[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2032* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ..........Tafiya mai d'an tsawo sukae cikin sand'a suka karaso katangar dake bayan gidan wadda take gajera bata da tsawo sosae Fatuu ce ta taimaka ma Haulat ta dira ta mik'a mata jakunkunan nasu sannan itama ta hau ta dire duk suka d'auki kayan suka bar wurin da sauri, Tafiya suke cikin sauri sosae Haulat duk a tsorace take ganin ko ina dumd'um ga haushin karnuka da ya karad'e ko ina cikin ranta tana ta yin Addu'oi Fatuu kuwa sam bata wani jin tsoro burinta kawai taga sun bar k'auyen ita ke ma Haulat jagora tana haska masu da fitilar wayarta saidae tana yi tana kashe wa ne, cikin sa'a suka k'araso bakin garin lokacin aka fara kiran sallar farko na Asuba tsaye sukae suna jira ko zasu samu abun hawa amman har bayan wani lokaci ba mai abun hawan da ya wuce Fatuu duk ta damu ganin an fara kiran salla tasan yanzu ayi sallar gari ya fara wayewa, Haulat dae saboda tsananin gajiya duk'ewa tay a wurin ga gabanta dake ta faman fad'uwa can Fatuu tace mata ta daure su d'an yi gaba kar azo a gan su ta yunk'ura da k'yar ta mik'e ganin haka yasa Fatuu ta d'aura trolley d'inta a saman kai ta d'auki jakar Haulat d'in a hannu tanata ta kawo ta ruk'e tace mata a'a ta bashshi zata iya, tafiya suka ci gaba da yi k'arfin hali kawae Fatuu ke yi amman ta gaji itama ga kaya, suna cikin haka sai ga wani mai amalanken shanu ya taho ta gabansu zai wuce da sauri Fatuu ta tsaida shi amman sai yak'i tsayawa tana ganin yana niyyar wuce wa ta sha gabanshi da sauri tana fad'in Don Allah ya tsaya, tsayawa yay cikin harshen fulatanci yace ta bashi wuri ya wuce hakan yasa ta fahimci k'ilan bai jin hausa ta bud'a murya cikin fulatanci tace Don Allah ya taimaka masu ya kaisu Jimeta, wani kallo yay mata duk da duhu ne yace bazai d'auke suba don ba can yay ba, rok'on shi ta shiga yi tace zasu biya shi yana kallonta yace yasani ko Aljanu ne su zai d'aukesu ta shiga yi mashi rantsuwar Mutane ne su zasu koma garin su ne, shiru ya d'anyi kafin ya tambayi nawa zata bashi ya kaisu da sauri tace dubu ukku d'an bud'e ido yay alamar mamaki sai kuma ya tambayeta ta tabbatar zata bashi hakan tace eh wllh yace to su hau cike da jin dad'i ta hau yi mashi godiya yace ba sai ta gode mashi ba su da zasu biya, saida ta taimaka ma Haulat ta hau suka saka kayan su sannan itama ta hau ya tambayi sun hau tace mashi eh sannan ya juya amalanken suka tafi Fatuu sai sauke ajiyar zuciya take Haulat dai tay zuru zuru jininta akan a kaifa yake in ba gani tay sun fita daga garin ba gaba d'aya hankalin ta bazai ta6a kwanciya ba, Anata sallar Asuba suka isa Jimeta suna shiga garin yace to su sauka anan zai aje su Fatuu ta rokeshi ya kaisu tasha sai sun je can zata fitar da kud'in da zasu biyashi basu dasu a hannu, fuska d'aure yace dama tasan ba kud'in suka ce zasu bashi tace ai akwae kud'in a cikin banki suke a tashar motar tasan ana fitarwa sai su bashi yana kunkuni yace to gaskiya saidae su k'ara mashi dubu biyu sannan ya kaisu da sauri Fatuu tace suje zasu bashi, Lokacin da suka isa cikin sa'a akwae mai Pos Fatuu ta fitar da sauran kud'in da suka rage mata gaba d'aya wanda Baffanta yace ta bari 20k ta biya mai amalanken dubu biyar d'inshi yana ta washe baki yay masu Allah ya kiyaye, Cikin sa'a suka samu Motar da tay Katsina direct suka hau aka shigar masu da kayan su aka ce su shiga seat d'in baya su zauna, bayan sun zauna zuru sukai kowacce kirjinta na bugawa zuciya na raya masu za'a zo a kama su sai Addu'oi suke acikin ran su, shiru shiru Mota bata cika ba har gari yay haske gaba d'aya tsoro ya kama su can Fatuu tace ma Haulat su sauka su hau ta Kano kawae tace to anata ce masu su k'ara hakuri mana ta cika suka ce sauri suke dole aka fiddo masu da kayan su suka koma ta Kano da ta kusa ciki suna shiga duka Mutum biyu suka k'aru Motar ta tashi har saida Fatuu ta d'an saki murmushi, Sai fatan Allah ya sauke su Lafiya. Koda Yadikko ta shigo da safe sam bata kula da babu su a saman gadon ba duk tunaninta sunyi salla sun koma bacci, sai bayan da ta gama had'a Breakfast a falo tace ma Mino taje ta tashe su Suzo su karya in sun gama sun ci gaba da baccin ko don bak'uwa, lokacin da ta shiga bata ga kowa ba ta dawo ta sanar mata sam yadikko bata kawo komae ba a ranta tace k'ilan ko sun fita ne ko wurin Amadu, bayan su Mino sun gama suka wuce Makaranta, har Yadikko ta gama gyara d'akin shiru basu shigo ba tana tunanin zuwa ta duba su sai ga Kamalu ya shigo amsar masu abun karin kumallo nan ta tambaye shi ko su Fatuu na wurin su yace a'a su yanzu ma suka tashi da mamaki ta ce to ina suka je da sanyin safiya Kamalu yace basu nan ne tace eh yanzu aka je taso su aka ga basu nan yace k'ilan wani wuri suka je zasu dawo, tun dae abun bai damun yadikko har ta fara damuwa ta fara neman su har bathroom d'in cikin d'akin ta duba duk da tasan ba yadda za'ai su shiga nan su biyu, cikin gidan ta fita ta zaga d'akuna tana tambayarsu cikin hikima ta yadda baza'a zargi wani abu ba ko ina aka ce basu zo ba, bayan ta dawo d'aki zaune tay kan kujera tana ta tunanin to ina suka je ne can ta mik'e ta nufi k'uryar d'aki tay tsaye tana kalle kalle idanunta suka sauka akan babban akwatin Fatuu ta k'ura mashi ido tana kallo can ta ankare da guda d'aya ne a wurin kuma tasan guda biyu ne, to ina d'ayan ta jefa ma kanta tambaya tare da nufar wurin shi da sauri, duk iya dubawar da tay bata ga trolley ba nan ta tuna da jakar Haulat da ita ta aje mata ita da hannunta ta juya da sauri inda ta aje ta idanunta suka gane mata wayam wani irin bugu k'irjin Yadikko yay lokacin da zuciyarta ta raya mata kodae guduwa sukae in ba haka ba mi zai sa aga ba kayan su kuma babu su, nan da nan jikinta ya fara rawa k'afafuwanta sukai mata nauyi da k'yar ta koma falo ta zauna kan kujera ta rafka uban tagumi. Sai Azahar Allah ya sauke su kano baiwar Allah Haulat ta mugun gajiya anan tasha Fatuu ta siya masu Abinci suka ci bayan sun gama ba 6ata lokaci suka hau Motar Katsina da gasu nan available sai ka za6a ka darje nan da nan suka hau hanya sai fatan a sauka Lafiya, kiran duniya Yadikko tay ma layin Fatuu amman sai ace mata a kashe yake har waje ta fita tasa Kamalu ya kira wai ko laifin wayarta ne kiran yak'i shiga shima yayi mamakin jin har yanzu basu gidan, to shima dae a kashen aka ce mashi wayan take dole ta dawo cikin gida tama rasa tunanin da zata yi da k'yar jiki ba kwari ta tashi don yin girki, Bayan da su Fatuu suka kama hanyar Katsina ne ta bud'e wayarta sakamakon tunanin halin da su Yadikko suke ciki daya tsaya mata a rai, sak'o ta rubuta ta tura ma Kamalu ta sanar dashi bata son Auren nan don haka ta koma gida tana tura mashi ta k'ara kashe wayar, lokacin suna tare da Amadu a kopar gida message d'in ya shigo wayarshi da tsananin mamaki yake karantawa har Amadu ya lura da yanayin fuskarshi ya shiga tambayar shi ko lafiya ya mik'a masa wayar shima ya karanta, kasa Magana Amadu yay Saboda tsabar mamaki da Al'ajabi shi yazo biki Amarya ta tafi ta barshi, tare da Kamalu suka tashi suka shiga cikin gidan don sanar ma yadikko a d'aki suka isketa ta rafka uban tagumi su Mino da suka dawo daga Makaranta suna zaune suna cin Abinci ita ta kasa ma ko ci don zuciyarta ta gama yanke mata cewa Fatuu guduwa tay ita da k'awarta tana ganin su Kamalu sun shigo ta mik'e tana tambayar su ko sun dawo Kamalu ya girgiza mata kai da alamun damuwa ya fad'i mata sak'on da Fatuu ta turo ba shiri Yadikko ta saki salati tana fad'in dama tayi zargin hakan wllh yanzu ya zasu yi da wannan babbar matsalar, miyasa Fatuu tay tunanin ta gudu ba tare da ta yi tunanin abunda zai iya biyo baya ba duka saura yan kwanaki a d'aura Auren, jin hakan yasa su Mino mik'ewa ba shiri jin Adda d'in su ta gudu, gaba d'aya sun yi jugum jugum sai kiran layin Fatun ake kaman yadda Yadikko ta buk'ata saidae kiran bai shiga sakamakon wayar da ake cewa a kashe take can Yadikko ta d'aukko wayarta ta kira Baffan su Fatuu hankali tashe ta sanar dashi abunda ke faruwa yace ya akai tun d'azun bata sanar dashi halin da ake ciki ba tace sam ita bata yi tunanin guduwa suka yi ba yace gashi nan zuwa gidan, zama su Amadu sukae haka su yadikkon duk suka zazzauna sai jimami kowa yake suna a haka har Baffan ya dawo, lokacin da ya shigo da alamun tashin hankali a kan fuskarshi yana shigowa yadikko ta mik'e shima tsayen yay murya na rawa ya k'ara tambayarta game da abunda ta fad'a mashi a waya nan ta sake kora mashi bayani da tsantsar tashin hankali yake kallonta can ya tsugunne don kafafunsa nema suke su kasa d'aukarshi yadikko na ganin hakan ta juya tace ma su Mino da tuni sun fara zubar da k'walla su fita waje ko su shiga cikin kuryar daki, suna tafiya Kamalu ma ya fara kokarin tashi Yadikko ta ce ya tsaya ya kawo wayarshi yaga sak'on da ta turon, bayan ya shiga cikin message d'in ya mik'e ya kai ma Baffan nasu hannu na rawa ya amsa ya k'ura ma screen d'in ido can ya d'ago ya mik'a ma Kamalu wayar ya idasa zaunewa k'asa idanunsa har sun canza sun yi ja cikin tashin hankali ya fara fad'in "Miyasa inna wuro zata man haka, in tasan bata son auren ai da tun farko bata nuna ta Amince ba sai ta k'yale mu duk halin da zamu shiga mu shiga ba sai yanzu da lokaci ya k'ure ba, sam inna wuro bata kyauta mana ba ban ta6a zaton zata iya aikata haka ba duk da tasan irin halin da hakan zai k'ara jefa mu amman ta za6i mu shiga cikin matsala, da ina Alfahari da ita don ta damu da damuwar mu tana jin tausayin mu ashe sam ba haka bane tunda zata iya za6ar k'ara jefa mu cikin mawuyacin halin yanzu ina amfanin haka ya take so muyi, duka saura fa yan kwanaki bikin nan....." Kasa cigaba yay sakamakon Muryar shi da ta karye kwalla suka fara zubo mashi da sauri Yadikko tace "Don Allah kar ka zubar mata da hawaye kar hakan ya zame mata matsala wllh duk abunda kaga ya faru laifin su Zakiyya ne har cikin ranta ta amince da Auran nan amman sune suka fara cusa mata k'in auran ta hanyar fad'a mata Maganganun da suka tashi hankalinta" nan take ta kwashe komae ta sanar mashi ba iya wannan ba harda abubuwan da shi Khalid d'in ke mata da gidan gona daya kaita yasaka mata maganin bacci a lemu duk bata 6oye mashi ba duk da su Amadu na a wurin gaba d'ayan su sun matuk'ar girgiza da jin hakan kowa ran shi ya sosu ba kamar Baffan nata da tsananin mamaki yake bin yadikko da kallo kafin rai 6ace yace yanzu dama yaron bai canja hali ba aka fad'a mashi ya shiryu yadikkon tace wai don ya biya sadaki a fusace Baffan yace biyan sadaki d'aura aure ne da zai nemi lalata yarinya su Kawu Amadu dae sun kasa cewa komae saidae kowa ran shi ya 6aci da jin wannan Magana shi dama Kamalu ya tsani Khalid d'in sanin halayen shi marasa kyau da yay shi kam Kawu Amadu wani irin tausayin Fatuu ne ya kama shi taya nutsattsiyar yarinya kamarta za'a had'a ta da irin wannan Mutumin nan take cikin ran shi ya goyi bayan guduwar da tayi duk da yana shakkun ba lalle Gwaggo ta saurareta ba amman tabbas zai kira gwaggon ya k'ara tunzura abun duk yadda za'ai a fasa, shima Baffan tunani na daban ya fara yi a cikin ranshi yana jin bai kamata ya k'yale a Aura mata wannan Mutumin ba saidae taya zai dakatar da auren shine abunda ya tsaya mashi a rai, tsam ya mik'e ya fice daga d'akin yana fita Kamalu ya fara Maganganu kan rashin dacewar Aura ma Fatuu Khalid yana fad'in shi dama yasan ba wani canzawar da yay za'a cuce ta ne kawai. Sai wurin la'asar suka iso tun kafin su shigo Katsina Fatuu na hango Welcome to Katsina taji wani irin sanyi a ranta koda suka shigo har saida ta juya suka had'a ido da Haulat tay mata Murmushi itama ta yi mata amman fa na yak'e don ta gaji har ba sauran wuri, suna zuwa roundabout d'in Liyafa suka ce a sauke su anan don in suka wuce tasha tafiyar ta k'ara nisa, bayan sun sauka suka tsaida Keke Napep suka hau bayan sun fad'i mashi inda zai kai su yaja suka tafi Fatuu sai kalle kalle take sai take ganin kaman ta shekara da barin garin, tunda suka k'araso bakin Unguwar su gabanta ke fad'uwa har suka iso kopar gidan, bayan ya tsaya suka fito harda kayan suka biya shi, tsaye Fatuu tay tana zare ido suna kallon juna da Haulat itama dae gabanta fad'uwar yake don bata san irin tarbar da gwaggon zata masu ba can dae tace ma Fatun su shiga, Gwaggo na a wurin filin wanke wanke tana yin Alwala gamawarta kenan ta yunk'ura zata mik'e Fatuu ta sako kai ba tare da tayi Sallama ba, cak ta tsaya sakamakon had'a ido da sukae da gwaggon da ta ida mik'ewa tsaye, bin Fatun da ido kawai tay saidae a bad'ini ta matuk'ar razana da ganinta a ranta ta fara tunanin ko gizo take mata saidae kuma ganin Haulat ta sako kai itama yasa ta gasgata Fatun ce dae, hannu Haulat ta sa ta d'an zunguri Fatuu a hankali suka had'a ido tay mata alamar taje da ido, aje trolley d'in tay anan slowly ta nufi gwaggon duk ta kame kanta a d'an gabanta ta tsaya murya na rawa tace "G.. gwaggo......" kallon ta kawae take can kuma ta fara k'ok'arin wucewa ciki aikuwa da sauri Fatun ta durk'ushe gabanta ta kama k'afarta guda ta fashe da matsanancin kuka tana fad'in "Don Allah gwaggota ki yi hak'uri ki yafe man nasan nayi maki laifi, ke mahaifiyata ce dama ya'ya suna yi ma iyayen su laifi kuma su yafe masu Saboda k'aunar da suke masu, kiyi hakuri gwaggo banda hankali ne banda wayau shiyasa na kasa gane abunda kike jiye mun...." Dakatawa tay tana cigaba da kukan Gwaggon ta d'age kanta sama tana jin wani iri a ranta har idanunta sun fara tara kwalla, tun da Fatuu ta tafi bata k'ara lafiya ba kusan kullum sai ta zubar da kwalla har rama tayi Amadu bai fad'i ma Fatun bane don kar ta tada hankalinta, Allah ya jarabeta da tsananin k'aunar Fatuu kallon Ayshar ta take mata, ganin tak'i cewa komai ga Fatuu nata kuka yasa Haulat k'araso wa ciki inda suke itama ta duk'a ta kai hannu ta kama d'ayar kafar itama kwalla suka fara zubo mata cikin muryar kuka tace "Gwaggo don girman Allah kiyi hakuri ki yafe mata ta gane kuskuren ta na k'in goya maki baya" d'an ta6e baki gwaggon tay still kanta na d'age sama, cigaba da rok'on ta suka yi can ta sauke ajiyar zuciya tana kokarin maida kwallan idonta ta saddo kan tana kallon Fatuu da fuskar ta tay jage jage itama kallon gwaggon take, d'an nisawa tay kafin murya can k'asa tace suje ciki aikuwa da sauri Fatuu ta mik'e ta fad'a jikinta ta k'ank'ameta tana wani irin Kuka saida dai tasa k'wallan gwaggon zubowa ta d'agota suka nufi ciki ta kalli Haulat itama tace mata ta taho, wucewa tay da sauri inda kayansu suke ta jawo trolley d'in da jakar ta sannan ta bi bayansu suna zuwa saitin d'akin Fatuu Gwaggo tace su shiga kafin tay salla har suna had'a baki wurin cewa to suka nufi ciki Haulat ma ta shiga da kayayyakin, Gwaggo na shiga d'aki kujera ta nufa ta zauna tay tagumi tama rasa tunanin da zata yi kan dalilin dawowar Fatun don tasan tabbas ba hakanan ta dawo ba ana saura yan kwanaki a d'aura mata aure dole da dalili can ta mik'e dai ta kabbara sallar bayan tasa Hijab, bayan ta sallame ta kai hannu saman gado ta d'aukko wayarta da tunda tana salla taji tana ta ringing tana dubawa taga Amadu ne tabi bayan kiran ringing d'aya ya d'aga bayan sun gaisa yana d'an inda inda ya tambayeta Fatuu ta iso k'asa k'asa tace mashi eh, dama tun d'azun yake son ya kira zullumi ko Fatun bata iso ba yasa yak'i kiran sai yanzu da yay tunanin sun isa isowa sallama yay mata kawai don baisan ko basu yi Magana ba ta kashe wayar, suma su Fatun sallar sukae bayan sun gama sukae Zaune jugum, bayan da gwaggo ta gama Addu'oi shiru tay kaman mai nazari can bayan d'an wani lokaci ta k'wala ma Fatuu kira wani kalan fad'uwa gabanta yay ta amsa suna Kallon juna ita da Haulat har taje d'akin gwaggon tace ta kira Haulat itama ta dawo ta kirata, duk a k'asa suka zauna idon gwaggo a kansu sai da ta nisa sannan ta fara Magana, "Miya faru kuka dawo?" Shiru sukai suna kallon juna kafin Fatuu ta sauke idanunta kan gwaggo murya na rawa tace "b..ban son Auren ne" zuba mata ido kawae gwaggo tay ganin kallon da take mata yasa Fatuu d'an sunnar da kai can taji tace "Baki son auren, kenan gudowa ki kai?" a hankali ta d'aga mata kai still gwaggo tay tana kallonta kawae da alama tama rasa mi zata ce mata ne, "Saura kwana nawa a d'aura maki Auren?" a sanyaye Fatuu ta bata amsa da hud'u, kya6e baki gwaggo tay tace "Saura kwana hud'u shine zaki ce baki son auren to yanzu da kika zo man nan ni mi zan maki??" Idonta akan gwaggo idanunta sun kawo kwalla tace "Don Allah gwaggo kar ki bari ayi man Auran nan" d'an murmushin takaici gwaggon tay kafin ta d'aure fuska a kausashe tace "ni ba abunda zan iya yi maki yanzu, lokacin da nike tunanin inada yadda zanyi nuna wa ki kai baki son hakan don haka yanzu bakin Alk'alami ya riga da ya bushe dole ki koma ai maki Auren, kuma ke da kika amince don ki taimaki Mahaifinki ki fitar dashi daga halin da yake ciki shine yanzu zaki za6i k'ara jefa shi a wani halin saura kwana hud'u bikin ki kice wai baki so kina da hankali kuwa!" tuni Fatuu ta fara kuka gwaggon ta juya kan Haulat rai 6ace tace "Ke Haulat ke kika bata shawarar ta gudo ne da kuka taho tare?" Da sauri murya na rawa Haulat tace "a..a gwaggo jiya bayan munje ne shine da tsakar dare ta tashe ni tace man gida zata taho lokacin nima na nuna mata had'arin dake tattare da hakan nace tayi hak'uri amman sai tay man bayanin irin mijin da ake so a aura Matan tace dama kema baki so in ta dawo zaki taimaka mata a fasa, to da ita kad'ai ma zata taho daga baya nace bari mu taho tare" d'an ta6e baki gwaggon tay tace "to ni kam yanzu ba abunda zan iya yi kan hakan don haka sai ku tattara ku sake komawa tayi hakuri taje a d'aura mata Auren kaman yadda tun farko ta amince...." Kuka sosae Fatuu take yi ta fara mata Magiya tana fad'in "Don Allah gwaggo ki taimaka man wllh ban iya rayuwar Aure da shi in aka aura man shi mutuwa zan yi d'an iska ne mai neman mata kuma mashayi...." Nan Fatuu ta kashe komae duk abunda ya ta6a yi mata ta fad'i ma gwaggon, a zahiri sai kace abun bai dake ta ba amman a bad'ini ba k'aramar kad'uwa gwaggo tay ba da jin hakan ba kamar gidan gonar da ta ce ya kaita har ya zuba mata maganin bacci ya ta6a ta duk da haka fuskarta ta nuna tashin hankalinta rai 6ace ta tambayi Fatun ta fad'a ma wani cikin iyayenta wannan zancen da sauri tace eh ta fad'a ma Yadikko amman sai ta bata hak'uri tace lokaci ya k'ure kuma wai itama tana ganin don ya biya sadaki ne yasa yay mata hakan kamar yadda yace, a fusace gwaggo tace "Zancen banza kenan! a ina biyan sadaki ya zama aure da har zai samu damar ta6a ki???" Shessheka kawae Fatuu ke yi gwaggo taci gaba da fad'in "ni dama tun farko abunda na guda kenan don Kamalu ya fad'a ma Amadu yaron ba nutsattse bane in ba don haka ba wllh bazan tsani yi maki aure ba, tabbas nasan zan ji ba dad'i don ina son ki yi karatu amman kuma nasan darajar kowace yarinya d'akin mijinta ne ba kamar zamanin nan da mazajen aure ke wuya sai kaga yarinya ta gama karatun kuma sai mijin aure ya gagara shiyasa iyaye masu dubara da yarinya ta gama secondary suka ga tana da tsayayye sai kiga sunyi mata aure sun ce taci gaba da yin karatun a d'akin mijinta don kar a rasa damar da aka samu, to ke kanki da ace naji an yaba da yaron wllh zan goyi baya ne in kin je can Kya yi karatun amman Kika watsa man k'asa a ido kika nuna ke kin amince, nasan da niyya mai kyau kikai hakan amman yanzu baka cewa zaka kashe kan ka don ka raya wani ba kaman akan abunda ansan da matsala yanzu in akai maki Auren matsala ta biyo baya ke ce a ciki shi kan shi mahaifin naki ba samun kwanciyar hankali zai yi ba kina cikin matsala shiyasa maganin kada ayi to kada a fara da kin ban dama da nayi duk yadda zan yi inga an fasan in dae Allah ya nufi hakan in kuma nayi bakin k'ok'ari na naga na kasa sai abar ma Allah, Yanzu ni gaskiya bansan ya zanyi in tsaida Al'amarin nan ba lokaci ya k'ure" rai a tsananin 6ace take Maganar ta k'arasa tana girgiza kai Fatuu ta matsa gabanta ta kamo hannuwanta tana cigaba da rok'onta Haulat sai matsar k'walla take to itama dae gwaggo kasa jurewa tay saida kwallan suka zubo mata Fatuu nata mata Magiya tana fad'in ita bata san ashe dalilin da ya sa bata son ai mata Auren ba kenan can gwaggo ta nisa tace mata abar ma Allah komae tayi Addu'a ya tabbatar da abunda yafi zama Alkhairi ta jinjina kai, mik'ewa gwaggo tay ta fita bada jimawa sosae ba ta dawo hannunta ruke da tray ta aje masu tace ga Abinci nan su ci ta sake fita sai gata ta dawo da ruwa da lemu ta aje masu kafin ta nufi bakin gado ta zauna hannunta dafe da ha6arta gaba d'aya kanta ya gama k'ullewa ta rasa tunanin ma da zata yi, a hankali suke cin Abincin jikin kowannan su ya gama yin sanyi ba laifi sun ci sosae bayan sun gama atare suka fitar da kayan gwaggo tace suje suyi wanka tunda Magrib bata k'arasa yi ba suka amsa da to ta bi su da ido gwanin tausayi, Haulat ce ta fara yo wanka sannan Fatuu gaba d'aya sun ji dad'in jikin su saidae kowa da fargaba a cikin ran shi ba kamar Fatuu, bayan sun canza kaya zaune su kae a cikin d'akin jigum saida akai sallar Magrib suka fito bayan sun gama sallar gaba d'aya suka 6ingire a kan abun salla suna baccin gajiya lokacin da akai Isha da k'yar Gwaggo ta tashe su suka yi salla tayi masu Maganar Abinci duk suka ce basu jin yunwa tace to su hau gado dama Haulat bata ma yi tunanin tafiya gida ba tunda tsugunne bata k'are ba, Allah sarki gwaggo sam ta kasa ma kwanciya sai kai da kawowa take a cikin d'akinta wani lokacin ta zauna a bakin gado abun duniya duk ya isheta ba k'aramin k'una ranta ke mata ba can ta d'auki waya ta kira Mahaifin Fatuu bayan ya d'aga sun gaisa ne take ce mashi yanzu ashe sun san halin wanda za'a aura ma Fatuu amman suka amince a jefa rayuwar yarinya a cikin matsala kamar zai kuka ya fara mata rantsuwa yana fad'in harda k'arin hakan yasa shi kwanciya ciwo lokacin da Ard'o ya fad'i mashi hakan kuma har wurin mahaifin yaron yaje don ya rok'eshi a kan a fasa harda Maganar halin yaron nashi yay mashi amman sai ya tabbatar mashi da cewa ya kwantar da hakalinshi yaron ya canza hali ya shiryu shiyasa ma ya nema mashi aurenta ya kuma tabbatar mashi da ko bayan bikin yaci gaba da yin hali mara kyau shi da kan shi zai d'auki mataki gwaggon ta tambaye shi yaji abubuwan da yay ma Fatun yace eh Yadikko ta fad'a mashi tace to yanzu ina canza hali anan yace babu kam, tambayar shi tay yanzu wane mataki zai d'auka ko kuwa a hakan za'a aura mata shi cikin karewar murya yace shi wllh ya rasa mafita amman har ga Allah bai son ayi mata auran gwaggo na jiyo sheshshekar shi sake tambayar shi tay an san Fatun ta gudo yace ba wanda ya sani iya su ne tace to abunda za'ai in Allah ya kaimu yaje ya fad'i ma Ard'o harda dalilin da yasa ta gudon kar ya rufe komae, d'an jimm yay kafin ya amsa mata da to sukae sallama, koda suka gama wayar cigaba da tunanin mafita tay gashi Hajiya bata nan bare taje neman shawara jiya da yamma Senator yasa aka tafi da ita Abuja Saboda ciwon kafar da ya taso ta gaba, k'arshe dai Alwala taje tayo tazo ta kabbara salla don neman mafita wurin Allah, Washe gari bayan da su Fatuu sukae salla komawa sukai sai da gwaggo ta gama breakfast taje ta tashe su sukai breakfast d'in bayan sun gama suka gyara gidan tsaff gwaggo na d'aki bata je aiki ba dama kwana biyu tana gida Saboda bata jin dad'in jikinta sai jiya ta koma yau kam gaba d'aya bata jin dad'i damuwa tay mata yawa hakan yasa ta kira ta fad'a bazata samu zuwa ba, har d'akin ta suka je don su gyara tace su bar shi in ta tashi sai a gyara, Wanka su kai Fatuu ta tsuke cikin jeans da t-shirt har ta jita ta dawo Fatunta ta da duk da da sauran rina a kaba ta ba Haulat doguwar rigar Material don kayanta masu nauyi ne duk na cin biki ne ta tafi da su, tsaye Fatuu tay gaban dressing mirror tana kallon kanta tana ce ma Haulat wai kaman yadda fuskarta ta rame hips d'in ta ma sun rame don ita ji take kaman sun rage girma dariya kawae Haulat d'in ke yi can ta tuno da abunda Khalid yay mata ta d'aure fuska ta dawo gefen gado ta zauna Haulat na ganin yanayinta ya canja ta fara tambayar ta abunda ya faru idanun Fatuu cike da kwalla tace ta tuna abun da Khalid yay mata ne yanzu shikenan ya gane mata jiki Haulat ta dafata tace "ki daina damuwa k'awata yaje don kan shi kuma bi'iznillahi ta'ala ya yi mashi ganin farko kuma na k'arshe" a sanyaye Fatuu tace Allah ya sa suna haka wayarta ta fara ringing ta d'aukko tana duba mai kiran ganin Abbas ne yasa tay picking bayan sun gaisa yace "Mom Zarah Amarya kwana biyu inata jira baki turo man invitation card ba shiyasa nace bari in kira in ji Date d'in" shiru ta d'anyi sai kuma tace mashi "ai na dawo gida fa" da alamar mamaki yace "wane gida?" Tace "Nan Katsina" still da mamakin yace "ba dae har an d'aura Auren ba anan zaku zauna ne?" Har saida Fatun tay yar guntuwar dariya jin abunda yace kafin tana tura baki tace "a'a ba'a d'aura ba banson auren ne shine na gudo jiya" Abbas yace "What! Kin gudo?" kaman zatai kuka tace "Eh Ya Abbas ni ban son Auren" tana jin yadda ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yayi d'an shiru kafin ya tambaye ta yanzu haka tana gidan su tace eh yace Ok gashi nan zuwa yanzu................. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._ [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2033* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........After some minutes sai gashi ya kira yace mata yana waje tace to, babban gyale ta d'aukko a cikin wardrobe ta d'aura saman kayan jikinta tace ma Haulat tana zuwa ta d'aga mata kai, bayan ta fito daga d'akin saida ta shiga d'akin gwaggo har sannan tana kwance saman gado ta fad'i mata ga Ya Abbas nan yazo zata je gwaggon ta d'ago da kai ta kalleta tace kiran shi tay ta fad'i mashi ne Fatun tace "a'a d'azun ya kirani wai ban tura mashi Iv ba har yanzu shine nace mashi ai na dawo ya tambaye ni yadda akai shine nace ban son Auren ne na gudo" ta k'arasa tana d'an sunnar da kai, shiru gwaggo ta d'an yi kamar mai tunanin wani abu sai kuma ta d'aga kai tace taje, tana fitowa daga cikin gidan Abbas ya bud'e kopar Motar ya fito idon shi akanta har ta k'araso ta tsaya d'an gaban shi tana ta kikkafta ido ta gaishe da shi, da alamun mamaki yace "Mom Zarah so u'r serious kin gudo d'in dae kenan" d'an tura baki tay bata ce komae ba yace "Amman miyasa kikai hakan ba kince man kin amince bane Saboda Daddy en ki yanzu da kika gudo baki tunanin zaki k'ara jefa shi a wata matsalar da ta fi wanccan?" Yamutsa fuska ta fara nan da nan idanunta suka kawo kwalla cikin rawar murya tace "Ya Abbas ban son wanda za'a aura man d'in ne....." Katseta yay "ai nasan hakan Zarah kuma dama ai ba don kina son nashi kika amince ba why saida aka kusa zaki hakan" ya kafeta da ido rasa abun ce mashi tay kawae sai ta saka mashi kuka tana fad'in "Ya Abbas mai neman mata kuma mashayi ake son aura man fa" waro ido Abbas yay da alamun ya d'an razana da jin Maganar tata ita kuma sai kuka take, nuna mata other side en Motar yay yace su shiga ciki ta juya tana matsar k'walla shima ya juya ya shiga, bayan ta shiga cigaba da kukan tay Abbas da shima ya shigo yace mata is ok ta daina kuka, d'an tsagaitawa tay yanata kallonta yace "Mom Zarah ya akai kika san abunda kika fad'a game da shi" shiru tay tana tunanin ko ta fad'a mashi shima tunda ta ga da ta fad'i gwaggo hakan ta saukko Abbas d'in ya lura kaman tana 6oye wani abu hakan yasa yace mata kar taji komae ta fad'a mashi yankewa tay gwara ta fad'i mashi kawai ta d'aga kai ta kalli gefen shi cikin muryar kuka ta fara fad'i mashi tiryan tiryan tun farko abunda ya fara mata har zuwa gidan gonar da ya kaita da washe gari da suka dawo daga wurin gyaran jiki tana kai wa k'arshe ta sake fashewa da kuka mai cin rai, iya girgiza Abbas ya girgiza da jin abunda ta fad'an fuskar shi har ta nuna yama kasa Magana sai kawae ya maida kan shi jikin heardrest ya d'age sama wani irin bak'in ciki ne ya turnuk'e shi, ya d'an d'auki lokaci a hakan kafin ya sauke kan yana kallonta sai kuka take hannu ya kai ya bud'e glove box ya curo tissue ya yagi mai d'an yawa bayan ya maida ya mik'a mata yace tayi shiru ta daina kukan hakanan, amsa tay ta fara goge fuskar saida ta gama ta ruk'e tissue d'in a hannu sannan ya fara mata magana cikin murya mai tattare da 6acin rai yace "But Mom Zarah are sure daga hakan bai cutar dake ba?" ta fahimci mi yake nufi hakan yasa ta fara girgiza kai tace "Wllh daga hakan bai man komae ba, ko lokacin da na gane yasa man maganin bacci ina mashi Masifa har nace mashi Mazinaci shine ya fara man fad'a har yana cewa da shi Mazinaci ne ai da bai k'yale ni ba duk da damar da ya samu" tana kai k'arshe ta d'ukar da kanta d'an yamutsa baki kawai Abbas yay cike da takaici, suna cikin hakan sai ga Haulat ta fito ta zagayo side d'in da Fatuu take ta d'an kwankwasa glass tana ganinta ta bud'e kopar ta d'an duk'a kan ta ta gaida Abbas da k'yar ya amsa mata tace mashi dama gwaggo ce tace tana Magana yace Ok gashi nan zuwa daga haka ta juya ta koma, kallon Fatuu yay suka had'a ido yace su je a tare suka fito daga cikin Motar, lokacin da suka shiga Parlon gwaggon na zaune tayi mashi sannu da zuwa ya amsa yana kokarin zama, nuna ma Fatuu wuri tay tace ta shiga ta zauna ta kalli Abbas cike da damuwa tace "d'ana Abbas tayi maka bayanin abunda ke faruwa ne?" d'aga mata kai yay alamar eh ta sauke Ajiyar zuciya taci gaba "abun dae sam ba dad'in ji gashi ni na rasa mafita shiyasa nace a kira man kai koda shawarar da kake ganin zaka bani, na so ace Hajiya na nan to kuma bata nan gashi lokaci ya riga ya k'ure amman sam bai kamata ta auri Mutumin nan ba tunda daga ji baida hali" girgiza kai Abbas yay yace "tabbas bai dace ta aure shi ba gaskiya, amman su can yanzu da ta taho mi suka ce ne?" d'an yarfa hannu tay tace "to jiya dae da daddare munyi Magana da Babanta yace Matar tashi ta fad'a mashi dalilin tahowar Fatuun ya nuna shima bai son ta auri Mutumin saidae baisan taya zai dakatar da Al'amarin ba, anan nake tambayar shi ko mutan gidan nasu sun san Maganar tahowar tata yace ba wanda ya sani to dae nace ya je ya sanar da Ard'on komae dake faruwa, har yanzu dae bai kira ni ba balle in san halin da ake ciki" sigh Abbas yay yana d'an jinjina kai kafin yace "Yanzu za'a jira shi ne aji ko akwae abunda kike ganin za'a yi?" a sanyaye tace "eh to ni da na yanke shawarar zan tafi can garin ne gobe gwara ayi wacce za'ai tun kafin ranar d'aurin auren tunda su can dangin Angon bama su san ita Fatuun ta taho ba" d'an biting lower lip d'in shi yay ya k'ura ma carpet d'in k'asan parlon ido da alama yana tunanin wani abu ne can ya d'ago yace mata shikenan ta shirya gobe idan Allah ya kaimu zai zo da Asuba sai suje can garin tare gwaggon tace "a'a d'ana Abbas ai ba'ayi haka ba kaima ai kana da hidindimun ka da za'a k'ara d'aura maka nauyin tafiya dama dae shawara nike nema don kaina ya k'ulle gaba d'aya gashi dama ba cikakkar lafiya ce da ni ba" tana k'arasa Maganar tasa k'asan rigarta tana goge kwallan idonta, tsananin tausayin ta ne ya kama Abbas d'in ya shiga bata baki yana ta kwantar da Hankalinta in sha Allahu Allah zai kawo mafita duk yadda za'ai baza'a yi auren nan ba, sosae gwaggo tay mashi godiya da Addu'oi daga baya yay mata sallama yace sai yazo goben suka fito gaba d'aya, daga bakin kopar fita gwaggo ta komo ciki ita kuma Fatuu ta bishi har waje, jikin Motar ya jingina yana kallonta kanta a k'asa gaba d'aya duk tausayin su yake ji yasan dole zuciyoyin kowannansu na cikin wani hali, kiran sunanta yay ta d'ago suka had'a ido yace ta daina damuwa in sha Allahu zai yi iya bakin k'ok'arin shi wurin ganin ba'ayi mata Auren da mutumin ba tay d'an murmushi had'i da jinjina mashi kai yace gobe in Sha Allah zasu je can ai masu Addu'a tace to daga haka yace ta shiga ciki ta saida tay mashi Allah ya kiyaye hanya sannan ta juya ya bita da ido har ta shige cikin gida kafin ya koma cikin Motar yaja ya tafi, tana shiga d'akinta cike da farinciki ta nufi gado ta fad'a tana sakin murmushi Haulat dake kallonta ta tambaye ta ya akai ta fad'i mata game da tafiyar da Gwaggo zatayi da Ya Abbas itama d'an murmushin tay tayi fatan Allah ya kaisu lafiya yasa ayi nasara suna cikin haka wayar Fatuu tayi ringing ta kai hannu ta d'aukko tana d'aura idonta akan screen d'in wayar mood d'in ta ya canza tay rejecting kawae ta kife wayar Haulat dake bin ta da ido ta tambayi waye kaman bazata fad'i mata ba sai kuma tace "wanccan d'an iskan ne" nan take haulat ta fahimci wanda za'a aura mata ne, k'ara kira yay Fatun ta buga uban tsoki ta kai hannu a fusace ta d'auki wayar ta saka ta a silent kawae ta sake aje ta ganin yadda ranta ya 6aci yasa haulat yin d'an murmushi tace "ina ma ace Ya Haisam yaji kawae yazo yasa a d'aura auran da shi" wani kallo Fatuu ta bita da shi baki bud'e Haulat d'in ta d'age mata gira tace "in shine ai nasan zaki yarda ko?" D'an ta6e baki Fatuu tay tace Uhmm kawae Haulat dake dariya tace "ko yanzu kin daina son nashi ne?" Shiru ta d'an yi sai kuma ta sauke ajiyar zuciya yanayin fuskar ta ya k'ara canzawa a sanyaye tace "kema Haulat ai kin san in nace na daina son shi nayi k'arya tunda son gaskiya nike mashi kawai dae nasan ba ta6a samun shi zanyi ba zan ta wahala ne shiyasa na rarrashi zuciya ta kawai" d'an girgiza kai Haulat tay itama dama ta fad'a ne kawae tasan har Abada ba lalle ta daina son Ya Haisam ba saidae ta hakuran kawae, "Amman in ace yace zai aure kin zaki yarda" wani kallo Fatuu tay mata tace "Fad'a ma 6ata baki ne Haulat" gaba d'aya su kai yar dariya Haulat tace "in Allah ya kaddaro mijin ki ne duk aje a dawo wllh sai kin aure shi kina zaune zai kawo kan shi ma" d'an ta6e baki Fatuu tay tana murmushi ta gyad'a mata kai kawae, a ranar da daddare gwaggo tace suzo su je gidan su Haulat tace ma Fatuu ta d'aukko kayan da zatai amfani dasu don a can zata zauna kafin ta dawo Fatun tace to, bayan sun je Innar su Haulat ta matuk'ar girgiza da jin abunda ke faruwa da gwaggo ta mata bayani, itama sam bata goyi bayan ai auran ba daga baya tay ma gwaggon fatan sa'a, tare dasu Fatuu ta dawo zasu kwana nan da safe sai su koma gidan su Haulat d'in. Washe gari ana gama sallar Asuba Abbas yazo ba 6ata lokaci gwaggo dasu Fatuu suka fito bayan an rufe gidan suka shiga cikin Motar Abbas ya gaishe da gwaggo tay mashi ya kwanan iyali su Fatuu ma suka gaida shi, a daidai bakin lungun su Haulat aka aje su suna d'aga masu hannu suna Allah ya tsare saida suka ga tafiyar au sannan suka nufi gidan. Alhamdulillah kafin la'asar wurin k'arfe ukku na rana suka isa da yake Motar gida ce ba tsaye tsaye tun suna akan hanya Abbas ya tsara ma gwaggon abunda yake ganin yakamata suyi har ya nuna ace Fatun tana da wanda suke son juna hakan zai sa asamu sauk'in matsala tsakanin Mahaifinta da kuma shi Ard'on in Allah yasa aka janye batun Auren sosae gwaggo ta fahimce shi, a kopar gidan Motar Abbas ta parker duk idanun mutanen dake wurin ya dawo kanta gwaggo ce ta fara fitowa akan idon Kamalu da Amadu dake zaune a bakin teburin saida raken shi aikuwa da sauri suka tashi suka nufo ta baki washe itama dariyar take masu, a gabanta suka tsaya suna mata sannu da zuwa tana amsa masu lokacin Abbas ya fito shima yana sanye da manyan kaya shadda ash da hula da takalma yayi too match Amadu na ganin shi ya nufe shi da Murmushi shima murmushin yake mashi yana zuwa ya mik'a mashi hannu suka gaisa Kamalu ma ya zagaya suka gaisa, tuni su Mino sun je sun fad'o ma Yadikko zuwan gwaggon, kallon su Abbas gwaggo tay tace mashi su shigo suka nufi hanyar shiga gidan ta lura da kallon da Mutanen gidan dake zaune a wajen ke mata basu da niyyar yi mata ko sannu da zuwa hakan yasa itama ta share su sai Abbas ne ke d'aga masu hannu yana gaida su suma suna d'aga mashi, suna shiga Yadikko ta tarbe su da fara'a tana masu sannu da zuwa tace su shiga ciki mutan gidan kaman ko yaushe sai lek'owa suke suna ba ido hakkin shi yan kad'an ne suke ma gwaggon sannu da zuwa itama ta gulma, a falo suka zauna yadikko ta zauna a k'asa tana gaishe su fuska a sake Abbas ya amsa mata su Amadu ma suka zazzauna shiru ta d'an biyo baya can gwaggo tace "sai muka ga Amarya ta dawo" d'an rausayar da kai yadikko tay bata ce komai ba gwaggon ta tambayi ina Baffan Fatuu tace yana d'aki bai jin dad'i ne bari tay mashi Magana, saida ta fara kawo masu Abinci da fura sannan taje ta fad'o ma Baffan game da zuwan nasu suka dawo tare yana biye da ita, bayan sun shigo a k'asa ya durkusa yana gaida gwaggon da fulatanci ta amsa Abbas ma ya gaishe dashi suka k'ara yin shiru Yadikko ce ta katse shirun da ce masu su ci Abincin gwaggo tace ba damuwa zasu ci basu jin yunwa ne don sun ci Abinci a hanya, maida idon ta tay kan Baffa da ya sadda kai k'asa ta tambaye shi yayi ma Ard'o Maganar halin da ake ciki ya d'ago yace eh, "To ya kukai da shi ne?" Gwaggo ta tambaya shiru ya d'an yi yana motsa baki kafin cikin rawar murya yace "ran shi ne ya 6aci yace wai ai ba wani abu bane ita tamkar Matar shi ce tunda ya biya sadaki, yanzu haka yau zuwa gobe ya bani in je in dawo da ita in ba haka ba ko bata nan za'a d'aura Auran wai sai mijin nata yaje ya d'aukko ta k'arshe ma cewa yay mu muka k'ulla komae muka sa ta gudu duk yabi mutan gidan ya fad'a masu mun sata ta gudu" wani murmushin takaici gwaggo tay ta maida idonta kan Abbas da shi ma 6acin rai ke kwance akan fuskar ta shi tace "d'ana Abbas kaji wani son zuciya ko" jinjina mata kai yay kawae gwaggon tace "to sam bazan yarda a lalata ma yarinya rayuwa ba wllh tunda shi kan shi kawae ya sani..." Maida idonta kan Baffan tay ta tambaye shi ance yaron a Jimeta yake ko yace mata eh yaron chairman ne ta kalli Abbas tace ya ci Abinci in sun huta sai suje Jimetan farko cewa yay ya k'oshi Baffan Fatuu yace don Allah ya ci sun kwaso hanya kuma yace bazai ci Abinci ba sai a lokacin gwaggo ta gabatar masu da Abbas a matsayin abokin Haisam duk sukai mashi godiya suka ce Allah ya bar zumunci, ba laifi ya ci Abincin ba kamar da yake yadikko akwae tsafta d'akin tass yake suma tsab da su bayan ya gama ne Baffan yace su je d'akin shi sai ya huta yace to suna fitowa daga falon idon Abbas ya sauka akan Mino dake zaune da k'annanta a gefe don yadikko ta hana su shiga murmushi yay ganin sak fuskar Mom Zarah ya kirata ta mik'e taje gaban shi itama tana mashi murmushi ganin yana yi mata, dafa Shoulder d'in ta yay yace ya sunanta tace mashi Ameenatu amman Mino ake ce mata ya tambayeta tana zuwa makaranta tace mashi Eh aji ukku ma take, sake tambayar ta yay yaushe itama zata zo Katsina still murmushin take tace ai tana son zuwa su Baffane suka hana wai tunda Adda Fatuu na can jinjina kai kawae yay daga haka ya wuce Baffa dake tsaye gefe yana masu d'an murmushi yay gaba suka nufi d'akin nashi, bayan tafiyar Abbas gwaggo ma cikin k'uryar d'akin ta shiga ta shiga band'aki ta watso ruwa tazo ta kwanta don ta rage gajiya saidae tunane tunane sun hanata ta hutan don in dae ba fasa auren nan akai ba to fa bazata samu kwanciyar hankali ba gashi bata san ya zasu kwashe da iyayen yaron ba. Sai da akai la'asar wurin k'arfe biyar suka shirya tafiya Jimeta lokacin da ta fito ne ta shiga gaida Yaya duk aka bita da ido yayar ta nuna mata abun zama ta zauna suka gaisa da ita da sauran Mutanan da ta taras a d'akin Yaya ta kya6e baki tace ma gwaggon ashe sai suka sa Amarya ta gudu, yar guntun murmushi kawai gwaggon tayi Yayar tace "to dae ko bata nan sai an d'aura Auren ta gama guje gujenta ta dawo" still gwaggo bata ce mata komae ba don bata son Maganar tay tsawo k'arshe ma sai ta mik'e tay masu sallama ta nufi hanyar fita sauran Mutanan duk suka ta6e baki suka bita da d'an iskan kallo bayan ta fita aka dasa tsegumi har suna cewa a Wurin gwaggon idanun Fatuu suka k'arasa k'ek'ashewa, tana fitowa waje tay ba tare da ta tsaya gaisawa da Ard'o ba don tasan shima surutan zai mata cikin sa'a kuma bai fito waje ba ta nufi Mota da tuni Abbas ya shige dasu Amadu da Kamalu da zai nuna masu hanya Baffan Fatuu dake tsaye yay masu Allah ya kiyaye yasa a dace tace Amin ta shige. Cikin 30 minutes suka isa gidan bayan Abbas yay horn maigadi ya fito suka gaisa ya tambayi daga ina suka ce su baki ne daga rugar Baffa Ard'o yana jin haka yace ko dangin Amaryar Khalid ne banza gwaggo tay sai Kamalu ne yace mashi eh kawae yana washe baki ya juya ya bud'e masu gate d'in suka shiga, har Main falo ya shigar dasu ya fara kwala ma mai aikin Hajiya kira bayan ta fito yace taje ta sanar ma Hajiya ga bak'i anyi dangin Amaryar Khalid ne tace to bayan ta gaishe dasu ta juya, bada jimawa ba sai ga Hajiyar ta Fito tana sanye da doguwar riga jallabiya ta yafa mayafinta ta nufo su fuskarta d'auke da murmushi ta zauna, gaisawa suka shiga yi a mutunce tay masu an zo lafiya gwaggo tace lafiya lau daga baya suka d'an yi shiru can tana murmushi tace "an ce man daga ruga ko?" Gwaggo tace "eh amman ba yan rugar bane daga Katsina muke" Momy tace "Allah sarki yan biki ne kenan, ya hanya an zo lafiya" gwaggo ce ta k'ara amsa mata da lafiya lou lokacin mai aikin ta kawo masu lemu da ruwa ta aje masu ganin basu da niyyar sha Momy na murmushi tace don Allah su sha ruwa lokacin gwaggo tace "dama mun zo wurin mai gidanne in yana nan sai ai mana iso" d'an jimm Momy tay kafin tace "eh yana nan bai dad'e ma da shigowa ba kuwa" gwaggo tace to don Allah a sanar mashi tace to ta mik'e lokacin su Kamalu suka bud'e bottle water d'in da aka kawo suka tsiyaya a cup suna sha ita gwaggo ma bata jin zata iya ko shan ruwan in ba anyita ta k'are ba can sai gata ta dawo bata k'araso cikin parlon ba tace masu bismilla su shigo gwaggo ce ta fara mik'ewa tace ma Amadu yaje ya shigo da Abbas ya amsa da to, parlon chairman ta kai su yana zaune shima jallabiyar ce a jikinshi da murmushi yake kallon su suna shigowa ya nuna masu Sofas alamar su zauna, bayan sun zauna su Abbas suka shigo da sallama ya amsa masu suma ya nuna masu wurin zama duk suka zazzauna, gaisawa suka fara yi cikin girmama juna daga baya shiru ta biyo baya Chairman d'in ne yace yaji ance dangin Amaryar Khalid ne daga Katsina ko gwaggo tace "Eh hakane nice kakarta dake ruk'onta" yana fara'a yace Allah sarki to sun zo lafiya tace lafiya lau Momy ma dake zauna ta k'ara fad'ad'a murmushin ta tace mata sun zo lafiya ta amsa da Alhamdulillah suka k'ara dan yin shiru, again Chairman d'inne yace yaji ance suna son ganin shi Allah yasa lafiya sauke ajiyar zuciya gwaggon tay ta juya ta kalli Amadu tace su jira su a Parlor suka amsa da to had'i da mik'ewa, saida suka fita sannan ta maida kallon ta kan chairman ta fara Magana "Alhaji nasan ba lalle in kun san abun da ke faruwa ba..." da sauri suka had'a ido da Momy kafin ya d'an gyara zama ya tambayeta Mike faruwa ne gwaggo taci gaba "game da auran yaron ku da ita yarinyar waje na, to dae zancen da nike maka ta komo gida tun shekaran jiya tace bata son auren har tayi ikirarin mutuwa zatai in ka d'aura mata aure da shi" waro ido sukae gaba d'aya a rud'e Chairman yace to mi yay zafi haka gwaggo taci ba "koma miya faru Alhaji laifin yaron ku ne shine ya k'ara cusa mata k'iyayyar auren har hakan ta faru sakamakon wasu abubuwa da basu dace ba da ya rink'a yi mata...." Nan gwaggo ta kwashe komae ta fad'a masu a razane su duka suke kallon gwaggo har ta gama kora masu bayani chairman yasa hannu ya kama ha6arshi ya kasa cewa komae ma Saboda Al'ajabi sai faman jinjina kai yake can ya kai hannu gefenshi ya d'auki wayarshi, Khalid ya kira yace komi yake ya bari yazo yanzun nan gida yana son ganin shi daga haka yay cutting kiran, ganin yadda duk fuskokin su suka nuna tsantsar damuwa yasa gwaggo tace masu sai hakuri yara ne ka haife su amman baka haifi halin su ba jinjina kai kawae sukae bada jimawa ba sai ga Khalid d'in don dama yana kan hanya ya kira shi yayi shigar complete black riga mai dogon hannu da ma6allai harda necktie sai bakin wando mahad'in rigar da gani daga wurin aiki yake, da yar sallama ya shigo parlon ya bi bak'in fuskar da ya gani da kallo kafin ya nufi gefen Momy ya zauna suma su Abbas kallon suka bi shi da shi gwaggo a ranta tana raya gashi dai in ka ganshi a ido baka cewa yana da aibu in ma da abunda za'ai mashi sharrin shi to rashin jiki ne, gaida Dad d'in shi yay kaman bazai amsa ba sai kuma k'asa k'asa ya amsa ya kalli Mom d'in shi itama ya gaida ta kafin ya k'ara bin su gwaggo da kallo Chairman ya d'an yi gyaran murya Khalid d'in ya kalle shi yace bai ga Mutane bane sai lokacin ya gaida gwaggo ta amsa mashi tun kafin ya tanka ma Abbas ya d'an d'aga mashi hannu alamar gaisuwa shiru ta sake biyo baya, "Khalid yaushe rabon ka da wadda zaka aura?" Yaji Dad d'in shi ya jefo mashi tambaya idon shi akan shi yace tun shekaran jiya da ya maidata daga wurin gyaran jiki dad d'in yace shikenan basu k'ara had'uwa ba Khalid yace a'a jiya ya kirata yana son yaje saidae bata yi picking ba sai kuma wani uzurin ya taso mashi bai je ba amman d'azun wurin 12:00 yaje sai brother d'in ta yace bata nan sun fita, shiru dad yay yana d'an jinjina kai idanun shi akan carpet Khalid nata bin shi da ido don ya lura da canzawar da yanayin fuskar shi tay, d'agowa chairman yay a kausashe yace "miya kai ka gidan gona da ita???" Rasss gaban Khalid ya fad'i don tambaya ce da bai tsammaci jin ta ba shiru yay ya rasa amsar da zai bashi don yasan tunda yay mashi tambayar to tabbas yasan yaje da ita gidan gonar, har saida ya sake maimaita mashi sannan cikin trembling voice yace "b...ba komae just na biya ne da ita" Dad yace "ka biya da ita ka ci zarafin ta ko!" da sauri ya girgiza mashi kai yace "No Dad na kaita ta ga gidan ne" d'an murmushin takaici Dad d'in yay gwaggo ma ta kya6e baki Abbas kuwa d'an juyar da kan shi yay gefe wani irin haushi yake bashi, Dad yaci gaba "shi maganin bacci da ka saka mata a drink fa ko shima duk cikin ganin gidan ne?" Wani abu Khalid ya had'iya ya shiga motsa baki saidae ya kasa cewa komae ganin haka yasa Dad buga hannun Sofa ya daka mashi tsawa yace "Am asking my Friend!!!" runtse ido kawae Khalid yay bai taba zaton maganar zata je kunnan wani ba bare yay tunanin iyayen shi zasu sani can ya kalli Dad d'in cike da k'arfin hali yace "Dad ban bata wannan ba" duk kowa kallon shi yake Dad d'in ya yamutsa baki yace Ok bari ya d'aukko mashi Al'qur'ani sai ya rantse mashi, ganin yana kokarin tashi yasa da sauri Khalid d'in ya dakatar da shi ta hanyar fad'in "No Dad ba sai ka d'aukko ba it's true na saka mata saidae bada niyya bane sharrin shaidan ne kuma ban cutar da ita ba" komawa yay ya zauna cike da takaici yace "ka bata maganin bacci ka gane mata jiki har ka ta6ata shine baka cutar da ita ba! Idan aka ma k'anwarka Sadeeya haka zaka ji dad'i???" cije lower lip d'in shi yay remorsefully yace "am so sorry dad wllh sharrin zuciya ne tasa naga ai ni zan Aureta amman nasan nayi kuskure don Allah ka yafe man" banza Dad d'in yay mashi ya juya ya kalli Mom d'in shi da ido tay mashi alamar ya duk'a ya bashi hakuri slowly ya sauka on his knees ya shiga bashi hakuri can ya d'ago idanun shi sun yi ja yace ba shi zai ba hakuri ba ga dangin ta nan su suka cancanci ya ba hakuri don su yay ma laifi har suka tako suka zo garin Saboda hakan, juyawa yay ya kalli Gwaggo ya fara bata hak'uri yana yasan yayi ba daidai ba don Allah su yafe mashi Abbas dae sadda kan shi yay yana jinjina shi gwaggo ma rasa abun cewa tay can taji muryar Dad yana fad'in "Don Allah Hajiya ku yi hakuri kaman yadda kika ce yaro ne ka haife shi baka haifi halin shi ba amman ina mai tabbatar maki zan d'auki kwakkwaran mataki kan abun da ya aikata ai man Alfarmar hakan" yana rufe baki Mom ma ta d'auka ta hau bata Hakuri can gwaggo ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace "Hakuri ya zama dole Alhaji tunda aikin gama ya riga da ya gama" gaba d'ayansu murmushi suka saki suna mata godiya ta sake cewa "Amman Alhaji nima ina son in rok'e ka wata Alfarmar kuma ina fatan za'a yi man" jinjina kai Dad yay yace in sha Allahu ta fad'i yana ji, gyara zama gwaggo tay taci gaba "Ina son ka dubi girman Allah ka janye batun auren nan....." Zaro ido sukae shi kam Khalid wani kallo ya bita dashi cikin yar in ina Dad yace "a... amma Hajiya yanzun nan kika ce fa kin hak'ura kuma na fad'a maki zan d'auki mataki to miya kawo Maganar a janye batun auren kuma ko baki hakuran bane?" Girgiza kai tay har idanun ta sun ciko da k'walla tace "dalili na na son a fasa auren shine saboda ba auran had'i bane auren dole ne za'a ma ita yarinyar kuma nasan duk kun san illolin da auren dole ke haifarwa ba kamar yanzu da ita yarinyar ta tsani auren har tana ikirarin mutuwa zatayi in aka mata" dakatawa tay tana goge kwallan da suka fara zubo mata gaba d'aya kan su ya gama d'aurewa ganin tana kuka yasa Chairman cewa "Hajiya ai abun duk bai kai na haka ba kuma ni nasan tun tsawon shekaru ukku na nemi auren ita yarinyar don da bakinta ta fad'a man lokacin tana aji ukku na matuk'ar yabawa da komae nata shiyasa nayi sha'awar ta shigo Family na saidae a lokacin tayi k'arama kuma sai ya kasance shima yaron nawa lokacin yana k'asar waje bai ida gama karatun shi ba shiyasa sai nace a bari ta k'arasa Secondary d'inta ala bashshi in sukae Auren sai taci gaba aka kuma amince man" yana rufe baki gwaggo ta d'auka "to mudai bamu san da Maganar an bada itan ba sai sati biyu zuwa ukku da suka wuce kawae aka kira mu wai za'a zo d'aukar yarinya an bayar da ita, wllh Alhaji bazan 6oye maka ba rabon da in shiga tashin hankali irin na jin wannan batun tun rasa Mahaifiyarta da nai bawai ina k'in ai mata aure bane saidae abu ne da ban ta6a zato ba don nayi tsammanin an bani ita kuma ko za'a raba ni da ita bai kamata a nuna man fin k'arfi ba, ban ta6a samun sa6anin da har nay fushi da ita ba sai akan auren nan, na zubar da kwalla har bansan adadin ta ba ba kuma don komai ba sai Saboda amincewa da tayi wanda ita kanta don bata da yadda zatayi ne Mahaifinta ya kira yana kuka ya sanar mata cewa shima bai son a mata auren amman mahaifin shi Ard'o yace in har bai amince ba zai yafe shi ne kuma dole ya bar mashi gida........." Nan gwaggo ta kwashe duk yadda akai har Fatuu ta taho don amata auren da niyyarta na k'in zuwa biki Saboda bacin ran da take ciki har halin ciwon da take ciki, lokacin da ta gama rufe fuskarta tay tana ta kuka, sam Chairman bai ji dad'in jin abubuwan da suka faru ba don shi ya d'auka tuni sun san da Maganar, sai lokacin Abbas ya fara Magana cikin natsuwa da nuna shi mai ilimi ne ya shiga kwatanta ma Alhajin illar da yin auren zai iya haifarwa tunda har yarinyar ta gudu yanzu to in aka matsa mata za'a iya ganin ba daidai ba don yanzu kwata kwata abun ya fitar mata a rai a k'arshe ya tabbatar ma da Chairman d'in tana da wanda take so kuma shima yana sonta bai k'asar don haka shi abunda yake gani a k'yale ta ta auri wanda take so kawae kar a mata dole don ko addininmu ba'a ce ai ma yarinya dole ba a aure, shiru Chairman yay hannunshi ruk'e da ha6arshi har Abbas ya gama cike da gamsuwa ya shiga jinjina kai kafin ya fara Magana "Duk na fahimci bayanan ku kuma har ga Allah ni dama ba wai son zuciya ne yasa zan had'a auren su ba kawae don yarinyar ta kwanta man ne kuma wllh da ina da wani yaron ba Khalid ba to da shi zan nema ma auren ta, amman yanzu daga abunda ya aikata mata na fahimci sam basu dace da juna ba sannan Hajiya ki sani duk abunda bazan so ya faru da yata ba to bazan so ya faru da yar wani ba tunda d'a ai na kowa ne kuma ta cika yar halak da har ta sadaukar da farin cikinta don mahaifinta ta k'ara burge ni sosae ta cancanci itama a faranta mata Saboda haka zan maki Alfarma kamar yadda kika buk'ata matuk'ar hakan zai saka ki farinciki, Hajiya a yanzu na Janye maganar auren su a barta ta auri wanda take so Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi" ido waje Khalid ke kallon mahaifin nashi har ya rufe baki ita kuwa Hajiya Rabi'atu girgiza kai kawai take sam bata so hakan ya faru ba don tasan wata matsalar ce zata kunno kai tsakanin Khalid da Mahaifin na shi saidae har cikin ranta Gwaggon da Fatuu sun bata tausayi................. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._ [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2034* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *Wannan page kyauta ne a gareki Mommy Kubra ki yadda kika ga dama dashi🤩 Allah ubangiji ya bar mana zumunci Amin🤝😍* *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ..........cike da farinciki gwaggo ta hau yi mashi godiya had'i da Addu'oi yana jinjina mata kai yana fad'in ba komae haka ma Abbas godiyar yay mashi daga baya gwaggo tace kar dai ya gaji don Allah tana k'ara neman Alfarmar yaje suyi Magana da Ard'o yace ba komae yanzu dae yamma tayi amman zuwa da safe yana nan zuwa karta damu duk abunda ya kamata za'a yi sosae suka k'ara yi mashi godiya suka Mik'e zasu tafi Mom ma ta mik'e jikinta duk ya mutu a sanyaye tace su bari su ci Abinci mana Gwaggo tace sun gode wllh saida suka ci Abinci suka taho, ita ta rakosu bayan fitar su Khalid ma ya mik'e zai tafi Dad ya ce bai sallame shi ba ya koma ya zauna, bayan tafiyarsu d'aki Momy ta koma duk ta rasa mi ke mata dad'i ta d'auki wayarta ta kira su Sadeeya suna can suna shirin Bridal shower da zasu yi gobe ta sanar mata da su dakata da komai su dawo gida matsa mata tay da tambayar abunda ya faru nan ta kwashe komae ta fad'i mata ba k'aramin tashi hankalin Sadeeya yay ba Mom na jiyo yadda take ta sakin salati. Tsitt kake ji sai Ac da tv dake ta aiki Chairman nata d'an jinjina kai da k'afa Khalid kuma ya sadda kan shi k'asa sai da aka d'an d'auki lokaci sannan Dad yay ajiyar zuciya cikin karyayyar murya ya fara fad'in "Ka kyauta mun Khalid ka nuna man irin muhimmancin da nike dashi a wurin ka....,amman ka sani ba ni kai mawa ba kan ka kai mawa, kanka ka zubar ma da k'ima da daraja koda yake dama baka da su don duk mai su bazai rungumi sa6on Allah ba....." Dakatawa yay har saida Khalid d'in ya d'an d'ago ya kalle shi kafin yaci gaba "Allah ne shaida ta na fita hakkin ka a matsayi na na uba duk wani hakki na sauke kuma nasan ban yi maka tarbiyar da zata sa ka rink'a sa6a ma Allah ba hasali ma har Al'qur'ani ka sauke ba sau d'aya ba sannan kuma ka haddace wasu bangarori nashi masu yawa amman duk da haka ka za6i take sanin da ke gare ka kake aikata manyan laifukan da Allah ne shaida ta ban aikata su balle in ce abun da nike yi ne nima ake man...." Kwalla ne suka ciko idanun shi ya sa hannu yana gogewa sosae hankalin Khalid ya tashi sai zare ido yake kallonshi Dad yay yace "Khalid ka rasa abun da zaka rink'a aikatawa sai Zina!! duk da ka sani ka karanta kasan illolinta k'asan hukuncin mai aikata ta, mina rage ka dashi ne a rayuwar nan? Duk wata ni'ima Allah ubangiji yayi maka ita ya baka lafiya ya wadata ka ta yadda idan mata hud'u kake so ka aura a rana guda zaka iya amman shine ka za6i sa6a ma wanda yay maka wannan baiwar, Ya Allah! d'ana na ciki na shi ke neman mata shi ke shaye shaye....." Muryar shi ce ta karye ya fashe da kuka a gigice Khalid ya saukko ya durk'ushe a gaban shi ya fara fad'in "billahi Dad kaji na rantse maka na daina tun last Maganar da mukae da kai akan yarinyar nan Danejo ban k'ara aikata hakan da kowa ba, Yes nasan in na 6oye maka bazan 6oye ma Mahallici na ba ina ta6a mata kuma nasan hakan baida kyau kawae son zuciya ne amman nayi maka alk'awarin na daina daga yau Dad kuma ko shaye shaye da kace shima nasan ina yi amman wllh na rage kaji na rantse, don Allah Dad ka daina man kuka kar abun ya k'ara man yawa" dakatawa yay yana goge k'wallan dake zubo mashi duk wannan abun akan idon Mom da tun d'azun ta shigo tana tsaye gefe itama kukan take jin sheshshekar ta yasa Khalid juyowa ya hau rokonta kan ta taya shi rok'on Dad kar ya k'ara yin fushi da shi girgiza kai kawae take dama dalilin auren Fatuu suka k'ulla yarjejeniya har ya amince yasa suka shirya da Mahaifin nashi yanzu kuma ga wannan, matsawa Mom tay itama ta duk'a suka taru suna ta bashi hak'uri, sosae fasa Auren ya ta6a mashi zuciya don yarinyar ta shiga ran shi kuma yana tunanin ta silar ta Khalid d'in zai natsu to amman duk da da laifin Khalid d'in yasan haka Allah ya k'addara yarinyar ba Matar shi bace, can ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya d'ago ya kalle su d'an murmushin takaici yay yace ma Khalid "Ka tashi kaje komi kai don kan ka kuma kowa yay da kyau zaiga da kyau sannan ka sani kayi ma kanka don ban tunanin zaka k'ara samun nagartacciyar Matar aure kaman Yarinyar nan kuma ba baki nay maka ba wllh I assure u sai kayi da na sani u should mark my words" daga haka ya mik'e yay hanyar Bedroom d'in shi ya shige, yana shigewa Mom ma ta mik'e ta bi bayan shi idon Khalid a kan ta, ya rage saura shi kadae tunanin rayuwarshi ya shiga yi tabbas yasan bai kyauta ma kan shi ba abubuwan da yake yi daga zuwa karatu ya biye ma gur6atattun abokai ya canza daga halayar shi mai kyau zuwa maras kyau tabbas yasan ya cuci kan shi, a hankali tunanin shi ya gangaro kan Maganar Dad d'in shi ta k'arshe da ya ce sai yay dana sanin rashin Auren Fatuu ko bai fad'a mashi ba shi yasan yayi asarar mace har mace yarinya ce mai tarin baiwa lokaci guda suffarta ta fara mashi gizo ya dingi tariyo lukkuttan da suka kasance a tare yanzu shikenan ya rasata! Wani Sarawa kan shi yay mashi da k'yar ya yunk'ura ya mik'e hannunshi guda dafe da gaban kan shi ya nufi hanyar fita daga parlon, Uhmmmm dama ance rashin hakuri na rana guda kan iya ja ma mutum dana sani na har Abada Bature kuma yace Once Opportunity lost would never be regain, Allah ya kiyashe mu aikin dana sani ya k'ara shirya mu ya shirya mana zuri'a Amin ya hayyu ya kayyum. Cike da farinciki Gwaggo ke sanar ma dasu yadikko da Baffa lokacin da suka koma kowa yay murnar jin hakan don abu ne da basu tsammaci fasuwar shi cikin sauk'i ba saidae kuma a d'ayan bangaren na zuciyoyin su suna fargabar abunda zaije ya dawo in Ard'o ya sani gwaggo ce ta nuna su kwantar da hankalin su in sha Allahu komae zai zo cikin sauk'i kaman yadda ya faru yanzu. Washe gari Misalin k'arfe 11 na Safe sai ga Chairman Alhaji Lawal harda Hajiya Rabi'atu a Fadar Ard'o suka sauka yasa aka kira kowa manyan gidan harda mata su Yaya da Gwaggo da Baffan Fatuu Abbas da dai sauran su bayan an gaggaisa a nutse cikin Fahimta ya bayyana masu ya janye Maganar aure Saboda yarinyar bata so tana da wanda take son Aure aikuwa nan aka fara zantuttaka Ard'o yace sam baza'a fasa auren ba wllh Yaya ma a harzuk'e take fad'in ba'a fasa shi su za'a maida kananun mutane aja masu abun kunya, harda ce ma Alhaji Lawal duk wannan makarkashiya ce ba wani wanda yarinya ke so komae tsarawa akai don wata manufa ta daban, gwaggo bata tanka ba Abbas ne ya shiga nuna masu da gaske ne tana da wanda take so bai K'asar ne shi Amininsa ne kuma da ya dawo zai zo a d'aura masu auren, da k'yar Alhaji Lawal yasa kowa ya natsu nan ya shiga nuna masu illar dake tattare da yi ma yaro auren dole tunda har bata so to a kyaleta shi bai ji komae ba don yasan komae mukaddari ne daga Allah, Allah ya k'addaro ba Matar yaron shi bace tun bai rufe baki ba Ard'o yace sam fa yana raye hakan bazai faru ba dole abi Maganar shi ai ba itace ta farko da aka fara za6a ma miji ba kuma suma sauran ai basu rasa wad'anda suke so d'in Yaya sai k'ara tunzurashi take tana Kumfar baki haka wasu daga cikin yan uwan Baffan Fatuun ma k'arshe dae da k'yar Alhaji Lawal ya shawo kan Ard'o ta hanyar nuna mashi ita yarinyar a birni ta taso ba za'a had'ata da sauran yara na nan ba kuma a birni in hukuma taji za'a ma yaro auren dole baiso to kuwa d'aukar kwakkwaran mataki suke don har kotu ake zuwa don haka gwara su kyaleta, abun ka da mutumin k'auye da tsoron hukuma ta haka ya samu suka sassauto k'arshe Ardon yace yaji za'a fasan amman sai dae a d'aura da wanda aka ce suna son juna don tayi girma da yawa ba aure kuma shi karatun nasaran ai ana yin shi ko bayan anyi aure ko, har saida cikin Abbas ya Murd'a shi da ya tsara hakan suka d'an saci kallon juna da gwaggo, da k'yar cike da k'arfin hali yay masu bayanin bai nan ne yaje yin wani aiki ne shiyasa ayi hakuri ya dawo Ard'on yace ai ko miji bai kusa ana yin aure ganin yadda ya d'auki zafi sosae yasa Alhaji Lawal sa baki yace ayi hakuri ya dawon sai ita yarinyar ta fara ma karatun ta da k'yar dae aka tankwara kafaffen tsohon harda kukan shi Yaya kam kamar ta had'iya zuciya ta mutu sam Al'amarin bai mata dad'i ba duk da haka bata hak'ura ba saida ta kawo zancen wai to a maida auran kan Mino mana sosae hankalin Baffan su ya tashi bashi kad'ai ba har su gwaggo da Abbas saida hakan ya bayyana a fuskokin su, d'an murmushi Alhaji Lawal yay ya tambayi wacece ita aka ce mashi k'anwar ita Fatun ce still da murmushin yace ya gode amman ba sai anyi hakan ba a k'yaleta ta auri wanda take so itama sannan ya tambayi bata karatu ne Abbas ya bashi amsa da tana yi har ta kai J.s 3 ma, Chairman d'in ya shiga fad'i masu muhimmancin karatun ya'ya mata yace don haka a k'yaleta tay karatun ta, Jama'a zuciyar Yaya zata buga a fusace tace ma Baffa ai sai aje a kwaso masu kayan su tunda ba gadon su za'a ci ba Chairman na a barsu ai ko daga baya a turo a d'auka amman Yaya ta kafe sai an d'aukko, tsamm Gwaggo ta mik'e ta bita da wani mugun kallo bada jimawa ba suka dawo tare da Yadikko dasu Kamalu suka shigo da akwatunan duk da haka saida tasa aka bud'e kowanne wai kada a nemi wani abu a rasa anan aka ga kud'in da Fatuu ta saka Yadikko tace shi Khalid d'in ya bata su ranar da ya zo chairman ya jinjina kai, daga baya taro ya tashi wasu na farinciki yayin da Zuciyoyin wasu ke k'una aka fitar masu da akwatunan suka tafi. A hayye shagali zo kaga farinciki wurin su Gwaggo har bai 6oyuwa. Washe gari Juma'a yanda kasan ranar ake bikin don kuwa musamman Baffa ya yanka masu k'atuwar tunkiya su gwaggo aka hau suya wad'anda suka ga zasu yi ma kan su buk'ulu ba Arzik'i suka shigo akai aikin da su aka yi Abinci mai uban yawa Yaya dai na can zazza6in bak'in ciki ya rufeta, da rana kowa yaci gayun Juma'a aka ci aka sha harda lemuna da Abbas ya kawo daga Jimeta da ya je Salla tare dasu Kamalu, a ranar da yamma sai ga akwatuna guda biyu da kit d'in su daga wurin Chairman yace akai ma Fatuu harda kud'i dubu d'ari kowa yayi tsananin mamakin hakan duk d'inkakkun kayan da akai mata ne a ciki da wasu abubuwan su Cosmetics takalma komae saida aka d'ebo gwaggo murna kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha wai akace hassada ga mai rabo taki ranar dae ta shiga tarihin su, sosae Kamalu ya zagaya da Abbas yaga rugan ya kuma yi hotuna da daddare suka fara shirye shiryen tafiya don dasu Yadikko za'a tafi kamar yadda suka buk'ata Baffa ma na zaune a parlon Abbas kuma basu kaiga dawowa shida su Amadu ba anan yake ma Gwaggo Maganar kayan kitchen d'in Fatun yace daga baya zai sawo su a Mota a maido tace hakan yayi tay mashi Maganar yadda za'ai da kayan d'aki da aka riga aka siya yace wannan ba matsala bane tunda kayan amfani ne yasan za'a samu yadda za'ai dasu zai tuntu6i wad'anda suka yisu ko zasu fanshe su tace to duk yadda ake ciki sai ya sanar mata sai kuma kayan gara nan tace kowanne su d'auki d'ai d'ai suyi amfani dashi buhun shinkafa, taliya, macaroni, aka fiddo su man shanu da su dublan aka zuzzuba su Mino suka hau rabo sauran gidajen har 6angaren Yaya saida aka kai. Washe gari ana gama sallar Asuba aka fara shirin tafiya aka zuba kayan da za'a tafi dasu su shinkafa da akwatunan da aka ba Fatuu a booth bayan duk sun yi sallama da yan gidan suka hau Mota, gwaggo da yadikko sai su Mino a baya gaba kuma Amadu da Kamalu shi Baffa banda shi sai zai maida kaya yana tsaye yana murmushi had'i da d'aga masu hannu suka tafi Katsina za tay di6a su Mino sun kasa 6oye farincikin su yau dae Allah ya kira su zasu je Katsina Yadikko ma bata ta6a zuwa ba haka Kamalu sai fatan Allah ubangiji yasa su isa lafiya Amin. KATSINA TA DIKKO DAKIN KARA KUNYA GARE SU BA DAI TSORO BA. Tun suna kan hanya Fatuu keta faman kira tana tambayar gwaggo sun kawo ina sam bata san da su Yadikko aka taho ba kuma bata san an fasa Auran nata ba don duk inta kira don jin halin da ake ciki sai gwaggo tace mata tay ta Addu'a dai ko jiya da ta kira kaman zatayi kuka ta hau rok'on Gwaggo kan ta fad'i mata wai gabanta sai fad'uwa yake Saboda zullumi nan ma cewa dai tay taci gaba da Addu'a gobe zasu dawo zata ji komi ake ciki, yau da Asuba bayan sun tashi ne gwaggo ta kirata tace mata su koma gida ita da Haulat suyi Abinci mai d'an yawa. Kaman dae lokacin da suka je yau ma cikin ikon Allah kafin la'asar suka iso zo kuga su Mino yan kauye an zo birni sam sun kasa tsaida idanun su a wuri d'aya sai zuba k'auyanci suke su gwaggo da Abbas na masu dariya yadikko ce kadae bata k'auyanci ita da tay zaman Abuja amman har Kamalu kasa rufe baki yay, tun suna shigowa gari Amadu ya kira Fatuu ya sanar mata lokacin da suka isa Unguwar tun kafin su k'arasa kopar gidan suka hangota a tsaye tana sanye da doguwar rigar atampa ta yafa d'an mayafi a kanta ai koda ta gane sune tun kafin Motar ma ta tsaya ta nufo ta da sauri, lokacin da tay arba da su Mino da yadikko kuwa wata uwar k'ara ta fasa ta hau tsalle tana kwad'a ma Haulat kira gaba d'aya gyalenta ma ya fad'i k'asa sai tulin gashinta dake a fake, suma sai murnar ganinta suke kowa baki yak'i rufuwa sai gwaggo ce ta d'aukko gyalenta dake yashe a k'asa ta yafa mata a kan, tana cikin murnar take tambayar yadikko an fasa Auren da sauri Mino tace mata eh, tafin hannuwanta tasa ta rufe baki cike da tsantsar farinciki, gwaggo ce tace to su shiga ciki sai ai murnar da kyau duk suka juya gwaggo ta kalli Abbas dake jingine da Mota tace ya shigo ya ci Abinci amman sai yace mata a'a zai k'arasa gida duk yadda tay dashi yak'i yace kada ta damu, sosae tay mashi godiya da fatan Alkhairi tace sai tazo har gida yanata dae dariya har ta juya sai kuma tace ya d'an jira zata aiko da sak'o a kai ma su Abdul yace to, har Fatuu zata shige gidan sai kuma ta dawo ta tsaya gaban Abbas d'in tana ta washe baki kamar gonar auduga da tsananin mamaki tace "Wai ya Abbas da gaske an fasa Auran?" K'ura mata ido yay da d'an murmushi kaman bazai ce komae ba can yace "Eh an fasa amman an d'aura maki da ni" waro ido tay baki bud'e ganin hakan yasa shi sakin dariya itama sai tay dariyar don ta fahimci wasa yake ta sake tambayar shi wai ya akai aka fasan yace mata ikon Allah sun dogara da shi shiyasa aka samu mafita ta jinjina kai cike da gamsuwa kafin tace "Alhamdulillah" yar dariya Abbas d'in yay ya jinjina mata kai suka d'an yi shiru sai faman kallonta yake har ta kula ta d'an yamutsa fuska sai ya fad'ad'a murmushin shi suna haka Haulat ta fito ruk'e da babbar leda ta ba Abbas tace inji gwaggo ya amsa yay godiya harda tsokanarta wai mai rako Amarya ta gudo ta saki dariya haka Yadikko ma tace mata da ta ganta, juyawa yay ya bud'e back door ya saka bayan ya rufe ya d'ago suka had'a ido da Fatuu yana murmushi yace "Wai Mom Zarah ban ji kin yi Maganar Mutumin naki ba" tace "Wa?" d'age gira yay yace "Wa kike tunanin zan maki Maganar shi ko na Jimetan?" Tura mashi baki tay yasa dariya tace "Wai Ya Haisam ai ya manta da ni" ta d'an d'aure fuska Abbas dake dariya yace "Haba shi ya isa ya manta da Mom Zaraah d'in shi kawae nasan k'ilan aiki ne yay mashi yawa" tace "tun fa da na tafi sau d'aya mukai waya" Abbas yace "kingane bai nan ne Company d'in su sun tura shi wata seminar ina tunani bai samun isasshen time ne" d'an ta6e baki tay yace "shi kike tura ma bakin?" Yar dariya tay tace a'a, sigh yay yace bari ya wuce sai sunyi Magana ta d'aga mashi kai tace ya gaida su Abdul sai tazo ya d'aga mata kai ta wuce gida shi kuma ya shige Mota ya tafi. Koda ta koma cikin gidan farin cikin suka ci gaba da yi anata murna bakin kowannan su yak'i rufuwa su Mino sai santin gidan suke basu kad'ai ba har Yadikko da Kamalu gidan ya burge su a d'aki Fatuu ke tambayar Mino yadda akai aka fasa Auranta tace ita bata sani ba gaskiya, sai bayan da suka huta gwaggo ta k'wala mata kira anan ta nuna mata Akwatunan da aka bata Fatuu was completely speechless tayi matuk'ar mamakin jin an bata su a rud'e ta shiga tambayar gwaggon yadda akai aka fasa har aka bata wannan uban kayan ta kwashe komae ta fad'i mata Yadikko nata yabon kirkin Chairman gwaggon ma tace wllh ita kanta ta matuk'ar yabawa da karamcin da yay masu ta hau yi mashi Addu'oi tana Allah ya shirya mashi yaron nashi da sauran yara ita dae Fatuu shiru tay tana bin ta da ido tunowa da Khalid, gwaggo tace ta kwashe su ta kai d'akinta ta k'wala ma Haulat kira tace su zo ita da Mino, bayan sun maida su d'akinta ne ta fara k'ok'arin gwada kayan wanda ada ta k'i sosae kowanne ya amsheta su Haulat nata santin yadda kayan su kai mata kyau tana fad'in ita gaba ta kaita gobarar titi a Jos Fatuu na dariya tace amman dae ai anyi asarar k'walla galan galan duk suka sa dariya, sai dare Haulat tace zata tafi gwaggo ta bata su dublan tace ta kai ma innarta tay ma Yadikko sallama tana sai tazo gidan su, Fatuu da su Mino ne suka rakata har gida, sosae innar su Haulat tay farinciki da jin zancen an fasa tay ma su Mino an zo lafiya daga baya Haulat ta rako su bakin lungu suka tafi. Washe gari da safe bayan sun yi Breakfast sai ga kiran Abbas bayan sun gaisa yace mata tace ma su Mino su shirya zai zo ya kaisu su ga gari, zo kaga murna ba tare da 6ata lokaci ba suka hau shiri Fatuu ta taimaka masu sukai kwalliyar yan birni Mino ma ita ta bata kaya ta saka koda Kamalu yaji cewa yay aikuwa ba za'a bar shi ba shima ya fara shiri gwaggo tace ma Yadikko itama to ta shirya tace abun yara ta bisu kuwa tace eh mana ba ganin gari bane tace to daman tana so, Wurin k'arfe sha biyu na rana yazo d'aukar su duk sun shirya har Fatuu ma ta d'auki ado da wata fitinannan fitted gown ta Atamfa acikin kayan da aka kawo mata koda ta fito yadikko taga shigar da tayi ga d'an mayafi da bai rufe ta ba sosae kasa hak'uri tay tace mata gaskiya kayan sun kamata kuma ga mayafin ba babba ba gwaggo ta k'arasa fitowa daga cikin d'akinta cikin fad'a take fad'in haka take fama da ita da son saka matsattsun kaya kuma tasan ba kyau, k'arshe cewa tay kodae taje ta saka babban mayafi ko kuma ta cire kayan ba sai an je da ita ba tana tura baki ta koma cikin d'aki, yadda Rigar tay mata sai taji data saka babban mayafi gwara ta cireta ta saka wasu riga da skirt na lace bayan ta d'aura kallabi ta laga mayafin kayan sannan ta fito, koda suka fito waje Abbas na ganin ta yace ta koma ba da ita za'a ba tunda ita ba bak'uwa bace tasan ko ina, cikin sigar shagwa6a tace Allah sai an je da ita Yadikko nata dariya yace su shiga Mota yana ta yaba Kwalliyar su Mino da Aysha suna dariya, Sosae ya zaga gari da su ko ina da yakamata haka ya rink'a siya masu abubuwan ciye ciye har park and zoo ya kai su da Fatuu taga zasu yi k'auyanci sai ta taka masu burki Abbas ya rink'a masu hotuna da wayarshi sai yamma ya wuce da su gidan shi sosae Feenah tay murnar ganin su ta tarbe su hannu bibbiyu bayan sun zazzauna aka shiga gaisawa ta kalli Fatuu cike da zolaya tace "Amarya Sai kika gudo munata shirin zuwa mu sha biki" duk akai dariya daga baya ta tayata murna tace Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi suka amsa da Amin, bada dad'ewa ba Abdul ya dawo daga Tahfiz yana ganin Fatuu ya ruga suka rungume juna bayan ya d'ago yace "Aunty Fatuu Daddy yace man an fasa Auran ki ko" kai ta d'aga mashi ya k'ara cewa "gara da aka fasa dama ban son ki tafi yanzu kin ga sai ki zaman ki anan in ma zaki Auren sai kawae ki auri Baba Zakee kin ga shi Babana ke kuma Mamana" gaba d'aya aka sa dariya Fatun tace to shikenan hakan za'ayi, sai bayan Magrib Abbas yazo maida su Feenah na fad'in kamar kar su tafi sunata dariya harda kayan shafa taba su Mino, Washe gari Monday wurin k'arfe sha d'aya da wani abu Yadikko da Fatuu suna aikin Abincin rana Yadikko na cikin kitchen Fatuu na daga waje tana yanka Alayyahu suna fira taji wayarta ta fara ringing Aysha ta kwad'a mata kira tana fad'in "Adda Fatuu an bugo maki waya" d'an d'aga murya tay tace ta kawo mata, Koda ta kawo mata ta duba screen d'in taga mai kiran nata har saida ta d'an bud'a ido ta d'ago ta kalli yadikko dake kallonta a bakin Kitchen ganin yadda ta kame kanta yasa yadikko yin yar dariya tace halan Ya Handsome ne itama yar dariyar tay ta jinjina mata kai ganin tana niyyar d'auka yasa tace mata ta d'an ke6e mana murmushi kawae tay ta mik'e tana tunanin inda zata can ta nufi d'akin Kawu Amadu Saboda bai nan suna shago shida Kamalu, a bakin mattress d'in shi ta zauna bayan tay picking ta karata a kunne, shiru ba wanda yay Magana har bayan wasu sakannai sannan taji yace "Zaraah" wani yammm taji jikinta yayi harda d'an runtse ido tunda take a rayuwarta bata taba ganin Namijin dake da murya mai sanyin dad'i ba irin ta Haisam, a hankali tace "uhyum" sigh yay kafin ya k'ara cewa "kin picking and u can't talk" d'an tura baki tay kaman yana kallon ta tace "Fushi nike da kai" har saida ta d'an ji sautin murmushin da yay, "Did I offended you?" can taji ya tambaya tana tura baki tace eh sigh ya k'ara yi kafin ya tambayeta tana cikin Mutane ne tace a'a ita kadae ce yace Ok bari ya maida Video Call yaga angry face din tay d'an murmushi, bayan ya maida zaune yake kan Sofa jikin shi sanye da silky sleeping dress riga da wando farare ya zuba mata ido suna kallon juna tana sanye da yar riga v-neck ta mata cib burst d'inta ya fito sosae kanta d'aure da d'an bak'in gyale daya d'an zame bak'in gashinta ya d'an bayyana bai hango skirt d'in dake jikinta ba wanda iya gwuiwa ne don a zaune take, ita shamm tama manta a yadda take Fuskar shi a sake kaman zai murmushi ya tambayeta suna lafiya tace mashi lafiya lou sai kuma taji yace "So tell me laifin mi na maki?" d'an yamutsa fuska tay a d'an shagwa6e wanda hakan yama zame mata jiki tace "ba ka manta dani ba" still yay yanata kallonta kaman bazai tanka ba har saida ta d'an tsargu da kallon ta d'an kauda idonta can taji yace "am sorry it wasn't intentionally, naje wani wuri ne and I have been trying to call but u'r out of reach kinsan k'auyen ku ba Network mai kyau" wani kallon k'asan ido tay mashi kawae sai taga yay dariya har jerarrun fararen hak'oran sa suka d'an bayyana, idasa d'agowa tay tana ta kallon shi ya d'age mata gira ya tambayi ta yi hak'uri bata san ma ta d'aga mashi kai ba alamar eh, ya furta mata "thanks" tay yar dariya, shiru ta d'an biyo baya kafin ta tambaye shi ina Aunty Fanan yace mata tana wurin aiki da d'an alamun mamaki tace amman ba taga kaman dare bane yace eh acan zata kwana ne ta jinjina kai, "Sai kika gudo ko" tura mashi baki tay tana kikkafta ido tace "to ai ni ban son Auren fa" d'an d'age gira yay da d'an murmushi kawae tana dai ta kallon shi ta lura kaman yanayin face d'in shi ya canza yana nan yadda yake saima wani fresh daya k'ara yi gashi ya d'an tara suma a sajen shi ba kaman da ba duk yana lura da kallon da take mashi duk da sai kace ba kallonta yake ba can taji yace ya akai take k'are mashi kallo haka, yar dariya tay dama tasanshi da rashin son kallo tace "naga fuskar ka kaman ta canza" fuska sake yace mi face d'in nashi tay tace kaman ta d'an fad'a ko bai lafiya ne, hannu yasa ya shafi forehead d'in shi slowly yace "Yea but na samu sauk'i" tace Allah ya k'ara sauk'i ya amsa da Amin ta sake cewa "Amman a haka kana ciwon ka tafi wurin da ka ce ka je?" idon shi a kanta yace eh, cikin nuna damuwa tace "ai da sai kace baka lafiya kai zaman ka gida" d'an ta6e baki yay yace "ai ni ba lazy bane kaman ke" waro ido tay tace itace lazy d'in yace "yeah komae kuka" aikuwa a shagwa6e ta fara yarfa hannu tana fad'in wllh ita ba raguwa bace shima ai ya sani still yay yanata kallonta da d'an murmushi komae nata burge shi yake ba kaman in tana shagwa6a duk da ba ita kadai ke mashi hakan ba Fanan ma na yi mashi sosae amman sai yafi ganin kyaun abun in Zaraah tayi, har saida yace wasa yake sannan ta daina mitar, cigaba da firar sukae har yana ce mata daga yanzu in tasan tana cikin Matsala ta rink'a sanar dashi in ma bata same shi ba ko Abbas ne ta kira ta fad'a mashi Koda wani abu ne take so ta amsa mashi da toh, fira tayi fira saiga su Fatuu harda kwanciya kan Katifar shima can ya mik'e ya d'auki laptop d'in ya koma Bedroom d'in shi, gado ya hau ya jingina da headboard ya d'aura laptop d'in akan laps d'in shi, Hira da Masoyi dad'i😍 sai ga Fatuu da fara yin gyangyad'i tun tana yi tana bud'e idon har takai baccin ya kwashe ta dai abun sai ma ya bashi dariya kamar ba ita bace ta tada jijiyar wuya ba don an ce mata lazy, sam ya kasa disconnecting ya kafeta da ido sai kallon face d'in ta yake ba kamar eyelashes d'inta da lips d'inta da tun ba yanzu ba yake ganin kyawun shape d'in su yadda na k'asan yake da d'an fad'i sosae, slowly ya mik'a hannunshi kan screen d'in ya sauke dogon yatsan shi manuni daidai lips d'inta ya fara zagaye su tamkar mai tracing ya d'an d'auki lokaci yana hakan can kuma ya janye hannun ya katse kiran ya maida laptop d'in saman bedside drawer bayan ya rufeta, idasa kwanciya yay idon shi na kallon sama tamkar mai tunanin wani abu a hankali kuma ya lumshe su........... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._ [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2035* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ..........Yadikko tayi zaton wayar suke tayi hakan yasa taci gaba da aikin ita kad'ai, sai da aka kira sallar Azahar su Amadu sun shigo yin salla ne ya ganta baje kan katifarsa tana ta sharar bacci d'an tsoki yay ya girgiza kan shi kaman bazai tashe ta ba sai kuma ganin lokacin salla yayi yasa ya tada ita yace ta je tay salla, tay matuk'ar yin mamakin yadda akai tayi baccin daga yin waya, Koda ta fito bata iske Yadikkon a cikin Kitchen d'in ba don tuni ta gama komae ta wuce d'aki don tayi salla itama Fatuu d'akin ta nufa, jibi su Yadikko zasu tafi hakan yasa washe gari talata suka hau shiri har Kasuwa gwaggo ta rakata tayo siyayya Fatuu duk ta damu bata son su tafi haka ma Mino tun ranar ta fara kuka Fatuu na bata hak'uri gwaggo ma tace mata in sha Allahu bada jimawa ba zata dawo da ita nan ta dae dage da karatun ta tace to, akwati guda na kaya Fatuu ta bata hakan yasa ta washe tana ta murna gwaggo ma tayi masu siyayya sosae shima Kamalu kaya sosae Amadu ya bashi, Washe gari da Asuba Abbas yazo kai su tasha dama tun jiya ya kira Fatuu sanin yau zasu tafin yace zai zo ya kaisu Fatuu ta so bin su tasha amman gwaggo ta hana don kar asa Abbas wahalar dawowa sai Fatan Allah yasa a sauka Lafiya, bayan tafiyar su duk kad'aici ya damu Fatuu don ma Haulat na nan, Ranar Juma'a da daddare bayan Isha Fatuu na zaune tare da gwaggo a Parlor gwaggon na zaune akan Carpet don ba kasaifai take son zama kan kujera ba har ta dad'e Fatuu ce zaune akan kujerar can ta tambayi gwaggon in jarabawar su ta fito a ina zata ci gaba da karatu, d'an jimm tay kafin tace a nan Katsina Fatuu ta d'an bud'a ido tace "amman gwaggo ai ba'a fa karatun Medicine anan sai Kano ko Zaria ko sakkwato" gwaggo dake kallonta ta d'an girgiza kai tace "ina tunanin ai kawae zaki canza abunda zaki karanta ne" da yar damuwa Fatuun ta tambayeta Saboda me tace "gaskiya banson ki tafi wani gari karatu ko ba don komae ba don abunda ya faru kinga yanzu idanun dangin mahaifin ki na akan ki abu kad'an suke jira tunda dama ba son karatun suke ba, ni a shawarce ki fara yin School of Nursing ta nan ala bashshi tunda naji ance gab ake da a fara karatun likitancin anan har an maida Asibitin Medical center na koyarwa don hakan kinga Ko kina cikin karatun aka fara sai ki koma shi in kuma har kika gama wannan d'in ba'a fara ba tunda shekara ukku ne lafiya lou ai shima duk aikin Asibitin ne kuma ko lokacin aka fara karatun likitancin zaki iya yi zaki ma fi jin sauk'in karatun tunda kin karanci abunda ya dangance shi" d'an shiru Fatun tay kamar mai yin tunani bata son abunda zai sa ta k'ara samun sa6ani da gwaggon har ta 6ata mata rai hakan yasa tace Shikenan Allah yasa haka yafi zama Alkhairi murmushin jin dad'i gwaggon tay tace Amin haka yakamata duk abu ya faru da mutum yay fatan kasancewar shi Alkhairi in har ba Alkhairin bane sai kaga Allah ya canza ma, cike da gamsuwa Fatun na yar dariya tace "Hakane gwaggo ni shaida ce" duk suka sa dariya kafin gwaggon tace "in ce dai kun rabu dashi yaron kwata kwata ko?" Fatuu ta gane Khalid take nufi hakan yasa yanayin fuskarta ya d'an canza ta ta6e baki tace "Eh, da dai Farko yana ta takura man da kira har da kina can ma sai yay ta kira na har message ya turo man yana rok'on wai don Allah in yi hakuri in saurare shi yana son muyi wata Magana ne ni kuma kawae sai nayi blocking d'in shi ma" jinjina kai gwaggon tayi tace hakan ya kamata tunda an rabu ba shikenan ba yaje kowa Allah ya had'a shi da rabon shi, can ta d'an kya6e baki tace wai da fa Mino za'a k'ak'aba ma shi, zaro ido Fatuu tay da Al'ajabi tace "Mino kuma!" gwaggon tace "Eh wllh duk tuggun Yaya ne Allah dai ya taimaka hakk'atta bata cimma ruwa ba, in ba don mugun nufi ba ba akwae sauran yara ba a gidan a bashi mana" ta6e baki Fatuu tay ta shiga fad'in ai dama ko itama tasan duk k'ullin su Yayan ne su suka tunzura komae Gwaggon tace "ai da yake da Allah muka dogara kuma shi ba azzalumin bayin shi bane gashi nan ai ya bamu mafita da basu ta6a zata ba" ta k'arasa tana sakin murmushi wanda da gani ba k'aramin dad'i take ji ba a ranta Fatuu dake kallon ta itama tana murmushin tace "Wllh Gwaggo ina son in ga kina farin ciki kyau kike sosae" yar harara ta wurga mata tace bayan ta gama sata kukan da rabon da tayi irin shi har ta manta da sauri Fatuu ta sauka daga kan kujera taje ta rungumeta tana fad'in "Am very sorry my lovely Kakus in sha Allahu bazaki k'ara zubar da hawaye Saboda ni ba zan ta saka ki farin ciki kuma zamu rayu tare har in yi aure inyi ya'ya harda jikoki" sosae gwaggo ke dariya tana fad'in anya bata so kanta ba da yawa ita ina zata kai wannan lokacin da sauri Fatun tace insha Allahu zata kai, jin tak'i ta d'aga daga jikinta yasa gwaggon ce mata ta d'agata ta fara d'aura mata gajiya shiru Fatun bata tanka ba kuma bata d'agata ba hakan yasa gwaggon ta kira sunanta da d'an k'arfi sai lokacin ta d'ago tana d'an murmushi ganin yanayin idonta yasa tace mata badae har tayi bacci ba tana muttsike idonta guda tace Wllh har ta fara gyangyad'i da d'an mamaki gwaggo tasa hannu ta ruk'e ha6arta tace "Wai ni kodae shawara ke damun ki ne Fatuu, na lura dake kwanan nan kin fiye bacci bunu bunu kin 6ingire bacci" tana yar dariya tace "Ramuwar baccin da ban samu yi da ina cikin damuwa ba ne" d'an ta6e baki gwaggo tay Fatuu ta k'ara cewa "Haka rannan ma fa Ya Haisam ya kira ni Video Call muna cikin yin Magana nay bacci ban sani ba" bud'a ido gwaggo tay alamar mamaki sai kuma tace "ashe kun yi Magana bayan kin dawo" Fatuu tace "Eh tun ma su Yadikko na nan" kai gwaggo ta d'aga sai kuma ta tambayeta suna lafiya dai ko Fatuu tace "eh lokacin yace Aunty Fanan ma na wurin aiki amman shi naga fuskarshi kamar ta d'an fad'a shine na tambaye shi ko bai lafiya ne yace eh baijin dad'i amman ya samu sauk'i" girgiza kai gwaggo ta shiga yi alamar jajantawa kafin tace "Allah sarki Allah ya k'aro sauki, amman to kin k'ara kiran nashi kin ji ya jikin ko" d'an bud'a ido Fatuu tay ta girgiza kai alamar a'a gwaggon tace "Amman baki kyauta ba gaskiya ai Kya kira ki ji ya ya k'ara ji ke in kece yaji baki lafiya kina tunanin zai dau kwanaki bayan jin hakan bai kira ki ya k'ara jin ya kike ba?" hannu Fatuu tasa ta rufe baki tana dariya sai kuma ta cire tace to ta kira shi yanzun gwaggon tace haka dae yakamata da sauri ta mik'e ta nufi hanyar fita daga parlon don wayar na d'akinta gwaggo ta bita da ido fuskarta da d'an murmushi har ta fice. Tana shiga ta nufi gado ta fad'a saman shi tay rubda ciki, bayan ta kai hannu ta d'auki wayar tay sending mashi kira saidae har wayar ta katse ba'a d'aga ba tana kokarin sake kiran sai gashi ya kira picking tay ta kara a kunne gudun kada yay complain kamar ranar nan na k'in yin Magana yasa tace "Hello Assalamu alaikum" cikin cool voice en shi ya amsa mata, d'an murmushi tay tace "Ya Handsome ina kwana nasan ku nan safiya ne ko?" d'an murmushi ya saki jin sunan data kira shi dashi ya bata amsa da eh, tace "Dama na kira in ji ya jiki rannan da kace baka jin dad'i" shiru ya d'an yi sai kuma slowly yace ta damu da ciwon da yake ne, tura baki tay a shagwa6e tace "A'a nifa kawae na tuno ne shiyasa na kira", "Dat's mean baki damu da ciwon ba kenan" ya tambaya tace "a'a....na damu ba kai ne ba..." Sai kuma tay shiru ya tambaye ta shine mi tace sai yace ta damu, d'an murmushi mai sauti yay yace to ba gashi tace ta damu ba miya fad'i ba daidai ba, shiru tay ta rasa mi zata ce ma har saida ya kira sunanta a shagwa6e ta amsa yace mata ya warke ya gode da kulawa tace to, bai cika son ya kara waya a kunne yay ta Magana ba hakan yasa ya maida kiran video call yana zaune da gani a Office ne jikinshi sanye da Maroon suit yayi kyau har ya gaji ganin bai ganinta sosae yasashi tambayar ta ba wuta ne tace eh amman ai akwae sola bari ta kunna wannan hasken na rechargeable globe ne ya amsa da Ok, bayan ta kunna haske ya gauraye d'akin ta koma kan gadon ta zauna ta d'age k'afafuwan ta ta jingine wayar ajikin su, tambayar shi tay ya Aunty Fanan yace tana nan lafiya da bud'ar bakinta sai cewa tay wai tana da ciki shiru yay kawae yana bin ta da kallo hakan yasa tasha jinin jikinta ita kanta hakanan taji tayi tambayar ba tare da shiri ba su6utar baki ce, duk ta kame kanta sai nonnoke fuska take ganin yadda take yi yasa shi yin d'an murmushi yace zata zo ne kallon shi tay kaman bazata ce komae ba sai kuma tace tazo ina yace nan in Fanan d'in ta haihu da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a fuskar shi a sake yace "Why ba sai ki mata rainon ba" tana tura baki tace ita bazata yi karatu ba sai raino, yar guntuwar dariya yay sai kuma ya tambayeta yaushe zata ci gaba da karatun ta kwashe yadda sukae da gwaggo ta fad'i mashi a tunaninta ko zai ce zaiyi Magana da gwaggon kan a barta taje tay Medicine d'in amman sai taji yace hakan yayi yace amman ai kaman dole saida Jamb tace a'a taji ana cewa Basic Nursing ba saida Jamb ba yace Ok tace mashi yanzu result kawae take jira yace Ok Allah yasa aga Alkhairi ta amsa da Amin, shiru suka d'an yi can tace mashi yaushe zai zo idon shi akanta ya tambayi tana son ganin shi ne da sauri tace a'a ba gashi ko yanzu tana ganin shi ba kawae ta tambaya ne yay nodding kai kafin yace mata bazai samu zuwa yanzu ba tunda bai dad'e da yazo ba kuma Hajiya daga Abuja zata zo nan ta d'an zauna dasu Saboda ganin likita tace Allah ya bata lafiya ya amsa da Amin daga baya da kanta tace bari ta k'yale shi ta hana shi aiki yay d'an murmushi kawae yace mata take care ta d'aga kai daga haka ta katse kiran, d'akin gwaggo ta nufa don ta fad'i mata ya warke ta iske har tayi bacci. Fatuu an samu natsuwa har ta koma islamiyya washe gari yan islamiyyar sunyi farinciki da ganinta sai tambayarta ake yadda akai ta dawo tace an fasa auren ne kawae Malam Nazifi har ke6ewa yay da ita ya tambayeta Allah yasa dae lafiya ta dawo tace mashi lafiya lou dama bata son auren na dole ne za'a mata to kuma an fasa daga yanayin fuskar shi ta fahimci yaji dad'in hakan yace ba komae bane ya ja hakan face Addu'a shiyasa ake son bawa ya mik'a lamuransa wurin Ubangiji to kuwa a komae zai samu mafita Fatuu ta jinjina kai tay mashi godiya sosae har yana tsokanarta yace sai a dasa rashin ji ko tana dariya tace ai ta daina wannan yanzu ta girma, Washe gari bayan ta dawo daga islamiyyar safe ne Amadu ya shigo d'akinta lokacin tana cikin gyara wardrobe d'inta ta kalleshi tana murmushi shima murmushi yake mata yace "Amaryar mu" tura mashi baki tay tace don Allah ya bari bata so, wayarta ya kawo mata yace ta bashi tashi tace a'a Ya barta kawae yace don me ai itama tana son abunta ko kuma ga Makaranta zata fara tace ai tashin ma lafiya lou daga baya ta canza, duk yadda yay da ita k'in amsa tay k'arshe yay mata godiya ya tafi, acikin satin da ya kama Haulat ta koma Nijar don bikinta bai fi saura sati biyu ba, ranar Laraba sai ga Baffan Fatuu sun kawo Kayanta na kitchen kamar yadda yace Fatuu tay farincikin ganin shi sosae, a d'akin Fatun can gefe akai masu wuri manyan kuma su freezer aka kai su d'akin Amadu bayan sun zauna da gwaggo ta tambaye shi yadda akai da furniture d'in yace wad'anda suka yi su sun fanshe su duk da sun rage kud'in gwaggo ta girgiza kai tace Allah ya kyauta bayan Gwaggo ta tafi Fatuu taje wurin shi d'akin Amadu da aka sauke shi sukai fira anan ya bata kud'i dubu d'ari yace ta d'auki 50k d'inta da ta bashi tay amfani da sauran dubu hamsin d'in gun shirye shiryen fara karatun ta dama cikon dubu d'arin data bashi kud'in sadakin ta ne, k'in amsa tay tace ai ba sai ya maido mata ba itama ai Saboda auren aka bata yana dariya yace to ai ba'ai auren ba ko ta dingi zuba mashi shagwabar bazata amsa ba yana dariya daga baya da k'yar ya sata ta amsa kwanan shi biyu ran Friday ya tafi, Bayan sati guda suka shirya zuwa Niamey K'asar Nijar bikin Haulat harda Kawu Amadu gwaggo tayi masu hidima sosae don kayan kitchen d'in Fatuu ta d'ibar mata masu yawa harda zannuwan gado da labulaye innarsu haulat d'in kafin su tafi lokacin tay tsananin farinciki da yake su da wuri suka tafi su kuma su Fatuu saida bikin ya zo, Tafiya yankin Azaba Fatuu an ji jiki sai lokacin ta gane daga Katsina zuwa Adamawa ba komae bane akan wannan tafiyar da sukae don farko Marad'i suka fara zuwa daga can suka hau luxurious bus suka kwana suna tafiya don ma Motar nada dad'in hawa akwae su Ac harda Tv, lokacin da suka isa da k'yar take iya taka k'afafunta don tafiyar tayi daga Katsina zuwa Lagos in ma bata fi ba, Haulat tay tsananin farinciki da zuwan nasu haka danginsu sun tarbe su hannu bibbiyu an sha shagali an ci an sha anyi wadaqa da nama don mutan Nijar badai cin nama ba bakamar in suna hidima gashi ba Laifi dangin mijin nada d'an hali saidae wani Abincin fa su Fatuu kasa ci sukae sai wanda yay irin namu na nan, Alhamdulillah ranar Asabar aka d'aura auren Haulat da Angonta wanda yake d'an uwanta ne wato Nuraddeen suna zaune Fatuu na dariya tace mata da rabon dae sai ta rigata yin aure duk sukae dariya, Sosae Fatuu akai kasuwa don wanka na Mutunci ta rink'a d'auka da bikin don ma gwaggo na taka mata burki har samari ta hanata saurara tace ba wannan ne a gabanta ba to itama dai dama ba mai kula samarin bace, bayan biki da kwana biyu suka sake d'aukko hanya aka taita yi har Allah ya maido su Lafiya Fatuu cike da kewar Aminiyarta, tun suna can aka saki result d'in Waec suna dawowa Abbas yazo ya dauketa suka je dubawa gaba d'aya ta samu credit saidae chemistry ne ta samu pass tun can ta fara k'walla don bata tsammaci hakan ba sakamakon tasan ta maida hankali lokacin da sukae exams d'in gashi dole saida shi zata iya yin School of nursing din Abbas ne ya shiga kwantar mata da hankali yace a jira Neco ta fito in sha Allahu yasan zata samu, koda ta dawo gida ma gwaggo duk da bata ji dad'i ba amman bata nuna mata damuwa ba sosae itama tace a jira d'ayar daga baya ma sai ga Haisam ya kirata don Abbas ya fad'i mashi komae harda yarda ta tashi hankalinta sosae ya kwantar mata da hankali yace ai akwae alternative so a jira Neco fuska jage jage tace mashi to anan ma saida ya k'ara ce mata lazy ta tura mashi baki daga baya sai gashi har saida yasata dariya, bayan sati biyu Neco ta fito wannan karon k'in zuwa tay dubowar saidae Abbas ne yaje, a k'opar gida ya tsaya bayan ya dawo ya kirata ta fito tunda ya tafi dubowar dama gabanta keta fad'uwa duk ta sha jinin jikinta ba kamar da taga fuskar Abbas d'in bai dariya a gefe ta tsaya ta gaida shi a sanyaye ya amsa duk ya d'an damu kaman zatai kuka tace mashi itama akwae matsala ko ya d'aga mata kai alamar eh nan da nan tasa hannu zata fara matsar kwalla ya fiddo result d'in daga gefen shi ya mik'a mata, k'in amsa tay tace ita mizatai dashi tunda bata ci abunda ake so ba saida ya d'an matsa mata sannan ta amsa ta amman ta k'i dubawar yace ta duba mana, hannunta har rawa yake ta d'aga da ido d'aya ta d'an kalli paper d'in da sauri kuma ta ware idanun a tunaninta ko abunda take gani gizau ne ba gaske ba, tabbatar ma da kanta tay da sauri ta kalli Abbas taga yana murmushi a rud'e tasa hannu ta rufe bakinta ganin ta cinye duka harda su A (distinctions) nan da nan ta fara murna tana yarfa hannu sai faman fad'in Alhamdulillah take Abbas na mata dariya, koda ta shiga gida gwaggo ta gani tay matuk'ar murna harda duk'awa wai Fatun ta hau ta goyata ta kuwa haye aikuwa da k'yar ta mik'e don ma gwaggon k'akk'arfa ce dik'ir take, ganin tana ta nishi yasa Fatun saukkowa tana ta kyalkyatar dariya, Lokacin da aka fara saida Form na Makarantar Abbas ne yaje Bank ya siyo mata ya kawo mata suka cike tare suka maida can School d'in bayan wani lokaci suka je don yin jarabawar shiga wato Entrance exam a lokacin ne ta had'u da wata da suka zauna tare har ta fad'a mata sunanta Fauziyya Ahmad ta tambayi Fatun itama ta fad'i mata nata Fauziyyar tay masu Fatan Nasara Fatuu ta amsa da Amin, bayan sun gama ne tace ma Fatuu ta bata phone no d'inta ta bata don ta lura tana da kirki ga fara'a bunu bunu tayi murmushi, bayan kaman sati biyu da yin jarabawar aka kafe lists d'in wanda suka ci Fauziyya ce ta kira Fatun ta sanar mata ta samu itama haka don taga sunanta cikin yan Katsina local Government itace ma ta biyu sosae Fatuun tay murna duk da da sauran rina a kaba don dama farko sai su d'auki Mutane fin d'ari cikin mutane wurin 500 koma fi da sukai applying sai a hankali za'ai ta zubar da su don bai wuce Mutum 130 ko 150 bane zasu ci entrance exam d'in suma kuma wurin interview za'a k'ara zubar da wasu haka Bayan an fara karatunma, cikin Nasara Fatuu taci interview da sukae ta samu Admission d'in Kasimu Kopar Bai School Of Nursing Katsina dake acikin General Hospital, kowa yay farin ciki karma dae gwaggo taji haka Abbas ma har Haisam saida ya kira ya tayata murna daga baya suka fara Class ranar farko har Video call sukai da Haisam tana cikin fararen Uniform d'inta da takalma sai faman zabga dariyar dad'i take ya k'ara tayata murna ya kuma ce sai ta d'age don still bata zama cikakkar daliba ba har sai tayi passing Intro Exam tace in sha Allahu, tun ranar da suka je interview Fauzy kamar yadda Fatun ta fara kiranta dama kuma tace haka ake ce mata ta tambayi Fatuu Day zatai ko Boarding tace mata Day Fauzyn tace mi zai hana tayi Boarding don itama ita zatai Fatuu ta tambayeta ba'a nan garin take bane tace eh ita yar Funtua ce amman akwae Yayarta dake Aure nan Katsina a Goruba Road, Fatuu tace to ba sai ta zauna a wurinta ba Fauzyn tace ita tafi son zama a school don mutum yafi samun time na karatu balle wannan Makarantar da ba'a wasa da karatu dole sai Mutum ya dage zadai ta rink'a zuwa wurinta weekend, to bayan sun fara shiga Class ma saida ta k'ara yi ma Fatuu Maganar tace an bata d'aki dama akwae wata yar garinsu da suka gama a d'akinsu zata zauna Don Allah ta dawo boarding sai su zauna tare ganin yadda ta dage tana ta nuna mata Muhimmancin zama a cikin Makaranta ne yasa Fatuu tace to in ta koma gida zata tambaya in an barta sai ta dawo Fauzy harda yi mata Addu'ar Allah yasa a barta ita dae Fatuu yar dariya kawae tay, A ranar da daddare bayan sallar Magrib ta iske gwaggo a d'aki ta gama salla ta zauna gefenta bayan tay mata sannu ne tayi mata Maganar komawarta boarding, shiru gwaggo tay tana kallonta can ta nisa ta tambaye ta miyasa take son zama a Makarantar Fatun tace an fi samun lokaci kuma ko Assignment aka bada mai wuya za'a taru ayi tare sannan ana tattaunawa game da abunda aka koya, d'an jimm gwaggo tay kafin tace "Gaskiya ni banson zaman Makarantar nan don yana da illoli ba kuma wai don ban yarda dake bane amman nafi son ki rink'a zuwa kina dawowa" gyad'a kai Fatuu tay tace Shikenan Gwaggo ta fahimci yanzu duk inta nuna ga yadda take son abu bata gardama mata hakan yasa tace mata in kamar an basu aikin ko zasu tattauna kan karatun zata iya tsayawa can amman ba wai ta koma gaba d'aya ba Fatun tace to ta tashi ta koma d'akinta............ _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._*ASM Bk2035* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ..........Yadikko tayi zaton wayar suke tayi hakan yasa taci gaba da aikin ita kad'ai, sai da aka kira sallar Azahar su Amadu sun shigo yin salla ne ya ganta baje kan katifarsa tana ta sharar bacci d'an tsoki yay ya girgiza kan shi kaman bazai tashe ta ba sai kuma ganin lokacin salla yayi yasa ya tada ita yace ta je tay salla, tay matuk'ar yin mamakin yadda akai tayi baccin daga yin waya, Koda ta fito bata iske Yadikkon a cikin Kitchen d'in ba don tuni ta gama komae ta wuce d'aki don tayi salla itama Fatuu d'akin ta nufa, jibi su Yadikko zasu tafi hakan yasa washe gari talata suka hau shiri har Kasuwa gwaggo ta rakata tayo siyayya Fatuu duk ta damu bata son su tafi haka ma Mino tun ranar ta fara kuka Fatuu na bata hak'uri gwaggo ma tace mata in sha Allahu bada jimawa ba zata dawo da ita nan ta dae dage da karatun ta tace to, akwati guda na kaya Fatuu ta bata hakan yasa ta washe tana ta murna gwaggo ma tayi masu siyayya sosae shima Kamalu kaya sosae Amadu ya bashi, Washe gari da Asuba Abbas yazo kai su tasha dama tun jiya ya kira Fatuu sanin yau zasu tafin yace zai zo ya kaisu Fatuu ta so bin su tasha amman gwaggo ta hana don kar asa Abbas wahalar dawowa sai Fatan Allah yasa a sauka Lafiya, bayan tafiyar su duk kad'aici ya damu Fatuu don ma Haulat na nan, Ranar Juma'a da daddare bayan Isha Fatuu na zaune tare da gwaggo a Parlor gwaggon na zaune akan Carpet don ba kasaifai take son zama kan kujera ba har ta dad'e Fatuu ce zaune akan kujerar can ta tambayi gwaggon in jarabawar su ta fito a ina zata ci gaba da karatu, d'an jimm tay kafin tace a nan Katsina Fatuu ta d'an bud'a ido tace "amman gwaggo ai ba'a fa karatun Medicine anan sai Kano ko Zaria ko sakkwato" gwaggo dake kallonta ta d'an girgiza kai tace "ina tunanin ai kawae zaki canza abunda zaki karanta ne" da yar damuwa Fatuun ta tambayeta Saboda me tace "gaskiya banson ki tafi wani gari karatu ko ba don komae ba don abunda ya faru kinga yanzu idanun dangin mahaifin ki na akan ki abu kad'an suke jira tunda dama ba son karatun suke ba, ni a shawarce ki fara yin School of Nursing ta nan ala bashshi tunda naji ance gab ake da a fara karatun likitancin anan har an maida Asibitin Medical center na koyarwa don hakan kinga Ko kina cikin karatun aka fara sai ki koma shi in kuma har kika gama wannan d'in ba'a fara ba tunda shekara ukku ne lafiya lou ai shima duk aikin Asibitin ne kuma ko lokacin aka fara karatun likitancin zaki iya yi zaki ma fi jin sauk'in karatun tunda kin karanci abunda ya dangance shi" d'an shiru Fatun tay kamar mai yin tunani bata son abunda zai sa ta k'ara samun sa6ani da gwaggon har ta 6ata mata rai hakan yasa tace Shikenan Allah yasa haka yafi zama Alkhairi murmushin jin dad'i gwaggon tay tace Amin haka yakamata duk abu ya faru da mutum yay fatan kasancewar shi Alkhairi in har ba Alkhairin bane sai kaga Allah ya canza ma, cike da gamsuwa Fatun na yar dariya tace "Hakane gwaggo ni shaida ce" duk suka sa dariya kafin gwaggon tace "in ce dai kun rabu dashi yaron kwata kwata ko?" Fatuu ta gane Khalid take nufi hakan yasa yanayin fuskarta ya d'an canza ta ta6e baki tace "Eh, da dai Farko yana ta takura man da kira har da kina can ma sai yay ta kira na har message ya turo man yana rok'on wai don Allah in yi hakuri in saurare shi yana son muyi wata Magana ne ni kuma kawae sai nayi blocking d'in shi ma" jinjina kai gwaggon tayi tace hakan ya kamata tunda an rabu ba shikenan ba yaje kowa Allah ya had'a shi da rabon shi, can ta d'an kya6e baki tace wai da fa Mino za'a k'ak'aba ma shi, zaro ido Fatuu tay da Al'ajabi tace "Mino kuma!" gwaggon tace "Eh wllh duk tuggun Yaya ne Allah dai ya taimaka hakk'atta bata cimma ruwa ba, in ba don mugun nufi ba ba akwae sauran yara ba a gidan a bashi mana" ta6e baki Fatuu tay ta shiga fad'in ai dama ko itama tasan duk k'ullin su Yayan ne su suka tunzura komae Gwaggon tace "ai da yake da Allah muka dogara kuma shi ba azzalumin bayin shi bane gashi nan ai ya bamu mafita da basu ta6a zata ba" ta k'arasa tana sakin murmushi wanda da gani ba k'aramin dad'i take ji ba a ranta Fatuu dake kallon ta itama tana murmushin tace "Wllh Gwaggo ina son in ga kina farin ciki kyau kike sosae" yar harara ta wurga mata tace bayan ta gama sata kukan da rabon da tayi irin shi har ta manta da sauri Fatuu ta sauka daga kan kujera taje ta rungumeta tana fad'in "Am very sorry my lovely Kakus in sha Allahu bazaki k'ara zubar da hawaye Saboda ni ba zan ta saka ki farin ciki kuma zamu rayu tare har in yi aure inyi ya'ya harda jikoki" sosae gwaggo ke dariya tana fad'in anya bata so kanta ba da yawa ita ina zata kai wannan lokacin da sauri Fatun tace insha Allahu zata kai, jin tak'i ta d'aga daga jikinta yasa gwaggon ce mata ta d'agata ta fara d'aura mata gajiya shiru Fatun bata tanka ba kuma bata d'agata ba hakan yasa gwaggon ta kira sunanta da d'an k'arfi sai lokacin ta d'ago tana d'an murmushi ganin yanayin idonta yasa tace mata badae har tayi bacci ba tana muttsike idonta guda tace Wllh har ta fara gyangyad'i da d'an mamaki gwaggo tasa hannu ta ruk'e ha6arta tace "Wai ni kodae shawara ke damun ki ne Fatuu, na lura dake kwanan nan kin fiye bacci bunu bunu kin 6ingire bacci" tana yar dariya tace "Ramuwar baccin da ban samu yi da ina cikin damuwa ba ne" d'an ta6e baki gwaggo tay Fatuu ta k'ara cewa "Haka rannan ma fa Ya Haisam ya kira ni Video Call muna cikin yin Magana nay bacci ban sani ba" bud'a ido gwaggo tay alamar mamaki sai kuma tace "ashe kun yi Magana bayan kin dawo" Fatuu tace "Eh tun ma su Yadikko na nan" kai gwaggo ta d'aga sai kuma ta tambayeta suna lafiya dai ko Fatuu tace "eh lokacin yace Aunty Fanan ma na wurin aiki amman shi naga fuskarshi kamar ta d'an fad'a shine na tambaye shi ko bai lafiya ne yace eh baijin dad'i amman ya samu sauk'i" girgiza kai gwaggo ta shiga yi alamar jajantawa kafin tace "Allah sarki Allah ya k'aro sauki, amman to kin k'ara kiran nashi kin ji ya jikin ko" d'an bud'a ido Fatuu tay ta girgiza kai alamar a'a gwaggon tace "Amman baki kyauta ba gaskiya ai Kya kira ki ji ya ya k'ara ji ke in kece yaji baki lafiya kina tunanin zai dau kwanaki bayan jin hakan bai kira ki ya k'ara jin ya kike ba?" hannu Fatuu tasa ta rufe baki tana dariya sai kuma ta cire tace to ta kira shi yanzun gwaggon tace haka dae yakamata da sauri ta mik'e ta nufi hanyar fita daga parlon don wayar na d'akinta gwaggo ta bita da ido fuskarta da d'an murmushi har ta fice. Tana shiga ta nufi gado ta fad'a saman shi tay rubda ciki, bayan ta kai hannu ta d'auki wayar tay sending mashi kira saidae har wayar ta katse ba'a d'aga ba tana kokarin sake kiran sai gashi ya kira picking tay ta kara a kunne gudun kada yay complain kamar ranar nan na k'in yin Magana yasa tace "Hello Assalamu alaikum" cikin cool voice en shi ya amsa mata, d'an murmushi tay tace "Ya Handsome ina kwana nasan ku nan safiya ne ko?" d'an murmushi ya saki jin sunan data kira shi dashi ya bata amsa da eh, tace "Dama na kira in ji ya jiki rannan da kace baka jin dad'i" shiru ya d'an yi sai kuma slowly yace ta damu da ciwon da yake ne, tura baki tay a shagwa6e tace "A'a nifa kawae na tuno ne shiyasa na kira", "Dat means baki damu da ciwon ba kenan" ya tambaya tace "a'a....na damu ba kai ne ba..." Sai kuma tay shiru ya tambaye ta shine mi tace sai yace ta damu, d'an murmushi mai sauti yay yace to ba gashi tace ta damu ba miya fad'i ba daidai ba, shiru tay ta rasa mi zata ce ma har saida ya kira sunanta a shagwa6e ta amsa yace mata ya warke ya gode da kulawa tace to, bai cika son ya kara waya a kunne yay ta Magana ba hakan yasa ya maida kiran video call yana zaune da gani a Office ne jikinshi sanye da Maroon suit yayi kyau har ya gaji ganin bai ganinta sosae yasashi tambayar ta ba wuta ne tace eh amman ai akwae sola bari ta kunna wannan hasken na rechargeable globe ne ya amsa da Ok, bayan ta kunna haske ya gauraye d'akin ta koma kan gadon ta zauna ta d'age k'afafuwan ta ta jingine wayar ajikin su, tambayar shi tay ya Aunty Fanan yace tana nan lafiya da bud'ar bakinta sai cewa tay wai tana da ciki shiru yay kawae yana bin ta da kallo hakan yasa tasha jinin jikinta ita kanta hakanan taji tayi tambayar ba tare da shiri ba su6utar baki ce, duk ta kame kanta sai nonnoke fuska take ganin yadda take yi yasa shi yin d'an murmushi yace zata zo ne kallon shi tay kaman bazata ce komae ba sai kuma tace tazo ina yace nan in Fanan d'in ta haihu da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a fuskar shi a sake yace "Why ba sai ki mata rainon ba" tana tura baki tace ita bazata yi karatu ba sai raino, yar guntuwar dariya yay sai kuma ya tambayeta yaushe zata ci gaba da karatun ta kwashe yadda sukae da gwaggo ta fad'i mashi a tunaninta ko zai ce zaiyi Magana da gwaggon kan a barta taje tay Medicine d'in amman sai taji yace hakan yayi yace amman ai kaman dole saida Jamb tace a'a taji ana cewa Basic Nursing ba saida Jamb ba yace Ok tace mashi yanzu result kawae take jira yace Ok Allah yasa aga Alkhairi ta amsa da Amin, shiru suka d'an yi can tace mashi yaushe zai zo idon shi akanta ya tambayi tana son ganin shi ne da sauri tace a'a ba gashi ko yanzu tana ganin shi ba kawae ta tambaya ne yay nodding kai kafin yace mata bazai samu zuwa yanzu ba tunda bai dad'e da yazo ba kuma Hajiya daga Abuja zata zo nan ta d'an zauna dasu Saboda ganin likita tace Allah ya bata lafiya ya amsa da Amin daga baya da kanta tace bari ta k'yale shi ta hana shi aiki yay d'an murmushi kawae yace mata take care ta d'aga kai daga haka ta katse kiran, d'akin gwaggo ta nufa don ta fad'i mata ya warke ta iske har tayi bacci. Fatuu an samu natsuwa har ta koma islamiyya washe gari yan islamiyyar sunyi farinciki da ganinta sai tambayarta ake yadda akai ta dawo tace an fasa auren ne kawae Malam Nazifi har ke6ewa yay da ita ya tambayeta Allah yasa dae lafiya ta dawo tace mashi lafiya lou dama bata son auren na dole ne za'a mata to kuma an fasa daga yanayin fuskar shi ta fahimci yaji dad'in hakan yace ba komae bane ya ja hakan face Addu'a shiyasa ake son bawa ya mik'a lamuransa wurin Ubangiji to kuwa a komae zai samu mafita Fatuu ta jinjina kai tay mashi godiya sosae har yana tsokanarta yace sai a dasa rashin ji ko tana dariya tace ai ta daina wannan yanzu ta girma, Washe gari bayan ta dawo daga islamiyyar safe ne Amadu ya shigo d'akinta lokacin tana cikin gyara wardrobe d'inta ta kalleshi tana murmushi shima murmushi yake mata yace "Amaryar mu" tura mashi baki tay tace don Allah ya bari bata so, wayarta ya kawo mata yace ta bashi tashi tace a'a Ya barta kawae yace don me ai itama tana son abunta ko kuma ga Makaranta zata fara tace ai tashin ma lafiya lou daga baya ta canza, duk yadda yay da ita k'in amsa tay k'arshe yay mata godiya ya tafi, acikin satin da ya kama Haulat ta koma Nijar don bikinta bai fi saura sati biyu ba, ranar Laraba sai ga Baffan Fatuu sun kawo Kayanta na kitchen kamar yadda yace Fatuu tay farincikin ganin shi sosae, a d'akin Fatun can gefe akai masu wuri manyan kuma su freezer aka kai su d'akin Amadu bayan sun zauna da gwaggo ta tambaye shi yadda akai da furniture d'in yace wad'anda suka yi su sun fanshe su duk da sun rage kud'in gwaggo ta girgiza kai tace Allah ya kyauta bayan Gwaggo ta tafi Fatuu taje wurin shi d'akin Amadu da aka sauke shi sukai fira anan ya bata kud'i dubu d'ari yace ta d'auki 50k d'inta da ta bashi tay amfani da sauran dubu hamsin d'in gun shirye shiryen fara karatun ta dama cikon dubu d'arin data bashi kud'in sadakin ta ne, k'in amsa tay tace ai ba sai ya maido mata ba itama ai Saboda auren aka bata yana dariya yace to ai ba'ai auren ba ko ta dingi zuba mashi shagwabar bazata amsa ba yana dariya daga baya da k'yar ya sata ta amsa kwanan shi biyu ran Friday ya tafi, Bayan sati guda suka shirya zuwa Niamey K'asar Nijar bikin Haulat harda Kawu Amadu gwaggo tayi masu hidima sosae don kayan kitchen d'in Fatuu ta d'ibar mata masu yawa harda zannuwan gado da labulaye innarsu haulat d'in kafin su tafi lokacin tay tsananin farinciki da yake su da wuri suka tafi su kuma su Fatuu saida bikin ya zo, Tafiya yankin Azaba Fatuu an ji jiki sai lokacin ta gane daga Katsina zuwa Adamawa ba komae bane akan wannan tafiyar da sukae don farko Marad'i suka fara zuwa daga can suka hau luxurious bus suka kwana suna tafiya don ma Motar nada dad'in hawa akwae su Ac harda Tv, lokacin da suka isa da k'yar take iya taka k'afafunta don tafiyar tayi daga Katsina zuwa Lagos in ma bata fi ba, Haulat tay tsananin farinciki da zuwan nasu haka danginsu sun tarbe su hannu bibbiyu an sha shagali an ci an sha anyi wadaqa da nama don mutan Nijar badai cin nama ba bakamar in suna hidima gashi ba Laifi dangin mijin nada d'an hali saidae wani Abincin fa su Fatuu kasa ci sukae sai wanda yay irin namu na nan, Alhamdulillah ranar Asabar aka d'aura auren Haulat da Angonta wanda yake d'an uwanta ne wato Nuraddeen suna zaune Fatuu na dariya tace mata da rabon dae sai ta rigata yin aure duk sukae dariya, Sosae Fatuu akai kasuwa don wanka na Mutunci ta rink'a d'auka da bikin don ma gwaggo na taka mata burki har samari ta hanata saurara tace ba wannan ne a gabanta ba to itama dai dama ba mai kula samarin bace, bayan biki da kwana biyu suka sake d'aukko hanya aka taita yi har Allah ya maido su Lafiya Fatuu cike da kewar Aminiyarta, tun suna can aka saki result d'in Waec suna dawowa Abbas yazo ya dauketa suka je dubawa gaba d'aya ta samu credit saidae chemistry ne ta samu pass tun can ta fara k'walla don bata tsammaci hakan ba sakamakon tasan ta maida hankali lokacin da sukae exams d'in gashi dole saida shi zata iya yin School of nursing din Abbas ne ya shiga kwantar mata da hankali yace a jira Neco ta fito in sha Allahu yasan zata samu, koda ta dawo gida ma gwaggo duk da bata ji dad'i ba amman bata nuna mata damuwa ba sosae itama tace a jira d'ayar daga baya ma sai ga Haisam ya kirata don Abbas ya fad'i mashi komae harda yarda ta tashi hankalinta sosae ya kwantar mata da hankali yace ai akwae alternative so a jira Neco fuska jage jage tace mashi to anan ma saida ya k'ara ce mata lazy ta tura mashi baki daga baya sai gashi har saida yasata dariya, bayan sati biyu Neco ta fito wannan karon k'in zuwa tay dubowar saidae Abbas ne yaje, a k'opar gida ya tsaya bayan ya dawo ya kirata ta fito tunda ya tafi dubowar dama gabanta keta fad'uwa duk ta sha jinin jikinta ba kamar da taga fuskar Abbas d'in bai dariya a gefe ta tsaya ta gaida shi a sanyaye ya amsa duk ya d'an damu kaman zatai kuka tace mashi itama akwae matsala ko ya d'aga mata kai alamar eh nan da nan tasa hannu zata fara matsar kwalla ya fiddo result d'in daga gefen shi ya mik'a mata, k'in amsa tay tace ita mizatai dashi tunda bata ci abunda ake so ba saida ya d'an matsa mata sannan ta amsa ta amman ta k'i dubawar yace ta duba mana, hannunta har rawa yake ta d'aga da ido d'aya ta d'an kalli paper d'in da sauri kuma ta ware idanun a tunaninta ko abunda take gani gizau ne ba gaske ba, tabbatar ma da kanta tay da sauri ta kalli Abbas taga yana murmushi a rud'e tasa hannu ta rufe bakinta ganin ta cinye duka harda su A (distinctions) nan da nan ta fara murna tana yarfa hannu sai faman fad'in Alhamdulillah take Abbas na mata dariya, koda ta shiga gida gwaggo ta gani tay matuk'ar murna harda duk'awa wai Fatun ta hau ta goyata ta kuwa haye aikuwa da k'yar ta mik'e don ma gwaggon k'akk'arfa ce dik'ir take, ganin tana ta nishi yasa Fatun saukkowa tana ta kyalkyatar dariya, Lokacin da aka fara saida Form na Makarantar Abbas ne yaje Bank ya siyo mata ya kawo mata suka cike tare suka maida can School d'in bayan wani lokaci suka je don yin jarabawar shiga wato Entrance exam a lokacin ne ta had'u da wata da suka zauna tare har ta fad'a mata sunanta Fauziyya Ahmad ta tambayi Fatun itama ta fad'i mata nata Fauziyyar tay masu Fatan Nasara Fatuu ta amsa da Amin, bayan sun gama ne tace ma Fatuu ta bata phone no d'inta ta bata don ta lura tana da kirki ga fara'a bunu bunu tayi murmushi, bayan kaman sati biyu da yin jarabawar aka kafe lists d'in wanda suka ci Fauziyya ce ta kira Fatun ta sanar mata ta samu itama haka don taga sunanta cikin yan Katsina local Government itace ma ta biyu sosae Fatuun tay murna duk da da sauran rina a kaba don dama farko sai su d'auki Mutane fin d'ari cikin mutane wurin 500 koma fi da sukai applying sai a hankali za'ai ta zubar da su don bai wuce Mutum 130 ko 150 bane zasu ci entrance exam d'in suma kuma wurin interview za'a k'ara zubar da wasu haka Bayan an fara karatunma, cikin Nasara Fatuu taci interview da sukae ta samu Admission d'in Kasimu Kopar Bae School Of Nursing Katsina dake acikin General Hospital, kowa yay farin ciki karma dae gwaggo taji haka Abbas ma har Haisam saida ya kira ya tayata murna daga baya suka fara Class ranar farko har Video call sukai da Haisam tana cikin fararen Uniform d'inta da takalma sai faman zabga dariyar dad'i take ya k'ara tayata murna ya kuma ce sai ta d'age don still bata zama cikakkar daliba ba har sai tayi passing Intro Exam tace in sha Allahu, tun ranar da suka je interview Fauzy kamar yadda Fatun ta fara kiranta dama kuma tace haka ake ce mata ta tambayi Fatuu Day zatai ko Boarding tace mata Day Fauzyn tace mi zai hana tayi Boarding don itama ita zatai Fatuu ta tambayeta ba'a nan garin take bane tace eh ita yar Funtua ce amman akwae Yayarta dake Aure nan Katsina a Goruba Road, Fatuu tace to ba sai ta zauna a wurinta ba Fauzyn tace ita tafi son zama a school don mutum yafi samun time na karatu balle wannan Makarantar da ba'a wasa da karatu dole sai Mutum ya dage zadai ta rink'a zuwa wurinta weekend, to bayan sun fara shiga Class ma saida ta k'ara yi ma Fatuu Maganar tace an bata d'aki dama akwae wata yar garinsu da suka gama a d'akinsu zata zauna Don Allah ta dawo boarding sai su zauna tare ganin yadda ta dage tana ta nuna mata Muhimmancin zama a cikin Makaranta ne yasa Fatuu tace to in ta koma gida zata tambaya in an barta sai ta dawo Fauzy harda yi mata Addu'ar Allah yasa a barta ita dae Fatuu yar dariya kawae tay, A ranar da daddare bayan sallar Magrib ta iske gwaggo a d'aki ta gama salla ta zauna gefenta bayan tay mata sannu ne tayi mata Maganar komawarta boarding, shiru gwaggo tay tana kallonta can ta nisa ta tambaye ta miyasa take son zama a Makarantar Fatun tace an fi samun lokaci kuma ko Assignment aka bada mai wuya za'a taru ayi tare sannan ana tattaunawa game da abunda aka koya, d'an jimm gwaggo tay kafin tace "Gaskiya ni banson zaman Makarantar nan don yana da illoli ba kuma wai don ban yarda dake bane amman nafi son ki rink'a zuwa kina dawowa" gyad'a kai Fatuu tay tace Shikenan Gwaggo ta fahimci yanzu duk inta nuna ga yadda take son abu bata gardama mata hakan yasa tace mata in kamar an basu aikin ko zasu tattauna kan karatun zata iya tsayawa can amman ba wai ta koma gaba d'aya ba Fatun tace to ta tashi ta koma d'akinta............ _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._ [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2037* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........A bakin gate ta tsaya suka gaisa da Officer har yana ce mata yaushe za'ai mashi allura tana dariya tace sai ya shirya daga haka ta shige, lokacin data shiga Parlon ba kowa saidae a gyare yake tsab sai daddadan k'amshi ne ke tashi, Bedroom d'in Hajiya ta wuce ta tura ta shiga a hankali da yar sallama idonta suka sauka akan Hajiyar dake kwance saman gado ta d'ago kai don ganin mai shigowa suna had'a ido Fatuu ta sakar mata murmushi Hajiya ta yunk'ura tana kokarin tashi zaune itama da murmushin akan fuskarta, daga gaban gadon ta tsaya tace "Hajiyar Sanata ina wuni an dawo lafiya" da hannu ta nuna mata gefen ta alamar ta zauna tana amsa gaisuwar tata, dafa Shoulder d'inta tay da murmushi tace "Ma sha Allahu Fateema yar Makaranta naji dad'in ganin ki haka sosae, ashe abu haka ya kasance da bani nan?" Kai Fatuu ta d'aga a hankali tace mata eh, tace "An gode ma Allah daya kawo k'arshen Al'amarin cikin sauk'i duk aikin Addu'a ne da kuma biyayya da kika ma mahaifin ki shiyasa ya za6a maki abunda yafi zama Alkhairi" ita dae Fatuu murmushi kawae take can tace mata ya jiki still da fara'a ta amsa "Ah k'afa Alhamdulillah na samu sauk'i tuni fa sune suka hana ni dawowa wai sai in zauna can" yar dariya Fatuu tay tace "suna son su rink'a ganinki a kusa dasu ne Hajiya" ta6e baki tay "suda suke tafiyar su aiki su barni yini zungur daga ni sai mai aiki to ba gwara a k'yale ni in dawo ba, shiyasa ina ganin Azumi ya taho nace to wllh gida zan dawo in yi shi cikin yan'uwana ba Arziki da suka ga ina niyyar hana masu sukuni aka barni na dawo" ta k'arasa tana yar dariya itama Fatun dariyar take Hajiyar tace "To ya Karatun Fateema ana maida hankali ko" kai ta d'aga tace mata eh sosae, tace "Kin iya allura?" Fatuu na dariya tace "na iya ta tuni bama ita kadae ba na iya abubuwan duk da aka nuna mana sosae don yanzu muna cikin Asibiti ne" jinjina kai Hajiya tay tace "Ma sha Allahu kice ni yanzu ina da mai duba ni a gida, Allah Ubangiji yasa ma karatun Albarka ya bada sa'a Amin" itama Fatuu ta amsa da Amin, shiru suka d'an yi can Hajiyar tace "Fateema kije ki ci Abinci naga kaman yanzu Kika dawo daga Makarantar dama Akwae na Yayan ki da bai ci ba akan table d'in" da sauri Fatuu ta d'aga ido ta kalli Hajiya jin abunda tace kafin da mamaki akan fuskarta tace "Ya Haisam yazo ne?" Hajiya tace "Eh tare muka zo shi ya maido ni saida nace ma ya tsaya Saboda aikin shi zan iya dawowa amman ya k'iya sai kace zan 6ace, tunda muka dawo ma ya fita kinga har yanzu bai dawo ba k'ilan ko wurin Abbas yaje" shiru Fatuu tay fuskarta da d'an murmushi sai kuma ta sunkuyar da kanta ta rasa gane farinciki take da jin yazo ko kuwa can ta d'ago tace ma Hajiya bari ta barta ta huta anjima ta dawo hajiyar tace bazata ci Abincin ba tace a k'oshe take daga haka ta mik'e tay mata sai anjima Hajiyar nata mata Murmushi sosae take jin dad'in ganin Fatuu haka da ka kalleta yanzu kasan bata da damuwa ta dawo kamar da koma ta fi don har kumatu ta k'ara sai kace ba Student ba ga Fuskarta ta k'ara yin Smooth hakan yasa Farinta ya fito sosae, Fatuu na fitowa ta maida glasses d'inta a fuska dama da zata shiga d'akin Hajiyar ne ta cire, kamar taje d'akin Saude sai tay tunanin k'ilan ma bacci take hakan yasa ta nufi hanyar fita daga parlon, tana zuwa kopar Fita Haisam na shigowa har saura kad'an su bangaje juna da sauri Fatuu ta dawo baya ta tsaya ta kai idonta kan shi shima kallon nata yake yana sanye da farar shadda k'al anyi mata Fav d'inkin shi wato sen style ta amshe shi Sosae d'inkin ya bayyanar da kirar shi ta k'akkarfa kan shi ba hula sai sumar shi dake faman salk'i, wani fitinannan k'amshi ke tashi daga jikin shi, bin juna sukae da ido Fatuu ta kasa tanka mashi sai faman had'iyar abu take a yadda taga Fuskar shi ta dawo daidai ba kamar can baya ba da ta fad'a Saboda ciwon da yace mata yayi gashi yay wani irin fresh Fatar nan ta k'ara mulkewa to weather ba d'aya ba ga sajen da ya fara bari sumar ta d'an k'ara yawa a kwance lub amman bai barta ta taru sosae ba, wani kalan kallon k'urulla yake mata tun daga sama har k'asa ganin haka yasa ta kai hannu a hankali ta cire glass d'in fuskarta ta ruk'e a hannu kafin da k'yar Saboda tunda ta gan shi k'irjinta ke wani irin bugu ga wani abu da ya tsarga mata tun daga kanta har zuwa babban yatsan ta tace "Sannu da zuwa, anzo lafiya" bai bata amsa ba sai yay mata alamar su shiga da hannu ta ja gefe ya fara wucewa kafin ta bi bayanshi tana kallon yadda yake tafiyar shi mai cike da isa duk da ba don nuna isar yake yin ta ba haka yake tafiya dama, saman sofa 3 seater ya zauna Fatuu na kokarin zama kan 1 seater dake can gefe yay mata nuni da d'an can gefen shi alamar ta zo ta zauna, bayan ta zaunan shiru tay tana d'an kallon shi sai kuma ta kauda kai shima still idanun shi na akanta sai duk ta tsargu da kallon nata da yake tayi sanin shi ba mai kafe mutum da ido bane kamar yadda shima bai son a kafe shi da idanun, "Ya School?" taji saukar cool voice d'in shi lokacin ta d'an duk'ar da kanta tana wasa da glass d'in hannunta, d'agowa tay suka had'a ido a hankali tace mashi Alhamdulillah ya jinjina kai sai kuma ya k'ara cewa "hope u'r concentrating?" Da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh bai ce mata komae ba sai ita tace mashi ya Aunty Fanan ya amsa da tana lafiya tana gaisheta tace tana amsawa suka d'an k'ara yin shiru ta maida kanta k'asa kaman daga sama taji yace "baki tambayi ko ta haihu ba" da sauri ta kalleshi sai taga yay d'an murmushi d'an kwa6e fuska tay tace "ai in ta haihu zan ji ko" ta6e baki yay kawae wata shirun ta biyo baya sai take ganin kaman ya canza mata don a waya sosae yake sakar mata baki suyi Magana duk da a nan ma d'in wata Maganar sai ya d'an ja lokaci kafin yayi ta tunawa tayi da koda can ai baya Maganar sosae itace ke ja har yayi yasa bata kawo komae a ranta ba, wayarta ce da ke acikin Aljihun rigar uniform d'inta ta fara ringing ta kai hannu ta ciro sunan Fauzy ne ya bayyana akan Screen d'in tay picking bayan ta kara a kunne suka fara magana tambayarta tay ya taje gida ya su gwaggo ta amsa mata da lafiya lou suke itama ta tambayeta Aunty Mareeya daga baya suka yi sallama Fatun na jin da ita kad'ai ce da ta fad'i mata Ya Haisam yazo, bayan ta cire wayar ruk'eta tay a hannu tana d'an tatta6a ta jin shirun Haisam d'in yay yawa yasa ta juya ta kalleshi sai taga shima ya d'ago ya kalleta ranta ne ya bata wayar hannunta yake kallo hakan yasa lokaci guda ta kama kanta cikin d'an rawar murya tace "D....dama ba waccan wayar bace daka siya man, ita lokacin da zan tafi Yola ne sai mukai musanya na amshi ta Kawu Amadu Saboda naga shi zata fi mashi amfani a nan tunda mu bamu da network mai kyau to dana dawo aka fasa auren shine ya maido man sai nace ya barta nak'i amsa da ya matsa man, to da Baffana yazo maido kaya ne ya bani dubu d'ari duba hamsin Ya Abbas ne ya bani sai dubu hamsin shi ya bani yace in yi amfanin Makaranta to shi ya Abbas dama Saboda Auren ne ya bani su da nayi mashi maganar su daga baya sai yace ai ya riga ya bani ne kyauta shine na had'a da wayar Kawu Amadun da kud'in na bashi ya canza man wannan" ta k'arasa tana nuna mashi wayar shi kam tunda ta fara mashi Maganar bakinta kawae yake kallo har ta gama ganin tana mik'o mashi wayar ya d'an ta6e baki kawae had'i da d'an murmushin gefe don ya fahimci tayi tunanin wayar yake kallo yasa tay mashi dogon bayanin abunda bata sani ba shi yanzu yama manta wace irin wayace ya siya mata, ganin ya k'i amsa ya bita da ido kawae yasa ta d'an tura mashi baki ta janye wayar shi kuma gyara zama yay ya d'an kwantar da kan shi yana facing sama ganin haka yasa tace "Bazaka ci Abinci ba?" d'an jimm yay sai kuma ya jiyo da fuskar shi ya kalleta ta sake cewa "Hajiya tace baka ci Abincin ba ka fita" fuskar shi a sake ya d'age mata gira yace "Tambayarta kikae ne?" Da sauri ta girgiza mashi kai ta fad'i mashi yadda akai ta sani yay shiru kawae, ba wata yunwa yake ji ba amman jin ita bata ci ba yasa ya yunk'ura ya fara kokarin mik'ewa bayan ya tashi yace mata zaije Masallaci in ya dawo sai su ci daga haka ya nufi hanyar fita don da suna zaune aka fara kiran sallar la'asar, bin shi tay da ido har ya kusa kai bakin kopar ta ga ya d'aga hannunshi na dama ya had'e yatsunshi biyu suka d'an yi sauti nan take ta gane mi hakan ke nufi wato yasan kallon shi take, murmushi tay ta jingina da kujera komae na shi mai burgewa ne Allah ne shaidar ta tana tsananin son shi saidae ba yadda zatai k'addara ta riga fata, ganin zuciyarta na kokarin maida ta ruwa don har k'walla sun fara taran mata a idanu yasa tay saurin kawar da tunanin ta yunk'ura ta mik'e itama, d'akin Saude ta nufa lokacin data shiga Sauden ta fito daga toilet da alamu Alwala tayi tana ganinta ta washe baki tace "Fateema yan Makaranta an dawo" itama murmushi take mata tace "Eh Aunty Saude kin dawo lafiya" ta amsa mata da lafiya lou Fatun tace mata zata yi salla ne ta amsa da to ta nufi Toilet, bayan tayo Alwalar a kusa da Sauden ta shimfid'a abun salla ta kabbara, saida suka gama sannan Saude tayi mata Maganar Aurenta da aka fasa tace d'azun da gwaggo ta shigo take fad'a masu taji mata dad'i Allah yasa haka yafi zama Alkhairi Fatuu ta amsa da Amin can wayarta ta fara ringing ta kai hannu gefen Katifa ta d'aukko sunan Ya Haisam ta gani hakan yasa ba tay picking ba ta yunk'ura tay ma Saude Sallama ta fice, Zaune a Dining area ta hango shi ta nufi can yana ta lallatsa wayar shi ganin haka yasa ta fara k'ok'arin serving nashi ta tambaye shi mi zai ci yace mata abunda ya kamata d'an murmushi kawae tay ta fara zuba mashi gaba d'aya sanyayyan k'amshin da jikinta ke saki ya cika mashi hanci saidae bazaka ta6a gane yanayin shi ba lokacin idon shi na akan wayar hannun shi baya ta gama ne tace "Ya Haisam bismilla" Slowly ya d'ago ya kalli Abincin da ta zuba mashi shak'e da plate kafin ya d'aga idon ya kalleta ta nufi d'ayan bangaren ta zauna opposite dashi ganin kallon da yake mata ta kuma san dalili yasa ta yin yar dariya tace "ai nasan yanzu kana cin Abinci sosae shiyasa na zuba maka haka" d'an murmushin da iyakar shi lips d'inshi yay kafin yace "Who told u?" tura baki tay tace "Ba kayi aure ba" wani kalan kallo yake mata har saida tasha jinin jikinta a d'an rud'e tace "dama na ta6a ji Ya Abbas yace in kayi aure zaka rink'a cin Abinci hannu baka hannu kwarya lokacin daka fara kaini gidan shiyasa nace haka" ta k'arasa had'i da sunnar da kai still kallonta yake ya kuma tuna da lokacin da Abbas d'in yay Maganar kusan 4yrs yanzu amman bata manta ba, hannu ya kai ya d'auki spoon ya fara cin Abincin a nutse itama ta fara kokarin zubawa saidae kaman rabin nashi ta zuba tana yi tana satar kallonshi yay kaman bai ganin mi take yi, tana fara ci ya dakata yace "how can u eat comfortably da wannan" yay Maganar yana mata nuni da kan shi ta gane Hijab d'in jikinta yake nufi hakan yasa ta kai hannu ta cire ta dama yar k'arama ce saidae kuma kanta ba kallabi sai tulin gashita dake fake ganin bai kamata ta zauna ba kallabi ba kuma ana cin Abinci yasa ta ninka Hijab din tay irin d'aurin ture kaga tsiyar nan taci gaba da cin Abincin, wohoho maza masu abun ban mamaki wai kuma sai yadda d'aurin yay mata yay mashi kyau ba kamar yadda tulin gashin ya fito waje ko don matarshi ba irin gashin gareta ba kuma ita ta saba sakin shi oho dae shi yasan dalili, duk in ta d'ago sai sun had'a ido yana kallonta sai ta d'an mashi murmushi abun mamaki saiga Haisam ya take Abinci ba tare daya ankare ba abun shima ya matuk'ar bashi mamaki Fatuu kuwa ta hau yi mashi dariya tana fad'in ashe Ya Abbas da gaske yake saidae kawae yay mata murmushi, kusan a tare suka gama Fatuu ta kwashe kayan da sukayi amfani dasu takai kitchen saida ta wanke su sannan ta fito ta maida hijab d'inta lokacin shi har ya koma cikin parlon hakan yasa ta nufi can tana zuwa a gefen shi ta tsaya tace zata wuce gida d'an shiru yay yana kallonta sai kuma ya mik'e yace suje zai bata abu yay gaba tabi bayan shi, hanyar part d'in shi ya nufa hakan yasa tabi shi lokacin da ta shiga Falon har bata san sadda ta saki murmushi ba bata yi zaton zata k'ara shigowa cikin shi ba duk da tasan dama dole zai rink'a zuwa to amman a tunanin ta zai rink'a zuwa da Matar shine, ce mata yay ta zauna shi kuma ya nufi hanyar Bedroom ta ci gaba da k'are ma parlon kallo tamkar yau ta fara shigowa kuma yana nan yadda yake ba abunda ya canza sai gyara da yasha k'amshi na tashi, bayan wani lokaci ya fito hannun shi ruke da abu da bata gane ko minene ba a gefenta ya ajiye sai lokacin ta gane sabuwar Laptop ce ya koma daga can gefe ya zauna ganin ta bishi da ido yasa a hankali yace tata ce tayi amfani da ita d'an waro ido tay sai kuma tay murmushi tace mashi ta gode Allah ya saka da Alkhairi ya k'ara bud'i ya jinjina mata kai can kuma sai ta d'an kwa6e fuska ganin haka yace "What?" A shagwa6e tace "ban wani iya amfani da ita ba" still yay yana kallonta kafin yace a Secondary school ba'a koya masu ba ne tace "an koya mana amman ai duk theory ake duka bai fi sau a k'irga ba aka kaimu Lab yin practical kuma mudae in munje game d'in jirgi dana had'a bangarorin jikin mutum muke" yadda tay Maganar sai kace wata k'aramar yarinya yasa shi yin dariya batare da ya shirya ba ta zuba mashi ido tana kallon tsantsar kyau bayan ya dakata ya d'age mata gira yace "shikenan ai sai kici gaba da game d'in jirgin" tura mashi baki tay tana yamutsa fuska ganin haka yasa shi mik'a dogon yatsan shi ta kalli tissue box d'in da yake nuna mata sai kuma ta kalleshi cikin rashin fahimta yace mata in ta fara kuka sai ta yaga ta goge tunda kuka bai mata wuya sai lokacin ta fahimci abunda yake nufi tay dariya sigh yay yace taje da daddare zai zo ya koya mata abunda ya kamata tace to ta d'auki laptop d'in had'i da mik'ewa tace mashi sai anjima ya jinjina mata kai kawae ta nufi hanyar fita, bayan ta fice d'age kan shi yay yayin da a ranshi ya fara tunanin wani abu da shi kadae yasan minene, ya dan d'auki lokaci a haka kafin ya yunk'ura ya mik'e duk jin jikinshi yake wani iri hakan yasa shi yin tunanin tafiya Gym ya nufi Bedroom don ya shirya. Cike da farinciki Fatuu take nuna ma gwaggo Laptop d'in itama sai washe baki take tana saka Albarka kamar yasan Fatun dama ta fara Maganar siyan computer d'in har tambayarta gwaggo tayi ko ita tace ma shi tana buk'atar ta ne da sauri tace mata a'a wllh da kan shi ya kawo mata tace yayi kyau bata son ta rink'a tambayarshi abu ta bari sai in shi ya tambayeta sannan Fatun tace mata to dama ita bata hakan kokarin tashi ta fara yi don taje tayi wanka, bayan ta gama ta shiryawa da doguwar riga mai gajeran hannu gwaggo ta shigo cikin d'akin Fatuu ta kalleta da murmushi ta nufi bakin gado ta zauna itama Fatuu zama tay gwaggon tace har ta gama shiryawa tace eh, shiru ta d'an yi sai kuma tace "da nace wai tunda Abinci tazarce muka yi ko za'a had'a mashi wani abu maras nauyi haka?" Fatuu dake kallonta tace "wai Ya Haisam" tace "Eh ba kince zai zo koya maki Computer d'in ba?" d'aga kai tay tace "Eh haka yace, to mi za'a had'a?" d'an shiru gwaggo tay alamar tunani kafin tace "ko ayi mashi fatan dankalin turawa yaji Alaiyahu" Fatuu tace "eh kuma kinga ba Abinci bane mai nauyi dama asa harda kifi" yar dariya gwaggo tay tace to bari sai a siyo gasasshen kifi tarwad'a ayi amfani dashi ta tambayeta da ta wuto shagon Amadu yana ciki tace mata a'a a rufe yake tace to bari ta kira taji k'ilan ma kasuwa ya wuce daga Makaranta in yana can ma sai ya siyo komae daga haka ta mik'e ta nufi hanyar fita, bayan ta koma d'aki ta kira Amadun cikin sa'a kuwa yace mata yana kasuwa taji dad'in haka nan ta bashi saftun duk abunda take so, gab da Magrib Amadu ya dawo ya siyo komai Gwaggo ta kira Fatuu tazo ta fara feraye dankalin ita kuma gwaggo ta fara gyara kifin zuwa bayan Magrib sun kammala komae gwaggo tace ma Fatuu sai taje tayi wanka kada taje wurin mutane tana k'arnin kifi duk da ba ita ta gyara ba amman yana iya kama mata jiki tace to, tana fitowa daga wanka tayi Alwala bayan ta shiga d'aki ta tsaya gaban wardrobe tana tunanin kayan da zata saka can ta fiddo wasu light blue riga da skirt yan kanti kayan na da d'an k'auri amman roba ne ta saka sun mata kyau sosae shape d'inta ya fita har ba'a Magana tasa bak'ar hula a kanta bayan ta gama ta kabbara sallar isha, ana gama salla sai gashi yazo lokacin itama Fatuu bata dad'e da gamawa ba ta jiyo cool voice d'in shi yana sallama mik'ewa tay tasa hannu ta cire hijabin ta aje bakin gado sannan ta fito lokacin yana tsaye gefen Parlor jikin shi sanye da k'ananan kaya da murmushi ta isa gabanshi shima ya d'an yi mata tace ya shigo mana tay gaba ya bi bayanta, a saman 3 seater ya zauna tana tsaye sai kuma ta juya ta nufi Freezer don d'aukko mashi lemu da ruwa yabi bayanta da kallo har ta bud'e ta d'aukko yana ganin zata juyo ya kauda idon shi kanshi baisan miyasa yake yawan kallonta ba abunda ba halinshi bane, a saman Carpet ta ajiye su ta bud'e Coke d'in ta tsiyaya mashi a cikin glass cup kafin ta mik'e still da murmushin ta d'an rankwafa tana mik'a mashi yana kokarin kallonta idanunshi suka sauka akan saman boobs d'inta da suka d'an bayyana sakamakon duk'awar da tay da sauri ya kawar da idanun shi had'i da amsar cup d'in ya furta thanks ta koma gefe ta zauna kan kujera one seater kamar sau ukku yay sipping ya ajiye bayan ya d'ago suka had'a ido Calmly yace "go and bring d Laptop" tace to ta mik'e still dae kallon yabi ta da shi har ta fita, tana fita gwaggo ta shigo da fara'a ta zauna suka shiga gaisawa ta k'ara mashi ya gajiya don d'azun sun gaisa da taje gidan, godiyar Laptop tay mashi yace ba wani abu ta k'ara mashi godiya da Addu'oi yana amsawa a hankali daga baya ta mik'e ta fita Fatuu ta shigo ta mik'a mashi ya amsa ya gyara zama yana kokarin bud'e ta ita kuma ta sake juyawa ta fita, kayan Abincin taje ta kawo ta tambaye shi ta zuba mashi yanzu ya d'an d'aga mata hannu alamar a'a idon shi akan Screen hakan yasa ta mik'e tana kokarin komawa inda ta tashi ta zauna ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata gefen shi alamar ta zauna nan bayan ta zaunan ganin ya d'aura laptop d'in akan laps d'in shi yasa tace ko ta daukko d'an table ya d'aga mata kai alamar eh, bada jimawa ba ta dawo ta aje a gabanshi ya d'aura laptop d'in a sama daga haka ya fara nuna mata abubuwan da yakamata ta iya dama duk ya tura mata Apps ba laifi kuma tana catching yafi koya mata Ms-Word inda zatayi typing duk in yayi abu sai itama tayi abunda yafi bata wahala in tazo yin highlighting dasu dragging sai ya rik'a kubce mata dama sun fi sauk'i yi inda mouse ne tana cikin yi taji ya kawo hannunshi ya kama hannun nata da sauri ta d'an kalleshi ganin bai ko kalleta ba yasa ta maida idon kan screen d'in yana ruk'e da hannun ya rink'a koya mata tun tana jin wani iri hardae ta saki jiki saidae gaba d'aya kamshin jikinshi wani irin narkar mata da zuciya yake sakamakon kusancin da suke dashi a zaunen,sosae ta koyi abubuwa harda yadda zata tura abu a turo mata da yarda in kamar zasu yi online class da dae sauransu lokacin da suka gama kusan goma saura ganin yana niyyar ta shi yasa a shagwabe tace to Abincin fa still yay yana bin ta da kallo kafin yace bai son Abinci mai nauyi da daddare da sauri ta sauka ta fara bud'ewa tana fad'in ai tasani ya gani ba mai nauyi bane light food ne wani irin daddad'an kamshi ne ya buge parlon ganin baice komai ba yasa kawae ta fara zuba mashi kaman d'azun ta shak'e mashi plate tana yi tana kallon shi tana yar dariya ganin tana kokarin d'aura mashi saman table d'in ya dakatar da ita yace zai ci a kan carpet ta aje a nutse ya sauko ya mik'ar da k'afaffun shi ta yadda Abincin ke a gefen shi ya kalleta yace ta d'aukko wani spoon d'in tace to bayan ta dawo ta mik'a mashi da kai yay mata alamar ta ci ta langa6ar da kai tana fad'in nashi ne ai bin ta yay da wani irin kallo hakan yasa ta matsa gaban Abincin suka fara ci a nutse, sosae Abincin yay ma Haisam dad'i can sun yi nisa Fatuu ta d'ago da d'an murmushi suka had'a ido ta d'age mashi gira tace "da dad'i?" murmushin gefen baki yay bai ce komae ba, ba laifi sosae suka ci Abincin don har k'ara masu Fatuu tay saida suka gama ya kalleta cikin ido yace "Yayi dad'i da yake bake kika yi ba" waro ido tay sai kuma ta fara rantsuwar ita tayi abu kad'an gwaggo tayi still yay yana ta kallonta fuskar shi a sake sai faman rantsuwa take a shagwa6e tana fad'in ai shima dae yasan ta iya girki ko can Calmly ya furta "Ok kin yi kokari" tace ta gode sannan ta mik'e ta kwashe kayan ta kai kitchen, lokacin da ta dawo har ya mik'e zai tafi ta tsaya gabanshi suna Facing juna tace tafiya zai yi ya d'aga mata kai tace suje to ta raka shi ta fara K'ok'arin juyawa kawae sai taji ya kamo hannunta cak ta tsaya ta zaro ido kafin slowly ta juyo still yana ruk'e da hannun suka zuba ma juna ido kan Fatuu ya gama d'aurewa gaba d'aya ganin shi take tamkar bashi ba Saboda bak'in abubuwan da yake mata wanda ko ada can da bai da aure bai mata hakan ya lura da irin kallon da take mashi hakan yasa a hankali ya saki hannun kafin Slowly ya furta "It's already late ba sai kin raka ni ba" tamkar yar k'adangaruwa ta jinjina mashi kai kawai don gaba d'aya jin ta take wani iri don kallon da yake mata bai saba yi mata shi ba, kokarin bi ta gefenta ya fara da sauri taja gefe tana ci gaba da kallon shi har ya fice ............. Mun gama Sabon salo da An yanka ta tashi yanzu mun shiga WASA FARIN GIRKI😂 _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2036* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Sosae Fatuu ta dage da karatu ita da Fauzy don seat d'in su guda a hankali suka zama abokai sosae duk da ita Fatun Day take yi tare suke yin break wani lokacin daga gida tana kai mata abubuwan ci, Bayan wata ukku sukayi jarabawar pre intro wadda daga ita bayan wasu wata ukun zasu yi intro exam d'in wadda itace yar bala'en wadda kowa ke tsoro don mutane sosae ake zubar wa, cikin Nasara ita da Fauzy sun ci pre intro din wad'anda basu ci ba kuma aka rink'a karfafa masu guiwa don su dage kafin ai d'ayar. A bangaren Khalid yana can yana fama da ciwon so don tun bayan da aka fasa Auran su Allah ya jarabe shi da tsananin son Fatuu gashi yasan ya rasata kenan har Abada don mahaifin shi kaifi dayane kuma ita kanta Fatun ta rufe duk wata kafa da zai samu yin Magana da ita gaba d'aya ya zama salihin k'arfi da yaji ga Dad d'in shi bai kula shi sosae bai dae yi fushi da shi ba amman bai shiga har kar shi Mom ce kawae ke kula shi ta damu sosae da halin da yake ciki haka Sadeeya ma da tuni ta koma school tana yawan kiran shi don jin yadda yake da kuma k'arfafa mashi gwuiwa kan ya daina damuwa, har Abokan aikin shi wasu sun fahimci yana cikin damuwa, Ciwon so ba dad'i Khalid ma an d'and'ana Allah ya bada lafiya. Zaune suke a cikin d'akin su na Hostel da yake Saboda jarabawar dake gaban su yasa Fatuu ta dawo cikin Makarantar kamar yadda sukae da gwaggo don itama tasan had'arin dake tattare da ita shiyasa ta barta ta dawo don yin karatu sosae duk ranar Monday in tazo sai juma'a da an tashi take komawa gida, gado biyu ne acikin d'akin nasu d'aya a 6angare dama d'aya kuma a hagu, d'akin baida girma sosae sun gyara shi komae tsab, Fatuu na zaune saman gadon dake hagu tana facing Fauzy dake zaune a saman na dama kowannen su ruk'e da littafi suna karatu akai akai suke tambayar juna abu, can bayan wani lokaci Fatuu ta d'ago da niyyar yi mata magana sai taga ta kife fuskarta akan gwuiwowinta wanda da ba haka take ba, kiran sunanta Fatuu tay shiru bata amsa ba hakan yasa tay tunanin ko bacci ne ya kwashe ta daga karatu, d'aga murya tay tace "Fauzyyy tashi baki ga ta yin bacci ba a wannan lokacin in ba munyi passing Intro ba" shiru bata tanka mata ba bata kuma d'ago ba ta sake kiran sunan ta da d'an k'arfi k'asa k'asa taji muryar ta tace "ba bacci nike ba" yadda Fatuu taji sautin muryar ta sai taji kaman tana kuka da alamun mamaki tace "to mi kike, naji kaman ma kuka kike ko" daga yadda take ta girgiza mata kai Fatun tace to ta d'ago ta gani, a hankali ta sak'a hannunta ta cinyoyinta Fatuu na ganin haka ta gane so take ta goge kwalla ne da sauri ta saukko daga kan gadon tana sanye da Vest da dogon skirt kan ta ba d'an kwali, gadon da Fauzyn take ta haye tasa hannu ta d'ago da face d'inta, Har saida gabanta ya fad'i ganin fuskar ta jage jage da hawaye sai kace ba ita bace suke karatu suna magana ba a d'an rud'e Fatuu ta shiga tambayarta abunda ya faru take kuka shiru bata ce mata komae ba sai faman sheshsheka take hakan yasa Fatuu cewa "Saboda Exam d'in da zamuyi kike kuka?" Girgiza kai tay da yar damuwa Fatuu tace "To don Allah Fauzy miye?" cikin muryar kuka tace "Mujaheed........" Sai kuma ta Sake fashewa da kukan kan Fatuu ne ya d'aure jin sunan da ta ambata ta rasa gane wanene shi sannan kuma miya faru da shi, ganin wayarta a gefenta yasa Fatun cewa "Rasuwa yayi ne?" Da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a, d'an yarfa hannu Fatuu tay tace "to don Allah ki fad'a man waye shi kuma miya faru kinsa ni na rud'e fa" shanye kukan Fauzy tay tasa hannu tana goge k'wallan kafin ta fara magana "Mujaheed shine silar zuwa na wannan Makarantar Zarah na kasa man cewa da abunda yay man duk yadda naso na manta" cikin d'aurewar kai Fatuu ta tambayi waye shi kuma miya mata, goge kwalla ta k'ara yi taci gaba "Tsohon saurayi nane kusan in ce ma shine saurayi na farko kuma na k'arshe kusan shekararmu hud'u tare...." Dakatawa tay ganin hakan yasa Fatuu sake tambayar ta abunda ya faru tsakanin su, cigaba tay "Mun had'u dashi ne lokacin da na dawo gida nayi Jsce da yake Boarding nayi lokacin na raka wata Yayata wadda muke uba d'aya don Matan babanmu biyu mamarmu da tasu dinner party d'in k'awarta to lokacin da muka je sun tashi su da k'awayen su suna rawa an bar ni ni kadae zaune sai gashi ya zo inda nike da murmushi ya tambayeni ya na zauna ni kadai bazan je nima in yi rawar ba na d'an yi mashi murmushi kawae a tunani zai tafi ne sai kawai naga ya zauna kujerar kusa dani yaci gaba da latsa wayar shi lokaci bayan lokaci yake d'agowa ya kalle ni da murmushi nima sai in d'an yi mashi can ya k'ara d'agowa ya tambaye ni sunana na fad'a mashi Fauziyya da bud'ar bakin shi sai cewa yay sunan ya dace da mai shi ina dae ta dariya daga baya ya mik'e ya bar wurin har yana ce man wai ya zo ya tayani fira ne dama kyauta nace mashi Nagode, ba'a kaiga tashi ba muka fito don tafiya Saboda in muka kai har lokacin da za'a gama to zamu ja ma kan mu ne wurin Abban mu dama da K'yar aka bar mu muka zo ba tare da ya sani ba, muna fitowa sai ga mutumin ya biyo bayanmu yace man tafiya zamuyi na d'aga mashi kai sai yace to bari yay dropping namu muka bishi inda ya parker Motar shi,lokacin da muka isa layin gidan mu bamu k'arasa ba muka ce ya ajiye mu anan Farko farko ya tambayi ina ne gidan namu muka ce yana a d'an can gaba yana murmushi yace to ya k'arasa damu mana da sauri muka ce a'a Ya tambayi dalili anan Yayata Fareeda tace mashi bamu son baban mu ya gan mune yace Ok, dama ni ce a seat d'in gefen shi kafin mu fita yace na bashi no d'ina nace ai ni ban fara rike waya ba ya tambayi dalili nace Saboda nayi k'arama kuma Makarantar kwana nike yi yana yar dariya yace shi bai ga wata k'aranta tawa ba anan ya tambayi ajina nawa nace mashi Jsce nayi zan tafi s.s 1 ganin ita Fareeda nada waya ne yasa yace to ko tata ce a bashi sai mu rink'a gaisawa ya zama yayana harda tambayata ko ban so ina dariya nace mashi ina so aka bashi ta Fareeda d'in, tun daga wannan lokacin muka fara yin waya dashi daga baya watarana har yazo gidan mu da yake ba'a hana mu tsayawa da samari Saboda da mun gama Secondary Matan gidan mu ake mana aure maza ne ke cigaba da karatu, yan gidan mu suka fara tsokanata nayi saurayi don sun san ban saurarar samari ko zancen su ma ban so ay man inta faman rantse masu shi ba saurayi na bane don bai ce yana so na ba sai su ce wai ai in aka ga kare na Sunsuna takalmi to d'auka zai, lokacin dana tashi komawa S.s One sosae yay man hidima kinga uban provisions d'in da ya siya man muka raba ni da K'anwata da muke makaranta d'aya ko Fareeda ma boarding tay amman ita lokacin da nayi Jsce ta gama, bayan mun koma Makaranta Zaria saida nay yadda mukae muka rink'a waya da shi da wayar wani malami mai shago da muke siyayya har lokacin kuma bai furta man so ba kuma har Visiting yake zuwa man in dae yana Funtua...." D'an dakatawa tay tana maida numfashi Fatuu dae ta zuba mata ido duk ta k'agu taji abunda yay matan can taci gaba "Saida muka shiga Ss 2 wato aji biyar sannan ya furta man yana so na bayan mun dawo wani hutu, Sosae naji dad'in hakan don dama tuni ni na Kamu da son shi Saboda Mujaheed Namiji ne wanda da wuya mace tay rejecting soyayyarshi yana da kyau sosae duk da ba fari bane bak'i ne amman bak'in nashi mai kyau ne ba kamar da Yake hutu ya zauna mashi da yake Family d'in su sanannu ne a garin suna da Kud'i, lokacin da ya furta man so na sanar da shi mu gidan mu da an gama Secondary ake yin aure saidae mutum yaci gaba da karatu a d'akin mijin shi in yana so yace man lafiya lou ai shima ya kusa kammala Karatun shi da yake a K'asar Malaysia ranar da farinciki na kwana Zarah, koda yan gidan mu suka ji suma duk sunyi murna ba kamar mahaifiyata, tunda ya furta man so ban sake kula wani Namiji ba don ya nuna man zai aure ni duk da kuwa lokacin sosae ake cewa ana sona,tunda nike da Mujaheed a wannan lokacin bai ta6a nuna yana son ta6a jikina ba hakan ne ma yasa nike k'ara bala'en son shi don a gani na mutumin kirki ne sai Bayan da na gama Secondary ne ya fara kaman man hannu haka in muna zance wani lokacin har d'an kiss yake man a bayan hannu, sam hakan bai canza daga kallon da nike mashi ba a ganina bai wuce iyaka ba, Bayan mun gama Secondary da kamar wata d'aya watarana da yazo duk sai na ganshi a cikin damuwa na fara tambayar shi mi ke damun shi farko ce man yay ba komae sai dana matsa mashi ne yace zai fad'a man don Allah in fahimce shi kar in tada hankali na tunda naji hakan gabana ya fara fad'uwa amman sai nace mashi to kawai ya kama hannuwana ya fara fad'a man wai a gidan su ne ake son had'a shi aure da wata Cousin d'in shi an matsa mashi sai ya aure ta shi kuma baison ta ni yake so, wllh tunkan ya rufe baki jikina ya fara rawa nan da nan sai kuka ban san lokacin da na fara rok'on shi kan ya fad'a man gaskiyar Magana in ita zai aura amman sai ya nuna man shi fa ba wanda zai masa dole don haka in kwantar da hankali na dama kawai ya fad'a man ne, sosae ya kwantar man da hankali lokacin har da hugging d'ina yay saida yaga hankali na ya kwanta sosae sannan muka rabu...." K'ara dakatawa tay tana share kwallan da suke zubo mata kafin taci gaba "bayan kaman sati biyu da yin hakan Mahaifina yasa in yazo in ce yana son ganinshi akayi hakan bayan sun gama naje wurin shi yana murmushi yake fad'i man cewa akai ya turo sosae nai murna har na kasa boyewa anan yake ce man amman yaba Dad d'ina hak'uri sai after 1 Month don Dad d'in shi bai K'asar nace Allah ya maido shi lafiya, tun bayan wannan Maganar sai ya rage zuwa sai dae muyi waya har tambayar shi nayi sai ya nuna man ba ya fad'i man Dad d'in shi bai nan ba to ai shike kula da harkokin kasuwan cin shi nace na Fahimta, ina ganin acikin watan da yace a bashi bai fi sau biyu ko ukku ya zo ba aka shiga wani watan to shi kwata kwata ma bai zo ba saidai waya har dae na k'ara mashi Maganar turowa sai yake ce man tafiya ce ta kama shi in fad'a a gida ayi hak'uri sai ya dawo lokacin jikina ya fara yin sanyi amman sanin yana tafiye tafiye yasa ban kawo komae ba nayi mashi fatan ya dawo lafiya, tun daga wannan ranar inaga sau d'aya na k'ara yin waya da shi kullum wayarshi bata shiga haka in nayi mashi Magana ta chat itama bata shiga a haka har akayi 1 month aka shiga wata na biyu tun ban damuwa sosae hardai na fara ganin haka yasa Momynmu ta tambayeni kodae wani abu ya faru ne ko munyi fad'a nace mata nidai nasan ba muyi fad'a ba kuma ban masa komae ba na fad'a mata Maganar da yay Mun kafin ace ya turo ta auren Cousin d'in shi tunda naga yanayin fuskar ta a lokacin na fara sarewa tace man kar in damu in ci gaba da Addu'a nace to, abu sai gashi har anyi wata ukku ba Mujaheed babu dalilin shi a lokacin harna fara tunanin ko in je gidan su in duba in lafiya duk da bansan ta ina zan fara ba don gidan su Babban gida ne, ban kaiga zuwa gidan ba bayan kwana biyu an aike mu bakin kasuwa nida sister d'ina da muke boarding tare lokacin ta dawo Hutu muna tsaye bakin titi zamu tsallaka kaman ance in juya sai na hango wani abokin Mujaheed mai suna Usman wanda sun sha zuwa wurina tare da shi har da ina Makaranta ya ta6a zuwa dashi kusan sau biyu ya fito daga Motar shi ya nufi wani shagon Pos aikuwa da sauri nace ma Ummi muje wurin shi, lokacin da ya ganni har saida naga kaman ya d'an razana bayan Mun gaisa nace mashi ina Mujaheed ne farko shiru yay yanayin shi ya canja lokaci guda na rud'e cikin rawar murya na tambaye shi kodae ya mutu ne da sauri ya girgiza man kai yace yana nan raye na hau rok'on shi kan ya fad'a man yana ina da k'yar ya iya bud'e baki ya gaya man Maganar da tunda nike a rayuwata ban ta6a jin abunda ya razanar da ni ba irin ta wai Mujaheed yayi aure kusan wata ukku....." K'ara dakatawa tay tasa kuka sosae Fatuu da itama idanunta har sun cika da kwalla ta jawota jikinta tana bata hakuri, bayan ta d'an tsagaita ne ta d'ago taci gaba ".....nidae tunda ya fad'a man hakan ban san miya faru ba kawai dae na farka na ganni a gadon Asibiti ake sanar dani kwanana biyu anan, Zaraah ko ban fad'a maki ba kema kinsan dole na shiga wani hali na samu Heartbreak, nayi kuka har na gode Allah saida nayi sati biyu a Asibiti koda muka koma gida ma bai lafa ba sai sambatu da koke koke ganin abun yay yawa yasa aka k'ara maida ni Asibiti anan likita ya tabbatar kwakwalwata ta d'an ta6u a maida ni psychiatric muga likitan can a tak'aice dae can ma d'in nayi wani watan har Doctor yace yakamata a nemo man abunda nike so amman da yake ran Abbanmu ya 6aci sosae yace ko da wasa kar wani yace zai nemo Mujaheed har ya kira shi inyi hak'uri kawae don ko dawowa yayi wllh bazai bashi aure na ba, sam banga laifin shi ba Saboda ya matuk'ar yarda dashi bashi kad'ai bama duk yan gidanmu saboda yardar da Abbanmu yay dashi yasa har yake barin mu muna yin zance a cikin Mota wanda ba wanda ya ta6a ma hakan dole saidae aje sitting room d'in shi ko kuma a tsaya a waje amman badai a shiga cikin Mota ba, haka naci gaba da jinya a gida duk da yadda kowa ke kokarin ganin ya faranta man kaman yadda likita ya bada shawara amman abun gaba yake k'arawa don na kasa mantawa ga zuciya tay ta tunzura ni akwae ranar da har na d'aga maganin kwari zan sha k'arfin imani ne ya hana, na dau tsawon lokaci ina cikin hali hardae na fara rarrashin zuciyata da kaina kaman yadda kullum Mahaifiya ke nuna man in yi hakuri kar in ma kaina illa don shi yana can da matarshi bai san ina yi ba, akai akai Usman ke zuwa duba ni dana fara warwarewa ne watarana nike ce mashi Mujaheed ya zalunce ni da yayi man hakan don mi bazai gaya man zancen auren ba kamar yadda da farko ya gaya man gidansu an matsa ya aure ta ai ni da zan fahimce shi ko mu biyu ne sai ya aura banda matsala da hakan cike da tausayawa Usman yace bari ya fad'i man gaskiya ba wani matsa mashi da akai dama can yana tare da ita cousin d'in tashi don tare ma sukayi karatu a Malaysia kawai ni yace ina bala'en burge shi ne, yace man tun kafin mu dad'e tare dashi saida ya bashi shawarar indae yasan ba Aure na zaiyi ba ya rabu dani Amman sai yace wai yasani ko Allah yasa ya aure nin ko da zai yi auren saida yace mashi ya had'a mu ya aura sai yace wai gidan su baza'a bari ba, Saboda haka har d'an sa6ani suka samu lokacin dashi har yana ce mashi wai to shi ya aure ni mana yace ba don sa rana dake a kan shi ba wllh da ya Aure ni, wannan bayanin da Usman yay man yasa raina ya 6aci sosae wani irin haushin shi yakamani don na fahimci shi d'in mugu ne macuci kuma Azzalumi in ba haka ba yasan akan shi nasan miye so kuma Ba wanda nike tare dashi sai shi ko da wasa ban ta6a tunanin ba wani dama ba sai shi amman bai ji komae ba ya iya rabuwa dani, ba abunda ya k'ara bani haushi irin cewa da yay wai burge shi nike...., amman ba komae ai akwae Allah shi mai ji ne kuma mai gani ban mashi ko Allah ya isa ba amman nasan sai Allah ya saka man wllh....." Fashewa tay da matsanancin kuka ta fad'a jikin Fatuu da ta kumbura baki tamkar zata fashe wani irin takaici had'i da haushin Mujaheed d'in ne suka turnuk'e ta a yadda take ji da yana a kusa da ita ba abunda zai hana ta d'udd'ura mashi ashar har bugu ma in tasamu dama Wannan zalunci har ina kuma ita bata ga aibun Fauzy ba indae kyau ne Tubarkallah tana da shi don su rumawa ne harda tsagar 11 gareta a gefen fuskarta ga farinta mai kyau ga gashi duk da bata kai Fatuu ba amman tafi Fatuu tsawo sannan tana da d'an dirinta daidai gwargwado ko a hostel d'in ce ma d'akin su ake d'akin kyawawa, (Uhmm irin hakan na faruwa ko a zahiri don wani 6angare na labarin nan true life story ne, bansan miyasa wasu mazan ke yaudarar mata haka ba duk da a Matan ma ana samun masu yaudarar maza amman ba kamar Mazan ba wanda hakan tsagwaron zalunci ne ko ba'a fad'a ba, ka 6ata ma yar mutane lokaci kayi mata k'arya ta d'auki dukkan yardarta ta d'aura akanka amman kazo ka cuce ta wllh duk mai irin wannan yasani Allah bazai k'yale shi ba don kuwa ya haramta zalunci a tsakanin bayin shi ba yadda za'ai mutum yay haka kuma yaci bulus, duk da mun san wani bai auren matar wani haka wata bata auren mijin wata in ma rabuwar ta kama to ayi ta ba tare da an zalunci juna ba misali kana son ta tsakani da Allah itama haka sai kuma Allah yasa kaddaro dole a rabu amman bawai tun farko ayi tarraya ta k'arya ba kasan bazaka aureta ba initially don me zaka rufe, wasu Matan ta dalilin irin hakan sun samu ta6in hankali wasu sun Kamu da ciwon zuciya wasu ma d'ungurugum kashe Kawunan su suke Saboda an samu irin hakan ba sau d'aya ba ba sau biyu ba ko 6angaren labarin dana ta6o wanda ya danganci yaudarar da akai ma Fauzy ita yarinyar ma tasha maganin k'warin Allah ne yasa da sauran numfashinta gaba bata mutu ba amman ta shiga mawuyacin hali, anan nike son kira ga yan'uwana mata musamman wad'anda aka yaudara da su rungumi hak'uri su d'auki hakan matsayin jarabawa suna zaune Allah zai saka masu kar ki kuskura ki halaka Saboda wani k'ato wanda ba lalle ko gaisuwa yaje gidan ku ba in kin mutu, nasan abun da rad'ad'i da ciwo dole zuciya ta girgiza amman in akayi hakuri duk na d'an lokaci ne a yak'i zuciya kar a biye mata azo ai dana sani mara amfani yin hak'uri shine mafi Alkhairi domin Allah yana tare da mai hakuri kuma bai barin zalunci). "Yanzu ina Mujaheed d'in yake" Fatuu ta tambaya a zuciye, shanye kukan Fauzy tay tace "lokacin da Usman ya fad'a man yace basu K'asar tunda sukae Auren amman daga baya watarana Mun ta6a had'uwa a bakin hanya ya tsaya zai man Magana na k'i sauraren shi na tsallaka titi nay tafiyata, tun bayan lokacin na tsani zancen soyayya balle kuma ace ana sona bana saurarar Mutum har lokacin kuma ban daina jin son Mujaheed ba saidae kawae ina matuk'ar kokarin yakar zuciya ta kan ta manta shi, daga baya ne ganin na warware Mijin Yayata na nan yayi ma Abban mu Magana kan ya barni inzo in yi Karatu hakan zai sa in mance komae in ina shiga Mutane to shima din yana son in mance hakan yasa bai gardama ba ya barni wanda nice mace ta farko a gidan mu da ta cigaba da karatu ba tare da tayi Aure ba don ko ita Yayata Mareeya ta nan garin saida tayi aure tayi degree d'inta a nan" sauke ajiyar zuciya Fatuu tay cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Fauzy nasan yadda kike ji don nima na shiga irin wannan halin nasan yadda rad'ad'in yake a zuciya duk da ba....." Da sauri Fauzy ta d'ago ta katseta "Zarah kema an yi breaking heart d'in ki kenan?" Girgiza mata kai Fatuu tay tace "kusan hakan saidae ni ba wani ne yayi man hakan ba nice na ja ma kaina don son maso wani nayi koma ince nike yi Saboda har yanzu nima abun na damuna acikin zuciya amman na samu sauk'i sosae don ma still ina tare dashi shiyasa na kasa cire shi a raina kwata kwata" idanunta ne itama suka ciko da k'walla cike da mamaki Fauzy ta tambaye ta wanene don ita kallon wadda bata kula samari take mata, ganin tayi shiru yasa ta k'ara ce mata don Allah ta fad'i mata mana ko bata yarda da ita bane kamar yadda ita ta yarda da ita Fatun tace a'a ta yarda da ita mana nan ta fad'i mata ko waye take so, da tsananin mamaki Fauzy tace "Ya Haisam dai da na san pictures d'inshi a wayanki wanda rannan ina maki wasa nace don Allah ki had'a ni da shi?" d'aga mata kai Fatun tay Fauzy ta sake cewa "Amma ba kince man Yayanki bane dama ba d'an gidan ku bane?" Ajiyar zuciya Fatun ta sauke kafin ta fara bata labarin tsakaninta da Haisam tun daga farkon haduwarsu har zuwa lokacin da ya tafi harda bayan tafiyar tashi da auranta da aka fasa har ta fara karatu, da tsananin mamaki Fauzy tace "Dama a gaske akwae irin wannan Mutanen da zasu rink'a yi ma mutum Alkhairi haka don Allah! Kai gaskiya koma akwae to da wuya a samu sai dace, gaskiya banga laifin k'awar ki Haulat ba don ko nice wllh irin tunaninta zanyi akan shi, ko bata fad'a bama irin wannan dole zuciyar mutum ta kamu da son shi don ita tana son mai kyautata mata ni kaina iya labarin nan da kika ban baki ji yadda ya k'ara burge ni ba sosae wllh, amman na matuk'ar tausaya maki Zarah irin wannan a kwae ciwo ace kana son mutun amman bai sani ba" d'an ta6e baki Fatuu tay tasa hannu tana goge sauran kwallan dake fuskarta can Fauzy tace "Amman fa da ace lokacin muna tare dake ni zan baki shawarar ki fad'a masa ne koma in je in fad'i mashin" d'an waro ido Fatuu tay Fauzy ta jinjina kai tace "am serious duk da ita Friend en ki da Uncle d'inki sun fad'a maki abunda yake daidai amman ni nayi la'akari da yanayin shi na Mutum ne da yasan darajar mutane mara wulakanci mai fahimta sannan mai son yaga farincikin wani don kin fad'a mashi bana tunanin zai k'i fahimtar ki tunda ai yasan yadda zuciya take kuma yana daga cikin wad'anda suka fi kowa sanin halin ki balle ace k'imar ki zata zube ko yaga baki da kunya" d'an murmushi Fatuu dake ta bin ta da ido tay kaman bazata ce komae ba sai kuma a sanyaye tace "to ko na fad'a mashin ai bashi da wani amfani kamar yadda kowa yace tunda yana da wanda yake so zai aura k'arshe hak'uri kawae zai bani" Fauzy tace "Yes he might do dat and he might not also kar ki manta yana son farincikin ki ina tunanin zai iya amincewa ko don farincikin ki ita kuma Matar tashi in har tana son shi da Gaske zata amince" d'an murmushi Fatuu ta sake yi tana girgiza kai tace "Don baki san yadda take son shi bane wannan ai dole tay tsananin kishin shi ma wllh ban tunanin zata iya amincewa ya aureta ita da wata ko dangin shi ba lalle su yarda ba tunda yar uwar shi ce" gyad'a kai Fauzy tai kafin tace "ina rok'on Allah yasa rabon ki ne shi ya cusa mashi tsananin son ki har ya kasa zama ya dawo yace a d'aura maku aure ko baki gama karatun ba" wani kallo Fatuu ta bita dashi Fauzyn tay yar dariya tace ko bata so ta d'an ta6e baki kawae kafin tace itama tana mata Addu'ar Allah ya bata Wanda take so da sauri tace "Mujaheed ne kadae na so kuma a yanzu ko ya dawo wllh tllh bazan Aure shi ba duk da kuwa har yanzu da sauran son shi a zuciyata amman ko ke ai bazaki ban shawarar in Aure shi ba" jinjina kai Fatuu tay "hakane nima na fad'a ne kawae amman ban fatar wannan azzalumin ya zama mijin ki don baisan darajar dan'adam ba ki manta da shi kawae kina zaune Allah zai kawo maki wanda ya fi shi a komae yanzu mu dage da karatun dake gaban mu shi yafi ba tunanin wasu da basu san ma muna yi ba k'arshe Muzo muja ma kan mu matsala su sun riga sun gina rayuwarsu" sosae Fatuu ta shiga bata shawarwari kan ta daina damuwa da wani Mujaheed su maida hankali, mik'ewa Fatun tay tana fad'in itafa wllh yunwa ma take ji ta koma gadonta Fauzy da ke kallonta tace ko ta dafa masu indomie ne, "Ni dae na gaji da cin wata indomie wllh" yar dariya Fauzy tay tace "to ai itace mai sauk'in dafawa a halin karatun nan da muke ciki yar gidan Ya Handsome, to ko in dafa mana Macaroni sai asa sardine nasan zata yi dad'i" d'an yamutsa baki Fatuu tai ta fara k'ok'arin saukkowa daga gadon tana fad'in ita dae bari ta fara shan Cornflakes gaskia bata iya jira har sai an dafa wani Abinci ta nufi inda Provisions d'in su suke idanun Fauzy a kanta can tace "Wai ashe Ya Handsome d'in ki ne yasa maki Zarah da kika ce man haka ake ce maki" daga inda take ta d'aga mata kai ta k'ara cewa "Allah sarki wllh k'awar nan taki ta burgeni tana ina?" tace mata tayi Aure tana Nijar "Da wuya yanzu ka samu irin su don k'awance yanzu ya zama abunda ya zama shiyasa ni tsoron tara k'awaye ma nike ko da can, amman dae ke nasan nayi dace don tunda na gan ki kika burge ni kuma in sha Allahu nima zan zamar maki madad'in Haulat bazan ce fin ta ba don duk abunda ake so a k'awa tana dashi, tana son ki da Alkhairi bata maki bakin ciki da hassada farin cikin ki shine nata haka damuwar ki damuwarta ce bata maki kallon bare face Yar'uwa wad'annan abubuwan duk an rasa su a k'awancen yanzu da k'yar ake samun masu wasu daga ciki Allah yasa mudace mufi k'arfin zukatan mu dae" daga inda take ta amsa mata da Amin tana murmushi, "Amman dae watarana yakamata mukai mata ziyara har Nijar d'in" Fauzy ta fad'a, da sauri Fatuu ta kalleta ta zaro ido tace "tabb ai saidae ko in ta haihu kin kuwa san yadda tafiyar take a kwana a wuni ana abu guda lokacin da muka je bikinta baki ga yadda kafafuwana suka sumbuk'e ba" dariya Fauzy tasa lokacin Fatun ta kawo mata cup d'in Cornflakes data had'a mata itama ta amsa tana murmushi tace mata thanks suka fara sha. Sosae su Fatuu suka dage da karatu don tsallake ma had'arin dake tattare da jarabawar intro dake gabato su, Bayan wata ukku da yin pre intro suka yi ita intro d'in, cikin hukuncin ubangiji Fatuu ta tsallake don sunanta ma ne farko a list d'in haka Fauzy ma ta tsallake sai faman murna wad'anda suka ci suke suna kiran clean pass yayin da wad'anda basu samu ba ke a mawuyacin hali harda masu suma abun ba dad'i wllh to amman haka tsarin yake dole sai Mutum ya dage yanzu wata shiddan da suka 6ata ya tashi a banza sai dae hak'uri, bayan cin jarabawar ne akai masu clinical posting nan cikin Asibitin saidai ba'a kai Fatuu da Fauzy wuri d'aya ba Fatuu Gyne aka kaita ita kuma Fauzy tana a A&E (Accident & Emergency), su Fatuu an fara kama hanyar zama ma'aikaciyar lafiya hadda su farin glasses take sanyawa yanzu kuma ba k'aramin kyau yake mata ba sai tayi kaman cikakkiyar nurse ba Student ba patients da masu jinyarsu sai dae kaji anata Sister sosae Fatuu ke jin tausayin irin halin da Matan wurin ke ciki masu lalurar data danganci haihuwa da sauransu. Ranar Friday bayan sallar Juma'a Fatuu ta dawo daga Makaranta don sun tsaya Hostel saida aka yi salla tana shiga gida ta aje Bagpack d'inta mai kyau mai manne da Yar teddy jikinta sanye da sababbin uniform d'in data canza da suka zama cikakkun dali6ai, a gefen kitchen ta aje jakar ta nufi toilet abun ya riga ya zame mata jiki da wuya ta shigo gida bata wuce toilet ba, bayan ta fito ta d'auki jakar ta wuce ciki, d'akin gwaggo ta nufa ta d'aga labulan lokacin tana kwance akan gado saidae ba bacci take ba suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi Fatuu ta shiga ta zauna a bakin gadon Gwaggo tace "ai na ji shigowar ki halan saida akai abunda aka saba?" Dariya tayi tace "ni gwaggo banson yin fitsari a wani wuri wllh kyankyami nike ji ga toilet infection da ake kamuwa da shi in mai cutar yayi using wuri kaima kayi shiyasa ko a Makaranta in ina can indae zan yi amfani da toilet to sai na wanke shi fess sannan fitsari ma a tsaye nike yi sai in bi da ruwa aita ce man sarkin tsafta kuma ni infection d'in nike tsoro don muguwar cuta ce" jinjina kai gwaggo tay tace "tabbas kuwa don har haihuwa take hanawa, akwae wasu saiwowin magani ma da nasa a kawo sai ki rink'a amfani dasu har acan Makarantar na tsarki ne akwae kuma na sha don wani lokacin duk yadda kake kiyayewa sai kiga ka kamu baka sani ba gara kana yin riga kafi" d'aga kai Fatun tayi gwaggo ta tambayeta ya Makarantar tace Alhamdulillah nan ta shiga bata labarin maras lafiyan dake ward d'in da take gwaggon nata girgiza kai tana Addu'ar Allah ya basu lafiya can tace mata bata jin yunwa ne taga bata nemi Abinci ba tace eh da yake sun biya hostel sun ci abu gwaggo ta tambayeta Fauziyya tace itama ta tafi Weekend gidan Yayarta tace Allah sarki daga haka suka d'an yi shiru can tace "Na manta ban fad'a maki ba Hajiyar Sanata fa ta dawo d'azun bayan kin tafi Makaranta don har na ma shiga na gano ta" waro ido Fatuu tay sai kuma tay yar dariyar farinciki tace "Allah sarki Hajiyata ashe ta dawo wllh nayi missing d'inta" gwaggo na murmushi tace "itama haka don sai tambayarki take wllh ba kamar da ta ji abunda ya faru ta jajanta sosae har tace ta k'osa ta ganki" mik'ewa Fatuu tay da sauri tace bari taje to gwaggo ta d'aga mata kai ta nufi hanyar fita, bayan ta aje jakar goyon tata a d'aki ta fito ba tare da ta cire uniform d'in ba da glass d'inta manne a fuska ta nufi gidan Hajiyar Sanata............. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._ [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2038* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .......Da k'yar taja k'afafunta ta koma kan kujera ta fad'a da6as duk jikinta yay weak ta kasa gane wannan bak'in Abubuwan da yake mata na miye, bai jin komae yanzu yake ta6a ta ga wani irin kallo da yake mata wanda ada sam ba irin shi yake mata ba, shiru tay kamar mai nazari can wata zuciyar ta ayyana mata kodai son ta yake tunda ada da bai mata hakan ai ba son ta yake ba kuma ko Fanan da tazo itama yana ta6a ta lokacin kuma soyayya suke can kuma wata zuciyar ta tuno mata da labarin Fauzy wanda itama ai tace Mujaheed na ta6ata kuma k'arshe ya yaudareta, rasa tunanin ainihin dalilin canzawar Haisam d'in tay k'arshe jiki a sanyaye ta mik'e ta d'auki laptop d'in bayan ta kashe hasken parlon ta nufi d'akinta don ta san tuni gwaggo tay bacci, kayan jikinta ta cire ta sa na bacci ta haye gado sam tunanin Haisam yak'i barinta wani iri take ji ran ta sai bata yake ko dae da gaske son nata yake in kuwa haka ne da zata yi farinciki to amman mizai sa sai yanzu zai so ta bacin yana da mata wata zuciyar ta k'ara raya mata nan fa ta shiga wasi wasi k'arshe ganin tana neman harmutse kwakwalwarta da tunane tunane ta bar ma ran ta ba son ta yake ba kawae, Fauzy ce ta fad'o mata a rai tay tunanin ko ta kirata ta sanar mata game da zuwan shi sai kuma ta ayyana kamata yay ta bata surprise suje tare da shi to amman ya zata yi wata zuciyar tace in kince ya kai ki ai zai kai ki ne, d'an murmushi kawae tay k'arshe ta jawo d'ayan pillow dake gefen kanta ta rungume shi sosae ta lumshe ido a haka bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba, Haisam na komawa part d'in shi ya nufa duk da bai dad'e da yayi wanka ba da zai je gidansu saida ya k'ara watso ruwa ya fito d'aure da farin towel a k'ugun shi ya nufi press don saka sleeping dress, yana gamawa ya nufi switch ya kashe hasken d'akin kafin ya kunna bedside lamb guda d'aya ya haye gado ya kwanta yana facing sama da alama dae Haisam ya d'aura aure da tunani yana haka wayarshi ta fara ringing ya kai hannu gefen shi ya d'auka sunan Lovely Wife ya bayyana wato Fanan ce ta kira picking yay yasa speaker ya aje wayar kusa da kan shi cike da k'auna ta fara Magana tana nuna yadda tay missing nashi shima yace yayi nata ta tambaye shi ya akai bai bacci ba ko rashin ta by his side ne ya hanashi yi d'an murmushi kawae yay sai kuma yace mata Yeah, haka suka cigaba da hiran yawanci itace mai Maganar shidae saidae yay murmushi mai d'an sauti ko ya bata amsa a tak'aice daga baya sukai sallama har tana ce mashi zata zo a cikin dream d'in shi tayi mashi duk abunda ya kamata yana murmushi ya furta mata Ok had'i da take care, yana cire wayar ya aje akan bedside ya koma yana facing sama kaman da farko had'i da lumshe ido saidae bansan ko duniyar tunanin ya k'ara tafiya ba ko kuma baccin ya yi ba. Washe gari sai wurin k'arfe 10 na safe Fatuu ta tashi tunda weekend ne ba school, bayan tayi breakfast ta fara gyara gidan zuwa k'arfe sha d'aya da rabi ta gama komae taje tayo wanka ta shirya cikin short skirt da yar vest zaman school ya koya mata sa guntayen kaya dama kuma zafi ake, saman gado ta haye ta d'auki wayarta ta fara lallatsawa nan ta fara doubting na kota kira Haisam d'in tayi mashi Maganar zuwa gidan su Fauzy ko kuwa ta k'yale shi,to in ta Kira kawae sai tace tana son ya kaita gidan k'awarta ita bata iya zuwa ne dole zai ya kaita haka tay ta wasi wasi can dai ta yanke kiran nashi lokacin da kiran ya shiga yana zaune a Parlor bai jima da gama yin Breakfast ba anan part d'in na shi don ko kayan ma ba'a kaiga zuwa an d'auke ba yanata Operating system jikin shi sanye da farar jallabiya jin ringing d'in wayar yasa ya kai hannu gefenshi ya daukkota ya kalli screen d'in kafin yay picking yasa speaker ya aje ta agefen laptop d'in d'an shiru sukae Fatun ce ta fara cewa "Ya Haisam ina kwana an tashi lpy" amsa mata yay da "Alhamdulillah and how was ur night?" Itama tace Alhamdulillah sai kuma tay shiru shi kuma yana ta lallatsa computer d'in gabanshi rasa ta yadda zata fad'i mashi tay sai kawae tace "d..dama na kira in k'ara maka godiyar Laptop" jinjina kai yay tamkar tana gani sai koma ya furta is Ok suka k'ara yin shiru can taji ya furta "then What else?" d'an gwale ido tay jin ya gano akwae abunda take son fad'a cikin yar inda inda tace "d....dama so nike in ba damuwa ka kaini gidan wata k'awata zaku gaisa da ita na ta6a bata labarin ka" shiru yay ita kanta sai taji kaman she sounds stupid da ta fad'i mashi hakan can taji yace "Magana ta kike da wasu kenan" rud'ewa tay bata zaci zai fad'i hakan ba cikin shaky voice tace "a...a wllh Ya Haisam kaji na rantse ni ba Maganar ka nike yi ba ita kadae ce itama don k'awata ce sosae kuma saida taga pic d'in ka a waya na ne ta tambayeni na fad'a mata kai yayana ne shine...shine..." sam ta rasa mi ma zata ce, shikam d'an ta6e baki yay fuskarshi d'auke da d'an murmushi can taji ya kira sunanta "Zarah" kaman zatayi kuka tace "Na'am" yace "unhun am listening shine what" abu ta had'iya da k'yar tace "na fad'a mata lokacin baka K'asar kayi Aure, kawae dama don ku gaisa ne amman a bashshi ma" still murmushin yake yi kafin yace "by what time?" d'an waro ido tay had'i da yin d'an murmushi tace "duk lokacin da yayi maka ni yau ba abun da nike yi" taji yace "is it Ok by 4:00?" Da sauri tace eh yayi yace Ok till then tayi mashi godiya kafin ta kashe wayar yaci gaba da latse latsen shi, murna ce ta lullu6eta bayan ta gama ta fad'a saman gadon harda su mirgina mirgina can kuma a fili ta furta "Ya Haisam kai na daban ne wllh I so much luv u" ta rungume hannayenta a k'irji had'i da runtse ido. Misalin k'arfe hud'u saura kwata ta gama shiryawa har Salla tayi kaya kawae ya rage ta saka tay tsaye gaban wardrobe d'inta tana tunanin wanda yakamata ta sa, in ta janyo wannan sai taga bai yi ba ta maida ta fiddo wasu sai faman ruwan ido take k'arshe dai ta fiddo wasu riga da skirt na atampa da bata ta6a saka su ba cikin kayan da Chairman ya bata, atampar na da zanen flowers army green da kuma light green ba k'aramin amsarta kayan sukai ba dama kuma saida aka aunata kafin aka yi su, yar light make up tayi tasa yan kunne da sark'a silver sai Agogo haka gyale da jaka da takalma duk mahad'in kayan ne takalman half cover ne masu tsini jakar ma mahad'insu ce bata sa turare sosae ba don gwaggo ta hana ta iya roll on ta goga sai ta shafa Humra a jiki kayan kuma dama suna sakin kamshinsu sakamakon turaren kaya da suke amfani dashi, k'arfe hud'u saura yan mintuna da basu wuce 2 ba sai ga kiran shi yace in ta gama yana waje tace to, bayan ta fito saida ta lek'a d'akin gwaggo don yi mata sallama dama tun lokacin da tay Magana da Haisam d'in ta sanar mata, sosae gwaggo ta hau yabon kyaun da tay tana ce mata sai kace Amarya ita dae Fatuu sai dariya take har waje gwaggo ta biyota ta tsaya a bakin kopar d'akinta tana kallon Fatun cike da jin dad'i har ta fice sannan ta koma ciki, tunda ta fito ya kai idonshi kanta ta zagayo ta gaban Motar ta zo d'ayan side d'in duk idonshi na akanta saidae ita bata gani don glass d'in blacktinted ne, bud'e kopar gaban tayi ta shiga bayan ta rufe ta juya da murmushi ta gaida shi shima kallonta yake ya jinjina mata kai kawae wani abun mamaki sai kace yasan kayan da zata saka don kuwa shima wani d'anyen Voile ne army green ya saka sumar nan tasha gyara hatta Agogo da takalman kafarshi duk army green ne sosae kayan suka fito mashi da farin shi ita kanta Fatuu a cikin ranta saida tay mamakin kalar kayan ganin sun hau dana jikinta sosae, saida suka hau hanya idon shi akan titi ya tambayeta ina zasu tace mashi Goruba road yaci gaba da tafiya ba tare daya ce komae ba, tsit kake ji ba wanda ya k'ara cewa uffan Fatun ta juyar da fuskarta tana kallon hanya yayin shi kuma yake driving saidae akai akai yake d'aga ido ya kalleta ta cikin mirror a haka har suka iso ita ta rink'a nuna mashi hanyar da zai bi har suka k'araso gaban gidan ya parker, da murmushi tace mashi zata shiga tay mata magana ya d'aga mata kai ta fita idon shi akanta, da sallama ta shiga Parlon gidan saidae ba kowa a ciki ta wuce d'akin Fauzy ta tura kopar da yar sallama ta shiga lokacin Fauzy na kwance saman gado tayi rubda ciki wayarta ruk'e a hannu da alama wani abu take kallo tana sanye da doguwar rigar material koda ta d'ago taga Fatuu ce mai yin sallamar wata yar k'arar farinciki ta saki ta saukko da gudu ta tarbeta, kama hannunta guda tay tana k'are mata kallo kafin tace "Yar matar nan wai kinga kyaun da kika yi kin wanku wllh sai kace wata Amarya" dariya Fatun tayi Fauzyn ta sake cewa "koda yake in sha Allahu Amaryar ce ta Ya Haisam da zai yi" zaro ido Fatuu tay ta d'an bud'e baki tace "ki rufa Asiri kar Aunty Fanan ta ji mu" yar dariya Fauzy tay tace "to sai me in Allah ya k'addaro ai bata isa ta hana ba wllh duk min kishinta" Fatun tace "amman dae Fauzy ai ana barin halak ko don kunya ko" wani kallon kina da hankali tay ma Fatuu tace "Halak....Kunya, ke yanzu idan yazo yace yana son ki zai aure ki sai kice a'a kenan duk da son da kike mashi Saboda matar shi?" Fatuu tace "Uhmm Fauzy mubar Maganar nan tunda bai ce ba d'in, ni kinga zo muje waje zaki gaisa da wani ne" da mamaki ta maimaita wani kuma Fatun tace mata eh still da mamakin ta sake ce mata wanene tace tazo dai suje ta gani ta juya taje ta d'aukko gyale ta dawo suka nufi waje tana ce ma Fatun kodae Sabon saurayi tayi ita kuma tay murmushi tace suje dae, tunda suka fito take bin Motar da kallo duk ta k'agu taga wanene a ciki a tare suka isa driver side d'in yana ganinsu a bakin kopar Motar glass d'in ya fara sauka slowly lokacin da fuskarshi ta bayyana mutuwar tsaye Fauzy tay har saida kirjinta ya buga don bata ta6a kawo ma ranta irin halittar da zata gani kenan ba jin saukar muryar Fatuu tay tace "Fauzy ga Ya Haisam ya zo" tana murmushi tay mata Maganar har saida ta had'iye miyau Kutt kafin tay murmushin yake tamkar yar koyo tace "Ina wuni Ya Haisam an zo lafiya" da k'yar ta k'arasa a haka ma ba k'aramin kokari tay ba wurin daidaita Maganar amman duk da haka saida muryarta tay d'an rawa cikin cool voice d'in shi yace "lpy ya School" wohoho Fauzy na ganin Mujaheed ya gama had'uwa acikin Mazan Nigeria to yau ga Kakanshi ta gani wanda komae nashi mai tafiya da mutum ne amsa mashi tay da Alhamdulillah ya jinjina mata kai kawae daga haka bai k'ara cewa komae ba, a hankali ta matso gefen Fatuu cikin rad'a tace "bari in yi ma Aunty Mareeya Magana su gaisa don Allah na bata labarin da muka yi da ke" bata jira cewar Fatuu ba ta juya da sauri ta tunkari gate shi kam bai ma san suna yi ba don ya maida kanshi jikin Headrest, bata dad'e ba ta dawo tun daga bakin gate d'in tay ma Fatuu alamar su shigo ta juya ta kalli Ya Haisam d'in sai ma ta rasa ya zata ce mashi can dae ta kira shi ya juyo da face din shi kanta cikin yar inda inda tace wai zai shiga su gaisa da Auntynta da take zaune wurin ta wani kallo ya bita dashi da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa can taji yana kokarin bud'e Motar ta d'ago da sauri sai kuma taja gefe ya fito, alamar suje yay mata da kai tay gaba yana biye da ita suka nufi gidan, lokacin da suka shiga Parlon da yar Sallama ya shiga Aunty Mareeya dake a tsaye da fara'a ta shiga yi mashi sannu da zuwa ta nuna mashi wurin zama ya zauna itama ta zauna gaidashi tay duk da da gani ta girmeshi tayi mashi an zo lafiya ya iyali a nutse ya amsa mata shiru ta biyo baya idonshi a kan carpet Fauzy ta fito ruk'e da k'aton tray data d'auro ruwa da lemu ta d'aura saman c-table Aunty Mareeya ta kalli Fatuu dake zaune tace "Zarah zuba mana" tana niyyar tashi ya dakatar da ita ta hanyar d'an d'aga mata hannu ya furta "am Ok" Aunty Mareeya na murmushi tace ai yakamata yasha ruwan zumunci ko yace bai jin kishi ne can kuma sai ya mik'e yay mata sallama itama ta mik'e tana mashi godiya ya fita, kallon juna sukae su duka ukkun Aunty Mareeya ta d'an gwalo ido har saida ta basu dariya su duka tace "Zarah dama Akwae irin wad'annan Mutanen a Nigeria" Fauzy ta kar6e "wllh Aunty nima lokacin da ya sauke glass nay arba da face d'in shi har tsoro naji nafa san shi a picture amman gaba d'aya ban gane shi ba don sai naga ma ya fi kyau a fili....." Aunty Mareeya ta sake cewa "Tubarkallah ma sha Allah kai kace hausa bazata fito daga bakin shi ba koda yake ai kun ce ruwa biyu ne koma ace ukku, Zaraah banga laifin ki ba wllh kin yi namijin kokari da kika iya danne son shi baki furta mashi ba ai inni ce wllh ban san lokacin da zan fad'a mashi ba" gaba d'aya suka sa dariya dama Aunty Mareeya yar barkwanci ce anan Fatuu ta gaya ma Fauzy zancen Laptop d'in daya kawo mata ta hau murna tana fad'in su Shar sun yi computer suma Aunty Mareeya ta hau yabon kirkin shi tana fad'in ita ko a labari bata ta6a jin mutum da ya had'a abubuwa irin nashi ba ga kyau ga kud'i ga tsananin kirki k'arshe ta hau yi ma Fatuu Addu'ar Allah ya mallaka mata shi in rabon ta ne Fauzy ta amsa da Amin ita kuma tay murmushi kawae can tace bari taje kada yay ta jiranta Aunty Mareeya harda fad'in yi maza kar ki rink'a 6ata mashi rai kita mashi biyayya har mu samu yazo hannu duk suka kwashe da dariya, tare da Fauzy suka fito lokacin ya rufe glass d'in side d'inshi suka zagaya d'ayan side d'in Fatuu ta bud'e ta shiga Fauzy ta d'an rankwafa tana ce mata sai sun had'u a School ran Monday kafin ta kalli Haisam tay mashi sai anjima da godiya, kud'i ya mik'a ma Fatuu yace ta bata yan dubu dubu ita kanta bata san ko nawa bane lokacin har Fauzy ta juya Fatun ta kirata ta juyo ta mik'a mata tace in ji Ya Haisam waro ido tay alamar mamaki sai kuma ta amsa ta sake lekawa tay mashi godiya kai kawai ya d'aga ba tare daya kalleta ba, a d'an can gefe ta tsaya saida taga tafiyar su sannan ta nufi cikin gidan da gudu a Parlor ta iske Aunty Mareeya bata shiga ciki ba ta nufeta tana dariya ta d'aura mata kud'in saman jikinta tace shi ya bata, hannu tasa ta ruk'e haba Fauzy ta zauna gefen ta da yake saman 3 seater take nan suka dasa hirar Haisam har Aunty Mareeya na cewa wannan dole ma Matar shi ai tay kishin shi. Bayan sun baro Unguwar EE ya wuce da ita tunkan ya tsaya Fatuu ta fara yin Murmushi tunawa da randa ya zo da ita, bayan yayi parking a parking space ya kalleta yace su je a tare suka fito suna shiga entryway ya nufi shagon saida wayoyi Fatuu ta bishi lokacin da suka shiga da fara'a masu shagon suka tarbeshi suna mashi sannu da zuwa ya amsa kafin ya tambayi wanda ke gabanshi ko sun kawo iPhone 15 yace mashi a'a amman in sha Allahu gobe zata iso akwae ma wad'anda suka bada akawo masu zai iya yin payment shima ya fiddo card ya mik'a mashi ba 6ata lokaci ya fitar da kud'in ya bashi receipt yace a zo dashi goben ya furta Ok daga haka suka fito, waje suka nufa wurin packing space ya bud'e ya saka receipt d'in da aka bashi a shagon waya Fatuu na tsaye gefe ya juyo bayan ya rufe Motar suka kalli juna Calmly yace mata yana son shiga gym ko zata jira shi a pack wani kallo tay mashi kafin ta d'an tura baki tace ita mi zata yi a park kaman wata k'aramar yarinya komawa yay ya jingina da jikin Motar ya bita da ido kawae ganin kallon da yake Matan ne yasa ta yamutsa fuska tace "Ko fa da can ma da muka zo ai na girmi wurin balle yanzu" d'an murmushin gefe yay ya jinjina kai kaman bazai ce komae ba sai kuma yace to ta shiga Mota su tafi da sauri ta kalleshi tace ina ya bata amsa da gida tana kallon shi tace ya fasa yin gyming d'in ko zai dawo yace mata yadda ya yuwu ganin zai bud'e Motar duk sai bata ji dad'i ba don sai take ganin kaman zata hana shi yin abun da yake so da sauri ta dakatar dashi ta hanyar fad'in "To muje gym d'in tare mana ba sai in tsaya wurin Aunty Anah ba" juyowa yay ya kalleta Calmly yace "bata nan yanzu" tace tana ina ya bata amsa da dama Service ya kawo ta garin ta d'an zauna yanzu ta koma garin su, jinjina kai Fatun tay tace "Allah sarki Aunty Anah, to ai nasan baka rasa sanin wasu ba sai ka had'a ni da su ba nima inyi exercise d'in dama wllh ina d'an jin nauyin jikina" d'age gira yay yana mata wani kallo tace "bafa zanyi bane da kaina sai a koya man nike nufi" kaman bazai ce wani abu ba sai kuma yace "taya zaki da wannan dressing d'in?" Yay tambayar yana mata nuni da kan shi ta d'ukar da kanta ta kalli kayan jikinta skirt din straight skirt ne yay mata k'yam a jiki ko tafiya da sauri bata tunanin zata iya yi balle kuma exercise d'agowa tay ta bishi da ido kawae ya juya zai bud'e Motar ta sake tambayar shi tafiya zasuyi baza su je gym d'in ba yace ta shigo zasu je su dawo ne tace to ta zagaya ta shiga, yar tafiya sukai bayan sun bar wurin ba mai tsawo sosae ba suka iso bakin wata plaza yace su je ta bud'e Motar, Wani k'aton shago suka nufa wanda kayan sports ne kawae a ciki shak'e, bayan sun shiga ya gaisa da masu shagon ya fad'i masu irin kayan da suke so aka d'aukko masu kamar kala biyar don su za6a da kai ya nuna ma Fatun yace ta d'auki wanda take so ta bishi da kallon mamaki don bata yi zaton inda zasu zo ba kenan k'arshe ta zabi wasu riga da wando rigar tight long sleeve ce sai wandon ta shigen wanda Fanan ta ta6a sawa a gabanta, bayan ya biya su aka saka masu a babbar leda mai tambarin wurin suka fito, within Few minutes suka dawo EE d'in yace ta d'aukko kayan suka nufi ciki, lokacin da suka shiga gym d'in a bakin bangaren mata ya tsaya ya fiddo wayarshi ya kira wata mai suna Deborah yace ta fito yana son Magana da ita suna gama wayar sai gata ta fito cikin shigar gym tana ganinshi ta washe baki tana gaishe da shi ya amsa, nuna mata Fatuu yay yace pls ta shiga da ita ta taimaka mata tay gyming bata iya ba da sauri ta amsa da Ok ta kai idonta kan Fatuu lokaci guda taga kaman ta san Face d'inta can ta tuna tace mashi kaman itace suka ta6a zuwa ko yace mata yeah sosae tay mamakin ganin girman da Fatun tay ta gaishe da ita ta amsa da fara'a ta kama hannunta suka shiga shi kuma ya wuce side d'in su dama ya taho da jakar shi komae na ciki har kayan da zai canza, bayan su Fatuu sun shiga ne ganin bak'uwar fuska yasa aka fara tambayar Deborah bak'uwa akayi ne tace eh, wad'anda suka dad'e suna zuwa wurin tay masu bayanin kowacece nan fa suma sukai ta mamaki suna fad'in ta girma ita dae murmushi kawae take, wata k'opa Deborah ta nuna ma Fatuu tace change room ne taje tasa kayan tace to ta nufi d'akin after some minutes sai gata ta fito uhmm nasan ko ban fad'a ba kowa yasan kayan zasu yi mata kyau ko don dirinta zo kaga idanu gaba d'aya ta janye hankulan su nan fa aka shiga yabawa ana Maganar shape d'inta duk da kasancewar ta mai k'ananun shekaru gashi dama kanta ba kallabi shima gashin ba'a k'yale shi ba sai da suka tanka ganin abun yayi yawa yasa Fatuu ta rink'a fad'in Tubarkallah a hankali, Sosae tay exercise d'in kuma ta matuk'ar jin dad'i don komae ta iya a nutse Deborah ta kokkoya mata cike da kiyayewa gudun kada a sake samun matsala,Sai lokacin da aka tashi sannan suka dakata ganin kowa na fita a yadda yake yasa Fatuu yin tunanin ba sai tasha wahalar mayar da kayanta ba tunda ga gyale sai tay rolling d'in shi kawae ta shiga ta d'aukko kayan data cire dama ta saka su a cikin ledar kayan, lokacin da ta fito Deborah na tsaye tana jiranta da murmushi ta ce suje H.zakee na nan waje yana jiranta suka nufi hanyar fita, yana d'an can gefe suka fito suka nufe shi idon shi akan Fatuu har suka k'arasa Deborah na murmushi tace mashi gata nan tayi kokari don ta iya komae kuma tayi sosae ya d'aga mata kai kafin ya furta mata thanks tay masu sallama ta tafi, kallonshi Fatuu tay tana murmushi ganin sun yi tsaye tace su tafi tana kokarin yin gaba kawai taji ya kamo hannunta guda yay pulling d'inta back har saida ta d'an bangaji gefen jikinshi, zaro ido tay tana kallon shi lokaci guda hankalinta ya tashi ganin kallon da yake mata ya d'an 6ata rae ta fara tunanin mi tayi mashi a kausashe taji yace "How can u go out like dis!" Sai da yay Maganar ta fahimci laifinta murya na d'an rawa tace "n...naga wai Mota zamu hau ne kuma nasa gyale" kallonta kawae yake wai tasa gyale komi wannan d'in yay mata ganin ta d'an tsorata yasa shi sassauta d'aure fuskar da yay yace "amman haka kika fito gida?" da sauri ta girgiza mashi kai ita sai lokacin ma ta tuna da ba hakan ta fito ba da sauri tace bari taje ta maida kayanta ta juya sam ya kasa janye idon shi daga kanta har ta shige wurin, lokacin data fito ta maida kayanta bata ganshi a wurin ba hakan yasa ta nufi hanyar fita saida ta fita can waje ta hango shi a tsaye jikin Mota yana ganinta ya bud'e ya shiga itama ta k'arasa ta bud'e ta shiga ba tare da ya ce mata komae ba yaja suka tafi.......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2040* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ............Washe gari Fatuu na gama sallar Asuba bata koma bacci ba kasantuwar ranar Monday ce ta hau yin shirin tafiya School, Misalin k'arfe bakwae saura tana cikin yin breakfast jikinta sanye da Uniform wayarta dake a gefenta ta fara ringing ta kai hannu ta d'auka sunan Ya Haisam ta gani a screen d'in har saida ta d'an yi mamaki kafin tay picking, gaishe da shi tayi bayan ta d'aga ya amsa yay mata ta tashi lpy tace lpy Lou tambayarta yay k'arfe nawa zata je School tace mashi yanzu tana yin Breakfast ne sai wurin kaman k'arfe 7:15 zata tafi yace Ok zai zo ya kai ta daga haka yay cutting kiran, bin wayar tay da kallo bayan ta cireta daga kunne tana kallo can kuma ta d'an ta6e baki ta ajeta taci gaba yin breakfast d'in ta, K'arfe bakwae da Minti goma ya kira yace in ta gama yana waje ta amsa mashi da to dama Hijab kawae zata saka sai jakar goyon ta ta nufi gaban dressing mirror ta dan k'ara gyara fuskarta ta saka glass d'inta daga haka ta fita, sai da ta lek'a d'akin gwaggo tay mata sallama ta bata kud'in abun hawa da Abinci tace ta barsu Ya Haisam ne yazo zai kaita kuma dama akwae wasu canji zata yi break d'in dasu tana murmushi ta d'aga mata kai kafin tay mata Allah ya tsare ya bada sa'a ta amsa da Amin tana nufar Kopar fita, bayan ta shiga Motar ta rufe ta juya ta kalle shi yana sanye da jallabiya ash mai gajeran hannu da d'an murmushi ta gaishe shi fuska a sake ya amsa yana kallonta kafin ya juya ya ja Motar suka tafi, shiru ba wanda ya k'ara tankawa sai itace ke ta d'an kallon shi sai kuma ta juya duk yana lura da ita ta mirror can ta k'ara juyowa shima ya juya karaf suka had'a ido ya d'age mata gira yace "What?" d'an motsa baki ta fara yi a marairaice tace "dama akan wayan da ka siya man jiya ne" idonshi akan hanya yace mi ya samu wayan tace "ba komae, d..dama Kawu Amadu ne ya fad'i mana kud'inta to shine muka ga tayi kud'i da yawa don har gwaggo ma tana cewa zata yi maka magana kud'in sun yi yawa sosae" d'an guntun murmushi yay kaman bazai ce komai ba yana ta driving ita kuma ta kafe shi da ido can yay sigh yace "yanzu ya za'ai da shi kenan?" Da sauri tace "a barta kayi wani abun da kud'in" d'age gira yay yace "to in ba abunda za'ai da kud'in fa?" Tura baki tay yana kallon ta ta mirror a shagwa6e tace "ya za'ai ace ba abunda za'ai da kud'i?" shiru yay yana cigaba da driving da d'an murmushi akan face d'in shi ita kuma sai faman k'unak'uni take tana yamutsa Fuska sai kace abun tsiya akai mata bana Arziki ba duk yana kallonta ta mirror can taji yay sigh yace shikenan akwai yadda za'ai to, da sauri tace to ta kai hannu k'asa ta d'aukko jakarta ta bud'e dama ta sako wayar don ta bashi, fiddota tay ta maida jakar ta mik'a mashi d'an kallon wayar yay ya maida idon kan hanya taji yace "ai ba nine zan yi ba kece" da d'an mamaki kan fuskarta tace "ni kuma, to ni zanje in maida masu ne?" girgiza mata kai yay kafin yace "I mean zaki iya bayar da shi in baki so" waro ido tay da alamun Al'ajabin jin abunda yace ya d'an kalleta ya d'age gira alamun tabbatar da abunda yace d'in ta cuno baki tana mashi wani kallo batare da ya kalleta ba taji yace shi take harara a shagwabe tace ita ba hararan shi take ba, tasan tunda ya fad'i hakan ba amsa zai yi ba dole ta maida ita cikin bag d'in, Lokacin da suka iso ya parker tay mashi godiya tana niyyar juyawa ta bud'e kopar yace mata wait ta dakata ya bud'e glove box tana ganin kud'i zai ciro ta tsuke fuska bayan ya d'aukko 5k ya mik'a mata yace tay break tak'i amsa tana kallon shi yace ta amsa mana kawae sai ta fara jujjuya mashi kai tana mashi magiyar ya bassu gwaggo ta bata, bin ta da ido kawae yake yace tunda ya fiddo ta amsa sai ta k'ara kawae sai ta juya mashi k'eya still yay yanata kallonta irin abubuwan shagwabar nan da take yi ba k'aramin tafiya take dashi ba sai tai ta burge shi, jin yayi shiru yasa ta juyo ganin kallon da yake mata ne yasa itama ta kafe shi da nata idon suka cigaba da bin juna da wani irin kallo mai wuyar fassarawa dole Fatuu ta sare don bazata iya jurewa ba ba shiri ta sadda kanta jikinta duk yayi weak d'an guntun murmushin gefe yay ya kira sunanta ta amsa jin bai k'ara cewa komae ba yasa ta d'ago ta kalleshi alamar ta amshi kud'in Yay mata da kai sai ta kasa k'ara yi mashi gardama don duk ya kashe mata jiki a sanyaye ta mik'a hannun ya bata ta furta ta gode ta kai hannu ta d'aukko jakarta zata fita taji ya tambayi k'arfe nawa zasu tashi d'an kallon shi tay tace k'arfe biyu ya d'aga kai ta juya ta bud'e Motar ta fita, nufar class area tay tana yi tana waiwayen Motar yana kokarin juyawa har ya tafi, tunani iri iri a ranta har ta isa Class tana shiga Fauzy dake ta zuba idon ganinta ta mik'e da sauri ta nufo ta tana mata welcome ta d'an mata side hug Fatun na murmushi suka nufi seat d'in su, bayan sun zauna Fatuu tace da wuri ta taho kenan tace mata a'a ai tun jiya da daddare ta dawo suna haka malamin su ya shigo, basu k'ara samun daman yin hira ba har saida akayi break sannan Fauzy ta shiga tambayarta ya Haisam Fatuu tace mata shine ma ai ya kawo ta da d'an mamaki tace "kai haba, shi dae bai gajiya da yin hidima dake bawan Allah amman mudae ba wannan muka fi so ba kawae ya fito ya mana Wuff da ke don Allah" d'an ta6e baki Fatuu tay tace "Uhm ai ke Fauzy wannan ba komae bane hidima ai sai jiya da muka fita dashi" cike da k'aguwa tace "ya kai bani in sha" nan Fatuu ta kwashe komae na kayan da ya siya mata har zuwa wayar daya siya mata hannu Fauzy tasa ta rufe baki da tsananin mamaki ta maimaita sunan wayar Fatun tace wllh bari ma ta gani ta kai hannu ta d'aukko jakarta bayan ta bud'e ta zura hannu ta fiddo da kwalin wayar ta mik'a mata, zaro ido Fauzy tay baki bud'e da d'an k'arfi tace "Wllh iPhone 15 d'in ce da gaske" wannan Maganar da tay ta jawo hankalin yan seat d'in bayan su wata Aisha ta ja hijab d'in Fauzy ta waiga tace taji tana iPhone 15 su ganta ta mik'a masu kan kace mi sauran wad'anda suke cikin ajin basu fita break ba harda maza duk suka taso ganin wayar ana tambayar wake da ita Fauzy na nuna masu Fatuu wani harda cewa ashe dae ita big girl ce mai babbar harka haka, wata student ma tace ashe dae ita babbar Hajiya ce basu sani ba wani dake gefe ya tambayi wai nawa take ne 15 d'in na kusa dashi ya bashi amsa nan fa wasu suka zaro idanu wasu suka hau jinjina kai, lokacin da Fauzy ta amshi wayar ta juya don ta ba Fatuu ganin yanayin fuskar ta yasa ta tambaye ta lafiya miya faru ne kaman zatayi kuka tace "ni fa Fauzy ban so aka san da wayar nan ba wllh don ni tsoro nike ji ina zaman zamana in ja ma kaina bala'e" dafa Shoulder d'inta tay tace "in sha Allahu ba abunda zai same ki ki kwantar da hankalin ki" a sanyaye tace Allah yasa, don ta k'awar mata da damuwar tace "Amman fa gaskiya Zarah ina tunanin Ya Haisam son ki yake wllh" waro ido Fatuu tay tace "ke waya fad'a maki da har zaki rantse" tace"uhum haba Zarah kiyi tunani mana nasan ba yau ya fara maki hidima ba amman fa hidiman ta canza salo ke baki fahimta ba tunda yake dake ya ta6a maki hidima irin wannan ya d'auki abun har million kacukam ya baki, je ki asa ma shi mai yawan Alkhairi ne mizai sa bazai siya maki wata irin waya ba tunda gasu nan iri iri in ma masu uban kud'i ne duk akwae su amman sai ya za6i wannan da fitowarta kenan kuma ba kowa ne zai iya riketa ba ke in ba don kina da wani matsayi a wurin shi ba da yafi wanda kika sani taya zai maki hakan?" bin ta da ido kawae Fatun take dama kanta duk a d'aure yake game da sabbin abubuwan da yake mata Fauzy ta ci gaba "ba fa wani abun mamaki bane don ya kamu da son ki kema da ai yadda ya d'auke ki kika d'auke shi ko ta zo ta canza zani to shima d'in zai yuwu hakan ce ta faru dashi ni wllh in hakan ta kasance sai nafi kowa farinciki ko ba komae Allah ya amshi Addu'ar mu zuciyarki kuma ta samu abunda take muradi" sai lokacin Fatuu tay d'an murmushi had'i da yar ajiyar zuciya, "Yanzu ace sai ya bayyana maki yana son ki kuma yana son kuyi aure zaki hak'ura da karatun ki bi shi?"Fauzy ta tambaye ta had'i da d'age gira wani kallo Fatuu ta jefa mata kafin tace "har ma sai na baki amsa ai kema kinsani" dariya Fauzy ta sa tace "baki tsoron matar shi kawae sai ta ganki da mijinta matsayin Matar shi?" Fatun tace "to ai cewa kikae in yace yana sona kuma ya aure ni kinga tunda shi ya 6allo ruwa ai shi zai san yadda zai da ita ko" duk suka sa dariya Fauzy na fad'in uwar wayo wato shi yace yana so sai kace ita irin bata so d'in nan Fatun na dariya tace to ai irin hakan saida basaja suka ci gaba da dariya har Fauzy na Addu'ar Allah ya nuna mata ranar da zaice yana son ta a kur kusa Fatun tace shida ma zai tafi yau tace ai duk inda yake zai iya furta mata hakan ba wata matsala bace, daga baya Fatun tace suje suyi break lokaci nata tafiya kar a dawo suka tafi, k'arfe biyu daidai Haisam ya kirata yace yana inda ya ajeta da safe, tare da Fauzy suka taho suka zagaya d'ayan side d'in Fatuu ta bud'e gaban ta shiga Fauzy ta leka tana murmushi ta gaishe da shi fuska a sake ya amsa mata tace Zarah ta fad'a mata yau zai tafi Allah ya kiyaye a gaida Aunty Fanan ya amsa da Ok zata ji daga haka tace ma Fatuu sai sun had'u Gobe tace to, tun bayan da ta shiga cikin Motar ta gaishe da shi ya amsa bata k'ara cewa komae ba har suka hau hanya can ta kalleshi tace "sai k'arfe nawa zaka tafi?" Fuska sake yana kallon hanya taji yace ta k'osa ya tafi ne da sauri tace a'a ta dae tambaya ne kawae gyad'a kai yay suka d'an yi shiru sai kuma taji yace "ko za ki ne?" da sauri ta kalleshi tace ina yace "U.s" d'an bud'a ido tay tace "ni da nike karatu" shiru ya d'anyi still bai kalleta ba can yace "da ba karatun za ki je kenan?" itama shirun ta d'an yi har saida ya d'an juyo ya ce mata bata ji bane cike da jin kunya a hankali ta d'aga mashi kai alamar eh kawae sai gani tay yay d'an murmushi ya maida idon shi kan hanya saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya sake cewa "kin daina tsoron matana kenan" tsuke fuska tay ta d'an tura baki tace "ai ni dama ba tsoron ta nike ba kawae dae ina ganin in naje bazata ji dad'i ba taga bamu had'a komai ba na bika har can karshe ma ta koro ni" d'an murmushi yay kafin yace "to yanzu da kika ce da ba karatun zaki kin daina tunanin zata ji ba dad'in ne?" d'an watsa hannu tay tace "to ai kaine ka tafi dani ko bani nace ba in ma taji ba dad'i kai kasan yadda zaka yi" wani kallo ya juyo yay mata duk sai tasha jinin jikinta ta fara sussuna kai kamar daga sama taji yace "yanzu in tafi dake d'in kenan?" Da sauri ta kalleshi suka had'a ido ya d'age mata gira alamar ta bashi amsa da sauri ta girgiza mashi kai tace "ni fa ba so nike in bika ba tun farko na tambaye ka lokacin da zaka tafi ne don in raka ka Airport" murmushi kawae yay yaci gaba da driving d'in shi itama ta juyar da kanta taci gaba da kallon hanya har suka iso gida ba wanda ya k'ara tankawa tay mashi godiya ta d'auki jakarta tana kokarin bud'e kopar ta ji yace mata before 4:30 zai tafi ta d'aga mashi kai ta fita yaja Motar ya wuce gida. Tana shiga gidan ta wuce d'akin gwaggo tay mata sannu da gida anan ta sanar mata zancen tafiyar Haisam gwaggon tace bari ta tashi to taje tay mashi sallama, d'aki Fatuu ta nufa ta aje jakarta kafin ta wuce kitchen ta zubo Abinci ba wani mai yawa ta ci ba don sunci abubuwa sosae da break ita da Fauzy tana gamawa ta wuce toilet don yin wanka, Misalin karfe hud'u da yan mintuna lokacin angama sallar la'asar Fatuu ta isa part d'in Haisam tana sanye da riga da skirt na atampa mai jajayen flowers had'i da mayafi mahad'in su tayi d'aurin kallabi mai kyau ga glasses d'inta manne a idanun ta, a hankali ta tura kopar parlon ta shiga da yar sallama idanun ta suka sauka kan Abbas dake zaune kan L-shape yana sanye cikin k'ananun kaya kasumbar shi tasha gyara gashin sai kyalli yake suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi yace mata ta shigo mana tayi tsaye a bakin kopa ta nufi armchair ta zauna ta gaida Abbas d'in da murmushi ya amsa mata ta tambayi Abdul yace yana school bai dawo ba da yake yana yin lesson ta jinjina kai shiru suka d'an yi ta juyar da kanta can taji yace tazo raka mutumin nata ne d'an murmushi tay kawai bata ce komae ba shima yar dariya yay bai k'ara cewa komae ba can kuma sai ya mik'e yace yana zuwa in Haisam ya fito tace mashi yana Mota ta d'aga mashi kay ya nufi hanyar fita, after few seconds sai gashi ya fito yana janye da d'an trolley da kuma jakar laptop yana sanye da kananun kaya kai idonta tay kan shi har ya k'araso cikin parlon ya tsaya gefenta yana kallonta ganin hakan yasa ta mik'e tana cigaba da kallon shi da d'an murmushi ta gaida shi ya amsa ta fad'a mashi Ya Abbas yace yana Mota yana dai ta kallon ta tana Maganar kawae sai ji tay slowly yace "baki tsawo ne?" bud'a ido tay alamar mamaki sai kuma ta d'an tura baki tace "duk tsawon da nayi, dafa a iya nan d'in ka nike yanzu kuma kad'an ya rage in kawo shoulder d'in ka" tay Maganar tana nuna mashi inda ada tsawonta yake a jikin shi daga inda take, shiru bai ce komae ba yana cigaba da kallonta fuska a sake ganin bai ce komae ba yasa a d'an shagwa6e tace "to tunda baka ganin tsawona kai sai ka samman naka tunda kana dashi kai sosae" shirun dai yay sai kuma ya d'age gira yace tana so ta d'an k'ank'ance ido ta d'aga kai alamar eh, aje jakar laptop d'in dake a d'ayan hannun shi yay kan d'ayar armchair d'in dama ya saki trolley d'in tunda ya tsaya kawae sai gani tay ya kai hannu d'aya ya jawota jikin shi a razane ta zaro ido tana kallon shi shima haka still holding onto her motsa baki ta fara amman ta kasa cewa komae bata ankara ba sai ji tay ya ida yin hugging nata sosae ta yarda har ya d'aura Ha6arshi a saman kanta, zaro ido Fatuu tay ta d'an bud'e baki alamar Al'ajabi k'amshin turaren shi ne ya cika mata hanci har bata san lokacin da slowly ta lumshe idanunta ba zuciyarta ta fara melting sun d'an d'auki lokaci a haka can wata zuciyar ta fara raya mata hakan fa da sukae ba kyau miyasa zata bari ya rungume ta haka bacin tasan ba matar shi bace ita ko har ta manta da labarin yaudarar da aka ma Fauzy ne da sauri ta bud'e idonta jin tana kokarin d'ago da kanta yasa shi cire beard d'in nashi daga saman kanta ta d'ago ta kalle shi sam bazata iya karantar yanayin fuskar shi ba, ganin baida niyyar sakinta yasa ta kira sunan shi cikin disasshiyar murya ya d'an bud'a ido alamar amsawa da ido tay mashi nuni da rok'on da yay mata alamar ya saketa ya kafeta da ido kamar bai gane mi take nufi ba hakan yasa ta d'an 6ata fuska sigh yay slowly ya saketa had'i da furta "am sorry" shiru tay ta sadda kanta ya kai hannu zai kama trolley d'in ta d'ago tace mashi bari ta rike bai ce komae ba ya d'auki jakar laptop d'in yay gaba ita kuma taja trolley d'in tabi bayan shi, saida suka je part d'in Hajiya harda Abbas ta rako su har bakin Mota tana ma Haisam Allah yasa a sauka Lafiya ya gaida su Farha da yake Lagos zai sauka daga can gobe zai wuce Us, Abbas ne ya shiga driver seat sai Haisam na gefen shi ita kuma Fatuu ta shiga baya ya tashi Motar Hajiya nata d'aga masu hannu har suka fuce, bayan sun hau hanya sama sama Abbas da Haisam d'in ke yin hira can Abbas ya kalli Fatuu ta cikin mirror yace "Mom Zarah yau ba kuka kenan Ya Handsome zai tafi" dariya tay mashi bata ce komae ba Haisam ya d'an juyo ya kalleta ta rufe Fuskar ta da gyalen ta Abbas duk yana kallon ta ta cikin mirror yana dariya yace "yakamata yau ma a d'an rera mana gaskiya" d'an tura baki tay tace "ai ko wanccan lokacin ma don ina tunanin ya tafi kenan ko zai zo sai an dad'e" Abbas yace "Hajiya na raye ai dole zai rink'a zuwa ko don ita yanzu ma ai in ya tafi baza'a dad'e ba sosae zai dawo don akwai bikin wani Friend d'in mu da za'a yi bayan babban salla kuma shine best friend d'in shi a cikin musulmai" waro ido Fatuu tay tace shi kenan ba musulmi bane yace eh Christian ne d'an sarkin inyamurai ne sun d'an zauna anan amman yanzu ba'a nan suke da zama ba amman shi wanda zai auren shi ke kula da wasu wurare na mahaifin shi kamar Hotels da wasu kamfuna tare sukae Secondary da shi, jinjina kai Fatun tay kawae shi dai Haisam bai tanka masu ba, bayan sun iso Airport d'in gaba d'aya suka fito Haisam ya zagaya wurin Abbas ya bashi hannu yay mashi godiya shima yay mashi fatan sauka lpy ya juya ya kalli Fatuu dake d'ayan side d'in tana kallon shi da d'an murmushi shima yay mata daga haka ya juya ya tafi har ya d'an yi nisa Fatun ta k'wala mashi kira ya tsaya ya juyo ya kalleta da faffadan murmushi ta d'aga hannu tana yi mashi bye bye yana murmushi ya jinjina mata kai kafin ya juya Abbas dake dariya ya kalleta suka had'a ido ganin dariyar da yake mata yasa ta d'an cuno mashi baki yace shidae ai bai ce komae ba ta shige cikin Motar shima ya bud'e ya shiga ya ja suka tafi. Sati biyu da tafiyar Haisam aka fara Azumi saida ya turo mata kud'i masu yawa na siyan kayan Azumi tuni ta kai kayan da ya siya mata wurin Kb don a d'inka da aka fara Azumin har tana zolayar gwaggo wai ya taga bata da niyyar yi mata d'inkin salla tana dariya tace ai ita Haisam ya d'auke mata nauyin wannan kuma, a cikin kayan da ya siya mata taba gwaggon atampa da lace amman sai ta amshi lace d'in kawae tace ta bar atampar ta k'ara ba yadda bata yi da ita ba amman tak'i karba sai taba Fauzy ita kawai dama tana da wani material da bata d'inka ba ta had'a mata sosae Fauzy taji dad'in kayan tay ta godiya a tare suka kai d'inkin bayan Fauzy tasa Fatuu ta rakata itama shagon Zee ta siyo kayan sallanta har Fatuu ta k'ara siya mata wasu abubuwan Zee taji dad'in kawo mata Customer da Fatun tay har tay adding nasu a groups d'inta da take business koda zasu ga abu suna so, Alhamdulillah angama Azumi lpy ranar salla tare da Hajiyar Sanata harda Fauzy suka je Masallaci ko k'unshi ma tare suka je gidan su Nanah kamar kowacce Salla, da Fauzy gida zata tafi yin salla amman Saboda tana son su yi yawo tare da Fatuu ta fasa sai bayan sallan zasu tafi tare da Aunty Mareeya, su Fatuu an zama yan mata sun dai sha kyau da sallar abun ba'a Magana Tk ne ya kaisu wurare kamar yadda Haisam ya bashi umarni ko ina tare da Fauzy take zuwa har gidan Abbas suka je da sauran wurare sun sha zafafan hotuna da iPhone d'in Fatuu harda Vedios suka daddaura a status anan Haisam ya gani har ya yaba sosae taji dad'in yabon da yayi har saida ta kasa hak'uri ta ma Fauzy forwarding sai ga Voice note d'inta harda su shewa tana fad'in "Zarah da alamu mutumin nan fa ya kamu wllh kawae miskilanci ne ke d'awainiya da shi amman muje zuwa gab yake da ya shigo hannu" ita dae Fatuu dariya kawae take, har gida Aunty Mareeya tazo tayi ma gwaggo an sha ruwa lpy bayan salla haka ma Abbas ya kawo Feenah da suka zo gidan Hajiya, ana gama salla Fauzy ta tafi Funtua Fatuu taso ta bita amman gwaggo ta hana satin ta d'aya ta dawo suka koma Makaranta sun ci gaba da karatu ba tare da wasa ba a haka har babbar salla tazo wannan lokacin Yola gwaggo tace zasu je yin salla Fatuu taji dad'i sosae ana saura kwana biyu suka tafi Hajiya ma wannan karon saida babbar salla taje Abuja don da k'arama cewa tay bazata je ba ai bata dad'e da dawowa ba Fauzy a Katsina tay salla cike da kad'aici saida suka gama aikin naman layya sannan suka tafi Funtua, su Yadikko sun matuk'ar yin murna da zuwan su kar ma Mino taji ta kasa boye murnarta harda d'inki gwaggo tayi masu su duka harda baffan Fatun da shima yay farin cikin ganin su, kud'i masu yawa da zasu siya lafiyayyun raguna biyu Haisam ya turo ma Fatuu yace suyi layya harda kud'in da zatayi hidiman salla lokacin da ta kira don yi mashi godiya yake sanar da ita sun zo suna Abuja har tana ce mashi zai je katsina ne yace ai Hajiya bata nan kuma suma basu nan wurin wa zai je tace ai da an gama salla zasu koma yace suma bazasu dad'e bane amman yana nan zuwa bikin abokin shi da Abbas ya fad'a mata tace Allah ya kaimu, ana gama salla da kwana biyu suka dawo don ba wani Hutu suka samu ba just salla break ne, washe garin da suka dawo Fauzy ma ta dawo suka cigaba da karatun su. A bangaren mutanen Us ma tuni sun koma lokacin Auren su ya cika shekara harda kusan wata a lokacin Fanan ta matsa lamba kan lalle sai suje a duba lafiyar su ta bangaren haihuwa don tun auren su bata ta6a yin 6atan wata ba koda kuwa sau d'aya gashi tana period lpy lau, wannan karon ma dai kaman sauran lokutta Haisam d'in cewa yay basu bukatan hakan yanzu ta bari a k'ara lokaci in bata samu ba sai su je amman shi a wurin shi still yayi wuri amman tak'i gaba d'aya ta burkice mashi wai dole tasan wani cikin su bai rasa matsala tunda har sun shekara amman har yanzu batai conceiving ba, sosae ta hana mashi zaman lafiya harda su koke koke to shi mutum ne mara son yaga wani cikin damuwa balle ma ace shine sila hakan yasa yace tayi duk abunda ya kamata sai su je d'in, sosae taji dad'i ba 6ata lokaci tay making appointment da Doctor d'in da zasu gani a Asibitin da take aiki washe gari suka je aka fara masu diagnosis daga baya kuma yay referring nasu wani Asibitin suga Fertility specialist anan aka cigaba da yin binciken tun daga Family history nasu ko akwae wanda bai haihuwa zuwa su awon jini da hotuna sosae akai investigations saidae an fi yi ma Fanan don ita yake ganin kaman in ma matsala ce to daga ita ne sakamakon wasu tambayoyi da yay mata sai washe gari suka gama likita ya fara masu bayanin result na binciken da akayi masu anan yake fad'i masu Fanan ce mai matsalar don tana da Polycystic ovary syndrome (PCOS) Wato matsala ce data shafi kwan da take saki har saida Fanan ta firgita jin wannan Maganar a razane tace how comes ita da take having regular periods! Shima Doctor d'in yayi mamakin hakan daya kasance bata ga wani symptoms ba don yawanci indai mace nada matsalar to zata rink'a samun irregular periods ne bazata rink'a yin period very often ba saidae kuma a tambayoyin da yayi mata farko ta tabbatar mashi wani lokacin periods d'in yana d'an dad'e mata in yazo amman bata maida kai kan hakan matsala bane don tun kafin tay aure ma tana hakan wanda hakan ma na daga cikin alamomin matsalar tata sai kuma a Family history nan ma ta tabbatar mashi da Kakarta wato Hajiyar Sanata tana da Matsalar yawan miscarriage lokacin tana haihuwa hakan yasa iya yara biyu ta Haifa a rayuwarta daga Mahaifin Haisam d'in sai kuma Mahaifiyarta hakan ma ya k'ara tabbatar da yuwuwar tayi gadon matsalan ne daga wurinta, tuni hawaye suka wanke mata fuska don tasan tabbas indae tanada wannan matsalar to zata iya hana ta samun ciki balle harta haihu rarrashinta suka fara yi suna bata hak'uri Doctor yace bai kamata ta tashi hankalinta ba tunda is treatable za'a iya dacewa ta samu cikin nan ya shiga bata shawarwari da abunda yakamata ayi, tun bayan da suka baro Asibitin take ta cizgar kuka tana fad'in "Ya Haisam am barren! I cannot give birth I can't give u child!!!" Duk ta firgice abunka da fara jijiyoyin kanta duk sun firfito fuskarta ta yi jajir ya kai hannu ya ruk'o nata yana d'an murza shi alamar rarrashi sai faman kuka take tana fad'in ta bani bazata iya haihuwa ba shikenan bazata bashi d'a ba har shakewa take wurin yin Maganar Saboda kuka shi kam sai faman rarrashinta yake a nutse yake fad'in ta kwantar da hankalinta hakan ai ba yana nufin kwata kwata bazata haihu bane Allah na iya nuna ikon shi a kowane lokaci a haka har suka iso gida still yana ruk'e da hannunta suka shiga Parlor a saman 3 seater suka zauna ya rungumeta yana cigaba da rarrashinta sai faman fad'in tasan da wuya ta haihu tunda tayi gadone kuma gara ita Hajiya ma tana yin miscarriage amman itafa ko sau d'aya bata taba samun cikin ba balle ma tayi 6arin, suna cikin hakan can ya ji ta tayi tsit kamar ba ita ke rizgar kuka ba da sauri ya d'ago fuskarta da tay jage jage yaga idanunta a rufe alamar ta suma a razane ya mik'e ya kwantar da ita akan kujerar ya nufi fridge ya d'aukko bottle water ya dawo bayan ya cire murfin ya d'an zuba a cikin hannun shi ya yayyafa mata a fuska sai gashi ta ja wata irin doguwar ajiyar zuciya da sauri ya rufe robar ya aje gefe ya duk'a a gabanta ya kai hannu yana d'an bubbuga face d'inta had'i da kiran sunanta slowly ta bud'e idanun suka k'ura ma juna ido can kawae sai ta k'ara fashewa da wani Sabon kukan daga kwancen tana girgiza kai hannu yasa yana shafa gefen fuskarta a hankali yaci gaba da rarrashinta can ta yunk'ura ta mik'e da gudu ta nufi d'aki ya mik'e ya bi bayanta.......