu yi magana dake" da sauri ta mik'e tsaye ta dan tattare skirt din sama sannan ta koma ta zauna kaman wadda zata ci tuwo ta zuba masa ido tana jiran taji abunda zaice mata gabanta na dan bugawa amman ba sosai ba saboda ganin fuskarsa adan sake, "Zan yi hakuri,in kuma yafe kaman yadda kika roke ni,amman on one condition,dole akwai abunda zansa ki.." da sauri ta katseshi"to wllh koma miye zanyi indai bai sa6a ma addini ba,koma ya sa6an zanyi sai na roki Allah ya yafe man" sosai ya daure fuska yace"nayi maki kama da wanda zai saki hakan??" da sauri tace"a'a yaya handsome don Allah kayi hakuri wllh bansani ba na fadi hakan...", "karya kike,u said it intentionally yanzu ke har Allah kike sa6a mawa don kar ayi maki hukunci!" Ganin yadda yayi maganar a kausashe yasata rudewa tsoronta kar yace ya fasa yafewar,lokaci guda ta fara kokarin kara yin kneel down baki na kerma tace"na rantse da Allah ban ta6a sa6a ma Allah ba don a yafe mani,kwarankwatsi kaji na rantse,ni ai bamma ta6a yin irin wannan laifin ba tunda na dawo garin nan" gaba daya ta rude jikinta sai faman rawa yake,alamu yayi mata ta zauna da hannu,komawa tayi ta zauna, "to amman yanzu miyasa kika za6i ki sa6a mashi don kawai a yafe maki?"da sauri tace"daman naji malamin mu na islamiyya yace shi Allah mai hakuri ne yafi kowa hakuri,indai kayi masa laifi ka roke shi ya yafe maka to zai yafe makan"ta k'arasa maganar tana ta dage baki, Girgiza mata kai yayi"You didn't get him right,banda laifin da akayi masa da gangan,in kinsan abu ba kyau kuma kika aikata even if u ask for his forgiveness he won't forgive u,saboda kinsani kika take,so duk hukuncin da za'a yi maki is better ayi maki da ki zabi ki sa6a ma Allah saboda hukuncinsa yafi na kowa tsanani,Understand? Ya tambayeta hadi da dage girarsa sama,da sauri ta daga kai sama,tace"Astagfurrullah,Allah,Allah na tuba"ta tofa a hannu ta shafa,girgiza kai ya d'anyi ganin abunda tayi. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *28⃣* Haisam speaking calmly"kaman yadda nace zan yafe amman abisa sharad'i guda,shine i want u to promise me bazaki k'ara fada da kowa ba,kar in sake ganin ana fada da ke,indai kina son zama Doctor like you said to sai kin natsu don in kina rashin ji koda kina da kokari you won't be a doctor,saboda sai masu natsuwa ne ke wannan aikin" Sakin baki tayi tana kallonshi,ganin hakan yasa shi dage gira yace"is too harsh for u ko,nasan bazaki iya bari ba..." da sauri tace"a'a wllh,nifa mamaki nike,wai iya abunda zanyi kenan ka yafe miliyan din,kuma bazaka fadi ma hajiyanka ba da gwaggotah?" d'aga mata kai yayi alamar eh,cike da farinciki ta washe baki tana fadin"wllh,wllh,kwarankwatsi kaji na rantse nayi maka alkawarin na daina,kam yo wannan abun mai sauki ai ko cin tuwon gwaggo yasin yafi shi wahala" ta k'arasa maganar sai faman daria take dimples dinta duk sun lotsa,shi dai sai kallonta yake ya dan ta6e baki, ta ci gaba"Uhm nasan gaye sai yayi mamaki sosai idan yaji ka yafe man,shida yace wai ko dan gidanmu ne kai bazaka yafe man ba,dole sai an biya ka ko kuma akaini gidan yari,aiko sai na fad'a masa to ka yafen in na ganshi,nasan yanzu haka suna can kangon da suka saba zuwa yin shaye-shayensu,Allah dai ya shirye su", ganin yadda take ta faman farinciki yace"kibar wani murna i know u can't maintain,kin saba rashin ji,nasan sai kinci gaba" da sauri tace"ai wllh na bari fa,kam gidan yari fa za'a kai ni ko aman aure ai nama bari baruwana da kowa yanzu komi aka man zanyi hakuri, daman haulat tace Allah yana tare da masu hakuri kuma in aka cuce ka kayi hakuri shi zai saka maka ta hanyar da baka yi zato ba" dan murmushin gefe yayi yace "we shall see,ai inma kika kara ina zaune zan gani so karma kiyi tunanin yiman wayo kiga ai ban gani,kuma da kin breaking promise din zan tada maganar glass din don akwai camera a motana tayi recording lokacin da kika fasa glass din kinga dole a biya ni and I will not forgive again" a nutse yake maganar, Baki sake take kallonshi har ya gama maganar sannan tace"ai fa ko kare mai bak'in baki ne ya cije ni bazan k'ara fad'a da kowa ba,kwarankwatsi kaji na rantse kuma zaka gani" ta k'arasa tana daga hannu sama alamar rantsuwa,haisam dake kallon abunda tayi yace"miye wannan din da kike fad'i? tace"kwarankwatsi?" daga mata kai yayi alamar eh,tace "rantsuwa ce,in dai ka rantse da ita kuma ka karya to fado ma mutum take ta kashe shi" hannu yasa ya rike beard dinsa kafin calmly yace"to ba kyau ki bari,is a kind of shirk,kinsan miye shirka?" ya tambayeta,zaro idanu tayi a rude tace"shirka!hada Allah da wani kenan,malamin islamiyyar mu yace kaman kayi mashi kishiya wurin bauta masa" Yace "haka ne,kinga ke yanzu wannan abun da kike fadi kaman kishiyan ki ka masa tunda kina rantsewa dashi,kuma ba'a rantsewa da ko wani abu bayan Allah don komai a karkashin ikonsa yake, Hannuwanta ta d'ora asaman kai tace"na shiga ukku,wllh ni ban san ba kyau ba fa tun a garinmu nike rantsewa da ita,kuma malam yace babban laifine shirka,shine laifin da Allah bai yafewa in aka mutu ba'a tuba ba"tayi narai narai da idanu zata fara kuka, ganin hakan yace"ai shirkan iri iri ne,wannan tunda kince baki sani ba sai ki tuba ki bari,in kuma kika ci gaba kinga kinsani kin take like i told u before, Da sauri ta daga hannu sama tace"Allah,Allah na tuba ka yafe man,bazan kara rantsewa da ita ba,ban san shirka bane,daga yanzu da kai kadae zan rinka rantsewa" ta tattofe a hannu ta shafa,girgiza kai kawai yayi ganin wata bidi'ar kuma. Shuru sukai na wani d'an lokaci,ita dai sai faman murmushi take, "daman haka ake barin ki kina fita da dare ki dade batare da an neme ki ba? taji ya jefo mata tambaya,daga kai tayi ta kalleshi tace"a'a Gwaggo bata bari na ina fita da dare,nan gidan ne kawae nike zuwa ina kaiwa dare,da fa har kwana ma nike amman yanzu na daina kwana sai dae inzo taya hajiyanka fira to wani lokacin sai bacci ya kwashe ni,sai ta aiko kawu Amadu ya tafi dani,yanzun ma ce mata nayi zanzo wurin hajiyar tana nemana shiyasa ta barni,da tace ma dare yayi,sai kuma tace inzo amman kar in bari har kawu Amadu ya tashi daga shago" dage gira yayi yace"k'arya ko" daria tayi tasa tafukan hannu ta rufe fuskarta tana fadin"ai gidan hajiyan nazo ko,kuma malam yace akwai inda wata k'aryar ke hallata mutum yayi,kaga da banzo ba har gobe tayi shikenan da sai gidan yari,ko kuma ka matsa abaka shanu ni kuma aman aure" ta k'arasa maganar tana turo baki, Fuskarshi dauke da dan murmushi yace"ai ba wani abu bane in an maki auren.." da sauri ta katseshi"kam,ni d'in yar karama dani hakan ai child abuse ne(cin zarafin yara)" waro ido yayi cike da mamaki sai kuma yayi daria har hakoransa suka bayyana yana jinjina kai yace"Child abuse!waye ya fada maki hakan?" tace"malamar social studies dinmu" jinjina kai kawai yayi ya mik'a hannu ya daukko gwangwanin lemun ya idasa juye sauran ya kai bakinsa yana sha,bin lemun tayi da kallo ko kyaftawa batayi,can ya d'ago idanunsa suka hada ido,dan murmushi tayi batare da ta janye idon ba,yatsa ya mika yana nuna mata fridge yace "je ki daukko" girgiza masa kai tayi alamar a'a, "baki shan lemu ne?"ya tambaya,tana ta murmushi tace"ina sha,amman gwaggo ta hana ni rok'o" dan guntun tsoki yayi kafin yace"kin rok'e ni ne daman,in kika roke nima bazan baki ba don ba abu ne mai kyau ba shiyasa grandma d'in taki ta hana ki,C'mon je ki daukko"mikewa tayi ta nufi inda fridge din yake, Hannu ya kai ya dauki remote yayi turning tv on,yana cigaba da shan lemun yana kallo,dawowa tayi tai tsaye gabanshi ba tare da ta d'aukko lemun ba,kallon ta yayi"ina lemun?" hannu ta dan watsa tace "babu" da dan mamaki yace"babu,to duk ina suka tafi?? tace"a'a akwai sauran wasu irin wannan da kake sha ne babu" wani kallo yayi mata mai kaman harara"to wannan shikenan dama aciki kuma baki bukatan shi,ki daukko wani" "giya ce?" yaji ta jefo masa tambaya yana niyyar kai cup din bakinsa,da wani irin expression ya d'ago yana kallonta,sosai gabanta ya fad'i ta shiga ja da baya tafukan hannunta dafe da bakinta furiously yace"zo nan!" sosai ta tsorata da yadda fuskan shi ta canja,a hankali ta fara matsawa dan nesa dashi ta durkushe tana girgiza kai alamar yayi hakuri don ta kasa ma magana,sassauta d'aure fuskan yayi yace"nayi maki kama da mai aikata abunda kika fadi ne...?da sauri ta girgiza masa kai,yace"to miyasa kika tambaye ni? Baki na kerma tace"naga kalan shi wani iri ba irin na lemunan dana sani bane shiyasa nayi tunanin ko itace tunda ni bansan ya take ba,amman don Allah yaya handsome kayi hakuri na tuba" ta d'aga hannuwa, Sauke ajiyan zuciya yayi ya kwantar da bayanshi jikin kujeran kaman bazai tanka mata ba,gaba daya ya gaji da magana,dama duk duniya a yanzu dai mutum biyu ne ke sa shi magana da yawa,daga Abbas sai hajia,yanzu kuma ga fatuu dama dazun Abbas ya gama nashi,ita abunda yasa ya biye mata dama don akwai abubuwan da yake son sani game da ita don dan kwana biyu da ya santa ya fahimci bata jin magana sosai kuma shi tunda yake bai ta6a cin karo da yarinya irin haka ba,haka yanzu ma da tazo wurinshi sai yaga kaman ba daidai take ba,shiyasa yayi tunanin ko tana da matsalan kwalwa ne,to amman daga baya ya fahimci kaman lafiyarta lau kawai halinta ne hakan. "Don Allah yaya handsome kayi hakuri kar kayi fushi,wllh bansan irin wannan lemun bane" kwalla ce ta fara gangaro mata a daidai lokacin ya d'ago da kansa yana kallonta itama shi take kallo tana matsar kwalla,gently yace"is okey,amman ki rage yawan surutu mara amfani" da sauri ta d'aga kai alamar toh,alama yayi mata da hannu tazo ta mike a hankali ta tsaya gefensa ya d'aga gwangwanin lemun ya fara magana a nutse"akwai lemu kala kala,wani a roba,wani a can,wani a kwalba,wasu manya wasu k'anana,so ba iya wad'anda kika sani bane lemu kawai,kar ki k'ara ganin wani yana shan wani kalan lemu da baki sani ba kice giya,Understand?" Da sauri ta daga kai,ya ci gaba"abunda yasa nace baki bukatan sa,Energy Drink ne,kuma yana da d'an karfi ne", bude baki tayi da mamaki tace Energy..! Yace"yea,ko baki san miye energy ba?da sauri tace "nasani,is the ability to do work" cike da confidence tayi maganar d'an murmushi yayi,hakan yasa itama tayi "mi kenan yake nufi?, Tace"karfi,karfin yin aiki,shi kake sha kenan shiyasa ka ke da power?" ta fad'a tana nuna damtsen hannunshi dake a murd'e,banza ya mata taci gaba"don dai kace in aka roke ka abu bakayi da nace kabar lemun da zaka bani yanzu sai nima ka samo man iri wannan din,wallahi aiki yawa yake man,inna dawo daga makaranta sam ban hutawa ba kaman gwaggo in tana nan,fatuu yi tankad'e,fatuu dibo ruwa,fatuu fito ki shara,komai ni", Murmushi ya sake yi yace "wannan ai ba wasu aiki bane,and being a girl dole ki koya irin wannan aikin..." tace "to ai sai in mutum aure za'a masa sannan ni kuma fa ba yanzu zanyi ba sai nan da dadewa,ba na fada maka..." da sauri yace "yea,is a child abuse,je ki daukko wani zan kawo maki wannan din" tace "toh,ta juya,ya bita da kallo,kafin ya maida kallon kan t.v. Lemu fanta ta daukko ta dawo ta zauna a inda ta tashi,ta rike lemun tana d'an wasa da robar sai faman murmushi take da ka kalli fuskarta zaka san tana cikin tsananin farin ciki,sai kallon haisam take wanda idanunsa ke kan tv,juyowa yayi suka hada ido kaman jira take ta d'aga lemu daya tace"Allah yaya hansome kana da kirki wllh,kafi kowa na duniyar nan kirki,wai har kudin shanu gomaa ka yafe tabb,nagode thank u so much,God bless you" ta k'arasa maganar tana noke kai,gyara zama yayi ya d'an kwanta yana kallonta, "in kuma kika karya promise din,na dawo nace ban yafe ba sai kice ni mugu ne,nafi kowa rashin kirki a duniya,right? Girgiza masa kai tayi tace"a'a ai wannan ni naja ma kaina kuma,bama fa zan kara ba tunda nasan da nayi zaka sani,ai nagan ma abubuwan da ke fadi maka abu in akayi baka nan" yace "a ina?" Juyawa tayi tana nuna dakin da taje yin fitsari tace"a cikin dakin naga wani abu babba mai uban wayoyi ajiki,kuma ma naga wasu jajayen abubuwa manne a bango,bokayen turawa ne ko?" shiru ya mata,ya lura ta cika tambaya ta rashin kan gado ita kanta ba kan gadon gareta ba,ganin tana ta kallonshi alamar jira take ya bata amsa,ya d'age gira yace"bokayen fulani ne" da farko waro ido tayi waje cike da mamaki,can kuma sai ta gane gatse ne yayi mata don gwaggo ta saba yi mata,hakan yasa ta d'age kafafunta ta tura kanta ciki tana daria gyalenta ya zamo kasa, Dago kanta tayi a hankali suka had'a ido dashi tana murmushi tace"ashe kaima ka iya irin abun gwaggo"banza ya mata,ganin ta rungume lemun yace"kisha mana" girgiza kai tayi tace"ba yanzu zan sha ba,dashi zanje makaranta gobe in yi break" jinjina kai yayi sai kuma yace"je ki k'aro wani" daga na hannunta tayi tace"ai wannan ya ishe ni" "What about ur friend,bazaki bata ba,ko ba school daya kuke ba?" tace"wai haulatu,ajin mu ma daya kuma seat dinmu daya da ita,tare ma muke yin break din,ai sai mu raba" shiru yayi yana tunanin halinta ne haka bata da had'ama ko kuwa don yace bai son roko shima" je ki daukko mata wani,in nace kiyi abu just do it banson jayayya" da sauri ta mik'e tana cewa"yi hakuri yaya handsome,taje ta daukko coca-cola ta dawo tana daria ta nuna mashi tace"ita haulatu tunda bak'a ce sai in bata wannan ni kuma tunda fara ce sai in sha wannan jan" ta koma ta zauna hadi da rungume roban lemunan,shidai dan murmushi yayi kawai kafin yace"karfe nawa Uncle din naki ke kulle shagon? tace "k'arfe tara da rabi ko goma cikin sanyi amman da zafi kaman yanzu yana kaiwa har sha daya" time ya duba a wayansa yaga 9:50,yace mata "shi zai zo ya tafi dake ne? tace "a'a haka gwaggo tace dai kar na bari ya tashi,amman in ban koma ba har ya tashin zata aiko ya tafi dani" jinjina kai yayi kawae yaci gaba da kallo,can ya mike don ya gaji bacci yake son yi,gashi gobe akwae aiki,ya wuce bedroom dinsa tana ta kallon bayan shi har ya shige,tana ganin ya shige ta kyalkyace da dariyar farinciki,tana tillah robobin lemun hannunta tana cafewa. Sanye cikin jallabiya mai gajeren hannu ash color ya fito,komawa yayi inda ya tashi ya zauna yana kallon yadda take wasa da robobin lemun,dagowa tayi suka hada ido tayi dan murmushi a hankali tace"Yaya handsome" shiru yayi kaman mai tunanin wani abu kafin yace"ba sunana haka ba" sakin baki tayi da mamaki tace"amman ai haka naga ansa a jikin riganka" yace"yeah,but wannan rubutu ne kawai", "ya sunanka to?"ta tambaya, d'an k'ankance idanunsa yayi yace"Haitham" cike da mamaki ta rika maimaita duka sunan,haisam da handsome can tace"ai to duk d'aya ne ko wancan da turanci wannan da hausa ko"d'age gira yayi yace"koh? Jinjina kai tayi"eh mana,kuma ni nama fi iya fadin handsome din kuma ai shi ya dace da kai,baka san mi yake nufi bane?" ta fad'a tana daria,dan murmushin gefe kawai yayi baice komai ba,daman saida yayi tunanin zata iya cewa sunan daya ne. Kallon time ya k'ara yi a wayansa lokaci guda ya mike yana fadin"it's already late,tashi na raka ki" toh tace ta fara kokarin mikewa hannuwanta rungume da lemunan,ta wuce gaba yabi bayanta daidai bakin kofan fita ta juyo da murmushi tace"in ringa zuwa ina gaida ka?"daga mata kai yayi alamar eh,daga haka suka fice. Unguwar shiru ga duhu saboda an dauke wuta,gidaje kad'an ne gaban su ke dauke da hasken wutar generator da suka kunna wasu kuma solar saidai gaban gidan hajiyan yafi ko ina haske saboda fitulun jikin gidan da suke akunne gaba daya,ko alluran mutum ta fad'i a wurin zai iya ganinta,gaban shagon Amadu ma akwai hasken kwai mai caji ga wasu mutane biyu a tsaye suna siyayya,suna kaiwa daidai rabin bangon gidan hajiyan yaja ya tsaya agaban fence itama tsayawar tayi tana kallonshi hannu yasa ya shafi forehead dinshi gently yace"Good nyt" murmushi tayi itama tace"to good night yaya handsome" jinjina mata kai ya yi daga haka ta wuce. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story._ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *2️⃣9️⃣* Haisam na ganin ta kai k'arshen katangar ya juya ya nufi gida don yaga akwai mutane gaban kiosk din. Tana gab da isa shagon Amadu taja ta tsaya tana tunanin wani abu sai kawai ta juyo ta nufi lungun dake tsakanin gidajen su da gidan hajia,daidai haisam na niyyar shigewa kwanar gate kaman ance ya juya yaga tasha kwana saboda hasken da ya haska lungun da tabi,tunani yayi a ranshi ina kuma yarinyar zata da daren nan,juyowa yayi ya tsaya yana kallon hanyar data bi,a hankali ya fara tafiya ya koma hanyar daya baro,daidai lokacin da ya kai karshen bangon ya juya yana kallon lungun lokacin ta karya kwanar dama ta shige ya daina ganinta,tsaye yayi yana ta kallon inda tabi yana cigaba da tunani,can ya ayyana kilan aikenta akai bata je ba sai yanzu,"ai kuma cewa tayi ta tambayi zata zo gidan hajiya don ta baka hakuri",wani bangare na zuciyarshi ya ayyana mashi can dai ya d'an ta6e baki hadi da d'age kafad'a daga haka ya juya ya koma gida. A daidai gaban kofan kwangon ginin data 6uya ranar juma'a lokacin data fasa ma haisam glass ta tsaya,tura kanta tayi tana lek'en ciki wanda yake dund'um ba haske,lokaci guda ta shige ciki ko tsoro bata jiba,ta nufi wata kofa, Zaune suke su ukku saman windunan wani babban d'aki,da gani falo ne aka fitar,suna ta busa hayaki sunyi mankas da wiwi(Allah ka shiryi al'ummar Annabi,Amin),jin motsin mutum ya shigo yasa daya daga cikinsu fad'in"kwalawa yasin...."da karfi yayi maganar duk suka dire na karshen na niyyar direwa da karfi fatuu tace "kai Gaye nice fa" jin hakan yasa shi tsayawa ya juyo yana k'are mata kallo cikin duhu,fiddo wayarsa yayi ya kunna fitila ya haska inda take tsaye,cike da mamaki da kuma fargaba cikin muryarsa ta wanda ya bugu da wiwi yace"Aljana!,kece ko kuwa Aljanar gasken ce" turo baki tayi tace"ni fa ka daina ce man Aljana banso" jin hakan ya tabbatar mashi da itace,juyawa yayi jikin windown yace"Goga,6aure ku dawo ba kwalawa bane" daga haka ya juyo ya nufo fatuu yana fad'in"ke Aljana miya kawo ki fadarmu da daren nan?", "ba kaine kace mutumin nan ko d'an gidanmu bane bazai yafe abunda nayi masa ba,to yace ya yafe kuma ko gwaggotah bazata sani ba" ta k'arasa tana murmura idanu, Gaye yace"wai mi kike magana akai kiman gwari-gwari don ni ba fahimtarki nike sosai ba na riga na dau caji kingane ko" yana maganar ya kasa tsayar da kanshi awuri guda,bude murya tayi tace"wannan mutumin dana fasa ma glass din mota wanda kace kudin gilashin yakai miliyan kuma inba'a biyashi ba gidan yari za'a kaini..." yace "eahh hakane,to minene?", "to yace ya yafe,yanzun nan daga wurinshi nike,naje na bashi hakuri kaga ma har lemunan roba ya bani" ta d'aga lemunan tana nuna masa,waro idanu yayi yana kallon robobin ta hasken fitilan daya kunna ya fara karanta sunansu a wawware"Co,co ca,co-la,da fannntah...", "Wai Gaye yane,mike faruwa ne anan wurin naga ana d'aga lemu ko kawo mana akai mu k'ara ne?" Goga ne yayi maganar wanda tuni suka diro ciki shida dayan suka zauna inda suke da suka ci gaba da bushe-bushensu,Gaye ya waiga yace"baabah ina yarinyar nan wanda muka hadu d'azun da safe na baka labarin ta rotsa ma wani mutum gilashi harma na nuna maka gidansu mutumin?" Goga yace"eah baabah na ganeta wata yar fara mai kumatun nan ko,mi ya faru da ita ne?", "kaganta nan tazo wai abun mamaki mutumin nan yace ya yafe mata,yanzun nan ta dawo daga wurinshi kaga harda lemunan gora ya bata,shine tazo ta fada man" wata yar iskar dariya gogan yayi yace"yo kai baabah wannan ai ba wani abun mamaki bane,taje ta basa gurasa ba dole ya yafe ba" Gaye ya juyo yana kallon fatuu fuskarsa dauke da yar dariya yace"shegiya Aljanna yar k'arama dake kinsan takan abun,ashe gurasa kika gutsira masa,ahh dole ya yafe kam" cikin rashin fahimtar zancensu da sauri tace"ni wllh ba wata gurasar dana kai masa,yo ni ina naga wata gurasa,dama a bokonmu ake saidawa to kuma yau bama ranar zuwa bace..." Wata mahaukaciyar dariya gaba dayansu suka kwashe da ita harda gaye,ganin haka yasa fatuu ta d'an tsorata ta juya zata tafi,caraf taji gaye ya ruk'o hannunta,da sauri ta juya tana kallonshi cikin fushi tace"kai Gaye miye haka da Allah sake man hannu ni in tafi gida" kai tabar wiwin dake hannunshi yayi wurin bakinta yace"haba Aljana ya zaki kawo mana ziyara har fadarmu kitafi ba tare da kin ta6a komai ba,kinsan mu akwai karamci,kidan busa kema" da karfi ta buge hannunshi cike da masifa tace"Allah ya tsari kakata Dije,Allah ya kyauta in sha wannan abun,ni ba yar iska bace..." jin hakan yasa Goga da 6aure durowa daga saman windunan da suke zaune suka nufosu a kausashe goga ke fadin"kee,to su waye yan iskan kenan,ai kece ma babbar yar iskar da daren nan fa kika je wurin wani k'ato ya gama dak'una ki,shine don kin raina mu kin d'auke mu masu kawunan kifi zaki wani zo kice wani ya yafe maki hakanan,k'anin gyatumarki ne shi ko na gyatumin ki iyehh??" shuru tayi tana kallon shi ganin yadda yake maganar yasa taji tsoronsu ya kamata gashi sunyi mata rumfa,da sauri ta juya zata fice Goga yasa kafa ya tad'iyota ta yo baya ta fad'i kasa da6ar ass dinta ya daki wani dutsi,da karfi ta saki wata razananniyar kara tace"Wayyo Allah gwaggo!!" Haisam na komawa falon ya kashe laptop din ya kaita saman desk ya ajiye kafin ya dawo ya dauki cup da can din lemun daya sha ya jefa cikin wastebin din parlon shi kuma cup din ya nufi fridge dashi saida ya dauraye shi a wani d'an madaidaicin basin dake makale a bango gefen fridge din kafin ya maida shi ciki,yaje ya kashe kayan kallo ya rage hasken fitilun wurin baifi guda biyu ya bari a kunne ba,daga haka ya nufi Bedroom hannunshi ruk'e da wayarsa,yana shiga ya jefata saman gado ya wuce cikin laudary,toilet ya shiga yayi brush daga haka ya fito,yaso ya watsa ruwa duk da yayi after ishaa sai dai ya gaji so yake kawai yaji sa a kwance,yadda yake ba tare da yasa sleeping dress ba ya haye gado,saida yayi addu'ar kwanciya kafin ya mika hannunshi yai switching fitilan dakin off daga haka ya kwanta ya lumshe idanunsa alamar bacci. *** *** *** Duk'awa Goga yayi inda take zaune tana ta murza wurin da dutsen ya cakar mata yace"kina nufin tafiya zaki batare da muma kin d'an sammana ba,haba ke kuwa,ai ance yaba kyauta tukuici,da gaye bai sanar dake gilashin nada tsada ba ai bazakiyi tunanin kije ki rokesa ya yafe maki ba ta hanyan basa abun dadi" yunkurin mikewa ta fara yi duk da radadin da take ji,hannu yasa ya dannata ta koma kafin yasa duka hannuwansa yana k'okarin kwantar da ita,lokaci guda fatuu ta gane abunda yake kokarin yi mata da sauri ta shiga kiciniyar mikewa tana fadin"ni ka kyaleni,wllh ba abunda naje yayi man saboda Allah ya yafe man,cewa yayi in daina rashin jin magana..." ganin abunda goga ke yi yasa Gaye da sauri ya duk'a gabansa"baabah mi kake kokarin yi haka ne,don Allah rabu da ita ta tafi,zai iya yuwuwa ya yafe mata hakanan kasan suna da kudi sosai fa,miliyan ba wata tsiya bace a wurinsu kyautarta ma sai suba mutum" harara Goga ya dalla ma Gaye yace"koma dai miye yasin bazan ga samu inga rashi ba,abu har gida dama na jima ban k'ara samun irin damar nan ba tunkan yarinyar nan hajara", juyawa yayi yace ma dayan"kai 6aure zo ka kama man in daure shegen bakin nan nata inba haka ba zata tona mana asiri ne" jin haka yasa fatuu kwara baki tace"Wayyo na shiga ukkuna,a taimaken...bata karasa ba ya buge bakin da karfi,a fusace ya juya yace ma Gaye"dallah kai kuma ka rike man kafafunnan nata" baki na rawa yace"don Allah Goga ka kyale yarinyar nan,abun da fa kake shirin yi ba k'aramin laifi bane wllh,hukuncinsa fa daurin rai ne,kana jin yadda kullum ake sanarwa,kuma kaga ta san mu, ba kamar ni har gidan iyayena ta sani wllh asirinmu tonuwa zaiyi baabah" tsawa ya daka mashi yace"to ni wawa ne da zan bari ta tona mana asiri,dallah zo kaji yanda zamuyi" matsawa Gaye yayi gab da shi,alamu yayi masa na ya kawo kunnansa,ya rad'a masa wata magana,a firgice Gaye ya d'ago yana kallon Goga ta hasken fitilan wayansa dake rike a hannunshi,lokaci guda ya shiga girgiza masa kai alamar a'a,ganin haka yasa fatuu k'ara rudewa duk da bata san miya fada masa ba,kara k'arfin wurga kafan da take tayi saboda Goga da 6aure sun riketa gam,ga gefen bakinta ya fashe saboda bugun da yakai mata........, A hankali ya bud'e idanunsa cikin duhu yana kallon ceiling,duk yadda yaso ya kwanta don yayi bacci ya kasa baccin,abunda yafi d'aure mashi kai tunanin ina yarinyar taje da ya tsaya masa a rai,bai ga dalilin da hakan zaisa ya zama restless ba,juyawa yayi ya koma yana facing window yayi shiru yana tariyo hiran da sukai da ita cikin ransa kaman maison gano wani abu...., "_*_uhm nasan gaye sai yayi mamaki sosai idan yaji ka yafe man,shida yace wai ko dan gidanmu ne kai bazaka yafe man ba,dole sai an biya ka,ko kuma akaini gidan yari,aiko sai na fada masa to ka yafen inna ganshi,nasan yanzu haka suna can kangon da suka saba zuwa yin shaye-shayensu,Allah dai ya shirye suu...._" tuno wannan maganar ta fatuu yasa shi tashi zaune da d'an sauri hannu ya kai ya kunna fitila haske ya gauraye d'akin ya jingina bayansa ajikin headboard,a fili yace"kar dae yarinyan can wurin wannan Drug abuser din taje da daren nan don ta fad'a masa I forgive her..."da sauri ya saukko da kafafunsa ya dau wayarsa ya nufi kofar fita a korido ya tsaya ya sanya wasu slippers a kafarsa daga haka ya fice. Tsawa Goga ya kwatsa ma Gaye"dallah ka rike man kafafunta,in kai baza kai ba mu zamu yi,kasan kuma ba fita zakai ba,gara ma ka bamu hadin kai kawai muyi yadda na fada maka" ba yadda gaye ya iya dole yabi umarnin goga don shine babbansu ko kayan harkar ma shike kawo masu su siya wani lokacin ma kyauta yake basu don shi mutumin manyan mutane ne,d'an bangar siyasa ne na kirki. Rike kafafuwan fatuu ya fara kokarin yi ta han6arar dashi tana girgiza masa kai,a fusace Goga yace"dalla ka riketa da kyau shegen karfi ne da ita kaman doki" tasowa yayi ya kama kafafun da kyar ya danne su,Goga ya kalli 6aure yace"ina wannan hankacin naka cire sholin ciki ka daure mata baki" ya amsa da toh shikuma goga ya rike ta gam dama duk yafi su girma,bayan ya d'aure bakin,goga yace mashi ya zagayo ya fiddo nashi a cikin aljihun shi ya daure mata hannuwa,6aure ya sake amsawa da toh yayi yadda yabashi umarni,wata yar iskar daria goga yayi yace"yauwa komai ya zama ready,6aure zo ka rike hannuwan don tana iya kwancewa" rike hannuwan 6aure yayi shi kuma ya mike tsaye....., Tsaye Haisam yayi cikin center din yana haska gidajen wurin da fitilan wayansa,kokari yake ya gano ko akwai kango a wurin,sai dai a iya haske-hasken da yake baiga wani kango ba yawancin uncompleted buildings din dake layin duk arufe suke da kofofi wasu Gate,dan k'ara gaba yayi yana ci gaba da haskawa har yazo kusan karshen layin baiga kango ba hakan yasa ya fara tunanin ko he was wrong about d girl..." Daidai saitin kafafun fatuu Goga yazo ya fara kokarin cire belt din tsohon jeans din jikinshi,duk da rirriketan da sukai bai hana ta girgixa kai ba tana dan motsa kafafunta kad'an saboda danne su da Gaye yayi,ga wani gurnani da take,ganin goga na k'okarin cire wandonsa yasa ta k'ara karfin gurnanin da take yi...... *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *3️⃣0️⃣* Juyawa haisam yayi da niyyar barin layin gurnanin da fatuu ke yi ya sauka cikin kunnuwansa abun ka da dare gari yayi tsit da sauri ya juya baya trying to locate inda abun ke fitowa,yana d'an kara taku ya ga kofan shiga wurin wanda take bude ba kofa daidai lokacinne kuma fatuu ta kara k'arfin gurnanin,da sauri ya kutsa kai without second thought ya nufi inda yake jin abun na fitowa, ".....dallah Gaye ka riketa da kyau,wai ya zaka bari k'aramar yarinya tafi karfinka ne,na gaya maka idan kai bazaka yi ba mu wllh sai munyi......." Wannan maganar ta Goga ita tayi ma Haisam jagora zuwa dakin da suke,yana isa bakin kofan d'akin ya haske su da fitilan wayansa da take da haske sosai lokacin goga na niyyar afka ma fatuu,ai suna ganin an haskesu su duka suka nufi windunan wurin da gudu zasu dire,cikin zafin nama haisam ya bisu yana k'okarin kamo goga wanda ke gudu saman wandonsa rik'e da hannunsa,cakk haisam ya tsaya sakamakon wani rad'adi daya ji tun daga kasan kafarsa har tsakiyan kansa,a hankali ya maido kafansa ta dama baya ya haska kafan hagunsa don a jikinta ne yake jin rad'ad'in,kwalba ce ya taka ta hudo ta k'asan takalminshi ta shige cikin kafan sosai,a hankali ya duk'a yasa hannunsa na dama yana kokarin cire kwalbar,sai dai ba karamin yanka tayi masa ba radadi yake ji sosae,runtse idanunsa ya yi yasa hannu ya cije lip dinsa na k'asa da k'arfi ya fisgo ta,har saida yayi dan sound a hankali"ahhh..." saboda azabar da yaji,aikuwa nan da nan jini ya fara zubowa kaman yana jira... Ita kam fatuu tana ganin duk sun ruga ta fara kiciniyar kwance hannuwanta cikin sa'a d'aurin ya saki ta samu ta fiddo hannuwanta a gigice ta mike ko tsayawa kwance bakinta bata yi ba ta nufi hanyar fita cikin rashin sani saboda kidimewa da tayi ta kaima bango karo a tunaninta nan ne kofar fita,taga-taga tayi tayo baya gabadaya zata fad'i,ganin haka yasa Haisam da ke haskata tun lokacin data mik'e tarbota cikin zafin nama don ba k'aramin buguwa tayi ba,ba kamar goshinta ji kake wani K'UMM!, Sosai ya rungumeta ganin tana ta son kwacewa ta gudu a hankali ya dan duk'a yakai bakinsa saitin kunnanta wanda kanta ke saman cikinshi cikin calm and cool voice yace "is okey,u are safe now" lokaci guda ta gane voice dinshi hakan yasa ta lafe ajikinsa ta kankameshi sosae jikinta sai faman rawa yake da gani ta razana sosae,yayin da shi kuma azaba da radadi keta damunsa a tafin kafarsa haka ya daure ya kai hannu ya kwance hanki din dake rufe da bakinta ya jefar cike da kyankyami don k'auri kawae yake, bayan wani dan lokaci ganin ta daina kermar ya janyeta a hankali gefe guda ya haska mata tasa takalmanta ya duka ya d'aukko gyalenta dake agefensa ya d'an yarfe shi sannan ya mika mata,ta amsa ta yafa shi saman kanta wanda tuni gashinta ya warware yayi kaman fanka don tana da cikar gashi sosai,a hankali yace"mu tafi"yayi maganar yana haska mata hanya,da kyar ya daga kafansa ya fara tafiya duk da zafin da take masa haka ya daure ya rik'a takata a hankali jini naci gaba da zubowa saboda taka tan da yake, Tana gaba yana bin ta a baya yana haska mata hanya har suka iso bakin kofan fita daga ginin gidan,yana k'okarin sa kafanshi a hankali ya fita yaga ta juyo da sauri zata koma ciki tsayawa yayi yana kallonta ganin haka yasa da sauri tace"lemunana zan daukko" ji yayi kaman ya fizgota ya wawwanka mata mari saboda haushi da ta bashi,tsawa ya kwatsa mata yace"C'mon leave this place...!bakinki ne lemun" da sauri ta juya taci gaba da tafia sumi-sumi. Tana zuwa k'arshen lungun gidan Hajiya ta juya zata karya kwanar gidansu Haisam dake can bayanta saboda a hankali yake tafiyan ya dan d'aga murya yace"muje gidan hajia" ba musu ta juya ta nufi gidan,ta riga shi isa hakan yasa tayi tsaye a bakin kofan parlonsa,bayan d'an lokaci ya k'araso tana ganin ya shigo part din ta tura kopan falon da sauri ta shige,tsayawa yayi bakin tap din da ake ba flowers ruwa ya wanke kafan da takalmin wanda gaba daya kalansa ta koma ja saboda jinin da kafansa keta fitarwa har lokacin,abunka da dan madara,tana shiga ta nufi can gaban armchairs inda tayi kneel down d'azun ta durkushe, Shigowa yayi bai ko kalli inda take ba a hankali ya nufi kujera ba tare daya cire takalman kafansa ba ya zauna,hannu ya kai ya dauki tissue box ya 6allo mai d'an yawa ya ninninkata kafin ya tura kasan foot dinsa dake zubar da jini,bayan yayi hakan ya mike ya nufi hanyar bedroom d'insa yana dan jan kafan a hankali,binsa da kallo fatuu tayi ta d'an yamutsa baki alamar tausayi,sai da ya shige sannan ta juyo,fitowa yayi hannunshi rike da dan first aid box na karfe ya tsaya ya kunna fitilan sama don ba haske sosai kafin ya nufo cikin parlon,komawa yayi inda ya tashi ya zauna,ita dai fatuu sai binshi da ido take, d'age kafan yayi saman table ya bude akwatin ya fiddo d'an scissors ya fara yanke bakin wound din da kwalbar taji masa,ganin haka yasa fatuu cije hakora tayi wani d'an sauti"shuuu! Sai lokacin yayi mata kallon kasan ido hakan yasa da sauri ta sunkuyar da kanta,dressing din ciwon yayi ya nad'e saitin ciwon da bandage, Bayan ya gama ya d'ago ya kalleta itama kallon shi take,alamu yayi mata da kanshi tazo da sauri ta mike ta matsa gab dashi ta duka cotton ya ciro ya dangwali spirit ya mika mata yace"goge nan" ya fad'a yana nuna mata gefen bakinsa,hannu na rawa ta kar6i audugan ta fara goge inda ya nuna mata sai dai sam ta kasa goge jinin dake a wurin wanda har ya fara bushewa,wata cotton din ya ciro ya dan duk'u yayi mata alamu da hannu ta matso da kanta,goge mata jinin yayi kafin yace"kije wancan room din da kika je d'azun ki wanke face dinki ki ciccire abubuwan dake a kanki ki kulleshi"yadda yayi maganar kaman an masa dole, Da sauri ta mik'e ta nufi d'akin don yin abunda yace tayi,kaman sabon kamu haka kan ya mayar da ita,a hankali ya cira kai yana kallon bayanta har ta shige d'an guntun tsoki yayi kafin ya mik'e ya daukko dustbin ya kwashe cottons din da sauran abubuwan ya zuba ya maida shi wurinshi ya dawo ya rufe box din bayan ya maida komai ciki,jingina bayansa yayi yad'an kwanta jikin kujeran, Fitowa tayi bayan duk tayi yadda yace gefen c-table ta durkusa saida ya dau wasu seconds sannan ya d'ago ya kalleta fuskan nan babu yabo ba fallasa hakan yasa tasha jinin jikinta,goshinta ya kalla wurin yayi ja amman bai fashe ba,dawo da kallon yayi cikin idanunta ganin yadda ya d'aure fuska yasa tayi saurin sunkuyar da kanta,can ta d'an d'ago taga har lokacin kallonta yake kasa dauke idanunta tayi itama ta rinka kallonshi tana motsa baki kaman zata ce wani abu sai kyakkyafta idanu take, yatsansa ya mik'a ya nuna mata fridge"je ki daukko" sumi-sumi ta nufi fridge din ta bude ba tare da ta tsaya za6a ba kawai ta daukko guda ta juyo,kafin ta k'araso inda ta tashi ya mike yana nuna mata hanyar fita,ta juya ta nufi kopan shi kuma ya bi bayanta a hankali yake taka kafar, Fitowa gwaggo tayi daga d'aki hannunta rike da buta ta nufi band'aki,bayan ta fito har ta nufi dakinta zata shiga sai kuma ta juyo ta nufi dakin fatuu don ta kashe mata hasken wutan da aka maido bada jimawa ba,tana d'aga labulan da niyyar ta sak'a hannunta ta latsa switch ta hango gadonta wayam bata a kwance ajiye butan bakin kopar dakin tayi ta shiga ciki don tabbatar da abunda ta gani aikuwa dai bata a ciki da mamaki cikin ranta tace"to ina fatuun take ne?ko bandaki ta tafi...ai kuma daga can nike tabbas ba can taje ba" rike ha6a tayi tana d'an tunani can ta tuno da d'azun ta tambayeta zata gidan hajiya ai,a fili tace"kar dai wai har yanzu yarinyar nan bata dawo gidan nan ba" tsoki tayi ta juya hanyar fita tana cewa"fatuu ho badai ayi abun arziki da ita ba sai tasa mutum surutu" hanyar zaure ta nufa tana shiga suka hade da Amadu ya shigo hannunsa dauke da kwali ya kwaso kaya aciki ganin gwaggon yasa shi ajiye kwalin a k'asa yana fadin"gwaggo lafia?" tace"lafiya lau fatuu zaka taimaka kaje ka taho da ita kaman yadda aka saba dai"tayi maganar tana yar dariya,shima murmushi yayi yace"wai dama bata gidan ashe" gwaggo tace"eh dazun bayan na dawo tace man wai hajiyar na nemanta shine nace taje amman kar ta bari har ka tashi amman kaga har yanzu bata dawo ba..." daria yayi yace"yanzun haka suna can bacci ya kwashe su,watarana fa haka zaki ga sun hada kawuna sun saki baki suna ta bacci ita da hajiyar sai naje ne nake tashinsu ita hajiyar ta wuce daki" gwaggo dake dariya tace"ina ruwan hajjaju" Amadu yace"amman ki barta ta kwana kawai mana" tace"ba kwanan ke banson tayi ba inda kamar yau asabar ne da sai ta kwana to gobe Monday kaga akwai makaranta kuma na daina barinta tana kwana saboda makarar da take yi duk in ta kwanan kaga kwanaki fa akwai ranar da saidai fasa zuwa makaranta tayi saboda bata dawo gidan nan ba sai wurin karfe tara na safe,shiyasa ma in na aika a taho da ita hajiyar bata cewa abarta saboda tasan makara take tunda ita ba da wuri take tashi ba" jinjina kai Amadu yayi yace"Ok zanje in taho da ita,amman bari in k'arasa shigo da kayan in kulle shagon" gwaggo tace"eh kagama,ni bari in koma in kwanta bacci nike ji sosae wllh dama farkawa nayi naga bata dawo ba"tana maganar ta juya ta nufi dakinta. Fatuu ce gaba Haisam na bin ta a baya sai faman waigawa take tana satar kallonshi don duk ta tsorata da yanayin shi ga ciwon da yaji saboda ita, suna zuwa gab da k'arshen katangar gidan hajiya Amadu ya fito daga gida ya tsaya yana kulle kiosk dinshi,haisam na hango shi yace ma fatuu "hey..." alamar ta tsaya,juyowa tayi ta kalle shi,taku ukku yayi ya k'araso inda take a hankali yace"don't disclose what happaned to anyone" jinjina masa kai kawai tayi,ganin haka yace"kin gane mi nace" da sauri tace"eh,cewa kayi kar na fada ma kowa abunda ya faru" alama yayi mata da hannu ta tafi ta juya ta tunkari Amadu dake tahowa Haisam na niyyar juyawa Amadu ya dan d'aga murya yace"Ina yini" tsayawa haisam yayi ya d'aga masa hannu ba tare daya amsa ba, Juyawa Amadu yayi tare da fatuun yana cewa"dama baki yi bacci ba shine kika ki kidawo kaman yadda gwaggo tace maki,kawai don kibani wahala" ya kai hannu zai rankwasheta tai saurin janye kan tace"wad muyal kawu(yi hakuri kawu)" Amadu ne ya fara shigewa kafin fatuu saida ta dan juya ta kalli haisam da har lokacin yake tsaye da sauri ta shige ganin sun hada idanu. ______________________ Zama haisam yayi kan kujera bayan ya koma ya shiga cikin contacts din wayarsa yayi dialing wata number mai dauke da sunan SP khamis,wayan na shiga aka daga gaisawa sukai da mutumin wanda daga ji abokinsa ne daga yanayin yadda suka gaisan,Haisam ya sanar dashi game da incident din daya faru yace ya samu rauni ne a k'afarsa shiyasa ba zai iya zuwa station din yayi reporting ba,Sp khamis najin abunda ya faru yace ma Haisam ya bari zaizo yanzu wannan ba maganar waya bace daga haka ya katse, kwanciya yayi saman kujeran gaba daya ma ya nemi baccin da yake ji ya rasa al'amarin ba k'aramin tada masa hankali yayi ba,imagining kawai yake da baije wurin akan lokaci ba abunda zai faru,d'an guntun tsoki kawai yake ja. Bayan kaman 30 minutes SP khamis ya iso a bakin gate ya parker motarsa ya fito matashi ne da bazai wuce 33yrs ba, jikinsa sanye da uniform din yan sanda riga blue sai black wando su Officer na ganinsa suka sara masa,Officer p ne yayi masa jagora ba tare da 6ata lokaci ba zuwa part d'in haisam bayan ya sanar dasu wurinshi yazo, Tura kopan yayi bakinsa dauke da sallama,k'okarin tashi zaune haisam yayi bayan ya amsa masa,fuskarsa d'auke da murmushi ya mika ma Haisam hannu yana fadin"H, Zakee the big COE" haisam da shima yake murmushi yace"SP,ya aiki", "Alhamdulillah gamu a cikinsa" ya fad'a yana kokarin zama a daya daga cikin armchairs din dake parlon, haisam yace"am sorry nasa ka baro aikinka..." SP khamis ya katseshi"Oh no,don't say dat, nan ma ai aikin na zo ko,uhum kana fad'a man yadda incident din ya faru ta waya inason k'ara jin cikakken bayanin al'amarin", Sigh haisam yayi kafin ya sake mashi bayani a takaice,Sp khamis nata jinjina kai,cike da takaici yace"yanzu ina yarinyar take?" haisam yace"tana gidansu and I ave instructed her not to tell anyone about d incident" jinjina kai Sp yayi"hope basu yi nasarar yi mata komai ba dai??" shiru haisam ya d'an yi yana tunano maganar da yaji goga yayi,yace"bana tunani gaskia", gyara zama SP yayi"Ok yanzu inason statement dinka sannan itama dole zamu bukaci nata" haisam yace"Owk,lokacin da kuke bukata just inform me,ni bari in rubuta maka" ya k'arasa maganar yana kokarin mikewa SP nace mashi yabi a hankali,d'akin da fatuu ta shiga fitsari ya shiga,hannunshi rike da plain sheet da pen ya dawo cikin kankanin lokaci ya rubuta duk bayanin daya sani ya mika ma Sp khamis dubawa yayi kafin yace"gud,yanzu shi guy din da yarinyar ta fada maka baka san gidansu bane?" girgiza kai kawai haisam yayi alamar baisani ba, SP yace"dole kenan sai wurin yarinyar za'a samu information din da ake bukata gashi yanzu dare yayi gaskia" shiru haisam yayi kaman mai dan tunani can yace"I think u can get that from the security at the gate,tunda kagan sun dan jima suna aiki anan bazasu rasa sanin guy din ba" Sp yace"yauwa bari in tuntu6e su don so nike zuwa gobe su zo hannu in sha Allah" d'aga mashi kai haisam ya yi yayin da SP ya fara kokarin mikewa hannunshi rike da takardar da haisam ya bashi,ganin haisam din na kokarin mikewa don ya raka sa yace"kai zamanka kawai da na samu information din da nike so zan wuce,komai ake ciki I will inform u,amman kafan nan kaje a dubata gaskiya" haisam dake d'an murmushi yace"don't worry nayi mata duk abunda ya dace yanzu" SP dake sauraranshi yace"bafa Hardware ko software bace da zaka ce kayi abunda ya dace,u need to go hospital saboda ba dressing kawai kake bukata ba you also need TT Injection and some drugs like anti-biotics nd pain reliaver" Komawa yayi ya kwantar da bayansa yana murmushi yace"I have taken d pain reliever,amman dama zanje asibitin first thing tomorrow Morning in sha Allah", SP yace"better,ko kazo na kai ka wani pharmacy a duba ka" girgiza masa kai yayi"thanks,ba sai kayi wahala ba" ta6e baki yayi jin abunda Haisam d'in yace daga haka ya nufi hanyar fita yana fadin"My regard to hajiya pls" haisam yace"Owk zata ji,sai da safe" SP yace"Allah ya tashe mu lpy" daga haka ya fice. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *3️⃣1️⃣* Washegari da safe Gwaggo ce acikin kitchen tana ta kwala ma fatuu kira "fatuu,fatuu.." fitowa tayi jikinta sanye da uniform d'in makaranta ta nufi kicin daidai lokacin da ta iso bakin kicin din zata shiga gwaggon ta fito"wai mi kike yi ne nike ta faman kwala maki kira kin k'i fitowa?" fatuu tace"shiryawa fa nike,a gwallijam" gwaggo dake ta kallon fuskarta tace"Jam sumul,kije wurin Amadu ki kar6o madara da milo ki maza kizo ki karya kumallo karki makara" tace "to biredi fa?", "a'a akwai wani saura zai ishe ki"gwaggo ta bata amsa, "To ke bazaki ci ba,ai badai tuwo tunda bakiyi ba jiya?" Gwaggo tace"eh zan bada a siyo man waina gidan ladidi,ke ki ci biredin kawai" gyada kai fatuu tayi har ta juya gwaggon tace"miya same ki a goshi ne naga yayi ja?" Damm gaban fatuu ya buga, juyowa tayi tana kyakkyafta idanu tana tunanin k'aryar da zata yi ma Gwaggon don dama ko Haisam baice karta fad'a ba,ba fadin zata yi ba, "Bugewa kikai ne?"gwaggo ta sake tambaya,da sauri tace"eh jiya ne da Hajiya tagan na fara bacci ta tada ni in taho gida shine cikin magagin bacci na bugi bango awurin fitowa, bayan na fito ne na hadu da kawu Amadu" ta k'arasa tana dan kare gefen bakinta da hannunta don kar ta lura da bakin duk da daga ciki ne ya fashe,girgiza kai gwaggo tayi tace"maganin mara jin magana kenan da kin taho da wuri kafin baccin ya kwashe ki ai da ba haka ba,tafi ki amso abunda nace maki lokaci na tafiya" juyawa fatun tayi ta nufi hanyar fita. Tunda ta fito zata tafi makaranta take kallon gidan hajiya ji take kaman taje sai dai tasan kawu Amadu sai ya tambayi abunda zata je yi tun da safe kuma lokacin tafiya makaranta,hakan yasa ta mik'i hanya kawai don biya ma haulatu, Tana tafiya tana waiwayen bayanta wai ko zata hango Haisam ya taho a mota amman har ta kawo lungun su haulat bata ga wata mota ta taho ba balle tasa ran shine,lokaci guda gabanta ya fara fad'uwa ta fara tunani a ranta ko dai saboda ciwon da yaji jiya ne yasa bai fito ba,a fili tace"kar fa kuma ya dawo yace bai yafe gilashin ba saboda nasa yaji ciwo,daman naga sai d'aure fuska yake jiyan..." jikinta ne yayi mugun sanyi ta shiga damuwar da har fuskarta ta bayyana, Tana zuwa kopar gidan haulatun ta fito,fuskarta d'auke da dan murmushi tace"ashe kin taho har inata sauri inje mutaho tare..." kasa karasa maganar tayi saboda yanayin fuskar fatun da ta gani,a hankali tace"miya faru kawata?baki je kin basa hakurin bane ?", "ba komai,mu tafi karmu makara" daga haka ta wuce gaba,bin bayanta Haulat tayi jiki asanyaye tana ta faman tunane-tunane cikin ranta. Har akayi masu break fatuu bata saki jikinta ba duk ta shiga damuwa ganin duk yan ajin sun fita yin break fatun na a zaune yasa haulat tace mata"ki taso muje muyi break fatuu" kifa fuskarta tayi saman desk tace"ki tafi kawai bana jin yunwa" jin hakan yasa Haulat da har ta mik'e komawa ta zauna,hannu tasa ta d'an bubbugi bayan fatun tace"wai miyake damunki ne,kodai mutumin cewa yayi bazai yafe bane?kinji ki fada man" Dagowa tayi fuskarta a d'aure tace"wai bana ce maki ba komai ba,ki kyale ni kije kiyi break dinki" daga haka ta sake maida kanta ta kifa a saman desk din. Shiru Haulat tayi,sai taji duk zuwa break din ma ya fita ranta dama kuma naira ashirin ce da ita,can ta mike da niyyar zuwa ta siyo ruwa saboda kishin da ta fara ji, "Haulat" taji fatuu ta kira sunanta,a hankali ta juya ta kalleta fuskarta a dan d'aure don bata ji dadin abunda fatun tayi mata ba,kudi fatun ta mik'o mata,kallon kudin tayi kafin ta kalli fatun tace"mi zan siyo maki?", girgiza kai tayi"ba komai ki had'a kiyi break"shiru Haulat tayi duk da bata da isassun kudi amma tace"a'a ki barshi"daga haka ta juya, "Fushi kika yi?" fatuu ta jefo mata tambaya,banza ta mata taci gaba da tafiya,ganin hakan yasa da sauri fatuu tace"ki yi hakuri to...."tsayawa da yin tafiyar haulat tayi ta juya ta d'an kalli fatun hakan yasa ta cigaba"banje na bashi hakurin bane shiyasa kika ga duk na damu,tsoro na yau Monday kada maganar Gaye ta tabbata" sai da kirjinta ya buga data ambaci sunan gayen,ita kuwa Haulat jin hakan yasa ta koma inda fatun take ta tsaya a gaban desk din tace"to kuma sai inta faman tambayarki ki k'i gaya man abunda ke damunki", "to ai nace kiyi hakuri ko" fatun tace, "Shikenan,in sha Allahu ba abunda zai faru ma,yanzu ki taso muje muyi break din,alabashshi da yamma in aka taso mu islamiyya sai muje tare mu bashi hakurin,nasan in Allah ya yarda zai hakura" mik'ewa fatuu tayi har ta fito daga cikin seat d'in ta koma ta janyo jakarta,bude ciki tayi ta fiddo lemun da Haisam ya bata daga haka suka fuce. *** *** *** *** Wuraren karfe 9 na safe Haisam ya farka daga bacci tun bayan da yayi sallan Asuba anan cikin dakinsa,yana farkawa kiran Hajiya ya shigo wayarsa don tana ta kiran telephone bai dauka ba sai tayi tunanin ko bai tashi bane,ganin lokaci nata tafiya yasa ta kira wayarsa,bayan ya d'aga kiran sun gaisa take tambayar ko ya wuce wurin aiki ne,don bata ga yaje sun gaisa ba kaman yadda yake yi kullum kafin ya tafi don bai cika yin breakfast ba a cewarshi yayi safiya da yawa,sai hajiyan ta matsa masa ne ma wani lokacin yake shan tea kawae,sanar mata yayi cewa yana nan bai tafi ba bada wuri zai je bane,in ya gama abunda yake zai shigo. Toilet ya nufa don yin wanka bayan ya gama ya shirya cikin wata navy blue jallabiya mai gajeran hannu ya fito falo hannunsa rike da wayarsa yana d'an dangyasa kafan mai ciwo ya nufi kujera ya zauna,fara latsa wayan yayi ya kira Tk,yana d'aga kiran yace"t.k are u at home?" da sauri t.k yace "a'a wllh na tafi skul.."kafin ya k'ara cewa wani abu Haisam ya katse kiran,d'an kwantar da kansa yayi yana tunanin yadda zai tafi asibiti, don jiya da tsakan dare kafan ya takura masa da zogi duk da pain reliever din da ya sha,sai wuraran asubahi ya samu yin bacci sosae,duk motocin da zai yi amfani dasu manual ne dole sai yayi amfani da kafan mai ciwo in zai tuka su,gashi a yadda yake jin kafan ba zai iya yin tuki da ita ba. Bayan wani lokaci ya mik'e, komawa yayi cikin corridor yasa takalma slippers kafin ya dawo cikin parlon ya fuce,wajen gate ya nufa ta k'aramar kopa ya fita,tunkarar Officer CD dake zaune saman benci shi kadai yayi,Officern na ganin haisam din ya tunkaro sa yana d'angyasa kafa ya mike da sauri ya nufo sa yana zuwa wurinsa yace"yalla6ai barka da safiya..."hannu haisam ya mik'a masa suka gaisa kafin yaci gaba"yalla6ai rauni ka ji haka?" d'aga masa kai kawai yayi,cike da jajantawa Officer ya shiga girgiza kai yana fad'in"wai sannu,Allah ya kyauta gaba" "Amin" haisam ya amsa kafin yace"in ba damuwa inason zaka kaini hospital ne,sai dai motan is manual I don't know if u could drive it" ya tambaye shine don yasan ba kowa ya iya tuka mota manual ba, d'an sosa k'eya Officern yayi yana d'an murmushi yace"wllh yalla6ai kwata kwata ma ni ban iya tukin mota ba.." d'age gira haisam yayi yace"really?" Officer dake ta murmushi ya daga masa kai alamar eh kafin yace"sai dai ko in ma Officer Jamil magana don shi ya iya tuka mota don wani lokacin ma yakan fita da Hajiya in t.k baya nan" jinjina kai Haisam yayi yace"ok bari in koma ciki in yazo sai kayi masa magana..."da sauri Officer ya katseshi"ai yana nan,ya shiga ciki ya kimtsa da yake ba dashi mukai aikin dare ba bai jima da zuwa ba,bari in masa magana" ya k'arasa maganar tare da juyawa ya nufi cikin gidan, Ba da jimawa ba suka fito atare Officer police ne Jamilun da aka kira ya nufo haisam yana gyara hulansa yana zuwa ya mika mashi hannu suka gaisa yace"yalla6ai ashe tsautsai ka had'u dashi" d'aga masa kai kawai yayi yace"to Allah ya kiyaye gaba" a hankali haisam yace"Amin", "Yauwa wani motan za'a fiddo ne?Nura yace kana so a kaika asibiti" daga masa kai haisam yayi tare da mika masa makullin mota dake rike a hannunsa na hagu" amsar key d'in Officer jamil yayi ya d'an duba shi kafin ya juya don fiddo motan,Officer Nura kuma ya fara sliding gate din,ba 6ata lokaci ya fito da motan Haisam ya shiga suka tafi. Wuraren karfe biyu na rana gwaggo na zaune a tsakan gida jikinta sanye da kayan aiki ita da wata mata dukkansu suna zaune a saman kujera yar tsugunno da alama bak'uwa tayi,da gudu fatuu ta shigo daga bakin kopar shigowan ta wurgo jakarta tsakar gida tayi bandaki da gudu,gaba dayansu sai da suka tsorata bakuwar matar ce ta juya ta kalli gwaggon tace"kaman fatima ko?" girgiza kai gwaggo tayi ta d'an ta6e baki tace"itace wllh,haka take don iskanci sai ta tara matsuwa,maimakon tun can makarantar tasan tana ji tayi" Yar dariya matar tayi tace"ina ruwan fatuu" adaidai lokacin fatun ta fito tana gyara wandonta ta duk'a inda jakarta take ta dauka ta wuce ciki,kallon bakuwar tayi tace"Ladidi mai waina ina yini" amsawa tayi"lafiya lau fatima yan makaranta" kallon Gwaggo tayi tace"sannu da gida gwaggo" yar harararta gwaggon tayi batare da ta amsa mata ba,hakan yasa fatuu yin dariya ta wuce d'aki don tasan hararar ta shigowar da tayi da gudu ce, "....Oh ladidi kina fadi man wannan al'amari mai cike da tashin hankali" ladidin ta kar6e"wllh bari,ni fa ina cikin tuyan waina da safe naji yara suna cewa wai gashi can an zo kama Gaye nace wane gayen? wai Ashiru d'an gidan Malam Tanimu,shine fa su Bilki suka fita don jin ba'asi nidai bansamu fita ba saboda tuyan wainan da nike,da suka dawo ne suke ban labarin wai yunkurin fyade su kai ma wata jiya da daddare shi da abokanansa Allah baisa sun kaiga yin nasarar aikatawan ba wani mutumi ya gansu,ance ma tun jiya da daddaren yan sanda suka zo neman shi basu same shi agida ba shine suka fad'a ma mahaifinsa mlm tanimun laifin da ake tuhumar d'an nasa,suka kuma bukaci ya basu hadin kai da zarar yaron ya dawo gida ya kira su ya sanar dasu kuma kar ya bari ya fita in ba haka ba zasu dawo su kamashi tare da mahaifiyar Ashirun wato Zulai,aikam yau da safe sai gashi ya dawon don bai kwana a gida ba,yana ko zuwa malam tanimun ya kira yan sandan" Nannauyar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke cike da takaici tace"kai jama'a duniya dai ta idasa lalacewa yanzu ace kaman Ashiru yasan ya hakkewa mace,yanzu dai indai kana da yaya mata agabanka baka da kwanciyar hankali wllh masifar fyaden nan tayi yawa kullum gargadi ake nasiha ake amman a banza abun sai kara gaba yake na jiki ma sai ya cutar maka da y'a,Allah kai mana maganin wannan masifa ka shiryi al'ummar Annabi..." ladidi ta amsa"S.a.w,ke dai bari Dije Amin ya Allah,ni wllh malam tanimun ma ke bani tausayi shi kuma ta nan Allah ya jarabe shi gashi malami" gwaggo tace"wllh ai abun a tausaya masa ne jarabawar ya'ya ai babbar jarabawa ce mutum baida yadda zaiyi dole ya rungumeta har Allah ya yaye inda rabo,Allah ka shirya mana zuria shirin addinin musulunci", "Amin" ladidi ta amsa tana kokarin mikewa tace"na tsaida ki zaki tafi aiki ga lokaci nata tafiya" mik'ewa itama Gwaggon tayi tana fadin"to daman dai wani lokacin dole ai uzuri yasa ka makara kaman yadda wani lokacin kaima ba'a zuwa a amshe ka da wuri saboda wani dalilin haka dai ake ta fama" yar dariya ladidi tayi"hakane kam rayuwan gaba daya sai da uzuri,ku kunma ji dadi kunata aikin ku wllh kai bawa kullum sai fama da wuta kake" gwaggo tace"to ya za'ai kowa da hanyar da Allah ya tsaga masa cin abincinsa,Allah dai ya kara rufa mana asiri duniya da lahira" ladidi ta amsa da Amin yayin da suka nufi hanyar zaure a tare, Da sauri fatuu ta koma gefen d'an gadonta ta zauna daga inda ta la6e tana sauraron hirarsu gwaggo,hannu tasa ta ruke ha6arta a fili tace"kai,wai yaya handsome har yasa an kama su gaye kenan" kwafa tayi ta sake cewa"ai maganinsu kenan mugaye kawai,kilan ma su za'a kai gidan yarin ba ni ba,wayyo har naji tausayin Gaye wllh shi baiso ba amman abokanansa sun ja masa" idasa fadawa tayi saman gadon ta kwanta tana kallon sama ta ci gaba"yakamata inje in gaida Yaya handsome tunda saboda ni yaji ciwo,ko yama akai yasan naje kangon nan,kilan yagan sanda na juya nabi lungun ne,ashe dai haka yake da mugun kirki ni wllh farkon dana fara ganinshi nayi tunanin baida mutunci ba kaman daya falla mun marin nan" kyalkyacewa tayi da dariyar farinciki kafin tace"ai da har naji tsoron ko yana can bai iya tafiya ne shiyasa ban ganshi da safe ba,ashe har wurin yan Sanda yaje ya kai kara,ohooo shiyasa yace kar na fadi ma kowa abunda ya faru nagano dalilin...,Oh da ansan nice da sai aita nuna ni wasu ma su ki yarda ba ai man fyaden ba,gwara ma da ba wanda yasan ni ce"ta k'arasa maganar tana ta faman watsa hannuwa kaman da wani take maganan, "Fatuu" gwaggo da ta dawo daga rakiyar da tayi ma ladidi ta kwala mata kira,da sauri ta saukko daga gadon ta nufi kopa tana amsa kiran,d'aga labulan tayi ganin gwaggon a bakin kopan yasa ta tsaya tace"gani" kallon kanta gwaggon tayi wanda ke bude ba dankwali ta d'an girgiza kai tace"wai ke don Allah fatuu sai yaushe ne zaki hankali,kisan abunda ya dace ne iye?yanzu wannan kan naki tun yaushe yake a tsefe ne,kudi fa kawai zaki dauka kije a kitse maki amman abun duniya ya gagara so kike sai na kama hannunki naje na kaiki ne?" turo baki fatuu tayi"Allah gwaggo bazaki gane ba fa,wllh balaraban nan mugun zafin hannu gare ta,kitson da tayi man na karshe fa har dan guntun fitsari sai da nayi fa" ta6e baki gwaggo tayi tace"wannan kuma ai kin saba in dai sakin fitsari ne,kullum mutum bazai yi abu lokacin da yake jin sa ba sai ya matse shi ba dole ya zubo ba,ke dai kika sani,gashin ma naki bai da zuciya ne yadda baki gyara shin nan kamata yayi ace zuwa yanzu duk ya zube ya bar ki da kwaikwaidon kai", Langa6ar da kai tayi tana turo baki"kai gwaggo harda mugun fata,to ke ki mun ko kalaba ko kuma ki man na fulani da kike man" gwaggo tace"Uhmm sai ki ta jira na ai har in samu lokaci,nasan hakan ba matsala bane a wurinki,kinga ni zan wuce wurin aiki nama rigada na makara,ga abinci nan a kicin in Amadu ya dawo ki dau nasa ki kai masa,sannan kema in kin ci kiyi wanka sai ki share tsakan gidan da kuma kicin din don duk ya 6aci ban samu na gyara ba" daga haka ta juya can kuma sai ta sake juyowa tace"fatuu na roke ki don Allah ki zauna agida kar kije ko ina da lokacin islamiyya yayi ki tafi ana tasowa kuma ki dawo gida kinji?, d'an sosa kai tayi"to,amman zan dan je gidan hajia in nagama abunda kika sani kafin lokacin islamiyyar yayi" wani kallo gwaggon tayi mata kafin tace"wai mi kike yi ne a gidan hajiyar ba jiya kinje ba kuma ma da dare,to mi kuma zaki je yi yanzu?anya fatuu ba wata rigimar kike shirin jawo man ba kike fakewa da zuwa gidan hajia?" da sauri ta girgiza kai tace"Allah ni ba wani rigimar da zan jawo maki,yaushe rabon ma da kiji an kawo karata,kawai banson in zauna ni daya shiru tunda kinga shi kawu Amadu da ya dawo ya dan huta shago zaije ya bude" ta6e baki gwaggon tayi"ai jin shirun ba'a kawo k'arar taki ba kwana biyu yasa ni nike zullumi don in kikai kwance kwancen nan to ba k'araman rigima za'a jawo man ba", kyalkyacewa da daria fatuu tayi tace"to ki kwantar da hankalinki kakus ba wani rigiman da zan jawo na bari na shiryu ba ruwana yanzu" gwaggo tace"da nafi kowa farin ciki,sai dai nasan a iya baki ne don nasaba jin hakan" daga haka ta juya ta nufi hanyar fita fatuu ta d'an daga murya"inje ko? batare da gwaggo ta juyo ba tace"ai sai kita zuwa ko na hana ma nasan sai kinje" fatuu da ke ta dariya da karfi tace"si to a warti kakus" hannu gwaggon ta d'ago mata lokacin kuma ta idasa ficewa daga gidan,fatuu na ganin ta fice ta koma d'aki da sauri don daukko gyalenta dan gado ta tafi gidan hajiyar Sanata. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story._ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *32⃣* Fitowa tayi da sauri tana yafa gyalen saman uniform din jikinta,a daidai zaure suka had'e da kawu Amadu ya dawo daga Makaranta shima,wani kallo yayi mata yace"yawo ko?" Da sauri ta girgiza mashi kai"a'a gidan hajiya zani kuma na tambayi gwaggo ma yanzun nan ta fita" gyada kai yayi yace"eh na hadu da ita,mashin d'in da ya kawo ni ma ta hau,yanzun je ki kawo man abinci na sai kita tafiya" to tace ta juya don daukko masa abincin, Yana zaune agefen yar katifarsa yana cire safar kafarsa ta shigo,aje masa yar kular abincin da cokali asamanta tayi a gabansa tace"gashi nan" tana k'okarin juyawa yace"ruwa fa?"wani kallo tayi masa tana turo baki "kai kawu wai ruwan ma baka iya zuwa kasha in ka gama don kawai ka wahalar dani" harararta yayi cikin d'aure fuska yace"Imi fijirma(ina wasa dake)!zaki kawo man ruwan ko sai na tattaka ki anan,kin iya jin wahalan asa ki yin abu amman baki jin wahalan yawo"tana ta faman turo baki ta koma ta d'ebo masa ruwan ta kawo masa,yar harara ya watsa mata kafin yasa cokali ya fara cin abincin,juyawa tayi zata fita ta hango kwali d'auke da su biscuits dasu sweet aje a jikin bango, d'an juyowa tayi ta saci kallonsa taga hankalinsa na kan abincin da sauri tasa hannu ta rarumo sweet jin karar ta6a kwalin yasa shi dagowa da sauri yace'Fatuu...."da gudu ta fice daga gidan. ________________ Haisam zaune a parlornsa hannunsa ruke da wayarsa yana karatun Al'qurani a hankali ta cikin app d'in Vmuslim,tun bayan da suka dawo shi da Officer direct part din hajiya ya nufa don yin breakfast yasha magungunan da aka bashi,anan ne taga raunin daya ji a kafan,ba k'aramin tashi hankalinta yayi ba taita faman tambayan shi yadda ya samu rauni bacin jiya lafiya lou suka rabu,bai 6oye mata ba ya fad'i mata kwalba ce ya taka amman a part d'in sa yace mata bai fad'i mata ainihin yadda akai ya samu raunin ba,aikam ba k'aramin jimami ta shiga ba mamaki ya cikata na yadda akai akasamu kwalba apart dinsa har ya taka don tasan ko lemun kwalba basu amfani dashi haka dai taita faman jajanta al'amarin,da kanta ta had'o masa breakfast har yunkurin bashi a baki tayi ya hanata yana ta faman dariya,tsare shi tayi sai da ta tabbatar yaci sosae sannan ta 6allo masa magungunan yasha,ci gaba su kai da hira har ya tambayeta miyasa bata je aiki ba,ta sanar mashi cewa tana aikin wani project ne sai ta gama gaba daya sannan zata je,bayan wani lokaci ne hajiyan tayi bak'i hakan yasa haisam din baro part din hajiar,har cewa tayi yaje dakinta ya kwanta yace mata baijin bacci zai koma part d'insa. A hankali fatuu ta kama handle din kopan ta tura ta d'an leka ciki,hango shi tayi zaune yaba kopan baya ta yadda duka kafafunsa na asaman kujeran ya mik'ar dasu,k'ira'ar karatun da yake na tashi a hankali, Shiga tayi da yar sallama a bakinta gabanta na d'an faduwa ta nufi can gefen c-table ta durkushe,bai kalleta ba amman yaji shigowar mutum,cigaba yayi da karatunsa ita kuma tana ta kallonshi tana wasa da yatsun hannunta,sai da yakai karshen surar da yake karantawa ya aje wayan a gefensa,tsawon wasu seconds ya d'auka kafin ya juya ya kalleta fuskar nan ad'aure tamkar bai ta6a dariya ba,lokaci guda fatuu tasha jinin jikinta ta shiga motsa baki gabanta na bugawa da karfi da karfi,tana son ta bud'a baki ta gaishe shi amman sam ta kasa saboda ganin yanayin shi,yadau d'an lokaci yana kallonta "Dama ke yar iskace" ya jefo ma fatuu tambaya,a gigice ta zaro idanu tana kallonshi jin abunda yace,girgiza kai ta fara yi a tsananin rud'e tace"A..a...a'a wllh ni ba yar iska bace,na rantse da Allah ban ta6a iskanci da kowa ba kaji na rantse maka...." ta6e baki ta fara yi nan da nan hawaye suka fara zubowa daga idanunta, Juyar da kanshi yayi gefe sam ba abunda yaso fada ba kenan, it was just an unfortunate slip of the tongue,shi kanshi yaji nauyin abunda yace d'in,kuka sosae take yi tasa hannu tana murzar idanunta sai faman rantse rantse take na ita ba yar iska bace, "Tashi ki tafi" haisam daya juyo yana kallonta yace har lokacin fuskarshi a d'aure,kallonshi tayi tana niyyar magana ya daka mata tsawa"just leave!" da sauri jiki na kerma ta yunkura zata mike gocewa tayi ta bigi c-table d'in dake gefenta sosai ta bugu har sai da haisam ya d'an yamutsa baki,kopar fita ta nufa tanayi tana waiwayenshi tana kuka a tunaninta ko zaice ta tsaya amman bai ko juyo ba balle ya kalleta har ta fita, bakin kopar ta tsaya kaman bazata tafi ba sai shesshekar kuka take yi, A hankali ta fara tattaka stairs din balcony"yanzu shikenan kin 6ata masa rai zai fasa yafewar da yayi hajiya da gwaggo duk zasu sani kuma sannan gwaggon zata san ke ce wadda su Gaye suka kusa yima fyade a kangon su....."zuciyarta ce take raya mata hakan,cikin tsananin rudewa ta juya ta koma jikin kopan kama handle d'in tayi ta dan tura ta kad'an ba tare da ta lek'a kanta ba ta fara magana"Don girman Allah yaya handsome kayi hakuri don darajar Annabi,in kana kaunar maman ka hajiya,wallahi tallahi ni ba yar iska bace kowa ya sani a unguwar nan,wllh ko Bello na gidansu Umar makwabcin mu kwanaki da ya rike man hannu sai da na daddage na falle shi da mari kuma ko haulatu zaka tambaya zata fad'i ma hakan,ko gwaggota ma tasan anyi hakan don har cewa tayi na kyauta dana mare shin" dakatawa tayi taci gaba da kuka tana shessheka, Duk maganganun nan da take haisam din na jin ta,don tun bayan da ta fita yake zaune still,bai motsa ba ko wayarsa ma bai d'auka ba,gaba daya tun bayan da fatuu tazo wurin shi he felt distubed,shi mutum ne da baison hayaniya,ji yake gaba daya ya takura, Tsam ya mike ya nufi hanyar fita,fatuu najin an kama kopan za'a bude taja baya da sauri sai faman zare ido take,tsaye yayi a bakin kopan bayan ya bud'e yana kallonta ya goya hannayenshi a kirji,itama shi take kallo da kumburarrun idanu fuskarta tayi jage jage da hawaye ganin yana ta kallonta baice komai ba kuma har lokacin fuskarshi a tamke take yasa ta sunnar da kai k'asa had'i da sa gefen gyalenta tana goge hawayen fuskarta hakan kuma yasa gyalen sa6ulowa daga saman kanta,jin shiru bai yi magana ba yasa ta d'an saci kallonshi ta kasan ido suka hada idanu hakan yasa ta d'ago ta marairece fuska ta fara motsa baki kaman zata yi magana amman ta kasa cewa komae saboda kafetan da yayi da ido, Sauke Ajiyar zuciya yayi calmly yace"ki tafi kawae,in don laifin da kika yi man ne na fasa glass I hv forgiven u already,so karki damu bazan tada maganan ba,kije ki ci gaba da yin rayuwan ki the way you want" yana gama maganar ya juya zai koma cikin parlorn da sauri tace"to don Allah kar kayi fushi dani..."juyowa yayi ya d'an kalleta,ta langa6ar da kai taci gaba"Don Allah,wallahi ni ba yar iska bace,kawai zuwa nayi in fad'i ma gaye ka yafe man shida yace bazaka ta6a yafewa ba shine..."bata k'arasa ba ya juya ya shige, Matsowa tayi jikin kopan wadda bata idasa rufewa ba,ta kama handle din ta ci gaba"Don Allah kayi hakuri kar kayi fushi dani,wllh ko gwaggota da haulat in naga sun yi fushi da ni banjin dad'i" Haisam dake a zaune tun bayan da ya shige yana jinta sai faman ta6a kopan take tana yin yar k'ara,hannun daman shi yasa ya dafe forehead d'insa,wannan shi ake kira da karfen kafa😂. A hankali ya zame hannun daga kan goshin ya juya ya kalli kopan"Come in" ya fad'a da wata irin dishasshiyar murya,turo kanta tayi jin kaman yayi magana sai dai batasan miya ce ba"kira na kayi"ta tambaya ta inda ta sak'o kan,a hankali ya cira kai ya kalleta,yadda tayi yaso ya bashi dariya amman ya share ya d'an daga kanshi alamar eh,aikuwa da sauri ta idasa shigowa ta nufi inda ta tashi dazun ta durkushe gaba daya gyalen ma ya dawo a hannu daga ita sai Uniform riga da wando ga gashinta yayi wani tumm a d'aure, Shiru sukai na wani lokaci shi yanata kallonta ita kuma sai faman murzar idanu take da gyalen hannunta,a hankali ta saci kallonsa ganin ita yake kallo yasa ta dakata da abunda take yi itama taci gaba da kallonshi tana kyakkyafta idanu hadi da motsa baki, hannu yasa yana shafa beard dinsa cikin cool voice yace"ga ki kaman zaki wayo ashe baki da shi" kya6e fuska tayi tace"wllh ina da wayo fa" d'an ta6e baki ya yi"da kina dashi ai bazaki je can wurin ba at dat time,da banje in a right time ba baki san mi zai faru da ke ba....", "Nasani,fyade zasu yi man"ta fad'a tana sussunar da kai,still yayi sai dai sam baiyi mamakin jin haka daga bakinta ba,don yarinyar da bata kaita bama yanzu zata san kalmar fyade koda bata san ainihin abunda yake nufi ba saboda yadda ake fadakarwa game da aikatashi a kafafen sadarwa irinsu tv,radio da sauransu,gashi a jiya tace yima yarinya k'arama kamarta aure is a child abuse,yana ganin tasan miye ne auren shiyasa har ta fad'i hakan don inba haka ba ai a garinsu ya tabbatar ana ma yaran da basu kaita bama aure, ci gaba da magana tayi"ai shima a makaranta anyi mana bayani akanshi kuma an fad'a mana abubuwan da zamu yi don mu kare kanmu,ance in wani da bamu sani ba ya kira mu yace zai aike mu wani gida da bamu sani ba to kar muje,ko ya kira mu a wani wuri kaman kango yace zai bamu wani abu nan ma kar muje,ko kuma mu ga wani yana ta6a mana jiki to mu hana shi in bai bari ba muje gida mu fad'i ma iyayenmu,shiyasa da Bello na gidansu umar ya kama man hannu na felle shi da mari" ta kai maganar tana gwada yadda ta mare shin har sai da Haisam ya dan juya fuska, Juyowa yayi yace"to ai ba gwaninta kikai ba tunda jiya da kafafunki ki ka kai kanki inda za'a cutar da ke" da sauri tace"ni fa wllh kawai zuwa nayi in fad'a ma gaye cewa ka yafe d'in,shida yace wai bazaka ta6a yafewa ba,shine fa abokansa suka ce wai k'arya nike hada cewa wai kai kanin babanane ko mamata da zaka yafe man hakanan wai zuwa nayi ka da....." da sauri ya d'aga mata hannu"shikenan,since they've been arrested duk wannan bayanin zasuyi acan ne ba sai kin maimaita man ba", Jinjina kai tayi tace"za kau suyi bayani mai dalili,duk sai sun yabawa aya zakinta tunda su yan iska ne,amman kasan mi yaya handsome?"Girgiza mata kai yayi alamar a'a tace"wllh shi fa Gaye ba ruwanshi baiso ayi man abun ba,har cema su yayi su kyale ni inyi tafiyata don Allah,don abunda zasu yi man babban laifine hukuncin sa d'aurin rai da rai,amman wannan banzan abokin nashi gago ne ko gogo oho ni ban iya sunan ba,ya ki ya kyale ni wai suma sai na basu abunda na baka,har rantsuwa nayi masu ba abunda kai man don Allah ka yafe man kace kawae in daina rashin ji,amman katoton banzan yaki yarda..."d'an dakatawa tayi tana maida numfashi kafin taci gaba"harfa cewa yayi wai rabon da ya samu irin wannan daman tun akan wata ko hajara,kenan kaga dama sun saba yima yaran mutane fyade ko?" Haisam da yayi still yana saurarenta tamkar ya kunna radio,ya dan ta6e baki kafin yace"whatever dai zasu yi bayani acan,ke ma in kika je sai kiyi masu duk wannan bayanin" wata zabura tayi ta kwalalo idanu"ni kuma!to ni mi zanje yi police station?nifa ba laifin da nayi Allah,kuma abunda yasa naje wurin gayen da dare saboda banyi tunanin zai cutar dani ba saboda shi wllh ko hannuna bai ta6a rukewa ba,kawae dai in ya ganni yana tsokana na yana ce man wai Aljana", D'an kankance idanu yayi yace"aikam dole zaki je can...." tun kafin ya k'arasa ta fara kokarin rage tsawonta har idanunta sun kawo ruwa alamar zata fara kuka,d'agowa yayi yana mata nuni da hannu yace"No,yi zamanki zaki je ne don akwae bayanai da suke so daga gare ki,yadda incident d'in ya faru,dat's all" komawa tayi ta zauna had'i da yin dan murmushi lokacin kuma kwallan da ta taru ta zubo sharrr,haisam dake kallonta ya dan girgiza kai calmly yace "kuka bai maki wuya ko" tsayawa tayi da goge kwallan da take da gyalen tace"wllh hankalina ne ya tashi,nayi zaton nima kulle ni za'ai,amman kaine zaka kai ni can din?" d'aga mata kai yayi alamar eh,tace"A motar mai fasassan gilashin?" banza ya mata yana mata kallo mai kaman harara,da sauri tace"au na manta kuna da su da yawa,to amman fa gwaggota da hajiyanka basu san abunda ya faru ba,kar kuma su zo su sani,dama yau da na dawo daga makaranta na iske Ladidi mai waina tana ba gwaggo labarin anzo an kama Gaye wai jiya wani mutum ya gansu suna k'okarin yima wata fyade,baka gan yadda hankalin Gwaggota ya tashi ba fa" ta k'arasa had'i da rike ha6a, "Don't worry bazasu sani ba,amman akwae abunda zan fad'i maki yanzu shima yana cikin sharadinmu na glass indai baki kiyaye ba you know what would happen" kasak'e tayi tana kallon shi,d'agowa yayi daga jikin kujeran ya d'an duk'u hadi da linke hannuwansa asaman cinyoyinsa,ganin hakan yasa itama ta goyo hannayenta saman kirjinta ta yi masa kuri da idanu, On a serious note ya fara magana"I don't want u to repeat same mistake u made yesternight" da sauri tace"ba zan k'ara ba Allah kuwa" tayi maganar tana girgiza kai,Haisam ya ci gaba"kowa da kike gani zai iya cutar da ke,including your own blood brother..." zaro ido fatuu tayi tasa hannu ta rufe bakinta alamar mamaki,haisam yace"yeah.."cire hannun tayi tace"to amman ai ni yayana fa ba anan yake ba yana can garinmu sai dai kawu Amadu harshi kenan zai iya cutar dani din?" nodding kai yayi kafin yace"baki ji nace ko d'an uwanki na jini ba" shiru ta d'an yi alamar tunani can tace"kenan yanzu da kawu Amadu ya kara rike man hannu in gaya ma gwaggo?" girgiza kai ya yi"ba irin wannan ba,ai shi d'an uwanki ne zai iya rike ki..." shiru yayi don bai san taya zai mata bayani ba,fatuu dake ta kallonshi ganin yayi shiru tace"ko kana nufin ta6a cikin jiki?" kai kawae ya d'aga mata,da alama ta kashe bakinshi,jinjina kai tayi alamar ta fahimta can ta d'ago tace"HAR KAI.......?" *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story._ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *3️⃣3️⃣* ".....Har kai in kayi man hakan in fad'i ma hajiyanka ko gwaggotah?" komawa yayi ya jingina da kujeran yasa hannu ya rike gemunsa da bakinsa, kallonta kawai yake,fatuu ta wuce duk yadda yake tunani,tai mashi zuru da idanu da alama amsa take jira,ganin haka yasa ya daga mata kai alamar eh,can kuma ya cire hannunsa daga bakin gently yace"But i will never do dat..." da sauri ta katseshi"dama nasan kai baza ka cutar dani ba,kai mutumin kirki ne ai" shi dai kallonta kawae yake kaman yana nazarin wani abu. "Kin ta6a yin ciwo aka kai ki asibiti?" ya jefa mata tambaya, tace "A ina?can garinmu ko nan" yace"ko ina" dan langa6ar da kai tayi"acan garinmu ba'a ta6a kaini asibiti ba in ma ban lafiya jik'a man magani ake in sha ko asaman a abinci,kuma ma ni ina dad'ewa banyi ciwo ba fa,yauwa na tuna kaka na yana sawa ana man turaren magani,ba na fad'a maka yace wai shedanu ne su kai man fitsari aka ba,to fa yana nufin wai aljanu gareni" "da gaske kina da su?" haisam ya tambaya,girgiza kai tayi tace"nidai wllh bani da wasu Aljanu amman sai aita cewa su gare ni ko a makarantar bokonmu ma kowa kallon mai aljanu yake yiman tun daga wata rana da displine master ya bugan man kai na fad'i ina bori shikenan akace aljanu gare ni kuma wllh ina sane nayi borin,to fa haka nan ya tsaneni ko laifi mukai mu da yawa ko bai bugi kowa ba sai ya buge ni,ni kuma shiyasa nayi masa bori dama kuma banson a bugan man kai ai kai ma kasan baida dadi ko?" daga mata kai yayi alamar eh, ta ci gaba"amman kasan mi,tun daga lokacin wasu malamai suka daina buguna ma ajiki sai a hannu su duk atunaninsu aljanun gare ni harda sauran yan makarantar ma tsoro na ake,sai su rika cewa wai k'arfin da ke gareni ba nawa bane na aljanun ne" ta k'arasa maganar tana ta dariya,shima d'an murmushi yayi sai kuma yace"to ita grandma d'in taki bata fad'a maki ko da gaske kina dasu ba?" gyara zama tayi tace"ai ita dama bata cewa inada su,ko da na fad'a mata abunda ake cewa a makarantar cewa tayi k'aryane in rabu dasu,amman kuma tana cewa zata kaini asibiti wai a binciki kwakwalwata wai banda cikakken hankali,ba kaman in na siyo mata rigima"ta k'arasa maganar tana tikar dariya had'i da sussunar da kai k'asa,shi dae kallonta kawai yake, "ko kaima kana ganin banda cikakken hankalin ne?" fatuu ta jefo mashi tambaya,girgiza mata kai kawai yayi alamar a'a tace"nifa wllh zafin marin da kayi man ne yasa na jefan maka gilashi kuma nayi zaton in ya fashe kawai za'a walde shi ne kaman yadda ake walde kofa,ashe shi wai sai dai a canja,Allah yaso ni mai kudi kuma mai kirki na jefan mawa ai da kuwa an kai ni asibitin mahaukata mai dalili na gidan yari"ta k'arasa tana dariya hadi da jinjina kai,shi dai d'an ta6e baki yayi baice mata komae ba, jin kafarsa mai ciwo ta sage masa yasa ya d'agata yana k'okarin d'aura ta saman kujerar,ganin haka yasa fatuu cije baki tana yin d'an sauti"shiiii.." juyowa yayi ya kalleta bayan ya d'aura kafan da sauri tace"sannu,da zafi ko?"yar harara ya wurga mata ba tare da yace komae ba ganin haka yasa ta sake cewa"kayi hakuri Yaya handsome,kaji ciwo ta dalili na" ta k'arasa maganar tana turo baki hadi da langa6ar da kai, d'an daure fuska yayi"ban yin hakurin,kin zaunar dani a gida ban je aiki ba ke gashi kin je school" yar dariya ta yi tace"nama san wasa kake ai,kai da nayi ma asarar million amman ka yafe balle wannan" cike da mamaki yace"kenan ita asarar kudin yafi wannan?" tace"eh mana,million fa kudi ne da yawa", "to kuma in k'afan ya lalace fa saboda ciwon?" tace"da million ai za'a iya yi mata magani har ma arage canji" jinjina kai kawai yayi yana kallonta underneath his breath ya furta"this's serious!", wayarsa ce ta fara ringing ya kai hannu ya d'auka yana duba mai kiran Henry shine sunan da ya gani,d'aga kiran yayi kafin ya kara a kunne cikin harshen turanci ya fara magana daga ji wanda yake wayar dashi bature ne don slang english yake yi,ita kuwa fatuu k'ura masa idanu tayi kaman mujiya baki bude,yana cikin yin wayar yayi dariya har hakoransa suka bayyana a lokacin kuma wani abu yaja hankalinta a fuskar tashi,k'ara kura masa idanu tayi cike da mamaki ta ke bin fuskarsa da kallo har d'an kwantar da kanta take yi tana lek'o d'ayan 6arin fuskarshi,duk abunda take yana lura da ita ta wutsiyar idonsa,juyowa yayi ya kalleta bayan ya gama wayan fuskarshi ad'an d'aure tana ganin haka da sauri ta kama kanta tace"naga kana da irin abuna anan amman a dayan 6arin ban ganshi ba"tayi maganar tana nuna masa dimples d'inta bayan ta yake baki tana dariyar yak'e wai don yaga dimples din", still yayi yana kallonta kafin yace"d'ayan kike nema kenan?" d'aga masa kai tayi alamar eh,ya jinjina kai kaman bazai ce komae ba sai kuma yace"to babu" da sauri tace"kenan kai guda d'aya kayi gado?", d'age gira yayi"meaning?" "ina nufin wurin mamanka ko babanka ka gaje shi,kasan fa in mutum guda d'aya gareshi to cikin iyayenshi guda ke dashi,kaga ita hajiya nasan bata da shi,to kenan a wurin babanka ka gada" jinjina kai yayi yace"ko?" tace"eh mana" can kuma ta rik'e baki da sauri "kai,to ai nima babana bai dashi wllh gashi kuma biyu gare ni,to ya akai hakan ta faru?" ta jefa mashi tambaya,watsa hannuwa yayi yace"how do i know" d'an tunani ta yi kafin tace"nifa dama wata kawata ce itama tana dasu ta fad'i man hakan,amma yanzu na ma gane yadda take nufi,in cikin iyayen mutum guda d'aya na dashi duka biyun to sai mutum ya gaji duka shima,in kuma cikin iyayen d'aya nada guda d'aya to sai mutum ya gaji guda d'aya shima kaman kai kenan" tana maganar tana d'aga hannu kaman malama na bayani, Gyara zama yayi yace"what if duka iyayen na dasu kuma guda biyu kowa,ya kenan za'ai? dage idanu tayi sama alamar tana nazarin tambayar tashi can ta kalleshi tace"sai mutum ya gaji guda hudu kenan" jinjina kai haisam yayi cike da son jin yadda hakan zata faru yace"ta ya ya?" yatsun hannuwanta manunai tasa ta nuna saitin da dimples d'inta suke tace"kaga nan biyu,sai kuma asamansu ko ak'asan su wasu biyun su fito" shiru haisam yayi yana imagining yadda dimples hudu zasu fito ma mutum a fuska,can yace"ke kin ta6a ganin mai su haka?" shiru tayi tana zare idanu can ta fashe da dariya tace"wllh ban ta6a gani ba,kam yo mutum ma ai kaman Aljani zai koma" dariya shima haisam din yayi har fararen hak'oransa suka bayyana, yace"kawae kin zauna kina shirya man k'arya... " da sauri ta katse shi tana turo baki "wayyo Yaya Handsome wllh bafa k'arya nike ba,baka ji nace wata kawata ce ta fad'i man hakan ba,kaga ita ce ke yin karyar ba ni ba ko", Sigh yayi ya shafi gefen fuskarshi,ita kuma sai sussunar da kai take alamar taji kunya,d'an Murmushi yayi yace"is okey na fahimta ba k'arya kikai ba" da sauri ta kalleshi tayi yar dariya,shima har lokacin da Murmushi a fuskar tashi "What's ur name?" ya tambayeta,tace"Fatuu,baka ji jiya ina fad'a ba a labarin dana baka",dage gira yayi yace"I mean your real name" "Fateema"ta bashi amsa, jinjina kai yayi kawae,shiru sukae na wani d'an lokaci,tana ta wasa da yatsun hannunta, remote haisam ya dauka yai turning tv on,da sauri fatuu ta juya jin sautin tv din, ganin yadda take ta d'age kai tana yin kallon don a k'asa ta ke zaune haisam yace"Zarah..." shuru bata waigo ba da alama bata ji shi ba,d'an daga murya yayi ya kara kiran nata aikuwa da sauri ta waiwayo tace"ni kake kira da Zarah?" "yeah,ko ba sunan ki bane?" dariya tayi tace"sunana ne,Fateema zahra,amman fa ba wanda ke kira na da haka" tayi maganar tana jaddada mashi da kai,hannu yasa ya shafi beard d'insa kafin yace"nima sunan da kike kirana dashi ba wanda ke ceman haka" kyalkyacewa tayi da dariya tace"ka rama kenan" bai ce mata komae ba, "ka kira ni to" fatun ta fad'a, yace"just to say u can have a seat,naga kina ta d'age kai zai iya maki ciwo" jin haka yasa ta mik'e tana d'an yake baki"wllh fa harma naji kaman ya fara zafi,to a ina zan zauna wannan ko wanccan" ta nuna d'ayan 6arin kujerar da yake zaune da kuma armchairs d'in dake a d'ayan bangaren "duk inda ya maki" ya bata amsa,yar dariya tayi tace"to bari in zauna can gefen kujeran nan naga kafi zama asamanta nasan tafi dadi ne ko?" dan ta6e baki yayi fuskarshi a sake kaman zaiyi murmushi"in kin zauna zaki ji" tace "to"daga haka ta nufi dayan 6arin L-shape d'in ta zauna ta daidaita zamanta sosae kafin ta juyo tana dariya tace"taushi wllh"d'an Murmushi yayi yasa hannunsa na dama ya shafi forehead dinsa,ita kuma ta juya taci gaba da kallon, Juyowa fatuu tayi bayan wani d'an lokaci ta yamutsa baki, "yaya handsome wai baka da Arewa24 ne,nifa wllh wannan bangane abunda suke cewa" haisam dake daddana wayarsa ba tare da ya kalleta ba yace"ba kina fahimtar turanci ba" tace"ai nifa irin namu na nan nike dan ganewa ba irin wannan suri surin ba" ta k'arasa maganar tana turo baki,sai lokacin ya d'ago ya kalleta"to ai duk abu d'aya ne.." ta katse shi"to ai nasu gudu yake ban ganewa kai naji ka iya d'azun kana yi,ni sam ban iya ba,in dai akwae Arewan ka maida man" nodding kai yayi yace"baza'a rasa ba sai dai bansan a ina yake ba,let me search" searching Arewan ya fara "kenan kai baka kallon Arewan?"fatuu ta jefo masa tambaya,kai kawai ya d'aga mata alamar eh,tace"tabb kai yan turancin kenan kawai kake kalla shiyasa ka iya kaima,zaka koya man?" nan ma kai ya d'aga mata alamar eh,"to yaushe zaka fara koya mun?" sai lokaci yayi magana ba tare da ya kalleta ba yace"ba yanzu ba,sai ansamu enough time yanzu ina busy" jinjina kai tayi tace"zan jira kuwa,haulat ta bani dani in na iya har malaman makarantarmu ma sai na nuna masu su basu iya turanci ba...." da saura ta juya ta kalli tv jin ana magana da hausa lokaci guda ta washe baki tace"yauwa ga inda muka fi wayo nan...." juyowa ta sake yi a kalli haisam rai adan 6ace tace"wllh su Arewar nan sai suyi ta maimaita film" d'ago kai yayi ya kalli tv din sai kuma ya maida kan akan wayar da alama wani abu yake da ita, "Don Allah yaya handsome ka maida Tauraruwa ko Hijira suma duk hausa ake yi" ba tare da ya dago ba yasa hannu ya dauki remote din ya mik'o mata,bin shi tayi da ido ba tare da ta taso ba,hakan yasa ya dago yace"ki zo ki amsa mana" tashi tayi ta nufesa tsayawa tsaye tayi a gabansa bayan ta kar6i remote d'in tace"nifa ban san ya ake yi ba,bamu da dish agidanmu" dagowa yayi da d'an mamaki ya kalleta,to in basu dasu ya akai duk tasan channels din da ta fadi mashi yanzu,kaman tasan mi yake tunani tace"dama a makwabtanmu nike zuwa yin kallo,mu yar tv garemu da vedio to daga baya aka saida vedion aka siyo DVD muna kallon cassette,kuma sai tv din ta lalace aka kaita gyara bayan ta gyaru munci gaba da kallo kuma wai rannan sai aka maido wuta da karfi ta sake lalacewa da aka kai gyara sai aka ce ai ta kone ne,tun daga lokacin ne bamu da kayan kallo,ita kuma banzar Naja'atun da nike zuwa gidansu kallon rannan muka yi fad'a har na falleta da mari shine tayi man gori tace karna k'ara zuwa gidansu kallo,ni kuma sai na daina zuwa don banson inje ayi man wulakanci don ba kyalewa zanyi ba ko innarsu ce tayi man sai na rama ehe,ai dai arziki na Allah ne suma ba finmu sukai ya basu ba" ta k'arasa ranta a 6ace ta kumbura baki da alama abun yayi mata ciwo,ganin haisam din yayi shiru yana kallonta yasa da sauri tace"ina nufin fa ada lokacin da banjin magana shine ba zan kyalen ba,ni yanzu bama ruwana dasu,anan gidan nike yin kallo in na zo wurin hajiya,kuma kai naga abun naka ba irin nata bane shiyasa bansan ya zanyi amfani da shi ba", Sigh haisam yayi Calmly yace"kome ta maki laifin ki ne miyasa zaki mare ta,ke komae aka yi maki sai bugu" ya k'arasa maganar ya dan 6ata fuska,ganin haka yasa fatuu marairaicewa tana nannok'e kai muryarta kaman zata yi kuka tace"to ai ita ta ja ni fa,raina man wayo tayi ni kuma naji bazan iya hakuri ba,kai ma rannan dana yi maka ba daidai ba ai mari na kayi ko amaimakon kayi hakuri", "Oh kinma san ba daidai ki kai man ba har na mare ki,amman still kika jefan man glass" ganin kaman ransa a 6ace yayi maganar yasa da sauri tace"Don Allah kayi hakuri,na fa gaya maka wllh marin ne mai zafi kayi man,amman yanzu ai na bari ko"har kwalla sun taru a idonta,ga rashin ji ga saurin kuka, Jimm ya d'an yi kafin ya mik'a mata hannu alamar ta bashi remote din,da sauri ta mika masa ba tare da ya kalleta ba yace"matso ki ga yadda ake,if u want to change another channel ba sai kin tambaye ni ba,tace to had'i da matsowa gabanshi tana k'okarin dukar da kanta taga yadda zai yi d'an gyalenta ya silalo ya fada saman hannun shi, Dagowa yayi ya kalleta tana tsaye daga ita sai riga da wando na uniform da sauri tasa hannu ta d'auki gyalen ta fara k'okarin yafawa,tun d'azun yana lura da yadda gyalen keta zamewa hakan yasa shi cewa"ki rolling din shi mana" tace"ai ko nasa bai zama,gashina ne ke da sul6i shiyasa" shiru yayi da alama bata fahimci mi yake nufin tayi da gyalen ba,kaman ance ya kalli tv ya hango wata mata tayi rolling gyale a film din da ake hakan yasa haisam mik'a yatsansa yace"ki yi yadda tayi" da sauri ta juya ta kalli in da ya nuna kafin ta juyo tace to,cuku cukun laga gyalen ta shiga yi sai dai sam ta kasa saboda bata iya ba,ga gyalen ba wani babba bane,ganin yadda take ta fama yasa haisam fara nuna mata yadda zata yi da hannu,can tace"to tunda ka iya ka nad'a man mana,daga nan kagan sai in koya" wani kallo yayi mata, ganin hakan tace"ai shi ba ta6a ni kayi ba ko" shiru yayi ya duk'ar da kansa yana kallon k'asan parlon da alama nazari yake don al'amarin Fatuu saida nazari kam😹. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story._ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *34⃣* D'agowa yayi yai mata alamar ta duk'u da dogayen yatsun hannunshi,kneel down tayi a gabanshi ahankali yace"ki bud'e gyalen ki d'aura shi asaman kanki" tace "to" yin yadda yace tayi,hannu yasa ya kama ha6ar gyalen ta gefe guda ya janyo shi ta yadda zai fi d'ayar ha6ar tsawo,ba tare da ya ko kalleta ba ya shiga nad'a mata shi,daga k'asan wuyanta ya dan d'aure gyalen don in ba d'aurewar akayi ba bazai tsaya ba,har ya gama hannunshi bai ko ta6a gashin kanta ba, cikin cool voice d'insa yace"U can get up now,an gama" bata mik'en ba sai ma washe baki da tayi tace"Yaya handsome ya akai kai ka iya kana namiji amman ni ban iya ba,kuma dai ai baka da k'anne balle ace awurin su ka koya" komawa yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran fuskarshi a sake yace"ko" tace"eh mana ai kai kad'ai ne anan gidan baka da k'anne,Aunty Saude kuma yar aiki ce...." dan dakatawa tayi alamar tunani kafin taci gaba"ko a wurin ya'yan yayanka Senator ka koya" nodding kai yayi alamar eh, tace"ashe shi yasa ka iya, to nayi kyau?" ta tambaya tana d'age idanu,hannu yasa ya dauki wayarsa ya shiga camera,mik'o mata wayar yayi "ki duba" kar6ar wayar tayi ta fara kallon kanta aciki lokaci guda ta kyalkyace da dariya"wllh nayi d'an banzan kyau sai kace irin larabawan nan da ke yin wak'a a wata tasha a tv d'in hajiya suma haka kumatunsu ke yi in suka nad'a gyale kaman an tura biredi" yar dariya haisam yayi jin abunda tace, Mikewa tayi tace"to ka nuna man yadda zan canja kallon,d'agowa yayi ya shiga nuna mata sannan ya mik'a mata ta koma inda ta taso ta fara caccanja channels d'in,in ta fara kallon wannan sai ta canja ta koma wannan shi dai yana ta bin tv d'in da kallo,can ta kamo wata tasha ta turawa saurayi da budurwa suna romance,budurwar nata kakkaucewa shi kuma saurayin na kara jawota kaman wani maye k'okarin saka bakinshi yake a cikin nata da sauri Fatuu tace "A'uzubillahi minash shaitanir rajim,wannan d'an iska ne irin su Gaye.." k'okarin juyowa tayi haisam na ganin hakan yai saurin d'age kansa akan bayan kujeran yana facing sama pretending he's not watching the tv, "Yaya handsome", fatuu ta kira shi,shiru yayi kaman bai ji ba,ta k'ara kiranshi sai lokacin ya dago ya kalleta had'i da d'an dage gira" ya akai?" turo baki tayi tace"wannan tashar ta yan iska ce wllh ka cire shi,ko kuma in baka iya ba kasa azo acire ta,irin su gaye ne fyade ake yi,kalli ka gani..." ta juya zata nuna mashi lokacin budurwar ta amince mashi har sun had'e bakunansu sun wani rurruke juna,da sauri fatuu tasa tafin hannun hagunta ta kare gefen fuskarta, "ka gani ko,itama ashe yar iska ce,wllh ka daina kallon irin wannan kar kaima su maida kai d'an iska kai da ba ruwanka atoh" still haisam yayi ya d'an daure fuska,duk da tun farko taso bashi dariya, jin abunda tace yasashi cewa"don kin ganshi sai aka ce maki ina kalla", "to amman kai kasa ko?" girgiza mata kai yayi Calmly yace"haka suke", "a cikin dish din?" kai kawai ya daga mata,ta6e baki tayi tace"so suke su iskanta mutane,Allah ya shirye su,don Allah yaya handsome duba man kaga sun daina"ta fad'a har lokacin hannunta na kange da gefen fuskanta, D'aga idanunsa yayi ya d'an kalli tv kafin ya maida idon kanta"to mi ya kai ki nan,ba inda ake yin hausa kika ce kina son kalla ba?" ya yi maganar fuskarsa ad'an daure,da sauri tace"gani nayi su duk basu wani sabon abu fa shine nike neman tashar yan indiyawa kawae sai gani nayi na fad'o awannan,k'ilan ma wllh su suka ja ni na kamo nan don inga iskancin da suke", yar harara ya wurga mata yace"jiyan ma inda kika je ai jan ki akai ko" da sauri ta sunnar da kai k'asa,can ta d'an dago idanunta taga ita yake kallo hakan yasa ta d'ago kan gaba daya tana kallonshi itama,sigh yayi kafin ya fad'i mata lambar da zata kamo Mbc Bollywood d'in,da sauri ta juya ta canja sai gashi ta kamo ana yin wakar india,gaba daya ta maida hankalinta kan tv d'in ta fara d'an jujjuya kanta tana yin rawar itama, Kallonta haisam yai tayi ganin yadda take rawa daga zaune hankalinta a kwance,hakan yasashi cikin ranshi yin tunanin da suna da kayan kallon k'ilan da bata rinka fitowa tana yin rigima ba don zasu rinka dauke mata hankali,bayan wasu mintuna ya duba time a wayansa ukku saura kwata,hakan yasa ya mik'e ba tare da ya d'auki wayarshi ba ya nufi Bedroom dinsa,juyowa fatuu tayi ta bi shi da ido tana kallon yadda yake yin tafiyan a hankali har ya shige cikin corridor d'in sannan ta juya kan tv taci gaba da kallo. Almost 40 minutes ya d'auka kafin ya fito,k'amshin turaren jikinshi ne ya bugamma fatuu hanci hakan yasa ta d'ago da sauri ta kalli bakin corridor din,baki bude take kallon haisam da ya fito cikin jeans bak'i da t-shirt fara ta mashi cif a jiki,k'irarsa ta kakkarfa ta bayyana,a gaban rigar anyi babban rubutu bak'i ansa XL,gashinshi a nad'e yasha gyara sai salki yake,ganin ta k'ura masa idanu yasa ya kauda nasa idon dama shi baison kallo,nufo inda fatuu take zaune yayi daga gefenta ya aje mata abubuwan da ya ruk'o a hannunsa kafin ya juya ya nufi inda desk yake,laptop d'in dake asamanshi ya d'aukko ya dawo cikin falon,inda ya tashi ya koma ya zauna ya jawo c-table ya d'aura computer d'in,budeta yayi ya fara kokarin kunnata, K'ura ma abubuwan da ya aje mata ido tayi wanda Milk pop corn ne anyi sealing dinsa a leda da k'aton biscuit sai wasu manyan chocolate guda biyar wanda ko ledar da aka nade su abun kallo ce,cike da mamaki ta juya ta kalli haisam wanda keta operating laptop d'in gabanshi, "Yaya Handsome" fatuu ta kira sunanshi,ba tare da ya kalleta ba ya d'age gira"yess"ya amsa, ta ci gaba"wannan abubuwan da aka ajiye a gabana fa,mi za'ai dasu?" still bai kalleta ba yace"kallonsu zaki yi" tace toh, bayan wasu yan mintuna ya yi mata kallon k'asan ido yaga ko ta fara ci,don yaga jiya da yayi mata gatse ta gane har tace irin abun gwaggo,aikuwa cike da mamaki ya idasa d'ago kanshi yana kallon ikon Allah,ashe bata ma d'auki komae ba, yadda yace matan tayi,wato k'ura masu ido sai kallonsu take tana hadiye miyau,Murmushi Haisam yayi ya d'an girgiza kai"Zarah" ya kirata, juyowa tayi ta kalleshi ta gwalo ido,gently yace"u can eat" fuskarta d'auke da mamaki ta juya ta kalli abubuwan kafin ta sake juyowa ta kalli haisam "yanzu duka wannan ni ka ba in ci?" kai kawae ya d'aga mata, d,aukar Pop corn din tayi ta fara kokarin budewa dama duk shi yafi tafiya da ita saboda madarar da ke cikinsa, "Wllh Yaya handsome kai mutumin kirki ne,yanzu duk abunda nayi maka kuma ka bani wannan kayan dadin,harfa ciwo naja maka" "Gashi ma kinzo ko abun ciwo baki kawo man ba" haisam dake ta latsa computer ya fad'a, "To ai mu fa bamu da irin wad'annan kayan dadin wllh,ko Kawu Amadu bai saida su,to ko inje in zubo maka abinci"? Girgiza mata kai yayi alamar a'a,tace"shinkafa ce fa"sosae ta bashi dariya amman sai ya basar,ya lura tana son shinkafa don ko jiya ta ambace ta, "Ko baka cin shinkafa ne?"ta tambaya, "Ina ci,amman yanzu na koshi ne" gyad'a kai tayi daga haka ta fara tura Pop corn din a baki,wani kalan dadi ne ya ratsa cikin bakinta,lokaci guda ta fara k'okarin gyara zamanta gaba daya ta d'aura kafafunta asaman kujeran ta lankwashe su tayi zaman cin tuwo,mutsu mutsun da take yi ne yasa ya d'an yi mata kallon k'asan ido dai dai ta juyo da alama magana zatayi suna had'a idanu tace"don kar na 6ata maka k'asan parlon yasa nayi haka" jinjina kai yayi kawae. "Wllh yan gayu sun ji dadinsu,Allah muma kasa mu a Aljanna muci kayan dad'i tunda nan mu ba masu kudi bane balle muci,komai na masu kudi na daban ne" tana maganar tana taunar Pop corn d'in har wani lumshe ido take da alama santi takeyi,haisam na jin duk abunda take fad'a bai dae tanka mata ba, can ta juyo ta kalleshi"Amman dae Yaya handsome wannan guggurun na kasar yan turanci ne ko?" ya fahimci tana nufin yan kasan waje,girgiza mata kae yayi"na yan kasan hausa ne" ya bata amsa, "To a ina ake yin shi Abuja ko lagos", " ki duba jikin takardar ciki" da sauri ta ciro yar takardar tana dubawa,cike da mamaki tace"kai wai anan garinma ake yinshi,tabb lalle amman mu an raina mana wayo,kasan wanda ake kawo mana makaranta wllh duk tsakuyoyi gashi ba madara kuma duhu gare shi duk ya k'one,kasan mi?" girgiza mata kai yayi alamar a'a, "Shi fa ko sugar babu sosae kuma da gishiri suke had'awa da sugan kana ci kana cin gishiri,kawae dai mu don anga talakawa ne ake mana irinshi mugaye kawae" daga haka ta ci gaba da taunar Pop corn d'in tana jujjuya kai, "Ba kina zuwa Islamic school ba?"haisam da ya d'ago yana kallonta ya tambaya, "Eh amman lokaci bai yi ba sai an kira sallah,sai inje in shirya" nodding kai yayi,sai kuma yace"dama kenan baki wanka", Cakk ta tsaya da taunar pop corn d'in ta juyo baki cunkushe"wllh ina yin wanka,duk yanmatan unguwan nan nafi so yin gayu" jinjina kae kawae yayi da d'an murmushi ya maida kan aranshi yana fad'in wai duk yanmatan unguwannan ko ina abun yake, K'okarin mikewa tayi ta kwashe su biskit d'in ta rungume ta nufi hanyar fita tana fad'in"bari inje inyi wankan to kafin a kira sallan" d'aga mata kae yayi ba tare da ya kalleta ba,ita kam tana nufar kopar fita amman idonta na akanshi ba k'aramin kyau yayi mata ba,yadda ya duk'ar da kanshi sumar kanshi mai matukar kyau da tsawo ga daukar ido a nad'e,ga ta gefen fuskan a kwance luf haka hannunshi da yake latsa computer dashi duk suma liya liya a kwance, tana kaiwa bakin kopan ta tsaya"Yaya handsome"ta kira sunanshi,sai lokacin ya d'ago ya kalleta had'i da dage gira alamar amsa kiran nata,fuskarta d'auke da murmushi tace"thank u so much da abubuwan da ka bani"d'an murmushi yayi ya jinjina kanshi,daga haka ta juya ta kama handle d'in kopan ta bude,sake juyowa tayi ta k'ara kiran sunanshi,kallonta yayi "What" runtse idanunta tayi tace"A wodi masha Allah" tana fad'in hakan ta juya da gudu ta fita,shiru yayi yana tunanin ko mi take nufi da abunda ta fad'a don ya fahimci fullanci ne tayi,koma dae miye yasan ba rashin kunya tayi ba don ta had'a da masha Allah,dan ta6e baki yayi yana k'okarin juyawa aka turo kopan,itace ta lek'o da kanta tanata dariya duk dimples dinta sun lotsa sosae"yaya handsome kasan mi nace?" d'an girgiza mata kai yayi alamar a'a, "Cewa nayi kana da kyau masha Allah" rasa abunda zaice mata yayi kawae yaci gaba da kallonta,hakan yasa ta kyalkyace da dariya ta janye kanta ta turo mashi kopan,haisam dake kallon side d'in kopar d'an murmushi hadi da girgiza kai yayi daga haka ya juya ya ci gaba da abunda yake. Sai da ta koma gidan sannan ta tuna da gwaggo tace ta share kitchen da tsakar gidan,da sauri shaf shaf ta share su kafin ta zuba ruwa ta shige band'aki don yin wanka,bayan ta fito tasa Uniform tayi sallah sai lokacin ta dan zubo abinci ta ci kafin ta d'auki jakarta ta fito don tafiya islamiyya lokacin kusan karfe hudu da rabi. Da sauri take tafiya bayan ta fito ta hau hanya tana gab da shan kwanar gidan hajiya taji an kwala mata kira"Fatuu" da sauri ta juyo ganin haulat ce yasa ta tsaya har ta k'araso wurinta"ya akai kika makara yau keda baki makara?"haulat ta tambayeta, "Gwaggo tasa in yi mata wani aiki" fatuu ta bata amsa bayan sunci gaba da tafiya,jinjina kai haulat tayi kafin tace"in muka dawo sai muje in raka kin abashi hakurin" kallonta fatuu tayi ta d'age gira"wa kenan"ta tambaya cike da rainin wayo, "D'an gidan Hajiya mana da kika fasa ma glass ko" wata yar iskar dariya tayi tace"sai dae ko ni in rakaki ki bashi hakurin"da sauri Haulat ta kalleta" yo ni hakurin mi zan bashi kamar dae ni na fasa masa glass din...." fatuu ta katseta"to wadda ta fasan taje ta bashi hakuri kuma ya hakura" zaro ido haulat tayi cike da zumudi tace"don Allah da gaske kinje fatuu,kuma ya hakuran?" "Bari kiga dil" fatuu ta fad'a tana kokarin bud'e cikin jakarta,biscuit da chocolate din da haisam ya bata ta fiddo harda ledan d'an sauran Pop corn da bata k'arasa cinyewa ba,ta mik'a ma haulat, Cike da mamaki baki bude haulat ta kar6a"wai don Allah da gaske kike shi ya baki wadannan abubuwan?" fatuu tace"eh mana shi ya bani,kuma yace ya hakuri amman fa sai da yasa nayi masa alkawarin na daina rashin ji ko fad'a yace kar ya sake ganina ina yi"ta k'arasa tana yar dariya, cike da farinciki haulat tace"kai amman wllh naji dadi da ya hakura,daman nayi tunanin zai hakuran don ni banma yarda da maganganun gaye ba,amma fa nayi mamakin saukin kanshi keda kika yi masa laifi wai kuma har ya baki wadannan kayan dadin", "kinsan ni d'in jinin sa'a ce" fatuu ta fad'a tana murmura idanu ", "Ah lallai ni ce sheda,jinin sa'a mai kukan za'a kaita gidan yari ta rink'a cin gabza kwarkwata ta gwaigwaye mata kai ba,yar rainin wayo zaki wani gaya man jinin sa'a bayan kin gama 6are ma mutane baki"haulat ta fad'a tana dariya itama fatun dariyar take,ta bude chocolate guda ta tura baki,kallon haulat tayi "ke ba zaki sha ba", "Gani nayi akan hanya muke..." fatuu ta katseta"yo miye ina ruwanki da wani kuma ma hanyar ai ba wasu mutane" haulat tace to ta 6are guda itama ta tura cikin baki ta fara taunawa"wai fatuu micece gabza?"fatuu da dad'in chocolate ya ratsata har cikin kwanyarta ta d'age idanu tace"oho ni wllh bansan miye gabzar ba,kaman dae abincin gidan yari ne,kuma ni abunda ya tada man hankali dana ji gaye yana neman tsari da ita,har fa cewa yayi wai yana taka tsantsan kar akaisa gidan yari saboda tuwon babarsa..." tunda ta fara magana haulat ke kyalkyatar daria hada dafe ciki"yanzu ashe dama baki san ma micece gabzar ba amman kika tashi hankalinki,nifa wllh tun farko ma ban yarda da duk abunda ya fad'a ba tunda d'an shaye shaye ne fa yawancin kalamansu duk k'arya ne,amman gwara ma da akayi hakan koma karyan ne ni wllh naji dadin hakan..." fatuu ta katseta"wayace maki karya yake,da gaske ne don saida yace wai lauya d'insa ne bai a gari shiyasa ba'azo aka kamani ba", Jinjina kai kawai haulat tayi don daga jin maganar ta san mutumin wasa yake amman bata nuna ma fatun ba tace"yanzun dae ai dole ki daina rashin ji tunda kinyi masa alkawari in ba haka ba atafi a had'e da gabza tunda dae ba kudin shanu gomaa da za'a biya shi" ta k'arasa tana ta tik'ar dariya,hakan yasa fatuu d'aga jakarta zata buga mata da sauri haulat ta ruke jakar"ke fatuu baki da hankali ne akwae fa Al'qurani aciki" cigaba da tafiya sukae haulat nata tsokanar fatuu har suka kae islamiyyar,sun dae makara sosae hakan yasa aka yi masu bulalar makara kafin suka shige aji. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _*A heart touching love story.*_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *3️⃣5️⃣* Bayan antashi islamiyyar atare suka taho kaman yadda suka saba sai lokacin suka bud'e biskit d'in suna ci,hannu fatuu tasa ta dafa kafad'ar Haulat"wllh Yaya handsome na da kirki sosae" wani kallo haulat tayi mata tace"waye haka?" "Yo Dan gidan hajiya mana mai gilashi", "Haka sunanshi yake handsome? Biscuit fatuu ta tura abaki"a jikin rigarsa naga an rubuta call me handsome daya ji ina kiransa da sunan shine yace man wai ba sunanshi haka ba sunan shi ko Haisam to ni kuma sai naga ai duk d'aya ne ko" kyalkyalewa da dariya Haulat tayi"wllh fatuu kin cika iskanci ta ina handsome da haisam suka zama d'aya,handsome fa turanci ne haisam kuma ai kaman larabcine" fatuu dake taunar biscuit tayi wata yar iskar dariya"to ni dae nafi jin dadin cewa handsome kuma ai ya dace da sunan tunda yana nufin mai kyau kuma shi d'in mai kyaun ne"girgiza kae kawai haulat tayi suna ci gaba da tafiya, "k'awata nagode sosae da shawarar da kika bani kinga tayi man amfani kaman dae yadda duk in kika ban shawara take yi,Allah ya barmu tare har abada"fatuu ta k'arasa maganar had'i da k'ara dafa kafad'ar haulat din, Murmushi Haulat tayi"ai shiru nayi na zuba maki ido inga in zaki man godiyar kaman yadda kika ce jiya in bari sai shawaran tayi aiki sannan ki goden" fatuu ta langa6ar da kai"ai kinsan dai inada hankali nasan daidai ko,dama ai zan maki godiyar...."katseta haulat tayi"ah kina da hankali kam,ni ce dil nafi kowa sanin k'awata yar fillo d'an kai ne da ita" a fusace fatuu ta juyo ta kalleta"ni ce mai d'an kai?mara hankali fa kenan" ganin haulat d'in tasa hannu ta guntse dariya yasata d'aga hannu zata kai mata bugu, aikuwa da gudu haulat ta juya fatun ta rufa mata baya suka yanki hanya suna ta gudu,cikin haki haulat ke fad'in"Don Allah fatuu yi hakuri kinsan ni ban iya yan guje gujen nan ba,wllh har na fara ganin juwa", Suna isowa bakin lungun gidan hajiya haulat ta tsaya tafin hannunta guda asaman kirji sai faman haki take,ita kam fatuu koda ta zo wurin amaimakon itama ta tsaya sai kawae ta mik'i hanya straight taci gaba da gudun,cikin d'aga murya haulat tace"fatuu ina za ki?" hannu ta d'ago mata"kije sai mun had'e gobe da safe,zanje wani wuri ne"daga haka tayi gaba,gyada kai haulat tayi ta juya ta shige cikin lungun. Juyowa fatuu tayi ganin haulat d'in ta tafi yasa ta tsaya da gudun ta ci gaba da tafiya,bakin titi take son zuwa don ta siyo ma Haisam wani abu,bata son haulat d'in ta sani ne shiyasa tayi mata hakan don in suka tafi tare tasan sai ta tambayeta dalilin siya mashi abun kuma gashi ya gargad'eta kada ta fada ma kowa abunda ya faru game dasu gaye. A dai dai bakin titin ta tsaya ta shiga tunanin mi ya kamata ta siya mashi,ko taje wanccan shagon taga in akwae abunda ya kamata ta siya...."yanmata zo ga kayan marmari masu kyau..."fatuu taji an fad'a daga d'an can gefenta,juyawa tayi ta kalli mutumin da yayi maganar,ya ci gaba"zo ki siya zan maki sauki"shiru tayi tana kallonshi sai kuma ta fara tafiya ta nufi wurinshi, "Yauwa yar fillo to mi za'a baki" wani kalan kallo ta yi mashi"ni ba sunana haka ba sunana fatuu"ta k'arasa tana turo baki,yar dariya yayi"to ai daga jin sunan naki na fillon ne,ba fatima yake nufi ba?" tace"to ni dae ka kira ni da sunana kawai in ba haka ba in tafiyata" da sauri yace"ah to yi hakuri hajiya fateema dami dami za'a baki ne?" shiru tayi kaman tana tunanin wani abu"kasan mi,wani ne fa zan siya mawa bai lapiya to kuma su yan gayu ne,ni sai ina ganin kaman ma bazai ji dad'insu ba tunda suna shan su kullum,har lemunan roba dana gwangwani suna dasu cike a fridge", "Kice saurayinki ne bai lafiya zaki siya masa karin ciwo,hakan nada kyau...." cike da tsiwa ta katseshi"ni nace maka saurayi na ne,yayana fa ne shine zaka ce wai saurayina to bamma siya"ta juya zata tafi,da sauri yace"yaki zo mana,ai ni bansan yayanki bane,to yi hakuri yar fil...au fatima"tsayawa tayi tana mashi wani kallo ta kumburo baki, "Yauwa kika ce su masu kudine ko,to ai hajiya fatima dama masu kudi ana masu kyauta ne ba wai don abun yafi karfinsu ba sai don kyautatawa da nuna damuwa kuma hakan na sasu farinciki sosae,baki ga iyayenmu in zasu kaima manyan mutane ziyara ba sai su kai masu yar kuka dasu daudawa ba kuma kiga suna ta farinciki duk da sunfi kafinsu nesa ba kusa ba,to shima ina tabbatar maki in kika kai masa zai yi farinciki sosae yaga kindamu dashi hakan kuma zai k'ara dankon kauna a tsakaninku" wani kallo tayi mashi kaman zata kai masa bugu da sauri yace"ina nufin kaunar yan'uwantaka fa", Ajiyar zuciya ta sauke,ta bud'e jakarta kudi ta fiddo yan hamsin hamsin,ishirin,goma harda naira biyar biyar ta mik'a masa"gashi kaban na duka kuma cika man leda zaka yi komae ka zuba"kar6ar kudin yayi yana fad'in"wannan kudi haka hajiya fateema,nawa ne da har za'a cika leda"fara k'irga kudin yayi kafin ya kalleta"dari biyar ne"daga masa kai tayi alamar eh, "To amman d'ari biyar har acika leda,za'a dae zuba na iya d'ari biyar din" da sauri tace"a'a nidae komae zaka zuba man"tayi maganar tana tura baki,shiru yayi hannunsa rik'e da kudin yana mata kallon mamaki"taya zan zuba maki komae na wurin nan a d'ari biyar,kayan nan fa ba wata riba ce dasu ba don sunyi tsada yanzu,in ban ci riba ba ai bana fad'i ba ko,kinga wannan yankin kankanar naira dari take zansa maki ita,sai lemu da ayaba,sai in had'a maki da wannan yankin abarbar shima dari ne...." katseshi fatuu tayi"harda Apple zaka sa man" d'an bude ido yayi"Apple!taya zan had'a maki da shi abunda duk d'aya 300 yake,to kuwa saidai abaki apple d'in sai yankin kankanar nan sai asa maki lemu..", "to ayaba da abarbar fa" fatuu ta tambaya, "To indae harda su kike so gaskia sai kin karo kudi,ki k'aro wata dari biyar din asa maki komae,a cika maki ledar" "To ni ina naga wata d'ari biyar din,wannan ma kasan ko kudin miye na baka,nidae ka zuba man yadda kace din da farko sai ka saka man Apple d'in" shiru mai kayan marmari ya yi,lokaci guda ya fahimci rigimamma ce yarinyar,yar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"kingane ko hajiya fateema kar6i kudin nan,ki d'an k'ara gaba can gaban wanccan wurin wankin motocin,akwae wani mai saida kayan marmarin k'ilan nashi su fi nawa sauki don ni gaskiya ban iya baki yadda kike so,fad'uwa zanyi", k'in amsar kudin tayi tace"tabb wllh ba inda zani,ai kai ka kirani kace inzo za kai man sauki ko sai kuma kace wai inyi gaba ba inda zani sai kaban yadda nike so...."a fusace yace"to na fasa saidawar kije wani wurin,kar6i kudinki" turo baki tayi ta juya masa k'eya tana fad'in "Allah ko kaban ko in tara maka mutane ehe" zaro ido yayi"ki tara man mutane akan me,ana dole ne a kasuwa,yau naga karfin hali ni Rabi'u,fitsara zaki man nida kaya na" juyowa tayi ta kalleshi"ba wata fitsara,in mutanen suka taru ai sai suyi mana sharia aga wanda baida gaskia atsakaninmu,tunda dae kai ai ka kira ni ko"shiru yayi yana tunani cikin ranshi,anya yarinyar nada cikakken hankali kuwa,gara ya lalla6ata su rabu lpy, "Yanzu kingane to ki k'aro d'ari biyu sai in baki harda Apple d'in,ai kema nasan bazaki so in fadi ba ko hajiya fateema ki tausaya mani mana,nima sai nayi ciniki nike samu ina ma iyalai na cefane"lalla6ata ya shiga yi,ta k'ara bud'e jakar tana fad'in"ni bani da wata d'ari biyu naira d'ari ta rage man itama ajewa nayi don kar in rasa ko sisi" sababbin yan ishirin ta fiddo da gani kudin da hajiyar Sanata ta bata ne,mik'a mashi tayi bayan ta zare naira ashirin wai bazata zauna ba ko sisi ba,girgiza kai kawae yayi ya kar6i tamanin d'in ya fara kokarin zuba mata a leda bayan ta matsa masa saida ya kara lullube su kankanar da leda bayan wacce ke a jikinsu,yana zubawa tana masa korafin masu kyau zai bata don d'an gidan hajiyar Sanata ne zai sha in yaga ru6a66e bazai sha ba, Dakyar aka gama wannan ciniki ta juya ta tafi mai kayan marmarin ya d'an d'aga murya cike da tsokana"to yar fillo sai kin k'ara zuwa ko,Allah ya ba masoyinki lpy ki gaida man shi don Allah" juyowa tayi cikin fushi tace"ban k'ara zuwa siyan wani abu wurinka"daga haka tayi gaba, Dariya mai kayan marmarin yayi a fili yace"in kana sana'a kaga mutane kala kala". **** **** **** Fitowa Haisam yayi daga cikin Bedroom ya nufo cikin falo yana d'aura agogo a wrist d'insa,da gani alwala yayi,wurin da laptop dinsa take ya nufa don ya kashe ta,turo kopan da akai ne yasa shi dakatawa ya tsaya yana jiran ganin wanene ke k'okarin shigowa,bakinta d'auke da sallama ta shigo,tana ganinshi ta saki Murmushi shima d'an murmushin ya yi mata,tsaye tayi tana kallonshi tana ta kunshe ledan hannunta cikin Hijab,bangaren da armchairs suke ya nuna mata"get seated"ya fad'a gently, Shigowa ta k'arasa yi ta nufi wurin kujerun ta zauna saman d'aya,shima zaunawa yayi kan L-shape d'in,sai faman Murmushi take saki tak'i cewa komae hakan yasa shi cewa"har an tashi" kai ta d'aga masa alamar eh,shima jinjina kae yayi kafin ya juya yana k'okarin kashe laptop din, juyowa yayi ganin tana ta nuku nuku da abu cikin hijab yace"ba aiken ki akai bane,kije ki kai ni zanje masallaci" jin haka yasata fiddo ledan ta aje saman carpet kafin tasa hannu ta rufe bakinta tana k'umshe dariya,kallon ledan yayi sai kuma ya kalleta"What is it?" ya tambaya, "Abun ciwon ne na kawo maka"ta fad'a har lokacin hannuta na rufe da bakinta,he was speechless,cike da mamaki Haisam ke kallonta jin abunda tace wai abun ciwo ne ta kawo masa,cire hannun tayi ganin kallon da yake mata"ba d'azun kace ban kawo maka komae ba,shine yanzu na kawo" tayi maganar tana turo baki, d'an Murmushin mamaki yayi yana jinjina kai"Open it let me see what's inside", hannu tasa ta bud'e ledan ta d'an turata gabanshi,bin fruit din yayi da kallo,tunani ya shiga yi cikin ransa yana fad'in wani irin yarinya ne wannan,d'agowa yayi ya kalleta"baki san wasa bane,ni wasa nayi maki ai ba ina nufin ki kawo man wani abu ba...."katseshi tayi"ai yakamata dae in kawo d'in tunda dama saboda ni kaji ciwon ko"dan ta6e baki ya yi kawae,in ya biye mata haka zasu yi ta jan maganan"a ina kika samu kudi haka?"ya tambaya yana ci gaba da kallonta, d'an langa6ar da kai tayi tace"Kud'in adashe ne da muke yi nida kawayena yan makarantar bokonmu,to ni ce ke yin tari don ban yarda ba in ba wata kudina ta cinye", "amman ai ke gashinan sun yi trusting dinki sun baki kuma kin kashe masu, "ai zan biyasu dama d'ari biyar ce kawae ta adashen naira d'arin tawa ce hajiyanka ta bani,itama d'ari biyar d'in dama nida wata za'a ba kwasa yanzu,to rabi nawa ne rabin ne nata" "Yanzu ina zaki samu rabin ki biyata da kika kashe mata?" yar dariya tayi"zan samu mana ai gwaggo na bani kudin break kuma sai nayi kalaci nike tafiya makarantar kaga sai in tara kudin,kuma hajiyanka ma na bani,ga kawu Amadu ma in nace ya ban wani abu zai ban duk sai in had'a in bata"shiru Haisam yayi yanata kallonta, "ko bazaka sha bane"ta tambaya jikinta a d'an sanyaye,girgiza mata kai yayi"zan sha,amman karki k'ara yin haka,ni wasa nike maki" dan ta6e baki tayi"kenan ni baka son in baka abu?" "Ina so,amman ba wanda zaki ta6a ma mutane kudi ba,understand?"jinjina mashi kae tayi tace"to ban k'arawa Yaya handsome,da ai abinci ma zan kawo maka kace bazaka ci ba,shiyasa ma na siyo wannan din", "Na koshi ne,da zan ci ai" ya fad'a da d'an murmushi,itama Murmushin take tana kallonshi, k'okarin mik'ewa ya fara yi"nafa yi wankan" fatuu ta fad'a, d'aga mata kai yayi yana kallonta daga tsaye,ta ci gaba"wllh nayi,ina komawa gida kafin na tafi islamiyyar nayi kawae ban shafa turare bane shiyasa baka ji kamshi ba"ta k'arasa tana d'an sunsuna hijab dinta "miyasa baki sa turaren ba"haisam ya tambaya, "ai bandashi yanzu,dama gwaggo ke siyo man a wurin abokiyar aikinsu irin wanda ake sawa a yar kwalbar nan irin ta fiya fiya,ka santa?" kai ya daga mata alamar eh,taci gaba"to irinshi,wanda garan rannan ina cikin shafawa ya fad'i ya fashe,amman tace zata siyo man wani"jinjina kae yayi alamar toh,cikin cool voice d'insa yace"yanzu zanje masallaci time yayi" da sauri fatuu tace"to su kankanar fa bazaka sha ba?", "Zan sha mana,amman yanzu kinga sallah zanje,abunda za'ai ki tafi man dasu part d'in hajiya in nagama zanzo sai in sha,kema sai kiyi sallan ko" kai ta d'aga alamar toh ta mik'e bayan ta d'auki ledan,harta nufi kofa ya tsaidata"Zarah"juyowa tayi ta kalleshi,"wait,am coming"d'aga haka ya juya ya nufi bedroom d'insa,bai jima ba ya dawo,mik'a mata wani had'add'an kwalin turare yayi yace"kiyi amfani da wannan baida karfi sosae,za'a samo maki wasu" zaro idanu waje tayi ganin tana niyyar yin magana ya rigata da fad'in"ba rokona ki kai ba" dariya ta saki tace"ya akai kasan abunda zance Yaya handsome"shima yar dariya yayi"amsa kisa a bag d'inki" kar6a tayi tace"thank you Yaya Handsome" kai ya d'aga kawae daga haka suka nufi hanyar fita tana gaba yana bayanta. Suna zuwa daidai fence door d'in fita daga part d'in nasa ta juyo da sauri da yake shi a hankali yake tafiyan saboda kafansa mai ciwo,ad'an rude tace"akwae matsala Yaya handsome,in na kae maka wannan fruit d'in part d'in hajiya kuma ta gane abunda ya faru fa ko ka gaya mata ne??"ta kai maganar tana ta zare ido,d'an lumshe ido yayi ya girgiza mata kai alamar a'a kafin Calmly yace"don't worry ur self bazata gane ba"jinjina kai tayi harta juya sai kuma ta sake juyowa "Yaya handsome ko ka dafa kaina mutafi naga dakyar kake tafiyan"da'n bude idanu yayi da murmushin da iyakarsa saman lips d'insa yace"sai dae in rankwashi kan" dariya ta kyalkyace da ita ta juya, A harabar gidan ta tsaya tana yima dawisu wasa can ta d'aga kai ta kalli haisam da ya kusa isa kopan shiga masallaci ta kware murya tace"Yaya Handsome,don Allah kai man Addu'a Allah yasa in zama likita" hannu ya d'ago mata ba tare da ya juyo ba daga haka ya shige cikin masallacin lokacin ana cikin tada ik'ama,saida ta gama shiriritarta a harabar gidan kafin ta nufi part din Hajiya. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *3️⃣6️⃣* Lokacin da fatuu ta shiga parlon ba kowa,deep freezer dake a Dining area ta nufa ta bud'e ta saka ledan fruit d'in kafin ta nufi corridor d'in d'akunansu,bedroom d'in hajiya ta fara zuwa ta isketa tana yin salla hakan yasa ta fito ta nufi d'akin Saude itama sallan ta taras da ita tana yi, shiga ciki tayi ta aje jakarta a gefen k'atuwar katifar sauden ta nufi toilet ta d'auro alwala itama tazo ta kabbara sallan, Juyowa fatuu tayi ta kalli Saude dake zaune tana yin lazimi bayan ta gama sallan tace"ina yini Aunty Saude "fuskarta da fara'a ta amsa" lafiya lou fatima yar gidan hajiya,ya makaranta? "Lafiya lou" ta bata amsa,daga haka ta mike ta fita,bata jima ba ta dawo har lokacin sauden na a zaune,kallonta fatuu tayi bayan ta zauna"Aunty Saude kin daina koya man abincin yan gayu", Yar dariya tayi"ai ba lokaci ne fateema kinga kullum kina zuwa makaranta ga kuma islamiyya ki bari in aka sake yin hutu sai in ci gaba da koya makin ko kuma tunda Azumi ya kusa ma kinga sai mu yi a lokacin don an fi yin abubuwa da yawa"jinjina kai fatuu tayi, Saude ta ci gaba"wai ina kawar nan taki ne kun rabu da zuwa tare", "wai Haulat,tana nan,sai azumi yazo za ki ganta tana lalla6owa shan A.c"dariya saude tayi, fatun ta sake mik'ewa ta fita bata jima ba ta sake dawowa,ganin tana ta zarya yasa Saude fad'in"Hajiya kike jira ne,kinsan in tayi magriba sai ta yi isha'e take fitowa... "Fatuu ta katseta"a'a ba ita nike jira ba,Yaya hansome ne yace in jira shi anan" ba tare da saude taji sunan da ta kira shi da shi ba tace"ai kuwa shima wani lokacin sai anyi isha'in yake shigowa" d'aga kai fatuu tayi"to bari inje in gaisa da mutumina Aku kafin ya shigo"ba tare da ta jira abunda sauden zata fad'i ba ta juya ta fice, Hajiya ce ta shigo cikin parlon bayan angama sallan isha,zama tayi akan kujera 2 seater ta d'au remote tana kokarin canja channel Haisam ya shigo da sallama 3 seater ya nufa ya zauna,hajiya ta juyo tana kallonshi da d'an murmushi, shima murmushin ya mayar mata"hope u'r ok sweethrt", "lafiya kalau nike" hajiyar ta bashi amsa tana shirin k'ara yin magana fatuu ta shigo cikin falon da gudu ta kofar baya,juyawa hajiya tayi tana kallonta har ta k'araso ciki a gefen hajiyar ta zauna tana ta dariya"ke kuma yaushe kika shigo?" hajiya ta tamabaya, maimakon ta bata amsa sai cewa tayi"wllh hajiya wancan Akun ya raina ni na kusa in mashi jan bugu"ta k'arasa tana nuna yadda zata buge shin da hannu, hajiya tace"toh,yau kuma miya hada ki da mutumin naki ne?" "wai daga nace Aku mai fitsari a tsaye shine yace man fatuu mai kashin kwance" hajiya tace"ah laifinki ne don mi zaki ce masa mai fitsarin tsaye a ina kika ga yana fitsari a tsaye"turo baki tayi"to ai ni wasa nike masa ko" hajiya tace"ai shima wasan yake maki nasan,ina Dije ko tana wurin aikin?", "Eh tana can tana faman share-share da goge goge" hannu hajiya tasa ta d'an bugi kafad'arta"ja'ira aikin nata kike ma tsiya,ai da share sharen take biya maku buk'atunku ko,ita dije yanzu ai saidae ma tasa ayi don babba ce ita,ta jima tana aikin gashi har ta iya allura ciwo ma in bai tsanani ba tana fad'in maganin da za'a ba mutum.... " fatuu ta katseta"har k'arin ruwa ma tana sa ma mutane"hajiya ta jinjina kai"to kin gani,ai dije akwae kwazo", Juyawa tayi ta kalli haisam dake danna wayarsa ya d'an kishingida hadi da mikar da kafafunsa saman kujeran sai kuma ta saci kallon hajiyan ganin ta maida hankalinta kan tv yasa ta mik'e taje gabanshi a hankali kaman mai rad'a tace"in kawo maka fruit d'in?" ba tare da ya kalleta ba ya d'aga mata kai alamar eh,juyawa tayi ta nufi hanyar kitchen,sai da ta bud'e freezer ta fiddo ledan kafin ta shige cikin kicin din,a saman plate mai dan fad'i ta jero mashi bayan ta cire bawon su ta yayyanka amman bata yanka Apple d'in ba,yadda ta jera su sunyi gwanin sha'awa. Gefen kujeran da haisam yake ta aje kafin ta juya ta kinkimo sofa table hakanne yajawo hankalin hajiya kanta ta bita da ido ganin abunda take,gaban Haisam ta aje table d'in ta daukko plate din fruit din ta d'aura,fuskarta d'auke da d'an murmushi bayan ta mik'e tace"Yaya handsome gashi nan"sai lokacin ya juyo ya kalli fruit din kafin ya d'aga kai ya kalleta shima murmushin yayi ahankali yace"thanks", hajiya da ta saki baki tana kallonsu tace"ina aka samu fruit ko Tk ya dawo ne?shi naba sakon ya taho dasu d'azun da nace Saude ta had'a man fruit salad take sanar dani sun k'are", juyowa fatuu tayi ta dawo wurin hajiyan ta zauna"ba shi bane wannan na Yaya handsome ne", "toh yaya handsome kuma?" hajiya ta tambaya,kai fatuu ta daga mata alamar eh,juyawa tayi ta kalli haisam wanda gabadaya hankalinshi na akan wayansa da alama chatting yake sai faman Murmushi yake tace"kai ka zo da ftuit dinne?" Kafin ya bata amsa fatuu ta amshe"ni na kawo masa abun ciwo ne,baki ga bai lpy ba" da mamaki hajiya ta kalleta"ke kika kawo masa?" jinjina mata kae fatuu tayi alamar eh sai kyakkyafta idanu take hajiya tace"daman kinsan Haisam ne?", "Eh mana baki ji har sunanshi na fad'i ba" dan ta6e baki hajiya tayi sai kuma tace"amman baki ta6a ceman kin sanshi ba,shi dae nasan magana bata dame shi ba daman ba lalle ya fad'a man ya sanki ba..." da sauri fatuu ta tari numfashinta"to nima ai ina da sirri ko" bud'e idanu hajiya tayi cike da mamakin maganar fatuu tace"ah lalle kam ni shaida ce,amman yaushe kika san ya samu raunin ne?naga jiya da dare ya hadu da tsautsayin" wuki wuki da idanu fatuu tayi ganin kaman hajiyan nason ganota,turo baki tayi tace"kai hajiya bafa kyau zurfafa bincike nasan kin sani,nace maki na sanshi baki ji ma yaya nike ce masa ba,ai d'azun bayan na dawo boko nazo shine naga bai lafiya to ban shigo nan ba saboda lokacin islamiyya yayi shine fa na tafi" jinjina kae hajiyan tayi alamar gamsuwa, Kallon Haisam tayi ganin hankalinshi na akan waya bai shan fruit din tace"Yaya handsome kasha mana" ta6e baki hajiya tayi"uhmm karma ki wahalar da bakinki...." maido idanunta tayi kan hajiya"bai shan fruit ne?"ta tambayaa, "Yana sha amman shi fa komae sai an matsa masa yake ci kaman wani k'aramin yaro,kwata-kwata baison cin abinci ina ga dae tsukakkun yan hanji ne dashi" zaro ido fatuu tayi ta juya ta kalleshi har lokacin idonsa na kan wayar tamkar bai jin abunda ma suke cewa,hajiya taci gaba"kinga dae yadda yake k'ato tubarkallah, kamata yayi ace yana cin abinci hannu baka hannu kwarya,amman sam baison cin abinci k'irar tasa duk bogi ce ta k'arfe ce,yanzu fa inda zai sha fruit dinnan to wllh kina iya ganin ba lalle ya k'ara cin wani abu ba da daren nan,k'ilan sai dae ko tea da biscuit ko snacks,yafa iya yan ciye ciye maras amfani shi ga bature", ta k'arasa tana turo baki, daman rashin cin abincin nashi na damunta,ita kam fatuu tsura mashi ido tayi tana tunani cikin ranta"ashe abubuwan da ya bata d'azun sune abincin shi bai son cin abinci.."ji yayi ajikinshi idanu na yawo akansa hakan yasa ya juyo ya d'an kalleta tana ganin sun had'a ido tayi masa alamun ya sha fruit d'in da hannu tana yamutsa fuska,wani kallo yayi mata mai kama da harara ya juya yaci gaba da lallatsa wayansa. A hankali yasa hannu ya d'auki Apple d'in ya kai bakinsa ya gatsa,lokaci guda fatuu dake kallonshi ta saki Murmushin jin dadi dama tasan zai so Apple d'in tunda shi d'an gayu ne shiyasa ta matsa sai da mai kayan marmarin yasa dashi,juyo idanunsa yayi ya kalleta, washe baki tayi tana dariya hakan yasa ya d'an mata side chuck kafin ya mayar da kanshi kan wayar yana ci gaba da cin Apple d'in, "U have a message" Haisam ne yayi maganar,juyowa hajiya tayi tace"sak'on mi?" batare da ya bata amsa ba ya d'an d'aga mata wayarshi lokaci guda wata zazzakar murya ta fara magana,_"Hi Granny!how are u,kin manta dani ko?"_ daga yadda mai muryan tayi magana da hausa zaka fahimci hausar tata bata nuna ba sosae, lokaci guda hajiya dake kallon haisam ta washe baki tana fad'in"Allah sarki Fanan,ai in dae na manta dake na manta da kaina kenan,kira man ita don Allah in wanke kaina" sauke wayan yayi ya fara kokarin kiran fanan d'in,tana fara ringing haisam ya kalli fatuu yayi mata alamar tazo ta amshi wayan ta mik'a ma hajiyan,tasowa tayi ta kar6i wayan kaman yadda ya mata umarni,hajiya na amsa aka d'aga kiran suka fara waya da Fanan din, A hankali fatuu ta mik'e ta nufo wurin da haisam ke zaune,tsayawa tayi daga gefe tana kallonshi had'i da yin d'an murmushi,hannu yasa ya daukko ayaba yakai bakinsa yad'an gatseta kafin ya d'ago idanunsa ya kalli fatuu dake atsaye,sauke kafansa guda k'asa yayi d'ayar kuma mai ciwon ya mik'ar da ita kan kujeran,kallonta ya sake yi yace"Seat" a hankali ta zauna d'ayan 6arin kujeran ta d'aura hannunta d'aya kan hannun kujeran tayi tagumi dashi har lokacin da Murmushi akan fuskarta,ci gaba da shan fruit din yayi idonsa akan tv can suka had'a ido da ita,ganin tana ta kallonshi ne yasa shi tunanin ko fruit d'in take so ne,ita kuma yadda yake sha ne abun yayi mata dad'i tayi zaton ba zai sha ba kaman yadda hajiya tace, d'aukko plate d'in fruit din yayi ya aje agabansa ta yadda ya kasance atsakiyansu kenan,kallonta yayi a hankali yace"eat"da sauri ta girgiza mashi kai"ni da na kawo maka kuma sai in shanye ma" yar harara ya wurga mata"what did i told u yesterday?ba nace in nace kiyi abu ba kawae kiyi"ganin yadda yayi mata maganan yasata saurin cewa"yi hakuri to"hannu takae ta d'aukko 6allin kankana ta fara sha tana satar kallonshi,shikam hankalinshi na kan tv,duk wannan abun hajiya na akan waya sai faman hira suke da Fanan din da aka kira mata, Hannu fatuu ta kai zata d'auki fruit carab Haisam yaji ta kama yatsan hannunshi,da sauri ya kae idonshi kan hannunta dake ruke da yatsan nasa,da mamaki ya d'ago ya kalleta sam hankalinta na akan tv da ake Indian film,batama san ta kama yatsan nasa ba,jan yatsan ta fara duk a tunaninta fruit d'inne,jin yaki daukuwa yasa ta juyo takai idonta kan fruit din,zaro ido tayi ganin ta kama yatsan Haisam,da sauri ta saki ta dago suka had'a ido dashi a rude tasa tafin hannun damanta ta rufe baki tana girgiza masa kae alamar batasan tayi ba,cire hannun tayi tana kokarin yin magana ya dakatar da ita da hannunshi,cigaba yayi da shan fruit din yana kallo,ganin haka yasa itama taci gaba da sha tana kallon sai dae duk in zata dauka sai ta juyo ta kalli fruit d'in gudun karta k'ara ruke masa yatsa, Juyowa hajiya tayi bayan ta gama wayan ta kallesu, mamaki ta shiga yi cikin ranta na yadda akae suka san juna haka,shidae haisam tasan ba mai shiga harkar mutane bane balle kuma yarinya kaman fatuu,tunowa da halin fatun na sam bata jin magana kuma bata da shariya sannan tana da saurin shiga ran mutum yasa ta kawar da mamakin, "Abun yar wariyar launin fata ce kenan" hajiya ce tayi masu maganar,juyowa fatuu tayi ta kalleta tana dariya hajiyar taci gaba"wato don kun ganku farare shiyasa ni bak'a aka ware ni ko"sosae fatun ke dariya,shima haisam d'in da idonsa ke akan tv d'an murmushin gefe yayi jin abunda hajiyan ke cewa,fatuu tace"ai akwae saura a kitchen in kawo maki ne?" kafin hajiyan ta bata amsa haisam ya maida dubansa kan fatuu da ta juyo ta kalleshi tana dariyar maganar hajiya"d'auka kikae mata" da sauri tace"da gaske fa akwae saura bari in..." katseta yayi"ki kai mata wannan na koshi" sukuku tayi da fuska ganin haka yace"zan sha sauran anjima" yayi maganar idanunsa ad'an lumshe,mik'ewa tayi ta dauki plate din ta nufi wurin hajiyan, "Sauranku zaku ban in sha don kun raina ni ko" d'an murmushi fatuu tayi"to ai shi yace in kawo maki ya koshi"ta aje plate din a gefen hajiyan itama ta raku6a gefe ta zauna,hannu hajiya takai ta fara shan fruit din,itama fatun tasa hannu zata ci gaba da sha,da sauri hajiya tace "a'a sauran ma bazaki barman ba,ke baki koshin bane?"dariya fatuu tasa ta jingina kanta da kujeran,atare suke shan fruit d'in suna kallon Indian film d'in da ake a Bollywood da alama yana masu kyau ne, Haisam ne ya fara k'okarin gyara kafarsa mai ciwo jin ta sage masa,hakanne ya jawo hankalinsu kanshi, "Sannu kabi a hankali" hajiyace tayi maganar,d'aga mata kai kawae yayi taci gaba da magana"ni wllh har yanzu mamakin yadda ka taka wai kwalba nike,muda ko lemun kwalba bama amfani dashi,in kaga kwalba a gidan nan sai ta turare ko tasu salad cream su kuma wannan dama iyakarsu cikin kicin ne,da sun k'are kuma sai cikin dustbin amman sai gashi wae ka taka kwalba a part d'inka,abun ya d'aure mun kai,wae ko dai ka fita waje ne?" ta k'arasa maganar idonta akan haisam tana jiran ya bata amsa,fatuu kau gaba d'aya ta zaro idanu ganin kaman hajiyan nason gano gaskia, da sauri fatuu tace"a...ai hajiya k'ilan a k'asan take fa"a rude tayi maganar, "taya hakan zai yiwu bacin harabar part d'in nasa interlock ne,bafa k'asa bace balle ace kwalbar ta shige ciki ne" sosae gaban fatuu yake bugawa"ai ko shi d'in kwalbar zata iya shiga..." hajiyar ta katseta"bulo ne fa fateema" duk maganganun da suke Haisam d'in na jinsu don yana niyyar yaba hajiyan amsa lokacin da ta tambayeshi fatun ta rigashi yin maganar shiru yayi yana sauraransu idanunsa akan tv,so yake yaji yadda zata fidda kanta, Fatuu taci gaba"ai a bulonma kwalba na mak'alewa" hajiya tace"kai fateema anya kuwa,su masu yin bulon har basu gani ba lokacin da suke yi su cire" fatuu dake ta zare ido tace"to ai ba inji bane yake kwa6a masu simintin da yashin ba,ai ba lalle fa su gani ba,ni nasha ganin kwalba ajikin bulo a gidajen da ake ginawa a hanyar islamiyyarmu" cike da al'ajabi hajiya ta ruke ha6arta"kuma fa hakane wllh,dama kinga part d'in nasa sabone kafin ya dawo akulle yake,ko ada in yazo kafin ya dawo nan,acikin nan yake zama,yanzu saboda zai dade ne aka idasa gina can d'in.."fatuu dae sai gyad'a kai take,hajiya taci gaba"aikuwa bari zansa Tk ya samo almajirai abi k'asan part d'in nasa adudduba inma akwae saura su cire saboda gaba kar ya k'ara takawa..." fatuu ta kar6e"haka yakamata nima zan tayasu aduban", "Yauwa haka kawae za'ayi ma..." hajiya bata k'arasa maganarta ba sakamakon sautin yar dariyar da haisam ya saki,abunda ya bashi dariya shine yadda yarinya k'arama ta zauna tana mata wayo, "kaji wulakanci muna tattauna yadda zamu kare lafiyarsa yana mana dariya" Hajiya ce tayi maganar idonta akan haisam,d'an juyowa yayi ya kalleta suka hada ido tace"mu kake ma dariya don mun damu da lafiyarka" d'an girgiza mata kai yayi"baki ga ina kallo bane",ya kai idanunsa kan fatuu bayan yayi maganar,tayi wuki wuki gaba daya tayi kalan rashin gaskiya,wani kallo yayi mata da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa kafin ya ci gaba da kallonshi, "Fateema yakamata kizo ki tafi gida dare yayi sai kuma Allah ya kaimu" hajiyace tayi maganar idonta akan agogon dake parlon, "Ni yau nan zan kwana" ta ba hajiyar amsa,kallonta tayi"amman dae kinsan gobe akwae makaranta ko,ki bari ran juma'a in Allah ya kaimu sai kizo nan kiyi weekend ma tunda ita islamiyyar bada sassafe ake zuwa ba" turo baki tayi tana niyyar yin magana haisam ya jefo mata wani kallo nan da nan taja baki tayi shiru,dama abunda yasa tace anan zata kwanan saboda ta kasa ta tsare don kada ta gano gaskiya,jiki a sanyaye ta mik'e zata tafi,hajiya tace"gashi ko abinci ma baki ci ba,mun zauna munata zance....", "na koshi"ta fada fuskarta a yamutse, "A'a bari dae a zuba maki ki tafi dashi in ke bazaki ci ba ai Dije da Amadu sa ci" tana kai maganar ta juya tana kwala ma Saude kira,fitowa sauden tayi ta nufo cikin parlon hajiya ta dakatar da ita"ki zubo ma fateema abinci cikin kula"amsawa sauden tayi da to ta juya ta nufi kicin,sai lokacin fatuu ta tuna da jakarta dake a d'akin sauden taje ta daukko,lokacin da ta fito sauden ma ta fito daga cikin kicin wurin fatun taje ta mik'a mata,amsar kular abincin tayi ta rungume a hannunta d'aya,gudan kuma yana rataye da jakarta,daga haka ta dawo cikin parlon kallon hajiya tayi"sai Allah ya kaimu hajiya", "To fateema Allah ya tashemu lafiya,ki gaida dije",kai kawai ta d'aga mata,hajiya ta maida kanta kan tv,juyawa tayi ta kalli haisam da idanunsa ke kan tv shima"Yaya handsome sai da safe" jinjina mata kai yayi batare da ya kalleta ba,ba haka fatuu taso ba,so tayi ya kalleta don ta k'ara rokonshi akan karya fad'a ma hajiyan, Hanyar fita daga parlon ta nufa tana yi tana waiwayen haisam wai ko zai juyo amman har takae bakin kopan bai juyo ba,tsaye tayi tana ta kallonshi ta kasa fita,kaman yaji ajikinsa ne yasa shi waiwayawa ya d'an kalli kopan fitan,da sauri fatuu ta aje kulan abincin ak'asa ta had'a hannayenta ta fara rokonshi tana magana kasa kasa had'i da jujjuya kanta,still yayi yana kallonta fuskarshi a sake kaman zaiyi murmushi,suna cikin haka hajiya ta juyo da niyyar yi mashi magana,ganin inda yake kallo yasata juyawa ta kalli bakin kopan karaf idanunta suka sauka akan fatuu,cike da mamaki ta furta"Fateema......."aikuwa da sauri fatun ta d'auki kulan ta fice. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* _Gashi nan 2 pages ne,ku da update sai Next week in Allah ya kaimu kar inji wani yace yau ba'a posting ne,within the Weekend🤨_ *3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣* Da sauri Fatun ta d'auki kulan ta fice,maido idanunta tayi kan haisam da shima ya d'an kalleta kafin ya mayar da idanunsa kan tv,kanta ne yai matuk'ar d'aurewa,tunanin anya ba wani abu suke 6oye mata ba ta shiga yi,tasan halin kowannensu sarai shiyasa tun farko tayi mamakin ganin suna shiri sosae, "Haisam" hajiya ta kira sunanshi,juyowa yayi ya kalleta ba tare da ya amsa ba,taci gaba"mike tsakaninka da fateema ne?" d'an guntun murmushin da iyakarsa kan lips dinsa yayi"kinji ki da wani magana sweetheart mike tsakanina da ita fa..." katseshi tayi"ina nufin ya akai kasanta,ko tayi ma wani abunne don nasan halinta bata jin magana,kuma naga kaman kuna 6oye man wani abun" shiru haisam yayi yana tunanin ko ya fad'i mata kawae don ta san halin da ake ciki agame da yaran da yasa aka kama,yasan dole zata fi shi sanin abunda ya akamata ayi dangane da case din don ita aikinta ne, Ganin yayi shiru yasa hajiya fad'in"talk to me haisam ka kafe ni da idanu,da akwai wani abu ne???" kai ya d'aga mata alamar eh,kafin a nutse ya soma magana"I first saw her On Thursday when i was Coming back frm Work........"nan take ya kwashe duk abunda ya faru tun ranar daya fara ganin fatun har zuwa jiyan"tunkafin ya rufe bakinshi hajiya ta shiga zabga salati,hannuwanta duka biyu dafe da kirjinta"innalillahi wainna ilaihir rajiun,hasbunallahu wa'niimal wakeel!!yanzu fateeman ce jiya mutum ukku suka kusan hakke mata?"cike da tashin hankali tayi mashi tambayar,lumshe ido yayi alamar eh, "Kai jama'a wannan masifa dami tayi kama ni Hauwa'u,rape cases everywhere,everyday,fyade dae fyade dai,duk gargad'in da ake ana fadakarwa a banza kaman ma ana tunzura mutane" cike da takaici take maganar ci gaba tayi"Amman fateema bata yi wayo ba,wannan sakarci har ina,ina ganinta kaman mai wayau bazata bari a cucetaba ashe doluwa ce" sigh haisam yayi"tace Guy din wae bai ta6a ko ruke mata ko hannu ba shiyasa bata yi tunanin zai cucetaba", Tsoki hajiya taja"sakarci dae kawae,wannan har hujjace da zata sa tabi shi kango karfe goman dare bacin tasan bashi kadae ke yin shaye shaye a wurinba kuma don bai ta6a ruke taba ai baikamata shima ta yarda dashi ba tunda tasan halinshi sarae daya samu dama zai iya cutar da itanne..."kwafa tayi kafin taci gaba"zata zo ta same ni ne,wato shiyasa ta zauna tana ta tsaran zance ta maida ni shashasha....harda cewa wani nan zata kwana,haba nifa wllh nayi mamakin ganinku tare don nidae nasan ba saninta kayi ba", Sauke 6oyayyar Ajiyar zuciya haisam yayi"ina ganin ki kyaleta kawae...."da sauri hajiya ta tari numfashinshi"ta tafka wannan rashin wayon amman kace wai a kyaleta...", "No kingane,duk wani abu da yakamata afad'i mata don ta kiyaye gaba i hv done dat,kuma nasan bazata k'ara yin makamancin hakan ba tunda nace mata nasa shi a yarjejiniyar glass da ta fasa man and kinga tana tsoron ki sani hakan zaisa ta k'ara kiyayewa sosae", Cike da takaici hajiya tace" Fateema bata jin magana wllh,kar kaso kaga yadda kakarta Dije ke k'okari akanta,ni kaina nan kullum cikin yi mata fadan ta daina rashin ji nike,yanzu ina amfanin hakan,sannu kaima kayi Babban taimako,Amman ka tabbatar dae basu cutar da ita ba?ko dae akaita asibiti ne??"Hajiya ta tambayeshi fuskarta a yamutse,Al'amarin ya Matuk'ar tashi hankalinta, D'an girgiza kai yayi"gaskia basu yi mata komae ba,kawae dai sunyi tying Bakinta da Hannu so tana ta basu wahala don naji wani cikinsu yana magana kan hakan lokacin da naje,Da sunyi matan ma i think da ba'a ganta haka ba", jinjina kai Hajiyan tayi"yanzu wani mataki kake ganin ya dace a daukar masu?" gyara zama Haisam yayi"shiyasa ai na fad'i maki don ke aikinki ne,d'azun da Sp khamis ya kirani ya sanar dani sunyi arresting nasu gaba daya so suna bukatan akai ita Zarah station d'in,na sanar dashi sai zuwa Friday lokacin kafana ya k'ara warkewa yace ba matsala"Jinjina kae tayi"shikenan before then zamu yi magana" "Ok,amman shi guy din kin sanshi?", "Uhm sani kam,ai Ashirun babanshi d'aya daga cikin limaman masallacin gidan nan ne malam tanimu,ko last da aka kamashi akan case d'in sata ni nayo mashi belinshi,amman yanzu ai ba batun insa kaina tunda wannan babban Case ne,shi kuma tanan Allah ya jarabeshi,Allah ya shirya mana zuria", "Ameen" haisam ya amsa,Saude ce ta k'araso cikin parlon,A gefen kujerar da hajiya take ta tsaya"Hajiya na gama shirya table tun d'azun,kai kawae ta d'aga mata alamar toh,juyawa tayi ta kalli haisam"ka tashi kaje ga abinci can kaci dare nayi"har lokacin fuskarta akwae alamun damuwa, "Ke bazaki ci abincin ba" haisam dake kallonta ya tambaya,"kaje zan taso"mik'ewa yayi ya nufo wurinta,agabanta ya tsaya"C'mon,Stop Worrying ur Self,taso muje kici abinci"ganin tana niyyar yi masa gardama yasa shi sa hannu ya sunkuceta sai kace ya dauki k'aramar yarinya,hajiya na bugun hannunsa tana ya sauketa amman saida ya kaita har Dining area din. _______________ Ranar laraba da yamma gwaggo zaune atsakan gida saman tabarma tana jiran lokacin magrib ya k'arasa yi fatuu ta shigo da gudu,a gefen kopar zauren ta aje jakar islamiyyarta ta nufi toilet,girgiza kai gwaggon tayi a fili tace"Allah ya shirya"fitowa tayi tana gyara wandon uniform din islamiyyar jikinta ta d'auki jakarta kafin ta nufo cikin gidan,fuskarta d'auke da dariya tace"sannu da gida kakus"ta6e baki gwaggo tayi"yauwa"daga haka ta juya zata shiga daki,"in kin cire kayan islamiyyar ki fito in gyara maki kanki,zuwa gobe in sha Allah tunda ba islamiyyar sai in kitse maki shi"amsawa tayi da toh kafin ta shige dakin,bata dade ba ta fito jikinta sanye da doguwar rigar material kanta ba kallabi, "Ki shiga cikin dakina ki dauko masharci da mai" gwaggo tace mata, A saman tabarmar ta kwanta ta d'ora kanta saman cinyar Gwaggon,warware fakin d'in da akai ma gashin gwaggo tayi ta shafe gashin da mai kafin tasa comb ta fara taje mata,duk yadda take bi a hankali amman fatuu sai cije baki take tana k'orafin zafi can tace "gwaggo tun da dadewa kika ce zaki ban labarinki amman har yanzu kinki ki bani"yar dariya gwaggo tayi"to ke miyasa kike son jin labarina,ba kinsan garinmu da yan'uwana ba...", "Amman ai bansan su waye iyayenki ba ko,kawu shi6ado na Daura kawae nasani da matansa da ya'yansa sai wasu dae yan'uwanki yan kad'an"gwaggo da har lokacin fuskarta ke d'auke da Murmushi tace"to ai na fadi maki sun rasu tuntuni ko...", "a ina" fatuu ta katse ta, "Tunda labarin dai kike so bari in baki a takaice,mu Asali Fulanin tashi ne wato masu caccanja wurare,na taso a kudancin kasarnan acan nayi wayo,fad'a tsakanin manoma da makiyaya ne ya rutsa da mahaifina har ya rasa ransa,to a lokacinne kawuna k'anin mahaifina ya dawo damu arewacin kasarnan ta dalilin wani Abokinsa wanda ke kai shanaye can kudun amman ba'a can yake zaune ba d'an nan Daura ne,bayan wasu shekaru da dawowarmu nan itama mahaifiyata ta rasu sakamakon jinya da tayi daganan ya rage bani da kowa sai kawu shi6adon da kika sani na daura....", "amman to ke kad'aice baki da yayye ko kanne?" fatuu ta tari numfashinta, "Ni kad'ae iyayena suka haifa,ina shekara goma sha biyu aka man aure,lokacin wani abokin su kawu ne Bello ya kwallafa rae akaina saida aka bashi ni ba don ina son shi ba amman bani da yarda zanyi,can yankin Safana aka kaini cikin matansa biyu nice ta ukku,matansa suka hade man kai,ba k'aramar wahala nasha ba agidan wannan bawan Allahn k'arshe dae matansa saida sukayi yarda sukae suka sa ya sake ni lokacin shekararmu biyar da aure,to bayan na dawo Daura ne Allah ya had'a ni da kakan ki Abdullahi a kasuwar mashi ina kai tallan nono,farko k'in saurararshi nayi don lokacin tsoron maza nike saboda wahalan dana sha a gidan Bello,daga karshe dae na Amince mashi muka fara soyayya har Allah yasa mukayi aure....", d'ago kai fatuu tayi"Enye su Gwaggo ashe ansha soyayya" harara gwaggon ta wurga mata kafin taci gaba"shi asalinshi bahaushe ne d'an nan katsina wannan dalilinne ya kawo ni katsina shima lokacin yana da mata guda d'aya Habiba,Mutuniyar kirki ce sam bata d'auke ni kishiya ba face d'iya duk abunda zata yima yayanta shi take man,wani lokacinma in taga kakannaku nayi man fad'a in nayi masa ba daidai ba ita ke kwa6ar shi ta rinka cewa baka ganin yarinyace,shekararmu biyu da aure sannan nasamu cikin Innarki bayan na haifeta kuma saida nayi shekara sha biyu har ma na fidda ran sake haihuwan don nayi tunanin nima irin inna tace haihuwa d'aya zanyi sai ga cikin Amadu to tun daga kanshi ne ban sake haihuwa ba kuma yana shekara biyar babansu ya rigamu gidan gaskiya sakamakon had'arin mota da suka yi"d'an dakatawa tayi alamar jimami, "Allahu kakana,Allah ya jikanka da rahama yasa ka huta,yanzu to ina ita Habiban gwaggo" Gwaggo ta amsa da "Ameen,ita ma yanzu kusan shekara bakwae da rasuwarta sakamakon jinya da tayi,sai dae ya'yanta da muke ta zumunci,ai kinsan zaliha ko ta kopar k'aura?" kai fatuu ta daga alamar eh,"to ai diyarta ce,da shehu dake zuwa gidannan..."katseta fatuu tayi bayan ta d'ago kanta"Baba Shehu?"Gwaggo tace"eh shi,to shima d'an habiban ne,yaranta shida", "Allah ya jikansu gaba daya" fatuu ta fad'a, "Ameen" gwaggo ta amsa. Shiru sukae na wani lokaci gwaggon nata gyara mata gashin,can fatuu tace"Amman gwaggo ya akai to Innata tayi Aure a Yola?" fatuu ta tambaya,Ajiyar zuciya tayi kafin ta d'aura"bayan mungama takabar kakanku Abdullahi dole na koma daura don bani da kowa anan,alokacinne kuma kawu shi6ado ya matsa aima Aisha aure acewarshi tayi girma da yawa kuma dae da gaske yake don lokacin duk yankinmu ba babbar budurwa kamarta don shekararta 17 gashi tubarkallah sam jikinta ba irin na ainihin yanmatan fulani bane hakan kuma ya samu asali ne daga mahaifinta da yake cikakken bahaushe dama fuskarta sak shine,yana da kyau da dogon hanci amman baki ne,ita kuma Aisha sai ta daukko haskena don harma ta fini fari sosae kuma batada tsawo ba kuma gajera bace,sannan Allah ya hore ma Aisha kugu tun tana yar k'ankanuwarta ya fara bayyana lokacin da take shekara sha bakwae d'innan in ka kalli kafadunta bazakace k'ugun nata bane don ya bude sosae harda shi kesawa ana ganin tayi girma da yawa,kema naga alamun jikinta ne zaki daukko don sam baki da tsawo gaki nan yar dumurmur...."kyalkyacewa da dariya fatuu tayi"kice nima zanyi hips,ai kaman ma ya fito fa,innasa skirt yana nunawa, Allah shiyasa nike son sa skirt", Yar harara gwaggo ta wurga mata kafin ta d'ora"lokacin da ake ta maganar ayi mata aure ita bata so karatu take son taci gaba da yi don a katsina tana makaranta harma ta shiga Sakandire,amman fir kawu shi6ado yace baisan zancen wani karatun nasara ba,kan kice mi samari sukayo mata ca bayan komawarmu amman ita bata son kowa ganin tak'i fiddo miji ne yasa kawu yace shi zai za6a mata duk wanda yayi mashi,ana haka sai ga Muhammadu wanda abokin wani yarone makwabcinmu shi kuma yaron abokin dan wajen kawu ne,Muhammadu Dan jahar Adamawa ne,manyan kasuwannin yankin Katsina suka fara kawu shanaye to shine ya fara sauka a wurin abokin yaron kawun dama kuma yan uwansu ne,yana ganin Aisha Allah yasa mashi sonta itama kuma ta amince dashi don tubarkallah ko ni lokacin na yaba dashi ga kyau ga biyayya ba 6ata lokaci akayi bikinsu,to kinji yadda mamanki ta auri baffanki,bayan shekara guda da auren ta haifi yayanki Kamalu nayi murna sosae ganin ba'a dau wani lokaci ba,Kamalu na shekara ukku ta Haifeki kar kiso kiga Murnar da nayi don na fahimci ita bata gado ni ba,ashe duk salesalin Ajali ne....",dakatawa gwaggo tayi fuskarta a yamutse, "Kina shekara ukku Allah ya kar6i ran Aisha,ba lokacin aka fara man mutuwa ba amman naji mutuwar Aisha nayi kuka su kenan gareni su biyu ita da Amadu,ba yarda banyi ba alokacin amaido man ita nan amman sai kakanki ardo ya hana yace wai ba ciwon Asibiti bane to sanin Aishar nada iska ne yasa na amince da Maganarshi ashe ashe cutace kunshe acikinta....", Dan ta6e baki fatuu tayi kaman zatayi kuka"Allah ya jikan mamata yasa tana Aljanna"gwaggo ta amsa da Amin ya Allah,kafin ta d'aura"Aisha ba ruwanta tana da halin kirki,har yau ina jin radadin mutuwarta sai dae ba yadda zanyi Allahn daya fi ni sonta ya d'auke abunshi,Wani lokacin sai inta ganin hada sakaci yasa ta rasu,da tun wuri an kaita asibitin angano cutar dake damunta k'ilan da ta rayu,amman Wannan nasan kawae rudun shaidan ne,ko ankaitan in Allah ya k'addaro a ciwon Ajalinta yake nasan dole sai ta mutu,baffan ki ma yaji mutuwarta wllh don yana son Aisha duk soyayyarta ce ya maido kanki,tun lokacin da ta rasu naso ya bani ke,amman duk kunya irinta fulani haka ya dinga rokona yana hawaye akan na barki acan,lokacin duk da halin da nike ciki ya bani tausayi hakanne yasa na kyale mashi ke kawae don nasan zai kula dake yadda ya kamata," Dago kai fatuu tayi"to gwaggo ki k'ara yin aure mana ba sai ki haifi wasu yaranba"harara ta wurga mata,fatuu ta fashe da dariya"Allah gwaggo baki tsufa ba sosae da anyi maki makeup aka nad'a maki gwaggwaro zaki koma kaman Yar budurwa,kinga sai muyi baba anan gidan",banza gwaggon tayi mata, "Amman to ya akai kika dawo nan garin?", "wai tambayoyin na miye fatuu,sai kace wata yar Jarida komai sai kin sani", "Don Allah ni dae ki fad'a man,kinga ko tambayana akae watarana nasani", "Akwae wani d'an uwan kakanki likita ne sunan shi Doctor Kabeer anan katsina yake,to watarana muka kawo mashi ziyara daga Daura ni da Amadu lokacinne yayi mun tayin aiki yace in inaso zai samarmun don insamu abunda zanci gaba da kula da rayuwarmu,nayi matukar farinciki nan take nace mashi inaso na bashi duk wani bayani da yake bukata,bayan komawarmu da yan kwanaki sai gashi ya kirani ya sanar dani nasamu aikin,lokacin da nazo na iske shi yake tambayata ya na tsara fara yin aikin don bai yuwuwa ince zan rinka zuwa daga daura nan nake sanar dashi zan samu gidan haya in zauna,sai yace in ba damuwa to in fara zama a gidanshi kafin wani lokaci,nan nayi ta mashi godiya naji dadi sosae,cikin sa'a na fara zuwa aikin lokacin Amadu nacan daura amman duk cikin sati sai nasamu lokacin dana je na duba shi,da tafiya ta fara mikawa sai na fara fuskantar matsala da matarshi Rukayya Wanda farko ba haka take mun ba muna zaman lafiya tana jin dadin yadda nike kama mata ayyuka da yake itama lokacin tana aikin koyarwa,amman daga baya duk irin hidiman da nike mata bata yabawa,don lokacin indai banje Aiki ba nike share mata gida,inma yaranta wanka har girki yi mata nike amman duk da haka sai tayi ta wani shan kunu gashi tayi ta nuna man iyaka da wasu abubuwan nasu Abinci ma sai in dafa amman iya wanda taga dama zata zuba man,ta hana yaranta guda biyu Mace da Namiji zuwa wurina da kuwa haka zasu zo muyi ta hira ina masu wasa har Assignment dinsu suke zuwa dashi suyi d'an abunda na sani in fad'i masu dayake lokacin na d'an iya karatu don lokacin da Aisha ke karatun boko tana koya mun,wata rana mai gidan ya aiko wani yaro lokacin tana a d'aki tayi bakuwa,wata aminiyarta ce tazo shine na nufi dakin don in sanar mata sai naji suna wata magana da ta d'aga man hankali,wai ashe dama kawartata ce ta zugeta take man abubuwan da take man alokacin,taci gaba da zugata tana fad'in"yanzu kike yin abunda ya kamata,don wllh da kinyi sake sai dae kiji ana shafa fatiharsu tunda ba wasu shekarune da ita sosae ba gata da kyan jiki,yanzu kamata yayi ki fara yi mata kora da hali har ta gaji ta tattara tabar gidan" jiki a sanyaye na shiga na fad'i mata an aiko wani,daga haka na fito suna bina da wani irin kallo..."dan dakatawa gwaggo tayi tana sauke numfashi, "Tun daga ranar na fara tunanin barin gidan don kuwa kora da halin ta fara yi man,in suna kallo ita da yaranta dana shiga zata kashe kayan kallon tace kallon ya isa,haka zan fito Jiki a sanyaye,duk wannan abun Dr bai sani ba don bata yi man wulakancin agabanshi,watarana ina zaune a d'aki da daddare inata tunanin yadda zan bar gidan ba tare da Dr din ya tuhume ni ba don banson in haddasa masu fitina,can na tuna da wata tsohuwar gona da muka gada ta marigayi kakanku dake can gefen gari wanda alokacin inda gonar take ya d'an fara shigowa cikin gari don akwae yan gine ginen gidaje da aka fara yi a wurin,gari na wayewa na tafi daura wurin kawu shi6ado don kar6o wasu kudadena dake awurinshi anan nake sanar dashi inason zan gina koda d'aki daya ne a wannan gonar in koma,ya tambayeni dalili na kwashe komae na fad'i masa nan take ya goyi bayana yace daman bai kamata in yi masu zaune agidansu ba,shima ya k'ara man kudi na had'a harda na aikina dana d'an tara,ta hanyar wata Abokiyar aikina na samu wadanda suka gina man daki daya da kewaye aka kuma katange gidan,sai da aka gama ginin nasamu Dr kabeer A asibiti na sanar dashi cewa zan koma gidan,anan yake tambayana ko anyi man wani abu ne,nace mashi a'a inason zan daukko yaro nane nasa shi a makaranta to banson na k'ara d'aura mashi nauyi ne gana iyalinshi kuma,ya fahimce ni sosae yayi man fatan alkhairi ya kuma bani kudi masu yawa wanda zan sa Amadun a makaranta,Matar Dr na Zaune a falo ita da yaranta ba zato ba tsammani ta ganni d'auke da jakar kayana nayi mata godiya na sanar da ita zan bar gidanne daga haka nayi mata sallama na fito yaranta nata yi mun bye bye harda yar kwallarsu,wannan shine dalilin dawowata wannan gidan da muke zaune", "Lokacin dana dawo na d'an shishshiga makwabta don agaisa in kuma gabatar masu da kaina amatsayin sabuwar makwabciyarsu,alokacinne nashiga gidan Hajiyar Sanata wanda ada bai kai yadda yake yanzu girma ba da k'ayatuwa,hannu bibbiyu ta kar6e ni ba kamar da ta ji ni yar daura ce don itama Asalin yar can ce tana ma da dangantaka da Masarautar Dauran,daga nan muka fara zumunci da ita sosae tamkar uwa haka na dauketa don ta haifeni,koda na daukko Amadu nasashi a makaranta kusan duk dawainiyar karatunshi ita keyi,banda damuwar inda zan barshi in zan tafi aiki don da ya dawo bannan zai tafi gidan hajiya daga baya tukur ya zama d'an gidan suka fara abota tare ma suke tafiya makarantar allo da yamma,rashin sa Amadun makaranta da wuri ne yasa tukur d'in ya wuce shi don duk tsararraki ne amman Amadu ya dan girme mashi,kinga shi tukur yanzu yana makarantar gaba da Secondary shikuma Amadu har yanzu a sakandiren yake,A hankali ahankali da Kud'in da nike samu na albashi naci gaba da ginin gidan nan har yanzu ya koma haka,to Hajiya Fatuu yar Jarida,yanzu kinji komae ko?" Kyalkyacewa da Dariya fatuu tayi tace"Amman wannan matar Dr din shegiya ce,daman kin Aure shin muga yadda zata yi,Oh da yanzu muna gidan Dr shine kakana kuma kinga da cikin sauki zai taimaka man in zama likita,Allah ya isa na matar Dr",Dariya gwaggo tayi tana girgiza kai jin shirmen fatuu"bana hana ki zagi ba,ni sam banga laifinta ba wllh kishi take akan mijinta ba wani abu ba,duk da hakan bai hana ayi mata kishiyoyin ba har ma guda biyu,yana nan yanzu shi Medical Director ne", Fatuu tace"Allah ya kara,yasa ma ya cike ta hud'un",girgiza kai kawae Gwaggo tayi, Hannu fatuu ta kai ta shafo kanta da sauri tace"Gwaggo ya naji kamar kina man kitso kuma", "Eh wai in rage hanya,bana fulani kika ce kina so ba,na gaban ne nike yi maki goben in Allah ya kaimu sai in k'arasa maki",kai fatuu ta daga alamar toh, Shiru sukae na wani lokaci kafin fatuu tace"Gwaggo kinsan Yaya Handsome?", "yaya Handson kuma wani abu ne hakan?" gwaggo ta tambaya,kyalkyacewa da dariya tayi"kai gwaggo mutum ne fa,d'and'an Hajiyar Sanata nike nufi fa" ta6e baki gwaggo tayi"Haisam dinne wani handson,kuma waya fad'i maki d'and'an Hajiya ne,ke ko fadi maki akae ita ta haife shi kya yarda,Jikanta ne,Senator d'in da kika ji ana cewa shine d'an hajiyar shikuma Haisam d'an Senator dinne",waro ido fatuu tayi"haba ashe shiyasa kwata kwata basu kama,ni wllh dana ganshi zaune Agidan nayi zaton danta ne ashe anko muka yi dashi shima kakarshi ce ita", "Itama Hajiya yaranta biyu a Duniya,amman ita ba kamar ni ba tana haihuwar kawae tana samun matsala ta yawan 6ari,wani cikin kuma inta samu har sai ta haihu sai d'an yazo ba rai,to daga baya ma sai aka juya mata mahaifar kawae,Shi Senator d'in shine babban d'an hajiyan daga shi sai Hajiya Maryam tana lagos tana aure Bature ne take aure,Allah cikin ikonsa su duk suna haihuwa sosae shi Senator Ali bansan ainihin yawan yaranshi ba,amman ita hajiya Maryam din tana da yara biyar yanzu,yaranta tubarkallah suma kaman turawan suke don duk farin ubansu suka daukko ga gashi kwayar idanunsu kala daban daban,da suna yawan zuwa amman yanzu sun rage zuwa ita Hajiyar ke zuwa can ta d'an kwana biyu......", Cike da mamaki fatuu tace"Bature mai jan kunnuwa,Gwaggo ina ta same shi har ta aure shin?", "Oho bansani ba,amman kya iya zuwa ki tambayi hajiyan"cike da gatse tayi maganar, "To shi Yaya Handsome d'in Gwaggo waya biyo ne,naga shima kalan yan kasan waje ne", "Senator Ali mai Kud'in gaske ne,Don a yadda naji yafi duk wani Senator d'an Arewa kudi,yana da kamfanoni iri iri har a kasashen dake makwabtaka damu,yana da gidajen Mai,da kamfanonin saida Motoci,Wanda wasu ya gaje sune daga Mahaifinsa,Mahaifiyar Haisam ba yar nan kasar bace Asalinta yar kasar Ethiopia ce...." katseta fatuu tayi"Wace k'asa ce kuma Ethiopia Gwaggo?", "Kasar Ethiopia tana a cikin nahiyar Africa,kinsan akwae nahiyoyi bakwae a Duniya,Akwae Nahiyar turawa,Larabawa,Indiyawa....." da sauri Fatuu ta katse mata hanzarinta"Continent ake cewa gwaggo an yi mana shi a Makaranta guda bakwae ke akwai", "Yauwa to Contilet d'in..." wata Mahaukaciyar Dariya fatuu ta saki"kai Gwaggo wayace maki Contilet yake,kalli bakina kiga yadda nike fad'i,CONTINENT" ta dashe baki tana nuna ma gwaggon, d'an guntun tsoki taja"to ban fad'in yadda kike cewan ki kyale ni da yanda na iyan" Fatuu dake ta dariya tace"Aikam wllh in turawa suka ji ki garkameki zasu yi a gidan yarin kasan teku kije kita cin gabza", "Tunda Sarauniyar Engila na zaga ba" gwaggo ta fad'a fuskarta ad'an daure, "To ci gaba kice Contilet d'in..." a harzuke gwaggo tace"banci gaban", "Haba Kakus,kinsan fa wasa nike don Allah kici gaba da bani labarin Yaya Handsome d'in" ta hada hannuwanta tana rokon gwaggon, "Zanci gaba,amman wllh kika kara katseni na gama"d'aga kai fatuu tayi alamar ta yarda, "Mahaifiyarshi Fateema Fulanin Ethiopia ce,yayin da Mahaifinta yake Balarabe wato Kakan Haisam din na wurin Uwa,a yadda Hajiya ke ban labari Aiki ne ya kaishi kasar Ethiopian har ya Auri Kakar Haisam d'in wadda yar sarauta ce acan,suka haifi Mahaifiyarshi Fateema wadda yan biyu ne su,Wani taron Yan kasuwa ne yakai Senator Ali kasar Ethiopian anan ya had'u da Mahaifiyar Haisam din,shi da Abokinshi suka Aure su ai na fada maki yan biyu ne su,Fateema da Zainab,ita Zainab d'in yanzu haka Mijinta shine Gwamnan Jahar Nasarawa,ita kuma Fateema tana Abuja Gidan Senator Ali,da farko kafin ya zama Sanata din anan Katsina suke zaune a G.R.A,nan yake da katafaren gida,Hajiya ta ce lokacin da ta dawo Katsina don da a Abuja take lokacin Mijinta na Minister a gidan ta fara zama,to lokacin da shikuma zai koma Abuja yaso ta Zauna a Gidan don tace bazata bisu Abujan ba Amman taki acewarta yayi mata girma,shine aka gina mata wannan wanda kusan rabin Unguwar nan duk filayenshi ne da ya saida ma mutane,Allah yasa ma Hajiya kaunar Haisam tunda aka haifeshi Wanda hakanne yasa ta roki abata shi har yayi Primary da k'aramar Sakandire awurinta acan Abuja kafin ta dawo nan ya karasa Secondary d'in anan daganan kuma ya tafi kasar waje yayi Degree dinsa na farko bayan ya gama bai dawo wurinta ba ya fara aiki a Abuja sai dae yana yawan zuwa daga baya ya sake fita wata kasar yayi Degree na biyu shine da ya gama ya dawo nan,to kinji game da Haisam din",ta k'arasa tana kallon fatuu, "Ohh,yanzu nagane dalilin dayasa bai ceman Fateema kamar yadda Hajiyan ke kira na shi saidae yace man Zarah,ashe sunan Mamanshi ne" fatuu tayi maganar tana jinjina kai, "To gwaggo wannan Sojan na d'akin Hajiyan waye shi??" ", kai gaskiya fatuu na gaji da wadannan tambayoyin haba,wannan dama yar Jarida kawae kika zama,shi d'in Mijin Hajiya ne General Adamu Zakee,Asali d'an nan Katsina ne kuma Soja ne tun Zamanin turawa,bayan ya kai matakin janar yayi retire daga nan aka bashi Ministern tsaro wanda yana ruke da mukamin ne ya rasu Sakamakon had'arin Jirgin Sama da ya rutsa dashi anan kasar....."katseta Fatuu tayi"Allahu Aikuwa nasan lokacin da yayi hadarin wll....."bata k'arasa ba sakamakon bugun bakinta da Gwaggon tayi tace"in buge bakin mai karya kawae,Mutumin da ya rasu kusan Shekaru Goma Sha biyar yanzu shine zaki ce wani kinsan lokacin,ashe har yanzu baki daina wannan muguwar k'aryar ba", Turo baki Fatuu tayi"wllh ba karya nike ba,nayi zaton sune suka yi wani had'ari da akace Jirgi ya fad'o a Yola" Gwaggo dake harararta ta ture mata kai"d'aga ni in tashi inyi Sallah anata kira,kinga naso ma ki daka man daddawa wllh gashi har an kira Sallah,yi sauri kiyi sallar sai ki d'an kwankwatsa man ita"Wani kallo Fatuu ta bita dashi ta cuno baki"kai Gwaggo,kai gwaggo,wai an gama hiran yan gayu kuma zaki wani ce a daka daddawa,maimakon kice inje in kama kaza daya a keji in yanka", Ruke ha6a gwaggo tayi"Waye zai wani baki ki yanka masa kaza,ance maki na manta kazan da kika matsa kwanaki in baki ki yanka kika gutsire ma kaine,ba wata kazar da za'a yanka sai Azumi in Allah ya kaimu,Nama dae ai daidai gwargwado ina siyowa,kuma inma tuwo kike tunani zanyi to bashi bane taliyar hausa ce za'a dan 6ararraka"Lokaci guda Fatuu ta washe baki"Yauwa Kakus yanzu naji magana,ni zan dafa to", "To tashi kiyi sallah sai ki dafan"da sauri ta mike jelar kitson da gwaggo ta fara yi mata nata reto agaban kanta ta saukko har wurin kirjinta. Bayan sun gama Sallan a gefen kitchen ta fiddo Gas d'in ta fara dahuwar taliyan gwaggo dake zaune kan tabarma tana nuna mata yadda zata sa abubuwan,lokacin da ruwan ya tafaso gwaggo tace ta d'aukko taliyar a kicin,ta dibar mata wadda zata dafa,fatuu tace"ki k'ara Gwaggo zan kaima Hajiya" ba musu tace toh,sai dae acan kasan zuciyarta ba hajiyan zata kaimawa ba Haisam zata kaimawa,Tashin Sense,Mutumin da Hadaddan Abinci ma bai dameshi ba,shine za'a kaima Taliya mai daddawa,Haisam yaga ta kanshi😂, "Wai nikam ko kin daina rashin ji ne Fatuu? Kwana biyu ba wanda ya kawo man k'ararki inata mamaki wllh", gwaggo dake zaune tayi maganar, Wata yar Isakar Dariya Fatun tayi"Na daina kakus,ance man indae inason in Zama Doctor to sai ma Natsu,don ko inada Kokari indae banda Natsuwa to bazan zama ba", "waye ya fad'a maki hakan" Fatuu tace"Yaya Handsome na gidan Hajiya",jinjina kai gwaggo tayi"Har shima yasan halinki kenan,ai ni da ina fad'i maki hakan shashasha kika mayar dani shiyasa kika ki daukar maganata...."katseta Fatuu tayi"ai shi mai ilimi ne yasan yanda Abun yake"hannu gwaggo tasa ta ruke baki"ni kuma Jahila ce ko shiyasa baki yarda da maganata ba kenan", Fatuu dake Dariya tace"to kice Continent sai in yarda ke mai ilimi ce",Juyawa gwaggo tayi gefenta ta rarumo takalmi ta jefo mata,da gudu Fatuu ta fad'a cikin kicin sauran kad'an ta ham6arar da Tunkuyar Taliyan🤣. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *39⃣* Ta cikin Kitchen d'in ta lek'o da kanta,kitson da gwaggo tayi mata gefe da gefe nata reto"Gwaggo Don Allah kiyi hakuri,Wllh ni bance ke Jahila ba ce,ai nasan kwanaki kinje Makarantar yaki da jahilci kuma har d'an turanci kina ji",banza gwaggo tayi mata tana cigaba da Sauraron Radion wayarta da ta kunna, "Pls Sorry Kakus"Fatuu ta fad'a, d'aga kai gwaggo tayi tana kallon kanta da ta leko dashi,dan ta6e baki tayi,tasan in ba tanka mata tayi ba haka zatai ta mata surutu, "bazaki fito ki duba girkin ba sai ta dafe"jin haka yasa Fatun fitowa daga cikin kicin d'in don ta fahimci gwaggon batayi Fushi ba. *** *** *** *** Hajiya zaune ita da Haisam a parlor kaman yadda suka saba bayan isha, "Tahir ya turo man sako yace naki ne" kallonshi hajiyar tayi"Waye Tahir kuma?wane sako?" "Matsalar kin tsufa da yawa baki gane mutane,Tahir na gidan Mota Kaduna", Dariya Hajiya tasa"Allah Sarki wai Wannan Yaron tahir,rabona dashi tunda ya kawo man waccan 406 d'in kuma mun kwana biyu bamu gaisa ba, kasan Mutane yanzu sunfi gane ma tarkacen chatting d'innan ni kuma ido ba wani isasshen lafiya ba,ban iya inta k'ura ma waya ido shiyasa ba son yin shi nike ba,Miya ce ne?", "Yace sunyi magana da Dad akan Mota da za'a kawo maki shine ya turo pictures ki Za6a" Yamutsa Fuska Hajiya tayi"Ali ho,ni bansan mike damunshi ba wllh", Sai lokacin Haisam ya d'ago idanunsa daga kan Wayar dake hannunsa yace"Mi kuma Dad d'in yayi?", "To wai daga Munyi magana yake tambayana cikin Motoci ba mai Matsala,shine na fad'i masa game da Waccan Vibe d'in da ta lalace yace za'a zo a d'auka,ni ai nayi tunanin gyarota Za'ai kawae Amman shine zai wani ce a turo hotuna in zaba", Haisam dake d'an kishingid'e ya d'an ta6e baki"Shine har yayi laifi,ke da ba'a maki gwaninta...."da sauri hajiya ta katseshi "To mai Uba kaji nace yayi man Laifi ne,Kawae dai kamata yayi a gyaro Wanccan d'in,ba sai an wani sake ba,Duk ma ga Matoci nan a Gidan,kai kanka akwae biyu naka da kazo dasu ga d'ayar tawa,Sannan acan GRA ma akwae Motoci,to duk miye na sai an Kawo Watan," "Ba ruwanki da nawa kowa yayi Amfani da nashi,Kuma na Gra da kike Magana ai Dad yasa Manager d'inshi na nan garin ya kwashe su Saboda anata ajesu ba'a Amfani dasu, in Buk'atar amfani dasu ya tashi zasu yi replacing wanda suka d'aukan,tunda dae so yake a canja maki kawae ki za6a,already i ave selected it for u", Hajiya dake kallonshi tace"Wacce ka za6ar man?", bai bata amsa ba sai mik'ewa da yayi ya koma kusa da ita ya zauna yana nuna mata pic d'in Motar da ya za6a matan, "Kai Masha Allah tayi kyau wllh,kuma gata itama yanayin Vibe din gareta inason Mota haka,kamar jeep ce ma ko,Ya sunanta ne,ince dae bata da tsada ko?" Kwantar da kanshi yayi ajikin kujeran ya d'an zamo"Rav 4,jeep ce,bata da wani kudi sosae just 12 million take..."tun kafin ya k'arasa Hajiya ta waro idanu hannunta d'aya ruke da ha6arta"Million sha biyun ne ba tsada don baka tsoron Allah Haisam,haka kurum jama kai Surutu,aji dadin cewa kudin talakawa yake sata yana kashe man tsofaitsofai dani ko,su Mutane da basa raina abun magana", "Ina ruwanki da Mutane,let dem say what they want,tunda Allah ya baki iko sai ki denying kanki abunda kike so", ta6e baki hajiya tayi tace"Uhm surutun Mutane ai abun tsorone haisam,in dae akwae wata wadda bata kai wannan kudi ba in gani", "Yeah Akwae wasu,ga wata sunanta Venza" yayi maganar yana nuna mata hoton Motar,Hajiya tace"Oh,kaji sunayen Mota iri iri,kuma masha Allah itama ba dae kyau ba,to ita bata kai waccan ba dae ko?" "Yeah,bata kaita ba,ita 10m take...", da sauri hajiya ta katseshi tana d'an harararshi "yo miye marabarsu,ni nayi zaton Banzar ce ashe ta kirki ce,kaga nifa banson wadda takai miliyan goma gaskia,in dae akwae na k'asa da hakan to sai in za6a,amman bazan za6i wad'annan ba,ita waccan d'ayan taka d'in nawa take ne?" "Mercedes kike magana,55m take",Wata Uwar harara Hajiya ta wurga mashi"da Allah ni ba ita nike magana ba,yo ni miya rage man yanzu a Rayuwar da zan rinka hawa Motar Miliyan hamsin harda biyar,d'ayar nike Nufi navy blue dinnan" Sigh yayi"Corolla S kike nufi,bai da wani tsada 6m yake..."da sauri ta tari numfashinshi"Yauwa to kaga kamar itan ko wadda ma bata kaita ba yar 5 zuwa 4m" Still yayi ya d'an dage gira yana kallonta, "Kayi man shiru,bakaji mi nace bane?" Gyara zama ya danyi"Rav 4 da na za6a maki shi za'a kawo period,dama na sanar dake ne don kisan za'a kawo,kina son abu sai ki hana kanki saboda wani Mutane" A harzuk'e Hajiya tace"To tunda nace banso ba sai akawo man irin wadda nike son ba",banza yayi mata saima latsa wayarshi da ya fara,dama tasan tunda har ta nuna Motar tayi mata to fa sai yasa an kawo ta, a k'ule tayi kwafa"To wllh da an kawota bada waccan 406 d'in zanyi",d'age gira yayi ba tare da ya kalleta ba yace"as u wish" tana niyyar bud'e baki ta sake yi mashi Magana Muryar Fatuu ta katse mata hanzari"Assalamu Alaikum,ga bak'uwa daga Makka", Juyawa hajiya tayi ta kalli entry d'in adai dai lokacin Fatuu ta sake maimaita abunda ta fad'a,d'an girgiza kai Hajiya tayi tace shiryayya kafin ta amsa"Wa'alaikumus Salam Maraba da Mutan Makka ku shigo",shigowa tayi tana Dariya hannunta ruke da yar madaidaiciyar warmer ta yafo d'an bakin gyalenta na gado,da Hijabi ta fito ganin gwaggo zaune a tsakan gida,tana zuwa zaure ta cireta ta sagale ajikin windon Amadu kaman yadda ta saba yi daman ta 6oyo gyalen shine ta yafa kafin ta fito, Tana shiga haisam ya koma inda yake zaune da farko,hakan yasa ta nufi gefen hajiyan ta zauna tana dariya"Hajiyan Sanata ina wuni", "Lafiya lou fateema,yau Allah yayi kenan an kitse kan nan", "Ai ba duka akayi ba iya biyun nan ne,tace sai gobe da yamma tunda ba islamiyya zata k'arasa man sauran", Jinjina kai hajiya tayi kafin tace"wani abun arzikin nasamu da daren nan" tayi maganar idonta akan kulan da fatuu tazo da ita,janye kulan fatuu tayi gefe"Ba naki bane,Yaya handsome na kawo mawa,naje part dinshi naga bai nan shine na kawo masa nan", Hannu Hajiya tasa ta ruke baki alamar mamaki tace"iyee, yanzu Fatima ni zaki gwasale,duka yaushe kika san haisam d'in da zaki man tawaye,lalle Nagode da wannan babban dizgin da kika man,amman zamu had'u ne",langa6ar da kae tayi tana ma hajiyan dariya kafin ta mik'e tana niyyar nufar inda haisam d'in yake,kwafa hajiyan tayi tana jinjina kai,ganin dae da gaske haisam d'in ta kawo mawa yasa Hajiya juyawa side d'in kitchen ta fara kwalama Saude kira"Saude,Saude lek'o ki tayani Jimami,yau ni Fateema ta wulak'anta",fitowa Sauden tayi ta tsaya bakin kopar kicin d'in hajiya ta shiga fad'i mata abunda fatuu tayi mata,Dariya ta fara yi daga inda take tsaye, A gabanshi ta tsaya tana ta Murmushi,shima kallonta yake don duk draman da suke da Hajiyan yana sauraransu,hannu tasa tana d'an kange bakinta"kai na kawo mawa Yaya Handsome"ta fad'a da alamun kunya,kai ya d'aga mata,hakan yasa ta d'aura warmer d'in kan hannun kujera ta kinkimo sofa table kafin ta d'auko kulan ta d'aura,Hajiya dae nata bin ta da ido haka Saude ma har lokacin tana a bakin kicin sai faman Murmushi take, A hankali Fatuu tasa hannu ta fara k'okarin bud'e kulan,k'amshin daddawa ne ya kaima hancin haisam karo bayan ta bud'e,da Sauri ya juyar da fuskarshi gefe had'i da runtse Idanuwanshi,waro ido Fatuu tayi ganin abunda yayi, "Miya faru ne naga Wanda aka kawo mawan ya kauda kai hada rufe idanu??" hajiya ce tayi tambayar,a sanyaye fatuu ta juya ta kalleta"nima ban sani ba,dana bud'e ne sai naga yayi haka", "Miye kika kawo masa ne?" Fatuu tace"Taliyan hausa ce mai daddawa",bud'e idanu hajiya tayi hannunta ruk'e da ha6arta"ai baya son daddawa Fateema,kamshinta tada mashi Zuciya yake yi shiyasa bai cin duk wani abu da akayi da ita", Damm gaban fatun ya buga,juyawa tayi ta kalleshi,ya bud'e idanun sai dai kwata kwata bai kalli bangaren da take ba idanunsa na akan TV,jikinta ba k'aramin Sanyi yayi ba,a hankali tasa hannu ta d'auki kulan,juyawa tayi ta kalli hajiya dake kallonta fuskarta d'auke da Murmushi,a hankali ta nufi wurinta,agabanta ta tsaya ta mik'a mata kulan"gashi to Hajiya ki ci" fuskarta a yamutse tayi maganar, Dan ta6e baki tayi"saida shi bazai ci ba sannan zaki kawo man,wato ni ga kwad'ayayya ko,to nima bazan ci ba...."fuskarta kaman zatayi kuka ta katse Hajiyan"Don Allah kiyi hakuri ki ci", "Uhm dama kin daina Wahalar da kanki Fateema bafa zanci ba,har ni zaki ma Wulakanci,wato ke mai Yaya ko,to tunda ba zai ci ba sai ki koma dashi kawae" ba alamun wasa a fuskarta tayi maganar,ganin haka yasa Fatuu d'aga kai ta kalli Saude da har lokacin take tsaye a bakin kicin ta dan d'aga murya"Aunty Saude in kawo maki zaki ci?" kafin Sauden ta bata amsa Hajiya ta amshe"bazata ci ba itama tunda tun farko bamu kika kawo mawa ba,saida aka gwasale ki shine zaki mana neman kai da ita,to ba wanda zai ci"maido kallonta tayi kan hajiya da tayi maganar ganin ba alamun wasa a fuskarta yasa ta fara ta6e baki alamar zata fara yin kuka,ganin haka yasa Hajiyar juyar da kanta gefe alamar ko a jikinta,a hankali ta juya ta nufi hanyar fita idanunta cike tabb da kwalla,sharr kwallan ta fara zubowa,gefen gyalenta tasa tana gogewa yayin da hannunta guda ke rungume da kulan taliyan, "ZARAH....",Haisam ne ya d'an d'aga Murya ya kirata,a hankali ta waiwaya ta kalleshi,alamar tazo yayi mata da kanshi hakan yasa ta koma cikin parlon tana yi tana goge kwallan dake zubo mata,A gabanshi ta tsaya kanta na kallon k'asa, "Keep it" yayi Maganar yana nuna Sofa table,a hankali ta d'aura kulan saman table d'in kaman yadda yace,d'agowa tayi bayan ta aje ta saci kallonsa,shima ita yake kallo saidai bazaka iya gane tak'amaimai yanayin fuskarsa ba, "Go and bring plate with fork" gently yayi maganar,da alamun mamaki ta idasa d'agowa tana kallonsa hakan yasa ya d'an lumshe idanunsa alamar eh,da sauri ta juya don daukko Plate da cokali mai yatsu,suna had'a idanu da Hajiya ta wani sha kunu ta nufi hanyar kicin,hakan ba k'aramin dariya yaba hajiyan ba,tana shiga kicin d'in Saude ta mik'o mata abunda taje d'aukan kallon Sauden tayi fuskarta ba yabo ba fallasa ta kar6a,daga haka ta juya ta fuce, Ba k'aramin daurewa Haisam yayi ba lokacin da ta bud'e kulan zata fara zuba mashi, don ma ba sosae aka cika daddawan ba sannan ga k'amshin Curry da aka sa hakan ya rage mata kaifi sosae,tana zuba kamar cokali biyar ya dakatar da ita alamar ta isa,maida marfin kulan tayi ta rufe ta d'an ja gefe ta tsaya,Slowly ya kai hannu kan fork din ya d'ebo yar kad'an,lokacin da zai kaita bakinshi har saida ya d'an dauke numfashin shi kafi ya sakata ciki,a hankali ya fara chewing dinta kafin ya had'iye,abunda ya bashi mamaki kwata kwata baiji daddawan ya canja taste d'in abincin ba,kamshinta ne kawae ake ji,k'ara kai fork d'in yayi ya debo har ta dan fi ta farko yawa ya kai bakinsa,bayan ya hadiye ya d'ago fuskarshi ya kalleta a inda take tsaye ta zuba mashi idanu,fuskarshi ad'an sake kaman zai yi Murmushi yace"it tastes good", Waro idanu tayi"Kenan tayi maka dad'i Yaya Handsome?, Kai ya d'aga mata da d'an murmushi alamar eh,wata k'arar farinciki Fatuu ta saki lokaci guda ta fara tsalle had'i da juyawa saitin da hajiya take tana fad'in"Yeeee,an gwasale hajiya,an gwasale hajiya....",Sosae take tsalle kitson gaban kanta sai dagawa yake sosae, gaba daya ma gyalen ya zamo k'asa,ita kam hajiya mi zata yi in ba Dariya ba,sosae take tik'ar dariya,hakan ya jawo hankalin Saude ta leko,cike da farinciki fatuu ta tsaya da yin tsallan tace"Aunty Saude Yaya Handsome yaci abincin hajiya taji Kunya",hannu Saude tasa ta rufe baki tana dariya,ita kam Hajiya throw pillow ta d'aukko ta jefo ma Fatun,abunda bata sani ba Hajiyar ita tasa haisam d'in yaci abincin,dama da biyu taki ci lokacin da fatuu ta nufi kopar fita daga falon hajiya ta kalli haisam d'in da kai ta rinka lallashinshi tana magana kasa kasa akan ya daure ya ci abincin, "To a samman in ci nima tunda wanda aka kawon don shi yaci" hajiya ce tayi maganar tana kallon Fatuu dake zaune a gefen Haisam,mak'e kafad'a tayi"baza ki ci shi ba kuwa,shi zai cinye abunshi"ta k'arasa tana murmura ido, Dan gyaran murya haisam yayi ta juya ta kalle shi"ki yi hakuri ki bata", "To ai baka ci da yawa ba fa" a shagwa6e tayi maganar,yace"Owk ki d'an kara man kad'an sai ki bata sauran" mik'ewa tayi taje gabanshi ta k'ara masa kafin ta nufi Hajiya da kulan,a gefenta ta dangwarar da kulan"gashi nan don ba Halin ki ba...."bata k'arasa ba sakamakon damkota da hajiya tayi ta daddage ta d'uma mata dundu tana fad'in"Kin raina ni ko Fateema"Fatuu dake ta dariya tace"to ai ke ba kakata bace ba",Sakinta tayi tace"Je ki d'aukko man fork nima in ci inji in kin iya girkin"cike da Zumudi tace to,har ta nufi kicin ta juyo"banda plate hajiya?"kai ta d'aga mata"eh bani cokalin kawae zanci acikin kulan, Bayan ta kawo mata cokalin a gefenta ta zauna ta k'ura mata ido tana jiran taji mi zatace game da Abincin,jinjina kai hajiya tayi lokacin da takai lomar farko"Ah Masha Allah, tayi dadi sosae wllh,amman dae nasan dije ce tayi shi....."da sauri fatuu ta katseta"Wllh ni nayi shi na rantse da Allah,ita kawae nuna man yadda zansa abubuwa tayi amman tana zaune nayi har na gama" hajiya tace"lalle kinyi kokari"sosae fatuu ta washe baki alamar taji dadi. Yana gama cin Abincin ya mik'e don gaba daya jin bakinsa yake yana warin daddawan,Bedroom d'in Hajiya ya nufa fatuu ta bishi da kallo har ya shige corridor kafin ta maido idonta kan hajiya"Wai hajiya da gaske Yaya Handsome baison daddawa?" cinye abincin bakinta ta fara yi tace"Wllh kwata kwata baisonta tun yana yaro,warinta yake ji sosae,wani lokacin har Amai yake yi in yaji kamshinta,shiyasa ma bai shan miyan duk da akasa ma daddawa yanzu haka da kika ga ya nufi dakina na tabbatar Brush zai je yi", Jinjina kai fatuu tayi a sanyaye tace "ai da bai ci ba tunda bai so,ni fa koda nayi kuka saboda ke kinki kici ne", dariya hajiya tayi" karki damu,yaji zai iya ne shiyasa yaci,nima kuma dama don yaci d'in tunda shi kika kawo mawa yasa nace maki bazan ci ba,yanzu da yaci ba gashi nima ina ci ba"gyad'a kae fatuu tayi sai faman fara'a take ba k'aramin dadi taji ba da suka ci, Fitowa yayi yana goge face d'inshi da tafin hannunshi da alama ruwane a fuskar,hanyar fita ya nufa don duk da yayi Brush d'in still jin bakinsa yake ba dai dai ba,Part dinsa zaije Don ya fesa had'addan Mouth spray dinsa ko zaiji daidai, "in fita zaka yi don Allah ka d'an raka Fateema dare nayi"hajiya ce ta katse mashi hanzari,kai kawae ya d'aga ba tare daya kallesu ba, "To Fateema tashi ki bi shi sai kuma Allah ya kaimu,Nagode duk da bani aka kawo mawa ba", mikewa tayi ta dauki kulan don tuni hajiyan ta gama ci, "Sai da safe Hajiya" kai ta d'aga"Allah ya tashe mu lafiya", har Fatuu ta nufi hanyar fita cike da tsokana hajiya ta dan d'aga Murya"Gobe ki kawo ma Yaya Handsome Tuwo da Miyan kuka",a sukwane fatuu ta juyo ta kalli hajiya dake ta dariya,ganin haka yasa itama tayi dariya tace"ai bazan k'ara kawo masa abu mai daddawa ba",daga haka ta juya tabi bayan haisam wanda tuni ya fice, Da sauri ta isko shi don a hankali yake tafiyan,jerawa tayi dashi ta d'ago kae ta kalleshi"Yaya handsome don Allah kayi hakuri nasa kaci abunda baka so,wllh ni bansan baka sonta ba"d'an juyawa yayi ya kalleta da dan Murmushi calmly yace"Don't worry ur self,naji dadin abincin ai,thanks",jinjina kai tayi tana ta zabga uban Murmushi daga haka suka fuce daga Gate din gidan, Fatuu na ganin har sun wuce katangar gidan Hajiya bai tsaya ba tace"Yaya handsome yau har gida zaka rakani ne?"kai ya daga mata alamar eh,taci gaba"ko dae don kar na sake zuwa kangon nan ne,ai bazan k'ara zuwa ba duk da ma an kamasu,oh lemunana ko suna can ko wani ya d'auke su"tayi maganar hannunta ruk'e da ha6arta, "Ko zaki je ki duba ne" haisam yayi maganar idonshi akan hanya,dariya kawae tayi don ta gane gatse ne yayi mata,gab da kiosk d'in kawu Amadu Haisam ya ja ya tsaya,hakan yasa itama ta tsaya tana kallonshi"kije sai da safe"fatuu tace"to bari inma kawu Amadu magana ku gaisa,bata jira cewarshi ba ta juya tana kwala ma Amadu kira"Kawu Amadu ka lek'o ku gaisa da Yaya handsome", lek'o da kai ta cikin kiosk d'in Amadu yayi tun kafin yayi magana Fatuu ta nuna masa haisam dayake an maido da wuta akwae haske sosae,,Haisam na ganin Amadun na k'okarin fitowa ya matso ya mik'a masa hannu suka gaisan,fatuu na ganin zai juya bayan sun gaisan tace"Yaya haisam bari abaka biscuit da sweet" yadda tayi maganar sai kace wani k'aramin yaro,wani kallo yayi mata da sauri tace"pls"ta marairaice fuska,jin baijin dad'in bakinsa yasa shi cewa"just a Sweet"da sauri tace to,ta juya ta nufi cikin shagon,can sai gata da ledan sweet ta mik'a masa,d'an bude ido yayi batare daya amsa ba, "Gashi nan duka yace a baka" girgiza mata kai yayi"yayi yawa inada shi a d'aki,just one ya isa"Wani kallo tayi masa"kai Yaya Handsome ya zaka ce d'aya ya isa,don Allah ka amsa duka" k'in amsa yayi ya bita da ido tace"to in d'ibar maka rabi?"girgiza mata kai yayi alamar a'a,ya d'aga mata dogon yatsansa guda alamar guda daya zata bashi, "To bari kagan yanda za'ayi,zan baka na yawan sunanka ka yarda?" kai ya d'aga alamar eh, "YAYA HANDSOME"ta d'aga hannunta tana k'irga yawan sunan da yatsunta kafin ta kalleshi"guda sha biyu kenan zan baka"jinjina kai yayi cike da mamakin wai shi zata ma wayo, Fatuu tace"Kawo hannunka to"ba musu ya bud'e kyakkyawan hannunsa mai d'an fadi da tsawo,tafin hannun sumul dashi tamkar ka ta6a jini ya fito,bud'e ledan sweet d'in tayi ta fara saka mashi da dai daya tana saka gudu shidda ya rufe tafin hannun,da sauri ta d'ago ta kalleshi tun kafin tayi magana ya rigata da fad'in"HAISAM is six letter word,so guda shida ne daidai sunana" cike da shagwa6a ta d'age kai"Wayyo Yaya handsome ni zaka ma wayo..."katseta yayi cikin Sanyayyar Muryarshi yace"Nima ai wayon kika so yiman ko"jin haka yasa fatuu kyalkyacewa da dariya tana fad'in"ashe ka gano ni"shima dariyar yayi har jerarrun hakoransa masu tsari suka bayyana,dimple dinshi guda d'aya ya lotsa sosae"kije dare yayi,Gud nyt" kai fatuu ta d'aga"Gud nyt yaya handsome kabi a hankali kar ka sake taka kwalba"Wani kallo yayi mata mai kaman harara kafin ya juya, Tana ganin ya tafi ta juyo,tsayawa tayi ta bud'e kulan hannunta ta fara zazzaga sweet d'in ciki,kamar ance Amadu ya lek'o,ya ganta da karfi yace"Fatuu dama bashi zaki ba...."bai k'arasa maganar ba ta wurga ledan sauran sweet din cikin shagon ta nufi gida da gudu. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D2Y0l2ZoRx8FLdjdi2Te0F _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *4️⃣0️⃣* Washegari Misalin karfe biyu da rabi na rana,Haisam zaune a parlor ya tasa laptop d'insa gaba yana lallatsa ta,Tun bayan da ya samu rauni daga gida yake aiki don bai iya zuwa wurin aikin,gaba daya ya gaji Don aiki biyu yake yi, gana nan ga kuma na U.S,Kullum wuni yake aikin latsa Computer,Wani irin bacci ne ke fizgarshi don ya gaji Sosae,A hankali yasa hannu ya d'an ture laptop din gefe ya idasa hayewa kan kujeran ya kwanta,hannu ya kai ya d'aukko throw pillow ya tura ak'asan kanshi ya mik'ar da kafafunshi,A hankali idanunsa suka fara lumshewa alamar bacci ya fara zuwa. Turo kopar falon akayi tare da sallama,Cikin zuciyarsa ya amsa ba tare daya kalli mai shigowan ba don yaji Muryarta,k'arasa shigowa tayi jikinta sanye cikin Uniform amman yau da Hijab,kitsonta sun fito gefe da gefe yayin da k'asan kitson ki acikin hijabin,ba k'aramin kyau hakan yayi mata ba, gaban kujeran da yake kwance ta tsaya tana kallon fuskarshi,Slowly ya bud'e idanunsa akanta,murmushi ta sakar masa hakan yasa shima ya d'an yi mata wanda iyakarsa saman lips d'inshi,ganin tayi tsaye k'erere yasa shi mik'ar da yatsansa yana nuna mata 6arin da armchairs suke alamar taje ta zauna,girgiza masa kai tayi tace"bari in Zauna anan"tana fad'in hakan ta zauna a saman Carpet ta lankwashe kafafunta tayi zaman cin tuwo still idanunta na akanshi, kallonta yayi a kasalance yace"kindawo",kai ta d'aga masa "eh yanzun nan na dawo na iske ba kowa a gidan,Gwaggo tana wurin aiki,kawu Amadu kuma har yanzu bai kaiga dawowa ba,shine nace bari nazo na tayaka fira",nodding kai yayi kawae,hannunta ta fiddo daga cikin hijab ta mik'a masa ledar dake ruke a hannun,bin abunda take mik'o masan yayi da ido kaman bazai kar6a ba,can kuma ya mik'o hannu ya amsa,jujjuya faran ledan yayi kafin ya d'ago ya kalleta da gani bai gane miye aciki ba, "Tsaraba ce nayo maka,su tuwon madara ne,da gwullisuwa da baban dudu da mandako sai kantun gana" d'an bud'e idanu yayi jin wasu sunaye da take fad'a,yasan tuwon madara da gwullisuwan don akwae wata Abokiyar aikinsu dake kawo su,sai dae sam ba irin wannan bane,nata masu aji ne,wurinta ne ma ya siya Popcorn d'in da ya ba fatuu rannan,sauran abubuwanne bai sani ba bai ma ta6a jin sunansu ba, ganin yana ta jujjuya su tace"ko bazaka sha ba" d'ago idanunsa yayi"zan sha,but ba nace ki daina kashe kudi kina siyo man abu ba"da sauri tace"ai kudi nane nasiyo maka dasu ba na wasu na ta6a ba,kuma duka Naira d'ari ce ma,komai na ishirin ishirin",kallonta kawai yake da lumsassun idanuwansa kafin Calmly yace"thanks zaraah"daga haka ya aje ledan a gabanshi, "Nafa san miyasa kake ce man Zarah" kallonta yayi ba tare daya ce komae ba,taci gaba"Gwaggo tace man sunan mamanka gareni hakane wai??"ta d'an bud'e idanu alamar amsa take jira,kai ya daga mata alamar eh, "Kenan nazama mamanka", Yace"ko", "Eh mana,tunda ina da sunanta ai kaga nazama mamanka ko",still yayi yanata kallonta, "Mom zaraah yakamata ka rinka ce man,kuma ka rink'a yiman Dariya kana man Magana sosae"ta kai maganar tana d'an tura baki alamar shagwa6a,d'an muskutawa yayi ya juyo sosae"ai ina maki wannan ko" tace"to ai ba sosae kake yi ba,in zaka yi dariyan haka kake ko kayi haka"tayi maganar tana nuna mashi yadda yake dariyan,sosae ta bashi dariya yadda ta wani d'age baki amman sai yayi murmushi kawae, "To ai hakan ma normal ne" d'an girgiza kai tayi"a'a,haka yakamata ka rink'a yi..."ta washe baki tana nuna mashi wai hakan zai rinka yin dariyar,Fuskarshi a sake yace"Wannan ai irin naku ne na Manya Mom zaraah"sosae ta washe baki jin ya kirata da sunan da tace ya rink'a ce mata, Hannu ya kai ya dafe gaban kanshi don rashin baccin da baiyi ba har ya fara developing headache,sosae ya runtse idonshi yana d'an yamutsa bakinsa,ganin hakan yasa Fatuu cewa"Yaya handsome mike damunka ko baka lafiya ne?"sai da ya d'an dauki lokaci kafin ya janye hannun,a hankali ya fara bud'e idanun,yana son yace mata bacci yake ji amman baison taga kaman yana korarta ne don wani lokacin kaman bata fahimtar abu daidai, K'ura mashi ido tayi"idanunka sunyi wani iri yaya handsome,baka lpy ko?"girgiza mata kai yayi yace"lafiya na lou,kawae ina jin bacci ne"d'an murmushi tayi"to bari in tafi"tayi maganar tana k'okarin mikewa,bin ta da kallo yayi kaman mai son gano wani abu har ta karasa mikewa zata tafi, "Zaraah..." ya dakatar da ita,tsayawa tayi tana kallonshi,shima kallon nata yake yana nazarin fuskarta sai dae sam ya kasa fahimtar yanayinta,"Yaya handsome ka tsaida ni", "Yeah,dama ba ina nufin ki tafi ba,ba kince gidan ba kowa ba?" kai ta d'aga mashi alamar eh, "Owk,ko ki je ki gaida hajiya sai ku d'an yi firan kafin in tashi" yayi maganar idanunshi akan fuskarta yana nazartarta,d'an murmushi yaga tayi"to Yaya Handsome bari inje"murmushi yayi don yaji dad'i da bata fahimce shi ba daidai ba,har ta fara tafiya ya sake kiran sunanta,juyowa tayi ta kalleshi ya d'ago ledan abubuwan da ta kawo mashi ba tare daya kalleta ba yace"ki kai ma hajiya"shiru tayi tana bin shi da ido, jin bata amsa ba yasa shi d'ago da kai ya kalleta,lokaci guda ya gane bata ji dadin hakan daya ce ba, "Ki kai mata kice ta dauki rabi sai ta aje man sauran,kinga itama duk in ta samu abu sai ta bani" sai lokacin ta mik'o hannu ta kar6i ledan tana fad'in"to ai leda biyu ce,bari in raba maku",raba masu ta fara kokarin yi shi dae yana ta bin ta da ido, bayan ta gama ta mik'o mashi"to ga nakan ita kuma sai in kai mata wannan"hannu yasa ya amsa Fuskarshi ad'an sake ya furta"Thanks"daga haka ya aje ledan gefenshi,ita kuma ta nufi kofa ta fuce, ____________________ Sam baijin dadin Baccin da yake kan kujeran,hakan yasa ya fara motsi alamar zai farka,A hankali ya fara bude idanunsa kafin ya idasa ware su sosae,k'uri yayi cike da mamaki yake kallon abunda ke gabansa har saida ya d'an sa bayan hannunsa ya goge idanunsa don ya tabbatar,Fatuu ce zaune saman C-table d'in parlon tayi dare dare a sama tana facing dinshi hannunta guda tayi tagumi dashi gaba daya ta k'ura masa idanu, A kasalance ya furta"Zarah!what are u doing up there,ba nace kije kuyi hira da hajiya ba?", Cire tagumin tayi ta zuro kafafunta k'asa a shagwa6e tace"to ai naje na iske itama hajiyan bacci ya kwashe ta a Parlor,baka gan yadda ta saki baki ba sai munshari take wllh kaman rago"bud'e idanu yayi sosae yace"Hajiyan ne rago!" da sauri ta shiga girgiza kai"a'a,wllh na manta rago Namiji ne,kaman shanuwa nike son cewa",Still yayi yana mata wani kallo hakan yasa tasha jinin jikinta duk da ita gani take wai ta gyara,yunkurawa yayi ya tashi daga zaune ya jingina bayansa da jikin kujeran,ita kam tayi tsuru tana bin sa da ido,ya fahimci gani take abunda ta fad'a daidai ne hakan yasa shi cewa"ba'a kwatanta Mutum da dabba kar ki k'ara"da sauri ta d'aga masa kai"to Yaya Handsome bazan k'ara ba",jinjina kai yayi,yana jin dadin yadda da yayi mata gyara take cewa bazata kara ba,kuma ya tabbatar bazata k'aran ba. Shuru suka yi na wani d'an lokaci tana ta kallonshi tana faman sakin Murmushi,shi kuma fuskarshi ad'an sake yake kallonta, "Duk kujerun dake parlon nan baki iya zama sai nan,in kika fasa man abu fa", Hannu tasa tana shafa saman C-table din"Ai yana da kwari bazai fashe ba kuma ni bani da nauyi ma,kasan mi?" kai ya girgiza mata alamar a'a,taci gaba"nafa dad'e da dawowa ina shigowa nagan kanata bacci...." katse ta yayi"shine kika zauna kina bina da ido"fuska ad'an d'aure yayi maganar, Da sauri tace"a'a Yaya handsome lokacin da na shigo naga kana baccin wllh har zan tafi gida kawae sai naga wani abun mamaki,kasan mi?"kai ya girgiza"wllh dana kalle ka kana baccin sai naga ka koma man kaman Karan na cikin Kaddarar rayuwa da ake a Arewa 24,ka gane shi"shiru yayi mata,tace"au ashe fa kace baka kallon tashar,amman wllh kunyi kama shiyasa na haye nan ina k'ara kallonka sosae har gashin kanku iri daya ne,kuma shima yana da dimple amman kai kafi shi tsawo gaskia shi kuma yafi ka yin dariya sosai"ta k'arasa tana ta watsa hannuwa,shi dae zuru yayi mata don bai ma san wanda take magana akai ba,ganin yayi mata shiru tace"Ka bari lokacin da ake yin shirin zan nuna maka shi",kai ya daga mata alamar toh,daga haka ya d'age kansa sama yana kallon ceiling gaba daya baijin dadin jikinshi,baccin sam bai ishe shi ba, "Yaya handsome ka gama baccin ne?"a yadda yake ba tare da ya d'ago ba ya girgiza mata kai, "to ka kwanta ka cigaba da baccinka",still bai d'ago ba yace"I can't sleep if there's someone around", jin tayi shiru yasa shi d'agowa ya kalleta,don kar tayi tunanin korarta yake yasa da sauri yace"Hajiya ma in tana kusa dani ban iya yin bacci" jinjina kai tayi alamar ta gamsu kafin tace"to ka tafi d'aki mana ka kwanta", "In barki ke kad'ai?" tace"Eh mana ba sai in yi maka gadi ba kar wani ya shigo ta katanga su Officer basu sani ba",d'an murmushin gefe yayi jin abunda tace kafin yace"Yau ba aikin da zaki yi ne"hannu tasa ta ruke ha6a ta d'age ido sama alamar tunani"ba aikin da zan yi,amman yau gwaggo tace zata k'arasa man kitso bansan ko ta dawo ba yanzu", "Ok,kije ki gani in ta dawon ko", "To,amman sai na fara gyara ma d'ana parlon shi", tayi maganar tana kare ma falon kallo,shima d'aga ido yayi yana kallon falon kafin ya maida idon kanta"ai ba abunda yayi" jinjina kai tayi"eh amman dae akwae abubuwan da ya kamata a gyara",d'an ta6e baki yayi ya dage shoulders d'inshi daga haka ya mik'e ya nufi Bedroom dinshi,yana kaiwa daidai Corridor fatuu ta juya kai daga kan C-table d'in da take tace"My son kayi bacci mai dadi kuma kayi mafarkin mamanka",d'ago mata hannu yayi murya a kasalance ya furta"Owk,Mom Zaraah",daga haka ya tura kofa ya shige Bedroom d'in. *** **** **** Ba k'aramin bacci yayi ba don sai can bayan la'asar ya farka,hannu ya kai ya d'auki wayansa yana duba time,da sauri ya mike zaune ganin karfe hudu da rabi hakan na nufin yayi missing Sallan la'asar,da k'yar ya saukko da kafafunsa ya nufi Toilet don ya watsa ruwa saboda duk kasala ta baibayeshi, Sanye cikin jeans da T-shirt ya fito ya nufi masallaci duk da lokaci ya kure,bayan ya gama sallan zama yayi cikin Masallacin yana yin azhkar d'in yamma,bayan ya gama yana fitowa daga cikin Masallacin wayarsa dake ruke a hannunsa ta fara ringing,duba mai kiran yayi kafin ya d'aga,tun kafin yayi magana on the other hand akace"Kana ina ne naje part dinka baka nan,nazo na Hajiya ban samu kowa ba", "Ina a masallaci gani nan fitowa",daga haka yayi rejecting kiran,yana fitowa kopan masallacin ya hango Abbas tsaye agaban part din hajiya,juyowa Abbas yayi ya kafe Haisam d'in da ido ganin yana dangyashi hakan yasa Abbas din k'arasawa wurinshi,hannu ya bashi suka gaisa kafin yace" What happened, naga kana dangyashi "Na samu rauni ne a kafan", "rauni,wane irin rauni"Abbas ya tambaya, "Na taka kwalba ne" ya bashi amsa a takaice,cike da mamaki Abbas yace"kace shiyasa jiya na tambayi ko kana wurin aiki kace man a'a kenan?" "Yeah,bana zuwa sai na samu sauki sosae" Cike da jimami Abbas yace"wai garin yaya?A ina ka samu kwalba har ka taka?" bai bashi amsa ba sai cewa yayi"Muje ciki mana"ya kai hannu ya kamo hannun Abbas d'in daga haka suka nufi part d'in haisam, Lokacin da suka shiga cikin parlon atare suka ja suka tsaya suna bin shi da kallo,gaba daya Fatuu ta harmutsa shi,sam Haisam bai lura ba d'azun don yanata sauri yaje yayi sallan la'asar da ta wuce shi,Flower vases d'in dake a bakin corridor ta kinkimo su ta jara su a kan carpet d'in falon,yayi mamakin yadda ta iya daukko su don ba karamin nauyi ne dasu ba,ta d'aukko telephone da lamps d'in dake akan desk ta maido su kan C-table,haka Sound systems d'in falon ta rarraba su wasu dogaye ta jajjerasu a bayan kujera L-shape, Kallonshi Abbas yayi"Waye yayi wannan gyaran,ko duk gwaurancin ne yasa baka iya gyara falo ba" fuskar haisam d'auke da Murmushi ya nufi kujera ya zauna yana fad'in"kasan dae nafika iya komae na cikin gida Abbas,wani yarinyane tayi gyaran"cike da mamaki Abbas ya maimata abunda haisam d'in ya fad'a yana kokarin zama kan armchair, "Yaushe ka fara shiga harkar yara ko ince yaushe yara suka fara shiga harkar ka?" "Wannan tafi karfi na ne" "Tafi karfin ka,wannan wace Yarinyace haka da har tafi karfin ka?"da tsananin mamaki Abbas yayi tambayar idonsa akan haisam d'in,kwantar da bayanshi yayi ajikin kujeran a takaice ya fara bashi labarin Fatuu sai dae ba komae ne ya fad'i masa ba kaman kango da taje har ya taka kwalba duk bai fad'i masa ba,Dariya sosae Abbas ke yi,lokacin da haisam ya gama bashi labarinta yace"kai gaskiya yarinyar yar bala'e ce gashi ta cika abun dariya,amman fa wllh da ni ta fasa ma glass bazan yarda ba" wani kallo haisam yayi masa"what u would hv done,zaka ce a biyaka ne,or what?", "Ai inma nace a biyanin ba laifi bane kuma ko ba ni ba adai halin da ake ciki yanzu kowa tayi ma hakan wllh cewa zai yi sai an biyasa,ta dae ci sa'a kawae da kaine ta fasa mawa", Wani kallo haisam ke bin shi dashi ya d'an ta6e baki"in kuma basu da halin biyan naka fa Abbas?" A d'an harzuke yace"to kuwa jikinta zai gaya mata wllh,don har gidan nasu zan je in zaneta "sosae yaba haisam dariya don yasan da gaske yake maganar don shima Abbas d'in dan balae ne, "U Know what Abbas,irin yaran nan duka bai masu sai ma k'ara masu rashin ji,yanzu da ban taking wani action kan hakan ba,ba gashi ta canja ba har ta zama Mom d'ina" ya k'arasa maganar yana ta dariya, Jinjina kai Abbas yayi"U'r right,amman shima gayen daya fad'a mata kudin glass d'in ya iya zuka karya koda yake d'an shaye shaye ne abunda yafi hakan ma zai fad'i,just abunda ba zai wuce 50k ba yace wai 1 million,amman shima ya taimaka tunda yasa ta tsorata har tayi alk'awarin ta daina rashin jin"ya k'arasa maganar shima yanata daria, "Ina My boy" haisam ya tambaya, "yanzu haka na baro shi yanata kuka wai sai nazo dashi" Haisam yace"baka kyauta ba ai da ka kawo man shi mun gaisa yaga babanshi daya dade bai gani ba", "rabu dashi kawae rigima zai zo yayi maka ba wani abu ba" "Why? haisam ya tambaya a takaice, gyara zama Abbas yayi kafin yaci gaba"kagane wani toy ne that looks exactly like a real laptop da ake talla a mbc,shine yasa rigima sai an siya masa ya takura man,so ganin toy d'in zai yi amfani wurin taimaka ma yaro ya koyi abubuwa,don akwae educational apps da cartoons sannan yaro zai iya yin typing kuma za'a iya tura masa wasu apps din kaman islamic haka,so na neme shi anan ban samu ba gaskia,sai nayi ma wata colleague d'ina lecturer magana da yake tana ordern kaya daga waje ko zata samo masa,tace zata bincika man,nace amman in ansamun ta fara fad'a man price d'in kafin tasa akawo,aikuwa kaman yadda nayi zaton zai yi kudi sai gashi tace man ansamu price din zai kama 40k,ai sai kawai nace ta barshi yayi ta rigimar in ya gaji ya daina,aikuwa yaron nan ya kaunaci Allah ya hana man zaman lpy dole na samo mashi wani karami dan 5k ai koda nakai mashi sai yayi wurgi dashi wai shi bai son shi har ya d'an fashe da yake roba ne,ya ban haushi na zane shi,aikuwa sai na k'ara tado ma kaina rigima dole na koma lallashin shi nace ya fara amfani da wannan d'in babanshi Zakee yana can k'asar da ake saida waccan da yake so zan mashi waya in zai dawo zai kawo masa,shine fa nasamu ya shafa man lpy,wai d'azun da nike fad'a ma Feenah zanxo wurinka in na fito yaron nan ashe bai manta ba da yake banzan kai ne dashi kaman naka,bai mantuwa kawae sai yaje ya sanyo takalma wai zaizo ya kar6i kwamfuta d'in shi wurin Baba zakee tunda ya dawo,kasan Allah ni nama manta,dubara ta fad'o man nace mashi wannan wanda zani ba shine baba zakee ba shi H,zakee sunanshi baiji na fad'a ma Momynshi ba,yace shi H,zakeen baida ita,nace mashi eh ai shi tare muka dawo daga Abuja ba shine a k'asan da ake saida computer din ba,shine fa na samu na gudo,feenah nata man Dariya" Sigh haisam yayi yace"ai da ka siya masa tunda zai masa amfani,from d way kai describing nashi it will help him learn things easily so kudinsa ba abun damuwa bane" "Uhm kudinsa kam abun damuwa ne,ka kuwa san da kudin zaka mallaki buhun shinkafa harma ka hada da d'an galan d'in mai,koda yake kai fa ba siyan shinkafar kake bama shiyasa zaka ce hakan,kyale sa kawae yanzu ba komai dama ake so akuma samu ba,rayuwan yayi tsada ta abinci ake ba wani abun wasa ba" k'ura masa ido haisam yayi ya cije lip d'insa na kasa kaman ba zai kara cewa komae ba, "Da kana yaro me ka ta6a nema ka rasa Abbas? shine kai yanzu za kai denying yaro abunda yake so" sosae Abbas ya kyalkyace da daria "wuuuh h,zakee kai fa na manta you don't give up easily,shi yasa ko da muna skul abokan adawan ka na debate ke shan wuya,is hardly ai nasara akan ka,kai baka ganin rayuwan yayi tsada yanzu," girgixa kai haisam yayi"kawai dae zaka cutar man yaro,thank God he has another father,ka turo man picture din toy en,akwae computers da za'a turo man next week zan tura masu su bincika masa sai a hado man nasan baza'a rasa ba,koda ba exact irinshi nasan za'a samu mai irin features din shi" Abbas yace"ah haba ka rabu dashi wllh...."haisam ya katse shi da fad'in"ina ruwanka ne,wait Abbas....,badai so kake ka nuna man iyakata a gun yarona ba..."da sauri Abbas ya daga hannuwanshi alamar ban hakuri yace"Apology baban Abdul "ta6e baki haisam yayi kafin yace"Don ma he's too young ai da ta gasken za'a kawo masa,don so nike ya zama expert tun yanzu don babanshi zai gada shima Computer engineer zai zama insha Allah" "Allahu yashaa,Hakan nada kyau ai daman kyan d'a ya gaji mahaifinsa"Abbas ya fad'a yana murmushi don kar ya k'ara wani laifin,shi dai Haisam d'an ta6e baki yayi ba tare da yace masa komae ba. "Wani zaka kawo ma computers ne? Abbas ya tambaya, "yeah,wani company ne a lagos suka ban contract zan je nayi masu aiki but sai kayan sun iso"haisam ya bashi amsa, "Allah ya kawo su lafiya,ya bada sa'a,kaga ba don mun koma aiki ba ai danayi rakiya" d'an murmushi haisam yayi yace"ai in zanje zan bi flight d'in yamma ne ran friday,inason yin komae within weekend zuwa Monday sai in dawo,kagan just rana d'aya ne bazaka aikin ba" Abbas yace"alright sir,zan dauki excuse,Allah ya kaimu" "Ameen" ya amsa,daga haka Abbas ya fara kokarin mikewa"bari na wuce Zakee inason zan biya round din Gra ne,Allah ya baka lpy ya kiyaye gaba" mik'ewa haisam yayi,Abbas na fad'in ya bar rakiyar yace ba matsala ai yasamu sauki sosae suje ya rakashi wajen,suna fitowa waje inda yayi parking motarshi ya tuna da wata magana da yake son yi ma Haisam d'in hakan yasa suka haye saman boot d'in Motar suka zauna don suyi maganar,suna cikin tattaunawa kamar ance haisam ya waiga gefensa ya hango Fatuu na tahowa daga bayansu dayake Motar Abbas din gab da shiga kwanar gate din ya parker ta, bata shiga cikin lungun gate d'in ba,underneath his breath yace"here she comes"kallonshi Abbas yayi"wa?"haisam bai kaiga bashi amsa ba ta zagayo inda suke hannunta ruke da bokitin ruwa,jikinta na sanye da riga da skirt na atampa yayin da ta yafa d'an gyalenta na gado saman kai,kitsonta sun zuba gaban kan,har lokacin ba'a idasa kitson ba don daga baya gashin a fake yake yayi tum,aje bokitin tayi a gabansu ta zuba ma Abbas ido shima bin ta yayi da ido yana kallonta. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *4️⃣1️⃣* A hankali ta fara matsawa kusa da Haisam,a gefenshi ta tsaya,kasa kasa da murya tace"Ya handsome bak'o kayi?"kafin ya bata amsa Abbas ya rigashi"ba bak'o bane dan'uwansa ne Mom zarah"waro ido tayi baki bud'e take kallonshi,mamaki ne ya kamata jin yace mata Mom zaraah,nufo inda yake tayi ta tsaya agabanshi tace"kenan Yaya Handsome ya baka labarina?"kai ya d'aga mata"Eh yace wai munyi sabuwar Mom",tafin hannuwanta tasa ta rufe baki tana dariya alamar mamaki, "To kai ma sunan mamanka gare ni ne?fatuu ta tambaya bayan ta cire hannun, "Ba kiji nace ni dan'uwansa bane,ai Mom dinmu daya..." tun kafin ya rufe baki ta fara jefa masa wani kallo irin ban yarda ba d'in nan, "kenan kana nufin kaima Senator babanka ne?"cike da tuhuma tayi tambayar,kai ya daga mata alamar eh, Juyawa tayi ta kalli Haisam daya sadda kai yana latsa waya kafin ta juyo tana kallon Abbas wanda ya d'an k'ankance ido fuskarsa d'auke da Murmushi yana d'an girgiza kai,ganin hakan yasa ta buga kafa cike da shagwa6a tace"Wllh ban yarda ba,kamm yo ya zanga wake da shinkafa amman kace man wai gidanku d'aya",Sosae Abbas ke 6a66aka dariya jin abunda tace,tsagaitawa yayi"waye wake waye shinkafar"tana turo baki tace"yo kai da kake baki ai kaine waken shi kuma da yake fari shine shinkafar", "To ai ni Senator na biyo shi kuma sai ya biyo Mom dinmu, ko baki ta6a ganin senator din bane?" shiru tayi tana kallonshi still bata yarda ba"to amman ni ai shi kadai nasani anan,kuma shima baice man yana da wani dan'uwa ba anan,kuma ko gwaggota da hajiya ma basu fad'i man ba", "To k'ilan dae bakuyi Maganar da zasu sanar dake hakan bane,amman ni dan'uwansa ne Uwarmu daya Ubanmu daya" ya k'arasa yanata Murmushi,kallonshi kawae take ba don ta yarda ba,ganin yanata faman zabga murmushi yasa ta fara bubbuga k'afa tana jujjuya kai sai kace wata yar k'aramar yarinya,murya kaman zatayi kuka tace"bafa kyau k'arya kuma kai babba ne kasani,don Allah ka fad'i man kai waye"a marairaice tayi maganar,karfin halinta ba k'aramin Dariya yake ba Abbas ba,ganin tana ta masa magiya yace"Owk,bari in fad'i maki gaskiya to daman wasa nike maki,ni Amininsa ne tare mukayi Senior Secondary anan garin amman yanzu mu mun wuce abokai yan'uwa ne"washe baki tayi"daman nasan ba gaskiya kake fad'a man ba,kenan kaima kaman Haulatu ne", "Wacece haka?Abbas ya tambaya, "nima Aminiya tace yanzu haka makarantarmu d'aya da ita kaman yayata take" jinjina kai yayi, taci gaba"muna ta yin anko da Yaya Handsome,kaga shima awurin kakarshi yake nima haka,sannan yana da Amini nima ina da Aminiya"ta kai maganar tana ta dariya duk dimples dinta sun lotsa,shima dariyar yake mata, "To kai ya sunanka?" "Sunana Abbas", jinjina kai tayi ta kuma cewa"A nan garin kake?" kai ya daga mata alamar eh, "To ina ne gidanku?" "Gidana dae,a Fatima shema Estate nike,kinsan wurin ko?", "Ina dae jin sunan amman ban ta6a zuwa ba,ka ce anan gidanka yake,kana da aure ne?" Kai ya d'aga"ina da Aure sunan matata Nafeesat kuma inada yaro guda d'aya sunanshi Abdul"hannu fatuu tasa ta ruke ha6a alamar mamaki,a hankali ta juya ta kalli haisam wanda har lokacin kanshi na k'asa yana latsa waya tamkar bai jin ma abunda suke tattaunawa, D'an matsawa tayi kusa da Abbas kasa kasa da murya tace"to ya akai shi bai yi auren ba?" Abbas na niyyar bata amsa haisam ya d'ago fuska a d'an d'aure yace"Zaraah!"a firgice ta juya ta kalleshi,"ba aiken ki akai ba?"da sauri ta kai hannu ta d'auki bokitin ruwan ta juya zata tafi,Abbas dake guntse dariya yace"Ah Mom ya haka kuma d'anki ne fa shi ai ke yakamata ki bashi umarni ko"juyowa tayi tana mashi wani kallo"da ya baka labarina bai gaya maka akwae yarjejiniyar gidan yari tsakaninmu ba"daga haka tayi gaba,Abbas kau dariya yasa harda dafe ciki,ganin yadda ruwan keta zubowa yana jik'a mata k'asan skirt yasa shi d'aga murya"Mom ki d'aura saman kai mana"bata juyo ba hannu tasa tana nuna mashi tudun gashinta dake afake alamar bazai bari ta d'aura ruwan akan ba, K'ara daga murya yayi"to Mom zaraah sai yaushe zamu kara had'uwa mu gaisa",d'an juyowa tayi ganin haisam d'in ya maida kan k'asa yasata dakatawa ta aje ruwan"yaushe zaka k'ara dawowa?"ta tambayeshi, "Kowane lokaci,ina yawan zuwa ai", "To kaga wannan gidan mai kiosk shine gidanmu,idan kazo kana son ka ganni nan zaka zo,kace a kira maka Fatuu,in kuma ba wanda zaka aika ka shigo ciki kawae,in kaga gwaggota sai kace mata kai Abokin Yaya Handsome ne wurina kazo...." tana ganin haisam yana niyyar d'agowa ta kai hannu da sauri ta d'auki bucket din ta juya, Sosae Abbas keta dariya don maganar tata dariya ta bashi wai in bai samu wanda zai aika ba ya shigo kawae yace ita yake nema sai kace wani zararre,kallon haisam yayi wanda ya d'ago yana kallonshi don duk maganganun da suke yana jinsu dama shima Abbas din bakinshi sake yake,d'an ta6e baki yayi yana girgiza kai,Abbas yace"yo kai H,zakee ashe Mom d'in naka kwarkwar ce"gaba daya suka sa dariya, Bayan ya tsagaita da yin dariyar yace"let me take my leave zakee,magrib ma ya kusa",atare suka saukko daga kan boot d'in,Abbas ya zagaya side din driver shi kuma haisam ya tsaya a other side d'in, "Gaskia Abbas kaci mota,motan ya tsufa,wai a haka yan matan naka suke shiga?" Har Abbas ya kai hannu zai bude kopar motan ya dakata"yo kar yarinya ta shiga in akwae kamarta a gidansu"fuskarsa d'auke da murmushi yayi maganar, "I thought so,sai dae babun"haisam ya fad'a da murmushi daga haka Abbas ya bud'e motar ya shige suka sake yin sallama yaja Motar bayan ya tafi haisam ya juya ya koma gida. _____________________ Washegari Juma'a,misalin karfe 11 na safe Hajiya ta kira gwaggo tace mata in Fateema ta dawo daga Makaranta tazo zasu je Unguwa,cike da girmamawa Gwaggo ta amsa mata da toh. Bayan sallan Juma'a,Hajiya zaune ita da Haisam saman Dining suna cin lunch,Haisam yasha shadda gizner Ash colour hannunsa sanye da wani hadaddan Diamond watch,kafarsa sanye cikin dakakkun takalma na zallar fata suma Ash,Hajjaju ma ansha atamfa babbar Holland kunnanta sanye da yan kunnan zinari harda sark'arsu da zobuna tayi d'aurin kallabi irin nasu na dattawa,kamshi ne kawae ke tashi daga jikinsu, Bakinta d'auke da sallama ta shigo,gaba daya suka juya suna kallon entry d'in,tana hango su a Dining area ta nufi can,har ta isa idanunsu na a kanta, "Tubarkallah,maa sha Allah,wannan kwalliya haka Fateema,kice saboda kinci gayu yasa yau ba ayi man irin sallamar da aka saba ba" Cike da jin kunya tasa tafin hannuwanta ta rufe fuska tana dariya,sanye take da riga da skirt na lace brown mai d'auke da kwalliyan fulawoyi Coffee brown,ta yafa gyale coffee yau Allah ya yi ta canza gyale, kafafunta na sanye da takalma masu tudu bak'ake hannunta ruke da yar k'aramar bak'ar jaka,yayin da wuyanta ke sanye da sarka mai kyau da yan kunnanta harda yan hannu,tayi kwalliya harda jan baki maroon,haka kitsonta an ida mata shi ta zubo shi ta gaba har ya wuce kirjinta,cikin kayanta ne na sallan bara tasa,ta Matuk'ar yin kyau,kalan lace din ya hau da fatar jikinta sosae,ganin tana ta tsayuwa Hajiya tace"Zo ki zauna kema kici abincin"cire tafukan tayi daga kan fuskan ta k'arasa wurin table d'in,dama saboda zumudin zasu fita unguwa ita da hajiya lokacin da gwaggo ta sanar da ita yasa ta kasa zama taci abinci,kujera taja ta zauna idonta akan haisam dake cin Abinci a nutse,Saude hajiya ta fara kwala ma kira don tazo tayi serving fatun,A hankali haisam ya cira kai ya kalli side d'in da take,suna had'a ido ta sakar mashi murmushi"Yaya handsome ina wuni"jinjina mata kai kawae yayi don akwae abinci a bakinshi,daga haka ya maido idanunshi kan Abincin, Fitowa Saude tayi jikinta sanye da doguwar rigar shadda,ba karamin kyau tayi ba sai kace ba mai aiki ba,tsaf tsaf da ita tayi d'aurin kallabi mai kyau,tana karasowa Dining d'in tun kafin tayi magana hajiya tace"ki zuba ma fateema abinci"amsawa tayi da toh,ta kalli fatun"inyee wannan kyau haka fateema"Saude ta fad'a fusakarta da murmushi,itama fatun murmushin take,janyo katuwar Warmer d'in dake kan table din tayi ta bud'e,White rice ce tasha peas da green beans harda carrot gwanin ban sha'awa,Plate ta daukko ta zuba mata sai da ta tambayeta in ya isa Fatun ta ce eh,sannan ta rufe Warmer d'in ta bud'e ta biyu,jar miya ce taji uban nama kitif da ita ta zuba mata a saman shinkafar, sannan ta kuma janyo wata warmer d'in yar babba ta bude,farfesun kaza ne ciki sai uban k'amshi ke tashi,cikin wani d'an bowl ta zuba mata sannan ta rufe,nuna ma fatuu coleslow tayi"gashi nan kisa wanda zai ishe ki"fatuu ta amsa da toh,bayan ta gama zuba mata komae ta tsiyaya mata Ginger Drink a Cup daga haka tace"Aci lafiya"tana shirin juyawa Hajiya ta dakatar da ita"ki d'aukko ma haisam lemu wai ginger d'in tayi mashi yaji"kallon haisam din Saude tayi"Wanne iri za'a daukko?" batare daya d'ago ba ya bata amsa"Coke",amsawa tayi da toh,daga haka taje ta kawo masa,kallon hajiya tayi cikin girmamawa"akwae abunda za'ayi?"hannu ta d'aga mata alamar taje. Sam fatuu ta kasa sakewa taci Abinci yadda ta saba ci,idonta na akan haisam tana kallon yadda yake tsakuran nashi,hakan yasa itama take ci a hankali,hajiya ta lura da bata sake ba kuma tasan saboda haisam d'inne don taga yadda take ta kallon abincin da yake d'ebowa, Gyaran murya Hajiya tayi, hakan yasa duk suka d'ago suna kallonta,kallon fatuu tayi tace"muyi yar rigen cinyewa Fateema,wanda ya riga shi yayi nasara"aikam tana fad'in hakan fatuu ta fara yin loma da sauri,itama Hajiyar lomar take sai dai bata kai ta fatun ba,shi kam haisam zuba masu ido yayi cike da mamakin yadda suke tura abinci a baki,kan kace mi Fatuu ta cinye,kyalkyacewa tayi da Dariya tana fad'in ita tayi Nasara,d'an girgiza kai haisam yayi ya fara kokarin mik'ewa,kallon fatuu hajiya tayi"yi maza kisha ginger d'in,dashi wai zaku fita"da sauri ta kalli haisam don ta fahimci inda zasu,a tunaninta hajiyar bata san ina zasu ba,mikewa tayi bayan tasha ginger d'in ta bi bayan haisam da tuni ya bar wurin, "Don Allah haisam kasa hulan ka an fi ganinka da kamala,akan kabar wannan gashin awaje kasa manyan kaya" d'aga mata kai yayi ba tare daya juyo ba,nufar kujerar da ya aje hulan shi lokacin da suka dawo masallaci yayi ya dauki hulan wadda ash colour ce itama,sawa yayi saman kan ya d'an dannata ta d'an shiga sai dae duk rabin sumar ta fito ta gefe gefe da bayan kan hakan kuma ba k'aramin kyau ya k'ara masa ba,daga haka ya nufi kopar fita daga falon fatuu dake tsaye tana jiransa ta rufa masa baya hajiya na masu adawo lpy. Yana isa bakin parking spot ya juya yace ma fatuu ta jira,shiga yayi ciki ya nufi wata jeep ash colour sai d'aukar ido take,ba kowace mota bace fa ce Motar da ya za6ar ma Hajiya shekaranjiya har an kawota jiya da yamma yau da safe tahir d'in ya koma,budeta yayi ya shiga ya fara kokarin fiddota waje,fatuu dae sai bin motar take da kallo don sam bata ta6a ganinta ba,sai dae bata yi mamakin ganintan ba don gidan hajiya bai rabuwa da bak'in Motoci,bayan ya fito cikin harabar yasa hannu ya bud'e kopar dake gefenshi fatuu na ganin haka ta matsa gaban kopar tayi tsaye tana kallonshi, "Sai nace ki shigo ne?" jin haka yasa da sauri ta haye ciki,bayan ta shiga tasa hannu ta jawo kopar a hankali, "Bai rufu ba,ki bud'e ki sake rufewa da karfi",yin yadda yace tayi,sai dae har lokacin bata rufun ba,rankwafawa yayi don ya rufe da kanshi,da sauri fatuu ta kame jikinta ajikin seat ta runtse idanunta, don sai taga kaman zai had'a jikinshi da nata ne,dakatawa yayi cike da mamaki yake kallonta,a hankali ta fara bud'e idanun,lokaci guda ya fahimci dalilin da yasa tayi hakan,hannunshi ya d'aga yana nuna mata kopan idonshi a kanta yace"bai rufu bane shine zan gyara", jinjina mashi kai tayi,maimakon ya gyaran sai kawai ya juya ya fita daga cikin Motan ya zagaya side d'in da taken ya bud'e kopar ya sake rufewa sannan ya koma cikin motan daga haka ya tasheta,fuu ya tunkari gate din da tuni Officer ya zuge masu shi suka fuce. G.R.A POLICE STATION Slowly ya parker motar agaban Station din,hannu ya kai ya d'auki wayarsa dake aje a gefe yayi dialing number din Sp khamis,tana fara ringing yayi picking bayan yayi masa sallama ya sanar dashi yana a waje, Ba'a dau wani lokaci ba Sp ya fito jikinshi na sanye da Uniform bai dad'e da ya zo station d'in ba,don yanzu a Police headquarter yake aiki, saboda case d'in haisam yazo,haisam na ganinshi ya bud'e motan ya fito,nufo shi yayi yana fad'in"H,zakee d big COE",hannu haisam ya mik'a masa suka gaisa fuskan kowannansu d'auke da murmushi,bayan sun gama gaisawa Sp khamis yabi motan da haisam yazo da ita da ido"H,zakee kune mota,duk wata hadaddar mota da ta amsa sunanta ku ake fara gani da ita,gaskia Motan nan ta tafi da ni Ma sha Allah",haisam dake d'an Murmushi yace"ka shiga kawae,bai da wani tsada..."wani kallo Sp ya bishi dashi"haba zakee ai koda ni makaho ne dana laluba jikin motan nan wllh zan gane mai kudi ce" kafin haisam yace wani abu Fatuu ta fito daga cikin motan ta zagayo inda suke atsaye idonta akan Sp, "Wow,what a beautiful girl", gaidashi tayi ya amsa yace"ya sunanki?"tace"Zarah", "Fatima zahrah,ya School kina zuwa ko?" kai ta d'aga mashi alamar eh, Kallon haisam yayi"is she d girl?"kai haisam ya d'aga masa alamar eh,jinjina kai Sp yayi kafin yace"let's get in"jerawa suka yi da haisam,yayi ma fatuu alamar ta biyo su,bin bayansun tayi suka nufi cikin station din,Office d'in DPO ya nufa dasu, A zaune suka iske dpo d'in bayan sun shiga yana cikin duba wasu files,nuna masu kujerun dake agaban table sp yayi alamar su zauna,hannu dpo ya mik'o ma haisam bayan ya d'ago suka gaisa,gaishe da shi Fatuu tayi,fuska a sake ya amsa mata kafin yace"Fine girl,what's ur name?"fuskarta da Murmushi tace"Zarah"jinjina kai yayi,ya maida idonsa kan Sp,bayaninsu yayi mashi nan take ya gane case d'in,hannu ya kai ya jawo wani file gabanshi,bude ciki yayi yana sake duba statement d'in haisam kafin ya dago ya bada Umarnin a kawo mashi su gaye,lekawa cikin corridor din Sp yayi yace "Sergeant" da hanzari Sergeant d'in yazo gabanshi hadi da sara mashi,umarnin kawo su gaye ya bashi daga haka ya dawo cikin Office din, After few minutes sai ga su gaye an shigo dasu da ganinsu sunji jiki sosae,don farko da aka kamosu aka fadi masu laifin da ake tuhumarsu dashi sai suka karyata don basu san waye ya kawo kararsun ba,shi kuma Sp yasan haisam bai ta6a yi masu karya,ko ba haka ba gama shaidar raunin da haisam d'in yaji,sai da suka ci na jaki sannan sukai confessing,tun lokacin suke cikin mawuyacin hali don ba wanda yayi yunkurin zuwa belinsu jin babban laifin da sukae yunkurin aikatawa,a k'asa suka zube kan gwuiwoyinsu, Kallon Fatuu Dpo yayi"kinsan wad'annan"kai ta daga mashi alamar eh, "Mi sukai maki?"gyara zama tayi ta fara kora mashi bayanin yadda sukai yunkurin yi mata fyade a kango" jinjina kai dpo yayi"tun farko ya akai kika san su"shiru tayi ta d'an saci kallon haisam dake opposite da ita,alamar ta fad'i masa yayi mata da kai,nan take ta juya ta fara kora mashi bayani tun daga kan glass da ta fasa ma haisam har zuwanta kangon,ta k'arasa sai faman nishi take, Kallon su gaye dpo yayi fuska a murtuke yace"gaskiya ne abunda ta fad'a" inda inda suka fara Sp ya kwatsa masu tsawa nan take goga ya fara magana don Gaye gaba d'aya ya firgice,tsoronshi kar ace za'a kaisu kotu don yasan daga can sai gidan yari,tsananin tashin hankali ne akan fuskarshi, "Yalla6ai hakane,duk abunda ta fad'a gaskiya ne,amman wllh sharrin shaidan ne bada niyya ba...."da sauri Fatuu ta katseshi"Wllh karyane,kar ka yadda yalla6ai so yake ya maida kai sakarai baka san aikin ka ba,Allah da niyya sukae kokarin yi man fyaden,shi wanccan gayen shine baiso ayi mun ba,yace a kyaleni don Allah don babban laifi ne hukuncinshi daurin rai ne,amman wannan katoton banzan gogo ne ko miye sunanshi ma yace sai yayi",ta k'arasa tana ta nishi ta kumburo baki,gyalenta gaba d'aya ma ya dawo hannunta don da tana bayanin har d'an yunkurawa take kaman zata mik'e daga kan kujeran,Sp khamis sai faman Murmushi yake don confidence din yarinyar ya burge shi,irinsu zai yi matukar wuya a cucesu suyi shiru, A kausashe Dpo ya fara magana idonshi akan su goga"akwae wani shaidan da ya wuce ku masu lalata yaran mutane,duk irin yadda aketa fadakarwa da gargad'i amma abanza bakwa ji ko,kun lalata rayuwarku da shaye shaye hakan bai ishe ku ba sai kunbi yaran mutane kuna lalatawa,to tunda bazaku daina ba mukuma bazamu yi kasa a gwiwa ba wurin ganin an yanke ma duk wanda yake aikata irin wannan laifin hukunci,Don ubanku duk sai kunje gidan yari",a fusace ya kai maganar,gaba dayansu suka rud'e,gaye har ya fara kuka,kwalla nata zubowa daga idanunshi,magiya suka shiga yi ma dpo suna sun tuba bazasu kara ba, "Yalla6ai ka wa Allah da manzonsa ka yafe mana,wllh ba halinmu bane sharrin zuciya ne,amman munyi alkawari bazamu sake yunkurin aikata hakan ga kowacce yar......" tun kafin goga ya rufe baki fatuu ta katseshi a fusace"sa6a lamba(sarar su ce a makaranta da mutum yayi k'arya ko ya fad'i abu ba daidai ba,sai suce sa6a lamba),karyane yalla6ai,wllh k'arya yake lokacin da suke k'okarin yi man fyaden wannan gayen na hanashi cewa yayi wllh sai yayi wai rabonshi da ya samu irin damar tun akan wata hajara,to yalla6ai sunan Akuya ne hajaran ba mutum ba?kar ka yarda wayo zai maka"ta k'arasa tana ta huci tana hararar goga,kaman zata kai mashi bugu,hannu Dpo ya d'aga mata alamar ta zauna"it's Okey,bazan bari suyi man wayo ba,nagode da bayani" shi kam Sp khamis d'an juyar da kanshi yayi yana dariya,haisam dai na zaune yayi shiru kanshi na kallon k'asa yanata sauraransu don yasan abunda yafi hakan Fatuu zata fada ne. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oummu Imam)~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *4️⃣2️⃣* Kallonsu Dpo yayi tun kafin ma yayi magana goga yasha jinin jikinshi sai faman zare ido yake, "Wacece ita hajarar??"zare ido goga yayi ya fara inda inda,hannu Sp ya d'aga zai kwasa mashi mari da sauri goga ya idasa durkushewa yace"zanyi bayani..." sauke hannu Sp yayi fusakarshi a d'aure yace "uhun" alamar yayi magana, Juyawa yayi ya kalli Dpo"Yalla6ai ita wannan Hajarar wllh ba fyade nayi mata ba,dama ita ta saba,yar talla ce in dae za ka siye abunta to zata baka had'in kai da ka buk'aci hakan,sau d'aya wani abu ya shiga tsakanina da ita,kuma ko lokacin ta riga ta saba kuma tun daga nan ban k'ara yin wani abu da ita ba,an ma dad'e da hakan ta faru,ni yanzu ma wllh bansan a ina take ba ga 6aure nan ka tambayeshi wllh zai fad'a maka gaskiya don shima yasan hajarar kuma shima wani abu ya ta6a shiga tsakaninsu", gaba d'aya idanunsu suka koma kan 6aure dake ta zaro ido yayi wuri wuri,tun kafin ma a tambayeshi ya fara magana"Wllh yalla6ai duk abunda ya fad'a gaskiya ne,yanzu mu bama musan a ina take ba", Jinjina kae Dpo yayi,a kausashe ya fara magana"I don't care da ta saba ko bata saba ba,all i know is that kun bada gudummawa wurin lalata rayuwar ita yarinyar,Ku yanzu idan k'anwarku ce ko diyarku zaku so ai mata haka?wato don ita ba wata bace a wurinku shiyasa baku damu da yadda rayuwarta zata kasance ba saboda tsabagen mugunta,kun manta da cewar duk abunda kayi ma yar wani kaima za'ayi ma yarka ko kanwarka ko ma matarka,yanzu idan ku ka auri mata irin ita hajaran na tabbatar bazaku zauna da ita ba,in kuma kun zauna da itan tofa zata rayu ne cikin Wulakanci da kaskanci saboda ta riga ta saida mutuncinta tun awaje bakuyi wannan tunanin ba akan ita hajaran da kuka aikata ma hakan ba saboda son zuciya,kuma da kuke cewa an dade da kuka aikata hakan gareta ai ba bari kukai ba tunda gashi yanzu kunzo kuna yunkurin aikata ma Wata"dakatawa yayi yana maida numfashi,su haisam dae sun natsu suna saurararshi yaci gaba"Addininmu addini ne na yanci,ya bamu damar auren mata daga daya har zuwa hudu,idan son abun kuke why not bazaku yi aure ba...." Fatuu ta katse shi tace"atoh"tayi maganar had'i da gyad'a kae,kallon k'asan ido haisam yayi mata da sauri ta sadda kai, Dpo ya d'aura"gaba daya kun bi kun lalata rayuwarku,look at u don Allah,sam baku da wani buri kuna matasa masu jini a jika amman kuna neman kashe rayuwarku,ku kalle ni,ku kalli kowa dake wurin nan muma mutane ne kaman ku, inda munso sai muma mu lalata tamu rayuwar amman bamu za6i yin hakan ba don munsan ba hanya bace mai 6ullewa,mun tsaya munyi karatu gashi yanzu muna cin ribarshi,gaba daya munyi aure muna da iyali kowa girmama mu yake,kufa ba wani uba na gari da zai baku auren diyarshi a irin halin da kuke ciki,mutane gudunku suke saboda kun zama tamkar liability a garesu da kun gansu sun san da wuya in baku rok'e su kudi ba,yan siyasa su yi amfani daku don su ci za6e a d'irka maku kwayoyi don kuyi hatsaniyar da zata sa dole su ci,da zarar sun samu mulkin shikenan amfaninku ya k'are a wurinsu,wani kuda ku ganshi sai dae ko a TV,yana can yana jin dadi shi da iyalinshi,Wani fa ko da mahaifiyarka da ta tsugunna ta haifeka har yaci moriyarka kaje magashiyyan rai hannun Allah da sunan kana son ganinshi ya taimaka maka baza'a ta6a bari ka ganshi ba,kana ji kana gani karshe sai dae ta fadi ta mutu a gabanka akan wasu yan Kud'in da dakun tsaya kun gyara rayuwarku wallahi tallahi kunfi karfinsu,ko dama ba duka ba baku rasa wata hanyar da zaku samu,ina maku wannan Nasihar ne ba wai don bani da aikin yi ba ko ba za'a yanke maku hukunci ba,na kuma tabbatar ba lalle ku d'auka ba,sai dae duk wani wanda aka kawo mana nan ina kokarin ganin nayi mashi Nasiha,idan Allah yasa yana da sauran dama agaba in ya gadama yayi amfani da ita in bai gadama ba yayi watsi da ita,Amman mu munfi son ayi amfani da itan don ba dad'i muke ji ba ayi ta kawo mana masu laifi,burinmu kowa ya zamo nagari"d'an dakatawa yayi,a hankali fatuu ta kalli haisam ganin ba ita yake kallo ba yasa ta kalli Dpo tace"Yalla6ai,d'azun naji kace duk kuna da mata da ya'ya,shifa Yaya Handsome bai yi aure ba har yanzu" tun da yayi maganar ashe abun ya tsaya mata,tana son tayi masa magana tsoron kallon da haisam yayi mata d'azun ne yasa tayi shiru,amman sam ta kasa jurewaa saida ta tanka, d'an Murmushi Dpon ya yi, don daga d'an zaman da suka yi tsaf ya karanci halin Fatuu, "To ai k'ilan ra'ayin auren ne shi Yaya h......", kasa fad'in sunan yayi don bai fahimci yadda tace ba,kallon haisam yayi"wai ya sunan yake ne?"kafin ya bashi amsa Sp ya rigashi"Haisam ne sunanshi,ita naji kaman Handsome take cewa"ya k'arasa yana dariya, jinjina kai Dpo yayi da d'an murmushi yaci gaba"Yauwa to kilan bai tashi yin auren bane,amman nasan yana da kudin yin auren tunda yana aiki ko"kai ta d'aga"eh yana aiki "gyad'a kai Dpo yayi"to kinga shima yayi karatunshi yana aikinshi,su wad'annan sun ki tsayawa su yi karatun balle suci moriyarshi,kan Naira hamsin sai su fitar ma junansu jini" dan kya6e baki tayi tana kallon su goga, "Yanzu Sp ina ganin kawae zamuyi filing case d'inne mu mik'a su kotu...." tun kafin ya rufe baki Gaye ya d'aura hannu aka"Don girman Allah yalla6ai ka rufa man asiri,wallahi tallahi ni ba ruwana ba yadda banyi dasu ba akan kar ayi mata ko itama ta fad'i hakan"yana yin shiru Goga ya kar6e"Yalla6ai mun tuba,a yafe mana don Allah zamu yi amfani da nasihar da kayi mana,dama wllh ba wanda ya ta6a zaunar damu ya nuna mana illar abunda muke yi shiyasa...."tun kafin ya rufe baki Dpo ya daka mashi tsawa"karya kake,har ni zaka fad'i ma hakan,duk irin fadakarwar da ake yi ba dare ba rana a kafafen sadarwa, besides,baku da iyayene?ko kana son kace man suna jin dad'in halin da kuka jefa rayuwarku??" shuru goga yayi ya duk'ar da kanshi,sai lokacin haisam ya d'ago ya kallesu tun bayan da aka shigo dasu,Calmly ya fara magana yana nuna gaye"shi wannan babanshi ma is an Imam a Juma'at mosque dake nan Unguwarmu"girgiza kai suka shiga yi gaba dayan su, "Look at it pls,kana d'an liman kake wannan rayuwar ina amfani don Allah,na tabbatar banda fad'a da yake ma har zubar da kwallarshi bai rasa yi akan ka....."hannu fatuu ta d'an daga alamar zatayi magana,har saida gaban su goga ya fad'i rass duk da basu san abunda zata fad'a ba,kallonta sukai gaba daya Dpo yace"Zarah akwae abunda kike son cewa ne?" kai ta d'aga mashi"na tuno wani abu ne,ai na fad'i maka shi wannan gayen baiso ba ko,shi wanccan gagon ne ya matsa masa,to lokacin da yace mashi a kyaleni babban laifine sai kuma yace na san gidansu in suka aikata man Asirinsu zai tonu ne,to shi gagon sai cewa yayi wai shi wawa ne da zai bari asirinsu ya tonu,wai akwae abunda zasu yi,shine yace ma gayen ya kawo kunnansa ya rad'a masa wata magana ni dae bansan miya ce mashi ba amman naga gayen ya firgita ya zaro ido yana girgiza mashi kai alamar a'a,to Yalla6ai ka tambayesu kaji miye yace zasu yi man don kusan abunda suke aikatawa in suka yi fyaden don kar a gane su",tun kafin takai k'arshen maganarta cikin gaye yayi wani kuka ji kake kuuuu,gaba daya suka shiga tsantsar tashin hankali,da ka kalli fuskokinsu zaka gane basu da gaskia, Gaba daya idanun kowa ya dawo kansu alamar su ake jira suyi magana,su kam sai faman zare ido suke,gaye tuni jikinshi ya fara kerma,a hankali goga ke dan ta6a cinyarshi alamar ya natsu amman ina tuni zufa ta fara wanke mashi fuska, "Bazakuyi magana bane,miye zaku yi mata bayan kun yi mata fyaden wanda bazai sa agane ku ba???"Dpo ne yayi maganar ya tsaresu da ido ba alamun wasa atattare dashi,inda inda suka fara an rasa wanda zai yi magana sai faman zungurin gaye goga ke yi alamar kada ya fad'a,suna cikin hakan ta bayansu ba zato ba tsammani Sp ya shiga faffaska masu mari hannu bibbiyu,gaba dayansu sai da suka baje suna ta faman zabga salati, Furiously Sp yace"zaku yi magana ko sai ansa ku" gaye ne ya d'ago yana motsa baki kamar zai yi magana,sai dai tsoro ya hanashi, "Kai naga kafi su gaskia,tell me miye yace zaku yi mata" Dpo ya fad'a yana kallon Gaye,baki na kerma ya soma cewa"Yalla6ai zan fad'i maka gaskiya,amman don Allah na rokeka ka yafe man,wllh ni ba ruwana"kai ya d'aga masa alamar to,kafin yace"ina jinka" Duk yadda goga yaso hana gaye ya k'asa,don gaba daya idanunsu na akan gayen,cikin en ina gaye ya fara magana "C...ce...cew...cewa ya..yi in munyi mata mu k....kashheta" Wata zabura fatuu tayi lokaci guda kallabinta ya fad'o kasa,ya rage daga ita sai riga da skirt din jikinta dama gyalenta tuni yabar jikinta,lokaci guda ta furgice ta gigice,kwayar idonta kaman zasu fad'o kasa,ta matukar razana,nan da nan jikinta ya fara rawa kamar mai jin sanyi da kyar ta iya bud'e baki ta fara magana"Yalla6ai DOP kaji da kashe ni zasu yi in sunyi man fyaden,Yaya handsome da baka zo ba kashe ni zasu yi...."maido idonta tayi kan Sp"d'ayan Yalla6ai kaji wai kashe ni suka so yi acikin kangon in sun gama...."baiwar Allah duk ta furgice,sai kiran Dpo take da dop,dama tunda zasu shigo taga sunanshi asaman kopan shiga office d'in,gaba daya hankalinsu ya matukar tashi haik'am da jin abunda su gaye sukai niyyar aikata ma fatuu,gaye kam kuka yake wi wi yana fad'in shi ba ruwanshi wllh,Wata gigitacciyar tsawa Sp ya kwatsa masa had'i da buga table"ka rufe mana baki,idan ba ruwanka uban miyasa ka bashi had'in kai,shi ubanka ne da zai tursasa maka dole ka aikata ba daidai ba,ko ubanka yace ka aikata ba daidai ba ba'ace kai masa biyayya ba bare wani,duk zaku yabawa aya zakinta wllh", shi dae dpo zuru yayi yana kallonsu hakan yasa goga fara yi mashi magana"Wallahi tallahi Yalla6ai,na rantse da sarkin da yake busan numfashi ba ina nufin zamu aikata mata hakan bane,shi gaye ne naga kaman bazai bamu hadin kai ba saboda ta sanshi,shiyasa na fad'i masa hakan,amman wllh bani da niyyar kashe ta kaji na rantse"Dpo da yayi still yana sauraranshi ya daki table yace"Ubanku zaku ci"d'ago kai yayi ya kwalama sergeant dake bakin kopa kira,shigowa yayi ya sara mashi,dpo yace"take dem back,where is corpral Gajere?", "Ya fita siyo abu ne", "Ok,in ya dawo tell him to have meeting with dem", "Okey Sir"daga haka ya tasa su gaba,gaye nata kuka shida 6aure,goga kam idanunsa sun kad'a sunyi jawur tsananin tashin hankali,Allah sarki Gaye,dama ance son zuciya bacin zuciya,Saboda kar a hanashi kayan maye ya jefa kansa a tsaka mai wuya,Allah ya rabamu da aikata aikin danasani,Ameen. Ana fita dasu gaye fatuu dake tsaye tayi tsuru har lokacin jikinta kerma yake,ta kalli Dpo tace"Yalla6ai Dop fitsari nike ji"jinjina kai yayi kafin yace wani abu Sp ya leka waje yana kwalama Corpral Jummai kira,ba tare da 6ata lokaci ba jumman tazo sanye cikin uniform,tana da d'an tsawo da jiki,hakan yasa kayan suka yi mata cuf cuf,sara masu tayi had'i da fadin"Sir",nuna mata Fatuu Sp yayi"ki kaita Toilet ",ta amsa da Ok,daga haka ta nufi fatuu idanunta akan haisam da ya sadda kai yana ta6a wayarsa,ruko hannun fatuu tayi tace ma haisam" Barka da rana",Slowly ya d'ago suka had'a ido,cikin cool voice dinsa yace"Yauwa,ya aiki",da sauri tace"Alhamdulillah,gamu a cikinsa",kai kawae ya jinjina kafin ya maida idonsa kan wayarsa,still dpo yayi yana kallonta,shikam Sp khamis juyar da kanshi yayi yana dariya,cikin ransa yake fad'in"su jummai anga kyakkyawa", Tsaye Jummai tayi tana jiran fatuu ta fito daga cikin toilet",fitowa tayi tana gyara skirt dinta,jummai ta kalleta da murmushi"har kin gama?" kai fatuu ta d'aga mata, "Ya sunanki ne" tace"Fateema"dama abunda yasa tace ma su Dpo sunanta Zarah saboda haisam ne kada ta fad'i sunan mamanshi a gabanshi,jinjina kai corpral jummai tayi,kafin tace"Wannan da kuka zo dashi yayanki ne?" kai ta kara d'aga mata, Inda inda jummai ta shiga yi kafin ta kuma cewa"kinsan Number d'in wayarshi ki bani?"wani kallo fatuu tabi ta dashi har sai da tasha jinin jikinta,a hankali ta girgiza mata kai"ni bansan number din shi ba,nida ba waya gare ni ba", Hannu jummai ta kai ta dafa kafadarta"Ok muje,amman karki fad'a ma kowa na tambayi no dinshi kinji",a hankali tace toh,uhmm jummai bata san wacece fatuu ba,ba don halin da fatun take ciki ba nasan tana komawa cikin Office din sai ta fallasa ta, Suna zuwa bakin office din,jummai tace mata ta shiga ita kuma ta wuce,bayan fatuu ta shiga iske su tayi su ukkun suna cikin tattaunawa,nuna mata kujerar da ta tashi Sp yayi alamar ta zauna,idonta akan haisam ta zauna,d'an kallonta yayi kafin ya janye idonshi,gyaran murya Dpo yayi"Kema Zarah kina da laifi"a firgice ta kalleshi,yaci gaba"miyasa zaki je wurinsu karfe goman dare bacin kinsan me suke aikatawa awurin,ko bama shaye-shaye suke ba bai kamata kije wurin wani a irin wannan lokacin ba",ta marairaice fuska kaman zatayi kuka tace"ai ni banyi tunanin zai cutar dani ba don ko hannuna bai ta6a kamawa ba shiyasa naje,amman Yaya Handsome yayi man fad'a ya kuma ce ko yayana ma wanda muke uwa daya uba daya zai iya cutar dani,yanzu bazan kara yarda da kowa ba,duk wanda ya ta6a man jiki yaya handsome yace in fad'i ma gwaggota kuma yace har shima",jinjina kai sukayi bayan ta gama,dpo yace"Gud,kuma ki daina rashin ji,in ba haka ba duk ranar da aka kawo mana ke zamu kulleki ne"a rude tace"ai na daina tuntuni wllh yanzu ba ruwana ka tambayi yaya handsome ma", "Owk,kin kyauta,yanzu ina son zaki yi mana aiki..." zaro ido tayi"kana nufin in zama yar sanda?"d'aga mata kai yayi da sauri tace"to ai ni fa likita nike son zama ya zaka ce kuma in zama yar sanda", "Ai lafiya lou,dama mutum zai iya yin aiki biyu,kuma ai sai kin girma zaki zama likitan shi kuma aikin yar sandar yanzu zaki yi mana shi" Sp ne yayi maganar, Kallon Dpo tayi"to na yarda,mi zanyi?" "Yauwa,zaki zama Jami'ar mu ta sirri ne,ina son kisa mana ido anan unguwar taku,duk wanda kika ga ya shiga kango da wata indae kinsan yarinyar to ki ruga gidansu ki fadi ma iyayenta,in kuma baki sansu ba to kije ki fad'i ma yayanki cewa kinga wani ya shiga da wata kango kar kice zaki bisu fa,sannan k'awayenki da kuke tare suma ki fad'i masu abunda yayanki ya fad'a maki game da yadda zasu kare kansu kuma kada su yarda da kowa", "To zanyi,sai abani kayan yan sandan nima"yar dariya su kae harda haisam, "to ai ke aikin sirri zaki yi mana,in kika sa Uniform kuma ai za'a gane ke yar sanda ce,kuma kinga masu aikata laifin zasu guji aikatawa a inda zaki gansu,wasu kuma suna iya zuwa gida suce zasu yi maki wani abun,amman kinga in babu Uniform d'in ba wanda zai sani sai iya mu kawae"kai ta d'aga mashi cike da gamsuwa, "To Albashi fa" gaba daya suka tuntsire da dariya shi dae haisam d'an Murmushi yayi,Sp yace"ai mun zata zaki yi mana kyauta ne,to ga yaya handsome ne shi zai rink'a biyanki" zaro ido tayi"shi kuma,a'a abarshi to zanyi kyauta",had'a baki sukai wurin ce mata sun gode, daga haka haisam ya kalli Dpo"Sir,are u done wit her?" d'aga mashi kai yayi"yes"kallon fatuu yayi gently yace"Zarah ki jirani a Mota"kai ta d'aga mashi daga haka ta mike ta nufi hanyar fita,Sp yace"ba ki d'auki gyalenki ba"sam ta manta ma da tazo da wani gyale harda yar jakarta duk suna akasa,komawa tayi ta d'aukko daga haka ta fuce su Dpo na mata sai anjima, Bayan fitarta suka ci gaba da tattaunawa akan su Gaye,da shi haisam tunkan su zo ma ya sanar da Sp so yake a yafe masu tunda basu kaiga aikatawa ba,ayi masu horo sannan suyi rubutun cewa bazasu kara ba sai kuma ga wata babbar maganar,don haka yace ma Dpo ya bar komae a wurinsu su yanke masu hukuncin da ya dace kawae,duk hadin kan da suke bukata zai basu,daga haka suka yi sallama da Dpo din suka fito, Atare suka nufo cikin station d'in bayan sun fito daga cikin corridorn Office d'in Dpo, "Kawai ni a tura mu kotun zaifi don wasa da hankali zai tayi mun,tun yaushe yake cewa a k'ara mashi lokaci zai kawo amman shiru" atare Sp da Haisam suka juya inda suka ji anyi maganar,wani babban mutum ne sanye da malum malum a tsaye gaban kanta yake yin maganar daga gabanshi kuma wani dattijo ne sanye cikin tsohon yadi duk yaji jiki kanshi sanye da wata tsohuwar hula duk ta yankwane gashin fuskarshi da kanshi duk hurhura, "Sergeant mike faruwa ne?" Sp ne yayi tambayar, "Sir game da case din su Alhaji Ubale ne,shi wanda zai kawo masa kudin gashi nan ya zo,sai dae dubu biyar kawae ya kawo,to shine yace wai a tura su court kawae" jinjina kai Sp yayi yana niyyar juyawa su tafi muryar dattijon ta katse mashi hanzarinsa"Yalla6ai wallahi tallahi bani da halin kudinne ba irin kokarin da banyi ba don insamo su in kawo amman abun yaci tura,wannan dubu biyar din ma dana kawo wllh yar wayata ce naje na sayar,yanzu haka gidana ko abincin rana ba'ayi ba ga yarana guda biyu kwance,don su na siyar da wayar amman saboda ba yarda zanyi na kawo kudin nan"cikin karyayyar murya yake magana,yana kaiwa karshe kwalla suka fara zubo mashi yasa tafin hannunshi yana gogewa,ba k'aramin sanyi jikin Sp yayi ba,kallon Sergeant yayi"let me come back"daga haka suka fita, tunkarar inda motar haisam take sukai bayan sun fito daga cikin station din, "Miye case dinshi ne?" haisam ne yayi tambayar idonshi akan hanya, "Wllh wai wannan Alhajin ne ke yin gini a unguwarsu shine yaronshi da abokinshi suka je gidan suka sace kofofi da winduna so bayan asirin yaran ya tonu an kamosu shine aka yi ma abubuwan da suka sata kudi don tuni sun salwantar dasu,to shi d'ayan yaron mahaifinshi ya biya,wannan dattijon ya rage ya biya nasu,d'azun da nazo ne na iske shi Alhajin nata korafin wai sau ukku ana mashi uzurin ya kawo bai kawo ba,lokacin dattijon bai kaiga zuwa ba" jinjina kai kawae haisam yayi a lokacin suka iso bakin motar,jingina bayanshi yayi da murfin motar ya kalli Sp,"Nawa ne kudin?" "Gaba daya 150k ne so da aka raba kowa zai bada 70k an cire 10k" d'aga kai haisam yayi kafin ya maida idonshi kan wayarshi dake a hannunshi ya fara daddannata, "Your Account no pls", "U mean my account details?"Sp dake kallonshi ya tambaya,kai haisam ya daga mashi ba tare da ya d'ago ba,nan take ya fara karanto mashi acct details din, Da sauri Sp yasa hannu cikin trouser pocket dinsa ya fiddo wayarsa jin k'arar shigowar message,duba wayar yayi da sauri ya dago ya kalli haisam"naga ka turo kudi har 200k,na minene?" A nutse yace"kaba mutumin 150k sai ya biya kudin sauran kuma ya yi amfani dasu"daga haka ya juya yana k'okarin bude Motar, "What about d remaining 50k,mi za'ayi da ita?",banza yayi mashi,ganin hakan yasa Sp k'ara tambayarshi don yayi tunanin ko bai ji shi bane,d'age mashi kafada yayi"i ave no idea"lokaci guda sp ya gane bashi yayi,shine ba zai iya fadi mashi hakan ba, Girgiza kai Sp yayi" H,zakee u will never change",fuskar haisam da d'an Murmushi yace"I was born like dat"hannu Sp ya kai ya d'an bugi shoulder dinshi suka yi dariya gaba daya da alama wata sarar su ce ,godiya ya shiga yi mashi sosae shi dae bai tanka mashi ba,saima bud'e mota da yayi ya shige, Lek'awa ciki Sp ya yi"To sabuwar ma'aikaciyarmu sai munji daga gareki ko"da fara'a yayi maganar,kai kawae fatuu dake zaune ta d'an kwantar da kanta ajikin seat ta d'aga mashi,daga haka sukayi sallama da haisam ya tashi Motar Sp na d'aga masu hannu ya jata suka tafi. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *_RAMADAN KAREEM_☪️* _Allah ya kar6i ibadunmu yasa muna daga cikin yantattun bayi,Amin ya Sami'ud dua🤲_ *4️⃣3️⃣* Lokacin da Sp khamis ya koma ciki dattijon nan nata matsar kwalla don kuwa Alhaji Ubale ya matsa akan a turasu kotu kawae, "Ya Allah na dogara da kai,fadar kace,duk wanda ya dogara da kai ka isar masa,Ya Ubangijina kafi kowa sanin halin da nake ciki na rashi,nayi imani da jarabani da kake yi, nasan ba don baka sona bane sai don ka gwada imanina,Allah ka shirya man yarona da ya saka ni acikin wannan halin da Sauran Al'ummar Annabi(S.A.W)", Dattijon na gama yin Addu'ar ya kalli Sergeant cike da k'warin gwuiwa yace"Ku tura mu kotun,duk da nasan ko anje banda halin biyanshi, Amman ubangijin dana dogara dashi nasan zai kawo man Mafita",ta6e baki Alhaji Ubale yayi ya juyar da kanshi gefe irin ko ajikin shin nan, duk wannan abun akan idon Sp,yaji duk maganganun da dattijon yayi,nufar inda suke ya yi fuskarshi d'auke da Murmushi,yana isa gaban Dattijon ya mik'a masa hannu,kasa kama hannun SP yayi ya bishi da ido yana mashi kallon mamaki,hakan yasa SP jinjina mashi kai alamar ya bashi hannun,jiki na kerma ya mik'a masa hannu suka yi musabaha SP yace"hak'ika fad'ar Allah ce acikin Suratul D'alaq aya ta ukku'....Waman yatawakkalu alallahi fa huwa hasbuun....,ka dogara dashi ya kuma isar maka ta hanyar kawo maka Mafita"fuskar Sp d'auke da Murmushi yake maganar don ba k'aramin burgeshi dattijon ya yi ba, gaba d'aya bin Sp sukayi da ido cikin rashin fahimtar abunda yake nufi,dattijon kuwa har lokacin hannunshi dake acikin na Sp sai kerma yake yi, "Baba Mutumin da muka fita tare dashi ya baka Kud'in,ya turo su ta Account d'ina don ka biya shi" lokaci guda su Sergeant suka fara sakin Murmushi had'i da fad'in Alhamdulillah,don suma ba k'aramin tausayi dattijon ya basu ba, Murya na rawa ya fara Magana"Yalla6ai ban fahimce ka ba,wani ya biya Kud'in kace? ko dae ba daidai kunnena suka ji ba?" "Baba daidai kaji,ai kasan bazan zolaye kaba da magana irin wannan kuma a irin wannan lokacin" jin hakan yasa dattijon duk'awa k'asa yayi Sujjadar godiya ga Allah ,mik'ewa yayi hawaye cike a idanuwansa"Don Allah waye wannan d'an arzikin,waye mai kirkin nan haka,bai sanni ba, hakanan ya d'auki wannan uban Kud'in ya bani...."yana Maganar kwallan idonshi na zubowa ga kuma Murmushi yana yi duk alokaci d'aya,Sp shima dake Murmushi yace"Baba kada ka damu da sai kasan ko waye,don Allah ya baka", "Nasani Yalla6ai,amman dae yakamata ai insan waye wanda yayi man wannan abun alkhairin da bazan ta6a mantawa ba asauran rayuwar data rage man", "Ok shikenan tunda kana son sanin ko waye bari in fad'i maka,Sunan shi Haisam,shi d'an gidan Senator Ali Adamu Zakee ne" Sp na rufe baki Alhaji Ubale ya kar6e, "ahaf d'an gidan dan siyasa ne dake kan mulki,su da ake satar kudinmu ana tara masu ai dole su rinka bada su yadda suka gadama.....", Wata gigitacciyar tsawa Sp ya kwatsa mashi"Enough!!!kai ka tabbatar kud'in sata ne ya bada?shikenan duk wani mai mulki ya zama 6arawo?idan har cikin mutane akwae na kirki da kuma na banza to tabbas suma shuwagabannin dole asamu na kirki da kuma na banzan tunda daga cikin mutanen ake za6arsu,kuma da kake maganar wai an tara mashi,tabbas kuwa zancenka gaskiya ne an tara masa,sai dai ina son ka sani kud'in halal aka tara masa,kowa anan nasan ya san Mahaifinsa Shahararren mai kud'i ne wanda ya tara dukiyar da har su kare rayuwarsu zata ishesu yin rayuwa cikin jin dad'i,amman hakan bai hana Wannan bawan Allahn tashi ya nemi na kansa ba,injiniya ne na na'ura mai kwakwalwa,aiki yake ba dare ba rana,Kamfanoni da Manyan Ma'aikatu har ma da kananu wad'anda suka danganci aikinsa dake a Jahohin k'asar nan ake gayyatarsa yaje yayi aiki ba tare da girman kai ba ana biyansa kudin da ba komae yake dasu ba face yin aikin Alkhairin da yafi kowanne lada kamar yadda Manzon Allah(S.A.W) yace,Ka Shigarwa da Mutum Farinciki a rayuwarsa,ko ka yaye masa bakinciki,ko ka d'auke masa wata damuwa,babu aikin da yafi Wannan lada,ban tsaya ina maka wannan dogon bayanin ba don baka cancanci hakan ba,inda naso zan iya sa a kulle man kai saboda wannan maganar da kayi akanshi,amman banyi hakan ba don nasan da yawan Mutane irin wannan tunanin naka garesu akan duk wani mai Mulki,a k'arshe ina mai gargad'inka da ka rink'a kiyaye harshen ka don Mutum irin wannan da kayi ma kazafi nada daraja ba awurin Mutane kawai ba har a wurin Ubangiji don yana daga cikin mafi Alkhairin mutane kaman yadda Manzon Allah(SAW) yace,khairun nas man yan faun nas,khairun nas anfa'uhun lin nas,(Mafi Alkhairin Mutane wanda yake amfanar mutane,mafi Alkhairin Mutane wanda Mutane suke amfanuwa dashi). Ranshi a Matukar 6ace ya k'arasa Maganar,shikam Alhaji Ubale yayi wuri wuri da ido sai faman bashi hakuri yake yana fad'in su6ul da baka ne,banza yayi mashi,ganin yanayinshi yasa su Sergeant had'a baki wurin fad'in"Sorry Sir," shima Dattijon Mutumin hakurin yake bashi,sai da ya d'auki d'an lokaci ba tare daya tanka masu ba kafin yaba Alhaji Ubale Umarnin ya fad'o masa Account details d'inshi,baki na rawa ya soma fad'i mashi,ba tare da 6ata lokaci ba Kudin suka shiga yace mashi ya duba,dubu 70 cuf ya gani ya d'ago ya fadi mashi cewa sun shigo,shiru Sp yayi mashi don ba k'aramin kule shi yayi ba,ba don ya kai Zuciya nesa ba da sai ya hukunta shi, k'okarin barin cikin Station d'in Alhaji Ubale ya fara,dakatar dashi Sergeant yayi"Hey,Alhaji waya baka izinin tafiya ne?"da sauri ya dawo yana fad'in"Oh kuyi hakuri pls,nazata shikenan" a rud'e ya yi Maganar, K'aton littafin da ke abud'e saman kanta Sergeant ya duk'a ya d'an yi rubutu kafin ya d'ago yaba Alhaji Ubale Umarnin yasa masu hannu,cikin kermar hannu ya fara sa hannun bayan ya gama Sergeant ya duba sai kuma ya kalli dattijon ya nuna masa inda zai sa hannu,bayan duk sun sa hannun yaba Alhajin Umarnin tafiya,hannu ya d'aga yana yi masu Sallama ya nufi Hanyar fita buguzum buguzum, Bayan fitarshi su Sergeant da dattijon suka shiga k'ara ba Sp hakuri,sauke ajiyar zuciya yayi yace masu ya wuce kawae,daga haka ya bukaci su zauna saman wani benci dake acan gefe shida dattijon,bayan sun zauna ne yayi masa bayanin ainihin kud'in da aka bashi,ya nuna mashi dalilin da yasa bai fadi mashi tun farko ba don yana ganin hakan na bukatar sirri ne don haka yanzu idan yana da Account ya bashi details dinshi zai tura mashi cikon dubu tamanin din, Jin dattijon yayi mashi shiru ne yasa shi kallonshi yace"Baba kaji abunda nace?"shiru har lokacin bai ce uffan ba,hakan yasa Sp kai hannu saman kafadarshi ya d'an girgiza shi had'i da fad'in"Baba!"gaba d'aya Mutumin ya kifo jikin Sp,cikin tsananin tashin hankali ya d'ago shi yanata faman girgiza shi had'i da fad'in"Baba!Baba!!...."da alama fa kaman ba rai a jikin Mutumin,a rud'e Sp ya juya gun su Sergeant da k'arfi yace"Sergeant Bala pls come and help me!" suna jin haka suka zagayo da sauri inda su Sp suke,suma jijjiga dattijon suka shiga yi Sp dake kallonsu cikin tashin hankali yace"Sergeant ya Mutu ko?innalillahi wa'inna ilaihir rajiun....", Sergeant dake tatta6a jikin Mutumin yace"I don't think ya Mutu sir,da alama suma yayi ne..."da sauri Sp yaba Inspector dake k'okarin k'arasowa inda suke Umarnin kawo masu ruwa,ba tare da 6ata lokaci ba ya kawo masu pure water guda daya,cikin sa'a ana yayyafa ma Dattijon sai gashi ya farfado,Sosae Sp ya shiga yin murna yana fad'in Alhamdulillah don ya d'auka Mutumin ya mutu ne saboda irin hakan tasha faruwa saboda tsabar farinciki Mutum ya rasa ransa,ganin ya farfado yasa su Sergeant tambayar dalilin sumewar nashi,Sp bai 6oye masu ba yayi masu bayani,gaba d'aya suka shiga yin dariya harda Sp d'in don sunga ba k'aramin rud'ani ya shiga ba,anan ne Dattijon ke fad'i masu cewa tsabar farinciki ne yasa shi sumewa don ahalin da yake ciki bai ta6a tunanin wani zai mashi irin wannan kyautar ba,kwalla na zuba yake masu maganar,gaba daya sun jinjina ma kirkin Haisam lokaci guda suka ji ya kwanta masu a rai, Bayan su Sergeant sun bar wurin Sp ya sake tambayar ko yana da Account,dattijon yace eh yana da wanda ake biyansa albashi lokacin da yake yin aikin gadi,Sp yace ya bashi don ya tura masa kudin,karanto mashi Account no d'in yayi don k'arfin hali harda cewa wai Sp ya d'auki rabin kudin ya tura masa sauran,Murmushi kawae Sp yayi,maimakon ya dauki rabin sai shima ya k'ara masa dubu goma yace baza a barshi a baya ba a aikin ladan,kuka sosae Mutumin ya shiga yi yana k'ara gode ma Allah daya kawo masa Mafita ya kuma sa ya mallaki kud'i har Naira dubu 90 lokaci guda, Mikewa Sp yayi don tafiya yace mashi yazo ya rage mashi hanya,sai da ya tura ma Sergeant da corpral dubu biyar biyar kafin suka wuce su Sergeant nata faman yi mashi godiya,tabbas zancen Sp game da Haisam gaskiya ne,ta dalilinshi Mutum hudu sun kasance cikin Farinciki,Allah ka bamu ikon sanya ma Junanmu Farinciki a koda yaushe,Amin. Bayan sun hau hanya ne dattijon ya rok'i Sp da ya kira mashi haisam yayi mashi godiya tunda shi baida waya,Sp ya sanar dashi cewa ko ya kirashi ba lalle ya d'aga ba don yasan bai wuce ace za'ai mashi godiya ne dalilin kiran shi, kuma shi baison aita yi mashi godiya,dattijon yace a jaraba dae don yana Matuk'ar son yi mashi godiyar,kaman yadda Sp ya fad'a sau ukku yana kiran haisam d'in bai d'aga ba, a k'arshe yace ma dattijon kada ya damu da sai yayi mashi godiya ya gode ma Allah kawae,cigaba da tafiya sukae Mutumin na yima Sp yan tambayoyi game da haisam har yake ce mashi ba a Abuja Senator Alin yake bane,nan Sp ya sanar dashi cewa shi Haisam d'in a wurin Mahaifiyar Senator d'in yake anan garin wato Hajiya Hauwa Adamu Zakee, A bakin titi Sp ya sauke shi don sauri yake ya koma Headquater,kafin dattijon ya sauka Sp ya tambayeshi sunanshi yace mashi Sunanshi Malam Garba, "To Baba ina son in d'an baka shawara game da kudin nan daka samu in ba damuwa" baki na rawa yace"Ah haba yalla6ai ai ko Umarni ne kaban zan bi wllh", Murmushi Sp yayi"dama so nike in baka shawarar ka nemi Sana'a duk da bansan ko kana da wadda kake yi ba,amman nasan yanayin rayuwar yanzu ko sana'ar mutum ke yi in ba wata babba bace nan da nan sai kaga ta durkushe", "Hakane wllh,tabbas ina sana'ar yin faci tun bayan dana bar yin gadi kuma ba laifi ina samun yan kudaden yin hidindimun rayuwa,Allah cikin ikonsa kwanakin baya sai injin d'in da nike yin sana'ar ya lalace dama ya tsufa sosae haka ma kompressor din,koda na kai wurin gyara sai aka ce yayi kondem sai dae in sake wani,to yalla6ai kadae san yanayin rayuwar yanzu kudi basu taruwa in ba samunsu ake da yawa ba,lokacin banda wasu kudi da zan siya wani,a dole na hakuri naci gaba da noma wata yar gona da nike da ita acan kauyenmu to da amfaninta naci gaba da gudanar da rayuwata da ta iyalina,to matsalar da ance kaka ta wuce sai kaga anata fama,Amman dae Alhamdulillahi", Jinjina kai Sp yayi"To yanzu ina ganin sai ka siya sabon injin din facin ko", "Eh in sha Allahu abunda nike niyyar yi kenan,sannan akwae d'ana Habu yaron kirki ne,shi Allah yasa nutsattse ne ga hakuri,to yana da son yin sana'a tun ba yanzu ba,da ya samu yan kud'i sai kaga ya kafa trader a kopar gida bayan d'an lokaci kuma sai ta rushe saboda cinye mashi jarin da ake cikin gidan,to yanzu zan bud'e mashi dan kes sai azuba kaya sosae muga abunda Allah zai yi"fuskarshi d'auke da Murmushi ya k'arasa maganar, "Ma sha Allah hakan yayi sosae,Allah yasa Albarka a duka kasuwancin,shi kuma dan'uwan nashi kaci gaba da yi mashi Addu'a kar ka gaji in sha Allah zai shiryu shima", "Kullum acikin yi mashi Addu'a nike bama shi kadai ba,ina kuma da yakinin Allah zai amsa man wataran", jinjina kai Sp yayi"Allah ya amsa,yanzu zan baka kati na akwae lambar wayata ajiki tunda kaga ba waya gareka ba bamu san kudin ko sun shiga ba amman ina sa ran sun shiga ma,gashi baka tare da Atm card dinka da sai mu bincika awurin masu Pos,amman yanzu in ka koma gida sai ka daukko katin kaje a bincika aga in sun shiga,komi ake ciki sai ka sanar dani", "To,to in sha Allahu,ai Habu ma nada yar waya in na koma sai in amshe ta in sa layina inga ko sun turo man sakon sun shigan kafin inje in siya wata nima", daga haka suka yi sallama bayan ya amshi card d'in Sp yasa a Aljihun rigarsa,atare suka fito daga cikin Motar Sp ya tsaida masa Keke Napep ya biya masa kud'in,Mlm Garba nata faman cewa ya barshi ai akwae kud'in wayarsa daya saida sai ya biya cikinsu,Godiya sosae ya shiga yi masu shi da Haisam had'i da Addu'oi yana d'aga mashi hannu,har saida Napep d'in tayi nisa kana ya daina dagawa Sp hannu,daga haka Sp ya koma cikin Motar shi ya jata. **** **** **** **** Tun bayan da suka baro Police Station din ba wanda ya tanka ma wani a cikin su,idonshi na akan hanya yana ta driving yayin da Fatuu ta kwantar da kanta tana kallon gefen hanya,da ka kalleta zaka fahimci ba k'aramin Sanyi jikinta yayi ba,ta firgita sosae da jin abunda su Gaye sukai niyyar aikata mata, A hankali Haisam ya juya ya kalleta,d'an Murmushin gefen baki yayi ganin yadda duk tayi laushi sai kace ba ita ta tak'alo Maganar ba,A daidai gaban wani Babban Shopping Mall Haisam ya parker motar,kallon inda suka tsayan tayi kafin ta juya ta kalleshi, "Come out"Calmly yayi maganar kafin ya bud'e Motar ya fita,bud'ewa tayi itama ta fito ta yafa gyalenta asaman kai kallabin kuma na acikin Motar ta barshi,nufar cikin Mall d'in yayi ita kuma tayi tsaye bakin motar, tsayawa yayi ya juyo"What are waiting for?" jin hakan yasata bin bayanshi suka shiga ciki,wurin shopping carts ya nufa ya turo guda daya ya dawo inda take tsaye tanata faman kalle kalle, "muje"yace mata,wurin da Cosmetics suke ya nufa yana tsayawa wayarsa ta fara ringing,fiddota yayi daga cikin Aljihun rigarshi ya duba mai kiran nashi,kallon Fatuu yayi"ki fara selecting perfumes ina zuwa"daga haka ya juya ya nufi hanyar fita waje, After few minutes ya dawo,tsaye ya isketa a inda ya barta bata saka komae cikin cart d'in ba,wani kallo yabi ta dashi fuska a d'an daure yace"baki ji mi nace kiyi ba kafin in fita ne?", ta6e baki ta fara tana d'an jujjuya kai"to ni ai bansan wanda zan d'auka ba,bana ce maka irin na kwalbar fiya fiya muke amfani dashi ba,sai irin wanccan d'an dogon(body spray) shima gwaggo na siyo shi,kuma ma ni banta6a zuwa irin wurin nan ba a TV kawae nike gani",tana kai Maganar kwallah suka zubo mata sharrr,dama tunda ta fara Maganar idonta ke cike tab da kwalla,ahankali ta sadda kanta tana shessheka,still haisam yayi yana kallon ikon Allah, yanzu har yayi maganar da zata sa ta kuka ne?, Sigh yayi cikin sanyin murya ya kira sunanta"Zaraah",amsa mashi tayi ba tare da ta d'ago ba, "Zarah look at me",a hankali ta d'ago ta kalleshi, "na buge ki ne??"ya tambaya had'i da d'age mata gira,girgiza masa kai tayi alamar a'a, "to mi nayi da yasa kike kuka?" Cikin Muryar kuka tace"ba kai man komae ba Yaya Handsome,kukan ne ke zuwa da kanshi",har lokacin idanunshi na a kanta,ya lura tunda suka baro PS ranta a dagule yake,da ka kalleta zaka fahimci akwae damuwa atattare da ita, d'an matsawa yayi kusa da ita yace"is okey,mantawa nayi kin fad'a man,ki daina kukan",d'aga mashi kai tayi alamar toh daga haka tasa k'asan gyelenta tana share hawayen, da kanshi yasa hannu yana za6o turarurrukan,sealed guda ukku masu kyau da tsada ya d'auka sai body spray shima guda ukku,roll-on biyu duk ya zuba a cikin cart din,d'an matsawa yayi saitin mayuka nan ma set biyu ya d'auka harda na Olive,kowanne Complete set d'inshi ya d'auka su Body Cream,lotion,hair oil and lotion,conditioner,shampoo,soap,shower gel da dai sauransu harda Mouth freshner spray ya saka,abunda zai baka mamaki shine ya iya za6en abubuwan mata masu kyau wanda ko wata macen yar gayu ba lalle ta iya za6arsu ba,alamu yayi mata na ta biyo shi,lafiya lou ta tura cart d'in don taga yadda wasu ke tura nasu kuma ko a tv ma tana ganin yadda ake amfani dashi,6angaren Underwear ya tsaya,d'an shiru yayi yana kallon kayan wurin kafin ya kai hannu ya ciro wasu yan rigunan bacci masu kyau da taushi,dogaye guda biyu sai mai had'e da wando guda d'aya ya juya ya zuba su cikin cart d'in,kallon kayan ya sake yi sai kuma ya juyo ya kalli Fatuu wadda gaba d'aya hankalinta na a wani wuri ta d'aga kai tana ta kallon wurin har gyalenta ya sauka daga kanta,kai ido yayi inda yaga tana kallo,6angaren da jallabiyu suke ne ta k'ura ma ido tana ta kallon rigunan,tana bala'en son dogayen riguna,in taga mace tasata ta nad'a gyalen ko a tv ne burgeta take ita kuma guda d'aya gareta wata Brown,saboda yawan sawar da take mata yasa tuni ta tsufa,gyalen rigar ma gurin guga ta k'one shi, "Zarah"ya kirata,bata ji shi ba har saida ya maimaita kiranta da d'an karfi,firgit ta juyo ta kalleshi,hannunshi ya d'aga yana nuna saitin da undies d'in suke"in kina buk'atar wani abu anan ki d'auka"maida idonta tayi inda yake nuna matan,ai tana yin arba dasu bras da pants da sauri ta duk'ar da kanta kasa sai kace wadda taga wani mugun abu,zuba mata ido yayi yana kallon ikon Allah,ganin bata da niyyar d'agowa yasashi cewa"Don't u need anything?"d'aga mashi kai tayi da sauri,dan ta6e baki yayi hadi da d'an murmushin gefen baki,ashe tasan kunya ya ayyana a ranshi,gaba yayi abunsa bai dauki komae ba tunda tace bata buk'ata,har zai karya kwana ya juyo don yaji kaman bata biyoshi ba,aikuwa dai tana a inda ya barta har lokacin kanta na duk'e, "zaki kwana anan ne?"d'agowa tayi ta kalleshi ya d'age mata ido hakan yasa ta tura cart d'in tabi bayanshi,6angaren da Jallabiyun suke ya tsaya,itama ta tsaya, kallonta yayi yace"Choose d colours you want"zaro ido tayi,sai ta kalleshi sai kuma ta kalli rigunan, "baki ji bane?"da sauri ta d'aga hannu ta nuna wata Yellow,kallon rigan yayi sai kuma ya kalleta ya d'an yamutsa baki da alama bata yi mashi ba kuma da gani tayi mata yawa ma,sake kallonta yayi sama da k'asa kafin ya kai hannu ya curo wata Maroon mai ratsin brown,ya sake ciro wata Black sai kuma Red colour su kenan colours masu kyau da zasu yi mata,daga d'an gaban jallabiyun ya daukko wasu riga da skirt pink color sun matukar had'uwa kayan shima kyau suka yi mashi,alama yayi mata su tafi tabi bayanshi sai da ya tsaya 6angaren su Sweets ya d'ebo wasu chocolate masu kyau ya watsa acikin kayan,daga nan suka nufi wurin biya,card ya bada aka cire kud'in wanda ba k'ananun kudi ya kashe ba don ko iya dogayen rigunan da riga mai skirt wata 50k ce ta tafi banda sauran kayan,kwashe masu kayan aka yi acikin wata katuwan Shopping bag mai d'auke da tambarin Mall din,d'aya daga cikin ma'aikatan ya bisu da ledan har mota,Back door Haisam ya bud'e mashi ya saka masu daga haka yayi masu Godiya ya koma, ganin tana ta tsaye bata da niyyar shiga motan yace"Get into d car", yamutsa fuska tayi tace"k'ishin ruwa nake ji" juyawa yayi ya kalli gefen Mall d'in,akwae wasu shaguna ciki harda na kayan sanyi,kallonta yayi"am coming"daga haka ya nufi shagon ta bishi da ido,bai jima ba ya dawo hannunshi ruke da leda ya mik'a mata kafin ya zagaya ya bud'e motan itama ta shiga suka bar wurin. Har suka hau hanya sosae bata bud'e ledan ba Haisam da idonsa na kan titi yace"dama ba kishin kike ji ba kenan don ki wahalar dani ne ko?", kallonshi tayi"a'a da gaske ina ji", "So what are u waiting for da baki sha ba" a hankali ta bud'e ledan,bottle water ne had'i da babbar robar ice cream,fiddo ruwan tayi ta bud'e ta kafa baki tana sha,sai da tasha kusan rabi sannan ta cire robar daga bakinta ta rufe ta mayar da ita cikin ledan,shiru tayi sai ta kalli ice cream d'in sai kuma ta saci kallon haisam,can dai tasa hannu kaman mara gaskiya ta ciroshi,a hankali ta bud'e tasa d'an cokalin ta fara d'ebowa tana kaiwa bakinta,d'an juyowa haisam yayi ya kalleta aikuwa da sauri ta d'ago robar tana mik'a mashi,maida idonsa yayi kan hanya ba tare da ya amsa ba, "mi zanyi dashi",ya tambaya, "ka sha kaima", d'an guntun murmushi yayi, "baki ga ina driving bane....', katseshi tayi"to in rage maka?", waro ido yayi irin mamakin nan ya d'an k'ara kallonta kafin ya juya"ni bana shan saura ai"shiru tayi ta aje robar kan laps d'inta,ganin ta daina sha ya kalleta"ki sha abun ki,na k'oshi ne da zan sha"ya kai maganar had'i da d'an dage mata gira,jinjina mashi kai tayi taci gaba da sha a hankali. A daidai kopar gidansu ya tsaya,tana ganin haka ta fara k'okarin bud'e motar,kallon ledan sauran ice cream da ruwan data aje yayi"kije dasu"ba tare da tace komai ba tasa hannu ta d'auka ta had'a da kallabinta da yar jakarta ta fita,har zata rufo mashi kopar yace"ki d'auki kayan baya",barin kofar Motar tayi a bud'e ta bud'e ta bayan ta kinkimo ledan ta dawo gaban tana k'okarin shigar da ita,ganin abunda take yi ya dakatar da ita"Zaraah,i mean ki shiga dasu gida naki ne", waro ido tayi baki bud'e take kallonshi don ita tsakani da Allah bata yi tunanin kayanta bane ko da yace ta za6i kalar riga ta zata yana nufin ta za6ar mashi kaloli ne, "ki d'auke ina son in tafi"yayi maganar ganin ta kafe shi da idanu, Murya kaman zata yi kuka tace"to in Gwaggo tace ina na samo su fa?"wani kallo ya bita dashi jin wata tambaya mara kan gado da tayi mashi, k'ank'ance ido yayi yasa hannu yana shafa beard dinsa"kice mata wani Mutum ne kika had'u dashi shine yaje dake inda ake saida su ya siya maki", zaro ido tayi sosai cikin rawar murya tace"wani mutum kuma,ba kaine ka siya man ba", harararta yayi"Oh ashe kinsan hakan kike tambayana,C'mon d'auke su ki shiga gida",jiki a sanyaye ta fiddo ledan kayan waje ta aje ta a gefe,dawowa tayi don ta rufe masa kopar,suna had'a ido tace"Nagode",kai kawae ya d'aga mata sai kuma yace"kisa sauran kayan aciki don kiji dad'in d'auka, "to"tace ta rufo masa kopar da karfi,yin yadda yace tayi har ta nufi hanyar shiga gidan,ya kirata bayan ya sauke glass k'asa,aje ledan tayi ta komo bakin kopan tana kallonshi, "U look worried,ki saki ranki in ba haka ba grandma d'inki zatai ta tambayan ki abunda ke damunki,ko kina son tasan abunda ya faru ne?",da sauri tace"a'a" jinjina kai yayi yai mata alamar ta tafi da hannu,tana kaiwa bakin kopan shiga zauren gidan ta aje ledan ta juya ta kalli haisam da har lokacin bai ja motan ba kuma bai rufe glass d'in ba yanata kallonta,suna had'a ido tayi mashi Murmushi shima Murmushin ya maido mata,tunda suka je PS har suka dawo sai yanzu tayi Murmushi,hannu ta d'aga tana mashi bye bye hakan yasa shima ya d'an d'aga mata hannun daga haka ta d'auki ledan ta shige,yana ganin ta shige ciki yaja motan dama a kunne take,bai wuce gida ba reverse yayi ya mik'i hanya don zuwa gidan Abbas. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ _Barkanmu da Sallah,fatan kowa yayi sallah lpy,Allah ubangiji ya maimaita mana ya kar6i ibadunmu,Amin._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *4️⃣4️⃣* Tana shiga cikin gidan gwaggo ta fito daga cikin d'akinta hannunta ruke da parker da alama shara tayi dama gwaggo ba dai tsafta ba in dai tana gida bunu bunu ta share wuri ko ya taga d'an dirty,fuskarta d'auke da Murmushi ta nufo Fatuu tana fad'in"Yan unguwa har kun dawo",kai fatuu ta d'aga mata alamar eh ta nufi cikin gidan ita kuma gwaggo ta nufi inda dustbin yake ta zuba sharan kafin ta dawo tsakar gidan,a tsaye ta samu Fatun agaban d'akinta, tana zuwa inda take tace"to ki shiga cikin d'aki ki huta ko",ledar kayan ta nuna ma gwaggo tace"gashi", bin ledan kayan da ido gwaggon tayi tace"minene?", Shiru bata ba ta amsa ba, duk'awa tayi ta bud'e ledan tana duba kayan ciki,idasa durk'ushewa tayi tana k'ara bincike kayan,kallon fatuu tayi"kayan wanene haka?", K'yakkyafta idanu ta fara"wai nawa ne Yaya handsome ne ya siya man", da mamaki gwaggo ta k'ara kallon kayan kafin ta kuma kallon fatuu"daman dashi ku ka fita ne?, "Eh shi ya kaimu,to da muka dawo ne ya biya da mu kantin da ake saida kayan"ta k'arasa tana cigaba da kyakkyafta idanu, jinjina kai gwaggo tayi"duk wannan uban kaya haka,kai Haisam ba dai kirki ba wllh,shima kaman hajiya yake duk kirki ne dasu ga yin Alkhairi,Allah ya saka masu suma da alkhairi,amman fa fatuu bansan rok'o,kar kiga yana maki abu kice zaki rok'e shi"tayi Maganar idonta akan fatuu, da sauri fatun tace"Wllh gwaggo ban rokonshi,ko turaren da ya bani bana fad'a maki yadda akai ba,yanzun ma ban rok'e shi ba wllh,kinji na rantse", jinjina kai gwaggo tayi"ai dama bance rokonshi kikai ba nasan halinshi sarai haka yake, to amman dae ko ba yanzu ba banson ki rokeshi abu kin ji,kuma idan ya maki abu ki rink'a mashi godiya", amsa mata tayi da toh, gwaggo tace"to yanzun wad'annan uban mayukan kinma san yadda ake amfani dasu kuwa"fuskarta da fara'a tana kallon fatun ta fad'a, Yar dariya tayi tace"ai ajikinsu duk akwae sunayen kona miye da yadda ake amfani dasu in na karanta zan gane"gyad'a mata kai gwaggo tayi kafin ta kuma cewa"to ki kwashe ki kai d'aki,an dae gode wllh da gani ba kudi yan kad'an ya kashe ba,ji rigunan nan masu kyau dasu,to koma kibar su sai Sallah", turo baki tayi"ni dae so nike in sa,in sallan tazo ba sai kiyi man ba",d'an girgiza kai gwaggo tayi"don kawae baki son na huta,kud'in dinkin ba sai a siya wasu abubuwan ba",cike da tsokana gwaggon ke mata Maganar, "To zan aje guda d'aya,ai dae na rage maki ko,kuma in ban sawa ai kinga zai gani ko", Dariya gwaggo tayi"To shikenan mai wayau,nima wasa nike maki", dariya fatuu tayi,gwaggo tace ta kai kayan daki, "to gwaggo baki dau komai ba", mik'ewa tayi tana fad'in"to ni mi zan d'auka anan wannan duk sai ke,sai dae ko turare kuma tunda suna a gidan in ina buk'ata zanyi amfani da su", amsa mata tayi da to,daga haka ta d'auki ledan kayan ta nufi d'akinta dasu,har ta kusa shiga gwaggo ta tsaida ta, "Fatuu ki d'ebi ko kayan shafanne da turare ki kaima Haulatu", "To daman zan d'ibar mata" ta bata amsa daga haka ta shige cikin dakin, Lokacin da ta shiga cike da Murna ta fad'a saman gadonta,da duk damuwa ta hana tayi murnar,sai faman Murmushi take saki,zazzage kayan tayi saman gadon tana sake dubawa,sai faman sambatu take tana yaba kirkin haisam,saukkowa tayi ta fara kokarin gwada rigunan,ba k'aramin kyau suka yi mata ba,sun hau da fatarta sosae gashi duk sunyi mata daidai sai kace ya gwada mata ne kafin ya za6ar mata,guda d'aya ce bak'ar ta d'an so yi mata yawa itama ba sosae ba,data sa takalmi mai tudu zatayi mata daidai kuma ita ta yanke shawarar bari sai sallah don ta had'u sosae har wani d'aukan ido take,duk wadda tasa sai taje ta nuna ma gwaggo,cike da farinciki gwaggon ke yabawa don ba karamin dad'in kayan taji ba,kowa na jin dadi in yaga anyi ma nasa,ba kamar fatuu yar lelenta, **** **** **** Ranar Lahadi Misalin k'arfe ukku na rana haisam ya shigo cikin parlon Hajiya bakinshi dauke da sallama,hajiya dake zaune saman 3-seater ta d'an kishingid'a idanunta sanye cikin gilashi ta amsa mashi, juyawa tayi tana kallonshi har ya k'araso,agefenta ya zauna yana mata murmushi,itama murmushin take mayar masa, "Yau ba aikin latse latsenne naga ka fito"d'an kwantar da kanshi yayi"yea,ai gobe zanje Office", "Haka fa tunda kasamu sauki,Allah ya tsare gaba",can k'asan makwoshinshi ya amsa "Amin", shuru sukayi na d'an lokaci,to break the silence hajiya tace"ko akawo ma wani abu ka dan ta6a?", d'age mata gira yayi"not too long naci fa abinci", "Eh ai dama ba abincin nike nufi ba d'an abu mara nauyi haka da zaka d'an tauna",lumshe mata ido yayi nan take ta gane abunda yake nufi,Saude ta kwala ma kira ta bata umarnin kawo abun da zasu dan tauna,bada jimawa ba ta kawo masu meatballs cikin plate da fork hajiya ta amsa,tana k'okarin kinkimo sofa table hajiya ta dakatar da ita tace taje kawae,a tsakiyansu ta aje plate d'in tace mashi gashi nan ya ci,kai ya d'aga mata kafin yasa fork ya dau d'aya ya d'an gutsira yana chewing a hankali yana kallon Tv,itama hajiyar d'auka ta fara tana ci suna d'an yin fira,can ta kai hannu cikin sumar kanshi ta nutsa shi ciki"wai wannan sumar ba'a aske ta ne tayi tsawo da yawa,koda yake dole ai tayi tsawon tunda kud'i ake kashe mata,don ma a nad'e take wannan da ba k'aramin tsawo kitso zai yi ba in akayi maka", Wani kallo yayi mata da d'an murmushi"ko zaki man kitson ne", "In kana so ai sai in maka, kasan k'aramin aikina ne,sai dae ba lalle ma kitson ya tsaya akan wannan sumar ba ta cika santsi",ta k'arasa maganar har lokacin hannunta na acikin sumar tana d'an sosa mashi kan,shi dae murmushi kawae yake don abunda take mashin dama ta saba tun yana k'arami haka zata sa hannu cikin sumarshi tana sosa mashi,ba kamar in ranshi ya 6aci ko yayi fushi a haka take rarrashinshi, cire hannun tayi tace"ya kamata a rik'a rage maka ita, kaima kasha iska", Sigh yayi"ai ana rage shi,shiyasa kike ganinshi haka da yafi hakan sosae", jinjina kai tayi suka ci gaba da cin abunda ke gabansu sai dae ita shi yake bata a baki idonta akan tv, "Motan ki da kika ce zaki bada waye zaki ba?", maido idonta tayi kanshi"wani abu?, girgiza mata kai yayi"i just want know in akwae wanda zaki ba", "Eh,kawunku Mani nike son ba,don kwanaki da suka zo naga tashi ta fara tsufa dama tun wadda Senator ya basu ce,ko za kai wani abu da ita ne?"idasa cinye abunda ke bakinsa yayi kafin yace"No,ki bashi kawae,i thought baki fidda wanda zaki ba bane,da zan ba Abbas ne,amman zansa akawo mashi wani, "to ka bashin kawae,ai shima d'an gidane wani lokaci aba Manin" lumshe ido yayi yana d'an girgiza kai alamar a'a,shiru tayi tana kallonshi,tasan tunda ta ambaci wanda zata ba,zai yi wuya yayi amfani da ita, "To ba ni nace ka bashi ba" "Ki ba wanda kikai niyya rabonshi ne,za'a kawo ma Abbas d'in period",daga haka ya aje fork d'in asaman plate alamar ya k'oshi ya maida kanshi saitin tv,itama hajiyar kallon taci gaba da yi, "to mi zai hana ka kira Nameer,nasan baza'a rasa motan da basu amfani da ita acan Abujan ba tunda wasu aje suke kawae kaga sai ka tambayeshi in akwae lafiyayya sai aba Abbas d'in kawae",kai ya d'aga mata alamar toh batare da ya kalleta ba,ta kuma cewa"ko ni in kirashi kawae don nasan ma ba lalle ka kirashin ba", "Ba sai kin kira ba,zanyi abunda ya kamata",d'an ta6e baki tayi suka ci gaba da yin kallon, "Wai nikam Fateema ko Lafiya,jiya fa banga tazo gidan nan ba,yau ma gashi har yamma,ko tazo wurinka?"hajiya tayi maganar idonta akan haisam,girgiza mata kai yayi"tun Friday da nayi dropping nata ban k'ara ganinta ba", "To Allah yasa dae lpy,don in lafiya lafiya baka k'i ganinta agidan nan ba,ba kamar ma weekend",shi dae shiru yayi baice mata komai ba, can tace"kai bari dai in kira Dijen muji lafiya",juyawa tayi ta d'aukko wayarta akan hannun kujera ta fara k'okarin kiran Gwaggo,tana fara ringing ta d'auka,bayan sun gaisa take tambayarta lafiya bata ga Mutuniyarta ba cikin weekend d'innan,anan gwaggon ke sanar da ita cewa bata lafiya ne tun ranar Juma'a da zazza6i ta kwana,jiya jikin ya d'an yi tsanani don har sai da aka mata allura amman zuwa yau ta samu sauki sosae,salati hajiya tayi tace ai bata sani ba,tace agaida mata ita sai ta shigo dubata in Allah ya yarda,Gwaggon nace mata ai ba sai tazo ba tunda da sauk'i sosae a haka suka yi Sallama,cire wayar tayi daga kunnanta idonta akan haisam da tunda ta saki salati ya juyo yana kallonta,tace"kaji ashe wai bata lpy tun ranar juma'a da zazza6i ta kwana jiya jikin yayi tsanani har saida aka mata allura,amman dai tace da sauki", "Allah ya bata lafiya",yace still idanunsa akanta, hajiya taci gaba"aikam zuwa dubiya ya kama ni,ance wai ka gaida mai gaidaka,sam Fateema bata da kyaliya,kar kaso kaga yadda take tashin hankalinta in ban jin dadi,wani ciwo da nayi kwanaki tasani gaba tayi tana kuka wai bata so in Mutu"takai maganar tana dariya,shima d'an Murmushi yayi bai dai ce mata komae ba, "Ko zaka je ka dubata ne,kaga ma sai ku gaisa da Gwaggonta don ta sanka sosai,kaima nasan zaka santa,matar akwai kirki wllh",shiru ya d'an yi,hajiya ta bishi da ido can ya furta"Ok", "Yauwa,ka gano ya jikin nata,ko zuwa da daddare ne sai in lek'a",jinjina mata kai yayi daga haka ya mik'e,hajiya tace"in can d'in zaka ko Saude ta zuba abinci ka tafin mata dashi?" Wani kallo ya jefa ma hajiyan kaman harara"ni zaki aika da abinci", dariya tayi"wai ai naga kaima da baka lpy ta kawo maka abun dubiya ko", "Ba can zani ba yanzu sai after asr,in zaki bada abu akai mata ki bada"daga haka ya nufi hanyar fita hajiya nata dariya dama tsokana ce kawae tasan bazai ta6a daukar warmer din abinci ba da sunan zuwa dubiya, Yana isa part d'inshi ya fad'a toilet don yin wanka,after some minutes ya fito jikinsa sanye da Bathrobe ya nufi Closet dinshi,within few minutes ya shirya cikin Red polo shirt da farin Jeans itama rigar daga cikin collar dinta fari ne sai faman sakin daddad'an kamshi yake,a corridor ya tsaya yasa fararen takalma,Masha Allah shigar Red and White nasan ba sai na fad'i kyan da yayi cikin kayan ba,a parlor ya d'au wayarsa da ya aje lokacin da ya shigo daga haka ya nufi Masallaci da aka gama kiran sallan la'asar. Yana fitowa daga masallacin bayan an gama sallan ya nufi gidansu Fatuu,a bakin shagon Amadu ya tsaya shima bai dad'e da ya dawo daga sallar ba,yana ganin haisam d'in ya shiga washe baki yana gaidashi,hannu ya mik'a masa suka gaisa,cikin cool voice d'inshi yace mashi ya shiga ya sanar yazo duba Zarah ne,da sauri ya amsa mashi da toh kafin ya nufi cikin gidan,bai jima ba ya fito yace mashi ya shigo,atare suka shiga Amadu na gaba shi kuma yana binsa a nutse yake yin tafiyar har suka shiga ciki,suna shiga gwaggo dake abakin kopar d'akinta ta tarbeshi da fara'a"Maraba da d'ana Haisam",fuska a sake ya amsa mata nan take kuma ya ga ya santa da Hajiya,gashi ma har ta kirashi da d'anta,cikin d'akin tace mashi ya shigo wanda ke d'auke da gado six by six da wardrobe d'inshi mai gida biyu da d'an k'aramin Dressing Mirror sai kujera two seater da kuma one seater, d'akin sai k'amshin incense stick da aka kunna ke tashi,a bakin kopar d'akin ya cire takalmansa ya shiga da yar sallama,fuskar gwaggo da fara'a ta nuna masa kujera don ya zauna,bayan ya zauna ita kuma ta koma bakin gadon ta zauna,cikin muryarsa mai sanyi ya fara gaisar da ita ta amsa,shiru ya d'an yi can kuma ya d'ago don tunda ya shigo kanshi na a k'asa, "Ya mai jiki", "Ah maijiki da sauk'i sosae,oni Hajiya sai da ta taso ka ai nace mata ta samu sauki da bata wahalar da kai ba wllh", shi dai shiru yayi idonshi na kan floor d'in dakin,ita kam gwaggo idonta na akanshi bata ta6a tunanin zai zo gidan ba don iyakarta dashi su gaisa ne in yazo gidan hajiya, can tace"Mun ga d'awainiyar abun Arziki,inata son inzo in yi godiya wllh jikin nata ne ya hana,don jiya gaba d'aya bansamu na fita bama saboda jikin nata,yau nike niyyar in shigo da daddare sai kuma ga ka,da nasan zaka zo ai da tunda safe na shigo"fuskarta d'auke da fara'a take yin maganar, d'an guntun Murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba yace"ba wani abu ai", Godiya ta shiga yi mashi sosae tana shi mashi Albarka,tun yana amsawa kasa kasa har dae yayi shiru yana ci gaba da amsawa acikin ransa,tana cikin yin godiyar Amadu ya shigo dauke da plate ya d'auro ruwa pure water da yan k'ananun robobin lemu guda biyu don irinsu kawae yake saidawa saboda yan makaranta don ba freezer gareshi ba a shagon,a gaban haisam ya aje ya k'ara gaidashi kafin ya fita,shiru sukayi na d'an wani lokaci don Mutumin ba gwanin yin fira bane ba kaman kuma a inda yake bak'o, "Kasha mana", d'an d'agowa yayi"Nagode,bana jin kishi", gwaggo tace"duk da haka ya kamata kasha na zumunci,sai dae kuma kar in matsa ma bansan ko baka shan irinsu ba"da yar zolaya tayi Maganar, sai dae kuma tabbas bai shan ruwan leda da irin lemun da aka kawo masa don ba kowane irin lemu yake sha ba ko a gidansu,daurewa yayi ya cije ya d'auki ledan ruwan gwaggo tai saurin mik'ewa"bari in kawo maka Cup",tsayawa yayi don dama hakanan ya d'auka ba don yana son sha a ledan ba, dawowa tayi hannunta ruk'e da cup na jug mai kyau,ita ta zuba mashi ruwan kafin ta mik'a mashi ta koma inda ta tashi,kur6a yayi kaman sau ukku ya aje cup d'in,gwaggo dake kallonshi tace"da ina niyyar zubo abinci gashi ruwan ma ka k'i sha sosae",kallonta yayi da d'an Murmushi"a'a Nagode ban jima da naci ba", dariya gwaggon tayi tace"ai nasanka sarai baka son cin abinci shiyasa ma ban zubo ba", bai dai ce mata komae ba,can tace"gashi anzo gaida mara lafiyar tana ta bacci,bari in taso ta...."da sauri ya katseta"No a kyaleta,Allah ya bata lafiya"daga haka ya mike zai tafi, Shi ya fara fitowa yasa takalmanshi kafin Gwaggo ta biyo bayanshi tana ta faman godiyar zuwan da yayi,suna kaiwa tsakiyar gidan yaji an kwala mashi kira, "Ya Handsome", atare suka juya shi da gwaggo inda kiran ya fito,Fatuu ce tsaye a bakin kopar dakinta tana sanye da pink riga da skirt d'in da ya siya mata acikin kayannan kanta a bud'e,ba k'aramin kyau suka yi mata ba musamman skirt din box pleated ne irin mai fad'in nan mai tattara daga sama kuma bai kai har can k'asa ba,kayan sun mata cif a jiki ba kamar daba ramamma bace sai ta koma kamar rainon madara da bournvita itama koda yake rainon madarar shanu ce😂,Slowly ya nufi inda take,tsayawa yayi yana kallonta,ta d'an fad'a ba kamar idanunta da ka kallesu zaka gane bata lpy, "Ya handsome kai ne a gidanmu" ta fad'a tana mashi murmushi,kafin yace wani abu Gwaggo tace"Eh,ke yazo gaidawa da jiki", kallonshi tayi"to amman shine zaka tafi kuma baka ganni ba", dan Murmushi yayi calmly yace"kina bacci ne,ya jikin naki?" "na samu sauk'i",jinjina kai yayi, "To ka shigo d'akina tunda gaida ni kazo", still da Murmushi akan fuskarshi"to ba gaki na gan ki ba", turo baki tayi ta langwa6ar da kae"to ka shigo kaga d'akina",d'an bude mata idanu yayi,tana ganin hakan ta fara mashi magiya harda buga kafafu,shi dae still yayi yana kallon ikon Allah, "Ina ruwan Fatuu uwar rikici tana lafiya ma ya aka cika balle bata lpy,ka shiga d'ana Haisam"Gwaggo dake jingine da bangon d'akinta ta fad'a,dariya fatuu ta fara"to an dae ce ka shigo ato", d'an girgiza kai yayi kafin ya fara k'okarin cire takalmanshi gwaggon na cewa ya shiga dasu amman saida ya cire,sai da ya d'an duk'a da zai shiga cikin d'akin,tsaye yayi atsakiyar d'akin bayan ya shiga,ita kuwa sai faman dariyar jin dad'i take yau Yaya Handsome acikin dakinta, "Ya handsome kaga dakina ni kadai nike kwana acikinshi,wannan kayan fa cikin na Mamata ne da ta rasu aka bani gado"Murmushi yayi yana bin d'akin da kallo, "gashi ma baki gyarawa"da sauri ta juya tana kallon dakin kafin ta juyo"wllh kuwa ina gyarawa fa", Yatsanshi ya mik'a yana nuna kayan dake a gefen gadonta"wannan nan yakamata a aje su?" da sauri tace"wanki ne jiya kawu Amadu yayi man,to ban lafiya shiyasa ban ninninke su ba amman gwaggo tace zata ninke man su"ganin yana mata wani kallo tace"wllh Allah ina yin tsafta,ai gwaggo ma bata bari in yi kazanta",nodding kai yayi, nufar gadon tayi ta ture kayan can k'arshen gado ta kalleshi"kazo ka zauna Ya handsome kana ta tsayuwa",hannu ya d'an daga"No zan tafi ne,Allah ya baki lpy",daga haka ya nufi hanyar fita ta biyo shi,yana niyyar sa hannu ya d'aga labulen d'akin yayi tuntu6e da inda ledan k'asan ta fashe,da sauri Fatuu ta ruko hannunshi tace"kai Ya Handsome kabi a hankali,wllh kada Mutum take yi,rannan fa na shigo da gudu ta tad'iye ni na fad'i baka gan yadda hancina ya bugu ba,ni nama yi tunanin ya ta6e wllh", he couldn't help it but laugh,Calmly yace"My hand"da sauri ta saki hannun"Yi hakuri,don karka fad'i ne na ruke ka"d'an ta6e baki ya yi wato in ma faduwar zai yi ita a tunaninta zata iya ruke shi ne,daga haka ya fita itama ta fito gwaggo da ta shige d'akinta ta fara kwalama kira, "Gwaggo!gwaggo..."fitowa tayi tun kafin tace wani abu fatuu ta fara magana, "Kinga ina ta fama dake ki canja man leda kin k'iya,ai gashi nan sauran kad'an ta kada Ya Handsome wllh"waro ido gwaggo tayi kafin tace wani abu haisam dake kallon fatuu yana Murmushi yace"ko an canja zaki lalata ne,gara abar maki shi ahaka", Da sauri gwaggo ta kar6e"Wllh kaman kasani,mutum kullum shine shigowa da fita da gudu ba dole ta lalace ba,shiyasa nace ban canja mata ai"tana dariya tayi maganar,ita kam fatuu turo baki tayi"Wayyo don kun ga ban lafiya shine zaku yi man taron dangi ko"gaba d'aya su kae dariya,kallon gwaggo haisam yayi ya k'ara mata sallama daga haka ya nufi hanyar fita fatuu na biye dashi a baya,ita kam gwaggo tana rako shi bakin kitchen ta juya ta koma d'aki, Yana shiga cikin zauren gidan ya juyo ya kalleta"ki koma,a ina kika ga patient na rakiya" dariya tayi tace"ai na warke", shiru yayi yana ta kallonta itama shi take kallo,d'age mata gira yayi"damuwa kika sa aranki shiyasa kike ciwo ko?" turo baki tayi tace"to fa so sukayi su kashe ni ba dole in damu ba,da shikenan washe garin ranar sai dae a tsinci gawata acikin kangon,wllh nasan gwaggo itama sai ta mutu inta rasa ni kaman mamana,kawu Amadu ma ko bai mutu ba nasan sai ya sume,kai nasan bazaka damu ba ko?"still kallonta yake yace"Why", "Saboda baka dad'e daka sanni ba", d'an Murmushin gefen baki yayi"Yanzu dae ai bai faru ba,so stop worrying ur self en" kai ta d'aga mashi kafin tace"ai daman hakanan naji ciwon yazo man aranar da daddare"jinjina mata kai yayi yana niyyar juyawa tace"baka ga kayan dake jikina ba?", tsayawa yayi"na gani sunyi maki kyau", ruke ha6a tayi alamar mamaki tace"wai Ya handsome ya akai kasan kayan da zasu yi man ba tare da ka gwada ni ba,kasan fa duka kayan sunyi man daidai wllh", fuskarshi a sake yace"Ke in naje dake wurin siyan kaya bazaki iya za6ar man daidai dani ba?"kallonshi ta fara yi from head to toe can tace"gaskiya sai dae in kanga maka kayan inga in sunyi maka,kuma ma sai dai inyi d'agyal,ko nayi ma ba lalle in kamo ka ba don tsawo gare ka nikuma yar gudul ce"ta k'arasa tana ta dariya shima yar dariyar ya yi,abunda fatuu bata sani ba shine tsananin lissafin dake akan haisam yasa daya kalli Mutum zai iya estimating abunda zai mashi daidai saboda karatun da yayi ya kunshi lissafi sosae, "Go back Zarah"ya fad'a yana niyyar fita,maimakon ta koma d'in sai ta biyoshi tana fad'in"bari in raka ka waje sai in dawo,tun ranar juma'a da muka dawo ban sake lek'o waje ba"shiru baice mata komae ba har suka fita,adaidai gefen kiosk d'in Amadu ya juyo yace to ta koma,murmushi tayi mashi tace"Nagode Ya Handsome mai kirki"kai kawae ya d'aga mata,da baya baya ta fara komawa ciki tana mashi bye bye,yana dae tsaye yanata kallonta da d'an murmushi akan fuskarshi,cikin rashin sani ta tafi zata bugi bangon kopar shiga cikin gidan,da d'an k'arfi ya furta"Zarah!be careful"juyawa tayi ta kalli bayanta sai kuma ta juyo tana ta dariya,girgiza mata kai yai yayi mata alamar ta shige daga haka ya juya ya tafi. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *4️⃣5️⃣* Misalin karfe takwas da wani abu na dare Haisam ya parker motarsa abakin shagon Amadu,fitowa yayi ya zagaya d'aya bangaren ya bud'e back door,wata k'atuwar farar leda ya fiddo ya nufi kiosk d'in bayan ya rufe kopar Motar,yara guda biyu ne ke yin siyayya,saida ya d'an jira a gefe aka sallamesu kafin ya matsa,Amadu na ganinshi ya fara washe baki ya shiga gaisar dashi,hannu ya bashi suka gaisa kafin ya d'aura ledan agaban kiosk d'in yace ya kai ciki,juyawa yayi ya nufi motarshi Amadu sai faman godiya yake mashi,hannu kawai ya d'aga mashi daga haka ya bud'e Motar ya shige ya jata, Lokacin da ya shiga gidan,gwaggo na zaune saman darduma dake shimfide'e akan tabarma a can k'arshen bangon dake tsakankanin d'akunansu da alama salla tayi gashi ba wutan Nepa amman tsakar gidan akwai hasken globe mai caji,Fatuu na kwance agabanta ta d'aura kanta saman cinyar Gwaggon suna fira tana d'an shafa mata kai,wurinsu ya nufa ya aje ledan agabansu, "gashi Yaya Haisam yace in kawo", zumbur fatuu ta d'ago jin ance haisam,ita kuwa gwaggo da mamaki ta bud'e ledan tana fad'in"yace ka kawo...", d'agowa tayi ido waje ta kalli Amadu bayan ta duba abunda ke a ciki tace"shi bai gajiya ne,wannan hidima ai tayi yawa", Amadu yace"wllh yanzun nan ina shago ya tsaya da Mota yazo har bakin shagon yace in kawo ciki....", katseshi fatuu tayi"gwaggo miye aciki?", fiddo kayan cikin ledan ta fara yi tana fad'in"abubuwan ciye ciye ne", zaro ido fatuu tayi ganin kayan da aka kawo,Manyan gasassun kaji guda biyu,manyan robobin yoghourt da ice cream guda ukku ukku sai wata leda shak'e da kayan Marmari ba abunda babu su kankana,Apple,Abarba,lemu, Ayaba,shamman,pear da sauransu dae wasu ma bata san su ba,fatuu na ganin fruit d'in tasa hannu ta rufe bakinta, "Wannan dai da gani kayan mara lpy ne" gwaggo ce tayi maganar, "To gwaggo wake da lpy,ai yanzu kowa kika gani ba lafiya ne dashi ba,in d'aukko Plate ki zuba man kasona na baro shago ba kowa", kallonshi gwaggo tayi tace"Oh ni bansan wane kalan uba bane kai,yarinya bata lafiya baka siyo mata ba,an kawo mata kuma kana niyyar cinye mata", "amman dai ai kinsan wannan kayan sunyi mata yawa ko,dama can harda mu aka kawo shiyasa ma wasu abubuwan aka sako ukku ukku", dariya gwaggo tayi tana girgiza kai tace"Wannan dae da sunanta aka kawo don haka nata ne",tana kai Maganar ta tura ma fatuu ledan kayan,da sauri Amadu yace"Gwaggo ya da haka,kinsan fa Yarinyar nan ba hankali ta cika ba kin tura mata ledan kuma gaba d'aya",ita dai dariya kawai take ganin yadda ya harzuka, Hannu fatuu ta kai cikin ledan kayan ta fiddo duka ice cream d'in ta aje agabanta daga haka ta tura ma gwaggo ledan tace"ni su nike so", kallon Amadu gwaggo tayi"to kaga ita abunda ma ya dameta nan,sai ka d'aukko plate a kicin in zuba maka ko ka koma shagon,juyawa yayi ya nufi kicin d'in yana fad'in"atoh yanzu naji bayani,amman kyace wai kayan mara lafiya ne", Bayan ya kawo plate d'in ta yagar mashi naman mai d'an yawa,ta bashi robar Yoghourt d'aya tana niyyar dibar mashi fruit d'in yace ta barshi ba yanzu ba sai ya gama da wad'annan tukun,daga haka ya nufi hanyar fita kopar gida gwaggo nata mashi tsiya,ita kam fatuu tasa ice cream d'in tayi gaba taita sha gwaggo na ce mata kada sanyi ya kamata fa,har saida ta shanye roba biyu sannan ta fara cin naman,gaba dayansu ba wanda yaci abincin dare don ba k'aramin k'oshi sukai ba,d'ayar robar Yoghourt d'in data rage gwaggo tace ma fatuu ta k'ara da ita tace to saidai ta tafi da ita Makaranta gobe,acikin d'an tsohon fridge d'insu dake acikin kicin suka saka sauran abubuwan da suka rage harda fruit masu yawa don basu sha su sosae ba,naman ma sun rage,daga haka gwaggo tasata ta d'aukko magunguna ta sha suka ci gaba da yin hira har aka maido da wuta suka nufi d'akin gwaggon gaba d'aya don su kwanta dama tunda ta fara ciwo anan take kwana. MONDAY Wuraren k'arfe 7:00 na safe Haisam tsaye agaban Dressing Mirror d'in bedroom d'inshi ya gama shiryawa cikin tsadaddun suit black color,yar cikin fara ce sai Bow tie red color,daga gaban aljihun ta saman anyi adon red harda wata yar sarka mai walwali,k'afafunshi na sanye da dakakkun takalma penny loafer na zallar bak'ar fata wad'anda sababbi ne fil yau ya fara saka su harma da suit d'in,ba k'aramin had'uwa yayi ba acikin kayan,da ka kalle shi zaka yanke cewa ba d'an Nigeria bane sai kaji yayi magana sannan zaka iya gasgata hakan,bayan ya gama gyara sumarshi ya kai hannu ya d'auki kwalbar turare ya shiga feshe jikinshi dashi,aje shi yayi ya d'aukko wata kwalbar ya k'ara fesawa sai da ya fesa kala ukku kana ya dakata ya feshe sumarshi da hair spray mai daddad'an kamshi,agogon Diamond d'inshi dake a ajiye ya d'auka ya sanya a wrist d'insa daga haka ya nufi kopar fita, Bayan ya fita kopar d'akin da Fatuu taje fitsari ya bud'e ya shiga,bai jima ba ya fito hannunshi ruk'e da wata yar babbar bak'ar jaka irin ta ma'aikata,cikin parlon ya fito daga haka ya nufi kopa ya fice, A nutse yake tafiya cikin harabar gidan bayan ya fito ya nufi part d'in hajiya,tunda ya fito Tk dake tattara busassun ganyayyakin da suka fad'o a harabar ya dakata da aikin da yakeyi gaba d'aya ya zuba ma Haisam na mujiya,ba k'aramin tafiya yayi dashi ba,yadda Haisam ke d'aukar wanka in zaije aiki yasa tk k'agara yaga ya fara aikin shima don ya rink'a daukar wankan kamar yadda yake yi,lokacin da yazo saitin tk d'in da hannu yayi mashi alamar yazo aikuwa da sauri ya wurgar da tsintsiyar kwakwar ya nufe shi,gaidashi ya shiga yi bayan ya isa,amsa mashi yayi fuska asake ya mik'a mashi jakarshi had'i da bashi Umarnin ya k'ara goge masa Mercedes Benz kafin ya fito daga haka ya wuce,juyawa tk yayi hannunsa ruk'e da jakar ya tunkari parking space d'in bakinshi a washe kaman gonar auduga,a fili yake fad'in"Yau shegiyar za'a hau..", yana isa ya bud'e d'ayan side d'in driver ya aje jakar ya maida kopar ya rufe,lallausan farin yadin da yake goge motoci dashi ya d'aukko acikin wurin ya fara goge jikin Motar wadda dama tuni agoge take sai faman kyalli take don kullum ne sai Tk ya gogeta duk da ba hawanta Haisam d'in ke yi ba tun bayan da ya zo da ita. Bakinshi d'auke da Sallama ya shiga cikin parlon,Hajiya dake zaune saman Sofa 2 seater jikinta nad'e da lifaya Milk Color mai Manyan fulawoyi light blue idanunta sanye cikin glasses ta amsa mashi had'i da kai idanunta gareshi,suna had'a ido ya sakar mata k'ayataccen Murmushinshi itama Murmushin takeyi,nufar inda take zaune yayi yana fad'in"Gud Morning My Sweethrt ", Hannu ta mik'o mashi" Morning a Shining Star,How was ur nyt?", "Alhamdulillah"ya fad'a yayin da ya kai hannu yana tattara takardun dake gefenta ya zauna, "Yau zaki fita kenan", "Eh,muna da bak'in turawane, shiyasa zan fita da wuri don mu tar6esu",jinjina mata kai yayi, "Bari akawo maka ko tea ne ka sha", hannu ya kai Saman Sofa table dake gabanta ya d'aukko tea cup dake d'auke da kakkauran tea mai zafi yana d'an tiriri yace"let me take this" kai ta d'aga masa ya fara sipping tea d'in,yana cikin sha Saude ta k'araso inda suke hannunta d'auke da d'an babban plate an rufeshi ta aje asaman table din,kallonshi tayi tace"Barka da Safiya Yalla6ai", "Barka"ya amsa mata,juyawa tayi gun hajiya"Hajiya gashi nan,za'a zubo masa ne?" kafin ta bata amsa Haisam ya girgiza mata kai alamar a'a,hajiya tace ta tafi kawae, Hannu hajiya tasa ta bud'e plate din,kallon haisam tayi"ka d'an had'a da wad'annan kafi jin nauyin cikinka", kallon plate d'in yayi,sliced bread ne da wainar kwai,ganin bai ce komai ba yasa hajiya kai hannu ta d'aukko yankan biredi d'aya ta yago wainar tasa aciki ta fara k'okarin bashi a baki,a hankali yake gatsar bread d'in yana sipping tea d'in har ya cinye ahaka yaci guda biyu ganin tana kokarin d'aukko wani yasashi mik'ewa da sauri yace"am Ok Sweethrt",k'yaleshi tayi don tasan baison cin abinci da sassafe wannan bread d'in ma da ya ci sa'a aka ci,duk'awa ya yi saitin fuskarta ya manna mata kiss a gefen fuskar wanda hakan yake mata kullum in zai tafi aiki,mik'ewa ya yi ya tunkari Corridor d'in dakinta bayan d'an wani lokaci ya fito da alama bakinshi ya wanko,hanyar fita daga falon ya nufa yana fad'in"Till i come back", Hajiya dake Murmushi ta fara yi mashi Addu'ar da ta saba yi mashi kullum"Allah Ubangiji Ya tsare,Ya baka ikon yin abunda kaje yi,ya kuma maido man da kai lafiya", Hannu ya d'ago mata"wish u same Sweethrt",daga haka ya fuce,hajiya dake kallon bayanshi tana ta murmushi ta d'an girgiza kai,tana matuk'ar kaunar Haisam ba kamar kuma da ya kasance akwae yanayin Mijinta da ya d'aukko wato Gen. Adamu Zakee. __________________ Mik'ewa tayi bayan ta gama sanya igiyoyin Sandals dinta ta goya yar jakarta ta makaranta, kallon gwaggo tayi dake tsaye abakin kopar d'akinta, "Zan tafi Gwaggo", "kindai matsa sai kinje Makarantar nan,da kin bari kin k'ara samun sauki sosae", turo baki tayi tace"ai na samu sauk'in zan iya zuwa,kuma in na zauna ma ai ni kad'ai za'a bari tunda kema aiki zaki ko", "Ai shikenan,dama ina gudun kar jikin ya dawo maki ne a Makarantar...." katseta Fatuu tayi"in ma ciwon ya dawo ba ga Haulatu ba ai sai ta rakani clinic ko akan dae in zauna ni kadai a gida", gyad'a kai gwaggo tayi kawae dama ita niyyarta ta tura Fatun gidan hajiya in zata aikin to ta matsa sai taje makarantar,kud'i gwaggo ta mik'o mata ta amsa daga haka ta juya ta nufi hanyar fita, "ba kin ajiye abu ba a fridge jiya kince dashi zaki makarantar",Gwaggo ce tayi Maganar,da sauri ta juyo ta nufi kicin tana fad'in"Yauwa kakus nagode da kika tuna man don har na manta",d'aukko robar youghout d'in tayi ta hado da fruit a bakin kicin ta saukko da jakar ta zuba su ciki kafin ta maidata bayan,nufar kopar fita tayi tana fad'in"na tafi kakus", "A dawo lpy,Allah ya tsare", juyowa tayi ta kalli gwaggo,"yau baki cewa banda rigima don Allah Fatuu?", Yar dariya gwaggon tayi tace"ai na lura dae kaman da gaske kin daina rashin ji,da alama Allah ya kar6i Addu'ata",dariya kawai tayi ta d'aga mata hannu tana mata bye bye itama gwaggon hakan tayi mata har ta fuce,girgiza kai Gwaggon tayi,tana Matuk'ar jin Fatuu cikin ranta,tamkar Aysha d'inta take kallonta,juyawa tayi ta shige cikin d'aki don ta idasa shiryawa itama ta tafi wurin aiki. Parking Space ya nufa bayan ya fito,a tsaye ya iske tk yana d'an k'ara kakka6e jikin Motar, yana ganin haisam ya dakata da abunda yake yana mashi dariya,yana isowa kusa dashi yasa hannu da sauri ya bud'e mashi Motar,har zai shiga ya juyo ya kalli tk dake ta faman bin sa da ido, "Any problem?"ya tambaya fuskarshi a sake,maimakon ya bashi amsa sai yasa hannu yana d'an sosa k'eya,a zahiri tabbas yana da buk'ata,sai dae bazai iya fad'i mashi ba don gani yake buk'atar tashi tana da d'an girma,wani mashin ne da ake yayi yake so ya mallaka sai yaba kaninshi nashi da yake da,tuntuni yake rok'onshi ya bashi mashin d'in yace mashi ya bari sai ya siya wani to kuma yanzu baida kudin da zai siya wanccan din don ba wata sana'a yake ba illa kud'in da hajiya ke saka mashi a Account a duk k'arshen wata saboda Karatunshi da yan hidindimun kanshi,duk da yana balaen son mashin d'in bai ta6a tunanin tambayarta ba don dama tk yana da hangen nesa sam baida had'ama ya iya bin komai a hankali kuma hada hakan yasa yake zaune lafiya da hajiya, Jin yayi shiru yasa Haisam gane akwae wani abu, "tell me,kana da matsala ne?", Haisam da ya rik'e murfin motar ya sake tambaya,d'an Murmushin yak'e Tk yayi yace" ba wani abu Yaya haisam", shigewa yayi cikin Motar tk ya matsa don ya rufe masa kopar, "U can send me a message", Haisam ya fad'a ba tare da ya kalli tk d'in ba,rufe masa kopar yayi bayan ya amsa mashi da toh,sai da yayi Warming d'in Motar kafin ya fita daga cikin parking space din,shima tk fitowa ya yi ya tsaya gefe guda yana kallon Motar,da gudu ya ja Motar ya fice daga gidan su officer na d'aga mashi hannu ya sakar masu Horn. ************, Tafe take ta raba hanya biyu tana ta tafiya sai dai yau tafiyar tata da yar natsuwa ba kaman yadda ta saba wurga k'afafu ba in tana tafiya,horn d'in da aka yi mata da k'arfi ne yasa ta koma gefen hanyar da sauri ba tare data waigo ba,cigaba da tafiya tayi aka k'ara yi mata horn d'in aikuwa a fusace ta juyo cike da tsiwa ta bud'e baki zata yi magana,tana yin arba da Bak'ar Motar dake a bayantan ta kasa magana,bin ta kawae tayi da ido ba tare data san ko waye a ciki ba,slowly glass d'in kopar gaban ya fara sauka k'asa,tana yin arba da fuskar Haisam tasa duka tafukan hannayenta ta rufe baki alamar mamaki,jingina kanshi yayi ajikin headrest d'in seat yana kallonta fuskarshi a sake, "Ya Handsome ashe kaine kake ta man horn" fatuu ta fad'a bayan ta cire hannun, "Yea,ni ne za'ai ma masifa" ya bata amsa, Tura baki tayi"ni fa ba masifa zanyi ba,da naji an k'ara yi man horn dinne shine na juyo ince ai na kauce",d'an ta6e baki yayi don yasan ba gaskiya ta fad'a ba, "Kin samu sauki ne zaki school?" "Eh,kuma ma in ban je ba ni kad'ai za'a bari agidan", jinjina kai yayi"Ok,get into d car", hannu ta d'aga tana nuna motar tace"in shigo kace?" kai ya d'aga mata alamar eh,matsawa tayi ta kai hannu zata bud'e kopar baya taji ta a rufe,komawa tayi saitin haisam tace"Ya handsome tak'i bud'ewa ko ba ta nan ake shiga bane?",daga yadda ya kwantar da kanshi ya daga mata kai alamar eh, "To ta ina ake shiga?",ta tambaya, yatsanshi guda ya d'aga sama,zaro ido tayi"kenan ta sama ake hawa?",gyad'a kai yayi,cike da mamaki take kallon saman Motar can tace"itama kaman jirgi ce kenan ta,to mi zan taka in hau,ko itama tsani ke gareta?" Still yayi yana kallonta ganin da gaske ta d'auka ta saman ake hawa,tunanin ranar da zata daina wauta ya shiga yi tana ganin handle ajikin kopan bayan amman take tambayan ko bata nan ake shiga ba,ganin tana ta kallonshi tana jiran amsa yasashi cewa"ke zaki hau da kanki", hannu tasa ta ruke ha6arta ta fara tunanin yadda zata hau saman Motar,kallonshi tayi tace"Ya Handsome kodae ka idasa sauke glass d'in sai ka matsa man in shigo ta nan inda kake",wani kallo ya bita dashi kafin ya kai hannu ya bud'e k'ofofin ta gaba,juyawa yayi yace"ki shigo", "Ta ina?"ta tambaya, "Ta ina kika san ana shiga Mota?" hannu ta d'aga ta nuna mashi k'opa,kai ya gyad'a mata alamar tanan zata shigo,da sauri ta kama handle din ta ja sai gashi ta bud'e,shigewa tayi ta rufe kopar da karfi don kar yace bata rufu ba irin rannan,tsakiyar backseat d'in ta zauna ta kame wuri guda,wani irin ni'imtaccen sanyin Ac had'e da kamshi suka fara ratsata sai faman sakin Murmushi take,d'aga kai tayi suka had'a ido da Haisam ta cikin madubin gaban Motar,dariya tayi mashi tace"ashe wasa kake man kace ta sama ake shigowa", shi dae kallonta kawae yake bai ce komai ba, "to na shigo Ya Handsome mu tafi", D'age mata gira yayi ta cikin madubin"ina?" zaro ido tayi"ba kai kace in shigo ba,ai nayi zaton Makarantar zaka kai ni fa", K'ara gyara kanshi yayi a jikin headrest, "yeah can zan kaiki amman in kin zauna a inda ya dace",cikin rashin fahimta tace"to a ina zan zauna?"hannu ya kai ya d'auke jakarshi da yatsanshi ya nuna mata kujerar dake a gefenshin tace toh,maimakon ta bud'e Motar ta fita ta zagaya sai ta kutsa ta tsakankanin kujerun gaban,har saida haisam yaja gefe guda,zaunawa tayi a kujeran gefen nashi ta kalleshi, "to na dawo", kai ya d'aga mata ya maida jakar baya daga haka ya ja Motar suka fara tafiya, "Ki sauko bag d'in mana"yace mata ganin ta takure don da jakar a bayanta ta zauna,curo jakar tayi ta aje ak'asan seat din, "wllh sanyin ya fi yawa anan gaban"ta fad'a tana lullu6e jikinta da hijab dinta,hannu ya kai ya rage mata Ac din ba tare da yace komai ba,curo hannuwanta tayi daga cikin hijabin jin sanyin ya rage ta kalli haisam da idonsa na akan hanya cikin natsuwa yake driving din, "Ya Handsome"ta kira Sunanshi,d'age mata gira yayi alamar amsawa ba tare da ya kalleta ba, "Wai kaima abun dubiya ne ka kawo man jiya?"shiru ya d'an yi kaman ba zaice komai ba, ganin tayi kasak'e tana jiran amsarshi yasa shi cewa"ko nayi laifi ne?", Da sauri ta girgiza kai"a'a ba kai laifi ba,kawae dae naga kayan da yawa nasan ka kashe uban kud'i amman naji dadinsu wllh,kasan mi?" kai ya girgiza still idanunsa na a kan hanya, "Duka fa ice cream d'innan roba ukkun ni kadae na shanye su,na bar masu Yoghourt din,amman su d'aya d'aya suka d'auka aka bani sauran roba d'ayan ka ganshi ma nan a jakata zani Makaranta dashi harda ma fruit na d'ebo,naso ma in aje ice cream d'in shima roba d'aya amman na kasa saida na shanye shi duka tun jiyan sannan hankalina ya kwanta"ta k'arasa tana ta dariya, sai lokacin ya d'an kalleta yace"kina shan sanyi da yawa zaki ciwo fa", langa6ar da kai tayi cike da shagwa6a"to ai bakina ne bai man dad'i shiyasa da nasha naji yana da d'an banzan dadi na kasa hakuri saida na shanye shi duka"d'an Murmushi yayi ya cigaba da driving, "Thank u so much Ya Handsome mai kirki,May Allah give u more Money"yadda tayi turancin gwanin dad'i ba kaman da yake Muryarta har yanzu akwae d'an sautin fulani dama kuma in bafullatana tayi turanci sound d'in ba dai dadi ba, Juyowa yayi ya kalleta"Ameen yar fillo" fuskarshi d'auke da Murmushi yayi maganar,turo baki tayi sai kuma tayi dariya tace"ai kai Yayana ne ko kace man hakan bazan ji haushi ba", cigaba yayi da driving fuskarshi a sake,can tace"Wai Yaya Handsome kasan makarantarmu ne?naga muna ta tafiya kuma baka tambayeni inda take ba, "Kaman haka"ya bata amsa, "to ya akai kasan Makarantarmu?ko ka ta6a kai wata ne?ko kana da Budurwa acan ne?" "bani da ita", "Budurwar?"kai ya daga mata alamar eh, "To ya akai baka da ita?baka ta6a cewa kana son wata bane?",yace"yea", "kuma wata bata ta6a cewa tana sonka ba Ya Handsome?kai ya daga mata alamar eh,jinjina kai tayi"nasan akwae masu son ka kawai tsoronka suke ji balle su gaya maka kasan fa ko Ya Handsome,wllh in Mutum bai sanka ba da ya ganka zai yi tunanin kai masifaffe ne mara kirki,nima da farko nayi tunanin hakan"shiru ta d'an yi kafin taci gaba, "Don dae ni k'arama ce da sai ka so ni,kuma ma ni ko na gama Secondary Skul ba zan yi aure ba sai na zama likita na fara aiki ma", Wani kallo ya juyo ya yi mata kafin ya maida idon kan hanya yace"to ko in jira ki ne?", zare ido tayi"ka jirani har in zama likitan?" "Yeah, "tabb lokacin ai ka fara zama tsoho",d'an jinjina kai yayi da d'an Murmushi yace"ba zaki so tsoho ba kenan", "Gaskiya lokacin fa ni nazama babbar Budurwa kuma sai in auri tsoho,kuma kai ai yanzu yakamata kayi budurwa ko kayi aure kaima kaman abokinka,in kana so sai in yi ma Budurwa a Makarantarmu, a Ajinmu akwae wata Sofiya Moussa tana da kyau,kasan mi?" Haisam da yayi still yana saurararta ya girgiza mata kai alamar a'a, "Itafa Safiyar buzuwa ce yar Nijar baka ganta ba fara ce sosae tana da gashi,kuma doguwa ce,nasan in ta ganka da gudu zata amince don yan Makarantarmu ko Malami suka gani mai kyau mai yin gayu sai su fara sonshi kaga sunata rububinshi balle kai,in gaya mata kana sonta?" D'age gira yayi ya d'an kalleta itama shi take kallo tana jiran amsarshi yace"wa kenan?" "Safiyar", girgiza mata kai yayi"bansa ki ba", gyad'a kai tayi tace"shikenan dama ba lalle ma ka sota ba don k'aton baki ne da ita kuma hak'oranta sun d'an turo haka,gata bata da jiki wllh kaman sandar suluka take,cewa ma akai na fita kyau sosae fa kawae dai tafi ni fari sosae don ita har tayi kaman zabaya kuma ta fini tsawon gashi amman na fita yawan gashi,kuma ni duk in za'ai wani abu a makarantar ana za6ar masu kyau harda ni ake sawa ko a House d'inmu in za'ai inspection nice Flower Girl",jinjina kai yayi ba tare da ya ce mata komae ba, shuru sukai na wani d'an lokaci can tace"Yaya Handsome kayi kyau sosae wllh,wannan kayan in ka sasu k'ara yin kyau kake ko ranar dana fara ganinkan nan ka sasu kayi kyau kaman Aljani,akwae irinsu na mata ko?"kai ya daga mata alamar eh, tace"aikam nima idan na zama Doctor irinsu zan rinka sawa"jinjina kai ya k'ara yi daga haka suka iso bakin Main Gate na shiga kwalejin gwamnati ta yan mata dake a Katsina. *_💖A SANADIN MAKWABTAKA💖_* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH*_🌹 *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *4️⃣6️⃣* ....... Suna shiga ta cikin gate d'in fatuu ta kalleshi,"lah Ya Handsome ashe da gaske kasan makarantarmu ɗin" Murmushi yayi baice mata komae ba yana ci gaba da shiga cikin Makarantar gaba d'aya hankalin Mutane ya dawo kan Motar ba kamar Students dake ta faman shigowa, "Yauwa Ya handsome wannan gate ɗin na farko ne section dinmu", Juya kan Motar yayi yai horn don a idasa bud'e mashi d'ayan 6arin gate d'in,lek'owa Maigadi yayi koda yai arba da Motar da tai horn d'in da sauri jiki na kerma ya shiga bud'e d'ayan side d'in don a zaton shi Babban bak'o ne yazo Makarantar kamar yadda aka saba yin Manyan Baki,kutsawa yayi cikin Makarantar ya nufi gaban Admin Block inda akai parking wasu motocin ciki harda ta Principal ya parker shima ba tare da ya kasheta ba, kallon fatuu yayi tare da lumshe ido"here we come",calmly yayi maganar, yar dariya tayi ta kai hannu ta ɗauko jakarta dake aƙasan seat, "Zarah"taji ya kirata, kallonshi tayi,wallet ce ruk'e a hannunshi ya fiddo 1k yana miko mata, "Ta micece Ya Handsome?" ta tambaya ba tare data kar6a ba, "Ba ki yin break ne", "ina yi,amman gwaggo ta bani ai kud'in break d'in" "Ok,ki ƙara", zaro ido tayi"ai wanda ta bani fa zasu ishe ni,in na amshi wannan bansan ya zanyi da ita ba",shiru yayi yana kallonta yayin da itama take kallonshi, "Owk ki amsa sai ki biya kuɗin friend ɗinki da kika kashe mata"he said calmly, "Wai kana nufin kud'in da na siyo maka fruit?" kai ya d'aga mata alamar eh, wani kallo tayi mashi"kam kenan kai zaka biya kud'in abun ciwon naka kuma" "Ai ba wani abu bane nasan ke kika siya man am grateful for dat,wannan na baki ne kyauta sai ki biya", wani kallo take mashi a shagwa6e tace"ni dae gaskia ban yarda ba Ya Handsome Allah wayau kake son yi man,salon kayi man gorin kai ka biya abun ciwon dana kawo makan", Haisam baisan lokacin da ya saki dariya ba jin abunda ta fad'a ya d'an juyar da kanshi,kallonta ya sake yi still yana dariyar,ita kam Fatuu sai binshi da ido take don ba k'aramin kyau yake yi ba in yayi dariya har jerarrun fararen hak'oransa suka bayyana,ko dan bai cika yi bane, "Do i look like wanda zai maki gori?",kai ta girgiza masa alamar a'a, "to ki amsa ba zan maki ba ai baida kyau", "kayi Alkawari?"kai ya d'aga mata, "To ka rage kud'in sunyi yawa sosae don har na tara 150 sauran 100 zan cika", hannu yasa ya shafi beard d'insa kafin ya mayar da 1k d'in cikin wallet ya zaro 500 ya mik'a mata, "Itama tayi yaw...." katseta yayi"just collect it Zarah!", tana tura baki had'i da kyakkyafta idanu alamar bataso ba ta mik'a hannu ta amsa"Nagode", har ta juya zata kama door d'in ta bud'e taji yace"Wait"dakatawa tayi ta juya tana kallonshi,hannu ya kai ya d'aukko jakarshi dake a seat d'in baya,d'aurata yayi saman laps dinshi ya bud'e ciki,wani k'aton biscuit ne ya fiddo ya zuge zip d'in ya mayar da jakar,mik'a mata biskit d'in yayi"ki had'a da Yoghourt d'in da kika ce kin taho dashi", k'in amsa tayi tasa hannu tana d'an sosa gaban kanta"kai Ya Handsome banda kud'in kuma,don Allah ka barshi wllh kud'in ma fa sunyi man yawa,kuma ba sai in siya biscuit din ba in inaso acikinsu", Wani kallo ya jefa mata mai kaman harara"What did i told u initially?ba nace maki banson jayayya ba?", yana rufe baki ta juya mashi k'eya ta yadda fuskarta ke kallon k'opa,still yayi cike da mamaki yake bin ta da kallo, "ZARAH!"ya kirata a kausashe, amsawa tayi ba tare da ta juyo ba,aikam a fusace yace"Zarah ina wasa dake!" jin sautin yadda yayi Maganar yasata juyowa ta kalleshi ganin ya d'aure fuska sosae yasa ta fara ta6e baki alamar zata yi kuka"Don Allah Ya Handsome ka barshi nasan don ka ci ka taho da shi, dama Hajiya tace baka son cin abinci sai irinsu",sai yanzu ya gane dalilin da yasa taki amsa,ganin yayi shiru kaman ranshi a 6ace taci gaba"Don Allah kaje dashi ka ci,wllh in Mutum bai cin abinci Ulcer ke kamashi"ta k'arasa tana mutsustsuke ido da hannunta, Sigh yayi had'i da nodding kanshi"baki so Ulcer ya kama ni?"da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh, "Why" ya tambaya idonshi a kanta, "Saboda tsinka ma mutum yan hanji take ya Mutu", hannu yasa ya ruk'e ha6arshi"To baki son na mutu ne?" ɗaga mashi kai tayi"eh ai baka yi aure ba kuma ance in mutum bai yi aure ba ya Mutu aza6a ake mashi", bud'a mata ido yayi alamar mamaki"waye ya fad'a maki hakan?"turo baki ta ɗanyi"haka naji ana cewa", jinjina kai yayi"to ba haka bane,ai Auren ma is not compulsory and akwae wad'anda Allah bai k'addara masu ma zasu yi auren ba a rayuwansu,amman dae yana da kyau Mutum yayi in Allah ya bashi iko don sunna ne kuma yana da falala sosae and daga cikin falalanshi ake samun yara wanda zasu rinka yi ma Mutum Addu'a in ya mutun don Addu'ar ya'ya ga parents dinsu kar6a66a ce, kuma ni nasan zan samu masu yi man wannan kema nasan zaki yi man ai ko?", da sauri ta d'aga mashi kai ta kuma ce"amman dae banso ka Mutun"d'an Murmushi yayi kawai, "yanzu ki amsa tunda na riga na fito dashi a hanya zan siya wani", d'an yamutsa baki tayi"to kuma in baka samu ba fa yanzu fa safiya ne" "In naje wurin aiki sai in siya wani abu in ci", "a wurin aikin ana saida irin shi ne?" "Yeah,har ma abinci dasu snacks akwae", "To kayi man Alk'awari zaka ci abinci ka ƙoshi",tayi Maganar tana mik'o masa yatsan hannunta da ta d'an lanƙwasa, kallon yatsan yayi"mi kenan"ya tambaya, "Alk'awari zamu k'ulla don kar ka k'i cin" dariya ya sake yi har fararan hakoransa suka sake bayyana"No ba sai munyi hakan ba,ai nace zan ci so don't worry", hannu ta kai ta d'auki biscuit d'in don ya aje shi akan lap dinshi,ta bud'e jakarta ta saka hada kud'in da ya bata daga haka ta juya zata fita, "Mom Zarah rigima" yar dariya tayi lokacin ta bud'e kopar motar ta zura kafarta guda,juyawa tayi ta kalleshi "Ya Haisam mai balaen kirki" daga haka ta fita daga cikin motar tana zuge zip d'in jakarta,tana fitowa aka bita da ido don glass din motar black tinted ne sam ba'a ganin wanda ke aciki,dama kowa ya k'osa yaga wanda ke cikin Motar ba kamar wasu Students yan section d'in da suka ga shigowar Motar tun a main gate,Maigadi ma tsaye yayi yana jiran wanda yazo d'in ya fito ya kasa k'arasawa wurin Motar don fargaba,a tunaninshi bak'on wurin principal yazo to kuma yasan bata Office d'inta tana wurin Assembly kasantuwar yau Monday hakan yasa Maigadin yin tunanin ita yake jira shiyasa bai fito ba, Idasa fitowa tayi waje,tana niyyar rufe mashi kopar Motar ya hango Principal cikin shigar alfarma tare da muk'arrabanta sun tunkaro Admin block d'in don angama Assembly d'in,cire seat belt dake ajikinshi yayi ya bud'e Motar ya fito,fatuu da ta rufe kopar ta bishi da ido ganin ya fito, "Ya Handsome ko raka ni aji zaka yi ne?", shaking kai yayi alamar a'a,tsaye tayi tana kallonshi ganin ya zagayo ta bayan Motar,cike da tafiyarshi ta k'asaita ya tunkari principal d'in,Yasalam!zo kaga idanu ba Students din ba,ba malaman ba mai gadin ba,kowa ya zuba mashi na mujiya,tun bayan da ya fito daga cikin Motan principal d'in taja ta tsaya haka ma Vice principal dake a gefenta da sauran malaman da suka rufo mata baya,cike da mamaki take kallon Haisam har ya k'araso gabanta,tunkan yace wani abu ta rigashi, "Who am i seeing in my School like Haisam?",fuska a d'an sake yace"it's me Maa",gaidata yayi ta amsa,dama haisam Mutum ne mara shariya duk inda yaga wanda ya sani in dai da dama sai ya tsaya sun gaisa koda yana cikin mota ne,hakanne ma yasa da ya hango principal din ta kopar da Fatuu ta bud'e ya fito don ya gaidata, "Haisam mi kazo yi school d'in nan,ko dama kana zuwa baka ta6a zuwa mun gaisa ba?", "No,i just drop off a sis",ya bata amsa, "A sis...", principal ta maimaita yayin da ta maida idonta akan Fatuu dake jingine da Motar haisam sai hura hanci take yi,kai ya d'aga mata itama ta jinjina mashi kai kafin ta kalli malaman da suke gefe da gefenta tace"Malamai Meet Haisam,Son of Senator Ali Adamu Zakee",gaba daya suka shiga gaisawa dashi bayan ya gaisa da kowa ya yi mata sallama tana cewa ya gaida mata da Hajiya kwana biyu bata samu taje sun gaisa ba,amsa mata yayi da Ok,daga haka ya nufi Motarshi,kallon Fatuu dake mashi Murmushi yayi shima ya maida mata tana ganin zai shiga motan ta d'aga mashi hannu tana mashi bye bye maigadi dake atsaye a sukwane ya sha gaban haisam d'in ya bud'e mashi motar yana gaishe dashi jinjina mashi kai yayi ya amsa daga haka ya shige cikin motar maigadin ya fara mashi Allah ya kiyaye yalla6ai,Allah ya tsare,Wallet dinshi dake ajiye agefe ya d'aukko,kud'i ya kirgo yan dubu dubu ya mik'o masa daga haka yakai hannu don ya rufe kopar da sauri mai gadin ya rufe masa yana cigaba da yi mashi Addu'a yana d'aga mashi hannu,adaidai lokacin d'ayan baba maigadin da ya zagaya toilet d'in cikin d'an d'akinsu na masu gadi ya fito hannunshi ruk'e da yar buta,ai yana hango abunda ke faruwa ga kudi a hannun abokin aikin nasa yai saurin aje butan ya tunkaro su da hanzari saidai ko kafin ya k'araso haisam ya tashi motar yana yin reverse, hannu ya fara d'aga mashi shima duk da baida tabbacin ko yana gani don glass d'in motan dind'im yake,yana juya kan motan ya tunkari gate d'in fita daga section din,jiki a sanyaye baba maigadin ya tunkari abokin aikin nasa, "Ashe bak'o akayi", ba yabo ba fallasa ya amsa mashi"umm wata ya kawo kuma ma kaman d'an uwan Hajiya ne don naga suna gaisawa", gyada kai yayi can kuma yace"naga ma har alheri yayi maka,ai sai ka d'an samman wani abu tunda ba rabona, dama wllh fankan fayau na tashi tun jiya nike istigfari ashe ta wajenka arzikin zaizo" ya k'arasa da d'an murmushi akan fuskarshi,shi kam wanda aka ba kudin tunkan ya k'arasa maganar yake wurga mashi harara,k'okarin saka ma kud'in acikin aljihunsa ya fara yi Horn d'in da akayi ne yasasu d'aga kansu su duka,a wani irin slow glass d'in kopar driver ya sauka,zuro da santalelen hannunsa yayi yai alamar kira,don sonkai irin na wasu Mutanen da sauri mutumin da aka ba kudin ya nufi motar,alamar bashi yake kira ba yayi masa da hannun nan take yaci burki yai turus awurin shikam wanccan bawan Allah sai yayi tsaye bai tunkari motan ba gudun kada ace shima bashi ake kiran ba,haisam dake hangensa ta side mirror ganin bai taho ba yasashi zuro da kanshi ya yi masa alamar yazo da kan nashi aikam da sassarfa ya nufe shi,yana zuwa haisam ya mik'o masa kud'i masu yawa shima yan dubu dubu da gani sunfi na wancan yawa sosae,hannu na kerma ya kar6a nan take ya durkushe yana mashi godiya harda hawayen farinciki,alamar ya mik'e yayi mashi daga haka glass d'in ya fara rufewa sama yana gamawa yaja Motar mutumin na ci gaba da yi mashi godiya,ko kallon inda wanccan yake bai yi ba ya nufi d'an d'akinsu na gadi, Uhmm har na tuno da baitin wakar Naziru sarkin wak'a da yake cewa, *_in rabo ya tsago da kai,kuma abun ya tabbata da kai,Rabbi ne yace saida kai in saida kai kawae sai da kai,in abun yazo babu kai,rabbi ne yace babu kai,in babu kai kawai babu duk duniya ba mai sa dakai.....😍_ Duk wannan abun akan idonsu Principal da sauran malaman dake a wurin harda ma wasu Students ɗin,Murmushi principal d'in tayi bayan Haisam ya fuce ta furta"That's haisam",ba k'aramin burge duk wanda ke a wurin yayi ba,kallon Fatuu dake tsaye itama tana kallon abunda ya faru principal tayi ta kirata da sauri ta taho wurinta ta tsaya a gabanta,bin ta da ido tayi ta shiga tunanin tasan yarinyar a Makarantar,kuma tabbas ta santan don irinsu fatuu masu k'okari yawanci zaka ga duk an sansu a makaranta ba kamar ita dake a English Club na Makarantar, "Which class are u?" principal d'in ta tambayeta, "Am in class 3c"ta bata amsa,jinjina kai tayi ta waiga gefenta in da discipline master yake tare da wasu prefects da zasu fara taren yan makara bada jimawa ba, "Malam Mahadi ka kaita Class"da sauri yace"Ok Ma",kallonta yayi yai mata alamar su tafi ta wuce gaba yabi bayanta daga haka principal d'in da sauran malaman da suka rako ta suka nufi cikin Admin block din, Tafiya take hankalinta kwance sai fanan shan kamshi take,yayin da wasu Students din keta faman bin ta da kallo,shi kanshi discipline master din kanshi ya d'aure,tsananin mamaki yake ta yadda akai yarinyar keda dangantaka da Senator Ali don yafi kowa sanin halin fatuu a Makarantar shiyasa kullum cikin yi mata horo yake ita kuma tana ganin ya tsaneta ne,kasa daurewa yayi ya dawo daga gefenta yace"dama kina da alak'a da Senator Ali?", d'aga kai tayi ta kalleshi sai kuma ta sauke kan fuska adan d'aure ta furta"eh", jinjina kai yayi can kuma ya sake cewa"Amman ya kike dashi ne?"shiru ta d'an yi tana tunanin amsar da zata bashi, tsoronta kar tace ita d'iyarshi ce ace kuma shi yasan ya'yanshi tunda gashi ya sanshi, "Kawu nane shi"ta fad'a cike da fargaba, "ke yar Daura ce?"da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh, "To amman ya akai kike wannan makarantar"turo baki tayi"to ita ba makaranta bace?"shiru yayi ya rasa amsar da zai bata,lokacin da suka iso bakin class d'insu har ciki ya shiga da ita Malamin English dake da period d'in farko tuni ya shiga kuma shima ya ga lokacin da aka kawo Fatun, hannu discipline ya d'an d'aga mashi"Sannu da aiki malam",amsa mashi yayi da"Yauwa",kallon fatuu yayi"jeki ki zauna"ta amsa da toh ta nufi seat d'insu sallama ya yi ma malamin ya juya ya tafi,saida ta isa seat d'in nasu sannan ta tuna da Haulat ganin bata a zaune sai d'ayar da suke zama atare ita kadae dama su ukku suke zama, Sai da malamin yaci kusan rabin first period sai ga Haulat ta shigo cikin ajin da yar sallama,nufo cikin ajin tayi sumimi sumimi zata wuce, "From where are you?" taji Malamin dake yin note a allo ya fad'a,tsaye tayi duk tasha jinin jikinta,juyowa yayi ya kalleta, "Baki ji bane,daga ina kike?" cikin en ina tace"daga bakin gate tare mu akai", "Ok ki fita idan na gama kya shigo", Magiya ta fara yi mashi tana rokon ya barta ta zauna,daka mata tsawa yayi"I said get out!kinsan kina son ki zauna a class kika ƙi zuwa da wuri", Jiki a sanyaye ta juya zata fita fatuu dake kallonta duk bata ji dad'i ba don sai taga kamar laifinta ne da bata biya mata ba kallon Malamin tayi Cikin sanyin murya tace"Sir pls Sorry,Wllh tare muke zuwa kullum da wuri",wani kallo yayi ma fatun ta d'an marairaice mashi fuska dama suna shiri da ita saboda k'okarinta gashi tana a Club din shi,juyawa yayi yaci gaba da yin rubutu, "Go and sit down"yace ma haulatu da har tasa ƙafarta guda waje,juyowa tayi ta dawo ciki tana zuwa saitin shi tace" thank u sir",kai ya d'aga mata ta nufi seat d'insu don ta zauna,suna had'a ido da Fatuu dake ta faman sakar mata Murmushi ta galla mata harara ta fara k'okarin fiddo English Note Book d'inta don tayi copying note d'in da malam ke yi,fatuu kuwa sai faman k'umshe dariya take don tasan laifin da tayi ma haulatun. Tun bayan da haulat ta shigo basu samu damar yin magana ba don Malamin English din double period gareshi yana gamawa kuma Malamar dake da Next period ta shigo har saida akayi break sannan fatuu ta kalli haulat, "Sorry k'awata wllh Mantawa nayi in biya maki saboda...." a harzuk'e Haulat ta katseta"Yar rainin sense,ba dole ki manta dani ba ankawo ki cikin had'addar mota,sanyin Ac ya ratsaki ta ina zaki tuna da wata Haulatu"fashewa Fatuu tayi da dariya, "Ya akai kika san a Mota aka kawo ni?", Dan ta6e baki Haulatu tayi"harma wanda ya kawo ki na sani ba Dan gidan Hajiyar Sanata bane?"da sauri fatuu tace"shine ya akai duk kika sani wai?", "Inata jiranki naga baki zo ba kuma nasan kin tabbatar man yau zakizo to don kar mu makara yasa na nufi gidanku ina zuwa bakin kopar gidan Umar na gidansu Bello yace man wani mai mota ya tsaya kin shiga kun tafi,ina jin hakan na juyo na nufi bakin hanya inata tunanin ko waye ya d'auke ki don sam ban kawo d'an gidan hajiya araina ba,koda nazo bakin hanya wani Mutum yace man Bus ta wuce baki ji takaicin dana ji ba dole na hawo mashin koda na iso har an fara taren yan makara,a bakin gate d'inne naji prefects nata Maganar Motar da aka kawo ki suna kuma zuzuta Mutumin da ya kawo kin,kinsan fa A.Sp Asma'u Kabeer har tambayata tayi wai ya kuke dashi.....", katseta Fatuu tayi da sauri,"ya kika ce mata muke dashin?", Dariya haulat tayi"Yo cewa nayi Yayanki ne", "Yauwa Allah gwara da kika ce masu hakan yan sa ido kawae,wai kinga yadda aka rink'a bin Motar da ya kawo nin da ido sai ma da ya fito zai gaisa da Principal ashe ya santa innalillahi!ke kinga kuwa yadda ake kallonshi", "Ai naji ance wai har kud'i yaba masu gadi,Binta Musa duk ta rud'e wai yadda ya kira Baba maigadi mai kirki ya bashi abun kaman a film..." da sauri fatuu ta amshe"Wllh baki ga uban kud'in da ya mik'o mashi ba,dafa inaga Maigadi Masifaffen hana shi yaso yayi wanda aka bashi aikau ashe Ya Handsome d'in na kallo shine ya kira shi shima ya bashi", "Ai in gaya maki suna can sun rud'e sai faman santinshi suke yi anga Mijin Novel,Labour Prefect Binta Musa ma wai zata zo kamun k'afa a wurinki,kinsan ma lokacin da aka samu a layi za'a kaimu muyi punishment ita tasa ni in gudo wllh sauran na can suna shara wasu na wankin toilet,ke hardae Sp Ni'imatu Abdullahi da take miskila saida ta tanka akanshi wllh",Wata Mahaukaciyar dariya Fatuu tayi, "Ƙyale banzar tazo d'in,yama za'ai Ya handsome ya sota da fuskarta kaman an ƙona baƙar leda",hannu Haulat ta kai ta d'an bugi kafadarta"wllh baki da kirki fatuu,aikam tana da kyawunta daidai gwargwado kawae don dai tana bak'a sosae ne,kuma ba ita kadai ke son nashi ba Asma'u Kabeer ai ba laifi tana da kyau kuma wankan tarwada ce...." "Allah yasa wankan kada ce wllh Ya Handsome ba abunda zaiyi da ita,ce man fa yayi shi baida budurwa", ita dae haulat dariya kawae tayi tace"wai bazamu fita break bane sai an dawo", "Wane break ai yau a aji zamu yi break d'inmu basai munsha wahalar fita ba"Fatuu tayi Maganar yayin da ta kai hannu ta d'aukko jakarta ta zage zip, fiddo abubuwan dake aciki tayi ta d'aura su saman desk,bin yoghourt da fruit da k'aton biscuit d'in haulat tayi kafin tace wani abu Fatuu ta fara bata labarin kayan dubiyar daya kai mata jiya da daddare da biscuit had'i da kud'in daya bata lokacin da ya kawota, "Kai Amman Mutumin nan yana da Mugun kirki wllh...." katseta Fatuu tayi"Mugun kirkin ma,ba kinga kayayyakin daya siya man ba lokacin da kika zo gaida ni", "Gani kai,nida har na samu rabona,da wani ne kika ma laifin da kikai mashi tun farko ko kallonki ma zai sake yi ne in ma bai d'au mataki akanki ba kenan,amman shi ji abun arzikin da ma yake maki wllh yaji dadi,ga kyau ga kudi ga kirki ko nayi rantsuwa bazan yi kaffara ba samun irinshi a wannan lokacin zaiyi Matuk'ar wahala wllh", Murmushi kawae fatuu ke saki ta bud'e masu biscuit da yoghourt d'in suka fara ci, Suna cikin yin break d'in sai ga prefects su biyar sun shigo,su Binta musa ne,Asma'u Kabeer,Amina Aminu,Halima lawal,sai Sp,dama mate dinsu ne suma duk Js 3 suke itama Fatun lokacin da suka shiga aji ukkun harda ita cikin wad'anda aka za6a za'a basu prefect d'in Displine master ne ya hana a bata don cewa yayi in aka bata watarana sai ta kashe wata tunda kaman yar dambe take bunu bunu an kai k'arar ta bugi wata harta raunata ta,gashi kuma lokacin sam bata da wani tsawo yar k'arama ce kan sauran da aka za6an, tana ganin sun shigo ta wani sha murr,saman Desk din wasu suka zauna wasu kuma suka tsaya a tsaye,tambayarta sukae wai haulatu ta gaya mata sak'onsu tace masu eh,nan suka shiga zuzuta haisam din suna fadin basu ta6a ganin mutum mai irin kyawun shi ba a Nigeria,tambayoyi suka rink'a yi mata cike da rainin wayau take basu amsa wani lokacin kuma ta 6a66ake masu da dariya ganin yadda duk suka susuce kan Ya Handsome,ba kamar Binta Musa da Asma'u Kabeer su da gaske sonshi suke sai faman rokonta suke wai ta shigar dasu wurinshi da taga dae bilhakki da gaske suke sai tace masu ita bata iyawa don bai wasa da ita duk wadda ke sonshi in ya k'ara zuwa taje da kanta ta fad'i mashi,nan take duk suka ce gaskia bazasu iya ba,bai yi wasa da ita bama ita dake yar'uwarshi balle su, kuma sunga yasan principal kar su ja ma kansu,fatuu tace to sai suyi hakuri kawae,k'arshe dai atare suka idasa cinye kayan break d'in su Fatun kafin suka tafi. Kallon Haulat Fatuu tayi fuska a tur6une"banzayen sun zo sun cinye mana abu gashi ma ban k'oshi ba", d'an Murmushi tayi tace"rabonsu ne ya tsaga suma", ta6e baki tayi"to sai kiyi sauri ki taso muje mu siya wani abu kafin adawo",tayi Maganar had'i da mik'ewa tsaye itama Haulat d'in ta tashi suka fita daga cikin class din. *💖ASANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching love story._ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *4️⃣7️⃣* Lokacin da suka tunkaro gate d'in,Discipline master na tsaye awurin masu gadi sunata yi mashi zancen Haisam,sai faman yaba kirkinshi suke,Dariya Malam Mahadi yayi yace"ai kufa dama kunfi kowa shaida kirkinshi tunda ya cika maku Aljihunanku,amma dae nima na yaba da kirkin shi gaskiya", adaidai nan su Fatuu suka k'araso bakin gate d'in,kallon masu gadin Malam Mahadi yayi"to ga wadda tayi maku sanadin Alkhairin da kuka samu nan sai kuyi mata godiya" ya yi Maganar yana nuna Fatuu,atare suka kalleta da mamaki Maigadi mai kirki kaman yadda suke cewa ya furta"Dama Fulani ce ya kawo?",sunan da yake kiran fatuu dashi kenan saboda sun sa6a sosai da fulatanci ma yake mata magana duk in tazo bakin gate d'in kuma dayake shi yana a toilet lokacin da fatun ta fito daga Motar Haisam shiyasa baisan itace aka kawon ba, "Eh Yayanta ne" Malam Mahadi ya fad'a,aikuwa nan suka shiga yima Fatuu godiya gaba d'ayansu suna fad'in Allah ya k'ara Arziki shi d'ayan da fulatanci yake mata godiyar ita dae sai faman sakin Murmushi take ba tare data ce masu komai ba, "Ku sai yanzu zaku je Break d'in an kusa dawowa"Malam Mahadi yace, turo baki tayi"to ai da a aji zamu yi break d'in bazamu fito ba sai kawai......"da sauri Haulat ta tari numfashinta tace"munci kayan break din tare da wasu ne to sai muka ji bamu k'oshi ba shine zamu je mu siyo wani abu mu k'ara" kai ya jinjina masu daga haka suka wuce, Bayan sun fita gate d'inne Haulat tace"kefa yanzu yakamata ki zama mai aji don d'an gidan Hajiyar Sanata ya kankaro maki girma,shiyasa na katseki da kina ma Malam Mahadi magana don nasan halinki sarai shima kina iya ce mashi banzayen prefects ne suka cinye mana abun break d'in wanda hakan ba girmanki bane kina dangin Senator",ta k'arasa tana tik'ar dariya,itama Fatun kyalkyacewa tayi da dariyar tace"Dangin Senator masu shanu ba,sufa duk sun yarda baki ga yadda Malam mahadin ma ke man magana ba cikin mutunci inda da ne wllh kora mu zaiyi ya hana ni fita break d'in tunda bamu fito da wuri ba",dariya suka ci gaba da yi Haulat nata tsokanarta tana fad'in dangin Senator. __________ Misalin karfe 4:30 na ranar,Haisam na zaune a falon hajiya saman Sofa 2 seater yana cin abinci,jikinshi sanye cikin Sportswear da gani gym zai tafi, "Wai wace yarinya ce yau ka kai Wtc ne?" hajiya ta jefo masa tambaya,sai da ya cinye abincin dake acikin bakin kafin yace"Wani abu?", "A'a,dama principal ce ta kira ni muka gaisa shine tace man yau ta ganka a Makarantarta kun gaisa har kake ce mata sister dinka ka kawo shine nike ta tunanin wacece ka kai Makarantar ne?" "Zarah" ya bata amsa ba tare daya kalleta ba, "Dama saida nayi tunanin itace ka kai", shiru yayi baice mata komae ba,ganin yana k'okarin mik'ewa tace"halan har ka k'oshi?", Kai ya d'aga mata"Yea,i ate too much food at work"d'an ta6e baki tayi"ka dae ci abunda ka saba ci ba dae abinci ba,ni da nasan hali ai saidae ka fadi ma wani hakan ya yarda badai ni ba", d'an murmushi yayi"Am serious yau naci abinci,Zarah tasa nayi alk'awarin zan ci abinci in k'oshi"fuskar Hajiya d'auke da tsananin mamaki tace"Fateemar ce tasa ka yin hakan?"kai ya d'aga mata alamar eh,ganin tana ta binshi da ido har lokacin da mamaki akan fuskarta yasashi fad'i mata yadda akai tasa shi yin Alk'awarin,Lokaci guda tayi Dariya ta furta"Ina ruwan Fateema,ta man daidai itama tasan ba yadda za'ai tarkacen su biskit su ruke Mutum kamar ka", daga haka ya nufi Dining area ya kuskure bakinsa had'i da wanke hannayensa a Washbasin duk da badasu yaci abincin ba,hanyar fita daga parlon ya nufa ya d'aga ma Hajiya dake kallonshi hannu alamar bye bye,itama hannun ta d'aga masa tace"A dawo lpy,Allah ya tsare. Yana fita parking space ya nufa ya fiddo bike dinsa cikin harabar gidan,jakarshi dake rataye ajikin bike d'in ya curo ya goyata a bayansa daga haka ya tasheshi bayan yasa helmet ya nufi gate da tuni an bude masa shi ya fuce. **** ***** ***** Bayan Sallar isha'i Haisam ya shigo gidan,parking space ya shige ya parker bike din,jakarshi rataye a hannunsa na hagu ya nufi part d'inshi,yana niyyar shiga cikin corridor wayarsa ta fara ringing alamar ana kiransa,hannu yakai cikin Aljihun wandonsa ya fiddota, tsayawa yayi ganin hajiya ce ke kiran nasa,picking call din yayi ya kara wayar a kunnansa, "Naji ka shigo ka d'an lek'o nan kana da bak'o", amsa mata yayi da"Ok" daga haka ya cire wayar,yaso ya isa part d'in nasa don ba abunda yafi buk'ata ayanzu face yayi wanka to amman baisan wane bak'o bane kuma baisan tsawon lokacin da ya d'auka yana jiransa ba hakanne yasashi aje jakar anan bakin corridor din ya juya ya nufi part d'in Hajiya, Da sallama ya shiga cikin falon lokacin daya isa,Hajiya na zaune tana opposite da wani dattijo sanye cikin manyan kaya riga da wando kanshi sanye da hula harda rawani,amsa mashi sallamar sukayi ya nufi sofa one seater dake kusa da wadda hajiya ke azaune ya zauna,gaida mutumin yayi cikin girmamawa ya amsa mashi, "Yauwa Mahaifin Ashiru ne yazo yana son ganinka" hajiya ta fad'a,shiru haisam yayi yana son ya tuna waye ma Ashirun,kallon Dattijon hajiya tayi"Malam bismillah kuyi magana", Amsawa yayi da toh ya d'an matso daga kan kujeran kafin yayi gyaran murya ya fara Magana "Dama naje can caji office ne don in dubashi to ananne nasamu labarin kaine ashe ka kai case d'in..."d'an dakatawa ya yi,sai yanzu Haisam ya gane Ashirun da ake nufi wato Gaye, d'agowa Malam Tanimu yayi cikin sanyin murya ya d'ora da fad'in"tun bayan da al'amarin ya faru banyi niyyar sa baki ba saboda babban laifi ne sukayi niyyar aikatawa ba don Allah ya kiyaye ba,kuma yakamata dama arinka bada goyon baya wurin hukunta masu aikata irin wannan laifin ta hakanne za'a samu saukin al'amarin,amman ina kowa baison a hukunta nashi,sai mutum ya aikata mummunan laifi amman kiri kiri kaga danginshi sun shiga sunyi yadda sukai an sake shi ba tare da an hukuntashi ba yadda yakamata,shiyasa kullum k'ara samun yawaitar masu aikata munanan laifuka ake tunda sunga ko an kama ma saki ake ba tare da anyi wani tsattsauran hukunci ba,Allah ya kyauta ya rabamu da son zuciya" gaba daya suka amsa da Amin, Gyaran murya ya k'ara yi kafin ya sake d'aurawa"Yau da naje tasani gaba yayi yanata kuka yana rok'ona akan kar na bari wai akai shi gidan yari shi wllh yasan yana shaye shaye da yan d'auke d'auke amman bai ta6a yunkurin aikata fyade ba,na nuna masa komae ya faru dashi shi yaja ma kansa da ya za6i yin irin wannan rayuwar har yayi abokai gur6atattu irinshi,bayan an maidashi cikine muka tattauna da wani d'an sanda nan mai kirki har yake nuna man ya tausaya ma yaron don ya jefa kanshi cikin matsala gashi yanzu da kyar ne in ba'a kaisu gidan yari ba,kuma matsalan wasu in aka yanke masu hukunci kan laifin da basu aikata ba in suka fito sai kaga sunzo suna aikata laifin saidae wanda Allah yasa yana da sauran imani,wasu kuma sukan had'u da manyan masu laifine sai kaga sun koyo mugayen laifukan da sunfi wanda suke aikatawa muni da sauransu dai..."dakatawa yayi yana maida numfashi kafin yaci gaba"atak'aice dai ni Uba ne,duk yadda naso k'arfafa zuciyata saida tayi rauni,maganganun d'an sandan nan sun tsaya man araina,kullum bani da fata da burin daya wuce inga Ashiru ya shiryu,shin yanzu in aka kaishi gidan yarin ya halayyarsa zata koma kuma?wannan tambayar ita ta tsaya man arai ta kuma saka ni jin tsoron zuwansa can d'in don bazan so yafi hakan lalacewa ba tunda dai ba'a ta6a canja ma tuwo suna,shi d'in d'ana ne ni na haifesa hakan bazai ta6a canjawa ba,ba komae ya bani kwarin gwuiwar zuwa gareka ba face furucin da ya rink'a yi yana kuka na ya yarda zai koma Jos in dae na ku6utar dashi lokacin da za'a maidashi cikin cell....", "Wani abu ake a Jos d'in?" Hajiya ce ta katseshi da wannan tambayar, "Eh akwai wani Yayana acan babban malamin tsangaya ne,ana tura mashi kangararrun yara ba kamar masu irin halin Ashirun wato masu yin shaye shaye da kuma sata kuma akan dace su shiryu,da farko lokacin da ya jefa rayuwarshi cikin wannan halin nayi tunanin zan iya gyarashi amman ina,ganin abun nashi yana yin gaba ne yasa nayi ma yayan nawa magana akanshi yace in kaishi can,wllh banfi sati guda da kaishi ba sai gashi ya gudo,bayan wani lokaci na sake d'aukarshi na maidashi amman sai ya sake guduwa kuma abunda ya tada man hankali shine da ya gudun ba nan gida ya dawo ba gaba yayi bamu san inda ya nufa ba,hankalinmu ya matukar tashi don ba irin neman da bamu yi mashi ba amman shiru ba labarinshi,haka muka hakura kuma muka dukufa da yin Addu'ar Allah ya bayyana shi kwatsam, wata rana sai gashi kamar an jefo shi,nayi Matuk'ar farincikin dawowarsa duk da canjin dana gani atattare dashi,wai ashe lagos ya tafi bayan ya gudun,to tun dagananne na hak'ura da turashi jos d'in duk da halin nashi saima abunda yayi gaba bayan yaje lagos d'in", sauke ajiyar zuciya suka yi gaba dayansu, "Yanzu mi kake bukata a wurina ne?" Haisam ne ya yi Maganar,shiru yayi ya d'an sadda kanshi k'asa kafin ya d'ago yace"idan zai yuwu ina neman alfarmar ayi mashi duk hukuncin da ya dace amman don Allah kar akaishi kotu don daga can ne za'a iya tura su gidan yari,na dad'e ina mashi Addu'ar shiriya watakil lokacinne yayi don tabbas naga nadama a idanuwanshi kuma sanin basu kaiga aikata laifin bane yasa nayi karfin halin zuwa nema mashi wannan Alfarmar,wallahi tallahi kaji arantse da ace yau sun aikata laifin koda shi Ashirun bai yin ba bazan ta6a nema masa sassauci ba duk kuwa yadda raina zai sosu zan bada goyon baya d'ari bisa d'ari akan ayanke masa hukunci", Jin ya dakata yasa Haisam fara Magana"at first munso ayi masu afuwa ne tunda basu kaiga aikatawa ba so bayan munje can da Yarinyar ne kuma ta kawo wani issue wanda yasa dole aka fasa yi masu afuwan da akai niyya bansan ko kasamu labarin hakan ba",da d'an rud'u Malam tanimu ya girgiza mashi kai"bansan wani abu ba bayan abunda ake tuhumarsu dashi,dayake tunda aka kamasu ni banje ba sai yau,yan uwansa dae na zuwa Mahaifiyarsa ma taje",jinjina kai Haisam yayi nan take ya fad'i masa dalilin da yasa aka fasa yi masu afuwar,cike da tashin hankali ya saka salati yana tafa hannuwa,a razane, a kuma firgice yace"Wllh sam bansan hakan abun yake ba da ban fara ma zuwa nema masa afuwa ba,ashe rashin hankalin Ashiru har yakai haka,yanzu ace saboda kayan maye zai goyi bayan wannan aika aikar da suka so yi ba don Allah ya takaita Al'amarin ba",lokaci guda idanunsa suka cuccuko tab da kwalla,girgiza kai hajiya tayi cike da takaici ta fara magana"nima dai na Matuk'ar girgiza wllh da jin hakan,sam Ashiru bai yi man wayo ba,yadda bai goyi baya ba tun farko kamata yayi jin wannan Mummunar niyyar tasu yasashi bujire masu ta hanyar tona masu asiri amman ina,saboda tsabar rashin hankali ya za6i ya jefa kanshi cikin matsala ta hanyar goya masu baya duk da yasan mummunan kudirinsu ", "Ai Hajiya ni yanzu ma wllh na cire hannuna daga lamarinshi daman rashin sani ne,duk hukuncin da ya dace ai mashi ai mashi kawae shi ya ja ma kanshi" yana kai Maganar kwallan daya taru suka zubo mashi sharrr ya sunkuyar da kan k'asa, Sigh Haisam yayi gently yace"We should thank Allah da bai basu nasarar aikatawa ba gaba daya,lamarin zai fi zuwa da sauki,in sha Allah zanyi ma wanda case din ke ahannunsu Magana za'a duba ayi abunda zai yuwu", Hajiya ce ta shiga bashi baki tana cewa kar yasa damuwa aranshi yaci gaba da yi mashi Addu'a kawae don ita kadai ce magani inda rabon shiryuwa wataran komae zai zamo tarihi. Mik'ewa Haisam yayi ya kalli Hajiya"is that all?"ya tambayeta,kallon Malam tanimu dake ta matsar kwalla tayi tace"Malam ko akwae wani abu?"da sauri ya girgiza mata kai"Babu komae hajiya Nagode kwarae,Allah ya k'ara girma",jin hakan yasa Haisam yi mashi sallama ya nufi hanyar fita daga falon don duk a takure yake bazai ta6a samun natsuwa ba har sai yaji saukar ruwa ajikinsa,d'an k'ara tattaunawa sukai kan halin da yara matasa ke jefa rayuwarsu daga bisani Malam Tanimun yayi mata sallama ya tafi. ____________ Washegari da Safe misalin k'arfe 7:30 Fatuu ta fito kopar gida jikinta sanye da kayan makaranta,tsaye tayi gefen kiosk d'in Amadu tana d'an tunanin ko Ya Handsome ya wuce,zuciyarta ce ta raya mata wani abu hakan yasa ta mik'i hanyar zuwa gidan Hajiya,tana karya kwanar Gate aka zuge gate d'in,tsaye tayi tana kallon Motar da ta fito wadda suka je Police Station da itace,adaidai inda take tsaye Motar ta tsaya glass d'in ya fara sauka ahankali tana had'a idanu da Haisam ta sakar mashi Murmushi,shima murmushin ya maida mata yana sanye cikin Suit Ash and black colour,alamar ta shigo yayi mata da kai hakan yasa takai hannu da sauri ta bud'e Motar ta shiga,rufe glass d'in yayi bayan ta rufe kopar,daga haka yaja Motar suka fara tafiya, "Gud Morning Ya Handsome",fuskarshi asake yace" Morning,how a'r u", "I'm fine" ta bashi amsa,jinjina kai yayi ba tare da ya k'ara cewa kamae ba, "Ya Handsome ashe kasan Principal d'inmu?" kai ya d'aga mata alamar eh, "Ashe shiyasa kasan Makarantar da nike"nan ma kai ya d'aga mata,ganin sun wuce kwanar gidansu Haulat yasata sakin salati "kai innalillahi...."kallonta yayi yace"What?", "Wllh jiya mantawa nayi ban biya ma kawata Haulatu ba hakan yasata ta makara aka tareta,ranta ya 6aci har tana ceman wai tunda an kawo ni a Mota sanyin Ac ya ratsa ni ai dole in manta da ita", d'an bud'a idanu yayi yace"baki kyauta ba" turo baki tayi cike da shagwa6a"to ai mantawa nayi ko,kowa ba yana yin mantuwa ba",d'an ta6e lips d'insa yayi sai kuma yace"to yau sai ki biya matan ko", "To ai saidae ka aje ni sai inje in biya mata mu hau Bus" kallonta ya d'anyi "Why,ko wannan ba Mota bane?", langa6ar da kai tayi idonta akanshi"to ai kai naga baka son ana zauna maka a bayan mota to kuma in tazo ita a ina zata zauna?"d'age mata gira yayi yace"mukai dake ba'a zauna man a bayan Mota?" zaro ido tayi cike da mamaki"to amman jiya dana zauna ba k'in tafiya kayi ba kace sai na zauna a inda ya dace ka nuna man gaba", "Yea,ai ni ba Driver dinki bane da zaki zauna a baya kuma gaban ba kowa" bud'a baki tayi alamar mamaki"wai dama saboda hakan ne kace in dawo gaba?'kai ya d'aga mata kafin yace"ina ne gidansu Friend d'in naki?", "To ai mun fa wuce kwanar tana baya" gyad'a kai yayi ya fara k'okarin juya motar,kallonta yayi bayan ya juya"shi center d'in nasu yana fita titi ne?" "Eh,amman fa bansan ko Wannan k'atuwar motar zata wuce ba don lungun nasu d'an tsukuku ne,yauwa ga lungun nan" takai Maganar tana nuna masa lungun da yatsanta,kallon lungun yayi nan take ya fahimci motan zata iya wucewa hakan yasashi kutsawa ciki,suna zuwa daidai gidansu Haulat tace "wait, wait ga gidan nan",tayi Maganar tana nuna gidan,ganin tana k'okarin fita yace"ki bari ayi mata horn mana ta fito",da sauri ta kalleshi ido waje"Haulatun za'ai ma horn,ita da ba mota garesu ba taya zata gane ita ake kira bari dae inje in kirata" yadda tayi Maganar sai kace ita Motar garesu,tana shiga cikin zauren gidan suka kusan cin karo da ita ta taho tana sanya hijabin Makaranta,tana ganin fatuu tace"ai na zata yauma a Motar aka daukeki kin manta dani..."da sauri Fatuu tasa hannu ta rufe mata baki, "Dalla kiyi shiru da Ya Handsome d'in fa muka zo" da mamaki Haulat ta d'an bud'a idanunta"bangane ba?", "Shi d'an gidan hajiyan nike nufi gashi nan kopar gidanku shi yace in kirawo ki zai kaimu Makarantar" zaro ido Haulat tayi ta kasa magana,ita kam Fatuu hannu takai tana gyara mata wuyan hijab d'inta da ya jirkice ta goge mata maikon kosai data gama ci agefen bakin, "Ki taho mutafi kada yayi ta jiranmu,amman fa kada kiyi mashi hauka ko kauyanci da kin shiga motan ki gaidashi sai kija bakinki kiyi shuru don shi baison Surutu" daga haka tayi gaba Haulat da tayi sototo tana saurarenta tabi bayanta,har zata fita ta juyo da sauri"ki saka wannan jakar ledan taki cikin hijab ki 6oyeta har muje class don kauyanci ne ki shiga wannan had'addar Motar da Jakar leda",kai kawai ta gyad'a mata tayi yadda tace daga haka suka fita,nuna mata kopar baya Fatuu tayi tace"ki bud'e ta ki shiga,in baki iya ba in bud'e maki kuma in kin shiga ki kulle da karfi don kar taki rufuwa" d'an Murmushi kawai Haulat tayi takai hannu taja Door handle d'in sai gashi kopar ta bud'e fatuu na ganin ta shiga itama ta bud'e gaban ta shige, "Ya Handsome gata nan na kirata" kai ya d'aga mata yana k'okarin jan motan Haulat data kame kanta agefe guda tace"ina kwana",kai kawae ya jinjina mata daga haka suka tafi,tunda suka hau hanya Fatuu keta faman zuba kaman burkakkar radio,cike da mamaki haulat ke kallonta ita data gama mata hud'ubar taja bakinta tayi shiru baison surutu amman ita ji yadda ta cika su da surutun,ita dai saidai ta d'an girgiza kai kawae kai kace bata acikin Motar ma. Yauma har gaban Administrative Block ya kaisu,yana tsayawa Haulat ta rasa yadda zata bud'e Motan ta fita hakan yasa tayi zugudum kirjinta na bugawa, kallon haisam Fatuu tayi tace"Yauwa Ya Handsome inata son in tambayeka wai jiya kuwa ka cika alkawarin daka yi man?" Kwantar da kanshi yayi jikin headrest ya d'aga mata shi alamar eh, "To kaci ka koshin?" daga yadda yake ya d'an juyo ya kalleta"Yea,sosae naci i can't even remember when last dana ci abinci haka",kyalkyacewa tayi da Dariyar farinciki harda d'age kai sama,shi dae sai kallonta yake yana d'an Murmushi, kallonshi tayi bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"to yauma ka d'aukko biscuit d'in?"kai ya daga mata alamar eh, "To ka bani shi sai mu sake kulla Alkawarin yauma" yar harararta yayi"nak'i wayon yau ni zanci abuna in kina so sai ki siya", Magiya ta fara yi mashi tana jujjuya kai wai ya bata ai anan ba'a saida irinshi,Haulat dake baya batasan lokacin da ta fara sakin Murmushi ba ga mamaki tanayi yadda ya sake ma Fatun sai kace dan'uwanta da gaske, "Zarah bafa zan baki ba,in kuma na bakin i won't promise u zanci wani abinci a wurin aiki"turo baki tayi ta kai hannu ta d'aukko jakarta dake ajiye akasan seat ta juya zata fita, "Zarah" ya kirata,juyawa tayi ta kalleshi fuska a d'aure alamar tayi fushi,d'an Murmushi yayi ya girgiza kai daga haka yakai hannu baya gefen haulat ya d'aukko jakarshi,budeta yayi ya fiddo biscuit har yafi na jiya girma,mik'o mata biscuit d'in yayi ganin tak'i amsa yace"take it!" tana tura baki tace"to ai baka yi alkawarin ba" shiru ya danyi yana kallonta,karfin halinta na bashi mamaki,sigh yayi"to zan ci wani abu in naje wurin aiki shikenan?" "Abinci ko mi?" "Duk abunda na samu zanci kedai ba so kike in ci in koshi ba?" da sauri ta d'aga mashi kai, "Owk zanyi hakan,ki amsa kina sani ina makara fa", da sauri takai hannu ta kar6i biscuit d'in tasaka acikin jakarta tana d'agowa ya sake mik'a mata N500 yace su samu drink su had'a batare da musu ba ta amsa tayi mashi Godiya, Haulat dai nata bin ta da ido,so take kawai taga yadda zata bud'e kopar,aikuwa tana ganin yadda Fatun tayi itama tayi sai gashi kopar ta bud'e,wani irin sanyi taji aranta dama bata son agane bata iya bud'ewarba ba kamar Fatuu yanzu tayi mata surutu, tsaye Fatuu tayi tana mashi bye bye yayinda aketa faman binsu da ido saida ya gama juya kan Motar ta kalli Gate sannan ya sauke glass d'in side din da Fatuu take tsaye,alamar tazo yayi mata da kanshi,mik'a ma Haulat jakarta tayi ta nufi Motar,tsaye tayi abakin kopar tace"gani" hannu ya kai cikin jakarshi dake a gefe sai gashi ya fiddo wani Biscuit d'in irin wanda ya batan fuskarshi d'auke da k'ayataccen Murmushinshi yace"I ave another biscuit,so shi zanci in naje aikin tunda ban yi alkawarin cin wani abu daban ba" zaro ido tayi tasa tafin hannun damanta ta rufe baki alamar mamaki,ganin yanata Murmushi yasa ta cire hannun rai a 6ace kaman zatai kuka tace"ni za kaima wayo Ya Handsome?"d'an harararta yayi"ke kika so yi man wayo bare ni,C'mon Go Class Yar Yarinya", daga haka glass d'in Motan ya fara rufewa sama a slow yana gama rufewa yaja motan ya tunkari gate,yana zuwa gate masu gadi suka fara d'aga mashi hannu don sai yanzu suka gane ko waye ganin Fatuu da sukai,tsayawa yayi ya sauke glass d'in side d'inshi yana amsa gaisuwar da suke mashi har wani d'an russunawa suke,ganin ya tsaya yasa Fatuu tsallakawa side d'in masu gadin taci gaba da kallonshi fuska atur6une ita ala dole ya 6ata mata rai yayi mata wayau,ta cikin side mirror ya hangota hakan yasashi d'an lek'o da kanshi suna had'a ido da ita ya saki Dariya ganin yadda ta cika fam kaman zata fashe,Sauran Mutanen dake kallonshi suma basu san lokacin da suka fara yin dariyar ba duk da basu san tak'amaimai dalilin yin dariyar tashi ba kawae ya burgesu ne,Wohoho mai kyau ya huta(Allah sarki,sarar kawayena na sec skul😍),maida kanshi yayi yaja motan ya fuce daga cikin Makarantar. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 4️⃣8️⃣ .......tsallakowa Haulat tayi inda take tsaye ganin tak'i tahowa su tafi aji, "Mu tafi" tace mata, k'wafa tayi "Wllh Ya Handsome sai yasan ni ya yi ma haka" Murmushi Haulat tayi tace"wai mi yayi maki ne?" tana tura baki ta fara bata labarin rashin cin abincinshi da Hajiya ta fad'i mata da yadda suka yi jiya daya bata Biscuit d'in da sukai break da kuma yadda yau yayi mata wayo ya bata ashe yana da wani, Dariya sosae Haulat ke yi,ita mamaki ma fatun ta bata wannan k'arfin hali har ina, "To kema in banda abunki ga abunda ya saba ci sai kice lokaci guda sai ya canja ya rink'a cin abunda kike so" a harzuk'e tace"To Wannan biscuit d'in abinci ne,ta ina Mutum zai wani k'oshi da biscuit ", "To ai tunda ya saba cinsu yana k'oshi dasu ne,kinsan kowa da kalar halittarshi akwae Mutane da yawa da basu son cin abinci gara ma shi yana d'an ci kuma duk da ba sosae yake ci ba zaki ga ahakan yana k'oshi halittarsa ce shima haka", ta6e baki tayi "sai yaje yai ta cin su in Ulcer ta kamashi ba shi ya sani ba"daga haka suka iso bakin class d'insu ta shige ita kam Haulat girgiza kai tayi cikin ranta ta ayyana"Fatuu ta cika rigima,ko ina ruwanta da wani cin abincinshi ma"daga haka itama ta shige cikin ajin. Bayan sun dawo daga Break Malaminsu na lissafi ya shigo,single period gareshi yana cikin yi masu bayani Malamar Basic science dake da Next period tazo ta sanar cewa bazata samu shigowa ba saboda wani uzuri daya taso, don haka in period d'inta tayi su d'aukko darasin da tayi jiya su k'ara karantawa daga haka tayi ma Malamin Maths d'in godiya ta fita,lokacin da period d'inshi ta kar'e maimakon ya fita sai yace masu zaiyi amfani da lokacin Malamar tunda bazata samu shigowa ba yana so su gama topic d'in yau gobe sai kawae su shiga sabon darasi,duk ba haka suka so ba don da har sunji dad'i zasu wataya in ya fita don period din Malamar Double ce, Tun yana masu bayani suna ganewa har abun ya gundiresu dama kuma mafi akasari ba son lissafin suke ba don ba kowa ke ganewa ba,juyawa Fatuu tayi tana k'arema sauran yan ajin kallo ganin kowa ya tur6une fuska da gani sun gaji yasa ta juyo ta kalli malamin rai a6ace,can taja d'an guntun tsoki a hankali,da sauri Haulat ta kalleta,hannu biyu tasa tayi tagumi ganin Malamin baida niyyar tsayawa da alama duka double periods d'in yake son yin amfani don har ya shiga sabon Darasi, "Malam gaskiya mun gaji fa" Fatuu ce tayi maganar,a fusace ya juyo don lokacin da tayi Maganar yana cikin yin rubutu a board ne, "Who said that" ya tambaya, gaba d'aya yan ajin suka yi tsit kamar bada su yake ba, "Wacece tayi wannan Maganar" nan ma shiru kowa yayi suna jin tsoron su nuna Fatun,aikuwa nan take ya harzuk'a cikin tsawa yace"U're Very Stupid!baku ji mi nace bane,ko ku nunata ko kuma ku ja ma kanku ku duka wllh, "Sir ni ce" Fatuu ta fad'a fuska a d'aure,wani kallo ya bita dashi cike da mamaki ya furta"kece!" kai ta d'aga mashi alamar eh, "Ke mara kunya ko?" turo baki tayi "a'a ba rashin kunya bane,duk mun gajine kuma ko ganewa ma bama yi yanzu,kace so kake ka gama topic d'in gashi har ka fara wani",still yayi yana kallonta da alama ta d'aure mashi kai,can yace"su yan Class d'inne suka ce maki sun gaji kuma basu ganewa?"kai ta d'aga mashi alamar eh, jinjina kai yayi ya kalli sauran yan ajin fuskarshi a murtuke"Class ku kuka ce mata kun gaji baku ganewa?"tsiit suka yi kowa ya kasa tanka mashi saboda sabon Malami ne d'an bautar k'asa ne shima kanshi rawa yake gashi ya cika zafi, tsawa ya daka masu"baku ji mi nike tambayarku bane!"gaba d'aya suka had'a baki wurin cewa "a'a", "To mara kunya sunce basu suka ce maki ba,dama na lura kinfi kowa rashin kunya aduk classes d'in da nike d'auka to zan cire maki duk wani rawar kanki,i will definately deal with u,fito gaban allo ki kama kunnanki" wani kallo tayi mashi kafin ta fito d'in,tana zuwa gaban allon tayi tsaye k'erere tana turo baki,a fusace yace" baki ji mi nace kiyi bane!", kallonshi tayi"to ai ni ban yin kamun kunne" da mamaki ya maimaita abunda tace, "Miyasa baki yin kamun kunnan?" shiru ta mashi hakan yasa yan ajin had'a baki wurin cewa"Malam bata lafiya" juyawa yayi"mike damunta?"ya tambayesu, "Aljanu gareta in tayi kamun kunne ko aka bugar mata kai tashi suke" wata mai zazzak'ar murya daga can baya ta fad'a,juyowa yayi ya kalli fatun lokaci guda kuma ya yarda da aljanun gareta, "Ki rage tsawonki anan" ya fad'a yayin da ya koma gaban Allon yana ci gaba da yin rubutun,su kuwa gaba d'aya yan ajin idanunsu na akan Fatuu data kumbura kamar zata fashe,tafi jin haushinsu fiye da malamin,ganin anata kallonta ne yasa tayi kwafa da karfi tace"Wllh in dae aka bugeni bazan k'yale ko wacce banza ba,duk sai na rama tunda baku san abun arziki ba" ta k'arasa tanata huci,Malamin na jinta yayi shiru bai tanka ta ba,hakan yasa ta k'ara cewa"dallah kowacce banza ta daina kallona duk baku kuka ja man ba,matsoratan banza da wofi kawae....." "Keep quiet!" Maths teacher d'in ya daka mata tsawa yayin da ya juyo yana kallonta fuska a murtuke,turo baki tayi tana kallonshi k'asa k'asa,tsoki yayi ya juya yaci gaba da rubutun duk da hakan bata kyalesu ba kasa kasa ta rink'a yi masu Masifa tana yarfa d'an yatsanta manuni alamar zata kamasu, Juyowa yayi bayan ya gama rubutun yace"kuyi copying wannan,tomorrow i will explain it",amsa wa sukai da"Ok sir" nuna dayan 6arin board d'in yayi ya tambayesu sun gama kwafar rubutun suka ce eh,hakan yasa ya goge wurin ya rubuta Assignment,a Wayarshi ya ringa kallo Question d'in yana rubutawa a Allo,bayan ya gama rubutawa suka tambayeshi suyi copying Assignment d'in yace masu a'a ba nasu bane,kallon Fatuu yayi yace nata ne Assignment d'in ta tabbatar gobe tayo shi ta kawo mashi kuma a Allo zata yi ma yan ajin bayanin yadda ta fidda shi in kuma ta kasa to duka filin dake gaban classes d'insu ita zata share shi ta kuma wanke duka toilets dinsu har tsawon sati guda sannan ya k'ara mata da bugu,k'ank'ance idanu tayi tana kallon Assignment d'in da ya batan kafin ta kalleshi tana tura baki tace"ai baka yi mana irinshi ba", "Eh nasani,kece zaki yo shi kiyi ma sauran yan ajin bayani,ga amsar da nike so ki samo nan na rubuta a k'asa in dae amsar da kika samu bata yi daidai da ita ba to baki yi shi daidai ba" cike da isa yana wani shan k'amshi yake mata Maganar daga haka ya kwashe kayanshi da yayi amfani dasu ya kalli sauran yan ajin yace"Till we meet tomorrow" ya fuce abunshi, Mik'ewa tsaye Fatuu tayi tana k'are ma Assignment d'in kallo,sam bata san ta ina zata fara yinshi ba bare har ta gano amsar daya rubuta a k'arshen,lokaci guda ranta ya k'ara 6aci ta harzuka juyawa tayi tana kallon yan ajin da suma ita suketa kallo tun bayan da malamin ya fita nan take ta fara zuba masu ruwan bala'e tana yi tana buga desk ta kuma ci alwashin indae har bata yo Assignment d'in daidai ba yasata yin abunda yace wllh kowa sai taci ubanta,tun tana masifar a k'asa har abun yakai ga hawa saman desk yadda zata ji dadin ganin kowa kuma kowa ya jita,gaba daya kowa yayi tsit ba wanda ya tanka mata don sun san halinta sarae bata iya fad'an cacar baki ba sai nakai bugu kamar yar dambe da mutum ya tanka mata yanzu ta hau shi da bugu koda kuwa ya girme mata haka zatayi suka kan mutum ta mak'alkale shi kaman biri,Haulat dai girgiza kai kawae take don tasan in tayi irin wannan zuciyar bata jin lallashi,saida tayi mai isarta don kanta ta hakura ta saukko daga saman ta zauna saman seat taci gaba da kwafar rubutun tana yi tana kwafa had'i da tsoki, sai bayan da aka tashi ne lokacin da Bus ta saukesu Haulat ta fara bata hakuri ta nuna mata duk laifinta ne da batayi Magana ba tunda ba ita kadae ta gaji ba kuma ba wanda yasata tace mashi hakan dama dole zai ga tayi mashi rashin kunya ne data k'yaleshi yai tayi har ya gama ya fita,shiru tayi bata ce mata komai ba, "Yanzu to shi Assignment d'in daya bakin kin iya ne?" Haulat ta tambayeta,nan ma shiru tayi mata kaman bazata ce komae ba can kuma tace"ko ban iya ba sai na dage nayi shi ko don in bashi kunya,mugu kawae ai da biyu ya bani shi bacin yasan bai mana shi ba,baki ga ma a wayarsa ya kwafe shi ba" kai Haulat ta d'aga"Eh nagani,Allah ya taimake ki kiyi shi daidai",a hankali ta amsa da Amin,adaidai nan suka rabu da Haulat d'in, Fatuu tayi gaba ita kuma ta shige kwanar gidansu. Tun bayan data koma gida ta baje a tsakar d'akinta tanata faman kokarin yin Assignment d'in,saidae sam ta kasa,har wani textbook d'inta na maths ta duba wai taga ko zata ga irin tambayar amman ina ko mai kama da ita bata gani ba gashi matsalar ma bata san sunan topic d'in Assignment d'in ba balle ta duba table of contents na text book d'in ta gano page din da akayi irin topic d'in ko zata samu koda shigen tambayar ne,duk ta had'a uban gumi,k'arshe data gaji ta buga littafin da kasa tana ta faman huci ga uwar yunwa dake faman cinta don dole ta mik'e ta nufi Kitchen ta zubo abinci,bata wani ci na kirki ba taji duk ya fita aranta don hankalinta ba'a kwance yake ba bata da burin daya wuce taga tayi Assignment d'innan ba kuma don tana tsoron hukuncin da za'a mata bane sam ta saba da Wannan kawae so take ta k'ure Malamin da sauran yan ajin,can ta tuna da bata yi sallah ba zuciyarta ta raya mata k'ilan ma shiyasa ta kasa yin Assignment d'in,zumbur ta mik'e taje tayo Alwala tazo tayi Sallah data gama harda yin Addu'ar Allah yasa tayi shi daidai,bayan ta gama ta k'ara d'aukko littafin Maths d'in don ta k'ara gwadawa ko tayi daidai amman ina ko steps d'in dama zata bi har tasamo irin amsar daya batan bata sani ba,duk da hakan bata sare ba taci gaba da jagwalgwalawa a paper in tagama taga baiyi ba sai ta yaga paper din ta ciro wata ahaka sai da ta yaga fefofi masu yawa da abun ya isheta sai kawae ta zabga uban tagumi fuskarta a yamutse ta rasa yadda zatayi tai solving dinshi,tana cikin wannan yanayin Kawu Amadu ya fad'o mata arai aikau zumbur tayi ta mik'e ta nufi waje duk da batasan ko ya dawo bama don bata ji motsin shigowarshi ba kuma bata ji ya shigo d'aukar Abinci ba a kicin,tana zuwa zauren taga kopar d'akinshi a rufe alamar bai dawon ba,komowa tayi cikin gida amma ta d'an ji sanyi cikin ranta don zuciyarta na tabbatar mata da k'yar inba shi zai iya fidda mata shi ba tunda shi d'an Senior ne kilanma su anyi masu irinshi dama kuma yana yi mata Assignment in bata iya ba,cike da kwarin gwuiwa ta koma daki don ta jira dawowarshi,can ta mik'e tace bari taje tayi wanka kilan kafin ta gama ya dawo. Bayan tayo wanka ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ko mai bata shafa ba burinta kawae taji Kawu Amadu ya dawo,zaune tayi ak'asa ta tasa littafin Assignment d'in agaba tayi zugudum ahaka ta fara gyangyad'i amman taki bari baccin ya d'auketa duk da tana jinshi sosae,tana hakan ta jiyo k'arar bud'e d'akinshi aikuwa a sukwane ta rarumi littafin Assignment d'in da biro tayi waje,tana zuwa d'akin nashi ta banka ko sallama babu,lokacin yana cikin cire Uniform d'inshi don har ya cire rigar daga shi sai singileti amman bai kaiga cire wandon ba,kallonta yayi fuska amurtuke, "Kina da hankali zaki shigo man d'aki haka ko sallama babu!" shiru tayi tana kallonshi fuska a yamutse, ganin hakan yasashi cewa"lafiya?", cikin yar en ena tace"Daman tun d'azu nike jiranka Assignment ne don Allah zaka yi man ni nayi nayi amman na kasa",yar harararta yayi"shine don baki da hankali daga dawowana zaki banko man d'aki ko,to banyi ki futa ki ban wuri",ta6e baki ta fara yi kaman zatayi kuka ta hau yi mashi Magiya,fuska a d'aure yace ta fita to ya gama cire kaya,da sauri tace to,ta juya ta fita,abakin kofar d'akin nashi ta tsaya bayan wani d'an lokaci ta kware baki tace"in shigo ka gama?"banza yayi mata ta k'ara maimaitawa,jin shiru yasa ta d'an lek'a kanta cikin d'akin lokacin yana tsaye daga shi sai d'an boxer shorts amman sai cewa tayi"Kawu ka gama ne in shigo"a fusace ya kai hannu ya rarumo jakar Makarantarshi zai jefo mata tana ganin hakan ta janye kan da sauri, ci gaba tayi da tambayar kawu ka gama in shigo,daga wajen ta maida abunma kamar wak'a,d'an guntun tsoki yaja lokacin daya gama shiryawa yace"in kin gadama ki kawo man Abinci",da sauri ta amsa da toh, Kawo mashi Abincin tayi harda ruwa masu sanyi,tana ajewa a gabanshi ya d'an rankwashi kanta"shegiya dayake buk'ata kike awurina harda su ruwa baccin kullum sai nayi fama dake kafin ki kawo man" ya k'arasa Maganar yayin da yake zaunawa a gefen yar katifarsa, itama zaunawa tayi ak'asa hannunta guda tana d'an sosa inda ya rankwashetan,fara cin abincin yayi ita kuma tayi mashi k'uri da ido,yana cikin ci ya kware ya hau yin tari ta hau yi mashi sannu,a fusace ya kalleta bayan tarin ya lafa"Sannun ubanwa,kin k'ura man wad'annan idanuwan naki uwa na mujiya ba dole in kware ba ko ki daina kallona ko ince banyi wllh"turo baki tayi ta juyar da kanta gefe har ya gama cin abincin, "Kawo muga Assignment d'in in zan iya ko kya tashi kiban wuri kin wani tsareni sai kace wanda yaci maki bashi"da sauri ta mik'a mashi Littafin bayan ta bud'o daidai inda Assignment d'in yake,kar6ar littafin yayi ya k'ura idanu yana kallon tambayar da za'a fiddan, "Wannan wane topic ne,Quadratic Equation ne ko mi?"yayi tambayar had'i da kallonta,watsa hannuwa tayi tace "wllh nima ban sani ba ya dae ce wai ga amsar da za'a samo nan ak'asa in ba'a samo irinta ba to ba'ayi daidai ba,amman na duba ma Quadratic equation d'in da akayi mana naga kwata kwata basu kama da wannan har a textbook d'ina na Maths na duba banga wanda yayi ko shige dashi bama" k'ara kallon Question d'in yayi kafin ya d'ago yace"to shi wannan din a wane topic yayi maku shi?", "Bansani ba,kawae tambayar ya bada" jinjina kai yayi"aikau dae wllh dakyar in zan iya yinshi nima don gaskiya ba'ayi mana irinshi ba,amman bari dai in duba textbook d'ina nima muga ko za'a samu irinshin"da sauri tace to,don da har gabanta ya fad'i, Ba irin k'okarin da Amadu baiyi ba don ya fidda mata shi amman abun yaci tura duk ya had'a uban gumi, shima sai faman yago papers yake yana jagwalgwalawa kaman dai yadda Fatun tayi, a k'arshe dakyar ya samo wani problem anyi solving mai shige dashi acikin textbook d'inshi, a hankali ya rink'a bin steps d'in da akayi waccan wai ko zai iya fidda mata,sai faman sharce zufa yake Fatuu nayi mashi sannu,can ya d'ago a fusace ya wurga mata bangon littafi yace tayi mashi firfita baiwar Allah da sauri tace to ta d'auki bangon ta fara yi mashi don bata da burin da ya wuce taga yayi mata Assignment din,abu fa ya ture,lissafi an koya maka ma ya gagareka yi balle wanda ba'a koya maka ba,baka ma san hanyar da zaka bi kayi shi ba,kwalwar Amadu fa ta cazu iya cazuwa gashi ba abun yace zaiyi goggling ba tunda wani abunma ba yadda za'ai ya rubuta shi da wayarshi,ak'arshe dae da ya fusata sai ya cillar da biron ya d'auki paper d'in da yake solving d'in ya kekketata a fili yace"ina dalili,haka kawae in haukata kaina,ke nifa dama wllh ban kaunar Maths don ba yarda zanyi nike yinshi tunda ya zama dole", Fatuu na jin haka idanunta suka cicciko da kwalla ta fara ta6e baki zatai kuka,cikin muryar kuka ta fara mashi Magiya,a harzuke kaman zai kai mata bugu yace"to wai ya kike son inyi ne?ba kiga duk irin kokarin dana yi bane,inda na iya ai zan maki ko,shima malamin daya baku Assignment dinnan ina tunanin yaci kai,taya zai baku abu alhalin bai maku irinshi ba,kuma ya rubuta question kawae ba wani d'an bayanin da mutum zai gane ko wane topic ne",ita dae Fatuu sai faman matsar kwalla take,wani kallo ya wurga mata mai kama da harara ya dan ja guntun tsoki can ya kai hannu ya daukko wayarsa, "Bari in kira wani abokina d'an Class dinmu yana da kokari sosae shi ke yin na daya a ajinmu kilan shi ya iya yinshi", har Fatuu taji dan sanyi a ranta,bayan ya kirashi yayi mashi bayani kan Assignment din,yace kanwarshi ce aka ba shi kuma yayi iya bakin k'okarinshi ya kasa,Abokin nashi yace ya tura mashi Question d'in ta Whatsapp ya gani,bayan sun gama wayan ya d'auki hoton tambayar ya tura mashin daga haka suka yi jugum jugum suna jiranshi,bayan wani lokaci sai gashi ya kirashi a waya,Amadu na d'auka tambayar daya fara yi mashi itace wai under wane topic ne aka ba sister d'in nashi wannan question d'in,Amadu yace itama bata sani ba kawae tambayar ya rubuta masu yace ga irin amsar dayake so su gano nan,nan take Abokin yace to gaskia wannan zasuyi ta wahala ne kawai,tunda ko su ba'ayi masu irinshi ba balle su san hanyar da zasu bi su gano irin amsar da yake son ba,abunda za'ai ya bari gobe in sunje Makaranta sai su ba Malamin Maths d'insu yayi masu bayanin yadda za'a fidda shi kawae,nan take Amadu yace hakan za'ai,ai shi sam yama manta yayi wannan tunanin kuma yasan Confirm Malamin nasu zai fidda masu don ya had'u a lissafi,daga haka suka yi sallama yayi mashi godiya, Koda yayi ma Fatuu bayanin shawarar da suka yanke da Abokin nashi sai tasa mashi kuka tana fad'in"ai gobe zai amsa fa,kuma da safe muke dashi",a fusace Amadu ya d'auki littafin ya wurga mata ajikinta, "Gashi nan to sai kije kisan yadda zaki fidda kayanki,ni ina zargin ma wllh wani laifin kika aikata aka baki wannan aikin mai dan banzan wahala shine zaki zo ki wahalar da Mutane a banza a wofi,da ganin yadda kika tashi hankalinki baki da gaskiya,in ma laifin kikai aka baki Allah ya k'ara yasama karki iya fidda shi har goben tayi a zane ki tunda haka kika fi so,kinga in halinki ne gobe ma sai ki k'ara yin laifin da za'a baki irinshin,dalla tashi ni ki fita ki ban wuri kinzo kin hanani hutawa balle ko shago inje in bud'e", Cikin tsananin fushi ta mik'e har wani huci take tana d'an harararshi,d'aukar littafin tayi da bironta da ya wurgar can gefe ta nufi hanyar fita,adaidai bakin koparshi ta tsaya,juyowa tayi lokacin yana niyyar kwanciya, A tsiwace tace"Eh laifin nayi,kuma inna k'ara yin laifin an sake bani wani ai ko na kawo makan ba iya yimun zakai ba tunda yanzu ma gashi ka kasan balle kaman surut....."bata k'arasa ba sakamakon wani kukan kura da yayi ya nufo ta a fusace,aikuwa da gudu kaman walk'iya ta fice kopar gida da gudu,tsaye tayi tsakiyar center tana kallonshi yayi tsaye cikin zaure sai huci yake,yasan in ya biye mata wahalar dashi kawae zatayi ta maidashi kaman Mahaukaci,kwafa yayi a fili ya furta"zaki dawo gidan",daga haka ya shige cikin d'akinshi, Tsaye tayi awurin abun Duniya duk ya isheta,wani kunci take ji acikin ranta na rashin yin Assignment d'in gashi tasan in dai ta sake ta koma cikin gidan to kuwa kashinta ya bushe,yadda Gwaggo bata nan ai sai kawu Amadu ya kusa kasheta gashi dama bak'ar zuciya ce dashi sam bai iya bugu ba,sai lokacin ta fara danasanin abunda ta gaya mashin,tana cikin tsayuwar nan Ya Handsome ya fad'o mata arai,nan take ta fara tunanin ta kai mashi Assignment d'in kilan shi ya iya shi tunda ya gama karatu har yana aiki,lokaci guda ta saki Murmushi duk da bata da tabbacin ya iya d'in,har ta juya zata tafi ta tuna ai ko kallabi bata dashi kuma gashi tana tsoron shiga gidan ta d'aukko,nan take dubara ta fad'o mata,bud'e tsakiyar littafin tayi ta kifa asaman kanta daga haka ta nufi gidan Hajiyar Sanata. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 4️⃣9️⃣ Haisam zaune saman kujera L-shape ya dan kishingida jikinshi sanye cikin bak'ak'en kaya jeans da t-shirt gaban rigar anyi rubutu golden colour hannunshi sanye da Agogo golden,tun bayan daya dawo daga aiki wanka kawae yayi ko part d'in Hajiya baije ba yaci abinci ya zauna yana yin video call,yana yin firan yana d'an gutsiran cake dake ajiye gefen laptop dinshi dake kan c-table hannunshi guda na ruke da glass cup mai d'auke da ruwan lemu yana d'an sipping ahankali, Turo kopar tayi bakinta d'auke da sallama ta shigo,a gefen kujeran ta tsaya idonta akanshi,a hankali ya wurga eyeballs d'inshi kanta suna had'a ido ya d'an yi Murmushi hakan yasa itama tayi mashi, "Who is dat?" wata zazzak'ar murya daga cikin laptop d'in ta tambaya da alama wadda yake yin video call d'in da itace,maido idanunsa yayi kan screen d'in slowly ya furta"Zarah"yayi Maganar had'i da lumshe ido, "Oh really?" mai muryar ta tambaya,d'aga mata kai yayi alamar eh, "I wanna see her,where is she" ta sake fad'a alamar tana son ganin Fatuu,daga yadda take turancin zaka yanke ba bahaushiya bace,kallon fatun yayi yai mata alamar tazo da kanshi,sai lokacin tasa hannu ta cire littafin dake asaman kanta ta d'an matso gaba kadan,da yatsanshi ya nuna mata Laptop dinshi yace"zaku gaisa da ita ne"cikin rashin fahimta tace"wa?", wani kallo yayi mata"ki duba inda nike pointing mana" da sauri ta juya ta kalli inda yake nuna matan,Matashiyar budurwa ce da zata iya kai shekara 21 zuwa 22 haka,tana zaune asaman gado ta jingina bayanta da kan gadon,lokacin da Fatun ta kalli Computer d'in budurwar ta juya gefe ta dauki ruwan roba dake aje saman bedside drawer ta daga tana sha hakan yasa bata ga ainihin fuskarta ba sai dai dogon gashinta dake gefe da gefen fuskar ya zuba har kan cikinta wanda launinsa brown ne sosae haka fatar jikinta ma fara ce sosae wanda kallo d'aya zakai mata ka kirata da farar fata,sai dae sam kalar hasken fatarta dana haisam ba iri daya bane kowa da launin haskensa, Ai Koda Fatuu tayi arba da ita a firgice ta juya ta kalli haisam tace"Ya Handsome da wannan zamu gaisa din?"fuskarshi a sake kaman zaiyi dariya ya d'aga mata kai don yadda ta firgitan taso bashi dariya, a rud'e ta kuma cewa"to amman ai ni fa ban iya irin turancinsu ba mai saurin nan,ba rannan na fad'a maka ba har kace zaka koya man amman sai ka samu isashshen lokaci to yanzu ya zanyi magana da ita....."kafin ta k'arasa budurwar ta katseta da fad'in, "karki damu nima bahaushiya ne ai" yadda tayi hausar gwanin dad'i,da sauri Fatuu ta maida kallonta gareta lokacin ta gama shan ruwa ta juyo da fuskarta sosae,Tubarkallah Ma sha Allah,kallo daya zakai mata ka shaida kyawun fuskarta,kyakkyawa ce matuk'a ga kwayar idonta brown ce har wani kyalli take,waro ido Fatuu tayi tana kallonta arazane,ba kyawunta ne kad'ai ya razana ta ba, harda furucin da tayi na wai itama bahaushiya ce to ta yaya?shine abunda ya tsaya ma fatun arai. Hannu ta d'aga ma Fatuu"hi,Zarah how're u?", Cike da mamaki fatuu tace"da gaske ke bahaushiya ce?" "Yeah,kuma ina jin hausa kaman jakin kano ba" tayi Maganar tana dariya haka kuma ba k'aramin kyau ya k'ara mata ba,kan fatuu fa ya Matuk'ar daurewa hannu guda tasa ta rufe bakinta alamar mamaki kafin tace"wai har sunan jaki ma kin sani kenan!",ba budurwar ba har Haisam dake saurararsu saida ya d'an murmusa, "Na fad'a maki nima bahaushiya ne ko baki yarda ba,nasan komae ai saboda nima yar Nigeria ne, anan aka haifeni, anan nayi wayo har na girma", kai abunfa nayi ne,neman wurin zama Fatuu ta fara don da a duk'e take tayi ruku'u,ganin haka yasa Haisam janye kafarsa daya mik'e kan kujeran ya matsa can gefe,zama tayi sosae tace"to ke wacece,kuma wane gari kike ko ke yar gidansu Ya Handsome ce amman kuma naga ba kalarku daya ba"duk ta jero mata tambayoyin nan, Murmushi tayi tasa hannunta tana gyara gefe da gefen gashinta kafin ta fara magana"sunana FANAN,ni yar Lagos ne and ni kanwarsa ce but am his Cousin sis kinsan me cousin ke nufi ko?"da sauri Fatuu ta d'aga mata kai"Eh nasani anyi mana shi a English,diya ko dan kanin ko yayan iyayen Mutum", "Yeah,You're right Zarah ni d'iyar kanwar babanshi ce", cike da mamaki Fatuu tace"wllh nama gane ki,Mamanku diyar Hajiya ce wadda ke lagos kuma Babanku Bature ne ko?" Fanan na dariya ta d'aga mata kai alamar eh, "To ke yaushe zaki zo nan Katsina?" fatuu ta tambaye, "Currently now am not in Nigeria,ina India ina karatu,sai dae watarana in nazo" zaro ido Fatuu tayi"India!yanzun nan da nike yin magana da ke kina India?"kai Fanan ta d'aga mata alamar eh, "To mi kike karantawa anan d'in?", "Medicine"ta bata amsa, "had'a Magunguna kenan?", "No,karatun likita kenan",cike da mamaki Fatuu ta ruk'e baki tace"kai ashe wai shine Medicine,shifa nike son in karanta amman bansan sunan karatun ba kenan,ni karatun Doctor kawai nike cewa",sosae Fanan d'in ke dariya jin shirmen Fatuu nan suka shiga yin hira sosae atsakaninsu da alama itama Fanan d'in bakinta asake yake har Fatuu na tambayarta wai tana zuwa wurin yan Film d'in suburbud'a dasu Sharukhan,tace mata a'a ai Karatu ne ya kawota amman dae wani lokacin suna ganin yan Film d'in in sunzo makarantarsu shooting ko akan hanya ko a Mall in sunje Shopping da dae sauran wurare kaman wurin shak'atawa haka,anan Fatuu ke ce mata wai in zata zo tayo mata tsarabar sari amman ba wanda ake nad'awa ba wannan kada ita zai rink'a yi irin masu wando take so irin wanda Roshni d'in Aman na cikin film d'in Shu'umin iko take so,nan Fanan d'in tace mata bata gane irinsu ba don ba kallon film d'in take ba,Fatuu tace mata in anayi a tauraruwa zatasa Ya Handsome ya d'auki hoton irinsu ya turo mata tace to,daga haka Fanan d'in tace mata zata tafi tutorial yanzu sai wani lokacin zasu sake gaisawa Fatuu ta amsa da toh, "Beb where are u?" Fanan ta fad'a tana d'an kallon gefen Fatuu,Haisam na jin hakan yayi ma Fatuu alamar ta juyo mashi da Laptop d'in,kallonta yayi fuskarshi da Murmushi itama Murmushin take mashi tace"I will be offline now so u can have more time wit ur Funny Mom"lumshe ido yayi still da Murmushi akan fuskarshi slowly ya furta"Ok,Bye Sweethrt", "Bye Beb"ta d'an ja Maganar daga karshe had'i da yin kiss daga haka ta sauka,waro ido Fatuu tayi tasa tafukan hannayenta duka biyun ta rufe baki alamar mamaki tana kallonshi,kallonta yayi,ganin abunda tayin yasashi cewa" What?" cire tafukan tayi tana d'an murmushi tace"Nagane Budurwarka ce,amman shine kace man baka da Budurwa ko" ta k'arasa tana tura baki tana yi mashi wani kallo irin ya raina mata wayon nan, Murmushi yayi yace"Who told u dat?" tana tura baki tace"ba gashi nan kace mata Sweethrt ba kuma tayi maka..." kasa k'arasa Maganar tayi tana guntse dariya,shiru yayi yana kallonta still da Murmushi afuskarshi,ita kuma sai faman guntse dariya take, Sigh yayi"ai wannan duk wanda ka damu dashi who is important to u zaka iya ce mashi hakan ba sai wanda ake Soyayya dashi ba" daina yin dariyar tayi tace"da gaske?" gira ya d'aga mata"yeah,kaman Grandma d'inki da Uncle d'inki duk zaki iya ce masu hakan is normal",cike da mamaki tace"ashe ba dole sai wanda ake Soyayya ba?"kai ya d'aga mata kafin ya kuma cewa"Mutum mai kirki ma zaki iya ce mashi hakan,kaman wanda yayi maki wani abu kika ji dadi" zaro ido tayi "to kuma in Namiji ne kada yayi tunanin sonshi nike fa",hannu yasa ya shafi forehead dinshi"ai zaki ce ne yadda zai fahimta kaman kice,u're such a Sweethrt"dariya tayi tace"Ya Handsome u are such a Sweethrt" shima dariyar yayi har hakoransa suka bayyana ya furta"thanks,har kin gama fushin dani kenan" turo baki tayi"ai na kyaleka kaci gaba da cin abunda ka saba", "Kin daina damuwa da Ulcer zai kamani na mutu kenan" d'an yamutsa fuska tayi"to ai tunda su ka saba dasu kilan kana koshi ko,kuma koma na matsa ma ba bari zakai ba" ta k'arasa da sigar shagwa6a,d'an ta6e baki yayi kafin ya kai hannu ya d'aukko sauran cake din da ya aje agefen Laptop,har yakai baki zai gutsira suka had'a ido hakan yasa ya dakata don baida sauranshi da zai bata,mik'a mata yayi ta kalli cake d'in ba tare data amsa ba hakan yasashi cewa"take"maimakon ta amsa d'in sai ta turo mashi baki tace"Nima bancin sauran wani", waro ido yayi lokaci guda ya gane Magana ta gaya mashi,wato abunda ya fad'i mata rannan data bashi ice cream acikin motane itama ta gaya mashi yanzu,ganin yadda yake kallonta yasata fashewa da dariya tana rufe bakinta da hannunta,aikuwa baisan lokacin da ya dauki throw pillow dake a gefenshi ba ya jefa mata a fuskar,dukar da fuskar tayi tanata dariya kitsonta ya zuba yaraf akan kujeran,still yayi yanata Murmushi shima,can ta d'ago ta mik'a mashi hannu alamar ya bata,shiru yayi yana kallonta kaman bazai bata ba sai kuma ya mik'a mata ta amsa tace"thank u Sweethrt ya Handsome"dariya yayi ya d'an girgiza kai kawae ita kuma ta fara cin cake din, "Mi yasa kike fitowa haka,where is ur headtie?" yayi mata tambayar had'i da dan kwantar da kanshi jikin kujeran,sai lokacin ta tuna da abunda ya kawo tan,baki cunkushe da cake tace"ba kawu Amadu bane ya biyo ni zai bugeni shiyasa ban koma na daukko kallabin ba", "Mi kika yi mashi?" idasa cinye cake d'in tayi sannan ta fad'i mashi abunda ya had'a su,idonshi akanta yace"har yanzu kina rashin kunya ko Zarah!"ta6e baki tayi kaman zatayi kuka"to ya kasa yi mun kuma maimakon ya barni inji da abunda ya isheni sai yake ta man maganganu ni kuma naji haushi bansan lokacin dana fad'i mashi hakan ba wllh kaji na rantse,amman bazan k'ara ba" ta k'arasa maganar tana d'age baki had'i da jujjuya kai alamar nadama,still yai yana kallonta ya d'an 6ata fuska,ita kuma sai sussune kai take, Sauke ajiyar zuciya yayi yace"Let me see d Assignment " aikuwa da sauri ta juya gefenta ta d'aukko littafin,mik'a masa tayi bayan ta bud'o daidai inda tambayar take,hannu yakai ya amshi book din, "Wai wannan tambayar za'a fidda kuma ga amsar da yake so asamo nan a k'asa wai in batayi irinta ba to ba'ayi daidai ba",shiru yayi yana kallon Assignment d'in can k'asan mak'oshinshi ya furta" CALCULUS" janye littafin yayi ya kalleta da mamaki"Ajin ki nawa kika ce ma?" da sauri ta bashi amsa"Js 3 nike kuma ban dade dana shiga bama" d'an jinjina kai yayi ya k'ara d'aga littafin yana sake kallon question d'in,yasan lissafin sosae tun yana 100lvl yake yinshi,yana da wahala amman awurin wasu don shi lokacin yana degree d'insa na farko yana koya ma mutane shi sosae wadanda basu ganewa in akayi masu,yayi mamakin ganin tana js 3 an bata shi, dama a Senior Secondary take anayinshi a Further math ga wad'anda suke yin Subject d'in shima kuma wanda ake yi masun introduction ne ba'a nitsa masu can ciki don lissafi ne mai rikitarwa sosae gashi yana da yawa, "Mi kika yi aka baki wannan Assignment d'in?" ya tambayeta fuska a d'aure,nan ta fara inda inda tana zaro ido ba abun tayi mashi karya ba don ta fahimci ya gane laifi tayi, "Am asking u Zarah!" ya d'an yi mata tsawa aikuwa a rud'e ta fara kora mashi bayani bata 6oye mashi komai ba,tana gama fad'i mashin kwalla suka zubo mata sharrr,shiru yayi baice mata komae ba,a zahiri ta wani 6angaren tana da gaskiya yadda ya rikesu tsawon lokaci dole su gaji kuma dama lissafi in rana tayi ba kowa ke fahimta ba shiyasa mafi akasari aka fi sa period dinshi da safe,ko kuma ana dawowa break kaman yadda tashi take sai kuma ya had'e masu da double periods d'in malama dole ma su gaji ai,matsalan yadda Fatun tayi Maganar dole zaiga tayi mashi rashin kunya, "Ke kad'ai ne ajin?" haisam ya tambayeta,girgiza mashi kai tayi idanunta sunyi rau rau, "Ke kika fi kowa rashin kunya kenan", da sauri ta k'ara girgiza kan tace"a'a wllh nifa bada niyyar rashin kunya nayi Maganar ba,kawae gaskiya na fad'i mashi don ya sani"shiru yayi yana ta kallonta fuskarshi still a d'aure hakan yasa ta sunnar da kanta k'asa tana ajiyar zuciya, Sigh yayi"as from today,i don't want u to dat again,ba ko ina mutum keda right na ya fad'i abu ba koda yana ganin yana da gaskiya hakan na iya zama ma mutum matsala like it happens to u now,ki koyi yin shiru understand?", da sauri ta d'aga mashi kai"to ya Handsome wllh bazan k'ara ba",jinjina kai yayi yai shiru yana d'an tunanin yadda zai solving mata don lokacin Sallar la'asar ya riga yayi gashi sai dae ya hakuri da zuwa gym don ko zata fahimta sosae har ta yi bayani a aji sai an d'auki d'an lokaci,ana haka aka fara kiran sallar la'asar mik'ewa yayi tsaye yana gyara rigarshi Fatuu ta d'aga kai tana kallonshi, "Zanje sallah sai na dawo zan nuna maki yadda yake",jin haka yasa lokaci guda ta saki Murmushi,hanyar Bedroom dinshi ya nufa yana shigewa ta hau yin murna tana bubbuga kujeran kaman sabon kamu, bayan wani lokaci ya fito lokacin ta natsu har ta kwanta ma asaman kujeran,tana ganinshi tayi saurin mik'ewa zaune yana zuwa zai wuce yace"ke bazaki sallan bane?"tana kallonshi tace" to ai banda Hijabi" "Kije wurin Hajiya sai kisamu kiyi sallan inna gama zanzo nan" amsawa tayi tare da mik'ewa tabi bayanshi, _________________ Lokacin data shiga parlon hajiyan ba kowa aciki hakan yasa ta nufi dakin Saude don tasan Hajiyan Salla take,da sallama ta shiga cikin dakin lokacin Sauden na niyyar tada salla,juyowa tayi ta kalli bakin kopan shigowan tana ganin fatuu ta saki Murmushi, "Fateema ce" "Eh Aunty Saude ina yini" "Lafiya lou ya Makaranta an dawo ko", " Eh,Don Allah hijabi zaki ban zanyi salla",amsa mata tayi da to ta nufi wardrobe din bango ta d'aukko mata wata wadda take tunanin bazata yi mata yawa ba sosae ta aje mata agefen Katifarta don fatun ta riga ta shige toilet. A tare Haisam da Hajiya suka shigo parlon sai kace tare suka je masallacin,yana ganinta ya sakar mata Murmushi ya nufeta,hannunta ya kamo suka nufi kujera 3 seater ya zaunar da ita kafin shima ya zaunan, "Sai yanzu kaga damar shigowa bacin tun d'azu kana gidan nan" yana niyyar bata amsa Fatuu ta shigo cikin parlon ta nufi kujera one seater ta zauna tana yima hajiyar Murmushi, "Ke kuma yaushe kika shigo?" gaidata ta fara yi kafin tace"da aka fara salla", Kai hajiya ta d'aga sai kuma tace"yau baki zuwa islamiyya ne kuma ina kallabinki?"amsa ta biyun ta bata tana tura baki"ban zo dashi ba,kawu Amadu ne zai bugeni shine na taho haka" "Laifi kikai mashi ko" shiru bata ba ta amsa ba hakan yasa Haisam fad'i mata laifin data yi mashi,girgiza kai hajiya tayi"Fateema hoo,baki dai daina rashin ji wllh,Allah ya shiryeki"maida kallonta tayi kan haisam tana yar dariya"kace yau ba zuwa d'aga karfe kenan,yar gidanka ta jawo aiki,Allah ma yasa kai ka iya ai da tasha punishments ja'ira"ta k'arasa idonta akan Fatuu tana dariya itama dariyar tayi tana sunna kai k'asa, "Ko har kayi mata ka fitan?" hajiya ta tambaya jin baice komae ba, "No,we need enough time,zanje Gra after magrib sai inyi acan", kai hajiya ta d'aga"wannan abu dae shima kaman shaye shaye yake ace dole sai mutum yayi zai jishi daidai ya zauna lafiya"wani kallo yayi mata ba tare da yace komae ba, "a zubo maka Abinci ne ko yau ma yar gidan taka tasa kaci Abinci awurin aiki?"da sauri Fatuu ta d'ago ta kalleshi lokacin shima ya d'an kalleta suka had'a ido ta tura mashi baki,d'an murmushin gefen baki yayi ya janye idonshi Hajiya dai nata murmushi, "Yanzu nagama cin abu,amman zanci bada yawa ba", Saude hajiya ta kwala ma kira,bayan ta fito ta bata umarnin kawo mashi Abinci,kallon Fatuu tayi tace" ko kema zaki ci?"kai ta d'aga mata alamar eh dama kuma bata wani ci abincin kirki ba, "bi Sauden kice wai ta zubo harda ke acikin nashin sai kuci tare" amsawa tayi da to ta mik'e ta nufi kitchen d'in,shi dae Haisam shiru yayi bai tanka ba dama Hajiyar da biyu tayi hakan wai ko yaci sosae,bayan ta kawo abincin tashi Hajiya tayi ta koma saman 2 seater tace ma Fatun ta zauna sai su saka abincin a tsakiya,yin yadda tace tayi,ganin Haisam d'in idonshi na akan waya ahankali tace"Ya Handsome ga abincin"ba tare daya kalleta ba yace"ki ci" k'in ci tayi ta bishi da ido fuska a daure alamar fushi can ya d'an d'ago ya kalleta ganin yadda tayi yasashi d'an yamutsa baki ya kai hannu ya d'auki spoon d'in ya fara ci,sai lokacin itama ta d'auki nata cokalin ta fara ci,abun mamaki,in yaci sai taci,in ya tsaya sai ta tsaya itama,duk wannan abun hajiya dake kallo na satar kallonsu sosae abun ya bata dariya amman sai tayi kaman ma bata san abunda suke ba,ganin zata 6ata mashi lokaci yasashi aje wayar ya maida hankali kan abincin,ba 6ata lokaci suka kusa cinyewa ya aje spoon d'in tana niyyar ajewa ya wurga mata wata uwar harara hakan yasa ta idasa cinyewa, Mik'ewa yayi "ki same ni can" yace mata daga haka ya fara k'okarin nufar hanyar fita daga parlon, "Ba za'ayi anan ba nima in koya" Hajiya ce tayi Maganar cike da zolaya, "Yana da d'an yawa we need to do it on board" ya bata amsa yana tafiya,mik'ewa Fatuu tayi tana niyyar d'aukar tray d'in da aka d'auro kayan abincin ta kai kitchen, "Ki barshi za'a d'auke kije ya koya maki yamma na yi" amsawa tayi da to tana niyyar juyawa Hajiya ta kira sunanta,amsawa tayi tare da kallonta, "Badai zaki daina rashin ji ki natsu ba ko Fateema!" fuska a Matuk'ar d'aure tayi Maganar, nan da nan Fatuu ta rud'e ta nufi gabanta ta duk'a"Don Allah Hajiya kiyi hakuri wllh na daina ko rannan saida Gwaggo ta fad'i hakan yanzu ba ruwana da kowa", "Amman ai har yanzu kina rashin kunya ko tunda gashi kinyi ma kawun ki da Malaminku",idonta cike tabb da kwalla tace" shi Malam wllh bansan rashin kunya bane nayi tunanin gaskiya ce na fad'i mashi amman Ya Handsome ya man fada yace in rinka yin shiru,shi kuma kawu Amadu raina ne ya 6aci da baiyi man ba kuma yana ta yiman fad'a,amman wllh tllh kinji na rantse bazan k'ara ba",sauke ajiyar zuciya tayi"in kika k'aran fa mi zanyi maki?"da sauri tace"komi"jinjina kai tayi tace"tashi kije" mik'ewa tayi tana goge kwallan da suka gangaro mata ahaka ta fita daga parlon....... *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣0️⃣ Lokacin da ta shiga parlon yana zaune saman kujera yana daddana Laptop d'inshi,yana ganin ta shigo ya mik'e, "ki daukko Book d'in" yace mata yayin da ya nufi corridor d'in Bedroom,d'akin da Fatun ta ta6a zuwa yin fitsari ya tura ya shiga itama tabi bayanshi bayan ta dauko littafin da biro,d'akin kaman d'an Computer Lab yake duk IT tools ne aciki gaba d'aya d'akin zagaye yake da Desk,abud'e yabar d'akin ya tokare k'opar da kujera,Desk chair ya jawo ya nuna mata alamar ta zauna ta yadda zata iya kallon d'an madaidaicin whiteboard d'in dake manne a bango,wata drawer dake jikin desk ya jawo,marker ya fiddo ya dawo gaban allon ya fara yin rubutu,abun mamaki tambayar ya rubuta ba tare da ya duba littafin ba kenan har ya haddace tambayar,ak'asan tambayar ya rubuta Solution yaja layi kafin ya fara fidda mata tambayar a nutse yake mata bayani kai kace shi d'in Malami ne gashi ko Calculator bai dubawa da ka yake fidda komae ita dae tayi kasak'e tanata kallon ikon Allah,Abunfa ashe aiki ne ja,ashe sai anyi amfani da wasu formulas da wasu rules an gano wace tsiyace,kai ni dai bama ganewa nike ba balle in ma masu karatu bayani🤣,tambaya guda d'aya amman sai da ya kusa cika allon wai ahakan ma don yayi mata shi atak'aice ne yadda zata gane,lokacin daya fitar da amsar k'arshen kallonta yayi yace ta duba taga tayi iri d'aya da wadda Malamin ya bata, cike da mamaki tace"Kai Ya Handsome, kodae kaima Malami ne?kaga yadda kake yin bayanin wllh har kafi duka malamanmu iyawa ma" goya hannuwansa yayi a k'irji yana kallonta fuskarshi ba wasa yace"is dat what i asked u to do?" da sauri ta girgiza mashi kai ta bud'e littafin daidai inda Assignment d'in yake tana kallon amsar da malamin yace ta samo,d'agowa tayi ta kalli wadda haisam ya gano ta sake kallon ta littafin nata,cike da Al'ajabi ta d'ago tafin hannunta guda rufe da bakinta ta mik'e tsaye,wani tsalle tayi cike da farinciki tace"wllh tllh iri d'aya ne ba bambanci Ya Handsome, kai innalillahi....? "Sosae take washe baki tana dan d'add'aga hannuwa, "Can u do it?"ya tambayeta, hakan yasa ta tsaya cakk jin yace zata iya yi,zaro ido tayi tana kallonshi ya d'age mata gira alamar amsarta yake jira,a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a, "Baki da baki ne!" "A'a,bazan iya yi ba don ban gane ba sosae" wata uwar harara ya wurga mata"taya zaki gane dama tunda attention d'inki bai anan"ganin kaman ransa ya 6aci yanata kallonta yasa ta duk'ar da kai, "I will explain it one more time,idan baki maida hankali kika iya ba,ba k'ara maki bayani zanyi ba" ya yi maganar yana jaddada mata abunda yace d'in da marker din hannunshi,hakan yasa ta tattara dukkan natsuwarta guri guda ta goya hannayenta a kirji ta k'ura ma allon ido,su fatuu an natsu kaman duka kenan,goge wanda yayi akan allon yayi ya faro mata daga farko,a nutse yake mata bayanin dalla dalla kuma sau biyu yake fad'i mata abu kafin ya wuce gaba ahaka har ya sake fidda irin amsar da malaminsu ya batan,kallonta yayi yace akwae abunda bata gane ba tace ta gane,hakan yasa yace mata ta taso tayi mashi bayani kaman yadda yayi ba tare daya goge ba,tsayawa yayi ajikin bango ya goya hannayensa akirji yana kallonta ta fara yin bayanin kaman yadda yayi har tazo k'arshe,jinjina kai yayi ya nufi board d'in yasa duster ya goge ya bar iya tambayar daga haka ya nufi kujerar data zauna da farko ya zauna,mik'a mata marker d'in yayi yace ta fidda da kanta har saida gabanta ya d'an fad'i jiki asanyaye ta amshi marker d'in ta koma gaban allon,a d'arare ta fara fiddawa hannunta har Dan kerma yakeyi ganin hakan yasashi kiran sunanta ta waigo yace ta kwantar da hankalinta ta natsu zata iya,jinjina kai tayi ta juya taci gaba da solving a nutse har saida ta wuce rabi sannan ta kakare,tayi tayi ta tuna abunda zatayi agaba ta kasa,jiki a sanyaye kaman zatai kuka ta juyo ta kalleshi ga mamakinta sai taga yayi mata d'an murmushi don ba k'aramin kokari tayi mashi ba data kawo har nan d'in ma,daga inda yake ya tadata taci gaba ahaka yana d'an tada ita in ta kakare har tazo k'arshe,mik'ewa yayi ya amshi marker d'in ya sake yi mata bayani a wawware yadda zata gane sosae har kusan sau ukku yana maimaita mata sake gogewa yayi ya bata tayi shi kuma ya zauna,wannan karon a nutse ta fara fiddawa har ta samo amsar k'arshen,juyowa tayi asanyaye ta kalleshi ya d'aura kafa daya kan daya still hannuwanshi na goye a kirjin sam ta kasa karantar ko tayi daidai daga yanayin fuskarshi,ganin yak'i cewa komae yasa tasha jinin jikinta, "Banyi daidai ba ko Ya Handsome?" murya na rawa ta tambayeshi,daga yadda yake yace"check your book"da sauri ta nufi saman Desk inda ta aje littafinta ta d'aukko shi ta dawo gaban allon tana duba amsar data samo da wadda Malamin Maths d'in ya bata,sai ta kalli cikin littafin sai ta d'ago ta kalli allon,wata uwar k'ara ta fasa ta daka uban tsalle kai kace zata ta6o ceiling d'in dakin ne,cike da farinciki ta fara fad'in"Wllh iri d'aya ne,nayi daidai...."sai faman tsalle take wutsiyoyin kitsonta na tashi sama suma,sai lokacin ya saki wani k'ayataccen Murmushi ya sauke hannayenshi daga kan kirjin ya d'an had'a tafin hannunshi ya tafa mata sau ukku kafin ya saka yatsun cikin na juna yana ci gaba da kallonta da d'an murmushi,(Jama'a wai Fatuu bata san ta fara girma bane wannan uban tsalle haka,yakamata team Fatuu kuyi mata karatun ta natsu fa😂),cike da murna tanata dariya duk dimples dinta sun lotsa sosae ta nufi haisam dake zaune yana kallonta,tana zuwa ta d'aga mashi hannu alamar su tafa,d'an bud'a mata ido yayi had'i da dage gira hakan yasa da sauri tasa bayan hannunta ta rufe bakinta,ganin yana mata wani kallo yasa ta sunnar da kai k'asa alamar taji kunya, "Zarah!" taji ya kira sunanta,koda ta d'ago abun mamaki sai taga ya bud'e mata tafin hannunshi fari kwal dashi,bud'a ido tayi alamar mamaki shi kuma ya d'an lumshe nashi had'i da jinjina mata kai,washe baki tayi ta buda tafin hannunta na dama ta buga a nashin da k'arfi ji kake fasss har saida ya d'an cije baki,tana ganin abunda yayi ta kyalkyace da dariya tace"thank u,God bless u Sweethrt"girgiza kai kawae yayi tare da mikewa, "Ki copying solution d'in Magrib ya kusa" daga haka ya fita daga cikin d'akin,da sauri ta d'aukko littafinta da tuni ya fad'i a k'asa da tana tsalle ta zauna saman kujeran ta fara kwafar rubutun kaman yadda yace mata tana yi tana sakin Murmushi, Yana fita fridge ya nufa ya daukko bottle water mai sanyi da glass cup ya nufi kujera ya zauna inda ya tashi lokacin da Fatuu ta shigo,tsiyaya ruwan yayi kaman rabin cup d'in kafin ya rufe robar ya kai cup d'in baki ya fara shan ruwan ahankali,yana niyyar aje robar ruwan akan c-table Fatuu ta fito har ta gama kwafar rubutun dama saurin rubutu ne da ita,kan d'aya daga cikin armchairs ta zauna idonta akanshi, "Ko zaki sha ne?" ya tambayeta bayan ya cire cup d'in ta d'aga mashi kai alamar eh, sauran na cikin robar ya mik'o mata ta mike ta kar6o kafin ta dawo ta zauna, "Ki d'aukko cup acikin fridge" girgiza mashi kai tayi"ai shanye shi zanyi bari insha a robar" kai ya gyad'a mata shiru ya biyo baya na d'an wani lokacin, "Wai Ya Handsome kodae kaima malami ne naga ka iya bayani fa sosae"girgiza mata kai yayi alamar a'a,ganin tana ta binshi da ido yasashi cewa" hakan is part of my work,ina yawan presentation kinsan miye hakan ko?"ya tambayeta idonshi akanta,d'aga mashi kai tayi"eh yima mutane bayani"jinjina kai yayi daga haka ya d'aura kafarsa d'aya akan c-table d'in gabanshi ya d'age kanshi yana facing saman d'akin,duk jinshi ake wani iri ya saba kaman yanzu yana gym, "Ya Handsome" Fatuu ta kira shi,amsa mata yayi ba tare daya d'ago ba, "In tambayeka?" ta sake cewa,shiru ya d'an yi ya maimaita abunda ta fad'an acikin ranshi,saboda duk in zata tambayeshi kai tsaye take jefo mashi kowacce irin tambaya,daga yadda yake ya d'an juyo da fuskarshi side d'in da take, "Am all ears" ya fad'a, "Wai don Allah da wane irin dutsen goge kaushi kake amfani ne kafanka tayi haka kaman ta jarirai sumul ba kaushi?" ta k'arasa tana nuna kafarshi da ya d'aura saman c-table, kai jama'a ashe tunda ya dauran ta k'ura ma k'afar ido tanata kallonta har ta kasa daurewa saida ta tambaya, shi kuma sam bai gane ma mi take nufi ba,ganin tanata kallonshi yasa shi ce mata"miye shi abun da kika fad'in?"idanunshi a lumshe ya tambaya, "Dutsen goge kaushin kake nufi?" kai ya d'aga mata alamar eh, "Wannan fa dutsen mai gurjigurji wanda ake sakawa acikin kwandon wanka ana gurje tafin k'afa dashi mai kaushi ko faso"tayi maganar tana kwatanta mashi yadda ake goge k'afan dashi da tafin kafanta da ta d'an d'age sama,still idanunshi alumshe suke ahakan yake kallonta,yanzu ya gane abunda take nufi duk da shi bai san ma dutsen ba, "kina son abunne?"da sauri ta girgiza mashi kai "a'a bani ke so ba Kawu Amadu zan sai ma irin nakan k'ilan ya gyara mashi k'afarshi ta koma kaman taka, wllh baka ga kafarshi bafa, ina...kasan dawon fura in ya kwana,to haka k'afarshi ke komawa cikin sanyi haka zaka ga yanata dirzarta a gefen inda nike yin wanke wanke,har wani k'aton dutsen goge kaushi gwaggo ta siyo mashi a kasuwar yar kutungu yana amfani dashi,kwanaki fa cewa tayi in kafarshi nayin hakan in yayi Amarya zai rinka yaga mata zanin gado"ta k'arasa tana 6a66aka Dariya,d'an bud'e idanun yayi yana kallonta fuskarshi d'auke da dan guntun Murmushin gefen baki, "Shiyasa na tambayekan in ka fad'i man inda ka siyo naka sai in siyo mashi k'ilan ta daina tunda ni dai banso yayi Amarya ya yaga mata zanen gado kuma in ta canja wani taga ya k'ara yaga mata ai kaga tana iya yin yaji ko?" tsakaninta da Allah take yin Maganar😂, d'ago kan yayi gaba d'aya daga saman bayan kujeran yace mata"bani amfani da abun ina kaita ana wanke man ne" wata zabura tayi ta zaro ido tace "kafan kake kaiwa wanki sai kace kayan wanki!" tayi maganar hannunta guda ruk'e da ha6arta alamar mamaki,kai ya d'aga mata kafin yayi mata bayanin yadda ake pedicure d'in,cike da Al'ajabi take kallonshi hakan yasa ya d'age mata gira"zaki kaishi arika wanke mashi kafan ko?" a razane tace "wa!ba ruwana wllh,ban shirya zuwa gidan yari ba,haka kawae muje kafan tashi ta lalata masu inji ace sai na biya miliyoyi,ai ma yanzu ta d'an gyaru tunda zafi ake sai sanyi yazo take tsatstsagewan sosae zan dai gaya mashi in yana so to sai yaje amman ba ruwana ni dai" tana Maganar tana d'aga hannuwa sama alamar ba ruwanta,gyad'a kai yayi kawae yana niyyar k'ara kwantar da kan nashi aka fara kwala kiran sallar magrib hakan yasa ya dakata, "kije gida kiyi salla sai ki kara duba Assignment d'in karki manta ko" kallonshi tayi ta d'an marairaice "to ai yanzu gwaggo bata isa dawowa ba, kuma wllh in na koma kakkarya ni kawu Amadu zaiyi kaman kara dama ya ta6a gota ni a hannu,kofa Gwaggon na nan yana buguna balle yanzu da bata nan"shiru baice komae ba can ya mik'e tsaye yana gyara rigarshi ta daga kai tana kallonshi, "Ki jira in dawo" yace mata ganin bata da kallabi kuma magriba tayi bai kamata ta fita haka ba,da sauri tace mashi toh tana gyara zamanta,Bedroom d'inshi ya nufa yayo alwala,yana fitowa zai wuce tace ya kunna mata kallo,remote ya dauka asaman c-table ya latsa power daga haka ya mik'a mata ya fita. Ana gama sallan ba 6ata lokaci ya dawo part din nashi,lokacin daya shigo parlon iske Fatuu yayi ta baje a d'ayan 6arin L-shape sai sharar bacci take,(nima inyi ta hajiya ja'ira ta gaji),dama tun agida take jin baccin amman tak'i yi saboda rashin yin Assignment,tsaye yayi tsakiyan falon yana kallonta yayinda ya shiga tunanin yadda zaiyi da ita don fita yake son yi gashi da gani tana enjoying baccin,tunanin ko ya barta yaje ya dawo ya shiga yi sai kuma yayi tunanin za'a iya zuwa nemanta wurin hajiya kuma bata san har yanzu tana wurinshi ba kuma ma is'nt proper taci gaba da zama anan wannan lokacin, yin wannan tunanin yasashi fara kiran sunanta daga nan inda yake atsaye sai dai ko motsi bata yi ba tun yana kiran ahankali har ya d'an k'ara d'aga murya amman ina tuni sanyin Ac yasa tayi nisan kiwo acikin barcin da alama ma bata Nigeria,d'an k'ara matsawa yayi gabanta ya k'ara kiran sunanta nan ma shiru,still yayi da alama baison zuwa kusa da ita ne balle yasa hannu ya tasheta,har zai juya yaga ta motsa zata gyara kwanciya da d'an karfi ya furta"Zarahh"slowly idanunta suka fara bud'ewa suna kuma d'an lumshewa duk alokaci d'aya alamar dae baccin take ji sosae, yana ganin zata juya mashi baya ya sake kiranta wannan karon da k'arfi yace"Zarah!" amsawa tayi tare da bud'e idon sosae cikin Muryar bacci tace"Na'amm", "Tashi muje na raka ki gida" amsawa tayi da toh ta fara k'okarin tashi zaune idonta akanshi tace"wai bacci nayi?"kai ya daga mata alamar eh, "Wllh bansan ma nayi ba,kallo fa nike yi shine ya sace ni shiyasa ma ake ce mashi 6arawo ashe"da wata irin kasalallar murya take maganar,d'an murmushin gefe yayi yace"tashi muje", "Gidan zaka kaini" kai ya d'aga mata alamar eh, "To amman fa gwaggon bata isa dawowa ba yanzunma kar kawun ya dokeni", "zamu je sai ki bashi hakuri",da sauri ta jinjina kai ta fara k'okarin tashi tsaye,har zai nufi kopar fita sai kuma ya juya yace mata yana zuwa,Bedroom d'inshi ya nufa bada jimawa ba ya fito lokacin har ta zauna don jikinta ba kwari,hannunshi ruke da wani bakin abu ya nufi inda take,mik'a mata yayi"kisa wannan akan ki" amsa tayi tana dubawa,hula ce skullcap irin mai matse kai,sawa tayi akanta kuma tayi mata da yake roba ce,kallonshi tayi tana da murmushi tace"thank u Sweethrt ya handsome"d'an kya6e baki yayi da Murmushi ya nuna mata hanya alamar su tafi, saida ta d'auki littafinta data aje kan armchair kafin ta wuce yabi bayanta suka fita daga parlon. Unguwar ko ina da haske da yake akwae wutan nepa,lokacin da suka iso bakin shagon Amadun ba kowa sai sautin waka dake tashi saidae bai k'ure sautin ba ta yadda har zai takura Mutane,Fatuu ce agaba Haisam na bayanta tana zuwan gaban shagon ta tsaya lokacin ya juya baya da alama wani abun yake nema ko zai daukko, "Kawu" Fatuu ta kirashi, aikuwa a fusace ya juyo ya kalleta fuska a tamke yace "kin gama guje gujen naki kin dawo ko,to sai ki shiga ciki zanzo in samek...." bai k'arasa ba sakamakon Haisam da idonshi ya hango mashi a gefen kiosk d'in don da duk bai ganshi ba,washe baki yayi ya fara gaidashi,hannu ya mik'o masa suka gaisa kafin calmly yace"naji laifin da tayi maka bata kyauta ba,but u know she's still a child dat's why take behaving haka sai kana hakuri and she's here to apologize" maida kallonshi yayi kan Fatuu yace"Say sorry to him" tana jin haka da sauri ta kalli Amadun"Kawu pls Sorry,wllh raina ne ya 6aci saboda ba'a fidda Assignment d'in ba shiyasa har bansan lokacin dana fad'i ma abunda nace ba amman don Allah ba don ni ba kayi hakuri bazan k'ara ba" takai Maganar tana girgiza mashi kai,wani kallo yai mata mai kaman harara sai kuma yai saurin sakin fuskar don mugun nauyin Haisam d'in yake ji,d'an Murmushin yak'e yayi mata yace"shikenan ya wuce" Dariya tayi cike da farinciki tace"Nagode kawuna kuma yayana"yar harararta yayi cikin wasa da sauri ta bud'e mashi littafinta tana nuna mashi Assignment d'in da aka fiddan"kawu kagani Ya Handsome ya fidda man shi, ashe ya iya shi sosae baka gani ba" kai ya d'aga fuska asake yace"na tayaki murna", "Ki shiga gida Zarah" Haisam yace mata,amsawa tayi da to ta rufe littafin kafin ta nufi gidan tana yi mashi bye bye sai lokacin da zata shige ne ya d'an d'aga mata hannun shima,bayan ta tafi ne Amadu ke ce mashi wllh Assignment d'in da aka ba Fatun shi bai ko ta6a ganin shegenshi bama anan Haisam ke mashi bayaninshi yace itama don tayi laifi ne aka bata irinshi,Amadu yace shi dama yayi tunanin hakan wllh,hira yaci gaba da yi ma haisam d'in shi kuma yana tankawa jefi jefi hakan kuma ba k'aramin dadi yayi ma Amadun ba don bai ta6a tunanin ma watarana haisam zai tsaya agaban kiosk d'inshi ba balle har su danyi fira haka, "Yaya Haisam ko abaka wani abu kad'an ta6a gashi ma kanata tsayuwa"Amadu ya fad'a yana washe baki, "Don't mind,zan tafi ne yanzu", "To kad'an ci wani abu don Allah" yayi Maganar cikin marairaicewa,shiru haisam din yayi,yasan in ya amsa zaiji dad'i don da dad'i kaba mutum abu ya amsa hakan yasa yace ya bashi sweet guda d'aya duk yadda yaso ya k'ara mashi yaki amincewa daga haka yayi mashi sallama ya tafi,yana komawa gida ya fiddo bike dinsa don tafiya gidansu na GRA ko kaya bai canza ba don acan akwae wanda zai iya amfani dasu. Tana shiga gidan cike da farinciki ta nufi dakinta ta fad'a saman gado,can kuma sai ta mik'e ta nufi gaban d'an fasassan madubin daya rage a jikin d'an Dressing mirror dinta tana kallon hular da Haisam ya bata tasa,ta Matuk'ar yi mata kyau ba kamar da igiyoyin kitsonta suka zuba gefe da gefe gashi ta fito mata da haskenta sosae kasantuwar bak'a ce hular,tana ganin yadda tayi matan ta saki kayataccen Murmushi tasa hannu tana shafa jikin hular,komawa tayi kan gadon ta bud'o Assignment d'in tana k'ara bin yadda aka fidda tana cikin hakan ta tuna ai batayi sallar magriba ba hakan yasa ta mik'e da sauri ta d'auro alwala tazo tayi salla bayan ta gama har gode ma Allah tayi acikin Addu'a ta kuma yima Ya Handsome addu'a tace Allah yashi mashi Albarka ya biya mashi bukatunshi ya kuma saka shi a Aljanna,bayan ta gama Addu'ar a saman abun sallan bacci ya sake d'aukarta ko abinci bata ci ba har saida Gwaggo ta dawo ta tasheta sannan taci abincin tayi sallan isha daga haka ta koma baccin. Washe gari tunda asussuba Fatuu ta farka da kanta ba tare da gwaggo ta tasheta ba dama akagare take da garin ya waye ta tafi Makaranta,bayan tayi sallar Asuba ta sake daukko littafin Assignment d'in lafiya lau ta k'ara bin yadda aka fidda shi ba tare da ta kakare ba,a gurguje ta shirya ta dan ci abun kalaci kad'an daga haka ta nufi dakin gwaggo tace zata tafi,amsa mata tayi da to duk da tayi mamakin shiryawarta da wuri haka don ko bakwai da rabi bata ida ba,da ta bata kudin break ce mata tayi ta barsu jiya Ya Handsome ya kaisu ita da Haulat kuma ya basu kudi sun kuma rage canji,godiya gwaggo ta shiga yi tana fad'in shi bai gajiya da hidima ne don ranar Monday ma daya kai Fatun saida ta fad'i mata har Biscuit da kudin daya bata,tana fitowa kopar gida taga Amadu a bayan kiosk dinshi yana yin brush,Murmushi tayi tace"Gud Morning my Uncle"aikuwa wata uwar harara ya zabga mata ta kyalkyace da dariya don tasan ta mecece,jiya ba don Allah yaso taba data yaba ma aya zakinta,wucewa tayi tana fad'in"sai na dawo My Uncle"daga haka ta nufi gidansu Haulat don yau ko tunanin zuwa wurin Haisam bata yi ba burinta kawae ta ganta a makaranta don Malamin lissafin garesu farko...... *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣1️⃣ Tana shiga gidansu Haulatun ta iske innarsu acikin yar rumfar da take yin sana'ar koko,wurinta ta nufa tana zuwa tace"innarsu haulatu ina kwana" Da fara'a ta amsa mata"lafiya lau Fateema har an shiryo yau da wuri haka" ɗan murmushi Fatuu tayi tace eh, "Ita haulatun ma ban tunanin ta shirya don bata ma daɗe da dawowa daga kai markade ba,amman ki shiga ciki ki duba ko ta shirya" amsa mata tayi da toh kafin ta nufi dakinsu haulatun da sauri,madaidaicin daki ne fentin bangonshi duk ya kode ya kankare bazaka ma gane ainihin kalar fentin ba,kasan dakin siminti ne ba leda shima wasu wurare duk ya farfashe yayi ramuka haka saman dakin leda mai kyalkyali ce akayi rufin da ita,ba wasu kaya adakin daga yar lamusassar katifa sai wata tsohuwar wardrobe mai gida biyu taji jiki ba laifi don murfi guda ma akasa yake ya balle dayan kuma da bai ballo ba shima bai rufuwa sosae gefen wardrobe din dan tebur ne an jajjera tarkacen kayan shafa akasanshi kuma takalma ne,Haulat na zaune da daurin kirji agefen katifar tana shafa mai daga can gefenta kuma kannanta ne zaune akasa suna karyawa da koko da kosae Fatuu ta shigo da sallama,bud'a baki haulat tayi alamar mamaki k'annanta suka shiga gaida fatun ta amsa masu tana nufar inda haulat d'in ke zaune, "Wai ba dai har kin shirya ba?" haulat ta tambaya, "Ba ga zahiri kin gani ba" Fatuu da tayi tsaye k'erere ta bata amsa, "Amman nayi mamakin ganinki yanzu lokaci fa bai ida ba", " nasani so nike muje da wuri kafin banz....kafin malamin math din nan ya shiga"da har zata zagi malamin ta tuna da fad'an da Ya Handsome da Hajiya suka yi mata, washe baki haulat tayi "kenan kinyi Assignment d'in?"girgiza mata kai Fatuu tayi alamar a'a tana wani Murmushin rainin wayo, "Allah ban yarda ba kinyi,ai da baki yi ba bazaki doko wannan uban safkon ba,kuma gashi ma kina Murmushi" haulat tayi maganar tana dan harararta, "Don Allah haulat ki tashi kisa Uniform d'inki mu tafi mana" Fatuu ta fad'a cike da kosawa harda d'an yarfa hannu, "To amman fa ko karya kumallo banyi ba" tayi maganar a yayin da take kokarin mikewa tsaye,daukar uniform dinta dake aje agefen katifar tayi ta wuce dakin innarsu ta shirya,da kyar tasamu ta dan sha kokon Fatuu nata azalzalarta akan su tafi harda cewa ta bari in sunje kan hanya sai su sayi wani abu haulat tace ga dai abun kari agida kuma ba makara suka yi ba ta dae bari ta karya kumallon. A kan hanya haulat ke tambayarta yadda akai tayi Assignment din nan take ta kwashe komae ta fadi mata harda wuyar da suka sha ita da kawo Amadu don su fidda amman suka kasa da yadda Ya Handsome ya fidda mata,Dariya sosae Haulat ke yi mata tana fadin"wllh kedai baki da dama,baki san mutunci ba,yanzu duk irin kokarin da kawu Amadun yayi maki amman shine kika yi mashi rashin kunya,ni dama ya zane ki"wata yar iskar dariya fatun tayi kafin tace"wllh da kawu ya matsa sai ya fidda Assignment din nan kilan sai ya haukace shegen wuya ne dashi,wai kinga yadda yayi uban gumi yanata hura hanci karshe daya kasa ya wurgo man shi,harda wani cewa shi dama ba kaunar lissafi yake ba"dariya sosae suke yi kafin suka tsagaita suka koma yabon Haisam,haulat ta jinjina ma basirarshi jin yadda yayi solving mata Assignment din har tana cewa lalle shi dan baiwa ne komai Allah ya bashi,Lokacin da suka iso bakin titi Fatuu hanawa tayi su jira Bus tace su hau keke napep kawai kuma hakan suka yi ba 6ata lokaci suka iso Makarantar. Fitowa Amadu yayi jikinshi sanye da uniform ya rataye jakarshi a kafada da alama shima ya gama shirin tafiya makaranta ne,yana kokarin hawa saman hanya wata galleliyar mota fara sol kirar Hyundai ta parker agabanshi,slowly glass din motar ya dan sauka nan take fuskar mai Motar ta bayyana,Amadu na yin arba da haisam ya washe baki don da har ya dan tsorata da motar ta tsaya agabanshin,jiya da yaje gidansu na Gra ne ya taho da motar yabar Bike din acan, "Yaya Haisam ina kwana" Amadu ya fad'a,kai kawai ya jinjina mashi fuskarshi asake kafin calmly yace"Zarah fa?" da sauri Amadu yace"Wllh ta rigada ta tafi,dazun ina brush anan waje ta fito ta tafi yanzun ma ina ganin ta isa makarantar", lumshe ido yayi ya dan jinjina kai,a tunanin Amadu wucewa zaiyi hakan yasa ya dan ja da baya amman sai yaji yace mashi ya shiga Motar, "Yaya Haisam da kaje kar na 6ata maka lokaci zan hau aca6a" cike da girmamawa yayi Maganar harda dan rankwafowa, "No problem ka shiga" cikin cool voice dinsa ya fada amsawa yayi da toh ya nufi d'ayan 6arin Motar,gaba ya bude ya shiga ya zauna wani ni'imtaccen sanyi hadi da sanyayyan kamshi suka kai ma hancinshi ziyara har saida ya dan lumshe ido bayan ya rufe kopar haisam yaja suka tafi,tsit kake ji idon haisam na akan hanya shi kam kawu Amadu yayi shiru yana kallon gefen hanya wani irin nishadi yake ji har dan murmushi yake saki,bayan sun hau hanya ne haisam ya tambayeshi wane school yake ya fadi mashi nan take ya gane Makarantar don acan wurin Airport take wato kambarawa,bayan d'an lokaci suka iso Amadu yace ya ajeshi a bakin gate sai ya shiga hannu kawai haisam ya daga mashi alamar ba wani abu ya shige dashi ciki,har gaban Admin block ya kaishi yana kokarin fita ya mika masa kudi 2k yace yayi break, da tsananin mamaki Amadu ya kalli kudin kafin ya kalli haisam,yana so yace mashi ya barsu sai dai sam ya kasa don wani irin kwarjini gareshi gashi ko kallon Amadun ma bai yi ba,hannu ya kai ya amsa hadi da yi mashi godiya daga haka ya bude motar ya fita daidai wasu Abokansa sun taho suna ganinshi suka ja suka tsaya suna kallonshi da mamaki ganin had'addar Motar daya fito wanda a iya saninsu ba'a ta6a kawo shi makarantar a Motar gida ba,tsaye yayi saida haisam din yayi reverse ya juya ya nufi gate kafin ya tunkari abokan nashi yana wani bouncing suna ganin hakan suka sa sowa suna kuranta shi,saida suka gama shegantakar tasu irin ta dalibai sannan suka nufi class. *** **** **** Lokacin da su Fatuu suka isa class dinsu Mutum biyu suka iske aciki wurin zamansu suka nufa don su zauna dayake a layin tsakiya suke kuma seat dinsu ne na farko,suna zama Fatuu ta fiddo Assignment dinta tana kara bitar shi haulat dae nata saurararta don ba gane inda ta dosa take ba,a hankali dalibai suka cigaba da zuwa nan da nan ajin ya cika period din farko ta shiga shiru Malamin lissafin bai shigo ba Fatuu duk ta kagara bunu bunu ta kalli kopar shigowa ajin, "Fatuu gashi nan" Haulat ta fada tana gyara zamanta da sauri fatuu ta kalli kopar daidai malamin ya shigo cikin ajin,wani murmushi ta saki tana kallon haulat,sanye yake da blue jeans da riga mai dogon hannu ya dad'e da bak'in glass,yana shigowa yan ajin suka mike suna gaidashi,seat din farko na layin karshe ya nufa ya d'aura textbook da Allin dake ruke a hannunshi sannan ya kalli Students din fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa masu gaisuwar kafin yace su zauna,bayan sun zaunan ya juya ya nufi blackboard ya rubuta subject din da yake yi da date yaja layi kafin ya rubuta sabon topic din da suka shiga jiya ya juyo ya dauki textbook din math ya rubuta wasu misalan bayan ya gama ya juyo ya fara masu bayani,itakam Fatuu ganin bai tanka mata ba yasa ta fara tunanin ko ma ya manta da Assignment dinne,saida ya gama yi masu bayanin misalai guda ukku yace in akwae wanda bai ganeba ko mai tambaya yayi,wasu suka fadi abunda basu ganen ba wasu sukayi tambayar saida ya gama dasu kafin ya kalli Fatuu fuska a matukar d'aure yace"where is my Assignment?", shiru tayi tana binshi da ido hakan yasashi ce mata ta fito gaban Allo,mikewa tayi littafinta a hannu ta fita, " Who is the class monitor?"ya tambayi yan ajin, "Malam itace monitar" wasu suka fad'a, jinjina kai yayi ya tambayi ina mataimakiyarta aka nuna mashi Haulat,umarni ya bata taje Staff room ta daukko mashi kujera ta amsa da to kafin ta mike ta nufi hanyar fita,bada jimawa ba ta dawo hannunta ruke da kujerar ta kai mashi inda yake jingine da window ta aje agefenshi kafin ta koma ta zauna,gyara kujerar yayi ya zauna daga haka ya nuna ma Fatuu Allo da hannunshi, "Ki rubuta Question din dana baki da kuma amsar danace ita zaki samo"amsawa tayi da to,yadda ta amsan a dan sanyaye sai kace batayi Assignment din ba,bayan ta rubuta ta juyo ta kalleshi tun kafin tace wani abu ya tambayi yan ajin sun gama kwafar rubutun tsakiyan allon suka amsa da eh,nuna mata wurin yayi yace ta goge rubutun tayi ma yan ajin bayanin aikin da ya bata har ta gano amsar,shiru tayi tana kallonshi ya dan daka mata tsawa" baki ji mi nace bane!" dan tura baki tayi tace"naji" juyawa tayi ta kalli yan ajin da kowa idonshi na akanta sunyi mata tsuru ba wanda yake tunanin zata iya don sam yanayinta bai nuna ta iyan ba ta galla masu harara,hada ido sukai da haulat ta tura mata baki itakam haulat din dariya tayi ta girgiza kai kawai don halin Fatuu sai ita,shidae math teacher din sai girgiza kafa yake ya dan kya6e baki cikin ranshi kuwa ya tabbatar bazata iya ba hakan yasashi cin alwashin sai ya koya mata hankali,littafinta ruke ahannunta ta fara rubutu a allo bayan ta goge rubutun jikinshi,tambayar ta fara rubutawa kafin ta fara fiddawa tana juyowa tana ma yan ajin bayani,tun tana yi ahankali har ta daga murya ta zage sai uban bayani take kai kace malama ce ke yima dalibai bayani,shin ina malam yake ne?yana dai azaune yayi tsitt sai bin ta da ido yake cike da mamaki abun ya matukar daure mashi kai don bai ta6a tunanin zata iya ko kusa da yadda take yi ba,gashi abunda ma yafi bashi mamaki shine yadda take bayanin ba tare da tana kallo a wani wuri ba da kai take yi,lokacin data zo karshe ta gano irin amsar tashi sai ta juyo ta kalli yan ajin da suka yi sototo suna sauraranta wasu bakinsu a bud'e saboda mamaki, "kun gane ko asake yi maku bayani?"ta tambayesu tana murmura idanu had'i da sa hannu guda ta dafa kugu,gaba daya suka ce sun gane,juyawa tayi ta kalli malam da har lokacin idonshi na sanye cikin gilashi tace" Gashi nan na fidda har na gano amsar irin taka,nayi daidai ko?"ta tambaya da d'an Murmushi tana d'age ido,farko shiru yayi yana ta kallonta har saida ta k'ara tambayar tayi daidai sannan ya daga mata kai alamar eh, "To tunda nayi daidai kace a tafa man ko" ta fad'a tana tura baki,d'an jinjina kai yayi yai wani guntun Murmushi da alama ta kashe shi da mamaki sai kace ba mai laifi ba har wani neman atafa mata take, ganin haka yasa tace"yanzu duk wannan uban aikin da nayi malam baza'a tafa man ba" ta k'arasa tana ta tura baki,kallon yan ajin yayi yace su tafa mata aikam kaman da gayya suka fara uban tafi kilan kuma murna suke Allah ya raba su da alakakai, "Malam shikenan inje in zauna ko tunda dai nayi daidai ae ba batun punishment ko?" ta fad'a tana gwalo ido,d'aga mata kai yayi alamar eh, har ta juya ya tsaidata don ya kasa hakuri so yake yaji yadda akai ta fidda Assignment din don shi kanshi yana a shekararshi ta k'arshe aka basu Assignment d'in wanda ba karamar wuya yasha ba wurin fidda shi, " Waya koya maki?" yayi tambayar fuskarshi ba wasa,d'age gira tayi tace"Assignment d'in?"kai ya daga alamar eh,d'an murmushi tayi da bud'ar bakinta sai cewa tayi"wani Aljani ne acikin Aljanuna yazo ya koya man",tashin hankali!hannu ya kai ya cire gilashin idonshi yabi ta da wani irin kallo mai kama dana wanda ya razana duk da ya d'an dake,ganin irin kallon da yake mata ne yasa taci gaba da cewa"ba kaji yan ajin nan jiya sunce ina da Aljanu ba,to cikinsu ne ai wani yazo ya koya man har na iya", ba iya malam d'in ba har yan ajin sun razana da jin abunda take cewa don duk d'aukar mai Aljanu kowa kema Fatun ita kanta Haulat in Fatuu tayi wani abun takan yi kokonton anya ba da gaske tana da Aljanu ba tunma farkon kawota garin amman yanzu tasan k'arya take ma malamin nasu tunda ta gaya mata wanda ya koya matan kawae iskancinta ne, "Dama Aljanu suna zuwa wurin mutum in yana dasu ne" malam da yayi sototo yana kallonta yayi tambayar, "Eh baka ga ko bokaye a film ba suna magana da Aljanu kuma suna ganinsu to ai a fili ma hakane,ni dama in dae raina ya 6aci to suna zuwa ko in wani ya ci zalina,to daka ban Assignment d'in naje gida nayi nayi na kasa shine raina ya 6aci har nayi kuka aikuwa sai ga wani cikinsu ya bayyana da suffar saurayi baka ganshi ba kyakkyawa ne sosae kamar balarabe gashinshi liya liya shine ya rarrashe ni ya koya man nan da nan na iya" ta k'arasa tana wani dashe baki ita ala dole dariya take shikam malam din was completely speechless bin ta kawae yake da ido daka kalle shi zaka fahimci hankalinshi ya tashi Haulat dai sai faman girgiza kai take don ta fahimci ya yarda da Maganar Fatun dama kuma shi bak'o ne bai dad'e da zuwa ba balle yasan halinta da cikin tsoffin malamansu ne ta fad'i ma wani hakan ba lalle su yarda ba tunda sun san halinta, "Ko in ce mashi kana son ganinshi ne?" ta tambayi malamin ganin yanayin fuskarshi, "Waye?" adan rud'e ya tambaya, "Shi Aljanin da yayi man Assignment d'in" wani kallo yabita dashi irin kallon mahaukaciya ce ke kafin yace"ni bance maki ba"daga haka ya d'auki littafin shi da sauran allin daya rage ya nufi hanyar fita ko uffan baice ma kowa ba ya barta atsaye,tana ganin ya fita ta nufi seat d'insu tana kyalkyatar dariya ta fad'a jikin haulat, "Wllh baki da hankali Fatuu shine kika tada mashi hankali ko", Murguda baki tayi tace" to da ba mugunta yaso yayi man ba daga na fad'i gaskiya", "Amman ai ta sigar rashin kunya ki kai mashi magana ko", " ni wai komae nai sai ace rashin kunya kuma ni ai bansan ita nayi ba ko"tayi Maganar tana tura baki,girgiza kai haulat tayi kafin tace"yakamata dai ki bari wllh kinsan fa komae kayi kaima sai anyi maka ba kamar malamai su tamkar iyayenmu suke abunda kasan bazakai ma iyayenka ba bai kamata suma kai masu ba,don Allah Fatuu ki natsu duk abunda kikasan zaisa ayi maki surutu ki bari kinji yar kawata kuma kanwata"ta k'arasa hadi da dafa kafadarta, "Ai nace ma Ya Handsome da Hajiya na bari in sha Allahu bazan kara ba", "yauwa yar gidan Ya Handsome Aljani ko ke fa",zaro ido Fatuu tayi ta kalli Haulat d'in kafin tace wani abun Haulat ta rigata"ko bashi ne Aljanin da kika suffanta ma Malam yayi maki Assignment ba",tana jin hakan ta kyalkyace da dariya itama Haulat din dariyar take tace sai ta fad'i mashi Fatun ta fara mata magiyar tayi hakuri daga haka suka ci gaba da hira don dama period d'in malam mai lissafi bata kare ba Fatuu tasa shi ya fita ba shiri, _____________ A ranar da yamma bayan ta fito zata tafi islamiyya ne Kawu Amadu dake cikin kiosk dinshi ya fadi mata yau Yaya Haisam yazo tafiya da ita Makaranta ya iske bata nan sai dai ya daukeshi yakaishi har Makarantarsu,jin hakan yasa washe gari da safe taje har gidan Hajiyar suka tafi tare bayan an biya an dauki Haulatu,bayan Haisam ya aje su a gaban Admin kaman yadda ya saba yana kokarin juya Motar ya tafi wani Malami ya tunkaroshi yana dan d'aga mashi hannu alamar tsaidashi,tsayawa Haisam din yayi bayan malamin ya k'araso ya zuge glass d'in motar kasa,gaidashi yayi haisam din ya mik'a masa hannu don su gaisan,bayan sun gama gaisawa ne yace mashi in ba damuwa yana son yin magana dashi haisam yace ba matsala,ganin yana kokarin fitowa ne malamin yace yayi zamanshi ba wata magana bace mai tsawo jin hakan yasa haisam cewa ya shigo daga cikin motan amman nan ma yace ba matsala zai tsaya daga waje wanda yayi hakanne gudun surutun mutane da basu raina abun magana yanzu ayi masa wata fassarar ta daban ba kaman in aka ga ya shiga motar,lokacin su Fatuu har sun kai wurin Hall dinsu don yana aje su bayan ya bata kudin break yau harda irin Popcorn din daya ta6a bata tai ta santi ya basu yace su wuce class,kamar ance Haulat ta waiga ta hango malamin tsaye gefen kopar driver ya d'aura hannunsa guda asaman motar, "Fatuu ji Uncle Bash a wurin dan gidan hajiya" haulat ta fad'a bayan ta ja ta tsaya,da sauri Fatuu da har tayi gaba ta juyo a sukwane jin abunda Haulat ta fad'a,a d'an rude tace"kai,to mi yake ce mashi,ko ya sanshi ne?"hannu Haulat ta yarfa alamar bata sani ba sai kuma tace"Allah yasa dai ba wani abun yake fad'i mashi ba game dake,kinsan yanzu kowa kallon d'an uwanki yake mashi" jin hakan yasa fatuu zaro ido a rud'e tace"to ni mi nayi mashi kuma in ba sharri zai ja man ba,bari inje inji mi yake ce mashi" ta k'arasa Maganar tana niyyar nufar bakin gate d'in da sauri Haulat ta kamo hannunta, "In kin je kice mashi mi,kika sani ko ya sanshi ne yanzu kuma kije ki fad'i wani abun aga kinyi rashin kunya ki kyalesu kilan wani abun suke tattaunawa ba lalle in abunda ya shafe ki bane" jin hakan yasa ta fasa zuwan Haulat tace mata su tafi kawae suka juya suka nufi aji saidai sam zuciyar fatuu ta kasa samun natsuwa sai faman waiwayensu take har suka kai aji tana ta sak'e sak'e acikin aranta. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣2️⃣ ........Sosae Haisam ya fahimce shi,bayan sun gama Maganar yayi mashi godiya shima Uncle Bash d'in yace ya gode da saurararshi da yayi ya kuma fahimce shi daga haka suka yi sallama da juna glass d'in Motar ya rufe yajata dama akunne take ya tunkari gate ya fuce , Har aka tashesu bata bar tunanin mi Uncle Bash yace ma Ya Handsome ba,bayan ta koma gida ma abun na ranta saidai bata yi tunanin zuwa ta tambayeshi ba saboda zullumin ko wani abun ya fad'i mashi game da ita gashi ma tasan ba lalle in ya dawo daga wurin aiki ba,wuraren karfe ukku da wasu mintuna suna zaune atsakar gida saman tabarma ita da gwaggo ita ta kwanta tayi shiru gwaggo kuma na sauraren radio,ganin Fatun tayi shiru ne yasa gwaggon tambayarta ko bata jin dad'i ne tace mata a'a lafiyarta lau kawae ta gaji ne,suna cikin zaman Amadu ya shigo gidan yana hango su azaune ya dakata a bakin kopar zauren yace"ke kije Yaya Haisam na kiranki"daga haka ya fara k'okarin juyawa zai fita gwaggo ta tsaidashi da fad'in"gidan kaje ne?" "A'a yanzu ina shago yazo zai wuce cikin Mota shine ya tsaya yace in kira mashi ita", "yana wajenne?" gwaggo ta tambaya, "Ya wuce gida" ya bata amsa daga haka ya juya ya fuce,jin Fatun tayi shiru yasa gwaggo cewa"Fatuu ko har kinyi bacci ne?"daga yadda take ta girgiza mata kai alamar a'a, "To kitashi kije baki ji ana kiranki bane", shiru tayi kirjinta na d'an bugawa tsoron zuwan take don yanzu ta tabbatar da kyar in ba wani abu Uncle Bash ya fad'i mashi game da ita ba, " Fatuu baki ji bane wai"gwaggo ta fad'a da d'an d'aga murya hakan yasa ta yunkura ta tashi zaune,ganinta sukuku yasa gwaggon tambayarta"lafiya?ko wani abu ya faru shiyasa yake nemanki ne?"da sauri ta girgiza mata kai tace itama bata sani ba, "To tashi kije,Allah yasa dai lafiya" mik'ewa Fatuu tayi ta shiga cikin d'akinta ta d'aukko d'an bak'in gyalenta ta yafa asaman kanta kafin ta fito zata tafi gwaggo ta bita da ido bata dai tanka mata ba ganin doguwar rigar atamfa ce ajikinta.Tana fitowa ta nufi kiosk din Amadu a sanyaye tace"Kawu ina Ya Handsome din?"wani kallo ya bita dashi mai kaman harara yace"A'a Ya Ugly,yar rainin wayo kawai Haisam dinne bazaki iya cewa ba"tura mashi baki tayi kawai bata ce komai ba, "Saurayinki ne shi da zai tsaye yanata jiranki,ya wuce gida sai ki iske shi can", Juyawa tayi ta nufi gidan Hajiya jikinta duk yayi sanyi sai faman zurfin tunanin ko tayi wani laifi a Makaranta kwanannan banda na Malam mai Maths take yi har ta iso part d'in nashi,tura kopar tayi ta shiga da yar sallama,abakin kopar ta tsaya ganin ba kowa a parlon,tunanin ko yana wurin Hajiya ne ta shiga yi har zata juya ta hango kopar Bedroom d'inshi a d'an bud'e bata idasa rufewa ba hakan yasa tayi tunanin ko yana ciki,d'an shiga tayi cikin falon ta tsaya gab da corridor ta k'ara yin sallama har sau biyu, " Who's there?"ta ji muryarshi can ciki ya tambaya, "Fatuu ce" ta bashi amsa, "Ok,am coming", jin hakan yasa ta koma can bakin kujerun tayi tsaye tana jiranshi,after some minutes taji ya bud'e kopar Bedroom d'in da sauri ta kai idonta gareshi,sanye yake da wando 3 quarter ruwan madara sai farar riga armless irin mara hannuwa ta mashi cif cif kirar karfinsa ta bayyana ba kamar damtsen hannuwan dake a murd'e ga suma duk ta kwanta luf a hannun nan da nan kamshin turaren jikinshi ya k'ara karad'e falon banda wanda dama falon ke saki,bai kalli inda take ba ya nufi kujera 6arin daya saba zama ya zauna ya d'an jingina,sai lokacin ya kalleta suka had'a ido da sauri ta gaidashi, maimakon ya amsa sai ya zuba mata ido kawae yana nazarin yanayinta don yaga kaman ba yadda ya saba ganinta ba,ita kuma ganin kallon da yake matanne yasa ta k'ara shan jinin jikinta, " Zaraah..."taji ya kirata,aikam tun kafin ya rufe baki ta durkushe a inda take ta fara cewa"Wallahi Ya Handsome kaji na rantse maka tun bayan dana fasa maka gilashin mota ban k'ara yi ma kowa laifi ba, ba ruwana da kowa ko Malamin math da ya ban Assignment d'innan ai na fad'i maka ni bansan rashin kunya bane da bazan fad'i mashi hakan ba amman ni ba abunda nayi ma Uncle Bash wllh tun dae can da dad'ewa ne ya ta6a cewa nayi mashi tsoki kuma dae gaskiya nayi mashin amman ya bugeni kuma tunda na shiga English club ma muke shiri dashi don shine shugaba amman wllh in dae ce maka yayi nayi mashi wani abu to karya yake man kawai sharri yake son ja man" cikin karyewar murya ta k'arasa Maganar nan da nan idanunta suka kawo ruwa ta duk'ar da kanta k'asa,still yai yanata sauraranta har ta gama kafin ya d'an girgiza kai had'i da yin guntun Murmushi aranshi yake ayyana ita dae kuka bai mata wuya,a yadda halinta yake bai kamata ace tana da saurin kuka ba ko kuwa shi take ma hakan saboda yarjejeniyar dake tsakaninsu ta glass oho, Sigh yayi kafin calmly yace"Zarah sit down"da sauri ta d'ago ta kalleshi ya d'an lumshe ido alamar eh,maimakon ta hau saman kujera sai ta raku6e agefen kujeran ta zauna kan Carpet,shi dai kallonta kawai yake bai dai yi mata magana ba, "Why zaki ce malaminku yayi maki k'arya kinsan mi yace man ne?" Da sauri ta d'ago tana zare ido ta dan girgiza kai alamar a'a, yaci gaba"kar ki k'ara cema babba yana k'arya ba teacher dinki kadae bama"da sauri tace"toh"idonta akanshi,shiru yayi kaman bazai k'ara cewa komae, "shi teacher d'in da kike magana akwae wani list na textbooks da ya ta6a baki right?" jinjina mashi kai tayi alamar eh, "Ok,ina list d'in?" "Paper d'in na wurin gwaggo tun lokacin da aka bani nakai mata nace ance asiyo wad'annan littattafan to sai ta ba kawu Amadu tace ya tambayo mata kudinsu lokacin da zaije kasuwa to daya dawo ne yace mata duk shagon daya je babu su sai da aka mashi kwatancen wani Babban Bookshop acan ne aka samu wasu acikinsu wasu kuma suka ce sun k'are amman za'a kawo ita kuma gwaggo data ji suna da d'an kudi don akwae ma wani na English dubu biyar yake shi kadae sai tace gaskiya bata da kud'in da zata siye su lokaci guda amman akwae adashe da take yi wanda zata siya ma kawu Amadu freezer saboda azumi daya kusan zuwa ya rinka saida kankara in ta kwashi kudin zata siya mansu duka shi kuma sai ta nemi ciko ta siya mashi,to ita nike ta jira fa kuma shima Uncle Bash d'in in ya tambaya ai inace mashi ance za'a siyo"ta k'arasa tana ta nishi sai kace ya tambayeta duk wannan bayanin,shi dai yayi shiru yana sauraranta har ta gama, Gently yace" je ki amso man paper d'in", Bud'a idanu tayi"siyo man zakayi?" d'an k'ank'ance idanu yayi"ko baki so?" A shagwa6e tana tura baki tace"to amman ai tsada garesu fa sai a saka ka kashe kudinka hakanan,shima ba ance za'a siyo ba", "Shine ai yanzu za'a siyo d'in ko saboda kina bukatansu" "Ni dai gaskiya banso kaita kashe kudinka fa,in kuma suka k'are fa", d'an Murmushi yayi jin abunda tace,d'an gyara zama yayi ya jingina sosae yana kallonta, " bazasu k'are ba inada su da yawa so don't worry about dat, yanzu kije ki kawo man and daga yanzu duk in kina bukatar wani abu game da karatunki ki sanar man" zaro ido ta k'ara yi a d'an rud'e tace "kai kuma ba gwaggo ba?" "Yeah"ya bata amsa fuskarshi still da Murmushi, " to saboda me?"ta sake tambaya, "Saboda na fita kudi kuma abubuwa sunyi mata yawa kinga sai in rage mata burden ko", d'age kai tayi gyalen ya idasa sa6ulewa ya tsaya kan kafad'arta a shagwa6e tace "to amman kai ai ba d'an gidanmu bane kuma sai ka d'aura ma kanka nauyi" "Yanzu ai nazama ko baki so?" "To ai sai ka dawo gidanmu zaka zama d'an gidan" "Ok sai in dawo in kin tanadar man inda zan zauna", " sai ka dawo d'akina ni kuma sai in koma na gwaggo,tunda akwae gado sai ka d'auki wannan kujeran daka fi zama tunda d'akin bazai isa asa dukkansu ba"still da Murmushi akan fuskarshi da alama yana enjoying hiran ne, "Ok zanyi hakan,sai ki fitar man da ranan da zan dawo but ki fara sanar da Grandma d'inki", Wani kallo ta bishi dashi baki bud'e alamar mamaki sai kuma tace" wllh nasan karya...au wasa kake ba dawowa za kai ba,tabb yama za'ai kabar wannan Aljannar duniyar ka koma gidanmu d'an kut dashi kaman zuciyar talaka,ai zafi da sauro ma kadae sun isheka ka gudu sai dai mu farka muga Ya Handsome ya tsere"ta k'arasa tanata dariya shima dariyar yake har hakoransa sun bayyana sosae ba kaman da tace wai gidansu kaman zuciyar talaka ko a ina ta iya wannan Maganar ya fad'a aransa, "Yanzu dae kije ki kawo man abunda nace" ya fad'a bayan ya gama dariyar,amsa mashi tayi da to kafin ta yunk'ura ta mik'e tsaye har zata juya sai kuma ta juya da yar damuwa a fuskarta tace"to kuma Ya Handsome in Gwaggo tace ni na fad'i maka Maganar littattafan fa,tana iya duka na fa don tace kar na rok'e ka abu", Shiru ya dan yi kaman mai tunanin wani abu sai kuma yace"ki fad'a mata shi teacher dinne yayi man magana"still da yar damuwa akan fuskarta tace"to Allah yasa ta yarda" har ta juya zata fita ya kirata ta juyo,tambayarta yayi Uncle d'inta nada waya tace mashi eh,yace tasan number dinshi tace eh ta sani yace ta karanto mashi dama wayarsa na aje akan kujera tun bayan da ya dawo,bayan ta bashi lambar wayar kawu Amadun yayi dialing kira yana jin ta fara ringing yace mata taje gidan kawai za'a bata ta kawo mashi, Lokacin da ta isa kopar gidan Amadun bai acikin kiosk dinshi,tana shiga gidan ta ganshi atsaye shi da gwaggo abakin kopar d'akinta, k'arasawa tayi ta tsaya agefe tana ta faman zare ido, "To shi bai gajiya ne yai ta faman hidima" gwaggo ta fad'a yayin da ta maida idonta kan Fatuu da sauri fatun tace "Uncle Bash ne yayi mashi Maganar d'azun daya kaimu Makarantar shine yanzu yace wai in kawo mashi takardar",jinjina kai kawae gwaggon tayi kafin ta k'ara cewa wani abu Amadu ya rigata da fad'in" to wai duk minene na damuwa da jan Maganar ma tunda dai ba rok'onshi mukai ba shi yace abashi ki bata ta kai mashi kawae", "Hakane amman dai wai kar abun yayi yawa aita d'aura ma Mutum hidimar da ba tashi ba" gwaggon ta fad'a da yar damuwa, "Ba wani abunda zaiyi yawa tunda yana da hali,ki d'auka kawai Allah ne ya dubi duminiyarki kinsan in bawa ya dogara ga Allah sai ya bud'a mashi ta hanyar da bai ta6a zata ba,kuma kinga dama ni da ita duk marayu ne haka kike ta kula damu,to ki d'auka sauk'i ne Allah ya kawo maki ta hanyarshi don haka ki d'aukko takardar ki bata ayi mashi godiya kawai", jin hakan yasa da sauri Fatuu ta kar6e" haka ma yace wai duk in ina buk'atar abu game da karatuna in sanar mashi,da nace saboda mi sai yace wai ke abubuwa sunyi maki yawa zai rage maki nauyi", Da sauri Amadu yace"Kinji ko,kar ki wani damu", jinjina kai tayi cike da gamsuwa"shikenan,Allah ya saka masu da mafificin Alkhairi,yasa ya gama da duniya lafiya ya biya masa bukatunshi na Alkhairi" gaba d'aya suka amsa da Amin,daga haka ta shiga ta d'aukko mata takardar dake d'auke da sunayen littattafan ta bata ta kai mashi. Lokacin data koma bai cikin parlon hakan yasa tayi tunanin ko ya koma cikin Bedroom ne,nufar corridor d'in tayi ta d'an shiga daga ciki ta rafka uwar sallama, "Assalamu alaikum Ya Handsome ga takardan" jin shiru yasa ta sake maimaitawa still bata ji yayi Magana ba hakan yasata k'ara d'aga murya tace"Ya Handsome na dawo ga takardan ko in shigo in kawo maka ne?" "Tunda d'akin ki ne ba sai ki shiga ba" ba zato ba tsammani taji daga bayanta ya fad'i haka,aikuwa a furgice ta juya ashe bai cikin d'akin fita yayi ya d'aukko abu a Mota,hannu tasa ta rufe baki tana gumtse dariya shi kuma ya d'an harareta ya nufi inda ya tashi ya zauna bayan ya aje abunda ya d'aukko kan c-table, nufo shi tayi tana zuwa gefenshi ta mik'a masa takardar kafin ta zauna kan carpet,dubawa ya d'an yi itama ya d'aurata kan c-table din, "Kasan inda ake saida su?" kai ya d'aga mata alamar eh, "To yaushe zakaje ka siyo?" shiru ya d'an yi sai kuma yace"After Asr prayer", "Kai wai yanzu ma ba dadewa kenan,to yau bazaka je d'aga karfen bane?" wani kallo yayi mata ba tare daya ce komai ba hakan yasata gwalo ido don a tunaninta ko tayi laifi ne da sauri tace"haka naji Hajiya tace rannan shiyasa nima nace", D'an lumshe ido yayi calmly yace"ba sunanshi kenan ba exercise ne,kinsan mi kenan ko?"da sauri ta d'aga kai tace"to bazaka je exercise d'in ba?" "Zanje amman sai na dawo" "To kullum kake zuwa exercise din?" Girgiza mata kai yayi"bani zuwa weekends but nakan yi saturdays wani lokacin, sundays dai bani yi" "Yauwa to tunda baka zuwa ranar lahadin ka bari sai ranar sai kaje ka siyo man kaga ranar Monday ba sai inje dasu ba kawai" Kai ya k'ara d'an girgizawa"No,tunda yayi Magana gobe yakamata ki shiga dasu,lafiya lou har naje na dawo ai", kai ta d'aga alamar gamsuwa sai kuma tace"to don Allah zan raka ka Ya Handsome " Shiru ya danyi sai kuma yace"Ai ba wani dad'ewa zanyi ba zan dawo", " to ba sai mu wuce wurin exercise d'in ba in ka gama sai mu dawo ko",wani kallo ya bita dashi, "Pls don Allah kaje dani,wllh ni da kake gani na kifin rijiya ne duk bansan wurare ba in baya ga kasuwa sai asibitin da gwaggo ke aiki sai wasu yan wurare kad'an fa" still kallonta yake,yana ganin k'okarinta intayi wata Maganar just cikin 3 years ta iya hausa sosae bacin ko agida tace wani lokacin Grandma d'inta fulatanci take mata, "Pls don Allah Sweetheart ka tafi dani" Fatuu ta katse mashi zancen zucinshi,tunani ya shiga yi ina zaije da ita in ya tafi da ita,yana da register da gym ukku so baisan wanne zaije da ita ba duk da mata na zuwa amman ba kamarta ba, "Don Allah Sweetheart Ya Handsome ka tafi dani inga gari" ta k'ara fad'a a shagwa6e, sigh yayi idonshi akanta yace"in matana taji ki kina ce man Sweetheart d'innan zata fasa maki baki fa" yayi Maganar fuskarshi a sake kaman zaiyi dariya, "Nasan wasa kake,Kai da ma baka da ko budurwa balle mata kuma", jinjina kai kawai yayi sai kuma yace" to mi zaki fad'i ma grandma d'inki?" da sauri tace"yo zance mata zan bika siyo littattafan daga nan zan raka ka wurin exercise in ka gama sai mu dawo", nodding kai yayi"Ok kije ki fad'a mata,if she agrees sai kizo in an gama salla", Yar k'arar murna ta saki ta fara mashi godiya daga haka ta mik'e ta nufi kopar fita da sauri,har zata kama kopar ta bud'e ya kirata ta juyo, " Ki fad'i mata exactly as u said,in kikai man karya....." kafin ya ida maganar ta katseshi ta idasa mashi ".....in kika man k'arya ina zaune zan gani" tayi Maganar tana kwaikwayon yadda yake Magana harda wani d'age gira daga haka ta fuce da gudu Haisam bai san lokacin da kyalkyace da dariyar da bai tunanin ma ya ta6a yinta, arayuwarshi ba mai mashi irin abunda Fatuu ke mashi haka kuma bai ta6a sake ma wani mutum 6are kaman yadda yake mata ba ko k'annenshi bai sake masu kaman yadda yake ma Fatuu ayanzu,wato ashe ta ruke Maganar da yayi mata lokacin da tazo bashi hakuri ta dau alkawarin ta daina fada da kowa yace inma tayi yana zaune zai gani kar tayi tunanin zata mashi wayo,girgiza kai yayi a fili ya furta"ZARAH". Tana komawa gida cike da farinciki ta sanarma gwaggo kaman yadda tace zata fad'i matan sai dai da farko nunawa tayi bata yarda ta bishi ba kawai salon taje ta takura mashi,magiya ta shiga yi mata tana rantsuwar bazata takura shi ba,da kyar gwaggon ta amince bayan taja kunnanta sosae,cike da zumud'i ta nufi bandaki don yin wanka tana cikin yi aka fara kiran sallar la'asar da sauri ta gama ta fito tayi walwala kafin ta nufi dakinta ta fiddo sabuwar maroon jallabiyarta mai ratsin brown ta zumbula bayan tasa undies sannan ta duddungura sallar shaf shaf tana gamawa ko addu'a bata yi ba ta mik'e ta nufi gaban mirror ta fara yin kwalliya dama ta jere kayan shafan da Haisam ya siya mata,kwalliya tayi simple ba mai hayaniya ba ga powder din ta kwanta mata sosae tayi wani fayau,dama yanzu fatarta ta k'ara yin smooth saboda mayukan da take amfani dasu,ta shafa maroon janbaki wow,jama'a kuzo kuga Fatuu yanmata,fita tayi taje wurin gwaggo tace ta bata takalmanta na sallar bara dama ita ta 6oye su don Fatuu in tana son abu bata san ta kyaleshi ya huta ba yanzu ya tsufa,ba don gwaggon na adanawa ba shima takalmin da tuni ya tsufa koma ya lalace,d'aukko mata tayi da yar jakarshi bak'a shima bak'i ne mai tudu nan da nan ta idasa fitowa a yar budurwa,sark'a da yan kunne harda d'an agogo golden gwaggo ta fiddo mata harma ta tayata sakawa,tana niyyar juyawa ta fita gwaggo tace"wannan kitson na gaba ki maida shi baya ki hade ki kulle kar ki fita haka dashi",amsa mata tayi da toh daga haka ta koma dakinta tayi yadda gwaggon tace ta feshe jikinta da turare harda bakinta ta fesa mouth freshner dama tayi brush da ta shiga wanka,tsayawa tayi tana kallon kanta a madubi,kayataccen Murmushi tayi a fili tace"Fatuu kinyi kyau kaman sarauniya" tuntsirewa tayi da dariya daga haka ta fita daga d'akin ta d'aga murya tana fad'in "Gwaggo sai na dawo" lek'owa gwaggon tayi tana kallon bayanta har ta fita bayan tace mata adawo lafiya,d'an girgiza kai tayi ganin yadda Fatunta ta fara zama Budurwa. Tana niyyar shiga part d'inshi ya 6ullo daga corridor d'in da zai kai ka cikin harabar gidan,tana ganinshi ta tsaya,suna had'a ido ya d'an buda mata ido alamar mamaki hakan yasa tasa tafukan hannayenta ta rufe fuska alamar kunya, "Nayi kyau?" ta tambayeshi bayan ta bud'e fuskar,kai ya d'aga mata alamar eh kafin yace taje parking space ta jira shi,amsa mashi tayi da toh tabi ta gefenshi ta shige cikin gidan shi kuma ya ida shigewa part din nashi,tana shiga ta nufi part d'in hajiya don ta gaidata Saude ta sanar da ita Hajiyar bata nan bayan ta gama yabon gayun nata hakan yasa ta juya ta fita,tana isa wurin aje motocin Haisam ya fito ya nufo parking space d'in yana sanye da Sportswear ya ratayo jakarshi a hannu guda,k'ura mashi ido Fatuu tayi tana kallonshi don shi komi yasa kyau yake k'arawa,ganin kallon da take mashin yasashi sadda kanshi k'asa har ya k'arasa cikin wurin,back door na mota ya bud'e ya saka jakar,yana k'okarin bud'e gaban motar Fatuu tace"Ya Handsome mu hau wanccan mashin din" juyawa yayi ya kalli bike d'in da take nunawa kafin ya juyo yana kallonta, imagining ya fara abunda zata iya yi mashi in ya hau bike d'in da ita hakan yasashi girgiza mata kai yace"zamu a Mota",turo baki tayi tana d'an yamutsa baki alamar ba haka taso ba,ganin hakan yasashi cewa"wani lokacin" ya jaddada mata da kanshi itama ta d'aga mashi alamar toh daga haka ya bud'e Motar ya shige yace mata ta zagaya ta shiga,bayan ta shiga ya fiddo motar cikin harabar daga haka yajata suka fuce. *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣3️⃣ Wani Babban Bookshop ya nufa dasu, a gefen wurin ya parker motar, da har zaice mata ta jirashi sai kuma yace ta fito sakamakon tunawa da Maganar data yi na cewa ita kifin rijiya ce duk bata san wurare ba, suna shiga ciki Fatuu tabi wurin da kallo don an tsarashi sosae gashi k'ato ne akwae duk wani abu da Mutum zai iya bukata a Bookshop, wani k'aton Alhaji ne zaune saman kujera acan ciki yana ba yaran shagon umarnin d'aukko ma Mutane abubuwa hannunshi ruke da calculator da littafi da alama lissafi yake, yana hango Haisam ya fara washe baki yana mashi dariya, "Barka da zuwa yalla6ai" Alhajin ya fad'a lokacin da suka k'arasa, "Yauwa Alhaji,ya kasuwa" ya fad'a cikin cool voice dinsa, "Kasuwa Alhamdulillah gamu cikinta" Alhajin yayi maganar still da fara'a a fuskarsa, maida kallonshi yayi kan Fatuu data k'ura mashi ido tanata kallon tumbinshi cikin ranta kuwa tunani take wai ko dai ciki gareshi ne, "Sannu yanmata"Alhajin yace mata, saidai sam hankalinta na kan tumbinshi har saida Haisam ya kira sunanta sannan ta maido idonta kanshi yay mata nuni da ana mata Magana, kallon Alhajin tayi dake mata Murmushin yake don ya fahimci abunda take kallo ya sake ce mata sannu sai lokacin ta gaidashi ya amsa mata, d'aura takardar yayi saman wurin dama ya fiddota daga cikin pocket d'in wandonsa yace ma Alhajin wannan yake so, da sauri ya kira wani matashin saurayi acikin yaran shagon yace ya mik'o masa takardar, bayan ya duba ya d'ago yace ma Haisam duk akwaesu nan take ya nuna ma saurayin inda zai d'add'auko su, bayan an fiddo mashi su duka Alhajin ya tambayi shikenan, Haisam yace a d'aukko mashi Calculator guda biyu da Math Sets, da sauri Fatuu ta kalleshi tace" Ya Handsome guda biyu biyu ai sunyi yawa kuma ma ina dasu don dai sun tsufa ne wasu abubuwan maths set d'in duk sun 6ace, amman dai guda d'aya ya isa" shiru yayi mata duk idanun mutane suka dawo kanta dama kuma tunda suka zo wurin tun a waje aketa faman kallonsu,(dama abu mai kyau badai jan hankali ba), jin baice mata komae ba yasa ta sake maimaita mashi cewa guda daya fa ya isa, "Ba kinada Friend ba,ki bata" taji yace ba tare daya kalleta ba, shiru tayi sai yanzu ta gane ashe harda Haulat ya siya, da itama ance ta siyo littattafan harda ita zai saimawa kenan ta ayyana aranta, bayan an d'aukko su yace a bashi bandir d'in littafin rubutu,kwalin biro dana pencil da eraser da sharpener, wata zabura tayi ta zaro ido tana kallonshi shikam baima san tana yi ba, ganin duk an d'aukko mashi yasa a rud'e tace"Ya Handsome wannan ai sunyi yawa sosae duk ina zan kaisu?" banza ya mata ganin hakan yasata ta d'an buga k'afa tana jujjuya kai irin na shagwababbun yara hakan yasa Mutane yin Murmushi harda Alhajin yace "ai abun amfani bai yin yawa, in aka siya da yawa kinga zaki dade baki nema ba, ko baki son ayi mana ciniki ne" tura mashi baki tayi batace komae ba, bayan duk an d'aukko komae aka zuba masu acikin katuwar leda mai tambarin shagon ya basu card suka cire kudinsu daga haka suka yi sallama da Alhajin har sun juya zasu tafi ya kira Fatuu ya bata kyautar jotter mai cover din frozen had'e da dan bironta in ana rubutu dashi da daddare yana sakin haske kala kala, fuska a tur6une tace ta gode ta nufi hanyar fita ita ala dole anyi mata laifi gashi ma Ya Handsome d'in yaki tanka mata hakan ya kara fusata ta, Har suka hau hanya tana ta tura baki tana d'an satar kallonshi, duk yana kallonta ta cikin mirror can ya d'an juyo suka had'a ido tayi narai narai da idanu kaman zatai kuka, "In kana da abu har yayi maka yawa wasu basu dashi suna bukata sai ka basu" taji ya fad'a bayan ya maida idonshi kan hanya, Kallonshi tayi don bata fahimceshi ba,ci gaba da magana yayi" duk abunda kike ganin yayi yawa ki nemi wanda basu dashi ko kuma suke bukatar k'ari sai ki basu",shiru tayi tana ta kallonshi hakan yasashi sake kallonta ya d'age mata gira yace"Understand? " da sauri ta jinjina mashi kai don yanzu ta fahimci dalilin dayasa ya siya da yawa, yana cikin driving d'in ya yanke shawarar zuwa Electronics Empire (E.E) da ita don wurin suna da park na yara sai kawae ya siya mata ticket ta shiga wurin kafin ya gama workout dinshi, lokacin da suka k'arasa wurin Babban ginin bene ne mai girman gaske, duk wani abu mai amfani da wutar lantarki ko mai samar da wutar zaka samu a wurin bama su kad'ai ba akwae katon shagon wayoyi da abubuwan da suka danganceta wato accessories,akwae internet cafe wato inda mutum zai shiga ya hau yanar gizo a Computer, wannan duk ak'asan benen suke, acan sama kuwa nan Gymnasium d'in yake wato wurin motsa jiki, k'aton wuri ne shaqe da kayan motsa jiki, daga can bangare guda glass ne mai dishi dishi irin wanda ba'a ganin abu sosae akayi amfani dashi wurin fitar da bangaren mata saidai zaka d'an iya hango kawunansu don glass din baida tsawo sosae, bayan gym d'in akwae wani babban parlor koparsa na kallon ta gym d'in an k'awata shi sosae da kujeru na alfarma ga had'addun Flowers da frames masu d'aukar hankali, ba komae ake aciki ba face Electronic games iri iri, bayan su kuma akwae Cold Store wato wurin kayan sanyi mai d'auke da freezers kala kala komai zaka samu nau'in kayan sanyi awurin har kayan itatuwa ana matsewa ayi ma mutum juice in yana bukata, shima dae ya kawatu wurin, Bayan yayi parking motar a wurin da aka fitar don aje motoci atare suka fito da ita yace ta biyo shi, bangaren da park yake daga can gefen benen ya nufa,ticket ya siya mata kafin ya shigar da ita don an sanshi sosae a wurin, park d'inma ya kawatu sosae, akwae lilo kala kala aciki da abubuwan da zasu dauke ma yaro hankali, lilon da yasan inta hau su baza'a samu matsala ba ya biya mata daga haka yace mata shi zai shiga ciki ta tsaya tayi wasa in ya gama zai dawo sai su tafi, tana jin abunda yace ta turo baki tana yamutsa fuska ganin hakan yasashi cewa "any problem?" A shagwa6e tace "to ni bazaka je dani wurinku ba sai kace wai in tsaya nan inyi wasa kaman wata k'aramar yarinya" d'an bud'a ido yay jin abunda tace yace "to ke ba Yarinyar bane?" "Eh mana ni yanzu ba yarinya bace matashiyar budurwa ce" d'an guntun tsoki yayi ya d'an girgiza kai, "Wurin namu to Matashiyar budurwa bata zuwa sai Babba,in bazaki tsaya anan ba to kizo in maida ki gida kar ki wasting time d'ina" tana jin hakan tace to zata tsaya, dama wurin ya burgeta Sosae kawae rigimar tace saida yaga ta hau lilo sannan ya tafi bayan ya gargadeta kan babu ruwanta da kowa da komae tayi wasanta kawae tace mashi to,bayan ya fita saida ya koma wurin motarshi ya d'auko jakarshi sannan ya nufi cikin wurin. Sosae Fatuu take jin dadin wurin tana ta nishadi, in ta hau wannan lilon sai ta sauka ta hau wannan har abokai tayi harda yan yara anata yi masu hotuna tare hakan yasa tayi tunanin zuwa ta amso wayar Ya Handsome don itama ayi mata hotunan da wayarsu,lokacin data zo fita hanata akai akace inta fita shikenan sai dae ta sayi wani ticket d'in in zata sake shigowa ita kuma tace wllh ba wani ticket d'in da za'a k'ara siya daga zata je ta amso wayar yayanta ayi mata hoto sai ace sai ta k'ara wani biyan kudi wannan ai salon sata ne ma,k'arshe dae dole aka barta ta fita ba kamar dayake ansan wanda ya kawota, tana shiga entryway din benen ta tsaya a wurin tana yan kalle kalle wai ko zata ga wurin exercise d'in amman bata ga an rubuta a ko ina ba hakan yasa ta tsaida wani mutum daya fito daga cikin internet cafe ta tambayeshi inda ake motsa jiki yace Gymnasium kenan ta hau saman bene zata ga wurin an rubuta asaman kopar shiga tace mashi to ta gode, tana hawa ta kalli kopar bangaren dama taga an rubuta Game Zone asama hakan yasa ta juya hagu ai kuwa sai gashi taga an rubuta yadda Mutumin nan ya fad'i asama da sauri ta nufi babbar kopar shiga wurin saidai tana zuwa mai tsaron wurin ya hanata yace masu register da wurinne kadai ke shiga, turo baki tayi tace to ai wurin yayanta tazo, yace saidai ta kirashi awaya ya fito,rokonshi ta fara yi akan ya barta ta shiga,don daga inda take tana d'an hango cikin wurin ganin yadda ya had'u ne yasa taji ta matsu ta shiga ciki har d'an d'agyel take tana k'ara hango cikin,hakuri ya bata yace haka dokar take ne ba laifinshi bane amman ta fad'i sunan yayan nata sai akira mata shi,tana niyyar fad'i mashi kaman ance ta d'aga kanta ta hango Haisam d'in ya bullo wuyanshi rataye da farin short towel yana goge zufa da