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2039* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *Wannan page tukuici ne agare ki Mrs Haisam Kano ina matuk'ar godiya Allah ya k'ara dankon kauna keda Haisam ya sauke ki lpy Amin🤲😍* *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Tunda suka hau hanya ba wanda yace uffan idon shi na akan hanya ko ta mirror bai kalleta ba yanata driving itace ke d'an juyowa ta saci kallon shi, a hanya ya tsaya bakin wani Masallaci ba tare da ya kalleta ba yace zai yi salla ta d'aga mashi kai tana ta kallon shi har ya fita, bayan an gama ya dawo suka tafi saida ya k'ara tsayawa bakin wani Cafe ya fita bada jimawa ba ya dawo hannunshi ruk'e da ledoji masu d'auke da tambarin wurin guda biyu ya bud'e back door ya saka sannan ya dawo ya shige driver seat ya ja suka tafi duk jikin Fatuu yay sanyi ganin ko kallonta bai yi, a bakin kopar gidansu ya tsaya ta kalleshi a sanyaye tace "Nagode" sai lokacin ya d'an kalle ta ya jinjina mata kai kawae har ta bud'e Motar taji voice d'in shi yana fad'in ta d'au abun dake baya a hankali tace to ta idasa fita ta rufe kopar, ganin ledojin biyu ne yasa ta d'auki guda d'aya ta k'ara mashi godiya still kan ya jinjina mata ta rufe mashi kopar ta nufi gida shi kuma yaja ya tafi, tsaye tay a bakin wurin tana kallon bayan Motar har saida yasha kwanar gate d'in gidan sannan ta juya sukuku da ita ta nufi cikin gida, d'akin gwaggo ta nufa ta shiga da yar sallama lokacin tana zaune akan abun salla tana yin tasbih Fatun ta nufi ciki ta zauna akan kujera, juyowa gwaggo tay da d'an murmushi tace sun dawo Fatuu ta d'aga mata kai ta k'ara cewa "Amman dai ba iya gidansu Fauziyyar kuka je ba ko" kai Fatuu ta d'aga tace "Eh daga can gym muka wuce" cikin rashin fahimta gwaggo ta tambayi ina ne hakan tace mata wurin motsa jiki gwaggon ta jinjina kai suka d'an yi shiru sai kuma tace ma Fatun ya taga kamar wani abu ma damunta da sauri ta k'ak'alo murmushin yak'e tace ba komae ta gaji ne ta yunk'ura ta aje ledar hannunta a gaban gwaggon tace shine ya siyan mata gwaggo ta hau godiya tana shi Albarka, ganin Fatun na niyyar mik'ewa tace ta d'auka ta d'iba sai ta d'ibar ma Amadu shima ta mik'a mashi tace to ta d'auki ledar ta nufi kopa ta fita, bayan ta d'an d'iba su shawarma ne harda ice cream ta kaima Kawu Amadu waje har yana tsokanarta yana fad'in Amaryarmu harda tsaraba ta d'an tura mashi baki yasa dariya don yasan bata so shiyasa yake tsokanarta yana ce mata hakan tun bayan da aka fasa aurenta, da k'yar ta ci don duk komae bai mata dad'i bayan tayi sallar isha ta watso ruwa ta canza kaya zuwa na bacci ta haye gado, tana son ta d'an duba littattafan ta amman ta kasa tay kwance kawae. Tun bayan da ya koma gidan saida ya fara zuwa part d'in Hajiya ya kai mata d'ayar ledar ganin yana niyyar tafiya tace ya tsaya yaci Abinci mana sai ya tafi gaba d'aya yace Ok tasa Saude ta kawo mashi anan Parlor yana ci Hajiya dake zaune tana mashi fira har ya gama sukae bankwana ya koma part d'in shi, wanka yayi ya shirya cikin sleeping dress yana son ya d'an yi wani aiki a computer amman sai yaji bai iyawa ya haye gado kawae ba tare da ya kashe Switch d'in d'akin ba ya kwanta yana facing sama hannunshi na dama ruk'e da beard d'in shi kafarshi d'aya a mik'e d'ayar kuma ya d'an d'agata a lankwashe yana d'an girgiza ta da gani akwae abunda yake tunani. Sai faman juyi take don ta kasa ma yin bacci ga Maganar Aunty Mareeya dake ta mata yawo ta d'azun da tace kar ta rink'a 6ata mashi rai gashi ta fahimci kamar ranshin ya 6aci ta ayyana ita sam bata san hakan zai 6ata mashi rai ba ai da bata fito hakan ba ta tsaya ta canza kayan, wata zuciyar ce ta bata ta kira shi kawai ta bashi hak'uri zai fi kaman bazata yi hakan ba can kuma sai ta tashi zaune ta kai hannu ta janyo wayar ta bud'e ta shiga call log sai da ta d'an yi jimm kafin can kuma tay sending mashi kira, yana a yadda yake kiran ya shigo ya juya ya kalli wayar dake akan bedside kafin ya mik'a hannu ya d'aukko ta idon shi suka sauka kan screen d'in ya bi kiran da kallo kaman bazai picking ba can ya d'aga yasa speaker ya juya daman shi ya aje wayar saitin fuskar shi, shiru sukae ba wanda ya tanka har bayan d'an wani lokaci sannan yaji cikin sanyin murya ta fara Magana "Ya Haisam dama ina so in baka hak'uri don Allah in ranka ya 6aci am sorry" yanayin fuskar shi ne ya canza kamar zai yi murmushi kafin yay sigh taji yace "kin man wani abu ne?" d'an yamutsa fuska tay tace "Abunda ya faru d'azun naga kaman kayi fushi" lumshe ido yay sai kuma slowly ya ware su taji yace karta damu bai yi fushi ba har saida ta d'anyi murmushi, "Miyasa baki bacci ba har yanzu?" Tura baki tay a shagwa6e tace "ba Kaine ba ka canza man fuska" d'an murmushi yay har saida ta jiyo sautin shi a ranshi ya ayyana har yanzu bata canza ba kaman yadda ya san ta da bata son taga anyi fushi da ita duk sai ta damu, ce mata yay ya wuce ta daina damuwa tace to suka d'an yi shiru can taji yace yanzu sai tay baccin ko tace ai bata fara jin baccin ba yace Ok suka d'an k'ara yin shirun, kaman daga sama taji yace to ta bashi labari ba shiri ta waro ido don abun da bata zaci jin shi ba daga bakin shi bane tana murmushi tace "to ai ni banda labaru don daga gida sai Makaranta nike zuwa saidae in baka na Asibiti" sosae yake jin dad'in voice d'inta in tana Magana a shagwa6e, shima murmushin yake yace mata bai son wannan ta manta matarshi Doctor ce tace Shikenan suka k'ara yin shiru, "Baki fad'a man yadda akai calling off Auren ki ba" wannan karon k'irjinta ne ya buga jin tambayar da ya jefo mata har saida ta had'iye miyau Kutt, taya zata fad'a mashi abunda Khalid yay mata wanda shine silar komae, lokaci guda taji bata ma iya yi mashi wannan bayanin jin tayi shiru yasa shi ce mata yana saurarenta cikin dabarbarcewa tace "Ya Abbas bai fad'a maka ba?" Yace ya d'an fad'a mashi yana son yaji komae ne daga wurinta, a rud'e don har wata yar zufa taji a fuskarta tace mashi to ai abunda ya fad'i mashi shi ya faru ya furta mata Ok har saida ta dafe k'irji irin tasha da k'yar d'in nan, "Zaka dad'e ne anan?" ta tambaye shi d'an shiru yay kafin yace "Nah Next tomorrow zan wuce" d'an zaro ido tay tace ranar Monday kenan yace mata Yea shiru ta d'an yi duk sai taji wani iri jin tayi shiru yasa shi tambayar ta koda wani abu ne da sauri tace "a'a Allah ya kaimu" a hankali ya amsa da Amin sai kuma ta k'ara ce mashi sai Allah ya kaimu yace baccin yazo kenan tace eh yace "Ok gud nyt" tace to ta kashe wayar a hankali ya lumshe ido, to bansan dai ko bacci bane shima yazo mashi ba, aje wayar tay gefe ta koma ta kwanta tay lamo hakanan take jin wani iri tunda taji yace jibi zai tafi a haka da k'yar bacci ya kwashe ta. Washe gari wurin k'arfe 11 lokacin ta gama gyaran gidan tana zaune a d'aki saman gado tana duba littafin ta idanunta sanye cikin glass sai ga kiran Haisam ya shigo d'an murmushi tay ta d'aga ta gaida shi yay mata ta tashi lpy ta amsa da Alhamdulillah d'an shiru yay daga baya kuma sai yace mata ta fad'a ma gwaggo zasu d'an fita around 3:00 tace mashi to suka yi sallama ta sauka daga gadon ta iske gwaggon a d'aki tana kwance, koda ta sanar mata d'an murmushi tay tace ba komai Allah ya kaimu Fatun ta amsa mata da Amin kafin ta fito ta dawo d'aki, kasa cigaba da karatun tay ta tattare books d'in ta mayar cikin bag ta nufi wardrobe don ta za6i kayan da zata za ba sai lokacin ba ta kasa za6a, wani dark purple material lace ta fiddo yana da kananun flowers light purple da tsabu tsabun ash mai kaman silver d'inkin straight gown ne yayi kyau sosae ta fiddo gyalen shi light purple da takalma sai yan kunne da sarka silver da yar please purse itama silver komae ta aje a gefen gado sauran jiran lokacin saka su, zuwa k'arfe biyu da rabi tayi wanka taci Abinci ta hau shiri ba 6ata lokaci ta gama lokacin ukku ta d'an gota da Minti biyar daidai ya kirata yace yana waje tace to, saida taje tay ma gwaggo sallama yau ma tana ta yabon gayun nata Fatun sai dariya take tace mata sai sun dawo ta fito, idon shi a kanta har ta zagayo ta bud'e gaban Motar ta shiga bayan ta rufe ta juya suka had'a ido tana murmushi ta gaishe shi shima fuskar shi a sake ya amsa yana sanye da complete bak'ak'en kananan kaya jeans da t-shirt haka agogon dake d'aure a hannunshi itama bak'a ce sumar nan tasha gyara sai salk'i take ga k'amshi da ya cika Motar abun ba'a Magana kasa d'aurewa Fatuu tay ta d'an juyar da kanta gefe ta lumshe ido ya Haisam naso ya ida kasheta da salon gayun shi, jan Motar yay suka tafi ba tare da wani ya k'ara cewa komae ba sai sanyin Ac dake ratsa sassan jikin kowannen su, a daidai wata k'atuwar plaza ya karya kan Motar ya shiga ciki lokaci guda Fatuu ta ga kaman tasan plaza d'in bayan ya parker a wurin da aka tanada ya kalleta yay mata alamar suje da kai ta bud'e ta fito ya nufi cikin plaza din tabi shi saida ta ga shagon da suka tunkara mai d'auke da sunan Zee Collections sannan ta gane wurin har saida tay d'an murmushi, shi ya fara shiga tabi bayanshi ba kowa a Parlon sai wata yarinya da gani ba ita bace wadda ke a shagon ba lokacin da suka ta6a zuwa wato Esther saidae itama yarinyar Christian ce k'ilan ko k'anwar waccan ce tana ganin su ta mik'e da sauri tana ce masu welcome kafin ta gaishe dasu cikin harshen turanci suka amsa Haisam ne ya tambayeta Ogar tata tace tana ciki bari ta kirata ta juya da sauri Fatuu tabi kanta da kallo da akai ma k'waryar molo kamar dae waccan Esther d'in a ranta take ayyana kawae a aske mata gashi ai sai tayi hauka wllh, zama Haisam yay kan doguwar Leather sofa d'in dake a wurin yay ma Fatuu alamar ta zauna ta nufi can gefen shi ta zauna lokacin Zee ta fito tana sanye da doguwar rigar Boubou ta Atamfa tana yin arba da Haisam ta waro ido alamar mamaki shi kuma yay mata d'an murmushi can daga gefensu ta zauna saman wata kujerar tace "Zakee Manyan gari ko in ce Manyan dawa kai ne a K'asar tamu saukar yaushe?" Fuska a sake ya fad'i mata lokacin da yazo tana ta murmushi tace mashi an zo lafiya ya amsa mata lokacin Fatuu ta gaishe da ita ta kai idonta gareta tana amsawa da fara'a can tace "Wai kaman Zarah ko?" Yar dariya Fatuu tay tace itace Zee ta bud'a ido had'i da ruk'e ha6a tace "Zarah kece kika girma haka halan kin gama Secondary ma?" Fatuu tace mata eh ta gama ta tambaye ta taci gaba da karatu tace mata eh, "Wani School kike ne?" Zee d'in ta tambaya Fatuu ta bata amsa da "School of Nursing" jinjina kai zee tay tace "Gud, Allah ya bada sa'a" ta amsa mata da Amin, maida idonta tay kan Haisam dake latsa waya tace "H,Zakee ya Matan ka ta haihu kuwa ai ina jin kaman anyi 9 Months da auren ku ko?" Kai ya d'aga mata alamar eh, tace "halan ta haihun don nasan ba lalle ka fad'a ba koda yake da ta haihu ko a wurin su Jidderh na ji ai, ba da ita ka zo bane?" Kai ya sake d'aga mata alamar eh tace Allah sarki sai kuma ta kalli Fatuu dake ta murmushi itama tayi mata ta sake maido dubanta kan Haisam tace "Wai ni H,Zakee ko dae kai zaka mana Wuff da Zarah ne?" Kamar saukar aradu haka Fatuu taji Maganar ba shiri da sauri ta kalli Zee dake ta murmushi sai kuma ta juya kan Haisam suka had'a ido da sauri ta kauda idon nata ta sadda kanta k'asa wani kallo yay ma Zee tana ganin haka tasa dariya tace "Serious ka Aure ta kawai kaga kayi kiwon abun ka kenan?" d'an murmushin gefe kawae yay bai ce komai ba ta kai idonta kan Fatuu da har lokacin kanta ke sadde tace "Zaraah ko baki son Yayan naki?" Shiru bata ce mata komae ba bata kuma d'ago ba hakan yasa Zee cigaba da yin dariya Haisam yay sigh kafin yace mata zata za6i kaya ne Fatuu na jin haka ta d'ago da sauri ta kalle shi tana niyyar yin magana Zee tace "a'a Zarah kar muyi haka dake fa kaya aka ce zaki za6a ki tashi kawae muje dama Akwae d'ibar farko ta salla suna ciki ban kaiga fiddo su ba sai an fara Azumi kin ga rabon ke zaki fara za6a ne" shiru Fatuu tay don ta riga ta kashe mata baki tace suje tana kokarin mik'ewa itama Fatun ta mik'e har sun tafi Zee ta juyo tace ma Fatuu ta shiga ciki tana zuwa ta koma gun Haisam ta tambayeshi kaman kala nawa yace ta tambayeta tace Ok sai kuma ta d'an rankwafa yadda zai ji ta cikin kaman rad'a tace "Serious H,Zakee ka auree yarinyar nan kawae wllh don bata dace da kowa ba sai kai kaga kaci ribar rainonta da kai duk da nasan don Allah kai amman fa gida bai k'oshi ba ba akai ma dawa ba" ba shiri Haisam yay dariyar da har fararen hak'oransa suka bayyana Calmly ya furta "Zee Who told u gida bai k'oshi ba?" Kanne ido guda tay tace "a ina gidan ya k'oshi ai sai Mutum yayi hud'u sannan kuma yarinyar nan da kake gani mai zafi ce don haka da irin ka mai zafi ta dace willh" tana k'arasa Maganar ta mik'e ta juya tana dariya tana fad'in kar ya fad'i ma Matar shi fa ya girgiza kai kawae shima yana yar dariyar, duk yadda Fatuu taso kar ta d'auki kaya da yawa saida Zee tasa ta d'auki kala biyar da k'yar gashi duk masu tsada, laces kala biyu sai Atamfa ma biyu sai wani had'addan cotton material harda doguwar riga jallabiya saida ta lik'a mata sannan aka d'auki mahad'in kayan su gyale da takalma harda jaka dasu sarkoki don ma Fatun ta kafe kan ba kowanne zata d'aukar ma mahad'in ba wanda zai hau da kaman kala biyu take d'auka, koda tay mata Maganar English wears da Undies Fatun cewa tay duk tana da su, bayan sun fito Zee ta zauna ta kalli Haisam tana yar dariya tace "da alama har yanzu Zarah tana tausayin ka bata son kana kashe kud'i don yanzu ma da k'yar aka za6i kayan kaman dai other time" d'aga ido yay ya kalli Fatun ta d'an tura baki ta juyar da kanta gefe, card ya ciro ya ba Zee d'in ta fitar da kud'in yau ma saida yace ta k'ara 30k ta siya sugar Azumi tay ta godiya Fatuu kam shiru tay a ranta tana mamakin yadda yake kashe kud'i kamar baisan zafin su ba kai kace kawae umarni yake badawa ake buga mashi, har Mota Zee ta rako su da kayan aka saka booth tay wishing Haisam Safe flight tace ma Fatuu tana jiranta tazo mata yawon salla ta amsa da to suka shige Motar ita kuma ta juya ta koma, bayan sun bar plaza d'in ganin hanyar da yabi yasa ta tambaye shi shagon Kb zasu ne ya d'aga mata kai alamar eh tace mashi a bari ba yanzu ba ya tambayi dalili tace tana so sai ta samu styles sai ta kai mashi baki d'aya ya furta Ok suka canza hanya, Fatuu tay mamakin ganin sun tsaya gaban Shagon Maman Abdul mai saloon ganin tana kallon shi yace mata taje a wanke mata kai gudun kar tay mashi gardama ta 6ata mashi rai yasa ta juya ta fita, tun kafin ta shiga ciki Maman Abdul d'in ta fito ta tarbeta da alama hangota tay suka shiga ciki ta nuna mata kujera bayan Fatun ta zauna ta hau gaidata ta amsa sannan cikin washe baki anga customer ta tambayeta abunda za'a mata tace Wash and Set ta amsa da okey har zata juya sai kuma ta tsaya tana kallon fuskar Fatun da d'an alamun nazari can tace "Ma, ur face look familiar as if u ave came here before" d'an murmushi Fatuu tay ganin yadda dimples d'inta suka lotsa yasa maman Abdul d'in tabbatar da tasan face d'in ta koda ba anan ba ganin ta dage sai ta tuna inda tasan ta yasa Fatun yi mata bayani aikuwa da tsananin mamaki ta ruk'e haba tana fad'in itace wai ta girma haka miyasa ta dad'e bata zo ba Fatuu dai dariya kawae take can ta tambaye ta ina yayanta d'in nan da ya ta6a kawota tace mata yana nan waje shine ya kawota yanzu ma, da sauri tace "let me greet him I will come back now" tayi Maganar had'i da juyawa ti6i ti6i ta nufi hanyar fita Fatuu ko mi zatayi ba dariya ba ganin yadda duk ta rud'e su maman Abdul anji kud'i sun zo, tana isa driver side d'in ta d'an kwankwasa glass d'in slowly ya fara sauka tana ganin shi ta washe baki ta sunkuya tana fad'in "Good after....oh good Evening sir" duk ta rud'e sai washe baki take, d'an murmushi yay mata ya amsa yay mata ya kasuwa ta amsa da Alhamdulillah nan ta shiga fad'in taga Fatuu tay girma sosae shidae murmushi kawae yake tace amman ya akai suka d'auki tsawon lokaci basu k'ara zuwa bane ko aikin nata bai masu ba fuska a sake Yay mata bayanin tana gyarawa a gida ne Maman Abdul ta marairaice fuska tace ya kamata dae don Allah a rik'a kawota don za'a fi gyara mata anan yace Ok in sha Allahu tace bari tay sauri ta gyara mata kar ai keeping nashi yana jira ya jinjina mata kai ta juya da d'an sauri sauri gudu gudu ta koma, yana zaman jiran nata akai sallar la'asar ya fita yaje Masallaci dake gefen benen yay salla bayan ya dawo bada jimawa sosae ba aka gama ma Fatun Maman Abdul ta rakota har bakin Mota tana fad'in tana jiranta sai ta k'ara ganinta ta amsa da Ok ta kopar da Fatun ta bud'e ta d'an duk'a tace ma Haisam ashe yayi aure bai K'asar ma saida suna fira ne ta fad'i mata ya d'aga mata kai tayi mashi Allah yasa Alkhairi ya amsa da Amin ta koma kan Fatuu tace mata pls ko bai nan ta rink'a zuwa tace to, kud'i masu yawa ya fiddo yaba Fatuu ta mik'a mata zo kaga godiya tana yi tana sunkuyawa saida yaja Motar ta koma shagon, yana ta driving ita kuma tana ta kallon hanya can taji kamar yayi magana ta juya ta kalle shi tace Magana yake ne kaman bazai tanka mata ba idon shi akan hanya sai kuma taji yace "cewa nay ba za'a nuna man ba yau" dariya tay tasa hannu ta rufe baki tasan wasa yake mata don ya tuna mata da wanccan lokacin ne shima fuskar shi d'auke da d'an murmushi yake driving d'in, suna akan hanya ya kira Abbas ya tambaye shi yana gida yace eh yanzu da la'asar d'in nan ya dawo yace Ok gashi nan zuwa, lokacin da suka isa yay horn Abbas ne yazo ya bud'e mashi ya shigar da Motar bayan ya parker ta ya bud'e ya fita Abbas dake gefe yana mashi dariya ya bashi hannu sukai shaking yana niyyar yin magana Fatuu ta bud'e kopar ta fito da mamaki Abbas yace "Mom Zarah tare kuke kenan" d'aga mashi kai tay kafin ta gaishe da shi ya amsa yana murmushi yay mata ya School ta amsa da Alhamdulillah ya sake cewa "sai kika ga mutumin naki yazo ba ko notice?" Ita dai murmushi kawae take kafin ta tambaye shi Aunty Feenah yace ta na ciki tace to ta nufi cikin idon shi akanta yanata wani irin murmushi can ya juya suka had'a ido da Haisam dake jingine jikin Mota Abbas d'in ya furta "Perfect Match" wani kallo mai kaman harara yay mashi Abbas yasa dariya yace "Wllh kun matuk'ar dacewa am telling u d truth" dan ta6e baki Haisam d'in yay yace zai bar shi a tsaye ne da sauri yace tuba nike Angon Mom Zarah mu shiga ciki Haisam d'in ya d'an girgiza kai kawae suka wuce, lokacin da ta shiga ba kowa a Parlon hakan yasa ta wuce Bedroom d'in Feenah anan ta iske ta, tay matuk'ar jin dad'in ganinta tace halan ita da H,Zakee ne Fatun na murmushi tace mata eh ta mik'e tace suje su gaisa, anan Parlor suka suna hira bayan Feenah ta kawo masu abun ta6awa daga baya Haisam da Abbas suka ce zasu je su dawo suka ci gaba da hirarsu su biyu har Abdul ya dawo daga islamiyya, sai bayan Magrib suka dawo Haisam d'in bai shiga ba sai Abbas ne ya shiga ya kirata su Feenah suka rako ta da gudu Abdul ya nufi Haisam ya kankame shi yana dariya can ya d'ago ya kalli Haisam dake murmushi shima yace "Baba Zakee don Allah ka auri Aunty Fatuu" d'an d'age gira Haisam yay Feenah da Abbas suka sa dariya ita kuwa Fatuu sunkuyar da kai tay gabanta ya fara fad'uwa bata ta6a zaton zai mashi wannan Maganar ba, ganin yak'i cewa komae yasa Abdul jujjuya kai yace mashi "kaji Baba zakee kuyi aure kai da Aunty Fatuu don Allah" sigh Haisam yay slowly yace mashi Saboda mi yake son hakan yace "kaga kai babana ne ita kuma sai ta koma mamana" Haisam na murmushi cikin cool voice d'in shi yace "but kai kace ai tayi k'arama ta zama mom en ka" waro ido yay baki bud'e yana son tuna sadda yace hakan can yace "gaskiya baba zakee ni ban ce hakan ba fa" Abbas dake dariya yace ya dae manta ne a shagwa6e yace "to in ma nace haka ai yanzu ta zama babba zata iya zama mamana kaji kuyi Auren" gaba d'aya aka sa dariya Haisam yace "ai sister na ce ita..." Da sauri Abdul d'in ya katse shi yace "Amman dai ai ba gidan ku d'aya ba ko kai a Abuja gidan ku yake ita kuma anan kuma a islamiyya ance sai sister d'in da ake gida d'aya ne ba'a iya aure" nan ya shiga lissafo mashi wad'anda aka ce masu ba'a iya aure Abbas sai dariyar k'eta yake shi ma Haisam murmushi ne akan fuskar shi yasan yaron da shegen wayau duk yadda zai zame sai ya gane hakan yasa ya d'aga mashi kai yace to kawae nan fa ya hau tsallan murna ya tambaye shi to yaushe za'a yi bikin Haisam yace in an shirya zai ji a wurin Dad d'in shi cike da farinciki ya nufi Fatuu da ji take tamkar ta nutse don kunya ya kama hannunta yana dariya yace taji Baba Zakee zai aureta ko ta kasa ce mashi komae saida Abbas yace ya k'yaleta ai taji sannan ya bar Maganar Haisam yay masu sallama Abbas yace sai yazo kai shi Airport gobe Feenah ma tay mashi Allah ya kiyaye ya gaida Fanan yace Ok duk suka yi ma Fatuu sallama da k'yar ta iya d'agowa ta kalle su da yake wurin fayau yake da hasken fitilu ta amsa masu kafin jikinta sukuku ta zagaya ta shiga Motar lokacin Haisam ya shige ya fara kokarin fidda ta dama gate d'in a bud'e yake da suka shigo, bayan sun baro gidan Abbas EE ya nufa da suka isa yace mata yana zuwa ya fita tana ta kallon shi ta glass da yake wurin akwae haske sosae har ya shige after some minutes sai gashi ya fito hannunshi ruk'e da yar jakar kwali mai d'auke da hotunan abubuwan da ake saidawa a wurin ya bud'e Motar ya shiga ya aje jakar a gefe bayan ya rufe kopar yaja suka tafi, akai akai yake d'an kallonta ta juyar da kai dama tunda suka baro gidan Abbas a haka take, lokacin da suka k'araso kopar gidansu ya parker da k'yar ta kalleshi tay mashi godiya ya bita da ido kawae duk sai ta tsargu tana niyyar juyawa ta bud'e taji yace ga abu nan nata ne ta juyo saida ta kalle shi kafin ta kai hannu ta d'auka tay mashi godiya sam bata san miye a ciki ba zata fita yace mata tay ma Amadu magana yazo ya d'aukar mata kayan baya tace mashi a'a zata iya ya d'aga kai ta juya ta fita ta rufe kopar, bayan ta fiddo kayan ta wuce har saida yaga ta shiga gidan sannan yaja ya tafi, tana shiga d'akin gwaggo ta wuce tana zaune kan abun salla bata jima da gama sallar isha ba, da sallama Fatun ta shiga ta amsa mata a gefenta ta aje ledar kayan da kuma jakar gwaggon ta kalli kayan sai kuma ta kalleta a sanyaye tace mata Ya Haisam ne ya siya mata, bud'e baki gwaggo tay da tsananin mamaki tace "kuma dae wai shi baya gajiya da hidima ne don Allah" ta k'arasa idonta kan Fatuu ta d'an ta6e mata baki ta nufi kujera ta zauna, hannu gwaggo ta kai ta fara duba kayan tana yi tana girgiza kai har ta gama sannan ta bud'e ledar kwalin ta fiddo kwalin dake ciki wanda ke nuni da na waya ne gwaggo ta bishi da ido daga inda Fatuu take zaune ta saki baki tana karanta sunan wayar har saida cikinta ya d'an yamutsa ganin iPhone 15 wayar da take taji anata zancen ta fito a social media ba wannan ne abun mamakin ba irin kud'inta da taji ana fad'a nan ta fara shakkun anya kuwa haka kud'in nata suke, suna haka sai ga Amadu ya shigo da sallama yana dariya yace "nazo a bani rabo na don naga Amar....au Hajiya Fatuu ta shigo mana da k'atuwar leda" kallon shi Fatuu tay yace "tuba nike ai dae ban k'arasa cewa Amaryar ba" d'an ta6e baki kawae tay yana niyyar duk'awa gaban kayan idanun shi suka sauka akan kwalin wayar dake hannun gwaggo wani kalar waro ido yay with mouth agape a razane yace "Wannan fa ta gasken ce ko kuwa kwalin ne kawae" ya kai hannu gwaggo ta mik'a mashi a kidi'me yace "kai wllh itace da gaske ta waye??" da kai gwaggo ta nuna mashi Fatuu ba shiri yasa hannu ya rufe baki yana fad'in "kai kai kai..." ganin yadda duk ya rud'e yasa gwaggo cewa "halan mai kud'i ce, in ce tafi waccan da ya siya mata ko?" Wani d'an murmushin Al'ajabi yay yace "mai kud'ad'e ce zaki ce gwaggo ba kud'i ba, iPhone 15 pro ce fa wayar data fito kwanan nan aketa Magana kusan miliyan d'aya take wannan in ma bata fi ba" duka hannuwanta gwaggo tasa ta rufe baki ido waje kafin a tsananin razane tace "Kai Amadu!! yanzu wannan abun ke har miliyan d'aya! ka kuwa san nawa ne miliyan!!!" Rantse mata yay haka kud'in ta suke har yana cewa in bata yarda ba bari yay mata Googling d'inta yanzu ta gani girgiza kai gwaggo ta fara yi tana fad'in gaskiya bazai yuwu ba dole tay mashi Magana wannan ai almubazzaran ci ne Amadu dake kallonta da alamun mamaki yace "kaji gwaggo da wata Magana ina ruwanki, nasan dae ba rok'onshi tay ba yaji zai iya ne miye naki na shiga Maganar, kuma da kike Maganar Almubazzaran ci ne kin dae san shi ba mai hakan bane in aikin Alkhairi ne yana yi, ba don ma bai yin yawa ba da sai ace nashi Alkhairin har yayi yawa, kawae wadata ce in Allah yasa mutum nada ita sai yay abunda ya ga dama" zugudum gwaggo tay tana bin shi da ido kawae Amadun ya juya kan Fatuu yana fad'in lalle ita mai k'ashin Arzik'i ce bin shi da ido kawae Fatuu tay jikinta duk ya mutu ita tsoron ma wayar take ganin yanayin ta yasa Amadu cewa ya yaga kaman bata farinciki kaman zatayi kuka tace mashi ita dae wllh tsoron wayar take gashi yanzu anata sare mutane wasu ma kashe su ake kan waya Amadun yace in sha Allahu ba abunda zai sameta tunda tana Addu'a da kuma Azkhar amman dae ta rink'a kiyayewa kar tay ta nuna ma Mutane a yanzu ta d'an rink'a amfani da tsohuwar tata kafin tay yawa ta d'aga mashi kai kawae yace zai koya mata yadda zata yi amfani da ita don yasan 13 sosae kuma ance bambancin su kad'an ne da wannan, sai zuba yake yana taya Fatuu murna gwaggo dae ta zuba mashi ido kawae da alama takaici ya hana ta Magana, daga baya Amadu ya tashi ya fita sukae zugudum kowa ya kasa cewa komae can gwaggo ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace ta kwashe kayan ta kai d'akinta, bayan ta koma d'akin zaune tay a gefen gado ta zuba ma kwalin wayar ido kamar mai tsoron ta6a shi can dai ta kai hannu ta d'auka ta bud'e ta zuba ma wayar ido kirjinta na ta fad'uwa ta d'an d'auki lokaci a hakan kafin da k'yar ta mik'e don yin salla, bayan ta gama ta d'an ci Abinci sannan taje tayo wanka ta zo ta shirya cikin kayan bacci ta haye gado ta shiga duniyar tunani, ita dae tasan Haisam na mata abubuwan Alkhairi sosae amman wannan ya matuk'ar d'aure mata kai taya za'ai ace hakanan ya siya mata irin wannan wayar gaba d'aya ta rasa tunanin ma da zatayi da k'yar bacci ya kwashe ta........... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2041* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ........Sai dae ko kafin ya kai har ta kulle kopar, knocking ya fara yi yana kiran sunanta shiru har bayan wani lokaci tak'i ta bud'e hakan yasa ya koma cikin parlon ya zauna had'i da had'e hannuwan shi ya d'aura beard d'in shi, shi dama initially hakanan zuwa binciken lafiyar bai kwanta mashi ba kawai don ta matsa ne yasanta sarai da k'wallafa rai akan abu in bai goya mata baya ba haka za tay ta damuwa yanzu kuma ga wata damuwar data fi wancan, tunanin yadda akai tana da wannan problem d'in amman ko ita bata gane ba a matsayin ta na likita ya shiga yi daga baya kuma ya tuna in Allah yaso ya 6oye Al'amari dama ba lalle a gane ba yana ta zaune can ya mik'e ya koma kan 3 seater ya d'auki wayar shi ya fara kokarin kiran Hajiya tana fara ringing ta d'auka suka gaisa ta tambayi ya Fanan jin ya d'an yi shiru dama ta ji yanayin voice d'in shi kaman yana cikin damuwa, tambayar shi tayi lafiya taji kaman yana cikin damuwa saida ya d'an nisa sannan cikin natsuwa ya fara mata bayanin komae to itama dae Hajiyar ta girgiza da jin bayanin matsalar tabbas itama haka tay ta fama da lalurar yawan 6ari wani lokacin sai cikin yayi kaman zai tsaya sai kuma ya zube ko kuma bayan ta haife ya koma saidae kuma tayi mamakin jin Fanan nada irin matsalar ba tare da an ta6a fuskantar wata babbar alama ba, cikin tashin hankali ta tambaye shi tana ina yace mata tayi locking kanta acikin d'akin tace bari ta kira wayar ta ya sanar da ita wayan na nan parlor, cike da damuwa tace dole ta shiga mawuyacin hali ba kamar yadda take da son ta haihu, ce mashi tay ya samu ya lalla6a ta ta bud'e kar wani abun ya sameta ba kamar da yake rarraunar zuciya gareta ya rarrasheta sosae itama zata kira suyi Magana ya amsa mata da Ok, mik'ewa yay walking slowly ya sake komawa bakin kopar yana knocking had'i da kiran sunanta shiru bata bud'e ba hakan yasa shi fara tunanin kar wani abu ya sameta nan take ya yanke zuwa yasa azo a 6alle kopan yana shirin juyawa yaji tana bud'e wa da sauri ya dakata ya kai idon shi jikin kopar yasa hannu ya tura, a tsaye ya ganta har saida gabanshi ya fad'i ganin yadda cikin kankanin lokaci duk ta yamutse ga hancinta duk alamun jini da alama nose bleeding tay dama yasan tana hakan tun tana k'arama in ranta ya 6aci ko ta buge sai tayi ha6o, hannunta ya kama suka koma cikin d'akin ya zaunar da ita gefen gado shima ya zauna idon shi a Kanta sai faman ajiyar zuciya take saukewa still yana ruk'e da hannunta guda slowly ya furta "Fanan" kaman bazata amsa ba sai kuma a hankali tace "Na'am" cigaba yay "Why all dis? Do you want to harm your self?" Shiru tay bata ce komae ba ya cigaba "I know how u'r feeling but kiyi hakuri muyi Addu'a Allah ya yaye matsalan yakamata ba damuwa ba tunda is curable kowane lokaci zaki iya samun lafiya" a hankali ta d'ago da rinannun idanunta ta kalle shi cikin disasshiyar murya tace "Babe ina tsoron ace bazan haihu ba bansan ya zaman mu zai kasance ba" ta k'arasa kwalla na zubo mata ya kai hannu ya jawo ta jikin shi yay mata side hug ya d'aura ha6ar shi a saman gashin ta gently yace "In sha Allah zaki haihu and nothing will change tsakanin mu ko kin haihu ko baki haihu ba ina son wife ena itama tana sona hakan ya wadatar dani" lumshe ido tay koba komae taji dad'in Maganar shi kuma tasan har cikin ranshi gaskiya ya fad'a mata shiru tay tana cigaba da shak'ar daddadan k'amshin da jikinshi ke fitarwa tana jin wata irin natsuwa na shigar ta, Allah ne shaida tana matuk'ar son Haisam tana jin tamkar da son shi aka halicce ta tabbas tasan rasashi babbar barazana ce ga rayuwarta tana wannan tunanin wata zuciyar ta ayyana mata wani abu da yasa gabanta fad'uwa ba shiri ta d'ago da kanta ta kalle shi shima ita yake kallo ganin kaman tana son yin Magana yasa ya tambayeta akwae wani abu ta d'aga mashi kai alamar eh yace ta fad'a mashi miye d'an jimm tay kafin tace "pls Ya Haisam I want a Favour from you" jinjina mata kai yay alamar to k'ara yin shiru tay tama rasa ta ina zata fara ya lura da ta kasa fad'i mashi Alfarmar da take son yay matan ya kai hannuwan shi ya kama duka hannuwanta yace kar ta ji komai ta fad'a mashi zai yi iyakar kokarin shi yay mata abunda take so in dai zai sakata farin ciki kuma ta daina damuwa haka, jin wannan batun nashi yasa ta samu k'warin gwuiwa ta fara magana cikin d'an rawar murya tace "I.... i want u to promise me dat you'll not marry another wife" bin ta kawai yay da ido bai ta6a zaton abunda zata fad'i ba kenan don bai ga dalilin da zata fad'i hakan ba, kaman ta san tunanin da yake ta had'iya abu kafin tace "ina nufin koda ban haihu ba don Allah ya Haisam kai man Alk'awarin bazaka k'ara aure ba tunda akwae hanyoyin da zamu iya samun yara zamu iya adopting ma in muna so" still kallon ta kawai yake hakanan ya kasa ce mata komai ganin kallon da yake Matan yasa taci gaba "isn't dat am trying to be selfish kawai ban son rasa ka ne babe in ya kasance ban haihu ba ka auro wata ta zo ta haihu zata rink'a man gori tana kirana juya k'arshe ma ta raba ni da kai hakan ya sha faruwa wllh and I can't survive without u" ta k'arasa kwalla na shararo mata taci gaba da tabbatar mashi da hakan zai faru in dae ya k'ara aure rayuwarta na cikin had'ari ya taimaketa su ci gaba da zaman su tare, gaba d'aya ya rasa mi zai ce mata bawai bazai iya yi mata alk'awarin bane amman yasan ta dama can tana da kishi ko ba don wannan matsalar ba tana yawan rok'on shi kan kada yay mata kishiya don bazata iya sharing nashi da wata ba da dai sauran maganganu, ganin yak'i yace komae yasa ta k'ara sautin kukan ta tana fad'in ya taimaketa yay mata alk'awari hakan ne kawae zai sa ta samu natsuwa a cikin zuciyarta da yanzu take mata rad'ad'i sauke ajiyar zuciya yay ya d'an yi jimm kafin calmly yace mata shikenan yayi mata alk'awarin hakan tun kan ya rufe baki ta fad'a jikin shi ta wani k'ank'ame shi tanata mashi godiya had'i da d'agowa tana yi mashi kiss a dukkan side d'in fuskar shi d'an murmushi kawai yay can yace ta tashi tay wanka zata fi jin dad'in jikinta tace to suyi tare mana yace mata zai d'an yi wani abu yanzu taje tayi yana zuwa ya fara kokarin mik'ewa yana ruk'e da hannunta ya d'agata saida ya kaita har cikin toilet d'in sannan ya fito, Bedroom d'in shi ya nufa yana shiga bayan ya rufe kopar ya nufi bakin gadon shi ya zauna, had'e dukkan hannuwan shi yay ya d'aura ha6arshi hakanan yake jin kaman bai yi daidai ba da yace yayi mata alk'awarin to amman yasan in har ba yayi mata yadda take son ba bazata ta6a natsuwa tabar damuwa ba ya d'an d'auki lokaci a haka yanata sak'e sak'e kafin can ya mik'e da k'yar don duk jin jikin shi yake ba dad'i ya nufi toilet, sosae taji dad'in jikinta da ta fito daga wankan duk da da sauran damuwa da kuma fargaba a cikin ranta na ko zata warke ta haihu ko bazata warke ba press ta nufa ta ciro wata yar riga iya gwuiwa tasa ta nufi gaban dressing mirror iya turare da roll on kawae ta sa ko mai bata shafa ba ta nufi Parlor don ta d'aukko wayarta, bayan ta dawo a bakin gadon ta zauna ta kira Momynta gaisawa suka fara yi tace ya taji muryarta ta canza bata lafiya ne aikuwa kaman tana jira ta saka mata kuka nan fa Hajiya Maryam ta rud'e ta hau tambayarta abunda ya faru cikin kuka ta shiga fad'i mata komae sosae itama ta girgiza ta hau yin salati harda ce mata ta tabbatar an yi aune aunen daidai kuwa tace mata eh kwararran likita ne suka gani sosae ta shiga damuwa amman Saboda kada ta k'ara tada ma Fanan d'in hankali sai ta hau rarrashinta tana nuna mata kada ta damu in sha Allahu zata samu lafiya tunda ana warkewa tambayar ta tay mi Haisam d'in yace da yaji zancen matsalar tace hakuri yake ta bata yana rarrashinta sam bai damu ba yama yi mata Alk'awarin koda bata haihu ba bazai k'ara aure ba zasu cigaba da zama a haka sosae Hajiya Maryam taji dad'i tace mata in sha Allahu ma zata haihu bama d'a guda ba yanzun dae ta tabbatar ta kwantar da hankalinta tunda Haisam d'in ma bai damu ba dama shine abun ji daga baya ta tambaye ta ta fad'a ma Daddy d'in su ne tace a'a Hajiya maryam d'in tace to ta bari yanzu zata kira ta sanar mashi tasan zai kirata tace to ta tambayeta su Farha da sauran yan'uwanta daga baya sukae sallama tana niyyar aje wayar kan gadon sai ga kiran Hajiya ya shigo bayan tay picking suka gaisa ta hau jajanta lamarin kafin ta shiga kwantar mata da hankali sosae tana mata nasiha daga baya sukai sallama ta aje wayar ta kwanta tana facing ceiling ba tunanin kowa take ba face Haisam ita tasan ta gama yin dacen miji ba k'aramar baiwa Allah yay mata da samun shi ba slowly ta lumshe ido wani irin son shi na ratsa zuciyarta tana haka wayarta ta sake yin ringing ta kai hannu ta d'aukko sunan Dad d'in ta ne ya bayyana kan screen d'in da sauri ta yunk'ura ta tashi zaune, bayan tay picking ta gaishe dashi shima dai rarrashin ta ya shiga yi yana kwantar mata da hankali yace kada ta damu za'ai iya bakin k'ok'ari ay treating problem din yana nan zuwa ma sosae taji dad'i harda su murmushi bayan sun gama wayar ne ta tuna da basu ci lunch ba gashi har yamma tayi sosae da sauri ta mik'e ta fita daga d'akin ta nufi Bedroom d'in Haisam tana shiga ta iske shi saman gado a kwance jikin shi sanye da jallabiya don yana fitowa ita kawae ya zura ya kwanta da alama dae wani abun na damun shi ko kuwa alk'awarin da ya daukan ne Allah masani, tana isa bakin gadon ta zauna ta kwantar da kanta a saman chest d'in shi can ta d'ago suka had'a ido ganin yanayin shi yasa da sauri ta tambaye shi mike damun shi ne slowly yace mata ba komae ya gaji ne tace tasan harda yunwa yay hak'uri bata bashi Abinci ba har yamma yayi sosai ya taso suje table ta mik'e tana kokarin d'aga shi ta hanyar kama hannun shi, baida yadda zai yi dole ya tashin ya zuro da k'afafun shi amman yafi buk'atar kwanciyar ya ji shi shiru, a daren ranar sosae Fanan ta faranta mashi duk da damuwar da take ciki da alama tukuicin Alk'awari ne aka bashi, Allah dai yasa a wanye lpy. A daidai kopar gidansu Keke Napep d'in ta tsaya Fatuu ta fito jikinta sanye da fararen Uniform d'inta ta biya shi kud'in shi ya ja ya tafi tana juyawa zata nufi gida taje da d'an k'arfi ance mata "wait!" da sauri ta juyo idanunta suka sauka akan wanda yay Maganar Matashi ne kaman tsaran Kawu Amadu ko ya d'an girme mashi yana sanye da manyan kayan shadda blue harda hula tsaye tay tana kallon shi ya nufo ta a gabanta ya tsaya yana mata murmushi ita kuma ta k'ura mashi ido gani take tasan mai fuskar amman tana kokonton in shine d'in don ya canza mata sosae ganin irin kallon da take mashi ne yasa shi cewa "halan baki gane ni ba, ko sai nace Aljana sannan" waro ido Fatuu tay baki bud'e da tsananin mamaki tace "GAYE!" d'an d'aure fuska yay yana mata wani kallo yace "Point of correction, ba wannan sunan yanzu Ashiru zaki ce ko kice Malam Ashiru" k'ara bud'a baki Fatuu tay tasa hannu ta rufe baki mamaki ya gama kasheta abunda bata ta6a zaton gani ba ne take gani a gabanta shi kuwa sai faman murmushi yake don ya fahimci Al'ajabi ya hanata magana can yace tunda bazata tay mashi Magana ba bari ya tafi da sauri tace "to ai ni Gaye wllh mamaki yama hana ni yin magana wai don Allah da gaske kaine?" Yar harara ya wurga mata yace "ba nace maki ba wannan sunan ba yanzu ko so kike ki zubda ma Malam Mutunci ne" Fatuu kau mi zatay in ba Dariya harda tafa hannu ta ruk'e ha6a bin ta da kallo yay daga sama har k'asa yace "Oh su Aljana an girma nayi k'ok'ari ma dana gane ki koda yake d'azun da safe naga Amadu na tambaye shike ke yace man kina makaranta shiyasa yanzu ina ganin ki na gane kece a ina kike karatu ne?" ta fad'i mashi still da mamaki akan fuskar tata don gaba d'aya ya canza Maganar ma cikin natsuwa yake yin ta irin ta masu hankali, tambayar shi tay wai ina ya tafi ne ta daina ganinshi yace mata yana Jos, "Kaci gaba da karatu ne?" ta tambaya yace "Eh mana, ke da ban cigaba ba Kya ganni haka na gama Nce" bud'a ido Fatuu tay tace "inyee yayi kyau gay....au Malam Ashiru, mi ka karanta ne?" "Islamic studies kinsan d'an Malam ne ni nayi gado" Fatuu na murmushi tace da kyau ta taya shi murna Allah yasa Alkhairi ya amsa mata da Amin tace "ina Abokan ka su goga" wani kallo yay mata irin baiso tambayarba tay yar dariya tace don Allah suna ina yace duk sun yi laifi suna gidan yari Fatuu ta zaro ido tace "kace saida dai suka je gidan yarin saura kai kenan" cike da zolaya tay Maganar aikuwa ya galla mata harara yace "amman gaskiya ke mak'iyata ce yanzu Malam d'in kike ma fatan zuwa gidan yari Saboda rashin Mutunci" sosae Fatuu ke dariya tana fad'in ashe har yanzu bai daina tsoron zuwa gidan yari ba yakamata ya d'an je ko don yaci gabza shima dariyar yake yace wannan ai tata ce ita yakamata ta ci ta koda sau d'aya ne, "Sai Mutumin ki yay aure" tambayar shi tay wa yace "Yaya Haisam na gidan Hajiya mana ai nayi zaton ke zai aura" yanayin murmushin fuskarta ne ya d'an canza tace waya fad'a mashi son ta yake da zai aureta yace "kawae yanayin yadda naga yana kula ki ya damu dake acan baya yasa nay tunanin ko yana ciki ne" d'an ta6e baki tay bata ce komai ba yace "da kin aure shi da kin more miji wllh ni tunda nike a rayuwa ta ko a labari ban taba jin mutum mai kirki irin nashi ba don kirkin nashi har ya yi yawa kinsan fa shine ya d'auki nauyin karatun da nayi bayan daya sa aka yafe mana laifin nan....." Nan ya kwashe komai tun daga ranar da suka je da mahaifin shi yin godiya ya fad'a mata yace yanzu ma da ya dawo nan aikin teaching za'a samar mashi har ma yasa ya kai ma Hajiyar Sanata takardun shi gyad'a kai Fatuu tay tace mashi ai yasan mijin wata bai auren matar wani kowa da wanda Allah ya kaddaro zai aura yace tabbas hakane tace shi yaushe zai auren ne yana dariya yace "ai bani da budurwa saidae ko in ke zaki taimaka ki aure ni" wata muguwar harara ta watsa mashi kafin tay dariya tace ai ni nafi k'arfin ka gaye ko da can ma saidai ka zama driver na sosae yake dariya yana fad'in yanzun Malam d'in ne zai zama drivern ta, ganin kaman ta gaji yace ta shiga gida ya tsayar da ita kuma yasan ta kwaso gajiya da yunwa ta tambaye shi sai yaushe yace ai ya dawo kenan don haka zai zo su sha hira tace to sai yazo yace ta gaida mashi gwaggo daga haka suka rabu,tana shiga gidan bayan ta shiga toilet ta fito ta nufi d'akin gwaggo tana zaune bata dad'e da gama cin Abinci ba don ko plate d'in bata kaiga d'aukewa ba, zama Fatuu tay akan kujera ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata an dawo tace eh nan ta hau bata labarin Gaye cike da mamaki gwaggon tace ai ba abu mamaki ba ne Allah yana shiryar da bawan shi a lokacin da yaso duk mun munin abunda yake aikatawa da Allah yasa yana da rabon shiryuwa sai kaga ya bari shiyasa ba'a so aita hantarar mutum ana aibata shi in yana aikata ba daidai ba an fi so aja shi a jiki da fad'a da nasiha in da rabo sai kaga ya bari ya dawo kan daidai daga k'arshe ta hau yabon Haisam da Hajiya had'i da yi masu Addu'oi Fatun na amsawa tace taje ta zubo Abinci ta amsa da to saida ta d'auki plate d'in da gwaggo tay amfani ta fita. Haisam ya fasa zuwa sakamakon d'aga bikin da zai zo da akai aka maida shi sai cikin farkon sabuwar shekara wato bayan Christmas da new year kamar yadda ya sanar da Fatuu da suna waya tace mashi Allah ya kaimu lokacin, a cikin lokacin su Fatuu sukai jarabawar kammala aji d'aya suka shiga aji biyu. Hajiya zaune a Parlor ta tasa Saude dake zaune akan Carpet gaba tun bayan data sanar mata cewa Officer ya mata Maganar yana son aurenta ta sunnar da kai ba tare da ta ce komae ba, "Saude kin k'i cewa komae ko bakya son shi ne?" a hankali ta d'ago da alamun damuwa akan fuskar ta tace "Hajiya ba wai ban son shi bane ni gaskiya nafi son in ci gaba da aiki na" d'an murmushi Hajiya tay tace "amman Saudatu ai yin auren yafi ko kyata zama ne gashi da sauran yarintar ki ba wani tsufa kikai ba ki dai duba kema in kika yi ai Kya fi samun natsuwa" d'an mommotsa baki ta shiga yi tana kikkafta idanu Hajiya tace indai bata son shi ne karta ji komai ta fad'a mata ita tasan yadda zatai in kuma har tana son shi to tafi son ta amince mashi suyi Auren kawae sai gani Hajiya tay ta fashe mata da kuka da mamaki take kallonta tace to miye na kuka kuma ba tace in bata son shi ba ta fad'i sai ta kama kuka kaman wata k'aramar yarinya girgiza kai ta fara yi cikin kukan take fad'in "Hajiya ba wai auren shi ke banson yi ba nasan aure rufin asirin mace ne ni kawae har ga Allah ban son rabuwa da ke ne shiyasa tun farko da yay man Maganar tun ba yanzu ba na nuna mashi yay hakuri kawae tunda nasan k'arshen ta garinsu zai kai ni ya had'a ni da d'ayar matar shi" yar dariyar jin dad'i Hajiya tay tace "nima ba don dole ba Saude ai bazan so rabuwa dake ba to amman hakan bazai sa in so kaina ba in hana ki yin abunda yakamata ba kuma shi Officern ma yace ke a nan zai sama maki gida ya ajiye ki wannan sai ya daina damun ki" cikin muryar kuka tace "to aikin fa zan ci gaba ko?" dariyar dai Hajiya ke yi ta lura dae da gaske bata son barin gidan can taji tace "to ko ku zauna anan?" Ba shiri da sauri Saude ta kalleta don bata tsammaci jin hakan ba Hajiya taci gaba "in dai kuna so tunda ga d'akuna nan biyu a kusa da na Tukur sai kuyi amfani da su kawae" Saude tace "to Hajiya ba matsala kuwa?" tana dariya tace "Wace matsala kuma ba wata matsala in dae wurin yayi maku ai sai kuyi zaman ku kici gaba da zama da Hajiya kafin mai rabawa kuma ta raba" shiru Sauden tay don Maganar Hajiyar ta k'arshe ta kashe mata jiki kuma dai abune da ya zama dole ko ba dad'e ko ba jima saidae fatan dacewar Ubangiji, ganin tayi shiru yasa Hajiyar cewa shikenan ko tace mashi ya tura Daura Sauden ta jinjina mata kai had'i da sadda shi k'asa alamar kunya Hajiya nata dariya tana fad'in to miye abun jin kunya..... Ba yawa but manage it pls😔 _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2042* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah har anyi New year su Fatuu sun dawo daga Hutu sun cigaba da karatu, Ranar Monday misalin k'arfe biyu saura suka dawo daga Area d'in class an tashi zasu tafi Hostel da yake yanzu Fatuu tana d'an yawan zama a Makarantar sai Weekend ta koma gida wani lokacin ma a Makarantar suke weekend d'in kaman Asabar sai lahadi ta je gida, tafe suke kowanne yana rataye da jakar shi Fauzy sai faman rangaji take ta d'aura kan ta saman shoulder d'in Fatuu can tace mata "Wai Fauzy so kike ki sauke man kafad'a ne, duk kin bi kin sakar man nauyi" a marairaice Fauzy tace "wllh Zarah wata irin yunwa nike ji baki ji ba gashi bak'in cikina in mun koma Hostel d'in ma dole sai mun dafa" yar dariya Fatuu tay tace "to ba sai ki nemi emergency food ki fara ci ba" yamutsa fuska Fauzy tay tace "irin yunwar da nike ji wannan bazasu rike ni ba kin san fa bamu yi break ba Saboda discussion d'in da muka yi just d'an biscuit muka ci" Fatuu tace to ta d'aga mata kafad'a ko sun yi sauri suje suyi girkin, jin haka yasa Fauzy d'agowa tana kallon Fatuu tace "Gaskia Zarah yakamata kiyi saurayi ko don irin haka kinga da yanzu kawae sai kisa ai mana take away ba 6ata lokaci" Fatuu na dariya tace "to kema kiyi saurayin mana" yar harararta tay tace ai ita ta gama yin saurayi har abada yanzu karatun ta ne saurayinta in ta gama kuma aikinta ne zai zama mijinta Fatuu sai dariya take tace ai shikenan sai suyi ta zama ba samarin tunda haka suka za6a Fauzy ta fara mata magiyar don Allah ta fara saurar su tunda ana cewa ana sonta, d'an ta6e baki tay tace "kema ai ana cewa ana son kin ko don da wuya mu fita wani bai mana Magana ba ji wannan da ya maki Magana a Mall kika k'i saurarar shi da gani d'an gayun mai kud'i ne ga Motar shi had'add'a" yamutsa fuska tay tace "k'yale wad'annan masu Motocin duk mayaudara ne" yar dariya Fatuu tay daidai lokacin suka iso wurin Admin Fauzy ta kai idonta daga gefen wurin parking space d'in Malamai kaman daga sama Fatuu taji tace "Wow ji wata zazzafar Mota can kalar su Yaya Haisam" da sauri Fatuu ta kalli direction d'in idanunta suka sauka akan Motar kalar army green da sai faman d'aukar ido take da gani sabuwa ce kuma da gaske ta had'u ba k'arya d'an murmushi Fatuu tay ta juya tana fad'in wato kalar su Ya Haisam ce kenan Fauzy tace "Eh mana ai ko wacce kalar mota da kalar irin mutanen da ke hawanta waccan ko ban fad'a ba kinsan kalar shi ce inama ace shine tun da kince wannan Month d'in zai zo" wani kallo Fatuu tay mata tace "da yake daga Funtua yake zamu gan shi kwatsam ko" dariya sukai su duka suna niyyar wuce saitin Motar suka ji an latsa horn Fauzy ta d'an juya ta kalli Motar sai kuma ta maida idon kan hanya tana fad'in "Zarah ko dae kin yi kasuwa ne" ta6e baki kawae Fatuu tay suna k'ara taku aka k'ara yin horn d'in Fauzy tace Allah da gaske kodae dasu ake Fatun tace da yake su kad'ai ne a wurin ko wannan Maganar tasa Fauzy yin tunanin k'ilan bada su ake ba suka cigaba da tafiya wayar Fatuu suka ji ta fara ringing ta kai hannu cikin pocket d'in rigar uniform d'inta ta fiddo ta tana kallon screen d'in taga sunan Ya Haisam ya bayyana da d'an mamaki tace "Fauzy da alama Ya Haisam yaji kin yi Maganar shi" kai idonta Fauzy tay kan wayar da d'an mamaki take tambayar ta shine ya kira Fatuu ta d'aga mata kai itama tana kokarin yin picking, bayan ta d'aga tun kafin tay magana taji yace bata ji yana mata horn bane ba shiri ta kai idonta akan Motar da tsananin Al'ajabi take kallonta yana fad'in hakan yay cutting kiran Fauzy da itama ta kalli in da Fatun ke kallo ta juya tace mata ya akai ne with surprise written ol over her face ta fad'i mata abunda yace waro ido Fauzy tay with mouth agape ta sake kallon Motar kafin tace "kenan shine??" Kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh sosae itama Fauzyn tay mamaki wani irin arashi ne haka ita tayi Maganar ta duk don ay raha sai gashi ta tabbata kama hannun Fatun tay tace suje, a gaban driver side suka tsaya idonsu akan glass d'in duk da basu ganin shi slowly glass d'in ya fara sauka k'asa har fuskar Haisam d'in ta bayyana, zuba mashi ido su kai su duka yana sanye da riga turtle neck army green irin rigar nan mai kaman ta sanyi wadda ake nad'e wuyanta tana da dogon hannu kuma dama har lokacin akwae yanayin sanyi sai bak'in Jeans har k'iba taga ya d'an k'ara don fuskar shi ta k'ara cikowa ga sajen da ya bari sumar ta d'an k'ara yawa yanzu kwance luff da k'yar Fauzy tay murmushin yak'e tace "Ya Haisam ina wuni an zo lafiya" jinjina mata kai yay kafin cikin cool voice d'in shi ya amsa mata da Alhamdulillah ta k'ara ce mashi ya Aunty Fanan yace tana lafiya juyawa tay ta kalli Fatuu jin bata ce komae ganin ta zuba ma Haisam d'in ido yasa tay d'an murmushi ta kai hannu tace ta kawo jakar bari taje ta yi masu Abincin bayan ta amsa ta juya tace ma Haisam sai anjima ya d'aga mata kai, sam Fatuu ta kasa bud'e baki ta tanka mashi Saboda mamaki don ko jiya sunyi waya fa amman bai ce mata yau zai zo ba ga wani irin bugu da k'irjinta ke yi tunda tay tozali dashi, ganin irin kallon da yake mata ne yasa tay k'arfin halin cewa "an zo lafiya" still bin ta da ido yay dama ya jingina kanshi da headrest kaman bazai ce komai ba can taji yace ta shigo cikin Motar jiki a sa6ule ta zagaya d'ayan side d'in ta bud'e kopar gaba ta shiga har saida ta d'an lumshe ido bayan ta rufe kopar ta juya suka had'a ido ta sake gaida shi had'i da yi mashi an zo lpy sai lokacin ya amsa mata da lafiya suka d'an yi shiru tana kallon glass d'in gaba shi kuma yanata kallonta ta cikin mirror can ta juya ta kalle shi shima ya juyo suka had'a ido tace "ashe yau zaka zo amman baka fad'a man ba kuma ko jiya mun yi waya" d'an murmushi yay calmly yace "komae sai an fad'a ne?" d'an tura baki tay ta sadda kan ta k'asa taji ya k'ara cewa ko yayi laifi ne da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ba tare data d'ago ba suka d'an yi shiru can ta ji yace mata ya School sai lokacin ta d'ago tace mashi lpy Lou ta tambaye shi Aunty Fanan yace tana Lagos shima daga can yake Fatun ta d'aga kai suka k'ara yin shiru can ya kai hannu yana kokarin tashin motar ta juya ta kalle shi batare da ya kalleta ba taji yace su je a samo masu Abinci bata ce komae ba ta d'an juyar da kanta gefe had'i da yin murmushi ta ayyana Ya Haisam ba dae sanin yakamata ba, saida suka fita daga cikin Makarantar ta tuno da girkin da Fauzy zata masu ta ayyana yakamata ta kirata tace ta bashshi dama wayar na akan cinyoyinta ta d'auka ta fara kiranta bugu d'aya ta d'auka tace "love birds ya ana nan anata soyewa?" d'an murmushi Fatuu tay bata ce mata komae ba gudun kar tay wata Maganar yasa ta tambayeta ta d'aura Abincin ne tace a'a biscuit da Madara ta fara sha don bata iya jurewa har sai ta gama amman gashi yanzu zata d'auran Fatun tace mata ta bar shi gashi za'a siyo wata k'arar murna Fauzy tay tace "Allah maji kan bawa muma ga saurayin zai mana take away" yar dariya kawae Fatuu tay Fauzyn tace "in fad'a maki abunda nike so" tace mata eh, harda su gyara murya ta fara zayyano mata shawarma,pizza,farfesun yan ciki, sakwara......, saida ta fad'i abu ya kai goma cike da mugunta Fatuu tasa speaker tace mata bata ji abubuwan da ta lissafa tana so ba muryar na yankewa ta sake fad'i mata ba tare da ta sani ba ta hau sake lissafo mata Fatuu nata guntse dariya ta d'an waiga ta kalli Haisam shima murmushi ne akan face d'in shi bayan ta gama lissafawa Fatuu tace mata duk ya zatayi dasu tace kara'i zatay yaushe rabon da su ci kayan dad'i da yawa saidae suga ana kawo ma masu samari to suma tunda Ya Haisam d'in su yazo ai dole su ci dad'i, sosae Fatuu ke dariya jin irin dariyar da taken ne yasa Fauzy tace badai yana ji ba cikin dariya tace a'a sai ta dawo ta kashe, bayan sun je Eatery d'in duk abunda Fauzy ta fad'a saida yasa aka basu Fatuu nata ce mashi wasa fa itama take saidae yay murmushi kawai haka akai masu ledojin takeaways suka taho a bakin gate d'in Makarantar ya tsaya don an riga an tashi ba'a bari a shiga, juyawa tay ta kalle shi da d'an murmushi tay mashi godiya yay shiru har zata juya taji yace bazata koma gida ba ta rink'a zuwa ko tafi son ta zauna a school tana kallon shi tace "to in koman ne?" guntun murmushi yay jin tayi mashi tambaya cikin tambaya yace in tana so ya rink'a kawo ta kafin ya koma tace "to in kai mata Abincin sai in dawo?" shiru ya d'an yi kafin yace taje zai zo bayan Magrib ya d'auketa tace to daga haka ta fita daga Motar ta rufe ta bud'e back seat ta tattaro ledojin ta nufi cikin gate d'in tana yi tana d'an waiwayen shi duk yana kallonta ya juya Motar ya tafi, Fauzy baje saman gado tana latsa waya Fatun ta shigo da yar sallama suka had'a ido da sauri ta yunk'ura ta tashi zaune tana fad'in welcome ta Ya Haisam, a gabanta Fatuu ta aje dukkan ledojin tace "ga dukkan sak'on ki nan sai kita kara'in" waro ido Fauzy tay tabi ledojin da kallo kafin da mamaki ta kalli Fatuu tace "Wai badai fad'a mashi kikae ba?" zama Fatuu tay gefen gadon tana cire Hijab d'inta tace "kedai ba Kin fad'i abubuwan da kike so ba kuma an kawo maki kawae kici gaba da shagali" wani kallon rashin yarda take ma Fatun ba kamar data ga tana yin dariya magiya ta shiga yi mata kan ta fad'i mata ya akai aka siyo wannan uban kayan daga baya Fatun ta fad'i mata shi yaji da kunnanshi tace kenan speaker tasa ta tay shiru tanata mata dariya aikuwa tay kukan kura zata jawo ta Fatuu ta mik'e tanata kyalkyatar dariya Fauzyn na Fad'in "U'r wicked wllh yanzu don rashin Mutunci shine kika sa man speaker na saki baki inata maganganu don Allah ba sai ya d'auke ni acici ba kuma mai son abun duniya" ganin kaman ranta ya 6aci yasa Fatun ta koma gefen ta tana bata hak'uri tace ai shima yasan wasa take kar ta damu kawai suyi shagalin su aikuwa saida ta jawota ta d'uma mata dundu tana niyyar k'ara wani Fatuu ta k'wace tana fad'in daga abun arzik'i in dai ta k'ara bugunta to bazata ci komai ba a ciki Fauzy ta harareta tace "kin ma isa ki zubda man Mutunci kuma kice bazan ci komae ba" ta k'arasa Maganar tana fiddo takeaways d'in tana yi tana jinjina kai tana fad'in Fatuu ta gama da ita ganin duk abunda ta fad'a an siyo shi, saida suka wanke hannuwan su a jikin windown d'akin nasu dake a saman bene sannan suka zauna zaman ci Fauzy tana ci tana saka wa Haisam Albarka Fatuu nata dariya anan take sanar da ita zancen tafiyar ta anjima ta 6ata rai tace "Ya Haisam ya kuma zai mun haka don Allah na samu yanzu kina zama zai dawo mun da kad'aici" ita dae Fatuu dariya kawai take can Fauzy tace "na gano shi wato bai iya jure rashin ki kusa da shi shine zai d'auke ki yace wani zai rink'a kawo ki ke miyasa bazaki ce kin fi son zama nan ba don Allah" ta k'arasa a marairaice kafin Fatun tace wani abu ta sake cewa "koda yake saida hakan zaki janyo mana zuciyar shi don na lura bata jawuwa cikin sauk'i amman gaskiya ban ji dad'i ba" Fatun ta hau ce mata sorry, duk cin su basu iya cinye rabin Abincin ba don wasu abun ma Fatun bata ci ba tace ta bar ma Fauzyn ta rage loneliness da su. Zuwa bayan Magrib ta gama shirya kayanta a trolley d'inta tayi wanka ta shirya cikin straight skirt da riga na atampa sun mata k'yam ta kashe d'auri Fauzy sai yabonta take dama ba tun yanzu ba take fad'in bata ga wadda straight skirt ke ma kyau ba irin Fatuu, yar light make up tayi da ba zata ma yi ba Fauzy ta matsa mata ta d'an shafa humra a jikinta bayan ta gama ta zauna gefen gado suna d'an yin fira da Fauzy har tana fad'in yau dole ta nemo mai tayata kwana don yanzu ta riga ta saba kwana ba ita kad'ai ba Fatuu dai nata mata dariya ganin yadda take Maganar tana tura baki ita ala dole an mata laifi, suna zaunen saiga kiran shi ya sanar da ita yana a bakin gate tace to ta yafa gyalenta a kafad'a tare da Fauzy suka fito tana ruk'e da trolley d'in suka sauka k'asan benen, suna tunkarar gate Fauzy taja ta tsaya ta mik'a mata trolley d'in Fatuu tace "girlfriend bazaki idasa raka ni ba" yar harararta tay tace "in dawo ni da wa kuma ko bama haka ba Allah ban zuwa kin gama zubda man Mutunci" dariya Fatuu tay tace "ki share kawae tunda buk'ata ta biya anci dad'i har an ture" kafewa tay kan bafa ta k'arasawa gate d'in dole Fatun ta amshi trolley d'in tayi mata saida safe sai sun had'u gobe daga haka ta tafi itama Fauzy har ta juya sai kuma ta sake juyowa ta k'wala ma Fatuu kira ta tsaya cikin d'an d'aga murya tace "ki tabbatar kafin ya koma kin ida sace zuciyar ta yarda har ya kasa sukuni sai ya fad'i maki yana son ki don duk wannan kame kamen mun gano shi" dariya sosae Fatuu ke yi ta d'aga mata hannu kafin ta juya ta tafi itama Fauzy ta koma Hostel, tunda ta kusa isowa bakin gate d'in ya fara hangota sakamakon hasken fitilun dake a gefe da gefen hanyar data zo bakin gate saida ta tsaya suka gaisa da baba mai gadi da yake kusan ba wanda bai santa ba a Makarantar tun daga kan d'alibai har zuwa Malamai sosae take da farin jini uwa uba kuma tana da abubuwan dake sa mutum ya rink'a burge mutane kaman kokari ga kyau kuma tana da kirki duk da bata d'aukar nonsense yanzu ta sauke ma mutum kwandon bala'e, tunda ta nufo Motar ya zuba mata idanun shi da ya d'an lumshe su yana mata kallon k'urulla har ta k'arasa ta bud'e back door ta saka d'an trolley d'in kafin ta rufe ta bud'e kopar gaban ta shiga yanzu ma dae k'ananan kayan ne a jikinshi bayan ta zauna ta jawo kopar ta rufe da murmushi ta juya suka had'a ido ta gaishe da shi ya jinjina mata kai daga haka ya juya Motar suka tafi, tsit sukai ba wanda ya k'ara tankawa yanata driving ita kuma tana kallon gefen hanya a bakin wani Cafe ya tsaya yace mata yana zuwa ta d'aga mashi kai ya fita tanata kallon shi lokacin da ya zagayo har ya shige cikin Cafe d'in ta d'an lumshe ido tana murmushi bai d'auki lokaci sosae ba ya fito hannunshi ruk'e da ledoji guda biyu masu d'auke da tambarin wurin ya bud'e baya ta can side d'in driver ya saka sannan ya koma driver seat d'in yaja suka tafi, saida ya k'ara tsayawa wurin masu Fruit saidae bai fita ba ya sauke glass ya fad'i abubuwan da yake so aka cika manyan ledoji guda biyu yace ma mai fruit d'in ya saka mashi a baya bayan ya biya shi suka tafi, lokacin da suka k'araso kopar gidan su Fatuu anata kiran sallar isha ta kalle shi da murmushi tayi mashi godiya bai amsa ba sai ya jinjina kai had'i da lumshe ido har zata bud'e kopar taji voice d'in shi yana fad'in da safe zai zo ya kaita school ta kalleshi tace to ya k'ara ce mata ta d'auki abun baya, kowanne leda guda ta d'auka ta fruit d'in da ta Eatery d'in ta yi mashi godiya suka had'a ido ta mirror kasa d'auke idon tay tana ta kikkafta su can taga yay d'an murmushi duk sai kunya ta kamata ta janye kan ta ta rufe Motar saida ta fidda kayan can gefe sannan yaja Motar Amadu na ganinta ya fito ya zo gabanta yana washe baki yace "wato ya kasa hak'uri saida ya d'aukko ki kenan" wani kallo tay mashi had'i da tura baki ya kai hannu ya d'auki ledojin yana fad'in Juliet ta Romeo suka nufi gidan, d'akin gwaggo suka nufa suna shiga tana sallame salla ta d'aga kai tana kallon su tana ganin Fatuu tay murmushi Amadu yace "ga autar ki nan Romeo ya kasa hak'uri saida ya d'aukko ta" tur6une Fuska tay tace "kai Kawu Amadu miye haka" dariya yaci gaba da yi yana fad'in tuba yake kar a hana shi tsaraba yasan kayan dad'i ne, zama Fatuu tay kan kujera ta gaida gwaggo dake ta fara'a ta amsa mata tace an dawo Fatun tace eh Ya Haisam ne ya d'aukko ta yace zai rink'a kaita kafin ya koma gwaggon ta d'aga mata kai Amadu sai faman k'umshe dariya yake can ya juya yace bari ya d'aukko plate a bashi kason shi gwaggo ta d'an ta6e baki tana girgiza kai koda ya dawo da kan shi ya d'ibi komai harda fruit d'in ya mik'e yana fad'in Allah ya barta da Romeo suyi ta cin dad'i gwaggo ta kai hannu zata make shi ya nufi kopa yana dariya ya fuce gwaggo ta maida idonta akan Fatun tace "ai d'azun bayan ya iso ya shigo nan mun gaisa anan na fad'i mashi kina can Makarantar ashe zuwa yay" d'an murmushi Fatuu tay ta d'aga mata kai itama gwaggo murmushin take duk sai Fatun ta tsargu ta mik'e tace bari ta kai kayanta d'aki ta nufi kopar fita gwaggo ta bita da ido, bayan ta koma d'akinta saida ta cire kayan jikinta tasa na bacci bayan ta fito ta nufi kitchen ta d'aukko plates sannan ta dawo d'akin gwaggo ta zuba masu abubuwan suka fara ci tare suna yar hira har tana tambayarta Fauzy anan ta bata labarin abunda ya faru d'azun gwaggon tanata dariya tace amman bata kyauta ba Fatuu tace to ba gashi tayi kara'in ba, bayan sun gama ta fidda kayan wanda suka rage ta kai fridge ta zauna yin kallo dama ba salla take ba shiyasa bata yi sallar isha'i ba, Washe gari talata da safe Haisam yazo ya d'auketa kamar yadda yace yaci gaba da kaitan, Ranar Alhamis bayan sallar la'asar Haisam na zaune a Parlor tare da Abbas da ya kawo mashi dress code na Dinner d'in da za'ayi gobe Friday ta Abokin su Prince Obinna Eze ganin harda na mata lokacin da ya bud'e kayan yasa Haisam d'in cewa shida wa zai je da zai kawo mashi rigan mata kuma yasan Fanan bata nan dariya Abbas yay yace to haka aka tsara daya je amso kayan aka bashi su haka kowa da matar shi zai je ko budurwar shi don haka dole ya nemi wadda zai je da ita Haisam d'in na kishingide jikinshi sanye da jallabiya tun bayan da ya d'aukko Fatuu ya dawo ya watsa ruwa ya kwanta bacci saida akai la'asar ya farka ana gama sallar Abbas d'in yazo kawo mashi kayan, k'arshe ce ma Abbas d'in yay shi kadae zai je in yaje a koro shi Abbas na dariya yace "haba H,Zakee kaifa kana cikin manyan Abokan shi ya zaka kwafsa bayan ga yadda aka tsara kawai ka samu wata kuje tare badai na d'an lokaci bane" wani kallo mai kaman harara yake bin shi dashi jin Maganar da yay wai ya samu wata suna haka aka turo kopar duk suka kai idanuwan su Fatuu ce ta shigo tana sanye da riga da skirt na material kanta ba dankwali sai gyalen kayan data d'aura asaman kan shima baida wani girma sosae gashi sai zamewa yake gashin ta na fitowa tana rungume da k'aton littafi hard cover suna had'a ido ta sakar masu murmushi Abbas yace ta shigo mana ta nufi cikin parlon ta tsaya tana ta murmushi ta rasa ina zata zauna Haisam na kan L-shape Abbas na kan armchair guda Abbas ne yace ta zauna mana ga wuri nan yay Maganar yana nuna mata daga gaban inda Haisam yake zaune saida ta kalleshi suka had'a ido fuskar shi a sake ta nufi wurin ta zauna ta gaida shi ya jinjina mata kai ta kalli Abbas ma ta gaishe da shi ya amsa yana yar dariya yace "Mom Zarah ko ince Nurse Zarah" gumtse baki tay bata ce komae ba can taji ya sake cewa "Mom Zarah wannan dressing haka yakamata a rink'a sa babban mayafi" wani iri taji kunya ta kamata ta sadda kan ta k'asa ganin haka yasa shi cewa "am sorry gudun yin laifi yasa nayi maki Magana tunda an zama d'aya" d'agowa tay tana d'an murmushi tace "ba komae na fahimta yanzu ma don gwaggo bata ganni bane da bazata bari in fito da k'aramin gyale ba" jinjina kai yay yace "to yakamata ana kiyayewar" tace "in sha Allah dama don naga nan zan zo ne kuma inata sauri don kar ya fita Assignment ne na kasa nike so a nuna man" kai ya d'aga alamar ya fahimta ta juya ta kalli Haisam tace don Allah ya duba mata kafin yace wani abu Abbas yace "Mom Zarah ya zaki kawo ma wanda computer kawae ya sani Assignment d'in ku yan Asibiti" tana dariya tace ai tasan zai iya Abbas d'in yace in yayi browsing ko tace ko bai yi ba yace ta kawo ya ga Assignment d'in ta mik'e ta kai mashi ya amsa yana dubawa yana dariya yace wannan nashi ne bana Zakee ba ita dae dariya kawae take can ta mik'e tace bari ta kawo mashi lemu to yaji dad'in yi mata yace yauwa kaman tasan yana buk'ata H,zakee bai iya tarbar bak'o ba ta mik'e tana dariya ta nufi fridge d'in idon Haisam a kanta Abbas na d'an satar kallonshi yana guntse dariya slowly ya maida idon kan Abbas suka had'a ido ganin dariyar da yake yasa shi d'an ta6e baki ya maida idon shi kan Tv, bayan ta d'aukko lemun da glass cup ta tsiyaya ta ba Abbas ya amsa had'i da yi mata godiya daga inda take ta kalli Haisam tace zai sha shiru bai ce komai ba sai bin ta da ido da yake Abbas ne yace ta kai mashi kawai irinsu ba'a jiran sai sun yi magana tana dariya ta wuce saida ta janyo c-table ta aje a gabanshi sannan ta d'aura lemun ta juya ta je ta d'aukko wani cup d'in ta dawo ta duk'a tana tsiyaya mashi yau ma dae kaman rannan idonshi suka sauka akan boobs d'inta saidae yau sam ya kasa kauda idon har ta d'ago don ta mik'a mashi bai sani ba ta kama shi farko bata fahimci inda yake kallon ba har saida ta sadda kanta taga saman boobs d'in ya fito sosae duk sai taji wani iri ta mik'e tsaye hakan ya maido shi cikin hankalin shi ya d'aga ido ya kalleta tay mashi nuni da lemun da hannu ya d'an jinjina kai had'i da furta thanks jiki a mace ta koma inda ta taso ta zauna duk sai bata ji dad'i ba tasan da tasa babban mayafi ta rufe jikinta ko hijab da hakan bata faru ba, bayan Abbas ya gama shan lemun yace tazo taga yadda Assignment d'in yake saida ta gyara gyalenta sosae sannan ta nufi inda yake ta zauna akan d'ayar armchair d'in ya d'aura book d'in akan hannun kujerar ya fara nuna mata ba'a dau wani lokaci mai tsawo ba ta gane sosae tay mashi godiya had'i da mik'ewa tay masu sallama ta tafi, tana fita Abbas ya kalli Haisam yace "mi zai hana kaje da Mom Zarah kawai ma?" Kallo kawae Haisam d'in ya bi shi da shi Abbas yaci gaba "nasan bazata k'i zuwa ba kawae ka fad'i mata zata raka ka dinner party sai ka bata rigar nasan dad'i ma zata ji kuma hakan yafi da a maida masu rigan" shiru yay da alama nazari yake. Washe gari Juma'a bayan ya d'aukko ta daga school lokacin da suka k'araso kopar gidan kafin ta fita yay mata zancen Dinner d'in yace in ba damuwa yana so ta raka shi tace to yace amman ta fara tambaya nan ma to d'in tace ya kai hannu baya ya d'aukko jakkar da rigar take ya bata yace wannan zata saka amman ta fara dubawa in bazata yi ba sai a canzo before time d'in, bayan ta amshi jakar ta kai hannu ta fiddo rigar wadda doguwar riga ce Red colour mai bud'ewa daga k'asa hannun Net gareta d'an k'arami haka ma k'asan rigar inda ya bude hawa biyu ne yadin rigar da kuma irin net din hannun sai wuyan ta ma wani irin design akai mashi ba k'arya dae rigar ta had'u iya had'uwa Fatuu na ganinta ta saki k'ayataccen murmushi don harma ta hango ta cikinta, bayan ta gama dubawa ta kalli Haisam tace lafiya lou zata yi shiru ya d'anyi yana kallon ta yace amman kaman zatai tighting nata yaga tayi k'arama tace mashi a'a lafiya lou ai roba ce zatayi ya k'ara cewa tsawon ma kaman yayi mata yawa shima tace ai dogon takalma zata sa lafiya lou duk da haka saida yace in ta shiga ta gwada in bata yi ba ta kira shi sai a canzo tace to daga haka ta fita, tana shiga gidan cike da zumudi ta wuce d'akinta dama tasan gwaggo bata nan tana wurin aiki, gado ta nufa ta aje bag d'inta ta fara cire uniform d'in hannuwan ta har kerma suke ta k'agara taga yadda Rigar zata mata, bayan ta cire kayan ta fara kokarin saka rigar sai dae da k'yar ta shigeta don ta kamata sosae don ma roba ce yasa ta shiga, tsaye tay a gaban mirror tana kallon kanta hannunta rufe da baki ganin yadda shape d'inta yay bala'en fitowa tana jin tunda take bata ta6a saka kayan da suka fiddo mata da dirinta haka ba har jujjuyawa take tana k'are ma kanta kallo tunanin anya yakamata ta je da ita wurin ta fara yi kodae ta kira shi tace a canzo d'in haka taci gaba da yin wasi wasi saidae ita kanta yadda Rigar tay mata ya burgeta can ta yanke kawae ta tafi da ita komawa tay gefen gado ta d'auki wayarta ta kira gwaggo ta sanar mata zancen zuwa dinner d'in tace to Allah ya kaimu. Da daddare tana cikin yin shirin tafiya don ya sanar mata sai k'arfe 10 za'a fara gwaggo ta dawo makeup tay sosae ta saka rigar tunanin wane kalar takalma zata saka ta fara can wata zuciyar ta raya mata ta kira shi taji su wane kalar kaya zasu saka sai tasa irin takalmin da sauri ta juya ta d'auki wayarta tay sending mashi kira bayan ya d'aga ta gaishe dashi ya tambayi ta shirya ne cikin yar in ina tace eh tana son taji shi wane kalar kaya zai saka yace mata Ash suit ne da red tie tace to ta katse kiran ash d'in takalma masu tsini ta d'aukko da hadaddar purse d'in su tasa d'an kunne mai yar ziririyar sarka silver da agogon su ta jiguno dai ba k'arya, bayan ta gama ta fara tunanin gyalen da zata saka sai kuma tay tunanin tabbas ta fita da gyale gwaggo bazata barta ta fita da rigar ba haka ma Ya Haisam d'in tasan in ya gani ba lalle ya bari ba dubara ce ta fad'o mata ta yanke sa ash d'in jallabiyarta in suka je sai ta ajeta a Mota sosae hakan yay mata ta d'aukko rigar dama a goge take ta saka ta zuge zip d'in gaban yadda ta cikin zata fito tay rolling veil d'in rigar ko a hakan ma ba k'aramin had'uwa tay ba sai faman sakin murmushi take tana haka goma saura yan mintuna ya kira yace in ta gama yana waje tace to, bayan ta fito ta nufi d'akin gwaggo tayi mata sallama lokacin har ta kwanta amman idonta biyu ta tashi zaune tana kallon Fatun da murmushi ta hau yaba Kwalliyar tana fad'in had'in yayi kyau Fatun ta sanar mata shi ya kawo mata rigar ita za'a saka ta d'aga mata kai tace taje kar yay ta jira ta ce to ta juya tana fad'in sai sun dawo, a Ash d'in Mota zasu tafi tana zuwa ta bud'e front seat ta shiga bayan ta rufe kopar ta juya ta k'ara gaida shi a hankali ya amsa dama Motar a kunne take ya ja suka nufi Paramount Event Center inda za'ai dinner d'in......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2043* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ........ Lokacin da suka iso harabar Event Center d'in shak'e take da jigunannun motoci masu numfashi kai ko ba'a fad'a ba kasan wani wanda ya kai ne zai yi aure, bayan ya parker Motar ya kai hannu ya d'auki phone d'in shi dake ajiye gefe bayan ya bud'e ya shiga call log ya fara kokarin kiran Abbas ringing biyu ya d'aga kafin yace wani abu Abbas ya riga shi tambayar sun isa wurin ne yace mashi eh yace Ok shima gashi nan ya kusa shigowa jin haka yasa yay cutting kiran ya maida wayar inda ya d'auke ta ya d'ago ya kalli Fatuu suka had'a ido da yake wurin fayau yake kai kace da rana ne don ba abunda ba'a gani hakan yasa har cikin Motar akwae d'an haske da za'a iya ganin mutum duk da glass d'in blacktinted ne amman widescreen d'in gaban bai da duhu sosae kamar na k'opopin, maida kan shi yay jikin headrest itama ta juya tana kallon abubuwan dake faruwa a wajen cikin ranta tana jinjina irin Motocin Alfarmar da aka tara ga Mutane ne sai kai da kawowa suke, bada jimawa ba Abbas ya shigo akan idon Haisam bayan ya parker Motar ya bud'e ya fito yana lallatsa wayar shi ganin hakan yasa Haisam ce ma Fatuu yana zuwa ta d'aga mashi kai ya d'auki wayar shi ya bud'e ya fita, tunkarar Abbas dake k'ok'arin kiran wayarshi yay yana ganinshi yay dariya suka ba juna hannu ya d'an kalli gefen shi ganin bai ga Fatuu ba yace "ina Zarah badai kai kad'ai d'in ka taho ba?" Fuskar shi a sake yai mashi nuni da tana cikin Mota ya jinjina kai shima ya tambaye shi ina Feenah bai bashi amsa ba sai dariya kawae yake can ya juya ya bud'e Motar ya d'an duk'ar da kan shi da alama Magana yay ya fiddo ya rufe aka bud'e front door d'in d'ayan side d'in ta fito tana sanye da irin rigar Fatuu tunda ta fito Haisam ya tsuke fuska yana mata wani kallo ganin ba Feenah bace wata ce daban yar doguwa ce don zata fi Fatuu tsawo saidae bata da jiki amman ba za'a kirata siririya ba kuma fara ce duk da da gani an k'ara dana kanti ko daga yanayin hasken fuskarta zaka gane, rigar ta amshe ta da yake roba ce amman fa da gani wurin hips d'in anyi ciko don bai tafi sosae ba kamar na gaske, tana k'arasowa Haisam ya kauda idon shi ba kamar ganin yadda ta kafe shi da ido Abbas ne yace mata ga Aminin shi Haisam su gaisa cike da kwanare da kisisina cikin mak'e murya ta gaishe dashi k'asa k'asa ya amsa ba tare da ya sake kallonta ba suna haka Motar ango ta iso wata rantsattsar jeep mai bugun zuciya tasha adon su balloons ga security gefe da gefe Motocin suka ja layi suka tsaya ba tare da wani ya fito ba Abbas ne yace ma Haisam ya kamata Zarah ta fito tunda sun iso yanzu za'a shiga ya d'aga mashi kai kawae dama wayar shi na ruk'e a hannun shi ya kira ta bayan tayi picking yace ta fito da yake yasan tana ganin su tunda Motar a saitin su take, saida ta cire jallabiyar ta aje anan cikin Motar ta gyara rolling d'in gyalen ta yadda daga bayan kan ta ya d'aga sosae Saboda gashin ta dake a fake ta kai hannu ta bud'e Motar ta fito bayan ta rufe ta tunkare su tana tafiya slowly hips d'inta na wani sama da kasa sakamakon takalmanta dake da tsini sosae kai kace da gayya take yin tafiyar saidae ita tsakaninta da Allah lafiya lou take yin tafiyarta tunda ta fito Abbas ya kafeta da ido bako k'yaftawa haka budurwar tashi, kallon Abbas Haisam yay da niyyar yi mashi magana ganin gaba d'aya attention d'in shi ya tafi kan wani abu yasa shi d'an juyawa ya kalli direction d'in da idanun Abbas d'in suke idanun shi suka sauka akan Fatuu da take nufo su har bai san ya hadiyi abu ba lips d'in shi suka d'an motsa kad'an wani iri yaji ganinta haka sam bai yi tunanin zata cire jallabiyar bane ganin ta hau da dressing d'in sosae yama kasa gane dad'in ganinta haka yaji ko kuwa akasin hakan kawai dae abunda ya sani shine sam bai dace a ganta a haka ba, tana murmushi ta k'araso ta tsaya gefen Haisam tana kallon Abbas da shima yake d'an murmushi shi kan shi bai so ganin ta haka ba har saida yay mamakin yadda akai Haisam ya fito da ita a haka, rigar ta kamata sosae shape d'inta ya fita over ita kanta budurwar Abbas d'in duk sai ta raina kanta sai faman kikkafta ido take tana had'iyar abu bakinta na d'an motsawa ta kafe Fatuu da ido tana mata kallon k'urulla Abbas ne ya katse shirun da fad'in "Mom Zarah an yo rakiya kenan" tana murmushi ta d'aga mashi kai kafin ta gaishe dashi ya amsa ta kalli budurwar Abbas d'in suka had'a ido ganinta da irin kayan jikinta yasa tay tunanin tare take da Abbas tana murmushi tace mata sannu ta d'an yi murmushin itama amman na yak'e tace yauwa had'i da d'an juyar da kai, d'aga kai Fatuu tayi ta kalli Haisam da shima kallonta kawai yake bazaka gane yanayin fuskar shi ba d'an murmushi tay mashi bai ce komai ba kuma bai maida mata martanin murmushin ba suna haka aka sanar amarya da ango zasu fito a shirya entrance Abbas yace su je kaman Haisam d'in bazai je ba saida Abbas ya k'ara cewa su tafi sannan slowly ya kalli Fatuu yay mata alamar suje tana a gefen shi suka tunkari wurin, cikin shiga ta Alfarma da ni kaina bazan iya k'iyasta adadin dukiyar dake a jikinsu ba Bride and Groom suka fito suna ruk'e da hannun juna Amaryar na sanye da rantsattsiyar farar wedding gown da ke sakin wani irin k'yalli mai d'aukar ido da alama dai stones d'in da akai adon rigar kilan diamond ne dama tun daga kunnanta wuyanta har hannunta duk diamond ne sannan aka bi da kuma irin sark'ar su da suke sawa ta duwatsu mai kaman murjani har a saman kanta tayi kyau ba k'arya dama gasu jajur da su shima Ango Prince Obinna fararen suit ne a jikinshi sai bak'in tie da bak'ak'en takalma shima kunnuwan shi na manne da barimar diamond haka agogon hannunshi ma, bayan duk an fito an jera layi abun gwanin burgewa ashe ba iya shigar su Fatuu bace wasu bak'ak'e suka sa Matan na sanye da fararen gown wasu marron suit Matan na sanye da gown golden brown da sauran shiga kala kala sosae suka tsaru duk masu shiga iri d'aya sun jera wuri guda ga makad'an su na gargajiya sunyi shigar su suna irin kid'an su suna ma ango da Amaryar shi kirari bayan komae ya tsaru yadda ake so aka nufi cikin Hall d'in, Wow wow just wow don bansan ma ta ya zan fara bayyana tsaruwar wurin ba don duk iya hasashen mai hasashe ba zai iya k'iyasta ainihin nawa aka kashe ba wurin tsara wurin don wurin ya fitinu abun ba'a Magana suna shiga duk na ciki aka mik'e tsaye police bands suka d'auka busar sarewa kake ji ta ko ina ga kid'an su da ke sa mutum ya tausaya ba tare da yama sani ba wuri fa ya kacame da kid'e kid'e ga yan rawar gargajiya ma na nasu jikin Fatuu har tsuma yake sai faman sakin murmushi take ji take ina ma anzo da Fauzy tazo taga sha'ani da ya amsa sunan sha'ani, saida suka je suka zauna a high table sannan sauran Mutane duk aka zazzauna aka dakatar da kide kiden don fara gabatar da abunda aka zo yi, bayan MC yay welcoming kowa wani abokin ango ma yazo tare da budurwar shi ce ko matar shi oho yay ma kowa sannu da zuwa da gabatar da abunda aka taru yi bayan ya gama babban Abokin Ango da Amarya inyamurai suka fito suka bada tarihin Ango da Amarya bayan suma sun gama aka buk'aci Bride and Groom suka fito don taka rawa zo kaga yadda suke cashewa abunsu cike da nuna ma juna kauna abun sai yama ba Fatuu kunya sai faman sunnar da kai take yayin da ake ta masu ruwan lik'i masu lik'a dollars nayi masu lik'a Naira nayi manyan mutane masu sanye da shigar su ta gargajiya ta ko ina sai tasowa suke suna lik'i daga baya aka bukaci kowa ya koma Abokan Ango da Amarya inyamurai suka fito aka fara casu mai sunan casu Fatuu sai dariya take haka ma su Abbas ji take kaman tay tsuntsuwa ta ganta a cikin filin itama tayi rawar saidae ba dama, bayan duk an gama abubuwan da ya dangance su aka dawo kan hausawa shi Angon da kanshi ya fara bayanin irin alak'ar shi da mutanen Katsina da irin karar da suka yi masu tun bayan da suka tsinci kan su a cikin garin ba tare da nuna k'yama ko tsangwama ba Saboda bambancin Addini ya tabbatar ma Mutane da musulunci addinin zaman lafiya ne sa6anin wasun su da suke masu kallon yan ta'adda yace shi shaida ne game da Mutuncin hausawa don sun nuna masu k'auna ta yadda har sun zama daga cikin Family d'in shi a k'arshe yay godiya ga musulman da suka zo wurin ya nuna hakan ba k'aramin abu ne a wurin shi ba yay fatan Allah ya k'ara had'a kan su suci gaba da zama da juna da Amana yay Addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata ga K'asar mu Nigeria sannan yay godiya ga Governor d'in Katsina da Sarakunan D'aura da Katsina da sauran manyan mutane Mutane nata amsawa da Ameen bayan ya gama itama Amaryar aka bata tayi godiyar bayan duk sun gama aka buk'aci babban Abokin Ango bahaushe da ya fito ya bada tarihin Ango na nan garin irin alak'ar shi da mutane da sauran su MC ya tambayi angon waye zai fito ya nuna mashi Haisam duk ido ya dawo kan shi a nutse ya mik'e ganin zai fito shi kadae MC yace the equation isn't balanced nan take duk aka gane abunda yake nufi da yake d'an barkwanci ne duk aka sa dariya dakatawa Haisam yay ba wai fita da Fatun ne bazai yi ba sam shigar ta bata dace da wurin ba a matsayinta na Musulma Abbas ne ya kalli Fatuu yace ta tashi suje ganin Haisam d'in bai ce komae ba yasa ta mik'e ta fito suka jera wohoho all eyes on them ita kanta Fatuu duk sai ta ji ta takura, tunda suka fara saukkowa daga kan steps d'in MC ya saki baki galala kamar rainon sakarai yana bin su da kallo tun daga sama har k'asa, lokacin da suka k'araso gaban shi suka tsaya fuskar Haisam dai ba wata walwala don duk ji yake wurin ya fice mashi a rai maimakon MC d'in ya bashi loudspeaker d'in sai yace mashi wait ya juya kan Mutanen wurin yace "People are u seeing what am seeing???" gaba d'aya aka sa dariya ya sake juyawa kan angon harda d'an rankwafawa alamar girmamawa cikin harshen turanci da yake dashi ake Magana a wurin yace ya gafarce shi amman abokin shi bahaushe ya tambaya ba Arab ba ko Indian gaba d'aya wurin aka kwashe da wata irin dariya har dai shi Haisam d'in saida ya d'an dara Fatuu ma haka daga inda Angon yake zaune yace ma MC ya ba Haisam d'in speaker ya tambaye shi tarihin shi da Hausa anan zai gane wanene shi ya juyo kan Haisam yace suna rok'on Alfarmar jin tarihinshi da hausa farko kafin ya fad'i abunda aka bukace shi ya fito yi, shiru ya d'anyi MC d'in nata fad'in please can ya kai hannu ya amshi speaker d'in cikin cool voice d'in shi ya fara bada tarihinshi a tak'aice cikin harshen hausa aikuwa masu jin hausa a wurin aka hau tafi da sowa Haisam d'in na d'an murmushi MC sai faman jinjina kai yake baki bud'e alamar mamaki bayan ya gama ya canza harshe zuwa turanci ya fara bada tarihin Ango da mu'amalar shi da mutane anan sai ka rantse ba shine ya gama Magana da Hausa ba gaba d'aya ya gama tafiya da mutane sai faman sakin murmushi ake bayan ya gama ya mik'a ma MC d'in speaker d'in amman sai yak'i amsa yace yana son yay mashi few questions ba yadda Haisam d'in ya iya dole yace mashi yana jin shi farko tambayar shi yay miye alak'ar shi da Fatuu har saida gabanta ya fad'i Haisam d'in yay d'an shiru kamar mai nazari Abbas kuwa mi zaiyi in ba Dariyar mugunta ba can ya nisa yace mashi girlfriend d'in ce da sauri Fatuu ta kalle shi sai kuma ta kauda kanta gudun kada a gane ba gaskiya ya fad'a ba saidae bata yin zaton zai boye gaskiya ba, tambayar shi yadda akai suka had'u ya k'ara yi anan bai 6oye ba yace mashi Neighbor d'in shi ce daga baya ya koma kan Fatuu itama ya tambayeta tsakanin su waya fara cewa yana son wani shiru tay ta rasa amsar da zata bashi kawae sai ji tay Haisam d'in yace mashi shi ya fara MC d'in ya k'ara tambayarta ya taji da ya furta yana sonta tace taji dad'i sosae har bata san yadda zata bayyana ba tana fad'in hakan ta sunnar da kai, haka dae yaci gaba da yi mata tambayoyi daga baya Haisam yace ya d'an yi excusing nasu yay ma Fatuu alamar su je suka juya MC nata kod'a su yana fad'in "What a match, What a perfect Match......." Maimakon su koma high table d'in sai gani tay ya nufi hanyar fita daga hall d'in hakan yasa ta bi bayan shi suka fice, inda Motar su take ya nufa tay tsaye tana kallon shi ya bud'e ya kalleta yace ta shiga cikin rashin fahimtar dalilin fitowar su ta kai hannu ta bud'e ta shiga tana ta kallon shi har yay ma Motar Key ya fara yin reverse tana dae ta kallon shi da alamun mamaki har ya juya Motar suka tunkari gate d'in fita, suna hawa hanya sai ga kiran Abbas yana yin picking tun kafin Abbas yace wani abu yace mashi yaba Prince hak'uri he has an urgent call ya tafi daga haka yay cutting call d'in yaci gaba da driving baki bud'e Fatuu ke kallon shi sam bata yarda da Maganar da yay ba a yaushe aka kira shin, d'an juyawa yay ya kalleta yace mata lafiya fuska a tur6une tace mashi ya akai suka baro wurin daga farawa shiru yay kaman ba zai ce komai ba sai kuma yace mata gida zai maida ta kamar zatai kuka murya na rawa tace "to Saboda me, duka fa bamu wani dad'e da zuwa ba" nan ma shirun yay tana ta k'unk'uni sai da ya d'an d'auki lokaci sannan yace "ban ce in akwae wani problem da kayan ba u shall inform me a canzo?" tura baki tay yanzu ta gano dalilin kaman zatay kuka tace "to ai naga ta shige ni ne" banza ya mata taci gaba da k'una k'uni da jan majina alamar zatai kuka can ya juya ya kalleta sai kuma ya maida idon kan hanya calmly yace "ai mun je ko miye na damuwar?" kallon shi tay kaman bazata tanka ba ta d'aure fuska a shagwa6e tace "to wannan zuwa ne, kofa Abinci bamu ci ba gashi serve ur self za'ai harda bank'ararrun raguna mutum yaci iya cin shi ga wannan yar giyar ma da aka aje mana saman table ko sha bamu yi ba" Haisam baisan lokacin da yay dariyar da har hak'oran sa suka bayyana ba jin wani shirmen ta wai giya d'an juyawa yay still yana dariyar yace "Har yanzu baki daina ganin lemu kice giya ba ko" tana tura baki tace "to ai giyar ce wannan ko ga kwalaben nan manya manya masu duhu kuma dama ai su suna shan ta" d'an shaking kan shi yay yana d'an murmushi yace "to wannan ba giya bane is non Alcoholic suna respecting addinin mu bazasu bamu giya ba saidae in mutum na sha yay Magana a bashi ko nama ma musulmai suke ba suyi processing nashi" shiru kawae tay still bakinta a ture yake can ya d'age gira yace "da giyan ne sai ki sha kenan?" Kikkafta ido tay tace "to ai in a rashin sani na sha ba wani abu ko" yace "to waya kai ki inda za'a bakin balle har kisha?" Shiru ta d'an yi kafin tace "kai ka kai ni kuma kasan za'a banin" yana murmushi yace "in nasan za'a baki bazan kai ki ba" shiru tay shima yaci gaba da driving d'in shi yana yi yana d'an kallonta still da murmushi a kan face d'in shi ganin yadda ta 6ata rai ita ala dole an mata laifi, a gaban wani babban soya spot ya parker Motar gefen titi ya fita part d'in gasasshen rago mai yawa yasa aka yanko mashi had'i da gasasshar kaza bayan ya biyasu ya dawo a back seat ya bud'e ya saka ya rufe ya koma driver seat d'in suka tafi, a gaban wani Cafe ya k'ara tsayawa ya fita bada jimawa sosae ba ya dawo ruk'e da k'atuwar leda mai tambarin wurin ya shiga suka tafi har lokacin bata washe ba sai fushi take, ganin sun bi wata hanya wadda ba ita suka biyo ba da zasu zo yasa ta d'an juya ta kalle shi yanata driving bata ce komae ba ta maida kan ta jikin seat har suka k'araso wata unguwa suka shiga Fatuu ta bi manyan gidajen da suke wucewa da ido lokaci guda mamakin ina ne suka zo ya cika ta tana niyyar juyawa ta tambayi ina suka zo idonta suka sauka agaban wani d'an sign board mai d'auke da sunan road d'in da Unguwar nan take ta gane G.r.a ne da mamaki ta juya ta kalle shi tace mi zasu yi a Gra kamar bazai tanka ba sai kuma taji yace saida ita zai yi ta tura baki, suna hawa wani titi ya tunkari wani tangamemen gate na wani katafaren gida ya tsaya yana latsa horn sau biyu wani mutum mai sanye da kayan yan sanda ya d'an manyanta ya lek'o ta k'aramar kopa yana ganin Motar ya koma da sauri ya zuge masu gate d'in Haisam ya shige, bai nufi k'aton parking space d'in ba sai ya parker ta gaban ginin gidan wanda mansion ne na Gaske ya kalli Fatuu yace ta fito ya kai hannu ya bud'e kopar ya fita itama ta bud'e ta fito baki bude take k'are ma gidan kallo duk da ba bene bane amman yana da girma sosae ga ginin kan shi abun mutum ya saki baki yana kallo ne ga had'addun shuke shuken da suka zagaye ko ina sun k'ara k'awata harabar sosae ta ko ina k'awatattun fitilu ne sun haske gidan security d'in ne ya iso gaban Haisam yana washe baki yay mashi sannu da zuwa ya amsa mashi kafin ya kai idon shi kan Fatuu itama ya gaidata duk sai ta ji wani iri hakanan ta amsa, bud'e back door yay ya fiddo da ledojin ciki security d'in ya mik'a mashi hannu yace ya kawo ya rage mashi Haisam d'in yace ya bashshi bayan ya rufe kopar yana shirin wucewa security d'in yace "Yalla6ai mai gyaran nan ya dawo yace abun nan sai ya kai zuwa gobe dole sai a Kano aka samu goben za'a kawo sai ya idasa gyaran" kai ya jinjina sai kuma ya tambaye shi tun yaushe aka maido wuta yace mashi ai duk yau akwae wuta gaskiya Haisam d'in ya amsa da Ok ya juya shima security d'in ya koma gate kallon Fatuu yay bayan ya zagaya side d'in da take yace suje tay tsaye tana kallon shi har zai juya ya dakata yace bata ji bane d'an yamutsa fuska tay tace ina ne nan d'in wani kallo yay mata kafin ya bata amsa da inda zai sayar da ita ne ta d'an zaro ido ganin bata da niyyar tahowa yasa shi cewa shi ya shiga ciki tay ta tsayuwa har azo a tafi da ita aikuwa tun kan ya rufe baki tabi shi da sauri tana yi tana waiwayen bayanta ita duk sai ta tsorata da gidan ma da yayi Maganar, Wani jigunannan Parlor suka shiga mai d'auke da Sofas set biyu ya tsaru iya tsaruwa ya bi wani Corridor dake gefe Fatuu na bin shi a baya sai waige waige take har suka iso bakin wata babbar kopa ya tura suka shiga Fatuu tay tsaye tana bin d'akin da kallo wanda Bedroom ne amman mai girman gaske daga can gado yake da bedside drawers d'in shi sannan daga gaban shi inda table d'in gaban gado yake set d'in leather Sofas ne ta yadda sun sa gadon a gaba daga tsakiyar su lallausan carpet ne a bangon da suke facing k'atuwar plasma TV ce manne sai can gefe kuma dressing mirror yake daga d'an gaban shi wata budaddar kopa ce ta corridor a gabanta kuma akwae k'atuwar window a wurin kayan motsa jiki ne sai dae basu da yawa harda irin mai sa gudun nan wanda Fatuu ta hau sanyin Ac ta koina, suna shiga taja ta tsaya har ya nufi ciki ya dakata ya juya ya kalleta ganin tayi tsaye ya nuna mata inda kujeru suke yace taje ta zauna bata motsa ba ta bishi da ido hakan yasa ya dawo d'an gabanta ya tsaya yana kallonta ta sadda kai can ta d'an d'ago ganin ya kafeta da ido yasa a marairaice tace "baka gaya man ina bane nan d'in da muka zo" d'an kauda idon shi yay tana ta kallon shi ya juyo yace bata yarda dashi bane da sauri tace "a'a kawai dae ina son sani ne" sigh yay yace "gidan Dad d'ina ne a G.r.a" kai ta d'aga har zai juya ta k'ara cewa "to mi muka zo yi bazamu koma gida ba?" Idon shi a Kanta yay d'an murmushin gefe yace "zaki ida abunda na hanaki ne kike fushi sai mu koma" d'an tura baki tay yace taje ta zauna ta shige shima ya wuce saida ya aje ledojin kan Carpet yace mata yana zuwa ya nufi Corridor d'in cikin d'akin tabi shi da kallo har ya shige kafin ta maido su tana k'are ma d'akin kallo ya dae tsaru sosae sam ba hayaniya ga katafaren gadon yasha farin bedsheet gwanin burgewa, sanye da milk jallabiya mai gajeran hannu ya fito ya nufi hanyar da suka shigo ya fita Fatuu dae tayi tsuru a saman kujera bai dad'e ba ya dawo hannun shi ruke da plates harda yar wuka da glass cups ya nufi wurin kujeru ya d'aura akan Carpet ya d'ago ya kalleta yace ta saukko ta taso tazo wurin ta zauna, da kan shi ya shiga fiddo abubuwan da ya siyo yana sawa a plate d'in harda take away d'in Fried rice da irin lemun da tace ma giya yana fiddo shi ya d'aga ido ya kalleta yana d'an murmushi ta tura baki ta kauda fuskarta, bayan ya gama yace ta ci ya d'auki wasu da ya rage a cikin leda yace mata yana zuwa ya nufi hanyar fita don kai ma security, bata fara ci ba har ya dawo ya zauna kan kujera yana kallonta yace taci mana tana d'an kikkafta ido tace to shi fa yace zai ci ta gama tana d'an yamutsa fuska tace wato ita acici ko in dae bazai ci ba itama ta k'oshi d'an murmushin gefen baki yay yana kallonta itama kallon shi take can ya tashi ya sauka kan Carpet d'in ya lankwasa kafafun shi saida taga ya fara ci sannan itama ta sa hannu tun dai bata saki jiki ba har ta saki suna ci suna kallon Tv sai gashi sun ci sosae harda k'arawa bayan sun gama yace in bata k'oshi ba ta k'ara tace itama ta k'oshi ya bud'e mata lemun ya tsiyaya mata yana d'an murmushi yace ta d'auka ta kai hannu ta d'auka ta d'an sha sai taji shi lafiya lau lemu ne yana murmushi yace saura ta k'ara gani tace giya ce tay d'an murmushi taci gaba da sha a hankali, wayarshi ce ta fara ringing ya mik'e ya nufi gaban dressing mirror ya d'auka da turanci yake magana bayan ya gama ya aje wayar ya juya ya nufi daga can gefen inda kayan Motsa jiki suke saman wani desk ya d'aukko laptop dake a sama ya dawo wurin kujerun ya zauna saman 3 seater ya aje laptop d'in a gabanshi bayan ya bud'eta ya fara operating nata Fatuu da itama ta koma saman one seater ta zauna tana kallon Tv bayan wani lokaci ta kalleshi ta kira sunan shi ya juyo ya kalleta tace ba yanzu zasu tafi bane gently yace ta d'an yi hak'uri ya k'arasa abu ana jiranshi ne tace to ta maida idon kan Tv can ta tuna da bata yi sallar isha'i ba da yake tayi wankan tsarki jiya zumud'in zuwa dinner ya hana ta tsaya tayi Sallar kallon shi tay tace tana son tayi salla ya d'ago ya nuna mata corridor d'in da ya shiga ya canzo kaya yace in ta shiga akwae kopa mai kallonta anan toilet yake tace to ta mik'e, lokacin data k'arasa ta tura kopar tasha mamaki don tayi zaton toilet d'in zata gani amman sai taga laundry room irin nashi na gidan Hajiya amman wannan yafi kayatuwa don aciki press d'in kayan shi take wadda ta glass ce kana kallon kan ka a jiki ga kuma wall cabinet a ciki su kayan wanka suke sosae wurin ya burgeta don ita bata san yana dashi a can d'in ba tunda ko bedroom d'in shi bata ta6a shiga ba, kopar da ta gani a cikin wurin tay tunanin nan ne toilet d'in ta nufeta ta tura aikuwa toilet d'in ne wanda ya amsa sunan toilet, bayan tayo Alwalar ta fito tsaye tay a bakin corridor d'in tana tunanin to da mima zatay sallar d'an gyalen data nad'a iya kafad'ar ta yake tana tsayen ya d'ago ya kalleta ya tambaye ta da matsala ne tace eh ba hijab yace ina jallabiyar ta tace ta baro ta a Mota mik'ewa yay yace yana zuwa bada jimawa ba ya dawo ya kawo mata tay mashi godiya ya d'aukko mata prayer mat ta tambayi inda gabas take ya nuna mata kafin ya koma yaci gaba da aikin shi, bayan ta gama sallar komawa tay wurin kujerun ta zauna kan 2 seater taci gaba da kallon a hankali kuma ta fara gyangyad'i tun tana yi tana bud'e ido har takai ta d'an kwanta ta fara baccin sosae can ya d'ago ya ganta tana baccin don bai ma san tayi ba juyawa yay yaci gaba da aikin da yake bayan wani lokaci Fatun ta bud'e ido da sauri kuma ta tashi zaune tana d'an murza ido tace "Ya Haisam yakamata mu tafi dare yayi sosae" kallon agogon jikin laptop d'in yayi yaga sha biyu saura saukko da d'ayar kafar shi yay ya mik'e yace suje itama ta mik'e ganin bai kashe laptop d'in ba yasa tayi mashi magana yace zai dawo ne in ya kai ta ta d'aga kai ta d'auki purse d'inta ta fita daga wurin kujerun shi kuma ya nufi gaban dressing mirror ya d'aukko cay key yana nufo ta kwatsam aka d'auke wuta aikuwa Fatuu ta saki k'ara tana fad'in "Wayyo ya Haisam kana ina don Allah ka kunna haske wllh ban ganin komae" shi Maganar tata ma dariya ta bashi sai kace wata yar k'aramar yarinya wai tsoron duhu ya lura da ita abunda bai kai ya kawo ba shi take ji ma tsoro jin baiyi magana ba yasa ta k'ara kware murya tana fad'in ta bani don Allah yayi magana abun ma shi nishad'i ya saka shi sai kawae yay shiru aikuwa ta k'ara rud'ewa dama ta tsorata da gidan tun farko cigaba da fad'in yana ina tay tana lalube duk ta firgice a haka har ta k'araso gabanshi tana kai hannu ta ta6a chest d'in shi ga k'amshin jikinshi kuma aikuwa ta fad'a mashi ta fashe da matsanancin kuka tana fad'in shine yana jinta zai yi banza da ita sosae ta k'ank'ame shi jikinta sai kerma yake sai kuma duk bai ji dad'i ba baiyi zaton ta tsorata haka sosae ba slowly ya kai hannu bayanta alamar rarrashi ya shiga furta mata "am sorry" lamo tay a hankali rawar da jikinta keyi ta fara raguwa cikin muryar kuka tace ya kunna haske su tafi ya furta Ok bari ya duba wayan bai san takamaimai inda take ba aikuwa ta k'ara rikeshi gam ganin haka yasa ya fara moving da ita a kokarin shi na su koma inda kujerun suke don yafi tunanin anan ya aje wayar bayan da aka kira shi cikin rashin sani ashe ta bayan kujerun suka bi har baisan sun zo bakin gado ba kawae sai jin su sukae sun fad'a saman shi rikica gaba d'aya hankalin su ya tashi don abu ne da basu tsammaci faruwar shi ba tsit kake ji kowa na maida numfashi ba kamar Fatuu da yake a samanta sun dan d'auki lokaci a haka kowa ya kasa yin kwakkwaran motsi tamkar anyi glueing nasu da k'yar Fatuu cikin rawar murya ta ambaci sunan shi shiru bai amsa ba ta kai hannu da niyyar ta d'aga shi hannun ya nutse acikin sumar kanshi wani irin shock yaji a jikin shi da sauri Fatuu ta janye hannun tana breathing rapidly wannan d'agawa da saukar da chest d'inta keyi ya fara turning nashi on slowly ya d'ago face d'in shi ta yadda numfashin su ke had'uwa gaba d'aya kasala ta lullube Fatuu da k'yar ta iya k'ara bud'e baki tace "Ya Haisam ka......" Cak ta tsaya tana zare ido jin abunda bata ta6a zato ba lips d'in Haisam a saman nata a rud'e ta fara kokarin k'ara yi mashi magana kawae sai jin tongue d'in shi tay cikin bakinta bata ankare ba sai ji tay ya fara mata hot French kiss lokaci guda Fatuu ta rud'e ta kidi'me ta gigice, gaba d'aya Haisam ya gama gigita yar Mutane har bata san ta zura hannunta acikin sumar shi ba tana squeezing nata hakan da take ya k'ara turning nashi completely on hot romances ya shiga yi mata tamkar yana operating laptop d'in shi to Fatuu dae ba k'arfe bace cikakkar mace ce da jini ke yawo a jikinta tana cin mai kyau ta sha kuma mai kyau dole kota k'i ko taso jikinta na buk'atar abunda ke faruwa da ita hakan yasa kwata kwata ta kasa hana shi abun har ya kai wani mataki da ita kanta bata ankare da an kai ba ba abunda take sai sakin numfashi da k'arfi had'i da nannauyar ajiyar zuciya a wata kalar duniya take jin ta da babu gwaggo babu Kawu Amadu ba Hajiyar sanata ba ba....., Fatuu bata tashi dawowa hayyacin ta ba saida taji wani rikitaccen Al'amari dake shirin faruwa da ita wanda sam bata san an kawo nan ba aikuwa a gigice ta kai hannu ta kama damtsen shi tana girgiza mashi kai tana fad'in ya bari ba kyau abunda suke Allah zai kama su kada ya cutar da ita, da alama Haisam fa ya rasa control kokarin penetrating d'in ta yake ta k'arfi ganin haka yasa Fatuu ta fara k'ok'arin kwatar kanta ta hanyar kai mashi bugu da yakushi amman sam kamar bai jinta ma abunda yasa gaba kawai yake as if his life depends on it cikin k'araji Fatuu ke fad'in "Don Allah Ya Haisam na rok'e ka in kana k'aunar iyayen ka kana k'aunar Hajiyar Sanata ka k'yale ni kada ka cutar dani ni fa kanwarka ce......" bata k'arasa Maganar ba ta saki wata irin razanannniyar k'ara koma in ce kururuwa........... innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un! Jama'a miya hwaru ne😳 _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2045* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ........lokacin da suka iso kopar gidan k'arfe d'aya da rabi na dare Unguwar tayi tsit ba kowa sai hasken fitilu da yake akwae wuta, yana parker Motar ta kai hannu don ta bud'e ta fita amman sai taji kopar a rufe cikin muryar fushi tace ya bud'e mata ta fita bai ce komae ba wayar shi na a hannun shi yana kokarin kiran Amadu dama tun suna Asibitin bayan an shiga da Fatuu yay tunanin kiran shi cikin sa'a ya d'aga kiran anan ya sanar dashi cewa ayi hak'uri sun yi dare ne da yake ba'a fara program d'in da wuri ba amman gasu nan dawowa in ba damuwa kada yay bacci sai ya bud'e mata k'opa, yanzu ma da ya kira shin bayan yay picking yace mashi gasu nan k'opar gida ya amsa da to ya katse kiran ya aje wayar a gefe sannan ya d'auki wayarta dake aje kan seat ashe anan ciki ta barta tun bayan da ya kirata a wurin dinner yace ta fito, bud'e k'opopin Motar yay Fatuu na jin ya bud'e ta kai hannu ta bud'e shima bud'e ta side d'in shi yay ya fito ya zagayo inda take lokacin har ta zuro k'afafun ta hannu ya kai don ya taimaka mata tak'i 6ari ya ta6ata dole ya k'yaleta yana ta kallon ta cike da tausayawa har ta fito hannunta ruk'e da takalmanta ya duk'a cikin Motar ya d'aukko purse d'inta da ledan magungunan har ta fara tafiya ya bita ya tsaya a gefenta ta kauda fuskar ta tana niyyar cigaba da tafiya cikin wata irin murya ya kira sunanta shiru bata amsa shi ba sai dai ta tsaya bai damu ba yaci gaba da fad'in "am so sorry pls kiyi hak'uri nasan ban kyauta maki ba amman kamar yadda nace zan gyara laifi na in sha Allah zamu yi Magana kinji?" Shiru dae bata tanka ba ya mik'a mata ledan da purse yace "ga drugs en ki ki d'aure ki sha....and sun...ce ki rink'a sit bath with lukewarm water da d'an salt nasan baki rasa sanin hakan but kaman yadda nace kar ki fad'a ma kowa abunda ya faru pls" a wawware yake Maganar duk muryar shi ta canza ga wani nishi da yake yi in yana Maganar shiru dai tayi kanta na gefe jin k'arar ta6a k'opar gidan su alamar za'a bud'e yasa ta kai hannu ba tare data kalle shi ba ta amshi purse da magungunan daidai lokacin Amadu ya bud'e k'opar tunanin yadda zata cigaba da tafiya ta shiga yi tayi tsaye Haisam ya fahimci hakan sai ya kira Amadun ya nufo shi ya juya ya koma Mota Amadun na biye dashi a jikin Motar ya jingina Amadu ya iso ya tsaya gaban shi da murmushi ya gaishe da shi ya amsa yana kokarin daidaita voice d'in shi yace "am sorry na hanaka yin bacci ko?" Murmushi Amadu yay yace "ai lokacin da ka kira ni d'azun ban ma kaiga kwanciya ba ina chatting ne" jinjina kai Haisam yay ya d'an saci kallon Fatuu dake k'ok'arin shigewa cikin gidan yace ma Amadu "kana zance kenan?" Yar dariya mai sauti Amadu yay don bai tsammaci jin irin Maganar daga wurin Haisam ba yace mashi a'a, d'an yamutsa fuskar shi yay a kokarin shi na ya d'an yi murmushi kafin yace "Ok in ka shiga pls ka basu hak'uri" Amadu yace "toh naga ma tayi bacci yanzu d'azun ne da ta ga k'arfe 12 tayi naga kamar ta d'an damu tana cewa ko lpy shine har ta kira wayarta sau biyu ba'a d'aga ba sai na nuna mata ba lalle in an fara da wuri ba don irin wannan ana yin African time sai akai har tsakar dare wasu ma kwana ake" d'an lumshe ido Haisam yay ya bud'e yace mashi ya shiga gida ya gode sosae yayi mashi saida safe ya juya idon Haisam akan shi har ya shiga gidan ya maido kopar ya rufe, hannu Haisam yasa ya dafe forehead d'inshi gaba d'aya ran shi a cunkushe yake rashin kwanciyar hankali ta hana yaji zafin zazza6in daya rufe shi ya d'an d'auki lokaci a haka shi kadae kaman Aljani acikin tsohon dare daga baya ya cire hannun daya dafe goshin ya rufe kopar da Fatuu ta fito kafin ya zagaya driver side ya bud'e ya shige bai yi tunanin zuwa gidan Hajiya ba duk da yasan ko ya koma Gra ba iya k'arasa aikin da ada shine zai maida shi can d'in ba, bayan ya tashi Motar ya juyata ya koma Gra, lokacin da Amadu ya shiga gidan har ta shige d'aki shima nashi ya shige tana shiga ta nufi gado ta aje ledar maganin da purse a gefe tay zaune tana ta sakin ajiyar zuciya a hankali can ta kai kwance ta kife fuskarta a jikin katifa kwalla suka fara gangaro mata abunda bata ta6a tunani zai faru da ita bane ya farun wai Ya Haisam ne yay raping d'inta wani ma in yaji wannan Maganar ai ba zai ta6a yarda ba wllh ita yanzu shikenan tasan ko aure tay mijinta bazai ta6a d'aukarta da daraja ba in ma ya zauna da ita kenan, runtse idonta tay tasa kuka mai ta6a zuciya ta fara raya miyasa Ya Haisam zai mata haka miyasa Ya za6i ya cutar da ita har hakane ko dai Khalid da kowa yasan halin shi ne bai cutar da ita kamar yadda Haisam yay ba shi da ma yake da aure wata zuciyar ce ta fara kokarin k'are shi tana ayyana mata sharrin shaid'an ne ba komae ba tunda shima ai tasan ba halin shi bane ko, wata zuciyar kuma tace koda ba halin shi bane dama ya so ya aikata mata hakan tunda ai ta rok'e shi amman yak'i saurarenta kuma dama yana yi mata wasu abubuwa da bai saba mata ba ko jiya a parlon shi ai saida ta gan shi yana kallon mata boobs hakan na nufin sha'awarta yake! tana yin wannan tunanin ta k'ara sautin kukanta abun da ciwo Mutumin da take tsananin k'auna amman shi sha'awarta yake ta yadda har ya kasa dannewa saida yay mata wannan aika aikar saida tay mai isar ta kanta na kife kafin ta rarrashi kanta ta yanke a ranta bazata bari kowa yasan abunda ya faru ba kuma ba ruwanta da Ya Haisam ta fita daga harkar shi daga yau wata zuciyar ta raya mata kar tace haka ta bari ya zo suyi Maganar da yace goben ta raya koma yazo ai bai wuce yace zai bata hak'uri ne ba wani abu ba, "in kuma yace zai aure ki fa??" ta sake raya mata shiru tay tana kikkafta ido k'arshe ta yanke tasan hakan ma ba mai yuwu bane mutumin da duka shekara d'aya da rabi kenan da auren shi koma ba haka ba taya Aunty Fanan zata amince ya aureta ta san hakan ba mai yuwuwa bane, "in shi yaga zai auren ki duk abunda zai faru ya faru fa?" Wata zuciyar ta k'ara raya mata wannan karon yunk'urawa tay ta tashi zaune fuskarta a tamke a fili tace "Bazan Aure shi ba wllh tunda ba don yana sona zai aure ni ba sai don ya goge laifin da ya aikata man ba zan ta6a amincewa ba yaje yaci gaba da zama da matar shi da yake so" idanunta ne suka sauka akan ledar magungunanta ta kai hannu ta d'aukko ta tana kallo ta raya yakamata ta 6oyeta can kuma tay tunanin dole fa sai tayi wankan tsarki kuma, shiru tay zuciyarta ta fara tariyo mata farkon yadda abun ya faru a hankali ta lumshe ido tana ta tuno lokacin kafin ta fita hayyacinta ji take inama ace da aure suka aikata hakan cike da so da k'aunar juna wasu kwalla ne masu zafi suka fara gangaro mata tunowa da haramun suka aikata da sauri tasa tafin hannunta cikin kuka take fad'in "Ya Allah ka yafe man na tuba bazan k'ara ba ba hali na bane sharrin shaid'an ne" can ta mik'e tana tafiya a hankali ta nufi wardrobe ta aje ledar magungunan bayan ta rufe tsaye tay tana tunanin yadda zata yi wankan in tace ta bari saida safe to saidai fa ta bari har gari ya waye bata yi sallar Asuba ba tunda ba yadda za'ai ta yi da Asuba sanin lokacin gwaggo ma ta tashi wata zuciyar ce ta ayyana mata kawae tayi yanzu tay tsaye tana jin tsoron kar ta je tana yi gwaggo kuma ta fito taga tana yin wanka cikin tsakar daren nan wata zuciyar ce ta raya mata in ma ta kamata sai tace sun dawo ne jikinta ba dad'i ta kasa yin bacci shine ta fito ta watsa ruwa still kaman hakan bai kwanta mata ba don gani take kaman duk da haka zata gane can dae tay shahada ta nufi wajen kitchen taje don tasan ana aje ruwan zafi a Electric kettle koda yaushe cikin sa'a kuwa akwai ruwan ta d'aukko butar gaba d'aya cikin fad'uwar gaba ta fito ta nufi Toilet har ta shige ba wanda ya fito, a ciki ta had'a ruwan tay wankan ta d'an zauna wasu duk da bata sa gishiri ba bata d'auki lokaci ba Saboda tsoron kada wani yazo ya ganta doguwar rigar ta maida ta d'aukko butar ta fito saida ta cikata da ruwa ta lalla6a ta maida ta kitchen d'in ta jona ta fito don tasan in ya tafasa zata mutu, har saida ta saki ajiyar zuciya ganin ta shige d'akinta ba tare da wani ya ganta ba wardrobe ta nufa ta fiddo doguwar rigar bacci ta cire ta jikinta tasa ta duk'unk'une wadda ta cire ta cusa ta a cikin Wardrobe d'in daga haka ta nufi switch ta kashe hasken d'akin kafin ta nufi gado ta haye taja bargo ta lullu6e ba laifi sosae rad'ad'in da take ji ya rago sai dae k'afafunta ne bata iya rufe su ba kamar in tana tafiya, lamo tay idanunta a waje tana kallon sama ta shiga ayyana yanzu da ace aure tay hakan ta faru tasan da yanzu mijinta na nan yana tarairayar ta amman yanzu gata tamkar mara galihu iya cuta dae ya Haisam ya cuceta wllh, a hankali take goge kwallan dake zubo mata ba laifi zazza6in ya sauka saidae jikinne duk ba dad'i take jin shi......... Lokacin da ya isa bakin gate d'in yana yin horn sau biyu Security yazo ya bud'e mashi ya shige, inda ya parker ta d'azun da suka zo anan ya k'ara parker ta bayan ya kashe d'an jimm yay kaman ba zai fito ba can ya kai hannu ya bud'e ya d'auki wayar shi dake gefe ya fita ya nufi cikin gidan, yana shiga Bedroom d'in idanun shi suka sauka kan gadon ya nufe shi a bakin gadon ya zauna idanun shi akan blood stains d'in dake jikin Farin bedsheet d'in tunanin yadda zai yi da shi ya fara zuciyar shi ta raya mashi wankewa yakamata yayi ya mik'e ya kai hannu ya fara cire bedsheet d'in bayan ya cire yana ruk'e da shi ya nufi hanyar corridor ya shiga laundry room ya bud'e Washing machine ya saka ya fara wankewa bayan ya gama koda ya fiddo shi sai yaga stain d'in na nan amman dai ya d'an rage zuciyar shi ta bashi ba lalle ya fita ba don ya bushe a jiki tunanin ko ya sa hannu ya wanke yaga in zai fita yay saidae shi bai iya wankin hannu ba don iya underwear d'in shi dana Fanan yake wankewa suma kuma a washing machine can dae ya yanke gwada wankewa da hannu ya juya yana tunanin a inda zai wanke don ba bucket a toilet d'in sai dai ya tafi part d'in Mom d'in shi ya d'aukko kuma da akwae tazara, dubara ce ta fad'o mashi ta ya toshe hanyar fitar ruwa ta bathtub d'in ciki sai ya wanke anan, bayan ya toshe a ciki ya k'ara wanke shi sam bai sha wata wahala ba duk da ba yin wankin yake ba saidae shi ba rago bane don ma jikin yayi weak ga zazza6in dake damun shi don har yanzu akwae shi a jikinshi cikin sa'a sai gashi ya fita don ma ba bleach a toilet d'in duk da bai sha wahalan wankewa sosae ba tunda fari ne, bayan ya d'auraye shi tunanin inda zai shanya shi yay ya yanke saidae ya fita can ta k'opar bayan gidan nan keda fence ta hanyar zuwa swimming pool har zai tafi can idon shi ya sauka akan k'opar laundry d'in yaga lafiya lou zai iya d'aura shi anan yay hakan sannan ya dawo ya wanke itama jallabiyar shi da ta 6aci, saida yay wanka ya tsarkake jikin shi ya canzo wata jallabiyar sannan ya dawo cikin bedroom d'in ya nufi inda kujeru suke ya zauna ya d'aura ha6ar shi kan hannuwan shi da ya dunkule tunanin halin da Zarah take ciki ya shiga yi gaba d'aya tsananin tausayin ta ya gama mamaye mashi zuciya ba kamar in ya tuna yadda yay da Fanan a first night d'in su nan da can ma sai ya d'auketa ya kaita ta dingi yi mashi rigima, gashi daga yadda Al'amarin ya faru yasan Zarah ta fita jin jiki kawai don tana da k'arfin hali ne, slowly ya lumshe idonshi underneath his breath ya furta "Am very sorry Zaraah I knew i hurt u..." tunanin ya kirata yaji halin da take ciki yay ya bud'e idanun a hankali kafin ya yunk'ura ya mik'e ya nufi can gefen gado inda ya aje wayar shi Lokacin da ya shigo saida ya kalli time biyu da rabi har ta wuce shiru yay yana tunanin ko ya kiratan can dae ya bud'e wayar yay sending mata kira lokacin har bacci mai nauyi ya d'auketa hakan yasa har kiran ya yanke ba'a d'aga ba ya sake wani kiran shima ba'a d'aga ba tunanin ko tayi bacci ko kuma fushin da take ne yasa bata d'auka ba yay ya aje wayar akan mattress yai zugudum can ya mik'e ya nufi gaban mirror ya jawo drawer chest ya fiddo wani d'an madaidaicin first aid box bayan ya d'aura saman mirror ya bud'e Panadol ya d'aukko ya 6alli guda biyu ya maida bayan ya rufe box d'in ya maida shi inda ya d'aukko wurin kujeru ya nufa walking very slowly ya zauna ya d'auki robar ruwa a cikin kayan Abincin da suka ci ya bud'e ya sha maganin kafin ya rufe ya ajeta, maida bayan shi jikin kujeran yay ta d'age kai hannun shi d'aya dafe da forehead d'inshi, ya d'an d'auki lokaci a haka can ya d'ago ya mik'e ya kwashe kayan ya fita dasu daga d'akin bada jimawa ba ya dawo ya nufi Corridor toilet yaje ya d'auro Alwala bayan ya dawo ya shimfid'a prayer mat ya kabbara sallar Nafila raka'a hud'u yay don k'arfin hali kawae yake bayan ya d'aga hannu ya d'an jima yana Addu'oi kafin ya mik'e ya nufi gado har wani duhu duhu yake gani ko tunanin shimfid'a wani bedsheet bai yi ba a haka ya hau kan mattress d'in yaja duvet ya lullu6e jikinshi har kan shi nan da nan kuwa temperature d'in jikin shi yay high sosae numfashin shi ya fara fita da zafi a haka bacci ya d'auke shi amman bana dad'i ba, gab da kiran sallar Asubar farko k'arar wayar shi ta tashe shi alamar ana kiran shi ya bud'e fuskar shi duk ta canza kala da alamun mamakin mai kiran na shi a time d'in, yunk'urawa yay ya tashi zaune ya kai hannu daga d'an gaban shi ya d'auki wayar yana kai idon shi kan screen d'in ganin sunan mai kiran har saida gaban shi ya d'an Fad'i ya shiga tunanin ko lafiya jiki a sanyaye yay picking kafin ya kara a kunne.., Har aka gama Sallar Asuba Fatuu bata farka ba rashin jin motsinta yasa gwaggo bayan ta gama azkar ta mik'e ta nufi d'akinta don tasan ta dawo lokacin da ake kiran sallar farko da ta fito ta d'aga labulan d'akin ta ganta a kwance, lokacin da ta shiga tana a kudundune har sannan gwaggo ta tsaya a gaban gadon ta fara kiran sunanta shiru har sau kusan ukku hakan yasa ta d'an duk'a ta kai hannu tana d'an bubbuga jikinta can ta fara motsi a hankali ta cire bargon dake rufe da fuskarta ta d'an juyo da fuskar da yake taba gwaggo baya ba saitin da take ba ta ke kallo koda tay arba da fuskarta da sauri tasa hannu ta dafe goshin ta ta yarda har idanuwanta ta d'an rufe ganin ta farka yasa gwaggo ta zauna a bakin gadon tana kallonta tace "Wane irin bacci kike ne haka baki san Asuba tayi ba ga gari har ya fara washewa baki tashi kin yi salla ba" d'an yamutsa fuska tay murya k'asa k'asa tace mata bata san gari ya waye ba bari ta tashi, ganin ta dafe kai yasa gwaggon tambayarta lafiya ta dafe kai haka wani irin bugu kirjinta ke yi tay k'ok'arin daidaita Maganar ta tace "Wllh kan ne ke man wani irin ciwo" da d'an alamun mamaki gwaggon tace "ciwon kai kuma to ya akai?" abu Fatuu ta had'iye ta fara tunanin abunda zata ce mata can tace "Wurin ne hayaniya tayi yawa sosae sai faman kid'e kid'e ake harda yan police band fa ga masu irin kid'an su na gargajiya in suka buga har tsakiyar kan Mutum wllh" yar dariya gwaggo tay tace to tunda shagali suke ai dole suyi kafin ta kuma cewa "gashi kuma kun dad'e sosae don har sha biyu ta wuce fa idona biyu ina dakon ki amman shiru ga wayar ki na kira ba'a d'aga ba........" Da sauri Fatuu ta tari numfashinta tace "a cikin Mota na barta kuma ba'a fa fara ba da wuri anata jiran wasu manyan mutane da yake bikin fa d'an sarkin inyamurai ne sai wurin sha d'aya in ma bata wuce ba aka fara da aka gama da Aunty Feenah ma akace in bi gidanta wai in kwana ni kuma na matsa sai na dawo tunda ba haka mukae da ke ba" jinjina kai gwaggo tay da d'an murmushi tace "Allah sarki ai da kin bitan ba wani abu dama dai aji shiru shine matsala amman indai ansan inda ake ai ba komae" juyar da kai Fatuu tay gefe jin k'walla na son zubo mata don wani irin tausayin gwaggon taji ta bala'en yarda da Haisam ta yadda ko kusa ranta bai bata wani abu mara kyau a game dashi, kokarin mik'ewa ta fara yi tana fad'in ta tashi tay sallar in tayi breakfast sai tasha magani akwae ruwan zafi a cikin flask a cikin kitchen da bread ita bari taje ta kwanta ta huta tunda yau bazata aiki ba daga haka ta fuce, wani irin kuka mai cin zuciya Fatuu ta saki zuciyarta ta raya mata yanzu fa ba kuka bane a gabanta ta fara tunanin yadda zatai jinyar kan ta ba tare da an gane ba don a iya tafiyarta ma kawae da gwaggo ta gani to tabbas zata iya zargin wani abu koma ta gane yin wannan tunanin yasa da sauri ta goge kwallan ta fara k'ok'arin sauka daga kan gadon a hankali ta fara tafiya k'afafu a wawware tana d'an yamutsa fuska don wurin yay tsami tana buk'atar ruwan zafi, saida ta d'an lek'a fuskarta ta labule ta kalli kopar d'akin gwaggo tsoro take kada ta fita itama ta fito su had'e ta d'an d'auki lokaci a haka can dai tay Addu'a ta yaye labulen ta fita gabanta na wani irin bugu tamkar ana mata luguden ta6are, kasa tafiya tay tayi tsaye a wurin can ranta ya bata ta lek'a taga mi gwaggo ke yi ta nufi d'akin a yadda take tafiya har ta k'arasa without making any sound a hankali hannu na rawa ta d'an d'aga labulan ta hangota saman gado ta lullube rabin jikinta har saida taji wani sanyi ta saki labulan ta juya, sosae ta d'aure tana cije baki ta rink'a tafiya yadda zata d'an yi sauri ta nufi kitchen ta d'aukko electric kettle ta nufi Toilet bayan ta fito, saida ta zauna ruwan zafi sannan ta d'auro Alwala, zaune tay bayan ta gama sallan da k'yar ta shiga tunanin yadda zatai don yadda take tafiya tsab asirinta zai tonu tana ta sak'e sak'e can dubara ta fad'o mata ta ta tafi Makaranta kawae kafin gwaggo ta tashi ko Kawu Amadu don shima ta san yanzu bacci yake tunda weekend ne sai d'an anjima zai tashi ya bud'e shago da wannan tunanin ta lalla6a da sauri ta tashi bayan ta d'auke abun sallan ta nufi Wardrobe ta fiddo wata doguwar riga ta zumbula ta ciro yar madaidaiciyar hijab ta saka lokacin idanunta suka sauka kan ledan magungunan ta d'aukko su bayan ta rufe ta d'aukko jakar goyonta da komae na karatun ta ke ciki ta bud'e ta saka magungunan ta sake bud'e wardrobe ta d'auki k'ananun kaya kala biyu da undies don acan tana da kaya bayan ta rufe wardrobe d'in ta d'auki wayarta dake ajiye gefen gado itama ta saka ta kauda duk wani abu da zata kauda daga haka ta nufi hanyar fita hannunta ruk'e da jakar saida ta lek'a ta tabbatar ba kowa sannan ta fita ba sai na fad'i yadda gabanta ke fad'uwa ba sai Addu'a take a cikin ranta cikin sa'a har ta kai zaure bata ji motsin wani ya fito ba ta bud'e gidan wanda sakata ce kawae Amadu ya sa da ya dawo daga sallar Asuba. Lokacin da ta fito wajen kwalam ba mutane bata bi ta hanya ba ta lungun gidan Hajiya tabi tana yi tana dafa bangon gidaje in ta gaji sai ta d'an tsaya ta huta kafin taci gaba tana cikin hakan tazo daidai kangon da su goga suka so raping nata wanda yanzu gida ne masu shima har sun dawo yanayin fuskarta ne ya canza ta shiga tuno yadda abun ya faru a lokacin har Haisam yazo ya ceceta da kuma lokacin da ta je part d'in shi daga baya har yace mata dama ita yar iska ce, a hankali kwallan da suka taru suka fara gangaro mata a fili ta furta "Ya Haisam yanzu ai kasan in ni yar iska ce ko....." Cigaba da lalla6awa tay tana yi tana cigaba da goge kwalla ta d'auki lokaci kafin ta kai bakin hanya don ba ranar aiki bace sam bata ga wani abun hawa a layin ba saida taje bakin hanya nan ma saida ta d'an yi jiran samun Napep don babu sai masu mashin ne keta tsayawa tana girgiza masu kai don tasan ba iya hawa zata yi ba daga baya ta samu Napep d'in ta fad'i mashi inda zata je suka tafi, lokacin da suka isa da kanta ta rok'i mai gadi kan ya bari a shiga da ita ciki bata lafiya ne da yake sun saba sosai yace to amman yay sauri ya fito suka shige bayan tayi mashi godiya, har bakin Hostel ya kaita bayan ta fito ta biya shi shima saida yay mata Allah ya sawak'e tay mashi godiya sannan ya juya Napep d'in ya tafi, harta shige bata ga kowa ba anata baccin weekend wad'anda suka rage a hostel d'in wanda ba yan gari ba don yan cikin gari da garuruwan kusa duk weekend suke tafiya wani lokacin, data zo hawa bene nan abun ya zama aiki tana yi tana dafa bango tana runtse ido had'i da cije baki a haka har ta haye ta nufi d'akin su a cikin bag d'inta ta fiddo makullin da yake hannunta don Fauzy ma ta tafi gidan Aunty Mareeya Weekend, bayan ta bud'e ta shige ta turo kopar ta nufi gado ta zauna ta aje jakar a gefenta har taji d'an sanyi yanzu sai tunanin abunda zata fad'a ma gwaggo in ta kira ta shiga yi, tana ta zaune jugum ga wata irin yunwa da take ji tun a gida can ta mik'e don ta samu abunda zata ci d'an gas d'insu ta kunna ta d'aura ruwa acikin yar babbar tukunya ta koma gefen gado ta zauna har ya tafasa sannan ta tashi ta d'ibi wanda zata had'a tea cikin d'an Flask ta saka Lipton kafin ta rufe sauran ruwan zafin ta juye a cikin bucket ta d'an sa gishiri sannan ta fita zuwa toilet, sosae taji dad'i bayan ta fito saida ta soya k'wai sannan ta had'a tea d'in ta had'a da biscuit ta ci data gama tasha magungunan ta haye gado ta kwanta ta lullu6e rabin jikinta tay ma bango k'uri zuciyarta ce ta raya mata Ya Haisam yace zasu yi Magana gashi har yanzu bai kira ba balle ma yaji ya take d'an ta6e baki tay ta raya ita tasan ba wata Magana data wuce ya bata hak'uri, a hankali ta fara lumshe ido a haka har bacci Yay awon gaba da ita. Lokacin da gwaggo ta fito sam bata yi tunanin tashin Fatun ba don tasan tace mata kanta na ciwo hakan yasa ta k'yaleta ta wuce kitchen koda ta shiga bata gane bata yi breakfast ba don Amadu ya shiga ya d'iba sai tay tunanin ko Fatun ce itama had'a nata tay ta koma d'aki, bayan ta gama ta fito da kayan ta maida kitchen kafin ta fara kokarin gyara gidan a haka har lokacin d'aura Abincin rana yay ta d'aura tana cikin yin girkin tace bari ta duba Fatuu baccin yayi yawa ko ciwon kan yayi tsanani ta nufi d'akin ta.......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2044* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ...........tun bayan daya dawo hayyacin shi ya k'ank'ame ta sosae jin yadda jikinta keta kerma gashi an kai wata ga6a da bata ma iya yin kukan mai sauti sai na zuciya k'walla nata gangaro mata ga zazza6i daya rufeta ruf lokaci guda, to shima dae kermar nashi jikin yake duk ya rud'e yanata bata hak'uri cikin wata irin murya mai nuna tsantsar tashin hankali gaba d'aya jin jikinshi yake tamkar ba nashi ba ga zazzabi dake neman rufe shi shima a haka bacci ya d'auke su su duka saidae Fatuu bana dad'i bane don sai sakin ajiyar zuciya take had'i da d'an firgita, suna haka aka maido da wuta sanyin Ac ya karad'e bedroom d'in kermar jikin Fatuu ta k'aro ba kamar da yake ba kaya a jikinta iya duvet ne da ya rufa masu, da k'yar ta bud'e idanunta da sukae mata wani irin nauyi jikinta na cigaba da yin kerma ga wasu kwalla masu zafi na gangaro mata a gefe da gefen idanunta sam ta kasa wani kwakkwaran motsi don duk ilahirin jikinta ciwo yake ga rad'ad'in azaba dake ratsa cikin jikinta ga kanta dake wani irin Sara mata ta k'ura ma ceiling ido idanuwanta a d'an lumshe she wishes what happened was a dream ba gaske ba saidae koda ga yanayin da take jin jikinta tasan gaske ne ya farun cikin ranta ta fara ayyana wannan wane irin bala'e ne miyasa Ya Haisam ya akaita mata hakan anya kuwa da gaske ne ba mafarkin ba, a hankali ta fara tariyo abunda ya faru tun daga farko ita dae tasan zata iya tuna lokacin daya kai hannu ya zuge mata zip dama rigar nada dogon zip har kusan k'ugu kuma bata sa bra ba sakamakon kamata da rigar tayi sosae sai tasa yar half vest kawae tunda kuma ya kai kan su ta fita hayyacin ta bazata iya tuna ga abubuwan da suka cigaba da faruwa ba sai lokacin da taji yana kokarin penetrating d'inta, hannu tasa ta rufe bakinta tana wani irin kuka mai cin rai miyasa hakan ta faru ya akai suka aikata hakan wata Zuciya ta raya mata sharrin shaid'an dama duk in mace da namiji suka ke6e ai na ukkun su shaidan ne ta k'ara ayyana to amman miyasa da tana rok'on shi kada ya aikata mata hakan yak'i sauraron ta mi zai sa ya cutar da ita har haka yanzu shikenan ya rabata da budurcin ta ya Haisam ya cuceta bai tunanin abunda zai je ya dawo ba Saboda son zuciya ya keta mata haddi wannan wace irin Masifa ce mutumin da ko a mafarki bata ta6a tunanin zai mata haka ba balle a zahiri mutumin da shine ya bata kariya hakan bai faru da ita ba a baya amman shi da kan shi ya aikata mata hakan mutumin da kowa nata ya yarda dashi ba kamar gwaggo har take iya barinta ta fita da shi da daddare sosae shine ya aikata mata wannan d'anyen aikin da tasan in gwaggo taji har zuciyarta na iya bugawa, innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un! haka take ta maimaitawa tana juya kanta tafin hannunta guda dafe da goshinta tana haka taji fitsari ya matseta ta fara kokarin janye jikinta don ta tashi sai faman nishi take da k'arfi sai lokacin ta gane ba kaya jikinta ta k'ara sakin wani Sabon kukan da K'yar taja jiki ta matsa can gefe inda ta hango jallabiyar ta ta d'auka daga zaunen ta zurata don bata ma ga jar rigar ba da dubara ta isa k'arshen gadon a hankali ta zura kafafun ta k'asa saida ta daddafe gefen gadon da hannunta sannan cike da k'arfin hali ta yunk'ura ta mik'e har wani Jiri ke dibarta tasa hannu ta dafe kai tana d'aga k'afarta don ta fara tafiya ba shiri ta koma da6ar ta zauna har saida ta saki yar k'ara Saboda wani rad'ad'in azaba da ta ratsata, hannu tasa ta rufe baki ta fashe da wani sabon kukan jin fitsarin na niyyar zubowa yasa dubara ta fad'o mata ta duk'e k'asa ta fara yin rarrafe tana cigaba da yin kuka a haka ta nufi Toilet d'in baiwar Allah duk wannan abun Haisam bacci yake ta shara sai kace matacce, a wahalce ta isa toilet d'in da K'yar ta shiga cikin bathtub don ma tana da k'arfin hali lokacin da fitsarin ya fara zubowa wata zabura tay a gigice tace "Wayyo Allah na!!!" ta k'ara fashewa da kuka Saboda azaba da kyar ta gama tana ta gunji ta kai hannu ta kunna fanfon ruwan zafi ko da tai tsarkin sai taji wani dad'i ya ratsata aikuwa taci gaba da yi ta bar fanfon a kunne tana tayi har bayan wani lokaci sannan ta kashe sai gashi ta samu relieve sosae bata sha wahala ba wurin fitowa kamar da zata shiga, da k'afafunta ta fito sai dae da K'yar take tafiyar tana yi tana dafa bango ga k'afafun sun d'an bud'e bata iya had'e su a haka har ta fito cikin d'akin idanunta suka sauka akan Haisam dake ta bacci sumar shi duk ta yamutse wani irin haushin shi taji ya turnuk'e ta ya aikata mata wannan aika aikar amman baccin shi ma yake sha nan da nan ta ayyana dama da niyya yay mata hakan k'walla ne suka cigaba da zubo mata tana sharewa wata zuciyar ta raya mata kawai ta tafi gida tunda ko ta zauna in ya tashi bai wuce yace zai bata hak'uri tunda ba iya dawo mata da abunda ya rabata da shi zai yi ba da wannan tunanin ta lalla6a ta d'auki gyalen rigar kota kan jar rigar bata bi ba dama tashi ce ta bar mashi kayan shi a hankali take tafiyar ta nufi kofa akan hanya ta ga purse d'inta yashe a k'asa ta d'auka bayan ta fita a bakin k'opa dama ta aje takalmanta saidae tasan bata iya tafiya dasu hakan yasa ta ruk'e su a hannunta, ta d'auki lokaci kafin ta k'araso bakin gate d'in tsit kake ji da alama dare ya tsala sosai a bakin kopar security ta tsaya ta kai hannu tana kwankwasa wa sai gashi ya fito hannun shi ruk'e da bindiga ya bita da kallo ta d'an kauda fuskar ta ya ganeta hakan yasa shi cewa "Madam lafiya kuwa" kaman bazata yi Magana ba k'asa k'asa tace ya bud'e mata kopa zata tafi ne da alamun mamaki yace "tafiya kuma cikin daren nan ina shi yalla6an yake" nan ma shirun ta k'ara yi ta rasa mi zata ce mashi don kar ya zargi wani abu can dubara ta fad'o mata tace "wani aiki yake a computer shine yace in jira ya gama mu tafi to sai bacci ya d'auke ni yanzu bayan na farka kuma sai naga shima yayi baccin ban son in tashe shi ka bud'e man zan iya tafiya" daga jin yadda take Maganar zaka fahimci ba daidai take ba sai faman nishi take ga Maganar a wawware shiru Officer yay yanata kallonta ya lura da har jikinta ma kerma yake hakan yasa shi ce mata kamar ma bata lafiya ko tace mashi eh zazzabi ne ya rufeta shine ma yasa ta farka yace to bari shi yaje yay mashi magana sai yazo ya kaita don dare yayi sosae k'arfe d'aya saura da kyar ma in bata wuce ba da sauri tace ba sai ya kira shi ba zata iya yace "Madam bari dae in mashi magana don a irin wannan lokacin ba'a fita da k'afafu don karnuka keda akwae ta ko ina da sun ganta zasu yi mata tara tara su aikata mata d'anyen aiki yana gama fad'in hakan ya nufi cikin gidan Fatuu na k'walla ta ayyana d'anyen aiki ya wuce wanda aka aikata mata yanzu, kasa cigaba da tsayuwar tayi da K'yar ta zauna kan saman wurin k'afafunta na a k'asa ta takure jikinta dake ta rawar sanyi wani irin fayau take jin ta, yana shiga corridor d'in d'akin Haisam ya tunkari kopar ya tsaya yasa hannu yana kwankwasa wa tun yana yi a hankali har ya kai ya k'ara sautin bugun amman shiru kake ji ba alamun za'a tanka kuma dae ba zai yuwu ya kutsa kai ba, cigaba da kwankwasawa yay can cikin bacci bugun ya kai ma Haisam da K'yar ya fara bud'e idanun shi da sukai wani irin nauyi gashi har kala sun canza sun d'an yi ja d'ago kan shi yay da mamaki yake kallon kopar da ake bugawar can ya tambayi waye da kasalalliyar murya saida ya tambaya sau biyu sannan k'asa k'asa Officer ya jiyo shi da d'an k'arfi yace Officer ne cikin ranshi ya maimaita sunan Officer d'in kafin ya kai hannu ya yaye duvet d'in wani irin bugu gabanshi yay lokacin da idanun shi sukai tozali da jinin da ke a jiki kallon jinin yake with mouth agape can ya furta "ZARAAH!!!" aikuwa cikin zafin nama ya saukko da sauri ya nufi hanyar corridor ya nufi toilet don ganin ko tana ciki yaga wayam da sauri ya juyo lokacin idanun shi suka sauka kan milk d'in jallabiyar shi da itama ke d'auke da stains na jini ta cikin mirror d'in jikin press d'in shi k'ara rud'ewa yay ya nufi hanyar fita yazo bakin kopar ba tare da ya bud'e ba sosae ya d'an lek'a kanshi ya tambayi Officer ko lafiya anan ya fad'i mashi dama Madam ce da suka zo tare gata can bakin gate ta matsa sai ya bud'e mata ta tafi kuma ma bata lafiya don sai kerma take da sauri Haisam d'in yace mashi yaje gashi nan zuwa ya koma cikin Corridor d'in yana wani irin sauri da shi kanshi bazai iya tuna ga ranar da yayi irinshi ba wata jallabiyar ya zuro wuya a jirkice ya fito tun kafin ya k'arasa ya hangota raku6e a jikin pillar yana k'arasawa ya tsaya akanta ya kira sunanta shiru bata amsa ba bata kuma kalleshi ba sai ajiyar zuciya take yi da gani kukan zuci take Slowly ya duk'a a gabanta Officer na ganin haka ya juya ya koma cikin d'akin shi, k'ara kiran sunanta yay still bata amsa ba ya kai hannu ya kamo hannunta aikuwa ta fusge zafin da yaji a hannun ne ya k'ara tada mashi hankali cikin trembling voice yace "am so sorry Zaraah mu koma ciki sai muyi magana" banza tay mashi ganin bata da niyyar tashi yasa shi mik'ewa ya kai duka hannuwanshi zai d'auketa aikuwa ta fashe mashi da kuka mai sauti tana fad'in ita ya kyaleta yasa a bud'e mata gate ta tafi, fasa d'aukar tata yay ya mik'e tsaye don bai son Officer ya ji har ya zargi wani abu can ya sake duk'awa gabanta a hankali yace "kin ga yanzu dare yayi sosae kiyi hakuri mu koma ciki zan kira Uncle d'in ki sai in sanar mashi dare yayi mana sosae matar Abbas ta wuce dake gidanta in mun shiga ciki zamu yi magana kiyi hak'uri kinga ma baki lafiya sai kisha magani" da ga voice d'in shi zaka fahimce shima a rud'e yake har wani d'an nishi yake don shima zazzabi ne a jikinshi, duk yadda yay da ita su koma ciki tak'i sai ma ta kife kanta tana ta kuka har cikin ran shi yake jin kukan don yasan shine silar shigarta halin da take ciki yama rasa tunanin da zai yi cikin ranshi yanata ayyana miya faru dashi ne ya akai ya aikata wannan d'anyen aikin ina hankalin shi ya tafi ne, yasan tunda ta kafe to bazata koma ban hakan yasa shi ce mata to bari ya maida ita gidan cikin fushi tace ita bata so a bud'e mata gate kawae bai yi mamakin yadda tay mashi Maganar ba don yasan girman shi ya gama fad'uwa a wurin ta rarrashin ta ya shiga yi yana nuna mata illar fitar ta a wannan lokacin in dai bata bari ya kaita ba to saidae su kwana anan ala bashshi sai ya kira Amadun ya fad'a mashi abunda yace zai fad'i mashin, shiru tay saida aka d'an d'auki lokaci sannan tace suje ya kaita ya mik'e da sauri kai kace ba Haisam ba da alama bai ma san ina yake wurga k'afarshi ba dama Motar ba'a parking space take ba yana d'aukko makullin ya shiga ya tada bayan ya juyata ya iso gaban gate d'in ya bud'e ya fito ya koma wurinta yace ta taso suje ganin yadda take kokarin mik'ewa yasa shi kai hannu ya taimaka mata tana ta k'ok'arin kwacewa bai biye mata ba saida ta mik'e sannan ya saketa da k'yar taja k'afa ganin ta nufi kopar baya ya je ya bud'e mata saida dubara ta shiga ya rufe shima ya shige driver seat yay ma Officer horn sai gashi da sauri ya fito yaje ya zuge masu gate d'in Haisam yaja suka fice, bayan officer ya rufe gate d'in tsaye yay da alamun tunani yake saidai ya kasa hasashu komae k'arshe ya gyad'a kai ya koma cikin d'aki, tunda suka taho taci gaba da kukan da take k'asa k'asa tana sheshsheka shiru bai ce mata komai ba tunanin yadda zai maida ta gida acikin wannan halin yake can wata zuciyar ta raya mashi yakamata ma ya kaita Asibiti don da alama akwae matsala Saboda jinin da ya gani duk da first night dinsu da Fanan itama tay shedding blood d'in amman nata d'an kadan ne bai kai yawan na Fatuu ba da wannan tunanin ya yanke wucewa da ita Asibiti kawai, kanta na duk'e har suka iso jin an tsaya yasa ta d'ago lokaci guda ta gane Asibiti ne bayan ya kashe Motar ya bud'e ya fita saida ya rufe ta da Makulli sannan ya nufi ciki Fatun na mashi wani kallo ta cikin glass wa zai yi tunanin zai iya aikata mata haka ta raya a ranta, yana shiga reception sai ga wata Nurse zata wuce da sauri yay mata magana ta dakata baiwar Allah har saida ta saci kallon k'afafun shi don taga in ba kofato bayan yay mata ya aiki tace Alhamdulillah yace don Allah Doctor mace yake son gani tace mashi gaskiya ba mace duk maza ne shiru yay kawai yana tunanin bai kamata ace namiji ne zai duba ta ba ganin haka yasa tace mashi dole sai mace yace eh yafi son haka har zai juya tace "Yalla6ai akwae wata Mama tsohuwar nurse ce ba likita ba amman kusan ma kamar likitan ake d'aukarta don ta san abubuwa sosae in kana so tana nan sai ka ganta" da sauri ya kalle ta yace Ok tana ina tace suje ta juya hanyar da ta fito yana biye da ita har suka isa wata kwana a bakin wata k'opa ta tsaya ta juya tace mashi tana zuwa ya d'aga mata kai, lokacin data shiga mamar wadda dattijuwa ce tana kwance a saman gadon da ake duba mara lafiya ta d'age kai baki bud'e tana bacci ga gilashin fuskarta ya zame a gabanta nurse d'in ta tsaya ta kira sunanta har sau biyu bata farka ba hakan yasa ta d'an matsa ta kai hannu ta d'an bubbuga gefen kanta aikuwa sai gashi ta bud'e ido kaman an latsa mata remote ta k'ura ma nurse d'in ido ita kuma tana mata murmushi can ta yunk'ura ta tada kanta cikin fushi tace "Nurse Bilki ke wace irin muguwa ce ne?" D'an bud'a ido bilkin tay tace "Mama nice muguwa kuma" tsuke fuska tay tace "eh mana in ba mugunta da rashin tausayi ba duka fa ban dad'e dana samu na kwanta ba bayan gama kacaniyar Labour room shine kuma zaki zo ki katse man bacci?" Sanin halin ta na mita yasa bilkin cewa "to yi hakuri Mama dama bak'o kika yi ne shiyasa na tashe ki" d'an yamutsa baki tay tace bak'o kuma da tsakan daren nan waye shi bilkin ta fad'i mata yadda sukai da Haisam wata uwar harara ta zabga mata tace "to in banda iskanci baki ji likiciya yake son gani ba zaki tada ni ni likita ce?" d'an murmushi bilki tay tace "ai kema mama kaman likitan kike kuma don naga kaman yana cikin tashin hankali ne yasa nace bari in maki Magana k'ila wata matsalar ce yake son fad'i maki" cigaba da harararta tay kafin can ta yunk'ura ta saukko tana d'aure da zanin Atamfa saman farar doguwar rigar aikinta tambayarta tay yana ina tace yana nan bakin kopa ta nufi kopar tana mita bilkin na dariya a ranta tana ayyana dama ina ma'aikacin Asibiti yaga wata damar yin bacci mai yawa, Mama na bud'e kopar idonta suka sauka kan Haisam dake jingine da bangon dake opposite da Office d'in har saida tasa hannu ta gyara gilashin ta yadda zata gan shi da kyau ta bishi da kallo tun daga sama har k'asa ganin yana kallonta yasa tace shine mai neman ta yace eh yana kokarin matsowa gabanta tace tana d'an zuwa to yace Ok ta koma ciki suka had'a ido da bilki dake murmushi tace "Ke kin tabbatar wannan mutum ne kuwa ba Aljani ba nifa ban yarda da shi ba don kwanakin nan dama ina yan gane gane" Bilki mi zatayi ba dariya ba ganin yadda mama tayi zuru zuru da alama dae ta tsorata da Haisam d'in cikin dariya tace "Wllh mama nima dana gan shi har saida na kalli k'afafun shi dama banga lokacin da ya shigo ba sai dae naji anyi man Magana kawae ga abu na dare" turo baki Mama tay tace mata yanzu ya zasu yi bilkin tace ita tana ganin lafiya lou Mutum ne in ba haka ba mi zai sa yazo wurin su har yace yana son ganin likita Mama tace "Bilki raba kan ki da sharrin Mutanen 6oye" juyawa tay tace suje tare koma mi zai faru ya faru dasu duka bilkin ta bita tana fad'in kai Mama kefa dama kin tsufa ni kuma yanzu nike kuruciya ta a tare suka fita bawan Allah Haisam yana jingine da bango duk yayi zuru zuru bayan ta fito tace mashi tana ji miye matsalar yake son ganinta ba tare daya ji komae ba ya shiga yi mata bayani bayan ya d'an daidaita natsuwar shi tana ta jinjina kai ta d'an ta6e baki har ya gama saidae a yadda yay mata bayanin nuna mata yay matarshi ce, tambayar shi tay yanzu ina take yace tana Mota ta tambaye shi tana iya tafiya yace eh amman ba sosae ba ta kalli Bilki tace taje ta d'auki Wheelchair ta taho da ita su fara tsayawa Nurses room a turo ta tace to ta kalli Haisam tace suje, da taimakon Bilki Fatuu ta fito ta taimaka mata ta hau wheelchair d'in kafin ta tura ta tana biye da ita suka shiga saida ta tsaya aka tura sunanta ta computer sannan suka wuce wurin Mamar da zasu shiga tace ma Haisam ya jira ta nuna mashi waiting seats dake gefe alamar ya zauna yace ok, bayan an shiga da ita tare da Mamar aka taimaka mata ta hau gadon ta sanya hand gloves ta fara dubata tana yi tana yamutsa baki can ta fara mita tana fad'in "ni wllh irin wannan duk nafi ganin laifin iyayen ku su same ku suyi ta yi maku banke banken magungunan mata to su mazajen naku duwatsu ne da bazasu rikice har suyi maku aika aika ba, kamar ke yanzu ai baki wani bukatan magunguna iya lafiyayyen Abinci ma ya Wadatar kuma da gani ana ci sai abu ya faru kuzo kuyi ta ma Mutane jan ido" bilki dai na tsaye daga can gefe tana k'umshe dariya sosae ta duba ta bayan wani lokaci ta gama ta fara cire safar ta jefar a cikin dust bin kafin ta juyo ta kalli Fatuu tace "Allah ya taimaka baki buk'atar stitches kin samu rauni ne a farko wurin shiga da alamu ansa ma wurin k'arfi ne halan hana shi hakkin shi kika so yi ya nuna maki k'arfi haka?" sunnar da kai Fatuu tay idanunta suka ciko da k'walla da tasan halin da take ciki da batai mata wannan Maganar ba kallon bilki tay tace ta kamata su shiga toilet d'in cikin Office d'in ta taimaka mata da ruwan zafi ta zauna ta d'an samu relieve tace to ita kuma ta juya ta fita Haisam na ganin ta lek'o ya mik'e yaje gabanta tayi mashi bayanin komae tace yanzu dole ta dage da zauna ruwan zafi amman ba mai zafi ba sosae da d'an gishiri sai magungunan da za'a bata ta rink'a sha in tana haka zata samu sauki yace to d'an zare mashi ido tay tace "Amman fa ka k'yaleta ta huta sosae har ta warke garas kafin ka k'ara tunanin yin wani abu" jinjina mata kai kawae yay tace ya jira zata tura magani yaje Pharmacy yace to tana niyyar juyawa ya dakatar da ita ta hanyar rok'on ta ko ya samo mata wani abu a bata taci sai in ya amso magungunan a bata ta fara sha daga nan d'an kya6e baki Mama tayi tace halan fushi take dashi yasan in ya bata bazata ci ba d'an guntun murmushi kawae yay tace yaje ya kawo ya amsa da Ok ya wuce, bada jimawa ba ya dawo Cake da lemu ya samo a shop d'in cikin Asibitin su kadae ne yake tunanin zata d'an ci don ba Abinci a wurin bayan ya kwankwasa Nurse Bilki ce ta fito ta amsa kafin ya juya ya nufi Pharmacy d'in aka tura kud'in yaje ya biya kafin ya amsa magungunan suma ya kai masu ya koma ya zauna, saida Mama ta matsa mata ta cinye duka har lemun tana yamutsa fuska alamar bata so bayan ta gama suka rakota waje ba laifi tafiyarta ta d'an k'ara warwarewa yana ganin ta fito ya mik'e ta kauda kai gefe Mama tace to gatanan sai a kiyaye ya amsa da Ok yay mata godiya kafin ya rok'eta ta d'an bashi Account details nata farko kaman bazata bashi ba tace ai ba sai ya bata wani abu ba ai aikinta ne yace ya sani just kyauta ce sannan ta fad'i mashi nan take yay mata transfer d'in 70k yace taba Nurse Bilki 20k suka hau godiya har tana zolayar shi tana in Amarya ta haihu a sanar masu ya d'an dai yi murmushin yak'e kawae suka tafi yana ruk'e da ledan magungunan da bilki ta bashi, a hankali take tafiyar yana biye da ita a haka har suka fito shi ya bud'e mata back door d'in kaman bazata shiga ba yanata kallon ta ita kuma ta juyar da fuskarta gefe saida ta ga dama sannan ta shiga ya rufe kopar koda ya zagaya maimakon ya shiga driver seat d'in sai shima ya bud'e bayan ya shiga tana ganin ya shigo ta juya mashi k'eya shiru yay yana kallon bayan kan nata Magana yake so suyi saidae ya rasa ta inama zai fara can ya nisa yace "Zaraah" shiru bata amsa ba balle ta kalle shi cigaba yay "I know i ave wronged u dat sorry isn't enough to make u forgive me but I will still use it to apologize for what I have done am very sorry Zaraah" banza ta mashi yaci gaba "nasan na cutar dake saidae billahi bada nufi hakan ya faru ba ni kaina I don't know what came over me da har hakan ya faru amman koma miye laifi na ne cos am the one who took u there" nan ma dae tsit tay sai yar sheshsheka da take yi a hankali shiru yay yana ta kallonta a cikin ranshi kuwa bai mamakin duk abunda tay mashi ba don yasan dole ma girman shi ya fad'i a idonta sigh yay yace "in sha Allah zan gyara laifin da na aikata gobe zamu yi Magana da ke but before then pls don't disclose what happened to anyone" cikin fushi ta juyo fuskarta jage jage da hawaye tace "ai in ban fad'a ma kowa ba Allah shi ya sani miyasa zaka man haka ka cutar dani bayan laifin da kasa muka aikata hakan bai isa ba har sai ka cutar da rayuwata....." Fashewa tay da matsanancin kuka still yay yana kallon ta komae ya gama kwance mashi ya rasa ta ina zai taro matsalan ta gyaru gashi shi kanshi ba lafiya gareshi ba don zazza6i tuni ya gama rufe shi k'arfin hali kawae yake k'arshe dai hak'urin yaci gaba da bata yana zasu yi Magana gobe da k'yar ya samu ta d'an tsagaita da kukan ya bud'e Motar ya fita bayan ya rufe ya bud'e driver seat ya zauna kafin ya rufe yaja suka tafi........... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2046* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ..........Tana d'aga labulan d'akin ta sauke idanunta akan gadon dake wayam ba kowa da d'an mamaki ta k'arasa shiga don ta tabbatar da abunda take gani, tabbas ba Fatuu kwance tsaye tay ta fara ayyana ina taje ne acikin ranta can tace ko tana band'aki ne, sai kuma ta raya anya dae tana can tun d'azu fa tana kitchen kuma bata ga fitowar ta ba in ba dai tun kafin ta fara aikin girkin ta shiga ba to amman mi zai sa ta dad'e har haka ta jefa ma kanta tambaya, can dae ta juya ta fita daga d'akin ta nufi hanyar toilet don ta tabbatar tun ma kafin ta k'arasa ta hango kopar shi a bud'e alamar ba mutum d'an tsayawa tay sai kuma ta juya ta nufi hanyar fita daga gida, a bakin k'opa ta tsaya ta fara k'wala ma Amadu dake cikin shago kira ya bud'e ya lek'o ganin itace yasa shi k'arasa fitowa ya nufo inda take ya tsaya yana kallonta yace gashi tambayar shi tay ina Fatuu da d'an mamaki yace "bata ciki ne?" Gwaggon ta d'aga kai tace mashi bata nan ta duba har toilet d'an jimm yay kafin yace "gaskiya ni banga ta fito ba tunda na bud'e shagon" shiru gwaggon tay tana tunanin to ina ta shiga Amadu ya katseta da tambayar ta kira wayar ta ta girgiza mashi kai alamar a'a yace to bari ya kirata ya juya ya koma shagon, bayan ya fito ruk'e da wayar ya dawo gaban gwaggon ya fara k'ok'arin kiran Fatuu lokacin da kiran ya shiga tana ta sharar bacci har kiran ya yanke bata ji ba sai da ya k'ara kira ne can a cikin bacci ringing d'in ya kai mata ta fara motsi a hankali ta fara bud'e idanunta jin wayan nata k'ara yasa ta yunk'ura ta tashi zaune tana kai hannu zata d'auka kiran ya katse, bayan ta d'auka ta duba mai kiran nata har saida gabanta ya fad'i ganin sunan Kawu Amadu tana haka sai gashi ya sake kira tay shiru kaman bazata d'aga ba can dai tay picking ta kara ta a kunne daga can bangaren Amadun ya kira sunanta ta amsa a hankali ya tambaye ta tana ina ne tace mashi ta tafi Makaranta ya maimata abunda tace jin haka yasa ya mik'a ma gwaggo ta amsa ta kara a kunne ta kira sunanta itama ta amsa mata had'i da gaishe da ita tace "naji kin ce kina Makaranta lafiya kika tafi baki fad'a ma kowa ba?" Had'iyar abu tay ta fara tunanin k'aryar da zata mata cikin yar rawar murya tace "d..dama na manta ban fad'a maki ba da yake jiya baki nan na dawo akwae wani malamin mu to ba'a cika gane abunda yake koyawa ba ana ta mashi complaining shine ya ware mana lokaci a cikin wannan weekend d'in da safe yace zai yi mana lesson tunda lokacin da yake dashi cikin ranakun aiki bai isar shi ya rink'a yin bayani sosae yadda za'a gane" gwaggo dake sauraronta tace "to yanzu sai yaushe zaki dawo?" shiru Fatuu ta d'anyi kafin tace "sai Allah ya kaimu Juma'a" "Har sai Juma'a kuma ba da safe zaku rink'a yin lesson d'in ba in aka gama ai sai ki taho gida ko?" Fatuu tace "eh amman da yamma ma zamu yi group Assignment" sauke yar ajiyar zuciya gwaggon tay tace "to amman shi yayan ki fa daya maido ki yace zai rink'a kaiki baki tunanin zaiga kaman kin k'i jin Maganar shi ko baki gode ba" d'an runtse ido Fatuu tay ta bud'e yanayin fuskar ta kaman zata yi kuka tace "Na fad'i mashi ai" gwaggon tace Shikenan Allah ya bada sa'a Fatuu na gumshe kuka ta amsa da Amin da sauri ta kife wayar akan katifa ta jingina da bango ta kifa fuskarta a tsakankanin cinyoyin ta wannan wace irin cin Amana ce sukai ma gwaggo gaba d'aya ta yarda dasu ji yanzu daga fad'i mata hakan har ta amince, da kanta ta rarrashi kanta bada jimawa ba aka kira sallar Azahar ta sauka daga kan gadon don tayi salla, wasa wasa har dare bata ga kiran Haisam ba balle tasa ran zai zo suyi Maganar da yace bayan taci indomie da ta dafa taje tay wanka ta zauna ruwa data dawo ta sha magungunanta ta kwanta saidae sam ta kasa yin bacci abubuwa ne da yawa ke mata yawo a rai ba kamar rashin zuwan Haisam duk da ba wai tana son zuwan nashi bane kawae sai take ganin kaman bai damu da halin da ya jefatan bane daga baya ta dasa tunanin yadda rayuwarta zata kasance nan gaba ba kamar in tayi aure, "anya ma ni zan yi auren kuwa?" ta ayyana a ranta sai dae itama tasan fad'a kawae take ba yadda za'ai ta rayu ba tare da ta yi aure ba tasan ai baza'a ma ta6a k'yaleta ba, tana ta tunane tunane sai can dare bacci ya d'auketa, Washe gari Lahadi haka taci gaba da jinyar kanta ranar ma har dare yayi Haisam d'in bai kira ba a lokacin Fatuu har ta gama yankewa ranta dama dad'in baki ne kawae yay mata ba wani abu ba, bayan sallar isha sai ga Fauzy ta dawo da mamaki ta shigo d'akin ganin kopar a bud'e idanunta suka sauka akan Fatuu dake kwance saman gado hannunta ruk'e da waya tana ganinta ta fara mata murmushi ta nufi gadon da take ta zauna a gefe surprisingly tace "wai da gaske ke ce?" Tana murmushi tace "a'a Aljana ce" gyara zama Fauzy tay sosae tace "amman ya akai na ganki anan bacin kin koma gida?" d'an yamutsa fuska Fatuu tay tace "to na dawo" waro ido Fauzy tay tace "Don Allah da gaske?" Kai ta d'aga mata alamar eh Fauzy tace "to ina Ya Haisam d'in yake da kika dawo ko har ya tafi" d'an shiru tay idonta a kanta ta rasa wace amsa ma zata bata can tace "Ya tafi Abuja" d'an tura baki Fauzy tay tace "to har kin siye mana zuciyar tashi ne da kika bari ya tafi" d'an murmushi kawae Fatuu tay a cikin zuciyar ta ta raya in ni ban siye zuciyar shi ba shi ai ya siye man Mutunci bin ta da ido Fauzy tay ta kalleta suka had'a ido duk sai ta tsargu can taji Fauzyn tace "ya naga kamar wani abu na damun ki har face d'in ki ta nuna?" damm k'irjinta ya buga tasa hannu tana d'an Sosa gefen kanta tace ba abunda ke damunta kawae bacci take ji kuma ta tsaya latse latsen waya tay Maganar tana niyyar komawa ta kwanta bayan ta kwanta Fauzy dake kallonta tace "amman yau kika dawo ne?" Kai ta d'aga mata alamar eh ta sake cewa taci Abinci ne Fatun tace eh taci d'azun gyad'a kai tay ta mik'e tana fad'in ga wani Abincin ta taho dashi ta tashi su ci ta tambaye ta minene tace tuwon shinkafa ne miyar d'anyen kubewa Fatuu tace to ta zuba masu, suna cikin ci Fauzy tace bata ba ta labarin dinner d'in data fad'i mata a waya zasu da Ya Haisam, d'an yamutsa fuska tay kafin ta d'an bata labarin sama sama bayan sun gama suka sha lemun data had'o masu dashi Fatuu na son tasha magungunan ta amman ta rasa yadda zatayi don tasan da Fauzy ta gani sai ta tambaye ta dalilin shan su tunda tasan magungunan na miye gashi ita ba wani rauni ke a jikinta da zata gani ba shiyasa ma ta bar su a cikin bag d'inta bata fiddo su waje ba gudun hakan k'arshe kawae sai tay kwanciyar ta Fauzy na ce mata bazata duba book d'inta ba tace mata bacci take ji. Washe gari Monday suka cigaba da zuwa class kaman ko yaushe ba laifi tafiyarta ta d'an daidaita in dae ba kallon k'urulla kai mata ba bazaka gane ba daidai take tafiya ba don sosae ta d'aure take tafiya yadda ba za'a zargi wani abu ba musamman Fauzy, wasa wasa sai gashi har Friday tayi ba Haisam ba dalilin shi balle kiran wayar shi bayan sallan juma'a suka fito tare don tafiya weekend saida aka fara sauke Fauzy Fatuu ta rok'i mai Napep zata d'an shiga yace to suka shiga gidan tare ta gaisa da Aunty Mareeya itama saida ta tambayeta Haisam tace mata ya koma kawae daga baya sukai sallama Fauzy ta rakota har bakin Napep suka k'ara yin bankwana ta tafi, a k'opar gida suka tsaya bayan ta fito ta biya mai Napep d'in ta nufi ciki don shagon Kawu Amadu a rufe yake, lokacin da ta shiga d'akin gwaggo ta nufa ta d'aga labule da yar sallama ta hango gwaggon kwance tana bacci d'an murmushi tay har zata juya ta fita taji ta kira sunanta ta juya ta kalleta suka had'a ido ta nufeta ta zauna a bakin gadon tana ta mata murmushi itama gwaggon tashi tay zaune ta jingina bayanta da kan gadon tace mata an dawo Fatun tace eh ta gaishe da ita ta amsa kafin ta tambaye ta Fauzy tace yanzu suka sauke ta a gidan Aunty Mareeya ta d'aga kai shiru ta biyo baya idon gwaggo a kanta ita kuma ta sunkuyar da nata still murmushi take can taji gwaggon tace taje ta zuba Abinci tace to ta mik'e ta nufi hanyar fita tana ruk'e da jakar goyon ta jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa A-shape ta yafa gyale dama ko ba don abunda ya faru da ita ba duk in ta san zata zo gida su had'u da gwaggo bata sa matsattsun kaya don tasan da gwaggon ta gani sai tayi fad'a kuma dama tunda abun nan ya faru da ita bata sa kayan da suka matse ta tafi zumbula doguwar rigar material, d'akinta ta nufa bayan ta shiga ta aje jakar a gefe ta nufi bakin gadonta ta zauna duk yadda taso kar ta damu da rashin kiranta da Haisam bai yi ba ta kasa abun ya matuk'ar d'aure mata kai tunaninta dama kenan k'arya yake mata, ita dama tasan ba wani abun da zai iya yi ya gyara laifin shi kawae dae ya cuceta, jiki a sanyaye ta mik'e tana kokarin maida k'wallan da suka tarun mata bayan ta fita kitchen ta nufa ta zubo Abinci, da daddare bayan tayi sallar isha ta watso ruwa ta zura doguwar riga yar kanti mai gajeran hannu ta saka hula akanta ta nufi d'akin gwaggo a zaune ta isketa akan kujera tana kokarin kunna Radio tana ganinta ta sakar mata murmushi itama Fatuu shi take mata ta zauna daga gefenta tace "wai gwaggo miyasa baki son zama a Parlor ne kullum indae kina gida kin fi son ki zauna a d'aki?" yar dariya tay tace "nafi sabawa da d'akin ne ni mantawa ma nike da wani Parlor" d'an tura baki tay tace "ga kayan kallo can maimakon kije ki kallo sai ki zauna kina ta faman jin radio sai kace wata tsohuwa" dariya sosae gwaggo ke yi tace to ai tsohuwar ce ko Fatun tace "a'a da sauran ki Allah" murmushi kawae tay sai kuma tana kallon Fatun tace "Oh ya mai jiki kuma" kallon rashin fahimta Fatuu ta bi ta da shi ganin haka yasa gwaggon cewa "Senator Alee na Hajiya nike nufi, ni kwata kwata ban sani ba sai ranar Laraba nan data wuce na shiga gaida Hajiyar anan Saude ke fad'a man wai ashe basu K'asar harda shi Haisam suna Germany nace ai ban sani ba ke kuma baki fad'a man ba ko ta waya" zuru Fatuu tay zuciyarta ta ayyana ashe bai K'asar muryar gwaggo ta katseta da fad'in "Bawan Allah, Allah ya bashi lafiya ya tashi kafadun shi" a hankali Fatuu dake ta kallon ta tace Amin suka d'an yi shiru can tace ma gwaggon miya ke damun shi ne, da d'an alamun mamaki tace ba dae bata san bai lafiyan ba Haisam bai fad'i mata ba a dabarbarce Fatun tace "....a'a na san bai lafiyan amman ban san abunda yake damun shi bane" gyad'a kai gwaggo tay da alamun damuwa tace "yanke jiki yay ya fad'i to an kaishi Asibiti nan Abujar daga baya likitocin suka bada shawarar ayi saurin fita dashi don ya kusa samun stroke Saude tace a ranar Juma'ar da ta wuce da Asuba aka kira Hajiyar ake sanar mata tun kafin gari ya waye suka tafi Kano ita da Haisam d'in daga can suka hau jirgin Abuja" gyad'a kai Fatuu tay tace Allah ya bashi lpy mai dorewa gwaggo ta amsa da Amin shiru tay da zuwa tayi taja gwaggon su je suyi kallo amman jin wannan Maganar yasa ta fasa ta mik'e tace mata bari taje ta kwanta taji bacci take ji ta d'aga mata kai tace Allah ya tashe su lpy, bayan ta koma d'aki zaune tay a gefen gado tama rasa tunanin da zatayi kenan wannan dalilin ya hana shi zuwa suyi Maganar kaman yadda yace can ta ayyana to amman ai ko a waya dai ya kirata tunda yanzu kwana takwas kenan da faruwar abun k'arshe dai ta yanke kawae bashi da abunda zai fad'a mata ne shiyasa bai kiratan ba a hankali ta kai kwance ta lumshe ido. Washe gari Asabar tana gama yin Breakfast ta gau gyara gidan tana cikin gyara d'akinta wayarta ta fara ringing ta aje bedsheet d'in da take kakka6ewa ta d'aukko wayar daga kan dressing mirror tabi kiran da kallo ganin bak'uwar lamba kuma da gani bata Nigeria bace bakin gadon ta nufa ta zauna ji take kaman kar ta d'aga kiran don tana tunanin ko Haisam ne gab da kiran zai katse tay picking ta kara a kunne tun kafin tay magana taji ance "Hello Kanwata kuma K'awata ya kike?" Zaro ido Fatuu tay ta washe baki jin muryar Haulat tace "Na'am Haulat ashe kece naga ba number d'in ki bace wannan" tace mata eh ta mijinta ce tana ta washe baki tace "to ya kike ya Nijar d'in?" itama Haulat bakin ta a washe yake tace mata nijar lafiya lou Fatun tace "kwana biyu sai inta trying layin ki bai shiga gashi tunda ki kai nauyi kin daina chat saboda ragwonci" tana jiyo dariyar Haulat d'in kafin tace "ashe ma ragwonci ne ba zan ce maki komai ba yanzu sai kema kin samu na Ya Haisam zan rama don nasan ke k'ilan ma ko wayar bazaki iya ta6awa ba" d'an yamutsa fuska Fatuu tay bata ce mata komae ba Haulat d'in ta tambaye ta Haisam tace mata yana nan bai dad'e da zuwa ba amman ya koma daga baya tace mata dama ta kira ne ta sanar da ita tayi D'iya Fatuu ta k'ara zaro ido ta rufe bakinta da hannu guda kafin tace "Don Allah Haulat da gaske kike ko wasa" tana jiyo dariyar ta tace Wllh ba wasa take ba ta haihu ran Alhamis da tsakar dare jiya aka sallamota yanzu haka ga babyn nan a hannunta da tsananin mamaki Fatuu tace "ikon Allah abun ba wuya ni wllh banyi zaton kin kusa haihuwa ba" Haulat na dariya tace "ashe abun ba wuya ki bari in lokacin da kema zaki haihun yayi zan tuna maki sai ki tantance" Fatuu na dariya tace ai ita haihuwar ne kawai bata yi ba amman tasan komai su da ke shiga Labour room kawae dae taga saurin abun ne daga lokacin da sukai wayar k'arshe, fira suka cigaba da yi har Fatuu na rok'onta ta turo mata picture d'in baby tace in suka gama zata sa ya turo mata ta tambaye ta zata dawo gida wanka ne tace mata eh amman sai an yi suna Fatun tace aikuwa dole su zo suna amman sai Haulat d'in ta hau rok'onta kan su barshi ba sai sun zo ba ai da anyi sunan zata dawo daga baya Fatun tace Shikenan tunda haka take so sukai sallama tace ta gaida mata gwaggo da Kawu Amadu, suna gama wayar cike da zumud'i taje d'akin gwaggo tana ta washe baki ta sanar mata zancen Haihuwar Haulat itama gwaggo tayi murna sosae tayi masu Addu'oi, bayan ta fito daga d'akin gwaggo hanyar waje ta nufa dama d'an gyale ne d'aure a kanta ta ciro shi ta yafa shagon Amadu taje shima ta sanar mashi yay murna sosae yayi mata Allah ya raya tayi D'iya sai faman washe baki take, saida ta amshi sweets da chocolate Amadun na fad'in komi take so ba zai hanata ba kar shima in tazo da kayan dad'i ta hanashi ta nufi gida tana dariya, da daddare bayan sallar Magrib ita da gwaggo suka tafi yin barka gidan su Haulat d'in, Ranar Monday da safe ta gama shirin ta tsab na tafiya Makaranta bayan tayi breakfast data fito d'akin gwaggo ta shiga tayi mata sallama tace mata sai yaushe tace Friday tasan zuwa lokacin k'ilan Haulat ta dawo tana murmushi tace mata to Allah ya kaimu ta amsa da Amin ta tafi, bayan taje Makarantar saida akai break take sanar ma Fauzy zancen Haihuwar Haulat ta hau murna tana fad'in zuwa suna Nijar ya kama su kenan Fatuu na dariya tace to murnar ta koma ciki da anyi suna zata dawo saidae su isketa gida tsuke fuska Fauzy tay tace ita gaskiya ba haka taso ba ta so zuwa Nijar don bata ta6a zuwa ba Fatuu nata mata dariya, a ranar da daddare suna cikin fira Fauzy ta kalli Fatuu tace "wai ni Zarah ina Ya Haisam ne kwana biyu ban ji kinyi Maganar shi ba?" bin ta da ido Fatuu dake zaune saman gadon tay tana tunanin abunda zata fad'i mata can ta sauke ajiyar zuciya ta fad'i mata halin rashin lafiyar da mahaifin shi ke ciki yanayin fuskar Fauzy ne ya canza cike da jajantawa ta yi mashi Addu'ar samun lafiya, Ranar Laraba da yamma Fatuu na zaune tana yin Assignment Fauzy kuma ta fita wayarta dake ajiye gefe tay k'ara alamar shigowar sak'o kallon wayar tay sai kuma ta aje biron hannunta ta d'aukko wayar ta shiga cikin messages d'in lokacin data bud'e sakon da ya shigon wani irin bugu k'irjinta yay da tsananin mamaki take kallon alert d'in 500k daga wurin Haisam lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya zuwa 6acin rai a ranta ta fara raya lalle ma Ya Haisam wato zai iya turo mata kud'i amman ba zai iya kiranta ba ita ga uwar son kud'i ko a tunanin shi zai siyeta da kud'i ne, a yadda take ji da tasan yadda zata maida mashi dasu da kuwa ta maida ranta ne ya bata ko ta kira Abbas ta tura mashi tace ya tura ma Haisam d'in sai kuma tay tunanin zai zargi wani abu tunda ai ba yau ya fara turo mata kud'i ba kuma har ta Account d'in Abbas d'in yana turowa cikin fushi ta fita daga cikin messages d'in ta wurga wayar gefe taci gaba da abunda take tana yi tana jan tsoki koda Fauzy ta shigo bata fad'i mata zancen kud'in ba don ta sa aranta bazata ta6a mashi kud'i ba, da daddare wuraren k'arfe goma saura sai gashi ya kira hakan kuma ba k'aramin tunzura ta yay ba wato ya turo kud'i shine ya samu k'warin gwuiwar kiranta k'in d'aga kiran tay har ya yanke wani ya sake shigowa k'arshe ma sai ta saka wayar a silent kawae, Ranar Friday da safe suna yin breakfast jikinsu sanye da Uniform ba tare da sun saka Hijab ba Fatuu ta fara kokarin tashi tana fad'in ta k'oshi Fauzy tay sauri ta gama su tafi, tana mik'ewa wani irin jiri ya kwashe ta da sauri tasa tafin hannunta na dama ta dafe goshinta tana yin salati hakan ya ja hankalin Fauzy ta kalleta ganin halin da take ciki yasa ta mik'e da sauri ta kamata tana tambayar ta lafiya, a gefen gado suka zauna Fatun na maida numfashi da d'an sauri Fauzy dake kallonta tace "What's happening Zarah?" Sai lokacin ta cire tafin hannun tace mata ba komae kawae data mik'e ne taji jiri ya kwashe ta amman yanzu lafiya lau, d'aga kai Fauzy tay tace "Sannu Allah yasa ba Malaria ke son kama ki ba don kinsan yanzu haka take tai ta sa mutum jin jiri ga matsanancin ciwon kai" shiru kawae Fatuu tay tace mata ta k'arasa su tafi yau Friday yanzu sun makara tace to tama k'oshi bari su saka Hijab kawai su tafi, a saman gadonta ta d'aukko masu hijaban ta mik'a ma Fatuu ta ta itama ta sa ta nufi wurin kayan shafan su dake jere saman table ta d'aukko turare ta shiga fesawa bayan ta gama ta nufi Fatuu itama ta fesa mata koda k'amshin turaren ya d'aki hancinta da sauri ta kauda kanta Saboda wani irin tashin zuciya da taji, bayan Fauzy ta kauda komae da sukae amfani ta goya jakarta ta mik'a ma Fatun tata ta yunk'ura ta mik'e suka tafi, sosae k'amshin turaren da Fauzy ta fesa mata ke damunta ji take kamar zata yi amai a haka har suka k'arasa class d'in suna shiga Malamin su na Farko na shigowa, tunda ta zauna take yan juye juye tana yamutsa fuska sam ta kasa natsuwa wani irin tashin zuciya ne ke addabarta can malamin na cikin bayani taji wani irin yunkurin amai ya taho mata da sauri ta mik'e hannunta rufe da bakinta ta d'an bubbuga shoulder d'in Fauzy alamar ta bata hanya koda ta kalleta ganin yadda take yasa da sauri ta mik'e Fatun ta fita daga cikin seat d'in da gudu ta nufi hanyar fita gaba d'aya idanun yan class d'in ya koma kanta harda malamin nasu dakatawa yay ya bita da ido gaba d'aya Fauzy ta rud'e sai zare ido take can ta kalli malamin tace "Sir pls let me help her" kai ya jinjina mata da sauri ta nufi hanyar fita ta bi bayan Fatuu................ _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2047* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ..........A can k'arshen barandar Classes d'in su Fauzy ta hangota tsugunne bayan ta fito ta nufeta da sauri tana zuwa ta duk'a ta dafa Shoulder d'inta tana kallon yadda take faman maida numfashi gaba d'aya ta amayar da breakfast d'in da ta ci cike da damuwa Fauzy tace "Sannu Zarah abun har ya kai haka" shiru tay tana cigaba da yin nishi ta d'age kai sama Fauzy ta sake cewa "to ko cikin ki ne ya 6aci?" a hankali ta girgiza mata kai alamar a'a Fauzyn tace "to gaskiya ina tunanin Malaria d'in ce dai muje famfo ki wanke Fuskar ki sai mu wuce cikin Asibiti kiga Doctor" sauke ajiyar zuciya tay tana kokarin daidaita natsuwar ta a sanyaye tace "ba sai mun je ba Fauzy nasan Malaria d'in ce ma kawae in mun koma Hostel zan sha magani" cike da damuwa Fauzy tace "to amman ai bamu da maganin Malaria d'in iya paracetamol ne sai na ciwon ciki" tace "shikenan bari muga zuwa a tashi in ban samu sauk'i ba sai mu siya in mun fita" shiru Fauzy tay ganin Fatun na kokarin tashi yasa ta kai hannu da sauri ta taimaka mata suka nufi famfo ta wanke face d'inta sosae da bakinta ta sha ruwan kafin suka nufi Class, lokacin da suka shiga gaba d'aya aka maido idanu kan su Malamin su dake tsaye yay mata sannu ta amsa kafin ya tambayi abunda ke damunta Fauzy ta bashi amsa da Malaria ce ya jinjina kai suka nufi seat, tunda ta zauna ta kife fuskarta akan desk nan da nan bacci ya kwasheta har akayi break sannan Fauzy ta tada ta ta tambayeta mi take so ta siyo mata tay d'an shiru don ji take bata son komae can tace mata ta amso mata youghort kawae ta amsa da to ta tafi, bada jimawa ba sosae ta dawo lokacin har taci gaba da yin baccin Fauzy ta tashe ta ta bata bayan ta bud'e mata ta amsa a hankali ta fara kur6a Fauzy na mata sannu tana d'aga kai sai gashi har ta shanye kuma bata ji zuciyar na tashi ba, sosae Fauzy taji dad'in ganin ta d'an warware har tana dariya da suna magana koda malamin su ya shigo bata koma ta kife kan ba ta tsaya ta saurari abunda yake koya masu, cikin sa'a har aka tashi bata sake yin aman ba suka nufi Hostel suna zuwa suka fara shirin tafiya Weekend Fatun tace ma Fauzyn tazo suje gidan su tayi weekend d'in acan in Haulat ta dawo sai suje tace to bari ta tambayi Aunty Mareeya, koda ta kirata ce mata tay Fatun ce bata lafiya zata kaita gida daganan za tay weekend d'in a can Aunty Mareeyar tace Subhanallahi miya sameta tace mata ba ciwo bane Sosae Malaria ce harda amai ta sata tayi mata Addu'ar samun sauk'i tace taje dama itama gobe Daura zata je sosae Fauzy taji dad'i tayi mata godiya da Allah ya kiyaye hanya Fatuu ma nata murmushin jin dad'i, gaba d'aya riga da skirt na lace suka sa sukai d'an makeup kowacce ta rataya jakar goyonta bayan sun yafa gyalensu sun yi kyau sosae abun ka da farare a tare suka fita suka rufe d'akin kafin suka tafi Lokacin k'arfe ukku na rana, lokacin da suka isa gidan gwaggon bata nan sai kawu Amadu shima bacci yake a d'akin shi, a d'akin Fatun suka sauka wannan ne zuwan Fauzy tayi Weekend a gidan na biyu don lokacin da Suke aji d'aya ta ta6a zuwa, bayan Fatuu ta aje jakar ta ta cire mayafi ta fito ta nufi kitchen don ta zubo masu Abinci waina da miya taga anyi ga kuma tuwon dare shima anyi murmushin jin dad'i Fatuu tay a ranta ta ayyana gwaggo ba dae kokari ba har tayi Abinci haka kafin ta tafi, wainar ta zuba masu ta nufi d'aki itama Fauzy tana ganin wainar ta washe baki don ta kwana biyu bata ci ta ba sosae suka ci Fatuu harda sud'e plate, saida akai sallar la'asar sun fito yin Alwala suka had'e da Kawu Amadu shima ya fito yin Alwalar yana ganin Fatun yace mata yaushe suka zo tace mashi yanata sharar bacci lokacin da suka zo gashi ya bar ma Mutane gida a bud'e salon a shigo ai masu sata ya wurga mata harara yace ta bar ganin fa ta girma har yanzu bata wuce bugu a wurin shi ba Fatun tay wata yar iskar dariya tace "ni yanzu Kawu Amadu ai mai buguna sai dae ko ruwan sama amman ko gwaggo ai na mata girma da bugo balle kai" jinjina kai yay ya d'an cije leben shi na k'asa yace "kawai dae kawae shikenan..." Fatuu ta katse shi tace ya fad'a mana kawai dai mi yana yar dariya yace "kawae dai bazan buge ki ba don kada Romeo yasa a kama ni don naga shima kaman ya shigo hannu" ya k'arasa yana tik'ar dariya ba kamar da ya ga yadda ta tamke Fuska Fauzy ma sai dariya take ganin yadda suke drama sai kace ba kawunta ba sai lokacin ta gaishe da shi yana murmushi ya amsa yay mata ya Makaranta tace lafiya lau daga haka ya wuce ya d'ibi ruwan ya nufi hanyar waje yana cigaba da yi ma Fatuu dariya, sai bayan sallar isha gwaggo ta dawo suka tare ta tana ganin Fauzy ta washe baki tana amsa mata sannu da zuwan da take mata tay mata ya Makaranta da Auntyn ta tace lafiya lau daga baya ta wuce d'akinta Fatuu tace ma Fauzy tazo su zuba Abinci suka nufi kitchen tare bayan ta zuba suka kai cikin parlor ta fito ta nufi d'akin gwaggo lokacin ta gama cire kayan aikin Fatuu tace mata ta taho Parlor suci Abinci tana yar dariya tace to a bari tayi wanka sai tazo ta mak'e mata kafad'a sai kace wata k'aramar yarinya gwaggon nata dariya saida ta tasata gaba suka tafi parlon a tare ta zuba masu tuwon alkamar da miyar karkashi mai kyau gwanin yauk'i taji kifi tarwad'a da suka fara ci sosae tuwon yay ma Fatuu dad'i don har wani lumshe idanu take wasa wasa sai gashi har suka k'oshi amman ita bata k'oshi ba saida ta k'ara gwaggo na fad'in bari cikinta ya fashe duk sukai dariya bayan sun gama suka fita da kayan gwaggo ma ta fita don yin wanka tana fitowa tay sallar isha ta haye gado su kuwa suna a parlon suna yin kallo saida dare yay sosae Fatuu ta kashe kayan kallon suka nufi d'aki don su kwanta, Washe gari a tare suka gyare gidan tsab bayan sun gama suka d'aura girkin rana koda gwaggo ta fito don ta kama masu ce mata sukae sun yafe taje ta huta tana dariya ta shi masu Albarka cike da farinciki suka amsa ta koma d'akin, bayan sun gama suka zuba mata Fauzy ta kai mata d'akin ta Kawu Amadu ma aka zuba mashi su kuma suka yanke su fara yin wanka sai su ci, bayan duk sun yi wankan lokacin gwaggo ta tafi aiki saida sukai sallar Azahar sannan suka zuba abincin suka shiga Parlor akan Carpet suka zauna, Fatuu na fara cin Abincin wanda shinkafa da wake da miya ne taji zuciyarta ta fara tashi hakan yasa ta d'an dakata ta gumtse baki kwata kwata Fauzy bata lura ba don tana ci tana kallon Tv gaba d'aya hankalin ta ya tafi saida ta d'an d'auki lokaci jin tashin zuciyar ya lafa yasa taci gaba da ci can wani irin yunkurin amai ya taso mata ta tashi da sauri ta nufi hanyar waje hakan ya maido hankalin Fauzy kanta ta bita da ido can ta jiyo ta tana ta Kwara amai da sauri ta mik'e ta fita ta nufi inda take a duk'e ta tsaya kanta tana ta mata sannu sai ga Kawu Amadu ya fito ya nufo inda suke ya tsaya da d'an alamun razana ya tambayi Fauzy miya faru take amai haka itama duk damuwa ce akan fuskarta tace mashi tana tunanin Malaria ce ke damunta dama jiya a School ma saida tayi yace to bata je taga likita ba Fauzyn tace eh da yake tunda tayi bata k'ara yi ba kuma duk alamu sun nuna malaria d'in ce don harda jiri tace tana ji da yake yanzu haka take ma Mutane, jinjina kai yay ya kalli Fatun dake k'ok'arin mik'ewa yay mata sannu ta d'aga mashi kai ta nufi famfo ta kunna tana wanke fuskarta da bakinta ta kora aman, Amadu dake kallonta yace inta gama ta duba d'akin gwaggo yasan ba'a rasa maganin Malaria d'in ta d'aga mashi kai yace mata Allah ya sawak'e ya juya, bayan ta gama kama hannunta Fauzy tay zasu koma Parlor Fatuu tace mata bari taje d'aki kwanciya take son yi tace to taje ta d'aukko maganin sai ta sha bari ta kawo mata ruwa ta saki hannunta ta nufi Parlor don d'aukko ruwan, a d'akinta ta iske ta bayan ta d'aukko ruwan tana ruk'e da Maganin data d'aukko ta bud'e mata ruwan ta bata ta sha maganin bayan ta gama ta mik'a mata robar ita kuma ta kwanta gefenta Fauzy ta zauna cike da damuwa tace mata to yanzu mi zata ci tunda ta amayar da wanda ta ci da sauri ta girgiza mata kai alamar bazata ci komae ba kafin ta lumshe ido nan da nan bacci ya d'auketa duk sai Fauzy taji Abincin ma ya fitar mata a rai ta mik'e ta koma Falon ta kwashe kayan ta kai Kitchen bayan ta fito ta nufi d'akin a gefen Fatun itama ta kwanta bada Jimawa ba itama bacci ya kwasheta, sai bayan da akai sallar la'asar Amadu ya shigo ya tashe su don suyi salla tun Fatuu na cikin yin sallan ta ji wani irin kwad'ayin shawarma ya kamata bayan sun sallame ta kalli Fauzy tace mata bakinta ba dad'i ta zo suje su siyo shawarma daga nan sai su biya shagon Aunty Zee su siyo ma Babyn Haulat kaya tunda tana hanya tace to, gaba d'aya jallabiya suka sa sukai rolling veil d'in kowacce ta rataya yar side bag lokacin da suka fito Amadu na ganinsu yace ma Fatuu yo har ta warke tana d'an murmushi tace mashi eh da sauki bata son ta kwanta ne ciwon ya rufeta zasu je su dawo ya tambayeta ina zasu tace bakinta ba dad'i shawarma zasu siyo yana murmushi yace "to ta Romeo a had'o dani" tura mashi baki tay taja hannun Fauzy dake murmushi suka tafi, shagon Zee suka fara zuwa sosae tay farincikin zuwan su ta kar6e su hannu bibbiyu suka gaida ta bayan sun zauna tay masu ya karatu daga baya suka fad'i mata abunda suke so cike da zolaya tace ma Fatuu ko tayi aure har zata Haifa masu baby bata sani ba ta d'an waro ido tana dariya tace "ai in nayi Aunty zee zaki sani don zan fad'a maki" jinjina kai tay tace "hakane nima ina wasa ne ai in sha Allahu tuwo na mai na za'ai kinga mune k'irjin biki kenan" yanayin fuskar Fatun ne ya sauya still da d'an guntun murmushi ta d'an sunkuyar da kai anan Zee ke mata zancen rashin lafiyar Senator tace su Jidderh ne suka fad'a mata Fatuu da ta d'ago tace mata eh yana Germany aka ce tace eh haka aka fad'i mata Addu'ar Allah ya bashi lpy tayi duk suka amsa da Amin ta mik'e tace su shiga sai su za6i kayan da suke so, bayan sun shigan kaya sosae suka siya tarkacen kayan jarirai harda su mayukan su sannan ta siya ma Haulat itama atampa mai kyau da harda lace ma taso ta siya mata to bata da isassun kud'i gashi tasa ma ranta bazata ta6a wanda Haisam ya turo ba, saida suka baro shagon sannan suka biya wani Cafe suka sayi shawarmar harda ice cream da youghort kafin suka wuce gida, da daddare bayan gwaggo ta dawo ta gama kintsawa suka kai mata kayan don ta gani sosae ta yaba kyawun su tana fad'in su Fatuu fa anyi D'iya dole a gwangwaje ta duk suka yi dariya har suka baro d'akin ba wanda yay zancen ciwon Fatuu don ta gyagije baka cewa ma itace tay amai d'azun, a ranar sai wurin goma ta wuce su Haulat suka iso ita da wasu yan uwansu lokacin data kira Fatuu ta sanar mata ta iso sha d'aya tayi cike da zumud'i Fatuu tace in Allah ya kaimu tana nan zuwa a shafa mata kan Baby ace Mamanta na mata sannu da zuwa Haulat na dariya ta amsa da to Maman Baby, Washe suna gama gyara gidan suka shirya don tafiya gidan su Haulat da yake gwaggo bazata je aiki ba ita zatayi Abincin rana ta basu sak'on suyi ma Haulat barka da zuwa sai ta shigo anjima suka amsa da to suka tafi, Lokacin da suka shiga gidan a tsakar guda suka iske innarsu da fara'a tay masu sannu da zuwa duk suka gaidata ta amsa tana fad'in "Fatima yan Makaranta karatu ya 6oye mana ke" d'an murmushi kawai Fatun tay tace Allah ya bada sa'a suka amsa da Amin kafin sukai mata barka d'an murmushi tay tace ai ita za'a ma barka su shiga Haulat d'in na cikin d'akinta suka amsa da to had'i da nufar d'akin, da sallama Fatuu ta shiga idonta suka sauka akan Haulat dake zaune saman gado tayi wanka tana sanye da riga da zani na atampa tana rungume da babyn itama an yi mata wanka an shiryata tana Feeding d'inta d'akin sai k'amshin jego yake suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi Fatuu ta nufe da sauri ta d'an yi mata side hug tana fad'in "Allah sarki Aminiyata nayi missing d'inki over wllh" dariya Haulat tay tana fad'in itama haka Fatuu ta zauna gefen gadon Haulat ta kalli Fauzy dake tsaye tana murmushi tace mata ga wuri ta zauna mana ta nufi wurin daga gefen Fatuu ta zauna, k'ura ma Babyn ido Fatuu tay yadda take ta shan nono abunta ta bud'e ido mamaki kawae Fatuu ke yi wai Haulat ce da D'iya Haulat dake ta kallon Fatuu ganin yadda take kallon babyn yasa tace "halan mamaki kike?" Da sauri ta kalli Haulat tace "wllh abun ba wuya da anyi aure sai kiga an haihu" Haulat dake dariya tace "Uhm dama ai yanzu haka zaki gani sai zaki haifa ma Ya Haisam tukunna zaki gane inda wuyar ko babu" d'an 6ata fuska tay had'i da ta6e baki Haulat d'in tace "ko an daina yayin shi ne anyi new catch?" Kafin tace wani abu Fauzy dake murmushi tace "yana nan daram a cikin zuciyar don ta shi ce ba sauran space da wani zai samu" Haulat dake kallonta tana yar dariya tace "Fauzy bamu gaisa bama ya karatu?" tace "Alhamdulillah barka mun samu karuwa Allah ya raya mana ya Albarka ci rayuwar ta" Haulat ta amsa da Amin da sauri Fatuu ta kai hannu ta d'an bugi gefen hannunta tace ba'a amsawa fa rashin kunya ne dariya kawae Haulat ke yi Fauzy tace "barta ta amsa abunta wllh ita tasan kwakwar da ta ci kafin ta same ta sai kuma ayi Addu'a tak'i amsawa, ko ni da zan yi aure in haihu duk wanda yay ma babyn Addu'a sai na amsa" Haulat dake dariya tace "ai zaki yin in sha Allah da lokaci yayi" d'an girgiza kai tay tace ta yafe ba sai tayi ba Haulat dae murmushi kawae take don tasan labarinta tun bayan da suka had'u da Fatuu ta bata labarin ta can Fatuu ta kai hannu tace ita dae gaskiya ta gaji da jira duk ta k'osa ta d'auketa Haulat ta mik'o mata ita ta kai hannu ta amshi babyn, Fatuu na murmushi take kallon yarinyar Tubarkallah kyakkyawa da ita gata fara hasken babanta ta d'aukko don yafi Haulat d'in haske amman fuskarta tana kama da Haulat sosae, kallon Haulat tay ta tambayi sunanta tace Umma Salma Fatuu ta d'an 6ata fuska tace maimakon a saka mata sunanta duk suka yi dariya Haulat ta kalli Fauzy tace "Fauzy ya fama da k'awar nan ta ki" tana dariya tace "ai ke kika sha fama ni yanzu da Sauk'i ta girma tayi hankali" juyawa Fatuu tay ta d'an harareta tace da bata da hankali kafin Fauzy ta bata amsa Haulat tace da Sauk'i dai hankalin nan gaba d'aya suka kwashe da dariya, hira suka cigaba da yi Haulat nata ba Fauzy labarin kuruciyar Fatuu tana ta tik'ar dariya suna haka har Azahar tayi suka tashi sukae salla bayan sun gama ne k'anwar Haulat ta kawo masu abinci a cikin yar babbar kula ta koma ta kawo plates da ruwa daga baya ta kawo ma Haulat nata ganin sun k'i fara ci tay masu magana tace ma Fauzy don Allah taci itace bak'uwa tana murmushi tace itama ai yanzu ta zama yar gida Haulat tace hakane, hannu ta kai ta bud'e warmer d'in dafa dukan shinkafa da taliya ne a ciki ta fara zubawa a cikin plate bayan ta gama ta rufe ta kalli Fatuu tace suci kowa ta d'auki spoon suka fara ci, d'an kad'an Fatuu taci jin zuciyarta ta fara tashi yasa ta aje spoon d'in Fauzy dake kallonta tace har ta k'oshi ta d'aga mata kai alamar eh, sai bayan da suka gama suka ba Haulat kayan da suka kawo mata sosae tay farin ciki ta hau yin godiya har da k'wala ma innar su kira ta shigo itama ta ga kayan tay godiya sosae tana fad'in lalle Mama Fatima ta fito da d'iyarta wannan kaya haka k'arshe tay Addu'ar Allah yasa suma su ga yaran su kowa ta sunnar da kai suna d'an murmushi Haulat na fad'in su Fatuu ashe yanzu an san kunya innarsu dake dariya tace ai daman can da kunyarta daga baya ta fita, har akai la'asar suna gidan bayan an gama salla gwaggo tazo itama harda kayan ta kawo masu sosae suka ji dad'i sai bayan Magrib sukai masu sallama Haulat na tambayar Fatun yanzu Makarantar zata koma tace eh amman zata dawo cikin satin ta k'ara ganin Baby tace to Allah ya bada sa'a suka amsa da Amin kafin su tafi aka basu naman suna mai uban yawa har gwaggo na fad'in kar su kwashe ma mai jego fa innar su tace a'a bakomae godiya sukai suka tafi. Washe gari da safe sukai shirin tafiya bayan sun gama yin breakfast suka je d'akin gwaggo sukai mata sallama tay ma Fauzy godiyar ziyara harda kud'i ta basu ta rako su har bakin zaure Kawu Amadu ma ya fito sukai sallama, Lokacin da suka isa Class kawae suka wuce don duk suna tare da jakunkunan su da akayi break suka fita, tun bayan da suka dawo zuciyar Fatuu ta fara tashi ga wani ciwon kai daya far mata lokaci guda daurewa kawai take bayan da malamin su ya shigo yana cikin yi masu bayani yau ma kamar rannan amai ya taso mata ta fita da gudu Fauzy ta d'auki excuse ta bi bayanta, saida ta gama ta kamata suka je bakin famfo ta wanke fuskarta da bakinta bayan ta gama Fauzy dake kallonta cike da damuwa tace gaskiya suje taga likita ciwon ya fara yin yawa Fatun ta d'aga mata kai don itama abun ya fara damunta class Fauzy ta koma ta fad'i ma malamin zata kaita taga likita ya bata izini ta d'aukar masu jakun kunan su, lokacin da suka isa Opd office d'in wani Doctor Madugu suka nufa don sun san shi son Fatuu yake ita kuma tak'i saurarar shi ba kamar da yake tasan halin shi ya cika son mata, saida suka jira patient d'in dake ciki ta fito sannan suka shiga yana ganin su ya sakar masu murmushi suka zauna a kan kujerun gaban table d'in shi yabi Fatuu da wani kallo yana sakin k'ayataccen murmushi ta d'an d'aure fuska Fauzy ce ta fara gaishe dashi sannan Fatun kaman an mata dole yace ba zai amsa ba in bazata saki face en ta ba k'ara tamke fuskar tay Fauzy ce tace mashi bata lafiya ne d'age gira yay ya tambayi abunda ke damunta har Fauzy zata bashi amsa yace ita yake son yaji daga bakinta d'an shiru fatun tay kafin ta fara mashi bayanin abunda ke damunta bayan ta gama yana d'an murmushi yace "kinga da mun yi aure sai in yi tunanin ko mun samu rabo ne" a d'an harzuk'e ta kalle shi bata dae ce komai ba ya fara rubutu a Computer d'in gabanshi can ya d'ago yace suje lab ya tura test ayi mata suka mik'e yabi bayanta da kallo har suka fice, suna zuwa lab d'in ba 6ata lokaci akai mata awon don sun san masu yi awon Malaria da typhoid ne aka mata bayan an tura ma likitan suka koma Opd d'in lokacin daya duba result d'in akwae malaria d'in amman ba typhoid ya fad'i masu kafin ya tura masu magunguna yace suje pharmacy bayan sun mik'e ya kira Fauzy ya bata kud'i yace su biya tay mashi godiya suka tafi, bayan sun amshi magungunan suka tafi ganin an kusa tashi Fauzy tace su wuce hostel kawae sai ta sha magungunan ta d'aga mata kai, bayan ta fara shan magungunan sosae ta samu sauk'i ta daina yin aman saidae bata da appetite ba komae take iya ci ba tafi shan youghort sai kuma lemu Fanta sai abu mai d'an tsami ko yaji a haka har Friday tayi suka tafi weekend, lokacin data koma gidan gwaggo bata nan bata dawo ba sai dare Fatun ta fito tsakar gida ta tareta tay mata sannu da zuwa tana niyyar zuwa kitchen don ta kawo mata Abinci tace mata ta barshi in tayi wanka zata ci ta ce to ta koma d'aki, washe gari bayan ta gama gyara gidan tay wanka ta shirya cikin doguwar rigar material tay rolling veil d'in ta shiga d'akin gwaggo lokacin tana kishingid'e saman gado amman ba bacci take ba a bakin gadon Fatuu ta zauna suna kallon juna da gwaggon da ta d'ago kanta tana kallon Fatun sosae tana murmushi ta gaishe da ita ta amsa tace mata zatace gidan su Haulat shiru gwaggon tayi tana ta kallonta saida Fatun ta maimaita mata sannan ta d'aga mata kai alamar to har ta mik'e ta nufi kopa tana fad'in sai ta dawo taji gwaggon ta kirata ta dakata ta juya da kai tay mata alamar ta zo ta koma ta tsaya daga d'an gabanta tace gata gwaggon ta yunk'ura ta tashi zaune sosae tana kallonta tace "wani abu na damun ki ne??" Cikin rashin fahimta Fatuu ta tambayeta wani abu tace tana nufin bata lafiya ne d'an murmushi Fatuu tay tace "Eh ciwo nayi har ma naje naga likita ya tura ni aka man test aka ga malaria ce ke damuna sosae ya rubuta man magunguna yanzu haka cikin shan su nike amman na samu sauk'i ai sosae" shiru gwaggo tay kafin tace mata basu saka net ne in zasu wanta tace suna sawa wllh kawae ciwon ya kamata ne kuma kafin su shiga net d'in saurayen na cizon su ko in sun fita class da daddare,jinjina kai gwaggon tay tace taje Allah ya sawak'e amman dole su k'ara kulawa tace to ta tafi, tunda tazo gidan wani ikon Allah lafiya lou take cin Abinci washe gari lahadi harda cin cin tayi masu ranar Monday da safe ta tafi. tun bayan da ta koma sai ciwon ya k'ara dawowa sosae ga yawan amai da take yi kusan kullum sai tayi amai a class wani lokaci in Malam na ciki ko kuma da break haka a Hostel ma in ya taso mata ta window take zura kanta tai tayi ga magani tana ta sha amman abun yak'i lafawa har fuskarta ta d'an rame tayi wani fayau da ita ranar laraba Fauzy tace mata kodae ta rakata gida amman sai tace tunda har anzo ranar ta bari Friday ta je tace to kodae ta saka mata drip ko taji k'arfin jikinta Fatun tace eh, da kanta ta fita taje ta siyo drip d'in bayan ta dawo ta saka mata shi lokacin daya k'are sosae ta samu k'arfin jikinta washe gari Alhamis taje class lpy lou har aka tashi, da yamma Fauzy taje siyo abu a shop bayan ta dawo ta nufo Hostel hannunta ruk'e da leda taji ana k'wala mata kira ta bayanta ta tsaya da ta juya sai taga wata yar class d'in su ce mai suna Zainab Muhammadu wadda ake ce ma suda (sarkin labari) tana ta sauri ta k'araso ta tsaya gaban Fauzy tace "dama tambayar ki nike son yi ya jikin Fatima Ard'o?" Wani kallo Fauzy tay mata tace bata ganta bane yau a class da sauri tace ta ganta taga ma duk ta rame Fauzy tace eh ai ciwo take ko daga haka ta fara kokarin wucewa Zainab d'in tace "wai kinsan abunda ake fad'a kuwa game da ciwon da take?" Cakk Fauzy ta tsaya tana kallonta tace mi ake fad'an yar in ina ta fara tace "j....ji nayi ana cewa wai kamar ciki ne da ita don ciwon da take yayi kama da laulayin ciki" rassss gaban Fauzy ya fad'i ta zaro ido waje gaba d'aya hannunta guda dafe da bakinta can ta cire cikin bacin rai tace "uban wa yace ciki gareta dama mara aure na samun ciki ne ko kuwa ana sha a ruwa ne ban sani ba???" Yarfa hannu Zainab d'in tay tace "nima fa bani nace ba abunda aketa fad'a ne nagaya maki don ku sani" daga haka ta wuce tay tafiyarta Fauzy tabi bayanta da kallo fuska a matuk'ar d'aure can ta wuce fuuu itama ta shige cikin hostel d'in idonta har rufewa yake Saboda tsabar bacin rai da bibbiyu ta rink'a hawa staircases d'in ta nufi d'akin su, lokacin data shiga Fatuu na kwance saman gado tana jiranta ta kawo mata Fanta gado ta nufa ta aje ledar hannunta gefe ta zauna fuska a d'aure ta kumbura baki ganin yanayinta yasa Fatuu yunk'urawa ta tashi zaune ta fara tambayarta lafiya bin ta da ido kawae tay kaman bazata tanka ba can cikin bacin rai tace "wllh magulmaci bai ji dad'i ba yaji haushin asara!!" A d'an rud'e Fatuu ta hau cewa ta fad'i mata gulamar mi akayi don Allah tace "wai shikenan mutum bazai yi ciwon Allah da Annabi ba sai an ja mashi sharri yanzun nan da zan shigo wai Zainab Muhammadu ta tsaida ni take fad'a man maganar da ake tayi game da ciwon ki.." a rud'e Fatuu tace mi ciwon nata yayi kaman bazata fad'i mata ba ganin yadda take mata Magiya yasa tace "ke wai ciwon da kike wai kaman ciki gare ki don ciwon yayi kama da laulayi Kiji jan sharri don Allah kawae don aja maki, ta ina zaki samu ciki tunda ba aure gare ki ba!!" Zaro ido waje Fatuu tay tasa hannu guda ta dafe kirjinta a kidi'me ta maimaita "ciki kuma!" Wani uban tsoki Fauzy taja jikin Fatuu har ya fara rawa kaman zata yi kuka tace "ni a ina zan samu ciki bacin kowa yasan ba aure gare ni ba!" Wani tsokin Fauzy taja tace "dalla rabu dasu magulmantan banza kawae an fad'a ne tunda kika ji Zainab Muhammadu ta fad'a don in dae tace abu to tabbas an yi ne ki k'yale su ta Allah ba tasu ba duk mai neman ki da sharri saidae ya koma mashi wllh" tana k'arasa Maganar ta fiddo mata Fanta d'in ta mik'a mata hannun Fatuu sai rawa yake ta amsa sai ta aje ta a gefenta kawae tsananin tsoro da fargaba ne suka kamata jin abunda zuciyarta ke ayyana mata na kada ace daga abunda Ya Haisam yayi mata ta samu ciki sosae kirjinta ke bugawa tunanin yaushe yakamata tayi period ta shiga yi a lissafin ta gobe Juma'a wata guda kenan da abun ya faru kuma tayi wanka da kwana d'aya hakan ta faru kenan yanzu kusan kwananta talatin da yin wanccan tasan kuma bayan kwana ishirin da d'aya wato sati ukku koda biyu take yin sabon period yanzu kenan lokacin ya wuce kuma ko alamun zata yi bata fara ji ba wani abu ta had'iya Kutt lokaci guda zufa ta fara tsattsafo mata ta koma tamkar an dasa ta a wurin ko kwakkwaran motsi ta kasa yi kallonta Fauzy tay ganin halin da take ciki da alama ta rude yasa tace mata wllh kada ta sake ta wani damu da zancen munafurcin su tunda ita dae ai tasan ba shi gare ta ba ko, zuru da ido kawae tay ma Fauzy k'arshe Fanta d'in ma kasa sha tay don ko kallonta ma bata k'ara yi ba Fauzy ta hau lallashin ta tana don Allah ta d'auka tasha kada ta tada hankalin ta a banza ita data san haka zata shiga damuwa da bata fad'a mata bama, a wannan daren yadda Fatuu taga rana haka ta ganshi sam bacci ya k'aurace ma idanunta sai juyi take tana zullumin kada ace da gaske ciki ne da ita don duk alamu sun nuna kaman laulayi take yin da gaske yin wannan tunanin har saida tasa hannu ta rufe bakinta, akan kunnanta aka kira sallar Asuba da k'yar ta iya yin salla tana gamawa ko Addu'a kasa yi tay ta koma gado ta kudundune lokacin da gari ya waye Fauzy ta d'an bubbuga ta tace ta tashi ta shirya kada su makara tana a kudundunen tace mata ta shirya ta tafi ita bazata je ba jin hakan yasa Fauzy zama a gefen gadon da take tace "kamar ya bazaki class ba kuma, ko don Maganar jiya to ke miye abun wai damuwa har haka ne tunda kin san kina da gaskiya ki tashi kawae ki shirya mu tafi in mutum ya isa ya tunkare mu yayi mana Maganar mu mana" duk yadda tayi da ita ta kafe kan bazata je class ba har ran Fauzyn ya 6aci tace "to ko dae Zarah da gaske cikin ne da ke???" shiru Fatun tay bata bud'e fuskarta ba kirjinta na wani irin bugu can Fauzy ta kai hannu ta yakice bargon data lullu6a Fatun ta kalleta da sauri suka zuba ma juna ido baiwar Allah duk ta firgice sai numfashi take da k'arfi wani irin kallon tuhuma Fauzy ta fara yi mata ganin haka yasa Fatun sunkuyar da kai cikin d'aurewar kai Fauzy tace "Zarah na tambaye ki baki ban amsa ba ki fad'a man gaskiya ko dae Maganar da ake gaskiya ce??" Girgiza kai ta fara yi da k'yar ta d'ago ta kalleta idanunta sun ciko da Kwalla tace "Fauzy ya zaki fad'i hakan kema bacin kin fi kowa sanin wacece ni kuma kin san ba aure ke gare ni ba" sauke Ajiyar zuciya tay tace "to don mi zaki k'i zuwa class??" Cikin rawar murya tace "h.... hakanan kawae, hankali na ya tashi sosae da jin Maganar ban so inje class haka su k'ara tabbatar da Maganar su gara in tafi gida kawae in fad'i ma gwaggo halin ciwon da nike ciki a nema man maganin hausa" da k'yar ta kai Maganar, shiru Fauzy tay tana nazarin Maganar can tace mata shikenan ta fahimta amman ta bari a tashi sai ta rakata gidan tace mata to kawai, saida ta matsa mata sosae sannan ta d'an sha ruwan tea da yar wainar kwae, tun bayan da Fauzy ta shirya ta tafi class take ta faman kai da kawowa a cikin d'akin gaba d'aya ta gama firgicewa kanta ko kallabi babu ta rasa tunanin da zata yi tsoron ta ace da gaske tana da ciki duk in tayi wannan tunanin sai yan hanjinta sun juya can wata Zuciyar ta raya mata taje ta siyo Pt strip ta auna in shine tun wuri ta d'auki matakin daya dace, yin wannan tunanin yasa da sauri ta nufi kayan su ta d'auki hijab ta bud'e jakarta ta d'auki kud'i har zata fita tay tunanin ta saka nikab d'in Fauzy ta tafi dashi ta juya ta d'aukko shi ko sakawa daidai bata yi ba a haka ta tafi....... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2048* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ...........Tafiya take bata san inda take wurga k'afafunta ba don sam bata cikin hayyacin ta a haka har Allah yasa ta fito cikin Asibitin tasan in taje pharmacy d'in asibitin ba za'a bata ba tunda ba Doctor ya turo ba hakan yasa ta yanke zuwa d'aya daga cikin pharmacies d'in dake wajen Asibitin tana ta tafiya gani take tafiyar ma bata sauri tamkar maidota baya ake hakan yasa ta yanke hawa Napep duk da ba wani nesa bane tama kusa isa, bayan ta tsaida ta fad'i mashi inda zai kaita shima mai Napep d'in har saida ya d'anyi mamaki yace mata nan wajen gate tace eh amman zai jira zata siyo abu ne sai ya maido ta makaranta yace nan school of nursing tace mashi eh yace to ta hau, bayan sun tsaya ta nufi cikin pharmacy d'in gabanta sai fad'uwa yake har ta kusa rubzawa k'atuwar kwalbatin dake wurin batare da ta ankare da slab din ya fashe ba mai Napep d'in ne ya d'an d'aga murya yace tabi a hankali don ya lura duk a firgice take ta d'aga mashi kai kawae, bayan ta shiga ta fad'i abunda za'a bata ba 6ata lokaci aka d'aukko mata ta je wurin biya ta bada d'ari biyar ta juyo saida cashier d'in yace mata canjin ta fa sannan ta juya ya bata ta amsa ta fito bayan ta hau Napep d'in suka komo Asibitin, a bakin gate ya aje ta ta mik'a mashi duka sauran canjin dake hannunta ta juya, ganin a rud'e take yasa yay tunanin ko bata san nawa ta bashi ba ya tsaidata yace kud'in sun yi yawa tazo ta amshi canji hannu kawae ta d'an girgiza mashi alamar ya bassu ta nufi ciki yana ta kallonta gashi dai baisan wacece ba don ta rufe face d'inta amman dae ta bashi tausayi don tabbas da gani akwai abunda ke damunta k'arshe yay mata Addu'a yaja napep din ya tafi, nan da nan ta iso d'akin su ta shige bayan ta cire nik'ab d'in zaune tay a gefen gado tana ta zare ido wani irin tashin hankali take ciki tsoronta ta gwada taga cikin ne can wata Zuciyar ta bata shawarar ta daure ta gwadan in ma shine tunda wuri ba sai taje ta siyo allurar zubda ciki ba tay ma kanta, sosae hakan yay mata ba tare da tayi tunanin wata matsala ba ta mik'e saida ta samu wani d'an murfi sannan ta fita zuwa toilet d'in su bada jimawa ba ta fito ko kallabi babu a kanta haka taje tayo fitsarin, a bakin windown d'akin ta tsaya ta d'aura robar fitsarin ta koma bakin gado ta d'aukko ledar pt d'in ta dawo, tsaye tay cike da fargaba take kallon fitsarin ba don komai sai Allah ya k'addara ba da iya tashin hankalin da take ciki ya isa yasa in ma cikin ne ya zube, can zuciyarta ta raya mata time fa na tafiya gashi yau Friday tayi abunda yakamata da sauri tasa hannu ta cizge ledan hannu na rawa ta fiddo tsinken gwajin ta tsoma shi a cikin fitsarin kaman yadda ake yi bayan ta fiddo ta aje ledar data fiddo shi a ciki ta d'aura tsinken flat hannunta nata k'akkarwa, a hankali ya fara washewa idonta akan shi tun ma kafin ya gama ta fara girgiza kai had'i da gumtse baki a haka har ya gama jajayen layuka biyu suka bayyana daro daro alamar akwae cikin, kwata kwata ta kasa yin kuka sai faman girgiza kai take tana fitar da numfashi da k'arfi da karfi ga jikinta dake ta kerma da k'yar ta kai jikin bango kusa da window d'in ta jingina bayanta sai lokacin kwalla suka fara zubo mata masu d'umi cikin wata irin murya ta fara fad'in "ciki ne da ni! Ciki....Na shiga ukku na lalace na bani! Mi maye ni Fatuu na mutu, Ya Haisam ka cuce ni, kaci amanata na shiga ukkuna in gwaggo taji wannan Maganar nasan mutuwa zatayi wllh..." tana Maganar tana Jujjuya kai, tana cikin wannan halin taji motsin kaman ana tunkaro d'akin bata gama gasgatawa ba taji muryar wata tana fad'in "Fauzy kema kin dawo kenan" Fauzyn ta bata amsa da "Eh wllh Maryam toilet ya koro ni" ta k'arasa Maganar tana dariya jin muryar Fauzy yasa a firgice Fatuu ta kai hannu ta rarumi ledar strip d'in da tsinken gwajin ta nufi gado a sukwane taja bargo ta lullu6e har kan ta, tana gama rufe jikin Fauzy na shigowa ta bita da ido sam bata kawo idonta biyu ba ta duk'a ta d'aukko bucket ta fita don flushing d'in su bai yi saidae mutum ya cika bucket da ruwa ya shek'a, tana jin lokacin data fita amman bata bud'e jikinta ba don tasan da ta ga fuskarta zata zargi wani abu tay lamo tafin hannunta toshe da bakinta, after some minutes saiga Fauzyn ta dawo ta maida bucket d'in k'ark'ashin bed tana kokarin mik'ewa kwatsam idanunta suka sauka akan pt strip d'in dake yashe a k'asa wanda sam Fatuu bata san ya fad'i ba iya ledar ce a hannunta, slowly Fauzy ta kai hannu ta d'aukko shi ganin abunda ke a jikin shi yasa ba shiri ta mik'e idanunta still na akan shi tana kallo da tsananin Al'ajabi had'i da mamaki ta d'an gyad'a kai cikin ranta ta ayyana pt strip kuma a d'akinsu mai nuna akwae ciki to waya kawo shi??? A wani irin slow ta d'ago ta kalli Fatuu dake kudundune lokaci guda kirjinta ya buga jin zuciyarta na raya mata kodae itace tunda ai ba kowa a d'akin sai ita kuma duk sauran students na Class hannu ta kai ta rufe bakinta gabanta na cigaba da fad'uwa can kuma ta cire hannun murya na rawa ta kira sunan Fatun amman bata amsa ba bata kuma nuna idonta biyu ba hakan yasa ta k'ara kiran sunan da k'arfi nan ma still bata amsa ba nan take Fauzy ta shiga girgiza kai cikin murya mai nuni da tashin hankali tace "Zarah I know u'r not asleep idonki biyu to ki tashi don na riga nasan abunda kike 6oyewa gashi ma a hannuna!!" runtse ido Fatuu tay sosae ta kasa gane mi Fauzy ke magana akai tana haka taji Muryata tana fad'in "Ki tashi Zarah ina son sanin wannan abun na waye!" Jin haka yasa a kidi'me ta yaye bargon tana juyowa idanunta suka sauka akan abunda Fauzy ta d'aga tana nuna mata wani abu Fatuu ta had'iye Kutt sai zare idanunta da sukae jawur take yanayin fuskar ta kadae ya tabbatar ma da Fauzy abunda take zargi, ganin irin kallon da take mata ne yasa cikin rawar murya Fatuu tace "m....miye wannan d'in...?" Wani d'an murmushin takaici Fauzy tay kafin tace "abun ki ne da kikai amfani dashi, yanzu ashe da gaske ciki ne da ke Zarah!!" A razane Fatuu ta hau girgiza mata kai tana fad'in ita fa bata san mi take magana ba akai ya za'ai wannan ya zama nata ita da tasan ba aure ne da ita ba, Fauzy tace "Yes Zarah ba aure ne dake ba amman kina da ciki ai ba dole sai ta aure ake samun shi ba ko" Fatuu na jin haka ta saka mata kuka tana fad'in sharri zata ja mata ita data san halinta ko samari bata saurara, duk yadda Fauzy ta so ta fad'a mata gaskiya abun yaci tura k'arshe ma sai cewa tay ta sani ko sharri ake son ja mata tunda dama anata fad'in ciki ne da ita jin wannan Maganar yasa Fauzy ta d'an sauko ta fara tunanin zai iya yuwuwa hakan ne to amman abun da d'aure kai mi ta tsare ma wani da har za'a mata sharri irin wannan ita da take zaune da kowa lafiya sannan kuma ana k'aruwa da ita sosae Saboda k'ok'arin ta, kan Fauzy ya gama d'aurewa ta rasa tunanin da zatai sai kallon Fatuu da ta duk'e kanta tana kuka take can ta juya gefe idanunta suka sauka akan hijab da nikab d'in da Fatuu ta ajiye slowly ta nufe su tasa hannu ta d'aga nikab d'in wanda nata ne kuma a cikin Akwatin kayanta tasan ta ajiye shi to miya fiddo shi? bata kaiga ba kanta amsa ba idanunta suka sake sauka a kan robar fitsarin da Fatuu tay amfani da shi harda sauran fitsarin ganin shi ya tabbatar ma da Fauzy gaskiyar Al'amari cike da tashin hankali ta juyo tana kallon Fatuu yayin da acikin ranta ta furta innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un! Kiran sunan Fatuu tay ta d'ago da jajayen idanunta ta kalleta jiki a mace ta nuna mata robar fitsarin tace itama kawo ta akai? Wani abu Fatuu ta had'iya cikin kuka ta hau rantse rantsen itafa ba ita tay amfani dasu ba k'ilan tana cikin bacci wata ta shigo d'akin don kar a kamata tayi amfani dasu anan still Fauzy tay tana kallonta kawae jin wata magana ta rashin hankali duk wuraren dake da akwae a Hostel d'in sai wata tazo d'akinsu duk da ga Fatun kwance tay hakan, ta lura in ba da gaske tay ma Fatuu ba bazata fad'i mata gaskiya ba duk da ta riga ta gama yarda itace tay amfani dasu kawae tana son taji daga bakinta ne, sauke nannauyar ajiyar zuciya tay tace "Ok fine tunda kince bake kika yi amfani dashi ba kin k'i ki fad'a man gaskiya I know what to do" tana gama Maganar ta juya zata fita da sauri Fatuu ta mik'e ta sha gabanta fuskarta jage jage cikin rawar murya tace mi zatayi d'an murmushi Fauzy tay tace ina ruwanta ta bata hanya, k'in kaucewa Fatun tay duk tay zuru zuru sai motsa baki take ta rasa abunda zata ce ganin haka yasa Fauzy cewa "tunda kina son ki sani to bari in fad'a maki, daga nan in na fita gidan ku zan wuce zan je in kai ma gwaggo wannan pt strip d'in in mata bayanin komae harda ciwon da kike tayi ba tare da saninta ba kin fake da baki son hankalinta ya tashi alhali ba haka bane sai yanzu na gano dalili" tana k'arasawa ta fara kokarin ra6awa ta gefen Fatun ta wuce da sauri ta kamata tana girgiza mata kai cikin kuka tace "Fauzy don't do dis to me na fad'a maki bani nayi amfani dashi ba nan fa Hostel room ne kowa zai iya shigowa kuma ai bani kad'ai ce a d'akin ba ko" ita kanta Fatun bata san mi take fad'a ba, d'an murmushin takaici Fauzy tay tace "Yess Zarah u'r not d only one a cikin d'akin ni dake ne so in kina tunanin ko sharri zan maki duk abun mai sauk'i ne yanzu ki sako Hijab d'in ki mu fara zuwa gidan Aunty Mareeya akai mata pt strip d'in sannan mu wuce gidan ku akai ma gwaggo kin ga duk sai a taru a tuhume mu baki d'aya" zuru Fatuu tay tana ta motsa baki cikin d'aure Fuska Fauzy tace taje ta sako Hijab d'in su tafi mana, yarfa hannu Fatuu ta fara yi ta shiga fad'in ta shiga ukku ta lalace karta yi mata haka don Allah ganin zata 6ata mata lokaci yasa Fauzy tureta gefe ta wuce har ta kai kopa taji muryar Fatun tace "ki dawo zan fad'a maki gaskiya to" cakk Fauzy ta tsaya ta runtse ido wani irin tashi hankalinta ya k'ara yi jiki a mace ta juyo ta kalli Fatuu dake tsaye bayanta tana ta kuka cike da Al'ajabi tace "so it's true Zarah u'r pregnant?" Jinjina mata kai tay alamar eh wani irin jiri ne ya kwashi Fauzy da sauri ta dafe kanta tana salati kafin da k'yar ta nufi gadonta ta zaune idonta akan Fatuu dake tsaye can itama ta lalla6a ta koma gefen nata gadon ta zauna suna facing juna, sun d'an d'auki lokaci a haka kwata kwata Fauzy ta kasa magana Saboda tsabar rud'ewa baki bud'e take kallon Fatuu abun ya matuk'ar tada mata hankali wai Zarah data sani bata ko kula samari bare ayi zancen soyayya ko aure itace da ciki, how on earth?" Fatuu dae sai kuka take ta sadda kai can Fauzy ta sauke ajiyar zuciya rai a 6ace ta kira sunan Fatun ta d'ago ta kalleta a kausashe tace "am highly disappointed in you Zarah, ina hankalin ki da na sani ina tunanin ki ya tafi, duk irin kamun kan ki da na sani har kika iya ba wani dama ya ku sance ki ba tare da kinyi tunanin girman zunubin hakan ba, to ko dama kina aikatawa mu kika lullu6e...." Da sauri Fatuu tace "Don girman Allah Fauzy ki daina fad'in hakan wallahi tallahi billahillazi ba hali na bane yadda kika d'auke ni haka nike, Fauzy k'addara ce ta fad'a man nima ba da son rai na ba hakan ta faru wllh fyad'e aka man" zaro ido Fauzy tay baki bud'e ta maimaita fyade aka mata da sauri Fatuu ta d'aga mata kai alamar eh salati Fauzy ta shiga yi hannunta dafe da goshinta can ta cire tace "amman ke ya akai har kika bari hakan ta faru ina kika je har aka maki hakan kuma waye yay raping en ki??" yarfa hannu Fatuu tay ta langa6ar da kai tace "Don Allah Fauzy kada ki man wannan tambayar nasan kin yarda dani to ki yadda wllh raping ne bada son raina bane" jinjina kai Fauzy tay tace "tabbas na yarda dake Zarah amman taya daga kin fad'i man rape in ki akai sai in kama bacin baki fad'i man yadda akai ba" Magiya Fatuu ta shiga yi mata kan ba sai taji yadda akai ba kawae ta taimaka mata ta san yadda zata rabu da shi amman fir Fauzy ta k'i amincewa tace lallae fa sai ta fad'i mata yadda akai har a kai raping inta in ba haka ba to da son ranta a kai kuma ba makawa sai taje gidan su ta fad'a, kuka wiwi Fatuu ta ke yi hakanan bata son ta fad'i mata wanda yay mata hakan don duk da haushin shi da take ji sai taji bata son Mutuncin shi ya zube a idon mutane gwara ta rufa mashi Asiri, k'arshe da Fauzy taga ta kafe tak'i fad'i sai ran ta ya 6aci sosae ta mik'e Fatuu na ganin haka itama ta mik'e da sauri ta nufeta ta kama hannunta guda tana kuka tana mata Magiya a fusace Fauzy tace "Wllh tllh Zarah ko kukan jini zaki indae baki fad'i man wanda yay maki hakan ba Allah a yau d'innan sai gwaggo tasan halin da ake ciki wato shi baiji komae ba yay maki hakan sai kece zaki kare shi da alama dae magana ta na akan hanya da son ran ki komae ya faru" tana rufe baki ta fara k'ok'arin k'wace hannunta daga ruk'on da Fatun tay mata cikin k'araji Fatuu ta fara fad'in "to don Allah Fauzy ki tsaya zan fad'i maki" bin ta tay da wani kallo kafin tace to ta sakar mata hannu bayan ta saki ta koma gadonta ta zauna itama ta zauna a bakin nata ganin yadda Fauzy ta kafeta da ido yasa ta fara motsa baki tana d'an nishin kuka ta rasa ta ina ma zata fara Fauzy dake kallonta tace "am listening Zarah, tell me who impregnated u??" Ba alamar wasa a fuskarta tay Maganar saida Fatuu ta had'iyi wani wahalallan yawu kafin da k'yar ta bud'e baki tace "zan fad'a maki Fauzy amman don Allah don son Annabi ki man alk'awarin bazaki fad'a ma kowa ba koda gwaggo ce kuma zaki taimaka man" kai Fauzy ta d'aga mata alamar eh hakanan taji gabanta ya fara fad'uwa tun bata ji wanene ba don ta gane Fatun na jin nauyin ta fad'i ko waye, ce mata tay ta fad'i tayi alk'awarin da bakinta Fauzyn ta bud'e baki tace tayi mata alk'awarin hakan suka zuba ma juna ido da k'yar murya na rawa Fatuu tace "Y....YA HAISAM NE!!!" Kaman saukan aradu haka Fauzy taji Maganar gaba d'aya ta zaro ido waje baki bud'e k'irjinta ya fara wani irin bugu k'arshe ta mik'e da sauri ta nufi kopar d'akin ta d'aga labulan ta d'an lek'a wajen ta tabbatar ba kowa sannan ta maido kan ta ciki tasa hannu ta tura kopar cikin tashin Hankali ta dawo ta zauna inda ta tashi a kidi'me tace "Zarah kina da hankali kuwa? have u gone mad! Saboda na matsa maki sai kin fad'a mani wanda yay maki hakan shine zaki raina man hankali don ki kare kan ki, mi Ya Haisam yay maki da ya cancanci wannan bak'in k'azafi daga gare ki???" Jujjuya kai Fatuu ta shiga yi ita dama tasan zai yi wuya duk wanda yaji Maganar nan ya yarda da ita tana sheshsheka tace "Wllh Fauzy da gaske nike shine yay rapi...." Tun kan ta k'arasa Fauzy tay mata yar tsawa tace "Enough Zarah, enough pls wannan Maganar taki ba abu bane da hankali zai d'auka wllh haba how on earth ace mutum kaman ya Haisam wai shine yay raping d'in ki, kawae na gane kina mashi sharri ne don ai saurin barin Maganar amman wllh kin ban mamaki mi ya Haisam yay maki da zaki mashi bak'in k'azafi?" Cikin kuka tace "Fauzy akan wane dalili zan mashi k'azafi miya man tunda nike dashi in ba Alkhairi ba ba abunda yake shiga tsakanin mu sai yanzu da yay man wannan mummunan abun shiyasa tun farko kika ga na kasa fad'i maki wanda yay man d'in Wallahi tallahi kinji na rantse shine kuma in zaki lura ke kan ki rannan ba sai da kika tambaye ni wai lafiya kika ga ban ciki Maganar shi ba yanzu kuma ko waya baki ganin muna yi kaman da har nace maki hankalin shi ne ba kwance ba tunda jinyar mahaifin shi yake to kawae na fad'a maki ne don abar Maganar wllh" da alama mutuwar zaune Fauzy tay ko idonta bai motsi ba k'aramar razana tay da jin zancen ba k'irjinta kai kace ana mata daka a wurin, ba wai bata yarda da zancen Fatun bane kawae ta kasa believing Haisam zai iya aikata wannan d'anyen aikin ga wata ma ba Fatuu ba, ta d'auki lokaci bata ce uffan ba sai da aka d'an jima sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya idonta akan Fatuu tace ta fad'a mata ya akai hakan ta faru nan Fatun ta shiga bata labari tiryan tiryan bata 6oye mata komae ba har yadda ta kasa hanashi da farko da kuma yadda har ya aikata mata hakan tana gamawa ta fashe da matsanancin kuka tana Fad'in ya cuceta ya gama da rayuwarta gashi yanzu yaja mata abun kunya, itama Fauzy kuka ta saka suka taru sukai tayi aka rasa mai rarrashin wani da k'yar Fauzy ta mik'e ya nufi gadon Fatun ta hau ta jawota jikinta ta shiga rarrashinta tana cewa ta daina fad'in abunda take fad'i akan shi daga jin yadda abun ya faru bada niyya bane kawae kaddara ce da sharrin shaid'an jin hakan yasa Fatuu d'agowa cikin kuka tace "duk da hakan harda son zuciya Fauzy dama yanzu na fahimci yana man wasu abubuwa da bai saba ba rannan fa a parlorn shi kama shi nay yana kallon man boobs ena gashi yay ta yawan ta6a ni bai jin komae ranar da zai koma wancan zuwan da yayi harda hugging ena fa yayi kawae na fahimci ya fara sha'awata ne shiyasa ya kasa daurewa duk da magiyar da na rink'a mashi amman saida ya cutar da ni" shiru Fauzy tay kaman tana nazarin wani abu Fatun ta maida kanta jikinta don wani irin Sara mata yake can bayan wani lokaci Fauzy tace "Yanzu miye abun yi don ni wllh kaina ya riga ya k'ulle saboda wannan ba k'aramin Al'amari bane ba kowace zuciya zata iya d'auka ba" da sauri Fatuu ta d'ago ta kama hannuwanta cikin muryar kuka tace "mu zubar da shi kawae Fauzy ba tare da kowa ya ji ba" waro ido Fauzy tay a razane tace "abortion kuma keda kan ki kike fad'ar hakan sai kace baki san tarin illolin shi ba......" Katseta Fatuu tay "Eh nasani Fauzy amman shi kadae ne mafita wllh in ba haka ba ba k'aramar matsala cikin nan zai jawo ba na farko kinga da an sani za'a kore ni daga school d'in nan kuma bazan k'ara samun damar yin karatu anan ba ga suna na da zai 6aci, duk ba ma wannan ba gwaggo nafi ji wllh taji zancen nan zuciyarta na iya bugawa ta mutu kinga Saboda fa wanda za'a aura man d'in nan ba shiryayye bane yana neman mata ta kasa natsuwa har da su ciwo to ina ga yanzu in taji ina d'auke da cikin shege...." tana kai k'arshen Maganar ta fad'a jikin Fauzy tana cigaba da yin kukan, shiru Fauzy tay ita dae har ga Allah tsoron abortion take can tace "ni gaskiya Zarah ban goyon bayan ki abortion Saboda abunda kan iya faruwa duk da ba fata ake ba za'a iya samun matsalar da asirin mu kuma zai zo ya tonu kinga anyi ba ai ba kenan ga laifin kisan kai kuma a wurin Ubangiji gaskiya dae muyi tunanin wata mafitar ba wannan ba", Fatuu da ta d'ago daga jikinta tace "wace mafita kike tunani data fi wannan Fauzy, in ba hakan muka yi ba duk abunda zamuyi asirinmu tonuwa zai yi ni kuma abunda ban so kenan kar ki manta akwae aminci mai k'arfi tsakanin Gwaggo da Hajiyar su shekaru masu yawa suna zumunci na tabbatar in wannan abun ya bayyana sai zumuncin nan ya lalace abubuwa da yawa Al'amarin nan zai shafa don Allah Fauzy ki bani goyon baya in sha Allahu ba wata matsala da za'a samu kuma Allah zai yafe man tunda yasan ba da son raina hakan ta faru ba sannan cikin kinga k'arami ne ko kwana arba'in bai yi ba duka watan shi guda" shiru kawae Fauzy tay tana bin ta da ido ita dae hakanan hankalin ta bai kwanta da a zubar da cikin ba ba kamar wasu abubuwa da take nazari, magiya Fatuu ta shiga yi mata kan azubar d'in can ta nisa tace "kin gane Zarah ni wllh raina bai kwanta da a zubar da shi ba ba kamar dana yi la'akari da wasu abubuwa shin Ya Haisam ya ta6a kai ki gidan tunda kuke dashi?" a hankali ta girgiza mata kai alamar a'a shiru Fauzy tay tana sake yin nazari tsawon shekara biyar da suka san juna amman bai ta6a kaita gidan ba sai yanzu sannan tace yana yawan ta6a ta ba tare daya ji komae ba wanda a yadda ta bata labari a da sam bai mata haka hasali ma bai son su ke6e su biyu to miyasa yanzu yake mata hakan? wata Zuciyar ta raya mata k'ilan don yanzu ta girma ta zama cikakkar budurwa shiyasa ya fara jin sha'awarta kamar yadda itama Fatun take tunani can kuma nazarinta ya gangaro kan Alkhairin da yake mata wanda harda su wayar miliyan hakanan ba dangin iya bana baba nan ma wata zuciyar ta sake raya mata wannan ai daman ya saba yi mata Alkhairin kuma zai iya yuwuwa ko ya fara son ta ne shiyasa har Yay mata irin kyautar, k'arshe dae kan Fauzy ya k'ulle tamau ta kasa yin tunanin wani kwakkwaran dalili don komae a bud'e yake amman tana jin kaman something is amissing k'arshe dole ta bar ma ranta kawae kaddarar su ce a hakan, kallon Fatuu tay tace "zan amince a zubar kamar yadda kike so amman da sharad'i guda" da sauri Fatuu tace miye sharad'in Fauzy taci gaba "Dole Ya Haisam yasan da cikin nan kafin mu zubar d'in" wani kallo Fatuu tay mata a marairaice tace "miyasa za'a sanar mashi Fauzy abunda shi baima damu da abun da yay man ba kina gani tunda hakan ya faru sau biyu ya kirani ban d'aga ba daga nan fa bai sake kira ba dama shima kiran sai kusan da akai 2 weeks sannan don Allah mu rabu dashi kawae ni nasan ba wani abunda zai yi" d'an girgiza kai Fauzy tay tace "karda idon ki ya rufe Zarah zubda ciki fa ba k'aramin abu bane da za'a ce ayi ba tare da mai shi ya sani ba yanzu ba fata nike ba azo Asiri ya tonu wurin zubarwar taya zamu kare kan mu tunda shi ba sanin da cikin yay ba think about it Zarah" d'an shiru Fatuu tay duk ranta bai so ba tace mata ita tana ganin in sha Allahu ba abunda zai faru ai cikin k'arami ne they should just go ahead and do d abortion ba tare da ya sani ba amman Fauzyn ta kafe kan ita dae a sanar mashi don bata tunanin hakanan yak'i kiranta dole da dalili Fatun tace to taya zata sanar mashi shi da bai nan kuma dae ai bai dace ta kira shi yana can wurin jinyar ba, d'an jimm Fauzy tay sai kuma tace "mi zai hana ki kira Kawu Amadu ki tambayi ko sun dawo baki sani ba" gyad'a kai tay ta juya can kusa da pillow ta d'aukko wayar ta fara k'ok'arin kiran Amadun ringing biyu ya d'aga ta gaishe shi ya amsa ya tambayeta ta dawo gida ne don shi yana Makaranta tace mashi a'a sai anjima d'an shiru tay jin hakan yasa ya tambayeta da wani abu ne tace a'a kawae tana son ta tambaye shi ko Hajiyar Sanata ta dawo ne, yar dariya yay yace "ke dai fad'i gaskia kodae ran ki ne ya baki Romeo d'in ki ya dawo shine kike son ki tabbatar" d'an yamutsa fuska tay tace "kai Kawu Amadu ni don Allah ka fad'a man ai Hajiya dae na tambaye ka ba wani ba ko" tana jiyo dariyar shi kafin yace mata eh ta dawo jiya da yamma harda ma Romeo d'in nata, ko sallama bata yi mashi ba ta katse kiran da ta kalli Fauzy har bata san tayi d'an murmushi ba tace mata ya dawo jiya itama murmushin tayi tace "yauwa kinga Allah ya taimake mu komae zai zo da Sauk'i in sha Allah" cike da farinciki Fatuu ta fad'a jikinta tana Fad'in "Thank u so much Fauzy u'r more like my blood sis than Friend, Nagode ma Allah da yake had'a ni da k'awaye Nagari wanda duk in ina cikin damuwa suma suke shiga damuwa har su bani shawara mai kyau da zata fitar dani" d'agota Fauzy tay tana murmushi tace "What are Friends for, haka yakamata aboki na gaskiya ya kasance wani lokacin in kai dacen aboki sai kaji ma har yafi maka wani dan'uwan naka na jini hakan nake ji a tattare dake Zarah" k'ara fad'awa tay jikinta tana murmushi can taji Fauzyn tace "How I wish ace cikin nan na halak ne lokacin da zamu gama makaranta kuna da d'an yaron ku ko yaranku in twins ne lokacin nasan har sun d'an tasa ma, wai za'a ga ruwan kyau dae wllh amman ba komae komi Allah yay mai kyau ne fatana dae ya shige mana gaba a duk abunda zamu yi" Fatun ta amsa mata da Amin a hankali Fauzyn tace mata to ta tashi tay wanka ta shirya sai taje ita kuma zata jirata har ta dawo bazata tafi weekend ba, sosae Fatuu taji dad'i ta mik'e, ba'a d'au wani lokaci ba tayo wankan ta zura doguwar riga bak'a ta yafa gyalenta Saboda zumud'i har ta ma manta da ita mara lafiya ce, tare suka fito har wajen gate cikin sa'a suka samu Napep da Fatuu zata shiga Fauzy ta kama hannunta tace "kiyi man alk'awari nima zaki same shi kiyi mashi Maganar" kai ta d'aga mata tace "nayi maki Alk'awari kuma in zan dawo zan taho da allurar sai kiyi man" d'an jimm Fauzy tay kafin ta gyad'a mata kai tace shikenan amman dae ta tabbatar sun fara yin Magana da shi daga haka ta shige Fauzy na d'aga mata hannu suka tafi. Tunda suka shigo Unguwar gabanta ke fad'uwa har d'an rufe fuskarta take don kada gwaggo ko Kawu Amadu wani ya ganta Saboda bazata shiga gidan su ba don kada gwaggon ta gano halin da take ciki ba kamar da ta tuna Maganar data yi mata rannan, har bakin gate mai Napep d'in ya kai ta bayan ta biya shi tana ruk'e da yar purse d'inta ta tunkari gate d'in Office yay mata ya Makaranta ta amsa bayan ta gaishe da shi ta shige, part d'in Hajiya tay tunanin fara zuwa don tayi mata ya mai jiki kuma k'ilan ma ta iske Haisam d'in a can tunda yau Friday, lokacin data shiga Hajiyar na zaune a parlor tayi gayun Juma'a bak'i tayi bayan ta dawo daga Masallaci basu dad'e da tafiya ba ta zauna tana kallo idanunta sanye da medical glasses d'inta, tunda Fatuu tay sallama ta maido idanunta kanta tana kallonta har ta k'araso cikin parlon ta zauna kujerar dake opposite da ita da d'an murmushi tace "Hajiya ina wuni an dawo lafiya" still kallonta take fuska a sake ta amsa mata, Fatun ta sake cewa Ya mai jiki, d'an girgiza kai Hajiya tay tace "mai jiki sai dae mu ce Alhamdulillah don an sha jiki kam amman cikin hukuncin Allah ya warke garas abunda ake gudu Allah ya tak'aita faruwar shi" itama Fatun Alhamdulillah tace kafin tay Addu'ar Allah ya k'ara mashi lafiya Hajiya ta amsa, d'an shiru sukae Fatun ta lura da Hajiyar sai kallonta take hakan yasa tasha jinin jikinta ta sadda kai tana wasa da yatsunta can ta d'ago tace ma Hajiyar Ya Haisam na part d'in shi ne zata mashi ya mai jiki d'an girgiza kai ta k'ara yi tace "bai nan tun jiya da muka dawo yana G.r.a da yake har yanzu shi kaman jikin nashi bai idasa warwarewa ba" shiru Fatuu tay tana maimaita abunda tace a cikin ranta can ta tambaye ta bai lafiya ne, Hajiyar ta ruk'e ha6a tace "ai ciwo yasha shima a can jinya biyu akai wllh dama dae tun da muka bar nan zamu Kano na lura da yanayin shi har na tambaye shi sai yace man fever ke damun shi to da yake mutum ne mai k'arfin hali a hakan har suka fita da Mahaifin na su da yake mu sai daga baya muka bi bayan su Germany d'in, to a can ma bai samu ya huta ba bayan sun je aikuwa sai ciwo ya buge shi wani irin zazza6i mai zafi da ciwon kai suka taru suka rufe shi dama kuma shi yana dad'ewa bai yi ciwo ba, amman fa duk randa ya kwanta yana jin jiki wllh don ni bazan iya tuna ma yaushe yay irin wannan ciwon ba amman dae Alhamdulillah ya samu sauk'i sosae nayi ma tunanin zai wuce can U.s d'in da yake suma su Fanan d'in sun zo nan Germany kusan ita tay jinyar mijin nata har ya samu sauk'i to da zamu dawo ne ita ta wuce can shi kuma muka dawo dashi" duk sai jikin Fatuu yay d'an sanyi a hankali tace Allah ya k'ara basu lafiya Hajiyar ta amsa har zata mik'e taji tace "amman kema dae Fateema kaman baki lafiyar ko?" Damm gabanta ya fadi a dabarbarce tace mata eh itama malaria ke damunta, Hajiyar tace to taga likita ko don fuskarta ta fad'a da yawa gashi tayi fayau kamar mara jini da sauri tace mata eh taje taga likita har test an yi mata an kuma bata magunguna yanzu haka tana cikin sha ma Hajiya tace to Allah ya k'ara lafiya ta amsa da Amin had'i da mik'ewa zata tafi Hajiyar tace ba ta bari taci Abinci tace a'a ta k'oshi taci Abinci daga haka sukai sallama ta nufi hanyar fita, lokacin data fito har saida ta saki yar ajiyar zuciya bayan ta fito wajen gate sai taji dama ta san bai nan da bata bari mai Napep d'in ya tafi ba, ta bayan gidan Hajiyar ta bi saida ta kusa bakin titi sannan ta samu mai Napep ta fad'i mashi G.r.a zai kaita yace to ta hau suka tafi, bayan sun iso ya tambayeta road d'in da zai kaita tace bata san sunan road d'in ba da yake sau d'aya ta ta6a zuwa kuma da daddare ne amman zata rink'a nuna mashi hanya yace to, da yake G.r.a ba kaman geto bace sam Fatuu ta kasa gane gidan sai faman uban zagaye layuka suke a kokarin ta na ta gano, sun d'auki lokaci tana dudduba gidajen Unguwar har dae mai Napep d'in ya gaji ya parker a gefen hanya yace mata gaskiya fa ba lallae su gane gidan ba tunda bata san sunan layin da yake ba k'arshe zasu yi ta yin wahala ne, shiru tay da alamun damuwa bata son ta koma ba tare data gano gidan ba don ta san k'arshe ba lalle Fauzy ta bata goyon baya ba ganin yadda ta damu yasa mai Napep d'in tambayarta bata san sunan mai gidan bane d'an Jim tay ta tuno da Haisam yace ai gidan baban shi ne hakan yasa tace ta sani gidan Senator Alee Adamu Zakee ne yace to bari yaga in za'a samu wanda za'a tambaya da sauri tace to ya fita daga cikin Napep d'in yana duba hanya can saiga wata Mota ta taho ya d'aga ma mai Motar hannu cikin sa'a ya tsaya daga d'an gaban Napep d'in ya nufi Motar da sauri, slowly glass d'in driver side ya sauka wani Alhaji ne a ciki mai Napep d'in ya gaishe da shi bayan ya amsa yace don Allah tambaya suke yace to Allah yasa ya sani mai Napep d'in yace "dama wani gida ne muke ta nema mun kasa ganewa gidan wani Senator Alee....." kakarewa yay yana niyyar d'aga kai ya tambayi Fatuu yaji Alhajin yace gidan Senator Alee Adamu Zakee da sauri mai Napep d'in yace yauwa eh nan, kwatance yay mashi mai Napep d'in ya gane yay mashi godiya yaja Motar shi kuma ya koma Napep d'in Fatuu ta tambaye shi an gane gidan yace eh sosae taji dad'i duk da fargabar da ta cika ta, suna shiga titin layin da aka masu kwatance Fatuu ta hango gidan ta nuna ma mai Napep d'in ya tunkare shi, a gaban tangamemen gate d'in ya parker ta fito su Officer na zaune a saman benci ta nufe su idanun su a kanta har ta k'arasa ta tsaya daga d'an gaban su, bayan ta gaishe dasu tace don Allah ko Ya Haisam na nan d'ayan Officern da tunda ya ganta ya ganeta yace mata eh yana nan, d'an shiru tay ganin haka yasa shi ce mata ba wurin shi tazo bane tace eh yace to ta shiga, juyawa tay ta koma wurin mai Keke Napep d'in tace don Allah ya jirata ba dad'ewa zatay ba sai su koma yace ba matsala hajjaju a fito lafiya harda ce mata wai ta taho mashi da lemu mai sanyi mak'oshin shi ya bushe Saboda yawon da suka sha ta d'aga mashi kai kawae, ta k'aramar kopa ta bi ta shiga gidan tunda ta tunkari ginin gabanta ke fad'uwa abubuwan da suka faru rannan suka shiga dawo mata, saida tay yar tafiya mai d'an tsawo ta isa ginin gidan ta shiga Parlon kafin ta bi ta Corridor ta nufi kopar Bedroom d'in shi......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2049* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........tsaye tay a bakin kopar k'irjinta na ci gaba da bugawa da sauri da sauri ga tsoro da ya kamata ta d'an d'auki lokaci a haka kafin tay k'arfin halin kai hannu yana d'an rawa ta d'an kwankwasa shiru bata ji an yi magana ba hakan yasa ta k'ara d'an kwankwasawa da d'an k'arfi k'asa k'asa ta jiyo Muryar shi yace "Who is dat" shiru tay har saida ya sake tambaya amman ta kasa bud'e baki tace itace jiyo shi tay yace a shigo kopan a bud'e take da turanci d'an jimm tay kaman bazata shiga ba can ta d'an runtse ido kafin ta bud'e fuska a d'aure slowly ta tura kopar, tana shiga suka had'a ido da shi yana zauna akan kujera 3 seater yana operating system jikin shi sanye da jar armless gabanta anyi bak'in rubutu sai bak'in wando 3-quater abu dae sai dae ace Tubarkallah daga gefen shi c-table ne a saman table d'in kwalin lemu ne aje sai tumbler daga gefe kuma ledar take away ce mai d'auke da tambarin wani Eatery, bin ta da ido yay ya yi matuk'ar mamakin ganinta duk da fuskar shi bata nuna hakan ba itama tsaye tay tana mashi wani irin kallo cike da 6acin rai don bata tsammaci ganin shi haka ba wato dae zargin ta ya tabbata na bai damu da abunda ya aikata mata ba tunda gashi zaune ya warke har yana latse latsen computer ba tare daya nemeta ba tunda suka dawo, "Come inside" taji cool voice d'in shi ta fad'a kaman bazata shigan ba ta d'aure fuska tamau can dae ta nufi cikin a gefen shiga inda kujerun suke ta ja ta tsaya tana kallon gefe kallonta kawae yake ya lura da yadda ta d'aure Fuska can yace "come and have a seat" banza ta mashi kuma bata kalle shi ba har saida ya k'ara mata magana kan taje ta zauna a d'an fusace ta kalle shi tace "ba shi ya kawo ni ba" still idon shi na a kanta ita kuma ta k'ara juyar da fuskarta can yay sigh yace "am listening miya kawo ki?" d'an yamutsa baki tay alamun mamakin jin yadda ya tambayeta seemed he doesn't care at all aikuwa sosae ranta ya k'ara 6aci idanun ta suka ciko da k'walla ta juya cikin rawar murya ta fara magana "Zuwa nai in fad'a maka ka cuce ni, ka zalunce ni Ya Haisam, an yarda da kai amman kaci Amana kayi man abunda wani ma ban tunanin zai man hakan balle kai, kace ni matsayin k'anwar ka ta jini ka d'auke ni amman abunda kai man ya tabbatar da k'arya ne don in hakan ka d'auke ni baza ka ta6a son wani yayi man hakan ba balle kuma kai da kan ka, kowa nawa ya amince maka amman duk da haka ka ha'ince su kai man abunda na tabbatar ba kuskure bane da niyya ne tunda sai da na rok'e ka amman ka k'i saurare na Saboda dama kana neman dama ne don ka fara nuna alamomin kana son ta6a jikina...." dakatawa tay tana goge kwalla shidae sai kallonta kawae yake bazaka gane yanayin da yake ciki ba, tsayawa tay da goge kwallan cikin muryar kuka tace "..gashi nan sakamakon abunda kai man ka jawo mana abun kunya wanda na tabbatar gwaggo in taji zuciyarta na iya bugawa ta mutu...." dakatawa tay tana sheshsheka sai lokacin yanayin fuskar shi ya canza ya d'an k'ank'ance ido alamar tunani kan abunda ta fad'a kan shi ne ya d'aure gashi tak'i cigaba da Maganar sai kuka take faman yi tsam ya mik'e ya nufo ta ya tsaya gabanta Slowly ya furta "What is it?" d'ago kai tay ta kalle shi cikin kuka tace "CIKI gare ni!!!" yanayin kallon da yake mata ne ya sauya with surprise written boldly al over his face ya furta "U'r pregnant???" Kai ta d'aga mashi alamar eh kan shi ya d'aure ya ayyana taya hakan zai faru sai kallonta kawai yake ita kuma tana cigaba da yin kuka ta juyar da face d'inta gefe can taji yace "how did you know dat u'r pregnant?" shiru tay mashi don sai taji tambayar ma ta rainin wayau ce tunda ai yasan karatun da take, "am asking you Zarah" ya k'ara fad'a ba tare da ta kalli face d'in shi ba ta fara gaya mashi ciwon da take da yadda aka fara gulman ciwon da take a school har zuwa yadda taje ta siyo Pt strip ta auna tana gama fad'i mashi ta kai hannu ta bud'e yar purse d'in dake ruk'e a hannunta ta fiddo shi dama bayan ta shirya Fauzy ta saka mata shi tace in tazo ta nuna mashi mik'a mashi tay ya kai hannu ya amsa ya fara dubawa nan take ya tabbatar ma kan sa da gaske cikin gareta, d'agowa yay mamaki shimfid'e akan fuskar tashi ya kafeta da ido sai lokacin ma ya lura da canzar da tayi tay wani fayau dama gashi bak'ak'en kayane a jikinta, shiru ya rasa mi ma zaice abun ya matuk'ar bashi mamaki abun da akai just once amman ace har ciki ya shiga jin yayi shiru yak'i yace Komae yasata cewa "Dama nasan bazaka iya cewa komae ba, iya cuta dae ka cuce ni Ya Haisam yanzu da an san da wannan abun kunyan shikenan Mutuncin mu ni da gwaggota ya gama zubewa a idon mutane ga school ma da an sani korata za'ai ga dangin Baffana su bansan iya abunda zai faru ba in suka ji zasu ce dama abunda gwaggo ke sani ina aikatawa kenan shiyasa tai duk yadda zatayi ta hana in auri wanda suka za6a man Saboda manemin mata ne to gashi nan nima ashe abunda nike aikatawa kenan, wllh Ya Haisam ka zalunce mu kayi amfani da son zuciya wajen tarwatsa mana farinciki ko wanda a da za'a aura man da yake halin shi bai cutar da ni har haka ba don nasan Ya Abbas ya fad'a maka dalilin fasa auren mu sai kai da aka amince mawa kai da nake kallo matsayin Yayana uwa d'aya uba d'aya...." Kuka sosae take shi kam zuba mata ido kawae yay don a rayuwar shi wani bai ta6a tutsiye shi haka ba itace mutum ta farko, d'an tsagaitawa tayi tace "zuwa nayi dama in fad'a maka game da shi sannan in sanar da kai zubar dashi zan yi don bazan bar wannan abun kunyar a tare da ni ba ko don gwaggota da sauran dangi na kuma kai ma hakan zai rufa maka asiri duk da kai ka za6i zubar man da Mutunci to ni bazan so in zubar maka da naka ba don har yanzu kana da girma a idona sai dae ina k'ara tunasar da kai ka cuce ni ka ci amanar yarda" tana kai k'arshen Maganar tay gaba abunta fuu bai juya ya kalleta ba har ta fuce ya zuba ma abun hannun shi ido jikinshi yay weak sosae slowly ya d'an matsa ya zauna akan hannun kujera ya d'aura ha6ar shi akan hannun shi guda da ya dungule ya rasa ma murna zai yi ko kuwa don tunda yake bai ta6a jin fargabar wani abu ba irin wannan sosae kuma yay mamaki bai ta6a kawowa hakan Zai faru ba runtse ido yay ya shiga tariyo kalaman Fatuu har zuwa k'arshe da tayi zancen zubar da cikin tunanin abunda yakamata yayi ya fara zuciyar shi ta raya mashi yakamata yay saurin dakatar da ita fa don zata iya aikatawa wani abun kuma yazo ya sameta..... Tana ta faman goge k'walla ta fito daga cikin gidan ko kallon inda su Officer suke zaune bata yi ba ta nufi Keke Napep d'in bayan ta shige tace mashi su tafi bai tanka mata Maganar lemun da ya ce ta fito mashi da shi ba ganin halin da take ciki, bayan ya ja Napep d'in sun bar wurin d'ayan Officer wanda bai san Fatun ba ya kalli abokin aikin nashi yace "ita waccan d'in wacece naga kaman kasan ta" yana murmushi yace "nima ban san wacece ba kwanaki ne Yalla6ai yazo tare da ita" da alamun mamaki yace "nan gidan suka zo?" Kai ya d'aga yace "eh da daddare inaga wurin k'arfe 11 ma" jinjina kai d'ayan ya hau yi alamar mamaki kafin yace "wato ya fara kawo mata kenan amman nayi mamaki koda yake dama irin Mutanen nan sun fi bada mamaki" yar dariya d'ayan yay yace "nidae ban ce maka ya fara kawo mata ba ka sani ko yar uwarsu ce" "Kai tunda kake aiki a gidan nan ka ta6a ganinta koda in masu gidan na nan kuma koda yar uwarsu ce mi zaisa ya zo da ita a wannan lokacin tunda yasan gidan ba kowa kai dai Allah ya kyauta kawae gata ma ta fito tana goge fuska da gani kuka take" da alamun mamaki d'ayan yace "na gani wllh kasan ko rannan ma haka ta fito tana kukan wurin d'ayan dare....." Katse shi yay ya maimaita lokacin da ya fad'an had'i da ruk'e ha6a d'ayan yace "wllh amman dae tace ya tsaya yin wani aiki ne a computer sai bacci ya kwashe ta lokacin da ta farka kuma shima ya riga yay bacci" d'ayan yace "to in haka ne miye na ta fito tana kukan?" Still da murmushi yace "zazza6i ne ya rufeta tace dalilin farkawar tata kenan amman dae.....kawai muyi mashi kyakkyawan zato kaman ko yaushe" dan ta6e baki d'ayan yay yana wani murmushi. Tana cikin Napep d'in wayarta ta fara ringing duk a tunanin ta Fauzy ce ta bud'e purse d'inta ta fiddo wayar tana kallon screen d'in taga sunan Haisam ya bayyana wani irin tamke Fuska tay tak'i yin picking ta d'aura wayar a kan laps d'inta har ta katse can sai ga wani kiran ya sake shigowa still tak'i d'auka saida ya kira na ukku mai Napep d'in yace mata ana waya cikin disasshiyar murya tace mashi tana ji ya jinjina kai yana kallonta ta side mirror ganin tana ta goge kwalla yasa shi ce mata tayi hakuri ta d'aga mashi kai kawae. Tsaye yake wayar shi ruk'e a hannu ganin ya kira har sau ukku bata d'aga ba yasa shi yin shiru kaman mai yin tunani can ya juya ya nufi inda bed d'in shi yake ya zauna a edge d'in gadon ya kai hannu ya d'auki wayar landline dake aje a saman bedside ya kira gate saidae har ta tsinke itama ba'a d'aga ba don su Officer d'in na wajen gate maidawa yay ya aje ya fara k'ok'arin kiran shi ta wayar dake hannun shi ringing biyu Officer d'in ya d'aga tun kafin yace wani abu Haisam yace mashi akwae wata da ta fita yanzu ya bita ya tsaidata gashi nan fitowa Officer na jin haka ya gane wadda yake magana akai yace mashi ai tare da mai Keke Napep take kuma tana fitowa suka tafi yanzu ma yasan sun yi nisa tun kafin ma ya k'arasa Haisam ya katse kiran yay zaune jigum ya rasa miya kamata ma yayi gaba d'aya ya shiga damuwa har fuskar shi ta nuna sanin abortion ba k'aramin hadari ne dashi ba komai zai iya faruwa gashi yasan halinta har yanzu she's stubborn tunda ta fad'a abunda zatai kenan, k'ara kiranta yay still ba ta d'aga ba bayan kiran ya yanke d'an shiru yay can kuma sai ya shiga cikin messages ya tura mata sak'o kamar haka, Don't do anything Zarah, pick my call now. Bayan ya tura da yan mintuna ya sake kira still bata d'aga ba tafin hannun shi ya kai ya rufe daga hancin shi zuwa ha6arshi yana breathing heavily yasan shi yay mata laifi amman bai yi tunanin zata iya mashi haka ba, lokacin da sak'on ya shigo wayar ta ta duba d'an ta6e baki tay a ranta tace ko na d'auka ba abunda zaka fad'a man k'arshe kace kar na zubar tunda ba kai ne a matsala ba dama ance komi namiji yay ado ne to wllh sai na zubar dashi k'arshe ma sai ta saka wayar a silent kawae, suna hawa titi mai Napep d'in ya tambayeta ina zai kaita ta ce babban Asibiti suka d'auki hanya, Yanata zaune can ya yanke yabi bayanta ya mik'e da sauri ya nufi cikin Corridor bada Jimawa ba ya fito ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt bayan ya d'auki wayar shi da car key ya fice da sauri, parking space ya nufa ya bud'e Motar da zai hau ya shiga bayan yayi mata key ya fito ya tunkari gate yana sakin horn da k'arfi tuni su Officer suka mik'e aka zuge mashi Gate d'in ya fice ko ta kan d'aga mashi hannun da suke bai bi ba, bayan wanda ya bud'e gate d'in ya rufe ya dawo yace ma abokin aikin ka lura da yadda ya fita kaman akwae abunda ke faruwa yace mashi eh shima ya lura kuma yana tunanin game da yarinyar nan ne da ta zo tunda ya kira yana a tsaidata d'ayan ya d'an jinjina kai yace Allah ya kyauta to ya amsa mashi da Amin, Har ya fito daga Unguwar bai ganta ba dama bai yi tunanin zai gantan ba tunda ance a Napep take tunanin inda yakamata ya nufa ya shiga yi ganin ranar Juma'a ce yasan tana komawa gida Weekend yasa ya yanke zuwa can, Suna zuwa gab da Asibitin tace ma mai Keke Napep d'in ya d'an tsaya wanccan Pharmacy d'in zata amshi abu yace to ta ciro gyalen jallabiyar ta ta nad'a shi kaman nikab ta yadda ba za'a gane face d'in ta ba bayan ta gama ta bud'e purse ta fiddo yar takardar data rubuta sunan allurar da zata siyan dama tun kafin ta fito ta rubuta ko Fauzy bata sani ba, nufar cikin pharmacy d'in tay mai Keke Napep d'in nata kallonta cikin d'aurewar kai ganin tayi basaja wanda da ba haka take ba, bayan ta shiga ta mik'a ma d'aya daga cikin yan shagon takardar tace ita take so in akwae ya amsa yana dubawa can ya d'ago ya kalleta yace akwae amman basu yi ma Mutane da sauri tace Owk dama ba yi mata za'ai ba ya juya bayan ya d'aukko yace taje ta biya ta nufi cashier d'in ta biya aka bata receipt ta dawo ta amshi allurar ta juya yana ta kallonta har ta fice k'arshe ya d'an girgiza kai kawae, bayan ta koma cikin Napep d'in yaja suka nufi cikin asibitin, a daidai gate d'in School d'in su ya tsaya bayan ta fito ta bud'e purse d'inta ta fiddo 1500 ta mik'a mashi ya amsa ya duba da mamaki ya kalleta ganin kud'in sunyi yawa tun kafin yace wani abu tace yasha lemun da bata d'aukko mashi ba da sauran ta juya ta nufi ciki yana ta washe baki yana mata godiya, tana shigewa tasa hannu ta kwance gyalen ta nufi Hostel. Sosae yay gudu nan da nan ya iso kopar gidan su bayan ya parker ya bud'e ya fito lokacin Amadu na cikin shago yana hango shi da sauri ya bud'e ya fito ya nufo shi suka had'e ya gaishe dashi bayan ya amsa mashi yace "Zaraah na ciki?" d'an shiru Amadu yay alamar tunani can yace "gaskiya kaman bata nan don tunda na dawo daga school ban ganta ba kuma da ina cikin shago ban ga ta zo ba, shiru Haisam d'in yayi Amadu ya lura yanayin shi ya canza hakan yasa yace mashi bari dae yaje ya tambaya ko ta dawo da bai nan ta fita kai kawae Haisam ya d'aga mashi ya juya da sauri ya nufi cikin gidan, d'akin gwaggo ya nufa lokacin tana kwance kan gado tana bacci tayi wankan juma'a wurin kanta ya tsaya ya fara kiran sunanta a hankali ta ware idonta akan shi tana ganin shi ta yunk'ura ta tashi zaune tace mashi lafiya tambayarta yay Fatuu ta dawo ne tace "a'a lafiya?" Yace "dama Ya Haisam ne yazo yana tambayarta yana waje" tace "ba ta kaiga dawowa ba har yanzu kace mashi tana Makaranta k'ilan zuwa zai ya d'aukko ta" d'an shiru Amadu yay sai kuma yace mata k'ilan to daga haka ya juya yana fad'in bari ya fad'i mashi, bayan ya fito ya sanar dashi har yanzu bata dawo ba kai kawae ya d'aga mashi ya juya ya koma Motar bayan ya juyata ya koma ta hanyar da ya biyo da gudu. Lokacin da ta shiga d'akin nasu Fauzy na kwance tana bacci ta yi wanka tasa kaya a bakin gadon da take Fatuu ta zauna ji tay kamar karta tasheta ta bari sai ta tashi amman kuma bata iya hakuri don ta k'osa ai komae a gama hannu ta kai ta fara dan bubbuga jikinta a hankali ta fara motsawa kafin ta bud'e idonta tana ganin Fatuu da sauri ta yunk'ura tana murza ido ta jingina da bango cikin muryar wanda ya tashi daga bacci tace "kin dawo Zarah" kai Fatuu ta d'aga mata d'an shiru Fauzy tay tana ta kallonta can tace "kin gan shi?" nan ma kan ta sake daga mata ta k'ara cewa "to ya ku kai dashi?" d'an ta6e baki tay yanayin fuskar ta ya canza cikin bacin rai tace "bai ce komai ba sai faman bi na da ido kawae, ni dama nasan fa ba abunda zai iya cewa shi kanshi daga yanayin fuskar shi na fahimce ya rud'e da jin zancen cikin ba kamar dana nuna mashi pt strip d'in" shiru Fauzy tay saidae a ranta ta matuk'ar yin mamakin jin wai bai ce komae ba can tace "to da ya ji Maganar zaki zubar da shi miya ce??" tace "dana fad'a mashi shima tsaye yay man yana bina da ido har na baro mashi d'akin saida ina kan hanya ne naga ya kira ni ni kuma ban d'aga ba" Fauzy tace "to Saboda mi Zarah ba sai Kiji mi zai ce ba" yamutsa fuska ta fara yi idanunta suka ciko da k'walla cikin rawar murya tace "Fauzy da akwae abunda zai fad'a man tun ina can da ya fad'i man kawai nasan bai wuce yace kar in zubar ba zai handling komae kuma wllh wannan ba yar k'aramar matsala zai jawo ba ni gwaggota nafi ji Fauzy tun ina k'arama take bani labarin wata d'iyar yar wajen aikin su da tay cikin shege a koda yaushe tana man misali da ita in tana gargad'i na koda na fara period saida tay ta gargade ni akan kada na bari wani ko hannuna ya kama in ba haka ba zan samu ciki Fauzy ki taimake ni ko don ita da karatu na da kuma kallon da za'a koma yi man ba kamar dangin mu har ma dashi Ya Haisam d'in gara mu kawo k'arshen komai ba tare da kowa ya sani ba" ta k'arasa hawaye na zuba daga idanunta had'i da kai hannu ta kamo hannun Fauzy shiru tay tana bin ta da ido wani irin fad'uwa gabanta ke yi hakanan ita dae bata son a zubar da cikin ga fargabar mi zai iya zuwa ya dawo magiya Fatuu taci gaba da yi mata can ta ja dogon numfashi cikin karyayyar murya tace "Zarah tsoro nike wllh kada wani abu ya faru sakamakon yin allurar nan kinsan tana da illa fa" da sauri Fatuu tace "in sha Allahu ba abunda zai faru raina na bani hakan kuma nayi maki Alk'awarin koda wani abun ma ya faru bazan mentioning d'in ki ba zan d'aura ma kaina alhakin duk abunda zai faru pls k'awata wadda bata son damuwata ki taimaka man" hannu Fauzy ta kai baki ta d'an cije yatsun ta tana nazari Fatun na cigaba da kallon ta a marairaice can ta cire hannun cikin disashewar murya tace mata ta had'a allurar nan da nan Fatuu tay d'an murmushin farin ciki ta fara kokarin had'a allurar......... Sosae yake gudu yana driving d'in yana kai hannu bakin shi ya d'an ciza had'i da d'an bugun steering d'in cikin lokaci kankani ya iso bakin gate d'in Makarantar su ya Parker sai lokacin ya fara tunanin yadda za'ai ya samu ganinta in ma tana a cikin school d'in hannu ya kai gefe ya d'auki phone d'in shi ya fara kiranta sai dae har ta katse bata d'aga ba haka saida ya kira sau biyar amman bata d'aga ba cikin tashin hankali ya kai hannu ya d'aki steering d'in da k'arfi ya furta "ZARAH....!!!" shiru yay yana numfashi da sauri da sauri kan shi ya gama k'ullewa bai san taya zai gan ta ba gashi bai san number d'in Fauzy ba balle ya kirata zuciyarshi ce ta raya mashi the more yake 6ata lokaci the more rayuwar ta ke shiga hadari he has to do something quickly hannu ya kai da sauri ya tashi Motar bayan ya juya ta ya jata da gudu ya tafi, yana ta sak'e sak'en abunda yakamata yayi a ranshi k'arshe zuciyar shi ta yanke mashi kawae yaje ya sanar ma Hajiya, bai d'au tsawon lokaci ba duk da da yar tazara ya iso Unguwar taso tun da ya karya kwanar gate ya fara latsa horn wani na bin wani Officer na jin hakan ya tashi da sauri ya zuge mashi Gate d'in ya shige fuuu bai nufi parking space ba ya wuce da Motar har kusa da part d'in Hajiya sannan ya parker ta ya fito ko rufe kopar bai yi ba ya wuce ciki, lokacin da ya shiga Parlon kwalam ba kowa da sauri ya nufi Bedroom d'in Hajiya yana shiga nan ma ya ga ba kowa har toilet ya nufa yay knocking tsit bai ji anyi alamun da mutum ba hakan yasa ya juyo da sauri ya fito Parlor ya nufi hanyar fita har ya kusa kaiwa k'opar fitan yaji motsi a bayan shi ya juya da sauri Amarya Saude ce don an d'aura mata aure da Officer tarewa ce kawai ta rage, daga kopar baya ta shigo hannunta ruk'e da yar roba mai fad'i Haisam na ganinta ya tunkare ta yana tambayarta Hajiya ko amsa gaisuwar da take mashi bai yi ba da hannu tay mashi nuni da inda ta fito tace mashi tana baya wurin su d'awisu ya amsa da Ok ya nufi kopar ita kaita saida tay mamakin ganin yanayin shi, yana fita bayan ya hango ta can a zaune akan kujera a gefen wurin Aku da alama fira suke hannunta d'aya ruk'e da sandar ta ta alfarma da take amfani da ita yanzu wurin yin tafiya, tun kan ya isa Aku yace ma Hajiya wai ga d'an ta nan jin haka yasa ta juya ta kalli Haisam dake tunkaro ta kafin ta juyo tana dariya tace ma Akun bata fad'a mashi jikan ta bane ba d'anta ba Akun ya dae yi shiru tamkar bai fahimci mi take nufi ba lokacin Haisam ya iso ya tsaya gefenta ta d'aga kai ta kalle shi sai yama kasa ko gaida ita sai d'an motsa baki yake lokaci guda ta gane akwai abunda ke damun shi tace mashi miya faru d'an shiru yay har saida ta maimaita sannan yace yana son yin Magana da ita ne tace to ta taso ne ko anan zasu yi yace suje Parlor tace Ok ta fara kokarin mik'ewa Aku na fad'in sai kin dawo Hajiyata tace to ya jirata suka nufi parlon tana gaba Haisam na bin ta a baya, bayan sun iso wurin kujeru akan 3 seater ta zauna shima ya zauna daga can gefenta idanunta akan shi yay shiru yana kallon carpet ganin haka yasa tace mashi shi take sauraro ya akai, shirun dae yaci gaba da yi ya rasa ta ina ma zai fara tunda yake bai ta6a jin fargabar gaya ma wani magana ba irin yau saida Hajiya ta k'ara tambayar shi da d'an k'arfi tace "miye wai ka fad'a in wani abu ya faru kayi man shiru zaka tada man hankali!" Sauke ajiyar zuciya yay ya d'an kalleta idanun shi har sun canza sai kuma ya maida su yana kallon gefe cikin raunanniyar murya ya fara cewa "...I want to tell u dat Zarah is pregnant and a.....am responsible for it" daga haka ya dakata wani kallo Hajiya ke bin shi dashi baki bud'e cikin rashin fahimta tace "Fanan nada ciki shine abun damuwa kai da zaka yi farinciki kiran ka tay ta sanar maka?" Tayi tambayar tana murmushi ya fahimci bata fahimci sunan da ya fad'i ba gashi ta kafe shi da ido alamar tana jiran amsa juyawa yay yayi facing d'in ta sosae cike da k'arfin hali yace "I said Zarah Not Fanan" lokaci guda yanayin fuskarta ya canza ta tsuketa cikin d'aurewar kai tace "Wace zarar?" Jimm yay sosae yake jin fargaba can dae ya dake yace "Zarah our neighbor I impregnated her yanzu haka tana d'auke da ciki na a jikinta" da alama mutuwar zaune Hajiya tay baki bud'e take kallon shi shima kallon nata yake sun dan d'auki lokaci a haka kafin ta kai hannu ta gyara zaman gilashin ta wai taga in shi ne da kyau a rud'e tace "Haisam kana da hankali kuwa kasan mi kake fad'a kuwa dama ashe ciwon da kake ba wani abu bane shaye shaye ka koya wurin turawan shine yanzu ka shawo abunda ya fi k'arfin ka kazo kana man zancen hauka to Allah ubangiji ya tsare mu da irin wannan abun kunyan ka bari muji dana shaye shayen da ka fara, yanzu kai Haisam duk yadda muke d'aukar ka mai hankali kowa na yaba halin ka nagari shine har ka bari turawa sukai galaba a kan ka wannan wane irin abun kunya ne ni Hauwa!" tana k'arasawa ta kai hannu ta ruk'e ha6a tay mashi zugudum tana mashi kallon bak'on mutum ba Haisam ba still yana ta kallon ta yasan dama bazata fahimta ba cikin sauk'i d'an matsawa yay kusa da ita yace "ni fa ba wani abu da nake sha ko kuma na sha yafi k'arfi na what am telling u is true Zarah da kika sani tana da ciki 1 month and nawa ne yanzu taje G.r.a ta sanar mani don nima ban san tana dashi ba...." Nan ya kwashe yadda sukai da Fatuu data same shi yanzu harda K'in d'aukar wayar shi da tayi da neman ta daya zo da kuma makarantar su da ya je duk ya fad'a mata, tana ta kallon shi har ya gama mata bayani tay shiru kawae, zuciyarta ta fara gasgata mata zancen shi Saboda yanayin da ta ga Fatun a d'azun tabbas yanayin ta ya nuna kaman na mai d'auke da yaron ciki iya girgiza Hajiya ta girgiza cikin tsananin tashin hankali murya na rawa tace "K.. kenan kana nufin raping d'in yar mutane kai???" d'an cije lips d'in shi yay ya d'aga mata kai alamar eh ta zabga uban salati tana tafa hannuwa ta shiga fad'in ".....Wannan wace irin musiba ce Haisam ya jawo mana, duk yadda nike Addu'ar Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani ashe kai ne zaka jawo hakan Haisam, miya faru da kai ne ka aikata ma Yarinyar Mutane wannan d'anyen aikin yarinyar da take tamkar k'anwa a gare ka, mika sha ne ka aikata mata hakan, ka fad'a man ko don ance matar ka nada matsala shi ne kai tunanin samun d'a ta wannan hanyar kasan mi ka aikata kuwa???" Sigh yay ya kai hannu ya dafa goshin shi kafin ya cire yace "I ave told you ba wani abu dana sha fa abunda ya faru wasn't intentionally kema kin san bazan aikata hakan da wani niyya ba ko don wai Fanan na da matsala nasan nayi kuskure na biye ma son zuciya wannan dalilin ne ma yasa na kasa natsuwa har na dawo nan ban wuce Us ba" kallon dae kawai take bin shi dashi tsananin tashin hankali yasa ko kuka ta kasa yi ganin shi take a matsayin wanda ba daidai yake ba don kuwa da alama ya manta girman laifin da ya akaita da wadda ya aikata mawa, cigaba yay "Yanzu dae isn't the right time da zamu cigaba da Maganan ya kamata ai stopping nata daga aikata abunda tace zata yi u know abortion nada matsala and nayi k'ok'arin in tsaidata but she refused to pick my calls kuma kinsan tunda karatun ta ne zata iya aikatawa pls do something in ya kama ko gidansu ne muje sai a fad'a ma Grandma d'inta" wannan karon kallon mahaukaci Hajiya ta koma yi mashi mahaukacin ma mai hauka tuburan don Maganar k'arshe da yayi a wurinta ta mara hankali ko miskala zarratin ce kaman yasan mi take ayyanawa yasa shi fad'in "nasan abun nada tashin hankali but bai kai na in aka samu Matsala ba don she may lose her life fa in hakan ya faru kuma ya tashin hankalin zai kasance so is better a sanar mata ta dakatar da ita and I will take responsible of everything" bakin Hajiya dai ya gama mutuwa sai ido kawae can ta yunk'ura ta mik'e shima ya mik'e ta nufi kopar fita daga parlon ganin zata fita haka yasa shi cewa veil d'in ta fa banza tay mashi tana dogara sandar ta har ta fice daga parlon shima haka........... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2050* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ..........tana fitowa ta nufi hanyar gate shi kuma Haisam ya nufi Motar shi dake a bakin part d'in dama a bud'e ya barta ya shige yay reverse kafin ya juyata ya nufi hanyar gate d'in a daidai saitin Hajiya ya tsaya ya sauke glass yace mata ta shigo, banza tay mashi tana cigaba da dogara sandar ta ganin haka yasa shi bud'e Motar ya fito ya sha gabanta tay mashi wani kallo kafin tace ya jaye ya bata wuri kawae sai ya kama hannunta ya nufi Motar da ita tana ya k'yaleta amman yak'i sakin ta har saida ya bud'e kopar baya ta shiga sannan ya koma gaban ya shige tuni Officer ya zuge mashi gate ya fice yabi Motar da kallo a ran shi yana tunanin ko lafiya, A daidai gaban gidan su ya parker da sauri ya fito ya bud'e ma Hajiya kopar bayan ta zuro sandar ta kafin ta fito ya maida duka kopopin ya rufe suka nufi gidan tana gaba yana biye da ita Amadu dake cikin shago yana ganin su ya bud'e ya fito yazo gaban Hajiya ya gaishe da ita ta amsa mashi kafin ta tambaye shi Dijen na ciki yace eh ta wuce ya k'ara gaishe da Haisam ya jinjina mashi kai kawae, bin su da ido Amadu yay lokaci guda hankalin shi ya tashi don ya fahimci akwae abunda ke faruwa tun ma d'azun da Haisam d'in ya zo neman Fatuu Addu'ar Allah yasa dae lafiya yay kafin jiki a sanyaye ya koma cikin shagon, suna shiga zauren gidan Haisam yaja ya tsaya Hajiya har ta shiga ciki ta juyo ganin bai shigo ba yasa ta tamke fuska tace "Wato ka d'auke ni mutuniyar banza ko ni ce zan shiga in sanar da aika aikar da kayi?" Yana kallonta yace "No just to ask for permission first" wata uwar harara ta zabga mashi tace "kai a tunanin ka yanzu kana da wata kamala ne wanda ya aikata abunda ka aikata ai bai buk'atar a bashi izinin shiga gidan mutane ba kamar Mutanen da ya za6i zubar ma da Mutunci ka shigo muje" wani kallo yake mata ya d'an girgiza kai yay mata alamar suje da hannu ta juya lokacin ta fara yin sallama saida tayi sau biyu sannan gwaggon ta amsa ta lek'o don ganin waye koda ta gansu da sauri ta k'arasa fitowa tana washe baki jikinta sanye da riga umbrella da zani na atamfa ta d'aura kallabi nufo su tay tana masu maraba Hajiya dake bin ta da ido ganin yadda take ta washe baki yasa nan da nan tausayinta ya mamaye zuciyar ta don ta tabbatar da ta san abun da ke tafe da su to tabbas manta yadda ake dariya ma zata yi balle har tayi, gaida Hajiyar tay ta amsa mata tana kokarin daidaita natsuwar ta ta kalli Haisam still da fara'a tace "d'ana Haisam barka da juma'a ya k'arfin jikin?" Slowly ya amsa mata da Alhamdulillah Hajiya ta kya6e baki tana girgiza kai gwaggon tace su shigo cikin parlor, bayan sun shiga a kan one seater Haisam ya zauna Hajiya ta nufi 3 seater gwaggo kuma ta zauna akan 2 seater ta shiga k'ara gaida Hajiyar tana mata barka da juma'a ta amsa fuska a kwa6e shi kam Haisam tunda ya zauna ya sadda kan shi k'asa, shiru duk suka yi gwaggo sai d'an murmushi take sai dae a cikin ranta ta lura kaman akwae abunda ke faruwa ba kamar Hajiya data gani ba ko mayafi saida aka d'an d'auki lokaci sannan Hajiya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya idonta akan Gwaggo ta fara magana "Dije gamu mun zo saidae ba irin zuwan da aka saba bane zuwa ne mara dad'i mun zo maki da Al'amari wanda ban tunanin ya ta6a faruwa a kaf dangin ku...." Dakatawa tay sakamakon kukan da ya taho mata nan fa hankalin gwaggo ya tashi haik'am ba kamar da ta ga Hajiyar na kuka ga Haisam ya sadda kai baida alamar d'agowa bare tasa ran jin bayani daga gare shi a rud'e ta hau ba Hajiya hak'ura tana had'ata da Allah ta daina kuka k'arshe ma sai ta tashi ta koma kusa da ita tasa hannu tana goge mata kwallan tana cigaba da bata hakurin can ta shanye kukan tace "Dije nasan ki ke mace ce mai tsananin k'arfin hali ba k'aramin abu bane ke ta6a maki zuciya don Allah ina rok'on ki da ki k'ara kan wanda ke gare ki don Al'amarin da muka zo da shi zai iya tarwatsa maki zuciya wllh ni kaina da nake maki Maganar nan tuni zuciyar tawa ta tarwatsa Allah ne kawae ke bani iko nake yin komae" tuni jikin gwaggo ya fara rawa duk ta bi ta rud'e a kidi'me ta hau ce ma Hajiyar to tana ji in sha Allahu ba abunda zai faru da ita ta sanar mata abunda ke faruwa cigaba Hajiya tay "Dije kin san duk inda ake zaman lafiya Shaid'an bai da sukuni har sai yaga ya tarwatsa ni dake zumunci ne mai k'arfi a tsakanin mu tsawon lokaci Saboda dage wa da Addu'oi da su Azkhar yasa tsawon lokaci bai yi nasara akan mu ba sai yanzu, dije sai yanzu....." Share k'walla taci gaba da yi hankalin gwaggo in yayi dubu ya gama tashi a lokacin ta rasa ma hasashen da zata yi kan abunda ke faruwa ganin Hajiyan tak'i fad'a mata abunda ke faruwa yasa ta juya kan Haisam tace "d'ana Haisam don Allah ka sanar dani abunda ke faruwa in sha Allahu zan fahimta ai ni musulma ce...." Tun kan ta k'arasa Hajiya ta katse ta da Fad'in "k'yale wannan Dije dashi shaid'an yay amfani yayi galaba yake son ganin ya tarwatsa mana farinciki zan sanar maki abunda ke faruwa amman ina rok'on ki da girman Allah ki fahimce ni" da sauri gwaggo ta hau jinjina mata kai alamar zata fahimtan Hajiya tace mata ina Fateema gwaggon tace mata bata kai ga dawowa ba har yanzu amman dae yau zata dawo Hajiyar tace mata ta kirata a waya yanzu ta ce mata duk abunda take ta bari ta taho gida da sauri baiwar Allah gwaggo ta mik'e ta nufi hanyar fita tana Fad'in bari ta d'aukko wayar to, bada jimawa ba ta dawo hannunta ruk'e da wayar ta fara kiran Fatuu ba tare da ta koma ta zauna ba saidai har ta yanke bata d'aga ba wasa wasa sai da ta kirata sau kusan goma amman ba'a d'aga ba Hajiya dake ta kallonta tace "halan tak'i d'agawa?" Kai gwaggo ta d'aga mata ta girgiza kai tace "dole ta k'i d'agawa don itama tana cikin tashin hankali" a razane gwaggo dake kallon ta tace "kodae wani abu ya faru da Fatun ne ko tayi had'ari ne, don Allah Hajiya ki sanar man!" ganin yadda ta rud'e yasa Hajiyar kwantar da murya ta na kokarin fahimtar da ita ba abunda take tunani bane ya same ta kawai dae akwai dalilin da ya sa ba lalle ta d'aga kiran ba, ta nuna mata lalle dole sai Fatun tazo zata ji abunda ke faruwa gwaggon tace to yanzu ya za'ai gashi ta k'i ta d'aga kiran, tambayar ta Hajiya tay ko tasan d'akin da Fatun take a can Makarantar tace a'a ta dai san Hostel d'in amman bata san d'akin su ba tunda bata ta6a zuwa ba Hajiyar ta sake tambayar ta bata san wata k'awar Fatun ba ta kirata tace ta sani amman bata da lambar wayar ta don duk in zasu gaisa da wayar Fatun suke gaisawa, shiru kowa yayi gwaggo dai na tsaye k'ik'am can Hajiya tace "ina ga tashi zamu yi mu tafi Makarantar tasu kawae alabashshi sai mu nemi d'akin nasu in mun je" shiru gwaggo tay fuskarta duk ta canza an barta a duhu sai faman sak'e sak'e take a ranta can tace ma Hajiyar "ina tunanin Amadu bai rasa lambar k'awar tata bari in mashi magana" da sauri Hajiya tace to taje taji in akwai ta juya har tana yin tuntu6e wurin fita daga parlon Hajiya na ta bi a sannu, bayan fitar ta ta maida idonta akan Haisam da still kan shi na sadde ta hau jefa mashi wani mugun kallo fuska a kwa6e, Saboda tsabar rud'ewa a yadda take ba lullu6i babu itama ta fita har bakin shagon Amadu yana ganinta ya bud'e ya fito ya hau tambayar ta lafiya ba kamar yadda yaga yanayin fuskarta murya na rawa tace "ban san abunda ke faruwa ba Amadu amman dai gaskiya da matsala gashi sun k'i sanar dani abunda ke faruwa wai sai Fatuu ta zo Hajiya harda kuka fa gashi anata kiranta a waya tak'i d'agawa" zaro ido Amadu yay ba kamar daya ji tace Hajiya harda kuka yama rasa mi zai ce Gwaggon ce ta tambaye shi ko yana da lambar Fauziyya da sauri yace "eh akwae Fatuu na kira na da ita" tace to ina wayar ya d'aukko mata ita yace to had'i da juyawa da sauri ya koma cikin shagon without wasting time ya dawo ruk'e da wayar ya fara kokarin kiran Fauzy........., Tun bayan da ta yi mata allurar ta haye saman gadon ta ta jingina da bango duk ta takure a guri d'aya har yanzu jikinta rawa yake d'an yi Saboda zullumin abunda zaije ya dawo idanunta akan Fatuu dake kwance akan gadonta ta rufe ido bacci ne ya kwashe ta tana cikin jiran tsammani bayan da aka mata allurar, duk in tayi motsi sai gaban Fauzy ya fad'i daramm! Tana haka wayarta dake gefe ta fara ringing da sauri ta kalle ta kafin ta kai hannu ta d'aukko lokacin da tay arba da sunan Uncle Ahmad kamar yadda tay saving no d'in shi har saida gabanta ya fad'i tabi kiran da kallo har ya kusa yankewa kafin hannu na rawa tay picking yana jin ta d'aga da sauri ya mik'a ma gwaggo wayar ta karata a kunne ta rafka sallama wani irin rassss Fauzy taji murya na rawa ta gaishe da ita ko amsawa gwaggo bata yi ba ta jefa mata tambayar suna tare da Fatuu ne da sauri tace mata eh gata nan kwance tana bacci gwaggon tace "wani abu ya samu wayarta ne inata kira bata d'aga ba kema kuma baki d'aga mata ba?" A rud'e Fauzy tace "a....a'a banji kiran ba k'ilan ko wayar bata a tare da ita don ban ganta ba tun d'azun" "To ki tasheta ki bata wayar taki ina son magana ne da ita" Fauzy ta amsa da to da sauri tana k'ok'arin sauka daga kan gadonta ta nufi Fatuu ta sunkuya ta kai hannu tana tashin ta a hankali ta bud'e idanunta da sauri don kada ta fad'i wani abun Fauzy ta kanga mata wayar a kunne tace "gwaggo ce ke son magana da ke kiyi magana" waro ido Fatuu tay saida ta had'iya miyau Kutt kafin tayi sallama gwaggon bata amsa mata sallamar ba tace "ina kika jefa wayar ki ne anata kira tana shiga amman ba'a d'agawa?" Kikkafta ido ta fara yi a d'an razane jin yanayin voice d'in gwaggon tace mata wayar na a silent ne shiyasa ita kuma bacci ya d'auketa cike da bada umarni tace "to duk abunda kike yi ki bari yanzu yanzun nan ki taho gida ina jiran ki" zaro ido Fatuu tay sosae gabanta ya hau fad'uwa cikin inda inda tace "s..sai anjima da daddare zan taho gwaggo zamu yi wani group......" Bata samu damar k'arasawa ba sakamakon tsawar da gwaggon tayi mata tace yanzu take son ta taho ba sai anjima ba da sauri Fatun tace mata to gata nan tahowa daga haka ta kashe kiran, kallon Fauzy Fatuu tay idanu waje itama kallon nata take a d'an kid'ime ta tambaye ta abunda ke faruwa Fatun ta yarfa hannu tace "nima ban sani ba tace dai komi nake yi in bari in tafi gida yanzu gashi a muryar ta kaman akwae alamun tashin hankali" wani kuka cikin Fauzy yay tace "to kodae tasan da Maganar cikin ne?" tay Maganar hannunta guda ruk'e da ha6arta Fatuu dake kallonta tace "taya za'ai ta sani baccin daga ni sai ke muka sani...." da sauri Fauzy tace "sai kuma Ya Haisam ba" wani kallo Fatun tay mata tace "kina nufin shi zaije ya gaya mata?" Fauzy tace "Eh mana shiyasa nace da kin d'auki kiran shi kin ji mi zai ce maki yana iya yin tunanin kar kije ki samu matsala wurin yin abortion d'in ya yanke gwara yaje ya gaya ma gwaggon" wani kallon anya kina da hankali Fatun ke bin Fauzy dashi tace "Saboda tsabar baida hankali ya aikata man hakan sannan yaje ya fad'i mata haba da Allah kema Fauzy ai baya ma fara ba wllh k'ilan dae akwae abunda ya faru kawae ba wannan ba" uhmm kawai Fauzyn tace, "Ni tsoro na ma kada sai ina gidan cikin ya zube tunda har yanzu shiru, koda yake tunda ba wani babba bane nasan ba wani jini zan zubda ba in sha Allahu in ma ta fuskanci wani abu sai in ce mata period d'ina ne ya zo yau" tana k'arasawa tay d'an murmushin jin dad'in samun mafita ta mik'e Fauzy dae nata bin ta da ido gaba d'aya a tsorace take, bayan ta had'a duk abunda zata d'auka a jakar goyonta ta yafa mayafin jallabiyar jikinta tace ma Fauzy ta tafi jiki a mace tace bari ta rakata ta hau Napep, bayan sun fito daga Hostel d'in sun nufi gate Fatuu ke tambayar ta sai yaushe zata tafi weekend d'in Fauzyn tace sai d'an anjima bayan Magrib in ta gama kimtsawa, bayan sun fito suka samu Keke Napep Fatun ta shige Fauzy tace mata duk abunda ake ciki don Allah ta kirata don a tsorace take wllh Fatun tace ta kwantar da hankalin ta in sha Allahu ba game da wannan abun bane ta d'aga mata kai kawae suka tafi Fauzy ta juyo sukuku da ita ta koma Hostel, lokacin da suka iso layin gidan nasu tun kafin su tsaya a kopar gidan ta hango Motar Haisam dake fake wani irin bugu k'irjinta ya shiga yi har Mai Napep d'in ya tsaya a gaban Motar ta fito da tsananin mamaki take kallon Motar, bayan ta biya shi ta juya suka had'a ido da Kawu Amadu dake kallonta ta cikin shago nan da nan ta sha jinin jikinta da k'yar ta d'aga k'afarta ta nufi wurin shi ta tsaya a gaban Shagon ta gaishe da shi duk ta kame kanta ya amsa yanata kallonta don shi kan shi ya lura da canzawar da tayi kafin yace mata ta shiga gwaggo na jiranta, a kid'ime ta tambaye shi Ya Haisam na ciki ne yace mata eh tay jimm kaman bazata wuce ba har saida yay mata magana sannan ta nufi hanyar shiga gidan k'irjin ta tamkar ana mata luguden ta6are kanta ya gama d'aurewa ta tabbata dae Ya Haisam d'in zuwa yay gidan su ya fad'a, tunanin abunda yazo yace ta shiga yi ba kamar yadda taji gwaggon na mata Magana da ta kira waya "ba dai kaina aka d'aura laifin ba!!!" ta raya a cikin zuciyar ta, lokacin data shiga zauren gidan d'an jimm tay kaman bazata shiga ba can dae ta shiga cike da fargaba ta nufi Parlor ganin takalman su anan tana zuwa bakin kopar parlon taja ta tsaya ido waje ganin Hajiya a zaune ita bata ma ganta ba saida gwaggo tace mata ta shigo ciki sannan Hajiyar ta juya ta kalleta, a d'arare ta shiga ta k'ara togewa a bakin kopar tana ta zare ido wani irin kallo gwaggo ke bin ta da shi Lokaci guda jikinta yay lakwas don ko ba'a fad'a mata ba ta gane mike faruwa da Fatun Hajiya ce ta nuna mata gefenta tace tazo ta zauna ta nufi wurin jikinta tamkar ana zare mata lakka, bayan ta zauna murya na rawa ta gaishe da ita kafin ta d'an saci kallon Haisam da idanun shi ke akan Carpet itama ta sunkuyar da kan nata tana kallon yatsun hannunta dake yin rawa ji take inama ta 6ace bat daga wurin Hajiya ce ta katse shirun da fad'in "Dije ga Fateema ta zo yanzu zan sanar dake abunda ke faruwa amman kaman yadda na rok'e ki kafin yanzu ina sake rok'on ki don girman Allah kiyi hakuri kiyi hakuri dije duk da wannan yayi kad'an ya hana zuciyar ki girgiza amman dai ina rok'on ki kar ki tashi hankalin ki sosae ta yarda zaki cutu don aikin gama ya riga da ya gama sai ayi tunanin mafita kawae tunda ko an tashi hankalin ba abunda zai canza...." d'agowa gwaggo tay ta kalli Hajiyar fuska a kwa6e ta jinjina mata kai kawae, d'an jimm Hajiya tay ita kanta bazata iya tuna ranar da taji fargabar sanar da wani abu irin yau ba gani take kamar zuciyar gwaggo zata iya bugawa ita kanta Fatuu tuni kwalla sun fara gangaro mata tasa hannu ta rufe bakinta ji take kamar kar a sanar ma da gwaggon don in dai wani abu ya sameta to bazata ta6a yafe na kan ta da kuma Haisam ba, sosae kuma tay mamakin k'arfin halin shi da har ya iya zuwa ya sanar da abu irin wannan, jin Hajiyar tak'i cigaba yasa gwaggo ce mata karta ji komae ta sanar mata kawae ita ai musulma ce ta yarda da k'addara mai kyau da kuma Maras kyau jin haka yasa Hajiya d'an gyara zama ido cike da k'walla tace "Dije Fateema dai.....CIKI ne da ita, kuma ba kowa ne yay mata ba sai wannan k'aton kawai d'in da bai dubi girman zumunci ba bai dubi girman yarda ba ya iya cin Amana har haka ta hanyar biye ma son zuciya...." Fashewa tay da matsanancin kuka Fatuu ma haka ita kuwa Gwaggo ta sadda kanta ta yadda bazaka iya gane halin da take ciki ba can Hajiya ta d'ago taci gaba "Don girman Allah dije kiyi hak'uri a taru a rufa ma juna Asiri tunda abun nan duk na gida ne iya cuta dae nasan an cuceku shiyasa ma ake baku hakuri......." kallabin ta ta kwanto taci gaba da share hawaye da shi, duk da kasancewar ta tsufa kan cike yake da gashi wanda rabin shi duk hurhura ce anyi mata kitso all back, duk abun nan sai yanzu Haisam ya d'ago da kan shi ya kalli Hajiya kafin ya maida idon kan Fatuu da sadda kai tana ta kuka slowly ya maido kallon kan Gwaggo cikin sa'a ta d'ago da fuskarta suka had'a ido d'an jinjina mata kai yay had'i da d'an lumshe ido kafin ya mayar da kallon k'asa nan take ta fahimci abunda yake nufi, d'agowa Hajiya tay ta kalli Fatuu dake ta kuka tace "Fateema ya akai kika biye mashi, ki ka bari ya cutar da ke har haka keda nike ganin ki mai hankali da wayau baki tunanin ke zaki fi cutuwa ba a matsayin ki na yarinyar budurwa shi kuwa yayi auren shi!" d'agowa Fatuu tay cikin kuka tace "Wllh Hajiya ba laifi na bane shine yace zan raka shi dinner d'in abokin shi to da muka je bamu dad'e ba muka bar wurin...to da muka taho shine nay fushi Saboda bai bari mun dad'e ba shine ya wuce dani G.r.a bayan ya siya abubuwan ci, koda muka je ni ban so shiga cikin gidan ba hakanan na bi shi.....da muka je wani d'aki nan ma saida na tambaye shi abunda muka zo yi shine yace wai zan k'arasa abunda bai bar ni nayi ba a wurin dinner d'in har nike fushi......to bayan mun ci Abinci tare da shi sai aka kira shi a waya shine ya d'aukko laptop ya fara latsawa da na ga dare yayi sosae nayi mashi magana akan yakamata mu tafi shi...shine yace in bari zai d'an ida wani aiki ne to nan har nace bari in yi salla bayan na gama na koma kan kujera ina kallo sai bacci ya fara d'aukata ina haka na farka nace mashi mu tafi dare yayi sosae yace to ya mik'e nima na mik'e bayan na fita wurin kujeru shima ya tafi ya d'aukko makullin Mota kawae sai aka d'auke da wuta shi......." Kafin ta k'arasa gwaggo ta daka mata wata irin tsawa tace "DUM HETSI FATUU!!!" a razane Fatuu ta kalli gwaggon haka ma Hajiya da mamaki take kallon gwaggon jin yadda ta daka mata tsawa bayan ita aka cutar idanun gwaggon ne suka ciko da kwalla gani take sam ba'a kyauta ma Haisam ba wannan tonon sililin har ina ya muzanta, cikin harshen fulatanci murya na rawa ta hau yi ma Fatuu Magana tana rufe baki a wani irin zabure Fatuu ta mik'e tana zare ido baki bud'e idonta akan Haisam da still kan shi na k'asa, cikin d'aurewar kai Hajiya tace "a'a Dije, a'a, kada muyi haka dake ya za'a cuci yarinya har haka sannan ki hau daka mata tsawa tamkar itace mai laifi bugunta za'ai kuma a hanata kuka? to mi Haisam d'in yayi maki da har ya shanye ki haka??" rai 6ace take Maganar ita kuwa gwaggon maida kan ta tay k'asa ba alamar zata yi magana Hajiya ta maida idonta kan Fatuu da ke tsaye cike da tashin hankali jikinta sai 6ari yake tace "fad'a man mi tace maki ne Fateema? ba don ma na watsar ba ai nima ina d'an jin fullancin za'a canza harshe a cuci yarinya" sake tambayar Fatuu tay kan ta fad'a mata abunda tace mata a d'imauce Fatun tace "C...cewa cewa tay w...wai shi MIJINA NE!" sakin baki Hajiya tay jin wata magana kamar ta wanda ya sha giya Haisam mijin Fateema ta ina!!! wani kallo Hajiya ke bin gwaggo dashi cikin d'aurewar kai tace "Dije ko dae kema chemicals d'in da Kike amfani dasu a wurin aiki suna bugar da ke ne da har yasa kike magana mara kan gado haka?" d'agowa gwaggo tay fuskarta share share da hawaye ta girgiza kai tace "Hajiya da suna bugar da ni zuwa yanzu ai da ban tunanin za'a same ni da cikakken hankali....." Da sauri Hajiya ta katse ta tace "ai Maganar da ki kai Dije ta nuna babu cikakken hankali a tare dake kwata kwata Haisam fa kika ce wai mijin Fateema ne Saboda Allah har ki tunanin kina da Hankali? A yaushe aka d'aura masu auren da har mu bamu sani ba???" Shiru gwaggo tay ita kuwa Hajiyar ta kafeta da ido can ta juya ta kalli Haisam da still kan shi na k'asa ganin yadda bai ce komae bane yasa jikin Hajiyar idasa mutuwa don da alamu da gaske ne kenan tunda gashi bai ce komae ba cikin daka tsawa tace masu bazasu yi mata bayani ba ta ya akai Haisam ya auri Fateema?? Had'iye abu gwaggo tay cikin rawar murya tace "tabbas akwae igiyar auren shi ukku akanta hakan ne ma yasa aka fasa auren ta da wanda aka so aura mata bayan munje can ni da Abbas lokacin da ta gudo, saidae ita Kanta bata san da hakan ba Saboda wani dalili Abbas ne zai yi maki bayanin komae" da alama Hajiya mutuwar zaune tay don kuwa idanunta ko kyaftawa basa yi ita kuwa Fatuu jin wannan bayanin na gwaggo ya k'ara jefa ta cikin matsanancin tashin hankali nan take taji mararta ta fara murd'a mata ta kai hannu ta dafeta tana nishi da k'arfi, wani abu mai d'umi taji ya fara zubo mata ta k'afafun ta hannu na rawa ta d'an d'aga jallabiyar nan take idanunta su kai tozali da jinin dake ta zubowa tamkar ana koro shi a razane ta d'ago ta kai idon ta kan Haisam da shima idon shi ke akan jinin dake zubowar shi kadae ya lura da abunda ke faruwa wani irin jiri ne ya kwasheta ta kai hannu ta dafe goshi kafin ta tafi gaba d'aya zata kifa cikin zafin nama ya yunk'ura ya isa gareta ya tarbeta ta fad'a jikin shi.......... Yau akwae yak'i tsakanin team Fatuu da team Haisam🤣 Wllh yan team Haisam kada ku yarda ku bi mashi hakkin shi gurin duk wanda ya zage shi ko ya muzan tashi da munanan kalamai☹️ _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2051* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .............A razane duk suka mik'e ganin abunda ke faruwa Hajiya ta fara fad'in" gashi nan ai zaku kashe masu D'iya..." Gwaggo duk ta rud'e hannunta sai rawa yake daukarta Haisam d'in yayi yay hanyar fita parlon da ita duk suka rufa mashi baya, yana fita ya kira Amadu da k'arfi ya fito daga cikin shagon da sauri koda yaga abunda ke faruwa da gudu ya nufi Motar ya bud'e mashi baya ya sakata lokacin Hajiya ta fito ta nufi Motar itama ta shige bayan ta d'aura kan Fatuu akan cinyoyinta sai ga gwaggo itama ta fito tana kokarin sanya hijab hannunta ruk'e da wata hijabin da sauri Amadu ya tunkare ta cikin tashin hankali ya fara tambayarta abunda ke faruwa idanu cike da k'walla tace "Maganar da tsawo ka kula da gidan" daga haka ta nufi Motar Haisam yay mata nuni data shiga gaba tace to ta bud'e kopar ta shiga shima ya shiga driver seat ya tashi Motar bayan ya juyata suka tafi Amadu na tsaye jikin shi gaba d'aya ya mutu yabi Motar da kallo har ta 6ace ma ganin shi sannan jiki a mace ya koma shago, tunda suka hau hanya Hajiya ke sababi tana Fad'in "Wllh idan wani abu ya samu yarinyar nan duk sai nayi k'arar ku tunda kun d'auki aure abun wasa abu kamar a shirin film ko littafi ace wai Haisam ya auri Fateema ba tare da sanin mu ba Saboda bamu da amfani ke Dije da nike gani mai hankali amman kika goyi baya...." Dakatawa tay tayi k'wafa kafin ta maida idonta kan Haisam dake driving tace "ko ba abunda ya faru da ita sai na bi mata hakkinta hakanan kusa yarinya tay ta yawo da aure a saman kanta ba tare da ta sani ba kaman baku san darajar shi ba, sannan wllh kukan daka sani shima sai na bi hakki na hakanan kasa ni kuka share share ko mahaifin ka daya kwanta ciwo bamma shi kuka haka ba don iskan ci kasan yarinyar matar ka ce shine bazaka sanar dani ba da kazo sanar man da aika aikar da kayi mata ka nuna man raping d'inta kai kana ganin kuma yadda hankali na ya tashi na d'imauce amman ko a jikin ka Saboda shegen miskilanci wato in mutu ma kai ko a jikin ka ko bari dae Allah ya tashi Fateema dani kake zancen" tsit kowa yay gwaggo kanta na k'asa shi kuma idon shi na akan hanya yanata driving bai ko kalleta ba ta cikin mirror can ya kai hannu cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo wayar shi kokarin kiran Dr Habeeb wanda ya ta6a duba Fatuu da ya kaita har yasan ta fara period ya shiga yi saidae layin nashi baya shiga kusan 3 times yana jarabawa but isn't available Abbas ya koma kira ringing biyu ya d'aga tun kafin yace wani abu Haisam d'in ya riga shi ta hanyar kiran sunan shi Abbas d'in ya amsa yace mashi Don Allah idan yana da wani phone no d'in Dr Habeeb ya kira shi yaji in yana Hospital gasu nan kan hanya zasu kai Zarah and is Emergency, hankalin Abbas d'in ne ya tashi ya hau tambayar shi abunda ya faru da ita yace mashi yana driving ne zasu yi Magana pls ya kira Dr d'in yanzu daga haka ya katse Hajiya ta kya6e baki tace "ai da sai kayi mashi bayani yarinyar mutane zaku kashe tunda shima da sa hannun shi" still bai tanka ta ba sai dae ya d'an kalleta ta cikin mirror suka had'a ido ta wurga mashi uwar harara ya maida idon kan hanya yana cigaba da driving. YADDA HAISAM YA AURI FATUU, A Lokacin da Alhaji Lawal yazo wurin Ard'o ya sanar da batun janye Maganar auran Khalid da Fatuu Saboda yarinyar bata so tana da wanda take so kamar yadda Abbas ya sanar mashi firrr Ard'o yaki amincewa yace sam baza'a fasa auren ba su Yaya suka harzuk'a suka hau tunzura shi kan baza'a fasan ba nan Abbas ya shiga nuna masu da gaske ne tana da wanda take so baya K'asar ne shi Aminin sa ne kuma da ya dawo zai zo a d'aura masu auren, lokacin Alhaji Lawal ya shiga nuna masu illolin dake tattare da auren dole tunda har bata so to a kyaleta Ard'o fa ya hau sama ya tuma yace muddin yana raye hakan bazai faru ba wllh dole abi Maganar shi ai ba itace ta farko da aka fara za6a ma miji ba lokacin Alhaji Lawal ya k'ara nuna mashi ita baza'a had'a ta da yaran nan ba tunda a birni ta taso kuma a birni in hukuma taji za'a ma yaro auran dole bai so to kuwa d'aukar kwakkwaran mataki suke don har kotu ake zuwa mutumin k'auye da tsoron hukuma jin haka yasa Ard'o cewa yaji za'a fasan amman saidae a d'aura mata auren da Wanda take so don tayi girma da yawa ba aure nan fa cikin Abbas ya d'uri ruwa a rud'e ya shiga yi masu bayanin shi wanda take son baya K'asar ai yaje yin wani aiki ayi hakuri ya dawo amman Ard'o ya kafe har da cewa ai ko miji bayanan za'a iya d'aura mashi aure kuma tunda shi yace Aminin sa ne ba sai ya amsar masa ba sosae Abbas ya rud'e suka shiga kallon kallo shida gwaggo Alhaji Lawal yasa baki yace ayi hak'uri ya dawon kafin nan sai ita yarinyar taci gaba da karatunta aifa zancen suke so shine abunda Ard'on yace ya kafe kan ba'a isa yayi yadda ake so ba tunda daga yarinyar har uban nata shike iko dasu, su Yaya aka hau Kumfar baki ana zuga Ard'o don ita bata ma so ya janye da Khalid d'in k'arshe ma sai Ard'on ya fashe masu da kuka wiwi yana fad'in tunda yake nuna iko da ya'yan gidan ba wanda suka ta6a watsa mashi k'asa a ido sai iyalan Muhammadu don haka in dae ba'a d'aura da wanda take son ba to dama k'arya ne kawai so ake a yaudare shi to kuma Wallahi tallahi da kwarankwasa sai an d'aura da wanda aka za6a mata in ba haka ba a yau d'in nan ba gobe ba saidae Muhammadu ya tattare iyalin shi su bar mashi gida ya yafe su tunda basu da wani amfani a wurin shi sai saka shi jin kunya yana rufe baki ya hau yin tari aikuwa kan kace mi fadar ta rikice aka hau fad'in Baffan Fatuu da Gwaggo zasu kashe Ard'on hankalin gwaggo yayi matuk'ar tashi haka ma Abbas don yasan mutumin k'auye da iya jan sharri a rud'e ya hau lalla6a su yace a d'an jira zai kira shi ya sanar mashi sai a d'aura masu auren sai lokacin Ard'on ya d'an sassaukko yace ya bashi kafin gobe Juma'a Yaya ba haka taso ba tamkar zata fashe nan ta kawo Maganar a ba Khalid d'in Mino Chairman ya nuna itama a barta tay karatun ta k'arshe tasa aka fiddo masu da akwatunan lefen su, bayan an watse waje Abbas da gwaggo suka nufa suka tsaya jikin Motar Abbas d'in fuskokin su d'auke da matsananciyar damuwa Abbas yama rasa mi zai ce Gwaggo ce tay k'arfin halin cewa "d'ana Abbas ai da baka ce zaka yi ma wanda take son magana ba tunda dai babu dama an tsara hakan ne don asamu mafita kawae" cike da damuwa yace "amman muddin ba'ai yadda yake son ba saidae fa a d'aura mata waccan mutumin" yar ajiyar zuciya gwaggon ta sauke tace "in hakan Allah ya k'addaro mu bamu isa mu hana ba kuma koma dae miya faru ai harda laifin ta tun farko da anyi ma tufkar hanci tun da wuri ai kaga da ba'a ma kawo yanzu ba da lokaci ya riga da ya k'ure ni dama nasan fasa wannan auren ba abu bane mai sauk'i a wurin wanccan kafaffen tsohon" hannu Abbas yasa ya dafe fuskar shi yama rasa tunanin da zai yi can ya yanke kiran Haisam don ya sanar dashi halin da ake ciki Saboda yasan da Maganar zuwan shi garin kallon gwaggo yay yace mata ta shiga ciki in sha Allahu za'a samu mafita zai yi mata magana cike da damuwa tace mashi kar yace zai takura kan shi don ba samun mafitar za'ai ba kawae suje a sanar da Ard'on wanda take son yace bai shirya ba sai a d'aura mata da wanda suke so d'in kawae, girgiza mata kai Abbas yay yace a d'an dai jira ta shiga ciki tace mashi to kawae ta nufi komawa cikin gidan a ranta tana tunanin taya za'a samu mafita bacin ita Fatun bata da wani wanda take so da har za'a d'aura masu aure, bayan tafiyar gwaggon ya shiga kiran Haisam saidae sam wayar tak'i shiga Saboda rashin Network mai kyau k'arshe dole ya yanke komawa Jimeta ya juya ya bud'e Motar ya shige bayan ya tashe ta ya ja ya tafi, a can cikin gidan bayan gwaggo ta koma sukai zaune jugum harda Baffan Fatuu cike da damuwa ya tambayi gwaggon dama da wanda Fatun suke son juna, ba tare data 6oye mashi ba ta sanar mashi babu wani wanda suke soyayya don karatun ta tasa a gaba kawae shi Abbas yasa a fad'i hakan ne don a samu mafita yanzu kuma ga yadda abu ya kasance Yadikko dai sai bin su da ido kawae take ita tasan Fatun nada wanda take so to amman shi ba lalle in yana son ta ba balle aje ga zancen aure bacin ma bai dad'e da yayi aure ba, k'arshe shima Baffan ce ma gwaggon yay kawae ayi hakuri a k'yale shi ya aura mata wanda yake so sai su bita da Addu'a tace itama tayi ma Abbas Maganar hakan amman yace a jira shi sai su jira suga abunda Allah zai yi duk suka ce Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi. Cikin mintuna talatin ya isa jimetan bayan ya shiga gari ya samu wani ya tambaye shi ko akwae wani Hotel mai kyau yace mashi eh yay mashi kwatance, bayan ya isa ya kama d'aki aka bashi makulli ya nufi d'akin wanda d'an madaidaici ne akwae duk abun buk'ata na cikin bedroom da yake Hotel d'in ba wani babba bane, toilet ya fara shiga ya watso ruwa daga baya ya fito daga shi sai singlet da d'an short ya aje kayan daya cire a saman gadon shima ya zauna daga gefe ya kai hannu ya d'aukko wayarshi da ya aje lokacin da ya shigo ya shiga kiran Haisam saidae duk iya kokarin da yayi layin nashi yak'i shiga har mik'ewa yay ya d'an zagaye d'akin ko ya samu kiran ya shiga amman da yay dialing sai ya yanke k'arshe dole ya dawo bakin gadon ya zauna had'i da cillar da wayar asaman gadon ya had'e hannuwan shi ya d'aura ha6ar shi abun duniya duk ya dame shi yama rasa tunanin da zai yi, maida bayan shi yay saman gadon ya kwanta yana kallon ceiling sai sak'e sak'e yake a haka bacci yay awon gaba dashi, ba shi ya farka ba sai bayan Azahar lokacin har angama salla jiki a mace ya mik'e ya nufi toilet saida ya k'ara watsa ruwa ya d'auro Alwala sannan ya fito ya zura wandon shi ya kabbara salla anan cikin d'akin, bayan ya gama ya d'aga hannu yana Addu'a aciki ya rok'i Allah daya kawo masu mafita a Al'amarin nan ya za6a abunda yafi zama Alkhairi, bayan ya gama ya mik'e ya koma kan gadon ya shiga duniyar tunani ga yunwa ya fara ji can yaji wayar shi ta fara ringing ya juya ya kai hannu ya d'aukko ta yana kallon screen d'in yaga sunan da ya saka ma Haisam ya bayyana har bai san lokacin da yay murmushin farinciki ba duk da baida tabbacin za'a samu mafita a wurin shi, bayan ya d'aga suka gaisa yace mashi tun d'azun yake trying kiran shi amman yak'i shiga Haisam d'in ya tambaye shi yadda suka k'are da Mutanen cike da damuwa Abbas yace "Wllh H,Zakee bamuyi nasara ba k'arshe ma abun nema yay ya zama wani issue na daban" cikin cool voice d'in shi ya tambaye shi abunda ya faru nan Abbas ya kwashe komae ya fad'i mashi tun daga kan zuwa gidan Alhaji Lawal har zuwa zaman da akai d'azun a fadar Ard'o yace "Wllh kafaffen tsohon nan ya kafe kan lalle sai dae a d'aura mata auren da wanda nace suna son juna and ni na fad'i hakan thinking that za'a samu mafita ya amince kamar yadda shi Dad d'in yaron ya amince" shiru Haisam yay can yayi sigh yace "So what's d way out now?" Yarfa hannu guda Abbas yay kan lap d'in shi yace "ban sani ba H,Zakee cos am completely confused abunda nasani dae shine muddin ba wanda nace d'in to tabbas wancan guy d'in zasu aura mata wllh don tsohon ya d'auki zafi da yawa nema ma yay ya suk'e mana fa yaja aka mana caa wai in ya mutu mune and yace muddin ba'a d'aura mata da wanda aka ce tana so ba kuma ba'a bari ya aura mata wanda ya batan ba to ya yafe Dad d'inta dole ya bar mashi gida a yau d'in nan sosae ya shiga tashin hankali abun ba dad'i but he's in serious dilemma har ma da ita Zarah wllh, ni tsorona ma aje a aura mata shi ba fata ake ba wani abun mara dad'i yazo ya faru tunda ta nuna bata son shi ta tsane shi so everything can happen" shiru Haisam kaman ba zai ce komae ba saida ya d'an d'auki lokaci har Abbas d'in na fad'in "H,Zakee are u there?" Yay sigh yace mashi "yeah" Abbas d'in yaci gaba da fad'in "da akwae wanda take so sai a aura Matan kawae ba wani abu bane karatu ko a d'akinta ne sai tayi wannan ba wani problem bane har haihuwa in suna so zasu iya dakatar wa har ta gama karatunta to ni ta fad'a man ba wani wanda take so gaskiya Saboda karatu ta saka a gaba" still shirun Haisam yay can Abbas yaji yace "I think u should just marry her Abbas" har saida Abbas ya d'an zaro ido jin Maganar Haisam d'in yay d'an guntun murmushi a ranshi ya ayyana da ace ba wani a zuciyar ta tabbas da zai yadda ya aureta to amman yanzu ba zai iya auren ta ba gaskiya don yasan zuciyarta na wurin wani har saida Haisam ya k'ara mashi magana sannan yace "ba wai bazan iya auren ta ba H,Zakee saidae gaskiya itama ba lalle ta amince ba Saboda akwae shakuwa mai k'arfi tsakanin ta da Feenah hakan zai jawo babbar matsala azo a kasa samun kwanciyar hankali kuma" shiru Haisam yay yana nazarin Maganar shi can yaji yace to ko Yayi ma Najeeb magana yasan zai amince tunda yana sonta dama, yanayin fuskar Abbas d'in ne ya sauya da sauri yace "haba H,Zakee ban tunanin zaka yi wannan Maganar ba duk don mi ake gudun wannan d'in da za'a aura mata ba Saboda halin shi ba to miye marabar shi da Najeeb d'in duk abunda yake Najeeb ma nayi k'ilan ma ya take shi" sai lokacin ma shi Haisam d'in ya tuna da wannan yace "gashi Saleem was already engaged da sai in mashi magana" wani d'an guntun murmushi Abbas yay jin yadda Haisam d'in keta kawo mutane can yay ajiyar zuciya yace "H,Zakee kai why not ka aureta kawae dama kaga ance wanda take so bai K'asar kaga kenan kai ka dace matsayin wanda za'a aura mata" wani d'a murmushin gefen baki yay yama rasa wace amsa zai ba Abbas d'in har saida ya sake mashi magana kan abunda ya fad'a sannan yace "I thought k'arfi kowa sanin yaushe nay aure zaka k'ara man Maganar wani auren and Maganar shakuwa da kai itama Fanan d'in ai sun shak'u" Abbas yace "amman ai hakan ban tunanin zai hana ka aureta matuk'ar kana so ko don ka taimake ta duba da irin shak'uwar da ke tsakanin ku....." Tun kan ya k'arasa Haisam d'in ya girgiza kai tamkar yana ganin shi yace "isn't possible Abbas bansan yadda zan kawo wannan issue d'in ba just 3 months da yin aure na so let think of another solution" Abbas yace "H,Zakee Maganar aure fa ba magana bace mai sauk'i da kawae za'ai tunanin da anyi ma wani magana zai amince kuma yakamata ka rink'a tuna dalilin son fasa wannan auren nata, ni ina ganin in dae zaka amince ba wani abu bane zaka iya auranta ba tare da kowa ya sani ba just to help her ya zamana iya mu nan muka sani ko ita ba sai an sanar da ita ba kaga bayan an d'aura maku auran zaka iya rabuwa da ita ba tare da idda ta hau kanta ba" Haisam d'in yace "but baka tunanin still sunanta zai canza?" Da sauri Abbas jin kaman ya fara yin nasara yace "No, ai kaga yanzu su nan dama an sanar dasu wanda take son bai K'asar to in aka d'aura auran daga baya in tayi nisa a karatun ta sai a sanar masu ka warware auren don ba yanzu zaka dawo ba ita kuma kar tay ta zama da aure a kanta ba miji" wani kalan murmushi Haisam yay yace "what if suka maido Maganar auren wanccan din?" Abbas yace "ban tunanin hakan ai ba wai daka raba auren za'a sanar masu ba sai an samu kaman 2 years haka lokacin kuma nasan yayi auren shi tunda ba yaro bane kuma nasan ko don ya shirya da Dad d'in shi zai yi sauri yay aure in ma lokacin sun kawo zancen yi mata wani auren nasan k'ila bata rasa wanda take so then" shiru Haisam yay yana nazarin Maganar Abbas sai Addu'ar Allah yasa ya amince yake a cikin ranshi don yana da tabbacin ba lalle ya saketa ba in ya aureta don ya fahimci kamar shima yana son Zarah d'in kawae bai gane bane bayan wani d'an lokaci yace mashi shikenan in yana ganin hakan za'a samu mafita ba tare da wata matsala ba ayi hakan Abbas ya washe bakin farin ciki yace in sha Allahu ba wata matsala da za'a samu Haisam d'in yana murmushi yace shi zai zaman mashi Waliyyi kenan yace eh yana dariya ya tambaye shi nawa za'a bada sadaki Abbas yace ko nawa yadda yaga yayi mashi yace zai turo mashi 1 million ya bada 500k sadakin sauran 500k d'in ai abunda yakamata sosae Abbas yay mamaki jin sadakin daidai da na Fanan ya bada hakan ya k'ara tabbatar mashi da zargin shi na yana son Fatuu kawae ya kasa ganewa ne nan take ya d'auki aniyar sai ya yi yadda yay auren ya d'ore in sha Allah, suna gama wayar sai ga kud'in ya turo mashi murna a wurin Abbas har saida ya d'an taka rawa kafin ya d'aga hannu yay ma Allah godiya ya rok'i yasa hakan yazama Alkhairi, ba 6ata lokaci ya saka kayan shi ya d'auki wayarshi ya fice, ko ta kan ya nemi Abinci bai bi ba ya hau Motar shi bayan ya fito ya nufi komawa rugar akan hanyar shi zuciyar shi ta raya mashi yakamata yaje ya sanar ma da Alhaji Lawal don ya zame masu shaida sosae hakan yay mashi ya nufi hanyar zuwa gidan cikin sa'a ya gane kuma ya same shi yana gida, bayan ya shiga Parlon shi suka gaisa Abbas ya tambayi ko ya gane shi yana fara'a yace ya gane shi mana ba duka d'azun suka rabu ba shima Abbas murmushi yake kafin ya sanar dashi yazo rok'on Alfarma ne yace to Allah yasa zai iya nan ya sanar dashi wanda take son ya amince a d'aura masu auren har ma ya turo da sadaki shine yake son don Allah ya shige masu gaba, sosae yaji dad'i yace ya taya Fatuu murna anan ya tambaye shi game da Haisam d'in Abbas ya sanar dashi sunan shi da kuma waye Mahaifin shi sosae Alhaji Lawal yay mamakin jin d'an Senator Alee Adamu Zakee ne wanda ba 6oyayyen d'an siyasa bane kusan ko ina an san shi ba kamar daya kasance shine Senator d'in daya fi kowane Senator kud'i a Arewa ba 6ata lokaci yace ya tsaya ayi sallar la'asar sai su koma rugar tare a shirya yadda za'a d'aura masu auren Abbas yace to nan Yasa aka kawo mashi Abinci yaci ya k'oshi daga baya yace zai d'an je cikin gari ya dawo yace to, kud'i yaje ya fiddo ana gama sallar la'asar ya dawo ba 6ata lokaci bayan Chairman ya dawo daga Masallaci suka tafi rugar Abbas na a Motar shi shima yana a Jeep d'in shi driver na tuk'a shi, lokacin da suka isa Ard'on na a kopar gida zaune da mutane suka nufi wurin su bayan sun zauna aka shiga gaisawa Ardon yace su shiga cikin fada Alhaji Lawal yace a'a nan ma lafiya lau tunda dama abunda ke tafe dasu ana son mutane su shaida nan Abbas yay ma Ard'on bayani game da amincewar da Haisam yay ya fiddo kud'i 500k ya aje a gaban shi yace ga sadakin ta sannan ya k'ara fiddo 200k yace wannan kuma na su ne su raba inji Angon jama'a zo kuga idanu baki bud'e kowa ke kallon kud'in Alhaji Lawal dae sai murmushi yake a rud'e Ardo ya hau tambayar wai waye wanda zai aure tan ko dai d'an yankan kai ne wannan iyayen kud'i a sadaki Alhaji Lawal ne yay masu bayanin ko wanene Angon Ardo daya gama rud'ewa harda cewa da tana da saurayi irin wannan tuntuni bata kawo shi an d'aura masu aure ba, Kamalu da Amadu da tunda suka ga isowarsu suka taso suka zo gefe don jin abunda zasu tattauna ai suna jin zancen Haisam ne za'a d'aura dashi suka nufi cikin gida da hanzari har rige rigen shiga d'akin suke lokacin su gwaggo duk suna a parlon tun bayan da suka gama sallar la'asar har saida su gwaggon suka tsorata ganin yadda suka fad'o masu Amadu na washe baki ya hau yi mata bayanin abunda ke faruwa a waje cikin d'aurewar kai ta maimaita sunan Haisam matsayin wanda za'a d'aura aure dashi yace mata eh wllh har sadaki ma an kawo Naira 500k zaro ido gwaggo tay tama kasa cewa komae Yadikko ko bata san lokacin data fara sakin murmushi ba Kamalu ne ya juya da sauri ya nufi d'akin baffan su ya sanar mashi lokacin yana kwance ya kasa fita Saboda damuwa ai yana jin zancen ya mik'e ba shiri ya nufi wajen anan aka shirya d'aura auren gobe Juma'a a Masallacin Juma'a dake Jimeta bayan gama Sallar juma'a Lokacin da Alhaji Lawal zai tafi har kud'i Abbas ya basu don su sha mai amman yak'i amsa yace da Haisam da Fatuu duk ya'yan shi ne k'arshe saidae yay ma driver d'in shi Alheri suka tafi kan sai goben, sam gwaggo ta rasa farin ciki zatai komi gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa ta yadda akai Al'amarin ya kasance haka, sai bayan sallar isha sannan duk suka hallara a parlon Yadikko harda Abbas cike da damuwa gwaggo tace "d'ana Abbas ya akai hakan ta faru Saboda mi zaku takura kan ku har haka shi Haisam bai ganin bai dad'e da yin aure ba zai k'ara wani wanda nasan ba don yana so bane kawae k'arfin hali ne irin nashi shiyasa ya za6i cire mu a matsala shi kuma ya jefa kan shi a matsalar aure ba ba k'aramin abu bane, gaskiya ni ban goyon bayan auren nan kwata kwata shima nasan bai yi nazari yadda ya kamata ba kafin ya amince, gaskiya ban amince ba kawae a k'yaleta ta auri wanda suke so hakan zai fi nima hankali na zai fi kwanciya fiye da ace Haisam ta aura" ganin yadda duk ta damu yasa Abbas warware mata komae yace shi yana ganin hakan zai fi kan ta auri wanccan da bata so kuma shima Haisam d'in hakan yayi mashi tunda ba takura shi yay ba ta bari kawae ayi yadda suka tsaran Allah yasa haka yafi zama Alkhairi" Yadikko itama tace "nima ina ganin hakan zai fi kawai ai dama Addu'ar abunda yafi zama Alkhairi duk muke tayi to hakan shi yafi Alkhairin" Baffan Fatuu dae ya rasa ta cewa su Amadu da Kamalu ma duk suka goyi bayan yadda aka tsaran gwaggo dae tay shiru fuskarta d'auke da damuwa duk da ta ragu sakamakon jin ba auren dundundun bane nan Abbas yaba gwaggo sauran 300k d'in yace ayi abunda yakamata tace yaba Baffan dama an bashi sadakin Fatun amman saida Ardo yasa aka bashi wani abu a ciki wai ai sun riga sun gama mata komae, Yadikko ta zubo ma kowa Abinci bayan an gama ci duk akai sallama kowa ya nufi wurin kwanciya Amadu har ya fita ya dawo yace ma gwaggo yana son magana da ita ta mik'e ta fito wajen jiki sukuku acan gefe suka ke6e ganin yadda duk ta damu ya shiga kwantar mata da hankali yace shi yana jin hakan wata hikima ce ta Ubangiji nan ya kwashe komae game da son da Fatuu kema Haisam d'in har ciwon da tayi acan baya suka zata na Aljanun ta ne tsananin mamaki ne ya kama gwaggo har saida tasa hannu ta ruk'e ha6arta baki bud'e ta shiga fad'in yanzu dama duk wannan halin data shiga Saboda Haisam ne Amadun yace mata tabbas don da bakinta ta fadi mashi ya bata labarin lokacin d'aya isketa cikin mawuyacin hali tana amai a d'aki har ta sanar mashi hakan tafa hannu gwaggo ta shiga yi tana salati Amadun yace don haka ta bi su da Addu'a kawae k'ilan Allah ne ya cika mata burinta, a daren ranar kasa runtsawa gwaggo tay sosae tausayin Fatuu ya mamaye mata zuciya biri yayi kama da Mutum ashe shiyasa tak'i sake ma Fanan duk da hakan ji take ba yadda za'ai auren ya dore abunda za'ai iya su ba tare da sanin dangin shi ba ita kanta bazata so Fanan taji zancen auren nan ba Saboda yadda ta d'auke su gani take hakan zai zama tamkar cin Amana ne, Washe gari Juma'a aka fara shirye shiryen d'aurin aure tunda safe Abbas da Baffan Fatuu suka tafi kasuwa suka yo siyayyar kayan Abincin da za'ai harda tunkiya da za'a yanka bayan sun dawo dole gwaggo ta washe suka fara hidiman Abinci da soyen nama bayan sallar Juma'a Mutane masu yawa suka shaida d'aurin auren Haisam da Fatuu sosae Alhaji Lawal yay kokari don kuwa shi ya kawo take aways na abinciccikan da aka raba ma Mutane, bayan sun koma gida aka ci gaba da hidiman biki saidae yawanci yaran gidan ba kowa ne yasan da Maganar auren ba sun dae ga anyi Abinci ga nama kuma an soya Yaya ranar wuni tay a d'aki tana ciwon bakin ciki tun bayan da taji da wanda aka d'aura ma Fatuu aure to ai dama ita Hassada ga mai rabo taki ce, Washe gari ana gama sallar Asuba suka kamo hanya harda su Yadikko aka taho Katsina.......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2052* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ............. Lokacin da suka iso Katsina wannan dalilin ne yasa lokacin da Fatuu ta tambayi Abbas da gaske an fasa auranta yace mata eh amman an d'aura da shi haka da zata bi su Mino lokacin da Abbas yazo kai su suga gari ta saka fitted gown Yadikko tay magana kan rashin dacewar ta fita da rigar da d'an k'aramin gyale har gwaggo ta saka baki k'arshe dai saidae ta canza kaya haka lokacin da Haisam ya kirata vedio call da tace fushi take dashi har bacci ya kwashe ta ya kai hannu yana zagaye lips d'in ta saman screen lokacin duk matar shi ce ita, bayan an samu natsuwa su Yadikko sun koma aka fara shirin cigaba da karatun Fatuu lokacin gwaggo ta nemi Abbas yazo suka zauna a parlor bayan sun gaisa ne ta fad'i mashi dalilin kiran nashi dama kan Maganar sakin Fatuu ne don suna shirin cigaba da karatun ta kuma ga aure akan ta shiyasa take so ya tuntu6i Haisam da Maganar dama sadakin shi na nan a wurin Baffan ta za'a maido mashi amman sai yace shi yana ganin ba sai an yi mashi magana ba tunda ai yasan da auren shi a Kanta kuma dole zata cigaba da karatu don haka a k'yale shi taci gaba kawae cike da damuwa gwaggo tace "amman baka ganin akwae had'ari ace ta tafi wani gari karatu da auren da bata san dashi ba a kanta ni ina ganin d'ana Abbas gara ai mashi Magana ya saki kaman yadda aka tsaran" Abbas d'in ya nuna mata shi fatan da yake dama auren ya d'ore ba wai su rabu ba gwaggo ta hau girgiza kai tace "gaskiya ni bana son hakan duk da zan yi matuk'ar farin ciki in ta samu miji kamar shi to amman ana barin halak ai ko don kunya yanzu in matar shi tasan da Maganar auren da wane ido zan kalleta ita kanta zata ga an ci Amanar ta ba kamar yadda ta d'auke ni tamkar itama ni kakarta ce" cikin kwantar da murya Abbas yace "gwaggon mu wannan duk ba abun damuwa bane in dae Allah ya kaddaro dama zasu kasance miji da mata ai mu bamu isa mu hana ba kuma duk abunda zamu yi yanzu wllh bamu isa mu raba ba don haka mu bar ma Allah komae shi zai shige mana gaba kiga komae yazo da sauk'i" ba don taso ba tace mashi shikenan amman dae gaskiya bai kamata ta tafi wani gari karatu da aure a kanta ba shine ya kawo mata shawarar Fatuu ta fara yin School of Nursing tunda an kusa fara yin Medicine anan ko bayan ta gama ne sai tayi k'arshe gwaggon ta amince ta kuma rok'e shi kan ya taimaka mata wurin kula da Fatun yace in sha Allahu, tun daga wannan lokacin duk abu in ya shafi Fatuu sai gwaggo ta tuntu6i Abbas ko lokacin da zasu bikin Haulat Nijar sai da tay mashi magana shi kuma ya kira Haisam don neman izini lokacin yace mashi duk inda zasu suje ba sai an rink'a tambayar shi ba ya bada izini haka lokacin da taso zama a Hostel farko gwaggo tak'i amincewa tace saidae in ya kama ko zasu yi wani abun kaman yadda ta fad'a mata daga baya ta tuntu6i Abbas da Maganar yay ma Haisam Maganar shi da kan shi yace abarta in dae tana so ta zauna shiyasa gwaggon ta k'yaleta take zama saidae duk da haka tana saka ido sosae a kanta kaman wurin sa kaya da kuma tabbatar da tana a Makarantar duk da ta yarda da ita sosae. ***** ****** ***** Suna isa Abincin Haisam ya hango Dr Habeeb a bakin main Entrance gefen shi nurses ne guda biyu suna ruk'e da gadon d'aukar mara lafiya ya nufi inda suke ya parker a gefe ko kashe Motar bai yi ba ya fito lokacin itama Hajiya ta bud'e kopar bayan ta fara K'ok'arin fitowa, d'ayan side d'in Haisam ya nufa yaima nurses d'in alamar su zo suka turo gadon zuwa inda yake bayan ya bud'e kopar ya duk'a ciki ya cicci6o Fatuu da take a kwance ba numfashi ya juya ya d'aurata akan gadon Dr Habeeb ne ya basu umarnin su nufi Amenity da ita ya juyo kan Haisam da Fuskar shi ta bayyana tashin hankali hakan yasa ko gaisawa basu yi ba ya tambaye shi abunda ke faruwa nan yay mashi bayanin cikin da ke gareta da kuma yadda ta fara zubda jini sakamakon razana da tayi saidae ya nuna mashi akwae yuwuwar tayi wani abu dama don ta zubar da cikin da sauri yace mashi su je suka nufi ciki gwaggo da Hajiya ma suka rufa masu baya, lokacin da suka isa har an shigar da ita d'aki an kwantar da ita Dr yaba d'aya daga cikin Nurses d'in umarnin abubuwan da zata kawo mashi da sauri ta amsa ta juya da d'an gudu gudu ya kalli Haisam yace su jira ya shige d'akin dama d'ayar Nurse din na ciki bada jimawa ba wadda ya aika ta dawo ta shige had'i da maida kopar ta rufe, tsaye duk sukae kowa ya jingina da bango ga seats nan na zaman jira amman duk sun kasa zaunawa Saboda fargaba da ta cika kowannan su Hajiya sai k'wafa take tana kai hannu tana ruk'e ha6arta da bakin ta gwaggo dae tayi jugum sai ido kawae ita kadae tasan halin da take ciki sai Addu'oi take a zuciyarta Haisam kuma ya d'age face d'in shi sama yana kallon ceiling yayin da hannuwan shi ke zube a cikin Aljihunan jeans d'in shi, sai bayan kusan 15 minutes Dr ya bud'e kopar ya fito da sauri Hajiya tace "Dr ya ya?" d'an murmushi yay yace mata lafiya lou in sha Allah ya juya kan Haisam da ya sauke face d'in shi yana kallon shi yace mashi bari ya gan shi a Office aikuwa a harzuk'e Hajiya tace "Dr kamar ya ka gan shi a Office baka ga yadda duk muka damu bane har ma mun fi shi shiga damuwa duk abunda zaka fad'a mashi ai mu ya cancanta ka fad'a mawa ba shi da yayi silar jefata a halin da take ciki ba saboda son zuciya har da ma wannan" ta kai Maganar tana nuna gwaggo da sandar hannunta sadda kai k'asa gwaggo tay ita kanta ta k'osa taji halin da Fatun ke ciki ganin yayi shiru yasa Hajiya cewa suna jin shi a wane hali take ciki ne gyara tsayuwar shi yay yace "ta razana sosae ne shiyasa tay doguwar suma hakan kuma ya haddasa mata bleeding d'in da take don cikin dake jikinta ya fita amman akwae yuwuwar dama anyi kokarin zubar dashi don bleeding d'in yayi yawa ace iya razanar tasata zubar da jini haka sosae amman mun samu jinin ya rage ita kuma har yanzu bata farfado ba amman dae ba wani abu zata farfado in sha Allah yanzu tana buk'atar Oxygen don level d'in nata yayi k'asa sosae sannan already an samata drip yanzu tana buk'atar jini kusan leda biyu...." Tun kan ya rufe baki Hajiya ta shiga nuna mashi Haisam da sandar hannunta tace "gashi nan ja shi ku tafi a de6i nashi in ma fiye da leda biyu ake so duk shi zai bada su" Dr dake d'an murmushi yace "ai Hajiya sai in yayi daidai...." Katse shi tay da fad'in "ko ma bai yi daidai ba ku d'iba sai kuyi ma canza ku bata wanda yay daidai da nata, amman in fad'a maka gaskiya bai dad'e daya tashi daga jinya ba don haka ku binciki jinin in ba wata cuta kar aje a d'irka mata wani abun ya faru a lik'a man sharri nima a saka ni cikin wad'anda suka cuceta" d'an ta6e baki Haisam yay yayi ma Dr alamar suje da hannu yana murmushi suka tafi nurse dake ruk'e da jinin Fatuu da aka d'iba tabi bayansu suka nufi Lab, bayan sun je aka d'ibi jinin Haisam d'in duk aka gwada aka ga zai iya bata kuma cikin sa'a bai da ko malaria har Dr Habeeb na cewa da yake ba anan yake zaune ba shiyasa bai da yar Malariar zamani shidae d'an murmushi kawae yay sai kuma yace mashi a ka'ida leda guda yakamata ya bata Haisam d'in yace in dae za'a iya samun leda biyun a d'iba kawae Dr yace shikenan aka fara shirin d'ibar jinin baida yadda zai yi duk irin kyankyamin shi haka ya kwanta akan gadon, ana gama d'ibar leda guda wata irin juwa ta taso mashi har ya kasa jurewa saida ya kai hannu ya dafe forehead d'in shi Dr Habeeb na ganin hakan ya tambaye shi halan bai ci Abinci ba sai lokacin ya tuna da baici Abincin rana ba an dae siyo mashi bai kaiga ci ba Fatuu taje mashi da zancen cikin da ke gare ta, kai ya d'aga mashi alamar eh Dr d'in yace yana zuwa ya fita bai d'au lokaci ba ya dawo ya kawo mashi Maltina da cake yace bari aje a fara saka mata wanda aka d'iba ya d'aga mashi kai, Bayan an tafi a d'ibi jinin Haisam d'in Hajiya da gwaggo suka shiga cikin d'akin gwaggo ta tsaya daga gefen gadon idonta akan Fatuu dake kwance ido a rufe kanta ba kallabi gashinta ya tarwatse, a gefen gadon Hajiya ta zauna fuskarta cike da tausayi ta kai hannu ta shafa fuskar Fatun tana Fad'in "Baiwar Allah Fateema hakanan an d'auki alhakin ki ana neman asa ki rasa rayuwarki gashi ansa kin aikata babban laifi in ke kika zubar da cikin koda yake su Allah zai kama da laifi ba ke ba...." Haka tay ta surutai gwaggo dae tay shiru, Dr na fitowa ya nufi Amenity anan suka had'e da Abbas daya shigo ya nufe shi bayan sun gaisa fuskar shi d'auke da damuwa ya tambayi Dr d'in abunda ke faruwa don yaga Motar Haisam a waje alamar suna Asibitin nan ya kwashe komae ya fad'i mashi da tsananin mamaki Abbas ya maimaita Zarah ta samu ciki, jin yadda cikin ya zube ne yasa bai nuna farinciki ba tare da Dr suka nufi Amenity d'in, bayan sun shiga d'akin wata uwar harara Hajiya tabi shi da ita nan take yasha jinin jikin shi ya gaishe da gwaggo da ke zaune kan yar doguwar kujerar da take cikin d'akin da d'an murmushi ta amsa yace ya mai jiki kafin ta bashi amsa Hajiya ta amshe da fad'in "Mai jiki da kuka jefe halin da take ciki? to ai gata kana gani don haka sai ka ba kan ka amsa ba sai ka tambayi wani ba" hannu ya kai ya d'an sosa k'eyar shi ya gaishe da ita tay banza da shi ta kya6e baki Dr Habeeb ya wuce ya fara kokarin sama Fatuu jinin bayan ya gama zai fita Abbas na niyyar bin bayan shi Hajiya tace ya tsaya zatai magana dashi yace to, bayan fitar Dr tana mashi wani mugun kallo tace "Yanzu Abbas abunda ku kai kun kyauta, domin Allah kun kyauta ma Fateema dubi halin da kuka jefa yar mutane kiri kiri kusa yarinya tay ta yawo da aure a kanta ba tare data sani ba taya zaku aikata wannan d'anyen aiki haka??" d'an rankwafar da kai yay yace "Wllh hajjaju gaba d'aya hakan ya faru ne Saboda samun mafita gudun jefa rayuwar ta a matsala......" Nan ya kwashe yadda komai ya faru ya sanar da ita cikin fushi tace "to ai gashi nan matsalar da kuke gudan mata ku kun jefata a wata shi kuma in bada niyyar rabuwa da ita ya aure taba ai sai ya fito ya bayyana ma Mutane duk abunda zai faru ya faru yafi da ya kama baki yay shiru shi ga miskili sannan kuma yay kwance kwance ya d'irka ma yar mutane ciki ba kunya ba tsoron Allah banda fyaden da yay mata, iya cuta dae wllh an cuci Fateema kuma harda ku a cutar da ita don haka ku zauna da shirin in dae wani abu ya sameta ba fata nike ba sai an bi mata hakkinta, a ina aka ce don yarinya matar ka ce ka afka mata hakan ai bashi da maraba da fyad'e" kan Abbas na sadde k'asa haka ma gwaggo jin tayi shiru yasa ya d'an d'ago don duk kunya ta rufe shi ya shiga bata hak'uri yana fadin sun yi kuskure ta ta6e baki tace su dae suka sani ita dae ai yanzu jiran Fateema take sumi sumi ya juya ya nufi hanyar fita bayan ya fito ya nufi Lab duk ran shi ba dad'i, sosae baiji dad'in yadda Al'amarin ya kasance ba kamar cikin da ya zube, lokacin da ya isa d'akin da Haisam yake a lab yana shiga suka had'a ido dashi ya jingina da bango hannun shi ruk'e da abubuwan da Dr ya kawo mashi yana ci a hankali Abbas ya shiga da yar sallama can k'asan mak'oshi ya amsa mashi ya nufi inda yake ya zauna daga bakin gadon yana kallon shi da yar damuwa yace mashi sannu kai kawai Haisam d'in ya d'aga mashi suka d'an yi shiru idon Abbas akan shi shi kuma ya maida nashi k'asa can Abbas yace "ashe haka abu ya faru ba dad'i yanzu Hajiya ta tutsiye ni tana ta fad'a" ido kawae Haisam ya bi shi dashi Abbas dake kallon shi yace "to wai ya akai hakan ta faru ba tare da ka warware mata komae ba, nasan da kayi mata bayani duk hakan bazata faru ba" still idon ya bishi dashi ba alamar zai tanka mashi wata yar dariya Abbas yay yace "look dude ba fa wata fuska da zaka man bayan ka aikata 6arna ka cuci yar mutane kaja har muma ta shafe mu" shigar da lip d'in shi na k'asa yay ya d'an ciza suka bi juna da ido Abbas nata sakin murmushin iskanci can ido a d'an lumshe slowly yace "What do u want me to say Abbas? It was intentionally or what?" Abbas dake murmushi yace "kusan hakan mana in ba da niyya ba mi zai sa ka aikata?" Still idon shi na akan shi ya d'an ta6e baki kafin yace "isn't as u think, it was mistake" Abbas yace "to ya akai har kai irin wannan kuskuren, ni mamaki na a ina hakan ya faru ko a part d'in naka" ya k'arasa yana yar dariyar iskanci d'an langa6ar da kai Haisam yay kaman bazai tanka shi ba ganin haka yasa Abbas gumtse Dariyar yace ya bari don Allah ya fad'a mashi don kan shi ya daure sai da yay d'an Jim kafin a nutse ya soma bashi labari tun daga barin su wurin dinner d'in Prince da dalilin kaita G.r.a d'in har zuwa yadda Al'amarin ya fara cike da damuwa bayan yazo nan a bayanin yace "I don't know what came over me and how everything happen dat way, i completely lost control as if my life depends on it dat moment...." dakatawa yay ran shi a 6ace Abbas nata girgiza kai had'i da d'an murmushi Haisam d'in ya cigaba "She said she was pleading me then I dont even heard her" yar Dariya Abbas yay mai d'an sauti Haisam d'in ya jefa mashi wani kallo mai kaman Harara cikin dariyar yace "Da alama akwae bambanci kenan?" Ya d'age ma Haisam d'in gira d'an guntun tsoki yay sai kuma yay d'an murmushin gefe had'i da juyar da kan shi, hannu Abbas ya kai ya dafa k'afar shi guda da ya mik'ar a saman gadon yace "Wllh H,Zakee ba wani abu bane face rabo Allah ya k'addara a wannan ranar a kuma daidai wannan lokaci Mom Zarah sai ta samu cikin ka shine kawae kuma Allah ya kaddaro dama can ita matar ka ce shiyasa wata kil hakan ya faru don asiri ya tonu" shiru bai ce komae ba dae Abbas ya dasa "amman miyasa daga baya ba kai mata bayani ba har abun ta kasance haka" sigh yay yace "ranar da hakan ya faru naso in mata hakan but tana cikin mawuyacin hali gashi ta matsa sai ta tafi gida don ni bamma san lokacin da ta je gate ba saida security yazo ya sanar dani bayan na fita naso mu koma ciki a lokacin I intend to explain myself but sai tak'i and banso muyi jayayya don dare yayi sosae ga security zai iya tunani na daban shiyasa nai mata yadda take so sai ma dana fara kaita hospital don tay shedding blood sosae" d'an bud'a ido Abbas yay fuskar shi tay yanayin tausayi ya hau girgiza kai can yace "to amman daga baya fa, da kai mata bayani ko kuma ni kayi man magana nayi mata na tabbatar da bata yi tunanin yin abortion ba in shi d'in tayi" hannu yasa ya d'an shafo forehead d'in shi kafin yace "a ranar nima kwana nay ban lafiya dama tun da abun ya faru naji ni abnormal daga baya fever mai tsanani ya rufe ni wurin Asuba sai ga kira daga Mom ta sanar dani halin da Dad ke ciki so I have no option dole in tafi muna zuwa can nima ciwo ya rufe ni kuma harda abunda nay ma yarinyar ke damuna duk da nasan mata ta ce amman nasan ban kyauta mata ba hakan ya k'ara worsen condition d'ina bayan na d'an samu sauk'i na Kirata amman tak'i picking dama ko ranar da abun ya faru na kira bata yi picking ba, a lokacin da ina can da ta d'auki wayan zan mata bayani ne in ma bata yarda ba zance taje ta tambayi grandma d'inta so ganin bata d'auka ba I just decided in rabu da ita in na dawo sai in mata bayanin komae" Abbas dake ta kallon shi jin ya dakata yasa shi cewa "to amman data gane tana da cikin bata sanar da kai bane?" Yanayin face d'in shi ne ya k'ara canzawa yace "Yau d'in nan nasan da Maganan Abbas, ta same ni can G.r.a lately anan take sanar man tana ta ciwo a School har an fara rumours d'in ciki ne da ita shine ya ja hankalinta......" Nan ya kwashe yadda sukai da ita d'azun ya sanar mashi Abbas sai girgiza kai yake har ya gama sannan cike da damuwa yace "Wllh harda rashin rabo Allah ya k'addaro dama ba za'a haife shi ba saidae Al'amarin ya bayyana kawae" shima Haisam d'in ran shi a d'an 6ace yace "with her stubbornness also, if she had listened to me this wouldn't hv happened......" Shiru yay bai k'arasa ba ya juyar da fuskar shi ganin yanayin shi yasa Abbas cewa "Kayi hak'uri nasan dole kaji ba dad'i kaga tak'i jin Maganar ka amman na tabbatar in ma zubar da shi d'in tay tayi hakan ne don Saboda ku duka bazata so sunan ku ya 6aci ba tunda kallon da take ma cikin bana halal bane" shiru bai ce mashi komae ba kafin Abbas ya k'ara cewa wani abu Dr Habeeb ya shigo ya nufo su da d'an murmushi kallon Haisam yay da shima ya kalle shi yace ya gama ya d'ibi d'ayan kai ya d'aga mashi Abbas yay saurin tambayar wani jinin za'a d'iba yace mashi eh cewa yay a d'ibi nashi in zai yi Dr yay yar dariya yace "Malam bari dae a diba nashi d'in tunda akwae don na tabbatar ko naka yayi sai an samu Malaria a ciki" dariya sukae gaba d'aya shidae Haisam d'an guntun murmushi kawae yay, bayan an fara d'ibar jinin Dr ke tambayar Abbas wai mara lafiyan matar H,Zakee ce yace mashi eh ya sake cewa amman yaga kaman ba itace suka je bikinta ba Abuja yace mashi eh wannan Amaryar shi ce da d'an murmushi yace "ai da yake su manya ne shiyasa har ya k'ara, itama wanccan din ai Amaryar ce tunda duka yaushe akai bikin" Murmushi kawae Abbas yayi bayan an gama d'iba saida ya zauna ya huta sosae lokacin Dr ya tafi daga baya suma suka mik'e Abbas nata mashi sannu saidae ya d'aga kai kawae bayan ya tashi tsaye Abbas ke ce mashi yakamata yaje yay wanka ya canza kaya don jini ya 6ata mashi gefen hannun shi da gefen rigar shi saima lokacin shi Haisam d'in ya lura yace suje Office d'in Dr ya wanke hannun zuwa anjima yaje yayi wankan Abbas yace to yasan in ba don ta kama dole ba ba yadda za'ai Haisam ya zauna da rigar nan, bayan sunje ya wanke suka nufi d'akin da Fatuu take lokacin da suka shiga jinin da aka saka mata nata shiga jikinta tunda Hajiya ta kalle su sau d'aya ta kauda kai Gwaggo ce tai mashi sannu ta mik'e tace suzo su zauna har yace tay zamanta tace zata shiga toilet ne lokacin Magrib ya yi ta nufi toilet d'in su kuma suka zauna yana ta kallon Fatun can suka had'a ido da Hajiya tana hararar shi ya sunkuyar da kan shi k'asa Abbas dae sai d'an murmushi yake, fitowa gwaggo tay tana gyara hijab d'in jikinta bayan ta daidaita ta kalli Abbas tace suje suyi salla kar lokaci ya shige ya amsa mata da to hannun shi ruk'e dana Haisam suka mik'e suka tafi gwaggo ta kalli Hajiya tana son yi mata magana amman tana jin shakka can dae ta tay k'arfin halin ce mata an fara kiran salla a fad'ace tace tana ji ai d'an murmushi gwaggo tay ta k'ara ce mata ga Hijab nan a jikin kujera ta d'aukko mata tace bata so ai batasa ta ta d'aukko mata ba yadda take Maganar ta d'aure fuska irin tayi fushin nan kwantar da Murya gwaggo tay ta shiga bata hak'uri har saida taga ta d'an saki Fuska ta fara k'ok'arin mik'ewa sannan gwaggon ta nufi gefe ta kwanto kallabinta ta shimfid'a ta kabbara salla, suna fita yace ma Abbas ya tsaya nan yay salla shi bari yaje yayi wanka sai ya dawo Abbas d'in yace to suje tare mana yace No ya tsaya koda za'a buk'aci wani abu sannan yace Ok sukae sallama ya tafi, ana gama sallar Abbas ya koma d'akin nan gwaggo tasa shi ya kira mata Amadu don ta baro wayarta a gida har Hajiya ma bata zo da waya ba a gida ta baro ta tun lokacin da Haisam ya sanar mata zancen cikin Fatuu, bayan ya kira ta fara ringing ya mik'a mata yana d'auka yaji muryar gwaggo ya hau tambayar ta ya Fatuu ko gaida ita bay ba dama tunda suka tafi hankalin shi ba kwance yake ba k'arshe ma kulle shagon yay ya koma gida bayan ya shiga kuma hankalin shi ya k'ara tashi haik'am ganin d'igo d'igon jini a tsakar gidan har zuwa cikin Parlor, saida ya gyara duk inda ya 6aci sannan ya shige d'akin shi ya kwanta cike da zullumi gashi duk yaga wayoyin su a Parlor balle ya kira yaji halin da ake ciki, jin yanayin muryar tashi tace mashi ya kwantar da hankalin shi da Sauk'i sosae ana mata k'arin jini ne cike da damuwa yace mata zasu iya yin Magana tace ai bata kaiga farkawa ba tukun, nan tace mashi ya zubo Abinci a Warmer da plates ya kawo da ruwa sannan ya d'aukko abun salla da buta da kayanta kala d'aya sai bargo ya tambayi Asibitin da suke sai lokacin ta tuna da bai sani ba ta fad'a mashi yace to, Haisam na barin Asibitin G.r.a ya nufa bayan ya shiga Bedroom d'in shi dole wanka ya fara ya zura jallabiya kafin yay sallar Magrib anan cikin dakin don lokacin ta ya shige, bayan ya sallame zaune yay jigum duk ya rasa mike mashi dad'i daka kalle shi zaka fahimci yana cikin damuwa don fuskar shi ta nuna, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin yay Addu'a ya mik'e ya nufi cikin Corridor, sanye cikin wasu k'ananan kayan ya fito fess da shi ya d'auki Car key da wayarshi ya fita, saida ya tsaya yay sayayya mai yawa su lemu da ruwan roba katan katan da uban fruit harda gasassun kaji da balango mai yawa sannan ya wuce Asibitin, bayan ya isa ya parker Motar ya fara d'aukar lemu da ruwan ya shiga dasu lokacin Amadu har ya k'araso yana zaune cikin d'akin yay zugudum sai kallon Fatuu yake Haisam na shigowa ya mik'e da sauri yaje zai amshi abunda ya shigo dashi yana gaishe shi amsawa yay yace ya bashshi yaje Mota akwae wasu ya d'aukko ya amsa da to da sauri ya juya ya fita shima ya k'arasa ciki gwaggo na mashi sannu da zuwa cikin cool voice d'in shi ya amsa ya gaishe da ita kafin ya gaishe da Hajiya dake zaune akan Carpet d'in da Amadu ya kawo gwaggo ta mik'e ta koma gefen gado tace ya zauna, bayan ya zauna d'akin yay tsit Amadu ya dawo ruk'e da manyan ledoji ya aje a gefen inda sauran kayan suke ganin yay tsaye Haisam yace yazo ya zauna mana ya nufi gefen shi ya zauna shiru ta sake biyo baya har aka fara kiran sallar isha lokacin Haisam yace ma gwaggo ga kaya nan nasu ne tay mashi godiya ya mik'e ya fita Amadu ma ya bi bayan shi, bayan sun gama sallar isha ta bud'e ledojin ta d'aukko plate ta fara zuba ma Hajiya koda ta mik'a mata cewa tay bata ci da alama dae ran ta ya 6aci sosae hak'uri ta shiga bata suna haka suka dawo daga Masallaci harda Abbas nan fa ya sa baki aka cigaba da ba Hajiyar hak'uri sannan tace taji zata ci, k'ara zuba wani tay taba Amadu ya kai ma su Abbas harda Fruit d'in shima Amadun ta zuba ma shi kowa ya fara ci banda Haisam da tunda aka kai masu Abbas ya aje a tsakiyar su yay mashi magana sai yace ya fara ci yay zaune shiru idon shi na kallon floor gwaggo ta lura da bai ci hakan yasa tay mashi magana tana lallashin shi kan yaci kar yunwa tay mashi illa dama gashi bai warware sosae ba ga kuma jinin shi an d'iba da yawa jin haka yasa Hajiya ta ta6e baki tace "ai itama wadda ya kwantar bata ci ba waya san ma ko duk yau bata ci komae ba don haka ki rabu dashi" shiru gwaggo tayi shi kuma ya d'aga ido ya kalleta suka had'a ido tana ta tura baki yanayin fuskar shi ne ya d'an canza kamar zai yi murmushi amman bai bayyana ba sai daga baya ya fara ci a hankali don yana jin yunwa sosae kuma d'akin fess yake tamkar ba Asibiti ba ko d'azun gab da Magrib saida aka shigo akai Mopping tiles d'in kasan da bazai ma ci ba, wurin k'arfe tara Dr Habeeb ya shigo ya duba ta ya sanar masu da ta farfad'o don numfashin ta ya dawo bacci take yi yanzu ko wane lokaci zata iya farkawa shi lokacin tashin shi yayi amman akwae Doctor da yazo in da wani abu sai ai mashi Magana ga Nurse nan zata cigaba da kula da ita sukae mashi godiya Abbas da Haisam suka raka shi ita kuma Nurse d'in ta gaishe dasu tay masu ya mai jiki duk suka amsa tace zata tafi amman zata rink'a lek'owa in kuma da wani abu sai ai mata magana tana a Nurses station gwaggo ta amsa da to ta juya ta tafi, bayan wasu mintuna Haisam ya dawo shi kadae ya tsaya a gefe cikin girmamawa yace ma gwaggo su je Abbas na waje zai maida su gida tana jin haka tace mashi a'a Don Allah suje su ita zata tsaya ta kwana tun kan ta rufe baki a harzuk'e Hajiya tace "Yau naga ikon Allah ni Hauwa, shin wai shi d'in ba mijinta bane kuma shine sanadin kwanciyar ta to waya kamata yay jinyar ta dama bashi ba ko kuwa ya ja ma yar Mutane wahala sai kuma yaje yay share share akan gado yana bacci to kuwa bai isa ba shi zai zauna yay jinyar ta duk da kema bai kamata kiyi baccin ba shima Abbas d'in muje ya kaimun dole ya dawo nan ai jinyar ta dashi" tana gama Magana ta fara k'ok'arin mik'ewa duk gwaggo bata ji dad'i ba wllh don Haisam d'in na buk'atar isasshen bacci saidae ba yadda ta iya dole tabi Maganar Hajiyan itama ta mik'e ta d'auki kayan da Amadu ya kawo mata na sawa amman banda su bargon dama Amadu a tsaye yake sukai mashi sallama yana tsaye ya d'aga masu kai sai da ya raka su bakin k'opa yay tsaye har suka bar wurin sannan ya koma ciki, bakin gadon ya nufa ya tsaya hannuwan shi zube cikin Aljihun jeans d'in shi yanata kallonta bazaka iya karantar yanayin fuskar shi ba ya d'an d'auki lokaci a haka kafin yay yar ajiyar zuciya ya kai hannu ya shafi forehead d'in shi kafin ya juya walking slowly ya koma kan kujera ya zauna, suna hawa hanya Hajiya ta amshi wayar Amadu ta kira saude bayan ta d'aga ta gaishe da ita tace mata taga bata ganta a gida ba ko abu ne na gaggawa ya taso shiyasa batai mata ko sallama ba ta fita Sauden tay Addu'ar Allah ya maido ta lafiya tace ai gata nan ma a kan hanya so take tay sauri ta feraye dankali tay Faten shi yaji Alaiyahu sai kuma ta d'ibi yan ciki tay d'an ferfesu karta 6ata lokaci don Allah da sauri ta amsa mata da to ta kashe wayar, su gwaggo aka fara ajewa kopar gida sukai ma Hajiyar saida safe ta amsa ba yabo babu fallasa aka wuce da ita su kuma jiki a sanyaye suka nufi cikin gida gwaggo taso taga tashin Fatun, bayan sun isa gidan Hajiyan sawa tay dole Abbas ya tsaya har aka gama Abincin don ma ba me d'aukar lokaci bane aka zuba a k'ayatattun Warmers Saude ta bi shi dasu har zai fita daga parlon Hajiya ta tsaida shi tace ma Saude ta je ta daukko mosquito spray bayan ta kawo ta ba Abbas d'in tace gashi nan a fesa a d'akin kar sauro ya ciji Fateema ya k'ara mata wata cutar banda wadda suka jaza mata shi dae d'an murmushi kawae yay yasan harda don Haisam ta bada shi yay mata saida safe ya tafi Saude na biye dashi ruk'e da basket d'in Warmers suka nufi Mota, yana shiga ciki sai ga kiran gwaggo tace ya wuce ne yace mata a'a yanzu dae zai tafi tace to don Allah ya d'an tsaya zata bashi kayan Fatuu akai mata in ta farka sai ta canza yace to, lokacin da ya tsaya horn yay Amadu ya fito ruk'e da yar jaka mai d'auke da kayan Fatuu harda undies da pad bayan ya saka a back seat yay mashi saida safe ya juya shi kuma yaja Motar ya tafi, lokacin da isa Asibitin k'arfe goma ta wuce bayan ya Parker ya fito ya bud'e back door ya fiddo basket d'in kayan Abincin da jakar ya rufe ya nufi ciki, Haisam na zaune kan kujeran ya d'an kishingid'a had'i da lumshe ido Abbas d'in ya shigo da yar sallama ya bud'e idon a hankali ya kalle shi Abbas d'in ya d'an yi mashi murmushi ya nufi inda yake, a gaban kujeran ya aje kayan hannun shi ya zauna gefe idon shi akan Haisam yace mashi sannu ya jinjina mashi kai nuna mashi kayan yay yace ga Abinci nan da kayan matar shi an ce inta tashi ya bata ya kuma taimaka mata tay wanka ta canza kaya wani kallo yay mashi Abbas d'in yay dariya kafin ya juya ya kalli Fatuu ya d'an girgiza kai ya juyo yace ma Haisam wai har yanzu bata farka ba ya d'aga mashi kai yace "Allah sarki Mom Zarah wllh na tausaya mata sosae Allah ya bata lafiya" shiru Haisam d'in yay Abbas yace "bazaka amsa ba ko baka so tay saurin samun sauk'i ka maida bugu nan da nan asamo mana twins" still banza yay mashi fuska a d'aure Abbas ya tuntsire da dariya yace "Serious kasan wani rabon na kore wani fa gashi Mom Zarah na fahimci ba ta wasa bace da an bata take amsa" d'an k'ank'ance ido yay yana kallon shi Abbas d'in sai dariya yake can slowly yace ya tashi ya tafi gida dare yayi Abbas d'in yace wato ya ishe shi kenan daga yana taya shi hira ya rage kad'aici yace mashi ya gode bacci yake ji ne Abbas d'in ya fara kokarin mik'ewa yana fad'in ai shikenan, tare suka fito saida ya raka shi har bakin Mota Abbas ya bud'e ya shige driver seat yay mashi saida safe ya juya ya koma ciki, yana shiga d'akin ya k'ulle kopar ya nufi kujerar ya zauna idon shi akan Fatuu can kuma ya kai hannu ya dauki wayar shi ya fara lallatsawa bayan wani lokaci ya ajeta don bacci yake ji daurewa kawae yake mik'ewa yay ya d'auki bargo ya shimfid'a a saman kujerar kafin ya kwanta saidae bata d'auke tsawon shi ba gaba d'aya a hankali ya fara lumshe ido yana yi yana bud'ewa har baccin ya d'auke shi, Misalin k'arfe sha d'aya da yan mintuna ta fara mutsu mutsun farkawa slowly ta fara bud'e idanuwan ta tana yi tana sake lumshe su a haka har ta bud'e su gaba d'aya akan ceiling d'in d'akin ta k'ura ma Fanka ido tana kokarin gano a ina take, d'ago hannuwanta tay duka jin su kaman ba daidai ba nan idonta ya sauka akan kanular dake a jikin kowanne nan take ta gane inda take, sauke su tay ta fara juya kan ta a hankali tana bin d'akin da kallo har idanunta suka sauka akan Haisam da idanun shi ke a rufe wani irin bugu kirjinta yay ta k'ura mashi ido lokaci guda abubuwan da suka faru suka fara dawo mata har zuwa lokacin data san shi Mijinta ne ta shiga tunanin ashe duk abubuwan da yake mata Saboda wannan dalilin ne ita bata sani ba tay wani tunani na daban a hankali ta saki d'an murmushi tana cigaba da kallon shi zuciyar ta na raya mata yanzun nan shi Mijinta ne wani irin dad'i take ji a cikin ranta can kuma ta tuno da Maganganun da ta gaggaya mashi a G.r.a nan take yanayin fuskar ta ya sauya damuwa ta bayyana tamkar yaji ajikin shi tana kallon shi ya fara motsi yana kokarin bud'e ido sam ta kasa janye idanunta kirjinta sai bugu yake da sauri da sauri a hankali ya bud'e idanun suka sauka akan ta ya bita da kallo suka zuba ma juna ido........... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2053* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ...........kasa jurewa tay a hankali ta maida idonta k'asa shima maida nashi yay ya lumshe bayan wani lokaci ta d'ago ta sake kallon shi har lokacin bai bud'e idanun nashi ba hakanan sai taji wani iri don kallon da ta ga yana yi mata ba kalan wanda yake mata bane a kwanakin baya kafin hakan ta faru, maida idon tay tana kallon gaban ta cikin ran ta tana k'ara tariyo abubuwan da suka faru gaban ta ne ya fad'i tunowa da jinin data gani nan ta fara kokonton anya cikin bai fita ba kuwa lokaci guda ta yanke ta san ma zai yi wuya in yana nan, wani iri taji damuwa ta bayyana kan fuskar ta sai kuma ta hau yin tunanin halin da gwaggo da Hajiya suke ciki tana haka taji fitsari ya matseta ta fara kokarin yunk'urawa ta tashi dama an riga an cire mata k'arin jinin da aka saka mata na farko a can gefe ta hango gyalenta dama yana jikinta aka zo da ita Saboda rolling d'in shi tay sai bayan an kawo ta d'akin ya kwance, bayan ta yafa gyalen saman kanta zuro k'afafun ta tay a hankali ta saukko daga saman gadon wani irin fayau taji ta kwata kwata ba k'arfi a jikinta ga juwa na niyyar kwasar ta ba shiri ta koma ta zauna tasa tafin hannun ta guda ta dafe forehead d'inta duk Haisam na kallonta don tunda ta fara k'ok'arin saukkowa ya bud'e ido jin mutsu mutsun da take, bin ta yay da kallo ba tare da ta sani ba can ya yunk'ura ya tashi tsaye walking slowly ya nufe ta duk bata sani ba har saida taji k'amshin shi jikin shi ya cika mata hanci sannan ta d'ago da fuskar ta da d'an sauri idanunta suka sauka a cikin nashi wani irin bugu kirjinta yay ta kafe shi da ido had'i da d'an motsa baki kamar zata ce wani abu amman ta kasa furta komae Slowly taji cool voice d'in shi ya furta "Let me Help" ya mik'a mata hannu duk tayi tsuru tsuru kamar mara gaskiya ta kai hannu a d'arare ta kama santalelen hannun nashi jajir dashi ga taushi kai kace ba hannun babban namiji ba don kuwa banda yanayin halittar fata shi kan shi hannun yana shan tsadaddun mayukan gyara masu saka taushi, bayan ta mik'e tsaye zame hannun na shi yay ya zagaya dashi ya tallabo Shoulders d'in ta suka fara tafiya fuskarta a k'asa gaban ta naci gaba bugawa har suka isa bakin kopar toilet d'in sannan ya dakata ya zame hannun nashi ta d'an kalle shi sai taji yace "Can u....or I should call Nurse?" d'an girgiza kai tay a hankali tace zata iya shiru bai ce komae ba ta juyar da fuskarta ta tura ta shige ta maido k'opar, toilet d'in tsaf kai kace bana asibiti ba duk da ba bathtub amman har heater ta ruwan zafi akwai da shower, butar data gani wadda gwaggo tasa Amadu ya kawo ta d'auka ta tari ruwan zafi daidai yadda zafin zai mata, lokacin data tattare rigarta gabanta ne ya fad'i ganin cinyoyinta jage jage da jini bata yi mamakin rashin ganin pant d'in data sa ba don tasan a ina take zai yuwu an cire shi ne, jiki a mace ta duk'a ta fara yin fitsarin bayan ta gama tay amfani da ruwan wurin wanke k'asan nata sosae bayan ta gama ta mik'e tsaye da k'yar, tunanin yakamata tay wanka ta shiga yi don tasan duk jini ne a jikin rigar don ma tana bak'a saidae bata san kuma ko akwai wasu kayan da zata canza ba, matsawa tay ta jingina da bango tay shiru sam ta kasa karantar yanayin da ta ga fuskar Haisam don sai take ganin kaman yana d'aure fuska, tana ta tsaye ta rasa mike mata dad'i gashi bata san ya zata yi ba tana son yin wanka amman bata san ko akwae kaya ba kuma sai take ta jin fargabar fita tana haka taji an yi knocking kopar har saida kirjinta ya d'an buga damm da sauri ta kai ido kan kopar k'ara knocking d'in akai ta nufi kopar cikin rashin k'arfin jiki tasa hannu a hankali ta bud'e tay arba da Fuskar shi, bin shi tay da ido ya mik'o mata abun hannun shi wanda towel ne da soap dish ta kai hannu ta amsa murya k'asa k'asa tace mashi ta gode bai ce komai ba ya juya itama ta koma ciki, yana bata kayan waje ya nufa yaje yay ma Nurse Magana kan azo a gyara mata bed har ya dawo bata fito ba ya zauna kan kujera yana nan aka zo aka gyara gadon aka canza Bedsheet can ya tuna da Magungunan da Dr Habeeb ya tura pharmacy don yace akwae yuwuwar ba sai an yi mata wankin ciki ba don yana tunanin komae ya fito sakamakon jinin da ya zuba sosae zuwa washe gari za'ai mata scanning don a tabbatar mik'ewa yay ya tafi ya amso, bayan ta gama wankan tsaye tay ta kasa fita da towel d'in jikinta wanda iyakar shi tsakiyar cinyoyin ta, tana ta tsayuwa gashi jiki ba kwari can dae ta nufi kopar saida tay d'an jimm kafin hannu na rawa ta kama handle d'in ta bud'e sai dae tana sa kai taga d'akin wayam ba kowa wani sanyi taji ta shiga ta nufi gadon da taga an gyara mata shi zaunawa tay tana ta yan kalle kalle ta hango jakar kayanta a gaban drawer d'in gadon ta tashi ta d'aukko ta a gefen gadon ta d'aurata ta bud'e, hannu ta kai tana d'an d'aga kayan kafin ta fiddo wata doguwar rigar material ta aje gefe ta ciro pant da pad data gani suma ta aje tunanin ko ta koma toilet tasa kayan ta shiga yi wata zuciyar ta raya mata tunda ita kadae ce ta sa anan mana k'ilan har ta gama bai shigo ba, yin wannan tunanin yasa da sauri ta bud'e pad d'in ta ciro wadda zatai amfani da ita tasa a jikin pant d'in bayan ta gama ta saukko daga saman gadon ta zura pant d'in tana kokarin sanyawa taji an turo kopar aikuwa da sauri ta d'ago ta kalli kopar ba tare da ta ankare ba kuma towel d'in ya kwance Saboda d'agowar da tayi ba shiri nan take boobs d'in ta suka bayyana duk ta dabarbarce don kuwa idon shi na akanta ganin haka yasa da sauri ya koma yaja mata kopar, ta d'ago da towel d'in da sauri had'i da dafe k'irji tana kallon kopar kafin a kasalance ta duk'a taci gaba da sakawa bayan ta gama ta zura doguwar rigar ta fiddo hula ta saka ta zuge jakar har ta koma ta zauna sai kuma ta mik'e ta d'auki towel d'in da ledar da ta ciro pad da yan takardun ta nufi toilet da ganin yadda take tafiyar jikinta sam ba kwari, bayan ta dawo still bai shigo ba ta koma bakin gadon ta zauna tana facing kopar tama rasa tunanin da zatayi tay zuru sai kikkafta ido take tana haka ya turo kopar da yar sallama ya shigo suka had'a ido a hankali ta amsa kafin ta maida idonta k'asa da sauri ta fara d'an wasa da yatsun ta, wurin gadon ya nufa a saman yar drawer d'in gefe ya d'aura ledar drugs d'in ya juyo ya d'an kalle ta kan ta a k'asa kaman yana son cewa wani abu ji tay a jikinta ita yake kallo ta d'an d'ago a hankali suka had'a ido taji yace "How are u feeling?" a sanyaye tace "Alhamdulillah da Sauk'i" shiru bai ce komae ba can taji yace "are u done with this?" jin tambayar yasa ta kai idon ta kan jakar kayan da ke gefen ta kafin ta kalle shi ta d'aga kai alamar eh ta gama amfani da ita hannu ya kai ya d'auke ta ya maida ita inda take da, duk'awa yay wurin kayan Abincin ya d'auki plate da spoon sai bottle water ya mik'e ya nufi window d'in d'akin bayan ya zuge net d'in jiki ya fara d'auraye su Fatuu nata kallon shi har ya gama ya rufe ruwan tana ganin zai juyo ta maida idonta k'asa ya dawo ya tsugunna gaban basket d'in Warmers masu d'auke da abincin ya fara bud'ewa, Faten dankalin ya zuba ya saka spoon d'in kafin ya mik'e ya kai mata ta mik'a hannu ta amsa nan ma saida ta furta mashi ta gode bai ce komae ba ya juya tabi shi da kallo, rufe warmer d'in yay ya koma kan kujerar ya zauna had'i da jingina bayan shi ya d'an d'age kan shi, gaba d'aya jikinta ya mutu Saboda canjin da ta gani a tattare da shi da k'yar ta d'auki spoon d'in ta fara ci duk yadda Abincin yay mata kyau a fuska sam ta kasa jin dad'in shi a baki hakanan dae take ci kad'an kad'an saida taci kaman rabi sannan ta tashi zata maida wurin kayan Abincin lokacin ya sauke fuskar idanun shi suka sauka a kan ta wani kallo ya jefa mata ta sadda kanta k'asa cike da bada umarni taji yace mata ta cinye shi duka d'agowa tay ta kalle shi still kallon dae yake mata jiki a sa6ule ta koma ta zauna don sai taga kaman ma hararar ta yake, ba yadda ta iya haka ta dingi turawa ba don tana jin dad'in shi ba har ta samu ta cinye tana niyyar mik'ewa taga ya taso yazo gabanta, amsar plate d'in yay ya maida ya k'ara d'aukar wani yaje ya wanko shi bayan ya dawo ya zuba mata farfesun yan cikin shima ya mik'a mata ta amsa yanzu bata ce mashi ta goden ba saidae ta d'an kalle shi, bayan ya juya plate d'in da ta 6ata ya d'aukka yaje ya wanko shi ya maido, kujerar ya koma ya zauna ya k'ara d'age kan kaman d'azu, sosae farfesun yay mata dad'i saidae damuwa ta hana taci shi sosae don gani take kaman dai da gaske fushin yake, bayan ta d'an sha kawai sai ta aje spoon d'in tsam ta mik'e zata aje shima sai gashi ya sake juyowa ya kalleta nan take tay pause tana kallon shi fuska a yamutse daga inda yake taji yace "Eat it up!" d'an yamutsa fuska tay cikin rawar murya tace "na k'oshi" shiru bai ce komae ba idon shi akanta itama ta kasa motsawa balle ta aje can ya mik'e ya nufo ta yazo daga gabanta ya tsaya suna facing juna abu ta rink'a had'iya ta sak'a d'ayan hannun da bada shi ta ruk'e plate d'in ba gefen wuyanta tana d'an sosa wurin kasa jure kallon shi tay ta maida idon t k'asa, hannu taga ya mik'o ya amshi plate d'in ta kalle shi da kai yay mata alamar ta zauna ta koma gefen gadon kawae sai gani tay shima ya zauna a gefenta ya fara d'ibowa zai bata ta yamutsa fuska idanunta har sun ciko tace mashi ta k'oshi wani kallo ya wurga mata ba shiri ta bud'e bakin ya zuba mata ta fara taunawa tana kikkafta ido, haka yaci gaba da bata har ta dai ta saki Fuska taci gaba da ci tana yi tana satar kallon shi wani lokacin su had'a ido sai tay saurin janye idon ga k'amshin shi da ya gama cikata, saida ta cinye shi duka sannan ya mik'e ya maida plate d'in ya d'aukko mata ruwa bayan ya bud'e mata ya mik'a mata ta amsa tasha da d'an yawa sannan ta cire robar daga bakinta ta mik'a mashi ya amsa ya rufe, ledar fruit ya bud'e suma ya zuba a plate d'in ya mik'a mata k'in amsa tay ya wani d'aure fuska kawae sai ta saka mashi kuka still yay yana kallon ta komi yay mata na kuka shida ko tanka mata bai yi ba cike da shagwa6a duk da ita ba da niyyar shagwabar take yi ba nature d'in ta ne haka taci gaba da yamutsa fuska tana d'an ta6e baki kalan yadda take kuka tun yarinta tana ta faman kikkafta ido kwalla na gangaro mata shi dai kallon ta kawai yake ga abu ta barshi dashi a hannu sigh yay ya d'age gira yace mata "na buge ki ne?" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ya sake cewa "to wannan d'in na miye?" yay mata nuni da k'wallan dake zubawa da ido shiru tay ta sadda kanta k'asa har saida yace ba magana yake mata bane sannan ta d'ago tana d'an share kwallan cikin muryar kuka tace "ba komae" shiru bai ce komae ba sai ya koma gefen ta inda ya tashi ya sake zaunawa ya d'aukko 6ararrar ayaba zai bata tana ta goge kwalla ba tare data kalle shi ba hakan yasa bata san yana mik'o mata ba saida taji yace "FATUU" damm k'irjinta ya buga a ranta ta maimaita sunan daya kira ta dashi don tunda yasan sunanta bai ta6a kiran ta da hakan ba sai yau nan take jikinta yay lakwas tamkar an watsa ma kaza gishiri a sa6ule ta kai idon ta gare shi taga ayabar da yake mik'o mata a hankali ta bud'e baki ta d'an gutsira ta fara taunawa, haka yaci gaba da bata har saida ta shanye komae ya maida plate d'in ya d'aukko ledan magungunan daya aje da ruwa ya sake zaunawa suma ya shiga 6aro mata yana mik'a mata tana sha da ruwan har ta gama dama bata gudun magani allura ce wani lokacin ake fama da ita shima kafin ta girma haka yanzu saidae in za'a yi mata ta cije baki da runtse ido, bayan ya maida komae duk plates d'in ya wanko su ya bud'e warmer d'in ya zuba Abincin don shima yunwa yake ji bayan ya saka spoon ya nufi kujera tana ta bin shi da ido har ya zauna a nutse ya soma ci, Allah sarki true love sai kawae taji tausayin shi ya kamata ta shiga tunanin k'ilan ma ya dad'e bai ci Abincin ba tunda hakanan ma tasan ba ci yake sosae ba, tana ta zaune tana kallon duk wani motsi da yake wurin cin Abincin kama daga kai cokalin ya d'ebo zuwa kai wa bakin shi saida ya d'an d'auki lokaci da farawa tukunna ba tare data ankare ba taga ya juyo sun had'a ido duk sai ta kame kanta sum sum kaman munafuka ta haye gadon ta kwanta had'i da juya mashi baya, cigaba da cin Abincin yay har ya gama ya tashi ya d'ebo farfesun bada yawa ba shima ya sha da ya gama ya je ya wanke abun da 6ata ya d'auki bottle water ya koma kan kujeran ya bud'e yasha da d'an yawa bayan ya gama ya rufe murfin ya ajeta a gefe ya maida bayan shi jikin kujerar ya kai idon shi kan Fatuu data duk'unk'une wuri d'aya ya d'an d'auki lokaci yana kallon ta kafin ya janye idon ya kai hannu ya d'auki wayar shi ya fara latsawa can kuma ya aje ya mik'e bargon daya shimfid'a ya d'auka ya nufeta yana zuwa bakin gadon ya bud'e shi ya lullu6a mata lokacin idon ta biyu tay ma bango tsuru taji ya rufa mata, lumshe ido tay yana daga abunda ke k'ara mata k'aunar Haisam wato sanin yakamata don kuwa kaman yasan sanyi take ji kuma ta rasa yadda zata sanar mashi, yana gama rufa mata wayar shi ta fara ringing ya nufi inda take bayan ya zauna ya kai hannu ya daukko sunan daya sa ma Fanan ya bayyana akan Screen yasan su can gari ya waye, picking yay ya kara ta a kunne tun kafin tace wani abu yace mata "Good Morning" cikin sigar shagwa6a ta amsa mashi ta tambaye shi ya akai bai yi bacci ba yace mata yayi farkawa yay da bud'ar bakinta sai cewa tay wai ba dae yana soyayya da wata bane ta waya d'an guntun murmushi yay yace mata ai da taji yana waya ko tace ai wai ko chat fuska a sake yace mata yana wani aiki ne tace mashi Ok, tambayar shi tay mai jiki yace mata ya samu sauk'i sosae shima ta tambayi na shi yace ya warke cike da shagwa6a tace "so when are u coming back, serious am missing my husband ina daurewa ne kawae" d'an murmushin da ta ji sautin shi yay kawae tace "seems like u'r not missing me babe" sigh yay yace waya fad'i mata tace gashi nan ta fad'a mashi tayi missing nashi but bai nuna shima yana nata ba, yana murmushi yace ai abunda ta sani ne dole yayi so ba sai ya fad'a ba, d'an murmushi tay tace tama manta waye mijin nata, tambayarta yay waye shi tana yar dariya tace wanda magana ke ma wuya d'an Murmushin gefe yay kawae, "I asked when are coming back baka fad'a man ba" shiru ya d'an yi kafin yace mata ya kusa yanzu yana Katsina ne da alamun mamaki ta tambayi mi yaje yi Katsina kuma yace ya rako Hajiya ne sai kuma wani aiki ya rike shi a shagwa6e tace to yanzu har sai yaushe kenan yana murmushi yace "Don't worry I will come back soon" da sauri tace "not soon babe soonest in ba haka ba zan zo ne nan" yar dariya yay har hak'oran sa suka d'an bayyana yace mata aikin nata fa tace shima ai yana aikin ko yace ai shi yana da strong reason Dad d'in shi ke bai lafiya, "But tun kafin ya fara ciwo ka taho ai" yace ai wannan ya nemi permission ne sai kuma ya k'ara nema yanzu Saboda ciwon kuma ko daga nan zai iya yin wani aikin tace itama sai ta nema ai tana da babban dalili tunda wurin mijinta zata zo yace banda wanda aka bata taje Germany tana yar dariya tace zata k'ara nema ne kaman yadda shima yay, nan yace mata kar ta damu zai dawo bada dad'ewa ba tace Ok, suna cikin wayan ta tambaye shi Zarah har saida ya d'aga ido ya kallo Fatuu kafin ya bata amsa da tana lafiya tace ai ta yada ita ko waya ta manta last da sukai itace ma ke mata magana ta WhatsApp wani lokacin sigh yay yace mata tasan yanayin karatun da take may be bata samun isashshen time ne tace hakane Allah ya bada sa'a slowly ya amsa da Ameen, tun dae yana wayan a zaune har ta kai ya d'an kishin gida ya aje wayan a hannun kujera yasa speaker saidae ya rage volume dama baida juriyar ya kafa waya a kunne yay tayi, duk wannan abun idon Fatuu biyu ta ji tun lokacin da ya fara yin wayan saidae kwata kwata bata jin mi yake fad'a don dama bai d'aga murya ko a waya balle kuma da yake da Sweetheart d'in shi yake wayar, duk da Fatuu bata gane da ita bane amman ran ta ya bata itace, runtse idonta tay ta shiga jefa ma kan ta tambayoyin da bata da amsar su, tambayar farko wadda tafi d'aure mata kai itace yanda akai Ya Haisam ya aureta ba kamar data ji gwaggo tace dalilin fasa aurenta da Khalid kenan wanda ita dae tasan tun bayan data je ruga sau d'aya ma su kai waya da shi har sai bayan da suka dawo nan ta ayyana ashe ranar da sukai Vedio call da yace zai ga fushin da take dashi ita matar shi ce, tsananin mamaki ne ya cika ta sai kuma ta d'an yi murmushi, tambaya ta biyu data sake jefa ma kanta itace ya matsayin auren yake tunda ba wanda ya bayyana mata har sai yanzu da Al'amarin nan ya faru shin auren zai d'ore ko kuwa ba zai d'ore ba don ta fahimci kamar ba don hakan aka yi shi ba, gashi kamar yana fushi da ita kuma tasan don abunda ya faru ne ga maganganun data je ta fad'a mashi har tak'i d'aga wayar shi wanda tasan da ta d'aga kiran nashi da hakan bai faru ba, tambaya ta k'arshe da har saida gaban ta ya fad'i sosae itace yanzu in auren zai d'ore ne ya Aunty Fanan zata ji anya zata amince da ita matsayin KISHIYA tunda ta tabbatar itama ba ta san da auren ba kaman yadda ko Hajiya bata sani ba wata zuciyar ta raya mata ga dangin su kuma suma ba lalle ma su amince ba, wani irin sanyi jikinta yay ta raya ita dama ta dad'e da fahimtar Ya Haisam ya fi k'arfinta ba iya samun shi zatai matsayin miji ba hakanan zuciyarta ke azabtar da ita da son shi duk kuwa yadda taso ta cire shi abun ya gagara duk aje a dawo son shi na nan mak'ale a zuciyar, wasu siraran hawaye ne suka fara gangaro mata masu d'umi taci gaba da tunane tunane a haka bacci ya d'auketa, shima tuni sukai sallama da Fanan d'in ya nuna mata bacci yake ji, gaba d'aya kwanciyar bata mashi dad'i dama d'azun harda k'arin da bargo ne ya samu har bacci ya d'auke shi yanzu kuwa ji yake ya takura ga kayan jikin shi daya kwanta dasu su kan su a takure yake da su don bai saba kwana da kaya ba bai ma tunanin ya ta6a kwana da kaya haka, hakanan dae ya d'aure yana ta faman gyara kwanciya akai akai, bai fesa maganin daya gani a cikin basket d'in ba don ba sauro a d'akin tunda akwae Ac ga kuma fanka sannan windows d'in akwae Net, sai can dare ya raba ya samu bacci ya d'auke shi, A kan kunnan shi aka fara kiran farko na sallar Asuba hakan yasa ya tashi zaune ya kai idon shi kan Fatuu dake ta bacci, d'auke idon yay ya shiga tunanin yadda zai yi salla don bai using wani toilet ba wanda ya saba amfani ba balle kuma na Asibiti gashi bai yuwuwa yace zai tafi gida ya barta can yay deciding ya shiga na cikin d'akin kawae ya mik'e ya nufi toilet d'in, after few minutes ya fito harda Alwala yayo ya koma wurin kujeran ya ciro prayer mat dake jikin ta ya shimfid'a ya kabbara raka'atanil fajr bayan ya sallame zaune yay yana tasbih ta hanyar yin amfani da wayar shi har lokacin salla yayi sannan ya mik'e saida yay d'an jimm yana kallon gadon sai kuma ya juya ya tafi, har aka gama sallar ya dawo bata farka ba ya koma kan kujerar ya zauna ya bud'e wayar shi ya fara yin Azkar bayan ya gama ya ajiye wayar ya d'an zamo jikin shi daga kan Sofa d'in ya d'age kai had'i da lumshe ido yana haka yaji motsin ta slowly ya sauke kan ya kai idon shi kan gadon lokacin ta tashi zaune suna had'a ido tay saurin maida kanta k'asa, "Do u need anything?" taji cool voice d'in shi yana tambaya daga inda yake d'agowa tay ta kalle shi a sanyaye tace toilet zata je d'an shiru yay sai kuma yace "Do u need Help?" Girgiza mashi kai tay alamar a'a bai ce komae ba ta fara kokarin saukkowa daga kan gadon, ba laifi taji k'arfin jikin ba kaman jiya ba idon shi a kan ta har ta shige cikin toilet d'in, bata d'au lokaci ba ta fito idon ta a k'asa ta nufi gadon ta zauna a gefe kan ta a sadde, pad da pant take son ta d'auka don ta canza amman ta kasa d'auka tana haka taji yace "U need to take bath" da sauri ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido kaman yar k'adangaruwa ta d'aga mashi kai sai kuma murya na rawa ta gaishe da shi ya amsa had'i da tambayar jikin ta tace da Sauk'i sosae ya d'aga mata kai kawae ya janye idon shi daga kallon ta har yanzu dae canjin da ta gani a fuskar tashi yana nan, mik'ewa tay ta nufi inda jakar kayan take ta duk'a bayan ta bud'e ta d'auki abunda take buk'ata ta rufe jakar ta mik'e tana rungume da su ta nufi Toilet d'in still kallon ya bita dashi har ta shige, saida ta gama kimtsawa a ciki sannan ta fito bata gan shi a cikin d'akin ba saidae attender dake Mopping sarkin tsafta har yaje ya kira azo a goge suna had'a ido da matar Fatun ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata ya jiki tace da Sauk'i ta nufi gadon ta haye ita kuma bayan ta gama har kujerar ta kakka6e ta nufi cikin toilet d'in don ta gyara shi tana shiga sai gata ta fito ruk'e da dustbin ta yi hanyar fita, saida aka gama gyara d'akin fess sannan ya shigo lokacin Fatuu na zaune ta jingina da kan gadon ta bishi da ido har ya zauna sannan ta janye idon, tsit kake ji sai kace ba mutane a d'akin ko kuma kurame ne a ciki bayan d'an wani lokaci ya fara tunanin ya samo mata wani abu ta ci sai dai kuma yasan yayi safiya da yawa ko ya fita ba lalle ya samo wani abu ba hakan yasa shi tunanin ya bari garin ya d'an k'ara wayewa, suna ta zaune can ta d'an saci kallon shi karaf suka had'a ido kasa janyewa tay shima kallon nata yake kawai sai ji tay yace "kina jin yunwa ne?" tambayar ma saida taso ta d'an bata dariya amman ba halin yi da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a sai kuma kamar mara gaskiya ta zame ta kwanta ta juya mashi baya don ta fahimci Saboda kallon data yi mashi ne yasa shi yi mata tambayar bin bayan ta yay da kallo can kuma ya d'age kan had'i da lumshe ido, karfe bakwae saura yan mintuna aka kwankwasa kopar ya sauke kan ya kai idon shi kan kopar saida aka k'ara knocking d'in sannan yace a shigo kopan a bud'e take aka turo Amadu ne ya fara shigowa yana ruk'e da basket mai d'auke da kayan abinci gwaggo na biye da shi itama tana ruk'e da wasu kayan harda bucket da kujera yar tsugunno ta roba yana ganin su ya mik'e tsaye fuskar shi a sake yake kallon su suka nufo ciki suma duk suna yi mashi murmushi, a gefen gadon ya aje basket d'in gwaggo dake gefe da murmushi tace "Sannu d'ana Haisam ya kwanan Asibiti" d'an murmushi yay yace mata Alhamdulillah had'i da gaishe da ita bayan ta amsa tace "Amman dae nasan baka samu yin bacci ba kwanan Asibiti akwae takura gashi ba'a shirya mashi ba" still murmushin yake yace mata yayi bacci yar dariya tay tace ya dae fad'a ne Amadu ya gaishe dashi yayi mashi ya mai jiki ya amsa, ganin yayi tsaye tace mashi yay zaman shi zata zauna a gefen gadon ya koma yace ma Amadu yazo ya zauna itama gwaggo ta zauna idonta akan Fatuu dake ta bacci ta lullu6e tana son ta tambayi ko ta farka amman ta kasa Saboda kunya can dae ta kalle shi tana murmushi tace "ya mai jikin?" Kallonta yay calmly ya furta "da Sauk'i sosae tun jiyan around 11 ta farka yanzu bata dad'e data koma ba" wani sanyi gwaggo taji cikin ranta Amadu ma har saida yay d'an murmushin jin dad'i gwaggon tace Allah ya k'ara lafiya duk suka amsa da Amin shiru ta biyo baya, bayan d'an wani lokaci gwaggo tace ma Haisam ko a had'a mashi breakfast taga safiya ce sosae bata san ko zai ci ba yace mata a'a tace to ko tea ne a had'a mashi ya gasa cikin shi fuska a sake yace mata ba zai iya sha ba bai wanke baki ba tana murmushi ta jinjina kai kawai don ta san shi sarkin tsafta ne da gaske ba zai iya cin ba, Shiru suka k'ara yi Amadu na latsa waya ita kuma gwaggo kanta a k'asa tana yi tana d'an juyawa ta kalli Fatuu can ta juya ta kalli Haisam daya had'e hannuwan shi ya kifa goshin shi tace "d'ana Haisam Don Allah ka tashi kaje gida ko ka samu ka huta sosae" slowly ya d'ago ya d'an kalleta suka had'a ido sai kuma ya kawar da idon bai ce mata komae ba dae hakan yasa ta k'ara ce mashi yaje ba wani abu ai tunda gasu sun zo, a hankali ya furta to tare da yin godiya ya mik'e bayan ya d'auki wayar shi sukai sallama ya nufi kopa ya fita, "Bawan Allah ni tausayi ma ya bani da gani bai samu isashshen bacci ba" Amadu ne yay Maganar gwaggo tace "taya zai samu yin isashshen bacci a nan duk da dai kamawa take amman nasan da wuya in ya ta6a jinyar wani haka suda suka saba kai mara lafiya K'asar waje shiyasa wllh ban so ya kwana ba don dole zai takura to ba yadda zan yi da Hajiya" shiru Amadu yay can ta mik'e ta cire hijabin jikinta ta d'auki bucket d'in da kujerar ta nufi toilet, bayan ta shiga fess ta gan shi dama niyyarta in yana buk'atar gyara sai ta gyara anan taga rigar Fatuu data cire jiya da undi ta d'aukko su ta saka acikin bucket d'in don ta wanke, Amadu na zaune ruk'e da wayar yana lallatsawa kaman daga sama yaji muryar Fatuu ta kira sunan shi da sauri ya d'aga kai ya kalli gadon suka had'a ido da ita ta tashi zaune gaba d'aya hankalin shi na akan wayar har baiji motsin tashin ta ba, mik'ewa yay ya nufi gadon yana washe baki ya zauna a gefe itama murmushi take mashi cike da farin ciki yace "Sannu kin tashi?" Kai ta d'aga mashi a sanyaye ta tambayi yaushe ya zo yace basu dad'e ba harda gwaggo tana cikin toilet ta d'aga mashi kai ya tambayi ya jikin nata tace da Sauk'i sosae yanayin fuskar shi ne ya canza "ashe haka abu ya faru ni ban sani ba koda nazo lokacin baki farka ba saida muka koma gida da daddare gwaggo ke sanar dani" shiru tay ta zuba mashi ido can yaji tace "Kawu Amadu miyasa baka ta6a fad'a man zancen auren ba duk da kasan ni ban 6oye maka abu" yadda tay Maganar kaman zatai kuka shima yanayin fuskar tashi ne ya sauya zuwa yanayin damuwa ya kai hannu ya kamo hannunta guda yace "ba hakanan na k'i fad'a maki ba gwaggo ce ta hana tace kar in sake inyi maki Maganar shine dalili" d'an ta6e baki tay kwallan da suka taru suka zubo sharr da sauri ya kai hannu yana goge mata yana bata hak'uri had'i da nuna mata komi ya faru haka Allah ya k'addara suna haka gwaggo ta bud'e kopar toilet d'in ta fito............ _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2054* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ...........Nufo cikin d'akin tay tana d'an yarfe ruwan fuskarta da alama wanke ta tay, a gefen gadon ta tsaya idon ta akan Fatuu da itama ta kafeta da nata idanun, da d'an murmushi tace "sannu kin tashi" itama murmushin take mata ta d'aga mata kai kafin ta gaishe da ita ta amsa tay mata ya jiki, shiru suka d'an yi suna ta kallon juna Amadu na kallon su da murmushi yar ajiyar zuciya gwaggo tay tace mata ga breakfast nan kai ta k'ara d'aga mata, kina iya saukkowa ne?" Gwaggo ta tambaya a hankali tace mata eh ta fara matsowa zuwa bakin gadon ta zuro da kafafun ta har zata mik'e gwaggon ta dakatar da ita tace yakamata a k'ulle gashin ta kai hannu ta fara tattara mata shi bayan ta gama ta juya cikin kayanta ta d'aukko mata brush da toothpaste ta tambayeta zata iya zuwa toilet nan ma kai ta d'aga mata alamar zata iya amman duk da haka saida ta kai hannu ta d'agota ta nufi toilet d'in da ita Amadu nata kallon su cike da k'auna, Bayan da Haisam ya fito yana shiga reception zai nufi hanyar fita wata mata sanye da farar doguwar rigar uniform kanta d'aure da kallabi ba hijab a jikinta ta sha gaban Haisam tana Fad'in "wa nike gani kaman ango?" dakatawa yay ya kai idon shi kan ta nan take ya ganeta mama ce wadda ta duba Fatuu lokacin da abun ya faru da d'an murmushi ya gaishe da ita yay mata ya aiki bayan ta amsa fuska a d'age tana kallon shi ta cikin glasses d'inta tace "wani ke bai lafiya ko kai?" Fuska a sake yace mata ita matar tashi ya kawo tambayar shi tay Mike damun ta kuma yace "She had a miscarriage" waro ido mama tay "Subhanallahi yaushe hakan ya faru?" Ya bata amsa da jiya ta tambayi yanayin cikin yace mata just 1month ne ruk'e ha6a tay "Oh kace dai tun wannan karan battan aka samu abu bai dad'i ba kuwa" shi dae d'an murmushi kawae yay tambayar inda Fatun take tayi ya fad'i mata tana Amenity da room no d'in ta jajanta mashi kafin sukai sallama ya tafi, tare suka fito bayan tayi brush d'in saida Gwaggo tace ko zatai wanka tace tayi d'azun da asuba, bayan sun fito kan kujera gwaggo ta sata ta zauna ta fara had'a mata breakfast, kakkauran tea da slice bread sai wainar k'wai ta had'o mata ta aje a gefen ta tace ta ci ta k'oshi kallonta tay da d'an murmushi tace mata ta gode, kallon Amadu da har lokacin yana a bakin gadon Gwaggo tay ta tambaye shi yanzu zai yi Karin kumallon ta had'a mashi yace a'a ta bari sai d'an anjima gefen Fatuu ta koma ta zauna cikin sanyin murya Fatun tace ita ba yanzu zata ci ba tana mata murmushi tace sai ta gama, a hankali take cin Abincin akai akai gwaggo ke kai idonta kan ta tay mata sannu ita kuma sai tay d'an murmushi ta amsa suna haka aka turo k'opar Mama ce ta shigo da sallama idonta akan su Gwaggo dake zaune ta amsa mata tunda Fatuu ta kalleta ta gane ta, k'arasowa ciki tay gwaggo na kokarin mik'ewa tace tay zamanta su ai sun saba da tsayuwa, gaisawa suka shiga yi Amadu ma ya gaishe da ita ta amsa kafin ta maido idonta kan Gwaggo tay mata ya mai jiki da fara'a tace mata gata nan da Sauk'i ta maida kallon ta kan Fatuu cike da jajantawa tace "Sannu Amarya ai yanzu na had'u da Angon naki zai fita shine yake sanar da ni kina nan kin samu miscarriage" wani abu Fatuu ta had'iya tay mata zuru da ido Gwaggo kuwa kan ta ne ya kulle cikin ranta ta hau mamakin jin sunan data kira Fatuu Saboda a tunanin ta iya su kadae suka san da Maganar auren to ya akai ita ta sani gashi ba sanin ta ma tayi ba ko a yan'uwan Haisam d'in, kamar Mama tasan zancen zucin da Gwaggon ke yi ta kalleta tace "ai bayan auren nan ya kawo mana ita magashiyan cikin mawuyacin hali hankalin shi a tashe" wata irin kunya ce ta rufe Fatuu ta sadda kai gabanta na fad'uwa gwaggo ma d'an murmushin yak'e tay ta maida idon ta gefe Amadu kuwa dama wayar shi na a hannun shi sai kawae yay kaman yana kira ya mik'e ya nufi hanyar fita, cigaba Mama tay "ai har fad'a saida nay tayi kan yadda ake d'irka ma yara magungunan da suka fi k'arfin su don harda hakan ke haddasa irin wannan aika aikar azo kuma aita jan ido Allah ma yaso ita ba'a dangana da yin d'inki ba, ashe har an samu rabo sai kuma abu mara dad'i ya faru" gwaggo dake ta murmushin yak'e a kunyan ce tace mata "Wllh kam" ta fahimci irin Mutanen ne da bakin su a sake yake komi yazo fad'i suke ba tare da sun ji komae ba, "To Allah ya maida mafi Alkhairi ai abun ba wuya yanzu kin ji an samu wani ba kamar yaran yanzu fitinannu ne wllh jarabar tsiya gare su" Fatuu tamkar ta nutse a wurin haka taji ba ita kadae ba har gwaggo wata irin kunya ce ta rufe ta saidae ta sadda kan ta k'asa ita kuwa Mama ko a jikin ta tambayar gwaggo tay wai Fatuu d'iyarta ce ta d'ago da d'an murmushi tace mata a'a jikarta ce a wurin ta take nan fa ta hau yi ma gwaggo tambayoyi sai kace yar jarida harda tambayar ta amma dae Haisam d'an manyan mutane ne ko don taga ranar da ya kawo Amaryar tashi har kyautar dubu hamsin yay mata nurse da ta kawo shi wurinta kuma dubu ashirin nan gwaggo ta sanar da ita ko d'an waye harda su ruk'e ha6a tace koda taji ai biri yay kama da mutum sai kuma tace ma gwaggo wai kaman ta san fuskarta a wani wuri tace mata ba mamaki ita attender ce a k'aramar Asibiti Mama tace ba shakka anan tasan fuskar sai k'ara cewa ikon Allah wai su kaman masu d'an rufin asiri ne daga amsoshin da ta bata shi kuma gashi d'an shahararran mai kud'i da aka sani a haka kuma ya auri ita Fatun don taga yanzu auren jari hujja ake ita dae gwaggo sai murmushi take tace mata ai su ba irin wad'annan masu kud'in bane kud'in su basu sa masu girman kai ba kowa na su ne ko mai kud'i ko talaka duk d'aya suka d'au kowa, sosae ta shiga yabon su tana fad'in dama tana jin ana fad'in alkhairan mahaifin shi da kakar tashi ma har a tv tana ganin aiyukan Alkhairin da suke yi harda ce ma Fatuu tayi dace ta k'ara gode ma Allah samun irin wad'annan mazan a yanzu ba k'aramar baiwa bace don tsananin wahala gare su don haka ta rik'e shi gam ta bishi sau da k'afa still kan Fatun na k'asa Gwaggo dae sai murmushi take daga baya ta hau yi ma Fatun tambayoyi tace anyi mata wankin ciki ne gwaggo tace mata a'a jiya har suka bar asibitin da daddare ba'ai ba da yake ta suma ne sai daga baya ta farfad'o Allah yaso bata tambayi dalilin suman nata ba sai ta kalli Fatun tace "kina zubar da jini ne sosae har yanzu?" Kai ta girgiza mata ba tare data kalleta ba a hankali tace "a'a ba sosae bane" tace "akwae gudaji gudaji?" d'an shiru Fatun tay alamar tunani sai kuma ta d'an kalleta tace a'a babu, nufar gado mama tay tana fad'in k'ilan ma ba sai anyi Mata ba to da alama komae ya fice tunda dama cikin k'arami ne sosae, a gaban drawer d'in gefen gadon ta tsaya ta kai hannu ta fara duba magungunan dake sama tana yi tana d'age ido had'i da cuno baki da alama dae kaman bata gani sosae sai da gilashin, bayan ta gama dubawa ta dawo wurin su tace tunda an bata wadancan magungunan tasan za'ayi mata scanning in anga komae ya fita ai shikenan dama amfanin wankin cikin don a fitar da komae koda wani abu ya mak'ale a mahaifar gwaggo ta d'aga mata kai daga baya tace bari ta tafi tana shirin tafiya gida ne aikin kwana tayi zuwa da daddare in ta shigo zata shigo taji yadda sukai da likita gwaggo ta mik'e tay mata rakiya har bakin k'opa tana mata godiya ta tafi, tunda gwaggo ta juyo ta dawo kan Fatuu ke a k'asa inda ta tashi ta koma ta zauna d'akin yay tsit wata irin kunyar gwaggon ce ta lullu6e Fatuu yayin da ita kuma Gwaggo ran ta yay mata wani iri sosae abun ya ta6a mata zuciya jin Haisam har Asibiti ya kawo Fatun wato yanzu da ba aure a tsakanin su kuma Al'amarin cikin bai biyo baya ba shikenan ita ba sanin an aikata zatay ba, sosae jikinta yay sanyi lalle mutum bai isa ya shiryar da wani ba face Allah yaso kaidae kawae saidai kai iya bakin kokarin ka ka had'a da Addu'a amman wani tsananin ka ko sa ido ko wani wayon ka ko dubara duk basu yi wllh tarbiyar yara yanzu sai an dage da Addu'oi don duk yadda kake kaffa kaffa wllh bai hana yaro lalacewa ba tare da ka ankare ba Allah Ubangiji ya shirya mana zuri'a ya tabbatar dasu akan daidai ya taya mu tarbiyyantar dasu kada yaba wani abokin halitta damar canza su daga kan tarbiyyar da akai masu mai kyau ya shirye mu baki d'aya darajar fiyayyen halitta Manzo (S.A.W). Haisam na fita daga Asibitin gidan Hajiya ya nufa, bayan ya isa yay parking Motar part d'in shi ya nufa yana zuwa Toilet ya shige don yin wanka, after some minutes ya fito k'ugun shi d'aure da Towel ga wani short yana goge sumar shi da shi wata irin yunwa yake ji shiyasa bai tsaya busar da ita da dryer ba shi kan shi saida yay mamakin yunwar don bai cika yin Breakfast da sassafe ba sai wurin 11 haka amman yanzu duka k'arfe takwas da yan mintuna, gaban dressing mirror ya tsaya ya shafe jikin shi da body cream d'in shi mai daddad'an k'amshi bayan ya gama ya shafa roll on ya feshe jikin shi da body spray kala ukku har wani mai ya d'aukko ya matsa a tafin hannun shi ya kai kan kwantacciyar sumar chest d'in shi ya shafe nan take ta k'ara kwanciya luff ya k'ara d'aukko hair spray ya feshe sumar kan kafin ta k'irjin ma ya d'an fesa mata bayan ya gama yan shafe shafen closet ya nufa ya ciro jallabiya da short ya dawo bakin gadon ya fara kokarin sawa, sanye cikin jallabiyar wadda coffee brown ce mai gajeran hannu ya fito bayan ya zura takalma a cikin Corridor ya shigo cikin parlorn dake a gyare tsaf kaman ko yaushe ya nufi kopar ya fita, part d'in Hajiya ya nufa lokacin da ya shiga Parlon ba kowa hakan yasa ya wuce Bedroom d'inta ya turo kopar ya shiga da yar sallama, tsayawa yay a bakin kopar yana kallon Hajiyar dake kwance tana ta sharar bacci ta rufe rabin jikin ta da lallausan bargo baki a wangame d'an murmushi kawae yay ya juya ya bud'e kopar yana fitowa Saude ma ta fito daga cikin d'akin ta zata kitchen dakatawa yay cikin girmamawa ta gaishe dashi ya amsa mata tay mashi ya mai jiki don jiya bayan Hajiya ta dawo saida ta bata labari kaf tana ta fad'a tana fad'in Haisam bai d'auke su da mahimmanci ba bama kamar ita yanzu ta gane bai damu da ita ba bai k'aunar ta shiyasa ya iya fad'i mata abunda hankalin ta zai tashi harda uban kukan ta ko ta mutu ko tay rai shi ko ajikin shi nan fa Saude ta hau rarrashinta tana bata hak'uri saidae a can k'asan ranta ta ji ma Fatuu dad'i sosae da Haisam ya kasance mijinta duk da bata ji dad'in zubewa da cikin yay ba har Addu'a tay kan Allah yasa auren ya d'ore, umarnin ta kawo mashi breakfast ya bata ta tambayi abunda zata kawo yace wanda ya samu daga haka ya wuce saida ya fita daga cikin corridor d'in sannan itama ta wuce, a parlor ya zauna bai koma part d'in shi ba ta bishi da shi can don yanzu yasan ita matar aure ce, ba'a d'au lokaci ba ta shigo cikin parlorn ruk'e da d'an babban tray saida ta janyo c-table gaban shi sannan ta d'aura mashi tace aci lpy ya jinjina mata kai had'i da furta thanks, kakkauran tea ne a cikin mug sai babban plate mai gidaje da marfi bayan ya bud'e soyayyar plantain ce a gida d'aya sai chips a wani gidan na k'arshe kuma soyayyar wainar k'wai ce daga d'ayan gefen tea d'in ledar biredi mai yanka yanka ce duk da komae d'an daidai ta zuba sun mashi yawa, fara ci yay a nutse yana yi yana d'an kallon Tv a haka har ya gama ya rufe sauran da ya rage ya idasa hayewa kan kujerar ya kwanta sosae yana ci gaba da yin kallon bada jimawa ba bacci ya kwashe shi. Sai wurin karfe goma Hajiya ta fito jikinta sanye da doguwar riga cotton ta nufo cikin parlorn da sandar ta ta alfarma tana zuwa bakin kujerun tay turus idon ta akan Haisam da ya d'aura hannun shi d'aya ya rufe idon shi yana ta bacci, d'an ta6e baki tay ta wuce ciki a kujerar kusa da tashi ta zauna ta bishi da kallo kaman yaji a jikin shi ya fara motsi ya sauke hannun slowly ya fara bud'e idanun shi suka sauka akan Hajiya da ta tura baki tana bin shi da ido shima kallon ya bita dashi kafin ya yunk'ura ya tashi zaune ya jingina da jikin kujerar cikin muryar wanda ya tashi daga bacci ya gaishe da ita "Gud morning Sweetheart" wata uwar harara ta zabga mashi a d'an fusace tace "ai ka daina yaudara ta kaje can kai ma wata dad'in baki ba dai ni ba" wani kalar kallo yake bin ta da shi idanu a d'an lumshe can yay sigh slowly ya furta "am sorry" k'ara tura bakin tay ta kauda idon ta gefe ganin haka yasa shi jan jiki ya matsa can k'arshen kujerar ya kai hannu ya kamo hannunta ta fara k'ok'arin kwacewa sai dae ta kasa a fad'ace tace "ai tunda kaga zuciyata bata buga ba sai ka k'arasa ni ta hanyar k'arya man hannun" d'an guntun murmushi yay remorsefully yace "I said am sorry I regret what I did, I dont know what came over me har hakan ya faru" yana Magana yana wani lumshe mata idanu sai kace wata budurwar shi ko matar shi k'in kallon shi tay tana cigaba da tura bakin had'i da kikkafta idanu d'an matsa hannun yay aikuwa ta juyo a fusace tace "Ka gama raina ni Haisam, kai wato har kana da k'arfin halin yi man wannan iskan cin ko" har sai da ya d'an yi yar dariya jin abunda tace cigaba tay "in ba don ka raina mu ba ka d'auke mu maras amfani wai har kasa a d'aura maka aure ba tare da sanin mu ba" rai 6ace tay Maganar yace "kiyi hak'uri Allah ne ya kaddara hakan zai faru ni kaina I never thought zan yi hakan" wani kallo take jefa mashi can tace "uhmm kai ka sani" sakin hannun nata yayi ya maida bayan shi ya jingina da kujerar idon shi na kallon gaban shi ita kuma Hajiyar idonta na akan shi can cikin d'aure fuska ta tambaye shi jikin Fateemar ya kalleta fuska a sake yace mata da Sauk'i tace ta farka ne yace mata eh tun jiya tay shiru can kuma ta sake cewa "ita waccan ta K'asar wajen kunyi magana da ita ne karta ji shiru tunda dae ba yadda za'ai ka tafi kabar yar mutane da ciwo" d'aga mata kai yay sai kuma yace mata sun yi magana jiya tace "kadae zabga mata k'arya tunda naga ka iya ta yanzu" bai ce komae ba ya d'age kan shi kawae yana facing saman Parlon yaji tace in baccin zai cigaba ya tashi ya koma part d'in shi ko a gyara mata parlonta yazo ya kama yi mata bacci ya hana a gyara, sauke kan yay suka had'a ido sai kuma ya mik'e ya nufi hanyar fita yana tafiya a hankali tabi shi da ido har ya fita ta maida jikinta jikin kujerar tay shiru da alamun damuwa akan fuskar ta ta, part d'in shi ya koma ya shige bedroom ya kwanta a kan gado nan da nan wani baccin ya sake d'aukar shi. Saida Amadu yaga fitar Mama sannan ya koma cikin d'akin yana niyyar komawa bakin gadon Gwaggo ta mik'e tace yazo ya zauna bari ta had'a mashi breakfast d'in yaci yanzu in ba haka ba ba lalle ya samu damar ci ba d'an anjima mutane zasu iya fara zuwa yace to, bayan ya fara ci Fatuu dake gefen shi ta tambaye shi ko yaga wayarta kafin ya bata amsa gwaggo tace gata nan cikin Aljihun ta jiya ma bayan sun koma Fauziyya ta kira ta d'aga ta fad'i mata tana Asibiti shiru Fatuu tay cikin ranta ta shiga raya da ta bi Maganar Fauzy da yanzu cikin na nan ta tabbatar ma inda tasan kiran da Haisam yay mata a waya da yawa ne harda text message bazata bari a zubar ba wani, wani irin sanyi jikinta yay nan take taji wata irin nadama tazo mata da kanta ta zubar da cikinta na halak cikin mutumin da take tsananin k'auna, gaba d'aya ji tay breakfast d'in ya fitar mata a rai ta mik'e ta tattara kayan ta nufi gefen gado dasu gwaggo na ce mata har ta k'oshi tace eh ta tashi ta bata magungunan ta, bayan ta gama sha idasa hayewa gado tayi tay lamo har gwaggo na tambayar ta ko jikin ne tace a'a bacci ne bai ishe ta ba tace ai sai taci gaba ta lumshe ido kaman baccin zatai da gaske amman tunane tunane da zancen zuci kawae take a haka baccin ya d'auketa ba, bayan Amadu ya gama yace ma gwaggo zai tafi sai anjima zai dawo tace to k'ilan ta kira shi ya dafa Abinci ya zauna cikin shiri sukai sallama ta bashi kayan Abincin da aka gama dasu ya tafi. Wuraren k'arfe sha d'aya Fatuu ta farka taga d'akin wayam ba kowa tana kwance aka turo k'opar sai ga Fauzy ta shigo da yar sallama da sauri Fatuu ta yunk'ura ta tashi zaune tana kallonta itama Fauzy da sauri ta nufi gadon ta zaune a gefe fuskarta d'auke da matsananciyar damuwa tayi mata sannu ta d'aga mata kai d'an shiru sukai sunata kallon juna fuskar Fatuu a yamutse kaman zata saka kuka can Fauzy tace "ashe haka abu ya faru harda kwanciya Asibiti tun bayan da muka rabu inata so in kira ki zullumi da fargaba suka hana ganin har dare yayi baki kirani ba kin sanar da ni halin da ake ciki yasa nai k'arfin halin kiran ki saidae kusan sau ukku ba'a d'aga ba tsoro ya kama ni sosae na shiga tunanin to ko lpy gashi na kasa kiran ko Kawu Amadu, sai can dare wurin karfe 11 nace bari in k'ara jarabawa k'ilan ki d'aga tunda lokacin kwanciya ne ina kira sai gwaggo ta d'auka nan take sanar dani wai an kwantar dake Asibiti wayar na gida aka barta wllh sosae hankali na ya tashi bazan 6oye maki ba ko bacci ban yi ba saboda fargabar abunda ya faru har aka kwantar da ke, Aunty Mareeya har ta gane ina cikin damuwa tanata tambayata Mike damuna saidae in ce mata ban jin dad'i kawai don ban san taya zan mata bayani ba" dakatawa tay ta kai idonta kan ledar Karin jinin dake rataye cike da damuwa tace "harda k'arin jini ma akai maki kenan, cikin ne ya fita kika zubda jini sosae?" Kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh, girgiza kai Fauzy tay "Sannu, wllh irin abunda nake ta gudu kenan kinga ko a Makarantar hakan ta faru sai an san dalili, to yanzu da su gwaggon suka sani miya faru?" Shiru kaman bazata ce komae idanunta suka ciko da k'walla a hankali suka fara gangaro mata cikin muryar kuka tace "Fauzy na aikata babban kuskure wllh ashe cikin nan na halak ne ba yadda na zata ba" waro ido Fauzy tay with mouth agape a rud'e tace "cikin halak! Kenan kina son kice man Ya Haisam Mijin ki ne???" Cikin kuka ta d'aga mata kai k'ara zaro idon tay ta kai hannu ta rufe baki kafin ta cire cike da Al'ajabi ta tambayeta yadda hakan ta faru nan ta shiga fad'i mata komae da ya faru bayan ta dawo gidan har zuwa yanzu, salati Fauzy ta shiga yi tana yi tana kai hannu tana dafa gaban kanta da kuma bakin ta cikin tsananin tashin hankali ta hau fad'in "ni wllh dama raina saida ya bani anya ba wani abu a k'asa kwata kwata na kasa yadda Ya Haisam zai aikata maki hakan Saboda son zuciya kawae dai bani da wata hujja ne, innalillahi abu dae bai yi dad'i ba wllh aka ce rashin sani yafi dare duhu" sosae ta shiga damuwa har fuskar ta ta nuna idanun ta sun sauya kwalla ta kwanta cikin su sosae Fatuu ke kuka tana fad'in "nayi danasani Fauzy duk da na d'aga wayar Ya Haisam bayan dana je na sanar mashi da hakan bata faru ba, saida yay ta kira na harda message ya turo man yace kar in yi komae in picking kiran nashi amman na k'iya k'in Fad'a maki nay don kar ki hana a zubar na nuna maki sau d'aya ya kira, wllh ban yi zaton na halak bane tunda ni bansan komae ba ai gashi naga kaman ma yayi fushi Saboda hakan " itama Fauzy k'wallan ne suka fara zubo mata suna cikin haka suka ji karar bud'e kopa duk suka kai idon su kan kopar toilet sai ga gwaggo ta fito idon ta a kan su suma suka bita da ido cike da rashin gaskiya............... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2055* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ......Kauda idon ta tay daga kallon su ta nufo cikin d'akin cikin kame kai Fauzy ta gaishe da ita ta amsa tare da d'an kallon ta tay mata ya mai jiki nan ma ta amsa kafin ta nufi kujera, a jikinta ta janyo Hijab d'inta ta nufi hanyar fita daga d'akin tana kokarin sakawa, bayan ta fita Fauzy ta kalli Fatuu da yar damuwa tace "ta san kin yi wani abu ne don zubar da cikin?" d'an shiru Fatun tay fuskar ta duk hawaye tace bata sani ba ko likita ya gane ya sanar masu tunda ta dad'e bata farfad'o ba amman in ma ta sanin to bata nuna mata ba, ajiyar zuciya Fauzy tay tace "to k'ilan bata sani ba amman yanzu kaman ma taji abunda muke cewa" shiru kawae Fatun tay idon Fauzy akan ta wani irin tausayin ta ne ya kamata tasan dole ta shiga matsananciyar damuwa yadda take son Ya Haisam bazata ji dad'i ba ace ta samu cikin shi na halak kuma ta zubar da hannun ta gashi tace yayi Fushi, hannu Fauzy ta kai ta kamo nata ta fara lallashin ta "ki kwantar da hankalin ki Zarah nasan dole Kiji ba dad'i amman kada kisa damuwa a ranki ki d'auka komae rubutacce ne dama haka Allah ya k'addaro kuma shima Ya Haisam d'in na tabbatar zai fahimce ki kawae dae dama dole ne ya nuna maki 6acin ran shi Saboda zai ga kin k'i jin Maganar shine har hakan ta faru wanda nasan bai yi zaton hakan daga wurin ki ba a yadda kuke da shi amman dae komai zai daidaita in sha Allahu, ki daina damuwa ko don halin da kike ciki kada ki samu wata matsalar kuma" tana kai Maganar ta kai hannu tana goge mata kwalla daga baya tace bari ta sanar ma Aunty Mareeya, bayan ta kirata ta sanar mata zancen kwantar da Fatun Asibiti salati ta saka hankali a tashe ta hau tambayar Fauzy abunda ya samu Zarah nan ta kwashe komai ta fad'i mata tana jin yadda take zabga salati a rud'e tace tana nan zuwa wane Asibitin take ta sanar mata, bayan sun gama wayar yar hira Fauzy ta shiga yima Fatun duk don ta daina damuwa harda zancen irin shagalin da zasu yi in komae ya daidaita da kalar su ankon da za'ai daga baya kuma yanayin fuskar ta ne ya canza tace tasan ma d'auke Fatun zai yi su bar K'asar amman dae gaskiya a bari sai sun gama karatu lokacin tasan ta k'ara samun wani cikin harma ta haihu, harda Addu'ar Allah yasa next cikin da zata samu na twins ne, tun dai Fatuu na d'an murmushi sai gata harda su dariya, Bayan sallar Azahar sai ga su Feenah Abbas ya kawo su lokacin da suka shigo su Fatun na Zaune akan gadon Fauzy na gefen ta Abdul na hango ta ya nufi gadon da gudu ya fara k'ok'arin hawa Fauzy ta taimaka mashi yana hayewa ya fad'a jikin ta Feenah na fad'in bai ganin mara lpy ce, a gefen gadon Feenah ta tsaya bayan ta aje basket d'in kayan Abincin data shigo da shi tana sanye da doguwar rigar Atamfa tayi d'aurin kallabi mai steps ga gyale mahad'in kayan ta yafa a kafad'a hannun ta na dama ruk'e da hannun Nasreen da itama tasha yan kanti, da alamun damuwa Abdul dake kallon face d'in Fatuu yace "Aunty Fatuu ashe baki lpy" itama kallon shi take da d'an murmushi ta d'aga mashi kai alamar eh ya juya ya kalli ledar K'arin jini fuskar shi kaman zai kuka idanun shi har sun kawo kwalla yace mata sannu ta rungume shi ta gefe Feenah ma tayi mata ya jiki ta amsa mata kafin ta gaishe da ita Nasreen ta fara rigimar itama a d'aurata kan gadon Feenah tace ya duk zasu haye gadon mara lafiya Fatuu ta mik'o hannu tace ba wani abu ta d'auro ta Fauzy ta kai hannu ta d'aukko ta, ganin Feenah nata tsayuwa yasa Fatuu ce mata "Aunty Feenah ga kujera can ki zauna" d'an murmushi tay tace "bari in gama ganin ki to, ashe abu kuma haka ya faru jiya Dear ke fad'a man banji dad'i ba wllh nace da an sani ai da an tari abun da wuri duk da hakan bai faru ba, shima yace man bai san abunda ke faruwa ba sai jiyan" idanun Fatuu ne suka ciko da k'walla bata dae ce komae ba sai kikkafta idanu take don kada su zubo suna haka Abbas ya shigo dama yana waje wurin gwaggo suna gaisawa, bakin gadon shima ya tsaya Fauzy ta gaishe dashi ya amsa yay mata ya karatu ya maida kallon kan Fatuu cike da kulawa yace "Mom Zarah ya jikin?" Kallon shi tay a sanyaye tace da Sauk'i, "Allah ya baki lafiya ashe haka abu kuma ya faru?" Aikuwa kaman tana jira ta fashe masu da kuka dama daurewa kawae take, girgiza kai Abbas ya shiga yi cike da tausayi Feenah ma Fuskarta kaman zata sa kukan Fauzy kuwa tuni kwalla sun ciko mata, sosae Abdul ya rud'e ya d'ago yana fad'in "Aunty Fatuu don Allah kibar kuka zaki samu lafiya in baki yi shiru ba nima zan yi kukan" k'ok'arin shanye kukan ta fara tana girgiza ma Abdul kai alamar kada yayi ya kai hannu yana goge mata kowa jikin shi yayi sanyi Abbas ne yace "Kiyi hakuri Mom Zarah nasan an maki ba daidai ba don da kin sani hakan ba zai faru ba to amman komai ki ka ga ya faru dama rubutacce ne" kallon shi tay cikin muryar kuka tace "Amman Ya Abbas Saboda mi aka 6oye man ko kai ba sai ka fad'i man ba tunda ni ban 6oye maka komai" da alamun Damuwa kan face d'in shi yace "kiyi hak'uri don Allah haka aka tsara ne ba za'a sanar maki ba shiyasa..." Katse shi tay "to Saboda mi?" Shiru yay don bai son yace mata auran tsarawa akai don a taimake ta ba don ya d'ore ba, ba kamar kuma yanzu da abu ya shiga tsakanin su, Feenah ta fahimci Abbas bai son sanar da ita game da auren hakan yasa ta kai hannu tana share mata hawayen dake zubowa tana fad'in "Haba Mom Zarah d'in mu kefa nasan mai k'arfin hali ce kiyi hak'uri komae ya wuce ko ma samu ki warke da wuri a k'ara samo mana cikin wani Baby d'in in sha Allahu ma twins za'a maida mana tunda da yawa wani rabon ke kore wani" d'an murmushi Fauzy tay ta sadda kan ta haka ma Fatuu d'an juyar da fuskar ta tay Abdul kuwa k'ura ma Feenah da tayi Maganar ido yay can ya kasa jurewa ya d'ago daga jikin Fatuu yace "Momy Aunty Fatuu tayi aure ne?" D'an shiru tay sai kuma tace mashi "Mi yasa ka tambaya?" yace "naji kin ce ta Warke ta haifo babies?" shiru Feenah tay sham ta manta dashi a wurin tay Maganar tasan shi bai ji ya k'yale Abbas kuwa d'an d'age gira yay yana kallon Feenah da murmushi alamar jiran yaji amsar da zata ba Abdul don ya kafeta da ido can ta d'aga mashi kai tace eh tayi aure, waro ido yay alamun mamaki ya juya ya kalli Fatun ya sake juyowa ya kalli Mom d'in tashi yace "Yaushe tay auren ni ban sani ba kuma waye ta aura?" ta biyun ta amsa mashi tana d'an murmushi tace "Baban ka Zakee" har saida yay wata yar zabura ya tsuke fuska cikin fushi yace "Kamm shine sukai auran ban sani ba kuma bani nace ma ya aure ta ba" a hak'ik'an ce yay Maganar sai bin su yake da kallo ya kumburo baki sigh Abbas yay yace mashi "ai ba'a yi bikin ba tukun an dai d'aura masu aure ne....." Katse shi yay kaman zai kuka "to ni miyasa ba'a je dani d'aurin auren ba ba inada babban riga ba" har saida ya basu dariya su duka Fatun ma saida tay d'an murmushi wato shi a tunanin shi saida babban riga ake zuwa d'aurin aure, kafin wani ya bashi amsa aka turo k'opar da yar sallama k'asa k'asa ya shigo, Wow Tubarkallah Angon Fatuu shine abunda na fad'a, wankan bak'in Voile yay ana d'an hango hasken vest d'in shi kad'an hannun shi d'aure da Agogo ta bak'ar fata haka k'afafun shi dakakkun half cover ne masu kyau da tsada Sumar nan tasha gyara ta k'ara bak'i sai salk'i take, sosae yay kyau tun ma kafin ya k'arasa shigowa k'amshin turaren shi ya baza d'akin kai kace shi kadai kamfanonin turaren suke ma irin nashi don koda yaushe k'amshin shi na daban ne, tunda Fatuu tay arba da Fuskar shi gaban ta ya fara wani irin bugu gaba d'ayan su idanun su na akan shi yayin da Fauzy acikin ranta ta hau fad'in Tubarkallah sam bata ganin laifin Fatuu da take son shi ita a yadda take ji ma da itace abu ya shiga tsakanin su har ta samu ciki wllh bazata zubar da shi ba bari zatai har ta haife tunda tasan bazai ta6a wofintar da ita ba duk surutun da za'ai aje ai ta yi, Abdul na ganin shi ya saukko daga kan gadon ya nufe shi da sauri lokacin har ya zo tsakiyar d'akin a gaban shi ya tsaya yana kallon shi fuska a d'aure hakan yasa Haisam d'in tsayawa yana kallon shi Fuska a sake su Abbas nata murmushi daga inda yake yace ma Haisam "Baba Zakee yau fa ka ta6o d'an gidan ka kay mashi laifi" d'an kallon Abbas da yay Maganar yay sai kuma ya maido idon kan Abdul daya kumbura kamar zai fashe cikin cool voice d'in shi yace "What's happening?" Ya kai hannu zai dafa kan Abdul d'in da sauri ya janye kan yasa hannuwan shi duka ya ruk'e k'ugun shi alamar dai abun yau baram baram za'ai Abbas kau mi zai yi in ba dariya ba haka ma su Fauzy still Haisam murmushi yake calmly ya furta "kaga dariya suke mana tell me laifin mi nayi?" Yana tura baki yace "ashe dana ce ka auri Aunty Fatuu ka aureta ban sani ba kuma ko d'aurin auren ba'a je dani ba!" Abbas ya amshe da fad'in "kuma dae yana da babban riga ato" duk sukai dariya shima Haisam d'in yar dariyar yay ya kamo hannun shi yana fad'in yayi hak'uri to ya fara bubbuga k'afa k'arshe Haisam d'in ya sunkuce shi ya d'aura shi a bayan shi sai k'unk'uni yake cike da shagwaba, yana zuwa bakin gadon Fatuu ta sunkuyar da kanta Fauzy dake kallon shi ta gaida shi ya amsa tay mashi ya mai jiki haka Feenah ma duk ya amsa Fauzy ta sauka daga kan gadon ta nufi Kujera Feenah ma ta bi bayan ta ya rage daga shi sai Abbas tsaye a bakin gadon, kai idon shi yay kan ta kaman ance ta d'ago suka had'a ido Slowly ya furta "Ya jiki?" a sanyaye tace da Sauk'i ya jinjina kai kawae still da canjin da take gani akan Fuskar tashi, mai da kallon yay kan Abbas dake mashi wani kallo irin na wanda yay abu ba daidai ba shi kuma ya maida mashi martani da nashi mai kaman harara suna haka Dr Habeeb ya shigo cikin d'akin da sallama su Feenah suka amsa had'i da gaishe dashi yay masu ya mai jiki ya nufi su Abbas, hannu ya basu suka gaisa gaba d'aya ya kalli Haisam yay mashi ya mai jiki k'asa k'asa yace da Sauk'i kafin ya d'an matsa gaban gadon da murmushi yace ma Fatuu ya jiki tace da Sauk'i ta gaishe dashi ya amsa, tambayarta yay tana jin wani ciwo ko a marar ta haka tace a'a bata jin komae ya k'ara tambayar yanayin jinin da ke zuba da yanayin yawan shi a kunyance take bashi amsa tana yi tana d'an sadda kai don duk su Abbas na ji, "To ya kike jin yanayin jikin ki?" tace "kawae ba k'arfi ne sosae" jinjina kai yay "Ok sai a hankali k'arfin zai dawo zuwa anjima sai a ida saka maki sauran jinin" kai ta d'aga ya juya kan Haisam yace "Yanzu ina ganin muje ai mata Scanning d'in mu ga" kai Haisam ya d'aga ya juya ya kalleta suka had'a ido sai taga kaman ma harararta yake da sauri ta sunkuyar da kan ta, Abbas ya yi ma Feenah magana kan tazo ta taimaka mata suje wurin scanning tace to ta mik'e su kuma suka wuce tare da Dr d'in, bayan ta saukko daga kan gadon Fauzy ma ta taso lokacin gwaggo ta shigo tazo wurin su tana fad'in bari a bata abunda zata yafa ta wuce wurin jaka ta ciro mata d'an gyalen ta dama kan ta da hula suka tafi Feenah ta tallabo Shoulders d'in ta, a kan hanyar su ne Fauzy ke yin Addu'ar Allah yasa aga cikin na nan Feenah tace ai gaskiya da wuya ne Saboda Dear ya fad'a mata ta zubar da jini sosae gashi cikin dama d'an k'arami ne zai wuya ya tsaya kuma already Dr ma yace masu ya fita, lokacin da suka isa a bakin wurin suka iske su Haisam tunda ta kalle shi sau d'aya ta kauda idon ta Abbas ne yace mata ta shiga Dr d'in na ciki ta d'aga kai ta shiga suma su Feenah suka tsaya a bakin kopar don su jirata daga baya Dr ya fito yace ma su Abbas suje Office, sai bayan wasu mintuna Fatun ta fito Feenah ta tambayi an gama tace mata eh ance za'a tura ma Dr tace Ok ta k'ara kamata suka tafi, Suna zaune a Office suna yar hira aka turo result d'in ya fad'a masu gashi an turo ya fara dubawa bayan wani lokaci ya d'ago ya kalli Haisam yace "ya nuna ba sauran wani abu mahaifar ta is empty so ina ganin kawae taci gaba da shan magungunan tunda tace jinin ma ba mai yawa bane ke zuba yanzu a hankali zai d'auke, in kuma kun fi so ayi mata D&C d'in to wani lokacin yana taimakawa wurin k'ara conceiving da wuri amman dama ciki k'asa da 10 weeks ba dole sai an yi ba indai ba wata matsala haka" Wani kallo Abbas yay ma Haisam cike da shak'iyanci yace "H,Zakee ina ganin ayi matan ko Saboda ai saurin k'ara samun wanin" banza yay ma shi cikin cool voice d'in shi yace ma Dr shikenan ba sai anyi ba ya gode yana fad'in hakan ya mik'e Abbas ma ya tashi yana mashi dariyar iskanci shima Dr Habeeb d'in mik'ewa yay yana yin dariyar don daga baya Abbas yay mashi bayani game da auran da yadda aka samu cikin, saida ya rako su bakin Office d'in yace tayi duk abunda zata yi bada jimawa ba zai zo ya sa mata jinin Haisam ya amsa da Ok kafin suka tafi, Bayan su Fatuu sun koma kan kujera Feenah tasa ta zauna don taci Abinci cikin wanda ta kawo mata ta zubo mata tace ma Fauzy itama ta zuba tana murmushi tace to, tasa Fatuu gaba tay wai sai ta ci shi sosae Abdul ma na gefen ta yana fad'in taci ta k'oshi ta warke su tafi gida tare tay yar dariya suna haka Hajiya ta shigo harda Saude ruk'e da k'aton Basket din kayan Abinci da kuma Tk, Feenah ta mik'e taba Hajiyar wuri don ta zauna, bayan ta zauna idon ta akan Fatuu ta kai hannu ta dafa kafad'ar ta tace "Sannu Fateema kin ji an ja maki jinyar dole" d'an murmushi kawai Fatuu tay ta gaisheta bayan ta amsa taci gaba "an gode ma Allah daya tashi kafad'un ki, jiyan nan ai hankali na ya tashi sosae wllh yarinya tamkar ba rai ga uban jini da kika zubda, to ya jikin naki yanzu?" tana d'an murmushi tace da Sauk'i sosae Hajiya tace "to Alhamdulillah Allah ya k'aro sauk'in, su Dije sun auna Arziki don da wani abu ya same ki duk sai nayi k'arar su an bi maki hakk'in ki wllh duk da haka ba k'yale su zan ba" kowa yay murmushi su Sauden sukai mata ya jiki ta amsa masu ana haka gwaggo ta shigo cikin d'akin d'auke da plastic chairs guda biyu ta aje tace ma Saude su zauna, bayan sun zauna duk suka gaishe da ita Sukae mata ya mai jiki ta amsa masu dama ta gaisa da Hajiya tun a waje tana ta tura baki ta amsa mata, lokacin Abbas da Haisam suka shigo Hajiya ta bisu da wani wani kallo fuska a tsuke Abbas ne kawae ya gaishe da ita ta amsa mashi ba yabo ba fallasa ya kalli gwaggo yay mata bayanin da Dr yayi game da scanning d'in yace ba sai anyi Mata wankin cikin ba taci gaba da shan magani gwaggon tace to in sha Allah Hajiya tace "ai gwara dae kada ayi matan a kyaleta da wahalan da aka d'ora mata ba sai an k'ara mata wata Azabar ba" kowa dae murmushi kawae yake banda Haisam dake tsaye can ya juya zai fita Abbas yabi bayan shi, Sai da akayi la'asar Abbas ya kira Feenah ta fito su tafi lokacin an k'ara sama Fatuu jinin Abdul yasa rigimar bazai tafi ba shi anan zai tsaya dama da yaga za'a saka mata jinin harda kukan shi da kyar gwaggo ta lalla6a shi tace Asibitin ba'a barin yara su zauna da an ganshi za'a zo a tafi dashi ya bari in suka koma gida sai yazo ya zauna har ta warke gaba d'aya yace to yaushe zasu koma gidan tace bada dad'ewa ba da an sallame su zata kira daddy d'in shi ta gaya mashi sannan ya yarda suka tafi Fauzy tay masu rakiya har bakin Mota, tana niyyar dawowa ciki sai ga Aunty Mareeya mai Keke Napep ya tsaya da ita Fauzy ta nufe su tana murmushi tay mata sannu da zuwa ta amsa tace ta d'aukko basket a ciki tace to, bayan ta d'aukko ta sallami mai Napep d'in suka nufi cikin Asibitin, lokacin da suka shiga d'akin Aunty Mareeya ta gaida su Hajiya da Gwaggo tay masu ya mai jiki suka amsa sannan ta nufi gadon Fatuu na kwance jinin nata shiga ta kalli Aunty Mareeyar da d'an murmushi ta gaishe da ita saida ta zauna a bakin gadon da alamun damuwa tay mata sannu da jiki Fatun ta amsa bayan Fauzy ta aje basket d'in tazo daga d'ayan gefen itama ta zauna Aunty Mareeya ta kalleta k'asa k'asa da murya tace "d'azun kina gaya man abun Al'ajabi ashe duk abunan mutumin nan mijin Zarah ne" gyad'a kai Fauzy tay kawae ta sake cewa "amman dai ni kun yi man rashin hankali wllh haba kaman baku san halin shi ba ai bai kamata kuyi saurin zubar da shi ba" cike da damuwa Fauzy tace "wllh nima Aunty ban so akayi saurin zubar dashi ba..." Nan ta fad'i mata yadda sukai da Fatuu kan zubar da cikin gaba d'aya k'asa k'asa suke Maganar yadda baza'a ji su ba, bayan ta gama fad'i mata ta kalli Fatuu tace "na fahimci dalilin ki Zarah haka Allah ya k'addara amman dae da kin bashi dama kin ji abunda zai ce wllh tunda mutumin nan kin fi kowa sanin halin shi bai kamata ki k'i saurarar shi ba koda ace babu auran yayi maki haka na tabbatar zai yi abunda ya dace ya samar maku mafita bazai ta6a bari ki wulakanta ba nasan k'arshe ma cewa zai ya aure ki kuma ai mu abunda muke so kenan" shiru kawae Fatuu tay ita kanta yanzu dana sani kawae take ta rasa ya akai ta kasa yi ma Ya Haisam uzuri amman tasan Saboda son da take mashi ne shi kuma sai taga kaman ya fara sha'awarta ne can taji muryar Aunty Mareeya tana fad'in "ni wllh dana san da Maganar bazan bari a zubar ba, ni in nice ma wllh bazan yi tunanin zubar dashi ba yaushe ma ai ko shi yace a zubar bazan yarda ba adai nemi mafita kawae" hannu Fauzy tasa ta gumtse Dariya ta kai hannu ta bugi shoulder d'in ta tace "to uwar gulma ai don kar a akaita laifi biyu na fad'i hakan" cire hannun Fauzy tay tana ta dariya Fatuu ma saida ta d'an yi, Sai bayan Magrib duk suka tafi har da Fauzy tace nan zata kwana gwaggo tace a'a taje gida ta huta tunda ta wuni, a daren Abinci saidae gwaggo ta ba wasu don yayi yawa sosae, Misalin karfe tara na daren Fatuu na kwance jikinta sanye da english wears riga da skirt bayan tayi wanka ta saka su gwaggo kuma na kishingid'e kan kujera ta kunna Radio d'in wayarta tana saurara aka kwankwasa kopar d'akin gwaggo tace a shigo kopan a bud'e take, da sallama ya shigo bayan ya turo kopar tana ganin shi ta yunk'ura ta tashi zaune tana murmushi ta hau yi mashi sannu da zuwa, shima yayi wanka ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt hannuwan shi ruk'e da manyan ledoji ya nufi daga can wurin drawer ya aje ya juyo yana gaishe da gwaggo ta amsa tare da mik'ewa tace ya zauna ita kuma ta koma gefen gadon ta zauna shiru ta biyo baya Fatuu dae tayi zuru can ya d'ago a nutse yace ma gwaggo yanzu Abbas zai zo zasu koma gida da sauri ta tari numfashin shi tace "a'a baza'a yi Haka ba yau dae ni zan kwana ka koma gida kai baccin ka zurga zurgar da ake ma ta isa tasa a gaji ai" d'an shiru yay yana kallon gabanshi shi bai iya gardama ba can ya d'ago yace mata ba wani abu ai zai kwana da sauri ta sake cewa "yau dae da wani abu gaskiya d'ana Haisam" har saida yay d'an guntun murmushi tace ya kira Abbas d'in yace basai ya zo ba kar yay wahalar zuwa ya furta Ok sai kuma ta mik'e ta nufi hanyar fita, bayan ta bud'e kopar ta fita suka rage su biyu d'akin yay tsit Fatuu dae na kwance lamo can ta d'an d'aga ido ta saci kallon shi yana zaune idon shi na kallon gaban shi tana ta kallon shi can taga yana niyyar juyowa da sauri ta maido idonta, gaban ta ne ya fara fad'uwa Jim k'amshin shi ya fara cika mata hanci alamar kamar yana tunkaro ta har dai taji k'amshin ya gama cika ta gaba d'aya hakan yasa ta d'aga ido da sauri ta ganshi tsaye a bakin gadon hannuwan shi zube a cikin Aljihunan jeans d'in shi gabanta ne ya hau fad'uwa suka k'ura ma juna ido ta fara d'an motsa baki ganin irin kallon da yake mata a dabarbarce tace mashi ina wuni shiru bai amsa ba hakan yasa ta sauke idanun ta k'asa cikin mutuwar jiki, saida ya mula yasha iska sannan taji yace ya jikinta ba tare data d'ago ba ta amsa mashi da Sauk'i taji ya k'ara cewa ko akwae abunda take buk'ata da turanci ta girgiza mashi kai alamar a'a still bata d'ago ta kalle shi ba, "So this is d result of being stubborn" taji ya fad'a ba shiri ta d'ago suka had'a ido ya d'aure fuska kai kace bashi yay Maganar ba, idanun ta ne suka ciko da k'walla kan kace mi suka fara zubowa shar cikin raunanniyar murya ta furta "kayi hakuri" shiru bai ce komae ba idon shi akan ta itama kallon shi take k'wallan na cigaba da zubowa can kawai sai ya juya ya nufi hanyar fita ta bi bayan shi da kallo yana ficewa ta kife fuskar ta a jikin pillow ta saki kuka mai cin rai, sai bayan wani lokaci taji shigowar gwaggo hakan yasa tay saurin shanye kukan ta gyara kwanciyar ta ta yadda taba gwaggon baya, ledojin da ya kawo ta shiga bud'awa su Fruit ne da uban nama harda su shawarma da ice cream har saida gwaggo ta d'an girgiza kai ta d'auki shawarma guda da ice cream ta nufi gadon, a gefe ta zauna ta kira sunan Fatun shiru bata amsa ba har saida ta k'ara sannan ta amsa k'asa k'asa tace ta tashi ga shawarma da ice cream tasan zata ji dad'in su ba tare data juyo ba tace mata ta k'oshi gwaggon tace "to ai in aka bar su lalacewa zasu yi" daga yadda take tace mata ai akwae fridge ko sai a saka bazasu yi komae ba, shiru gwaggon tay tana kallon ta kaman mai nazarin wani abu can ta kira sunanta ta amsa tace ta tashi zaune har saida gabanta ya fad'i bata da yadda zatayi dole ta yunk'ura ta tashi kan ta a k'asa, "Kuka kike yi ne?" Gwaggo ta tambaya da sauri ta girgiza mata kai tana k'ara d'ukar da kanta, d'an jimm gwaggon tay kafin tace "miya faru ne ko kina jin wani ciwo ne?" Nan ma kai ta girgiza, "in baki fad'a man damuwar ki ba wa zaki fad'a mawa ko kin fi son ki 6oye abu har wani ciwon ya kama ki?" jin yadda tay Maganar a tausashe yasa ta d'ago ta kalleta idanunta cike da k'walla cikin karyayyar Murya tace "Ya Haisam ne ke fushi kan abunda ya faru" d'an guntun murmushi gwaggon tay tace "to ba dole yay fushi ba ko ke baki ga laifin da kika aikata mashi ba, ba d'azun nan naji kina fad'a ma Fauziyya saida yay ta kiran ki harda sak'o ya tura maki amman kika k'i saurarar shi sai ke yanzu kike son ya saurare ki kome?" Shiru bata ce komae ba k'walla na zubo mata gwaggo taci gaba "ni kaina da naji hakan in fad'a maki gaskiya ban ji dad'i ba wllh nayi zaton zaki amfani da hankali kafin ki yanke hukunci" cikin muryar kuka tace "Gwaggo ni ban sani bane nayi zaton hakanan hakan ya faru shiyasa naji tsoron abunda zai biyo baya gashi Makaranta har an fara gulman ciwon da nike ina tsoron abun ya fito in samu matsala ga kuma ke da kuma zumuncin dake tsakanin ku da Hajiya da kuma surutan mutane in aka sani shiyasa na k'i saurarar shi don nasan yana iya cewa in bar shi" 6ata rai gwaggo tay sosae tace "wato kin fi tsoron wad'annan abubuwan akan Mahalliccin ki? Ko baki san girman laifin zubar da ciki ba?" d'an yarfa hannu tay "na sani gwaggo naga cikin k'arami ne sosae kuma bada son raina na same shi ba sannan in na barshi zan fuskanci matsaloli da yawa shiyasa naga gara in zubar" d'an ta6e baki gwaggo tay "baki tunanin matsalolin shi kuma zubar da cikin ba? Baki tunanin har ranki zaki iya rasawa ba?" shiru tay ta sadda kai gwaggo taci gaba "nayi mamakin duk irin yardar dake tsakanina dake har kika iya 6oye man wannan babban Al'amarin ashe zaki iya cutar dani har haka Fatuu??" A rud'e ta fara girgiza mata kai k'walla na zuba ta kai hannu ta kamo hannunta guda tace "a'a gwaggota don Allah kar kice haka wllh tallahi kin ji na rantse bada son raina nayi hakan ba saboda gudun matsalolin da zasu biyo baya ne kuma wllh ke na fi ji ma Saboda ni bansan ya aure ni ba nayi tunanin in kika ji zaki shiga mawuyacin hali ne Saboda kina yawan gargadi na da bani misali da yar wajen aikin ki gashi naga kuma shi an yarda dashi an amince mashi hakan yasa naji tsoro don nayi tunanin zuciyar ki ma zata iya bugawa wllh wannan ne dalili amman Allah ne shaida ta ban ta6a yunkurin aikata abu makamancin wannan ba, wllh gwaggo ko saurayi bani dashi duk da ana yawan nuna ana so na amman ban saurarar su balle ta kai ni ga aikata wani abu ba daidai ba shi kan shi koda muka je can G.r.a d'in raina bai so in shiga ba kawae don na yarda dashi nasan bazai cutar dani ba yasa na bi shi" yar ajiyar zuciya gwaggon ta sauke tace "amman miyasa tunda abun ya faru baki sanar da ni ba in har akwae yarda a tsakanin mu, washe garin ranar har d'akin ki nazo da safe kika nuna man kan ki na ciwo miyasa baki fad'i man ba sai kika za6i ki 6oye man k'arshe ma kika gudu Makaranta wannan abun ya ta6a ni Sosae bazan 6oye maki ba yasa na fara tunanin zaki iya cuta ta" idanunta ne suka ciko hakan ya k'ara tada hankalin Fatuu ta k'ara k'ank'ame hannunta dake cikin nata a rud'e tace "a'a gwaggota kar ki wannan tunanin a kai na don Allah wllh bansan taya zan fad'i maki abu irin wannan ba ina tsoron wata matsala ta biyo baya ne banson in rasa ki kaman yadda na rasa Mahaifiyata ke nike gani madad'in ta ban son rasa ki gwaggota ganin Al'amarin na da girma, ki yarda dani Don Allah wllh ban taba munafuntar ki ba kinji na rantse" sosae take kuka itama gwaggon har kwallan sun fara zubo mata can ta sa hannu ta fara goge ma Fatun k'wallan ta tace "shikenan ya isa kar kija ma kan ki wani ciwon amman daga yanzu kar ki k'ara 6oye man koma miye da ya shafe ki zan fahimce ki tunda ai ni musulma ce na yarda da k'addara mai kyau da kuma mara kyau komi ya faru da bawa dama can an riga da an rubuta tuni alkalumma sun bushe ko wata matsala gare ki kar Kiji komae ki fad'a man in inada iko sai in maki maganin ta in kuma ban iyawa sai in taya ki rok'on mai kowa da komae tunda shi yace mu rok'e shi zai amsa mana wannan shine amfanin Mahaifiya daga inda ta gane kana 6oye mata abubuwa kana rushe yardar da ke tsakanin ku ne" da sauri Fatuu ta jinjina mata kai tace "in sha Allahu bazan k'ara 6oye maki komai ba mahaifiyata" hannu gwaggon ta bud'e mata tana murmushi ta fad'a jikinta ta rungume ta sosae wata irin natsuwa zukatan su suka samu sun d'an d'auki lokaci a haka kafin gwaggo ta d'agota tana fad'in tasan halinta yanzu ta kama yin bacci Fatun tay murmushi, warware mata shawarmar tay tace "ki saki jikin ki kici tunda dae shi ba sanin baki cin zai yi ba nasan kawae yana maki hakan ne don ki gane kin yi mashi ba daidai ba amman nasan zai fahimce ki sai kuma muga abunda Allah zai yi dangane da Al'amarin auran na ku" shiru Fatun tay ta mik'a mata shawarmar ta amsa ta fara ci a hankali, tana cikin ci tace ma gwaggo itafa in ba wata shawarmar su ci tare tace akwae zata ci, matsa mata tay saida ta d'aukko harda youghort ta k'aro ma Fatun, suna cikin ci Fatun ta tambaye ta yadda akai Ya Haisam d'in ya aureta tana murmushi ta fara bata labari tiryan tiryan har ta gama, sosae Fatuu ta jinjina abun a ranta wato ashe ma taimakon ta yay ita dama abun ya matuk'ar d'aure mata kai data ji wai ya aureta gashi yanzu abunda ya k'ara bata mamaki irin kud'in da ya biya matsayin sadaki nan take taji bata ji dad'i ba data 6ata mashi rai saidae ta wani bangaren kan ta ne ya kulle kan tunanin dalilin da ya sa bai sake tan ba kamar yadda aka tsara har abu yazo ya shiga tsakanin su, kamar gwaggo tasan abunda ke ranta taji tace "nayi zaton bayan auren zai sake ki to amman sai bai yi hakan ba k'arshe har Abbas na tuntu6a don yay mashi Magana Saboda kar kici gaba da karatu ga auren da baki sani ba akan ki amman sai ya nuna a k'yale shi kawae tunda ai yasan da hakan aka tsara k'arshe ma sai ya nuna shi dama yafi son auran ya d'ore to farko dae ni gaskiya ban so ko don Saboda Matar shi ganin amincin dake tsakani to amman kuma daga baya sai nay tunanin in hakan Allah ya k'addaro ba yadda za'ai" kallon Fatuu tay da ke taunar abu a hankali tana saurarar ta wani murmushi tay tace mata "Ke ma kina son auren ya d'ore ne??" Waro ido Fatun tay ta dakata da taunar abun bakin ta batay tunanin zata mata wannan tambayar ba, ganin yadda ta kafeta da ido alamar jiran amsar ta yasa ta girgiza kai a hankali alamar a'a, wata dariya taga gwaggon tayi har saida ta tsargu ta bita da ido can ta furta Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi daga haka ba wanda ya k'ara cewa komae suka cigaba da cin abubuwan da Suke ci har fruit da naman gwaggo ta k'ara d'ebo masu saida suka ci suka k'oshi sauran ta saka acikin Fridge dake a d'akin, bayan sun gama Fatuu taje tayo brush lokacin data fito har gwaggo ta gyara mata gadon ta maida brush d'in ta haye gado ta kwanta gwaggo ma saida ta wanko bakin bayan ta fito ta d'aukko bargo ta rufa ma Fatun kafin itama ta fiddo wani bedsheet ta nufi kujera tana fad'in tunda harda fruit suka sha tasan zai taimaka wurin saurin narkar da abunda suka ci tunda ba'a son da an ci Abinci a kwanta gashi bacci take ji ta haye kujerar bayan tayi Addu'oi ta tottofe a 6angarorin d'akin ta kwanta, lamo Fatuu tay tana tunanin masoyinta ta ayyana tunda take dashi ba abunda ke shiga tsakanin su face Alkhairi amman bata ta6a tunanin zai amince ya aureta ba don kawae ya taimaketa wani kalan son shi taji ya ratsa zuciyar ta har saida ta lumshe ido Slowly ta furta "Am so sorry for my mistake Ya Haisam and my beloved husband also" wani irin murmushin dad'i ta saki nan ta fara tariyo abunda ya faru tsakanin su a G.r.a tun farko da suka fad'a saman gadon da lokacin da tay mashi magana taji shiru bai ce komai ba ta kai hannu ya nutse cikin sumar shi mai taushi ga santsi wani irin dad'in ta6awa ne da ita, a hankali ta gangaro kan lokacin da ta bud'e baki don sake yi mashi magana bata samu damar k'arasawa ba ya had'e lips d'in su wannan karon kankame jikinta tay tunowa da yadda ya rink'a bata hot and deep French kisses the way she felt at dat moment was like her breathing would cease, haka tay ta tunano abubuwan da suka faru wani lokacin tay murmushi wani ta tsuke fuska wani ta kankame jiki a haka har bata san lokacin da bacci yay awon gaba da ita ba........... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2056* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ........Washe gari lahadi tun wurin karfe 8:30 Tk ya kawo masu Breakfast daga gidan Hajiya haka wurin 9 ma sai ga Fauzy itama ta kawo masu tace ma Fatun zata je ta dawo Aunty ta aiketa Kasuwa, da har gwaggo ta kira Amadu kan ya had'o masu abun karin kumallo ganin sun kakkawo yasa ta kira shi tace ya barshi, wurin karfe 12 na rana saiga Haulat harda innar su sunzo gaida Fatun take ce mata ita bata san tana Asibiti ba sai da k'anwar ta taje siyayya shagon Kawu Amadu yake fad'a mata, cike da nuna damuwa ta tambayi Fatun wai miyake damunta da har ya kaita ga kwanciya Asibiti tana rungume da Babyn Haulat d'in da ta k'ara girma Tubarkallah ta bata labarin sanadin ciwon, sosae ita ma Haulat ta girgiza da jin zancen Aurenta da Ya Haisam tace Allah kenan mai yin yadda yaso a kuma lokacin da ya so cike da farinciki duk da bata ji dad'in rasa cikin ba tace "K'awata kinga abun Allah ko gashi har kin ci ribar hakurin da ki kai, muna ta ganin kaman shi ba rabon ki bane ashe da rabon a kusa ma" ta k'arasa tana murmushi shiru Fatuu tay da damuwa akan face d'in ta Haulat da ta lura da hakan tace "ko baki farinciki ne Allah ya cika maki burin ki, ko kuwa Saboda rasa cikin ne, kiyi hak'uri duk rashin sani ne ya jawo haka Allah ya k'addara hakan sai ya faru" yar ajiyar zuciya Fatun tay a sanyaye tace "haka ne Haulat na sani kawae dae ina ganin auren ba zai d'ore ba tunda ga dalilin yin shi" da sauri tace "in sha Allahu zai d'ore mutu ka raba keda ya Haisam bi'iznillahi ki kwantar da hankalin ki ni ina ganin hakan hikima ce ta Ubangiji dama ya kaddaro shine mijin ki shiyasa komae ya faru, baki ga da akai auran ba duk da ga yadda aka tsara amman kuma sai bai sake ki d'in ba k'arshe ma ga abu har ya shiga tsakanin ku harda rabo ni na tabbatar auran nan zai d'ore ke yama d'ore kawae" ta k'arasa tana yar dariyar farinciki still da yanayin damuwa Fatuu tace "amman fa Haulat Ya Haisam d'in Fushi yake dani kan wannan abun daya faru yana ganin nayi mashi taurin kai Saboda nak'i in saurare shi naje na zubar da cikin" itama yanayin fuskar ta ne ya sauya ta kai hannu ta kamo hannun Fatun guda tace "kinga wannan ma kadae ya isa yasa ki gane ya Haisam ba don ya sake ki ba ya aure ki in ma farko da wannan niyyar ne to daga baya ya canza ra'ayi tunda gashi har bai ji dad'in zubewar cikin ba wanda da yana da niyyar rabuwa dake ai shi dad'i zai ji koma da kan shi yasa a zubar Saboda kar abun da ya shiga tsakanin ku ya bayyana, nasan shi mutum ne mai fahimta sosae zai fahimci dalilin ki yay maki uzuri tunda ai sun san ke baki san da auren ba kuma Saboda ku duka kika aikata hakan, don haka ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai faru kawae yana fushin ne don ya nuna maki kin mashi laifi kuma ki gane bai ji dad'i ba ko don Saboda gaba, keda ma kike yar gidan shi dama ko kin 6ata mashi rai da kin bashi hakuri yake hak'ura ki tuna fa tun farkon sanin shi kafin ku saba ma babbar asara kikae mashi harta kud'in shanu goma kuma kina sane kika aikata mashi amman kina zuwa kika bashi hakuri ya hak'ura balle kuma yanzu da kuka zama abu d'aya ya kuma san abunda kika yi kuskure ne sakamakon rashin sani da Kin san komae baza ki aikata hakan ba kuma yanzu da ya baki dama zaki gyara laifin ta hanyar biyan shi abunda ya rasa ba kamar na shanu ba" ta k'arasa tana dariya itama Fatun yar dariyar tayi ba kamar da ta tuno mata da can baya, kwantar mata da hankali taci gaba da yi har saida taga ta washe bayan sallar Azahar suka tafi, wurin k'arfe ukku Fauzy ta dawo harda Abincin rana ta kawo masu Gwaggo tay ta godiya tana fad'in ba'a gajiya da d'awainiya Fauzy na murmushi tace ai an zama d'aya gwaggon tace hakane tay Addu'ar Allah ya bar zumunci, Fauzy da kanta ta zuba ma Fatun ta kai mata saman gado tana ci suna yar fira nan take fad'i mata zancen zuwan Haulat ta nuna bata ji dad'i ba da basu had'u ba amman in suka koma gida zata je ta k'ara ganin Baby d'in su, bayan ta gama cin Abincin Fauzy ta d'aukko mata drugs d'in ta tare da bottle water ta sha, gab da la'asar sai ga su Feenah sun k'ara zuwa yau ma harda Abinci, da Abbas ne zai kawo amman Abdul ya sa rigimar sai anzo aikuwa tunda suka zo ya haye gadon suka kankame juna shida Fatun daga baya Abbas ya shigo ya gaishe da ita tana ta murmushi ta amsa har yana fad'in "Alhamdulillah da alamu Amaryar mu da wuri zata warware ta biya mu abunda muka rasa" murmushi Fauzy da Feenah sukai ita dai d'an sadda kai kawai tay tana d'an murmushi ya tambayi ta ci Abinci tasha magungunan ta Fauzy tace eh, sai bayan la'asar suka tafi da daddare bayan isha Haisam yazo yau ma kaman jiya da manyan ledoji yana sanye da k'ananun kaya yana shigowa Fauzy da har lokacin tana nan don tace yau a nan zata kwana ta mik'e daga kan kujera da suke zaune tare da gwaggo taje ta amshi ledojin tana mashi sannu da Zuwa ya d'aga mata kai ya juya suka gaisa da gwaggo ganin tana niyyar mik'ewa don ta bashi wuri yasa shi ce mata ta zauna zai wuce ne tace to ta koma Fauzy ma bayan ta aje ta dawo kusa da gwaggon ta zauna, slowly ya nufi gadon Fatuu na zaune jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa ta jingina da bango kanta sanye da hula ta kallabin rigar tayi wani fayau da ita ta k'ara haske sosae saidae ta rame ba kamar Fuskarta har idanunta sun fad'a, a gefen gadon ya tsaya tunda ya shigo ta sadda kai k'asa saida taji tsayawar shi a wurin ta d'an d'ago suka had'a ido ta gaishe da shi jinjina mata kai yay slowly ya tambayi jikinta ta bashi amsa da Sauk'i, shiru yay idon shi akanta itama shi take kallo tana yi tana d'an maida idon k'asa tana sake d'agowa da su duk ta kame kan ta can ya d'an ta6e baki ya juya ya nufi hanyar fita su gwaggo su kai mashi saida safe ya amsa, tunda ya tafi tay zugudum Fauzy ta taso ta zo gefen gadon ta zauna ganin yanayin Fatun ta tambaye ta har yanzu fushin yake cikin raunanniyar murya tace mata eh Fauzyn tace "ki daina damuwa k'ilan ma fa ba wani fushin da yake tunda irin su dama gane masu yana da wuya kawai k'ila yana canza maki fuska ne don ki gane kin mashi laifi" shiru kawai tay amma ita ai ta karance shi sosae tana gane yanayin shi, yau ma dai kaman jiya suka sha shagalin su da abubuwan da ya kawo gwaggo ta zubo masu itama ta zuba ta koma kan kujera da Fatuu tak'i ta ci Fauzy ta tursasa mata harda yin k'asa k'asa da murya tace "ki saki jiki ki ci ki k'oshi ta hakane zaki samu sauk'i sosae cikin d'an lokaci ko Kya yi sauri ki biya shi abunda kika sa ya rasa ya daina fushin in ma shi yake yi" wani kallo mai kaman harara tay mata Fauzyn ta sa dariya tana d'an gumtse baki daga baya Fatun ta fara ci suna cikin ci cikin rad'a Fauzy tace "akwae wata mai magunguna da Aunty ke siye jiya dana koma muke Maganar da ita tace yakamata a amsar maki su don suna da mugun kyau wllh tunda ita tana amfani dasu ta shaida ingancin su, haka tace su maza ta haka ake kama su Aunty harda cewa wai ba kamar irin wad'annan miskilan mazan an fi kama su ta nan wai har zaucewa suke kaita mamaki kaman basu ba kinsan mijinta shima miskili ne duk da bai kai Ya Haisam ba" cikin rashin fahimta Fatuu da tayi sototo tace mata wai wane irin magunguna ne Fauzy tay mata wani kallo tasa hannu ta ruk'e ha6a tace "yanzu nan wai ke baki gane inda aka dosa ba sai kace wata yar primary magungunan mata fa ake nufi wanda mata ke sha don gyara jikin su Saboda su kama mazajen su badai wai baki san su ba?" Shiru Fatuu tay kaman mai tunani can tace mata ta san su taga ana tallan su a Tv kuma da suna secondary school lokacin da suka kusa gamawa wad'anda zasuyi aure da sun gama suna zuwa da su suyi ta sha harma su samma su har da wani mai kaman chocolate da kwakwa a ciki tana son shi yana da dad'i don Haulat har badawa tay aka siyo mata da yawa suna sha, da sauri Fauzy tace "Chocolate gumba kenan akwae ma ta kwakwa da dabino d'an banzan dad'i ne da ita wllh duk ni ke sace ta Aunty Mareeya tay ta fad'a harma ta gaji yanzu in aka kawo mata sai ta d'ibar man a yar roba ta bani tace in na satar mata nata wuta bal bal" gaba d'aya suka sa dariya Fauzy ta k'ara cewa "kinsan akwae su fa da yawa wasu gari ne da Madara ake sha wasu da Zuma wasu na ruwa ne ke harda itatuwan tsarki tarkace ne sosae ake had'o ma mutum, kuma fa wai kinsan kaman gumbar nan da kika ce kina son ta tana da dad'i wai fa haka suke ji mazan in ku kai Meeting" waro ido Fatuu tay don ta gane meeting d'in da take nufi Fauzy tasa hannu ta gumtse dariya Fatun ta girgiza kai a hankali tace "Allah ya shirye ki Fauzy nidai ba ruwana" da sauri tace "ke kau keda ruwa wllh don ba k'aramin gyara zaki sha ba Aunty tace duk sai an sauke mashi miskilancin da Matarshi ta kasa sauke mashi wai sai an sa duk inda ya zauna sai ya ambaci sunan ki nace mata Aunty kaman wani zautacce tace ai haka zai koma a kan ki" gaba d'aya suka saka dariya har saida suka ja hankalin gwaggo dake cin abu tana saurarar radio ta juyo ta kalle su Fauzy data lura ta wutsiyar ido ta zaro ido had'i da rufe baki da ido tay ma Fatuu nuni da gwaggo itama ta gumtse dariyar, suna haka Amadu ya shigo dama gwaggo ta kira shi don ya kawo mata abun shimfid'a ta kwanta k'asa ita kuma Fauzy sai ta kwanta kan kujerar da fara'a ya shigo ya nufi gwaggo ya kai mata kayan suka gaisa ya juya ya nufi gadon ya tsaya a bakin gadon yana fad'in "kuce kuna nan kuna shagalin ku wannan to jinya kuke ko party" duk dariya su kai Fauzy ta gaishe dashi ya amsa Fatuu ma haka ya tambayi jikinta tace mashi ta samu sauki yace ai gashi nan kam ya gani suka k'ara sa dariya Fauzy tay mashi bismilla yace suci gaba da shagalin su ya juya ya koma wurin gwaggo ya tambaye ta yaushe za'a sallame su ne yaga ai ta samu sauk'i sosae tace to suna dae jiran Dr har yanzu bai ce komae game da sallamar, da zai tafi ta k'ulle mashi sauran abubuwan da suka rage tace in yaje sai yaci ya amsa yay godiya sukai sallama ya tafi, Washe gari wurin k'arfe tara da yan mintuna Dr ya shigo lokacin Fauzy ta tafi tuni Saboda zata makaranta Fatuu tayi wanka tana zaune gefen gado tana yin Breakfast da Tk ya kawo masu bayan sun gaisa da gwaggo dake zaune kan kujera tana shan tea yay mata ya mai jiki ta amsa ya nufi Fatuu ya tsaya bakin gadon itama ta gaishe shi da murmushi ya amsa yay mata ya jiki tace ta samu sauk'i yace Alhamdulillah haka ake so ya tambayi tana cin Abinci sosae ko tace mashi eh, jinjina kai yay daga nan ya shiga yi mata wasu tambayoyin tana bashi amsa daga baya yace bari ya duba bp d'inta ta maida kayan breakfast d'in kan drawer ya fara gwada ta harda idon ta ya bud'e ya duba bayan ya gama yace zata iya cigaba da yin Breakfast d'inta tace to, juyowa yay ya dawo wurin gwaggo yace mata yana ganin tunda komae lpy lou za'a sallame su yanzu sai taci gaba da shan magungunan ta a gida tana murmushi ta amsa da to had'i da yin godiya ya juya ya tafi, bayan ya koma Office ya kira Haisam ya fad'i mashi za'ai discharge d'in su yace mashi gashi nan zuwa yana kan hanya, bayan ya iso Office d'in Dr ya nufa yana sanye da jallabiya bayan sun gama tattaunawa ya fito ya nufi Amenity, kwankwasa kopar yay aka bashi izinin shiga sannan ya tura da yar sallama gwaggo da har ta fara packing kayan su ta juyo tana kallon shi da murmushi ta amsa sallamar tay mashi sannu da zuwa bayan ya gaishe da ita ya fad'i mata Dr ya sallame su tace to Alhamdulillah Allah ya k'ara mata lafiya ya kyauta gaba a hankali ya amsa da Amin kafin ya tambayi ko akwae kayan da za'a fitar tace eh ga wasu nan ta juya ta d'aukko mashi jakar kayan Fatuu da Basket ya amsa yana shirin juyawa Fatuu tace mashi ina kwana ya dakata ya kai idon shi kan ta bai amsa ba slowly yace mata ya jiki ta amsa sannan ya juya tabi bayan shi da kallo, bayan ya fita gwaggo ma ta d'auki su bargo da wani basket d'in tabi bayan shi, bayan an kai komae Mota Fatuu ta saukko daga saman gadon ta yafa gyalenta suka tafi bayan sun fito saida gwaggo ta lek'a d'akunan dake kusa da nasu tay masu sallama da Addu'ar samun lafiya sannan suka wuce, lokacin da suka isa Motar Haisam d'in bai ciki gwaggo ta bud'e mata gaba ta shiga itama ta bud'e kopar baya ta shige basu dad'e da shiga ba sai gashi ya fito hannun shi ruk'e da ledar magunguna da Dr ya sake rubutawa bayan ya iso ya bud'e driver seat ya zauna ya rufe kopar a gefen shi ya aje ledar ya tashi Motar suka tafi, tunda suka taho idon Fatuu na gefe tana kallon hanya har suka iso Amadu dake cikin shago yana ganin Motar ta parker da sauri ya bud'e ya fito ya nufo Motar yana washe baki shi ya bud'e ma Fatuu kopar ta fito lokacin itama gwaggo ta fito yana ta washe baki alamar yaji dad'i yace ma gwaggo ashe yau za'a sallame su tace eh suma basu sani ba saida safen nan da likita yazo, kallon Fatuu dake tsaye yay yayi mata sannu ta d'aga kai ya juya ya nufi Haisam da ya fito yana kokarin bud'e boot ya gaishe dashi, tare suka fiddo kayan ciki Amadu ya d'auki wasu ya nufi gida Haisam d'in na niyyar d'auka gwaggo tace mashi don Allah ya barshi za'a kwashe hakan yasa ya dakata, godiya ta shiga yi mashi had'i da Addu'oi a hankali yake amsawa ta d'auki wasu kayan ta juya Fatuu dake tsaye ta bita suka nufi gidan tana tafiya a hankali har ta kusa shiga ta juyo ta kalle shi suka had'a ido har lokacin yana tsaye a bakin boot d'in jiki a sanyaye ta juya ta shige, suna shiga gidan tsaf da gani ma da safen nan an share shi anyi Mopping dama Amadu baida ganda ya iya komai na cikin gida, d'aki Fatuu ta nufa gwaggo tace ta shiga parlor bari ta canza mata zanin gado tace to, bayan ta d'aukko wankakke a d'akinta ta shiga ta canza mata sannan Fatun ta koma d'akin tana shiga ta nufi gado ta hau ta kwanta, bayan gwaggo ta koma d'akinta ta kira Hajiya a waya ta sanar mata an sallamo su tay mata barka tace sai ta shigo tare da tambayar jikin Fatun suna gama wayar gwaggo ta cire kayan jikinta ta fito don yin wanka dama ita bata yi ba a Asibitin sosae taji dad'in sallamo sun da akai don komi dad'in wuri naka yafi ba kamar kuma wuri irin Asibiti da sam baida dad'in zama sai dole, tana kwance lamo can ta tuna da bata fad'i ma Fauzy an sallamo su ba kuma tasan yanzu an isa yin break hakan yasa ta kai hannu ta d'aukko wayarta dake a gabanta ta kira ta, sosae taji dad'in jin an sallame su tace in aka tashi tana nan zuwa sukai sallama, bayan ta gama wayar ta aje shiru tay tana tunanin Mijinta ta rasa gane mashi yanzu ada in tayi mashi abu ba daidai ba da ta bashi hak'uri yake hak'ura amman yanzu ta lura kaman bai hak'ura ba koda ta bashi hakurin gashi kuma ita a ganinta in ma tana da laifi ai shima yana da shi miyasa tun da abun ya faru bai sanar mata shi mijinta bane koda lokacin da suka je Asibiti ne bayan an gama dubata da suka dawo Mota ya shigo baya yana bata hak'uri har yana fadin zai gyara laifin shi ai tun lokacin ya kamata ya sanar mata, sannan ko da bai K'asar da ya turo mata kud'i har ya kirata daga baya da bata d'auka ba ai ko message ba sai ya turo mata ba yayi mata bayani haka tay ta raya abubuwa a ranta har bacci ya kwasheta, gwaggo na fitowa daga wankan ta sa yar doguwar rigar shan iska ta haye gado don tana da bashin bacci aikuwa nan da nan ya kwasheta, ba ita ta farka ba sai wurin sha biyu ta fito don d'aura girki ta lek'a d'akin Fatuu da har lokacin bacci take sakin labulan tay tana niyyar shiga kitchen ta jiyo wayarta na ringing ta koma d'aki ganin Hajiya ce yasa ta d'aga da sauri bayan ta gaishe da ita tace mata ba sai sun yi Abinci ba gashi nan Saude nayi ta kira d'azun ba'a d'aga ba tasan bai wuce bacci suke gwaggon tace eh wllh tay mata godiya bayan sun gama wayar sosae ta ji dad'in hakan a ranta dama baccin bai ishe ta ba ta koma ta kwanta cikin ranta tana jinjina kirki irin nasu shiyasa sam bata ji dad'in Al'amarin nan da ya faru ba don gaba d'ayan su sun shiga tashin hankali ba kamar Hajiya data sha kuka, Bayan sallar Azahar Saude ta kawo Abincin lokacin Fatuu ta farka saida ta shiga d'akin tay mata ya jiki sannan ta tafi gwaggo ta zubo ma Fatuu Abincin da aka kawo wanda lafiyayyar sakwara ce miyar egusi da tasha ganyen ugu ga ganda da kuma nama sai farfesun yan ciki wanda hanta tafi yawa a ciki sai uban k'amshi ke tashi ta kai mata d'aki itama Abincin ya burgeta tun bata ci ba, saida ta wanko bakin ta sannan ta fara ci, bayan gwaggo ta zuba ma Amadu ta mik'a mashi itama ta zuba ta koma d'akin Fatun ta zauna kan Carpet tana ci suna d'an yin fira da Fatun dake zaune a bakin gado tana cin Abincin, wurin la'asar Fauzy tazo harda Abinci ta kawo masu bayan ta shiga sun gaisa da gwaggo ta aje mata basket d'in tana ta mata godiya ita kuma tana murmushi tana cewa ba komai ta fito ta nufi d'akin Fatuu lokacin tana kwance tayi wanka ta canza kaya zuwa doguwar rigar material itama Fauzy ita ce a jikinta tayi rolling veil tana rataye da side bag suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi ta nufi gadon Fatuu ma ta tashi zaune, hayewa gadon Fauzy tay ta yadda suke facing juna tace "sannu Amaryar mu ya k'arfin jiki?" Yar harararta Fatuu tay Fauzyn tana dariya tace "ai dai ba k'arya nayi ba ko kuma wasa da gaske amaryar ce ke, kinsan kuwa a Makaranta dana fad'a cewa ke matar aure ce akaita mamaki" Fatun tace miyasa ta fad'a tace "to ai kinga dama anata gulma gashi yau baki je ba sai tambayata ake wai badai jikin naki bane yay tsanani shine nace masu miscarriage ki kai dama ke matar aure ce mijin naki ne ba zaune yake a K'asar ba yana dai zuwa, aikuwa kinga yadda akaita mamaki kuma wllh nan da nan suka yarda har wasu na cewa wai shiyasa wani lokacin kike zama hostel wani lokacin kuma kiyi day nace masu eh har na bud'e pictute d'in ki wanda kikae tare dashi na nuna masu wasu suka ce sun ta6a gani ya kawo ki wasu kuma ya zo d'aukar ki Zainab Muhammadu ma cewa tay tabbas ta ta6a ganin shi har sukai ta yaba kyawun shi ita da su Sa'adatu nan fa ta hau shela harda hawa saman Desk tana fad'in to masu gulmar Fatima Ard'o na da ciki tabbas tana da shi kuma na halal ne don da auren ta kuma gashi nan sun ja sakamakon gulmar da suke cikin ya zube sai Allah ya saka mata bak'in k'azafin da akai tay mata, sosae ta bani dariya wllh" d'an murmushi Fatuu tay ta d'an ta6e baki tace "Auran dake lilo" da sauri Fauzy tace "in sha Allahu ba wani lilon da yake komai zai daidaita mu sha biki...." Katseta Fatuu tay "har yanzu fa Fauzy fushi yake" Fauzy tace "zai yi ya gama ne amman ni na tabbatar ya riga ya gama shigowa hannu tunda abunnan ya faru kin ma tuna man ga sak'o Aunty Mareeya ta bani in kawo maki" tana kai Maganar tasa hannu ta ciro side bag d'inta ta bud'e wata kullin bak'ar leda ta fiddo bayan ta bud'e ta ciro wata yar kwalba madaidaiciya ta mik'a ma Fatun ta amsa ta fara karanta sunan maganin da bayanin yadda ake amfani dashi ba Arzik'i tasa hannu ta rufe baki Fauzy ta kyalkyace da dariya tace "Wllh nima sunan maganin ya ban dariya lokacin da zata bani sak'on fa hana ni tay in duba aikuwa ina hawa Napep na bud'e nima saida na rufe baki nace Ya Haisam ya bani ana shirya mashi makaman da zasu tarwatsa miskilancin shi" yar dariya Fatuu tay tare da d'an girgiza kai Fauzy ta shiga fiddo sauran tana mata bayani wani da Madara zata sha wani da nama haka tay ta mata bayani ita dae tayi zuru saida ta gama sannan tace "Dama sana'ar kika fara yi kinga yadda kike bayani sai kace kece mai maganin" Fauzy ta kyalkyace da dariya Fatun ta k'ara cewa "kema yakamata Fauzy ki manta da abunda ya faru ki fara saurarar samari ko Kya samu miji kema kiyi auranki, lokaci tafiya yake muna k'ara shekaru gashi mutuwa ake yakamata muyi auren ko don mu samu masu yi mana Addu'a" idanun Fauzy ne suka ciko da k'walla cikin raunanniyar murya tace "Wllh Zarah na kasa mantawa da Mujaheed duk da irin abunda yay man ba kuma wai ace in ya dawo gare ni zan iya auran shi ba wllh tllh ko da ace misali dole sai shi zan aura to saidai in mutu ban auren ba, kawae zuciyata ce sam bata man Adalci data kasa cire man shi a rai", Fatuu tace "matsalar daga wurin ki ne Fauzy kin k'i ba wani namiji dama da zaki daure ki ba wani da yake son ki dama a hankali zaki ga kin fara cire shi a ran ki, ki daure Pls" ta kai hannu ta kama hannunta guda, d'an murmushin yak'e Fauzy tay tace "zan jaraba in sha Allahu duk da a yanzu ba wani da zan ba damar amman k'ilan ko da bikin ki kinsan ance a bikin wata wata ke samun miji" ta k'arasa tana d'an murmushi haka Fatun ma tace "wai wane biki abunda an riga da an d'aura tuni" da sauri tace "aikuwa dole in komae ya daidaita mu sha shagali sai kace wani auren mak'iya za'a yi shi lami dole musha anko mu cashe bikin d'an Senator guda" dan ta6e baki Fatun tay can tace "Don Kawu Amadu bai had'u ba dana had'a ku" yar harara Fauzy ta wurga mata "Kawu Amadun ne zaki ce bai had'u ba santalelen saurayi dashi ga tsawo gashi fari ga kyau daidai gwargwado" dariya Fatuu tay tace "ai ba wannan had'uwar nike nufi ba ta kud'i nike nufi shi baida kud'i ke kuma na fi son ki auri wanda Mujaheed zai girgiza in yaji" d'an murmushi Fauzyn tay "Allah ya za6a mana abunda yafi zama Alkhairi a gare mu" Fatuu ta amsa da Amin suka cigaba da hira har Fauzy na ce mata ta tashi ta 6oye magungunan kada gwaggo ta shigo ta gani tace to tana k'ok'arin sauka daga gadon. Tun bayan da Haisam ya maido su G.r.a ya wuce don yin wani aiki a computer sai da akai Azahar sannan ya dawo gidan Hajiya ya kwanta bacci, saida aka fara kiran sallar la'asar sannan ya tashi yay wanka ya shirya ya wuce Masallaci, bayan ya fito daga Masallacin parlon Hajiya ya wuce lokacin da ya shiga ba kowa ya nufi ciki ya zauna kan 2 seater ya d'auki remote yana canza channel, bai dad'e da zama ba Hajiya ta fito jikinta sanye da doguwar riga da mayafinta hannunta ruke da sandar ta haka idanunta na saye cikin medical glasses d'inta hango shi da tay yasa ta nufi cikin parlon don da gidan su Fatuu ta fito zata, tana zuwa cikin parlon ya d'aga ido yana bin ta da kallo har ta zauna a kan one seater d'in dake gefen shi itama kallon shi take bayan ta zauna tace "ashe ka tashi" kai ya d'aga mata, "ai tun d'azu nike dakon ka bansan ma ka dawo gidan ba saida Saude ta dawo daga gidan su Fateema nike tambayarta ko taga Motar ka a parking space tace man eh" shiru kaman bazai ce komae ba sai kuma yace "ba sai ki kira ba" d'an ta6e baki tay tace ai na kira ka sau biyu ko, farko landline na kira ba'a d'aga ba na kira wayar ka itama baka d'aga ba nan nagane bacci kake" yana ta kallonta har ta gama sannan ya d'an d'age gira yace "Wani abu?" tace "kaci Abinci ne?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, "to sai kai zaune da yunwa baka iya shiga kaman magana" tay Maganar tana d'an hararar shi d'an guntun murmushi yay "ban jin shi sosae ne" tace "uhmm kai dai ka sani wa zai zauna yay ta fama da kai kan abunda amfanin kan ka ne alhali kai ba damuwa kai da halin da mutum zai shiga ba ya mutu ko yay rai ba abunda ya dame ka" d'an murmushi yay kawae ya fahimci kan zancen ciki daya zo yay mata take Magana da alama dae abun yay mata zafi, "Am all ears da wani abu ne?" Fuska a kwa6e tace ya ci Abinci tukun ta juya tana k'wala ma Saude kira bayan ta fito ta bata umarnin kawo mashi Abincin, akan c-table ta d'aura tray d'in kayan Abincin tana kokarin yin serving nashi ya d'aga mata hannu alamar ta bashshi ta mik'e tace aci lafiya ya jinjina mata kai, a nutse ya fara cin Abincin yana yi yana kallon channel d'in daya kamo Hajiya ma idonta na akan Tv d'in tana kallon American film d'in da ake yi tana yi tana d'age kai had'i da yamutsa fuska wani lokacin har hannu take d'an d'agawa in anyi abun tashin hankali, bai d'auki lokaci mai tsawo ba ya gama ya yago tissue yana goge baki, kallon Hajiya yay bayan ya gama yace mata "am done" ta maido idonta kan shi saida ta gyara zama ta fara magana "dama game da Fateema ne tunda an sallamo ta ina son in ji miye matsayin ta tunda bai yuwuwa a barta tay ta zama da aure a kanta ba kamar yanzu da tasan da shi" shiru yay yana kallon gaban shi har saida tace mashi kar ya 6ata mata lokaci ya bud'e baki yay mata magana don fita take son yi, sigh yay ba tare da ya kalleta ba yace "I will divorce her" wani kallo Hajiya ta bishi da shi jin bata ce komae ba yasa ya juya ya kalleta ganin kallon da take mashi yace "dama haka aka tsara ai ba Abbas ya fad'a maki ba?" a k'ufule tace "eh ya fad'a man hakan aka tsara amman bai ce acikin tsarin anyi da kai zaka rabata da budurcin ta ba" yana jin haka ya juyar da fuskar shi daga barin kallon ta taci gaba "Yanzu kai irin Adalcin ka kenan? Sai da ka raba yarinya da pride d'inta sannan zaka ce ka saketa wato k'aramar bazawara kake son mayar da ita kenan, idan k'anwar ka ce zaka so ai mata haka?" Shiru bai ce komai ba bai kuma kalleta ba a fad'ace tace "ba tambayar ka nike ba Haisam! idan Jidderh ce Fateema zaka so ai mata haka?" Sai lokacin ya d'an juyo slowly ya furta "am sorry for dat" daga haka yay shiru itama bata k'ara cewa komae ba sai da aka d'an d'auki lokaci sannan ta dasa fad'in "ko kusa ban amince wai kace zaka saketa ba yanzu ta riga ta zama Matar ka dole kaci gaba da zama da ita don haka yanzu dole ta baro gidan su akawo ta part d'in ka nan zata cigaba da zama kafin muga abunda Allah zai yi sai kasan yadda in ka koma zaka sanar ma Matar ka ni kuma daga baya zan kira iyayenka su zo harda ita ta Lagos din sai in sanar masu su kuma ganta ko don Saboda halin rayuwa bai kamata ace duk basu san da Maganar ba auren ba" shiru yay can ya kalleta yace "is dat all?" Kai ta d'aga mashi ganin yana K'ok'arin mik'ewa yasa da alamun mamaki tace "au tashi za kai bazaka ce komae ba?" Dakatawa yay yace "So What do you want me to say ba kin tsara komae ba kiyi yadda yay maki" wannan karon bud'e baki tay galala tana kallon shi ganin hakan yasa shi d'an d'age gira "ba haka ya yi maki ba so just go ahead do as u wish" ta6e baki tay tana mashi wani kallo tace "to yalla6ai shikenan" mik'ewa yay ya nufi hanyar barin parlon walking majestically Hajiya ta saki baki tana bin bayan shi da kallo har ya fuce, hannu ta kai ta ruk'e ha6a a fili tace "tabbas Yau na shaida Miskili yafi mahaukaci ban haushi kaji fa yaron nan don Allah wai ni zai ma duniyanci, in da farko ya aure ta don ya taimaketa wannan na yarda don zai iya yin hakan amman na tabbatar yana son zama da Fateema shiyasa bai saketa ba kamar yadda suka tsara" ta kai Maganar tana ta6e baki had'i da yin k'wafa tana niyyar mik'ewa Saude ta kawo mata wayarta data baro d'aki tace anata kira ta amsa ta duba mai kiran kafin ta d'aga suka hau yin wayar, sun d'auki lokaci suna wayar kafin sukai sallama ganin yamma tayi sosae yasa ta yanke barin zuwa gidan su Fatun sai da daddare............. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2057* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ............. Bayan gama sallar Magrib Hajiya ta nufi gidan su Fatuu lokacin da ta zo daidai shagon Amadu ta d'an d'aga Murya tace "Ahmad ya kasuwa" jin haka yasa ya kallo wajen yana ganinta da yake akwae wuta da sauri ya fito lokacin har ta karya kwanar shiga suka had'e da fara'a ya gaishe da ita ta amsa ta k'ara ce mashi ya kasuwa yace Alhamdulillah, ganin yana k'ok'arin bin ta su shiga gidan tace ya koma wurin sana'ar shi ta gode yay mata a fito lafiya ya juya, tana shiga cikin gidan tay sallama jin ba'a amsa ba yasa ta k'arasa wurin kopar parlon ta k'ara yin wata sallamar da d'an d'aga murya lokacin gwaggo dake cikin d'aki ta ji ta amsa, tana lek'owa ganin mai yin sallamar yasa ta k'arasa fitowa da sauri ta nufeta jikinta sanye da hijab tun bayan da ta gama sallar Magrib bata Mik'e ba zaune take tana yin tasbih ta jiyo sallamar, sannu da zuwa tay mata ta gaishe da ita tana d'an murmushi Hajiyar ta amsa ta nufi cikin parlon tun ma kafin gwaggon tace mata ta shiga, bayan ta shige tabi bayanta daga d'an can gefen kujerar da Hajiya ta zauna itama ta zauna tana k'ara gaishe da ita bayan ta amsa tace "Barka an dawo" gwaggo tace "Yauwa eh wllh", "to Allah ya kyauta gaba ya k'ara mata lafiya, ai kun auna Arziki da Allah ya tashi k'afadun ta ba tare da wata matsala ba" yadda tay Maganar fuskar ta a d'an d'aure cike da girmamawa Gwaggo ta hau bata hak'uri tace ai hak'uri ya zama dole tunda aikin gama ya riga da ya gama wanda aka cuta an cuce shi" d'an murmushi kawae gwaggon tay Hajiyar tace "Ya jikin Fateemar?" tace mata da Sauk'i bari a kira ta tana d'akinta, "In tana bacci ne ki rabu da ita", tace "ban tunanin shi take yi kawae dai tana kwance ne tun bayan da muka dawo sai da dalili take fitowa" tana k'arasawa ta mik'e ta nufi hanyar fita Hajiya na fad'in ai dole tay ta kwanciya wannan uban jini da ta kwararar, lokacin da ta d'aga labulan a kwance ta same ta idanunta a rufe tana sanye da doguwar rigar bacci kanta sanye da hula, nufar ta gwaggo tay ta tsaya a bakin gadon ta kira sunanta jin shiru bata amsa ba yasa ta gane bacci take ta sunkuya ta kai hannu ta d'an bubbuga shoulder d'inta, a hankali ta bud'e idanun suka sauka akan gwaggo tace mata "Sannu ya k'arfin jikin?" hannu ta kai tana muttsike idanun tace mata da Sauk'i gwaggon tace "ba abunda ke maki ciwo?" Kai ta d'aga kafin tace "kawae jikin ne ba k'wari" kai ta jinjina "Wannan dama sai a hankali, ga Hajiya nan tazo ganin ki ki taso" amsa mata tay da to ta fara kokarin saukkowa, a tare suka tafi gwaggon na gaba tana biye da ita suka nufi parlon, bayan gwaggo ta shige da yar sallama itama ta shiga idon Hajiya a kanta ta mik'a hannu tana ce mata tazo ta zauna kusa da ita da yake a saman 2 seater take zaune, a gefenta Fatun ta zauna a hankali ta gaishe da ita ta amsa kafin ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tana tambayar ta ya jikin tace mata ta samu sauk'i sosae, "To Ya jinin yana zuba sosae ne?" ta tambaya sunkuyar da kai Fatuu tay tace "a'a kad'an ne kaman zai d'auke" jinjina kai tay tace "ai kin zubar da jini dole yay saurin d'aukewa" shiru Fatun bata ce komae ba Still kanta na k'asa, "Yanzu akwae abunda ke damun ki a jikin?" d'an girgiza kai tay tace "a'a kawae k'arfi ne babu sosae" tace "Wannan sai a hankali zai dawo kina dae cin Abinci sosae ko?" Kai ta d'aga mata alamar eh tace yayi kyau kafin ta sake tambayar tana shan suma magungunan da aka bata tace mata eh, shiru ta d'anyi kafin ta dasa "Fateema ina son tambayar ki kuma gaskiya nike son ki fito ki fad'a man kin ji ko?" d'agowa tay ta kalleta ta d'aga mata kai alamar to, "Ina son inji shin zaki cigaba da zama da Yayan ki matsayin mijin ki ko kuwa baki so in raba ku?" Dammm! gaban Fatuu yay wani irin bugu ta kasa d'agowa balle tace wani abu ganin haka yasa Hajiya cewa ba shiru zata yi ba ta bud'e baki tay Magana a hankali ta saci kallon gwaggo suka had'a ido tana ganin haka ta juyar da fuskar ta daga barin kallon Fatun ta koma kallon gefe Hajiya tace "ki daina kallon ta ba abunda zata ce maki tunda ai ba ita zata zauna da shi ba dole kece zaki yanke kar Kiji wani abu ki fad'i man ra'ayin ki kan hakan" wani abu Fatuu ta had'iya ta rasa ma wace amsa zata bata duk ta rud'e kanta a k'asa sai zare ido take tana motsa hannuwan ta da bakin ta, da d'an d'aga Murya Hajiya tace mata dare nayi tayi magana d'agowa tay duk ta dabarbarce murya na rawa tace ".....Duk abunda...kuka za6a man yayi man" d'an murmushi Hajiya tay tace "To Fateema in muka za6a maki abunda bai maki ba fa tunda mu ba sanin abunda ranki zai fi so mukai ba kuma dae baso muke mu takura maki ba shiyasa aka baki dama ki fad'i abunda ranki ke so, kinga mu bamu zamu zauna da shi ba don haka kar Kiji komae ki fad'i kina son cigaba da zama dashi matsayin miji ko kuwa a raba ku" k'ara kallon gwaggo tay taga bata kallonta ta maida idon k'asa abu biyu ne suka hanata magana na farko kunya na biyu kuma tana kokonton amincewa ba kamar yanayin da take gani tattare da Haisam d'in, "Shikenan tunda baza kiyi Magana ba bari in tashi in tafi, ni dae bazan yanke hukunci ba yazo kuma bai maki dad'i ba tunda ai harda irin hakan tasa aka fasa wanccan auren ko an za6a maki wanda baki so duk da harda k'arin halin shi" ganin tana k'ok'arin mik'ewa yasa gwaggo ta canza harshe tay ma Fatun Magana da d'an d'aga murya tace bazata bud'e baki tay magana ba, tana yamutsa fuska kaman zata saka kuka itama ta juya harshen tace mata tana so amman kunya take ji ta fad'i mata hakan, Hajiya da ta fasa mik'ewa ta kya6e baki tana bin su da ido har suka gama sannan tace "wato matsalar ka zauna cikin wad'anda ke yin yaren da baka iya ba kenan har gulmar ka sai ayi a kuma zage ka tass ba tare da ka sani ba k'arshe ma har kai ta washe baki kana tunanin abun kirki ake fad'a kaiga sakarai" murmushi kawae gwaggon tay Hajiya dake kallonta tace to mi suka ce a fad'i mata gwaggo tay mata bayani, wata irin kunya ce ta lullu6e Fatuu kan ta a sadde, d'an murmushi Hajiya tay tace "ina ruwan Fateema to miye abun jin kunya mutumin da dama Mijin ki ne kawae amsa zaki bada, shikenan Allah Ubangiji ya shige mana a Al'amarin tashi kije Allah yay maki Albarka ya k'ara maki lafiya damu baki d'aya, a hankali ta amsa da Amin ta mik'e ta nufi hanyar fita sumi sumi har lokacin bata d'ago fuskar ta ba, Bayan fitar ta Hajiya ta kalli gwaggo tace "Sai ku fara shiri ran Juma'a in Allah ya kaimu zata tare a d'akin mijinta nan part d'in shi" rasss kirjin gwaggo yay bata yi tunanin haka da wuri ba a d'an rud'e tace "to..Amman Hajiya bai yi wuri ba kuwa har a shirya ta tare a ranar?" Hajiya dake kallon ta ta cikin glasses tace "to Dije wane irin shiri ne za'ai da har nan da Juma'a bai isa a gama ba?" Cikin yar inda inda tace "dama wai Saboda kayan d'aki tunda wanccan wanda suka yi su sun fanshe su yanzu dole sai nayi ma Mahaifin nata Magana sai a siya wasu koda anan ne sai kuma sauran dae abubuwa" tana Maganar tare da yin nuni da hannuwan ta har ta k'arasa Hajiya da ta ta6e baki tana saurarar ta tace "To wane kayan d'aki kuma, ina ce a part d'in nashi akwae su kuma ba abunda sukai yanzu in an siya mata wasun su wanccan ya za'ai da su, ki bar zancen wasu kayan d'aki tay amfani da wanda ke akwae acan abunda ma nasan zaman na d'an lokaci ne Saboda karatun ta data gama ai dole ta bi shi inda yake zaune tunda ba yadda za'ai tay zaune nan mijin ta na wata uwa duniya, kuma ko bayan ta taren kina iya ganin ma ya canza mata wasu kayan d'akin tunda wanda ke akwae yanzun ma ai daga can K'asar wajen ya siyo su don haka ki bar zancen su kiyi sauran yan shirye shirye da ba'a rasa ba suma kada kice zaki wani takura kan ki tunda an riga an d'aura ba wani abu da ake buk'ata kawae ki sanar ma makwabta da Abokan Arzik'i don a shaida auren tunda abun surutu bai ma Mutane wuya kuma ma dai wani surutun dole ayi tunda yanzu tazo ta samu ciki kuma tazo daga baya ta haihu duk mutane basu san da auren ba ai kinga dole ayi surutu ko, in da wata matsala kiyi magana ina sauraren ki" godiya gwaggon tay mata daga baya tace "akwai kayan kitchen da ya siya mata na waccan auren suna nan ajiye ban san ko za'a iya kai mata ba tayi amfani dasu" tace "Eh to bai kamata aita ajiye su ba, bari muga tunda akwae d'ayan d'akin da yake aikin injiniyan cin nashi kuma an kwashe komae tunda yanzu ba'a nan yake ba sai abunda ba'a rasa ba inaga sai a jera mata kayan a cikin shi ya zama kaman kitchen dama kuma zagaye yake da table sai a k'ara gyarawa yadda zai yi Sosae, shikenan ko in kuma da wani abun sai ki fad'a don nafi son mu gama Maganar da ta danganci tarewar yanzu" d'an shiru gwaggo tay akwae abunda ke damunta a rai saidae ta rasa ta yadda zata yi mata Maganar Hajiya ta lura hakan yasa tace mata tayi magana inda wani abu ta kalleta cikin yar in ina tace "d...dama wai naga su can sauran dangin nashi da Matar shi basu san da Maganar auren ba shi ne nace...to ba matsala ta taren?" Hannu Hajiya tasa ta ruk'e ha6a "Oni Dije kin fi ni sanin abunda ya dace ne ko kuwa tsoro kike in sun sani za'a cinye maki Fateemar?" da sauri gwaggo ta girgiza kai alamar a'a ta hau bata hak'ura Hajiya ta dasa fad'in "ki bita da Addu'a kawae in sha Allahu komae zai zo da Sauk'i tunda shi ya k'addaro komae nasan hakan duk cikin hikimar sane shiyasa nima na d'auki Al'amarin da Sauk'i" kai gwaggo ta jinjina tay Addu'a tare da k'ara yi mata godiya daga haka ta fara k'ok'arin mik'ewa gwaggo ma ta tashi don tay mata rakiya, Fatuu na komawa d'aki ta nufi gadonta ta haye can k'arshe ta zauna had'i da jingina bayanta a jikin bango sai zare ido take tama rasa shin murna ya kamata tayi ko mi, canjin da take gani a wurin Haisam duk shi ya Sagar mata da gwuiwa har take jin shakku game da zaman su tare gani take kaman shi bazai so hakan ba saboda in don laifin da ta yi ne ai ta bashi hak'uri, gani take da yana son ta ko yana son cigaba da zama da ita ai da ya hak'uri ya sake mata, tana haka Gwaggo ta shigo bayan ta dawo daga raka Hajiya, gadon ta nufa ta zauna a baki idonta a kan Fatuu da itama ta k'walalo ido tana kallon ta can tay yar ajiyar zuciya ta fara Magana "Sai ki fara shiri ranar Juma'a in Allah ya kaimu zaki koma gidan Hajiya can part d'in Yayan naki" dadamm! k'irjin Fatuu yay wata irin Fad'uwa ta zaro ido kaman zasu Fad'o a razane take kallon gwaggo jin abunda ta fad'a wanda kwata kwata bata zaci jin hakan ba, ko da ta amince ba tay tunanin da wurwuri haka ba, jin bata ce komae ba yasa gwaggo cewa bata ji abunda tace bane ta d'an yamutsa fuska kaman zatai kuka tace "Gwaggo da wuri haka kuma ya za'ai hakan bacin ba wanda ya sani a dangin shi ko ita fa Aunty Fanan bata sani ba" da alamun damuwa akan fuskar gwaggo tace "to nima nayi ma Hajiya Maganar hakan amman tace ayi Addu'a kawae Allah ya shige mana gaba" idanun ta ne suka ciko da k'walla ita tasan hakan ba k'aramar matsala za'a iya samu ba can suka fara zubowa sharr gwaggo dake kallonta tace mata ai ba kuka yakamata tayi ba suyi Addu'a kaman yadda Hajiyan tace komai sai aga yazo da Sauk'i cikin kuka tace "amman gwaggo ni ina tsoron kada azo a samu matsala fa in daga baya suka sani suka ce basu yarda bafa basu son auren tunda kinga Aunty Fanan yar'uwar su ce" shiru gwaggo tay ta sauke idanun ta k'asa ita kanta abunda yafi damunta kenan a cikin rai can ta d'ago tace "Addu'ar dae kawai zamuyi tunda ba abunda yafi k'arfin ta, koda nayi mata magana kan hakan nuna wa tay ban fi ta sanin abunda ya dace ba kin ga ai bazan yi jayayya da ita ba ko" shiru Fatuu tay tana goge kwallan dake zubo mata ana haka Amadu ya d'aga labulan d'akin ganin gwaggo yasa shi shigowa yana fad'in ashe tana nan yaje d'aki bai sameta ba hannun shi ruk'e da k'atuwar leda ya nufo su a bakin gadon ya aje ledar yace gashi nan in ji Ya Haisam yana gaida mai jiki kai gwaggo ta d'aga, ganin yanayin fuskar ta yasa shi tambayar ta lafiya ya juya kan Fatuu dake ta goge k'walla ba shiri ya kai zaune yana tambayar gwaggo jikin nata ne ta girgiza mashi kai alamar a'a, "To miya ke faruwa ne naga kunyi jugum jugum ga damuwa akan fuskokin ku ita harda kuka don Allah ku fad'a man?" Shima har yanayin fuskar ta shi ya sauya yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke ta fad'a mashi zancen da Hajiya tazo tayi, d'an bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma ya washe baki yace "to shine abunda yasa maku damuwa ku da zaku yi farinciki auren zai d'ore wanda mu hakan dama muke fata" d'an murmushin yak'e gwaggon tay tace "ba wai ba'a farincikin bane kawae damuwar tamu game da dangin nashi ne da basu san da zancen auren ba ita gudun ta kar daga baya kuma azo a samu matsala suce basu amince ba" da sauri yace "ku ma cire wannan tunanin in sha Allahu ba wata matsala da za'a samu koda ma an samu Allah zai kawota da Sauk'i don haka mu mik'a komae gare shi ayi Addu'a kaman yadda Hajiyan tace, kuma kun manta ne gaba d'aya dangin na shi da matar ta shi duk tana da iko da su don haka ayi yadda tace kawae" jinjina kai gwaggo tay ya juya kan Fatuu yana murmushi ya d'an kwanta kan gadon ya kai hannu ya kamo hannun Fatuu guda yana fad'in "u should be happy Allah ya amince Romeo ya zama naki ba kuka ba" tura mashi baki tay yasa dariya gwaggo ma murmushi ta bisu da shi, sakin hannun Fatun yay ya koma ya zauna yana kallon gwaggo yace "to yanzu ya za'ai Maganar kayan d'aki gashi an sa k'urarren lokaci ko da yake ai indai da kud'i har a siya ko?" Fad'i mashi yadda sukai da Hajiyar game da hakan tay yace "shikenan ma an hutar da mu naji dad'i wllh in akwai buk'atar ayin ko nan gaba sai ayi matan in kuma zai tafi da Ita can d'in ne bama sai an yin ba" juyawa yay kan Fatuu dake ta bin su da ido yana dariya yace "Waya ga su yar fillo a jirgi za dai asha hauka nasan" k'ara tura mashi baki tay ta d'an harare shi yace "ni kike harara, kifa bar ganin wai ke matar aure ce baki fi k'arfin in kikai man ba daidai ba in zane ki ko da kin bar gidan nan ne zan iya bin ki har can gidan in maki hukunci" gwaggo dake dariya tace "shi kuma mijin nata sai ya bika da ido kai ta dokar mai mata ko", "Wllh yadda yake tubarkallan nan ma sha Allah yace zai rama mata ai sai ya karairaya ni nasan" ya k'arasa yanata dariya itama gwaggon dariyar take Fatun dai sunkuyar da kai tay tana d'an murmushi yayin da zuciyar ta ke suffanto mata surar Haisam, "To yanzu shikenan sai dae a jira ranar akaita ko akwae abunda zaki?" Amadu ya tambaya tace "Eh zan bada ayi mata su cin cin tunda za'a sanar da makwabta zancen Auren nasan daga baya za'a shishshiga sai ranar Juma'a d'in ayi Abinci Saboda wanda zasu zo" kai ya jinjina "hakan yayi amman fa kar kiyi su da yawa ayi daidai daidai, to su yan Adamawa fa za'a sanar masu ne naga kaman lokaci ya k'ure ko?" d'an jimm tay kafin tace "zan kira Baffanta in sanar mashi komai amman zance mashi ba sai sun zo ba su bari sai daga baya in an samu natsuwa" kai ya jinjina yace hakan yayi sai kuma yace "Yanzu shikenan haka za'ai bikin Romeo da Juliet d'in lami ba wani d'an cashewa gaskiya yakamata a d'anyi mana ko yar dinner ce mu shaida muna biki" gwaggo dake murmushi tace "aikuwa dai haka zaku yi hak'uri don ba wani abu da za'ai" gyad'a kai yay "shikenan amman fa mun biyo bashi ko daga baya ne dole ayi mana in komae ya daidaita dangin shi sun sani" ta6e baki gwaggo tay "tunda ibada ne ya zama Farilla dole sai an yi ko" k'ok'arin mik'ewa ya fara yi yana fad'in bari ya d'aukko plates su yi shagalin abun farinciki ya nufi hanyar fita, plate guda biyu ya d'aukko babba da k'arami ya duk'a ya bud'e ledar abubuwan daya saba kawo wa ne a ciki ya zuzzuba a plate d'in ya mik'a ma gwaggo ta kar6a shima ya d'auki wanda ya zuba a k'aramin plate ya mik'e idon shi akan Fatuu data takure a guri guda yace "ki saki jiki Amaryarmu dis is worth celebrating don haka ki saki ran ki kici ki k'oshi" ya nufi hanyar fita yana fad'in dole ma ya d'inka sabuwar shaddar kai Amarya daga haka ya fice gwaggo ta d'an girgiza kai da d'an murmushi ta juya kan Fatuu da tay zuru tace ga abu nan taci, girgiza mata kai tay alamar a'a ganin ta damu sosae yasa ta shiga kwantar mata da hankali tace ta saki jiki taci don jikinta na buk'atar su ko kuzarin ta ya dawo cike da tsokana tace mata ko so take a kaita d'akin miji haka sukuku da ita Amarya da ake son ta da kuzari Fatun ta duk'ar da kan ta gwaggon nata murmushi, daga baya ta d'ago suka fara ci tare da gwaggon lokacin take ce mata ta kira Fauzy ta fad'a mata don su fara shirye shiryen su k'unshi da gyaran kai har tana cewa yakamata ma in an gyara kan ai kitso ita dae Fatun shiru tay, bata wani ci sosai ba tace ta k'oshi amman gwaggo ta matsa mata saida ta k'ara ci daga baya ta bar d'akin da sauran da suka rage, tun bayan da gwaggo ta fita tay zaune zugudum ta rasa Mike mata dad'i ita dai har ga Allah zallumin zama part d'in nashi take ba tare da dangin su sun san da auren ba sam hankalinta bai kwanta da hakan ba, tana haka Gwaggo ta k'ara shigowa hannunta ruk'e da cup mai d'an girma a bakin gadon ta tsaya ta mik'a mata ta ce ta shanye abun ciki maganin sanyi ne ba tare data ce komai ba ta amsa ta kafa baki nan da nan ta shanye shi tass don dama ta saba bata tun kwanakin baya harda itatuwan tsarki da na sha duk ce mata take na sanyi ne, bayan ta shanye ta mik'a mata Cup d'in ta amsa ta juya Fatun ta bita da kallo don a yanzu ta gane ko magungunan miye take bata da sunan na sanyi, can wata zuciyar ta raya mata ko shiyasa ma lokacin da abun ya faru Ya Haisam d'in ya rikice mata tamkar bashi ba duk da rok'on shi da ta rink'a yi amman a banza, tuno lokacin yasa ta saki d'an murmushi tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamar kunya tana haka ta tuno da magungunan da Fauzy ta kawo mata na yar kwalbar inserting d'in shi ake bayan wasu mintuna sai a wanke da ruwan d'umi wata zuciyar ta raya mata tay amfani dashi yanzu sai kuma ta tuna da jinin da take hakan yasa ta bari sai ya d'auke sai wanda ake ci da nama gashi yanzu ta gama cin naman saidae ba dama ta sa a gaban gwaggo d'ayan kuma da peak milk tunanin ko taje shagon Kawu Amadu ta amso Madarar tay amman kuma ta k'oshi sosae gashi yanzu gwaggo ta bata wani k'arshe ta yanke gobe tayi amfani dasu kawae ta sauka don taje ta wanko hannu ta sha ruwa, tun bayan da ta kwanta bacci ya k'aurace ma idanunta sai juye juye take tana tunanin wane irin zama za tay da Ya Haisam matsayin miji kuma ta koma part d'in shi ganin abun take kaman wasa wllh, can kuma ta koma tunanin ya Aunty Fanan zata ji in taji Maganar auran na su ita da yan gidansu har saida gabanta ya fad'i tunowa da Mahaifiyar Fanan d'in wato Hajiya Maryam jikinta ne yay wani mugun sanyi don ta santa tana da kirki amman fa jarababbiya ce ta gaske a hankali tunanin ta ya koma kan yan gidan su Haisam su wannan bazata iya yanke hukunci a kan su ba kawai dae tasan suna da kirki sosae kuma tana Mutunci da wasu daga cikin yan gidan kaman Nameer, Jidderh dasu twins wannan sun ma maidata tamkar yar'uwar su haka Mahaifiyar Haisam d'in ta san ta sosae kuma duk in tazo tana zuwa ta gaishe da ita cikin sakin fuska take amsa mata bata san in suka ji zancen auren ko zasu amince ba, damuwa ce kwance akan fuskar ta haka taci gaba da tunane tunane har bata san lokacin da bacci ya kwashe ta ba, Washe gari da niyyar zuwa Makaranta ta tashi ta hau shiri ba 6ata lokaci gwaggo na cikin Kitchen ta iske ta bayan ta amsa mata gaisuwar ta ta bita da kallo ganin ta sanye da Uniform yasa tace mata ba dai Makaranta wai zata je ba tace eh ai ta samu sauk'i, girgiza kai gwaggo tay "koda kin samu sauk'i bazaki je ba gaskiya har sai shi Mijin naki ya baki izini tukun kar ai rashin hankali" yamutsa fuska tay kaman za tai kuka tace "amman gwaggo ko da ai da auren nike zuwa ko har ma in zauna a can" gwaggo dake kallon ta ta d'an d'aure fuska tace "da kika ce lokacin baki san da auren ba yanzu kuma kin sani don haka duk abunda zaki sai da izinin shi" idanunta cike da k'walla tace "to gwaggo in kika ce sai ya bada izini har sai yaushe kenan zan ci gaba da zuwa kina gani fa ko jiya bai shigo ba Kawu Amadu ya ba sak'o" tace "ba kina da waya ba ki kira shi mana ki fad'i mashi" tura baki tay tana cigaba da yamutsa fuska had'i da kikkafta idanu gwaggon ta mik'o mata abun breakfast tace taje tayi yadda sukai da shi to ta amsa ta juya, tana komawa d'aki ta aje kayan Breakfast d'in akan Carpet ta koma bakin gado ta zauna sai k'unci take ita sam bata son ta kira shi don bata san mi zata ce mashi ba da sunan neman wani izini shi da ko kiranta bai yi ba tun bayan da suka dawo har yanzu sai ita ce zata kira shi, tana ta zaune cikin 6acin rai can dubara ta fad'o mata da sauri ta kai hannu ta d'aukko jakar goyonta ta bud'e wayarta ta fiddo ta fara kiran Abbas tana fara yin ringing ya d'auka bayan ta gaishe da shi yay mata ya jikin ta amsa daga nan tay shiru jin haka yasa shi tambayar ta da wani abu ne murya kaman zata yi kuka ta fad'i mashi makaranta take son zuwa amman gwaggo ta hana wai har sai Ya Haisam ya bada izini kuma tun jiya daya maido su ma ita bata k'ara ganin shi ba tambayar ta yay har ta samu sauk'in da zata iya cigaba da zuwa School tace mashi eh har yana cewa kodae ta bari ta k'ara warwarewa amman ta kafe kan ta samu sauk'i ko ta zauna ba abunda take sai kwanciya kuma can ana ta wuce ta, sigh yay jin haka yace ta bashi wasu mintuna zai sake kira tace to, bayan sun gama wayar ta saukko ta fara yin breakfast don ranta ya bata zata je Makarantar tana cikin yi sai gashi ya sake kira bayan tayi picking yace ta zama cikin shiri ga Mijin nata nan zai zo ya kaita ya k'arasa yana yar dariya tace ta gode, cire wayar tay ta bita da kallo jikinta ne yay sanyi jin shi zai kaita aje wayar tay taci gaba da yin Breakfast d'in, tana gamawa ta jiyo horn d'in shi har saida gabanta ya fad'i ta d'an yi jimm lokacin taji ya k'ara yin wani ta yunk'ura ta mik'e, gado ta nufa ta goya jakar ta ta sa hijab dake aje saman gadon bayan tasa fararen takalman ta na makaranta ta d'auki tray d'in kayan breakfast d'in ta fita, kitchen taje ta aje su ganin gwaggo bata ciki yasa ta fito ta nufi d'akinta tana zaune kan carpet itama tana yin breakfast d'in ta shiga ta d'aura idonta a kanta Fatun tace mata gashi nan yazo zata tafi gwaggon tace "to a dawo lafiya kinga ai hakan yafi da ai abu kai tsaye" bata ce komai ba tana shirin juyawa gwaggo ta sake cewa "amman fa gida zaki dawo don zama a Makaranta ya k'are in ma kina da kaya ki kwaso su yau kin ji ni?" Kai ta d'aga mata kawai ta juya ta fita, bayan ta fito ta nufi d'ayan side d'in Motar ta kai hannu ta bud'e lokacin da ta shiga idonta ya sauka akan shi har saida gaban ta ya d'an fad'i tay saurin d'auke idon ta ta rufo kopar, juyawa tay ta d'an kalle shi yana sanye da jallabiya ta gaishe dashi ya amsa ba tare da ya kalleta ba yaja Motar suka fara tafiya ta juyar da fuskar ta gefe wani abu taji ya tokare mata k'irji wai ita Ya Haisam ke sharewa haka idanunta ne suka ciko da k'walla da sauri ta fara K'ok'arin maida su don bata son su zubo mata, har suka isa fuskar ta na gefe ya parker inda ya saba aje ta tace mashi an gode ba tare da ta kalle shi ba tana niyyar juyawa don ta bud'e kopar taji yace mata "Wait" dakatawa tay still bata kalle shi ba saida taji yace mata ta amsa sannan ta juya ta kalli kud'in da yake mik'o mata yan dubu duba bin kud'in tay da ido kafin ta d'ago a raunane ta kalle shi suka had'a ido da sauri ta kawar da nata ta furta "ka bar su" shiru bai tanka mata ba bai kuma janye kud'in ba yamutsa fuska ta fara yi tana d'an kikkafta ido a K'ok'arin ta na kada tay kuka ta sake juyawa still kallonta yake fuskar shi ba yabo ba fallasa ta sake ce mashi tana da kud'i nan ma bai tanka ba bai kuma janye kud'in ba bata da yadda zatay ba don ta so ba tasa hannu ta kar6a wani irin bak'in ciki ne ya turnuk'e ta ta shiga ayyana wato ita ga mayyar kud'i, ko tambayar ta ya jiki bai yi ba sai wasu kud'i zai bata, can k'asan mak'oshi ta furta mashi ta gode tana shirin juyawa ta bud'e taji yace mata ya jikinta har bata san lokacin data juya ta kalle shi ba kaman mai jin zancen zuci, d'auke idon tay ta ce mashi ta samu sauk'i daga haka ta juya ta bud'e Motar ta fice, saida taji ya juya Motar ya tafi sannan ta tsaya da tafiya ta juyo tana kallon Motar idanun ta cike da k'walla sharr suka fara zubowa tasa hannu tana gogewa kafin ta juya ta nufi aji, tana shiga suka had'a ido da Fauzy aikuwa ta taso da gudu ta nufo ta tana fad'in Oyoyo Bestie nah, tana zuwa ta kankame ta gaba d'aya hankalin yan ajin ya dawo kan su, sakin ta tay tana kallonta da murmushi da alamun mamaki tace mata wai har ta warke ta d'aga mata kai, kama hannuta tay suka nufo cikin ajin ana ta mata sannu da jiki tana amsawa, koda suka zauna akan seat d'in su haka a kaita tasowa ana zuwa yi mata ya jiki harda Zainab Muhammadu nan ta hau ce ma Mutane wllh su zo su nemi yafiyar ta zargin ta da sukai na tana da ciki bada aure ba aikuwa wasu sukai ta ce mata ta yafe masu su basu san ita matar aure bace tace ta yafe suna haka malamin su ya shigo kowa ya koma seat d'in shi, gaba d'aya damuwa tay mata yawa har ta kasa tsaida hankalin ta kan abunda ake koya masu saidae ta sunkuyar da kai kota kai hannu ta dafe goshi ko ta d'an cije baki Fauzy duk tana lura da ita saidae ba damar tayi mata magana, basu samu damar yin Magana ba don malamin na fita wani na shigowa har saida akai break sannan Fauzy ta tambaye ta wai mi yake damunta ne ta lura tana cikin damuwa nan ta kwashe zancen tarewar ta ta fad'a mata har Fauzy bata san lokacin data saka yar k'arar murna ba cike da farinciki tace "to keda zaki farinciki ma Allah ya cika maki burin ki Aure ya d'ore Ya Haisam ya zama naki sai kita damuwa" d'an yarfa hannu tay ta cije baki tace "Fauzy bazaki gane ba ne ina hango gagarumar matsala a tattare da hakan dangin shi fa basu sani ba haka ma Matar shi Hajiya ce kadae ta sani yanzu in suka zo daga baya suka ce basu amince da auren bafa?" Da sauri Fauzy tace "ni wllh ban ganin za'a samu wata matsala, karfa ki manta gaba dayan su Hajiya na iko dasu tunda kuma ta amince ai ta zauna na tabbatar bazata bari a raba auren ba kawae muci gaba da Addu'a" shiru kawae tay idanunta sun cika da k'walla can suka zubo sharr da sauri Fauzy ta dafa Shoulder d'in ta ta shiga bata hak'uri cikin kuka tace "Fauzy abunda yafi damu na Ya Haisam ya canza man yanzu da nike ganin ya zama mallaki na, in don laifin dana yi mashi ne na bashi hak'uri duk da in zai man Adalci ai bani kadae keda laifi ba ko, ni ina ganin gaskiya kaman gara in hak'ura da auren shi tunda na fahimci bai sona kawae nasan zai amince ya zauna da ni ne k'ilan don Hajiya tay mashi dole kinga to wane irin zaman aure zamu yi haka, koda nike son shi nafi son shima ace yana sona ko d'an yaya ne" yar ajiyar zuciya Fauzy ta sauke tace "ni gaskiya ina tunanin k'ilan akwae wani dalili da ya sa ya canza maki amman ba wannan ba kuma da dukkan alamu yana son ki shiyasa tun farko bai sake ki ba kaman yadda aka tsara, kuma in ma fushin yake Saboda rasa cikin kinga hakan ya tabbatar da yana son kine shiyasa yake son cikin har yay fushi da kika zubar, kuma da bai son ki gaskiya a ganina bazai amince yaci gaba da zama da ke ba tunda shi fa namiji ba'ai mashi dole irin wannan" shiru tay kaman mai nazarin wani abu can tace "ina ganin kaman hakurin da kika bashi bai isa ba mi zai hana ki same shi ki bashi hak'uri sosae, da kaman ki k'ara iske shi can G.r.a d'in nike gani" d'an waro ido Fatuu tay tace "in je in k'ara bashi hak'uri kuma, gaskiya ni bazan je ba Fauzy hakanan ya wulakanta ni ai na bashi hakurin ko" hannu Fauzy ta kai ta dafa Shoulder d'inta tace "k'ilan abun yay mashi ciwo ne sosae, kinsan su irin su gane masu yana da wuya amman tunda har kika ga ya nuna to tabbas bai ji dad'in abun bane kije ki same shi ki bashi hak'uri sosae ba fad'uwa bane wllh karki manta shi Mijin ki Aljannar ki na a tafin kafar shi kuskurene ace yana fushi dake haka indae fushin yake da gaske Saboda abunda kika aikata don haka nidai a gani na kije ki bashi hak'uri tun kafin ranar Juma'ar tayi" shiru Fatuu tay tana juya zancen zuwa bashi hakurin a cikin ranta can wata zuciyar ta tuno mata da lokacin data fasa mashi glass har Haulat ta bata shawarar taje ta bashi hak'uri kuma shawarar tayi mata amfani wanda itace silar komae a tsakanin su, yin wannan tunanin yasa ta kalli Fauzy tace "shikenan zan je d'in amman bansan lokacin da yake can ba gashi in na koma gida bansan yadda zan ce ma Gwaggo ba har ta barni in fito" Fauzyn ta tambaye ta yana zuwa aiki ne tace mata a'a ya bar aiki nan tunda ya bar K'asar, sake tambayar ta tay yaushe rabon data gan shi tace mata shi ya kawo ta tace "kinga da ace can ya tafi sai kiyi sauri tunda anyi break duk da ma an kusa dawowa sai kije ki dawo mai Napep d'in da ya kai ki sai ya jira ki ku dawo" d'an jimm Fatun tay kaman mai yin tunani can tace bari ta gwada zuwa k'ilan can ya wuce in kuma bai can sai ta dawo ta mik'e Fauzy ma ta mik'e tace bari ta rakata, suna fitowa waje suka samu Keke Napep Fatuu har zata shiga ta dakata takai hannu cikin aljihun rigarta ta fiddo kud'i cikin wanda ya bata ta mik'a mata tace tay break ta shige cikin Napep d'in Fauzy ta d'aga hannu tana mata sai ta dawo da fatan Allah yasa ta iske shi ta amsa da Amin yaja suka tafi ita kuma ta juya............... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2058* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Tunda suka taho take ta faman zullumin abunda zai biyo baya in ta iske shi, wannan karon bata wani sha Wahalar gano gidan ba da suka iso don ta rik'e sunan Road d'in, a bakin tangamemen gate d'in tace ma mai Napep d'in ya tsaya bayan ta fito tace zai jirata ne su koma yace to ba matsala ta juya ta nufi k'aramar kopar a d'arare, Officer dake zaune shi kadae yana ganin ta ya hau washe baki harda mik'ewa yana mata sannu da zuwa abun har saida ya bata mamaki a hankali ta amsa mashi ta tambaye shi ko Ya Haisam na ciki da sauri ya d'aga mata kai yace eh yana nan tace zata gan shi ne yace mata ba Komai ta fito lafiya ta wuce, tunda ta shiga harabar gidan gabanta ke ta fad'uwa tana tafiya tana yan waige waige har ta isa bakin mai entrance na gidan ta turo kopar ta shige, ba kowa a cikin parlon farko ta wuce Corridor d'in da zata kaita d'akin nashi cike da fargaba har ta iso bakin dakakkar kopar dake a rufe, tsaye tay ta kasa kwankwasawa sai faman wasi wasi take a cikin ranta ta had'e hannawun ta tana cakud'a su, can dae ta kai hannu yana d'an rawa ta fara knocking a hankali, kusan sau biyar ta kwankwasa amman shiru bata ji an yi magana ba, dakatawa tay da knocking d'in tay jimm tana tunanin ko dae bai nan wata zuciyar ta ayyana mata amman ai Officer yace yana nan kuma da ya fita bazai ce mata haka ba ta raya to ko bacci yake yin Wannan tunanin yasa ta yanke ko dae ta tafi, har zata juya sai kuma ta dakata tay tunanin k'ara d'an kwankwasawa k'ilan tay sa'a yay Magana, can cikin bacci yaji knocking d'in sama sama har dai yaji shi sosae ya fara motsa idanuwan shi kafin slowly ya bud'e su dai dai lokacin ya k'ara jin anyi knocking d'in cikin disasshiyar murya irin ta wanda ya tashi daga bacci ya tambayi wanene shiru ba'a amsa ba saima k'ara yin knocking d'in da akai ya k'ara tambaya nan ma shiru, tunani yay k'ilan Officer ne ko ya kira landline bai ji ba hakan yasa ya yaye lallausan duvet d'in daya rufe rabin jikin shi da shi ya saukko da k'afafun shi kafin ya idasa mik'ewa daga shi sai farar singlet fara kal sai short da iyakar shi rabin cinyoyin shi, saida ya zura takalman da ke a bakin gadon sannan ya nufi kopar, ganin ta k'ara kwankwasa har sau ukku ba'a bud'e ba yasa ta hak'ura tana shirin juyawa ya bud'e kopar da sauri ta kai idon ta kan shi suka had'a ido, wani irin bugu kirjinta yay ta d'an zaro ido tana kallon shi shima irin kallon baka tsammaci ganin mutum ba ya bita dashi, gaba d'aya ta kame kanta ba kamar a yadda ta ganshi hannuwan ta da ta had'e sai d'an rawa suke, sakin kopar yay ya juya ba tare da ya ce mata komae ba, d'an jimm tay kaman bazata shiga ba sai kuma ta shiga ta maido kopar wani irin ni'imtaccen sanyin Ac had'i da daddad'an k'amshi mai ratsa zuciya suka tarbeta har saida ta d'an lumshe ido taja numfashi, in da kujeru suke ya nufa ya zauna kan 2 seater ta nufi can walking slowly gaba d'aya a d'arare take, a gefen wurin ta tsaya tana kallon shi ya sa duka tafukan hannayen shi ya dafe goshi alamar baccin bai ishe shi ba aka katse mashi, saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya cire ba tare daya kalleta ba da hannu yay mata nuni da kujera alamar ta zauna jiki a sa6ule ta nufi cikin wurin ta zauna akan one seater tana facing d'in shi, gaba d'aya ta tsorata da yadda ta ganshi don bata ta6a ganin shi haka ba duk ilahirin jikin shi inda gashi ke fitowa suma ce a kwance liya liya ga farin shi gaba d'aya ya tafi bai d'aya skin d'in shi sumul da ita ba ko d'an ta6o ko bambancin kala harta gwuiwar shi ba bak'i ko tabo kamar bai yi rarrafe ba da yana yaro kawae dae skin d'in wurin jan ta ya d'an fi cizawa ga suffar k'arfin shi ta bayyana muraran gaba d'aya a murde yake, tana cikin k'are mashi kallon ya kai idon shi kanta suka had'a ido ta fara motsa baki da k'yar ta k'ak'alo Kalmar ina kwana tace mashi kaman ba zai amsa ba sai kuma ya amsa can k'asan makoshi ganin yana mata kallon da take ganin na fushi ne yasa ta sunkuyar da kanta yaci gaba da kallon ta, "Why are u here not in School?" Bayan wasu sakanni taji cool voice d'in shi ya fad'i hakan, d'ago kanta tay ta kalle shi ta fara motsa baki tama rasa ta ina zata fara mi zata ce mashi duk ta dabarbarce ba kaman da ya kafeta da kaifafan idanuwan shi masu k'ara mashi kwarjini gathering much courage ta fara magana cikin yar rawar murya "d...dama zuwa nayi in baka hak'uri kan abunda ya faru....nasan nayi maka laifi amman ni bansan komai bane shiyasa na aikata wannan kuskuren....don Allah Ya Haisam kayi Hakuri" da k'yar ta k'arasa Saboda idon shi dake a kanta tana yi tana maida kan ta k'asa tana d'agowa, bin ta kawae yake da ido kaman ma bashi da niyyar tanka mata duk tasha jinin jikinta sai yan kame kame take, "Ba zan yi hakurin ba!" Kaman saukar aradu haka taji Maganar da sauri ta tsaida idanunta akan shi ta zaro su don bata ta6a tunanin zata ji ya fad'i haka ba, d'agowa yay daga jinginar da yayi da kujeran a kausashe yace "da baki san komae ba banyi k'ok'arin sa ki sani ba? Tell me how many times did I call u to explain everything amman Saboda taurin kai kika k'i picking all my calls har message na tura maki warning u not to do anything amman Saboda abu ya faru bani da sauran girma da mutunci a wurin ki shiyasa bazaki bi umarni na ba, ni da kika zo nan I gave u chance kin fad'i duk abunda kike so u even shouted at me kin kira ni Azzalumi, macuci, maci Amana which I never expect to heard from u and dat's d worst thing that ever happened to me....." Dakatawa yay yana d'an girgiza kai fuskar shi d'auke da tsantsar 6acin rai ya d'an cije baki Fatuu ko tunda ya fara magana ta kid'ime don bata ta6a ganin irin yanayin da yake Maganar ba tunda suke da shi sai zare ido take tana sakin numfashi da k'arfi ta had'e hannuwan ta akan k'irji tama kasa bud'e baki tace wani abu, "Nayi tunanin koda ace hakan ya faru ne kuma ba aure tsakanin mu zaki man uzuri, for how long muna tare dake na ta6a maki wani abu makamancin wannan? duk wani dama da zan iya aikata maki hakan na samu amman ban ta6a jin ina sha'awan hakan ba kaman yadda kika fad'a man wai ina son jikin ki God forbid! ban ta6a jin hakan ga wata wadda ba halal d'ina ba, kallon da nike ma siblings d'ina shi nike maki before aure ya shiga tsakaninmu amman kin yanke man mummunan hukunci har kin nuna guy d'in da aka so aura maki yafi ni duk da halin shi da aka fad'a man Saboda shi bai cutar dake ba sai ni right?" rai 6ace yake Maganar yana jinjina kai da alama maganganun nata sun tsaya mashi a rai, a rud'e Fatuu ta taso tazo daga d'an gaban shi ta duk'a tana girgiza mashi kai ya bita da ido cikin kuka tace "Don girman Allah ya Haisam kai hak'uri nasan nayi maka ba daidai ba sharrin zuciya ne, wllh ita tasa na kasa maka uzuri duk da nasan halin ka ta raya abubuwa ba daidai ba akan ka, kuma wllh ni ban daina ganin girman ka ba kawae dai nak'i d'aga wayan ka ne Saboda ina tunanin zaka hana ni aiwatar da abunda nai niyya ni kuma ina tsoron matsalolin da zasu biyo baya don bansan da aure a tsakanin mu ba shiyasa naga yin hakan yafi kuma wllh harda k'arin don kada k'imar ka da Mutuncin ka su zube kaji na rantse maka, amman don Allah kayi hak'uri na gane kuskurena ba zan k'ara ba" ta k'arasa fuskarta jage jage da hawaye tana yi tana gogewa wasu na sake zubowa, shiru yay ya jingina da kujerar yana ta kallon ta ita kuma sai motsa baki take ta marairaice fuska can yay sigh yace "is Ok,ai ke zan ba hak'uri na aure ki bada sanin ki ba daga baya kuma na cutar dake am really for dat" da sauri tace "a'a ai ni taimako na kayi kuma ba cutar dani kayi ba don ban sani bane nace haka kuma da na saurare ka da na san komai kayi Hakuri da abunda nayi" ta k'arasa tana ta6e baki yadda ta saba kuka tun yarinta still idon shi na akan ta sai yan kame kame take taji ya sake cewa "I know kinsan girman zunubin laifin da kika aikata amman kika za6i ki aikata and kinsan had'arin da ke tattare dashi but still kika aikata kawae don gudun matsaloli, baki ji tsoron sa6a ma Ubangiji ba?" hannu ta kai tana d'an sosa gefen wuyanta tana kikkafta ido ganin ya kafe ta da nashi idon yasa tace "Sharrin zuciya ne, kuma har yanzu banda cikakken hankali tunda ban girma ba sosae amman na rok'i Allah ya yafe man" bin ta kawae yay da ido ita kuma tsakani da Allah tay Maganar ta, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace "shikenan kawae you can go back to School nayi hak'urin" kallo ta bi shi dashi har saida yace bata ji bane sannan ta fara k'ok'arin mik'ewa tace mashi ta gode ta juya, har ta fita daga wurin idon shi na akan ta sannan ya maido su yana kallon gaban shi kaman mai tunanin wani abu lokacin yaji k'arar rufe kopar ya mik'e ya nufi hanyar corridor, bada jimawa ba ya fito sanye da jallabiya ya nufi gaban mirror ya d'auki Car key ya fice, lokacin daya fito a harabar gidan ya hangota ta tunkari gate tana tafiya tana goge fuskarta da hannu, parking space ya nufa sai lokacin ta lura da shi ya d'aga hannu yay mata alamar ta tsaya, bayan ya fiddo Motar ya nufo gate d'in a saitin inda take ya tsaya ta zagaya d'ayan side d'in ta bud'e kopar gaba ta shiga, sai da suka fito sannan ta tuna da mai Keke Napep dake ta faman jiranta sam bai ji ya gaji da jira ba don yana sa ran zai samu biya mai kyau ba kamar da ya ga gidan da ta shiga, Haisam na ganin Napep d'in tun kafin ma tayi magana ya tambaye ta tare suke tace mashi eh ya tsaya gefen shi ya kai hannu ya bud'e glove box ya k'irgo 5k ya bata yace ta kai mashi tace to ta amsa ta bud'e kopar, lokacin data ba mai Keke Napep d'in washe baki yay ya shiga yin godiya harda biyo ta bayan ta bud'e kopar ya duk'o da kai yana mashi godiya ya d'aga mashi kai kawae bayan ta shiga yaja suka tafi, A daidai inda ya aje ta da safe ya parker tuni an koma break ba kowa a wajen ta juya ta kalle shi idon shi na kallon gaban shi a sanyaye ta furta ta gode ya d'aga mata kai ta juya zata bud'e kopar lokacin taji muryar shi yace in an tashi ta jira zai zo ya d'auketa, d'an juyawa tay suka had'a ido a hankali tace mashi to kafin ta sake juyawa ta bud'e kopar, bayan ta fita ya juya Motar ya tafi tabi bayan Motar da kallo har ta daina ganinta sannan ta juya jiki ba kwari ta nufi class, tana zuwa bakin barandar benen da ajin su yake kawae sai ta zauna a wurin ta jingina da pillar ta d'an d'age kanta sama kwalla suka fara gangaro mata wani irin dana sani take yi ta rasa ya akai ta kasa yi ma Ya Haisam uzuri kaman yadda ya fad'a yakamata ace tunda tasan halin shi bata yi mashi yadda tay mashi ba, amman tasan harda bak'in abubuwan da taga ya fara yi mata ne yasa tay tunani na daban akan shi, tuno yadda ya rink'a yi mata Magana da tsantsar 6acin rai ta shiga yi dama Fauzy tace k'ilan abun yay mashi ciwo sosae ashe hakane ta fahimci bai so ta zubar da cikin ba, girgiza kai ta fara yi a fili ta shiga fad'in "am sorry my husband nasan na aikata kuskure amman cikin rashin sani ne bazan k'ara ba..." haka tay ta sambatu k'walla na zuba, Sa'adatu ce ta fito daga cikin class d'in su zata je toilet ta hango ta saida taje ta dawo sannan ta nufi Fatun ta tsaya gefen ta ta kira sunanta har sau biyu sannan tay d'an firgigit ta sauke kai ta kalleta, ganin hawaye a fuskar ta yasa tay saurin zama a gefen ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tana tambayar ta lafiya Fatun tay shiru, ta k'ara tambayar ta ko jikin nata ne sai lokacin ta d'aga mata kai alamar eh cike da tausayawa ta hau yi mata sannu ta tambayi to ta sha magani ne ko suje ta rakata Asibiti tace mata daga can take tace to ta taso su tafi aji amman sai tace taje kawae tafi jin dad'in zama anan ta ce to, ta k'ara yi mata sannu tare da mik'ewa ta nufi komawa aji, da yake akwae malami cikin class d'in hakan yasa bata fad'i ma Fauzy game da Fatun ba har saida ya fita sannan ta tashi da sauri taje seat d'in su ta fad'i ma Fauzy aikuwa tun kafin ta gama fad'i matan ta mik'e zumbur tay hanyar fita, tana hangota ta nufe ta da sauri, tana zuwa ta zauna gefenta hankali tashe ta kai hannu ta dafa Shoulder d'in ta ta hau tambayar ta miya faru, tace ta iske Ya Haisam d'in kai Fatuu ta d'aga mata alamar eh, tace to ya sukai dashi, cikin muryar kuka ta shiga fad'i mata Fauzyn nata girgiza kai itama har idanunta sun kawo kwalla bayan ta gama fad'i mata yadda sukai dashi tace "ashe abun ya mashi ciwo ne sosae kaman yadda kika ce Fauzy, ban ji dad'i ba da na kasa yi mashi uzuri har komai ya faru if I had known I would have listened to him da komai bai faru ba nayi dana sani sosae" janyo ta Fauzy tay ta rungume ta ita kanta bata ji dad'in abubuwa data fad'i ma Ya Haisam din ba wanda ta 6oye mata hak'ik'anin yadda sukai dashi lokacin data dawo, jin tana ta kuka yasa tace "shikenan kukan nan ya isa hakanan kinga ba ki idasa warwarewa sosae ba kada kuma wani ciwon ya kama ki, tunda yace ya hak'ura ai shikenan sai a kiyaye gaba" d'ago kai tay ta kalleta tace "ni gani nike kaman bai hakuran ba ya dae fad'a ne kawae tunda har yanzu yanayin da nike gani bai canza ba" Fauzyn tace "kar ki damu tunda yace ya hak'ura to ya hak'uran kin dae san ai ba zai magana biyu ba daga baya yace bai hak'ura ba wannan ai k'aranta ne, dama burin mu ya hak'uran naji dad'i sosae abunda kuma ya rasa in sha Allahu bada jimawa ba za'a biya shi wani" wani kallo Fatun ta d'aga kai tay mata Fauzy tasa dariya, "Yanzu kinga sai muji dad'in fara shirye shiryen duk da banji dad'i ba da ba wani shagali da za'ai amman mun biyo bashi koda in kika haihu ne sai mun yi shagali sosae, yanzu yaushe kike ganin zamu je ai maki k'unshi da gyaran kan?" d'agowa tay daga jikinta ta zauna sosae tace mata itama bata sani ba Fauzy tace "tun yau yakamata a fara maki gyaran jiki gobe ma a k'ara sai a gyara maki gashi jibi in Allah ya kaimu sai ayi maki k'unshi bari in aka tashi zan je gida sai in sanar ma Aunty Mareeya zuwa da la'asar sai muje wurin gyaran jikin" kai Fatun ta d'aga mata alamar to Fauzy ta kai hannu taja kumatun ta tana fad'in ta saki ranta Amarya da farinciki aka santa ta d'anyi murmushi kawai ta kama hannunta tace ta tashi su koma aji suka mik'e, Bayan an tashi Hostel suka wuce ta tattara kayan ta da suke a nan kaman yadda gwaggo ta bata umarni Fauzy nata fad'in zatai missing d'inta kad'aici zai dameta amman tana farinciki da abun Alheri ne yasa zata bar zama hostel d'in, Fatun nata murmushi itama duk wani iri take ji tasan dole ta damu da tafiyar ta, indomie Fauzy ta dafa masu harda kifi sardine suna cikin ci Haisam ya kirata yace yazo ta fad'i mashi suna cin Abinci ne amman sun kusa gamawa yace ba wani abu ta gama, bayan sun gama Fatuu tace mata to tazo ba sai a ajeta a gidan ba kawae, cike da tsokana Fauzy tace a'a wai kada ta shiga tsakanin Masoya ta hana su sakewa inta gama kimtsawa zata tafi Fatun ta harareta ta saka dariya, tare suka fito Fauzy ta kamo mata trolley d'inta dama iya shi kadae ne sauran abubuwa kaman provisions wannan ta bar ma Fauzy, lokacin da suka iso inda ya parker Motar back door ta bud'e ta saka akwatin bayan ta rufe ta bud'e kopar gaba ta shiga yana sanye da k'ananun kaya Fauzy ta lek'o ta gaishe da shi fuska a sake ya amsa yay mata ya karatu daga baya ta k'ara yi ma Fatuu sallama tace sai ta zo anjima ta rufo mata k'opar, saida ya ja Motar ta gaishe dashi ya amsa idon shi a kan hanya ta juyar da kai tana kallon gefen hanya har suka iso kopar gidan su ya parker, d'an kallon shi tay tace ta gode ya jinjina mata kai still bai kalleta ba ta juya ta bud'e kopar bayan ta fita har zata rufe sai kuma ta tuna da fitar da zasu yi anjima da Fauzy tasan in ta fad'i ma gwaggo sai tace ta tambaye shi hakan yasa ta duk'ar da kan ta ciki a sanyaye ta fad'i mashi sai lokacin ya juyo suka had'a ido, jinjina mata kai yay tay mashi godiya bayan ta janye kan ta rufo mashi kopar ta bud'e back door ta fiddo trolley din, har saida ta shige gida sannan yaja Motar, tana shiga d'akin gwaggo ta nufa ta d'aga labulan taga bata ciki ta saki ta nufi d'akinta, tana shiga ta aje trolley d'in a bakin gado ta aje jakarta saman gadon ta cire Hijab d'in itama ta d'aura ta saman gadon, tana juyawa zata nufi hanyar fita taji wayar ta tayi k'ara alamar shigowar message ta koma bakin gadon bayan ta bud'e jakar ta ta fiddo wayar ta fara dubawa, alert ne na 500k daga Haisam har saida ta d'an zaro ido dama wanccan da ya turo mata suna nan bata ta6a ko sisi ba yanzu ga wasu sun kama 1 million kenan d'an jinjina kai tay ta ayyana in gwaggo ta dawo sai ta nuna mata, har zata aje wayar wata zuciya ta raya mata yakamata tay mashi godiya d'an jimm tay tana yin wasi wasi na ta kira ko kar ta kiran, can dae ta kira saidae har ta yanke bai d'aga ba jikinta ne yay sanyi lakwas ta ji dama bata kira ba don a tunanin ta yana tare da wayar tunda yanzu ya turo mata sak'o, har zata ajeta kan gado sai gashi ya kira tabi kiran da kallo kaman bazata d'aga ba can dae tay picking ta kara a kunne bai tanka ba cikin yar inda inda tace taga sak'o ta gode sai lokacin ya furta Ok tay shiru can taji ya furta "da wani matsala ne?" da sauri tace a'a ta katse kiran, bin wayar tay da kallo a ranta ta ayyana halin Ya Haisam sai shi ta d'an ta6e baki sai kuma tay d'an murmushi ta aje wayar ta juya, d'akin Kawu Amadu ta nufa ta iske shi yana ta bacci hakan yasa ta juyo ta koma d'akin ta, a bakin gado ta zauna ta d'auki wayar tana kokarin kiran gwaggo, tana fara ringing ta d'aga bayan ta gaishe da ita ta tambayeta ta dawo ne tace mata eh ta iske bata nan ko ta tafi aiki ne tace a'a taje inda zata kai aikin su dublan ne, ta tambayi taci Abinci ko tace mata taci a Makaranta bata jin yunwa amman duk da haka saida tace mata ta k'ara taci ta k'oshi tace to, daga baya ta sanar da ita zancen zuwa gyaran jikin da zasu yi da Fauzy a kunyace gwaggon tace mata to amman ta kira shi ta sanar da shi har saida ta d'an yi murmushi dama saida ranta ya bata ta fad'i mata ta tambaye shi daya kawo ta harma da kud'in daya turo da wanccan daya fara turowa itama gwaggo saida ta jinjina yawan kud'in tace saidae ta dawo tay amfani dasu suyi duk abunda zasu yi tace to, bayan sun gama wayar ta mik'e ta nufi kitchen ba laifi taji damuwar da take game da yanayin Ya Haisam ta ragu, Saida Fauzy tay wanka ta shirya sannan ta fito don tafiya gida, bayan ta isa bata iske kowa a parlor ba yaran Aunty Mareeyar basu kaiga dawowa daga School ba don suna tsayawa extra lesson, Bedroom d'in ta ta nufa tay knocking ta jiyo Muryar ta tana a shigo sannan ta tura kopar da sallama ta shiga, tana kwance saman gado tayi wanka jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa kallabin ta aje a gefe kanta yasha kitso yar yar Tubarkallah dama akwae gashin kitson ya zubo gefe da gefen wuyanta tana ruk'e da wayar ta, tana ganin Fauzy tace lafiya dai ko ta dawo don jiya ta tafi, a bakin gadon Fauzy ta zauna tana kallon ta da murmushi tace mata lafiya lau, Aunty Mareeyar tace "kenan hakanan kika dawo, ko missing d'ina kike shine kika zo ki gan ni?" Yar dariya tay tace mata eh amman harda Albishir tazo yi mata, tana jin hakan ta aje wayar ta maido hankalin ta gaba d'aya kan Fauzy tana fad'in ta bata ta sha, cike da tsokana Fauzy tace "Dama Daddyn su Hanif ne na gani ya kai wata Makarantar mu amman shi bai ganni ba saida ya sauketa ya tafi naje muka gaisa nike tambayarta inda ta san shi take ce man wanda zata Aura ne har an sa masu rana shine nace bari in zo in fad'i maki kin kusa yin k'anwa mu kuma zamu yi sabuwar Aunt......" bata k'arasa ba Aunty Mareeya ta kai hannu ta janyo ta ta daddage ta d'uma mata dundu tana fad'in bari ta fara ta kanta ita yar zuwa ta fad'i, wata irin gantsarewa Fauzy tay sosae taji zafin dundun har saida ta saki k'ara tana fad'in "Aunty Mareeya so kike ki kashe ni kika buga man wannan k'aton hannun naki tubarkallah" sakin ta tay tana dariya tace gobe ma ta k'ara fad'i mata irin wannan mummunan labarin Fauzyn ta tashi zaune tana yamutsa fuska kaman zatai kuka har kallabinta ya cire Aunty Mareeya dake ta dariya tace mata tana jin ta wane Albishir ne zata mata, tana tura baki tace ta fasa fad'i mata ta fara k'ok'arin mik'ewa da sauri ta janyo ta ta fad'a saman gadon ta rungume ta tana bata hak'uri sannan ta shiga fad'i mata zancen tarewar Fatuu, har saida Aunty Mareeya ta rangad'a gud'a ta shiga washe baki tana fad'in Alhamdulillah an zo daidai inda take so, ta bata labarin zuwa da tayi d'azun bashi hak'uri da yadda sukai dashi, yamutsa baki Auntyn tay tace "in ma bai hak'uran ba ta lalama zai hak'ura ne don dole, wllh ni dama fatana auren dai ya d'ore duk wannan miskilancin sai an sauke mashi shi sai ya rasa sukuni duk in bai ji Zarah a gefen shi ba, shiri za'ai mata na musamman ba boka ba Malam amman fa sai ya susuce a kanta mu da muke da AUNTY BEE KAYAN MATA AND SUPPLEMENTS ai zance kuma ya k'are, mu mata da Allah yay mu masu daraja ai duk kika ga mace bata da k'ima da daraja a wurin mijinta wllh ita taso, macen data san kanta wllh bata zama ba tare da gyara kan ta ba musamman da kaya masu tsananin inganci na Aunty Bee, ai ance ko kana da kyau to ka k'ara da wanka" Fauzy da tay sototo tana sauraren ta tace "Aunty su kayan Aunty Bee d'in nada kyau sosae kenan" hannu Aunty Mareeya tasa ta ruk'e ha6a tace "Uhmm bazaki gane ba yarinya tunda baki san yadda karatun yake ba, amman wllh kin ji na rantse kayan ta Kat ne ingancin su ba'a magana sai mutum yayi amfani dasu zai shaida don sha yanzu ne magani yanzu, gashi abun burgewa abubuwan mune na gargajiya ake sarrafawa ayi magungunan sam basu da wata illa sa6anin wasu magungunan ke da kinji kin san harda surkulle" Fauzy ta tambayeta a ina Aunty Bee d'in take tace "a Kano take nima yadda akai na santa nan Neighbor d'ina Maman taufiq taji ina complain kan sai aita zuzuta magani amman in na siya sai inji ba haka ba k'arshe ma na daina siya nace gwara in cigaba da shan su Fruit dasu Fresh milk shine fa tace ai in jaraba kayan Aunty Bee d'in, farko k'iyawa nay nace kowane Magani haka ake cewa amman ta matsa man ta bani wasu in gwada....." Hannu tasa ta ruk'e ha6a tace "Fauziyya...." Itama Fauzyn ruk'e ha6ar tay tana gumtse dariya tace "Aunty..." ajiyar zuciya Aunty Mareeya ta sauke tace "naga abun Al'ajabi wllh, amman mu bar Maganar daga nan bari in kira ta in mata zancen Zarah" tana rufe baki Fauzy ta kyalkyace da dariya itama Aunty Mareeyar dariyar take ta fara k'ok'arin kiran layin Aunty Bee kamar haka, 08144224934 wayar na fara yin ringing Aunty Mareeya ta d'aga ma Fauzy gira tace "yanzu zata d'auka ta bala'in iya haba haba da customer da kin kirata ko kika tura mata sak'o ta WhatsApp ba 6ata lokaci zaki ji ta d'auka saidae in wani babban uzurin ya hanata d'agawa da wuri amman data gani ko daga baya ne zatay ma mutum magana..." Jin Aunty Bee d'in ta d'aga kiran yasa tay shiru suka shiga gaisawa cike da mutunta juna daga baya ta shiga yi mata bayanin K'anwarta take so a gyare mata sosae kaman yadda aka saba harda cewa mijin miskili ne na gaske so take asa ya magantu ba tare daya shirya ba Aunty Bee d'in tay dariya irin ta mata da suka amsa sunan su tace mata karta damu wannan ba matsala bane saidae in bata yi amfani da magungunan ba amman tabbas zai magantu, gaba d'aya suka saka dariya Aunty Mareeya tace tana son ta turo mata hotunan packages na magungunan zata tura ma Mamar Amaryar tace ba matsala ta duba WhatsApp yanzu zata turo mata in sha Allahu sukai sallama, suna gama wayar ta shiga WhatsApp d'in dama anan take Fauzy ta shigo, ba 6ata lokaci sai ga hotunan ta turo Aunty Mareeya tay ma Fauzy alamar ta matso ta gani ta k'arasa hayewa kan gadon, baki bud'e take ganin hotunan magunguna ba kamar package na Amaren ya burge Fauzy sosae tun ma a ido, magunguna ne sosae Aunty ta shiga fad'i mata sunayen su, su Zakaran mak'alemata, kazar gadali, zabuwa, cicci6i, tsumi kala kala masu wanke mara suyi maganin sanyi, gumba ma kala kala ga garirrrika wato daka akwae d'akan yar gata, k'orama, green emergency, bata gaban kishiya , a ciji kunne....." Aunty bata k'arasa fad'in sauran ba Fauzy ta kwashe da dariya harda tuntsirawa ta d'ago tana fad'in Aunty badai kunnan Zarah za'a cije ba da sauri Aunty Mareeya ta kai mata bugu tana fad'in mara kunya kawae ita tana nuna mata ne don in za'a ma k'awayen ta aure ta taimake su ta tallata masu don su gyara kansu, k'arshe sai ta fita daga cikin hotunan Fauzy nata rok'on ta taci gaba da mata bayani tace bata yi, "To amman Aunty kince a Kano take yanzu yaushe har aka kawo su Zarah tai amfani dasu saura fa kwana ukku ta taren" murmushi Aunty Mareeya tay tace "ai wannan ba matsala bane Aunty Bee bata da wasa a kasuwarta in yanzu nace duk ana son wannan kayan a gobe insha Allahu zaki ga ta turo su ke ko Lagos kike kika ce kina son kayanta cikin kwana biyu zasu iso maki kuma abun mamakin kayanta basu lalacewa yadda ta turo su haka zaki amshe su ba cuta ba cutarwa, kuma koda yan kud'i k'alilan zaki samu kayanta, kai ai Allah yaba Aunty Bee gaskiya ba k'aramin taimakon mata take ba shiyasa a koda yaushe Allah ke k'ara ma kasuwarta Albarka wllh" Fauzy tace "to yanzu tura ma Zarah za'ai ta gani in mata bayani?" Yar harara Aunty ta wurga mata "wata Zarah can, kenan ita zata gyara kanta sai kace mara gata gwaggon zaki kira man in mata bayani kina da no d'inta?" tace mata ba'a rasawa ta ciro wayarta a cikin jaka ta fara dubawa cikin sa'a akwae lambar tace ta kirata, tana fara ringing ta d'auka Aunty ta amsa cikin girmamawa ta gaishe da ita tay mata Allah yasa alheri Fauzy ta fad'i mata zancen tarewar Zarah, daga baya ta shiga yi mata bayanin magungunan sosae gwaggo taji dad'i tay ta godiya tana shi Albarka tace duk kud'in da ake buk'ata tay ma Fatun Magana zata turo sai a kawo tace to, daga baya sukai sallama suna gama wayar gwaggo ta kira Fatuu tace mata Auntyn Fauziyya zata kira inta fad'i mata kud'i ta tura mata tace to, ba tare da 6ata lokaci ba bayan ta kira Fatuu ta tura mata kud'in ita kuma nan take ta tura account d'in Aunty Bee daga baya ta kirata tace ta tura mata receipt ta duba, bayan ta gani ta tabbatar mata gobe in Allah ya kaimu wurin k'arfe 10 na safe magungunan zasu iso tace harda gudummawarta ta k'ara aba Amarya, dama haka take da wuya kai siyayya bata k'ara maka ba Aunty tay mata godiya sosae sukai sallama har Fauzy na yamutsa fuska tana ita baza'a siyar mata koda kazar bace Aunty tace asarar kud'i kenan, ana yin sallar la'asar Fauzy tay ma Aunty Mareeya sallama ta tafi gidan su Fatuu don zuwa gyaran jikin........... (Aunty Bee Kayan Mata And Supplements TESTED AND TRUSTED duk abunda Aunty Mareeya ta fad'a game da kayanta gaskiya ne ni shaida ce don haka kar ki bari a barki a baya wllh ki zama tauraruwa a idon oga ta hanyar amfani da kayan Aunty Bee, Mace mai gyara bata boranci) _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2060* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ......... Lokacin da su Hajiya suka fito Abbas na tsaye bakin Jeep d'in da ya zo da ita har an shiga da Fatuu, Aunty Mareeya da Feenah da inna Zaliha da Matar Baba shehu duk suka shiga ya juya kan sauran k'awayen Fatuu da suka rage don wasu sun tafi ya nuna masu Jeep d'in Saleem yace su je su shiga harda Fauzy ita ta shiga gaba sai Haulat, sauran wad'anda suka rage Abokan aikin gwaggo Hajiya ta nuna masu Motar da Tk ya zo da ita suka shiga Amadu na a Front seat, kowa ya samu wuri sai wasu daga cikin Makwabta ne basu samu ba Hajiya tace su taka a k'asa itama a k'asan zata duk akai dariya ta kira Abbas yazo gaban su tace mashi su d'an zagayo da su Fateemar ita ma ta shaida an yi mata d'aukar Amare yana murmushi yace to ya juya, Motar Saleem ya nufa ya zagaya driver side ya bud'e yana zauna ya d'an d'age kan shi jikin headrest ya sanar dashi zasu d'an zagayo dasu roundabout ya jinjina mashi kai ya rufe mashi kopar, saida yaje ya sanar ma Tk shima sannan ya dawo Motar tashi, lokaci guda gaba d'aya suka kunna motacin sai lokacin gwaggo dake tsaye ta tuna da kayan Fatuu ta yi ma Hajiya Maganar ko a d'aukko kafin su tafi tace ta bari in suka dawo sai Tukur yazo ya d'auka tace to, Tk ne ya fara jan tashi dama shine a gaba lokacin da suka baro gidan Hajiya da zasu zo ya mik'i hanya Abbas ne a tsakiya sai ta Saleem k'arshe suka tafi, Bayan tafiyar su Hajiya tace masu su tafi su jira su acan gidan, har zasu tafi ganin an bar gidan a bud'e yasa Hajiya cema gwaggo akwai sauran mutane ne a gidan za a bar shi a bud'e, sai lokacin ta ankare da sauri ta juya tana fad'in ta manta Hajiya na cewa ko duk tafiyar Fateemar ce tasa ta rikicewa, bayan ta shiga ta d'aukko wayar ta da makulli ta fito ta rufe gidan suka tafi, ta k'aramar kopa suka shiga suka nufi part d'in Haisam, lokacin da suka shiga a gyare harabar take tsaf an gyare shukokin flowers d'in wurin gwanin sha'awa suka nufi kopar shiga parlon, suna shiga makwabtan da aka je da su suka saki baki galala suna bin parlon da kallo ga wani ni'imtaccen sanyin Ac had'i da fitinannan k'amshi da ya karad'e cikin parlon, gwaggo dae sai d'an murmushi take itama tana k'are ma parlon kallo, parlon yana nan yadda yake amman an k'ara wasu abubuwa kaman daga bayan L-shape ansa dining table mai kujeru hud'u suma leather ne bak'ak'e sai daga gaba bangon dake kallon su an sa wani jigunannan console mai jan hankali golden haka saman kujera L-shape an canza throw pillows an sake wasu masu design mai kyau da d'aukar hankali, Carpet d'in k'asa ma an canza wani sabo wanda ke akwae da an maida shi wurin dining table, haka flowers d'in dake a angles d'in parlon an k'ara wasu, d'an madaidaicin Fridge d'in dake parlon an maida shi cikin kitchen sai sabon freezer da aka siya mata a cikin kayan kitchen aka aje shi a parlon daga can wurin dining table, a jikin bangon parlon an manna manyan Frames harda mai Ayatul kursiyyu, blinds d'in jikin Windows ma an canza su zuwa manyan labulaye wanda daka kalla ba sai an fad'a maka ba zaka shaida masu kud'i ne Saboda had'uwar da sukai kuma sun hau da parlon sosae, komae ya hau daidai nan aka shiga yabawa ana sa Albarka tare da Addu'oi, Hajiya tace masu su shiga suga sauran d'akunan suka ce to suka nufi hanyar corridor, Bedroom d'in ma tsab dashi sai k'amshi ke tashi nan ma an canza labulayen ciki haka gadon ma yasha babban bedsheet mai pillows da yawa ko a ido ka kalle shi kasan zai yi mugun taushi, nan ma sosae suka yaba daga baya Hajiya tace suje su ga Kitchen ta juya gaba suka bi bayanta, d'ayan d'akin da yake matsayin Lab d'in shi a da shine aka maida mata kitchen d'in, bayan sun shiga ciki sosae shima suka yaba komae an tsara shi har a sama anyi cabinet haka k'asan ma cikin kankanin lokaci an maida d'akin Kitchen na yan gayu, bayan sun gama gani suka nufi Parlor sai faman yabo da san barka ake, duk suka zazzauna suna dakon isowar su Fatuu farinciki Fal cikin zuciyar gwaggo har fuskar ta ta kasa 6oyewa sai d'an murmushi take ganin wai autar ta ce zata rayu a cikin wurin, sai godiya take ga Allah acikin ran ta, Tun da suka tafi Fatuu ke ta faman kuka har Abbas saida yay mata Magana yace gidan fa Ya Handsome d'inta za'a kaita ba wani wurin ba ai farinciki yakamata tayi ba tay ta yin kuka ba sai kace za'a kaita inda za'a cuta mata, Aunty Mareeya itama tace abun ya bata mamaki wannan kuka haka sai kace za'a kaita gidan makiyinta Feenah ce tace "ai dole duk da hakan sai taji ba dad'i barin gidan da ka saba rayuwa a ciki ka koma wani wuri ba abu bane da ba za'a ji komai ba", inna Zaliha tace gaskiya ne ba kamar yadda suka shak'u da gwaggon ta, Aunty Mareeya tace "hakane, amman dae kukan yayi yawa bai kamata ta sama kanta damuwa ba tunda dai ga baki ga hanci ba nisa tayi da gida ba, muda aka d'aukko daga wani gari sai an dad'e kafin muje gida ita kuwa data fito fa zata ga gidan koda bata shiga ba zata ji dad'i, gani ma zatayi tamkar ba ta bar gidan ba tunda duk unguwa d'aya ne kuma in taso ma kullum taje nasan ba zai hana ba" inna Zaliha dake d'an murmushi tace "hakane amman dai kar ace kullum sai anje d'in hakan bai kamata ba, ita mace ta zauna a d'akinta shi yafi mutunci ba kullum ai ta ganinta tana sunturi a waje ba hakan bai dace ba" gaba d'aya suka ce gaskiya ne harda Abbas, saida suka shawo roundabout na Barhim sannan suka koma. A cikin kwanar gate suka parker Motocin bayan sun iso duk aka firfito Aunty Mareeya na ruk'e da Fatun gefenta Abdul ne ruk'e da hannunta guda suka shiga ta k'aramar k'opa da sauran Mutane, lokacin da suka k'araso bakin kopar shiga parlon Aunty Mareeya ta tsaya da ita tace tayi Addu'a sannan ta shiga da k'afar dama wad'anda ke a bayan su duk suka tsaya saida ta gama sannan suka shige sauran suka bi bayan su, suna shiga d'aya daga cikin makwabtan dake zaune suna jiran isowar su ta mik'e ta rangad'a gud'a mai sautin gaske su Hajiya suka shiga sakin murmushi itama ta mik'e ta nuna masu inda zasu shiga da ita kowa ya baza ido yana k'are ma parlon kallo, hardae Aunty Mareeya da Feenah bin parlon suke da kallo don ba k'aramin had'uwa yay ba ya matuk'ar burge kowa ga wani irin k'amshi mai had'e da sanyin Ac da ya baza ko ina na parlon, Fauzy ma ta jinjina had'uwar wurin har d'an jinjina kai take haka sauran k'awayen su Zainab Muhammadu ma baki bud'e take k'are mashi kallo, ba wanda ma yay tunanin kayan ciki wai ba sababbi bane don kana kallon su zaka ga sabunta a tattare dasu tunda dama iya Haisam d'in kadae ne ke amfani dasu kuma masu matuk'ar inganci ne hakan yasa sam basu canza daga yanayin da aka siyo su ba, Saude ce tay masu jagora zuwa Bedroom d'in nan ma saida aka sa Fatun tayi Addu'a a bakin kopar shiga sannan ta shiga da k'afar dama aka wuce ciki da ita wurin gado, nan ma dae sosae Mutane suka yaba anata Addu'oi, a can tsakiyar gadon aka sa ta haye ta zauna ta jingina da headboard kanta na sadde cikin gyale Fauzy ma ta hau ta zauna gefen ta haka Abdul ma har lokacin yana ruk'e da hannunta duk ya damu tun da yaga tana kuka shima a Mota har kukan yayi yana fad'in ta daina kuka, bayan an gama ganin Bedroom d'in har Laundary room da toilet saida mutane suka shiga suka gani harda su Aunty Mareeya, bayan sun gama dubawa suka fita zuwa Kitchen ya rage daga Fauzy sai sauran k'awayen su, su Zainab dake zaune a bakin gadon sai faman santi suke suna Allah ya maida su damshin Fatuu Fauzy na dariya take amsa masu Zainab tace suje suga sauran wuraren suma duk suka mik'e suka nufi laundry Fauzy ta juya ta kalli Fatuu da har lokacin bata d'ago ba ta kai hannu ta d'an d'aga gyalen ta lek'a fuskar ta suka had'a ido idanun nata sun yi jawur Fauzy ta jawota jikinta tana Fad'in "Haba Amaryar Ya Haisam kukan ya isa hakanan, keda zaki murna ki farinciki Allah ya cika maki burin ki yau gaki a gidan shi a d'akin ki mallakin ku keda shi, don Allah kiyi hakuri kar kija ma kan ki wani ciwon a wannan daren mai daraja da zaku idasa dunk'ulewa ku zama abu d'aya" d'aga idanunta da suka sauya kala tay ta d'an kalli Fauzyn dake ta sakin murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, yar harara Fatuu ta jefa mata ta maida kan ta k'asa Abdul dake a jikinta shima yace "Aunty Fatuu kar ki k'ara yin kuka don Allah, Baba Zakee ba zai cuce ki ba kuma zai rink'a siya maki kayan dad'i da yawa harda Computer ki rink'a yin game" d'an murmushi tay ta d'aga mashi kai kafin ta kai hannunta da ya sha k'unshi da had'add'un awarwaro yan manya guda hud'u sai zobba guda biyu ta shafi fuskar Abdul d'in yaron yana k'aunar ta sosae, d'aga ido Fauzy tay tana k'ara kallon d'akin tace yakamata a k'ara sa turaren wuta cikin wanda Aunty Mareeya ta kawo tace bari tay mata magana ta sauka daga saman gadon ta nufi kopar fita, tana fita parlon taga ba kowa a ciki tun bayan da suka gama dudduba ko'ina Hajiya tace atafi part d'in ta a ci Abinci kar a 6ata ma Amarya nata shine aka d'unguma aka tafi can, wayar ta ta fiddo daga cikin side bag d'inta ta fara k'ok'arin kiran Auntyn bayan tayi picking ta tambaye ta suna ina ta fad'i mata tace gata nan zuwa, fita tay daga cikin parlon bayan ta fito part d'in duk da bata san in da part d'in Hajiyar yake ba bata sha wuyar gane hanyar da zata bi ba saboda ko ina fayau yake da haske tamkar da rana, tana shigowa harabar ta hango part d'in ta nufe shi, bayan fitar Fauzy a hankali Fatuu tasa hannu ta yaye gyalen kanta yadda fuskar ta ta fito sosae, d'aga kai tay ta fara bin bedroom d'in da kallo har yanzu ganin abun take tamkar ba gaske ba kaman mafarki ne, wai yau itace a cikin bedroom d'in Ya Haisam a saman gadon shi kuma ma a matsayin matar shi Allah kenan buwayi gagara misali acikin ikon sa komai mai yuwuwa ne cikin sauki, cigaba da k'are ma d'akin kallo tay iya fentin shi abun burgewa ne balle kuma rantsattsun tsadaddun furniture d'in ciki, sam d'akin baida hayaniya ga wasu jigunannan labulaye, bedsheet d'in saman gadon cikin wanda Hajiya ta siya mata ne lokacin da za'ai mata aure da kayan kitchen har saida ta kai hannunta ta d'an ta6a jikin shi gwanin taushi, tana haka ta shiga tunano can baya tun daga kan farkon ganin shi lokacin da ya raba su fad'a da Jameela mai awara, a nutse taci gaba da tunanin baya sai faman sakin murmushi take lokacin ta tuno da ran da tazo kawo mashi takardar list d'in littattafan da yace taje ta d'aukko bata gan shi a parlon ba ta zo bakin corridor ta tsaya tana yin sallama tace ga takardan, jin shiru bai amsa ba yasa tace ko ta shigo ne ta kawo mashi ya bata amsa da tunda d'akin ta ne ai sai ta shiga daga bayanta ashe bai a cikin d'akin, wani irin murmushi ta saki har fararen hak'oran ta suka d'an bayyana a ranta ta ayyana yanzu gashi ya zama nawa d'in gani ma zaune a saman gadon ka, k'ara tunano lokacin da zai kaita makaranta tay da tace don dai ita k'arama ce da sun yi soyayya kuma in ta gama Secondary School cigaba zatai da karatu yace to ko ya jirata ne tace ai lokacin ita ta zama babbar budurwa shi ya kuma ya tsufa, tace in yana so zata had'a shi da yar ajin su sofiya moussa yace bai sata ba daga baya kuma ta hau yi ma safiyar sharri har tana ba ma lalle ya so ta ba don k'aton baki gare ta hak'oranta kuma sun d'an turo kuma bata da jiki kamar sandar suluka take, tunano hakan har saida tay dariya mai d'an sauti, ita kanta tasan tayi ma Haisam hauka iri iri kafin ta girma amman bai ta6a yin fushi da ita ba ko ya canza mata, in ma tayi abunda ya nuna ta 6ata mashi rai da ta bashi hak'uri yake hak'ura, tabbas dole ne ka ra6i Haisam sai ya burge ka don komai nashi na musamman ne samun irin shi wanda ya had'a abubuwan da ya had'a zai matuk'ar wahala, ga tsantsar kyau, ga kud'i, ga kirki, ga hali mai kyau, ga ilimi, ita kam ko iya haka ta gode ma Allah don ya gama mata komai samun Haisam a matsayin miji ba k'aramar baiwa bace wllh, wata zuciyar ce ta raya mata in kuma bai son ta fa kuma dangin shi suka k'i amincewa da ita, sosae jikinta yay sanyi lakwas yin wannan tunanin, tasan koda bai son ta bazai cutar da ita ba tana da tabbacin hakan inda za'a samu matsala wurin dangin nashi ne in basu amince da ita ba ga kuma matar shi Fanan, sosae Fatuu ke jin zullumin abunda zai je ya dawo in ta samu labarin auren nasu don ita shaida ta kan irin son da take ma Ya Haisam ga hirar da ta ta6a ji yana yi da Abbas da ta tabbatar da cewa Fanan d'in ce ta fara son shi da ya nuna baiso shine har ta kwanta gadon Asibiti, tsayawa tay da yin tunane tunanen Saboda gaba d'aya jikinta ya mutu ta zuba ma bangon da take facing ido a ranta ta shiga ayyana ita bazata so Ya Haisam ya shiga matsala Saboda ita ba, in dae bai son ta da bai cigaba da zama da ita ba, wata zuciyar tace ki ka sani ko yana son ki kaman yadda ake hasashe tunda har abu ya shiga tsakani kuma ya nuna rashin jin dad'i da kika zubar da cikin, shiru tay don a wannan ga6ar baza ta iya yanke hukunci ba duk da a yanzu tasan gaba d'aya abunda ya farun bada niyya bane kuma da ya nuna yayi fushi kan abunda tay k'ilan don aikata hakan laifi ne kaman yadda ya fad'a mata da taje bashi hak'uri da kuma gudun kar wani abu ya faru da ita ba wai don yana son cikin ba ko ita, haka tay ta sak'e sak'e, jin Abdul yay tsit yasa ta kai idonta kan shi taga ashe yayi bacci ta fara k'ok'arin gyara mashi kwanciya a gefen ta tana cikin haka taji an turo kopar Bedroom d'in ta kai idonta da sauri, Kawu Amadu ne ya shigo yana sanye da sabuwar shadda light blue da ya d'inka musamman Saboda ranar, suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi ya iso bakin gadon ya zauna sai faman murmushi take mashi ta kasa yi mashi magana, "Amarya, Allah dai ya amince Romeo ya zama naki" ya fad'a yanata murmushi still itama murmushin take ta k'i cewa komae, "Ko duk Farin ciki ne ya hana ki magana?" Ya fad'a yana murmushi da sauri tasa tafukan hannuwanta da suka sha k'unshi ta rufe fuskar ta, bayan ta cire tana kallon shi yace "kinga ikon Allah ko?" Kai ta d'aga mashi alamar eh, "zaki iya tuna abunda na fad'a maki a can baya lokacin dana iske ki a d'aki cikin mawuyacin hali har kika fad'a man Saboda Ya Haisam ne?" Shiru bata ce mashi komae ba ta maida idanun ta k'asa, yaci gaba "lokacin na fad'i maki in Ya Haisam rabon ki ne kina zaune ba tare da wata wahala ba za ki ga yazo ya Aure ki har kita mamakin yadda akai hakan, kin tuna?" d'agowa tay ta kalle shi tare da d'aga mashi kai, yaci gaba "kin ga maganata ta tabbata, Wannan kad'an ne daga cikin ikon Allah, in dae zaka dogara gare shi to tabbas zaka samu biyan buk'ata ba kamar in ka had'a da hakuri da kuma Addu'a, in kika ga duk kin yi wannan amman bukatan ki bata biya ba to abun ba Alkhairi bane gare ki sai ya musanya maki da wanda yake Alkhairin, shi yasa ake son bawa ya kasance mai yawan godiya ga Allah, in ka samu ka gode mashi haka in ka rasa, a koda yaushe in zaka yi Addu'a to ka rok'i abunda yafi zama Alkhairi a gare ka, duk abunda kaga kasamu to shine yafi Alkhairi, Allah ubangiji da kan shi acikin suratul baqara yace zaku so wani Al'amari alhali ba Alkhairi bane a gare ku, haka zaku K'i wani Al'amari alhali Alkhairi ne a gare ku, Allah ne mafi sani ko baku sani ba, to kinga ba buk'atan ka matsa ma kan ka akan dole sai ka samu wani abu tunda ga mai badawa wanda ya san abun Alkhairi ne a tare da kai ko sharri sai ka mik'a komai a Wurin shi ka dage da Addu'a, a k'arshe ina taya ki murnar samun abunda ran ki ke so ina fatan kuma ku zame ma juna Alkhairi, Allah ubangiji ya bashi ikon ruk'e ki da Amana ya kauda dukkan wata fitina, kema Allah ya baki ikon yi mashi biyayya ya albarkace ku da zuria d'ayyiba Amin" idon shi a Kanta ya k'arasa fuskar ta da d'an murmushi take kallon shi ba tare da ta ce komae ba, d'an tsuke fuska yay yace "ba zaki ce Amin ba" d'an yamutsa fuska tay ta d'an sa hannu ta rufe wurin idanun ta alamar kunya, yace "ke ni zaki wani nuna ma ke mai kunya ce, miye abun kunya an roka maka abun Alkhairi ba sai ka amsa ba" jin haka yasa ta ce Amin a hankali tare da d'an kallon k'asa, kafin ya kara cewa wani abu aka turo k'opar bedroom d'in gaba d'aya suka kai idanun su wurin Tk ne ya shigo shima yana sanye da irin shaddar Amadun da alama anko su kai suna had'a ido da Fatuu ya washe baki ya tunkaro su yana fad'in "Amaryar mu, amaryar mu" yadda ya furta sautin kaman Wak'a Fatun tana ta murmushi ya k'araso bakin gadon shima ya zauna kusa da Amadu ya k'ara ce ma Fatuu dake kallon shi Amaryar su ta gaida shi, da sauri yace "ah ai yanzu ni ne yakamata in rink'a gaishe dake tunda kin koma Aunty na" bata ce komae ba tana dae ta murmushi ya juya kan Amadu yace "kaga ikon Allah ko, yanzu fa dole in rink'a girmama ta tunda ta zama Matar Yayana kuma uban gidana" yar dariya Amadu yayi Tk d'in ya juya kan Fatuu yace "Aunty Amarya Allah yasa dae a rink'a rangwanta man, a da daba k'ark'ashin ikon ki nike ba ma baki d'aga man k'afa ba balle kuma yanzu da kike da cikakken iko dani...." Maida kallon shi yay kan Amadu yace "AA (Ahmad Abdullahi) ka tuna can baya lokacin da aka sa in kaita yawon salla ta maida ni kaman yaron ta tay ta wahalar dani?" "na tuna mana har saida kay ciwon k'arya" ya k'arasa yana dariya shima Tk tuntsirewa yay da dariya tunowa da lokacin, Fatuu ma dariyar take dama lokacin daga baya ta gane ciwon k'arya ne har ta fad'i ma Haisam bayan ya dawo tace bata gama yawon ba har ta rok'e shi ya idasa kai ta hakan ne silar farkon zuwan ta gidan Abbas, Amadu dake kallon shi yace "har ka kai Yayar Fauziyyar ta d'aukko sauran kayan?" d'an girgiza kai Tk yay "No tace in bata makullin Motar ta iya sai su d'aukko ni in huta shine na bata" kai Amadu ya d'aga Tk ya juya kan Fatuu dake kallon su, da murmushi yace "na taya ki murna yar k'anwar mu yanzu kuma Auntyn mu, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya baku zaman lpy, wllh baki ji dad'in dana ji maki ba lokacin dana samu labarin auren, Ya Haisam cikakken mutum ne harda ma rabi, samun shi matsayin abokin rayuwa abun a taya mutum murna ne sam bani da shakku a kan shi don yayi 100% kuma kun bala'en dacewa wllh, zaku ji dad'in yin rayuwa tare don kun riga da kun gama fahimtar juna, shine zai iya maki don ma yanzu naga kin natsu....au tuba nike Hajiya tah su6ul da baka ne" gaba d'aya suka sa dariya ya k'ara cewa "dama ni ne mai kula da part d'in nan wurin gyara shi, to yanzu Aunty zan ci gaba da aiki na ne ko yaya?" Yay tambayar idon shi akan Fatuu dake ta faman sakin murmushi ta kasa ce mashi komae, Amadu ne yace "ah dama ai don ba mata ne, yanzu kuma tunda gata na me kaci gaba ita zata rink'a gyarawa" da sauri Tk yace "No ka bar Hajiyata ta yanke hukunci don itama tana da iko dani yanzu" ya juya kan Fatuu yana fad'in ta yanke yadda za'ai sai Faman dariya take, da k'yar tace mashi ai ba ita zata yanke hukunci ba Ya Haisam ne yace shikenan, ya juya kan Amadu yace "gaskiya AA yakamata muma fa mu fara haramar shigewa daga ciki, ko da yake k'ilan ma sai na riga ka kai da ko budurwa nasan baka da ita, ko kayi ta Yanzu?" Amadu dake murmushi ya girgiza mashi kai alamar a'a, "Gaskiya yakamata ace by now kana da budurwa ko kuma ka tsaida wadda zaka aura tunda nasan ba'a rasa masu son ka kaine kawae baka basu dama" Amadu dake yar dariya yace "No k'yale budurwar nan bari dae in nemi kud'i su taru tukunna in lokacin auren yayi zaka ga bazan sha wahalan samu ba tunda na gama had'uwa" dariya sosae Tk yasa bayan ya tsagaita yace "kuma wllh in dae kana da kud'i bazaka sha wata wahalan samun irin Matar da kake so ba, wai ni yanzu yan mata na soyayya tsakani da Allah kuwa? Ni kaina nan wai d'an ganin da ake ina fantamawa da motoci aka kuma ji gidan da nike kar kaso kaga yadda yan mata suke lik'e man, nan basu san Almajiri bane" gaba d'aya sukai dariya Amadu yace ai yanzu yafi k'arfin a ce mashi Almajiri shima ya zama dangin Senator d'in, suna haka aka turo k'opar duk suka kai idanun su kan masu shigowar, Abbas ne da Saleem da k'yar Abbas ya matsa mashi suka shigo don ya k'iya yace mi zai shigo ya yi, su Amadu na ganin su suka mik'e suna gaishe dasu kafin suka nufi kopar fita su kuma suka k'arasa shigowa ciki idanun su akan Fatuu da itama kallon su take da d'an murmushi haka Abbas ma murmushin yake mata, a gaban gadon suka tsaya yana kallon ta yace "Mom Zarah Amaryar mu, an daina kukan ko?" Kai ta d'an d'aga mashi alamar eh kafin a Sanyaye ta gaishe dasu suka amsa, "haka yakamata ai kar ya haddasa maki wani ciwon muda muke so a biya mu abunda muka rasa a yau......", bai rufe baki ba daga bayan shi yaji an ce "mi kake ci na baka na zuba ai kunsan dai ita d'in bata wasa bace da kun bata zata biya ku" Aunty Mareeya ce da ta shigo ruk'e da kwalin kwalaben kayan k'amshi tay Maganar duk suka juya har da Saleem suka kalleta Fatuu kuwa wata irin kunya ce ta rufe ta da sauri ta sadda kan ta k'asa, shigowa tay cikin d'akin ta nufi wurin dressing mirror Abbas ya bita da murmushi don sai ya d'an ji kunya duk da tun a Mota wurin kawo Fatuu ya fahimci bakin ta a sake yake itama, Saleem ne ya kalli Fatuu cikin cool voice d'in shi yace mata Allah yasa Alkhairi bata amsa ba sai d'an murmushi kawae tay mashi Aunty Mareeya ce ta amsa tare da juyowa ta kalle shi kafin ta maida idon kan Abbas dake ta murmushi itama ta yi had'i da d'an girgiza kai tana a gaban dressing mirror, ta fiddo wasu had'add'un kwalaben humra da turaren wuta tana jerawa a wurin a parlor ma ta jera wasu a cikin gidajen da su tv suke sosae suka k'ara k'awata wurin, Saleem ne ya juya zai tafi Abbas dake kallon Fatuu yace mata bari su je sai ya kawo mata Angonta Aunty Mareeya tay carab tace suna jiran shi yazo ya siya bakin Amarya a wurin su tay Maganar tana dariya shima Abbas d'in dariyar yake ya juya suka fita, bayan fitar su Fauzy ta shigo ruk'e da burner data gama turara parlor ta jona ta anan aka zuba turare Bedroom d'in ya fara turaruwa shima Aunty Mareeya da ta gama ta shiga yi ma Fatuu bayanin yadda zatay amfani da wasu daga cikin kayan kamshin ita dae kai kawai take d'aga mata, bayan an gama turara d'akin Fauzy ta hau gyara bedroom d'in duk da ba wani 6aci yay ba tana cikin gyaran Aunty Mareeya ta sake shigowa hannunta ruk'e da cup ta nufi side d'in da Fatuu take ta zauna a bakin gadon ta bata tace ta shanye abun ciki, ba musu ta amsa ta kafa baki saida ta shanyen ta mik'a mata Cup d'in tace ta taso zata nuna mata abu a kitchen tace mata to ta zuro da k'afafun ta ta mik'e suka nufi hanyar fita Fauzy nata sakin wani kalan murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, bayan sun je kitchen d'in bin d'akin Fatuu tay da kallo an tsara shi ya koma babban Kitchen a ranta ta shiga tuna lokacin da ta fara shigowa cikin shi yin fitsari da ta zo ba Haisam hak'uri da kuma lokacin da yay mata Assignment d'in maths tuna lokacin har saida ta saki murmushi, waya ta6a tunanin wai d'akin zai zama kitchen d'inta gaba d'aya part d'in ma, wata drawer Aunty Mareeya ta jawo ta ce ta matso, nuna mata abubuwan dake ciki tay wanda sauran magungunan ta ne da aka siya mata a wurin Aunty Bee ta shiga yi mata bayanin yadda zata rinka amfani da kowanne Fatun na d'aga mata kai har ta gama, tambayarta tay ko a cikin kitchen d'in akwae abunda bata iya amfani da shi ba ta gwada mata, a sanyaye tace duk ta iya tana ganin yadda Aunty Saude mai aikin nan gidan ke amfani da su Aunty Mareeyar tace da kyau daga haka suka fito suka koma Bedroom d'in, suna komawa Feenah ta shigo tace ma Aunty Mareeya ance su fito za'a maida kowa gida tace to dama sun gama mata komae ai, ta kalli Fatuu da tay zuru jin zancen zasu tafin ta tambaye ta akwai wani abu ta girgiza mata kai sukuku da ita ta juya ta nufi wurin k'atuwar wardrobe d'in d'akin, a gefenta ta d'aukko jakar ta ta dawo bakin gadon Feenah na tsaye, zuge zip d'in jakar tay ta kai hannu ta ciro wata farar shopping bag mai d'auke da tambari ta d'aura ta akan cinyoyin Fatuu tace "Yar k'anwata Amarya ga tawa gudunmawar nan saura kuma kice zaki k'i yin amfani dasu Saboda wai kunya, ke da shi yanzu ba sauran wata kunya don kun riga kun zama abu d'aya, an san kunya abu ce mai kyau amman yanzu a wani wurin in kika ce zaki saka kunya to zaki k'wari kan ki ne da kuma shi Mijin naki don haka ba a komai zaki rink'a nuna kunya ba....." Katse ta Feenah tay da fad'in "ba kamar yadda take da kishiya kuma ma baturiya, gaskiya dole sai kin zage wllh don su ba wata kunya gare su ba don ma ita tana ruwa biyu....." Aunty Mareeya ta kar6e "kin ji dai ko, wannan nasan har yawo daga ita sai d'an pant in ma tasa kenan tana iya yi a gaban shi, don haka ki zage wllh balle ke da ma kike da surar jan hankali Tubarkallah, ki kuma dage da gyara jikin ki ciki da waje, duk magungunan da nayi maki bayani kada ki wasa da shan su sannan kuma kada ki k'asa a guiwa wurin faranta mashi irin su ta nan wajan aka fi kama su, ki sashi ya susuce ta yadda duk in zaiyi Magana sai ya ambaci sunan ki alamar kece a ran shi koda yaushe" gaba d'aya suka sa dariya harda Fauzy dake can d'ayan side d'in gadon raku6e, Feenah ta d'aura da fad'in "Bayan wad'annan kuma sai a had'a da biyayya don itace zata k'ara taimakawa wurin siye zuciyar shi duk da nasan ke mai biyayya ce a gare shi tun ba yanzu ba, to ki k'ara akan wadda kike mashi don yanzu ne zata fi yin aiki kuma zaki fi cin ribar yin ta, a k'arshe ina Addu'ar Allah yasa Alkhairi a zaman ku ya had'a kawunan ku gaba d'aya da abokiyar zaman taki ya kauda fitina ya bashi ikon yin Adalci a tsakanin ku, ya albarkace ku da zuria d'ayyiba" su Aunty Mareeya ne suka amsa ita kuma Fatun kan ta na a k'asa, lokacin Abbas ya lek'o cikin d'akin yace su suke jira fa duk suka mik'e ya d'aga murya yana ma Fatuu sai da safe, yana shirin juyawa Feenah tace don Allah ya taimaka mata da Abdul yadda yay baccin nan ba iya d'aukar shi zatay ba ya k'arasa shigowa cikin d'akin ta kinkimo mashi Abdul d'in ya kar6e shi ya sa6a a Shoulder yana fad'in Allah ma ya taimake su da yayi baccin ai da ba k'aramar rigima za'ai dashi ba don yana iya cewa nan zai kwana ba kamar yana ganin gidan Baban shi da Momy d'in shi ne duk sukai dariya ya juya ya nufi kopa suma suka bi bayan shi Fatuu ta fara k'ok'arin saukkowa daga saman gadon Fauzy dake kallonta tace ina zata, jin haka yasa su Aunty Mareeya juyowa suma suka tambayi inda zata fuskar ta kaman zatai kuka murya na d'an rawa tace raka su zatai, waro ido tay tace a ina ta ta6a ganin Amarya tayi rakiya ta koma ta zauna kafin Angon ta ya zo, ba yadda ta iya dole ta koma ta zauna suka tafi banda Fauzy da tay tsaye ta kasa tafiya yanayin fuskar ta ya sauya itama kaman zata saka kukan, bin juna da ido sukai can k'walla suka zubo ma Fatuu sharrr Fauzy ta d'an girgiza mata kai daga inda take tsaye tace "ki daina kuka Zarah lokacin farinciki ne yanzu, Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya sai mun had'u School" da k'yar ta k'arasa Maganar, jin kuka na niyyar k'wace mata yasa ta juya da sauri ta fita, tana fita Fatuu ta d'age k'afafunta ta kife fuskar ta tana kuka a hankali................. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 *ASM Bk2060* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ......... Lokacin da su Hajiya suka fito Abbas na tsaye bakin Jeep d'in da ya zo da ita har an shiga da Fatuu, Aunty Mareeya da Feenah da inna Zaliha da Matar Baba shehu duk suka shiga ya juya kan sauran k'awayen Fatuu da suka rage don wasu sun tafi ya nuna masu Jeep d'in Saleem yace su je su shiga harda Fauzy ita ta shiga gaba sai Haulat, sauran wad'anda suka rage Abokan aikin gwaggo Hajiya ta nuna masu Motar da Tk ya zo da ita suka shiga Amadu na a Front seat, kowa ya samu wuri sai wasu daga cikin Makwabta ne basu samu ba Hajiya tace su taka a k'asa itama a k'asan zata duk akai dariya ta kira Abbas yazo gaban su tace mashi su d'an zagayo da su Fateemar ita ma ta shaida an yi mata d'aukar Amare yana murmushi yace to ya juya, Motar Saleem ya nufa ya zagaya driver side ya bud'e yana zauna ya d'an d'age kan shi jikin headrest ya sanar dashi zasu d'an zagayo dasu roundabout ya jinjina mashi kai ya rufe mashi kopar, saida yaje ya sanar ma Tk shima sannan ya dawo Motar tashi, lokaci guda gaba d'aya suka kunna motacin sai lokacin gwaggo dake tsaye ta tuna da kayan Fatuu ta yi ma Hajiya Maganar ko a d'aukko kafin su tafi tace ta bari in suka dawo sai Tukur yazo ya d'auka tace to, Tk ne ya fara jan tashi dama shine a gaba lokacin da suka baro gidan Hajiya da zasu zo ya mik'i hanya Abbas ne a tsakiya sai ta Saleem k'arshe suka tafi, Bayan tafiyar su Hajiya tace masu su tafi su jira su acan gidan, har zasu tafi ganin an bar gidan a bud'e yasa Hajiya cema gwaggo akwai sauran mutane ne a gidan za a bar shi a bud'e, sai lokacin ta ankare da sauri ta juya tana fad'in ta manta Hajiya na cewa ko duk tafiyar Fateemar ce tasa ta rikicewa, bayan ta shiga ta d'aukko wayar ta da makulli ta fito ta rufe gidan suka tafi, ta k'aramar kopa suka shiga suka nufi part d'in Haisam, lokacin da suka shiga a gyare harabar take tsaf an gyare shukokin flowers d'in wurin gwanin sha'awa suka nufi kopar shiga parlon, suna shiga makwabtan da aka je da su suka saki baki galala suna bin parlon da kallo ga wani ni'imtaccen sanyin Ac had'i da fitinannan k'amshi da ya karad'e cikin parlon, gwaggo dae sai d'an murmushi take itama tana k'are ma parlon kallo, parlon yana nan yadda yake amman an k'ara wasu abubuwa kaman daga bayan L-shape ansa dining table mai kujeru hud'u suma leather ne bak'ak'e sai daga gaba bangon dake kallon su an sa wani jigunannan console mai jan hankali golden haka saman kujera L-shape an canza throw pillows an sake wasu masu design mai kyau da d'aukar hankali, Carpet d'in k'asa ma an canza wani sabo wanda ke akwae da an maida shi wurin dining table, haka flowers d'in dake a angles d'in parlon an k'ara wasu, d'an madaidaicin Fridge d'in dake parlon an maida shi cikin kitchen sai sabon freezer da aka siya mata a cikin kayan kitchen aka aje shi a parlon daga can wurin dining table, a jikin bangon parlon an manna manyan Frames harda mai Ayatul kursiyyu, blinds d'in jikin Windows ma an canza su zuwa manyan labulaye wanda daka kalla ba sai an fad'a maka ba zaka shaida masu kud'i ne Saboda had'uwar da sukai kuma sun hau da parlon sosae, komae ya hau daidai nan aka shiga yabawa ana sa Albarka tare da Addu'oi, Hajiya tace masu su shiga suga sauran d'akunan suka ce to suka nufi hanyar corridor, Bedroom d'in ma tsab dashi sai k'amshi ke tashi nan ma an canza labulayen ciki haka gadon ma yasha babban bedsheet mai pillows da yawa ko a ido ka kalle shi kasan zai yi mugun taushi, nan ma sosae suka yaba daga baya Hajiya tace suje su ga Kitchen ta juya gaba suka bi bayanta, d'ayan d'akin da yake matsayin Lab d'in shi a da shine aka maida mata kitchen d'in, bayan sun shiga ciki sosae shima suka yaba komae an tsara shi har a sama anyi cabinet haka k'asan ma cikin kankanin lokaci an maida d'akin Kitchen na yan gayu, bayan sun gama gani suka nufi Parlor sai faman yabo da san barka ake, duk suka zazzauna suna dakon isowar su Fatuu farinciki Fal cikin zuciyar gwaggo har fuskar ta ta kasa 6oyewa sai d'an murmushi take ganin wai autar ta ce zata rayu a cikin wurin, sai godiya take ga Allah acikin ran ta, Tun da suka tafi Fatuu ke ta faman kuka har Abbas saida yay mata Magana yace gidan fa Ya Handsome d'inta za'a kaita ba wani wurin ba ai farinciki yakamata tayi ba tay ta yin kuka ba sai kace za'a kaita inda za'a cuta mata, Aunty Mareeya itama tace abun ya bata mamaki wannan kuka haka sai kace za'a kaita gidan makiyinta Feenah ce tace "ai dole duk da hakan sai taji ba dad'i barin gidan da ka saba rayuwa a ciki ka koma wani wuri ba abu bane da ba za'a ji komai ba", inna Zaliha tace gaskiya ne ba kamar yadda suka shak'u da gwaggon ta, Aunty Mareeya tace "hakane, amman dae kukan yayi yawa bai kamata ta sama kanta damuwa ba tunda dai ga baki ga hanci ba nisa tayi da gida ba, muda aka d'aukko daga wani gari sai an dad'e kafin muje gida ita kuwa data fito fa zata ga gidan koda bata shiga ba zata ji dad'i, gani ma zatayi tamkar ba ta bar gidan ba tunda duk unguwa d'aya ne kuma in taso ma kullum taje nasan ba zai hana ba" inna Zaliha dake d'an murmushi tace "hakane amman dai kar ace kullum sai anje d'in hakan bai kamata ba, ita mace ta zauna a d'akinta shi yafi mutunci ba kullum ai ta ganinta tana sunturi a waje ba hakan bai dace ba" gaba d'aya suka ce gaskiya ne harda Abbas, saida suka shawo roundabout na Barhim sannan suka koma. A cikin kwanar gate suka parker Motocin bayan sun iso duk aka firfito Aunty Mareeya na ruk'e da Fatun gefenta Abdul ne ruk'e da hannunta guda suka shiga ta k'aramar k'opa da sauran Mutane, lokacin da suka k'araso bakin kopar shiga parlon Aunty Mareeya ta tsaya da ita tace tayi Addu'a sannan ta shiga da k'afar dama wad'anda ke a bayan su duk suka tsaya saida ta gama sannan suka shige sauran suka bi bayan su, suna shiga d'aya daga cikin makwabtan dake zaune suna jiran isowar su ta mik'e ta rangad'a gud'a mai sautin gaske su Hajiya suka shiga sakin murmushi itama ta mik'e ta nuna masu inda zasu shiga da ita kowa ya baza ido yana k'are ma parlon kallo, hardae Aunty Mareeya da Feenah bin parlon suke da kallo don ba k'aramin had'uwa yay ba ya matuk'ar burge kowa ga wani irin k'amshi mai had'e da sanyin Ac da ya baza ko ina na parlon, Fauzy ma ta jinjina had'uwar wurin har d'an jinjina kai take haka sauran k'awayen su Zainab Muhammadu ma baki bud'e take k'are mashi kallo, ba wanda ma yay tunanin kayan ciki wai ba sababbi bane don kana kallon su zaka ga sabunta a tattare dasu tunda dama iya Haisam d'in kadae ne ke amfani dasu kuma masu matuk'ar inganci ne hakan yasa sam basu canza daga yanayin da aka siyo su ba, Saude ce tay masu jagora zuwa Bedroom d'in nan ma saida aka sa Fatun tayi Addu'a a bakin kopar shiga sannan ta shiga da k'afar dama aka wuce ciki da ita wurin gado, nan ma dae sosae Mutane suka yaba anata Addu'oi, a can tsakiyar gadon aka sa ta haye ta zauna ta jingina da headboard kanta na sadde cikin gyale Fauzy ma ta hau ta zauna gefen ta haka Abdul ma har lokacin yana ruk'e da hannunta duk ya damu tun da yaga tana kuka shima a Mota har kukan yayi yana fad'in ta daina kuka, bayan an gama ganin Bedroom d'in har Laundary room da toilet saida mutane suka shiga suka gani harda su Aunty Mareeya, bayan sun gama dubawa suka fita zuwa Kitchen ya rage daga Fauzy sai sauran k'awayen su, su Zainab dake zaune a bakin gadon sai faman santi suke suna Allah ya maida su damshin Fatuu Fauzy na dariya take amsa masu Zainab tace suje suga sauran wuraren suma duk suka mik'e suka nufi laundry Fauzy ta juya ta kalli Fatuu da har lokacin bata d'ago ba ta kai hannu ta d'an d'aga gyalen ta lek'a fuskar ta suka had'a ido idanun nata sun yi jawur Fauzy ta jawota jikinta tana Fad'in "Haba Amaryar Ya Haisam kukan ya isa hakanan, keda zaki murna ki farinciki Allah ya cika maki burin ki yau gaki a gidan shi a d'akin ki mallakin ku keda shi, don Allah kiyi hakuri kar kija ma kan ki wani ciwon a wannan daren mai daraja da zaku idasa dunk'ulewa ku zama abu d'aya" d'aga idanunta da suka sauya kala tay ta d'an kalli Fauzyn dake ta sakin murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, yar harara Fatuu ta jefa mata ta maida kan ta k'asa Abdul dake a jikinta shima yace "Aunty Fatuu kar ki k'ara yin kuka don Allah, Baba Zakee ba zai cuce ki ba kuma zai rink'a siya maki kayan dad'i da yawa harda Computer ki rink'a yin game" d'an murmushi tay ta d'aga mashi kai kafin ta kai hannunta da ya sha k'unshi da had'add'un awarwaro yan manya guda hud'u sai zobba guda biyu ta shafi fuskar Abdul d'in yaron yana k'aunar ta sosae, d'aga ido Fauzy tay tana k'ara kallon d'akin tace yakamata a k'ara sa turaren wuta cikin wanda Aunty Mareeya ta kawo tace bari tay mata magana ta sauka daga saman gadon ta nufi kopar fita, tana fita parlon taga ba kowa a ciki tun bayan da suka gama dudduba ko'ina Hajiya tace atafi part d'in ta a ci Abinci kar a 6ata ma Amarya nata shine aka d'unguma aka tafi can, wayar ta ta fiddo daga cikin side bag d'inta ta fara k'ok'arin kiran Auntyn bayan tayi picking ta tambaye ta suna ina ta fad'i mata tace gata nan zuwa, fita tay daga cikin parlon bayan ta fito part d'in duk da bata san in da part d'in Hajiyar yake ba bata sha wuyar gane hanyar da zata bi ba saboda ko ina fayau yake da haske tamkar da rana, tana shigowa harabar ta hango part d'in ta nufe shi, bayan fitar Fauzy a hankali Fatuu tasa hannu ta yaye gyalen kanta yadda fuskar ta ta fito sosae, d'aga kai tay ta fara bin bedroom d'in da kallo har yanzu ganin abun take tamkar ba gaske ba kaman mafarki ne, wai yau itace a cikin bedroom d'in Ya Haisam a saman gadon shi kuma ma a matsayin matar shi Allah kenan buwayi gagara misali acikin ikon sa komai mai yuwuwa ne cikin sauki, cigaba da k'are ma d'akin kallo tay iya fentin shi abun burgewa ne balle kuma rantsattsun tsadaddun furniture d'in ciki, sam d'akin baida hayaniya ga wasu jigunannan labulaye, bedsheet d'in saman gadon cikin wanda Hajiya ta siya mata ne lokacin da za'ai mata aure da kayan kitchen har saida ta kai hannunta ta d'an ta6a jikin shi gwanin taushi, tana haka ta shiga tunano can baya tun daga kan farkon ganin shi lokacin da ya raba su fad'a da Jameela mai awara, a nutse taci gaba da tunanin baya sai faman sakin murmushi take lokacin ta tuno da ran da tazo kawo mashi takardar list d'in littattafan da yace taje ta d'aukko bata gan shi a parlon ba ta zo bakin corridor ta tsaya tana yin sallama tace ga takardan, jin shiru bai amsa ba yasa tace ko ta shigo ne ta kawo mashi ya bata amsa da tunda d'akin ta ne ai sai ta shiga daga bayanta ashe bai a cikin d'akin, wani irin murmushi ta saki har fararen hak'oran ta suka d'an bayyana a ranta ta ayyana yanzu gashi ya zama nawa d'in gani ma zaune a saman gadon ka, k'ara tunano lokacin da zai kaita makaranta tay da tace don dai ita k'arama ce da sun yi soyayya kuma in ta gama Secondary School cigaba zatai da karatu yace to ko ya jirata ne tace ai lokacin ita ta zama babbar budurwa shi ya kuma ya tsufa, tace in yana so zata had'a shi da yar ajin su sofiya moussa yace bai sata ba daga baya kuma ta hau yi ma safiyar sharri har tana ba ma lalle ya so ta ba don k'aton baki gare ta hak'oranta kuma sun d'an turo kuma bata da jiki kamar sandar suluka take, tunano hakan har saida tay dariya mai d'an sauti, ita kanta tasan tayi ma Haisam hauka iri iri kafin ta girma amman bai ta6a yin fushi da ita ba ko ya canza mata, in ma tayi abunda ya nuna ta 6ata mashi rai da ta bashi hak'uri yake hak'ura, tabbas dole ne ka ra6i Haisam sai ya burge ka don komai nashi na musamman ne samun irin shi wanda ya had'a abubuwan da ya had'a zai matuk'ar wahala, ga tsantsar kyau, ga kud'i, ga kirki, ga hali mai kyau, ga ilimi, ita kam ko iya haka ta gode ma Allah don ya gama mata komai samun Haisam a matsayin miji ba k'aramar baiwa bace wllh, wata zuciyar ce ta raya mata in kuma bai son ta fa kuma dangin shi suka k'i amincewa da ita, sosae jikinta yay sanyi lakwas yin wannan tunanin, tasan koda bai son ta bazai cutar da ita ba tana da tabbacin hakan inda za'a samu matsala wurin dangin nashi ne in basu amince da ita ba ga kuma matar shi Fanan, sosae Fatuu ke jin zullumin abunda zai je ya dawo in ta samu labarin auren nasu don ita shaida ta kan irin son da take ma Ya Haisam ga hirar da ta ta6a ji yana yi da Abbas da ta tabbatar da cewa Fanan d'in ce ta fara son shi da ya nuna baiso shine har ta kwanta gadon Asibiti, tsayawa tay da yin tunane tunanen Saboda gaba d'aya jikinta ya mutu ta zuba ma bangon da take facing ido a ranta ta shiga ayyana ita bazata so Ya Haisam ya shiga matsala Saboda ita ba, in dae bai son ta da bai cigaba da zama da ita ba, wata zuciyar tace ki ka sani ko yana son ki kaman yadda ake hasashe tunda har abu ya shiga tsakani kuma ya nuna rashin jin dad'i da kika zubar da cikin, shiru tay don a wannan ga6ar baza ta iya yanke hukunci ba duk da a yanzu tasan gaba d'aya abunda ya farun bada niyya bane kuma da ya nuna yayi fushi kan abunda tay k'ilan don aikata hakan laifi ne kaman yadda ya fad'a mata da taje bashi hak'uri da kuma gudun kar wani abu ya faru da ita ba wai don yana son cikin ba ko ita, haka tay ta sak'e sak'e, jin Abdul yay tsit yasa ta kai idonta kan shi taga ashe yayi bacci ta fara k'ok'arin gyara mashi kwanciya a gefen ta tana cikin haka taji an turo kopar Bedroom d'in ta kai idonta da sauri, Kawu Amadu ne ya shigo yana sanye da sabuwar shadda light blue da ya d'inka musamman Saboda ranar, suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi ya iso bakin gadon ya zauna sai faman murmushi take mashi ta kasa yi mashi magana, "Amarya, Allah dai ya amince Romeo ya zama naki" ya fad'a yanata murmushi still itama murmushin take ta k'i cewa komae, "Ko duk Farin ciki ne ya hana ki magana?" Ya fad'a yana murmushi da sauri tasa tafukan hannuwanta da suka sha k'unshi ta rufe fuskar ta, bayan ta cire tana kallon shi yace "kinga ikon Allah ko?" Kai ta d'aga mashi alamar eh, "zaki iya tuna abunda na fad'a maki a can baya lokacin dana iske ki a d'aki cikin mawuyacin hali har kika fad'a man Saboda Ya Haisam ne?" Shiru bata ce mashi komae ba ta maida idanun ta k'asa, yaci gaba "lokacin na fad'i maki in Ya Haisam rabon ki ne kina zaune ba tare da wata wahala ba za ki ga yazo ya Aure ki har kita mamakin yadda akai hakan, kin tuna?" d'agowa tay ta kalle shi tare da d'aga mashi kai, yaci gaba "kin ga maganata ta tabbata, Wannan kad'an ne daga cikin ikon Allah, in dae zaka dogara gare shi to tabbas zaka samu biyan buk'ata ba kamar in ka had'a da hakuri da kuma Addu'a, in kika ga duk kin yi wannan amman bukatan ki bata biya ba to abun ba Alkhairi bane gare ki sai ya musanya maki da wanda yake Alkhairin, shi yasa ake son bawa ya kasance mai yawan godiya ga Allah, in ka samu ka gode mashi haka in ka rasa, a koda yaushe in zaka yi Addu'a to ka rok'i abunda yafi zama Alkhairi a gare ka, duk abunda kaga kasamu to shine yafi Alkhairi, Allah ubangiji da kan shi acikin suratul baqara yace zaku so wani Al'amari alhali ba Alkhairi bane a gare ku, haka zaku K'i wani Al'amari alhali Alkhairi ne a gare ku, Allah ne mafi sani ko baku sani ba, to kinga ba buk'atan ka matsa ma kan ka akan dole sai ka samu wani abu tunda ga mai badawa wanda ya san abun Alkhairi ne a tare da kai ko sharri sai ka mik'a komai a Wurin shi ka dage da Addu'a, a k'arshe ina taya ki murnar samun abunda ran ki ke so ina fatan kuma ku zame ma juna Alkhairi, Allah ubangiji ya bashi ikon ruk'e ki da Amana ya kauda dukkan wata fitina, kema Allah ya baki ikon yi mashi biyayya ya albarkace ku da zuria d'ayyiba Amin" idon shi a Kanta ya k'arasa fuskar ta da d'an murmushi take kallon shi ba tare da ta ce komae ba, d'an tsuke fuska yay yace "ba zaki ce Amin ba" d'an yamutsa fuska tay ta d'an sa hannu ta rufe wurin idanun ta alamar kunya, yace "ke ni zaki wani nuna ma ke mai kunya ce, miye abun kunya an roka maka abun Alkhairi ba sai ka amsa ba" jin haka yasa ta ce Amin a hankali tare da d'an kallon k'asa, kafin ya kara cewa wani abu aka turo k'opar bedroom d'in gaba d'aya suka kai idanun su wurin Tk ne ya shigo shima yana sanye da irin shaddar Amadun da alama anko su kai suna had'a ido da Fatuu ya washe baki ya tunkaro su yana fad'in "Amaryar mu, amaryar mu" yadda ya furta sautin kaman Wak'a Fatun tana ta murmushi ya k'araso bakin gadon shima ya zauna kusa da Amadu ya k'ara ce ma Fatuu dake kallon shi Amaryar su ta gaida shi, da sauri yace "ah ai yanzu ni ne yakamata in rink'a gaishe dake tunda kin koma Aunty na" bata ce komae ba tana dae ta murmushi ya juya kan Amadu yace "kaga ikon Allah ko, yanzu fa dole in rink'a girmama ta tunda ta zama Matar Yayana kuma uban gidana" yar dariya Amadu yayi Tk d'in ya juya kan Fatuu yace "Aunty Amarya Allah yasa dae a rink'a rangwanta man, a da daba k'ark'ashin ikon ki nike ba ma baki d'aga man k'afa ba balle kuma yanzu da kike da cikakken iko dani...." Maida kallon shi yay kan Amadu yace "AA (Ahmad Abdullahi) ka tuna can baya lokacin da aka sa in kaita yawon salla ta maida ni kaman yaron ta tay ta wahalar dani?" "na tuna mana har saida kay ciwon k'arya" ya k'arasa yana dariya shima Tk tuntsirewa yay da dariya tunowa da lokacin, Fatuu ma dariyar take dama lokacin daga baya ta gane ciwon k'arya ne har ta fad'i ma Haisam bayan ya dawo tace bata gama yawon ba har ta rok'e shi ya idasa kai ta hakan ne silar farkon zuwan ta gidan Abbas, Amadu dake kallon shi yace "har ka kai Yayar Fauziyyar ta d'aukko sauran kayan?" d'an girgiza kai Tk yay "No tace in bata makullin Motar ta iya sai su d'aukko ni in huta shine na bata" kai Amadu ya d'aga Tk ya juya kan Fatuu dake kallon su, da murmushi yace "na taya ki murna yar k'anwar mu yanzu kuma Auntyn mu, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya baku zaman lpy, wllh baki ji dad'in dana ji maki ba lokacin dana samu labarin auren, Ya Haisam cikakken mutum ne harda ma rabi, samun shi matsayin abokin rayuwa abun a taya mutum murna ne sam bani da shakku a kan shi don yayi 100% kuma kun bala'en dacewa wllh, zaku ji dad'in yin rayuwa tare don kun riga da kun gama fahimtar juna, shine zai iya maki don ma yanzu naga kin natsu....au tuba nike Hajiya tah su6ul da baka ne" gaba d'aya suka sa dariya ya k'ara cewa "dama ni ne mai kula da part d'in nan wurin gyara shi, to yanzu Aunty zan ci gaba da aiki na ne ko yaya?" Yay tambayar idon shi akan Fatuu dake ta faman sakin murmushi ta kasa ce mashi komae, Amadu ne yace "ah dama ai don ba mata ne, yanzu kuma tunda gata na me kaci gaba ita zata rink'a gyarawa" da sauri Tk yace "No ka bar Hajiyata ta yanke hukunci don itama tana da iko dani yanzu" ya juya kan Fatuu yana fad'in ta yanke yadda za'ai sai Faman dariya take, da k'yar tace mashi ai ba ita zata yanke hukunci ba Ya Haisam ne yace shikenan, ya juya kan Amadu yace "gaskiya AA yakamata muma fa mu fara haramar shigewa daga ciki, ko da yake k'ilan ma sai na riga ka kai da ko budurwa nasan baka da ita, ko kayi ta Yanzu?" Amadu dake murmushi ya girgiza mashi kai alamar a'a, "Gaskiya yakamata ace by now kana da budurwa ko kuma ka tsaida wadda zaka aura tunda nasan ba'a rasa masu son ka kaine kawae baka basu dama" Amadu dake yar dariya yace "No k'yale budurwar nan bari dae in nemi kud'i su taru tukunna in lokacin auren yayi zaka ga bazan sha wahalan samu ba tunda na gama had'uwa" dariya sosae Tk yasa bayan ya tsagaita yace "kuma wllh in dae kana da kud'i bazaka sha wata wahalan samun irin Matar da kake so ba, wai ni yanzu yan mata na soyayya tsakani da Allah kuwa? Ni kaina nan wai d'an ganin da ake ina fantamawa da motoci aka kuma ji gidan da nike kar kaso kaga yadda yan mata suke lik'e man, nan basu san Almajiri bane" gaba d'aya sukai dariya Amadu yace ai yanzu yafi k'arfin a ce mashi Almajiri shima ya zama dangin Senator d'in, suna haka aka turo k'opar duk suka kai idanun su kan masu shigowar, Abbas ne da Saleem da k'yar Abbas ya matsa mashi suka shigo don ya k'iya yace mi zai shigo ya yi, su Amadu na ganin su suka mik'e suna gaishe dasu kafin suka nufi kopar fita su kuma suka k'arasa shigowa ciki idanun su akan Fatuu da itama kallon su take da d'an murmushi haka Abbas ma murmushin yake mata, a gaban gadon suka tsaya yana kallon ta yace "Mom Zarah Amaryar mu, an daina kukan ko?" Kai ta d'an d'aga mashi alamar eh kafin a Sanyaye ta gaishe dasu suka amsa, "haka yakamata ai kar ya haddasa maki wani ciwon muda muke so a biya mu abunda muka rasa a yau......", bai rufe baki ba daga bayan shi yaji an ce "mi kake ci na baka na zuba ai kunsan dai ita d'in bata wasa bace da kun bata zata biya ku" Aunty Mareeya ce da ta shigo ruk'e da kwalin kwalaben kayan k'amshi tay Maganar duk suka juya har da Saleem suka kalleta Fatuu kuwa wata irin kunya ce ta rufe ta da sauri ta sadda kan ta k'asa, shigowa tay cikin d'akin ta nufi wurin dressing mirror Abbas ya bita da murmushi don sai ya d'an ji kunya duk da tun a Mota wurin kawo Fatuu ya fahimci bakin ta a sake yake itama, Saleem ne ya kalli Fatuu cikin cool voice d'in shi yace mata Allah yasa Alkhairi bata amsa ba sai d'an murmushi kawae tay mashi Aunty Mareeya ce ta amsa tare da juyowa ta kalle shi kafin ta maida idon kan Abbas dake ta murmushi itama ta yi had'i da d'an girgiza kai tana a gaban dressing mirror, ta fiddo wasu had'add'un kwalaben humra da turaren wuta tana jerawa a wurin a parlor ma ta jera wasu a cikin gidajen da su tv suke sosae suka k'ara k'awata wurin, Saleem ne ya juya zai tafi Abbas dake kallon Fatuu yace mata bari su je sai ya kawo mata Angonta Aunty Mareeya tay carab tace suna jiran shi yazo ya siya bakin Amarya a wurin su tay Maganar tana dariya shima Abbas d'in dariyar yake ya juya suka fita, bayan fitar su Fauzy ta shigo ruk'e da burner data gama turara parlor ta jona ta anan aka zuba turare Bedroom d'in ya fara turaruwa shima Aunty Mareeya da ta gama ta shiga yi ma Fatuu bayanin yadda zatay amfani da wasu daga cikin kayan kamshin ita dae kai kawai take d'aga mata, bayan an gama turara d'akin Fauzy ta hau gyara bedroom d'in duk da ba wani 6aci yay ba tana cikin gyaran Aunty Mareeya ta sake shigowa hannunta ruk'e da cup ta nufi side d'in da Fatuu take ta zauna a bakin gadon ta bata tace ta shanye abun ciki, ba musu ta amsa ta kafa baki saida ta shanyen ta mik'a mata Cup d'in tace ta taso zata nuna mata abu a kitchen tace mata to ta zuro da k'afafun ta ta mik'e suka nufi hanyar fita Fauzy nata sakin wani kalan murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, bayan sun je kitchen d'in bin d'akin Fatuu tay da kallo an tsara shi ya koma babban Kitchen a ranta ta shiga tuna lokacin da ta fara shigowa cikin shi yin fitsari da ta zo ba Haisam hak'uri da kuma lokacin da yay mata Assignment d'in maths tuna lokacin har saida ta saki murmushi, waya ta6a tunanin wai d'akin zai zama kitchen d'inta gaba d'aya part d'in ma, wata drawer Aunty Mareeya ta jawo ta ce ta matso, nuna mata abubuwan dake ciki tay wanda sauran magungunan ta ne da aka siya mata a wurin Aunty Bee ta shiga yi mata bayanin yadda zata rinka amfani da kowanne Fatun na d'aga mata kai har ta gama, tambayarta tay ko a cikin kitchen d'in akwae abunda bata iya amfani da shi ba ta gwada mata, a sanyaye tace duk ta iya tana ganin yadda Aunty Saude mai aikin nan gidan ke amfani da su Aunty Mareeyar tace da kyau daga haka suka fito suka koma Bedroom d'in, suna komawa Feenah ta shigo tace ma Aunty Mareeya ance su fito za'a maida kowa gida tace to dama sun gama mata komae ai, ta kalli Fatuu da tay zuru jin zancen zasu tafin ta tambaye ta akwai wani abu ta girgiza mata kai sukuku da ita ta juya ta nufi wurin k'atuwar wardrobe d'in d'akin, a gefenta ta d'aukko jakar ta ta dawo bakin gadon Feenah na tsaye, zuge zip d'in jakar tay ta kai hannu ta ciro wata farar shopping bag mai d'auke da tambari ta d'aura ta akan cinyoyin Fatuu tace "Yar k'anwata Amarya ga tawa gudunmawar nan saura kuma kice zaki k'i yin amfani dasu Saboda wai kunya, ke da shi yanzu ba sauran wata kunya don kun riga kun zama abu d'aya, an san kunya abu ce mai kyau amman yanzu a wani wurin in kika ce zaki saka kunya to zaki k'wari kan ki ne da kuma shi Mijin naki don haka ba a komai zaki rink'a nuna kunya ba....." Katse ta Feenah tay da fad'in "ba kamar yadda take da kishiya kuma ma baturiya, gaskiya dole sai kin zage wllh don su ba wata kunya gare su ba don ma ita tana ruwa biyu....." Aunty Mareeya ta kar6e "kin ji dai ko, wannan nasan har yawo daga ita sai d'an pant in ma tasa kenan tana iya yi a gaban shi, don haka ki zage wllh balle ke da ma kike da surar jan hankali Tubarkallah, ki kuma dage da gyara jikin ki ciki da waje, duk magungunan da nayi maki bayani kada ki wasa da shan su sannan kuma kada ki k'asa a guiwa wurin faranta mashi irin su ta nan wajan aka fi kama su, ki sashi ya susuce ta yadda duk in zaiyi Magana sai ya ambaci sunan ki alamar kece a ran shi koda yaushe" gaba d'aya suka sa dariya harda Fauzy dake can d'ayan side d'in gadon raku6e, Feenah ta d'aura da fad'in "Bayan wad'annan kuma sai a had'a da biyayya don itace zata k'ara taimakawa wurin siye zuciyar shi duk da nasan ke mai biyayya ce a gare shi tun ba yanzu ba, to ki k'ara akan wadda kike mashi don yanzu ne zata fi yin aiki kuma zaki fi cin ribar yin ta, a k'arshe ina Addu'ar Allah yasa Alkhairi a zaman ku ya had'a kawunan ku gaba d'aya da abokiyar zaman taki ya kauda fitina ya bashi ikon yin Adalci a tsakanin ku, ya albarkace ku da zuria d'ayyiba" su Aunty Mareeya ne suka amsa ita kuma Fatun kan ta na a k'asa, lokacin Abbas ya lek'o cikin d'akin yace su suke jira fa duk suka mik'e ya d'aga murya yana ma Fatuu sai da safe, yana shirin juyawa Feenah tace don Allah ya taimaka mata da Abdul yadda yay baccin nan ba iya d'aukar shi zatay ba ya k'arasa shigowa cikin d'akin ta kinkimo mashi Abdul d'in ya kar6e shi ya sa6a a Shoulder yana fad'in Allah ma ya taimake su da yayi baccin ai da ba k'aramar rigima za'ai dashi ba don yana iya cewa nan zai kwana ba kamar yana ganin gidan Baban shi da Momy d'in shi ne duk sukai dariya ya juya ya nufi kopa suma suka bi bayan shi Fatuu ta fara k'ok'arin saukkowa daga saman gadon Fauzy dake kallonta tace ina zata, jin haka yasa su Aunty Mareeya juyowa suma suka tambayi inda zata fuskar ta kaman zatai kuka murya na d'an rawa tace raka su zatai, waro ido tay tace a ina ta ta6a ganin Amarya tayi rakiya ta koma ta zauna kafin Angon ta ya zo, ba yadda ta iya dole ta koma ta zauna suka tafi banda Fauzy da tay tsaye ta kasa tafiya yanayin fuskar ta ya sauya itama kaman zata saka kukan, bin juna da ido sukai can k'walla suka zubo ma Fatuu sharrr Fauzy ta d'an girgiza mata kai daga inda take tsaye tace "ki daina kuka Zarah lokacin farinciki ne yanzu, Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya sai mun had'u School" da k'yar ta k'arasa Maganar, jin kuka na niyyar k'wace mata yasa ta juya da sauri ta fita, tana fita Fatuu ta d'age k'afafunta ta kife fuskar ta tana kuka a hankali................. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2059* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .............Fauzy na zuwa ba 6ata lokaci suka tafi don itama Fatun ta gama shiryawa, sai Magrib ta dawo Fauzy an sauketa a School, daka kalli fuskarta ma zaka gane tasha gyara ga wani k'amshi da jikinta ke fitarwa, lokacin data shiga gidan d'akin gwaggo ta nufa ta isketa ta dawo tana yin salla hakan yasa ta juya ta nufi d'akin ta, a gaban dressing mirror ta tsaya bayan ta cire veil d'in da tayi rolling ta fara k'are ma kanta kallo tana sakin murmushi, hannu ta kai tana shafa kumatun ta da har wani glowing suke, skin d'in ta ta k'ara yin sumul gwanin taushi dama a mulke take Saboda tsadaddun mayukan da take amfani dasu, bayan wani lokaci ta d'auki gyalen ta da ta ajiye a gefen mirror ta fita, d'akin gwaggo ta koma ta iske ta gama Sallar tana zaune kan darduma tana tasbihi, gefen ta Fatuu ta nufa ta zauna suka had'a ido ta sakar mata murmushi saida ta shafa sannan itama ta mayar mata da murmushin tace "Auta ta ta fara fitowa sak Amarya" murmushi kawae Fatun ke yi ta gaishe da ita bayan ta amsa ta tambaye ta Fauzy tace mata an aje ta a Makaranta ta d'aga kai, d'an shiru su kai suna ta yi ma juna murmushi daga baya Fatuu tay mata Maganar kud'in d'azu da aka turo da wanccan da tay mata Maganar su gwaggon ta tambaye ta ta tura ma Aunty Mareeya tace mata eh, tace to ai nata ne ba zatay amfani dasu bane, d'an shiru Fatun tay kafin tace "ni ba abunda zan yi dasu kawae dae ina tunanin zuwa shagon Aunty Zee in siyo wasu kaya" gwaggo dake kallonta ta tambaye ta wane irin kaya ko na sawa tace mata eh, tace "Yanzu duk kayan da ke gare ki sai kin k'ara,wasu ma fa baki ta6a sakawa ba sai aita tara kaya don ma ana bayarwa, duka yaushe Chairman ya baki akwati biyu na kaya ga shima Yayan naki da zai tafi yay maki akwatunan kaya ga wad'anda kike siya duk basu isa ba ki tattara abun ki ki tafi dasu sai kin k'ara wasu" da d'an alamun kunya Fatun tace "d...dama wai ko wanda zan sa ranar Juma'a d'in ne da yan underwear" da k'yar ta k'arasa Maganar had'i da sunkuyar da kai gwaggon tace "ni ina ganin tunda lokaci ya riga ya k'ure kawae ki bar shi yanzu yaushe har aka d'inka ma tunda kina da sababbin kayan da baki ta6a sawa ba ko cikin su ne ki za6i d'aya sai ki saka, nasan ma ko daga bayane zai maki suturar tunda hakanan ma yayi bare kuma yanzu, kawae don lokaci ya k'ure ne amman su underwear d'in zaki iya siyowa" kai ta d'aga mata alamar to, "to wai ma kin had'a kayan naki ko kuwa baki had'a ba?" a hankali ta girgiza mata kai alamar a'a, tace "to har sai yaushe ko sai lokaci ya k'ure kizo Kita faman duminiya" d'an yamutsa fuska Fatuu tayi kaman zatai kuka tace "ni wllh gani nike kaman wasa ba gaske ba wai zan bar gidan nan" yar dariya gwaggo tay tace "ki bari sai ranar zaki shaida in wasa ne ko gaske, in Allah ya kaimu ranar Juma'a kaman yanzu ai ina sa ran kin ma bar gidan nan" cike da shagwaba tace "Wayyo Allah, wllh gwaggo ban jin dad'i zan rabu daku zan koma wani wuri" tana rufe baki k'walla suka zubo mata sharr gwaggo dake ta dariya tace "ni kuma kinga dad'i nike ji..." Katse ta tay da fad'in "kai gwaggo dama ashe kin gaji dani" tace "ai abun farinciki ne yanzu ka ga naka yayi aure ba kamar da auren yay wuya yan mata da dama nata neman mijin aure babu, gashi ke kin samu d'aya tamkar da miliyan don wannan wuce dubu, in na ce banji dad'i ba ai na zama butulu ban gode ma Allah ba daya amsa man Addu'ar da nike maki koda yaushe ta ya baki miji na gari" d'an murmushi Fatun tay ta sunkuyar da kai can ta d'ago tace "nama ji dad'i daba nesa bane zan rink'a zuwa koda yaushe...." Da sauri gwaggo ta tari numfashin ta "ki rink'a zuwa ina? aikuwa dana sa6a maki wllh mi kika d'auki aure ne, abun wasa ko mi to a hir d'in ki kika ce zaki rink'a yin sunturi kina zuwa sai na sa6a maki kuwa, Mutuncin mace ta zauna a d'akinta sai ta kama ta fito" tana ta yamutsa fuska tace "kaman ma ke bazaki missing d'ina ba" tana yar dariya tace "ba kuwa zan yi ba tunda na samu madadin ki, Mino zan d'aukko ta dawo nan dama nayi mata alk'awarin zata dawo" d'an waro ido Fatuu tay ta fara sakin murmushi cike da farinciki tace "Yanzu Mino nan zata dawo kenan?" Kai ta d'aga mata, "amman kuma ai bata gama Secondary d'in ba" gwaggo tace "Eh aji biyar ta shiga in ta dawo nan sai ta k'arasa ai" sosae Fatuu taji dad'i sai faman washe baki take, tana matuk'ar son yan'uwan ta don kuwa mahaifiyar su itama tana son ta suma kuma haka don in ba ka sani bama baka cewa ba uwar su d'aya uban su d'aya ba ba kamar dae Mino d'in bala'en kama take da Fatuu, tana zaune a d'akin akai sallar isha gwaggo ta tashi tayi ita kuma ta koma d'akin ta, bayan gwaggo ta gama d'akin Fatun ta nufa tana shiga ta iske ta a kan gado tana latsa wayarta tace mata ta tashi ta taya ta su had'a kayan nata tace to, saukko da akwatunan ta sukai daga saman wardrobe gwaggo ta bud'e wardrobe d'in ta fara za6o mata wanda zata tafi dasu ita kuma tana jerawa, suna cikin haka taci karo da k'umshin ledar magungunan da Aunty Mareeya ta fara aiko mata ta fiddo tana fad'in miye aciki, d'an zaro ido Fatuu tay ganin gwaggon na kokarin kwancewa yasa gabanta ya hau fad'uwa ta sadda kanta k'asa, bayan ta bud'e k'ura ma abunda ke ciki ido gwaggo tay ta kai hannu ta fiddo da yar kwalbar ciki ta d'aga tana duba takardar jiki lokacin Fatuu ta d'an d'ago gwaggon ta jefa mata wani mugun kallo ba shiri murya na rawa tun ma kafin ta tambaye ta ta hau yi mata bayanin wadda ta bata, har saida gwaggo taji d'an sanyi don da hankalin ta har ya tashi ta maida kwalbar ciki kafin ta kalleta sai yan kame kame take ta tambayeta ta yi amfani dasu ne tace mata a'a gwaggon tace to Saboda mi ba bata akai don tayi amfani da su ba, cikin yar in ina ta ce mata na kwalbar dole sai jinin ya d'auke su kuma sauran wani da nama ake cin shi wani kuma da peak milk tana Maganar tana sussune kai, yar ajiyar zuciya gwaggon tay tace mata taje wurin Amadu ta amso Madarar da sauri tace to ta juya gwaggon ta bita da ido har ta fita, bayan ta amso tasa ta d'aukko Kofi da cokali a Kitchen ta tambayeta yadda aka ce a had'a ta fad'i mata da kanta ta shiga had'a mata bayan ta gama ta bata ta shanye daga baya suka cigaba da abunda suke. Washe gari wurin Misalin k'arfe sha d'aya saura na safe aka kira Aunty Mareeya daga tasha cewa ga sak'o an kawo mata daga Kano tace to suka fad'i mata tashar da suke, kiran Daddyn su Hanif tay ta sanar dashi zata je ta dawo, ba 6ata lokaci dama tana ta dakon isowar kayan ta tafi, bayan ta amshi sak'on magungunan direct gidan su Fatuu ta nufa lokacin tana Makaranta sai gwaggo ta tarbeta tana ta fara'a suka shiga Parlor, gaisawa suka shiga yi daga baya Aunty Mareeya ta warware kwalin da aka sako sak'on ciki ta shiga firfito dasu tana yi tana ma gwaggo bayanin kowanne ta shiga yabawa tana sa Albarka ita kanta taga sauk'in kayan gasu da yawa, bayan ta gama fiddo su ta nuna mata wanda yakamata a fara ba Fatun zuwa ranar tarewar sauran kuma sai ta tafi dasu taci gaba da amfani dasu a can gwaggon tace to da ta dawo sai a fara batan, sosae tay ma Aunty Mareeya godiya tana Allah ya bar zumunci daga baya ta tambaye ta ko akwae wani abu gwaggon tace ehh kayan k'amshi take so an mata kwatancen in da zata samu to ita kuma ba sanin kan su tay ba Aunty Mareeya tace wannan ba matsala bane akwae inda za'a same su masu kyau jera mata kawai za'ai don already a kwalaben su masu kyau suke nan ma godiya gwaggon tay mata ta tambayi kaman nawa zasu isa ta fad'i mata, bayan sun gama Maganar kayan k'amshin suka shiga Maganar Abinci da za'ai ranar Juma'ar, saida suka gama tsara komae Gwaggon ta bata kud'in abubuwan da zata siyo sannan ta tafi. Tun Aunty Mareeya na kan hanya ta kira Fauzy ta sanar mata zancen isowar sak'on Magungunan taji dad'i sosae ta sanar ma Fatuu ita dae d'an guntun murmushi kawai tay, bayan an tashi Hostel suka wuce Fauzy ta had'a kayanta a cikin d'an trolley zata bi Fatun kaman yadda suka tsara a aji ita da dawowa cikin Makaranta sai bayan ta tare daga baya Haisam yazo d'aukar su, tun bayan da suka shiga Motar suka gaida shi ba wanda ya k'ara cewa uffan har suka isa gida, suna shiga d'akin gwaggo suka wuce tana ta fara'a tay masu sannu da dawowa suka gaishe da ita tace in sun kimtsa su zuba Abinci yana Kitchen suka ce to suka nufi d'akin Fatuu, suna cikin cin Abincin gwaggo ta k'wala ma Fatun kira bayan taje ta bata wasu daga cikin Magungunan da aka kawo kaza da cicci6i da kuma zabuwa duk ta d'ibar mata tace taje ta cinye su duka harda romon su tace mata to ta koma d'aki Fauzy na zaune tana cin Abincin ta shigo ta koma inda ta tashi ta zauna, koda Fauzy taga abunda ta shigo dashi nan take ta gane na maganin ne tunda taga hotunan su jiya ta hau yin murmushi Fatuu ta aje tace su ci Fauzy ta zaro ido tace ta rufa mata Asiri wannan yafi k'arfin ta saidae itan tay d'an murmushi kawae ta kai hannu ta yago naman kazar ta kai baki koda taji taste d'in ta ba Arziki ta d'an yamutsa baki da k'yar ta had'iye na bakinta a tunanin ta ko kazar ce kad'ai haka sai ta d'ibi cicci6i shima tana kaiwa baki taji shi salaf sai kaifin magani bayan ta had'iye ta kalli Fauzy tace don Allah ta ci da dad'i sosae jin haka yasa ta cewa tunda ta matsa mata bari ta d'an ci ta kai hannu ta yagi kazar Fatuu nata gumtse dariya gaba d'aya ta kai naman baki ba Arziki itama ta tsaya cak ta kasa taunawa ta d'an zaro ido Fatuu kau mi zata yi in ba dariya ba, da k'yar Fauzy ta had'iye tana d'an yamutsa fuska ta kai hannu ta d'auki ruwa ta kwankwad'a bayan ta aje tace "tabb, ni fa koda na ganta na zata Normal farfesun kaza ne ashe ashe duk farfesun magani ne wannan dole ma tay aiki a jiki kam" koda Fatuu tace mata ta k'ara don Allah cewa tay wllh in ta ganta a lahira kaita akai hakanan taja ma kanta bala'e ta kasa zaman lafiya ita dae daya zamar ma dole taci Fatuu tay ta mata dariya, daurewa tay taci gaba da ci daga baya ma lafiya lau ta rink'a ci har ta cinye ta shanye romon kaman yadda gwaggon tace, bayan sun gama suka hau shirin tafiya gyaran jiki da wankin kai don gwaggo tace kitso za'a yi mata, da daddare bayan sun dawo sun ci Abinci gwaggo ta kara kiran Fatuu ta bata tsumi kusan kala ukku ta sha harda na magarya mai wanko mara yay maganin sanyi aikuwa sosae yay ma Fatuu aiki don duk wani sauran jini daya rage saida ya fito a daren, Washe gari Alhamis da safe bayan sun yi breakfast suka hau shirin tafiya Makaranta Haisam ne yazo ya d'auke su, Bayan an tashi ya d'aukko su suna dawowa Abinci kawae suka ci suka hau shirin tafiya k'unshi lokacin da Fatuu ta shiga toilet yin wanka har saida ta d'an yi mamaki ganin Pad d'in data sa da safe Kandas ba jini alamar dae ya d'auke hakan yasa bayan ta gama wanka ta had'a dana tsarki tayi sannan ta fito, tana komawa d'aki ta zura doguwar riga don yin salla Fauzy na ganin haka tay yar shewa ta hau tsokanar ta tana fad'in an yi a daidai abun ya mata dad'i wllh, ita dai d'an murmushi kawai tay ta girgiza kai, bayan duk sun shirya suka tafi, Ana gama sallar la'asar sai ga Saude tare da Tk rike da wasu jakunkuna masu shegen kyau guda ukku Gwaggo ta tarbe su suka shiga cikin parlor, bayan sun gaisa Saude tace mata gashi in ji Hajiya tace Fateema ta fara amfani da kayan ciki gwaggo ta hau godiya Saude ta k'ara cewa da Mota suka zo tace a kwaso kayan kitchen da sauri gwaggo tace to ta mik'e suma suka mik'e gaba d'aya suka fita, saida ta lek'a waje ta kira Amadu ya shigo aka fara kwashe na cikin d'akin shi ana kaiwa cikin Hilux d'in da suka zo da ita daga baya aka kwashe na cikin d'akin Fatuu, sai bayan da suka tafi ne gwaggo ta koma parlor ta bud'e jakunkunan ta fara dubawa, kaya ne ciki dinkakku lace kala biyu atampa kala ukku sai shadda data sha uban aiki itama kala biyu sai lifaya da dogayen riguna suma kala bibbiyu a cikin d'ayar jakar mahad'in sune wato takalma da mayafai harda hijab da jakunkuna sai cikin ta k'arshen underwear ne harda rigunan bacci dasu sark'ok'i da kuma kayan shafa duk da kayan basu da yawa amman fa da ka gani kasan masu kud'ine ba k'ananun kaya bane, bayan gwaggon ta gama dubawa ta hau jinjina kai cikin ranta take raya ita dama ranta ya bata da wuya ba'ai ma Fatun kaya ba, maida komai tay ta mik'e ta fita, d'akin ta ta koma tana zuwa ta kira Hajiyar a waya tay mata godiya ta tambayeta ba wata matsala tace mata eh ta k'ara yin godiya sosae da Addu'oi. Bayan su Tk sun kai kayan ta k'aramar kopa suka rink'a shiga dasu shida Amadu da gwaggo tasa ya bisu Saude ma ta fara d'auka Officer ya taso yace ta barshi ya kama aka rink'a shigar dasu tare da shi ita kuma ta nufi cikin part d'in don ta fara jerawa kaman yadda Hajiya ta bada umarni har aka shigar da komae. Yau ma sai bayan Magrib suka dawo har Fauzy ma anyi mata k'unshi gwaggo na gani ta hau yabawa don ba k'aramin kyau yay ba ya zanu rad'am abun ka da farare kuma gashi ja da bak'i ne yay gwanin burgewa gwaggo ta nuna masu kayan da aka kawo suka fara dubawa Fauzy nata santi ita dae Fatuu murmushi kawai take. JUMA'AT BABBAN RANA Washe gari da wani irin yanayi Fatuu ta tashi ta kasa gane farinciki take ko damuwa gaba d'aya kasala ta baibaiye ta har Fauzy ta fahimci hakan ta tambayi Mike damunta tace ita dae gatanan ta rasa Mike mata dad'i ma yar dariya Fauzy tay tace zullumin barin gida ne, Bayan sun yi breakfast suka yi shirin tafiya Makaranta, koda Fatuu taje yima gwaggo sallama cewa tay ai tayi zaton zasu hak'ura da zuwa yau Fatun da tay sukuku tace ai ko sun zauna ba abunda zasu yi gara su tafi gwaggon tace shikenan itama ta lura da yanayin ta har saida ta tambayeta wani abu ke damunta ne tace mata ba Komai ta juya zata fita gwaggon ta bita da kallo tana d'an murmushi, tana komawa d'aki ta jiyo horn d'in Haisam suka fito, Bayan tafiyar su makwabta suka fara shigowa don gwaggo duk ta sanar dasu zancen auren da tarewar kowa yaji sai ya taya ta murna har innar su Haulat ma tazo nan aka fara shirin d'aura girki duk da ba wani abu za'ai ba miyar waina ce da sinasar da ta bada ayo mata sai Fried rice itama Aunty Mareeya ta amsa zata bada ayo harda su coleslaw, bayan an d'aura miyar aka fara had'a kunun Aya da zobo lokacin wasu daga cikin Abokan aikin gwaggon suka zo har an taho da su dublan d'in data bada aikin su nan aka cigaba da hidima, lokacin da su Fatuu suka dawo wurin k'arfe d'aya saura mutane sun d'an taru a gidan ba laifi harda Zaliha d'iyar kishiyar gwaggon da iyalanta da kuma iyalan baba shehu suna shigowa aka hau ce ma Fatuu Amarya Amarya ita dae d'an murmushi kawae take tana gaishe dasu suka wuce d'aki, suna shiga Fatuu ta nufi gado ta zauna dabar Fauzy dake k'ok'arin cire Hijab tace ba zama yakamata tay ba ta tashi taje tay wanka ta shirya kar aita ganin Amarya kamar an koro ta kallo kawae ta bita dashi bata da niyyar mik'ewa, suna haka gwaggo ta shigo ruk'e da plate d'in Abinci da kuma na sobo da kunun aya ta aje masu akan Carpet tace gashi nan su ci in sun gama taje tay wanka ta d'aga mata kai, bayan sun fara ci bata ci wani mai yawa ba ta cire hannunta Fauzy na tambayar ta badae har ta k'oshi ba tace eh rarrashin ta ta shiga yi kan ta k'ara tace mata bata jin dad'in bakin ta ne dole ta rabu da ita tace to taje tayo wankan, bayan tayo wankan itama Fauzy taje tayi suka fara shiryawa doguwar rigar shadda ta fiddo mata a cikin kayan da Hajiya ta aiko ta taimaka mata ta d'an yi make up ta koma saman gado ta zauna Fauzy ma ta hau shiryawa lokacin Haulat ma tazo bayan ta gaisa da gwaggo ta bata gudunmawar data kawo tana ta godiya ta koma d'akin Fatuu, a bakin gado ta zauna ganin yanayin ta yasa ta hau tambayarta lafiya ita da za'a gani tana farinciki Fauzy na yar dariya tace fargaba ce itama Haulat dariyar tayi. Ana gama sallar Juma'a su Feenah suka iso sun ci gayu Abdul harda babbar riga tunda bai sa yaje daurin aure ba yasa yazo tarewa, harda katan katan d'in lemu da ruwa suka kawo da kwalin Warmers masu kyau harda na had'addan glass jug ga kuma kud'i gwaggo tay murna sosae sai godiya take, daga baya ta koma d'akin Fatuu tana zaune saman gado ta rungume Abdul da tunda suka shigo gidan ya nufi d'akin, bakin gadon Feenah ta zauna ta kalli Fatun da murmushi tace "Amaryar mu kin sha kyau" d'an murmushi kawai tay ta gaishe da ita aka kawo masu Abinci, su Feenah basu dad'e da zuwa ba Aunty Mareeya ta iso tare da k'atuwar kular Fried rice da trays d'in coleslaw anyi sealing, su Amadu ne suka shigo da su tare da Tk da wani abokin su ita kuma suka kamo k'aton kwalin kayan k'amshi ita da Maman taufiq makwabciyar ta da suka taho tare, gwaggo tay farinciki sosae har ta kasa rufe baki sai faman godiya take tana shi Albarka daga baya wasu daga cikin k'awayen su na makaranta da Fauzy ta gayyata suka zo ciki harda Zainab Muhammadu da wadda zatayi ma Fatuu make up dama sana'ar ta ce ba 6ata lokaci aka fara yi mata, lokacin da aka gama baka jin komai sai Tubarkallah da kowa ke fad'a don ba k'aramin kyau kwalliyar tay mata ba ba kamar da yake ba'a ta6a yi mata irin ta ba,nan fa aka shiga yi mata hotuna daga baya aka sa ta canza kaya tasa lace shima akai mata hotunan, haka aka ci gaba da hidima aka ci aka sha abun sai godiyar Allah, Bayan sallar la'asar Haisam na Zaune a Bedroom d'in shi na G.r.a tare da Abbas da Saleem da yasan da zancen auren daga baya Najeeb dae bai sani ba don bai K'asar yana Canada, basu dad'e da gama cin Abinci ba da Abbas ya kawo daga gidan Hajiya don anan ya iske su bayan ya kai su Feenah, gaba d'ayan su kowa na ruk'e da wayar shi yana latsawa jefi jefi suke yin Magana, can Abbas ya mik'e daga kan kujerar da yake ya nufi Haisam dake kishingid'e jikin shi sanye da ash d'in shadda ya zauna daga gefen shi yana fad'in "gafa Amaryar ka ta fito ma sha Allah" d'aga ido yay ya kalli wayar, Abbas yaci gaba da bud'e mashi sauran dama Feenah ce ta d'aura su a status har saida suka k'are sannan Haisam d'in ya janye idon shi ba tare da yace komai ba, Abbas ya mik'e ya nufi Saleem dake sanye da farar shadda yana latsa waya shima ya shiga nuna mashi d'an guntun murmushi yay cikin cool voice d'in shi tamkar Haisam yace wai yarinyar nan ce har ta girma Abbas na dariya yace mashi eh mana gashi ma har ta d'auke nauyin H,zakee Haisam din na jin shi bai ko kalle su ba Saleem d'in ya k'ara yin d'an guntun murmushi kawai, suna nan har aka yi sallar Magrib suka tafi Masallaci suna can har akai isha ana gamawa Hajiya ta kira Abbas tace mashi ya taho suje su d'aukko Fateema yace to bayan sun gama ya kira Feenah ya tambaye ta akwae Mutane ne da yawa tace mashi ba laifi, Saleem yay ma Magana da yake da Jeep ya zo kan suje su d'aukke su yace ok, kallon Haisam Abbas yayy yana murmushi yace ya taso suje ya d'an girgiza mashi kai alamar ba zai je ba ya juya yace ma Saleem su je ya mik'e har zasu tafi Haisam ya dakatar dasu Abbas ya juyo yana kallon shi ya mik'e yace yana zuwa, dressing mirror ya nufa ya jawo drawer chest ta tsakiya ya fiddo wani makulli, bayan ya rufe ya dawo wurin su ya mik'a ma Abbas yace yay amfani da Motar duba makullin yay ya d'ago da d'an bud'a ido yace "Lalle kana ji da Amaryar nan a Jeep d'in Dad d'in za'a d'auketa" shiru yay mashi ya nufi komawa kan kujera yace ma Saleem suje suka nufi hanyar fita daga Bedroom d'in, Bayan Hajiya ta kira Abbas tay mashi Magana ta kira gwaggo tace mata a shirya Fateema za'a zo a d'auketa tace to, d'akin ta ta nufa su Aunty Mareeya da Feenah da sauran k'awayenta duk suna ciki anata hira Aunty Mareeya sai basu dariya take gwaggo ta shiga ta sanar dasu, wani irin bugu k'irjin Fatuu yay gabanta yaci gaba da Fad'uwa Aunty Mareeya kau harda gud'a ta rafka ta mik'e tana fad'in Fatuu ta tashi ta canza kaya, Wani farin dankareren lace mai adon golden cikin kayan da aka kawo mata ta fiddo mata da gyalen shi golden da takalman shi half cover masu tsini suma golden harda purse d'in su dama barin su akai sai za'a kaita ta saka su, ba 6ata lokaci aka gama shiryata abun saidae ace Tubarkallah tayi kyau har ta gaji sai yi mata hotuna ake ba'a dad'e da gama shiryata ba Hajiya da Saude suka zo Hajiya na fadin gasu sun zo biko tana sanye da lifaya Saude ma tasha doguwar rigar lace da mayafi, nan aka shiga gaishe gaishe Gwaggo tace ma Hajiyar su shiga tace a'a basai sun shiga ba dare nayi a fiddo ta su tafi tace to ta nufi d'akin, tunda taji zancen an zo tafiya da ita ta saka kuka da duk ganin abun take kaman wasa sai yanzu ta tabbatar gaske ne, nan aka shiga rarrashin ta Aunty Mareeya data ruk'ota cike da zolaya take ce mata waya fad'i mata amare na kuka yanzu k'auyanci ne, bayan sun fito aka kaita gaban Hajiya dake tsaye tana jira tace akaita Mota duk aka firfita ta kalli gwaggo dake tsaye jikinta duk yayi sanyi tace itama tazo aje da ita ta rakata d'akinta tace to ta juya don d'aukko Hijab bayan ta dawo suka fita tare da Hajiya............. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2061* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .......bayan su Aunty Mareeya sun fito saida suka koma part d'in Hajiya suka k'ara yi mata Allah yasa Alkhairi sannan sukai mata sallama tana ta godiya duk aka fito harda su inna Zaliha da tun d'azu suka so tafiya Hajiya tace su bari za'a maida su gwaggo ta biyo su tace suje gida don Allah zata basu kayan biki, Motar Saleem Abbas yace su Aunty Mareeya da Feenah su shiga gwaggo ma ta shiga shi kuma ya d'auki su inna Zaliha da iyalan baba shehu sai wasu abokan aikin gwaggo da suka rage su biyu, a daidai kopar gidan su Fatuu suka tsaya gwaggon ta shiga ta d'ebo ma kowannensu su cin cin harda man shanu, bayan ta kawo masu suka yi sallama tana ta godiya tace ma Fauzy saura ta daina ganin ta tunda k'awar ta ta bar gidan tana yar dariya tace a'a zata rink'a zuwa har weekend ma zata rink'a zuwan mata, sosae gwaggo taji dad'i tace to Allah ya bada iko suka tafi tana ta k'ara godiya tare da d'aga masu hannu, saida sukai nisa sannan ta koma ta kullo gidan ta nufi gidan Hajiya don bata yi mata sallama ba ta taho, tana tafiya tana tunanin autar ta sai murmushi take wani lokacin ta d'an girgiza kai, har ta fara jin kewar ta tana son ta gan ta saidae ba dama don bazata iya zuwa part d'in ba a yanzu. Feenah aka fara ajewa gida don tafi kusa tay ma Saleem d'in godiya sukai sallama dasu Aunty Mareeya har tana fad'in taga gida zasu rink'a zumunci in sha Allahu tace to shikenan ta gode, dama sun yi musayar lambar waya tun a gidan su Fatuu kafin akai ta, daga nan Goriba road suka nufa aka kai Aunty Mareeya, bayan ta nuna mashi gidan ya parker tay mashi godiya ya jinjina mata kai ba tare da ya ce komae ba ta bud'e kopar ta fita Fauzy dake a gaba ma ta fito bayan sun rufe mashi kopopin yaja ya tafi, tsaye Aunty Mareeya tay baki bud'e tabi bayan Motar da kallo kafin tace "da alama shima wannan lalurar gare shi" kallon bayan Motar da har tayi nisa Fauzy tay kafin ta juyo ta kalli Aunty Mareeya cikin rashin fahimta ta tambayi wace irin lalura gare shi, tace "irin ta mijin Zarah mana, daga gani shima miskili ne na gaske" yar dariya Fauzy tay "na lura da hakan don ko d'azun da za'a kai Zarah da muka hau Motar shi bai ce ma kowa uffan ba sai d'an Music da ya kunna sama sama" Aunty Mareeya dake kallon ta tace "da gani dai wani shege ne ko kuma d'an wani shegen shiyasa harda rufe lambar Mota, baice yana son ki ba?" ta kafe Fauzy da ido alamar jiran amsa, dariya Fauzy tay "taya zai ce yana sona na fad'i maki tunda muka hau Motar shi bai ce mana uffan ba, kema ba gashi kin gani ba har kin fad'a" k'wafa tay tace "Allah ya yabawa aya zak'in ta, ai da ya sake yace yana son ki har abun ya kai ga aure da an taimaka mashi an sashi ya rink'a magana shima yadda za'a sa abokin shi, Allah sarki Zarah...." Murmushi tay kawae bata ida abunda zata ce ba ta nufi gate Fauzy tabi bayanta acikin ranta tana tuna k'awarta Fatuu dama tunda suka baro ta ta tsaya mata a rai, a yanzu kuwa sai taji ta fara sha'awar yin aure itama. Gwaggo na isa part d'in Hajiya a parlor ta same su kaman yadda ta barsu ita da Saude sai dae ita Sauden tana kitchen tana yin girki musamman don su Fatuu kaman yadda Hajiya ta bata umarni, zama gwaggon tay Hajiya tace har ta sallame su tace mata eh suka d'an ci gaba da yin hira suna kallo, can gwaggo tace bari ta tafi sai Allah ya kaimu ta k'ara yi mata godiya da Addu'oi, tana k'ok'arin mik'ewa Hajiya tace ta tsaya zasu je wurin Zarah yanzu sai suje tare tasan dae bata rasa mararin son ganin ta, cike da Zolaya tay Maganar gwaggo dai d'an murmushi kawai tay ta sadda kai, bada jimawa ba Saude ta shigo cikin parlon hannunta ruk'e da wani had'add'an basket mai d'auke da k'awatattun Warmers, a gefen kujera ta tsaya cike da girmamawa tace ma Hajiya an gama, kokarin mik'ewa ta fara yi tace ma gwaggo suje itama ta mik'e, har zasu tafi tace ma Saude taje saman gadon ta towels na nan da aka manta ba'a saka mata a kaya ba ta d'aukko a kai mata tace to, bayan ta dawo ta d'auki basket d'in d'ayan hannun rungume da towels d'in da ta d'aukko suka tafi. Tun bayan da su Fauzy suka tafi ta kife fuska tana kuka sai da ta d'an d'auki lokaci a haka sannan ta d'ago idanunta duk kwalla tay zuru tana d'an kalle kallen d'akin, can ta kai hannu ta cikin ledan da Aunty Mareeya ta bata ta fiddo abun da ke ciki, bata gane ko miye ba saida tasa d'ayan hannun ta bud'e sannan ta ga ashe rigar bacci ce orange colour ta dai had'u ba karya yadin ta gwanin santsi irin mai bin jiki d'in nan kuma bazata wuce guiwa ba tana da d'an fingilallan pant mak'ale a jikinta, ajeta tay gefe ta zazzago sauran da ke ciki guda biyu, d'aya baby pink ce shara shara wannan da k'yar ta wuce mazaunan mutum irin wadda in aka sa a naked za'a ga mutum har saida Fatuu ta d'an bud'a ido ganin rigar, d'ayar ta karshe cream ce yadinta cotton ne mai dad'in tabawa gwanin taushi daga wurin wuyanta da k'arshen hannun ta da zai iya wuce guiwar hannu duk gashi gashi ne gazar gazar yana d'an walwali harda ribbom gareta, itama tana da pant sai dai gabanta a bud'e yake kawai yan igiyoyi gareta wuri ukku da zaka daure, har saida Fatuu ta d'an sauke ajiyar zuciya fuskarta a d'an kwa6e take bin rigunan da kallo ita kam bata jin zata iya amfani dasu a yanzu gani take zai iya mata kallon mara kunya, maida su tay cikin ledan ta d'an yi jimm can kuma ta mik'e ta nufi wardrobe don ta 6oye su a ciki, saidai duk yadda tay ta bud'e wardrobe d'in ta kasa ta rasa ta ya ake bud'eta don bata ga wani handle da zaka kama ka bud'e ba a jikinta, k'arshe d'aya daga cikin jakunkunan ta dake a gefen wardrobe d'in ta duk'a ta bud'e, a can k'asa ta tura ledan bayan ta rufe ta mik'e, a gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta, ita kan ta taga had'uwar da tayi don lace d'in ba k'aramin had'uwa yayi ba kuma ko ba'a fad'a ba da ka kalle shi zaka gane ba mai k'ananun kud'i bane, ga sark'a da yan hannun ta suma tamkar gold sun yi ma hannunta da ya sha k'unshi kyau ba kad'an ba, zuciyarta ce ta fara hasasho mata Haisam tsaye a bayanta har bata san lokacin da ta d'an yi murmushi ba, bayan ta gama kallon kan nata juyawa tay jiki a sanyaye ta koma bakin gadon ta zauna ta jingina da headboard, bada jimawa ba aka turo kopar ta kai idonta da sauri kan mai shigowar, Saude ce ta fara shigowa suka had'a ido tay ma Fatun murmushi itama tana niyyar mayar mata Gwaggo ta shigo aikuwa zumbur tay ta mik'e da sauri gudu gudu ta nufo kopar tana zuwa ta fad'a jikinta ta fashe da kuka lokacin Hajiya ma ta shigo tana dogara sandar ta idanun ta sanye da glasses har lokacin lifaya d'in ce nad'e a jikinta, sosae ta k'ank'ame gwaggon sai kace zata shige cikin jikinta sai faman kuka take har kallabinta ya fad'i haka gyalen ma ya zamo daga saman kan ta gashinta da ya sha gyara baki wuluk sai salk'i yake an yi parking d'in shi ya bayyana, har cikin ran gwaggo take jin kukan hakan ya karya mata zuciya daurewa kawai take tasa hannu guda ta d'an dafa bayan ta, "To wannan kukan shagwa6a ne ko na me, sai kace wadda zaku rabu kwata kwata, duka yaushe kika baro gidan kuma gashi har kin gan ta to miye abun kuka Fateema" Hajiya dake tsaye gefe tay Maganar Saude nata kallon su gwanin ban tausayi, d'ago da ita Gwaggo tay suka had'a ido Fuskar ta duk tayi jage jage da hawaye a sanyaye tace mata ya isa hakanan ta kamata suka nufi gado ta zaunar da ita, Hajiya ta kalli Saude tace ta kai towels d'in saman jakunkunan dake gefen Wardrobe in ta tashi ta canza masu wuri tace to, tsaye gwaggo tay a gaban Fatun tana d'an murmushi Hajiya ma ta maido idon ta kan Fatun tace "Fuskar Amarya duk tayi jage jage haka, kar kija Angon naki yazo yay tunanin wani abun mukai maki ya d'auki mataki a kan mu" cike da zolaya tay Maganar Fatun ta sunkuyar da kan ta k'asa, "Amman Dije ya akai aka bar mata kai haka ba'ai kitso ba" Hajiya dake kallon kan Fatun ta fad'a, gwaggon tace "Wllh naso ai mata shafa'a nayi gashi yau anata hidima ban ko tuna ba" jinjina kai tay tace "shikenan bari in Allah ya kaimu gobe sai a kira Balaraba tazo tay mata" gwaggo tace to cike da girmamawa, sake kallon Fatuu tay "Fateema ga Abinci can a saman Dining table in zaki ci in kuma zaki jira Angon naki ne sai ku ci tare dama can baya ke kike sa shi yaci da yawa yanzu ma sai ki dasa don har yanzu ba wani cin Abincin kirki yake ba" gaba d'aya d'an murmushi sukai banda Fatuu da ta sadda kai Hajiya ta kalli Saude tace suje, ganin gwaggo na niyyar bin su yasa tace in bata gama da ita ba ta tsaya zasu jirata a parlor cike da jin nauyi tace to, don dama bata samu yi ma Fatuu Nasiha ba, bayan fitar su Fatuu ta kalli gwaggon ta kamo hannunta cikin muryar kuka tace ta zauna sai ta girgiza mata kai alamar a'a, magiya Fatun ta hau yi mata kan ta zauna tace bazata zauna a gadon suruki ba tay Maganar da yar dariya dole Fatuu ta k'yale ta sai kuma ta nuna mata bedside drawer tace to ta zauna saman ta, bata musa ba ta nufi inda take ta zauna Fatun taja jiki ta matsa kusa da ita ta k'ara kama hannunta tana yar ajiyar zuciya irin ta wanda yay kuka, bin juna sukai da ido Fuskar gwaggo da d'an murmushi ita kuma Fatun ta d'an kwa6e fuska idanunta sunyi raurau kaman zata cigaba da kukan, nannauyar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke ta fara Magana a nutse, "Ina matuk'ar godiya ga Allah daya nuna man wannan ranar gaki a cikin d'akin ki na aure hakan ba k'aramin abun farinciki bane, dad'in dad'awa kuma wanda ya kasance a matsayin mijin naki mutum ne da kowacce uwa zatay Alfahari in d'iyar ta ta samu irin shi a matsayin miji, bani haufi akan yadda zaki gudanar da rayuwar gidan auren ki don nasan wacece ke fiye da kowa, duk yadda ake son Mace ta kasance a gidan aurenta na tabbatar zaki kasance, saidai ina so in k'ara jan hankalin ki, a yanzu kin baro shek'ar da kika taso cikinta kika saba rayuwa kin dawo wata sabuwa da baki saba ba, dole zaki ga yanayin rayuwar ya bambanta sosae, kada kiga ai kinsan abokin rayuwar naki kun saba dole wasu abubuwan zasu canza, ki k'ara wasu ki kuma rage wasu don yadda kuke dashi a da da kuma a yanzu ba d'aya bane, yanzu shi Mijin ki ne wanda Aljannar ki na a tafin k'afar shi dole ki k'ara girmama shi kiyi mashi biyayya fiye da yadda kike mashi, ki bishi sau da k'afa sannan ki zama mai wadatuwa da duk abunda yay maki kada kiga yanzu kina da hakki akan shi kice zaki rink'a rainuwa kan abunda yay maki, duk abunda yayi maki ki zama mai godiya had'i da Addu'ar k'arin budi a gare shi, sannan kada kice zaki rink'a yawan kai mashi buk'atu kiga ai yana da halin yi maki in dai abu ba ya zama dole ba to ki hak'ura don yawan tambayar abu na sa ka gundiri mutum koda bai fito ya nuna ba, na tabbatar zai tsare maki dukkan hakk'in ki don haka sai ki zama mai kauda kai, sannan 6angaren tsafta nasan baki da kyuwa ko ganda, ki k'ara dagewa wurin gyara jikin ki da Mahallin ku ki hana idon shi ganin abunda zai munana mashi haka ki hana hancin shi shak'ar abunda zai 6ata mashi...." D'an dakatawa tay idanun Fatuu akan ta sun yi rau rau, bayan ta d'an nisa taci gaba "a zaman farkon nan da zakuyi anan zaki k'ok'ari ki fahimci miye yake so da kuma miye bai so ma'ana miye in kinyi zai ji dad'i ya faranta mashi rai miye kuma in kinyi ba zai ji dad'i ba ko zai bakanta mashi, in kin fahimci hakan sai ki kiyaye sai kiga kun zauna lafiya har in kin ji wasu na korafin tsakanin su da mazajen su kita mamaki, a k'arshe inason in ja hankalin ki game da abokiyar zaman ki, ki sani ku biyu keda shi Saboda haka kada ki zamo mai son kai, duk abunda baza ki so ya faru dake ba to itama kada ki so mata haka duk abunda kika so ma kan ki itama ki so mata, ki zauna da ita tsakani da Allah, nasan in Maganar auren ku ta bayyana rai zai iya 6aci kiyi hakuri da duk abunda zai biyo baya ba kamar daga gareta don tabbas an mata ba daidai ba, in Allah ya daidaita tsakanin ku ki ci gaba da daukarta tamkar Yayarki uwa d'aya uba d'aya kar kiyi mata kallon kishiya balle har zuciyar ki ta samu damar sak'a maki wani abu ba daidai ba game da ita, in abun farinciki ya faru da ita ki taya ta murna in na jajantawa ne ki taya ta jajantawa kada ki sake ki bari shaidan yay galaba a kanki game da ita in ma zaki kishi da ita to akan kyautata ma mijin ku ne, haka dangin shi ma ki d'auke su tamkar naki ki zauna da kowa lafiya sannan ki dage da yin ibada don neman dacewa, a K'arshe ina Addu'ar Allah ubangiji ya sanya Alkhairi a zaman ku gaba d'aya Amin,(Wannan Nasiha ce ba ga Fatuu kadai ba ga duk wata Amarya da ke karanta Novel d'in nan, duk abun da kika ji mai muhimmanci ki aiki da shi zai maki amfani in sha Allah). A tare suka fito parlon Hajiya da Saude na zaune suna kallo, tana ganin su ta fara k'ok'arin mik'ewa Saude ma haka, Hajiya tay ma Fatuu saida safe tace taje ta jira Mijinta yazo daga haka ta nufi k'opa, kallon juna sukai ita da gwaggo ganin idanunta sun ciko yasata girgiza mata kai alamar kada tay kukan had'i da yi mata d'an murmushi da k'yar itama ta d'an yi mata gwaggon ta nufi kopa har zata fita ta juya ta kalli Fatuu da tay tsaye tay mata alamar ta koma ciki a sanyaye ta d'aga hannu ta d'an yi mata bye bye ta jinjina mata kai daga haka ta fuce, bin parlon ta shiga yi da kallo har ta kai idanunta sama kan chandelier taga an canza wata da ta fi ta da k'awatuwa, d'an murmushi tay ta sauke idanunta ta juya har zata shiga corridor sai kuma ta juya ta nufi Dining Area tana tafiya kaman mai yin sand'a, tsaye tay tana bin wurin da kallo ya burgeta sosae can ta nufi wurin table d'in ta kai hannu ta fiddo Warmer guda ta bud'e farfesun yan ciki ne sai zuba uban k'amshi yake, fiddo d'ayar tayi wadda tafi girma itama ta bud'e taga Fried Spaghetti ce da tay brown tasha vegetables daga gefe manyan soyayyun tsokokin nama ne a jere, maida murfin tay ta rufe ta jera su kan table d'in kafin ta d'auki basket d'in ta wuce, Kitchen ta shiga don ta aje nan ma ba k'aramin burgeta yay ba fuskarta d'auke da d'an murmushi take k'are mashi kallo, daga baya ta juyo ta fito ta koma Bedroom. ***** ***** Bayan Abbas ya aje su inna Zaliha direct G.r.a ya wuce, Haisam zaune acikin Bedroom d'in shi saman 3 seater ya d'an kishingid'a ya cire rigar shaddar jikin shi daga shi sai farar singlet da wandon shaddar, Video call yake da Fanan ta cikin computer d'in dake ajiye saman c-table sai faman zabga mashi shagwa6a take kan ya koma tana missing d'in shi sosae shi kuma yana rarrashin ta kan ta kwantar da hankalin ta ya kusa komowa, daga ita sai wasu yan fingilallun half vest da wandon ta wanda da kad'an ya d'ara ma pant sai faman yin abubuwan jan hankali take yanata d'an murmushi don ya gane mata sam bata da Sauk'i ta wannan 6angaren don in dai yana a kusa da ita hana mashi sakat take, suna cikin haka Abbas ya turo kopar Bedroom d'in ya d'an juya ya kalli wurin kafin ya juyo kan screen Fanan d'in ta tambaye shi waye can k'asan makoshi ya furta Abbas aikuwa da sauri ta tashi ta sauka daga saman gadon da take kwance tayi ruf da ciki ta nufi closet, Zama Abbas yay gefen shi yana sakin murmushi ya tambayi da wa yake Video call ne slowly ya furta mashi Fanan, fad'ad'a murmushi Abbas yay yace "kace da uwar gida kake ganawa, to in ka gama ga Amaryar ka can mun kai maka tana jiran ka" wani kallo Haisam d'in yay mashi mai kaman harara, ba don Fanan d'in ta mik'e ba da tabbas sai taji abunda Abbas d'in yace, dariya sosae Abbas ke yi yana fad'in ya gama boye boyen shi dole asiri ya tonu, Haisam d'in bai tanka mashi ba saima ya maida idon shi kan Screen, lokacin Fanan d'in ta dawo ta zura doguwar riga kanta tasa hula sa6anin da babu hulan sai brown sumar ta da ta zuba gefe da gefen fuskarta duk da haka yanzun ma ta fito daga gefen wuyanta, tambayar ina Abbas d'in yake tay Haisam ya juya laptop d'in ta kalli Abbas dake dariya yace "gani nan uwar gida", itama yar dariya take tace "uwar gida and also Amarya" wata yar iskar dariya Abbas yasa har saida haisam yay mashi wani kallo suka had'a ido hakan ya k'ara bashi dariyar da k'yar ya tsagaita Fanan d'in tace mashi ko ta fad'i ba daidai bane da sauri yace "No, no daidai kika fad'a kawae yanayin yadda kikai Maganar ne naga kaman akwae son kai a ciki, da sai ki tsaya a uwargidan ita kuma Amaryar sai tazo" wani kallo ta watsa mashi ta had'e giran sama da ta k'asa tace ashe bai k'aunar ta har haka bata sani ba, da sauri ya d'aga hannu yana fad'in tuba yake, cikin d'an d'aure fuska tace to ya daina mata irin wannan mummunan fatan ita kad'ai ce ba k'ari wannan Alk'awari ne Until death do them part itama d'in tare zata d'auke su, jinjina kai Abbas ya hau yi yana k'ok'arin danne dariyar dake ciyo shi yace to ya bari Allah ya bada ikon ruk'e Alkawari tace Amin ai yasan waye mijinta tunda ya d'auka zai ruk'e da sauri Abbas yace gaskiya ne, "To amman wai ya akai kika k'yale shi yay zaune anan ne naga ma kaman bai da niyyar dawowa nan" d'an 6ata fuska tay "nima na k'osa ya dawo bana jin dad'in rashin shi a kusa dani duk na takura, amman yace man wani aiki ne ya ruk'e shi ya kusa dawowa" d'an ta6e baki Abbas yay ya jinjina kai yace "Tabbas hakane na manta, ko yau ma ya k'ara samun wani babban aikin mai cike da Alkhairi don haka sai kin d'an k'ara hakuri kin d'aga mashi k'afa" d'an rausayar da kai tay tace shikenan ya zata yi tana yi mashi fatan nasara, da sauri Abbas yace "Yauwa, haka ake son matar kwarae duk in mijinta yazo mata da wani Al'amari ta fahimce shi ta yiwu Alkhairi ne" murmushi tay kawai tace bari ta k'yale su suyi hira yace ok, juyo da Laptop d'in Haisam yay sukai sallama cike da nuna kauna kafin ya katse, maida idon shi yay kan Abbas dake dariya ya hau jinjina kai yace "Wato har na fara tausaya maka wllh, waya fad'a maka ana ma mata irin wannan Alk'awarin? Ai koda baka da ra'ayin k'ara Aure bai kamata kai mata Alk'awari ba don bamu ke da iko da kan mu ba komai na iya canza wa just like it happens now, yanzu in tazo ta san da zancen wane kallo kake tunanin zata maka in ma ta saurare ka kenan" bin shi da ido kawae Haisam d'in yay kaman ba zai ce komae ba, can yay sigh slowly ya furta "she was already my wife then" Abbas yace "amman ai ita bata sani ba ko" d'an d'age gira yay yace zai fahimtar da ita in buk'atan hakan ya ta so, d'age kafad'a Abbas yay yana murmushi yace Allah ya taimaka bai amsa mashi ba saima ya juyar da idon shi, "Yanzu ka tashi muje in kai ka an bar yar mutane ita kad'ai kuma kasan ba sabawa tay ba" ba tare daya kalle shi ba yace yaje kawai, still dariya Abbas ke yi can ya mik'e ya nufi hanyar fita sai lokacin ya juyo ya kalle shi, bayan wani lokaci Abbas d'in ya dawo abunka da wanda yasan gidan hannun shi ruk'e da mug d'an tiriri na fitowa alamar abunda ke ciki mai zafi ne, wurin kujerun ya nufa ya koma inda ya tashi ya zauna ya kai hannu ya kama igiyan tea bag d'in data lek'o waje yana dan tsoma ta ciki yadda zai yi Sosae, bayan wani lokaci ya mik'a ma Haisam dake kallon shi yana murmushi yace ga shi ya sha, wani kallo ya bi shi da shi kafin ya maida kallon kan cup d'in baida niyyar amsa, k'ara kallon Abbas yay ganin irin murmushin da yake yi yasa ya fahimci ko na minene tunda ko da bikin su da Fanan ya bashi irin su, d'an girgiza mashi kai yay slowly ya furta "No need" Abbas d'in yace "kai dai ka amsa don kuwa kana buk'atar shi ko an gaya maka ita ma hakanan za'a kawo maka ita ba tare da an gyara taba ba kamar yadda kai mata aika aika" kallon shi kawai Haisam d'in ke yi baida niyyar amsa, duk yadda Abbas yay dashi kan ya amsa ya sha ya k'i k'arshe dole ya k'yale shi yace yayi ma kansa shi bari yasha Allah yaso zai mashi amfani, bayan ya shanye ya mik'e yace bari ya maida mug d'in daga can zai wuce, mik'ewa Haisam yay ya taka mashi suna zuwa bakin k'opa Abbas yace yaje ya shirya ya tafi gun yar mutane tana can ita kadae, tsaye yay yana kallon shi ya fita yana murmushi har zai rufe kopar sai kuma ya dakata yace "saura ka k'ara bari ka zama uncontrollable kazo kana fad'a man k'auli da ba'adin u feel like ur life depends on it" sai lokacin Haisam ya saki murmushin da har hak'oran shi suka d'an bayyana Abbas d'in ma dariya yake yi yace makullin Motan na nan a wurin da ya zauna ya d'aga mashi kai daga haka sukai sallama ya tafi, Wurin kujerun ya koma ya zauna kan ta farko ya d'aura kafa d'aya akan d'aya ya zuba ma gaban shi ido da alama tunani yake yi, ya d'an d'auki lokaci a haka can ya mik'e ya fita daga wurin ya nufi hanyar corridor, saida ya d'auki kusan 30 minutes sannan ya fito da alama wanka ma yayi don ya canza kaya zuwa farar shadda Sol sai salk'i take da alama sabuwa ce bata ga ruwa ba, hannun shi d'aure da agogon diamond k'afafun shi na sanye da fararan half cover, kan shi ba hula sai nad'add'ar bak'ar sumar shi da gani an gyara ta don sai shining take yana janye da d'an madaidaicin trolley, saida yaje ya kauda laptop d'in dake saman c-table sannan ya dawo bakin dressing mirror ya d'auki Car Key ya kai hannu ya kama trolley d'in da ya aje, bayan ya latsa switch hasken d'akin ya d'auke ya bud'e kopar ya fita, Wani irin tsoro ne ya fara kama Fatuu ganin dare yayi sosae don sha d'aya ta kusa, duk ta takure kanta a saman gadon sai wuwwurga ido take ga wata irin yunwa da take ji, lokaci bayan lokaci take duba time a jikin wayar ta dake a gabanta har ta fara fidda ran zuwan Haisam d'in ta shiga tunanin yadda zata kwana ita kadae a part d'in, can bayan wani lokaci taji ana k'ok'arin bud'e kopar aikuwa a tsorace ta tashi zaune jikinta har ya fara yar rawa kanta ba kallabi ta zaro idanu tana kallon kopar, a hankali ya turo k'opar ya shigo da yar sallamar da ko Fatun bata ma ji ba, yana shigowa idanun shi suka sauka cikin nata da ta zaro ya dakata suka bi juna da kallo, ya lura da a tsorace take hakan yasa shi k'ara yin sallama a hankali sai lokacin taji ta amsa tare da sauke nata idanun saman gadon shiru ta biyo baya, jin bai k'ara cewa komai ba yasa ta d'ago ta kalle shi, still yana tsayen suka k'ara had'a idanu cikin yar rawar murya tace "Sannu da zuwa" kai ya d'aga mata kawai ya juya ya nufi wardrobe yana janye da trolley d'in ta bishi da kallo, aje trolley d'in yay ya kai hannu gefenta ya latsa sai gashi ta fara zugewa da kanta sai lokacin Fatuu ta gane yadda ake bud'e ta, bayan ta gama bud'ewa ya kai hannu ya zuge trolley d'in ya fara k'ok'arin fiddo kayan ciki tana ta kallon shi, bayan ya saka na farko ta kai hannu ta d'auki kallabinta ta yafa saman kai ta sauka daga saman gadon a d'arare ta nufe shi, lokacin data isa ya saka na biyu yana juyowa ya ganta a gefen shi ya bita da ido, saida ta had'iyi abu sannan cikin yar in ina tace "b....bari in saka.." bai ce mata komai ba sai kawai ya juya ya tafi tabi bayan shi da kallo, Laundry room ya nufa ya tura kopar ya shige, a sanyaye ta kai hannu taci gaba da fiddo kayan tana jerawa har da su underwear d'in shi, har ta gama bai fito ba ta zuge trolley d'in ta maida shi gefe wurin jakunkunan ta ta aje, komawa tay wurin gado tana niyyar zama ya bud'e kopar ya fito fuskar shi da alamun ruwa haka k'asan hannun rigar shi mai links, tsaye tay ta kasa zaman tana kallon shi tana yi tana maida idon k'asa, tsayawa yay daga d'ayan bangaren gadon yana kallon ta kaman zai yi magana, sai da ya d'an d'auki lokaci sannan taji yayi Maganar saidae bata ji mi ya ce ba ta bishi da kallon rashin fahimta, ya gane bata ji mi yace ba ya d'an maida idon shi k'asa sai kuma ya d'ago slowly da turanci yace ta samu tsarki, kai ta d'aga mashi alamar eh tare da maida idon ta k'asa taji yace taje tayo Alwala tace to, ba tare da ta kalle shi ba ta nufi hanyar Laundry room d'in sumi sumi, lokacin data fito har ya shimfid'a prayer mat guda biyu a saman lallausan carpet d'in dake a gaban gadon yana zaune a bakin gado, wurin jakunkunan ta nufa ta bud'e ta curo Hijab ta fara k'ok'arin saka wa ya mik'e ya daidaita kan abun sallar gaba ita kuma ta hau kan ta baya ya kabbara salla, Nafila raka'a biyu sukai sam Fatuu batayi mamakin jin yadda yake sakin kira'a ba don ba yau ta fara jin shi yana karatun Qur'ani ba yana yawan yi ta cikin wayar shi, gaba d'aya Allah ya bashi ilimin boko dana Addini abun saidae ace ma sha Allah, zama sukai suna lazimi tana ta kallon sumar bayan kan shi ba zato sai gani tay ya juyo har saida gabanta ya fad'i don sun yi gab da juna, had'a ido sukai ta d'an waro nata yay mata alamar ta matso da kan shi, matsawa tay dab da shi ya kai hannu ya dafa kanta ta d'an sunkuyar da kan tana kallon k'asa gaba d'aya k'amshin shi ya gama cikata, Addu'ar da Manzo (S.A.W) ya koyar mutum yayi in yay Amarya ya shiga yi bayan ya gama ya sauke hannun nashi ta d'ago suka k'ara had'a ido, bai yi tunanin tambayar ta wani abu ba don duk abunda yake son sani game da ita ya sani, juyawa yay ya d'aga hannu ya fara jero Addu'oi da sauti kad'an itama ta d'aga nata hannuwan bayan ya gama a tare suka shafa ya yunk'ura ya mik'e tana dai ta bin shi da ido, har yayi taku d'aya zuwa biyu ya dakata ya juyo ya furta akwai abu akan dining table daga haka ya juya ya nufi kopar ya fita, zugudum tay ta bi k'opar da ido tama rasa tunanin da zata yi, gaba d'aya ta kasa gane mashi duk ya canza mata sai kace ba Ya Haisam d'in da ta sani bane, in don abun da tayi ne ai taje ta bashi hak'uri kuma ya nuna ya hak'ura to miyasa taci gaba da ganin shi haka wanda ada da ta bashi hak'uri yake hak'ura kuma bata ganin canji a tattare dashi kamar yanzu, gaba d'aya jikinta ne ya k'ara yin sanyi, tunowa da Abincin da su Hajiya suka kawo yasa ta yunk'ura ta mik'e, cire Hijab d'in tayi ta linke ta mayar ta dawo ta kwashe abubuwan sallan suma ta linke ta je ta ajiye ta d'auki kallabin ta dake a saman gadon ta yafa saman kan nata ta nufi hanyar fita, d'an jimm tay a bakin k'opar tana zullumin fita can dai ta kama handle d'in ta ja kopar ta bud'e a d'arare ta fita, Tana zuwa bakin corridor d'in ta hango shi zaune akan L-shape ya d'an kishingid'a yana kallo, had'a ido sukai da sauri ta kawar da nata sum sum ta nufi hanyar dining d'in, tana zuwa taga manyan ledoji guda biyu ta fahimci sune yay mata magana akai ta kai hannu ta fara bubbud'a su taga miye a ciki, d'aya su ice cream da Youghort da kuma snacks d'ayar kuma fruit ne, shiru ta d'anyi tana tunanin yadda zata yi dasu can ta d'auki guda ta nufi freezer ta bud'e ta saka, dawowa tayi ta d'auki d'ayar ma taje ta kai ba tare data d'au komai ba don ta ci, bayan ta dawo tsaye tay gaban table d'in tana tunanin ko zai ci Abincin ma, wata zuciyar ta bata taje ta fara tambayar shi, kamar bazata je ba sai kuma ta tafi tana tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, bata zagaya cikin parlon ba sai ta bi ta bayan kujeru ta tsaya a d'an gefen bayan kujerar da yake zaune ta bi shi da ido ta kasa cewa komai, kamar yaji ajikin shi da mutum a wurin ya d'an juyo da kan shi suka had'a ido, d'an kikkafta idanu ta shiga yi da k'yar tace mashi dama Abinci ne aka kawo daga part d'in Hajiya, shiru ya d'anyi still idon shi na akan ta sai kuma ya d'an girgiza mata kai alamar bazai ci ba, maimakon ta tafi sai tay tsaye tana kallon shi ganin haka yasa shi cewa "Dare yayi" saida ta had'iyi abu kafin a sanyaye tace "ai Abincin ba mai nauyi bane" yanayin kallon da yake mata ne ya sauya da sauri ta maida nata idon k'asa tana haka taji ya mik'e ta d'ago tana kallon shi, saida taga ya zagayo sannan itama ta nufi Dining d'in ta d'ayan side d'in da ba ta nan ya bi ba............. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2062* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ......... Zama yay akan d'aya daga cikin chairs d'in sai lokacin ta tuno da bata d'aukko plates ba da d'an hanzari ta juya ta nufi hanyar corridor Slowly ya juya yana kallonta har ta shige sannan ya janye idon, bada Jimawa ba ta dawo hannuwanta ruk'e da plates da bowl sai serving spoon da kuma spoons da forks duk ta d'aurayo su don da alamun lemar ruwa a jikin su, bayan ta aje ta bud'e babbar warmer d'in ta fara zuba mashi tana sa kaman rabin plate taga ya d'an d'aga hannu alamar ya isa ta d'aukko k'atuwar tsokar nama ta d'aura tana niyyar k'ara wata nan ma ya k'ara dakatar da ita ta hanyar k'ara d'aga mata hannu ta tsaya, saka mashi fork tay ta tura gaban shi ta bud'e Warmer d'in farfesun ta zuba mashi kad'an ta tura mashi, Fridge ta nufa ta d'aukko bottle water da lemu ta dawo ta aje daga gaban shi ta sake juyawa ta koma ta d'aukko glass cups daga cikin fridge d'in ta dawo, tana niyyar bud'e robar lemu ya dakatar da ita a hankali ya furta ruwa kawae yake buk'ata ganin zata bud'e nan ma yace sai ya gama a hankali ta furta to, zuba nata abincin tayi bada yawa ba tasa fork ta d'auka tana niyyar juyawa ya d'ago ya kalleta suka had'a ido ta kasa tafiya, "zaki je ina ki ci Abinci?" taji cool voice d'in shi ya tambaya, shiru kaman bazata ce komai ba ganin ya kafe ta da ido yasa tace d'aki zata je, still yay yana kallon ta can taji yace "shi nan don me aka yi shi?" Shiru bata ce komae ba ta maida idon ta k'asa, "Sit!" cike da bada umarni taji ya fad'a, ba yadda ta iya dole ta aje Abincin ta zauna, duk da tana jin yunwa ta kasa cin Abincin sosae don duk sai taji ya fitar mata a rai sai d'an tsakura take tana yi tana satar kallon shi yanata cin nashi a nutse, bata wani ci da yawa ba ta mik'e ta d'auki Abincin yana kallonta tun kan yace wani abu tace mashi ta k'oshi zata kai kitchen ne ya d'an d'age mata gira "da kika ci mi?" yanayin Fuskar ta ne ya sauya idanuwan ta sukai rau rau kaman zatai kuka yace ta zauna ta cinye shi, komawa tay jiki a sanyaye taci gaba da ci ba don tana jin dad'in shi ba don ta rasa mike mata dad'i kamar ta fashe da kuka take ji, ya rigata gamawa amman sai yay zaune ya kafe ta da ido har saida itama ta cinye sannan ya mik'e ta bi shi da ido, Fridge ya nufa ya bud'e ya d'aukko babbar robar ice cream da wasu daga cikin Snacks ya dawo, aje mata yay gabanta da sauri ta kalle shi ba tare da ya kalle ta ba yace suma ta cinye aikuwa kaman jira take ta fashe mashi da kuka ta kife kanta a kan table d'in kallabin ta ya zamo ya baro saman kan ta, bin ta da ido yay yana kallon ta da alamun mamaki ita kan ta kawai ji tay kukan yazo mata, d'an kwankwasa saman glass table d'in yay ta d'ago fuskar ta jage jage da hawaye ta kalle shi, "na buge ki ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira ta girgiza mashi kai alamar a'a, "then miye abun kuka?" cikin muryar kuka tace "ni na k'oshi" bin ta da ido yay can yace "shine na kuka, ko akwai abunda ke damun ki ne?" Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, "Ok, kin ci wani abu ne before I came?" Kai ta sake girgiza mashi, "kuma shine har kin k'oshi?" tana d'an tura baki tace to ba ta ci Abinci ba yanzu, yanayin fuskar shi ne ya sauya kaman zai d'an yi murmushi "ai baki k'oshi ba so ki k'ara da wannan" kallon shi tay ba dama tay mashi musu don kuwa yasan yanayin yadda take cin Abinci, ganin ya kafeta da ido yasa da sigar shagwa6a ta d'an juya kai tana yamutsa fuska tace to ai sunyi mata yawa dare yayi sosae bazata ci Abinci da yawa ba tunda kwanciya zata yi, ganin yadda yake kallon ta tana Maganar yasa ta juyar da fuskar ta gefe can taji yay sigh ya furta Ok, komawa yay ya zauna duk abunda ya d'aukko ya raba biyu saidae d'aya yafi d'aya girma ya bata wanda suka fi girman shi kuma ya fara cin sauran itama ta fara ci tana yi tana d'an kallon shi har lokacin ba kallabi a kanta, kusan a tare suka gama ya bud'e mata robar ice cream d'in ya tura mata ganin yana niyyar mik'ewa da sauri tace to shi bai rage ba ai yayi mata yawa shi ma, wani kallo ya jefa mata sai taga kaman ya harareta ta d'an tura baki ta sauke idon ta k'asa, d'an guntun murmushin da iyakar shi lips d'in sa yay taji yace in ta rage tasa a fridge daga haka ya juya ta d'ago ta bi shi da ido, dakatawa yay ya juyo yace in ta gama yana buk'atar fruit bada yawa ba ta d'aga mashi kai ya juya ya tafi, sai gashi ta shanye ice cream d'in duka dama harda rashin sake mata fuska da ta ga baiyi ba yasa taji komae ya fitar mata a rai, bayan ta gama ta nufi Fridge ta fiddo ledar fruit d'in tunanin ko ta had'a mashi fruit salad tay tasan zai fi jin dad'in sha tayi ta juya tana ruk'e da ledar ta nufi hanyar corridor yana zaune a inda yake da kafin ya tashi ya d'an kai idon shi kanta kafin ya maida su kan tv, ba 6ata lokaci ta had'a mashi ba mai yawa ba sosae a cikin d'an bowl mai kyau ta bud'e fridge d'in cikin kitchen ta d'aukko k'ank'ara ta d'an kwankwatsa ta a ciki ba mai yawa ba don tasan bai son abu mai sanyi sosae, saka ledar fruit d'in tay a cikin fridge d'in nan ta d'auki bowl d'in ta nufi parlon, tunda ta fito ya maido idon shi kanta itama kallon nashi take tana isa ta d'aura saman c-table ta ja shi gaban shi ta d'ago suka had'a ido tace gashi nan da d'an murmushi ya jinjina kai tare da furta thanks, juyawa tay ta koma Dining Area ta fara kwashe kayan Abincin, wanda zata saka a fridge ta saka tay clearing wurin, saida ta wanke duk abunda suka 6ata a cikin kitchen ta maida su ma'adanar kowanne sannan ta fito ta nufi bedroom, tana shiga ta koma can bakin gado inda ta zauna d'azun ta zauna tay shiru kaman mai tunanin wani abu, gajiya tay da zaman ta kai kwance amman k'afafun ta na a k'asa, har bayan wani lokaci tana a hakan can taji an bud'e kopar da sauri ta tashi zaune suka had'a ido, rufe kopar yay ya nufo ciki ya tsaya gaban dressing mirror ya fara k'ok'arin cire Diamond Watch d'in wrist d'in shi, bayan ya cire a saman wurin ya aje ta ya juyo idanunshi suka sauka cikin nata da take ta faman bin shi dasu taga ya nufi hanyar Laundry room tana ta kallon shi har ya shige sannan ta juyo, komawa tay yadda take kafin ya shigo taci gaba da wurga ido tana tunane tunane, kusan Mintuna 15 ya d'auka sannan taji ya turo kopar ya fito tana kwancen ya zagayo wurin gadon, wani irin bugu k'irjinta yay mata don kuwa daga shi sai towel d'aure a k'ugun shi ya fito, tunda take bata ta6a ganin namiji haka ba balle shi da yake Tubarkallah, a rud'e ta juya ta yadda ta bashi baya yana jin mutsu mutsun ta bai ko kalle ta ba ya nufi gaban dressing mirror, duk mayuka da turarurrukan da yake amfani dasu suna a wurin saidae an k'ara wasu dasu kwalaben humra da turaren wuta, mai din shi ya d'an shafa sama sama bayan ya gama ya hau feshe jikin shi da turare Fatuu da tay lamo tana ta kikkifta idanu tana jin yadda yake fesa turarurruka ta d'an lumshe ido had'i da d'an yin murmushi, yana da son k'amshi sosae har da hakan ke k'ara mata k'aunar shi gashi koda yaushe zaka ji k'amshin shi na daban ne, bayan ya gama closet ya nufa ya bud'e bayan ta zuge ya fiddo sleeping dress riga da wando ya juya ya k'ara nufar laundry idon shi akan Fatuu da ta takure guri guda ya d'an ta6e baki da yanayin murmushi kan face d'in shi ya wuce, jin k'arar k'opa yasa ta d'ago da sauri ta kalli kopar Bedroom d'in sai dai bata ga alamar ita aka bud'e ba nan ta gane laundry ya shiga, bada jimawa ba taji motsin zai fito aikuwa da sauri ta maida kan yadda take da, fitowa yay ya saka kayan baccin ya nufi k'opar fita, har ya kama handle d'in sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon ta, ta ji lokacin da ya kama k'opar amman bata ji ya rufe ba hakan yasa ta d'an d'ago zata saci kallon shi karaf suka had'a ido nan take ta kama kanta ta k'arasa d'agowa ta tashi zaune sai waro ido take tana d'an motsa baki, "Zaki kwanta haka ne?" taji ya fad'a, shiru tay tana kallon shi ba tare da ta ce komai ba, d'age mata gira yay "am I not talking?" abu ta d'an had'iya a hankali tace "a'a", "U should go and take bath" kai ta d'aga mashi alamar to ta mik'e sumimi sumimi ta nufi wurin wardrobe, towel d'in da ta gani saman jakunkuna ta d'auki wani light blue ta juyo idanun ta suka sauka cikin nashi yana tsaye har lokacin da sauri ta sauke kanta k'asa ta wuce, tana kaiwa bakin k'opar zata shiga taji k'arar bud'e kopar shi ta juya lokacin ya fita, After some minutes ta fito tana d'aure da towel d'in a k'irji da yake yana da d'an girma ya saukko mata ta yafo kallabin lace d'in da ta cire, nufar wurin jakunkuna tay ta duk'a ta bud'e wadda ke d'auke da kayan bacci, wata doguwar riga cotton ta fiddo cikin kayan da Hajiya ta aiko jikinta gwanin taushi ta bud'e cikin Akwatunan ta ta d'aukko hula ta mik'e ta koma bakin gado, saida ta d'an shafa mai sannan ta shafe jikinta da wata humra mai Masifar k'amshi don kuwa nan da nan k'amshin ta ya karad'e d'akin ta d'aukko roll on ta goggoga a hammata, bayan ta gama yan shafe shafen da goge gogen ta dawo bakin gado ta saka rigar, komawa tay gaban dressing mirror d'in ta hau feshe jikin rigar da turare saida ta fesa kaman kala ukku sannan ta dawo bakin gadon ta d'auki towel d'in ta nufi laundry don ta baza shi ya bushe, bayan ta fito zama tay a bakin gado tay shiru gaba d'aya bata jin bacci gashi dare yayi sosae don tuni k'arfe 12 tayi ko don Saboda bak'unta ne oho, tana ta zaune can ta idasa hayewa gadon ta kwanta tay k'uri tana kallon bangon da k'opa take, bata dad'e da kwanciyar ba ya turo k'opar ya shigo suka had'a ido ya tunkaro gadon har saida gabanta ya fad'i, yana isa bakin gadon ya kai hannu ya d'aukko babban pillow guda ya d'ago idon shi a Kanta ya furta mata "Gud nyt" kai ta jinjina mashi kaman yar k'adangaruwa, har zai juya sai kuma ya kai hannu jikin lamb dake gefen gadon ya kunna sannan ya juya Fatuu dai nata kallon shi, saida ya kashe switch hasken d'akin ya d'auke sai na fitilar da ya kunna sannan ya bud'e kopar ya fita, zuru Fatuu tay a ranta ta fara tunanin kenan a parlor zai kwana Saboda ita, sam ran ta bai mata dad'i ba ba kuma don wani abu ba sai don kwanan da zai yi a parlon tasan ba lalle yaji dad'in kwanciyar ba duk da kujerar nada taushi sosae amman zai iya takura, tana ta zancen zuci can zuciyar ta ta raya mata wani abu tay d'an jimm tana tunanin tayi ko kuwa, tashi tay zaune ta saukko daga saman gadon ta nufi hanyar fita har ta kusa kaiwa kopa sai kuma ta dakata ta juyo ta koma wurin kayanta, golden gyalen da ta cire ta d'auko ta yafa sannan ta nufi kopar fita. Lokacin da ta fito cikin Corridor d'in tsayawa tay tana kallon cikin parlon ya kashe hasken cikin shi sai na wasu da ya bari na gidajen wurin su Tv sune suka d'an haska parlon, nufar cikin parlon tay sai kace mai yin sand'a ta hango shi kwance kan L-shape side d'in da ya fi zama, tunda ta bud'e k'opa ta fito ya hangota ya zuba mata ido yana ta kallon ta har ta k'araso, daga bakin kujerar taja ta tsaya tana kallon shi ta gane kallon ta yake shima, kasa isa wurin shi tay tayi tsaye sai d'an wasa take da yatsun hannunta tana d'an kikkafta ido had'i da motsa baki alamar tana son fad'in wani abu, yunk'urawa yay ya tashi zaune idon shi akanta yay mata alamar ta zo da hannu ta matsa a d'ayan side d'in ta tsaya ya k'ara mata alamar ta zauna a hankali ta d'an d'osana ta zauna, "Any problem?" Ya tambaya, cikin yar inda inda tace "D...dama cewa nay kaje ka kwanta ciki ni zan kwanta anan" da k'yar ta k'arasa Maganar Saboda kallon da yake jefa mata mai wuyar fassaruwa ba Arzik'i ta sunnar da kan ta bayan tayi Maganar, maida bayan shi yay jikin kujeran still idon shi na akanta kaman bazai ce komae, jin shirun yayi yawa yasata d'an d'agowa suka had'a ido, sigh yay "ba wani abu kije ki kwanta" yanayin fuskar ta ne ya sauya hakanan taji kaman idanunta na son tara k'walla da sauri ta maida fuskarta gefe tana kikkafta idanu don kar su tarun, "Fatuuh" ya kira sunanta ta d'an yamutsa fuska had'i da d'an cije lower lip d'inta ba tare da ta juya ba, hakanan bata son Fatuu da yake kiranta duk da sunan ta ne kuma yafi kowa iya fad'ar shi don a gayance yake furta shi amman duk da haka bata so sai take ganin kaman bai huce bane yasa yake kiran ta haka ko kuma matsayin da take dashi a wurin shi da yanzu ya ragu, k'ara kiran ta yay sai lokacin ta juya suka had'a ido fuskar shi a d'an sake yace "Don't worry am comfortable here kije ki kwanta it's already late" ba tare da ta ce mashi komai ba ta mik'e ta nufi hanyar corridor walking very slowly don duk jikinta ya mutu, idon shi na kanta still yana zaune bai kwanta ba har ta shige cikin Corridor d'in yana ji ta bud'e kopar Bedroom d'in ta shige, maida kanshi yay jikin kujera ya d'age shi yana facing sama had'i da lumshe ido ba zaka iya karantar yanayin shi ba a lokacin, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin ya maido kan k'asa ya koma ya kwanta. Tana shiga d'akin ta nufi bakin gado ta zauna ta zuba ma wuri guda ido, ta d'an d'auki lokaci a hakan can ta idasa hayewa saman gadon ta kwanta ba tare da ta cire gyalen ba, kwata kwata bacci ya k'aurace ma idanuwan ta sai juye juye take ba kuma wai don tana son wani abu ya kasance tsakanin su ba kawae dai ta rasa mike mata dad'i ne, sam ta kasa gane mashi har ta fara kokonton anya yana son Auren ba Hajiya ce ta matsa ba kuwa, haka tay ta tunane tunane zuciyar ta na sak'a mata abubuwa har dare ya tsala da k'yar bacci ya d'auketa shima kuma ba mai nauyi ba, Akan kunnanta aka fara kiraye kirayen farko na sallar Asuba ta bud'e ido saidae bata tashi ba tay zuru, ba'a dad'e da gama kiran sallar ba taji an turo kopar ta kai idanun ta wurin tana ganin shi ya shigo da sauri ta rufe ido, saida ya kalleta sannan ya wuce wurin closet ya bud'e, jallabiya ya fiddo yana ruk'e da ita ya nufi laudary room jin k'arar bud'e kopar yasa ta bud'e idon nata, bayan few minutes ya fito ta sake rufe idon nata, saida taji k'arar bud'e kopar Bedroom d'in sannan ta d'an bud'e idon taga ya saka jallabiyar ya fita da alamun Alwala yayi, bayan fitar shi bada jimawa ba itama ta tashi ta saukko ta nufi laundry room d'in, Alwala tayo bayan ta fito ta wuce wurin jakunkunan ta ta ciro wata doguwar riga tare da hijab d'in da sukai salla da Haisam ta dawo bakin gado don ta saka, bayan ta gama ta shimfid'a prayer mat ta kabbara raka'atanil fajr, tana zaune tana ta tasbih har lokacin sallar Asuba yayi ta mik'e don tayi, bayan ta gama tayi Addu'oi ta shafa, zaune tay a wurin kaman an dasa ta ta kasa tashi can sai ma ta kwanta a wurin cikin sa'a bacci ya d'auke ta. Bayan an gama salla saida gari ya d'an fara washewa ya dawo daga Masallaci, a bakin kopar parlon ya cire takalman shi ya nufi kujera ya zauna, had'e hannuwan shi yay ya d'aura ha6ar shi yana kallon wuri guda ya d'an d'auki lokaci a hakan can ya mik'e ya nufi hanyar corridor, Slowly ya tura kopar Bedroom d'in ya shiga idanuwan shi suka sauka akan ta kwance kan Carpet ta takure cikin Hijab d'in kaman mai jin sanyi, tsaye yay a bakin kopar yana ta kallon ta can ya idasa shiga ciki wurin Ac ya nufa ya rage mata ita sannan ya dawo inda take, kiran sunanta yay shiru bata motsa ba ya k'ara nan ma bata farka ba, d'an jimm yay sai kuma ya rankwafa ya kai hannu ya d'an bubbuga shoulder d'in ta nan ta fara motsi ya d'ago, a hankali ta bud'e idanun ta ta d'an d'ago suka had'a ido da sauri ta k'arasa d'agowa ta tashi zaune tana gyara hijab, kallon shi ta d'an yi k'asa k'asa tace mashi ina kwana ya d'aga mata kai, "taya zaki ji dad'in bacci anan, ki koma kan bed mana" taji cool voice d'in shi ya fad'a, bata ce komae ba ta mik'e ta d'auke abun sallar ta maida sannan ta nufi gadon idon shi akanta, ganin zata hau ba tare da ta cire k'atuwar hijab d'in ba yasa shi k'ara yi mata magana kan taya zata kwanta da ita zai iya shak'e ta nan ma ba tace komai ba tasa hannu ta cire, saida ta linke ta ta mayar wurin kayan ta sannan ta dawo still yana a inda yake ta hau saman gadon sannan ya juya ya fita, da k'yar ta koma baccin shima parlon ya koma ya kwanta, ba laifi ta d'an yi baccin don sai k'arfe tara saura ta farka ta tashi zaune tana yin yar mik'a da hamma, sosae ta ji dad'in baccin da tayi jin jikinta ba k'arfi yasa ta saukko daga kan gadon ta wuce laundry don ta shiga toilet tay wanka, d'aure da towel a k'irji kanta sanye da hular wanka ta yafo wani short a kafad'arta ta fito, gaban dressing mirror ta tsaya tana k'ara goge ruwan jikinta bayan ta gama ta aje short towel d'in ta fara shafa mai cike da fargabar kar ya shigo ya iske ta haka, bayan ta gama ta shafa su humra nan da nan k'amshin su ya karad'e Bedroom d'in, wurin jakunkunan kayan ta ta nufa bayan ta gama ta duk'a ta janyo babbar mai d'auke da kayan sawa ta bud'e nan ta fara tunanin kayan da zata saka tsakanin lace shadda da kuma atamfa ga kuma jallabiyu, ta d'an d'auki lokaci tana ruwan ido can dae ta fiddo wata hadaddar atamfa mai red flowers riga ce da straight skirt tana ganin kayan ta gane kb ne ya d'inka su don yasan kalan d'inkin da tafi so kuma dama ba'a amshi ko measurement d'in ta ba tunda yana dashi, maida jakar tay ta bud'e mai d'auke da undies ta fiddo wanda zata saka, bayan ta fiddo komae da take buk'ata ta maida jakunkunan ta dawo bakin gado, d'aura kayan tay ta fara k'ok'arin sakawa gabanta na d'an fad'uwa don kar a maimaita na Asibiti, har ta gama bai shigo ba ta koma gaban mirror tana kallon kanta abun saidae ace Tubarkallah, sosae kayan suka amshe ta shape d'inta ya fita kamar an zana ta gashi straight skirt d'in irin mai tsaga ta gaba ne rigar ma tayi mata k'yam k'yam daga wurin hips d'in ta ya bud'e sosae kaman zai fashe yadda ya kamata, d'an jujjuyawa tay tana k'are ma kanta kallo har saida ta d'an yi murmushi don ita kanta taga yadda kayan suka mata kyau, yar light make up tayi tasa red janbaki wow just Ma sha Allah, gashinta ta warware ta sharce shi har zata kulle wata zuciyar ta bata ta bar shi haka a sake tay d'an jimm tana tunanin yin hakan don bata yi mashi haka, can ta yanke barin nashi taga in zata yi kyau ta d'aukko k'aton kallabin atamfar ta lankwasa shi ta gaba ta kashe d'auri gaban sai yay kaman daurin Zarah buhari duk da bata sa komae ba ciki amman ya yi sosae da yake atamfar sabuwa ce, Jama'a ku zo kuga Fatuu ta fito sak Amarya ita kanta sai d'an sakin murmushi take wani irin kyau da bata ta6a ganin tayi ba taga yau tayi ga bak'in gashinta mai santsi yay mata rumfa a k'afadun ta abun dai sai wanda ya gani, turarurruka ta feffesa bayan ta gama ta nufi gefen gado ta kwashe towels d'in da tay amfani da hulan wanka ta wuce laundry don ta kai su, baza su tayi yadda zasu sha iska ta nufi hanyar fita, daidai tana fitowa Haisam ya turo kopar Bedroom d'in ya shigo idanun shi suka sauka cikin nata tay tsaye cak kaman an dasa ta da alamun yar razana take kallon shi shima yanayin kallon da yake Mata irin na baka tsammaci ganin mutum ba balle kuma a yadda take, sakin fuska yay yanayin d'an murmushi ya bayyana itama d'an murmushin tay da hannu yay mata alamar ta wuce ta tafi a nutse, saida ta wuce sannan shima ya wuto ya shiga laundry room d'in, a gefen gado ta zauna a ranta tana raya kar fa yace Saboda wata manufar tay kwalliyar wata zuciyar ta sake raya mata amman dama can ai yasan dai tana yin gayun ta ko, yin wannan tunanin yasa ta kauda wanccan tunanin sai kuma ta k'ara yin tunanin k'ilan wanka zai yi yakamata ta fita ta bashi wuri in ya fito ya shirya koma ta je ta had'a masu Breakfast, mik'ewa tay har zata nufi kopa sai kuma ta wuce wurin kayanta ta bud'e inda takalma suke ta curo wasu flat shoe da suka hau da kayan jikinta ta saka su sannan ta tunkari kopar fita don zuwa Kitchen. Bayan da ta shiga cikin Kitchen d'in duk iya dubawar da tayi bata ga wasu kayan abinci ba da zata yi amfani da su sai iya su cincin da dublan kawae, tsaye tay ta jingina da drawer tana k'are ma Kitchen d'in kallo a ranta tana k'ara yaba kyan shi ganin abun take har yanzu kaman al'mara wai nan Kitchen d'in ta ne, idanunta ne suka sauka akan drawer d'in da Aunty Mareeya ta nuna mata da ta zuba mata magungunan ta, a yadda ta fad'a mata yakamata da safen nan ta sha amman sai taji kaman bazata sha d'in ba tunda tasan dalilin shan magungunan, tana ta tsaye k'arshe ma sai tay d'an tsalle ta haye saman drawer d'in ta zauna sai yan kalle kalle da yan tunane tunane take, ta d'auki kusan minti talatin a haka ta jiyo k'amshin Haisam cikin hancin ta da sauri ta kalli kopar shigowa daidai lokacin ya sawo kai cikin wurin wato tun ma kafin ya shiga wuri Kamshin shi ke sanar da isowar shi, ya yi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya bak'in jeans da farar t-shirt daga gabanta an d'anyi style d'in bak'in rubutu, sosae kayan suka amshi jikin shi yay wani Fresh sumar nan sai kyalli take tasha gyara haka sajen shi ya kwanta luf, daga can bakin kopar ya tsaya tana ganin shi ta diro k'asa tana kallon shi, tambayar ta yay mi take yi a nan ba ga parlor ba, "Dama na shigo inyi breakfast ne amman na duba banga kayan Abinci ba" a sanyaye tay Maganar sai faman bin bakin ta da ya sha jan jambaki yake da kallo har ta gama, ganin yadda yake ta kallon ta kaman ba zai ce komae ba yasa ta d'an sunkuyar da kan ta, "Ba sai kin yi ba za'a kawo" taji ya fad'a, d'agowa tay ta d'aga mashi kai alamar to suka ci gaba da kallon juna tana yi tana d'an maida idanunta k'asa da d'an motsa baki, "ko kina buk'atar wani abu ne?" da sauri ta girgiza mashi kai ta nufi inda yake don ta fita ta gefen shi ta wuce, bin bayanta yay shima ya fito ganin zata shiga bedroom yasa shi ce mata taje ta zauna a parlor mana, juyowa tay ta kalle shi tace zata gyara d'akin ne ya d'aga mata kai ya wuce cikin parlon ta bi bayan shi da kallo yana tafiyar shi mai cike da k'asaita, d'an murmushi tay ta tura Kopar ta shige.............. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2063* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ...........Bayan shigarta tsayawa tayi daga gaban gado tana tunanin abunda zatai ma d'akin don fes yake, can dai ta fara gyaran gadon ta kakka6e abunda zata kakka6e bayan ta gama da gadon laundry ta nufa ta d'aukko floor wiper ta dawo ta fara gyara tsakar d'akin, bata d'au wani dogon lokaci ba ta gama ta maida ta ta dawo da d'an towel mai taushi ta goge furniture d'in, bayan duk ta gama ta kunna burner dake jone jikin socket ta zuba turaren wuta nan da nan daddad'an k'amshi ya fara karad'e d'akin, bayan d'akin ya turaru ta cire burner d'in ta nufi Parlor don shima ta turara shi, yana zaune a inda ya saba zama ya d'an kishingid'a Tv nata aiki wayar shi ruk'e a hannun shi yana lallatsawa, tana fitowa ya d'aga ido ya d'an kalle ta kafin ya maida su kan wayar, anan wurin kayan kallon ta jona ta tsaya tana jira ya gama turaruwa, tana cikin tsayuwar aka k'wank'wasa kopar parlon Haisam ya bada izinin a shigo, Saude ce ta shigo hannun ta ruk'e da d'an babban basket mai d'auke da kayan Breakfast ta tsaya daga bakin kujerun tana gaishe da shi ya amsa tare da d'an kallon ta ta nufi c-table zata d'aura yace ta kai dining area ta amsa da to ta wuce, Fatuu na tsaye tana kallon ta da murmushi tun da ta shigo itama murmushin take mata ta nufo in da take, tana zuwa Fatuu ta amshi basket d'in tana gaishe da ita ta fad'ad'a murmushin ta tana amsawa, godiya Fatun tayi mata k'asa k'asa da murya tace "Yayi kyau Amaryar mu, naji dad'in ganin ki haka sosae" yar kunya ce ta kama Fatun tana ta murmushi ta d'an sadda kan ta, tambayar ta tay mi take so a dafa masu da rana ta d'ago tace mata ko mi ta dafa tana ta murmushi tace in dai akwae abunda take so ta fad'i kar ta ji nauyi Fatun tace mata da gaske duk abunda ta dafa yayi tace to shikenan sukai sallama ta juya, kan Dining table ta kai basket d'in ta d'aura sama, juyowa tay ta nufi Kitchen plates da cups da sauran abun da zata buk'ata ta d'aukko saida ta d'auraye su tare da hannuwan ta da tay aikin sa turaren wuta sannan ta fito ta koma dining d'in, wata babbar Warmer a cikin kayan ta fiddo ta bud'e nan take wani irin k'amshi ya bugi hancin ta, Kaza ce guda d'aya babba ta gasu tasha kayan yaji da spices sun manne a jikinta daga k'asanta kuma a tsage yake tasa spoon ta juyata ta bud'e wurin nan take taga ashe Chicken and Chips ne ta ta6a gani Sauden tayi ba dai dad'i ba soyayyen dankalin turawa da dafaffen kwai ake cusawa a cikin Kazar bayan an tafasa ta sai a d'inketa a shafe ta da butter a bad'a kayan yaji da spices sai a gasa su tare a Oven, gani tay in ta yaga zata 6ata ta hakan yasa ta k'yale ta fiddo ledan sliced bread dake ciki ta aje kan table d'in sannan ta fiddo kayan tea da Flask mai d'auke da ruwan Lipton da ya sha kayan k'amshi sai wani bowl mai murfi ta bud'e shi nan kuma wainar k'wai ce murtuka murtuka, tunanin ta fara mashi magana kafin ta had'a tay hakan yasa ta nufi cikin parlon tana tafiya a hankali kai kace yanga take saidai kamata da kayan sukai ne yasa hakan, tana zuwa bakin kujeru kafin ta k'arasa taga ya mik'e ya tunkaro inda take yana zuwa saitin ta yay mata wani kallo ya wuce abun shi ta juya ta bi bayan shi, bayan ya zauna ta fara had'a mashi tea d'in tana yi tana tambayar yadda zata saka mashi komai har ta gama ta tura gaban shi ta fiddo kazar ta d'aura akan plate itama ta tura mashi ta curo waina d'aya daga cikin bowl d'in tasa a wani plate ta tura mashi sauran dake a cikin bowl d'in duka sannan ta d'aukko ledan biredi ta bud'e ta curo yanka biyar ta d'aura a gefen wainar k'wan da ta d'auka ta tura mashi ledan itama yana dai ta kallon ikon Allah, har ta gama had'a tea d'in ta ta zauna bai ta6a komae ba, hannu ya kai ya ciro slice na bread ya yagi wainar kwai ya had'e sannan ya d'auki cup d'in tea ya fara sha a nutse, kallon shi tay bayan wani lokaci ganin bai ta6a kazar ba yasa a hankali tace "gashi nan ka ci while it's still hot kar ta huce" shiru bai ce Komai ba bai kuma kalleta ba saida ya k'ara sipping tea kaman sau biyu sannan ya d'aga ido suka sauka cikin nata, da hannu tay mashi nuni da kazar ya kai idon shi kan ta kafin ya sake maido su a kanta "miye wannan d'in?" d'an waro ido tay jin wata tambaya kenan ma bai gane shi ta aje mawa ba, cikin yar inda inda tace "C... chicken and Chips ne" hannu ya kai ya d'an ruk'e ha6ar shi taji yace "mi za'ai dashi?" "Kai na aje mawa ka ci" tay Maganar tana d'an kikkafta idanu, "Na zama ke kenan?" ya tambaya had'i da d'an d'age mata gira ta d'an zaro ido sai kuma ta d'an tura baki "ai ba ina nufin ka cinye shi ba duka kawae naga in na 6ara ta zan 6ata ne shiyasa na bar maka in ka ci ka rage sai in ci, kuma ma ai nima ba iya cinye ta zan yi ba ko" yadda tay Maganar cike da shagwa6a saidae ita matsayin lafiya lou take Maganar ta, d'an guntun murmushi taga yayi gashi ya kafeta da ido ita kuma sai faman kikkafta nata take tana d'an juyar da fuskar, wani plate ya d'auka ya rufe kazar ya kai hannu ya d'auki cup d'in shayin ya cigaba da sha, bayan ya cinye waina d'aya ya tura mata bowl d'in ta d'an kalle shi, saida ya k'arasa shanye tea d'in ya bud'e kazar ya d'aukko fork ya fara k'ok'arin 6alla sai dai kuma tak'i 6alluwa ta dad'i, aje fork d'in yayi ya kai hannu wurin cutlery set d'in dake a tsakiyar table d'in ya curo yar wuk'a, d'an jim yay bai sata jikin Kazar ba ganin tana buk'atar a wanke ta tunda anan suke aje lokaci guda Fatuu ta fahimci dalilin dakatawar tashi ta mik'e ta mik'a hannu alamar ya bata ya d'aga ido ya kalleta kafin ya bata, bayan ya mik'a mata ta fita daga cikin kujerar ta nufi hanyar kitchen ya bi bayan ta da kallo har ta shige Corridor sannan ya juya da wani irin yanayi akan Face d'in shi, had'e hannuwan shi yay ya d'aura ha6ar shi a ranshi ya raya yakamata a sa washbasin a wurin Saboda zaryar da yaga tana yi, bada jimawa ba ta dawo ta wanko wuk'ar ta mik'a mashi amman sai bai amsa ba yay mata alamar ta zuba mashi, ganin kazar ta d'an mata nisa yasa ta zagaya daga gefen shi ta jawo plate d'in ta fara yankar mashi, gaba d'aya sun cika juna da fitinannan k'amshin jikin su Haisam har d'an lumshe ido yay slowly ya bud'e ba tare da ta gani ba, tana yanko wurin cinye ta d'aura mashi a plate zata k'ara ya d'aga mata hannu alamar ya isa ta kai idon ta kan shi suka had'a ido, d'an tura baki tay ta marairaice fuska a hankali ta furta mashi gaskiya bai isa ba yayi kad'an, ido ya bita dashi da alama ya kasa ce mata komai ta k'ara yanko wani ta d'aura, kallon shi tay ta d'an bud'a ido ta tambayi ta k'ara ya d'an wurga mata harara ta saki murmushi tace to bari a zuba mashi mahad'in kazar ta d'ebo dankalin ta zuba tana shirin sake d'ebowa ya kai hannu ya ja plate d'in ba tare da ya ce komae ba ta k'ara yin murmushi, tana shirin komawa wurinta taga ya kai hannu ya tura plate d'in kazar wurin da ta zauna, bayan ta koma ta zauna a nutse suka cigaba da yin Breakfast d'in tana yi tana d'an satar kallon shi, saida ya cinye wanda ta zuba mashin ya yago tissue ya goge bakin shi, mik'ewa yay zai bar wurin ya juya suka had'a ido taji yace ya bata space ta cinye komai ta d'an bud'a ido ya juya ya tafi tay d'an murmushi had'i da d'an girgiza kai, ba laifi ta d'an ci sosae bayan ta gama ta mik'e ta fara kwashe kayan tana kaiwa kitchen, saida ta wanke abubuwan da suka 6ata kazar da ta rage ta saka ta fridge wainar k'wan kuma da ledan biredin ta ajiye su saman counter, bayan ta gama fitowa tay ta wuce Bedroom saida ta d'aukko wayar ta daga cikin purse ta koma gefen gado ta zauna, bayan ta bud'eta tunanin wa zata kira ta shiga yi can ta kira Fauzy tana fara ringing ta d'aga, yar shewar farinciki tay tace "K'awata Amarya ai ban tsammaci ganin kiran ki ba don banyi tunanin zaki tuna da wata Fauzy ba da wuri haka" d'an murmushi mai sauti Fatun tay ta tambayi ya suke da Aunty Mareeya tace mata duk suna lafiya ta k'ara ce mata ya gajiya had'i da yi mata godiya, tana dariya tace ai ita ke tattare da gajiya su tasu tabi jiki tuni har saida Fatun ta d'an girgiza kai, tambayar ta Ya Haisam Ango tayi tace mata yana parlor, hiran School suka shiga yi ta tambayi yaushe zata dawo Fatun tace mata jibi in Allah ya kaimu, "ah haba dae jibi, ki bari sai kin gama cin Amarci kaman after a week sai ki dawo" tana murmushi tace mata so take ta samu matsala kenan Fauzyn tace to ta bari sai kaman Wednesday tazo amman ba jibi ba, tuna mata tay tace kar Amarci yasa ta manta da Assignment d'in da aka basu ran Friday dai, Fatun tace to zata yi jakarta ma na gida amman yanzu zata kira Kawu Amadu ya kawo mata, daga baya sukai sallama tana ce mata ta gaishe mata da Ango tana murmushi tace zai ji, Bayan sun gama wayar Kawu Amadu ta kira har saida ta kusa yankewa sannan ya d'aga ta gaishe dashi yana yar dariya yace "Amaryar mu kun tashi lafiya" amsa mashi tay da lafiya lou suma ta tambayi ya suka tashi yace mata lafiya, jin ta d'an yi shiru yasa shi tambayar ta lafiya dai ko cikin yar in ina tace mashi dama don Allah so take ta rok'e shi ya kawo mata jakarta ta makaranta, farko cewa yay shi ba zai kawo ba ta marairaice tana rok'on shi k'arshe sai cewa tay shikenan bari tazo ta d'auka da kanta yana dariya yace ai dama yana cikin shago ya sake ya ganta sai ya zane ta kuma da tsallan kwad'o zai maida ta, itama dariyar take a hankali tace mashi ai yanzu ta wuce wannan a wurin shi yace eh lalle ta isa shi take gaya ma haka ko to ta gwada fitowar zata sha mamaki, rok'on shi ta k'ara yi yace bari ya kawo mata tay mashi godiya ta tambayi gwaggo yace ta na cikin gida, bayan sun gama wayar d'an jimm tay tana son kiran gwaggo amman kunya take ji, can dai tay dialing lambar ta ta fara ringing, bayan ta d'aga a kunyace ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata sun tashi lafiya da tambayar d'anta Haisam Fatun tace mata yana parlor tace to ta gaishe mata da shi tace to, d'an shiru sukai can gwaggon ta ce badai wata matsala ko da sauri tace mata eh ba komai, tambayar ta tay wai ta fad'a ma baffanta zancen gwaggon tay yar dariya tace ta fad'a mashi mana yayi farinciki sosae ma, cikin yar shagwa6a tace amman shine bai kirata ba tace k'ilan ya bari sai an samu natsuwa ne, bayan sun gama ta shiga kiran Baffan nata cikin sa'a ta shiga ya d'aga ta gaishe da shi yana murmushi ya amsa ya tambayi ya take ita da maigidan nata, cike da shagwa6a tace "Baffa shine kasani amman baka kira ni ba gaba d'aya ma ka manta dani" yar dariya yayi "haba ni na isa in manta da inna wuro gaba d'aya, dama zan kira na bari a nutsu tukun, na matuk'ar yin farin ciki da jin abun Alkhairi wllh har bazan iya kwatanta maki ba ashe dai rabon shine mijin naki yasa komae ya faru, kinga sakamakon yi ma iyaye biyayya Allah ya juya komai, Nagode inna wuro ina matuk'ar Alfahari dake matsayin jinina, ina rok'on Allah ya k'ara ma rayuwar ku Albarka ya jikan Mahaifiyar ku" har k'walla sun taru a idanun ta ta amsa mashi da Amin, tambayar ya karatun ta yay tace mashi Alhamdulillah yace Allah ya bada sa'a, bayan ta amsa ta tambaye shi Yadikko yace tana d'aki bari ya mik'a mata tace to, bayan ya kai ma Yadikkon cike da Farinciki tana washe baki suka gaisa tana fad'in Amaryar su, tambayar ya gida da Angon ta tay Fatun ta amsa mata ta shiga yi mata Allah yasa Alkhairi da nuna yadda tay murna da Al'amarin tace Addu'ar da suke tayi ce Allah ya amsa taji mata dad'i sosae wllh da Al'amarin ya juye haka dama haka take ta fata, daga jin yadda take Maganar Fatuu ta fahimci ba k'aramin farinciki take ba, tambayar ta su Mino tay tace basu kaiga dawowa daga islamiyya ba tace to in sun dawo zata kira ta tambayi yaushe zasu zo tace suna nan zuwa in ta Haihu, a shagwa6e tace a'a ita dae bata yarda ba wllh tana dariya tace suna nan zuwa bada dad'ewa ba, bayan sun gama Magana da Yadikkon ta ba Baffan wayan suka cigaba nan yake tambayar ta Haisam yace bai da Lambar shi yana son yi mashi godiya tace ai yana nan ko a kai mashi yace to, mik'ewa tay da sauri ta nufi hanyar fita, Yana kishingid'e kan kujera ta tunkaro shi Wayar kare a kunnanta, tana zuwa daga gefe ta tsaya ta cire wayar daga kunnan ta a hankali tace mashi Baffan ta ne yake son Magana da shi ya d'an d'aga mata kai ta mik'a mashi wayar ya amsa, gyara zama yay a nutse ya gaisa da shi nan ya hau yi mashi godiya sosae da Addu'oi, k'asa k'asa yake amsa wasu wasu kuma yay shiru daga baya sukai sallama ya mik'a mata phone d'in idon shi cikin nata da d'an murmushi ta amsa ta maida ta kunnan ta, har ta juya kaman zata tafi sai kuma ta dakata tana tambayar Baffan yaushe zasu zo to jin yana mata sallama yace mata ba yanzu ba sai an d'an jima, aikuwa cike da shagwa6a ta hau Jujjuya jiki tana ita dae bata yarda ba don Allah su zo kwanan nan kai kace da gayya take juya jikin saidae ita bata ma san tana yi ba kuma da alama ma ta manta da a gaban Haisam d'in take, shi kuwa kafe bayan nata yay da ido da wani kalan expression mai wuyar fassaruwa yake kallon nata, bayan sun yi sallama ta juyo suka had'a ido ta sakar mashi d'an murmushi shima ya d'an yi mata, juyawa tay zata tafi taji yace in ta gama abunda take zasu gaishe da Hajiya ta juyo tace mashi to sannan ta tafi, tana komawa Bedroom d'in bada jimawa ba akai knocking kopar ya bada izinin shigowa, Amadu ne ya shigo ruk'e da jakar Fatun da d'an murmushi ya nufi cikin parlon ya tsaya daga gefe yana gaishe da Haisam d'in, bayan ya amsa ya nuna mashi armchair yace ya zauna mana, mik'ewa yay ya nufi hanyar Bedroom d'in da alama kiran ta zai yi, yana tura kopar daidai ta kawo bakin kopar zata bud'e ta yafo mayafi golden da ta sa jiya da yake a atamfar akwae golden brown harda takalman da ta saka jiyan mahad'in gyalen half cover masu tsini sun k'ara mata tsawo ta tattara gashin ta a baya ta sa red ribbom sai yayi kaman ta saka hular gashi don ya rufe gefe da gefen fuskar, tura kopar da yay ta buge mata goshi da sauri taja baya had'i da sa hannu guda ta dafe wurin da ta bugen, bai yi zaton tana a bakin kopar ba yay moving zuwa inda take tsaye ya kai hannu ya cire hannun ta da ta dafe goshin wurin har ya d'an canza kala, bin wurin yay da kallo ya kasa furta komae don gaba d'aya wata irin kasala yaji ta fara saukar mashi sakamakon K'amshin ta da ya cika mashi hanci, jin yayi shiru yasa ta d'aga ido ta kalle shi suka sauka cikin nashi nan take gabanta ya fad'i ganin irin kallon da yake mata da sauri ta sauke idon ta k'asa, d'ayan hannun nashi slowly ya zagaya dashi bayan ta ya matso da ita suka had'e da juna nan take wutar Fatuu ta d'auke ta fara shiga wani irin yanayi dama kuma a tsume take har saida ta d'an runtse ido, jikinta ne ya canza wata irin kasala ta baibaiye ta wani abu ya fara mata yawo a jiki ga k'afafuwan ta na neman kasa d'aukarta, sauke gudan hannun shi da ke ruk'e da natan yay k'asa ya d'an sunkuyar da face d'in shi Slowly ya d'an fara matsawa da ita saitin tata, jin saukar breathing d'in shi a gab da Fuskar ta yasata d'agowa da sauri har saida gabanta yay wani irin bugu ganin fuskar shi kusan saura kad'an ta had'e da tata, wani irin kallo mai wuyar fassarawa suka shiga bin juna da shi, da k'yar Fatuu ke daurewa gudun kada ta zaqe don ta kai wata ga6a da take neman rasa control idanun ta har sun fara lumshewa sai k'ok'arin daidaita su take amman abun yaci tura kawae sai ta rufe su gaba d'aya, bin dogayen eye lashes d'in ta yay da kallo sai d'an far far suke sakamakon idanun nata dake motsi, numfashin ta ne ya nemi tsayawa jin ya had'e faces d'in su nan take jikinta ya fara d'an rawa ta koma yin numfashi da sauri da sauri shima nashi da d'an k'arfi yake fita yana had'uwa da nata, sun d'an d'auki lokaci a haka suna ta shak'ar scent d'in juna, can ya janye fuskar ta shi a hankali ya maidata gefen tata ta yadda kwantaccen sajen shi ya had'e da gefen tata fuskar cikin wata irin murya mai fuzgar mai sauraro ya furta "am sorry, bansan kina a wurin ba...." Kasa ko d'aga mashi kai Fatuu tay idonta still na a rufe taji ya k'ara furta "Uncle d'in ki na jiran ki a parlor" yana yin Maganar ya d'ago ya cire hannun shi dake tallabe da ita ya juya ya nufi hanyar Laundry ba tare da ya ko kalleta ba, da k'yar ta d'an bud'e idanun ta da suka gama canza kala tabi bayan shi da kallo kar ya shige ya rufe kopar, kasa cigaba da tsayuwar tay don gaba d'aya jikinta ya gama mutuwa da k'yar ta ja jiki zuwa bakin gado ta zauna dabas still breathing heavily, hannu tasa ta dafe goshin ta ta d'an sadda kai, ita kad'ai tasan mi take ji a jikinta, da k'yar ta fara k'ok'arin daidaita kanta tunowa da yace Kawu Amadu na a parlor, mik'ewa tay jiki a mace ta nufi kopar ta bud'e, bayan ta fito saida ta k'ara tsayawa a cikin Corridor ta k'ara daidaita natsuwar ta sannan ta nufo cikin parlon, tana shiga suka had'a ido ta fara mashi murmushi wanda yafi kama dana yak'e shima d'an murmushin yake mata ta nufi inda yake, a d'ayar armchair d'in ta zauna ta gaishe da shi ya amsa shiru ta biyo baya don sai taji kaman muryar ta ba a daidai take ba, hannu ya kai ya d'aukko bag pack d'in daga k'asa ya d'auro ta kan hannun kujera yace mata ga ta nan da k'yar tace mashi ta gode, ganin ya mik'e alamar tafiya zai yi yasa cikin yar rawar murya tace don Allah ya tsaya yay breakfast yay mata wani kallo mai kaman harara ya juya ya tafi ta k'ara ce mashi ta gode ya d'aga mata kai kawae lokacin ya bud'e kopar ya fita, zaune tay turus tama rasa mi yake mata dad'i a hankali ta d'aga ido ta kallo kopar Bedroom d'in ta shiga tunanin zuwa zatai tay mashi magana su tafi ko kuwa, ji tay bazata iya zuwan ba tay zaune zuciyar ta na tariyo mata abunda ya faru a tsakanin su, tana haka bayan wani lokaci taji k'arar bud'e kopar Bedroom d'in aikuwa da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, nufo cikin parlon yay idon shi akanta ya tsaya daga gefen ta taji yace zasu iya tafiya sai lokacin ta d'ago ta kalle shi ta d'an d'aga mashi kai, mik'ewa tay har zai juya sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon ta ta d'an kawar da fuskar ta, "How are feeling, ko wurin na ciwo muje Hospital?" D'an kallon shi tay had'i da girgiza kai a hankali tace a'a yama daina zafin ya jinjina kai yay gaba ta bi bayan shi a ranta ta shiga raya kenan duk abunda yay mata d'azun ban hak'uri ne Saboda ya buge ta, yana gaba tana biye dashi suka shigo harabar gidan, suna cikin tafiyar ta kai idon ta can gefe wurin parking space ta hangi d'awisu ya bud'e jikin shi yana kuka gwanin burgewa, murmushi Fatuu ta saki tunowa da can baya lokacin da ta kawo ma shi Fruit na karin ciwo ta iske zashi Masallaci har suka fito tare ta tsaya a harabar tana ma d'awisun wasa shi kuma ya nufi hanyar Masallacin yana d'an d'angyasa k'afa Saboda raunin da yaji da kwalba, gab da zai shiga ta kware murya tace Ya Handsome kayi man Addu'a Allah yasa in zama likita ya d'aga mata kai ba tare da ya juyowa ba, fad'ad'a murmushi tay bata ta6a kawo wa a ranta wai zasu yi aure ba don ita auren ma bai gabanta a lokacin duk da kuruciya, ko ba aure a tsakanin su Haisam nada daraja a wurinta ta silar shi ne ta san kanta ko lokacin da ta kasa mashi uzuri da abu ya Faru tsakanin su harda girman da yake da shi yasa duk da tana tunanin laifi yayi mata amman bata son girman shi ya fad'i ne gashi hakan ba K'aramin karya mata zuciya yay ba don tana ganin ita tana k'aunar shi shi kuma sha'awar ta yake ashe duk ba haka bane, Kallon bayan shi taci gaba da yi wata irin k'aunar shi na ratsa mata zuciya har tana d'an yin murmushi a haka har suka k'araso part d'in suka shiga, lokacin da suka shiga basu samu kowa a cikin parlon ba an dai gyara shi fess sai k'amshi ke tashi, Hanyar Bedroom d'in ta ya nufa ta bi bayan shi, knocking kopar ya d'an yi daga ciki ta bada izinin a shiga ya tura da yar sallama ya shiga, tana zaune a bakin gado idanunta sanye cikin glasses hannunta ruk'e da Littafin Addini tana dubawa bata dad'e da komawa cikin d'akin ba bayan ta yi Breakfast, d'ago ido tay ta kalle shi tana niyyar yin Magana Fatuu ma ta shigo da sallama Hajiya ta saki murmushi tana amsa mata kafin tace "Maraba da Amaryar mu" d'an sadda kai tay Hajiyar ta nuna mata gefen ta da hannu alamar tazo ta zauna, tsaye Haisam yay daga gaban gadon bai zauna ba ya gaishe da ita ta amsa tay mashi an tashi lafiya, kai idon ta tay kan Fatuu da ta d'an sunnar da kai da murmushi tace "Amarya an tashi lafiya ya bak'unta kuma?" a hankali tace Lafiya lou, "Ba dai yar kunya muka fara dake ba" Hajiya ta tambaya tana murmushi hakan yasa Fatun d'agowa itama murmushin ne akan fuskar ta a hankali tace mata a'a, "Yauwa to, ni ba surukar ki bace Kakar kice a hakan zaki cigaba da kallo na muci gaba da wasa da dariya kaman da, don ma yanzu anyi hankali natsuwa tazo an rage sani nishad'i" yar dariya Fatuu tay ba tace komai ba, kallon Haisam tay "Kai kayi tsaye kaman wani Security ka samu wuri mana ka zauna, ko gadin Matar taka kake?" Fuskar shi a sake kaman zai murmushi ya kalleta ta nuna mashi Stool a gaban mirror tace ya d'aukko shi sai ya zauna, yin yadda tace yayi suka d'an yi shiru kafin ta fara magana, "Alhamdulillah, duk abunda Allah yayi mai kyau ne, a koda yaushe muna rok'on Alkhairi so duk abunda muka ga ya faru damu in ma mai kyau ko akasin hakan Alkhairi ne, Fateema ina maki barka da shigowa wannan Family don a yanzu kin zamo wani 6angare nashi, ina fata zaki d'auke mu a matsayin dangin ki, ki rungumi kowa matsayin dan'uwan ki duk da bani da shakku akan ki nasan ki farin sani nasan baki da matsala to sai kinyi hak'uri don shi mataki ne nasara ba kamar a yadda Auren naku ya kasance, dole daga baya za'a iya fuskantan yan matsaloli bama fata in sha Allahu muna fatan Allah zai shige mana gaba, sannan ina son ki saki jikin ki kada wai ko don kiga ga yadda akai auren naki ki takura kanki Ki k'i yin walwala, duk aure aure ne duk kuwa yadda aka yi shi ki walwala ki farinciki ki Alfahari da Auren, gidan mijin ki naki ne so ba buk'atar takura kai, duk yadda bani da haufi akan mijin ki ance wai zo mu zauna zo mu sa6a, so a duk lokacin da yay maki wani abu da baki ji dad'in shi ba ki k'ok'arin yi mashi Magana kada kice zaki bar abun a ranki duk d'an Adam ajizi ne zai iya yi maki laifi ba tare da ya ankare ba, ta hanyar yi mashi magana ne zai gane har ya gyara laifin shi, in kuma bai gyaran ba wanda bana tunanin hakan ni kizo ki sanar dani kar kiji wani abu, duk yay maki wani abun da kike tunanin fad'i ma wani don neman mafita ko shawara kizo wuri na kar kice zaki kai k'ara gidan ku hakan ba komai yake jazawa ba face matsala, zai iya maki abu kije ki fad'a daga baya ku shirya ki manta ma amman su kuma abun na nan a ran su watak'il su k'ullace shi ko makamancin hakan, don haka k'opa ta a bud'e take duk in kina da wata matsala kizo gun Hajiyar Sanata ki fad'a mata ni kuma in sha Allahu zanyi k'ok'arin ganin na daidaita komai, ina Fatan zaki cigaba da yi mashi biyayyar dana san kina mashi kada don ya zama mijin ki kice zaki rage kan hakan a'a a yanzu k'arawa ya kamata kiyi don muhimmancin shi a yanzu yafi na da ya tashi daga Yayan ki Handsome ya koma Mijin ki wanda Aljannar ki ke a tafin kafar shi" d'an dakatawa tay kan Fatuu a k'asa haka Haisam d'in Fuskar shi na a gefe, "Na dawo gare ka Zakee manyan dawa, ga Fateema nan Amana ce a wurin ka duk da nasan kasan da hakan amman ina fad'a maka ne don kada ya zama ba wanda ya fad'a maka hakan, ka ruk'e ta Amana dama can kai kamar guardian ne a gare ta to yanzu matsayin ka ya koma biyu don haka sai ka linka komae, kuma don ta zama taka ba yana nufin ta zama baiwar ka ba duk kyautatawar da zaka yi mata lada zaka samu haka in har kaci zarafin ta ka munana mata tabbas zaka samu zunubi don haka ta zama taka ne don ka kyautata rayuwar ta, sannan ina son jan hankalin ka kayi k'ok'arin zama adali ga matan ka nasan ba sai nayi maka bayanin yadda zaka zama adali ba kasan miye yin Adalci tsakanin mutane, idan har ka za6i yin rashin Adalci to ka bud'e ma kanka da kanka kopar matsalolin da zasu hana maka kwanciyar hankali ga kuma zunubi a wurin ubangiji, a k'arshe ina Addu'ar Allah yasa Albarka a Auren ku ya kauda duk wata fitina, yasa ya zame maku silar shiga Aljanna gaba d'ayan ku, Amin ya Rabbi" a hankali Haisam ya amsa da Amin Fatuu kuma a cikin rai ta amsa Hajiya ta kai hannu ta d'an bugi shoulder d'in ta tace ita bazata amsa ba ta d'ago tana yar dariya tace ai ta amsa, "Oh Fateema ni wannan in nayi sakaci ban yi da gaske ba yar gaisuwar da nike samu yana zuwa ma ai sai ki hana shi ya tattara ni ya zuba a dustbin" cikin rashin Fahimta Fatun ta d'an waro ido Hajiya taci gaba "eh mana, kina irin wannan kwalliyar ina zai rink'a tunawa da wata tsohuwar matar shi..." Tun kan ta rufe baki Fatun tasa tafukan hannuwan ta ta rufe fuska Hajiyar nata dariya, a hankali Haisam ya d'ago ya kalli Fatun suka had'a ido da Hajiya ta d'an harare shi cikin wasa yay d'an guntun murmushi ya juyar da fuskar shi gefe, "Yanzu dae ki bani cin hanci sai in yafe maki shi in kuma fad'a maki abubuwan da zasu sa ki kama shi a hannu" cire tafukan hannuwan tay tana murmushi bata ce komai ba, mik'ewa yay yace ma Hajiyar zai d'an je G.r.a tace a dawo lafiya ya nufi hanyar fita, kallon Fatuu Hajiya tay ta d'an kai mata bugu tace bazaki tashi ki raka shi ba yaran zamani duk baku san abunda ke sa ana kama miji ba, mik'ewa tay a kunyace ta nufi hanyar fita Hajiya ta bita da ido tana murmushi a ranta ta ayyana Allah kenan gwanin hikima, wasu mutanen na shigowa rayuwar mu ne in ma su amfane mu ko mu mu amfane su, wasu su tsaya wasu kuma su tafi bayan sun taka rawar da zasu taka, a fili ta furta "Allah kasa Mudace", tana fitowa har ya kusan fita daga parlon taja ta tsaya a bakin corridor, kamar yaji a jikin shi ya juyo suka had'a ido, dakatawa yay ganin haka yasa ta nufe shi walking slowly, a d'an gaban shi ta tsaya tana bin shi da kallo ganin ya kafeta da ido yasa cikin yar inda inda tace "D...dama Hajiya ce tace in rako ka" da k'yar ta kai Maganar Saboda kallon da yake bin ta dashi ba Arzik'i ta sunkuyar da kanta, "Ok thanks, ki koma" taji yace ta d'ago, kai ta d'an d'aga mashi yana shirin juyawa tace "Sai ka dawo Allah ya tsare" dakatawa ya sake yi ganin yanayin fuskar shi kaman zai murmushi yasa itama ta d'an yi mashi, "Do you need something?" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ya d'aga kai ya wuce, saida taga fitar shi sannan ta juyo tana d'an sakin Murmushi ta nufi komawa Bedroom d'in Hajiya.............. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2064* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ..........tana shiga tace mata ya tafi ta d'aga mata kai kafin tace eh a hankali , a inda ta tashi ta koma ta zauna Hajiya ta fara magana "irin nuna kulawa haka yana k'ara dank'on k'auna tsakanin ma'aurata, yanzu kinga kece abu na k'arshe da ya gani kafin ya fita to zaki ga kin tsaya mashi a ran shi yana tafiya yana tunanin ki har ma kiga yana d'an murmushi kaman ta6a66e, ba kamar yadda kika ci gayun nan" Dariya Fatuu ta saki ba kaman da tace kaman ta6a66e ta bata dariya sai Maganar ta tuno mata da Maganar Aunty Mareeya, itama hajiyar Dariyar take taci gaba "naji dad'i dana gan ki haka tsaf kin sha gayu wannan ma zai taimaka wurin siye zuciyar shi don shi mutum ne mai tsananin son tsafta nasan kin san da hakan, ga son k'amshi don haka ki dage da tsafta, amman fa kuma kar tay yawan da zaki janye man hankalin shi gaba d'aya" ta d'an ta6e baki, sosae Fatuu ta saka dariya, cigaba tay bayan ta d'an murmusa, "Komai nashi Sak kakan shi wllh, yana tuna man dashi a koda yaushe shiyasa bazan 6oye ba a duk jikokina nafi jin shi a raina kowa ma ya sani, hatta y'ay'an cikina ban jin su kaman yadda nake jin shi, Duk irin halayen shi na kakan shi ne, koda ake ganin Sojoji kaman basu da kirki basu da tausayi ba haka bane kowa da irin halin shi kaman dae a sauran mutane....." D'an dakatawa tay tana kallon hoton Gen. Adamu Zakee dake a jikin bango cikin shiga ta Alfarma, da gani akwae k'auna mai k'arfi a tsakanin su kuma rashin shi ba k'aramin ta6a mata zuciya yay ba, "Shima haka yake da son K'amshi, ko 6ata mashi rai kikai in dae zaki je bashi hak'uri ya kasance kina sakin k'amshi to Magana ta k'are tuni zai yafe maki, koda ma ba ke kika 6ata ran ba in dae zaki rarrashe shi kina k'amshi yanzu ya saukko" idonta akan hoton take Maganar, tausayin ta ne ya kama Fatuu itama ta kai idon ta kan hoton ta d'an girgiza kai, bayan d'an wani lokaci Hajiya ta sauke idon ta tare da ajiyar zuciya, kallon ta Fatuu tay da d'an murmushi tace "Allah ubangiji ya jik'an shi da rahama yasa ya huta, Allah ya h....had'a ku a Aljanna" tana murmushi ta amsa da Amin sai kuma tace "muci gaba da soyewa acan ko?" Dariya Fatuu tay suka d'an yi shiru, can ta kalle ta tace bari taje wurin Aunty Saude ta taya ta aiki, "to ke waya fad'a maki Amarya na wani aiki, ki zaman ki ki huta, ki k'yale ta tayi aikin ta lokacin yin aikin zai zo sai kita yi" shiru tay ta maida kanta k'asa, "in kina son zuwa kije k'yama k'ara koyon wasu abubuwan tunda Saude ba daga baya ba wurin iya girki tasan hannun ta, sai ki dage ki k'ara koya duk da ma Mijin naki ba gwanin cin Abinci bane, amman k'ilan ya rink'a cin na Matan shi" tana d'an murmushi ta mik'e zata tafi, har ta juya Hajiya ta dakatar da ita, "Yauwa na tuna, Maganar gyaran part d'in naku Tukur ne ke yi, to tun kafin ki tare yayi man magana kan zai cigaba ne ko a'a nace ya bari ki zo duk da dai shi Namiji ne ina ganin baida Matsala, amman ke ya kike so" d'an jimm Fatun tay ta rasa mi zata ce Hajiyan tace ta bud'e baki tay magana, a sanyaye tace duk yadda ta yanke yayi, "Shi d'in ne ya nuna yana so, tun farko ma ni ba shi naso yayi aikin ba bayan Haisam d'in ya dawo sawa nayi ya nemo wani amman ya matsa, kwanaki har zaunar dashi nayi nai mashi Magana kan hakan tunda ko ni bai bari akai kayana wurin wanki ga Karatu lokacin amman sai cewa yay wai baida abunda zai saka mana sai dai hakan kawai, nace to mu duk abunda ya ga an yi masa ai don Allah ne ba wai don ya saka mana ba, dama can Allah ya k'addaro akwae rabon shi a tare da mu" ta k'arasa tana murmushi itama Fatun shi take yi, "Yanzu tunda naga ya nuna yana so ke ki rink'a gyara Bedroom da Kitchen ala bashshi shi sai ya rink'a gyara maki parlon tunda dama yana da girma ko in kin tafi Makaranta sai ya shiga ya gyara, Wankin k'ananun kayan mijin naki kuma kyaci gaba in zai mashi na manyan kaya sai yazo nan yay amfani da injin d'in nan, koma kawae bari na mashi magana tunda ga naki sun k'aru ya bari a rink'a kaiwa dry cleaning kawai", kallon Fatun tay "lafiya lou zaki rink'a gyara Bedroom d'in da Kitchen d'in ba takura tunda naga karatu kike?" Da sauri tace mata eh, a ranta ta raya ita da ke yin fin wannan aikin a gida wannan ai ba wani aiki bane, ce mata tay taje tayi mata godiya ta juya ta fita, Kitchen ta nufa a ciki ta iske Saude na shirye shiryen d'aura girkin rana, da yar sallama ta shiga ta juyo tana murmushi ta amsa mata ta nufi gefenta gaban drawer ta jingina fuskar ta da murmushi tace "Sannu da aiki Aunty Saude", "Yauwa Amaryar mu kun shigo" kai ta d'aga mata suka d'an yi shiru, "Aunty Saude aiki na zo taya ki" d'an waro ido tay "aiki kuma Fateema keda kike Amarya, ki rufa man Asiri kar nayi laifi" tana murmushi tace "kai Aunty Saude daga taya aiki sai yin laifi ai na fad'i ma Hajiya zan zo in taya kin" tace "to amman ai ina iya yin laifi wurin Angon naki yaga duka daga kawo mashi Amaryar shi jiya yanzu na saka ta aiki" d'an tura mata baki tay tana murmushi "Kai Aunty Saude shi ina ruwan shi kuma ma ai ya fita bai gidan" "Ya kamata dai kije ki huta don kina buk'atar shi ansha hidima" still tura bakin ta k'ara tana kallon ta itama Sauden kallon ta tay tana yar dariya, Fatuu tace "ni dae na huta har na gaji ma" kafewa tay kan sai ta taya ta aikin girkin tace ai ta k'ara koya ma Sauden tace shikenan tunda ta kafe, "Mi kike so a dafa tunda ban kaiga d'aura komai ba sai ayi gaba d'aya kawai" d'an bud'a ido tay alamar mamaki tace "Aunty Saude ni zan fad'i mi za'a dafa" yar dariya tayi "Eh mana ki fad'i abunda kike so a dafa maku keda Angon naki" d'an jim tay ta maida idon ta k'asa alamar kunya, ganin ta tsaya tana kallon ta alamar amsa take jira yasa ta d'ago tana d'an far far da ido tace "Aunty Saude kiyi abunda kikai niyya kawai" tace "to ko shi ki fad'i abunda yake so sai ayi" d'an jimm ta k'ara yi sai kuma tace "to ai kin fi ni sanin abunda yake so ni dai kawai nasan bai son tuwo da miyan yauk'i" "Eh bai cin tuwon masara ko dawa da miyar yauk'i sai na shinkafa da yake yana son Abinci irin haka su sakwara har teba ma yana ci" Fatuu dake kallon ta tace "to ko ayi ebar?" Dariya tay "haba Fateema ya za'a had'a ango da teba kuma" itama Fatun dariyar tay bata ma san ya akai ta furta hakan ba, "ina ganin ko ayi sakwara don gaskiya yana son ta" Saude ta fad'a, da d'an sauri ta d'aga kai tace to ayi, amsar gyalenta tayi ta kai mata d'akinta bayan ta dawo suka fara aikin Pounded Yam d'in ba 6ata lokaci, Fatuu na tsaye tana yanka su alaiyyahu da Albasa harda ganyen ugu tace "Aunty Saude wai sai yaushe zaki tare?" tana juya miya tay yar dariya "ai na riga na tare Fateema" da alamun mamaki "kin tare, amman kuma yanzu ba d'akin ki na cikin nan kika kai man gyale na ba?" "Eh ai ban bar d'akin ba har yanzu matsayin nawa yake inna shigo ina aiki kinga ba sai nata zarya zuwa baya ba, kuma ma in ya tafi garin su wurin d'ayar matar shi a nan zan cigaba da kwana" kai Fatun ta d'aga alamar gamsuwa sai kuma tace "Amman Aunty Saude tarewa ba sanarwa balle ai mana d'an shagali" tana yar dariya ta k'arasa, itama dariyar tayi "Kai Fateema har kin bani dariya wane shagali kuma tsofe tsofe dani wannan ai sai ku, kema kawai nasan don ga yadda Al'amarin ya kasance ne da ba k'aramin shagali za'ai ba duk da haka kina iya ganin anyi daga baya" murmushi kawai Fatun tay tana fad'in ba wani tsufan da tayi wllh ai da ko yar Walima an yi masu, Sauden tace Hajiya ma taso tayi itace ta nuna bata so, cigaba da aikin sukai har Sauden na tambayar Fatuu turaren da ta shafa k'amshin yayi mata dad'i in ba tsada zata siya irin shi tace mata ai Humra ce duk da ta shafa turaren kad'an amman dai k'amshin na Humra ne, ta fad'i mata wadda ta siyo mata tace aikuwa tana so gaskiya zata bada a siyo mata Fatun tace ta bari zata d'ibo mata, nan fa suka hau yin yar jayayya Saude na fad'in a'a karta kwashe abunta ta bari a siyo mata kawai tace to ai kafin a siyo mata sai ta fara amfani da wadda zata batan tunda akwai da yawa, basu d'au wani lokaci mai tsawo ba suka gama had'a komai saura k'arashe, bayan an kwashe Fatuu tace bari ta nik'a cikin Food processor Sauden tace ta bari ta daka a turmi tafi dad'i Hajiya ma tafi son a daka, bayan ta fiddo turmin ta wanke ta fara d'akan sakwara Fatuu ta kafe kan sai itama ta daka farko Sauden ta k'i bata k'arshe da ta matsa ta bata tana faman fad'in tabi a Hankali don Allah kada tsautsayin Amarci ya gifta Fatun sai dariya take, kan kace mi daddad'an k'amshi ya karad'e Kitchen d'in har cikin Parlor, bayan an kammala hada miyan egusi da ta sha ganye ga ganda da kuma nama tayi wani irin kitif bata ko juya jikinta sai an juya ta, a tare suka nannad'a sakwarar a farar leda, bayan sun gama a wasu jigunannun luxury Warmers aka zuba tasu Fatun, "Ban taho da Warmers d'in jiya da kuma kayan breakfast d'in da aka kai yau ba da yake duk akwae sauran Abinci na saka a fridge, sai dai inna koma sai in kawo ko Almajirai in suna zuwa sai a basu kada ya lalace" Fatuu tayi Maganar tana kallon Saude, tace "ai Almajiran ma sun zo tun d'azu da safe na tattara masu wanda za'a basu, amman Abincin nada yawa ne?" d'an jimm Fatuu tay alamar tunani "Eh gaskiya da d'an yawa don na jiyan bamu ci sosae ba sai breakfast d'in yau shima bread d'in da saura sosae sai itama kazar wurin rabi ce don shi cinya kawae yaci ma sai chips d'in shima ba sosae ba" Jinjina kai Saude tay sai kuma tace "amman mi zai hana ki aika dasu gida kawae kinga itama gwaggo ta huta da yin girki tunda daga ita sai Amadu" d'an waro ido Fatuu tay "Aunty Saude in aika dasu gida kuma, in aka gani fa zai zama kaman fa nayi rashin gaskiya ne", yar dariya tay ganin yanayin fuskar fatun tace "to miye abun rashin gaskiya fita da Abinci gidan nan ai ba wani abu bane, kullum cikin fita ake dashi ba wanda zai maida kai ya ga kinyi wani rashin gaskiya" shiru tay kaman tana nazarin Maganar tata can ta kalleta "amman Aunty Saude ba ance ba kyau ka d'auki abinci bada izini ba ka bayar" Saude ta fahimci abunda take nufi wato bada izinin miji ba tace "Wannan ai ana nufin d'anyen Abinci Fateema, amman dafaffe ba laifi in ka bada gudun kada ya lalace ya zama anyi Almubazzaranci kuma kai laifi" d'an gyad'a kai tay alamar ta fahimta, saida suka had'a kunun Aya mai shegen dad'i kafin a tare suka kai wanda za a kai dining table, bayan sun gama Fatuu cikin d'an jin kunya tace mata bari taje tana son tayi wanka Saude na dariya tace ai haka yakamata, da kanta taje d'akinta ta d'aukko gyalenta bayan ta fito ta shiga Bedroom d'in Hajiya don yi mata sallama, bayan ta shiga ta iske ta kwance akan gado tana bacci hakan yasa ta juya zata tafi sai kuma taji muryarta ta kira sunanta ta juyo ta ga ta d'ago da kanta tana kallonta, nufar gadon tay tana niyyar duk'awa kan Carpet da hannu tay mata alamun ta zauna a bakin gadon, cikin Muryar wanda ya tashi daga bacci tace "Bacci ne ya d'auke ni halan Azahar ma tayi tuni?" tace "A'a an dai fara kiran sallar" ta fad'a tana d'an kallon gefe, jinjina kai tay suka d'an yi shiru sai kuma ta sake cewa"har an gama aikin girkin ne" kai ta d'aga "Eh mun gama zan koma can ne" kanta a k'asa tay Maganar, "Ok, sai ki tafin maku da naku ma" amsawa tay da to tana k'ok'arin mik'ewa Hajiya ta dakatar da ita da fad'in "kinga na manta jiya nace zan sa a kirawo balaraba tay maki kitso ko a bari sai yamma kawai" shiru Fatun tay kanta a sadde tana d'an wasa da yatsun hannunta, ganin bata ce komai ba yasa Hajiya tambayar ko bata son kitson ne ta d'ago ta d'an kalleta fuskar ta da d'an murmushi ta d'aga mata kai alamar eh, yar harara Hajiya ta wurga mata "ashe har yanzu halin ki na rashin son kitso na nan Fateema?" Shiru bata ce komai ba Hajiya tace "yanzu in baki yin kitson zaki takura ne, in gayun Amarci kike son kiyi na k'yale ki aita gayu lafiya, amman dole ki rink'a yin kitso, amsa mata tayi da to a kunya ce tace mata taje ta mik'e tay mata sallama. Bayan ta fito Kitchen ta nufa don ta d'aukko Basket d'in Abincin su ta taras da Saude na gyara Kitchen d'in, bayan ta d'aukka tay mata sallama ta fito, tana isa part d'in nasu bayan ta shiga parlon ta nufi Dining Area, a saman table ta d'aura Basket d'in ta shiga fiddo da warmers d'in tana jerawa, bayan ta gama d'aukar Basket d'in tay ta wuce Kitchen don ta aje, tsaye tay a gaban drawer bayan ta aje ta shiga tunanin Maganar Aunty Saude tana wasi wasin ta aikata yadda tace ko a'a, can ta yanke yin yadda tace d'in ta bud'e fridge ta fiddo sauran Kazar da Abincin jiya ta fara k'ok'arin dumama su a cikin Oven, bayan ta gama ta d'aukko kwalin Warmers masu kyau ta bud'e, mai d'an girma a ciki ta d'auka bayan ta wanke ta juye Abincin, sake d'aukko wata tayi itama bayan ta wanke ta juye Kazar, shiru ta d'an yi tana tunanin yakamata ta samu leda ta saka su ba ta aika dasu haka ba can ta tuno da ledar kayan baccin da Aunty Mareeya ta bata tana da girma Warmers d'in zasu shiga ciki, da sauri ta juya ta fita ta nufi Bedroom, bada jimawa ba ta dawo ruk'e da ledar ta fara saka Warmers d'in ciki hannun ta har d'an rawa yake, gaba d'aya sun shiga harda sauran wuri ma nan ta tuno dasu Snacks da ice cream d'in dake a Fridge d'in parlor ta juya da sauri ta fita daga cikin Kitchen d'in, d'ebo su tay ta saka harda robobin yoghurt da ice cream guda guda, bayan ta had'a komai tay tunanin kiran kawu Amadu don ya turo mata yaro da sauri ta juya ta fito ta shiga Bedroom, Wayar ta ta d'aukka ta kira shi yana d'agawa tunkan tayi magana yace mata miye kuma, yar dariya tay tace ba komai don Allah yaro take son in akwae wanda yazo siyayya ya turo mata shi yace to, aje wayar tayi ta juya ta fita tay tsaye bakin corridor tana dakon isowar wanda za'a turon, bada Jimawa ba akai knocking da sauri ta nufi kopar ta bud'e, wani yaro ne d'an unguwar ya turo tana ganin shi tace mashi tana zuwa ta juyo, ledar ta d'aukko harda dublan ta d'ebo mashi bayan ta kawo tace gwaggo zai kai mawa ta bashi ta dublan d'in tace gashinan ya ci yana washe baki yay mata godiya da Allah yasa Alkhairi ta amsa, juyawa tay da sauri ta koma Bedroom ta nufi gaban mirror bayan ta cire su sark'a da yankunnan ta ta cire kayan jikinta ta d'aura towel ta nufi laundry room, after some minutes ta fito jikinta sanye da bathrobe da ta gan su cikin cabinet d'in laudary ta d'auka, bayan ta fito doguwar riga tasa da hijab ta shimfid'a abun salla ta kabbara sallar Azahar da har angama ta a Masallacin gidan, bayan ta gama ta cire kayan ta linke da abun sallan ta maida kowanne wurin shi ta d'auki towel ta d'aura sannan ta nufi gaban mirror ta fara shafa, tana cikin yi wayarta ta fara ringing ta nufi gefen gado ta d'auka har saida gabanta ya fad'i ganin gwaggo ce mai kiran, bayan tayi picking ta gaidata nan tace mata mi ta aikata haka da sauri ta tari numfashin ta ba kamar yadda taji tayi Maganar cikin yar rawar murya ta fad'i mata duk yadda sukai da Saude, yar ajiyar zuciya ta sauke tace mata duk da haka yayi wuri da yawa ta fara hakan tace to zata kiyaye daga baya sukai sallama, bayan ta gama shafe shafen da goge gogen ta nufi wurin jakunkunan kayanta ta duk'a, tunanin kayan da yakamata tasa ta shiga yi, tana son saka k'ananun kaya don ko a gida tafi saka su ba kamar in ba inda zata je saidae tana gudun yay wani tunanin na daban, d'aya daga cikin Akwatunan kayan ta na gida ta bud'e ta fara ruwan ido can dae ta fiddo wata fitted gown d'in lace yellow da touches d'in dark ash bayan ta rufe akwatin ta bud'e na Undies ta d'auki wanda zatai amfani dasu, bakin gado ta nufa ta fara k'ok'arin sakawa bayan ta gama ta koma gaban mirror tana k'ara gyara kwalliyar da tayi yar light, sosae rigar ta amshe ta dama ita duk kayanta suna amsar jikinta Saboda irin d'inkin da ake yi mata dake fiddo dirin ta sosae, irin d'aurin kallabin d'azun tayi ta k'ara zubo da gashin gaba can kuma sai ta raba gashin na 6arin hagu ta maida shi baya na 6arin dama ta barshi a gaba, sosae hakan da tayi ya k'ara mata kyau sai kace wadda zata gasar kyau, bayan ta feshe jikinta da turare ta gyara komai ta maida bathrobe d'in, a gefen gado ta zauna ta fara tunanin ko akwae abunda yakamata tayi can ta mik'e ta nufi dressing mirror ta d'aukki robar Air Freshener ta shiga feshe Bedroom d'in Bayan ta gama ta juya ta nufi kopar fita, parlor tazo nan ma ta shiga feshe ko ina tana haka taji an turo kopar parlon ta kai idanun ta da sauri, Haisam ne ya shigo shima da alama wanka yayi don ya canza kaya zuwa farin jeans sai yellow polo shirt daga jikin tsayayyar collar d'in akwae ratsin fari haka a k'asan hannuwan ma sannan daga gaba 6angaren dama akwae farin tambarin polo d'in, yadda yasa Yellow d'in riga abun kaman had'in baki da itama tasa kaya Yellow, Cikin parlon ya shigo ya nufi inda ya saba zama ya zauna, slowly ta nufi inda yake hannunta ruk'e da robar freshener d'in, daga d'an gefe ta tsaya tayi mashi sannu da zuwa ya jinjina mata kai tay tsaye suka bi juna da ido tana d'an motsa baki, "Ya gida?" taji ya tambaya har saida taji mamakin tambayar ganin ya kafe ta da ido fuska a sake yasa ta yin d'an murmushi tace mashi lafiya lau ya d'aga kai, "Sit" ganin tana ta tsayuwa yasa shi ce mata haka, zama tay a bangaren inda take shiru ta biyo baya da d'an murmushi take kallon shi tana yi tana maida idanun k'asa, "Kin yi kyau" kaman daga sama taji Maganar ta kalle shi had'i da d'an waro ido mamaki kwance akan fuskar tata, ya fahimci hakan sai kawai yay d'an guntun murmushin gefe idon shi a Kanta ya maida bayan shi ya jingina da jikin kujerar, Maganar sai ta tuno mashi da Fanan ita ta koya mashi cewa hakan duk in tayi kwalliya bai yaba ba sai tay ta k'orafi daga nan ya fahimci mata basu son suyi kwalliya a k'i yabawa, da k'yar ta furta mashi ta gode bai ce mata komae ba sai ma ya maida idanun shi kan wayar shi dake a hannun shi ya fara latsa ta, "k..Kai ma kayi kyau" da k'yar ta tattaro kalmomin muryar ta na d'an rawa ta furta mashi, shiru kaman ba zai ce komai ba can taga yay mata kallon k'asan ido fuskar shi a sake ya furta thanks kafin ya maida idon kan Screen, bin shi da ido tay ta ayyana sam baka ta6a gane mashi, tana cikin kallon shi ya d'ago suka had'a ido, d'age mata gira yay ya tambayi da wani abu da sauri ta girgiza mashi kai sai kuma tace ga Abinci can kan table ya jinjina kai, saida ya d'an k'ara lallatsa wayar kafin ya aje ta a gefe ya mik'e ganin haka yasa itama ta mik'e ta bi bayan shi, Kitchen ta wuce anan ta aje Freshener d'in ta wanke hannuwan ta sannan ta d'auki duk abunda zata buk'ata na cin Abinci ta fita, bayan ta iso dining d'in ta fara zuba mashi tana sa sakwara guda d'aya ya d'aga mata hannu alamar ta isa kawai sai gani yay ta k'ara d'aukko guda ya d'ago ya kalleta ta d'an tura baki ta fara k'unk'uni a shagwa6e tace "ya za'ai abu d'aya ya ishe ka" wani kalan kallo ya ke bin ta da shi ya d'an d'age gira, "Ba zai isheka ka k'oshi ba sai dae ko biyu" tana gama Maganar ta k'ara mashi d'ayar tana yi tana kallon shi, yanayin fuskar shi ne ya sauya taga kaman ya d'aureta ta fara d'an kikkafta idanu a marairaice tace "har yanzu fa in baka cin Abinci sosae Ulcer zai iya kama ka" still yay yana bin ta da ido without saying anything, jikinta ne yay sanyi ta kai hannu da niyyar ta cire wadda ta k'aran taji yace "in ya kama ni I have got married now" da sauri ta kalle shi taga ya d'an d'age mata gira kuma ya saki fuskar lokaci guda ta saki murmushi jin bai manta da Maganar data ta6a yi mashi ba, bayan ta gama serving nashi itama ta zuba ta fara ci tana yi tana satar kallon shi yana cin nashi a nutse, sunyi nisa da farawa ta dakata idon ta a kan shi tana d'an murmushi slowly ya d'aga ido ya kalleta don yaji kallon shi take, "ya yi dad'i Abincin?" ta tambaya, bai bata amsa ba ya maida idon shi kan Abincin, saida ya k'ara ci sannan taji yace miye na tambaya tunda ba ita tayi ba, a hak'ik'an ce tace ai tare fa suka yi kuma ko ita kad'ai zata iya yin shi, d'an guntun murmushi kawae yay yaci gaba da ci, sai ga shi ya take duka sakwarar cikin wasa ta tambayi ta k'ara mashi ya d'an wurga mata harara, bayan ya sha kunun ayar ya yago tissue ya goge mouth d'in sa sannan ya mik'e zai bar wurin idon Fatuu a kan shi, dakatawa yay ya kalleta suka had'a ido Slowly taji ya furta "the empty plate is ur answer for d question u asked" daga haka ya juya yana tafiyar shi ya nufi cikin parlon tabi bayan shi da kallo tana Murmushi shi komai nashi na daban ne, saida taci ta k'oshi don ita kanta Abincin yayi mata dad'i sosae, bayan ta gama ta fara kwashe kayan da sukai amfani ta kai Kitchen, saida ta gyara Dining table d'in sannan ta koma Kitchen ta wanke komae da suka 6ata ta maida shi a wurin shi, bayan ta gama har zata fita idanunta suka sauka akan bokitan su cin cin a ranta ta raya tunda aka yi su bata ci ba wata zuciyar ta ayyana shi k'ilan ma baya cin su, tunanin ta d'iba ta kai mashi taga in yana ci tay ta d'aukko plate mai kyau ta bud'e ta d'ebo kowanne bada yawa ba harda alkaki, bayan ta zuba ta nufi hanyar fita yana kishingid'e kan kujera idon shi akan Tv yana kallon American film ta nufo shi tana tafiya a nutse sai kace mai yin yanga, tunda ta tunkaro cikin parlon ya maida idanun shi kanta har ta k'araso ta d'aura plate d'in kan c-table ta k'ara matsar dashi kusa dashi ta d'ago tana murmushi suka had'a ido tace mashi gashi nan ya ci, maida idon yay kan abunda take maganan kafin ya d'ago ya kalleta tana tsaye still Murmushin take tana d'an wasa da yatsun hannunta da ta had'e, ji tay yace a ina zai saka wannan d'in da sigar shagwa6a tace ai su ba Abinci bane, "Who told u ba Abinci bane, yanzu kaci wannan kasha ruwa bazaka k'oshi ba?" Ya tambaya had'i da d'age gira, d'an tura baki tay "Ya za'ai su kosar da Mutum, saidae in da yawa aka ci kuma ai kai kad'an ne na kawo maka ko" tana Maganar ya kafe bakinta da kallo, sigh yay ya d'an shaking kan shi "bansan ina zan sa shi ba as am stuffed, I couldn't eat another bite" bin juna sukai da kallo na d'an wani lokaci can ta kai hannu a sanyaye ta d'auki plate tana shirin juyawa taji yace zai ci wani lokacin ta juyo suka had'a ido ya d'an bud'a mata ido alamar taji abunda yace ta d'aga mashi kai daga haka ta wuce ya bita da kallo, bayan ta maida su ta fito ta wuce Bedroom, bada jimawa ba ta fito hannunta ruk'e da laptop d'inta da babban hardcover ta nufo cikin parlon ya maido idon shi kanta, a gefen shi ta tsaya a d'an marairaice tace "please, could you help me with this Assignment, ta email malamin yace mu tura mashi gashi harda drawing nayi k'ok'arin in d'aukko in saka na kasa" shiru yay just staring at her har saida tasha jinin jikinta ta d'an juyar da fuskar ta, tana haka taji cool voice d'in shi yace ta kawo ya gani ta matsa, akan c-table ta d'aura ta shiga nuna mashi yadda Assignment d'in yake bayan ta gama ta d'ago ya kai hannu ya fara latsa Computer din, can bayan d'an wani lokaci ya d'ago suka had'a ido yace mata sai ya d'aukko abu a G.r.a za'a iya tura mashi zuwa dare zai nuna mata, murmushi ta shiga yi tayi mashi godiya bai ce mata komai ba ya koma ya jingina bayan shi jikin kujerar, hannu ta kai zata d'auki laptop d'in slowly taji yace an hana ta zama a parlor ne, kallon shi ta d'an yi still da murmushi ta fasa d'aukar laptop da littafin ta koma d'ayan side d'in kujeran ta zauna, remote ya d'auka ya canza daga channel d'in da yake kallo zuwa Arewa 24 lokacin suna cikin yin maimaicin shirin dad'in kowa da yake k'arfe ukku yayi, d'an juyawa tay ta kalle shi ta d'an yamutsa baki nan take ya gane mi hakan ke nufi ya k'ara canza channel zuwa tauraruwa ganin suna yin wak'ok'i yasa ta d'an yi murmushi, voice d'in shi taji yana tambayar yayi mata ta juya ta d'aga mashi kai ya aje remote d'in dama ta dalilin ta ya san channels d'in hausa, tana kallon wakokin tana d'an bi wani lokacin har d'an juya kai take akwae wata da ya lura tana mata dad'i don sosae take bin wak'ar tana juya kai, still yay yana ta kallon ta kai kace ita ta raira wak'ar saidae kuma kunnan shi na akan wak'ar yana sauraro can kaman taji kallon ta yake ta juya suka had'a ido yar dariya tayi mashi shi kuma ya d'an yi mata guntun murmushi, ana yin wakokin kaman guda biyar suka datse suka sako tallar magunguna, juyowa tay tace mashi ya maida channel d'in da yake kallo sun gama fuskar shi a sake kaman zai murmushi ya kalle ta, tambayar ta yay ba wani da ake irin shi, ta gane wakokin yake nufi tace mashi ko an canza ba lalle ana yi ba dama nan an fi sa su, shiru yay can ya kai hannu ya d'auki remote d'in ya canza channel d'in da yake kallo farko suka cigaba da kallon American film d'in tare, gaba d'aya Fatuu ta takura don sai yin abubuwan sa kunya suke, suna cikin kallon aka nuno jarumin Film d'in da budurwar shi suna romancing juna ji Fatuu tay kaman ta nutse a wurin don abun bana Arziki bane, can abun ya kai ga an sa6ule rigar budurwar har boobs d'inta sun bayyana Fatuu na ganin hakan ta mik'e zumbur ta nufi hanyar corridor without even looking at him ya bi bayanta da kallo shi sai ma ta so bashi dariya yadda tayi, tana shiga Bedroom d'in ta nufi gado ta zauna a baki ta d'an waro ido tay shiru kaman mai tunanin wani abu, a hankali ta kwanta ta takure a guri guda tana cigaba da tunanin da take yi, bata dad'e da kwanciyar ba aka kira sallar la'asar, har tayo Alwala ta zo ta kabbara sallar bai shigo ba, bayan ta gama zaune tay kan abun sallar ta jingina da gado tana haka taji wayar ta na ringing ta mik'e ta nufi bedside drawer inda wayar take ajiye, d'an jimm tay ganin shine ke kiran kafin ta d'auka a hankali tayi sallama amsa mata yay yace mata ya je ya dawo ta yi mashi adawo lpy, tambayar ta yay akwae abunda take so tace mashi a'a daga haka yay cutting kiran, bin wayar tay da kallo bayan ta cire ta daga kunnan ta a ranta ta shiga raya shi d'in ba dai kula ba duk zai fita sai ya tambayi ko tana son wani abu, d'an murmushi tay tana jin k'aunar shi na k'ara ninkuwa a cikin ranta, tunanin tafiya part d'in Hajiya tay ta taya Saude girkin dare tunda ko ta zauna ba abunda zata yi ta mik'e, bayan ta d'aukko gyale da takalma ta k'ara gyara fuskar ta a gaban mirror sannan ta tafi, saida ta tsaya Kitchen ta d'aukko wasu daga cikin kayan da aka kawo masu Abinci don ta maida sannan ta tafi, tare sukai aikin Abincin daren kaman da rana a nan tayi sallar Magrib da isha'i sannan ta baro part d'in tare da Abincin su ta dawo part d'in su har lokacin Haisam d'in bai dawo ba, bayan ta aje kayan Abincin kan table ta wuce Bedroom, har ta zauna bakin gado zata fara latsa wayar ta Zuciyar ta ta ayyana mata yakamata tayi wanka ta mik'e bayan ta aje wayar ta nufi gaban dressing mirror ta cire jewellery d'in jikinta ta maida komai ma'ajiyar shi sannan ta wuce laundry room, after some minutes ta fito sanye da bathrobe kanta ba kallabi sai short towel tana goge fuskar ta da gefen gashin ta, gaban dressing mirror ta tsaya ta shafa mai da su humra bayan ta gama ta wuce wurin kayanta a ranta ta ayyana yakamata ta jera kayan a cikin closet ta yanke gobe tunda ba Makaranta zata je ba tayi hakan, ruwan idon kayan da zata sa ta shiga yi daga k'arshe ta yanke ta saka sleeping dress kawai tunda dare ne kwanciya zatayi ta bud'e jakar da suke ta fiddo wasu riga da wando silk cikin wanda aka kai mata rigar gajeran hannu gare ta ta d'an saukko zata kai cinyoyin ta, gefen gado ta koma ta fara saka su ba tare da ta d'aukko undies ba tunda dare ne, gaban mirror ta koma ta k'ara gyara parking d'in gashinta, bayan ta gama ta maida su bathrobe d'in ta d'aukko phone d'inta ta haye gado ta fara latsa ta, bata dad'e da hawa ba taji an turo kopar da sauri ta kai idonta suka had'a ido dashi ya shigo da yar sallama tana d'an murmushi ta amsa mashi, a gaban gadon ya tsaya tayi mashi sannu da zuwa ya d'aga mata kai, mik'a mata ledar daya shigo da ita yay ta matso ta amsa tana kallon shi kafin ta maida kallon kan ledar shi kuma ya nufi gaban mirror ya fara cire Wrist watch d'in shi, bud'e ledar tay ta lek'a sai kuma ta kai hannu ta fara fiddo abubuwan dake ciki nan taga Pop corn ne da tuwan Madara harda gullisuwa sai Chocolates manya manya with surprise written on her face ta d'ago tana kallon shi don bata tsammaci ganin su ba tunda bata ce mashi tana so ba, hanyar laudary room ya nufa ba tare da ya kalle ta ba da d'an d'aga murya tace "Thank u so much, Allah ya k'ara bud'i na Alkhairi" d'an juyowa yay ya kalleta fuskar shi a sake ba tare da ya ce komae ba ya juya yaci gaba da tafiya har ya shige, tana ta sakin murmushi da alama taji dad'in kawo mata su da yay ta bud'e ledar tuwon madara ta fara sha nan take wani dad'i ya ratsa ta harda lumshe ido lokaci guda zuciyar ta ta tariyo mata can baya irin su ne kyauta ta farko da ya fara mata da hannun shi ta dingi zuba mashi santi harda bashi labarin irin Pop corn d'in da ake kawo masu a Makaranta duk tsakuwowi da gishiri don an raina masu wayau, tunowa da lokacin yasa tay ta dariya can tay tunanin yakamata ta bashi wuri tasan wanka yake in ya fito ya shirya ta saukko daga kan gadon ruk'e da ledar ta nufi hanyar fita, tana zaune a parlor tana cigaba da cin abubuwan ta tana yi tana kallon sabon shirin dad'in kowa ya fito shima ya shirya cikin sleeping dress riga da wando tun kafin ya k'arasa shigowa k'amshin shi ya karad'e parlon, tana ganin shi ta mik'e da hannu tay mashi alama da Dining area ya nufi can ta bi bayan shi, ba wani Abinci sosae yaci ba ya dawo cikin parlon, bayan ta gama ta gyare wurin ta had'o mashi Fruit salad, a kan c-table ta d'aura mashi tace gashi nan ya sha ya furta mata thanks tay d'an murmushi ta koma inda ta taso ta zauna taci gaba da kallon ta, bayan an gama ta juyo suka had'a ido lokacin har ya gama sha tay mashi d'an murmushi taji yace zasu iya yin Assignment d'in yanzu tace eh, bud'e Computer d'in yay dama tana nan ba'a d'auke ba ya fara operating nata tana ta kallon shi can taga yay mata alamar tazo da hannun shi ba tare daya d'ago ba ta mik'e ta nufe shi, a gefen shi ta ja ta tsaya ya k'ara mata alamar ta zauna a kusa da shi still bai kalleta ba, a d'arare kaman mai jin tsoro ta raku6a gefen nashi ta zauna ya shiga nuna mata yadda zatai, tun dai bata saki jiki ba har ta washe suka cigaba da yi har ta kai ya kama hannunta yana koya mata yadda zata d'aukko zanen, tuni jikin su ya had'e da na juna gaba d'aya sun cika juna da fitinannan k'amshi, ba'a d'au wani dogon lokaci ba suka gama har an tura ma malamin tana ta murmushin jin dad'i ta hau yi mashi godiya, d'an murmushi kawae yake ba tare daya ce komai ba ta mik'e ta kai hannu ta d'auki book d'in tana shirin juyawa ta tafi kwatsam tay tuntu6e da kafar shi ta tafi gaba d'aya zata kifa aikuwa cikin zafin nama ya jawo ta tayo baya ta fad'o jikin shi gaba d'aya, tsit kake ji Wutar Fatuu ta d'auke don ba k'aramar razana tayi ba gaba d'aya ta runtse idanunta gam jikinta sai d'an rawa yake tana fitar da numfashi da sauri da sauri, still yay yana bin fuskar ta da kallo ya kasa cewa wani abu idanunta sai rawa suke, bayan wani lokaci natsuwar ta ta daidai ta a hankali ta fara bud'e idanun ta, bayan ta ware su gaba d'aya suka sauka akan face d'in shi dake gab da ta ta, sam kowa ya kasa yin kwakkwaran motsi sunyi tsit gazing in to each other's eye and inhaling each other's sweet scent, Fatuu ce tay k'arfin halin ce mashi ta gode da taimaka da yay ta fara k'ok'arin d'agowa sai dae ta kasa don ya ruk'e ta tightly, slowly ya d'ago da fuskar ta ta yadda saura kad'an su had'e Fatuu na ganin haka da sauri ta runtse idonta breathing d'in su ya fara had'uwa zuciyarta ta fara beating da sauri da sauri, numfashin ta ne ya nemi tsayawa jin ya had'e bakunan su......