alama motsa jiki ya gama ga headphones asaman kanshi sai dae ya cire kan speakers d'in daga jikin kunnanshi, da sauri tace "yauwa gashi can yayan nawa" juyawa mutumin yayi don ya ganshi daidai Haisam d'in na niyyar shigewa aikuwa fatuu na ganin haka ta kware murya ta kwala mashi kira"YA HANDSOME!" da sauri ya juyo don bai tsammaci jin muryarta ba a wurin,hannu ta d'aga mashi tana d'an tsalle wai don ya ganta,yana hangota ya nufo kopan cikin tafiyarshi ta kasaitacce kuma maji karfi,da d'an mamaki yake kallonta lokacin daya fito inda take ita kuma sai faman washe mashi baki take, "What are u doing here Zarah?" ya fad'a ya d'an 6ata rai, ganin haka yasa ta marairaice fuska ba tare da ta ce mashi komai ba, "Ba nace ki tsaya acan ba!" ya k'ara fad'a idonshi a kanta da d'an yanayin bacin rai a fuskarshi, " To ai ba hakanan nazo ba fa" ta fad'a tana kyakkyafta ido ta d'an yamutsa fuska, jin hakan yasa ya d'an sassauta d'aure fuskar da yayi ya fara tunanin ko wata matsala ce ta kawo ta, "What's d problem?" ya tambaya, " Dama wayarka nazo ka bani za'a man hotuna, duk mutane yan uwansu nata dauk'arsu banda ni" ta k'arasa tana tura baki, bud'a ido yayi ya d'an jinjina kai " Wayana zan baki?" kai ta daga alamar eh, " waye zai maki hoton?" "Ai akwae mutane awurin zan samu wani sai in bashi yayi man kuma harma nayi abokai fa" ta k'arasa tana Murmushi shima murmushin yayi amman nashi na mamakin maganarta ne, "Yanzu idan na baki wayana aka gudu dashi fa? baki san ana satan waya sosae ba a irin wurinnan" zaro ido tayi jin bunda yace sai kuma tace" to muje tare kai sai kayi man" d'age mata gira yayi yace "Zarah bazaki barni nayi exercise d'ina ba ko", Langa6ar da kai tayi tana dariya tace "ai yanzu zaka dawo" gyad'a mata kai yayi kafin yace bari ya d'aukko wayar tana ciki,tana jin hakan tace don Allah ya shiga da ita taga yadda wurin yake,sosae take mashi magiya har saida ya shiga da ita,daga baki bakin kopa ya tsaya da ita bai shige da ita can ciki ba,baki bud'e take bin wurin da kallo don ba k'aramin haduwa yayi ba kaman a kasar waje,ko iya haduwar wurin tasa mutum ya ringa kwakwar zuwa kullum,kayan motsa jiki kala daban dabanne a wurin an jerasu a tsare ga maza nan masu k'irar karfi sanye cikin workout outfits iri daban daban nata yi gwanin burgewa, ga sanyin Ac ya karad'e wurin sai kace ba wurin fidda zufa ba, ga wak'a an kunna sautin kid'an na tashi a sifiku ji kake wani dudum dudum abun dai sai wanda ya gani, nuna mashi d'ayan bangaren tayi tace nan kuma inane yace mata wurin mata ne tana jin hakan tace bari ta d'an leka ta gani, kafin yace wani abu tuni tayi gaba,tana lekawa cikin wurin da sauri tasa hannu ta rufe bakinta, cike da al'ajabi ta dawo wurin Haisam dake tsaye tace "amman dai Ya Handsome wad'anccan matan ba musulmai bane ko suke sanya irin wannan kayan na jikinsu,wai kaga wata,wllh wandon jikinta da kad'an ya wuce girman d'an pant gashi bata da riga sai....." kasa k'arasa abunda zata ce tayi ganin kallon da yake mata, "Tunda kin shigo kin gani ki koma waje ki jirani ina zuwa" amsa mashi tayi da toh tana juyawa daidai wata mace ta shigo wurin dama kopar daya ce tanan kowa ke shigowa sai ya nufi bangarenshi, tana ganin Haisam ta nufo shi tana murmushi, sanye take da tight long sleeve shirt irin rigar nan mai kama jiki mai dogon hannu purple colour kuma bata rufe mata cikinta ba duka sai bak'in wando pant irin dogon wandon nan roba shima mai kama jiki don har shaidar pant d'inta na can ciki ana gani tasa hular gashi baka har tsakiyar bayanta ta d'aure da ribbom purple, kafafunta sanye da kambas farare ba laifi tayi kyau kuma kayan sun fitar mata da shape dinta sosae amman dai da ganinta ba musulma bace, "Hi zakee" ta fad'a tana ta faman washe mashi baki, kasa kasa ya furta"Anah",kallon Fatuu tayi dake ta faman bin ta da ido tana mata kallon k'urulla tunda ta shigo tayi kafin ta kalli haisam tace "is she ur sis?",kai ya d'aga mata alamar eh, tambayar sunanta tayi yace mata Zarah,jinjina kai tayi ta kalli Fatuu tace "kina lafiya?" mamaki ne ya kama Fatun don bata yi tunanin ta iya hausa ba tace "Lafiya lau", "Gud,tunda kin kawo mana ziyara yakamata kiyi exercise kema" ta fad'a still da fara'a a fuskarta, ita dai Fatuu bata ce mata komae ba, sai ta kalleta sai kuma ta kalli haisam da ta kasa gane yanayin fuskarshi, hannun Fatun ta kamo tace ma Haisam zata je da ita wurinsu don ya samu yayi workout dinshi, "No Anah, she's going now" ya fad'a fuskarshi ba yabo ba fallasa, "Don Allah Ya Handsome ka barni in bita ina son nayi nima" Fatuu ta fad'a kaman zatayi kuka, girgiza mata kai yayi yace ba'a yi da irin kayan jikinta,da sauri tace "to ai sai in nad'e rigar sama" wani kallo ya bita dashi jin wani shirme data fad'a, "Don Allah Ya Handsome ka barni ko irin wannan wanda akeyi mai kaman tafiya ne inje in danyi, wllh dama ina ganin Hajiya Rabi Bawa mai kada na shirin kwana cas'in na hawa irinshi yana burgeni sosae" ta k'arasa tana d'an hade hannu alamar rok'o, " Tana nufin treadmill kabarta sai in rage mata Speed din k'arshe" Anah ta fad'a,shiru ya danyi kaman bazai ce komai ba da alama nazari yake acikin ranshi, kallon Fatun yayi da ta kafe shi da ido da gani tana Matuk'ar son taje duk tayi kalar tausai, d'an lumshe ido yay yai mata alamar taje, sosae ta saki dariyar farinciki tace mashi ta gode, hannunta Anah d'in ta kama suka nufi bangaren matan bayan Haisam yace mata ta kula da ita sosae don bata ta6a yi ba, Suna shiga aka fara tambayar Anah wacece ita tace masu sister d'in zakee ce, nan da nan suka shiga d'aga ma Fatuu hannu suna mata welcome don suna yin Haisam, da yawansu sun fada tarkon sun shi sai dae ba fuska, ita kanta Anah din bala'en sonshi take har haisam din ya gane mata don tafi kowa shishshige mashi acikinsu shiyasa bai sakar mata fuska, ita dae Fatuu sai faman binsu take da ido tana ganin yadda suke motsa jikin,Anah da kanta ta tattare ma Fatuu rigar sama dama rigar nada mad'auri ta d'aure mata ita sannan ta cire mata mayafin rigar ta aje shi gefe, dama yar jakarta tunda suka zo ta barta a mota, wurin wani treadmill da bakowa ta nufa da ita, saida ta fara hawa ta nuna mata yadda ake amfani dashi ta tabbatar ta gane sannan tace ta hau bayan ta rage gudunshi karshe yadda zata yi kaman tana tafiya a hankali, sosae Fatuu ke sakin Murmushi tana tayi dad'i duk ya kamata abunda take gani a tv anayi yau gashi itama ta hau tanayi, kallon Anah tayi dake gefenta tace ta d'an k'ara mata gudunshi,ganin tana yi ba wata matsala yasa ta k'ara mata gudun kad'an,tana cikin yi aka kira Anah din waya tace ma Fatuu zata yi waya kar ta ta6a komae ta amsa mata da to, dan matsawa kad'an tayi tai picking call d'in saidai bata ji sosae saboda k'arar kid'an dake tashi a wurin hakan yasa ta nufi can bakin kopar shigowa wurin taci gaba da yin wayar, Fatuu na cikin yi hankalinta ya tafi kan wasu tanata kallon yadda wasu ke yin nasu har bata san ta d'aura hannunta kan malatsin dake d'auke da alamar + ba, wato k'ara gudu saidai taji gudun ya k'aru hakan yasa ta rud'e ta daddafe kan abun ashe tanata k'ara gudunne bata sani ba,lokaci guda ta rud'e ta kidime ta gigice gaba d'aya taga duniyar na juya mata hakan yasa ta saki wata gigitacciyar k'ara ta kwala ma Haisam kira "YA HANDSOME.......!!!" duk tabi ta daddafe kan machine d'in sai falla uban gudu take,k'arar data saki ce ta jawo hankalin Mutane kanta harda masu sanye da earpiece saida suka ji don ba k'aramar k'ara tayi ba, a gigice Anah ta saki wayar ta nufo ciki da gudu sai dai ko kafin ta kai wurin wata wadda ke kusa da fatun tayi kukan kura ta kai ma fatun d'auki cikin zafin nama ta kasheshi, Anah na isowa wurin fatun tayi baya luuu zata fad'i kasa da sauri ta tarbota ta riketa gam adaidai lokacin kuma Haisam ya fado cikin wurin don yana jin k'arar yasan Fatun ce, akasan wurin ta kwantar da ita tanata faman girgizata sai dai ko motsi bata yi ba hakan kuma ba k'aramin tada mata hankali yayi ba har ta fara zubda kwalla, " Zarah, Can u hear me? Open ur eyes please!" haka Anar keta fad'i tana ci gaba da zubar da kwalla, shidai Haisam tsaye yayi yana kallon Fatuu dake yashe a k'asa bata motsi,tsananin tashin hankali ne yake ciki sai dai ba lalle ka gane hakan ba, yama kasa yin tunanin takamaimai abun yi gashi duk matan sunyi mata rumfa hakan ne yasa bai k'arasa wurin Fatun ba,ko wurin ma don baida zabi ne dole tasa ya shigo saboda maza basa shigowa, a hankali ya matsa kusa dasu yace su d'an matsa duk suka dare ya kasance yana kallon fuskar Fatun, dagowa yay ya tambayi ko akwae ruwa awurin da sauri wasu suka amsa da eh don duk basu yi tunanin ma su samata ruwan ba, bayan wata ta kawo bottle water Haisam d'in ya amsa ya duk'a gaban Fatun ya zuba ruwan ahannunshi dama a bud'e aka bashi robar, yayyafa mata a fuska yayi nan da nan taja wani dogon numfashi don ruwan nada dan sanyi, "Zarah" haisam din ya kirata, a hankali idonta ya fara motsi,Anah na ganin haka ta ci gaba da kiranta tana cewa ta bud'e idonta, bud'e idon ta fara yi tanayi tana lumshe su, "Zarah look at me" haisam ya fad'a, a hankali ta d'an ware idon akanshi, kura mashi ido tayi kamar bata sanshi ba can kuma sai ta fashe da kuka tana wani dashe baki dama haka take kukanta kamar yar k'aramar yarinya, Sai lokacin ya kalli Anah fuska a d'aure yace "how does it happened?" baki na rawa ga kwalla a fuskarta ta kora mashi bayani, tana kaiwa karshe yay ma Fatun wani kallo hakan yasa cikin sheshsheka ta fara mashi bayanin yadda abun ya faru "Wllh Ya Handsome bani na k'ara gudun ba, bansan na d'aura hannuna kan abun k'ara gudun ba, da naga gudun na karuwa shine na rurruke kan abun ashe na k'ara latseshi ban sani ba" shiru yayi don yama rasa abunda zaice,wad'anda suka ji abunda tace sai faman yi mata sannu suke yayin da wad'anda basa jin hausa suka shiga tambayar abunda tace aka fad'a masu suma suka shiga ce mata sorry, "Zan sha ruwa" ta fad'a da disashshiyar murya, sauran ruwan dake hannunshi ya mik'a mata Anah ta d'an d'ago kanta ta kafa baki saida ta shanye shi tas tasa hannu ta cire robar daga bakinta Anah ta amshi robar ta aje gefe guda, "Zaki iya tashi" haisam ya tambayeta, d'aga mashi kai tayi alamar eh ta fara k'okarin mikewa tsaye da taimakon Anah shima ya mik'e tsaye,hannu Anah takai ta kwance mata rigarta ta d'aukko mayafinta ta yafa mata tana k'ok'arin kama hannunta Haisam yace ta bashshi, kallon Fatuu yayi yace suje ta fara tafiya ahankali tana jan k'afa matan wurin na k'ara yi mata sannu, ita kam Anah tayi tsaye sototo duk ta d'aura ma kanta laifin faruwar hakan gashi ma taga haisam d'in kamar yayi fushi, tai tsaye tana kallonsu har suka fita daga wurin, a hankali take taka matattakalar benen hannunta dafe da bango haisam d'in na bayanta, haushi yaji shiyasa yace Anah ta kyaleta don tun farko shi dama baiso fatun taje wurinba jin tace zata kula da ita ne yasa ya bari dama kuma ita taja hankalin fatun har tasa ran zuwa wurin, suna fitowa waje Fatun ta duk'e don tunda ta saukko daga kan benen taji amai na tuk'arta, "Lafiya Zarah?" haisam dake gefenta ya tambaya, "Amai nake ji " ta bashi amsa, "Ok ki d'aure ki matsa can kada kiyi masu amai nan",tashi tayi tana daddafe cinyoyinta ta nufi can gefe guda ta duk'a shi kuma yana bayanta bai kallon fuskarta don arayuwarshi ya tsani amai ko kusa da mai yinshi bai zuwa don yanzu zuciyarshi ta tashi shima yaji aman,kuma in har hakan ta faru ba k'aramar wahala yake sha ba don ba k'aramin abu ne ke sashi amai ba, shiru aman yak'i zubowa hakan yasa ta mik'e ta juyo, Haisam ya tambaye ta ya akai, tace bai zubo ba yace mata su tafi to, wurin da yayi parking d'in motarshi ya nufa suna zuwa bakin motar Fatuu tace" Ya Handsome ina zamu?" "Daga ina muka zo?" shima ya tambayeta, "Daga gida" ta fad'a tana yin nishi, yace to can zamu, da sauri tace "Don Allah Ya Handsome kar mu koma gida yanzu, wllh in gwaggo taji abunda ya faru har buguna tana iya yi dama saida ta gargad'eni kan kar inyi wani abu ba daidai ba, yanzu ko na fad'i mata yadda abun ya faru ba lalle ta yarda ba" da ganin yadda take yin Maganar tana d'an jin jiki, shiru yayi yana nazarin maganarta don shi kanshi bazai so ya maida ita gida haka ba don kallo d'aya za'ai mata a fahimce wani abu ya faru da ita, Allah ma ya tak'aita abun don irin wannan har zuciyar mutum sai ta buga saboda firgici, " To ya kike so ayi" ya tambaya idonshi akanta, " Mu koma inda ka fara kaini naga akwae kujerun siminti sai in d'an k'ara hutawa yanzu juwa nike gani" jinjina kai yayi yace suje can d'in, a daddafe suka isa wurin masu tsaron gate d'in wurin nata tambayar miya sameta ganin lafiya lou ta fita bayan ta gama yi masu masifa, Haisam yace masu ta fad'i ne suka shiga yi mata Allah ya kyauta, wani ticket ya siya masu kafin suka shiga ciki, a gefe gefen cikin wurin dogayen kujerun suke,nufar guda sukai yace mata ta zauna zaije ya dawo, bayan ya tafi tabi wurin da kallo wai ko zata ga abokanta da tayi saidai duk babu su sun tafi dama sun rigata zuwa wurin, bai jima ba ya dawo hannunshi ruke da robar ice cream da bottle water tana zaune ta d'age kanta saman bayan kujerar,zaunawa yayi gefenta ya kira sunanta ta d'ago tana kallonshi, ice cream d'in ya mik'a mata ta girgiza mashi kai da sauri alamar bazata sha ba, shiru yayi yana kallonta don hakan ya tabbatar mashi batajin dad'i sosae tunda har tai rejecting ice cream saboda yasan tana sonshi ne ma ya siyo mata, "Zan sha ruwa" ta fad'a, bud'e mata yayi ya mika mata, ta kafa baki ta shiga kwankwad'a har saida yace kar yasata amai sannan ta daina sha, amsar robar yay ya rufe ya aje su agefenshi harda ice cream din,shiru sukai na d'an wani lokaci ya jingina bayanshi da jikin kujeran yana kallon yadda yara keta wasa, ba zato ba tsammani yaji Fatuu ta kwantar da kanta saman kafadarshi, d'an juyo da fuskarshi yayi ya kalleta sai kuma ya d'ago yaci gaba da kallon yaran, a hankali ta rinka shakar daddadan turaren jikinshi mai sanyin kamshi da yaketa kaima hancinta ziyara, nan take kuma tashin zuciyar da take ji ya fara raguwa ta fara lumshe ido, bayan wasu mintuna Haisam ya fara tunanin ko dai ya kaita asibiti don ya fara gajiya da zaman hakan yasa ya kira sunanta don yaji ya take ji yanzu, jin shiru bata amsa bane yasa ya k'ara kiran nata still shiru bata amsa ba, d'an juyawa yayi ya kalleta sai dae bai iya ganin fuskarta don ta d'an dukar da ita kasa, dago fuskarshi yay yaci gaba da kallon wurin can kuma sai ya kai hannu ya d'aukko wayarshi dake gefenshi, camera din wayar ya shiga ya maida camerar ta gaba ya kaita saitin fuskar Fatuu, nan take ya saki d'an Murmushi ganin yadda taketa bacci abunta numfashinta na fita a hankali ga gashin idonta yai wani irin tsawo da tana baccin, janye wayar yayi ya fita daga camera d'in ya ajeta agefenshi, gyara zamanshi yay ya d'an zamo kafin ya kai hannun damanshi ya gyara mata kan nata yadda zai kwanta kan kafad'ar sosae,almost 30mins ta d'auka tana yin baccin kafin ta fara motsa kanta lokacin yanata latsa wayarshi, kallonta yay ya kira sunanta don dama ko bata tashi ba yana niyyar tadata saboda Magrib ta gabato wurin ma duk an yaye sauran mutane kadan, "Zarah how are u feeling now?" ya tambaya bayan ta amsa kiranta da yayi, d'ago kanta tayi daga kan kafadarshi tana kallonshi shima ita yake kallo ya dage mata gira alamar uhhuym, "Na daina jin juwar, aman ma ya koma" ta fad'a da sanyayyar murya, jinjina kai yayi ya juya, "Ya Handsome..." yaji ta kirashi, juyawa yayi ya kalleta ba tare daya amsa ba, "Don Allah kayi hakuri naja baka yi abunka ba, wllh ni bansan na ta6a wurin ba" shiru bai ce komai ba yana dai ta kallonta acan kasan zuciyarshi kuma mamakin yadda tayi mashi Maganar yake, ba yau ta fara bashi hakuri ba sai dai ba anutse kaman yanzu ba, "Kayi hakuri" ta kara fad'a ganin baice komai ba, jinjina kanshi yayi "it's ok", " To zaka kara fitowa dani?" ta dan bud'a ido, Murmushin gefen baki yayi sai yanzu ya gano dalilin natsuwar, "Ki tashi muje magrib yayi" yayi maganar yana kokarin tashi, da sauri ta kai hannu ta kama hannunshi tace "bakai man hotunan ba" yar harara ya wurga mata, wato ta samu har Maganar pics take, fasa mik'ewar yayi dama wayar na ahannunshi, camera ya shiga ya juya zai mata hoton amman sai ta d'aga mashi hannu alamar ya tsaya,tace "To ai da fa nida abokai na zaka yi man yanzu kuma basu nan sun tafi sai kayi mana tare ni da kai" ba tare daya ce komae ba ya maida camerar ta gaba yayi mata alamar ta lek'o kawai sai ji yayi ta dafe kafadarshi, ta cikin camera d'in yayi mata wani kallo hakan yasa da sauri ta cire hannun tana d'an murmushin da ba har Zuciya take yinshi ba tana d'an kallonshi, alamar ta maida hannun yayi mata da kanshi, a sanyaye ta d'an dafa shi yayi masu hoton, ya d'auku sosae saidai ba wanda yayi dariya,sake shiga camerar yayi kafin ya d'auka yace "baki iya dariya bane" jin hakan yasa tayi dariya duk dimples dinta suka lotsa, yana shirin sake d'auka itama tace "to kaima baka iya dariya bane" jin Maganar tata yasashi yin d'an murmushin da bai shirya ba, tana ganin hakan da sauri tace "yauwa to kar ka daina yi" ta k'ara dafeshi sosae ta d'an kwantar da kanta tana k'ara yin irin dariyar da tayi daga haka ya dauka, lokacin da ya bud'e hoton har wata yar k'ara fatuu tayi don murna saboda hoton ya matukar yin kyau gashi ya d'auku tar tar dashi, ita tayi dariya shi kuma murmushi gaba daya dimples dinsu ya fito sosae, kitson fatun na gaba daya zubo gefe da gefe yasa tayi kyau sosae dama tunda ta gigice har ta suma ya warwaro daga daureshin da gwaggo tasa tayi, (Nima dae saida na leka hoton, Ma Sha Allah shine abunda nace kuma masu karatu duk wanda ya kalla yace Ma sha Allah kar a lashe masu kyau 🤪) "Ya Handsome bari in hau lilo ka dauke ni hoton" tana fad'in hakan ya mik'e yace"Next time" daga haka yace ta daukko ice cream da robar sauran ruwan da ta rage suka fita daga wurin. (Uhmmm Allah ya kyauta gaba to, ni dama jinina kan akaifa yake game da wannan zuwa Gym din, team Fatuu ina mik'o sakon jaje su Fatuu anga bala'e harda su suma😹) *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣4️⃣ ......Suna niyyar shiga mota Anah ta fito tana rataye da jakarta, nufo su tayi fuskarta a kwa6e ba walwala, agaban Haisam ta tsaya yana ganinta ya dakata don har ya bud'e kopar Mota, a sanyaye ta fara Magana, "Am so sorry Zakee about what happened, i know it's all my fault but it was a mistake" ta k'arasa idonta cike da hawaye, Sigh yayi a tausashe don yaga hankalinta ya tashi sosae yace " it's ok Anah, just let it be past " d'an guntun Murmushi tayi tace "thank u" kai ya d'aga mata kawai ta nufi inda Fatuu take tsaye ta dafa kafad'arta, " Zarah ina fata kina lafiya?" jinjina mata kai tayi alamar eh,, " akwae abunda ke maki ciwo yanzu?" girgiza mata kai tayi alamar babu, "Am sorry kinji, ki hakuri pls" ta fad'a a marairaice, Murmushi Fatuu tayi mata hadi da d'aga kai, maida idonta tayi kan Haisam tace mashi sai gobe, kai ya d'aga mata ta wuce wurin da ake aje mashina don mashin take hawa roba roba, har ta d'anyi nisa Fatuu ta kwala mata kira " Aunty Anah", juyowa tayi ta kalleta Fatun tace " zan k'ara dawowa ki koya man wani kala", zaro ido tayi sosae jin abunda fatun tace hakan yasata kyalkyacewa da dariya, itama Anar dariyar tayi ta girgiza kai daga haka ta juya ta tafi, shiga cikin motar tayi donshi tuni ya shige ya jata suka bar wurin, saida ya tsaya yayi mata siyayyar kayan kwalama yayi sallar Magrib a wani Masallaci sannan suka wuce, A bakin kopar gidansu ya tsaya da motar Fatuu ta fito shima ya fito ya zagayo bangaren da take, kopar baya ya bud'e ya fiddo ledojin siyayyar da yayi mata harda ta littattafan, Amadu na hango su ya fito ya nufo su, gaida haisam yayi ya amsa kafin yace ya tayata shiga dasu ya amsa da to,bayan ya tafi Fatuu ta kalleshi tana Murmushi tace "Nagode Sweetheart", wani kallo yayi mata ta kyalkyace da dariya, tana ganin zai juya tace "Don Allah Ya Handsome karka fad'i ma Hajiya abunda ya faru fa", d'an juyawa yayi ya kalleta sai kuma ya d'aga mata kai alamar to, har zai shiga cikin motar ya dakata ganin tayi tsaye bata shiga gida ba yace "ki shiga kiyi sallah sai ki kwanta, in kinyi bacci sosae u wll feel much better" kai ta d'aga ta kai hannu ta d'auki ledar data rage, ganin zaija motar yasa ta d'aga hannu tana mashi bye bye yay mata horn daga haka yaja motar, Washe gari Friday bayan ya ajesu a Makaranta ya bata wata envelope yace in ta kaima malamin nasu littattafan ta bashi, lokacin da ta kaima Auncle Bash sak'on Haisam d'in da mamaki ya bude, kudi ne ya gani a ciki yan dubu duba har saida gabanshi ya fad'i, kallon fatuu yayi ya tambayeta ta tabbatar shi akace taba tace mashi eh, sosae ya jinjina abun kafin yace in tasan lambar wayarshi ta bashi tace batasani ba, ba haka yaso ba eson gobe ba makaranta balle yayi mashi godiya, mik'a mashi littattafan da aka siyo Fatuu tayi ya amsa yace sai zuwa Monday za'a fara mata amfani dasu amman duk da haka saida ya bata wani English Grammar ya nuna mata inda yake so ta duba cikin weekend, kamar yadda Haisam yace mata tayi da abubuwan da ya siya mata da yawa hakan tayi, ta babba wasu wanda basu dashi harda ma wad'anda suna dasu ta k'ara masu hakan ba k'aramin mutunci da girma ya siya mata ba, Haulat ma ta d'ibar mata duk abubuwan dasu Calculator d'in da yace ta bata sosae tai farinciki tanata gode masu su duka har Fatuu nace mata ai itace silar komae da ta bata shawarar zuwa bashi hakuri, ita dai Haulat d'in d'an Murmushi kawai tayi tace dama Allah ya rubuta hakan. A cikin wani satin daya kama Haisam ya siya ma Tk sabon mashin d'in daya tura mashi sakon yana so kaman yadda sukai dashi duk da dak'yar yayi k'arfin hali ya tura mashi Message d'in don bukatar tashi yana ganin babba ce don mashin din yayi wurin dubu dari biyar, sosae Tk yay farinciki har ya kasa 6oyewa ba kamar da ya kasance shima zai biya ma kaninshi bukatarshi na mashin d'inshi da yaketa so ya bashi, sam Haisam bai bashi damar yi mashi wata doguwar godiya ba, bai 6oye ma Hajiya komae ba yay mata bayanin yadda akai Haisam ya siya mashi mashin din, batace komai ba sai murna ma da ta tayashi don tasan halin tk yana da kawaici kan abu irin hakan sam baida zari, tambayarshi ma tayi yadda zai aika ma kaninshi da nashin yace mata akwae wasu yan garinsu dake zuwa cin kasuwa nan to da babbar mota mai bud'addan baya suke zuwa su zai ba su kai mashi tace hakan yayi. A cikin satin kuma aka sako su Gaye bayan anyi tsatstsauran rubutun cewa za'a saka masu idanu in aka k'ara kama kowannansu ya aikata ko k'ara yunkurin aikata laifi makamancin wannan to za'a tado wannan ahad'a ayi masa hukunci, daka kallesu zaka fahimci sunji jiki ba laifi duk sun k'ara yin bak'i sun jeme ga wata uwar rama (ba tuwon gyatuma), gaye har wasu kuraje suka fito mashi banda uban cizon sauron dake kan fatarshi, A daren ranar da aka sakosu mahaifinsa Malam tanimu ya tasa shi gaba suka je gidan Hajiya don yi mata godiya, sosae ya shiga yi mata godiya hajiya tace ba wani abu ai d'a na kowa ne, yace in ba damuwa yana son ganin Haisam, Hajiyar na niyyar kiransa awaya sai gashi ya shigo cikin parlon don lokacin ba'a dad'e da gama sallar isha ba, sosae malam tanimu yayi mashi godiya shima had'i da sama rayuwarshi da iyayenshi Albarka, yayi masa Addu'oi sosae kafin yace ma Gaye dake ta faman sussunar da kai tunda Haisam d'in ya shigo yayi mashi godiya, kallonshi ya d'anyi cike da jin kunya yay mashi godiya, sai lokacin ya bud'e baki yay Magana dama shi baison ayi tayi mashi godiya shiyasa koda Malam tanimu nayi saidae ya jinjina mashi kai in kuma Addu'a ce can kasan makoshi yake amsawa da Amin, yar nasiha yayi ma gaye ya nuna mashi yana da damar da zai gyara rayuwarshi a yanzu tun kafin lokaci ya k'ure mashi don a rayuwa komae yana da limit idan lokaci ya k'ure mashi koda ya gyara hakan bazai amfaneshi da komae ba, bayan ya gama ya kalli Mahaifinshi yace idan ya gyara halinshi ya natsu zai d'auki nauyin karatunshi in yana son yi, in kuma kasuwanci yake so to zai bashi isasshen jari, sosae Malam tanimu yaji dadin wannan Maganar don harda yar kwalla yayi ya kalli gaye yace mashi yaji dai da kunnanshi wannan dama ce agare shi, bayan ya gama yi mashi magana Hajiya ta tambayeshi yanzu Jos d'in zai kaishi yace ehh, duk da Ashirun yace mashi wai ya bari amman yasan in ya kyaleshi ruwa zai koma saboda gurbatattun abokai don haka gobe in Allah ya kaimu zasu tafi zuwa wani lokaci in yaga ya gyara halin da gaske sai ya maido shi nan, Hajiya tace hakan yayi, da zasu tafi ta basu kud'i masu yawa tace su sha ruwa a hanya Allah ya kiyaye bayan itama tayi ma gayen nasiha, Bawan Allah harda yar kwallarshi yace in sha Allahu zai yi amfani da nasihar da suka mashi zai dage don ganin ya gyara rayuwarshi daga haka suka yi masu sallama suka tafi, (Allah sarki Gaye inayi maka fatan Alkhairi, Allah ya baka ikon gyara rayuwarka ya shiryi duk masu irin halinka ya shirya Al'ummar Annabi(SAw) gaba d'aya Amin, nasan masu karatu ma nayi maka fatan Alkhairi don ka taka muhimmiyar rawa a labarinnan muna godiya) Kwanaki sun shud'e sun bada satittika haka suma sun shud'e sun bada wasu yan watanni har gashi yau Asabar saura sati biyu cub a fara azumin watan Ramadan, da yammacin ranar Misalin k'arfe shidda saura Tk ya parker hilux ta wurin aikinsu Hajiya a kopar gidansu Fatuu, fitowa yayi ya zagayo d'ayan 6arin ya tsaya yana yin yar mik'a, kallon Amadu dake cikin shago yana ta faman binshi da ido tunda ya tsaya yay yace "ka fito ka d'auki Amaryarka" cikin rashin fahimtar zancenshi Amadun yace "Amarya kuma,wace amarya" da alamun mamaki akan fuskarshi yay Maganar, Tk yace ya fito mana ya gani, lokacin daya fito yaje bayan motar turuss yay yana kallon katon kwalin da ke nuni da freezer ce acikinshi, cikin rashin fahimta ya kalli Tk daketa murmushi tun kafin yace wani abu ya rigashi cewa tashi ce Yaya Haisam yace ya kawo mashi, zaro ido Amadu yayi a rude ya maimaita tashi ce! Tk ya bashi amsa da eh kafin yace yazo su sauke, da taimakon wasu mutane aka sauke freezer d'in suka nufi cikin gida da ita, Gwaggo na zaune asaman tabarma a inda ta saba zama in ba wuta taji anata kiciniyar shigo da abu, sakin baki tayi tanata kallon ikon Allah har suka samu shigowa da ita suka nufo cikin gidan a gaban gwaggon suka ajeta, tun kafin tayi magana Amadu dake ta faman washe baki yayi mata bayani, abun bana zama ne, mik'ewa tayi ba shiri tana kallon kwalin freezer d'in cike da mamaki, maida idonta tayi kan Tk dake tsaye gefe tace ya tabbatar nan akace ya kawo, tambayar tata har saida ta bashi dariya kafin yace mata eh, ita mamakinta yadda yasan da Maganar zata siya freezer d'in har ya aiko, wanda yau bai wuce saura yan kwanaki bama ta siyo ma Amadun ba donma kud'in sun samu gi6i ba da tuni ta siya mashi, suna cikin tsayuwar Fatuu ta rafko sallama ta shigo jikinta sanye da uniform d'in islamiyya, baki bud'e tabi kwalin itama da kallo cike da mamaki ta furta "kai,wai Gwaggo harkin siyo ma kawu Amadu freezer d'in?" Wannan Maganar yasa gwaggon tunanin ko ita tayi ma Haisam zancen hakan yasa ta tambayeta ko tayi mashi zancen siyan freezer d'in, da farko cewa tayi ita batayi mashi Maganar ba gwaggon tace ta dai tuna, don ita abun yasata al'ajabi indae ba wani ya gaya mashi ba taya zai sani tunda gashi ance Amadu aka siya mawa, can Fatun tace ta tuna lokacin da Uncle Bash yayi mashi maganar littattafan nan daya ta6a siya mata, to lokacin ne ta gaya mashi gwaggo ma tace zata siya littattafan amman bata da kud'i sai ta kwashi kudin adashen da take wanda zata saima kawu freezer, jin hakan yasa gwaggo sauke nannauyar ajiyar zuciya tama kasa cewa komai don Al'amarin Haisam akwae d'aure kai, ko acikin mutane masu yin Alkhairi shi na dabanne, tambayar Tk tayi ko Haisam d'in na gida yace mata a'a yana can wurin exercise shima kiranshi yay awaya yace ya d'aukko mota ya iskeshi a wurin, jinjina kai gwaggo tayi kawae tk d'in yayi mata sallama zai tafi ta shiga yi mashi godiya harda cewa don Allah ya tsaya abashi tukuici, wata yar iskar dariya yayi yace "haba dae Kakus" dayake shima d'an barkwanci ne, bayan ya tafi tsaye sukai su duka farinciki duk ya cikasu sai fara'a suke Fatuu kam harda rawa tayi, Da daddare bayan sallar isha suka d'unguma zuwa yin godiya lokacin Haisam na a part d'insa hakan yasa suka je can, karo na farko kenan Gwaggo da Amadu suka shiga sashen nashi, ba k'aramin burgesu wurin yayi ba suna ta yabawa acikin ransu, lokacin da suka shiga falon bai ciki yana can cikin bedroom d'inshi saida kawu Amadu ya kirashi a waya ya sanar dashi zuwansu sannan ya fito, fuskarshi a sake ya gaida gwaggo shikuma Amadu ya gaida shi ya amsa, wuri ya nuna masu yace su zauna kowa ya zauna saman armchair d'aya, bayan sun zaunan gwaggo ta fara mashi godiya tana cewa anga abun arziki angode Allah ya saka da mafificin Alkhairi ya albarkaci rayuwa yasa agama da duniya lafiya, sosae take mashi godiya had'i da Addu'a har saida sautin muryarta ya d'an karye kaman zatayi kuka, shidae abu d'aya yace shine ba wani abu, sai kuma Addu'ar daya rink'a amsawa jefi jefi, tana tsagaitawa kawu Amadu ma ya shiga yin godiya, kallon Fatuu yay data zauna akan carpet gefenshi yay mata alama da kanshi nan take ta gane abunda yake nufi don yanzu da yayi mata alama da kai ko da ido take ganewa, mik'ewa tayi ta kalleshi k'asa k'asa tace "Lemu ko ruwa?" wani kallo yayi mata kafin ya k'ara mata alama da kai ta juya ta nufi Fridge d'in, lemu da ruwa ta d'aukko ta kawo ma gwaggo kafin ta juya ta kalleshi ya lumshe idanunshi hakan yasa ta juya ta k'ara d'aukko wasu ta kawo ma kawo Amadu, "Ki kawo cups ko" Haisam ya ya fad'a, tana juyawa ya mik'e ya fara kokarin matsar masu da c-table don a hannun kujerun ta d'aura ma kowa, gwaggo na ganin hakan ta mik'e tace ba sai ya wahala ba tafiya zasu yi ma hakan yasashi dakatawa, Fatuu na ganin sun miken ta dawo ba tare da ta dauko kofunan ba, ganin duk basu d'auki lemun da ruwan ba yasa tace" Gwaggo kin bar lemunki da ruwa fa" banza tayi mata ta fice Haisam yace ta d'aukar masu, tace "to nima in d'aukko" yana niyyar fita yace "wani ya hanaki ne" daga haka yabi bayansu, daukowa tayi itama ta zubasu acikin hijabin jikinta daga haka itama tabi bayansu niki niki da abu rungume, bayan sun fito gwaggo tace mashi don Allah ya koma don part d'in hajiya zasu je, sallama yay masu suka shiga k'ara yi mashi godiya ya juya kawae Fatuu na cewa "saida safe Ya Handsome" ya d'aga mata hannu daga haka ya shige, itama dai hajiyar godiya sukai mata tace ita batama san anyi ba ai, sosae gwaggo ta shiga mamakin hali irin na haisam wannan shine kyauta da dama ba tare da hagu ta sani ba, masu yi don Allah kenan, yar hira suka ta6a kafin suka yi sallama da ita suka koma gida, bayan sun koma ne suka shiga kiciniyar bud'e sabuwar freezer din don su had'a ta, a cikin d'an ginin d'akin da ba'a k'arasa ba dake gefen na gwaggo suka yanke shawarar ajeta don ta rinka samun isashshiyar iska amman sai anyi mata yar baranda asama saboda rana wannan kuma duk sai gobe in Allah ya kaimu suka yanke shawarar za'ai hakan. Ana saura kwana ukku a fara Azumi ranar laraba kwatsam sai ga Mahaifin Fatuu yayi masu zuwan bazata, wannan ne zuwanshi na biyu tun bayan da ta dawo nan ba kuma don baison zuwa ba sai don kunya da kawaici irin na Fulani, da farko lokacin data dawo ya fara turo masu kudi akai akai gwaggo ta dakatar dashi tace bata d'auki Fatuu don yaci gaba da kula da ita ba, d'aukar d'awainiyarta bazai gagareta ba in sha Allah, sosae yaji dad'i amman duk da hakan lokaci bayan lokaci yana masu aike ta hanyar yan garinsu dake zuwa manyan kasuwannin yankin Katsina tunda shi yanzu ya daina zuwa sai dae k'annanshi da y'ay'an yan'uwanshi, haka kuma yana yawan yin waya da fatun don ko bai kiraba ita tasa gwaggo ko kawu Amadu wani ya kira mata shi, Mahaifi mai dadi (Allah ka jikan namu da suka rasu, Amin), Jama'a kuzo kuga Murna agun Fatuu duk tabi ta kankameshi shidae sai dariya yake, fari dashi mai kyau har yafi Fatuu fari saidai daka kalli fuskarshi zaka ga kamanninshi da Fatun yayi shigar dogayen kayan yadi mai kyau kanshi sanye da hula tsaf tsaf dashi kaman ba daga k'auye yake ba, amman daka ganshi kaga cikakken bafullatani, A d'akin Amadu aka sauke shi fatuu sai faman tambayoyi take mashi tana tambayar yan'uwanta yana bata amsa da muryarshi mai sanyi daga ji baida hayaniya kuma ya iya hausa sosae don Fatun da hausa take mashi Magana koda yayi mata da fullanci amman sam basuyi hausa ba da gwaggo da ta shigo don su k'ara gaisawa, sam Fatuu tak'i barinshi ya huta yaci abinci sosae, tunda ta kawo mashi ta tasashi gaba tana ta bashi labarin Ya Handsome da duk Alkhairan da yake masu kuma har labarin yadda akai suka saba dashi saida ta bashi wanda ko gwaggo batasani ba har yake cewa ashe har yanzu baki daina rashin ji ba inna wuro (sunan da yake kiranta dashi kenan wato uwar masu gida don sunan Mahaifiyarshi ne aka sanya mata), rantsuwa ta hau yi mashi kan ta daina rashin ji kuma ma ya tambayi gwaggo, atare suka ci abincin gwanin burgewa har abaki take bashi, bayan sun gama ya d'an kishingida don ya huta ita kuma tace mashi zataje ta dawo, kopar gida ta nufa wurin kawu Amadu don tunda yaje suka gaisa ya dawo shagon, rok'onshi tayi wai ya kira mata Ya Handsome yace bai kira, Magiya ta fara yi mashi ta hanashi sakat har saida ya kira mata shi, cikin murna ko gaidashi bata yi ba ta sanar dashi Babanta yazo tana ta faman dariya, cemata yay yana tayata murna in ya dawo zaizo su gaisa tace mashi to, Bayan sallar la'asar yazo gidan yana sanye cikin jeans da t-shirt gaba dayansu navy blue ne, hannunshi sanye da agogo bak'a hakama takalmanshi bakake ne sai sakin kayataccen kamshi yake, Amadu ya shigar dashi wurin Baban Fatun lokacin tana like dashi sai faman zuba take mashi ko islamiyya tace bata zuwa, bayan Amadu ya shigo ya sanar mashi cewa zasu gaisa da bako ya juya waje yace ma Haisam ya shigo, fatuu na jin muryarshi yayi yar sallama ta wani zabura ta tashi zaune, ganin shine da gaske yasa ta washe baki tace ma babanta to ga Ya Handsome d'in da take bashi labari nan, ganin ba abun zama yasa Amadu cewa bari ya d'aukko mashi kujera acikin gida haisam yace ya barshi, d'an duk'awa yayi suka gaisa cike da mutuntawa anan yake mashi godiya yace inna wuro ta fad'i mashi abun arzikin da yake masu, to shi d'inma dai cemashi yay ba wani abu, daga haka shiru ta biyo baya don gaba d'ayansu ba gwanayen Magana bane kai kace bashi ne Mahaifin Fatuu ba ta wannan fannin, muryarta kawai ake ji sai zuba take tana zuba uwar shagwa6a da shirme kala kala kanta na akan kafafunshi, " Baffa na gaya maka Ya Handsome dinnan yana da motoci, in kana so sai ya kaika kaga garin nan" Fatuu ta fad'a,shiru baice mata komai ba hakan yasa ta d'aga idanunta tana kallonshi tace "ko baka son ganin garinne?", fuskarshi da fara'a yana kallonta cikin harshen fulatanci yace mata ai ba dad'ewa zaiyi ba gobe da safe zai tafi, tana jin hakan ta fara bori tana tittirza k'afa akan katifar cike da shagwa6a tace " kai da ka dad'e baka zo ba kuma sai kace wai gobe zaka tafi, ni dai ban yarda ba Allah kwan", Still Haisam yay yana kallonsu fuskarshi a sake shi kuma mahaifin nata sai murmushi yake da gani dai yana da fara'a sosae, ganin yadda take ta zuba shagwa6a ne yasashi cemata yaso zuwa tuni Ardo ne yay jinya shiyasa bai zo ba kuma har yanzu bai idasa warwarewa ba shiyasa bazai zauna ba don shi ke kula da harkokinshi da yawa acan, da bud'ar bakinta sai cewa tayi " Allah yasa ma ciwon mutuwa ne yakeyi kowa ya huta da masifa " tana yin Maganar suka had'a ido da haisam ya d'an harareta shi kuma baban nata kama kunnanta guda yay ya d'an ja ta saki yar k'ara tana fad'in " wad' muyal baffa, ba ya tsufa ba", murmushi Haisam ya danyi kafin ya mik'e yay mashi sallama ganin yana kokarin tashi shima yace yay zaman shi da mota yake zai wuce ne, mik'ewa Fatuu tayi tana sanye da riga da skirt na shadda kanta ba kallabi tace ma babanta bari ita ta raka shi waje yanzu zata dawo, Haisam da har ya nufi mota ya juyo sakamakon kiran sunanshi da tayi, tsayawa yayi ta k'araso tana ta dariya ta kasa ce mashi komae, " U'r Happy Dad yazo ko" jinjina mashi kai tayi sai kuma ta kwa6e fuska tace " bacin ma wai gobe da safe zai tafi", " yana da uzuri ne" ya fad'a yana kokarin juyawa, " gida zaka koma?" ta tambayeshi, kai ya girgiza alamar a'a, " To ina zaka?" "Gym" ya bata amsa yana nufar mota, " ko in zo in raka ka?" sai lokacin ya tsaya yay mata wani kallo ta kyalkyace da dariya, " ina Aunty Anah?" ta tambayeshi bayan ta daina dariyar, " tana tambayarki" ya bata amsa a takaice, " wayyo, don Allah zaka k'ara kaini in ganta, wllh tana da kirki", girgiza mata kai yay alamar a'a aikuwa ta fara d'an bubbuga kafa tana jujjuya kai, kai kawai ya d'an girgiza ya kai hannu ya bud'e motar ya shiga kafarshi guda awaje, ganin tak'i daina abunda take yasa yay mata alamar tazo da hannunshi, sealed Popcorn da tuwon madara ya mik'o mata ta amsa sai kuma cewa tayi "Ya Handsome na gane wayonka, ina yi maka rigima shine kaban wad'annan abubuwan don inyi shiru ka maida ni karamar yarinya ko", d'an cije peach lip dinsa na kasa yay da alama ta kashe shi da mamaki, murya can kasa ya furta "kinsan ma rigima ne kike man ko Zarah?" jin haka yasa ta 6oye a gefen motar tana dariya, d'an leko da kanshi yay ya kalleta aikuwa da sauri ta kife fuskar, girgiza kai yay yace "ki koma kin bar dad shi kadae" yana fad'in hakan ya maida kafarshi ciki ta lek'a kanta tana kallonshi yay mata alamar taje da hannu, har saida ya tashi motar ya tafi tana ta d'aga mashi hannu, lokacin data koma cikin d'akin kawu Amadu Babanta har yayi bacci, bawan Allah tun karfe hudu na asuba ya taho ya sauka a Kano kafin ya hau motar Katsina, ya kwaso gajiya don akwae nisa tsakanin Katsina da Yola kusan fin awa goma yana hanya yazo kuma ta hanashi hutawa, Allah yaso yan hankali sunzo mata ta kyaleshi ta nufi cikin gida, tare suka ci abunda haisam ya bata da gwaggo amman fa sai da ta rage ma Baffanta, da daddare aka aiketa gidan hajiya ta kai mata tsaraba ananne tasan baban nata yazo tace ta tayata murna in Allah ya kaimu sa gaisa dashi, bayan ta dawo rigima tasa wai awurinshi zata kwana dole saidai Amadu ya tafi dakinta ya kwana, Washe gari da safe Haisam ya parker akopar gidansu lokacin zai tafi wurin aiki, kiran Amadu yayi a waya yace ya d'an fito waje, bayan ya fito ya gaidashi cike da girmamawa, amsawa yay yace ya bud'e back door akwae sako ya kaima bako, wata katuwar leda ce mai hannu ya fiddo saida yay mashi godiya kana ya shige gida shi kuma ya tafi, gwaggo ya kaima sak'on yace inji Yaya haisam yace aba Baffan Fatuu, jinjina kai kawae tayi tana Murmushi ta jawo ledan ta bud'e, kaya ne ciki sosae, shaddoji dinkakku guda biyu daya mai babbar riga daya kuma dogayen riga da wando ne, sai guda daya da ba'a dinka ba sai kuma manyan yadi kala biyu, takalma da huluna kala bibbiyu sai agogo ma guda biyu sai kwalin turare guda ukku, duk yadda gwaggo taso kin yin mamaki saida tayi shi haka Amadu ma sai faman jinjina kai yake don Haisam ya iya yin kyautar ban Al'ajabi, lokacin da aka kai mashi kayan shima saida ya d'an rude ba kamar dayaga duka fa jiya ya sanshi gwaggo tace mashi haka halinshi yake, koda ya buk'aci zuwa yi mashi godiya Amadu ya sanar dashi ya tafi wurin aiki saidai ya kirashi awaya, koda ya kira bai d'aga ba almost 3 times gwaggo tace ya kyaleshi kawai in ya gama shiryawa ya kaishi wurin hajiya su gaisa sai yay mata godiyar, Lokacin da suka je gidan cike da mutuntawa hajiya ta kar6e shi tana ta fara'a don bata ta6a ganinshi ba sai yau sai kuma a wani hoto da Fatun ta ta6a kawo mata can da dad'ewa shida mahaifiyarta, har Saude da Tk saida Hajiya ta kirawo tace suzo su gaisa da Baban Fatuu, suma cikin girmamawa suka gaidashi yana ta dae fara'a Fatuu na lik'e dashi har hajiya na tsokanarta tana cewa to ko zata bishi ne, ta mak'e kafad'a tace in taje aure za'ai mata gaba daya suka sa dariya,sosae yayi mata godiya lokacin da zai bar gidan, kud'i hajiya ta ba Amadu abashi acikin envelope ba tare da saninshi ba, har Amadun zai yi mata gaddama yak'i amsa tace yaushe ta fara yin wasa irin wannan dashi dole ya kar6a, bayan sun koma yay sallama da gwaggo alokacin Amadu ya bashi kudin da hajiya ta bashi yace suyi amfani dasu amman gwaggo taki amsa tace shi aka ba adole ya amsa don bai iya yin jayayya da ita, Fatuu da Amadu ne zasu raka shi tasha don anyi hutun Azumi shiyasa basuje makaranta ba, har kopar gida gwaggo ta rako su tana yi mashi Allah ya kiyaye Amadu na ruke da jakar da gwaggo ta zuba mashi kayan da aka bashi don yar jakarshi da yazo da ita bazata dauki ko kwatan kayan ba don yar k'arama ce iya kayan da zai canja ya sako a ciki hakan yasa ta bashi babba mai zip wadda ta d'auke duka kayan harda jakar da yazo da ita, akan hanyarsu ta zuwa bakin hanya don hawa keke napep ne ta tuna da Haulat, rokon Kawu Amadu tayi su bi ta lungun gidansu don Haulat d'in ta gaisa da babanta, bai mata musu ba suka bi ta lungun lokacin da suka karasa, da zata shiga kiran haulat d'in yace mata kar ta 6ata masu lokaci tace yanzu zata fito, bada jimawa ba kuwa sai gata ta fito da haulat d'in tana sanye da hijab har k'asa ta duka ta gaidashi tana ta murmushi ya amsa mata shima yana murmushin, ce masu tayi bari taje ta tambayo innarta sai su rakashi tare, lokacin da ta dawo wajen harda innar tasu itama ta lek'o don su gaisa, atare suka durkusa suna gaida juna kafin tayi mashi Allah ya kiyaye hanya, k'arasawa sukai bakin hanya suka hau Napep don zuwa tasha, lokacin da suka sauka Haulat taba kawu Amadu dubu dayar da innarsu tace abashi har yana cewa ai da bata bada ba, Motar Kano ya hau lokacin bai fi saura mutum biyu ba ta cika, Fatuu tace bazata tafi ba sai sun tafi yanata cewa su tafi tana mak'e mashi kafada saidae yay Murmushi kawai don ya fahimci har yanzu da sauran rigimarta amman acan k'asan zuciyarshi ba k'aramin farinciki yake ji ba da ganin yadda ta koma gaba d'aya ta canja daka kalleta zaka san tana cikin jin dad'i, ba'a dau wani dogon lokaci ba mutum biyun suka samu motarsu ta tashi suna ta d'aga mashi hannu suna cewa Allah ya tsare Fatuu na fad'in wayyo babana ya tafi harda yin baya kaman zata fadi haulat ta tareta tana mata dariya, (To Baban Fatuu, muma muna yi maka Addu'ar Allah ya kiyaye hanya,Allah yasa a sauka lpy,Amin) Ana gobe za'a fara Azumi Tk ya kai uban kayan abinci gidansu Fatuu, dama duk azumi Senator Ali na aiko da kayan abinci masu yawan gaske a rarraba gida gida sai dae wannan karon kayan da aka kai gidansu Fatun sunfi na baya yawa sosae sakamakon Haisam da ya kara masu, bama su kadae ba harda sauran mutane saidae nasu yafi yawa don babu abunda babu wanda mutum zaiyi lafiyayyan buda baki da sahur, bayan d'anye da ake rarrabawa anayin lafiyayyan dafaffen abinci na sadaka agidan hajiyar, musamman ma'aikata masu yin girkin duk azumi ke akwae, a can bayan part d'in hajiyar ake kafa rumfuna ana yin aikin, bayan abinci ana yin kunu da kosai da kuma abunsha kamansu zo6o kunun aya wani lokacin harda fruit acikin wanda ake kaiwa masallacin gidan alokacin bud'a baki, **** **** **** An fara azumi lafiya gashi yau in an kai na bakwae kenan wato sati guda da farawa,Misalin karfe sha daya na safiyar ranar wadda take Asabar Fatuu ta shigo gidan hajiya ta Gate don tunda aka fara azumi ta rage zuwa part d'in Haisam don da safe yana wurin aiki ko tazo bai nan dayake ita an basu hutu in ya dawo da rana kuma mafi yawancin lokutta ko taje bacci yake da yamma kuma in aka gama sallar la'asar tsayawa yake wurin tafsir hakan yasa basu cika haduwa ba sai a part din Hajiya, tana shigowa ta hango shi acikin parking space ya bude boot d'in mota ya d'an dukar da kanshi da alama wani abu yake yi, wurinshi ta nufa ta tsaya daga gefenshi ganin alamar mutum yasashi d'agowa ya kalleta, gaidashi tayi tana d'an d'age baki tana yamutsa fuska, "Miya faru?" ya tambayeta,kaman zatayi kuka tace "ba azumin ne ke bani wahala ba" jinjina kai yayi yace "tunda wuri haka" tana ta faman yamutsa fuska ta d'aga mashi kai, dama kullum in sun hadu haka take complain d'in Azumin wuya, "Ki shiga ciki sai ki kwanta ki huta", amsa mashi tayi da to ta nufi part d'in Hajiya, lokacin da ta shiga cikin parlon ba kowa amman an gyara shi tsaf sai dan sanyayyan kamshi ba mai karfi ba ke tashi don tunda aka fara azumi aka rage sa turare da yawa, kitchen ta nufa wurin Saude don tasan war haka Hajiya bacci take, tana shiga ta isketa tana yin wanke wanke, "Aunty Saude ina kwana", da fara'a ta juyo ta kalleta "lafiya lou Fateema har an dawo daga islamiyyar" kai ta d'aga mata alamar eh, "Ina fata dai yau kina yin azumin?" tana tura baki tace "banyi,ni wllh wuya yake bani shiyasa nike karyawa" jinjina kai Saude tayi tace "ki rink'a daurewa kina yi ta hakane zaki saba" d'aga mata kai tayi alamar toh tana dai atsaye can ta matsa tace bari ta tayata, d'auraya ta fara yi mata suna cikin yi sauden tace "Don Allah jeki part d'in Yayanki ki d'aukko man basket d'in kayan sahur da aka kai mashi da asuba na manta ba'a d'aukko su ba", amsa mata tayi da to ta juya ta fita, lokacin data fita harabar gidan bata hango shi a cikin parking space d'in ba hakan yasa tayi tunanin ya koma part din nashi, da sallama ta shiga lokacin data isa saidai bai amsa mata ba don bai cikin parlon, k'ara yin sallamar tayi wai ko zai jiyo ta don kilan yana cikin Bedroom ne amman bata ji ya amsa ba hakan yasa ta nufi center table don d'aukar basket d'in da ta gani a samanshi cikinshi dauke da kayan tea da warmer, maimakon ta d'auka din sai takai hannu ta bud'e warmer dake ciki nan take ta zare ido ganin soyayyan dankalin turawa mai d'an yawa aciki, shiru tayi tana kallonshi ta fara hadiye miyau,d'an d'agowa tayi ta kalli kopar Bedroom d'in nashi jin bata ji wani motsi ba yasa ta kai hannu ta d'ebo dankalin mai yawa ta tura abaki tana taunawa idonta na a corridor d'in Bedroom din, tun tana ci atsaye har ta duk'a tayi ruku'u tana yi tana kallon corridorn don kar ya fito ya ganta, "Can't u sit properly, haka zai iya shake ki ai" taji daga bayanta ya fad'a aikuwa a firgice ta juya ta kalleshi baki cike da dankali, ashe bai cikin d'akin kuma da ta shigo bata kulle kopar falon ba hakan yasa bata ji shigowarshi ba, can 6arin L-shape ya nufa ya zauna ya d'aura abunda ya ruko ahannunshi saman c-table wanda da gani wani abun computer ne, ci gaba da duba abun yayi alamar gyara yake yi ajikinshi, shin wai ina Fatuu???? ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIGAR KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCE💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari Muna kawo kalolin kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni ima da jimawa yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso tabini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣5️⃣ .......tsaye tayi tanata binshi da ido gashi ta kasa k'arasa cinye dankalin bakinta ta d'an d'age hannun da take ci dashi kamar mai shanyayyan hannu, saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya d'ago ya kalleta, ganin yadda ta k'ame yasashi d'an ta6e baki yay mata alamar ta zauna da kanshi, zaunawa tayi idonta akanshi shima kallonta yake ya dan 6ata fuska, "Har yanzu baki daina k'arya ba ko?" da sauri ta girgiza mashi kai kaman zatayi kuka, "Miya hana ki yin fasting ko karya shi kikai?", sai lokacin ta idasa cinye dankalin bakinta ta fara Magana murya kaman zatayi kuka, "a'a dama bana yi, wllh dana d'auka in rana tayi sai inji kirjina ya fara ciwo numfashina har d'aukewa yake kaman zan mutu", " guda nawa kikai?" zaro ido tayi jin tambayar da yayi mata gashi ya kafeta da ido tasan da ta yi k'arya zai ganeta, " Banyi ko d'aya ba" buda ido yayi alamar mamaki ya d'an jinjina kai kafin yace "ita grandma d'in naki ta kyaleki baki ko daya ba?" "A'a tana tada ni inyi sahur to in rana tayi bata nan sai in karya, in kuma tana nan naga tana yin bacci sai inje kicin in karyashi ko kuma in shige toilet in ci wani abu", k'ara bud'a idon yayi ya d'an yamutsa fuska jin abunda tace,maida kanshi yay yaci gaba da abunda yake yi ganin hakan yasa tace "in ci gaba da ci?" da hannu ya bata amsa, ta kai hannu ta fiddo warmer d'in dankalin ta d'aurata asaman cinya taci gaba da ci har wani jujjuya kai take tana lilo da kafafunta, can ya d'ago ya kalleta tai saurin kame kanta, "A islamic school naku ba'a fad'i maku hukuncin wanda ya karya azumi da gangan ba?" cakk ta tsaya jin tambayar da yayi mata tace "an fad'i mana,ance Mutum sai yayi kaffara duk azumi guda sai ya rama sittin harda guda d'ayan da ya karya", jinjina kai yay a kausashe yace "shine kuma kike karyawa!" " To ai ance sai wanda ya balaga ne ya zamar ma dole nikuma fa ban balaga d'in ba tunda ance sai mutum ya fara wai jinin haila shine ya balaga nikuma har yanzu ban fara ba, da bamma gane abunda ake nufi ba dashi saida na tambayi Haulatu tayi man bayani dayake ita ta fara ko wanccan azumin duka tayi, tasha wuya kuma saida ta rama wanda tasha, nan gidanma take biyoni ta lalla6o shan Ac, ni dae Allah yaso ni har yanzu bai zamar man dolen ba shiyasa ma nike karya shi" ta tura dankali abaki tana yar dariya lokacin da takai k'arshen Maganar, still yay yanata binta da ido, ba yau ta fara kwa6o Magana ba amman yayi Matuk'ar mamakin yadda ta gaya mashi wannan batare da taji komae ba duk da tasan mi abun ke nufi, d'agowa tayi suka had'a ido ganin kallon da yake mata yasa tayi tunanin ko bai yarda da Maganarta bane hakan yasata cewa "Wllh da gaske nike fa ban fara ba, ba kasan shekaruna ba, ko kwanaki wasu Mutane sunzo Makarantarmu suka raba mana panties da pad da turare harda sabulu mai kamshi acikin yar jaka, suka koya mana yadda wai zamu tsaftace kanmu in muna yi to nidai pad din sai dai naba Haulatu ita,nasan kai baka san miye pad d'inba tunda kai Namiji ne, ita wai ake sawa a pant sai ta tar......", "Enough Zarah!!!" ya daka mata tsawa har saida ta firgita ta k'ame tana kallonshi idanu waje Jikinta na yar kerma......., fuska a matukar d'aure yace " ke baki san ba komai ne Mutum ke sakin baki yana fada bane,did i ask u all dat!", a tsorace tace "naga kai yayana ne shiyasa na fad'i maka amman ba wanda na fad'i ma wannan", ganin ta d'an tsorata yasashi d'an sakin fuska yace "nima ba komae ne zaki fad'i man ba cos wani abun yakamata ki barshi as a secret and kowa da kike gani yana da sirrinshi wanda bai fad'a ma Mutane ko ni ina fad'i maki abu game da kai na ne?" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, "To ki daina fad'i man abu irin wannan, ko matsala gareki data shafi kanki ki fad'a ma grandma d'inki, kingane mi nike nufi?" ya d'age mata gira,kai ta d'aga tace "eh kaman jikina kake nufi ai ko" kai ya d'aga mata daga haka ya maida kanshi kan abun da yake yi, "In sha tea d'in" kai ya k'ara d'aga mata alamar eh, mik'ewa tayi ta aje warmer dankalin don ta cinyeshi ta fara kokarin had'a tea, D'an kallonta yay yace "zaki had'a ba tare da kin wanke cup ba" jin hakan yasa ta d'auki cup d'in ta nufi washbasin dake can gefen fridge d'inshi don ta wanko shi, d'agowa yay ya bi bayanta da kallo kafin ya d'an girgiza kai, sam baiyi mamakin jin bata fara menstruation ba duk da baiyi zaton hakan ba amman yasan ba wata babba bace kawae dai tana da d'an jiki ne da zai iya sawa ai tunanin takai matakin yi, lokaci guda ya fad'ad'a Murmushinshi don hakan ya tuna mashi da wani abu wanda shi kadae yasan ko minene ya maida kanshi kan abunda yake yi, tea mai kauri ta had'a ta zauna kan kujera tana sha idonta akan tv tana kallon Mbc Bollywood, tallar man gyaran gashi aka fara wata mata nata juya gashinta da ya zuba a gadon bayanta, "Ina son nima gashina ya koma haka wllh amman ni banzan nawan nad'ewa yake" ta fad'a tana kur6ar tea, can aka nuno wata kuma mai gashi brown tace "lah, ga mai irin gashin wannan yar'uwan taka ta India" sai lokacin ya d'an d'ago ya kalli tv d'in kafin ya maida kan k'asa, cigaba tayi da santin gashin tana fad'in Allah yasa nata ma ya koma haka liya liya yabar nad'ewa, " baki mai abunda ya kamata bane" taji ya fad'a ba tare da ya kalleta ba, " To ai man farming ake sawa, waccan sallar da aka saka ma haulatu nace nima inaso sai gwaggo tace baza'a saman ba gashin wai lalacewa zaiyi" jinjina kai yay sai kuma yace "ba dole sai ansa relaxer cream ba ai", tace " to mi za'a sa yayi liya liya ya mik'e?" d'agowa yay hannunsa guda yana d'an shafa beard d'insa calmly yace "in kina so sai a kai ki" da sauri tace "inda ake maida shi hakan?" kai ya d'aga mata alamar eh, " To kai zaka kaini?" shiru ya danyi kaman bazai bata amsa ba sai kuma ya d'an d'aga mata kai don wani lokacin gajiya yake da tambayarta bata iya dunk'ule tambayoyinta tayi at once, " To yaushe zamu ko sai Salla ta kusa?" ta sake tambaya cike da zumud'i, " i wll talk to u" haka kawae yace tare da maida bayansa ya jingina sosae da kujerar ita kuma taci gaba da yin kallo tana shan tea d'in fuskarta d'auke da murnar za'a kaita inda za'a maida mata kai liya liya har wani d'an jujjuya kai take, duk wannan abun idanun Haisam na akanta kaman yana nazarin wani abun, " Zaraah" taji ya kirata, amsa mashi tayi "uhhuym" tare da juyowa, on a serious note ya fara magana " daga yau ki rinka yin azumi!" cike da bada umarni yay Maganar, tana jin hakan ta tsaya cakkk kaman an latsa mata pause, " did u hear me" yace fuskarshi ba alamun wasa, marairaice fuska tayi tace "to amman ai bai zaman man dole ba ko" " who told u bai zaman maki dole ba? Shima malamin da yayi maku bayanin kan hakan baki fahimceshi bane sosae dole zaki rink'a yi ko ba wannan abun da kika fad'i ai cos kin girma ko bake kikace ke matashiyan budurwa bane?" ya d'age mata gira alamar ta amsa mashi, (ya fad'i mata hakanne donta rink'a yi, duk da a ilimin dake gareshi kan hakan yasan bai zamar mata wajibi ba sai dae dole arinka sata tana yi as ladab kuma ta hakane zata saba kan yazaman mata dole), hannu tasa tana d'an sosa gaban kanta ta d'age baki, " ki rinka yi sai kina hutawa like in kika yi 3 sai ki huta one day" zaro ido tayi a rud'e tace " har sai nayi ukku zan huta, gaskiya ai yayi yawa sosae" takai Maganar kaman zatayi kuka, Sigh yay yace "Owk mu barshi biyu to" tana tura baki tace "kadai k'ara rage man kabar man d'aya in nayi sai in huta" yadda tayi Maganar sai kace suna ciniki, girgiza kai yayi strictly yace " 2 days zaki rika yi ki huta 1 day" ganin zata k'ara magana ya dakatar da ita da fad'in "Zarah dat's my final say, kinyi 7 days batare da kinyi fasting ko guda ba and shine bazaki iya yin 2,2 days ba, even yara younger than u suna yi kullum ko kunya ma baki ji", kwa6e fuska tayi tana mommotsa baki saidae ta kasa yin magana don ba alamun wasa a tattare dashi, mik'ewa tayi dama ta gama shan tea d'in ta saka cup d'in acikin basket ta d'auka zata tafi, har zata bud'e kopar ya kirata ta juya, " ki fara tomorrow, kuma kada kice zaki shiga kitchen ko toilet tunda ke kazama ne kici wani abu, in kika yi hakan mi zai faru?" ya kafeta da kaifafan idanunsa, baki a kumbure tace "kana zaune zaka gani a Computer" jinjina kai yay yayi mata alamar ta tafi, d'an girgiza kai yay bayan ta fita ya mik'e ya nufi Bedroom. Lokacin da ta koma sashen Hajiya, Saude har ta gama wanke wanken tana ganinta tace sai yanzu ni harma na manta dana aike ki, anan take fad'i mata kamata Ya Handsome yayi tana cin abinci kuma yace dole ta rink'a yin azumi kwana biyu kafin ta huta kwana daya kuma wai daga gobe zata fara, fuska a tur6une take gaya mata hakan yasa saude yin yar dariya itama tasan dama yakamata ace tanayi ko don ta saba, in ba haka ba wuya zata sha nan gaba in ya zamar mata dole karshe ma ta rink'a karyawa don ko shekarar data wuce bazata manta ba karyawar ta rinka yi don batama tunanin tayi cikakken azumi sai dae wani lokacin tana kaiwa azahar sannan ta karya wai intayi na gobe sai yazama d'aya, bata wani dad'e ba tace gida zata tafi Saude nace mata ko ta samar mata wani abu ta k'ara ci tace ta k'oshi, a haka ta nufi gida ranta a jagule don ance tayi azumi kuma dai ba damar tayi yadda ta saba don ta yarda Haisam d'in zai gani. Da Asuba lokacin da gwaggo ta tada ita sahur dagewa tayi ta ci uban abinci wai don karta ji yunwa bata san in kaci Abinci da yawa bama kafi jigatuwa, da gari ya waye ko islamiyya k'in zuwa tayi wai in taje taya zata dawo cikin rana tana azumi tai wucewarta gidan hajiya lokacin batama tashi ba sai Saude dake gyaran gidan, bayan sun gaisane tace zata je d'akinta ta kwanta sauden ta tambayate ba islamiyya zataje ba tace bata iyawa Azumi take, Maganar har saida taba saude dariya, daga haka tai wucewarta d'akin Saude. Bacci sosae tayi don sai wuraren sha biyu ta farka tana jin wata irin yunwa saukinta ma acikin Ac take, tana cikin juye juye Saude ta shigo d'akin, ganin ta farka ne yasa tace masu Azumi antashi kenan, tambayarta Fatuu tayi wai an kusa kiran Magriba don taga tayi bacci sosae, Dariya saude tayi tace to dama ta k'ara kwantawa don ko karfe sha biyu bata yi ba, sosae gaban Fatuu ya fad'i jin hakan, bayan fitar saude duk yadda taso ta koma bacci abun ya gagara sai faman juye juye take tana yin tsoki dakyar ta samu ya d'an dauketa amman sama sama, shigowa saude ta k'ara yi lokacin an fara kiran Sallar azahar, ganin Fatun ta motsa tace mata ta tashi tayi salla ta amsa da to saidae har ta idar Fatuu bata da niyyar tashi, kiranta ta k'ara yi tace ta tashi tayi sallar inta gama sai ta kwanta, tana tura baki ta tashi zaune, koda ta saukko daga kan katifar ta mik'e tsaye sai taji d'an jiri ya kwasheta, da sauri ta koma ta zauna tanata faman k'unci hannunta guda dafe da cikinta ita dae saude tana ta lazimi bata tanka mata ba, saida ta dau d'an lokaci kafin ta sauka k'asa ta fara yin rarrafe ahaka ta isa kopar toilet din, Saude data saki baki tana bin ta da ido bata san lokacin data saki dariya ba tana girgiza kai tace Allah ya shiryeki Fateema, koda tayo Alwalar matsar da abun sallan tayi can jikin bango ta jingina dashi ahaka ta kwa6a sallar tana gamawa ta baje awurin, da Saude ta lek'o d'akin wurin karfe biyu har kwalla tayi mata wai mutuwa zatayi sauden tace mata bazata mutu ba don da ana mutuwa suma da suke yi duk shekara kuma duka ai da tuni sun mutu, tace wannan zaman d'akin da take yi ne yake sata jin wuyar azumin da zata d'aure ta fita tayi wani d'an aiki zata rage jin wuyarshi, tana jin hakan tace tabb wllh ita ko mik'ewa ma bata iyawa, Ana gab da kiran sallar la'asar Hajiya na zaune a falo tana kallon tafsir aka aiko wata yarinya kiran Fatuu, da mamaki Hajiya tace anya Fateema na gidan nan kuwa, k'wala ma saude kira tayi ta fito daga cikin kitchen tun kafin ta k'araso cikin falon hajiya tace "wai Fateema na gidan nan kuwa?", Murmushi tay tace "tana nanl" da mamaki Hajiya ta maimaita tana nan kafin tace "yaushe to tazo gidan ban sani ba?" Saude na dariya tace " Azumi take yi yau tun safe tana cikin dakina kwance" da mamaki Hajiya ta k'ara maimaita maganar Sauden kafin tace "to dama sauran ranakun da take cewa tana azumi bayi take ba?" " Eh wai wuya yake bata shine take karyawa wani lokacinma wurina take zuwa in bata abinci to jiya na aiketa ta d'aukko Basket a part d'in yalla6ai haisam shine ya kamata tana ci ", Salati Hajiya ta saka ta ruke ha6a cike da mamaki tace "yanzu dama duk marairaicewar da take tace tana yin azumi k'arya ne bata yi ko d'aya ba, kai Fateema Allah dai ya shiryata wllh, ke kuma ya da haka Saude ya zaki rink'a goya mata baya tana karyawa?" Hajiya ta kafeta da ido hakan yasa ta dan sunnar da kai kafin ta d'ago tace "ta ce man wai bata fara jinin al'ada bane kuma a islamiyyarsu ance sai Mutum ya fara azumi ya zamar masa dole kuma nima haka nasani shiyasa", jinjina kai Hajiya tayi tace " to ai koda bata faran ba tunda alamomin balaga sun fito mata ya wajaba arinka sata tanayi amatsayin ladabi shiyasa ma Dijen ke sawa tana yi, kuma in bata saba da azumin ba taya zata rinka yi inya zamar mata dolen, aikuwa ya kyauta daya sata dole tayi in ba haka ba to kuwa ba ranar da zata yi azumin, kema kuma kar ki k'ara goya mata baya ta hanyar bata abinci abarshi a yadda Haisam d'in yace ta rinka yi" jinjina kai Saude tayi cike da ladabi tace "insha Allahu bazan k'ara ba", Umarnin tado Fatun Hajiya taba sauden, lokacin da taje dakin tana nan dae malale a k'asa kaman ruwa tana ganin sauden ta fara juye juye tana fad'in wayyo cikinta, " Sannu Fateema, ki daure ai ankusa ma shan ruwa tunda la'asar ta kusa", wani kallo tayi ma Sauden tace "wai har yanzuma bata yi ba kenan, Aunty saude kodae lasifinkan masallacin ne ta lalace shiyasa baki ji ankira ba" ta k'arasa Maganar tana ta nishi, yar dariya tayi tace lafiyar lasifikan masallaci lau kawae lokacinne bai idasa ba, lokacin da ta sanar mata Hajiya tace akirata don an aiko kiranta cewa tayi ita wllh bata iya tashi sauden tace to taje ta fad'i ma hajiyan hakanne tace a'a ta kamata sai suje, kamar wata mai jinya haka Saude ta kamota suka fito hajiya na ganinsu ta saki baki tana kallon ikon Allah, a tsakiyar falon ta zauna tana gaida hajiyar da kyar, "Yanzu duk azumin ne haka Fateema?" kai ta d'aga mata kawae, "To sannu, ki tashi kije Dije ta aiko kiranki" Yamutsa fuska tayi kaman zatayi kuka ta kalli saude tace don Allah ta k'ara kamata suje gidan, Hajiya ta hana tace ta daure ahaka zata saba, da k'yar ta tashi ganin hajiyar ta d'an d'aure fuska ta tafi tana layi kaman wata yar maye, tana fita waje ta dawo cikin falon kamar wadda wani abu ya biyo har saida hajiya ta d'an tsorata takai idanunta kopar shigowan, can gefen Hajiyar taje ta zauna ta jingina da kujerar da take zaune idanunta cike tab da kwalla, ganin hakan yasa hajiya tambayarta lafiya,murya kaman zata yi kuka tace "Wllh Hajiya rana yayi yawa baki ji ba dana fita kaman an watsa man wuta a fuska, ban iya zuwa gidan cikinta" tana kai Maganar kwalla suka zubo mata sharr, jinjina kai Hajiya tayi tana kallonta tace "to yanzu ace ma Dijen baki zuwa kenan duk da tun safe baki gidan?" shiru ta d'anyi sai kuma tace "A'a zani amman don Allah ki ara man lemarki" waro ido hajiya tayi bata san lokacin data sa dariya ba tace "lema kuma fateema" kai ta d'aga mata tana ci gaba da zubda kwallah, kwala ma Saude kira tayi tace ta aro ma fateema lemarta wai bata iya zuwa gida cikin rana, Saude nata dariya ta d'aukko mata lemar, dakyar ta mik'e tun acikin falon ta bud'eta ta d'aga saman kanta daga haka ta fita sunata mata dariya hajiya na fad'in yau Manya na Azumi..... ( A daidai wannan gabar zanyi karin bayani dangane da wajibci ko rashin wajibcin azumin Fatuu, ni ba malama bace ta wannan fannin daliba ce, hakanne yasa nayi amfani da ilimin da aka koyar dani kan hakan, Fatuu bata balaga ba saboda bata fara jinin haila ba saidae alamomin balagar sun fara bayyanar mata kaman fitowar mama wanda wannan ba ainihin balaga bace, a ka'ida na cika azumin mace da namiji, shi namiji sai ya balaga ma'ana yayi mafarki shine malamai suke cema iza balagal luhuma, ita kuma mace sai ta fara jini, su abubuwan da zasu fara fitowa ajikinta wato canjawar jikin anace masu alamun balaga amman ba ainihin balagar ba, a ka'ida ta musulunci da malamai suke badawa shine wanda hukunci ya fara hawa kanshi wanda in baiyi abu ba na wajibi za'a bashi zunubi in kuma yayi za'a bashi lada shine mace ko namiji su balaga, wato cikakkiyar balaga ga mace takai lokacin da zata fara yin jini, in kuma kaman aka samu matsala mace tazo da lalura cewa ita bata jini, to malamai suka ce akwae abunda ake cema,'addaruriyati tud'id' iful ma'azurat, shine lalura tana kauda duk wani abu da yake na uzurine to sai a kiyasta shekarunta aga sun kai nawa, ko kuma a duba wanne ne karshen shekarun da mace take kaiwa ta fara jini in dai lafiya lafiya to sai ace ta fara cika azumi tana da matsala kilan tana daga cikin matan da basu jini, Kaman Fatuu da alamomi suka bayyanar mata amman bata fara jini ba to azumi bai zama wajibi akanta ba sai ajira har sai tafara sai kuma ayi mata ladabi kaman yadda Manzon Allah (S.A.W) ya fad'i cewa ku hori yaranku suyi sallah suna yan shekaru bakwai, idan suka kai goma basu yi ba ku bugesu, ba ana nufin idan sun kai shekara goma basuyi sallah ba suna tare da zunubi, ana so akoya masu yin sallar ne sai sunkai lokacin da zasu balaga ne in basu yi ba za'a rubuta masu zunubin wannan anayi masu ladabi ne don akoya masu su saba, to haka yarinya in bata balaga ba bata fara jini ba ana koya mata ta cika azumine saboda in yazamar mata wajibi ta saba, anan nike son jan hankalin wasu Iyayen da suke goya ma yayansu bayan kin yin azumi saboda basu balaga ba basu fara jini ba duk da alamomin sun bayyana wai don yana basu wuya, wannan kuskurene ba soyayya bace in dae wuyar ba lalura take zamar masu ba ya kamata ayi masu dole su rinka yi don in basu saba ba ko ya zamar masu wajibi zasu iya su rinka karyashi ba tare da sanin kowa ba, yakamata ayi ma yaro ko yarinya ladabi su saba kaman yadda ake yi masu na salla, Allah yasa mu dace Amin, Ga wadanda fahimtata su ba haka bane agare su, ba haka aka koyar dasu ba, Wannan kuma sa6ani ne na malamai, Wallahu a'alamu). ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣6️⃣ ......dakyar ta fito daga gidan don ko tanka ma su Officer dake tambayarta lafiya ko duk azumin ne batayi ba, har saida ta zauna gaban fence d'in gidan hajiyan ta d'an huta kafin ta samu ta mik'e da kyar ta k'arasa gidan tanata had'e hanya don ko kawu Amadu baiga sanda ta wuce ba saboda ta kifa lemar asaman kanta don ruk'on ma lemar aiki ya zamar mata, koda taje gidan bata iya tsinana ma gwaggon komae ba don tana shiga ta kwanta a k'asa ta aje lemar gefe tana ta nishi dayake yamma tayi ba rana a tsakar gidan, a d'an rud'e Gwaggo ta rink'a tambayarta lafiya kafin ta iya bata amsa wayarta ta fara ringing hakan yasa ta juya ta d'aukkota asaman window, ganin sunan Hajiya yasa ta d'auka da sauri don tasan k'ilan Maganar da ta shafi Fatun zata yi mata, aikam bayan sun gaisan hajiyar tayi mata bayani dangane da yanayin da fatun take ciki ta nuna mata karta sare tace zata sata ta karya ta kyaleta inba haka ba bazata ta6a sabawa ba, cike da girmamawa tace mata in sha Allahu bazatayi hakan ba, sosae ta shiga yi masu godiya ita da haisam, bayan sunyi sallama ta aje wayar, bin fatun tayi da kallo cike da mamakin ashe duk azumin da tayi ba cikakku bane ita ta mayar shashasha, kyaleta tayi nan yashe taci gaba da ayyukanta saboda taga tana jin jiki sosae don tasan dama bata da jumurin yunwa, MAGRIB Lokacin da aka sha ruwa jiki na kerma Fatuu ta d'auki Jug d'in ruwan sanyi ta kafa baki gwaggo na karta sha da yawa amman ina saida ta shanyeshi tasss sannan ta dire jug d'in aikuwa nan da nan ta fara kwara amai anan tsakan gidan gwaggo na fad'in maganin mara jin Magana kenan, sosae jikinta ya mutu ta kwanta asaman tabarmar da daddumar da gwaggo ta shimfida sam tama kasa cin komai gwaggo nata faman yi mata sannu, lokacin da Amadu ya shigo shan ruwa yana ganinta ya hau tambayar lafiya ko bata lafiya ne gwaggo ta bashi labarin abunda ya faru, sai can bayan Magrib d'in ta samu ta iya cin wani abu, duk burin da take dashi na taci uban abinci in ansha ruwa yatashi abanza tana niyyar k'ara kwanciya gwaggo tace ta tashi tayi wanka zata ji k'arfin jikinta sai tayi sallah in ma kwanciyar zatai sai ta kwanta, da farko cewa tayi bata iya yin wankan gwaggo tace ta dai daure bari ta kai mata ruwan band'aki, aikuwa tana yin wankan sai gashi taji ta dawo daidai har saida ta k'ara cin wasu abubuwan sannan ta had'a Magrib da Isha tayi, anan kan sallayar ta sake bajewa sai bacci don da lokacin kwanciya yayi saidae gwaggo ta kaita cikin d'akin dakyar, Da Asuba lokacin da gwaggo ta tada ita sahur kuka ta saka mata wai in ta k'ara yi yau mutuwa zatayi don Allah ta rokar mata ya Handsome ya kyaleta ba sai tayi ba tunda bai zamar mata dole ba aikuwa nan ta tok'alo gwaggo dama yanayinta a jiyan yasa bata tanka mata ba akan karya azumin da ta rink'a yi har bata yi ko d'aya ba, fada sosae tayi mata tace waye yace mata don bata fara Al'ada ba shikenan bazata rinka yi ba ai dole zata rink'a yi don Al'adar na kan hanya, tana kuka a haka ta rink'a tura Abinci ranta ajagule sai dai bata yi irin cin da tayi jiya ba abinci d'an daidai ta ci harda fura gwaggo ta bata tasha don ita tafi sha da yawa lokacin Sahur sai abinci kad'an anan kuma taci alwashin da gari ya waye zataje ta bashi hakuri akan ya kyaleta ko dayan ne ta rink'a yi, bayan ta gama tana niyyar kwanciya gwaggo tace ta tsaya tayi sallar asuba sai ta kwanta in ba haka ba da ta kwanta cikinta na iya 6aci tace ta d'aukko Alqur'ani ta karanta, lokacin da tayi sallar asubar har Addu'a tayi wai in taje ba Ya Handsome hakuri Allah yasa ya yarda ta rinka yin daidaya kuma Allah yasa ta daina shan wuya harda su kwalla da tana yin addu'ar. Karfe takwas da rabi Gwaggo ta tada ita don tayi shirin islamiyya don yanzu da safe suke zuwa karfe 9 saboda anyi hutun boko kafin itama islamiyyar abasu hutun ranar Laraba, lokacin da ta shirya ta fito cikin Uniform direct gidan hajiya ta wuce, tana zuwa part d'in haisam ta iske kopan shiga falon a kulle lokacin da ta tura, shiru tayi tana tunanin k'ilan bai tashi ba, ko ta tafi sai anjima sai kuma ranta ya bata yau ba lalle Aunty Saude ta kyaleta ba batare da ta tafi islamiyya ba kuma lokacin da za'a taso rana ta fara gara ta bashi hakuri in ya yarda sai ta karya azumin kawae, Knocking kopar ta fara yi ahankali, jin ba'a da shirin bud'e mata yasa ta k'ara sautin bugun amman shiru har ta fara tunanin ko dai ya tafi aiki ne, har ta juya taji an bud'e kopar hakan yasa ta waiwayo da sauri, tsaye yay jikinshi na sanye da sleeping dress riga da wando Army green ba k'aramin fito mashi da farinshi kayan sukai ba, da ka kalli fuskarshi zaka gane daga bacci ya tashi, kallonta ya rink'a yi daga sama har k'asa fuskarshi a d'aure hakan yasa tayi saurin sunnar da kai k'asa, juyawa yay ya koma cikin falon ya zauna kan kujera had'i da d'age kanshi sama don har ya fara sara mashi, a rayuwarshi ya tsani yana bacci a tasheshi, bama wanda ya ta6a gigin yi masa hakan, ko Hajiya take da bukata awurinshi indae tasan yana bacci bata tadashi ko acan Abuja ma indae ba abu na gaggawa ne ya taso ba wanda dole dole sai ya tashin shine aka tashinshi, in kau ba haka ba duk wanda ya tasheshi sai ya fuskanci bacin rai, shi kanshi yasan yana d'aga ma Fatuu kafa sosae don a yadda ya taso da wani ne tabbas sai ya fuskanci bacin ranshi koda da dalili duk da itama fuskarshi ta nuna, Tsaye tayi awurin ta kasa shiga ciki saboda yadda taga ya daure fuska tunani ta rink'a yi kodae ta tafi amman kuma tana bukatar rokonshi don lokacin da za'a taso islamiyya tasan rana tayi kuma indae tana azumin tasan sai tasha wahalar dawowa gida, wannan tunanin yasa ta fara tafiya ahankali kaman mai yin sand'a ta shiga cikin falon, ganin yadda ya d'age kai sama yasa taji tsoron k'arasawa ciki tai tsaye daga gaban kopan tana kallonshi, Bayan wani d'an lokaci taji yace "Just to interrupt my sleep?" da wata irin murya mai kaushi yay Maganar, shiru tayi tana kyakkyafta ido, jin bata amsa mashi ba yasa ya d'ago kan ya kalleta, ganin kallon da yake matanne yasa ta matsa zuwa gefen kujerun ta tsugunna, yar sheshsheka ta fara yi kafin ta fara magana, " Ya Handsome da..dama..don Allah zuwa nayi in rok'eka ka kyaleni in rink'a yin azumi kwana daidaya, wllh jiya kusan mutuwa nayi ko islamiyya ma banje ba saboda ban iyawa a d'akin Aunty Saude na wuni lokacin da aka sha ruwa kuma har amai nayi" ta k'arasa cikin karewar murya tana goge kwalla da hijab dinta, Sigh yay ya d'an gyara zamanshi kaman bazaice mata komai ba idonshi akanta tana ta nannok'e kai, "Kinsha ruwan da yawa next time sai kisha kad'an, ko ki fara shan something warm in zaki iya and karki k'ara zama baki je skul ba saboda kina fasting " ya fad'a bayan ya daidaita temper dinshi, d'agowa tayi ta kalleshi still tana murzar ido cikin marairaicewa tace "to zan rink'a yin hakan kuma bazan kara kin zuwa islamiyyar ba amman in rinka yin d'ayan?" girgiza mata kai yay ba alamun wasa tana niyyar k'ara magana ya dakatar da ita da hannunshi yace "Zarah kije karki late" tana jin hakan ta mik'e tana k'ara sautin kukan da take, shiru yay yana bin ta da ido lokaci guda yaji wani abu ya fara ratsa zuciyarshi mai kaman tausayi dama Haisam baison yaga mutum yana kuka don shi Mutum ne mai tausayi sosae ba kaman ita da ta kasance mace kuma ma yarinya saidae bazai iya yi mata yadda take so ba don alamu sun nuna inba hakan aka yi mata ba to bazata ta6a sabawa da azumin ba, "Zaraah" taji ya kirata lokacin har ta kama handle d'in kopar zata bud'e, da muryar kuka ta amsa tace "Na'aaam", " wait let me drop u" daga haka ya mik'e ya nufi bedroom dinshi, bai jima ba ya fito hannunshi ruk'e da Car key batare da ya cire sleeping dress d'inba, tana ganin ya fito ta juya ta fita, bayan sun fita daga gidan amota ya tambayeta inda Islamiyyar take ta fara kwatanta mashi, ba tare da sun d'au wani dogon lokaci ba suka k'arasa, tanata faman cin magani tace mashi ta gode kaman anyi mata dole, d'an Murmushin da bai bayyana kan fuskarshi ba yay a fili kuma sai ya tambayeta k'arfe nawa suke tashi baki kumbure tace 11:00 daga haka ta bud'e kopar Motar ta fice, lokacin da taje aji ta makara amman saboda azumi ake yasa ba'ayi mata komae ba, koda taje ta zauna bin ta da ido Haulatu tayi ganin yanayinta, bayan malamin dake ajin ya fitane ta tambayeta mike damunta kaman bazata fad'i mata ba, can da haulatun ta matsa matane ta fadi mata yadda Ya Handsome yasata yin azumin dole duk da bai zamar mata dole ba da kuma irin wuyar da tasha jiya ta k'arasa kwalla na zubo mata tana sa bayan hannunta tana gogewa, ita dae haulatu jinjina kai kawae tayi tace tayi hakuri amman acan k'asan zuciyarta ta masifar jin dad'in hakan don ita kanta ba k'aramin fama take da Fatun ba akan ta daure ta rink'a kai azumi amman sai tace ana wannan uwar ranar zatayi azumi bacin bai zamar mata dole ba wllh batayi don dama sam bata da jumurin yunwa in har kaga bataci abinci ba kuma tana jin yunwa saboda wani dalili to kuwa babban daliline, har aka tashi tana ta bak'in rai don har ta fara complain din yunwa ita dae Haulat d'an Murmushi kawae take, suna fitowa daga cikin islamiyyar ta hangi Motar Haisam, da farko tsaye tayi tana kallon bayan motar kaman bazata je ba saidai tsoronshi da take bazai bari tayi hakan ba kuma ko ba wannan bama tana buk'atar shiga motar don rana ta bud'e sosae, kallon Haulat tayi tace mata suje ga Ya Handsome can yazo daukarta, nufar Motar sukayi Haulat nata jinjina kirki irin na Haisam acikin ranta lokacin da suka k'arasa bakin motar baya haulat ta bud'e ta shiga haka itama fatun sa6anin d'azun da zai kawota agaba ta zauna don tasan baison ba kowa a agaba a zauna baya, yana sanye da Jallabiya fara sol ga d'an kamshi mai sanyi ba mai hawa kai ba na tashi had'i da ni'imtaccen sanyin Ac, suna zaunawa Haulat ta gaidashi tace mashi ya ibada ya amsa da Alhamdulillah ba tare daya kallesu ba daga haka ya tashi Motar Fatuu batace mashi komae ba, lokacin da suka zo center d'in gidansu tana ganin zai nufi gidansu tana tura baki tace gidan Hajiya zasu hakan yasa ya nufi can, bayan yayi parking d'in Motar a Parking Space Haulat tayi mashi godiya ya jinjina mata kai ganin fatun bata yi ba yasa ta d'an zungureta amman sai ta kalleta ta tura mata baki hakan yasa ta bud'e motar ta fita, tana shirin fita itama kamar ance ta d'aga kanta suka had'a ido ta cikin madubin gaban motar, ganin kallon da yay mata ne yasa da sauri tace "An gode" banza yai mata saima ya bud'e motar ya fita bayan ya rufe kopar ya nufi part d'insa, Haulat dake atsaye tana jiran Fatuu tabi shi da ido Allah kadae yasan mi take ayyanawa aranta, Jin Fatun ta fito ne yasa ta maida kallonta kanta fuska ad'an daure tace "Wllh Fatuu baki san baki san mutunci ba, yanzun mutumin nan yaje har islamiyya ya d'aukko mu amman shine bazaki iya ce mashi angode ba sai ma wani tura baki kike ke ala dole yayi maki laifi daga abun arziki wanda inma kinyi ke zai amfana bashi ba", " to ba nace mashi ba yay banza dani" ta fad'a tana d'an hararar Haulatun, " To shi tsaranki ne ko ko ajeshi kikai da sai kingadama zaki ce mashin, kuma dayake tsoronki yakeji sai ya amsa ko" a tsiwace tace "dalla ni ki k'yale ni, Mutum na azumi ki wani cika shi da Surutu" daga haka ta nufi part d'in Hajiya, d'an girgiza kai Haulat tayi cikin ranta ta ayyana samun wuri, a fili kuma da d'an d'aga murya yadda Fatun zataji ta furta "Don kin samu yana kulaki ne ai, amman bari kija ma kanki bake kika sani ba" daga haka tabi bayanta, Lokacin da suka shiga ba kowa acikin falon hakan yasa ta nufi d'akin Saude Haulat d'in tabi bayanta, lokacin da suka shiga Sauden na kwance tana hutawa don bata jima da gama gyaran gidan ba tana jiran ayi azahar ta fara aikin bud'a baki don ita ke yin na cikin gidan kuma ba laifi shima aikin yana da d'an yawa don ana yin abubuwa sosae don Hajiya na gayyato yan shan ruwa wani lokacin, da sallama suka shiga ta d'ago fuskarta da fara'a ta amsa, mik'ewa tayi zaune tace suzo su zauna ta nuna masu bakin katifa, "Sai yau muke ganinki" Saude ta fad'a tana kallon haulatu da Murmushi, gaishe da ita ta fara yi kafin tace "ai ina zuwa amsar sadaqa ban dai shigowa nan d'in" jinjina kai saude tayi ta maida idonta kan Fatuu dake zaune fuska a d'an d'aure tace "Fateema ya azumin kinayi yau d'in ko?" kai ta d'aga mata kawae, taci gaba da cewa "in kika daure a hankali zaki ga kin saba" sai lokacin ta bud'a baki tace "amman ai wuya nakesha fa, ko jiya da akasha ruwa har amai nayi" ta k'arasa idanunta sunyi rau rau alamar kwalla, d'an Murmushi saude tayi tace "eh haka naji d'azun abakin Hajiya data kira gwaggonki, amman tace mata ai ruwa kikasha da yawa kuma dama ko babba ne yakai azumi yasha ruwa da yawa wani lokacin amai yake sawa, ki rinka shan d'an daidai daidai in aka kira sallar daga baya sai ki k'ara kinji" ta k'arasa Maganar ta sigar lallashi ita dae kai kawai ta d'aga mata, hira suka ci gaba da d'an ta6awa sai dae yawanci ita da haulat ne suka fi Magana ita kuma ta kwanta gefe guda,suna ahaka aka fara kiran sallar azahar lokacin Fatuu har tayi bacci, alwala suka yo suka kabbara sallah, bayan sun gama ne saude ta tada Fatuu itama tayi sallar, anyi arziki yau batayi rarrafen ba saidae d'an yamutsa fuska da take tana dafe ciki ahaka har ta shige toilet d'in, haulat dake kallonta ta girgiza kai afili tace " naga randa Fatuu zata saba da azumi", " zata saba ne ahankali tunda gashi yau da kafafunta ta shiga toilet jiya ai rarrafe tayi" bud'a ido haulat tayi ta maimaita abunda saude tace sai kuma ta fashe da dariya tana fad'in Allah ya shiryi fatuu, saude da itama ke dariyar don abun ba k'aramin dariya yabata ba a jiyan ta amsa da Amin, suna zaunen saude tace zataje kitchen ta fara aiki haulatu tace bari tazo ta tayata suka fita atare bayan duk sun cire hijjaban suka bar Fatuu na yin sallah, Bayan wasu mintuna saiga haulat ta dawo d'akin lokacin Fatuu ta dad'e da gama sallar tana kwance kan abun sallar, " ki taso mu tayata aikin tare zaki ji kin rage jin yunwa, dama in kana yin aiki baka fiye jin azumin ba" haulat dake tsaye akan Fatuu ta fad'a,banza tayi mata sai kace ba da ita take magana ba, har k'ara maimaita mata Maganar tayi amman ko ci kanki bata ce mata ba hakan yasa ta juya ta koma kitchen d'in, suna cikin feraye dankali da doya sai gata ta shigo fuskarta sam ba annuri ta kasa bacci saboda yunwa gashi kuma ta d'an damu da fushin da taga kamar Haisam yayi hakanne yasa ta fito ta d'anyi wani abu wai ko ta daina jin yunwar kamar yadda haulat tace, saude na ganinta tayi d'an Murmushi tace "masu azumi anzo taya mu ne?" kai ta d'aga mata alamar eh, "To zo ki zauna kuci gaba nikuma sai in gyara cefane" ta fad'a yayin da ta mik'e don fatuu ta zauna saman kujerar, cigaba da feraye dankalin sukai tana yi tana d'an watsa ruwan dankalin a fuska Haulat dai nata kunshe dariya ita kuma tana harararta, bada dadewa ba suka gama Haulat tayi ma Saude sallama zata tafi gida sauden nacewa gashi ba'a gama komai ba haulat d'in tace ba komai, amman duk da haka saida ta bata lemun roba da fruit tai mata godiya tace ma Fatuu kawata asha ruwa lafiya daga haka ta tafi tana dariya ganin hararar da fatun ke mata ta d'aga murya tace ba ita ta kar zomon ba rataya aka bata. Bayan tafiyar Haulat bada jimawa ba fatuu ta tambayi Saude karfe nawa tace mata ukku saura yan mintuna kad'an nan take tayi yar dariyar da duk ranar bata yi ba jin lokacin yayi sauri, ci gaba da taya sauden aiki tayi har tana ce mata taje ta huta tace ai lokacin baya gudu in ta kwanta, dama kuma Fatuu ba raguwa bace tana da zafin nama kawae azumine yasata tayi laushi, duk bayan d'an lokaci sai ta tambayi Saude karfe nawa yanzu kuma, da ta d'anyi aikin sai ta zauna ta huta in na tsayuwa ne, tana cikin yankan fruit da za'ai fruit salad aka kwad'a kiran salla cike da mamaki tace "kai, wai har la'asar tayi?" gyad'a mata kai Saude tayi tana yar dariya aikuwa nan take ta fara murna tana washe baki, ashe da sauran dariyar azumi bai k'arar da ita ba, bayan sunyi sallar la'asar ne saude tace taje gida ta taya Gwaggo aiki amman da ansha ruwa ta dawo susha ruwa tare tace to, dama ko ba wannan azumin ba agidan hajiya take wuni tana taya saude aiki don ita da wuri take farawa, gwaggo kuma sai yamma wani lokacin ma in aikin rana take tunda safe take yin rabin aikinta koma fi ta bar ma Fatun d'an wanda zata karasa, koda ta koma gidan bata kwanta ba aiki ta shiga taya gwaggo wanda hakan ba k'aramin mamaki ya bata ba don tayi zaton tana can baje bata iya ko mik'ewa ganin yadda ta tashi hankalinta da Asuba shiyasa ma bata yi niyyar kiranta ba sai ankusa shan ruwa tunda can zata fi shan iska, gab da kiran sallar Magrib sun gama komae fatun ma ce ke jera abubuwan shan ruwan asaman katuwar darduma hakan kuma ba k'aramin dad'i yay ma gwaggo ba, ba kamar da ta tambayeta kodae ta karya azuminne ta rantse mata da Allah bata karya ba tace to taje ta watsa ruwa kafin akira sallar, lokacin da tayo wankan ta fito wani nishadi ta rinka yi tanata washe baki sai kace ba Fatuu mai kukan azumi ba gwaggo dae sai girgiza kai take tana Murmushi tace taje ta samu kaya maras nauyi tasa ta amsa da to, yar shimi da wani dogon wando ta sanyo tazo ta zauna gaban kayan shan ruwan da ta jere kiran Salla kawai take jira, aikuwa bata dad'e da zama ba liman ya kwad'a kiran salla kaman don taji, da sauri takai hannu zata dauki jug d'in ruwan sanyi sai kuma ta tuna da abunda Ya Handsome yace na tasha abu mai dumi in zata iya hakan yasa ta aje Jug d'in ta janyo bokitin kunu ta kafa baki ta kurba kaman sau ukku sannan ta aje ta d'auki ruwan sanyin shima ta kafa baki saidae sam bata sha da yawa sosae ba sakamakon abu mai d'umi da ta fara sha kuma tajita tayi wasai cikinta daidai kuma bata jin wata kasala, bud'a baki ta fara hankalinta kwance sai ta janyo wannan ta d'an ci ta maida ta janyo wani ta tsakura tana ci har wani rawa take da kai ita kam gwaggo saida tayi sallah sannan tazo ta zauna alokacin shima Amadu ya shigo suka ci gaba da yin bud'a bakin atare yana tayi ma Fatuu tsiyar abunda tayi jiya sai faman kyalkyatar dariya take sai kace ba ita ba, bata cika cikinta sosae ba don tasan Saude zata aje mata kayan shan ruwa dama ko ba yanzu ba tana aje mata intaje sallar asham sai taci ko kuma bayan angama sallar shekaranjiya dae saboda ansata azumin dole da jiya duk bataje sallar ba, Mik'ewa tayi ta d'aukko Hijab acikin d'aki bayan ta fito tace ma gwaggo ta tafi salla Amadu na fad'in shifa bai yarda da ita ba anya cikakken azumi tayi yau, lokacin da ta kai bakin kopar zaure ta juyo da karfi tace "Da kenan" daga haka ta fuce sunata mata dariya, Lokacin da ta shiga Falon Hajiya suna saman table ita da Haisam jin sallamarta yasa ta juyo ta kalleta banda haisam d'in, alamar tazo tayi mata da hannu hakan yasa ta nufe su ta tsaya agefen hajiya tace "Hajiyar Sanata ansha ruwa lafiya" saida ta cinye abunda ke bakinta sannan tace "Lafiya lou kema kinsha ruwan lafiya ko?" kai ta d'aga mata tana satar kallon haisam da bai ko kalleta ba yanata bud'a bakinshi a nutse, " Ya Handsome barka da shan ruwa" ta fad'a a sanyaye don taga kamar yayi fushi da ita, hannu kawae ya d'an d'aga mata ba tare da ya ce mata komae ba hakan kuma ya tada mata hankali sosae, " Zo ki zauna kici abinci dama saude ta ban labarin yau harda ke tayi aikin, naji dad'i sosae ki rink'a daurewa kinji a hankali zaki saba" a hankali ta amsa mata da to taja kujerar gaba ta zauna dama hajiyar facing d'in juna suke da Haisam d'in, cemata tayi ta zuba duk abunda take so daga haka ta mik'e tace bari taje ciki kafin a kira salla dama kuma ta riga Haisam zama shi bai dad'e da ya shigo ba, soyayyar doya da dankali ta zuba bada yawa ba sai farfesun yan ciki dake ta zuba uban kamshi, koda ta zuban sam sai ta kasa ci sai bin Haisam take da ido shikam tamkar ma baisan da ita awurin ba yana ta cin hadaddan chips din dake gabanshi ga farfesun kifi tilapia agefe, "Ya Handsome" ta kirashi a d'arare, shiru bai amsata ba balle kuma ya kalleta yana ta cin abunda ke gabanshi a nutse, K'ara kiran sunan nashi tayi aikuwa ya d'an juya ya jefa mata wani kallo da bata ta6a ganin yayi mata shi ba, nan da nan ta razana har saida tasa tafin hannu ta rufe bakinta, ganin hakan yasashi maida idonshi kan abunda ke gabanshi ya d'an kara ci kad'an kafin ya janyo wani luxury flask ya bud'e, hadaddan kunun gyad'a ne da yaji peak milk musamman shi aka had'a mawa don bai shan kunun tsamiya ko na kanwa, a glass cup ya tsiyaya kaman rabi kafin ya aje flask d'in ya maida marfinshi ya rufe, cikin aji yake d'an kurbarshi gwanin burgewa duk wannan abun idon fatuu na akanshi ta d'an kwa6e fuska kaman zata yi kuka yayin da take tuno da Maganar Haulat ta d'azun da tace bari taja ma kanta ya daina kulata da alama hakan ce ta faru kirjinta sai bugawa yake, tsam ya mik'e bayan ya gama sha ya rage d'an kad'an acikin Cup d'in, saida ya gyara rigarshi kafin ya nufi cikin Falon idon Fatuu a kanshi ta zaro su, tana ganin alamun fita zaiyi ta wani zabura ta mik'e kamar walkiya sai ganinta yay tasha gabanshi lokacin har ya fita daga cikin falon yana niyyar shiga harabar gidan, shiru yay yana bin ta da ido da yake akwae haske ya gauraye ko'ina kaman da rana, ganin hakan yasa ta kama kunnuwanta da hannayenta murya na rawa tace "am sorry Ya Handsome, don Allah kar kayi fushi dani" yadda tayi yaso bashi dariya dama gata ba wani tsawo ne da ita ba amman sai ya basar ya k'ara tamke fuska, cigaba da yi mashi magiya tayi har kwalla sun fara zubo mata duk tabi ta tashi hankalinta saidae baiyi mamakin hakan ba don yasan dama bata so taga anyi fushi da ita, Kokarin bi ta gefenta yay don ya wuce tai saurin matsawa ta tare shi harda bud'a hannuwa alamun kar ya wuce, goya hannuwansa yay a k'irji yana kallonta daga sama har k'asa wata yar guntuwa da ita, acan k'asan zuciyarshi kuma mamaki ne ya cikashi don tanayi mashi abubawan da ba wani mahalukin da ya taba yi mashi, wannan daba yarjejeniya atsakaninsu bai tunanin ma zata ji shakkarshi balle harta aikata abu in ya bata umarni ya ayyana hakan aransa don ya gama fahimtar sam bata da tsoro, "Don Allah kai man Magana" tayi Maganar kaman mai niyyar rushewa da kuka tana wani ta6e baki, Sauke hannuwan yay ya zurasu cikin Aljihunan wandonshi kaman an masa dole yace "kin yi man wani abu ne?" shiru tayi tana kyakkyafta ido ta rasa mi zatace, " baki man komai ba, nine nayi maki dana takura kiyi abunda bakya so but yanzu zaki iya yin yadda kike so i won't care anymore........." ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣7️⃣ .......tun kafin ya k'arasa ta fara girgiza mashi kai da sauri Murya na rawa tace "a'a baka takura man ba zan rink'a yin yadda kace bazan k'ara cewa komae ba wllh", Shiru yay yana dai ta kallonta dama yafi son tasama ranta yin azumin ta hakane kadae zata daina jin wuyarshi sosae, jin baice komai bane yasa tace "kaji ya Handsome, zan rink'a yi", Dan d'age kafad'a yay ya furta " Is Ok" daga haka ya fara kokarin wucewa, " To bakai dariya ba" cakk ya tsaya ya juyo yay mata wani kallo kafin yace " kin raina ni ko!" zare ido tai gudun kada ta kara wani laifin da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, "Dama ina wannan ne?" tanata zare ido tace " eh wani lokacin kana yi sai ka juyar da kanka amman kana yin haka..." ta dan jirkice bakinta ita ala dole irin murmushin da yake yi na gefe ta kwaikwaya aikuwa baisan lokacin daya d'aga hannu zai rankwashi kanta ba ta janye da sauri tana dariya, dan Murmushin gefen dai yay ya girgiza kai daga haka ya juya, "Masallaci zaka?" ta tambaya jin ana kiran sallar isha, kai kawae ya d'aga mata alamar eh ba tare daya juyo ba, "In zo mu tafi tare?" sai lokacin ya juyo ya kalleta ya saki fuskar sosae, "Ba kina cin abu ba" da sauri tace "a'a zan barshi inna dawo sai inci" jinjina kai yay ya tambayi ta rufeshi ne tace a'a umarnin taje ta rufe ya bata ta juya da sauri tana ce mashi ya jirata fa, Sauke ajiyar zuciya yay bayan ta shige cikin falon a fili ya furta "Zaraah Rigima", bada jimawa ba ta fito suka tafi. Bayan angama sallar asham atare suka dawo parlon hajiyan, haisam ya d'an kishingida saman 3 seater ita kuma ta nufi dining ta daukko abincinta da ta rufe, a gefen Haisam d'in ta aje kafin tasa hannu ta cire hijab dinta, ba tare data ji komae ba ta zauna daga ita sai yar shimin jikinta ga gashinta dama atsafe yake yayi wani tum abaya hakan kuma yasa ta k'ara kyau, fuskarta da d'an Murmushi tace mashi su ci, girgiza mata kai yay alamar bazai ci ba, ta langa6ar da kai tana ce mashi don Allah, yasan in ba cin yay ba haka zatai ta faman yi masa magiya shiyasa yace mata yafi son abu mai ruwa, tana jin hakan ta mik'e tace bari taje ta amso mashi abu mai ruwan ta nufi kitchen da sauri batare data jira mi zai k'ara cewa ba. Bada jimawa ba sai gata ta dawo hannunta ruke da bowl d'in Fruit Salad da spoon ta mik'a masa idonsa akan Tv ya dan kalleta ya furta " Thanks" tana ta Murmushi tayi gwaninta ta koma ta zauna, a hankali yake d'ebowa yana kaiwa bakinshi itama tana cin nata suna yi suna kallon tv, ganin dare nayi yasashi cemata tayi sauri ta gama taje gida tace to, bayan ta gama ta mik'e don kai Plate da bowl d'in data yi amfani ya mik'a mata nashi yace ta kai duk da bai k'arasa shanyewa ba, bayan takai kitchen ta aje ta fito ta nufi d'akin Aunty saude tayi mata saida safe kafin ta nufi Bedroom d'in Hajiya don itama tayi mata saida safe lokacin da taje har ta fara bacci saidae baiyi nisa ba, saida safe tayi mata tace taje wurin Saude tace ta zuba mata tuwo ta kaima Dije ta amsa mata da to, bayan ta gaya ma Saude atare suka je kitchen d'in ta zuba mata tuwon acikin bakar leda wanda na semovita ne an nad'e shi a farar leda, bata dade da gama yinshi ba don Hajiya tafi son cin tuwo da Asuba, a yar madaidaiciyar warmer ta zuba mata miyar Alaiyahun mahad'in tuwon suka sake yin sallama ta nufo cikin falon, tana zuwa gabanshi ya mik'e yay gaba tabi bayanshi rungume da warmer d'in, jerawa tai dashi bayan sun fita tana ta faman zuba shi dai sai dai ya jinjina mata kai ko kuma ya bata yar gajerar amsa in ta matsa mashi da tambaya. Saida suka gaisa da Amadu yayi mashi ansha ruwa lafiya kafin ya wuce da ita har cikin gidan don yana son yi ma gwaggo barka da shan ruwa, a zaure ya tsaya yace mata ta shiga ta fad'i ma gwaggon zai shigo, cike da zumudi ta shiga cikin gidan lokacin gwaggon na kwance a tsakar gida tayi shimfida ga maganin sauro ta kunna agefe don ba wutan Nepa, a gefenta ta aje tuwon tana sanar mata cewa tare da Ya Handsome take yana zaure yace zai shigo, da sauri gwaggon ta tashi zaune tace mata tace ya shigo don a kimtse take, da gudu taje tace ance ya shigo, a tare suka shigo tana gaba yana baya lokacin gwaggo ta fito daga d'akinta ruk'e da darduma ta shimfida mashi tana ce mashi sannu da zuwa, bayan ta gama ta nuna mashi alamar ya zauna saida ya cire takalmanshi agefe kafin ya hau ya zauna ita kuwa Fatuu can gefe inda sauran kayan bud'a baki suke ta nufa ta fara bubbud'awa tana fad'in " Gwaggo Allah yasa dae baki cinye komai ba kin rage man" har saida Haisam ya d'an kalli inda take sai kace ba yanzu ta gama cin abinci ba, shuru gwaggon tayi mata suka shiga gaisawa da Haisam tace bari akawo mashi abun ta6awa, tana k'okarin mik'ewa ya dakatar da ita yace yanzu ya gama cin abu tace to ai ko ruwa yasha nan ma yace ya gode tace to ta kyaleshi yanzu amman dole yazo shan ruwa kafin agama azumin, d'an Murmushi kawae yay kafin ya d'an d'aga kai ya kalli Fatuu dake can gefe sai ta tsakura wannan ta ci wannan acikin ranshi kuwa mamakin yadda take cin abinci yake yanzu ya gano dalilin dayasa ta tashi hankalinta daya sata yin azumi dole, godiya gwaggo ta fara yi mashi game da azumin dayasa Fatuu take yi tace ita sam bata san rashin hankalin da take yi kenan ba da tuni ta tsawatar mata don duk atunaninta in tayi azumi cikakkene, nan ma dae d'an Murmushi yayi ita kuwa fatun tana jin abunda gwaggon ke cewa ta taso tazo inda suke, agefenta ta zauna tace, "Gwaggo ni ce banda hankali?", " ina kika ganshi fa" ta bata amsa cikin harshen fulatanci, turo baki tayi da hausa tace "Wllh Allah inada cikakken hankali kuma ga Ya Handsome nan ki tambayeshi kiji don shi yasan inada hankali" jinjina kai gwaggo ta shiga kafin tace " dama ai yanzu yana daga cikin wad'anda zasu fad'i rashin hankalinki Fatuu" jin hakan yasa ta fara kukan shagwa6a tana d'an tuttura kafa, girgiza kai gwaggo tayi tace "yanzu shi wannan abun da kike ai duk cikin hankalinne ko, ke sam ba ranar da zaki girma ne?" turo baki tayi ba tare data ce komai ba idonta akan Haisam daya d'an sadda kai yana kallon k'asan gidan, d'agowa yay ya d'an kalleta suka hada ido ya d'an girgiza kai kafin ya kalli gwaggo yay mata sallama yana kokarin mik'ewa, atare suka rako shi gwaggon na k'ara yi mashi godiyar dawainiyar da yake masu, suna zuwa bakin zaure ta koma ciki ita kuma Fatuu ta rako shi har waje dama bata cire hijab d'in jikinta ba, suna fitowa kan hanya yace ta koma tayi tsaye bakin hanyar tace sai ya tafi zata koma, har ya d'an wuce shagon Amadu ta kwala mashi kira, "Ya Handsome",tsayawa yay ya juyo ya kalleta, " ai gobe dae ba Azumi ko?" shiru ya danyi da farko sai kuma ya d'aga mata kai alamar eh, kawae sai gani yay ta fara yin rawa, bud'a ido yay alamar mamaki aikuwa tana ganin hakan dayake akwae haske ta ruga tana ta dariya, girgiza kai kawae yay daga haka ya nufi gida. Washe gari da bata yin azumi sam bata yarda taji yunwa ba,duk wani abun ci data gani sai taci, tunda safe kafin ta tafi makaranta ta cinye duk abunda suka rage haka bayan antaso data je gidan Hajiya bunu bunu taci wani abu wai daga yau sai bayan kwana biyu Saude nata mata dariya, da yamma data koma gida ma tana taya Gwaggo aiki tana cin abubuwan da aka fara na bud'a baki ba tare da ta 6oye ba kamar yadda take yi da don yanzu gwaggon tasan yau ba ranar yin azumi bace har gwaggon nace mata wannan kafin asha ruwan ma ai saita cinye komae sai da tayi da gaske ta hanata. Haka taci gaba da yin azumin duk in tayi biyu sai ta huta kwana d'aya kuma bata k'ara yima Haisam korafi game da azumin ba gudun kada yay fushi da ita sai dae in yana bata wuya tai ma su gwaggo ko Saude korafin, ana saura kwana takwas agama azumi bayan gama sallar asham yace mata ta shirya gobe karfe 10 na safe zai kaita inda za'a gyara mata kai, lokacin zai rakata gida kaman yadda kusan kullum yake rakata don yanzu da angama sallar saita koma part d'in hajiya daga baya ya rakota sa6anin da tare da Haulat suke tafiya gida da angama sallar yanzu kuwa tun a Masallacin suke rabuwa suyi ma juna saida safe, cike da murna ta amsa mashi da to sai kuma ta tuna goben ranar yin azumi ce hakan yasa ta rokeshi akan ya barta ba sai tayi gobe ba tunda fita zasuyi, da farko k'in yarda yay ganin yadda ta marairace mashi ne kuma ba wuri daya yake son suje ba yasashi ce mata in ta yarda zata rama shi next tayi ukku sai ya amince, cike da zumud'i tace to ta yarda ahaka suka rabu, **** **** ***** Washegari tunda sassafe ta tashi don fitar da zasuyi na ranta shiyasa da tayi sallar Asuba ta kasa komawa, kuma dama tunda ya gaya mata tana isa gida ta sanar ma gwaggo tace karta tada ita sahur don bazata yi azumi ba, tana tashi shaf shaf ta share tsakar gidan tayi wanke wanke don indae bata azumi ita ke yinsu in tana yi kuma gwaggon ke kama mata wani abun kaman wanke wanke sai suyi tare in tana gida wani lokacin ma ita kad'ai ke yi ita Fatun sai ta share duka gidan don tuni anyi masu hutun Islamiyya, tana gamawa ta fad'a bandaki tayo wanka bayan ta gama ta nufi d'aki don ta shirya, Misalin k'arfe 9:30 saura ta gama shiryawa cikin jar jallabiyarta harda su makeup ga jan janbaki tasa abakinta tayi kyau sosae ba kamar yanzu da skin d'inta ta canza saboda mayukan da take amfani dasu sun fito da ainihin kalarta don bana bleaching bane, koda ta lek'a yi ma gwaggo sallama isketa tayi tana bacci hakan yasa ta fito ta tafi don tasan ta sanar da ita tun jiya, lokacin da ta fito wajen wayam ba kowa duk anata baccin safe ko kawu Amadu ma bai tashi ba dama yanzu bai bud'e shago da wuri wani lokacin ma yan kawo kud'in kankara ne ke tada shi dole, ta Gate tabi don k'aramar kopar arufe take har Officer na zolayarta cewa da ganin wannan kwalliyar bata azumi tace mashi tana yi daga haka tai wucewarta don a k'agare take da su tafi, da sallama ta shiga cikin falon nashi don abud'e ta iske kopar sai dai koda ta shiga bai acikin falon hakan yasa ta zauna don ta jirashi tunda tasan lokacin daya dibar masu zasu fitan bai idasa ba kuma koda wasa bata ta6a shiga Bedroom dinshi ba don bata ma ga fuskar yin hakan ba a wurinshi, shiru shiru har bayan wani lokaci bai fito ba hakan yasa ta gaji da zaman ta d'an kwanta a d'ayan 6arin kujerar, nan da nan sanyin Ac ya bugeta ta fara d'an gyangyadi dama jiya bata samu isasshen bacci ba saboda zumudin yau tayi, jin sanyin Ac d'in yayi mata yawa don har kafafunta sun fara rawa yasa ta mik'e ta daukko throw pillows d'in dake akan kujeran ta rufe kafafunta dasu ta linke hannuwanta akirji nan da nan ba tare da ta ankare ba bacci mai karfi yai awon gaba da ita, Karfe goma daidai ya fito cikin falon jikinshi sanye da rantsatstsen Voile Coffee Brown haka takalmanshi da agogon hannunshi ma duk Coffee ne, Ma sha Allah shine abunda na fad'a yayin da yake nufo cikin falon da tafiyarshi ta kasaita, tsaye yay d'an nesa da ita yana kallon fuskarta fuskarshi d'auke da d'an Murmushi don ganinta da yay yasashi k'ara fahimtar yadda take son agyara mata gashin, kai idonshi yay kan kafafunta da ta jera throw pillows lokaci guda ya fadada Murmushinshi had'i da d'an girgiza kai, juyawa yay ya koma Bedroom dinshi, bada jimawa ba ya fito hannunshi d'auke da lallausan farin Duvet, saida ya cire pillows d'in sannan ya lullu6a mata shi har zuwa cikinta daga haka ya juya ya nufi dakin lab d'inshi ya fito hannunshi ruke da wata bak'ar laptop ya zauna a inda ya saba zama ya fara operating dinta bayan ya daurata kan c-table, Bacci sosae Fatuu take yi, duk in tayi motsi sai ya d'aga idonshi ya kalleta sai kuma taci gaba, saida ta d'auki kusan awa kafin ta fara motsi sosae, a hankali ta fara bud'e idanunta kafin ta idasa ware su sosae, kuri tayi tana kallon Haisam dake ta daddana computer da mamaki tace "Ya Handsome" gira ya d'age mata kafin ya d'aga ido ya kalleta, mik'ewa tayi zaune idonta akan duvet d'in dake jikinta tace "Ya Handsome kai kasa man wannan abun?" kai ya daga mata alamar eh sai kuma yace " kina jin sanyi ne", " to munje wurin gyaran gashin ne?", shiru yay jin wata tambaya mara kan gado, can kuma tace "Wai ashe bacci nayi, to mun fasa zuwa ne" jinjina mata kai yayi ba tare daya kalleta ba yace "Yea, time d'in ya wuce yanzu ina abu ne", kaman zatayi kuka tace "to ai ba laifina bane tunda da sassafe nazo kaine baka fito ba ka ganni ba har bacci ya kwashe ni", " Yanzu laifi nane kenan tunda ni nace kiyi bacci ko?" ya d'ago ya kalleta tai narai narai da idanu har kwalla ta fara taruwa, " Saboda ba sayar da su ake ba shiyasa da kin so sai ki zubosu without any strong reason, baki tsoron su k'are?" yay Maganar idonshi akanta aikuwa kaman tana jira kawae sai tasa mashi kuka harda shashsheka, bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma ya mik'e ya d'auki laptop d'in ya maida ita dakin daya daukkota bayan ya fito wurin tv ya nufa ya daukko tissue box yazo gabanta, yagowa yay ya mik'a mata bayan ya kira sunanta ta d'ago idanunta sun d'an yi ja gashi duk ta 6ata kwalliyarta, fuskarshi a sake cikin cool voice dinshi yace "Wipe ur tears, ina maki wasa ne ai yanzu zamu tafi dama am just waiting for u to wake up" hannu ta mik'a ta amshi tissue ta fara goge idonta tanayi tana d'an kallonshi ganin ya kafeta da ido, " Zan sha ruwa" ta fad'a a sanyaye, " Owk " ya furta kafin ya aje box d'in kan c-table ya juya ya nufi inda fridge yake, bottle water da lemu fanta ya d'aukko ya dawo ya mik'a mata ta amsa tace ta gode, bud'e ruwan tayi ta d'an sha har zata aje yace su tafi dashi ko zata bukata ta amsa da to, daga haka yace zasu iya tafiya ta mik'e tabi bayanshi, yana gaba tana biye dashi suka fito harabar gidan, bata yi tunanin zuwa gaida hajiya ba don tasan ba lalle inta tashi ba, bayan sun hau mota sun fitane ya kira wata mai suna Nana a waya ya tambayeta wurin salon mai kyau tace zata turo mashi Address d'in mai yi masu yay rejecting call d'in bayan yace mata thanks, ba wani 6ata lokaci ta turo mashi ya duba dama bai aje wayar ba tana hannunshi, aje wayar yay ya dan juya ya kalli Fatuu da tunda suka fito batai magana ba ta kwantar da kanta tana ta kallon hanya ta glass d'in kofa, maida idonshi yay kan hanya yaci gaba da driving bayan wani d'an lokaci suka k'araso wurin wanda bene ne dauke da jerin manyan shaguna a sama da kasa, acan gefen benen ya hango shagon da aka turo mashi mai dauke da sunan MAMAN ABDUL BEAUTY SALOON, hayewa yayi sama ya parker motar acan gaban shagon tun kafin ma ya kashe sai ga wata mata mai kiba tana sanye da doguwar rigar atamfa mai gajeran hannu kanta daure da kallabi ta nufo Motar da sauri fuskarta dauke da fara'a da gani an sanar mata game da zuwan su ne, daidai lokacin da suka bud'e Motar ta k'araso tana ta faman washe baki cike da girmamawa tace ma haisam " U'r welcome sir, Nana told me about ur coming" jinjina mata kai yay ta shiga gaidashi tana ce mashi ya ibada, dama itama musulma ce amman bayerabiya ce, bayan sun gama gaisawa ne yay mata bayanin yadda yake son gashin yayi amman bai son asaka mata relaxer, da sauri tace mashi kar ya damu hakan aikinta ne zata yi mata yadda yake so insha Allahu, kallon Fatuu tayi dake tsaye jikin kopa tace su shiga ciki, saida ta gaidata kafin ta bar jikin kopar ta rufeta har zata bita ta juyo ta kalli haisam tace " Ya Handsome kai bazaka shigo ba?" girgiza mata kai yay yace "kije zan jiraki cikin mota" jinjina mashi kai tayi ta juya matar na tsaye ta kama hannunta suka nufi shagon, komawa yay cikin motar ya rufe, kwantar da seat din yay ya d'an kwanta yana cigaba da sauraron karatun Alqur'anin da dama tunda suka taho ya kunnashi, Bayan kaman minti goma sha biyar da shigar su Fatuu cikin shagon kawae sai gata ta fito da gudu kanta duk an nad'a mata rollers yayi kaman an kifa mata d'an kwando, tana fitowa matar ma ta biyo bayanta da yar sassarfa don bata iya yin gudu saboda kiba a yadda ta biyotan sai kace giwa ta biyo yar akuya, side d'in driver ta nufa lokacin idanun Haisam na a lumshe saidai yaji ana kokarin bude kopar, da sauri ya ware idanunsa koda yay arba da Fatuu ba arziki ya tashi zaune ya fara kokarin fitowa daga cikin motar don har ta bud'e kopar, tun kafin yace wani abu matar ta riga cewa "Sir, she refuses to stay in d dryer" maida idonshi yay kan Fatun dake ta hura hanci ta kumburo baki lokaci guda takaici ya rufeshi, kallon matar yay yace taje kawae ta amsa mashi da okey kafin ta juya, kallon kallo suka shiga yi da ita yama rasa mi zaice kawae sai ya juya ya tada seat d'in motar ya shige tare da jawo kopar ya rufe, tsaye tayi awurin can kuma sai ta zagaya a d'arare ta bud'e kopar ta shiga ba tare da ta rufe ba, shiru tayi tana binshi da ido ya d'age kanshi sama ya lumshe idanunshi, bayan wani lokaci ganin bai tanka mata ba yasa ta kira sunanshi "Ya Handsome" shiru bai amsa ba hakan yasa ta k'ara kiran sunanshi sai lokacin yace mata taje su cire rollers d'insu tazo su tafi, jin hakan yasa tace " Fushi kai....." tun kafin ta k'arasa a fusace ya juyo yace "A'a ba fushi nayi ba tunda ni dutse ne, an gaya maki bani da abun yi ne da zaki sa in kawo ki wuri and ki k'i yarda ayi maki, ko kuwa ance maki bana jin azumin bakina ne da zaki sa in wahalar da kaina, tell me did i brought u here ba tare da amincewarki bane da zaki nemi tozarta ni!!" zaro ido tai jin yadda yake mata Magana a kausashe daga ji ranshi ya matukar 6aci sosae don ko lokacin da ya mareta bata ga irin bacin ran dake fuskarshi ba ayanzu, " U are wasting my time Kije su cire abubuwan su don inada abun yi" ya sake fad'a a fusace aikuwa sai ta rushe mashi da matsanancin kuka acikin kukan ta fara fad'in "to ai ba hakanan nak'i yarda ba ko, ba ji nayi abun yana da zafi ba ni kuma ina tsoron kada ya guntile man kai tunda ai ban ta6a shiga irinshi ba ko, shine za kai ta man fad'a", still yay yana kallonta sai kuma da ta yi Magana ya tuna da wacece ya kawo wurin hakan yasa ya daidaita yanayinshi calmly ya kira sunanta cikin muryar kuka tace " Na'aamm", " look at me Zarah" a hankali ta d'ago ta kalleshi fuskarta sha6e sha6e da hawaye, hannu yakai ya bud'e glove box ya ciro mata tissue yace ta goge fuskar, amsa tayi ta fara gogewa tana sakin ajiyar zuciya, " Do u think zan kawo ki inda za'a cuceki ne?" ya tambaya bayan ta tsagaita da goge fuskar, girgiza mashi kai tayi alamar a'a, "Then miyasa kike tunanin dryer d'in zai cire maki kai ne or what?" cikin disashshiyar Murya tace " to ai kai Namiji ne baka san ya abun yake ba" d'an girgiza mata kai yay yace "Nima ina dashi ai, amman nawa na hannu ne, yana busar da gashi ne kawae bai cire kai" d'an yamutsa fuska tai irin bazaka gane d'innan ba tace "to ai kace naka na hannu ne kaga ba irin wannan k'aton bane, shifa wani iska mai mugun zafi yake busowa" d'an Murmushi yay yace "Zarah duk d'aya ne ai, kawae iskan zai drying gashi ne ba zai cutar dake ba, kuma ko ni bansan irinshi ba ai Sisters d'ina na zuwa ana yi masu amfani dashi kuma bai ta6a cire ma wani kai ba saidae ya gyara gashin ya koma irin yadda kike so", " A can Abuja" ta tambayeshi ya d'aga mata kai alamar eh, shiru tayi ta kafeshi da runannun idanu hakan yasashi cewa " in baki so kije su cire rollers d'in sai mu tafi kawae" jin haka yasa tace "to amman ai fushi zakai?" tayi Maganar fuska a kwa6e, " bazanyi fushi ba but bazanji dad'i ba saboda kin nuna kina sone na kawo ki and bazaki k'ara nuna kina son abu ba inyi maki" yay Maganar ba alamun wasa, ta6e baki ta fara yi tace "to bari inje ayi man" shiru bai tanka mata ba saidae idonshi na akanta, "Kaji" ta fad'a ganin baice komae ba, jinjina mata kai kawae yay ta juya zata fita sai kuma ta juyo tace " zafin bazai man komae ba dae ko" gyad'a mata kai yay ta sake juyawa ta fita daga cikin motar, shima fitowa yay ya d'aura hannuwanshi asaman Motar yana kallonta, nufar shagon tayi tana yi tana waiwayenshi ahaka har ta shige....... ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣8️⃣ .