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2066* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Tun bayan data shiga ta gaishe da shi ya amsa bata k'ara ce mashi komai ba ta juyar da kanta tana kallon gefen hanya, lokacin da suka iso Unguwar suna zuwa gab da gidan su ta juya ta kalle shi yana kallonta ta mirror ta d'an cije baki had'i da d'an yamutsa fuska, dage mata gira yay ba tare da ya kalleta ba yace "What?" A marairaice tace mashi don Allah ya bari ta shiga gida ta gaida gwaggo idon ta akan shi taga ya d'an girgiza kai alamar a'a, 6ata rai tayi idanunta sukai rau rau tana ta d'an kikkafta su bata yi tunanin zai k'i barin ta ta shiga ba, suna shiga kwanar gate tace mashi ya aje ta anan ta shiga ta k'aramar kopa ya parker ba tare da ya ce komai ba, saida ta juya zata bud'e kopar taji voice d'in shi yace ta bari wani time zata je yanzu in taje za'ai mata fad'a ne, juyowa tay ta kalle shi fuskarta a d'an kwa6e ya bud'a mata ido alamar taji ta jinjina mashi kai sannan ta juya ta bud'e, bayan ta fita yaja Motar ya tunkari gate ita kuma ta shige, tana isa part d'in a bakin kopar parlor ta cire takalmanta kafin ta wuce ciki, tana shiga Bedroom tay sensing k'amshin Haisam a ranta ta raya ko ya shigo d'akin ne, wata zuciyar ta ce k'ilan wanka yazo yayi, wucewa tayi ciki ta aje jakar ta ta cire Hijab sannan ta dawo wurin gado ta fad'a alamar ta kwaso gajiya, tana kwanciya taji k'amshin ya cika mata hanci fiye da yadda taji shi da ta shigo, hancinta ta kai jikin zanen gadon ta shinshina nan ta tabbatar da k'amshin shi ne ke tashi a jikin zanen sosae, cigaba da bin jikin zanen tai tana sunsunawa kafin ta d'ago mamaki shimfid'e akan fuskar ta, tambayar kanta ta shiga yi mi zai kawo k'amshin shi haka a wurin in dae ba kwanciya yay ba wata zuciyar ta bata kwanciyar yayi kenan, jikinta ne yay sanyi tay shiru a ranta tana raya kenan had'a gado da ita ne bai son yi, sosae abun ya dame ta don har Fuskar ta ta bayyana, ta d'an d'auki lokaci haka can ta tuna da bata yi salla ba ta saukko jiki sa6ule ta wuce laundry room, Alwala tayo tazo ta kabbara salla har ta gama bai shigo ba ta wuce Toilet don tayi wanka, bayan ta fito shiryawa tay cikin sabuwar doguwar rigar Atamfa tana tsaye a gaban mirror tana d'an yin light make up yayin da a ranta take ta juya kwanciyar da yayi akan gadon tana haka ya turo k'opar ya shigo suka had'a ido ta cikin mirror d'in, ganin yayi tsaye yana ta kallon ta ba tare daya ce komai ba yasa ta juyo ta kalle shi lokacin yace mata ga Abinci can an kawo ta fito ta ci ta d'aga mashi kai daga haka ya juya ya fita ta bi shi da ido, Bayan sun gama cin Abincin ta gyara wurin ta wanke komai a ranta ta yanke tafiya part d'in Hajiya don ta bashi wuri k'ilan ya k'ara kwanciya kan gadon in zai yi bacci, tana can har yamma suka fara aikin girkin dare da Saude, suna cikin yin girkin ne ta tambayi Sauden akan yau da safe ita ta dafa mata indomie, yar dariya tayi don ta d'ago dalilin yin tambayar tata tace mata ba ita ta dafa ba wanda ya kai mata shi ya dafa, ganin Fatun tayi d'an jimm yasa tace mata tayi mamaki ko ta d'aga mata kai tace "nima sosae nai mamaki lokacin dana fito na gan shi a cikin Kitchen yana dahuwar, na kuma rud'e don abu ne da ban ta6a gani ba, ni tunda nike da shi ban ta6a ganin yazo ko bakin Kitchen d'in nan ba balle ta kai shi da yin girki, bamma yi tunanin ko ruwan zafi ya iya dafawa ba sai gashi da yin girki kuma da ga ji Abincin yayi dadi don baki ji yadda k'amshi ya cika wurin Kitchen d'in ba" Murmushi kawae Fatuu ke yi a cikin ranta tana raya a haka kai kace Saboda yana son ta ne yayi amman kawai kulawa ce, ji tay Sauden ta k'ara cewa "ni bansan zaki Makarantar bane ai da nayi maki Breakfast din da wuri, saida ma nace ya bari in yi amma yace in bar shi kawae dai in rink'a tashi da wuri ina maki" shiru Fatuu tay still da murmushi akan fuskar ta Saude ta shiga tsokanar ta tana fad'in ai daga yau da tayi sallar Asuba bazata koma ba kar tayi ma Ango laifi kan Amaryar shi, sai bayan da tayi sallar isha'i ta koma part d'in su tare da Abincin nasu, lokacin da suka yi shirin kwanciya tana zaune akan gado tana yin rubutu ya shigo tana ganin shi ta san mi ya shigo yi da kanta ta d'auki pillow d'in ta mik'a mashi ya amsa Fuskar shi a sake ya furta mata thanks da kuma Gud night ya juya tabi shi da kallo ta d'an kwa6e fuska. Ranar Laraba bayan ya d'aukko ta daga Makaranta sun gama cin Abinci ta gyara wurin, tana cikin Bedroom ya turo kopa ya shigo tana zaune a bakin gado ta juya ta kalle shi, daga bakin gadon ya tsaya Fuskar shi a sake itama da murmushi take kallon shi ya d'an d'auki lokaci ta fahimci kaman wani abu yake son cewa amman kuma yayi shiru, tambayar shi tay ko akwai abunda zata yi ya girgiza mata kai slowly taji yace in tana so taje gida yanzu da daddare zai zo ya d'aukko ta, waro ido tay baki bud'e take kallon shi ta kasa ce mashi komai don Maganar tazo mata a bazata, ganin yadda tayi yasa shi d'an d'age mata gira yace ko bata son zuwa ne aikuwa da sauri ta mik'e tana girgiza mashi kai had'i da yin murmushi ta hau yi mashi godiya farinciki bayyane akan fuskar ta ta nufi wurin wardrobe don ta shirya ya bita da ido, ba 6ata lokaci ta gama shiryawa da wata rantsattsar sabuwar shadda a cikin kayan da aka kawo mata ta ca6a ado ta fito a Amaryar ta sak sai k'amshi take bazawa, lokacin da ta fito yana zaune akan kujera yana lallatsa Computer ya d'ago ido yana kallon ta har ta k'araso ta tsaya daga gefen shi tana ta murmushi shima murmushin ya mayar mata tace mashi ta tafi ya d'aga mata kai ta juya, har ta fice idon shi na akan kopar sai bayan wani lokaci ya janye idon ya maido shi kan abunda yake, tana tafiya tana faman sakin murmushi sai kace wadda ta shekara bata je gidan ba, lokacin da ta iso kopar gidan shagon Kawu Amadu a kulle yake dama tunda suka wuce da aka d'aukko ta daga Makaranta taga shagon a kulle, a ranta ta raya k'ilan yana Makaranta daga haka ta shige cikin gidan, daga bakin k'opa ta tsaya tsakar gidan wayam ba kowa tana murmushi ta kwad'a sallama ba'a amsa ba saida ta k'ara d'aga murya tayi wata sallamar sannan ta jiyo Muryar gwaggo ta amsa, d'an lek'o da kanta tayi don taga waye nan tay arba da Fatuu dake tsaye tana mata murmushi, hannu gwaggo ta kai ta rufe baki sai kuma ta janye kan ta koma ciki bada jimawa ba sai gata ta fito hannun ta ruk'e da tsintsiya ta d'agata alamar bugun Fatun zatayi ita kuwa mi zatay in ba dariya ba ta nufe ta da gudu suna had'e wa ta k'ank'ame ta gaba d'aya harda tsintsiyar, dariya itama gwaggon tasa tana fad'in waya fito da ita Fatun tace Ya Haisam din ne ai yace tazo ko, d'aki suka nufa Fatun tay ma gwaggon side hug, bayan sun shiga a bakin gado suka zauna idon su a cikin na juna sai faman dariya suke ma juna, sosae gwaggo taji dad'in yadda ta ganta duk da Fuskar ta ta d'an fad'a amman wannan dama tun kafin ta tare ne Saboda ciwon laulayin da tayi amman ta k'ara haske fuskar ta sai sheki take fatar nan tayi lukui ko d'igon k'urji babu, Fatuu ce ta katse shirun ta gaishe da ita bayan ta amsa ta tambayi suna lafiya tace mata eh, "Amman ya akai kika fito haka da wuri, bana ce banson ki rink'a zaryar zuwa ba miyasa wani lokacin baki jin magana" tay Maganar ta d'an d'aure fuska, a shagwa6e tace "Wllh shine fa yace in zo..." tunkan ta rufe baki ta katseta "to tunda kin matsa ba dole yace ki zo ba" da sauri ta ce mata wllh bata matsa mashi ba nan ta kwashe yadda akai ta fadi mata gwaggon ta gyad'a kai alamar ta yarda, tambayar ta tayi Kawu Amadu tace bai dawo ba yana Makaranta tace dama saida tayi tunanin haka, hira suka shiga yi kai kace sun dad'e da rabuwa, suna cikin yin Hiran Fatuu ke mata Maganar kud'in da suke a cikin Account d'in ta tace ana ta ajiyar su zata turo mata tayi wani abun dasu, gwaggon na yar dariya tace to ita mi zata yi da su tunda nata ne tayi wani amfanin dasu mana, tace ai ita ba abunda zata yi dasu, "amman tunda kince zaki d'aukko Mino ba sai kiyi amfani da su ba wurin karatun ta" yar harara gwaggon ta wurga mata ta d'an girgiza kai tace "Ke da na d'aukko ki na amshi kud'in karatun ki ne, tunda ni nasa kaina ai bazai gagare ni ba" shiru suka d'an yi can ta sake cewa "ina ganin ko a tura ma Baffan ki sai a siya maki shanaye dama rannan yake man Maganar Sadakin ki duk da Ard'o ya amshi wasu amman yace zai cika maki kinga sai a had'a da d'an kunnan zinarin ki a canzo" da sauri Fatun tace ita dai ba sai an bata wani sadaki ba suyi amfani dasu kawae gwaggo na yar dariya tace ai sai ta kira Baffan nata ta fad'a mashi tace to, sai can yamma Amadu ya dawo shima sosae yay farin cikin ganin Fatun anan d'akin Gwaggon ya zauna harda sakata ta d'ebo mashi Abinci a Kitchen tace to gwaggo na dariya tana fad'in yanzu fa Yayar shi ce ita ya zai sakata aiki, shima dariyar yake yace "haba dai yaya ta, ai koda goma ta lalace tafi biyar Albarka kuma ba'a ta6a canza ma tuwo suna ai", bayan ta kawo mashi Abincin suka cigaba da hira Kawu Amadu nata tsokanar ta yana fad'in wai ita nan Matar aure ce ko shi ganin abun yake kamar wasa gwaggo tace "ai dole kaga hakan tunda kai baka da niyya ko Maganar auren ma banji kana yi ba" yana dariya yace "ai shi lokaci ne, ita ai tama fi ni rashin niyyar auren tunda kin ta6a ganin saurayi yazo kopar gidan nan wurin ta Saboda bata basu dama, komai tace ita likita zata zama sai ga shi ta tafi gidan Romeo karatun likitancin" gaba d'aya sukai dariya, ana gama sallar isha bada dad'ewa ba Haisam yazo shima yasha shadda wadda ta hau da ta jikin Fatuu don ajikin aikin tata akwae kalar daya sa sai baza k'amshi yake, a parlor suka zauna suna gaisawa da gwaggo ta k'ara yi mashi godiya sosae nan tace bari a kawo mashi Abinci yace a'a a barshi bai jin yunwa, daga baya sukai sallama taje tay ma Fatuu dake cikin d'akinta Magana suka fito tare ta rako su har kopar gida, bayan sunyi sallama da Amadu ya rako su har bakin Mota suka tafi, mik'ar hanya Fatuu taga yayi suka fito daga Unguwar suka hau titi sosae tana ta kallon hanya, wani k'aton Shopping mall suka je bayan ya parker Motar a inda aka tanada yace ta fito, da kanshi ya d'aukko shopping cart tana tsaye yazo yace ta d'auki duk abunda take so, rasa abunda zata d'auka tay don gani take kusan komae tana dashi k'arshe dai sai shi ya shiga d'aukar mata kayan har saida cart d'in ya cika ya bata yace ta kai wurin biyan kud'i sai ta d'aukko wani aikuwa ta marairaice mashi a shagwa6e ta hau rok'on shi kan a barsu hakanan itafa tana da komai, har jakunkunan kayan da Hajiya ta aiko mata ta fad'i mashi don a tunanin ta ko bai sani ba, k'arshe dole aka barsu hakanan d'in suka je suka biya aka kai masu kayan Mota bayan an juye a manyan Shopping bags, bayan sun baro wurin wani babban Cafe ya kaisu yace ta fito su ci Abinci, sosae Fatuu taji dad'in wurin kowa ya za6i abunda yake so aka kawo mashi da suka gama su ka tafi, a gaban wani babban cold store ya k'ara Parker Motar yace mata yana zuwa ta d'aga mashi kai bayan ya fita ya zagaya ya shiga wurin tana ta kallon shi ta cikin glass, ruk'e da babbar leda mai d'auke da tambarin wurin ya fito ya zagaya driver side d'in ya koma ciki, saida ya mik'a mata ledar sannan ya ja Motar, yana ta driving ganin ta aje ledar akan cinyoyin ta bata ko bud'e ba yasa shi d'an kallon ta yace nata ne, da d'an murmushi tace mashi Thanks har saida ya sake juyowa ya kalleta yaga tana dariya dama ya gane kwaikwayon shi tay, maida idon yay kan hanya yaci gaba da driving ita kuma ta bud'e ledar, su ice cream ne da youghort ta fiddo ice cream d'in ta fara sha, lokacin da suka iso gida tare suka d'auki kayan suka nufi part dinsu, saida ya kai mata su cikin daki sannan yace mata yana zuwa ya fito ya nufi part d'in Hajiya, cire gyalenta tayi ta hau jera kayan cikin Wardrobe harda nata dama tana ta so ta jera su, sosae taji dad'in kayan ba kamar English wears d'in ciki don tana son k'ananun kaya, bayan ta gama shirya komai wad'anda ba yanzu zata yi amfani dasu ba ta sasu daga can k'asan wardrobe d'in, takalmanta kwasa ta fita cikin Corridor suma ta jera su a jikin shoe rack inda takalman Haisam d'in suke, bayan ta gama ta wuce Kitchen tana shiga ta saki baki tana bin kayan Abincin da ta gani a ciki su kwalayen indomie da spaghetti, macaroni su doya da dankali harda buhun shinkafa gasu madara, milo, Cornflakes harda custard, sugar harda crates d'in k'wai ya kai biyar ba dai abun da babu na kayan Abinci irin na yan gayu, taji dad'in ganin kayan a ranta ta raya zata fara yin girki kenan, shirya kayan Abincin ta shiga yi lokacin data gama ta gaji sosae ta wuce d'aki tana shiga ta nufi laundry don yin wanka, saida ta gama shiryawa ta kwanta akan gado tay rubda ciki tana latsa Computer d'in ta ya shigo, bayan ya cire agogon hannun shi ya d'aura kan dressing mirror ya wuce laundry tana ganin haka ta tashi ta d'auki laptop d'in ta fito daga d'akin don ta bashi wuri ya shirya. Washe gari Alhamis bayan ta dawo daga Makaranta sun ci Abinci a parlor suka zauna shi yana kallo ita kuma tana typing a laptop d'in ta jikinta sanye da k'ananun kaya riga da skirt sun kamata da yake roba ne kanta sanye da hula, suna cikin zaman taji yayi Magana ta d'ago ta kalle shi da alamun bata ji ba tace mashi Magana yake, saida yay d'an jimm sannan yace abunda ta kawo mashi rannan zata zubo mashi nan take ta gane su cin cin yake nufi, d'aga kai tay alamar to da d'an murmushi ta mik'e ta nufi Kitchen a ranta tayi mamakin cewa da yayi ta zubo mashin, tunda ta mik'e yabi bayanta da kallo har ta shige cikin Corridor sannan ya d'age kanshi ya kalli ceiling had'i da d'an lumshe ido, a saman c-table ta d'aura bayan ta zubo mashi ta kalle shi har lokacin yana a yadda yake tace mashi gashi sannan slowly ya sauke Fuskar ya d'an d'aga mata kai ta koma inda take ta zauna, a nutse ya fara ci Fatun ta rink'a satar kallon shi wani lokacin su had'a ido ta d'an yi mashi murmushi, kiran sallar la'asar da aka fara yasa shi mik'ewa ya nufi hanyar corridor, after some minutes ya fito yana gyara hannun rigar shi da gani Alwala yayi ya nufo cikin parlon Fatuu ta d'aga ido tana kallon shi, ganin yadda ta kafe shi da ido yasa shi dakatawa ya tambayi da wani abu ne cikin yar in ina tace dama so take ta tambaye shi har yanzu yana zuwa Gym, shiru ya d'anyi sai kuma ya d'aga mata kai tay d'an jim tana jujjuya ido da alama magana take son yi ta kasa, d'an moving yay ya tsaya ya tambayeta ya akai, marairaice fuska tay tace dama so take taje ne wani kallo taga yayi mata kaman harara ta d'an tura mashi baki had'i da rausayar da kai, jimm yay can yayi sigh yace taje ta shirya har bata san lokacin da ta saki yar k'arar farin ciki ba ta k'ame hannuwan ta had'i da d'an runtse ido, sototo yay yana kallon ta tana bud'e idon suka had'a ido ganin yadda yake kallon ta yasa ta kai duka tafukan hannuwanta ta rufe fuska alamar kunya yay d'an guntun murmushin gefe ya juya, yana fita ta tattara komae ta nufi Bedroom da sauri don ta shirya, salla ta fara yi tana gamawa ta hau shiri ba 6ata lokaci ta shirya cikin wando skin tight bak'i da top bak'a ta d'aukko sabuwar jallabiya cikin siyayyar da aka yi mata ta d'aura saman kayan ta nufi gaban mirror tana rolling veil d'in lokacin ya shigo ya wuce laundry, daga gida ya shirya don jakar shi bata nan tare suka fito suka nufi parking space suka hau Mota don yanzu bike d'in shi bai nan. Sai bayan Magrib suka dawo a cikin kwanar gate ya ajeta yace zai je ya dawo, sosae Fatuu taji dad'in jikinta tana shiga Bedroom ta wuce toilet tayo wanka don ta had'a gumi sosae, bayan ta fito doguwar riga mai gajeran hannu mara nauyi ta sa ta d'an shafa mai da humra ta fesa turare, saman gado ta zauna tana latsa wayar ta a haka har lokacin isha yayi ta mik'e tayi salla, bayan ta gama jakar ta ta d'aukko ta Makaranta anan ta fara duba books d'inta, tana cikin karatun ya shigo yayi wanka yana sanye da k'ananun kaya tay mashi sannu da zuwa bayan ya amsa yace ta fito su ci Abinci tace to ta mik'e, bayan sun gama ta kwashe kayan da sukai amfani ta kai Kitchen saida ta wanke komai kaman ko yaushe ta koma dining d'in ta gyara table lokacin data gama Haisam d'in bai cikin parlon don yana gama cin Abincin ya fita, bayan duk ta gama abunda zatayi Bedroom ta koma ta zauna a kan gado tana cigaba da yin Karatu, ji tay ta fara jin bacci ta tattara littattafan ta maida a cikin jakar ta saukko ta maidata inda take sannan ta dawo ta haye gado taja duvet ta rufe rabin jikinta, bata dad'e da kwanciya ba har ta fara gyangyad'i ya turo k'opar ya shigo ta bud'e ido tana kallon shi shima ita yake kallo ya nufi gadon, duk a tunanin ta pillow zai d'auka kaman ko yaushe amman sai taga ya zauna daga bakin gadon ta can 6angaren da yake har saida ta d'an ji mamakin hakan da yayi don bai ta6a hakan ba, shiru suka d'an yi ya kauda idon shi yana kallon gefe ta lura kaman magana yake son yi, sai da ya d'an d'auki lokaci sannan taji cool voice d'in shi yace "You will sleep without switching off the light" yay Maganar idon shi a kanta ta d'an had'e lips d'inta sai kuma a hankali tace ta manta ne ta fara k'ok'arin tashi ya gane wutar zata kashe taji yace ta bari zai kashe in zai fita ta d'aga mashi kai amman duk da hakan sai ta tashi daga zaune, shiru suka d'an yi idon shi na kallon gaban shi ita kuma sai kallon shi take a ranta tana mi yake son ce mata ne, "Am leaving tomorrow" bayan wani lokaci ya d'an kalle ta taji ya fad'i haka, bin shi da ido tay da alamun rashin fahimtar Maganar tashi taji ya k'ara cewa "I mean am going back to Us, zan je Abuja gobe daga can zan wuce" yanayin yadda yake Maganar kaman bai so don dole yake yin ta, ido kawae Fatuu take bin shi dashi ta d'an bud'e baki da gani Maganar tazo mata a bazata ne zuciyarta ta fara bugu da k'arfi don kaman saukar aradu haka taji Maganar wai zai koma Us duka yaushe aka kawota da zai tafi, goben fa zata yi sati d'aya amman shine zai ce zai tafi haka take ta ayyanawa a cikin ranta, tana haka taji Muryar shi yace bata ce komai ba sauke kanta tayi k'asa nan da nan kwalla suka fara taruwa ta shiga kokarin maida su da k'yar murya na d'an rawa tace mashi "Allah ya kaimu, ya kiyaye hanya" shiru bata ji ya amsa ba tasan kallon ta yake hakan yasa tak'i d'agowa don tasan data kalle shi tana iya yin kuka, sun d'an d'auki lokaci a haka shiru can taji ya kira ta da Fatuuh ta amsa ba tare da ta kalle shi ba ya tambayeta da matsala ne, jin tambayar tay kaman ta rainin wayau ta girgiza mashi kai kawai alamar babu komai, mik'ewa yay ya nufi hanyar laundry sai lokacin ta d'ago tana kallon shi, yana shigewa wani irin kuka ya taho mata tasa hannu ta toshe bakin ta da sauri ta koma ta kwanta ta kife fuskar ta jikin mattress, after some minutes taji k'arar bud'e kopar shi da sauri taja duvet ta lullube har kanta, sanye da bathrobe ya fito saida ya kalleta kafin ya wuce ciki, shiryawa ya fara yi yana yi yana kai idon shi kanta ko kwakkwaran motsi tak'i yi, bayan ya gama yasa kayan bacci ya nufi bakin gadon ya kai hannu ya d'auki pillow taji yace Good Night bata motsa ba balle ta amsa mashi irin ita ala dole bacci take saida ya kashe mata hasken d'akin gaba d'aya ya kunna mata lamb ta gefen da yake sannan ya juya ya nufi kopa, tana jin k'arar fitar shi ta bud'e fuskar taci gaba da kukan da take yi k'asa k'asa, saida tay mai isarta don kanta tayi shiru, duk yadda ta kwaso gajiya amman gaba d'aya bacci ya k'aurace ma idanunta sai juye juye take tana zancen zuci, saida dare ya raba sannan da k'yar baccin ya d'auketa shima ba wani mai nauyi ba, ana fara kiraye kirayen sallar Asuba ta farka da wani irin yanayi mara dad'i jikinta yayi weak har wani zazzabi zazzabi take ji, cike da k'arfin hali tayi shirin zuwa Makaranta ko breakfast d'in kirki ta kasa yi haka ta d'an tsattsakura ta barshi, tunda suka hau hanya ta juyar da fuskar ta gefe har suka isa Makarantar bata kalle shi ba saida zata fita sannan ta d'an juya suka had'a ido tace mashi ta gode ya fiddo kud'i ya bata bayan ta amsa ta bud'e Motar ta fita, ko a Class ma Fauzy ta lura da yanayinta ta hau tambayar ta abunda ke damunta tace mata kawae bata lafiya da zazza6i ta kwana amman ta sha magani, nan ta hau tsokanar ta wai kodai har ta biya Ya Haisam saidae kawae tay mata d'an murmushin yak'e, bayan an tashi ya zo ya dauketa, tunda ta koma ta shige d'aki ta kwanta sai daga baya ya shigo ya iske ta a kwancen ko Uniform bata cire ba ya tsaya daga bakin gadon yana tambayar ko bata lafiya ne da k'yar ta d'aga ido ta kalle shi ta girgiza mashi kai ya bita da kallo ta maida nata k'asa taji yace to ta tashi ta shirya zasu yi lunch a part d'in Hajiya ta d'aga mashi kai kawai ya juya ya fita, a daddafe ta shirya don har lokacin jin jikinta take ba dad'i tasa riga da skirt na lace iya powder da lip glow kawai tasa suma don kada a gane mata ne, lokacin data gama shiryawa bai nan tasan bai wuce Masallaci ya tafi don an fara hud'uba ta fito ta wuce part d'in Hajiya, bata samu kowa a parlon ba ta wuce Bedroom d'in ta bata same ta ba a ciki ta fito ta wuce d'akin Saude itama bata nan ta raya k'ilan suna Masallaci ta nufi Katifar Sauden ta kwanta sai daga baya ta mik'e ta nufi toilet tayo Alwala, bayan sun dawo ne ta fito ta iske su a parlor taje ta gaishe da Hajiya har tana tambayar ta ya akai bata zo sunje Masallaci ba tace lokacin da tazo har sun tafi shine tayi a d'akin Aunty Saude, daga baya Sauden tazo tace ma Hajiya ta shirya table tace masu su tashi suje su ci Abinci, da k'yar Fatuu ke turawa ba don tana jin dad'in Abincin ba, ita ta fara tashi Hajiya tace badai har ta koshi ba da d'an murmushin yak'e tace mata eh tace amman ai bata wani ci na kirki ba tace ai taci ne a Makaranta shiyasa ta gyad'a kai Fatun ta wuce idon Haisam a kanta, d'akin Saude ta koma bayan barin ta wurin Hajiya tace "Yanzu har sai yaushe zaka dawo in ka tafi?" Shiru ya d'an yi idon shi akan Abincin gaban shi kaman mai nazari can ya d'ago ya kalleta yace mata saidae yaje zai gani, gyad'a kai tay da alamun damuwa tace "banso ka tafi da wuri ba haka tunda Yarinyar nan ba'a dad'e da kawo ta ba, amman kana da kwakkwaran dalili yakamata ace ka koma aikin kaman yadda kace tunda kusan watan ka biyu kenan rabon ka da aikin fa, an taho bikin aboki sai kuma jinya kusan wata guda, yanzu da dawowar mu kuma inaga sati biyu kenan, ita kanta Fanan d'in nasan ta k'agara ka koma don ma tazo Germany d'in" d'an dakatawa tay sai kuma taci gaba "ba don karatun Fateemar ba ai da ka tafi da ita ala bashshi kasan yadda zakai in ka je, amman dai kai k'ok'ari in ka koma ka sanar da ita zancen auren naku sannan kayi k'ok'arin fahimtar da ita don kada kuma a tauye hakkin Fateema tunda itama zata so ku kasance tare ba kamar yanzu dai bai kamata ace har ka tafi ba, nima zanyi k'ok'arin sanar da iyayen naku bayan ka tafi, Allah ya shige mana gaba" a hankali ya amsa da Amin, bayan sun gama yace ma Hajiyar zai je G.r.a ya dawo, gab da sallar la'asar ya dawo ya nufi part d'in su ganin bai ga Fatun ba ya gane bata dawo ba, shirya kayan da zai d'auka anan yayi cikin trolley d'in shi, ba wasu kaya masu yawa ya d'auka ba ya bar wasu bayan ya gama aka kira sallar la'asar ya tafi Masallaci, bayan an gama sallar ya dawo ya zauna akan kujera yasa hannu ya d'an ruk'e ha6ar shi kaman mai yin tunanin, ganin lokaci nata tafiya don 4:30 jirgin su zai tashi yasa shi kai hannu ya d'auki wayar shi, kiran Fatun yay bayan tayi picking yace tazo yana jiranta a part d'in su a sanyaye ta amsa da to, bada jimawa ba ta turo kopar parlon ganin shi zaune yasa tayi yar sallama ya amsa idon shi a kanta har ta k'arasa shigowa ta zauna daga d'ayan 6angaren, ganin yadda ya kafeta da ido yasa ta juyar da face d'inta gefe tana haka taji yay sigh ya fara magana, ce mata yay yanzu zai tafi duk abunda take buk'ata tayi ma Abbas Magana, jin yayi shiru yasa ta d'an juyo suka had'a ido da k'yar murya na rawa tace mashi to ta maida kanta k'asa, wani irin kuka ne ke taho mata sai k'ok'arin maida shi take tana haka taji yace taje Bedroom ta d'aukko mashi trolley d'in shi ta mik'e ba tare data ce komai ba ta nufi hanyar corridor yana ta kallon ta har lokacin hannun shi na ruk'e da beard d'in nashi, janye da trolley d'in ta fito yana ganin ta ya mik'e tsaye, daga gaban shi ta tsaya ta mik'a mashi a hankali tace gashi bai amsa ba ya kafeta da ido kawae, jin yayi shiru yasa ta d'ago idanunta cike da k'walla ta kalle shi suka had'a ido da sauri ta juyar da fuskarta, k'ara ce mashi tay gashi ba tare data kalle shi ba taji yace "Won't u accompany me to the Airport?" Shiru bata bashi amsa ba don tasan tana bud'e baki zata saki kuka sai yamutsa fuska take ta gumtse baki, hannu ya kai ya kamo hannun ta ya matso da ita har lokacin Fuskar ta na gefe, kiran sunanta yay aikuwa kaman tana jira ta k'wace hannun nata ta juya da gudu ta nufi hanyar corridor, tana shiga ta nufi gado ta fad'a ta fashe da kuka mai cin rai, ta d'auki lokaci tana ta rizgar kukan, ganin bai biyo ta ba yasa ta gane ya tafi hakan ya k'ara tunzura ta, tashi tay zaune kallabin ta ya kwance fuskar ta jage jage da hawaye idanunta sun yi ja a fusace ta fara magana cikin kuka "Yanzu na tabbatar baka sona Ya Haisam baka kaunata, kawae ka amince kaci gaba da zama dani ne hakanan ba don kai rayuwar Aure dani ba Saboda ni ban kai matsayin da zan zama matar ka ba, da kana sona na tabbatar bazaka tafi yanzu ka barni ba, shiyasa ka tafi wurin matar ka da kake so ka bar ni, hada cewa duk abunda nike so in ma Ya Abbas Magana wato Saboda baka son in rink'a ma magana ko, to shikenan bazan kira ka ba kasha soyayya da matar ka lafiya zan ma fita daga rayuwar ka kwata kwata sai ka huta" tana kaiwa nan ta sake fashewa da kuka ta fad'a saman gadon, ta jima haka har idanunta sun d'an kumbura can ta mik'e ta nufi mirror ta d'auki wayarta dama da ta shigo d'aukar mashi trolley ta d'aura ta anan, call log ta shiga ta kira lambar Fauzy tana fara ringing ta d'aga tace "Amaryar mu ya kika koma gida" fashe mata da kuka Fatuu tay a rud'e Fauzy ta saki salati ta hau tambayarta lafiya cikin kuka tace "Fauzy na gaya maki ya Haisam bai sona gashi nan har ya tafi ya barni" a kid'ime ta hau tambayar ta ina ya tafi ya barta tace mata ya koma Us, cike da mamaki Fauzy ta maimaita abunda tace Aunty Mareeya dake gefen ta tana sauraron su ta kai hannu da Sauri tana fad'in ta bata wayar, bayan ta amsa ta kira sunan Fatun cikin muryar kuka ta amsa tace "naji kina cewa ya koma?" Tace "Eh Aunty Mareeya yanzun nan ya tafi kuma bansan da zai tafin ba sai jiya da daddare yake fad'i man" salati Aunty Mareeya ta rafka ta kai hannu ta ruk'e ha6arta cikin bacin rai tace "Amman wannan anyi d'an jakar uba wllh....ke yi hak'uri na zagar maki miji raina ne ya 6aci, to wai miyasa zai tafi duka sati guda da kai mashi Amarya, mi ya koma yi ne yaushe yace maki zai dawo" cikin kuka tace "nifa Aunty Mareeya ce man yay kawae zai tafi bai fad'i man ko wani dalili ne yasa zai koma d'in ba kuma bai ce man ga ranar da zai dawo ba" salati ta k'ara sakawa sai faman fad'in kai take, "amman Zarah wani abu bai shiga tsakanin ku bane?" Ta jefa mata tambaya, ta fahimci abunda take nufi tace mata eh, da tsantsar mamaki tace "Yanzu kina nufin tsawon sati gudan da kikai kallon ki kawai yake ba abunda ya wakana" k'ara amsa mata tay da eh, cike da takaici da har muryarta ta nuna tace "Amman dai wannan anyi sak'ago wllh, sai kace ba jini a jikin shi, to ko dai bai lafiya....Amman ma ai mu shaida ne in ma bai lafiyan tsabar iskanci ne ba wani abu ba, haka suke dama irin Mutanen nan akwae ban haushin tsiya wllh..." Dakatawa tay tana numfasawa can ta d'aura "Yanzu ina magungunan da aka siyo maki kina ta amfani da su ne?" tace "a'a, tun bayan da aka kawo ni na daina sha dana ga......" Shiru tay ta kasa k'arasa Maganar Aunty Mareeya tace "Yauwa Nagode ma Allah kin yi kyaun kai gara da kika daina amfani dasu duk da haka nasan kin k'waru, don Allah kiyi hak'uri Zarah kin ji, nasan dole ki shiga wani hali komai anyi maki ne don a nema maki k'ima" amsa mata tayi da to, taci gaba "bari mu zuba mashi ido muga iya gudun ruwan shi, ki k'ara hak'uri kinji in sha Allahu zaki ci ribar hakurin da kikai, ina nan dake sai reshe ya juye da mujiya a lokacin kuma zaki murza kambun sarautar ki sai yadda kika so zaki yi, in dai bada wani kwakkwaran dalili yay maki hakan ba bi'iznillahi ta'ala shima sai ya yi kuka share share" sosae ta shiga kwantar mata da hankali har saida taji ta d'an saukko sannan su kai sallama Fauzy ma ta rarrashe ta tace mata tana nan zuwa daga baya sukai sallama, tana niyyar aje wayar taji kira ya shigo ta kai idonta taga sunan da ta sa ma Abbas ya bayyana, d'an jimm tay kaman bazata d'aga ba can ta kusa yankewa tay picking ta kara a kunne, tun kafin tace wani abu ya tambayi tana ina tace mashi tana cikin d'aki yace yana a parlor ta fito a hankali ta amsa mashi da to, gyalen ta dake saman gado ta d'auka ta yafa ta nufi k'opa, dan jimm tay a bakin k'opar a ranta ta shiga raya komi ya kawo shi can dai ta kai hannu ta bud'e kopar ta fita........ _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2065* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ........... Kissing d'in ta ya shiga yi deeply a nutse hannun shi duka biyun talla6e da kanta da ba kallabi gashinta dake fake yayi k'asa, Fatuu kam tuni ta k'ame ta kasa ko d'aga hannunta don abun yazo mata unexpected sai numfashin ta da ke fita rapidly kirjinta na hawa da sauka da sauri da sauri, sun d'auki lokaci a haka kafin slowly ya kwantar da ita akan kujeran tayi Flat still idanunta na a rufe, had'e fuskokin su yayi ta yadda tsinin hancin shi ya had'e da nata inhaling each other's breathe wanda gaba d'aya yake fita da k'arfi, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin slowly ya janye fuskar ya fara Moving dinta around her neck yana inhaling scent d'in jikinta, a wannan lokacin a wata irin duniya ta daban Fatuu take jinta the world around her faded away, sai faman sakin nishi take ta kai har saida ta d'an bud'e bakinta don ji take numfashin ta na neman katsewa, wani irin salo yake mata mai rikita kwakwalwa a nutse cike da gwanancewa, suna cikin haka ya kai hannu ta k'asa a hankali ya fara tattare rigar ta, Fatuu na jin haka bugun zuciyar ta ya k'aru, dakatawa yay da shak'ar K'amshin wuyan ta da yake ya fara jawo fuskar k'asa har ta sauka kan flat tummy d'in ta daya bayyana sakamakon dama iya rigar baccin ce ta rufe shi, har saida Fatuu ta d'an gantsare lokacin da taji ya kai nan jikinta ya fara d'an rawa ta fara mommotsa k'afafun ta, bin cikin nata ya fara yi yana cigaba da shak'ar Scent d'in da jikinta ke saki giving her soft kisses at the same time, she's savoring every touch and every kiss ji take tamkar zata suk'e, cigaba da moving face d'in shi yay yana yi mata abunda yake mata, a haka har ya rage da ya k'ara janye rigar boobs d'in ta zasu bayyana a lokacin numfashin Fatuu kusan d'aukewa yay, yana k'ok'arin k'ara janye rigar hannun shi ya gogi boob d'in ta, dakatawa yay da abunda yake matan tamkar an latsa mashi pause yay d'an jimm can kuma sai ya d'ago daga jikin nata, dakatawar da yay yasa da k'yar ta d'an bud'e idanun ta da sukai mata wani irin nauyi ta hango shi zaune daga gefe kan shi a k'asa yasa hannu guda ya dafe gefen fuskar tashi, k'arasa bud'e idanun ta da tuni sun canza daga ainihin kalar su da yanayin su tayi ta bi shi da kallo har lokacin numfashin ta da d'an k'arfi yake fita, sun d'an d'auki lokaci a haka can wata zuciyar ta raya mata zaman me take ta tashi ta tafi d'aki, da k'yar ta yunk'ura ta tashi zaune ta saukko da k'afafawun ta k'asa kafin ta mik'e, ko ta kan littafin ta da laptop d'in bata bi ba ta nufi hanyar corridor tana tafiya a harhard'e gaba d'aya jikinta jin shi take kaman ba nata ba sai kace na wadda ta tashi daga ciwo sam ba k'arfi a jikin nata kwata kwata, Slowly ya d'aga idon shi da suka sauya daga yanayin su yana kallon ta har ta shige d'aki sannan ya maida kan nashi k'asa yasa dukkan hannuwan shi ya talla6e shi, tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna dabas ta kankame jikinta da har lokacin yana d'an yin rawa, gaba d'aya ji take kamar har lokacin yana cigaba da yi mata abubuwan da suka wakana tsakanin su, gaba d'aya ya tado mata da urge d'in ta dama kuma a tsume take a yadda take ji ma sai tayi wanka, ta d'an d'auki lokaci a haka can ta kai kwance k'afafunta na a k'asa tay tsuru tana ta imagination hakan ya k'ara kashe mata jiki sosae, zuciyar ta ce ta fara raya mata anya Ya Haisam na son ta kuwa, inda yana son ta bata tunanin yadda suka kai wani mataki haka zai k'yale ta, wata zuciyar ta k'ara raya mata da bai son ta zai yi mata abubuwan da yayi mata ne sai kuma ta sake raya ai k'ilan bada niyya bane kaman yadda ya faru a G.r.a dalili ne ya sa komai ya faru to k'ilan yanzu ma haka ne tunda ita ta fad'a mashi, idanunta ne suka ciko da k'walla ita kad'ai tasan abunda take ji a jikinta can ta runtse idanun ta suka fara gangaro mata, ta d'an d'auki lokaci a haka saida taji ta d'an samu sassaucin abunda take ji a jikinta sannan ta yunk'ura ta tashi zaune sai kuma ta mik'e tana tafiya a hankali ta nufi wurin kayanta ta d'aukko hula tasa, gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta kwalla na ci gaba da zubo mata daga baya ta sa hannu ta goge ta juya ta nufi hanyar laundry, d'aure da towel ta fito ta koma wurin kayanta ta curo doguwar riga ta zumbula daga haka ta nufo gado ta kwanta ta ja duvet ta lullube har kanta. Tun bayan da ta shige yake zaune a yadda yake tsawon lokaci sai daga baya ya mik'e ya nufi hanyar fita daga cikin parlon walking slowly, not too long da fitar shi ya dawo hannun shi ruk'e da wani abu har ya zauna sai kuma ya mik'e bayan ya aje abunda ya d'aukko a kan kujerar ya nufi hanyar Dining, bottle water ya d'aukko daga cikin freezer ya dawo, zaunawa yayi ya shiga bud'e ruwan bayan ya bud'e ya aje shi akan c-table ya kai hannu gefen shi ya d'aukko abunda ya aje wanda d'an kwali ne kamar na magani ya bud'e, ciro abunda ke ciki yay ya 6allo guda d'aya ya saka cikin bakin shi ya kai hannu ya d'aukko robar ruwan, bayan ya shanye ya rufe robar ya aje ya maida abun cikin kwalin wanda kaman magani ne, bayan ya rufe kwalin ya sake mikewa ya nufi hanyar fita, bada jimawa ba ya dawo ya nufi wurin Switch ya kashe hasken Parlon ya bar na wasu k'ananun fitilu kaman yadda yake yi ya koma wurin Kujerar, Zaune yay idon shi akan Corridor kaman mai tunanin wani abu, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin ya kwanta yau ko pillow d'in babu saidae ya tada kan shi da hannun kujera yasa tafin hannun shi d'aya ya rufe fuskar shi, ta dad'e bacci bai d'auke ta ba sai tunane tunane take tana juye juye har dare ya yi sosae tana a haka, har Addu'a tay a cikin ranta kan Allah yasa tayi baccin, sai bayan wani lokaci sannan baccin ya d'auketa cike da mafarkan abunda ya faru. Sai da gari ya fara wayewa sannan ta farka lokacin har anyi sallar Asuba tuni, bayan tayo Alwala tazo ta kabbara salla, zaune tay da ta gama cikin ranta tana ayyana Ya Haisam bai shigo bane yin Alwala da bai tashe ta ba, haka tay ta zancen zuci ita kad'ai sai bayan wani lokaci sannan ta mik'e ta cire Hijab d'in data yi sallar ta ninke ta d'auke prayer mat duk ta maida su wurin da suke, komawa tay gado ta kwanta ta kudundune taci gaba da yin sak'e sak'e a ranta, tsawon lokaci tana a hakan bacci yak'i d'aukar ta har taji ta gaji da kwanciyar ta mik'e don ta gyara d'akin, bayan ta gama gyaran d'akin tasa turaren wuta toilet ta wuce tayo wanka, bata canza kaya ba doguwar rigar jikinta ta bari haka jikinta ma iya mai kawai ta shafa sai turare data fesa ta koma bakin gado ta zauna, hakanan rashin shigowar Haisam d'in ta tsaya mata ta raya k'ilan don abunda ya faru ne k'ilan kuma ya shigo tana bacci, gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i har wayarta ta daukka don tayi ko chatting ne amman k'arshe sai dai ta aje ta ta haye gado tay shiru, tana kwancen taji anyi knocking kopar d'akin ta tashi zaune da alamun mamaki, jin an k'ara kwankwasawa yasa ta mik'e ta nufi kopar, tana bud'ewa taga Saude ce tayi mata murmushi itama ta d'an yi mata ta gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata dama Breakfast ne ta kawo to bata iske kowa a parlon ba kar ta aje ta tafi kuma ba'a san ta kawo ba yasa tace bari tayi mata magana, Fatuu ta d'an yi mamakin jin tace ba kowa a parlon kenan ma baya nan godiya tay mata har Sauden zata juya ta tafi sai kuma ta dakata idon ta akan Fatun tace "amman ko baki lafiya ne?" d'an fad'uwa gaban ta yay tayi d'an murmushi tace mata a'a lafiyar ta lau, Sauden tace "amman Fateema naga idanunki sun canza kaman ma kuka kikai ko?" da sauri ta girgiza mata kai "a'a Aunty Saude" tana kai Maganar ta sunkuyar da kanta k'asa don sai taji idanunta na tara k'walla, hakan da tayi yasa Saude zargin da wani abu ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tace "in wani abu ke damun ki Fateema ki fad'a man in da taimakon da zan maki, barin damuwa ba abunda yake ma mutum sai haddasa mashi ciwo" da k'yar ta maida k'wallan ta kalle ta da d'an murmushin yak'e ta girgiza mata kai tace "ba abunda ke damuna Aunty Saude kawai na tashi da ciwon kai ne" kai Sauden ta jinjina ta yarda da abunda tace ta tambayi to tasha magani tace mata eh tun jiya da daddare, "to yanzu ai yakamata ki k'ara sha tunda ga Abinci nan na kawo ki zo ki ci sai ki sha maganin in kuma kinji bai daina ba gara kiyi magana akai ki Asibiti, kinsan yanzu haka malaria ke sa mutane suyi ta ciwon kai mai tsanani" kai ta d'aga mata tace ta zo tayi breakfast d'in, ba musu ta fito suka shigo parlon tare Sauden tace suje tay serving nata da sauri tana murmushi tace mata lafiya lau zata yi ai ba wani ciwo yake mata sosae ba tay mata godiya ita kuma tay mata Allah ya sawak'e ta tafi, zaune tay a dining d'in ta kasa yin Breakfast sai tunanin inda Haisam d'in ya tafi take wata zuciyar ta raya mata k'ilan ma ba gidan ya kwana ba k'arshe ta yanke watak'il yana G.r.a, ta d'auki lokaci a haka kafin ta fara yin Breakfast din, bata wani ci da yawa ba ta mik'e ta koma d'aki, ji tay duk zaman bai mata dad'i ta yanke tafiya part d'in Hajiya bayan ta d'aukko gyale ta yafa ta fita, tana kaiwa bakin k'opar parlon zata bud'e taga an turo ta kalli mai shigowar da sauri, Haisam ne ya shigo jikin shi sanye da k'ananun kaya da gani wanka yayi sai sakin uban k'amshi yake, suna had'a ido ta sadda kanta k'asa da sauri, k'arasa shigowa yay idon shi a kanta ya tsaya daga gefe, kirjinta ne ya fara bugu da sauri sauri da k'yar ta bud'e baki ta gaishe dashi ba tare data kalle shi ba ya amsa, shiru ba wanda ya k'ara tanka wa balle ya motsa still idon ta na k'asa shi kuma ya kafeta da nashi idon wata irin kunyar shi taji ta rufe ta, jin bai k'ara cewa komae ba kuma yayi tsaye yasa ta d'an d'ago ta kalle shi suka k'ara had'a ido da sauri ta juyar da face d'in ta gefe ta fara motsa baki murya na d'an rawa ta fad'i mashi zata part d'in Hajiya ne, shiru bai ce komae ba hakan yasa ta d'an juyo still kallon ta yake sai kace mai nazarin wani abu, tambayar ta yay bata lafiya ne ta d'aga ido ta kalle shi sai kuma ta girgiza mashi kai had'i da maida idon k'asa, ji tay ya k'ara cewa in bata lafiya ne su je Hospital ba tare da ta kalle shi ba a sanyaye tace mashi lafiyar ta lau k'asa k'asa ya furta Ok ya fara k'ok'arin wucewa ciki, har zata fita sai kuma ta tuna da breakfast d'in da aka kawo ta juya ta koma ciki daga gefe ta tsaya ta d'an kalle shi yana zaune kan kujera tace mashi ga breakfast can an kawo ya jinjina kai yana kallonta, ganin tayi tsaye yace taje in da zata tace zatay serving nashi ne yace no problem zai yi da kan shi ta je, kallon shi ta sake yi idon su ya k'ara had'uwa da sauri ta juya ta nufi kopa ta fita, Tana tafe tana zancen zuci gaba d'aya ta kasa gane ma wannan auren nasu, tasan ana aure ne in ana son juna to su ita ce ke sonshi shi ba son ta yake ba kawae ya aure ta ne don ya taimaka mata ba don suyi rayuwar Aure ba abun kuma turns out this way, yanzu haka zasu cigaba da yin tasu rayuwar auren? Ta jefa ma kan ta tambaya, ta so ace shima yana jin son ta ya kuma nuna mata tasan da ba k'aramar rayuwar Aure mai dad'i zasu yi ba, idanun ta ne suka ciko da k'walla daga baya suka fara zubowa, saida ta iso bakin part d'in sannan tasa gefen gyalenta ta goge Fuskar sosae sannan ta shiga, ganin ba kowa a parlon yasa ta wuce Bedroom d'in Hajiya nan ta iske ta tana bacci ta fito ta nufi Kitchen ba kowa a ciki ta juyo ta nufi d'akin Saude, ciki ta isketa tana ganinta ta washe mata baki tana fad'in har ta samu sauk'i da ta fito, a gefen Katifarta ta zauna tana murmushi tace mata ai fa dama ba sosae yake mata ciwon ba yanzu ma ta samu sauk'i ta zo ta taya ta aikin Abinci Sauden tace a'a yau dae ta huta ko ta k'ara samun sauk'i Sosae tay murmushi kawae, kwanciya tay akan Katifar Sauden don tak'i yarda ta taya ta aikin bada jimawa ba kuma bacci yay awon gaba da ita, saida akai sallar Azahar Saude tazo ta tashe ta don tayi salla, bayan ta gama sallar ta nufi Bedroom d'in Hajiya ta isketa zaune akan prayer mat tun bayan da ta gama salla bata tashi ba ta nufi gefen ta ta zauna tana gaishe da ita da murmushi ta amsa tana tambayar ina Angonta ta sanar da ita ai tun d'azun tazo ta iske tana bacci shine ta wuce d'akin Aunty Saude nan bacci ya kwashe ta, tana zaune a d'akin Hajiyar sai ga Haisam ya shigo tunda suka had'a ido ta maida kanta k'asa ya zauna a bakin gado bayan ya gaida Hajiyar suka shiga d'an yin fira jefi jefi daga baya Saude ta shigo ta sanar da ita an shirya table tace ai sai su tashi suje suci gaba d'aya tunda suna nan, Fatuu ce tay Serving d'in su bayan itama ta zuba nata ta zauna saidai kasa sakin jiki tay taci sosae sai faman Jujjuya cokali take har Hajiya ta gane ta tambaye ta ko bata son Abincin ne da sauri tace mata a'a tace to taga tak'i sakin jiki taci sosae in bata son shi tayi Magana sai a samar mata wani abun tace a'a tana so dole ta daure ta rink'a turawa, bayan sun gama Haisam ya tafi dama shi ya fara tashi su kuma suka koma Parlor suna kallo, sai bayan la'asar sannan Fatuu ta koma part d'in su tana zuwa ta wuce toilet don tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa A shape ta d'an shafa powder da lip glow ta fesa turarurruka, wayarta ta d'auka ta haye gado ta fara yin Azkar bayan ta gama tay tunanin kiran Haulat don tun ranar tarewar ta rabon ta da ita, ta dai san da ita aka kawo ta amman bata san lokacin data tafi ba, sai bayan isha Haisam ya dawo yau ma harda ledar su ice cream ya kawo mata tayi mashi godiya daga baya suka wuce dining area don cin Abinci, bayan Fatuu ta gama duk abunda zata yi na shirin kwanciya ta d'aukko Al'qur'ani ta zauna a saman gado tana karantawa lokacin Haisam ya shigo shima tuni yayi shirin kwanciya, dakatawa tay da karatun ta kalle shi ba laifi ta rage jin kunyar tashi Fuskar shi a sake ya nufo gadon ya d'auki pillow yace mata "Gud night" kai ta d'aga mashi ya juya ta bishi da ido har ya fita sannan taci gaba da karatun, Washe gari ana kiran sallar Asuba ta farka, tana gama yin sallar ta wuce toilet tayo wanka, bayan ta fito ta fara shirin zuwa Makaranta, Yana kwance kan kujera idanun shi a rufe ta fito sanye da Uniform ta nufo cikin parlon, daga gefen shi ta tsaya tana kallon fuskar shi ta fara tunanin ko bacci yake yi, slowly taga ya fara bud'e idon suka sauka a kanta, gaishe da shi tayi ya jinjina mata kai cikin yar inda inda tace mashi dama Makaranta take son zuwa, kafeta yay da ido ba tare da yace komai ba hakan yasa ta maida nata k'asa, tana haka taji yace tayi breakfast ne ta girgiza mashi kai alamar a'a, shiru yay ta d'ago ta kalle shi yace to zata tafi School d'in ne ba tare da tayi breakfast d'in ba tace mashi eh, "Dama kina yin haka?" taji ya tambaya, ta gane yana nufin dama tana zuwa Makarantar ba tare da tayi breakfast d'in ba, a hankali tace "a'a, amman in na tsaya jira zan iya makara, nasan bata san da zanje Makarantar bane yasa bata yi da wuri ba" tana Maganar ya kafeta da ido, sigh yay taji yace sai tayi breakfast zata je ta kalle shi yanayin fuskar ta ya sauya, tunawa tay da ice cream d'in daya kawo mata ko roba d'aya bata sha ba tace mashi bari tasha ice cream da cin cin to, wani kallo yay mata ya d'an yamutsa fuska yace ya zata sha abu mai sanyi da safe ta yamutsa fuska a shagwa6e tace to ai lafiya lau in ta tsaya jira sai an kawo zata makara ne fa, shiru yay kaman bazai ce komai ba can yay mata alamar ta zauna da hannu, bayan ta zauna ya yunk'ura ya mik'e tana ta kallon shi ya nufi kopa ya fita, bayan fitar shi tana zaunen idanunta suka sauka akan pillow tay tunanin ta d'auke tunda tasan shi zai kai ta School d'in kuma daga can ba lalle ya dawo nan ba, mik'ewa tay ta nufi kujerar ta kai hannu ta d'aukko filon, wani abu ta ji ya fad'o akan k'afarta ta kai idanunta k'asa don taga minene, duk'awa tay ta kai hannu ta d'aukko abun, k'aramin kwali ne wanda ya d'aukko jiya ta bishi da kallo, daga yanayin sunan dake jiki da hotunan jiki ya nuna magani ne saidae ta kasa gane maganin ko na miye daga sunan shi amman daga yanayin hoton jiki ya nuna kaman na ciwon ciki ne don wani mutum ne a jiki ya daddafe cikin shi ya d'an duk'e sai kuma daga gaba gashi nan bayan yasha maganin a kwance yanata bacci harda d'an murmushi akan fuskar shi, jujjuya kwalin ta shiga yi a ranta tana raya Ya Haisam bai lafiya ne amman bata ga alama ba wane irin ciwon ciki yake yi, ranta ne ya bata ta bud'e k'ilan akwae leaflet a ciki sai ta duba k'ilan ta gane na ko wane irin ciwon ciki ne, har zata bud'en sai kuma wata zuciyar tace mata bafa kyau yin bincike hakan yasa ta fasa sai ma ta maida pillow d'in kawae ta tura maganin a karkashi don tana tunanin anan yake ya fad'o, bata dad'e sosae ba da komawa ta zauna sai gashi ya shigo hannun shi ruk'e da d'an babban tray ta bi shi da ido har yazo ya aje akan c-table, matsar mata yay da table d'in yace gashi nan ta kalli tray d'in sai kuma ta kalle shi ya koma ya zauna, hannu ta kai ta bud'e plate d'in da aka rufe wani plate nan take k'amshi ya bugi hancin ta taga indomie ce tasha vegetables harda soyayyun cinyoyin kaza guda biyu tayi gwanin kyau a ido daga gefe kuma Cup d'in tea ne an had'a shima an rufo shi, da alamun mamaki ta d'aga ido ta kalle shi ya jingina bayan shi yana kallon ta mamaki ta shiga yi a cikin ranta na badai shi ya dafa ta ba, hannu ta kai ta d'auki fork ta fara ci sosae tay mata dad'i, kasa jurewa tay tana cikin ci ta dakata ta kalle shi yana ta latsa wayar shi, "Amman kai ka dafa ta ne?" da k'yar ta tattaro kalmomin ta tambaye shi, shiru kaman bai ji tambayar da tayi ba har ta fidda ran zai amsa taga ya d'ago ido ya kalle ta taji yace ta tambayi Abincin mana, d'an tura mashi baki tay ta maida idon ta kan Abincin, tana cikin ci taji yace shi ya dafa akwai matsala ne, har saida ta maimaita Maganar tsabar mamaki ba wai don ya dafa matan ba sai don bata ta6a tunanin ya iya girki ba koda dafa tea ne, saida ta cinye ta duka farko ta rage yace mata wa zata bar mawa tana d'an murmushi tace shi d'an murmushi yay kawai ya gane wasa take mashi tunowa da can baya, naman ne ta rage ta kwashe kayan ta kai Kitchen, saida ta wanke komae ta d'ebi su dublan don ta kai ma su Fauzy harda ice cream ta d'aukar mata sannan ta koma Bedroom ta d'aukko jakar ta da takalma dama ta saka safa tun da tasa uniform. Bayan sun isa ya fiddo kud'i ya bata ba tay mashi musu ba don tasan ba maidawa zai ba tayi mashi godiya ta bud'e Motar ta fita, tun kan ta shiga aji wasu da suka ganta sukai shelar zuwanta, tana zuwa bakin Class d'in su Zainab suka fito da gudu suna mata oyoyo Amaryar su suka rungume ta tana ta masu dariya, bayan sun saketa ta tambaye su Fauzy suka ce bata kai ga zuwa ba suka nufi cikin ajin suna ta tsokanar ta wai k'amshin Amarci take gashi tayi Fresh ita dai sai murmushi take kawai, bata dad'e da zuwa ba Fauzy tazo tun daga bakin Class ta hango ta ta shigo da gudu tana fad'in k'awarta Amarya tana zuwa seat d'in ta rungume ta Fatun nata dariya, zama tay sai kallon Fatun take tana sakin murmushi tace "ai banyi tunanin zaki zo yau d'in ba, nayi zaton zaki k'ara kwana biyu kaman yadda na baki shawara" d'an girgiza mata kai tay alamar a'a, "wai badai duk Amarcin bane yasa baki magana" Fauzy ta fad'a baki bud'e Fatun ta sa dariya tace mata a'a, "Amarci dad'i, Wai kinga yadda kikai Fresh duka kwana ukku, gaskiya nima na fara jin son aure wllh" ta k'arasa tana dariya itama Fatuu dariyar take suna haka malamin su ya shigo, bayan anyi break sun fito ne Fauzy ke tambayar Fatuu wai ko wani abun na damunta ta lura da suna class kaman tana yawan yin tunani a sanyaye tace mata ba komai saidae Fauzyn bata yarda ba tace in wani abu ke damunta ta fad'i mata in na shawara ne sai ta bata barin damuwa ba zai mata magani ba har da ce mata ko bata yarda da ita bane tace mata a'a, ganin yadda duk ta damu da son jin ko wani abu na damunta yasa a sanyaye tace "ba wani abu ke damuna ba Allah Fauzy, kawai dai....na rasa gane kan Ya Haisam, gani nike bai so na kaman yadda ake hasashe kawai ya yarda yaci gaba da zama dani ne ba wai don yana sona ba" idanun ta ne suka ciko da k'walla da sauri ta fara k'ok'arin maida su, ajiyar zuciya Fauzy ta sauke duk da bata san dalilin da ya sa tace haka ba ranta ya bata wani abu, tambayar ta tay dalilin daya sa tace haka tay d'an murmushi tace mata ba komai kawae dai yak'i sake mata ne, hak'uri Fauzyn ta bata tace ita tana ganin a k'ara bashi lokaci k'ilan da dalilin hakan amman tana kokonton ace bai sonta kuma ya za6i cigaba da zama da ita to miye ribar hakan, ai indae dama ya aure ta tun farko don ya taimaka mata ne to ba dalilin da zai cigaba da zama da ita Fatun tace bata ganin ko don abunda ya faru yaga bai kyauta mata ba in ya rabu da ita yasa, Fauzy ta girgiza kai tace gaskiya bata tunanin hakan koda da hakan to akwae wani dalilin wanda kuma tana ganin so ne Fatun tay shiru kawai, Fauzy na son ta yi mata Maganar magunguna amman dalilin wannan Maganar yasa ta fasa, ana tashi Haisam yazo d'aukar ta saida Fauzy ta rakata har bakin Mota ta gaisa da shi sannan ta wuce Hostel su kuma suka tafi........ _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2068* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Har tuntu6e take yi tsabar sauri, tana zuwa part d'in su ta shiga parlor ta wuce Bedroom, tana shiga ta maida kopa ta k'ulle harda saka Key ta juya da gudu ta nufi gado ta Fad'a sai faman numfarfashi take ta zaro ido hannuwan ta har d'an kerma suke sai tuno abunda ya faru take Fuskar Hajiya Maryam na mata gizo, tafin hannunta ta kai ta rufe baki tasa Kuka, Sosae Senator yaji Fatuu ta burge shi da Hajiya na bashi Labarin ta da Haisam Fuskar shi d'auke da Murmushi, suna nan har aka yi La'asar ya tashi don yaje Masallaci yace mata daga can zai wuce G.r.a ya d'an huta, fuskar ta da murmushi tace to ba ga d'akinta ba in ya dawo ya kwanta ya huta yana dariya yace mata to ta bari zai zo ya kwana akan gadon nata itama dariyar take ta mik'e don taje tayi sallar itama, Lokacin da ta shiga cikin d'akin nata anan ta iske Hajiya Maryam aciki pacing up and down sam ta kasa zama tun d'azu abunda take kenan, sai ta zauna sai ta mik'e ranta a tsananin 6ace, Hajiya na shigowa suka had'a ido da ita ba tare data ce mata komai ba ta nufi hanyar toilet, Alwala tayo ta fito ta nufi cikin d'akin, saida ta shimfid'a abun salla sannan ta kai idonta kan Hajiya Maryam da ta zauna a bakin gado k'afar ta d'aya akan d'aya idon ta na kallon wuri guda ta cije le6en ta na k'asa tana d'an jinjina kai, ce mata tay bata ji an kira salla bane ba tare data kalle ta ba tace taji zatayi, saida Hajiya ta fara yin Salla sannan ta mik'e ta nufi Toilet, ita ta fara tashi bayan sun gama ta cire Hijab d'in jikinta ta aje a gefen gado ta koma ta zauna kaman yadda take d'azun sai faman d'an jijjiga jiki take tsananin bacin rai kwance akan fuskar ta, bayan Hajiya ta shafa Addu'a ta juyo ta kalleta na d'an wani lokaci ta d'an girgiza kai, tasan halin ta tana da d'aukar zafi sosae sam bata 6oye fushi, a nutse ta fara mata magana "Yanzu Maryam abunda kika aikata ma Yarinyar nan daidai ne, ita miye laifin ta a ciki ne, kusan fa ita akai ma ba daidai ba ma, an aureta bada sanin ta ba kuma sannan yazo ya hakke mata tunda ita bata san da ya aureta ba abu ya kai ga har da samun ciki yazo kuma ya 6are wanda hakan yasa ta a mawuyacin hali, in rai ya 6aci ai bai kamata hankali ya gushe ba sai a bi komai a sannu asa tunani, komai ki ka ga ya faru to dama can haka Allah ya k'addara, don haka sai mu d'auka dama Allah ya k'addaro Aure tsakanin su" Tunda Hajiyar ta fara Magana bata juyo ta kalleta ba sai da tay Maganar k'arshe sannan ta juya a zafafe tace "Pls Hajjaju stop saying that, komai sai ace kaddara, Yes an san komae sai Allah ya amince yake Faruwa amman harda sa kai, don uban shi in son taimaka mata yake ai akwae hanyoyi da yawa da zai yi hakan, Why not yayi amfani da kud'i akwai abunda basu yi bane balle kuma su da suke yan k'auye ma tuni zai sa a fasa yi mata auren in yay amfani dasu, kuma ma wai miye nashi na damuwa da wanda zata auran kowa ai da kalar k'addarar sa, watak'il in ta aure shi ya canza amman Saboda ya isa da kan shi shine yay gaban kan shi shiga isasshe ko, to zamu nuna mashi haihuwar shi akai ba a komae yake da iko da kan shi ba" tana huci ta k'arasa Maganar, d'an guntun murmushi Hajiya tay "kinga dae kenan Magana ta na kan hanya, kince kowa da kaddarar sa to suma hakan kaddarar su ce kenan shiyasa komai ya juye hakan sai kowa ya rungumi Al'amarin a matsayin hakan" wani kallo take bin Hajiya dashi ta yamutsa fuska cikin k'unar rai tace "Hajjaju na fahimci goya mashi baya kike shiyasa ma har ya samu k'warin gwuiwar cigaba da zama da ita, haba! ta ya zaki goyi bayan wannan kaskantaccen Auren, Auren wulakanci, in ma k'ara Auren zai yi ai wannan ba class d'in shi bace wllh, kuma ba kowa za'a wulakanta ba face Fanan taya ma za'a had'a ta kishi da wancan abun" sai huci take tayi mitsi mitsi da idanu, d'an murmushi Hajiya tay idonta akanta tace mata ba mace bace ita Fateemar kuma miye aibunta, d'an jim tay fuska a yamutse tana ma Hajiya kallo irin na baka zaci jin Magana daga bakin mutum ba, "Hajjaju wato na lura dae kin za6i faranta ma bare fiye da naki ko, kin sani matuk'ar auren nan aka ce ya d'ore ba wanda zai cutu irin Fanan, don Allah duka yaushe aka yi auren nasu da za'a ce har an yi mata kishiya, da mi zata ji ne da damuwar lalurar dake tare da ita ko kuwa da wannan damuwar da ake neman k'ara mata, wai ko don cikin da ta samu ne yasa kike goyon bayan auren, Saboda ance Fanan nada lalura ai ba yana nufin bazata haihu ba, tunda anata kokarin nema mata magani sai a bari zuwa wani lokaci aga in bata haihu ba sannan ai tunanin auro wata, kuma shi in ba don ya nuna irin halin nasu na maza ba da ba yan goyo bane ba har alk'awari yayi mata zai zauna da ita a halin da take ciki koda kuwa bata haihu ba shine tun ba'a je ko ina ba zai watsa mata k'asa a ido ya nemi tarwatsa mata zuciya wato ta mutu ma shi ba damuwar shi bane, to wllh bazan zuba ido ta cutu ba Saboda wata kaskantatta can" tana kaiwa k'arshen Maganar ta kai hannu ta warto wayar ta ta mik'e, har ta nufi hanyar k'opa sai kuma ta dakata ta juyo ta kalli Hajiya data bita da ido ta d'an sassauta d'aure fuskar da tay tace mata sun gama Maganar zata fita, d'an murmushi Hajiya tay ta sani duk irin zafin zuciyar ta mai d'a'a ce a gareta yanzu ma tasan Saboda tsoron abunda zai iya faruwa da Fanan yasa ta zauna tana ta mata Magana cikin 6acin rai kuma bata d'auki hakan a wani abu ba don ta san yadda soyayyar d'a da Mahaifi take, kai ta d'aga mata alamar sun gaman ta juya ta nufi kofa, cikin nuna ma kopar k'arfi ta bud'eta ta fuce, Kuka Fatuu tasha har ta gaji tay shiru don kanta, kiran sallar la'asar ya tada ita taje tayo Alwala tazo ta kabbara salla, bayan ta gama zaune tay kan abun sallar ta langa6ar da kanta jikin gado ta shiga duniyar tunani. Hajiya Maryam na fitowa daga d'akin Hajiya Visitor room ta nufa, tana shiga ta d'aga wayarta tana k'ok'arin yin kira ba tare data zauna ba, d'an kai da komowa ta fara lokacin da wayar da ta kira ta fara ringing , Haisam zaune kan kujera a cikin d'akin da yake aikin injiniyancin shi kira ya shigo wayar shi, hannu ya kai saman desk d'in gaban shi ya d'aukko wayar, bin screen d'in yayi da ido ganin mai kiran lokaci guda ya yanke ba lafiya tasa ta kira shi ba ba kamar da yake dare ne kuma yasan tasan lokacin da suke ciki, shima abu ne ya ishe shi bacci ya k'aurace mashi yasa shi zuwa wurin yay zaune yayin da Fanan ke d'aki tana bacci, saida kiran ya kusa yankewa yay picking ya kai wayar kunne, sallama yayi mata tayi mashi banza cikin cool voice d'in shi ya gaida ita aikuwa kaman tana jira a fusace tace "Ka rik'e gaisuwar ka ban so, ai bamu da girman da zaka gaishe da ni tunda kai isashshe ne ka kai kayi gaban kanka, ashe Haisam baka da Mutunci ban sani ba! mu zaka wulakanta ka nuna bamu kai ba a wurin ka, kai ka Haifi kan ka ne ko mu muka haife ka da har zakai Aure ba tare da sanin mu ba, da izinin wa kaje kai auren???" Shiru yay bai da niyyar tanka mata aikuwa hakan ya k'ara hasala ta cikin daka tsawa tace "bazaka bud'e baki kai man Magana ba don ubanka" d'an lumshe ido yay ya bud'e, in ba ya manta ba tunda yake ba'a ta6a zagin shi haka ba, slowly ya bata hak'uri yace yayi ne don taimako, a fusace tace "then what are u waiting for da baka saketa ba kaman yadda kuka tsaran? Mi ya zaunar da ita" shirun ya k'ara yi saida tace bai jita bane sannan yace "Hajiya ce ta hana" "Hajiya ce zata zauna da ita ko kai" d'an jimm yay sai kuma yace "I can't argue with her" shiru tay cikin ranta ta fara tunanin kenan ba don Hajiya ba zai saki yarinyar ne, d'an sassauta murya tay tace mashi shikenan zata yi Magana da Hajiyar he should be expecting her call kowane lokaci don ya saki Yarinyar, amsa mata yay da toh tace tasan Fanan bata sani ba to Kada ya sake ya bari ta samu labarin har zuwa lokacin da zai sake ta nan ma da toh ya amsa mata tay mashi sai da Safe ta kashe Wayar, bin wayar yay da kallo tun bayan daya cireta daga kunnan shi, can yay sigh ya fara latsa ta na d'an wani lokaci ya dakata ya zuba ma Screen ido kaman mai kallon wani abu..., tana ta zaune a wurin cikin duniyar tunani, a hankali take kai hannu tana goge yar kwallan dake zubo mata daga cikin idanuwan ta da har sun d'an kumbura, wayar tace ta fara ringing ta d'aga kai ta kallo ta a saman gadon, ganin zata iya jawo ta yasa ta kai hannu ta jawo tan ta kalli screen d'in, Abbas ne mai kiran nata har saida ta d'an ji sanyi dama duk yau bai kirata ba, d'aga kiran tay ta kara wayar a kunne muryar ta can k'asa tay mashi sallama, bayan ya amsa ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru, jin yanayin muryar ta yasa shi tambayar ta lafiya nan ma tayi shiru, ce mata yay ta fad'a mashi inda matsala cikin rawar murya ta fara fad'i mashi duk abunda ya faru, sosae Muryar Abbas ta bayyana rashin jin dad'in abunda ya farun ya shiga bata hak'uri daga baya ya tambaye ta game da reaction d'in Senator nan ta gaya mashi komae tana gamawa ya furta "Alhamdulillah, dama nasan ta 6angaren shi ba za'a samu wata matsala ba, itama Momy Maryam d'in kawae tana taya d'iyar ta kishi ne ba wani abu ba, so kar kisa damuwa a ranki in sha Allah komai zai daidai ta na d'an lokaci kad'an ne" a hankali ta amsa mashi da to, "Yanzu kin ci Abincin ne?" D'an girgiza kai tay tace mashi a'a, "Ya zaki sa damuwa har ta hana ki cin Abinci hakan ai sai wani ciwon ya kama ki, ba wani Abincin da zaki ci ne?" bashi amsa tay da eh tace amman bari taje ta dafa indomie yace ta d'an jira ba sai ta dafa ba, har zai cutting kiran sai kuma taji yace bata tambaye shi Mijin ta ba, tura baki tay kaman ya gani yay yar dariya yace koda yake ai yanzu tafi shi kusa da shi daga haka ya katse, wayar na ruk'e a hannunta ta maida kan ta jingina da gadon kaman yadda take ada ta runtse idanu ta sake fad'awa duniyar tunani wanda duk na Haisam ne, gama wayar su da Abbas bada jimawa ba aka k'wank'wasa kopa ta bud'e idanunta ta kallo kopar zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri, mik'ewa tay a d'arare ta nufe ta hannun ta har yar rawa yake da zata bud'e, tana bud'ewa suka had'a ido da Saude tana mata murmushi itama ta k'ak'alo d'an murmushin tayi mata a sanyaye ta gaishe da ita, hannu ta kai ta kamo hannunta guda suka nufo cikin parlon, akan kujera ta zaunar da ita itama ta zauna nan ta fara lallashin ta tace ita bata ma san abunda ke Faruwa ba don tana baya sai yanzu da aka kira ta a waya ai da tun d'azun ta kawo mata Abincin kuma itama ai data kirata sai tazo ta kawo mata amman zama da yunwar ga damuwa ai sai suyi mata illa, tasata gaba Saude tay saida tasa taci Abincin sosae daga baya ta k'ara kwantar mata da hankali kafin ta tafi. Bayan Hajiya Maryam ta yi waya da Haisam a bakin gadon cikin d'akin ta zauna hannunta ruk'e da wayar ta d'aura ha6arta saman shi, tunanin ta yadda zata 6ullo ma Hajiya har ta amince a saki Fatuu ta shiga yi, ta d'an d'auki lokaci a haka kafin ta idasa hayewa saman gadon ta kwanta da tunanin zata yi mata Magana anjima. Da daddare bayan kowa yayi shirin kwanciya Hajiya Maryam ta nufi d'akin Hajiya ta shiga da sallama Hajiya dake zaune a bakin gado sanye da kayan bacci idanunta na sanye cikin glasses tana duba wayarta ta amsa mata ta nufo ta, a bakin gadon daga d'an gefe ta zauna tayi mata sannu da hutawa da d'an murmushi Hajiya data d'ago kai ta amsa mata, shiru suka d'an yi Hajiyar ta maida idon ta akan Wayar ita kuma tana kallon k'asa, juyowa tay ta kalli Hajiya tace mata dama Magana take son su yi ne ta d'ago tare da jinjina mata kai idonta a kanta alamar ita take jira, "Mun yi Magana da Haisam ya fad'a man ke kika hana ya saki Yarinyar can, kinga kenan shima ba wai son zaman yake da ita ba kawai yayi maki biyayya ne don haka ni ina ganin tunda shine mai zama da ita kuma ba so yake ba sai ki bashi dama ya rabu da ita hankalin kowa ya kwanta" d'an murmushin dattako Hajiyar tay jin abunda aka ce Haisam d'in yace, gyara zaman glass d'inta tay idonta akan Hajiya Maryam a nutse ta fara magana "Kaman yadda kika ce biyayya yay man yaci gaba da zama da ita to kema ina son kiman biyayya ki bi yadda nike so, ki yi masu Fatan Alkhairi a auren shikenan komai ya wuce" wani kallo take bin ta dashi baki bud'e alamar Al'ajabin Maganar tata rai 6ace tace "to wai Hajjaju akan mi zaki mashi dole ya zauna da ita ne, ya aureta don taimako da nufin zai saketa sai a sa ya saketan barin shi ya ci gaba da zama da ita ba komai zai ja ba sai 6acin rai" girgiza kai Hajiya ta fara yi "Ba zai rabu da ita ba Maryam dole yaci gaba da zama da ita, in kece ko Fanan a matsayin ta bazan so abunda kike so mata ba" ta k'are Maganar tana girgiza kai bakinta a kwa6e, yarfa hannu tay ta yamutsa fuska tamkar zata saka kuka cikin breaking voice tace "Wai Hajjaju ya kika za6i faranta ma bare ne fiye da naki, kin san idan Fanan ta samu labarin nan ba K'aramin mawuyacin hali zata shiga ba, dame zata ji don Allah ko so kike zuciyarta tay bursting ne, sai nike ganin kaman kin fi damuwa da ita yarinyar ma fiye da Fanan, in don haihuwa ne a ba Fanan d'in time mana kaman yadda nace d'azun duka ai ba dad'ewa sukai da yin auren ba ko" shiru Hajiya ta d'anyi still idanunta na akan ta sai faman huci Hajiya Maryam din take ta gumtse baki idanunta sun Kad'a da gani kiris ya rage ta saka kuka, cikin kwantar da murya Hajiya tace "idan aka zo Maganar Adalci Maryam baka duba bare ko naka indai Adalcin tsakani da Allah za'ai, koda Fateema take 6are ai itama tana da dangi kuma suna son ta suna son farincikin ta, sannan Maganar halin da Fanan zata iya shiga ita ai Musulma ce kuma inada yak'inin tana da cikakken imani hakan kuma na nufin ta yadda da k'addara mai kyau ko akasin hakan don haka in sha Allahu ina sa ran zata rungumi hakan matsayin k'addara kaman yadda ta rungumi ta lalurar ta ake ta neman Magani" Kuka ne ya taho mata tace "Hajiya kar azo ai dana sani, na fad'i maki har Alk'awari fa yayi ma Fanan kan bazai k'ara aure ba koda bata haihu ba kuma akan hakan suke zaune in taji ya k'ara auren nan har matar ta samu ciki mi kike tunanin zai iya biyo baya don Allah, dama kuma ga yanayin ta" cewa Hajiya tay in sha Allahu ba abunda zai faru kuma tasan lokacin da yay mata Alk'awarin ya riga ya auri Fatuu ne don haka shi yasan yadda zai rarrashe ta, a k'arshe ta tabbatar mata da indai ba yarinyar ce tace bata son zama dashi ba to wllh ba zai saketa ba, mik'ewa tay zumbur ta nufi hanyar fita Hajiya na kallonta ta kwa6e fuska. Bayan ta koma d'aki kai da komowa ta shiga yi ta cize baki, abun ya matuk'ar d'aure mata kai yadda Hajiya ta kafe, a tunanin ta koda cewa akai Fanan bata haihuwa kwata kwata Hajiya bazata matsa ayi mata kishiya ba tunda abun na gida ne, dogon tunani ta shiga a k'arshe zuciyarta ta bata wani tunani kan dalilin Kafewar Hajiyar, A daren Hajiya Maryam ta yanke komawa lagos a yadda take ji ba don dare yayi ba da bazata ma kwana ba, a daren tayi duk wani cuku cukun tafiya saidae ba jirgin da zai je Lagos direct washe gari sai dae Kano ta yanke tafiya Kano d'in daga can sai ta hau na Lagos, a ranar baccin ta ragagge ne Saboda tsabar 6acin rai har gani tay daren yayi mata tsawo, Washe gari tana gama sallar Asuba ta hau shiri duk da bada wuri jirgin nasu zai tashi ba, Misalin k'arfe takwas na safiyar ta kira Senator take sanar dashi zancen komawar tata, tambayar dalilin tafiyar ta a yau yayi tace mashi hakanan ta canza shawara yace da yaushe jirgin nasu zai tashi ta fad'a mashi, ce mata yay in ta shirya kafin ta wuce ta same shi a G.r.a tace to, Misalin k'arfe tara da yan mintuna ta gama shirin ta tsaf cikin wani dandatsetsen leshi ruwan Madara da fulawowi maroon da golden brown, ba K'aramin had'uwa leshin yay ba idanun kansu zasu shaida maka tsadar shi don kuwa d'an dubu d'aruruwa ne, a da tazo da shirin fita taje wasu wurare kafin ta koma, gyale da jaka da takalma maroon ta saka ta fiddo wasu sarka da yan kunne da yan hannu na zinari ta saka ta fito a babbar macen ta, tana janye da d'an madaidaicin trolley d'in kayanta ta fito, Bedroom d'in Hajiya ta wuce bayan ta tura K'opar da yar sallama ta shiga, ganin Hajiyar bata cikin d'akin yasa ta kai idon ta wurin toilet nan ta gane tana ciki ta nufi bakin gado ta zauna, bada jimawa ba ta fito idanunta suka sauka akan Hajiya Maryam d'in ta nufo gadon itama ta zauna, kallonta tay ta gaishe da ita bayan ta amsa ganin tayi shiru yasa ta tambaye ta lafiya ta ganta cikin shiri da safe ko wani wuri zata ta girgiza mata kai kafin tace zata koma ne, d'an jimm Hajiya tay sai kuma tay d'an guntun murmushi tace "an 6ata maki rai shine kikai Fushi zaki tafi kenan" shiru bata ce mata komai ba idanunta na kallon k'asa, Hajiya ta k'ara cewa "shikenan bazan hana ki tafiya ba Allah ya tsare, kin yi Breakfast ne?" Girgiza mata kai tay tace in ta isa tayi ta gyad'a kai, d'an shiru sukai can ta mik'e ta kalli Hajiyar tace ta wuce, Addu'ar Allah ya tsare ta k'ara yi mata ta kama trolley d'in ta juya, har ta kusa k'opa Hajiya ta kira sunanta ta dakata ta juyo, "Kiji tsoron Allah, Kada soyayyar d'a ta tunzura ki kice zaki cutar da yarinyar can domin duk abunda kai ma d'an wani kaima za'ai ma naka ne, idan ranki ya 6aci Kada ki bari hankalin ki ya gushe, ki d'auki Al'amarin a matsayin Alkhairi sai kiga ya kasance hakan, tada hankalin ki shi zai taimaka wurin faruwar abunda kike gudu, ki gaida man Mazajena da K'awaye na" d'an jimm tay tana kallon ta kaman bazata tafin ba can ta furta mata ta gode ta juyo tana janye da trolley d'in ta fice, Itama Fatuu a jiya bata yi wani baccin kirki ba wanda ta samu yake d'aukar ta ba wani mai nauyi bane gashi cike da mafarkin abunda ya faru tsakanin ta da Hajiya Maryam, kiran sallar farko na Asuba ta farka taje tayo Alwala, bayan ta fito ta zo ta kabbara raka'atanil fajr data gama ta d'aura da karatun Al'qur'ani har lokacin sallar Asuba yayi, bayan ta gama yin sallar kwance tay akan prayer mat d'in cikin sa'a bacci ya d'auketa, Misalin k'arfe tara saura ta farka jin jikinta duk ba dad'i yasa ta tafi toilet tayo wanka, bayan ta fito ta shirya cikin riga da wando, wandon skin tight ne bak'i sai rigar ta kai mata har gwiwa tana da gajeran hannuwa jikinta bak'i da fari ne, bata sa hula ba sai gashinta dake fake yayi tumm, bayan ta gama gado ta koma ta zauna tay tsuru, tana jin yunwa amman fargabar fita take sai kawai ta kai hannu ta d'auko wayar ta daga kan Bedside drawer ta fara dannata, bata dad'e da zama ba aka k'wank'wasa kopar ranta ya bata k'ilan Saude ce amman duk da haka saida taji tsoron bud'ewa, bayan ta bud'e taga Sauden ce suka gaisa harda ce mata tayi kyau inama Angonta na nan sai yafi ganin kyaun kwalliyar yar dariya tayi tace ita ai ba wata kwalliya tayi ba, daga baya tace mata ta fito tayi Breakfast gashi can ta kawo tace to, ce mata tayi ta fito suje taci a gabanta kaman jiya tay yar dariya tace mata zata ci Allah sannan ta fito, Hajiya Maryam na fitowa sukai kacibus da Saude data dawo daga part d'in su Fatuu, gaishe da ita tay ta d'aga mata kai kawai ta mik'a mata trolley d'in tace ta biyo ta dashi, suna fitowa harabar gidan tay mata nuni da parking space da hannunta tace ta kai shi can ta je ta kirawo mata Tk tace mashi ya jirata anan, amsa mata da to Saude tay ta nufi parking space d'in tana tafiya tana waiwayen ta ganin ta nufi part d'in su Fatuu, Har Fatuu taje dining area d'in ta tuna da bata d'aukko cup da sauran abunda zata buk'ata ba ta juyo ta nufi Kitchen, hannunta ruk'e da plate da tea cup da spoon a saman shi ta fito zata koma dining, tana fitowa daga corridor zatai kwanar dining area taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta suka shiga cikin na Hajiya Maryam, wani mummunan Fad'uwa gaban ta yay ba shiri ta saki abun hannunta nan take cup d'in yay tsalle ya fad'o ya d'aki tile ya tarwatse, tsaye tay cak ta zaro idanu zuciyar ta na wani irin harbawa ganin yadda Hajiya Maryam d'in ke jefa mata wani kallo fuskar ta ba d'igon annuri, daurewa kawai Fatuu ke yi amman jikinta har ya fara rawa daga ta ciki a yadda take ji tamkar ta watsa da gudu ta shige d'aki, cikin parlon ta k'araso tana tafiya a k'asaice ta tsaya a tsakiyar parlon, d'an d'aga murya tay tace ma Fatun ta k'araso wurinta ne ta d'an girgiza mata kai kafin ta fara tahowa cikin parlon a d'arare, a d'an nesa da ita ta tsaya murya na d'an rawa ta gaishe da ita tay mata banza still idanun ta na akanta ba alamun sauk'i a cikin su, cike da yarinta ta Fatuu tay tunanin wai ko don bata ce mata ta zauna ba yasa tay tsaye cike da k'arfin hali tace mata ta zauna aikuwa tamkar ta watsa mata wuta ta k'ank'ance ido a fusace tace "Samun wuri! Wato Ni zaki kalla ki ce ma in zauna! daga gidan ku aka kawo kujerun ko kuwa?" Da sauri ta girgiza mata kai a hankali tace tayi hak'uri....a zafafe ta amshe "Ke zan ce ma kiyi hak'uri ki tattara ki bar gidan nan don kuwa bai dace da ke ba baki samu kar6uwa ba, idan kuwa kika k'i to kuwa kin tattaro ma kan ki abunda bazaki iya d'auka ba, in ba ganganci irin naku ba k'auyawan mutane ke ko a mafarki kin isa kiyi kishi da d'iyata balle kuma a zahiri, wato har kuna da k'warin gwuiwa har haka ko? Fad'a man Asiri kukai ma shi don yaci gaba da zama dake ko??" a rud'e Fatuu ta hau girgiza mata kai aikuwa ta daka mata wata uwar tsawa "K'arya kike! dole Asiri ku kai mashi shi da Hajiya shiyasa har ta goyi bayan yaci gaba da zama dake" kuka Fatuu ta saka tana fad'in wllh su ba Asiri sukai masu ba Hajiya ce tasa yaci gaba da zama da ita, wani kallon rashin Arzik'i take bin ta da shi tun daga sama har k'asa, ada Haushin ta take ji yanzu kuwa abun sai ya juye zuwa tsana can ta buga wani uban tsoki ta d'aga yatsa tana nunata tace "To zan baki shawara tun cikin Arzik'i ki fita daga rayuwar shi, kice baki son cigaba da zama da shi idan ko ba haka ba to rayuwar ki zaki jefa a matsala don kuwa provided that am alive d'iyata bazatai kishi da ke ba da kowa ma, idan har baki d'auki shawarata ba kika fita daga rayuwar su ta lalama ba to zaki danasanin da har ki mutu bazaki daina ba don sai na salwantar da kaskantacciyar rayuwar ki, ta yadda ko kallon gidan nan aka baki shawarar kiyi sai kin zagi wanda ya baki shawarar balle ta kai ki ga cigaba da zama a cikin shi, kinsan Asirin ma mataki mataki ne iya nauyin jakar mutum iya girman wanda za'ai mashi, if u wise enough nasan zaki abunda ya dace" daga haka ta juya, har tayi d'an taku ta dakata ta juya ta kai hannu ta ruk'e kunnanta guda ta furta "idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira!!!" daga haka ta nufi k'opa ta fuce, Fatuu na ganin ta fita ta juya da gudo ta nufi Bedroom, Lokacin data fito bakin part d'in su a parking space ta hango Tk tsaye jikin Mota har ya saka trolley d'in nata ciki, da yatsa tay mashi alamar ya fito da Motar ta tsaya a wurin, yana tsayar da Motar ta bud'e baya ta shiga yaja suka fita su Officer na d'aga mata hannu a K'ok'arin su na su gaishe da ita don ta saba yi masu Alheri bata ba Tk Umarnin ya tsaya ba hakan yasa ya wuce, Suna zuwa gab da gidan su Fatuu ta nuna gidan tana tambayar Tk nan ne gidan su waccan yarinyar da aka kai gidan Hajiya ko yace mata eh, Umarnin ya tsaya a gaban gidan ta bashi, bayan ya tsaya ta bud'e kopar ta fito tace mashi tana zuwa, cike da isa ta nufi gidan Tk dake kallonta ta cikin glass ya girgiza kai a fili ya furta "Allah ya kad'e fitina", a bakin kopar shiga cikin gidan ta tsaya tana bin tsakar gidan da yake wayam ba kowa da kallo, Sallama tayi shiru ba'a amsa ba hakan yasa ta d'aga murya tace "ina masu gidan nan?" Amadu ne ya fito daga cikin d'akin shi yana sanye da jallabiya, wani kallon rashin Arziki ta bi shi dashi shima kallonta yake don ya ganeta, gaishe da ita yay bata amsa ba tace mashi ina take da alamun rashin Fahimta ya tambaye ta wa ya lura da yanayin ta kaman ba Arzik'i, "Kai da waye a gidan?" Ta tambaya ta yamutsa fuska, kafin ya bata amsa gwaggo ta fito daga cikin d'aki hannunta ruk'e da tsintsiya dama shara take shiyasa bata ji sallamar ta ba, juyawa Hajiya Maryam tay ta kalli Gwaggo data tsaya bakin k'opa tana kallon su don ta lura kaman ba lafiya ba, "In k'araso ne?" Hajiya Maryam d'in ta tambaya tana kallon gwaggon shekeke, aje tsintsiyar da parker gwaggo tay ta nufo su, daga gaban Hajiyar ta tsaya da k'ak'alallen murmushi don tana kallon Fuskar ta tasan akwai matsala, gaishe da ita tay kaman bazata amsa ba sai kuma kaman an mata dole ta amsa daga haka gwaggo tayi shiru, d'an matsowa gaba tay yadda gwaggon zata jita da kyau, cikin isa ta fara Magana, "Mun ji abunda ya faru tsakanin d'an mu da jikar ki, to na zo inji cigaba da zaman su tare na minene? Taimakon ta yay to don mi zaku goyi bayan su cigaba da zama ko baku san yana da Mata bane?" Shiru gwaggo tay kanta k'asa abunda take ta fargaba game da Auren kenan don sarai tasan wacece Hajiya Maryam, cigaba tay "in dai kunsan halacci to bai kamata ku goyi baya ba, tun farko yakamata ace kun yi Magana akan ya saketa kaman yadda ku kai da shi, saidai kuma in dama akwae wata a k'asa kuna so kuyi amfani da damar don cimma wata manufa, to idan dai hakane wannan ba matsala bane ki fad'i man ko nawa kike so zan baki ta ruwan sanyi ki raba jikar ki da mijin Y'ata don bata kai tayi kishi da ita ba balle har ta zame mata matsala!" Yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke cikin kwantar da murya ta fara bata hak'uri tace ita wllh basu da wata manufa akan auren hasali ma itama bata goyi bayan auren ba tun da farko kawae don abun ya juye ne kuma Hajiya ta nuna tana so, a zafafe ta katseta da fad'in "tunda baki goyi baya ba sai kema ki nuna baki so, ba jikar ki bace ke kike da cikakken iko da ita!" D'an jim gwaggo tay yanayin fuskar ta ya sauya a sanyaye tace "Kiyi Hak'uri, Hajiya tana da girma ne a wuri na bazan iya musa mata ba" tamkar ta gaya mata magana taji a hasale tace "to kin mata biyayya don tana so mu kuma sauran dangi yanzu bamu so ba muyi Na'am da auren ba don haka bazamu kar6e ta ba sai ki maido abun ki in dai da gasken ba ki da wata manufa akan auren, bijire ma hakan daidai yake da bijirema Farincikin kowannan ku, zan iya k'arar da duk wani abun da na Mallaka akan bijirema hakan don kuwa ba zan ta6a zuba ido wata kaskantatta ta zama shamaki ga farincikin Y'ata, tana son Mijinta shima kuma yana son ta don haka basu buk'atar wata ta shigo rayuwar su, a shawarce sai kiyi abunda ya dace" ta k'are Maganar tana jinjina kai had'i da kanne ido, ba K'aramin 6aci ran Amadu yay ba ganin yadda take ta gaya ma Mahaifiyar shi Magana daurewa kawai yake yana danne zuciyar shi, tana zuwa ga6ar data kira Fatuu da Kaskantatta yaji bai iya jurewa ya matso inda suke rai 6ace yace "Hajiya gaskiya ita ba kaskantatta bace, don tana talaka hakan ba yana nufin bata da galihu ba, a wurin Ubangiji duk d'aya muke wanda yafi tsoron shi yafi bauta mashi shi ya fi ba wai mai kud'i ba ko nasaba kawai mutane ne ke bambantawa, in Allah yayi mutum mai kud'i ba hakan na nufin yafi son shi ba ko rayuwar shi tafi amfani ba haka talaka ma ba yana nufin Allah bai son shi ba ko rayuwar shi bata da amfani, ki sani gaba d'ayan mu Allah yayi mu a yadda muke ne don mu bauta mashi don haka gaba d'ayan mu rayuwar kowa talaka ko mai kud'i nada amfani, kuma Maganar aure ai bamu muka sa ya aureta ba, hasali ma bamu san yadda akai ba saidai muka ji zai aureta balle kice ko dama da niyya, sannan Maganar zaman su ma bamu muka rok'a ba tun farko shi ya k'i sakin ta aka zo kuma aka buk'aci zasu ci gaba da zama tare Saboda biyayyar mu ga wadda ta buk'ata muka amince, in zaki ga laifin mu kan hakan shi miyasa bazaki ga laifin shi ba da tun lokacin bai bijire ya nuna bazai cigaba da zama da ita ba, mi yasa tun farko bai saketa ba kaman yadda akai dashi ba, Maganar hallaci kuma ai shi muka yi, ya aureta don ya taimaketa daga baya kuma an buk'aci suci gaba da zama a tare in muka k'i ai kinga mun yi butulci kenan amincewar da mukai kuma hallaci mu kai domin d'an halak shi yake maida Alkhairi da Alkhairi, Yanzu tunda baku amince da auren ba duk miye abun zuwa da tada jijiyar wuya kusa ya sake ta mana........! A fusace ta kai hannu zata wanka mashi mari ya goce Fuskar shi a tamke yana huci nan da nan Fuskar shi tay jajir kaman an watsa jini abunka da Fari, itama Hajiya Maryam d'in huci take tana mashi wani kallo mai cike da tsantsar 6acin rai zuciyarta tana boiling da burning a lokaci guda, cikin wata irin murya ta nuna kanta da yatsa manuni tace "ni kake gaya ma magana haka!!!" D'an tura baki yay yace "ni ba Magana na gaya maki ba saidai in ke kika d'auka haka amman duk abunda na fad'a ai daidai ne, ikon baro gidan nata na a hannun ku sai ku sa ta......." Tsawa gwaggo ta kwatsa mashi cikin harshen fulatanci tace ya bar wurin, wani kalan murmushin yaro bai san wuta ba sai ya taka Hajiya Maryam tayi tace "ki k'yale shi, yay man duk rashin kunyar da ya iya ai gada yay tun daga tushe, kowa ya san baku da kunya ai, bama iya hakan kuka tsaya ba gashi nan kun addabi K'asar mu" idonta da suka sauya kala akan shi tay Maganar nan da nan idanun gwaggo suka ciko da k'walla, nuna shi tay da yatsa tace "Ni ba sa'ar yin ka bace, kaff dangin ku ma ba sa'ar yi na, idan kaci gaba da yi man rashin kunya You will definitely find ur self behind BARS....!!!" A tsiyace ta furta Kalmar Bars d'in ta cize hak'ora, Shiru yay bai ce komai ba gwaggo na girgiza mashi kai alamar kar ya tanka sai huttai yake kamar wanda yay gudu da gani dai ba k'aramar zuciya gare shi ba, juyawa tay kan gwaggo ta had'e yatsanta biyu suna making sound tace "Zan yi komae don Farincikin Y'ata in kuma tabbatar bata samu wata matsala ba in kin so zaki iya yin hakan ga Jikar ki......." Tana kaiwa nan ta juya cike da tafiyar isa ta nufi hanyar k'opa ta fice........ [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: ASM Bk2067* _Destiny may be delayed but cannot be changed...._ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Tana zuwa bakin corridor ta hango shi zaune akan L-shape inda Haisam ke zama, da sauri ta maida idanun ta k'asa ganin ya zuba mata ido, a d'ayan side d'in ta zauna sai lokacin ta d'ago ta kalle shi still kallon ta yake a sanyaye ta gaishe da shi ya amsa, shiru suka d'an yi kafin taji ya fara magana, "dama mun had'u da H,Zakee a Airport ne ban ga kin rako shi ba har nike tambayar shi kina ina yace kina gida shine nace bari in zo mu gaisa" d'an d'agowa tay ta kalle shi da k'ak'alallen murmushi bata ce komai ba, shiru suka d'an k'ara yi ganin yanayin ta yasa shi cewa "Mom Zarah ko akwae wani abu ne u look abnormal" k'walla ne suka taho mata da sauri ta maida fuskarta k'asa had'i da girgiza mashi kai alamar babu komae, bin ta da ido yay kaman mai nazarinta can ya kira sunanta ta amsa ba tare da ta kalle shi ba yace ta d'ago, saida tay d'an jimm kafin ta d'an d'ago suna had'a ido k'wallan suka zubo mata sharr kawae sai tasa mashi kuka ta kai hannu ta rufe bakinta, a d'an rud'e yace "Subhanallahi, Mom Zarah Mike faruwa ne pls tell me" girgiza mashi kai ta hau yi cikin kukan tace mashi ba komae bata lafiya ne, tambayar ta yay Mike damunta tace kan ta ke ciwo, shiru ya d'an yi yana kallon ta ya cije lower lip d'in shi can yay sigh yace "ba gaskiya kika fad'a man ba Mom Zarah, in har baki lafiya na tabbatar H,zakee bazai tafi ya barki a halin ciwo ba koda kuwa baki fad'a mashi cewa baki lafiya ba nasan zai yi noticing don yana d'aya daga cikin Mutanen da suka karance ki sosae kusan ma zan iya cewa yafi kowa karantar ki, so don't hesitate ki fad'a man in akwae wata matsala" cire hannun data rufe bakin tay ta fara goge k'wallan tana yi tana kallon shi tana d'an bud'e baki, gaba d'aya tama rasa to mi zata ce mashi bata san ta ina zata fara ba, "Ko mun fara 6oye ma juna abu ne?" Cikin muryar kuka tace "ba kai ne ka fara ba, ka 6oye man cewa shi miji nane" d'an shaking kan shi yay tun a Asibiti ya fahimci bata ji dad'in abun ba, "am very sorry for dat Mom Zarah, kaman yadda na fad'a maki haka aka tsara so bai kamata ace na fad'a maki ba tunda bamu san yadda Al'amarin zai kasance ba, duk da muna fatan auren ya d'ore ba lalle hakan ya faru ba kuma kinga in kika sani sai kin fi shiga mawuyacin hali fiye da farko, da naga bai sake ki ba kaman yadda aka tsara lokacin na fara sama rai na auren zai d'ore, a lokacin da abu ya shiga tsakanin ku da ace kin fad'a man da tabbas zan bayyana maki komai ne to amman sai baki sanar man ba kema kika 6oye man har abu mara dad'i yazo ya faru, amman nasan haka Allah ya k'addaro komae ba mu isa mu canza ba, yanzu shikenan abar shi a munyi ma juna laifi, kiyi hakuri nima kuma nayi hakuri sai muci gaba kaman farko, in kina da wata matsala feel free ki fad'a man ta yuwu in iya taimaka maki ko yaya ne, kinsan ance a Problem shared is a problem half solved" idon ta a kanshi tana ta kikkifta su a kokarin ta na ta dakatar da cigaba da yin kukan, ce mata yay yana Jin ta ta fad'i mashi Mike damun ta ta fara motsa baki cikin karyayyar murya tace "ba wani abu bane Ya Abbas, kawai dai na fahimci Ya Haisam bai sona ne, ya za6i yaci gaba da zama dani ne don dalili biyu, ko don abunda ya faru tsakanin mu ne yana ganin in bai cigaba da zama dani ba bai man Adalci ba ko kuma k'ilan Hajiya ce ta matsa mashi amman ba wai don yana son yin rayuwar Aure dani bane" da k'yar take tattaro kalaman take fad'i mashi, shiru yayi daga Maganar da tayi ya fahimci komae dama kuma tafiyar Haisam d'in tasa shi kokonton in wani abu ya shiga tsakanin su, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yama rasa ta ina zai fara shi kanshi ya rasa gane ma Haisam d'in game da auran, jin yayi shiru yasa Fatuu cigaba da Magana a sanyaye "I decided to get out of his life tunda ba son zama yake dani ba ni bazan so in zame mashi matsala ba, yayi man dukkan Alkhairi a rayuwata bai kamata in hana mashi kwanciyar hankali ba" girgiza kai Abbas yay "kar kice haka Mom Zarah nasan dole ki shiga damuwa game da hakan amman ina ganin mu bashi lokaci tunda kinga duka sati guda kenan da kasancewar ku tare" da alamun bacin rai tace "to Ya Abbas wane lokaci zamu bashi abunda komai a bayyane yake da yana sona ba zai tafi ya barni ba, koda ta kama ma ya tafin ai a k'alla zai man bayani kan dalilin tafiyar da kuma lokacin da zai dawo, amman fa jiya da daddare kawai yace man wai zai koma kuma yau d'in yay tafiyar shi" idanunta ne suka kawo ruwa da alama abun ba k'aramin 6ata mata rai yay ba, hannu ta kai ta goge k'wallan tace "gara mu rabu kawai tunda na gane his heart belongs to his wife alone ni na hak'ura, da ai har na hak'ura dashi na amince ai man auran abun yay turning haka, ni yanzu ya Abbas ka taimaka man kasa ya sake ni kawai, dama yace duk abunda nike so in maka magana, to ka fad'i mashi ya sake ni don Allah kaga sai suci gaba da rayuwar shi da Matar shi cikin farin ciki ba tare dana takura su ba, kaga bama sai ya dawo ba" fuska a kwa6e ta k'arasa Maganar Abbas dake kallonta ya d'an yi guntun murmushi don ba abunda ke acikin Maganar tata face sheer jealous, sigh yay "kar muyi saurin yanke mashi hukunci Mom Zarah, mu dai k'ara bashi lokacin kiyi hakuri, ina d'aya daga cikin Mutanen dake fahimtar shi sosae amman da yawan lokutta is very difficult to understand him completely, ni raina na bani shima yana son ki don kuwa H,Zakee adalin Mutum ne zan iya rantsuwa akan hakan, indai yasan zai aure ki ya takura rayuwar ki bazai ta6a amincewa yaci gaba da zama dake ba so mu bashi lokaci, in har ya dawo komai bai canza ba na maki Alkawarin da kaina zan je wurin Hajiya in fayyace mata komai game da zaman ku na tabbatar zata raba ku bazata goyi bayan a cutar da wani ba" shiru tay taji ta amince da Maganar ta shi, tambayar ta yay hakan yayi mata ta d'aga mashi kai, lallashinta ya shiga yi yana kwantar mata da hankali har ta d'an saukko, tambayar ta yay yaushe zasu yi exam ne tace mashi kafin Azumi yace to ta dage tunda Azumin ya taho kar tasa damuwa a ranta har tazo ta samu matsala tace mashi to, shiru suka d'an yi can ta mik'e tace bari ta kawo mashi lemu ya dakatar da ita yace daga gida ya fito yaje Airport bai jin k'ishi tace to bari ta kawo mashi cincin nan ma yace mata ta barshi ai an basu da yawa sun ci sosae, duk da hakan saida ta tafi tana fad'in bari ta kawo mashi ya kaima su Abdul ta nufi hanyar corridor yabi ta da kallo har ta shige sannan ya d'an girgiza kai a fili ya furta "DESTINED HEART", bada jimawa ba ta dawo ruk'e da leda ta d'aura akan c-table ta koma ta zauna, rok'on shi tayi kan ya kawo mata Abdul ya zauna na wani lokaci ya nuna mata yanzu in ya kawo mata shi aiki zai zamar mata tunda ba hutun school akayi ba kuma itama gashi tana zuwa Makaranta amman ta bari in akayi hutu yayi mata Alk'awari zai kawo mata shi har hutun ya k'are ta ce to, shiru ta danyi sai kuma tace "yace duk abunda nike so kai zan tambaya yanzu in ina son fita fa?" D'an murmushi yay yace ina zata ne tace a'a tana nufin in fita ta kama ko zuwa gida haka, still murmushin yake yace ba wani abu duk inda take so ta je tunda yasan bazata je inda bai kamata ba, daga baya ya mik'e yay mata Sallama yace zai je su gaisa da Hajiya tace ya gaida su Aunty Feenah, bayan tafiyar shi d'aki ta koma ta kwanta rub da ciki ta fad'a duniyar tunani wanda kusan duk na Haisam ne, can ta mik'e ta d'aukko wayarta ta shiga cikin gallery, tsofaffin hotunan su ta shiga gani wanda yawanci duk shi ya tura mata a ranta ta rink'a jin inama ace irin rayuwar nishad'in da suke har yanzu kenan, a hankali take kai hannu tana goge k'wallan dake zubo mata daga baya ta kife wayar tay lamo akan gadon, tana haka har Magrib sannan ta mik'e don tayi salla jikinta duk jin shi take kaman na wadda ta tashi daga ciwo. Haisam ya sauka lafiya tuni dama yaje ne don ya duba jikin Mahaifin shi kafin ya wuce, ya iske ya samu sauk'i sosae dama ciwo ne kawai Allah ya kawo mashi don mutum ne mai cikakkar lafiya don ko hawan jini bai da shi hakan yasa ma wasu sukai tunanin ko Asiri ne ba kamar da yake d'an siyasa ne saidae shi yace ya d'auke shi ciwo ne kawai Allah ya kawo mashi, da daddare suna cin Abinci ne Mom d'in shi ke tambayar wai ko har yanzu bai lafiya ne taga still da rama a fuskar shi gashi kaman baida kuzari yana d'an murmushi yace mata ya samu sauk'i sosae Dad d'in shi yace ai bai cin Abinci sosae gashi ya yi ciwo dole yay ta zama hakan, shidai d'an murmushi kawai yake, bai ci wani Abincin kirki ba ya mik'e Senator ya kalli Mom d'in shi yace "you see, taya zai maida jikin shi da wuri" d'an 6ata fuska tay tace mashi ya zauna ya k'ara to shi bai iya gardama ba ba kamar kuma da iyayen shi kawae sai ya koman ya k'ara ci daga baya ya tashi ya nufi upstairs idanun Mahaifiyar tashi a kanshi, bayan ya haye ta maido idon ta kan Senator tace bai lura kaman yana cikin damuwa ba ya d'an watsa hannu yace ba lalle ba tunda gane mashi nada wuya, haka ta bar Maganar amman a ranta tana ganin kaman akwai abunda yake damun shi. Daren ranar baccin Fatuu ragagge ne, Washe gari bayan tayi sallar Asuba Al'qur'ani ta d'aukko ta fara karatu, ta dad'e tana yi bayan ta gama ta nufi toilet don tayi wanka, tana cikin sa kaya Saude ta kawo mata breakfast, bayan ta gama Part d'in Hajiya ta nufa ta isketa a d'aki suka gaisa tay mata ya kewar mai gida ita dai d'an murmushi kawai tayi, nan ta bata hak'uri tace mata daga wurin aikin shi ne suka buk'aci ya koma tasan bai rasa fad'i mata, tace ai sun ma yi mashi mutunci suda basu wasa da aiki don ma yana yi masu wani daga nan, ita dai Fatuu shiru tay daga baya tace zata je wurin Aunty Saude, tare sukai aikin Abincin rana, gaba d'aya ta koma sukuku da ita ga tunanin Haisam da ya addabi zuciyar ta komi take shike mata yawo a rai har Saude ta lura da yanayin ta ta tambayi ko har yanzu ciwon kan take tace mata a'a da Sauk'i, anan taci Abincin rana tare da Hajiya bayan sun gama suka koma falo suna kallo saidai ita idanun nata na kan tv d'in ne ba don tana fahimtar mi ake ba wani lokacin sai ta sauke idanunta tay shiru, Hajiya da ta lura da yanayin ta tace "Fateema anata kewar miji ko?" d'an firgit tay ta kalli Hajiya lokacin idanunta na k'asa tay Maganar ta d'an k'ak'alo murmushin yak'e ba tare da tace komai ba, "ko kije gida nasan in kika ga Dije Kya rage kad'aici" sosae taji dad'in Maganar a hankali tace mata to ta mik'e, har zata tafi Hajiya tace taje Kitchen ta zuba Abinci ta kai mata nan ma ta amsa da to ta nufi Kitchen d'in, Yau ma data je gidan saida gwaggo tayi mata fad'a kan miyasa zata rink'a zaryar zuwa a sanyaye ta fad'i mata yadda sukai da Hajiyar, duk a zaton ta bata san Haisam d'in ya tafi ba amman sai taji tace ai yazo yayi mata sallama kafin ya wuce jiya ma harda kayan Abinci Tk ya kawo, ta d'ora da fad'in ai dama yakamata ya koman tunda bada shirin zama yazo ba, gwaggo ta lura da yanayin ta amman bata ce komai game da hakan ba sai kawai ta nuna mata tayi mashi Addu'a da fatan Alkhairi in ya samu lokaci tasan zai dawo ne Fatun ta d'aga mata kai kawai, jefi jefi suke yin fira nan Fatun ta rok'i gwaggo kan ta d'aukko Mino yanzu sai ta taya ta zama, cikin wasa tace kenan ma ita zata d'aukko ma ita, a sanyaye tace a'a ko kwana ne sai ta rink'a taya ta tace ta kusa zuwa ai, sai bayan isha ta koma gida a part d'in Hajiya taci Abincin dare lokacin da zata koma part d'in su Hajiyar tace mata in tana so ta kwana anan tace to don a tunanin ta in anan ne k'ilan ta samu tayi bacci sosae ba kamar jiya ba, komawa tay part d'in nasu ta shiryo sannan ta dawo, a d'akin Saude ta kwanta da yake ita ba anan zata kwana ba, Washe gari bayan sallar Azahar tana part d'in Hajiya sai ga kiran Fauzy bayan ta d'aga tace mata bata nan ne gasu sun zo da Aunty Mareeya amman ba kowa a part d'in, da sauri tace mata gata nan tana part d'in Hajiya ne, tana shigowa parlon ta nufi Aunty Mareeya da yar sassarfa ta fad'a jikin ta sai kuka, rarrashinta ta shiga yi tana d'an bubbuga bayanta daga baya ta washe, sosae ta shiga bata baki tana kwantar mata da hankali ta nuna mata sam bata ji dad'in halin da take ciki ba amman in sha Allahu komai ya kusa zama labari, fira suka shiga yi daga baya Fatun tace bari ta d'aura masu girki suka ce suda daga gida suke sun ci Abinci ta kafe kan ai anjima sai suci in ta dafan, ta fad'i masu bata ta6a yin girki ba sai yanzu Aunty Mareeya tace ah lalle taje tayi masu su ci girkin Amarya harda cewa Allah yasa akwae sauran man shanu tana yar dariya tace eh akwai ai bata ma wani amfani dashi, tare da Fauzy suka fara yin aikin girkin wanda Fried rice ce zasu yi, suna cikin yin girkin Aunty Mareeya ta shigo Kitchen d'in tay masu sannu da aiki kafin ta nufi drawer din da ta saka mata magunguna ta bud'e, wasu daga ciki ta fiddo tace mata zata tafi dasu don kar su lalace in buk'atar su ta taso daga baya zata aiko mata da wasu, d'an tura baki tay tace ita tama kwashe su duka tana dariya cike da tsokana tace karfa daga baya ta kirata tana mata yar muryar Aunty Mareeya dama Maganar Magungunan nan ce, duk sukai dariya tace ita bazata k'ara amfani dasu ba, bayan sun ci Abincin duk in suka ce zasu tafi sai Fatuu ta marairaice kan su bari sai anjima a haka har dare yay sai da akai sallar isha sannan suka tafi bayan sun je part d'in Hajiya sun gaisa, Washe gari tana yin shirin zuwa Makaranta a ranta ta raya ko wama zai rink'a kaita, k'arshe ta yanke in ta gama shirin kawae ta tafi ta hau abun hawa, bayan ta gama shiryawa a parlor ta zauna tana yin breakfast da Saude ta kawo mata tana cikin yi aka k'wank'wasa kopa ta bada izinin a shigo, Tk ne ya shigo yana ganinta ya fara mata dariya ya shigo ciki, akan armchair ya zauna har suna had'a baki wurin gaishe da juna yace mata dama zuwa yayi yaga in ta shirya nan ta gane shine zai rink'a kaita kenan, yana zaune har ta gama taje ta d'aukko jakarta da takalma suka tafi. A Ranar wadda ta kama Monday Haisam ya tafi U.S, Bayan ya isa Fanan ta d'aukko shi ta sha kwalliyar k'ananan kaya, gaba d'aya Farinciki ya cikata har fuskarta bata iya 6oyewa, tun a Mota ta fara nuna mashi tayi missing d'in shi don ma ita ke driving d'in, bayan sun isa gida zo kaga tarairaiya har wanka ita tayi mashi, haka Abinci ma a baki ta rink'a bashi, bai dakatar da ita daga yi mashi duk abunda ta saba mashi ba, ita kanta saida tayi Maganar fad'awar da fuskar shi tayi da har yanzu bata ciko ba, cike da nuna damuwa ta shiga tambayar ko har yanzu bai lafiyan ne yace mata ya warke nan ta yanke harda stress tace ya tashi daga ciwo bai huta ba ya tafi wani aiki, sosae ta bashi dama ya huta don har saida ya d'an yi mamakin hakan harda su massage aka mashi, daga baya ne bayan ya huta sosae abu ya shiga tsakanin su a lokacin kuma ta nuna mashi how badly tay missing nashi to shima d'in bai yi k'asa a gwaiwa ba wurin sauke mata abunda ya tara, daga baya suka cigaba da gudanar da rayuwar su yadda suka saba. Ba k'aramin yak'i da zuciyar ta Fatuu ke yi ba, ta matsa mata da tunanin Haisam gaba d'aya ta koma sukuku da ita gashi tunda ya tafi basu yi waya ba ko text message balle kuma chat, sosae take daurewa a haka har yayi sati guda da tafiya, a ranar wadda ta kama Friday bayan ta dawo daga Makaranta tana cikin Bedroom ta fito daga wanka tana shiryawa taji wayarta ta fara ringing ta nufi bakin gado inda take ajiye ta d'auka, har saida gaban ta ya fad'i ganin Haisam ne ke kira, tamke Fuska tay wata zuciyar ta bata kar ta d'aga ta bi kiran da kallo har ta yanke, zama tay a bakin gadon nan da nan mood d'in ta ya canza damuwa ta bayyana a kan fuskar ta a ranta ta shiga raya ace tunda ya tafi bai kira ta ba sai yau a haka za'a ce wai yana son ta Abbas da bata had'a komai dashi ba kullum sai ya kira yaji ya take wata rana ma sau biyu yake kiran nata, tana ta zancen zuci wani kiran ya sake shigowa ta k'ara bin screen d'in da kallo, har ta kusa yanke wa wata zuciyar ta raya mata hakan ba daidai bane tunda shi ya kira ba ita ta neme shi ba ta d'auka, picking tay ta kai wayar kunne jin shiru yasa can k'asan makoshi tay sallama, amsa mata yay daga haka tay shiru shima shirun ya d'anyi sai kuma taji ya tambayi yadda take k'asa k'asa ta bashi amsa da lafiya lau, sake tambayar karatun ta yay nan ma tace lafiya lau, jin sun yi shiru yasa tace mashi sai anjima yace Ok, bin wayar tay da kallo fuska a kwa6e bayan ta cire ta daga kan kunnan ta, can ta cillar da ita ta kife fuskarta a saman gadon. ***** ****** Ranar Friday da ta kama satin Haisam biyu da tafiya daidai, Misalin k'arfe sha biyu da rabi na rana Jirgin su Senator da Hajiya Maryam ya sauka a Airport d'in Katsina don amsa kiran da Mahaifiyar su tayi masu kwana ukku da suka wuce, tun ranar data kira su ta sanar dasu tana son ganin su suka hau tambayar ta lafiya tace masu Kada su tashi Hankalin su lafiya lau sai Alkhairi kawae tana son ganin su ne in sun samu lokaci, shine daga baya suka kira Junan su suka yanke ranar da zasu zo, gaba d'aya sunyi shiga ta Alfarma Senator na sanye da babbar rigar shadda haka takalman shi ma fararen cover ne da hular shi hannun shi sanye da dankareren agogon diamond yayin da Hajiya Maryam ke sanye da rantsattsiyar bak'ar shadda data sha aiki golden takalmanta ma golden ne masu d'an tudu haka jaka da gyalen jikinta duk golden ne tsadaddun gaske to coge d'aurin kallabi, tun daga kan kunnan ta da wuyan ta da kuma hannunta kerarrun gold ne, dole ma ka kalle ta ko bakai niyya ba sai faman baza k'amshi suke ba kamar dai Senator d'in, in ka kalle su zaka ga basu kama saidai kamar jini don shi mahaifin su ya biyo ita kuwa Hajiyar Sanata ce sak, A dankareriyar Jeep aka d'aukko su Motar Escorts na biye da su suka nufi gidan Hajiya, bayan sun isa cike da Farinciki Hajiya ta tarbi y'ay'an nata abun Alfaharin ta itama ta ca6a adon leshi, kan kace mi kopar gidan ya cika da Jama'a Mutanen Senator, a nan Parlor suka zauna suna gaisawa daga baya wasu daga cikin Mutanen Senator d'in Abokan shi na hannun daman shi da suka zo yi mashi sannu da zuwa su kuma gaida Mahaifiyar tashi suka shigo a bisa Umarnin shi, nan fa hira ta 6alle baka jin komai sai dariyar manyan mutane masu tumbin Naira, Saude da wata da aka d'aukko don ta kama mata aiki suka shigo masu da abubuwan sha da na ta6awa kafin lokacin cin Abinci yayi, daga baya sukai ma Hajiya sallama bayan sun mata Alheri irin nasu na manya Senator yace mata zaije Government House su gaisa da Governor, bayan tafiyar su ya rage daga ita sai Hajiya Maryam, hannu ta kai ta kamo na Hajiya da yake a kujera d'aya suke 2 seater da murmushi tace "Hajjajutah fatan dai kina lafiya?" itama murmushin take tace mata tana lafiya Alhamdulillah, "Ya k'afafun da Sauk'i dai ko" cike da nuna kulawa tay tambayar tare da d'an kallo k'afafun Hajiyar, nan ma ce mata tayi da Sauk'i sosae da taimakon sandar ta ba inda bata zuwa, "Ma sha Allah haka muke so, Allah ya k'ara maki lafiya da nisan kwana our Heartbeat" Hajiya na yar dariya ta amsa da Amin, "Sai muka ji kira kina neman mu, nifa har hankali na ya d'an tashi kawae don kin ce ba komai sai Alkhairi yasa na d'an kwantar da hankali na amman duk da hakan naji na k'agara in zo in ji miye" still da fara'a a fuskar Hajiya tace mata in sha Allah Alkhairin ne kaman yadda ta fad'a masu tace to ta fara fad'a mata kafin Yayan ya dawo, tace "Saurin mi kike, ki bari ya dawo kaman yadda kuka zo tare sai muyi Maganar tare ko yau zaku koma ne?" tana yar dariya tace mata a'a kawai ta k'osa taji ne nan zasu yi mata Weekend, "Shine don rowa ko a taho man da d'aya daga cikin mazajen nawa ko k'awayen nawa koma a kwaso man su duka" dariya ta saka da yar kakkausar muryarta tace "Wllh kuma sun so biyo ni k'in tahowa nayi da kowa hakanan kai ta yawo da yaro tunda saida na je Abuja sannan muka taho nan" Hajiya tace to miye tunda ba'a k'afa za'ai yawon ba tace a'a in suna so in akai masu hutu sa zo, "Amman dai nasan banda uwar ji da kai aka nuna ana son zuwa ko" still dariya take tace "Wai Farha, aikuwa kaman kin sani ko in gaida ki bata ce ba" ta6e baki Hajiya tay "taji da shi, nima ba son tace tana gaida nin nike ba tunda inada wanda suke gaida nin ta rik'e kayanta ban so" haka suka cigaba da hira cike da raha. Duk wannan abun Fatuu na Makaranta bata dawo ba daga can ma Hostel zata wuce sai Fauzy ta shirya zasu taho tare a sauketa a gidan Aunty Mareeya sai ta dawo tunda akai Break dama ta kira Tk ta sanar dashi don Kada yazo in an tashin shima kawai sai ya wuce cikin gari bai ma san su Senator d'in sun zo ba, tare da Hajiya Maryam d'in suka tafi Masallaci sallar juma'a, bayan an gama nan fa aka fara tururuwar zuwa gaishe dasu da yake da yawa sun santa wasu kuma sai sun zo gaida Hajiyar suke sanin wacece wasu ma ba sai an fad'a masu ba tunda ga kama nan, bayan sun dawo ne suka zauna cin Abinci, suna cikin ci Senator ya dawo ya nufo Dining area d'in Hajiya tace ya zauna su ci Abinci yana murmushi yace mata sunci Abinci tare da Governor, d'an 6ata fuska tay tace to itama sai yaci nata tunda don su akai yana yar dariya yace tuba yake zai ci ba sai ta 6ata rai ba yaja kujera ya zauna duk sukai dariya, Bayan sun gama cin Abincin suka dawo parlor nan Hajiya Maryam tace mata tunda Yayan ya dawo sai ta fad'a masu abunda yasa ta buk'aci ganin su, numfasawa Hajiya tay ta gyara zaman glass d'in fuskarta sannan ta fara Magana a nutse "Farko dai muyi ma Annabi salati" gaba d'aya suka amsa da sallallahu alaihi wa sallam, bayan kowa yayi taci gaba "dalilin kiran ku abu ne ya taso wanda dole kuna da buk'atar sani ko ba don komai ba don halin rayuwa, ta wata fuskar ba lalle ku kalle shi a matsayin abun Alkhairi ba amman ina fatan ku natsu kuyi amfani da hankalin ku ku kar6e shi a matsayin Alkhairin domin duk abunda kaga Allah yayi to mai kyau ne" dakatawa tay tana maida numfashi duk sun natsu suna sauraronta Hajiya Maryam na gefen ta yayin da Senator ke facing d'in su acan d'ayan bangaren, Maganar da tayi yasa duk suka k'osa su ji miye abun da take son sanar da su d'in, kasa hak'uri Hajiya Maryam tay tace "muna jin ki Hajjaju" sauke yar ajiyar zuciya Hajiya tay ta d'aura "Haisam ne yayi aure, kuma yanzu haka da nike maku magana Matar tashi na zaune a gidan nan acan part d'in nashi" har saida Hajiya Maryam ta d'an zabura ta d'ago sosae idon ta akan Hajiya da alamun d'aurewar kai tace "Mi kike fad'a haka Hajjaju, Wane Haisam d'in yayi AURE!!!" tace mata wane Haisam ta sani banda d'an su, da tsananin mamaki akan fuskar ta tace "To ni ban gane mi kike nufi da yayi aure ba, ai dama duk mun san da yayi aure ko" d'an ta6e baki Hajiya tay kafin tace "dana ce yayi aure baki ji nace Matar na a cikin gidan nan ba, ko dama nan yake zaune da Matar tashi da kuka san ya aura?" da alama bakunan kowannen su ya mutu, shi dai Senator bin su da ido kawai yake ya jingine bayan shi da kujera yatsun hannun shi na had'e cikin na juna, Bayanin Yadda Al'amarin ya kasance Hajiya ta shiga yi masu tiryan tiryan har ta gama ba wanda ya katse ta sannan furiously Hajiya Maryam tace "kenan don uban shi har ya isa yayi aure without our Knowledge, Saboda bamu da amfani a wurin shi bai d'auke mu da daraja ba ko mi!!!" a tsananin fusace tayi Maganar har huci take, kallon Senator tay tace "Yaya kana ji fa, wai yaron nan har ya kai yayi aure bada sanin mu ba!" d'an girgiza kai kawai yay still bai yi magana ba, "ke kuma Hajjaju ya aikata wannan d'anyen aikin har ki goya mashi baya kisa ya zauna da ita, tunda matsayin taimakon ta yayi to miyasa bazai saketan ba zaki bashi dama suci gaba da zama" a fusace idanunta akan Hajiya tay Maganar, Hajiya data kwa6e fuska tace "to miye amfanin sakin nata tunda abu ya shiga tsakanin su har rabo ya shiga tsakani...." A zafafe Hajiya Maryam ta katse ta don da ta ambaci rabo tamkar ta watsa mata ruwan zafi taji cikin k'unar zuciya tace "Don Allah ki daina wannan Maganar Hajjaju, wane rabo ba kince ya zube ba to cigaba da zama da itan na minene???" "Amman dai kinsan in aka saketa ai ba ai mata Adalci ba, da ya aure tan ai matsayin zai taimaka mata akai dashi ba'a yi dashi wani abu zai shiga tsakanin su ba ko, to tunda har hakan ya kasance sai a rungumi Al'amarin ai fatan ya zama Alkhairi ta yuwu dama Allah ya k'addara auren ba don su rabu bane" girgiza kai Hajiya Maryam ta shiga yi tana cigaba da yin huci can tace "Impossible wllh, bazai cigaba da zama da ita ba, duka yaushe yay Aure da za'a ce wai har ya k'ara, k'arin ma na wulakanci da kaskanci, dole mu nuna mashi bashi ke iko da kan shi ba akwae masu iko dashi da zai je yayi gaban kan shi, in ba iskanci ba da ya raina mutane a ina na ta6a jin irin wannan taimakon" idanunta har sun sauya kala tsabar 6acin rai, kallon Senator tay "Yaya kana jin rainin wayau ko, dole ma a raba su wllh kawai a kira shi ya saketa!!!" tana rufe baki Fatuu ta sawo kai cikin parlon da sallama tana sanye da jallabiya ta yafa veil d'inta duk suka maida idanun su kanta, nan take ta ja ta tsaya tana bin su da ido itama, da hannu Hajiya tay mata alamar ta k'araso ta nufe su a d'arare don kuwa duk ta gane su, tana zuwa bakin kujerun ta toge duk tasha jinin jikin ta ganin yadda suke bin ta da ido ba kamar Hajiya Maryam wadda bacin rai ke kwance k'arara akan fuskarta, Hajiya ce tace "ki k'araso mana Fateema" shiga tay duk ta kame kanta, nuna mata kujera Hajiya tay alamar ta zauna maimakon ta zauna samanta sai ta duk'e saman carpet daga d'an nesa da Hajiyar, fuska a sake tace "an dawo?" Kai ta d'aga mata, "amman ya akai baki shigo tun d'azu kin ci Abinci ba?" Cikin rawar murya tace "a..ai yanzu na dawo, na tsaya a Hostel ne wurin Fauzy mun yi Assignment" da k'yar ta k'arasa sakamakon mugun kallon da Hajiya Maryam ke jefa mata don kuwa ta santa tasan itace Matar Haisam d'in, tuni zuciyarta ta hau bugu da k'arfi da k'arfi, kai Hajiya ta jinjina sai kuma ta sake cewa "baki gaida bak'i ba to, kin gane su?" Kai ta d'aga mata alamar eh ta kalli Hajiya Maryam cikin rawar murya ta gaida ta tay mata banza, juyawa tay kan Senator dake ta kallon ta shima ta gaida shi ya jinjina mata kai kawai, juyowa tay kan Hajiya Maryam ta k'ara gaishe da ita aikuwa ta zabga wani uban tsoki ta mik'e ta nufi hanyar barin Parlon a fusace da sauri Fatuu ta fara k'ok'arin matsawa saidai ko kafin ta bata hanya ta cimmata aikuwa ta ham6are ta gefe ta wuce Fatun ta bugi kujera sosae aikuwa nan take ta fashe da kuka don ba K'aramin buguwa tayi ba, yamutsa fuska Hajiya tayi ta bi Hajiya Maryam d'in da kallo har ta shige Corridor sannan ta girgiza kai ta maido idon kan Fatuu ta mik'a mata hannu alamar ta matso ta jawo jiki tana cigaba da yin kuka tana gogewa da gyalen jallabiyar ta da ya zame daga saman kan, rarrashinta ta shiga yi tana bata hak'uri hannun ta guda a saman shoulder d'inta ta d'agota ta zaunar da ita akan kujerar kusa da ita tana cigaba da rarrashin ta, tana cikin goge k'wallan ta kai idonta kan Senator suka had'a ido kawai sai gani tay yay mata alamar tazo da kan shi, dakatawa tay tana kallon shi ya d'aga hannu ya k'ara kiranta Hajiya da ta gani tace taje ana kiranta ta mik'e a d'arare ta nufe shi, bayan ta isa gaban shi tana k'ok'arin zama akan carpet ya nuna mata kujerar kusa da shi yace ta zauna, zama tay tana cigaba da goge Fuskar ta tana yar ajiyar zuciya, a nutse cike da dattako ya fara magana, "Kiyi hak'uri kin ji, ranta ne a 6ace shiyasa tay maki hakan amman Kada ya dame ki, nasan ba ki rasa sanin cewa in rai ya 6aci mutum na iya aikata komai ko?" Kai ta d'an jinjina mashi, d'an murmushi yayi "Good, a wani School kike ne?" Still muryar ta rawa take don wani irin kwarjini ne dashi ta bashi amsa, jinjina kai yay "da kyau, kinyi nisa a Karatun ne?" tace "Eh ina aji biyu kuma mun kusa yin Exam" nan ma kan ya jinjina yace "sai ku shiga aji ukku kenan, ai kaman daga nan ma zaku gama ko don nasan kaman karatun 3 years ne" kai ta d'aga mashi a sanyaye tace eh, "kice watarana in bani lafiya za'ai man Allura kenan, koma har kin iya yanzu?" ya d'an bud'a mata ido sak irin yadda Haisam ke yi dabarbarcewa tay don bata tsammaci ganin hakan daga gare shi ba tace eh ta iya, wani kallo yay mata irin na baka yarda da Mutum ba yace "kai, ki fad'a man gaskiya fa, ko don Kada ince baki da k'ok'ari kika ce hakan" da sauri tace "Allah da gaske nike na iya harda sa drip ma da d'inki" jinjina kai yay yana murmushi yace "kice Daughter d'in nawa mai k'ok'ari ce kenan" d'an waro ido tay baki a d'an bud'e take kallon shi ya d'age mata gira yace ko bata da k'ok'arin da sauri tace tana da shi, kai ya jinjina taji yace taje taci Abincin da sauri tace to ta mik'e ta nufi hanyar barin cikin parlon duk suka bita da ido Hajiya na d'an murmushi dama tunda suke Magana dashi take kallon su tana murmushi, Ajiyar zuciya ya sauke ya kai hannu ya shafi fuskar shi yana kallon Hajiya yace "She's so cute" Hajiya dake murmushi tace mashi haka take sai ma ya zauna da ita tana da dad'in zama sosae, nan ta shiga bashi labarin rayuwar da sukai da Haisam a baya, Maimakon ta shiga Kitchen d'aukko Abincin sai ta zille ta bi ta kopar baya ta fuce, bata bi ta 6angaren da d'akin Hajiya yake ba tabi ta d'ayan 6angaren tana tafiya cikin sauri ta d'an d'age kasan rigarta tana yi tana waigen bayanta ta nufi part d'in su......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:28] +234 901 700 4868: ASM Bk2069 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Tana fitowa daga cikin gidan tay ma Tk dake cikin Mota alama da hannunta nan take ya fahimci mi hakan ke nufi ya bud'e kopar Motar da sauri ya fito, bud'e mata K'opar bayan yay tana zuwa ta shige ya maida kopar ya rufe mata ya d'an d'age gira tare da bud'a ido ya koma yaja suka tafi, sai faman jinjina kai take tana cije lower lip d'in ta tana d'an huci, Tana fita Amadu ya matsa gaban gwaggo ganin yadda idanunta sukai ja shima har lokacin ran shi a 6ace yake, kallon shi tay tace miyasa yayi abunda yayi ma Hajiya Maryam, cikin 6acin rai yace "to gwaggo sai mu zuba mata ido taci mana mutunci son ranta, miye laifin mu a ciki ko kuwa don muna talakawa" yar ajiyar zuciya ta sauke "kar ka manta ita d'in ko wacece, ko ba komai Mutanen nan nada k'ima da daraja a idon mu hakan da kayi mata bai kamata ba don kamar rashin kunyan ne, duk abunda ta fad'a ta fad'a ne cikin 6acin rai don tana ganin an mata ba daidai ba" dakata tay tana numfasawa idanunta na kallon gefe shi kuma nashi na akan ta, cigaba tay "Wllh abunda nike ta fargabar faruwar shi kenan, nasan dole irin hakan ya biyo baya shiyasa naso tun farko ace an tuntu6e su sun san da Maganar a nemi amincewar su tukun...." Dakatawa ta k'ara yi ta d'age ido sama, ganin yadda duk ta damu yasa Amadu cewa "Kar ki wani saka ma kan ki damuwa, tunda Hajiya tun farko ita ta nuna abar mata komai nasan in sha Allah zatayi abunda ya dace komai na d'an lokaci ne zaki ga ya wuce" girgiza kai tay ba tare data kalle shi ba tace dole tayi wani abu don ita bazata so silar hakan ace an samu rashin Fahimta ba yanzu na Hajiya Maryam d'in aka gani ba'a san ya sauran Yan'uwan nashi suma zasu d'auki Al'amarin balle kuma ita Matar tashi, tambayar ta yay to mi zata yi ta bashi amsa da abunda ya dace daga haka ta juya ta nufi d'aki ya bi bayanta yana ce mata ta kwantar da hankalinta ba sai tace zatayi wani abu ba yasan Hajiya bazata bari a cutar da Fatuu ba, tana shiga d'akin ta nufi gado ta zauna a baki Amadun ma ya shigo ya zauna gefen ta yaci gaba da rarrashin ta kan kar tace zata yi wani abu don anzo anyi masu barazana su yi Addu'a kawae, ce mashi tay to kawae daga baya da ya ga ta d'an saki ranta ya tashi ya tafi, Zaune tay a wurin tana tunanin abunda ya kamata tayi don ganin Auren ya rabu, k'arshe ta yanke zuwa ta samu Hajiya ta rok'e ta kawae a hak'ura da Auran, tana son ta kira Fatun taji halin da take ciki amman bata so taji abunda hankalin ta zai k'ara tashi wata zuciyar ta raya mata tunda ita bata kira ta ba k'ilan ba abunda ya faru da ita don Hajiya bazata bari ayi mata wani abu ba da wannan tunanin taji hankalin ta ya d'an kwanta. Bayan sun iso G.r.a sun shiga cikin gidan a gaban kopar shiga ya parker, bayan ta bud'e ta fito ta nufi ciki, Parlon Senator ta wuce wanda Had'add'an gaske ne ya tsaru ta samu wuri ta zauna, ganin bai a ciki yasata kiran shi ta sanar mashi ta iso, bada dad'ewa ba ya fito yana sanye da farar Jallabiya tun bayan daya dawo daga Masallaci ya koma ya kwanta zuwanta ne yanzu ya taso shi, a kujerar gefen ta ya Zauna Fuskar shi a sake ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru kanta a k'asa tana kallon Carpet 6acin rai bayyane akan fuskar ta, tambayar ta yayi tayi breakfast ne tace mashi a'a sai ta isa yace bari dai a kawo mata tayi anan, bata ce komai ba ya matsa can daga gefen kujerar inda landline take aje saman wani table, kira yay ya bada Umarnin akawo Breakfast, after some minutes sai ga wani cook ya shigo hannun shi ruk'e da babban tray dama aikin shi kenan girka ma Senator d'in Abinci in yazo bada iyalin shi ba, har zai kai inda dining table yake Senator yace mashi ya kawo nan, gaishe da Hajiya Maryam yay ta amsa k'asa k'asa ba tare da ta kalle shi ba ya d'aura a saman c-table Senator yace ya ja mata shi gabanta, saida yayi mata Magana sannan ta fara ci shi kuma ya fara daddana wayar shi da ya fito da ita, bata wani ci sosae ba ta cire hannunta ganin haka yasa Senator yi mata magana tace mashi ta k'oshi, k'ara kiran cook d'in yay yazo ya kwashe kayan, shiru suka yi Senator na cigaba da danna wayar can ya d'ago ya ajiye ta agefen shi yay yar ajiyar zuciya a nutse ya fara mata Magana yace miyasa zata tafi, kallon shi tay tace mashi ba komai kawae ta canza ra'ayi ne, shiru yayi yana kallon ta da d'an murmushi ita kuma idanunta na k'asa tana kallon Carpet har lokaci fuskar ta ba annuri, cigaba yay "nasan don abunda ya faru ne, ina son ki kwantar da hankalin ki abi komai a sannu sannan ayi fatan hakan ya zama Alkhairi kaman yadda Hajiya ta fad'a bamu san mi Allah ya 6oye a tattare da Al'amarin ba" kallon shi tay cikin 6acin rai tace "Kenan kaima Yaya goyon bayan auren kake?" d'an murmushi yay yace mata kawae yayi nazarin Maganar Hajiya ne shiyasa, Fuska a yamutse tace "Yanzu shikenan ya nuna bamu da iko dashi ya yi gaban kan shi sai kuma a k'yale shi hakan Yaya ai cin Fuska ne, gaskiya dole mu nuna mashi ba a komai yake da iko da kan shi ba kawai asa ya saketa" ta k'arasa tana d'an Jujjuya kai, numfasawa yay yace "ni ina ganin hukuncin da Hajiya ta yanke akan shi ya nuna ana da iko dashi, yaje yayi aure ba tare da sanin mu da niyyar zai saki Yarinyar kinga in aka sa ya sake ta shine yay abunda ran shi ke so amman matsa mashi ya zauna da itan hakan zai sa dangin yarinyar su san ana da iko dashi kuma mu ba k'ananun mutane bane, sakin ta kuma hakan gaskiya ina ganin zai zama k'aranta" idanun ta ne suka ciko da k'walla cikin karyayyar murya ta fara fad'in gaskiya ita bata goyi bayan yaci gaba da zama da ita ba duka yaushe yayi aure kuma in ma Auren zai k'ara wannan ai bata dace da shi ba ba sa'ar auren shi bace, shiru Senator yay still da d'an murmushi akan Face d'in shi don yasan dalilin da yasa duk take wad'annan abubuwan, rarrashin ta ya shiga yi yana nusar da ita aikuwa sai tasa mashi kuka tana fad'in shikenan ba wanda zai yi tunanin halin da Fanan zata iya shiga duk sun goyi bayan 6are sun za6i faranta mata da mi ake so Fanan taji ne ko don suna tunanin bazata haihu bane, nuna mata yay bai ji dad'in wannan Maganar da tayi ba sam ai yayi tunanin Fanan ta su ce da ta haihu da kar ta haihu hakan ba abun damuwa bane a gare su kuma don ance tana da matsala ai hakan ba yana nufin bazata haihu ba kawai yana son ta gane shi Al'amarin irin wannan in Allah ya kawo kamata yay a kar6a ai fatan ya zama Alkhairi ba kamar da Hajiya ta nuna tana so sai suyi mata biyayya su bi da Addu'a, hak'uri ta bashi kan Maganar da ta yin ya k'ara lallashin ta daga baya sukai sallama ta mik'e shima ya tashi don ya rakata. Bayan ya dawo inda ya tashi ya koma ya zauna ya d'auki wayar shi ya shiga kiran Haisam, picking yay tare da yin yar sallama Mahaifin nashi ya amsa mashi, bayan ya gaida shi yace mashi sun ji abunda ya aikata ya kyauta hakan ya nuna masu basu da amfani a wurin shi, hak'uri ya bashi yace mashi yayi don taimako ne, ce mashi yay to miyasa ya k'i sakin ta kaman yadda akai dashi har abu ya shiga tsakanin su, shiru yay bai ce mashi komai, sigh Senator yay yace mashi yana son ta kenan dama shiyasa har hakan ta faru don yaci gaba da zama da ita, Slowly yace mashi bada niyya bane kuma Hajiya ce tasa yaci gaba da zama da ita, d'an guntun murmushi Senator yay yace "Kenan baka son ta?" Shiru Haisam d'in yay, da d'an d'aga murya yace ya bud'e baki yay mashi magana kaman yadda yake mashi bai kira shi don yaja mashi aji ba, in bai son ta ya fad'i a raba su kowa ya huta, har saida Haisam d'in yay d'an guntun murmushi jin abunda yace dama ya saba ce mashi hakan in yana jira yay mashi magana, "Tunda Hajiya na so zan ci gaba da zama da ita" d'an ta6e baki Senator yay da murmushi irin na ka gane Mutum ba gaskiya ya fad'a maka ba, "ita Daughter ka sanar da ita ne?" Ya tambaya yace mashi a'a, "to kai k'ok'ari ka sanar da ita kasan yadda zaka kwantar mata da hankali don Momyn ku ta d'au zafi sosae rashin tada hankalin ta shi zai sa ta kwantar da nata hankalin" amsa mashi yay da to, tambayar yaushe zai dawo yayi yace sai ya samu time tunda bai dad'e da dawowa ba, "Ok, amman kai k'ok'ari ka dawo da wuri kar ita kuma ta nan d'in a shiga hakkin ta, in ta gama Karatun sai ka d'auketa kawai ta dawo nan" amsa mashi yay da to cike da tsokana yace "kai da alama ma sai ka wuce ni, tun yanzu kayi biyu gaba sai ka cike biyun dama an ce kyan magaji ya zarta" murmushi mai d'an sauti Haisam d'in yay shima Dad d'in nashi murmushin yake dama tamkar Abokai haka suke akwae kyakkyawar fahimta a tsakanin su, ce mashi yay shikenan Haisam d'in yayi mashi godiya shi kuma ya sa mashi Albarka sukai sallama. Saude na shiga cikin parlon bayan ta kai trolley d'in suka yi kacibus da Hajiya ta shirya cikin doguwar riga kanta sanye da hula, ganin ta nufi hanyar Dining yasa Saude ta bi bayanta don tay serving d'in ta Breakfast, bayan ta zauna Saude na zuba mata ta tambayi ta kai ma Fateema tace mata eh tun d'azu ma bayan ta dawo ne ta had'u da Momy Maryam shine ta bata trolley ta kai mata parking space, da d'an murmushi Hajiya ta girgiza kai tace ta tafi kenan, d'an jimm Saude tay ranta ya bata ta fad'i mata inda taga ta nufa don hankalin ta bai kwanta da zuwanta part d'in ba, fad'i mata tay cewa bata kaiga tafiya ba lokacin da suka fita taga ta nufi part d'in su Fateema, Yanayin fuskar Hajiyar ne ya canza ta maimaita ta je part d'in su Fateema to mi ya kaita, Saude tace itama bata sani ba, fara yin Breakfast d'in tayi Saude ta tambayi akwae wani abu da zata yi mata, tambayar ta tayi ita tayi breakfast d'in ne tace a'a tace to ta je tayi in ta gama ta zo zata rakata part d'in su Fateema ta amsa mata da to. Tun bayan da Fatuu ta ruga ta shige cikin Bedroom ta fad'a kan gado tana kuka sosae, tana cikin kukan ta fara bugun katifa da hannun ta a fili take fad'in "Ko ma mi akai man kai kaja man Ya Haisam! Baka damu dani ba, ka tafi ka barni Saboda baka so na baka k'aunata..., ni kawai ka zo ka sake ni na hak'ura da kai, na daina son ka, na daina......" Haka tay ta sambatu sai ta tashi zaune sai kuma ta koma ta fad'a saman Katifar, ba K'aramin kuka ta sha ba daga baya ta sassauta yin kukan tayi lamo akan Katifa ta k'ura ma wuri guda ido tana fitar da numfashi da sauri da sauri idanun ta sun yi jajur a ranta tana tunanin yadda zatay Haisam ya saketa, tunanin ko ta kira gwaggo ta fad'i mata halin da take ciki tay wata zuciyar ta raya mata hakan ba K'aramin tayar mata da hankali zai yi ba, tunanin Abbas tay shima ta raya tasan kota fad'i mashi hak'uri zai bata, a k'arshe ta yanke kawai taje wurin Hajiya tace mata bata son Auren tasa ya saketa tunda dama ai saida tace tana son cigaba da zama dashi sannan ta tare, tana haka aka turo kopar Bedroom d'in tay zumbur ta tashi zaune idon ta akan kopar ta zaro su sam ta manta ta kulle Saboda a yanayin da ta shigo, wani irin bugu da k'arfi zuciyar ta ta fara yi don a tunanin ta ko Hajiya Maryam d'in ce ta dawo, sandar data ga an sako yasa hankalin ta fara kwanciya, shigowa Hajiya tay ta yafo mayafi tana sanye da glass ta tsaya a bakin k'opar tana kallon Fatun, ganin haka yasa ta saukko daga saman gadon ta zagayo inda take, daga gabanta ta tsaya cikin rawar murya ta gaishe da ita tay d'an murmushi ta amsa kafin tace "ana nan ana ta shan kuka ko" sadda kanta tay k'asa bata ce komai ba Hajiyar tace mata ta biyo ta ta juya, bin bayanta tay har lokacin kanta ba kallabi, cikin parlon suka shiga Saude na zaune akan armchair Hajiya ta nufi L-shape ta zauna Fatuu na niyyar zama kan Carpet ta nuna mata daga gefen ta tace ta zauna, bayan ta zauna ta sadda kan ta k'asa Hajiya ta fara magana, "Maryam tazo duk ta firgita ko?" shiru tay bata d'ago ba sai d'an jan majina da take, "Fad'i man mi tazo tayi maki ne" d'agowa tay ta d'an kalli Hajiyar a hankali tace mata ba komai idanunta cike tab da k'walla, yar hararar ta tayi cikin wasa tace mata ba tambayar ta take ba umarni ne ta fad'i mata duk abunda ya faru, cikin rawar murya ta fara fad'i mata tiryan tiryan duk abunda ya faru, kwa6e Fuska Hajiya tay ta jinjina kai a fili ta furta sunan Hajiya Maryam d'in, sosae Fatun taba Saude tausayi tana ta kallon ta tana d'an girgiza kai, "To yanzu ke mi kika yanke kenan" Hajiya dake kallon Fatun ta tambaya aikuwa kaman tana jira tace mata bata son Auren tasa ya saketa, ta6e baki Hajiya tay "tayi nasara kenan akan ki, ke baki san duk barazana bace dama abunda take so kenan ta tsorata ki kice baki son Auren" kallon Hajiyar tayi da runannun idanu kwalla kwance a cikin su tace "Hajiya tunda dai basu son Auren don Allah ki raba mu kawai" Fuska a kwa6e take kallonta har ta rufe baki sannan tace "Waye bai son Auren, mu ba duk muna so ba ko baki ga Mahaifin shi ya kar6e ki hannu biyu ba, itama Mahaifiyar shi ina sa ran zata amince don duk abunda Mijinta yake so to itama tana so nasan zata fahimta, itace fa kadae ta nuna bata amince ba kuma itama ba wani abu yasa ba kawae tana taya d'iyar ta kishi ne ba kamar da yake itama ba kishiyar ce da ita ba shiyasa take ta wannan tada jijiyar wuyar", cikin muryar kuka tace "to amman tace fa zata yi man Asiri ni tsoro nike tayi man wani abu ko ta kashe ni" yadda tay Maganar har saida taba Hajiya dariya ta ta6e baki sai kace wata yar k'aramar yarinya, Hajiya ta lura Maganar ta tsorata ta sosae, hannu ta kai ta dafa Shoulder d'inta tace "Ki kwantar da hankalin Fateema nasan Wacece Maryam fiye da kowa tunda ni na haife ta, duk abunda ta fad'a maki ba abunda zata yi maki don ko k'adangare bata iya kashewa balle Mutum...." Katse Hajiyar tay tace "ai dama ba ita zata kashe ni d'in ba a Asirin da tace zata iya sakawa" yadda tay Maganar Hajiya ta kwaikwaya tace mata "Waya fad'i maki zata iya yi maki wani Asiri, duk fa burga ce ba wani abu ba kin wani tashi hankalin ki, kawai so take ta kwatar ma yarta mijin naku ya kasance nata ita kadai, kin san jik'an nawa badai nagarta ba son kowa k'in wanda bai samu ba shiyasa ake rububin shi, kiga fa ita matsayin d'a yake a wurinta itama d'iyar tata matsayin Yaya yake a wurin ta ko ba Aure akwai alak'ar yan uwan taka amman duk da haka suke k'wak'war shi, dama kinsan shi abu mai kyau da inganci shi yake siyar da kanshi, ko ke baki son shin ne?" ta d'age mata ido, dabarbarcewa Fatuu tay ta waro ido Hajiyar tace ta fad'i mata indai bata son shi to sai ta raba sun, kasa bud'e baki tay tayi Magana sai faman kikkafta idanu take ganin yadda duk suka kafeta da ido yasa ta sunkuyar da kanta zuciyarta na harbawa, Murmushi Hajiya tayi haka ma Saude, k'ara kai hannu Hajiya tay ta dafa kafad'ar ta tace "Ki kwantar da hankalin ki Fateema, ki jure duk wani abu da za'ai maki ki d'auki hakan matsayin yak'i akan abunda kike so, kinsan shi abu mai nagarta wani lokacin dama ba'a samun shi cikin sauk'i" tana yin Maganar Fatuu ta d'ago ta kalleta a hankali tace mata ita bata son shi Hajiyar ta harareta tace "K'aryar ki tasha k'arya yarinya, wannan d'an gold d'in jik'an nawa ai ba macen da zata ce bata son shi ai na riga na gano kina son shi tuni" d'an tura baki tay itama Hajiya ta tura mata nata harda yar harara aikuwa bata san lokacin data saki yar dariya ba har hak'oranta suka d'an bayyana, sosae ta kwantar mata da hankali har ta washe ta tambayi tayi Breakfast d'in tace mata a'a, Saude tasa taje ta d'aukko kayan daga kan Dining table ta kawo su nan kan c-table tace ta had'a mata, tsare Fatun tay saida taci sosae ta tabbatar ta k'oshi sannan tace taje ta d'aukko mayafi su tafi part d'in ta tace to, harda jakar Makarantar ta ta d'aukko don tayi Karatu suka tafi. Bayan jirgin su Hajiya Maryam ya sauka Mijinta Dr Mohammed ne yazo d'aukarta da yake Weekend ne yana gida yana hutawa, tun da ya ganta ya Fahimci tana cikin 6acin rai dama kuma ba ranar sukai da ita zata dawo ba, saida suka hau hanya ne yake tambayar ta abunda ke faruwa nan cikin 6acin rai ta bayyana mashi, shima ya jinjina Al'amarin amma da yake mutum ne mai sauk'in kai sai ya shiga rarrashinta ya nuna mata abi komai a hankali kaman yadda Hajiya tace, shiru kawai tayi dama tasan ba lalle ya d'auki abun yadda ta d'auka ba balle har ya goyi bayan ta d'auki mataki, bayan sun iso gida sun fito daga cikin Motar yaron gidan dake cikin ba flowers ruwa ya nufo inda suke yana masu sannu da zuwa Dr ne kad'ai ya amsa mashi ya fiddo trolley ya bashi ya kai ciki suma suka nufi ciki tare, Bedroom d'in ta suka wuce ta zauna a bakin gado shima ya zauna a gefen ta cikin salon nuna kauna ya shiga k'ara lallashin ta kan ta kwantar da hankalin ta, har lokacin ranta a 6ace yake tace mashi kenan shima goyon bayan auren yake yace mata a'a kawai tunda Hajiya tana so ba yadda za'ai dole suyi mata biyayya ta d'an ta6e baki kawae, yaran su ne suka fara shigowa yi mata sannu da zuwa don basu san ta dawo ba saida mai aikin su da ta ga dawowar ta ta sanar masu, saida Dr yaga ta d'an saki fuska sannan ya tafi, Abraham ne ya lura da yanayin Mahaifiyar tasu da Yazo yi mata sannu da zuwa yana fita ya wuce d'akin Farha don ya sanar mata, tana zaune a bakin gadon gaba d'aya ta rasa abunda yake mata dad'i sai tunanin ta ina ma zata fara take lokacin Farha ta shigo tana sanye da vest da d'an guntun wandon jeans fararen cinyoyinta tas masu k'auri don zuwa yanzu ta k'ara girma da k'iba sun bayyana, kunnuwanta sakale da earpiece ash d'in sumar ta ta faka ta a tsakiyar kanta jelar ta saukko bayanta, had'a ido sukai da Mom d'in nata ta sakar mata d'an murmushi ta nufe ta, a gefenta ta zauna ta kai hannu ta cire kan earpiece guda daga cikin kunnanta tayi mata sannu da dawowa da turanci ta d'aga mata kai kawai, itama ta lura da yanayinta da Abraham ya fad'a mata ta kai hannu ta kama hannunta guda tace "Mom what's happening, u look all worried, kince a can zaki Weekend amman miyasa kika dawo yau?" Kallon ta kawae tay ba tare data ce komae ba Farha d'in ta d'an yamutsa fuska a shagwa6e tace "pls Mom tell me mi ke damun ki ne?" d'an hucin numfashi tay tace "I can't Spend the Weekend there Farha...." Shiru tay tana jinjina kai 6acin rai shimfid'e a kan Fuskar ta, kan Farha ne ya d'aure da alamun mamaki tace mata Mike faruwa da bazata iya yin Weekend a gidan Hajiya ba, "Gidan Hajiya ya zama gidan 6acin rai Farha" ta kai hannu ta cize Yatsa, a shagwa6e Farha ta hau yi mata magiyar ta fad'i mata abunda ke faruwa tana d'an jijjiga hannunta da ta rike, Labarin abunda ya faru ta shiga bata baki sake Farha ke kallon ta har ta gama sannan da tsananin mamaki ta maimaita Ya Haisam yayi Aure ba tare da sanin kowa ba, gaba d'aya ranta bai bata Fatuu bace da yake ba komai ta fayyace mata ba saida ta tambaye ta wadda ya aura tay mata bayanin ta nan take ta ganeta ta wani irin zabura sai kace wadda shock yaja, baki bud'e cike da Al'ajabi tace "U mean he married that bitch!!" Uhmm kawai Hajiya Maryam ke fad'a, hannu Farha ta kai ta cire d'ayan kan earpiece d'in ta jefar tare da wayar a saman gado ta mik'e ta fara kai da komowa tsananin 6acin rai kwance akan fuskar ta ta wani kalan had'e rai sai huci take kai kace ita akai ma kishiyar, komawa tay ta zauna ta fara fad'in "impossible Wllh! That bitch can never be Sis Fanan's rival" nan da nan Fuskarta ta hautsine tay jajir har ta fi ta uwar nuna 6acin rai, cigaba tay "That's why from the day I first saw her i hated her completely, she's a gold digger!" shiru Hajiya Maryam tay sai d'an cize baki take tana jinjina kai, suna haka wayarta ta fara ringing ta kai hannu gefenta ta d'aukko, ganin Hajiya ce mai kiran yasa ta d'an yin jimm kafin tay picking ta kara a kunne tare da yin sallama, gaisawa sukayi tayi mata an isa lafiya ta amsa tace mata ana nan anata fushin tace Uhmm akwae, "Naji abunda kika je kika yi ma Yarinyar nan, wato don kin ji nace sai in ita tace bata son Auren shine kika je kikai mata haka don ki tsoratar da ita ko, anya Maryam! Yanzu Saboda soyayyar D'iya kike neman bijire man, a tunanin ki yanzu in ta nuna bata son Auren bazan gane ke ki ka sa ba? shikenan tunda kin za6i Farincikin d'iyar ki ita kad'ai kiyi duk abunda kike tunanin yi ban hana ki ba tunda kin za6i ki kauce hanya, sai dai ki sani a Matsayina na Mahaifiyar ki ban amince kiyi ma Yarinyar nan wani abu ba, ki gaishe man da kowa" daga haka ta katse kiran, wurgi tay da Wayar ta kai hannu ta bugi katifa tana yamutsa fuska tamkar zata fashe da kuka, nan da nan kwalla suka taru cikin idanunta ta fara fad'in miyasa Hajiya zata za6i Faranta ma 6are fiye da nata, ruk'e hannunta Farha ta k'ara yi fuska a yamutse tamkar itama zata saka kuka ta shiga lallashin ta tana tambayar mi Hajiyan tace mata, fad'i mata tay ta hanata ta d'auki kowanne mataki akan Yarinyar, fuska a kumbure kamar zata fashe tace mata ta daina damuwa idan suka yi hutu ita zata ce gidan sai ta fitar da ita da tsiya, jin haka yasa Hajiya Maryam samun sassaucin k'unar da zuciyarta ke yi Saboda tasan halin Farhar bata da Sauk'i dama itama ta nuna ma Fatun zata iya mata Asiri kawai don barazana amman sam bata bin Malamai ko bokaye iyaka ta bada ayi mata Addu'a kaman akan business d'in ta ko wani Al'amari, yanzu kam sai taji ta samu Mafita, nan ta fara kitsa ma Farhar wutar da zata hura ma Fatuu in ta je a 6oye ba tare da Hajiya ta sani ba har tasata da kanta ta bar gidan. Washe gari Lahadi da Yamma Senator ya koma Abuja bayan ya k'ara zuwa wurin Hajiya sun tattauna game da Auran tace mashi yay k'ok'arin fahimtar da matan shi yace in sha Allah, anan ya iske Fatuu suka k'ara gaisawa har yana tambayar ta in tana son wani abu tana murmushi tace ba abunda take so yace mata ta dage da karatu, da daddare bayan sun gama cin Abinci ya buk'aci ganin matan nashi a part d'in shi, bayan sun zo a nutse ya fara masu bayanin dalilin kiran nasu da Hajiya tay, gaba d'ayan su sun ji Al'ajabin Maganar ba ma kamar Mahaifiyar Haisam d'in, bazaka gane yadda ta d'auki Al'amarin ba daga yanayin Fuskarta ta tambaye shi mi Hajiya Maryam tace game da hakan, bai 6oye mata komai ba game da yadda ta ji zafin abun dama abunda tay tunani kenan a cikin ranta dole tasan baza su ji dad'in abun ba, ba kamar da taji yarinyar har ta samu ciki, jin tayi shiru yasa shi ce mata bata ce komai ba ta d'an watsa hannu tace to ita mi zata ce kawai dae Haisam bai kyauta ba ya zaiyi abu irin wannan ba tare da neman shawara ba tun farko gashi yanzu rayuka na neman 6aci na Hajiya Maryam aka gani ina ga ita Fanan d'in, nunawa tayi ita tana ganin gara a raba su kawae zai fi da azo asamu rashin Fahimta, Aunty tace "Gaskiya ni ina ganin in aka ce a raba su ba'ai ma Yarinyar Adalci ba kaman yadda Hajiya tace tunda shi ya fara sanin ta yanzu in aka raba auren dole sunanta zai canza zuwa bazawara, kuma ni ina ganin yana son ta ne shiyasa tun farko ma ya auretan ko kuma daga baya ya fara sonta shiyasa har abu ya shiga tsakanin su, haka da bai son ta sai inga kaman bazai yarda yaci gaba da zama da ita ba" d'an jimm Mom d'in shi tay alamar tunani kafin tace "zai iya auren ta don ya taimaka mata kawae and zai iya cigaba da zama da ita tunda Hajiya na son hakan koda bai son ta" gyad'a kai Aunty tay "hakane, nasan halin shi sarae zai iya kasancewa hakan, amman dai kamar yadda Hajiya tace ina ganin muyi masu Fatan Alkhairi kawae don ni ina ganin dama can Allah ya k'addaro matar shi ce shiyasa ma har suka san juna" jinjina kai Senator yayi Mom d'in Haisam da yanayin fuskar ta ya sauya tace basu ganin Hajiya Maryam zata ga suna supporting d'in shi Saboda d'an su ne basu damu da halin da Fanan zata iya shiga ba, Senator ne yace to tunda Hajiya haka take so ai dole su bi abunda take son sannan yasan damuwarta Saboda tunanin halin da Fanan zata shiga ne idan Allah yasa bata tashi hankalin ta kamar yadda take tunani ba yana ganin komai zai daidaita, cigaba da tattaunawa sukai daga baya suka bar part d'in nashi, Bayan Mahaifiyar Haisam ta koma Bedroom d'in ta, a gefen tanfatsetsen gadon ta daya sha k'ayataccen bedsheet ta zauna tay shiru tana kallon wuri guda da alama zurfin tunani ta shiga, sam ta kasa gane mi take ji game da Al'amarin, wayarta ta d'ago ta fara k'ok'arin kiran Haisam, bayan ta fara ringing ya d'aga suka gaisa tace mashi taji abunda ya aikata ba tare da sanin su ba batare da kuma yayi zurfin tunani ba mi zai sa yayi Aure da sunan taimako bazai yi amfani da wata hanyar ba, hak'uri itama ya bata tace tunda yaje yayi gaban kan shi ai dole suyi hak'uri amman yasan yadda zai yi ya fad'i ma Fanan ba tare da ta tada hankalin ta ba yace zai yi hakan in sha Allah cikin nuna k'auna yay mata Sallama tace Uhmm kawai, bayan sun gama wayar d'an jimm tayi sai kuma ta fara k'ara yin kira, Jidderh ta kirawo tace tazo d'akinta tana son ganinta, after few minutes ta shigo tana sanye da doguwar riga kanta ba kallabi sai bak'ar sumar ta wuluk da ta faka hannunta ruk'e da wayarta ta nufo gefen gadon ta zauna tace gata, "Akwai wani yarinya Neighbor d'in Hajiya I can't remember her name amman sun saba da Hajiya sosae...." Katseta Jidderh tay da fad'in "Sis Fatuu?" d'an d'age ido tay alamar tunani tace ta dai manta sunan k'ilan itace da sauri Jidderh tace bari ta nuna mata picture d'in ta ta gani in itace, shiga cikin gallery d'in wayarta tayi ta bud'o hoton Fatuu ta nuna mata tana gani ta shaida Fuskarta tace mata itace, tambayar ta Jidderh tayi miya faru da ita da d'an alamun rudu Mom d'in nasu tay d'an guntun murmushi tace ba komai she just wants know about her, cikin rashin fahimta Jidderh tace mi take son sani game da itan, tana d'an yarfa hannu tace kaman ya halayyarta take da mu'amalarta da Mutane haka, Murmushi Jidderh tayi harda gyara zama don tana bala'en k'aunar Fatuu nan ta shiga fad'i mata halayenta tace tana da kirki sosae ga faran faran ga son mutane gashi tana da dad'in zama bata da wuyar sabo kuma daka zauna da ita sai kaji ta burge ka, nan ta fad'i mata farkon saninta da ita lokacin data dawo daga Yola tazo gidan Hajiya da kayan Fulani har hoton da suka yi ranar ta bud'o mata da tasa Haisam ya turo mata don ta rasa shi, labarin tsakaninta da Ya Haisam abunda ta sani da wanda Hajiya ta basu labari ta shiga bata, tace mata yanzu haka suna gaisawa don ta zama kamar k'awarta ma, tambayar ta tayi zasu yi shekaru d'aya tace "No na girme ta da kusan 3 years ma, kawai dai she has a good shape kinga hips d'in ta kuwa Mom wllh kyace ba nata bane in kin ganta sun yi haka..." ta mik'e tana gwada ma uwar yadda hips d'in Fatuu suke ita dai sai murmushi take, komawa Jidderh tay ta zauna tace mata wai miyasa take son sanin abubuwa game da ita ne, shiru ta d'anyi tana rolling eyes ta kalleta da murmushi tace "Now she's part of this Family" waro ido Jidderh tay baki bud'e alamar mamaki cikin daurewar kai tace bata gane ba, ce mata tay Yayan su ya Aureta cikin rashin fahimta ta d'an waro ido tace Ya Nameer, yar harara ta wurga mata tace Nameer d'in da bai a K'asar Big bro d'in su take nufi, k'ara waro idanu waje tay tana kallon Mom d'in nasu da itama take kallonta ta d'an ta6e baki da d'an murmushi, cike da Al'ajabi ta tambaye ta yadda akai ta zama Matar Ya Haisam d'in nan ta fad'i mata, aikuwa ta washe baki cike da Murna tace "Oh my God! am so Happy to hear that Mom, wllh na dad'e ina masu sha'awar auran juna don sun dace sosae ba K'aramin fahimtar juna zasu samu ba, kaman fa shi ya raine ta Mom, bai son 6acin ranta bata son 6acin ran shi itama, sosae jinin su ya had'u baki ga yanda suke kulawa da juna ba, tun bayan dana santa dashi naga sun bala'en yin matching saidae kuma nasan ba zai aureta ba Saboda Maganar auren su da Aunty Fanan kuma lokacin tayi k'arama ma, daga bayan nan data girma inta ji inama suyi aure, ashe da rabon zasu yi d'in" cike da Farinciki take Maganar sai faman washe baki take, d'an d'aure Fuska Mom d'in tayi tace ai raba Auran za'ai nan da nan murnarta ta koma ciki tay mata wani kallo kaman zatai kuka tace "but why Mom, Don Allah kar a raba su" d'an ta6e baki tay tace Auren na son kawo rashin fahimta don Momy d'in su ta Lagos ta d'auki zafi sosae sannan Fanan ma tasan in taji za'a iya samun matsala, Fuska a yamutse Jidderh tace ai dama dole hakan ya faru Saboda kishi amman daga baya tasan komai zai daidaita zasu yi hak'uri ita dae don Allah kar su raba Auran, yar harararta Mom d'in tayi tace da yake ba ita akai ma kishiyar ba a shagwa6e ta kama hannun Momyn tana mata Magiya, ganin tana murmushi yasa ta gane wasa take cike da zumud'i tace bari ta kira mata Fatun su gaisa, har ta d'ago wayar ta dakatar da ita tace ba yanzu ba ta bari aga komai ya daidaita itama kar ta fad'i ma kowa cikin yan uwanta tace to, ce mata tay zata iya tafiya ta mik'e tana fad'in zatai ta yin Addu'a Allah yasa komai ya daidaita da wuri su sha shagali don duk abunda akai a bikin Aunty Fanan itama sai anyi Momyn tace Uhmm kawai ta nufi kopar fita tana ta murna ta fice............. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:29] +234 901 700 4868: * ASM 071* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........A nutse ta fara karanta sak'on wanda ke bayyana sirrin zuciyar wadda ta turo wato Zarah, bayanin tun lokacin da Allah ya jarabeta da son shi da irin wahalar da ta sha hakane ma yasa ta amince ai mata Aure Saboda ta rasa shi har Allah ya juya Al'amarin ya aureta, Hak'uri ta bashi kan zargin shi da tayi ta nuna bata san akwai Aure ba a tsakanin su kuma Saboda son da take mashi ne yasa taji zafin abun sosae hakane ma yasa data samu ciki tak'i saurarar shi harta 6arar don kuma bata son girman shi ya zube a idon mutane duk don k'aunar shi da take, a k'arshe ta nuna mashi tana cikin mawuyacin hali Saboda canza mata da yayi a yanzu da burinta ya cika ta zama Matar shi, Hak'uri ta k'ara bashi tace in don cikin da ta 6arar ne yake nuna mata halin ko in kula in sha Allah zata biya shi fin shi ma amman tana a cikin matsananciyar damuwa da har tana son shafar karatun ta........., Tun Fanan na karantawa lafiya lau har ta kai yanayin Fuskar ta ya fara sauyawa, lokacin data gama karantawa d'agowa tay da yanayin d'aurewar kai ta kallo hanyar Kitchen da Haisam ke ciki, k'ara maida idonta tayi akan Screen d'in tana sake biya sak'on lokaci guda hannuwanta suka fara yin kerma ta zuro da fararen k'afafuwan ta k'asa, Slowly ta mik'e har lokacin tana cikin k'ara karanta sak'on, saida ta karanta shi sau ukku tamkar mai yin hadda, gaba d'aya ta kasa gasgata abunda take karantawa gani take kamar ba daidai take karatun ba ko kuma ba sak'on Haisam d'in bane hakan yasa sai k'ara maida idonta take tana k'ara karantawa, zuciyar ta ce ta shiga gasgata mata sak'on shi ne in ba haka ba mizai sa ta turo mashi kuma ga alamu nan a bayyane har sunanta an ambata a ciki kan ciwon da ta yi lokacin da Fanan d'in tazo......."Kenan Auran Zarah ya yi a 6oye???" ta fad'a acikin ran ta, wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi mata ta fara numfashi da k'arfi har saida ta d'an bud'e baki jin numfashin na neman yi mata wuyar fitarwa, tana haka Haisam ya shigo cikin parlon yana sanye da wando 3 quarter da armless hannuwan shi duka biyun ruk'e da mug d'an tiriri na fitowa alamar abun ciki mai zafi ne, wani irin kallon tashin hankali ta shiga bin shi da shi hakan yasa shi dakatawa daga d'an gabanta yana kallon ta shima har saida gaban shi ya d'an fad'i ganin yanayinta da kuma wayar shi dake hannunta don yanayin kallon da take mashi na tuhuma ne, nufo shi tay a fujajen tana zuwa fuska a hautsine ta d'aga mashi wayar shi dake hannunta daidai kan sak'on a kid'ime tace "Don't tell me dis message is for you!!!" maida idon shi yay akan Screen d'in ya gane Zarah ce ta turo saidai bai fahimci miye akace a sak'on ba, wucewa yay yaje ya aje mugs d'in akan c-table ya juyo lokacin itama ta juyo tana kallon shi, hannu ya kai ya amshi wayar ya fara karanta message d'in a nutse har ya gama, d'agowa yay ya kalleta ta kafe shi da idanunta da ta zaro Fuskarta har ta fara yin ja alamar motsuwar jini, shiru yay kawai yana kallonta yama rasa mi zai ce mata don komai sak'on ya bayyana, girgiza kai ta shiga yi tana fitar da numfashi da k'arfi cikin d'an k'araji tace "so it's true, You married Zarah without my knowledge!" still bai ce mata komai ba aikuwa ta daka mashi tsawa a gigice tace "tell me! is she ur Wife??" d'an cize lip d'in shi yay na k'asa Slowly ya lumshe mata ido nan take ta gane mi hakan ke nufi, cikin fitar hayyaci ta fara ja da baya tana cigaba da girgiza mashi kai, bin ta ya fara yi yana ce mata "I can explain myself..." a haka har ta dangane da kujera kawai sai ta haye saman ta gudun kada ta yi ma kanta wani abu yasa shi kai hannu zai kamo ta ai kuwa ta tafi gaba d'aya ta wuntsila bayan kujerar ta fad'a saman tiles daga jin k'arar ba K'aramin bugawa tay ba, juyawa yay da sauri ya zagaya lokacin har ta mik'e tana k'ok'arin rugawa d'aki cikin zafin nama ya kamota ta fara kokowar kwacewa cikin k'araji fuskarta da idanunta sunyi jawur take fad'in "Leave me alone! Ya Haisam u'r a betrayer! u betrayed my trust, u broke the promise u have made to me! U deceived me....!" Gaba d'aya bata a cikin hayyacin ta idanunta sun jik'e da k'walla fatar k'asan idon tayi wani irin ja kamar jini, sai kiciniyar k'wace kanta take ta kansa sai rarrashinta yake yana ta tsaya zai mata bayanin yadda hakan ta faru amman ina tak'i sauraren shi fad'i take ba abunda zai fad'i mata ta san don ance tana da matsala shiyasa yayi tunanin bazata haihu ba yaje ya auri Zarah gashi nan har yayi mata ciki duk da Alk'awarin da yayi mata, abu fa ya ture gaba d'aya Fanan ta burkice mashi duk ta rud'a shi har fuskar shi ta bayyana, da dai taga ta kasa kwacewa kawae sai ta kai bakinta a jikin damtsen shi dake a bayyane ta daddage ta gartsa mashi cizo aikuwa ba Arzik'i ya saketa Saboda rad'ad'in Azabar da ya ratsa shi wurin har ya fashe nan da nan jini ya fara zubowa, ai yana sakinta ta watsa a guje hanyar Bedroom yana ganin haka shima ya bita don ya fahimci abunda take son aikatawa haka take da ranta ya 6aci sai ta ruga ta kulle kanta a cikin d'aki, ko kafin ya cimmata tuni ta shige lokacin daya kai hannu cikin zafin nama zai bud'e kopar data turo tuni har tasa Key, bugun k'opar ya fara yi da d'aga Murya yana kiran sunanta yana ta bud'e karta yi ma kanta illa, tana shiga d'akin a haukace ta nufi bango ta fara kai mashi bugu tana wani irin kuka na fitar hayyaci, har saida knuckles d'inta suka fara fitar da jini sannan ta daina ta nufi gado ta zauna dabar tana cigaba da kukan, a ranta ta fara tariyo sak'on aikuwa ta k'ara tsananta kukan ta fara sambatu tana fad'in Ya Haisam da Zarah sun ci amanarta, tunowa da Maganar ciki da ta samu tasa ta kai hannu ta fara bugun Katifar hakan bai sa ta samu sassaucin abunda take ji ba acikin zuciyarta sai ma k'ari nan fa ta mik'e ta fara wurgi da abubuwa abun har ya kai da fashe fashe, gaba d'aya hankalin Haisam ya gama tashi sai faman bugun k'opar yake da k'arfi yana kiran sunanta yana fad'in kada tayi ma kanta wani abu ta bud'e kopar, har ta kai ya fara mata Magiya ko tana jin shi ma oho ba dai alamun zata bud'e, sintiri ya shiga yi tsakanin Window wadda itama take a kulle da kuma kopar yana tunanin Mafita, zuciyar shi ce ta bashi ya fara bugun kopar k'ilan yaci sa'a ta bud'e duk da yasan mawuyacin abu ne don dakakkar k'opa ce, ba irin bugun da bai ma kopar ba iyakar k'arfin shi amman ba alamun zata bud'e dole ya dakata don shi kan shi ya gaji, Hajiya ce ta fad'o mashi a rai a rud'e ya nufi cikin parlon inda Fanan ta jefar da wayar ya nufa ya d'auka, tana fara yin ringing Hajiyar ta d'auka ko gaida ita bai yi ba ya shiga fad'i mata abunda ke faruwa itama rud'ewa tay ta shiga tambayar shi dama bai sanar mata ba duk da tasan inda ya sanar mata zata ji kawai ta rud'e ne, ce mata yay eh ya bari yayi 2 Months da dawowa sai ya d'auki hutun da basai an rink'a biyan shi ba su taho nan Nigeria su kwana biyu lokacin sai ya sanar mata dama irin haka yake gudu shiyasa, tambayar shi tayi to yanzu ya akai ta sanin yay d'an jimm hakanan sai yaji baison fad'i mata zancen sak'on da Zarah ta turo sai yace mata kawai a Wayar shi ta gane, ce mashi tay to yayi k'ok'ari ya 6alle kopar mana yace mata ba irin k'ok'arin da bai yi ba tak'i bud'ewa, tambayar shi tayi anan ba masu aikin 6alle k'opa ne sai lokacin ya tuna da sauri yace mata ba'a rasawa tace to yay hanzari don Allah ya kira azo a bud'e kar wani abu ya sameta ta razana ne sosae ba ta haka yakamata ta sani ba. Bai san ina zai samo wanda zai 6alle kopar ba amman da yake yana a K'asar da aka cigaba ne komai k'ank'antar sana'ar mutum zaka samu ya d'aura a internet, yana yin searching sai gashi ya samu, kiran su yay a waya ya fad'a masu aikin da yake so ayi mashi da Address d'in gidan, bayan sun gama komawa yay wurin d'akin yana cigaba da knocking wai ko zata bud'e amman shiru abunda ma ya k'ara tayar mashi da hankali jin shiru bai jin wani motsi sa6anin da yana d'an jin k'arar abubuwan da take yi, kai da komowa ya shiga yi duk fuskarshi ta harmutse, bada jimawa ba sai ga mai 6alle kopar ya iso, ba 6ata lokaci ya 6alle Haisam har yana yin tuntu6e Saboda saurin ya shiga, a kwance ya isketa k'asa ya nufeta da sauri ya duk'a, ganin bata motsi yasa a rud'e ya kai hannu ya fara jijjigata yana kiran sunanta yana ta bud'e idonta, gaba d'aya bata numfashi ga hancin ta duk jini alamar tayi ha6o haka hannuwanta ma glass ya d'an yayyanke ta, da sauri ya mik'e ya nufi closet ya bud'e ba tare daya tsaya za6a ba ya janyo wata doguwar riga dake sagale da mayafinta ya dawo inda take ya fara k'ok'arin zura mata, kinkimar ta yayi da taimakon wanda ya balle kopar aka sakata a Mota bayan ya sallame shi ya shiga yajata da gudu ya fice ko tunanin ya canza kaya bai yi ba, Tun bayan da Fauzy ta tura sak'on tay zaune tsuru gabanta na cigaba da fad'uwa sai fargabar abunda zai je ya dawo take a ranta ta shiga yin Addu'ar Allah yasa in yaga sak'on komai ya daidaita tsakanin su, saida aka kira sallar la'asar sannan ta tada Fatuu don tayi salla, bayan ta gama ta zuba mata Abincin ta fara ci, ta lura da yadda Fauzyn keta faman bin ta da ido hakan yasa ta tambaye ta lafiya ta d'an yi murmushi tace mata ba komai, kokonto Fauzy ta shiga yi na kodai ta fad'i mata kar daga baya ta gane taga tayi mata ba daidai ba, zuciyarta ce ta bata gara ta fad'i mata kawae in ma ta nuna bata ji dad'i ba sai ta bata hak'uri, bayan ta gama cin Abincin ne ta fara shirin tafiya, saida ta gama shiryawa ta maida Uniform d'inta sannan Fauzy tace mata tana son zasu yi magana, zama tayi a bakin gado Fauzy na facing din ta a d'ayan gadon a sanyaye tace "na maki katsalandan Zarah nasan yana iya zama laifi a wurin ki" da alamun mamaki tace laifi kuma wane irin laifi, Wayarta dake ajiye gefenta ta d'auka ta bud'o sak'on data tura ma Haisam ta mik'e ta kai mata, zuba ma Screen d'in ido Fatuu tayi tana karanta sak'on, tun kafin ta gama ta zaro ido ta kai hannun ta guda ta rufe baki alamar Al'ajabi, bayan ta gama karantawa ta d'ago tana kallon Fauzy dake tsaye gefe a rud'e tace "Fauzy miyasa kikai haka don Allah? Miyasa zaki tura mashi wannan sak'on haka?" Kamar zata yi kuka ta k'are Maganar tana yamutsa fuska idanunta har sun ciko da k'walla, zama Fauzy tay daga gefen ta cikin kwantar da murya tace "kiyi hakuri Zarah dama nasan ba lalle Kiji dad'in abunda na aikata ba, wllh tausayi kike bani ne abubuwa sun maki yawa daga wannan sai wannan ina gudun damuwar hakan tasa kizo ki fad'i Exam shiyasa nayi tunanin idan na tura mashi bayanin komai tunda shi mutum ne mai tausayi watak'il hakan yasa ya karkato da hankalin shi gare ki, nasan da kin samu kulawar shi zaki samu kwanciyar hankali" girgiza kai Fatuu tayi kwallan idonta suka fara zubowa tace ita dai da bata aikata hakan ba don hakan tamkar zubar da k'imar ta ne kuma yanzu koda bai son ta dalilin hakan zaisa ya cigaba da zama da ita Saboda tausayi ita kuma bata son hakan gara in bai sonta kawai su rabu, ganin yadda ta damu yasa Fauzy kama hannunta tace "ba wata k'imar ki da zata zube kar ki manta shi Mijin ki ne kuma dana bayyana mashi kina son shi ai kinga nace Allah ne ya jarabe ki shima yasan bake kika d'aura ma kan ki ba kuma tunda shi ba mutum bane mai wulakanci hakan bazai sa ya wulakanta ki ba sai ma kulawa dake, kuma ni nasan ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba koda kin nuna mashi ya sake ki bazai ta6a sakin ki ba domin da zaiyi hakan ai da bazai ma cigaba da zama dake ba gashi har mahaifin shi ya kar6e ki, uwa uba kuma Hajiya da take iko dasu gaba d'aya ita ta goyi bayan kuci gaba da zama tare kinga gara ya san kina son shi koda shi bai son ki in yana kula ki sai ki koya mashi son naki" a marairaice take Maganar, ita dai Fatuu sam hakan bai mata dad'i ba wllh sai yamutsa fuska take tana kwalla, k'ara duba sak'on ta shiga yi lokacin ta lura da marking d'in da yayi bai yi blue ba hakan yasa ta fara tunanin koma bai duba ba to, zuciyarta ce ta fara gasgata mata hakan ta shiga raya da ya gani tasan k'ilan ya ce wani abu don da wuya ya shareta, yin wannan tunanin yasa da sauri hannunta har yana rawa tayi delete for everyone duk Fauzy na kallon ta, wani sanyi taji a ranta fuskarta ta daidaita, ganin haka yasa Fauzy bata hak'uri tace tunda bata ji dad'i ba ta yi Addu'ar Allah yasa ba Gb WhatsApp gare shi ba Fatun tace mata ba komai tasan don Farincikin ta tayi hakan amman tafi son ya zauna da ita don yana son ta ba don tausayi ba idan ya dawo da kanta zata rok'eshi kan ya saketa, harda cewa in ma ya k'i zata ce mashi tana da wanda take so ne Fauzy tay d'an murmushi kawae a ranta ta raya fad'i kawai take tasan ba iyawa zatai ba don ba K'aramin kamu son shi yay mata ba, tare suka fito da Fauzy ta rako ta, ganin Fauzyn duk tayi sukuku yasa Fatuu bata hak'uri tace in ta 6ata mata rai Fauzyn tay murmushi tace a'a wllh ai ita zata ba hak'uri tayi mata ba daidai ba, Fatun tace itama bata d'auke shi a wani abu ba, saida ta hau Keke Napep sukai sallama tace ta gaishe mata da Mino sannan ta koma. Asibitin da take aiki ya kaita, nan da nan aka nufi Emergency da ita bayan Haisam d'in ya masu bayanin ta razana ne kuma ranta ya 6aci sosae, nan da nan likitoci suka taru kanta duk abunda ake mata Haisam d'in na gani ta faffad'an window d'in d'akin da yake gaba d'ayan shi transparent glass ne, Bayan wasu mintuna d'aya daga cikin likitocin ya fito ya sanar dashi tayi doguwar suma ne za'a bata treatment d'in daya dace zuwa kowanne lokaci zata iya farfad'owa, sai lokacin Haisam ya d'an ji hankalin shi ya kwanta da gaba d'aya jinin shi akan akaifa yake tsoron shi kar ace ta samu heart attack, daga baya bayan likitocin sun fito ya shiga cikin d'akin, a kan kujera dake a gefen gadon ya zauna yana kallon Fanan dake kwance fuskar ta sanye da Oxygen mask, a ranshi yake raya irin abunda ya guda kenan yasa bai fad'i mata ba don yasan fin hakan na iya faruwa, yana zaunen nurse ta shigo suka gaisa ta nufi gadon Fanan d'in, bayan ta gama abunda zatayi har zata fita sai kuma ta tsaya ta kalli Haisam d'in da murmushi ta nuna damtsen shi da jini mai d'an yawa ya taru tace mashi ya samu rauni ne, ce mata yay eh tace bari tayi mashi dressing d'in wurin yay mata godiyar kulawa, bayan ta gama mashi zaune yay shiru nan ya fara tunanin sak'on da Fatuu ta turo mashi, wayarshi dake ruk'e a hannun shi ya d'ago ya bud'e ya shiga cikin WhatsApp, koda ya bud'e chat d'in Fatuu sai ya ga an goge sak'on, wani kalan murmushi ya saki yay d'an jimm sai kuma ya fita daga chat d'in, Hajiya ya kirawo dama koda yana kan hanya da zai kawo Fanan d'in saida ta kira ta tambayi halin da ake ciki don ta kira bai d'auka ba hankalin ta ya k'ara tashi, fad'i mata yay an 6alle kopar da yanayin da ya iske Fanan d'in yace gashi ma a hanya zai kaita Asibiti, Har bayan wani lokaci bata farfad'o ba k'arfe sha biyu da wasu mintuna ya bar Asibitin don su ba'a kwana wurin mara lafiya duk abunda yakamata za'ai mashi sai dae in buk'atar ganin wani nashi ta taso a kira, yana driving yana tunanin sak'on Fatuu har ya iso gida, bayan ya shiga parlor ya tsaya ya d'auke Computer d'in Fanan da wayarta dasu takardun da ke ajiye ya nufi ciki, Bedroom d'inta ya wuce ya ajiye su ya fara gyara shi, lokacin daya dawo Bedroom d'in shi toilet ya wuce yayo wanka bayan ya fito d'aure da towel ya tsaya gaban mirror yana tsane ruwan jikinshi da short towel d'in daya ruk'o, gaba d'aya Fuskar Fatuu yake ganin tana mashi gizo a cikin Madubin sai d'an sakin Murmushi yake, bayan ya gama ya nufi closet ya fiddo kayan bacci ya saka, bayan ya kwanta tunanin abu biyu ya shiga yi wato Fanan da Fatuu sak'on data turo mashi sai yawo yake mashi a rai, bazaka ta6a gane yadda ya ji ba dangane da sak'on daga yanayin Fuskar ta shi. Washe gari bayan ya dawo daga sallar Asuba a Motar shi ya fito jikin shi sanye da farar jallabiya, Bedroom d'in shi ya wuce ya cire rigar ya bar short d'in jikin shi da singlet ya fito ya nufi Kitchen don had'a ma Fanan Breakfast koda zata farfad'o in yaje, Misalin k'arfe takwas na safiyar ya gama shiryawa cikin k'ananun kaya ya fito ya wuce Kitchen, bayan ya d'aukko basket d'in da ya zuba kayan breakfast d'in ya fito ya tafi, Har lokacin daya je bata farka ba ya aje basket d'in ya zauna, after some minutes ya mik'e yaje yay ma Nurse d'in dake kula da ita magana kan zaije ya dawo, bayan ya fito daga Asibitin wurin aikin shi ya wuce don yaje yay reporting kan ciwon matar ta shi. Wuraren k'arfe goma ya dawo still bata farka ba ya zauna idon shi akanta daga baya ya fara latsa wayar shi, bayan kusan awa guda da dawowar shi ta fara motsi yana ji da sauri ya kai idon shi kanta, a hankali ta fara motsa idanunta ta fara bud'e su tana yi tana lumshe su, tashi yay ya nufi gadon ya tsaya daga gefen inda kanta yake yana kallon ta, k'amshin turaren shi da ya cika mata hanci ne yasa ta bud'e idanun suka sauka a kan Face d'in shi, bin juna sukai da kallo Fuskarta har ta d'an fad'a, cikin cool voice d'in shi yace mata sannu aikuwa tamkar ya tuna mata da abunda ya faru ta kai hannu ta cire Oxygen mask d'in fuskarta, tashi tay zaune cikin fushi ta fara k'ok'arin cire cannular d'in k'arin ruwa da aka saka mata Haisam d'in na ta bari amman tamkar ma zuga ta yake, tana gama cirewa ta saukko daga saman gado ta kai hannu ta d'auki veil d'in rigar jikinta ta yafa saman kanta ganin abunda take shirin yi yasa shi zagayawa yasha gabanta ta fara k'ok'arin ture shi, ruk'e hannunta yay ya fara lallashin ta yana tayi hak'uri a gama dubata in sunje gida zai mata bayanin komai, a fusace take fad'in ya bata hanya ta wuce bin ta yay da ido sai kace ba Fanan d'in daya sani ba mai yi mashi biyayya sam bata tsallake Maganar shi, Nurse ce ta shigo ganin abunda ke faruwa yasa ta juya taje ta kira Dr, bayan ya shigo ya tambayi abunda ke faruwa Fanan d'in tace mashi gida zata tafi rarrashinta ya shiga yi shima kan ta bari ta samu sauk'i sosae ta kafe sai ta tafi fuskarta ba alamun sassauci k'arshe dole suka k'yaleta ta tafi, Haisam na niyyar bin bayanta Dr ya tsaida shi Magana yayi mashi kan halin da take ciki yace yayi k'ok'ari aga ta rage 6acin ran ko kuma ma asan yadda za'a rabata dashi don a halin da take ciki akwae yuwuwar ta iya samun heart attack saboda 6acin ran yayi yawa gashi har jininta ya hau, godiya Haisam yay mashi bayan ya gama mashi bayanin, koda ya fito harabar Asibitin bai ganta ba ya nufi inda ya parker Motar shi ya shiga, bayan ya fito daga Asibitin bai yi nisa sosae ba ya ganta a tsaye bakin titi, tsayawa yay ya sauke glass ta cikin Motar yay mata magana kan ta shigo su tafi amman ko kallon shi bata yi ba k'arshe ma sai taci gaba da tafiya gashi ba damar ya parker don ba'a parking a wurin, bin ta yaci gaba da yi da Motar har saida ta tsaida taxi ta shiga ya bi bayan su, bayan ta sun iso tana shigowa cikin gidan ta nufi Bedroom, wayar ta data hango saman bedside ta nufa ta d'auka, gefen gado ta zauna sai nishin 6acin rai take ta shiga kiran Mom d'inta, tana d'auka ta saka mata kuka a tsananin rud'e Hajiya Maryam ta shiga tambayar ta abunda ke faruwa cikin kukan tace mata Ya Haisam yaci Amanarta ya yaudare ta duk da Alkawarin da yayi mata yaje yayi aure bada sanin ta ba, cikin 6acin rai Hajiya Maryam ta tambaye ta shine ya fad'a mata tace a'a Wadda ya auran ce ta turo mashi sak'o ta gani, nan ta shiga fad'i mata halin da ta shiga, sosae Hajiya Maryam ta razana da jin a Asibiti ta kwana ta shiga kwantar mata da hankali tace itama tasan da Maganar Hajiya ta kira su ta fad'a masu ta nuna bata amince ba yanzu haka ma tana k'ok'arin raba su ne, cikin kuka Fanan d'in tace mata ita dae gida zata taho da sauri tace mata eh ta taho harda tambayar zata iya ko tazo ta taho da ita tace a'a zata taho, k'ara lallashinta ta shiga yi sosae tana kwantar mata da Hankali tace dole ma a raba Auran tunda bada izinin su aka yi shi ba, duk Maganar da take Haisam na tsaye daga gefen gadon tasan yana a wurin jin k'amshin turaren shi kuma taga lokacin daya shigo ta wutsiyar idon ta, tana gama wayar ta ajeta saman gadon ta mik'e, wardrobe ta nufa tana zuwa ta bud'eta, kayanta ta fara kwasowa ta kawo saman gadon tana shirin juyawa ta sake d'ibowa taji ya ruk'o hannunta, cikin fushi tace ya sakar mata hannu ba tare data juya ta kalle shi ba jin bai saki ba yasa ta juya a fusace tace "I said leave my hand!" kallonta kawai yake sam bai yi mamakin yadda take mashi ba don iya fuskarta kawae ta bayyana tsananin 6acin ran da take ciki, girgiza kai ta fara yi idanun ta suka ciko da k'walla cikin karyayyar murya ta fara fad'in "I feel deeply betrayed and disappointed by ur action, you broke a promise to me and now I can't trust you anymore...." Dakatawa tay tana fitar da numfashi da sauri kirjinta na hawa da sauka, sigh yay yana son mata magana yama rasa ta ina zai fara, k'ok'arin matso da ita yay don ya rungumeta aikuwa a fusace tace "Don't...!!!" ganin kallon da yake bin ta dashi ne yasa ta d'an sassauta murya idanunta na cigaba da zubar da k'walla tace "I can't believe dat you would betray my trust like this, u don't even care weather am gonna die.....Na daina son ka Ya Haisam! na daina, our relationship will end now sai kaje ka d'aukko Zarah kici gaba da Zama da ita" k'ok'arin fuzge hannun ta fara yi aikuwa ya janyota ta fad'o jikinshi ya sa duka hannuwanshi ya rungume ta gam ta yadda ko motsin kirki bazata iya ba, Kuka ta sakar mashi tana fad'in Ya saketa, ta tsane shi bazata cigaba da zama da shi ba, ganin bazata iya kwacewa ba yasa ta kifa Fuskarta a saman faffad'an chest d'in shi ta shiga raira kuka mai cin rai, Sigh yay ya kai bakin shi saitin kunnen ta cikin Magana mai kaman rad'a yace "am deeply sorry Fanan, I know I have wronged u, amman ban ci Amanar ki ba, lokacin da nayi maki Alk'awari Already akwai aure tsakanina da Zarah, if u could remember ban so yin Alk'awarin ba a lokacin" dakatawa yay dama tamkar Maganar na mashi wuya yake furta ta, shiru tay bata ce komai ba sai sheshsheka take, Cigaba yay "Now give a chance to explain Everything pls" shiru tay mashi saidae shesshekar da take ta ragu hakan yasa ya gane ta bashi damar, sakinta yay ya kama hannunta suka nufi bakin gado, zaunar da ita yay shima ya zauna ya juyo yana kallon ta ita kuma idonta na gefe, a nutse ya fara mata bayanin komai yadda akai Ya Auri Fatuu saida ta ji yayi shiru sannan ta juyo ta kalle shi still fuskarta a d'aure take tace mashi to miyasa ya kwanta da ita, d'an jimm yay kafin yace mata bada niyya bane shima baisan ya akai ya aikata hakan ba kuma ita kanta lokacin bata san ya aureta, shiru tay tana tunano sak'on data turo mashin a ciki ta bayyana bata san da aure a tsakanin su ba shiyasa ta zubar da cikin hakan yasa Fanan d'in gasgata Maganar ta shi wata zuciyar ta raya mata to amman miyasa zai nuna 6acin rai don ta zubar da cikin, kallon shi tay cike da tuhuma ta tambaye shi kan hakan tace kenan dae yana son Auren, nan ma saida yay d'an jimm kafin yace mata ita kanta ai tasan had'arin dake tattare da zubar da ciki hakan ne yasa bayan ta sanar dashi game da cikin tace zata zubar ya hanata gudun kada wani abu ya faru amman sai tak'i jin Maganar shi taje ta aikata sai gashi abunda ya gudan har kwanciya tayi Asibiti dalilin hakan, ji tay ta yarda da zancen shi hakan yasa ta d'an saki fuska tace mashi to tunda don taimako ya aureta ai sai ya saketa ko, ce mata yay Hajiya ta hana yanzu haka tasa an Kawo Zarah d'in part d'in shi, wani kalan d'aure Fuska tayi tace tunda shine mai zama da ita kuma bai so don me za'ai mashi dole, ce mashi tay ita gaskiya bazata zauna da Zarah matsayin kishiya ba in dai basu rabu ba to ita ta hak'ura da auren kuma yaci Amanarta, jin yayi shiru yasa tace mashi kawai ya tura mata sakin kaman yadda ta turo mashi sak'on, sai da ya nisa sannan ya d'an girgiza mata kai yace tunda Hajiya bata so bazai iya yin hakan ba tasan yadda take a wurin su, hakan ya k'ara 6ata mata rai tana d'an huci tay shiru tana d'an kallon gefe can ta jinjina kai ta kalle shi tace mashi suje Nigeria d'in tare ita zata ma Hajiya Magana shiru yay kawae yana kallonta ganin haka yasa da alamun zargi tace kodai dama shima yana son ta, d'an guntun murmushi yay yace mata kawai bai son a samu matsala ne dalilin hakan cike da tabbaci tace mashi ba wata matsalar da za'a samu tasan Hajiya zata goyi bayan abunda take so tunda dai duk basu son Auren, jinjina mata kai yay yace Shikenan ta tambayi yaushe zasu tafi yace nan da 2 weeks da sauri ta girgiza mashi kai tace mashi gaskiya yayi tsawo cikin satin nan zasu je yace Shikenan, sai gashi ta saki ranta harda d'an murmushi ta fad'a jikin shi cike da shagwaba take cewa an kusa asa zuciyarta tayi bursting yanzu haka da bai cire mata bak'in cikin da take ji ba tasan da wuya bata samu Heart attack ba, shidai murmushi kawai yake can ya d'agata yace suje tayi breakfast tace ya fara mata wanka bata jin dad'in jikinta, bayan an yo wankan ya taimaka mata ta shirya sannan suka fita don yin Breakfast, sai gashi ta sake sosae kamar ba ita ba suka cigaba da gudanar da rayuwar su yadda suka saba. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:29] +234 901 700 4868: *ASM070* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ........bayan sallar isha gwaggo ta nufi gidan Hajiya, lokacin data isa a parlor ta isketa ta yi mata maraba, ganin tayi tsaye ta nuna mata kujerar gefen ta tace ta zauna mana, bayan ta zauna ta gaishe da ita ta amsa tay mata ya aiki ta tambayeta Amadu kwana biyu bata gan shi ba tace yana nan, shiru sukai gwaggo ta d'an sunkuyar da kanta tama rasa ta ina zata fara, jin shirun nata yayi yawa yasa Hajiya cewa "Ya ya Dije, koda wani abu ne?" kallon ta tayi tay d'an murmushi kawai ba tare data ce komai, lokaci guda Hajiya ta fahimci abunda ya kawota tana murmushi tace mata ko itama Maryam d'in taje ta firgita ta, sai lokacin ta fara magana cikin sanyin murya tace "Hajiya dama zuwa nayi in rok'i Alfarma, don Allah tunda basu son auren ina ganin a hak'ura kawai don hankalin kowa ya kwanta, ban so silar hakan asamu rashin fahimta" d'an murmushi Hajiya tay ta d'an kya6e baki tace "to dawa dawa ye basu san Auren? Duka fa ita kad'ai ce ta nuna k'in amincewa kuma itama ba wani abu yasa ba face kishi da take taya yarta" shiru gwaggo tayi ita dai har cikin ranta tafi son a raba Auran kawae saidae bata iya yin jayayya da Hajiyar, ganin yanayin ta yasa Hajiya cigaba "ki kwantar da hankalin ki Dije ba abunda zai faru sai Alkhairi Fateema kuma tana nan Lafiya kuma ba abunda zai sameta in sha Allah, duk maganganun da taje ta fad'a maki barazana ce kawai ba wani abu ba" gyad'a kai gwaggo tayi tay shiru, can tace ma Hajiyar bari ta tafi tayi mata godiya Hajiya tace ta bari ta ci Abinci tana d'an murmushi tace mata a k'oshe bata jima da ci ba tace to bari a zubo mata ta kaima Amadu tace mashi tunda ya manta da matar ta shi gashi nan tana biko duk suka d'an yi dariya, Saude ta kira ta bata Umarnin zubo ma gwaggo Abinci, bayan ta kawo har zata bata Hajiya tace ta rakata part d'in Fateema ta ganta ko hankalin ta ya k'ara kwanciya ita dai gwaggo murmushi kawai take sukai sallama suka tafi Saude na ruk'e da Warmer d'in Abincin, Fatuu na cikin Bedroom ta fito daga wanka tana shiryawa da kayan bacci don tafiya part d'in Hajiya akai kopa ta nufeta ta bud'e, Saude ta gani sukai ma juna murmushi ta gaida ita tace mata ta zo ga bak'uwa ta kawo mata, d'an jimm Fatuu tay a ranta tana tunanin wace bak'uwa ce don rabonta da wani yazo tun cikin wanccan satin da Haulat tazo har take fad'i mata ta kusa komawa, juyawa tay ta d'aukko hula tasa ta fito, tana zuwa bakin corridor ta d'an wara ido tana son ganin wacece bak'uwar, gwaggo ta hango zaune akan armchair Saude na tsaye gefe aikuwa ta watso da gudu tana zuwa ta fad'a kanta cike da Farinciki take fad'in gwaggo dama ke ce bak'uwar, gaba d'aya dariya suke yi Saude na fad'in Fateema sai kace kin shekara baki ganta ba, ita dai gwaggo sai dariya take, sallama Saude tayi ma gwaggo tace ma Fatuu sai ta shigo ta juya ta nufi kopa, d'ago kai Fatuu tay suna kallon juna ita da gwaggo sai sakin murmushi suke, ganin gwaggon tak'i cewa komai yasa Fatuu tura baki a shagwa6e tace don Allah tayi magana mana, tana dariya tace taya zata yi Magana ta sakar mata nauyi jin haka yasa ta tashi maimakon ta zauna akan d'ayar armchair d'in sai ta haye saman hannun kujerar ta kama hannun gwaggon sai kace zata gudu, tambayar ta tana lafiya tayi tace mata eh sai lokacin ta tuna da bata gaishe da ita ba, shiru suka d'an yi Fatuu ta tambayeta Kawu Amadu tace ta wuto shi a shago yana gaishe da ita, shiru suka k'ara yi Fatuu nata wasi wasin ko ta fad'i mata abunda Hajiya Maryam tazo tayi mata, itama gwaggon tana son ta tambayeta ta rasa ta ina zata fara bata son Fatun ta fahimci taje gida kar ta tashi hankalin ta, "Daga wurin Hajiya nike, naji tace Mahaifin d'ana Haisam da Hajiya Maryam sun zo har sun koma" yanayin fuskar Fatuu ne ya sauya a hankali tace mata eh, "Yanzu sun san da Maganar auren kenan?" Kai Fatuu ta d'aga tace mata eh, amfani tay da canzawar fuskar Fatun tace mata ya taga Fuskar ta ta sauya ko da matsala ne, shiru tay tana d'an kikkafta ido tana son fad'i mata amman bata son hankalin ta ya tashi gwaggo ta fahimci da wani abu hakan yasa ta kwantar da murya tace inda wani abu ta fad'i mata in ba ita ba wa zata fad'i mawa, labarin abunda ya faru ta bata harda yadda Senator ya kar6eta, Fuskar gwaggon da murmushi tace mata ta kwantar da hankalin ta komai zai daidaita in sha Allahu itama kar ta k'ullace ta tana gudun abunda ka iya faruwa da d'iyarta ne tunda bata san da Maganar ba sai suyi ta Addu'ar Allah ya kawo komai cikin sauk'i, tambayar Fatun tay koda wani abu tace mata a'a ta mik'e Fatuu ma ta saukko tana fad'in don Allah ta bari su tafi tare ta kwana a can ta d'an harareta tace to bari ta d'aukko mayafi su fita tare ta rakata ita kuma ta wuce part d'in Hajiya tace to ta juya da sauri sauri gudu gudu ta nufi hanyar corridor gwaggo ta bita da kallo tana Murmushi. Bayan sati guda da zuwan su Senator Fatuu na a parlon Hajiya bayan la'asar suna yin kallo tana sanye da riga da skirt na atampa, akai akai Hajiya ke mata magana akan film d'in da suke kallo wani wurin ta bata amsa wani wurin kuma tay dariya kawai don Hajiya bata iya in tana kallo tayi shiru, Sallama akai daga can bakin kopar duk suka juya suka kallo mai sallamar, Kawu Amadu ne daga bayan shi kuma wata ce tana sanye da doguwar rigar Atamfa da Hijab Fatuu na ta son ta gane ko wacece ta kasa don sun d'an masu nisa gashi Kawu Amadu ya d'an kare ta, Hajiya ce ta d'aga murya tace su shigo mana sun yi tsaye sai kace parlon bak'on shi ne ya nufo ciki yana murmushi wadda suka shigo tare na biye dashi, suna zuwa bakin kujerun Fatuu tay zumbur ta mik'e da alamun Al'ajabi idon ta akan wadda yazo da ita, ganin murmushin da take mata yasa da k'arfi ta furta "MINO" dariya minon tayi aikuwa Fatuu ta watsa da gudu tana zuwa ta kankame ta Amadu nata dariya Hajiya ma kallon nasu take ta cikin glasses tana murmushi, zama Kawu Amadu yay ya gaishe da ita ta amsa tace kace da babbar bak'uwa kake tafe yace aikuwa, "To wai ni ba za'a bari in gaisa da k'awar tawa da ban sani ba sai a hoto" Hajiya tay Maganar idonta akan su Fatuu da suka saki juna suna ta ma juna dariya, kamo hannunta tayi suka nufo wurin Hajiya Mino na niyyar duk'awa ta gaishe da ita Hajiya ta mik'o mata hannu ta kama ta zaunar da ita a gefen ta, cikin hausar ta dake bayyana ita bafullatana ce sosae ta gaishe da Hajiyar tana fara'a ta amsa tay mata an zo lafiya da tambayar sauran yan'uwanta ta amsa Fatuu na tsaye gefe farinciki shimfid'e akan Fuskar tata, Hajiya ce tace mata ta zauna mana sannan ta zauna a kujerar kusa da su, "Ita Dije wannan shine Fateema ta tafi ga wata Fateemar ta zo" ta fad'a idon ta akan Mino da ke ta washe baki in ka ganta baka ce daga k'auye take ba tsaf tsaf da ita ba irin kwalliyar yan k'auyen nan iya jan baki kawae ta shafa ko jagira batayi ba don tana da gashin gira sosae kaman Fatuu gashi sai d'an k'amshin turare take, "kusan ma tsawon su d'aya da Fateema kawai yanayin jiki ne ba d'aya ba" Hajiya ta fad'a tare da kallon Amadu yana dariya yace eh ita da gani ma sai tafi Fatuu tsawo tace ba shakka, Fatuu dai sai murmushi take saki farinciki fal ranta yar uwa tazo, hannu ta kai ta dafo Shoulder d'in mino ta juya ta kalleta, tambayar ta tayi su Yadikko tace mata zasu zo amman ba yanzu ba sai daga baya Baffa ne dai suka zo tare da shi, "Kai haba! da Baffa kuka zo yana ina?" ce mata tay yana nan waje, kallon kopar shigowa Fatuu tayi ta nuna ta da yatsa tace bakin kopar nan ta d'aga mata kai alamar eh aikuwa zumbur ta mik'e ta nufi kopar da gudu, Kallon Amadu Hajiya tayi tace ya zai bar Mutum a waje yace mata shine yace ya fad'a tukun a bada izini, dariya Hajiya tay "wannan parlon na mutane har sai an nemi wani izini kaima Amadu ai da ka shigo dashi", ce mashi tayi yaje ya shigo dashi yace to, Fatuu na fita ta ganshi a gefe yana sanye da manyan kaya riga da wando na shadda brown kusan sun saje da kalar fatar shi kanshi sanye da hula saidai karin ta bai fita da kyau ba shima tsaf dashi harda su Agogo anzo gidansu suruki, da sassarfa ta nufe shi tana fad'in sunan shi tana zuwa ta kankame shi sai kace zata shige cikin jikinshi, yana ta dariya yasa hannu guda ya dafa ta, d'agowa tay da tsantsar farinciki tana kallon shi sai washe baki take ta kasa yin Magana shima idon shi na a cikin nata suna ta yi ma juna murmushi, suna haka Amadu ya fito yace mashi ance su shigo yace to, Fatuu na ruk'e dashi tayi mashi side hug suka shiga, suna isa cikin parlon ya fara k'ok'arin duk'awa ya gaishe da Hajiya ta dakatar dashi tace don Allah ga wuri ya zauna sai a gaisa, bayan sun gaisa tayi mashi ya aka baro mutan gidan yana ta murmushi ya amsa, kallon Fatuu dake gefen shi har lokacin tana a jikin shi Hajiya tay tace su Fateema an ga Baba an hana mashi sakat tasa dariya Amadu ya kai hannu alamar zai bugeta yace ta sake shi ya huta ta mak'e mashi kafad'a shi dae sai murmushi yake, godiya Baffan ya shiga yi ma Hajiya kan abubuwan Alkhairi da aketa yi masu da Addu'oi tana murmushi tace mashi ai ba komai an zama d'aya, kallon Fatuu tay tace "to mage sai a tashi aje a had'a masu Abinci ko" tana dariya ta d'ago a kunyace baffan yace a bashshi sun ci Abinci Hajiya tace eh ai tasan sun ci shima na nan d'in sai aci duka sukai murmushi ta kai hannu ta dafa jikin Mino tace ita ai ta samu k'awa minon nata mata murmushi, cikin parlon ta kawo masu Abincin tare da Aunty Saude da bata san da zuwan nasu ba saida Fatun taje Kitchen take sanar mata, gaisawa tayi dasu tayi masu an zo lafiya, daga baya bayan sun gama cin Abincin suka yi ma Hajiya sallama ta tambayi yaushe Baffan zai koma yace mata gobe in Allah ya kaimu, tambayar Hajiya Fatuu tay wai ta bisu can gidan ta d'an ta6e baki ta girgiza mata kai alamar a'a, marairaice mata tayi tace mata don Allah tayi yar dariya tace taje in ma kwana zata yi ta kwana, zo kaga murna harda d'an tsallen murna. Bayan sun fito ne Fatuu tace ma Baffan suje yaga inda take yace mata ba sai yaje ba ta marairaice mashi ta kama hannun shi guda tana mashi magiya, Amadu ne yace mashi ai ba wani abu suje sannan suka nufi part d'in nasu, sosae yay farincikin ganin inda yar tashi take rayuwa har fuskar shi ta kasa 6oye farinciki nashi, Mino ma sai washe baki take tana fad'in yanzu Adda Fatuu nan gidan ki ne tana ta kalle kalle, matsa mashi Fatuu tay wai yazo yaga sauran wurare ya k'i yace ba sai yaje ba tunda yaga nan Mino ko ai tuni ta nufi ciki. Bayan sun je can gidan mino tasa Fatuu ta kira mata Abbas tace ashe bata manta dashi ba tace ai suna waya dashi ta wayar yadikko, d'an waro ido Fatuu tay da d'an mamaki tace kodai wani abu ke tsakanin su ne da sauri Minon tace mata a'a wllh kawai yana kira yaji ya suke sai suyi hira wani lokacin har yasa tayi mashi magana da fulatanci har ma yace inta dawo nan zai siya mata waya kuma zata rink'a koya mashi fullanci jinjina kai kawae Fatuu tay, bayan ta kira shi sun gaisa taba Mino wayar ta sanar dashi game da zuwan su da alamun jin dad'i yace mata to yana nan zuwa, da daddare bayan sallar isha yazo a parlor suka zauna aka kira mashi Baffan Fatuu suka gaisa shima yayi mashi godiya sosae da Addu'oi yana ta fad'in ba komai, hira suka shiga yi gaba d'ayan su harda Kawu Amadu da gwaggo da Baffan Fatun Mino dai na a gefen Abbas, abun gwanin burgewa yadda suke yin hirar in akayi hausa wani lokacin sai a juye a koma fullanci Abbas yay ta murmushi har Mino nace mashi tunda tazo zata koya mashi ai, anan yake ma Gwaggo Maganar cigaba da karatun ta tace eh inda Fatuu tayi take son taci gaba in ta huta sai Amadu yayi mata cuku cukun samu Abbas d'in yace abar mashi komai, bayan Abbas ya tafi gwaggo tace ma Fatuu ita sai yaushe zata tafi dare yayi fa sosae tace ai anan zata kwana Hajiya ta amince tace a'a miya kai na wani kwana ta tashi ta koma ta marairaice kaman zata saka kuka gwaggon tace ko na jini zata yi sai ta tafi tace su tafi tare da Mino su kwana, jin hakan yasa ta washe ta basu tsarabar Hajiya da ta Fatun suka tafi, Bayan sun koma gida sun kaima Hajiya tsarabar suka dawo part d'in su, Bedroom suka nufa Mino sai faman washe baki take tana fad'in "Adda Fatuu wllh gidan ki Aljannar duniya ne" ita dai Fatuu sai dariya take, toilet ta jata don tayi wanka, a Laundary suka tsaya tasa ta cire kayanta ta d'aukko mata towel kanta yasha kitson fulani gwanin sha'awa, bud'e injin wanki tayi ta saka kayan data ciren nan fa Mino ta fara k'auyanci tana tatta6a shi cike da mamaki take fad'in ta ta6a ganin irin shi a kallo ashe tana da rabon ganin shi a fili har ta ta6a, gaba d'aya ta bi ta rurruk'e saman towel d'in da Fatuu ta bata ta d'aura, tana dariya tace mata in aka d'aure saki ake tace ai ji take kaman zai kwance ne, tare suka shiga toilet d'in ta fara nuna mata yadda zata yi amfani da komae ta waro ido tana bin shi da kallo, had'a mata ruwa tayi cikin bathtub ta fara nuna mata yadda zata shiga tayi wanka tana cikin mata bayani Minon tace wai ko kaman yadda ake yi a tafki ta d'an harareta, bayan ta gama nuna mata tace zata tsaya a cikin d'akin waje in akwae abunda bata gane ba tayi mata Magana tace toh, da yake tana da fahimta kuma k'auyancin nata da Sauk'i bai yawa ba sai gashi tayi wankan lafiya lou ta fito sai shinshina jikinta take yi tana washe baki tana fad'in yau tayi wanka da ruwan turare, Fatuu dai saidae tay dariya ta girgiza kai, bayan sun koma cikin Bedroom tasata ta shafa mai ta daukko mata rigar bacci, saida ta gama shiryata ta nuna mata gado tace ta kwanta a d'arare ta hau gadon tana yi tana tatta6a jikin shi sai kace tana jin tsoron shi, bayan ta kwanta Fatuu ta wuce don tayo wankan itama, bayan ta fito a takure ta iske Mino sai faman rawar sanyi take ita tama d'auka tayi bacci, rage mata Ac d'in tayi ta nuna mata duvet tace da shi ake lullubewa tace ai ta d'aukka kwalliyan gado akai Fatun tay d'an guntun tsoki tare da murmushi. Washe gari Baffan su Fatun ya tafi. A cikin satin Abbas ya gama yi ma Mino cuku cukun Makaranta ya kawo mata Uniform da su School back nan yake sanar da gwaggo Makarantar da zata cigaba wadda babbar private school ce da kusan duk an santa, da alamun damuwa gwaggo tace ya zai d'auki wannan babban nauyin ga dawainiyar iyalin shi nan yake sanar mata bashi ne zai d'auki nauyin Karatun ba Haisam ne shi yace akaita can tace to ai da ko wadda bata kaita ba tunda ita mai tsada ce yana murmushi yace mata tunda shi yace kar ta damu, bayan ya tafi tasa Amadu ya kira mata Haisam d'in bayan sun gaisa tayi mashi Maganar Makarantar tace dawainiyar zata yi yawa da asaka ta wadda bata kai ta ba yace mata ba wani abu, sosae tayi mashi godiya tare da Addu'oi. Cikin sati guda Mino har ta goge komai na part d'in Fatuu tasan yadda ake amfani dashi, anan take taya ta kwana da safe sai ta koma gida don taya gwaggo aiki, cikin satin daya kama ta fara zuwa Makaranta, sosae Uniform d'in suka kar6e ta kai kace itama d'iyar Senator d'in ce, Tk ne ke kaisu gaba d'aya kuma ya d'aukko su da yake kusan lokaci guda ake tashin su, duk wanda ya gan su sai yayi Maganar Kamannin su. Ranar Juma'a daya kama wata guda da sati d'aya da tafiyar Haisam bayan Fatuu ta dawo daga Makaranta an sauke Mino ta nufi part d'in su, Bedroom ta wuce ta aje jakarta ta nufi toilet, bayan ta fito ta fara shiryawa ta saka riga da skirt na lace da yake period take bazata je Masallaci ba kaman yadda suke tafiya tare da su Hajiya, bari tayi a gama sallar sai ta tafi part d'in Hajiyar taci Abinci don bata son taje tayi mata Maganar zuwa Masallaci, tana kishingid'e tana latsa wayarta har aka gama sallan, da yake ba wata yunwa take ji sosae ba sai can bayan an dad'e da gamawa sannan ta tashi don ta tafi, saida ta yafa d'an gyale mahad'in kayan jikinta sannan ta tafi, Tana shiga parlon Hajiya ta hango ta zaune tayi kwalliyar Juma'a daga d'ayan bangaren kuma wata ce zaune wadda Fatun bata gane ko wacece ba, tana kaiwa bakin kujerun taja ta tsaya sakamakon wadda idanun ta suka gani, Farha ce zaune tana sanye da wasu matsattsun jeans da top kanta ba kallabi kunnuwan ta sak'ale da earpiece idanuwan ta na akan wayarta dake ruk'e a hannun ta tana d'an taunar cingam sam bata ji shigowar Fatun ba, kallonta Hajiya tay fuska a sake tace mata an dawo tace eh tun d'azu ma tace to taje ta ci Abinci, suna cikin Maganar Farha ta d'ago ta kalli Hajiya ganin tana Magana yasa ta kai idon ta kan wanda take Maganar da shi suka had'a ido da Fatuu, wani mugun kallo ta jefa mata nan take Fatuu tasha jinin jikinta, maida kanta tay kan wayar har Fatuu zata juya Hajiya tace mata bata gane Farha bane, dakatawa tayi da d'an murmushin yak'e tace ta ganeta tace to basu gaisa ba, ce mata tay taga kaman bazata ji ba tunda ta saka earpiece shiyasa bata yi mata magana ba Hajiya tace ina ruwan uwar son kad'e kad'e, ce mata tayi taje sun gaisa daga baya hakan ba K'aramin dad'i yay ma Fatuu ba ta juya, ji tay kaman ta koma part d'inta kawai ba sai ta ci Abincin ba saidae ta san Hajiya dole tayi Magana, bayan ta shiga Kitchen tsaye tay gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i don tana zargin ba hakanan Farhar tazo ba ba kamar data ganta ita kadae, ita dake dad'ewa bata zo ba kuma saidai suzo gaba d'aya, zuciyar ta ce ta raya mata k'ilan ma yanzu d'in ba ita kad'ai tazo ba sai kuma ta sake raya ai kuma da taga sauran a parlorn, yanke tafiya da Abincin part d'in su tayi ta ci acan, bayan ta zuba har saida tay d'an jimm a bakin k'opa kafin ta fito, ganin hankalin Hajiya na akan tv yasa ta bi ta kopar baya idanun Farha a kanta, bayan fitar Fatun da d'an lokaci Farha ta mik'e ta nufi Hanyar Bedroom, tana zuwa ta d'an juyo ta kalli Hajiya ganin bata ganinta ta wuce itama ta bi ta kopar bayan ta fuce, Bayan ta koma part d'in nasu kitchen ta wuce ta zubo Abincin a plate ta dawo parlor ta d'aura akan c-table ta fara ci, bata dad'e sosae da fara ci ba taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta, Farha ce ta shigo har saida gaban Fatun ya Fad'i ta dakata da cin Abincin tana kallon ta, nufo cikin falon tay tana tafiya cike da isa ta tsaya daga gaban Fatun suka fara kallon kallo ta wani kalan had'e rai can ta ja wani dogon tsoki ta nuna Fatuu da yatsa a fusace tace "You bastard! how dare u married my sister's Husband!!!" Shiru Fatuu tay tana kallonta, a hasale ta matsa ta kai duka hannuwanta jikin c-table d'in ta d'ago shi ta kifa ma Fatun shi Abincin ya 6aro a jikinta da sauri ta mik'e don yana da d'an zafi ga c-table d'in ya dakar mata gwuiwa, hannu ta kai ta maida table d'in ta d'ago tana kallon Farhar tana fitar da numfashi da sauri da sauri ita kuma Farhar sai huci take, a zafafe taci gaba "U must leave dis house tunda ba gidan uban ki bane, wllh sai kin bar shi talakan banza talakan wofi a gold digger" tsoki ta k'ara ja ta juya har tayi d'an taku ta juya tana nuna Fatun tace "in na k'ara ganin kin je d'aukar Abinci sai na saka maki poison kin mutu kuma ba abunda za'ai man na kashe Banzaaa" tana fad'in hakan ta juya ta tafi, tsaye Fatuu tay a wurin tamkar an dasa ta zuciyarta sai harbawa take da k'arfi k'afafuwanta na d'an yin rawa, ta d'auki lokaci a hana kafin jiki a mace ta zauna kan kujera, sosae Maganar Farhar ta k'arshe tay tasiri a kanta don yadda take nuna mata tsana tasan zata iya aikata mata hakan, da k'yar ta mik'e gwuiwowinta a sanyaye ta nufi Kitchen don ta d'aukko abunda zata gyara wurin, bayan ta gama gyarawa Bedroom ta shiga ta nufi bakin gado ta zauna tay tsuru, in tace taji dad'in zuwan Farha tayi k'arya don tasan yanzu kwanciyar hankalinta ya k'are ba kamar data gane dalilin zuwan nata, k'arshe dai Abincin da bata ci ba kenan. Da daddare bata je part d'in ba balle taci Abinci sai kawae ta yanke ta dafa indomie taci, bayan ta gama dafawar bedroom ta wuce da ita, sam tama kasa sakin jiki taci indomie d'in don har bakinta ba dad'i take jin shi, yar kad'an taci ta mik'e ta maida ta kitchen, komawa tay Bedroom ta haye gado ta zauna ta shiga duniyar tunani, a ranta take raya ita bata ga amfanin wannan auren ba dama su rabu kawai ta huta don ba komai a cikin shi sai tashin hankali gashi wanda take zaune don shi ya yi tafiyar shi ya barta ko damuwa bai yi da ita ba, daga tafiyar shi zuwa yanzu zata iya k'irga sau nawa suka yi waya itama ba wani Magana mai tsawo ba iyaka ya tambayi yadda take ko chat basu yi, idanunta ne suka ciko da k'walla saidai bata bari sun zubo ba don itama yanzu har ta gaji da yin kuka, tana haka Mino ta shigo ta k'ak'alo murmushi tayi mata ta nufo ta itama tana murmushin, a bakin gadon ta zauna ta gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata gwaggo na gaishe da ita ta d'aga kai, tambayar ta tay ko bata lafiya ne ko wani abu na damunta taga kaman fuskarta ta canza tana murmushi tace mata lafiyar ta lau ta tambayi taci Abinci tace eh bata dad'e data gama ci ba, ce mata tay akwae sauran indomie data rage a Kitchen in zata ci, mik'ewa tay tace to bari ta d'aukko. Bayan sun gama shirin kwanciya Mino ta kwanta ita kuma ta d'aukko jakar ta don tayi karatun test da suke cikin yi Saboda exam d'in su ta matso, tana zaune a kan gadon tana karatun aka turo kopar ta kai idon ta da sauri don bata tsammaci wani ba a lokacin mantawa ma tayi bata kulle kopar ba, Farha ce ta shigo tana sanye da rigar bacci iya gwuiwa kanta sanye da hula, nufo cikin d'akin tay cikin d'acin rai ta tsaya bakin gadon tana masu kallon rashin Arzik'i, nuna Mino tay a wulakance tace "Who is she?" shiru Fatuu tay kaman bazata tanka mata ba sai kuma ta bata amsa da kanwarta ce, tafa hannuwa Farhar ta shiga yi da alamun mamaki tace wato har talakawan yan'uwanta ke zuwa kwakwa suma kenan" banza Fatuu tay mata tay k'wafa a fili ta furta duk zata yi maganin su, ce mata tay anan zata kwana don haka ta tasheta ta bata wuri, Fatuu dake kallon ta tace mata ai ga wuri nan sosae ba sai ta kwanta ba, yamutsa Fuska tay ta furta "God forbid! ni zan kwanta da pauper kina son ta goga man talauci ne" ta d'age ma Fatun gira tana kallon ta shek'ek'e, tasan fitina take nemanta da ita hakan yasa ta kai hannu ta fara tada Mino d'in, bayan ta farka tace mata ta saukko daga kan gadon, tambayar ta tayi lafiya tace mata eh kawai, saukkowa tayi ta tsaya sai lokacin ta lura da Farha dake mata kallon k'ask'anci, ganin yanayin fuskar ta yasa bata ce mata komai ba, wardrobe Fatuu ta bud'e ta fiddo bargo tazo ta shimfid'a ma Mino a saman Carpet ta d'aukko mata filo, bayan ta gama tace mata ta kwanta anan, da alamun rashin fahimta tace mata miya faru bazata kwanta a gadon ba kafin ta bata amsa a fusace Farha tace daga gidan uban su aka kawo shi ne, waro ido Mino tayi baki a d'an bud'e take kallonta ba tare data ce komai ba dama ita bata da rigima Fatuu ce mai rigimar yanzu kuma tayi sanyi lakwas, kwantawa Mino tayi itama Fatuun ta zauna a gefenta taci gaba da karatun, bata dad'e da zama ba taji Farhar ta watso mata zanin gadon dake shimfid'e a kan gadon da duvet harda pillows, hannu ta kai ta cire bedsheet d'in daya rufe mata fuska rai a 6ace tace mata ba gadon take so a bar mata ba kuma gashi nan an bar mata miyasa zata watso mata kaya tana yatsina tace ta d'aukko mata wasu wad'annan an goga masu talauci, sosae ran Fatuu ya 6aci bata dai ce mata komai ba kaman bazata d'aukko ba sai kuma ta mik'e taje ta fiddo wasu ta kawo mata ta aje akan gadon ganin zata juya tace mata bazata shimfid'a mata ba ko banda gadon rashin Arzik'i harda gadon rashin iya tarbar bak'o tayi, bata ce mata komai ba ta shiga shimfid'a mata, bayan ta gama ta koma ta kwashe wanda ta watso ta linke su ta kai Wardrobe, gaba d'aya Fatuu ta kasa yin karatun don tun bayan data kwanta ta fara kunna wak'ok'i gashi ta k'ure volume, k'arshe mik'ewa tay ta d'auki books da jakar tata ta fita daga d'akin ta koma parlor, bata dad'e sosae da komawa ba sai ga Mino ta fito a gigice tana kuka jikinta sharkaf da ruwa sai kerma take ta nufo cikin parlon, da sauri Fatuu ta mik'e ta tarbeta tun kafin ta tambaye ta abunda ya faru ta shaida, rai 6ace ta tambayi mi tayi mata ta watsa mata ruwa tace itama bata sani ba kawai tana cikin bacci taji ta watsa mata su da yawa, duk yadda Fatuu ta so kar tayi kuka ta kasa jurewa sosae Mino ta bata tausayi, zaunar da ita tayi kan kujera tace tana zuwa, Bedroom ta nufa saida ta tsaya a bakin k'opa ta goge Fuskar ta sosae sannan ta shiga, tsayawa tay daga bakin gado rai 6ace take kallon Farha dake latsa waya tace "mi tayi maki kika watsa mata ruwa haka!" banza ta mata sai kace bada ita take ba, k'ara maimaita tambayar Fatuu tayi saida ta mula sannan ta d'ago ido cike da isa tace snoring take mata daga haka ta maida idon kan waya, shiru Fatuu tay tana mata wani kallo jin sharrin data ja ma Mino na wai munshari take mata ita tasan bata yin shi tunda tare suke kwana, tunowa da ta baro Minon a jik'e yasa ta juya ta nufi wardrobe, kayan da zata canza ta d'aukko da su bedsheet d'in da Farha ta watso ta kinkima ta fita, bayan ta bata kayan ta canza tayi mata shimfid'a akan Carpet d'in parlon tace ta kwanta, kallon Fatun tayi ta tambaye ta wacece Farha nan ta bata labarin ta harda dalilin daya sa take mata hakan, "to ki fad'a ma Hajiya abunda take mana" shiru Fatuu tay tana nazari can tace mata suyi hak'uri kawai yanzu in ta fad'i ma Hajiya ta d'auki mataki akanta Mamar ta itama tana iya yi mata wani abun, kamar Mino zata yi kuka tace to yanzu haka zasu cigaba da zama tana masu haka, shiru Fatuu tay gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i can tasa Kuka bak'in cikinta wanda duk ake mata haka Saboda shi baima damu da ita ba ganin tana kukan yasa Mino d'in ma cigaba da yi, daina yin kukan Fatuu tayi tace itama ta daina komai zai wuce bada dad'ewa ba, rok'onta tayi akan Kada ta fad'i ma gwaggo tace to tace ta kwanta, zaune Fatuu tayi ta kasa cigaba da yin karatun ma idon ta akan Mino dake kwance ta lullube, wani irin tausayin ta take ji tunani take ko tace ta daina zuwa kwanan saidae tasan dole gwaggo zata tambayi dalili, haka tay zaune tsawon lokaci sai can dare ya nitsa sannan ta kwanta, Washe gari da wuri Fatuu tace ma Mino taje gida sai ta k'ara yin baccin acan tace to baiwar Allah harda ce mata to tazo suje tare tunda ba Makaranta itama tayi baccin tace mata a'a ko taje gwaggo korota zata yi, kaman bazata tafi ba tsoronta kada ta tafi Farhar tayi ma Fatun wani abu haka dai ta tafi, bayan tafiyarta Fatuu ta kwashe kayan shimfid'ar ta maida d'aki Farha na kwance baje baje ko salla bata tashi tayi ba, dawowa parlor Fatuu tay ta zauna tama rasa mi yakamata tayi, tsawon lokaci tana anan saiga Saude tazo kawo mata breakfast, akan c-table ta d'aura suka gaisa ganin yadda Fatun tayi tsuru yasa ta zauna tana tambayar ta miya faru a sanyaye tace mata ba komai, tana shirin k'ara yi mata magana sai ga Farhar ta fito duk suka kalleta ta wurga masu wata uwar harara ta wuce, bayan ta fita da alamun mamaki Aunty Saude ta kalli Fatuu tace mata mi tazo yi nan ne taga ta fito daga Bedroom, shiru Fatuu tay ta sunkuyar da kanta nan take Aunty Saude ta gane da wani abu dama gashi ta isketa tsuru a parlor, matsa mata tayi kan ta fad'i mata Fatun ta fara fad'i mata duk abunda tayi masu da cewar da tayi zata saka mata poison a Abinci tana yi tana goge kwalla, ran Saude ne ya 6aci tace aikuwa yanzu zata je ta fad'i ma Hajiya dama ita tasan ba abun Arziki ya kawo ta ba, rik'eta Fatuu tay ta hau yi mata Magiya kan karta fad'i na Hajiya tunda tasan ba dundundun ta zo ba ta k'yaleta tayi ta gama yanzu in aka fad'i ma Hajiya tana iya cewa ta koma gida kuma Hajiya Maryam zata ga an korar mata D'iya Saboda ita koma bata yi niyyar yi mata wani abu ba hakan na iya sawa ta cutar da ita tunda dama gani take suma kamar asiri sukai ma Hajiyar, shiru Aunty Saude tayi tana nazarin Maganar, da damuwa tace to yanzu haka zata k'yaleta tay ta mata rashin mutunci, d'an murmushi mai cin rai Fatuu tay tace mata ba komai kawae dai tana son ta taimaka mata zata daina zuwa cin Abinci bata son Hajiya ta gane koda tayi mata Magana tace tana zuwa amsa ala bashshi sai ta rink'a dafawa kawai, cewa Saude tay ta bari zata rink'a kawo mata tasan yadda zatayi Hajiyar bazata tuhumi dalilin daina zuwan nata ba Fatun tace ta barshi kawae tunda akwae kayan Abincin tace amman ya za'ai ace sai ta dawo daga Makaranta sannan ta dafa kawai zata cigaba da kawo matan in yaso randa ba Makarantar sai ta dafa tayi mata godiya. A daddafe tayi Weekend d'in nan, Ranar Monday tunda taje Makaranta Fauzy ta lura da yanayin ta tana cikin damuwa don har fad'awa fuskarta tayi, bayan anyi break ne ta tambaye ta abunda ke damunta nan ta kwashe game da abubuwan da Farha take mata ta fad'i mata, tun kafin ta gama yanayin fuskar Fauzy ya canza bayan ta gama fad'i mata rai a matuk'ar 6ace tace "inta fasa kashe ki bata haihu K'wara ba don ubanta! ke kika k'yaleta wllh" yamutsa Fuska Fatuu tay tace to ya zatayi, a hasale Fauzy tace "wane ya zaki yi, ba ita take neman ki da rigima ba, kamata zaki ki lakad'a mata shegen duka kinsan dama irin haka sai kun had'a jiki mutum yaji a jikinshi sannan yake shiga taitayin shi" sakin baki Fatuu tay tana kallonta Fauzyn tace "ko tafi k'arfin ki ne? In tafi k'arfin ki ni ki bari in zo mu had'u mu had'a mata jini da mijina wllh zaki ga ta kiyaye ki" da sauri Fatuu ta hau girgiza mata kai tace ba zasu yi haka ba a kyaleta kawai, a hasale Fauzy tace "Wato kin fi son tay ta cusa maki bak'in ciki ko har wani ciwon yazo ya kamaki ga jarabawa a gaban mu" watsa hannu Fatun tay ta yamutsa fuska kamar zatai kuka tace "Fauzy ko mi zatai man tayi ba kowa yaja man ba face Ya Haisam, duk abunda ake man Saboda shi ne kuma shi bai damu dani ba ya tafi ya barni Saboda bai sona, na tabbatar da yana sona ba yadda za'ai ya tafi tsawon wata guda da rabi ba tare da ya waiwaye ni ba tunda yana da halin ko duk sati yaso zuwa nan hakan ba wani abu bane a wurin shi, ni na rasa gane kan wannan Auren namu da yasan haka zai man da tun farko bai amince yaci gaba da zama dani ba, in don abunda ya faru ne naje na bashi hakuri kuma yace ya hak'ura to miyasa ya canza man, miyasa bai damu dani ba...., miyasa son shi yak'i barina kwata kwata, miyasa nike tunanin shi tunda shi bai damu dani ba....miyasa ba zai sake ni ba kawai in San ban tare dashi ko na cire shi daga cikin zuciya ta....." tana Maganar k'walla na zubo mata har tazo ga6ar da ta saki kukan mai cin rai ta fad'a jikin Fauzy da itama kwallan ne suka fara zubo mata, wani irin tausayin ta da bata ta6a ji ba ya kamata ta shiga d'an bubbuga bayanta tana rarrashin ta, ita kanta ta fara kokonton anya Ya Haisam na son Zarah kaman yadda suke hasashe kuwa, zuciyar ta ce ta fara raya mata aikata wani abu...... Kafin a tashi tace ma Fauzy zata rink'a bin ta Hostel sai yamma ta koma gidan don gaba d'aya bata jin dad'in gidan tace to Hajiya fa ba matsala taga bata komawa da wuri tace zata fad'i mata suna tsayawa karatun jarabawa ne tasan zata fahimta tace to, kiran Tk tayi ta sanar dashi kada yazo d'aukar ta ya d'aukko Mino kawai ita sai yamma zata dawo kuma ba sai yayi wahalar zuwa d'aukarta ba zata hau Keke Napep, bayan an tashi suka nufi Hostel, suna zuwa salla suka fara yi bayan sun gama Fauzy ta had'a mata Madara da biscuit tace ta fara sha bari ta dafa masu Abinci, tana gama sha lokacin Fauzy na cikin dafa masu Abincin ta mik'e tace bari taje ta watso ruwa har Fauzy nace mata zata iya shiga toilet d'in su kuwa tana yar dariya tace mi zai hana, cire kayanta tayi ta d'aura towel Fauzy ta kalleta tace mata wllh duk tayi d'an wuya tay murmushi kawai, bayan fitar ta Fauzy ta mik'e ta nufi inda ta tashi ta zauna ta kai hannu ta d'auki wayarta, zurfin tunanin anya Ya kamata tayi abunda take tunanin yi kuwa ta shiga, fargaba ce tay mata yawa ta maida wayar ta aje ta bar wurin, bayan Fatun ta fito tace ma Fauzy ta bata yar riga mara nauyi tasha iska kafin ta tashi tafiya ta d'aukko mata, bayan ta gama saka rigar hayewa tay saman gado ta kwanta suna d'an yin hira da Fauzy, a hankali ta fara lumshe ido Fauzy na fad'in kada tayi bacci bata ci Abincin ba tace ai ba yunwa take ji ba in ma tayi sai ta ci in ta tashi, baccin ne ya dauketa Fauzy ta zuba mata ido tana ta wasi wasin abunda take son yi acikin zuciyar ta can ta mik'e ta nufi gadon da take ta kai hannu ta d'aukko wayarta ta dawo ta haye saman gadon zuciyarta nata harbawa hannuwanta har d'an kerma suke ta shiga daddana ta......." ____________________ Fanan zaune asaman doguwar kujerar dake a cikin parlon su ta haye saman ta gaba d'aya tana sanye da yar fingilar riga da iyakarta tsakiyar cinyoyinta hannun ta kuma irin na vest kaman dai rigar bacci ce ta d'an rankwafa tana lallatsa computer d'in dake gabanta hakan yaba brown gashin ta damar zubowa ta gefe da gefen fuskar ta, daga gefen ta kuma takardu ne lokacin su can dare ne don har anyi sallar isha, tun bayan da Haisam ya aje wayar shi ya tafi had'o masu Coffee take ta damun ta da k'arar notifications, dakatawa tay ta kai hannu ta d'aukko wayar don ta kashe Wi-fi d'in wayar ko sakonnin sun daina shigowa, tana latsa power haske ya kawo jikin Screen d'in idon ta ya sauka akan sunan da tasan ya saka ma Fatuu alamar ta turo mashi sako, d'an murmushi Fanan d'in tayi a ranta ta raya wato da ita ne ta daina zumunci kenan, bayan ta kashe ta maida wayar ta aje, har taci gaba da abunda take kawai taji tana son ganin sak'on miye Zarah ta turo mashi, hannu ta kai ta d'aukko wayar ta sake kunna hasken ta bud'e, kan sakonnin WhatsApp ta danna ta shiga ciki, sak'on Fatuu ne last da aka turo hakan yasa ya kasance a sama ta kai hannu ta ta6a ya bud'e, gyara zama tayi ta fara Karantawa................... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 [5/8, 19:29] +234 901 700 4868: *ASM 072* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .......Ranar Laraba bayan su Fatuu sun tashi Mino ta tafi ta kwashe kayan shimfid'ar da tayi masu don yanzu da tsiya sun koma kwanan Falo don duk dare nan Farha ke zuwa ta kwana kuma duk abun nan Hajiya bata sani ba don ita a tunanin ta a d'akin da ta sauka take kwana dama bari take sai ta tabbatar Hajiya tayi bacci sannan ta taho, haka take ta faman yi masu cin kashi iri iri Harda ce ma Fatuu mayya ta lik'e tak'i tafiya gidan su, ita dae duk abunda zata mata bata biye ta, bayan ta maida kayan Farhar na kwance kan gado tana bacci, toilet ta wuce don tayi wanka, lokacin data fito cikin sauri ta fara shiryawa don yau test biyu gare su d'aya da safen nan za'ai masu d'ayar kuma sai After break so take taje da wuri don su k'ara yin karatu, bayan ta gama shiryawa ko tunanin tsayawa yin breakfast bata yi ba ta d'auki jakarta ta nufi k'opa zata fita, tana kama handle taji Muryar Farha tana mata magana hakan yasa ta dakata ta juya, tana kwance saman gadon ta d'an d'ago da kai tace mata wai taje tayi mata Breakfast, wani kallo Fatuu ta bita dashi kafin tace mata ai a part d'in Hajiya ake yi don haka taje can taci, yar tsawa ta kwatsa mata tace ita zata bata Umarni ta k'i yi mata to miye amfaninta dama in ba hakan ba miji bai son ta ya tafi ya barta yana can wurin wadda yake so suna shan soyayya amman ita da yake mayya ce ta lik'e to yau anan take son yin breakfast d'in, sosae Maganar ta daki zuciyar Fatuu har idanun ta sun fara tara k'walla amman sai tayi saurin maida su tace mata Aunty Saude zata kawo nata sai taci a fusace tace bazata ci shi ba ita take so ta dafa mata, d'an jimm Fatuu tayi sai kuma ta d'ago hannu ta duba agogon hannunta ganin da d'an sauran lokaci yasa ta juyo ta aje jakarta ta fita, bada jimawa ba ta dafo mata indomie ta kawo mata har lokacin tana a kwance, a saman bedside drawer ta aje mata tace gashi nan, tasowa Farhar tayi har Fatuu zata juya ta tsaidata ta juya tana yatsina tace mata ba ita take so ba Chips zata had'o mata, wani kallo Fatuu ta bita da shi kafin tace mata gaskiya bata da lokacin yi mata wannan School zata tafi tana da test kuma lokaci ya k'ure, tana gama fad'in hakan ta juya Farhar na mata magana cikin tsawa tay banza da ita ta tafi, Saida suka hau hanya bayan sun d'auki Mino ta kira Aunty Saude tace mata ta wuce ba sai ta kawo mata breakfast ba, tace da wuri haka ta sanar mata test gareta ne, har suka isa Makarantar tana ta tunanin irin wulakancin da Farha ke mata. Ana gab da tashi ta kira Tk tace mashi yau ya zo ya d'auketa lokacin tashi Fauzy tace mata yau bazata tsaya ba kenan tace mata eh akwae abunda zatayi sai dae gobe. Bayan ta koma gida tana shiga cikin parlon wani irin k'amshi ya bugi hancin ta, da mamaki ta shiga bin parlon da kallo tana son gane k'amshin na minene don yayi yawa kuma tasan ba haka ta bar parlon ba, hanyar corridor ta nufa tana zuwa saitin inda su Tv suke kaman ance ta waiga taga kwalaben turaren wutar ta dake jere a wurin gaba d'aya zube a k'asa sun yi kwatsa kwatsa turaren barbaje a koina, da Al'ajabi take bin su da kallo aranta ta shiga mamakin yadda akai sukai haka, ranta ne ya bata ko Farha ce tayi masu haka, da sauri ta juya ta nufi Bedroom tana tura kopar nan ma k'amshin ne ya dakar mata hanci tay tsaye tana bin kwalaben humra d'inta dake watse a k'asa da kallo gaba d'aya an fasa su harda su turaren fesawarta ga kayanta na cikin Wardrobe duk an watso su wardrobe d'in a bud'e, kai idonta tayi akan gado nan ma indomie d'in data dafo mata ce a warwatse ko ina, tsaye Fatuu tay ta kasa yin wani kwakkwaran motsi idanunta cike da k'walla take bin bedroom d'in da kallo, da k'yar taja k'afa ta idasa shiga ciki ta nufi bakin gado ta zauna a inda ba indomie d'in, kifa Fuskarta tayi cikin tafin hannunta ta fashe da kuka, tana cikin kukan ta tuno da Kitchen ta mik'e da sauri ta nufi k'opa ta bud'e, tana tura kopar kitchen d'in taja ta tsaya idanu waje take kallon cikin shi gaba d'aya duk wani abun fashewa ta fasa shi kayan Abinci ma bata k'yale su ba duka ta barbaza su harda mai duk ta zuzzubar dashi a k'asa wasu daga cikin Warmers d'in ta ma bata k'yale su ba saida tasa ta6arya ta faffasa su sosae tayi mata Asara abun ba kyan gani, wani irin 6aci ran Fatuu Yay tama kasa cigaba da yin kukan sai huci take, tana tsaye a wurin Aunty Saude ta shigo kawo mata Abinci, a kan c-table ta d'aura kayan Abincin ta nufi Bedroom a ranta tana Maganar k'amshin da take ji tayi tunanin ko turare ne ya 6are, tana shiga corridor d'in taga Fatun tsaye ta bata baya ta isa wurinta tana fad'in "Fateema an dawo yau da wuri kenan, Tk ne ya shiga d'aukar Abinci yake fad'a man kin dawo ai" jin shiru bata ce komai ba kuma bata juyo ba yasa Sauden kai hannu ta ta6o ta still bata juyo ba, matsawa tay tana fad'in Fateema lafiya mi kike kallo haka itama ta kallo cikin Kitchen d'in ba arziki ta bud'a baki tace garin Yaya haka ta faru ya akai kayan sukai haka, sai lokacin Fatuu ta juyo ta fad'a jikinta ta fashe da kuka, tambayar abunda ya Faru Sauden tay ta d'ago cikin kuka ta fara bata labari, Bedroom d'in Saude ta nufa ta shiga taga yadda shima tay mashi ta kai hannu ta ruk'e ha6a ta shiga jinjina kai, fitowa tay tazo taga na parlon ma sosae itama ranta ya 6aci don ba k'aramar asara tayi ma Fatun ba, juyowa Saude tay ta koma cikin Corridor inda Fatuu ke tsaye bakin Kitchen rai 6ace tace "Yanzu ke Fateema kin za6i ki zuba mata ido tay ta maki wannan cin kashin, nace in sanar ma Hajiya kin hana gaskiya to yanzu an zo ga6ar da dole ma in sanar mata" girgiza kai Fatuu tayi cikin kuka tace "Don Allah Aunty Saude kar ki sanar mata hakan ba k'aramar matsala zai Haifar ba...."Katseta Saude tay tace "to wai ita Mahaifiyar tasu ta isa tayi maki abunda Allah bai nufa akan ki bane" girgiza kai Fatuu ta k'ara yi "a'a Aunty Saude, nidai ki kyaleta kawai banso in shiga tsakanin su tayi ta gama ta tafi", Shiru Saude tayi tana kallon ta can tace "Shikenan indai kina son kada na fad'i mata sai kinyi abu guda in ba haka ba gaskiya bazan zuba ido ina ganin tana maki wannan iskancin ba" ce mata tay to mi zata yin, "so nike kiyi maganinta ta daina maki wannan wulakancin, kinsan irin haka saika had'a jiki da mutum yaji a jikin shi sannan yake kiyayar ka, nasan ba fin k'arfin ki tay ba wllh kawae jikin ne ba abunda zata iya maki don haka ki dawo Fateemar ki ta da ki sameta ki lakad'a mata dukan tsiya wllh zaki ga ta shafa maki lafiya" baki adan bud'e Fatun ke kallon ta jin kalaman sak irin na Fauzy, bayan ta gama tace mata tana ganin ba matsala ita bata son Hajiya ta sani, "Ba wata matsala, ai anan part d'in in tazo zaki mata hakan kuma tunda tasan ita ke bata da gaskiya bazata bari a ji ba tunda dama duk abunda take maki a 6oye take yi bata son Hajiya ta sani, shiru Fatuu tay tana nazarin Maganar, Sauden tace zata yi ko kuwa taje ta fad'i ma Hajiyar, kallonta tayi ta jinjina mata kai alamar zata yi tace to tazo taci Abincin ta k'ara samun k'arfin yin maganin mara mutunci ta kamo hannunta suka nufo cikin parlon duk fargaba ta cika Fatun don rabon data yi fad'a da wani har ta manta, da kanta ta zuba mata Abincin bayan ta cire Hijab d'inta ta aje a gefe ta fara ci, har saida taga taci ta k'oshi sannan ta bar part d'in bayan ta jaddada mata abunda take son tayi ma Farhar, Saude na fitowa cikin harabar ta hango Farhar ta fito ta baya ta nufo part d'in suna had'a ido ta wurga mata uwar harara ta kauda idon ta, Sauden tay d'an murmushin yau zaki gane kuran ki, bayan Fatun ta gama toilet ta je tayo Alwala ta dawo parlon don tayi sallar anan da niyyar inta gama sai ta fara gyara inda ya 6aci, tana kokarin sanya hijab taji an turo kopar ta kai idon ta da sauri, cikin isa kaman yadda ta saba ta nufo cikin parlon tana yatsina, a gaban Fatun ta tsaya hakan yasa Fatuu dakatawa da saka hijab d'in ta bita da ido gabanta nata fad'uwa kan abunda aka ce tayi matan, ce mata tayi tana fatan taga sakamakon k'in yi mata abunda ta sakata don haka gobe ma in ta k'ara sata abu tak'i yi zata ga abunda yafi wannan kuma tunda dai ita mayyace ta lik'e bada jimawa ba zatayi maganin ta gaba d'aya, tana rufe baki ta tsitta ma Fatun miyau a fuska aikuwa hakan ba K'aramin fusatar da ita yay ba duk da fargabar da take ciki a fusace ta kai hannu ta wanka mata mari ji kake Tasss! a gigice Farha ta kai hannu ta dafe kuncinta ido waje take kallon Fatuu data d'aure Fuska tana huci, nuna kanta tayi da yatsa tace ita ta mara a fusace Fatun tace eh taje ta mara aikuwa itama ta d'aga hannu zata sharara mata Mari da sauri Fatuu ta goce kafin Farha tay wani yunkurin ta shammaceta ta turata sai gata ta fad'a saman kujera tumm da alama k'ibar biredi ce dama, kan ta yunk'ura ta taso Fatuu ta haye samanta ta fara dukanta ba ji ba gani ta shiga sauke fushin duk wani bakin ciki data cusa mata dama kuma ita a yadda ta taso bata iya fad'an cacar baki ba tafi gane ta kai bugu kawai........... Saude na shiga parlor ta nufi Hajiya dake Zaune akan Kujera tana kallo, tana zuwa da alamun rud'ewa tace mata ga Farha can a part d'in Fateema suna fad'a tayi tayi ta raba su sun k'i rabuwa, ba shiri Hajiya ta mik'e ta d'auki sandar ta tace suje, suna kan hanya Hajiya nata faman dogara sandar tana yin sauri da alamun mamaki take tambayar abunda ya had'a su Sauden ta shiga fad'i mata asarar da tayi ma Fatun wani irin bacin rai ne ya bayyana akan fuskar ta, Har lokacin su Fatun fad'a suke sai tumurmusa suke a k'asa har ta fitar ma Farhar da jini, lokacin data ga ta fasa mata hanci da baki tsoro ya kamata ta fara k'ok'arin k'yaleta saidae ita Farhar tak'i sai k'ok'arin ganin itama ta cutar da Fatun take hakan yasa Fatun cigaba da kare kanta har jikin c-table taso bugata k'arshe ita Fatun ta buga, Saude ce ta fara shigowa sai Hajiya tana shigowa ta rafka uban salati tare da sakin sandarta ta fad'i k'asa tay k'ara aikuwa a firgice Fatuu ta k'wace ta mik'e tana ta huci, itama Farhar kokarin mikewa tay da k'yar tana ma Fatun wani kallo a fusace sai nishin wahala take tun daga k'asan hancin ta har zuwa k'asan bakin ta duk jini ne haka goshinta ma yayi jawur ita kuma ta kakkarce Fatun a wuyanta da kuma gefe gefen Fuskarta da yake k'umbuna gareta zak'o zak'o, cikin Fushi Hajiya ta kira sunan Farhar tace Saboda bata da mutunci da Matar Yayanta take fad'a haka, shiru tay sai nishi take ta kumburo baki da gani kiris take jira ta saki kuka don idanunta a cike suke taf da k'walla, kallon Fatuu data sunkuyar da kai Hajiya tayi ta tambayi miya had'a su ta d'ago cikin rawar murya ta fara fad'i mata daga breakfast da ta ce tayo mata zuwa dawowar da tayi ta iske abunda tayi mata Saude ce ta k'ara yi ma Hajiya bayani tun daga farko, sosae ran ta ya 6aci tay ma Saude nuni da ta d'ago mata sandarta, hanyar Bedroom ta nufa saida ta tsaya taga 6arnar da tayi mata a parlon sannan ta wuce ta gano sauran, bayan duk ta gani cikin parlon ta dawo Fuskarta a tamke ta tsaya daga gaban Farha rai 6ace tace "dama tunda na gan ki kinzo nayi zargin ba abun Alheri ya kawo ki ba kawae don anaso arinka kyautata zato yasa na kauda zargin hakan da tunanin mutum na canzawa, wato ke ta turo kizo kiyi mata abunda na hanata Saboda ta raina ni son d'iya yasa ta daina jin maganata, yayi kyau ai ga sakamakon ki nan kin zata don kina mata cin kashi tana k'yale ki tsoron ki take ji, uhmm baki san wacece Fateema kuwa, kin ci sa'a tayi sanyi ne da sai tayi maki fiye da hakan don har hak'oran gaban ki sai ta cire maki su, yanzu sai ki wuce muje ki tattara kayan ki kibar man gida ni ban sauke wanda ba abun Arziki ya kawo shi ba a gidana, don ma yamma tayi da wllh bazaki kwana ba amman Allah ya kaimu gobe ko ba Jirgin Lagos Kya hau na Kano daga can ki wuce, muje!" Ta daka mata tsawa ta juya tu6i tu6i ta nufi k'opa dama skin tight ne a jikinta, kallon Fatuu Hajiya tay ta bata hak'uri tace duk abunda tayi mata asarar shi za'a maida mata tace ma Saude ta taimaka mata su gyaggyra wuraren tace to daga haka ta juya itama ta nufi k'opa, bayan fitar ta hannun Fatuu dake d'an gunji da gani kukan zuci take ta kama ta zaunar da ita kan kujera, itama zama tayi ta fara lallashin ta aikuwa kaman tana jira ta saka mata kuka a cikin kukan take fad'in miyasa ta fad'o ma Hajiya ba sunyi da ita bazata fad'i mata ba Sauden tace to ba gashi ta kawo k'arshen komai ba, lallashinta ta shiga yi tana kwantar mata da hankali kan ba wani abunda zai faru in sha Allah, saida taga ta saukko tayi shiru sannan tace taje ta cire uniform sai su gyara wuraren tace to ta mik'e. Suna shiga cikin parlor Hajiya ta nuna mata hanyar Bedroom tace taje ta shirya kayanta, juyawa tay ta nufi hanyar ba tare da tace komai ba don ba alamun wasa a Fuskar Hajiyar, cikin parlon Hajiya ta wuce ta zaune inda take da kafin Saude tazo, Wayarta takai hannu ta d'auka ta shiga kiran Hajiya Maryam, bayan ta d'aga ta gaishe da ita Hajiyar tay banza bata amsa ba a kausashe tace "Ga yar Aiken ki nan zata dawo gobe in Allah ya kaimu, sannan a matsayina na Mahaifiyar ki in kika k'ara yin wani yunkuri don ki raba auren Fateema ko kuma ki cutar da ita BAN YAFE MAKI BA!!!" tana gama fad'in hakan ta katse Wayar. Da daddare lokacin tuni su Fatuu sun gyara ko ina bayan tayo wanka ta shirya cikin kayan bacci tana niyyar fita parlor don taci Abinci har ta kai k'opa taji wayarta na ringing ta juyo ta nufo bakin gado inda take ajiye, zama tayi ta kai hannu ta dauka tay Jim tana kallon sunan Haisam dake kan screen d'in alamar shi ke kira, Kaman bazata d'aga ba saida ta kusa yankewa sannan ta d'aga ta kaita kunne, shiru tay ko sallama bata yi mashi ba shima kuma bai ce komai ba, sai d'an bayan wani lokaci taji ya tambayi tana lafiya, sai data amsa mashi sannan ta gaida shi shima bai amsa ba ta d'an ta6e baki, tambayar ta karatun ta yay tace mashi Alhamdulillah suka d'an yi shiru taji yace sun kusa fara Exams ne a tak'aice tace mashi eh, tambayar ta yay tana karatu har saida ta curo wayar ta kalli screen d'in da alama so take ta tabbatar shi d'in ne ya kira ta, bayan ta ce mashi eh tana yi shuru suka k'ara yi daga baya yay mata saida safe ya kashe, bin wayar tay da kallo a cikin ranta ta fara kokonton kodai yaga sak'on ne wata zuciyar ta bata inda ya gani ba iya haka zai mata ba tunda dama ai duk in ya kirata yana tambayar karatun ta, tana cikin cin Abincin a parlor Mino ta shigo tana sanye da doguwar rigar material ta yafo gyale saman kanta daga baya yayi tudun kitson shukun da akai mata ta nad'e da k'aton ribbom, tun bayan zuwan Farha zuwa gidan bai mata dad'i sai jefi jefi zaka ga tazo da rana dama kuma ta fara zuwa islamiyya da daddare ne kullum sai tazo, cikin parlon ta shiga Fatuu dake kallon ta da murmushi ta nuna mata gefen ta alamar tazo ta zauna, bayan ta zauna ta gaishe da ita ta amsa tace mata suci suka cigaba da ci tare, bayan sun gama Minon ta kwashe kayan ta kai Kitchen ta dawo Fatuu tasa ta d'aukko masu ruwa da lemu cikin freezer d'in dining, kallo suka d'an yi daga baya Fatuu ta kalli Minon tace mata in tana jin bacci taje Bedroom ta kwanta, har saida fuskarta ta kasa 6oye mamakin Maganar data ji tace mata ba anan suke kwana ba, yar dariya Fatun tay tace yau suna da yanci a gado zasu kwana da tsananin mamaki tace mata ina ita mai idanun magen yau bazata kwana ba, dariya taba Fatuu jin sunan data kira Farha dashi dukda da gaske idanun nata kaman na magen suke, nan Fatuu ta bata labarin abunda ya faru tace mata gobe ma zata tafi, zo kaga murna a wurin Mino harda mik'ewa da yin tsalle daga baya suka je suka kwanta. Washe gari cikin nishad'i Fatuu ta tashi duk da tana d'an jin yar fargabar abun da zai iya zuwa ya dawo in Hajiya Maryam taji abunda ya faru, Bayan taje Makaranta Fauzy ta lura da yanayin ta ba kamar yadda ta saba ganinta ba da damuwa ta tambaye ta ko Ya Haisam d'in yaga sak'on sunyi Magana ne tace mata a'a itafa bata tunanin ya gani don ko jiya sunyi waya bata ga alama ba, nan ta kwashe abunda ya faru tsakaninta da Farha ta fad'i mata, cike da jin dad'i Fauzy tace amman ta burgeta wllh tuntuni abunda yakamata tayi kenan ai da duk ba'a zo nan bama. Lokacin da Fatuu ta dawo tuni Hajiya ta iza k'eyar Farha ta tafi. _______________________ Ranar Asabar da wuri Mino ta tashi ta had'a Breakfast bayan ta gama ci ta tafi gida don zuwa islamiyya lokacin Fatuu nata shan bacci, sai wuraren k'arfe 10 ta tashi ba dan ta gaji da baccin ba sai don yunwa data isheta, bayan ta gama yin breakfast d'in toilet ta wuce tayo wanka tazo ta fara shiryawa, doguwar rigar material tasa ta yafa d'an gyalenta bayan ta d'auki wayarta ta nufi part d'in Hajiya, tare da ita sukai Abincin rana da Saude bayan an taso su Mino ta isketa nan, anan suka ci Abincin rana bayan sun gama suka zauna parlor harda Hajiya da Saude suna yin kallo, wuraren k'arfe ukku da rabi Mino tayi masu sallama zata je tay shirin islamiyya Fatuu ma ta mik'e tay masu sallama suka fito tare, part d'in su ta koma ta wuce toilet tayo wankan rana dama kusan kullum wanka ukku take yi k'aranci tayi biyu, bayan ta fito gaban mirror ta tsaya tana yin shafa ta k'ura ma kanta ido ita kanta tausayin kanta take game da irin rayuwar auren da take yi, bayan ta gama shafe shafen bata yi wata kwalliya ba iya powder sai lip glow ta shafa, wata fitted gown ta Atamfa ta fiddo ta saka, bayan ta gama shiryawa ta shimfid'a qq abun salla ta d'aukko Hijab ta kabbara sallar la'asar, lokacin da ta gama zaune tay a wurin ta jingina da gado tay shiru hakanan take jin ta wani iri, ta d'an d'auki lokaci a haka daga baya ta mik'e ta d'auke abun sallar ta mayar inda yake ta cire Hijab d'in itama ta linke, saman gado ta haye ta zauna ta fara latsa wayarta can ta aje wayar ta mik'e ta d'aukko jakarta ta fiddo littafi don tayi karatu, shima karatun ji tay duk bata jin dad'in shi ta maida littafin cikin jakar ta zame ta kwanta ta runtse ido tamkar mai yin bacci saidae tunane tunane kawai take, bata dad'e da kwanciya ba sosae lokacin wurin karfe biyar da rabi wayarta ta fara yin ringing, bud'e ido tay kafin ta juyo ta kai hannu gefenta ta d'auka, ganin Hajiya ce mai kiran nata yasa tay saurin tashi zaune ta jingina da headboard,picking tay tare da yin sallama on the other hand Hajiyar ta amsa ta tambayi tana gida ne da sauri ta amsa mata da eh tana nan, ce mata tayi tazo part d'in ta to yanzu tace to, saukkowa tayi daga saman gadon ta nufi wardrobe ta fiddo d'an madaidaicin gyale da ba zai rufe bayanta ba gaba d'aya ta yafa, a cikin Corridor ta d'aukko takalma Flat shoe da suka hau da kayan jikinta ta wuce, Wata irin Fargaba take ji tun bayan data fito, ba yau Hajiya ta fara kiran ta ba amman wannan kiran duk sai take jin gabanta nata d'an fad'uwa, tana sanya kanta cikin parlon gabanta yay wani irin bugu mai k'arfi ba shiri taja ta tsaya, Zuba ma Mutumin da idanunta ke ganin mata ido tay wanda ko a nisan da ya ninninka wannan ta hango shi kallo d'aya zata gane shi, sosae tay Al'ajabin ganin su don bata ta6a zaton zata gan su ba, Haisam ne zaune akan 3 seater jikinshi sanye da Suit bak'ak'e saidai ya cire ta saman sai farar ciki mai santsi da dogon hannu sai bak'in wandon, daga gefen shi Fanan ce itama tana sanye da bakar doguwar riga jallabiya mai kayataccen adon stones gyalen rigar bai a saman kanta hakan ya bayyanar da brown sumar ta dake fake a tsakiya, gaba d'ayan su akan kujera d'aya suke zaune Haisam ya d'an zamo ta yadda ya jingina sosae da kujerar idon shi akan Tv ita kuma Fanan tana daga gefen shi itama ta jingina bayanta da jikin kujerar hannun ta d'aya dafe da forehead d'inta Hajiya har magana tay mata kan taje ta kwanta amman tace a'a sai an kirawo Zarah, sun d'an jima da zuwa don Fatuu bata dad'e da barin part d'in ba lokacin data koma tana toilet tana yin wanka suka iso, wani irin bugu da k'arfi da k'arfi zuciyar Fatuu ta hau yi ba kamar data ga Fanan ji tay kaman ta juya tunda ba wanda ya ganta ta koma, har zata juyan zuciyarta ta raya mata kenan k'in amsa kiran Hajiya zata yi hakan yasa ta dakata, Kamar Haisam yaji ajikin shi ana kallon shi a wani irin slow ya juyo da Fuskar shi ya kalli direction d'in da Fatun take nan take idanunsu suka shiga cikin na juna, zuba mata ido yay yana bin ta da kallo tun daga samanta har k'asa kafin ya tsaida su cikin nata, Hajiya ce ta kalle shi da niyyar yi mashi magana da yake Facing d'in su take a zaune ganin inda ya zuba ma ido yasa ta waiga ta kalli wurin, ganin Fatuu tsaye a wurin yasa ta d'an d'aga murya tace "Fateema ki shigo mana" har saida Fatun ta d'an firgita don bata san ta ganta ba, Fanan na jin Hajiya ta furta haka da wani irin sauri ta janye hannunta daga kan goshinta ta juya ta kalli inda Fatun take, gaba d'aya dabarbarcewa Fatun tay Hajiya ce ta k'ara mata magana kan ta shigo ta nufo cikin parlon idon ta a zare tana tafiya a d'arare, a bakin kujerun ta k'ara ja ta tsaya aikuwa kamar Fanan na jiran ta k'araso ta mik'e ta nufeta fuskar nan ba d'igon annuri, mik'ewar da tayi ta bayyana irin rigar jikinta mai bin shape d'in jikin mutum ce tayi kyau over, wani irin harbawa zuciyar Fatuu ke yi numfashinta ta fara kokowar fitar dashi, da za'a auna bp d'in ta a lokacin to kuwa daba makawa za'a ga ya hau, a gabanta ta tsaya daddad'an k'amshin jikin ta ya baza wurin, kyakkyawar Fuskarta a tamke take kallon fuskar Fatuun nan da nan jikinta ya hau 6ari ta hau kikkafta idanu, jin sun fara tara k'walla suna niyyar zubo mata da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, A kausashe Fanan ta kira Sunanta "ZARAHHH!!!" murya na rawa ta amsa mata, ce mata tayi ta d'ago ta kalle ta, da k'yar ta d'ago ruwan hawaye sun lullu6e k'wayar idon ta, "Zaraah u married my Husband!" Fanan ta fad'a muryarta har wani vibration take, shiru Fatuu tayi tana gunji kiris ya rage ta saki kukan, cigaba Fanan tay "na d'auke ki matsayin my own Sister Zaraah, amman shine kikai man haka, kin san yadda nike son ki na damu dake amman duk da haka kika iya auran man Miji?" Yanayin muryar ta tamkar itama zata saka kukan idanunta har sun canza, girgiza kai Fatuu ta fara yi fuska a yamutse da k'yar ta bud'e baki cikin trembling voice tace "D...on Allah Aunty Fanan kiyi hakuri wllh nima ban san ya Aure ni ba....kin ji na rantse maki..." Kuka ne yaci k'arfinta ta sadda kanta k'asa tana cigaba da yi, d'an ta6e baki Fanan tayi tace "But u loved him Zarah, Ur Message said it all!" d'agowa Fatun tay ta kalleta ta kasa cewa komai don ta gane sun ga sak'on da Fauzy ta tura, "Kinsan abunda ke tsakani na dashi tun farko amman kika fara son shi kuma kinsan ya Aure ni amman baki daina son na shi ba Saboda cin Amana!" Sautin kukan Fatun ne ya k'aru tace "Don Allah ki yi hak'uri Aunty Fanan wllh kinji na rantse maki ni bansan abunda ke tsakanin ku ba saida kika zo, bai ta6a fad'i man ke zai Aura ba kuma gashi can ki tambaye shi" yamutsa fuska tay "daga baya da kika sanin miyasa kika cigaba da son shi!" A fad'ace take Maganar, shiru tay ta maida idonta k'asa tana gunji, da d'an tsawa tace ta bata amsa miyasa ta ci gaba da son shi, "Kiyi hakuri nasan nayi maki ba daidai ba amman na daina son shi" d'age gira tay tace shine kuma ta turo mashi sak'o tana bayyana mashi son da take mashi, girgiza kai Fatun tay tace "Yanzu na daina son shi wllh kin ji na rantse maki" sai lokacin Fanan d'in ta d'an saki fuska tace "Good! haka yakamata" tana furta hakan ta juya tana tafiya cike da isa ta nufi wurin Haisam da har lokacin yana zaune a yadda yake, a gaban shi ta tsaya ta mik'a mashi hannunta dake sanye da zoben diamond, still yay yana kallonta ta wani yamutsa mashi Fuska, hannu ya kai gefen shi ya d'aukko wata takarda plain sheet dake nannad'e ya mik'a mata, juyawa tay ta koma wurin Fatun, a gabanta ta tsaya yanayin Fuskarta kamar zata yi murmushi tace "am sorry Zaraah we do not welcome u in our Fam, bazan iya yin kishi dake ba, not only u da Kowacce mace ma because yayi man Alk'awarin zamu rayu tare mu biyu until Death do us part" tunda ta fara Maganar Fatuu ke jinjina mata kai har ta gama ta mik'o mata takardar hannunta, tana amsa ta juya har cikin ranta taji dad'in hakan tana fara tafiya taji Muryar Hajiya ta kira Sunanta, juyawa tay ta kalleta da kai tay mata alamar tazo, daga gefenta ta tsaya da alamun damuwa akan Fuskarta ta fara Magana "Kiyi Hak'uri Fateema ban so hakan ta faru ba saidae gaba d'aya sun nuna basu son Auren ban so ki cutu ne shiyasa na goyi bayan ya sallame ki kawai, yanzu kije ki kai ma Dije ina nan zuwa" kai Fatun ta d'aga mata idanunta sharkaf da k'walla, har zata juya Hajiya tace mata ta bud'e ta fad'i mata saki nawa yayi mata Saboda sheda, hannunta sai kakkarwa yake ta fara warware takardar.............. ALHAMDULILLAH, Ba don na gama ba sai don nazo inda nike son in tsaya😀 _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 0816985626 *ASM 073* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .......bayan ta gama warware takardar, zuba ma content d'in ciki ido tay tana Karantawa, lokacin data gama a matuk'ar razane ta d'ago idanunta a waje ta kalli Hajiyar kawae sai taga tana mata dariya, kai idon ta tay kan Haisam shima taga yayi mata d'an guntun murmushi tare da lumshe ido, rud'ewa tay ta kasa Fahimtar komai hakan yasa ta k'ara maida idon ta kan takardar ta k'ara karanta abunda aka rubuta a ciki kamar haka, _WE ARE SO HAPPY TO WELCOME YOU INTO OUR FAMILY ZARAH_ _It's such a joy to be with u, We hope your presence will brightens up our days. You're a Wonderful person Zarah, we are so lucky to know u._ *We look forward to all the Wonderful things you'll bring to our lives. We love u so much Zaraah.