…...Yana ganin ta shige cikin shagon yay wani murmushi dama tun farko yadda ta fito da kan yaso bashi dariya ta wani bangaren, komawa yay cikin Motar yaci gaba da jiranta, Bayan wasu tsawon Mintuna sai gata ta fito gyalenta a hannu da gudu ta isa gaban Motar tasa hannu ta bud'e kopar gefen driver ta shige lokacin idanun Haisam na a lumshe, "Ya Handsome!" ta kirashi da karfin gaske dama yaji shigowarta kawae dae bai kalleta bane, a hankali ya ware eyes dinshi akanta, cike da farinciki ta juya masha bayan kanta tana nuna mashi gashinta daya sha gyara ya sauka sosae don har ya kai tsakiyar bayanta da gani harda stretching akai mata sai faman salki gashin yake, gyara zaman shi yay sosae fuskarshi d'auke da murmushi ya furta "yayi kyau" washe baki tayi sam ta kasa Magana saboda tsabar murna sai faman janyo gashin take ta gaba, suna cikin hakan Maman Abdul d'in ta k'araso bakin Motar, Haisam na ganinta ya bud'e kopar tun kafin yace wani abu tana ta fara'a ta tambayeshi gashin yayi yadda yake so ya amsa mata da yayi kafin ya tambayi kudin service d'in da sauri tace komi ya bada yayi, ba tare da ya k'ara cewa komai ba ya koma cikin Motar, glove box ya bud'e ya k'irgo kudi dubu goma Fatuu nata binshi da ido ya juya ya fita, a rude ta karbi kud'in lokacin da ya mik'a mata har da d'an duk'awa, sosae ta shiga yi mashi godiya tana fad'in "Thank u sir, May Almighty Allah increases ur wealth, May God bless u....." sai faman duk'awa take don ita kanta tasan bawae kudin aikinta bane ya bata kawai kyauta ce yay mata, shi dae jinjina mata kai kawae yay ya koma cikin Motar, kafin ya rufe ta lek'a da fara'a tace ma Fatuu tana jiranta ta k'ara zuwa tunda yanzu tasan Dryer d'in bai cire kai, kai fatun ta d'aga mata kawae ta juya ta nufi shago tana yi masu bye bye, yana Niyyar tashin Motar yaga Fatun na k'okarin bud'e mota ta fita ya tambayi lafiya, " zanje in daukko abunne", "Wani abu?" ya tambaya cikin rashin fahimta, "Shi abun yin, dryer sunanshi ko?" Bin ta da ido yay kafin yace "is it ur own?" " ai naga ka bata uban kudi ba siya kayi ba?" yar harara ya wurga mata ba tare da yace komai ba ya tashi Motar suka sauka kan titi yaja Motar suka tafi, Tunda suka bar wurin ta kasa natsuwa acikin motar, gaba daya ta aje gyalen rigar ma sai faman d'oki take tana ta6a gashinta har hannu take kaiwa ta juyo da rearview mirror bayan wani lokaci sai yasa hannu ya juya shi yadda zai ga bayanshi, da taga yana juyashi sai ta sauke glass d'in kopar da take ta rink'a lek'a madubin wajen tana ta washe baki, "Ki rufe shi ko wanda Grandpa d'inki yace sunyi maki fitsari su k'ara" taji ya fad'a ba tare daya kalleta ba, juyawa tayi ta kalleshi tana zare ido tace "Aljanu?" kai ya d'aga mata, " To ai banda su fa, in ma inadasu yanzu sun tafi", "In kinbar kan a bud'e ai zasu ga yayi kyau su dawo ko", hannu tasa ta rufe baki sai kuma ta kai hannu da sauri ta d'auki gyalen rigarta tasa ta rufe glass d'in don dama Gwaggo na yawan ce mata in bata son rufe gashinta shed'anun Aljanu zasu hau mata su shige jikinta, A daidai wata k'atuwar Plaza ya juya kan Motar ya shiga, can gefe guda ya parker Motar bayan ya kashe yace mata ta fito, wani katon shago mai d'auke da sunan Zee's Collection ya nufa tana biye dashi sai faman kalle kalle take, suna shiga wata wayayyar mata fara mai d'an jiki ba sosae ba kuma tana da dan tsawo jikinta sanye da bakar Jallabiya tayi rolling veil dinta ta nufo su da fara'a hakanne ya bayyana hakorin makkan dake bakinta, " The Big CoE, U'r welcome" fuskarshi da d'an Murmushi ya furta "thanks Zee" hannu ta mik'a ta nuna masu 2 seater leather sofa dake a shagon wanda yake dankam da kaya su laces, Atampopi, Materials harda dinkakku wato ready-made da kayatattun dogayen riguna, nufar kujerar yay ya zauna ta maida kallonta kan Fatuu dake ta bin shagon da kallo tace "Beauty ave a seat" kallonta tayi sai lokacin ta gaidata da fara' a ta amsa mata tace ta zaune, acan gefen Haisam ta zauna, "H,Zakee ya ibada" ta tambaya tana ta faman fara'a, "Alhamdulillah, Ya bussiness" " Alhamdulillah gamu munata kokartawa" jinjina mata kai kawae yay, Kallon Fatuu tayi tace "What's ur name?" "Zaraah" ta bata amsa "Sannu Fateema Zahra anata Azumi balle kisha ko ruwa" da sauri tace "ai banayi" d'an bud'a ido Zee tayi tace " bakya yi why?" "Ai bai zamar man dole ba saboda ban...." cakk ta kasa k'arasawa ta juya tana kallon Haisam da ya dan kishingida ajikin kujeran, lokaci guda Zee ta fahimci abunda zata ce hakan yasa tayi d'an Murmushi tace "to amman dae kinayi ko?" d'aga mata kai tayi "Eh, inna yi biyu sai in huta kwana d'aya" jinjina kai tayi tace gud, juyawa tayi ta kwala ma wata Esther kira sai gata ta fito yar matashiya ce da bazata wuce shekara sha biyar ba kuma tun daga kan shigarta da sunanta zaka gane ba musulma bace, tana zuwa ta d'an rankwafa ta gaida haisam da turanci ita kau fatuu sakin baki tayi cike da al'ajabi tana kallonta, abunda ya d'aure mata kai shine ganin kanta a aske kwal ga ba d'an kunne hakan yasa da farko tayi tunanin namiji ne sai kuma idonta ya sauka kan kirjinta dake dauke da breasts, Umarnin amso cake da lemu ta bata awani shago ta nufi hanyar fita Fatuu ta bita da kallo baki sake tace "kai! Wannan Namijine ko mace, kodae irin tane mata maza!" duk atunaninta acikin zuciyarta ta fad'i hakan bata san a fili tayi ta ba, Murmushi Zee tayi "ba Namiji bane Mace ne haka al'adansu yake" bin ta da ido kawae tayi lokacin esther d'in ta dawo ruke da leda mai dauke da abubuwan da kace ta amso, d'an durkusawa tayi taba zee tace mata ta kawo plate cikin inda ta fito ta koma sai gata ta dawo rike da plate d'in ta bata, fiddo cake d'in Zee tayi ta d'aura asaman plate d'in da lemun, da d'an Murmushi ta mik'a ma Fatuu ta amsa tace ta gode, a hannun kujera ta d'aura plate d'in ta fara ci bayan ta bud'e lemun, yar hira Zee suka ci gaba da yi da Haisam don kawarshi ce tare sukae Secondary school da ita sai dae ta d'an girmeshi, jefi jefi yake tanka mata Fatuu dai nata cin cake d'inta tana kurbar lemu, bayan wani lokaci ya duba wrist watch ganin lokaci ya tafi yace ma Zee ta duba mata kayan da sukae Magana ta amsa mashi da to kafin ta kalli Fatuu tace mata tayi sauri tazo ta za6i kaya, jin hakan yasa tai saurin tura sauran cake din gaba daya ta kwankwad'e lemun da sauri ta mik'e tace ta gama, Zee na murmushi ta mik'e suka nufi bangaren laces tace mata ta zabi wanda yay mata nan fa Fatuu ta zaro idanu tana tsuke baki ta fara bin kayan da kallo zee dae na tsaye agefe tana Murmushi, "Should i help u?" girgiza mata kai tayi tace "zan iya za6a" can ta nuna wani hadaddan swiss lace, "Wow, gaskia kin iya za6e" Zee ta fad'a yayin da takai hannu ta ciro mata lace din, sosae Fatuu ta shiga washe baki tana juya lace din a hannunta can idonta ya kai kan price d'inshi dake manne ajikin ledan lace din, kura ma kudin ido tayi cikin rashin fahimta tace ma Zee "Wannan kudinshi ne?" kai ta d'aga mata alamar eh, " To..Naira nawa ne naga ansa 64..,dubu shidda da dari hudu yake kenan?" tana ta Murmushi tace mata "No, ki duba sosae dai how many zeros are there?" K'ara k'ura ido Fatuu tayi tana kallon kudin can ta dago a d'an firgice tace "zero ukku ne, kenan dubu sittin da hudu yake?" "Yea, haka ne kin fad'a daidai" tana rufe baki ta tura mata lace d'in sai kace wani mugun abu, cikin rashin fahimta Zee ta tambayi miya faru ne tana tura baki tace " banson shi yay tsada da yawa, ace kudinshi har yayi kudin dan shanu wannan ma ai Almubazzaranci ne" sai yanzu Zee ta gano dalili kuma Maganar shanun da tayi tasa ta fahimci bafullatana ce nan take ta yanke aranta k'ilan cikin yan'uwan H,zakee ne na Daura, cikin d'an lallami tace "ai isn't an extravagance, in kana da hali ba laifi bane don ka siya abu mai kudi sosae, kuma ai kinga lace d'in is very fine and unique" turo baki tayi tace ita dae bata sonshi, Girgiza kai Zee tayi ta maidashi kafin tace to ta za6i wani, tambayarta tayi wanda basu kaishi kud'i ba ta nuna mata gabansu, wani Golden yellow mai sak'a Coffee brown ta nuna shima yay kyau sosae amman tun kafin aciro ta tambayi nawa yake, saida Zee ta d'anyi jimm kafin tace dubu 42, shima sai cewa tai yay kudi a nuna wadanda basu kaishi ba Zee ta nuna mata, wani blue mai kwalliya golden brown ta nuna tana washe baki alamar yayi mata don dama tana son blue har saida Zee ta sauke yar ajiyar zuciya don duk atunaninta shi zata d'auka amman koda ta ciro mata taga kudinshi dubu 34 sai tace shima bata so yayi tsada, lallashinta ta fara yi tace ta daukeshi kawae tunda tana sonshi kuma shi ai baiyi kudi sosae ba tunda kudinshi ma rabin na farkonne amman ta kafe akan yayi tsada shima, jagub zee tayi tana kallonta tana ta tura mata baki can ta tambayeta kaman na nawa take so ne tace kaman na dubu goma irin wanda gwaggonta ta siya mata waccan sallar, jinjina kai tayi tace to bata da irinshi gaskiya don ita laces d'inta masu kananun kudi duk sun kai 20k, tana jin hakan ta juya tana fad'in "bari in ma Ya Handsome Magana babu wanda nike so sai mu tafi wani wuri", Zee na jin tana niyyar yi mata asarar ciniki ta d'aga murya tana fad'in ya zatace ba wanda take so bacin duk gasu nan ta nuna, aikuwa tana yin Maganar sai a kunnan Haisam d'in dama hakan take so, tsam ya mik'e ya nufo su ya tambayi abunda ya faru Zee tayi mashi bayani, wani kallo yay ma Fatuu data tamke fuska, kallon Zee yay ya tambayi wanne ta nuna da farko aikuwa tana jin hakan tasa mashi kuka tana fad'in "Ni wllh bazansa wannan leshin ba don Almubazzaranci ne an fad'a mana a islamiyya, kudinshi fa sun kai na d'an shanu kuma ko gwaggo taji kudinshi wllh sai tayi fad'a, nidae banson shi don Allah Ya Handsome kar ka siya man shi" still sukai suna kallonta har fuskarta tayi sharkaf da hawaye gaba daya gyalenta ya zamo tana goge fuskarta yayinda Zee ke fad'in Masha Allah acikin zuciyarta ganin gashin kan Fatun, Sigh Haisam yay yasan halinta sarae tunda ta nuna bata so to fa yasan bata so d'in, umarnin suje su zauna ya basu ya fara duba kayan da kanshi, lace d'in data nuna tana so blue d'an dubu 34 shima shi ya d'aukko, sai atampa Chiganvy Gold mai shegen kyau, kiran Zee yay ta taso ya nuna mata kayan yace suje ta samo mata takalmi da veil da duk abunda yakamata kar ta k'ara tambayarta ta amsa mashi da toh, umarnin biyota taba Fatuu suka shiga kopar nan da wadda ta kira da Esther ta fito, suna shiga nan ma Fatuu sakin baki tayi tana kallo wurin don wani katon shagonne shake da takalma, jakuna, gyaluluwa, sarka da yan kunnaye, Undies Cosmetics harda English wears, akwae babbar kopar glass ta shigowa daga waje banda ta cikin d'ayan shagon, takalma golden da gyale guda biyu da jaka daya da zasu shiga da kayan ta d'aukko mata ta bata takalmin ta gwada wanda mai tsini ne amman heel d'in nada kauri kuma takalmin nada mad'auri, Jama'a kuzo kuga Fatuu cikin takalman sun mugun yi mata kyau ita kanta sai Murna take sai kace ba wadda ta gama kuka ba dama kuma tana son takalmi mai tsini amman gwaggo bata so shiyasa bata siya mata su sai mai tudu, sam bata ma tambayi su nawa suke ba saboda d'oki, sark'a da yan kunne da yan hannu gold plated ta daukko mata sai agogo, juyowa tayi don ta tambayeta ko akwae abunda take so kuma sai taga ta k'ura ido tanata kallon d'an mutum mutumin da aka sanya ma wasu had'addun wando jeans da riga sai kyalli suke , "Ko kina son su?" Zee ta tambayeta, maido idonta tai akanta tace "inaso amman fa ni ina jin tausayinshi ne banson sashi kashe kudi sosae saboda sai yayi wahala yake samunsu" ta k'arasa a marairaice, jinjina kai Zee tay da mamaki tace "ke waye ya fad'a maki sai yayi wahala yake samun kudi?" "Eh mana, ai ya fad'i man shi engineer ne rannan dana tambayeshi kuma yace man a filin jirgi yake aiki kinga kenan suke gyara jirgi in ya lalace in ma yak'i tashi su suke tura shi har ya tashi", bud'a ido Zee tayi sosae alamar mamaki sai kuma tasa Dariya tace "Yaushe H,zakee ya zama injiniyan jirgi kuma?" wuri wuri tayi da ido sai kuma tace "ko bashi bane?", girgiza mata kai tayi "yea bashi bane, shi Kwararran Computer engineer ne, he knows both the hardware and software da duk abunda ya danganci computer dae sosae, kuma yana samun kud'i sosae don yanzu we're in a Digital world so kullum cikin samun kud'i yake gashi Dad nashi ma mai kud'i ne sosae ke baki san Babanshi bane, ba yar'uwarsu bace?" da sauri Fatuu ta girgiza mata kai "a'a ni ba yar'uwarsu bace bafa makwabciyarsu ce", " No wonder dat's why kike cewa kina jin tausayinshi, to bari kiji in zai siye maki kayan shagonnan duka ba abunda zaiji kuma dukiyarshi bazatai ko gezau ba, a Abuja fa baki ga tangamemen gidansu ba gari guda in kika shiga zaki manta kina a Nigeria ne kuma bashi ne kadai gidansu ba don ko anan garin a GRA suna da wani katon gidan hadadden gaske..." "Ke kin ta6a zuwa gidansun ne?" Fatuu da tayi kasak'e tana sauraronta ta tambaya, " Yea sosae, don nasan yan gidansu suna siyan kaya awurina kuma wani lokacin ni ke kai masu in naje Abujar, yanzu haka akwae Sisters dinshi a Whatsapp group dina kuma suna fallowing handle ena na instagram da sunga kaya suna so zasu siya ne, akwae ma Stepmom dinshi da suke ce ma Aunty ita bata dad'e da auran dad dinshi ba, ita dama to tun kafin ta auri Senator d'in nasanta don yar Daura ce yar'uwarsu ce itama sosae take siyan kayana kuma wasu kyauta kawae take dasu, so su haka suke, yin babban Alheri ba wani abu bane a wurinsu, in ke kin k'i suna yi ma dubban Mutane gara ma kiyi amfani da damanki ki d'auki duk abunda ranki ke so" sauke ajiyar zuciya Fatuu tayi tace to ta bata kayan, juyawa zee tayi tana d'an girgiza kai ganin yadda tasata uban bayani kafin ta amince, wasu riga da skirt na jeans masu kyau ta daukko mata, rigar fara ce tana da ta sama kalar skirt d'in ta nuna mata wata kopa tace ta shiga change room ne ta sanya sai aga in sunyi mata, ba wani 6ata lokaci ta sanyo kayan don dama doguwar riga ce ajikinta,sosae kayan sukai mata kyau kuma sunyi mata daidai dama skirt din irin wanda bai kaiwa can k'asa ne, wasu riga da wando ta sake daukko mata har sunfi na jikin mutum mutumin kyau tace ta gwado su suma, cike da zumudi ta amshi kayan ta nufi dakin, suma bata dau wani dogon lokaci ba wurin sa su, lokacin data fito cikin jeans da shirt d'in har saida Zee ta furta Tubarkallah a fili ba tare da shiri ba don ba k'aramin amsar jikinta kayan sukai ba, babban abunda yaba Zee mamaki shine ganin yadda k'ugun Fatun ya fito sosae cikin wandon duk da kananun shekarunta amman hips ne da ita sosae, da alama dae Maganar gwaggo ta tabbata da tace da alama irin jikin mahaifiyarta gareta, Cike da Murna Fatuu ta nufi hanyar fita d'ayan shagon tana fad'in bari ta nuno ma Ya Handsome ba tare data jira mi Zee zata ce ba ta fice saidae tabi bayanta, tunda ta fita ta kwala mashi kira ya d'ago daga kan wayar da yake latsawa ya kalleta, tana ta washe baki ta nuna mashi kayan jikintan da hannu, bud'a ido yay ya d'age gira alamar mamaki, "Nayi kyau ko?" ta tambaya cike da zumud'i, jinjina mata kai yay alamar eh ai sai ta fara d'an tsalle gashinta dake zube a bayanta yana d'an watsowa har ta gefen fuskarta ita dae Zee na atsaye gefe tanata Murmushi, can tace mata tazo suje su ko sa gama don an bar Haisam d'in nata zaman jira, bin ta Fatuu tayi suka koma ciki suna shiga taci gaba da Murna tana ta ta6a jikinta, " I think u also need dis" Zee ta fad'a yayin da takai hannu ta ciro wata yar k'aramar bireziya ta mik'o ma Fatuu, ai koda idanunta sukai arba da ita da sauri kamar wadda shock ya ja ta matsa baya tana zare ido, "Kina bukatarta itama" Zee ta fad'a, da sauri ta girgiza mata kai "a'a ni bani sa ta, kawae so kike ace man yar iska", yar dariya tayi "to mu da muke sawa duk yan iska ne kenan?" turo baki tay "ai ku abunku manya manya ne" "To ai muma da kaman nakin ya fara mana kuma tun lokacin ake fara wearing nata", " to ai dana isa sawa gwaggota zata siya man ne", "Inaga ita gwaggon naki bata san yakamata ki fara sawa bane tunda baki sa irin wannan dress din ba agabanta, look at ur nipples yadda suke showing fa, haka kika je gaban Ya Handsome din naki da naji kina fad'a har kina tsalle" shiru tayi tana ta turo baki ita ala dole bata son sa bra d'in hakan yasa Zee ta kama hannunta ta kaita gaban katon mirror dake a shagon, "Look at ur chest very well, ko da breasts d'in basu da girma kiga yadda nipples dinki suka bayyana sosae" tayi Maganar tana nuna mata abunda take magana akai ta cikin Mirror d'in, aikuwa da sauri tasa hannu guda ta rufe bakinta alamar al'ajabi d'ayan hannun kuma ta kare kirjinta dashi alamar kunya, "Yanzu kin gan abunda nike Magana ko, in kina sa bra din baza'a rinka ganinsu ba", Fuska akwa6e Fatuu tace " to kuma gwaggota fa, kar ta bugeni in ta ganni dashi fa", da sauri Zee tace "No bazata yi maki komae ba, kice mata mai shagon da aka kawoki ce tace kina bukatarta", jinjina kai tay "to amman in bata yarda ba zansa Ya Handsome ya kawo ni in maido maki abunki" d'aga mata kai tayi alamar ta yarda daga haka ta shiga nuna mata yadda zata sa bra d'in har ta fahimta sannan tace taje ta gwada, tana shiga d'akin gwadawar Zee ta girgiza kai a fili ta furta "in kana sana'a kaga Mutane kala kala ( haka ma Rabiu Mai kayan marmari ya fada🤣), " Aunty a wane karfe ne kika ce zan makala ma?" Fatuu ta tambaya da d'aga murya, d'an matsawa tayi yadda zata jita tayi mata bayani yadda zata sa tace in taji ta matseta ko ta mata yawa sai tai adjusting karshe ta tambayi ko ta gane, da sauri tace "Nagane karki shigo" dariya Maganar taba Zee ta girgiza kai kawae ta koma kan stool d'in data taso ta zauna can sai gata ta fito ta maida rigar sai faman kakkare kirjin take, mik'ewa Zee tayi ta nufota tace ta cire hannun don taga intayi mata, da farko k'iyawa tayi saida tace mata to ba kina da riga ba sannan ta cire hannun, dubawa tayi taga tayi mata das ta kuma tambayeta lafiya lau breasts d'in sun zauna aciki batayi mata yawa ba, cike da jin kunya ta d'aga mata kai hakan yasa ta kamo hannunta ta sake kaita gaban mirror ta nuna mata yadda yanzu ba'a ganin nipples d'in nata ita dae dan Murmushi tay don duk jinta take wani iri ta takura, umarnin taje ta cire kayan tayi mata, bayan ta curo harda bra d'in ta saka jallabiyarta ta kawo mata kayan duk aka zuba su acikin k'atuwar leda, wata bra d'in Zee ta k'aro mata tace ta saka ta hannunta aciki don dama tana ahannunta ta dunkuleta, k'in sakawa tayi saima ta d'aukko d'ayar da aka saka tace wai bata so Ya Handsome ya gani, Zee tace to ai inta ruk'e a hannune zai ma fi gani sai kawai ta cusa su can cikin hammata ta mak'alesu, ba yadda Zee bata yi ba akan ta kawo a saka acan k'asan kayan amman tak'i wai ai zai iya duba kayan kuma ya ganta, k'arshe dole ta kyaleta suka fito d'ayan shagon, "Allah ya yi mun gama" Zee ta fad'a yayin da ta tunkaro Haisam da Murmushi, d'ago kai yay ya kallesu fuskarshi a sake, agabanshi ta aje kayan tana kokarin bud'a mashi ya dakatar da ita ta hanyar mik'o mata card yace ta cire kud'in kawae, saman wani d'an table dake d'auke da littafi da wasu yan takardu ta d'aukko Pos machine tasa card d'in, tana kokarin mik'o mashi don yasa pin kawae sai taji ya fad'i mata Pin d'in yace ta k'ara 20k sama tasha ruwa har saida ta d'an ware ido kafin tayi mashi godiya, Fatuu kuwa sakin baki tayi tana kallon yadda take fidda kudin ga kuma mamakin ance ta k'ara har dubu ashirin duk uban cinikin da akayi mata, tana sake da baki har bata san lokacin da bra guda ta fad'o ba, jin abu ya sauka kusa da kafarshi ne yasashi kai idonshi kasa ya d'an janye kafar kawae sai ga yar bireziya ta fito daga kasan rigar Fatun, kauda kanshi kawae yay ba tare da yace komae ba ita kam bata ma san abunda ke faruwa ba, kaman ance Zee ta kalli k'asan taga bra d'in yashe k'asan tiles bud'a ido tai ta kalli fatun suka had'a idanu, da kai tai mata alamar ta kalli k'asa hakan yasa tai saurin duk'ar da kai, ai koda tay arba da yar bra dinta sai ta wani zabura ta kwalalo ido ta d'ago tana kallon Zee dake yar dariya ta d'an rufe bakinta, juyawa tay ta kalli Haisam dake still azaune ta k'ura mashi ido duk ta sha jinin jikinta sai zare ido take, a hankali ya d'ago ya kalleta suka had'a idanu aikuwa a rude ta ida sakin d'ayar bra d'in ta nufi hanyar fita da gudu......... ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 5️⃣9️⃣ .......Bayan ta gama fitar da kud'in har ya mik'e sai kuma yace yana son atampopi guda ukku, Zee ta tambayeshi kaman wane kala yay mata bayani ta d'aukko mashi, sunyi kyau sosae tasaka mashi biyu a leda daban sai d'aya ma a leda daban kaman yadda ya buk'ata, bayan ya k'ara bata card d'in ta fitar da kudinsu atare suka fito daga cikin shagon yana ruk'e da babbar leda guda ita kuma ta ruko mashi guda saida ma tace ya bari Esther ta kai mashi yace ba wani abu, suna fitowa bakin shagon yace ta bashi d'ayar ledar ta koma, duk yadda taso ta kai mashi yace ta barshi kawae, sallama sukai tana tayi mashi godiya har tana cewa ya isar da sak'on sallamarta ga Zarah yace Ok, lokacin da ya iso bakin Motar back door ya bud'e ya saka ledojin kafin ya rufe, d'aga kanshi yay yana d'an kallon wurin da alama Fatuu yake nema, ganin bai ganta bane yasashi tunanin k'ilan ta shige cikin Motar, zagayawa yay da nufin shiga ciki kawae sai ganinta yay a duk'e jikin Motar, tana jin motsinshi ta d'ago suka had'a ido aikuwa da sauri ta sunkuyar da kan tana turo baki, d'an ta6e baki yay ya bud'e Motar zai shiga ganin bata tashi bane yasashi dakatawa yace mata "kina son in take ki ne?" jin hakan yasata mik'ewa sumi sumi ta zagaya d'ayan side d'in maimakon ta bud'e kopar ta shiga sai kawae tai tsaye a bakinta, ganin bata shigo ba bayan ya shigan yasashi sauke glass d'in kopar gefen nashi da d'an d'aga murya kad'an yace "zan fa barki a wurin", jin hakan yasa takai hannu a hankali ta bud'e kopar ta shiga tana ta sussunar da kai takai hannu ta rufe kopar, tashin Motar yay suka bar cikin Plaza d'in, tunda suka hau hanya batace uffan ba a hankali take satar kallonshi yanata driving idanunshi akan hanya, jin shirun nata yay yawa yasashi d'an juyawa ya kalleta daidai itama ta saci kallonshi suka had'a ido, kasa janye idanun nata tayi tana ta yamutsa fuska kaman zatayi kuka hakan yasashi d'an sakin Murmushi aikuwa kaman tana jira ta fara fad'in "Wllh Allah bani na d'auka ba fa, itace ta bani tace wai ina bukatarta kuma saida nace mata ni bani sawa amman ta matsa in d'auka kuma dama nace mata in gwaggota ta hana zaka kawo ni in maido mata kayanta" d'age gira yay kafin ya juya ya kalleta itama lokacin kallonshin take yadda ta wani kwa6e fuska ne yasashi sakin kayatacciyar dariyar dake Matuk'ar k'ara mashi kyau ba kamar daya kasance hakoranshi na gefe gefe sun d'an yi tsini daga k'asa, tana ganin dariyar da yake kawae sai ta fashe da kuka ta fara rantsuwar Allah ba ita tace tana so ba, ganin da gaske ta tashi hankalinta ne yasashi daina yin dariyar Calmly ya kirata "Zaraah" amsa mashi tai "uhhuym" cikin muryar kuka ba tare data kalleshi, "Is Okey, ai ba wani abu bane taga kina bukatan ne dat's why ta baki", Wani kallo tayi mashi baki kumbure kaman zata kai mashi bugu, d'an juyawa yay ya kalleta suna had'a ido sai kawae gani tai yayi mata Murmushi aikuwa sai ta k'ara kware baki tana fad'in " ni wllh ba yar iska bace bani nace ta bani ba ko" "Who said dat? Kinji na fad'i hakan ne?" Cikin muryar kuka tace "ba gashi nan kanata min dariya ba" "Owk, na bari calm ur mind" d'agowa tay don da ta d'age kafafunta sama ta cusa kanta ne, " isn't something to worry ur self about, kin reaching stage na amfani dashi ne so ba wani abu bane ai" "To ai na baro su kuma" ta fad'a da disashshiyar murya, juyowa yay ya kalleta fuskarshi sake kaman zaiyi Murmushi aikuwa sai ta fara yayyarfa hannuwa tana fadin "ni ka daina man dariya to" daure fuska yay yace "kinga yanzu na maki wannan ne?" kallonshi tayi ganin fuskar a daure yasata girgiza mashi kai alamar a'a, maida idonshi yay kan hanya yaci gaba da driving, "Ya Handsome to mu koma a daukko kar muyi nisa" ta fad'a a d'arare, shiru yai kaman bazai ce komae ba sai kuma ya daga ido ya kalleta ta cikin mirror suka hada ido, "an saka maki a kayanki " taji ya fad'a wai kuma sai ta sunkuyar da kai alamar kunya, d'an Murmushin gefen baki yay ya dan girgiza kanshi yaci gaba da driving dinshi ba tare daya k'ara ko kallonta ba itama bata k'ara cewa komae ba. A daidai wasu jerin shagona ya parker Motar agefen titi, wayarsa ya fiddo ya kira wani mai suna Kb yace mashi yana waje, ba 6ata lokaci ya fito daga wani shago acikin jerin shagunan wurin wanda na d'inki ne kamar yadda aka rubuta asaman shagon, matashi ne yana sanye da jeans da t-shirt yana zuwa bakin Motar Haisam ya bud'e kopar ya fito, cike da girmamawa ya shiga gaisar dashi yana tambayar ya ibada, bayan ya amsa mashi ne ya bud'e back door na Motar ya fiddo wata leda wadda yasa aka ware kayan da za'a dinka ma Fatuu, da sauri Kb ya kai hannu ya kar6a ya bud'e ledan ya duba kafin ya d'ago ya tambayi wa za'ai ma dinkinne kuma wanne iri, gaya mashi yay suna tare kafin ya lek'a ta gaba yace ma Fatuu ta fito, bayan ta fito yace ma Kb suje ya dau measurement nata sai ta za6i styles da take so, amsa mashi yay da to kafin ya nufi shagon yana zuwa saitin Fatun yace ta biyo shi, maimakon ta bishin sai ta kalli Haisam a rude tace "Ya tafi da abubuwan fa" cikin nuna rashin fahimta yabi Kb d'in daya kusa shigewa shago da kallo kafin ya maido kallon kanta, tana ganin hakan ta fahimci bai gane abunda take nufi ba hakan yasa da sauri ta sake cewa "Abubuwan da aka saka ciki nike nufi" still bin ta yay da ido kafin ya bude baki yace "i don't get u" jin hakan yasa ta d'aga hannu tana kwatanta mashi abunda take nufi harda d'an nuna chest dinta, wani kallo yabita dashi mai kaman harara aikuwa da sauri ta sunkuyar da kanta kasa, "Ki bishi" taji ya fada, juyawa tai sumi sumi ta nufi shagon haisam daya bita da ido yadan yi wani guntun Murmushi hadi da dan ta6e baki daga haka ya koma cikin Motar, Tana shiga cikin shagon wanda babbane yana d'auke da manyan kekunan d'inki kala kala masu amfani da wuta Kb ya nuna mata plastic chair yace ta zauna, zaunawa tayi gaba d'aya hankalinta na akan ledar kayan tsoronta kar ace bras din na ciki, saida ya fiddo kayan ya duba taga babu su sannan ta samu natsuwa ta fara tunanin kilan suna acikin sauran kayan, wayarshi ya bata bayan ya bud'o mata inda styles suke yace ta za6i wanda za'ayi mata aikuwa hannu na rawa ta amsa ta fara dubawa, duk Wanda ta gani sai ta wuce bai yi mata ba can ta samu wadanda suka yi mata d'aya fitted gown d'aya kuma riga da skirt, koda ta nuna ma Kb d'in sai cewa yay ta dae sake wani wad'annan na Manyan yan mata ne ko kuma Amare aikuwa a harzuk'e tace ai itama yan matance, nan fa suka fara jayyaya har sauran yan shagon saida suka amshi wayar suka duba style d'in da ta za6an kowa ya duba sai yace da de ta canja, wani ma har shawara ya bata yace kayanta masu kyau ne kar ta lalata su amman ta nace ita dae su take so tunda ai a jikin mutane ta gansu sun sa lafiya lou balle ace wani zata lalata kayanta shidae Kb kafewa yay akan ta canja in ba haka ba zaije ya nuna ma yalla6ai Haisam, ganin taki canzawar yasashi nufar waje aikuwa zumbur ta mik'e tabi bayanshi suka nufi Motar sai faman wawwatsa hannuwa take tana fad'in ita da kayanta ba abunda take so zata za6a ba, suna isowa bakin Motar taja kopar ta bud'e lokacin ya d'age kanshi jikin headrest yana sauraron Radio, sauke kan yay ya kalleta ta Matuk'ar d'aure fuska tanata hura hanci, "Miya faru" ya tambaya da kasalalliyar murya, hannu ta d'aga ta nuna mashi Kb dake gefe don shi baima ganshi ba, lek'o wajen yay ya zuro da k'afarshi guda ya kalli Kb d'in tambayarshi abunda ya faru yay, cike da girmamawa ya fara mashi bayani "Yalla6ai dama styles d'in data za6a ne naga kaman basu dace da ita ba don an fi yima Amare haka ko Manyan yan mata, ita in akayi mata karshe zasu takurata ne ma shine nace da ta canja wasu simple wanda zata mora sosae" tun kafin Haisam yace wani abu ta amshe a tsiwace tace "ai dae nima yanzu yar Matance ko, zaka wani ce na Manyan yan Matane to an gaya maka nima yanzu yarinya ce..." tsit ta dakata da Maganar ta juya tana kallon haisam daya d'an k'ank'ance ido had'i da d'an d'age gira yana kallonta lokaci guda tasha jinin jikinta ta fara d'an sussunnar da kai tana mashi kallon kasan ido, wani guntun bazawarin Murmushi yay tana ganin hakan ta turo baki tana kyakkyafta ido, "Kai mata wanda take so" ya fad'a ba tare daya kalli Kb d'in ba, kallonshi tai tayi mashi gwalo shidae Murmushi kawae yay yace suje ya dauki measurement dinta tabi bayanshi tanata surutai tana fad'in "ai daman nasan cewa zaiyi kayi man don duk abunda nike so yi man yake gashi nan ai kasha wahalar banza" ta k'arasa tana mashi dariya, girgiza kai kawae yay ba tare daya ce mata komai ba don ya fahimci rigimamma ce, bayan ya gwadata atare suka fito har yan shagon na mata sai anjima, suna isa ta bud'e Motar ta shige shi kuma ya zagaya wurin Haisam ya fad'i mashi an gama komae yace zasuyi Magana daga haka ya tashi motar, zuge glass Fatuu tayi tana jaddada mashi ya d'inka mata su suyi kyau kaman yadda na jikin matan data gani suke, cike da zolaya ya d'aga murya yace bazai mata irinsu ba zani jaka tsaye(zani single) da riga zai yi mata, atsiwace tace " Wllh in kayi man su sai ka biya ni kayana in ba haka ba a kaika gidan yariii" daga haka Motarsu tabar wurin shi kuma Kb ya nufi shagonsu yana dariya da alama shima d'an barkwanci ne, lokacin da ya koma shagon hiran rikicin Fatun suka cigaba da yi har Kb din na cewa shi abunda ma ya bashi mamaki da yarinyar irin hips din dake gareta duk da ba wani girma ne da ita ba, gaba daya suka tambayeshi measurement din hips din, da mamaki duk suka maimaita daya fad'i masu awon har wani na cewa kodae bai yi awon daidai ba yace wllh daidai awon yake don da farko ita yaba ta zagayo mashi da tape d'in kamar yadda suke yi in zasu auna chest da hips sai suba mai dinkin suce ya zagayo masu dashi, da ya duba awon sai ya kasa yarda hakan yasashi kama tape d'in ya auna da kanshi amman sai gashi same abu ya bashi, gaba daya suka jinjina kai wasu na fad'in hutu ne da cin kayan dadi kawae, "Kunsan kuwa dangin Senator Ali zakee ce" Kb din ya fada, "Haba nifa nayi mamakin ganin an kawo maka dinki a wannan lokacin kuma ka amsa kai da kace ka rufe amsar d'inki ashe babbar harka ce" wani dake yin d'inki cikin yan shagonne ya fad'i hakan, dariya Kb yay "ai kaima kasan har dinkin wasu sai in aje akan wannan, daga fa gidan uwar d'akina ne Hajiya Hauwa Zakee mai Alkhairin ban mamaki yake" "Waye ya kawo dinkinne ko wannan wanda take aikowa miye ma sunanshi?" wani daban ya tambaya, "Wai Tk, bashine ya kawo ba in shine ai shigowa zai yi jikinta ne Haisam dan Senator d'in" Kb ya bashi amsa, "Kace Balaraben nan ne, kai gaskiya mutumin nan wllh yana mugun burgeni yasin, kaga mutum kaman shi yay kansa.....", " ai in dae da irin wad'annan a gari to fa mu munshiga ukku wllh don mata ko kallon irinmu bazasu rink'a yi ba" wani da ya katse waccan ya fad'a aikuwa gaba daya suka kwashe da dariya suna fad'in shi damuwarshi kenan yace to ai gaskiya ya fada suna jin har maza yana burgewa inaga matan kuma, haka suka ci gaba da hiransu suna yin d'inki shi kam Kb fiddo kayan Fatun ma yay yace bari ma ya yanka su tun yanzu. A daidai kopar gidansu ya parker Motar lokacin anata yin sallar Azahar a Masallacin gidan Hajiya, batare daya fita ba ya mik'a hannu baya ya janyo babbar ledar sauran kayan yace ta fita sai ta d'auka, bayan ta fitan ta saukko ledan k'asa wasu guda biyu marasa girma ya sake daukkowa a bayan ya mik'a mata mai d'auke da atampopi guda biyu yace taba Friend dinta da Mom nata sai mai guda d'ayan yace taba Grandma dinta, gyad'a mashi kai tayi alamar to tana ta bin shi da ido kaman akwae abunda take son fad'a, kallonta yay ya dan kwantar da kanshi ganin tayi mashi tsaye ya furta "any problem" kaman wadda aka zarewa lakka ta girgiza mashi kai alamar ba komae, tana niyyar rufe kopar Motar taji yace "check inside suna nan" da sauri ta juya ta kalleshi shima ita d'in yake kallo fuskanshi a sake kaman zaiyi Murmushi, turo baki tay tace "nifa ban tambayesu ba ai ko", " kinji nace wani abu ne?" ya d'age mata gira, a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a, "Owk kije" ya fad'a bayan ya d'ago yana k'okarin jan Motar, "Ya Handsome" yaji ta kirashi a sanyaye, dakatawa yay ya kalleta ba tare daya amsa ba, "Nagode, Allah ya saka da Alkhairi ya saka ka a Aljanna" ,"Ameen yar fillo" ya fad'a da dan Murmushi, har ta juya ta sake juyowa, "Allah ya baka mata ta gari ta haifa maka yara masu kyau in rinka yi masu wasa ina kuma goya su" bud'a ido yay alamar mamaki hakan yasa ta kyalkyace da dariya ta rufo mashi kopar, baija Motar ba har saida ta kinkimi kayan ta shige sannan ya nufi gida, Lokacin data shiga cikin gidan d'akin gwaggo ta nufa ta taras ta gama salla tana zaune kan darduma tana lazimi, cike da zumud'i ta nufeta ko sallama bata yi ba ta zauna agabanta bayan ta ajiye kayan a gefe, hannu ta kai ta cire gyalen kanta ta juya ma gwaggo k'eya yadda zata ga gashin sosae, shafa Addu'a ta fara yi kafin ta kai hannu ta shafi gashin da fara'a tace "inyee, Fatuuta ce ta zama yar India haka" juyowa tayi tana ta dariyar farinciki ta hau bata labarin yadda aka gyara gashin tiryan tirya, "Yar kauye kawae" gwaggon ta fad'a bayan ta gama fad'i mata, ita dae sai faman tik'ar dariya take, hannu ta kai ta janyo ledar kayan ta fara curo wanda ya bata daga baya ta mik'a ma gwaggon tata "gashi nan yace in baki" jinjina kai tay ta ciro atamfar mai kyaun gaske tana ta Murmushi don al'amarin Haisam ya daina bata mamaki sai dae in yayi abu tayi godiya tasa mashi Albarka, fiddo na cikin d'ayar ledar Fatuu tayi wanda guda biyu ne daya mai Golden daya Normal Chiganvy irin ta cotonou mai laushin gaske itama ta gwaggon irin tace amman design ba daya ba, Fatuu na gani tace "lahh gwaggo wannan shigen irin tawa ce da aka kai dinki wllh, kinsan na waye?" girgiza mata kai tayi alamar a'a, "Haulat yace in kai mawa ita da innarta fa" bud'a ido gwaggo tayi sai kuma ta shiga yin godiya, jawo sauran kayan dake acikin babbar ledar tayi anan kuma tai kacibus da yan bras dinta tana ganinsu tai saurin d'agowa ta kalli gwaggo suka had'a ido don ita take kallo tana jiran ganin abunda zata fiddo a ciki, ganin ta k'ame yasa gwaggon tambayarta "lafiya" shiru tayi tana ta d'age baki hadi da dan sosa kai, ganin taki cewa komae ne kuma ga alamun rashin gaskia atattare da ita yasa gwaggo ta kai hannu ta jawo ledar ta lek'a ciki, da mamaki ta d'ago ta kalleta "wannan kuma na waye?" ta tambaya yayin da ta kai hannu ta fiddo da bras d'in, mar mar ta fara yi da ido kaman zata yi kuka cikin in ina ta fara magana "W..wa..wai mai shagon da akai siyayyar ce tace ina bukatarta...." katseta gwaggo tayi "ita ya akai tasan kina buk'atar tatan?" "Ai dayake shagon biyu ne,to da aka gama zabar lace da atamfar nawa sai Ya Handsome d'in yace mu shiga ciki a idasa daukko sauran abubuwa...." nan ta kwashe komae yadda Zee ta bata bras d'in ta fada mata, shiru gwaggo tayi had'i da sunkuyar da kai, tunani ta shiga yi dama can tayi tunanin yakamata ta siya mata bra din don irin breasts din nan masu nipples gareta koya tasa riga mara nauyi sai an gansu sosae, to ganin ba wani girma garesu bane yasa ta kyaleta don sam itama ba irin jikin ainihin yan Matan fulani ne da ita ba, su kansu breasts din nata da gani ba irin masu yin girman nan bane sosae wanda suke zubewa, jin gwaggon tayi shiru kuma ta duk'ar da kai ne yasa gabanta ya fara fad'uwa murya na rawa tace " Gwaggo in baki so dama nace mata zansa Ya Handsome ya kaini a maida mata su", d'agowa tay ta kalleta, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara magana " tunda ta baki taga ya dace ki rinka sawa ne, ki yi amfani dasu....,amman don Allah Fateema ki natsu kisan kin girma duk wani sakarci da wauta ki ajesu agefe, kada ki fara amfani dasu kice zaki bi mutane kina yamadidi kina nuna masu ko fadi masu, sam hakan bai dace ba don rashin kunya ne, ina son ki kama kanki mace da kunya aka santa ba kaman ke da kike bafullatana wadanda aka sani da tsananin kunya, idan naga kina rawar kai don kin fara saka su to kuwa tabbas zan hana ki amfani dasu ne, kinji ni da kyau?" da sauri ta d'aga mata kai alamar eh, duba sauran kayan tayi tasa albarka yayin da farinciki ya lullu6eta saidae sam bata bayyana a fuskarta ba dalilin Maganar da suka gama da Fatun, umarnin kai kayan d'aki ta bata bayan ta mik'e tace in an sha ruwa sai taje ta kaima su Haulatun tace ai ba azumi take yi ba bari taje yanzu ta kai masu gwaggon tace to ta fara yin salla ta amsa da to daga haka ta fice gwaggon ta bita da ido, girgiza kanta tayi lokaci guda kuma idonta suka ciko da kwalla don tunawa da yadda tai fama da Mahaifiyar Fatun kan saka bireziya sam bata so saboda tsananin kunya dake gareta sam ba halinsu d'aya da Fatuu ba duk da tasan dalilin dayasa wasu halayen nata take yinsu haka, d'aga hannu tayi ta shiga yi masu Addu'a gaba daya. Tana gama yin sallar ta nufi gidansu Haulatun, lokacin da ta kai masu kayan Golden d'in tace ta haulatu ce dayar kuma ta innar tasu, Murna sosae sukai dama rannan Hajiyar Sanata ta aiko masu da turmi ukku su dinka harda kannanta kaman yadda ta saba yi duk salla tana rarraba atampopin salla ga marasa k'arfi, har tukuici Innar tasu taba Fatun amman tak'i amsa Haulat tace bayan sallar asham zata rakata tayi mashi godiya, labarin irin kayan da ya siya mata ta shiga ba haulatun amman abun mamaki sam bata yi mata zancen bras din ba da alama taji fad'an gwaggo, sosae haulat ta tayata murna tana ce mata ita yanzu ai tazama yar lelen Ya Handsome, sai la'asar Fatuu ta koma gida, da dare bayan an gama sallar asham tare suka iske shi a part d'inshi don sun duba part d'in Hajiya bai je can ba, karo na farko da Haulat ta shiga part d'inshi sosae ta jinjina had'uwar falon acikin ranta, yana kishingide akan kujera yana lallatsa waya suka iskeshi Haulat d'in na k'okarin duk'awa kan Carpet yace ta zauna kan kujera lokacin ita Fatuu tuni ta haye, sosae tayi mashi godiya yace mata ba wani abu daga haka Haulat ta mik'e tace ma Fatuu tazo su tafi, sanin dama da angama sallar yake rakata gida yasa ta mik'e suka mashi sai da safe tana ta fama yi mashi Murmushi harda yi mashi bye bye shima ya d'an d'aga mata hannu suka fice. Washe gari ya rage saura kwana shidda salla da daddare bayan angama asham taje part d'in hajiya, lokacin da zata tafi ta bata wata babbar leda mai dauke da kaya tace ta kai ma Dije, cike da zumudi ta nufi gida don tasan bai wuce kayan sallar data saba yi masu, lokacin da ta isa gidan gwaggo na kan darduma a tsakar gidan bata dade da gama sallar asham din tata ba tana zaune ga haske ya haske tsakar gidan don tana cikin yin sallar aka maido da wuta, gabanta Fatuu ta nufa da sauri ta aje ledan tana fad'in "gashi Hajiya tace in kawo maki" saida ta shafa Addu'a sannan taja ledan ta bud'e, fiddo kayan ciki tayi gaba daya sannan ta fara daddaga su Fatuu na ganin hakan itama tasa hannu tana tayata d'agawar, d'inkakkun kaya ne d'aya Voile material ne bak'i mai d'auke da manyan fulawowi kala kala ya matukar yin kyau anyi dinkin doguwar riga wadda da gani ta fatuu ce gaban rigar sai sakin kyallin stones da akai ado dasu cikin flowers d'in Material yake, sauran kuma brown shadda ce aka dinka masu gaba daya, gwaggo riga da zani rigar umbrella ce tasha aiki sai ta Fatuu itama shaddar doguwar riga akai mata sai na kawu Amadu dogayen riga da wando ne akai mashi, dama ko sallar data wuce haka tay masu d'inkakkun kaya saidae wanccan karon atamfa tayo masu Amadu kuma yadi ne mai kyau kuma dama ko ba salla ba tana yi ma Fatuu d'inki lokaci zuwa lokaci, wata k'arar murna Fatun ta saki tana fad'in tafi kowa kayan salla wannan sallar gwaggo dai nata faman dariya, lissafi ta shiga yi Ya Handsome yayi mata kala hudu ga bakar doguwar rigar data aje kala biyar kenan sai ga biyu hajiya tayi mata bakwai kenan sai kuma baffanta da yazo ya kawo masu atamfofi ita da gwaggon anyi mata dinki kala biyu Amadu kuma ya kawu masa yadi mai kyau mai matsakaicin kudi dama ita gwaggo bata da niyyar yi mata d'inki wannan sallar tunda baffanta ya kawo mata kuma tasan hajiya dama zata yi mata ga kuma jallabiyar da ta aje, sam bata ma sa ran na Haisam ba iyaka dae ta siya mata gyale da takalma dasu sarka harda sabbin pants da undi da vest sai gashi kuma Haisam din shima ya siya mata, lallae da alama su Fatuu canjin wardrobe za'ai, cike da murna ta ruga waje ta fad'o ma Kawu Amadu suka dawo tare, sosae yay farinciki da ganin kayan, koda lokacin kwanciya yayi Fatuu tasa dukkan kayan tayi gabanta ahaka tai bacci.......... ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 6️⃣0️⃣ Washe gari da Safe suka d'unguma gaba d'aya suka tafi yin godiya, ana saura kwana ukku salla bayan la'asar lokacin gwaggo da Fatuu suna cikin aikin kayan shan ruwa Amadu ya shigo cikin gidan da sallama, nufar Fatuu yay dake jajjagen kayan miya aturmi ga kuma dankali na soyuwa kan gas agefenta, "Gashi nan in ji Ya Haisam" ya fad'a yayin da ya aje babbar ledar da ya shigo da ita daga haka kuma ya juya don ya baro Mutane a shago, cike da zumud'i ta janyo ledan ta bud'e, koda ta yi arba da kayanta da aka kai d'inki sai ta saki dariyar farinciki ta fara kwala ma gwaggo kira tana fad'in tazo taga dinkinta gasu an kawo, fiddo kayan ta fara yi tana dubawa nan take tsananin farinciki ya lullu6eta ganin yadda dinkin sukai bala'en kyau, a atamfar akai mata fitted gown d'in lace din kuma sai akai mata riga da skirt, sunkutar gown d'in tayi ta nufi d'aki don ta gwada, bayan shigarta da d'an lokaci gwaggo ta fito daga cikin kitchen tana fad'in taga dinkin, ganin ba Fatun a wurin yasa takai hannu cikin ledar ta fiddo rigar lace d'in ta d'aga sama, waro ido gwaggo tayi gannin dinkin rigar ba arziki ta d'aurata a saman kafadarta ta curo skirt d'in shima ta d'aga tana k'are mashi kallo bata gama al'ajabin d'inkin da akai masun ba sai ga Fatuu ta fito cikin fitted gown d'in ta kamata tayi mata d'as ajiki daga k'asa ta bud'e sosae yayin da hannuwan ma suka wani kumbura anyi masu wani kalan design d'in dinki da wani abun kwalliya mai kyau, nufo gwaggo tayi tana faman washe baki tana fad'in bari tazo ta idasa zuge mata zip d'in, cakk taja ta tsaya sakamakon jin salatin da gwaggon ke rafkawa hannu a baki, tsaye tayi ta kwalalo ma gwaggo ido, "Yanzu Fatuu wannan d'inkin akai maki sai kace wata kifi, waye yace ai maki shi ne?" ta tambaya rai a 6ace, shiru tayi tana ta zare ido ganin yanayin fuskar gwaggon, har saida ta kwatsa mata tsawa sannan cikin en ina tace "n..nice na za6a" cike da takaici gwaggo ta maimaita abunda ta fad'an kafin tace "saboda baki da hankali ko shine bazaki za6i d'inkin arziki ba sai wannan duk da irin fad'an da nike maki akan matsatstsun kaya shine don kin raina ni baki jin maganata kika za6i wannan dinkin na rashin arziki duk an matse halitta ta bayyana, to naga yadda za'ai ki saka su da sallar in Allah ya kaimu sai dae ki kallesu kuwa", yamutsa fuska ta fara tana jujjuya kai kaman zatai kuka tace " ni dae don Allah ki barni nasa abuna ai dae ajikin Mutane naga anyi nima na za6a ko" "To ni bazan bari kisa ba sai in ga ta tsiya" bubbuga kafafu ta fara tana k'unk'uni tana fad'in " Wllh nidae sai nasa abuna tunda ai bake kika siya man ba ko kuma....." cakk ta tsaya da yin Maganar ganin gwaggon na dube duben k'asa da alama abun bugu take nema, hannu takai cikin robar da fatun ta yanka dankali ta curo wuka, a rud'e Fatuu ta zaro ido tace "Gwaggo wuk'a ne fa!" "Wukan ne don kazan ki, in na illata ki ba sai inga yadda za'ai kisa su da Sallar ba" ta bata amsa lokacin da take d'agowa hannunta ruke da wuk'ar aikuwa Fatuu na ganin haka ta juya fatal fatal don ta kasa yin gudu sosae, maimakon ta jefa wukar saitinta sai ta jefata can gefe guda kafin ta duk'a da sauri ta curo slipper d'in kafarta ta jefa mata daidai fatun ta shige ya d'an sameta a gefen jikinta, tana shigewa d'akin ta rufo kopar, ita kuwa gwaggon cigaba da d'aga riga da skirt d'in tayi tana ta zabga uban tsoki don da gani suma kayan matseta zasuyi sosae gashi lace d'in ya Matuk'ar burge Gwaggo don ya had'u sosae kuma ko ba'a fad'a ba da an kalleshi an san mai kudine sosae, k'arshe dae da takaicin ya isheta sai ta jawo ledar kayan ta cusa su ciki ta ajeta can gefe taci gaba da aikinta cikin ranta kuwa takaicin Fatuu ne k'unshe, (Gwaggo ai ba laifin Fatuu bane ita kadai, harda haisam da ya goya bayan ayi mata shima yakamata kije ki hukunta shi gaskia🤣) A ranar bayan gama sallar asham atare da haisam suka nufi falon hajiya kamar dae kusan ko yaushe, basu dad'e da shiga ba itama Hajiyar ta fito jikinta sanye da hijab ta zauna suka ci gaba da yin fira sai dae tafi yi da Fatun, suna cikin yin firar ne Hajiyan ta juya tana ma Haisam zancen tafiyarsu Abuja jibi wato daren salla, har saida gaban Fatuu ya fad'i duk da tasan dama indae Hajiyan bata je Umrah ba to k'aramar sallah a Abuja take yinta babbar salla ce take yi anan, gaba d'aya jikinta yay sanyi jin harda Ya Handsome d'in za'a tafi lokaci guda walwalarta ta dushe, koda ya rakota lokacin zata tafi gida shiru tay mashi sa6anin yadda ta saba suna tafe tana mashi surutu, daren ranar dae cike da kunci ta kwanta har bacci ya kwasheta ba kuma komae yaja hakan ba sai don tunda tasan Haisam bai ta6a tafiya ba, ko lokacin baya kafin azumi daya tafi lagos shida Abbas sam bata san bai gari ba don in taje bata iske shi ba sai tai tunanin ya fita ne saida ya dawo ranar Monday da yamma taje bayan an taso su daga islamiyya ya bata tsaraba anan ne tasan tafiya yayi yanzu kuma tasan in suka tafi sai sun dade don in hajiya taje sallar tana dadewa bata dawo ba, Washe gari ya kama saura kwana biyu salla, tunda ta farka ba walwala a tare da ita komae sukuku take yinshi don Maganar ta tsaya mata arai, taci burin cin gayu suyi yawan salla tare dashi ya kaita wurare, gwaggo ta lura da yanayinta kaman akwae abunda ke damunta ba kamar data zauna gida bata je gidan hajiya ba hakan yasa ta kirata a d'aki ta tambayeta mike damunta ne (har an shirya kenan🥰) da farko ce mata tayi ba komae gwaggon tace ai in ba komai bazata ta6a ganinta haka ba dole akwae abunda ke damunta hakanne yasa ta fad'i ma gwaggo Hajiya ce zasu tafi Abuja ba anan zasu yi salla ba, "To dama wannan karonne ta fara tafiya Abuja salla" gwaggon ta tambaya da mamaki, "A'a nasan tana zuwa, amman wai fa harda Ya Handsome za'a tafi kuma da shi naso ya kaini yawon salla" ta fad'a fuska a kwa6e, jinjina kai gwaggo tayi jin wani karfin hali awurin fatun tace "to tunda bawanki ne ai sai ki hanashi tafiya gidan babanshi yin salla ya tsaya ya bauta maki tunda ke shashasha ce" turo baki tayi kaman zatayi kuka, can bayan wani lokaci a marairace tace ma gwaggon wai ko tace ma Hajiya zata bisu, aikuwa tun kafin ta rufe baki gwaggo ta hau zazzaga mata fad'a tana fad'in ahirr dinta karta sake taji hakan in ba haka ba ranta zai 6aci ne, duk da da hajiyar ke tafiya da ita dama ake zuwa ne, sosae ta 6ata ma gwaggo rai k'arshe ma tace ta tashi ta bata wuri kuma da taji ance za'a Abuja da ita to tasan ita tayi Maganar atafi da ita kuma wllh daga can tana dawowa Yola zata tafi tunda ita komae sai tasa rashin hankali, lokacin data koma d'aki kan gadonta ta fad'a tana share kwallar da suke zubo mata ita dae hakanan bata son yin salla ba tare dasu ba. Da rana Wuraren karfe sha biyu Hajiya ta kira waya tace Fateema tazo ga Balaraba nan ta kusa gama mata kitso sai ayi mata itama, lokacin da gwaggo ta sanar mata tana tura baki tace ita dae bata son ayi mata kitso tunda an gyara mata gashi gwaggo na jin hakan tace to taje da kanta ta fad'i ma hajiyan hakan, lokacin da ta shiga falon Hajiyar har angama mata kitson tana ganin yanayin Fatun ta tambayeta lafiya ko duk azuminne tace mata a'a bata jin dad'i ne, hajiya na jin hakan ta yarda don duk ranar sai lokacin taje gidan wanda lafiya lafiya tasan bazata k'i zuwa ba, tace to anma yi mata kitso kuma bata jin dad'i fatun tace a'a abarshi tunda Ya Handsome ya kaita an gyara mata gashin, daga haka tayi mata sallama ta nufi hanyar fita hajiyar nayi mata Allah ya sawak'e harda Saude dake jiran itama ayi mata kitson da Balarabar ma, _____________ "Zaraah" taji an kirata lokacin har ta kai gate d'in gidan tana niyyar fita, a hankali ta juya ta kalli haisam dake fitowa daga cikin corridor d'in part d'inshi da alama Masallaci zaije don an fara kiran salla, d'an matsawa tayi kafin taja ta tsaya ya k'araso gabanta yana kallonta, "Ina wuni" ta fad'a asanyaye, shiru bai amsa ba sai cewa yay "mike damunki ne" ya tambaya ganinta sukuku kuma yasan ba azumi ne yasata hakan ba don yanzu sam ta daina korafin azumi har ukku ukku take yi ma, "Am i not talking to u?" ya fad'a da d'an d'aga Murya, maimakon tayi mashi Magana sai kawae tasa mashi kuka hakan kuma yasashi Fahimtar tabbas akwae abunda ke damunta, "Kije part d'ina ki jira ni" ya fad'a yayin da yake wucewa ya nufi Masallaci, "Baki ji bane" ya sake fad'a bayan ya dakata ganin bata tafi ba, a hankali ta wuce part din nashi, ana gama sallar ya dawo yana shiga falon ya isketa tana yin salla dama hijab ce ajikinta kuma d'akin da ta ta6a zuwa yin fitsari taje tayo alwala, zama yay kan kujera ya d'auki remote ya fara canja Channel, zaune tayi kan Carpet bayan ta gama ta sunkuyar da kanta kasa, "Unhum am all ears, miye ne?" taji ya fad'a idonshi akan tv, shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta don tsoron fad'i mashi take saboda gargad'in da gwaggo tayi mata, aje remote d'in yay ya maido hankalinshi kanta a hankali ta d'ago suka had'a ido ganin kallon da yake mata ne yasa ta fara motsa baki amman ta rasa mi ma zata ce mashi, "Kina sani abubuwan da bana so Zarah, i think i ave told u since banason maimaita mgn right?" ya d'age mata gira, d'aga mashi kai tayi alamar eh, "Ok ina jinki" Cikin en ina ta fara Magana "da..daman naji ba anan zakuyi salla ba Abuja zaku tafi" Shiru kaman bazaice wani abu ba sai kuma yace "yea, akwae matsala da hakan?" girgiza mashi kai tayi "a'a, kawae dai nayi zaton anan zakuyi saboda ina son muyi yawan salla tare da kai", bud'a ido yay jin wata Magana mai nuna tsantsan yarintarta, d'an Murmushi yay gently yace "ni ai bani yawon salla Zarah" "Eh ina nufin ka kaini wurare dama, don duk salla ba inda nike zuwa in ba nan cikin Unguwar ba sai gidan wasu yan uwanmu yan kad'an" jinjina kai yay "Ko zaki bi mu Abujar ne?" ba zato ba tsammani taji ya fad'a aikuwa arud'e ta d'ago tana girgiza mashi kai alamar a'a, ya lura da razanar da tayi da jin abunda yace hakan yasashi tambayarta dalilin k'in bin nasu, farko shiru tayi sai kuma ta tuna da baison maimaita Magana hakan yasa kaman zatayi kuka ta fad'a mashi yarda sukae da Gwaggo harda rantsuwar da tayi na daga can tana dawowa sai Yola, shiru yay yana nazarin Maganar tabbas bai kamata ya gifta rantsuwar da tayi ba don yasan tana da dalilin hakan wanda bai wuce k'ok'arin da take yi na saita Fatun, "Owk tunda ta rantse shikenan ba sai kin bimu ba but ki daina damuwa kan yawon sallan zan sa akai ki duk inda kike so in ma ta hana i will talk to her" d'agowa tai ta kalleshi ya d'age mata gira "are u Happy now?" jinjina mashi kai tayi alamar eh, "To baki smile ba" ya fad'a fuskarshi a sake, da bud'ar bakinta sai cewa tayi "dama ina wannan ne?" wato abunda yace mata rannan itama ta fad'i mashi aikuwa ya jefo mata throw pillow yana fad'in kin raina ni da yawa Zaraah, duk'ewa tayi tana dariya hakan kuma ba k'aramin dad'i yay mashi ba don shi sam bai son yaga Mutum na k'unci duk sai yaji ya damu shiyasa in dae yana da iko yin yadda zai sa Mutum farinciki sai yayi, shiru su kai na wani lokaci can ta kalleshi idonshi akan tv, "Naga an kawo man dinkin jiya" kai ya daga ba tare da ya kalleta ba, "Nagode" jinjina mata kai yay sai lokacin ya kalleta tana ta wasa da yatsun hannunta, "Baki yin kunshi ne da salla" taji ya fad'a, Turo baki tay "da gwaggo ke yi man irin na hausa nan da ake d'ansa Salatef ni kuma yanzu banson tayi man irinshi nafi son irin wanda ake yayi a yayyanka salatef d'in ayi design mai kyau da kuma bak'i da ake zanawa" ta k'arasa tana kwatanta mashi wanda take nufi a hannunta, d'aga mata kai yay alamar ya fahimta ya maida idonshi kan tv, bayan wani d'an lokaci ya d'auki wayarshi yai dialing kira ya karata a kunne, wadda ya ta6a kira mai suna Nana lokacin da zai kaita saloon ita ya k'ara kira, yar wurin aikinsu ce zatayi tsararshi sai dae bata yi aure ba har yanzu amman ba zaune take ba tana ta aikinta da bussiness kuma tana jiran Allah ya kawo mijin (da duk masu neman mijin aure Allah Ubangiji ka albarkace su da mazaje na gari masu wadatar zuci wadanda zasu sosu su kuma ruke su saboda Allah ba don wani abu ba haka ma mazan, masu aure kuma ka kara zaunar damu lafiya da mazajenmu ka k'ara rufa mana asiri ka Albarkaci zuri'armu, Amin ya hayyu ya kayyum, ban mance da masu neman haihuwa ba Allah ubangijin samai da kasai mai ikon akan komae wanda da yace kun faya kun (kasance sai ya kasance (wani al'amari) ka albarkace su da samun zuria d'ayyiba Amin), suna mugun yin good time dashi dama kuma ita d'in yar barkwanci ce tana d'aya daga cikin Mutanen da ke sashi dariya ba tare daya shirya yin ba, kai tsaye take fad'i mashi itafa Mugun sonshi take ya taimaka mata ya shige da ita mana wato ya aureta, bayan ta d'aga kiran sun gaisa yace yana son ai ma Sister nashi henna ne tace ba matsala in zai yuwu ya kawota gidansu da safe mai kunshi zata zo yi masu sai ayi mata, amsa mata yay da owk daga haka yai rejecting call d'in, kallon Fatuu yay da ta k'ura mashi ido bayan ya aje wayar yace ta tambayi Grandma d'inta zai kaita k'unshi gobe da safe around 10 tace to, mik'ewa yay yace mata yana jin bacci ta d'aga mashi kai ya nufi Bedroom dinshi ita kuma ta koma kan kujera ta d'auki remote ta canja channel zuwa Bollywood ta kishingida tana yin kallon ahaka bacci yay awon gaba da ita, sai da akai la'asar ya fito don zuwa Masallaci ya ganta kwance tana baccin ta dukunkune cikin hijab d'in jikinta, babbuga kujera yay ta bud'e ido yace ta tashi taje gida tayi salla daga haka ya fuce bayan yaga ta mik'e itama. Washe gari jajibirin salla kaman yadda su kai dashi karfe goma tazo part d'in nashi tana sanye da riga da skirt na atamfa ta yafa gyale dama tun jiyan ta sanar ma gwaggo ba 6ata lokaci suka fito don tafiya gidansu Nanar, lokacin da suka hau hanya zasu wuce k'ura ma lungun gidansu Haulat ido tai Haisam din na kallonta ta Mirror "ko zaki je da ita ne" taji ya fad'a lokacin har sun wuce lungun, kallonshi tay ta d'an d'aga mashi kai alamar eh ba tare daya ce komae ba ya juya Motar suka nufi lungun gidansu Haulat din, abakin lungun ya tsaya bai shiga ba don ba tanan ne hanyarsu ba, ce mata yay taje ta kirata ta amsa da to ta fito, lokacin data shiga gidan ba kowa a tsakar gidan sai yan kannenta k'anana suna wasa hakan yasa ta nufi d'akinsu Haulatun, akwance ta isketa kan yar katifarsu ita da kannanta guda biyu da suma suke yin azumi sunata bacci, gefenta ta durkusa tasa hannu tana tada ita bayan ta farka ta tashi zaune Fatuu ta gaya mata ta taso za'a kaisu kunshi yanzu, tambayarta tayi wanda zai kaisu tace Ya Handsome, d'an jimm tayi tana tunanin anya za'a barta kuwa don da yau da daddare zasuyi na salatef, tana cikin tunanin taji muryar innarsu tana k'wala mata kira hakan yasa ta mik'e ta fita Fatuu ma tabi bayanta, gaishe da ita tayi ta amsa mata da fara'a cikin in ina haulat ta sanar da ita batun zuwa kunshin, da farko k'in amincewa tayi tace in ta tafi waye zai tayata aiyuka tunda tasan karshenta sai yamma koma dare zasu dawo don dole su iske layi sosae saida Fatuu tayi mata bayanin cewa ba gidan kunshi za'a kaisu ba gidan wasu yan uwan Hajiya ne nan mai kunshin zata zo, d'an jimm tayi haulat din ta marairaice fuska tana rokonta kan ta barta bazata dade ba in ma taga za'a kai yamma to zata dawo Fatuu ma ta tayata rokonta sannan ta amince suje, cike da farinciki sukae mata godiya haulat din ta nufi d'aki kaya kawae ta canja don ba lokacin yin wanka suka fice, Lokacin da suka isa gidansu Nanar dake a Kopar Marusa lowcost wanda da gani suna da hali ba laifi, kiranta yay a waya yace mata sunzo ba tare da 6ata lokaci ba Nanar ta fito, yar gajera ce mai k'iba bata da haske sosae saidae baza'a kirata da bak'a ba don akwae yanayin hutu a fatarta, daka kalleta zaka gane wayayyar yar boko ce tana sanye da kaftan ta atamfa ta yafo gyale asaman kai don bata da kallabi, cikin fara'a sosae ta tarbesu bayan ta gama gaisawa da haisam din ta jasu ciki tace in an gama zasu yi waya, sosae ta shiga haba haba dasu haka ma yan gidansu harda Mahaifiyarsu a mutunce suka kar6esu don tun kafin suzo tayi masu bayanin wadda za'a kawo kunshin saboda ba wanda baisan Haisam ba agidan sosae yake yi masu Alkhairi don wani lokacin shi ke maido Nanar gida in sun tashi daga aiki in bataje da Motarta ba suna ganin Fatuu suka yanke cewa itace kanwar tashi duk da Haulat ma sam ba mummuna bace sai dae yanayin fata, batare da 6ata lokaci ba bayan angama ma wadda suka iske anayi mawa aka fara yi ma Fatuu bayan an gama mata akai ma Haulat lokacin har azahar tayi, ba k'aramin had'uwa kunshin yay ba na salatef da kuma zane dayake ba mutum d'aya ce keyi ba akwae mai kama mata nan da nan aka gama, sosae suka rink'a yaba kunshin ba kamar na Fatuu daya fito sosae kasantuwarta fara, har kitso Nanar ta tambayeta in tanaso ayi mata don da ana kunshi kallabinta ya cire sunga gashinta sosae suka rinka santinshi cikin ransu tace mata bata son kitson dama ita Haulat ta riga tayi kitson sallan, bayan sunyi sallar Azahar a d'akin Nanar Fatuu tace mata ta kira ya handsome ta fad'i mashi yazo ya daukesu an gama tace bazasu bari su sha ruwa ba a gidansu ta fad'i mata ance haulat ta koma kafin yamma ne, bayan ta kirashi ta sanar dashi ba'a d'auki wani dogon lokaci ba sai gashi ya kirata yace yana waje, kayan shafa harda turare dasu Popcorn da gullisuwa irin wanda Haisam ke ba Fatun ta basu kowa ledarshi daban daman a wurinta ne Haisam din ke siya, a tare suka fito falo sukai ma yan gidan sallama har mamarsu Nanar na cewa basu tsayawa su sha ruwa Nana tayi mata bayanin ana jiran d'ayar ne kafin suka wuce ana tayi masu bye bye, Suna fitowa Nana ta nufi gaban Motar ta kwankwasa Haisam d'in ya bud'e kopar har yayi wanka ya canja kaya jeans da t-shirt, zuro kafarshi yay guda fuskarshi a sake suka sake gaisawa, juyawa tayi ta kalli su Fatuu da sukayi tsaye gefe tace tazo ta nuna mashi kunshin mana, matsowa tayi ta hade hannuwanta tana nuna mashi harda na kafafunta, dan Murmushi yay yace mata ya gani yayi kyau ita dae haulat na tsaye tana ta Murmushi, maida kallonshi yay kan Nana ya tambayeta nawa ne kudin aikin, " Ka barshi ni zan biya" girgiza mata kai yay alamar bai yarda ba, d'an farr tayi da ido tace "kaji zakee baka son na biya ma k'annen nawa ne?" Murmushi yay yasan halinta sarae in ya biye mata sai taita jan Maganar hakan yasa ya kai hannu cikin Motar ya d'aukko wallet dinshi, kud'i ya kirgo yan dubu dubu sabbi fill (da alama dae haisam bai kashe tsoffin kudi), mik'a mata yay amman sai taki Kar6a tace "tunda baka son na biya masu to ka rike na biyo ka bashi zan amsa", Cikin Cool voice d'inshi cike da tsokana yace "naki ne boyfriend dinki ya baki ki biya henna dinki kema" yana rufe baki ta saki wani k'arajin Murna ta zube kan gwuiwowinta, d'aga hannuwanta tayi sama tana fad'in " Allah Amin, Allah ka bani balaraben nan dama wani jinkirin alkhairi ne, kun ya Allah" tunda take mashi Maganar soyayya sai dai ya d'anyi mata Murmushi kawae yau ne kadae yayi mata Maganar data danganci hakan tunda ya bata kudi yace nata ne saurayinta ya bata duk da tasan wasa yake itama kuma kaman Comedian take ta cika ban dariya, su kuwa su Fatuu mi zasuyi in ba dariya ba ganin yadda ta durkusa k'asa dama gata yar 6asukuta shi ma Haisam Murmushi yake ta yunk'ura ta mik'e tsaye, mik'a mata kudin yay tasa hannu da sauri ta kar6a tana fad'in "dole in kar6i wannan babbar kyauta daga Muradin Zuciyata, kasan fa Zakee in dae ka aure ni sai nayi wata ina azumin godiya ga Allah sannan kuma inyi kyauta da duk abunda na mallaka, to mi zanyi dasu Allah na tuba na samu miji d'aya tamkar da miliyan" juyawa tayi ta kalli su Fatuu tace "ko baku so ya aure ni?" waro ido Fatuu tayi tana dariya Allah yaso dae bata ce komae ba don tana ganin wasa Nanar take, itama haulat dariyar take, girgiza kai Haisam yay ya furta "Nana u are too much" daga haka ya maida kafarshi cikin Motar yay ma su Fatuu alamar su shigo da hannu, tana ta d'aga masu hannu ya tashi Motar har zai tafi tai mashi alamar ya tsaya da hannu, sauke glass yay bayan ya dakata ta d'an lek'a tace ma Fatuu tana jiransu su zo mata yawan salla suka amsa mata da to daga haka tace ma Haisam masoyi asha ruwa lafiya, saida suka bar kopar gidansu sannan ta shige gate din gidansu....... ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 6️⃣1️⃣ .......Saida suka hau hanya ne ta nuna mashi abubuwan da Nanar ta basu ya jinjina kai kawae daga haka kuma suka yi tsit ba wanda ya k'ara tankawa don rana tayi Azumin ya fara bugu, lokaci bayan lokaci take d'an d'aga hannunta ta kalli k'unshin da aka yi matan, a daidai lungun gidansu Haulatu aka sauketa tayi ma Haisam godiya ya jinjina mata kai kawae tace ma Fatuu sai sun had'u anjima daga haka ta tafi, a kopar gidansu ya parker ta juya ta kalleshi tana Murmushi tace "thank u so much Sweetheart Ya Handsome", sigh yay kafin slowly yace "U'r Welcome Sweetheart Yar Fillo" waro ido tay tasa tafin hannunta guda ta rufe baki alamar mamaki don tunda take ce mai Sweetheart bai taba maido mata ba yace mata hakan sau yau, "Ya Handsome nima inada kirki ne kace man haka?" ta kafe shi da ido alamar jiran amsa take, shiru ya d'anyi kafin ya furta "U'r my sis", "kana sona kenan tunda na zama kanwarka?" lumshe mata ido yay alamar eh, yar Dariya tayi tace "Nima ina sonka Ya Handsome" jinjina kai kawae yay yace ta shiga gida, bud'e Motar tai ta fito bayan ta rufe kopar ta fara d'aga mashi hannu tana yi mashi bye bye har saida taga ya tafi sannan ta shige gidan, a tsakar gida ta iske gwaggo nata aiki ga kwandon cefane da kaji an aiko masu daga gidan Hajiya dama tana basu sai dae basu kai yawan na wannan karon ba wanda ba sai an fad'a ba kowa yasan aikin Haisam ne, basu kadai bama har makwabta tana basu kaji da Sallah don suna da k'atuwar gona mai suna ZAKEE's FARM wadda Mahaifin Haisam d'in suka gada awurin mahaifinsu Gen. Adamu, an zuba ma'aikata sosae dake kula da ita banda dabbobi, kaji tsuntsaye har kifi ake kiwatawa aciki dasu zuma Allah yasama gidan gonar Albarka, duk wani kwai da suke amfani dashi suke rabawa kuma da azumi da kaji daga gonar suke, Lokacin da gwaggo taga k'unshin bayan Fatuu ta nuna mata sosae ta shiga washe baki tana yabawa har zolayarta tayi tace itama da zata samu da an zana mata Fatun na jin hakan tace wai bari tayi ma Ya Handsome Magana aikuwa ba arziki gwaggo ta kwa6eta tace ita wasa take yau da daddare zata k'unsa abunta yadda ta saba, hutawa ta d'anyi sai can bayan la'asar ta fito kama ma gwaggo aiki saboda da ta dawo ta isketa tanata uban aiki don ma tuwon shinkafa kawae zatayi da kanta sai waina da alkubus wanda ta bada ayo mata kaman yadda ake yi yanzu a sauk'ak'e akwae wad'anda sana'arsu ce da hidima ko sallah sai ka kai kayan abincin da kake so ayi maka ka biya kai kuma sai kayi miyarka da kake so, itama gwaggon miya kala d'aya zatayi wadda za'a iya cin duka abincin da ita, ba abunda Gwaggo ke fad'a a fili da kuma cikin ranta face ALHAMDULILLAHI dama kuma kullum bakinta bai gushewa da fad'in hakan koda kuwa ba yadda taso abu ya kasance mata ba, kuma fad'ar Allah (SWT) ce idan ka gode mashi zai k'ara maka haka idan kayi takawa ya kasance ka kiyaye dokokin shi, yayi alkawari zai baka mafita a kowane irin al'amari sannan ya azurtaka ta hanyar da baka ta6a tunani ba, shiyasa ake so bawa ya kasance mai mik'a dukkan al'amuranshi ga Allah kuma ya kasance mai yawan gode mashi a koda yaushe to tabbas kuwa zai rink'a ganin bud'i kala kala (Alhamdulillahi ala kulli halin), gaba d'aya Azumin nan Gwaggo zata iya k'irga nawa ta kashe kud'inta don kuwa ba wasu kud'i masu yawa bane, ko su d'inkin salla da sauran siyayyar da ta yi masu duk cikin kud'in da tay niyyar siya ma Amadu freezer ne, ga Amadu yayi cinikin k'ank'ara sosae a haka ma don makwabta kyauta ake basu kuma sam basu cika mata kud'i ba kamar yadda wasu Mutane ke d'aura buri kan kankara cikin Azumi suyi ta saida ita da mugun tsada sai kace suma ba Musulmai bane suna yin azumin sun kuma san yadda mai azumi ke tsananin bukatar kankara, A maimakon su saukaka sai su tsawalla, A nan nike son jan hankalin masu saida kankara da suke tsawwalawa acikin Azumi da kuji tsoron Allah, kusani duk wanda ya ji tausayin Mutane ya rangwanta masu shima Allah zai tausaya masa akasin haka kuma kaima Allah bazai tausaya maka ba hadisi ne ingantacce, ba kuma iya masu kankara ba harda masu hali wannan ma ya shafe ku, wani sai kaga yana da hali amman har ya iya barin makwabcinshi ya kwana da yunwa wa'iyazubillah, saboda ba kyakkyawar alakar da d'aya zai iya sanin halin da d'aya ma ke ciki, sam wasu basa kiyaye hakkin makwabtaka wani ma ko cikakkiyar gaisuwa bai iya tsayawa yayi da makwabcinsa don yana ganin yin hakan tamkar alfarma ce yay masa, akwae hadisai da dama da sukae magana kan makwabtaka, Misali akwae wanda Manzo (SAW) yace, Mala'ika jibrilu bai gushe ba yana man wasiyya akan makwabci har nake tunanin idan na mutu makwabcina zai gajeni, haka akwae hadisi ingantacce da yay Magana kan duk wanda yay imani da Allah da ranar tashin Alkiyama to ya karrama makwabcinsa, amman sai kaga an koro yaran makwabci daga Makarantar da suke saboda littattafai ko Uniform kodae wani abunda bai kai ya kawo ba amma makwabcinsa nada hali bazai iya taimaka masu ba suna ta gararan ba acikin unguwa ko ajikinshi bai damu ma da ya tambayi dalili ba balle har ya taimakesu shi nasa yaran suna a Makarantu masu tsada har takai ta kawo wani fa ko rage ma yaran makwabcinsa hanya a Motarsa bai iya yi ya kaisu Makaranta yana kallo uban zai kama hannunsu yakaisu bakin titi don hawa abun hawa amman k'arshe saidae ya sakar masu horn ya wuce, ko kuma yaga yaran kan hanya suna d'aga mashi hannu alamar gaisuwa bazai iya tsayawa ya daukesu ba, abubuwan takaici dai da yawa wanda in nace in bayyanasu to fa har sai littafin nan ya idasa k'arewa ba tare da angama fad'in komae ba, Yakamata mu gyara masu hali ku rinka jin tausayin maras hali duk min yadda kake akwae wanda bai kaika ba so ko d'an yaya Allah ya bud'a maka kaima ka taimaki wani sai kaga an rage ma juna radadin talauci ba kaman a halin da muke ciki yanzu da babu tayi ma Al'umma yawa, kowa ya rinka kokarin ganin yasa farinciki ta hanyar yaye ma wani damuwarsa matuk'ar kana da halin hakan, kowa dae karshensa Mutuwa ce ko Mutum ya k'i ko ya so, duk kuma abunda ka mallaka dole anan gidan duniya zaka barshi su zama mallakin wasu, wad'anda suka aikata ayyukan Alkhairi Fisabilillah da dukiyoyinsu ne kadae zasu cigaba da cin moriyarsu ko bayan Mutuwarsu, ALLAH Ubangiji kayi mana Arziki mai amfani ka bamu ikon taimakon juna Amin. Sosae Fatuu ta taya Gwaggon aiki saidae bata yarda tayi aikin da zata ta6a ruwa ba sosae wai kada lallenta ya fice tun kafin sallan, zuwa dare sun kammala komae har kajin sun soya anyo markad'en miya an tafasa shi sai zuwa da Asuba za'a idasa had'a miyar ta kuma tuk'a tuwon, ana gama Sallar isha aka sanar anga wata don haka baza'ai sallar asham ba hakan yasa fatuu ta nufi part d'in Hajiya don ta nuna mata lallenta, suma sosae sukae santinshi ita da Saude anan kuma Fatun ta tambayi Hajiya ya akai basu tafi Abuja ba gashi gobe salla tace mata Haisam ne yace su tsaya sai sunyi salla gobe sai su wuce, dama ita hajiya tana son yin sallar anan Senator ne ke matsa mata take tafiya daren sallah ko saura kwana biyu sallah, sosae Fatuu taji dadi don tasan tare zasu je sallar idi Gobe. GOBE SALLA, GOBE💃💃 Allahu Akbar, Allahu Akbar La'ila ha ilallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar Walillahil hamdu, Allahu Akbar kabeera, Walhamdulillahi kaseera, Wa Subhanallahi Bukratan wa asila, shine abunda Mutane keta fad'a washe gari Safiyar sallah, tun kafin Asuba Gwaggo ta tuk'a tuwonta ta k'ukk'ula acikin farar leda ta ida had'a miyarta da taji naman kasuwa sai kamshi ke tashi, lokacin da Asuba tayi Fatuu ta farka bayan tayi salla gwaggo tace ta share tsakar gidan, ta fiddo mata wankakkun labulaye da zanin gado tace ta gyara dakinta zuwa karfe shiddan safe gidan ya fito fess sai kamshin turaren wuta ke tashi, shirin zuwa sallar idi suka fara gaba dayansu don tun jiya Hajiya ta sanar da gwaggon su shirya tare zasu sallah karfe bakwae don 7:30 za'ai salla masallacin da zasu je, gaba d'aya Fatuu ta baje kayanta saman gado sai faman ruwan ido take ta rasa wanda zata sanya har saida taje ta tambayi gwaggo tace tasa Jallabiyarta bak'a mana aikuwa cike da murna ta nufi d'akinta don sam bata yi tunanin sanya taba kuma tasan inta sata ba sai tasa wata hijab ba, k'arfe bakwai saura gaba d'aya sun gama shiryawa Amadu ya shigo cikin shadda ruwan madara kafafunshi sanye da bakin takalmi da agogo sai hula kalar shaddar ya matuk'ar yin kyau sai k'amshi yake saki haka gwaggo ma atamfa tasa da sabuwar hijab kalar zanen atamfar tayi fess da ita sai kuma Hajiya Fatuu ikon Allah mai jallabiya ta had'u harta gaji, takalmanta golden masu tsini da haisam ya siya mata ta sanya hakan yasa jallabiyar tai mata daidai don dama ta d'anyi mata yawa kad'an, sarka da yan kunnan da gwaggo ta siya mata ta sanya sai agogo Wow abun dae sai Mutum ya gani da idonshi dama bak'ar jallabiyar adon sak'a golden gareta da stones sai tayi kamar yar balarabiya, hotuna Amadu ya fara yi masu cike da farinciki kowa bakinshi a washe suna cikin yin hotunan Hajiya ta kirasu a waya tace su fito, bayan sun fita gwaggo ta rufe gidan suka nufi Jeep d'in hajiya dake fake ita da Saude ne a baya sai Tk dake tuk'a Motar sun sha adonsu suma Hajiya na sanye da rantsattsar lifaya sai salki take, baya tace gwaggon ta shigo shi kuma Amadu tace ya zauna gaba gefen Tk ita kuma Fatuu tace mata taje wurin Yayanta sai ya taho da ita daga haka tk yaja suka tafi, gidan Hajiyar ta nufa a nutse take tafiyar idonta akan kafafunta kaman mai counting steps dinta, tana gab da zuwa kwanar gate Mercedes Benz d'in Haisam ta karyo kwanar hakan yasa ta ja gefe da sauri, tsayawa yay saitinta ta bud'e gaban ta shige, tana shiga suka hada ido da Haisam ta sakar mashi murmushi yana sanye da wata kwankwatsetsiyar, dakakkar, bugaggar hadaddar kuma rantsattsar farar shadda wadda ko makaho ya shafa sai ya gane mai kudi ce sosae, shigar komae white yay ya fito a balarabenshi sak ga wani fitinannan kamshi mai cika hanci na tashi cikin Motar hadi da ni'imtaccen sanyin Ac mai ratsa sassan jiki, barka da salla tace mashi ya amsa ta hanyar jinjina mata kai yaja Motar suka tafi suna dab da lungun su Haulat sai gata ta fito tanata sauri don tun jiya Fatuu ta gaya mata ta shirya su bi su Hajiya sallah, sam bata gane su ba don ba'a gane wanda ke cikin Motar, "Lah ga Haulat gidanmu zata mutafi idi tare" Fatuu ta fad'a da sauri, burki yaja ya tsaya tana niyyar kai hannu ta bud'e kopar taga ya sauke mata glass d'in hakan yasa ta lek'a kanta ta kwala ma Haulat d'in kira, koda ta juyo taga Fatuu bud'a ido tai tana kallonta cike da mamaki, da hannu tay mata alamar ta taho hakan yasa ta nufo Motar, alamar ta shigo tai mata ta kai hannu ta bud'e kopar baya ta shiga, har sai da ta lumshe idanunta kafin ta daidaita zamanta yaja suka tafi, gaidashi tay tayi mashi barka da sallah ya amsa mata a hankali, bayan sun isa a waje can gefen Masallacin ya parker Motar don Area d'in wurin dankam take da Motoci bayan sun shiga sashen Mata suka nufa anan kuma suka hango su gwaggo don suma basu dad'e da isa ba, Alhamdulillah anyi salla an gama lafiya sai gaishe gaishe Mutane keyi suna yima juna barka da sallah da kuma fatan anyi ibada karbabbiya yayin da wasu suka fara daukar hotuna ciki harda su Tk da Amadu Fatuu na hango su taja hannun Haulat don suje suma ai masu hoton, Hajiya kam tuni Jama'a suka zagayeta suna ta yimata barka da salla, sosae take farinciki cikin fara'a take amsa ma Mutane don yin sallar anan ba k'aramin nishadi ta samu ba yayin da wadanda basu san wacece ba ke tambaya ana fad'a masu matar tsohon Ministan tsaro ce mahaifiyar Senator Ali Adamu Zakee kuma Mamallakiyar HAZ FOUNDATION, gidauniyar tallafa ma Marayu da gajiyayyu da kuma koya sana'oi, bayan masu kawo mata gaisuwar sun lafa ne Tk yazo yace bari yay masu hotona, sosae sukae Hotunan harda wanda Masu daukar hotuna wato photographers dake cikin Masallacin Hajiya tasa suyi masu, ganin anata hotuna ba Haisam ne yasa Fatuu wawwaigawa ko zata hangoshi amman sam bata ganshi ba hakan yasa ta fita daga cikin masallacin ta nufi Motarshi aikuwa sai gashi a ciki ya d'an kwantar da kanshi kafarshi guda ya zurota waje don kopar a bude take yanata latsa wayarshi, ba komae ne yasashi dawowa cikin Motar ba illa kallonshi da ake tayi shi kuma ya tsani kallo ba kamar Mata wasu har nunashi suke suna fad'in da gani ba d'an Nigeria bane, cikin Masu kallonshi harda Boss Bature can na hangota ta saki baki tana kallonshi har tana fadin " bala'i kuji wani wanda yaci uban Baby Junaid kyau🤣, Koda Fatuu tace mashi yazo suje ana yin hotuna girgiza mata kai yay alamar bazaije ba don shi baison yan d'auke dauken hotuna hakan a wurinshi ma kauyanci ne shiyasa in ba dole ba bai tsayawa ai ta yi mashi hotuna barkatai, jin bazaije bane yasata cewa to yayi masu ita dashi, da farko ki yay ta fara mashi magiya sannan ya shiga Camera d'in yay mata alamar tazo, ida fito da d'ayar kafarshi yay taje gefenshi ta d'an kwanto da kanta ya daukesu gaba d'aya sun d'anyi Murmushi, rok'onshi tay ya mik'e ya daukesu ta d'an jingina dashi tana dariya gashi tayi can k'asa ba tsawo amman dai ba k'aramin kyau hoton yay ba, ba kamar daya kasance sunyi shigar fari da bak'i ne, ( duk mai buk'atan ganin hotunansu yay ma Munah Bature Magana don a Masallaci d'aya sukai sallar wato Banu Commassie Masjid dake a GRA, can na hangota ta la6e ajikin wata bishiya tana d'aukarsu ba tare da saninsu ba, kwalelenki dae😹). **** **** **** Bayan sun bar Masallacin saida suka biya gidan Sarki, bayan sun fito daga gidanne gwaggo tace ma Amadu ya hau keke napep yaje ya amso mata aikin abinci data bada sai ya iskesu gida, Hajiya na jin haka tace to ba a Mota suke ba miyasa bazasu biya su amsa ba kawae gwaggon tace ai kada a 6ata masu lokaci Hajiyar tace ai ba wani abu bane suje kawae, bayan sunje sun amshi abincinne suka nufi gida lokacin tuni su Fatuu sun koma don suna baro gidan sarki Haisam ya wuce dasu gida ana sauke Haulat itama ta sauka tabita gidan nasu don tayi ma innarsu barka da Sallah, sosae Innarsu haulatu ta yaba da wankan Fatuu har barka da salla ta bata Haulat ta zubo masu abinci suka ci, su gwaggo na komawa gida ta zuba dukkan abincin tuwo, waina, Alkubus acikin Manyan Warmers taba Amadu ya kaima Hajiya, lokacin da ya kai mata sosae tai farinciki da abincin ba kamar Alkubus d'in ya burgeta don yayi kyau ya tashi sosae nan da nan tace ma Saude ta zubo masu su ci, kan kace mi gidan hajiya ya cika da yan yawon salla duk wanda yazo aka bashi barka da salla sai ya ruga ya fad'i ma abokanansa, haka iyaye mata duk wadda taji cewa Hajiya anan tayi Sallah sai ta zuba abinci tace akaimata nan aka cika hajiya da abinci sai faman farinciki take tana sawa ana daukarta hotuna da yaran unguwa daga baya kuma iyayen suka rinka shigowa suna yi mata barka da shan ruwa da fatan anyi salla lafiya. ( zaka kasance acikin farinciki matukar kaima kana sanya Mutane farinciki kuma Allah yana cigaba da taimakon bawansa matukar bawan na taimakon na kasa dashi) Ana yin sallar Azahar Fatuu ta canja kaya tasa fitted gown dinta don kuwa da gwaggo ta amshe tace bazata sakasu ba sai taje takai kararta wurin hajiya tace gwaggo ta amshe mata kayan da Ya Handsome ya dinka mata tace wai bazata sasu da salla ba hakan yasa Hajiyar kiran gwaggon a waya ta tambayi dalilin amshe kayan gwaggo tayi mata bayanin irin dinkin da fatun tasa akayi mata, karshe dae Hajiyar tasa gwaggon ta bata kayan tace tunda an riga an dinka ba yadda za'ai sai hakuri, wurin gwaggo taje ta d'aura mata kallabi, da tace bata d'aurawa daga baya kuma ta amsa tana d'aura mata tana k'orafin yadda rigar ta kamata, d'auri mai kyau tayi mata ga gashinta ta faka shi ya sauka abayanta don ma gwaggo ta lankwashe shi, tana komawa d'akinta tasa takalmanta ta dauresu ta kuma sanya sarkar da Haisam ya siya mata wadda tamkar gold haka take, d'aura gyalenta tay akan kafad'a ta d'auki yar jakarta mahadin takalman daga haka ta fito ta nufi gidan Hajiya, ta k'aramar kopa tabi ta nufi part d'in Haisam, tana shiga cikin falon taja ta tsaya a bakin kopa tana bin Mutanen dake a cikin Falon da kallo wad'anda maza ne guda ukku kowannensu yaci gayu cikin sabuwar shadda gaba d'aya falon ya k'ara hadewa da wani irin hadaddan kamshi mai bugun zuciya, wurga ido taci gaba da yi tana son hango Haisam saidae babu shi acikinsu, "Welcome Mom Zarah ki shigo mana" taji wani cikinsu ya fad'a hakan yasa takai idanunta da sauri kanshi, Abbas ne yana sanye cikin galleliyar shadda ash ya d'an kishingida ajikin kujera dama gaba dayansu suna akan L-shape ne ga kayan abinci birjik kan c-table da alama basu dad'e da gama ci ba don duk ga lemu nan acikin glass cups an rage, koda tay arba da Abbas sai kawae ta sakar mashi Murmushi don yanzu sun saba dashi sosae, mayar mata da martanin Murmushin yay ya nuna mata armchair alamar taje ta zauna saida ta duk'a ta cire takalmanta kafin ta nufi kujerar don ta zauna yayin da sauran Mutum biyun suka bita da ido, gaishe dasu tai gaba d'aya bayan ta zauna suka amsa banda Mutum d'aya da shi jinjina mata kai kawae yay fari ne don duk yafi su haske saidae sam bai kai Haisam ba yana sanye da farar shadda ya aje hularshi gefe kaman dae sauran suma duk sun cire hulunansu hakan kuma ya bayyanar da yalwatacciyar sumar kansu, d'ayan kuma za'a iya kiransa da Chocolate yana sanye da Brown shadda wadda ta hau fatar jinkinshi sosae har sun so sajewa, gaba d'ayansu ba mummuna kuma kallo d'aya zakai masu kasan yan hutu ne don shi mai farar Shaddar wato Saleem babanshi ne Deputy Governor na yanzu sai mai Brown shaddar wato Najeeb shi babanshi ba mai mukamin gwamnati bane saidae shahararren mai kudine a Katsina wanda idan za'a lissafa masu kudi a Nigeria to tabbas za'a fade shi, gaba d'ayansu Abokan Haisam ne tun yarinta don shi Saleem d'in ma tare su kae karatu akasar waje. "Mom Zarah ina barka da Sallah na?" Abbas ne yay Maganar, juyawa tai ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta rufe bakinta da tafin hannunta tana dariya, "Ba Dariya na tambayeki ba, ko bazaki bani bane?" girgiza mashi kai tayi alamar zata bashin yace to ta bashi, mik'ewa tay ta nufi inda yake ta fiddo yan d'ari biyu guda biyu sabbi dama yanzu Tk ya bata su ta mik'a mashi, mik'o hannu yay ya amsa yace ya gode har zata juya yace ta tsaya shima ya bata, sabbin yan d'ari biyar guda hudu wato 2k ya miko mata, da tak'i Kar6a yace to shima ga nata baiso hakan yasa ta amshi nashin tace ta gode tana niyyar sake juyawa taji ance "Mu don ba'a sanmu ba kenan baza'a bamu ba", da sauri takai idonta kan sauran Mutum biyun nan take ta gane wanda yay Maganar wato Najeeb saboda shine ke kallonta shi Saleem wayarshi yake daddannawa, mik'a mashi wanda Abbas ya bata kawae tayi don wani irin kallo yake binta dashi, "No ba nashi nike so ba, muma naki zaki bamu" ya fad'a yana wani lumshe mata ido dama kuma haka yanayin idonshi yake sai yaso yake waresu, murya na d'an rawa tace "ai ba sauran irin wanda na bashi yan k'anana ne suka rage" "No problem muna so" ya fad'a, hannu na rawa saboda kwarjinin da yay mata ta bud'e cikin jakar ta fiddo naira hamsin guda biyu da yan ashirin suma biyu naira d'ari da Arba'in, mik'a mashi su tayi duka sai ya cire hamsin d'aya da ashirin wato naira 70 ya bata sauran yace taba Saleem d'in da kanta, d'an matsawa tay ta mik'a mashi ganin bai kalleta ba yasa tace "gashi" a wani slow ya d'ago da kyakkyawar fuskarshi yabi kud'in da take mik'o mashin da kallo kafin ya d'aga manyan idanunshi ya kalleta, "Barka da salla ne aka baka kaima" Najeeb ya fad'a, wani kayataccen Murmushi ya sakar mata kafin ya d'an girgiza mata kai alamar a'a kaman an masa dole kuma ya furta "thanks" sak abubuwan shi shigen na Haisam ne ita kanta Fatuu hakan take ayyanawa aranta, juyawa tai ta mik'a ma Najeeb kud'in tace "gashi to ka had'a shi bai so" Murmushi ya sakar mata yana d'an motsa madaidaicin bakinshi ya kai hannu ya kar6a, har zata juya ya tsaidata da fad'in "nima bari in baki tawa Happy sallan" dakatawa tai ta tsaya tana kallonshi ya kai hannu cikin Aljihun rigarshi sai gashi ya fiddo sabbin yan dubu dubu zasu kai dubu goma in ma basu fi ba ya mik'a mata, zaro ido Fatuu tay lokaci guda ta fara girgiza mashi kai alamar a'a, "Abun wayo ne kenan, ke kin bani ni bazaki amshi nawa ba?" ya fad'a had'i da d'age mata gira, "Ai naka sunyi yawa sosae ni yan kad'an na baka" ta fad'a tana yamutsa fuska, d'an ta6e baki yay ya gyara kishingidar da yay kafin yace "abunda kike dashi kika ban nima kuma wanda nike dashi na baki ko" tana niyyar k'ara cewa wani abu taji Abbas yace ta amsa juyawa tai ta kalleshi ya jinjina mata kai alamar ta amsa d'in, ba don taso ba ta kai hannu ta kar6a saboda ita tsakaninta da Allah kud'in sunyi mata yawa bata san ya zata yi dasu ba, godiya tayi mashi tana juyawa Haisam ya fito daga Bedroom dinshi ya canja kaya zuwa shadda Navy blue an mata fav dinkinshi wato Sen style kanshi ba hula sumar nan tasha gyara sai salki take just Ma sha Allah, yana shigowa cikin Falon ya k'ara karad'ewa da wani kalan kamshi na daban, d'ayan 6arin L-shape d'in yaje ya zauna idanunshi akan fatuu da itama shi take kallo tunda ya fito tana ganin ya zauna ta nufeshi a lokacinne kuma Najeeb ya waiga yana tambayar Abbas wai wacece ita yana murmushi yace mashi Mom d'in H,zakee ce a gidajen makwabta take, jinjina kai Najeeb d'in yay kawae, tsaye tay agaban Haisam fuskarta da d'an Murmushi nuna mata gefenshi yay alamar ta zauna, tana zama ta mik'a mashi kud'in dake hannunta wanda suka bata, "Na miye ne?" ya tambaya idonshi akanta, " Barka da salla ne wai suka ban", jinjina kai yay "naki ne ai" "To ai sunyi yawa bansan ya zanyi dasu ba" shiru ya d'anyi sai kuma yace "ki kaima Grandma d'inki", d'aga mashi kai tayi alamar toh, ganin ta ruk'e su ahannu yace mata ta saka cikin bag d'inta, tana kokarin sakawa jakar ta kufce mata sai ga kayan kwalliya sun zubo waro ido tay ta d'ago ta kalleshi ganin kayan shafan yake kallo yasa ta rufe fuskarta alamar kunya, d'an ta6e baki yay ya kai hannu k'asa ya d'aukko lip glow d'in daya fad'a kan k'afarshi ya mik'a mata ta amsa tana sussunnar da kai, bayan ta saka komae cikin jakar ta d'ago ta kalleshi yasa hannunshi guda ya d'an shafi gaban kanshi can k'asan makoshinshi ya furta mata " Kije wurin Hajiya" yadda yay Maganar in ba ita dake kusa dashi ba ba wanda yaji abunda yace dama kuma duk Maganganun da Fatun tayi mashi k'asa k'asa da murya tai mashi su, d'aga mashi kai tayi alamar to kafin ta mik'e, k'ara yima su Abbas da Najeeb dake kallonta Godiya tai kafin ta nufi bakin k'opa tasa takalmanta daga haka ta bud'e kopar ta fuce........ ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 6️⃣2️⃣ .......Tana fita Najeeb ya maido idonshi kan Haisam yace "Zakee wannan Mom en naka gaskia am in", kafin Haisam ya bashi amsa Saleem ya d'ago ya kalleshi da expression na mamaki akan fuskarshi yace "Are u ok Najeeb, wannan abun ne zaka ce kana ciki?" ware ido Najeeb yay kafin yace "look dude in ana magana irin wannan just keep ur mouth shut, kai dama ai bakasan mi Duniya ke ciki ba kai da H,Zakee har gara ma shi yana da d'an dalili kai ko in ba cutar kanka ba ba abunda kake sam baka san miye dad'in duniya ba, to ni naga abunda nagani atattare da girl din can..." tun kafin ya rufe baki Abbas ya bushe da wata yar iskar dariya hakan yasa Najeeb ya maida idonshi kanshi "Yauwa My Man kai nasan kaga abunda nagani ko?" jinjina mashi kai Abbas yay alamar eh, "Obviously, Wannan yarinyan ta samu kiwo ba k'aramar Mace za'ai ba wllh so H,zakee in son Mom d'innan naka pls ya za'ai?", sai lokacin Haisam ya kalleshi don tunda ya fara Maganar idonshi na akan wayarshi amman yana jin duk abunda yake fadi, "Zatayi karatu ne" ya bashi amsa a takaice, "Daidai kenan, kaga sai kawae in wuce da ita Canada tana karatunta nima ina aiki na" dan ta6e baki Haisam yay sai kuma yace " ita wife en naka fa?" "Ita ai dama kaga ta gama karatunta kuma ta matsa tana son yin aiki yanzu zata zauna nan ne ba kowane lokaci zamu kasance tare ba kaga ita Mom d'in naka inna tafi da ita shikenan bani ba maraici sai taita karatunta acan......" "Ta kuma yi karatunka ba" Abbas dake ta dariya ya katseshi, shima Najeeb d'in wata yar iskar dariya yasa yace "yauwa My Man dad'ina da kai ganewa, ai dama dole ne wannan" yana kai Maganar ya mik'a ma Abbas hannu suka tafa, Sigh Saleem yay ganin da gaske Najeeb d'in yake yace "But kai can't u see she's young?" "Ba wata young tsaf zata dauki d'awainiya na, kai bakasan abun ba'a nan yake ba" d'an ta6e baki Saleem yay bai ce mashi komae ba, "Pls zaki am Serious wllh ni zan reneta indai zaka sa abani", sauke 6oyayyan ajiyar zuciya Haisam yay, sarai yasan halin Najeeb mugun son mata gareshi kaman Abbas gwara ma Abbas shi abunshi a bakine shi kam Najeeb d'an sharholiya ne banda neman mata har shaye shaye yana yi, sunsha zama su bashi shawara kan irin wannan mummunan halin sai yace masu ya bari amman kuma ba barin yake ba, koda ace Fatuu ta isa aure bai ta6a yarda Najeeb ya aureta balle kuma a yadda take d'innan, ganin ya kafeshi da ido alamar dae shi yake jira yasashi d'an tamke Fuska yace "She's young so she can't get married now, Period!" daga haka ya maida idonshi kan wayarshi yaci gaba da daddanata, d'an ta6e baki Najeeb yay bai k'ara cewa komae ba don ya lura kaman bai son ma Maganar, Fatuu na zuwa part d'in Hajiya ta iske sunata shirin tafiya Abuja don karfe 4:30 jirginsu zai tashi, Saude ma ta shirya tsaf da sun tafi zata wuce Daura dama yar can ce acan tayi aure har ta haifi yaranta biyu kafin auren nata ya mutu sanadiyar kishiya shiyasa take bama aikinta muhimmanci don ko tunanin ma k'ara aure bata yi don bataji da dadi ba agidan mijin nata, Hajiya ta had'a mata sha tara ta arziki kaman yadda ta saba yi mata, tayi ma yaranta dinkuna harma da Mahaifiyarta tun jiya take fama da ita akan ta tafi tayi salla acikin yan uwanta yaranta su ganta suji dadi amman tace sai taga tafiyar Hajiyar, tana shiga suka hau yabon kwalliyarta Saude na fad'in su Fateema an zama yan Mata har barka da salla Hajiya ta bata amman duk da haka saida tayi mata fad'a sosae kan d'inkin data sa akayi mata tace mata sanya matsattsun kaya sam baida kyau karta k'ara sawa ai mata d'inki irin wannan ta amsa mata da to, Bayan angama Sallar la'asar atare Haisam dasu Najeeb suka shigo cikin harabar gidan daga Masallaci, Parking space suka nufa don zasu raka Haisam Airport ne dalilin dayasa ma suka tsaya basu tafi ba tun dazun, wucewa Haisam yay part dinshi don daukko abu su kuma suka jingina da Motar Saleem wadda take Jeep Toyota Prado Land Cruiser dama acikinta suka zo su duka, suna tsayen yayinda Saleem ke daddana wayarshi Fatuu ta fito daga part d'in Hajiya janye da trolley, tunda ta fito Najeeb ya kai idonshi kanta yanata kallonta yayinda ta tunkaro parking space d'in har saida ta sadda kanta k'asa don taga kallon da yake matan, a gefen Jeep d'in Hajiya ta tsaya sai Saude itama ta fito da kaya inda Fatun take tazo ta aje ta koma ta d'aukko wasu don harda kayanta saboda daga Airport itama zata wuce tasha ta tafi daura, tana cikin tsayuwar a parking space d'in ta hango Haisam ya fito daga part d'inshi hannunshi guda janye da madaidaicin trolley don ba wasu kaya masu yawa ya d'aukka ba saboda acan ma yana da wasu kayan, a d'ayan hannunshi kuma jakar laptop ce ya ruko, Fatuu na hangoshi ta nufeshi cikin sauri, jin rigar tata bata barinta yin saurinne yasa tasa hannu d'aya ta d'an d'age ta sama, Najeeb dake ta kallonta ganin ta nufi Haisam yasa ya kalli Abbas da shima ita yake kallo yace "My Man tell me d truth, kodae h,zakee yana son girl dincan ne?" juyowa Abbas yay da d'an murmushi ya kalli Najeeb yace "No ba haka bane kaima ai kasan komai game dashi", "Yess, but is possible ai k'ilan shiyasa yak'i bani goyon baya" dariya sosae Abbas yake ganin yadda Najeeb d'in ya zauce kan k'ank'anuwar yarinya, "No ka fahimta dude wllh ba wani abu tsakininshi da yarinyan kawae dai he's like a guadian to her...." nan Abbas yaba Najeeb labarin yadda Haisam d'in yasan fatuu, d'an ta6e baki Najeeb yay kafin yace "if dat's it why bazai goyi bayana ba tunda kaman ma taimakon girl d'in zanyi kenan ai", "Serious Najeeb yarinyan can k'aramar yarinya ce sosae gaskia bai kamata ai mata aure ba" "Ba tagama sec skul ba?" girgiza kai Abbas yay "Ko Junior secondary bata gama ba" d d'an bud'a ido Najeeb yay alamar mamaki kafin ya waiga ya kalli Fatun ya furta "amman dae akwae wani abu" "What?" Abbas ya tambaya idonshi akanshi, juyowa yay ya kalleshi ya d'an yatsina fuska had'i da d'age gira yace "Shape, wato yarinyan nada k'ira ba k'araman Babe za'ai a wurincan ba wllh" dariya sosae Abbas ke yi hada dafe ciki kafin ya tsagaita yana kallon Najeeb d'in "wato kai indae mace tayi maka baka da sauran zaman lafiya ko?" d'age mashi gira yay "kaga laifina ne ai don mu akayi su ko, cikakken jin dadin duniyar nan ai bai samuwa saida su Mutumi na" "Hakane, amman nan dae saidai kayi hakuri toh aje aci gaba da samun jin dadin wurin ta gidan" cike da iskanci Najeeb yace "ita kadae ai bata isana" waro ido Abbas yay "Don't tell me har yanzu Najeeb ba ka daina womanizing ba?" wani d'an iskan kallo yay mashi kafin yace "Yea nabari since wannan d'in baka ji nace aurenta zanyi bane" daga haka ya kawar da kanshi shi kam Abbas girgiza kai kawae yay don yasan ba lalle in gaskiya ya fad'a ba, ba kamar yanzu da ba zaune yake anan kasar ba, Tana zuwa gaban Haisam ta tsaya tana mashi Murmushi hakan yasashi dakatawa yana kallonta fuska a sake, hannu ta kai ta kama trolley d'in tace "Kawo na ja Ya handsome" sakar mata yay batare daya ce komae ba suka nufi parking space d'in, "Ya Handsome yaushe zaka dawo?" ta tambaya had'i da d'an kallonshi, "I won't stay long" ya bata amsa ba tare daya kalleta ba, "Tk zai kai ki duk inda kike so" taji ya k'ara fad'a, kai ta d'aga mashi alamar to sai kuma tace "in ina son yin waya da kai fa?" "Ba Auncle d'inki nada phone no dina ba, ki amfani da wayanshi" turo baki tay "to ai shi wani lokacin sai yayi man wulakanci yake bani wayarshi" "Grandma dinki fa batada waya ne?" "Tana da ita amman yar k'arama ce ni kuma so nike muyi Vedio call don in nuna maka sauran gayun salla na" sai lokacin ya juyo ya kalleta suka had'a ido wai kuma sai tasa tafin hannunta wanda bada shi ta ruk'e trolley d'in ba ta rufe idanunta alamar kunya, d'an Murmushi yay kafin ya juya yana fad'in "in kinyi gayun ask Tk to call me" bud'e idon tay tace to lokacin kuma suka k'araso parking space d'in, amsar trolley d'in Abbas yay ya bud'e boot d'in Motar ya saka alokacin Hajiya da Saude suma suka k'araso wurin, k'ara gaidata sukai duk da dama da suka zo sunje har part d'inta sunyi mata barka da sallah, "Wai ina Tukur ne" Hajiya ta fad'a idonta akan Saude kafin ta bata amsa sai gashi ya taho daga baya yana k'arasowa ta bashi umarnin saka kayayyakin cikin Jeep dinta, "Yar Bafullatana zaki raka Yayanki ko?" fatuu dake tsaye taji an fad'a a gefenta hakan yasa da sauri ta waiga ta kalli wurin Najeeb ne zaune a back seat na Jeep d'in Saleem kafarshi guda awaje, Murmushi ta d'anyi mashi kafin tace wani abu Abbas dake a kusa dashi yace "ai dole ta raka Ya handsome d'inta ko?" jinjina mashi kai tay alamar eh, "Fateema taho to ki shiga mutafi kar mu makara jirgi bai jira, in kuka raka mu sai ku sauke Saude a tasha" Hajiya ce tai Maganar tana mik'o ma Fatuu hannu, shiga gaban Motar tayi Hajiya da Saude na a baya sai Tk da zai tuk'a daga haka ya fito da ita cikin harabar lokacin suma su haisam Jeep dinsu ta fito shida Saleem ne agaba sai Najeeb da Abbas a baya, Motarsu ta fara nufar gate da aka zuge masu suka fice sai ta Hajiya ta rufa masu baya bayan ta tsaya sun k'ara yin bankwana dasu Officer ita da Saude dama ita Gwaggo tun kafin su fito ta kirata tayi mata sallama har tana cewa bari tazo tayi masu rakiya tace tayi zamanta taji da bak'in Salla. A sauka lafiya Hajiyar Sanata 🛫. Duk ranta ba dad'i suka baro Airport d'in, su Abbas sun wuce su kuma suka nufi tasha don sauke Saude, suna zuwa ba 6ata lokaci ta samu mota sukai mata sallama daga nan Tk ya bazama dasu cikin gari, yawo sosae yay da ita don har gidan abokansa ma Makaranta ya kakkaita harda gidansu budurwarshi, sosae Fatuu ta samu barka da sallah don har jakarta ta cika da kud'i ga kayan kwalama da aka babbata iri iri ba kamar agidansu budurwar Tk d'in, basu suka dawo gida ba sai da akai Magrib lokacin tuni su Haisam sun sauka Abuja don har tayi waya dashi, lokacin data dawo gida ta nuna ma gwaggo kud'ad'en data samu sosae ta girgiza da ganin uban kudin ta hau tambayar a ina ta samu kudi haka nan ta kwashe duk inda ta samun ta fada mata harda wanda abokan Haisam suka bata karshe dae gwaggon taba kudin bayan ta ciri yan kad'an wanda zata ruke gwaggo kuma tai mata fadan banda rokon Mutane kudi ta rantse mata kan bata rokon kowa kuma in aka bata ma sai tace abarshi in aka matsa ne take amsa, tsakar gida ta baje tanata cin abubuwan data samo tanata zuba surutu gwaggo nace mata ta bi ahankali da ciye ciyen nan, karshe saida gwaggon tace in cikinta ya lalace ai taga yadda za'ai tayi yawon sallan sannan ta lafa da ciye ciyen don ta gaya mata Ya Handsome yasa Tk ya kaita duk inda take so. Washe gari tun 9 ta shirya cikin riga da skirt na lace dinta, tayi kyau har ta gaji kuma suma sun kamata sosae hakan yasa koda ta gama shiryawa bata shiga dakin gwaggo ba tai ficewarta dama kuma bacci take, gidan Hajiya ta nufa bayan sun gaisa da Officer dake zaune shi kadai yana ta yabon gayun data yi, ce mashi tay wurin tk tazo zasuje kallon hawan bariki yace ta shiga ta duba in ya tashi, tana shiga ta nufi Bq can bayan part d'in Hajiya don acan yake da zama, koda taje kopar dakin nashi a rufe take hakan yasa ta hau kwankwasawa shiru ba'a bud'eba har saida ta k'ara sautin bugun sannan taji muryarshi yana tambayar waye, ce mashi tay itace sannan yazo ya bud'e da ka kalleshi kasan daga bacci yake, yana ganin Fatun ya d'an buda idanunshi cikin muryar bacci yace " ya mukai dake jiya, ba sae goma nace zamu fita ba?" gaidashi tay tana tura baki tace " to ai goman ya kusa ko tunda yanzu tara fa ta wuce ba sai ka tashi ka shirya ba" d'an jujjuya kanshi yay alamar baccin bai isheshi ba, "Kije to in nagama shiryawa zanzo" "To ka kira man Ya handsome" amsa mata da ok yayi kafin ya juya cikin d'akin, hannunshi ruk'e da wayarshi ya dawo bakin kopar ya fara kokarin kira mata Haisam din, "Vedio call zaka kira shi" ta fad'a cike da zumud'i, "No bari dae in kirashi in ya d'auka sai kice ya kira ki Vedio d'in don bamma tunanin ya tashi bacci yanzu" sau biyu ya kira ba'a d'aga ba hakan yasa yace mata gaskiya bai tashi bacci ba amman tace wai a k'ara kira har ya tashi jin hakan yasashi bata wayar yace taje ta kira da kanta in ya fito zai amsa cike da murna tace to, gida ta koma ta shige d'aki tana ta kira dama tun kan hanya take kira bai d'aga ba sai can yai picking call d'in lokacin tana zaune gefen gadonta, da sauri ta kara wayar a kunne ko sallam bata yi ba ta kira sunanshi, "Ya handsome " shiru bai amsa ba har saida ta k'ara kira sannan cikin murya mai tattare da bacci ya fara Magana "Zarah hope u'r ok" maimakon ta bashi amsa sai cewa tay "tun d'azun nike kiranka amman kaki ka daga", "Wayan yana vibrate ne, any problem?" "A'a dama kwalliyata ta yau zan nuna maka ka maida Vedio call kaga uban gayun dana yi", ba tare daya k'ara cewa komae ba ya shiga maida kiran Vedio, yana kwance akan wani katafaren gado ya lullube rabin jikinshi da wani lallausan katon bargo blue don yanayin weather d'in can akwae d'an sanyi saboda samun ruwa da suke ba kamar Katsina ba gashi ya saba da Ac indae ba sanyi yayi tsanani sosae ba to bai zama ba tare da ya kunnata ba, Fatuu na ganinshi ta waro ido had'i da washe baki tana mashi dariya shima Murmushi yake mata yana daga kwance kanshi saman farin pillow haka rigar jikinshi kimono robe ce fara sol, "Ya Handsome wannan gadon kane?" kai kawae ya d'aga mata alamar eh, "To ina Hajiya da sauran yan gidanku,?" lumshe ido yay kaman bazai bata amsa ba da gani still da sauran bacci a idonshi a hankali kuma ya ware idon slowly yace "suna apartment nasu" "Kenan anan ma bangarenka dabanne?" kai ya d'aga mata alamar eh, "da an shigo bangaren naka yake kaman gidan Hajiya?" kai ya girgiza mata kafin cikin muryar bacci ya furta "Upstairs", zaro ido tay da mamaki tace "kai, gidanku na nan Abuja kenan benene tunda kace a Saman bene kake" kai ya sake d'aga mata ya fara kokarin tashi zaune don wani irin bacci ne ke fuzgar shi gashi sam baijin dad'in Vedio call d'in a waya don yafi sabawa da yayi a laptop, jingina bayanshi yay da kan gadon ya ruk'e wayar kan cinyoyinshi dake lullu6e da bargo, yana tashi zaunen da mamaki Fatuu ta kira sunanshi "Ya Handsome" bud'a mata ido yay ba tare daya amsa ba, "Ashe yadda kake da gashi a hannunka har anan ma kake dashi" cike da al'ajabi tay Maganar tana nuna kirjinta alamar inda take magana akai, a hankali ya d'an duk'ar da kanshi ya kalli kirjin nashi dake abude sakamakon rigar dake jikinshi haka take bata rufe kirji in ba'a sa wata a ciki ba ga gashin nan liya liya a kwance saidae baida yawa sosae don yana rageshi, d'agowa yay ya kalleta ganin ta kafe wurin da ido tanata kallo yasashi kai hannu ya idasa jawo bargon sama, kallon fuskarshi tay suka had'a ido don kar ta sake yin Magana kan gashin yasashi cewa "kince zanga kwalliyanki" da sauri tace eh tare da saukkowa daga kan gado ta mik'e tsaye tun daga kan k'afafunta ta fara nuna mashi har saman fuskarta tana ta dariya, "Nayi kyau sosae ko?" ta tambaya, fuska a sake ya furta "Yeah" shiru sukae na wani lokaci tana ta kallon fusakarshi tana dariya don dad'in Vedio Call din take ji shi kuma sai faman lumshe ido yake can yace "bazaki je yawo sallan ba?" da sauri tace "zanje, yanzu ai naje wurin Tk d'in don mu tafi kallon salla na iskeshe bai shirya ba amman yace yanzu zai shirya sai mu tafi" kai ya jinjina mata, "Kai bazaka kallon Sallan ba", " ba'a yi anan" "Hawan barikin?" d'aga mata kai yay, "Ai da yake ance Abujan duk yan gayu ne k'ilan baku zuwa kallo shiyasa ba'ayi, yanzu saidae kaita zama a gida kenan?" d'an Murmushi yay "No zan fita ba yanzu ba" gyad'a kai tay sukae shiru ita dae tana ta Murmushi shima fuskarshi a sake take yana cigaba da lumshe ido alamar dai har yanzu baccin yake ji can ya d'an langa6ar da kanshi da alama baccin yake, tsuru Fatuu tay tanata kallon fuskarshi, "Wllh Allah Ya Handsome kanada bala'en kyau" yaji Maganar ta doki dodon kunnanshi, a hankali ya bud'e idanun akanta yana kallonta tana ganin ya bud'e idon taci gaba da cewa "bakaga da ka rufe ido ba yadda ka k'ara kyau" shiru kaman bazaice komae ba can kuma yace "kije kiga if he's ready" "Tk d'in?" ta tambaya, kai ya d'aga mata alamar eh, "To amman in bai shirya ba zan k'ara kiranka" shiru ya d'anyi sai kuma ya d'age gira yace "bazaki barni nayi bacci ba ko" kyalkyacewa tay da dariya ganin yadda yai mata Maganar tace "to na barka kayi bacci Sweetheart Ya Handsome d'ina, amman fa in muka dawo zan kiraka kaima ka nuna man gayun sallan ka" tay Maganar tana jaddada mashi da kanta, d'an guntun Murmushin gefe yay ya daga mata kai alamar to daga haka ta daga hannu tana yi mashi bye bye shima ya d'aga mata hannu guda kafin ya katse kiran, Lokacin data maida ma Tk d'in wayar yana cikin shiryawa don bayan tafiyarta kwanciyarshi yay ya k'ara yin bacci, cewa tay zata jirashi a parking space yay sauri ya fito yace mata to, bayan wani lokaci tana jingine da Motar Hajiya sai gashi ya fito ya dau wankan voile sai kamshi yake zabgawa, tana ganinshi ta fara kokarin bud'e Motar ya dakatar da ita da fad'in "Yau ba cikinta zamu fita ba" "To a wacce zamu?" ta tambaya, Corolla S d'in Haisam wadda ranar data fara ganinshi ita ya hau tk ya nuna mata, da mamaki tace "To baya rufe abunshi ba taya zamu hau ta?" "Ai ya bani makullinta yace ko zamuyi amfani da ita" ya fad'a yana kokarin zura key d'in ya bude Motar,Murmushi ta saki tana jinjina kirkin Haisam a ranta, Bayan sun fita saida suka tsaya suka d'auki Haulat kafin suka wuce. ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 6️⃣3️⃣ .......Bayan sun gama kallon sallan bazama sukae cikin gari ana yin la'asar Tk yace bari ya maidasu gida don akwae taron da zaije shida abokanshi Fatuu tace to ai basu gama zuwa inda suke so ba yace ta bari gobe tunda ba wani hawan za'a k'ara yi ba sai su fito da wuri suje duk inda suke so sannan ta amince ya maidasu gida, a gidansu Haulat suka sauka sai Magrib ta koma gida ana gama sallan isha taje shago wurin kawu Amadu tace don Allah ya kira mata Ya Handsome, tsawon lokaci ta d'auka tana waya dashi duk da shi ba wata Magana yake ba itace mai surutun wani lokacin tayi Maganar arziki wani lokacin kuma mara kan gado shi dae sai dai yay murmushi ko ya bata yar gajerar amsa har tambayarshi Hajiya tayi yace bai gidan ta kira wayanta, karshe dae saida ya nuna mata zaiyi wani abu sannan ta kyaleshi sukayi sallama, Washe gari ma kaman jiya tunda wuri ta shirya taje wurin tk lokacin ya tashi amman bai gama shiryawa ba tace bari taje wurin Haulatu in ya fito sai ya kirata a gidan harda jaddada mashi kar ya dad'e fa ya dai amsa mata da to, bayan yaje ya d'aukesu sosae sukayi yawo don duk wani wurin shakatawa kama daga park, zoo da sauransu dae har wani had'addan eatery ya kaisu suka ci duk abunda suke so suka kuma dauki wanda zasu tafi dashi duk ya biya kud'in, dama kuma duk inda suka je shike biyan kudin shiga da sauran abubuwan don Musamman Haisam ya bashi kudi saboda hakan, sai Magrib suka koma gida sun gaji likis sun kuma yo guzurin abubuwa sosae sannan duk inda suka je saida Fatuu tasa photographer dake wurin yay mata hotuna za'a turo ma Tk shi kuma sai ya tura ma haisam wad'anda akayi masu kuma da Haulat tace in an turo zata yi ma kawu Amadu magana sai ya tura mashi su, Washe gari ya kama kwana ukku da salla tk na cikin sharar baccinshi da safe ya jiyo sautin bugun kopar dakinshi koda yace waye Fatuu tace itace har saida gabanshi ya fad'i kafin ya taso ya bud'e mata, bin ta da ido yay bayan ya bud'en tana tsaye taci gayu da shaddar da hajiya ta d'inka mata don jiya voile d'in tasa, tana ganinshi ta turo baki tace "kai Tk wai bacci ma kake yi baka shirya ba kullum sai na jira ka" "Ina zamu kuma" ya tambaya da mamaki, "Yawon salla mana" jinjina kai yay yace "yanzu duk uban yawon da muka yi bai isa ba, ko inafa munje ina kuma zamu k'ara zuwa?" "To ai kayan sallan nawa basu k'are ba, ko sai in sanyasu in zauna gida" ta fad'a tanata faman tura baki, d'an Murmushin yak'e Tk yay kafin ya tambayi kayan sallan nata kala nawane tace mashi kala tara ne yau tasa na biyar yanzu saura kala hud'u, waro ido Tk yay jin har nan da kwana hud'u masu zuwa sai sun fita, ce mata yay ta bari to sai zuwa d'an anjima sai su fitan tunda jiyan sun je wurare da yawa, da farko k'in yarda tay sai daga baya ta amince akan kafin sallar azahar zai zo su fita yace to, tana tafiya ya fara tunanin nemawa kanshi mafita don tsakani da Allah ba k'aramin takura zaiyi ba ace har nan da kwana hudu masu zuwa yana fita da ita kuma dae ba yadda zaiyi dole yai mata yadda yake so in ba haka ba yasan fad'i ma Haisam zatayi shi kuma ba zai so hakan ba koda kuwa haisam d'in ya fahimce shi, Wuraren karfe 12 yaje ya dauketa koda suka biya ma Haulat cewa tai su tafi kawae Innarta tace yau bazata fita ba ita zata kula da gidan don innar tasu ta tafi Unguwa hakan yasa suka tafi, Gaba d'aya Tk baiji dad'in fitar ba har saida ta k'ule shi don gidaje tasa ya rink'a kaita na yan'uwansu su Zaliha da gidan Baba shehu har gidansu Nana saida taje da gidajen wasu k'awayenta gashi in ya ajeta yace zaije ya dawo sai tace a'a sai dae ya jirata ta fito abunda kuma yafi 6ata mashi rai kenan yadda ta maidashi kaman driver d'inta don ko Hajiya bata ta6a yi mashi haka ba ita iyaka in ma zai jirata in ya kaita wani wuri to baifi suje gida biyu ba, sam bai nuna mata 6acin ranshi ba amman yana ta sak'a yadda zai yi daga yau kar su k'ara fitowa, yau ma dae sai wuraren Magrib suka dawo da daddare bayan sallan isha suna zaune a tsakar gida gwaggo ke ce mata amman dai daga yau sun gama yawon sallan ko tace mata a'a ai bata sanya sauran kayanta ba gwaggon tace yakamata dae ta kyale tukur ya huta hakanan amman sai ta turo baki tace to ai dai Ya Handsome yace ya kaita duk inda take so don haka ita sai tagama sanya kowanne kaya sannan zata gama yawon sallan, washe gari ganin jiya basu fita da wuri ba yasata bari sai kaman lokacin sannan ta nufi gidan Hajiyan bayan taci gayu da d'aya daga cikin atampopin da Babanta ya kawo mata anyi mata riga da skirt ga gyale wanda gwaggo ta siya mata da takalma yauma dae tayi kyau abunta atamfar ta amshi fatarta sosae da yake adon flowers pink gareta, lokacin da ta je bakin Gate bayan sun gaisa da Officer ne yake ce mata anya kuwa Tk zai iya fita yau, cikin rashin fahimta ta tambayeshi dalili, "Ai jiya kwana yayi ba lafiya don da daddare har saida na kaishi asibiti" cikin rashin yadda take bin shi da wani irin kallo bayan ya gama Maganar tace "Tk d'inne bai lafiya bacin ko jiya lafiya lou muka dawo" yar dariya Officer yay kafin yace "in baya ga abunki hajiya fatuu ai yanzu yanzu sai Allah ko, ina tunanin wani abu yaci ya lalata mashi ciki shine ya d'ingi gudawa harda amai gaba d'aya yau da safe dana duboshi baida kuzari don ko Magana ma da k'yar yake yi" sototo tay tana kallon Officer alamar kaman dae bata yarda ba ganin hakan yasahi cewa ta shiga ta ganshi, wucewa tay ta nufi cikin gidan yana ganin ta tafi ya d'aga waya da sauri ya kira Tk lokacin yana kwance yanata sharar baccinshi kiran wayar ya tada shi don tana kusa da kanshi, bayan ya d'auka ne da sauri Officer ya sanar dashi ga Fatun nan ai kuwa wata wuntsilawa yay ya saukko daga kan k'atuwar katifarshi ya d'aukko wasu tarkacen Magunguna acikin drawer ya watsasu agefen katifar, bottle water dake saman drawer d'in ya d'aukko ya ajeshi a k'asa kusa da katifar, da sauri ya nufi kopa ya bud'e kafin ya koma kan katifar agurguje ya kwanta hadi da lullu6e jikinshi gaba d'aya da bargo yaba kopar baya, sai bayan d'an wani lokaci ta k'araso don akwae yar tazara daga gate zuwa bayan, tana niyyar kwankwasa kopar ta ganta a bud'e, d'an tura kopar tay ta rafka sallama shiru bai amsa ba ta k'ara yin sallamar sannan ta jiyo muryarshi can kasa yana cewa ta shigo kopar a bud'e take, a hankali ta tura kai ta shiga tana hango shi taja ta tsaya kaman taga abun tsoro ganinshi a kudundune cikin bargo, d'an matsawa tayi ta kira sunanshi shiru bai amsa ba ta k'ara sannan ya amsa da kyar, "Ashe wai baka lafiya?" ta tambaya tanata zare ido, kai kawae ya jinjina mata ba tare da yayi Magana ba, "Mike damunka?" shiru kaman bazai bata amsa ba can ya dan fiddo fuskarshi amman bai juyo ba don yasan daya kalleta yana iya yin dariya don dama akwae shi da yawan yin dariya, da kyar cikin irin muryar mara lafiya yace "ina tunanin Food poison ne naci ya lalata man ciki, jiya nasha wahala dakyar na samu na kira Officer ya kaini hospital har saida akai man k'arin ruwa na d'an samu sauki" yadda yake Maganar sai ka rantse da Allah bai lafiyar ita kau Fatuu k'ara zaro ido tai a rud'e jin harda k'arin ruwa akai mashi don ita a wurinta da anyi ma Mutum drip to ciwon yayi tsanani, kaman zatayi kuka ta shiga yi mashi sannu don dama ita badai tausai ba in taga mutum na ciwo duk ta damu, da kai ya rinka amsa mata can tace ya kawo wayarshi ta kira Ya Handsome ta fad'i mashi, da sauri yace " a'a ki kyaleshi kar a tada masu hankali tunda Officer ya kaini asibiti" "To bari inje in fad'i ma gwaggo, in ta gama abinci kuma zan kawo maka" ta kai Maganar tana nufar hanyar fita da sauri, yana jin k'arar rufe kopa alamar ta fita ya yaye bargon daga jikinshi tare da juyowa yana dariya a fili yace "haka kawae ki nemi maida ni bawanki, ko shi Yaya Haisam d'in nasan da yasan wahalar dani zaki bazai sani kaiki wani yawon salla ba" ya kai hannu ya d'auki wayarshi ya hau yin chat abunshi, Ko ta kan Officer dake tambayarta ta gano shi bata bi ba iyaka ta d'aga mashi kai kawae tayi gaba, gaban kiosk din Amadu ta tsaya da damuwa ta fad'a mashi Tk bai lafiya don Allah ya kira ya Handsome ta fadi mashi, ganin yadda ta damu ne yasashi tambayarta miya samu Tk din ta fadi mashi, kiran Haisam din ya shiga yi bugu d'aya ya d'aga ya mik'a mata wayar bayan ta gaidashi ne ta kwashe komae game da ciwon Tk din ta fadi mashi a rude tana ta zuzuta ciwon yace zai kirashi daga haka sukai sallama, tana shiga gida ta iske gwaggo cikin kicin itama ta hau fad'i mata, sosae ta shiga jimami har tana cewa ko wannan yawon ai yasa ma mutum ciwo, jin abunda gwaggon tace ne yasa fatun yin wuri wuri da ido jin kaman harda laifinta yake ciwon. Tk na cikin yin chat kiran Haisam ya shigo har saida gabanshi ya fadi don yasan tabbas Fatuu ta gaya mashi bai lafiya ne, a d'arare ya d'aga kiran bayan sun gaisa ne ya mashi ya jiki yace da sauki sosae jin hakan yasa haisam din cewa Zarah tace har drip aka mashi shiru yay ya kasa cewa eh don mugun jin nauyin yi mashi k'arya yake kuma yasan in yace eh zai iya tada masu hankali ba kaman Hajiya in taji, "Any problem?" yaji haisam d'in ya tambaya, cikin sanyin murya yace "ba wani abu daman ba ciwo nike ba ita na fad'i ma hakan kawae" shiru Haisam d'in yay kaman bazaice komae ba can kuma ya furta "why", ba tare daya yi mashi karya ba ya kwashe yadda sukae da Fatun na cewa sai kayan sallanta sun kare zasu daina yawon sallan kuma duk inda ya kamata suje sun je, sigh Haisam yay ta cikin wayar jin rikicin Fatun, "kayi hakuri Ya Haisam in banyi maka daidai ba" Tk ya fad'a cike da girmamawa, gently yace "No, i understand, amman kana ciwon k'arya in ya kamaka fa?", yar dariya Tk yay yace "ai ya haisam akwae inda dole saida karyar" d'an guntun murmushi yay ta yadda har saida Tk d'in yaji daga haka yay mashi sallama tare da rejecting call din, cike da murna Tk ya fad'a kan katifarshi don sai yaji kaman wani nauyi ya sauka daga kanshi, yana kwancen Amadu ya turo kopar ya shigo, turus yay ganin Tk d'in kwance yana mashi dariya hakan yasa Amadu murza idonshi don wai ko ba daidai yake gani ba, "Kaga patient na dariya ko" Tk ya fad'a yana tashi zaune, nufarshi Amadu yay yace "to ai ni waccan burkakkar ce man tayi wai kana kwance magashiyyan fa" k'ara sautin dariyar tk yay "ai hakan ta ganni ne, amman fa lafiya ta garas wllh" nan ya yi ma Amadun bayani dalilin ciwon karyar "Yarinyar nan fa ba hankali ne da ita ba wllh kai jakinta ne, amman baka ce mata ka gaji sai kayi ciwon karya?" "Ai hakanne kawae zaisa mu rabu da ita lafiya tunda kaga sani akai yi mata hakan" jinjina kai Amadu yay alamar ya fahimta suka k'ara d'an yin fira kafin ya mik'e zai tafi, "Amman ya baka kawo man abun ciwo ba to" Tk ya fad'a yana dariya, "Wake ta wani abun ciwo nida akace ma cikin ka ya lalace kana ta amai da zawo har na fara tunanin ko wucewa zakai" Amadu yay Maganar yana dariya shima, "to na biyo ka bashi ka aiko man da kayan dubiya" Tk ya fad'a lokacin Amadun zai fita, akan hanya ya had'u da Fatuu ruke da kula zata kai ma Tk Abinci kallonta kawae yay ya d'an girgiza kai ita kuma ta tura mashi baki, tana wucewa ya kira tk a waya yace sai ya shirya ga Boss dinshi nan zata kawo mashi Abinci, koda ya isa bai tsaya shago ba dama wani yaro ya bari ya jire mashi, cikin gida ya nufa ya sanar ma gwaggo game da ciwon Tk din don ta tashi hankalinta har lekowa tay waje bayan Fatuu ta sanar da ita tace don Allah yay sauri yaje ya gano ya jikin nashi yana ciwo shi kadae a gida ya sanar mata dama yanzu yake niyyar zuwa, Salati Gwaggon ta saka ta shiga tafa hannu jin ciwon bana gaske bane, "Wllh dama nasan dole ya gaji da wannan yawon, ai yama yi kokari kwana nawa suna fita kuma kullum sai wurin Magrib za'a dawo, ai da baiyi ciwon k'arya ba dama ina niyyar taka mata burki tunda ita bata da hankali bata san daidai ba" girgiza kai Amadu yay ya juya hanyar fita yana fad'in Allah ya shiryi Fatuu, tun daga ranar ba'a k'ara fita yawon ba. **** **** **** Bayan kwana tara da yin salla ranar Laraba da yamma Fatuu ta dawo daga islamiyya don sun koma tun salla da sati daya wato shekaranjiya litinin kenan, tana shigowa cikin zaure suka yi kacibus da Amadu da ya shigo daukar abu acikin d'akinshi, da sauri taja gefe don tasan yana iya rankwashinta, yar harara ya wurga mata ya nufi waje ita kuma ta nufi cikin gida, har ya fita ya juyo yace "Ke Ya Ugly d'inki ya dawo d'azun nan naga Tk ya d'aukko shi daga Airport" waro ido tai tasa tafin hannunta ta dafe kirjinta alamar mamaki, juyawa tai zata wurga jakar cikin gidan Amadu ya daka mata tsawa "baki da hankali ne ba akwae Alqur'ani ba!" sai da yay Maganar ta tuna ta nufi cikin gidan da sauri ta ajeta a gefen dakinta kafin ta juya da gudu ta fita daga gidan ta nufi gidan Hajiyar sanata, lokacin data k'arasa part d'in nashi tura kopar Falon tay ta shige cike da zumudin son ganin Ya Handsome saidae bata samu kowa a falon ba sai daddad'an kamshi da sanyin da yake saki kamar ko yaushe, kware baki tayi ta rafka uwar sallama amman shiru bata ji ko motsinshi ba hakan yasa ta nufi bakin Corridor ta k'ara d'aga Murya tayi wata sallamar nan ma dai shiru ba'a yi Magana ba tana shirin yin ta ukku taji an bud'e kopar Bedroom d'in, sanye cikin Maroon din jallabiya mai gajeren hannu ya fito fuskar nan tai wani fresh ai koda tai arba dashi gaba daya hannuwanta tasa ta rufe bakinta tana dariyar farinciki, tsaye yay a gabanta cikin Corridor d'in ya goya hannuwanshi a kirjinshi yana Murmushi don ta tare mashi hanyar da zai fita cikin falon, sosae farinciki ya lullu6e Fatuu har tama kasa Magana ji take kaman ta ruga ta kankameshi don bata ta6a tunanin zai dawo yanzu ba saboda Hajiya in ta tafi salla sai tayi sati ukku bata dawo ba wani lokacin ma har wata don daga can tana biyawa Lagos, ganin tayi mashi tsaye yasashi yi mata alamar zai wuce da hannu da sauri ta matsa gefe ya fito ta jera dashi suka nufi cikin falon, nuna mata armchair yay alamar ta zauna shima ya zauna a inda ya saba zama, maimakon ta zauna kan kujeran sai kawae ta zauna akan carpet gabanshi tana ta faman sakin Murmushi, "Duk Murnan ganin Ya Handsome d'in ne yasa kika kasa Magana" ya fad'a had'i da d'age mata gira, d'aga mashi kai tay alamar eh sai lokacin tace "Ya Handsome ashe yau zaka dawo?" shima kai ya d'aga mata, "Tare da Hajiya kuka dawo?" girgiza mata kai yay alamar a'a, "To ya akai kai ka dawo?" fuska a sake yace "aiki" jinjina mashi kai tay tana dae ta dariyar hakan kuma ya bayyanar da tsantsar farincikin da take ciki shidae sai kallonta yake da d'an Murmushi saidae acan kasan zuciyarshi yaji dadin ganin yadda take ta farinciki saboda dawowar tashi, "Amman Ya Handsome ya akai baka gaya man zaka dawo yau ba kuma ko jiya fa munyi waya" ta fad'a ta d'an turo baki, "Nayi laifi ne?" "Eh mana daka fad'i man ba sai in dafa maka abinci ba" ta fad'a a shagwa6e, Dariya Maganar tata ta bashi yace "ai bana jin yunwa" "Amman dae ai daga tafiya kake yakamata kaci abinci ko" d'an kwantar da kanshi yay jikin kujeran idonshi akanta yace "Don't worry naci abinci kafin na taho kuma tafiyan baida tsawo so bana jin yunwa yanzu" "To anjima fa da daddare ina zaka samu abinci tunda Hajiya bata nan?" "Zan siyo a restaurant" ya bata amsa, "A'a gaskiya ka bari sai in kawo maka kawae" d'age gira yay ya bud'e ido ganin hakan yasa tace "ko bazaka ci na gidanmu ba?" Shiru kaman bazai bata amsa ba can yace "to ai bada ni akai ba kar in cinye maku" "Ni dai ko nawa ne sai na kawo maka" ta fad'a tana turo baki, "Ke kici mi kenan?" "Yo ko garin kwaki sai in sha" waro ido yay alamar mamaki yace "zaki ci wannan ki kwanta zai saki ciwo ai" "Ai ina sha in banson cin abincin" d'an ta6e baki yay kawae can kuma ta ruk'e ha6a tace "kai na manta wllh tuwo miyan busassan ku6ewa gwaggo tayi kuma ansa daddawa fa" d'an Murmushi yay "kinga dole ki bar ni in siyo kenan" da sauri tace "to sai in dafa maka indomie", "Da indomie d'in kika ce zaki sha wannan abun ki kwanta?" da alama Maganar shan garin kwakin ta tsaya mashi, d'an sosa kai tayi tace "ai indae akwae abinci nace banci to ko nace zan amso indomie din wurin kawu Amadu na dafa gwaggo hanawa take tace in banci in bari amman yanzu tunda kai zan dafa mawa nasan zata barni na amso" girgiza mata kai yay "ki k'yale kawae" Magiya ta fara yi mashi tana rantsuwar ta iya dafawa ko kawu Amadu ita yake ba ta dafa mashi ganin yak'i amincewa tace "Allah in baka yarda ba kuka zan maka kuma bazan ci abincin dare ba nima" dariya yay har fararen hakoransa suka bayyana yace "You can start now akwae tissue da yawa" tana jin hakan ta d'age kafafunta sama ta tura kanta ciki, kallonta kawae yake yana Murmushi sanin halinta na saurin kuka yasashi kiran sunanta ta d'ago aikuwa abun mamaki sai ganin kwalla yai sharere a fuskar, ta6e baki ta farayi alamar kukan zata yi sosae, girgiza kai yay cikin cool voice d'inshi yace to zai ci indomie d'in kawae sai ta kyalkyace da Dariya tana fad'in dama tasan ai data yi kuka zai amince tunda baison kukanta shi dae Murmushi kawae yake yana kallonta, "Ya Handsome kaga hotunan sallan da tk yace ya tura maka?" d'aga kai yay yace "yea sunyi kyau yan mata" rufe fuskarta tay alamar kunya adaidai lokacin aka fara kiran sallar Magrib, kokarin mikewa ta fara yi tace bari taje tayi salla sai ta dafo mashi indomie din, ce mata yay sai bayan sallan isha zai ci ta bari sai lokacin ta dafa kar ya huce don bai iya cin shi in ya huce, amsa mashi tayi da to har zata tafi kuma yay tunanin bayan isha dare yayi bai kamata tazo kawo mashi ba a wannan lokacin hakan yasashi tsaidata yace ta bari zaizo gidan bayan isha prayer sai ta dafa mashi lokacin, cike da murna ta amsa mashi da to ta nufi kopa tana jaddada mashi da an gama sallar ya taho fa ya d'aga mata kai daga haka ta fuce shima ya mik'e ya nufi Bedroom don yin Alwala........ ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *6️⃣4️⃣* .......tana komawa gida ta iske gwaggo ta dawo dama makwabta ta shiga, cike da zumudi ta sanar mata game da zuwan haisam cin indomie gwaggon tace to tayi sallar magrib sai taje ta amso wurin Amadu ta amsa da to,bayan ta gama sallar ta tambayi gwaggo guda nawa zata amso tace to kuma ba'a san nawa zata ishe shi ba ko abari yazo sai ta tambayeshi Fatun tace to, mikewa tay ta nufi kitchen ta fiddo d'an gas d'insu da zatayi amfani dashi ta aje acan gefen kicin d'in, komawa tayi ta fiddo tukunya da sauran abubuwan da zatayi amfani dasu duka ta aje, attarugu da albasa ta de6o bayan ta wanko su ta daukko d'an turminsu zata jajjaga gwaggo tace karfa ta cika tunda ba'a san ko yana son su ba tace ai kad'anne dama haka take masu in zata dafa ma Amadu saboda bai son ganinsu zak'o zak'o ba kaman Albasar, bayan ta gama ta kwashe su acikin wani d'an bowl ta rufe ta aje awurin sauran kayan ta koma kusa da gwaggo ta zauna ana fara kiran sallar isha ta mik'e tayi, tun bayan data gama ta zuba ma kopar shigowa ido tana dakon zuwan Haisam shiru shiru har bayan wani d'an lokaci bai zo ba hakan yasa ta fara mita can dai tace bari taje taga miyasa bai zo ba har yanzu, tana shirin mik'ewa gwaggo ta dakatar da ita tace ta kyaleshi tunda yace zaizo ai zaizo ne k'ilan wani uzurin ya tsaidashi, tana rufe bakinta Amadu ya lek'o ta cikin zaure yace ga Yaya Haisam nan zai shigo zumbur Fatuu ta mik'e ta nufi hanyar zauren tana fad'in ya shigo kawae mana, atare da shi suka shigo tana gaba yana biye da ita a nutse yake tafiyar jikinshi sanye da riga turtle neck da jeans sai faman juyawa take tana kallonshi bakinta a washe suka karasa ciki, fitowa gwaggo tay hannunta ruke da k'atuwar darduma tana mashi maraba ta nufi can gefen d'akin Fatuu ta shimfida mashi, bayan ta gama tace ya zauna saida ya cire takalmanshi a gefe kafin ya hau kan dardumar, gaisawa suka shiga yi gwaggo na mashi an dawo lafiya da tambayar ya ya baro sauran yan gidan da Hajiya, a nutse ya rinka bata amsa Fuskarshi a sake, "Ya Handsome indomie nawa zan dafa maka?" Fatuu da tay tsaye k'erere a gefenshi ta tambaya,shiru bai bata amsa ba hakan yasa ta k'ara cewa "kaji Ya Handsome guda nawa zata ishe ka?" kallonta yay da d'an Murmushi ya d'aga mata dogon yatsansa alamar guda d'aya tana ganin haka ta zaro ido tace "d'aya kuma, amman dae babba ko?" girgiza mata kai yay a hankali ya furta "small pack" bud'a baki tay sai kuma ta tura shi cike da shagwa6a tace "kam ya za'ai k'araman indomie ta ishe ka" gwaggo dake d'an Murmushi ta amshe da fadin "adai dafa babba ko d'ana Haisam k'arama d'aya ai bazata kosar da Mutum ba...." da sauri Fatuu ta katseta "kuma ma tun Abuja fa bai k'ara cin wani abu ba nidai Allah manya guda biyu zan dafa maka ka ci ka koshi" tana kai Maganar ta nufi hanyar fita, har ta shige zaure sai kuma ta lek'o da d'an d'aga murya ta tambayeshi harda kwai ya daga mata kai alamar eh sai kuma tace "to guda nawa kwan?" kafin ya bata amsa cikin harshen fulatanci gwaggo tace ta amso ukku Fatun tace to tare da juyawa ta nufi waje shagon Amadu, bata d'auki wani dogon lokaci ba ta dawo ruk'e da bak'ar leda ta aje gefen sauran kayan kafin tasa hannu ta cire hijab d'in jikinta ta kaita can gefen tabarmar da gwaggo ke zaune ta aje tana niyyar komawa wurin da zata yi girkin gwaggo tace ahaka kai ba kallabi zata yi dahuwar, da sauri tace au ta manta ta nufi d'akinta ta dauro kallabi, bayan ta fito ta d'auki tukunyar taje ta debo ruwa ta kunna gas d'in sannan ta daura, cike da nuna kwarewa take dahuwar nan da nan k'amshi ya gauraye wurin lokacin data kusa gamawa, "Ya Handsome ka fara jin kamshi ko?" ta juya tana tambayarshi da yake tsakan gidan fayau yake da hasken globe mai caji, kai ya d'aga mata yana Murmushi gwaggo ma dake zaune tana mashi fira jefi jefi itama Murmushin tayi, tunawa tayi bata dafa kwan ba hakan yasa ta tambayeshi ta soya mashi ko yafi son dafaffen yace ta soya, bayan ta dahu ta shiga kicin ta daukko plate mai kyau tana fitowa gwaggo tace ta sake wanko shi kafin ta zuba, ba 6ata lokaci ta wanko shi tazo ta juye indomie d'in ta nufi inda haisam yake tace ya fara ci kafin ta soya mashi kwan kada ta huce ya jinjina mata kai, mik'ewa gwaggo tay don yafi sakewa yaci ta nufi d'akinta, kicin Fatuu ta shiga ta d'aukko fraying pan da duk abunda zatayi amfani dashi saida ta daurayo su kaman yadda gwaggo tace tayi d'azun sannan tazo ta fara had'a kwan bayan ta zuba ta juya ta kalli haisam ganin baici yasa tace yaci kada ta huce mana, aje wayar yay gefe guda ba tare daya ce mata komae ba ya d'auki fork d'in cikin indomin ya d'ebo yar kadan ya kai baki ya fara ci a nutse, "Ya Handsome ya kaji, da dad'i ko?" maimakon ya bata amsa sai ya mik'a yatsanshi yana mata nuni da kwan da take soyawa da sauri ta duk'a ta juya bayan kafin ta d'ago tana k'ara tambayarshi da dad'i indomie d'in jinjina mata kai yay ta washe baki ta shiga kod'a kanta tana cewa ai ta iya dafawa don kawu Amadu ma inta dafa mashi har santi yake shidai haisam jinjina mata kai kawae yake yana d'an cin indomie din can suka fara jin k'auri alamar kwan na k'onewa, a rud'e ta juya gun kwan koda ta juyashi har bayan ya yi bak'i amman ba sosae ba, kashe gas d'in tayi da sauri kafin ta juyo a sanyaye tana kallon haisam da shima kallonta yake fuskarshi a sake kaman zai dariya, "Chef Zarah kin k'ona man egg ko" ya tambaya had'i da d'age gira, d'aga mashi kai tay alamar eh adaidai lokacin gwaggo ta fito hannunta ruke da buta zata bandaki ganin Fatuu tsaye sototo ga haisam na Murmushi yasa ta tambayeta lafiya tace mata kwan ne ya kone, "Dama komae Mutum zai yi bai sa kula ba dole yaga ba daidai ba,sai ki maza kije ki amso wani kizo ki soya kafin ya gama" ta fad'a da d'an 6acin rai ta nufi hanyar toilet, tana niyyar juyawa taje ta amso Haisam yace ta barshi, kallonshi tay a sanyaye tace "amman ai bayan ya k'one fa" d'aga mata kai yay yace "sai ki cire wurin", "Inda ya k'one d'in?" kai ya d'aga mata alamar eh, da sauri tace to ta kwashe acikin plate ta kawo mashi, duk'awa tayi zata cire inda ya konen yace taje ta wanko hannunta tana zuwa wurin gwaggo ta fito ganinta yasa ta tambayeta ta amso wani kwan ne tace mata ai yace ta barshi sai ta cire inda ya k'one d'in wucewa tayi ta nufi cikin gidan tana zuwa inda yake tace mashi miyasa ba zai bari a soya mashi wani ba yace lafiya lou abar wannan daga haka ta shige d'aki, bayan ta dawo ta cire inda ya konen tass ta d'ago tana kallonshi da d'an Murmushi, "Go bring another fork" taji yace, mik'ewa tayi taje kitchen ta d'aukko wani cokalin mai yatsu kaman yadda ya mata umarni, tana mik'a mashi yace ta zauna taci indomie d'in, da mamaki ta kalleshi kafin tace wani abu ya rigata cewa "kinsan ai ya min yawa kika yi shi haka so da kanki dama kika yi" rantsuwa ta fara mashi wai shi kadai ta dafa mawa yace to ta zauna taci, zaunawa tayi ya juya plate d'in sukae facing juna, suna cikin ci gwaggo ta fito daga cikin d'aki don d'aukko ma Haisam d'in ruwa da lemu don yanzu Amadu harda manyan lemuna yake saidawa, tana ganin Fatuu na cin indomie d'in cikin harshen fulatanci tace ya ta dafa mashi abu kuma zata zauna ta cinye mashi, kafin Fatuu ta bata amsa Haisam d'in yace ba wani abu shi yace taci yayi mashi yawa, ba Gwaggo ba har Fatun saida tayi mamakin jin ya gane abunda gwaggon tace basu san guessing kawae yay ba daga yanayin yadda gwaggon tayi Maganar, Fatuu na ganin ta nufi inda freezer take da karfi tace "Gwaggo Coca cola zaki d'aukko mashi" tana juyowa suka had'a ido tasa dariya tana fad'in ai tasan kalan lemun daya fi sha kenan, ba laifi yaci sosae kafin ya aje fork d'in alamar ya koshi tana niyyar aje nata yace yasan bata koshi ba ta cinye, dariya tayi kafin taci gaba da ci shi kuma yaci gaba da latsa wayarshi, saida ta cinyeta tass ta tsiyaye sauran lemun daya bari mai yawa ta shanye sai lokacin ya d'ago ya kalli plate din kafin ya kalleta aikuwa da sauri ta sadda kanta tana dariya, "Acici kawae" taji ya fad'a da sauri ta kalleshi ta turo baki tace "Kai Ya Handsome bakai kace in cinye ba" dan ta6e baki yay kafin yace wani abu wayarshi ta fara ringing kai idonshi yay kan screen d'in kafin yay picking call din fara magana a nutse, sanar da mai kiran yay cewa zai kirata in ya koma gida on the other hand aka tambayi yana inane yace yana gidansu Zarah, "Oh Zarah where is she, let me speak wit her" wadda yake wayar da ita fad'a, mik'a ma Fatuu wayar yay ta amsa tana tambayar waye daga cikin wayar taji ance "is ur Sis Fanan" washe baki Fatuu tayi tace "Aunty Fanan ashe kece, ya India" amsa mata tayi da lafiya lou, "Ai ina ce ma Ya Handsome ya gaida man ke in naga kuna waya yana fad'i maki?" amsa mata tayi da eh, "To rannan nasa ya d'auki hoton kayan dana ce ki siyo man ya turo maki?" nan ma amsa mata tayi da eh ya tura mata, "To kin siyo?" tace "No, na bari sai zan dawo kinga in an siya yanzu zai iya maki kad'an lokacin" "To shikenan,amman fa in suna da tsada ki barsu kawae kar ki kashe kud'inki kuma ki rasa na dawowa" har saida ta bata dariya kafin tace "Don't worry sis Zarah, i will definately buy it for u ko don yadda kike kulawa da Ya Handsome d'inki" jin hakan yasa Fatuu washe baki cike da gwaninta ta shiga bata Labarin indomie din data dafa mashi yanzu ya ci saboda Hajiya bata nan, sosae Fanan d'in ta nuna jin dad'inta tay mata godiya, hira suka shiga yi har saida Haisam yaji ya gaji da zaman ya mik'e sannan Fatun tayi sallama da ita tace Ya Haisam din zai tafi, d'akin gwaggo ta leka ta sanar mata zai tafi, fitowa tayi suka yi sallama yayi mata godiya tana fad'in haba ai ba wani abu bane duk yima kaine tunda ai anzama d'aya daga haka ya nufi hanyar fita tana mashi sai Allah ya kaimu Fatuu ta bi bayanshi suka fita tare, suna fitowa waje ya juya yace mata ta koma saida safe, har ya juya ta kirashi ya sake juyowa, "In shirya gobe tunda ba islamiyya muje yawo?" ta tambaya tana d'an kare fuskarta da tafin hannunta guda, still yay kaman bazai ce komae ba sai kuma calmly yace "baki gajiya da yawo ne?" a ashagwa6e tace "ai to tun fa salla ban k'ara zuwa ko ina ba, kuma koda sallan ma ban gama yawon ba Tk din ya kwanta rashin lafiya kuma ma ciwon kaman na k'arya wllh don washe garin ranar da yace bai lafiyan na ganshi kan sabon mashin dinshi yaci gayu ya fita da nace ma gwaggo zanje mu idasa yawon tunda naga ya samu sauki sai ta hana ni" still idonshi na akanta slowly yace "ina zan kaiki?" watsa hannuwa tay "duk inda ka kaini" shiru yay yana d'an tunanin inda zaije da ita can ya tuna d'azun bayan ya iso sunyi waya da Abbas yake ce mashi ya kamata su kaima Najeeb ziyara don ya kusa barin kasar, "Zaki je gidan Abbas?" da sauri tace "eh dama ban ta6a zuwa ba" "Owk ask ur Grandma in ta barki zan kaiki..." tun kafin ya rufe baki ta katseshi "ai zama ta barni wllh", "ki dai tambayeta, kuma bani nace ba" dariya tasa tana fad'in ai bazata yi mashi karya ba, ganin yana shirin juyawa yasa tace "to da yaushe zamu?" dakatawa yay "ba kince lokacin islamiyya tunda ba'ayi", "Eh amman dai ba ina nufin da yamma d'in ba, mutafi tunda safe tunda bani zuwa makarantar boko saboda wannan satin aka koma kuma duk mutane basu zuwa" juyawa yay yana fad'in zai sanar ma Auncle d'inta time din da zasu fita, cike da murna ta d'aga murya tace "Thank u Sweetheart Ya Handsome d'ina" hannu guda ya d'an d'aga mata ba tare daya juyowa ba ta juyo da gudu ta koma cikin gidan, lokacin data shiga gwaggo ta kauda komae har ta shige d'aki hakan yasa ta bita cikin dakin ta sanar da ita zancen zuwa gidan Abbas don itama yanzu ta sanshi sosae, cewa tayi Allah ya kaimu kafin kuma tayi mata fad'a kan ta rage takura mashi tace to daga haka ta nufi d'akinta cike da farinciki. Yana komawa part d'inshi ya zauna kan kujera ya kira Abbas, yana d'aga kiran ya hau yi mashi iskanci yana fad'in wai baisan lokacin daya dace ya kira mai aure bane, shidae d'an Murmushi kawae yay bayan sun gaisa ya kara yi mashi ya gajiya Haisam d'in ya sanar dashi game da zuwansu gobe shi da Zarah, sosae yaji dadi dama yana ba Feenah labarinta yace ma Haisam amman dae yini zai kawo ta ko yace mashi bai kaiga fidda time ba nan Abbas d'in yace ya kawo ta da wuri sai ya ci Abincin rana anan gidan tunda Hajiya bata nan kuma daga nan ma sai suje gidan Najeeb din ya amsa masa da owk, daga haka yai mashi saida safe Abbas d'in na fad'in bai bari suyi hira yace No baiso yayi mashi kora da hali daga haka yay rejecting call d'in Abbas nata kyalkyatar Dariya, sanin Amadu na shago lokacin yasashi kiranshi ya bashi sakon ya fad'i ma Zarah zasu fita around karfe 1:00 na rana cike da girmamawa ya amsa mashi da to, bayan ya katse kiran ya kira Fanan Vedio call ya hada a laptop dinshi dake kan c-table suka ci gaba da yin hira. ____________ Washe gari da safe lokacin da Amadu ya shigo d'aukar abun karin kumallo ya fad'i mata sak'on Haisam, cike da zumudi ta gama yin kalaci da sauri tayi aikin da zata yi tana gamawa ta fad'a wanka, ba 6ata lokaci ta fito ta nufi daki ta hau yin kwalliya, cikin kankanin lokaci ta gama ta zumbula wata yar doguwar riga mara nauyi saboda lokacin fitan baiyi ba, sam ta kasa zama sai tayi nan tayi nan ji take kamar ta matso da lokacin don gani take bai sauri, karshe dai data gaji sai tasa hijab ta fita waje wurin Kawu Amadu tace don Allah ya ara mata waya zata fad'i ma Ya Handsome wani abu jin hakan yasa ya bata wayar bayan ya kira mata layin nashi, tana jin ta fara ringing ta nufi zaure da sauri wayar kange a kunnanta, yana d'agawa cike da shagwa6a tace mashi ta shirya tun d'azun zaune take kawai ba abunda take yi don Allah yazo su tafi, shiru yay yana saurararta har ta gama sannan yace mata ba gaisuwa, da sauri tace au ta manta ya yi hakuri don Allah ta hau gaidashi yace baiso tunda saida ya roka, Magiya ta shiga yi mashi akan ya amsa sannan ya amsa gaisuwar yace ta jira shi zaizo yanzu, maida ma Amadu wayar tayi kafin ta shige gida da gudu don tasa kaya, cikin kankanin lokaci ta ci gayu da jeans da riga ta gyara gashinta ya zuba a gadon bayanta don har yanzu ba ai mata kitso ba, nan da nan ta koma kamar yar balarabiya, golden d'in gyalenta da takalma tasa don rigar nada adon flowers golden mai walwali agabanta, wow kuzo kuga Fatuu ita kanta data kalli kanta a d'an Mirror dinta saida tasa hannu ta rufe bakinta ganin fitinannan kyaun da tayi, da sauri ta juya ta nufi hanyar fita don ta gwado ma gwaggo gayun da tayi, tana fita ta fara kwala mata kira hakan yasa gwaggon lek'owa daga cikin kitchen dama bata dad'e da ta shiga ba don d'aura girki, sototo tayi tana kallonta da alamun al'ajabi akan fuskarta ita kuwa Fatun sai faman washe baki take tace "gwaggo kinga na zama kaman yar kasar waje ko", "Ina zaki je haka?" ta tambayeta fuskarta a d'an daure hakan yasa Fatun dakatawa da dariyar da take yi tace "gidan Abbas da na fad'a maki Ya Handsome zai kaini jiya ko" canza harshe gwaggon tay ta fara mata fada sosae tana fad'in "saboda baki da hankali shine zaki fita haka kaman ba musulma ba, to ki koma ki canja sutura ba dai wannan ba!!" kwa6e fuska tay kaman zata yi kuka ta fara mata magiya tana fad'in a Mota fa zasu je kuma su dawo, shiru gwaggon tayi tana kallonta kafin tace to taje ta saka hijabi dogo Fatun tace ai bata da dogon hijab tace to kuwa dole ta cire kayan, tana shirin k'ara mata magiya ta daka mata tsawa hakan yasa ta nufi dakinta da gudu tana kuka, saman gadonta ta fad'a ta shiga rusa kuka kai kace wani abu akai mata, jin irin ihun da take mata ne yasa ta bita d'akin daga waje ta d'age labulan a kausashe tace wllh in bata yi wasa ba har fitan ma zata hanata ne tunda bata da hankali bata san daidai ba, jin Maganar gwaggo yasa ta tsagaita da kukan don tasan in ta k'uleta tsab zata hanata fitan, saukkowa tay daga kan gadon ta nufi wardrobe d'inta ta fiddo d'ayar atamfar da babanta yayi mata wadda bata sata ba da salla anyi mata d'inkin doguwar riga, bayan ta gama shiryawa tasa bak'in gyale da takalmi ta d'auki yar jakarta daga haka ta fita daga d'akin ta nufi hanyar fita, kaman zata wuce sai kuma ta tsaya a bakin Kitchen d'in baki kumbure tace ma gwaggon ta tafi kallonta tayi kafin tace mata adawo lafiya ta juya ta fuce daga gidan, tana fita Motar Haisam na tsayawa hakan yasa ta nufeta,bud'e d'ayan side d'in driver tayi ta shiga idonta cike da kwalla ta d'an kalli Haisam da shima yay adon k'ananan kaya sai fitinannan kamshi yake saki, gaidashi tay ya amsa yana kallon cikin idanunta, "What's d problem?" ya tambaya yana kallonta, shiru ta d'anyi kafin cikin shashsheka tace "ba gwaggo bace saida naci gayu na da kayan da nike son sawa wannan riga da wandon da ka siya man awurin Aunty Zee d'innan tace wai bazan fita dasu ba sai nasa babbar hijab kuma ni banda ita duk hijabai na basu kai har k'asa ba" ta k'arasa Maganar kwalla na gangaro mata da gani ranta a 6ace yake sosae, still yay yanata kallonta ya d'an jingina kanshi jikin headrest ya kuma fahimci dalilin dayasa gwaggon ta hanata fita da kayan, "Ko muyi cancelling fitanne?" taji ya fad'a, da sauri ta kalleshi ta girgiza mashi kai alamar a'a, "But look at ur face taya zamu fita haka?" shiru tayi tana binshi da ido sai kuma tace ta bari tasa hannu tana goge kwallan dake zubo mata bayan ta gama ta kalleshi ba tare da tace komai ba, har zai tashi Motar ya dakata yace mata "ba kina da Abaya ba?" cikin rashin fahimta tace "ai tace sai wadda takai man k'asa kuma na fad'i maka banda ita" shaking head dinsa yay yace "i mean dogon riga" "Jallabiya?" kai ya d'aga mata alamar eh tace tana da wad'anda ya siya mata, "Akwae mai bud'ewa?" ya tambaya yana nuna mata da hannunshi tace "eh guda biyu na budewa in an zuge zip d'insu" "Ok kije ki saka kayan sai ki d'aura dogon rigan sama" sai da yayi Maganar sannan ta tuna da yadda take ganin larabawa nayi a tv, da sauri ta amsa mashi da to ta bud'e kopan ta fita, lokacin data shiga gidan gwaggon bata cikin kicin bata bi ta kan nemanta ba ta wuce d'akinta, shaf shaf ta canza kayan jikinta zuwa riga da wandon ta bude wardrobe ta d'aukko Maroon jallabiyarta ta daura sai faman washe baki take, takalman data cire golden ta maida ta bud'e zip d'in rigan yadda za'a rinka ganin kayan ciki, har ta nufi kopa zata fita ta tuna da gwaggo hakan yasa ta rufe zip d'in tana fita suka yi kacibus da gwaggo ta fito daga dakinta, kallonta tayi tana ta washe baki ta k'ara ce mata sai sun dawo ta nufi hanyar fita da sauri gwaggon ta bita da ido har ta fice kafin ta d'an ta6e baki ta nufi kicin duk a tunaninta kaya ta dawo ta canza, tana shiga zaure ta zuge zip d'in sannan ta fita wajen tayi d'as da ita, tana shiga cikin Motar suka had'a ido ta washe mashi baki tana dariya, yar harararta yayi ta rufe fuskarta da sauri alamar kunya, "rigimamma kawai" taji ya furta, cire hannun tayi ta kalleshi tana tura baki yaja Motar suka tafi........ ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 6️⃣5️⃣ .......A nutse yake driving d'in yayin da Fatuu keta kallon gefen hanya ta 6angaren da take can ta juya ta kalli Haisam ta kira sunanshi, d'age mata gira yay idonshi akan hanya tace "ka kunna mana waka" shiru ya d'an yi kafin yace mata babu wakar, "To a wayanka fa baka da wak'oki?" "Ba wanda kike so" ya bata amsa a takaice, "To ka kunna mana radio k'ilan suna yin wakokin" ba tare daya kalleta ba yace "baki iya kunnawa bane?" jin hakan yasa ta kai hannu ta kunna radio d'in don ta iya, jin ba'ayin wak'okin yasa ta canja wani gidan radion nan ma wani shiri sukeyi d'an tsoki ta ja a fili tace "duk ma basu yin wakokin" har ta koma ta zauna ta tuno da sabon gidan radion da aka bud'e wanda kullum cikin sa wak'oki suke, da sauri ta kai hannu ta kamo shi aikuwa sai gashi suna cikin yin wak'okin Umar m sharif ana gama wadda ake yi aka sako wakar zan rayu dake, Murmushi Fatun tayi ta fara bin wakar kai kace ita ta rairata, tana cikin bi ta juya ta kalli haisam dake driving tace "Ya Handsome muma atare zamu cigaba da rayuwa har mu Mutu ko?" d'an Murmushi yay ba tare daya kalleta ba bai kuma ce komai ba hakan yasa ta cigaba da cewa "kaga tunda kana da bangarenka agidan Hajiya in kayi aure sai akawo maka Matarka nan in ka tafi aiki sai in rink'a zuwa ina tayata fira in kuma ta haihu sai in rink'a goya babyn ina yi mashi wasa" sai lokacin ya juyo ya kalleta da Murmushi suka had'a ido yace "ke bazaki yi auren ba kenan?" tace "zanyi mana, amman fa sai nazama likita" jinjina kai yay "zamu rabu kenan tunda zaki aure kema" yay Maganar yayin da yake maida idonshi kan hanya, tace "ai lokacin na fara aiki sai in sayi gida anan unguwar ko kuma tunda gidan Hajiya akwae k'aton fili sai nima abani in gina kaman naka ba shikenan ba sai muci gaba da yin rayuwa atare" d'an ta6e baki yay hadi da jinjina kai sai kuma yace "kyauta za'a baki ki gina kenan", "Sai na biya? Ta tambaya ta d'an waro ido, d'aga mata kai yay alamar eh tace "to sai in biya tunda lokacin na fara aiki shikenan kaga sai mu cigaba da rayuwa atare tunda muna gida d'aya ko?" kai ya d'aga mata ta koma ta jingina bayanta a jikin seat tana ci gaba da bin wakar da ake, basu dad'e ba suka k'arasa estate d'in da Abbas yake, a gaban gate d'in gidan ya dakata ya latsa horn sau biyo sai ga Abbas d'in ya lek'o yana ganinsu ya shiga idasa bud'e gate din, yana gama wage masu shi ya kutsa kan Motar ciki, can gefe inda Motar Abbas take fake ya nufa, yana parker Motar Fatuu ta bud'e ta fito tana ma Abbas Dariya, shima dariyarce akan Fuskarshi ya nufeta yana fad'in "u'r highly welcome Mom Zarah" still dariyar ce a fuskarta bata ce mashi komae ba adaidai lokacin Haisam ya bud'e Motar ya fito,nufarshi Abbas yayi ya mik'a mashi hannu suka gaisa yana k'ara yi mashi an dawo lafiya, hanyar shiga cikin gidan suka nufa yayi ma Fatuu alamar ta taho, suna zuwa bakin entrance d'in yaron Abbas wato Abdul ya fito da gudu yana sanye da jeans da t'shirt ya nufi haisam yana fad'in "Oyoyo Baba zakee" haisam na ganinshi ya ca6eshi had'i da d'aga shi sama suna ma juna dariya ya saka hannunshi cikin sumar haisam d'in yana cakud'ata, sauke shi yay yana fad'in in ya lalata mashi gashi sai ya gyarashi Abdul d'in yace Mommyn shi nada Comb da yawa sai ya gyara mashi gaba d'aya sukai dariya harda Fatuu dake ta binsu da ido tana mamakin yadda haisam kema yaron don batai tunanin yana ma yara wasa har haka ba, juyawa yay ya kalli Fatun irin kallon rashin sani kafin yace "Baba zakee wacece wannan?" d'an kallon Fatun yayi yace mashi "wata rigimamma ce" waro ido yay ya kalli haisam yace "rigimamma irina?" gaba d'aya suka sa dariya haisam d'in ya kai hannu yaja hancinshi yace "ashe kasan kai rigimamme ne" kafin ya bashi amsa sai ga Feenah ta fito tana sanye da doguwar riga A shape ta atamfa tayi daurin dankwali mai kyau, fara ce saidae ba irin tas d'innan ba tana da kyau ba laifi kuma doguwa ce sam bata da jiki kana kallonta zaka fahimci wayyayar yar boko ce kuma haskenta Abdul din ya d'aukko harma ya fita fari amman sak da babanshi yake kama, "Ni dae na gaji da jiran bak'uwar tawa ta shigo na biyo sahu" ta fad'a idonta akan fatuu tana mata Murmushi itama Murmushin take mata kafin ta gaidata, bayan ta amsa tace su shigo mana duk suka nufi ciki wanda madaidaicin falo ne daka shiga yana d'auke da duk wani abu da akan samu a falon yan gayu masu matsakaicin k'arfi, kujera ta nuna ma fatun tace ta zauna shi kam haisam tuni ya zauna saman 3 seater sofa Abdul na akan cinyarshi Abbas ma ya zauna agefenshi, gaida Haisam din ta shiga yi tayi mashi anyi salla lafiya duk da da sallan tayi mashi ta waya, bayan sun gama gaisawa Abbas ya nuna mata fatuu yace "yau dae ga Mom Zarah" Murmushi Feenah tayi tace "aikam H,zakee ya kyauta man ai da ya kawo man ita inata jin labarin Mom d'inmu ba tare dana ganta ba" ita dae fatuu Murmushi kawae take, kallonta Abdul yayi kafin ya juya yace ma haisam "wai wacece wannan Baba zakee" kafin ya bashi amsa Abbas yace "Mom din shi ce" zaro ido yay yana bin fatuu da kallo itama kallonshi take tana Murmushi, d'aga kai yay ya kalli haisam yace "Wannan yar k'aramar ce mamanka?" kai ya d'aga mashi alamar eh da mamaki ya k'ara kallon fatun sai kuma yace "kodae matarka ce baba zakee" gaba d'aya suka sa dariya Abbas yace "wato tayi k'arama ta zama mamanshi kenan saidai matarshi ko, to sister d'inshi ce" dariya Abdul d'in yayi yace "kenan yayata ce ita?" "Mamanka dae" Abbas ya bashi amsa, cike da rashin yarda yace "kam ni ba mamata bace wannan yar karamar ga mamata nan babba" Feenah dake dariya tace "zata iya zama mamanka mana,ba Hafsa mamanka bace itama kuma ai yar k'aramace ko" turo baki yay yace "ai ita mamata ce ta k'arya ko wannan ma ta k'arya ce?" ya tambaya yana nuna Fatuu, girgiza kai Abbas yayi yana dariya yace "No ka barta a yayar taka dai" mik'ewa Feenah tayi ta kawo masu abun sha ta zuba ma kowa kafin ta koma ta zauna suka shiga yar hira harda Haisam d'in, tambayar Abbas tayi ko a shirya table yace no ta bari sai sun dawo salla tunda lokaci ya kusa tace to, juyawa tayi ta kalli Fatuu dake ta faman binsu da ido bata cewa komae tace "wai dama Mom Zarah bata magana ne?" d'aga ido haisam yay ya kalli Fatun suka hada ido tayi Murmushi Abbas yace "Magana kai,kawae dai k'ilan bakunta take maki ne" tace "Ah Mom Zarah kada muyi haka dake gaskiya,inata murna za'a kawo man ke musha fira kuma sai kizo ki man shiru alhalin kina magana" hannu tasa ta rufe bakinta tana dariya jin abunda Feenah din tace, "Ba dariya zaki man ba bud'a baki zaki muyi fira" cire hannun tayi ta amsa mata da to, saukkowa Abdul yay daga kan cinyar Haisam yaje gaban fatuu yace "zo muje dakina kiga Computer d'ina da Baba zakee ya siyo man a k'asan waje" amsa mashi tayi da to ta mik'e zata bishi Feenah tace ta cire Abayar mana ta sha iska, sa6ule rigan tayi ta daurata kan kujera harda gyalen rigar ta bi bayanshi suka nufi wani Corridor, bin ta da ido sukae gaba d'aya har ta shige kafin Feenah ta juyo suka had'a ido da Abbas tayi dan Murmushi kawae don shima Murmushin yake yi, basu jima ba suka fito Fatuu na ruk'e da computer d'in Abdul na biye da ita, akan carpet ta ajeta duk suka zauna suka cigaba da yin game d'in da suka fara yi anan Feenah ta fara jin muryarta wurin yin gardama da Abdul sai kace wani tsaranta sudae dariya kawae suke yi masu, bayan wani lokaci ta fita daga game din ta shiga wani app na koyon karatu nan ta fara koya mashi da turanci sosae ta burge su Abbas don daga yadda take koya mashin zaka fahimci tana da k'ok'ari da abun ya nisa ma duk sai suka kwanta akan carpet, kiran sallan da aka fara ne yasa Abbas da Haisam mik'ewa don zuwa masallaci Haisam yace ma Abdul ya taso suje suyi salla,mik'ewa yay yana cema Fatun sai sun dawo ta d'aga hannu tana yi masu bye bye, bayan sun fita itama Feenah mik'ewa tayi tace ma Fatuu ta taso suje suma suyi sallar ta amsa mata da to, atare suka nufi Bedroom dinta taba Fatun hula tace ta rufe kanta kafin ta nuna mata toilet tace ta shiga tayo Alwala ita kuma ta nufi d'akin Abbas ta d'auro Alwalar, atare sukayi sallar suna gamawa Fatuu ta koma Falo ta cigaba da abunda take ita kuma Feenah tana fitowa Kitchen ta nufa don shirya abinci kan Table, Fatuu na hangota tana fitowa da kayan abinci ta mik'e taje tace bari ta taya ta suka cigaba da shirya table d'in suna cikin yi su Haisam suka dawo Abbas na hangota ya d'an d'aga murya yace "Mom Zarah an saki jiki kenan har ana taya Feenah aiki" ya yi Maganar yana dariya Feenah tace "aikuwa dae ta zama yar gida dama haka yakamata ai" Abbas d'in yace gaskiya yayin da yake zama kan kujera, bayan sun gama Feenah tace su taso table yazama ready Abdul ya fara rugowa ya zauna kusa da Fatuu don ita tuni ta zauna, atare suka nufo Dining area d'in da Haisam kowa yaja kujera ya zauna Feenah ta hau serving nasu bayan ta gama Abdul yace "kowa yayi Addu'a kada yaci da shedan" gaba d'aya suka jinjina kai suna dariya, a nutse suka fara cin abincin baka jin komae sai k'arar cokulla hankali kwance Fatuu ke tura abinci har ta k'ara abunda bai yi mata ba, Haisam ne ya fara mik'ewa alamar ya koshi Feenah ta d'aga kai ta kalleshi tace"badai wai har ka koshi ba?" kai ya d'aga mata alamar eh, tace"amman fa baka ci wani na kirki ba, har yanzu dae kana nan da rashin cin Abincin ka kenan" d'an Murmushi yay ba tare daya ce komae ba ya fara kokarin barin wurin Abbas dake kallonshi yace "ki rabu dashi lokaci na zuwa da zai rink'a ci hannu baka hannu kwarya in har yana son samun kuzarin yin noma yadda ya kamata" shiru bai tanka mashi ba bai kuma kalleshi ba yabar wurin amman sarae yaji abunda yace ita kuwa Feenah d'an runtse ido tayi ta sadda kanta k'asa alamar kunya, kusan atare suka gama Abbas ya nufi parlor Feenah kuma ta fara clearing wurin tana cikin kwashe kayan abincin da su Abbas sukae amfani Fatuu ta mik'e alamar itama ta gama ta tambayeta ta tabbatar ta koshi tace mata eh, tayata gyara wurin tayi kafin ta nufi parlor wurin Abdul suka ci gaba da abunda suke a Computer dinshi su kuma su Haisam suna kallo a tv, duba agogo yayi ganin ukku tayi yace ma Abbas suje gidan Najeeb ya amsa masa da ok duk suka mik'e a tare har zasu nufi hanyar fita yace ma haisam "bazamu je da Mom zarah ba su gaisa" shiru yay mashi kaman bai jishi ba har saida ya k'ara Magana sannan ya amsa masa da No kawae daga haka ya fuce,dariya Abbas yayi dama tsokana ce yasa yayi mashi Maganar Fatun, saida ya lek'a Bedroom ya sanar ma feenah zasu je su dawo tayi mashi Allah ya tsare sannan ya dawo falon su Fatuu dai gaba d'aya hankalinsu na akan abunda suke hakan yasa ya fuce kawae. Bayan tafiyarsu ne Feenah ta fito tayi wanka ta canja kaya zuwa doguwar rigar Material ta zauna tana kallon abunda su Fatuu keyi in sukae abun dariya tayi in kuma wani yai gwaninta ta tafa mashi haka in suna gardama sai ta rabasu sosae ta saki jikinta daga baya ta koma kan kujera suka shiga yin fira da Feenah har sata tayi ta rink'a yi mata fullanci ta kuma bata labarin garinsu, Lokacin da su Abbas suka k'arasa gidan Najeeb dake a Gra wanda katon gidane na gaske, sosae yay farinciki da zuwan nasu haka ma Matarshi Sofeeyat wadda irin matan nan ne da suka waye over tana da kyau daidai gwargwado kuma tana da haske saidae kana gani kasan hasken harda na kanti, taci gayu cikin k'ananan kaya wando da riga sun kamata hakan ya bayyanar da d'an dirin dake gareta, kanta anyi mata kitson k'arin gashi miri miri amman yay kyau sosae ta d'aura bak'in veil ta zameshi daga gaban yadda kitson ya fito sosae haka k'umbunanta an k'ara mata dana kanti shima Najeeb d'in yana sanye da kayan shan iska armless da wando 3 quarter,suna shiga cikin tangamemen falon wanda yake shak'e da kayan alatu suka zauna asaman d'uma d'uman sofas d'in dake kewaye acikinsa set biyu, zama itama soffyn tayi tana facing d'insu cike da kisisina ta shiga gaidasu idonta akan Haisam amman Abbas ne kawae ya kalleta shikam Haisam bai ko kalleta ba ya amsa mata a takaice, "H,zakee manyan gari ashe ka dawo nan da aiki rannan My ke gayaman" ta fad'a cike da salo, shiru bai ce mata komae ba da alamu ma bai jita bane don ya sadda kanshi yana danna wayansa, d'an ta6a shi Abbas yay yace mashi ana magana sannan ya d'ago ya kalleshi kafin yace wani abu ta k'ara cewa "da alama ta janye mashi hankali ne" kallonta ya d'anyi da d'an Murmushi ba tare daya ce wani abu ba, Najeeb ne yace tasa akawo masu drinks mana tace dama yanzu zata sa ta bari su gama gaisawa ne, mai aikinta ta fara kwalama kira "Murja,Murja" ta kirata har sau biyu sannan ta fito yar dattijuwar mata ce in a auren k'auye mane zata haifeta, "Baki ji anyi baki bane" ta fad'a ta d'aure fuska had'i da d'aura kafa d'aya kan daya, murya na rawa Murjar tace "ayi man afuwa Hajiya ina can ciki ne banji shigowarsu ba" shiru ta d'anyi kafin cike da bada umarni tace taje ta kawo masu abun sha kuma ta shirya abinci akan table Abbas na jin hakan yace "adai bamu abun shan amman abincin dae abarshi basai an shirya ba....." katseshi Najeeb yay "kana nufin bazaku ci abincin gidana ba?" yar dariya yayi yace "ba haka bane kaima kasan by dis time mutum yaci lunch so duk a k'oshe muke" d'an ta6e baki yayi baice mashi komae ba adaidai lokacin murja ta karaso ruk'e da babban tray ta d'auro bottle water da drinks da glass cups, daurashi tayi kan c-table kafin ta kinkimeshi da k'yar don murtukeke ne ta matsar masu dashi gabansu, tana shirin juyawa ta tafi aikuwa soffy ta daka mata tsawa tace "wai ke dak'ik'iyan inane,da kika aje masu waye bawanki da zai zuba masu?" har saida ta d'an tsorata jiki na kerma ta hau bata hakuri ta juya zata zuba masu Abbas yace ta barshi zasu zuba shidae haisam baima d'ago ba balle ya kallesu saidae yaji tsawar da tayi matan har cikin ranshi don ya tsani wulak'anta dan'adam don shi a wurinshi duk d'aya muke,tsaye Murjar tayi tana binta da ido ta kasa tafiya ita kuma Soffyn taba banza ajiyarta sai juya k'afa take tana wani shan kamshi, a hankali Haisam yay ma soffyn kallon kasan ido cikin sa'a suka had'a ido don dama bunu bunu sai ta kalleshi, ganin kallon da yayi mata ne yasa tasha jini jinkinta ta kalli murjar tace taje amman karta shirya table d'in ta kawo masu abunda zasu ta6a ta amsa da to harda dan rissinawa tayi mata godiya soffyn ta d'aga mata kai kafin ta juya ta tafi, bada jimawa ba ta dawo d'auke da wani hadaddan trayn ta d'auro plates d'in soyayyan naman kaza da kuma na snacks ta aje masu gefe tayi masu aci lafiya gaba daya harda haisam suka d'aga mata kai, fira suka shiga yi ganin haisam bai ta6a komae ba yasa Soffy yunk'urawa tana fad'in "kunsan fa H,zakee saraki ne bari nai serving nashi" dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu kafin yace ba yanzu zai ci ba, bata san shi k'yamar k'umbunan hannunta ma yake ba, tana zama wayanta ya fara ringing alamar ana kiranta mik'ewa tayi tace masu "excuse me" Abbas ne ya d'aga mata kai ta nufi ciki tana wani karairaiya jiki ba kunya ba tsoron Allah, suna cikin hiran Najeeb ya kalli Haisam yace "H,zakee ina Mom d'inka bafullatana?? Kafin ya bashi amsa cike da tsokana Abbas yace "aikuwa kasan tana gidana ya kawota da har nace mashi mu taho tare ku gaisa" Najeeb yace "halan yak'i ko?" dariya Abbas d'in yasa yace "nidae ai baka ji na fad'i haka ba" d'an ta6e baki kawae yay baice komae ba, hira suka cigaba da yi har aka kira sallar la'asar sukaje masallaci suka yo salla suna dawowa suka ce bazasu shiga ciki ba zasu je wurin Saleem ne Najeeb na jin haka yace su jira su tafi tare ya nufi cikin gidan yana fad'in bazasu yi sallama da soffy ba Abbas yace ya gaya mata sun wuce, bayan wani lokaci ya fito sanye cikin jeans da t-shirt hannunshi ruke da wayarshi yasa bak'in glass ya fito a d'an madararshi, yana k'arasawa wurunsu suka shiga cikin Motar suka fuce, Bayan sunje har wurin Mahaifiyar Saleem d'in sukaje suka gaidata kafin suka shiga part d'inshi sai karfe biyar da wani abu suka baro wurin Saleem d'in Abbas ya tambayi Najeeb gida zasuyi dropping nashi ne dayake shi ke tuk'a Motar Haisam na gefenshi sai Najeeb d'in a baya, ce mashi yay su wuce gidanshi ya gaisa da Feenah, Murmushi kawae Abbas yayi don yasan ba wata Feenah kawae Zarah yake son gani, lokacin da suka isa bakin gate d'in gidan Abbas d'inne ya fita ya bud'e gate kafin ya dawo cikin Motar ya kutsa cikin gidan, suna shiga ciki daidai lokacin Abdul ya fito da gudu sai kuma ga Fatuu ta biyo bayanshi da gudu gaba d'aya gashinta a tarwatse ya zubo mata gefe gefe da kuma bayanta, tun kafin su tsaya Najeeb ya zuba mata idanu, suna yin parking suka firfito da gudu Abdul ya nufi bayan Haisam ya 6oye yana fad'in "Baba zakee kaga Aunty Zarah zata bugeni" d'agowa yay ya kalleta tayi tsaye agabanshi ba damar ta kamo Abdul d'in cikin cool voice d'inshi ya tambayi abunda yayi mata tana tura baki tace "ba game mukeyi ba duk wanda yay winning ya bugi mutum tun d'azun nike cinyeshi amman sai yak'i bari in bugeshi kuma ni da shi yay winning na tsaya ya bugeni har ma ya cire man ribbom" still yay yana kallonta Abbas kuma sai dariya yake Najeeb ma murmushi yake don ba k'aramin burgeshi take ba ba kaman yadda ya ganta a yanzu gashi tana Magana cike da sangarta, "Baki ga yaro ne ba kiyi hakuri" Haisam ya fad'a, tura mashi baki tayi alamar bata yi hakurin ba, ruk'o hannun Abdul d'in yayi ya dawo dashi gaba yace mashi "Say sorry to her" da sauri yace "Aunty Zarah Sorry" yayi Maganar yana dariya, harararshi tayi kawae haisam yace taje ta d'aukko Abaya dinta su tafi tace to, tana shirin juyawa Najeeb yace "yar bafullatana ba gaisuwa" dakatawa tayi ta juya ta kalleshi sai lokacin kuma tama ganshi don da duk bata lura dashi ba,ganin yana mata Murmushi yasa itama tayi mashi don ta ganeshi ta gaidashi ya amsa mata bayan ya cire glass d'in fuskarshi, nufar cikin gidan tayi Abdul yabi bayanta yana tambayarta tafiya zata yi tace mashi ehh, bada jimawa ba ta fito Feenah da Abdul na biye da ita suka k'araso wurin Motar, gaida Najeeb Feenah tayi tana cewa shine yazo gidan amman bazai shiga su gaisa ba Abbas yace kuma dama wurinta yace zai zo Najeeb d'in yace to yaga ya tafi bai shigan bane ita dae dariya kawae tayi ta mik'a ma Fatuu yar babbar ledar data ruk'o a hannunta, amsa tayi ta lek'a ciki kafin tasa hannu ta fiddo wani Material mai kyau tare da veil d'inshi can k'asa kuma kayan shafa ne wai sai ta rungume Material d'in ta mik'a mata ledar kayan shafan tace "Aunty Feenah ki bar wad'annan na d'auki wannan" d'an waro ido Feenah tayi tace "saboda me ki tafi dasu duka" tace "ai inada su da yawa Ya Handsome yana siya man" kafin tace wani abu Abbas ya riga cewa"ai na Ya Handsome daban wannan daban Mom Zarah don haka ki tafi dasu" kallon Abbas d'in tayi kafin ta kalli haisam ta d'age gira tace "in tafi dasu??" har saida tasa ya d'anyi murmushi yadda tayi mashi tambayar, ganin tayi mashi tsuru tana jiran amsa kuma kowa shi yake kallo yasa ya d'aga mata kai alamar eh, maida Material d'in tayi tace mata ta gode ta nufi Motar da sauri Abdul ya nufi Haisam yace "Baba zakee zaka k'ara kawo man ita?" kai ya d'aga mashi alamar eh ya juya gun Fatun ya kama hannunta yana tambayarta yaushe zata dawo tace sai Ya Handsome ya kara kawota daga haka ta nufi gaban Motan zata shiga Najeeb yace ta shiga baya zasu tafi tare tace to ta shiga bayan shi kuma ya shiga gaban Haisam ya zagaya side din driver ya shiga, lek'awa Abbas yay yana yi masu sallama yace ma Najeeb sai sunzo rakiya Airport, tada Motar yay su Feenah nayi ma Fatuu bye baye Abdul kamar zaiyi kuka suka fuce daga gidan........ ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *6️⃣6️⃣* ......Suna komawa cikin parlon Abbas ya fad'a kan 3 seater Abdul ma ya haye saman jikinshi yana mai rigimar shidae adawo mashi da Aunty Zarah d'inshi Abbas d'in ya shiga rarrashinshi yana ce mashi zata k'ara zuwa, zama Feenah tayi gefenshi tana dariya kafin tace "kasan mi Dear?" girgiza mata kai yay alamar aa, tace"wllh ni kaina yarinyar ta shiga raina sosae d'an zaman da nayi da ita nima na fara jin kewarta" fuskarshi d'auke da dariya yace "ai haka take shiyasa suke shiri da H,zakeen sosae though dae dama shi sai kayi mu'amala dashi zaka fahimci sauk'in kanshi" jinjina kai tayi alamar gasgata zancenshi sai kuma tace "dama ya aureta don sun matuk'ar dacewa wllh kuma a yadda take yanzu kaga sai yay playing role biyu, gashi matsayin Yayanta kuma mijinta, kai abun zai bada citta fa" ta k'arasa tana dariya shima Abbas dariyar yake yi yana ayyana yadda zamansu zai kaya matsayin miji da mata kafin yace "kema kinsan hakan bamai yuwuwa bane ai", da sauri tace"yo dear mi zai hanashi yuwuwa sai dae in bai sa kanshi auren nata ba but it's possible" d'an ta6e baki kawae yay yana murmushi bai dae ce komai ba. Suna hawa hanya Najeeb ya fad'i mashi sunan wata shopping mall yace ya kaisu zaima Zarah shopping, kai ya d'aga mashi kawae, bayan sun k'arasa awurin da ake yin parking ya parker Motar Najeeb ya bud'e ya fita kafin ya bud'e ma Fatuu yace ta fito, k'in fitowa tayi ta bishi da ido yace "ko nima sai Ya Handsome din ya baki izini ne?" shiru bata ce komae ba hakan yasa ya duk'a yace ma Haisam "ka bata permission" kallonta Haisam yay ta cikin madubi suka had'a ido da ita ya lumshe mata ido alamar taje sannan ta fita daga cikin Motar Najeeb yai wani Murmushi had'i da jinjina kai yay mata alamar suje,maimakon ta tafin sai ta lek'a ta kopar data fito tace ma Haisam "Ya Handsome banda kai zamu?" d'aga mata kai yay kafin yace "kuje ina nan" janye kan tayi ta rufe kopar tabi bayan Najeeb d'in suka nufi cikin Mall d'in, da kanshi ya d'aukko shopping cart yace ta d'auki duk abunda take so,tsaye tayi mashi tana kallonshi yace "Zarah baki ji mi nace ba?" yay Maganar ya kafeta da lumsassun idanunshi, d'an yamutsa fuska tayi kaman zata yi kuka tace"to ai fa ni ba abunda nike so ina da komae" d'an murmushin gefen baki yay yace"i know,amman ai k'ari baya k'in dad'i ko,ko dae ni baki d'auke ni kaman yayanki bane?" tace "to ai shi an sanshi a gidanmu kai kuma ba'a sanka ba in ka siya man abu fad'a za'ai man", "Owk in muka siyan sai in biki muje gidan in fad'a masu nine na siya maki don kar ayi maki fad'an hakan yayi maki?" shiru tayi sai kuma ta d'aga kai alamar ta yarda, zagayawa suka fara yi yana tura cart d'in saidae sam ta kasa d'aukar komae hakan yasa ya fara daukar mata da kanshi, sosae ya jidar mata kaya har saida tace mashi amman dae duk ba nata bane ko yace to na waye, tana jin hakan tace ita gaskiya sunyi yawa ganin zata yi mashi rigima ne yasashi dakatawa ya nufi wurin biya tana ta faman tura baki sai kace ba abun arziki akai mata ba, bayan ya biya aka juye kayan acikin manyan shopping bags ma'aikatan wurin suka biyo su dasu, boot yace ma Haisam ya bud'e aka zuba kayan kafin ya shiga Motar suka tafi, tambayarshi Haisam yay gida zai dropping nashi ne yace a'a ya fad'i mashi yadda sukae da Fatuu na zaije gidansu ya fad'i shi ya siya mata kaya kar a doketa yayi Maganar yana dariya ya dan juya ya kalleta ta tura mashi baki, shima haisam Murmushi yayi kafin yace ya rabu da ita kawae, gida ya maidashi suna isa mai gadi ya wangale masu k'aton gate d'in ya nufi parking space, tunda suka shiga Fatuu ke bin gidan da kallo har suka tsaya, juyawa Najeeb yay ya kalleta da Murmushi yace "to Zarah gaki a gidana zaki shiga ku gaisa da matana ko?" d'an murmushi tayi batare data ce komae ba hakan yasashi cewa "Oh I forgot, ashe kefa sai Yayanki ya baki permission d'in yin abu kike yi" kallon Haisam yayi yana niyyar magana ya rigashi cewa "permission not granted" dariya Najeeb yasa yace"gaisawa kawae zasuyi nothing else" Haisam yace "Inason na kaita gida before Magrib and it's almost time" ya kai Maganar yana duba wrist watch d'in hannunshi, jinjina kai Najeeb d'in yayi alamar gamsuwa kafin yayi mashi sallama yace sai sun had'u gobe ya juya kan Fatuu yace "to yar bafullatana sai watarana ko don ni gobe zan bar kasar nan" zaro ido tayi alamar mamaki sai kuma tace "ina zaka?", da Murmushi yace "k'asan da nike zaune" da mamaki ta k'ara cewa "amman ba kace nan ne gidanka ba?" "Yeah but bamu cika zama nan ba saboda acan nike aiki sai in munzo" cike da jin dadin yadda ta bud'e baki tana yi mashi Magana yake bata amsa, gyad'a kai kawae tayi yace "ko kina da waya ne mu rik'a gaisawa tunda nima na zama yayanki" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a yace "to ya za'ai,ko shikenan bazamu k'ara gaisawa ba?" shiru ta d'an yi sai kuma tace "in ka kira Ya Handsome in ina nan sai mu gaisa" jinjina kai yay ya sakar mata kayataccen murmushi kafin ya juya ya bude Motar ya fita yace ta dawo gaba, bayan ta koma Haisam yaja Motar Najeeb na d'aga mata hannu har suka fice daga gidan. Tunda suka hau hanya ba wanda yace komae shi idonshi na akan hanya ita kuma tana ta kalle kallenta har suka karaso gida, bud'e Motar tayi ta fita yace ta d'auki abunta data aje a bayan tace to, bayan ta d'aukko ledar kayan da Feenah ta bata juyawa tayi zata nufi gida don duk a gajiye take ganin haka yasashi sauke glass ya kirata, komawa tayi ta tsaya tana kallonshi ta gaban yace "kayan boot wa kika bar mawa ne?" ita sai lokacin ma ta tuna dasu don ta manta tace "to duka zan d'auka?" wani kallo ya bita dashi kafin yace "ke dawa aka siya mawa?" shiru tayi tana kallonshi bata ce komae ba, bud'e Motar yay ya fito ya nufi baya,bud'e boot d'in yayi ya fito da jakunkunan ya aje gefe bayan ya rufe yace ta kai wasu sai ta dawo ta d'auki sauran, maimakon ta daukan sai ta fara yamutsa fuska kaman zatayi kuka tace "to ai gwaggo na iya buguna in taji wani ne ya siya man wannan uban kayan" shiru ya d'anyi sai kuma yace taje ta kira mashi uncle d'inta in yana nan don shagon a rufe yake tana shirin nufar gidan Amadun ya fito yana gyara hannun rigarsa da alama alwala yayi yana ganinsu ya nufi Haisam yana washe baki ya shiga gaisar dashi, bayanin kayan yayi mashi yace ya fad'i ma gwaggon ya amsa mashi da to da sauri ya d'auki shopping bags guda biyu ya nufi gidan Haisam yace ta d'auki dayar ta bishi ya juya zai shige Mota sai yaji tace "kai bazaka dauki komae ba?" d'an kallonta yay bai ce komae ba hakan yasa tace "akwae turare da yawa" sai lokacin ya d'an girgiza mata kai da d'an Murmushi alamar a'a yay shigewarshi Mota,ganin bata tafi ba yasashi sake fitowa yace ta shiga gida sai lokacin ta kai hannu ta dauki d'ayar jakar ta nufi gida tana yi tana waiwayenshi har ta shige sannan ya tafi, Lokacin data shiga a gefe ta samu kayan da Amadu ya shigo dasu gwaggon kuma tana band'aki, aje d'ayar jakar da wadda Feenah ta bata tayi a wurin sauran kafin ta shige cikin d'akinta ta canja kaya zuwa doguwar riga ta fito lokacin gwaggo tayo Alwala tana shirin tada salla tana ganin Fatun tace an dawo d'aga mata kai tayi alamar eh tace taje tayi salla to, saida suka gama sallan ne gwaggon ta jawo jakunkunan ta fara duba kayan ciki fatuu dai na gefe sai zare ido take, uban kayan shafa ne kala kala da turarurruka, takalma jakuna yan kunne fashion harda jallabiyu guda ukku da kuma kananan kaya, tana cikin dubawa Amadu ya shigo don shima yana son ganin kayan da abokin haisam d'in ya siya mata, da tsananin al'ajabi gwaggo ta d'ago ta kalleta kafin tace "yanzu duk wannan uban kayan abokin nashi ne ya siya maki?" da sauri ta d'aga mata kai ta kuma cewa "to hakanan zai kashe uban kud'i ya sai maki kaya har haka sai kace lefe?" da sauri Fatun ta fara mata bayanin yadda ya siya matan har zuwa gidanshi da suka maidashi ta kuma ce mata shine ya bata kud'i masu yawa barka da salla ranar salla, shiru gwaggon tayi tama kasa Magana don mamakine kunshe cikin ranta har fuskarta ta bayyana, Amadu ne yace "su fa masu kudin nan basu d'auki wannan a wani abu ba wllh don haka kar ma ki wani damu" ya juya kan Fatuu yace "inyee kefa yanzu kin zama mai sa'a abun arziki kota ina samu kike bari nima in d'auki rabona to duk da ma bai wuce turare tunda duk abubuwan kune na mata" ya kai hannu bayan ya gama Maganar ya d'auki manyan turare guda biyu yace "na d'auki wad'annan don turaren ma duk na mata ne, daga yanzu in za'ai maki siyayya ki rink'a d'aukko abubuwan maza ba naki kadae ba" ya kai Maganar yana jaddada mata da hannu kafin ya nufi hanyar fita gwaggo ta dan ta6e baki ta bishi da ido har ya fuce, juyawa tayi ta kalli Fatuu data yi mata k'uri da ido ta sauke ajiyar zuciya kafin tace ta kwashe kayan ta kai cikin d'aki an gode Allah ya saka da Alkhairi, a sanyaye fatun ta amsa da Amin, bin ta da ido tayi tana kwashe kayan har ta gama, bayan sallar isha gwaggon ta bata warmer guda biyu babba da k'arama mai dauke da abinci tace ta kai ma Amadu tace ya kai ma Haisam Fatun tace ita takai mashi mana tace a'a dare yayi ta kai ma Amadun, ba don taso ba taje ta kai mashi, lokacin daya kai mashi abincin yana zaune a falonshi yana operating laptop, bayan ya gaida shi yace dama abinci ne gwaggo tace ya kawo mashi shiru ya d'anyi don shi ba kowane abinci yake ci ba da daddare yafi son mara nauyi duk da baisan miye aciki ba, godiya yayi mashi bayan Amadun ya tafi ne ya bud'e babbar warmer din mai dauke da farar shinkafa da taliya sai k'arama kuma miya ce aciki harda nama rufewa yayi ya d'auki wayarshi ya kira tk, tambayarshi yayi yana gida yace mashi eh yace ya kawo mashi plate da spoon ya amsa da to, bada jimawa ba sai gashi ya kawo masan bayan ya gaidashi yana kokarin d'aura plate d'in kan c-table haisam din yace ya wanko mashi su a basin ya amsa da to, bayan ya dawo ya d'aura kan c-table d'in yace "shikenan Ya Haisam?" alamar ya tsaya yayi mashi da hannu saida ya k'arasa abunda yake a laptop d'in sannan ya kalleshi yace "a ina kake cin abinci ne?" dariya tk yayi yace ina dafawa ne" jinjina kai yayi ya bashi umarnin ya zuba mashi abincin dake a cikin warmer d'in ya amsa da to, yana zuba d'an kad'an yace ya barshi haka ya bude miyan ya zuba mashi naman ma yana sa tsoka biyu yace ya isa,umarnin ya d'auki warmers din abincin yaje yaci ya bashi yace in ya gama ya kai warmers din gidansu Zarah ya amsa da to, har zai tafi sai kuma ya dakata cike da kulawa yace "amman ya Haisam wannan abincin kaman yayi kad'an ba zai kosar da kai ba" maida bayanshi jikin kujera yayi fuskarshi asake yace ba wani abu zai ishe shi yaje kawae, "to ko in had'o maka tea?" Tk d'in ya tambaya, shiru ya d'anyi sai kuma ya d'aga mashi kai alamar eh, cike da jin dadi ya nufi hanyar fita shi kuma ya fara cin abincin ba'a dau wani dogon lokaci ba Tk ya kawo mashi tea d'in ya zauna yana mashi yar fira har ya gama ya dauke abubuwan abincin kafin yayi mashi saida safe, cigaba da abunda yake yayi wayarshi ta fara ringing ya kai hannu ya d'auka, Murmushi ya saki ganin mai kiran nashi wato Hajiya, handsfree yasa ya aje wayar agefe hajiyar tayi mashi sallama, "Sweetheart hope u'r work" ya fada idonshi akan screen, "Lafiya lou nike kaifa?" "Same" ya bata amsa a takaice, "Yau mi kaci ne?" ta tambaya, har saida ya d'anyi Murmushi kafin yace mata abinci, tace "da safe kaci abinci?" yace mata eh yaci a wurin aiki, ta tambayi da rana fa yace mata yaci a gidan Abbas, "To yanzu da daddare fa?" ta sake tambaya, d'an girgiza kai yay kafin yace "in kin damu da wannan ki dawo mana" a d'an fad'ace tace "nima ai nan d'in kaman akan k'aya nike kawae banda yadda zanyi tunda an fi karfi na" dariya yayi har hakoransa suka bayyana kafin yace gidansu ne k'ayar tace eh mana, "Pls tell me kaci abinci yanzu kuwa, kodae insa Saude ta dawo ne dama don nasan tukur ya iya dafa abinci shiyasa nike kyaleta sai na dawo itama ta dawo amman yanzu ko don kai inaga zan sa ta dawo kawae tunda a gaban idona ma ba son ci kake ba balle yanzu da bani ba kuma mai dafa makan" d'an ta6e baki yay kafin yace ta kyaleta kawae sai ta dawo tace to ya fad'i mata abunda yaci yanzu, "Zarah ta kawo man" daga jin muryarta taji dadin hakan tace "yauwa naji dadin hakan wllh sun kyauta Allah ya saka, in kana son wani abun zaka iya sa tukur ma yayi maka don ya iya dafa abinci sosae" amsa mata yay da owk daga nan suka ci gaba da yin hira yana daddana Computer din. Washe gari Friday misalin Karfe bakwae Fatuu ta zo part d'inshi ganin bai cikin parlon yasa ta kware baki tana yin sallama sai gashi ya fito cikin suit Maroon Colour, sakin baki tayi tana kallonshi hakan yasa yay mata wani kallo mai kaman harara ta saki Murmushi, k'arasowa yay cikin falon ya zauna ganin tayi tsaye yace mata ta zauna mana sannan ta zauna ta gaidashi tana ta Murmushi dae, bayan ya amsa ta nuna mashi d'an basket da ta d'aura kan c-table tace "gashi nan abun kalaci ne na kawo maka" d'an waro ido yay ya kalli basket d'in kafin ya maido idon kanta calmly yace "breakfast dis early?" tura baki tayi tace "to ba aiki zaka tafi ba shiyasa ai na kawo maka da wurin" still idonshi akanta yace "ban iya breakfast a wannan time en" wani kallo tay mashi sai kuma ta juya mashi bayan kanta tana fad'in "Allah sai kaci shi" bin ta da kallo yay da d'an murmushi akan fuskarshi sanin in ya biye mata haka zasuyi ta jan magana kuma so yake ya tafi yasashi cewa ta had'a mashi amman d'an kadan in yaci da yawa zai iya yin amai ne da sauri ta kalleshi ta washe baki tace to, had'a mashi ta shiga yi dama an sako cup da spoon don ruwan tea ne acikin flask da ledar biredi mai kyau sai kayan hadawa madara da milo da sugar a gefe sai kuma soyayyen kwae rufe cikin bowl, komi sai ta tambayeshi in yayi bayan ta gama ta koma ta zauna kan carpet tana wasa da yatsunta shi kuma yana cin breakfast din a nutse can ya tambayeta ita ta yi breakfast dinne tace a'a sai ta koma gida, jinjina kai kawai yay don sauri yake, yana gamawa yace ta tafi da kayan tace ai ance in ya d'iba ta kaima Tk sauran ya amsa da owk yana nufar Bedroom dinshi, brush ya sake yi kafin ya fito ya shiga d'ayan d'akin bada jimawa ba ya fito hannunshi ruk'e da bak'ar jaka ya nufo falon, saida ya kira Tk a waya lokacin baima tashi daga bacci ba yace mashi in ya tashi yazo part d'inshi ya d'auki breakfast cike da girmamawa ya amsa mashi kafin yayi mashi adawo lafiya, ce mata yay tazo ya ajeta gida ta mik'e da sauri tabi bayanshi, Ana gama sallar Juma'a gwaggo tace ma Fatuu taje taga in Haisam ya dawo daga aiki lokacin ta ci gayun juma'a da d'aya daga cikin jallabiyun da Najeeb ya siya mata ash colour tasha adon duwatsu sai salki take, koda taje bai dawo ba sai kawae ta dawo ta d'auki rigar da gwaggo tace ta ba Haulat cikin kayan da aka siya matan da su kayan shafa ta tafi kaima Haulat, sosae tayi farinciki tana ta faman godiya harda innarsu sai washe baki haulat take don sam bata da jallabiya dama, sosae kuma ta yaba ta jikin Fatun gab da la'asar ta dawo gida ta k'ara zuwa ta duba ko haisam d'in ya dawo ta iske bai dawo ba,sai bayan sallar la'asar Amadu ya shiga yace ma gwaggo gashi nan ya wuce dayake tace in yaganshi ya sanar mata,zumbur Fatuu ta mik'e dama suna zaune a tsakar gidane don inuwa ta sauka, Kitchen ta nufa ta d'auki kayan abincin ta tafi kai mashi, da sallama ta shiga cikin falon saidae bai ciki sanin bai dade da dawowa ba yasa tayi tunanin kilan wanka yake, wuri ta samu ta zauna bayan ta d'aura basket d'in a saman c-table shiru bai fito ba hakan yasa ta d'auki remote ta kunna tv taci gaba da kallo abunta tun tana zaune har ta d'an kishingida sai can bayan wani lokaci ya fito cikin Sportswear suna had'a ido ya bud'a mata ido ita kuma tayi mashi dariya, wuri ya samu ya zauna ta gyara zamanta dama a d'ayan bangaren inda take zama ta zauna gaidashi tayi kafin tace "nayi kyau ko?" kai ya d'aga mata tace "cikin kayan da abokin nan naka ya siya manne wai ya sunanshi?" shiru ya d'anyi sai kuma a hankali ya furta "Najeeb" jinjina kai tayi ta kuma cewa "amman dai yana da kirki kaman kai hakanan bai sanni ba ya kashe uban kud'i ya siya man kaya,Allah ya saka maku da Alkairi ya saka ku a Aljanna ku duka" acikin ranshi ya amsa fuskarshi da d'an Murmushi don yadda tayi Maganar kaman ba ita tayi ta ba, "Yace yana gaidaki ya tafi d'azun" taji ya fad'a, da sauri ta kalleshi tace "kenan ya tafi kasar da yace man can yake?" kai ya d'aga mata tace "wayyo Allah ya kaishi lafiya" amsa mata yayi da amin ta nuna mashi basket tace ga abincinshi nan ta zuba mashi, shiru yayi yana kallonta har saida ta maimaita mashi sannan yace yaci abinci a wurin aiki tace to sai yaci da daddare, d'aga mata kai kawae yayi alamar to, sai kuma yace in taje gida ta fad'i adaina wahalar yin abinci dashi tunda yana ci awurin aiki da safe kuma baiyin breakfast da wuri tace "to da daddare fa?" yace "nafi son light food so Tk zai man wannan" jinjina mashi kai tayi can ya mik'e yace mata zai tafi gym,mik'ewa tayi itama tace "inzo in raka ka" girgiza mata kai yay yace "yawon zai yi yawa" daga haka ya nufi dakin lab ya d'aukko jakarshi ya fito suka fita tare, saida ta raka shi har parking space ya fiddo bike dinsa tace don Allah ya d'anata amman sai ya girgiza mata kai alamar a'a, tadashi yay ya fara tafiya a hankali yace suje suka tafi tana gefenshi sai tura baki take saboda yak'i goyata shidae sai murmushi yake kawae ahaka har suka je daidai gidansu sannan yasaka helmet ya fuzgeshi da gudu tana ta kallonshi har ya 6ace ma ganinta,tana shiga gidan ta nufi gwaggo dake zaune ta shiga fad'i mata abunda haisam d'in yace game da abincin da ake kai mashi, yar dariya kawae tayi tace ma Fatun ta kira mata shi a waya, farko data kira bai d'auka ba sai lokacin ta tuna tace mata ai fa ya fita yanzu da k'atoton mashin d'inshi kilan bai sauka ba, bayan wani lokaci sai gashi ya biyo kiran ta mik'a mata wayar, d'auka tayi ta kanga ta a kunnanta yana jin muryar gwaggon ya gaisar da ita ta amsa tace mashi taji sako wurin Fatuu ai ta d'auka anzama d'aya yana murmushi yace mata hakane tace kuma a ina yaga in uwa tayi ma danta abu yake zama wahala, nan ma dae Murmushi yayi kawae cike da zolaya tace mashi kodae bai jin dadin abincinne yaji shi ba irin wanda ya saba ci ba, wannan karon har saida yayi yar dariyar da itama taji sautinta yace mata ba haka bane tace to dole za'aci gaba da kawo mashi ai na d'an lokaci ne ko in yaje aikin ya rink'a cin kad'an in ya dawo sai ya k'ara, cike da girmamawa ya amsa mata da to kafin yayi mata godiya sukae sallama, Washe gari Asabar ana tashi islamiyya gidan hajiya ta wuce, lokacin data je part d'inshi yana zaune a falo yana aiki, bayan sun gaisa yace taje gida kar a nemeta har ta mik'e sai kuma ta tsaya tace "Ya Handsome wai baka ce zaka koya man irin turancin nan ba ko ka fasa ne?" d'agowa yay ya kalleta ya d'anyi shiru sai kuma yace "yaushe zamu fara?" da sauri tace "yanzu tunda na dawo daga makaranta ba abunda zanyi kuma" jinjina kai yayi yace taje ta cire uniform sai ta d'aukko book da pen ta amsa da sauri ta fuce, tana komawa gidan shaf shaf ta canja kaya taje kicin ta gaya ma gwaggo tace taje, lokacin data koma tana shirin zaunawa yace suje yai mata alamar waje, mik'ewa tayi suka fita, tana biye dashi suka nufi parking space can farko inda ba Mota dama ya kira Tk yace ya kawo masa kujeru guda biyu wurin harda d'an table dinsu, nuna mata d'aya yayi alamar ta zauna kafin shima ya zauna ba 6ata lokaci ya fara mata lesson din turancin, kiran sallar Azahar yasashi mik'ewa yace zaije yin salla itama taje tayi tace dakinshi ko gida yace mata taje gida sai taci abinci tace to shima zata kawo mashi kai kawae ya d'aga mata ya nufi part d'inshi don yin alwala, tana zuwa gida tayi sallar bayan ta gama taje d'aki wurin gwaggo tace ina abincin Ya Handsome zata kai mashi, tare suka fito suka nufi kicin ta bata kayan abincin nashi har zata tafi gwaggon tace ta dawo itama taci abincin tace mata zata ci acikin nashin, "Baku gama lesson d'in bane?" ta tambaya idonta akanta amsa mata tayi da eh, ganin ta kafeta da Ido yasa da sauri tace "wllh kuwa da gaske nike kuma in baki yarda ba ki aiki kawu Amadu ya dubo maki muna nan inda ake ajiye motoci anan yake koya man" jin hakan yasa gwaggon taji hankalinta ya k'ara kwanciya ba kuma don tana zargin wani abu ba sai don yakamata dama tasa kula duk da yardar da tayi da haisam d'in, ce mata tayi ta tafi, bayan ta koma bata iskeshi a parking space d'in ba tana niyyar zuwa part dinshi ya fito daga cikin Masallaci, komawa tayi ta zauna shima ya k'araso ya zauna ba tare data tambayeshi ba ta fiddo kayan abincin ta zuba mashi ta tura mashi kafin itama ta zuba tace mashi suyi yar rigen cinyewa, d'an murmushi yayi ya girgiza mata kai kawae, ba laifi yaci sosae bayan ya gama ya kira Tk a waya yazo ya d'auki sauran Abincin daga haka suka ci gaba da yin lesson din har saida aka kusa kiran la'asar sannan yace mata taje gida sai gobe, washe gari lahadi haka ya k'ara yi mata lesson d'in acikin parking space d'in kuma ba laifi tana kamawa sosae, ana shiga ranakun aiki ganin Haisam din yayi mata wuta daga ya ajeta a Makaranta bata k'ara ganinshi don lokacin da yake dawowa ta tafi islamiyya in kuma aka taso su shi kuma bai dawo daga gym ba gashi in tace zata kai mashi abinci da daddare sai gwaggo ta hana tace dare yayi sai ranakun da ba'a islamiyya ne kadae take samun ta dan ganshi in ya dawo kafin ya tafi gym wani lokacin kuma in gwaggon bata dawo daga aiki ba da daddare sai ta lalla6a ta saci hanya ba tare da Amadu ya ganta ba taje wurinshi kuma data je sun gaisa yake rakota gida karshe dae ta rokonshi tay wai don Allah duk in ya dawo da daddare kafin yaje gida ya tsaya ya kirata da layin gwaggo su gaisa yace mata a'a bazai kira ba tace to ya rink'a yi mata horn sai ta fito su gaisa sannan ya yarda ya rink'a yi mata hakan amman ba kullum ba. Salla da sati ukku Hajiya ta dawo, sosae Fatuu tayi farinciki kaman ta zuba ruwa a k'asa tasha don tasan yanzu zata rink'a zuwa gidan duk lokacin da take so ba tare da an hanata ba, rayuwa taci gaba da gudana kaman da bayan dawowar hajiyar a haka har babbar salla tazo wannan karon gallelliyar shadda Haisam ya dinka ma Fatun tasha uban aiki wanda in ka kalla sai ka k'ara kallo don a Abuja aka yo mata d'inkin sai dae kawae taje part d'inshi ya bata ana saura kwana biyu salla harda takalma da gyalen da suka shiga da shaddar, sosae Fatuu taji dad'in dinkin ba kamar da yake kuma wannan sallar a nan zasu yi ta hakan yasa sai faman d'okin zuwan sallan take, ranar sallar tare suka je salla kaman k'aramar salla ana dawowa aka fara yanka ragunan layya harda na gwaggo wanda Haisam ya siya mata katon gaske, shima Haisam din yayi layyar kusan rago biyar aka yanka gidan hajiyar don tana raba ma mutane d'anyen naman sosae shima Haisam nashi guda biyun duk rabar dashi akai, washe garin sallar Tk ya tafi gida dama duk babbar salla gida yake tafiya, yan Abuja basu samu zuwa ba, dama ba kowace babbar salla suke zuwa ba wani lokacin sai bayan sallan suke zuwa to wannan sallan Senatorn da matanshi duka da wasu daga cikin manyan ya'yanshi sun tafi Hajji yayin da sauran kuma suka tafi Lagos wurin Hajiya Maryam sai bayan sallan ne zasu zo Katsina....... *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *6️⃣7️⃣* ........Sosae Fatuu taji dadin sallar don sun fita yawo da haisam duk da bai biye mata ba na iya rana d'aya kawae suka fita tare kuma yawanci gidan Abokanshi yaje da ita ciki harda gidan Abbas sosae Abdul da Feenah suka ji dad'in zuwan nata taci gayu da shaddar da yayi mata, shima Abbas d'in bayan sallan da kwana ukku ya kawo Feenah yini gidan Hajiya suka wuni tare da Fatun harda ma Haulat tazo suka gaisa ta kuma je gidansu Fatun suka gaisa da Gwaggo bayan Magrib Abbas yazo ya daukesu. Bayan sallah da sati biyu su Fatuu suka fara jarabawar gama junior secondary wato JSCE, Haisam yayi mata abubuwan graduation sosae su littattafai masu d'auke da hotonta da key holder, biro, handkerchief jotter gaba d'aya tafi kowacce d'aliba yin abubuwa don har Malamai ta raba mawa,ranar da suka gama yakama ranar laraba ne cike da farinciki ta dawo gida da yamma sam bata ji wahalar jarabawar ba ba kamar da yake tana da kokari kuma Haisam ya taimaka mata wurin koya mata abubuwan da suka shafi jarabawar hakan yasa tayi ta cikin sauki ba tare data ji wahalarta ba, tana shiga Gwaggo ta taso ta rungumeta cike da farinciki, bayan ta gama tayata Murna ta kuma yi mata Addu'oi ta nufi gidan Hajiya ba tare data cire uniform d'inba gwaggo na ta tsaya taci abinci tace sai ta dawo, can ma Hajiyar Murna ta tayata da Addu'a ita da Saude, bata dad'e da zuwa ba Haisam ya dawo tana jin k'arar bud'e mashi gate ta tashi da sauri ta nufi hanyar fita,yana fitowa bayan ya gama parking Motar ya hangota ta nufo shi hakan yasashi dakatawa har ta k'araso sai faman washe mashi baki take, shima Murmushi yake yace mata Congrats tace mashi tagode, bud'e baya yayi ya fiddo flower da card na fatan sa'a a jarabawar da tayi mai shegen kyau sai d'aukar ido yake ya mik'a mata harda Flower d'in, waro ido tayi alamar mamaki kafin ta amsa tana kallonsu d'agowa tayi ta kalleshi baki washe tace nata ne ya daga mata kai alamar eh ta hau yi mashi godiya, hannu ya kai ya d'aukko jakarshi kafin ya rufe Motar da sauri ta amshi jakar suka nufi part d'inshi, bayan sun shiga ya amshi jakar ya nufi hanyar Bedroom ita kuma ta zauna tana k'ara kallon abubuwan daya batan sai faman dariya take, mamakinta abunda take gani yan kasan waje nayi a Tv suba mutum kyautar flower yau shine itama akai mata dama ba k'aramin burgeta hakan keyi ba, tana ta farincikinta har bata san lokacin daya d'auka ba saidae ganinshi tayi ya fito cikin workout outfit yace mata suje part d'in Hajiya ta mik'e tabi bayanshi, suna shiga cikin Parlon ta nufi Hajiya tana nuna mata kyautar da Haisam din ya bata ta yaba sosae sai bayan daya gama cin abinci zai fita ne tabi bayanshi yana tafiya itama ta nufi gida. Washegari Alhamis da rana Fatun na kwance kan tabarma gwaggo na gyara mata kai ta sanar da ita cewa ta shirya kayanta ranar Asabar zasu tafi Yola gaba d'ayansu amman su zasu kwana biyu ita dawowa zatayi, sam Fatuu bata ji dadin Maganar ba ba kamar da gwaggon tace can zata baro su ita da Amadu har ce mata tayi to su dawo tare mana tace a'a ai tunda ta baro garin bata je ba don haka yakamata taje ta kwana biyu, "To amman shi kawu Amadun ba yana zuwa Makaranta ba?" ta tambaya tana yamutsa fuska gwaggon tace "eh amman yace zai tambayi izini don shima yana son zuwan saboda ya kwana biyu baije ba, inaga ma da hankalinshi ai sau d'aya ya ta6a zuwa" turo baki tayi kawae ita dai har cikin ranta bata son taje ta wani dad'e, tana gama gyara mata aka fara kiran salla tace ta tashi tayi salla itama ta mik'e, can bayan sun gama sallan ne ta bata kudi tace tayi sauri taje ta siyo mata kuka da daddawa zata yi miya nata sun k'are sai taje kasuwa zata siyo, d'aukar hijab dinta data aje bayan ta gama salla tayi tasa ta mike ta nufi hanyar fita, tana fitan maimakon ta tafi aiken da akai matan sai kawae ta nufi gidan Hajiyar Sanata don taga in Haisam ya dawo, tana zuwa ta iske ya dawo amman bai cikin falon sanin kaman yanzu shirin zuwa gym yake yasa ta zauna kan carpet tana jiranshi sai faman kunci take, tana zaunen ya fito kallo d'aya yayi mata yasan akwae abunda ke damunta, gaidashi tayi bayan ya zauna ya amsa mata kafin ya tambayi abunda ke damunta kaman zatayi kuka tace "ba gwaggo bace....wai Adamawa zamu tafi ran Asabar kuma acan zata baro ni nida kawu Amadu wai sai munyi sati biyu zamu dawo" jingina bayanshi yay da kujera da d'an Murmushi akan fuskarshi yake kallonta yace "to ai ba wani abu bane u supposed to be happy instead, zakije kiga relatives naki especially ur beloved dad baki son ki ganshi?" tura baki tayi tace "inaso amman dae sati biyu yayi yawa ni banson ta baro ni can nafi son mu dawo tare" sigh yay gently yace "ai ba wani dad'ewa zaku yi ba 2 weeks is just like tomorrow da kunje zai yi ku dawo" d'aga kai tayi ta kalleshi kaman zatayi kuka tace "shikenan bazan rink'a ganinka ba har sai mun dawo?" fad'ad'a Murmushinshi yay dama yasan duk wannan damuwar saboda shi ne don ya lura bata son abunda zaisa ta daina ganinshi, hannu ya kai ya shafi gaban kanshi kafin yace "in kin dawo ai zaki ci gaba da ganina besides akwae vedio call ko" jujjuya kai tayi kaman zata yi kuka tace "to ai shi kawu Amadun ne fa ba lalle ya rink'a kira man kai ba yana iya hana ni wayan" shiru yay kaman yana tunanin wani abu can taji yace "ko in sai maki phone d'in?" a d'an rud'e ta kalleshi sai kuma ta fara girgiza mashi kai tace "Gwaggo bata son in rik'e waya yanzu ko ka siya man hanani amfani dashi zatayi, kasan miyasa?" ta bud'a ido girgiza mata kai yay alamar a'a, taci gaba "wai wata abokiyar aikinta ce wani saurayi yay ma d'iyarta wayo saboda ya siya mata waya yayi mata ciki kuma har ta haifi d'an shegen" bilhakki take bashi labarin shidae shiru yay yana binta da ido saidae sam bai ji komae ba don yanzu yama saba da halinta na ya6o Maganar da duk tazo mata, ganin yayi shiru yana kallonta yasa da sauri tace "bafa ina nufin kaima wayon zaka man ba kawae na fad'i maka dalilin dayasa bata son in ruke waya ne amman tace in zanje jami'a zata siya man da kanta ma" jinjina mata kai yayi yace ya fahimta zai rink'a kiran Amadun yace ya bata, amsa mashi tayi da to amman still ba don ranta na son tafiyar ba can tace "ko muje tare da kai?" d'age gira yay kafin yace "aiki fa?" tura baki tayi tace "to ai tunda ran Asabar zamu tafi kaga ba aiki sai ka rakamu ka dawo ran Monday kaga rana d'aya ne bazaka aikin ba" d'an Murmushi yay yace mata shima zai je Lagos gobe ne da mamaki tace "shine kuma baka gaya man zaka tafi ba ko wayo kaso yi man?" daga mata kai yay alamar eh yanata murmushi ta turo baki, shiru sukae na d'an wani lokaci tana ta jujjuya kud'in hannunta taji yace "ba an aike ki bane?" tana yamutsa fuska tace "eh wai kuka da daddawa zan siyo mata ita bata gajiya da yi mana tuwo wllh" Murmushi ya dan yi "ai shima abinci ne mai kyau" tace "to amman ai kai baka ci" "Ina cin wani" ya bata amsa tace "na shinkafa?" yace "yeah and semovita" tace "itama miya baka shan mai daddawa ko?" wani kallo yay mata ba tare da ya bata amsa ba tasa dariya dama da biyu ta ambaci daddawar sarae tasan bai shan, tura baki tay tace "nima wllh na tsani miyan yauki mai daddawa hakanan nike sha" yace "kije ki siya mata in na dawo sai kizo kici dinner nan" da sauri tace "amman tare zamu ci na bankwana?" tayi Maganar tana jaddada mashi, Murmushin gefe yayi kafin yace ai zata dawo ko tace eh amman dae ai sai ta dad'e yace owk tazo sai suci tare daga haka ya mik'e itama ta mik'e suka fita, Washe gari Friday bayan sallan Juma'a Haisam da Hajiya na cikin cin abinci Fatuu ta shigo tayi gayun juma'a, bayan ta gaishe su Hajiya tace tazo taci abinci tace ta koshi yanzun ta gama cin abinci tace bata yarda ba sai taci ko yaya ne tunda daga yau ai sai bayan wani lokaci ko, kujera taja ta zauna ta zuba d'an kad'an, Haisam ne ya fara tashi ya nufi cikin falon kafin fatuu ma ta mik'e tace ma Hajiyar ta koshi, kishingid'e ta iskeshi tana niyyar zama ya mik'e yace tazo suje ba tare da ta tambayi ina ba tabi bayanshi ya d'an daga murya yace ma Hajiya zasu je su dawo tayi masu adawo lafiya, parking space suka nufa ya fiddo Mota cikin harabar sannan Fatuu ta hau suka fice, saida ya tsaya adaidai gidansu yace taje ta fad'i ma gwaggo zasu je su dawo sannan suka wuce, Bayan tafiyarsu gwaggo ma ta fito ta nufi gidajen makwabta yi masu bankwana harda gidan Hajiya, saida suka hau hanya sosae sannan ta tambayeshi ya akai bai tafi Lagos d'in ba ko sai anjima yace mata ya fasa tafiya yau sai gobe tace sai yaga tafiyarsu kenan ya d'aga mata kai alamar eh, ganin suna ta tafiya ne yasa ta sake tambayarshi inda zasu yace mata bazata kai ma yan'uwanta tsaraba bane, jin haka yasa tace "tsarabar zamu je siyowa?" kai ya d'aga mata ta kuma cewa "to mi za'ai sai masu?" shiru yayi idonshi a kan hanya sai kuma yace "Biscuits, chocolate and so on" jinjina mashi kai tayi can kuma sai ta fashe da dariya tace "wayaga su Yaya na cin chocolate saniya kenan" d'an juyowa yay suka had'a ido nan take ta tuna da fad'an da ya ta6a yi mata na ba'a had'a mutum da dabba hakan yasa da sauri tace yayi hakuri, shiru yayi sai kuma ya tambayeta wacece yayar tace matar Ardo yace "Grandma d'inki kike ce hakan?" da sauri tace "ai ba itace kakata ba ni kakata ta rasu kuma sunanta ne ma aka sa man Fatee...." shiru tay bata k'arasa ba tunawa da sunan maman shi ne, jinjina kai yay yace "ai itama grandma d'inki ce ko" da sauri tace" Allah ya kyauta wannan muguwar ta zama kakata, kai baka santa bane bata da mutunci kuma ta tsaneni da ina can tai ta k'ala man sharri tana sawa ana buguna kuma har babana ma bata son shi saboda taga ardo yafi ji dashi haka lokacin da Mamata bata lafiya harda ita ta hana a kaita Asibiti da wuri" ta k'arasa Maganar kaman zata yi kuka, shiru yayi kawae matsalar kaima yaro abu kenan don kwakwalwarshi bata mantawa balle abu irin wannan ko babba ma bazai ta6a mantawa ba, juyawa yay ya kalleta ta kwantar da kanta da gani ranta a 6ace yake slowly ya kirata ta d'aga ido ta kalleshi yace "Do forgive her and forget everything" turo baki tayi yaci gaba "Allah ubangiji yana son bayinsa masu yafiya, don shima mai yawan gafara ne in dae ka sa6a masa ka roki ya yafe maka zai yafe maka so kema ki yafe mata ki manta don in kin rike abun zai dame ki ne" tura baki tayi batace komae ba har saida yace bata ji abunda yace bane sannan cike da shagwa6a tace "yanzu duk abunda tayi man sai kace in yafe mata......" katseta yayi "yeah in kin yafe mata Allah zai daga darajan kine kuma kema ai kina son ki laifi a yafe maki ko" da sauri tace "to ni wama na ta6a ma laif...." kasa karasawa tayi ta zuba mashi ido tana mashi kallon rashin gaskiya, ta cikin mirror ya kalleta suka had'a ido ya dan ta6e baki ganin hakan yasa tana tura baki tace "shikenan na yafe matan amman wllh indae nayi kudi zan kai kowa makka banda ita" d'an jinjina kai yay yace "baki yafe matan ba kenan" da sauri ta kalleshi "nace na yafe mata fa, ko kana nufin itama sai na kaita makkan?" kai ya d'aga mata alamar eh, wani kallo tayi mashi kaman zatayi kuka "yanzu duk abunda tayi man kuma sai kace itama sai na kaita Makkan" yadda tayi Maganar sai kace tayi kud'in kaisu makkan ne, cigaba da yi mata nasiha yay kan yafiya idonshi akan hanya har dae ta saukko tace to zata kaita makkan, wata supermarket suka je sosae ya jidar mata kayan zaki harda abubuwan wasan yara itama ya siya mata ice cream, bayan sun bar wurin zagayawa yayi da ita cikin gari tana shan ice cream d'in tana yi mashi fira k'arshe ya wuce da ita Gym duk da ba exercise d'in zaiyi ba don baizo da shirin yi ba, lokacin data je wurin Anah sosae tayi farinciki da ganinta harda ma sauran yan wurin wad'anda suka santa koda tace zata hau machine hanata Anah tayi mutane nata masu dariya sai gab da Magrib ya maidata gida, sosae gwaggo taji dadin tsarabar da yayo mata tasa Albarka da Addu'oin da ta saba yi mashi, Bayan sallar isha sai ga Hajiya tare da Saude wai ta k'ara zuwa bankwana, d'akin gwaggo suka shiga dayake akwae wutar Nepa, bayan sun gaisa suka shiga yin hira harda Fatuu data shigo ta gaishesu hajiyar na ce mata zatayi missing dinta Allah yasa kar in taje su ruketa su aura mata d'an Fulani Fatun tace da kuwa ta gudo wllh gaba d'aya suka sa dariya, suna cikin hiran tasa Saude ta bud'e ledar da ta ruko mai d'auke da kaya, atampopi ta nuna ma gwaggon tace gashi nan akai ma Yadikko da Fatuu ke yawan bata labarinta da kuma k'annenta su d'inka sai shaddoji suma tace na Baban Fatun ne da ardo sai kuma yayanta kamalu, saboda tsabar farinciki har gwaggo ta rasa wace irin godiya zatai mata sai faman washe baki take tana sa Albarka daga baya sukai masu rakiya da zasu tafi bayan sun k'ara yin bankwana da juna, Washe gari wuraren Karfe shidda na Asuba Haisam ya parker a kopar gidansu don kaisu tasha dama tun jiya ya kira Amadu ya tambayeshi lokacin da zasu tafin ya fad'i mashi yace zaizo ya kaisu, kiranshi yay a waya ya sanar dashi yana kopar gida aikuwa ba tare da 6ata lokaci ba Amadun ya fara fitowa da jakunkunansu Haisam ya bud'e mashi boot ya fara sakawa yana gamawa Gwaggo da Fatuu suka fito gwaggo na sanye da lace da Hijab kalar kwalliyar fulawoyin leshin itama Fatun lace d'in da Haisam yayi mata ne da k'aramar salla tasa ta yafa golden gyalenta da takalmanta masu madauri hannunta ruke da jaka sai dae sam Fuskarta ba walwala saida gwaggon tayi Addu'a tasa Fatun tayi don neman tsari sannan suka fito, Amadu ne ya bud'e ma gwaggon kopar baya ta shiga yace ma Fatuu ta zagaya ta shiga shi kuma ya koma ya kulle gidan kafin ya dawo ya bud'e gaba ya shiga, gaisawa sukae da gwaggon ita kuma Fatun saida suka had'a ido ta mirror sannan tace mashi ina kwana d'an Murmushi yay kafin ya amsa yana kokarin kunna Motar daga haka kuma yajata suka tafi, ktsta ya kaisu cikin sa'a kuma suka samu Motar da zata tafi direct Yola don da ta Kano zasu hau in suka je can sai su hau ta Yolan, yaron Motar da Amadu ne suka fiffito da jakunkunan daga cikin boot suka saka cikin Motar, bayan an gama kintsa kayan aciki aka nuna ma su gwaggo seats na biyun karshe akace nan zasu zauna shi kuma Amadu daga gaba inda maza suke, Godiya tayi ma Haisam ta k'ara mashi sallama yayi mata Allah ya tsare, shiga gwaggo tayi ita kuwa Fatuu k'in shiga tayi tay tsaye tana kallon Haisam daya jingina da Mota yana sanye da farar jallabiya shima idonshi na akanta yayi folding hannayenshi a kirji da dan Murmushi akan fuskar bai dai ce mata komae ba bai kuma kirata ba don ya lura abu kad'an take jira tayi kuka, daga cikin Motar gwaggo tace mata tsayuwar mi take yi ne wai bata shigo ba hakan yasa ta juya ta shiga, kiran Amadu Haisam yay ya fito yaje wurinshi, Mota ya bud'e ya shiga batare daya rufe ba ya kirgo kudi masu yawa ya mik'a mashi amsa yay tare dayi mashi godiya shi kuma yay mashi Allah ya tsare daga haka yaja kopar Motar ya rufe shi kuma Amadun ya koma Motar lokacin idon Fatuu na akan Haisam din ta dan lek'a kanta ta tagar Motar da yake glass din a bude yake, tada Motar yay lokacin kuma glass d'in kopar ya fara sauka kasa slowly d'an lek'a kanshi yay suka had'a ido da ita a hankali ya d'aga mata hannu itama a sanyaye ta d'aga mashi daga haka kuma yaja Motar ya tunkari gate d'in fita glass din yana komawa sama a hankali ya fice, tana ganin ya tafi ta kifa kanta a cinya bata d'ago ba har Motar ta tashi, sai Fatan Allah yasa a sauka lafiya, Haisam na komawa gida shima ya fara shirin tafiya Lagos don da wuri yake son ya sauka saboda baisamu tafiya jiyan ba, Tafiya akace yankin azaba Fatuu saidae tay ta kalle kalle tay bacci ta farka wani lokacin har dan tsoki take ja in ta farka ta tambayi gwaggo sun kusa tace mata da saura gashi bunu bunu tace yunwa take ji duk garin da aka tsaya sai tasa an siya mata abun ci, lokaci bayan lokaci Mahaifin Fatun ke kiran Amadu yaji ya hanya da yake in suka sauka jimeta wani abokinshi ne zai daukesu ya kaisu rugar saboda shi bai nan yaje kasuwar wani gari, lokacin da suka sauka jimetan yamma tayi lis Fatuu ko Magana dakyar take yi ba 6ata lokaci wanda zai daukesu yazo don suna gabda sauka Amadu ya kira Baban Fatun ya sanar mashi, gab Magrib suka isa rugar wadda da ka kalleta zaka fahimci ruga ce ta ainihin fulani tun daga kan jama'ar dake kai kawo wad'anda ke sanye da shiga ta fulani mafi akasarinsu daga kiwo suka dawo, garin nada albarkar shuke shuke ba kamar da yake damuna ta fara kankama ko ina yayi luff da korayen ganyayyaki sannan yawanci duk bukkoki ne masu ginin k'asa basu da yawa an zagaye su da dannin kara, tunda suka shigo garin Fatuu tayi kuri tana kallon masu wucewa a amalenken shanu dayake anfi amfani dashi saboda akwae yawan yashi a hanyar, daidai gaban wani babban gida na ginin kasa Motarsu ta tsaya nan da nan kuma yaran dake a kopar gidan suka yo ma Motar caa da ido wad'anda ke a tsugunne suka mik'e amman ba wanda ya tunkari Motar haka mutanen dake a gefe kasan bishiya suna yin Alwala suma duk suka maido hankalinsu kan Motar dama anan kopar gidan daga can gefe inda ardo ke zama ake taruwa ayi salla, adan can gefe guda kuma akwae teburi mai d'auke da rake a samanshi wanda yayan Fatuu Kamalu ne ke saidawa, tunda yaran gidan wadanda suka san Fatun suka ji batun zuwansu suke ta zaryar zuwa kopar gidan dalili ne kawae ke maidasu cikin gidan ba kamar k'annenta, Amadu ne ya fara fitowa duk suka kura mashi ido don basu sanshi ba wanda kuma suka ta6a ganinshi sun manta shi yana fitowa Fatuu ta fito gyalenta a hannu itama dae idon suka bita dashi da alama itama basu ganetan ba wasu kuma wasiwasi suka fara acikin ransu ba kamar kanwarta Ameena da ake ce ma Mino wadda suke bala'en kama da ita don itama Babansu ta biyo kuma tafi kowa d'okin ganin Fatun don suna kaunar juna kuma lokacin da tana garin bata bari wani ya ta6ata in kuwa akayi mata wani abu sai ta rama mata amman fa ita tana dukanta in tayi mata ba daidai ba, tsaye sukae suna kallon kallon da ita, ita Fatuu ta ganeta ita kuma sai kokonton anya itace take a ranta, gwaggo ce tazo inda suke bayan ta gama yi ma mutumin daya kawo su godiya Amadu kuma yana firfito masu da kayansu, "Ya aka tsaya ana kallon kallonne, Mino baki gane yar uwar taki bane" gwaggo ta fad'a cikin harshen fullanci, kallon gwaggo da tayi maganar tayi sai kuma ta maido idon kan Fatuu harararta tayi nan take ta gane itace ta saki wata uwar k'ara da fullanci take fad'in ga inna wuron sun iso hakan duk yaja hankalin mutanen wurin sauran yaran kuma suka watsa gida aguje don su sanar saiga Kamalu ya fito shima yana yanayi da Fatuun saidae ba sosae ba don yafi daukko kamannin mahaifiyarsu amman shima fari ne yana hangosu ya watsa a guje yaje ya rungume Amadu wanda yake matsayin babanshi kuma Abokinshi, ita kam mino ta kasa ma rungume Fatun saboda mamaki da kuma Al'ajabin yadda Fatun ta koma sai faman washe mata baki take kawae tana kare mata kallo daga sama har kasa fatun na mata Murmushi, wasu daga cikin mazan gidanne suka zo suna yi masu sannu da zuwa baka jin komae sai fullanci ke tashi yayin da kowa ke mamakin girman da Fatun tayi, ciki harda Yayanta Kamalu baki bud'e yake binta da kallo yana tambayar gwaggo wai wankan inji ta kaita akayi mata ne kuma mi take bata tayi girma haka ba kamar da yake takalma masu tsini ne a kafarta sun k'ara mata tsawo, ita dae gwaggo murmushi kawae take Fatun kuma na tura baki, Kamalu da wasu ne suka d'auki jakunkunan don shigar masu dasu su gwaggo suka rufa masu baya, Babban gida ne mai d'auke da gine ginen wasu gidajen aciki ma'ana yana da 6angarori sosae aciki don gaba d'aya a halin ardo na acikin gidan kowa da bangarenshi, suna shiga Yadikko da ta kosa su shigo tunda ta samu labarin isowarsu ta nufosu cike da farinciki tana masu maraba Mino dake ruk'e da hannun Fatuu ta nuna ma yadikko ita tana Fad'in taga yadda inna wuronsu ta koma, waro ido tay tasa hannu ta ruk'e ha6a alamar mamaki yayin da Fatun ke mata Murmushi buda mata hannu tayi bayan ta gama al'ajabin Fatun ta nufeta ta rungumeta cike da kauna da nuna kewa, saida gwaggo ta gama amsa sannu da zuwan da wadanda suka leko keyi mata sannan suka wuce ciki ita dae Fatuu ba kowa take tanka mawa ba saidae ta bi mutum da ido kaman yadda suma suke binta da idon fuskokinsu dauke da tsantsar Mamaki, koda suka shiga dakin wanda babbane ba laifi yana da shafen plasta amman ba fenti haka saman ma anyi ceiling irin na leda mai kyalkyali akwae gado babba mai rumfa sai kuma karami na katako yana da dan mirror mai dauke da tarkacen kayan shafa sai wardrobe mai gida biyu sai kuma cabinet mai dauke da jeren k'orai da kwalla da kwanoni jikin bangon d'akin ma anyi adon korai masu zane mai kyau da fayafai haka kasan dakin rufe yake da ledar tsakar daki akwae kujera mai mazaunin mutum ukku a gefe a samanta gwaggo ta zauna Fatuu kuma ta nufi gefen k'aramin gado ta zauna mino dai na gefenta sai faman kallonta take tana zabga Murmushi da gani ba karamin burgeta Fatun tayi ba, bayan sun k'ara gaisawa gwaggo ta mik'e don yin salla ita kam Fatuu kwanciyarta tayi koda gwaggo tace bazata tashi tayi salla bane cewa tayi sai ta huta bata iya tsayuwar sallan, bayan gwaggon ta gama saida tayi mata da gaske sannan ta tashi tayi sallan tana gamawa anan kan abun sallan bacci ya kwasheta, kan kace mi an cika d'akin da kwanoni da k'oran abinci dasu Fura da aka aiko ma baki ba yadda ba ai ba Fatuu ta tashi taci abinci amman ta kiya gwaggo tace su rabu da ita in taji yunwar sosae zata tashi ne, sai can bayan isha Mahaifin Fatun ya dawo cike da girmamawa ya duk'a suka shiga gaisawa da gwaggo dama shi Amadu sun gaisa dashi acan waje wurin Kamalu, sai lokacin gwaggo ta tada Fatun tace ta tashi to ga Baffanta ya dawo ai tana jin hakan ta mik'e zaune idonta akanshi shi dae sai faman Murmushi yake mata yadikko nace mashi ashe haka inna wuron ta koma da yake kwanaki da yaje bayan ya dawo yana ta basu labarin girman da tayi, bayan sun gama gaisawa ne gwaggo tace mashi yayi mata jagora zata gaishe da ardo, koda gwaggo tace mata tazo suje ta gaishe shi cewa tayi taje gobe taje ita yanzu yunwa take ji abinci zata ci hakan yasa ta rabu da ita, tana gama cin abincin lokacin gwaggo ta dawo tace ta watsa ruwa tafi jin dadin jikinta, bayan tayo wanka canja kaya tayi zuwa na bacci ta nufi d'akin Baffanta wai acan zata kwana da kyar ya lalla6ata yace ta dawo cikin yan'uwanta ta kwanta don sunyi kewarta sosae, saida ya rakota har kopar daki sannan ya koma maimakon ta shiga sai kawae tayi hanyar waje ta nufi dakinsu Kamalu dake acan soro lokacin tuni Amadu yayi bacci amman saida tasa aka tashe shi tace wai Ya kira mata Ya Handsome zata gaya mashi sun iso tunda da suna Mota ya kira ya tambaya, uban tsoki ya ja ya hau yi mata fadan tashinshi da tasa akai karshe rai 6ace yace bai kira tunda bai dade da yayi waya da Haisam d'in ba kuma ya sanar dashi sun iso lafiya don haka ta tafi ta bashi wuri, ba don taso ba tana kumbura baki Kamalu na mata dariya ta baro soron ta nufi cikin gidan dama don tasan gwaggo bazata bari ta kirashi a wannan lokacin bane yasa taje wurin Amadun. Washe gari tunda safe ko karyawa bata yi ba ta kira Haisam d'in yayi mata ya gajiyar hanya sai faman washe baki take suka d'an ta6a hira har ta tambayeshi ya tafi Lagos din yace mata eh yana can daga baya yace taje tayi breakfast tace to anjima ya kirata Video call da wayar Amadu ya amsa mata da owk, lafiyayyan abun karin kumallo aka shirya masu irin nasu na yan birni duk da dama a gidan sunfi kowa yin lafiyayyen abinci irin na yan birni don shi dama sam bai abubuwan k'auyawa saboda mu'amala da yake da yan birni da kuma yawan zuwa birnin, daga wasu gidajen cikin gidan ma an aiko masu da abun karin kumallon, tare da mino Fatuu tayi kalacin sauran yan kannansu guda ukku kuma suna gefensu da yake yadikkon yaranta hudu Mino ce ta farko zatayi shekara tara zuwa goma, suna gamawa gwaggo tace ma Fatuu ta shirya taje ta gaida Ard'o dasu Yaya tace to sai tayi wanka mino zata rakata, fiddo kayan tsaraba da suka kawo gwaggo tayi taba yadikko tace a rarraba kafin ta fito da sakon Hajiya ta bata, kasa rufe baki yadikkon tayi saboda tsabar farinciki tana fadin su basu Gajiya da alheri ne su dama ba'a sansu ba amman aka biyosu da abun arziki haka, dama tasan labarin hajiyan da haisam lokacin da Baffan Fatun yaje sosae take ta godiya kuma da hausa suke magana da gwaggon don tana jin hausa sosae sai jefi jefi suke canza harshe, fiddo kayan da ta tattaro na Fatun ta kawo ma mino tayi ta bata sosae tayi murna don kaya ne da yawa k'arshe mik'ewa tayi tana tsalle farincikinta itama ta samu kayan da zata rink'a yin gayu kaman Fatun, rigima kanwarta Aysha mai sunan maman Fatun tasa wai ita ina nata yadikko na dariya tace ai sunyi mata yawa tace to a maida mata su daidai ita mana tace mata to, sai wuraren karfe sha d'aya lokacin tayi wanka taci gayu da riga da skirt na atampa ta wani coge kallabi ta nufi soro inda fadar ardo take mino na biye da ita itama tayi kwalliya tasa doguwar riga cikin kayan da aka kawo mata na Fatun............ ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* *6️⃣8️⃣* .......Babban d'aki ne mai d'auke da abubuwan sarauta irin na gargajiya, lokacin data shiga zaune ta iskeshi akan kujerar da yake zama tare da wani babban Mutum yayi shiga ta alfarma yana zaune akan kujera daga gefen ardon da gani kuma wayayyan d'an boko ne kuma kana kallonshi zaka gane shima bafullatani ne, ard'on tsoho ne sosae don duk gashin fuskarsa hurhura ne ba bak'in gashi ko kwaya d'aya haka ma kanshi duk da a rufe yake gashi d'an tsamurmuri dashi wato baida jiki kwata kwata hakan kuma nada alak'a da tsufan da yayi sosae amman k'yam yake yana gani kuma yana ji amman dae tafiya saida sanda yake yi, da zasu shiga mino ce tayi sallama duk suka amsa harda mutumin ta duka k'asa kan shimfida ta gaishe dasu duk suka amsa ita kuwa Fatuu gaban ard'on ta nufa tayi mashi tsaye tana bin fuskarshi da kallo shima idonshi na akanta ya d'an k'ank'ance su da alama so yake ya gane wacece ita, haka shima wanccan mutumin da mino kallonsu suke, tambaya yayi wacece ita maimakon ta bashi amsa sai ce mashi tayi "wai har yanzun kana nan baka mutu ba?" da fullanci tayi Maganar jin hakan yasa nan take ya ganeta don kaf zuriyar gidan ba wanda zai iya mashi hakan in ba itan ba dama kuma yasan da zuwan nasu, hannu ya kai gefenshi ya janyo wata zungureriyar sanda zai buga mata ta ja baya da sauri tana dariya yace mata har yanzu shed'anun da ke kanta na nan kenan, tura mashi baki tayi yace ta girma amman har yanzu bata iya gaisuwa ba bata ga mutum ba in shi bazata gaidashi ba, juyawa tayi ta kalli Mutumin ta gaidashi ya amsa mata yana Murmushi sannan ta juya ta gaida ardon bai amsa mata ba sai ya nuna mata gabanshi yace ta zauna tace ai bugunta zaiyi yace bazai bugeta ba ai ita bak'uwa ce yanzu, zama tayi tana fuskantarshi yace to ta gaidashi yanzu bayan ta gaisheshi ne yace ta dawo ko tace a'a, "Ai kuwa bazan bari ki koma ba aure zanyi maki kin yi girma da yawa" ya fad'a da fullanci cikin dusashshiyar murya ta tsufa, tura mashi baki tayi tace "na rantse ba mai mani aure sai nagama karatu na zama likita har na fara aiki sannan zanyi aure kuma ni zan za6i mijin ba wani ba" jinjina kai yay kafin yace zata gani in zai barta ta koman,wani kallo tayi mashi tace "in ka hana ba sai in gudu ba ai nasan hanya" shiru yay yana ta binta da ido da d'an Murmushi tace "an kawo maka tsarabar dana kawo, koda yake kai bazaka iya cin biscuit ko chocolate da wannan bakin naka ba daba hakora kaman na......" bata k'arasa ba ya k'ara d'ago sandar taja baya daga zaunen tana Fad'in ita fa yanzu budurwar birni ce tafi karfin a bugeta yace ta matso taga in bai bugetan ba, su dai su mino sai Murmushi suke, jin tace sai tagama karatu ta fara aiki ko zata yi aure yasa Mutumin ce mata "What's ur name?" kallon Mutumin da yayi mata tambayar tayi sai kuma ta bashi amsa itama da turancin cigaba da yi mata tambayoyi yay game da alakarta da ardon da inda take da kuma yanayin karatunta duk da turanci ta rink'a bashi amsa itama, sosae ya yaba da yadda take turancin ba wani gargada ko tangard'a har ya tambayeta a Katsinar private skul take yi ne tace mashi a government skul ce nan take ya fahimci tana da kokari sosae mino dai na gefe tana kallonsu suna turancin gwanin burgewa don tasan yaren da suke saboda tana zuwa makaranta itama saidae ba wani turanci take ji ba inba dan guntu ba kaman tambayar sunan mutum haka shima ardon yasan yaren nasara ne suke yi bayan sun gama ta juya ta kalli ardo da ya zuba mata ido tace "kai fa baka san mi muke cewa ba ko?" d'an Murmushi yay kafin yace "kin zama nasara bama wanda zai aure ki sai nasaran" da sauri tace "ai nima ban iya auren d'an garin nan don duk basu da ilimi basu iya komae ba sai noma da kiwo samarin birni kuwa irina suke so don haka in na tashi aure sai ma na za6a" ta k'arasa tana murmura mashi baki shidae Mutumin sai Murmushi yake can ardon yace ta tashi su shiga ciki yana tattaunawa da bak'o tace to kafin suka mik'e tare da mino suka nufi hanyar fita, Bayan sun fito waje ta nufa don taga in kawu Amadu na nan ya kira mata Ya Handsome, koda ta duba inda Kamalu ke saida rake bataga kowa ba baima fito da raken ba acan gefe ta hango Mota Jeep dake ajiye ta kalli mino tace Motar mutumin ce tace mata eh tace wanene shi Minon tace "Chairman ne Alhaji lawal shine mai katon gidan gonar bakin gari da ardo ke kulawa" d'an ta6e baki tayi kafin ta juya suka koma ciki ta nufi d'akinsu nan ma basu nan ba don taso ba suka koma cikin gidan ganin sun nufi hanyar 6angarensu yasa mino cewa "Adda Fatuu bazaki gaishe da yaya ba?" tura baki ta d'anyi sai kuma ta tuna da Maganar da suka yi da Haisam hakan yasa ta juya tace suje, lokacin da suka je sashen yayan wadda take uwargidan Ard'o tana zaune gefen gadon karfe babbar mata ce jajur da ita tana da tsaga a bakinta kuma tana da jiki ba laifi ta manyanta sosae daga gefe da gefenta mata ne zaune harda kishiyarta guda da kuma matan ya'yanta guda ukku su biyar kenan dama haka suke wuni wurinta suna mata fadanci aita gulmace gulmace, mino ce tayi sallama suka shiga ba tare da sun amsa ba duk suka d'ago suna kallonsu saidae gaba d'aya idanunsu na akan Fatuu ne itama ta lura da kallon da suke matan hakan yasa ta wani sha kunu don tasan bana arziki bane, k'asa mino ta tsugunna tana gaishe da yayar kaman an mata dole ta amsa kafin ta kalli Fatuu da tayi mata tsaye k'erere aka tace ita bata iya gaisuwa bane tayi Maganar tana k'are mata kallo tun daga sama har kasa dama tunda suka zo aka kawo mata gulmar yadda Fatun ta koma wai kaman yar shekara ashirin, gaida ita tayi kaman yadda ta bukata amman sai tak'i amsa mata wai a haka zata gaishe da ita ba ladabi abunda ake koya mata a binnin kenan rashin da'a, sai kace dama da Fatun na garin ladabin take mata, idonta cikin nata tace "to ai ba abun zama" fuska a d'aure tace su sauran a ina taga sun zauna tace "a k'asa ni kuma ban saba zama kasa ba ai" shiru tayi tana kallonta yayin da sauran suka hau jinjina kai alamar al'ajabi, d'an Murmushi da bakai zuci ba Yayan tayi tace ta manta itafa yanzu yar birni ce ta kalli mino ta nuna mata buzun salla tace ta d'aukko mata, shimfida mata tayi tace adda ki zauna cike da kyankyami tana d'an yamutsa fuska ta hau ta zauna suna dae ta bin ta da ido, ganin ta zauna bata gaishetan ba yasa Babar Altine data ta6a karyama kafar kaza cewa "to sai ki gaishetan ko!" wani kallo Fatun tayi mata dama itama sam basu shiri kafin ta kalli Yayan ta gaidata kasa kasa, d'an ta6e baki tayi ta amsa tace ya birnin ta bata amsa da lafiya lou daga haka kuma suka d'an yi shiru Fatun na kallon gefe yayin da Yayar ke k'are mata kallo can tace "amman kin dawo ne ko" ba tare data kalleta ba tace "a'a ai karatu nike" jinjina kai tayi sai kuma tace "amman yakamata yanzu ace kinyi aure har kin haihu ma" wani kallo ta juyo tayi mata mai kaman harara a d'an harzuke tace "ni ba wani aure da zanyi sai na gama karatu na fara aiki" gaba d'aya kowa kallonta yake da mamakin yadda take ma Yayar Magana, d'an Murmushi tayi bata ce mata komae ba ta kalli d'aya daga cikin matan dake zaune tace "Bimbi in kin gama dama furan ki zuba ma bak'uwar birni" Fatuu na jin hakan tace ta koshi don tasan ba har zuci tayi maganar ba, mik'ewa tayi tace ma Mino ta taso su tafi tayi masu sallama suka tafi, tana fita matan suka hau jinjina kai suna fad'in an idasa lalata yarinya kawae wata tace yo dama an kai yarinya birni ai dole ta lalace Allah ma yasa bata san maza ba don yadda take Magana tsaitsayen nan sai dae ace Allah ya kyauta kawae wata tace ai tabbas ma wannan tasan maza daga ganin jikinta, ita dae Yayan nata saurarensu Allah kadae yasan abunda take kullawa acikin ranta don gani take fatun ta wulak'anta tane duk da ba yanzu ta fara yi mata hakan ba amman tafi jin ciwo don tana ganin yanzu ai ta mallaki hankali. Duk yadda taso tayi Video call da Haisam ranar abun ya faskara don yinin ranar Amadu bai nan sun fita tare da kamalu basu suka dawo ba sai bayan Magrib saidae tayi waya dashi kawae, washe gari ya kama Monday kwanansu biyu da zuwa a ranar gwaggo taso komawa saboda aiki amman suka rok'eta ta d'an k'ara ko kwana biyu ne cikin masu rok'on nata harda Fatuu kaman zata yi mata kuka hakan yasa ta hakura sai ranar laraba zata tafi, ranar da yamma tana sanye cikin Jallabiya ta d'aura kallabi akanta ta nufi kopar gida tana zuwa ta iske Amadu zaune saman benci gaban teburin raken Kamalu, gaidasu tayi tace don Allah ya kira mata Ya Handsome video call yace dama yasan ba gaisuwar Allah da Annabi bace to bai kira, rokonshi ta fara yi harda tsugunnawa k'asa Kamalu dae nata dariya don yar tsamarsu burgeshi take, saida ya gama ja mata rai sannan ya kirashi ya bata ta sanar mashi zasu yi Video call din bayan ya d'auka ta gaidashi ta sanar mashi ya amsa da owk, mik'a ma Amadu wayar tayi tana ta faman washe baki ya fara kokarin kiran nashi sai dae da yayi connecting sai kuma yayi disconnecting da kyar ya samu yayi ya mik'a mata, ta fara murnar ganin haisam d'in kenan kiran ya datse rai 6ace ta sanar ma Amadun yace to sai tayi hakuri ba network mai kyau, rokonshi ta fara yi ya daka mata tsawa yace to shine zaisa shi yayi, Kamalu yace in suna son network sai sunje bakin gari acan ake samu ta fara rok'on Amadun ya bata wayar taje can tayi, wani kallo yayi mata yace "matsalata dake baki da cikakken hankali nine zan baki wayata kije bakin gari salon a kwace man waya ko" Kamalu na dariya yace " a'a mu garinmu ba'a kwacen waya wama yasan yadda zai yi amfani da ita balle ya kwace ai sai d'aid'aikun Mutanan da yawanci ma ba a garin suke zaune ba" jin haka ta hau yi mashi magiya da k'yar ya bata yana jaddada mata tabi mai waya a hankali ta amsa da to cike da zumudi ta juya da gudu ta nufi bakin garin Amadun ya d'aga murya yana karfa ta fasa mashi waya, yar tafiya ce tayi ta isa wurin cikin sa'a tana kiran nashi yayi lafiya lou lokacin haisam d'in na kishingide kan gado tana ganinshi ta washe baki ta kira sunanshi, amsa mata yayi yace tana lafiya tace lafiya lou, "Ya Handsome ka koma Katsina ne?" girgiza mata kai yay tace "har yanzu kana Lagos d'in kenan" yace "Yeah ban gama abunda nazo yi ba sai tomorrow zan tafi, "to yanzu kana ina na ganka kwance ko Hotel?" girgiza mata kai yay "Nah" ta k'ara cewa to yana ina yace yana gidan Mommynshi ta Lagos tace mai auren Bature ya d'aga mata kai alamar eh wai harda cewa ina yake ta ganshi yace bai Nigeria, fira suka ci gaba da yi harda ce mashi wllh tayi missing d'inshi shima yayi nata yayi mata Murmushi kawae, can tace "Yauwa Ya Handsome don Allah jibi gwaggo zata taho kace ta taho dani pls" da d'an Murmushi ya girgiza kai yace "why, ba already kun gama magana ba" turo baki tayi sai kuma tace "to kai ka biyo ka d'aukeni" yace mata ai ba'a Mota zai dawo ba tace a jirgi yace eh, "Yauwa to tunda a jirgi ne ma kaga sai kace a biyo nan da kai zaka d'auki k'anwarka in kuka zo sai a zuro man igiya yadda ake yi a film sai kawae mu tafi in muka koma gida sai in kira su gwaggon in sanar dasu ni na koma gida" shiru yay kawae yana binta da kallo kaman zai yi dariya a shagwa6e ta langa6ar da kai tana ce mashi don Allah da bud'ar bakinshi sai ce mata yay "yaushe zaki girma Zarah" wani kallo tayi mashi tace "bana girman ba" d'an shaking head d'inshi yay alamar a'a bata girma ba ta tura baki tana cewa ita ai ta gaji da garin ne gida take son dawowa yace ta kwantar da hankalinta kaman gobe ne, ganin suna ta Magana bai ganin komae sai shuke shuke yasashi tambayarta tana ina ne tace tana bakin gari nan keda network ta juya wayar tana nuna mashi wurin yace bata jin tsoro ita kadae tace tsoron mi ai koda daddare zata iya zuwa wurin ba abunda zai sameta, yar hira suka k'ara yi yace ta koma gida Magrib ya kusa tace to amman kar ya kashe zata tafi suna hira har tazo inda ba Network yace owk, tafiya take ta raba hanya biyu tana bashi labarin garin nasu da yadda kowa ke mamakin girman da tayi a haka har tazo inda ba Network kiran yay disconnect da kanshi lokacinne kuma aka danna wani irin Horn mai karfi a bayanta har saida ta tsorata ta juya da sauri, da mamaki take bin Motar da tayi mata horn d'in da kallo wadda peugeot ce 406 irin wadda ta fasa ma glass lokacin da haisam ya mareta saidae ba Colour d'insu d'aya ba Wannan Navy blue ce, ganin tayi tsaye kan hanyar yasa na cikin Motar sauke glass a harzuke yace "ke mahaukaciyan inane nan d'in d'akin uwarki ne da zaki raba hanya biyu anata maki horn bazaki matsa ba!!" da hausa yayi mata Maganar don daga yanayin shigarta ya fahimci ba lalle in yar rugar bace, sototo tayi tana binshi da ido da alamar mamaki a fuskarta taji ya k'ara cewa "bazaki tashi man a hanya ba sai na bi ta kanki ne", a fusace tace "to shine sai ka zagar man uwa dake kwance cikin k'asa" bud'e Motar yay a fusace ya fito, dogo ne sosae don har yafi haisam tsawo saidae sam baida jiki yana sanye da jeans da t-shirt kallo d'aya zakai mashi ka gane bafullatani ne daga yanayin fatar jikinshi dake fara sannan sumar kanshi ma a nad'e take duk da bata da tsawo sosae kallonta yay a k'ule yace "Who d hell are u da baza'a zageki ba!" kallon up and down tayi mashi kafin tace "to wllh duk da an hana ni rashin kunya bazan kyaleka hakanan ka zagar man uwa ba don haka badae uwata ba" kallon mamaki ya bita dashi yace "badae zagina zaki ba!" tace "ai baka ji na zage kaba ko amman dae kasan in Mutum ya zagi iyayen wani bai rama ba to nashi ya zaga don haka taka ka zaga" a fusace ya idasa fitowa tana ganin hakan ta fara tattare rigarta dama akwae dogon wando a ciki nan take ya gane guduwa zatayi hakan yasashi tsayawa suna kallon kallo ta kumburo mashi baki, juyawa yayi ya koma cikin Motar dama a kunne take ya rufe tana dai tsayen bata kauce ba aikau ba zato ba tsammani yayo kanta da Motar tayi tsalle gefe guda hakan baisa ya kyaleta ba yayi kanta gadan gadan aikuwa ta watsa a guje don ta lura yafita hauka kan kace mi tayi mashi nisa don hanyar akwae yashi ya hanashi yin gudu sosae yana ganin ta 6ace ma ganinshi ya wani daki steering Motar yaja dogon tsoki abunda yafi bashi takaici wai ace wannan yar kankanuwar yarinyarce zata zageshi jan Motar yay ya k'ara yin gaba kafin ya karya wata kwana, Ranar laraba tunda sassafe gwaggo tayi sallama da kowa bayan an had'a mata sha tara ta arziki su Fatuu ne yan rakiya saboda Baffanta ne zai kaita jimeta a Motarsu Hijet da suke kai kaya kasuwa daga can sai ta hau Motar Katsina ko Kano, ita da Fatuu da kamalu da Mino ne abaya sai gaba Baffanta da Amadu Fatuu harda kukanta na atafi da ita, banza gwaggon tayi da ita sai yadikko ce ke rarrashinta tana cewa tayi hakuri ta k'ara kwanan masu biyu basu gaji da ganinta ba kuma in ta tafi ai sai an k'ara ganinta ko, Bayan sun dawo daga raka gwaggo kwance tayi saman gadon tana matsar kwalla a haka bacci yay awon gaba da ita lokacin data farka ne yadikko ta nuna mata abun karin kumallonta, bayan ta wanko bakinta rai a jagule take tsakuran abincin ganin tak'i sakin jiki yasa yadikkon ce mata tayi sauri ta gama ta shirya suje cin Kasuwar babbar hanya ita dasu mino tace bari ma tayi ma Kamalu Magana don tasan duk sati yana zuwa sarin rake, tana jin hakan ta d'an ji sanyi bada jimawa ba yadikkon ta dawo tace tayi ma Kamalun Magana zasu tafi tare, wuraren karfe sha biyun rana sun gama shirin zuwa kasuwar Fatuu tasha ado da shaddar da haisam yayi mata da babbar salla sosae yadikko da k'annenta ke yaba kayan bata 6oye mata ba tace ai Ya Handsome ne yayi mata don dama kullum ne sai tayi masu firarshi kaf ta basu labarin abubuwan da yake mata sosae suke yaba kirkinshi da kakarshi Hajiya, cike da tsokana yadikko tace kodae saurayinta ne don wannan hidiman tayi yawa, da sauri ta girgiza mata kai tace a'a ita ai bata da saurayi don karatu take son yi ta zama likita kuma shima baiyin soyayya koda ma zaiyi bazai yi da ita ba tunda ita karama ce shi kuma babbane kuma d'an gayu ita yadikko dan ta6e baki kawae tayi, itama Mino kwalliyar shaddar tayi cikin kayan da aka bata gwanin sha'awa yadikko ke kallonsu inda so samu ne Fatun ta dawo hannunta saidae ita kanta tafi mata sha'awar zama acan hannun gwaggon, lokacin da suka fito tsakan gidan gaba daya wadanda ke wajen sakin baki sukae suna kallonsu ciki harda Altine da tayi ado da kayan fulani suma zasu cin kasuwan ko ta kansu Fatun bata bi ba sukae fucewarsu a waje suka samu Kamalun harda ma Amadu shima yayi gayu da kananun kaya ba 6ata lokaci suka kama hanya, tun akan hanyar ake ta faman binsu dana mujiya don ba'a saba ganin irin shigar da suka yi ba wasu mutanen da basu iya hakura har tambayar Kamalu suke wai bak'i sukae ya basu amsa da eh wadanda suka san Fatuu kuma ya gaya masu itace da al'ajabi suke kallonta koda suka isa kasuwar ma nan ma dae abun kallo suka zama sai kace ansamu tv anan kuma suka hade da Jibo Mutumin da shine sanadin komawar Fatun Katsina wato wanda ta jefar ma Akuya ta mutu, yana sanye cikin shigan Fulani riga da wando da takalma fatalo shima kasa hak'uri yay ya tambayi Kamalu bak'in binni sukae yana dariya yace ya kalli Fatuu da kyau ya santa, k'ura mata ido yay saidae sam ya kasa gane wacece har saida Kamalun yayi mashi bayani sannan ya ganeta, cike da al'ajabi yake kallonta baki bude harda cewa ai shi yaga Mata wllh a tsiwace Fatun tace mashi Allah ya kyauta ta aureshi ko maza sun k'are mi zatayi dashi yadda tayi maganan yasashi cewa da kwarankwatsa itace kuwa sudae su Kamalu nata dariya, zagayawa sukae cikin kasuwa suka danyi siyayya yawanci duk abubuwan ci ne akafi saidawa su Awara, kosai, rake, danyen nono harda madarar shanu da kuma kayan noma sai yamma liss suka koma gida don daga kasuwar zagaya garin sukae har k'oramar dake bayan gidansu suka je mai tarin ni'ima da wadatar kayan itatuwa suka yi hotuna. _____________ Ranar Juma'a lokacin kwanansu Fatuu shidda da tafiya bayan sallan juma'a iyalan Senator harda shi sanatan da kuma Hajiya Maryam itama da nata iyalin suka sauka Katsina, Senator da Matansa guda biyu Mahaifiyarsu Haisam sai kishiyarta da suke ce ma Aunty da k'annen Haisam d'in guda bakwae don su takwas ne ya'yan Senator d'in ita Aunty bata haihu dashi ba sai dae akwae diyarta guda d'aya data Haifa da tsohon mijinta a wurinta don ba'a budurwa ya aureta ba kuma likita ce sa6anin Mahaifiyarsu Haisam ita full house wife ce bata aiki tunda Senator ya aureta da k'yar ya barta ta k'ara yin karatu anan amman tun lokacin data gama ya hanata yin aiki, k'annen haisam akwae Laila ita ke bi mashi wadda yanzu haka take karatun likitanci a k'asar Malaysia kuma ita Mahaifinsu ta biyo saidae ba bak'a bace ta d'an d'aukko hasken Mahaifiyarsu ba sosae ba sai Nameer shi yanzu ya gama Secondary skul sai kuma Hauwa'u mai sunan Hajiya suna ce mata jidderh zata yi shekara sha biyar zuwa sha shidda yanzu zata shiga s.s two sai Yasmeen dake j's 2 sai Adams mai sunan kakansu suna ce mashi Affan sai twins wanda sune auta wato Mubeen da Mubeena zasu yi shekara hud'u kusan gaba d'ayansu hasken Mahaifiyarsu suka d'ebo ba kamar Haisam Nameer jidderh da twins sun fi sauran fari sosae, a 6angaren Hajiya Maryam kuwa yaranta biyar saidae da guda hud'u tazo don cikon d'ayar wato Fanan bata k'asar sai Farha wadda ita ke bima Fanan d'in sai ibraheem suna ce mashi abraham sai muhammad da yar auta Noor itama sunan Hajiya gareta, a wata dankareriyar Hummer jeep aka je d'aukar Senatorn sai Haisam da shima yaje da Benz d'inshi sai kuma Tk da yaje da Jeep d'in Hajiya, cikin shiga ta Alfarma suka iso Arrival daka kallesu ko baka san su waye ba zaka fahimci akwae masu gidan rana ba kad'an ba a tattare dasu, Mahaifiyar Haisam wato Fateema tana sanye da wata jugunannan jallabiya da tasha adon stones sai d'aukar ido take tayi rolling veil d'in kallo d'aya zaka yi mata ka shaida balarabiya ce tun daga kan kalar fatarta da kuma suffarta don giant ce tana da tsawo da kuma jiki sai dai ba jiki sosae ba daidai, sai Hajiya Maryam ma tana sanye da dandatsetsen leshi red color mai touch din ash tasa gyale ash da takalma da jakka ash sai sarkar diamond dake wuyanta da agogo harda zobensu itama babbar macece saidae bata da tsawo sosae daka kalli fuskarta kuma zaka shaida kamanninta da Hajiyar Sanata sosae, shima mai gayya mai aikin wato Senator Alee zakee yasha farar shadda ta alfarma wanda basai na tsaya fadan kalan takalmi da hula da agogon hannunshi ba don kowa yasan na alfarma ne suma, Mutum ne mai tsananin haiba da cikar kamala ga kwarjini shima giant ne don sak Mahaifinsu shi kuma ya biyo wato Gen. Adamu zakee, su Jidderh da Laila sun ci gayu da had'addar embroidery atampa anyi masu riga da skirt kowacce ta d'aura gyalenta a kafada su kuma mazan suna sanye da jeans da t-shirt wasu rigunan polo ne sabbi dal, a 6angaren yaran Hajiya Maryam kuwa gaba d'aya yaran Mahaifinsu suka biyo hakan yasa daka kallesu zaka gane turawa ne tun daga kan kwayar idanuwansu da kuma sumar kawunansu, Farha na sanye da skinny jeans ya kamata had'i da farar top ta d'aura boyfriend jacket wadda gabanta ke hangame haka kafad'ar rigar a zame take, kaman yadda k'wayar idonta ke ash haka ma gashin kanta daya fito duk da akwae gyale bak'i akanta haka kafafunta na sanye da takalma bak'ak'e masu tsini sosae tana ruke da yar purse silver, shima Abraham kwayar idonshi brown ce kalar ta Fanan haka sumarshi ma take, Mohammed irin kwayar idon farha gareshi wato ash amman sumarshi bak'a ce sai yar auta Noor wadda ba k'aramar kyakkyawa bace tana da kwayar ido blue ga yalwatacciyar sumarta bak'a ce, suna hango haisam dake tsaye yana sanye da bak'in jeans da polo shirt yellow haka agogon hannunshi baki ne yayin da glass d'in ke bada launin yellow mai shining haka idanunshi ma na rufe da glass shima mai d'an launin yellow abun saidai ace ma sha Allah kawae, su Jidderh na hango shi suka nufo shi da d'an gudu gudu suna fad'in "Bro...." da Murmushi ya bud'e mata hannuwa ta fad'a jikinshi tana ta dariya side hug Laila tayi mashi tana murmushi, janye Jidderh yayi daga jikinshi ya janyo Yasmeen dake ta kokarin ture Jidderh don itama ta rungume Haisam d'in, yana rungume da ita ya hango su twins da sukae tsaye gabanshi sun kumburo baki alamar fushi dama gasu tubarkallah bul bul dasu da gani ba k'aramin 6arna da Madara suke ba kuma identical twins ne suna bala'en kama da juna gwanin sha'awa suna sanye da jeans da t-shirt kala d'aya wato unisex, janye Yasmeen yay ya duk'a ya bud'a masu hannu alamar su taho kawae sai suka had'e bayansu suka kalli 6angare daban daban, sanin halinsu rigimammu ne yasa ya nufesu duk da k'ibarsu suna a had'en ya d'agasu sama gaba d'aya aka sa dariya harda su, sauke su yayi ya nufi Mahaifiyarshi wadda sak ita ya biyo daka kalleta zaka gane cewa mahaifiyarshi ce rungume juna sukae a gefen kunnanshi a hankali ta furta "Habibie", d'agowa yay yana Murmushi kafin yace wani abu Hajiya Maryam tace "dayake bani na haife ka ba shiyasa ko kallo ma bazan samu ba ko" k'ayataccen Murmushin gefe ya sakar mata kafin ya yi mata side hug yana fad'in "So sorry lovely Mom", kallon Auntynsu dake gefe yay tanata Murmushi itama Maroon Abaya ce ajikinta murmushi yay mata ya gaidata tare da dan kama hannunta ta amsa mashi, "What about me Ya haisam" Farha ce tayi Maganar tana jujjuya ido, juyawa yay ya kalleta da Murmushi ya dafa kafad'arta lokacin ya hango Nameer tsaye yana kallonshi da Murmushi akan fuskarshi dama shi sarkin Murmushi ne yafi kowa fara'a a gidansu kullum zaka ga fuskarshi da Murmushi shiyasa ake saurin gane mashi in yana cikin damuwa gashi yana da mugun sauk'in kai suna kama da Haisam sosae saidae shi dimples biyu ne dashi kuma yanayin haskensu ba d'aya ba, tsaye sukae suna kallon juna ba tare da Haisam d'in yace mashi komae ba sanin halin yayan nashi yasa ya nufo shi yana dariya ya rungumeshi, suna cikin haka Senator ya dawo dama yana can wurin Mutanenshi da suka zo tarbarshi da fara'a ya bud'a ma Haisam hannu ya nufeshi suka rungume juna yana fad'in "My Pride...." d'agowa yay yana mashi Murmushi yace "U'r welcome Dad" Senator yace "thanks Son Hope u'r doing gud" kai kawae ya d'aga mashi daga haka kuma suka dunguma suka nufi wurin da Motocinsu suke yana tambayar Hajiya Haisam yace mashi tana gida shi ya hana tazo tunda can zasu yace owk bayan sun shisshiga cikin Motocin suka fita daga cikin Airport d'in Motar Escort na biye dasu, Lokacin da suka isa gidan Hajiya sam ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda tsabar farinciki don sun jima basu zo haka da yawa ba nan aka shiga gaishe gaishe da rungume rungume kan kace mi kopar gidan Hajiyan ya cika da Mutanen Senator wanda yawanci yan siyasa ne wai sunzo yi mashi sannu da zuwa da yake Mutumin kirki ne kuma adalin shugaba fita yayi suka gaisa kafin ya nemi suyi mashi uzuri ya gana da mahaifiyarshi in ya koma Gra duk maison ganinshi sai ya sameshi acan cike da mutuntawa suka yi sallama ya koma, yar kwarya kwaryar liyafa aka shirya musamman dama aka d'aukko kwararrun chefs suka shirya lafiyayyun abinci da abubuwan sha, bayan sun gama cin abincinne aka zauna ana k'ara gaisawa baka jin komae sai turanci da larabci dake tashi daga bakunan yaran jefi jefi kuma wasu sukan yi Hausa........... *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ Littafin A Sanadin Makwabtaka Kashi na Farko wanda nayi shi a kyauta yazo karshe, Ga mai bukatar cigaba da karanta kashi na biyu wato Book 2 zai biya kudin karatu Naira 300 kacal ta wannan Account din👇 1509618776 Zainab Bature Access Bank Za'a turo da shedar biya ta daya daga cikin wadannan Lambobin wayan ko kuma tuntu6a don neman karin bayani, 09013804524 ko 08169856268. Thanks and i luv u as u patronize🤝🥰 *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 6️⃣9️⃣ .........Sai bayan sallar isha Senator da matanshi suka tafi gidansu na G.r.a da tuni an gyara masu shi saboda zuwan nasu cikin Yaran nasu ba wanda ya bisu duk gidan Hajiya suka ce zasu tsaya gwaggo ma ta shigo sun gaisa ta gabatar masu da ita a Matsayin Makwabciyarta mutuniyar kirki mai kulawa da ita duk da wasu sun santa da Hajiyar ba kamar Hajiya Maryam, sosae sukae mata godiya harda Senator d'in tace ai itace da Godiya abun arzikin da ake mata, sosae tayi masu godiya da Addu'oi. Satinsu guda agarin suka koma lokacin kwanansu Fatuu sha ukku wato saura kwana d'aya su dawo saidae ba gaba d'ayansu suka tafi ba an bar wasu daga cikin yaran zasu k'arasa hutunsu dama saida aka jira suka yi hutun sannan aka taho cikin wanda aka barin harda Nameer da jidderh sai twins da suka nace suma sai an barsu wurin granny haka suke ce ma Hajiya sai Farha ma bata tafi ba tare zasu koma Abuja in sun tashi daga can sai ta koma Lagos ita Laila Makaranta zata koma dama bata dad'e da zuwa ba don bata samu zuwa da salla ba ita Fanan ma bata samu zuwa ba duk da taso zuwan Daddy d'inta ya hana yace ta zauna gidan d'an uwanshi wanda likita ne acan india d'in tayi sallar, A 6angaren Fatuu kuwa tunda sati na biyun ya kama ta kimtsa kayanta tsaf tana jiran ranar tafiya kullum in aka kwana sai tace saura kwana kaza yau da ya rage saura kwana d'aya su cika sati biyu sam ta kasa zaune ta kasa tsaye har bata iya 6oye farincikin da take ciki su kam su yadikko basu son ta tafi ba kamar kannenta tuni sun fara jin kewarta ba kamar Mino duk tafi kowa damuwa har cema Innarta tayi itama abarta ta koma can yadikkon tace a'a abun zaiyi yawa karma ta sake jin ta fadi haka, a ranar da daddare bayan Baffanta ya dawo ne yake sanar da ita tafiyarsu gobe Asabar bazata yuwuwa ba sai jibi in Allah ya kaimu don akwae siyayyar da yake son yi mata kuma sai goben ne Kasuwar da zaije ke ci cikin abunda zai siyo harda sak'on Fatun na tsarabar da zata kaima Haisam ba haka taso ba amman jin harda tsarabar Haisam za'a siyo yasa ta hak'ura hakan kuma ba k'aramin dad'i yayi ma Mino ba, a kwana a tashi ba wuya a wurin Allah duk abunda aka sama rana zai zo harma ya wuce a daren ranar Lahadi baccin Fatuu ragaggene saboda d'oki har k'agara tayi garin ya waye, Asubahin farko ta farka ko jiran yadikko batayi ba taje ta d'aura ruwan wankanta lokacin da yadikkon ta farka saidae ta ganta tana shiryawa da sabbin kayan Fulanin da Baffanta ya siyo mata Navy blue, Murmushi kawae tayi don ta gama fahimtar duk zumudin saboda taje taga Haisam ne, ana gama sallan Asuba suka fito don tafiya dama tun jiya da daddare tayi ma kowa sallama kuma ba laifi sun bata Abubuwa harda kudade haka Mahaifinta ma da Yadikko sun had'a mata sha tara ta arziki, har kopar gida suka rakota dama shi Amadu tuni sun fito shida Kamalu don zai rakasu ne, Mino nata matsar kwalla don itama sam batayi baccin kirki ba saboda tafiyar Fatun da ta saka a ranta gashi an hana tayi masu rakiya zuwa Jimeta inda zasu hau Mota, suna ta d'aga masu hannu bayan sun hau Mota Baffanta yaja suka tafi, Lokacin da suka isa jimeta basu samu Motar da zata kaisu direct Katsina ba hakan yasa suka hau ta Kano har saida suka ga tashinsu suna ta d'aga masu hannu cike da kewa suna masu Fatan Allah ya kiyaye hanya ya kaisu lafiya. Sam bata jin tafiyar ko bacci ta kasa yi burinta kawai ta ganta a Katsina hakan yasa bata takura ma Amadu ba sosae, sai bayan Azahar suka iso Kano ba 6ata lokaci suka samu Kano line mai zuwa Katsina, tunda suka kamo Hanya take ta sakin Murmushi don har ta fara jiyo kamshin Katsina, akace wai karfen Nasara ba Tabbas kwatsam Mota ta lalace masu a hanya har sunyo nisa sun kusa garin Kankia ta jahar Katsina, tun ana ganin zata gyaru har aka fara fidda ran gyaruwarta duk Mutanen ciki sun fito waje sun zazzauna a gefen hanya ciki harda Fatuu tana a wurin da Mata suke fuskar nan sam ba annuri murna ta koma ciki sai tsoki take bugawa Matar dake kusa da ita tun a Mota mai kirki ko abu zata ci sai ta bata ita ke bata baki tana nuna mata tayi hakuri komi Allah yayi mai kyau ne k'ilan da akansu matsalan zata faru ta faru akan Motar, ita dae jinta kawae take can ta mik'e ta nufi wani gida dake can gefe inda taga ana zuwa yin fitsari taje tayo bayan ta dawo ne ta nufi inda Amadu yake tana ta tura baki tace mashi wai ba'a kusa Katsinar bane su k'arasa ko a k'afa ne, wani kallo yayi mata kafin yace "an kusa baifi awa guda da wani abu ba sai ki taka ki k'arasan" yay Maganar yana harararta tana tura baki tace "ai wllh don bansan hanya ba dana tafiyata", d'an girgiza kai yay yace" indai hanya ce wannan ba matsala bace mik'ewa zaki sambal kita tafiya ba sai kin sha wata kwana ba zaki ganki har Katsinar" maimakon ta tafin sai ta tsaya tana tura mashi baki yace ta tafi ta bashi wuri ta juya Mutanen dake kusa dashi na mata dariya ganin tak'i ta tafi a k'afan ta koma ta zauna. Da kyar aka samu ta gyaru don da har direban ya fara tunanin buga waya a turo masu wata duk da hakan ba k'aramin dare zaisa suyi a hanya ba tunda yaushe Motar tazo har suka tafi, Hamdala Mutane suka shiga yi suna Addu'ar Allah ya kaisu lpy yasa kada ta k'ara lalacewa, ba tare da 6ata lokaci ba suka ci gaba da tafiya saidai direban bai yin gudu kaman da lalla6awa yake su samu su isa Lafiya, Allah sarki gwaggo tana can hankalinta duk ya tashi jin abunda ya faru da ta kira Amadun ya sanar da ita dama akai akai take kira tana jin sun iso ina haka ma can inda suka baro Mahaifin Fatuu da yaya Kamalu suma duk bayan d'an lokaci suke kira suyi masu ya Hanya, Alhamdulillah sai ana sallar isha suka k'araso duk sun gaji likis Fatuu kallabinta a hannu ta fito daga Motar kitson fulanin da yadikko tayi mata nata reto, suna sauka gwaggo ta kira lokacin Amadun na niyyar kiranta ya sanar mata ai koda taji sun sauka nan take ta hau yin hamdala harda yin sujjadar godiya ga Allah, ce ma Amadun tayi bari tazo ta taho dasu yace ta barshi kawae tunda sun shigo gari zasu k'araso lafiya lou, within some minutes suka iso gidan lokacin gwaggo na tsaye jikinta sanye da Hijab tana dakon isowarsu Keke Napep d'in na tsayawa ta nufeta tana masu Oyoyo, saida ta taimaka ma Fatuu ta fito cike da tsantsar farinciki ta rungumeta don tayi missing d'insu sosae duk sai gidan yayi mata ba dad'i saukinta ma tana zuwa aiki, bayan an sallami mai adaidaita sahun tare da gwaggo da Bello daya dawo daga Masallaci ya taimaka masu suka shiga da kayayyakin yay masu sannu da zuwa kafin ya fito lokacin tuni Fatuu ta baje a d'akin gwaggo don akwae wutan nepa atare suka shigo ita da Amadu ya zauna kan kujera ita kuma ta nufi gefen gadonta tana yi ma fatun sannu sam fuskarta ta kasa 6oye farincikinta sai faman tatta6a Fatun take tana yi mata sannu ita dae kai kawae take d'aga mata, mik'ewa tayi ta tafi kitchen ta fara kawo kayan abinci Amadu nayi mata sannu tace ai su keda sannu bayan ta gama kawo komae tace to su saukko suci Abinci, mik'ewa Amadu yay yace shi yafi bukatar yayi wanka kafin Abincin tana jin haka tace to bari ta had'a mashi ruwan wanka yana ta barshi zai had'a tace yay zamanshi, Allah sarki uwa mai dad'i ya ayyana a ranshi kafin ya koma ya zauna, bada jimawa ba ta had'a mashi ruwan dama akwae ruwan zafi a electric kettle data jona saboda su don garin a d'an kwai sanyin damuna, bayan ta dawo d'akin tace gashi can a bandaki yaje yayi yace to, kallon Fatuu tayi tace "to taso auta kici Abinci ko sai nazo na daukeki ne?" girgiza mata kai tayi alamar a'a tace "to daure ki tashi in kika ci abincin zaki ji karfin jikinki" tana jin haka ta yunkura ta fara kokarin saukkowa don tana bukatar karfin jikin saboda taje gidan Hajiya, zuba mata Abincin tayi ta zauna kan darduma ta fara ci ita kuma gwaggo ta hau kan kujera tana kallonta da Murmushi tana k'ara yi mata sannu, ta d'an ci ba laifi ta mik'e gwaggo na har ya isheta tace gidan Hajiya zata je ta fad'i mata sun dawo, "Ki bari ki huta gajiyar mana zuwa da safe ba sai kije ba" tura baki tayi tace ita dae yanzu zata je ba dad'ewa zata yi ba, d'aga mata kai tayi alamar taje da sauri ta nufi kayansu ta bud'e jakar kayanta ta d'aukko wata bak'ar leda dake k'ulle sai kuma ta bud'e ta tsarabar da suka yo ta kalli gwaggo tace "don Allah gwaggo kina da bak'ar leda yar babba?" tambayarta tayi mi zata yi da ita tace "zan d'ibar ma Hajiya tsaraba ne" gwaggon tace "to ki bari da safe ba sai akai mata ba ko", "To ai tsarabar Ya Handsome zan kai mashi tana iya cewa ita ina tata shiyasa zan fara kai mata wannan goben sai akai mata sauran" jinjina kai gwaggo tayi alamar gamsuwa ta mik'e ta samo mata ledan ta bata dama tasan duk zumudin na son ganin Haisam ne, bayan ta zuba abubuwan da zata d'iban tace ma gwaggo sai ta dawo ganin tana niyyar fita ko kallabi babu ta mik'e ta d'aukko mata kallabin ta bata tace ta yafa akanta tunda babba ne daga haka ta fuce. Lokacin data isa gidan kaman an jefota ta fad'o cikin falon Hajiyan kallabi a hannu ga ledoji a hannu tana ta zare idon son hango Haisam don taje part d'inshi bai nan kuma tasan yau ba ranar zuwa gym bace, Jidderh ce zaune a falon kan sofa 3 seater tana yin chat da wayarta ta d'aura duka k'afafunta saman kujeran jikinta sanye da jallabiya milk colour kanta ba kallabi tayi parking gashinta da yake bak'i sosae mai santsi sai twins dake gefenta suna yin game da ipad, atare suka d'ago suka kalleta kaman yadda itama ta kafesu da ido tana yi masu kallon rashin sani ko kyaftawa batayi, sai faman kallon juna suke an rasa wanda zai tanka ma wani can Mubeen ya kai bakinshi saitin kunnan Mubeena ya rad'a mata wata Magana ai kuwa a firgice ta kalleshi ta kuma kalli Fatun atare sai kace an latsa masu remote suka diro daga kan kujeran bayan sun aje ipad d'in suka ruga hanyar Bedroom d'in Hajiya suna kwala mata kira cike da razana sai kace kaji broilers yadda suke gudun, a daidai Corridor sukayi kacibus da ita ta fito jin kiran da suke mata jikinta sanye da hijab da casbaha a hannunta tun kafin tace wani abu atare suna haki suka ce "Ha...Hajiya a genie has appear" waro ido tayi tace "a genie?" da sauri suka jinjina mata kai alamar eh, tace"where is d genie" da hannu suka nuna mata cikin falonta, kama hannuwansu tayi tace "Ok let's go and see d genie" suka nufi cikin falon har wani sand'a suke tun kafin su k'arasa ta hango Fatun tsaye k'ikam har lokacin kuma Jidderh bata ce mata komae ba don ganin su twins sun ruga yasa ta d'an ji tsoron Fatun ya kamata, lokacin da suka k'araso cikin falon Hajiya na dariya tace "Lallai kuwa k'atuwar Aljana ce ta bayyana" da sauri Jidderh ta kalleta jin abunda tace amman ganin tana dariya yasa hankalinta kwanciya nan take kuma ta fara hasashen anya ba itace Fatun da Hajiya ke basu labari ba yar gidan ya haisam mai ce mashi Handsome don duk in suna fira sai ta sako masu labarin Fatun, kallon Hajiya su twins sukae suka nuna mata Fatuu wai ga Aljanar tana dariya ta zauna idonta akan Fatun tace "Manyan gari saukar yaushe?" tana tura baki tace "yanzun nan muka dawo Mota ta lalace mana a hanya" da mamaki su twins ke kallon both of them ganin suna Magana, Mubeena ce tace "Granny u know d genie?" kallonsu tayi tana dariya tace "she isn't a genie, she's d Fatuu i ave been telling u about" a tare suka zaro ido suka had'a baki suka ce "Fatuuuu!" kai Hajiya ta d'aga masu lokaci guda suka saki dariya suka nufeta aikuwa ta d'aure masu fuska tana yi masu wani kallo hakan yasa suka ja suka tsaya a gabanta suna kallonta itama kallonsu take da yar harara kawae sai suka fara ta6e baki irin na shagwa6a66un yara alamar zasu yi kuka hannunsu cikin na juna suka juya zasu koma Hajiya tace "ah Fateema ya da haka kuma?" tana tura baki tace "ba sune suke ce man Aljana ba" "To ai basu sanki bane baki ga bak'i bane gashi sun ganki da wata kalar shiga ga kanki a bud'e shiyasa suka tsorata ai" kallonsu tayi tace suje su bata hakuri a yadda suke ba tare da sun raba hannuwan ba suka koma,tsayawa sukae a gabanta sannan suka saki hannuwan kowa ya kama kunnanshi a tare suka ce"Sis Fatuu we're sorry" kawae sai gani sukae ta kece da dariya don yadda sukae ba k'aramin dariya suka bata ba dama ga uban kumatu tubarkallah suna ganin tayi dariya suka k'ank'ameta suna yi mata welcome, Jidderh da Hajiya ma dariyar suke, Hajiya ce tace ta zauna mana ta nemi wuri kan 2 seater suka zauna, gaida Hajiyar tayi kafin ta maida idonta kan Jidderh dake mata Murmushi itama ta gaidata ta amsa tace mata "an dawo lafiya" tana Murmushi tace "Lafiya lou amman munsha wahala tun Asuba sai yanzu muka iso fa" cikin sanyin muryarta tace "gaskia, sannu ko" amsa mata tayi da yauwa kafin ta kalli Hajiya tace "Hajiya su waye wad'annan?" tana dariya tace "ai kuwa ya kamata ace kin ganesu basai an fad'a maki ba, ki kallesu da kyau zaki gane ko suwaye" jin haka yasa ta k'ura ma jidderh dake Murmushi ido sai kuma ta maido kallon kan su twins tana k'are masu kallo can tace "wad'annan kumatunsu yayi yawa na kasa ganewa" hajiya tace "to ki kalli wannan da kyau" tayi Maganar tana nuna Jidderh, zuba mata ido ta k'ara yi ganin kaman tana yanayi da Haisam yasa tace ta daina yin dariya zata fi ganowa dariyar ta k'ara yi sosae jin Maganar Fatun kafin ta dakata suna kallon juna can ta kalli hajiya da sauri tace "yan gidansu Ya Handsome ne ko?" aikuwa gaba d'aya harda twins suka sa dariya jin tace Ya Handsome din, bayaninsu Hajiya tayi mata daga baya tace bayan bata nan suka zo, Ledar dake ruke a hannunta su twins suka fara ta6awa suna tambayar miye a ciki tace masu tsaraba ce, "Za mu ci" suka fad'a suna kara ta6a ledar da sauri ta janyeta tace"kai ba irin abunda kuka saba ci bane wannan shak'e ku zai yi" k'ara had'a baki sukae suka ce zasu ci koma minene tace "kai kuji man yara, so kuke ta shake ku kuja akaini gidan yari ko" kafewa sukae kan su dae ta basu suci su Hajiya na masu dariyar drama d'in da suke can Hajiya tace "miye a ciki ne?" da sauri tace "su goriba da kurna da magarya da aya ne fa na fara kawo maki sai gobe za'a ida kawo sauran tsarabar" kafin Hajiya tace wani abu Jidderh tace "ki basu ai sun iya cin su" da al'ajabi ta kalleta tace "ni ai nazata a Abuja ba'a saida irin wad'annan abubuwan don ance kaman kasar waje take" Jidderh na dariya tace "No akwae kasuwar da ake saida irinsu kuma cikin maids din mu akwae wata Iya yar Daura ce so in tazo tana kai mana tsaraban su har Dad ma naci yace suna Magani" cike da jin dad'i Fatun ta washe baki jin an yaba tsarabar tata, bud'e masu ledar tayi kowa ya d'auki goriba biyu yasa a cikin riga suka rungume sannan suka d'ibi magarya a hannu suka fara sha Hajiya dake kallonsu tace "wai bani aka kawo ma tsarabar bane to a mik'o man mana kuke ta kwashewa" mik'ewa Fatuu tayi ta kai mata ledar ganin tana ta mak'ale d'ayar a hammata tace to ita wannan miye aciki tace ba nata bane tsarabar Ya Handsome ne, bud'e ledar Hajiya tayi ta aje masu suka fara shan magaryar ita da Jidderh su twins suka ba Fatuu goribar wai ta cirar masu dama haka ake masu in kuma irin wadda aka 6an6are ce sai a jika masu tayi taushi sannan su ci suna cikin ci Fatuu ta tambayi Hajiya ina Saude tace tana d'akinta mura ke damunta ne tasha magani ta kwanta tace to ina Ya Handsome yake tace sun fita amman tasan sun kusa dawowa, Hajiya na rufe baki Nameer da Farha suka shigo hannunsu cikin na juna kowannansu na sanye da k'ananan kaya ta zame gyalen kanta ya dawo saman kafad'a, nufo cikin falon sukae Nameer na Fad'in "kai kai wato abun dad'i kuka samu kuna ta shagali shine ko ku tuna damu ko" yana rufe baki Mubeen ya nufe su yana nuna masu Fatuu yace "Ya Nameer guess who she is" d'aga ido yay ya kalli Fatun da itama shi take kallo da mamaki ganin tsananin kamarsu da Haisam, k'uri yay mata ya d'an k'ank'ance ido alamar yana son gano ko wacece d'in duk suka bishi da ido da Murmushi ita kuwa Farha kujera ta nufa ta zauna itama idonta na kan Fatun tana mata wani kallon rashin arziki don dama ita shirgin Mutane bai dameta ba, "She must be Fatuu yar gidan Ya Haisam" Nameer ya fad'a yana nunata da yatsa gaba d'aya suka sa dariya Mubeen na Fad'in "U guessed right" itama Fatun murmushi take mashi ya nufi hannun kujeran da take ya zauna yana mata Murmushi yace "saukan yaushe yar fillo" d'an tura mashi baki tayi yasa dariya dama yaji bata son sunan tace mashi bada dadewa suka dawo ba, "To ya rugar kuma ina tsarabarmu" yay Maganar ya d'age gira kaman yadda haisam ke yi, nuna mashi ledan abubuwan dasu Hajiya kesha tayi tace "ga tsaraban can" kallonsu yayi kafin yace "yo nida zanga Fura da Nono sai inga wanccan tarkacen" tace "ai suma za'a kawo su sai gobe" jinjina mata kai yay yanata dae yi mata Murmushi, Mubeena ce ta nufi Farha da tunda taji cewa itace Fatuu ta sadda kanta tana latsa wayarta tana zuwa wurinta tace "Sis Farha this's Fatuu we ave been told about" banza tayi mata kaman bata ji abunda tace ba har saida ta k'ara maimaita mata tana ta6ata aikuwa ta daka mata tsawa tace "leave me alone twin" yadda tayi Maganar har saida suka kalleta gaba d'ayansu, ta6e baki Mubeenar tayi sanin halinta yasa Hajiya tace mata ta kyaleta ana haka Haisam ya shigo shima k'ananan kaya ne jikinshi kafarshi na sanye da wasu slippers masu kyau da alama ba nisa sukae ba fuskar nan tayi wani Fresh ai twins na jin Muryarshi yayi sallama suka nufeshi atare da gudu suna cewa "Ya Haisam Fatuu has came back" sukae Maganar suna nuna mashi Fatun da itama idonta na akanshi ta guntse dariya da tafin Hannunta, kamo hannuwansu yay suka shigo cikin falon fuskarshi a sake da d'an Murmushi, mik'ewa Jidderh tayi ta nuna mashi kusa da Hajiya yaje ya zauna ita kuma ta koma saman hannun kujera tana facing inda Fatuu da Nameer suke Hajiya tace "ga Mutuniyarka fa an dawo sun dae sha wahala wai mota ta lalace masu a hanya tun Asuba sai da daren nan suka k'araso" d'an jinjina kai kawae yay kafin ya kalleta calmly yace "kun dawo lafiya?" tana ta sakin murmushi tace "Lafiya lou" nan ma jinjina kan yay kawae, Mubeen ne ya nufi wurin Fatun ya jawo ledar data k'ank'ame ta hana kowa ganin abunda ke ciki yace "ki bashi to" d'an harararshi tayi Hajiya dake dariya tace "atoh tunda ya dawo ai yanzu sai abashi muga abunda ke ciki ko, wai tsarabar kace tun d'azun ta kankame ta hana kowa gani" ta k'arasa idonta kan Haisam d'in shidae d'an Murmushi kawae yay, ganin Mubeen d'in yak'i kyaleta yasa ta mik'e taje gaban Haisam d'in ta mik'a mashi ya amsa ya furta mata "thanks", "Ya Haisam open it let's see what's inside" twins da suka k'agara su ga mike ciki suka fad'a, a nutse ya bud'e ledar ya fiddo abunda ke ciki, kayan fulani ne riga da hula kala biyu farare da kuma Navy blue kalan na jikin Fatun sun sak'u sosae da gani masu kyau da kud'i ne, d'an Murmushi yay ganin kayan duk suka hau cewa ya gwada don Allah suga yadda zasu yi mashi, shiru yay kaman bazai gwadan ba can ganin sunata rok'onshi yasa hannu ya cire rigar jikinshi k'irar karfinshi ta bayyana muraran don ma akwae farar singlet a ciki, masu duhun ya fara sawa lokacin da ya d'aura hulan akanshi wani ihu da sowa suka sa suna fad'in wllh yay bala'en kyau Nameer yace "gaskiya da sakel wllh ban yarda ba nima dole a bani irinsu" Fatuu dake dariyar jin dad'i tace" to ai bansan kana nan ba shi kadae na kawo mawa" yace dole tasan yadda zata samar mashi shi dae ya d'auki wayarshi iphone yace bari yayi mashi hotuna, da farko k'in yarda yay saida Hajiya tasa baki sannan ya bari ya fara yi mashi hoton suka ce ma Fatuu ta zo ayi masu tare tunda kayansu iri d'aya ne ta matsa akayi masu, Wow shine kowa ke fad'i don ba k'aramin kyau pic din yayi ba ba kamar da yake kan Fatun ba kallabi kitson fulaninta sun zubo, hotuna suka ci gaba da yi harda su twins da Jidderh da Nameer ita dae Farha ko ci kanku bata ce ba amman ta kan d'an d'ago ta kallesu, bayan ya cire masu duhun yasa fararen suma dae sun amshe shi sosae hakan ba k'aramin dadi yayi ma Fatuu ba tana cikin yin d'an tsallen Murna kawae taji an tadiyota tayi baya ta fad'i da6ar a kasan Carpet ba karamin buguwa tayi ba har saida ta yarfa hannu tace washhhh, tsit kake ji wutar kowa ta d'auke duk suka maido hankalinsu kan Fatuu daketa faman yarfa hannu sai kuma suka maida kallon kan Farha data d'aure fuska tamau tana hararar Fatun, "What's that Farha!" Hajiya ce tayi Maganar da d'an tsawa don daga kallon da Farhan kema Fatun suka fahimci abunda ya faru, jin Farhar tayi shiru ne yasa Hajiya maimaita Maganar Farhar tace "ta take man k'afa" a fad'ace tayi Maganar had'i da mik'ewa tana yamutsa Fuska ta nufi hanyar Bedroom walking slowly ita ala dole kafan ciwo take mata, bud'a ido Fatuu tayi alamar mamaki baki bud'e jin abunda Farhar tace wanda tasan ita dae bata taka ta ba suma sauran yan cikin falon kallon suka bita dashi har ta shige Corridor Nameer ne ya matso wurin Fatun ya mik'a mata hannu alamar ta kama ta tashi bin shi da ido tayi kaman zatai kuka ya jinjina mata kai alamar ta tashin, kama hannun nashi tayi ya d'agata ta mik'e suka nufi kujerar da suka zauna da farko ya zauna a kusa da ita yana ce mata sorry suma sauran hak'urin suka shiga bata su twins suka zo gabanta suna tatta6ata suna cewa "Sorry sis Fatuu Aunty Farha is wicked" duk abun nan Haisam na zaune shiru bai ce komae ba saidae daga yanayin fuskarshi zaka fahimci bai ji dadin abunda ya farun ba duk yadda taso kar tayi kuka ta kasa daurewa abun yayi mata ciwo gashi jikinta yayi sanyi don ta fahimci bata samu kar6uwa a wurin farhar ba dama d'azun taga yadda ta kwatsa masu twins tsawa da suna nuna mata ita, sharrrr kwalla suka fara zubo mata da sauri ta duk'ar da kanta Nameer nata bata hakuri yana k'okarin goge mata hawayen saidae ta hana, harda Hajiya da jidderh keta bata hakurin can ta mik'e tsaye cike da nuna damuwa Nameer yace "ina zaki?" a hankali tace "gida" mik'ewa yayi ya kama hannunta yace "muje in raka ki to" suna niyyar tafiya Haisam ya d'aga mashi hannu alamar dakatar dashi ba tare daya ce mashi komae ba, tsayawa yayi yana kallonshi haka ma Fatun, hannu yasa ya cire rigar Fulanin jikinshi ya maida tashi kafin ya mik'e idonshi akan Fatun yayi mata alamar su tafi da kanshi Nameer ya saki hannun nata ta bi bayan Haisam da yayi gaba duk suka bita da kallon rashin jin dadi Hajiya tace "Kiyi hakuri Fateema kinji, taji zafi ne shiyasa har tayi maki hakan" kai kawae ta d'aga mata suka fice, suna Fita Hajiyar ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom rai 6ace duk da ita tayi zaton da gaske takata Fatun tayi amman don mi zata yi mata haka, jiki asanyaye Jidderh ma ta nufi hanyar Bedroom su twins suka bi bayanta suna kunkunin Aunty Farha muguwa ce ya rage Nameer ne kad'ai a falon idonshi akan tv sai dai can k'asan zuciyarshi wani irin takaici ne ya turnuke shi lokaci bayan lokaci yake jan tsoki.............. ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ Littafin A Sanadin Makwabtaka Kashi na Farko wanda nayi shi a kyauta yazo karshe, Ga mai bukatar cigaba da karanta kashi na biyu wato Book 2 zai biya kudin karatu Naira 300 kacal ta wannan Account din👇 1509618776 Zainab Bature Access Bank Za'a turo da shedar biya ta daya daga cikin wadannan Lambobin wayan ko kuma tuntu6a don neman karin bayani, 09013804524 ko 08169856268. Thanks and i luv u as u patronize🤝🥰 *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 7️⃣0️⃣ ........Yana gaba tana biye dashi suka fito Harabar gidan, d'an dakatawa yay ta k'araso inda yake don ya d'an yi mata nisa ganin tana niyyar nufar gate ne yasa yace ta biyo shi part d'inshi, saida ya shiga kafin itama ta shiga ta tsaya gefen kujera shi kuma ya zauna, d'an kallonta yay suka had'a ido ta daina matsar kwallan amman idanunta sun d'an yi ja ba sosae ba, nuna mata armchair yay da hannu alamar ta zauna ta matsa a hankali ta zauna still kallonta yake yama rasa mi zaice mata, d'agowa tay a hankali suka sake had'a ido calmly ya furta "am sorry about what happened" jinjina mashi kai tayi tana d'an motsa baki ya sake cewa "Nagode da tsaraba" nan ma kai ta sake jinjinawa, "Ko baki yi hakurin bane?" a hankali tace "nayi" yace "Owk smile mana kin d'aure fuska bai maki kyau ba" bata san lokacin data saki Murmushi ba tana kare bakinta da tafin hannu hakan kuma ba k'aramin dad'i yay mashi ba ganin tayi Murmushi, shiru suka d'an yi can tace "kasan ya akai nasan wad'anda zasu yi maka" ta d'age ido, girgiza mata kai yay alamar a'a taci gaba "akwae wani d'an film d'in india mai irin jikinka to a wayan kawu Amadu akwae film d'inshi shine na nuna ma Baffa nace kaman wanda zai mashi zai sai ma yace man ai ya sanka zai gane wanda zasuyi makan" fuskarshi asake da d'an Murmushi cikin cool voice d'inshi yace "Wanda muke kama kenan?" da sauri ta girgiza kai tace "a'a shi wannan a fuska ne kuke kama amman jikinku ba iri d'aya ba wanda na nuna ma baffan shine keda irin jikin ka ni bansan sunanshi ba dae amman yana yawan yin Film d'in india kuma mai k'arfi sosae suke sa shi", still yay yanata kallonta har ta gama ya jinjina mata kai kafin yace "kina sa man ido sosae kenan har kika san jikinmu d'aya dashi ko" ya d'age mata gira, kyalkyace mashi tayi da dariya tana sunna kai tace "a'a wllh Ya Handsome ba saka maka ido nike bafa ba na sanka ba" d'an ta6e baki yay da d'an Murmushi akan fuskartashi can ya d'aga hannu ya duba wrist watch d'insa dake nuna karfe goma saura yan mintuna hakan yasa ya mik'e yace mata yana zuwa tace mashi to, hanyar Bedroom ya nufa tana ta kallon bayanshi yana kaiwa bakin Corridor ya d'ago mata hannu batare daya juyo ba ya furta "kallon ya isa hakanan" dariya tasa ta kwantar da bayanta a jikin kujeran, bai dad'e ba ya fito ruke da wata babbar leda mai d'auke da tambarin M. ZAKEE's STORE wato store d'in Mamansu Farha Hajiya Maryam, a gabanta ya ajiye ledar yace "nima ga nawa tsaraban" da sauri ta d'ago ta kalleshi tace "ta Lagos da kaje?" kai ya d'aga mata cike da murna ta duk'a zata bud'e yace ta bari sai taje gida yanzu dare yayi ta tashi ya rakata tace to, mikewa tayi tana kokarin d'aukar ledar ya rigata d'auka yace suje ta shige gaba yana biye da ita suka fita, suna akan hanya ta kai hannu tace ya kawo itama ta ruk'e hannu d'aya ba tare daya ce mata komae ba ya sakar mata suka cigaba da tafiya duk da ruk'on jakkar bai mashi dadi ba don bai yi balance ba, tana ta bashi labarin wuyar da suka sha saboda mota data lalace masu a hanya har suka k'araso kopar shiga gidan ya sakar mata Ledan yayi mata saida safe yana shirin juyawa ta kira sunanshi ya waigo tace "Nagode da tsaraba nima" Murmushi kawae yay mata ta d'aga hannu tana mashi bye bye shima ya d'an d'aga mata hannunshi guda kafin ya juya ya tafi. Lokacin data shiga ciki d'akin gwaggo ta nufa har lokacin Amadu na ciki ya kishingida kan kujera gwaggon na zaune a gefen gado da alama fira suke Fatun ta shigo da sallama ta nufi gwaggo tana washe baki Amadu yace "ai munyi zaton acan zaki kwana keda hankalinki ragaggene" bata tanka mashi ba ta aje ledar gaban gwaggo tana Fad'in tsaraba ce itama Ya Handsome ya bata ta Lagos daya je, fiddo abubuwan dake aciki ta fara yi, Wata hadaddar School Bag ce da takalma cambus guda biyu a cikin jakar akwae littattafai na karatu dana rubutu wato exercise books da textbooks masu yawa don duk manyan Subject d'in da ake a Senior secondary akwae textbook nashi ga uban biroka fensir shafana kilina da sauransu dae abubuwan gwanin burgewa irin na yan gayu don wannan da gani duk Makarantar tasu ba lallae asamu mai irinsu ba ba kaman jakar goyon irin mai trolley din nan ce, saboda tsabar farinciki har ta kasa Magana sai faman d'aga kayan take gwaggo ma dariya ce akan fuskarta, juyawa tayi tana nunnunama Amadu kayan yace "inyee yar gidan Ya Handsome sai nima ki dibar man rabona to" mak'e mashi kafad'a tayi yace wllh bata isa ba wannan uban kayan ya zata yi dasu tace ai tasan harda Haulat shiyasa ya siyo su da yawan yace to shima harda shi ai aka siyon gwaggo dae nata dariya tana girgiza kai, koda ta gwada takalman ba k'aramin kyau suka yi mata ba gashi sunyi mata daidai sai faman washe baki take tana nuna ma gwaggo kafar tata ita kuma tana yin Addu'a, mik'ewa Amadu yay yayi masu sallama dama tun d'azun yake jin bacci daurewa kawai yake yana ma gwaggo firan ruga, bayan ya tafi gwaggo tace "to ki maida su ciki kije kiyi wanka ko kya ji dad'in jikin kinje kin zauna gashi dare ma yayi sosae kije dae kiyi ki rufe kanki kuma ki tabbatar kinyi Addu'a" kai ta d'aga mata bayan ta mayar dasu suka fita tare don ta had'a mata ruwan wankan. Washegari suna gama yin karin kumallo taje tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atampa ta yafa mayafi ta nufi gidan Hajiya don kai mata sauran tsarabar lokacin k'arfe goma da wasu mintuna, lokacin data shiga Falon Hajiyar na zaune kan kujera tana kallon labaru su Jidderh kuma na kan Dining table suna yin breakfast don basu dad'e da tashi ba, da sallama ta shiga Hajiya ta amsa mata tana ganinta ta saki Murmushin jin dad'in ganinta don hakan ya tabbatar mata da bata yi fushi ba kan abunda ya faru jiya su twins ma na ganinta suka taso da gudu suna fad'in "Welcome sis Fatuu" suna k'arasowa suka fad'a jikinta tasa hannu ta dafa bayansu su duka, a kusa da kujerar da Hajiya take suka zauna ta gaidata tana dariya itama dariyar take tace "Yan tafiya ya gajiya?" tace " ba gajiya" aje mata ledar da ta shigo da ita tayi gabanta tace ga sauran tsarabar nan hajiyar tace "kuma dae muna ta shan tsaraba haka da dijen ma ta dawo ta kawo mana fa, to an gode Allah yasaka da Alkhairi" tana rufe baki Jidderh ta k'araso wurin jikinta sanye da doguwar rigar bacci brown mai santsi kanta ta yafa bak'in gyale tana kallon Fatun da Murmushi ta zauna kan Sofa Fatuu ta gaisheta ta amsa cikin muryarta ta yan gayu tace "ya gajiyan tafiya" amsa mata tayi da babu gajiya ta jinjina mata kai, kama hannun Mubeena mubeen yayi yace "zo muje mu gaya ma Ya Nameer Sis Fatuu tazo" suka nufi hanyar Bedroom da gudu, bada jimawa sai gasu sun dawo tare da Nameer d'in ya kamo hannuwansu da gani daga bacci yake don idanunsa sun nuna yana sanye da wando 3 quarter da riga armless da gani shima yana gyming don damtsen hannunsa ya gwada, da Murmushi ya k'arasa kujerar da Fatun take ya haye kan hannun kujerar idonshi akanta itama kallonshi take tana Murmushi cikin muryarshi da bata idasa washewa ba yace " yar fillo kin tashi lpy ya gajiyan tafiya" d'an tura mashi baki tayi tace "nifa ka daina ce man yar fillo ba kasan sunana ba" kawae sai ya dungure mata kai yace "to ke ba yar fillon bace" dariya ya basu gaba d'aya ganin abunda yayi mata, k'ura mata ido yay yana kallonta kafin yace "baki fushi ba kenan?" shiru ta d'anyi kafin ta d'aga mashi kai alamar eh yace "Gud haka ake so mutum ya kasance mai hakuri" Hajiya tace "aikuwa dai Fateema ba dai hakuri ba dama" wani kallo Fatun tayi mata alamar bata yarda da Maganar Hajiyan ba ba kamar da ta ga tana dariya alamar itama da biyu tayi Maganar duk suka yi Murmushi suma don sun san labarin Fatun na bata barin ta kwana duk wannan abun Farha na dining tunda ta juyo lokacin da Fatun ta shigo ta kalleta bata k'ara waigowa ba karshe ma sai ta mik'e ta nufi Bedroom, sai wurin Azahar ta bar gidan su twins na tambayarta zata dawo ko tace masu eh sai da daddare zata zo suyi fira lokacin Nameer har yayi wanka ya canja kaya suka fito atare yace bari ya rakata daga can ya wuce Masallaci, bayan sun fito ta tambayeshi Haisam yace mata yana wurin aiki dama tasani kawae hakanan ta tambayeshi, suna tafe suna fira sai kace sun dad'e da sanin juna har kopar gida ya rakota ya tsaya suka gaisa da Amadu Fatuu na gaya mashi k'anin Ya Handsome ne yace ai ya gane tunda ga kama nan ya gani, yayi mashi anzo lafiya fuska sake Nameer d'in ya ce mashi lafiya lou suma sun dawo lpy, cikin mutuntawa suka gama gaisawar ya kalli Fatuu yace "to yar fillo sai anjima ko" yar harara ta wurga mashi shima ya rama suka sa dariya harda Amadu daga haka ya juya ya tafi, bayan ta shiga gidan tsarabar Haulat ta d'auka ta nufi gidansu don bata san sun dawo ba tun ranar asabar data zo don da sukayi waya da Fatun lokacin suna can ta sanar mata ranar zasu dawo ta iske basu dawo ba Gwaggo tace mata sai washegari hakan yasa jiyan bayan la'asar ta sake zuwa still ta iske basu dawon ba, ba k'aramin farinciki Haulat tayi ba da ganin Fatun sai faman washe baki take kamar zata goyata innarsu ma da kannenta suka yi mata an dawo lafiya, lokacin data bata tsarabar harda ta haisam bayan sun shiga d'aki kasa rufe baki tayi don murna sai faman tatta6a abubuwan da haisam ya siyo masu take cike da zumud'i ta kwashesu taje ta nuno ma innarsu,bayan ta dawo ne innar tasu itama tazo d'akin tayi ma Fatun godiya kafin ta tafi, firan ruga ta shiga bata har akayi la'asar sannan ta baro gidan don tana son zuwa wurin Haisam in ya dawo tayi mashi godiyar tsaraba sosae don ba k'aramin dad'in kayan taji ba, tare da haulat d'in suka taho zata islamiyya tace ma Fatun ita bazata je ba tace eh sai gobe, a daidai kiosk d'in kawu Amadu suka rabu ta wuce, matsawa tayi gaban kiosk d'in ta tambayeshi yaga Ya Handsome ya wuce yace shi bai ganshi ba hakan yasa ta nufi cikin gidan tayi salla bayan ta gama ta fiddo da tsarabar kayan makarantar tana sake dubawa cike da jin dad'i ba komae yafi mata dad'i ba sai sanin cewa duk Makarantar baza'a samu mai irinsu ba, ganin hud'u da rabi ta wuce karfe biyar ta kusa yasa ta maida komae ta mik'e da sauri ta fita waje, wurin kawu Amadu ta sake komawa ta k'ara tambayarshi ko Haisam ya wuce da farko cewa yayi bai sani ba ta aje shi ne yay mata gadi, magiya ta hau yi mashi sannan yace eh ya wuce bada jimawa sosae ba, ko gidan bata koma ba ta nufi gidan Hajiyar ta k'aramar kopa tabi ta shiga part d'inshi tana niyyar hayewa balcony taji daga bayanta da d'an k'arfi ance "Hey!!!" da sauri ta juya don bata tsammaci ganin wani ba, Farha ta gani tsaye bakin fence door tana sanye da skinny fit bak'i wanda iyakarshi gwiwarta sai riga mai dogon hannu bak'a ta kamata sosae gashi daga k'asa bata rufe saman wandon sosae ba ana d'an hango k'asan cikinta da yake fari fat, kanta tasa bakar hula irin mai kama kai yayin da gashinta ash ke zube a gefe da gefen fuskarta hannunta ruke da wayarta wadda keda cover ash haka kafafunta ma na sanye da flat shoe ash ba k'arya tayi kyau sosae ta fito a baturiyarta dama gashi ba ramamma bace tana da yar k'iba sannan a shekaru ta girmewa Fatun sosae don zata kai shekara 18 zuwa 19, da wani irin taku ta nufo Fatun ta tsaya agabanta tana yi mata wani kallon rashin arziki itama Fatun kallonta take ta d'an d'aure fuska saidae jurewa kawae take saboda k'wayar idonta mutum bazai iya jure ma kallonta ba na tsawon lokaci, "What are u doing here?" ta tambaya, Fatun tai mata banza tana binta da ido ta k'ara cewa "am i not talking to u, why can't u sit in ur House, kullum ke kina gidan mutane ne?" sai lokacin Fatun tace "to ai ba wurin ki nazo ba ko wurin ya...." kafin ta idasa Maganar ta daka mata tsawa "Oh u shut up! Is he ur Father, babanki ne shi ko kin had'a wani abu dashi" ta tambaya ta kumburo baki tana huci haka itama Fatun ta kumburo baki jin abunda tace mata, nuna mata hanyar fita tayi tace "leave here now,mai kwad'ayi kawae baki iya tsayawa gidanku kullum kina gidan Mutane k'wak'wa, i don't wanna see u in dis house again" waro ido Fatun tayi baki bud'e take kallonta jin ta kirata da mai kwad'ayi da kwakwa lokaci guda idanunta suka sauya kala tsantsan bacin rai ne acikinsu sam tama kasa maida mata martani duk da yadda Maganar ta daketa kirjinta har wani d'agawa yake da sauri da sauri, "I said leave before i......." tsit tayi bata k'arasa ba sakamakon jin k'arar bud'e kopar Falon Haisam ta d'aga ido ta kalli saitin kopar, shine ya fito cikin shirin zuwa gym bin su yayi da ido yana tunkaro su ya tsaya a yar matattakalar ba tare daya idasa saukkowa k'asan ba, kallon Fatuu data sadda kai yay kafin ya d'ago ya kalli Farha data tamke fuska hakan ya tabbatar mashi da akwae abunda ke faruwa, What's happening here?" ya tambaya idonshi akan Farhar, shiru tayi ta d'an kauda kai tana tura baki, maida idonshi yay kan Fatuu yace "Zarah" da karyayyar murya ta amsa mashi yace "mike faruwa ne" girgiza mashi kai tayi alamar ba komae sam bai yarda ba ya sake tambayar Farha itama tace ba komae, shiru ya d'anyi yana nazarinsu gaba d'aya, a kausashe yace "Zarah tell me miye ne!" aikuwa kaman tana jira ta fashe da matsanancin kuka wanda daga jin sautinshi zaka fahimci tana cikin bacin rai, d'agowa yay yayi ma Farha kallon tuhuma kafin ya idasa sauka ya tsaya agaban Fatun ya kirata ta amsa yace ta d'ago ta gaya mashi abunda tayi mata, d'agowa tayi idanunta sunyi jawur cikin kuka ta fara fad'i mashi aikuwa tun kafin ta k'arasa ya juya yana ma Farha wani kallo fuska a matukar d'aure yace "Why, Why Farha!" tana tura baki tace "this is not their House so ta tsaya a gidansu mana zatai ta zuwa ma Mutane gida" takaici ne ya turnuke shi har baisan lokacin daya daka mata tsawa ba yace "shut up and leave my sight" wani kallo ta bishi dashi ya kara daka mata tsawa yace "i said leave else i will slap u!" d'an zaro ido tayi da alamun mamaki tace "u will slap me Ya Haisam because of dis pauper?" wani Murmushin takaici yayi ya jinjina kai had'i da maimaita kalmar pauper data kira Fatun da ita kafin yace "then isn't she a human being?" ya tambaya had'i da d'age gira jin tayi mashi shiru yasa ya fara moving inda take yana maimaita abunda yace mata "ki gaya man ita ba Mutum bace saboda talaka ce?" ganin yadda yake Maganar cike da 6acin rai yasa ta fara ja da baya kafin ta juya gaba d'aya ta nufi hanyar fita shi kuma yaja ya tsaya yana kallonta tana zuwa bakin fence door ta tsaya ta juyo tayi mashi wata magana da shi kad'ai yaji mi tace daga haka ta fuce, d'an guntun tsoki yaja jin abunda tace sai yanzu ya gane dalilin da yasa tayi ma Fatun haka juyowa yay ya kalleta ta fara kokarin bi ta gabanshi zata wuce yace mata su shiga ciki, d'agowa tayi ta kalleshi ya jinjina mata kai hakan yasa ta wuce gaba yana bayanta suka shiga cikin Parlon, armchair ya nuna mata yace ta zauna ta zauna sai faman sheshsheka take, wucewa yay ya nufi frigde ya d'aukko lemu fanta da cup ya dawo shima ya zauna akan d'ayar armchair d'in ta kusa da ita ya bud'e lemun ya tsiyaya acikin cup ya mik'e ya ajiye robar kan c-table kafin ya dawo ya mik'a mata, d'agowa tayi ta kalleshi ya d'an lumshe mata idanu alamar ta amsa maimakon ta amsan sai kawae ta k'ara fashewa da kuka tana Fad'in "wllh na rantse da Allah Ya Handsome ni ba kwad'ayi da kwakwa nike zuwa ba" d'an cije baki yay sam baison jin Maganar ma don yasan tana yi mata ciwo sosae saboda bai manta da labarin wadda tayi mata gorin kallo ba da ta ta6a bashi tun lokacin ya fahimci irin hakan na mata ciwo, shiru yay yana kallonta tana ta faman kuka fuskarta tayi jaga jaga da hawaye ga idanunta sunyi ja, Calmly ya fara Magana idanunshi akanta "i know who's Zarah, so i will never think of dat, ki daina damun kanki akan hakan ki manta kawae ita haka halinta yake ne kawae don ta 6ata maki rai tayi maki wannan Maganar but ni nasan ba haka halinki yake ba" da sauri ta kalleshi da jajayen idanu murya na rawa tace "to su sauran fa?" d'an Murmushi yay yace "suma bazasu yi maki kallon hakan ba don ba halinsu d'aya ba su zasu d'auke ki kaman sis nasu" shiru tayi tana kallonshi ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda ya fadan kafin ya sake mik'a mata lemun ta amsa ta d'an kur6a daga haka ta mik'e ta aje kan c-table ta kalleshi tace mashi zata tafi gida, shiru ya danyi yana kallon face d'inta kaman mai nazarin wani abu kafin ya d'aga mata kan alamar to har ta kama kopar zata bud'e ya kirata ta juyo yace "am so sorry and am apologizing on her behalf" shiru ta d'an yi sai kuma ta jinjina mashi kai daga haka ta fuce, zaune yay a wurin ya d'age kanshi sama na d'an wani lokaci kafin ya mik'e ya nufi hanyar Bedroom, ruke da jakarshi ya fito ya fita daga falon da farko da ya fito lokacin da yaga su Fatun part d'in Hajiya zaije yaci abinci amman yanzu yana fitowa Parking space ya nufa kawae ya hau bike dinsa ya fice, Hajiya na zaune a Falo hannunta ruke da Al'qurani idanunta na sanye cikin gilashi ta jiyo k'arar bike d'inshi,lokacin data kai karshen ayar da take cikin karantawa ta d'ago ta kalli Farha dake Facing dinta ta juya tana lek'en Haisam d'in ta window tace "Fita yayi kenan ba tare daya zo yaci abinci ba" juyowa Farhar tayi ta kalleta ta d'an ta6e baki daga haka ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom. Koda Fatuu ta koma gida bata gaya ma kowa abunda ya faru ba dama kuma gwaggon ta tafi aiki taja bakinta tayi shiru saidae acan k'asan ranta tana jin zafin Maganar sosae ba kamar dayake bata rama ba. Ranar Alhamis bayan Azahar duk suna zaune kan dining suna cin abinci banda haisam da bai kaiga dawowa ba Jidderh ta kalli Hajiya tace "wai nikam hajjaju ya akai kwana biyu yar gidan Ya Handsome bata zo ba ko dama ba ko yaushe take zuwa ba?" saida ta idasa cinye abincin dake cikin bakinta ta ajiye cokalin kafin tace "wllh kin riga ni ne a baki amman abun na raina ace yau har kwana ukku bata zo ba inata so in maganta kwana biyu da ba zaune nike ba shiyasa nama yi zaton ko tazo ban nan ne" girgiza mata kai jidderh tayi alamar a'a Hajiyar tace "to Allah dae yasa lafiya" tana rufe baki Nameer yace"Lafiyarta lau ko jiya naje gidansu mun gaisa da granny dinta" sai lokacin Farha ta d'ago tayi mashi wani kallon mamaki Hajiya tace "shanshani ashe har kasan gidansu kana ma zuwa kenan" murmushi yay gaba d'aya dimples d'inshi suka lotsa yace "Ran Monday da tazo na rakata ne naga gidan har muka gaisa da Uncle d'inta mai kiosk so wurinshi nike zuwa fira shine har na shiga cikin gidan" jinjina kai Hajiya tayi Jidderh tace "to muma zamu je mu gaisa", "haka yakamata kuje ku gaishe da kakarta har ku gano mana ita kuji ya akai bamu ganta ba kwana biyu" Hajiya na rufe bakinta Jidderh ta mike su twins ma suka saukko daga kan dining chair alamar suma zasu je kallon Farha tayi ganin yadda ta wani tamke fuska yasa bata ce mata komae ba ta nufi cikin falon Nameer na mata kwatancen gidan yace ko tayi ma Officer Magana zai nuna masu tace to, dama akwae gyale akanta don bata cika son zama ba kallabi ba suka fuce, suna fitowa bakin gate tayi ma Officer Magana ya tashi ya rako su har wurin kiosk d'in Amadu ya nuna masu gidan yayi masu adawo lafiya yana daga ma su twins hannu suma suna d'aga mashi, a bakin kiosk d'in ta tsaya ta gaida Amadu yana ganinta ya washe baki yana amsawa tace mashi sunzo gun Zarah ne ko tana nan yace eh bari ya rakasu ciki ya fito yay masu jagora yana gaba suna biye dashi har bakin kopar d'akin Fatun ya d'aga labulen baiwar Allah tana kwance kan gado tunda ta daina zuwa gidan Hajiya take jinta kaman bata lafiya ko gidansu Haulat ta daina zuwa duka sau d'aya taje shima kasa zama tayi ta dawo gida saidae taita kwanciya a d'aki har gwaggo ta gano akwai abunda ke damunta taita tambayarta amman sai tace mata ba komai, "Ki tashi kinyi bak'i" Amadu yace mata bayan ta d'ago ta kalleshi, idasa tashi tayi zaune ya juya yace masu su shiga su twins nata faman kallon gidan, da sallama Jidderh ta shiga Fatuu na ganinta ta saukko daga kan gadon ta mik'e tana kallonta da alamun mamaki ta amsa sallamar ita kuma tana tayi mata Murmushi, nuna mata gefen gadon tayi tace ta zauna ta amsa da to kafin ta nufi wurin ta zauna tace ma su twins dake ta bin d'akin da kallo suzo su zauna a tare suka haye saman gadon ko takalma basu cire ba Jidderh tace suje waje su cire Fatun tace ta kyalesu ba komai ai, "Zasu 6ata maki bedsheet" ta fad'a a nutse fatun tace ba komae, shiru suka d'anyi sai faman Murmushi suke ma juna can Mubeen yace "Sis Fatuu is dis ur House?" kai ta d'aga mashi alamar eh, Mubeena tace "but it's too small....." kafin ta ida Jidderh ta d'an yi mata tsawa tace "who ask u dat!" turo baki tayi Mubeen ya ta6a Fatun yace "ki dawo gidanmu babbane k'ato yana da kyau" yar dariya tayi tace "to zaku barni in zauna ko" da sauri suka d'aga mata kai alamar eh tace "amman a d'akinku zan zauna fa" a tare suka ce "to ai d'akinmu ma babba ne" suka yi Maganar suna nuna mata girman da hannu tayi Murmushi, suna zaunen Amadu ya shigo ruk'e da d'an babban plate ya d'auro masu ruwa da lemu harda Biscuits ya ajiye a k'asa kusa da k'afafun Jidderh ya d'ago da Murmushi yace mata bismillah itama Murmushin take tace mashi sun gode daga haka ya juya ya fita, kallonsu twins Fatuu tayi tace su saukko su ci atare suka mak'e Kafad'a suka ce "Abinci zamu ci bamu son wannan" wani kallo jidderh tayi masu Fatun tace "to bari in zubo maku...", katseta tayi "ki rabu dasu yanzu fa suka ci abinci" turo baki sukae suka ce su dae yunwa suke ci ai basu koshi ba suka taho binsu tayi da wani kallo Fatuu kuma ta nufi hanyar fita har zata fita ta juyo a sanyaye tace "amman bansan ko zaku iya cin abincin ba d'an wake ne ko in dafa maku indomie ko taliya?" da sauri suka hada baki suka ce "a'a zamu ci dan wakun" har saida tayi dariya jin yadda suka fad'i sunan d'an waken wai dan waku, bada jimawa ba ta kawo masu tasa masu fork guda biyu aciki da robar yaji ba yadda Jidderh batayi dasu ba akan su saukko k'asa suci amman suka k'iya wai ai ba table su bazasu zauna a k'asa ba Fatuu tace ta kyalesu ba komae dole asaman gadon suka ci sai faman tura biyu biyu suke ita Fatuu mamakin yadda suke cin d'an waken take don bata yi tunanin sun iya cinshi ba saida Jidderh tace mata ai suna yin abincin gargajiya Dad d'insu yafi son cin irinsu,jin hakan yasata cewa bari itama ta zubo mata to tace a'a ta barshi duk da ranta ya biya saboda ta jima bata ci ba, baki cunkushe su twins suka ce taci da dad'i sosae, Fatun tace ita dae sai ta zubo mata tace to kad'an zata kawo mata don daga kan abinci ta taso, bayan ta kawo matan sama sama suka shiga d'an ta6a hira saboda rashin sabo har ta tambayeta gwaggo tace mata tana wurin aiki, sai can bayan la'asar suka bar gidan Fatun ta rako su har bakin Gate Jidderh na cewa bazata shiga su gaisa da Hajiya ba tace ta gaidata ta baro gida ba kowa in gwaggonta ta dawo zata zo daga haka sukayi sallama ta juya ta komo gida. ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _A heart touching story of Love and Destiny_ 💔 *Mallakin* ⬇️ *🌹ZAINAB LALUH*📲✍ _~(Oummu imam)~_ Littafin A Sanadin Makwabtaka Kashi na Farko wanda nayi shi a kyauta yazo karshe, Ga mai bukatar cigaba da karanta kashi na biyu wato Book 2 zai biya kudin karatu Naira 300 kacal ta wannan Account din👇 1509618776 Zainab Bature Access Bank Za'a turo da shedar biya ta daya daga cikin wadannan Lambobin wayan ko kuma tuntu6a don neman karin bayani, 09013804524 ko 08169856268. Thanks and i luv u as u patronize🤝🥰 *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 7️⃣1️⃣ .......tunkarar gate d'in suka yi Officer na masu an dawo lpy Jidderh ta amsa mashi da lafiya lou kafin suka shige cikin gidan, suna shiga suka hango Haisam na tunkarar parking space zai tafi Gym da gudu su twins suka nufeshi ya bud'e masu hannu suna isa suka kankameshi suna murnar ganinshi, d'agowa sukai suka ce mashi daga gidansu sis Fatuu suke yace yayi kyau, lokacin Jidderh ta k'araso tana Murmushi ta gaidashi ya amsa har zata wuce ya tambayeta Zarah d'in na Lafiya tace eh har bakin Gate ma ta rako su tace gidansu ba kowa ne shiyasa bazata shigo ba, jinjina mata kai yay sam baiyi mamakin jin hakan ba su twins suka ce suma zasu je gym d'in yace ba'a zuwa da yara daga haka ya nufi parking space ya haye bike d'in ya fito su twins na yi mashi bye bye shima ya d'aga masu hannu bayan yasa helmet yaja ya fuce daga gidan. __________________ Washa gari Friday Misalin karfe takwas na safe Motar Haisam ta fito daga gidan don tafiya aiki kamar kullum, daidai lokacin Fatuu ta fito daga gida tana niyyar hawa hanya taga Mota ta tsaya gabanta wanda ko ba'a fad'i mata ba tasan haisam ne aciki, a hankali glass d'in ya sauka fuskarshi ta bayyana slowly ya juya ya kalleta itama idonta na akanshi duk tayi kalar rashin gaskiya murya na d'an rawa tace mashi ina kwana, shiru kaman bazai amsa ba sai kuma taji yace "bana amsa gaisuwan maikarya" waro ido tay jin abunda yace ya jinjina mata kai kamar zata yi kuka tace "to ai ban yin k'arya yanzu" d'an ta6e baki yay kafin yace "ni ai kinyi man saboda kin raina ni ko?" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a idanunta har sun kawo ruwa ganin yanata kallonta yasa tace "to karyan mi nayi maka?" da kai yay mata alamar ta shigo cikin Motan jikinta sukuku ta zagaya ta bud'e Motan ta shiga, kwantar da kanshi yay jikin headrest ya d'an juya yana kallonta ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta, "The other day bana baki hakuri ba kuma kin nuna kin hakuri miyasa kika daina zuwa?" taji ya fad'a, d'agowa tayi ta kalleshi kafin murya na rawa ta fara Magana "To ai ita wannan fa bata son ina zuwan nasan innaje data ganni sai ta karamin abunda tayi man kuma ko rannan data kada ni k'asa tace wai na taka mata k'afa wllh ni ban taka ta ba kawae bata sona ne shiyasa na daina zuwa" tana kai Maganar kwalla suka zubo mata sharrr tasa bayan hannunta ta goge, still idonshi akanta yace "bana gaya maki halinta ne hakan ba so u shouldn't mind her shit ki rabu da ita kuma a hakan zamu rayu a taren daga d'an abu har kin sare" da sauri ta kalleshi yace "ko ba ke kika ce haka ba?" ya d'age mata gira ta tura mashi baki yay murmushin gefe kafin yace "tunda kin zama matsoraciya ran Monday zasu tafi sai kici gaba da zuwa ko?" tana tura baki tace "ai ni ba tsoranta nike ji ba wllh don ko fad'a mukayi da ita bazata iya man komae ba kawai don ka hanani fad'a ne kuma banson inyi mata abu aga nayi mata rashin kunya kuma nima kamar yar'uwata na d'auketa tunda yar uwarkace" dan bud'e ido yay yana Murmushi jin tayi Maganar hankali tace "ko ba kace ni k'anwarka bace" still da Murmushin yace "Yeah sis d'ina ce Coward" cike da shagwa6a ta d'an jujjuya kai tana Fad'in"Wayyo Ya Handsome bana fad'i maka dalili ba wllh ni ba Matsoraciya bace" dariya yayi har hakoransa suka bayyana acikin ranshi kuma yaji dad'in abunda tayi, ganinta sanye da Uniform yasashi tambayar ta fara zuwa Skul ne tace a'a Registration zataje yi jiya sunje basu samu yi ba saboda akwae Mutane da yawa kai ya jinjina ya fara kokarin tashin Motar tace kaita zaiyi ya d'aga mata kai tace "to amman fa sai naje Kofar Marusa" ba tare daya kalleta ba ya tambayi abunda zata je yi, "Wai sai an siyo fatanya da tsintsiya in za'ai registration d'in ni sai jiya nasani" kai ya d'aga suka fara tafiya saida suka dauki Haulat kafin suka wuce, Kopar Marusan ya kaisu ya siya masu duk abubuwan dama itama Haulat d'in bata siyan ba yau sukai da Fatun dama zasu biya su siya kafin su wuce, sunata hira abunsu shi da Fatun ita dae Haulat iyakarta Murmushi sai in kuma Fatun ta sakota sannan ta tanka har suka iso Senior section d'in Makarantarsu ya ajesu a gaban Admin ya bata kudi da tak'i amsa wai ai suna da kud'i gashi kuma shi ya siya masu abubuwan saida yace ta rainashi ko sannan ta amsa, cikin sa'a yau suka yi suka koma gida da wuri tayi duk abunda zata yi na aikin gida tayo wanka taci gayun juma'a da fitted gown dinta ta atampa tunda ta gama shiryawar take ta wasi wasi aranta na taje gidan Hajiya ko kar ta je k'arshe dai bayan an gama sallar Juma'a ta yanke zuwa ko don ta nuna ma Haisam d'in ba tsoron Farha take ba kaman yadda yace, Suna zaune gaba d'ayansu harda Haisam saman dining table suna cin abinci kowa ya dau wanka sunci gayun Juma'a ta shigo cikin Falon da Sallama gaba daya suka kalleta ai su twins na ganinta suka saukko daga kan kujerun da suke suka nufota da gudu suna mata Oyoyo duk suka k'ank'ameta ta kamasu tana dariya su Jidderh da Nameer nata Murmushi shidae Haisam tunda ta shigon ya d'ago ya kalleta ya maida kan yana ci gaba da cin abincinshi, janta su twins sukae suka ce tazo suci abinci tana ce masu ta koshi amman suka ki kyaleta har saida ta bisu dining area din ta ja ta tsaya gefe Hajiya ta kalleta tace "Manyan gari sai yau ake ganinki" Murmushi kawae tayi ta gaidata kafin ta gaida sauran duk suka amsa mata fuska sake ba kaman Nameer sai faman sakar mata kayataccen murmushi yake, Hajiya tace ta zauna to itama taci Abincin tana niyyar yin Magana Haisam ya d'ago suka had'a ido ganin kallon da yake mata harda d'an satar kallon Farha da tunda Fatun ta shigo ta wani sha kunu ta duk'ar da kai bata kara kallonta ba yasa ta fahimci abunda yake nufi wato tsoron farhar take hakan yasa taja kujera kusa da Jidderh ta zauna Hajiya ta k'walama Saude kira bayan ta fito tace tayi serving Fatun aikuwa hakan ba k'aramin k'ara ma Farha bakin ciki yay ba a cikin Zuciya sai kace wata mai galihu a gidan harda sawa ayi serving nata, gaisawa sukai da Sauden kafin ta tambayeta abunda zata zuba mata ta fad'i mata tace ba mai yawa ba taci abinci a gida, bayan ta gama tace mata aci Lafiya su twins suka ce ta zuba masu drink, a nutse ta fara cin Abincin tana yi tana satar kallon Haisam duk abunda take akan idon Farha kasa jurewa tayi don zuciyarta har wani boiling take tsabar bakin ciki ta mik'e zata bar wurin suka had'a ido da Fatun tay mata wani kallo mai kaman harara aikuwa ba zato ba tsammani Fatun ta rama kafin ta maida idonta akan abincin gabanta wani uban tsoki ta ja tana niyyar wucewa ta ture Cup din lemu da hannunta ya zube kasa tay gaba abunta duk suka kalleta saidae gaba d'aya sunyi tunanin zubewar lemun ne yasa taja tsokin banda Haisam da duk abunda suke yana gani duk da basu yake kallo ba, girgiza kai kawae Hajiya tayi suka cigaba da cin abincinsu, bayan sun gama gaba daya Falo suka koma suka ci gaba da yin hira banda Haisam da sai ta kama yake sa masu baki yadda suke hiran da Fatuu sai kace sun dad'e da sanin juna saida akayi sallar la'asar suka tashi Mazan suka nufi Masallaci ita kuma Fatuu ta nufi d'akin Saude Jidderh na cewa tazo suje d'akinsu suyi sallan tace zata yi acan ba matsala, tana gama sallar ta fito ta nufi waje anan ta hangi Haisam ya dawo daga Masallaci yana nufar part dinshi ta tsaidashi ta hanyar kwala mashi kira, tana Murmushi ta nufeshi idonshi akanta, "Yanzu ka yadda ba tsoronta nike ba ko?" ta fad'a tana d'age ido harda ruk'e kugu da hannu guda, d'an Murmushin gefe yay kafin ya d'aga mata kai dama yana ganinta yasan saboda Maganar da yayi matanne tazo, tare suka nufi part d'inshi bada jimawa ba suka dawo tana goye da jakarshi suka nufi parking space ya haye bike bayan ya fiddo shi ta mik'a mashi jakar tana d'aga mashi hannu yaja ya fuce itama ta nufi gida. Ranar Monday bayan sallar La'asar ta shigo gidan yi masu Jidderh bankwana jikinta sanye da Uniform d'in islamiyya, tana shiga ta hangosu tsaye gaban parking space Haisam na kokarin fiddo mota don kaisu Airport, da Murmushi ta nufesu su twins na ganinta suka kamata suna fadin "Sis Fatuu yaushe zaki zo gidanmu" dariya tayi tace "karku damu ina nan zan zo" d'agowa tayi ta kalli Nameer dake ta faman sakar mata Murmushi itama Murmushin take mashi yakai hannu yaja kumatunta yace "Yar fillo sai wani lokacin ko" yar harararsa tayi kafin ta d'aga mashi kai yace "Don nasan baza'ayi man aure ba yanzu da ina komawa zance ma Dad nifa nayi mata kinga sai kawai in aureki ki koma Abuja" wani kallo tayi mashi su Jidderh da twins suka sa dariya yace "Yess ko bazaki aure ni ba?" kafin ta bashi amsa Hajiya ta nufosu tana gyara mayafinta zata yi masu rakiya Saude na biye da ita ta janyo trolley duk suka juya suka kalleta daidai lokacin Haisam ya gama fitowa da Motar ya sauke glass yace su taho su tafi Farha ce ta fara shiga dama duk abun nan tana gefe tasa earpiece ko kallon inda suke batayi ba, Nameer ne ya zauna agaba sai Hajiya da jidderh a baya suka rike su twins a jikinsu, Hannu Fatuu da Saude suka d'aga suna yi masu bye bye suma suka sauke glass suna yi masu yaja Motar suka tunkari gate su Officer na masu Allah ya kiyaye suka fuce, tun akan hanyarta ta zuwa islamiyyar ta rink'a jin kewarsu kamarsu dawo tana tunawa kuma da Farha a fili tace "Dama wannan mai idanun magen kad'ai ta tafi banda su" tana ta tuna abubuwan da suka faru tsakaninsu har ta isa islamiyyar ta shige. Rayuwa ta koma ma Fatuu kamar da bayan tafiyar tasu, taci gaba da zuwa gidan hajiya kaman yadda ta saba. Bayan wani lokaci Da Safe Misalin karfe 7 da rabi Motar Haisam ta fito daga cikin gidan don tafiya aiki kamar ko yaushe, yana hawa hanya wata yarinya ta fara d'aga mashi hannu alamar ya tsaya daga d'ayan bangaren, a hankali ya tsaida Motar bayan ya d'an wuceta kad'an tana ganin ya tsayan ta nufoshi da sauri ta tsaya bakin kopar sai zare ido take don bata hangen wanda ke ciki, Slowly glass d'in kopar ya fara sauka tana yin arba da fuskar Haisam din ta washe mashi baki tana dariya, bin ta da kallo yay ya kasa fahimtar wacece duk da yana ganin kaman ya ta6a ganin face dinta katseshi tay da fad'in "Yalla6ai ina kwana" kai ya daga alamar amsawa taci gaba da cewa "Yalla6ai baka ganeni ba ko?" nan ma kan ya daga mata tace "Jamila ce wadda ka ta6a ba kudi lokacin da ka ganmu muna fad'a da wata har ta fasa man bokiti" sai lokacin ya ganeta taci gaba "ai tun lokacin dana kai ma innata kud'in washegari ta bani awara mai yawa in kawo maka amman dana zo sai masu tsaron gate din suka hana ni shiga har ce masu nayi to su barni inje wurin Hajiyan amman suka hanani na basu awaran su baka nan ma suka ki amsa saidae na maida ma innata, kwanaki can ma na ganka ka shige na biyoka in gaidaka amman suka hanani har wani yace in ban tafi ba zai har6e man kafafuna shiyasa na tafi ban kuma zuwa gidan ba" jinjina mata kai yay da d'an Murmushi ita kuwa sai faman washe baki take kamar wadda akai ma albishir d'in Aljanna, "Bakya zuwa Skul ne" ya tambaya ganinta rungume da bokiti da alamun tallan take, da sauri tace "da ina zuwa amman yanzu na daina" still idonshi na kanta ya tambayeta miyasa ta daina zuwan cikin karewar murya ta fara mashi bayani "Babana ne ya kwanta jinya kuma ance sai anyi mashi aiki gashi bamu da kud'in, gidan da muke zaune ma an tada mu don Alhaji Sanin ya sayar da gidan amman yana da wani fili a gaban gidan shine yasa akayi mana d'aki guda biyu da kwano irin wanda ake rufin sama to yanzu anan muke kuma shi baban nawa bai iya komae dole sai munyi tallan ake samun kudin da zamu ci abinci a d'an kuma siya mashi magani tunda ba'a samu anyi mashi aikin ba shiyasa innata tace in hakura da makarantar zuwa wani lokaci in inada rabo don tasan ina son karatun" tana k'arasawa kwalla suka zubo mata tayi saurin sa gefen hijab d'inta ta goge don karfin hali kuma taci gaba da yi mashi dariyar, shiru kawae yay yana juya Maganarta acikin ranshi don ba k'aramin ta6a mashi zuciya tay ba, ba kamar da yaji inda suke rayuwa wai a dakin da akayi da zinc taya Mutum zaiyi rayuwa cikin irin wannan abun da ke mugun d'aukar zafi in rana tayi, "Zanje aiki ne ina makara, Allah ya bashi lafiya" ya fad'a da sanyayyar muryarshi, amsa mashi tayi da Amin kafin da sauri ta d'ago da bokitin tallan data ajiye a kasa tace "Yalla6ai bari in zuba maka kosai" da sauri ya girgiza mata kai tace "Don Allah Yalla6ai ka amsa nasan in na gaya ma innata zata ji dad'i sosae don lokacin data ban awara na kai maka bata ji dadi ba da ba'a samu baka ba" shiru ya d'anyi tace ta zuba mashi ya d'aga mata kai alamar eh kafin yace kad'an zata zuba, aikuwa cike da farinciki ta duk'a ta zubo mashi saida ta cika farar leda ta daura mashi yaji daban ta saka aciki sannan ta d'ago ta mik'a mashi ya mik'o hannu ya amsa da Dan Murmushi ya furta "Nagode" ta jinjina mashi kai still da dariya a fuskarta daga haka glass d'in Motar ya d'aga yajata ita kuwa Jamilar cike da murna ta sunkuci bokitin ta shige lungun gidansu don taje ta fad'awa innarsu, saida ya tsaya ya d'auki Fatuu kamar kullum suka biya suka d'auki haulat kafin suka wuce bayan ya ajesu ya basu kudin break ya had'a masu da k'osan don shi bai cin kosai kawae ya amsa ne don ya fahimci zata ji dadi in yayi hakan, Yana dawowa daga aiki da yamma ko part d'inshi bai wuce ba ya nufi na Hajiya don tunda yaje wurin aikin Maganganun Jamila sun tsaya masa arai, da sallama ya shiga lokacin Hajiya na zaune tana duba wani littafin addini don dama tafi ba karatun littattafan da suka shafi addini karfi fiye da karance karancen jaridu, kusa da ita yaje ya zauna yay mata sannu da gida don asaman 3 seater take zaune, tunda ya zauna take binshi da ido don ta lura kaman akwae abunda ke damunshi ba kamar da ya wuto part d'inta bai tafi nashi yay wanka ya shirya ba kaman yadda ya saba, "Any problem?" ta tambaya cike da kulawa, shiru ya danyi kafin ya gyara zama ya fara bata labarin Jamila da halin da suke ciki, lokacin daya gama da mamaki tace "Yanzu har akwae masu irin wannan matsalar a unguwar nan amman ban sani ba, ai yakamata ace sunzo neman taimako tunda mutum ba lallai ya sani ba" ta k'arasa da alamun damuwa akan fuskarta, "Zai iya yuwuwa sunzo basu samu ganinki ba" jinjina kai tayi alamar gasgata zancenshi kafin tace "aikuwa zanyi ma su Officer Magana indae mutum ya nuna yana cikin matsala su rink'a bari yana samun ganin wani inda rabo sai kaga an taimaka" Haisam yace "Better" idonta akanshi tace "to amman kai ya akai kasan yarinyar ma?" gyara zamanshi yay kafin ya bata labarin itace yarinyar daya raba Fad'a da Zarah ranar daya fara ganinta,jinjina kai tayi tace "Allah gwanin hikima, shiyasa akeso duk wanda Allah ya had'a mutum dashi yay kokari yaga abun arziki ya shiga tsakani haka kuma in za'a rabu to ai rabuwar arziki, mutane sukan shigo rayuwarmu da yuwuwar akwae rabonmu a tare dasu ko kuma rabonsu a tare damu" jinjina mata kai yay alamar gasgata Maganarta taci gaba "Allah ubangiji ya bamu ikon taimakama junanmu a koda yaushe" a hankali ya furta "Amin" idonta akanshi tace "Yanzu ya kake ganin za'ai to?" dan watsa hannu guda yay yace "Kiyi duk abunda ya dace game da Lafiyar Dad din nata and asama masu inda zasu zauna sannan ita yarinyar tabar talla ta koma school sai aba Mom din nata enough Capital da zata yi business ko a gida" yana gama Maganar yasa hannu acikin Aljihun suit dinsa ya fito da Wallet dinshi Card ya ciro ya aje ma Hajiyar akan jikinta kafin ya maida Wallet d'in, Hajiya dake binshi da ido tace "kana nufin duk zaka yi wannan?" kai ya d'aga yace "yea a fara abunda ya dace in akwae bukatar cheque let me know", wani kallo tayi mashi kaman harara tace "to baka isa ka wawushe ladan kai kadae ba duk da kai ka kawo aikin ladan nima dole zanyi wani abu aciki" dan Murmushin gefe yayi kawae ya fara kokarin mikewa tace "ka tsaya to ka ci abinci mana sai ka wuce gaba d'aya ko" dakatawa yay yace mata yana son yaje yay wanka ne ya rage kayan jikinshi, hannu ta kai ta fara kokarin cire mashi rigar saman tana Fad'in "anan ma ai zaka iya rage kayan" bayan ta cire ta k'walama Saude kira tace ta kawo mashi abinci. Washegari da Safe Hajiya da Tk suka je gidansu Jamila sam bai masu wuyar ganewa ba don Haisam ya fad'i mata jikin gidan Alhaji sani karofi filin da suke yake, lokacin da sukaje ba k'aramin tausaya masu tayi ba ganin halin da suke ciki ga Mahaifinnasu na jin jiki ba um ba umum don lalurar kwalwa yake fama da ita cikin nuna jimami Hajiya tace ma innar tasu miyasa bazasu zo su nemi taimako ba sai su barshi kwance a gida haka tace ma Hajiyar wllh sau wurin ukku tana zuwa bata samun ganinta shiyasa kawae sai ta hakuri da tunanin Alhaji sani zai taimaka masu tunda yasan da Maganar jinyar tashi kuma yace zai turo kud'in ai masa aikin don basu k'asar saidae har yanzu shiru amman dae ya turo masu wani abu saidae bazasu isa ayi aikin ba karshe ma abinci suka ci dasu, anan Hajiya ta tambayi inane za'ai masa aikin tace a Kano ne kuma kud'in aikin Miliyan 1 da dubu dari takwas ne Hajiyar tace ba wani abu su fara shirin kaishi aikin saboda tsabar farinciki innarsu Jamilan rushe ma Hajiya tayi da kuka ta kama kafafunta tana ta godiya da Addu'oi har saida kwalla suka taru a idanun Hajiyar ganin kan wasu yan kudi wanda ita a wurinta ba wani abu bane yasata farinciki har haka, (Allah Ubangiji ka bamu ikon sanya farinciki a zukatan junanmu Amin). Bayan sati biyu Cikin Nasara anyi mashi aikin Tk ne ya jagoranci tafiya kaishi aikin yanzu yana cigaba da shan Magani a sabon gidansu da Haisam ya siya masu wanda ke acan k'asan unguwar, gidan d'an madaidaici ne yana da d'akuna guda ukku biyu a jere sai daya a farkon shigowa yana da toilet aciki anan mahaifin nasu ke jinya akwae Kitchen mai d'an girma da toilet d'in tsakar gida, bawan Allah har yanzu bai fara yin Magana ba sai dae duk lokacin da aka ambaci su Hajiya sai yay ta zubar da hawaye wanda da gani na farinciki ne, Har gidan Haisam yazo ya dubashi a ranar innar Jamila ta fara ganinshi kuma shine wanda ta ta6a cema Jamila ta gani a gidan Hajiyar lokacin da suka je kar6ar tallafi, sosae tayi mashi godiya da Addu'oi harda kukanta sha6e sha6e shidae kai kawae yake d'aga mata yana fad'in ba wani abu, Jamila sai washe baki take tana farincikin ganinshi a gidannasu saida innar tasu ta tattaro yaran gaba d'aya tasa sukai mashi godiya kafin ya tafi. Fatuu taci gaba da zuwa Makaranta tana a Science Class wato s.s one Sci A ita da Haulat farko ba class d'aya aka kaisu ba ita haulat Sci C aka kaita da taimakon Discipline master dinsu na Junior da Fatun taje tayi ma Magana yasa aka maido Haulat din Class dinsu. AFTER 2 YEARS............... ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIJAR, KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCI💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621 Akwai zafafan kayan mata masu matukar kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah su isa har inda kike ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari. Muna kawo kalolin ingantattun kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-Maganin sanyi 2-Maganin gyaran nono 3-Maganin hips 4-Akwai gumba kala kala 5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa 6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni'ima da jimawa ajiki yana aiki 7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu 8-Akwai jigidar sirri kala kala Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇 1-dahuwar kaza 2-yan shila 3-ciccibi Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso ta bini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621, ALLAH YAYI MAKI KIMA DA DARAJA AMATSAYINKI NA MACE👰,KADA KI WOFINTAR DA KANKI A WURIN MIJI SABODA RASHIN GYARA KAI, BURIN MAMAN HAIDAR KO WACE MACE TA ZAMA TAURARUWA⭐YAR LELE AGUN MIJINTA😍 SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI🤝 *💖A SANADIN MAKWABTAKA💖* _*(Love and Destiny)*_ _*BY ZAINAB LALUH📲*_ ~(Oumm Imam)~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* 7️⃣2️⃣ Bayan shekara biyu Lokaci ya shude shak'uwa sosae ta shiga tsakanin Haisam da Fatuu a wannan lokacin ya zama tamkar dan uwanta na jini da yawan Mutane ma kallon da suke masu kenan wad'anda basu san ainihin tsakaninsu ba, a babbar sallar data wuce ne ta had'u da Mahaifiyar Haisam suka gaisa a gidan Hajiya lokacin sunzo salla su Jidderh suka nuna mata ita dama tana ta jin Labarinta a wurinsu, yanzu shekararta sha bakwae zuwa sha takwas har sun shiga ss 3 an bata muk'amin Senior prefect wato SP, a islamiyya kuma sunyi sauka an had'a masu gagarumar walima har Haisam sai da yaje wurin taron walimar da akayi a harabar Makarantarsu ya kuma bada gudunmawar kudi masu yawa yanzu a ajin hadda suke, gaba d'aya dawainiyarta Haisam ne ke yi mata ta canja sosae ta koma kalar yaran hutu gashi ta k'ara girma saidae bata da tsawo sosae tsaka tsakiyace baza'a kirata gajera ba ba kuma za'a kirata da mai tsawo ba, a bangaren jiki kuwa abun saidae ace Tubarkallah don tana da k'ira gashi hasashen da gwaggo tayi akanta ya tabbata sak jikin Mahaifiyarta ta d'aukko harma ta zarta ta haka gwaggon ke fad'a don kuwa in ka kalli kafadun Fatuu bazaka ta6a cewa k'ugun dake ajikinta nata bane don ya bud'e sosae har ta cikin Uniform d'inta ana gani haka mazaunanta ma fam suke hakan yasa Sauran Students ke kiranta da Fatuu Bum Bum, har Malamai ma sun san da irin k'irar dake gareta don akwae wata rana zasu yi Cultural dance a club d'insu na English tayi shigar fulani lokacin da suka shigo cikin Assembly hall ita da wad'anda sukayi shigan fulanin gabadaya hankalin malamai da d'aliban dake cikin Hall d'in ya dawo kanta nan da nan malamai mata suka fara Maganar rashin dacewar kasancewarta haka don kayan sun fito mata da shape sosae, jin hakan yasa Formistress d'insu Malama Lubabatu ta kirata bayan sun fita waje tace mata tasa kallabinta ta d'aura a kugu sai ta nemi hula tasa Fatun tace ai k'arami ne sai lokacin ta lura da bai rufe mata kai gaba daya ba tace ta jirata anan tana zuwa ta koma cikin Hall d'in ta samo mata aron farin gyalen wata Malama ta kawo mata ta rufe k'ugun. Zaune suke cikin Class kowa da abunda yake wasu na hira wasu na rubutu da yake free period ce malamin da ke garesu ya sanar bazai samu shigowa ba, Fatuu na zaune saman seat d'insu dake a farkon layin karshe na ajin ta juya ma allo baya suna hira da wata kawarsu mai suna Fiddausy dake zaune ita kad'ai a kujerarsu sauran wad'anda suke zaman sun tafi yawo wani seat d'in, can tace ma Fatun wai mi Haulat keyi ne ta duk'ar da kanta tun d'azun bata d'ago ba, juyawa Fatun tayi ta kalli Haulat dake gefenta can k'arshen bango ta duk'e kafin ta juya ta kalli Fiddausyn ta d'an ta6e baki tace "kema ai kinsan mi zaisa ta duk'e haka" yar dariya tayi tace "halan karatun Novel take" Fatuu tace "shine fa ta maida abu kamar ibada in batayi ba bata jin dadi Allah yasa ma in tayi auren ta rink'a kula da gidanta" "Wllh baki sani bane karatunne shiga rai gareshi in kika saba da wuya ki iya bari" d'an ta6e baki Fatun ta k'ara yi tace "tunda fa ana rubuta iskanci ba dole a rink'a jin dadinshi ba" waro ido Fiddausy tayi tace "ke waya gaya maki iskanci ake rubutawa?" "Haka naji ana fad'i nasan kuma shiyasa gwaggo ma ta hana ni karanta irinsu duk da dama ko bata hana ba nima bayi zanyi ba don banda lokacinshi ta karatuna nike bata shirme ba" girgiza kai Fiddausy tayi "Wllh ba yadda kike zato bane duk da ba k'arya bane Maganar gaskia akwae wanda ba komae ciki sai tsantsar batsa amman kuma akwae masu tsafta wad'anda in kana karantawa zaka k'aru sosae don ana fadakarwa da ilimantarwa ta fannin addini uwa uba kuma zaka koyi abubuwa masu mahimmanci da suka shafi rayuwa ba kamar gamu mata misali zamantakewar aure da dai sauransu wasu har abinci in suka sa anyi acikin littafi zaki ga sunyi bayanin yadda ake yi in kamar sun san ba irin wanda aka saba yi bane, ni kinga ina yin karatun Novel kuma ko Mamarmu ta sani itama tana yi kuma wani lokacin in ta karanta littafi taga yayi ma'ana da kanta take turo man tace in karanta sam bana karanta mara ma'ana don asarar lokaci ne wllh" still ta6e baki Fatuu tayi ta gyad'a mata kai, mik'ewa Fiddausy tayi tace "bari inje inyi Fitsari tun d'azun nike jinshi ina matsewa kar ya zubo man a wando in shiga ukku anma ce fa ba'a son rike fitsari don lalura yake sawa" har zata fita daga cikin seat d'in ta juyo tace ma Fatun bazata rakata ba, "Ke dai jeki, yadda kurata tayi kuka yanzu da an ganni waje sai ace nayi laifi, bari in baki ma ki siyo man aya" tayi Maganar tana kokarin curo kud'in acikin Aljihun wandon Uniform d'inta, naira dari ta fiddo ta bata tace ta siyo mata ta Hamsin ta d'auki sauran Hamsin d'in don yanzu Fatuu zama da Haisam ta koyi yin kyauta sosae sam abunta bai sha mata kai ba daka nuna kana son wani abu nata sai ta baka ko kuma kazo aro sai tace ta baka kyauta hakan kuma ba k'aramin farinjini ya k'ara mata ba kowa sonta yake tana matuk'ar burge mutane, Godiya Fiddausyn tayi mata bayan ta amshi kud'in ta tafi, juyawa tayi ta koma tana Facing allo ta duk'a a hankali ba tare da Haulat ta ankare ba taji ta fige yar wayarta da take karatun da ita, a wani firgice ta d'ago koda taga Fatuu ce sai ta wurga mata harara tace "Don Allah ki bani kar ki fitar man inda nike" itama hararar tata tayi tace bazata bata ba, magiya ta hau yi mata Fatun tace "to zan baki amman sai naga abunda kike karantawa in kuma baki bari ba Wllh bazan bari kici gaba da yin karatun ba" sanin halinta yasa tace to ta tsaya ta duba, kallon screen d'in wayar tayi ta fara karanta inda Haulat d'in take, suffar jarumin littafin ake bayyanawa bayan ta gama karantawa ta d'ago ta kalli Haulat tace "Waye wannan kaman Aljani?" dariya haulat d'in tayi tace "Mijin Novel kenan" "Mijin Novel haka sunanshi yake?" "A'a haka dae ake cewa wai ba'a iya samunsu a zahiri saboda kyaun da ake sawa suna dashi" da mamaki Fatuu ta k'ara duba wurin kafin tace "wannan ne ba'a iya samu a zahiri?" kai haulat ta d'aga mata "haka ake cewa" yar harara ta wurga mata kafin tace "to wllh ko ni nasan mai irin wannan suffar za'a wani ce ba'a samun irinshi a zahiri" haulat na dariya tace "nima nasan wani mai irin suffar amman ke wanene wanda kika sani mai wannan kamannin?" tace "yo Ya Handsome mana ke baki ga sak suffarshi ce aka bayyana ba" "Wllh nima ina karantawa shi ya fad'o man a rai" d'an ta6e baki fatuu tayi tace "to ke miye na zama kita karanta kamanin wani Namiji bayan an bayar dake" "To in banda abunki waya k'i abu mai kyau kuma dae nasan ba samun irinshi zanyi ba, ke dai ai kinji dad'i kinsamu mijin Novel" ta k'arasa tana dariya, da mamaki fatuu tace "ni kuma mukai dake ina da saurayi irinshi balle har ki kirashi da mijina" tayi Maganar tana harararta, "Ina nufin wanda yanzu kika ce yana da irin sufar da aka fad'i" waro ido Fatuu tayi harda d'an juyawa gefe wai taga ba wanda yaji abunda haulat d'in tace don kowa kallon yayanta yake mashi ido waje tace "ke, nina gaya maki Ya Handsome saurayi na ne yaushe mukai hakan dake?" wata dariya haulat tayi tace "habawa yan mata an gaya maki a banza nike karatun Novel, ai ko yaro yaji labarin tsakaninki dashi zai fahimci son ki yake shiyasa yake maki duk abubuwan da yake maki kawae dai nasan k'ilan lokacin da zai bayyana maki hakan baiyi bane shiyasa bai fito ya nuna maki ba amman ina nan dake zaki ce na gaya maki" wani irin kallo Fatuu ke binta dashi da alama ta kashe mata bakinta don ita tunda take da Haisam bata ta6a sawa aranta wai sonta yake ba can tace "amman dai ai kin fi kowa sanin halinshi in don abubuwan da yake man ne ai ba ni kadai yake ma abun alkhairi ba ko", "tabbas nasan hakan amman fa ba wanda yake ma kalan naki don ke alkhairin da yake maki special ne, haba Fatuu kiyi tunani mana tun farkon haduwarku abunda ya had'a ku har kawo yanzu gaba daya ya canja rayuwarki dubi uwar dawainiyar da yake dake, ya dauki nauyin ki gaba daya komae shi yake maki, yasa an gyara maku gida an jawo maku ruwa daga gidansu ya siya maku kayan kallo harda Solar aka sa maku ke kanki yanzu d'akinki carpet ne, gaba daya kayan gadonki an gyarasu sun zama na yan gayu don ma nasan saboda na mahaifiyarki ne yasa bai canja maki wasu ba, ji d'ayan d'akin nan da aka idasa gininshi yadda ya gyara maku shi ya zama hadaddan falo, da dai sauran abubuwa da yake maki har ni fa dana shafe ki yana mana alkhairi sosae, yanzu duk sai kice hakanan yake maki wannan d'awainiyar, Come to think of it mana" kasak'e Fatuu tayi tana kallonta don jin zancen take wani iri sam ta kasa yarda da Maganar Haulat d'in ta wani bangaren kuma zuciyarta nason gasgata hakan, "Ni ina tunanin bari yayi sai kin gama Makaranta sannan ya bayyana yana sonki shiyasa yake ta kulawa da abunshi" tayi Maganar tana dariya, ganin Fatun tak'i cewa komae sai kallonta take taci gaba da cewa "ko baki sonshi ne" ta d'age mata gira sai lokacin tace "amman ai yasan ni karatu nike son yi ni gaskiya ban tunanin hakan" ta k'arasa Maganar tana tura baki, Haulat tace "Uhm su karatu manya, ke yanzu in yace yana son zai aureki sai ki k'i yarda saboda wani karatu can kin kuwa san irin tsadar da maza irin Yaya Haisam ke yi in ma an samesu kenan, ke baki ganin yadda kowace mace ke sonshi tun da can ma, ai wllh kar ki sake ki bari damar nan ta wuce ki in ba haka ba zaki mugun dana sani ne, yana cewa yana son aureki ki wuff kice kin amince ya aureki kuyi tafiyarku k'asan da zai koma kinga acan cikin sauk'i zaki karatunki ga kuma mijinki a gefe inyee" bakin Fatuu fa ya mutu murus sai zare ido take ga zuciyarta sai wani irin bugu take mata tana fasalto mata face d'in Haisam yana sakin kayataccen Murmushinshi, "Sai wani faman bina kike da ido kema fa nasan kina son shi...." da sauri Fatuu tace "yaushe mukai haka dake?" tace "Uhm dama ai ke bazaki gane hakan ba tunda yana tare dake kullum, da zaki rasa shi misali kiga wata tayi wuff dashi a lokacinne zaki fahimci kina son shi" ajiyar zuciya Fatun tayi kafin tace a sanyaye don duk jinta take wani iri "amman kina ganin da gaske Ya Handsome na sona kuma zai aure ni?" "Shakka babu kema don baki karatun Novel ne da da kanki zaki gane haka Mrs Haisam Zakee, wai zanso inga ranar nan Allah yasa kafin inyi aure ne, ke wllh koda nayi aure ne sai nazo don dai nan da Niger ai ba wani abu bane mu da ke k'irjin biki, amman fa zanyi missing dinki sosae in kuka tafi kasan wajen nan ta wani bangaren kuma zanso hakan tunda cigaban kine yar'uwata, wayaga su Fatuu Amarya kuma a gun Handsome wai nasan dai zaisha hauka don ma dai kin d'an natsu yanzu, wata tara ki san6alo mana twins tunda naga suna da gadonsu, kai Ya Allah, har na hango kyawun da yaran zasu yi wllh Madarar kyau" da sauri Fatuu ta kai hannu ta bugi Haulat d'in tace "Wayyo Haulat stop it pls kinsa na fara imagining abubuwa wllh" tai Maganar kaman zatayi kuka Haulat na dariya tace "imagining din mi keda baki san kuna son juna bama, ni kinga bani wayata inci gaba da abunda nafi auki" tay Maganar tana mik'a mata hannu fatun ta bata wayar ta duk'a tana mata dariya taci gaba da karatunta. Tunda suka yi Maganar take jin wani bak'on yanayi a tare da ita ga suffar haisam da zuciyarta keta tariyo mata, mik'ewa tayi ta nufi hanyar fita daga Class d'in Haulat ta d'ago ta kalleta kafin ta girgiza kai ta koma taci gaba da abunda take, a saman barandar class d'in ta zauna ta jinginar da kanta jikin katangar data rufe gaban Office d'in dake tsakiyan ajin nasu da d'ayan ajin wato Sci B, shiru tayi tana ta tariyo rayuwarsu ta baya ita da Haisam tun daga farkon haduwarsu har kawo yanzu, sai faman sakin Murmushi take, jin shiru Fatun bata dawo ba yasa Haulat biyo sahunta nan ta ganta zaune yadda take da mamaki ta k'arasa wurinta tace "ni duk nayi tunanin fitsari kika je ashe da kina nan kin fad'a kogin tunanin sahibinki" ta k'arasa tana kokarin zama, da Murmushi Fatuu ta juyo ta kalleta tace "wani abu nike ji Haulat wanda ban ta6a ji ba game da Ya Haisam sai yanzu da muka yi Maganar nan dake" Haulat na dariya tace "So kenan yan mata, ai na fad'a maki wllh kina sonshi kawae dae baki san da hakan bane saboda baki san miye son ba to shima nasan hakan take a wurinshi tunda shima ba soyayyar yake ba balle yasan micece ita" gyad'a kai kawae Fatun tayi daga haka suka ci gaba da hiran Haisam d'in har Malamin da zai shiga yazo sannan suka tashi suka shiga Ajin. Misalin karfe 2 saura kwata aka tashi saidae basu samu fitowa da wuri ba saboda malamin dake da period d'in karshe ya rike su saida suka gama kwafar rubutu sannan, atare suka fito bayan sun gama zasu nufi gate kamar ance Haulat ta kalli gefenta ta hango Motar haisam yazo daukarsu dama wani lokacin in yasamu time ya kan zo ya daukesu amman wurin zuwa kullum shi ke kaisu, da sauri Haulat ta ta6o kafad'ar Fatuu tace "ke ga mijinki yazo d'aukarmu da alama yaji firar da mukayi a jikinshi" da sauri Fatuu ta juyo ta kalli inda Haulat d'in ke nuna mata kafin ta kalleta suka had'a ido suka sakar ma juna murmushi, lokacin da suka k'arasa bakin Motar hannu Fatuu tasa ta bud'e gaba haulat kuma ta bud'e baya ta shiga ganin yana waya yasa fatun yin tsaye ta dafa kopar tana ta kallonshi ba kaman yadda yake yin Maganar a nutse hakan yasata jin yanayin data rink'a ji dazun har bata san ya gama wayar ba ya kalleta ganin tanata kallonshi yasashi d'age mata gira yace "ya dae?" sam bata jishi ba har saida Haulat ta d'an d'aga murya tace Fatuu ana magana sannan ta dawo hayyacinta ta shige cikin Motar tana mashi Murmushi shima Murmushin ya mayar mata ta rufe kopar suka tafi, tunda suka hau hanya take ta faman zabga Murmushi tana juyar da kai saidae duk abunda take Haisam na lura da ita ba tare data sani ba can ya kira sunan Haulat idanunshi akan hanya ta amsa da sauri tace "Na'am Ya Haisam" yace "yau ko kun samu kudi ne a skul" d'an bud'a ido tayi cikin rashin fahimta tace bata gane ba, shiru ya d'anyi don dama sama sama yake Magana da ita can yace "naga friend dinki is in happy mood i thought ko kudi kuka samu" tana jin abunda yace tasa dariya itama Fatun kallonshi tayi tana dariya tace "ai Ya Handsome abunda na samu yau yafi karfin kudi don bai iya siyar manshi" d'age gira yay yace "really, dama akwae abunda yafi karfin kud'i yanzu" da sauri tace "eh mana baka sani ba" d'an ta6e baki yay bai ce komai ba can kuma sai taji yace "inason sanin wane abune haka" d'an juyawa tayi ta kalli Haulat suka yi dariya k'asa k'asa kafin ta kalleshi tace "sirri ne" d'an ta6e baki yay baidae ce komai ba, suna shan round about Fatuu tace "Lah Haulat kalli Baba mai ice cream gaban gidan man can shine yau yak'i kawowa makarantarmu ashe yana nan, juyawa haulat tayi tana kallon inda fatun ke nuna matan kawae sai ji sukai Haisam d'in ya tsaya kafin ya fara reverse da Motar ya tsaya saitin mai ice cream d'in yace ta bud'e ta siya ta amsa mashi da to ta juya zata bud'e kopar ta saci kallon haulat suka d'an bud'a ma juna ido suna guntse dariya, mai ice cream d'in na ganinta ya washe baki yana mata dariya tace Sannu Baba mai ice cream shine yau ka k'i kai mana ka tsaya anan" yace "wllh naje wanccan makarantar kudin ta kusa daku ne to lokaci ya k'ure ban samu na k'araso taku ba har aka koma tara" jinjina kai tayi tace abasu ya tambayi wanne tace Fan ice yace na roba tace a'a ya basu na leda zai fi dad'in sha tunda a mota suke, guda ukku ta amsa manya ta mik'a ma Haulat d'aya ta aje sauran gaban motar tana kokarin curo kud'i Haisam yace ta bud'e glove box ta d'auki 5k ta bashi tana Murmushi tace to, sosae ya shiga yi masu godiya da fatan Alkhairi bayan ta bashi suka tafi, mik'a ma Haisam d'ayan tayi ya dan kalleshi kafin ya girgiza mata kai alamar bazai sha ba cike da shagwa6a tace "pls ka amsa kaifa na amso mawa"? K'ara girgiza mata kai yay idonshi akan hanya yace ta had'a ta sha, kawae sai gani yay ta aje duka harda nata a gaban motan ta koma jikin seat tana tura baki, d'an kallonta yay ganin abunda tayi ya d'an girgiza kai da Murmushi yaci gaba da driving can bayan wani lokaci kawae sai gani tay ya kai hannu ya d'auka ya kai baki bayan ya fasa ya fara sha a hankali dama abunda yasa yace bazai sha ba saboda bai cika son shan abu a leda bane, wani kallo tay mashi kafin ta juya ta kalli Haulat ta kashe mata ido d'aya ta juyar da kai tana Murmushi, tabbas yanzu ta fara gasgata Maganar Haulat ta Haisam na sonta....... A takaice....... Tun daga wannan ranar kallon da Fatuu ke ma Haisam na yayanta ya canja ya dawo na masoyinta wanda kuma zata aura da zarar ta gama Makaranta don sosae take jinshi a ranta, ranar Juma'a bayan an sakko daga Masallaci suna zaune a falon Hajiya ita dashi hajiyar bata nan Saude kuma tana dakinta, bata je makaranta ba don anyi masu hutu wanda daga shi kuma sai gama Makarantar tana yin wanka ta taho gidan anan ma taci abincin rana don yanzu ta koma mai gida biyu har tama fi zama gidan Hajiya sai dae kuma yanzu sam Haisam bai bari tana zama a part d'inshi da taje suka gaisa in ba fita zaiyi ba sai yace suje part d'in Hajiya tun tana jin abun wani iri harma ta saba in yana aiki da laptop dinsa sai ta d'aukar mashi su tafi can yanzu ma da suke zaune aiki yake da laptop d'in ita kuma tana zaune tana kallon tv jikinta sanye da riga da skirt na atampa sun kamata ba laifi don son matsattsun kayanta na yarinta har yanzu bata daina ba kallabinta na akan kafad'arta tayi parking gashinta dake a kwance gyalenta kuma na ajiye a gefenta, tana cikin kallon aka sako irin sakon gaisuwar nan da tashar Arewa 24 ke ma garuruwa na Katsina anan suka nuno Masarautar daura tare da rijiyar kusugu mai dumbin tarihi dake garin idonta akan Tv din tace "Wllh ina son zuwa inga rijiyar nan anyi mana tarihinta a Hausa ance ma har ruwan ake d'ebo ma Mutum ya sha" shiru ya d'anyi yanata Operating laptop d'in gabanshi daya d'aura akan c-table can taji yace "ba'a kaiku excursion ba daga skul?" da sauri tace "eh an kai wasu amman mu banda mu da yake muna da yawa to sai aka raba mu gida biyu wasu suka je nijar da suka dawo ne aka tsaya dasu daura da kuma Ajiwa Dam mu kuma Kano aka kaimu, mukaje gidan zoo da gidan tarihi da kuma wani gidan fata da wurare dae da yawa, ba kasan lokacin da muka je ba farkon shigarmu s.s 3?" kai ya d'aga mata alamar eh taci gaba "sun zo sunata bamu labarin rijiyar da kuma Dam d'in sunce babban Dam ne ance masu shi ke ba Katsina ruwa" jinjina mata kai yay ta juya taci gaba da kallon, "Ki shirya within dis weekend sai in kai ki but ki fara tambayar Grandma d'inki" kaman daga sama taji Maganar da sauri ta juyo ta kalleshi daidai ya d'ago suka had'a ido tace "daurar zaka kaini?" "yea ko bakya so ne" da tsananin mamaki tace "ina so wllh,to harda Ajiwa Dam d'in zamu?" kai ya d'aga mata cike da farinciki ta fara mashi godiya sai washe baki take tana rufe fuska, da Murmushi yake kallonta kafin ya mik'e tace tafiya zai yi yace eh yana son zaije yayi shirin gym don la'asar ta kusa, jin haka yasa ta mik'e itama ta d'auki gyalenta ta d'aura saman kan ta ruke kallabin a hannu yana kokarin daukar laptop din ta nufeshi tana ya barshi ta d'auka, atare suka fito harabar gidan suka jera suna nufar part dinshi har yanzu bata ida kai kafadarshi ba suna zuwa bakin Corridor ya mik'a mata hannu alamar ta bashi laptop d'in tace bari ta kai mashi har bakin kopar shiga parlon bai ce komai ba ya wuce tabi bayanshi, yana hawa balcony ya juyo ta mika mashi tana sakar mashi Murmushi har zai juya tace "thank u Sweetheart for making me Happy always" d'an bude ido yay jin yadda tay turancin cike d kwarewa sai kuma ya jinjina mata kai ta juya ta nufi hanyar fita tana yi tana waiwayenshi don bai shiga falon ba tana kaiwa bakin kopar fita ta d'aga hannu tana yi mashi bye bye, d'an Murmushi yay ya d'aga mata hannu guda daga haka ta fuce shi kuma ya shige ciki, tana fitowa daga gidan bata nufi ko ina ba sai gidansu Haulat sauri sauri gudu gudu ta rink'a yi ta d'an d'age skirt dinta da hannu don a k'agare take ta ganta a gidan, lokacin data isa k'annenta kawae ta gani a tsakar gidan ta tambayesu ina Haulat suka ce mata tana cikin d'aki ko sallama bata yi ba ta fad'a ciki lokacin haulat d'in na kwance kan katifa tayi wankan juma'a tana karatun Novel a wayarta wani ihu Fatuu tayi ta fad'a samanta cike da farinciki da k'yar haulat ta tureta daga jikinta tana Fad'in "so kike ki kashe ni tun ban shiga d'akin mijina ba......" katseta Fatuu tayi da fad'in "Albishirinki kawata" da sauri Haulat tace "goro fari kal", "Ki tayani murna wllh ta tabbata Ya Handsome sona yake" da sauri ta yunkura ta tashi zaune cike da zak'uwa tace "ya fad'i maki ne?" girgiza mata kai tayi "a'a bai fadi man ba amman abunda zai man ya tabbatar da hakan" haulat tace "to bani in sha mana ya akai?" nan take Fatun ta kwashe komae game da inda zai kaita ta gaya mata, wata shewa haulat tayi tace "kice yawan shakatawa zaku kawae, ai k'ilan ma acan zai bayyana maki soyayyarsa fa" waro ido Fatuu tayi ta dafe bakinta da hannunta guda haulat tace "Wllh, Allah yasa ma hakane, ke ko bai furta makin ba iya hakan ma ya tabbatar da soyayyarsa gareki" ita dae Fatuu Murmushi kawae take saki duk farinciki ya lullu6eta har tafi jin dadin Maganar yana sonta fiye da inda zai kaita, hira suka ci gaba da yi yawanci duk kan soyayya ne har saurayin haulat wanda zata aura da zarar sun gama Makaranta kuma d'an uwan Mahaifiyarta ne d'an Nijar don Mahaifiyarta yar can ce ya kira har suka gaisa da Fatun, sai can gab da Magrib ta baro gidan Haulat tayo mata rakiya akan hanya take ce mata gaskiya ya kamata a tafi da ita ko don su samu photographer da zata yi masu hotuna don irin wannan fitar saida hotuna, harararta Fatuu tayi tace ba'a zuwa da ita salon ta takura masu haulat d'in tasa dariya tace wayaga sabon shiga a daidai nan suka iso inda zasu rabo suka yi sallama kowa ya tafi. Ranar Lahadi Misalin karfe goma da wasu mintuna Haisam ya parker a kopar gidansu don tun jiya ta gaya mashi gwaggon ta amince ya fad'i mata time d'in da zaizo, zuwa Amadu yay suka gaisa yace don Allah ya kira mashi Zarah yace to, bada jimawa ba ya dawo Fatun na bayanshi tayi shigan kananan kaya kaman Haisam d'in shima kananun kaya ne jikinshi amman ta d'aura bak'ar after dress asama mayafin kuma ta nada shi daga baya yayi tudu sosae kafafunta sanye da takalma masu tudu tayi kyau sosae, bud'e Motar tayi ta shiga tana Murmushi ta gaidashi fuskarshi a sake ya amsa mata kafin yaja Motar suka tafi, sama sama suke yin hira tana kuma yin kalle kallen hanya cikin awa guda da wasu yan mintuna suka isa Daura, Kofar sarki Abdurrahman suka nufa inda gidan sarki yake, sosae ya zagaya da ita gidan sarkin bayan sun je sai kalle kalle take daga baya kuma suka je inda rijiyar take tasa yay mata hotuna aka kuma dibo mata ruwan tasha shi dae bai sha ba, gidan yan uwansu dake nan ya wuce da ita har da gidan kawu Mani daya ta6a zuwa gidan Hajiya, duk inda suka je sai an tambayi wacece ita ya fad'a masu a makwabtansu take bayan anyi sallar Azahar suka bar daurar dama tun suna hanyar zuwa ta gaya mashi gwaggo tace in ba damuwa su biya su gaishe da kawunta shi6ado dake a karkarku garin Fulani ne don da wuya ka samu wanda ba bafullatani ba a kusa da garin daurar yake, ba k'aramin karramashi sukai ba lokacin da suka je don kawun yasan da labarin haisam a wurin gwaggo da duk abun alkhairin da yake masu sai faman zuwa ake gaishe shi a mutunce yake amsa ma kowa, basu wani dad'e ba suka yi sallama aka had'asu da uban dawon fura da fresh nono, wuri biyu akai masu wato na Haisam daban sai wanda Fatuu zata kaima Gwaggo, AJIWA DAM Babban Dam ne mai matukar girman gaske yana d'aya daga cikin wuraren da ake zuwa yawon bude ido a Jahar Katsina da Rijiyar kusugun da suka je, Farkon Dam din akwae masu saida kifi iri iri d'anye da soyayye akwae hanya da zaka bi kaje wurin ruwan wadda tun kana tafiya zaka fara ganin ruwan a gefen hanyar akwae Ofisoshin masu aiki a dam d'in a gefe guda, lokacin da suka isa Fatuu rudewa tayi don ba kamar irin ruwan data saba gani a garinsu bane cike da farinciki ta bud'e mota ta fito tana dariya shima Haisam din fitowa yay ya jingina da gaban Motar yana kallon ruwan, ganin tana matsawa yasashi cewa "Zarah u ave to be very careful" kai ta d'aga mashi sam fuskarta ta kasa 6oye tsantsar farincikin da take ciki wurin akwae kayatarwa sosae ga Mutane nan da suma suka zo ganin ruwan, akwae gadar karfe data bi ta cikin ruwan wadda zata kai ka har tsakiyar ruwan yadda zaka hangi ko ina mutane nata hawa suna zuwa tsakiyar ruwan, kallonshi tayi tace "nima in hau Ya Handsome?" girgiza mata kai yay alamar a'a ta marairaice tace "plssss" shiru yay yana kallonta tana ta langa6ar da kai yace taje amman ta kula cike da murna ta nufi wurin sai kuma ta tsaya ta juyo tace "kai bazaka hau ba?" shiru ya d'anyi da alama tunani yayi ya nufota yace suje, atare suka hau sai faman washe baki take ganin yadda take hango ruwan sosae saida suka je can k'arshe inda keda girma kaman dan gini mai rumfa suka tsaya sunata kallo fuskarshi a sake, tanan akwae inda zaka bi kaje kasan ruwan, ganin anata yin hotuna tace suyi suma don Allah ba tare daya ce komai ba ya fiddo wayar ya fara yi mata tace shima bari tayi mashi yace ta barshi karshe ma sai cewa yay su sauka hakanan don ya lura da yadda aketa faman kallonsu shi kuma baison kallo, koda suka saukan a kasan ma sawa tayi yayi mata hotunan a bakin ruwan cikin ciyayin dake wurin, Suna baro wurin ta fara gyangyad'i ganin hakan yasa yace ta sauke seat din ta kwanta sosae tace to, wuraren karfe biyar da wani abu suka shigo Katsina har saida suka iso bakin layin gidansu ta farka ganin inda suke yasa ta juya da alamun mamaki tace "wai ashe har mun dawo" kai ya daga mata idonshi akan hanyar layin ita kuma tana a kwance bata tada seat d'in ba,tunkan su k'arasa ya hango wata babbar bak'ar jeep fake a gefen gidan Hajiya tana facing d'insu da alama wanda ke ciki tafiya zaiyi daga jikin kopar motar ta wurin driver watace tsaye ta duk'ar da kanta da alama tana Magana ne da wanda ke acikin Motar, k'ura ido yay yana k'are mata kallo kafin da tsananin mamaki kan fuskarshi ya furta "What a Suprise!!!" jin abunda yace yasa Fatuu kallonshi ganin inda ya k'ura ma ido yasa ta juya ta kalli glass d'in gaban Motar itama ta kalli abunda yake gani, daidai gaban jeep d'in wadda Lexus GX460 ce ya parker tashi Motar lokacin kuma ta jikin kopar ta juyo, Tubarakallahu ahsanul khaliqin shine abunda na furta, kallo d'aya zakai mata ka yanke ba bahaushiya bace, doguwa ce ba kamar da yake takalman kafarta masu tsinine sosae tana sanye da straight gown ta babbar atampa glitter rigar ta bayyanar da dirinta sai dae sam bata da jiki ga d'amamman cikinta kai kace bata cin abinci, a bangaren kyawun fuska kuwa abun ba'a Magana don fara ce sosae tana da dogon hanci da d'an madaidaicin baki wanda lips dinsu ke jajur duk da da gani ta k'ara da janbaki, tayi d'aurin kallabi zara buhari yayin da yalwatacciyar sumarta brown ke d'aure da ribbom ta saketa saman gadon bayanta wuyanta na sanye da yar ziririyar sarka wadda da gani zinari ce haka ma d'an kunnan dake kunnanta barima ce ta zinari hannunta na hagu na sanye da golden agogo sam bata da mayafi ajikinta, tana juyowa ya bud'e Motar da sauri ya fita, nufarta yay tana ta faman sakar mashi kayataccen Murmushi koda ya isa gabanta kawae sai ta bud'e hannu ta rungumeshi can yasa hannu ya d'ago da ita suka had'a goshinsu suna ma juna dariya................End Of Book One, Shin wacece wannan? Mi kuma ke tsakaninta da Haisam? Da gaske Haisam na son Fatuu kuma zai aureta? Amsoshin wadannan tambayoyin na acikin A Sanadin Makwabtaka kashi na biyu. ALHAMDULILLAH, Anan na kawo karshen A Sanadin Makwabtaka kashi na farko wanda kamar gabatarwa ne ga ainihin Labarin dake a cikin kashi na biyu, ina rokon Allah yadda ya bani ikon kammala kashi na farko ya bani ikon kammala kashi na biyu cikin koshin lafiya, ya kuma bani ikon rubuta abunda zai amfaneni ya amfani Al'ummar Musulmi gaba d'aya Amin. Ga mai bukatar cigaba da karanta kashi na biyu wato Book 2 zai biya kudin karatu Naira 300 kacal ta wannan Account din👇 1509618776 Zainab Bature Access Bank Za'a turo da shedar biya ta daya daga cikin wadannan Lambobin wayan ko kuma tuntu6a don neman karin bayani, 09013804524 ko 08169856268. Thanks and i luv u as u patronize🤝🥰