* Lokacin data gama d'agowa tay ta waro idanu ta kalli Fanan dake tsaye a gabanta har lokacin kawai sai gani tay itama tay mata d'an murmushi, gaba d'aya sun rud'ata har Fuskarta ta bayyanar da hakan, d'age mata gira Fanan tayi Calmly ta furta "Nima na rama halin da Message d'in ki ya sani Zaraah" ta6e baki ta fara kawae sai ta fashe da Kuka Fanan ta kai hannu ta rungumo ta a jikinta a hankali take furta mata is okey, d'agota tayi bayan wani lokaci ta kama hannunta suka nufi ciki har lokacin Fatuu kuka take tasa gefen gyalenta tana ta goge k'wallan dake zubo mata, Kujerar data taso ta nufa da ita ta Zaunar da ita itama ta zauna a gefenta ta yadda suka saka Fatun a tsakiya har lokacin tanata sharar k'walla da gyalenta, Hannu Fanan ta kai ta dafa Shoulder d'inta tana ce mata ya isa haka kada tayi ciwon kai tayi mata wasa ne, Hajiya itama ta fara bata hak'uri tace mata sune suka shirya mata haka ita ba ruwan ta, daina yin kukan tayi ta sadda kanta k'asa har lokacin gabanta na d'an fad'uwa ganin komai take kamar a Mafarki don bata ta6a zaton haka daga Fanan d'in ba, a hankali ta d'an juyar da kanta ta saci kallon Haisam dake gefenta karaf suka had'a ido dashi ya kafeta da idanun shi dake a d'an lumshe da sauri ta maida kanta k'asa, Hajiya ce tayi d'an gyaran murya tace masu suyi ma Annabi salati (SAW), bayan sun gama ta fara masu Nasiha gaba d'aya kan zaman tare da kuma hak'uri da juna daga baya ta fara ma Haisam shi kadae kan rike amanar matan shi da kuma yin Adalci a tsakanin su, bayan ta gama dashi ta koma kan Fanan ta nuna mata kada ta dauki duk abunda ake fad'a akan kishiya ta d'auka ita d'in Alkhairi ce sai taga ta zame mata Alkhairin ta rufe idanunta ta kuma toshe kunnuwan ta daga dukkan wata zuga da za'ai mata kan Fateema, kada ta goyi bayan a cutar da ita domin tasan Allah baya barin cuta, tace ta ci gaba da yi mata kallon k'anwarta kamar yadda take yi mata a da, a matsayinta na babba ta zamo mai hak'uri sosae akan komai in taga tayi ba daidai ba ta nusar da ita...Sosae tayi mata Nasiha itama Fanan d'in dake jingina da kujera tana ta d'an jinjina mata kai, a k'arshe ta yaba mata sosae akan Namijin kokarin da tayi wurin yak'i da zuciyarta ta danne kishinta don Farincikin su ta nuna samun matan da zasu iya yin hakan yanada matuk'ar wahala ta nuna mata kar ta d'auki hakan gazawa face jarumta wurin yin abunda yake daidai, ta nuna more ma rayuwa shine ka sanya farinciki a zukatan mutane ba ka za6i ka saka kanka kad'ai ba hakan zai saya maka soyayya da k'ima a idon mutane, haka kuma ko bayan ba ranka za'a ji rashin ka baza kuma a manta da kai ba riba biyu kenan sa6anin ka za6i Farincikin kanka kai kad'ai ka cuta ma mutane su rink'a k'in ka k'arshe ka mutu aita murna tunawa ma da kai yayi wuya, Kallon Haisam tay dake kishingid'e yana sauraran ta tace "ina son ka sani Fanan masoyiyar ka ce ta hak'ika tunda har ta za6i Farincikin ka fiye da nata don haka indai ka wulakanta ta wllh sai Allah ya saka mata duk da bani da haufi a kan ka kawai tuni nake maka" jinjina mata kai yay a lokacin Fanan tasa hannu ta d'an dafe goshinta jin kuka na niyyar taho mata ita kad'ai tasan abunda take going through don ma tana ta yin Addu'oi a cikin ranta, komawa Hajiya tayi kan Fatuu da kanta ke a sadde tace ta dawo gareta, farko maraba da shigowa cikin Family d'in su ta k'ara yi mata tace tasan halinta itama bata da shakku a kanta don haka kada ta sake ta canza daga yadda ta santa ga Fanan nan taci gaba da d'aukar ta matsayin Yayarta kar ta sake daidai da rana d'aya tace zata mata kallon kishiya, in tana da matsala ta sanar da ita tana da yak'inin zata bata shawarar kirki sannan ta taimaka ma mijin su wurin ganin yayi masu Adalci hakan shine son gaskiya, in Fanan tana yi mata abunda bata jin dad'i ta fad'i mata idan bata gyara ba ita ta fad'i mata duk da tasan in sha Allahu hakan bazata faru ba, daga k'arshe bayan ta gama yi masu nasihohin da suka tsuma masu jiki sosae tayi masu Addu'oi tasa Haisam shima yayi duk suka d'aga hannuwa suna amsawa har ya gama gaba d'aya suka shafa, shiru ta biyo baya duk suka cigaba da yin kallo saidai kowa da abunda ke kai kawo cikin Zuciyar shi, gaba d'aya Fatuu ta kasa sakewa don jikinta na bata Haisam kallon ta yake hakan yasa duk ta takura ga kuma yanayin Fanan data lura tana a cikin damuwa k'arfin hali kawai take hakan yasa duk ta sha jinin jikinta, kiran sallar Magrib da aka fara yi yasa Haisam mik'ewa hannunshi ruk'e da rigar shi ta sama daya d'auka yace ma Hajiya zai je salla tai mashi a dawo lpy, d'an d'aga ido Fatuu tayi tana kallon bayan shi har ya kusa fita sannan ta maido shi k'asa, zuciyarta ce ta shiga raya mata wani abu game da shi, bayan fitar shi Hajiya ta mik'e tace masu suje suyi salla, Fanan ce ta fara mik'ewa da d'an murmushi ta kalli Fatuu data d'ago tana kallonta ta mik'a mata hannu, a sanyaye ta kama hannun ta mik'e suka nufi ciki. Yadda hakan ta faru, bayan Haisam sun gama Magana da Fanan kan zuwa Nigeria ranar talata, da yamma Hajiya Maryam ta kirata don ta ji halin da ake ciki game da tahowarta nan take sanar mata yadda sukai da Haisam kan zuwa Nigeria ta yi ma Hajiyar Magana da kanta, nan Hajiya Maryam taji dad'i sosae don tasan da wuya in Hajiyar bata bari an saki Fatun ba Saboda su duka sun nuna basu so kuma tasan yadda take ji dasu gaba d'aya, hakan ne yasa washe gari da Hajiya ta kira Hajiya Maryam game da zancen dawowar Farha da Maganar data yi mata sam bata damu ba, tun bayan da suka yanke zuwa Nigeria Haisam ya kasa samun natsuwa, damuwa tayi mashi yawa don yasan shi dae ba iya sakin Zaraah zai yi ba yadai biye mata ne don ya kwantar mata da hankali k'arshe kuma yasan indae suka zo Nigeria yak'i sakin Fatuu to abun zai k'ara kwa6ewa ne, hakan yasa ya yanke tunkararta akan hakan, Ranar Alhamis da daddare ya isketa a d'aki lokacin tana zaune akan gado tana latsa wayarta, tana ganin shi ta d'ago tana mashi dariya ya nufi bakin gadon ya zauna shima yana mata murmushi, aje wayar tayi ta matso inda yake ta kwanta a bayan shi ta yadda yay kaman ya goyata ta sak'alo hannuwanta a wuyan shi nan ta shiga fad'a mashi kalaman soyayya, sosae yaji fargabar sanar da ita abunda ya kawo shi k'arshe dai yay k'arfin hali yace mata magana yake so zasu yi, tana jin hakan ta sake shi ta dawo daga gefe tana kallon shi, d'an jimm yay ta kafe shi da ido daga baya ya fara magana gently, ce mata yay Alfarma yake son ya nema a wurinta for the first time a zaman su, jinjina mashi kai tay gaba d'aya ta maida hankalinta akan shi, ce mata yay ya zauna yayi dogon tunani gaskiya idan ya saki Zarah bai mata Adalci ba zai zama ya cuce ta ne Saboda shi ya fara saninta sannan tayi k'arama ace ta zama bazawara, wani kallo take bin shi dashi yanayin fuskar ta ya canza da alamun d'aurewar kai tace to mi yake nufi kenan, kauda idon shi yay tana ta kallon shi can ya juyo ya kalleta yace "I can't divorce her......" waro ido tay hankali tashe take kallon shi, hannu ya kai zai kama hannunta da sauri ta janye ta fara k'ok'arin nufar can d'ayan 6angaren gadon ta sauka, da sauri ya idasa hayewa saman gadon ya cafkota, rungume ta yay k'am ta fara kokowar kwacewa amman ta kasa kawae sai ta fashe da matsanancin kuka ta fara fad'in ita zai yaudara bacin sun gama Magana shine zai zo yace bazai saketa ba dama tasan yana sonta ne shiyasa ya aureta yanzu kuma daya san ita tana haihuwa shine zai ce bai iya rabuwa da ita to indai ya za6i zama da ita ita Allah bazata cigaba da zama da shi ba, sosae ta tashi hankalin ta sai k'ok'arin k'wace kanta take k'arshe kawai sai ya had'e bakunan su ya fara kissing d'inta deeply don yasan hakan zai iya calming nata, ya d'an d'auki lokaci yana mata hakan kafin ya saki bakin nata jikinta sai kerma yake tana sheshsheka, kwantar da kanshi yay saman kanta cikin sigar rarrashi ya fara magana yace mata yasan ita ba mai son kai bace tayi tunani, in ya saki Zarah zai cuceta ne yasan bazata so hakan gareta ba ko kuma sister d'inta Farha tayi aiki da Hadisin manzo SAW da yace love for ur brother what you love for urself, a yadda yasani tana son Zarah sosae miyasa bazata tausaya mata ba, sai huci take ta hau girgiza mashi kai tace ita dai bazata iya zama da ita matsayin kishiya ba, miyasa zai saka mata rai yayi mata alk'awarin zasu zauna su biyu, ce mata yay ya gaya mata already da aure a tsakanin su amman yanzu zai iya yi mata wani daga Zarah bazai k'ara Auren wata ba su biyu zasu zama matan shi har k'arshen rayuwar shi, shiru tay kaman mai nazarin wani abu can ta d'ago ta kalle shi idanunta sharkaf da hawaye tace "Tell me the truth, do you love Zarah?" Shiru ya d'an yi yana kallonta can ya jinjina mata kai kawai sai ta fashe da kuka ta fad'a jikin shi tana fad'in ita daman tasan son Zarah yake shiyasa tun farko ya auretan in ba haka ba miyasa bai sa Abbas ya aureta ba daga baya ya saketa sai shi daga baya kuma yazo ya kwanta da ita, tasan itace First love d'in shi dama ita ba son ta yake ba kawai tausayinta ne yasa ya aureta don haka zata bar shi sai suji dad'in zama da juna, sosae take kuka yana rungume da ita cikin kwantar da murya yace mata wayace mata bai sonta, da farko da akai mashi Maganar aurenta Saboda yasan ba soyayya suke ba shiyasa ya nuna bazai aureta ba don bai d'auka Maganar da ta yi mashi ta zai aureta ba da gaske take Saboda lokacin a wurin shi tayi k'arama da wannan Maganar, amman daga baya daya nuna ya amince Saboda yana son ta ne, kuma da bai sonta a zaman da sukai ai ya isa ta gane, tambayarta yay a zaman su tare ya ta6a cutar da ita ko hantarar ta ko dai yi mata wani abu na rashin so, d'an girgiza mashi kai tay yace to ta daina cewa haka he truly loves her kuma yana rokonta tayi mashi wannan alfarmar Saboda son da take mashi koda kuwa daga ita bazata k'ara mashi wata ba har k'arshen rayuwar su ya amince, gaba d'aya ya kashe mata jiki ganin haka yasa yaci gaba da rarrashinta, wai akace tsakanin mata da miji sai Allah d'agowa tay tace "Shikenan na Amince but don't break the promise u have made now kuma kayi man Alk'awarin zaka yi mana Adalci" sosae ta bashi tausayi don yasan Saboda son da take mashi ne yasa tayi saurin Amincewa, ce mata yay in sha Allahu zai yi masu Adalci tace ita bata yarda ba sai yayi mata Alk'awari da d'an murmushi yace to ya yi mata. Koda suna a jirgi saida ta jaddada mashi ya dai ce zaiyi Adalci a tsakanin su ko yana murmushi yace mata eh, Bayan sun iso a Bedroom d'in Hajiya suka sauka dama tun kafin su zo Haisam d'in ya fad'i mata game da amincewar da tayi itama Hajiya taji dad'i sosae, bayan sun gama gaisawa tayi masu Maganar Abinci duk suka ce mata basu jin yunwa a lokacin nan ta k'ara yi ma Fanan Nasiha sosae ta nuna mata ta d'auki abun a matsayin Alkhairi ta shiga bata misalai kan irin hakan sosae Fanan ta d'auki Nasihar Hajiyar daga baya ta tambayi Fatun Hajiya tace bata dad'e da barin Part d'in ba, ita da kanta ta tambayi Hajiya takarda ta rubuta abun ciki taba Haisam d'in tace zata mata wasa ne Hajiya na dariya tace ta dai tada mata hankali dama yar'uwarta da Mahaifiyarta sun gama nasu da alamun rashin fahimta Fanan d'in ta tambayi mi sukai mata nan Hajiya ta kwashe komai da Hajiya Maryam da Farha sukai ma Fatun, sosae ta bata tausayi har fuskarta ta bayyana, daga baya suka koma Parlor nan Hajiya ta kirata saidae ita bata san da Maganar sak'on da Fatuu ta tura ma Haisam ba saida tazo Fanan na mata Maganar ta fahimci ita ta tura mashi sak'o Fanan d'in ta gani. Sai bayan da aka yi isha sannan Haisam ya dawo lokacin suma sun dawo cikin parlon, Fatuu na ganin shi ta gane yaje part d'in su don har ya canzo kaya, har ya k'araso idon shi na akan Fatuu da tunda ta kalle shi ta maida idon ta akan Tv, Fanan ce tay mashi sannu da zuwa da murmushi ya amsa mata Fatuu tay d'an jimm zuciyar ta ta raya mata itama tace mashi mana, da k'yar ta d'an kalle shi da yake Facing d'in su yake murya na d'an rawa tace mashi sannu da zuwan ya jinjina mata kai kawae ya zuba mata ido da sauri ta maida nata kan Tv, wani abu take ji mai kamar haushin shi a ranta, bai dad'e da zama ba Saude tazo ta sanar dasu ta shirya Table, Hajiya ce ta fara mik'ewa tace masu su taso, bayan duk sun zauna Saude na niyyar Serving nasu bayan ta gama da Hajiya tace mata taje kawae, kallon Fatuu tay tace ta tashi tay Serving bak'inta ta d'aga mata kai, Haisam ta fara zuba mawa tana yi tana tambayar shi in yayi ya kafeta da kaifafan idanuwan shi da suke a d'an lumshe dasu yake bata amsa ko da kai gaba d'aya yana neman rikita ta, bayan ta gama ta juya kan Fanan itama ta zuba mata saidae d'an kad'an tasa ta zuba mata, zubawa itama tayi bada yawa sosae ba duk suka fara ci a nutse, baka jin komai sai k'arar cokulla, duk in ta saci kallon Haisam sai taga ita yake kallo yanayin fuskarta kamar a d'aure, tana lura da Fanan sam bata wani cin Abincin juya cokali ya fi yawa sai an d'auki lokaci take d'an d'iba ta kai baki tay ta taunar shi sai kaga kaman tana ci, duk Fatuu sai taji ba dad'i don gani take itace silar damuwar ta, can dae tay k'arfin hali murya na d'an rawa tace "A...unty Fanan baki ci sosae" da sauri Fanan d'in ta kalleta tay mata murmushi murya k'asa k'asa tace mata tana ci mana, Hajiya da ta d'ago ta kalli Fanan d'in da d'an murmushi tace an sha tafiya ko gajiya ce tasa ta kasa ci sosae in tana son wani abu ta fad'i sai a had'a mata, d'an girgiza ma Hajiyar kai tay tace wannan ma lafiya lou, kad'an ta k'ara ta mik'e duk suka kalleta tana murmushi tace ta k'oshi bata da appetite ne zata k'ara da tea daga haka ta fita daga cikin Kujerar ta nufi hanyar Bedroom idon Haisam a kanta ita kuma Fatuu lokacin ta samu damar kallonshi sosae bata Ankara ba ya juyo suka had'a ido, kayataccen murmushi taga ya sakar mata ta bishi da ido kawae, kaman daga sama suka ji muryar Hajiya tana fad'in suyi sauri su gama ba sai suje suji dad'in kallon Junan ba, sosae kunya ta kama Fatuu ta sunkuyar da kai, da k'yar ta cinye Abincin ta mik'e tace ma Hajiya saida safe ta kalleta tace to Allah ya basu Alkhairi, bayan ta fita daga cikin Kujerun Hajiya ta tsaida ita tace taje suyi sallama da Yayar ta tace to ta nufi hanyar Corridor tana tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, d'an jimm tay a bakin kopar visitor room d'in gabanta na d'an fad'uwa hakanan fargabar shiga take ji, can dai ta tura kopar a hankali tare da yin yar sallama, a kwance ta hangota ta kife fuska a jikin pillow kai da gani kasan da wuya in ba kuka take ba, bugun k'irjin Fatuu ne ya k'aru da sauri ta juya zata fita don ta lura kaman bata ji sallamar data yi ba, har zata fita taji Muryar ta ta kira Sunanta, juyowa Fatuu tay ta kalle ta taga ta tashi zaune, a sanyaye ta nufi gadon ta nuna mata gefen ta alamar ta zauna Fatuu na kallon idonta ta gane kuka take duk da goge idon da ta yi, shiru suka d'an yi kafin Fanan d'in tace mata har ta gama cin Abincin ta d'aga mata kai ta jinjina nata itama, shiru suka k'ara yi idanun Fatuu a k'asa wani irin tausayin Fanan d'in take ji can ta d'ago ta kalleta idanunta sun ciko da k'walla cikin karyayyar murya tace "Aunty Fanan don Allah kiyi hak'uri wllh ban ta6a nuna mashi ina son shi ba, ko wannan sak'on da kika gani bani na tura mashi ba wllh k'awata ce kuma sai da na nuna mata ban ji dad'i ba daga baya ma na goge shi ko tambayar shi zaki ko ki duba zaki ga an goge" idanun Fanan d'in suma cike tabb da k'walla take kallon ta harda Murmushin k'arfin hali har ta gama sannan ta kai hannu ta janyota ta kwantar da kanta a saman shoulder d'inta cikin sanyin murya tace 'its okey Zaraah I understand everything, kema bake kika d'aura ma kan ki ba, komai da yake Faruwa akan mutum was already written, Allah ya bamu ikon ruk'e Amanar juna and am sorry for what u'r going through itama Friend d'in tak'i taga kina wahala ne yasa ta yanke turo sak'on" shiru Fatuu tay wani irin tausayin Fanan ya mamaye mata zuciya, can ta d'ago daga kan kafad'ar tata ta kalleta a sanyaye tace mata to don Allah ta daina yin kuka bata jin dad'in ganin ta haka sai taita ganin kaman Saboda ita ne, da sauri ta girgiza mata kai tace ta bar sama ranta hakan kawai abunne gaba d'aya yazo mata a bazata so dole sai a hankali zata washe nan ta sanar mata da bata san komai ba sai da aka turo sak'on ita ta fara gani, sosae Fatuu taji ba dad'i Fuskarta a yamutse take kallonta can Fanan d'in tace mata ta k'ara girma sosae tana murmushi harda tambayar ta ta kai 20yrs ne yanzu, Fatun tace mata a'a 19 take ta jinjina kai tace tana da jiki mai kyau ita dai d'an murmushi kawai tayi sai kuma tace mata itama ai tana da kyaun jiki ga tsawo ita kuwa gajera ce har saida tasa Fanan d'in yar dariya, tambayarta karatun ta tayi tace ta kusa gamawa ko, ta bata amsa da yanzu zasu kama nursing 2 sai su shiga 3 daga nan zasu gama, jinjina kai tayi tace Allah ya basu sa'a bayan Fatuu ta amsa tace "in kika gama nasan U.S zaki dawo sai kiyi Medicine ki zama likita da kike buri" yar dariya Fatun tayi kawai, suna haka aka turo kopar d'akin duk suka kai idanunsa wurin, Haisam ne ya shigo hannun shi ruk'e da tea cup asaman saucer, har saida gaban Fatuu ya d'an fad'i ganin shi, ciki ya shigo ya nufo wurin su,a gaban Fanan ya tsaya idonta akan shi da d'an murmushi ya mik'a mata cup d'in tea d'in ta amsa a hankali ta furta mashi thanks Fuskar shi a sake ya jinjina mata kai, d'agowa yay idon shi akan Fatuu da ke kallon k'asa sai taji duk ta takura, mik'ewa tay ta kalli Fanan tace mata saida safe tace ta tsaya su sha tea d'in mana da d'an murmushi ta girgiza mata kai tace taci Abinci sosae dama saida safen ta shigo yi mata, godiya tayi mata tace sai sun had'u da safe daga haka Fatun ta juya ba tare data kalli inda yake ba ta nufi k'opa ta fuce. Tana tafiya tana ta zancen zuci har ta k'araso part d'in su, tun a parlor ta gasgata Haisam ya shigo jin k'amshin turaren shi, Bedroom ta wuce tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna tay zuru tana cigaba da zancen zucinta, sosae Fanan take bata tausayi tasan itama ba K'aramin so take ma Ya Haisam d'in ba yanzu kuma ace ya auri wata tasan dole ta shiga matsananciyar damuwa, mamakin ta yadda akai tay saurin amincewa ba kamar data ce mata saida aka tura sak'on nan ta sani duka kuma ba'a fi kwana shidda ba, wata zuciyar ce ta raya mata wato da ya kasa fad'a mata saida asiri ya tonu ta amince shine suka taho da hakan bata faru ba tasan baida niyyar zuwa, wani abu taji mai kaman 6acin rai ta raya yanzu dai ta tabbatar ba son ta yake ba tunda saida Matar shi ta amince zai waiwaye ta dama kuma tasan Saboda Hajiya yake zaune da ita, rayawa tayi to miye amfanin zaman ta dashi wai tunda bai son ta kawai ya saketa ya huta Aunty Fanan ma ta huta da damuwa, tunanin ta nemi ya saketa ta shiga yi, wata zuciyar ta raya mata tana tunanin a yanzu zai saketa bacin yasan sirrin zuciyarta ita kanta Fanan ai don ta nuna tana son shi ya aure ta, sosae taji bata ji dad'in sak'on da ya gani ba amman duk da haka ta sama ranta zata ce ya sake ta kawai, ta d'auki lokaci a zaunen kafin ta mik'e don taje tayi wanka, bayan ta aje gyalen ta gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta ta kai hannu tana cire yan kunnan ta fashion bayan ta cire su ta cire agogon hannunta ta d'aura su akan dressing mirror, daidai ta juyo aka turo kopar Bedroom d'in har saida gaban ta ya fad'i, shi ne ya shigo idon shi akanta yasa hannu d'aya ya tura kopar, a wurin ya tsaya suka kafe juna da ido fuskar shi a sake kaman zai yi murmushi ita kuwa yanayin tata kaman a d'aure, kauda idon ta tayi gefe zuciyarta ta raya mata tsayuwar mi take ta tafi tay wankan ta, nufar hanyar Laundry room tay idon ta a k'asa har tazo daidai inda yake a tsayen, tana niyyar wuce shi kawai taji ya kamo hannun ta na gefen da yake, yamutsa fuska tay fuskarta na kallon gefe wurin gado kirjinta ya hau bugu da sauri da sauri, wani irin haushin shi taji ya kamata wato sai yanzu da aka amince mashi ne zai yi lokacinta ta raya hakan, kaman daga sama taji ya furta "Zaraah" wani kalan murmushin takaici ta yi nan take ta fara k'ok'arin k'wace hannunta, k'ara kiran sunanta yay aikuwa a fusace ta juya idanunta har sun ciko da k'walla tace "ba suna na haka ba sunana Fatuu ka kira ni da hakan" cikin yanayin muryar kuka tayi Maganar tana rufe baki k'walla suka zubo mata sharr da sauri ta juyar da fuskar inda take kallo da, still yay yan kallonta don ya gane dalilin daya sa ta fad'i hakan, k'ok'arin matso da ita ya fara nan take ta fahimci rungume ta zaiyi aikuwa ta tirje ta fara jan hannunta sai ga abu ya zama kaman kokowa, da dai taga ta kasa kwace hannun sai ta fashe mashi da kuka ta fara fad'in ita ya sakar mata hannu, janyota yay ya had'a jikinsu ta kafe tak'i yarda ya mannata da k'irjin shi ta hau girgiza kan ta cikin k'araji take fad'in ita ya k'yaleta, sosae take kuka tana girgiza kai idonta a rufe gaba d'aya ta fara rud'a shi fuska a yamutse yake kallon tata fuskar, da k'yar ya manna ta da k'irjin nashi ya rungumeta gam sai faman kuka take, d'aura ha6ar shi yay a saman sumar ta mai santsi da tuni kallabin dake sama ya fad'i, lumshe idanunshi yay underneath his breath yake furta "am sorry for hurting u Zaraah, it was never my intention" shiru tay tana cigaba da kukan saidae sautin kukan ya d'an ragu sai sheshsheka take ga fitinannan k'amshin jikin shi duk ya cika mata hanci hakan ne yasa natsuwarta ta d'an daidaita, Moving yay da ita zuwa bakin gado ya zauna da ita ta kasance a saman cinyoyin shi har lokacin kuma yana rungume da ita gam, maida ha6ar shi yay saman kan nata breathing d'in shi na fita slowly idanun shi a d'an lumshe shi kad'ai yasan abunda yake ji a cikin ran shi ganin ta cikin halin nan, ganin kaman ta d'an natsu yasa shi janye beard d'in shi ya maida fuskar shi saitin kunnanta whispering in to her ear ya furta "I came all because of you" da sauri ta girgiza mashi kai ta d'ago idanunta sharkaf da hawaye ta juyar da fuskar ta gefe cikin fushi tace "ni ban son Auren ka sake ni!" jimm yay yana kallon ta can yay sigh calmly ya furta "Zarah kina fad'a man haka a matsayi na na mijin ki ba kyau fa" sheshshekar kukan ta ce ta k'aru, ji tay yace "Kin daina sona ne??" Kaman tana jira da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh har saida ya d'an runtse idon shi kafin slowly ya bud'e sai kuma ya d'an cize le6en shi na k'asa, nisawa yay yace "are u serious Zarah?"da sauri ta k'ara d'aga mashi kai alamar eh wannan karon har saida yaji gaban shi ya d'an fad'i, shiru yay idon shi a kan gefen fuskar ta, mutsu mutsu ta fara yi tana son ta k'wace daga jikin shi saidae ta kasa a hasale tace ita ya k'yaleta, still shiru yay bai kuma sake tankawa ba sai dae zuciyar shi ta fara gasgata mashi abun da take fad'an, muryarta ce ta k'ara ziyartar kunnan shi tace ya saketa, sigh yay Slowly ya furta "Ok, I want you to look into my eyes and tell that u don't love me sai in maki abunda kike so in hakan zai saki farinciki" yana rufe baki ta juyo ta kalle shi cikin idon da k'arfi gaban shi ya fad'i don yana ganin fad'in zata yi, bin juna sukai da ido tana d'an huci wani irin kallo yake bin ta da shi sai motsa baki take ta kasa furta mashi Maganar gaba d'ayan su gaban su fad'uwa yake bai ta6a jin zullumin magana ba sosae irin haka, da k'yar ta fara bud'e baki tace "ba.......n......." Zuciyarta ce ta fara tariyo mata Alkhairan shi a gareta ta shiga raya mata yanzu duk son da take mashi da wahalar da tasha Saboda shi ta za6i ta rabu dashi, kawai sai gani yay ta fashe da matsanancin kuka ta fad'a mashi, wani irin lumshe ido Haisam yay sosae yaji sanyi a ran shi, Kuka take sosae ta had'e fuskar ta da k'irjin shi, daga jin yadda sautin kukan ke fita yasan ba K'aramin K'ona ranta ke mata ba zuciyar shi ce ta shiga tunano sak'on data tura mashi irin wahalar data bayyana mashi ta sha Saboda son shi, wani irin tausayin ta ne ke ratsa shi sam bai jin dad'in yadda take kukan har Fuskar shi ta nuna fararen idanuwan shi sun d'an yi ja, hannun shi d'aya ya d'ago ya d'aura a saman kan ta ya fara shafa gashin ta alamar lallashi cikin breaking voice ya fara magana "am very sorry Wife, am not happy I caused u pain, kiyi hak'uri don Allah, bansan komai ba game da haka" cigaba da shafa kan yayi a hankali sautin kukan nata ya fara raguwa, sun d'an d'auki lokaci a haka saida yaji tayi shiru sai ajiyar zuciya da take ta faman yi ya d'ago da kanta suka fara kallon juna idanunta sun yi luhu luhu sunyi ja har lokacin ajiyar zuciyar take ta saki, "Forgive your Husband pls, bana jin dad'in ganin ki haka Wife, ba kamar in na tuna duk Saboda ni ne, ki manta komai ya wuce pls" yana Maganar d'umin numfashin shi na sauka akan Fuskar ta, shiru kawae tay tana kallon shi ba alamun zata tanka, fuskar shi a sake kaman zai murmushi yace mata tayi mashi magana pls sai lokacin ta d'an juyar da fuskar ta, hannu ya kai ya juyo da Fuskar ta sake kallonshi ya lumshe mata ido nan take ta gane Magana yake nufin tayi, da k'yar ta bud'e baki cikin muryar kuka da yar in ina tace "t...to ai kai baka sona ko shiyasa gara a bar Auren" d'an murmushi yayi yace mata in sun rabu to ya zatayi da son nashi, "A...ai dama baka sani ba ko na 6oye sai in yi hak'uri kuma nasan zan daina daga baya, d...dama ai har na hak'ura za'a min Aure ko" tana Maganar ya zuba ma bakinta ido Fuskar shi kaman zai murmushi har ta gama ta d'an tura baki, murmushi yay ya d'an d'age gira yace "in kuma ni ban son rabuwa dake fa Saboda nima ina son ki" ba shiri ta waro ido bakinta ya d'an bud'e, sosae taji Al'ajabin Maganar don ta gama yanke bai sonta, hannu ya kai ya rufe mata bakinta da ta bud'e ta tura mashi bakin had'i da d'an juyar da fuskar ta, ji tayi yace bata bashi amsa ba sannan ta maido idon ta kanshi a sanyaye tace ai tasan da wasa yake tunda da yana son ta ai da ya nuna mata, murmushi yay kawae suka zuba ma juna ido Fatuu sai d'an kikkafta ido take idan tace bata jin sabon son shi na ratsa zuciyar ta to ta shirga babbar k'arya, ganin bai da niyyar cewa komai gashi ta k'osa taji da gaske yana son ta yasa ta d'an yamutsa mashi Fuska, d'age mata gira yay yace "What?" a d'an shagwabe tace he should tell her da gaske abunda ya fad'a, Sigh yay kafin a nutse ya fara Magana, "Lokacin da Hajiya ta kira ni tay informing nawa game da Auren da za'ai maki na shiga damuwa because nasan miye burin ki kina son kiyi karatu, hakan yasa naji ba dad'i sosae har nayi mata magana kan bai kamata ayi maki Aure ba kuma ma wannan Auren dole ne I asked her to do something tunda hakan ya shafi aikinta na NGO but sai ta nuna man haka al'adan ku yake in ta shiga Maganar har ta hana ayi maki auren zai zama wani seriou issue Dad d'in ki zai shiga matsala sosae a lokacin ta fad'a man a halin da yake ciki kuma kema kin amince, karshe I have no option dole na bari suyi maki yadda suke so din, abun ya dame ni sosae bayan na kira ki kin sanar man kema baki so Saboda Dad d'inki kika amince haka nayi ta tuna Maganar ki da kukan da kike yi a lokacin, I thought damuwan nawa zai ragu tunda kin nuna man kin amince da Auren but sai abun yay ta gaba thinking of u all the time, nayi tunanin don na damu da halin da kike ciki ne a Lokacin amman abun sai yay ta k'aruwa damuwan yayi man yawa ko yaushe Zarah ce a raina abun har ya fara affecting bacci na bana samun enough ko ya d'auke ni it's Zarah gaba d'aya cikin shi, while eating, while driving ko mi nike Zarah ce abun har ya kaini ga hullicinations da naga yar baturiya daidai girman ki sai inta ganin ke ce inna zauna shiru sai inta jin muryar ki kina magana ko kuma in wata tayi magana naji kaman voice d'inki....." Dakatawa yay dama Maganar yana yi yana d'an tsayawa yake yin ta, idon su cikin na juna Fatuu tayi k'uri tana saurarar shi cike da Al'ajabi, d'an yamutsa mata fuska yay yace "kin man nauyi" wani kallo tay mashi ta d'an tura baki, K'ok'arin sauka daga saman jikin nashi ta fara ya maidota yay wrapping nata sosae, kai Fuskar shi yay gefen kunnanta whispering into her ear ya furta "just kidding wife, bana jin nauyin ki in ma kina da shi" yadda Maganar ke sauka acikin kunnanta har saida ta runtse ido fuskar ta d'auke da murmushi, shiru suka d'anyi can ta d'ago da fuskarta taga ita yake kallo, ganin baida niyyar cigaba yasa ta d'an yamutsa mashi Fuska tare da d'an motsa kai, murmushi yay don ya fahimci mi hakan ke nufi slowly ya kai bakin sa saman goshinta yay pecking wurin har saida ta d'an lumshe ido tana bud'ewa suka shiga cikin nashi kunya ce ta kamata da sauri ta kife fuskarta a broad chest d'in shi, hannu ya kai ya cigaba da shafa sumar ta mai santsi da laushi, "I don't know what's happening to me a lokacin,but I know am not alright don ban ta6a fuskantar irin hakan ga wani ba besides ni ban sa damuwa a raina, in dai abu naga zai zaman man damuwa da wuri nike maganin shi, a lokacin Fanan ta gane abu na damuna ta fara tambayana farko na nuna mata kawai banjin dad'i ne amman daga baya ta fara nuna man damuwarta kan sai na fad'i mata abunda ke damuna don ta ganni abnormal, na rasa mi zance mata yana damuna na barshi a banjin dad'i ne tace to muje Asibiti na nuna mata ba wani ciwo nike ba itace take ganin kaman ban lafiya, nasan kawai ta k'yale ni ne ba don ta yarda ba daga lokacin na fara k'ok'arin 6oye abunda ke damuna Saboda ita sai kuma na fara samun sleepless nights don sai damuwan ya dame ni in dare yayi hakan ke sa in kasa bacci, daga k'arshe na yanke zuwa inga Doctor, banje Asibitin su Fanan ba sai na je wani daban naga likita, bayan nayi mashi duk bayanin abunda ke damuna ban 6oye mashi komai ba shine yay assuring nawa cewa.....Na fad'a Son ki ne....." dakatawa ya k'ara yi suka k'ura ma juna ido cike da k'auna yayin da numfashin su ke had'uwa dana juna, kasa jurewa Fatuu tay ta sauke idanunta don wani irin kallo mai saukar da kasala yake mata, "Nayi mamakin jin hakan sosae Saboda tunda nike dake ban ta6a ji ko yi maki kallon hakan ba, ina d'aukar ki a matsayin blood sis tawa, kallon da nike maki kenan Zarah, saidae ban k'aryata Maganar shi ba na yarda da hakan, nan ya bani shawarwari saidae wadda yafi bani itace in mallake ki shine solution kawai a lokacin, jin hakan har saida na d'an yi murmushi sanin it's impossible, daga lokacin na dage kan sai na cire son naki a raina na dage da rok'on Allah akan hakan sosae nike yak'i da zuciyana, ban gane son ki yamun mugun kamu ba sai bayan na tafi wani Seminar da Company d'in mu suka tura ni, ina cikin yin bayani na rink'a ambaton sunan ki saida aka man magana sannan na gane shirmen da nike tafkawa, k'arshe dai ranar a gadon Asibiti na kwana don wani duhu na fara gani har ya kai na fad'i......", dakatawa ya k'ara yi ya d'age mata gira yace "tunda kike ciwon sona kin ta6a koda shan drug ne Saboda hakan?" d'an jimm tay alamar tunani kafin a sanyaye tace mashi a'a saidae maganin bacci da Kawu Amadu ya ta6a amso mata data kasa yin bacci, d'an murmushi yay yace "kin ga ni nasha drugs, na kar6i injections k'arshe harda drip all because u" wani irin tausayin shi ne ya mamaye mata zuciya nan da nan idanuwanta suka ciko da k'walla yana ganin haka ya girgiza mata kai da sauri alamar kar tayi kukan ta hau kikkafta idanu, cikin karyayyar murya tace mashi yaci gaba, d'an tura mata baki yay irin yadda take yi slowly yace mata ya gaji da Magana har saida yasa ta d'an yi yar dariya dama don ta washe kada tayi kukan yayi Mata hakan, "Kwana na d'aya a asibitin na nuna gida zan koma aka matsa man kan in bari in k'ara samun sauk'i, bayan nayi kwana biyu lokacin na warware sosai na dawo gida ba tare dana k'arasa abunda naje yi ba...., wani iko na ubangiji ranar Abbas ya kirani yake sanar dani ai gaki kin gudo wai baki son Auren da za'a maki na tambaye shi dalili nan ya sanar dani irin mijin da ake son Aura maki, lokacin na tambaye shi to miye mafita sai yace man ai ya yanke zuwa garin shida Grandma d'inki nace mashi Shikenan duk abunda ake ciki sai ya sanar man, a next wayan da mukai da Abbas lokacin yay man Maganar Auren ki, bazan 6oye maki ba lokacin duk da halin da nike ciki ban ji zan amince ba don ina ganin ba abu bane mai yuwuwa, ban dad'e da nayi Aure ba so nasan Matana da iyaye na bazasu amince ba, k'arshe da yake Allah ya k'addaro Aure tsakanin mu Abbas yay convincing ena ya tsara yadda za'ai, I guess you know everything about dat" kai ta jinjina mashi wani irin kallon tausayi mai had'e da tsantsar kauna take mashi, shima fuskar shi da d'an murmushi idanun shi a d'an lumshe yake kallonta shi kad'ai yasan irin nishad'in da yake ji a cikin zuciyar shi jin Zarah a jikin shi, cikin karyayyar murya tace mashi to miyasa bai saketa ba kaman yadda suka tsara, bin bakinta yay da kallo tana furta Maganar har ta gama yay d'an jimm yana ta kallonta hakan yasa Fatuu d'an motsa jikinta cike da shagwa6a tace yayi Magana mana, Slowly ya matsa da Fuskar shi ya had'e goshin su nan take yanayin fitar numfashin Fatuu ya canza ya koma fita da d'an k'arfi ta lumshe ido, shima nashi idon a lumshe yake kusan ma sun rufe wani irin yanayi mai dad'i suke ciki son junansu na sake sabuntuwa a cikin zuciyoyin su, sun d'an d'auki lokaci a haka suna inhaling sweet scent d'in juna, sai after some few minutes sannan ya d'ago da fuskar a hankali itama a hankali ta fara bud'e idanuwanta saidai ta kasa bud'e su gaba d'aya sun lumshe kaman yadda nashi ma suke a a d'an lumshen gashi sun k'ara cizawa, murya k'asa k'asa ya fara magana "after the marriage naji ban iya sakin ki and to my surprise tunda nasan kin zama tawa sai kawai na nemi ciwon da nike na rasa....." Dakatawa yay yana sakar mata wani k'ayataccen murmushi, itama murmushin take mashi, cigaba yay "if u can remember, akwae wani rana da muna Video call da kika ce ko kinga kaman face dina ya canza na tambaye ki mi yayi kika ce ya fad'a ko ban lafiya nace maki eh but na samu sauk'i, lokacin ina Tunanin bai fi 2 days dana dawo daga inda naje Seminar ba harna kwanta Medical bed" d'an jimm Fatuu tay alamar tunani nan take ta tuno lokacin bayan su gwaggo sun dawo ne tare da su yadikko har ta shiga d'akin Kawu Amadu suna cikin yin Vedio call d'in bacci ya d'auketa, da sauri ta maida idanunta cikin nashi tace "kenan lokacin ni Matar ka ce?" Ido ya lumshe mata still da murmushi akan Face d'in shi, murmushi tayi mashi ya kai hannu ya rungumota ta kwantar da kanta a chest d'in shi, shima kwantar da gefen fuskar shi yay suna kallon side guda, "Lokacin dana maido Hajiya that's why I can't take my eyes off u, sosae nike jin dad'i a zuciyana in ina kallon ki, akwae wani lokaci da nayi maki Maganar ko zaki bini U.S a cikin Mota bansan ko zaki tuna ba....." Kai ta d'aga mashi alamar ta tuna, ce mata yay lokacin da gaske yake data amince zai tafi da itan alokacin ya yanke ya sanar ma Hajiya game da Auran, jin tana k'ok'arin d'ago kanta ta kalle shi yasa shi janye face d'in shi, "To da na amincen ka tafi dani Aunty Fanan fa tunda nasan bata sani ba" a sanyaye tayi Maganar tana kallon shi, sigh yay yace zai kai ta wani wuri ne da bazata sani ba tunda lokacin ya fahimci bata son zuwa can Saboda Fanan d'in don akwae wani lokaci a baya sun ta6a Maganar yace ko zataje can taci gaba da karatu tace mashi Fanan d'in koro ta zata yi tace ta lik'e ma mijin ta, daga baya in ya yi mata bayanin komai sai ta koma gidan su, ce mashi tay to karatun ta fa bacin tayi nisa yana murmushi yace mata acan ma ai ana karatun sai tayi kuma bai d'aukar lokaci kamar na nan, shiru kawai tay suna cigaba da kallon juna can ya d'age mata gira yace "Are u satisfied now that I love you?" Lumshe mashi ido tay irin yadda yake mata nan take ya gane kwaikwayon shi tay, murmushi yay slowly ya kai bakin shi saitin nata ya manna mata kiss, da sauri ta kauda fuskarta alamar kunya, Hannu ya kai ya juyo da Fuskar tata ya furta "is dat all u want know ko da wani abu?" had'e lips dinta tayi ta d'an d'age ido alamar tunani, kallon shi tay cike da shagwaba tace "to amman miyasa kake gudu na?" kafeta da ido yay yana mata wani kallo ba tare da yace komai ba, ganin haka yasa ta fara nazarin Maganar da tayin a d'an rud'e tace mashi tana nufin miyasa bai sake mata bayan ta tare in kuma don abunda tayi ne ai ta bashi hak'uri kuma yace ya hak'ura, wani irin murmushi taga ya saki aikuwa ta fad'a mashi ta cusa fuskarta cikin broad chest d'inshi tana fad'in itafa ba wani abu take nufi ba wllh, rungume ta yay tightly yana ji a ranshi kaman su dawwama a haka bayan ya kwantar da Fuskar shi saman gashinta a nutse ya furta "ba gudun ki nike ba Wife, I always need u badly, abunda ya faru a G.r.a nasan nima inada laifi duk da ban kai ki can ba don hakan Allah ne ya kaddara hakan zai faru, banyi fushi da ke ba kawai abu biyu ne ban ji dad'in su ba, farko yadda nayi maki nasan na cutar dake sannan kuma da kika zo sanar man u'r pregnant duk abunda kika fad'a man banji komai ba don nasan nayi maki ba daidai ba kawae abunda banji dad'in shi ba yadda nayi k'ok'arin dakatar dake amman kika k'i saurarana bazan 6oye maki ba banji dad'i ba kaman yadda na fad'a maki da kika zo bani hak'uri, hankali na ya tashi a lokacin ba kuma don rasa cikin ba sai don tsoron abunda zai iya faruwa dake I might lose u i thought to myself, hakan yasa na je na fad'i ma Hajiya duk da dama ina niyyar inje in fad'a matan Saboda abunda nayi maki.....Tun bayan da abu ya shiga tsakanin mu...Sai na sha drug nike iya bacci peacefully" lamo Fatuu tay cikin ranta ta shiga tunanin ashe Maganin data gani kenan Saboda haka yake shan shi, kai bakin shi yay saitin kunnanta cikin magana mai kaman rad'a yace mata yana gudun ta k'ara samun ciki ne yafi son sai dangin shi sun sani komai ya daidaita don yasan dole farko za'a iya samun matsala hakan kuma na iya sata a damuwa wanda ba'ason mai ciki tana damuwa k'arshe ma cikin zai iya k'ara zubewa wannan ne dalilinshi duk da yana cutuwa amman in itama ta cutu sai yafi jin ciwo, nan ya bata hakurin abunda su Hajiya Maryam suka mata ya nuna bai ji dad'i ba sosae amman insha Allah hakan ya wuce ba wanda zai k'ara mata, k'ank'ame shi Fatuu tay lokaci guda yaji sheshshekar kukan ta a cikin kukan ta fara bashi hak'uri kan tunanin da tayi ba daidai ba a kan shi da kuma wahalar daya sha saboda ita, gaba d'aya ta gama kashe mashi jiki, d'ago Fuskarta yay har tayi jage jage da hawaye, idanun shi a lumshe yake kallon ta sai kukan take itama tana kallon shi, girgiza mata kai ya fara kafin ya kai bakin shi ya fara kissing hawayen, jin tayi shiru yasa shi dakatawa ya d'ago hannu yana share mata fuskar, bayan ya gama yana murmushi ya tambaye ta ya akai ta fara son shi itada yasan ba komai a ranta sai son karatu ta zama Doctor, cikin muryar kuka ta fara bashi labari tana yi tana yar ajiyar zuciya, bata 6oye mashi komai ba tun daga kan yadda Haulat ta nuna mata son ta yake shiyasa yake hidima da ita har ranar ta tuna mashi daya tambayi Haulat d'in ko yau sun samu kud'i ne a school yaga tana cikin farin ciki tace mashi tun daga nan ta fara jin son shi, ta sanar mashi tun ranar da Aunty Fanan tazo ta gane abunda ke tsakanin su ta fara wahala akan son shi, a shagwabe ta furta "Wllh Ya Haisam nasha wahala....maimakon tunda nasan kana da wadda zaka aura in daina jin son kan amman zuciyata taita k'ara man son ka gashi kuma tasan ba samun ka zan yi ba....." Fuskarta sharkaf take Maganar, wani irin tausayin ta ne ke ratsa shi har idanun shi sun k'ara sauyawa, cigaba da goge mata kwallan yay yana fadin "I promise you that this is the last time you will ever have to cry because of me" bayan ya gama goge mata rungumeta yay, suna haka yake ce mata ai da ta sani daya kirata ya tambayeta abunda ke damunta ta fad'i mashi tace mashi to ai tasan k'arshen ta ya bata hak'uri kaman yadda ta fad'i mashi su Kawu Amadu da Haulat sun ce mata a labarin data bashi kuma shima ba gashi yace lokacin da Abbas yay mashi Maganar aurenta duk da yana sonta da farko bai amince ba" shiru yay yasan kusan hakan ne zai faru, shafa bayanta ya shiga yi ana fadin she should forget about d pass, saida yaji ta samu natsuwa sosae sannan ya d'ago fuskar ta yana murmushi ya d'an dage mata gira yace yanzu yaushe zata biya shi abunda tasa ya rasa kaman yadda ta fad'a, kunya ce ta kamata ta fara mutsu mutsun son 6oye fuskar ta amman ya hana sai dariya yake hakanan sai ta kasa ce mashi ba ita ta tura sak'on ba, k'ara maimaita mata tambayar yay da k'yar tace mashi yana so ne, kai ya jinjina mata idonta a d'an runtse tace to miyasa Aunty Fanan bata haihun mashi ba tunda dai yana so, d'an jimm yay yana kallon ta har saida tasha jinin jikinta, saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya sanar da ita tana da problem ne daya hana hakan amman tana cikin shan Magani, wani iri Fatuu taji sai taji dama bata yi Maganar ba, a sanyaye tayi Addu'ar Allah ya bata lafiya ya amsa sai kuma yace "in bata haihun ba zaki bata kyauta cikin naki?" Da sauri ta jinjina mashi kai tace "dana haifi na farko ma zan bata" d'an bud'a ido yay yace mata to yaushe zata biya shin aikuwa da sauri ta kife fuskarta k'ok'arin d'agota ya fara amman ta k'ank'ame shi sosae sai yar dariya yake yi, tsit kake ji zuciyoyin su sai bugawa suke a tare kowanne ya rufe ido, sun dauki lokaci a haka kafin taji ya tambayi mi zata yi a cikin Laundry room daya ga d'azun ta nufi can, ce mashi tay wanka take son yi ba tare data d'ago ba, k'ok'arin d'agota ya fara yi yace "Ok, let me help u take the bath" da sauri ta k'arasa d'agowa ta waro ido tana kallon shi ya d'age mata gira aikuwa da sauri ta fara k'ok'arin sauka daga jikin shi nan take ya gane guduwa take son yi ko kafin ta ankare gaba d'aya ya mik'e tare da ita ya sa6ata a kan kafad'ar shi ya nufi Laundry d'in da ita sai faman wuwwuntsila k'afafu take tana fad'in don Allah ya bari zata yi da kanta shi abunma dariya yake bashi yana zuwa da k'afa ya tura kopar ta bud'e ya shige da ita..............(Wayyo! An yi magani na ina niyyar sa kai don d'aukko rahoto aka bugo man k'opa a goshi, maganina kenan mai son ganin sirrin ma'aurata) ....In zauna a bakin gado in jira su su fito, amman dai goshina ya bugu dama k'opar bata wasa bace.........Ina zaunen Fanan ta fad'o man arai, ko awane hali take baiwar Allah. *ASM 074* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ........... After some minutes sai gashi ya fito da ita yayi mata irin d'aukar jarirai gaba d'aya ta duk'unk'une a cikin bathrobe,gado ya nufa da ita ya d'aurata aikuwa kaman tana jira da sauri ta jawo duvet ta lullube, zama yay a bakin gadon idon shi a kanta fuskar shi d'auke da k'ayataccen murmushi tunawa da yadda akai wankan, shi ganin hakan yake bak'on abu don koda Fanan tana Amarya bata yi mashi haka ba saidae kuma sosae yadda take nuna kunyar ke burge shi, jin shiru bata ji yayi Magana ba yasa tayi tunanin ko da ya ajeta tafiya yayi, a hankali ta sa hannu ta d'an janye bargon da nufin ta d'an lek'o taga ko tafiyar yay, karaf suka had'a ido aikuwa da sauri ta ja bargon ta maida Fuskar, Murmushi kawae yake saki can taji ya kira ta "Baby" runtse ido tayi tana dariya ta cikin bargon, dama tunda yana mata wankan taji ya fara kiran ta da haka, ji tay ya k'ara kiranta still idanunta a runtse suke ta amsa mashi, taji yace yanzu shi bazata taya shi yay wankan ba, dama tun a toilet d'in yaso suyi tare tak'i yarda harda yi mashi magiya kan hakan, ya lura sosae take jin kunya don da k'yar yayi mata wankan hakan yasa shi k'yaleta, k'ara yi mata magana yayi ta cikin lullubar ta girgiza mashi kai, sigh yay yace mata Ok shi ya saba sai an taimaka mashi yake yin wanka bari yaje wurin Fanan in tayi mashi sai ya dawo, wani abu taji a ranta jin motsin mik'ewar shi yasa ta raya da gaske yake kenan aikuwa da sauri ta d'ago dama yana tsaye bai tafi ba, inda yake tazo still tana kudundunan kawai sai ji yay ta kamo mashi riga, gaba d'aya ta cure a guri guda shi yadda tayi ma sai ya bashi dariya har jerarrun fararen hak'oran shi suka d'an bayyana, "I will be back ai da an gama wankan" taji ya fad'a, da sauri ta girgiza mashi kai, d'an bud'a ido yay yace "kar in je?" Kai ta d'aga mashi, "Ok zaki taimaka man in yi kenan?" jimm ta d'an yi kafin a shagwabe tace "n...ni wllh Kunya nike ji" still dariyar yake dama wasa yake mata kawai komai nata nishad'i yake bashi ne, komawa yay ya zauna ya kai hannu ya janye duvet d'in Sumarta ta bayyana don ta kife fuskar a jikin mattress, bin ta yay da kallo cike da k'auna yana jin kaman don ita zuciyar shi ke beating, kiran ta yay ta amsa ba tare da ta d'ago ba yace tunda tana jin kunya zai k'yaleta yaje yayi amman har sai yaushe zata daina jin kunyar ta fara taimaka mashi wurin yin wanka, d'an jimm tay sai murmushi take zuciyarta ce ta tuno mata da zancen zuwa wurin Fanan da yayi kan tayi mashi wanka bata san lokacin data furta mashi gobe ba, jinjina kai yay yace promise ta d'aga mashi nata kan, ce mata yay to ta tashi ya taimaka mata ta shirya, girgiza mashi kai tayi murya can k'asa tace yaje yayi wankan zata shirya, hannu ya kai ya shafi sumar ta ya furta "Ok My Baby" daga haka ya mik'e, ta ji lokacin da ya tashi saida ta d'an bashi lokaci sannan ta d'ago ganin bata gan shi ba yasa ta tashi zaune ta juya hanyar laundry ta d'aga kai daidai zai tura kopar kawai sai gani tay ya d'ago mata hannu alamar yasan tana kallon shi, dariya ta saki ta maido kan ta k'asa, tana jin k'arar rufe kopar shi cike da Farinciki ta runtse idanunta tana d'an k'ank'ame hannunta, wani irin dad'i take ji tamkar ta saki ihu haka take ji sai d'an rawa rawa take da jikinta, idanunta a runtse ta shiga tariyo yadda akai wankan, a laundry ya cire mata rigar jikinta da k'yar lokacin da ya zo kan bra d'inta k'ank'ame jikinta tay idanunta a rufe ta hau yi mashi magiya kan basai an cire su ba ayi wankan da su, ganin bazata bari ya cire su ta dad'i ba yasa shi had'e lips d'in su ya fara kissing nata deeply nan take jikinta ya saki a haka ya cire bra d'in, lokacin daya raba mouth d'in nasu ai ko ido bata iya bud'ewa nan ya cire sauran undies d'in hankali kwance sai sakin murmushi yake, saida ya cire mata komai sannan ya sa6eta yay cikin toilet d'in da ita, cigaba da imagination na abunda ya faru bayan sun shiga cikin toilet d'in tay har zuwa fara yin wankan......., da sauri ta bud'e idanunta ta dawo daga tunanin da take yi jin kaman a lokacin hakan ke faruwa, k'ayataccen murmushi ta shiga saki tana haka Mino ta fad'o mata a rai, ita sham ta manta da wata Mino ta raya a ranta har saida tay yar dariya, tunanin ko lafiya bata zo ba ta shiga yi zuciyarta ta bata k'ilan zata zo sai kuma tay tunanin ai bata kaiwa haka bata zo ba, tun tana a part d'in Hajiya tara saura tayi yanzu kuma tasan karfe goma bata rasa wucewa, to ko dai bata lafiya amman kuma fa d'azun suka rabu, wata zuciyar ta ayyana mata to ai yanzu yanzu sai Allah ko, yin wannan tunanin yasa ta mik'e tasa hannu ta ruk'e gaban bathrobe d'in, gaban dressing mirror ta nufa ta d'aukko wayarta ta dawo bakin gado ta zauna, Kawu Amadu tayi tunanin kira tasan yanzu yana shago, bayan ta fara ringing yay picking, gaida shi tay ya amsa tace mashi dama so take ta tambayi ko lafiya Mino bata zo ba, cikin d'an fad'a fad'a yace mata to ba mijinta ya dawo ba zuwa kwanan mi zata yi kuma, d'an jimm Fatuu tay a ranta tana mamakin ashe sun san ya dawo, kaman yasan tunanin da take taji yace d'azun yana shago yaga zuwan su Tk ya d'aukko su har tsayawa yay suka gaisa, amsa mashi tayi da to tay mashi saida safe, saman bedside ta d'aura wayar tay shiru, zuciyar ta ce ta raya mata to bazata tashi ta shiryan ba sai ya fito kuma yaga bata shirya ba tace mashi zata shirya da kanta, mik'ewa tay ta nufi gaban mirror cikin fargabar kar ya fito ta fara yin shafa, bayan ta gama mulke jikinta da mai ta d'aukko wata yar sauran Humra da ta rage mata ta fara shafawa cike da takaicin sauran da Farha ta fasa mata tana ta so ma tayi ma Aunty Mareeya Magana kan tana son wasu don Hajiya tace tayi magana a fad'i kud'in, bayan ta gama shafe shafen wardrobe ta nufa, bayan ta bud'e wurin kayan bacci ta kai hannu har zata d'aukko wasu zuciyarta ta raya mata ta sa cikin wanda Aunty Mareeya ta bata ko ajiyar su zatai tayi, can k'asa ta kai hannu ta jawo su, tunanin wadda zata saka ta fara zuciyarta ta sake bata ta saka pink d'in, d'an jimm tay tana kallon rigar a ranta ta raya anya Ya kamata ta saka karfa yayi mata kallon yar iska, zuciyarta ta sake raya mata taya zai mata wannan kallon tunda dai shima yasan rigar bacci ce kuma Aunty Fanan bata rasa saka irin su kuma su Aunty Mareeyar ba sun ce ta cire kunya ba, da wannan tunanin ta d'auki rigar ta nufi bakin gado, gaban ta sai fad'uwa yake don kar ya fito ya ganta, hannunta sai d'an rawa yake ta fara saka rigar bayan ta gama gaban Mirror ta nufa, koda taga kanta ba shiri ta kai hannu ta rufe bakinta alamar Al'ajabin ganin yadda rigar tayi mata don ba abunda ba'a gani na jikinta gashi ta bi jikin ta lafe da kad'an ta wuce mazaunanta don da zata duk'a ma sai an gan su, amman fa tayi mata kyau Over yadda daga wurin k'ugunta ya bud'e, d'an juyi tay tana murmushi ganinta take kaman ba yar Nigeria ba, ranta ne ya bata ta kwance gashinta ta gyara, gaba d'aya ta shagala da alama ma k'ilan ta manta da Maganar fitowar Haisam d'in, gaba d'aya gashin yayi mata rumfa ya saukko har kusan tsakiyar bayanta tasa Comb tana sharcewa, tana haka taji k'arar bud'e k'opa da sauri ta juya ta kai idonta kan Haisam da ke fitowa daga cikin Laundry, rud'ewa tay gaba d'aya da sauri ta nufi wurin wardrobe da nufin ta d'aukko abu ta rufe jikinta kafin ta k'arasa ta tuno duvet d'in dake akan gado aikuwa da gudu ta juyo ta nufi gadon tana zuwa ta haye taja Duvet d'in ta lullu6e, shigowa yay ciki yana yar dariyar ganin yadda ta dabarbarce k'ugun shi d'aure da farin towel ga wani short rataye a wuyan shi, gaban dressing mirror ya tsaya yana goge lemar wurin kan shi da sauran jikin, juyowa yay ya nufi hanyar k'opar fita idanun shi akan Fatuu data duk'unk'une guri guda, fita yay ba tare da ya kulle kopar ba, jin k'arar bud'e kopar yasa ta d'an bud'e fuskar ta lek'o, bai dad'e ba sai gashi ya dawo da sauri ta maida kan ta rufe, Wani babban trolley ya shigo dashi yana ja dama yana ajiye a cikin Corridor d'azun da ya baro part d'in Hajiya zaije sallar Magrib yasa Tk ya kawo shi, bakin wardrobe ya kai shi bayan ya bud'e wardrobe d'in ya fara fiddo kayan ciki yana jerawa ciki, bayan ya gama ya fiddo wasu mayuka da turarurruka ya kai su kan dressing mirror, cikin mayukan ya bud'e wani ya fara shafawa, a hankali Fatuu ke bud'e duvet d'in tana d'an lek'en shi, da taga kaman zai juyo sai tay sauri ta maida kan, bayan ya gama turare ya fara fesawa ya d'aukko roll on ya shafa a armpit, wani mai ya matso a tafin hannun shi ya kai shi jikin kwantacciyar sumar chest d'in shi ya shafe nan da nan ta k'ara kwanciya luff duk abun nan Fatuu na kallon shi, bayan ya gama data chest d'in ta saman kan itama ya matso man ya fara shafe ta da shi saida ya shafa kala biyu sannan ya d'auki comb yana sharce ta bayan ya gama Hair spray ya d'aukko ya hau feshe ta da ita, sakin baki Fatuu tay tana kallon ikon Allah ko ita batai shafe shafen da yake ba, bayan duk ya gama ya matsa man tafin hannu ya murza sannan ya juya ya nufi wardrobe ta zuba ma bayan shi ido gaba d'aya a murde yake, rigar bacci kimono ya fiddo ruwan Madara itama sabuwa ce dal tana ganin zai juyo ta maida kan, a gefen gadon ya d'aura rigar yana k'ok'arin kwance towel d'in ta lek'o karaf suka had'a ido a sukwane ta koma ya d'an girgiza kai yana murmushi, bayan ya gama saka rigar ya d'aure, d'aukar towels d'in yay ya had'a da bathrobe d'inta data cire ya nufi hanyar laundry, bada Jimawa ba taji k'arar fitowar shi, side d'in da take ya zagayo ya zauna a bakin gadon idon shi akanta, kiran sunanta da ya fara kiranta dashi wato Baby yayi tay shiru saida ya k'ara kiran sannan ta amsa mashi, hannu ya kai zai janye duvet d'in ta k'ank'ame shi, Dariyar naki wasa ne yay ja d'aya yay mashi ya janyo shi, sosae ta k'ank'ame jikinta idanunta a runtse tana kallon gefe, hannu ya kai ya kamo hannunta guda ya d'ago da ita still idanunta a rufe suke, zuba mata ido yay yana bin jikinta da komai yake a bayyane da kallo kafin ya tsaida idon shi akan boobs d'inta dat look firm and pointed, kiran sunan ta yay da k'yar ta amsa yace ta bud'e ido ta kalle shi kaman bazata bud'en ba sai kuma ta dan bud'a su d'an kad'an har saida ta bashi dariya, d'age mata gira yay yace "didn't u wear it for me to see?" d'an jinjina mashi kai tay yace "then why are u hiding it from me?" yamutsa fuska tay da ido tay mashi nuni da fitila alamar haske, still yar dariya yake ganin da tsiya ta maida kanta kaman yar makauniya, sakin hannunta yay ya mik'e da sauri ta koma ta kwanta taja duvet d'in, wurin Switch ya nufa ya latsa hasken fitilun d'akin suka d'auke, dawowa yay side d'in da take kwance ya kashe lamp d'in wurin kafin ya juya ya zagaya d'ayan side d'in, bai kashe lamp d'in wurin ba ya barta a kunne amman ya rage haskenta ta yadda ta d'an haska d'akin, tana jin ya hawo saman gadon gabanta ya d'an fad'i ta runtse idonta, kwanciya yay ya d'aura kan shi saman pillow idon shi a kanta yana kallonta Fuskar shi d'auke da Murmushi, tsit kake ji ba mai motsi a cikin su saida aka d'an d'auki lokaci sannan ya matsa tsakiyar gadon, hannu ya kai ya janye duvet d'in kafin yay pulling d'inta ya had'e ta da jikinshi ta yadda Fuskarta na a saitin wuyan shi, sosae gaban Fatuu ya shiga fad'uwa sai kace wannan ne karo na farko da hakan zai kasance a tsakanin su, duk'o da Fuskar shi yay ta had'e da tata breathing d'in su ya shiga had'uwa, sun d'an d'auki lokaci a haka sai shak'ar daddad'an k'amshin juna suke can taji muryar shi k'asa k'asa yace "Baby, are u ready to make ur husband happy" k'ara runtse idanunta tayi sosae jin saukar hucin Maganar akan Fuskarta ga wani irin k'amshi da bakin nashi ke saki na Mouth freshener daya fesa acikin Laundry, da k'yar ta jinjina mashi kai, foreplay ya fara yi mata cike da salon gwanancewa nan take Fatuu ta fara losing mind dinta idanunta a runtse gam gasping heavily for breath sai d'an jan yar ajiyar zuciya, gaba d'aya jikinta ya saki sosae take savouring every bit of abunda yake mata, da kan shi ya fara nuna mata abunda yake son tayi mashi da k'yar ta fara maida mashi martanin ganin yana nuna mata yana enjoying sosae yasa ta d'an k'ara k'aimi nan take ya fara rasa control har ta kai ya zame hannuwan rigar jikinta ya saukko da ita wurin k'ugunta, a wannan lokaci gaba d'aya Fatuu d'imaucewa tay cikin fitar hayyaci take maida mashi martani hakan yasa shi rikicewa suka kacame ma juna and he got her all wet, sun d'auki tsawon lokaci suna faranta ma juna cike da tsantsar k'auna, daga baya ya fara kokarin getting in to her bayan ya karanto Addu'ar yin hakan, runtse idanu Fatuu tay sosae jikinta ya hau kerma ta fara jan numfashi duk da isn't the First time sosae take jin zafi shi kanshi Haisam d'in saida yayi Mamaki a hakan ma don akwae wetness sosae, gaba d'aya Fatuu gigicewa tay tun tana breathing rapidly da sakin nannauyar ajiyar zuciya har ta koma kiran sunan shi cikin fitar hayyaci ita kanta bata san mi zata ce mashi ba gaba d'aya Al'amarin yana nema yafi k'arfin kanta she's feeling like her heart is about to burst with joy k'arshe ma sai ta fashe da kuka, shima dae uban gayyar idon shi a runtse yake gam breathing heavily, he completely lost his mind har ta kai ya fara sakin layi........., Lokacin da suka samu natsuwa kife face d'in shi yay a saman tata ba tare daya raba jikinsu ba both of them were breathing rapidly, jikin Fatuu sai kerma yake don ba k'aramar jigatuwa tayi ba, cikin wata irin murya da bata san shi da ita ba taji ya fara fad'in "Thank u...thank u so much wife, thank u for coming in to my life Zarah.....I'm very proud of u, You have been a blessing...." Sai faman nishi yake, ba sosae take comprehending nashi ba idanunta a runtse gam, ji tay abu mai d'umi na d'iga akan Fuskar ta kaman ruwa, tunanin miye ta shiga yi da k'yar ta bud'e idanunta da sukai mata nauyi don ba K'aramin kuka tasha ba, lokacin ta fahimci kaman k'walla ne ta d'ago hannunta da ba k'wari ta sak'a shi tsakanin Fuskokin su ta ta6a fuskar Haisam nan take ta tabbatar da k'wallan shi ne duk da halin da take ciki saida ta d'an rud'e don abu ne da bata ta6a gani ba, murya a disashe ta fara ce mashi "Ya Haisam pls stop crying...." Shiru bata ji yace komai ba hakan yasa ta cigaba da yin kukan itama, d'ago Fuskar shi yay can k'asan mak'oshi ya furta mata ya bari, ya fara k'ok'arin raba jikin su har saida Fatuu ta d'an gantsare ya mirgina gefe, hannu ya kai ya matso da ita they were both nicked yay wrapping nata a jikin shi ta yadda ha6ar shi ke akan sumarta da ta gama fita hayyacin ta itama, shiru kake ji kowa da abunda yake rayawa a cikin mind d'in shi har lokacin da d'an k'arfi suke breathing, Haisam sai sakin k'ayataccen murmushi yake shi kad'ai yasan irin nishad'in da yake ciki, Zarah ta kai shi wata duniya da bai ta6a zuwa ba sai yau, mutsu mutsu yaji ta fara yi ya d'ago kanshi ya kai bakin shi saitin kunnanta ya tambayi miye ko tana son wani abu ne cike da tsantsar k'auna ya furta Maganar, juyo da Fuskar ta tayi suka had'a ido da sauri ta maida kan k'asa k'asa tace mashi fitsari take ji, Ok ya furta da sauri ya tashi da yake akwae d'an haske bai sha wahalar gano rigar shi ba, bayan ya saka ya saukko daga saman gadon ta bangaren da take har lokacin tana kwance kunyar tashi take, hannu ya kai zai d'agota cike da shagwa6a tace mashi bafa kaya a jikinta, murmushi kawai yay ba tare daya ce komae ba ya d'aukko ta ya nufi hanyar laundry da ita duk ta k'ank'ame shi, sun d'an d'auki lokaci kafin ya fito da ita jikinta d'aure da towel kanta ma an yafa wani short ta rufe fuskarta dashi, a bakin gadon ya ajeta ganin tana yar kerma ya juya yaje ya rage Ac tare da kunne d'ayar lamp d'in d'akin ya k'ara haske, dressing mirror ya nufa ya d'aukko man da yake amfani da shi ya dawo, a gefenta ya zauna ya kai hannu ya curo towel d'in saman kanta ya fara goge mata jikinta duk da ma ba wata lema Saboda bayan an yi wankan sun tsaya a Laundry ya d'an mata drying gashinta da hand dryer, gaba d'aya ta kasa had'a ido dashi saidae wani irin dad'i take ji a cikin ranta sosae take ta mamaki, who thought hakan zata kasance tsakanin ta da ya Haisam gaba d'aya ta fidda ran samun shi sai gashi cikin iko na ubangiji bada jimawa ba ta mallake shi sun zama abu d'aya ita da shi Allah mai yadda yaso a lokacin da ya so, ana ta ce mata tayi hak'uri tayi hak'uri zata ci riba sai gashi har taci ribar ba tare da an d'auki dogon lokaci ba, sai faman sakin murmushi take tana juyar da fuska bata san duk yana ganin ta ba shi kan shi murmushin yake, bayan ya gama da kan shi ya shiga shafa mata mai a jiki, mik'ewa yay ya nufi dressing mirror don ya maida mai ta juyo tana kallon bayan shi abubuwa na dawo mata da suka faru lately, bayan ya aje wardrobe ya nufa ya bud'e a wurin kayan ta ya fiddo wata doguwar riga tare da gyalenta ya dawo ta kauda idon ta gefe, bayan ya koma ya zauna yana k'ok'arin zura mata ta d'an kalle shi tace ya bari ta saka, yana ta kallonta tasa ta d'aure kallabin bayan ta gama ta maida kanta gefe, hannu ya kai yay tapping shoulder d'inta ta juyo ta kalle shi idanun ta adan lumshe d'age mata gira yay yace "bacci ko" kai ta d'aga mashi ya matsa ya rungumota jikinshi ta lumshe ido, shima nashi a d'an lumshen suke fuskar shi d'auke da d'an murmushi, Slowly taji ya fara magana in whispering "Baby na wahalar dake ko?" Kai ta d'an girgiza mashi, still da murmushi akan fuskar shi yasan ta fad'a ne kawae yace "am so sorry it was never my intention, I just wanted to make u forget about all the pain I caused you" shiru tayi sai kuma cikin disasshiyar murya yaji tace ai ba laifin shi bane yana murmushi yace amman ai dalilin shi ne, shiru suka d'an yi can ya tambayeta to yayi nasarar yin hakan nan ma kai ta d'aga mashi kafin tace ai tun d'azu ma daya bayyana mata yana sonta ta manta da komai, daga jin yadda tayi Maganar bacci ya fara cin k'arfinta, jin saukar numfashinta a hankali yasa shi kiran sunanta shiru bata amsa ba, d'ago Fuskarta yay yaga tayi bacci, bin Face d'in yayi da kallo, tunda yake bai ta6a ganin mutumin da komai nashi ke burge shi ba irin ta, tun farkon sanin shi da ita abubuwa da yawa a tattare da ita ke burge shi, kai bakin shi yay ya manna mata kiss akan lips d'in ta ya Furta "I love u so much Zaraah" yana rufe baki kawai sai gani yay ta d'an bud'e idanun ta cikin muryar bacci ta furta "I... love you...so much Ya Handsome" daga haka idanun suka rufe bakinta a d'an bude, faffad'an murmushi yay da alama acikin baccin taji Maganar da yayi sama sama shine itama ta maida mashi ta kuma kira shi da Handsome, Kwantar da ita yayi yaja duvet ya rufe mata jiki, saida ya yi pecking gefen fuskar ta sannan ya mik'e ya nufi toilet, bayan ya fito wardrobe ya nufa ya fiddo wasu kayan baccin riga da wando masu taushi ya saka, bayan ya gama ya nufi side d'in da take ya kashe fitilar daya kunna sannan ya nufo d'ayan bangaren gadon, bayan ya hau matsawa yay kusa da ita ya janyo ta yay cuddling nata sosae kaunarta na ratsa ko ina na jikin shi idanun shi a lumshe ya shiga tariyo abunda ya faru tsakanin su haka yay ta sakin murmushi kaman wani zautacce. Kiran sallar Asuban farko ya farka duk da baccin bai ishe shi ba saidae ya riga ya saba da lokacin yayi yake tashi, bayan yayo Alwala ya fito Wardrobe ya nufa ya d'aukko jallabiya ya canza kayan jikin shi, prayer mat ya d'aukko ya shimfid'a ya kabbara raka'atanil fajr, bayan ya gama mik'ewa yay yaje ya d'aukko Al'qur'ani ya dawo ya shiga karantawa, har saida lokacin salla yayi sannan ya mik'e ya maida Al'qur'anin, kallon Fatuu dake ta shan bacci yay da murmushi yasan dole tayi bacci sosae, saida ya duk'a yay pecking kumatun ta sannan ya tafi. Har ya dawo ko juyawa bata yi ba tana a yadda ya barta, gefen da take ya nufa ya zauna idon shi akanta yana jin kamar kar ya tasheta to amman lokacin ya dace tayi sallar, bayan ya tashe ta da k'yar ta bud'e ido tana kallon shi yace mata ta tashi tayi sallar saita koma ta d'aga mashi kai, sosae taga safiyar tayi saurin yi, saida ya rakata har toilet tayo Alwala sannan suka dawo, a gefen gado yasa ta zauna ya tambayi inda Hijabs d'in ta suke ta fad'i mashi ya nufi wardrobe d'in tana ta kallon shi sosae kulawar da yake nuna mata ke k'ara dulmiyar da ita acikin k'aunar shi, bayan ya kawo mata Hijab d'in tasa ta kabbara sallar ya juya ya fita daga d'akin, har ta gama bai dawo ba ta mik'e ta d'auke abun sallar, gado ta nufa ta haye taja Duvet ta lullube, shiru tay ta fara tunanin ko ina ya tafi da sassafe zuciyar ta ce ta raya mata k'ilan wurin Fanan ya tafi, shiru kawai tay ita kanta bazata iya fad'in mi take ji ba, bata dad'e da kwanciya ba idanunta a rufe taji an bud'e kopar da sauri ta bud'e idon tana ganin shi ta d'an ji wani sanyi a ranta, shigowa yay hannun shi ruk'e da d'an Babban try ya nufi gadon, aje tray d'in yayi a k'asa ya zauna bakin gadon yana kallonta itama ta juyo tana kallon shi, hannu ya mik'a mata yace ta tashi taci Abinci yasan dole tana jin yunwa yanzu, kama hannun tayi ta tashi ya matso da ita gefen shi, cup d'in tea ya d'aukko ya mik'a mata ta amsa ya d'ago da plate mai d'auke da wainar kwai ya aje a tsakiyar su, da kan shi ya 6allo wainar ya kai bakinta ta bud'e ya saka mata ta d'an kur6i tea din, bayan ta cinye na bakin ta ya 6allo wata zai saka mata tace "did u made it for me?" Fuskar shi a sake ya lumshe mata ido, bayan ta cinye ta bakinta daya saka mata ta furta mashi "thanks, I appreciate" d'an bud'a ido yay yana murmushi yace "I appreciate too" da d'an alamun mamaki tace What, shiru kaman bazai ce komai ba ya k'ara bata wainar, ganin tana ta kallon shi ya d'age gira ya furta "Yesternight" da sauri ta d'an juyar da fuskar ta, har mamaki take a cikin ranta yadda shi kwata kwata bai jin kunyar ta sai kace ba itace hakan ke faruwa tsakanin su ba, itama fara bashi tay yace ai ita kad'ai ya had'a mawa shi bai cin Abinci da sassafe ta tura mashi baki a shagwabe tace to ai shima tasan yana jin yunwa ko, bin ta kawae yake da ido gaba d'aya in tana shagwabe melting heart d'in shi take tun ba yanzu ba, dole ya bud'e baki ta rink'a bashi har suka cinye, mik'ewa tay don ta kai kayan Kitchen yace ta bari ya kai ta mak'e mashi kafad'a yay yar dariya, juyawa yay yana kallonta ta nufi hanyar fita tana kaiwa k'opa ta juyo suka had'a ido ta sakar mashi murmushi k'asa k'asa ta furta "I love u" ta fuce da sauri, mik'ewa yay ya nufi Laundry don ya wanko hannuwan shi yana ta sakin k'ayataccen murmushi, lokacin daya fito daidai ta shigo don saida ta wanke kayan, tsayawa tay daga bakin kopar tana kallon shi ya k'araso wurinta ba zato kawae taga yayi mata d'aukar jarirai har saida ta saki yar k'ara don abun yazo mata a bazata, a kan gado ya d'aurata ya dawo ya rufe k'opar, hawa yay saman gadon ya matsa kusa da ita ya jawota jikin shi, bin juna sukai da kallo da d'an murmushi na wani lokaci fuskokin su na a saitin na juna inhaling each others breathe, can ta fara motsa baki kaman tana son cewa wani abu, ya lura yace mata mi take son ce mashi ne, a hankali tace so take ta tambaye shi bai yin mamaki, murmushi yay ya d'age gira yace mamakin mi, tace "wai mune muka zama ma'aurata" da k'yar tayi Maganar yay yar dariya kafin ya d'an girgiza mata kai yace "ai ba abun mamaki bane baby, a rayuwa there is reason for everything, Allah ya k'addaro dama zamu zama married couple shine dalilin had'uwar mu and I blessed it" lumshe ido tay, slowly ya had'e face d'in su ya kai lips d'in shi kan nata he started kissing her deeply, sosae ta bashi had'in kai suka shiga ba juna hot romances a haka bacci yay awon gaba dasu....... Jama'a ina Baiwar Allah Fanan🤔 *ASM 075* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ............Sosae suka sha Bacci Haisam ne ya fara tashi wurin k'arfe goma, toilet ya wuce yayo wanka, bayan ya fito ya shirya cikin k'ananun kaya wanda da gani sababbi ne sai baza k'amshi yake, bayan ya gama shiryawa ya koma bakin gadon yana kallon Fatuu dake ta shan bacci gashinta duk ya tarwatse har ya d'an rufe mata fuska, murmushi yay ya juya ya nufi k'opa ya fita, Fanan kwance akan gado ta lullu6e da bargo tana bacci, she spent almost the whole Yesternight pacing up and down acikin d'akin, gaba d'aya zuciyarta ta hana mata zaman lafiya wani irin zafin rad'ad'i ta rink'a mata, she wept until there were no tears left, haka tay ta kai da kawowa kota kwanta tana son tayi bacci sai tay ta imaginations kan Haisam da Fatuu dole ta tashi, sosae ta jigata baiwar Allah har salla taso tayi amman ta kasa k'arshe a fili ta rink'a d'aga hannu tana rok'on Allah da ya sauk'ak'a mata abunda take ji fuskarta a yamutse, saida akai sallar Asuba bayan ta gama tayi Addu'oi sosae ta koma gado ta kwanta, ta d'an d'auki lokaci kafin cikin sa'a baccin ya d'auketa. Part d'in Hajiya ya zo lokacin da ya shigo ba kowa a parlon ya wuce hanyar corridor, Bedroom d'in Hajiyar ya nufa lokacin da ya shiga tana zaune a bakin gado tana shafa mai jikinta sanye da doguwar riga bata dad'e da fitowa daga wanka ba, bayan ta amsa mashi sallamar da yayi ya nufi inda take, a gefenta ya zauna Fuskar shi cike da annuri ga wani fitinannan k'amshi da yake saki, gaisawa sukai tayi mashi an tashi lpy ya amsa daga baya ta tambayi Fateema yace mata tana bacci, yar hira sukai sama sama kafin ya tashi yace bari ya ga Fanan tace to, A hankali ya tura k'opar d'akin da take ya shiga, a kan gado ya hangota ta duk'unk'une a cikin bargo, saida ya k'arasa gaban gadon yaga Fuskarta a d'an bude idanunta a rufe alamar bacci take, tsaye yay yana kallonta tun daga yanayin fuskar ya fahimci she isn't alright don Fuskar ta yi wani ja, ta cikin baccin k'amshin turaren shi ya fara kai mata, motsi ta fara yi ta fara bud'e idanunta a hankali, bayan ta bud'en bin juna sukai da kallo her eyes were red and swollen yana gani ya fahimci ba K'aramin kuka ta sha ba, yunk'urawa tayi ta tashi zaune ta kasa d'auke idanunta akan shi zuciyarta sai sak'a mata abubuwa da ke k'ara mata rad'ad'i take, wasu k'walla ne masu zafi suka taho mata jin zasu zubo yasa tay saurin sauke idanunta k'asa, gefenta ya matso ya zauna ya kai hannu ya matso da kanta saman kafad'ar shi sai sheshsheka take a hankali, shiru Haisam yay ya d'an rufe ido can ya bud'e ya juya yana kallon saman kanta, gently yace mata miyasa zata sa damuwa haka a ranta sai tayi causing mata wani ciwo, da damuwa akan fuskar shi yay Maganar don ba K'aramin tausayi ta bashi ba, cikin muryar kuka tace ita kanta ba yadda bata yi ba don kar ta damu amman zuciyanta ta takura mata ko bacci bata yi ba sai da Safe nan ta d'an samu ya d'auketa, daga jin yadda take futar da Maganar zaka Fahimci she's in serious grief, shiru yay he wished he could remove all the pain from her heart, a hankali ya kwantar da gefen fuskar shi a saman kanta cikin nuna damuwa yace "Am very sorry Sweetheart am not happy I caused you so much pain" d'an girgiza mashi kai tay suka yi shiru kowa yana kallon wuri guda can yay sigh ya d'ago itama ta d'aga kai tana kallon shi, tambayar ta yay tayi breakfast ta d'an girgiza mashi kai ya furta Ok bari ya kawo mata, yana k'ok'arin tashi ta kama hannun shi a marairaice tace mashi wanka take so tayi ko zata ji dad'in jikinta, mik'a mata hannu yay ta saukko daga saman gadon suka nufi Toilet. Bayan wani lokaci suka fito yana tallafe da ita k'irjinta d'aure da towel, taimaka mata yayi ta shirya cikin doguwar riga da hula ta zauna a bakin gado yace mata yana zuwa ya juya ya nufi k'opa ta bi bayan shi da kallo Zuciyar ta na raya mata abu game da shi da Zarah, k'walla ne suka shiga gangaro mata ta d'age kai sama, yana fita cikin parlor ya had'u da Hajiya ta fito yin Breakfast yay mata Magana kan yana son breakfast zai kai ma Fanan kai kawae ta d'aga mashi ta nufi Dining ya bita, bayan Saude ta zuba mashi ya juya ya koma, Magana Hajiya tay ma Saude kan ta had'a ta kai masu nasu can part d'in su tace to, bayan ta gama Serving nata ta juya Kitchen don ta had'a masu. A hankali Fatuu ta fara motsi kafin ta fara bud'e idanunta, hannu tasa ta janye gashin daya rufe mata fuska har saida ta d'an ji mamaki ganin ba Haisam kaman yadda suka kwanta tare, tunani tay k'ilan yana toilet tay shiru tana kallon wuri guda sai faman zabga murmushi take da gani tana cikin tsananin farinciki, can ta yunk'ura ta tashi Zaune ta jingina da Headboard, memory d'in rayuwar su ya shiga dawo mata sai faman sakin murmushi take, sosae take mamakin yadda komai ya kasance a tsakanin su, ta d'an d'auki lokaci a haka ganin shiru bai fito ba yasa ta fara tunanin ko dai bai cikin toilet d'in ne, saukkowa tayi ta nufi hanyar laundry tana gab da isa k'opar taji anyi knocking kopar Bedroom d'in, juyowa tayi ta nufi kopar ta tsaya a bakin ta, tambayar waye tayi ta jiyo Muryar Saude da sauri ta kai hannu tana tattare gashinta bayan ta d'aure ta kai hannu ta bud'e kopar, da d'an murmushi ta gaidata itama murmushin take mata ta amsa tace "Amaryar mu an tashi lpy, dama Breakfast na kawo ba kowa a parlon to da yake naga shi yalla6ai d'in a can shine nace bari in fad'i maki" still Murmushin take tace mata to kafin tayi mata godiya sukai sallama, bayan ta dawo cikin d'akin a gefen gado ta Zauna tay shiru kaman mai tunanin wani abu, ta dan d'auki lokaci can ta mik'e sukuku da ita ta nufi hanyar laundry, after some minutes ta fito jikinta sanye da bathrobe ta nufo cikin d'akin, shiryawa ta shiga yi bayan ta gama yin shafa ta nufi Wardrobe, saida ta d'an yi ruwan idon kafin ta fiddo wata doguwar rigar shadda kalar butter an yi mata red aiki, bayan ta gama shiryawa gaban mirror ta koma ta fiddo jewellery da suka hau da kayan ta saka, k'ara gyara fuskarta tayi ta goga jan jambaki ta goga maskara a gashin idonta ya k'ara mik'ewa gazar gazar kaman ta saka eyelashes, bata yi ja gira ba sai kawai ta gyara gashin don tana dashi da d'an yawa, ita kanta taga kyaun da tayi tana Fesa turare tana k'are ma kanta kallo da d'an murmushi, bayan ta gama komai komawa tay bakin gado ta zauna bata yi tunanin zuwa tayi breakfast d'in ba don ba wata yunwa take ji ba, Bayan ya kai mata Breakfast d'in da kanshi ya shiga bata a baki sai gashi ba laifi ta d'an ci da yawa kafin ta ce mashi ta k'oshi, kokarin mik'ewa tay tace bari ta fidda kayan ya rigata tashi yace ta zauna tana murmushi ta furta mashi thanks ya d'an lumshe mata ido, har ya kusa k'opa tace don Allah ya tambayi Hajiya in akwae paracetamol ya d'aga mata kai, bai jima ba ya dawo hannun shi ruk'e da glass of water ya nufi wurinta, da kan shi ya 6allo mata Maganin ya bata ta sha bayan ya d'aura glass cup d'in akan bedside drawer da Maganin ya d'aura idon shi akan ta cikin nuna kulawa yace "Your sacrifice means the world to me, it's the most generous thing anyone has ever done for me" daka kalli idanuwan shi zaka tabbatar da abunda yake fad'i, d'an murmushi tayi ta d'aura kan ta a saman shoulder d'in shi slowly ta furta "I can do anything for you my husband" lumshe ido yay fuskar shi d'auke da Murmushi, gyara zaman shi yay ya hau gadon sosae ya kwantar da kanta a saman cinyoyin shi fuskar ta na kallon shi tana mashi murmushi ya fara d'an shafa kumatunta can yaji tace "I love u so much babe, don Allah kar canza man zan iya mutuwa wllh" idanunta raurau tayi Maganar, lumshe mata ido yay ya furta " I will never forget how much you have done for me sweetheart" lumshe ido tay still da murmushi daga yanayin fuskar ta zaka fahimci ta samu sauk'in abunda take ji a cikin zuciyar ta, cigaba da shafa fuskar tata yay can ya d'an d'age kan shi sama ya lumshe ido nan take memory d'in shi da Fatuu ya shiga dawo mashi fuskar shi d'auke da d'an murmushi yayin da Fanan ta fara yin gyangyad'i daga baya bacci ya d'auketa. Tana ta zaune a bakin gadon ji take kaman taje part d'in Hajiyar saidae wata irin kunya take ji, tunanin gyara d'akin tayi ta mik'e, wani sabon Bedsheet taje ta d'aukko a cikin Wardrobe ta dawo ta cire na saman gadon da na pillows d'in ta fara shimfid'a wanda ta d'aukko, bayan ta gama laundry ta nufa ta d'aukko floor wiper tazo ta fara share dakin, data gama ta maida ta d'aukko bucket d'in Mopping ta dawo, tana cikin yin Mopping d'in har ta kusa gamawa taji an turo k'opar Bedroom d'in ta kai idonta da sauri, shine ya shigo suka had'a ido nan take zuciyarta ta shiga raya mata daga wurin Fanan yake, ganin yana mata murmushi yasa ta d'an yi murmushin itama, rufe kopar yay ya nufo inda take tsaye hannunta ruk'e da mop, a gabanta ya tsaya ya kai hannu ya ruk'o mop d'in ta sakar mashi, janye bucket d'in yay gefe ya kai duka hannuwan shi ya matso da ita gaban shi idonta a kanshi, ganin ta d'an yi mashi k'asa yasa shi rankwafawa ya had'e goshin su slowly yace mata waya sata yin wannan aikin yanzu, shiru bata ce mashi komai ba ya d'ago da fuskar shi yana kallon ta ya d'an d'age mata gira, da d'an murmushi tace mashi taga bata yin komai ne kuma d'akin na buk'atar a gyara shi shiyasa, tunda ta fara Maganar ya maida idon shi akan bakin ta daya sha jan jambaki har ta gama, ganin yadda ya kafe ta da ido ba tare daya ce komai ba yasa ta d'an tura mashi baki ya saki murmushi, juyawa yay da ita suka nufi wurin gado, shi ya fara zama sannan ya zaunar da ita kan cinyoyin shi ta yadda fuskokin su suka kusa yin saiti, shiru sukai gazing lovingly into each other's eyes kowa kokarin nuna ma d'an uwanshi yadda yake k'aunar shi suke ta cikin idanun, kasa jurewa Fatuu tay tana murmushi ta kwanta a jikin shi idanunta a d'an lumshe tana shak'ar daddad'an k'amshin da jikin na shi ke saki, hannuwan shi yasa ya rungumeta sosae ha6arshi a saman kanta taji ya furta tayi kyau sosae still Murmushi take ta furta mashi ta gode shima yayi kyau, shiru suka k'ara yi tayi lamo idanunta a rufe she felt safe in his embrace, suna haka taji Muryar shi yana tambayar tayi Breakfast ne ta d'an girgiza mashi kai alamar a'a, d'agota yay gaba d'ayan su idanuwan su sun d'an lumshe yace "miyasa zaki zauna da yunwa ko kina so ulcer ya kama man ke?" yay Maganar tare da d'age mata gira, yar dariya tayi don ta gane abunda take ce mashi ne yace mata da sigar shagwa6a tace to ba shi take jira ba, "Ok, kiyi hak'uri na bar ki da yunwa naje gaida Hajiya da Auntie d'in ki" jinjina mashi kai tayi ya kai bakin shi saitin nata ya manna ma lips dinta kiss, yana d'agowa ta d'an waro ido sai kuma ta saki dariya tambayar ta yay miye tace ya gogi jan bakin ta ganin abun ya saka ta nishad'i yasa shi kai hannu ya matso da kanta ya kad'e lips din nasu giving her a deep kiss, sun d'an d'auki lokaci kafin ya saki kan da k'yar take bud'e ido koda taga yadda bakin nashi yayi da jan bakin sosae ta sa dariya harda k'yak'yatawa sai kallonta yake yana yar dariyar shima sosae take burge shi, can ta kai hannu ta fara goge mashi tana yi tana k'ara sakin dariyar suna cikin haka ya mik'e da ita yay mata d'aukar jarirai har lokacin tana goge mashi bakin ya nufi hanyar k'opa da ita don suje suyi breakfast. Bayan sun gama yace su je ta gaida su Hajiya tace to, Bedroom ta koma ta d'aukko gyale bayan ta fito a corridor ta tsaya tasa takalma sannan ta dawo yana zaune a cikin parlor yana ganin ta ya mik'e yana mata murmushi ya kama hannunta suka tafi, suna zuwa k'arshen hanyar da zasu shigo cikin harabar gidan ta zame hannunta ya juya ya kalleta ta d'an yamutsa mashi Fuska, murmushi kawai yay baice komai ba don ya fahimci dalilin daya sa tayi hakan, lokacin da suka shiga cikin parlon Hajiya na zaune suka nufe ta idonta akan su tana murmushi, Haisam d'in ya nuna mata wuri ganin tayi tsaye ta zauna shima ya zauna a gefenta duk sai taji wani iri, da k'yar ta gaishe da Hajiya don duk ta sha jinin jikinta gani take kaman duk ansan abunda ya faru tsakanin su, bayan d'an wani lokaci ta mik'e tace bari su gaisa da Aunty Fanan Hajiya tace mata to, bata dad'e ba ta dawo idon Haisam a kanta ta koma ta zauna tun kafin tayi Magana Hajiya tace halan bacci take tace mata eh, kallo suka d'an yi daga baya Haisam d'in ya mik'e yace zai je ya dawo Hajiya tayi mashi a dawo lafiya ya nufi hanyar fita idon Fatuu a kan shi sai kuma ta juyo ta kalli Hajiya ganin ta maida idon ta akan Tv yasa ta mik'e sumi sumi ta bi bayan shi, lokacin da ta fita har ya nufi hanyar parking space ta kira shi da d'an d'aga murya ya dakata ya juyo, tana k'arasowa ta tsaya a gaban shi tana murmushi yace ai ya zata bazai ai mashi rakiyan ba, bata ce komai ba ya kai hannu ya kamo hannunta har saida ta d'an waiga bayanta suka nufi parking space, bakin Motar da zai hau suka tsaya ya tambayi ko tana son wani abu ta girgiza mashi kai ya furta Ok, saida yay kissing hannun nata sannan ya saki ya bud'e Motar ya shiga ganin tayi tsaye yace mata ta koma ta d'aga mashi kai alamar to amman bata da niyyar tafiyar, Maganar Hajiya ce ta fad'o mata a rai ta kwanaki data ce in itace abunda ya gani k'arshe to zaita tunaninta a waje har yay ta sakin murmushi kamar zautacce, k'ara ce mata yay koda wani abu dai ta d'aga mashi kai alamar eh yace to miye ko ya fito ne, da sauri ta girgiza mashi kai ta fara matsawa, tsaye tay gaba dashi tana ta faman murmushi, d'age mata gira yay ya d'an k'ank'ance ido yace "What do you want?" tsuke baki tay sai kuma ta runtse ido da hannu tay mashi nuni da kumatun ta, lokaci guda ya gane mi hakan ke nufi yace "Do you want to kiss me?" ba tare data bud'e idon ba ta d'aga mashi kai kawai sai ji tay ya kamo ta ya shigo da ita cikin Motar yana k'ok'arin zaunar da ita akan cinyar shi da sauri ta fara k'ok'arin kwacewa yak'i sakin ta ganin haka yasa a marairaice tace mashi wani fa zai iya ganin su ya d'age mata gira yace to shine mi, k'arshe ba yadda zata yi dole ta zauna idanun shi a lumshe yace tay kissing nashi iya yadda take so a kuma duk inda take so........ Bayan ta koma parlor duk ta bi ta kama kanta Hajiya tace ya tafi ta ce eh, bata dad'e da komawa ba Mino tazo jikinta sanye da Uniform d'in islamiyya taje can part d'in bata isketa ba, tana murmushi ta gaishe da Hajiya itama da fara'a ta amsa tace mata an dawo tace mata eh Fatuu ta nuna mata gefen ta alamar tazo ta zauna, bayan ta zauna Hajiya tace jiya bata zo tayin kwana ba maigida ya dawo, ita dai Minon murmushi kawae take yi cike da wasa ta sake ce mata ai da tazo ta taya ta ita duk suka d'an yi dariya, bata dad'e ba sosae ta mik'e zata tafi, bayan ta masu sallama Fatuu tace ta gaida mata da gwaggo, daga baya itama Fatun mik'ewa tay tace bari taje ta taya Aunty Saude aiki a Kitchen, Lokacin da akai Azahar sun gama komai ta wuce d'akin Aunty Sauden don tayi salla, bayan ta gama sallar ne ta fito ta nufi d'akin da Fanan take, da sallama ta tura kopar ta shiga, a saman abun salla ta hangota daga gaban gado tana jingine dashi ta juyo tana amsa mata sallamar da d'an murmushi, sosae gaban Fatuu ya fad'i da ta k'arasa wurinta taga idanunta a haka ma wai don ta samu bacci sun rage, gabanta ne ya shiga fad'uwa Fanan d'in ta nuna mata gefen gado tace ta zauna mana tayi tsaye, bayan ta zauna a sanyaye ta gaida ita ta amsa kafin tace taso taje ai can part d'in nata su gaisa bata tashi da wuri bane, cikin kama kai Fatuu ta d'an yi murmushin yak'e tace mata ai tun d'azu itama tazo ta shigo ta gaida ita ta iske tana bacci, sama sama suke d'an yin hira yawanci ma Fanan d'in ce ke kawo zance anan har take tambayar ta gwaggo tace zata shiga su gaisa in sha Allah, suna haka Haisam ya shigo duk suka yi mashi sannu da zuwa fuskar shi a sake ya amsa ya nufi mirror ya d'aukko stool ya dawo daga gefen gadon ya zauna, gaba d'aya Fatuu ta takura Saboda yawon kallon da yake mata har fakar idon Fanan tay ta d'an mashi alamar ya daina sai kawai taga yayi d'an murmushi, gaba d'aya su biyu ke yin hiran sama sama sai ta kama sannan Fatuu ta saka masu baki, daga baya Saude tazo tayi masu Maganar an shirya table bayan ta fita Fatuu ce ta fara mik'ewa dama duk a takure take cikin wasa Haisam d'in yace mata acici bazata jira su tafi tare ba sai kuma kunya ta kamata tana niyyar komawa ta zauna ya mik'e yana yar dariya Fanan ma yar dariyar tay ganin bata tashi ba yayi mata magana ta d'an yamutsa fuska tace gaba d'aya bata da appetite ne yace ta dai daure kar ta zauna da yunwa, mik'a mashi hannu tayi alamar ya taimaka mata ya kama hannun ya mik'ar da ita, bayan ta mik'e ta fara k'ok'arin cire Hijab din jikinta Haisam ya kai idon shi kan Fatuu dake kallon su suna had'a ido da sauri ta maida kan ta gefe, moving yay zuwa inda take yace su je ba tare data kalle shi ba ta wuce yana biye da ita Fanan kuma na gefen shi. Bayan sun fara cin Abincin Haisam na lura da Fanan bata wani ci kaman dai jiya can ya d'ebo ya kai spoon d'in bakinta da yake tana a gefen shi, kallon shi tay da murmushi yay mata alamun ta ci ta bud'e bakin ya bata, ci gaba yay da bata tunda Fatuu taga haka ta daina kallon su, sai gashi taci sosae, gaba d'aya Fatuu jin ta take wani iri hakan yasa taji Abincin ma ya fitar mata a rai hakanan take d'an tsakura gudun kada ta tashi ai tunanin wani abu, can bayan an k'ara lokaci ta mik'e duk suka kalleta da k'yar ta k'ak'alo murmushi tace ta k'oshi, Fanan ce tace mata amman ai kaman fa bata ci da yawa ba still da murmushin tace ai bata dad'e da yin Breakfast ba tazo ta d'aga mata kai alamar gamsuwa, idon Haisam a kanta ita dai Hajiya d'an murmushi kawae take a ranta ta raya aiki ya ga Haisam don tasan dama dole Fateema bata rasa jin wani abu a ranta a kan Abincin da yake ba Fanan d'in a baki, d'akin Saude ta wuce don acan ta aje gyalen ta, lokacin da ta shiga ba kowa a d'akin don Sauden na can baya ta nufi katifa ta Zauna tay shiru tana kallon wuri guda kaman mai tunanin wani abu, daga baya ma sai ta kwanta kawae, Bayan su Fanan sun gama cin Abincin Parlor suka wuce Suna kallo saidae gaba d'aya hankalin Haisam na a wurin Fatuu tunani abunda take a cikin d'aki yake ta yi, ana fara kiran sallar la'asar ya mik'e yace zai je Masallaci, bayan ya fito tsayawa yay cikin harabar yana kiran Fatuu a waya saida ya kira har sau biyu amman bata yi picking ba ya juya ya nufi part d'in su a ranshi yana wani tunani, bayan ya shiga Bedroom ne yaga wayar ajiye akan bedside ashe bada ita ta tafi ba ya wuce toilet don yin Alwala, bayan fitar shi Hajiya ma ta tashi itama Fanan d'in ta mik'e suka tafi suma su yi sallar, har Hajiya zata shiga d'aki tayi tunanin Fatuu tace ma Fanan ta duba Fateema a d'akin Saude watak'il bacci take tace to, bayan ta shiga taje ta tasheta tace lokacin salla yayi Fatun tay mata godiya ta mik'e ita kuma ta juyo ta fito, d'aukar gyalenta tayi ta fito daga cikin d'akin lokacin data shigo parlon ba kowa ta nufi hanyar fita ta wuce part d'in su, tana shiga Bedroom ta cire gyalenta a gefen gado ta wuce laundry, bayan ta fito ta yo Alwala ta shimfid'a prayer mat ta kabbara salla. Tun bayan data gama tayi zaune a wurin tay shiru k'arshe ma sai ta jingina da gado ta kwantar da kanta, Fauzy ce ta fad'o mata a rai ta raya yakamata ta kira ta sanar da ita Ya Haisam ya dawo bata samu ta hau online bane shiyasa data fad'a mata tuni, tana ta zaune can taji an turo k'opar ta kai idon ta, shine ya shigo suka had'a ido bayan ya rufe kopar ya nufota ta d'ago tana kallon shi, tayi tunanin saman gadon zai zauna amman ga mamakinta sai gani tayi ya zauna k'asa a gaban ta ya d'age kafa d'aya d'ayar kuma ya mik'ar da ita tana dai ta kallon shi fuskar ta a d'an sake, kallon ta yake shima saidai yanayin kallon kaman na mai nazarinta ganin haka yasa ta sunkuyar da Fuskar ta ta koma kallon k'asa, tana haka taji Muryar shi calmly yana fad'in "I want to try my possible best to be equitable to you, but I understand it would not be as easy as I think" jin abunda yace yasa a hankali ta d'ago ta kalle shi yanayin damuwa ya bayyana akan fuskar shi, bin shi tay da ido ta fahimci dalilin da ya sa yayi Maganar k'ilan yayi tunanin ko tayi fushi ne Saboda abubuwan da suka faru tsakanin shi da Fanan d'azun, d'an murmushi yaga tayi ta kai hannu ta ta6a gefen fuskar shi da turanci itama tace mashi kar ya damu zata taimaka mashi ya cimma hakan a tsakanin su, d'age gira yay ya tambayi da gaske ta d'aga mashi kai yace kenan bata yi fushi ba, tana yar dariya ta girgiza mashi kai tace fushin mi zatayi ya d'an kashe mata ido guda ya furta kishi, sosae ya bata dariya yadda taga yayi ta fad'a jikin shi a shagwa6e tace to yau ta fara gani ya ba Aunty Fanan Abinci a baki ai tasan yana bata dama, d'age mata gira yay ya tambayi a yaushe tasan hakan tace "a can baya mana lokacin ranar nazo nan gidan har na kawo mata wainar fulawa daga baya da aka ce an shirya table ta matsa man sai munje an ci Abincin da ni, koda naje ma kasa wani ci nayi na taso na dawo parlor, dama ranar da k'yar nazo sai da gwaggo ta ce ya kamata in zo ita ta damu dani tana ta zuwa" a shagwa6e take Maganar gaba d'aya ya zuba ma bakinta ido har ta gama sannan ya k'ara d'age mata gira yace "lokacin kina ciwon so na?" wani kallo tay mashi ta d'an tura baki ya ce ta bashi amsa kawae sai tasa hijab ta rufe fuskarta tana dariya, k'ok'arin bud'e Fuskar ya fara ta bi ta k'ank'ame ta, wani abu ya fara mata yana cigaba da k'ok'arin bud'e Fuskar sai ta ji yanayin yadda take jin abunda yake matan yayi mata kaman cakulkulo ai kuwa cikin d'an k'araji ta fara fad'in "Ya Haisam!....don Allah ka bari.... Wayyo Allah zan bud'e wllh, ka bari don Allah......" ba Arzik'i ta bud'e Fuskar tana haki da dariya, shima dariyar abunda ta rink'a yi yake, ce mata yay to ta fad'i mashi still tana a jikin shi saidai ta zame ta kwanta sosae, d'aga mashi gira tay irin yadda yake mata yace ta bud'e baki a shagwa6e tace "Ehhhhh" d'an bud'a mata ido yay yace "Eh What?" tura baki tay "kai Ya Haisam ba ka gane ba" d'an girgiza mata kai yay alamar bai gane ba ta tura baki, kawai taga ya d'ago hannu aikuwa da sauri ta tare hannun tana dariya tace "Ehh lokacin ina ciwon son ka" sosae yadda tayi Maganar ya bashi dariya sukai tayi a tare saidae ita tafi shi yi, bayan ya tsagaita yin dariyar yace "ni yaushe za'a canza man suna ne" d'age mashi gira tay "kana so ne?" da murmushi ya d'aga mata kai, tace "to wane suna kake so?" wani kallo yay mata mai kaman harara yace shi zai fad'i mata shi da ya canza mata ita ta fad'i mashi, d'an jimm tay ta kanne ido guda alamar tunani can tace "To Sweetheart?" shiru ya d'an yi sai kuma ya girgiza mata kai yace bai son shi ai dama tana ce mashi haka tace to ai da hakanan take ce mashi ko yanzu kuma da dalili yace to ai shiyasa yake son a canza, jimm ta k'ara yi tace to tunda shi yana da jinin larabawa bari ta rink'a ce mashi Habiby waro ido yay jin irin sunan da Mom d'in shi ke fad'a mashi ne ya girgiza mata kai yace a canza wani tace to Honey, wannan karon yar dariya yay yace to ai duk kusan d'aya ne da Sweetheart d'in, d'an yamutsa fuska tay ta d'an Jujjuya jiki cike da shagwaba tace to ita ta rud'e ta rasa wanda zata za6o yay shiru dae yana bin ta da ido da murmushi can tace "Yauwa to Hubby" Dariya yay kawai bata san shi yadda take mashi Maganar bane yake burgeshi shiyasa yake ta jan abun, tambayar shi tay yayi ya d'aga mata kai harda d'an d'aga hannuwa ta jinjina su alamar jin dad'i, shiru sukai suna ta kallon juna kowanne face d'in shi d'auke da Murmushi can yace mata mi ta zauna yi k'asa ne bata je Parlor ba ko ta hau gado tace mashi Sallah tayi da ta gama Addu'a sai kuma tayi zaune, tambayar ta yay Addu'ar mi tayi tace da yawa, hannu ya kai ya kama hannunta ya d'agata ta zauna sosae suna kallon juna yace to ta fad'a mashi Addu'o'in da ta yi, "Nayi ma mamana na rok'i Allah ya jaddada rahama a gare ta da sauran wanda suka rasu...." jinjina kai yay Slowly ya furta "Ameen" cigaba tayi "Sai Baffana da gwaggo harda Hajiya na rok'i Allah ya k'ara masu lafiya da nisan kwana mai Albarka" lumshe ido yay, ta sake cewa "Aunty Fanan ma nayi mata Allah ya bata lafiya ya kuma had'a kan mu, sai su Kawu Amadu da sauran yan'uwa harda k'awaye na su Fauzy na rok'i Allah itama ya bata Miji na gari wanda zai sota tsakani da Allah ya riketa da Amana harda su Mino ma" jinjina mata kai yay a hankali yace Allah ya amsa, shiru tay yace Shikenan ta d'aga mashi kai, wani kallo yay mata mai kaman harara tana ganin haka tasa dariya tace "to ai kai fa na fara yi mawa Allah, na rok'i Allah ya k'ara ma rayuwar ka Albarka yasa ka gama da iyayen ka lafiya ya k'ara maka lafiya da Arziki mai Albarka ya biya maka dukkan bukatunka na Alkhairi yasa ka dawwama a cikin farinciki ya kuma bani ikon yi maka biyayya" lumshe ido yay ya saki k'ayataccen murmushi sosae yaji dadin Addu'oin ya amsa mata da Amin, ce mata yay ita bata ma kanta bane tace tayi yace to ta fad'i mashi wacce tayi ma kanta wani kallo tay mashi tana dariya da alamun kunyar fad'i take ji yace yana jin ta, cikin jin kunya tace "Na rok'i Allah yasa....in samu ciki in haiho yaro mai kama da kai sak" da k'yar ta k'arasa Maganar tana rufe fuskarta da hannunta d'aya, yana murmushi yace bata son mai kama da ita ta d'aga mashi kai, tambayar ta yay miyasa take son mai kama da shi tace "Saboda nasan ba kowane lokaci zamu kasan ce a tare ba kaga in na haifi mai kama da kai ko baka nan zan rage kewar ka in ta kallon fuskar shi" tana yar dariya ta k'arasa Maganar, jinjina kai yay ya d'an kalli gefe alamar tunani kafin ya juyo yace mata to taji wani alama, ta d'an bud'a ido tace alamar mi, wani kallo yay mata da sauri ta maida fuskarta gefe, ce mata yay ta bashi amsa ba tare data kalle shi ba a shagwabe tace ita ya za'ai ta gane, "But, did you feel anything last time?" Yay tambayar ya kafeta da ido, d'an jimm tay sai kuma ta yarfa hannu cike da kunya tace itafa bata fahimci komai ba lokacin, yace "Ok I forgot, u were in severe pain lokacin ba zaki fahimta ba" ita dai shiru tayi taga ya mik'e, Hijab d'in jikinta ya cire da kan shi ya kaita wardrobe tana ta kallon bayan shi, dawowa yayi ya duk'a a gabanta yasa hannu ya duk'o da kanta saman chest din shi ya kai hannu ya cire mata necklace d'inta bayan ya dagota ya had'a da earrings d'in gaba d'aya jewellery d'in ya cire ya kai saman dressing mirror, saida yaje ya sa ma kopar Bedroom d'in key sannan ya dawo wurinta gaba d'aya ya ciccibo ta yana fad'in Let them try their luck now......... *ASM 076* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Gab da kiran sallar Magrib Haisam tsaye a gaban mirror ya gama shiryawa cikin jallabiya, bai dad'e da ya fito daga wanka ba bayan ya tashi bacci, gado ya nufa ya hau ya matsa kusa da Fatuu dake lullu6e da duvet tana ta shan bacci, hannu ya kai ya shafi fuskarta tare da kiran sunanta, ganin tak'i tashi yasa shi d'an bubbuga fuskar a hankali yadda bazata ji zafi ba, motsi ta fara yi kafin ta fara bud'e idanun tana yi tana lumshe su har ta bud'e su gaba d'aya sun d'an yi ja, bin juna sukai da kallo Haisam na d'an murmushi yace "My Lazy Wife" jin haka yasa ta tura mashi baki a shagwabe tace itace lazy d'in ya d'aga mata gira alamar eh, k'ok'arin rufe fuskarta da duvet ta shiga yi ta d'an d'aure ta ita ala dole tayi fushi, da sauri ya ruk'e Duvet d'in yace mata wasa yake mata ita ba lazy bace shi shaida ne, ganin irin kallon da yake mata yasa ta d'an juyar da fuskar ta tana yar dariya, ce mata yay ta tashi taje tayi wanka lokacin salla ya yi ta d'aga mashi kai, hannu ya kai zai d'ago da ita da sauri ta k'ank'ame duvet d'in tace yaje zata tashi yanzu, murmushi kawai yay ya juya ya saukko daga kan gadon, tanata kallon bayan shi har ya bud'e k'opa ya fita, lumshe ido tay tana ta sakin k'ayataccen murmushi da alama itama ta zaucen, daga baya ta saukko ta nufi toilet. Bayan ta gama sallar Magrib mik'ewa tay ta d'aukko wayarta ta dawo kan prayer mat d'in ta zauna ta shiga kiran Fauzy, tana fara ringing ta d'auka suka gaisa tace mata ya School Fauzyn tace ta manta Weekend ne tana gida ai, d'an shiru Fatun tayi jin haka yasa Fauzy tambayar ta lafiya, tace "kin san Fauzy Ya Haisam fa ya dawo" da alamun mamaki tace mata da gaske Fatun tace mata "Eh, kuma harda Aunty Fanan ma, ashe wannan sak'on da kika tura sun gani kuma lokacin daya shiga ma ita ta fara gani wayar na a hannunta" wani uban salati Fauzy ta buga har saida ta kusa sa Fatuu fashewa da dariya don a matuk'ar razane ta yi shi, a rud'e ta shiga tambayar ta yanzu ya akai, mi ya faru, da alamun damuwa Fatun tace mata bata yarda ba rigima tasa wai sai an sake ta shine suka taho, wani salatin Fauzy ta k'ara saki, a iya muryarta zaka shaida ba K'aramin tashi hankalinta yay ba, a kid'ime tace ma Fatun to shi ya Haisam d'in miya ce, don kada taci gaba da tada mata da hankali tasan hakan bashi da kyau yasa ta saki dariya tace "sorry k'awata ina tsokanar ki ne amman da gaske ya dawo kuma taren suka zo sannan da gaske ita ta fara ganin sak'on" da sauri Fauzy tace "to yanzu miya faru don Allah??" Fatuu na murmushi tace mata Alkhairi, nan ta kwashe yadda komai ya faru harda bayyana mata da ya Haisam yayi yana son ta shima, wata uwar k'arar murna Fauzy ta saki Fatuu nata dariya tana jiyo ta tana k'wala ma Aunty Mareeya kira tana fad'in the long expected day has come, d'akin Aunty Mareeyar ta nufa dama tare suke suna kallo a parlor ta tashi taje ta dawo, a daidai bakin k'opar bedroom d'in nata sukai kacibus don ta jiyo k'wala mata kiran da take, cike da farinciki ta hau bata labarin abunda ya faru tun kafin ta k'arasa ta mik'a hannu ta amshi wayar dama duk Fatun na jin su, tana amsa cike da Farinciki harta kasa rufe baki ta kira sunan Fatun itama tanata murmushi ta amsa mata kafin ta gaishe da ita, Cike da tsantsar farinciki tace "ashe wai haka abu ya kasance, shima bawan Allah ashe ashe yana ta gurzuwa" yar dariya Fatun tay tace mata eh, "Kai jama'a! Wannan cutar kai har ina kana son abu kuma abun nan ya zama mallakin ka Saboda tsabar cutar miskilanci ka tauye ma kan ka hakki" cike da jin kunya Fatun ta fad'i mata dalilin shi na yana son sai dangin shi sun sani, cikin washe baki tace "duk da yana da dalili amman ai da sai ya maki bayani ko yanzu da yasa zuciyar ki ta buga fa d'an bantan uba da yafi kowa shiga hali kuwa k'ilan ma tashi itama ta buga don na lura irin soyayyar laila da majnun kuke ma juna an sha yan ciwoce ciwoce" dariya Fatuun take ta yi Aunty Mareeyar ta shiga taya ta murna ta kuma yaba ma Fanan tace gaskiya tayi namijin k'ok'arin da ba kowace mace zata iya ba don ita kanta Maganar gaskiya bazata iya ba, daga baya kuma tace to kuma irin haka in har mutum ya fito ya bayyana maka in baka amince ba kai kanka ba samun kwanciyar hankali zaka yi ba, k'arshe kuma tace Allah ma kada ya kawo wacce zata siye mata zuciyar miji haka Fatuu dai sai dariya take, yar Nasiha ta d'an yi mata ta kuma ja hankalinta kan kula da miji dasu kwalliya tace sai sun had'u zata mata karatu sosae, "Yanzu Zarah nace sai in maido magungunan aro ko, dama shekaran jiya tayi promo jiya aka kawo man wanda na siya" shiru ta d'an yi kafin cikin jin kunya tace mata eh to tunda akwae, dariya Aunty Mareeya tasa tace "ja'ira da ba kince in ma kwashe duka ba, in ce dai na farkon sun yi maki aiki yadda nike ta fata Allah yasa ya magantu iya magantuwa" k'asa k'asa Fatun tace mata eh, kafin da k'yar tace mata harda kuka ma, wani irin ihu da Aunty Mareeya ta saki har saida Fatun ta cire wayar daga kunnanta tana dariya Fauzy ce ta taso da sauri tana tambayar Auntyn wai mi akai tay mata alamun ta tafi da hannu tace mata Maganar manya ce wannan, ce mata tay zata bada in zata je Makaranta gobe sai Fauzy ta tafin mata da su tace eh zata je, daga baya sukai sallama sai farinciki Aunty Mareeya ke yi, bayan Fauzy ta amshi wayar itama sukai sallama tace mata sai sun had'u School gobe, Fauzyn tace ita da ke shan Amarci ta bari ta gama, Fatuu na yar dariya tace yadda in jarabawa tazo zata rubuta hakan ko, duk suka yi dariya nan tayi ma Fauzy godiyar sak'on da ta tura tace dama koda ta nuna bata ji dad'i ba Saboda gudun abun da zaije ya dawo ne, Fauzyn na dariya tace mata haba ba komai ai tun lokacin ta fahimceta tayi mata Addu'ar Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lpy yasa nan da nine months su sha suna Fatuu dai nata dariya daga baya sukai sallama. Cikin parlon Fauzy ta koma ta zauna kusa da Aunty Mareeya nan suka dasa hirar farinciki Fauzy na fad'in ita wllh dama ranta ya bata shima yana son Zarah bawan Allah ashe ma ya fita shiga hali. Saida aka gama sallar isha Haisam ya dawo yace mata ta shirya suje part d'in Hajiya suci Abinci tace to, k'ananun kaya skinny jeans da riga wadda ta hau da shi ta fiddo, yana kwance saman gado ya jingina da headboard yana kallonta ta fara shiryawa, tana yi suna sakar ma juna murmushi in tazo kan abunda take jin kunya sai ta duk'e k'asa a haka har ta gama sakawa ta nufi gaban mirror tana gyara parking d'in gashinta, kasa jurewa Haisam yayi ya saukko daga gadon Slowly ya nufe ta, ba zato taji ya rungumota ta baya har saida ta d'an yi firgit, hannu ya kai ya janye gashinta data baza shi tana sharcewa fuskar shi da ya d'aura akan shoulder d'inta ta bayyana, murmushi suka shiga sakar ma juna ya d'an lumshe ido ya furta mata "Baby you're very beautiful" itama Lumshe mashi ido tay itama ta furta "Hubby you're very Handsome man" gaba d'aya sukai murmushi, hannuwan shi yasa yana bin shape d'in jikinta tamkar yana zana ta, d'an runtse ido da mak'e kafad'a Fatuu ta shiga yi, ganin bai da niyyar dainawa yasa tace mashi zai hanata ta gama shiryawa su tafi, juyota yay ya kai hannu ya fara k'ok'arin yi mata parking d'in gashin, suna haka take ce mashi wai a da can da ya fara saninta yana ganin kyaun ta, shiru yay yana d'an murmushi kafin yace bazai iya ganewa ba kawai dai yasan komai nata na burge shi, bayan ya gama d'aure mata gashin d'ago da ita yay ya d'aura ta akan k'afafun shi yadda ta d'an k'ara tsawo hannuwan shi tallafe da waist d'in ta itama ta zagayo da nata hannuwan ta bayan shi, bin juna sukai da wani irin azababben kallo kowa K'ok'arin nuna irin k'aunar dayake ma d'an uwan shi yake ta cikin kallon, As they held each other close, their bodies seemed to melt together like two puzzle pieces that were made for each other, Fatuu ce ta sare ta rufe fuskar ta a jikinshi idonta a lumshe can k'asan mak'oshi taji ya furta yana son ta itace best thing d'aya ta6a faruwa dashi tana mak'ale dashi ta furta mashi itama haka, d'agota yay suna sakar ma juna murmushi yace suje tace bari ta d'aura After dress, bayan ta d'aukko ta saka tayi rolling veil d'in ya kama hannunta suka tafi. Wuraren k'arfe goma da rabi lokacin basu dad'e da dawowa ba suna zaune a parlorn su suna kallon American film Fatuu ta cire after dress d'in tana mak'ale jikinshi kamar yar mage sai shak'ar k'amshin juna suke, d'aga kai tayi ta kalle shi tace mashi gobe zata je school, shiru ya d'an yi yana kallonta kafin yace bazata bari ta huta ba, a d'an shagwabe tace mashi Exams d'in su ta taho fa Upper week zasu fara bata son ayi wani abun bata nan kuma ma test ake ta masu, jinjina mata kai yay suka cigaba da kallon, bayan wani d'an lokaci taji ya fara magana ta k'ara d'aga kai tana kallon shi, shima kallon ta yake yace mata jibi Fanan zata tafi Lagos yana son zasu rakata, jimm Fatuu tay tana kallon shi ba tare data ce mashi komai ba hakanan sai taji bata son zuwa duk da bazata so ya tafi ya barta ba, ganin tayi shiru yasa shi tambayarta ko bazata rakata ba, da alamun yar damuwa tace ba wai bata son zuwa ba kawae dai bata son wani abu ya faru in taje gidan su, shiru ya d'an yi yana nazarin Maganar tata can yace mata Shikenan sai su sauka a Hotel kawai, bin shi da ido Fatuu tayi don hakan ma bata ji ya kwanta mata ba gani tay in suka yi haka kuma ai kaman ba'a kyauta ma Fanan d'in ba anan suna tare kuma acan ma su ware duk da bata san ya suka tsara da ita ba game da kwanakin da zaiyi da ita ba, tambayar shi tay kwana nawa zasu yi yace just 2 days, sauke idanunta tayi ta shiga tunanin tunda ba dad'ewa zai yi ba kodai ta k'i bin shi don k'arshen ta hakan ba komai zai k'ara mata ba face bak'in jini a wurin su Hajiya Maryam in dai suka san da ita yaje kuma ya sauka da ita a Hotel tunda dai tasan ai k'ilan duk in suka je da Fanan a gidansu suke sauka, tana haka taji ya tambayi koda wani matsalan ne, kallon shi tay ta d'an girgiza mashi kai kafin a sanyaye tace tana jin saidai yaje ya dawo don a jibin tana da test, shiru ya d'an yi sai kuma yace Ok bari a d'aga tafiyar sai bata da test d'in da sauri tace "Ai Hubby daga jibin fa kusan kullum sai munyi don upper Wednesday zamu fara exam, tunda just 2 days ne ka rakata kawai" shiru yay yana kallonta sai d'an yamutsa fuska take, sam ba haka ya so ba don a yadda ya tsara tare zasu, ganin yanayin shi yasa ta kai hannu tana shafa kwantacciyar sumar sajen shi cikin nuna damuwa tace "You shouldn't worry pls" d'an murmushi yay ya lumshe mata ido, cigaba da shafa beard d'in tayi shi kuma yaci gaba da kallon yana yi yana maido idon kanta, k'arfe 11 na yi yace suje su kwanta tunda zata school suka mik'e a tare yana ruk'e da hannunta sai kace k'anwar shi, bayan ya kashe kayan kallon ya rage hasken Parlon suka nufi Bedroom yana tallafe da ita. Washe gari bayan ta gama shiryawa tare suka fito da shi zai kaita, saida suka tsaya suka d'auki Mino sannan suka wuce, Mino aka fara ajewa suka wuce, a inda ya saba ajeta nan yayi packing ta kalle shi tana murmushi tayi mashi godiya tana niyyar juyawa ta bud'e kopar taji ya ruk'o hannunta ta juyo ta kalle shi, idanun shi a d'an lumshe ya jingina kanshi jikin headrest, tana kallon shi ta fahimci ruk'on kona miye tay mashi nuni da lip glow d'in da ta shafa ya ida lumshe idon, matsawa tay wurin shi ta kai baki ta manna mashi kiss a kumatun shi tana niyyar janye fuskar ya ruk'o kan, lokacin daya saketa gaba d'aya ba lip glow d'in, komawa tay ta zauna itama ta jingina kanta da kujerar tana breathing rapidly haka shima, bayan sun natsu ya tambayi tana tare da Atm d'inta ta d'aga mashi kai yace ok zai tura mata kud'i ta tabbatar taci Abinci mai kyau ta k'oshi nan ma kai ta d'aga mashi suna kallon cikin idanun juna, har zata juya taji yace ko ya kawo mata Abincin da break, da sauri ta girgiza mashi kai tace a'a ai anan akwae Abinci mai kyau zata ci. A class ta iske Fauzy don da wuri tazo Saboda zumud'in ganin Fatun, tana shiga ta taso da gudu tazo ta rungume ta cike da Farinciki itama Fatun sai dariya take, bayan sun je sun zauna gaba d'aya Fauzy ta kafeta da ido tana ta washe baki sai kace wadda aka ma Albishir mai dad'i tama kasa Magana, Fatuu na dariya tace "wai sai kallo na kike sai kace yau kika fara ganina" yarfa hannu tay tace "bazaki gane irin farincikin da nike ji ba wllh don abu ne da ban yi zaton shi kusa ba, kinga wai yadda kika canza cikin kwana biyu kacal har fa wani glowing kike wllh ga k'amshin amarci, koda yake dama fa irin su Ya Haisam ba dai iya zuba ruwan love ba wllh kina ganin su shiru shiru sai hum....." dariya kawae Fatuu take ta kasa cewa komai itama Fauzyn dariyar take can tace "k'awata kukan ya Haisam bai damu da ni ba bai sona ya k'are ko" bugu Fatuu ta kai mata tana fad'in "leave me alone Fauzy" gaba d'aya dariya suke a haka malamin su ya shigo, tun bayan da malamin ya fara masu bayani Fauzy na lura da Fatuu sai faman sakin murmushi take da gani ba K'aramin nishad'i take ciki ba, sai da akai break sun fito take ce mata ita wannan Amarcin anya ma zai bari tayi wani karatun Exams Malam na explanation tana sakin murmushi inaga in jarabawar tazo kar ta kai fa in aka tambayi zane ta zana Ya Haisam, sosae Fatuu ke dariya suka nufi inda zasu ci Abinci. Da yamma wurin sallar la'asar Fatuu ta fito daga wanka, bayan ta zura doguwar riga ta kabbara salla, tana gamawa ta nufi gaban dressing mirror ta fara shirin zuwa part d'in Hajiya, tun bayan daya d'aukkota daga school suna dawowa suka ci Abinci ko wanka bai bari tayi ba suka kwanta bacci, sai da aka fara kiran sallar la'asar ya farka yaje yayi wanka bayan ya fito ya shirya ne ya tasheta ya sanar da ita time d'in salla yayi, tana cikin yin shafan aka yi knocking k'opar Bedroom d'in ta juya ta nufi kopar, tana bud'ewa suka had'a ido da Fanan ta sakar mata murmushi tana sanye da fitted gown ta lace dark blue fuskarta ba wani makeup sai lip glow data shafa a baki sai kuma yanayin fuskar bata rasa shafa powder yar kad'an ta yafa mayafi mahad'in kayan a saman kafad'ar ta, murmushi itama Fatun tayi mata ta kira Sunanta kafin ta gaishe da ita, ce mata tayi ta shigo mana tace a'a bari ta jirata a parlor dama tana son zata rakata wurin gwaggo ne da sauri tace mata to, komawa ray cikin d'akin cike da zumud'i ta d'auki waya ta kira Haisam bayan yayi picking ta sanar dashi zancen fitar yace ai Fanan dama tayi mashi magana sai sun dawo sukai sallama cike da nuna k'auna, ba 6ata lokaci ta k'arasa shiryawa bata canza kaya ba sai kawae ta yafa mayafin rigar jikinta ta d'aukki wayarta ta fita. A parlor suka zauna gwaggo nata faman sakin murmushin yak'e dama tun lokacin da suka zo tayi arba da Fanan saida gabanta ya fad'i, wani irin nauyi da kunyar Fanan d'in ne suka kamata duk ta bi ta kama kanta a haka suka gaisa tayi mata an zo lafiya da tambayar yan gidan su, lokacin Mino ta tafi islamiyya Amadu kuma yana a shago saida ma suka tsaya ya gaisa da Fanan kafin su shigo, Fatuu ce ta mik'e taje ta d'aukko mata ruwa da lemu don ta lura da yanayin gwaggon, bayan ta zuba mata cup ta mik'a mata ta fara sha, da k'yar gwaggo ta mik'e tace bari a kawo mata Abinci, da sauri Fanan d'in tace "No gwaggo ban dad'e dana ci Abinci bana jin yunwa" still murmushin yak'e gwaggo ke tayi tace "amman d'iyata Fanan ai a d'an ci na zumunci ko Yaya ne tunda yaushe rabon da acin" tana Murmushi tace mata kar ta damu ai tasha ruwa da lemu sai kuma tace "Da dai akwae dambu da na ci" da sauri gwaggo tace "ah in shi kike so sai in yi maki yanzun nan" girgiza kai Fanan tayi tace ba sai tayi wahala ba tunda babu, da sauri gwaggon ta k'ara cewa "ai ba wani abun wahala tunda komai akwae bari kiga yanzun nan a yi" tana rufe baki ta juya ba tare data jira cewar Fanan d'in ba, tun bayan data fara aikin girkin dambun take ta faman sambatu ita kad'ai, wani lokacin ta girgiza kai duk ta bi ta damu, Kallo suka cigaba da yi sai dai Fanan ba wani kallon take ba tafi yawan d'aga kai ta kalli sama kaman mai yin tunani sai jefi jefi take sauke idon ta kalli Tv, gaba d'aya Fatuu duk ta damu da yanayin ta don akwae alamun damuwa a tattare da ita hakan yasa bunu bunu sai ta kalleta, suna haka can ta kalli Fanan d'in suka had'a ido ta k'ak'alo d'an murmushi itama Fanan d'in fuskarta a d'an sake tace mata "Sis Zarah kinata kallo na tun d'azun da wani abu ne?" da sauri Fatuu ta girgiza mata kai ta maida idon ta k'asa , kaman daga sama taji tace "ko ina baki tausayi ne?" da sauri ta d'ago ta kalleta idon Fanan d'in akanta da alama amsa take jira da k'yar Fatuu ta d'an d'aga mata kai alamar eh kawai sai gani tay ta mata wani kallo mai kaman harara tace tunda ta k'wace mata miji ba dole taji tausayin ta ba, a rud'e Fatuu tace "a...a Aunty Fanan don Allah ki yi hak'uri.... " idanun ta har sun ciko da k'walla sai kawae gani tay Fanan d'in ta yi dariya tace tana tsokanarta ne, cigaba da kallon sukai saidae duk Fatuu jin ta take wani iri don tasan dama damuwar Fanan d'in bata wuce kan Haisam, ba'a d'au wani dogon lokaci ba gwaggo ta gama yin dambun yasha zogale da gyad'a da albasa sai uban k'amshi ke tashi, saida tazo ta tambayi Fanan d'in da k'uli take so ko yaji tana murmushi tace a kawo duka sai tasa taji wanda yafi dad'i gwaggon tace to, a d'an babban plate ta zubo mata bayan ta aje ta kalli Fatuu da d'an murmushi tace itama zata ci ne ta d'an tura baki tace eh mana, tana niyyar fita Fanan tace ta bari su ci tare in basu k'oshi ba sai a k'aro masu gwaggo ta washe baki tace to, suna cikin cin Abincin Mino ta dawo daga islamiyya ta shigo tana ta fara'a ta duk'a ta gaida Fanan itama tana murmushi ta amsa mata daga baya ta gaishe da Fatuu kafin ta mik'e don taje ta cire Uniform, anan sukai sallar Magrib bayan sun gama suka fara shirin tafiya Fatuu taje ta sanar ma gwaggo zasu tafi, tana sanye da hijab da tayi salla tazo parlon lokacin Fanan na zaune a kan kujera itama ta zauna tana murmushi cike da k'arfin hali ta fara Magana "Y'ata Fanan inata so in baki hak'uri kan yadda abu ya faru tun d'azun nauyin ki yasa na kasa, nasan dole an maki ba daidai ba dole kuma hakan ya jefa ki a halin matsananciyar damuwa, don Allah kiyi hak'uri, duk ta wani bayani ba shi bane tunda mai faruwa ta faru" d'an murmushi tayi tace "No gwaggo ba komai, ni musulma ne na yarda da k'addara mai kyau da mara kyau and I hope wannan ya zama mai kyau, kawae ina son ki ma Zarah magana taci gaba da d'aukana matsayin sister nata ba kishiya ba, kuma duk abunda take so ma kanta ni ma ta so man....." Kuka ne ya taho mata da sauri tasa hannu ta rufe idanunta a rud'e gwaggo ta hau lallashinta kafin ta juya kan Fatuu ta fara mata Nasiha can ta maida Maganar da harshen fulatanci ta ce mata kar ta sake ta canza mata ta rink'a kyautata mata sosae samun abokiyar zama irinta a yanzu zai matuk'ar wahala idan ma tayi mata wani abu da bata ji dad'i ba ita ta fad'i mata zata bata shawara, haka tay mata fad'a sosae Fatun nata k'walla tana d'aga mata kai, daga baya ta had'a su gaba d'aya tayi masu Nasiha, sosae tayi ma Fanan godiya da Addu'oi tana ta amsawa a hankali, ce masu tayi bari ta zuba masu dambun su kai ma Hajiya, lokacin data zubo ta fito har sun fito tsakar gida Mino ma ta fito daga cikin d'akin Fatuu na da yanzu ita ce a ciki, har waje bakin shagon Amadu suka rako su Fatuu ta amshi kular dambun Amadu ma ya fito sukai sallama cike da nuna jin dad'i, jikin gwaggo ba K'aramin sanyi yay ba sai dai kuma yanzu hankalin ta ya fara kwanciya sosae. Bayan sun koma gidan part d'in Hajiya suka wuce, lokacin da suka shiga ba kowa a cikin parlon dama Hajiya sai tayi sallar isha take fitowa, d'akin da Fanan d'in ta sauka suka wuce bayan Fatuu ta je Kitchen ta aje dambun, yar hira suka shiga yi suna haka aka kira sallar isha. Bayan sun gama sallar Parlor suka fito suka zauna suna yin kallo, basu dad'e da zama ba Hajiya ta fito ta nufo cikin parlon, bayan ta zauna gaba d'aya suka gaishe da ita ta amsa tace masu an dawo ya Dijen, amsa mata sukai da tana lafiya tana gaishe da ita Fanan ta sanar da ita an bada dambu ma a kawo mata tace dambu Dijen tayi kenan aikuwa zata ci don ta kwana biyu bata ci shi ba, Fanan tace ita aka mawa, jinjina kai Hajiya tayi tana murmushi tace lallai Dije na ji da ita, Fatuu ma murmushi take ta mik'e don ta d'aukko mata, A plate ta zubo mata ta sako mata spoon ta dawo cikin parlon, tana niyyar d'aurawa saman sofa table ta kinkimo mata shi Hajiyar tace mata ta barshi ta bata, tambayarta tayi lemun da zata d'aukko tace ta bata ruwa kawae, juyawa tay ta koma hanyar Dining don ta d'aukko, sosae taji dad'in dambun tana ta yabawa Fanan na yar dariya tana fad'in kodai santi take, suna haka Haisam ya shigo cikin parlon hannuwan shi ruk'e da manyan ledoji, kusan a tare Fanan da Fatuu suka mik'e suka nufe shi kowa ya amshi leda guda tare da yi mashi sannu da zuwa yana murmushi ya amsa, Hajiya na yar dariya tace sun hutar da ita ita Uwargida duk sukai yar dariya, bud'e wadda Fanan ta amsa tayi taga su ice cream ne da snacks ta hannun Fatuu kuma Fruit ne, ce ma Fatuu tay taje ta zubo a plate sai ta taho da wasu a zuba snacks d'in ta amsa da to tana niyyar juyawa suka had'a ido da Haisam ya lumshe mata idanu tay d'an murmushi kawae ta wuce, bayan ta dawo kowa aka zuba mashi su shawarma suka d'auki ice cream Hajiya tace bazata sha shi ba Fanan d'in tace mata to akwae Fura a bata tace eh, k'arshe dai basu ci Abincin dare ba don duk sun k'oshi da abubuwan daga baya wurin k'arfe goma Haisam da Fatuu sukai masu sallama Fanan harda yi masu rakiya bakin k'opa bayan sun tafi ta dawo. Washe gari tun da Fatuu ta tashi take jin ta wani iri sanin yau Haisam d'in zasu tafi Lagos duk tayi wani sukuku da ita, Lokacin da zai kaita Makaranta bayan sun aje Mino sun wuce ganin yanayin ta yasa ya kai hannu ya kamo hannunta ya tambayi mike damunta ta d'an girgiza mashi kai kawai alamar ba komai, shiru yay kawai don ya fahimci dalilin canzawar tata yaci gaba da driving squeezing her hand lovingly. Bayan sun tashi ya d'aukko su saida aka aje Mino gida sannan suka wuce, Abinci suka fara ci kafin suka shiga faranta ran junansu, tare sukai wanka bayan sun fito ya fara taimaka mata ta shirya cikin doguwar riga kafin shima ya fara shiryawa tana zaune a bakin gado tana kallon shi, bayan ya gama shafe shafen jikin shi sanye da bathrobe ya nufo inda take zaune, zama yay daga gefenta cike da nuna damuwa ya kai hannu ya ruk'o hannunta yana ce mata karta damu kanta haka sosae is just 2 days ai zai dawo shima ba son tafiya yake ya barta ba shiyasa ma tun farkon yace a jira sai bata da test to kuma tace kusan kullum zasu yi gashi ya riga yace ma Fanan d'in zasu je tare, kuka ta saka mashi dama dannewa take ta yi, hannu ya kai ya jawo ta jikin shi, sosae ya shiga rarrashinta yana nuna mata ai zasu rink'a yin Vedio call kafin ya dawo, sai kace yana zugata sai k'ara sautin kukan take gaba d'aya ta fara rikita shi a da ma bai son kukan ta balle kuma yanzu, haka yay ta aikin rarrashi cikin salon k'auna, har aka kira la'asar suna abu d'aya k'arshe dai sai a d'aki yayi Sallah tare da ita bayan ya samu tayi shiru sai sakin ajiyar zuciya take, bayan sun gama ya fara shiryawa cikin shadda light blue itama d'aukko mata riga da skirt na atampa yay don doguwar rigar jikinta duk ta yamutse, kusan a tare suka sa kayan ya taimaka mata, bayan an gama saka kayan gaban dressing mirror suka nufa da kanshi ya shafa mata powder yanata mata murmushi itama tana d'an maida mashi, jambaki ya d'aukko zai shafa mata ta tare hannun ta d'an girgiza mashi kai yace bata so a hankali tace mashi bashi ba, yace Ok wanne ta nuna mashi lip glow ya d'aukko ya shafa mata, kai fuskar shi wurin tata yay ta d'aga ido ta kalle kawai sai gani tai ya kai bakin shi ya manna ma lips d'in ta kiss, yana d'agowa taga ya gogi lip glow d'in hakan yasa ta saki faffad'an murmushi, yar dariya yay dama so yake yaga ta saki fuskar yasa yayi mata hakan tunawa da yadda sukai na jambaki, bayan ya gama yi mata komai kama hannunta yay suka nufi bakin gado shi ya fara zama ya d'aurata akan laps d'in shi idon su cikin na juna, da d'an murmushi yace "za'a rakani Airport?" shiru tay ta kafeshi da ido sai da taga ya d'age mata gira alamar amsa yake jira sannan murya a disashe tace "kana so?" Lumshe mata ido yay ta d'aga ma shi kai alamar to, hannuwan shi ya kai ya rungumota jikin shi ya duk'a da kanshi saitin nata whispering in to her ear ya furta "promise me bazaki k'ara kukan ba har in dawo?" jimm tay ta kasa cewa tayi alk'awarin don ita kanta kawae ji taje kukan na zuwa, k'ara ce mata yay tayi mashi alk'awarin cikin karyayyar murya tace "ai shine ke zuwa da kan shi" k'ara matseta yay yace Ok amman ta daure ta daina yi hankalin shi ba zai kwanta ba in ya tafi ya barta tana kukan ta d'aga mashi kai alamar to, shiru suka d'an yi ha6arshi a saman kanta can taji yace mi take so ya siyo mata, d'an girgiza mashi kai tayi alamar ba komai yace bai yarda ba kullum sai tace ba abunda take so yanzu dai ta fad'a komi take so zai kawo mata, murya a disashe tace mashi da gaske ba abunda take so kawai sai ji tay yace "Ok I will buy you a teddy bear" ba shiri ta d'ago ta kalle shi da alamun mamaki akan fuskar ta, idanun shi a d'an lumshe yana d'an murmushi ganin kallon da take mashi ya d'age gira yace "or a Barbie doll wanne kike so ko duka?" tura mashi baki tay a shagwabe tace "to ni k'aramar yarinya ce da zaka siyo man wannan" still idanunshi a lumshe suke ya furta "Yes u'r my baby", murmushi tayi tace "to ni ban son su in ma abun wasan zaka siyo man to kan ka zaka siyo man" yana murmushi yace shi ai ta riga da ta mallake shi tuni, itama murmushin take tace to tana jira ya dawo sai tayi wasan da shi shine teddy d'in nata sukai yar dariya, wayarshi ce ta fara ringing ta sauka daga jikin shi tace bari ta d'aukko mashi, wurin mirror taje ta d'aukko ba tare data duba mai kiran ba ta kai mashi, sunan Fanan ya gani alamar ita ke kira bayan yayi picking ba tare da ya bari tayi magana ba yace gashi nan fitowa yanzu, yana gama wayar ya mik'e tana tsaye daga gefe ya kama hannunta suka nufi Wardrobe, bayan ya fiddo mata gyale da kan shi ya yafa mata shi suka tafi bai d'auki komai na kayan shi ba anan abunda ya ke son d'auka d'azun ya d'aukko a G.r.a da ya aje ta school harda jakar computer d'in shi, koda suka zo shiga harabar gidan ba yadda bata yi ba ya sake mata hannu amman ya k'iya haka da suka zo shiga part d'in Hajiya ma k'in sakin hannun yay suka shiga haka duk kunya ta kamata, a cikin parlon suka samu Hajiyar da Fanan ta shirya dama shi kad'ai take jira, zama sukai Fatuu ta gaishe dasu duka shima ya gaisa da Hajiya daga haka suka yi sallama duk suka mik'e don lokaci na neman k'urewa Hajiya na k'ok'arin mik'ewa tayi masu rakiya Haisam d'in yace tayi zaman ta kawae tayi masu Allah ya tsare, a parking space suka iske Tk a gefen Motar da zasu hau, ita da Fanan suka shiga baya shi kuma ya zauna a gaba Tk ya zauna a driver seat bayan ya rufe ya tashi Motar suka fito daga cikin wurin kafin yaja suka tunkari gate. Ba K'aramin k'ok'ari Fatuu tayi ba wurin hana idanunta zubar da k'walla har suka raka su suka dawo, gaba d'aya jinta take wani iri duk tayi sukuku da ita, suna zuwa kusa da gidan su tace mashi ya ajeta a gidan, lokacin data shiga Mino bata nan tana islamiyya sai gwaggo kawai ta iske a cikin d'akin ta tana zaune a saman gado tana linkin kaya, a saman kujera ta zauna bayan sun gaisa ta tambaye ta daga ina da d'an murmushi ta fad'i mata ta raka su Aunty Fanan ne nan gwaggon tayi masu Allah ya tsare, daga baya tsohon dakinta ta koma ta kwanta tayi lamo tana ta tunanin Masoyinta har Mino ta dawo ta isketa anan, tana a gidan har aka yi sallar isha lokacin har Haisam ya kirata ya sanar da ita sun sauka, bayan sun ci Abinci suka tafi tare da Mino zata taya ta kwana. Tun bayan da suka sauka Driver d'in gidan su Fanan ne yazo ya d'auke su, lokacin da suka isa gidan kusan ba kowa Hajiya Maryam bata nan ta d'an fita ta dawo haka sauran yara ma basu kaiga dawowa daga Islamic school ba Dad d'in su kuma na Asibiti wurin aiki sai Farha kad'ai tazo tayi masu sannu da zuwa, part d'in da suka saba sauka suka nufa, bayan Fanan ta aje masu kayan su kwanciya sukai don su huta har lokacin Magrib yayi sannan Haisam ya tashi don zuwa Masallaci itama ta tashi tayi sallar, ana gama salla Hajiya Maryam ta dawo, part d'in nasu tazo ganin ba kowa a cikin parlon yasa ta kira Fanan d'in a waya ta sanar mata tana a parlor, fitowa tay da murmushi itama Mom d'in nata d'an murmushin take mata tana zuwa ta rungumeta tana fad'in tayi missing nata itama tace tayi nata, bayan ta d'ago bin ta da ido Mom d'in tayi kaman mai nazarin wani abu can tace mata bata lafiya ne taga idanunta sun fad'a, har saida gaban Fanan ya d'an fad'i, tana murmushin yak'e tace mata tundai halin data shiga ne acan Us na sanin zancen Auren da Haisam d'in yayi a 6oye shiyasata har ta rame, jinjina kai tay cike da gamsuwa ta kama hannunta tace suje part d'in ta, Bedroom d'inta suka wuce suka zauna a bakin gado gaba d'aya ta maida hankalinta akan Fanan d'in ta tambaye ta ya suka k'are da Hajiya to, jimm tay tana tunanin abunda zata ce mata, tasan muddin ta fad'a mata ta amince to tabbas ran kowa sai ya 6aci har Haisam d'in ba k'yale shi zatai ba ita kuma bazata so hakan ba, d'an yamutsa fuska tay tace "Mom ki bari in huta sai mu yi Maganar we didn't arrive long ko Abinci bamu ci ba" wani kallo ta bita dashi tace to miyasa basu ci Abincin ba bacin already table a shirye yake tace mata sun bari su huta ne kuma basu jin yunwa sosae, tambayar ta Haisam tay tace yaje Masallaci daga baya gudun karta matsa mata kan Maganar ta mik'e tana fad'in bari taga in ya dawo sai su ci Abincin ta nufi hanyar fita Mom d'in ta bita da ido, tana komawa part d'in su ta shige Bedroom tay kwanciyarta a ranta tana raya ko zata fad'i mata sai Haisam ya bar gidan, sai bayan sallar isha ya dawo Fanan tace mashi suje suci Abinci, kusan gaba d'aya suka ci Abincin harda Farha da Hajiya Maryam da ba laifi ta sakar mashi fuska da suka gaisa, sai can wurin k'arfe goma na daren Dad d'in su ya dawo har part d'in nasu yazo suka gaisa Fanan ta rungume shi tana mashi shagwa6ar tayi missing nashi sosae shima yana fad'i mata yayi nata Haisam dai sai murmushi yake daga baya ya tafi, tun daga lokacin Fanan ta fara zille ma Mom d'in nata bata bari su zauna tare su dad'e don karta yi mata zancen, Sosae Haisam yake k'ok'arin faranta mata duk suka kasance tare, haka Fatuu ma yana yawan kiranta a waya tay ta zuba mashi shagwa6a, Ranar Alhamis da yamma ya shirya zai koma saidae a ranar da safe Mom d'in shi ta kira shi ta sanar dashi tana son ganin shi yaje Abuja kafin ya koma don tasan yana Lagos d'in, lokacin daya kira Fatuu ya sanar da ita yayi tunanin zata nuna damuwa amman ga mamakin shi bata nuna ba tana murmushi tace mashi ba komai Allah ya dawo dashi lpy sosae yaji dad'i dama duk itace damuwar shi, a ranar da yamma yayi sallama da Hajiya Maryam Fanan ce ta tafi kai shi Airport, ita ke driving Motar yana gefe hannun shi ruk'e da nata, cike da k'auna sukai sallama da shi ta dawo cike da jin kewar mijinta, bayan ta parker Motar a parking space, tana shigowa cikin parlor ta iske Hajiya Maryam zaune da Farha suna kallo a Tv, nufar su tay tana sanye da jallabiya tayi rolling veil ta tsaya a bakin kujerun tay mata sannu tana kallon ta tace har ya tafi tace eh, shiru suka d'an yi kafin ta juya zata tafi d'aki taji muryar ta tace "Wait I want to talk to you" daramm gaban Fanan ya fad'i, dakatawa tayi ta kai idonta akan Mom d'in su ta nuna mata sofa d'in gefen ta tace ta zauna, "Yanzu dai ai nasan kin huta sosae so am all ears ya kukai da Hajjaju ta amince an saki yarinyar nan?" Shiru Fanan tayi idonta a kan had'add'an carpet d'in k'asan parlon, maimaita mata tambayar tayi sannan ta d'ago ta kalleta gaba d'aya sun kafeta da ido harda Farha itama tana son taji amsar da zata bada, Sigh tay a sanyaye tace mata Hajiya ta k'i amincewa tace tayi hak'uri su zauna tare da ita, tun kan ta k'arasa Hajiya Maryam ta yamutsa fuska tana kallon ta har ta gama sannan cikin d'aga murya tace "You're telling a lie Fanan, daga yanayin face d'in ki nagane ba gaskiya kike fad'a man ba, kar ki manta ni na tsugunna na haife ki, so zan iya gane in kina 6oye man abu, dama tun da kika zo na fara zargin wani abu k'in tsayawa muyi magana ya k'ara k'arfafa zargin nawa, Now tell me the truth, else, ranki zai yi mummunan 6aci!" A fusace tay Maganar, abu Fanan ta had'iya kafin murya na rawa tace Ok zata fad'i mata gaskiyar, nan ta fara fad'i mata yadda sukai da Haisam ya nuna mata in ya saki Yarinyar za'a cuceta ne tunda shi ya fara saninta ya san hakan ne ma yasa Hajiya tun farko ta hana ya saketa, tun kafin ta gama ta katseta da tambayar "sai kika amince yaci gaba da zaman da ita???" Cikin yar in ina tace mata yayi mata alk'awarin zai masu Adalci kuma daga ita bazai k'ara Auren wata ba shiyasa ta amince don tasan ko sun zo wurin Hajiyar ba amincewa zata yi ba tunda shima ya nuna zai cigaba da zama da ita....., Buga hannun kujera Hajiya Maryam tayi tare da mik'ewa tsaye cikin daka tsawa tace "Enough Fanan! I never knew you were such a fool until Today, ba a iya sakarci ko wawanci kika tsaya ba har hankali baki da shi, yanzu ke ashe dama baki da wayau har haka, wato ya zauna yayi maki dad'in baki shine kika hau kika zauna ke gaki shashasha har ki ka kasa gane cewa son yarinyar yake shiyasa ya fake da hakan, in don abunda ya shiga tsakanin su ne ba sadaki ya biya ba to miye abun cuta ko wani cin zali a ciki......!" Sosae take fad'a ta inda take shiga ba tanan take fita ba a k'arshe tace sam bata yarda da amincewar da tayi ba don haka dole ta canza ra'ayi ta nuna mashi bata amince ba, shiru Fanan d'in tayi kanta a k'asa, ganin yadda ta d'auki zafi yasa ta d'ago kai idanunta cike da k'walla tace ma Mom d'in nasu ita gaskiya ta riga ta amince bazata canza ra'ayin ta ba tunda ya nuna yana son cigaba da zama da itan kuma Hajiya ma na so ita ta hak'uri sannan ita yarinyar sam bata da wata matsala zasu zauna lafiya, rai a tsananin 6ace Hajiya Maryam ta nuna kanta tace "Fanan! Ni kike fad'a ma haka! ni kike k'ok'arin nuna ma kin za6i faranta ma mijin ki fiye da ni duk da komai nike ina yi ne don ki dawwama cikin Farinciki, don in ga rayuwar ki baki shiga cikin matsala ba!" Girgiza kai Fanan ta fara yi k'wallan da suka taru suka fara zubo mata cikin karyayyar murya tace "No Mom ba haka bane wllh, is just dat in life Sometimes we must sacrifice our own happiness for the sake of those we love, yanzu in na za6i farinciki na kad'ai zan bak'an ta ma mutane da yawa, Hajiya bata so, shima baya so sannan ita kanta Zarah bazata so ta zama bazawara ba, sannan yan'uwanta ma bazasu so ace an sake ta ba that's why na hak'ura kuma nasan in sha Allah zan ci riba tunda Allah yace yana tare da mai hak'uri" wani kalan murmushin takaici Hajiya Maryam tay tana jinjina kai da alama ta kashe bakinta ta kasa ma magana, ganin yanayinta yasa Fanan sauka daga saman kujerar ta duk'a saman knees d'inta ta shiga bata hak'uri tana fad'in don Allah ta fahimce ta, can ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace "Ok, kiyi yadda duk kika ga yayi maki Fanan rayuwar ki ce ba tawa ba, dama katsalandan ne irin nawa yasa na zaqe, amman ki sani ba baki nayi maki ba indai Namiji ne gaki ga shi zaki nadama ne, ina zaune wataran zaki kira ni kina kuka tunda har kika za6i farincikin shi fiye da naki farincikin ma na k'arfafa mashi ya zauna da wadda yake so, uhmmm harna tausaya maki Fanan, duk da a lokacin bazan ji tausayin ba ko misk'ala zarratin!!!" A kausashe tayi Maganar tana huci ta na gamawa ta nufi hanyar Bedroom a fusace Fanan ta fashe da kuka tana bata hak'uri tana fad'in ta Fahimce ta don Allah hakan kaddarar ta ne....... *ASM 077* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Sosae Fanan ke kuka maganganun Hajiya Maryam sun ta6a mata zuciya sosae hakan ya k'ara tado mata rad'ad'in da take ji dangane da Auran Haisam d'in, dama ko a can Katsina ba K'aramin k'ok'ari take ba ta na dannewa, gaba d'aya abun yayi mata yawa a zuciya sosae take ta Kuka cikin kukan ta fara fad'in ita ya zata yi ne, tasan ko ta nuna bata so in dai hakan kaddarar ta ce dole sai yaci gaba da zama da Zarah k'arshe zata tada hankalin ta ne a banza, duk wannan abun Farha na zaune a inda take idon ta akan Fanan d'in dake a durk'ushe tana kuka bazaka gane yanayin da ke akan fuskar ta ba, mik'ewa Farhar tayi tana sanye da doguwar riga roba da ta kamata, wurin Fanan d'in tazo ta kai hannu tana k'ok'arin d'ago da ita Fanan d'in ta kalleta idanunta har sun yi ja fuskar jage jage da hawaye, ce mata tay ta tashi Fanan d'in ta mik'e ta koma kan kujera ta zauna itama Farhar ta zauna daga gefen ta idanunta akan ta, itama Fanan d'in kallonta take tana cigaba da zubar da hawaye can Farhar tace mata tayi shiru karta yi ciwo fuskarta a d'an yamutse tayi Maganar, hannu Fanan ta kai ta kamo hannunta guda cikin Muryar kuka ta fara Magana "Farha kema na baki haushi ko?" shiru tayi fuskarta kamar a d'aure dama ita yanayin fuskar ta a koda yaushe haka yake can tace a'a ita bata ji haushinta ba tunda taji zata iya kawae dai tayi mamakin yadda ta amince ta zauna da wannan yar talakawan a matsayin kishiyanta dama wadda suke the same level ne da sauki, hannu d'aya Fanan ta kai tana share hawayen fuskarta bayan ta gama a nutse ta fara ma Farha magana da sautin kuka tace "I want u to understand wacece Zarah ba yadda kike tunanin ta ba take, she's a very nice person bata da matsala wllh, kuma don ita talaka ce hakan ba yana nufin tana da illa ba Saboda da mai kud'i da talaka we're all the same a wurin Allah kuma in yaso zai iya canza rayuwar su suma su zama masu kud'in da baki ta6a zato ba, muma da kike ganin muna dasu bafa fin su muka yi ba ya bamu, kawai hikiman sa ne yasa ya raba don kowa yay benefiting da kowa, in ya bamu kud'i so yake muyi amfani da su wurin taimaka ma wanda bai ba bawai mu ci mu kad'ai ba kuma mu kyamace su, kinga kenan kamata yay mu rink'a girmama wanda bashi dashi tunda ta silar shi Allah zai k'ara bud'a mana because whenyou give you always get back more in return, sannan ta silar yi masu Alkhairi zai kai ka har Aljanna, Farha i advise u, stop hating the poor pls ki rink'a kyautata masu I assure u zaki ji dad'in rayuwar ki don kema Allah zai rink'a kyautata rayuwar ki zai rink'a baki way out a dukkan matsalolin ki....." Dakatawa tay tana numfasawa ita dai Farhar bin ta da ido kawae take still da yanayin da fuskar ta take tun farko, Cigaba Fanan tayi "bari in baki Misalin abunda nike fad'a maki, Ya Haisam yana tare da Zarah for almost good five years ba abunda ke tsakanin su face kyautatawa kuma duk abunda yake masu yana yi ne Saboda Allah ba don wani abu ba, tun lokacin daya fara saninta we were engaged bai ta6a sama ran shi son yarinyar ba balle yay tunanin ya aureta har mukai Aure, yanzu bayan mun yi aure an tabbatar inada problem da yasa ban yi conceiving ba already kuma ya auri yarinyar without my knowledge da niyyar ya taimaka mata daga baya sai ya sake ta saidai kuma bai yi hakan ba har Allah yasa abu ya shiga tsakanin su sai gashi ita tayi conceiving, don't you think Allah dama yasan ni k'ilan bazan haihu bane yasa tun farko ya had'a shi da yarinyar? Yanzu idan nace in takura ya rabu da ita kuma dama already an k'addaro matar shi ce ita zata Haifa mashi yara kina ganin na isa in sa ya sake ta ne? Wannan nazarin nayi yasa na d'auki komai da Sauk'i Farha, Allah yasan abunda mu bamu sani ba sai mu k'i abu kuma Alkhairi ne a gare mu, ina fatan zaki fahimce ni my lovely sis, kiyi man fatan Alkhairi sannan ina rok'on ki ki cire komai a ranki tsakanin ki da Zarah naji labarin abunda ya faru tsakanin ku, ina son kiyi hak'uri ki manta da komai, nasan duk abunda kuke yi Saboda ni ne kar in shiga matsala I really appreciate it, amman ina son ku fahimce ni ku bani goyon baya akan hakan in sha Allahu zai zama Alkhairi a gare ni" k'arasa Maganar tay tana k'ara share hawayen dake zubo mata, jin Farhar bata ce komai ba kallon ta kawai take yasa ta d'an matsa hannunta tace tayi mata magana pls, d'an yamutsa fuska tay tace tunda hakan yayi mata Shikenan tana mata fatan Alkhairi, har saida Fanan d'in tay d'an murmushi don taji d'an sanyi a ranta, rok'on ta tayi suje ta tayata ba Momy hak'uri Farhar tace anya zata saurare su don tayi fushi sosae Fanan d'in tace su jaraba, tare suka mik'e hannun su cikin na juna suka nufi Bedroom d'in Hajiya Maryam, lokacin da suka shiga a saman gado suka hango ta kwance ta d'aura kafa d'aya akan d'aya tana d'an Jujjuya su ta tada kanta da pillow tana kallon sama, sallama suka yi ta d'an kai idon ta kan su kafin ta janye ba tare da ta amsa masu sallamar ba, nufo gadon suka yi gaban Fanan na fad'uwa suka tsaya daga gaban gadon, sakin hannun juna suka yi Fanan d'in ta duk'a idanunta cike da k'walla ta kira sunan Hajiya Maryam d'in, banza tay mata sai ma cize baki da tayi ta rufe ido, kallon Farha Fanan d'in tayi tay mata alamar taci gaba da kai, maida idon tayi kan ta cikin rawar murya ta k'ara cewa "Mom do....." bata samu damar k'arasa abunda take son fad'a ba sakamakon d'agowa da Hajiya Maryam d'in tay a fusace cikin tsawa tace "Don't Mom Me Fanan! Don't....!!" ban son jin komai daga gare ki I heard enough pls, nace kije kiyi duk abunda kika ga ya fi maki don haka ki tashi ki ban wuri ko kuma ni zan bar maki d'akin" jujjuya kai Fanan ta shiga yi k'walla na zubo mata, fuska d'aure Hajiya Maryam ta saukko da k'afafunta Fanan na ganin haka ta gane barin d'akin zata yi da sauri har tana gocewa kaman zata fad'i ta matsa ta kama k'afafun nata cikin kuka ta ke fad'in "pls Mom don girman Allah ki fahimce ni kar ki fushi dani abun zai man yawa, nasan duk abunda kike Saboda farin ciki nane saboda k'aunar da kike man kuma wllh na yaba da hakan....." A fusace ta katse ta "K'arya kike Fanan baki yaba ba shiyasa kika za6i 6ata man rai duk da ni ina hango maki abunda kika kasa hango ma kan ki ne, ta ina kishiya take zamar ma mutum Alkhairi koda tana zama kafin a samu haka sau d'aya nawa ake samu da suke zama sharri, kina ji kina gani za'a raba ki da Mijin da kike tak'amar yana son ki zai maku Adalci kuma ya kasa tsinana maki komai a lokacin kuma ko kinyi k'ok'arin maido shi gare ki wllh bazaki iya ba don lokaci ya riga da ya k'ure maki" ta k'arasa tana huci, d'an shiru Fanan tayi kafin cikin kuka tace "Mom saida nayi nazari sosae sannan na Amince, in ka d'auki abu matsayin Alkhairi sai kiga ya zamar maka hakan koda bai zama ba hakan k'ilan jarabawar kace in kayi hak'uri kuma sai kiga kaci riba, idan baka yi cuta ba Mom ba wanda ya isa ya cutar da kai kuma ko na rantse bazan yi kaffara ba Zarah bazata ta6a cutar da ni ba balle har ta raba ni da miji na, haka shima Ya Haisam na yarda dashi bazai ta6a juya man baya ba don ya k'ara aure kema kin san waye shi Mom kin san halin shi, nayi dogon nazari Mom there is reason for everything dama can Allah ya k'addaro ita matar shi ce shiyasa ya had'a su idan kuma ba'a kaddara zasu rabu ba wllh ni ban isa in raba su ba duk abunda zanyi k'arshe zan wahalar da kai na ne a banza, Mom baki tunanin k'ilan ni Allah bai kaddaro zan haihu ba shiyasa ya had'a su itace zata Haifa mashi yara, nayi tunani in har na hana shi hakan ba soyayya bace tunda Allah ya bashi mafita kuma kema Mom Haisam d'an ki ne bazaki so ace ya rayu bai da ya'ya ba" tunda ta fara Maganar Hajiya Maryam d'in ta ta6e baki tana sauraren ta idon ta akan ta har ta dakata sannan ta d'an girgiza kai da murmushi wanda yafi kama da ace na takaici ta d'age gira tace "Good, sarkin iya yin dogon nazari da tsara zance, wato ni ban iya yin zurfin tunani ba ko sai ke shine harda yanke ma kan ki hukuncin bazaki haihu ba, sai ki fad'i man a ina aka ce bazaki haihu ba ko kuwa kin yi gadon rashin haihuwa ne?" Girgiza mata kai tayi "No Mom nima ba ina nufin wai bazan haihu ba ina fatan in samu lafiya kawae misali nike baki tunda hakan yana iya yuwa, kuma ko da ace na haihu ne in Allah ya k'addara zasu zama mata da miji wllh bazan iya hana hakan ba you know dat Mom, Koda ace nayi yadda nayi nayi nasarar raba su in zaman su bai k'are ba dole su k'ara kasancewa tare koda kuwa bayan RAI na ne" wani kallo Hajiya Maryam ke jefa mata taci gaba "it happened more than once Mom, sau da yawa iyaye zasu ce ya'yan su bazasu Auri wani ba sai dai bayan ran su kuma k'arshe su zo su Mutun ayi auran, Mom wllh hakan na iya faruwa dani in dai nace zan ja da ikon Allah, kuma indai na cutar da su don Farinciki na kinsan sai Allah ya saka masu, nasan a kullum fatan Alkhairi kike man a rayuwata don haka duk abunda ya faru dani ki d'auka Alkhairin ne Mom na kuma tabbatar zan ci ribar kar6ar kaddarata da nayi k'ilan silar hakan kiga Allah ya bani lafiya nima in ta haihuwa kuma ya d'aga daraja ta, koda ma ban haihu ba Mom wllh Zarah bazata ta6a man iyaka da yaranta ba tana so na sosae she has good intentions toward me, Mom ki bini da fatan Alkhairi Don girman Allah in kika juya man baya Saboda haka sai yafi ta6a man zuciya abubuwa zasu man yawa, don na Amince su zauna hakan ba yana nufin ban jin komai ba a rai na kawae ina daurewa ne nasan kuma hakan na d'an lokaci ne ba kamar in kika fahimce ni kikai man fatan Alkhairi" ta k'arasa Maganar tana share hawayen fuskarta, shiru Hajiya Maryam tay fuska a kwa6e a bad'ini jikinta yayi sanyi da Misalin da Fanan ta bata na Allah zai iya d'auketa don su zauna tare Saboda tabbas yana faruwa, Fanan d'in ce tace mata don Allah tayi magana, sauke nannauyar ajiyar zuciya tayi tace "Shikenan tashi kije ina maki fatan Alkhairi" ganin fuskarta ba a sake tayi Maganar ba yasa Fanan d'in cewa to ta daina yin fushi da ita, d'an guntun murmushi tayi had'i da d'an ta6e kawae, tunda suka shigo Farha na a tsaye sai lokacin ta matsa kusa da gadon Hajiya Maryam d'in ta d'aga ido ta kalleta Farhar ta d'an yamutsa fuska tace pls ta daina fushin, juyar da fuskar ta tay gefe duk suka bita da ido can ta k'ara sauke ajiyar zuciya ba tare da ta kalle su ba tace ta bari Allah yayi masu Albarka da sauri Fanan ta mik'e ta fad'a jikinta ta fashe da wani irin kuka mai ta6a zuciya Farha ma d'an murmushi tay ta duk'a ta manna mata kiss a kumatun ta, d'ago kai tayi tay mata wani kallo mai kaman harara kawae sai itama ta rungume ta ta baya, sun d'an d'auki lokaci a haka idanun Hajiya Maryam a rufe wani iri take ji Kukan da Fanan d'in ke yi can ta d'ago da ita ta fara share mata hawayen tana fad'in ya isa haka sai wani ciwon ya kamata, godiya Fanan d'in ta shiga yi mata da Addu'oi tana ruk'e da dukkan hannayenta, tana d'an murmushi take amsa mata, jin an fara kiran sallar Magrib yasa tace masu suje suyi salla suka amsa da Ok Fanan d'in ta mik'e ta kamo hannun Farha suka nufi hanyar fita idanun Hajiya Maryam a kan su har suka fita, girgiza kai ta shiga yi takai yatsa baki ta d'an cize, tasan bata da wata mafita da ya wuce ta zubar da makamanta dama abunda yafi damunta shine tunanin halin da Fanan d'in zata shiga sai gashi ta bata mamaki sannan kuma ga furucin da Hajiya tayi mata, dangane da yadda take ji game da Fatuu kuma bazata iya fad'a ba. Suna fitowa Fanan ta rungume Farha tana k'ara yi mata godiyar fahimtar ta da tayi, bayan ta saketa Farhar na d'an murmushi tace mata "We're blood sisters" Fanan d'in tace hakane, kowa d'akin shi ya nufa. Bayan Fanan ta gama yin sallar Magrib d'aga hannu tayi tana k'walla ta shiga rok'on Allah akan kada yasa Maganar da Mom d'in ta tayi d'azun ta tabbata, Allah yasa kada Ya Haisam ya juya mata baya ya had'a kan su ita da Zarah, sosae tayi Addu'oi bayan ta shafa zaune tay saman prayer mat d'in ta kwantar da kanta a jikin gado tana tunane tunane, Wayarta ce ta fara yin ringing ta juya ta kallo ta a saman gadon kafin ta mik'a hannu ta d'aukko, ganin Haisam ne mai kiran yasa ta saki murmushi tay picking, gaida shi tayi ya amsa ta tambayi ya isa yace mata eh ya bari yayi salla ne sai suyi magana, an isa lafiya tayi mashi yace mata lafiya lou ta tambayi yadda ya iske kowa, jin yanayin voice d'inta ta d'an disashe yasa ya tambayi ko wani abu na damunta ne, tana d'an murmushi tace mashi eh cike da kulawa ya tambayi abunda ke damuntan tana d'an murmushi tace mashi missing d'in shi, shima murmushin yayi yace mata ai saida yace ta bari ba yanzu ba ta tafi ta k'iya, ita dai murmushi kawai tayi don baisan ba K'aramin k'arfin hali take ba zaman ta a gidan Hajiya tana ganin shi yana kwana da wata, rarrashinta yayi yace ai bada jimawa ba zai dawo, sosae ya kwantar mata da hankali cikin salon nuna kauna kafin daga baya sukai sallama, *ABUJA NIGERIA* Bayan sallar isha iyalan Senator suka zauna cin Abincin dare harda Haisam da tuni ya isa, ba laifi Haisam yaci sosae har Senator na mashi tsiyar dama yanzu in bai rink'a cin Abinci ba Sosae sai ya rink'a fad'uwa Saboda figewa zai yi su Aunty da Mom sukai yar dariya don sun fahimci dalilin daya sa ya fad'i hakan, shima Haisam d'in murmushi kawai yayi, bayan sun gama gaba d'aya cikin parlon suka koma duk suka zazzauna kusan kowa na nan banda Mutum biyu Laila da Nameer duk basu K'asar suna Makaranta, Mom d'in su ce ta fara yin magana tace ma Haisam d'in sun ji dadin yadda Fanan ta amince bata tashi hankalin ta ba Senator ma ya karba yace sosae Daughter ta burge shi Allah ya had'a kan su duk suka amsa da Amin Aunty ma ta yaba mata tace tayi namijin k'ok'ari gaskiya, yar Nasiha Senator yayi mashi kan yin Adalci a tsakanin su, bayan ya gama Jidderh tace to yanzu ai sai a kawo Fatuu nan ayi shagulgulan biki ko, shiru Haisam d'in yay kawae Fuskar shi a sake ganin baice komai ba yasa a shagwabe Jidderh tace "Big bro talk pls, yaushe zaka kawo ta sai mu tsara programs da zamu yi" d'an murmushi yay ya girgiza mata kai kafin slowly ya furta ba sai anyi wannan ba tunda an wuce wurin, tura baki tay a shagwabe tace gaskiya basu yarda ba su suna so ya za'a ce ayi Auren ba wani celebration, Aunty ce itama tace gaskiya ya kamata ayi koda bada yawa ba Saboda she needs to be introduced as one of the Family tunda duk ba'a san da Auren ba, Mom d'in shi ma ta goyi bayan ayin ba yadda Haisam ya iya don an fi k'arfin shi yace su tsara abunda suke son yi, nan suka shiga tattauna abunda yakamata ayi Jidderh sai lissafo abubuwa take cike da zumud'i, Senator ne yasa baki yace tunda ba yanzu aka yi Auren ba yana ganin ba sai an yi abubuwa ba sosae dama ya lura Angon kamar bai so ko don kar a kalle mashi mata ne ko kuma kar a wahalar da ita oho gaba d'aya sukai dariya shima Haisam d'in murmushi yayi, k'arshe dai abu biyu suka yanke zasu yi Walima wadda zata kama ranar Friday ayi kaman yinin biki sai washe gari ayi Dinner party, ita Jidderh hakan bai isheta ba sai yamutsa fuska take tana shagwabar gaskiya a k'ara ita kenan Sis Zarah d'in baza ayi Ethiopian Night ba dasu Arabian Mom d'in su na yar dariya tace tayi hak'uri a barshi hakan, "Yanzu sai Maganar lefe ko, shi banji anyi Maganar shi ba" Senator ne yayi Maganar, Aunty tace "Eh nima ina niyyar yin Maganar shi" Mom d'in su ce ta kalli Haisam tace ya za'ayi lefen, yana a d'an kishingid'e yace suyi yadda ya kamata, Aunty tace "dama k'awata Hajiya Sakeena yanzu haka tana Dubai ina ganin duk abunda ake so za'a iya tura mata in sha Allahu nasan zata yi komai yadda ake so ta aiko batare da 6ata lokaci ba in ma ba yanzu zata dawo ba, sannan ga Zee Collections ma itama za'a iya yi mata magana sai a za6i abubuwan da ake so ta aiko da su" sosae hakan yayi ma kowa nan suka shiga tattaunawa kan yawan akwatunan da za'ayi kowa na fad'in yadda yake ganin yakamata Jidderh tafi kowa fad'in masu yawa a hakikance take fad'in Sis Fatun fa big girl ce gaskiya ayi mata masu yawa har saida Senator yasa baki yana yar dariya yace ya lura dai tana ji da wannan sabuwar Yayar tata, bayan sun gama yanke yawan akwatunan da za'ayi Aunty ta tambayi Haisam lokacin da zai kawota don ai fixing date da za'ai programs d'in, sanar dasu yay zata fara Exams ne next week kuma bai san date d'in da zasu gama ba sai dai ya tambaye ta tace Ok, daga baya suka shiga tattauna ankon da zasu yi Jidderh tace yakamata a kira Aunty Laila ta za6a tunda tasan takan gayu sosae duk suka yi dariya su Yasmeen da twins sai murna suke za'a sake yin biki a gidan, Haisam ne ya tambayi Shikenan ko akwae wani abu Mom d'in shi tace in aka gama tsara komai za'a mashi magana ya furta Ok daga haka ya mik'e yay masu saida safe Senator na dariya yace "halan Amarya tayi kira" faffad'an murmushi Haisam d'in yay ya mik'a mashi hannu Senator d'in ya dunkule na shi ya buga mashi ya wuce ya nufi upstairs yana murmushi duk suka bi shi da ido su Mom d'in suma dariya suke, gaba d'aya sun lura da canzawar da Haisam d'in yayi tun bayan da yazo yayi wani irin Fresh daka gan shi kasan yana cikin nishad'i, yana shiga part d'in nashi bedroom ya wuce har zai kira Fatuu sai kuma yayi tunanin ya fara yin wanka sai ya kwanta gaba d'aya ya nufi toilet, within 30 minutes ya gama shiryawa cikin sleeping dress, a bakin gado ya zauna ya kai hannu ya d'aukko wayarshi dake ajiye a gefe, Fatuu ya kira lokacin suna a parlor ita da Mino suna yin kallo basu dad'e da dawowa daga part d'in Hajiya ba, bayan tayi picking ya sanar da ita zasu yi Video call cike da Farinciki tace mashi to, dama tunda ya tafi sau d'aya sukai Vedio call d'in sai dai suna yin waya akai akai, mik'ewa tayi tace ma Mino in ta gama ta kashe kayan kallon ta nufi hanyar Bedroom da sauri... Next Day...... Washe gari Friday bayan sun gama shirin Makaranta harda Mino ma anan ta shirya suka nufi parking space. Lokacin da akai ma su Fatuu break ganin tayi zaune yasa Fauzy ce mata ta taso suje su yi break kawae sai ta fad'a jikinta a shagwabe tace "Wayyo Fauzy miji na, don Allah ya dawo wllh ina kewar shi" dariya Fauzy ta sa dama kullum sai tayi mata magana akan mijin nata tace "to mai miji kiyi hakuri zai dawo ai" d'agowa Fatuu tay tana dariya itama, Fauzyn ta k'ara cewa "da alama dai Magana ta zata tabbata in exams tazo inaga labarin mijin ki zaki rink'a rubutawa banda zana shi dana ce" lumshe ido Fatuu tay tare da langa6ar da kai hannunta dafe da k'irji Fauzy ta kai hannu ta 6aka mata bugu a shoulder, bud'e idon Fatuu tay tana dariya tace "Fauzy ina rok'on Allah ya baki miji wanda ya iya buga love irin Ya Haisam wato gaba d'aya jin ki zaki rink'a yi a wata duniya ta daban kina rayuwa mai cike da nishad'i" sosae Fauzy ke dariya tace "na lura dai giyar soyayyar Ya Haisam na bugar dake sosae da alama Maganar Aunty Mareeya akan ki ta faru wato ke kika zaucen kullum baki da magana sai ta mijin ki" cigaba da dariya Fatun tayi Fauzy ta k'ara cewa "Wai ni anya ma kina karatun jarabawa kuwa sosae a gida?" Kashe mata ido tay a hankali ta furta soyayya bata bari, jinjina kai Fauzy tay tana dariya tay yar k'wafa tace sai ki rinka rubuta hakan ai a jarabawar, da kuwa an kad'a k'eyar ki, murmura idanu tay tace "ba Shikenan bama sai inje in ta shan soyayya ta da hujja in muka gama soyewa har muka kone bayan mun koma US sai in yi karatun" dariya sosae Fauzy ta saka tana fad'in ina Magana kuma in aka k'one itama Fatun dariyar take Fauzy ta mik'e tana fad'in ta taso suyi sauri su dawo su k'ara duba book kafin a shigo yi masu Test d'in da zasu yi tace to ta mik'e. Wuraren k'arfe d'aya suka tashi da yake ranar juma'a ne, duk suka goya jakunkunan su suka nufi hanyar fita daga class d'in, suna fitowa wayar Fatuu ta fara ringing ta kai hannu cikin aljihun rigarta ta d'aukko ta, tana dubawa taga sunan Hubby ya bayyana ta kalli Fauzy dake kallonta ta kashe mata ido tace mijinta ne ke kira Fauzyn ta d'an yi murmushi kawae, picking tay ta kara wayar a kunne a shagwabe ta kira sunan shi shima kiran sunanta yay taji yace yana a inda yake tsayawa, cikin rashin fahimta ta tambayi inda yake tsayawa a ina yace a School d'in su, waro ido tay with surprise written boldly all over her face tace "Are u serious Hubby!" tana jiyo sautin murmushin shi yace mata ai tasan bazai mata irin wannan wasan ba, cire wayar tayi cike da murna ta kalli Fauzy tace mata mijinta ya dawo gashi ma har yazo d'aukarta, itama Fauzyn tayi mamaki da sauri ta kamo hannunta tace tazo suje su gaisa sai faman washe baki take ta kasa 6oye murnar ta, sosae take sauri tana ruk'e da hannun Fauzy itama dole ta rink'a yin saurin tana fad'in kar tasa su fad'i don Allah, tana hango Motar ta saki hannun Fauzy ta nufeta da sauri sauri gudu gudu Fauzy nata dariya tana girgiza kai, k'opar gaba ta bud'e tana sa kai wani fitinannan k'amshi tare da ni'imtaccen sanyin Ac suka tarbeta, had'a ido sukai dashi yana sanye da farar shadda sumar nan tasha gyara, k'ayataccen murmushi ya sakar mata itama murmushin take mashi ta matsa kusa dashi ta kai duka hannuwanta ta tallabo fuskar shi batai wata wata ba ta had'e lips d'in su, da k'yar suka raba fuskokin nasu breathing rapidly sai murmushi suke ma juna, saida ta samu natsuwa sannan ta tuna da Fauzy da sauri ta lek'a ta hango ta daga d'an can nesa ta tsaya, da hannu tay mata alamar tazo ta nufo Motar tana d'an hararar Fatun had'i da d'an murmushi, a bakin kopar ta tsaya Fatun ta juya tace mashi ga Fauzy zasu gaisa ya jinjina kai, da hannu tay ma Fauzyn alamar tazo ta duk'o da kanta tace mashi ina wuni fuska a sake ya amsa ta sake ce mashi an dawo lafiya nan ma ya amsa, janye kan tay Fatuu na murmushi tace mata sai Monday wani kallo Fauzyn tay mata itama tana murmushin kafin tace to sai sun yi magana, tana maida kai cikin Motar zata rufe Haisam d'in ya mik'o mata kud'i yan dubu dubu sabbi dal yace ta bata, da sauri ta lek'o lokacin Fauzyn har ta tafi Fatun ta fito daga cikin Motar tare da kiran sunanta da d'an k'arfi, tsayawa tay ta juyo Fatun ta nufota, tana zuwa gabanta ta mik'a mata kud'in tace gashi inji Mijinta har saida Fauzyn ta d'an bud'e ido ganin kud'in nada d'an yawa sai kuma ta amsa tana murmushi tace "tukuicin tura sako ne aka bani kenan" gaba d'aya sukai dariya daga baya tace tay mashi godiya, har Fatun zata juya Fauzy tace mata kar dai ta manta ran Wednesday zasu fara Exams sosae Fatuu ta saki dariya kafin ta juya ta tafi, Motar ta koma ta shiga bayan ta rufe ya ja suka tafi hannun shi d'aya ruk'e da nata nan fa ta shiga zabga mashi shagwaba tana fad'in miyasa bai fad'i mata yau zai dawo ba kuma ko yau da safe ba saida sukai waya ba, yana ta murmushi idon shi akan hanya, d'an kallon ta yay yace kawae yana son bata Surprise ne, tura baki tay tace amman daya fad'i mata ai ta shirya, tambayarta yay wane irin shiri tace tayi gayu mana harda kitso da lalle har saida yay yar dariya, ganin ta d'an d'aure fuska ita ala dole fushi take yasa shi d'an matsa hannunta ta kalle shi shima kallon ta yay yace kada ta damu ko bata yi su ba a koda yaushe k'ara mashi kyau take har bata san lokacin data saki murmushi ba ta d'ago hannunshi dake ruk'e da nata tay pecking d'in shi ya d'an lumshe ido tare da furta "Day's my Baby", A wani babban Eatery ya tsaya yace mata yana zuwa ta d'aga mashi kai, tana ta kallon shi ta glass har ya shiga cikin wurin, after some minutes ya fito hannun shi ruk'e da yan manyan ledoji masu d'auke da tambarin wurin, back door ya bud'e ya saka bayan ya rufe ya koma cikin Motar yaja suka tafi. bin hanyar da suka bi tay da kallon ganin ba wadda suke bi bace, sai daga baya ta fahimci G.r.a suka nufa........ *ASM 078* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ........Ganin inda zasu yasa ta fara k'ok'arin raba hannun su tana fad'in bari ta kira Tk ta fad'i mashi ba sai yaje d'aukota ba ya d'aukko Mino kawae, ba tare daya saki hannun ba yace mata sun yi magana dashi tace Ok, suna isa Officer ya bud'e masu Gate ya shiga da Motar, a bakin entrance ya parker Motar Fatuu ta juya suka had'a ido a tare suka sakar ma juna murmushi har lokacin yana ruk'e da hannun nata, jingina kan shi yay da headrest idanun shi a d'an lumshe ya furta mata zaije Masallaci ya dawo ta jinjina mashi kai, cewa yay bari ya kama mata ledojin Abincin tace ya barshi zata d'auka still da murmushi akan Face d'in shi ya tambayi zata iya, yar dariya Fatun tay tace to abunda ba wani nauyi ne da su ba kuma ko suna da nauyin ai zata iya d'auka ya jinjina kai yace ya manta Babyn shi mai k'arfi ta iya bugun mutane Fatun tasa dariya, saida yay pecking hannunta sannan ya saki tace mashi sai ya dawo, bud'e Motar tayi ta fito shima fitowa yayi ya zagayo side d'in da take har ta bud'e kopar bayan ya duk'a ya fiddo mata ledojin ta amsa tana murmushi ta furta "Thanks My Hubby" jawota yay jikinshi suka kafe juna da ido suna d'an murmushi can Fatuu ta hura mashi iska a fuska ya d'an kikkafta ido tasa dariya tace yaje kar ya makara a gama sallar bai samu ba, sakin ta yay ya ce mata sai ya dawo ta d'aga mashi kai, har ya juya tace yayi masu Addu'a sosae ya d'an juyo ya jinjina mata kai kafin ya cigaba da tafiya, tsaye tay hannunta d'aya ruk'e da ledojin ta d'aga d'ayan tana mashi bye bye, bayan ya juya Motar ta kalli gate tsayawa yay ya sauke glass da hannu yay mata alamar ta shiga ciki tana murmushi ta juya tana yi tana waiwayen shi har ta shige sannan ya ja Motar, Tana shiga ciki corridor d'in da zai kaita Bedroom d'in shi ta nufa, tura k'opar tay ta bud'e ta shiga, tana shiga ta tsaya tana k'are ma Bedroom d'in kallo tsaf tsaf da shi ga wani sanyi mai had'e da daddad'an k'amshi sun karad'e shi gadon ya sha lallausan bedsheet kai kace ba d'akin namiji bane, wurin kujeru ta nufa ta d'aura ledojin akan c-table kafin ta sauke bag pack d'inta ta aje a k'asa gaban kujera itama ta zauna akan kujerar fuskarta a sake tana k'ara bin d'akin da kallo, tunanin abunda ya kamata tayi ta shiga yi zuciyarta ta bata ta yi salla itama, mik'ewa tay ta nufi hanyar corridor d'in da toilet yake, bayan ta shiga cikin toilet d'in sai kuma ta canza ra'ayi ta yanke tayi wanka kawae, after some minutes ta fito cikin Bedroom sanye da bathrobe d'in Haisam har ta kusa kai mata k'asa ta nufi gaban mirror, kallon kanta ta shiga yi tana d'an murmushi ita kanta taga canzawar da ita fuskarta tayi wani sumul tayi wani Fresh, mai ta fara shafawa bayan ta gama ta fesa turarurruka ta goga roll on, tunanin to wane kaya ma zata sa ta shiga yi don bai kamata ta zauna da bathrobe d'in ba, zuciyarta ce ta raya mata taje ta duba cikin kayan shi k'ilan ta samu wanda zata iya sakawa, laudary room inda press d'in shi take ta nufa, bayan ta bud'e ta fara bin kayan ciki da ido ganin wurin su shadda ne yasa ta rufe ta bud'e d'ayan side d'in anan taga k'ananun kaya suke, hannu ta sa ta fara d'add'agawa idanunta ne suka kallo wata jar riga a linke ta raya bari ta duba k'ilan babbar t-shirt ce in zata d'an saukko mata sai ta saka ta kawae, bayan ta d'aukko tana warware ta ba shiri ta waro ido da sauri ta kai hannu ta rufe bakinta alamar Al'ajabin ganinta, cire hannun tay ta fara murmushi ganin jar rigar data sa ranar da suka je dinner party d'in abokin shi har suka wuto nan, tun lokacin da abun ya faru bata bi ta kan rigar ba tasa jallabiyar ta kawae da yake mai zip ce ta tafi, rigar sai sakin k'amshi take ta yanke bari ta saka ta ma kawai, cikin Bedroom d'in ta dawo ta tsaya a gaban mirror ta fara kiciniyar sakata dama ko wanccan lokacin da k'yar ta shige ta don ma tana roba, yanzu ma ta shigeta saidae ta kamata kaman lokacin data sakata da farko, sosae shape d'inta ya fita ita dad'in hakan taji don dama tana son kaya su kamata, bayan ta gama d'aukar bathrobe d'in tayi taje ta bazata a laundry kafin ta dawo gaban mirror ta fara gyara gashinta, tana cikin sharce shi a cikin ranta ta shiga raya yakamata tayi kitso duk da ba son kitson take ba amman ko rannan saida gwaggo tayi mata Maganar kitson har tace zata yi mata k'arshe ta zille ba'ayi ba, tana haka taji an turo k'opar da sauri ta kai idon ta, shine ya dawo aikuwa da gudu ta nufe shi kafin ta isa ya bud'a mata hannuwan shi tana isa ya kamata ya d'aga ta sama, sosae hakan ya burge ta sai dariya take shima dariyar yake fararen hak'oran shi har sun bayyana, sauke ta yay ya rungumota jikinshi ta d'aga kai tana kallon shi suna sakar ma juna murmushi a shagwabe tayi mashi sannu da zuwa cikin cool voice d'in shi yace yauwa, tambayar shi tay yayi masu Addu'ar ya d'aga mata kai alamar eh tace to wace iri, d'an jimm yay yana mata murmushi sai kuma ya rankwafo da kanshi ya kai bakin shi saitin kunnanta ya rad'a mata wadda yayi masu ba shiri ta kife fuskarta a jikinshi tana dariya, d'ago Fuskar tata yay sai d'an runtse ido take alamun kunya, bin fuskar yay da kallo yana jin wata irin sabuwar k'aunarta acikin zuciyar shi, bayan ta bud'e idanun tambayar ta yay taci Abincin ko ta girgiza mashi kai alamar a'a tace shi take jira ya bata a baki yace Ok, kama hannun ta yay suka nufi ciki anan take ce mashi bai ga rigar data saka ba yay murmushi ya had'eta da jikin shi yace ya gani tayi kyau, wurin kujerun suka nufa ya saketa, matso da c-table d'in yayi a gaban kujera bayan ya zauna ya mik'a ma Fatun hannu ya ruk'ota, a saman jikin shi ya d'aurata tana ta murmushi ya kai hannu ya fara bud'e ledojin Abincin, tambayar shi tay a ina kitchen yake ta d'aukko plates slowly yace ta barshi ai zasu iya ci haka, Fried rice suka fara ci shi yake bata a baki tace ya barshi ta ci yana d'an murmushi yace bai son ta wahala, cike da soyayya ake cin Abincin wani lokacin in ya bata sai yay ta kallon bakin yadda take taunawa tana murmushi wani lokacin kuma sai ya kai bakin shi yay pecking bakin nata, saida suka ci suka k'oshi ya bata lemu ta sha itama ta d'ago ta bashi, k'ok'arin mik'ewa tay tana fad'in bari ta d'auke kayan, maido ta yay jikin shi da sauri ta kalle shi tana ganin yanayin idon shi ta lumshe mashi nata, romancing juna suka shiga yi bayan wani lokaci ya dauketa ya nufi bed da ita, sosae suka shiga nuna yadda sukai missing d'in juna, kamar yadda ya tara mata gajiya haka itama, sun d'auki tsawon lokaci suna faranta ma juna, yau dai iya magantuwa d'an Senator yayi har dai Salati saida aka ma Manzo SAW da Aure ya kasance sunnar shi. Lokacin da aka fara kiran sallar la'asar Haisam ya farka daga baccin da suke tun bayan da sukai wanka, toilet ya nufa yayo Alwala jikin shi sanye da jallabiya ya fito don tafiya Masallaci, saida ya koma wurin gadon ya tsaya yana kallon Fatuu dake ta shan bacci yasan tana buk'atar shi hakan yasa ya yanke tafiya in ya dawo sai ya tashe ta tayi sallar. Motsi ta fara yi a hankali ta fara bud'e idanunta har ta ware su kallon gefenta tay taga ba Haisam ta maida idonta sama, k'ura ma ceiling ido tay tana yi tana lumshe ido Memory d'inta da Haisam na d'azun na dawo mata fuskar ta d'auke da k'ayataccen murmushi, ta d'an d'auki lokaci a haka kafin ta fara tunanin ina Haisam d'in ya tafi ne, tunawa da Salla yasa tayi tunanin k'ilan yana Masallaci, tashi tayi ta saukko da k'afafunta gaba d'aya jin jikinta take ba k'wari duk ga6o6inta kwankwasa suke sai faman langa6ar da kai take da k'yar ta mik'e ta nufi toilet, Bayan tayo Alwala ta fito a Laundry ta tsaya tana tunanin Hijab d'in da zata yi sallar don tata tayi k'arama bazata rufe k'ugunta gaba d'aya ba gashi rigar ta kamata sosae, k'arshe dole ita ta d'aukko ta sanya sai ta d'aukko kallabin uniform d'in ta d'aura a k'ugun nata da yake babba ne ya saukko k'asa, cikin Bedroom d'in ta dawo ta d'aukko prayer mat bayan ta shimfid'a ta kabbara sallar, bayan ta gama zaune tay ta shiga tunanin wai ina ya tafi ganin har lokacin bai dawo ba kuma bata san tun lokacin da ya fita ba, mik'ewa tay ta koma laundry ta cire hijab d'in da kallabin ta aje ta dawo cikin bedroom d'in, tsaye tay gaban mirror tana kallon kanta tana sakin murmushi gaba d'aya yanzu ji take bata da wata damuwa duk wani rad'ad'i da taji a baya ta manta shi, juyowa tay zata koma wurin gado sai kuma taji tana son fita ta d'an ga gidan, nufar k'opar fita tay kanta ba kallabi sai tulin Sumarta dake fake da ribbon daga baya ta bud'e sosae, tunkan ta k'arasa fita daga cikin Corridor da zai kawo ta cikin babban parlon ta hango Haisam a d'an kishingid'e akan kujera 2 seater, da sauri ta shiga cikin parlon ta nufe shi ya juyo yana kallon ta fuskar shi a sake, tana zuwa gaban shi ta fara k'ok'arin hawa jikin shi hakan yasa shi gyara zaman shi ta haye ya tallafe ta kamar wata jaririya, a shagwabe tace "Hubby shine zaka baro ni ni kad'ai a d'aki kazo nan kai zaune kuma ko salla baka tada ni in yi ba" Fuska a yamutse take Maganar ta d'an turo baki, murmushi kawae yake mata ba tare da yace komai ba hakan yasa ta d'an Jujjuya jiki tace yayi Magana mana, hannu ya kai ya shafi gefen fuskarta slowly yace ta yi hak'uri yaso ya tada ta bayan ya dawo daga Masallaci sai kuma ya manta, d'aga mashi kai tayi ya tambayi tayi sallan yanzu tace eh, shiru yay kawai yana murmushi ta kai hannu ta fara shafa kwantaccen sajen shi can kuma ta d'an d'ago ta tura hannun ta a cikin sumar shi tana sosa mashi har saida yay yar dariya, bayan ta cire hannun kai bakinta tayi ta manna mashi kiss a saman lips d'in shi ya d'an lumshe ido, bayan ta maida kanta tana kallon shi tace mi yake a anan in kallo zaiyi ba akwae kayan kallon ba a cikin Bedroom, a hankali ya furta mata yayi bak'o ne har saida ta d'an waro ido tace "bak'o? a nan gidan?" Kai ya d'aga mata tace "ina bak'on ko har ya tafi?" shiru yay yana d'an murmushi ganin ta kafe shi da ido ya d'an girgiza mata kai alamar a'a tace "to waye bak'on kuma yana ina?" Slowly ya furta "Abbas" k'ara bud'a ido tay tace shine ya zo yana ina, d'aga ido yay ya kallo can gefen shi still da murmushi akan Face d'in shi, zaro ido Fatuu tay don ta fahimci Abbas d'in yana a cikin parlon kuma shine ya kallo, gaba d'aya mutuwar kwance tay don ta kasa yin ko kwakkwaran motsi a ranta ta raya kenan duk abun nan Ya Abbas na kallon ta, bata gama zancen zucin ba ta jiyo Muryar shi yana fad'in "Mom Zarah barka da juma'a, kwana biyu ai nace da alama dai kin mance da ni, d'azun dana zo har nake tambayar H,zakee ke yace ai kina nan kina bacci ne" runtse ido gam Fatuu tay tare da cije baki wata irin kunya ce ta lullube ta taji kamar ta nutse a k'asa Haisam sai kallon ta yake yana murmushi haka Abbas d'in ma kawai sai gani sukai ta saukko da gudu ta nufi hanyar corridor Abbas ya hau yin dariya, tana shiga cikin Bedroom ta nufi gado ta fad'a saman shi tare da kifa fuskarta a jikin katifa can ta fara d'aga hannuwa tana bugun Katifar sosae taji kunya, bayan kaman minti talatin Haisam ya shigo cikin d'akin lokacin tana kwance ringingine idonta na kallon sama ta gama borin jin kunyar, tana jin shigowar shi ta kai idon ta suka had'a ido da sauri ta juya mashi baya ya k'araso bakin gadon ya zauna yana d'an murmushi, kiran sunan ta yay tayi shiru saida ya k'ara sannan cikin tura baki ta amsa mashi, hannu ya kai ya jawota inda yake ya d'agota jikin shi ta fara yamutsa fuska tana kukan shagwaba, tambayar ta mi akai yayi tay mashi wani kallo tace ba shine ba yasan suna tare da Ya Abbas amman bai fad'i mata ba, rarrashinta ya shiga yi yace bai san taya zai fad'i mata bane ta riga ta fito shiyasa amman kar ta damu ai ba wani abu bane tunda shi mijinta ne tay shiru tana tura baki, ce mata yay tazo su gaisa zasu fita ne sai after Magrib zai dawo sai su fita da ita suci Abinci tace gidan Hajiya zasu je cin Abincin ya girgiza mata kai kafin yace zasu Eatery ne, da yar damuwa tace to ita da bata da kaya sai wannan rigar kuma ai ba yadda za'ai ta fita da ita haka, d'an jimm yay sai kuma yace Ok in ya fita yanzu zai je can gidan sai ya d'aukko mata ta d'aga mashi kai, Maganar gaisawa da Abbas ya k'ara yi mata tace ita wllh kunya take ji ya fara k'ok'arin mik'ar da ita yana fad'in ba wani abu ai, saida taje laundry ta d'aukko Hijab d'in uniform d'inta bayan ta dawo ta sa suka nufi parlon, tunda ta shigo kanta na k'asa ta kasa d'agowa ta zauna a Kujerar gefen wadda Abbas d'in yake yana dariya yace "Mom Zarah yau na zama surukin ki kenan" yamutsa fuska tay da k'yar tace mashi ina wuni ya amsa ta tambayi su Abdul da Aunty Feenah yace duk suna nan lafiya lau, da k'yar ta d'ago tace mashi sai yaushe zai kawo mata Abdul still da dariya akan fuskar shi yace tayi Yaya dashi ga baban Abdul d'in tana kulawa dashi ba shiri tasa hijab ta rufe fuskarta, tambayar ta yay ashe sun kusa fara Exams ta bud'e fuskar tace mashi eh yace to tana dai karatun ko ga Amarci kuma ta d'an juya kai ba tare data ce mashi komai ba, "Mom Zarah nace yanzu kin gamsu Ya Haisam na son ki yana son yin rayuwar Aure da ke ko" maida kanta tay k'asa da k'yar ta d'aga mashi kai ya sake cewa "ina Maganar rabuwa da shi to ko kuwa tunda yanzu kin gane his heart belongs to not only his wife Shikenan" da sauri ta k'ara rufe fuskarta tana fad'in "Wayyo Ya Abbas don Allah ka bari" dariya sosae yake Haisam dai na zaune yana murmushi, ce mata yay ya bari sannan ta bud'e fuskar, tunano mata Maganganun da suka yi a baya kan k'addara da hak'uri ya shiga yi yace gashi nan yanzu har taci riba sai d'aga kai take daga baya ya taya ta murna yace in akwae wanda yay farinciki sosae yadda Al'amarin ya kasance bayan ita to shine k'arshe yayi masu Addu'oi sosae tana ta amsawa a hankali, bayan ya gama yace "Yanzu Mom Zarah bazamu d'aga k'afa ba dole a biya mu d'an G.r.a d'in mu gaskiya" da sauri ta tashi ta nufi hanyar Bedroom da gudu Abbas d'in nata dariya. Bayan Magrib Haisam d'in ya dawo da K'aramin trolley d'in kayan daya d'aukko mata ta tarbeshi ta amshi kayan yace Hajiya na gaishe da ita tay murmushi kawae, saida akai sallar isha suka yi tare a cikin d'akin sannan yace ta shirya su fita, doguwar riga tasa tay rolling veil bayan ta gama suka tafi, wani babban Eatery ya kaisu suka ci Abincin bayan sun gama sun baro wurin wata plaza ya nufa lokacin da suka shiga bin wurin da kallo Fatuu tayi tana jin kaman tasan wurin bayan yayi parking a inda aka tanada yace mata yana zuwa ya bud'e Motar ya fita, daga baya ta tuna sun ta6a zuwa da shi lokacin da ya siya mata kayan gym, shagon ya shiga bada jimawa ba ya fito hannun shi ruk'e da yar babbar leda mai d'auke da tambarin wurin ya dawo, bayan ya bud'e Motar ya shiga a seat d'in baya ya aje abunda ya siyo ya ja Motar suka bar wurin, zagaya gari ya shiga yi da ita hannun su ruk'e dana juna suna ta hira irin ta masoya masu tsananin k'aunar juna saidai ita Fatun wani lokacin harda sokana sosae kuma yake jin dad'i in tana mashi sangarta, sai after 10 suka koma gida bayan ya siya mata su ice cream, a daren ranar kusan kashe juna sukai da love da alama yanzu ne suke shan Amarcin, Washe gari wurin k'arfe goma na safe lokacin suna ta shan bacci Tk ya kawo masu break fast kamar yadda Haisam d'in ya buk'ata da ya je d'aukko mata kaya, a waya ya kira Haisam cikin bacci yaji ringing d'in ya tashi, bayan yayi picking ya sanar dashi game da zuwan shi yace ya shigo da shi parlor ya aje, bayan ya gama wayar saukkowa yayi daga saman gadon Fatuu na cikin bacci ya sungumeta yay toilet da ita. Wuraren k'arfe sha biyu saura lokacin tuni sun gama yin Breakfast d'in har Fatuu ta gyara d'akin tana zaune a kan kujera jikinta sanye da k'ananun kaya riga da skirt tana danna Computer d'inta Haisam ya fito daga cikin Corridor d'in laundry room daga shi sai short ta d'aga kai ta kallo shi ya sakar mata murmushi itama ta mayar mashi, hanyar fita daga d'akin ya nufa ya bud'e kopar ya fita, bai jima ba ya dawo hannun shi ruk'e da ledar abunda suka siyo a Plaza dama ita yaje d'aukkowa a cikin Mota, nufo inda Fatun take yayi tana kallon shi ya iso kusa da ita ya zauna, fad'awa tay jikinshi tana murmushi ya lumshe mata ido ta kai hannu ta fara shafa kwantacciyar sumar chest d'in shi can ya d'agota ya kai hannu ya fiddo abunda ke a cikin ledar yace bari tasaka wannan, da kanshi ya fara cire mata kayan jikinta sai faman nonnok'ewa take ita ala dole kunya take ji sai kace ba wadda yake sullewa ba a toilet, da k'yar ta tsaya ya saka mata rigar sai bayan daya gama ta gane irin rigar da take gani mata na sakawa a cikin film in zasu yi swimming ce wato Swimsuit, rigar bak'a ce da ratsin Ash ba K'aramin karbar jikinta tayi ba kai kace don ita aka yi ta tayi mata k'yam daga gefe da gefe cikinta a bud'e yake farar fatar wurin ta bayyana haka hips d'in ma duka a waje suke a bud'e abun saidai ace Masha Allah ga cinyoyinta masu d'an k'auri farare tas suma duk sun bayyana har zuwa k'asan k'afafun, bin jikin nata tayi da kallo sai washe baki take don ita kanta taga yadda rigar tayi mata kyau sosae, komawa yay ya jingina bayan shi da kujerar fuskar shi d'auke da Murmushi yake k'are mata kallo, kallon shi tay cikin farinciki tace "Hubby how do I look?" lumshe ido yay ya furta "Sexy....." fad'awa tay jikin shi tana dariya, tambayar shi tay hakanan ya siyo mata ya d'an girgiza mata kai alamar a'a ya matso da kanta yay pecking lips d'inta kafin ya d'aga ta yace yana zuwa, kayanta da aka cire ya kwashe ya nufi hanyar corridor, mik'ewa Fatuu tay tana ta faman Jujjuyawa tana k'ara k'are ma kanta kallo sai dariya take, fitowa yay ya tsaya daga can yay mata alamar tazo da hannu ta juya ta nufi hanyar fita daga wurin kujerun, ganin ya kafeta da ido yasa ta canza salon tafiyar ta koma yin catwalk hakan kuma ba K'aramin fizgar shi ta rink'a yi ba tana k'arasawa wurin shi ya jawota jikinshi ta kyalkyace da dariya, d'ukar da kanshi yay saitin kunnanta ya rad'a mata why is she driving him crazy always......, d'agota yay ya kama hannunta suka nufi k'opar fita daga Bedroom d'in, cikin Main Parlor d'in gidan suka shigo suka bi wata bud'add'iyar k'opa wani Corridor d'in ne suka shigo yar tafiya kad'an sukai suka k'ara shiga wani parlon a ran Fatuu ta fara raya ashe dai gidan ba K'aramin girma ne da shi ba, fita sukai daga parlon suka k'ara bin wata hanya, sunyi yar tafiya kafin suka k'araso wata dakakkiyar kopa mai biyu Haisam d'in ya kai hannu ya bud'e suka bi ta cikinta, cikin wani Corridor suka shigo an rufe gaban shi da K'ayataccen Fence, bud'e kopar Fence d'in yay suka fara tatttaka wata yar matattakala da ke jikin wurin sai gasu sun fito bayan gidan, waro ido Fatuu tay tana bin wurin da kallo don bata ta6a zaton haka yake ba, bayan nada girma sosae gashi gaba d'ayan shi korayen ciyayi ne a k'asan wurin kaman dai grass carpet ne, daga gefe guda na wurin su lilo ne iri iri sai daga can d'ayan gefen sport field ne akwae wurin yin basket ball sai Volley ball, daga tsakiyar wurin wani d'an babban Swimming pool ne anyi mashi wani irin shape mai k'ayatarwa ga ruwan cikin shi sunyi sky blue gwanin sha'awa, kasa boye mamaki fuskar Fatuu tay sai washe baki take tana bin wurin da kallo tama kasa tsaida idonta wuri guda, wurin pool d'in suka nufa suna zuwa ya fara k'ok'arin fad'awa ciki da ita aikuwa ta saki wata irin k'ara a gigice ta fara tirjewa tana girgiza mashi kai gaba d'aya ta rud'e shi dama wasa yake mata ba fad'awa zasu yi ba tunda yasan bata iya ruwan ba, ganin yadda yasa hankalinta ya tashi yasa shi jawota jikin shi ya rungumeta sosae ya duk'ar da kanshi yana bata hakuri kawae sai ta fashe mashi da kukan shagwaba don sosae ta firgita nan fa ya shiga aikin rarrashi bayan ya samu tayi shiru nuna mata inda zata zauna yayi yace sai ta saka k'afafunta ciki zai koya mata yadda ake yi, a shagwabe ta mak'e mashi kafad'a tace ita tsoro take ji karta fad'a yace bazata fad'a ma ai ga k'arfe nan da zata ruk'e, da k'yar ya samu ta zauna ta saka k'afafun nata a ciki amman fa hannu bibbiyu ta damke k'arfen, d'an ja baya yay yayi tsalle yayi suka ciki the water splashed everywhere har a fuskar Fatuu da sauri ta runtse ido taja numfashi, diving ya shiga yi cike da k'warewa Fatuu sai washe baki take tana daga zaune sosae ya burgeta yadda yake iyo acikin ruwan cike da salo daban daban har tsuma take saidai daga iya nan, ya d'an d'auki lokaci yana yi kafin ya tsaya a gabanta sumar shi ta kwanto har ta rufe mashi ido saida yasa hannu ya janye ta, lalla6a ta ya shiga yi kan ta shigo zai ruk'eta ya koya mata yace mata ruwan baida wani zurfin sosae, yarfa hannu ta shiga yi tana d'an ta6e baki a shagwabe take fad'in ita wllh tsoro take ji yace karta da mu ba abunda zai faru, da k'yar ta yadda ya kamo ta ya shigo da ita still hannunta d'aya na ruk'e da k'arfen, k'arshe dai daga koya ruwan sai aka 6uge da zazzafar soyayya suka shiga romancing juna passionately. Saida aka fara kiran sallar Azahar suka baro wurin sosae sukai enjoying moment d'in. Da daddare yau ma fita suka k'ara yi cin Abinci, bayan sun dawo tare suka shirya cikin kayan bacci sai lokacin Fatuu tayi tunanin yin karatu don ranar Monday tana da test, jakarta ta d'aukko ta nufi wurin kujeru ta zauna ganin haka yasa Haisam fita ya koma parlor don ya bata wuri Saboda yasan in dai tana ganin shi ba lalle tayi karatun ba , tana cikin yin karatun Haisam d'in ya shigo ya nufo inda take hannunshi ruk'e da wayar shi ta d'aga kai tana kallon shi, mik'a mata wayar yay yace "My Mom zaku yi Video call" d'an zaro ido Fatuu tay ta d'an yamutsa fuska tay mashi nuni da kayan jikinta da kuma kanta da ba kallabi da kai yay mata alamun ba komai, dole ta amshi wayar a kunyace ta kalli screen d'in tana ganin Fatun ta sakar mata murmushi itama ta d'an yi mata gaidata tayi tana ta murmushi ta amsa kafin tace "My Daughter hope you are doing well" kai Fatun ta d'aga mata kafin a hankali tace yes, gaba d'aya ta kama kanta har Mom d'in ta fahimta tay yar dariya tace mata ta saki jikinta ita Mom d'in ta ce Fatun tace to, tambayarta karatun ta tayi tace taji sun kusa fara Exams Fatun tace eh ranar Wednesday tayi mata fatan sa'a, tambayarta ya grandma d'inta da sauran yan uwan ta tayi tace mata duk suna lafiya, d'an shiru sukai sai murmushi suke ma juna can Mom d'in tace "Ok, bari in bar ki ance kina karatu ne kiyi sosae Allah ya bada sa'a" amsa mata tayi da "Amin Momy Nagode" d'aga mata kai tayi kafin tace mata saida safe itama tace mata haka, mik'a ma Haisam dake zaune gefe wayar tay ta d'an gwalo ido yay murmushi ya amsa, cigaba da Magana sukai saidae da larabci suke dama Fatun tasan yana Magana da ita da larabci harda ma wani yare nasu na Ethiopia kamar fulatanci Saidai shi Haisam d'in bai jin shi sosae in tana mashi yafi maida mata da Hausa ko turanci sai jefi jefi yake yi mata wanda ya iya, daga baya turanci suka koma yi suna cikin Magana Mom d'in ke ce mashi tunda ta kusa fara Exams d'in ya tura measurements d'inta da kuma size na takalmanta harda na undies yace Ok daga baya suka yi sallama, suna gama wayar ya juya ya kalli Fatuu itama ta d'ago ta kalle shi ta d'an yamutsa mashi fuska, d'age mata gira yay yace "What?" A shagwabe tace "ba karatun bane yak'i shiga sai ma wai inta ganin fuskar ka a littafin" baisan lokacin da yayi dariya ba yace shidai karta ja mashi sharri shida har space ya bata don tayi karatun, k'ok'arin mik'ewa ya fara yi yana fad'in bari ya k'ara bata wuri aikuwa da sauri ta nufo shi ta k'ank'ame shi tana fad'in ba inda zaije bacin ko bai nan karatun ba shiga yake ba ita dai yasa ta daina ganinshi a jikin littafin, sai ga abu ya zama kamar kokowa k'arshe suka baje a k'asa daga nan dai aka gama karatun. Washe gari ma Tk ne ya kawo masu break fast bayan sun gama ci Fatuu ta fitar da kayan Kitchen ta wanke komai, lokacin data dawo Haisam na Zaune saman kujera yana operating laptop d'in shi, d'aga kai yay yayi mata alamar ta zo ta nufo shi jikinta sanye da doguwar riga roba ta bi shape d'in jikinta, zama tayi a kusa da shi yana kallonta yace ta d'aukko bag d'in ta tazo tayi karatu tace to, bayan ta d'aukko a gefen shi ta zauna ta fara yin karatun, sun d'an d'auki lokaci a haka can Haisam ya dakata da aikin da yake ya jingina da kujera yana yin hamma Fatuu ta juya ta kalle shi tace ya gaji ya lumshe mata ido, hannu ta kai tana k'ok'arin kwanto da shi tace ya kwanta to ya huta, a saman laps d'inta ya kwantan ita kuma taci gaba da karatun tana yi tana d'an kallon shi idanun shi a lumshe, bai dad'e da kwanciyar ba ta aje book d'in ta kai hannu tana cakud'a sumar shi tace "Hubby wllh gashin nan naka in aka maka kitso ba K'aramin tsawo zai yi ba, slowly ya d'an bud'e idon shi suka sauka cikin nata, d'age mashi gira tayi tace "in maka kalaba ka gani" still yay yana kallon ta fuskar shi a d'an sake gaba d'aya in tana mashi abu koma mashi take kamar yar shekara ukku zuwa hud'u, ganin ta kafe shi da ido alamar jiran amsa take yasa calmly yace "bazaki karatu ba ko?" tura baki tayi tana yamutsa fuska tace "ai nayi fa da yawa kuma ya zauna yanzu, don Allah in maka kitson?" d'an murmushi yay kaman bazai ce komai ba sai kuma ya d'aga mata gira alamar eh, washe baki tayi ta sauke kanshi ta sauka daga saman kujerar tana fad'in bari ta d'aukko comb, bata dad'e ba ta dawo ta koma saman kujerar ta haye gaba d'aya ta juya ta maida kan saman cinyoyin nata, tambayar shi tayi tace "wane iri zan maka, shuku ko fashin kwakwa ko shade ko kuma 2 step, ko dai ma ayi na fulani?" Bai san lokacin da ya saki dariya ba ko ina shi yasan wani style d'in kitso, ce mashi tay ya fad'i idanun shi a lumshe yace tayi kowanne take so, yamutsa sumar ta fara can tace "kai wllh ta cika santsi ko anyi ma kitson ba zai zauna ba, bari kawai ayi kalaba sai in tuk'e bakin ta sosae yadda ba zai kwance ba" shidai murmushi kawae yake ta hau yi mashi kalabar, sosae yake jin dadin yadda take cakuda gashin sai gashi har da bacci, tana gamawa ta sa dariya tana fad'in wllh kan yayi kaman na mace, kiran sunan shi ta shiga yi cikin bacci ya jita slowly ya bud'e idon cike da murna tace ta gama ya tashi suje gaban mirror ya ga yadda ya koma wllh yayi kaman mace, ba yadda ya iya dole ya mik'e tana ruke da hannun shi suka nufi gaban mirror, tsaye yay yana kallon kan nashi da tayi ma kalaba yar manya manya sun zuba mashi ta gefe he couldn't help it but laugh, sosae itama Fatun ke dariya yana kallonta ta cikin mirror d'in, kasa daurewa yay ya jawota jikinshi......., Duk yadda yaso ya k'yaleta don tayi karatu ya kasa, k'arshe dai kalabar da kanta ta warware kanta sai d'an tukku tukkun ta, duk suna sanye da bathrobe suka dawo cikin d'akin daga toilet, kan front chair ta gaban mirror d'in yasa ta zauna da kanshi ya shafa mata mai ya d'aukko hand dryer ya fara busar mata da gashinta, bayan ya gama mata itama sawa tayi ya zauna ta fara yi mashi kamar yadda yayi mata tana busar mashi da gashin cike da tsokana ta k'ara cewa ta k'ara yi mashi kalaba d'in yayi mata wani kallo mai kaman harara tasa dariya, Bayan sun gama laundry room suka nufa don su saka kaya, wata rigar shi armless ta saka ta d'an saukko mata saidai duk cinyoyinta a bayyane suke, shima armless ya saka da wando 3 quarter, ce mashi tayi yaje parlor ita zata tsaya ta wanke Uniform d'inta yace bari suyi tare, a cikin washing machine suka fara yin wankin suna cikin yi tace mashi tana zuwa ta nufi hanyar fita da d'an sauri sauri gudu gudu, bata jima ba ta dawo hannunta ruk'e da wayarta ta fara lallatsata, wak'ar Hamisu breaker ta so gaskiya ne ta kunna tana bala'en son wak'ar tun lokacin da tana cikin yin ciwon so duk inta jita sai taji kaman don ita aka yi ta, tana ruk'e da wayar ta kwanta a bayan Haisam d'in tana bin wak'ar kai kace ita ta raira ta shidai sai murmushi yake yana yin wankin, bayan ta k'are wak'ar muradin zuciya itama ta breaker d'in ce ta shiga har saida ta runtse ido don itama wak'ar tana son ta, sakin Haisam d'in tayi ta koma gefen shi ta yadda zata rink'a kallon fuskar shi ta fara bin wak'ar, " _Burin zuciyaa, had'a da idaniyaa, su samu ganin ka yaaaa mai saka nayi dariyaaa, muradin duniyaaa son ka har yay lubiyaaaa a son ka duka zuciyaaa ta na bar maka taka ce.....🎼_ " tana yi tana nuna shi sai murmushi yake, can da tayi baitin " _Kai nike so....._" dakatawa tay ta turo mashi baki a shagwabe tace "Hubby kai ma ka rink'a yi man in nace _Kai nike so....._ sai kace _Na saniii...._ " bai san lokacin da yayi dariya ba slowly yace ai bai iya shi ba, sake kunna wak'ar tayi ta kanga mashi saitin kunne tace gashi nan ya saurara ya iya, wai aka ce kowa ya sayi rariya yasan zata zubar da ruwa😂 dole d'an Senator gwanin kamewa ya iya haka ya rink'a amsa mata Fatuu sai dariya take sosae abun ya sakata nishad'in, lokacin da aka zo kan baitin da take cewa " _....So nike ka zamo miji, a garan kai agaji..kaga ba wani jan aji...._ " tun kan ta k'arasa ya katseta da fad'in "ai nayi wannan ko" kyalkyacewa tayi da dariya ta fad'a jikin shi, haka dai akai ta shiriritar yin wankin k'arshe abun harda su yar watsa kumfa. Bayan sun gama cikin d'akin suka fito suka zauna akan doguwar kujera Haisam d'in yace bari ya kira mata Auntie d'in ta su gaisa tace toh, kiran Fanan d'in yay Video call ta cikin laptop Fatuu na gefen shi, suna ta ma juna murmushi Fanan d'in na zaune ta jingina da gado jikinta sanye da k'ananun kaya kanta ba kallabi, bayan sun gaisa suka shiga yin hira da Fatun shi sai jefi jefi yake saka masu baki har tana ce ma Fatuu wai ya Amarci tana dai kula da babe d'in sosae ko ita dai murmushi kawae tay, sun d'auki lokaci suna yin wayar cikin firar take ce ma Haisam sun yi magana ai da Mom da Dad harda Jidderh ma ta fad'i mata Maganar bikin da za'ayi tace harda anko in suka fidda za'ayi mata a can, da yanayin jin dad'i take Maganar shima Haisam d'in sosae yaji dad'i ba kamar data ce Mom da Dad d'in shi sun kirata, ita dai Fatuu bata fahimci Maganar bikin da suke ba don Haisam d'in bai fad'i mata ba, bayan sun gama ne ta tambaye shi wane biki za'ai ya fad'i mata har saida ta d'an waro ido alamar mamaki, tambayar lokacin da zasu gama Exams d'in yayi tace mashi zasu yi 2 weeks don harda practicals, kai ya jinjina sai kuma ya tambayeta ai Kb tailor nada measurement nata ko tace mashi eh, tambayar ta size na Undies nata yay don yasan na takalman da take sakawa, shigar da fuskar ta tayi a jikin wai kunya aikuwa ya kai hannu ya d'an ta6a gefen cikinta ta wani gantsare tana dariya kafin ta fad'a mashi. A daren ranar ya d'auketa suka fita siyo abun da zasu yi breakfast don gobe da wuri zasu tashi Saboda tafiyarta Makaranta. Washe gari tare suka yi sallar Asuba bayan sun gama komawa sukai suka kwanta Fatun nace mashi ya bari ta tashi tayi Breakfast yace karta damu zai yi ganin zata mashi rigima ya fara k'ok'arin sata yin baccin, ba'a d'auki lokaci ba ta koma baccin shi kuma ya mik'e ya nufi Kitchen, saida ya gama sannan ya tasheta, da kanshi ya rink'a bata a baki har ta k'oshi sannan aka hau shirin zuwa Makarantar dama tun da daddare ya goge mata Uniform d'in. Bayan taje Makarantar sosae Fauzy ta shiga tsokanar ta tana fad'in lalle da gani ba k'aramar soyewa sukai ba shiyasa ma ko tunawa da ita bata yi ba ace cikin kwana biyu ta k'ara canzawa har haske ta k'ara harda cewa Allah yasa hasken na rabo ne ita dai Fatuu dariya kawae take. Bayan an tashe su shi yazo ya dauke ta suka biya aka d'auki Mino tana ta murnar ganin Adda d'inta data kwana biyu bata gani ba, gidan Hajiya suka wuce don ya lura a G.r.a bazata yi karatun jarabawar ba sosae. Bayan komawar su sosae yake d'aga mata k'afa don tayi karatun yana kuma taimaka mata wurin k'ara yi mata bayanin wani abun da bata gane ba, a kwana a tashi ba wuya tuni sun fara jarabawar har ya rage saura yan kwana ki su gama, bayan sun fara da sati guda ne Haisam ya tafi Lagos wurin Fanan kwanan shi hud'u ya dawo, Ana saura kwana biyu su gama ranar laraba ya gama yi masu shirin zuwa Abuja harda Hajiya za'a tafi da sun gama jarabawar da kwana d'aya wato ranar Juma'a har su gwaggo sun san da zancen tafiyar don har an buga IV na programs d'in da za'ayi an aiko masu da shi IV d'in mai shegen kyau date d'in da za'ayi ya kama bayan gama jarabawar Fatuu da sati d'aya wato ranar Juma'a ta sama, cikin sa'a su Fatuu suka gama jarabawar sai farinciki suke lokacin Fauzy ke mata Maganar anko tace ta bari zata ma Jidderh magana in sun fiddo sai ta turo hoton shi, a ranar bayan Haisam yazo ya d'auketa sun koma gida ba K'aramin faranta ma juna sukai ba, da daddare ya d'auketa suka fita, shagon Kb mai d'inki suka fara zuwa ya amshi d'inkin dandatsetsen lace d'in daya bada a d'inka mata ita da Hajiya wanda ko ita Fatun bata san daya bada ba, sosae tayi murnar d'inkin gashi an mata Fav d'inkin ta wato straight skirt da riga fefflon irin mai bud'ewa daga k'asa yar daidai daidai hannun ma wani irin style akai mashi gwanin burgewa Hajiya ma riga Boubou akai mata harda kwalliyar bakin lace, sosae Fatuu tay murnar d'inkin abun yazo mata a surprise, bayan sun bar nan shagon Zee Collections suka wuce dama a wurinta ya siya leshin lokacin data kawo ba Jaka da takalma da gyalen da zasu hau dashi tace zata kawo mashi, cikin faran faran kaman ko yaushe ta tarbe su bayan sun zauna harda ita suka gaggaisa cike da nuna farinciki tace ma Fatuu ashe dai fatan su ya tabbata tace tayi murna sosae wllh data ji zancen Auren nasu, ita dai Fatuu murmushi kawae take Zee d'in tace ai in sha Allahu zata je Abujar, daga baya ta d'aukko mashi sak'on sukai sallama ta rako su waje. Saida suka tsaya wani Eatery ya siya mata kayan kwalama sannan suka wuce gida. Ranar Friday bayan gama sallar Juma'a suka hau shirin tafiya, sabon lace d'in wanda red color ne da torch d'in ash Fatuu ta saka sosae yay kyau d'inkin ya hau dashi Over, light make up tayi ta parker gashinta ta k'asa da ribbon dark ash, d'aurin kallabi Zarah buhari tayi ta yadda tulin gashinta ya lek'o ta k'asa, gaba d'aya jewellery d'in da ta saka silver ne suma sababbi ne masu tsada, bayan ta gama ta d'aukko takalman wanda ankle strap ne irin masu igiya da tsini sosae sai purse d'in su mai d'aukar ido gaba d'aya ash ne kalar kwalliyar lace d'in, Haisam bai nan ya tafi G.r.a ya dawo tuni shima ya gama shiryawa da ya dawo tafiya zasu yi, bayan ta gama shirin hanyar fita ta nufa jin ta take tamkar wata sarauniya sai faman murmushi take, tana shigowa cikin parlor Mino ta shigo tazo yin rakiya su sai cikin sati mai zuwa zasu je, waro ido tay ganin ta haka da mamaki ta "Furta Adda Fatuu kece haka!" Dariya kawae Fatun take ta taho da d'an gudu gudu tana zuwa ta rungumeta tana fad'in wllh tayi kyau sosae, part d'in Hajiya tace mata suje Minon tace dama gwaggo ma na can itama tazo yi masu rakiya Airport, lokacin da suka je itama Hajiya ta shirya cikin nata lace d'in duk suna zaune a parlorn harda Saude da Tk nan fa aka hau yabon gayun Fatun har Hajiya na fad'in wato Saboda son kai na Haisam shine ita akai mata d'inki mai kyau ita kuma akai mata burgujejiyar riga ai da itama sai ayi mata irin na Fateemar ta cakare duk suka sa dariya, a gefen gwaggo ta zauna suka gaisa, bata dad'e da zuwa ba Haisam d'in ya dawo yana sanye da farin danyen voile haka takalman shi da agogon shi duk farare ne, gaisawa sukai yace ma Hajiya in sun gama zasu iya tafiya tace to duk suka mik'e idon shi akan Fatuu dake sakar mashi murmushi, a gaban shi ta tsaya bayan duk sun tafi ya lumshe ido Slowly ya furta tayi kyau tace ai shi yasa tayi kyaun, tambayarta yay an fiddo kayan su tace a'a yace Ok suje suka nufi hanyar fita, bayan sun fito Tk yace ma ya biyo shi suka nufi part d'in nasu, basu d'auki lokaci ba suka dawo Tk na janye da trolley d'in Fatuu da wata jaka Haisam ma na janye da madaidaicin trolley, a boot aka saka su, Hajiya da gwaggo da Saude suka shiga Jeep Tk ne zai ja sai Mino da Fatuu da Haisam suka shiga k'aramar Mota Officer ne zai ja su, bayan duk sun shiga Motocin suka tunkari gate, bayan sun fito a daidai shagon Amadu Tk ya tsaya don shima yace mashi zai yi rakiyar, fitowa yayi bayan ya kulle shagon ya shiga gaban Motar sannan suka tafi, suna hanya Fauzy ta kira Fatuu ta tambayi sun fito tace mata eh tace to su had'e a Airport d'in, basu dad'e da isa ba Fauzy ta k'araso nan aka hau yin sallama yau su yar Fillo za'a hau Jirgi.......... *ASM 079* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........A business class na jirgi Suke kowa da kujerar shi ta Fatuu na kusa data Haisam sai Hajiya na daga d'an can gefe da yake kujerun ba had'e suke da juna ba saidae ta Haisam data Fatuu gab d'in su kad'an ne, in ka kalleta bazaka ta6a cewa hawa jirginta na farko bane don bata nuna wani k'auyanci ba amman fa gaba d'aya a tsorace take tun farkon ganin jirgin kafin su shigo yadda ta ganshi wani gingimeme dashi bata zaci haka yake ba don bata ta6a ganin shi a fili ba sai a sama kuma bai kai girman haka ba take ganin shi, sai faman d'an wuwwurga ido take tana k'are ma wurin kallo ta yadda baza'a ga k'auyancin ta ba dama kuma basu da yawa a class d'in kowa kuma harkar gaban shi yake, hannu Haisam ya kai ya kamo hannun ta da sauri ta kalleshi yay mata murmushi itama ta mayar mashi, nuna mata yadda zata saka seat belt in an sanar da ayi hakan ya shiga yi bayan ya gama yace tasa ya gani hannunta har d'an rawa yake ta shiga sakawa bayan ta gama ta kalle shi, murmushi yay mata ya jinjina mata kai had'i da d'an lumshe ido a hankali yace ta cire, ba'a dad'e ba aka sanar ai fastening seat belt ba 6ata lokaci Fatuu tasa har saida ta kalli Haisam yay mata murmushi, lokacin da jirgin ya fara tafiya wani irin bugu k'irjinta ya fara yi da zai d'aga sama ba shiri ta sauke kanta ta runtse idanunta da k'arfi Haisam ya kai hannu ya ruk'e nata da k'arfi, bayan ya kai kololuwa ya mik'i hanya ta bud'e idon ta juya ta kalle shi slowly ya furta "Are u okey?" Kai ta d'aga mashi ta d'an tsuke baki da d'an waro ido hakan har saida yasa shi yin yar dariya, daga baya sai gashi ta saki jiki taci gaba da yin kallo ma ita kuwa Hajiya ma d'an kishingid'awa tay idanunta a rufe da alama bacci take, Lokacin da suka iso bayan an sanar sun maida seat belt tun kan su k'araso yadda tayi da zai tashi haka ta k'ara yi da zasu sauka saidae na yanzu ma yafi don kamar zata sa kuka jikinta har rawa yake Haisam d'in ya k'ara ruk'e hannunta gam har jirgin ya tsaya sannan yace ta Kantar da hankalinta sun iso ta bud'e idanun tana numfarfashi, shi ya cire mata seat belt d'in tana mik'ewa tace mashi juwa take gani ya maida ta kan seat ya zaunar da ita Hajiya ta matso tana tambayar Yaya ko amai take ji yace mata a'a she feels dizzy, sannu Hajiyar tayi mata tace ai tama yi kokari tunda boarding d'in ta na farko ne wasu da zasu yi ta amai wasu harda bayan gida, bayan d'an lokaci ta mik'e cike da kulawa Haisam d'in yace mata zata iya tafiya tana murmushi ta d'aga mashi kai Hajiya sai sannu take mata, Haisam na janye da trolley d'inta dana Hajiya ita kuma tana ruk'e da K'aramin nashi sai Hajiya na ruk'e da yar madaidaiciyar jaka a hannunta d'aya d'ayan kuma tana dogara sandar ta ba yadda Fatuu bata yi da ita ba ta bata jakar ta ruk'e tace mata ta barshi zata iya, suna isowa Arrival Jidderh da Nameer da suka zo tarbar su suka hango su, da gudu Jidderh ta nufe su tana sanye da Turkish dress riga da wando pink colour ta yafa gyalen a saman kanta gaban bak'ar sumar ta ya d'an fito Nameer kuma na sanye da k'ananun kaya jeans da t-shirt duka Navy blue ba K'aramin kyau yayi a cikin kayan ba sun k'ara fito mashi da hasken shi gashi ya k'ara girma ya zama cikakken saurayi sumar shi shima dake a nad'e sai salk'i take duk da bata kai yawan ta Haisam ba, tana zuwa ta rungume Fatuu tana fad'in "Oyoyo sis Fatuu our bride" dariya kawae Fatuu ke yi, Nameer na k'arasowa ya nufi Hajiya ya rungumeta yana sakin k'ayataccen murmushi, bayan ya saketa tana yar dariya tace mashi yaushe ya dawo K'asar yace mata ranar laraba shima yazo biki ne tambayar shi Laila tayi yace mata itama tazo, sakin Fatuu Jidderh tay suna ma juna dariya tayi mata sannu da zuwa bayan ta amsa ta juya kan Hajiya tace "Welcome granny" yar harara Hajiya ta wurga mata tace sai yanzu zata yi lokacin ta da sauri ta nufeta ta rungumeta tana fad'in tayi hak'uri, kallon Haisam Nameer yayi yana murmushi yace "Welcome Big Bro" yana murmushi shima ya jinjina mashi kai kafin yace mashi yazo lafiya ya karatu ya amsa mashi, kallon Fatuu yay suka had'a ido tana mashi murmushi kawae sai gani tay ya d'an harareta sanin halin shi yasa bata ji komai ba taci gaba da yin Murmushin, Jidderh ce ta amshi trolley d'in hannun Fatuu shi kuma Nameer ya amshi jakar hannun Hajiya da trolley d'aya na hannun Haisam suka nufi hanyar barin wurin, ganin Nameer abu biyu ne hannun shi yasa Fatuu komawa kusa dashi tace "ka kawo jakar in ruk'e" hararar tata ya k'ara yi tana murmushi tace "laifin mi na maka ne kake ta hararata?" k'asa k'asa da murya yace "ai kin fi kowa sani, don wulakanci kin san ina son ki shine zaki auri big bro d'in mu" ba shiri Fatuu tay yar dariya sai kuma ta girgiza kai tace "wllh Nameer baka Ji Allah ya shirye ka" wani kallo yay mata yace "dole kice haka ai tunda kin yaudare ni" ya k'arasa Maganar tare da d'an murgud'a mata baki ita dai murmushi kawae take, wata dank'areriyar Jeep ce suka zo d'aukar su da ita, Hajiya da Fatuu da Jidderh suka shiga baya Jidderh ce a tsakiya sai Haisam a seat d'in gaba Nameer ya zauna driver seat bayan duk sun rufe kopopin yaja suka tafi, suna a kan hanya Hajiya ke tambayar Dad d'in su yace tunda yaje Masallaci bai dawo ba amman k'ilan da suka taho ya dawo, Jidderh sai jan Fatuu da hira take da sun had'a ido da Nameer ta mirror sai ya fakaici idon mutane ya harareta ita dai murmushi kawae take, Lokacin da suka iso gidan tun a babban gate Fatuu ta sha jinin jikinta ganin had'uwar gidan ga Jami'an yan sanda da civil defence dake tsaron gate d'in, ko tsaida su basu yi ba ganin Motar gidan ce suka shige, yar tafiya sukai suka k'araso wani gate d'in na k'arafa wanda ana hango cikin gidan ta cikin shi kuma a bud'e yake masu gadi biyu ne ke tsaron shi suka shiga d'aga ma Motar hannu da zata shiga, suna shiga suka nufi roundabout suka sha shi bai nufi parking space da su ba sai ya tunkari dank'areren ginin gidan, a gaban Entry Hall ya parker Hajiya ta furta Alhamdulillah ta bud'e k'opar, jiki a mace Fatuu ta bud'e ta side d'inta ta fito, wasu daga cikin ma'aikatan gidan ne jikinsu sanye da brown uniform suka nufo su don d'aukar kaya suka shiga yi masu sannu da zuwa suna d'an rankwafawa Fatuu dai sai wurga ido take, Haisam ne ya zo wurinta ta kalle shi yana murmushi yace mata su shiga kai kawai ta d'aga mashi suka nufi shiga cikin gidan, suna shiga hall d'in sai ga Senator ya fito dasu Momyn Haisam harda Aunty da Laila da sauran yaran gidan duk sun sha gayun Juma'a manyan na sanye da had'addan lace, iyayen dogayen riguna ne Laila kuma riga da skirt haka Yasmeen ma, a gaban su duk suka tsaya kowa fuskar shi da fara'a Senator dake sanye da riga da wando na farar shadda da gani yan cikin babbar riga ne ya cire babbar rigar yana faffad'an murmushi ya Mik'o hannu yana fad'in "You are Welcome My Daughter" ganin hannun da ya Mik'o yasa a sanyaye Fatuu ta k'ara matsawa kusa dashi ya dafa Shoulder d'inta kanta a k'asa ta gaishe dashi ya amsa yay mata ya hanya tace Alhamdulillah, nuna mata su Aunty yay yace taje su gaisa ta nufe su ta tsaya a gaban su, d'an rankwafar da kai tayi tace ma Mom d'in ina wuni tana murmushi ta amsa ta kawo hannu ta rungumo ta jikinta tace "Marhaban bik ya aibnati" d'agota tay ta nuna mata Aunty ta nufeta itama ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tana murmushi tace "Sannu da zuwa Daughter munyi farin cikin ganin ki" a hankali ta furta mata ta gode, Laila ce ta Mik'o mata hannu ta nufeta itama rungume ta tayi tana Fad'in "We're Welcome our bride" bayan ta d'ago ta suna ma juna murmushi ta furta mata Thank you, Hajiya ce dake tsaye tace "to in kun gama tarbar sabon jini sai ku ba tsohon jini hanya ta wuce kafin ta fad'i" Senator na dariya ya matso kusa da ita ya rungumota jikin shi tana fad'in sai da tayi magana sannan ya ganta, sosae ya rungumeta gaba d'aya ta shige cikin jikinshi kanta ko kafad'ar shi bai kai ba gaba d'aya sai dariya ake masu, bayan ya saketa ne su Mom da Aunty suka shiga gaishe da ita suma duk saida tay masu mitar sai yanzu zasu yi lokacinta wato don sun samu sabon jini shine suka shareta, suna dariya duk suka bata hak'uri, Jidderh ce tace ma su Yasmeen bazasu yi ma sabuwar Yayar su sannu da zuwa ba duk suka yi murmushi suna kallon Fatun suka hau yi mata Welcome tana murmushi take amsa masu kafin ta tsaida kallon ta akan su twins dake ta faman kallon ta sun girma sosae don yanzu zasu yi shekara tara, ganin suna ta kallon kallo yasa Jidderh cewa "ko baku gane sis Fatuu bane genie d'in ku" ta k'arasa tana dariya suma yar dariya suke sun san ta amman sun manta da lokacin da suka ce mata genie d'in, ganin ana ta tsayuwa yasa Hajiya cewa to a shiga ciki mana sai a gaisa sosae duk suka nufi ciki, ganin yadda su Mubeen da Mubeena keta kallon ta yasa ta kama hannuwan su suka shiga, bayan sun shiga mai parlor d'in sosae Fatuu ta raina kanta Saboda had'uwar parlon da irin dukiyar data ga an narka a cikin shi, bayan sun zazzauna aka shiga k'ara gaisawa Senator ya kalli Fatuu da murmushi yace "muna matuk'ar farincikin kasancewar ki cikin wannan family d'in muna fatan ki zamo Alkhairi a cikin shi" tana ta murmushi tayi mashi godiya duk idon kowa na a kanta da murmushi suke kallonta, kallon Hajiya yay yace "Hajiyata table ashirye yake muje sai ku ci Abinci ko" ce mashi tay ba wata yunwa suke ji ba sun ci snacks da lemu a jirgi a bari su d'an kara hutawa ya ce to, mik'ewa Laila tayi tana kallon Fatuu da murmushi tace suje ciki ta huta zumbur Jidderh ta mik'e a shagwabe tace d'akinta zata ta huta gaskiya, d'an bud'a ido Laila tayi Senator na dariya yace "Jidderh fa ba K'aramin ji take da Yayar nan tata ba indai tana kusa ban tunanin zata bari wani yayi mata wani abu" juyawa Laila tayi ta kalle shi tace "I see Dad" komawa tay ta zauna Jidderh ta na murmushin jin dad'i ta kama hannun Fatuu data Mik'e tace suje, ganin su twins ma sun mike yasa Fatun mik'a masu hannu tace su taho suka nufeta suna murmushi, bayan sun fito daga wurin kujerun Jidderh ta nuna kayan su tace wanne ne nata a ciki ta nuna mata, sakin hannunta tayi taje ta d'aukko trolley d'in da jakar Fatun ita kuma ta kama hannun su twins dawowa tayi tace ma Fatun suje, bayan tafiyar su Mom d'in su ta mik'e tace ma Hajiya suje ta huta ta mik'e Aunty ma da Laila suka mik'e suka tafi, kallon Haisam Senator yay yana murmushi yace "Ango kasha k'amshi" murmushi kawae yay haka ma Nameer, cigaba yay "dama inata son in yi maka magana amm....akwae wanda akace ya tsaya maka wurin d'aurin Auren ka ina tunanin yakamata yazo Walima da za'ayi" shiru haisam ya d'an yi kafin yace suna communicating da Abbas dama yana niyyar ya samu time yaje yayi ma shi godiya Senator yace to sai a tuntu6e shi aji in zai iya samun zuwa daga baya sai yaje har gida yayi mashi godiyar yace to, k'ara cewa yay "sai relatives d'in ita matar taka suma yakamata su zo, kayi mata magana kaji in sun yi zasu zo sai a tura masu Mota ta d'aukko su kawae" kai Haisam d'in ya jinjina suka cigaba da yin fira yana tambayar Nameer karatun shi na Software Engineering wanda Haisam d'inne yasa ya karance shi Saboda Company d'in da yake so ya bud'e. Wani corridor suka shiga sukai yar tafiya nan suka k'araso bakin wasu kopopi dake opposite da juna Jidderh ta tura ta 6angaren hagu ta juyo tace ma Fatuu ta shigo, d'aki ne mai d'an girma akwae madaidaicin gado daya sha bedsheet da side drawers d'in shi da dressing mirror sai wall cabinet sosae d'akin ya tsaru yasha decorations su frames da artworks da flowers harda wall stickers ga labulayen ciki ma masu kyau fentin d'akin ma kusan kala ukku ne amman yadda akai masu wani design sun k'ara k'awata dakin , suna shiga Jidderh ta juyo tace "Welcome to Jidderh's palace" jinjina kai Fatuu tay tana murmushi Jidderh tace "ya kika ga d'akin nawa" Fatuu tace "it's a beautiful palace gaskiya ya tsaru" dariya Jidderh tay tace ta gode, bayan ta aje trolley d'in a gefe ta nuna ma Fatuu gado tace ta zauna itama a gefe ta zauna su twins suka saka Fatun tsakiya, "Kinsan abunda nike karanta kenan interior design yanzu haka na kusa gamawa kuma ina gamawa zan tafi Dubai in k'ara yin wasu courses d'in kan hakan, so nike in bud'e babban company in nagama da zai rink'a supplying kayan decorations irin su furniture, labulaye, carpets, flowers harda fitilu da dai sauran su sannan kuma ba iya saidawar ba harda tsara wuri kamar gidaje, Offices, Hotel rooms da dai sauran su" Fatuu nata jinjina mata kai har ta gama sannan tace gaskiya tayi tunani mai kyau don irin aikin na kar6uwa yanzu Jidderh d'in tace sosae ma, kallon su twins tay ta d'an d'aure Fuska tace "wai ku bazaku k'yaleta ta huta ba ku tashi ku tafi tunda kun gaisa" mak'e mata kafad'a sukai suka tura mata baki sai kace ana latsa masu remote komai a tare suke Fatuu ta kai hannu ta rungumo su jikinta tace ta k'yale su ai an dad'e ba'a had'u ba, Jidderh na murmushi tace "koda yake suma zauna kita kallon su pls ki haifo mana irin su amman ba masu irin halin su ba don sai su haukata ki kullum cikin ba mutane ciwon kai suke" tana rufe baki suka murgud'a mata baki ta yunk'uro zata make su suka k'ank'ame Fatuu suna dariya itama dariyar take tace ma Jidderh tayi hak'uri don Allah, mik'ewa tayi ta nufi wardrobe, bud'eta tayi ta kai hannu ta fiddo wasu kaya dake a goge bayan ta rufe ta nufo gadon, a kan cinyar Fatuu ta d'aura su tace "kinga anko d'in da akayi na Walima da Dinner" sakin jikin su twins tay ta kai hannu ta fara d'aga kayan Jidderh tace ta warware mana ta gan su sosae, atamfar ta fara warwarewa sosae ta burgeta saidai da gani bata rasa kud'i, kallon Jidderh tayi tace "amman dae tayi kyau wllh" tace "sosae ma Chiganvy gold mix and match embroidery ne" jinjina kai Fatuu tay sai kuma ta tambayeta nawa take tace "kinga atamfan kaman kashi ukku ne, mutum zai iya yin Chiganvy gold d'in kawae ko yay mix and match da embroidery d'in ko kuma yayi embroidery d'in kawae gaba d'aya dai duka Atamfa kala d'aya ce ai kin gani kawae ita wannan normal atamfa ce mai gold ita kuma d'ayar sai akai mata aiki gaba d'aya jikinta, so mutum in yayi mai mix d'in zai iya ai mashi style mai kyau da mai aikin da mara aikin kaman yadda akai man, in Normal Chiganvy gold d'in mutum zai yi just 18k ne in kuma mix and match d'inne 37k sai kuma mai gaba d'aya embroidery 50k, su Aunty Laila mai gaba d'aya sukai nima naso ayi man ita amman aka k'i saida aka d'inka man mix and match d'in kuma sukai ta cewa dama ita sukai" ta k'arasa tana murmushi itama Fatuu murmushin take kafin ta tambayi lace d'in tace shi 35k yake, shiru Fatuu tay tana tunanin kawae dae in mutum zai yi ankon sai wurin 100k ya tashi harda kud'in d'inki saidai in ko mutum yayi normal Chiganvy d'in, tambayar ta tayi ina ake saida su Jidderh d'in tace Zee Collections ce ta kawo masu tace Ok zata mata magana tana son siya ma su gwaggon ta da k'anwarta da sauri Jidderh tace "ai fa Big Bro ya siya masu dama cewa yayi a bari kizo sai a tambaye ki wand'anda za'a d'inka mawa atamfa biyar da lace biyar yasa aka amsar maki yace in kinzo basu isa ba sai ayi mashi magana" d'an murmushi Fatuu tay yana daga abunda ke sawa tana k'ara son shi kenan akwae shi da sanin yakamata, tunanin wanda zata sa a d'inka ma su ta shiga yi nan ta yanke gwaggo da Mino sai Fauzy da Yadikko sai Aunty Mareeya, tunanin Haulat ko zata zo tayi don sunyi waya tace mata zata zo in sha Allahu k'arshe ta yanke tunda tana da number d'in Zee Collections d'in zata mata magana kawae ba sai Haisam din ya k'ara siya ba tunda tana da kud'i da yawa a account d'inta sai ta siya ma Haulat da k'annanta su Aysha tasan inta rok'i Kb mai d'inki zai d'inka masu, daga baya Jidderh tayi mata Maganar zuwa taci Abinci tace tunda Magrib ta kusa ta bari in tayi salla sai ta ci. Bayan sunyi sallar Laila ta shigo tana murmushi ta k'ara yi ma Fatuu ya gajiyan hanya tace mata ai ba wata gajiya, kallon Jidderh tay tace "ke haka ake kula da bak'o kin ruk'eta ashe har yanzu bata ci Abinci ba yanzu Mom ke man magana akan haka, so kika Big Bro yace mun bar mashi mata da yunwa ne" ta k'arasa tana d'an harararta tura mata baki tay tace ai saida tayi mata magana ita tace a bari sai tayi salla, ce mata Laila tayi ta taso suje taci Abinci tana murmushi tace to ta mik'e, ganin zata fita da Hijab Laila d'in tace ya zata je cin Abinci da Hijab, cire Hijab d'in tay Laila tabi jikinta da kallo ganin tana niyyar d'aukar gyalenta dake akan gado yasa Jidderh yin saurin d'auke shi tana dariya tace wai miye zatai ta wani lullube lullube nan fa gida ne Laila tace ato ta fad'a mata dai, ba yadda Fatuu ta iya haka ta bita duk ta takura suka fita. Da daddare sun gama shirin kwanciya cikin kayan bacci Jidderh ma tasaka nata Fatuu na kwance saman gado ita kuma tana zaune a gefen ta suna hira aka turo kopar d'akin duk suka kai idanuwan su wurin, Mom d'in su ce ta shigo da yar sallama itama tana sanye da kayan bacci riga da wando brown kanta ta yafa bak'in gyale, Fatuu na ganinta ta tashi zaune sosae tana mata murmushi, a bakin gadon kusa da Jidderh ta zauna itama fuskar ta d'auke da Murmushi Fatuu ta gaishe da ita ta amsa, kallon Jidderh tayi tace "nazo ki ban aron Yayar ki" yanayin face d'inta ne ya canza tace "aro kuma Mom, mi zata maki da daddaren nan" har saida tay yar dariya jin wata tambaya ta Jidderh tace to zasu je d'akinta ta kwanta ne, da sauri tana yamutsa fuska tace "gaskiya Mom a'a bacin gashi har ta kwanta anan lafiya lou" still Murmushi take tace mata ai ba lalle taji dad'in kwanciya anan ba gadon zai iya masu kad'an shiyasa, a hak'ik'an ce tace "No mom ba wani kad'an da zai mana yana fa da d'an girma in ma yayi kad'an d'in ni zan yi shimfid'a a k'asa", d'an bud'a ido Mom d'in tayi ta hau jinjina kai Fatuu dai sai faman murmushi take, kallonta Mom d'in tayi tace mata lafiya lou taji dad'in kwanciya anan da sauri tace mata eh harda ce mata ta tabbata ta k'ara cewa eh, mik'ewa tayi tana fad'in ai tasan Jidderh bazata bari ta fad'i mata gaskiya ba Saboda ta faranta mata duk sukai yar dariya tayi masu sai da Safe ta juya, tana fita wayar Fatuu ta fara ringing Jidderh ta d'aukko mata akan bedside drawer tana kallon screen d'in ta gane Haisam ne mai kiran kallon Fatuu tay ba tare data bata ba tace "Ya Haisam ne yanzu haka shima yana iya cewa kije part d'in shi ki kwana wllh, don Allah bari in ce mashi kin yi bacci" shiru Fatun tay don tana son jin muryar mijin nata Jidderh tace "pls is just for today gobe Kya je can in ma so yake ki kwana acan d'in" kunya ce ta kama Fatuu a dabarbarce tace mata a'a wllh ba haka bane lafiya lou tace mashi tayi baccin kiran na gabda yankewa ta d'aga tun kafin yayi Magana Jidderh tace mashi tayi bacci tun d'azun yay d'an shiru kafin ya furta Ok ya katse kiran Jidderh nata Murmushin jin dad'i. Washe gari da Asuba suka tashi don yin salla, bayan Fatuu ta yo Alwala ta d'aura doguwar rigar bacci asaman kayan Jidderh ta shimfid'a masu prayer mat suka kabbara a tare, bayan sun gama kowa ya cire Hijab d'in jikin shi ya linke Jidderh ta maida su cikin wardrobe, gaida Fatuu dake tsaye Jidderh tayi tana murmushi Fatun tay shiru itama murmushin take duk sai taji nauyin gaidatan da tayi don ta girme mata, ta fahimci dalilin k'in amsawar tata tace mata ita fa yanzu Yayar suce har Yaya Laila ma, ganin tayi tsaye yasa tace mata ta hau gadon mana su k'ara yin bacci kafin lokacin breakfast don malamin su mai masu karatun safe yayi tafiya, harda tambayar Fatuu wai ko tana jin yunwa ta had'o mata wani abun Fatun ta girgiza mata kai, suna kwanciya bada jimawa ba wayar Jidderh ta hau ringing ta kai hannu kan side drawer ta d'aukko, saida ta duba mai kiran nata kafin tay picking shiru tay tana sauraren abunda ake fad'i mata kafin ta furta "a'a" sai kuma ta k'ara cewa "Okey" daga haka ta cire wayar daga kunnanta bayan ta maida ta inda ta d'aukko ta juya ta kalli Fatuu data juya mata baya ta kira Sunanta, amsa mata tayi ta juyo tana kallonta da d'an murmushi tace "dama Ya Haisam ne wai yana main parlor yace in raka ki wurin shi" d'an jimm Fatun tay ta rasa mi zata ce Jidderh na murmushi ta tashi ta zura k'afafunta k'asa, mik'ewa tay tana kallon Fatuu ganin bata saukko ba tace mata yana jira fa, saukkowa tayi tace ma Jidderh ta bata Hijab d'in data cire tana murmushi tace sai tasa wata Hijab suje haka mana Fatun tace a'a ta bata dai, bayan ta d'aukko mata ta saka Jidderh tayi gaba tana biye da ita suka nufi k'opar fita, lokacin da suka iso cikin parlon yana zaune akan Royal sofa 2 seater dake kusa da tagwayen benayen da zasu kai ka sama ya d'aura kafa d'aya akan d'aya jikin shi sanye da farar jallabiya, basu dad'e da dawowa daga Masallaci ba suda Dad d'in su da sauran Mazan gidan kowa ya wuce d'akin shi, idon shi akan Fatuu har suka k'araso Jidderh ta zauna akan 1 seater Fatuu ma ta zauna akan d'ayar one seater d'in, gaida shi Jidderh tay ya amsa fuskar shi a sake tana murmushi tace "gata nan ko sauro d'aya ban bari ya cije ta ba in ma akwae shi" d'an murmushi yay ya furta mata thanks, gaida shi Fatuu tay ya bita da ido kawae ganin kallon da yake mata yasa taji kunya ta sadda kanta k'asa Jidderh dai sai murmushi take saki, ce mata yay taje tace zata jirata ne su koma yay mata wani kallo kafin yace zata 6ace ne, dariya tayi ta girgiza mashi kai alamar a'a ta mik'e ta nufi hanyar barin wurin, jin ta bar wurin yasa ta d'ago suka had'a ido dashi k'ara gaishe da shi tay kawae sai taga ya mik'e ya nufo wurinta, yana zuwa ya kamo hannunta ya mik'ar da ita Slowly yace suje inda ya kamata ta gaida shi, hanyar bene ya nufa da ita yana ruk'e da hannunta sai d'an waige waige take gudun kada wani ya gansu, sosae cikin ranta take jinjina tsaruwar ko ina na gidan don shima saman benen ba K'aramin had'uwa yay ba, part d'in shi ya nufa da ita bayan ya tura k'opar ta bud'e ya shige da ita, daddad'an k'amshi mai had'e da sanyin Ac ne suka tarbeta bayan sun shiga bin d'akin tay da kallo sosae ya burgeta, maido idon tay kan shi ya jawota jikinshi suka tsaya suna kallon juna da murmushi can tace mashi ina kwana Slowly ya amsa tare da d'an lumshe ido, had'e foreheads d'in su yay k'asa k'asa ya furta "I didn't sleep well last night because u weren't by myside" rufe idanunta tay tana shak'ar k'amshin shi daya cika mata hanci, ganin abun na neman yin yawa yasa ta fara k'ok'arin raba jikin su, k'in sakinta yay ya bita da kallo idanunshi a d'an lumshe har sun fara canza yanayin su tana yamutsa fuska tace "Hubby kar wani ya shigo" shiru yay yana kallonta kaman bazai tanka ba can kuma ya d'age mata gira yace "d'akin wani ne da zai shigo?" da yanayin damuwa tace "naga ai ba gidan mu bane nan d'in" d'an guntun murmushin gefe yay yace "gidan su waye?" rasa amsar da zata bashi tay sai yamutsa fuska take, sakin ta yay yace "i'm sorry ina damun ki, u can go" waro ido tay da sauri ta kama shi da d'an rawar murya tace "a'a Hubby ba haka nike nufi ba fa, kawai dai naga kaman ni matsayin bak'uwa ce ina jin kunya ne a ganni anan" shiru yay yana kallon ta kawae ta d'an jijjiga shi tace yayi Magana mana, still bai tanka mata ba sai kallonta kawae da yake shi kanshi yana mamakin kanshi yadda yake mata wanda sam ba haka ya saba yi ma Fanan ba mafi yawancin lokutta ma ita ke neman shi yanzu kuma sai abun ya juye duk in ya kasance da ita wata irin natsuwa ta daban yake samu, har idanunta sun ciko da k'walla kawae zai gani yay sun zubo mata sharr ta fad'a jikin shi tana fad'in don Allah kada yay fushi da ita sigh yay ya kai hannu ya d'agota Fuskar shi a sake yace mata waya fad'i mata zai iya hakan kawai dai bai son yana takura mata, da sauri tace "ni baka wani takura man hubby kawae ina jin kunya ne" murmushi yay yace to miye abun kunya nan fa d'akin mijinta ne dama ai anan yakamata ta zauna ba wani wuri ba, kai ta jinjina mashi ya kama hannunta suka nufi hanyar Bedroom yana fad'in har yanzu kuka bai mata wuya ko tay murmushi ta d'an fad'a jikinshi ya tallabo ta, Bayan tayi wanka zaune tayi jikinta sanye da bathrobe tana son ta koma d'akin Jidderh amman kunya ta hanata don ta d'auki lokaci anan, bin Haisam dake gaban mirror yana gyara sumar shi jikin shi sanye da k'ananun kaya jeans da t-shirt tay, bayan ya gama nufo inda take zaune yay ya tsaya a gabanta yace tazo ya rakata sai ta sa kaya, mak'e mashi kafad'a tay tana yamutsa fuska tace Allah ita kunya take ji tun d'azu fa take nan murmushi yayi sai kuma yay moving wurin side drawer ya kai hannu ya d'aukko wayar shi dake ajiye asama, Jidderh ya kirawo tana fara yin ringing ta d'aukka don lokacin itama ta tashi daga baccin data koma ta fito wanka tana cikin shiryawa, ce mata yay ta d'aukko ma Fatuu kaya a cikin trolley d'inta tace to, bayan ya gama wayar komawa yay wurin ta ya zauna daga gefen ta ta kai kanta ta kwantar a saman shoulder d'in shi k'asa k'asa da murya yace "Yunwa ko?" girgiza mashi kai tay alamar a'a yana murmushi yace yasan zuwa yanzu dole taji yunwa, ba'a jima ba Jidderh ta kawo kayan ta tsaya a bakin k'opa tana knocking, mik'ewa yay ya nufi kopar yana bud'ewa ta sakar mashi murmushi tana sanye da riga da wando skin tight sai rigar ta saukko mata zuwa rabin cinyoyin ta, mik'a mashi kayan tayi ya amsa ya furta mata thanks har zata juya sai kuma ta dakata lokacin shima har zai koma ciki tace mashi ko ta jirata su tafi tare d'an shiru yay sai kuma yace ta zauna a parlon ta jira ta fito tana murmushi tace to ta juya ta nufi wurin kujeru, bayan ya kai mata kayan waro ido tay tana kallon su ganin skinny jeans ne da riga wanda in tasa kayan sosae suke kamata, da alamun damuwa ta kalle shi tace gaskiya bazata saka su ba yace Saboda me, nuna mashi kayan tay tace baiga wanda ta d'aukko mata bane, "Ai weekend ne irin su ake sawa yau" ya fad'a yana murmushi k'ara waro ido tay a d'an rud'e tace "amman ni ai ba yar gidan bace bak'uwa ce kawae sai in saka wannan kayan in fita ai wllh cewa ma za'ai banda kunya" yar dariya yay jin Maganan da tayi wai ita ba yar gidan bace, tambayar ta yay to miyasa ta taho da su in bazata saka ba tace "ai dama ko zan sa zan d'aura after dress ne a sama ba hakanan ba sai dai in kasa a d'aukko man after dress d'in sai in d'aura" shiru yay yana bin ta da kallo kawae har saida ta k'ara ce mashi "ka ji hubby k'asa a d'aukko man tana nan acikin kayan" sigh yay ya tambayi ba wasu ne sai wannan da sauri tace mashi akwae mana su atampa da lace duk akwae lumshe ido yay ya d'an girgiza kai yace mata ba irin su yake nufi ba irin wanda aka d'aukko mata tace eh akwae wasu, mik'ewa yay daga zaunen da yake a gefen ta ya nufi hanyar fita daga cikin d'akin ta bi shi da kallo har ya fita sannan ta maido idon ta kan kayan ta fara imagining kanta sanye da su a fili tace "tabb wayaga mara kunya", yana fita parlor yace ma Jidderh suje ta mik'e, d'akinta suka nufa bayan sun shiga daga bakin k'opa ya tsaya yace ta d'aukko mashi trolley d'in Fatuu tace to, bayan ta d'aukko mashi ya amsa yace ta jirata anan zata dawo yanzu tace to, part d'in shi ya koma tana zaune ya shigo da akwatin ya nufi inda take, a saman gadon ya d'aura shi ya bud'e da kanshi ya hau duba mata wanda zata saka dama k'ananun kayan ba su da yawa basu fi ukku ba koda aka fiddo sauran biyun suma duk saida tayi k'orafin sun kamata yace dole ta saka d'aya ciki, k'arshe wani bakin pencil skirt da bakar riga v-neck mai dogon hannu tasa sai faman yamutsa fuska take tana fad'in ita gaskiya after dress zata saka yace da yake unguwa zata je ko, shi ya taimaka mata ta gyara fuskarta da gashinta bayan sun gama yace ta saka hula su tafi lokacin breakfast yayi kar a jira su rigima ta fara mashi tana fad'in wai ya za'ai ta fita haka don Allah dama gashi tazo d'akin shi kuma duk ansan ba anan ta sauka ba, still yay yana kallonta ya goya hannuwan shi a chest, suna haka akayi knocking k'opar har saida Fatuu ta d'an tsorata, nufar k'opar yay ya bud'e ganin Mom d'in shi yasa shi sakin k'ayataccen murmushi ya ambaci sunanta tana sanye da jar polo shirt ta mata da dogon bakin skirt kanta sanye da bakar hula abun sai dai ace Tubarkallah, k'arasa fitowa yay ya rungumota jikinshi yana gaishe da ita ta amsa tana murmushi, bayan ya saketa tace "nazo tafiya da wadda kaje ka d'aukko, in kai baka jin yunwa ita ce maka akai bata ji da zaka ruk'eta ka hana tazo tayi breakfast har kiran ka akai ta landline baka d'auka ba" tana d'an hararar shi ta k'arasa Maganar yana murmushi ya bata hak'uri yace dama yanzu zasu fito tace Ok su kad'ai ake jira, har zata juya yace bari ya kirata sai su tafi tare tace Ok, juyawa yay ya koma d'akin Fatuu dake zaune a bakin gado ta d'aga ido ta kalleshi ya nufa ta, a gabanta ya tsaya yace ta tashi ga Mom nan tazo tafiya da ita yamutsa fuska ta fara yi ya d'aure mata tashi kawae sai ta fara ta6e baki bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma yay murmushi yace bari yay ma Mom d'in magana sai ta shigo ta tafi da ita tana jin Haka ta mik'e da sauri, zuciyar tace ta bata ta d'aukko gyale tay rolling da sauri ta juya wurin kayan ta, bayan ta d'aukko ta nad'a duk da haka bai rufeta sosae ba amman dai taji gwara hakan, tare suka fito tana biye dashi Mom d'in har ta zauna akan kujera, suna had'a ido da Fatuu ta sakar mata murmushi, wurinta ta nufa a kunyace tana zuwa ta fara k'ok'arin zama a k'asa Mom d'in ta kamo hannunta ta zaunar da ita akan kujera kusa da ita, cikin jin kunya Fatuu ta gaishe da ita ta amsa mata tayi mata ta tashi lpy tace lafiya lau, mik'ewa tay ta kamo hannun Fatun tana fad'in suje tayi breakfast Habiby ya ruk'eta kuma tasan bata rasa jin yunya gaba d'aya kunya ce ta rufe Fatun, bayan sun saukko k'asan kasa d'aga ido tay ta kalli Mutanen dake a Dining area d'in wata irin kunya ta lullube ta, Haisam ne yaja seat yace ta zauna Mom ta koma gefen Senator ta zauna bayan ta zauna shima yaja kujerar gefen ta ya zauna, da k'yar ta d'ago ta gaishe da Senator idon shi akanta yana murmushi ya amsa yace "My Daughter how was ur night, hope u slept well" kai ta d'aga mashi yace haka yake so, juyawa tay ta gaishe da Hajiya itama ta amsa tana d'an murmushi, kallon Aunty tay ta gaishe da ita tana murmushi itama ta amsa tayi mata ta tashi lpy bayan ta amsa tana niyyar gaishe da Laila ta riga gaishe da ita a kunyace itama Fatun ta maida mata gaisuwar ta amsa tana mata murmushi komai nata burgeta yake bama ita kad'ai ba kusan kowa ma, dama akwae mutanen da zaka ga suna da farinjini sosae kowa son su yake sai wad'anda ba'a rasa ba tunda ance Abincin wani dama gubar wani ne amman dai Fatuu tana burge mutane sosae, sauran yaran ma duk suka gaishe da ita harda su twins Nameer k'in gaishe da ita yayi saidae ita ta gaida shi saida ya ga dama sannan ya amsa har Senator na ce mashi shi bai gaishe da ita ba tana Yayar shi kuma ta gaishe shi sai ya mula zai amsa ya kalli Dad d'in yana murmushi Hajiya tace wannan ya k'yale su kawai sun saba Senator d'in yace oh to ya gane duk akayi murmushi, Fatuu Senator yasa tayi masu Addu'a bayan ta gama suka fara cin Abincin a nutse tun Fatuu bata saki jiki ba har sai ta washe taci gaba da cin Abincin ta. Bayan sun gama Jidderh ta ja ta d'akinta Mom d'in Haisam tace mashi tana son zasu yi magana suka nufi cikin parlon , a saman doguwar kujera suka zauna suna kallon juna tace mashi dama Maganar dangin ita Daughter ne bata san ko anyi Magana ba yakamata suzo yace mata eh sunyi Magana da Dad jiya za'a tura Mota a d'aukko su tace hakan yayi amman a tura da wuri ba sai lokaci ya k'ure ba Saboda su kar6i lefen ta yace Ok, bayan sun gama Maganar sama ya haye ya koma part d'in shi, a parlor ya zauna ya fara k'ok'arin kiran Abbas, bayan yayi picking sun gaisa yayi mashi Maganar Alhaji Lawal kaman yadda sukai da Dad d'in shi Abbas d'in yace Ok zai kira shi da sun gama wayar sai aji in zai samu zuwa, Maganar dangin su Fatun ya k'ara yi mashi nan ma yace in suka gama zai kira gwaggo sai aji yadda za'ai Haisam d'in ya tambaye shi su yaushe zai taho da su yace yana tunanin ran Wednesday, hiran yadda abubuwa zasu kasance suka shiga yi kafin daga baya sukai sallama, Suna gama wayar ya kira Alhaji Lawal d'in bayan sun gaisa a mutunce Abbas ya fara mashi bayani game da bikin, sosae ya nuna jin dad'in shi yace ai wannan ba wani abu bane, shi a wurin shi ma girmama shi akai dama kuma lokacin yana a Abujar, nan yake sanar ma Abbas d'in yana shirin tsayawa takarar d'an majalissar tarayya ne a zabe mai zuwa Abbas d'in yayi mashi fatan Alkhairi yace in sha Allahu yana nan zuwa daga baya sukai sallama, Gwaggo ya kira bayan ta d'aga sun gaisa yayi mata Maganar zuwa d'aukko yan Adamawan cike da Farinciki ta hau godiya tace zata masu Magana sai su shirya dama jiya da daddare suke Magana da Baffan Fatun kan bikin yake tambayar ta ko za'a je daga nan tace ya bari sai ta tambaya Abbas na dariya yace ma gwaggo ai ba sai an wani tambaya ba suna da hakki suje itama dariya take tace hakane wai dai kar ayi ba daidai ba, nan yake sanar mata suma ran Wednesday zasu tafi tace to Allah ya kaimu suka yi sallama. Bayan Fatuu ta koma d'akin Jidderh wayarta ta d'auka ta hau online, sakonni na fara shigowa sai ga sak'on Haulat da sauri ta shiga voice note ne ta turo mata, bud'ewa tay ta fara saurara cike da farinciki take sanar da ita an barta zata zo, sosae Fatuu taji dad'i don tasan Haulat mai kaunarta ce kuma tana ganin komai ya faru da ita hada silarta, fita tayi daga cikin WhatsApp d'in ta fara k'ok'arin kiran Abbas bayan ya d'aga ta gaishe dashi ya amsa yana fad'in Amaryar su an je lafiya ta amsa mashi da lafiya lou, jin ta yi shiru yasa shi tambayarta ko da Wani abu da yar in ina tace dama so take ta tambaye shi yaushe zasu zo yace mata ranar laraba in Allah ya kaimu, k'ara tambayar koda wani abu yayi jin ta k'ara yin shiru tace eh dama don Allah k'awarta ce Haulat zata zo daga Nijar shine take son in ba matsala tazo nan sai a taho da ita, yana murmushi yace "an gama Amarya ai umarni kawai zaki bada bawai ki rok'a ba koda ba Mota da anyi ma Angon naki magana zai iya turowa a d'auketa koda ita kad'ai ce don na lura yanzu ke kike control d'in heart d'in shi" waro ido tay tasa hannu ta rufe baki sai kuma ta cire tana fad'in don Allah ya rufa mata Asiri kar Aunty Fanan taji dariya kawae yayi yace Shikenan dai abar Maganar, bayan sun gama wayar WhatsApp ta koma ta tura ma Haulat sakon voice note ta sanar da ita su gwaggo ranar laraba zasu taho tayi magana taje can sai a taho da ita, bayan ta tura mata sake fita tayi ta kira Fauzy suka gaisa Fauzyn tace ai ta kirata d'azun bata d'aga ba tace eh bata kusa ne, Maganar anko tayi mata tace ai Ya Haisam yayi masu harda Aunty Mareeya su turo measurements d'in su yanzu in sun gama wayar, wata irin k'arar murna Fauzy ta saka ta hau shi ma Haisam Albarka tana Addu'ar Allah ya k'ara mashi Arziki mai Albarka, Fatuu na jinta ta hau kwala ma Aunty Mareeya kira tana fad'in anyi masu anko wllh Fatuu sai dariya take, sanar da ita tay sunyi waya da Ya Abbas yanzu yace ranar laraba zasu taho Fauzyn tace eh Aunty Mareeya ma sunyi Magana da Aunty Feenah ta sanar mata, hira suka cigaba da yi nan Fatuu ke ce mata zata yi ma Aunty zee mai kaya magana tana son taje ta amsar mata sak'o sai ta kai ma Kb tailor Fauzyn tace to tana jira daga baya sukai sallama. Gwaggo suna gama waya da Abbas ta kira Baffan Fatuu bayan sun gama gaisawa tayi mashi zancen zuwa a d'auke su sosae yaji dad'i shima ya hau godiya nan cikin hikima ta nuna mashi ba gayya za'ai ba ya za6i wanda zasu je tunda ba irin bikin nan bane yace in sha Allahu za'a yi hakan daga baya suka yi sallama, d'akin yadikko ya nufa ya Sanar mata nan ta hau murna har Fuskarta ta kasa 6oyewa, tare da ita suka tsara yadda za'a fad'i ma Ard'o da kuma wad'anda yakamata suje. Shirye shirye sun kan kama a kwana a tashi ba wuya a wurin Allah ranar laraba Abbas ya taho da Aunty Mareeya da Feenah, Abdul sai Haulat da Mino sai Tk kuma ya taho da Amadu da Fauzy sai Aunty Saude harda Zainab Muhammadu k'awar su da Fatuu tasa Fauzy ta taho da ita don ta matsa tana son zuwa, lokacin da suka iso Sosae Fatuu tay farinciki kamar zata zuba ruwa a k'asa tasha yayin da su kuma wad'anda basu ta6a zuwa ba Al'ajabi ne ya kama su ganin irin d'aular da su Haisam suke ciki har fuskokin wasu sun k'asa boye Al'ajabin, a parlor aka tarbesu ana masu sannu da hanya Hajiya da Mom da Aunty dasu Laila duk sun fito cikin parlon anata gaishe gaishe a mutunce can sai ga Nameer ma ya shigo cikin parlon tarbar Abokin shi Amadu, yana ganin shi ya mik'e ya bashi hannu suka gaisa Nameer d'in yayi mashi an zo lafiya ya amsa yanata washe baki, matsawa yay wurin Tk shima suka gaisa ya zauna daga gefen shi, bin sauran Mutanen yay suka gaisa Aunty Mareeya na Fad'in ga mai kama da mijin Zarah duk akayi murmushi, tunda ya d'aura idon shi akan Mino ya bita da kallon k'urulla don yana ganinta ya gane yar uwar Fatuu ce, duk in Mino ta d'ago sai taga ita yake kallo hakan yasa tasha jinin jikinta ta fara yan kame kame kawae sai gani tay ya sakar mata murmushi har bata san lokacin data mayar mashi ba, bayan an gama gaisawa aka kira wasu daga cikin ma'aikatan da aka k'ara d'auka Saboda hidimar suka yi masu jagora inda zasu sauka, Mino na tafiya tana waiwayen Nameer da ya nufi bene dasu Amadu da Tk zai kai su part d'in shi shima waiwayen nata yake suna niyyar shigewa kopar da zata kai su baya ya d'ago mata hannu tay yar dariya, wani duplex ne a bayan gidan can wurin inda babban Kitchen yake nan aka kai su, ginin part biyu gare shi kowanne yana da babban parlor sai corridor guda biyu kowanne yana da d'akuna biyu da toilet, Fauzy da Haulat da Mino da Zainab Muhammadu d'aki guda suka shiga akwae gado da mirror sai wardrobe din bango kowanne d'aki haka yake tsaf an gyara, Feenah da Aunty Mareeya da Saude suma d'aki d'aya suka shiga ita gwaggo Hajiya taja ta d'akinta wai ta bar ma yara can, bada jimawa ba aka fara shigo masu da Abinci da abubuwan sha wasu suka fara yin salla wasu kuma suka fara cin Abincin, "Kai! Ashe dai bamu ga komai ba a kud'in su Mijin Zarah, wannan d'aula haka! Kuma fa kina iya ganin ba iya shine gidan su ba anan Abuja d'in" Aunty Mareeya ce dake cin Abinci tayi zaman cin tuwo asaman carpet tayi Maganar, jinjina kai Feenah tayi tace suna fa da kud'i bana wasa ba, Aunty Saude ce tace "aikuwa bashi kad'ai bane gidan su anan, Senator fa yana da kud'i sosae mutumin da keda gidajen mai da kamfanoni daban daban ba a iya Nigeria kad'ai ba ga gidajen haya ko anan Abujar yana da manyan estate guda biyu da ake haya harda babbar plaza ko a Katsina ma yana da gidajen haya da filaye, Unguwar da Hajiya take fa kusan duk filayen shi ne aka saida ma mutane" jinjina kai Aunty Mareeya ta hau yi cike da Al'ajabi tace "tabb kice dai ba K'aramin mai kud'i bane, wllh wasu masu kud'in sai inta mamakin yadda suke tara dukiya" dariya Saude tayi tace "shi kinga gaskiya harda wanda ya gada a wurin mahaifinshi duk da Soja ne yana da tarin dukiya don ko kamfanonin Motocin Senator yawanci asali na mahaifin shi ne, kuma kinsan ita dukiya in dai zaka tsare hakkin Allah ka rink'a kyauta da sadaqa to lillinkuwa take" cike da gamsuwa gaba d'aya suka ce tabbas haka ne kowa zai shaide su da hakan, haka suka cigaba da yin hirar su. Fatuu ma cikin su Fauzy ta zauna wani irin dad'i take ji sai murmushi take suna ta tsokanarta, bayan sun gama cin Abincin ne Fauzy ta bud'e jakar kayanta ta fiddo d'inkin da ta amso mata a wurin Kb, bud'e kayan Fatuu tay tana dubawa doguwar riga ce akayi gaba d'aya mix and match d'in da lace d'in duk sun yi kyau sosae sai kuma na k'annanta su Aysha suma duk dogayen riguna akai masu, Fatuu na murmushi ta mik'a ma Haulat kayan tace ankon ta ne, waro ido Haulat tayi haka ma Fauzy don ita bata yi tunanin sune ankon ba, kasa cewa komai Haulat tayi da mamaki Fauzy tace "wai dama sune ankon?" Kai Fatuu ta d'aga mata ta k'ara cewa "amman dai da gani zasu yi kud'i sosae" bayanin kud'in su tay mata gaba d'aya suka k'ara zaro ido da yanayin damuwa Haulat tace to maimakon tayi mata Mara kud'in sosae sai ta takura kanta tayi mata mai kud'i haka Fatuu na dariya tace ai ba takura kai bane tana da su ne kuma duk ita akayi sai full embroidery d'in, sosae Haulat ta hau yi mata godiya har kamar zata yi kuka Fatun ta kai hannu ta rungumo ta tana fad'in ai tafi k'arfin wannan a wurin ta, Zainab Muhammadu ce tace don dai lokaci ya k'ure itama da tayi ko normal Chiganvy gold d'in ce Fatuu tace bata san zata zo ba sai daga baya da itama anyi mata gashi yanzu lokaci ya k'ure ace a kawo har akai dinki masu yin d'inkunan ma aiki ya masu yawa don na su Fauzy ma ba'a kaiga gamawa ba da kuma nata zasu yi mata data bata tana murmushi tace ba komai tasa wasu kawai. A ranar bayan Magrib yan Adamawa suka iso, da Baffan Fatuu da Ard'o daya sha babbar riga da rawani shi ga mai Mulki yayi kaman wani d'an tsuntsu, harda Yaya da Baffan su Altine da innarsu Altinen sai d'ayar matar Ardo sai Yadikko dasu Aysha da Kamalu harda uban dawon furar su da Nono bokiti bokiti, k'auyanci kam ba sai an fad'a ba nan suka shiga zuba shi duk sun saki baki galala suna kallon Aljannar duniya in ka cire Yadikko da Baffan Fatuu ba wanda bai nuna k'auyanci ba a cikin su harda mai Mulki ya kasa sauke kan shi k'asa sai kace mai ciwon hangum, harda ce ma sauran dama yanata jin labarin cewa Abuja kaman Aljanna take shi dae babban su Fatuu murmushi kawai yake farinciki fal ran shi, su Yaya dai an kasa cewa komai sai faman jinjina kai take kaman k'adangaruwa baki a kwa6e, suma a mutunce aka tarbesu harda Hajiya ta fito suka gaisa tayi masu ya hanya sai faman kalle kalle suke su Aysha ma kaman tsoron gidan suke duk sun shishshige ma Yadikko, daga baya suma bayan akai masu jagora Mazan aka kai su d'ayan part d'in su kuma su Yadikko bangaren da su Aunty Mareeya suke, bayan sun zazzauna a cikin parlon su Feenah suka zo aka gaggaisa daga baya suka nuna masu bedrooms da zasu shiga, su dai ai sai yadda akai dasu ba baki sai idanu kawai suke wuwwurgawa, bayan sun shiga d'akin masu son shiga toilet Yadikko ce ta nunnuna masu yadda zasu amfani da komae gaba d'aya ma tsoron shi suke, Yadikko tunda tazo take ta son ganin Fatuu, kasa jurewa tayi ta fito a cikin parlor suka had'e da Saude ta nufeta tana murmushi ganin haka yasa ta tsaya, gaisawa suka k'ara yi tace mata don Allah ina zata ga Amaryar ne Saude tace basu had'u bane tace mata eh, ce mata tay ta koma d'aki bari ta dubo mata ita tayi godiya, bayan komawarsu aka kawo masu Abinci nan fa suka shiga ci hannu baka hannu kwarya a ran Yadikko ta shiga gode ma Allah daya sa su kad'ai ne, bada jimawa ba Saude ta dawo saida ta kwankwasa kopar sannan ta tura Yadikko na ganinta ta taso, ce mata tayi Fatuun bata nan wai sunje wurin amsar d'inki tace to tay mata godiya. Bayan Senator ya dawo har inda aka sauke su Ard'o yazo tare da Haisam da wasu yan uwan shi maza guda biyu da suka zo, a parlor suka zauna su Ard'on suka fito Kamalu dai Amadu yazo ya tafi dashi inda suke, ganin suna niyyar duk'awa kasa yasa yace masu don Allah kar suyi haka ga kujeru suma su zauna ai duk d'aya ake, bayan sun zauna aka shiga gaisawa suka yi masu an zo lafiya, Baffa ne ya nuna ma Ard'o Haisam yace shine mijin inna wuron ya hau jinjina kai da baban Altine yana fad'in ba shakka, godiya Senator yayi masu suka hau fad'in ba komai wllh ai sune yakamata suyi godiya nan suka hau yin godiya Ardo cikin hausar shi da bata fita sosae yace ai akwae shanu ma da suka taho dashi yana a kan hanya da daddaren nan zai iso, sai kace shi ya bada shanun ba Baffan Fatuu ba, baban Altine ne ya k'ara fad'i masu abunda yace su duka suka yi godiya suna fad'in Allah ya bar zumunci daga baya suka tafi. Fatuu na dawowa taji su yadikko sun iso tana sanye da riga da skirt na lace da gudu ta nufo bayan, tana tura kopar d'akin da suke suka had'a ido da yadikko ta nufeta tana zuwa ta fad'a mata tana dariyar farinciki sauran yan d'akin ma murmushi suke harda Yaya da alama abun yafi k'arfin ta don dole ta aje makaman yak'in nata, d'agowa tay ta juya tana gaishe da sauran sai washe baki suke suna amsawa ganin ta suke kamar Madara, zama tay a kusa da yadikko ta kama hannun Aysha tana tambayar ta ya Makaranta da d'an murmushi ta amsa mata, hira suka shiga yi gaba d'aya kowa Fatun burge shi take yadda ta koma kalar yan gayu, ganin kaman d'akin bazai ishe su ba yasa tace bari ta duba d'ayan d'akin in ba mutane sai wasu su je can, mik'ewa tay taje ta duba ta dawo tace masu ba mutane a d'akin wasu suje can suka ce to, hira suka k'ara yi da yadikko cike da Farinciki take fad'in taji mata dad'i wllh har bazata iya misalta mata ba tayi Addu'ar Allah ubangiji yasa gidan zaman ta ne na har abada ya kauda idon mak'iya, daga baya ta hau yaba irin kirkin dangin su Haisam tace samun irin su a masu kud'i yana da matuk'ar wahala, ta shiga yi masu Addu'oi Fatun na amsawa nan ta fad'i masu anyi masu anko ita nata sai zuwa gobe su Aysha kuma tace su zo suje ta d'aukko masu nasu suka mik'e cike da Farinciki suka tafi, suna fitowa cikin parlor tayi kacibus da Nameer da ya shigo, a gefen shi ta tsaya tana mashi wani kallo mai kaman harara ya sa dariya yana fad'in "kinga Yayata komai ya wuce tsakanin mu tunda naga wadda zata fanshe ki itama nazo nema don Allah ki turo man ita" cikin rashin fahimta Fatun tace wa kenan, kwatancen Mino yayi mata nan take ta gane ita ce, ta6e baki tay tace mashi to itama da sa rana akanta sai yayi hak'uri da sauri yace "No! Kar muyi haka dake pls am serious tayi man ba kamar kuma da ya kasance kuna kama tunda na rasa ki sai in maye gurbin ta dake" dariya Fatuu tay tace "wai Nameer a yaushe ka ta6a cewa kana sona ne da zakai ta man surutai haka" yar harararta yayi yace "kina nufin duk abubuwan da nike maki baki gane ba kawae fa ni don nasan ba yadda za'ai inyi aure a lokacin yasa na bari sai na gama karatu tunda kema naji likita kike son zama ashe ashe likiciyar gida ce zaki zama" dariya tay ta d'an girgiza kai tana fad'in Allah ya shirye shi, ganin zata wuce yasa da sauri yace pls ta turo mashi ita ta d'aga mashi kai, lokacin data shiga d'akin su Fauzyn suna ta faman gwada d'inkunan su da aka fara amsowa sai faman murna suke, kallon Mino tayi tace mata taje parlor ana neman ta da alamun mamaki tace ita ta d'aga mata kai, saukkowa tayi daga saman gado jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa A-line ta yafa d'an madaidaicin gyale a saman kanta, tana shigowa cikin parlorn suka had'a ido dashi ya sakar mata k'ayataccen murmushin shi tana ganin haka ta gane shine ke nemanta kenan, nufar shi tay ta tsaya daga gaban shi tana d'an murmushi ta gaishe dashi, amsa mata yayi kafin yace in ba damuwa yana son zasu yi magana ne ta d'aga mashi kai don Nameer ba irin samarin da za'a musa mawa bane, da hannu yay mata alamun suje suka jera, suna fita ya nufi Sport field d'in gidan da ita. A ranar saida su Fatuu suka kai tsakar dare suna hira sai daga baya ta koma d'akin Jidderh lokacin sun samu k'aruwar wata cikin yan uwan su na Daura da Suka zo k'awar Jidderh d'in ce, bayan ta shiga Jidderh d'in tace su kwanta ita bari tayi shimfid'a k'asa da sauri Fatuu tace a'a ai gadon zai ishe su. Washe gari bayan an tashi duk suka yi wanka aka fara yin Breakfast wanda lafiyayyun Abinci aka yi, daga baya kuma aka sa ma'aikatan dake hidiman Abinci suka dama furar da su Yadikko suka kawo aka rarraba ma mutane. Misalin k'arfe 12 na rana Aunty tazo d'akin Hajiya tayi ma gwaggo magana cewa za'a kawo lefen Fatuu cike da Farinciki tace to Hajiya tace mata taje ta sanar ma sauran iyayen nata tace to ta mik'e, d'akin su Yadikko taje bayan an gaggaisa ta sanar masu tace sai su fito parlor suka ce to, bayan ta fito d'akin su Aunty Mareeya taje ta sanar masu suma suka fito cikin Falon haka ma su Fauzy, bada jimawa ba aka fara shigowa da Akwatunan lefen aka shiga jera su a tsakiyar parlon har aka gama, akwati Set hud'u ne masu guda hud'u hud'u guda sha shidda kenan su kan su akwatunan abun kallo ne kala daban daban akwae set d'in bak'ak'e sai na maroon sai na brown sai kuma pink, Su Aunty ne da wasu yan uwan su Haisam d'in suka biyo kayan nan suka sa ma'aikatan da suka shigo dasu suka fara bubbud'a wa, ba abunda ka ke ji sai ma sha Allah da aketa fad'i kaya ne na gani na fad'a kusan duk ma an d'inka su harda wanda zata saka ranar Dinner, sai faman jinjina kai ake a wani d'an kit kusan duk zinarai ne a ciki harda gold su Fatuu anyi goshi hakanan ma Haisam yayi mata Akwatunan kaya inaga yanzu, bayan an gama dubawa aka hau yin godiya da Addu'oi, Fauzy ce ta koma d'akin da suka sauka da gudu da yake Fatuu na ciki ta hau bata labarin irin lefen da aka mata a rud'e sai faman zuzuta kayan take ita dai murmushi kawae take komai zuwa yake mata kaman a mafarki. A ranar bayan sallar Azahar Fanan ta iso Haisam ne yaje ya d'aukko ta a Airport ita kadae tazo sai autar su Noor, bayan ta iso a d'akin Mom d'in su ta sauka aka hau haba haba da ita ana mata sannu da zuwa daga baya tace bari taje su gaisa da Hajiya, Jidderh ce taje baya ta sanar ma Fatuu zancen zuwan Fanan d'in suka taho tare, bayan sun je d'akin Mom d'in aka sanar masu tana d'akin Hajiya suka nufi can, tana zaune a bakin gado su Fatuu suka shigo suna had'a ido ta nufeta da gudu suka rungume juna su Hajiya da gwaggo da wasu dake cikin d'akin suna ta murmushi don ba K'aramin burge mutane sukai ba, d'agowa Fatuu tay ta duk'a kasa hannunta cikin na Fanan d'in ta gaishe da ita tayi mata an zo lpy tana ta murmushi ta ke amsa mata tana fad'in Amaryar su, daga baya tare suka tafi harda Jidderh suka nufi baya, d'akin su Aunty Mareeya ta kai ta Feenah na ganinta ta mik'e tana murmushi take fad'in "You are Welcome Uwargidan H,Zakee" murmushi kawae Fanan d'in ke yi ta nufi bakin gado ta Zauna Aunty Mareeya ta bita da kallo don ta gane itace kishiyar Fatuu, gaidata Fanan d'in tayi tana murmushi ta amsa tayi mata an zo lafiya tace lafiya lou, hira suka shiga yi sosae ta burge Aunty Mareeya yadda bata da d'agin kai ko kad'an, suna haka Jidderh da Fatuu suka kawo mata abinci da abun sha Aunty Mareeya na dariya ta kalli Fatuu tana fad'in su Zarah anga Yaya sai washe baki ake duk suka kalli Fatun ta kai hannu ta rufe fuska Fanan ce tace mata ya Amarya ba k'unshi kuma tace anjima zasu je ba wani mai yawa ne za'a mata ba tace Ok, daga baya su Fatun suka fita Aunty Mareeya tace mata taci Abincin mana tace ok ta saukko kan Carpet ta zauna Noor dai na wurin Hajiya, sosae suka shiga yin hira anan har Aunty Mareeya da Feenah na yaba mata kan namijin k'ok'arin da tayi tana d'an murmushi tace ai haka yakamata don in kace zaka ja da hukuncin Ubangiji to kai ne a wahala gaba d'aya suka ce hakane wllh, karshe dai a nan ta wuni. Misalin k'arfe biyar na yamma lokacin su Fatuu na wurin kunshi dankara dankaran Motoci suka shigo cikin gidan da jiniya nan take aka gane Her Excellency Hajiya Zainab ce ta iso, a gaban Entry Hall na gidan Motocin suka parker nan da nan jama'ar cikin gidan suka fara fitowa wanda suka san itace da wanda ma basu san itace ba kawai jiniyar tasa su fitowa, wani Security ne daga cikin Escort d'inta na Motar gaba ya fito da sauri yazo ya bud'e mata k'opa ta zuro farar kafarta data k'unshi ga wani mayen takalmi golden sanye a k'afar, k'arasa fitowa tay tana sanye da rantsatstsen lace bak'i mai adon green da ratsin golden kad'an, tun daga kunnan ta zuwa wuyanta da yatsun hannunta duk gold ne ta yafa mayafi golden kalar takalmanta da jakarta abun sai dai ace Tubarkallah dama tana d'aya daga cikin Matan gwamnoni da suka san takan gayu, Security detail d'in ta mace ce ta fito tazo bayanta ta tsaya wani daga cikin Escort d'in nata ya nufi Motar dake bayan tata ya bud'e yaran ta ne suka fito cikin shiga ta Alfarma, Mota ta biyun k'arshe wani security d'in ya fito daga cikin Escort d'in Motar baya ya bud'e kopar bayan ta, kai kace ba mutum aka bud'e mawa ba don ba alamun wani zai fito, saida aka d'an d'auki lokaci sannan ya zuro da k'afar shi guda mai sanye da wani dakakken bak'in takalmi half cover daga haka bai k'arasa fitowar ba, Hajiya Zainab nata Murmushi ta tunkari Mutanen da suka fito tarbarta Momyn Haisam ta taho suka rungume juna gwanin burgewa kasantuwar fuskar su iri d'aya ce, bayan sun saki juna mutane suka hau gaishe ta ana mata sannu da zuwa wad'anda ma basu santa ba basu san lokacin da suka hau washe baki ba suna mata sannu da zuwa a mutunce take d'aga hannu tana amsawa, k'arasa fitowa Sameer yayi yana sanye da bak'in jeans da top bak'a sai maroon d'in riga a sama mai ma6allai saidai ba'a sanya su ba a bud'e take hakan ya bayyana bakar ta cikin idanun shi na sanye da wani mayen bak'in glass, agogon hannunshi ma bak'a ce saidae daga wurin glass d'in kan yana reflecting maroon d'in cikin agogon kai da gani ba sai an fad'a maka zata yi kud'i ba ga sumar shi da ta sha gyara a kwance, nufar inda su Mom d'in shi ke tsaye yayi yana tafiya cike da izza, yana zuwa ya tsaya a gefen ta Mom d'in su Haisam ta kalle shi da faffad'an murmushi tace "U'r welcome my son" kai kawai ya jinjina mata fuskar shi ba yabo ba fallasa Aunty ma sannu da zuwa tayi mashi to itama d'in dai kai ta samu aka d'aga mata, Laila ce ta matsa gaban shi tana kallon shi da murmushi tace ita bazata yi mashi sannu da zuwa ba sai ya bud'e idanun ta kuma tabbatar ba makancewa yay ba da yake suna d'an shiri dashi, d'age mata gira yay itama ta d'aga mashi tata sai lokacin yanayin fuskar shi ya d'an canza a K'ok'arin shi na yayi murmushi, hannu ya kai ya cire glass d'in tace Yauwa to amman da ya rufe idanu basu ma san ko yana ganin su ba, sannu da zuwa tayi mashi ya d'aga mata kai daga haka ya fara k'ok'arin wucewa ciki yana maida glass d'in all eyes on him nan aka shiga darewa ana bashi hanya har ya shige ciki, a wurin dai da yawa ya tafi da imanin wasu ba kamar yan mata Aunty Mareeya data saki baki tana kallon shi har ya shige ta jinjina kai tace "banga laifin ka ba wllh, ga kyau ga kud'i ga Mulki ai abun da yawa mutum bama zai san lokacin da zai ringa jin izza ba" Feenah dake gefenta ta saki dariya, nufo shiga ciki Her Excellency tay aka bata hanya security d'inta na biye dasu bayan tayi gaba aka rufa mata baya suka shige ciki........ *ASM 080* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Sameer na shiga cikin parlon ya nufi bene cike da isa ya haye ya nufi part d'in Haisam, bayan sun shigo d'akin Mom d'in su Haisam suka nufa, a parlor d'in ta duk aka zazzauna wasu akan kujeru wasu kuma a k'asa Security detail d'in ta na daga gefe a tsaye, gaisawa aka shiga k'ara yi ana mata an zo lafiya da fara'a take ta amsa ma kowa, bayan wani lokaci ta mik'e tace ma Mom zata shiga ciki ta d'an hutu before ayi sallar Magrib tace mata to Abinci ba, ce mata tayi bata jin yunwa saidai ko yara daga haka ta nufi hanyar Bedroom, dakatawa tay kafin ta shige tace ma security d'in tata ta zauna anan ta huta ta d'an rankwafa tayi mata godiya Mom ta bi bayanta suka nufi cikin Bedroom d'in. Abbas da Saleem wanda dama yana a Abujar zaune a cikin parlon Haisam Sameer ya turo k'opar ya shigo duk suka d'aga kai suka kalle shi, mik'ewa Abbas yayi da fara'a ya tarbe shi yana mashi sannu da zuwa kai kawai ya d'aga mashi Saleem dai na zaune yana bin su da ido don shima duk tafiyar su d'aya da Sameer d'in sai dai bambancin shi Salim miskilanci ne kawae Sameer kuma banda miskilanci harda izza ta bala'e, gaba d'aya kowa yasan kowa da kuma matsayin baban kowa tsakanin Sameer d'an Governor da Saleem d'an Deputy Governor, sai bayan da Sameer d'in ya zauna ya kai hannu ya cire glass d'in Fuskar shi sannan Salim ya d'an d'aga hannu yace mashi welcome Sameer d'in ya jinjina mashi kai daga haka ya maida idon shi akan Tv yaci gaba da kallon Film d'in da suke kallo, Abbas ne yace mashi Haisam d'in na wanka ne sai lokacin ya bud'e baki can k'asan mak'oshi ya furta Ok, hannu ya kai ya fiddo wayar shi daga cikin trouser pocket d'in shi ya fara latsa ta, bai dad'e da zama ba Haisam d'in ya fito yana sanye cikin k'ananan kaya kaman ko yaushe yana hango Sameer d'in ya d'an bud'a ido alamar mamaki don koda ya jiyo jiniya ya san Mom d'in shi ce amman bai yi zaton harda shi za'a zo ba don ko jiya sunyi Magana yake ce mashi ba zai zo ba yana da uzuri, nufo shi Haisam yayi yana zuwa ya zauna a gefen shi fuskar shi da murmushi ya mik'a mashi hannu tare da fad'in "What a surprise, u'r Welcome Bro" d'an gutsirin murmushi yayi a hankali ya furta mashi thanks, tambayar shi yay amman da yace bazai samu zuwa ba, kaman bazai bashi amsa ba sai kuma ya d'age gira yace to ya zo ko ya koma ne, yar dariya Haisam yay kawai Abbas dai yana ta kallon su da murmushi akan fuskar shi d'an Deputy kuwa tamkar ma bai san dasu a wurin ba, Jingina da kujerar Haisam yay idon shi akan Sameer yace "Kai wai sai yaushe zakai aure ne naga alamar ma baka da ko niyya" d'an yamutsa fuska yay idon shi akan Screen d'in wayar shi cikin husky voice d'in shi ya furta " I'm not as promiscuous as you are, ni ba dole sai nayi ba" d'an bud'a ido Haisam yay alamar mamaki yace "U call me dat!" Sai lokacin ya d'ago ido ya kalle shi yanayin fuskar shi yay d'an alamun murmushi Abbas sai dariya yake, ce mashi Sameer d'in yay ai ya fahimci ta farkon bata satisfying nashi ne shiyasa har ya k'ara itama yasan bada jimawa ba zai k'ara, a fiffizge yake Maganar yana yi yana d'age gira, Abbas sai dariya yake hakan ne ya janyo hankalin Salim ya maido idon shi kan su, shi dai Haisam murmushi kawae yake don bai san mi zai ce mashi ba, mik'ewa Sameer d'in yay idon shi akan Haisam yace yana bashi shawara daga wannan yayi hak'uri hakanan don a yawan aure ana samun cuta daga haka ya nufi hanyar Bedroom Haisam ya bi shi da ido yana murmushi haka Salim ma murmushin yake Abbas kuma sai dariyar k'eta yake, har ya kusa Bedroom d'in Haisam ya d'an d'aga murya yace Abinci fa, hannu ya d'an girgiza mashi ba tare daya ce komai ba bai kuma juyo ba har ya shige d'akin, bayan shigar shi ne Abbas yace "ashe ya iya tsokana haka" d'an girgiza kai Haisam yay yana dariya ya furta "d'an iska ne da kake ganin shi" Abbas din ya fashe da dariya. Sai bayan Magrib su Fatuu suka dawo anyi mata k'unshin a k'afa da hannu yayi kyau sosae ja da bak'i ne saidae jan yafi yawa kuma ba wani mai yawa bane sosae, su Fauzy da Mino duk ba'ayi masu ba don sun yi tun a Katsina kawai rakiya sukai, Jidderh ma anyi nata yan sarkoki masu kyau, d'akin Jidderh Fatuu ta wuce don kayanta na acan Fauzy kuma ta nufi baya, tana zuwa wanka ta shiga bayan ta fito Jidderh ma ta shiga, shiryawa tayi da doguwar riga bayan ta gama ta shimfid'a prayer mat ta kabbara salla da suna a hanya aka yi ta, bayan Jidderh ta fito tana cikin shafa mai su twins suka shigo ganin yadda suka fad'o cikin d'akin yasa ta kalle su tace daga ina suna dariya suka ce daga wurin Momyn Nasarawa suke, d'an waro ido tay tace "Momy ta zo kenan ashe shiyasa naga an k'ara security a gate, aikuwa bari in je mu gaisa" ta k'arasa tana ta washe baki, ba 6ata lokaci ta shirya itama doguwar rigar ta zura ta d'aukko Hijab ta kabbara salla, Fatuu na gamawa ta kalli su twins tana murmushi, wurin ta suka nufa suka zauna a gefen ta duk suka kama hannunta suna yabon k'unshin ta itama ta kamo hannun Mubeena tana yabon nata, Jidderh na sallamewa tace ma Fatuu tazo suje ta gaisa da twin sister d'in Mom d'in su First Lady d'in Nasarawa, d'an murmushi tay tace mata taje kawae Jidderh d'in ta matsa mata tace tasan ma za'a aiko kiran ta don su gaisa gara tazo suje kawae, dole ta mik'e Jidderh ta cire Hijab d'in jikinta ta d'aukko gyalen rigar itama Fatun tace mata ta cire hijab d'in mana, cirewa tayi ta d'auki gyalen rigar ta yafa su twins na ruk'e da hannuwanta suka tafi, part d'in Mom d'in suka nufa security detail d'in na a bakin k'opa suka gaishe da ita ta amsa a raina nace rayuwa kowa da hanyar cin Abincin shi wata na ciki tana hutawa ga wata k'ik'am tana gadin ta, nima dai sannu nace mata ta d'aga man kai na wuce sumi sumi, a parlor suka fara tsayawa suka gaggaisa da Mutanen ciki wasu na nuna Fatuu suna itace Amaryar ita dai sai d'an murmushi take tana Sunna kai, Bedroom suka wuce lokacin da suka shiga gaba d'aya Mom d'in su data Nasarawar suna zaune a saman gado jikin Her Excellency sanye da jallabiya cotton mai gajeran hannu bak'a anyi mata sak'a mai kyau orange a gaba itama Mom d'in su Haisam doguwar riga ce a jikinta gaba d'ayan su ba kallabi a kan su sai tarin sumar su dake a nad'e, daga d'an nesa Fatuu ta tsaya tana kallon su, ba don tasan dama su yan biyu bane to da ba k'aramar razana zata yi ba duk da yanzun ma saida ta d'an rud'e ganin Mutum biyu iri d'aya bata yi zaton haka suke kama ba komai nasu iri d'aya, nufar gadon Jidderh tay da gudu tana zuwa ta fad'a jikinta tana fad'in "Welcome lovely Mom" hannu tasa tana d'an bubbuga bayan Jidderh tace "thank you beloved Daughter" d'agowa Jidderh tay tana dariya itama murmushi take tace sun dawo kenan ai ta tambaye ta ance sun je k'unshi ne da bride d'in, ce mata tayi eh ai gata nan ma tare suka zo ta juya ta kallo Fatuu da tayi tsaye kamar an dasa ta, Mom d'in su Haisam ce tace mata ta k'araso ciki mana tana murmushi, nufo gadon Fatuu tay tayi mata alamar taje su gaisa ta nufi side d'in da suke, kokarin duk'awa tay k'asa Hajiya Zainab d'in ta nuna mata kusa da Jidderh tace ta zauna, a sanyaye ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tace mata ya hidima a hankali Fatuu tace Alhamdulillah, jinjina kai tayi tace Allah yasa Alkhairi Fatun ta amsa da Amin a hankali, daga haka bata k'ara ce mata komai ba ta maida idon ta akan Jidderh tana tambayar ta karatun ta nan ta shiga bata labarin yadda yanzu ta k'ware wurin tsara wuri, tana murmushi tace ma sha Allah zata gayyato ta Government House tazo ta tsara masu wasu wurare, washe baki Jidderh tayi tace da taji dad'i amman ai tasan wasa take tana murmushi tace mi zai sa tayi mata wasa indai ta k'ware yadda ta fad'a, sosae Jidderh ta shiga washe bakin jin dad'i Fatuu dai kanta na a k'asa sai jefi jefi take d'agowa ta kalle su ita mamaki ne duk yabi ya cika ta don bata ta6a ganin yan biyu ba haka masu bala'en kama, Mom d'in su ce tace ma Jidderh sun ci Abinci ne da suka dawo tace a'a ai basu dad'e da dawowa ba salla kawai sukai, tace to ta tashi suje kar a bar Amarya da yunwa Fatuu ta d'an kalleta tana murmushi, mik'ewa Jidderh tayi ta kamo hannun Fatuu ta mik'e suka nufi hanyar fita idon Hajiya Zainab akan Fatuu don Mom d'in su ta bata labarin komai game da yadda har akai Auren. Suna fita parlor Jidderh taga d'aya daga cikin ma'aikatan dake hada hadar Abinci tace mata ta kawo masu Abinci a d'akin su tace to, suna cikin cin Abincin wayar Jidderh ta fara ringing ta kai hannu ta d'auko, ganin mai kiran nata ta saki k'ayataccen murmushi Fatuu na ganin haka itama tayi murmushin, picking tay bayan ta kara ta a kunne ta furta Ok daga haka ta cire wayar tana yar dariya ta fara k'ok'arin mik'ewa tace ma Fatuu ta k'arasa cinyewa heartbeat d'inta ya zo, d'an bud'a ido Fatuu tay tana murmushi tace mata ashe tana da saurayi ai tayi zaton bata kula samari don bata ji tana Maganar su ba, "Ai Aunty Fatuu na kama dahir ne shiyasa ban Maganar wasu samari, d'an Abokin Dad ne Minister of finance" jinjina kai Fatuu tay sai kuma tace "dashi za'a yi kenan?" Jidderh dake a gaban mirror tana gyara fuskarta tace "in sha Allahu yanzu haka ma shi so yake a sa mana rana nice nak'i yarda nafi son sai Aunty Laila ta fara yi tukunna da ta k'arasa karatunta za'ayi bikinta don har an tsaida magana ma tuni" Fatuu dake saurarenta tace mi zai hana to ta bashi dama sai a had'a su kawae tana murmushi tace shima haka yace amman ita tafi son ta gama Karatun ta gaba d'aya don shima a cikin karatun yake a London yanzu in ko sunyi aure bazasu zauna a wuri guda ba tunda itama Dubai zata tafi k'arin karatu dama ya gama nashi ne tasan zai bita Dubai d'in gara ya gama tukunna, bayan ta gama gyara fuskar tambayar Fatuu tay ko ta canza kaya tace mata ai rigar jikintan ma lafiya lou tunda bata dad'e da sakata ba ta yafa mayafinta kawai tace Ok, nufar k'opa tay tana ce mata sai ta dawo Fatun tace a gaida mata shi. Bayan fitar Jidderh bada dad'ewa ba wayar Fatun ta fara ringing, ganin mai kiran nata yasa ta saki murmushi kafin tay picking, gaishe da shi tay bayan ya amsa ya tambayi sun dawo ne tace mashi eh tun d'an d'azu ma, "Shine ko ki kira ni kina mantawa da ni ko" murmushi tay a shagwa6e tace "zan iya mantawa da kai na kenan, ai kai ne ni so ban iya mantawa da kai Hubby u'r always in my heart, kai ne ma zuciyan nawa ai" tana jiyo sautin murmushin shi can yace "ya akai kika iya wannan d'in?" Dariya ta saki tace "ai da mutum ya samu abunda ran shi ke matuk'ar so yake iyawa" murmushin ya k'ara yi kafin ya tambayi mi take yi ne tace mashi Abinci take ci tama gama, ce mata yay in ba abunda zata yi tazo part d'in shi yana son su gaisa da Cousin brother d'in shi da suka zo tace to, bayan sun gama wayar mik'ewa tay ta nufi toilet don ta wanko hannuwanta, bata dad'e ba ta fito ta nufi gaban mirror ta fara gyara fuskarta ganin bata dad'e da saka rigar ba yasa ta yanke ta barta kawae ta gyara gyalen kanta daga gaban kanta ya kwanta sosae don harda salon aka mata, d'aukar kayan Abincin tayi ta nufi hanyar fita saida ta saka takalmanta dake a bakin k'opa sannan ta tafi, bayan ta aje kayan Abincin a Kitchen d'in nan parlon ta k'opar baya ta yanke ta bi sai tabi ta k'opar dake kai mutum sama don kunya take ji ta bi ta parlor wani ya ganta, tana fitowa bayan suka had'e da Fauzy itama tayi wanka tana sanye da k'ananun kaya riga da skirt ta yafo gyale, tsayawa Fatuu tay ta k'araso wurin ta tace dama wurin ta zata je ashe itama nan zata zo tace mata suje d'akin su to, Fatun tace mata ba nan zata ba Ya Haisam ne ke neman ta zata gaisa da wani d'an uwan su, "Ok bari in koma to, in kin dawo zaki shigo ne muyi fira?" Fatun tace "to ki zo mana ki rakani in muka dawo ba sai mu wuce nan d'in ba" kallon kanta Fauzy tay tace to bari taje ta sako Hijab ko babban gyale wannan kaman yayi k'arami Fatun tace tayi lafiya lau ai dare ne kuma zuwa kawae zasu yi su gaisa su juyo, tare suka tafi ta k'opar bayan suka bi, Haisam na Zaune a parlor jikin shi sanye da jallabiya mai gajeran hannu ya d'an kishingid'a yana kallo daga gefen shi Sameer ne a saman 2 seater daga shi sai farar vest Kal da short basu dad'e da suka dawo daga Masallaci ba yayi wanka Haisam yasa aka kawo mashi Abinci, a saman center table Abincin yake saida wadda ta kawo tayi serving nashi sannan ta tafi, knocking d'in kopar Fatuu tay k'asa k'asa ta jiyo Muryar Haisam d'in yana bada izinin a shigo, a hankali ta tura k'opar tana sa kai suka had'a ido ya sakar mata murmushi itama murmushin ta maida mashi ta idasa shigowa Fauzy ma ta shigo da sallama suka nufi cikin parlon, a kujerar dake Opposite da su Haisam d'in 3 seater suka zauna, Fauzy sai yaba had'uwar parlon take a ranta sosae ya burgeta don baida hayaniya, gaida Haisam d'in Fatuu tay tana murmushi ya amsa Fauzy ma ta gaishe dashi, kallon Sameer Fatuu tay ta gaishe da shi idon shi akan Abincin da yake ci ya jinjina mata kai ita Fauzy sai lokacin hankalinta ya kai kan shi itama ta gaishe shi yadda yayi ma Fatuun haka yayi mata, Haisam ne yace mashi ga wife en tashi, nan ma kai ya d'aga, gaba d'aya su Fatuu mamaki ne ya kama su suka bi shi da ido ganin ko kallon su ya k'i yayi, "If you Don't look at her ta ya zaka san ta?" Haisam yay Maganar yana kallon shi, shiru kaman bai ji abunda yace ba sai da aka d'an d'auki lokaci sannan slowly ya d'ago da fuskar, gaba d'aya saida gaban su ya fad'i ba don komai ba sai ganin kamar shi da Haisam d'in, nuna mashi Fatuu Haisam yay ya jinjina kai daga haka ya maida shi kan Abincin shi, gaba d'aya Al'ajabin shi ne ya kama Fauzy har ta kasa janye idonta daga kan shi ita kuwa Fatuu maida kan ta tay kan tv tana kallon Film d'in da Haisam ke kallo suna yi suna kallon juna suna sakar ma juna murmushi, Fauzy ta saki baki tana ta kallon Sameer dake cin Abinci a gayance ba zato kawai sai gani tay yayi mata kallon k'asan ido ba arziki ta sunnar da kanta ta koma kallon Carpet don da ganin kallon hararar ta yayi, can bayan wani lokaci ta k'ara d'agowa tana kallon shi kawai sai gani tay ya d'ago gaba d'aya Fuskar nan a tamke da sauri ta sauke idon ta k'asa gaban ta na wani irin bugu tsoron ta kar yace mata wani abu game da kallon shi da take, janye idon shi yay daga kanta ya yago tissue ya fara goge bakin shi, mik'ewa yay bayan ya gama ya nufi hanyar Bedroom Fatuu ta d'an kalle shi da sauri ta kauda idon ta ganin yanayin shigar jikin shi ita kuwa Fauzyn bin shi tayi da kallo har ya shige cikin d'akin sannan ta maida idonta kan tv, bayan wani d'an lokaci Fatuu ta mik'e tace mashi bari su tafi Fauzy ma ta mik'e, ganin shima ya mik'e yasa Fauzy yin gaba, tare suka fito har bayan gidan ya tsaya daga bakin k'opar wurin Fatun ma ta tsaya lokacin ita Fauzy ta yi gaba, tana murmushi tace mashi saida safe yay shiru yana kallon ta fuskar shi a sake, ganin ya k'i cewa komai yasa ta d'age mashi gira tace koda wani abu, slowly ya furta "ba zaki taya ni kwana ba" waro ido tay ta d'an bud'e baki sai kuma tay yar dariya tace "to taya zan taya ka kwana bacin ba kai kadae bane" shiru ya d'an yi idanun shi a d'an lumshe kafin yace "in zaki taya ni ai akwae wani d'akin" da d'an alamun mamaki tace "anan gidan?" Kai ya girgiza mata yace a wani wuri, d'an bud'a ido tay tace "Hotel?" d'an murmushi yay ganin yadda tayi Maganar yace mata ba dole sai hotel ba ai akwae wani gidan, shiru ta d'an yi tana kallon shi yace ko bazata je ba tay d'an murmushi tace in yana so sai taje, hannu ya kai ya shafi forehead d'in shi bayan ya cire ya ci gaba da kallon ta, gaba d'aya ta gama fahimtar shi hakan yasa tace mashi suje d'in, shiru yay lokacin ya tuno sun yi da Fanan zasu fita, sigh yay yace ba wani abu taje ta kwanta ta huta, yamutsa mashi fuska tay a shagwabe tace to ba tace suje ba yana murmushi yace ta bari to sai gobe, ce mashi tay ya tabbatar ba fushi yay ba yana murmushi yace Saboda bai da wuya, itama murmushin tayi yace taje Friend d'inta na jiran ta tace "Good night and dream of me" yana murmushi yace mata wannan ko yaushe ne in dai zai yi bacci, wani irin lumshe mashi ido tay tana dariya dimples d'inta suka lotsa sosae yadda tay ta tafi dashi ji yake kaman ya jawota jikin shi sai dai ba dama don Fauzy ta tsaya daga can gaba tana jiranta, yanata sakin k'ayataccen murmushi yace mata taje ta fara tafiya da baya baya tana murmushi tay blowing mashi kiss, lumshe ido yay ya furta "I love you so much Zaraah" washe baki tay da d'an d'aga murya ta furta "I love too Ya Handsome d'ina" dariya suka saki a tare yace ta tafi lafiya lau kar ta fad'i ta d'aga mashi kai, juyawa tay tana tafiya tana waiwayen shi tana mashi bye bye, sai da ta kusa isa wurin Fauzy sannan ya juya ya koma, tana zuwa wurin Fauzy ta dafa Shoulder d'inta tana dariya tace sorry ta barta tana ta jira tana sallama da Hubby d'inta ne, d'an ta6e baki Fauzyn tay tace "I see, luv birds" k'ara sautin dariyar Fatuu tay, har zasu tafi sai kuma Fauzy ta tsaya tana Kallonta tace "Wai wanccan mutumin da muka je ku gaisa ya suke da Ya Haisam ne?" fad'i mata tay cousin brother d'in shi ne d'an Governor d'in Nasarawa kuma maman shi twins ne da Mom d'in su Haisam nan ta shiga fad'i mata irin yadda suke kama sosae ita bata ta6a ganin yan biyu ba haka, jinjina kai Fauzy tay tace "amman dai ba K'aramin miskili bane, ke ni tunda uwar data haife ni ban ta6a ganin miskilanci irin nashi ba, kiga fa, wai ya iya ya d'ago ya kalle mu ma abun duniya ya gagara kuma yasan shi aka je gaidawa, ko ba haka bama matar d'an uwan shi ce fa tazo wurin ai ko ba shi aka je gaidawa ba ya dai d'ago a gaisa amman wai har saida aka mashi magana sannan yayi mana wani kallon rashin Arzik'i" dariya Fatuu ke ta yi ganin yadda take Maganar a d'an harzuk'e, cigaba Fauzy tay "nifa Al'ajabi ma ya sa na kasa daina kallon shi wllh, har ko ya kama ni ina kallon nashi akai man wani d'an iskan kallo da saida yan cikina suka juya dama gashi da suffar ban tsoro kinga uban Power d'in daya tara a damtsen shi ni ban ta6a ganin Namiji bama a yadda na ganshi sai ko dai yan gidan mu wannan kuma su ai kaman muciya damatsen su suke in aka had'a da nashi" dariya sosae Fatuu ke yi, cigaba da tafiya sukai Fauzyn ta k'ara cewa "amman dai suna bala'en kama da Ya Haisam wllh har k'irar jikin kawae bambancin kala ne, amman kin san mi, ni ina son Namiji haka banson wanda ya cika fari" harara Fatuu ta wurga mata tace da bata samu ba ko amman k'arya ne tace wai bata son Namiji fari, dariya Fauzy tay tace "Allah ya baki hak'uri matar fari maida wukar nima na fad'i ne kawai dana samu wanda nike so ni ina ruwana da wani fari ai ko Yellow ne in dai ina son shi auran shi zanyi" "Yanzu ace yace yana son ki zaki so shi?" tambayarta Fauzyn tay wa, Fatun tace "shi wanccan d'an uwan Ya Haisam d'in" zaro ido Fauzy tay ta kai hannu ta ruk'e ha6a tace "tabbb kema dai da wani bahagon tunani kike wllh, ke yanzu ko wani yace maki wanccan zai so ni zaki yarda mutumin da daga gani zai yi izza ba kad'an ba, ai irin wanccan mutumin wllh matar shi ta bani don kuwa ba k'aramar wahalar shi zata sha ba don daga gani baza'a iya mashi cikin sauki ba, irin su komai akai masu ba'ai masu gwaninta" Fatuu dake dariya tace kawae ta bata amsa in ya ce yana son ta misali da aure zata iya auren shi, shiru Fauzy tay kaman mai nazari can tace "kinga don Allah mu bar Maganar nan abunda baka samu aka ce had'a shi da baka so don haka bai man ba" dariya sosae Fatuu ke yi tana fad'in Allah don bai ce yana son ta bane amman tasan tabbas zata so shi don ta fahimci ya yi mata, murmushi kawae Fauzyn tay zuciyarta na suffanto mata shi a ranta ta raya wannan ta ina ma zai iya wani son ta mima zai yi da ita, daidai lokacin suka iso part d'in da suke suka shiga. Bayan sun shiga d'akin Toilet Fatuu ta wuce tayo Alwalar sallar isha, bayan ta gama hira suka dasa wadda yawanci duk akan Walimar gobe ce saida suka kai tsakar dare sannan Fatuu ta tashi don tafiya Fauzy tace ta kwana anan kawae mana tace ai gadon bazai ishe su ba tunda akwae wuri can bari taje kawae suka yi sallama dasu Haulat Fauzy ta rakota har waje kafin suka yi sallama ta koma. Washe gari Juma'a ana tashi aka fara shirye shiryen Walima ba kama hannun yaro masu aikin girki tuni sun fara dama tun jiya aka fara aikin nama banda shanun da Baffan Fatuu ya bada harda raguna da kaji aka yayyanka, Misalin k'arfe sha d'aya lokacin duk an gama breakfast Laila tasa Fatuu taje tayi wanka, da kanta taje d'akin Hajiya da yake nan aka kai akwatunan lefenta ta d'aukko mata kayan da zata saka wanda babbar Super ce ta had'u ba k'arya anyi mata straight skirt da riga half gown tare da sark'a da yankunan gold harda yan hannu da su jaka da takalmi da mayafi mahad'in kayan, bayan ta saka kayan Laila ta yi mata yar light make up kafin anjima wadda zata yi mata Bridal makeup d'in ta zo, da kanta ta d'aura mata kallabi abun sai dae ace Tubarkallah, nan fa aka hau yi mata hotuna bayan sun gama Laila ta kamata ta nufi d'akin Mom d'in su da ita, a parlor suka isketa da wasu mutane cikin yan uwan su da suka zo bikin Mom d'in na ganinta ta hau yi mata murmushi tace a kawota gefenta, bayan ta zauna ta gaishe da ita da sauran mutanen ana ta fad'in Ma sha Allah Amarya, mik'ewa Mom tayi ta kamo hannun Fatuu itama ta mik'e suka shiga cikin Bedroom harda Laila, wurin Hajiya Zainab ta kai ta, itama da murmushi ta tarbeta Mom ta sata ta zauna a bakin gado itama ta zauna a d'ayan gefen, gaida Hajiya Zainab d'in tayi da fara'a ta amsa ta yaba gayun nata tare da Addu'ar fatan Alkhairi Laila na amsawa daga baya ta kama hannun Fatun tace suje wurin Hajiya ta mik'e suka nufi hanyar fita idanun su Mom akan su, bayan sun fita Hajiya Zainab tace yarinyar nada kyau Mom dake murmushi tace sosae, part d'in Hajiya suka wuce bayan sun fito, duk suna zaune a parlor suna ta hira harda gwaggo suka shigo Laila tayi sallama duk suka maido idon su kan su suna amsa sallamar, gaishe da Mutanen parlon tay duk suka amsa, gefen Hajiya ta kai Fatun ta zaunar da ita tana murmushi tace "ga kishiyar ki na kawo kiga adon ta" d'an murmushi Hajiya tay ta ta6e baki tana kallon Fatuu da itama kallon ta take tana murmushi sai cewa tay ina ta wani yi kyau haka kamar an bad'a mata k'asa a fuskar, gaba d'aya yan d'akin sukai dariya suna fad'in duk kyaun nan da tayi wannan dai kishi ne ba wani abu ba Gwaggo dae sai murmushi take farinciki fal ranta ganin yadda Autarta ta fito sai kace d'iyar manyan mutane, gaishe da Hajiyar tayi bayan ta amsa ta juya kan sauran mutane ta gaishe da su da fara'a duk suka amsa suka hau yin Addu'oi Laila dasu Hajiya na amsawa daga baya suka bar part d'in, baya suka wuce inda su Haulat suke, lokacin da suka shiga cikin parlon su Yadikko dasu Yaya duk suna zaune suna yin kallo, wurin su Laila ta nufa duk suka maido idon su kanta suna washe baki, zama tayi akan kujera Fatuu ma ta zauna a gefen ta suka hau gaishe da ita, da fara'a ta amsa Yadikko ce tace "wannan kaman Amarya" sai lokacin Laila ta gane ashe basu gane Fatun ba tana yar dariya tace itace ta kawo masu suga gayun ta gaba d'aya suka k'ara washe baki suna fad'in ai su basu ganeta ba Fatuu dai sai murmushi take ta gaida su,Yadikko ce ta daddage ta rangad'a gwad'a sai ga su Mino sun fito da gudu ta nufo ta ai koda taga Fatuu da gudu ta koma cikin d'akin tana fad'in azo aga Adda Fatuu Amarya tayi kaman sarauniya, nan duk suka firfito harda su Aunty Mareeya Fanan ma na a d'akin su tafi zama a wurin su duk da a d'akin Laila ta sauka, nan fa aka shiga yabon gayun aka hau yin hotuna da ita Fanan tace ai yakamata a kawo photographer Saboda ayi hard copy na tarihi Laila tace zai zo sai anjima sunyi Magana yace na iPhone d'in ma lafiya lou zai wanke su tace Ok, bayan sun gama hotunan Laila ta k'ara kamo hannunta ta fito da ita, part d'in Haisam ta wuce da ita suka shiga ta baya, knocking k'opar tayi aka bata izinin shigowa ta tura, su biyar ne a zaune, Haisam, Sameer, Salim, Abbas sai wani abokin su d'an nan Abujar Na'eem, da murmushi Laila ta nufi cikin parlon idanun su gaba d'aya akanta banda Sameer da yake sanye da headphones da alama ma bai san ta shigo ba, tunda suka shigo idon Haisam na akan Fatuu suna ta sakar ma juna murmushi, gaishe su Laila tayi tace ga Amaryar su nan ta kawo masu su ga gayunta na farko duk suka maido idon su akan Fatuu, kunya ce ta kamata da sauri ta sunnar da kanta k'asa ta gaishe dasu Abbas ya shiga tsokanar ta, mik'ewa Haisam yay jikin shi sanye da k'ananun kaya basu dad'e da gama yin Breakfast ba, inda suke tsaye ya nufo yana zuwa ya kai hannu ya kamo Fatun kawai sai ya rungumeta gaba d'aya Abbas da Na'eem suka sa sowa shi dai Saleem murmushi yake, abunda su Abbas ke yi ne ya jawo hankalin Sameer ya d'ago ya kalle su Abbas ya fara masu Video, gaba d'aya wata irin kunya ce ta kama Fatuu ji take kaman ta nutse k'asa, kokarin d'ago da kanta ya fara yi ta kafe kan tak'i yarda ya d'ago ta, d'ukar da kan shi yay can k'asan mak'oshi ya furta tayi kyau sosae murya can k'asa tace don Allah kunya take ji ya fita da ita ya furta Ok, d'agota yay tak'i yarda ta kalli side d'in da su Abbas suke yace ma Laila suje yana ruk'e da Fatun yayi mata side hug suka nufi hanyar fita ta cikin parlon Sameer dake kallon su ya d'an ta6e baki da yanayin d'an murmushi akan fuskar shi, suna fitowa wayar Laila ta fara yin ringing tace masu tana zuwa pls ta d'an yi gaba tana amsa wayar, maido Fatun yay jikinshi ya rungumeta ta yadda suna kallon fuskar juna sai yamutsa mashi fuska take tana fad'in ita kunya take ji don Allah, yana murmushi idanun shi a d'an lumshe yace to mi yay mata da zai zama abun kunya da ido tay mashi nuni da rungume tan da yayi, ce mata yay wannan ba wani abu bane yake ma yan'uwan shi ma balle ita matar shi, sai faman tura mashi baki da ya sha jambaki take gaba d'aya hakan da take ya fara turning d'in shi on, kallon ta kawae yake tana mashi shagwabar kar wani ya gan su don Allah, slowly ya duk'ar da kan shi saitin nata ya kai bakin shi kunnanta ya rad'a mata magana, d'agowa yay ya d'age mata gira tace "Yaushe?" a hankali ya furta "after isha" shiru ta d'an yi kaman mai nazarin wani abu taji yace ko bata so da sauri ta girgiza mashi kai, Laila ce ta dawo wurin su tana murmushi da sauri Fatuu ta juyar da fuskar ta, ce ma Haisam d'in tayi ko ta barta a nan ne ba tare daya ce komai ba ya saki Fatun Laila ta kamo hannunta suka nufi sauka daga benen tana yi tana d'an waiwayen shi yana tsaye bai koma ba fuskar shi da d'an murmushi har suka sauka sannan ya koma ciki. Lokacin da akai Sallar juma'a hidima ta kan kama bak'i yan Walima tuni sun fara zuwa, bayan an yi salla mai makeup tazo lokacin Fatuu na d'akin Laila ta shirya cikin dandatsetsen lace Swarovski d'an dubu d'aruruwa anyi mata d'inkin riga da skirt tasa su sark'ar diamond abun ba'a magana jikin Fatuu ya zama kud'i ko ince kud'ad'e, ba 6ata lokaci aka fara mata bridal Makeup d'in, tun ana cikin yi ake aikowa kiranta daga d'akin Mom don tazo a ganta, Laila ce ta kira Mom d'in nasu ta sanar mata ana mata kwalliya ne in aka gama zata kawo ta, Jama'a kuzo kuga Fatuu ya fillo don Allah ni Saboda kallon ta ma har saida Alk'alami na ya fad'i, abun sai dai ace Tubarakallah Ma sha Allah an k'ara jik'a kyau da ruwan Naira abun ba'a magana, Nan aka shiga yi mata hotuna harda su Video mai makeup d'in ma tana ta mata don ta d'aura a handles d'inta na social media gashi da yake Fatun a wayancenta take abun sai ya tsaru sosae, ana cikin yi Jidderh ta shigo tasha ankonta an mata yar Arzik'in Fitted gown (bana ce matsiyaciya ba😂) sosae d'inkin ya had'u an tsara shi da mix and match d'in ta fito a yar matan Abuja, ce ma Aunty Laila tayi Mom tace a kawo ta hakanan Friends d'inta ne zasu ganta, wani had'add'an gele mai shara shara ana ganin komai na jikin mutum baida girma sosae ta d'aukko ta yafa mata tasa takalma nasu tsini sosae hannun ta ruk'e da yar purse d'in su Laila ta kama hannunta suka tafi, bayan sunje a parlor suka tsaya Mutanen ciki suka hau yabon gayun Amarya daga baya ta wuce da ita cikin Bedroom, duk k'awayen Mom ne a ciki wasu anko ne a jikin su na full embroidery har Hajiya Zainab ma da Mom ankon ne a jikin su anyi masu dogayen riguna sunyi kyau abun har ba'a magana, harda Hajiya Kubra ta Comment section a cikin su ashe itama mutuniyar First Lady ce tasha anko full embroidery, ciki Laila ta shiga da ita Jidderh ma na biye da su, bin su d'aya bayan d'aya ta shiga yi da Fatun suna ganinta tana gaishe dasu sai yabon kyaun ta suke nan aka shiga bata kyautar kud'i Laila na amsar mata harda wadda ta bata kyautar yan kunnan zinari ita dai Fatuu sai murmushi kawai take bakin ta ya mutu abun ya girmi tunanin ta, abun mata sai ya zama kamar gasa ma, ita Hajiya Zainab Account details d'in Fatun tace abata aka sa sowa ana mata kirari sai murmushi take daga baya aka kaita wurin Mom ta zaunar da ita kusa da ita a hankali Fatuu ta gaisheta tana murmushi tace "Ma sha Allah Daughter kin yi kyau" tace mata ta gode, bayan sun gama da nan Laila ta fito da ita suka nufi part d'in Hajiya daga nan kuma bayan sun fito baya suka nufa gaba d'aya rud'ewa su kai da ganin yadda Fatuu ta had'u, anan Laila ta barta ta tafi itama ta shirya don duk kusan kowa ya saka ankon shi kowa ka gani atamfar tayi mashi kyau daga bak'ak'en har fararen, sosae Fauzy da Mino suka yi kyau ita Fauzy fitted gown ce Mino kuma riga da skirt, su Aunty Mareeya da Feenah duk dogayen riguna aka masu styles masu kyau kalar na yan Abuja Fanan itama fitted gown aka mata sosae tayi kyau gashi a jikin atamfar akwae kalar gashinta, da Laila zata tafi ta bita don ayi mata makeup itama. Da lokacin cin Abinci yayi a parlor aka shiga jerawa saman Dining tables an k'ara wasu guda ukku suma masu cin mutum sha biyu sai aka matsar da set guda na kujeru aka had'e su, Abinci ne kala daban daban sai wanda Mutun ke so sai kuma mutum ya ci ya ture nama kuwa ba don kar inyi k'arya ba sai ince duk tsoka tayi dunkulan hannun mutum in ma bata yi ba to ta kusa🤧 ga kaji Malam, drinks da ruwa su wannan kaman company d'in su ka zo ma, bayan an gama tsara wurin aka je aka sanar ma Mom da Aunty suka fito da Mutanensu aka zazzauna yan baya ma su Aunty Mareeya aka masu magana suka fito, yadikko bata son suje ai kauyanci hakan yasa taje tayi ma gwaggo magana kan in zai yiwu akawo masu nasu can gwaggon ta fahimceta tace to, Table guda duk k'awayen Mom ne harda Hajiya Zainab Wani kuma Aunty ce da K'awayen ta wanda wasu k'awayen su ne gaba d'aya ita da Mom, a d'ayan table na ukku su Aunty Laila ne harda Amarya Fatuu da K'awayen su sai table na k'arshe nan su Aunty Mareeya suke harda Fanan da wasu yan uwan su yan Daura Ma'aikata nata Serving nasu abun gwanin burgewa kowa harkan gaban shi yake bai damu da yadda wani ke cin Abincin shi ba, a can cikin parlon ma a saman kujeru akwae mutane zazzaune suna cin Abincin, Haisam na part d'in shi da Abokan shi harda Najeeb da ya iso da daddare ya sauka a guest house d'in baban shi suma suna cin Abincin haka Nameer ma yana a part d'in shi da su Kawu Amadu da Tk da wasu Abokan shi, Senator ma na a part d'in shi da wasu Abokan shi da kuma yan uwan shi harda Baffan Fatuu dasu Ardo, sai da Baffan yayi masu hud'uba cikin hikima da zasu zo ya nuna masu abunda yakamata suyi don nan ba komai a ke masu ba sudai gyad'a kai ne nasu don yanzu mulkin ya koma kan Baffan Fatuu, duk wanda yazo sai Senator ya nuna masu dangin Amaryar sun gaisa, abun dai sai dae ace Ma sha Allah don Walima kam tayi Walima an ci an sha anyi hani'an kowa ka gani fuskar shi cike take da annuri bayan an gama aka hau yin hotuna gwaggo taje ta kira su Yadikko suka zo suma akayi hotunan da su, Fanan da kanta taje part d'in Haisam ta kira shi don ayi hotuna suka dawo dashi yana sanye da Farar shadda haka takalman shi da agogon shi duk farare ne yau dae Allah yayi an rufe kan da hula babbar rigar shi na ruk'e a hannun shi tare da Abbas suka fito shima yana sanye da riga da wando na farar shadda, idon Fatuu akan shi har suka k'araso wani irin dad'i take ji kaman ta kama yin rawa a yau ta k'ara jinjina girman Ubangiji ta k'ara gasgata Kalmar nan ta mahakurci mawadaci ne, bayan sun shigo Photographer yaci gaba da aiki, Mom da kanta ta kirawo Senator da Nameer don su zo ai hotuna dasu harda su Kawu Amadu su ka zo daga baya Senator d'in ya koma Saboda mutane d'aya baro, ana cikin hotunan Jidderh tazo wurin Fatuu tace mata ga bak'uwa Daddy yace akawo ta wurin ta, da farko Fatuu bata gane bak'uwar ba dake ta kallonta tana dariya hannunta ruk'e da yarinya da bazata wuce watanni ba, sai can da tay magana tace ma Fatun hala bata ganeta ba sannan Fatun ta d'an waro ido tace "Kaman Aunty Sadeeya?" tana dariya tace itace, mamaki ne ya kama Fatuu ganin k'anwar Khalid a wurin, hoton akayi masu tare bayan an gama ta nufi cikin parlon da ita suka zauna a saman 2 seater, "Amman Aunty Sadeeya ya akai kika san da walimar nan har kika zo?" Fatuu ta tambaya da alamun mamaki akan fuskar ta, tana murmushi tace "tare da Dad muka zo shi ya kira ni ya sanar dani yace zamu zo dashi, ni da yake ina nan ina Aure ban fi shekara guda da watanni ba, gyad'a kai Fatuu tay tace Allah sarki, "kin yi kyau sosae wllh kaman bake ba duk da dama kina da kyau an ma kin canza sosae kin k'ara girma kuma, na taya ki murna sosae Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya da zuriya d'ayyiba" Fatuu nata Murmushi ta amsa mata da Amin, shiru suka d'an yi dukkan su murmushi ne akan fuskar su can Fatuu ta tambaye ta Mom d'in su tace tana nan tama san zasu zo don sunyi waya take sanar mata tace ma ta kirata tayi mata Allah yasa Alkhairi, kai Fatun ta jinjina suka d'an k'ara yin shiru can Sadeeyar tace "baki tambayi Ya Khalid ba" har saida gaban Fatuu ya fad'i jin sunan Khalid, d'an murmushi tay a sanyaye tace ma Sadiyar yana ina, "Yana nan yanzu a koma Yola acan yake aiki tare ma akayi bikin mu don bayan an fasa naku yayi nadama sosae, don har gwuiwa k'asa ya rok'i Dad kan ya bashi dama ta k'arshe kada a fasa Auren anan yake sanar mashi ai an ma d'aura maki Aure don haka ya hak'ura dake ba matar shi bace, aikuwa anan ya sume mashi abun ya kai shi ga kwanciya har gadon Asibiti, sosae yayi nadama wllh don akwae lokacin da muka zauna dashi yana k'walla yake fad'i man Allah ya jarabe shi da son ki sosae dama tunda ya gan ki matsayin wadda zai Aura yaji kin mashi gajan hak'uri yaja mashi amman yasan Allah ne ya kama shi, lokacin da aka zo neman Aure na shine Dad yayi mashi Maganar ya fito da wadda yake so tunda yasan bai rasa yan mata sai a had'a shine yace ma Dad d'in ya bar mashi komai ya nemo mashi kowacece zai Aura, farko Dad cewa yay ya fidda hannun shi akan shi saida Mom tay ta rok'on shi tana nuna mashi da gaske ya canza ba zai bashi kunya ba anan har take mashi Maganar wata k'anwar ki wai da akayi magana da suka je Dad d'in yace ai kuma shi ba K'aramin mutum bane ya riga yace a kyaleta tayi karatun ta yanzu bazai Koma ba yace a bashi ko ba don haka ba ma don abunda Ya Khalid d'in yay maki bazai nema mashi k'anwar ki ba, k'arshe dai wata d'iyar Abokin shi ya samo mashi Hafsat itama Secondary ta gama ba laifi tana da kyau itama bafullatana ce a cikin Yola suke shine akayi bikin mu tare, Yanzu suna acan Yola d'in yasa taci gaba da karatu tana nan ma da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, gaba d'aya Ya Khalid ya canza ta sanadiyyar abunda ya faru, sosae yay sanyi duk wani hali mara kyau da kika sani ya bari wllh don ni bai 6oye man komai tun lokacin da yana cikin ciwon son ki ya maida ni kamar k'awar shi yay ta fad'i man damuwar shi in ta lallashin shi ina k'arfafa mashi gwuiwa yanzu haka shima yasan da zamu zo nan" idanun ta cike da k'walla ta k'arasa Maganar itama Fatuu sosae jikinta yayi sanyi zuciyar ta sai tunano mata abubuwan da suka faru tsakanin su take, Allah mai juya Al'amari a yadda yaso a kuma lokacin daya so da rabon ta silar hakan zata auri Haisam yanzu data k'i yarda kota yanke ta gudu da tayi ma kan ta, k'arshe rayuwarta ta wulakance ta kuma jefa iyayen ta a matsala, shiyasa ake son bawa ya rink'a yarda da k'addara mai kyau da mara kyau, duk abunda Allah yayi ma bawan shi mai kyau ne don yafi mu son kan mu, sau da yawa abubuwa marasa dad'i da suke faruwa damu wasu kan haifar da abubuwa masu dad'i agare mu matuk'ar zamu dogara da Allah muyi rik'o da yin Hak'uri, suna zaunen Laila ta zo tace mata Dad d'in su na nemanta tace to ta nuna mata Sadeeya tace bak'uwarta ce yar uwarsu ce a Adamawa tana aure anan, a mutunce suka gaisa harda tambayar ta Unguwar da take anan Abuja ta d'auki Baby d'inta, daga baya ta kira Jidderh ta had'a su tace a kaita d'akinta a bata Abinci kafin su dawo, part d'in Dad d'in suka wuce gaba d'aya parlon shi cike yake da Manyan Mutane masu tumbin Naira kama daga shahararrun masu kud'i zuwa masu Mulki, Laila ta shiga bin su da ita suna gaishe su suma dae har da kyautar kud'in suka mata daga baya Dad yace akawo ta wurin Alhaji Lawal dake a kusa dashi, a k'asa ta tsugunna ya kai hannu ya dafa Shoulder dinta da fara'a yace "Ma sha Allah Daughter, nayi matuk'ar farincikin yadda abu ya kasance, wannan aikin Albarkar da muke sa maki ne, matuk'ar zaka yi biyayya ga iyayen ka to kuwa rayuwar ka zata yi Albarka, Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya da zuria dayyiba yasa gidan zaman ki ne na har abada" Mutanen dake a kusa dashi sai amsawa da Amin suke harda wani abokin shi d'an Majalisa da suka zo tare, kasa jurewa Fatuu tay ta shiga yin hawaye komai daya faru a baya yana dawo mata, Envelope ya fiddo daga cikin Aljihun shi ya mik'a mata kawae sai ta fashe da kuka ya hau rarrashinta yana fad'in ai ba abun kuka bane, Senator dake ta murmushi yace "Kukan dad'i ne kasan shima yana sa ayi kuka" ya kalli Fatuu yace "Hakane ko Daughter?" A hankali ta d'aga mashi kai duk aka yi dariya daga baya Dad d'in yace ma Laila taje da ita. Bayan sallar la'asar Nameer ya d'auki Mino suka fita Tk ma ya d'auki su Kawu Amadu da Kamalu suka shiga gari, Lokacin Laila tasa Fatuu ta canza shiga zuwa rantsatstsiyar shadda gray data sha ubansun aiki harda alkyabba aka d'aura mata lokacin Malamar da aka d'aukko zata yi Wa'azi wadda sananna ce ta zo, tuni an gyara main parlor d'in tsaf anan aka zazzauna Malamar itama a kan kujera ta zauna ta fara Wa'azin hannunta ruk'e da lasifika da ta karad'e ko ina, Wa'azi mai tsuma zuciya kan rayuwar Aure tayi, sai gab da sallar Magrib aka gama nan aka shiga rabon souvenirs abubuwa kala kala masu d'auke da sunan Haisam Ali Adamu Zakee da Fatima Muhammad Ardo, ba masu hotunansu cikin abubuwan da aka raba don Haisam d'in ya nuna bai so. Alhamdulillah Walima ta tashi lafiya abun dai sai san barka wllh, mun ci mun sha munyi hani'an yan Comment section an sha da ku da baku yi anko ba kun zo, kar ku manta gobe in Allah ya kai mu akwae Dinner itama kuma in ba anko ba shiga zaku yi ba ato😹. Da daddare bayan isha gaba d'aya Su Fauzy bajewa sukai a parlor harda su Aunty Mareeya gaba d'ayan su dai yan part d'in ana hirar Walima cike da nishad'i, Wayar Fatuu dake hannun Fauzy had'e da tata ce ta fara ringing ta kai idonta kan screen d'in, ganin Haisam ne yasa ta mik'e don taje ta kai mata, har lokacin ankonta ne a jikinta rigar ta kamata kanta tayi d'aurin kallabi mai steps da akayi mata gashinta dake fake ya fito ta tsakiya ya bud'e sosae, sauri sauri gudu gudu ta nufi cikin gidan ganin kiran ya yanke ya kuma sake kira, hanyar d'akin Mom d'in su Haisam ta nufa don tun bayan da aka gama Wa'azi Fatun na can Mom tasa ta zauna Saboda masu son ganinta ba sai an ta nemota ba, tana zuwa daidai bakin corridor tana niyyar shiga da d'an gudu gudu kwatsam taci karo da Mutum wanda har saida tai taga taga tayo baya, ba arziki ta kai hannu ta dafe goshinta idanunta a rufe ta shiga fad'in "wayyo..wai...wai.wai...." A yadda taji sai kace ta bugi dutse, a hankali ta d'ago still hannun na a goshin slowly ta fara bud'e idanunta, koda tay arba da wanda tay karon ai ba shiri ta idasa bud'e idanun ta waro su, tsaye yake k'ik'am sai kace an dasa shi don koda sukai karon bai ko yi gezau ba, Sameer ne yana sanye da farin jeans da farar riga ta ciki sai aka d'aura Yellow a sama ma6allan ta a bud'e hakan ya bayyana ta cikin agogon hannunshi fara ce itama daga wurin glass d'in kan yana reflecting yellow sai k'afafun shi ma sanye suke da fararen takalma, daga wurin Mom d'in shi yake Hajiya Zainab data kira shi bayan ya fito ya d'aga waya yana magana sukai karon, gaba d'aya wayar shin da glass d'in shi daya ruk'o a hannu sun fad'i k'asa, bin shi da kallo Fauzy tay gabanta na wani irin Fad'uwa ganin mugun kallon da yake mata ya tamke fuska sosae, Murya na rawa tace "D...don Allah kayi hakuri bansan ka taho bane ina sauri ne zan kai waya ana kira" ta k'arasa tare da d'aga mashi wayar don ya gani, in bango ya tanka to shima ya tanka haka yanayin fuskar tashi ma bai canza ba, yan kame kame Fauzy ta shiga yi tana haka idanunta suka sauka akan Wayar shi da glass d'in dake yashe a k'asa, da sauri ta duk'a ta d'aukko su Allah yaso glass d'in bai yi komai ba, tana juya wayar zata mik'a mashi taga glass d'in yayi lafiyayyun tsaga har kusan hud'u, zaro ido tay ta bud'e baki gabanta ya shiga wani irin bugu, ganin reaction d'in fuskar ta yasa slowly ya kai idanun shi kan wayar idanunshi suka sauka akan glass d'in dake a tsattsage, wani irin kallo ya d'ago yana mata da sauri ta fara ja da baya tana yamutsa fuska daga d'an can gaban shi ta tsaya, kawai sai gani tay ya fara nufota, tana shirin k'ara ja baya cikin husky voice d'in shi ya furta "Stay where you are!!!" har saida cikinta ya yamutsa, a gabanta ya tsaya ya mik'a mata hannu da sauri ta mik'a mashi wayar ya k'i amsa ta bishi da ido cike da tashin hankali, a kausashe ya furta ta bashi glass hannunta har kerma yake ta mik'a mashi ya amsa, saka shi a idanun shi yayi bayan ya gama ya tsaida kallonshi akanta duk da bata ganin idanun, k'ara Mik'o mashi wayar tay murya na rawa tace don Allah yayi hak'uri wllh bada niyya bane, banza yay mata sai da ya mula sannan ya furta "ki biya shi!" Wani irin miyau Fauzy ta had'iya ko ba'a fad'i mata ba daga ganin wayar tasan mai tsada ce balle kuma daya kasance ga wanda ke rike da ita, da yake dare ne kowa ya gaji wasu kuma basu a gidan ba wasu mutane da ke shigowa wurin sai wanda ba'a rasa ba sun fito su kuma ba lalle su fahimci abunda ke wakana ba don daga yanayin su sai kaga kaman magana suke, Magiya taci gaba da yi mashi kan yayi hak'uri tana cewa tasan bazata iya biyan shi ba, ringing wayar ta fara yi ta kalli wayar kafin ta kalle shi tana kikkafta idanu, hannu ya mik'a ya amsa ya furta mata "ki biyo ni" daga haka ya juya, tsaye tay duk da taji abunda yace aikuwa ya juyo cikin daka tsawa tace "I told you to Follow me!!!" bin shi tay ya nufi hanyar fita daga cikin parlon, daidai gaban wata Mota da aka parker a gaban Entry Hall ya dakata itama ta tsaya daga d'an nesa dashi, dama wayar da ya taho yana yi umarni yake badawa na azo a d'auke shi suka yi karon, hannu ya kai ya bud'e kopar gaba, da kai yayi ma driver d'in alamun ya fito, bayan ya fito tsayawa yay daga gefe ya d'an russuna kai, ce mashi yay yaje zai driving da kan shi yayi mashi godiya ya juya, juyawa yay ya kalli Fauzy da tay tsuru tsuru a kausashe yace "come and get in to the car!" Nan take k'wallan da suka tarun mata a ido suka fara zubowa taci gaba da yi mashi magiya tana yayi hak'uri don Allah, kai ya jinjina ya d'an cize baki can cikin d'an d'aga murya yace "I don't allow anyone to argue with me! Ki shiga Mota else, yanzu zan sa aje a kulle ki!" yarfa hannu Fauzy ta shiga yi a hankali ta fara fad'in ta bani, matsawa ta fara yi a hankali tana tunkarar Motar, ganin yadda take tafiya ya k'ara ce mata kada tay wasting time nashi, tana niyyar bud'e k'opar baya ya galla mata wata muguwar harara ba shiri ta fasa bud'ewa da kan shi yay mata alamar taje ta shiga gaba ta zagaya tana kuka k'asa k'asa, saida ta shiga sannan ya kai hannu cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo wani farin hanky ya shimfid'a a saman seat d'in sannan ya shiga, bayan ya zauna da k'arfi ya rufo k'opar, dama Motar a kunne take aikuwa a tsiyace ya ja ta bayan yasha round d'in ya Mik'i hanyar Gate ya fuce............ *ASM 081* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* .........Suna fita daga cikin gidan suka hau hanya, hankalin Fauzy in yayi dubu to ya tashi tunanin ta ina zai kai ta kuma mi za'a mata, basu dad'e da hawa titi ba wayar Fatuu dake hannun Fauzy ta fara ringing, a hankali ta juya ta kalli Sameer da idon shi na akan titi yana driving, a d'arare takai hannu zata d'auka a kausashe taji yace "Don't pick it!" fasa d'agawar tay ta juya ta kalle shi fuskarta a yamutse har lokacin k'walla na zubo mata, wani kiran ne ya sake shigowa bayan wanccan ya yanke taji yace ta kashe wayan gaba daya, cikin muryar kuka tace "Don Allah ka bari in d'auka in fad'i mashi bana gidan, Ya Haisam ke kiran matar shi wayarta ce dama ita na taho in kai mawa Saboda yanata kira shine har na buge ka ban gani ba" banza yay mata yana ta driving d'in, saida kiran ya kusa yankewa ya bata umarnin ta d'aga, hannunta har d'an rawa yake tay picking kiran, tun kafin yace wani abu ta riga shi ce mashi k'awarta ce wayar na a hannunta kuma bata gida ya Furta Ok kawae daga haka ya katse kiran, tafiya suke ta faman yi a saman shimfidaddun titinun Abuja, tun Fauzy na yin k'walla tana kai hannu tana gogewa har ta saduda taci gaba da kallon hanya ta widescreen don glass d'in Motar blacktinted ne ba'a ganin waje sosae ta cikin su, saida suka d'auki kusan mintuna 30 sannan suka iso wata unguwa mai d'auke da had'add'un manyan gine gine ga fitilu ta ko'ina kaman da rana, yar tafiya sukai a kan titin Unguwar suka iso bakin wani katafaren gida da jami'an yan sanda guda biyu ke gadi kowannensu na rataye da bindinga a jikin shi, karya kan Motar yayi ya tunkari dank'areren gate d'in gidan da sauri su duka jami'an suka hau zuge gate din, bayan sun gama ya nufi shiga cikin gidan duk suka d'aga ma Motar hannu, ko horn baiyi masu ba balle ya tsaya ya shige ciki da Motar da gudu, babban parking space d'in gidan ya nufa bayan ya parker ya kashe Motar, sai lokacin ya juya ya kalli Fauzy tun bayan da suka fito ya furta mata "come out!" bud'e baki tay da niyyar yin Magana ya bud'e kopar ya fita, hannunta sai rawa yake ta bud'e kopar ta zuru k'afafunta dake sanye da takalma masu d'an tudu kafin ta k'arasa fitowa, hankali tashe take bin gidan da kallo wanda ba k'arya ya matuk'ar Had'uwa, ba wani mugun girma gidan gare shi ba kuma ba k'arami bane, bene ne hawa d'aya iya fentin gidan abun kallo ne don ya tsaru sosae, a harabar gidan akwae had'add'un Flowers su kan su an tsara shukar su gasu a gyare luf luf dasu, daga can gefe runfunan shak'atawa ne guda ukku kowacce na d'auke da k'ayatattun kujerun katako a zagaye da table, zagaye da runfunan akwae manyan shukokin Flowers harda irin Xmas tree da ake ma adon fitilu itama anyi mata hakan tana ta sakin haske kala daban daban haka sauran flowers d'in akwae masu reflecting hasken dogayen fitilun dake a wurare daban daban a cikin harabar gidan sun haske ko ina ta yadda ko allurar ka ta fad'i to zaka iya ganinta, a cikin hall d'in sama wata jigunannar katuwar fitilar sama ce mai adon sarkoki kai kace in mutum ya tsaya zata fad'o mashi, Bayan ya rufe k'opar hanyar fita daga cikin parking space d'in ya nufa, har ya kusa fita ya dakata ya juya yana kallon Fauzy da tayi tsaye a bakin kopar Motar da ko rufeta bata yi ba sai zare ido take a iya fuskarta zaka fahimci ba K'aramin tashi hankalin ta yay ba, cikin d'an d'aga murya yace zata tsaya anan ne, yamutsa fuska tay ta fara kuka tana mashi magiyar don Allah yayi hak'uri, tsaye yay yana mata wani kallon rashin Arzik'i ta cikin glass d'in daya maida bayan daya fito daga cikin Motar, ganin zata 6ata mashi lokaci yasa shi ce mata ta tsaya anan za'a shigo da ita, jin haka yasa ba shiri ta biyo bayan shi don gaba d'aya a tsorace take, har ta fito cikin harabar ya dakata ya juyo hakan yasa itama ta tsaya, ce mata yay waye zai rufe mata kopar da sauri ta juya ta nufi komawa cikin parking space d'in tana yi tana waiwayen shi yana tsaye yana kallon ta, bayan ta rufo k'opar ta dawo ya juya yaci gaba da tafiyarshi mai cike da k'asaita, ganin ya kusa shiga cikin ginin gidan yasa ta k'ara saurin da take, a bakin dakakkar kopar shiga gidan dake a cikin entry hall ya tsaya saida Fauzy ta k'araso wurin ta tsaya daga d'an nesa dashi sannan ya kai hannu cikin d'ayan Aljihun jeans d'in shi wata farar wallet ya fiddo ya bud'eta, wani d'an card ya ciro ya kai shi jikin kopar cikin wani d'an rami dake kusa da handle d'inta, yana zura shi sai gashi tayi wata yar k'ara, zaro katin yayi ya maida shi a cikin wallet d'in sannan ya kai hannu jikin handle d'in ya tura k'opar ta bud'e, shiga yay ciki ya juyo yana kallon Fauzy, ganin irin kallon da yake mata yasa cikin fad'uwar gaba ta tunkari k'opar tana tafiya a d'arare aikuwa ya daka mata tsawa yace kar ta 6ata mashi lokaci baiwar Allah har saida ta firgita da sauri ta nufi ciki, matsawa yay gefe ta wuce ya kai hannu ya rufe k'opar aikuwa a firgice ta kalli kopar kafin ta maido kallon kanshi ta fashe da kuka mai sauti ta hau rok'on shi don Allah yayi hak'uri ya k'yaleta ta tafi, kai kace bada shi take ba ya shige cikin Corridor d'in da suka shigo, yana niyyar karya kwana ya dakata ya juyo yana kallon Fauzy dake ta kuka tayi tsaye a wurin hannunta d'aya ruk'e da kopar sai jan ta take amman sai kace tana jawo bango, jinjina kai yay yace mata in ta bari ya shige zata ga abunda zai same ta a wurin aikuwa tun kafin ya rufe baki da sauri ta nufo shi, bene ne a wurin shi kan shi abun kallo ne don ya tsaru tunda ga kan Matattakalar zuwa yadda akai design d'in shi ya wani markwad'a, da sauri da sauri take hawa saman shi har tana yin kamar zata fad'i tana yi tana waiwayen bayanta, bayan ya haye a cikin wani Corridor ya tsaya cikin shi akwae flower vases masu kyau d'auke da kayatattun Flowers haka saman wurin akwae fitila mai kyau da tsari, kopopi ukku ne a wurin a gaban d'aya daga ciki ta bangaren hagu ya tsaya, hannu ya kai jikin kopar ya ta6a wani d'an circle na glass nan take k'opar tay wani d'an sauti alamar ta bud'e, tura ta yay ya shiga ya tsaya daga bakin kopar yana kallon Fauzy da tay fiki fiki duk ta firgice gata daga ita sai rigar jikinta ko gyale babu, "Come in" ya fad'a tare da yi mata nuni da kai, yamutsa fuska ta fara yi k'walla suka cigaba da zubowa ba tare data matsa daga inda take ba, hak'uri ta fara bashi kawae sai ya saki kopar yace mata ta bari ta rufe, a rud'e ta kutsa kai ciki bayan ta shiga kopar ta maida kanta ta rufe, Ya Allah kai mana Arziki mai Amfani shine abunda na furta, had'add'an parlor ne daya amsa sunan parlon masu Arziki sosae, komai na cikin shi fari da golden ne tun daga kan kujerun, labulaye, carpet, hatta fitilun cikin shi fari da golden ne kai kace da gold akai adon wasu abubuwan, sam parlon baida hayaniya komae tsaf tsaf sai ni'imtaccen sanyi mai had'e da daddad'an k'amshi ke tashi, a yanayin parlon kai kace mutane basu rayuwa a cikin shi yadda fararen abubuwan suke K'al da su, tsaye tay a bakin kopar duk da halin da take ciki sai da ta bi parlon da kallo fuskarta duk hawaye, cikin parlon ya shiga a saman farin c-table shima da adon golden ya d'aura wallet da wayar shi, hannu ya kai ya cire glass d'in Fuskar shi shima ya aje a wurin, saida ya d'an juyo ya kalleta suka had'a ido kafin ya juya walking majestically ya nufi hanyar wani Corridor ta bi bayan shi da kallo har ya shige, lokacin ta samu damar k'ara bin ko'ina na cikin Parlon da kallo baki a d'an bud'e, bai d'auki lokaci sosae ba ya fito ya cire yellow rigar ta sama sai farar ta ciki da ta kama jikin shi kirar k'arfin shi ta bayyana ya cire takalman k'afafun shi ya sanyo wasu bak'ak'en slippers masu d'an tudu, da sauri Fauzy ta maida idanunta cikin Corridor d'in jin sautin tafiya, yana fitowa suka had'a ido ya wani k'ara tamke fuskar da sauri ta maida idon gefe gabanta na bugawa da k'arfi da k'arfi, cikin parlon ya shigo ya nufi inda fridge yake a can gefe, bud'ewa yay bayan yaje gaban shi Fauzy ta kai idon ta wurin, hannu ya kai ciki ya fiddo wata k'atuwar bak'ar kwalba an nad'e saman marfinta da wata leda mai k'yalli haka ma a jikinta akwae takarda mai d'auke da rubutu zagaye da ita, d'aurata yay a saman fridge d'in ya k'ara kai hannu ciki ya d'aukko tumbler, bayan ya rufe fridge d'in ya kai d'ayan hannun shi ya d'aukko kwalbar tana ganin zai juyo da sauri ta kauda idonta daga barin kallon shi, cikin parlon ya dawo ya nufi kujera ya d'aura abunda ya d'aukko kafin ya kai hannu ya jawo c-table d'in gab da kujerar, d'aukar kwalbar da cup d'in yay ya d'aura su a saman table d'in kafin ya zauna ya kai hannu ya d'aukko kwalbar ya kaita baki yana cizge ledar da aka nad'e bakin ta, sakin baki Fauzy tay tana kallon shi cike da Al'ajabi don ita a saninta irin wannan kwalbar ta giya ce, lokacin daya gama bud'ewa ya fara tsiyayawa a cikin cup d'in wani irin harbawa zuciyar Fauzy ta shiga yin don kuwa ganin kalar abunda ya zuba a cikin cup d'in ta tabbatar ma kanta da giya ce, kaman rabi ya zuba bayan ya rufe kwalbar ya d'auka ya kai baki ya fara sipping a hankali, yana cikin sha yayi mata kallon k'asan ido da sauri ta sunnar da kanta k'asa gaban ta na cigaba da fad'uwa, yana cikin sha ya kai hannu kan table d'in ya d'aukko remote da ke a saman shi daga d'an can gefe ya kunna Tv, bayan ta kama ya shiga caccanza channel ya kamo wadda yake so sannan yaci gaba da shan lemun d'ayan hannunshi ruk'e da remote d'in ya d'aura kafa d'aya akan d'aya idon shi akan Tv yana kallo, fara gajiya da tsayuwar Fauzy tay daurewa kawai take don k'afafunta har sun fara mata zafi sai wuwwurga ido take sai ta kalle shi sai kuma ta kalli Tv shi kam gaba d'aya ya maida hankalin shi akan Tv ko kallonta bai yi sai kace ma ya manta da ita a wurin, sun d'auki lokaci a haka gaba d'aya Fauzy ta gaji da tsayuwar har k'afafunta sun fara mata zunga sai kallon shi take tana yamutsa fuska tare da kikkafta idanunta da suka cika da kwalla, matsawa ta d'an k'ara yi gaba kad'an cikin rawar murya tace "Don girman Allah kayi hak'uri ka k'yale ni in tafi, nasan ana can anata nema na wllh" da alama dae bango take ma magana don kuwa sipping d'in lemun shi da ya k'ara zubawa kawai yake, kuka Fauzy tasa sosae mai sauti sai lokacin ya juyo yana mata wani kallo, cigaba da magiya tay mashi tana nuni da hannuwan ta, janye idon shi yay daga kan ta ya ci gaba da kallon shi, bayan ya gama shanye abun cikin cup d'in d'aura cup d'in yayi saman table, tsam ya mik'e ya nufo cikin parlon ganin inda take yake nufowa yasa ta zaro ido ta fara ja da baya gabanta na wani irin bugu tamkar ana mata luguden ta6are, cigaba da tunkararta yay tana ja da baya can ta juya a rud'e ta kama k'opa ta fara jijjiga handle d'in a K'ok'arin ta nata bud'e tana yi tana waiwayen shi duk ta gigice ba kamar da take ganin giya ce ya gama sha, tana haka ya cimmata kokarin bi ta gefe ta ruga tay ya kai duka hannuwan shi ya dafe kopar ta yadda ya sakata a tsakiyar su yay mata rumfa, gaba d'aya jikinta 6ari yake har bakinta sai numfashi take da k'arfi tunda take a rayuwarta bata taba shiga firgici irin wannan ba, ko lokacin da aka sanar Mata Mujaheed yayi Aure batai irin wannan firgicewar ba Saboda sumewa tay lokacin yanzu kuwa bata fatan ma ta sume d'in, gaba d'aya ganin shi take a buge yake hakan yake k'ara tada mata hankali, kafeta da ido yay yana mata wani matsiyacin kallo sai kerma bakinta ke yi tama kasa cewa komai, wayarta ce da har lokacin tana ruk'e a hannunta tare da ta Fatuu ta fara ringing da sauri ta kai idonta kan screen d'in ganin Aunty Mareeya ce me kiran yasa a kid'ime ta fara k'ok'arin d'auka don ta sanar mata halin da take ciki kwatsam taji ya kawo hannu ya buge wayar ta fad'i k'asa ta daki tiles, daga jin sautin fad'uwar ba sai an fada ba glass d'in ya fashe, cikin rawar murya ta fara fad'in "D...don girman Allah, don son ka da Manzo SAW kayi hak'uri, wllh bada sani na na buge ka ba har wayan ta fad'i kaji na rantse..." abun ka da fara fuskarta har tayi jajur tunda take a rayuwarta bata ta6a kasancewa da Namiji haka ba don kusancin yayi yawa, bin ta kawae yay da ido da suke a d'an lumshe wanda suna daga cikin abun da ke tafiya da mata a tattare da shi, komai nasu da Haisam iri d'aya sai kace suma yan biyun ne don shima ya iya lumshe ido, kaman daga sama taji yace, "What is ur name" idanu waje cikin rawar murya tace "n..ni suna...na...Fauziyya" shiru yayi kafin ya k'ara cewa "What's your relationship with the bride?" har saida ta had'iyi abu kafin tace "Ni..Best Friend din ta ce tare muke karatu" da k'yar take bashi amsa don har lokacin a firgice take, tambayar ta ya k'ara yi a wani Makaranta suke karatu ta bashi amsa da School of nursing Katsina, "A nan kike?" da alamun rashin fahimta tace ina, kaman bazai bata amsa ba sai kuma taji ya furta sunan Katsina nan ta gane yana nufin a Katsina d'in take, ce mashi tayi ita yar Funtua ce, hannu ya kai ya shafi beard din shi bayan ya janye hannun yace mata ina ne Funtua, duk da halin da take ciki saida taji Maganar kaman ta rainin wayau don sai taga ya za'ai yace bai san garin ba, amsa ta bashi da babbar local Government d'in Katsina ce, dan ta6e baki yay ya juyar da Fuskar shi gefe, maido fuskar yay ya kalleta yace "Kinsan abunda kika fasa man yana da kud'i sosae?" da sauri ta jinjina mashi kai alamar eh, yace "Ok ina son ki biya shi" yamutsa fuska ta fara yi zata cigaba da kuka yay mata wani kallo ba shiri ta saki fuskar tace "Wallahi, tallahi kaji na rantse maka bazan iya biyan ka ba" still yay yana kallonta kaman bazai ce komai ba can yace "Ok sai ki sanar ma Dad d'in ki ya biya" girgiza kai ta hau yi "Wllh shima nasan bazai iya biyan ka ba....." Katseta yay ya d'age gira yace tasan kud'in shi ne, da sauri tace "a'a ban sani ba amman dai nasan zata yi kud'i sosae kuma mu wllh talakawa ne kawai dai muna da rufin asiri amman nasan baza'a iya biyan ka ba" tana rufe baki yace ai yasan basu rasa wani abu da za'a saida a biya shi, idanunta ne suka k'ara cikowa da k'walla suka zubo mata sharr ta kai hannu tana gogewa tace "saidae gidanmu kuma a ciki muke sai kuma gonar Baban mu ita kuma anan ake noma Abincin da muke ci wani kuma a saida ayi wasu hidindimun tunda baban namu ya aje aiki pension ake biyan shi kuma basu isa" shiru yay bayan ta gama kora mashi bayanin can yay sigh yace "Ok naji, but you must compensate me for the damage" yana rufe baki ta fashe mashi da kuka ya kai dogon yatsan shi jikin bakin shi yay mata alamar tay shiru, gunji ta koma yi tana yi tana kai hannu tana goge kwallan dake zubo mata ya kafeta da ido, hak'uri taci gaba da bashi can yace "Ok I will do u one favor" da sauri ta jinjina mashi kai tun bata ji Alfarmar ba har ta d'an ji sassauci a zuciyarta, kafe shi tay da ido tana jiran jin Alfarmar slowly ya sauke idanun shi yana bin jikinta da kallo daga baya ya d'ago da su ya tsaida su cikin nata k'asa k'asa ya furta "You can pay me with your... Body" wani irin zaro ido Fauzy tay kirjinta yay wani irin mummunan Fad'uwa a razane ta hau girgiza mashi kai tama kasa cewa komai, slowly ya fara matsawa da fuskar shi yana niyyar had'e ta da tata aikuwa a gigice ta hau girgiza kanta sosae ta runtse idanunta cikin k'araji ta hau fad'in "Na rok'e ka don girman Allah kada ka cutar dani, nasan kafi k'arfinta don Allah don darajar iyayenka ka yafe man kada kai man komai wllh ni ba yar iska bace ban ta6a yin haka ba" ji tay yace kenan tana nufin shi d'an iska ne, tana jin hucin Maganar tashi akan fuskar ta Saboda kad'an ya rage ya had'e ta da tata, da k'yar ta bud'e idonta cikin muryar kuka tace "a.. a'a wllh ni ba haka nike nufi ba kawae dae ina son fad'i maka ne ni ban ta6a aikata hakan ba don Allah kar kayi man komae" bin juna sukai da ido tana ta kikkifta nata dake jik'e da k'walla, shigar da lip d'inshi na k'asa yay cikin baki ya dan tsotse shi kafin ya fiddo dashi gently yace mata ai yanzu ba wanda zai sani kuma in tana tsoro ne zai mata yadda bazata ji komai ba sai dae tay enjoying, shiru tay tana ta kallon shi ganin haka yasa shi d'age mata gira yace "agreed?" motsa baki ta fara ta rasa mi zata ce mashi wata zuciyar ta shiga raya mata ta yadda kawai in dai sau d'aya ne, cikin rawar murya ta tambaye shi daga wannan Shikenan, kawae sai gani tay yay wani kalan murmushi mai wuyar fassaruwa ya jinjina mata kai, shiru tay gabanta na cigaba da bugawa da k'arfi, ganin yana matso da fuskar tashi yasa tay saurin runtse ido tana numfashi da k'arfi har yana jin hucin shi akan fuskar shi idanunta sai motsawa suke duk da suna a rufe, had'e face d'in su yayi tana jin lips d'in shi ya had'e da nata kawai sai ta zame k'asa ta rufe fuskarta da hannuwan ta da suka sha k'unshi ta fashe da kuka tana girgiza mashi kai da d'an k'arfi take fad'in "ban iyawa wllh, Allah na ganin mu in muka aikata hakan zai kama mu ne kuma zan lalata rayuwata na rok'eka ka yafe man nasan kafi k'arfin ta don Allah ka k'yale ni" yana a yadda yake bai cire hannuwan nashi ba ya sunkuyar da kan shi yana kallon ta abun mamaki Fuskar shi na d'auke da d'an murmushi, cire hannuwan shi yay daga jikin k'opar ya tsaya yana kallonta kallabin ta har ya fad'i kuma har lokacin hannuwanta na rufe da fuskar, yadda tayin ne yasa shi yin murmushi don hakan saiya zame mashi wani bak'on abu har ya d'an bashi nishad'i ganin shi da Mata ke son ya ta6a su yau an samu wadda ta samu hakan amman tak'i yarda saidai dama akwae abunda yake k'ok'arin ganewa shiyasa yayi mata hakan, juyawa yayi ya nufi inda wayarta ke yashe ya duk'a ya d'aukko ta, bai yi mamakin ganin yadda glass d'inta yay kwatsa kwatsa ba, latsa power button yay haske ya kawo, screen d'in wayar lafiyar shi lau ya k'ura ma hoton ta dake kan screen d'in tana sanye da fararen Uniform ba Hijab haka kanta ma ba kallabi sai gashinta dake a fake kunnuwanta sanye da Stethoscope ta rik'e kan a hannunta tana dariya, sosae tayi kyau a hoton don ma glass d'in wayar ya faffashe, juyawa yay ya koma inda take duk'e har lokacin fuskarta a rufe take tana ta sheshsheka, rasa yadda zai yi mata magana yay don har yama manta yadda ta fad'i mashi sunan ta, wayar yasa ya d'an bubbuga kanta aikuwa da sauri ta d'ago idanunta sunyi jajur har sun d'an kumbura, mika mata wayar yay yace ta bud'e hannunta yana ta rawa ta amsa ta bud'e ta mik'a mashi ko damuwa da yadda taga glass d'in yayi bata yi ba, amsa yay ya juya cikin parlon ta bi bayan shi da kallo, inda ya taso ya koma ya zauna yana latsa wayar, bayan wani lokaci ya d'aga kai ya kallo inda take Saidae bai hango ta Saboda duk'ewar da tayi, maida idon shi yay akan Wayar can ya sake d'agowa a kausashe ya furta "Where are you?" Da sauri ta mik'e tsaye suka had'a ido, kasa jure ma kallon shi tayi sai d'an maida idon ta k'asa take, da hannu yayi mata nuni da kujera har ta nufo cikin parlon ta tuna da kanta ba kallabi ta juya ta d'aukko ta yafa, a bakin kujerun ta tsaya tana kallonshi da kai yay mata alamar ta zauna, a saman ta kusa da ita ta zauna gaba d'aya a d'arare take, aje wayarta yay saman table ya maida idon shi akan Tv, wani irin fitsari take ji saidae bata san ya zata yi ba gashi sosae ya matse ta don tun d'azu ta fara jin shi tsabar firgici, yamutsa fuska ta shiga yi ta kafe shi da ido tana cikin kallon nashi ya maido idon kan ta yay mata wani kallo mai kaman harara da sauri ta maida idon nata k'asa, jin fitsarin na niyyar zubo mata yasa ta mik'e da sauri har bata san lokacin data tunkare shi ba ya maido kallon shi kan ta, daga d'an nesa da shi ta tsaya fuska a yamutse tace mashi don Allah toilet take son shiga, shiru yay yana kallonta saida ya ga dama sannan ya furta mata bai sharing toilet, jiki a mace ta juya har ta fara tafiya sai kuma ta dakata ta juyo tace to don Allah y bud'e mata kopar ta fita ta ga in zata samu wani, ta6e baki yay ya d'age gira yace mata gidan su ne nan da sauri ta girgiza mashi kai jiki a sa6ule ta juya ya bita da kallo, in da ta taso ta koma ta zauna, kasa natsuwa tayi a wuri guda sai yan matse matsen jiki take ba K'aramin k'ok'ari take ba tana ruk'e fitsarin, tana haka taga ya mik'e da hannu yay mata alamar ta biyo shi aikuwa zumbur ta mik'e, Corridor d'in daya shiga d'azun ya shiga ta bi bayan shi, a bakin wata farar kopa ya dakata ya juyo suka had'a ido, ce mata yayi ta shiga ciki zata ga toilet ta d'aga mashi kai, har ta kai hannu ta tura kopar zata shiga kamar wadda ta tuna wani abu da sauri ta juyo yana tsaye bai motsa ba, yamutsa fuska tayi idanunta rau rau cikin karyayyar murya tace "t...to don Allah kada kayi man wani abu in na shiga" wani kallon rashin Arzik'i yay mata ya kalleta daga sama har k'asa kawai sai yay d'an tsoki ya juya ya nufi komawa cikin parlon, k'irjinta na bugu da k'arfi ta kai hannu ta tura kopar ta shiga, tsaye tayi bayan ta shiga tana bin d'akin da kallo sai kace ba wadda Fitsari ya matsa ba, d'akin ya matuk'ar Had'uwa shima komai na cikin shi fari da golden ne, katafaren gadon yasha farin bedsheet K'al da shi, ba wasu tarkacen kaya a cikin shi gado ne da table d'in shi sai side drawers da dressing mirror sai tafkekiyar glass wardrobe itama fara ce sai glass d'in gaban yana da d'an launin golden ana hangen kayan cike wasu a hanger wasu a linke, daga can gefe guda farin table ne d'auke da wasu littattafai harda Alqu'ani daga gefen su fitila ce irin ta karatu golden, wata k'opa data gani ta nufa bayan ta gama k'are ma d'akin kallo, tana tura ta taga toilet ne a d'arare tana yi tana waiwayen bayan ta hakanan dai tayi shahada ta shiga, shima dai Toilet d'in komae na cikin shi fari ne kuma ko ban fada ba an san shima ya had'u, bata dad'e ba ta fito da sauri ta nufi hanyar fita, yana zaune a inda yake d'azun ta shigo cikin parlon sumi sumi ta nufi inda ta tashi bai ko kalle ta ba idon shi akan Tv, bata dad'e sosae da dawowa ba tana ta yan kalle kalle wayar shi ta fara ringing, yana ji amman ko kallon ta bai yi ba Fauzy ta bi shi da ido a ranta tana raya yana ji waya na ringing yak'i d'auka, bayan kiran ya yanke ba'a dad'e ba wani ya sake shigowa shima saida ya kusa yankewa sannan ya mik'a hannu ya d'aukko wayar, bai yi picking ba ganin mai kiran nashi sai ma ya mayar da wayar ya aje, can bayan wani d'an lokaci ya mik'e ya nufi hanyar corridor Fauzy ta bishi da ido har ya shige, gyara zamanta tayi ta hau kujerar sosae tay jugum gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i don bata san ko ya hak'ura ba gashi yazo ya jibgeta anan, saida ya d'auki kusan 30 minutes koma fi sannan ya fito da gani wanka yayi don ya canza kaya zuwa jeans da red t-shirt sai bazw uban k'amshi yake don yana fitowa ya kai hancin Fauzy, da sauri ta d'ago daga jingina da tayi da kujerar ta gyara zamanta, ciki ya wuce ya tsaya wurin table ya kai hannu ya dauko farar wallet d'in ya fiddo wasu abubuwa ya maida cikin wata dark blue kalar jeans d'in shi daya fito da ita, aje farar yay saman table d'in ya d'auki wayar shi daga haka ya juya ya nufi hanyar k'opar fita daga parlon, yana zuwa saitin Fauzy yace ta taso aikuwa da sauri ta mik'e, tana shirin bin bayan shi ya dakata ya juyo ta bi shi da ido, ce mata yay wata bar ma wayarta da sauri ta juya ta nufi wurin table da wayar ke a saman shi, har ta d'aukko ta juyo yana tsaye saida ta kusa zuwa wurin shi sannan ya juya yaci gaba da tafiyar, kamar yadda ya bud'e kopar ya shigo haka ya yi ta bud'e suka fita, da suka zo babbar k'opar shigowa gidan itama wani wuri ya ta6a ta bud'e bayan ya fita Fauzy ta bi bayan shi. Bayan da Haisam ya kira Fauzy ta d'aga ta sanar mashi wayar na a hannunta, wayar Jidderh ya kira bayan tayi picking yace ta ba Fatuu tace mashi tana d'akin Mom bari ta kai mata yace kawae in taje ta fad'i mata su had'u a main parlor tace to, lokacin data je part d'in Mom Fatun na a zaune a parlor da wasu mutane suna kallo, wurinta ta nufa ta zauna da murmushi tace mata "Sannu Amaryar mu nasan dai yau kin sha gajiya" murmushi itama Fatun take mata ba tace komai ba, gaya mata sak'on Haisam tay ta mik'e tace tazo su je, d'an jimm tayi kafin tace mata to ai Mom tasa tazo part d'in kuma sai ta tafi Jidderh d'in tace Ok bari tama Mom d'in magana, bedroom ta nufa tana shiga ta ganta zaune a saman gado ita da yar uwar ta suna hira, gadon ta nufa ta zauna a bakin shi Hajiya Zainab dake kallon ta da murmushi tace mata ya gajiyar Walima tana murmushi tace mata ba gajiya, maida idonta tayi akan Mom ta sanar mata zancen kiran da Ya Haisam ke ma Fatuu da abunda tace, salati ta saka tace ai ita wllh tayi zaton ma ta tafi ne tun bayan da Sameer ya shigo zasu yi Magana da Mom d'in shi ta fita, saukkowa tay daga saman gadon suka nufi Parlor, inda Fatuu take suka nufa Mom d'in ta zauna ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta ta shiga bata hak'uri kan wai ta aje ta Fatun nata murmushi tace ba komai ai, kallon Jidderh dake tsaye tayi tace suje in ta ga Haisam d'in ta tabbatar an bata Abinci ta ci tace mata to, mik'ewa Fatuu tay har lokacin shaddar ce a jikinta tayi ma Mom data Mik'e saida safe suka tafi, lokacin da suka isa parlon Haisam d'in na tsaye yana latsa waya jikin shi sanye da jallabiya, a gaban shi ta tsaya ya d'ago suka sakar ma juna murmushi, calmly yace mata tasan zasu fita shine bata neme shi ba, d'an yamutsa fuska tayi tace yayi hak'uri tana part d'in Mom ne kuma wayarta na a hannun Fauzy shiyasa bata kira shi ba, fad'i mata yay Fauzy d'in bata gida ne tace Ok, ce mata yay zasu iya tafiya tay d'an jimm kafin tace bari ta canza riga yace Ok bari ya d'aukko Mota in ta gama ta same shi waje ta d'aga mashi kai, d'akin Jidderh ta nufa lokacin data shiga mutum biyu ta iske cikin yan uwan su zaune a saman gado suna latsa wayoyin su, d'agowa sukai suna gaishe da ita tana murmushi ta amsa masu, wurin trolley d'inta ta nufa ta bud'e ta shiga tunanin kayan da zata canza har wanka taso tayi amman bazai yiwuwa ba saidae ko in taje can inda zasu, k'arshe doguwar rigar material ta d'auka ta nufi toilet don ta sa, bayan ta fito ta d'auki kayan bacci ta tura a jaka ta linke rigar data cire ta saka ta a cikin trolley d'in, d'an babban gyale ta fiddo sannan ta rufe akwatin, bayan ta nad'a gyalen ta d'auki jakar hannun ta nufi hanyar fita, lokacin data fito daga cikin gidan har ya kawo Motar bakin Entry Hall tana zuwa ta zagaya ta bud'e gaba ta shige bayan ta rufe k'opar ya ja suka tafi......... *ASM 082* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ........Bayan su Fauzy sun fito daga cikin layin gidan titi ya hau sosae suka cigaba da tafiya, Sameer na cikin driving cikin ran shi yake tunanin abunda yakamata yayi, dama bai san ma mi zai mata ba da ya d'aukko ta tun farko, akwae inda yake son zuwa ana jiran shi tunanin in yace ya maida ita gida hakan zai 6ata mashi lokaci yasa shi yanke zuwa da ita in ya gama abunda zai je yi sai ya maida ta, tafiyar kusan minti 20 sukai suka iso wani babban wuri wanda rabin katangar shi fence ne ta yadda zaka iya hango ciki haka daga gaban katangar had'add'un Flowers ne a tsare sannan a jikin katangar akwae fitilu da suka haska ko ina, karya kan Motar yay ta kalli gate d'in wurin wanda shima na k'arafa ne irin na jikin katangar, saida ya jira wata Mota ta k'arasa shigewa gate d'in sannan shima ya shige, k'aton parking space d'in wurin ya nufa bai k'arasa wurin shi ba ya parker Motar daga gefe don kuwa parking space d'in dankam yake da motoci masu numfashi don kowacce ka gani ta had'u, sakin baki Fauzy tayi tana kallon wurin ta cikin glass d'in gaba dama tunda suka taho ba abunda take sai aikin kalle kalle, hannu ya kai gefe ya d'auki wayar shi da wallet hakan yasa ta maido idon ta kan shi, kallon ta yay suka had'a ido ta hasken da ya d'an haska cikin Motar fuskar shi ba d'igon annuri ya mik'a mata hannu yace ta bashi wayoyin hannunta, da sauri ta mik'a mashi saida ya kashe su gaba d'aya sannan ya bude glove box ya saka su, ba tare da ya kalleta ba ya juya ya bud'e Motar bayan ya fita ya maido k'opar ya rufe, zuru tay tana kallon shi dishi dishi ta glass d'in kopar daya fita har saida ta daina hango shi sakamakon wasu da suka zo wurin shi suka tafi bata san ina sukai ba ta dai daina ganin su, maida kanta tay jikin headrest tay shiru ta shiga tunanin k'ilan ana can anata nemanta tunda ba wanda yasan ta fito sai Ya Haisam kuma shi tasan ba lalle in zai fad'i ma Fatuu ba cewa bata gidan ba kaman yadda ta sanar mashi, shiru shiru har kusan bayan mintuna talatin bai dawo ba gaba d'aya Fauzy ta gama gajiya ga wata bak'ar yunwa da take ji sakamakon bata ci Abincin dare ba ga zafi ya ishe ta don ma ta bud'e glass d'in gefenta, gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i sai yamutsa fuska take tana yan kalle kalle ta cikin Motar can ta kai hannuta a d'arare ta bud'e k'opar Motar, zuro kanta tayi tana k'are ma wurin kallo ba K'aramin had'uwa yay ba iya fitilun dake sakin haske a wurin abun kallo ne, kai idonta tay cikin wata had'add'iyar rumfa mai girma wadda mutane da d'an yawa ke acikinta, bazata iya gane Mutanen Musulmai bane ko Christians daga yanayin shigar su, wasu cikin su na tsaye suna buga snooker mata da maza yayin da wasu ke a zaune saman k'ayatattun kujeru zagaye da table suna kallon su yayin da saman table d'in ke d'auke da abubuwan ciye ciye dana sha wanda bazata iya gane ko su miye ba, daga gefen su kuma wasu ne ke yin ludu wasu kuma na yin wasan chess, ta d'an d'auki lokaci tana kallon su don yanayin wurin akwai d'aukar hankali can ta idasa fitowa daga cikin motar a tsorace gaba d'aya tayi kalar rashin gaskiya, jingina da kopar Motar tay ta na kallon cikin wurin Mutane sai kai da kawowa suke suma dai duk kalar irin shigar na cikin rumfar gare su wasu na fitowa daga cikin ginin wurin wasu kuma na shiga daga can gefen wurin wani irin k'aton swimming pool ne an k'awata shi mutane sai wanka suke mata da maza, daga inda take ta fara k'ok'arin ganin sunan wurin dake a sama yana ta sakin walwali saidae ta kasa gane mi aka rubuta dama bata gani ba da zasu shigo, gajiya tay da tsayuwar ta koma cikin Motar taja kopar ta rufe, shiru tay tana ta yamutse yamutsen fuska don Allah kad'ai yasan irin yunwar da take ji, wasa wasa ta shafe fin awa amman bai fito ba lokacin tuni ta fara yin k'walla abun har ya kai ta fashe da kuka a fili ta shiga fad'in "Wllh wannan mutumin mugu ne, in ya yafe man ba sai ya maida ni gida ba amman ya jibge ni a cikin Mota sai kace ba Mutum ba" haka tay ta sambatu. Sai wuraren k'arfe d'aya saura yan mintuna ya dawo, yana shiga cikin Motar idanun shi suka sauka akan Fauzy data langa6ar da kai, hannu ya kai ya kunna fitilar Motar haske ya gauraye cikin Motar ya bi ta da kallo, shi gaba d'aya ya manta ma da ya barta a Motar, da ganin fuskarta ta sha kuka da alama ma tana cikin yi baccin ya d'auketa don fuskarta duk jirwayen hawaye kallabinta data yafa ya zame, bayan wani lokaci ya fara k'ok'arin tada ita da fad'in "Hey...." Shiru bata ko yi motsi ba ya k'ara cewa hakan nan ma bata Motsa ba, hannu ya kai ya fara d'an bubbuga shoulder d'in ta lokacin ta fara motsi, a hankali ta fara bud'e idanuwanta tana yi tana k'ara rufe su cikin husky voice d'in shi ya furta "Wake up" aikuwa da sauri ta bud'e idanun gaba d'aya ai koda tay arba da Fuskar shi ba shiri ta shiga gyara zaman ta, bin juna sukai da kallo duk tayi wuri wuri da ita can k'walla suka zubo mata sharr da sauri ta juyar da fuskar ta daga barin kallon shi tana d'an yi sheshsheka a hankali, "da wa ya buge ki?" taji ya furta, shiru bata bashi amsa ba bata kuma kalle shi ba, ya k'ara furta "am I not asking you?" Sai lokacin ta juyo ta girgiza mashi kai alamar ba kowa, d'age gira yay ya furta "shi wannan d'in na miye?" ta gane kuka yake nufi ta fara motsa baki ta kasa yin magana, ce mata yay kar ta k'ara sa shi ya maimaita mata magana ya k'ara tamke fuska da sauri cikin rawar murya tace mashi yunwa take ji, bin ta yay da wani kallo ganin haka yasa cikin yar in ina tace mashi bata ci Abincin dare ba, ta6e baki ya d'an yi ya janye idanunshi daga barin kallon ta ya koma kallon gaban shi, bin gefen fuskar shi mai d'auke da kwantaccen saje sumar tayi luff tayi da kallo, juyawa yay dama bai datse kopar ba ya fita tana ta kallon shi ya maido kopar ya rufe, maida kanta tayi jikin kujera tay shiru ba abunda take gani sai fuskar shi, bayan wasu yan mintuna taji za'a bud'e Motar da sauri ta kai idonta, shine ya bud'e ya shigo hannun shi ruk'e da abu, bayan ya zauna ya mik'a mata d'an babban cake ne nad'e a leda sai lemu irin na cikin kaman d'an cup da straw manne a jikinshi, a hankali tayi mashi godiya bai ko kalle ta ba ya maida kan shi jikin headrest, ruk'e su tay a hannu bata da niyyar fara sha sai yan kame kame take tana haka taji yace zasu kwana ana ne, abu ta had'iya kafin ta fara k'ok'arin ciro straw d'in jiki, bayan ta saka a cikin lemun ta bud'e cake d'in ta fara ci tana yi tana satar kallon shi, bayan ta d'an ci da yawa ta rage sauran duka a hankali ta juya ta kalle shi ya d'age kan shi idanun shi a rufe, bin fuskar shi tay da kallo Idan tace ga wani abu da bai yi ba a fuskar tashi to kuwa ta shirga babbar k'arya, tana cikin kallon nashi ba tare data ankara ba ya bud'e idanun ya kallo ta, in ina ta kama yi tace mashi ta gama ya kallo sauran data rage a hannunta ba tare da ya d'ago ba kawai sai gani tay ya maida idanun ya rufe, bayan d'an lokaci taji yace "Don't waste my time, else zan barki anan ne" ai tana jin Haka da sauri ta kai lemun baki taci gaba da sha, saida ta cinye komai sannan ta kalle shi tace ta gama shiru kaman bai jita ba ta k'ara d'an d'aga murya ta maimaita ta gama, slowly ya fara bud'e idon ya d'ago daga jikin kujerar ya fara k'ok'arin tashin Motar yana haka yace mata wannan d'in wani zata kai mawa ta d'an girgiza kai kafin tace bata san ina ake aje wa ba ya juyo yay mata wani kallo da sauri ta juya ta bud'e kopar ta wurga ledar da d'an cup d'in, rufe kopar yay daga haka ya fara yin reverse bayan ya fita daga wurin ya shiga juya kan Motar Fauzyn nata kallon wurin har lokacin da mutane kusan ma yafi cika yanzu. Lokacin da suka iso gidan kusan k'arfe d'aya da rabi, a bakin Entry Hall ya parker Motar Fauzy ta bi shi da ido gudun kada tayi wani laifin, shiru kaman ba zai tanka ba can yace "Get out of my car" juyawa tay zata fita sai kuma ta dakata ta juya a d'arare tace mashi don Allah ya bata wayar kawar tata ta kai mata, sai da ya mula sannan ya kai hannu ya bud'e wurin da ya saka ba tare daya kalleta ba yace ta d'aukko, hannunta har d'an rawa yake ta kai shi ta d'aukko ta Fatun kawae a fusace yace waye ta bar ma d'ayar ta sake kai hannu ta d'aukko, d'an kallon shi tay tayi mashi godiya yay banza da ita jiki a sanyaye ta juya zata bud'e k'opar kaman daga sama taji yace ta sani dole zata biya shi damage d'in da tay ma wayar shi, juyowa tay fuska a yamutse tace "Don Allah kayi hakuri...Na fad'i maka wllh Allah ba zan iya biyan ka ba, d'age shoulder yay alamar bai dame shi ba kafin yace ta fita, bud'e k'opar tay bayan ta fita ta juyo idonta a kanshi ta kai hannu ta rufe mashi, nufar shiga cikin gidan tay tana yi tana waiwayen shi har saida ta kusa shigewa sannan taga ya ja Motar, Lokacin da ta shiga main parlor d'in tsit kowa yayi bacci, kopar baya ta nufa tana waige waige tsoron ta kar wani ya ganta ta dawo a lokacin duk da bata san k'arfe nawa ba amman daga yanayin da ta ga garin ta fahimci dare yayi sosae, har ta fita baya ko motsin mutum bata ji ba ta nufi part d'in da suke, lokacin data shiga cikin parlon kwalam yake da sauri ta nufi d'akin su, sai da tay d'an jimm kafin ta sa hannu a hankali ta d'an tura kopar, d'an lek'awa tay ta hango kowa yayi bacci sannan ta k'arasa tura kopar ta shiga, cikin tafiya mai kaman sand'a don kar tayi sauti wani ya tashi ta nufi cikin d'akin, a bakin gado ta zauna tana kallon su Haulat dake ta shan bacci, maido idon ta tay tana kallon gabanta tayi shiru zuciyarta ta shiga tunano mata dukkan abun da ya faru tsakanin ta da Sameer, tunano lokacin da yake mata magana gab da ita ta shiga yi yadda hucin bakin shi mai had'e da k'amshi ya rink'a bugun fuskarta, kokonton kodai ba giya bace ya sha ta shiga yi wata zuciyar ta raya mata to ita tasan yadda giyar take ne ai k'ilan kala kala ce akwae mai kamshi, tunano lokacin da ya kawo fuskar shi ya had'e da tata tayi har bata san lokacin data rufe ido ba sai kuma ta bud'e da sauri kawae sai ta saki murmushi, wasi wasi ta shiga yi na inda ta amince mashin da gaske zai yi mata wani abu ko kuwa, wata zuciyar ta k'ara raya mata kawai dae k'ilan hakanan yay mata hakan amman ai bata kai yayi hakan da ita ba in ma yana yin, har saida ta d'an ta6e baki, tunanin ko mi yaje yi a wannan wurin ta shiga yi tana raya wurin kaman Club a yadda ta fahimta kuma dai tasan ana cewa ba abun arzik'i ake ba a can, a hankali a fili ta furta "ko ma ina ruwa na" ajiyar zuciya ta sauke ita kanta tasan ba K'aramin firgici ya sata ba, tunanin ko ya yafe mata ko kuwa da gasken yake sai ta biya shin kamar yadda ya fad'a mata yanzu da suka dawo ta shiga yi can ta ta6e baki a fili ta furta "ni dai ai na fad'a mashi gaskiya bansan taya zan biya shi ba kuma" shiru tay tana kallon wuri guda can tay murmushi tunowa da abubuwan daya kawo mata taci ta raya ashe yana da kirki, kunna wayoyin tayi gaba d'aya nan taga ashe a fly mode yasa wayarta ta raya k'ilan ma Aunty Mareeya ta sake kiran ta, ta d'an d'auki lokaci a zaunen can ta tuna da ko sallar isha bata yi ba ta mik'e ta nufi hanyar toilet bayan ta aje wayoyin, saida tayi wanka ta d'auro alwala ta fito d'aure da kallabin ta, wurin akwatin kayanta ta nufa, doguwar rigar bacci ta fiddo bayan ta saka ta d'aukko Hijab ta wuce inda abun salla yake ta d'aukko ta shimfid'a, bayan ta gama sallar tayi Addu'a anan ta kwanta ba tare data cire Hijab d'in ba, gaba d'aya bacci ya k'aurace ma idanunta tay shiru tana kallon wuri guda can ta rufe su nan take zuciyata ta shiga tunano mata sufar Sameer a haka har bacci ya kwashe ta. Washe gari bayan sun tashi sallar Asuba kowa ya ganta sai ya tambayi ina taje ne jiya ba'a kwanta da ita ba cikin kama kai take basu amsa da sun fita ne bayan sun dawo kuma ta tsaya d'akin Jidderh fira, bayan ta gama sallar ta d'auki wayar Fatuu don ta kai mata, lokacin data je d'akin su Jidderh ma basu dad'e da gama sallar ba sun koma gado bayan sun gaisa ta tambaye ta Fatuu nan ta sanar mata ba a gidan ta kwana ba, bayan ta fito zata koma part d'in su a ranta ta shiga raya dama dalilin kiran da Ya Haisam ke ta mata kenan tay d'an murmushi, tana shiga cikin parlon suka had'e da Aunty Mareeya tana sanye da doguwar rigar bacci kanta sanye da hula har saida gaban ta ya fad'i, tana ganinta ta tsaya Fauzyn ta tunkareta tana k'ak'alallen murmushi, gaishe da ita tayi ta amsa tana mata wani kallo tace mata ina taje jiya, rasa amsar da zata bata tayi ta fara yan kame kame, tunanin ko tace mata tare suka fita da Zarah tay sai kuma ta tuna da har yanzu ita bata gidan k'ilan kuma Aunty Mareeyar tasan ba gidan zata kwana ba, hannu ta kai ta kama kunnanta tace "fad'i man ina kika je jiya har aka kwanta baki dawo ba, kuma na kira wayar ki baki d'aga ba k'arshe ma dana sake kira sai kika kashe" yamutsa fuska Fauzy tay alamar tana jin zafin kama kunnanta da tayi, hakanan taji bata son fad'i mata abunda ya faru don bata san ya zata d'auki zancen kai ta wani gida da Sameer yayi ba, k'ara murd'e kunnan tayi ta saki yar k'ara tace zata fad'i mata don Allah kar ta tsinka mata kunne, cikin yar in ina tace mata dama da wani abokin Ya Haisam ne suka fita, waro ido Aunty Mareeya tayi ta saki kunnan nata da alamun Mamaki tace "kuka fita ku ka je ina?" tana kikkafta ido tace gari suka fita ya zagaya da ita, hannu Aunty Mareeya ta hau tafawa da alamun d'an tashin hankali tace zaga gari shine har wurin sha biyu bata dawo ba don ma taji Zarah itama bata nan shiyasa hankalinta ya d'an kwanta tayi tunanin suna tare, abu Fauzy ta had'iya a ranta ta raya don ma bata san k'arfe nawa ta dawo ba, daga Maganar da Aunty Mareeya d'in tayi ta samu k'aryar da zata mata tace ai daga zaga garin wurin su Zarah d'in suka wuce, tambayar ta ina Zarah d'in taje tayi tace suna tare da Ya Haisam a wani gidan su, gaba d'aya tayi kalar rashin gaskiya don hakanan ta fad'i hakan bata san ina Fatun suka je ba, murmushi Aunty Mareeya tay tace "Uhm su Malam miskili kenan gaba d'aya yana neman takura ma Yarinyar Mutane" murmushi Fauzy tay cikin alamun kunya tace "to Aunty Mareeya ba duk ke ce ba" hannu ta kai zata kai mata bugu tana fad'in ita uban mi tayi Fauzy ta goce tana dariya, tambayar ta tay shi wanda suka fitan cewa yay yana son ta Fauzyn ta d'an girgiza kai tace a'a kawae dai sun fita ne, harara ta wurga mata tace ita kuma ga mara aji kawai sai ta bishi zararai zararai Fauzyn tay dariya, "Amman gaskiya Fauziyya yakamata kiyi saurayi ko kema Kya zo kiyi aure don Allah Zarah bata burge ki ba" tana murmushi tace "ta burge ni sosae Aunty, kuma dama tun lokacin data tare naji nima ina son in yi auren to amman ni fa har yanzu banda saurayi...." A hasale Aunty Mareeya ta katse ta "ta gidan uban wa zaki saurayin bacin har yanzu kin kasa cire wanccan shashashan mayaudarin daga cikin Zuciyar ki" yanayin fuskar Fauzyn ne ya canza cikin karyayyar murya tace "Aunty dole fa Mujaheed ya tsaya man a rai ko ya ya ne, kar ki manta bansan soyayyar kowa ba sai tashi, tun bansan kai na ba nasan miye soyayya ya koya man son shi daga shi kuma ban k'ara son wani abu, tsawon lokaci muna tare" idanunta har sun ciko tab da k'walla, ta6e baki Aunty Mareeya tay tace "Shikenan kada Allah yasa ki cire shi daga ran naki kiyi ta zama kar ki yi aure har mahadi ya bayyana" tana gama Maganar ta juya zata tafi da sauri Fauzy ta k'ank'ameta ta baya ta saki kuka tana fad'in don Allah tayi hak'uri wllh a yanzu a shirye take da tayi Aure indai ta samu mai son ta tsakani da Allah kuma itama taji tana son shi, juyowa tay ta rungume ta ta kai hannu tana goge mata hawayen tana fad'in ya isa, bayan ta yi shiru tace "Yanzu shi wanda kuka fita d'in da gaske bai ce yana son ki ba?" Kai ta d'aga mata ta sake cewa "to in yace yana son ki zaki amince" shiru Fauzy tay a ranta ta shiga tunanin to waima ita waye zai ce yana son nata Sameer dai tasan ko fad'uwa zatai a gaban shi tana mashi magiyar ya so ta ba son ta zai ba balle har ayi Maganar aure shiyasa ma bata sa ma ranta wai taji ko tana son shi ba, ganin ta kafeta da ido yasa tayi d'an murmushi ta jinjina mata kai alamar eh, sakinta Aunty Mareeya tayi ta d'aga hannuwa ta fara fad'in, "Ya Ubangiji ina rok'on ka da sunayen ka tsarkaka da suffofinka mad'aukaka, ga kanwata nan ka bata miji nagari wanda zai so ta Saboda kai, Ya Allah Idan wanda suka fita tare Alkhairi ne a tattare da ita kasa mashi son ta da k'aunar ta a zuciya ta yadda har Al'amarin zai kai su da Aure Alfarmar Annabin rahama SAW" a hankali Fauzy itama ta fad'i S.w.a ganin Aunty Mareeyar ta shafa itama ta shafa tana d'an murmushi ita tausayi ma Aunty Mareeyar ta bata wllh ganin ta shirga mata k'arya kuma ta yarda, a hankali tace mata ta gode da kaunarta da take tana dariya tace mata ai wannan dole ne ita dai fatanta ta cika masu burin su tace mata in sha Allah daga haka ta juya tana mata k'orafin Saboda ita bata koma bacci ba ta nufi hanyar Bedroom Fauzyn nata kallon ta har ta shige sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya. Misalin k'arfe goma sha d'aya na safen Haisam da Fatuu zaune a saman Carpet cikin parlon gidan da suka je wanda d'aya ne daga cikin gidajen estate d'in Dad d'in shi su suke amfani da shi, gaba d'aya ta shige cikin jikin shi kamar wata yar mage breakfast suke yi wanda da kan shi ya had'a masu tana ta bacci saida ya gama ya tasheta jikinta sanye da rigar bacci kanta ba kallabi sai sumar ta dake a fake, bayan sun gama ta mik'e ta fara tattara kayan, d'aukar babban tray d'in tayi ta juya zata kai kitchen ya bi bayan ta da kallo Fuskar shi cike da annuri, shi kad'ai yasan yadda yake jin yarinyar a cikin ranshi kullum da kalar nishad'in da yake samu a wurin ta, dawowa tay idon shi akanta yana mata murmushi itama murmushin take sakar mashi, ware mata hannuwan shi yay ta tafi da sassarfa ta fad'a mashi ya maida hannuwan ya rungumeta sosae ta d'ago fuska tana kallon shi, kai fuskar shi yay ya had'e da tata yana d'an danna hancin ta da dogon hancin shi, dariya tay tace "kai Hubby in ka k'ara shigar man dashi fa dama kana ganin shi d'an bajajje" yar dariya yay ba tare da ya raba fuskar tasu ba yace mata shi haka ganin shi yake yafi na kowace mace a duniya kyau, d'an bud'a ido tay har zata fad'i wani abu sai kuma tay shiru, sun d'an d'auki lokaci a haka suna ta shan love sai zuba ma juna sweet nothings suke suna dariya, d'agota yay yace taje ta shirya su koma gida aikuwa ta tura mashi baki ya d'age gira ya tambayeta minene a shagwabe tace "ni dai Allah bazan koma ba, kawai yanzu kowa ya tashi ansan ba gidan na kwana ba sai a ganni tsugui tsugui na dawo hakan ma ai rashin kunya ne" gaba d'aya ya zuba ma bakinta ido har ta gama idanu a lumshe yace mata ai ba wani rashin kunya don tana tare da mijin ta kuma ai su ba yanzu ne sukai auren ba ko" shagwaba ta shiga yi mashi harda su mak'e kafad'a sai sakin k'ayataccen murmushi yake, tambayar ta yay yanzu ya take so ayi tace ita dae bazata koma ba sai dare yace ta manta yau akwai dinner ne tace to ai tasan bada wuri za'a tafi ba in akayi Magrib lokacin gari ya d'an yi duhu sai su koma, d'aga mata kai yayi alamar za'a yi hakan can kuma tace koma kawai ta shirya daga nan sai ya kira Aunty Laila yayi mata magana yace Ok. Zuwa Azahar duk an san Fatuu bata gidan, sam Fanan bata wani ji hakan ya dame ta ba don itama shekanjiya da ta zo ba gidan ta kwana ba tana tare dashi a wani gidan nasu wanda tana tunanin can ya tafi da Fatuu. Ana gama sallar Magrib aka fara shirin dinner lokacin Aunty Laila ta d'auki kayan da Fatuu zata sa ta tafi can gidan da take a Motar ta, saida ta biya ta d'auki wadda zata mata Make up suka tafi tare, lokacin da suka je Fatun ita kad'ai ce a gidan Haisam ya fita tana sanye da doguwar rigar material d'in data sa jiya da zasu taho, ba tare da 6ata lokaci ba aka fara mata make up d'in don dama tayi wanka kafin su zo, a can gida ma tuni shirin yayi nisa su Jidderh da Fauzy da Mino harda Haulat Nameer ya d'auke su ya kai su wurin make up wanda daga can zasu wuce tsadaddiyar Event Center d'in da aka kama hall d'in da za'ayi dinner d'in, aikin Abinci da abubuwan sha wata k'awar Mom da Sana'ar tace aka ba kwangila, Tubarakallah Ma sha Allah shine abunda na fad'a dana dawo kan Amarya Fatuu, doguwar rigar material light ash tasa rigar tabi shape d'inta daga wurin k'ugun an yi wata yar tattara ta net ta d'an rufe k'ugunta da rigar ta kama ya fito sosae, daga k'asan rigan ta baya ya ja k'asa, head dark blue mai shining aka nad'a mata tseps d'in sun hau sosae daga tsakiya an nad'e mata gashinta ya d'an fito, sark'a da yan kunnan Diamond d'inta aka saka mata harda zoben su da yan hannu guda biyu sai d'ayan hannun aka sa hadaddiyar agogo silver, wasu jigunannun takalma half cover masu igiya da clutch d'in su duka kalar head d'in ta saka sai d'aukar ido suke haka Material d'in kai kace adon stones d'in jikinshi da diamond akayi su don ba K'aramin had'uwa yayi ba yana daga cikin kayan da aka siyo a Dubai, Jama'a ku zo kuga Amarya Fatuu ita kanta tasan ba k'aramar had'uwa tayi ba har ta kasa rufe bakinta sai washe shi take nan aka shiga yi mata hotuna da Vedios, ana gamawa Laila ta d'aura su a status d'inta mutane suka fara gani harda yan can gida, Fanan ce ta gani ta nuna ma su Aunty Mareeya da tuni suma sun saka leshin su na anko wanda kalar head d'in da aka d'aura ma Fatuu ne duk da bai ciza kalar shi sosae ba kamar head d'in, nan fa aka hau yabo haka su Jidderh ma acan inda suke duk sun gani, bayan an gama da Fatuu aka fara yi ma Aunty laila bayan ta saka ankonta da ta taho dasu, wasu yan Arzik'in riga da skirt ne aka mata kalar na manyan yan matan Abuja, bayan an gama yi mata make up d'in aka nad'a mata kallabinta sosae ya tashi kamar head don anyi mashi starch. Misalin k'arfe tara saura aka fara d'aukar mutane ana kaiwa wurin event d'in, saida aka gama d'aukar kowa sannan Haisam yazo gidan da su Fatuu suke Abbas ne ya tuk'o Motar galleliyar ash, suna cikin parlor suka shigo Haisam d'in na sanye da babbar shadda gizner light ash dinkin yan ciki da babbar riga kanshi sanye da ash d'in hula haka agogon hannun shi da takalman shi half cover duk kalar shaddar ne sai uban k'amshi yake bazawa kai kace wanke shaddar akai da ruwan turare, Abbas ma na sanye da tsadadden plain yard kalar lace d'in su Laila anyi mashi d'inkin Senator style wadda gaba d'aya irin d'inkin da sukai kenan mazan, kai, abun dai ba'a magana wllh sha'anin manya na daban ne, hotuna aka shiga yi masu shida Fatuu daga baya suka yi da su lailar harda mai makeup da itama ta saka fitted gown ta ankon, bayan sun gama ya kama hannun Fatun su Laila suka take masu baya suka nufo waje, duk son Fatuu da takalma masu tsini wannan dakyar take yin tafiya dashi, a bayan Motar da suka zo da ita shi da Fatun suka shiga Abbas ya shiga kujerar driver Laila kuma da mai makeup suka hau Motar ta a tare suka tafi. Bayan sun isa harabar wurin dankam take da motoci na Alfarma sosae Event Center d'in ya had'u, Laila ce ta fara fitowa taje Motar su ta sanar masu su jira kar su fito Abbas ya bud'e k'opar gaban ya fito, lokacin Motar Nameer ta danno kai cikin wurin, dakatawa Laila tayi suka k'araso bayan ya parker duk suka bud'e kopopin kusan a tare suka fito, kai Jama'a wannan gayu haka🤔 ai ni bamma gane su Fauzy da Mino ba gaba d'aya suma sun koma kalar yan Abujar, gaba d'aya anko ne a jikin su har Zainab ma na Fatuu ta saka amman saida aka sha mata su ba kamar wurin hips d'in, su duka riga da skirt ne banda Haulat ita doguwar riga ce kuma ita kad'ai ke da mayafi, Baby d'inta ma tayi mata gayu da yan kanti tana ruk'e a hannunta, Nameer ma ankon mazan ne a jikin shi yasa hula duk sumar shi ta fito ta baya da gefe abun saidai ace Ma sha Allah Angon Mino, wurin Aunty Laila d'in suka zo ta shiga yabon gayun su suna dariya haka ma Abbas yace ma Mino ai shi bai gane ta ba ma, ce masu tay su jirata anan ita da Abbas suka nufi cikin hall d'in, Motar saurayin Jidderh ce ta sake sako kai dama tare suke sun riga su isowa ne, bayan ya parker a tare suka fito ita straight gown ce aka mata shima saurayin nata Sadeeq ankon mazan ne a jikin shi suka zo wurin su Fauzy, kusan duk an hallara isowar Amarya da Ango kawae ake jira hall d'in yasha decorations, sosae ya had'u in nace in tsaya in bayyana tsaruwar wurin to kuwa dare yayi ba tare da na bayyana yadda Dinner d'in ta wakana ba, sosae kwalliyar hall d'in ta hau da dressing d'in mutanen wurin dama su suka za6i wanda za'ai masu, daga saman hall d'in nan aka aje leather chair mai kyau daga gabanta d'an table d'inta ne d'auke da abubuwan sha harda flower mai kyau, bayan wurin ya k'awatu sai sakin haske yake kala kala hatta saman hall d'in a lullube yake da irin decoration d'in da aka zagaye hall d'in, daga gaban hall anyi shimfid'u masu k'ayatarwa a gefen dama manyan speakers ne na masu DJ daga can bangaren hagu masu kid'an ganguna ne duk sun yi ready, daga su sai dogayen tebura suna kallon juna daga bayan su aka jera kujeru gaba d'aya an lullube su daga saman tables d'in an jera k'ayatattun flowers dake sakin walwali harda wasu sarkoki aka yi adon su abun dai sai wanda ya gani, a saman su k'awayen su Mom da Aunty ne da wasu Manyan mata yan uwansu, daga su sai wasu had'add'un royal sofas da aka jera suma suna kallon gaban hall an jera k'ananun table d'in kujerun a gaban su a nan Hajiya Zainab take da yaran ta daga gefe kuma Mom ce da wasu matan manya harda matar Speaker house of rep da wasu matan ministoci, daga can d'ayan side d'in nan hamshaki Sameer yake a hakimce dasu Salim da Najeeb da wasu Abokan su yayan masu fad'a a ji duk ankon mazan ne a jikin su kuma gaba d'aya d'inki iri d'aya, sauran cikin hall d'in anyi seat arrangements na kujeru masu round an zagaye su da kujeru guda hud'u kowanne table an kuma nad'e su da covers kalar da suka hau da decoration d'in bangon hall d'in a kowanne table an d'aura flower mai kyau, iya dai hall d'in ka gani kasan ba k'ananun kud'i ya ci ba, bayan su Laila sun shigo wurin yan mata taje ta za6o wasu ta wuce wurin dasu Aunty Mareeya suke tace ma Fanan ta taso a shigo da ita tace to itama tana sanye da ankon anyi mata fitted gown wuyanta sanye da yar ziririyar sark'ar diamond da barima harda d'an hannu tayi kyau ba k'arya, Su Yadikko ma da gwaggo duk suna zaune sun sha anko Yaya ma na sanye da k'uri adakan leshin ta mai kaman bambalasta, Abbas ma wurin su Najeeb yaje ya sanar dasu su taso a shigo dasu Haisam, saida Laila ta je wurin masu Dj ta sanar dasu wak'ar da zasu saka sannan ta yi ma babban MC magana kan shigowar, bada jimawa ba MC ya sanar da shigowar su aka saki wakar Aure Martaba gaba d'aya hall d'in ya d'auka, su Haisam d'inne a tsakiya yana ruk'e da hannun Fatuu na dama Fanan na ruk'e da na hagu daga bayan su su Jidderh ne a 6angare d'aya sai su Abbas a d'ayan bangaren hamshak'i Sameer dai dama bai taso ba, suna shigowa ciki aka saki wata k'ara mai kaman jiniya, saida aka raka su saman kafin suka dawo cikin hall d'in, sakin dry ice smoke akai gaban hall d'in ya turnuk'e da hayak'i ya shiga fita yana bada k'ayataccen design kowa kaga fuskar shi d'auke take da murmushi, bayan duk an natsu Mc yay welcoming kowa da bayanin dalilin daya sa sukai gathering a wurin, agenda ta farko Abbas aka kira yazo yayi jawabin maraba, bayan ya fito cikin harshen turanci bayan yayi Addu'a yay ma kowa sannu da zuwa da dalilin taruwar su k'arshe yay ma ma'auratan fatan Alkhairi yayi godiya ga mahalarta taron musamman manyan iyayen su, bayan ya gama Mc ya fad'i next abunda za'ai wanda takaitaccen tarihin Ango za'a bada ya ambaci sunan Sameer matsayin wanda aka sa zai bada tarihin, yana a Hakimce akan kujera ya d'aura k'afa d'aya akan d'aya kai kace ba sunan shi aka kira ba duk wanda suka san shi idon su na akan shi sai da ya mula bayan Mc ya k'ara kiran sunan sannan ya d'an d'aga hannu yayi mashi alamar ya kawo mashi lasifikan, da yawa basu yi mamakin hakan da yayi ba ciki harda wanda suka ga lokacin da suka zo gidan su Haisam, bayan an Kawo mashi sai da ya d'an d'auki lokaci sannan ya d'an kai ta kusa da bakin shi cikin isa ya fara magana, tsit kake ji kowa shi yake saurare cike da gwanancewa da kwarewa yake bada tarihin da turanci kai kace ba bahaushe bane duk da dai za'a iya cewa ba cikakken bahaushen bane, zuru Fauzy tay tana kallon shi ta can gefen shi da suke zaune duk da gefen fuskar shi kawai take iya gani, sosae yasa jikin wasu tsuma yana gamawa ya janye lasifikan ya d'aurata saman table d'in gaban shi duk da Mc d'in ya taho ya amsa aka shiga tafawa, bayan Mc ya d'auka harda yi mashi godiya bai ko kalle shi ba nan fa wad'anda basu san shi ba suka fara tambayar waye shi, abu na gaba da Mc ya fad'i za'ayi shine bada takaitaccen tarihin Amarya wanda aka kira sunan Fauzy itace zata yi, mik'ewa Fauzy tay duk da ta shirya ma hakan sai da gabanta ya hau fad'uwa, gaban hall d'in ta nufa a d'arare duk kunya ta rufe ta Saboda rashin mayafi don bata saba ba ko Yaya ne in zata je abu irin haka tana saka gyale, wurin Mc d'in taje ya mik'a mata lasifikan bayan ta amsa tana juyowa ta sauke idanunta kan Sameer suka had'a ido wani irin bugu kirjin ta yayi da sauri ta maida idonta ya koma kallon k'asa, a nutse ta fara godiya da yabo ga Allah da neman tsira da aminci ga fiyayyen halitta kafin ta fara bada tarihin Fatuu, sosae tay k'ok'ari wurin yi da turanci ba wata gargada duk da fargabar da take ji, tana gamawa aka shiga tafa mata bayan ta bashi lasifikan ta nufo cikin hall d'in idanunta a k'asa Mc d'in na yaba mata, abu na gaba Amarya aka buk'aci ta bayyana irin farincikin da take ciki da kuma tarihin yadda suka fara soyayya da Angonta har suka yi aure, mik'ewa Fatuu tay gabanta nata d'an fad'uwa ta nufo saukkowa daga saman Mc d'in nata kod'a ta, mik'a mata lasifikan yay ta amsa ta juya ta kalli Mutane, ta saba yin magana a gaban mutane tun a Secondary School hakan yasa bata ji komai ba a nutse cikin sanyin murya ta fara magana, godiya tay ga Allah sannan tayi ga mahalarta taron, tiryan tiryan ta shiga bayyana tun farkon haduwarta da Haisam zuwa dawainiyar da yayi da ita a rayuwa da yadda Allah ya jarabe ta da son shi sakamakon kyautatawar da yake mata da kuma yadda ya zama mijin ta a lokacin da bata ta6a zata ba, gaba d'aya komai a tak'aice take fad'i, juyawa tay ta kalli Haisam ta fara yi mashi godiya akan sadaukarwar da yayi a gare ta wurin ganin ya maida ita mutum, sosae ta shiga yi mashi godiya tana nuna bata da abunda zata iya saka mashi saidai tayi mashi Alk'awarin zama mai biyayya da saka shi Farinciki, Haisam d'in sai kallon ta yake da d'an murmushi wani abun in ta fad'a sai ya lumshe mata ido, bayan ta gama nashi komawa tay kan Fanan farko yabonta ta fara yi tace tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin mace irin ta ba, ta had'a komai na rayuwa amman hakan bai sa ta zama mai girman kai ba, ita a wurinta kirkinta har yayi yawa, tunda ta fara ganinta take k'aunarta har ta kai ta amince mata ta zauna da ita a matsayin kishiya ko kuma tace k'anwa Saboda farincikinta, nunawa tayi bata da kalmomin da zata iya yin amfani dasu wurin gode mata sai dai tayi mata Alk'awarin zama tamkar k'anwarta uwa d'aya uba d'aya da yardar Allah bazata zama matsala a gare ta ba saidae silar farincikin ta kuma tana son shaida masu ita da mijin su sune Mutanen da sukai mata kirkin da ba wanda ya ta6a mata irin shi a rayuwa duk da they're on a different level haka suka jata a jikinsu suka nuna mata duk d'aya suke, muryarta ce ta karye dama tuni k'walla sun fara zubo mata, Addu'oi ta shiga yi ma Fanan Mutanen cikin Hall d'in na amsa wa har ta kai kuka yaci k'arfinta kawai sai ta durk'ushe anan ana jiyo sautin kukan nata ta cikin loud speakers, Kusan a tare Fanan da Haisam suka mik'e suka nufota, Haisam ne ya riga saukkowa don da sauri ya nufo ta lokacin da Fanan ta k'araso ya d'ago ta tana zuwa kawae sai ta rungumeta ta saka kuka itama, baiwar Allah koda bata nuna kishi ba wai don bata jin shi bane ita kadae tasan battle d'in da take da zuciyarta kawai bata da mafita ne tasan hakan shi yafi mata Alkhairi, Hannu Haisam ya bud'e ya rungume su aikuwa gaba d'aya aka hau tafi da sowa wasu suka fara yi masu Vedio daga inda suke, d'agowa yay ya kai hannu cikin aljihun shi ya fiddo farin hanky, d'ago da fuskar Fanan yay ya shiga share mata hawayen fuskarta itama tasa gefen gyalenta tana goge ma Fatuu, bayan sun gama goge gogen hawayen a tare suka kama hannun Fatuu ta yadda suka saka ta a tsakiya suka nufi komawa saman nan Mc ya shiga kwarzan ta su yana fad'in "What an emotional occurrence, What a beautiful Family...." Bayan sun koma saman a tare suka zaunar da ita ta sadda kanta k'asa tana ta sheshsheka, Mc ne ya sanar za'a jira Amarya tayi shiru sai aci gaba duk akai murmushi, after some few minutes yace ma Haisam saura shi suna so ya bayyana farincikin da yake ciki, tun kafin ya rufe baki ya girgiza mashi kai alamar bazai ce komai ba Mc hada kwa6e fuska ya juyo yace to anyi ma Ango laifi an sa Amaryar shi kuka don haka bazai yi magana ba aikuwa su Laila suka mik'e suna basu yarda ba yadda itama tayi shima sai ya yi nan fa wasu ma suka sa baki harda su Aunty abun sosae ya bada nishad'i, ganin an fi k'arfin shi yasa shi yi ma Mc d'in alamar ya kai mashi lasifikan, da sauri ya nufi saman ya mik'a mashi, yana amsa abunda yace shine yana matuk'ar son matanshi kuma zai yi matuk'ar kokarin ganin ya zama mai Adalci a gare su, yana fad'in hakan ya mik'a ma Mc mike d'in gaba d'aya aka hau tafi da sowa harda Sameer sarkin kamewa saida ya d'an yi guntun murmushi, mik'ewa Laila tayi ta nufi bayan hall d'in, cikin wani d'aki ta shiga inda ma'aikatan da zasu serving mutane Abinci suke gaba d'aya jikinsu sanye da farar t-shirt mai d'auke da tambarin wurin da suke aiki na k'awar Mom, umarnin fara kai Abinci ta basu dama abunda suke jira kenan ba 6ata lokaci suka fara zuzzubawa suna d'aurawa a saman manyan trays, a wuri na musamman aka zuba ma su Her Excellency da sauran manyan matan, ko ban fad'a ba ansan abinciccika ne na musamman nan suka shiga kai ma mutane duk abunda mutum yake so zai d'auka in ma fin plate d'aya ne mutum ke so na wani Abincin zai iya dauka, masu raba lemuna ma suka shiga kawo ma mutane shima ko nawa mutum ke so zai d'auka, samun wuri Mc yay yana fad'in bari yay refilling cikin shi ya k'ara samun karsashi duk aka sa dariya don cike da barkwanci yayi Maganar, a nutse kowa ke cin Abincin kuma ba wanda ya damu da yadda wani ke cin nashi har lokacin Fanan na saman tare suke cin Abincin harda ba Fatuu a baki tana murmushi ta bud'e mata bakin daga baya itama ta bata, Mc na gamawa ya mik'e yana fad'in to basu da lokacin 6atawa bari aci gaba da abunda ya tara su duk aka sa dariya ana fad'in sai da ya gama yasan basu da lokacin 6atawa, abu na gaba Ango da Amarya aka buk'aci su sauko su taka Haisam nuna wa yay bazai je ba Fanan ta nuna mashi kar yayi hakan baza'a ji dad'i ba, tare suka mik'e ya kama hannun Fatuu ita tayi gaba suka biyo bayanta, tana saukkowa ta koma cikin hall din Mc ya nuna masu inda zasu tsaya, suna zuwa wurin kawai aka fara sakin fireworks da dry ice smoke, Ya Allah har tsuma nike Saboda kayatuwar yadda ake sakin hayakin da kuma tartsatsin wutar kowa ka gani murmushi ne akan fuskar shi wasu kuma washe baki sukai, ita Fatuu ma d'an tsoron abun ne ya kamata yadda hayakin ya turnuk'e su da kuma yadda tartsatsin ke fita da k'arfi, "Dama nasan da wuya H,Zee bai auri yarinyar can ba, tun da naga yak'i amince man in nemeta dama I ave suspected something ever since" Najeeb ne da yake zaune gefen Abbas yayi Maganar, yar dariya Abbas yayi yace mashi wllh ba wani abu a ranshi a lokacin daya wuce taimaka mata kawai Allah ne ya k'addaro zasu zama ma'aurata yace baya fad'i mashi yadda komai ya faru ba, hararar Abbas d'in yayi fuska d'aure yace "ai kaima ba sona kake da ita ba in ba haka ba why not ni ka kirani kai man Maganar Aurenta kaga in ban aureta ba" Sosae Abbas yake dariya bai dai ce komai ba acikin ran shi ya raya ai duk k'anwar ja ce, Salim dai d'an murmushi kawae yayi, kamata Haisam yay har hayakin ya washe, wak'ar Fall in love aka kunna masu yana rik'e da ita sai murmushi yake mata itama d'an murmushin take duk kunya ta lullube ta, a hankali yake d'an motsawa da ita har lokacin tartsatsin wutar na tashi a bangaren daman su da hagun su abun gwanin k'ayatarwa, masu hoto da Video nata yi harda wanda aka daukko, bayan d'an lokaci kafin wak'ar ta k'are Laila ta nufi wurin Dj ta fad'i mashi ya canza masu Wak'a tace yasa wak'ar breaker ta burina, a hankali taken wak'ar ya fara da kid'a mai sanyin dad'i kafin baitin wak'ar ya fara fita, _Dubaaa kan ki ana kallonaa....babban buri na ki kasance dab dani, in zaakii k'irga masoya naki ki sanyo danii, dubaaa kan ki ana kallonaa majnunii ni kuma nace in dai kai na ki ne baan fad'i ba, sak'o ya bayyana ni tun daga zuciya, sannan k'aunar ki tana kaman zuciya......_ Kowa kaga ni fuskar shi d'auke da Murmushi wasu suna d'an juya kai suna bin wak'ar, lokacin da aka zo baitin da ake cewa _" kin rikirkita dukka tunani na, taimaka ki bani wurin kwana, son ki ya hana min bacci na, ina ganin ki har a mafarki na, son ki yanaiii min dad'i ban san mu rabu......"_ Laila da ke tsaye tana masu Vedio ta d'aga murya tace "Big Bro yi mata zaka rink'a yi fa" Murmushi kawae Haisam d'in yay Jidderh ma ta k'ara d'aga murya tana cewa ya saurara za'a k'ara maido mashi, baitin na k'arewa Laila tace ma Dj d'in ya maido baitin, yana maido shi duk aka maida hankali kan su Laila da Jidderh harda sauran k'annansu da wasu yan uwansu suka shiga fad'in yayi mata har saida suka ba Haisam d'in dariya Fatuu ma haka duk kunya ta rufe ta, lokacin da baitin ya kusa zuwa k'arewa kawai sai gani sukai ya bi harda nuna ta, wani irin ihu aka sa Fatuu ta 6oye fuskarta tana dariya, sosae abun yaba mutane nishad'i, Hajiya Zainab ce ta mik'e tana murmushi Momy ma ta mik'e suka nufi gaban Security detail d'inta na biye dasu hannunta ruk'e da jakar ta, wurin su suka je ta mik'a ma security d'in hannu ta bata jakarta, bandir d'in yan dubu dubu ta fiddo guda biyu haka Mom ma su ta fiddo daga cikin jakarta nan fa suka fara masu ruwan nera, ai kamar sun bud'e k'opa sauran manyan bak'in ma duk suka mik'e suka nufi gaban ai masu kid'an ganga na ganin haka ba 6ata lokaci suka hau bugun gangunan su suna wasa manyan matan nan fa Hall ya karad'e kid'a ko ta ina abun sai ya ba mutane ma dariya, Laila ce tayi ma Dj magana sannan ya kashe nashi, Laila ma lik'in ta fara masu Jidderh ma saurayinta ya fiddo bandir d'in d'ari biyar biyar ya bata taje haka su Nameer ma, daga wurin lik'in su Her Excellency da Mom dasu Aunty sauran manyan bak'in duk tafiya sukai, nan aka cigaba da rawa ana lik'i, wai ashe haka Laila da Jidderh suka iya rawa harda kama Haisam suna yin rawar, Yadikko ma saida taje ta amshi canjin yan d'ari biyu biyu tayi ma d'iyarta lik'i koda Fatuu ta ganta rungume ta tayi, gwaggo dai bata yi ba Saboda kunya tana zaune sai dariyar farin ciki take, Kawu Amadu da Tk da Nameer ma duk saida suka yi, Haulat ma saida taje tayi canjin yan d'ari biyu taje tayi haka Saude ma Hajiya dai dama bata zo ba, rud'ewa Fauzy tay tana son yin lik'in amman bata da ko sisi duka yan kud'inta dasu ta siya takalma da jaka da mayafi da zasu zo, tana ganin Aunty Mareeya ta nufo cikin hall d'in ta gama lik'in nata da sauri ta tare ta kaman zata yi kuka tace mata don Allah ta bata kud'i itama taje tayi, wani kallo ta mata tace wllh bata da kud'in da zata bata itama wanda tayi k'arfin hali ne kawai, komawa tayi ta zauna jiki a mace Zainab ce tace mata tana da yan kud'i suje suyi canjin ko d'ari biyu biyu ne, girgiza mata kai tayi tace taje tayi kawai, ba yadda bata yi ba amman tak'i k'arshe ta tashi ta tafi ita, takaici duk ya kama Fauzy abu goma da asirin, ga Vedio ta kasa yi Saboda wayarta data kwankwatse bata iya fiddo ta a wurin ga rashin kud'i, k'arshe kife kanta tayi saman table d'in jin tana niyyar yin kuka, bata dad'e da kife kan ba taji ana mata sallama, d'agowa tayi ta kalli mai sallamar wanda d'aya daga cikin ma'aikatan dake hidiman Abinci ne, gaida ita yay da d'an alamun mamaki ta amsa mashi kawai sai gani tay ya Mik'o mata kud'i bandir d'in yan dubu dubu guda biyu dubu d'ari biyu kenan, ce mata yay gashi aka ce ya kawo mata taje tayi lik'i, waro ido tay da alamun Al'ajabi ta tambayi waye yace a batan, nuna mata saitin da su Sameer suke yayi yay mata kwatance wanda ya badan don ya juya kan shi yana a Hakimce iya sumar shi kawae suke iya hangowa, jimm Fauzy tay saida ya k'ara ce mata gashi sannan a tsorace ta amsa ya juya ya tafi, bin kud'in tayi da kallo kafin ta kai duban ta kan su Aunty Mareeya dake ta hira basu ma lura da abunda ke faruwa ba, a hankali ta juya ta kai idanunta kan Sameer ta bishi da kallo ji take kamar ta je ta maida mashi saidae tsoro bazai barta ba, tana haka kwatsam ta ga ya juyo ya kalleta suka had'a ido, wani mugun kallo yay mata ya janye ido ya koma yadda yake, ba shiri ta mik'e hannun ta ruk'e da kud'in ta nufi gaban hall din a d'arare, koda tazo saitin su ta kai idon ta kanshi bai ko kalleta ba, tana zuwa ta shiga yin lik'in bayan bandir d'aya ya k'are ta bud'e d'ayan ta raba biyu ta mik'a ma Zainab data saki baki tana bin ta da kallon mamaki, cikin makad'an ne wani yazo ya tambayi sunan Fauzy ita bata san dalilin ba ashe wak'e ta zasu yi kaman daga sama taji ana angaida Hajiya Fauziyya mai ruwan naira har bata san lokacin da tasa dariya ba tana d'an kare fuska, kirarin da ake ma Fauziyyar ne ya jawo hankalin Aunty Mareeya ta Ankara da lik'in dubu dubun da Fauzyn ke yi, wani jiri Fatuu taji yana niyyar kwasarta da sauri ta kai duka hannuwanta ta kama jikin Haisam, kallon ta yay ganin yadda take lumshe ido yasa shi tambayarta tana lafiya ta d'an yamutsa fuska ta kai hannu ta dafa gaban kanta a hankali tace mashi jiri take gani ba shiri ya kamata ya fara k'ok'arin barin wurin da ita wad'anda suka ankara suna tambayar lafiya yace masu eh, su Laila ne suka cigaba da yin rawar ya koma saman da ita, bayan ya zaunar da ita shima ya zauna cike da kulawa ya tambayi har yanzu tana ganin jirin, d'an murmushi tay ta girgiza mashi kai a hankali tace ya bari yace ta tabbata kodai su tafi gida still da murmushi tace mashi kada ya damu tasan tsayuwar da tayi ne yasa, Fauzy na son yin rawa amman ta kasa Saboda Sameer duk da bata san ko yana kallonta ba, bayan ta gama yin lik'in nufar komawa tay cikin hall d'in idon ta a k'asa, tana zuwa saitin Sameer ta saci kallon shi karaf suka had'a ido da sauri ta janye idon, tana zama a wurin zaman su Aunty Mareeya ta nufo ta da sauri har tana bugewa da kujera, zama tay a d'aya daga cikin kujerun ido a waje tace "Ke, ina kika samu kud'i haka da kikai lik'i har ana Wak'e ki?" murmushi tay tace mata Allah ne ya bata, wata uwar harara ta zabga mata tace zata gaya mata gidan uban wa ta same su ko kuwa, tana dariya tace mata wani ne ya bata, k'ara zabga mata harara tay tace wani wa, satar kallon Sameer tay sai sumar kan shi ta hango, maido idonta tay kan ta tace mata mutumin jiya ne ya bata, washe baki Aunty Mareeya tay a k'agare tace mata yana ina Fauzyn tay d'an jimm kafin tace mata ya fita bayan ya bata kud'in, "Da alama dai Addu'a ta zata amsu, koma har yace yana son kin?" dariya Fauzy tay ta girgiza mata kai, tace ai duk aje a dawo in kaga kare na sunsunar takalmi to d'auka zai yi, tambayarta tayi har nawa ya bata tayi lik'in ta fad'i mata, zaro ido tay tace "ba dai duka kika lik'a ba??" Kai ta d'aga mata kafin tace duka, bud'e baki tay alamar Al'ajabi tace "amman dai ke anyi shashasha wllh taya zaki je ki lik'a duka wannan uban kud'in ba tare da kin rage ba, maimakon ma ki saka bandir d'aya a jaka ki lik'a d'aya" fuska d'aure ta k'arasa Maganar, ce mata tay ai lokacin yana kallon ta fa taya zata d'au wasu Aunty Mareeyar tace eh to gara da bata d'auka ba kada yay tunanin tana da son abun duniya gara abi komai a hankali ya shigo hannu ita dai Fauzy dariya kawai take. Sai wuraren k'arfe sha biyu da wasu mintuna taron ya fara tashi, Kusan duk an tafi wasu daga cikin Abokan Haisam d'in ne suka rage su Abbas da Najeeb sai Na'eem Salim ya tafi haka Sameer ma tuni ya tafi, Aunty Laila bata tafi ba tana waje tana k'ok'arin ganin an maida kowa Nameer ma bai dad'e da tafiya dasu Fauzy ba, su Abbas suna tsaye a sama inda su Fatuu suka zauna Haisam ma na tsaye tare dasu suna magana, Laila ce ta lek'o cikin hall d'in ta sanar dasu kowa ya tafi fa Haisam ya d'aga mata kai, Abbas ne ya kalli Fatuu dake zaune yace "Mom Zarah an sha gajiya ko" d'an murmushi tay Najeeb ya kai idon shi kanta suka had'a ido shima d'an murmushin yayi mata, Kallonta Haisam yay yace ta tashi su tafi ta d'aga mashi kai, tana mik'ewa ta fara ganin jiri da sauri ta kai hannu ta dafe goshi bakin ta a d'an bud'e, wani irin duhu ta fara gani lokaci guda ta fara fita hayyacin ta, Abbas ne ya kai idon shi kanta yaga halin da take ciki da sauri ya furta "Mom Zarah lafiya??" gaba d'aya suka kai idon su kanta ko kafin suce mata wani abu gaba d'aya ta tafi zata fad'i cikin zafin nama Haisam ya tareta ta fad'a jikin shi, cikin tashin hankali ya shiga fad'in "Baby! Baby can you hear me? Mike faruwa?" tun tana lumshe ido tana bud'e su har ta k'arasa rufe su baki d'aya............ *ASM 083* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ...........Cikin tashin hankali yake jijjigata yana kiran sunanta, Abbas ne ya d'aukko robar ruwa bayan ya bud'e ya mik'a ma Haisam ya tara mashi hannun shi ya zuba mashi, sau biyu ya shafa mata amman ba alamar zata farfad'o, Najeeb ne da shima fuskar shi ta nuna tashin hankali yace bai kamata su tsaya suna wasting time ba ai rushing d'in ta hospital, Na'eem ne yace akwae wani private hospital daya sani bada nisa sosae ba, yana rufe baki Abbas yace ma Haisam ya d'aukko ta ya nufi hanyar fita Hall d'in da sauri sauri gudu gudu, d'agota Haisam yay ya d'auketa suka nufi hanyar fita dasu Najeeb, suna fita Abbas ya iso da Mota bakin wurin Najeeb ya bud'e baya Haisam ya saka ta ciki shima ya fara k'ok'arin shiga lokacin Laila ta k'araso hankali a tashe ta shiga tambayar wai mi ya faru da ita don Abbas ya sanar mata game da fad'uwar da tayi da ya fito, Najeeb ne yace hakanan suka ga ta fad'i, Na'eem ne ya shiga driver seat Saboda shi yasan Asibitin Najeeb da Abbas suka nufi inda Motocin su suke Abbas ya shiga Motar Na'eem haka Laila ma da gaba d'aya ta gama rud'ewa, a saman cinyoyin shi ya d'aura kan ta ya shiga shafa face d'inta yana kiran sunanta duk hankalin shi ya tashi, tashin Motar Na'eem yay bayan ya juya ya tunkari gate d'in wurin da gudu Motocin su Najeeb suka rufa masu baya, suna a kan hanya Laila ta d'aukko wayarta ta shiga kiran Mom d'in su, bayan tayi picking tun kan tayi magana cikin Muryar rud'u tace mata gasu a hanyar Asibiti, tambayar ta tay mi zasu je yi Asibiti tace mata Bride d'in Big bro ce hakanan ta yanke jiki ta fad'i, daga muryar Mom d'in zaka fahimci ba k'aramar razana tayi ba lokacin da ta sake maimaita abunda Lailar tace mata, tambayar ta tayi to miya faru da ita ne Fuskar Laila a yamutse kaman zatai kuka tace "Wllh ba abunda ya same ta kawae ta mik'e za'a taho gida ne aka ga ta yanke jiki ta fad'i" tambayar ta tayi an yayyafa mata ruwa tace mata eh an shafa mata har sau biyu amman bata ko motsa ba, salati Mom ta rafka a kid'ime ta tambayi wane Hospital zasu tace mata itama bata sani ba Abokin big bro ne yake jagorantar su shine yasan Asibitin, tun kafin ta rufe baki Mom d'in ta katse Wayar, hannu ta kai ta dafe gaban kanta tana salati Hajiya Zainab dake zaune duk taji abunda suke Magana akai itama daga yanayin fuskarta akwae alamun tashin hankali, tambayarta tayi miya faru da matar Son d'in tayi mata bayanin da Laila tayi mata, jinjina kai tayi tace to Allah yasa lafiya ta yuwu stress ne ya mata yawa Mom dake kallon ta tace to Allah yasa, kiran Senator tayi a waya saida ta kusa katsewa sannan yay picking, saida ta bashi hak'uri na tashin shi da tayi don tasan in ba bacci yake ba wayar bazata dad'e tana ringing ba batare da ya d'auka ba, ce mata yay ba komai Allah yasa dai lafiya cikin yar rawar murya ta sanar dashi abunda ke faruwa cikin daidaita natsuwa don kada ta tada mashi hankali, salati shima yayi ya tambayi asibitin da suka tafi ta fad'i mashi yadda Lailan tace yace Ok bari ya kira Son d'in, kiran Nameer Laila tayi a tunaninta ko basu kai gida ba don basu dad'e da rabuwa ba, ya tsayar da Motar kenan gaban Entry Hall kiran ya shigo, yana yin picking ta sanar dashi abunda ya faru cike da Al'ajabi ya maimata abunda tace su Fauzy dake niyyar fita daga cikin Motar cak suka tsaya suna sauraren shi, bayan ya gama wayar har suna had'a baki wurin tambayar shi abunda ke faruwa ya sanar masu, gaba d'ayan su razana sukai kar ma Mino taji gaba d'aya ta zaro ido kirjinta na mata wani irin bugu jin Adda Fatuu d'inta ta fad'i, Jidderh ce ta rok'e shi suje Hospital d'in yace Ok duk suka rufe kopopin Motar yaja suka tafi, tuni Mino ta fara kuka tana fad'in Allah yasa Adda Fatuu ba mutuwa tayi ba irin na mamanta, duk da su Fauzy na cikin tashin hankali haka suka shiga rarrashinta harda Nameer yace mata ta kwantar da hankalinta in sha Allah ba abunda zai sameta suyi mata Addu'a duk suka jinjina kai, nan fa Mino ta shiga yin Addu'oin a bayyane suna amsawa da Amin can ta kai hannu cikin jakarta ta fiddo wayarta ta shiga kiran gwaggo, lokacin da kiran ya shiga su gwaggon duk sunyi bacci, saida ya kusa katsewa ta farka lokacin data d'auki wayar kiran ya yanke, ganin mai kiran nata ta ambaci Mino to lafiya kira a wannan lokacin, tana niyyar kira saiga wani kiran ya shigo da sauri ta d'aga tun bata ji mi zata ce ba saida gabanta ya fad'i, cikin kuka ta sanar mata Gwaggon ta saka salati hakan ne ya tada Hajiya ta bud'e ido, bayan gwaggo ta gama wayar Hajiya dake kallonta ta hasken bedside lamps tace "Ya ya Mike faruwa ne miya samu Fateemar ne?" Cikin tashin hankali Gwaggo ta sanar mata ai ba shiri ta idasa tashi zaune, hannu ta kai ta d'aukko wayarta ta shiga kiran Haisam lokacin da kiran ya shigo mashi ya kife fuskar shi data Fatuu idanun shi a rufe sai Addu'oi yake mata, yana jin wayar na ringing amman a halin da yake ciki bai jin zai iya d'aukar waya, k'in d'aga wayar da yayi ya k'ara tada ma Hajiya da gwaggo dake kallon ta hankali, kiran layin Senator tayi tana fara yin ringing ya d'aga Hajiya tace mashi yaji abunda ke faruwa yace eh gashi nan ma zasu je Asibitin tace to bari su fito yace a'a ta yi baccinta in sha Allah ba abunda zai faru tace "taya wani bacci zai yuwu hankula duk sun tashi kaga uwar ta nan cikin tashin hankali gara dai muje da mu zauna zaman jiran tsammani" amsa mata yay da to, Gaba d'aya Haisam ya rasa inda zai tsoma ran shi, fargaba ta cika shi zuciyar shi sai raya mashi abubuwa take, bawan Allah in ta raya mashi wani abun sai ya girgiza kai da sauri ya k'ara k'ank'ame Fatun, wani iri yake jin zuciyar shi gaba d'aya rayuwar shi da ita sai dawo mashi take ba abunda yake gani sai fuskar ta d'auke da Murmushinta mai burgewa, "ko dai dama Allah bai yi zaku rayu tare tsawon lokaci ba" zuciyar shi ce ke raya mashi hakan da sauri ya hau girgiza kai kawai sai jin kwalla yay suna zubo mashi bai ko yi yunkurin gogewa ba, gaba d'aya gani yake tafiyar tayi tsawo har saida yayi ma Na'eem magana yace sun kusa, bada jimawa ba suka k'araso Asibitin a Jere motocin nasu suka shigo cikin harabar, Laila ko inda aka tanada don parking motoci bata k'arasa ba ta parker Motar, da sauri ta bud'e k'opar ta fito lokacin cikin security guards d'in dake bakin gate da ya biyo bayan Motocinsu yace mata pls ta gyara fakin ba'a yi anan bata ko kalleshi ba ta furta mashi it's an emergency daga haka ta nufi cikin Asibitin ko rufe Motar ma bata yi ba, Na'eem na fakawa da sauri Haisam ya kai hannu ya bud'e kopar ya fara k'ok'arin fitowa da ita Na'eem ya zo wurin ya taimaka mashi su Najeeb ma da sauri suka k'araso, yana d'auke da ita suka nufi cikin Asibitin a bakin main entrance suka had'e da Laila ta taho da nurses sun turo gado, d'aurata akai nurses d'in suka turata ciki suma suka rufa masu baya, Amenity suka nufa da ita Lokacin Doctor da wata nurse taje tayi ma magana ya nufo su, yana zuwa wurin ya gaidasu su Abbas ne suka amsa mashi ya shiga tambayar su abunda ya faru da ita suna tafiya suke bashi amsa, bayan sun iso aka shiga da ita d'aki Dr yace su jira shi ya shige, Shiru shiru tun bayan da likita ya shige bai fito ba sai nurses dake ta shige da fice cikin d'akin, can bayan kaman minti goma sai gashi ya fito nurse na biye dashi d'auke da sample na jini da gani na Fatun ne, tarar shi su Najeeb sukai suna tambayar ya ake ciki shi Haisam ido kawai ya bishi da shi don zuciyar shi tuni ta karye, ce masu yay in sha Allah she will be alright su d'an jira kad'an suna kan binciken dalilin sumar nata ne don da ran ta in sha Allah, har saida su Najeeb d'in sukai d'an murmushi tare da jinjina mashi kai ya wuce nurse d'in ta bi bayan shi, kallon Haisam daya jingina da bango Abbas yay fuskar shi tayi jajir haka idanun shi, dafa Shoulder d'in shi yay yace ya kwantar da hankalin shi in sha Allah ba wata babbar matsala bace da alama haka take suman ta don da ta yi miscarriage ma ai ta dad'e bata farfad'o ba duk da shi harda firgici yanzu kuma k'ilan gajiya ce tayi yawa, Na'eem ne ya matso shima yace "ni ina ma tunanin k'ilan harda smoke d'in nan duk da ance baida illa amman kasan kowa da kalan yadda jikin shi ke karbar bak'on abu" jinjina kai sukai cike da gamsuwa ba laifi Haisam d'in ya d'an ji fargabar shi ta ragu, after some minutes Likitan ya dawo saida ya d'an d'aga masu hannu sannan ya tura k'opar d'akin ya shige, su Nameer ne suka k'araso bayan Laila ta yi masu kwatancen inda Asibitin yake, gaida su Abbas sukai Mino dai ta kasa cewa komai sai bin su da ido take Fuskar ta sharkaf da hawaye Abbas ne ya shiga kwantar mata da hankali tana jinjina mashi kai, bada jimawa ba Laila ta dawo wurin tare dasu Dad da Mom sai Hajiya da gwaggo, gaidasu su Najeeb suka shiga yi gwaggo dai kai kawai take d'agawa don hankalinta in yayi dubu to ya tashi gaba d'aya jinin ta akan akaifa yake, Dad ne ya tambayi ya ake ciki Abbas ya fad'i mashi bayanin da likitan yayi yace "Ok sai mu jira shi Allah yasa muji Alkhairi" duk suka amsa da Amin, kallon Haisam yay da tunda suka zo bai tanka ma su ba sai ido kawae yake bin su dashi, ganin yanayin fuskar shi yasa shi kai hannu ya dafa Shoulder d'in shi da d'an murmushi yace "Don't worry Son, she will be fine in sha Allah muyi mata Addu'a" jinjina mashi kai yay Dad d'in ya kai hannu ya fara k'ok'arin cire mashi babban rigar yana fad'in bari a cire yasha iska don duk yayi zufa duk da yanayin wurin ba zafi, bayan d'an lokaci da zuwan su Hajiya tace ko dai a yi ma likitan magana aji halin da ake ciki an bar mutane da zullumi Gwaggo tace mata in ba ya gama binciken ba ba abunda zai iya fad'i tunda bai samu sakamako ba Hajiyar ta d'aga kai, Senator ne ya nuna masu waiting seat yace ma su Hajiya su zauna, Mino ma da duk hankalinta a tashe yake yace mata ta zauna ta d'aga mashi kai, basu jima sosae da zuwa ba Doctor d'in ya fito da sauri su Mom suka mik'e haka Hajiya ma da gwaggo, yana ganin Dad ya d'an sunkuyar da kai ya gaishe dashi bayan ya amsa yace ashe patient d'in su ce yace eh matar d'an shi ce, jinjina kai Doctor yay ya d'an yi shiru with confusion on his face Hajiya tace "Dr kai muke saurare, mi binciken naku ya gano yayi silar fad'uwar ta" nannauyar ajiyar zuciya yay idon shi akanta yace "pls zan iya ganin wani daga cikin danginta?" kan kowa ne ya d'aure duk suka zuba mashi ido, Dad ne yay saurin cewa "da wani abu ne?" d'an girgiza kai yay yace "No, kada ku damu yalla6ai inaso zamu d'an yi wata magana ne da d'aya daga cikin danginta wanda suke da kusanci sosae" kwa6e fuska Hajiya tayi tace "to ai nan duk danginta ne tunda alak'ar Aure ta shiga tsakani ai duk an zama d'aya, in ma mafi kusancinta ne ai Mijinta ne gashi sai kuyi Maganar" ajiyar zuciya doctor ya k'ara yi ya kai hannu ya gyara zaman glass d'in shi gaba d'aya jikin kowa yayi sanyi don sun fahimci bai son fad'i masu halin da ake ciki, sosae Doctor ya shiga rud'ani kawai sai ya yanke ya sanar da Mijinta abunda suka gano k'ilan shi yana da masaniya kan ciwon nata, tambayar ina Mijinta yay aka nuna mashi Haisam yace "pls let me see you in my Office" mik'a ma Abbas rigar shi yay wani irin Fad'uwa gaban shi ke yi ya juyo yay ma Dr alamar suje da hannu, "Shin wai Fateemar ko juna biyu ne da ita??" har likitan ya juya Hajiya ta furta hakan da sauri ya juyo ya kalleta, komawa yay wurinta a d'an fad'ace tace ya fad'i masu abunda ke faruwa duk miye na wani 6oye 6oye, d'an gyaran murya yay ya fara kora mata bayanin cewa abunda suka gano shine stress ne yay mata yawa ta yuwu tayi zurga zurga da yawa ta gaji sosae hakan yasa ta suma sai dai kuma abunda ya assasa suman nata shine sun gano tana d'auke da juna biyu na tsawon wata guda, ai tun kafin ya rufe baki suka hau washe baki su Jidderh da Mino harda sakin k'arar murna gwaggo ma bakinta a washe yake haka Mom dasu Abbas kowa ka gani sai washe bakin murna yake Senator ma fuskar shi d'auke da fara'a yanata fad'in Alhamdulillah nan aka kama anata fad'in Alhamdulillah, bawan Allah ango ai shi gaba d'aya ma ya kasa magana sai murmushi yake kawai sai gani akai ya duk'a yayi sujjadar godiya ga Allah duk aka kalle shi kowa fuskar shi da fara'a, bayan ya mik'e Senator ya dafa Shoulder d'inshi yace "Hankali sai ya kwanta ko Son" kawae sai Haisam d'in ya fad'a jikin shi Dad d'in yasa hannu ya rungume shi anata dariya shima Haisam d'in dariyar farinciki yake don kwata kwata ba abunda yake zato ba Kenan, sosae hakan da suke ya ba Dr mamaki har Fuskar shi ta kasa 6oyewa Dad ne da ya lura still Haisam na jikinshi yace ma likitan kada ya damu ba sabon Aure bane an kwana biyu da yi kawae yanzu ne ake shagalin bikin, wata ajiyar zuciyar samun relieve Dr d'in yayi don da he was completely confused ace ana cikin shagalin biki kuma ga Amarya da ciki hakan ba K'aramin Al'amari bane, shima sai ya shiga taya su murnar yanata murmushi, D'ago Haisam Dad yay suka had'a ido ya d'an bud'a ido yace "Son da alama ma har kuka kayi ko, halan kana tsoron kada Amarya ta tafi ana tsaka da shan Amarci ne" Yar dariya Haisam d'in yay sauran ma duk aka sa dariya, hannu ya kai suka gaisa ya furta "Congratulations my man, soon you will become a Father" cikin cool voice d'in shi ya furta mashi "Thank you Dad" Laila ce itama ta matso tana washe baki ta taya shi murna yay mata side hug ya amsa Jidderh ma ta matso tana washe baki tace "Congrats bro" jinjina mata kai yayi haka ma su Fauzy duk suka matso suna taya shi murna Nameer ma wurin shi yazo yana murmushi ya rungume shi yana taya shi murna, Abbas na tsaye tare da su Najeeb suma duk farinciki ne akan fuskokin su don ba K'aramin tashi hankulan su sukai ba, Abbas na dariya idon shi akan Najeeb da yake yasan da zancen wanccan cikin ya furta mashi "gaskiya Mom Zarah Sharp shooter ce ta gaske kaga fa har ta maida wani" kafin Najeeb d'in yace wani abu kaman daga sama suka ji ance "Shi kuma abokin naku jarababbe ko" gaba d'aya waro ido sukai suka sauke su akan Hajiya data yi Maganar kuma ko kallon su bata yi ba gwaggo dake gefenta sadda kai tay cike da jin kunya, gumtse dariya su Abbas d'in sukai ba wanda yace wani abu, Hajiya ce tace ma likitan zasu iya shiga su ganta da sauri yay mata alama da hannu ya furta "Yes you can" nufar d'akin sukai gaba d'aya harda Mom da Dad da gwaggo dasu Fauzy, su Haisam d'in suka tsaya jiran su gama shiga Najeeb da Na'eem suka matso wurin shi suna taya shi murna, Abbas na zuwa ya kamo hannun shi guda yay mashi side hug yace "Mom Zarah ta biya mu bashi da wuri kuma da alama dai a G.r.a d'in aka sake samo mana" washe baki Haisam d'in yay wanda shi rabon da yayi irin dariyar ma ya manta, tabbas a yadda aka fad'i lokacin shi da alama a G.r.a d'in ta same shi nan ya gane k'ilan harda shi yasa ta jin jiri da suka sauka Abuja Allah yasa ma bata samu wata matsala ba, daga baya suka shiga cikin d'akin, duk a tsattsaye suka iske su an zagaye gadon da take kwance har lokacin head dinta na a saman kanta fuskar ta sanye da Oxygen mask haka hannunta guda na sanye da drip, Addu'oin Allah ya bata lafiya aka shiga yi daga baya Doctor yace masu akwae buk'atar a d'aura ta kan Bed rest don akwai chance na zata iya miscarrying cikin in ta cika zirga zirga dole ta samu hutu sosae har ya zauna duk aka jinjina kai, Dad ne yace yakamata su tafi don dare yayi sosae sai wasu su tsaya, Aunty Laila ce tace a barta Hajiya tace a'a shi Mijin nata ya tsaya gwaggo dake murmushi tace a'a abar shi yaje ya huta ai an sha hidima Abbas yace kada shima ya fad'i duk aka sa dariya, shi da za'a barshin ma daya fi son hakan don zai so ace yana a kusa da ita ta farka, sallama Dad yayi masu ya juya Mom ma haka Nameer yayi ma su Mino magana suma suka tafi Fauzy sai faman sakin murmushi take ji take inama tana nan Fatun zata farka, kallon gwaggo Hajiya tayi tace suje ko tana d'an murmushi tace ba komai Laila taje don itama tasha hidima da yawa ita ta zauna, murmushi Hajiya tayi tace kawai dai K'aunar ta motsa bata son barin autar tata, kunya ce ta kama gwaggo tay yar dariya Hajiya tace ma Laila d'in suje kawai, har zasu juya Hajiya ta dakata tana kallon gwaggo tace bari suje sai a kawo mata abun shimfid'a da na lullu6a an taho hankali ba kwance ba, da sauri tace a'a tunda ga Hijab d'inta kuma doguwa ce lafiya lau zata yi mata ba sai an kawo komai ba abari sai zuwa gobe tunda ma dare yayi sosae tace to Shikenan suka juya suka tafi, Bayan fitowar su ganin Laila yasa Mom tambayar ya akai ta taho Hajiya ta fad'i masu yadda sukai da gwaggon Dad yace amman dai Laila din yakamata ta kwana Hajiyar tace mashi su je kawae ko gwaggon ta koma gidan ba bacci zata iya yi ba yar lelen ta na kwance a gadon Asibiti, yar dariya Dad yay yace ai ba ita kad'ai ce yau bazata iya yin baccin ba tana da d'an uwa yay Maganar idon shi akan Haisam duk akayi dariya, sallama su Najeeb da Na'eem sukai masu don wucewa zasu yi duk akayi masu godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci sukai ma Haisam Allah ya bata lafiya shima yayi masu godiya bayan sun shige Motocin su Senator yace ma Haisam suje shida Abbas su samo masu Abinci don tana iya tashi da yunwa yace Ok, a tare duk suka shiga cikin Motoci suka tafi. Lokacin da suka isa gidan tuni wanda suke cikin gidan sunyi nisa a baccin su, a gaban Entry Hall duk suka parker Motocin aka firfito, bayan sun shiga main parlor anan sukai ma juna sai da Safe Senator ya nufi part d'in shi haka ma Mom da Hajiya da Laila, Fauzy tare da Mino suka nufi hanyar baya har sun d'an yi nisa Nameer dake tsaye yana jiran su Mom d'in shi su shige ya kira sunan ta, juyowa tay yayi mata alamar ta zo ta juyo ta nufo shi, daga gaban shi ta tsaya suka sakar ma juna murmushi yace "Hankali ya kwanta ko Adda d'inki bata mutu ba" dariya tayi tasa hannu ta rufe fuska kafin ta cire, wani irin kallon love yake mata sai murmushi take a hankali ya furta "in muka yi aure I don't want you to get pregnant da wuri sai mun gama shan love sosae tukun" da sauri ta kai hannu ta rufe fuskarta ta juyar da fuskar wata irin kunya ce ta kama ta, ce mata yay miye abun wani kunya tunda auren zasu yi kuma ma bai son a d'auki time don ya yanke zai sanar da Hajiya sai ayi magana da parents d'in ta kafin su tafi, jin haka yasa ta juyo a sanyaye ta kalle shi, ya lura da canjin fuskar tata hakan yasa yace koda wani abu ba sun gama magana ba kuma ta amince zata aure shi, da d'an yanayin damuwa tace mashi eh kawai tana tsoron kar a k'i amince mashi ya aure ta, wani kalar murmushi yay yace "to akan mi za'a k'i amince man tunda ni nace ina so kuma in hakane shima Big bro ai da an k'i amince mashi" shiru yay ya d'age gira ya sake cewa "We are meant for each other shiyasa muna had'uwa muka fad'a son Junan mu so Don't Worry babe you will soon be Mrs Nameer Ali Zakee" k'ayataccen murmushi Mino tayi tace "Promise me bazaka dawo ka canza ra'ayi ba" wani kalan lumshe mata ido yay ya furta "I promise u My yar fillo" dariya Mino tayi shima yar dariya yay yace mata yana bala'en son yaji tana magana shiru tay tana ta murmushi bashi kad'ai ba ko a school haka ake cewa ba kamar in tana yin karatu, d'an juyawa tay ta hango Fauzy tsaye tana jiranta tace mashi bari taje ana jiranta, lumshe ido yay yace Ok amman tayi mashi abunda zai ta tunawa yay bacci mai dad'i, had'e lips d'inta tay tana murmushi a hankali tace "like what" rolling eyes d'in shi yay k'asa k'asa yace "blow me a kiss" sai da ta waiga taga Fauzy bata kallon su sannan ta d'aga hannu ta hura mashi kiss d'in ya bud'e hannu kafin ya rungume su ya wani lumshe ido dariya Mino tay ta juya da gudu ta bar wurin ya bita da kallo yana dariya, yana d'aya daga abunda ke k'ara burge shi da ita ta cika kunya, daina gudun tay data kusa zuwa wurin Fauzy, bayan taje inda take tsaye hak'uri ta bata tace ta sa tana ta jira Fauzyn ta d'an yi murmushi idonta a kanta tace "tsuntsayen love na lura dai ba k'aramar soyayya kuke sha ba da zafi zafi" rufe fuska Mino tay tana dariya suka tafi, bayan sun fito bayan sun tunkari part d'in Fauzy na murmushi tace inama su Aunty Mareeya basu yi bacci ba su ji abun farinciki Mino tace wllh itama tayi farinciki Fauzy tace sai fatan Allah ya inganta ya raba su lafiya wayaga su Zarah an haihu tayi Maganar had'i da sa dariya Mino ma yar dariyar take Lokacin suka iso part d'in suka shige. Bayan tafiyar su Hajiya wurin gadon da Fatuu take kwance gwaggo taje ta tsaya tana kallonta Fuskar ta d'auke da Murmushi, har bata san ina zata kai farinciki ba rayuwarta ta kasance fin yadda take mata mafarki, sai murmushi take tana haka fuskar Mahaifiyar Fatun ta rink'a dawo mata, girgiza kai ta shiga yi a ranta ta furta Allah kenan ya d'auke wata ya bata wata, a fili ta shiga yi ma mahaifiyar Fatuu Addu'a itama ta rok'a mata lafiya da kuma inganta abunda take d'auke da shi, juyawa tayi ta nufi kopar dake cikin d'akin wanda tasan toilet ne, Alwala ta dauro ta dawo cikin d'akin tunanin abunda zata shimfid'a tayi sallar tayi k'arshe ta yanke ta shimfid'a kallabinta kawai, bayan ta gama sallar Nafilar sosae tayi ma Fatuu Addu'a bayan ta shafa zama tayi taci gaba da tasbihi, tana haka aka k'wank'wasa kopar ta gyara zamanta tace a shigo, Abbas ne ya shigo da sallama hannuwan shi ruk'e da katan d'in ruwa da lemu bayan shi Haisam ne ruk'e da k'atuwar leda, sannu da zuwa gwaggo tayi masu suka amsa acan gaban gefen gadon suka aje kayan kafin suka juya suna gaishe da gwaggon da fara'a ta amsa tayi masu sannu, mik'ewa tayi ta d'auki kallabin tana ruk'e da shi ta nufi hanyar k'opa ta fita, tsaye sukai suna kallon fuskar Fatun gaba d'ayan su fuskokin su d'auke da Murmushi, wata irin sabuwar k'aunarta Haisam ke ji na ratsa zuciyar shi, "Allah kenan gwanin hikima masanin sirrin 6oye, wato a duk lokacin da na kalli Mom Zarah sai na tuno farkon gani na da ita a kopar gidan Hajiya ranar an aiketa ta d'ebo ruwa" Abbas ne yay Maganar idon shi akan Fatuu, Murmushi ne akan fuskar Haisam don bai mance da ranar ba, Abbas yaci gaba "lokacin har ta tambaye ka bak'o kayi na bata amsa da ba bak'o bane d'an uwan ka ne nace mata Mom d'in mu d'aya aikuwa ta buga k'afa tace ita bata yarda ba yo ya zata ga wake da shinkafa kuma in ce gidan mu d'aya, duk na tuna Maganar nan sai nayi dariya, lokacin dana fad'i mata inada mata da yaro ne tayi man magana k'asa k'asa wai kai to ya kai bakai auren ba, ina niyyar bata amsa ka d'ago kayi mata magana gashi tana tsoron ka hakan yasa ta tafi, k'ilan dana fad'i mata da sa rana akan ka da bata kamu da son ka ba" murmushi Haisam kawai yake yana tuna komai a lokacin, "Mom Zarah an yi kuruciya mai saka nishad'i ina rok'on Allah ya baku D'iya mai irin halinta sai kuyi ta tunawa da tata kuruciyar" yar dariya Haisam d'in yayi, Abbas ne yace mashi suje ko gwaggo ta komo ciki yace Ok ya sake cewa gashi ma ya gan tana salla asaman kallabi yakamata ace akwae prayer mat Haisam d'in yace zai zo da wuri sai ya taho dashi, matsawa yay wurin gadon ya sunkuya ya manna ma Fatuu kiss a saman goshinta Abbas nata sakin murmushi, gwaggo na zaune ta d'age kanta suka fito, sauke kan tayi ganin su yasa ta mik'e sukai mata saida safe ta koma ciki. Misalin k'arfe biyu da yan mintuna Fatuu ta fara motsi, a hankali ta fara bud'e idanunta har ta ware su gaba d'aya, k'ura ma saman d'akin ido tay tana kikkafta idanu, hannu ta d'ago ta ta6a mask d'in hancin ta nan take ta gane inda take, cire mask d'in tayi ta juya kanta idanunta suka sauka akan gwaggo dake kishingid'e akan kujera idanunta a rufe, bin ta da kallo Fatuu tay fuskarta da d'an murmushi, motsi gwaggon ta fara yi dama tana cikin yin tasbih baccin ya kwashe ta, kokarin gyara kwanciya ta fara cikin disasshiyar murya Fatuu ta ambaci sunanta, bud'e ido gwaggon tayi suka had'a ido, da sauri ta tashi zaune kafin ta mik'e ta nufi gadon, zama tay bakin gadon suna kallon juna da murmushi tace mata ta tashi ta d'aga mata kai, sannu tayi mata nan ma kai ta d'aga mata suka d'an yi shiru, "Gwaggo miya same ni ne har aka kawo ni Asibiti?" Fatuu ta fad'a tana ta kallonta, tana murmushi tace mata ta fad'i ne a wurin hidimar da akayi shine aka kawo ta, shiru Fatuu tay lokacin komai ya shiga dawo mata na lokacin data fad'i, "To mi akace yake damuna?" ta sake tambaya gwaggo dake ta murmushi tay d'an shiru idonta akanta can tace mata gajiya ce tayi mata yawa anata zirga zirgar hidima, shiru Fatun tay bata kawo komai a ranta ba don tasan hakan na faruwa, mik'ewa gwaggon tayi tace bari ta fad'i ma nurse ta tashi koda abunda za'a mata ta d'aga mata kai, bayan fitar gwaggo maida idonta tay tana Kallon sama ta shiga tunano komai daya faru a wurin dinner, tuno da lokacin da Haisam ya bi Wak'a yayi mata tay nan take ta fad'ad'a murmushi sosae taji dad'in hakan da yayi mata don ya nuna zai iya yin komai don son da yake mata, gwaggo ce ta dawo tare da nurse suka nufo gadon, sannu nurse d'in tayi mata tana murmushi Fatun ta d'aga mata kai, tambayar ta tayi ba abunda ke mata ciwo nan ma ta d'aga mata kai alamar eh, cire mata oxygen mask d'in tayi da drip d'in da aka saka mata bayan ta gama yi mata abunda zata yi mata ta k'ara mata sannu sannan ta tafi, bayan fitar ta Fatun ta fara k'ok'arin tashi zaune cike da kulawa gwaggo ke mata sannu, zuru k'afafunta tay gwaggo ta tambayi ina zata tace fitsari take ji ta mik'e ta taimaka mata, nad'e mata rigar tayi ta baya kafin ta kamata Fatun na murmushi tace mata zata iya, cewa tay bari dai ta taimaka mata, a bakin toilet d'in ta saketa ta bud'e mata kopar Fatun ta shiga gwaggo na fad'in tabi a hankali don Allah ta d'aga mata kai kafin ta maido kopar ta rufe, cikin d'akin gwaggo ta koma ta gyara mata gadon bayan ta gama ta nufi inda kayan da su Haisam suka kawo suke ta bud'e ledar, fiddo robobin take aways d'in da ke ciki tayi, bayan Fatuu ta fito tace mata tazo to ta ci Abinci ta d'aga mata kai don kuwa yunwa take ji, a saman kujera ta zauna gwaggo ta bud'e robobi biyu fried rice ce da naman kaza sai guda biyu kuma na sakwara ne gwanin sha'awa a ido da gani ta daku sosae, da murmushi ta tambayi to mi zata fara da shi ta nuna mata sakwara gwaggon tace dama tayi tunanin ita zata ce Fatun tay murmushi, bayan ta fara cin Abincin gwaggo ta mik'e tana fad'in bari a cire wannan d'aurin ko ta sha iska, bayan ta cire head d'in gado ta nufa ta d'aukko net d'in data yafa tazo ta d'aura mata akan Fatun nata murmushin jin dad'in yadda gwaggon ke ta bata kulawa, bayan ta zauna a gefen ta Fatun ta kalleta tace itama taci Abincin mana tace mata taci dai, tura baki Fatun tayi a shagwabe tace "Don Allah ki ci, in baki ci ba zan aje nima in daina ci" dariya gwaggo tay ta d'an girgiza kai tace mata wai sai yaushe ne zata girma ta daina shagwaba tafa girma yanzu, tana murmushi tace mata ba rana kuwa, gwaggo da har lokacin dariya take tace lallai kam za'a rinka abun kunya in ta haihu uwa na shagwa6a d'a na shagwa6a Fatuu dake dariya tace kyau kenan ai, daga baya gwaggon ta fara ci, sosae Fatuu taci Abincin don saida ta cinye sakwarar tass gwaggo tace ta k'ara ta d'ayar robar dama Saboda ita yasa bata ta6a ba ita ta d'auki shinkafa tana ci, ce mata tay bari taci shinkafar itama, sai gashi itama ta cinyeta ganin gwaggo na kallonta tana murmushi yasa tace "Gwaggo ko dai hada ciwon cin Abinci nike yi" yar dariya tay tace waya sani, mik'a mata robar sakwara d'in tay tace ta k'ara da sauri ta girgiza mata kai tace cikinta fashewa zai yi in ta k'ara, leda mai kyallin data gani a ciki ta fiddo ta fara warwarewa tana fad'in bari taga minene a ciki, bayan ta bud'e tsire ta gani yasha kayan had'i su tumatir da koran tattasai da albasa tun kafin ta fara ci ta hau had'iye miyau kallon gwaggo tayi tace wai ta ci tana dariya tace to dama ai don aci aka kawo ko, sosae yayi mata dad'i tace ma gwaggo su ci tace taci ta rage mata in ma duka zata cinye ta cinye da sauri tace a'a zata rage mata, sai ga wadda tace cikinta zai fashe sai faman cin tsire take tana zuba har da tambayar yadda aka kawo ta Asibiti gwaggon ta shiga bata labari don dad'i take ji ganin ta haka saidai bata fad'i mata ainihin abunda ya ja komai ba, tambayar gwaggon tay ina wayar ta tace mata ta barota gida bata ji dad'in hakan ba don tana son jin muryar mijin ta. Bayan su Haisam sun koma, wanka ya fara yi ya zura jallabiya Abbas ma ya shiga wankan, sallar Nafila yay ya kara godiya ga Allah da ni'imomin da yay mashi yayi ma Fatuu Addu'ar samun ingantacciyar lafiya harda Fanan ma yayi ma Addu'ar Allah ya k'ara bata lafiya, sosae yayi Addu'oi lokacin daya gama tuni Abbas ya kwanta Sameer yau ba anan zai kwana ba dama shi Abbas ranar da suka zo ne kawai ya kwana a wurin Salim yake kwana, bayan ya gama zaune yay yana ta tunanin ko zuwa yanzu Fatuu ta farka, sosae yake jin kewarta yana son jin muryar ta amman yasan ba waya a hannun ta daga baya ya mik'e yaje ya kwanta fuskar shi cike da annuri, ya d'auki lokaci idanun shi lumshe yana tunanin baby d'in shi a haka bacci yay awon gaba da shi.......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 *ASM 084* ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ *DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI* ............Washe gari bayan Haisam ya dawo daga sallar Asuba a main parlor ya tsaya ya kira Jidderh a waya, lokacin tana akan abun salla kiran ya shigo, mik'ewa tay ta nufi bakin gado ta zauna sannan ta d'aukko wayar, picking tay tun kafin tace wani abu taji yace ta same shi a parlor ta furta Ok, mik'ewa tay dama jikinta tana sanye da hijab ta nufi hanyar fita, yana zauna akan kujera one seater hannun shi ruk'e da waya ta iso wurin a kujerar kusa dashi ta zauna ya d'ago ya kalleta da fara'a ta gaishe da shi bayan ya amsa ta sake cewa "ya kwanan farin ciki" murmushi yayi ya amsa da Alhamdulillah, Addu'ar Allah ya bata lpy tayi bayan ya amsa yace mata so yake ta shiga Kitchen ta had'a mashi breakfast ba mai taking time sosae ba, tambayar shi tayi Asibitin zai kai ya d'aga mata kai, cike da zumud'i ta mik'e tana fad'in to yanzun nan zata had'a. Fauzy na gama sallar Asuba ta nufi d'akin su Aunty Mareeya lokacin data shiga a zaune kan abun salla ta iske ta da Saude Feenah na kwance kan gado don bata salla Abdul kuma dama tunda suka zo yana wurin su twins, da fara'a ta k'arasa cikin d'akin ta zauna daga gaban Aunty Mareeya, gaishe da Saude tay ta amsa tana murmushi ta maida idonta kan Aunty Mareeya dake bin ta da kallo, ganin tana ta faman zabga murmushi yasa tace ya zata zo tunda safe ta tasa su a gaba tana faman yi masu murmushi kamar wata zautatta, yar dariya Fauzy tay kafin tace Albishirinta da sauri tace goro harda su gyara zama shiru Fauzy tay Aunty Mareeyar duk ta k'agara ta ji miye har sai da ta kai hannu ta bugi shoulder d'inta tace dalla miye wai, fad'i masu abunda ya faru jiya ta shiga yi tana rufe baki Aunty Mareeya ta buga wata uwar shewa ta furta "Da kyau yar gidana Zarah, kwalliya ta biya kudin sabulu wllh wannan iya biyan bashi haka, kai Alhamdulillah Wllh naji dad'i nayi farincikin jin Maganar nan" Saude ma Alhamdulillah ta shiga fad'i, shewar da Aunty Mareeya tayi ce ta tashi Feenah ta bud'e ido, jin abubuwan da take fad'i yasa ta d'ago kai tana tambayar abunda ke faruwa cike da Farinciki Aunty Mareeya ta hau bata labari, jinjina kai Feenah ta hau yi fuskarta da faffad'an murmushi tace kai ma sha Allah abu yayi dad'i Allah ya bata lafiya ya inganta, amsawa sukai da Amin Aunty Mareeya tace ana ta shan Dinner d'in biki ashe Amarya da juna biyun ta mak'ale, labarin yadda likita ya kasa fad'a Fauzy ta shiga basu sukai ta dariya suna fad'in ai dole ya kasa fad'a don wannan ba K'aramin Al'amari bane. Bayan su Laila sun gama salla take ma Fanan Albishir don jiya ta riga tahowa kuma lokacin data dawo tayi bacci, waro ido Fanan tay ta kai hannu ta rufe bakinta alamar mamaki Laila nata Murmushi, cire hannun tayi cike da farinciki tace kenan duk abubuwan nan da ake Zarah is pregnant Laila tace wllh ai Allah ma ya taimaka da ba abunda ya same shi, mik'ewa Fanan tay da sauri ta nufi bakin gado ta kai hannu kan bedside ta d'auki wayarta, Haisam ta kira lokacin ya koma part d'in shi don ya shirya, yana tsaye a gaban dressing mirror kiran ya shigo ya juya ya kallo wayar dake saman bedside kafin ya nufeta, yana ganin mai kiran yay murmushi ya kai hannu yay picking, daga muryarta zaka fahimci tana cikin farinciki tace mashi ashe jiya abunda ya faru kenan bayan ta baro wurin yana ta murmushi yace mata eh, ce mashi tay shine ko ya kirata ya sanar da ita abun farincikin daya same su tama yi fushi dashi, yanayin yadda tay Maganar har saida yayi yar dariya, hak'uri ya bata yace tayi bacci ne yana son ta huta sosae tace to miyasa yanzu da aka tashi bai sanar mata ba ai kamata yay ace shine mutum na farko daya fara sanar mata, hak'uri ya k'ara bata yace mata yana niyyar yazo ne da kan shi sai yay mata Albishir yanzu haka yana gaban mirror yana mata Kwalliyar da zai zo yi mata Albishir d'in, yana jiyo sautin dariyar ta dama ya fad'i ne don ya faranta mata, ce mata yay gashi nan zuwa yi mata Albishir d'in a d'okan ce tace she's waiting for him, Bayan Jidderh ta gama komai ta had'a mashi a cikin basket part d'in taje ta sanar mashi ta gama yay mata godiya yace ta aje mashi a dining area tace to, har zata juya ya tsaidata, ce mata yay ta d'aukko ma Fatuu kayan da zata canza ta sa towel da brush d'inta sai ta aje mashi a wurin basket d'in tace to kafin ta tafi, bada jimawa ba ya fito yana sanye da k'ananun kaya bak'in jeans da dark blue t-shirt sumar nan ta sha gyara sai baza k'amshi yake, part d'in Laila ya wuce lokacin daya shiga ba kowa cikin parlon hakan yasa ya wuce Bedroom, knocking k'opar yay aka bashi izinin shigowa ya tura ya shiga da yar sallama, Duk suna kwance akan gado Laila tuni ta koma bacci sai Fanan ce idonta biyu ta kasa komawa baccin sai tunane tunane take, sosae taji farincikin samun cikin da Fatuu tay saidai ta wani bangaren zuciyarta ce ta k'ara sarewa ta shiga tunanin anya kuwa tana da rabon haihuwa a duniya ganin tana ta shan Magani kuma ana samun cigaba amman har yanzu ko 6ari bata yi ba tasan ma ko zata iya conceiving, a hankali take kai hannu tana share kwallan dake gangaro mata tana haka taji anyi knocking saida ta goge Fuskarta tass sannan ta bada izinin a shigo, tana ganin shi da sauri ta saukko daga gadon tana sanye da rigar bacci iya gwuiwa kanta ta saka hula gashin ta ya zubo ta gefe da gefe, nufo shi tay da sauri tun kafin ta k'araso ya bud'e mata hannuwan shi tana zuwa ta fad'a jikin shi ya maida hannuwan ya rungumeta sosae ta shiga fad'in she's happy for them bada jimawa ba zasu zama iyaye, murmushin jin dad'i ya shiga saki ya d'aura ha6ar shi a saman kanta tare da lumshe ido, daga lokacin data amince mashi ya cigaba da zama da Zarah ya gane irin son da yake mata, a yadda yake ji he can't live without her, jin tana k'ok'arin d'ago da fuskar ta yasa shi janye ha6ar tashi, d'agowa tay ta kalle shi suka shiga sakar ma juna k'ayataccen murmushi daka kalli fuskokin su zaka fahimci suna cikin farin ciki don cike suke da annuri, suna haka calmly taji ya furta mata "Thank you Sweetheart" d'an bud'a mashi ido tay tace akan me ya lumshe ido yace "For Everything" fad'awa tay jikin shi ta kwantar da kanta a chest d'in shi, yaci gaba da fad'in "har bansan ta yadda zan rink'a gode maki ba, nagode maki da kasance man mafi jin dad'in duniyar nan" wurin kunnanta ya kai bakin shi ya rad'a mata "al'mar'atussaliha" yana jin yadda ta k'ara shige mashi yana ta murmushi, d'ago kai tay ta kalle shi tace "komai daga wurin ka na koya babe, sadaukarwa halin ka ne, baka da buri sai na kaga kasa mutum farinciki hakan ne yasa kai ma kake kasancewa acikin farinciki koda yaushe, Babe duk yadda na kasance maka kai kaja hakan you're a selfless and just person, da maza zasu yi koyi da halin ka da sun zauna lafiya da matan su koda sunfi d'aya don hakan zai rink'a rage masu radadin kishi, amman da yawa su suke jefa matan su a mawuyacin hali k'arshe suzo suna kauce hanya wanda hakan bashi ne way out ba sai ma mutum ya halaka, Idan ba kayi cuta ba bazaka ga cuta ba all one needs to do shine hak'uri tunda Allah da kan shi yace yana tare da mai shi in mutum yayi sai yaci riba,ina rok'on Allah yasa in ci ribar hak'uri though nama fara cin ribar ga baby nan zamu samu" ta k'arasa tana murmushi, still yay yana kallonta wani irin tausayin ta ne ke ratsa shi, maida kanta yayi jikin shi yace in sha Allah zata samu lafiya itama ta Haifa mashi yara masu irin halinta, tana murmushi tace Allah ya amince amman in ya kaddaro mata bazata haihun ba ba komai tasan daga cikin hikimar sa ne ya kawo Zarah ta Haifa masu, murmushi kawai yake wani lokacin sai yay ta ganin kaman ba ita ba don da kuruciyarta bata da hak'uri ga kukan banza, sigh yay ya d'agota yace bari yaje, tambayar shi tay inda zashi ya fad'i mata da sauri tace to bari ta shirya sai su tafi tare, ba tare da ya sake ta ba gently yace mata yana son yaje da wuri ne Saboda grandma d'inta ta dawo gida jiya ta kwana ba shiri ko blanket babu yasan bata yi bacci cikin dad'i ba ta bari ta shirya a nutse sai suzo da Laila in ma ita bazata zo ba in ta shirya tay mashi magana zaisa a kawo mata makullin Mota sai ya bata address na Hospital d'in, kai ta jinjina mashi ya d'an sunkuyo yay pecking goshinta had'i da furta "I love u" farfar tay da ido ta furta mashi tana son shi da kowane bugu na zuciyar ta, yar dariya yay ya saketa tace in yaje yay kissing baby d'in su dariya Maganar ta bashi yace mata har ya zama baby kenan tace eh ai zai zama ne in sha Allah, bayan ya fito dining area ya nufa ya d'auki basket d'in da yar jakar kayan sannan ya tafi. Bakin gado ta koma cike da zumud'i ta d'auki wayarta ta fara k'ok'arin kiran Mom d'inta, saida kiran ya kusa katsewa sannan tayi picking, gaishe da ita Fanan tayi muryarta ciki ciki ta amsa, cike da Farinciki tace mata dama ta kira tayi mata Albishir Hajiya Maryam d'in tace mata miya faru ne, cikin washe baki ta hau bata labarin cikin da Zarah ta samu tana jiyo sautin d'an tsoki data buga kafin a hasale tace to shine zata tashe ta a bacci kaman dole kuma tasan a lokacin bacci take, hak'uri ta bata tace farinciki ne yayi mata yawa shiyasa ta kira don ta taya su murna, bata ce mata komai ba tay shiru can ta tambayi ina Noor ta bata amsa da tana a wurin su twins ta furta Ok, jin zata katse kiran yasa da sauri tace bata taya ta murna ba a dak'ile tace Allah yasa Alkhairi daga haka ta katse kiran sam Fanan bata ji komai ba, kiran Farha ta shiga yi bayan tayi ringing tay picking, gaishe da Fanan d'in tayi ta amsa ta tambayi ko bacci take ta bata amsa da No tana yin Assignment ne, ce mata tay ta tayata murna bride d'in su is pregnant Farhar tay d'an jimm sai kuma tace ta taya ta murna Fanan d'in tay mata godiya, tambayar ta tay yaushe zata dawo tace msta cikin week d'in da za'a shiga tay mata sai ta dawo daga haka sukai sallama. Gwaggo na zaune akan kujera tun bayan data gama salla ta koma saman ta tana tasbih jin k'asan sanyi yayi yawa Saboda Ac dake ta aiki tiles d'in duk ya d'auka, Fatuu na kwance saman gado ta koma bacci bayan tayi salla da hijab d'in gwaggo, bata dad'e zaunen ba akai knocking k'opar ta tashi zaune sosae tace a shigo, turo kopar akai Haisam ya shigo da sallama Nameer na biye da shi, da fara'a ta amsa sallamar suka shigo ciki, daga gefen gadon Nameer ya aje basket d'in da jakar kayan ya koma wurin gwaggo da ke cikin gaisawa da Haisam, da murmushi ya gaishe da ita ta amsa mashi tay mashi ya gajiyan hidima yace tabi jiki ai, shiru ta d'an biyo baya kafin cikin girmamawa Haisam yace mata ga Nameer nan zasu tafi tare, tana murmushi tace ai da basu wahalar da kansu sun fito da sassafen nan ba yace mata ba wani abu, k'ok'arin mik'ewa ta fara yi tana fad'i mashi game da farkawar Fatuu jiya da daddare yanata d'an murmushi, sallama suka yi Nameer ya juya ta bi bayan shi suka tafi, wurin gadon ya nufa ya tsaya yana kallon Fatuu dake ta bacci rabin jikinta lullube da farin bargo wani irin Fresh yaga tayi mashi, ya d'an d'auki lokaci a haka yanata kallonta da murmushi akan fuskar ta shi, matsawa yay ya zauna a bakin gadon ya kai hannu ya d'an janye bargon, hannunta guda ya kama yana ta kallonta can ya kai d'ayan hannun ya d'aura a saman cikinta wani irin farinciki yake ji, k'amshin turaren shi ne ya kai mata cikin baccin a hankali ta fara motsi da sauri ya janye hannun shi dake akan cikinta gudun kada ya tasheta kawai sai gani yay ta fara bud'e idanunta, tana gama bud'e su suka sauka cikin nashi yanata sakar mata k'ayataccen murmushi, k'ura mashi ido tay tamkar bata gane shi ba calmly ya furta ta tashi maimakon ta bashi amsa sai tace "Hubby kai ne?" yanayin yadda sautin Maganar ya fita muryar tata ta d'an dishe, lumshe mata ido yay nan take ta tabbatar da shi d'in ne da sauri ta juyar da kanta ta hango babu gwaggo cikin d'akin, maido kan tayi taci gaba da kallon shi a sanyaye ta gaishe shi, bai amsa ba sai ya matsa gaba ya sunkuyar da kanshi ya had'e fuskokin su, slowly ya furta "ni yakamata in gaida ki Baby, a huge thank you to u for the amazing gift" lumshe ido tay ba tare data ce komai ba, d'ago fuskar yay yana kallon ta a hankali ta bud'e idanun nata ta bi shi da kallon rashin fahimta, ganin irin kallon da yake mata ne yasa k'asa k'asa tace mashi wace kyautar ban mamaki ce ta bashi jin haka da yanayinta yasa ya fahimci grandma d'in ta bata sanar mata ba, maida Fuskar shi yay gefen tata ya rad'a mata "mun k'ara samun abunda muka rasa ne" waro ido Fatuu tay with mouth agape ya d'ago yana kallon ta da murmushi ya d'age mata gira aikuwa da sauri tasa duka hannuwanta ta rufe fuskar ta yay yar dariya, hannu ya kai ya janye hannuwan nata suka had'a ido ganin tana k'ok'arin juyar da fuskar yasa shi k'ara had'e fuskokin nasu taji yace "I don't even know how to thank you enough Baby" murmushin dad'i kawai take saki, d'agowa yay ganin tak'i sakin baki tay mashi magana sosae yace ko bata farinciki ne, da sauri ta girgiza mashi kai da hannu tay mashi nuni da bakinta nan take ya gane tana nufin bata wanke bakin ba kawai sai gani tay ya kai fuskar tashi ya had'e mouth d'in nasu wato tama gane bai k'yamar bakin nata, ya d'an d'auki lokaci kissing her deeply kafin ya d'ago da sauri ta juyar da fuskar ta tana dariya, hannu ya kai yana k'ok'arin d'aga ta zaune yace ta tashi taci Abinci, bayan sun Mik'e tace mashi zata je toilet yace Ok bari ya taimaka mata tana ta murmushi tace mashi zata iya nan ya sanar mata tana akan bed rest ne sai an bi a hankali ta jinjina mashi kai, zaunar da ita yay bakin gadon yace yana zuwa, jakar kayanta ya bud'e ya ciro towel da brush da toothpaste sannan ya dawo bayan ya mik'ar da ita yay mata d'aukar jarirai ya nufi hanyar toilet d'in suna ta sakar ma juna murmushi, bayan sun je toilet d'in taimaka mata yayi tay wanka har brush shi yayi mata tana ta dariya don abu ne wanda da wayon ta ba'a ta6a mata ba, kaman yadda ya d'auketa ya kai ta ciki haka yay mata ya fito da ita a gefen gado ya zaunar da ita, saida yaje ya kullo kopar d'akin ya dawo, shirya ta ya shiga yi harda mai cikin kayan ya shafa mata sannan ya fiddo kayan bayan ta saka undies, doguwar riga ce tasa da hula bayan sun gama ya kama hannunta suka nufi inda doguwar Leather sofa take ya zaunar da ita, d'aukko basket d'in yayi ya dawo wurin daga gefen ta ya zauna, warmer d'in ciki ya bud'e chips ne a ciki, d'aukar plate d'in cikin basket d'in yayi ya mik'e, wurin gado ya nufa ya d'auki bottle water ya nufi window don ya d'auraye shi Fatuu nata kallon shi, idon shi a cikin nata ya dawo suna ma juna murmushi, zuba mata Chips d'in yayi mai yawa ya bud'e ledar slice bread ya deb'o, d'aura plate d'in yay a saman kujerar ya shiga had'a mata tea mai k'auri, d'agowa yay tana ta kallon shi ya kai cup d'in bakinta ta fara sha, ganin yana ta bata yasa tace shi fa yace mata yayi safiya sosae ba yanzu zai ci ba ita dai da baby d'in su suci su k'oshi, mak'e mashi kafad'a tay ta tura baki tak'i amsar wanda yake bata a shagwabe tace in dai bai ci ba to itama ta k'oshi, d'an bud'a ido yay yana murmushi, hannu ta kai ta d'auki fork d'in itama ta d'ebo ta kai bakin shi dole ya bud'e ta ba shi, haka suka cigaba da ci a tare cikin salon kauna da k'yar ta yarda in aka bata sau ukku sai ta bashi da cewa tay bata yarda ba ayi sau d'add'aya dai yace mata to ai ita ba ita kadae bace akwae baby tana dariya tace ai bai fara cin Abinci ba ko, nuna mata yay ai sai tana cin Abincin zai girma ko tace to ita a bata sau biyu shi sau d'ayan yace ai yayi kad'an, da k'yar dai ta yarda da ukkun sai kace wata yar yarinya haka yake ta bi da ita, sosae taci ta k'oshi don saida ta cinye duka duk da dashi aka ci amman ba wani sosae ya ci ba, bayan sun gama ya kamata suka nufi toilet aka wanko baki da hannu duk da ba da hannun ma aka ci ba, akan kujera suka zauna suna kallon Tv ta kwantar da kanta a shoulder d'in shi, shima dai kallon ana yi ana shan love ake yin shi daga baya ta fara gyangyad'i har baccin ya d'auketa sosae, d'aukar ta yay ya kaita gado bayan ya kwantar da ita ta d'an bud'e idanunta ta kalle shi suka sakar ma juna murmushi, lullube mata rabin jikinta yayi ya sunkuyar da kan shi yay pecking goshinta ta furta mashi thanks, zama yay a bakin gadon yana ruk'e da hannunta guda yana d'an matsa mata shi tana ta murmushi a haka har ta koma baccin, mik'ewa yay ya koma kan Kujerar yaci gaba da yin kallon, ya d'auki lokaci a haka Yana yi yana kallo Fatuu dake ta shan bacci, wuraren k'arfe goma da wasu mintuna akai knocking d'akin sai lokacin ma ya tuna da kopar a rufe take ya mik'e don yaje ya bud'e lokacin Fatun ta bud'e idanunta sakamakon buga kopar da akai, Fanan ce ta shigo tana sanye da jallabiya coffee brown tay rolling veil d'in Laila na biye da ita itama tana sanye da jallabiya Navy blue ta d'aura gyalen saman kai, matsa masu yay suka shigo duk suna murmushi, Fatuu na ganin su ta fara k'ok'arin tashi zaune Fanan ta nufo ta da sauri, zama tay a bakin gadon tana washe baki ta kamo hannunta guda, gaidata Fatun tayi bayan ta amsa tace "we're really happy about this pregnancy Zarah" murmushi kawai Fatun ke yi mata ita kam sai washe baki take, Laila ce ta k'araso bakin gadon tana kallon Fatun da murmushi, gaishe da ita Fatuu tay ta amsa tay mata ya jiki tace taji sauki, Fanan ce ta tambayeta taci Abinci ta d'aga mata kai, kallo Haisam daya koma kan kujera tay tace mashi ya dai tabbatar taci ta k'oshi ko yana murmushi ya lumshe mata ido tace Yauwa to don kar abar masu baby da yunwa gaba d'aya Laila da Fatuu sukai dariya, komawa wurin Haisam Laila tay ita kuma Fanan ta shiga yi ma Fatuu tambayoyi da suka shafi cikin daga baya kuma ta koma yin hirar Babyn da za'a Haifa masu duk su Haisam na jinta sai dariya take ba su har Laila na cewa da alama tafi kowa murna da cikin tace mata abunda take ta fatan su samu kenan. A nan Haisam ya barsu Ya dawo gida, Wurin k'arfe sha biyu su Hajiya Zainab sun gama shirin tafiya, zasu biya Asibiti su gaishe da Fatuu daga can zasu wuce, bayan ta fito tare da Mom da su Aunty da wasu mutane Security detail d'inta na biye da ita, Jidderh na a part d'in da su Fauzy suke suna zaune a parlor harda su Aunty Mareeya suna firar Dinner d'in jiya da kuma tashin hankalin da suka shiga lokacin da suka ji Fatuu ta fad'i, Yasmeen ce ta shigo da gudu ta nufe su tana d'an haki idon ta akan Jidderh tace mata ga Momy d'in Nasarawa can zasu tafi, zumbur Jidderh ta Mik'e ta ce ma su Fauzy suzo suje duk suka mik'e harda su Aunty Mareeya tana fad'in bari suma suyi mata bankwana don mace ce mai mutunci wllh, suna akan hanyar zuwa Aunty Mareeya ke ce ma Feenah in ka ga Sameer sai kace ba itace ta haife shi ba ta 6angaren hali Feenah na murmushi tace shima k'ilan in aka zauna dashi aga Mutuncin shi Aunty Mareeya tace amman dai da gani ba sai an fad'a ba yana da girman kai ba kamar Mahaifiyar tashi ba, gaba d'aya an fito waje bakin Entry Hall inda Motocin su suke a fake, tun bayan da Fauzy ta fito take ta wurga ido wai ko zata ga Sameer amman bata gan shi ba sai dai K'annan shi, tunanin ko yana a cikin Mota tay tabi Motocin da kallo saidai bazata iya ganewa ko yana ciki ba, Sallama Her Excellency tay da kowa ta nufi Mota da sauri aka bud'e mata bayan duk sun shishshiga ta d'aga ma mutane hannu kafin aka rufe kopar, a jere Motocin suka tashi ana ta d'aga masu hannu suka tafi jiniya na tashi, juyawa sukai suka koma cikin gidan, hakanan Fauzy take jin ta wani iri sai ganin fuskar Sameer take, a ranta ta raya k'ilan Shikenan bazata k'ara ganin shi ba har saida taji jikinta yayi sanyi yin tunanin, can kuma wata zuciyar ta raya mata k'ilan kuma sai ko bikin Mino da Nameer in Allah ya k'addara zasu auri juna, sukuku da ita ta koma part d'in su, koda ta shiga d'akin su ta nufa ba kowa a ciki ta nufi gado ta kwanta ta shiga tunano abubuwan da suka faru a tsakanin su wani lokacin tay murmushi wani lokacin kuma ta yamutsa fuska can zuciyarta ta raya mata wai ko dai son shi take shiyasa take ta tunanin shi haka da sauri ta hau girgiza kai saima ta yunkura ta mik'e ta nufi Parlor. Wuraren sallar Azahar aka fara zaryar zuwa Asibiti ganin Fatuu, Yadikko tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, har su Baffan Fatun da Ard'o sai da suka zo gaba d'aya Asibitin saida aka shaida an kwantar da dangin masu Mota don Motoci ne iri iri ke ta sintiri cikin Asibitin, da la'asar Mom da Hajiya da Aunty da gwaggo suka zo, bayan sun shiga d'akin sun duba Fatun Hajiya tace ma Aunty ta duba ta in dai ba wata matsala gwara a sallameta su koma gida don anata faman zaryar zuwa in suka koma sai taci gaba da yin bed rest d'in a gida tace to, tambayoyi tayi ma Fatun daga baya ta fita ta nufi Office d'in Doctor, bayan sun gaisa tay mashi bayanin suna so ai discharging Fatuu tunda ba wata matsala a tattare da ita, bai da yadda zai yi dole yayi masu yadda suke so don ya gane Auntyn likita ce. Bayan sallar Magrib aka sallame ta suka dawo gida, d'akin Mom aka kaita nan fa akai ta zuwa gaishe ta ita dai sai faman murmushi take bayan an tsagaita da shigowa Mom ta tambayeta abunda take son ci tana murmushi tace mata komai aka bata zata ci itama da murmushi akan fuskar ta tace in akwae wani abu da take jin tana so ta fad'i tace mata ba komae, mik'ewa tay ta fita bada jimawa ba sai gata ta dawo ruk'e da plate mai d'an girma Fruit ne aka yayyanko wanda suke da amfani ga mai ciki ta kai mata tace ta fara shan su tay mata godiya, ganin tana k'ok'arin saukkowa daga saman gadon yasa ta tambayi zatai wani abu ne tace eh hannu zata wanko cike da kulawa tace Ok amman tabi a hankali tace to, tsaye tay har saida ta shiga ta wanko hannun ta fito bayan ta koma ta zauna sannan ta tafi, bada jimawa sosae ba sai gata ta k'ara dawowa hannunta ruk'e da babban tray, a saman Carpet ta aje tace ma Fatun ta zo ta zauna nan yadda zata ji dad'i sai ta ci tace to, bayan ta zauna da kanta ta bud'e mata plates d'in da aka rufo da wasu, d'aya tuwon semovita ne mulmule ukku sai miyar Alaiyahu data ji yan ciki a cikin bowl sai d'ayan plate d'in mai d'an zurfi farfesun kaza ne sai zabga uban k'amshi yake a ido kawai sai ya burge mutum daga gefe lemu da ruwa ne harda cup, tana murmushi tace mata ta ci ta k'oshi ta d'aga mata kai ta juya ta nufi hanyar fita daga d'akin, tun bata saki jiki ba har dai ta saki ta shiga kwasar Abincin wasa wasa sai gashi ta cinye mulmule biyu sannan ta koma kan farfesun, Ita kanta har mamakin kanta take yanzu lokacin da ba'a san da cikin ba kwata kwata bata cin Abinci sosae yadda ta saba take ci amman yanzu sosae cin Abincin ya k'aru, shima farfesun sosae ta ci shi don ba K'aramin dad'i yayi mata ba amman ta rage, bayan ta gama ta rufe komai ta d'auki tray d'in don ta fitar, a daidai bakin k'opa suka had'e da Haisam da dawowar shi kenan daga Masallaci, hannu ya kai ya amshi tray d'in yace mata wa yasa ta d'aukko ta langa6ar mashi da kai, ruk'e tray d'in yayi da hannu guda yasa d'ayan ya bubbud'e ganin bata cinye ba yasa shi kallon ta tana ganin haka ta tura mashi baki a shagwabe tace wllh ta k'oshi sosae ta ci, d'an d'aure fuska yay yace su koma ta ida cinyewa ta yamutsa fuska kamar zatai kuka tana fad'in Allah cikinta fashewa zai yi, suna Haka Mom ta sawo kai cikin d'akin har saida Fatuu ta ji kunya da sauri ta juyar da kai, tsayawa tay gefe da murmushi ta tambayi ya akai yace mata bata cinye ba, kallon Fatuu tay tace "Daughter ya akai baki cinye ba?" Juyowa tay a kunyace tace mata Allah ta k'oshi taci sosae, hannu Mom ta mik'a ta amshi tray d'in ta duba, jinjina kai tay tace ba laifi ta ci sosae ta juya ta fita da shi, had'a ido sukai tayi mashi wani kallo ya kai hannu ya jawo ta jikinshi ta saka dariya, ganin abun na neman yin yawa ta fara k'ok'arin k'wacewa tana fad'in kada Mom ta shigo don Allah, kawai sai gani tay ya d'auketa gaba d'aya ya nufi gado da ita gaban ta sai fad'uwa yake, a saman gadon ya d'aurata shi kuma ya zauna a baki yana murmushi yace hira yazo taya ta. Bayan Nameer ya shigo gidan daga Masallaci direct d'akin Hajiya ya wuce lokacin daya shiga parlon su gwaggo na zaune bata dad'e da gama yin salla ba suka zauna suna kallo ita da wasu yan uwan su da suke a part d'in Hajiyar, tsayawa yayi suka gaisa kafin ya wuce Bedroom, da sallama ya shiga ya hangota zaune akan prayer mat ta jingina da gado, wurinta ya nufa yana zuwa shima ya zauna a k'asa kan Carpet kusa da ita tana ta kallon shi fuskar ta a sake, ganin yayi shiru yasa ta ce mashi ya akai, gaishe da ita yay ta amsa, jimm yay sai d'an murmushi yake yama rasa ta ina zai fara, sake tambayar shi tay wai lafiya yazo ya tasata a gaba sai wani murmushi yake kaman wani zautacce, ce mata yay dama zuwa gaishe da ita yay ta d'an harare shi ya d'age gira yace ko bata so, d'an ta6e baki tay tace to ta gode sai kuma mi, saida ya d'an sosa k'eyar shi sannan ya fara Magana da yar in ina yace mata dama ya samu wacce yake so ne a wurin bikin nan kuma har sun daidaita ma to shine yake son don Allah tay ma Dad magana sai ayi magana da parents d'in ta, zuru tay tana kallon shi har ya gama tay d'an murmushi tace wacece ya ke son, fad'i mata yay k'anwar bride d'in Ya Haisam da d'an alamun mamaki tace wacce k'anwar tata yace mata Mino, d'an wara ido tay tace "Kai yaushe har kasan Ameenatun da zaka ce kana son ta kuma kun daidaita?" Fad'i mata yay anan bayan sun zo, shiru tay ta d'an jinjina kai idonta akan carpet shi kuma yanata kallonta yana jiran ya ji mi zata ce, maido idon tay kan shi tace Yanzu in aka yi magana da iyayen nata aurenta zai yi da sauri ya d'aga mata kai, d'an shiru ta k'ara yi sai kuma tace "ni da nayi tunanin kai ma yar gida za'a yi kai da yar'uwar matar yayan taka Farha" wata yar zabura yay ya bita da wani kallo na baka tsammaci jin abu ba, tana murmushi tace mashi eh ba sai a k'ara yin yar gida ba a k'ara dankon zumunci, da sauri ya girgiza mata kai yace "ni gaskiya bazan iya auren ta ba yarinyar da bata girmama mutane ko gaishe ni fa bata iya yi in ma na samu tayi man kallon arziki, d'auka na take wani tsaranta taya zamu yi aure haka, kuma ma dai ai saida soyayya ake aure ko to ni gaskiya ban mata irin wannan son" ya k'arasa Maganar ya d'an 6ata fuska, kallo kawai Hajiya ta bi shi dashi sai k'ara 6ata rai yake, jimm tay can ta tambaye shi ita Minon ya tabbatar suna son juna ba sai anyi magana ba kuma azo kuma daga baya wani cikin su ya canza ra'ayi da sauri yace mata wllh duk suna son juna sosae sun ma yima juna alk'awarin kan haka, harara Hajiya ta wurga mashi ya sunnar da kai yana dariya, ajiyar zuciya ta sauke tace Shikenan zata yi ma Baban nashi magana tana rufe baki ya matsa ya rungumeta yana fad'in shiyasa yake son ta, ture shi ta fara yi tana fad'in ba wani dad'in bakin da zai yi mata ina wani so yake yana k'ok'arin yi mata kishiya, sakin ta yay yana dariya har zai mik'e sai kuma ya dakata yace mata don Allah koda Dad zai k'i tay convincing nashi wllh yarinyar bata da matsala in ya aureta ya dace mata, hannu tasa ta ruk'e ha6a alamar mamaki ya mik'e yana dariya ya nufi k'opa yana fad'in Allah yasa yaji Alkhairi, bayan ya fita Hajiya ta d'an girgiza kai. Wuraren k'arfe goma da yan mintuna Senator ya dawo gidan yana sanye da babbar riga da yan ciki na brown shadda kan shi sanye da hula mahad'in kayan haka agogon shi da takalman shi da alama Haisam gadon yin to match yay, ta main parlor ya shigo bai bi ta k'opar da ke kai shi part d'in shi ba kamar yadda yake yi in ya dawo da daddare, hannuwan shi ruk'e da fararen ledoji nasu d'auke da tambari a jiki ya nufi part d'in Mom, Fatuu zaune a saman gado har tayi wanka ta saka doguwar rigar bacci kanta sanye da hula su twins da Abdul da Noor zagaye da ita gaba d'aya idanun su na akan tv d'in cikin d'akin suna kallon cartoon da akai ma Fatuu dole take kallo, da Sallama ya shigo duk suka kai idanun su kan shi aikuwa da sauri su twins suka sauka daga kan gadon suka nufe shi da gudu suna fad'in "Oyoyo Daddy" bud'a masu hannuwa yay suna zuwa a tare suka fad'a ya rungume su yana dariya, d'ago kai yay ya kalli su Abdul da suma suka saukko daga kan gadon daga d'an gaban su suka tsaya suna kallon su da murmushi, ce masu yay su bazasu yi welcoming d'in shi ba Noor ta ruga itama ya rungume ta ganin haka yasa Abdul ma yaje shima aka had'a dashi aka rungume, sakin su yay yana fad'in to su shiga ciki Mubeen da Mubeena suka kai hannu suna fad'in ya kawo su ruk'e ya sakar masu leda guda d'aya yace to su je su kai ma Yayar su ta saman gado, da gudu suka juya suna zuwa suka mik'a mata ta amsa tana murmushi, nufo ciki yay ya tsaya daga gaban gadon Fatuu ta gaishe da shi Fuska a sake ya amsa yay mata ya karfin jikin tace Alhamdulillah, tambayar ta yay taci Abinci ta ce mashi eh yace sosae tana murmushi ta k'ara cewa eh, "To ga Fura nan sai ki k'ara" kai ta jinjina a hankali tace ta gode, su twins ne suka dawo gaban shi Mubeena ta kai hannu tana k'ok'arin amsar leda guda tana fad'in suma a basu fura d'in, janye ledojin yay ya 6oye su a bayan shi yana fad'in babu na su, wani kallo Mubeen yay mashi ya turo baki yace to wannan duk na waye yace mashi d'aya na Hajiyar shi ne d'aya kuma shi zai sha, a shagwabe Mubeena tace to ya basu nashi furan, wani kallo yay masu mai kaman harara yace to shifa, har suna had'a baki wurin fad'in sai yayi hak'uri, girgiza kai yay ya d'an tura baki irin yadda suke yace "ni bazan hak'uri ba gaskiya ai don in sha na siyo ko, wai yama akai baku yi bacci ba?" dariya yadda yayi ya basu Mubeena tace rabon zasu sha furan ne yasa basu yi bacci ba yace to kuwa bazasu sha ta ba, k'ok'arin kamo ledar suka fara yi ta bayan shi yana kaucewa can ya d'age su sama yace in suka kama to zai basu, tsalle suka fara yi harda Noor da Abdul Fatuu sai dariya take sosae abunda suke ya saka ta nishad'i, ganin sun kasa kamowa don Dad d'in nasu ba gajere bane tur6une fuska su twins sukai suka hau yi mashi magiyar ya basu, suna haka Mom ta fito daga toilet tana sanye da bathrobe kanta ta nad'o towel, nufo su tay fuskarta da murmushi ta tsaya gefe, sannu da zuwa tay mashi ya amsa ta kalli su twins ta tambayi ya akai, kafin su bashi amsa Dad d'in yace fashi suke son yi mashi na furar shi kuma bada su ya siyo ba, yar dariya tayi tace a taimaka a basu tun da sun gani suka had'a baki suna rok'on shi ya basu, kwa6e fuska yay alamar zai yi kuka yana fad'in bazasu tausaya mashi ba su bar mashi furar shi, Noor da Abdul ne suka ce sun bar mashi ya sha su twins kuwa girgiza kai sukai suna bubbuga k'afa, mik'a masu leda guda yay suka saki k'arar murna Mom tace to suje Parlor su sha suka nufi hanyar fita daga d'akin suna fad'in "Thank you Daddy, We love you" yana dariya yace tunda sun raba shi da abun shi ba, wucewa Mom tay wurin mirror tana yar dariya ya kalli Fatuu ganin ta aje ledar yace ta sha yanzu Saboda ta bi jikinta cikin girmamawa tace to ta kai hannu ta fiddo robar furar ta fara bud'ewa, tambayar ta yay ko a kawo mata cup da sauri tace a'a zata sha a robar, jinjina kai yay sai kuma yace ta saki jiki duk abunda take so tayi magana sannan kada ta cika yin zirga zirga zuwa ta samu lpy sosae a hankali tace to, kai idon shi yay kan Mom dake yin shafa ta cire towel d'in kanta tana taje sumarta Tubarkallah gashin har k'ugunta gashi bak'i wuluk, maido idon shi yay kan Fatuu yayi mata sai da Safe ta amsa ya juya ya nufi hanyar fita idon ta akan shi tana murmushi. Bayan ya fito part d'in Hajiya ya nufa don kai mata Furar ta, dama in dai tana Abuja duk dare sai ya siyo mata in yana nan in kuma bai garin sai ya sa a siyo mata, a parlor ya isketa ya gaisa da Mutanen ciki kafin suka gaisa da Hajiyar ya bata ledar, mik'ewa tay tace mashi tana son magana da shi suka nufi Bedroom, bayan sun shiga a bakin gado ta zauna shi kuma ya zauna akan carpet tana ya zauna a bakin gadon shima mana yace lafiya lou nan ma, zancen da Nameer yazo mata da shi tay mashi, farko d'an jimm yay kafin ya kalleta yace to ya take gani tunda tasan yarinyar, ce mashi tay gaskiya ita a saninta bata da wata matsala ya sake cewa to tana ganin lafiya lau a barshi ya auretan tana murmushi tace tunda yace yana so kawai ai mashi fatan Alkhairi, jinjina kai yay yace to Allah ya tabbatar da Alkhairi ta amsa da Amin, shiru suka d'an yi kafin tace mashi Kakar ita Fateema d'in ta fad'i mata gobe zasu tafi don haka sai ayi masu magana da wuri yace in sha Allah, yar hira suka d'an ta6a daga baya ya mik'e sukai sallama ya tafi. Bayan ya koma part d'in shi toilet ya nufa don yayi wanka, after some minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe ya hau shiryawa cikin kayan bacci riga da wando, bayan ya gama parlon shi ya fito ya zauna ya kai hannu kan table d'in dake a gefen kujerar ya d'aukko jarida ya fara dubawa, bai dad'e da zama ba Mom ta shigo itama ta shirya cikin kayan bacci masu santsi bak'ak'e da layi layin ratsin fari kanta ta yafo d'an k'aramin farin gyale sosae tay kyau farinta ya fito, nufo cikin parlon tay hannuwanta ruk'e da d'an babban tray d'auke da kayan abinci, matsar da c-table tay gaban shi sannan ta d'aura tray din, kallon shi tay suka sakar ma juna murmushi, serving nashi Abincin wanda irin tuwon data kai ma Fatuu ne ta shiga yi, bayan ta gama a kujerar gefen shi ta zauna suna d'an ta6a hira tana kallo, bayan ya gama ta d'auke kayan ta fitar da su, Dawowa tay d'auke da had'addan flask milk anyi mashi adon golden kai kace da gold akai adon harda cups d'in shi tray d'in ma duk mahad'in shi ne a saman c-table ta d'aura, bud'e Flask d'in tayi ta tsiyaya mashi ruwan shayin da ya sha kayan k'amshi da Zuma dama duk dare wadda take da kwana sai ta had'o mashi shi yau ita ke da kwana don bak'in shi wasu sun tafi d'azun da rana Saboda gobe Monday akwae aiki wasu kuma ba anan zasu kwana ba Mutum biyu yan Daura da Suka rage suna a part d'in da aka sauke su Ard'o, fuskar ta da murmushi ta mik'a mashi dama tunda ta shigo idon shi na akanta, k'ayataccen murmushi ya sakar mata ya furta "Shukran laki Ya Uwargida sarautar mata" dariya tay ta koma kujerar dake gefen shin ta zauna ta kai idon ta kan Tv shi kuma yana ci gaba da kurbar shayin nashi, jefi jefi suke yin magana a haka har ya shanye ta tambayi a k'ara mashi ya d'an d'aga mata hannu "tukunna bari inason zamu yi magana ne" kai ta jinjina ta maido hankalin ta gaba d'aya kan shi, d'an gyaran murya yay a nutse ya fara mata Maganar da sukai da Hajiya ta Nameer, shiru tay tana saurarar shi har ya gama a hankali ta maida idonta ta koma kallon Carpet d'in k'asa yanayin fuskar ta ya d'an canza, idon Senator na kanta ganin yadda tay yasa shi tambayar ko da matsala, maido kallonta tay kan shi ta fara magana "Nameer d'iyar Yaya Othman na Qatar nike son ya Aura Jahad, har nayi mashi Maganar kwanaki kuma ya nuna ma ya amince yanzu kuma ya zai zo da wannan Maganar?" sigh Senator yay ya jinjina kai kafin a nutse ya shiga kwatanta mata k'ilan dama kawai don kar yayi jayayya da ita ne yasa ya nuna mata ya amince ko kuma da gaske ya amincen yanzu kuma ya ga wannan yaji ita yake so, to shi abunda yake gani zai fi kyau ai mashi yadda yake so tunda can ba'a riga an tsaida magana ba, nuna mata yay yaran zamani yanzu ba'a cewa za'ai masu dole a 6angaren aure sun auri wadda suke so ma wasu ya aka kare bare kuma wadda basa so, shiru kawai tay still da yanayin canzawar fuskar ta, "Ina son ki kwantar da hankalin ki nasan a koda yaushe kina masu Addu'ar mafi Alkhairi a rayuwar su don haka ki d'auka wannan d'in itace tafi Alkhairin a gare shi tunda Addu'ar mu karbabba ce a gare su, abunda ake mawa dama shine a samu asali mai kyau da kuma kyan hali Hajiya duk ta tabbatar man da wannan game da ita yarinyar hakan ne ma yasa ai tun farko ta goya ma shi Babban yayan nasu baya, kuma kinga yanzu in akace a hana shi zai ga anyi mashi ba daidai ba tunda shi yayan nashi an amince mashi, ba abunda zamu yi ma Allah sai godiya akan komai na rayuwar mu, Allah ya Albarkace mu da yara shiryayyu duk da yadda zamani ya canza ya cika da ababen rud'u amman hakan bai sa sun kauce hanya ba sam ni'imar da Allah yay masu bata sasu shagala ba a koda yaushe k'ok'arin su suyi abunda zai k'ara mana mutunci da k'ima suke suna mana biyayya bakin gwargwado ni ina ganin duk da mu muka haife su muna da cikakken iko dasu yakamata mu rink'a nuna godiyar mu a gare su ta hanyar faranta masu kamar yadda suke faranta mana sa6anin iyaye da dama ya'yan su sune silar bakin cikin su, wasu suna fama da cututtuka duk silar yaran su kullum Addu'ar su Allah ya shirya masu zuriar su don jarabawar yara babban jarabawa ce Saboda duk yadda hannun ka zai ru6e baka yanke shi ka yadda koda kuwa ka yanken to kuwa ba hutawa kai ba, don haka ni ina ganin mu k'ara gode ma Allah da ni'imar da yayi mana sannan duk abunda ya kawo mana matuk'ar abun nan baida illa to mu kar6e shi hannu biyu muyi mashi godiya don shi yasan sirrin dake tattare da komai sau da yawa abunda muke k'i sai kiga Alkhairi ne a gare mu" yar ajiyar zuciya ta sauke yanayin fuskar ta ya canza dama ita bawai Minon ce bata mata ba kawai tana son k'ara had'a dankon zumunci ne amman koda Nameer d'in ya nuna bai so bazata matsa mashi ba don ita mace ce mai matuk'ar son iyalinta bata da burin daya wuce ta faranta ma ya'yan nata da mijinta, d'an murmushi tay idonta akan shi tace Shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairi, faffad'an murmushi Senator yay ya furta "Ameen My Queen" wani kallon love ta sakar mashi ya wani lumshe ido ta saki dariya, shima dariyar yay can yace "ai tunda ma yaran ba k'arewa sukai ba in sha Allah za'a had'a Auren zumuncin, yanzu kinga ga Affan nan ya tasa nan da yan shekaru zaki ga shima ya isa Aure ga Mubeen nan shima, ko bama mazan ba ai kinga ga mata nan Yasmeen da Mubeena tunda shima Yaya Othman d'in yana da Maza sai kiga an had'a, koma ba'ai dasu ba akwae wad'anda za'a k'ara haifa ai" ya k'arasa Maganar yana sakin murmushi idon shi a kanta, wani kallo tay mashi tace waye zai k'ara haifo yara ya d'age gira yace ita mana tunda tasan Aunty ba haihuwa take ba, "ni kam dai na gama, yara takwas fa ai nayi k'ok'ari kai ma ai nasan wasa kake" Mom da ta d'an ta6e baki tace, tsuke fuska yay ya k'ank'ance ido yace wai taga wasa a idon shi har saida tay yar dariya, ce mata yay yara takwas sun mashi kad'an in son samu ne ishirin yake so to amman tunda ita kad'ai ce zai hak'ura da guda 12 yanzu sauran ta hud'u in kuma Allah yasa an k'ara samun twins Shikenan zai iya hak'ura da goma, da yanayin mamaki tace "pls are you serious?" Kai ya jinjina mata yana mata wani kallo yace yana son yaga yara yan dugui dugui a gidan, yamutsa fuska tay tace in dai wannan ne ai ga Daughter nan zata Haifa in Nameer ma yayi auren shima zasu Haifa, wani kallo yay mata mai kaman harara yace to wannan nasu ne kuma a gidan zasu cigaba da zauna ne abunda kowa kama gaban shi zai yi shi nasu yake so wanda koda yaushe zai rink'a ganin su, sosae ta kwa6e fuska tace hakan bazai yuwu ba taya yara na haihuwa itama zata wani haihu katseta yay yace ai yanzu hakan fashion ne shi ake yayi kana haihuwa yayan ka nayi ai duk Aure gare su ko, yamutsa fuska ta shiga yi a shagwabe take fad'in ita gaskiya wannan abun kunya ne wllh sai dariya yake mata can ya d'aga mata hannu yace Ok Shikenan tunda bata so ai duk ba abun daga hankali bane zai samo wata yar chick ya auro sai tazo taci gaba da haihuwar ita ta huta kawai, ai tun kafin ya rufe baki ta d'auki pillow d'in kujera ta jefa mashi ya ca6e shi yana dariya ita kuwa sai k'una k'uni take tana Allah ya gama k'aro wata a cikin gidan ta dai yi hak'uri ya auro Aunty to Shikenan an gama, d'age mata gira yay yace "to zaki k'ara haihuwa ko kuwa in nemo....." Kafin ya k'arasa ta taso da sauri ta zauna saman jikin shi ta toshe mashi baki sai 6a66aka dariya yake ni kam dai na yak'e baki abun ya ban nishad'i ashe ashe dai ko an manyanta ana buga love, ni wllh ma Senator kazo ina da k'anne don Allah ka za6i d'aya in ma basu yi maka ba akwai yar bahillot itama a kasuwa take abun ai duk namu ne🤓 cire hannun tayi har lokacin sai yamutsa fuska take shi kuma sai dariya yake, ce mashi tay don Allah yaran su sun isa haka tun kan ta rufe baki ya hau girgiza mata kai yana mata wani kallo yace "indai irin yaran da kike Haifa man ne basu ishe ni ba ina buk'atar K'ari" Murmushin jin dad'i tay ba tace komai ba ya d'age gira yace za'a k'ara Haifa mashi ko, d'an rolling eyes d'in ta tay tace Shikenan amman saidai tun daga rainon cikin har zuwa haife shi ba'a K'asar nan zata yi ba da sauri yace in hakan yayi mata ai ba matsala bane duk inda take so sai akaita kuma zai bi ta, dariya tay ta girgiza kai, tambayar shi tay ta k'ara mashi shayin ya d'aga mata kai, tashi tay daga saman jikin shi ta k'ara mashi, bayan ya shanye ta k'ara tambayar a k'ara yace a'a ya isa, mik'ewa tay zata dauke flask din yana kallon ta yace ta bari sai da Safe mana ta fitar da shi, mik'ewa tay tana d'auke da tray d'in tace mashi tana son taje ta tambayi Daughter ko akwae abunda take so kafin tay bacci ya jinjina kai ta juya, bin ta yay da kallo tana tunkarar hanyar fitan a kullum gani yake ta na k'ara mashi yarinta a maimakon manyanta, in yace ga wani nakasu nata daya sa shi k'ara Aure to yayi k'arya kawai dai yasan duk abunda Allah ya k'addaro ma bawan shi to tabbas sai ya faru da shi amman yana matuk'ar k'aunar matar shi a yanzu kam sam baida ma ra'ayin k'ara aure, su yar Munah da bahillot sai a fidda rai🤧 Misalin k'arfe goma sha d'aya da wasu mintuna su Fauzy na zaune a parlor suna kallo ita da Mino da Zainab Haulat dai tunda ta tafi kwantar da babynta bata dawo ba da alama tayi bacci, harda su Aunty Mareeya da su Yadikko ake ta kallon Film d'in, Fauzy na zaune jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta soke d'aurin kallabi ta yadda gashinta ya fito ta k'asa, wayarta ce dake a gefenta ta fara ringing ta kai idon ta, d'aukko wayarta tay ta zuba ma kwankwatsattsen glass d'in ido tana kallon bak'uwar lambar da ake kiran nata da ita, kaman bazata d'aga ba sai kuma tay picking, karata tay a kunne ba tare data ce komai ba tana jiran taji mi za'a je, jin shirun yayi yawa yasa tay sallama, "Meet me in the parking lot" shine taji an fad'a da yar kakkausar murya daga haka kuma akai cutting kiran, cire wayar tay daga kunnanta ta bita da ido, tunanin waye wannan da yace ta iske shi a wurin ajiye motoci ta shiga yi, tunanin muryar waye ta fara yi can zuciyarta ta raya mata ta Sameer ce har saida gabanta yay wani bugu, kokonto ta shiga na anya kuwa shida sun tafi kuma in ma shine ta ina ya samu lambarta, zuciyar ta ce ta raya mata taje ba sai ta ga koma waye ba, mik'ewa tay ba wanda hankalin shi ya kawo kanta duk idanunsu na akan Tv, d'aki ta nufa ta d'aukko gyale ta yafa sannan ta fito tana ruk'e da wayar, tana a kan hanyar zuwa aka k'ara kira da lambar, tana d'agawa taji ance "Don't waste my time!" tana jin hakan ta tabbatar da Sameer, sauri ta shiga yi gabanta na d'an fad'uwa sai fargabar dalilin kiran nata take, lokacin data k'araso tsaye tay tana kallon cikin parking space d'in wanda yake dankam da motoci rasa a ina yake tay sai faman waige waige take, horn d'in da taji anyi ne yaja hankalinta da sauri ta kai idon kan Motar da taga ta saki danja wadda ke a d'an gabanta daga wajen parking space d'in, nufar Motar tayi a d'arare ta zagaya d'ayan 6angaren, tsaye tay a bakin kopar ta sake ji anyi horn hakan yasa ta kai hannu har rawa yake ta bud'e k'opar, wani irin k'amshi ne ya bugi hancinta ta d'an lek'a kanta yana zaune a driver seat jikinshi sanye da k'ananun kaya, murya na rawa ta gaishe dashi yay shiru tamkar bai ji ta ba kuma bai kalle ta ba, saida ya mula sannan taji yace ta shigo, a tsorace ta shiga ta zauna a kujerar gaban ba tare data rufe kopar ba hannun ta guda na ruk'e da ita, juyowa yay ya kalli kopar kafin ya kalleta ya d'aure fuska tamau nan take ta gane mi hakan ke nufi ta rufo k'opar, k'ara gaida shi tay yay d'an Jim sai kuma taga ya jinjina mata kai, shiru sukai sai Ac dake ta aiki tana bugun fuskarta, a k'alla sun d'auki wasu mintuna a haka ba tare da yace mata komai ba sai latsa waya yake tana ta d'an satar kallon shi saidai sam bata ji ta gaji da zaman ba, tana satar kallon nashi ta lura da wayar hannun shi kamar ba wadda ta fashe ba don wannan ta hango glass d'in ta lafiya lau, sai can sannan yay mata nuni da wani abu dake a gefen shi da Hannun shi taji yace ta d'auka cikin d'aurewar kai ta kai hannu ta d'aukko abun wadda yar jakar kwali ce k'arama tana da yan igiyoyin kamawa daga jikinta akwae hoto saidai bata duba ba balle ta gane ko ta miye, rik'e jakar tay a jikinta ta maida idon ta akan shi lokacin taji yace gashi nan ya biya ta damage d'in da yay ma wayarta saura ita, yamutsa fuska ta fara yi a marairaice ta fara bashi hak'uri tana fad'in Allah tasan bazata iya biyan shi ba, banza yay mata kuma har lokacin bai kalleta ba can tace mashi to ga wannan d'in ya bar shi ba sai ya biya ta ba Shikenan, kawai sai gani tay yay wani guntun murmushi wanda yafi kama da a kira shi na mamaki, sai lokacin ya juyo suka had'a ido gabanta yay wani irin bugu ganin yadda ya d'aure fuskar, "kina da waya ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira wani miyau ta had'iya don ta fahimci tambayar yana nufin wayarta waya ce, a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a cigaba da kallon ta yay da yake wurin fayau yake da hasken fitilu kuma glass d'in Motar baida duhu sosae hasken ya d'an haska cikin Motar ba kamar da yake a inda suke akwae fitilar data haska saitin Motar, sai yan kame kame take ganin yadda ya kafeta da ido, janye idon yay taji yace ta tafi godiya tay mashi har ta juya zata bud'e Motar kamar daga sama taji yace "zaki aure yaushe?" Da sauri ta juyo ta kalle shi, sai ka rantse ba shi yay Maganar ba idon shi na akan Wayar shi, kokonto ta shiga yi na kodai kunnuwan ta ne suka ji mata ba daidai ba nan take ta gasgata hakan tana niyyar juyawa taji yace ba tambayar ta yay ba, maida idonta tay kan shi da tsananin mamaki take kallon shi har saida ta had'iyi abu kafin tace mashi ita ko rana ba'a saka mata ba ai, "Why?" taji ya fad'a ba tare daya kalleta ba, ce mashi tay bata da wanda ta tsaida zata aura, shiru ya d'anyi kafin taji yace ko dai bata da masu sonta ne, har saida tay d'an murmushi tare da girgiza mashi kai tace mashi ana cewa ana sonta sosae itace dai bata bada dama Why, ya k'ara ce mata tay d'an jimm kafin tace akwae wanda ta tsaida zata aura amman sai ya guje ta ita kuma sai bata k'ara jin tana son wani ba, dakatawa yay da latsa wayar ya juyo ya kalleta suka had'a ido har lokacin Fuskar shi kaman a d'aure take har ta fara tunanin kodai haka yanayin fuskar tashi take, tambayar ta yay mi tay mashi ya gujeta idon shi a cikin nata, kikkafta idanu ta shiga yi ta fara bashi labarin tun farkon had'uwar ta da Mujaheed har zuwa lokacin da ta samu labarin auren shi sai dai a tak'aice take gaya mashi, lokacin data gama idanunta ne suka ciko da k'walla da sauri ta sunkuyar da kanta tasa gefen gyalenta tana goge kwallan, tana haka taji yace ai wannan ba wani abu bane he found someone da yake tunanin is better than her so he left her, da sauri ta d'ago ta kalle shi cikin muryar kuka tace "amman fa tsawon lokaci muna tare da shi in yasan bazai aure ni ba miyasa tun farko zai sa ni in yarda da shi har yayi man Alk'awarin Aure, Saboda shi bana saurarar kowa kuma yasan hakan amman ya yaudare ni, dama ashe yasan ba aure na zaiyi ba wai haka yace ma abokin shi daya fad'a man zancen yayi aure wai burge shi nike shiyasa yake tare da ni" har ta gama Maganar idon shi na akan ta, janye idon yay yana wani d'an murmushin bata san miye duniya ba shiyasa ta d'auki hakan wani babban abu, tanata goge k'walla ya juyo suka had'a ido cikin Maganar shi mai cike da isa yace mata in a relationship she shouldn't trust completely don abunda yafi hakan ma za'a iya mata koma miya faru da ita shi a wurin shi itace tay kuskure amman yasan hada don bata da wayau ne tana rayuwa a k'auye, shiru tay tana sauraran shi saidai sam bata ji komai ba a Maganganun da yayi don ita bata ma yi zaton zai iya yin magana da ita ba haka, "You should forget about him and move on, in kin zauna a haka ke da shi waya ci gaba, I guess shine tunda yayi auren shi yana can yana enjoying life en shi, in kina ganin ya cuceki Allah yana nan ai, so you should focus on your self and your own happiness, ki ba masu cewa suna son ki chance you will definitely find the right person" jinjina mashi kai tay bayan yayi shiru, sosae taji ta samu k'warin gwuiwa ta wani bangaren kuma mamakin shi take yadda har ya yi Magana da ita haka, maida idon shi yay kan waya taji yace mata taje, godiya tay mashi ya jinjina mata kai ta juya ta bud'e kopar, bayan ta fita ta maido kopar ta rufe, nufar hanyar komawa baya tay sai murmushi take hakanan take jin wani irin nishad'i, jin k'arar rufe kopar Mota yasa ta juya baya shine taga ya fito daga cikin Motar ya nufo hanyar da take bi kawai sai ta tsaya tana kallon yadda yake tafiya irin ta kakkarfan namiji, tana tsayen har yazo saitin ta kaman bazai tsaya ba har ya d'an gota ta sai kuma taga ya tsaya taji yace mi taje jira, d'an murmushi tay tace taga ya taho hanyar ne shiyasa ta tsaya ya wuce, juyawa yay yaci gaba da tafiya, bai fi taku d'aya zuwa biyu yayi ba taga yayi mata alamun ta taho da hannun shi, a tare suke tafiyar tana daga d'an bayan shi, suna cikin tafiyar taji yace "When are you leaving?" amsa ta bashi da gobe bai ce komai ba yaci gaba da tafiyar shi can taga ya mik'o mata hannu cikin rashin fahimta ta kalle shi sai kawai ta mik'a mashi jakar hannun ta, girgiza hannun yay ya furta "Your phone" da sauri ta mik'a mashi wayar tata har zai bata ta cire password sai yaga a bud'e take don tunda ta fashe ta cire Saboda wuya take sha wurin bud'ewa, yana ta latsa wayar batare data san mi yake ba har suka iso baya, a daidai k'opar da zai bi ya tsaya ya mik'a mata wayar, amsa tay ya juya zai shige yaji tace "Kai yaushe zaka tafi?" Ita kanta sai dae jin Maganar tay ta fito, a wani slow ya juyo har saida gabanta ya fad'i ganin kallon da yay mata, motsa baki ta shiga yi ta waro ido duk ta sha jinin jikinta, "Na zo don ke ne?" taji ya tambaya da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, d'age gira yay yace to miyasa zatai mashi tambayar, cikin yar in ina tace "d...da..dama d'azunne naga yan gidan ku sun tafi,t.. to nayi tunanin ma harda kai aka tafi" da k'yar ta k'arasa Maganar, d'an k'ank'ance ido yay yace sa mashi ido take kenan a dabarbarce tace a'a wllh kawai don taga tare suka zo ne, yadda tay Maganar ne a tsorace yasa shi yin d'an guntun murmushi gefen kumatun shi ya d'an lotsa Fauzy ta bi shi da ido don ba K'aramin kyau murmushin ya k'ara mashi ba, juyawa yay ya nufi hanyar har zai shige ta ji da turanci yace gobe da sassafe zai tafi, da d'an d'aga murya tace "Allah ya kiyaye hanya" kaman bazai amsa ba sai kuma taji ya furta "Ameen" daga haka ya shige, washe baki Fauzy tay gaba d'aya yau abubuwan nashi burgeta suke, wucewa tay ta nufi part d'in da suke har ta kusa kaiwa taja ta tsaya, d'ago jakar kwalin tay sama tana duba hoton jiki wanda na inda ake saida wayoyi ne da kuma hotunan wayoyi kala kala da accessories nata, sauke jakar tay ta kai hannu ciki tana k'ok'arin fiddo abunda ke ciki, kwalin waya ne ta fiddo lokacin da idanun ta suka sauka akan rubutun jiki Kusan sik'ewa ta nemi yi ganin hoto da kuma sunan wayar wadda iPhone 15 ce irin ta Fatuu, wani irin bugu k'irjinta ya hau yi idanu waje baki bud'e take kallon kwalin, juyawa tay a razane ta kallo hanyar daya bi Al'ajabi ne ya kamata a ranta ta shiga raya don ya fasa mata waya shine zai bata wannan tsadaddar wayar, gaba d'aya tsoro ne ya kamata maimakon farinciki ta shiga tunanin yadda zatai da wayar, yankewa tay kawai taje ta nuna ma Aunty Mareeya ta kuma fad'i mata gaskiyar abunda ya faru tsakanin su, da sauri ta maida ta cikin kwalin kafin sauri sauri gudu gudu ta nufi part d'in nasu................. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 85 Lokacin da ta shiga parlon Aunty Mareeyar ta tashi ita da Feenah, har zata bita d'akin sai kuma ta fasa ta juya, bakin kopar shigowa ta komo ta tsaya ta fara k'ok'arin kiran ta,saida ta kusa tsinkewa sannan ta d'auka cikin murya ta wanda ya fara bacci tace mata ya akai ne har ta fara bacci ta tasheta, hak'uri ta bata daga haka tay shiru saida Aunty Mareeyar tace miye to ta kirata sannan murya na rawa tace don Allah tazo taga wani abu, tambayar ta tayi wani abu da alamun mamaki, rasa abunda zata ce mata tay kawai sai tace dama akan wannan ne data fad'i mata abokin mijin Zarah ai tana jin Haka da sauri ta mik'e ta zuro k'afafunta k'asa, hanyar fita daga d'akin ta nufa tana ce mata gata nan zuwa, bayan ta fito cikin parlon ganin bata ciki yasa ta nufi d'akin su, nan ma bata ganta ba sai su Haulat da Mino dake bacci Zainab dai tana a parlon suna son k'arasa kallon Film d'in, a bakin kopar d'akin ta tsaya ta fara kiran ta, bayan ta d'aga a d'an hasale tace wai tana ina tasa ta fito kuma ita bata ganta ba tace mata tana a bakin kopar shigowa, jin haka har saida gaban Aunty Mareeyar ya d'an fad'i da yar fargaba ta nufi hanyar fita, tana tsaye a gefen kopar ta fito suka had'a ido, bin juna sukai da kallo ganin yadda Fauzyn tay zuru zuru yasa ta bita da kallo tun daga sama har k'asa, tsaida idon ta tay kan yar jakar hannunta sai kuma ta maido idonta cikin nata tun kafin tace mata wani abu Fauzyn ta Mik'o mata jakar, hannu ta kai ta amsa ta bi jikinta da kallo kafin ta kalli Fauzy da alamun rashin fahimta ta tambayeta miye tace ta duba abun ciki, hannu ta kai ta fiddo kwalin wayar koda tay arba da sunan wayar da sauri ta kalli Fauzy tace "Wannan fa, ta waye?" Sai faman zare ido take tace mata wai cousin brother d'in Ya Haisam ne ya siya mata, cikin d'aurewar kai ta tambayi waye cousin brother d'in nashi muryarta na d'an rawa tace mata Sameer, waro ido Aunty Mareeya tayi cike da Al'ajabi ta maimaita sunan Sameer d'in Fauzy ta d'aga mata kai, gaba d'aya kanta ya gama daurewa tama kasa magana baki a d'an bud'e take kallonta can tace "to ke taya akai kuka san juna, mike tsakanin ku da har zai baki wannan tsadaddar wayar?" abu Fauzy ta had'iya kafin tace "d..dama shine wanda nace maki rannan ya d'auke ni mun fita tare kuma shine ya aiko man da kud'i in yi lik'i a wurin dinner" k'arasa bud'e baki Aunty Mareeya tay tsabar Al'ajabi, a rud'e tace mata amman taya wai ya santa da har hakan ta faru tsakanin su shi da ko kallon mutane bai yi balle ya tanka masu Saboda izzar bala'e, labarin yadda komai ya faru tsakanin su Fauzy ta shiga bata, lokacin data gama gaba d'aya Aunty Mareeya ta zaro idon ta sai kuma ta washe baki tana dariya cike da Farinciki tace "Allah buwayi gagara misali, wani hanin ga Allah baiwa ne, inyee yar gidan Hajiya, wannan dank'areren kamu haka, ashe ashe dai babban rabo ne ke bibiyar ki" dariya Maganar tata taba Fauzy tana yi tace mata itafa ba soyayya suke da shi ba bata fad'i mata yadda komai ya faru ba, baki a washe tace mata ai da hakan wani lokacin dama ake farawa, still dariya Fauzy ke yi tace "Wannan ne zai so ni kema dai Aunty Mareeya, mutumin da farko kafewa ma yayi akan sai na biya shi ko yanzu fa da zai bani wannan wayar sai da yayi man maganar saura ni in biya shi nayi ta mashi magiya, amman ina ganin yanzu dai ya hak'ura tunda yace in taho" karaf Aunty Mareeya tace "in ma bai hak'uran ba sai mu biya shi ai, don nasan tunda ya kafe bayan kin nuna mashi baku da halin biyan to na gane biyan da yake nufi da soyayyar ki zaki biya shi baki ga har gwada ki yay ba, ai yasha kurumin shi in dai wannan ne za'a biya shi fin yadda yake zato, ana son shi wllh" dariya sosae Fauzy ke yi jin wani hak'ilo na Aunty Mareeya gaba d'aya ta hak'ik'ance kan wai son ta yake bacin ita dai tasan ko abu d'aya mai kama da nuna so bai yi mata ba in ba tamke mata fuska ba wanda tasan hakan bai cikin alamun so gashi k'arshe ma ai cewa yay taba masu sonta dama zata samu mutumin daya dace, Aunty Mareeya sai faman farinciki take bakinta yak'i rufuwa sai juya wayar take tana jinjina kai, "Yanzu yaushe yace zai zo Katsina?" ta tambayeta taci serious Fauzy kau mi zatai in ba dariya ba, harara ta wurga mata tace ba tambayarta tay ba, cikin dariya tace "to ni Aunty Mareeya bansan mi zan ce maki ba sai kace baki fahimci bayanin dana yi maki ba, ni fa bai ce yana sona ba bai kuma nuna ko alamar hakan ba kece kike ganin haka, ba har na fad'i maki shawarar da ya bani dana bashi labarin abunda Mujaheed yay man ba" d'an jimm tay tana nazarin Maganar can ta sauke ajiyar zuciya tace "na fahimci komai, amman kinsan mi, ina tunanin yana son ki ba tare daya sani ba don mutum irin wannan hakanan bai iya sake maki haka gaskiya, in ma ace yana da kirki zai iya biyan ki wayar taki gaskiya bana tunanin da irin wannan tsadaddiyar duk gadai wayoyi iri iri nan cike da gari sai kawai ya siyo maki wannan don ya fasa maki glass d'in waya, ai kawae yar gidan Hajiya komar ki ta kamo mana gingimemen kifi wllh, Allah Ubangiji ka tabbatar mana da abun nan wllh har bansan irin farincikin da zan yi ba" ta k'arasa tana ta washe baki ita dai Fauzy murmushi kawai take can tace "to Aunty koda ace sona d'in yake ni ba sai in yayi man ba...." Tunkan ta gama Maganar ta kai hannu zata buge ta tana fad'in "Wllh yayi maki mak'aryaciya kawai, wannan d'in zaki ce wani bai maki ba, ke ko bai maki ba indai ya nuna yana son ki Allah kema sai kin so shi tunda ni yayi man, yanzu irin wannan yaushe ma ake jira sai sunce suna so ai da mutum ya samu dama yake cusa kan shi in da rabo sai kiga an dace haka kema ya kamata ki yi" tura baki tay tace Allah ita bazata wani cusa kanta a wurin shi ba hakanan ya wulakanta ta, "Ai dama ba ina nufin kice kina son shi ba, tunda kinga kin samu dama ke zaki rink'a yin abubuwan da zaki jawo hankalin shi gare ki har ya furta yana son ki" shiru Fauzy tay tana jinjina zancen wai Sameer ya bud'e baki ya ce yana son ta tirkashi, tambayarta tay ai tana da lambar shi ko tace mata eh d'azun daya kirata, tace Yauwa to yanzu ta kira shi tay mashi godiya, d'an waro ido Fauzy tay tace amman fa dare yayi sosae ta bari sai gobe mana, harararta tay tace da zafi zafi ake bugun k'arfe ai sai yaga ma bata yaba ba tunda yasan dole a daren zata bud'e ta gani su fa ta irin haka ake janyo hankalin su, ba yadda Fauzy ta iya haka ta fara k'ok'arin kiran nashi Aunty Mareeyar sai kwatanta mata yadda zatai mashi godiyar take ita kuwa gabanta sai d'an fad'uwa yake, kiran ya shiga yana ta ringing amman bai d'aga ba har ya yanke, cire wayar tay tace mata ta sake kira k'ilan bai kusa da wayar yanzu kuma tunda yaji ringing d'inta zai taho don ya d'auka, yamutsa fuska Fauzy tay tace ita gaskiya bazata sake kira ba hakanan ta ja ma kanta wulakanci sufa irin su ba'a zak'e masu don ba'a cika yi masu gwaninta ba, jinjina kai Aunty tay alamar yarda da Maganarta tace Shikenan suje, Fauzyn ta tambaye ta yanzu ya zatai da wayar ita bata son a gani gaskiya tace mata to ta 6oye ta in suka koma gida sai taci gaba da amfani da abunta ta d'aga mata kai, suna niyyar juyawa su shiga wayar Fauzy ta fara ringing da sauri gaba d'ayan su suka kai idanun su kan screen d'in, ganin lamba yasa Aunty Mareeya ce mata waye idon Fauzy a d'an ware tace mata shine, "Yauwa to, ki d'auka sai kice dama kinga wayar ne shine kika kira ki yi mashi godiya, kar kiyi mashi magana kaman wata sakarai kiyi exactly yadda na kwatanta maki d'azun" Aunty Mareeya da tay k'asa k'asa da murya ta fad'a har saida tasata dariya, picking kiran tay ta kai wayar kunne sai had'iyar miyau take Aunty na mata nuni da ta natsu da hannu, shiru yay bayan ta d'auka cikin kwantar da murya tay sallama nan ma shiru bai amsa ba, d'ago ido tay ta kallo Aunty da ta gwale ido tana kallon ta, alamun miye tay mata da hannu Fauzyn ta girgiza mata kai tay mata alamar bai yi magana ba, yi mata alamar taci gaba da magana kawai tay ta d'aga mata kai, a nutse tace mashi dama ta ga wayar ne shine ta kira tayi mashi godiya, tana rufe baki taji yace "You ave done that already" abu ta had'iya cikin yar in ina tace "eh, dama naga wayar babba ce shiyasa nace bari in k'ara yin godiyar, Allah ya saka da Alkhairi ya k'ara bud'i na Alkhairi" d'an shiru yay daga baya ya furta "Ameen" shiru sukai Fauzy sai kikkafta idanu take Aunty Mareeya tay mata k'uri sai tsuma take, can bayan wani lokaci taji ya furta "Gud nyt" da sauri tace mashi haka itama, tana ciro wayar Aunty Mareeya ta kai hannu kan kafad'unta ta jawota jikinta cikin washe baki tace haka yakamata tace "Gud nyt Masoyi na" yadda ta mak'e muryar ne yasa Fauzy kyalkyacewa da dariya itama dariyar farinciki take suka nufi ciki, lokacin da suka shiga cikin parlon ba kowa duk sun tashi an kashe kayan kallon, sakin kafad'ar Fauzyn tay cikin washe baki tace "ranki ya dad'e kije ki kwanta" dariya Fauzy ta saki tana fad'in kai Aunty Mareeya, sai da Safe tay mata tana washe baki tace "to your excellency Allah ya tashe mu lafiya" sosae Fauzy ke dariya ta juya ta tafi itama Aunty Mareeyar dariyar take ta nufi d'akin su, bayan Fauzy ta shiga bakin gado ta nufa ta zauna ta kai hannu cikin jakar ta fiddo kwalin wayar, bin shi tat da kallo can ta d'aura a saman cinyoyinta ta bud'e, bin wayar tay da kallo cikin ranta tana k'ara yin mamakin ta, Maganganun Aunty Mareeya ta shiga tunanowa na Sameer son ta yake, acikin ranta ta shiga mamakin taya hakan zata kasance wanda tasan tabbas dole yana da yan mata kuma bama k'ananu ba kamar ta, sannan y'ay'an Mayan masu kud'i da Mulki, zuciyarta ce ta tambaye ta yanzu in da gaske son nata yake zata so shi? jimm tay ta kasa amsa ma kanta don gaba d'aya ita gani take ba abu bane mai yuwuwa ma hakan yasa ta kauda ma tunanin gaba d'aya, d'aukar wayar tay ta fara jujjuya ta tana k'are mata kallo da d'an murmushi akan fuskar ta, aje wayar tay ta kai hannu ta tallabo ha6arta ta shiga tunano duk maganganun da sukai dashi a Mota, sosae tay mamakin yadda ya sake mata har sukai magana haka sai faman sakin murmushi take can ta maida wayar acikin kwalin ta saka cikin jakar ta mik'e, wurin kayanta ta nufa bayan ta bud'e akwatinta ta saka, ko tunanin ta saka kayan bacci bata yi ba ta wuce gado ta haye, rufe ido tay nan take zuciyarta ta shiga dawo mata da suffar Sameer. Washe gari da wuri akai gama Breakfast saboda masu tafiya kuma ranar aiki ce, Senator na cikin yin Breakfast jikin shi sanye da jallabiya yan'uwanshi da suka rage maza suka zo part d'in shi don su gaisa su kuma yi sallama wanda ya'yan yan'uwan mahaifinsu ne suma duk dattawa ne, bayan sun gaisa ya tambayi sunyi breakfast d'in suka ce eh yanzun nan suka gama, zancen wadda Nameer yake so yay masu yace bari ya gama sai suje suyi ma iyayen nata magana cikin nuna farinciki suka ce mashi to, bayan ya gama a tare suka mik'e har zasu tafi Senator ya dakata yace masu yana d'an zuwa duk suka tsaya suka ce to, hanyar Bedroom d'in shi ya nufa ya shige, bada jimawa ba ya fito ruk'e da babbar leda mai rubutu a jiki, d'aya cikin yan uwan nashi Alhaji Musa ne ya nufe shi da sauri wanda matsayin K'ani yake a wurin shi ya kai hannu ya amshi ledar suka nufi part d'in da su Ard'o suke, lokacin da suka shiga parlon ba kowa basu dad'e da gama yin Karin kumallo ba suna ciki suna shirin Tafiya, Alhaji Musa d'in ne yaje bakin k'opar tasu ya kwankwasa tare da yin sallama, Baban Altine ne yazo ya bud'e yana ganin shi ya k'arasa fitowa cikin washe baki ya gaishe dashi tare da d'an sunkuyawa bayan ya amsa ya sanar dashi tare suke da mai gidan suna son yin magana dasu ne yayi ma su magana, da sauri idanu a d'an waje ya tambayi lafiya dai ko yana murmushi yace mashi lafiya lou sai ma Alkhairi da sauri ya jinjina kai ya juya d'akin, ba'a d'au lokaci ba sai gasu sun fito su duka duk sun saka kaya da zasu tafi dasu Ardo yasha babbar riga da hula ha6ar kada, cikin parlon suka nufo su Senator na zaune suka nufe su da sauri, hannu suka basu suka shiga gaisawa don Senator ya hana su duk'awa k'asan da suke in zasu gaisa amman duk da haka in zasu gaisan dasu sai sun d'an sunkuya, bayan sun gama gaisawar yay masu nuni da su zauna duk suka nufi kujeru suka natsu, a nutse Alhaji Ibrahim ya fara magana yace dama abun Alheri ne suke tafe dashi duk suka jinjina kai, bayani yay masu d'an shi k'anin wanda ya auri yar wajen su ne shima ya ga yar'uwarta yana so to shine suka zo sake rok'on iri in ba'a yi mata miji ba, tun kafin ya rufe baki baban Altine ya hau girgiza kai bayan yayi shiru da sauri yace mashi ba'a yi mata miji ba wllh kuma koda an yi ma za'a warware a ba d'an wajen nasu ko don Mutuncin su a gare su, shi Baffan Fatun ma ya kasa magana tsananin mamaki had'i da farinciki ne suka lullube shi don kuwa yasan wadda ake Magana koma wacece d'iyar shi ce tunda da iya yaran shi su Aysha aka zo, shi Ard'o sam bai fahimci inda aka dosa ba tunda dama ba wani fahimtar hausar yake sosae ba cikin harshen fulatanci yake tambayar Baffan Altine abunda aka ce cike da farinciki ya hau sanar dashi, ai tun kafin ma ya k'arasa da sauri Ard'on har yana yin kaman zai fad'o daga kan kujera tsabar saurin yayi Magana Baffan Altine ya tare shi, cewa yay an ba yaron duka don haka yanzu ma sai a d'aura aure kawai, gaba d'aya murmushi su kai Senator yace masu yaron yana karatu ne yanzu kuma ba'a K'asar nan ba amman nan da shekara guda zai gama zuwa lokacin sai ayi masu Auren dama akwae Yayar shi da za'a ma Aure a lokacin sai a had'a su yanzu sun yi magana ne don asan da Maganar, Baban Altine ne ya k'ara yi ma Ardon bayani yadda zai fahimta sosae sai faman d'aga kai yake, Senator ne ya sake cewa yakamata a kira yaran aji ta bakin su don a tabbatar kafin a tsaida magana duk suka ce hakan yayi, kiran Nameer yayi a wayar shi bayan ya d'auka saida ya amsa gaisuwar da yay mashi sannan ya bashi umarnin ya iske shi a part d'in sannan ya kira itama yarinyar da yayi ma Hajiya Magana akan ta, bayan ya cire wayar ne daga kunnan shi ya kai hannu kan k'atuwar ledar da suka zo da ita ya d'an tura saitin su yace gashinan suyi amfani da su, Baban Altine ne ya taso ya d'auka har da duk'awa yana godiya haka Baffan Fatuu ma sai da ya d'an zamo daga kan kujera yay godiya Ard'o ma sosae ya hau yin godiya, after some minutes Nameer ya shigo jikin shi sanye da k'ananun kaya, amsa mashi sallamar da yayi sukai ya k'araso ciki kan shi a k'asa, daga gefen su Dad d'in shi ya zauna a k'asa duk idon su na akan shi, d'an d'ago da kai yay ya gaishe dasu Dad bayan sun amsa ya juya kan su Ard'o ya gaishe dasu cikin washe baki babban Altine ya amsa shi kuma Baffan su Fatun murmushi yake ya amsa, bai dad'e da shigowa ba Mino ta shigo da yar sallama jikinta sanye da Hijab duk suka kai idon su kan ta suna amsawa, kan ta a k'asa ta k'araso cikin parlon, a d'ayan bangaren ta zauna ya zamana suna facing juna da Nameer, gaishe dasu tay ba tare da ta d'ago kanta ba duk suka amsa, shiru suka d'an yi kafin Dad yay d'an gyaran murya idon shi akan Nameer yace mashi Hajiya ta fad'i mashi sak'on shi shine suke son ji daga gare shi da gaske yana son ta, shiru Nameer yay kan shi a k'asa gaba d'aya idanun su na akan shi, ganin yak'i magana yasa cikin d'an d'aga murya Dad yace, "C'mon Ka bud'e baki kai mana magana my friend! baka ji nauyin wadda ka ba sak'on ba sai mu" duk murmushi akai k'asa k'asa Nameer yace Eh, "Eh what?" da k'yar ya furta eh yana sonta ba tare da ya d'ago ba, "kuma zaka Aure ta?" kai ya d'aga kafin yace eh, "Ka sani in muka riga muka gama magana ba zancen ka dawo ka ce ka canza ra'ayi" da sauri ya jinjina mashi kai, maida idon shi yay kan Mino itama ya tambayeta tay shiru bata ce komai ba, k'ara tambayar ta yay nan ma tak'i tace komai baffan Altine ne cikin d'aga murya da fulatanci yace mata bata ji ana magana bane still bata ce komai ba idon Baffan ta na a k'asa, Ardo ne yay yar tsawa Dad yace su rabu da ita hakan data yi ta nuna masu ita cikakkiyar bafullatana ce, Albarka ya saka masu duk aka amsa da Amin yace su tashi su je, A tare suka mik'e dukkan su kan su na k'asa suka nufi hanyar fita daga part d'in su Dad suka cigaba da tattaunawa, suna fitowa bakin k'opar part d'in Nameer ya kai hannu ya kamo hannunta ta waro ido ya jata tana ta waige waigen kada wani ya gan su, bayan part d'in ya nufa da ita sannan ya sake ta suka bi juna da kallo fuskokin su d'auke da murmushi, "Yanzu hankalin ki sai ya kwanta sosae kin zama tawa na zama naki" Nameer ya fad'a yana dariyar farinciki, itama dariyar take sosae take ganin abun kamar a mafarki daga fara soyayyar su har an yi Maganar aure ta wani bangaren dad'i ne cike da ranta, "Yanzu ya za'ai Maganar karatun ki don ni gaskiya dana gama nan da one year in sha Allah za'a d'aura mana Aure tare da Yaya Laila" cikin tabbatar mata da hakan yay Maganar, shiru ta d'an yi sai kuma tace mashi to yayi duk yadda yake so, yana murmushi ya d'age mata gira "kenan k'in amince muyi aure ko baki gama Secondary d'in ba?" Kai ta jinjina mashi tace in dae zai barta taci gaba, "in kuma ban son kici gaba da karatun fa?" Still da murmushi akan fuskarta ta d'an yarfa hannu tace mashi Shikenan zata hak'uri, wani k'ayataccen murmushi ya saki yace ashe haka take son shi ita dai murmushi kawae take, "Ki sha kurumin ki zaki karatu har sai kin ce ya ishe ki, saidae gaskiya bana son a rink'a kalle man ke ya za'ai kenan?" Yar dariya tayi tace sai ta rink'a rufe Fuskar ta to, lumshe mata ido yay ya furta "that's what makes me love u more babe, duk abunda nike so kina so in sha Allahu zan yi bakin kokarina wurin saka ki farinciki bazaki ta6a yin dana sanin amince mani ba" jinjina mashi kai tay tana ta murmushi, "Kema zaki man haka?" Da sauri ta d'aga mashi kai kafin ta furta "in sha Allah" yace Allah ubangiji ya basu iko ta amsa da Amin, "Gaba d'aya ji nike inama ba sai nan da one year zamu zama ma'aurata ba don gaba d'aya kin mamaye heart ena" yar dariya tay sai kuma tace "ni kai ne heart d'in nawa" tana furta hakan tasa tafukan hannuwanta ta rufe fuska, sosae yaji dad'in Maganar sai zabga uban murmushin jin dad'i yake, hannu ya kai ya cire hannuwan nata suka zuba ma juna ido wani sabon son junan su ke ratsa zuciyoyin su, kasa jurewa Mino tay ta sadda idanun ta k'asa, "I'm going to miss you" d'ago ido tay a hankali tace itama haka, yar Ajiyar zuciya yayi yace yaso ya canza mata waya amman bai samu yin hakan ba, tambayar ta yay tana da bank account ta girgiza mashi kai alamar a'a, d'an jimm yay kafin yace Shikenan zai tura ma Uncle d'inta sai ya canza mata wayar don su rink'a yin Vedio call lafiya lou suna rage kewar juna, ce mata yay itama yakamata ace tana da account d'in zai sa a bud'e mata don ya rink'a tura mata kud'in da zata rink'a yin hidindimun ta, tana ta kallon shi har ya gama sannan tace mashi ya bar shi ba sai ya rink'a tura mata ba tunda ana mata komai, tun kafin ta rufe baki ya d'an yi mata hararar love yace tun yanzu ta sani hakkin ta ya hau kan shi tana dariya tace ai ba'a d'aura auren ba shima dariyar yake yace eh ai an bashi ita ko. Bayan su Nameer sun tafi Senator yay ma Alhaji Ibrahim Maganar bada kud'in neman Aure, daga cikin Aljihun jallabiyar shi ya ciro kud'in bandir d'in yan dubu guda biyu wato 200k ya ba Alhaji Ibrahim d'in, mik'ewa yay ya nufi su Ard'o da sauri Baban Altine ya mik'e shima ya tare shi ya bashi kud'in, bayan duk sun koma sun zauna aka yi Addu'oi aka shafa. Bayan tafiyar su Senator Baffan Altine ya bud'e ledar daya basu nan suka ga shaddoji ne guda shidda wato kowa kala biyu, sam bakunan su sun kasa rufuwa tsabar farinciki sai yabon kirkin su Senator suke, mik'ewa sukai don suje su k'arasa shiryawa kowanne su bakin shi a washe, tsayawa Baffan Fatuu yay bayan sun tafi ya fara k'ok'arin kiran Yadikko, lokacin da kiran ya shiga tana cikin d'aki suna shiryawa Kusan ma sun gama kimtsawa, bayan ta d'auka cikin ladabi ta gaishe dashi ya amsa, tambayarta yay sun gama shiryawa tace mashi eh, d'an shiru yay kafin kuma yace Albishirinta tana Jin hakan da sauri ta bashi amsa da goro fari Kal, yadda tay Maganar har saida ta d'an bashi dariya yace mata wani abun Alkhairin ne ya same su yanzun nan, cike da k'aguwa ta tambayi miye, fad'i mata zancen neman Auren Mino dasu Senator suka zo yanzu yay harda shaddoji daya basu da kuma kud'in neman Auren, tun kafin ya gama fad'i mata ta mik'e tsaye don da a zaune take a bakin gado, gaba d'aya mamaki ne ya kamata ta kai hannu ta rufe baki shi kuma sai murmushi yake don ya fahimci taji Al'ajabin Maganar, muryarta na rawa tace "Yanzun Mino itama yaron gidan nan zata aura, to yaushe suka san juna haka mu bamu da Labari" fad'i mata yay a wurin bikin nan kuma an kira shi a gaban su ya tabbatar yana son ta zai aureta, wani irin farinciki ne ya lullube yadikko wanda tunda take bata ta6a jin irin shi ba a rayuwar ta gaba d'aya ta kasa rufe baki su Aysha da suka zuba mata ido ganin yadda take farinciki yasa suma suka shiga washe bakin haka innar su Altine ma dake zaune a cikin d'akin idon ta na akan ta, bayan sun gama wayar da sauri ta tambayeta ya akai taga tana ta farinciki ne nan take sanar mata, itama tsananin mamaki ne ya kamata ta waro ido can kuma sai ta mik'e zumbur ta nufa hanyar fita, d'akin su Yaya ta nufa duk sun shirya suma suna zaune a bakin gado suna had'a jakunkunan kayan su ta fad'o kamar an jefo ta duk suka d'ago kai suka kallo ta, Yaya ce ta d'an 6ata fuska tace lafiya zata fad'o masu haka ba sallama, hak'uri ta basu tay tsaye tanata zare ido ta ma rasa ta ina zata fara, ganin yanayin ta yasa Yaya tambayar ta lafiya, ai kaman tana jira ta hau fad'i masu zancen an nemi auran Mino itama zata auri yaron gidan nan, wani kallon mamaki gaba d'ayan su suka bita dashi Yaya ta maimaita Maganar cikin d'aurewar kai Babar su Altine tace wllh yanzun nan mahaifin su ya kira innar su yana fad'i mata, hannu Yaya ta kai ta ruk'e ha6a tana jinjina kai ita kuwa kishiyar tata murmushi ta shiga yi tana fad'in "kaga ikon Allah, ashe da rabon zamu k'ara zuwa gidan nan shan wani bikin, lallai iyalin Muhammadu masu jinin sa'a ne....." A dak'ile Yaya ta katseta da fad'in "Uhmm wai jinin sa'a, ai ni gaba d'aya sai yanzun ma na fahimci komai, wannan sa'ar ba ta Allah da Annabi bace, wato da suka ga ita ta farkon ta samu mai Arziki shine itama wannan sukai kulle kullen su suka tura ta binni, kai da ganin wannan kasan aikin asiri ne ace yana ganin ta ya fara sonta har an tsaida magana, ita kadae ce yarinya a wurin bikin ba ga yan mata nan yan binni ba, ke ita kanta babbar ma ni yanzu ban yadda hakanan mijin nata ya aure ta ba tun farko k'ulla soyayyar ta su akai shiyasa ta tashi hankalin ta da taji Ard'o ya bayar da ita, gaba d'aya sai yanzu na gano komai, ita ce ta kitsa ma Yarinyar ta gudu ta koma bayan tayi shiri sosae kan shi mai kud'in da shi Alhaji Lawan d'in shine ta zo har tayi nasarar sa shi janye Maganar aka kawo ta wanccan" Fuska a hautsine take Maganar cikin harshen fulatanci duk sun zuba mata ido, mik'ewa tay ta cize baki idon ta a kan su rai 6ace tace "gaba d'aya sai yanzu na gane komai daya faru mak'ark'ashiya akai, shima Ard'o harda shi aka ma Asiri shiyasa ya yarda aka fasa da wanccan ya kafe kan sai anyi da wanda ta Auran" jinjina kai innar su Altine ta hau yi fuskarta a yamutse gaba d'aya wata irin hassada ce ta mamaye mata zuciya, kai da kawowa Yaya ta shiga yi ta k'ank'ance idanunta ta shiga zurfin tunani, "in dai ina raye to bazan bari Yaron ya auri Mino ba, tunda abun hakane nima zan yi abunda suka yin in sa a maida Auran kan d'aya daga cikin jikokina tunda ai ba fina iyawa su kai ba, ba abunda nike bari ya sha man kai, itama uwar Muhammadun da ta nemi zame man matsala ai ba k'aramar uk'ubata tasha ba kafin Allah ya d'auke abun sa, suma jikokin nata ban ta6a zaton haka abun zai kasance ba da tun wuri na d'auki mataki a kan su amman duk da haka lokaci ai bai k'ure man ba ko ya k'ure ba abunda zai gagara, har ita ta farkon sun ja bazan k'yaleta ba sai na raba Auran nata nasa ta dawo ruga anan zatai Aure...... 86 ...........bata samu k'arasa Maganar tata ba sakamakon buga katifa da d'ayar Matar Ardon mai suna Mero dake a zaune tayi fuska a matuk'ar d'aure ta fara magana "Sam bazan bari ki aikata hakan a gare su ba matuk'ar ina numfashi, duk abubuwan da kike yi mana k'yale ki kawae nike ba wai don ina tsoron ki bane, to yanzu an zo ga6ar da bazan zuba maki ido ba wllh sai in da k'arfi na ya k'are" gaba d'aya Al'ajabi ne ya kama su ganin yadda take maida mata martani ba tare da nuna shakkar ta ba kamar yadda suke yi tana juya su, hannu Yaya ta kai ta nuna kanta tace ita take gaya ma magana haka ta manta wacece ita, "Ban manta ba, ke Mutum ce kamar ni saidai muna da bambanci sosae, ke mushirika ce wadda bata yarda da Allah ba ni kuma na Yarda da Allah ban yarda da shirka ba, don haka a wannan karon na d'aura d'amarar yin yak'i da shirka za kuma muga wanda zai yi nasara tsakanin k'arya da gaskiya, hakanan Saboda tsabar mugunta da rashin tsoron Mahallici mi Mutanen nan sukai maki da kika d'au karan tsana kika d'aura masu, in don mahaifiyar shi da take kishiyar ki ai ta bar maki duniyar ko, in kuma don kina ganin Ardo yafi ji dashi ne ai don yafi sauran yaran nashi gaskiya ne da ruk'on Amana, wato don kina aikata shirka shine kike ganin ita kowa ma ke yi, to tsaya kiji sirrin, matuk'ar mutum zai tawakalli ya dogara ga Allah ya mik'a mashi dukkan lamuransa to zai ta samun cigaba a rayuwar shi wannan dalilin ne yasa kika ga a komai Muhammadu da iyalan sa suke nasara koda kuwa kin aikata masu wani abu ina mai tabbatar maki bazaki yi nasara ba da iznin ubangiji, Idan kuwa ya baki sa'a don wani lokacin yana tara bawa ne kafin ya d'au mataki akan shi in har kika aikata wani abu da yay sanadiyyar fasa yin auren nan to sai na tona maki Asiri kowa yasan ke kika aikata masu wani abu kuma kinsan Mutanan binni bazasu ta6a kyale ki ba kotu za'a kai ki daga can sai gidan yari kuma na tabbatar d'aurin rai za'a maki don sai na fad'a cewa kina da sa hannu wurin mutuwar Innar Muhammadun k'ilan ma harda matar shi innar su inna wuro, a yanzu zan zuba maki ido ne amman zan sanar da Muhammadu da matarsa harda su yaran da Kakar su akan su dage da Addu'a dama dai kinsan ai su ba daga baya ba wurin ruk'o da Addini to har nima zan taya su zamu ga tsakanin mu da ke wanda zai yi nasara" rai a tsananin 6ace tana huci ta k'arasa Maganar dama can tara Yayar take, sototo sukai suna bin ta da ido, mik'ewa tay tana d'an murmushi tace "ni zanje in taya murna don basu kad'ai abun Arzik'in ya shafa ba harda mu don haka ina mai baku shawara da ku kauda komai a ran ku kuyi farinciki hankali kwance ku dangwali Arziki, ke Yaya in kika kwantar da hankalin ki ma k'ilan Makka da kike ta mafarkin zuwa Masoyin ki Ardo da Ya'yan ki suka kasa kai ki duk da suna da halin hakan sai kiga ta sanadiyyar su kinje har ki k'ara ma sau ba adadi tunda kinfi kowa sanin halin iyalan Muhammadu basu da ruk'o in ba don haka ba da ko kallo a yanzu bazaki ishe su ba amman duk da tsangwama da tsanar da kike nuna masu hakan bai hana su jan ki a jiki ba wanda na tabbatar su wad'anda kike k'ok'arin ganin kin aikata shirka don ki jawo su a cikin Arzik'in ba lalle ko Habujar su bari ki rink'a zuwa wurin su ba balle har ta kai ga su biya maki Makka in ma ace burin naki ya cika kenan, in baki sani ba ki sani duk na kusa dake da kike ganin suna goya maki baya munafukan ki ne da sun samu dama zasu kaskantar da rayuwar ki kamar yadda kike masu" tana gama Maganar ta juya ta nufi k'opar fita, a razane Yaya ta bita da ido har ta fice haka Babar Altine ma, kallon juna sukai sun kasa cewa komai don abu ne da basu ta6a zato ba, sun d'an d'auki lokaci haka da k'yar innar Altine ta ja kafa ta matsa kusa da Yaya dake tsaye kamar an dasa ta, k'ok'arin k'arfafa mata gwuiwa ta shiga yi tana ce mata kada Maganganunta su dame ta ita tana tare da ita abunda za'ai kawae itama ai maganinta ta yadda bazata iya aikata abunda ta fad'an ba sai ayi yadda za'ai Auren ya koma kan d'aya daga cikin yaranta ita kuma ta mata alk'awarin duk abunda take so shi za'a rink'a yi in aka shigo cikin Arzik'in, bin ta da ido kawae Yayar tay daga yanayin fuskarta zaka fahimci ba k'aramar razana tay ba, ci gaba da k'arfafa mata gwuiwa tay can Yayar ta fara girgiza mata kai har saida gaban innar su Altinen ya fad'i, matsawa Yaya tay ta zauna a bakin gado cikin mutuwar jiki tace mata akwae babbar matsala, dama bokan ta ya ta6a fad'a mata sai ta bi a hankali don a cikin gidan su akwae wadda zata kawo k'arshenta lokacin ta buk'aci sanin ko wacece yace bai samu gano kowacece ba amman tabbas sai tayi taka tsantsan don ba K'aramin tagayyara rayuwarta zata yi ba, a lokacin ta rok'e shi ya bata abunda zatai amfani dashi wurin yin maganin ta amman sai ya nuna bazai iya ba don a yadda ya gani ita bada asiri zata yak'e ta ba da ayar Allah ne, baki bud'e innar su Altine data durk'ushe a k'asa take sauraren ta, nannauyar ajiyar zuciya Yaya ta sauke ta hau jinjina kai tace "yanzu na gano k'arshe na da yace zata kawo wato shine in ta tona man Asiri aka kai ni gidan yari" sosae Yaya ta tsorata abun ka da mutumin kauye, nazarin Maganganun kishiyar tata ta shiga yi a cikin ranta tabbas tasan abunda ta fad'a kan iyalan Muhammadu gaskiya ne duk abubuwan da take masu basu nuna rashin d'a'a a gareta in akwae wadda zata ce tana mata rashin kunya to Fatuu ce ita kuma wannan ba ita kad'ai take mawa ba halinta ne haka kuma bayan ta girma yanzu duk ta bari, zuciyarta ce ta raya mata in tayi wasa to fa zata tashi a tutar babu ne, da sauri ta kalli innar su Altine tace mata su hak'ura kawai in ba haka ba zasu shiga matsala in dai suka aikata wani abu gara su goyi baya suma su ci Arzik'in ala bashshi in bikin yazo sai su tattaro sauran yaran da basu da Aure suzo dasu watak'il suma su dace, cike da amincewa innar su Altine ta jinjina mata kai don itama ta tsorata da Maganar da tace bokanta yayi don tasan muddin asirin Yaya ya tonu to itama kuwa bazata sha ba, da sauri Yaya ta yunk'ura ta mik'e tace mata ta taso suje su nuna suna farinciki kar ayi tunanin wani abu, da sauri ta mik'e buguzun buguzun suka nufi kopa, Lokacin da Kishiyar Yaya ta shiga d'akin su Yadikkon bata isketa ba sai su Aysha kawai, da fara'a ta k'arasa wurin su ta tambaye su innar su suka ce mata ta fita taje ta dawo ta jinjina masu kai, a bakin gado ta zauna don ta jirata, bata jima sosae ba Yadikko ta dawo dama wurin gwaggo taje, a k'asa saman Carpet ta fara k'ok'arin zama ganin tana zaune a bakin gadon da sauri tace mata ya zata zauna a k'asa tazo ta zauna a bakin gadon mana Yadikkon na murmushi tace mata ai ba komai, gaisawa suka k'ara yi don sun gaisa da suka tashi, cikin nuna tsananin farinciki tace mata taji abun Alkhairin daya k'ara samun su a bakin innar su Altine taji dad'i sosae wllh, Addu'oi ta shiga yi Yadikkon sai murmushi take a cikin ran ta take amsawa Saboda nuna kunya ba kamar da Mino take y'a ta farko a wurinta, suna haka sai ga su Yaya sun turo k'opar kamar an jefo su gaba d'aya suka sauke idanun su cikin na kishiyar tata tana ganin su ta kauda fuskar ta, k'arasa shigowa ciki sukai ganin yadikkon zaune a k'asa yasa suma suka fara k'ok'arin zama a kan Carpet d'in, cikin girmamawa Yadikko tace masu don Allah su zauna a kan gado mana duk suka ce a'a bari dai suma su zauna a k'asan, gaisawa suka shiga yi sai faman washe baki suke kaman wad'anda akai ma Albishir da Aljanna su duk k'ok'arin da suke shine asan suna murna, bayan sun gama gaisawar ne suka shiga taya ta murna suna fad'in wllh sunyi farinciki jin abun Alkhairi da ya k'ara samun su, innar su Altine harda cewa ai ita d'azun tsabar farinciki ne ma yasa ta kasa cewa komai ta tashi da sauri ta nufi d'akin su don ta sanar ma dasu Yaya suma, Yaya ma cikin washe baki take fad'in ita shiyasa bata ta6a k'alubalantar komawar su binni ba wllh Saboda tana ji a jikinta hakan zai zame masu Alkhairi ashe kuwa hakan ne aikuwa su Aysha ma sai a maida su can binnin suma kawai, jin hakan har saida kishiyar tata ta d'an yi guntun murmushi ta ta6e baki ita kanta Yaya da tayi maganar duk ta bi ta kama kanta har d'an d'aga kai tay ta kalli kishiyar tata ita dai Yadikko murmushi kawae take don gaba d'aya farinciki ya gama cikata, Mero ce ta fara tashi tana k'ara taya yadikko murna ta nufi k'opa ta bud'e ta fita, kallon juna Yaya da innar su Altine sukai duk sun yi kalar rashin gaskiya, mik'ewa Yaya tay tana washe baki tace ma Yadikko bari taje ta idasa kimtsa kaya jin haka yasa innar su Altine itama ta mik'e tace haka, bin su da ido yadikko tay har suka fita, lokacin da suka koma d'akin nasu Mero na zaune a bakin gado jakar kayanta a gabanta ko kallon su bata yi ba, wurin ta Yaya ta nufa ta tsaya daga gaban ta sai lokacin ta d'ago ta kalleta, cikin kwantar da murya Yaya tace "ina son ki sani Wallahi tallahi kwarankwasa gajimare ni bani na kashe Fatima Mahaifiyar Muhammadu ba, koda kika ji nace na muzguna mata har Allah ya amshi abun shi bawai nice na kasheta ba, nasan da zalunce ta tun bayan da Ard'o ya auro ta na fahimci ba K'aramin son ta yake ba na fara muzguna mata k'arshe na had'a mata da asirin daya sa Ard'on ya rink'a gudun ta duk aka tsaneta to bak'in cikin hakan ne ya haifar mata da ciwo har yay tsanani Saboda ba'a kulawa da ita k'arshe ta rasu, ita kuma Aisha Mahaifiyar inna wuro sau d'aya nayi yunkurin yi mata Asiri don in raba su Saboda tana yar binni tafi sauran matan Y'ayana komai amman sai boka yace man bazai iya ba Saboda tana da iskokai masu zafi bazasu bari Asiri yayi tasiri ba a kanta gara in rabu da ita don zasu iya maido shi kaina, to daga nan itama na rink'a nuna mata tsana har tazo ta kwanta ciwo akai tunanin na iskar ta ne ashe cuta ce a cikin cikinta amman ni wllh bani da sa hannu a cutar" idon Mero a kanta har ta gama sannan ta sauke ajiyar zuciya tace ai Mahaifiyar Muhammadu itace tay silar mutuwarta don haka alhakinta na akanta gashi ta rasu balle ta rok'e ta yafiyar abunda tayi mata, a k'arshe tace mata tana bata shawara ta tuba ta daina shirka don malamin su dake koya masu karatun Addini yace itace laifin da Allah bai yafewa in aka mutu ba'a tuba ba sannan kuma duk wanda ta zalinta tun wuri ta nemi yafiyar shi don Allah bai yafe hakkin wani a kan wani, cike da nadama Yaya tace to yanzu ya zatay da hakkin Fatima data mutu, shiru Mero tay can ta nisa tace to ita gaskiya bata sani ba amman zata tambayi malamin su kuma suma yakamata su rink'a zuwa karatun hakan zai sa su daina aikata wasu abubuwan, atare suka had'a baki wurin cewa to zasu rink'a zuwa da sun koma, a marairaice Yaya tace mata to don Allah zata rufa mata Asiri Meron tay d'an murmushi tace ai ita bata isa ta tona mata Asiri ba in Allah bai yarda ba in kuna yaso ko ba ta silar ta ba to sai asirin nata ya tonu, sosae jikin Yaya yay sanyi lakwas kamar an watsa ma kaza gishiri. Bayan Fauzy ta gama shirin ta cikin bak'ar jallabiya tay rolling veil d'in ta, jakar wayarta ta d'aukko ba tare data bari kowa ya ankare ba don duk suna zaune a saman gado basu dad'e da gama yin murnar labarin da Mino ta shigo ta basu ba na neman auranta da akai, fitowa tay daga part d'in nasu ta nufi cikin gidan, part d'in Mom ta nufa lokacin data shiga a parlor ta isketa zaune itama jikinta sanye da jallabiya, tana murmushi ta kalli Fauzyn ta nufeta itama da murmushi akan fuskar ta, k'ok'arin zama take akan Carpet Mom ta nuna mata kujera tace ta zauna mana, bayan ta zauna gaishe da ita tay still da murmushi ta amsa mata, shiru suka d'an yi kafin tace mata ana ta shiri ko Fauzy ta d'aga mata kai a hankali tace eh tay Addu'ar Allah ya kai su lafiya ta amsa mata da Amin, shiru ta d'an yi kafin ta tambaye ta Zarah na nan tace mata eh ta shiga tana ciki, mik'ewa tay ta nufi hanyar Bedroom d'in, lokacin data shiga Fatuu na kishingid'e a gefen gado idon ta akan Tv tayi wanka tana sanye da doguwar rigar material mai red flowers ta yafa d'an jan gyale a kanta, jin sallama yasa ta kai idon ta kan kopar shigowa ganin Fauzy yasa ta washe baki tana gyara zaman ta, nufota tayi ta tsaya daga gabanta tana fad'in "mai ciki" dariya Fatun tay tayi mata alamar ta zauna da hannu, a gefenta ta zauna daga bakin gadon, "Kina ta hutawa abun ki" Fauzy ta fad'a idon ta akan Fatun tana murmushi, itama murmushin take jin abunda tace sai kuma tace "wllh har na fara gajiya ma ni, daga ci sai kwanciya in nayi wani aiki to bai wuce zuwa toilet fa" yar dariya tay "tun yanzu, duka mi akai a bed rest d'in" d'an tura baki tay "wllh ji nike inama ku tafi da ni duk naji na damu da tafiyar da zaku yi" d'an shiru Fauzy tay tana murmushi sai kuma tace "ai ba yadda za'ai a tafi dake tunda ga halin da kike ciki, amman yanzu ni abunda ma yafi damuna shine ya za'ai da School kinsan ranar Wednesday d'in nan zamu koma tunda dama hutun 2 weeks ne" yanayin fuskar Fatun ne ya d'an canza tace "nima harda ita yasa na damu nike jin dama in bi ku, amman zan ma Hubby magana kan hakan tunda bai yuwuwa in zaune anan ana can ana karatu tunda ba wani ciwo nike ba ba sai na dad'e anan ba gaskiya" kai Fauzy ta jinjina, shiru suka d'an yi sai kuma Fauzy tace "sai muka ji abun farinciki an nemi auren Mino wllh nayi matuk'ar murna baki ji ba" fad'ad'a murmushi Fatuu tay tace "wllh abun fa abun farinciki, ke ni farko ma da baffa ya kira ni ya sanar man tsabar mamaki kasa rufe baki nay jin abun kamar wasa duka yaushe suka had'u amman har an tsaida magana, sosae na taya Mino murna don Nameer sam bai da matsala wllh" "Haka abun Allah yake matuk'ar ya k'addaro abu sai kiga ya faru aita mamaki" kai Fatuu ta d'aga, "da rabon zamu k'ara zuwa shan wani shagalin don wllh bazan 6oye maki ba na nishad'antu da dukkan shagalin da akai kar ma dai dinner d'in nan duk aka zauna sai an tada zancen ta" "Ai naga har wak'e ki akai Hajiya Fauziyya mai ruwan Naira, wai ni don Allah ina kika samu wad'annan kud'in da kika rink'a man wanka da su" Fatuu ta tambaya tana murmushi idon ta akan Fauzy, murmura mata ido tay tace itama samun su tay daga sama, kafin Fatun tace wani abu ta d'ago jakar da ta shigo da ita ta mik'a mata, amsa Fatuu tay ta bi jikinta da kallo kafin ta maido kallon kan Fauzy alamar rashin fahimta, ce mata tay ta duba abun ciki, hannu ta kai ta fiddo kwalin wayar saida tay d'an jimm tana kallo shi kafin ta fara k'ok'arin bud'e shi, bayan ta fiddo wayar bin ta tay da kallo tana d'an Jujjuya ta, "Wannan irin wayata ce" kai Fauzy ta d'aga mata, "ta waye?" Fatuu ta tambaya, shiru Fauzy tay tana d'an murmushi Fatun nata kallon ta alamar jiran Karin bayani, "tawa ce wai, Cousin brother d'in Ya Haisam ya siya man" wani kallon rashin fahimta Fatuu ke bin ta da shi tace mata wane cousin brother d'in nashi, jimm Fauzy tay kafin ta bata amsa da "Sameer" a wani slow Fatuu ta fara bud'a idanunta tare da bakin ta duk a lokaci d'aya har saida taba Fauzy dariya, "Sameer fa kika ce! Wai wane Sameer d'in kike nufi?" ce mata tay wanda dai ta sani, "kina nufin wai Sameer Sameer d'an Governor???" Kai Fauzy ta jinjina mata, k'ara bud'e baki Fatuu tay idanu waje cike da tsantsar mamaki take kallon Fauzy tama kasa magana can ta sauke numfashi ta furta "this is unbelievable! Sameer ya siya maki wannan wayar! amman wai...taya akai kuka san juna ma tukun" Fauzy sai dariya take ganin yadda kan Fatun ya d'aure, labarin yadda akai suka san juna ta fara bata tiryan tiryan har da kud'in lik'in da ya bata zuwa jiya da ya bata wayar, lokacin data gama fad'i mata hannu Fatuu ta kai ta rufe bakinta tana dariya, "Yau da alama so kuke ku kashe ni da mamaki, Mino da Nameer an tsaida Maganar Auren su yanzu kuma ga ke da Sameer, wayyo dad'i kashe ni" Fatuu tay Maganar tana yarfa hannu, Fauzy dake ta dariya tace mata ai ita fa ba wani abu ke a tsakanin su ba, katseta Fatuu tay tace "ke dalla ai daga haka ake farawa, ga misali nan tsakani na da hubby dana fasa mashi glass duk da ni daga haka zumunci ne ya k'ullu kema shine zai k'ullu amman na soyayya in sha Allah" ta k'arasa Maganar sai faman washe baki take itama Fauziyyar dariya take can Fatuu tace "Allah ubangiji ya tabbatar da abun nan kai, wllh sai nafi kowa farinciki, zan so in ga Fuskar mayaudarin nan Muntari yake kowa, wannan babban kamu haka ai nasan wllh sai ya girgiza in ma bai zauce ba, kinsan da yawan mutane basu son su rabu da kai suga kuma kazo kaci gaba" girgiza kai Fauzy tay tana ta dariya jin sunan da Fatun ta kira Mujaheed, "Wai ku sai faman Maganar soyayya kuke haka ma Aunty Mareeya duk ta bi ta rud'e, nifa bai ce yana sona ba, mutumin da in banda harara da tamke fuska ba abunda yake man wannan ne son?" "Ai kin san kowa da kalar nashi salon soyayyar ba kamar da shi ga yadda halin shi yake, amman mutum kamar Sameer da kwata kwata bai shiga harkar mutane yake maki haka kuma tun farko ga abunda ya had'a ku laifi kikai mashi amman shine harda baki kud'in lik'i da yi maki Maganar yaushe zaki aure uwa uba ya siya maki wannan tsadaddar wayar, haba Fauzy, kema dai kin so a ja Maganar ne kawae Allah, ai koda baki soyayya kefa ba yar primary ko Secondary bace ko Yaya ne zaki gane in mutum na son ki, ke dai Allah ya tabbatar mana yasa komai yazo cikin Sauk'i kamar nasu Nameer, aikuwa zanje in zuge Aunty Mareeya ta koya maki yadda zaki kama mana shi a hannu don na lura kina buk'atar lakca gaskiya duk Muntarin nan yasa kin rasa karsashi ta wannan fannin kuma irin su Sameer sai anasa karsashi a yin love da su" dariya sosae Fauzy ke yi tana fad'in Allah ya shirye ta, tambayar ta tayi har su Haulat sun shirya ne suma tace mata eh ba wanda bai shirya ba, sake tambayar ta tay taga Mom da zata shigo tace mata eh tana a parlor zaune, maida wayar Fatuu tay tana fad'in Allah yasa Alkhairi ya tabbatar masu da abunda suke fata, saukkowa daga gado Fatun tay tace mata suje tana son zuwa part d'in Hajiya ne, a tare suka fito har lokacin Mom na zaune a cikin parlon, kai idon ta tay kan su tana kallon su da d'an murmushi suka nufo ta, daga d'an can nesa da ita suka zauna Fatuu tay mata sannu ta amsa mata, shiru sukai tana son yin magana ta kasa Mom data fahimci hakan tana murmushi tace "ya akai Daughter ko akwae wani abu ne?" a sanyaye tace mata dama part d'in Hajiya take son zuwa zata bada sak'o, jinjina mata kai tay tace Ok taje amman ta kula tana murmushi ta d'aga mata kai, har zasu mik'e tace yama sunan Fauzy suka fad'i mata,ce mata tay ta tayata kulawa tana murmushi tace mata to, bayan sun fito daga part d'in Fauzy tace ma Fatuu wai wannan cikin nata in ta haihu shine jika na farko a gidan ko tace mata eh, Fauzyn tace haba shiyasa wannan gata haka wani abun ma sai an haiho babyn ita dai Fatuu murmushi kawae take, bayan sun iso part d'in Hajiyar a parlor suka tsaya suna gaisawa da Mutanen ciki duk akai ma Fatun ya jiki ta amsa, wucewa sukai bedroom da sallama Fatuu ta shiga Fauzy na biye da ita, Hajiya na zaune a bakin gado gwaggo kuma nata had'a kaya duk suka amsa masu sallamar tasu, ciki suka shigo fuskar Hajiya a sake take kallon su haka gwaggo ma data d'ago tana kallon su, daga gefen gadon suka tsaya suna gaishe dasu bayan duk sun amsa Hajiya ta nuna masu bakin gado tace su zauna mana sun toge anan, duk suka zauna, "Hala an zo bankwana da Dije, ai da kin bari zata iske ki can sai kuyi bankwanan" Hajiya ce ta fad'a Fatun tay murmushi kawae haka Fauzy da gwaggon, tana son yi ma gwaggon Magana amman ta kasa sai bin ta da ido take, ganin yadda take ta kallon ta yasa tace mata ya akai, juya harshe tay ta fad'i mata abunda take son fad'i mata dama Haulat take son ba kyautar atampa a cikin kayanta, itama cikin harshen fulatancin tace mata itama tana son a bama su Yaya amman taga kayan duk manya ne kar ayi ba daidai ba, "In sirri kuke son yi ai sai kuce in baku wuri ba ku canza harshe ba in d'auka gulmata kuke" Hajiya ta fad'a ta d'an kwa6e fuska duk sukai dariya, gwaggo ce tay mata bayanin cewa wai tana son ba k'awar ta atampa ne shine itama take ganin ya dace a ba su Yaya da yadikkonta amman bata san ko zasu iya hakan ba, hannu Hajiya ta kai ta ruk'e ha6a tace "Oni yasu, to Dije mi zai hana, ai kaya yanzu sun zama naku waya isa ya hana kuyi yadda kuke so da su in banda abun ki" gwaggo na murmushi tace dama wai taga kayan manya ne Hajiyar tace to ko manyan ne fa ai dai nata ne ko, kuma ai akwae atampopi suna nan da ba'a d'in ka ba tasan k'ilan bai wuce ma don hakan yasa ba'a d'inka su ba tunda yawancin kayan duk an d'inka, duk abunda zaku bada ku bada ba ruwan kowa da wannan" godiya gwaggo tayi mata tana yar dariya sai kawai ma Hajiyar ta mike ta nufi hanyar fita, Fauzy gwaggo tay ma magana ta mik'e taje suka sauke akwatunan, na kayan suka fiddo bayan an bud'e gwaggo tace ma Fatuu ta zo ta d'aukar ma Haulat d'in, wata atamfa mai golden tayi kyau sosae ta d'aukar mata, Su Yaya da Kishiyar ta da Yadikko suma duk atampopin aka d'aukar masu, ta Yadikko ma glitter ce mai kyau, wani lace tasa aka d'aukar ma k'annanta su Aysha sai k'awarta Zainab ma ta d'aukar mata wata sarka da yan kunne masu kyau dama ankon lace d'inta ta bar mata, su Aunty Mareeya ma da Feenah da Saude yan kunne fashion aka d'aukar masu kai da gani kasan zasu yi kud'i don ba k'ananu bane, akwatin cosmetics tasa Fauzy ta bud'e mata ta k'ara ma su Aysha da kayan shafa, gudun abun kar yay yawa yasa gwaggo da fullanci tace mata a bar su haka Fatun tace da su Baffan ta take son d'aukar ma shadda tace mata a'a an basu ta k'yale su in ma tana son basu ta bari a basu daga baya, Fatun tace to bari a basu ko turare ta d'aukar masu guda ukku daga haka gwaggo tace to a bashshi, kallon Fauzy Fatuu tayi tace mata ta d'auki duk abunda take so da sauri ta girgiza mata kai tace wllh ba abunda zata d'auka duk uwar hidimar da akai dasu ga anko mai tsada har kala biyu gwaggo dai murmushi kawae take, madaidaicin akwati aka d'auko bayan an kwashe kayan cikin shi an maida cikin wani suka zuba kayan da suka d'aukar a cikin shi har Fauzy zata rufe Fatuu ta dakatar da ita, wani akwati ta nuna mata tace don Allah ta d'aukko mata, bayan ta jawo mata shi tasa ta bud'e, had'add'un dogayen riguna ne a ciki duk a Dubai aka siyo su Fatuu ta kai hannu ta ciro wata army green mai shegen kyau tasha adon stones, bayan ta saka cikin kayan tace ma Fauzy ta rufe, maida akwatunan sukai yadda suke da, tambayar gwaggo Fatuu tay jakarta da ta zuba kud'in da ta samu ranar Walima dama ita taba ajiya, bayan ta d'aukko mata ta bud'eta cikinta dankam take da kud'i, envelope d'in da Alhaji Lawal ya bata ta fiddo ta bud'e, kud'i ne a ciki bandir din yan dubu na dubu d'ari, maida su tay cikin envelope d'in ta d'auketa bayan ta rufe jakar ta mik'a ma gwaggo tace to ita da zasu tafi, ce mata tay ta tafin mata da ita kawae ba abunda zata yi da su don tana da kud'i sosae a account d'in ta. A tare suka fito daga cikin d'akin Fauzy na janye da akwatin kayan, a parlor suka iske Hajiya zaune tace ma Fatuu ta k'yale su suje ita ta koma taje ta natsu wuri guda a marairaice tace mata tana son yin sallama dasu ne, lokacin da suka isa part d'in bayan gaba d'aya a parlor suka iske su don Abbas ya kira Feenah yace bada jimawa ba zasu tafi su zama cikin shiri, gaishe gaishe aka shiga yi ana k'ara yi ma Fatuu ya jiki bayan sun gama gwaggo tasa Fauzy ta bud'e akwatun, fiddo kayan su Yadikko tay harda turarurrukan su Ard'o ta nufi d'akin da suke don ta kai masu, suma na nan parlon Fauzy ta shiga fiddo na kowa tana bashi farko duk cewa sukai don Allah a bashshi banda duk uwar Hidimar da akai masu, saida gwaggo ta fito ta saka baki sannan suka amsa suna ta godiya da Addu'oi cike da Farinciki su Yadikko ma duk suka fito suna nuna masu nasu sai murna suke karma su Yaya da innar Altine su ji sam sun kasa rufe baki, fiddo kud'in da Fatuu tazo dasu tay ta shiga ba kowa dubu biyar biyar Haulat dae dubu talatin ta bata harda wanda zata yi kud'in Motar komawa Niger, nan fa parlor ya kacame anata farinciki Aunty Mareeya harda cewa in haka ake yin biki ai ba abunda zai hanata zuwa in dai ba ciwo ya kai ciwo ba duk aka sa dariya dama tun ran Asabar duk aka basu abubuwan da akayi na bikin, fakaitar idanun mutane Fatuu tay ta d'aukko trolley d'in Fauzy dake a cikin parlon, bud'e shi tay ta d'aukko jallabiyar da ta sako cikin kayan ta tura acikin akwatin kayan Fauzy data lura saboda a kusa da ita take tana niyyar yin Magana ta hau yi mata magiyar kar tace komai, wani kallo tay mata mai kamar harara Fatun ta saka dariya, Gaba d'aya tare suka fito lokacin wuraren k'arfe goma yan Katsina da yan Adamawa harda wasu yan Daura, a gaban Entry Hall aka jere Motocin gaba d'aya duk an fito da yan tafiya da yan rakiya su Hajiya, Mom, Laila, Fanan, nan aka shiga yin bankwana Haisam da Abbas na daga can gefe sun jingina da Motar Abbas haka su Kawu Amadu da Tk da Kamalu ma duk suna gefe, Jidderh Saboda tafiyar tasu dama tak'i zuwa School Aunty dae ta tafi wurin aiki dama tayi sallama dasu kafin ta tafi Fatuu ji take kamar a tafi da ita, had'a ido sukai da Haisam ta yamutsa fuska ya saki murmushi don ya gane mi take nufi, Mino ma sai kallon love suke ita da Nameer suna sakar ma juna murmushi, Dad ne ya fito tare dasu Ard'o Fatuu ta nufe su ta gaishe su duk suka amsa Dad yay mata ya karfin jiki tace Alhamdulillah, kallon Baffan ta dake ta sakar mata murmushi tay itama murmushin take mashi sun kasa ce ma juna komai, kud'i Dad ya fiddo ya shiga raba ma duk masu tafiya aka hau godiya daga baya suka fara shiga cikin Motocin bayan an sassaka kayan su, d'aga ma juna hannu suka shiga yi kamar kar a rabu a Kusan tare duk suka tashi Motocin suna ta cigaba da d'aga ma juna hannu a haka suka tafi sai fatan Allah yasa a sauka lafiya, tsaye Fatuu tay idanun ta sun ciko da k'walla gaba d'aya har kewar su ta fara kamata, bayan barin Motocin aka tuk'o wadda Senator zai hau ta tsaya a gaban wurin dama a shirye yake, sallama yay da iyalin nashi duk sukai mashi sai ya dawo bayan an bud'e mashi k'opa ya shiga suka tafi, Haisam ne ya matso gaban Fatuu suka had'a ido a shagwabe ta tura mashi baki yay murmushi, Hajiya ce tace mata to suje ya kai hannu ya kamo hannunta duk kunya ta kamata suka nufi cikin gidan........ 87 .......Alhamdulillah matafiya duk anyi waya da su sun isa lafiya gaba d'aya sai fatan Allah ya huta gajiya, bayan sallar isha Fatuu ta gama sallar tana zaune a saman gado jikinta sanye da voile material pink d'inkin riga da skirt tayi d'aurin kallabi mai kyau daga cikin kayan lefenta ne yayi mata kyau sosae, ruk'e take da wayarta tana bin chat d'in group d'in su na School da ake hirar komawa Makarantar bayan sun gama taya Fatuun murna data tura masu pics d'in bikin nata da akai, Haisam ne ya shigo cikin d'akin jin sallama yasa ta d'aga ido ta kallo shi, k'arasowa yay ciki idon shi akanta suna ma juna murmushi, ta gefen inda take ya zagaya ya zauna a bakin gadon ta gaishe dashi ya jinjina mata kai, hannu ya kai ya shafi fuskar ta yace "Ya jikin ki?" tana murmushi tace mashi itafa lafiya lou take jin ta wllh, kai ya d'aga sai kuma yace to ya Baby d'in su tace yana nan lafiya bacci yake yanzu amman d'azun da suna fira yace ta gaishe mashi da Dad, dariya duk sukai yace Baby Boy ne kenan tace tana dai Fata amman duk wanda ta samu tana so ya jinjina mata kai, tambayar shi tay shi mi ya fi so ta haifa tun kan ta rufe baki ya girgiza mata kai yace kamar yadda ta fad'a duk abunda ta haifa zai yi farinciki yana fatan Allah ya k'ara mata lafiya da Babyn yasa ta haihu lafiya tana ta murmushi ta amsa da Amin, hannu ya kai ya jawota jikin shi da sauri ta shiga k'ok'arin kwacewa yay mata wani kallo, d'an yamutsa fuska tay tace mashi Mom take tsoron ta gan su haka, d'age mata gira yay yace in ta gan sun sunyi laifi ne a shagwa6e tace "to ai Hubby da kunya fa ka manta jinya nike" yadda tay Maganar ne yasa shi yin yar dariya har hak'oran shi suka bayyana, jawota yay sosae ya rungumeta a wurin kunnanta ya rad'a mata to Mom d'in bata nan sun fita da Aunty, shiru tay ta d'an ji hankalinta ya kwanta dama lokacin da ta gama sallar isha tana zaune kan prayer mat tana Addu'a taga shigowar ta bata jima ba kuma ta fita bayan ta yafa mayafi, tun bata saki jiki ba har dai ta saki ganin shi ba abunda ya dame shi, Maganar School tay mashi tace ran Wednesday suke komawa, jinjina mata kai yay yace ta bari zasu koma taci gaba da zuwa amman ba yanzu ba sai an d'an k'ara lokaci in ta kama sai ayi Magana can school d'in ta d'aga mashi kai, Wayar shi dake ruk'e a d'ayan hannun shi ya d'ago ya fara daddana ta idon ta akan Wayar, hotunan wasu Motoci ya fara nuna mata tana ta kallo har ya kai k'arshe guda Kusan Goma ne, maida idon shi kan Fatuu yay yace ta gan su ta d'ago ta kalle shi tace eh, tambayar ta yay wacce tayi mata da alamun rashin Fahimta tace bata gane abunda yake nufi ba, shiru ya d'an yi tana ta kallon shi kafin taji yace yana nufin tay choosing wadda take so a ciki, waro ido Fatuu tay da tsananin mamaki take kallon shi shima kallon nata yake da murmushi, "Amman Saboda mi to zan za6a" ta tambaya da alamun mamaki yace mata Saboda za'a kawo mata ne, k'ara zaro ido tay ta furta "Motar!" Kai ya d'aga mata had'i da d'an lumshe ido a shagwabe tace "ni dai Hubby a'a ka barshi ba duk akwae Motoci ba har acan gidan Hajiya ma" kallon ta kawai yake sam bai yi mamakin jin hakan ba don yasan halin ta kan hakan bata son ya kashe kud'in shi yay mata abu in bai zama dole ba gashi kuma ita ba tambayar shi abu take ba, ganin kallon da yake mata yasa ta fara tura mashi baki ya kai hannu ya d'an matse bakin ta yi d'an sauti alamun taji zafi, sigh yay yace shima kyauta ce zai bata kan wadda ta bashi cike da shagwaba tace to ai ita ba ita ta bashi ba ko Allah ne ya bashi, yana murmushi yace yasan da wannan amman ai a jikinta yake ko, yamutsa fuska ta shiga yi yana murmushi yace mata wannan ce kyauta ta farko da ya fara bata a matsayin su na ma'aurata dole sai ta amsa tace ba ga uban lefen da yayi mata ba nan, ce mata yay Wannan ai ba gift bane tunda ya zama al'ada kuma bashi kadae yayi shi ba, sai shagwaba take mashi kanta na a kan shoulder en shi da alama ma ta manta da inda suke, bud'e mata Motocin yay yace in bata za6a ba bazai ji dad'i ba yayi zaton zatai murna ne ya bata gift in kuma wannan bai mata ba ta fad'i duk abunda take so, da sauri ta kai hannu ta tallabo gefen fuskar shi tace "a'a Hubby naji dad'i wllh kawae naga kaman wannan kyautar tayi girma ne kuma naga akwae Motocin" ce mata yay to su motocin dake akwae d'in nata ne ta girgiza mashi kai yace to yanzu ta za6a sai ya zama itama tana da nata ko, kai ta d'aga mashi tana murmushi har ta maida idanunta akan Motocin sai kuma ta d'ago da sauri tace "amman Aunty Fanan fa?" d'an murmushin gefe yay ya furta banda ita, waro ido tay sai kuma ta hau girgiza kai tace a'a don Allah bazata ji dad'i ba wllh itama gaskiya a bata yana murmushi ya furta Justice for Fanan da sauri ta d'aga kai tace eh, sosae yaji dad'in hakan data yi ta tabbatar mashi da Maganar da tayi mashi na zata taimaka mashi yayi masu Adalci, ce mata yay kada ta damu Fanan ma nada Mota a can Us ya siya mata ba'a dad'e ba, "Da gaske?" ta d'age mashi gira shiru yay yana kallon ta, sake ce mashi tay da gaske yake ya siya mata yana murmushi yace "da k'arya" dariya ta saki don tasan wasa yake itama hakanan jan magana yasa ta tambayi da gasken tunda tasan bazai mata k'arya ba, maida idonta tay kan Screen d'in tace to bari ta za6a, gaba d'aya ta rud'e don kowacce ta had'u kama daga Camry, Hyundai, Corolla Mercedes da sauran su, wata Jeep ya bud'e har zai wuce da sauri tace mashi ya tsaya, k'ura ido tay tana kallon ta sosae ta burgeta don dama tana son Mota Jeep kuma tana son farar Mota to itama Jeep d'in fara ce, ganin tana ta kallon ta yasa shi ce mata tayi mata, jimm tay sai kuma ta d'aga ido ta kalle shi ya d'age mata gira alamar ta amsa mashi, kai ta d'aga ya furta Ok da d'an murmushi sai kuma da sauri Fatun tace "amman nawa take?" shiru kamar ba zai yi magana ba slowly yace tunda tayi mata Shikenan ai mi zatai da kud'in ta, a shagwabe tace ita dai ya fad'i mata gaskiya in mutum zai siya Mota ba sai an fad'i mashi kudin ba, dariya yay bai san ranar da zata daina wauta ba, ce mata yay to ita siya zata yi ne, "eh ai tunda kai zaka siya man to kaman ni zan siya ko" ta k'are Maganar ta d'an tura mashi baki, d'an lumshe mata ido yay ba zato taga ya matso da face d'in shi yay pecking lips d'in nata ta d'an waro ido ya d'ago yana murmushi, rigimar sai ya fad'i mata kud'in Motar taci gaba da yi ya tambayi to mi zatai wai in taji kud'in tace hakanan take so taji, still murmushi yake wasu abubuwan ta kaman Hajiya, ya gane wai wayo take son yi mashi in taji tayi kud'i sosae tace bata son ta, girgiza mata kai yay yace an gama Magana ba sai taji ba shima ba siya yayi ba, k'una k'uni ta fara tana ita dae Allah bata yarda ba tunda shi yace ta za6a to ya fad'i mata kud'in, gaba d'aya yadda take mashi ta tafi da shi sai kallon ta yake dama d'an kwana biyun nan har ya fara jin kewar ta a tare da shi, ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta dakata da abunda take suka zuba ma juna ido breathing d'in su na had'uwa, sun d'an d'auki lokaci a haka fuskar Fatuu da d'an murmushi kawai sai gani tay ya matso da fuskar shi ya had'e da tata, had'e lips d'in su yay farko fara k'ok'arin kwacewa tay amman yak'i bata dama daga baya kuma ta biye mashi don itama tayi kewar hakan, "To, to da kyau, sannun ku da aiki" kaman daga sama suka ji an fad'i hakan gaba d'aya sai da suka d'an firgita da sauri Fatuu ta janye jikinta daga nashi a tare suka juya don ganin mai Maganar, Hajiya ce ta shigo tana dogara sandar ta jikinta sanye da kaftan ta atamfa tayi d'aurin kallabi irin nasu na manya idanunta sanye cikin glasses, wata irin kunya ce ta rufe Fatuu da sauri ta sunnar da kanta duk da bata san ko taga abunda suke ba don sun ba kopar shigowar baya to amman gaba d'aya tana a jikin shi ya tallabe ta a ranta ta raya da k'yar in bata ga abunda yake matan ba, idon Haisam a kanta har ta k'araso ciki ta tsaya daga gaban su ta d'aure Fuska, murmushi yay ya gaishe da ita ta wurga mashi harara tace "Yanzu miye wannan d'in, kasan halin da yarinyar nan take ciki amman shine bazaka iya hak'uri ka bari tabi dokar likita ba ta samu hutun da take buk'ata saboda tsabar jaraba, anya Haisam!" ta k'arasa Maganar ta d'an 6ata rai, still Murmushi yake ya d'an d'age mata gira yace "Yanzu nayi wani laifi ne" a fusace tace bata sani ba, yar dariya yay yace in dai hutu ne ai gashi tana hutawa ko, kwabe fuska tay ta jinjina kai tace eh tabbas ta gani hutawa take, maida idon ta tay kan Fatuu da tai tsumu tsumu kanta a k'asa ji take kaman ta nutse a wurin, ce mata tay ta tashi ta gama hutun anan don ba barin ta za'ai tayi yadda ya kamata ba, zuru da k'afafun ta tay still bata kalli Hajiyar ba ta mik'e, da sandarta tayi mata nuni da hanya tace su je, har zata tafi sai kuma ta dakata Hajiya ta tambayi ya akai k'asa k'asa tace zata d'auki kayanta ne, tambayar ta tay suna ina da k'yar ta d'an d'ago tay mata nuni da inda trolley d'in ta yake, nufar wurin tay tana dogara sandar, jawo shi ta shiga kokarin yi Haisam dake zaune yay yar dariya ya mik'e, wurin ta yaje yace ta kawo ya taimaka mata fuska a d'aure ta kalle shi tace bata so, hannu ya kai ya amshi akwatin ya fara ja Hajiyar ma ta fara tafiya da sauri Fatuu ta juya ta nufi k'opa sumi sumi, Sun rigata zuwa bakin part d'in nata cikin d'an d'aga murya tace ma Haisam ya aje akwatin nan kar ya shigar mata d'aki ya kama gaban shi murmushi kawae yake ya shige dama ita Fatuu tuni ta shiga, tsaye tay a parlor yana shigowa suka had'a ido a tare suka saki yar dariya suna haka Hajiyar ta shigo da sauri Fatuu ta juyar da kanta, tambayar ta yay a ina za'a aje akwatin tace bata sani ba ya aje a duk inda ya ga dama tunda dai ya raina ta ai saida tace kar ya shigo amman ya shigo, shiru yay can kuma yace mata to tayi hak'uri don ya rage mata aiki ne kawai ba wani abu ba, kaman bazata tanka mashi ba sai kuma tace to ta gode yaje kar kuma ya sake ta k'ara ganin k'afafun shi a part d'in ta, yana dariya yace ai wannan dole ne ya zata d'aukko mashi mata tace kuma kar yazo ai dole yazo ko don ya duba tafiyarta ko, hararar shi tay tace ko don fitina dai, maida idonta tay kan Fatuu dake kallon gefe tace ta wuce ta shiga cikin daki ta nufi hanyar shiga d'akin ba tare data kalle su ba, hannu Haisam ya kai zai d'auki akwatin yana fad'in bari ya shigar mata da shi aikuwa ta d'aga sandarta zata kwad'a mashi da sauri ya kauce yana dariya yace "Sweetheart yau ni zaki buga" fuska a d'aure tace ai bai fi k'arfin shi ba in dai bai fita ya bata wuri ba Allah zata bubbuga nashi ita, cewa yay Allah ya bata hak'uri bari ya fita ai duk abu mai sauk'i ne, saida safe yay mata a dak'ile tace Allah ya tashe su lafiya ya juya ya tafi, d'an murmushi tay ta girgiza kai bayan ya fita ta kai hannu ta kama trolley d'in ta nufi Bedroom, lokacin data shiga Fatun na zaune a bakin gado suna had'a ido da sauri ta janye nata ta koma kallon k'asa, cikin d'akin ta nufo tazo bangaren da Fatun take zaune ta aje trolley d'in a wurin sauran akwatunan, juyowa tay ta kalleta ta tambayi taci Abinci a hankali tace mata eh bayan Magrib taci, "to yanzu kina jin yunwa" girgiza mata kai tay alamar a'a tace to ta kwanta, idasa hayewa gadon tay ta kwanta tay lamo duk tayi kalar rashin gaskiya, wucewa Hajiya tay ta nufi hanyar fita, jin fitar ta yasa Fatun d'ago kai ta kalli k'opar sai kuma ta saka dariya, wayarta ce ta fara ringing da sauri ta kai hannu ta d'agota taga Haisam ne ke kiran, picking tay tana kara wayar a kunne ta saka mashi dariya shima ita yake yi sai kuma a shagwabe tace mashi yaga abunda take ta gudu kenan yace kar ta damu ai ba wani abu bane kawae Hajiyar ce ta d'auke shi a wani abu, tambayar ta yay mi take yi tace mashi gata nan ansa ta kwanta yadda tay Maganar har saida ta bashi dariya itama ita take ta yi, "Ina Hajiyan?" Ya tambaya, tace mashi ta fita k'ilan tana parlor ya furta Ok bari ya k'yaleta ta huta kar su k'ara wani laifin, har zai mata saida safe sai kuma ya tambayi akwae abunda take so tace mashi eh cike da kulawa yace Ok minene tace "Kai" maimaita abunda tace d'in ya yi tace "Eh Hubby, kai nike so" tana jin sautin murmushin shi yace mata ai shi ta riga ta same shi, cike da tsokana tace "to baby yace so yake ya kwana a part d'in Dad d'in shi sai kazo ka d'auke shi ko ka d'auke ta" yana dariya yace saidae yazo ya d'auki Maman Baby wanda daidai yake da tada yak'i tsakanin shi da Hajiya, labarin buga mashi sanda da tace zatai ya bata Fatun nata dariya, sai da Safe sukai ma juna cike nuna k'auna da kuma kewar juna, Bayan su Mom sun dawo tana shiga Bedroom d'inta taga ba Fatuu bata kawo komai a ranta ba tay tunanin ko tana wurin Jidderh, bayan ta rage kayan jikinta a cikin Laundry room ta wuce toilet don yin wanka, tana cikin yin shafa Jidderh ta shigo zata fad'i mata abu nan ta tambayi Fatuu na d'akinta ne tace mata a'a ita rabon ta da ita tun kafin Magrib data shigo nan ta duba ta, bayan ta gama shiryawa cikin kayan bacci ganin har lokacin Fatun bata dawo ba yasa ta nufi k'opa, bayan ta fito daga part d'in nata part d'in Laila ta wuce tana shiga cikin parlon ta iske su zaune ita da Fanan duk suna sanye da k'ananun kaya suna kallo a Tv, maido kallon su sukai kanta jin sallamar ta suka amsa mata da murmushi, k'arasawa tay ciki ta zauna akan kujera Fanan ta gaishe da ita ta amsa Laila tace har sun dawo ta d'aga mata kai, tambayar ta tay Daughter na nan ne da alamun rashin fahimta ta tambayi wace daughter d'in tace mata Sis d'in Fanan d'an jimm tay don bata fahimci wadda take nufi ba, Fanan ce data gane tace mata Zarah take nufi, yar dariya tay tace ai cewa zatay matar big bro Mom d'in tayi d'an murmushi kawae, ce mata tay bata nan ai rabonta ma da nan part d'in tun kafin ayi D'inner, d'an jimm Mom tay duk idanunsu na akanta Laila ta tambayi Lafiya, fad'i mata tay tunda ta dawo bata iske ta a bedroom d'in ta ba kamar yarda ta barta tayi tunanin tana a wurin Jidderh kuma bata nan shine tazo nan, ce mata Laila tay to ba sai ta kirata taji ba Mom d'in tace ai bata da no d'in ta, "To ko dai Big Bro ya fita da ita bari a kira shi a ji don nima banda no d'in nata amman zan amsa ko don irin haka" jinjina kai Mom tay tace bata tunanin Haisam zai yi haka tunda yasan halin da take ciki, Fanan ce tace bari ta kirata sai aji, bayan ta kira layin Fatun ya shiga ta d'auka tana fara'a suka gaisa tace mata tana ina ne nan ta sanar mata tana d'akin Hajiya tace Ok sukai sallama, fad'i ma Mom inda take tay tace to ta mik'e ta nufi hanyar fita Laila na zolayarta tana fad'in duk hankalinta ya tashi kar ace ta 6atar da Amarya tana murmushi ta fuce, part d'in Hajiya ta nufa tana shiga parlon ta isketa zaune tana kallo, ciki ta shiga ta zauna kujerar gefen ta tana murmushi ta gaishe da ita itama fuska a sake ta amsa mata, shiru ta d'an yi can tace dama ta dawo ne daga unguwa da suka je bata iske Daughter ba tun d'azu shiru ashe tana nan, d'an ta6e baki Hajiya tay tace "eh tana nan ni naje na taho da ita nan kuma bazata koma ba" da sauri Mom ta kalleta da alamun mamaki ta tambayi Lafiya ba dai wata matsala ta faru ba, "Ba abunda ya faru saidai matsalar ake k'ok'arin janyo mata a an k'i barinta ta huta kamar yadda likita ya bada doka" fuska a kwa6e ta k'arasa Maganar, har saida gaban Mom ya d'an fad'i a ranta ta shiga tunanin to mi take ma Fatuu da zata ce haka ita a iya saninta tana hutawa yadda yakamata amman gashi tace wai an k'i barinta ta huta , tana cikin zancen zucin ta ji Hajiyar taci gaba da fad'in "in banda jarabar tsiya k'iri k'iri fa yasan halin da yarinyar nan take ciki amman yaje ya bi ya kaddadabe ta shiyasa na maido ta nan ai sai in ga ta yadda zai rink'a zuwa wurin nata balle har ya takura mata" har saida Mom ta d'an ji sanyi don ta fahimci wanda yay laifin, d'an murmushi tay ta bata hak'uri Hajiyar tace Uhm kawai, mik'ewa Mom tay tayi mata saida safe cikin sakin fuska Hajiyar ta amsa mata ta tafi, Misalin k'arfe goma da yan mintuna Senator ya shigo part d'in har lokacin Hajiyar na zaune a parlor tana kallo, amsa mashi sallamar da yayi tay idon ta a kanshi ya k'araso cikin parlon, zama yayi akan kujera gefen tata cike da girmamawa ya d'an sunkuyar da kai ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mashi an dawo yace eh, Ledar hannun shi ya mik'a mata yace ga furar ta, amsa tayi tay mashi godiya da sa Albarka ya amsa har zai yi magana ta riga shi fad'in da yayi ta wahalar siyo mata Furar kullum mi zai hana ya rink'a siyo ta kwana biyu tunda ga fridge nan sai ta saka, yana yar dariya yace mata ai ba abun wahala bane yafi son tana shan fresh ba wadda ta kwana ba kuma ai ba shi yake siyowa ba kawai dai shi yana shigowa da ita ne, jinjina kai tay alamar gamsuwa sai kuma ya k'ara cewa shi d'in ma zai iya zuwa ya rink'a siyo mata ai tunda neman Albarka yake, dariyar jin dad'i tay tace mashi wannan kullum cikin samunta suke koda ba furar saidae kuma don samun lada tunda tana jin dad'inta yana murmushi ya jinjina mata kai, d'ayar ledar ya d'ago yace ga ta Daughter nan yaje part d'in Mom ya kai mata aka ce ta dawo nan Hajiyar ta ce eh neman hanata ake ta bi dokar likita shiyasa ta maido ta nan, jinjina kai yay yana murmushi don Mom ta fad'i mashi komai, mik'ewa yay yace bari ya d'aukko mata cup tasha ko ta bi jiki tace mashi to ai taga ma kamar bata lalata ciki, d'an fridge d'in cikin parlon ya nufa ya bud'e bayan ya d'aukko cup d'in ya dawo wurinta da kanshi ya ciro robar furar ya zuba mata, bayan ta fara sha ya d'auki d'ayar ledar yace bari ya kaima Daughter d'in Hajiyar tace Allah yasa ma bata yi bacci ba saida tace mata in zatai kallo ta fito tace a'a kwanciya zatai, Bedroom d'in ya nufa saida yay sallama sau biyu sannan k'asa k'asa ya jiyo Muryarta tana amsawa, shiga yay Fatuu data d'ago kai tana ganin shi da sauri ta tashi zaune dama a kishingid'e take suna chat da Haisam da kuma Fauzy, cikin d'akin ya shigo ya tsaya daga gaban gadon da fara'a take kallon shi ta gaishe da shi, amsa mata yay ya tambayi ya yanayin jikin nata tace mashi lafiya lou ya jinjina kai, matsawa yay ya mik'a mata ledar yace to ga furar ta sai ta sha da sauri ta kawo duka hannuwanta ta amsa tay mashi godiya, saida safe yay mata ya juya ya tafi. Wuraren k'arfe sha d'aya da rabi Fanan ta gama shiryawa cikin had'add'iyar rigar bacci lokacin Laila tayi bacci, gaban dressing mirror ta nufa ta kwance gashinta ta fara gyara shi, bayan ta gama ta hau yan shafe shafe da feshe feshen turarurruka, press ta nufa bayan ta bud'e ta fiddo after dress cikin kayanta data jera, d'aura ta tay a saman rigar baccin tata da iyakar ta gwuiwa ta yafa veil d'in asaman kanta daga haka ta nufi hanyar k'opa, saida ta saka flat shoe dake a bakin k'opar sannan ta bud'e ta fuce, part d'in Haisam ta nufa bayan taje can ta cire rigar saman. Da Asuba bayan ya dawo daga Masallaci lokacin itama ta gama salla har ta koma ta kwanta, jikin shi sanye da farar jallabiya ya hau gadon idonta akan shi tana mashi murmushi ta gaishe da shi yay mata ta tashi lafiya ta amsa mashi, matsowa tay ta d'aura kan ta a saman chest din shi nan take mashi Maganar aikinta tace sunyi waya da Dad d'inta jiya yake tambayar yaushe zata koma don hutun data d'auka ya k'are har anyi mashi magana, shiru Haisam d'in yay kamar mai nazarin wani abu har saida ta d'aga kai ta kalle shi, ce mata yay nan da 2 weeks shima zai koma yana ganin in ba matsala ta bari sai su tafi tare tace Ok zata ma Dad d'in ta magana sai a k'ara mata hutun ya jinjina mata kai sai kuma ta k'ara mashi Maganar tafiyarta Lagos idon ta akan shi, d'age mata gira yay yace tana sauri ne tana murmushi tace a'a, ce mata yay ta bari ta k'ara ko 1 week tana murmushin jin dad'i tace to. Sam Fatuu bata wani laulayin ciki ba kamar wanccan data samu ba wannan cikin bata wani ciwo kuma komai ci take gashi sosae cin Abincin ta ya k'aru, kawai wani lokacin in taji k'amshin da bai mata ba take jin zuciyar ta ta d'an tashi sai kuma in taci Abinci wani lokacin nan ma tana jin tashin zuciyar har ta d'an yi amai shima zata iya k'irga sau nawa tayi. Gaba d'aya Hajiya ta kasa ta tsare tun abun bai damun Fatuu har ta fara shiga damuwar hakan ba kamar data ga har lokacin Fanan na a gidan kuma dai tasan dole wani abu na shiga tsakanin ta da Haisam, Haisam d'in na yawan zuwa duba ta sai dae bata wani sakewa da shi koda yazo Hajiyar bata a cikin d'akin d'an bayan lokaci take shigowa tace yazo ya wuce ya bata wuri, kullum daga kwanciya sai kallo sai latsa waya ko main parlor bata cika zuwa ba Saboda a ranakun aiki yan gidan ma ba zama suka cika yi ba a parlon. Bayan sati d'aya ranar asabar Fanan ta tafi dama Hajiya Maryam nata k'orafin ta maido mata yarinya ta hanata zuwa School, bayan tafiyar Fanan su Laila da Nameer suma suka fara shirin tafiya, ranar laraba Laila ta tafi Malaysia Nameer kuma Haisam yace ya bari su tafi tare tunda a can yake karatun dama, gaba d'aya Fatuu ta k'ara shiga takura dama dasu Fanan d'in take yin hira wani lokacin ga damuwar tafiyar da Haisam zai yi ranar Sunday zaije Lagos daga can ran Monday zasu tafi, sosae Fatuu ta shiga damuwa don in tace bata buk'atar mijinta to tayi k'arya ba kamar in ta tuna zai tafi tare da Fanan sai zuciyarta tay ta raya mata zasu je can suyi ta shan soyayyar su, Ranar Friday da yamma gaba d'aya Fatuu tunanin yadda zata je part d'in Haisam take tana haka dubara ta fad'o mata, tana sanye da riga da skirt na lace ta nufi cikin Bedroom lokacin Hajiya na zaune tun bayan data gama sallar la'asar take tasbih, daga gefenta d'an nesa da ita ta zauna akan carpet ta shiga yin wasa da yatsunta na k'afa, bata dad'e da zama ba taji Muryar Hajiyar tana tambayarta ya kai, shiru tay ta fara motsa baki da k'yar murya na d'an rawa tace mata dama tazo tambayar ta ne Ya Haisam ne yace taje ta had'a mashi kaya tay wuri wuri da ita ta k'arasa Maganar, bin ta da ido Hajiya tay ta shiga yan kame kame, "Rabu dashi bazaki je ba, da da babu ke wake had'a mashi bashi ke had'a kayan shi ba, duk da abu ne mai kyau amman ai yasan halin da kike ciki ko" kallon ta Fatuu tay tana d'an kikkafta ido a hankali tace mata ai lafiyar ta lau bata jin komai, yar harararta Hajiyar tay "dama ai ba'a ce baki lafiya ba ko saidai gudun janyo ciwon ake" da sauri Fatun ta juyar da fuskar ta, d'an murmushi Hajiya tay tace mata taje taci gaba da kallonta bazata hau bene ba a halin da take ciki in dole sai ita yake so ta had'a mashi kayan tace ya kawo nan sai ta tayata su had'a mashi, jiki sukuku Fatuu ta mik'e ta nufi hanyar fita ta koma parlor, idanunta ne suka ciko da kwalla ta zauna tay shiru. Bayan sallar isha Haisam yazo dubata kaman ko yaushe lokacin tana a cikin Bedroom zaune a saman gado, ya lura da yanayin ta cike da kulawa ya tambayi mike damunta kawai sai ta saka mashi kuka tace ba shine zai tafi ba, rarrashinta ya shiga yi da k'yar ya samu tayi shiru daga baya ya tafi, bayan tafiyar shi cigaba da matse kwalla tay wani irin k'unci take ji acikin ranta, tunani ta shiga yi na ko in Hajiya tayi bacci ta tafi wurin shi don shi kan shi ta fahimci yana son hakan kawai ba yadda zai yi ne, to kuma in ta farka fa don tabbas Hajiyar na tashi da daddare wani lokacin toilet take zuwa kuma bata da nauyin bacci don sau da yawa in Fatun ta farka ko zata toilet data ji motsinta ita ke kunna lamp har ta tambaye ta lafiya, tasan muddin ta tafi da k'yar in bata farka ba taga bata a d'akin hakan kuma itama tasan zai ja masu matsala, sak'e sak'e ta ci gaba da yi bayan zuciyarta ta raya mata wanccan tunanin tana haka kawai sai wani abu yazo mata a rai lokaci guda ta hau jinjina kai alamar ta samu mafita, saida ta kai idonta kan k'opar shigowa tay d'an jimm kafin ta kai hannunta gefe da sauri ta d'auki wayarta ta shiga call log, layin Nameer ta shiga kira bugu biyu ya d'auka ya furta "Yayata ta kaina" bata ce komai ba kan hakan k'asa k'asa da murya tana yi tana kallon kopar ta tambayi yana ina, ce mata yay bai nan yana cikin gari ta tambayi yaushe zai dawo gida yace d'an anjima, jin tayi shiru yasa shi ce mata in da wani abu ta fad'i mashi ko tana son wani abu ne, "Eh, don Allah akwae wani magani ne da nike son ka siyo man zan turo maka sunan shi saidae ni yanzu nike son shi gashi kuma kace sai d'an anjima zaka dawo" sai zare ido take tana kallon k'opa tay Maganar, da sauri yace mata ba matsala ai sai yazo ya kawo mata dama a kusa da inda yake akwae babban pharmacy, jin hakan har saida ta d'an yi murmushi tace to bari ta turo mashi, da sauri ta cire wayar daga kan kunnan ta hannunta har yar rawa yake ta fara k'ok'arin tura mashi sak'on sunan Maganin, bayan ta tura zuciyarta ta raya mata yanzu in ya kawo kuma Hajiya na zaune a parlor kuma ya bata fa gashi ansan ba kowanne magani take sha ba sannan tace mata na miye, wani irin bugu gabanta yay da sauri ta zuru da k'afafunta cikin sand'a ta nufi k'opar, a hankali ta d'an lek'a cikin parlon ta hango Hajiyar zaune da Aunty, wani irin waro ido Fatuu tay baki bud'e da sauri ta dawo cikin d'akin, can k'arshen gadon ta koma sosae hannuwanta ke rawa ta shiga sake kiran Nameer duk bugu d'aya tare yake da fad'uwar gabanta, har ta yanke bai d'auka ba a rud'e ta hau sake kiran nashi can k'asan mak'oshi take furta don Allah kayi picking Nameer, saida ta kusa yankewa sannan ya d'auka yace "Sorry Yayata ina cikin pharmacy d'in ne amman gashi nan na siyo yanzu zan kawo maki da sauri cikin rawar murya idanunta akan k'opa tsoronta kada Aunty d'in ta shigo dubata tace "N...namer..r ka gane, don Allah ban son asan da maganin kada ka bari kowa ya gani" d'an jimm yay sai kuma ya tambayeta amman to maganin miye, gabanta ne ya fad'i cikin yar in ina tace mashi maganin bacci ne saboda halin da take ciki bata samun isasshen bacci shine take so tasha ko tayi baccin amman in aka gani za'a iya hanata sha tunda ba kowanne magani take sha ba amman shi wannan baida wata illa zata iya sha, ce mata yay ta tabbatar dai bazai mata komai ba da sauri tace mashi eh wllh ai yasan dai bazata sha abun da zai mata illa ba yace Ok kada ta damu bazai bari kowa ya gani ba gashi nan zuwa, wani irin sanyi ta ji a ranta ta koma ta haye saman gadon, dama Aunty shigowa tay su gaisa da Hajiya bayan sun gama gaisawar ta tambayi ya mai bed rest Hajiya ta d'an ta6e baki tace tana cikin d'aki tana ta nukurci miji zai tafi, murmushi Aunty tay tayi mata sai da safe, bayan kaman minti ashirin da tafiyar Aunty Nameer ya shigo cikin parlon Hajiya na a d'an kishingid'e da yake yaran gidan duk yini suke a School shiyasa basu cika zuwa mata hira ba Saboda gajiya kuma wani lokacin da daddare aikin Assignment suke da angama kuma aka ci Abinci da wuri suke kwanciya sai Weekend suke samun lokaci sosae har ayi abubuwan nishad'i, kujerar kusa da ita ya nufa ya zaune yana sakin faffad'an murmushi idon ta akan shi itama d'an murmushin take mashi, gaishe da ita yayi ta amsa tana gyara zamanta idonta a kan farar ledar hannun shi mai d'auke da tambari an rubuta Special soya, ce mashi tay mi ta samu ne ya d'an kalli ledar kafin ya kalleta ya girgiza ma ta kai yace ba nata bane Yayar shi ya kawo mawa taci ko Babyn su shima ya ci, ta6e baki tay tace ai kafin ai d'aran akai kwand'i dai masu Baby, yana dariya ya mik'e yace bari ya kai mata in ta ci sai ta yan mata, Fatuu na kwance tayi tsuru ta ji sallamar shi aikuwa da sauri ta d'ago suka had'a ido, cikin d'akin ya nufo ta yunk'ura ta tashi zaune, a bakin gadon ya zauna idon shi akanta yana murmushi ya gaishe da ita ta amsa itama da d'an murmushin, hannu ya kai cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo maganin dake cikin farar ledar magani a jiki anyi alamar guda d'aya za'a sha ya mik'a mata da sauri ta kawo hannu ta amsa tace mashi ta gode, mik'a mata ledar hannun shi yay yace gashi nan aba baby d'in su tay murmushi kawai ta amsa yay mata fatan Allah yasa tay baccin yau harda miyau tana dariya tace Amin, mik'ewa yay yayi mata saida safe ta amsa, yana fita da sauri ta kai maganin ta tura a cikin bra dinta sannan taji ta d'an samu natsuwa sai kuma ta shiga tunanin yadda zata ba Hajiya, tunanin ko taje ta d'aukko lemu a fridge ta saka mata sai ta bata tayi wata zuciyar ta raya mata ai ba lalle tasha lemu ba da daddaren nan, gaba d'aya ta rasa tunanin yadda ya kamata tayi duk fuskarta ta yamutse can furar da Dad ke kawo masu ta fad'o mata a rai tabbas a ciki yakamata ta saka mata to amman ta Yaya, zuciyarta ce ta bata ta koma parlon don yanzu Dad ya kusa zuwa in yazo sai tasan yadda zatai ta zuba mata, da sauri ta saukko daga gadon har zata tafi sai kuma tayi tunanin tayi dubarar tafiya da abunda Nameer ya kawo mata ta kai mata, d'aukar ledar tay ta nufi parlon gabanta nata fad'uwa, cikin parlon ta fito Hajiya ta d'aga ido ta kalleta ta nufe ta, daga gefenta ta zauna tana d'an murmushi ta gaishe da ita bayan ta amsa tace mata Allah yayi kenan ta fito, shiru tay bata ce komai ba sai kuma ta mik'e ta kai mata ledar tace gashi, d'an ta6e baki tay tace ta ci abunta tunda ita ya kawo mawa da yayi niyya ai da ya had'o da ita dama ba so yake taci ba don haka ta k'oshi, hak'uri Fatun ta bata tay d'an murmushi tace mata wasa take mata taci, juyowa tay taja table gaban Hajiyar bayan ta d'aura ledar ta fiddo nannadaddar foil paper d'in ciki, warwareta tayi wani uban k'amshi mai dad'i ya daki hancin su baki d'aya, wani had'addan gasashen nama ne a iya ido kawai sai ya burge mutum irin kalar suyar da aka mashi yasha su Albasa da koran tattasai harda soyayyan dankalin turawa naman dai yayi ba k'arya😋 bayan ta bud'e ta kalli Hajiya tace don Allah taci tay d'an murmushi tace ta ci ta k'oshi in ta rage sai taci, a marairaice Fatun tace a'a ita ta fara ci in ta rage sai taci, ganin in ba ci tay ba bazata k'yaleta baà kuma dai naman ya burgeta yasa tace ta zauna to sai su ci tare sosae Fatuu taji dad'in hakan ta zauna, a nutse suke ci sai faman dakon shigowar Dad take can wata zuciyar ta bata ta tambayi Hajiyar ko zata sha lemu sai taje ta d'aukko mata daga nan ta saka mata maganin, koda ta tambaye tan ce mata tay a'a bazata sha lemu ba ruwa kawai zata sha shima sai sun gama in kuma ma an kawo mata Furar ta Shikenan ita zata sha tana d'an murmushi tace to, sai Addu'ar Allah yasa akawo furar take a lokacin, cikin sa'a basu kaiga gamawa ba Dad d'in ya shigo lokacin Fatun kad'ai ke ci Hajiya ta daina ci, yana ganin su yay murmushi yana sanye da farar shadda babbar riga ya k'araso cikin parlon yana fad'in shagali suke haka Hajiya na yar dariya tace Nameer ne ya kawo ma d'an su abun dad'i ita kuma ta cinye mashi duk sukai dariya, zama yay ya gaishe da ita bayan ta amsa Fatuu ma ta gaishe da shi ya amsa cike da kulawa ya tambayi ya take badai wata matsala ko tace mashi eh yace haka ake so, yunk'urawa yay ya mik'e ya nufi kan c-table ya d'aura ledojin yace to shima ga nashi a had'a aci gaba da party duk sukai dariya Hajiya tay mashi godiya da sa Albarka Fatuu ma tayi mashi godiya yay masu saida safe, wani irin bugu k'irjin Fatuu ke yi ga k'oshi ga kwanan yunwa, ga dama ta samu amman bata san taya zata zuba ba, can ta mik'e tana fad'in bari ta zubo mata a cikin cup Hajiyar ta d'aga mata kai, hannu ta kai za ta d'auki ledojin furar Hajiya tace mata ta bar su taje ta d'aukko cup d'in mana da sauri tace to, kaman ta saka ihu haka take ji ta nufi Fridge d'in, bayan ta d'aukko glass cups d'in ta dawo ta kai hannu ta fiddo robar furar tana cikin bud'ewa taji Hajiyar tace ta matsu bari ta je toilet ta dawo yadda zata sha a nutse har Fatuu bata san lokacin data washe baki ba tace to, d'aukar sandarta tay dake gefe ta nufi hanyar shiga d'akin ai tana shigewa jiki na rawa Fatuu ta kai hannu ta fiddo ledar maganin sai kerma hannun ta Keyi duk ta rud'e tana yi tana kallon kopar shigowa da kuma ta bedroom, fiddo guda d'aya tayi har zata saka zuciyarta ta raya mata ba lalle ya narke da sauri ba don furar kitif take kuma k'ilan ma guda d'aya bazai gaurayeta ba har yayi aiki, k'ara ciro d'aya tay da sauri ta maida ledar cikin bra d'in duk ta rud'e, kamo ha6ar kallabin ta tay ta saka magungunan ta rufe ta kai baki ta d'an tattauna sannan ta bud'e ta kai bakin robar furar ta zuba, sakin ha6ar tay da sauri ta rufe robar ta d'auka ta hau Jijjiga ta, maida ta tay ta aje a saman table d'in tana ta zare ido da sauri ta gyara kallabin ta sai faman zare ido take zuciyarta ta shiga raya mata ta daidaita natsuwar ta kar a gane ta, fiddo d'ayar robar furar tay ta bud'e har lokacin hannunta rawa yake ta zuba a d'ayan cup d'in bayan ta rufe robar ta d'auki cup d'in ta fara sha, gaba d'aya idanunta na akan kopar Bedroom har bata san tana kai cup d'in bakin hancinta ba sai taji take ankara, bayan wani lokaci Hajiya ta sako sandarta ganinta wani irin Fad'uwa gaban Fatuu ya hau yi, k'arasa fitowa tay ta shigo cikin parlon, bayan ta koma inda ta tashi ta zauna da sauri Fatuu ta aje cup d'in zata zuba mata tace ta barshi bari ta zuba, idanun Fatuu akan furar dake sauka cikin cup d'in tsoronta kar taga 6ar6ashin maganin, bayan ta gama zubawa ta d'auka ta kai baki duk da hakan hankalin Fatuu bai kwanta ba ta shiga tsoron kada kuma ta tauna maganin, har Hajiya ta shanye tata Fatun bata gama ba saida tayi mata magana kan tayi sauri ta gama ko taje ta watsa ruwa ta cire wannan d'amammun kayan ta kwanta tace to, bayan ta gama ta maida robobin cikin ledojin ta kwashe su ta nufi bakin k'opa inda dustbin yake ta saka, saida safe tay ma Hajiyar tace mata Allah ya tashe su lafiya, koda ta shiga toilet ba'a nutse tayi wankan ba, bata d'au lokaci ba ta gama bayan ta fito cikin sand'a taje ta lek'a cikin parlon ta hango Hajiyar zaune a inda ta barta idon ta akan Tv, jiki a mace Fatuu ta juyo ta dawo cikin d'akin ta nufi bakin gado ta zauna jikinta sanye da rigar wanka, tunanin kodai maganin bazai mata aiki ba ta shiga yi, ta dan d'auki lokaci a haka can ta mik'e sukuku da ita ta nufi wurin kayanta, doguwar rigar bacci ta fiddo bayan ta saka ta d'auki ta wankan ta nufi toilet, koda ta fito saida ta sake zuwa ta lek'a still Hajiyar na a yadda take, yanayin fuskar Fatun ne ya canza idanunta suka ciko da k'walla ta nufi gado, gajiya tay da zaman a hankali ta kwanta tay shiru k'walla suka fara gangaro mata, a hankali take kai hannu tana gogewa k'wallan, sosae ta damu da tafiyar da Haisam zai yi gashi bata san lokacin da zai dawo ba don da ta tambaye shi ce mata yake daya samu time zai zo ya ganta, "Fateema da kika ji ni shiru ba sai ki lek'o ba kiji lafiya ban taso ba ina can bacci ya fara d'aukata akan kujera" Hajiya ce data shigo tay Maganar tana yi tana hamma, gwalo ido Fatuu tay tayi shiru da sauri ta runtse idonta tana jin Hajiyar na fad'in ko bacci take a haka, gadon ta nufa bangaren da take kwanciya ta hau ta kwanta sai zabga uwar hamma take, tana kwanciya taci gaba da baccin dama da k'yar ta kawo kanta d'akin yau dai ko zaman yin Addu'a bata yi ba, Fatuu na jin saukar numfashinta da k'arfi ta gane tayi bacci, tashi tay zaune idonta akan Hajiya sai kace ta dad'e a kwance a yadda take baccin, hannu ta kai ta d'aukko wayarta ta duba time har k'arfe sha d'aya tayi, tunanin ta k'ara bata time tayi tay zaune tana yi tana kallon ta gaba d'aya ma sai taga time d'in bai gudu, bayan kaman minti goma ta yanke ta tafi sai kuma tay tunanin ta gwada tashin Hajiyar ta gani ko baccin bai yi nauyi ba in ta tashi sai tace mata dama taga bata canza kaya bane, da wannan tunanin ta mik'e ta zagaya side d'in da take ta fara kiran sunanta shiru hannu ta kai ta d'an bubbuga hannunta tana cigaba da kiran nata nan ma shiru, d'agowa Fatuu tay tana murmushi ta nufi wurin kayanta ta curo Hijab, bayan ta saka ta nufi bakin gadon ta d'auki wayarta, saida ta je ta ja duvet ta rufe ma Hajiyar rabin jikinta ta kashe wutar d'akin sannan ta nufi hanyar fita, a parlon ma saida ta kashe kayan kallon da hasken cikin shi sannan ta nufi hanyar fita, saida ta tsaya ta lallek'a ta tabbatar ba kowa sannan ta fito sauri sauri gudu gudu ta nufi hanyar baya, tana tafiya zuciyarta na raya mata to yanzu in Hajiyar ta farka kuma fa, girgiza kai tay ta tabbatar ma kanta tunda maganin yayi aiki bazata farka ba tasan har ta koma don maganin nada k'arfi gashi biyu ta saka mata, Lokacin data haye benen k'opar parlon nashi a rufe take, da sauri ta d'ago wayarta ta shiga k'ok'arin kiran shi, yana yin picking tun kafin yace wani abu tace mashi yazo ya bud'e mata k'opa saida yaji mamakin hakan ya tambayi wace k'opa tace mashi ta shigowa part d'in shi ta baya, yana bud'e kopar suka had'a ido ta sakar mashi murmushi yana sanye da rigar bacci kimono broad chest d'in shi a bud'e, d'an waro ido yay alamar mamaki da sauri ta fad'a mashi ya kai hannu ya rungume ta, komawa yay ciki da ita bayan ya tura k'opar ya d'ago ta har lokacin murmushi take, da alamun mamaki yace mata ya akai tazo nan yanzu, farko shiru tay ta shiga tunanin bazata ce mashi magani ta bata ba sai kawai tace mashi ba tun d'azun take fama da ita ta barta tazo ta had'a mashi kaya ba amman ta k'iya shine yanzu da taga tayi bacci ita kuma ta taho, d'age gira yay sai kuma yay faffad'an murmushi yace mata bata tsoron ta tashi taga bata nan ta d'an tura mashi baki bata ce mashi komai ba, "Yanzu kayan kika zo had'a man kenan?" ta d'aga mashi kai wani kallo ya bita dashi ta tura mashi baki, d'an murmushi yay yace mata to ai shi ya riga ya had'a kayan nashi ya za'ai kenan da sauri ta fad'a jikinshi tana fad'in suje a wargaza su ta sake had'a mashi, sosae yake dariya sai mutsu mutsu take mashi da kanta a chest nan take ta fara turning nashi on, hannu ya kai ya murd'a key k'opar ta rufe ya kai hannu ya d'auketa ya nufi ciki da ita. Duk yadda Haisam yaso kar ya xamo uncontrollable kaman yadda yake duk ya kasance da ita abun ya ci tura ba kamar kuma daya kasance ga halin da take ciki gaba d'aya ta canza mashi, bayan ya samu natsuwa hak'uri ya shiga bata yana tambayar is she Ok, shiru bata amsa mashi ba ta duk'unk'une guri guda, Jijjiga ta ya shiga yi yana kiran sunanta amman shiru, da sauri ya sauka daga saman gadon ya je ya kunna Switch, har saida gaban shi ya fad'i ganin yadda tay ta runtse ido hannunta guda dafe da cikinta, wani irin bugu gaban shi yay a rud'e ya dawo ya hau gadon, d'ago ta yay ya fara tambayarta lafiya miya faru shiru bata ce komai ba sosae ya razana, maida ta yay ya kwantar ya fara k'ok'arin sauka yana fad'in bari ya kaita hospital, ji yay ta ruk'e mashi hannu da sauri ya kai idon shi kanta kawae sai gani yay ta kyalkyace da dariya, wani kallo yake bin ta da shi ya d'an yamutsa fuska ta d'age mashi gira kawai sai ya yarfa hannu yace "Zarah wannan wasa ne?" Yadda ya kwa6e fuska yasa ta k'ara kyalkyacewa da dariya, hannu ya kai ya dafe goshin shi ya maida idon shi k'asa, da sauri ta tashi zaune ta kai hannu tana k'ok'arin cire mashi hannun tana fad'in yayi hak'uri, k'in bata dama yay ta cire hannun a shagwabe tace in bai hak'uri ba Baby zai fito ya bashi hak'uri yanzun, juyowa yay yayi mata wani kallo idanunshi sun d'an yi ja, wara mashi ido tay tana murmushi ya d'an harareta, ta6e baki tay ta kai hannu ta kama kunnuwanta ta furta "i'm very sorry My Hubby bazan k'ara ba" yadda tayi ne ya bashi dariya yayi har fararen hak'oran shi suka bayyana ya kai hannu ya jawota ya rungume ta a wurin kunnanta ya rad'a mata so take tasa heart d'in shi tay bursting ne da sauri ta girgiza mashi kai yace to karta k'ara mashi irin wannan wasan da sauri ta d'aga kai, tambayar ta yay wai yaushe zata girma ne tana murmushi tace mashi ba rana, zamewa yay ya kwanta tare da ita ta yadda kanta na a saman chest d'in shi, shafa kanta ya shiga yi wani irin nishadi suke ji suna haka taji ya furta Allah yay mata Albarka tana murmushi idanunta a lumshe ta amsa tace shima Allah ya yi mashi Albarka ya amsa da Amin a haka bacci yay awon gaba da ita, jin saukar numfashin ta a hankali yasa shi kwantar da ita ya saukko ya nufi toilet, Kiran sallar Farko ya farka kamar koda yaushe, tashi yay zaune ya kai hannu ya kunna lamp, juyowa yay ya sauke idon shi a kan Fatuu dake ta shan bacci, ji yay kamar ya k'yale ta amman bai son Hajiya ta tashi taga bata nan ya zama wani issue kuma duk da bai san ma ko ta tashi ba, tashin Fatun yay bayan ta bud'e ido yace ta tashi ya rakata kar Hajiya ta tashi tana jin hakan da sauri ta mik'e, tare suka fito ta baya, lokacin da suka shigo cikin main parlon a d'arare Fatuu take, tare suka shiga cikin parlon Hajiya ya tsaya anan yace ta duba taga ko ta tashi, gabanta na d'an Fad'uwa ta nufi Bedroom, cikin sand'a ta zagaya side d'in da take kwanciya saida ta d'an saurara sannan ta kai hannu ta kunna lamp d'in wurin,tsaye tay tana kallon Hajiya dake kwance kan gado tana ta bacci, d'an murmushi tay don ta fahimci bata tashi ba don data canza kaya zuwa na bacci Saboda bata kwanciya ba tare data saka kayan bacci ba, juyawa tay ta koma parlon ta fad'i mashi bacci take ya jinjina kai sai kuma yace mata to in ta tashi da daddare fa bata gan ta ba, d'an waro ido tay sai kuma tace ita dai in tayi mata magana kan hakan to zata ce shi yazo tana bacci ya d'auketa, yar dariya yay ya kai hannu ya kamo ta jikinshi yace sharri ko tanata dariya, saida yay pecking kumatunta sannan ya juya ya tafi ita kuma ta nufi Bedroom d'in, bayan ta shiga cikin sand'a ta nufi side d'in da take kwanciya ta cire Hijab d'in jikinta sannan ta hau gadon ta kwanta, tunawa tay da she needs to take bath a hankali ta tashi saida ta kallo Hajiya sannan ta mik'e ta nufi toilet, tana fitowa aka fara kiran salla na biyu nan take alarm d'in wayar Hajiya ya fara k'ara da sauri har tana yin tuntube da carpet taje ta haye gadon ta cure guri guda tana zare ido, har alarm d'in ya yanke ya sake fara wata k'arar shiru bata ji Hajiya ta tashi ba, a saninta tunkafin lokacin salla Hajiya ke tashi tayi raka'atanil fajr a wurin zata zauna har lokacin salla yayi, a ranta ta raya to miyasa yau bata tashi ba, bata kawo komai a ranta ba ta saukko ta nufi wurin kayanta, doguwar riga ta saka ta maida Hijab d'in data dawo da ita ta kabbara salla, har ta gama Hajiya bata ko motsa ba, tana zaune akan prayer mat ta kai idonta kan Hajiyar a cikin ranta ta fara raya to wai lafiya bata tashi ba, zuciyarta ce ta bata taje ta tashe ta, tun Fatuu na kiran sunanta har ta kai ta fara d'an bubbuga hannunta, tsoro ne ya kama Fatuu ganin yadda take ta tada Hajiyar amman ko motsi bata yi ba, tun tana bubbuga ta har takai ta fara jijjigata tana fad'in Hajiya ki tashi don Allah, gaba d'aya Fatuu ta kid'ime tuni ta fara kuka Fuskar ta share share da hawaye zuciyarta ta shiga raya mata kodai maganin nan data bata ya kashe ta, da sauri ta kai hannu ta ta6a saitin Zuciyar ta sam ta kasa gane komai, kai kunnanta tai saitin fuskar ta taji gaba d'aya bata numfashi, d'agowa tay a gigice ta d'aura hannuwa a saman kai tana fad'in ta bani ta lalace badai ta kashe Hajiya ba, Haisam ne ya fad'o mata a rai ta juya tana laluben wayarta don ta kira shi sai dai bata gan ta ba can ta tuna ta baro ta a part d'in shi, a sukwane ta sauka daga saman gadon ta nufi hanyar fita da gudu............. 88 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ ..........A daidai bakin k'opa tana k'ok'arin fita cikin parlor sukai karo da Mutum, a razane ta kai idon ta fuskar shi nan take ta gane Haisam ne don gari ya fara wayewa, dawowar shi kenan daga Masallaci ya zo don yaji yadda suka k'are, ganinta a rud'e fuska sharkaf da hawaye yasa shi saurin kama ta yana tambayar lafiya da hannu ta rink'a nuna mashi saitin Hajiya tana fad'in tak'i tashi, kamata yay suka nufi ciki ta bangaren gefen Hajiyar ya zauna a bakin gadon ita kuma ta zagaya ta haye saman gadon idanu waje take kallon Hajiyar sai kuma ta kalli Haisam dake bubbuga Hajiyar yana kiranta, hankalin shi ne ya fara tashi har Fuskar shi ta bayyana ya kalli Fatuu ya ce mata miya faru da ita ne, wani Wahalallan miyau ta had'iya sai motsa baki take gaba d'aya ta zaro ido duk tayi kalar rashin gaskiya, k'ara tambayar ta yay yace ta fad'i mashi miya faru da ita ne cikin kuka murya na rawa tace "Don Allah Ya Haisam kayi hak'uri, wllh bada nufin haka nayi ba na rantse maka da Allah" mamaki ne ya bayyana akan fuskar shi jin abunda tace wanda yake nuni da wani abu tay ma Hajiyar, ce mata yay ta fad'i mashi abunda ya faru zai fahimceta da sauri ta fara fad'i mashi tiryan tiryan abunda tay mata na maganin baccin data bata guda biyu, d'an waro ido Haisam d'in yay cike da Al'ajabi yake kallon ta ganin yanayin shi yasa ta hau yin rantse rantse, gaba d'aya shima Haisam d'in ya rud'e ya rasa tunanin da zai yi ga Fatun ta gigice sosae wanda a halin da take ciki bai kamata ace ta tashi hankalin ta haka ba, Hannuwanta ya kamo ya shiga rarrashinta yana fad'in ta kwantar da hankalin ta ya fahimce ta zata tashi in sha Allah, ganin ta d'an sassauto yasa shi tambayarta shi maganin data batan ta tabbatar baida illa, da sauri tace wllh baida illa na bacci ne ko su suna sha in sukai karatu sosae suka kasa bacci, jinjina mata kai yay ya maida idon shi akan hajiya, k'ok'arin tada ta yaci gaba da yi Fatun na taya shi, ganin tak'i tashi yasa shi kallon Fatun yace bai kamata suna 6ata lokaci ba bari yaje ya d'aukko Mota sai ya kaita Asibiti aikuwa a rud'e ta kamo hannun shi da duka hannuwanta tana girgiza mashi kai tace "Don Allah Yaya Haisam kada aje Asibitin wllh in aka je za'a gane an bata wani abu ne gashi Nameer ne ya siyo man kuma ba lalle a fahimce ni ba" shiru yay ya rasa miye abun yi don gaskiya ta fad'a saidae kuma yasan kaita Asibitin shi ya kamata, tambayarta yay an rage sauran Furan ne da sauri ta girgiza kai "a'a, duka muka shanye robobin na a cikin dust bin a parlor", "Ok, ki kwantar da hankalin ki Hospital d'in yakamata akai ta zan san yadda za'ai baza'a gane kin bata wani abu ba muyi Addu'a Allah yasa komai yazo da Sauk'i" da sauri tace Amin, har zai sauka daga saman gadon sai kuma ya maido idon shi kanta yace ta sa mata ruwa ne da sauri ta girgiza mashi kai tace a'a ko taje ta kawo, da hannu yay mata alamar ta tsaya shi ya mik'e ya nufi hanyar parlor, bada jimawa ba ya dawo hannun shi ruk'e da bottle water daya d'aukko daga cikin Fridge ruwan mai d'an madaidaicin sanyi ne, bayan ya koma ya zauna bud'e murfin robar yay ya tarba hannun shi ya cika shi da ruwan, sai da yay bismilla sannan ya watsa mata shi a fuska nan take tay wata ajiyar zuciya, k'ara zaro ido Fatuu tay suka kalli juna da shi atare suka shiga kiran sunanta saidae bata k'ara yin wani abu ba daga haka, da sauri Fatuu tace mashi ya k'ara watsa mata ruwan, yana k'ara zuba mata ta k'ara yin ajiyar zuciya suka cigaba da kiran sunanta, Motsi ta fara yi Fatuu ta fara d'an murmushi, Haisam ne ya rankwafa yasa hannu yana d'an bubbuga gefen fuskar ta yana fad'in "Sweetheart open your Eyes" a hankali ta fara bud'e idanun tana yi tana rufe su yana cigaba da ce mata ta bud'e idanunta, lokacin data bud'e su gaba d'aya sun yi ja sosae tabi Haisam da kallo tamkar mai son gane wanene shi kuma ya d'an rankwafa da kan shi sai murmushi yake mata, "Kai, wane gardi ne wannan a kai na, lafiyaaa???" da wani irin sauti tay Maganar nan take Fatuu ta bud'a baki Haisam ya d'aga ido ya kalleta gaba d'ayan su sun fahimci maganin bugar da ita yay da alama yayi mata k'arfi ne sosae, k'ara ce mashi tay waye shi ya d'age mata gira yace mata masoyinta ne ta wani k'ank'ance mashi ido fuska a tsuke, kallon Fatuu tay ta k'ura mata ido duk Fatun tasha jinin jikinta sai motsa baki take, hannu Haisam ya kai ya tada ita zaune ta jingina da kan gado yace mata ta kalle shi sosae ta kuwa zuba mashi ido, bayan wani lokaci yace mata to ta gane shi kawae sai ji yay tayi d'an guntun tsoki tace to shi d'in ne bata sani ba, murmushi yay tace wai mi ya faru ne shi kuma miya kawo shi nan, yana murmushi yace "da yake kin samu kan ki ko", kai idon ta kan Fatuu dake ta zare ido tayi tace ita kuma wannan mi akai mata tayi kuka Haisam d'in na k'ok'arin bud'e baki yay magana a rud'e Fatuu ta hau girgiza mashi kai alamar kada ya fad'i mata, yar dariya yay yace ma Hajiyar hankalinta ne ya tashi tana ta tada ita gari ya waye amman tak'i tashi, hannu ta kai ta dafe goshinta Haisam d'in yace mata lafiya tace ciwo yake mata, sannu yayi mata yace ta tashi tayi salla sai tasha magani, tambayar shi tay anyi salla ne yace eh tun d'azun, da alamun mamaki tace to wai miya faru da ita ne haka ya d'an ta6e mata baki, tunani ta shiga yi can tace mashi tana zargin furar data sha jiya ce ta sata Nauyin bacci haka don tun a parlor jiya ta fara yin bacci da k'yar ta dawo d'aki kuma daga nan bata k'ara sanin inda kanta yake ba gashi yanzu suma sun ce suna ta tada ita bata tashi ba tabbas Furar nan ce, gaba d'aya Fatuu ta rud'e sai zare ido take Haisam ya kalleta suka had'a ido yanayin fuskar shi kamar zai yi dariya, ganin tana ta Maganar furar yasa shi ce mata dama ya ta6a sata haka ne tace a'a yace to ba shi bane, da sauri tace ai dama fura na bugarwa wani lokacin fa yace to tunda tasan hakan ba Shikenan ba miye na dogon magana ta tashi taje tayi salla kawai Allah ya kyauta gaba, ganin tana ta k'ok'arin saukkowa yasa shi mik'ewa ya taimaka mata ta tashi tsaye tay mashi alamar ya bata sanda sai faman hamma take, ce mata yayi ko baccin bai ishe ta bane a k'ara nemo wani Furan ya saci kallon Fatuu suka had'a ido ta tura mashi baki yay yar dariya, duk da sandar saida ya kaita har bakin toilet don sai fad'i take jikinta ba kwari yace mata sai ta fara yin wanka taji k'arfi ta d'aga mashi kai, tura kopar toilet d'in tay yana ta fad'in tabi a hankali, saida yaga ta shige sannan ya juyo ya dawo wurin gadon ta side d'in da Fatun take idonta akan shi, zama yay a bakin gadon ya mik'a mata hannu ta matso, jawota yay jikinshi kawai sai ta fashe da kuka ya shiga rarrashinta yana fad'in ba Shikenan ba tunda ta farka, bayan tayi shiru ya tambayi ba abunda ke mata ciwo ta d'aga mashi kai alamar eh, shiru suka d'an yi kafin can k'asa k'asa da murya ya rad'a mata ta rage sauran maganin anjima da daddare a k'ara bata suje part d'in shi a zabure ta d'ago ta kalleshi kawai sai gani tay ya saka dariya aikuwa ta kai hannu ta bugi chest d'in shi ta fara k'ok'arin raba jikinsu ya matseta yana cigaba da yin dariyar yace shima ai wasa ne yayi mata ko irin wanda tay mashi tay d'an murmushi tare da lumshe ido ta maida kanta saman chest d'in nashi sosae yanzu hankalin ta ya kwanta amman ba k'aramar razana tayi ba, kai bakin shi yay saitin kunnanta cikin rad'a yace mata kar ta k'ara irin wannan kuskuren da sauri ta d'aga mashi kai kafin a hankali tace bazata k'ara ba ya jinjina mata kai. Da yake Weekend ne ana abubuwan nishad'i a gidan tuni Fatuu ta washe saidae taci alwashin ita da ta k'ara ba wani maganin bacci har a bada in dai ba patient ba a Asibiti shi ma sai in likita ne yace a bashi duk da tasan laifinta ne ita ta cika ma Hajiyar abun kuma ya had'u da shekaru, da daddare atare gaba d'aya wad'anda ke a gidan suka ci Abinci kamar dai da safe da kuma da rana, bayan sun gama cin Abincin daren sun koma part d'in su taje tayi wanka, bayan ta gama shiryawa da kayan bacci riga da wando tasa hula ta nufi Parlor wurin Hajiya da tuni ta wartsake tana zaune idanunta sanye da glass tana kallo, sannu tayi mata Hajiyar ta d'aga mata kai ta zauna itama, bata dad'e da zama ba Nameer ya shigo hannun shi ruk'e da ledojin Fura bayan sun gaisa ya d'aura akan c-table yace gashi nan Dad yace ya kawo daga haka yay masu saida safe, Fatuu ce tace mata ta d'aukko cup ta zuba mata Hajiyar ta d'an yamutsa fuska tace anya yau zata sha furar nan don gaskiya jiya itace ta bugar da ita wllh, duk sai Fatun bata ji dad'i ba ganin zata haramta mata abunda take so, wani tunani tay da sauri tace ma Hajiyar ita tana ganin ba daga furar bane k'ilan daga naman da suka ci ne ya had'u da furar shine suka bata reaction, Hajiyar tace anya sai kace dai kifi Fatun tace ai shima Naman yana iya sawa an koya masu a Makaranta Hajiyar tay mata wani kallo mai kaman harara tace to kuma shine ta bari suka ci, a dabarbarce tace ai bai cika sa wani abu ba kamar kifin ita tama dai fi tunanin k'ilan naman da aka sarrafa d'in ne keda matsala, ta6e baki Hajiya tay tace koma dai minene mai faruwa ai ta faru, da yake ranta na son furar tace mata ta zuba mata yar kad'an tasha in bata ji komai ba sai ta k'ara cike da jin dad'i Fatun tace to ta mik'e, bayan ta zuba mata ta bata itama ta zuba ta fara sha, suna cikin sha taji Hajiyar tace wai Haisam d'in ya had'a kayan tafiyar ko kuwa, d'an murmushi Fatuu tay ta sadda kai tace mata bata sani ba amman tasan k'ilan ya had'a zuwa yanzu tunda gobe zai tafi, d'an ta6e baki Hajiyar tayi sai kuma tace mata ta tashi taje ta gani in bai had'a ba ta had'a mashi in kuma ya had'a mata aiki ya tafi ya barta da wahala ita ta sani, kunya ce ta kama Fatun ta sadda kanta k'asa tana haka taji tace ta tashi taje, mik'ewa tay zata tafi Hajiyar tace to wa ta bar ma sauran furar ta d'auka taje da ita tana had'a kayan tana sha, d'auka tay sumi sumi ta wuce, a yadda take ta nufi hanyar fita daga parlon ta fuce, ta baya ta fita tana tafiya a ranta take raya gajen hak'uri gashi nan da kanta tace taje, wata zuciyar ta raya mata rabon kowa zai jigata ne tay yar dariya. Washe gari tunda Fatuu ta tashi cikin damuwa take, a part d'in Haisam tay wanka don nan ta kwana bayan ta koma part d'in Hajiya ta canza kaya, bayan sun gama yin Breakfast part d'in Haisam d'in ta koma, gaba d'aya yini yay aikin rarrashinta don sai kuka take mashi, lokacin daya dawo sallar la'asar tana zaune a bakin gadon shi itama bata dad'e da gama yin sallar ba, zama yay a bakin gadon suna kallon juna slowly ya furta mata zasu wuce don 4:30 jirginsu zai tashi zuwa Lagos yanzu yakamata su tafi don hud'u ta kusa, kai kawae ta d'aga mashi yace bazata raka shi Airport ba, a marairaice tace mashi bata son taje tay ta kuka tunda yak'i daina zuwa, kai ya d'aga mata ya kai hannu ya rungumo ta ya furta zai yi missing d'in ta sosae cikin muryar kuka tace itama, d'ago da ita yay suna kallon juna yay mata d'an murmushi ya kai bakin shi yay pecking duka kumatunta ya furta "I love you My Baby" itama tace mashi haka ce mata yay ta tashi suje ya rakata cikin gida tace mashi a'a zata zauna anan sai anjima zata koma, shiru ya d'an yi kafin yace tay mashi alkawarin ta daina kukan cikin karyayyar murya tace ai shi yake zuwa amman zata bari ya d'aga mata kai, mik'ewa yay ya nufi inda trolley d'in shi yake ajiye dama saida ya gama shiryawa sannan ya tafi Masallaci, juyowa yay ya kalleta ya furta ta kula da kanta sosae ta d'aga mashi kai tana kikkafta ido, har ya kai k'opa yaji ta kira sunan shi ya dakata ya juyo, mik'ewa tay ta nufo shi a gaban shi ta tsaya idanun ta cike da k'walla tace bari ta raka shi, murmushi yay yace indai bata so ta barshi tace a'a zata je, dama ranar k'ananun kaya ce hakan yasa ta d'aura after dress da zata zo wurin shi gyalen rigar na saman kanta, ce mashi tay ya kawo akwatin ta ruk'e ya girgiza mata kai ya kawo d'ayan hannun shi ya kama nata suka tafi, Gaba d'aya yan gidan sun fito bakin Entry Hall don yi masu rakiya lokacin da suka k'araso, harda Dad da Hajiya dasu Jidderh da Aunty ba wanda aka bari, a Jeep din da za'a d'auki Dad Aunty da Mom suka shiga sai Nameer ya shiga gaba, sai wata Jeep din Haisam ya shiga gaba Hajiya da Fatuu da Jidderh suka shiga baya sai k'aramar Mota Yasmeen da Affan dasu twins suka shiga a k'arshe kuma Hilux d'in escort ce a jere Motocin suka tafi. Bayan anje Airport d'in duk yadda Fatuu taso kar tayi kuka da zasu rabu abun yaci tura saida tayi akaita rarrashinta harda Dad a cikin masu rarrashin nata shi kan shi Haisam d'in wani iri yake jin shi, tana ji tana gani Hubby d'inta ya tafi. Bayan sun baro Airport d'in ba gida suka koma ba bazama sukai Outing, sosae suka zaga gari harda wani babban park suka je sukai ta hawa liluna iri iri ita dai Fatuu an hana ta hawa sai aikin kallo take tana nishad'i don harda Dad dasu Mom aka hau wasu lilon Hajiya dae itama aikin kallon tayi daga baya kuma suka yi hotuna, bayan sun baro park d'in wani babban shopping mall suka je nan aka ce kowa ya za6i abunda yake so, Su Mom duk kayan shafa da turarurruka suka d'auka haka Jidderh ma da Yasmeen suma cosmetics d'in suka d'auka suka had'a da Undies, Su Twins da Fatuu wurin kayan zak'i suka nufa saida suka cika basket dinsu da su Sweets, biscuits, chocolate da sauran su Fatuu sai ce masu take su barshi haka amman suka k'i wai ai harda Baby d'in su shima za'a d'aukar mawa Fatuu sai dariya take, Hajiya ita k'in d'aukar komai tay tace bata buk'atar komai Senator ne ya za6ar mata turarurruka Mom kuma ta d'aukar mata dogayen riguna da tasan tana sa irinsu harda Fatuu ta za6ar ma wasu dogayen riguna tace zata ji dad'in su nan gaba, Affan ma underwear ya d'auka sai turare da kayan zak'i, kowa dai ya d'auki abunda yake so, suna cikin shopping d'in Haisam ya kira Fatuu ya sanar mata sun isa Lagos ta hau yi mashi shagwabar tana missing nashi, anan Mall d'in suka yi sallar Magrib bayan sun gama suka shiga Eatery d'in wurin, kowa abunda yake so shi aka kawo mashi ya ci, daga nan bayan sun gama gida suka koma lokacin da suka dawo an fara kiran sallar isha kowa ya nufi part d'in shi cike da annashuwa, basu zauna cin Abincin dare ba don duk a k'oshe suke saidai wad'anda suka fara jin yunwa ne suka d'an ci harda Fatuu acici ta k'ara. Washe gari Monday da safe duk gidan ya rairaiye masu zuwa Makaranta sun tafi masu zuwa aiki ma sun tafi, Bayan Fatuu ta gama yin Breakfast na biyu don bayan da tayi sallar Asuba saida taci Abinci sannan ta koma bacci sai wuraren k'arfe goma saura ta tashi shine ta k'ara wani breakfast din, toilet ta wuce don tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin k'ananun kaya skirt d'in jeans da t-shirt kanta ta saka hula sosae tayi kyau, zama tay bakin gado bayan ta gama tay shiru gaba d'aya ta k'agara su koma Katsina don tafiyar Haisam ta k'ara sawa taji duk zaman gidan ya gundureta, hannu ta kai ta d'auki wayarta dake a gefe ta fara lallatsawa can tay tunanin kiran Fauzy don tasan lokacin anyi break, tana fara ringing Fauzyn ta d'auka suka gaisa ta tambayi jikinta, Fatun da yanayin damuwa tace mata ita fa lafiyar ta lau wllh bata jin komai hakanan take ta zama gashi anata wuce ta a Makarantar don ma tana turo mata abubuwan da akai, tambayarta Fauzy tay an yi Maganar ranar da zasu dawo ne tace mata a'a ita ba wanda yay mata magana kan hakan da Ya Haisam kawae suka ta6a yin Maganar tun lokacin da suka tafi yace ta bari zasu dawo in aka d'an k'ara lokaci gashi yanzu har Sati biyu shiru ba'a ce zasu dawo ba, shawara Fauzyn ta bata tace ko tayi ma Hajiya Maganar taji tace mata to, yar hira suka k'ara yi kafin sukai sallama, aje wayar tay a saman gadon ta mik'e ta nufi Parlor, bayan ta fito cikin parlon ta shigo Hajiya na zaune tayi wanka tana sanye da d'aya daga cikin dogayen rigunan da aka siyo mata jiya, zama tay daga gefen ta idanun su a cikin na juna da d'an murmushi Fatuu tay mata sannu Hajiyar ta amsa tace harta shirya tace mata eh, jinjina kai tay ta maida idon ta akan Tv, shiru Fatuu tay tana tunanin ta yadda zatai mata Maganar, Hajiya na lura da yadda tay sukuku can ta tsaida idanunta a kanta tace mata ya akai ne, kallon ta tay ta fara d'an kikkafta idanu a hankali ta fara magana tace dama Maganar Makarantar ta ne wurin sati biyu kenan da komawa Fauzy ta fad'i mata anata masu karatu, d'an murmushi Hajiya tay tace "to Fateema ai lafiya tafi komai ko yanzu taya zaki wannan tafiya bacin likita ya sa dokar kar ki rink'a yin zirga zirga sosae, kiyi hakuri zaki koma ne ni kaina dole tasa nike zaune Saboda ke bawai don ina son zaman anan bane" kai Fatun ta d'aga ba tare data ce komai ba saidae yanayin Fuskar ta ya d'an canza, cigaba da kallo Hajiya tay ita kuma tay shiru ta kasa tsaida idon ta wuri guda can bayan d'an wani lokaci ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom Hajiya ta maido idonta kan ta kafin ta maida su kan tv, tana shiga Bedroom d'in gado ta nufa tana zuwa ta fad'a kan shi nan da nan idanunta suka ciko da k'walla, kuka ta shiga yi k'asa k'asa ta rink'a kai hannu tana goge kwallan a haka bacci ya d'auketa. Bayan komawar su Gwaggo su Kawu Amadu suka fara shiryen shiryen zana jarabawar su ta k'arshe shi kuma Tk ya fara shirin yin bautar k'asa, tun bayan da Fauzy ta dawo Katsina bata yi waya da Sameer ba tun tana saka ran zai kira har ta fidda ita kuma bata yi tunanin kiran shi ba don bata san mi zata ce mashi ba tunda shi bai kira ba gashi ta fahimci mutane irin shi ba'a cika yi masu gwaninta ba kuma basa son shishshigi, akai akai Aunty Mareeya ke kira bayan dawowar su ta tambaye ta ko ya kira, haka in taje weekend ma taita tambayar wai da gaske bai kira ba har ce mata ta ta6a yi ta kira shi ita Fauzyn tace gaskiya bazata kira ba to tace mashi mi Aunty Mareeyar tace ta gaishe dashi, ce mata tay a'a gaskiya wannan ai zak'ewa ne, daga baya ita ma Aunty Mareeyar ta rage yawan tambayar ta game dashi, saidai sosae Fauzy ke tunanin shi duk ta zauna tay shiru sai tay ta tuno fuskar shi wani lokacin tay murmushi wani lokacin ta girgiza kai ko ta bud'o hoton shi na wurin Dinner tai ta kallo. A ranar Monday d'in bayan an tashi su Fauzy ta koma Hostel salla ta fara yi bayan ta gama ta nemi Abincin da zata ci tana gamawa ta nufi toilet tayo wanka, shiryawa tay cikin jan short skirt da bak'ar shirt mai gajeran hannu gashinta a fake, gado ta haye nan da nan bacci ya d'auketa, sai da akai sallar la'asar sannan ta tashi, bayan tayi salla jakarta ta d'aukko ta haye saman gado don tayi Assignment, bata d'auki lokaci ba ta gama ta d'aukko wani littafin ta fara yin karatu can ta aje ta kai hannu ta d'auko wayarta dake ajiye gefe, bud'eta tay ta kunna Data ta shiga WhatsApp, chat ta shiga yi da mutane daban daban harda Fatuu tana fad'i mata yadda sukai da Hajiya ta shiga kwantar mata da hankali tana nuna tasan in sha Allah bazata samu wata matsala ba a Makarantar k'ilan ma Ya Haisam d'in yayi Magana, bayan ta fita daga chat d'in Fatuu tana niyyar bud'e wani sak'o da wata k'awarta ta Funtua ta turo mata kawae taga sak'o ya shigo mata da wata bak'uwar lamba, bud'e sak'on tayi taga an rubuta, -"How are you doing?"_ iya abunda aka rubuta kenan, maimaita karanta sak'on tayi da alamun mamaki a cikin ranta ta raya to waye wannan, har zata tambaya waye sai kuma ta lura da a Dp d'in akwae hoto, hannu ta kai ta ta6a profile d'in ya bud'e ta ta6a kan hoton, har saida gabanta ya d'an fad'i ganin Mutanen dake a Dp d'in wanda mutum ukku ne kuma duk turawa ne suna tsaye a gaban wani k'aton jirgi gaba d'ayan su k'ananun kaya ne a jikinsu kansu sanye da irin hular kwanon da injiniyoyi ke sawa duk sun yi murmushi sosae hoton yayi kyau, kan Fauzy ne ya d'aure ta shiga tunanin to su waye wad'annan ita miye had'in ta da turawa kuma, zooming hoton tay yadda zata k'ara ganin fuskokin su da kyau lokacin data sauke idonta akan na tsakiyar wanda duk yafi su tsawo sannan bai kai sauran haske ba waro ido tay a fili ta furta "Sameer!" k'ura mashi ido tay ta tabbatar ma kanta da shi d'in ne kuwa, tunani ta shiga yi inane nan da sukai hoton kamar dae ba'a Nigeria bane tana haka taga kiran video ya shigo mata da lambar, d'an jimm tay ta d'age ido kafin ta daidaita natsuwar ta gabanta na d'an fad'uwa ta latsa d'auka video call d'in ya bud'e, lokacin da idanunta suka sauka akan shi wani irin bugu gabanta yay, babbar waya ta had'u da gingimemiyar waya hakan yasa tarr take ganin shi sai kace a fili, yana kishingid'e saman wani abu data kasa gane gado ne ko kujera jikin shi sanye da vest fara K'al data bayyana surar k'arfin shi don ta kama shi zanen jikin shi ya fito rad'am kai da gani kasan yana bodybuilding ga cikin shi a d'ame yake tamkar bai cin Abinci, murd'add'un damtsen hannuwan shi dake a bud'e sun bayyanar da chocolate fatar shi da take a mulke har wani sheki take alamar hutu ya zauna yadda ya kamata, wani abun mamaki kamar yadda ake gane iyayen su da Haisam ta bambancin ido to suma launin k'wayar idon su ta bambanta tsakanin shi da Haisam sai ka natsu zaka fahimta shi Sameer d'in kwayar idon shi brown ce sa6anin Haisam da take bak'a sosae saidai gaba d'aya idanun nasu farare ne tass haka ta bangaren lips d'in su na Haisam sun yi kaman peach ne shi kuma Sameer pinkish lips gare shi, kasa magana Fauzy tay sai faman motsa baki take da d'an murmushi shi kuma ya kafeta da ido hannun shi d'aya na aje gefe d'ayan kuma sai lokacin ta lura da akan pillow ne ya d'aura shi yadda yay zaman ya d'an zame da kuma yanayin yadda hannuwan shi suke zaka gane ta laptop ne yake Vedio call d'in, baida niyyar yin Magana da k'yar Fauzy ta bud'e baki tace mashi ina wuni, shiru yay mata bai amsa ba still kallon ta yake hakan yasa ta shiga yan kame kame sai lokacin ta ankare da a yadda take ko kallabi babu a kanta gashi rigar jikinta ta kama jikin ta don roba ce boobs d'inta sunyi fam gashi ko bra bata saka ba dama kuma tana dasu Tubarkallah ta wannan bangaren har tafi Fatuu don ita kuma su ta gada a wurin Mahaifiyar su da take barumaya harda ma Hasken Fauzyn duk da shima Mahaifin su barumayen ne kuma ba bak'i bane sai dai Mahaifiyar tasu tafi haske sosae don fara ce tass gasu duk ba gajeru bane hakan yasa Fauzy ke da tsawo har Aunty Mareeya ma irin giant d'in matan nan ne tana da tsawo da jiki ita ma kuma akwae k'irji Tubarkallah, "Can't you call people and greet them?" Sai da ya mula sannan ya furta mata hakan tare da d'an d'age mata gira, murmushin yak'e ta shiga yi cikin kama kai tace a'a tana ta son ta kira shi, shiru yay sai kuma taji yace miyasa bata kira ba ta shiga kikkafta idanuwa ta rasa mi zata ce, ganin ya kafeta da ido yasa tace mashi bata san ko bai son hakan bane, bai ce mata komai ba saima ya maida idon gefen da gani wani abu yake yi don hannun shi dake a kan gadon yana d'an motsawa, bin shi da ido tay tana ta k'are Mashi kallo ita sai ma yanzu take k'ara ganin kyaun shi sosae, tana cikin kallon nashi ya juyo suka had'a ido da sauri ta sunnar da kanta k'asa tana haka taji ya tambayi tana ina ne, "Ina a School" ta bashi amsa a hankali bayan ta d'ago sun sake had'a ido nashi idanun a d'an lumshe kamar dai yadda Haisam ke yi, ce mata yay yanzu nan a Class take da sauri ta girgiza mashi kai "a'a ina a Hostel ne an tashi daga Class" shiru ya d'an yi kafin ya tambayi mi take a Hostel ta bashi amsa da ai ita boarder ce, maida idon shi yay gefe yaci gaba da yin abunda yake yi wanda bata san ko minene ba, bayan d'an wani lokaci ba tare daya juyo ba yace mata ba ayin Day ne School en nasu, "A'a ana yi, ai ko matar Ya Haisam Day take ni kuma Saboda ba garin nike ba yasa nike yin boarding" sai lokacin ya juyo suka had'a ido yace mata amman ba tace tana a wurin Elder sister en ta bane, shiru tay tana kallon shi sam tama manta da tace mashi haka don lokacin da sukai Maganar a rud'e take, tana kikkafta idanu tace mashi eh haka ne amman da Weekend ne take zuwa wurin ta, shiru ya d'an yi sai kuma yace to miyasa bazata zauna a wurin ta ba, "Ai a boarding d'in an fi yin Karatu ne shiyasa" tana rufe baki taga yayi mata wani kallo mai kaman harara kawai sai ji tay yace sai dae dama in ita bata da k'ok'ari ne, waro ido tay ya d'age mata gira ya furta "Yeah" d'an murmushi tay tare da yamutsa fuska tace mashi wllh ita tana da k'ok'ari kuma sosae, tunda suka fara Maganar sai lokacin yanayin fuskar shi ya canza yay kaman zai murmushi tare da d'an ta6e bakin shi ganin haka yasa ta k'ara cewa "ai nan School d'in ma wllh mara k'ok'ari ma bai iya yin ta, da banda k'ok'ari ai da tuni ma sun kora ni tun kafin in fara karatun" yamutsa fuska yayi tare da d'an murmushi itama murmushin take tana kallon shi suna haka ya d'ago hannun shi ya d'an shafi beard d'in shi can ya furta dama ya ganta online ne shine yayi mata magana just to check on her, bata ji abunda yace ba sosae hakan yasa tace mashi bata ji mi yace ba dama tunda suka fara Vedio call d'in k'asa k'asa take jin voice d'in shi, shiru yay baida alamar zai k'ara fad'in abunda yace d'in, rantsuwa tay mashi tace bata ji ba yace mata Shikenan, marairaice mashi tay tana yamutsa fuska ta furta "Don Allah kayi hakuri wllh kaji na rantse banji mi kace ba" yanayin sautin Maganar tata da yar shagwaba tayi ta wanda ita bata san tayi hakan ba kawai sai gani tay yay d'an murmushi har gefen kumatun shi ya d'an lotsa, lumshe idon shi yay tare da yin yar hamma ya kai hannun shi ya rufe bakin bayan ya gama ya bud'e idon suka shiga cikin nata tay mashi zuru sai lokacin ya maimaita mata abunda yace d'in tay murmushi kafin tace ta gode, shiru bai ce komai ba sai ma d'age kai da yayi idanun shi a lumshe, bin shi da ido Fauzy tay sun d'an d'auki lokaci a haka can ya d'ago slowly ya fara bud'e idanun nashi suka shiga cikin nata, d'age mata gira yay ya furta "any problem?" da sauri ta girgiza mashi kai tace mashi sai anjima ya jinjina mata kai a hankali ya furta "Take care" kai ta d'aga mashi tana murmushi kafin ta kai hannu tay disconnecting kiran, bayan ta kashe kiran Murmushi ta shiga saki ba abunda take gani sai fuskar Sameer hakanan take jin komai nashi na burge ta bata ta6a zaton haka daga gare shi ba a yadda farko take mashi kallon mai girman kai, maida bayanta tay jikin bango ta d'age kai tana cigaba da sakin murmushi tana haka taji wayarta tayi k'ara alamar shigowar sak'o, sauke kanta tayi ta fara k'ok'arin duba sak'on, lokacin data ga sak'on wanda credit alert ne na kud'i dubu d'ari biyar aka turo mata gaba d'aya zaro idanu waje tay ta kai d'ayan hannunta ta dafe k'irji baki bud'e take kallon screen d'in wayar, mamaki ne ya cikata don ta gane Sameer ne ya turo su, "to ya akai ya san account number d'in ta??" Itace tambayar da ta shiga jefa ma kanta, zuciyar ta ce ta fara raya mata k'ilan lokacin da ya d'auki wayar a gidan daya kaita wanda dama a lokacin take tunanin ya d'auki number d'in wayarta can kuma ta k'ara yin tunanin ko kuma ranar da ya bata waya da suka taho a hanya ya amshi wayar tabbas a d'aya daga cikin hakan ne ya d'auka, tama rasa murna zatai ko mi don sosae mamaki ya kamata na yadda ya turo mata wannan iyayen kud'in, ta d'an d'auki lokaci tana ta mamakin kafin tay tunanin kiran shi don tay mashi godiya, sau biyu ta kira bai d'aga ba kiran na biyun ma kafin ya katse taji yayi rejecting, Aunty Mareeya ce ta fad'o mata a rai da sauri hannunta har yana rawa ta shiga kiran ta, tana yin ringing biyu ta d'auka, gaisawa sukai tay mata ya School da yake yau Fauzyn ta dawo daga Weekend, "Aunty Albishirin ki!" tana rufe baki da sauri tace "Goro d'an Governor ya kira ne? don Allah Fauziyya kice man shi ne ya kira" dariya Fauzy ta kyalkyace da ita Aunty ta buga wani tsoki a k'agare ta furta "dalla ni ki fad'i man in shine d'in ya kira" tsagaitawa da yin Dariyar tay tace mata eh ya kira, wata uwar hamdala ta saki ta fara fad'in Alhamdulillah Allah ya amsa Addu'ar da take tayi, "Ya kukai da shi da ya kira?" Cikin washe baki Aunty ta tambaya, "Kawai fa na hau online sai gani nayi an yi man magana da bak'uwar lamba na shiga cikin chat naga an tambayi ya nike to dana ga bansan ko waye ba sai na duba hoton dp naga shine ina cikin dubawar ma sai ga Vedio call ya shigo.. ......." Nan ta kwashe komai ta fad'i mata, a d'okance Aunty tace "Kai Ma sha Allah abu yayi dad'i wllh, ai kece da shegiyar kafiya wllh ba yadda banyi dake ba akan ki kira ki gaida shi amman kika k'i da yanzu an wuce wurin k'ilan anata Maganar saka rana ma, su mutane irin wannan ai ba'a masu sanya tunda dai an samu dama irin haka ma mantawa suke da mutum wllh shima nasan Allah ne ya amsa Addu'a ta ya karkato hankalin shi gare ki, to yanzu Shikenan iya gaisuwar kukai ko da wani abu?" Fauzy dake ta yar dariya tace "a'a....." bata k'arasa ba Aunty ta katseta "yace zai zo kenan?" Dariya Fauzy ta k'ara sakawa tace "ni fa Aunty bamu yi hakan da shi ba, kud'i ne ya turo man yanzu bayan mun gama wayar 500k bamma san ya akai ya samu account number dina ba amman nafi tunanin k'ilan dai d'auka yay a wayata" jin har ta gama Maganar Auntyn bata ce komai ba yasa ta kira Sunanta tace mata tana jin ta, wata uwar ajiyar zuciya Aunty Mareeya ta sauke a razane ta furta "Yar gidan Hajiya dubu d'ari biyar fa kika ce, rabin miliyan fa kenan!"cike da tabbatarwa Fauzy tace mata eh wllh gama alert d'in nan, shewa Aunty Mareeya ta saka tana fad'in "Wayyo Allah dad'i kashe ni ni Mariyatu, Yar gidan Hajiya na fad'i maki komar ki ta kamo mana gingimemen kifi wllh Manya masu babbar kyauta, wannan irin kyauta haka farko Wayar fin miliyan yanzu kuma kud'i rabin miliyan a hakan ma wai ba soyayya ake ba to inaga in an fara Soyewa kina sakar mashi kalamai ai sai baki ATM kawai wllh" dariya sosae Fauzy ke yi itama Aunty dariyar take ta farinciki, "Ina ganin yakamata a kira su Hajiya a sanar masu game da shi" da sauri Fauzy tace "a'a Aunty ni ina ganin bai kamata a sanar dasu ba...." Katseta tay cikin d'aga murya tace to Saboda me, Fauzyn tace "Saboda ban son suma su saka rai kamar yadda kika saka tunda kinga ba wani abu ke tsakanin mu dashi ba kece kawai kike ganin sona yake" ajiyar zuciya Aunty ta sauke "hakane, amman yanzu dole wani abun ya shiga tsakanin ku na fahimci in aka daka ta tashi ba ranar da zai fito ya bayyanar da abunda ke ran shi don haka ki zo gida inada Meeting da ke" Fauzy dake dariya tace duka ba yau ta dawo Makarantar ba tace eh tazo dai tana son ganinta, "amman yanzu fa yamma tayi Aunty ko a bari sai gobe in an tashi Class direct sai in taho nan" "Ok hakan yayi, yauwa in kika fito ki tsaya wurin mai gashin kazar nan na wurin Asibiti ki siyo mana dankwala dankwala guda ko ukku koma biyar sannan nasan baki rasa sanin inda ake saida su shawarma ki tsaya ki siyo mana har da pizza dasu ice cream ba sai kin siyo lemu ba tunda akwae anan ni kuma nan zan yi had'addan Abinci don wannan abun farincikin dole muyi Walima" dariya sosae Fauzy ke yi tace to sai ta turo kud'in da zata siyo abubuwan data lissafan aikuwa a hasale tace su kud'in da aka turo matan don ta kalle su ne ya turo mata, cike da ankararwa Fauzyn tace "amma Aunty an ta6a mashi kud'i kuwa....", Katseta tay "ajiya ya baki su ne, ko rok'on shi kikai, koma rok'on shi kikai sun halatta a ci su tunda ya baki" Fauzy tace "a'a Aunty kar fa a tada lissafi daga baya" tsoki ta buga tace "aita tadawar da yake ance maki shi K'aramin mutum ne, su irin su da sun ba mutum abu suke mantawa, ke in ma yace a biya shin ai muna da hali sai mu saida gonar gado" ta k'arasa tana kyalkyatar dariya itama Fauzyn dariyar take don ta gane dalilin da yasa ta sako zancen gona Saboda labarin data bata ne na Maganar gonar data yi mashi, cikin dariya Fauzy tace "Aunty ta ina ta zama gonar gado ga mai ita a raye, tace "ai shima gada yayi a wurin kakan mu ko kinga ai ta gadon ce kenan" dariya suka saka gaba d'aya daga baya sukai sallama kafin ta kashe ta tambayi to tayi mashi godiya ma kuwa ta sanar da ita yak'i ya d'auka tace ta kyale shi to sai wani lokacin in sun k'ara yin magana sai tayi mashi. A ranar da daddare misalin k'arfe goma da wasu mintuna Senator yazo kawo ma Hajiya da Fatuu Fura kamar ko yaushe, tana zaune a parlor ya shigo bayan ya zauna sun gaisa da fara'a ya tambayi yau ina yar taya ta hirar ya ganta ita kad'ai ko har tayi bacci, d'an ta6e baki Hajiya tay tace tana d'aki yau fushi take shiyasa ta k'unk'ume a cikin d'aki, cike da kulawa ya tambayi abunda yasa take fushin Hajiyar ta fad'i mashi zancen karatun ta ne so take su koma taci gaba da zuwa shine tace mata ba yanzu ba tunda ba yadda za'ai tayi tafiya mai tsawo a yanzu, d'an murmushi yay yace "ina ruwan Daughter lafiya ai tana gaba da komai, na fahimce ta tana da babbar hujja inaga abunda za'ai za'a tuntu6i Makarantar tasu in za'a iya yi man Alfarma sai taci gaba da yin karatun ta online zuwa a k'ara d'an lokaci ta k'ara samun lafiyar da zata iya yin tafiya ba tare da tunanin wata matsala ba" kai Hajiya ta jinjina mashi tace in zai yuwu to ayi hakan don ba K'aramin son karatun take ba in ba cigaba taga tayi ba ta dingi damuwa kenan kuma hakan ma na iya haddasa mata wata matsalar don ba'a son mai ciki da damuwa, kai ya jinjina mata tare da mik'ewa yace bari ya gan ta ya k'ara kwantar mata da hankali, a bakin Bedroom d'in ya tsaya yayi sallama, sau biyu yayi shiru ba'a amsa ba hakan yasa shi shiga, hango ta yay kwance ta lullube rabin jikinta da duvet nan ya gane tayi bacci, juyowa yay ya dawo cikin parlon bayan ya zauna ya sanar ma Hajiyar bacci take yace in ta tashi sai a k'ara kwantar mata da hankali in sha Allah yadda yace d'in yana tunanin zai yuwu tace to, yar hira suka ta6a kafin yay mata saida safe ya tafi. *Bayan Wata Biyu* A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji gashi cikin Fatuu har yayi wata ukku lokacin watan Haisam d'aya da rabi da tafiya, Sosae take samun kulawa a wurin dukkan Mutanen gidan ko tari tayi sai an tambaye ta lafiya, haka ta bangaren Abinci kullum ne da safe zuwa dare sai an tambayi abunda take so ta ci wani lokacin ta fad'i wani lokacin kuma tace zata ci abunda aka yi, sosae take hutawa don ko tsinke wannan bata kaudawa hakan yasa ta kara yin k'iba kumatunta sun k'aru ga wani irin fari data k'ara kamar Madara dama ita ba ja bace fara ce ta yi wani fayau ga fatarta tayi wani irin lukui lukui, ta bangaren jikinta ma hips d'inta sun k'ara saidai boobs d'inta sunfi k'aruwa sunyi fam dasu ga cikin nata har ya fito ana ganin shi ba kamar in tasa kaya da suka kamata sosae ake ganin shi, suna yin waya da Vedio call da Haisam akai akai don kullum ne sai sun yi wani lokacin wuni suke suna wayar in suna Vedio call har cikin take bud'e mashi ya gani haka Fanan ma sosae tayi murna ganin cikin ya fara fitowa tai ta kafa mata sharudd'a kan cikin ita kuma taita dariya, bangaren su gwaggo ma kullum sai tayi waya ko Vedio call da su gaba d'aya Mino ta k'osa ta dawo kullum sukai waya sai ta tambayi yaushe zata dawo, haka bangaren karatunta kamar yadda Senator yace ta Online d'in yanzu take yi har su Assignment da test duk ana mata hakan yasa ta kwantar da hankalinta, bangaren Fauzy itama tana kiran Sameer ta gaishe da shi saidai ba akai akai ba gudun kar ta zaqe saidai suna yawan yin magana ta chat wani lokacin shike fara mata magana ya tambayi yadda take da karatunta wani lokacin kuma ita ke mashi magana ta gaishe da shi sai dae tun Vedio call d'in da sukai rannan basu k'ara yi ba, Aunty Mareeya duk sukai waya ko ta koma weekend sai ta tambayi ko yace yana son ta tace mata a'a ita basu wannan Maganar da shi ba sai tay dariya tace ai sannu bata hana zuwa. Ranar lahadi lokacin cikin Fatuu ya k'ara sati guda suna zaune da daddare a parlor suna shan furar su da Dad yasa aka kawo masu don shi yayi tafiya tare da Mr. President basu K'asar dama shi na hannun daman shi ne ana hasashen ma shi ne d'an takarar shi da zai tsaida a Za6e mai zuwa, suna cikin shan furar Hajiya tace "Fateema ina ga fa barin ki zan yi anan don hankali na yayi gida na gaji da zaman Abujar nan dama Saboda ke ne in ba don haka ba ni ina zan zauna haka" idanu waje Fatuu data dakata da shan furar take kallonta har ta gama, a marairaice ta fara rok'onta kan to su tafi tare mana Hajiyar tace mata a'a tunda dai tana karatun ta lafiya lou ta zauna ta k'ara lokaci, kwa6e fuska tay nan da nan idanun ta sukai rau rau sun ciko da k'walla, tsam ta mik'e ta matsa gaban Hajiyar ta duk'a a gabanta ta fara mata magiyar su tafi tare don Allah wllh ita lafiya lau take jin ta ba abunda ke damunta in sha Allah lafiya lau zasu je, Hajiya dake kallonta tace ta tashi bata ga halin da take ciki bane zata duk'a haka, k'wallan ne suka fara zubo mata tace to don Allah zasu tafi taren, ce mata tay ta tashi ta zauna ta yunk'ura ta mik'e, bayan ta zauna cigaba da yin k'wallan tayi, ajiyar zuciya Hajiya tayi tace ita ba k'in tafiya da ita take ba kawai matsala take gudu da sauri Fatun tace "in sha Allahu Hajiya ba abunda zai faru tunda ban jin wani ciwo kuma zaki iya sawa ma Aunty ta duba ni" shiru tay tana kallonta ta cikin glasses d'inta fuskarta da d'an murmushi, tasan in ta tafi ta barta bazata kwantar da hankalin ta ba zatai ta damuwa ne dama hada k'arin hakan yasa ta zauna, ajiyar zuciya ta sauke tace Shikenan zata yi ma Dad magana kan hakan in ya amince cikin satin da za'a shiga sai su tafi dama shima jibi zai dawo, rok'onta ta shiga yi kan ai ita zata sa shi ya amincen don Allah Hajiyar nata dariya tana fad'in wai ba nan da Katsinar duk d'aya bane Fatun tace mata eh amman tayi missing d'in su gwaggo ne. Ranar talata da daddare Senator ya dawo sai washe gari da safe wurin k'arfe tara ya samu shigowa gaisawa da Hajiya ya shirya cikin galleliyar shadda light blue babbar riga da yan ciki sai hula da Agogo da takalma mahad'in kayan sai baza uban k'amshi yake, lokacin tana cikin Bedroom ya shigo bayan yayi sallama an bashi izinin shigowa, tana zaune a bakin gado jikinta sanye da cotton d'in doguwar rigar bacci Fatuu kuma na kwance itama jikinta sanye da kayan bacci riga da wando sai hula bata dad'e da gama yin Breakfast ba ta dawo ta kwanta, yana niyyar zama a kan Carpet Hajiya tace ya zauna a bakin gadon mana, tun bayan da ya shigo Fatuu ta tashi zaune idonta a kanshi tana d'an murmushi bayan ya zauna ta gaishe dashi ya amsa mata da fara'a tay mashi an dawo lpy ya amsa shima ya tambayi jikinta tace mashi Alhamdulillah, k'ok'arin sauka ta fara yi daga gadon yace mata tayi kwanciyarta ba dad'ewa zai yi ba, duk da haka saida ta sauka ta koma kan Carpet ta zauna, gaisawa sukai da Hajiya tayi mashi an dawo lafiya, bayan sun gama gaisawar ne ya fara yi mata maganar tafiyarta da suka fara ta waya tun yana can, tambayarta yay game da Fatuu yace in tana ganin ba matsala sai su tafi taren cike da zolaya tace "ai ina ganin ta zauna kawai in ta samu kaman wata biyar sai ta koma" ta k'arasa Maganar had'i da satar kallon Fatuu, tana jin haka ta yamutsa fuska idanunta sukai rau rau, ganin Hajiya na kallon Fatun tana yar dariya yasa Dad d'in shima kai idon shi kanta kawai sai ganin k'walla sukai sun zubo mata sharr da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, d'an murmushi Dad yay calmly yace "Daughter ko baki jin dad'in zama da mu ne" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ba tare data d'ago ba, "To kukan na miye?" Ya tambaya da fara'a, shiru tay bata ce komai ba ya sake cewa "Ko kina kewar yan uwanki ne?" Da sauri ta jinjina mashi kai, "Ok, ki daina kuka kin ji za'a duba in dai hakan bazai ja wata matsala ba sai ku tafi tare" kai ta d'aga mashi yace to ta d'ago yaga in ta daina yin kukan, saida ta goggoge fuskar da hannu sannan ta d'ago yana murmushi yace to yaga itama tayi ta d'an yi murmushin Hajiya dake kallonta ma ta yi murmushi, daga baya yayi sallama da Hajiyar tayi mashi Allah ya huta gajiya. Bayan fitowar shi part d'in Aunty ya nufa lokacin tana cikin d'aki ta koma ta kwanta da yake saida rana zata aiki, tana kishingid'e jikinta sanye da jallabiya kanta a bud'e yasha k'ananun kitso hannunta ruk'e da waya tana amsa kiran da shi ya tashe ta daga bacci ya shigo cikin d'akin da sallama, saida ta cire wayar sannan ta amsa mashi, nufar gadon yay ya zauna ta tashi da sauri tace ma wadda suke wayar tana zuwa, kallon shi tay da murmushi tay mashi barka da shigowa da yake a part d'in shi ta kwana sun gaisa, bayan ya amsa mata ne yay mata Maganar Fatuu yace yana son ta dubata taga in ba wata matsala zasu koma tare da Hajiya, a nutse ta fara mashi bayanin cewa a yanzu dai gaskiya lafiyar Fatun lau don tana duba ta akai akai ba wata matsala a tattare da ita sannan shi miscarriage yana iya faruwa unexpectedly koda ana kiyayewa wani lokacin hakanan ma sai ayi ita abunda take gani a barta ta bita sai a bita da Addu'a kawai tunda barin nata k'arshe zai jefa ta a damuwa ne kuma hakan ma had'ari ne a gareta, sosae tayi mashi bayani tare da nuna mashi duk abunda Allah ya k'addaro sai ya faru duk da kiyayewar nada kyau har ta bashi misali da zuwan su akwae cikin jikinta kuma k'arami ma sosae haka suka hawo jirgi kuma lafiya lou, sosae ya fahimta daga baya ya tafi. A ranar da daddare lokacin da ya kawo masu Fura Hajiya na zaune tare da Fatuu a parlor tana zaune akan kujera 3 seater ta haye saman ta gaba d'aya ta mik'ar da k'afafu gefenta bowl d'in Fruit ne tana ta sha dama bata dad'e da gama cin Abincin dare na biyu ba, da sallama ya shigo da sauri Fatun ta fara k'ok'arin gyara zama ya d'aga mata hannu yace tayi zaman ta, a kujerar kusa da Hajiya ya zauna bayan ya d'aura ledojin furan kan c-table, gaisawa sukai da Hajiyar Fatuu ma ta gaishe da shi ya amsa yana mata murmushi, juyawa yay kan Hajiya yace mata in Allah ya kaimu ranar Friday zasu tafi ta d'aga mashi kai tace Allah ya kaimu, maido idon shi yay kan Fatuu dake kallon su yace "Daughter sai a shirya in Allah ya kaimu ranar Friday zaku tafi" ba shiri ta washe baki duk dimples d'inta suka lotsa dama ga kumatun sunyi Tubarkallah da sauri takai duka tafukan hannuwanta ta rufe fuska alamar taji kunya duk sukai dariya, Maganar akwatunan ta Hajiya tay ma Senator yace ba matsala zuwa kafin su tafi za'a yi gaba da su. Tun daren Fatuu ta fara had'a kaya a ranar kwanan farinciki tayi. FRIDAY Akace komai aka sa ma rana zai zo har ma ya wuce, cike da Nishad'i Fatuu ta tashi har Fuskarta ta kasa 6oye farincikin da take ciki na tafiyar su yau ba kamar da Haisam ya sanar mata da sun koma zai zo, gaba d'aya ta gama shiryawa lokacin tafiya kawai take jira dama tun jiya Alhamis aka tafin mata da dukkan kayanta iya yar jakar kayan da zata yi amfani dasu ce zata d'auka haka Hajiya ma an tafin mata da akwatin ta iya yar jaka ce ta rage mata, da yake Friday ne da wuri yaran gidan suka dawo daga Makaranta bayan an saukko daga Masallaci a tare gaba d'aya suka ci Abincin rana a dining table kowa yaci gayun Juma'a, bayan sun gama cikin parlor suka koma harda Dad aka hau yin hirar bakwana dasu Hajiya har Jidderh na cewa ba don Makaranta ba wllh da bin su zatai taje tayi rainon Baby duk akayi dariya Mom tace da yake yazo duniya ko, Aunty ma cewa tay tana ganin Idan cikin ya kai wata takwas kamata yay ta dawo nan Abuja ta Haihu duk kowa yace haka yakamata ita dae Fatuu murmushi kawai take a k'agare take da su tafi har gani take Lokacin ma bai gudu, sai da akai La'asar sannan duk suka tashi don yin salla daga an gama kuma za'a tafi rakasu Airport.............. _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 89 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ .........Wuraren k'arfe biyar da rabi jirgin su Fatuu ya sauka a Airport d'in Katsina, Kawu Amadu da Tk da Mino ne suka zo tarbar su, Mino na sanye da riga da skirt na atampa ta yafa gyale a saman kanta sumarta a fake daga bayan kan yayi tudu sosae, gaba d'aya a k'agare take da taga Adda Fatuu din ta, lokacin da suka k'araso cikin Arrivals d'in Fatuu na sanye da Dubai Abaya fara Sol tasha adon stones tayi rolling veil d'in ta hannuwan ta sanye da yan hannunta na diamond da zobe sai k'afafun ta na sanye da takalma brown da suka hau da kalar aikin gaban rigar masu d'an tudu ne don Hajiya ta hanata saka masu tsini, in ka kalleta sai ka rantse bata san hanyar ruga ba balle har ayi zancen acan aka haifeta don gaba d'aya in ka ganta sai kace ba yar Nigeria ba ce ko kuma ace ruwa biyu, Hajiya ma na sanye da doguwar riga mai had'e da mayafi idanunta sanye cikin glasses, akan idon Mino suka shigo aikuwa da sauri ta mik'e ta nufe su da gudu Fatuu na hango su ta fara sakin murmushi, tana zuwa gaba d'aya ta tafi zata fad'a ma Fatun Hajiya tace "a hankali dai Ameenatu" hakan yasa ta dakata a gaban Fatun tana ta washe baki, hannu Fatuu ta kawo ta d'an rungumo ta bayan ta d'ago da ita tay mata sannu da zuwa tana ta murmushi ta amsa mata ta juya kan Hajiya ta gaishe da ita itama da murmushi akan Fuskarta ta amsa mata, lokacin su Kawu Amadu da Tk suka k'araso duk suna sanye da k'ananun kaya, gaishe da Hajiya sukai bayan ta amsa sukai mata an dawo lafiya kafin suka maida idanun su akan Fatuu, Tk na k'ok'arin gaishe da ita da riga shi gaishe dasu duk suka amsa sukai mata an dawo lafiya, bayan sun gama yan gaishe gaishen Tk ya amshi jakar Hajiya ita kuma Mino ta amshi ta Fatuu a tare suka nufi barin wurin sam Mino ta kasa rufe bakinta sai faman juyawa take tana kallon Fatuu da gaba d'aya ta canza mata, inda sukai parking Mota suka nufa daidai lokacin Fauzy ta k'araso cikin Keke Napep, fitowa tay tana sanye da doguwar rigar material tayi rolling bak'in veil a kanta bayan ta biya mai Napep d'in tana juyowa ta hango su Fatun cikin d'an d'aga murya ta k'wala mata kira hakan yasa Fatuu dakatawa ta juyo, nufar su tay gaba d'aya sun dakata suna jiran ta k'araso, tana zuwa ta d'an rungumo Fatuu tace "Welcome back Bestie nah" Fatun tayi mata godiya tana ta murmushi, bayan ta d'ago ta juya ta gaishe da Hajiya tare da yi mata sannu da zuwa, kallon su Kawu Amadu dake d'an murmushi tay suma tay masu sannu da zuwa Mino ma ta gaishe da ita ta amsa da fara'a, maida idon ta tay kan Fatuu da still Murmushi ne akan fuskarta ta kai hannu ta d'an ja kumatunta ta furta "Wannan kumatu haka da kika aje Tubarkallah ko dai ke kike cinye Abincin gidan ne" tana rufe baki Hajiya ta bata amsa da "kamar kin sani" duk sukai dariya, ce masu Hajiya tayi su je a k'arasa gaisawa a gida duk suka juya, ganin Motar kamar bazata ishe su ba yasa Fauzy cewa bari ta samu Napep sai ta bi bayan su Kawu Amadu yace lafiya lou zata isa bari su zauna a gaba shi da Mino, bayan duk sun shiga cikin Motar Hajiya da Fatuu da Fauzy ne a baya suka tafi. Lokacin da suka iso Unguwar su suna zuwa gab da gida Mino ta kira Gwaggo a waya ta sanar mata gasu sun dawo don da harda ita za'aje tarbar su to sai taga Motar bazata isa ba in aka d'aukko su hakan yasa ta fasa zuwa tace masu in sun dawo sai su sanar mata, A daidai bakin gate Motar ta tsaya su Officer suka taso da sauri suka zo bakin Motar aka zuge glass d'in cikin washe baki suka hau yi masu sannu da zuwa duk suka amsa, bayan an zuge gate d'in suka kutsa cikin gidan, part d'in Hajiya ya tunkara tace mashi ya kaisu cikin parking space kawai yadda ba sai yasha wahalar maido Motar ba tama mik'ar da k'afafunta, lokacin daya parker Motar Officer Jamil mijin Saude ya k'araso da sauri ya bud'e k'opar side d'in da Hajiya take Fauzy ta bud'e ta d'ayan side d'in haka su Kawo Amadu ma duk suka firfito, k'ara gaishe da Hajiya Officer yay cikin washe baki tayi mashi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah kafin yace sun yi kewarta sosae cikin Fara'a tace "to ai gani na dawo kewa ta k'are ko" yana yar dariya yace hakane, kallon Fatuu yay ya yi mata ya jiki tace Alhamdulillah, tambayar akwai kaya yayi Hajiya tace mashi ba wasu kaya duk anyo gaba dasu ya je kawai yace to tare da yi masu Allah ya huta gajiya ya nufi komawa gate, har zasu fita daga cikin wurin Hajiya ta kai idonta kan wata Mota dake a lullu6e da tamfal, dakatawa tay ta nuna Motar da sandar ta tace ma Tk wannan fa yace mata Tahir ne ya kawo ta kusan fin wata kenan yace Ya Haisam ne yace ya kawo, jinjina kai tay tace ko Mota ya canza ne Tk d'in yace bai sani ba, kallon Fatuu tay tace "Mijin ki ya fad'a maki yayi sabuwar Mota ne" shiru ta d'an yi kafin tace a'a bata san ko tashi bace amman dai ya nuna mata hoton motoci yace ta za6a tun ranar da su gwaggo suka dawo Hajiyar tace to k'ilan tata d'in ce, da sauri Tk yace bari ya bud'e taga in itace yace ma Amadu ya kama mashi, lokacin da suka bud'e Motar har saida gaban Fatuu ya fad'i ganin jigunannar Motar matsayin tata don ta shaida wadda ta za6a d'in ce, gaba d'aya maido idanun su sukai kan Fatuu suna son jin tata d'in ce saida Tk yace mata itace sannan ta d'aga mashi kai alamar eh jiki a mace, da tsananin mamaki duk suka shiga bin Motar da kallo don ta had'u dai ba k'arya, "Yanzu kina nufin wannan jibgegiyar Motar taki ce?" Amadu ne ya tambayi Fatun da mamaki, murmushi kawai take ta kasa magana don itama sosae taji Al'ajabin ganin Motar a matsayin tata, Hajiya ce tay d'an murmushi tace "tunda ta fad'a tata d'in ce, ai ba abun mamaki bane Ahmad, ko kamanta Mijinta sune Mota" Murmushi yay tare da jinjina kai Hajiya tayi mata Allah ya sanya Alkhairi suma suka shiga yi mata Mino sai washe baki take tana ta6a jikin Motar haka Fauzy ma taji ma Fatun farinciki sosae, Saude ce ta k'araso wurin don bata san sun iso ba tana d'akinta acan baya saida Officer ya kirata yay mata Albishir d'in dawowar Hajiyar, cikin washe baki ta gaishe da ita tare da an dawo lafiya Hajiya na murmushi ta amsa tay mata ya gida Sauden tace "gidan duk ba dad'i wllh da baku nan" yar dariya Hajiya tay tace to ai gata ta dawo sai su dasa daga inda suka tsaya Saude ta fad'ad'a dariyarta, kallon Fatuu dake kallonta tana mata murmushi tay suka gaisa itama tay mata an dawo lafiya da ya k'arfin jiki, maida idonta tay kan Motar da taga ana kallo Hajiya tace mata wai Motar Fateema ce suka tsaya kallo Sauden tace "Ma sha Allah, ashe ta Fateema ce amma dai Motar tayi kyau wllh" kallon Fatuu tay tayi mata Allah ya sanya Alkhairi ta amsa tana murmushi, nufar barin wurin Hajiya tay tana fad'in ita dai ta wuce in sun gama ganin Motar sun shigo Saude ta bi bayanta, tana barin wurin Mino ta had'e hannuwanta ta hau yin d'an tsallen Murna tana fad'in yanzu wannan Motar ta Adda Fatuu ce, dafa Shoulder d'inta Fauzy tay suka kalli juna tace mata ta taya ta murna wllh Allah ya sanya Alkhairi ya tsare ta amsa da Amin tare da Fad'in " kema Allah ya maida ke a damshi na" Fauzy tace "Wai.....to Amin dai" duk sukai yar dariya, "Ikon Allah, Yanzu wannan bugaggar Motar ta wannan yarinyar ce da aka raina tare da ni" Kawu Amadu ne ya fad'a yana ta tatta6a Motar don ba K'aramin tafiya tay da shi ba duk sukai dariya Tk yace "baka ji ance dare d'aya Allah kan yi Bature ba" da sauri Amadu ya jinjina kai "tabbas na shaida hakan akan yar fillo" duk suka kwashe da dariya, cikin washe baki Mino tace yakamata a d'ana su, Tk yace yanzu tunda yamma tayi kuma ga su Fatuu basu dad'e da dawowa ba a bari sai gobe tunda Weekend ne sai su zagaya gari cike da murna tace to, fitowa sukai daga cikin parking space d'in suka nufi part d'in Hajiya sai santin Motar suke ba ma kamar Amadu har Tk na fad'in ya lura dae Motar tayi mashi yace wllh ai ta had'u ba k'arya, "kuma kasan Motar can fa zata iya yin miliyan Ashirin wllh" Tk ne ya fad'a duk suka waro ido bama kamar Fatuu sai yanzu ta gane dalilin da yasa Haisam yak'i fad'i mata kud'inta, sosae suka jinjina kud'in Motar har Amadu na rok'on Fatuu akan wai tace a canzo mata guda biyu daidai kud'in wannan sai ta bashi d'aya harda cewa shi ko ma ba mai kud'i ba tata tafi tsada don Allah duk sukai dariya lokacin suka k'araso bakin entrance suka shige, lokacin da suka shiga Hajiya na zaune akan 2 seater gabanta Sofa table ne Saude ta kawo mata bottle water da cup har ta sha Saude na zaune kan one seater daga can gefe suna hira, ciki suka k'araso kowa ya samu wuri ya zauna aka cigaba da yin hirar, bada Jimawa ba gwaggo ta shigo da sallama tana sanye da dogon hijab Navy blue da ta fito da hasken ta sosae, da murmushi ta k'araso ciki duk idanunsu na akanta Fatuu na ganinta ta mik'e da sauri ta nufeta tana ga gwaggonta, tana isa gwaggon ta tareta ta hanyar ruk'e ta tana mata murmushi, a shagwabe tace "Don Allah gwaggota ki bari in rungume ki wllh nayi missing d'in ki sosae" yar dariya gwaggo tay Fatun ta k'arasa fad'awa jikinta, d'agota tay suka nufo ciki gwaggo na yar dariya Hajiya tace "ai ni dai bansan ranar da Fateema zata girma ba wllh, ga dai girman ya kamata amman tak'i ta gane" duk akai dariya, zama gwaggo tay ta shiga gaishe da Hajiya tare da yi mata an dawo lafiya bayan sun gama gaisawa Saude da Fauzy duk suka gaishe da ita da fara'a ta amsa masu, juyowa tay ta kalli Fatuu data sak'alo hannunta ta rungumo kafad'ar gwaggo suka bi juna da murmushi, "Gwaggo kinga Kumatun Adda Fatuu kamar an tura biredi ko" Mino ce tayi Maganar duk suka kwashe da dariya, Saude tace ma Hajiya table a shirye yake ko ta kawo Abincin nan ta d'an girgiza mata kai "ni kam dai a k'oshe nike saida muka ci muka k'oshi muka taho kuma a jirgi ma mun ci Snacks sai dai ko su Ameenatu in zasu ci k'ilan kuma uwar biyu taci don ba mamaki ta fara jin yunwa yanzu" a d'okance Mino tace "Adda Fatuu yan biyu zata Haifa" d'an yarfa hannu Hajiya tay tace "wama ya sani, in don ta Abincin da take ci ne in akace yan hud'u ma zata Haifa ai ba'a gardama ba" duk akai dariya, "Ga shi kun zo tarbar baki mu kuma ko tsaraba ba mu yi ba" duk suka ce a'a ba komai Hajiyar ta sake cewa "ai ko ba don ku ba ma dole in nemo tsaraba kafin yaran unguwa su fara shigowa" Saude tace aikuwa kullum ne akai akai ake shigowa tambayar Hajiya ta dawo, "Ai na sani, bari kiga asan na dawo yanzu a cika parlon anzo yi ma Hajiyar sanata sannu da zuwa" in ji Hajiya, Fatuu ce tace tana da su biscuits da chocolates a cikin kayanta da akayo gaba dasu sai a basu, tana rufe baki Hajiya tace "a'a ruk'e abun ki ban shirya ma rikicin mai juna biyu ba, yanzu in amsar maki abu kizo ki burkice man ke sai irin su kike so ni ina zan nemo maki su tunda ga Ahmad nan yaje shago ya kawo man hankalina a kwance" gaba d'aya aka sa dariya harda Fatun, mik'ewa gwaggo tay zata tafi tay ma Hajiya Allah ya huta gajiya zumbur Mino ta mik'e tana fad'in suje taga hadaddar Motar da aka Siya ma Adda Fatuu, da alamun mamaki tace Mota tayi kenan Amadu yace "Mota kam mai sunan Mota wllh" murmushin farinciki gwaggo tay kafin tayi Allah ya sanya Alkhairi ta juya kan Hajiya ta hau yin godiya Hajiyar tace "to miye na yin godiya kuma Dije don miji ya siya ma Matar shi abu, nima bansan da ita ba sai yanzu da na gani, kinsan ya samu sabbin jini ya watsar da ni" duk akai dariya Gwaggo tace aikuwa dole zai dawo mata don da tsohuwar Zuma ake Magana Hajiya ta ta6e baki tace bata so ta yafe masu shi, k'ok'arin mik'ewa tay itama tana fad'in bari ta shiga ciki Magrib ma ta kawo jiki, a tare da gwaggo duk suka fito suka nufi parking space, Tk da Amadu ne suka bud'e mata Motar ta gani ta hau yin faffad'an murmushi Mino tace "gwaggo ya kikab ga Motar?" jinjina kai tay tace "Ma sha Allah, tayi kyau sosae wllh, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya kuma tsare" duk suka amsa da Amin harda Fatun, Amadu ne yace ta matso ta ta6a tasa Albarka Mino harda fad'i mata kud'in da Tk yace Motar take sosae gwaggo ta jinjina kud'in, bayan ta gama gani an maida an rufe suka fito daga cikin parking space d'in Tk yay masu sallama ya nufi baya inda d'akin shi yake, Fatuu tace ma gwaggon tazo suje part d'in ta tana murmushi tace tayi mata mi tace su k'ara gaisawa sai tayi salla a can, girgiza mata kai tay tace ta dawo wani lokacin a shagwabe tace ita da ba wani zuwa take ba, magiya ta fara yi mata gwaggon tace bafa zata je ba tunda dai sun gaisa, sallama sukai da ita ta tafi tare da Amadu su kuma suka nufi part d'in su Fatuu, A bud'e kopar parlon take, lokacin da suka shiga wani irin k'amshi mai dad'i had'e da sanyin Ac ne suka tarbe su, parlon tsab da shi yasha gyara a wurin Saude, saman L-shape suka zauna wani irin farinciki Fatuu ke ji ganin ta a parlonta sosae tay missing part d'in nata, cire veil d'inta tay ta aje gefe Fauzy ta kalli kanta tace ba dai ta son kitso Fatun ta d'an yatsina baki tace wllh kitso takura mata yake, Fauzy tace harda don yana da yawa ne gashin ga kuma tsawo, hannu takai ta dafa Shoulder d'in Mino tace "Amaryar Nameer Ali Zakee ya Angon naki halan ana ta shan love?" dariya Mino tay sai kuma ta mik'a mata wayar hannunta wadda Samsung ce, bayan ta amsa Jujjuya ta tay tana k'are mata kallo kafin tace "Amman dai tayi kyau wllh, itace Wayar da aka Siya maki d'in" tay Maganar idonta akan Mino, d'aga mata kai tay "eh, 300k ya turo sai Kawu Amadu ya siyo man, rannan ma ya k'ara turo man 200k" d'an waro ido Fatuu tay tace "Lalle Nameer ba K'aramin ji yake da ke ba, shi da yake d'alibi yake turo maki kud'i haka, koda yake yi mashi komai ake gara shima ya fara hidiman iyalin shi" duk sukai dariya, "K'awata ke kuma ya ake ciki tsakanin ki da Sameer ince ko an samu cigaba kun fara shan love ku ma?" Yar dariya Fauzy tay kawai ba tare data ce komai ba, hannu Fatuu ta kai ta d'an bugi shoulder d'inta tace don Allah ta fad'i mata ya ake ciki, "To ni mi zance maki ai duk abunda ake ciki kin sani, har yanzu yadda kika sani muke muna dai gaisawa yaji ya nake shikenan" d'an jinjina kai Fatuu tay "ba komai ai anyi mai wuyar tunda kunsan juna duk ya gama nuk'u nuk'un shi zai fito ya bayyana abunda ke ran shi ne ai sannu bata hana zuwa zamu yi ta zuba mashi ido har muga gudun ruwan shi" Fauzy na dariya tace haka Aunty Mareeya ke cewa, "Allah sarki Aunty Mareeyata itama nayi missing d'inta Sosae wllh" Fatuu ta fad'a tana murmushi, Fauzy tace "kinsan kuwa da tare da ita zamu zo Airport don har ta shirya kawai sai tayi bak'uwa amma tace in maki sannu da zuwa sai tazo har gida" Fatun tace zama ta kirata kuma zata je har gidan ba sai ta zo ba. Sai da aka kira sallar Magrib sannan suka tashi suka nufin Bedroom, Fatuu ce ta fara yo Alwala sannan Fauzy ma ta shiga, ganin har zasu kabbara Mino na zaune yasa Fatuu dakatawa tace mata ita bazata tashi tayi sallar bane tay mata murmushi kawai, tambayarta tay bata yi ne ta d'aga mata kai Fatun ta d'an ta6e baki ta kabbara, suna gama sallar Saude ta zo ta sanar dasu ga Abinci can ta kawo kan table da sauri Fatuu ta mik'e daga kan prayer mat tana fad'in "Allah yay maki Albarka Aunty Saude kamar kinsan yunwa nike ji wllh" duk sukai dariya, bayan sun cire hijabs da sukai sallar gaba d'aya suka nufi parlon. Bayan sun yi sallar isha Fauzy ta mik'e tana fad'in bari ta tafi dare yayi Fatuu tace ta tsaya ta kwana mana, "Kwana kuma?" Fauzyn ta fad'a tana yar dariya, Fatun tace eh, "a'a gida zan tafi abu dai ana gari d'aya miye na in kwana kuma" Fatuu tace to ai wanda take mawa dai baya nan kuma Mino ma anan zata kwana, shiru Fauzyn tay Fatuu ta k'ara cewa "Ke Allah ma sai kin kwana, dama bakuyi man kwanan Amarya ba to shi zaki biya ni" gaba d'aya suka sa dariya, "To ai dama yanzu Kusan so ake a kashe kwanan gidan Amarya in an kaita wasu garuruwan ma dama ba'a yi don haka ba sai na biya ba" kafewa Fatuu tay kan ta kwana tace to ai bata tambayi Aunty Mareeya ba, hannu Fatuu ta kai ta d'aukko wayarta tana fad'in abu mai sauk'i in don wannan ne bari ta tambaya ma da kanta, tana fara ringing Aunty ta d'auka, "Yar gidana ta kaina an dawo lafiya" tana murmushi ta amsa mata da lafiya lau, "To ya jiki jikin?" Amsa mata tayi da Alhamdulillah, tace "anata laulayi kenan halan ma har ya fito?" k'asa k'asa ta bata amsa da eh, "ma sha Allah, Allah ya inganta mana, ai naso in zo tarbar ki wllh sai nayi bak'uwa" tace haka Fauzy ta fad'i mata ai ba komai, tambayarta tay ya mijinta yana can K'asar turawa ko tace mata eh tace to Allah ya maido shi lafiya, bayan ta amsa tace mata dama so take ta roketa don Allah Fauzy zata kwana anan, da sauri Aunty tace "kai haba ba komai Zarah ta kwana, nan gaba ma kad'an ai sai kin fini iko da ita in ta zama Matar d'an uwan mijin ki d'an Governor don ma d'an bantan uban izza ta hana ya fito ya bayyana da yanzu k'ilan Maganar aure ake tunda da gani son ta yake wllh ba don haka ba yaushe zata samu ma ya rink'a kula ta" dariya Fatuu tay tace haka Fauzy ta fad'a mata har yanzu yak'i bayyanawa, a k'ufule Aunty tace "k'yale shi yayi ya gama ai ina nan ina jiran shi ya shigo hannu sai ya rabu da wannan cutar miskilancin don shi sai yama fi mijin ki magantuwa" dariya sosae Fatuu ke yi bayan ta tsagaita tace to shima na Mino a had'a da shi da sauri tace "ahhh anya Zarah, shi ai kinga baida irin cutar su ta miskilanci bawan Allah bakin shi a sake yake adai kamanta don in akai mashi irin nasu ba wuya zai zare" wata uwar dariya Fatuu ta kyalkyace da ita har Fauzy na fad'in ta dai bi a hankali kar tasa Babyn su ya fito, bayan sun gama wayar tay mata godiya suna yin sallama da sauri Fauzy tace bari tayi mata magana, bayan ta bata wayar a d'okance tay ma Aunty Mareeyar Albishir d'in Motar da aka Siya ma Fatuu, wata uwar gud'a ta rangad'a tace taba Fatuu wayar, "Da kyau yar gidana, Wllh na taya ki murna Allah yasa Alkhairi ya tsare ya kuma raba lafiya, Wannan in dai za'a rink'a bamu kyautar Mota haka ai duk shekara sai mun haifa masa Baby" dariya kawai Fatuu ke yi tace mata sai tazo d'ani Fatun tace ai suna nan zuwa gobe da Motar a nuna mata tace to Allah ya kaimu tana jiran su, bayan sun gama wayar Mino ta kira Yadikko ta sanar mata zancen Motar sosae tay farinciki tasa aka ba Fatuu wayar ta taya ta murna da Addu'oi daga jin muryarta ba K'aramin farinciki take ba, tambayarta Fatun tay baffan su tace bai kaiga dawowa ba amman da ya shigo zata sana'ar mashi suka cigaba da yin wayar ta tambayi ya suka dawo da lafiyar Fatun duk ta amsa mata daga baya sukai sallama tana ta masu Addu'oi, bayan ta aje wayar mik'ewa tay har lokacin rigar da ta dawo da ita ce tace ma su Fauzy bari ta shiga tay wanka suka ce to kowannan su na latsa wayar shi, daga baya Mino ma ta mik'e tace bari taje gida ta canzo kaya Fauzy tace to bari ta rakata suka tafi tare, After some minutes ta fito d'aure da towel a k'irjinta ganin ba su Fauzy a cikin d'akin yasata yin tunanin ko sun tafi parlor suyi kallo, shiryawa ta shiga yi cikin silky kayan bacci riga da wando blue bayan ta gama saka kayan ta feshe jikinta da turare, tana cikin gyara gashinta wayarta dake a saman side drawer ta fara ringing ta juya ta nufeta, saida ta zauna a bakin gado sannan ta kai hannu ta d'auko, ganin mai kiran nata yasa ta saki k'ayataccen murmushi dama da suna Airport a Abuja sun yi waya da shi, idasa hayewa tay saman gadon sannan tayi picking, tana d'auka taji yace suyi Vedio call tace to, yana zaune a cikin Office d'in shi jikinshi sanye da blue suit shirt d'in ciki fara ce sai bak'in bow tie sosae kayan sukai fitting d'in shi sumar shi a gyare luff, murmushi suka shiga sakar ma juna kafin ta gaishe da shi ya amsa yay mata sun dawo lafiya tace lafiya lou, tambayar ta Hajiya yay tace tana part d'inta su sun dawo nasu part d'in da Fauzy da kuma Mino ya jinjina mata kai still da murmushi a fuskokin su, "What are u doing?" Ya tambaya idanunshi a d'an lumshe ta bashi amsa da wanka tayi yanzu ta gama shiryawa ya kira, shiru yay yana ta kallonta can ta tura mashi baki ya d'age gira "What?" A shagwabe tace "shine don kasan Mota d'in nan tana da kud'i sosae kak'i fad'a man ko" shiru yay yanata murmushi tace yayi Magana mana, tambayarta yay waya fad'i mata mai kud'i ce tace ita ta gane data ganta, "nayi laifi kenan?" ya k'ara d'age gira, a shagwabe tace "a'a, kawai dai naga akwai wasu hidindimun bai kamata ka siyan man mai tsada ba sosae" yana murmushi yace "anything for you Baby ko banda halin abu indae kina so zan yi bakin k'ok'arina ki mallake shi wannan kuma ina da halin shi ne in ma fin shi kike so zan siya maki" wani kalan murmushin dad'i tayi ta lumshe ido irin yadda yake yi bayan ta bud'e a tare suka sa dariya, "Where is our Baby, ya fara kicking?" waro ido tay ta d'an bud'e baki sai kuma ta saki dariya tace ai bai isa wannan ba ko abunda ko antenatal bata fara zuwa ba, tambayar ta yay sai yaushe zata fara zuwa tace kaman in yayi 4 Month amman ko yanzu tunda ta ya wuce 3 months zata iya fara zuwa ya jinjina mata kai, shiru suka d'an yi sai kuma tace bari babyn yaga Daddy d'inshi ta kai hannu ta d'aga rigarta farar fatar cikin da ya turo ta bayyana ta kai wayar saitin cikin, Kusan kullum ne in sukai waya sai yaga cikin wani lokacin shi ke cewa ta nuna mashi wani lokacin kuma ita ke nuna mashi kamar yanzu, maido wayar tay saitin fuskarta tana dariya shima ita yake yi yace mata yaga ya k'ara girma tace eh ai bata dad'e da gama cin Abinci ba taci ta k'oshi stiil yar dariya yake yace ai an fad'i mashi Abinci take ci sosae, jin haka yasa ta fara bashi labarin yadda a kai ta mamaki wai tayi uban kumatu harda Maganar da Hajiya tayi d'azun tace Saboda cin Abincin da take ko yan hud'u akace zata Haifa ba za'ai gardama ba dariya yay itama ita take yi, bin juna da kallo su kai mai cike da tsantsar k'auna bayan sun lafa da dariyar sun koma yin murmushi, "Yar fillo zata Haifa yaron Ya Handsome" suna cikin kallon junan taji ya furta hakan, dariya ta k'ara sakawa ta kai hannu ta rufe idanunta alamar kunya can ta cire idanunshi akanta yana murmushi tace mashi mamaki yake a hankali ya girgiza mata kai alamar a'a, tambayar shi tay yaushe zai zo d'in yay d'an jimm kafin yace mata yay postponing lokacin sai nan da 3 weeks, k'amewa tay tana mashi wani kallo ta tsuke fuska yay d'an murmushi, yamutsa fuska ta shiga yi kaman zatai kuka tace ita dae bata yarda ba kenan ma bai yi missing d'inta ba an kusa fa wata biyu da tafiyar shi kuma shine yanzu zai ce ya d'aga lokacin da zai dawo, sigh yay yace itama tasan ko bai fad'i mata ba yana missing nata in every second yana jin kewarta a tare da shi, "To miyasa ka d'aga dawowar" ta tambaya a shagwabe, hannu ya kai ya shafi gaban kanshi calmly yace mata an kusa bikin Saleem ne shine ya bari sai lokacin yazo so that he can stay a bit long, k'una k'unin shagwa6a ta shiga yi tana jujjuya kai ya hau bata hak'uri yana d'an murmushi, ganin tak'i barin abunda take yi yasa shi ce mata "Ok, in kina so in zo this coming week zan zo but bazan dad'e ba zan dawo tunda ina son zuwa bikin Saleem d'in amman hakan zai sa a ga na fara wasa da aiki tunda ban dad'e dana dawo ba kuma kinga na d'au lokaci anan" dakata tay da abunda take yi na shagwabar tace "Shikenan to na yarda ka bari sai lokacin ka zo amman fa sai ka maimaita man lokacin da kayi anan in kazo wata biyu da rabi zakai sannan ka koma" ta k'arasa ta d'an kumburo baki, yar dariya yay yace tayi mashi hak'uri kar tasa a kore shi a wurin aiki, kafin ta bashi amsa taji an turo k'opar bedroom d'in ta d'aga ido, Fauzy ce ta lek'o suka had'a ido tay mata murmushi, juyawa tay ta koma dama sun dawo ne shine ta lek'o taga mi Fatun ke yi, "To ba Shikenan ba in sun kore kan sai ka baro masu K'asar su ka dawo nan kawai" ta bashi amsa, d'age gira yay "to in na dawo ya zamu rink'a samun kud'i?" da sauri tace "to mi zamuyi da kud'in tunda muna da komai" yana yar dariya yace ta ta6a ganin rayuwa ta yuwu ba kud'i dole ai su buk'aci abubuwa kaman Abinci, kaya, da kuma kud'in yin wasu hidindimun gashi ma zata haihu dole su buk'aci kud'i, nok'e kai tay tace "to ba sai Hajiya dasu Daddy ba su rink'a mana wannan" fad'ad'a dariyar shi yay itama dariyar take yace mata ta dai bari gara su nemi nasu yadda bazasu takura ma kowa ba har a gaji da su, "to ai zaka iya samun wani aikin ma anan ko da baka fara ba kafin ka tafi" d'an rolling eyes d'in shi yay yace mata ai anfi samun kud'in sosae anan, tambayarshi tay wai dama Saleem bai yi aure ba yace eh an dai dad'e da akai engaging nasu to wadda zai auran tana karatu a London da za'ai auren sai tayi completing karatun a gidan shi daga baya kuma sai aka bari ta gama don shima Saleem d'in yaje ya k'aro karatu sai yanzu za'ai Auren, jinjina kai Fatun tay suka cigaba da hirar su ta k'auna, ganin ta fara hamma yace bari ya barta tayi bacci kar a takura ma Baby tay yar dariya, tambayarta yay ko akwae abunda take buk'ata da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh yace miye take so, ce mashi tay irin tuwan Madara da gullisuwa da Popcorn d'in da yake siyo mata take son ci yace Ok zai ma Nana magana sai a kawo mata tomorrow, jin sunan Nana yasata tambayar wai tana nan yace eh, ta tambayi har yanzu bata yi Aure ba yace eh amman anyi engagement, "Allah sarki na taya ta murna wllh, kai dai ai ka k'i ta" ta fad'a tana murmushi, shiru ya d'an yi sai kuma yace ai lokaci bai k'ure ba in tana son ya auretan da yayi Magana yasan za'a fasa da wanda aka sa masu rana sai ayi dashi, wani kallo tay mashi a d'an k'ufule tace "to a'a wllh, ba kasan da wasa nike ba" yadda ta yi ne ya bashi dariya yace "tunda tana sona da ki bari in k'ara da ita kinga kema kin yi man Alfarma irin na Fanan" yana rufe baki da sauri ta hau yamutsa tana girgiza kai tare da yarfa hannu tana fad'in "Don Allah Hubby mu bar Maganar nan, tunda an sa mata rana ba Shikenan ba nima dama ai wasa nike ko" dariya kawai yake ganin yadda tay k'utun k'utun da rai sai kace ba ita ta ja Maganar ba, ganin irin kallon da yake mata yasa taci gaba da fad'in "Allah ka gama aure, ba wata da zaka k'ara aura mu biyu mun ishe ka" dariya ya k'ara yi har jerarrun hakoransa suka bayyana sosae ita kuma taci gaba da yamutsa fuska tana k'una k'unin Allah bazai k'ara aure ba, "Ki kwantar da hankali, tunda na same ki Baby na gama aure am just teasing you" wani irin murmushin jin dad'in Maganar ta shiga saki harda d'age kai sama, sauke kan nata tay idanunta suka shiga cikin nashi a wani slow ta lumshe mashi ido ta furta "Ina son ka har abada abadan abada Hubby" shima lumshe mata idon yay cikin cool voice d'in shi ya furta "You are the best thing that has ever happened to me Baby, you made me feel complete" murmushi kawai take saki looking at him with much luv, sallama sukai yace ta kwanta shima sun samu break ne zai yi lunch tace to ai duk yama cinye lokacin suna hira yana murmushi yace ba wani abu ai ko bai ci komai ba ganinta da yayi ya k'osar dashi tana dariyar jin dad'i tace duk da haka dai yaje ya ci Abincin kuma Baby yace ya tabbatar yaci ya k'oshi, yace a fad'i ma Babyn Dad d'in shi zai bi umarni gaba d'aya sukai dariya daga haka suka gama Vedio call d'in, kwance tay saman gadon tana ta faman sakin murmushi wani irin nishadi na ratsata ita kanta tasan ba K'aramin so take ma Haisam ba a yadda take ji yanzu da suka zama d'aya she can't survive without him, a haka bacci yay awon gaba da ita, bada jimawa ba Fauzy ta shigo don tayi wanka ganin yadda Fatun tay bacci yasa ta yin d'an murmushi, saida ta tashe ta don ta gyara kwanciyar ta sannan ta nufi hanyar laundry, d'aure da towel a kirjinta ta fito ta nufi gaban mirror don ta shafa mai bayan ta gama ta nufi closet ta bud'e, wata doguwar rigar baccin Fatuu ta fiddo don ta saka, tana gama shiryawa Mino ta shigo ita dama tun a can gida da suka je ta shiryo cikin kayan bacci riga da wando, gado ta nufa tana fad'in wllh bacci take ji Fauzy data juya tana kallonta tace ta hak'ura da ganin k'arshen film d'in kenan tace eh ai taga basu da niyyar gamawa daga haka ta haye gadon ta ja duvet ta lullube, bakin gado Fauzy ta nufa ta zauna tay shiru, gaba d'aya ganin Fatuu da ciki ya k'ara mata jin son yin aure, dama dalilin auren Fatun taji ta fara sha'awar itama tayi, "gashi ba mijin..." wata zuciyar ta raya mata har saida tay yar dariya, ita gaba d'aya ma ta kasa gane ko tana son Sameer kawai dai tasan yana burgeta, wayarta dake ruk'e a hannunta ta bud'e ta fara latsa ta, gallery ta shiga ta bud'e inda hotunan bikin Fatuu suke ta bud'o wani hoton Sameer da aka yi mashi a wurin Dinner dama tana yawan kallon hoton, k'ura mashi ido tay yana a hakimce kan kujera fuskar nan ba annuri a cikin Zuciyarta ta shiga raya shin da gaske yana sonta, in hakane to miyasa yak'i bayyana mata, kai anya ma kuwa ita sam bata tunanin hakan gaskiya don tana ganin bata kai ya so ta ba, "in yanzu yazo yace yana son ki zai aure ki zaki amince?" wata zuciyar ta jefo mata tambayar tay shiru kamar mai nazarin wani abu lokaci guda jikinta yay sanyi tunowa da wasu abubuwa, fita tayi daga wurin hoton a sanyaye ta mik'e ta nufi bedside table ta aje wayar har zata juyo ta dakata ta kai hannu ta kunna lamp sannan ta juyo, wurin Switch ta nufa ta kashe hasken d'akin kafin ta juyo ta dawo wurin gadon ta haye gefe ta yadda sun saka Fatuu a tsakiya, lamo tay tana ta zancen zuci ta d'auki lokaci a haka kafin daga baya bacci ya d'auketa. Washe gari bayan sun yi sallar Asuba komawa Fauzy tay ta kwanta Fatuu kau Kitchen ta nufa don ta samu abunda zata ci ita kuma Mino dama bata tashi ba don ba sallar take ba, sauran Abincin da suka ci jiya data ga bai yi komai ba ta d'umama sai ta had'a da tea, anan cikin kitchen d'in ta zauna taci bayan ta gama ta koma d'akin itama ta koma ta kwanta, wuraren K'arfe takwas saura Mino ta farka lokacin su Fatuu nata shan bacci ta wuce toilet, bata dad'e ba ta fito tayo wanka ta maida kayan baccin jikinta gaban mirror ta nufa ta shafa mai bayan ta gama ta juya ta nufi k'opa, a parlor ta d'auki hijab d'inta data cire da daddare ta saka sannan ta nufi gida don tayi shirin islamiyya. Wuraren k'arfe sha biyu na rana suka fara shirin tafiya zaga gari kamar yadda akai jiya, bayan duk sun yi wanka suka shiga duba kayan da Fauzy zata saka saidai duk kayan Fatun bazasu yi mata daidai ba Saboda yanayin jikin su ba d'aya ba, k'arshe wata jallabiya suka samu da tayi mata daidai sabuwa ce acikin kayan lefenta da gani ita Fatun in tasa zata d'an yi mata yawa dama ko wadda taba Fauziyyar a Abuja itama tayi mata yawa yawanci dama da ganin dogayen rigunan wasu zasu yi mata yawa amman in ta saka takalma masu tsini ko tudu zasu iya yi mata daidai, itama Fatun shiryawa tay da riga half gown da straight skirt na atampa Fauzy ce tayi mata d'aurin kallabi mai kyau bayan an gama ta fiddo takalma da jaka da suka hau da atampar takalman masu dan tsini ne har Fauzy saida tay mata magana kansu tana murmushi tace ai tsinin nada gwa6i, rolling veil d'in jallabiyar Fauzy tay Fatuu kuma ta d'aukko mayafi daya hau da kayan sosae tayi kyau Fauzy ma ta yaba tace bari tayi mata hoto, atare sukai wasu hotunan bayan sun gama suka tafi gidan gwaggo don suga in su Mino sun shirya dama bayan sun yi Breakfast da suka je gaishe da Hajiya Fatuu ta sanar mata zancen fitar tasu. A can gidan suka ci Abincin rana lokacin Mino ta yi wanka kaya kawai zata saka haka Kawu Amadu ma ya shirya yana d'akin shi gwaggo ma da ita za'aje farko da tace bazata je ba suka matsa mata dole ta shirya, bayan kowa ya gama shiryawa Fatuu ta kira Tk ta sanar dashi yace gashi nan zuwa, bada jimawa ba yazo ya kira Kawu Amadu ya sanar dashi su fito, a tare duk suka fito gwaggo ta kulle gidan tana sanye da riga da zani na atampa tasa Hijab data hau da kayan hannunta ruk'e da purse, kowa fuskar shi da murmushi suka nufo Motar da sai shek'in sabunta take, ganin in suka zauna baya zasu iya matsewa yasa Kawu Amadu yace ma Mino tazo su zauna a gaba sai su kuma su ukku suka shiga baya, zagaya gari suka shiga yi suna hira cikin nishad'i ga Ac na ratsa sassan jikin su sai faman santin Motar suke ita dai Fatuu murmushi kawai take saki don ganin abun take kamar wasa wai wannan Motar ta ce, sosae suka zaga gari saida aka fara kiran sallar la'asar suka wuce gidan Aunty Mareeya, suna zuwa bakin layin gidan Fauzy ta kirata tace tazo ta tarbe su, Fauzy ce ta nuna ma Tk gidan yana Parker Motar gaban gidan sai ga Aunty Mareeyar ta fito tana sanye da doguwar rigar material ta yafa gyale saman kanta da ya bayyanar da gaban kanta daya sha kitso da alama dai tana son dogayen riguna koda yake mutane irin ta dama ita tafi dacewa da su don tana amsar su sosae, cikin washe baki ta nufo Motar duk suka bud'e suka fito, gaisawa suka shiga yi tana yi masu sannu da zuwa Fauzy ta nuna mata Motar tace ga Motar Zarah ta waro ido tana fad'in Don Allah wai wannan bugaggar Motar mai numfashi ce aka siya ma Zarah duk akai dariya, matsawa tay ta fara bin Motar tana dubawa sai faman fad'in ma sha Allah take tana zuba santi, bayan ta gama gani ta juyo tana fad'in wllh ta taya Zarah murna Allah yasa Alkhairi ya tsare gwaggo ta amsa tace masu suyi hak'uri tabar su a tsaye don Allah su shiga, a parlor duk suka zazzauna aka shiga k'ara gaisawa kafin ta mik'e tace ma Fauzy tazo suka nufi Kitchen, dawowa Fauzyn tay tana ruk'e da babban tray da aka jero kayan abinci Aunty Mareeyar ma ta biyo bayanta ruk'e da Warmers masu kyau babba da kuma madaidaiciya, tambayarta Fauzy tay ta kai dining table ne tace mata a'a akai cikin parlon yadda zasu fi jin dad'in bajewa su ci duk akai murmushi, farko cewa sukai duk basu jin yunwa don saida suka ci Abinci sannan suka fito Aunty tace ai tasan sun ci Abinci amman dole itama a ci nata ba kamar su Amadu da Tk da basu ta6a zuwa ba ta kalli Fatuu tace Maman biyu kedai ai nasan zaki ci ko ta d'aga mata kai tana dariya, Aunty tace "haba ai ina ganin wannan kumatukan da kika aje Tubarkallah nasan bakya wasa da Abinci" duk akai yar dariya ta sake cewa "ai angode ma Allah ma gara laulayin cin Abincin da ai ta amaye amaye" gwaggo tace aikuwa hakan yafi, saida kowa yaci Abincin bayan sun gama Amadu da Tk suka tafi Masallaci yin sallar la'asar da aka kira su gwaggo ma suka mik'e Aunty ta kai ta d'akin ta ita kuma Fatuu ta nufi d'akin Fauzy, bayan duk sun yi sallar har su Amadu ma sun dawo a parlon suka zauna aka shiga hira Aunty Mareeya na ta sasu dariya, sai wuraren k'arfe biyar suka fito Aunty tace ma Fauzy ita ta dawo gida ko da sauri Fatuu tace a'a sai gobe zata dawo Aunty tace "an gama ranki ya dad'e uwar biyu farincikin ki shi muke buk'ata yanzu" duk akai dariya tace gaskiya itama ya kamata ta d'ana Motar Tk yace to ta shiga sai ya zagayo da ita tace Yauwa to, seat d'in baya ta shiga ta wani hakimce har saida ta basu dariya, tsayawa sukai yaje ya zagayo da ita bayan sun dawo ta fito tana k'ara yabawa da Addu'oi, sallama sukai da mata tayi masu godiya tana fad'in taji dad'i sosae wllh Allah ya bar zumunci duk suka amsa tace ma gwaggo sai tazo yi mata yini tana murmushi tace to tana jiran ta daga haka duk suka shiga cikin Motar suna d'aga ma juna hannu suka tafi, k'ara zagaya gari sukai sai gab da Magrib suka koma gida harda tsaraba suka yo, gwaggo da Amadu aka fara ajewa tay ma Tk godiya da Allah ya huta gajiya suka wuce, har bakin part d'in Hajiya ya kai su bayan sun fito suka shiga ciki don kai mata tsaraba. A part d'in sukai sallar Magrib da isha suka ci Abincin dare bayan sun d'an yi mata hira sannan suka komo part d'in su Fatuu. Washe gari Lahadi bayan sun ci Abincin rana sun shirya suka tafi gidan gwaggo har saida tay ma Fatuu Maganar zuwan tace ba jiya ta zo ba tace ai jiya ba nan suka zo ba don zasu fita ne yau ne zuwan nata Fauzy nata masu dariya, bayan sallar La'asar lokacin Mino ta tafi Makaranta Fatuu tace ma Fauzy suje su gaida innar su Haulat suka tafi, lokacin da suka isa gidan sosae tay murnar ganin su tace ma Fatuu maimakon ta bari ita tazo ta dubata ai bata san ta dawo bane da tazo tana murmushi tace mata ba komai, sai gab da Magrib suka baro gidan suka koma gidan gwaggo, ana gama sallar Magrib tace ma Fatuu ta koma gida suka tafi tare da Fauzy da Mino, bayan sun yi sallar isha Fauzy ta fara yin shirin tafiya gida don gobe Monday, rigar material d'inta ta maida Fatuu na fad'in ta bar ta jikinta amman ta k'iya, duk da haka saida ta bata kyautar kayan shafa da turare guda biyu harda panties da vest mai had'e da wando sai sark'a da yan kunne masu kyau, farko k'in amsa Fauzyn tay tace ai abun yayi yawa ina laifin duk abubuwan Alkhairin da aka yi masu acan Abujar, magiya Fatun ta hau yi mata kan ta amsa tana fadin ai don tana da su ne ta bata ko k'arshe saida ta nuna mata 6acin rai sannan ta amsa tayi mata godiya da Addu'ar Allah ya sauketa lafiya, Tk ta kira ta tambayi yana gida yace eh yanzu dai yake niyyar fita ta rok'e shi kan ya aje Fauzy gida yace Ok ta fito, tare suka fito harda Mino suka nufi part d'in Hajiya don tayi mata sallama, tana zaune a parlor suka shigo bayan duk sun zauna suka gaishe da ita ta amsa Fatuu tace mata dama Fauzy ce zata tafi shine tazo yi mata sallama Hajiyar ta tambayi taci Abinci ne Fauzyn tace eh sun ci a gidan gwaggo, ce mata Hajiyar tayi bari a kawo mata ta k'ara sai ta tafi tana murmushi tace ta k'oshi ai basu dad'e da suka ci ba, Tk ne ya kira Fatuu yace gashi yazo parking space bai ganta ba ko bata fito bane tace mashi gasu nan zuwa, kallon Fauzy tay tace suje ga Tk d'in can yazo duk suka mik'e Hajiya tace ta bari a bata kud'in Napep Fatuu tace ai Tk ne zai kaita gashi can ma ya fito tace to hakan yayi tay ma Fauzy godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci ta amsa tana murmushi suka tafi, lokacin da suka fito har Tk ya fiddo Motar Fatun cikin harabar, bayan sun k'arasa a gefen Motar suka tsaya suna k'ara yin sallama Fatuu tace mata sai sun had'u gobe a School Fauzy tace "ai nayi zaton zaki k'ara hutawa tunda ana maki komai online" ce mata tay a'a zata cigaba da zuwa tunda ta dawo dama ba wani jin dad'in karatun take ta online ba tunda ba haka ta saba ba kawai don ya zama dole ne tace Shikenan to sai sun had'u goben tay ma Mino sallama ta shiga gaban Motar dama Tk na driver seat yaja suka tafi su kuma suka koma part d'in Hajiya..... 90 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ ..........Washe gari Fatuu na gama sallar Asuba ta tashi Mino suka fara shirin tafiya Makaranta, Mino ce ta shiga Kitchen don ta had'a masu breakfast ita kuma Fatuu ta shiga wanka, bayan ta fito ta fara shiryawa itama Mino ta shiga tayo wankan, anan ta shirya dama tun jiya da daddare taje gida ta d'aukko Uniform d'inta, saida suka gama shiryawa sannan suka yi Breakfast suna gamawa Fatuu ta kira Tk ta sanar dashi sun shirya yace to su fito, a cikin Motar ta suka tafi saida aka fara ajiye Mino kaman ko yaushe sannan aka wuce da Fatun, lokacin data je sosae yan class d'in su suka nuna murnar ganinta aka shiga zuwa yi mata sannu da dawowa da tambayar jikinta, bata dad'e da zuwa ba Fauzy ma ta zo. Bayan an tashi Tk yazo ya d'auketa suka biya suka d'auki Mino, a gida Mino tace a ajiye ta sukai sallama da Fatuu tace sai ta dawo islamiyya zata zo suka wuce, part d'in Hajiya ta nufa bayan sun isa gidan don wata irin yunwa take ji a haka ma wai taci Abinci sosae da break sannan gab da za'a tashi ma saida tasha youghort da cake da ta aje Saboda in taji yunwa, saida ta cika cikinta sannan ta koma part d'in su tana zuwa ko Uniform bata cire ba ta haye gado ta hau yin bacci, saida akai sallar la'asar sannan ta farka ta nufi toilet, wanka tayo ta dauro Alwala ta fara shiryawa cikin doguwar rigar Atamfa ta kabbara salla, bayan ta gama gaban mirror taje ta shafa yar powder da lip glow tana yi tana murmushi itama tana ganin canzawar da tayi sosae, gyale ta d'aukko ta yafa ta d'aukko jakar Makarantarta ta nufi part d'in Hajiya, lokacin data isa Hajiyar na zaune a parlon ta nufo ciki da sallama ta juyo tana amsa mata, kujera ta nufa ta zauna idon Hajiya a kanta ta gaishe da ita ta amsa kafin tace "an dawo" kai Fatuu ta d'aga "Eh tun d'azu nan ma na fara zuwa lokacin kina bacci naci Abinci sannan na tafi" kai ta jinjina mata, tana k'ok'arin fiddo littafi taji tace "Yanzun wannan rigar da kika saka baki ji kin takura ba, illar matsattsun kayan kenan dole wani lokacin kana ji kana gani baka iya saka su yanzun d'an nan gaba kad'an ya za'ai ki saka wannan rigar ai bata sanyuwa a wurin ki kinga da wadatattu ne ko yaushe zaki saka abun ki amman irin wad'annan kayan ko bayan kin haihu da k'yar in zasu yi maki don wani lokacin k'ibar ciki bin mutum take" shiru Fatuu tay idon ta akan littafin data fito tana d'an murmushi, "Sauran kayan da ba'a d'inka ba ki bada ayo maki wadatattun dinkuna da ko cikin naki ya tsufa zaki iya sakawa" d'agowa tay ta kalleta ta d'aga mata kai, karatu ta fara yi ita kuma Hajiyar na kallo can tace mata ko akawo mata fruit zata shi ta d'aga mata kai, Saude ta fara k'wala ma kira jin shiru bata amsa ba tace k'ilan tana baya jin haka yasa Fatun mik'ewa tace bari taje ta d'aukko har zata fita daga wurin kujerun ta dakata ta tambayi Hajiyar itama ta kawo mata tace eh, a cikin bowls ta yayyanko ta dawo saida ta fara aje ma Hajiya nata akan c-table sannan ta koma ta zauna, kallon Fruit d'in Hajiya tay ganin harda abarba ta d'ago ta kalli Fatun tace badai itama harda abarbar ta yanko ba tace mata a'a ai tun Abuja bata shan ta ta jinjina kai, cigaba da karatun tayi ta haye saman kujerar gaba d'aya tana yi tana shan fruit d'in, suna haka suka ji an yi sallama alamar wani ya shigo, a Kusan tare suka kai idanun su saitin k'opar suna kallon wanda yay sallamar, nufo ciki yay saida ya matso sannan Fatuu ta gane ko waye har saida gabanta ya d'an fad'i ganin shi, Gaye ne yana sanye da riga da wando na yadi kan shi ba hula harda agogo sanye a hannun shi yana ruk'e da leda gari yayi zafi, da murmushi ya k'araso inda suke ganin yana k'ok'arin duk'awa k'asa yasa Hajiya nuna mashi kujera tace ya zauna mana, bayan ya zauna ya gaishe da ita fuskarta a sake ta amsa ya juya suka had'a ido da Fatuu still da murmushi a fuskar shi itama ya gaishe da ita ta amsa a hankali tana d'an murmushi, hakanan taji wani iri ganin shi a parlon duk da suna had'uwa a hanya a haka ma don bata san da Hajiya tasan abunda ya ta6a faruwa tsakanin su ba, "kwana biyu Malam Ashiru ka daina lek'owa mu gaisa Allah yasa lafiya" Hajiya ta fad'a idon ta a kanshi yanata murmushi yace mata lafiya lou tace ma sha Allah, Fatuu dai sai kallon shi take abubuwa na dawo mata, mik'ewa yay ya matsa gaban Hajiya ya aje ledar daya shigo da ita ya koma ya zauna, kallon leda d'in tay ta ce "To, mi na samu haka" ta d'ago ta kalle shi yana murmushi yace mata yaje Jos ne kafin ya tafi ma yazo bata nan, jinjina kai tay tace sun je Abuja ne yace eh haka aka fad'a mashi, "kace tsaraba ce aka kawo man kenan" yace eh, godiya tay mashi ta tambayi ya ya baro Mutan Jos d'in yace duk suna lafiya, shiru suka d'an yi can ta tambayi ya aiki da yake ta sa an samu mashi aiki yana teaching a primary, amsa mata yay da Alhamdulillah "Yanzu sai aure ko tunda kana sana'a ga kuma aiki ai lafiya lou zaka iya rik'e iyali" yana murmushi cikin girmamawa yace mata sai nan gaba dai, "To Saboda mi, ai aure shine cika kamalar mutum ko baka son yin Auren ne?" da sauri ya girgiza mata kai yana yar dariya yace ba wadda yake tare da ita ne yan mata basu son malamin Makaranta, har saida Fatuu tay yar dariya Hajiya tace "to don me, aikuwa inda wanda yakamata aso to bayan malami ne tunda ai shine tushen kowane aiki ko, kawai dai ba'a basu k'arfin da Yakamata bane wannan kuma saidai aita Addu'a Allah ya kawo Shuwagabannin da zasu duba masu, in dai mutum zai rik'e ka ya tsare maka hakkokin ka ai kuwa ba abun gudu bane kwanciyar hankali shi ne abun buk'ata a gidan aure kuma ba Arzik'i ne ke samar da wannan ba, gaba d'aya Arzik'in ma ai na Allah ne in akai hak'uri sai akai matakin da ba'a ma ta6a zato ba ga misalai nan akan masu Arzik'in, da yawa in kaji ta yadda suka faru sai ka jijjina kai don mamaki rabon mutum ai baya ta6a wuce shi" gaba d'aya sun yi shiru suna saurarenta har ta gama duk suka jinjina kai, jin ta gama Magana yasa shi kallon Fatuu yana murmushi yay mata Allah yasa Alkhairin Auren ta tana murmushi tay mashi godiya, "In kana son yin Auren akwae yarinyar da zan had'a ka da ita bata da matsala akwai kyaun hali sai kaje in Allah yasa kun daidaita to sai muyi Addu'ar Allah yasa ayi damu" jinjina kai yay ta kai hannu gefenta ta d'aukko wayarta ta fara latsawa, alamun ya taso tayi mashi ya matsa daga gefen ta, mik'a mashi wayarta tayi tace ga Lambar yarinyar nan ya d'auka ranar da ya shirya zuwa su gana ya fara kiranta ya sanar mata yace to, bayan ya d'auka ya bata wayar cikin girmamawa yay mata sallama tace ya gaida Maman shi Allah yasa kuma su ji Alkhairi a kunyance ya amsa ya juya kan Fatuu dake cigaba da shan fruit idon ta akan shi itama yay mata sallama ya tafi ta bishi da ido gaba d'aya mamakin shi take sai ka rantse da Allah ba Gaye bane don sosae ya canza yay fresh hatta Maganar shi ma ta canza a nutse yake yin ta gashi kuma sam ba mummuna bane kuma yana da haske ashe dama can harda shaye shaye suka k'ara mashi bak'i. Bayan sallar Magrib Mino tazo har lokacin Fatuu na a part d'in Hajiya a d'akin Saude ta isketa lokacin bata dad'e da gama yin salla ba, suna anan d'akin aka yi sallar isha bayan Fatuu ta gama tace mata suje Parlor yunwa take ji, saida taje Kitchen ta zubo Abincin harda Mino sannan suka nufi cikin parlor don yanzu bata jin dad'in cin Abinci akan dining table, akan carpet suka zauna basu dad'e da fara ci ba Hajiya ta fito, bayan ta zauna Fatuu tace mata ta zubo mata Abincin ne tace a'a taci gaba da cin Abincinta in Saude ta zo ta zubo mata, bada jimawa ba Sauden ta shigo part d'in ta baya ta nufo cikin parlon, daga gefen Hajiya ta duk'a suka gaisa harda Mino kafin ta tambayi Hajiya a shirya table tace mata a'a waye mai ci a table d'in itama ta kawo mata nan tace to, bayan sun gama Mino ce ta kwashe kayan da sukai amfani dashi ta kai Kitchen ita kuma Hajiya tana cikin cin nata, suna Zaune suna yin kallo Tk ya shigo ta baya zai d'auki Abincin shi hango su da yay a zaune yasa shi nufo cikin parlon, daga bakin kujerun ya tsaya ya d'an rankwafa yana gaishe da Hajiya data juya tana kallon shi ta amsa Mino ma ta gaishe da shi, "Tk yaushe zaka fara koya man Motan?" har zai juya Maganar Fatuu ta dakatar da shi kafin ya bata amsa Hajiya ta tambayi waye za'a koya ma Mota ne Fatuu tace mata ita, wani kallo ta bita dashi kafin tace "kaman dole, kina a cikin wannan halin za'a koya maki wata Mota, in kinyi hakuri Allah ya sauke ki lafiya ba sai a koya maki ba" yamutsa fuska Fatuu ta fara yi tace in aka koya mata yanzu lokacin tasan ta k'ware, "kaji fitina don Allah, to bada ni za'ai wannan aikin rashin hankalin ba gaskiya ba wata Mota da za'a koya maki sai Allah ya sauke ki lafiya" ta k'arasa Maganar ta d'aure fuska, magiya Fatun ta fara yi mata Hajiya ta ruk'e ha6a tana fad'in wato ciki yasa ta koyi kafiya ko to ta ga ta inda za'a koya mata wata Mota, tana rufe baki kawae sai ji tay Fatun ta saka Kuka, waro ido Hajiya tay ta kai hannu ta rufe baki, "Ku ji jan sharri don Allah, daga nace kiyi hak'uri in kika haihu a koya maki shine zaki k'ware baki ki saka man kuka" cikin kukan tace to ai in ta Haihu Ya Haisam yace Us zasu tafi Shikenan kuma bazata yi amfani da Motar ba, "To a can Us d'in ba'a saida Motoci ne?" tace to Shikenan ita wannan d'in hakannan aka siya baza tayi amfani da ita ba, "Dole sai in ke kika tuk'a zai zama anyi amfanin da ita, baga Tukur nan sai yaci gaba da yi maki amfani da ita ba kuma in ita kike so sai akai maki ita US d'in bayan kin haihun" wani kallo take bin Hajiyar da shi fuska a yamutsa bayan ta gama Maganar ta shiga yi mata magiyar ta bari a koya mata Allah ba abunda zai faru in sha Allah, "Uhmm Fateema da alama wasa kika d'auki koyon Mota to iya fargaba ma ai tana iya haddasa maki matsala ni kaina har na manta yaushe rabon da in tuk'a Mota tun ma ban tsufa ba haka na hak'ura Saboda fargaba duk da na iya, sai ke kina d'auke da yaron ciki zaki ce wani a koya maki Mota" Kukan taci gaba da yi idonta akan Hajiyar itama kallonta take ta kwa6e fuska yadda sukai har saida yaba Mino da Tk dariya, ganin tana son a koya matan yasa Tk ce ma Hajiyar ko ya fara koya mata anan cikin gidan tunda akwae space lafiya lou tun kafin ta bashi amsa Fatuu tace "Eh don Allah Hajiya ki bari ya koya man d'in anan cikin gidan kinsan bai tuk'in ganganci zai koya man lafiya lou" fuska a kwa6e take kallonta Fatun ta shiga motsa baki, k'arshe dai dole hajiya ta amince da hakan ganin yadda Fatun ta k'wallafa rai kuma tasan duk aikin cikin jikinta ne amman tace ba ruwanta. Washe gari da safe lokacin su Fatuu sun tafi Makaranta Haisam ya kira Hajiya bayan sun gaisa ta tambayi yadda suke da aikin shi yace mata dama Maganar fara zuwan Fatuu awo zai mata sun yi magana da ita tace lafiya lou yanzu ma zata iya fara zuwa, ruk'e ha6a Hajiyar tay jin Maganar da yay mata tace wato shi ga mai d'a ita bata san abunda ya dace ba kenan yay yar dariya yace No ba haka bane, ce mashi tay to tana sane bari tay ya cike wata hud'u sannan ta fara zuwa tunda dai lafiyar ta lou duk abunda ya dace ana mata yace Ok, yar hira sukai ta tambayi lokacin da zai zo ya fad'i mata tay fatan Allah ya kaimu ya kawo shi lafiya daga baya sukai sallama. Kamar yadda sukai anan cikin gidan aka fara koya ma Fatun Motar da yake tana so sosae take ganewa, lokacin da cikin ya kai wata hud'u daidai ranar Laraba da yamma suka shirya zuwa yin booking d'in awon da yake a private hospital d'in da suke zuwa ne zata rink'a zuwa awon, tare da Hajiya suka tafi a Motar Fatun Tk yaja su, bayan sun isa Asibitin suna shiga Opd suka had'u da Nurse bilki tana ganin Fatuu ta ganeta ta nufo su, Fatuu na ganinta itama ta gane ta suka gaisa ta tambayi wani ne ba lafiya Hajiya tay mata bayanin abunda suka zo yi da sauri tace to suzo suje 6angaren Mama ne, a bakin d'akin da ake awon suka tsaya ta shiga ciki bada jimawa ba ta fito tace su shigo, lokacin da suka shiga Mama na zaune kan kujera idanunta sanye da glass ganin Hajiya yasa ta mik'ewa tana masu sannu da zuwa ta nuna mata kujerar data tashi tace ta zauna Hajiyar tace Fatuu ta fita buk'ata ita ta zauna, jin haka yasa tace ma nurse bilki taje ta kawo wasu kujerun tace to ta juya ta fita, gaisawa sukai a mutunce kai kace dama sun san juna Fatuu ma ta gaishe da ita ta maido idonta akanta bayan ta amsa tace ashe har an maida rabo abu har yama fara girma ita dai murmushi kawai tayi Hajiya ce ta bata amsa, nan mama ta hau fad'i mata ai kwanaki data yi 6ari taje ta dubata a Amenity Hajiya tace Allah sarki gashi ai har an samu wani Mama tace ai wuyar abun ace dama ba auren, bayan nurse bilki ta kawo kujerun duk suka zazzauna nan Hajiya tay mata bayanin abunda suka zo yi tace Ok, katin awo aka yankar ma Fatun daga baya Mama d'in tace ai bari ma a fara mata tun yanzu Hajiya tace aikuwa sun gode, Bp d'inta aka fara dubawa ya nuna normal sai aka auna tsawonta da kuma nauyin ta, bayan duk an gama Mama ta had'a ta da nurse bilki tace suje lab ta tura awon fitsari da na jini da za'a mata suka tafi nan fa suka hau yin hira da Hajiya, ba'a d'au wani dogon lokaci ba duk akayi mata awon har an turo result mama ta duba tace Alhamdulillah komai lafiya lou, gado tasa Fatun ta hau ta fara mata scanning gaba d'aya idanunsu ita da Hajiya da nurse bilki na akan computer d'in dake gwado cikin Fatun, tana cikin yin Scanning d'in tace "ni wannan cikin ma yadda nike gani kamar ba d'a d'aya bane" tai Maganar tana d'age idanunta dake a cikin glass Hajiya tace "ko?" mama ta amsa da "eh Allah, amman dai sai d'an nan gaba za'a tabbatar haka dai nike gani" jinjina kai Hajiya tay "ba mamaki ba d'ayan bane tunda shi Mijin nata suna da gadon abun Mahaifiyarshi yan biyu ne kuma cikin K'annan shi ma akwae yan biyu ni dama tunda naga yadda take d'irkar Abinci na yanke hukuncin da k'yar in ba yan biyun bane" dariya duk sukai Mama tace ai ko cikin d'ayan ma akwae mai saka cin Abincin Hajiya na dariya tace dama itama ta dai yanke hukuncin ne kawai tasan haka, bayan an gama komai aka rubuta mata date da zata dawo, a tare harda Mama suka fito tayo masu rakiya Fatuu dai ta kasa gane farinciki take ko fargaba jin zancen ana tunanin ba yaro d'aya bane a cikin nata, har harabar asibitin inda suka parker Motar su Mama ta raka su Hajiya nata mata godiya saida taga tafiyar su sannan ta nufi komawa cikin Asibitin. A kwana a tashi ba wuya har sati ukkun da Haisam yace zai dawo sun yi, tun ana gobe zai dawo Fatuu ke ta farinciki har Fuskarta ta kasa boyewa ranar ta kasance Juma'a Tk na d'aukko ta daga makaranta ita da Mino suka wuce kasuwa siyayyar kayan da zata mashi Abinci, Washe gari da wuri ta tashi ta hau shirin tarbar mai gida, anan part d'inta ta fad'i ma Hajiya za'ai abinci gaba d'aya hakan yasa Saude zuwa nan suka shiga Kitchen tare Mino kuma ta hau gyaran part d'in Tk kuma aka sa ya gyara harabar part d'in, zuwa sallar Azahar sun gama komai sai uban k'amshin girkin da sukai kala ukku ke tashi drinks ma kala ukku sukai harda lafiyayyen kunun Aya sannan sunyi had'addan tsiren hanta da grilled lamp daya gasu ya sha vegetables nad'e a cikin foil paper, bayan sun gama komai aka zuba na su Hajiya Saude ta tafi dashi Mino ma ta zuba mata wanda zata kai ma gwaggo tace ta shiryo daga nan zasu je d'aukko shi Airport a d'okance tace to ta tafi, tana shiga Bedroom ta fad'a toilet bata d'au lokaci ba ta fito don tafi son jirginsu yay landing suna a Airport d'in, shiryawa ta shiga yi tayi make up wadda rabon data yi irinta ta manta saidai ko wadda akayi mata da bikin ta, tana cikin yin shafar Haisam d'in ya kirata ya sanar mata gasu zasu taso daga Kano cike da zumud'i tace to tay mashi fatan isowa lafiya, shaf shaf ta k'arasa don tasan bada jimawa ba zasu iso, wata rantsattsar marron d'in shadda sabuwa dal a cikin kayan lefenta take tasha ubansun aiki ta fiddo, ba 6ata lokaci ta saka ta tayi d'aurin kallabi mai kyau ta fiddo jewellery da suka hau da kayan ta saka harda hannunta tasa Agogo da zobuna ita kanta taga kyaun da tayi data kalli Madubin, jaka da takalma da gyale ta fiddo wanda suka hau da aikin shaddar ta saka sosae tay kyau ga cikinta ya fito, tana gamawa ta kira Tk tace mashi sun kusa k'arasowa yace Ok su a had'u a parking space, lokacin data fito har ya fiddo Motar cikin harabar yana hangota ya tunkarota da Motar bayan ya tsaya ta bud'e baya ta shiga yaja suka tafi, a kan hanya suka had'u da Mino itama tayi wanka tayi kwalliya tana sanye da riga da skirt na blue lace ta yafa blue d'in gyale bakinta yasha jan jambaki sosae itama tayi kyau, gaban Motar ta bud'e ta shiga suka tafi. Basu fi minti biyu ba da zuwa jirgin su Haisam d'in ya sauka gaba d'aya Fatuu a k'agare take data gan shi don ba K'aramin missing d'in shi tay ba, gaba d'aya sun baza ido suna kallon masu shigowa can sai gashi ya shigo yana janye da trolley d'ayan hannun shi ruk'e da jakar laptop jikin shi sanye da bak'ak'en riga da wando ya d'aura jar coat, Fatuu na hango shi ta tafi da gudu har saida tasa hankalin shi ya d'an tashi ganin yadda ta nufo shi gashi takalman k'afarta half cover ne masu d'an tsini, da sauri ya saki akwatin itama jakar laptop d'in ya ajeta k'asa ya nufota da sauri yana fad'in ta tsaya tare da yi mata nuni da hannu amman ina ai saida ta k'araso tana niyyar fad'a mashi ya ruk'eta yana murmushi ita kuma ta washe baki gaba d'aya k'amshin jikin shi ya karad'e wurin, ce mata yay miyasa tasan halin da take ciki zatai gudu haka bata ce mashi komai ba sai faman dariyar farinciki take duk hankalin mutane ya dawo kan su, k'arasowa wurin su Mino da Tk sukai suna murmushi sukai mashi sannu da zuwa fuskar shi a sake ya amsa masu, kama trolley d'in Tk yay Mino kuma ta d'auki jakar laptop d'in ya tallabo kafad'ar Fatun gwanin sha'awa suka nufi barin wurin idonta akan shi sai faffad'an murmushi take shima haka, sosae yaga ta canza mashi kan yadda yake ganinta a Vedio call, inda Motar su take suka nufa ita dashi suka shiga baya Mino ta zauna a gaba suka tafi, kwantar da kanta tayi a saman shoulder d'in shi tana ta bashi labarai harda koya mata Motar da ake yana ta jinjina kai fuskar shi d'auke da Murmushi a haka har suka k'araso Unguwar su, a gida Mino tasa aka ajeta tayi ma Haisam Allah ya huta gajiya sukai sallama da Fatuu sannan suka wuce. Kwana ukku da dawowar shi ya tafi Abuja hidimar bikin Saleem Fatuu ji tay kamar ta bishi saidai Saboda makaranta ta hak'ura Saboda yanzu karatun suke da zafi zafi Saboda shekarar k'arshe ce. Ranar Friday aka d'aura ma Saleem aure da amaryar shi Saleema wadda d'iyar Minister of Health ce sai fatan Allah ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya da zuria dayyiba, Ranar Sunday Haisam ya dawo Katsina. Bayan sati biyu....... Ranar Friday Fauzy ta dawo Weekend gidan Aunty Mareeya kamar yadda ta saba, da yamma tana kwance akan gadonta cikin d'akinta tana lallatsa wayar ta, jin an turo k'opa yasa ta juyo taga Aunty Mareeya ce ta shigo tana sanye da riga da skirt na jan lace kanta ta d'aura kallabi daga baya ta lankwasa igiyoyin kitson ta Sosae kayan suka amshi jikinta sun bayyanar da k'irarta ta dirarrar giant d'in mace, gadon ta nufo hannunta ruk'e da wayarta ta zauna a baki idon ta akan Fauzy, ganin irin kallon da take mata ga yanayin fuskarta kamar da alamun tashin hankali ko kuma ace Al'ajabi yasa Fauzy tashi zaune itama riga da skirt d'in atamfa ne a jikinta kanta ba kallabi anyi mata kitso shuku jelar ta sauka k'asa, "Aunty lafiya?" Fauzy ta tambaya ta d'an waro ido da alamun fargaba akan fuskar ta, ajiyar zuciya Aunty ta sauke ta d'an motsa baki tama rasa ta ina zata fara, hakan da tayi yasa hankalin Fauzy tashi tace "Aunty don Allah minene, ki fad'i man kin ji" wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa ta yarfa hannu tace "to ai Fauziyya nama rasa ta ina ne zan fara tsabar mamaki wllh" da sauri tace mata mi akai, "Dama kun fara soyayya ke da Sameer ne baki fad'i man ba?" da mamaki Fauzy ta furta "Soyayya!" Kai Aunty Mareeya ta d'aga mata, girgiza kai ta hau yi "a'a wllh, ni ba wata soyayya da muke yi duk yadda muke da shi ai kin sani ko daga haka ba wani abu" shiru Aunty tay duk tayi zuru zuru, "Amman Aunty miyasa kika ce haka?" Hannu ta kai ta ruk'e ha6a tace "Wai kinsan yanzu Baba ya kira ni da alamun tashin hankali yake tambayata wai wane yaro ne kike tare dashi basu sani ba kuma Sameer ne yake magana akai" zaro ido Fauzy tay ba shiri ta gyara zama Aunty taci gaba "Wai kiran shi akai daga gidan gwamnatin Nasarawa kan ya bada rana za'a zo neman Auren ki kuma harda rana za'a saka" tun kafin ta k'arasa Fauzy ta k'ara zaro ido ta bud'e baki Aunty tace "Wllh, ke duk yadda nike fatan hakan baki ji yadda hankali na ya tashi ba don ban tsammaci abun haka ba" gaba d'aya bakin Fauzy ya mutu sai ido kawai sosae taji Al'ajabin Maganar don ita an fi sati ma ko ta WhatsApp basu yi magana da Sameer d'in ba, da k'yar ta iya cewa "Yanzu shi baban miya ce masu??" Aunty tace "wai ce masu yay don Allah su bashi lokaci zai kira su ya sanar masu don farko ma gardama masu yay kan bake bace saida aka tabbatar mashi ta hanyar yi mashi bayanin ki ya gasgata tabbas ke d'in shi shine ya kira ni yaji yadda abun yake baki ji yadda hankalin shi ya tashi ba bayan nayi mashi bayanin tsakanin ki da shi sosae yay mamaki" Fauzy ba baki sai ido kawai wani irin bugu k'irjinta yake mata sosae Al'amarin ya d'aure mata kai, "Yanzu shi Baba so yake wai aji ta bakin ki don yama rasa yadda zai tafi da Al'amarin" shiru Fauzy tay idonta acikin na Aunty can ta fara girgiza mata kai "Aunty kice mashi kada ya amince su zo ban son Auren shi" waro ido Aunty tay "amman Saboda me Fauziyya, ba abunda dama muke fata ba kenan??" Idanun Fauzy ne suka ciko da k'walla cikin karyayyar murya tace "Haba Aunty ina ake haka fisabilillahi, ko don mu talakawa ne shine zai nuna mana iko haka, bafa soyayya muke dashi ba hasalima bai ta6a nuna man wani alamu na yana so na ba kawai kuma sai ace wai zai aure ni to wane irin aure ne haka zamu yi dashi don Allah?" Shiru Aunty tay tana kallonta k'wallan suka fara zubo mata, ajiyar zuciya Aunty tay tace "amman Fauziyya ba kina son shi ba?" Da sauri tace "ko ina son shi Aunty ni bazan yarda ya nuna man iko haka ba, don ina talaka ai nima inada daraja ba yadda za'ai yayi man wannan ikon, a tunanin shi komai ne ake iya nuna iko, to bazan Aure shi ba gaskiya" ta k'arasa tana girgiza kai harda d'an huci ta kumbura baki, hannu Aunty ta kai ta kama hannunta cikin kwantar da murya ta fara magana "ni ina ganin tunda kinsan halin shi Fauziyya bai kamata ki tada hankalin ki haka ba, k'ilan shi ba da niyyar nuna iko yayi hakan ba...." Katseta tay "iko ne mana Aunty tunda ai yasan ba Soyayya muke da shi ba" d'an cize le6enta na k'asa Aunty tayi kafin tace "watak'il fa shi a wurin shi a hakan soyayya yake dake kinsan Mutane irin shi suna da wuyar fahimta wllh, kiyi tunani tun farko da kuka san juna laifi fa kikai mashi amman kuma ya cigaba da kula ki yana maki abubuwan Alheri kinga ta yuwu kamar yadda nace a wurin shi soyayya yake dake, kuma tabbas yana son ki shiyasa har yasa a zo nema mashi auren ki, tunda kinsan halin shi Fauziyya hakan bai kamata ya dame ki ba har ki fatali da wannan babbar damar da kika samu wadda ko a film da wuya kiga wata ta samu irin damar ace dai d'an Governor zai auri d'iyar talaka " shiru Fauzy tay har lokacin da k'walla a cikin idanunta, still hannun Aunty na a ruk'e da nata, "Tunda kina son shi ki amince kawai mu taru muyi fatan Allah yasa hakan Alkhairi ne kuma watak'il sakayyar abunda Mujaheed yay maki ne Allah yayi maki dama in dai aka cuci mutum yayi hak'uri ya bar ma Allah tabbas sai ya saka mashi" shiru tay tana ta bin ta da ido Auntyn tace mata tayi magana mana, motsa baki ta fara tana yamutsa fuska tace "to ni Aunty mi kike so in ce, wai ina aka ta6a Aure haka don Allah mutumin nan fa ko halin shi bamu sani ba shin yana da kyakkyawan hali ko mummuna ba wanda ya sani sannan kuma ni wllh ina zargin shi ma, akan ido na fa yasha giya kuma yaje Club taya mutum mai kyaun hali zai aikata hakan, ni dai gaskiya Aunty ina ganin gara mu hak'ura da shi kawai kar azo ayi abunda za'a dawo ana dana sani kema kinsan irin yaran masu kud'i da Mulkin nan sai a Hankali wllh" ta k'arasa tana girgiza kai, "Amman mijin Zarah haka yake? Kuma ai baki da tabbas din giya d'in ce kika ga yasha ko tunda ai ke ba saninta kikai ba, kuma da ya sha kinga ya bugu ne tunda ai kun d'an jima tare sannan yayi maki wani abu na kaucewar hankali? In da ya bugu kema kinsan yadda kuka kasance ku biyu kawai wllh sai dai Allah ya k'wace ki kuma ko da bai bugu ba inda d'an iska ne na tabbatar da sai ya nuna maki halin shi a wurin, sannan Maganar zuwa Club tare kuka shiga ne? Ina ce a cikin Mota ya bar ki kinga kenan baki da ikon zargin shi tunda ai baki san miya shiga yayi ba duk da ansan ba wurin Arziki bane amma ba kyau ki munana mashi zato" kallonta kawai Fauzy take fuska a kwabe, "Yanzu in don sanin halin shi ne ai Mijin Zarah na nan ko zan kirata in sa ta tambayar mana shi komai da muke son sani na tabbatar bazai 6oye mana komai ba, ni kuma na maki Alkawarin indai aka tabbatar yana da wani mugun hali da ya kamata a guje ma auran shi to zan goya maki bayan hakan" ganin bata ce komai ba yasa tace mata hakan yayi mata, d'an yamutsa fuska tay a raunane tace "to amman Aunty yanzu misali ace baida wata illa haka zan aure shi ko fa sona bai ta6a cewa yana yi ba, ni nafi tunanin ma Saboda labarin dana bashi na Mujaheed ne yasa ya yanke aure na matsayin ya taimaka man" d'an murmushi Aunty tay tace "in ma don hakan ne ai ba laifi bane sau nawa dama ake aure ba soyayya duk yawancin iyayenmu ba haka sukai auren ba kuma suka zauna lafiya, yanzu aure nawa ne akai a turbar soyayyar yazo ya lalace mudai fatan mu ai ya ruk'e mana ke da kyau ne kiji dad'in Auren, wani Maganar soyayya in kunyi auren kun yi in ma bai iya ba sai ki koya mashi abun ai duk mai sauki ne balle ma wllh irin wad'annan mutanen sun mugun iya love ki bari ayi Auren zaki ban labari dama yanzu ai bazai sake maki ba tunda yana ji da shegiyar izzar tsiya, ke ni ki bari indai damuwar ki ya furta yana son ki ne nayi maki Alkawarin sai furta wannan Kalmar ya zame mashi tamkar cin Abincin shi, yadda zai ci Abinci safe da rana da dare to ina mai tabbatar maki haka zai rink'a fad'in I love you Fauziyya", duk da yanayin da take ciki saida ta d'an yi dariya Aunty ta k'ara cewa "Allah kuwa, ke baki ga yadda mijin Zarah ba ya shigo hannu sai faman rawar k'afa yake akanta ko ba'a fad'a ba daka gani kasan ta kama shi gamm to shima hakan zamu kama shi wuyarta dai ayi Auren hakan ba wani abun wahala bane wllh" d'an ta6e baki Fauzy tay tana d'an murmushi, "Yanzu ya kika ce Your Excellency, a kira Zarah d'in ko mu fad'i mata abubuwan da muke so mu sani game dashi d'in?" wani kallo Fauzy tay mata tana yar dariya kafin a hankali ta d'aga mata kai alamar eh, da sauri Aunty ta kai hannu ta 6akar mata shoulder tace "su Excellency ana so ana kaiwa market" dariya Fauzy ta saka tana fad'in Allah ita ba wani son shi da take. Fatuu zaune a parlor tana kallo tana sanye da doguwar riga Boubou ta lace cikin kayan data ba Kb ya d'inka mata daga baya akai mata d'inkunan da Hajiya tace , bata dad'e da fitowa daga Kitchen ba tayi ma Haisam Abinci da yake tunda yazo ita ke mashi Abinci har ce mata yay ta bari a rink'a yi acan part d'in Hajiya ita ta huta amman tak'i, wayarta dake a gefenta ce ta fara ringing ta kai hannu ta d'aukko, ganin mai kiran nata yasa tay d'an murmushi ta kai hannu tay picking, "Aunty Mareeya ina wuni, barka da juma'a" ta fad'a bayan data yi sallama, amsa mata tayi ta tambayi ya suke harda unborn tana yar dariya tace mata duk lafiya lou suke ga unborn d'in ma yaji suna waya yace/tace a gaishe ta, dariya Maganar ta bata tace to tana amsawa ai in Allah ya yarda biyun ne duka ita dai Fatuu murmushi kawai tayi, "Yauwa Zarah nace don Allah ko mijin ki na nan?" Fatun tace "a'a Aunty yau da safe ya tafi Kano yin wani aiki amman dai a yau zai dawo yace man in sha Allahu da Magrib jirgin su zai sauka" jinjina kai tay tace to Allah ya dawo dashi lafiya bayan ta amsa tace "Amman Aunty lafiya dai ko?" "lafiya lou yar gidana sai ma Alkhairi in sha Allahu...." nan ta kwashe komai game da zuwa neman Auren Fauzy da za'ai da kuma yadda sukai da Fauzyn, tsananin mamaki ne ya bayyana akan fuskar Fatun gaba d'aya ta washe baki tana dariyar farinciki tace "Amman Aunty wllh naji dad'in wannan labarin wayyo Allah na, muna ta jiran ya furta yana son ta ko sun fara soyayya suyi aure ashe mai gaba d'aya zai yi.." Aunty ta amshe "Wllh haihuwa da hanji ba" dariya Fatuu tasaka nan ta fad'i mata abubuwan da take so ta tambayar mata Haisam a d'okance tace to in sha Allahu yana dawowa zasu yi Maganar Allah dai yasa suji Alkhairi Aunty tace "Amin ya Rabbi yar gidana shine abun da zamu yi fata kam" bayan sun gama wayar ta tambayi ina amarya Fauzy, yar dariya Aunty tay tace "ga abu nan tayi wuri wuri Sameer yayi mata bazata" Fatun nata dariya tace a bata, bayan ta amshi wayar tsokanarta Fatuu ta shiga yi ita dai sai uhhm take daga baya ta hau yin Addu'ar Allah ya tabbatar masu da Alkhairi. Bayan Magrib Haisam ya dawo bai dad'e da shigowa ba aka fara kiran sallar isha ya tafi Masallaci, bayan ya dawo toilet ya nufa yayo wanka ya zura jallabiya sannan ya fito don yaci Abinci da tuni Fatuu ta jera mashi akan c-table don in shi kad'ai zai ci yafi son a d'aura mashi anan, Serving nashi ta shiga yi saida ta tabbatar yaci ya k'oshi, tana k'ok'arin kwashe kayan Abincin ta kai Kitchen ya mik'e yace ta bari ya kai tace mashi tana son had'o masu Fruit salad ne, kallonta yay yana d'an murmushi yace zai had'o masu ta zauna huta, hura mashi kiss tay ta kashe mashi ido yay yar dariya, nufar Kitchen yay bayan ya d'auki tray d'in kayan ta d'an d'aga murya tana fad'in "Hubbyna I love you" kai ya jinjina mata ta k'ara fad'in "bazan iya rayuwa babu kai ba" tana fad'in hakan taji yace shima haka sosae yadda yay Maganar ya bata dariya, yana gab da shigewa cikin Kitchen d'in ta k'ara d'aga murya tace yabi a hankali kar ya yanke hannu Baby zai yi kuka in ya yanke, jinjina kai yay saida ya d'an juyo suka had'a ido ya sakar mata k'ayataccen murmushi tare da d'an girgiza kai ganin abunda take mashi da baki ya juya ya shige, after some minutes sai gashi ya dawo hannun shi ruk'e da acrylic bowl ana hangen fruit d'in, dayan hannun shi ruk'e da bottle water ya nufo ta suna ta sakar ma juna murmushi, a gefen ta ya zauna ya mik'a mata tasa hannu biyu ta amsa ta furta "thank you so much Daddyn Baby" hannu ta kai ta d'auki spoon d'in ciki ta fara sha tana yi tana bashi shima a baki can taga ya kawo hannu ya d'ago da k'afafunta ya d'auro su kan cinyoyin shi ya shiga matsa mata su sai murmushi take tana cigaba da sha shima tana bashi, yana ta matsa mata k'afafun idanun shi akan Tv yana kuma amsar fruit d'in in ta kawo can ya juyo yace mata tasha kada ya shanye ma Baby abu tay dariya, bayan ta shanye akan c-table ta d'aura bowl d'in ta d'aukko bottle water d'in, bayan tasha ta rufe ta maida kan c-table d'in, "Hubby" yaji ta kira shi ya d'aga gira kafin ya juya ya kalleta, ce mashi tay dama so take ta tambaye shi yasan da zancen zuwa nema ma Sameer Auren k'awarta Fauzy, yanayin fuskar shi ne ya canza da alamun rashin fahimta ya tambayi wane Sameer tace mashi cousin brother d'in shi, shiru ya d'an yi idon shi a kanta yace bai fahimce ta ba, bayanin Maganar zuwa nema mashi auren Fauzy ta yi, sosae mamaki ya bayyana akan fuskar tashi yace mata shi bai san da Maganar ba ai tace mashi aikuwa d'azun Aunty Mareeya ta kirata take mata Maganar, jinjina kai yay yama kasa cewa komai sosae kan shi ya d'aure don abu ne da bai zaton ji ba, "Ka yi mamaki ko?" Fatuu ta tambaya a hankali ya jinjina mata kai, tambayarta yay yadda akai suka san juna nan ta kwashe komai ta fad'a mashi harda wayar da ya siya ma Fauzyn tace ita ta mantane shiyasa bata fad'i mashi ba wllh, d'an tsoki yay ya furta "Sameer...." Shiru yayi Fuskar shi da d'an murmushi, sosae yaji mamakin yana son Auren Fauzy duk da yasan hakan ba wani abu bane in Allah ya k'addaro itace matar shi saidai shi yasan waye Sameer fiye da kowa bai ta6a tunanin zai iya Auren yarinya kamar Fauzyn ba sanin irin matan da yake tarayya da su, "Wai suna son sanin game da shi ne don ita ko cewa yana sonta bai ta6a yi ba fa kawai dai suna d'an gaisawa yana yi mata Alkhairi kuma sai kwatsam suka ji zancen neman auren ta", Yana murmushi yace "Yana sonta ne shiyasa yake mata hakan kawai bazai fito bane ya fad'i mata" gyad'a kai Fatun tay idon shi akanta yace mi suke son sani a tare da shi ne, ce mashi tayi kamar ya halin shi yake, "Ok, what I know is that baya da wani hali mara kyau da za'a k'i auren shi Saboda shi" ya k'arasa yana d'an girgiza kai, "amman ita wai tana zargin wasu abubuwa a tare da shi" tambayarta yay kamar mi take zargin, shiru Fatuu tay hakanan sai taji nauyin fad'in Maganar ya fahimci hakan ya d'age mata gira yace ta fad'i mashi duk abunda ya sani bazai 6oye masu ba, "D....dama wai cewa tayi taga ya sha giya" da k'yar ta k'arasa ganin yadda ya kafeta da ido, yana jin abunda ta fad'a ya d'an waro ido mamaki ya bayyana akan fuskar shi ganin haka yasa ta zaro ido, "A yaushe ne taga Sameer yasha wannan d'in?" da mamaki ya tambaya, wani abu Fatuu ta had'iya tana faman kikkafta ido tace "ai ba wai ta tabbatar bane fa, dama da ya je da ita gidan da na fad'i maka lokacin da sukai karon nan wayar shi ta fashe...to a nan ne taga wai ya bud'e Fridge ya fiddo kwalba irin ta giyar kuma bayan ya zuba a cup ma taga kalar kamar ita" ta k'arasa tana d'age baki, maida bayan shi yay ya jingina da kujerar fuskar shi a d'an kwa6e ita kuwa sai faman zare ido take can ya k'ank'ance ido yace "Kin koya mata taga mutane na shan lemu tace giya ko" hannu ta kai da sauri ta rufe baki ta hau girgiza kai yace mata eh mana, cire hannun tayi cikin yar rawar murya tace wllh ita fa ba ruwanta itace ta fad'i mata haka kuma ita ai bata ma ga abun ba ko, d'an ta6e baki yay yana murmushi can yay sigh yace "to bai shan giya inada tabbas akan hakan don shi yama tsane ta abunda taga yasha favourite drink d'in shi ne" da sauri ta jinjina kai yay mata wani kallo mai kaman harara tasa dariya, ce mata yay sai mi suke son sani, "To zan fad'i maka amman fa kar kace ni nace abunda aka fad'i ana son sani ne" murmushi yay ya d'aga mata kai, "tace wai taga yaje wani wuri da suka baro gidan kuma wurin wai kaman Club ne" d'an lumshe ido yay ya d'aga mata kai "Yeah, yana zuwa Club" shiru tayi tana kallonshi don ba iya abunda suke son su ji ba kenan, "da wani abu ne game da hakan" ya tambaya had'i da d'age mata gira, in ina ta fara "w..wai ita a tunanin ai ba abun Arziki ake yi a can ba, t..to shine wai...take ganin kaman yana...." dakatawa tay gaba d'aya ta waro ido yana dai ta kallonta taji yace uhum alamar taci gaba, "to na dai fad'i maka ai abunda ake son sani ne ba ana nufin yana yi ba" yana murmushi yace ai ta fad'i wannan ko yana jin ta, ce mashi tay wai ko yana neman Mata ne, ganin yayi shiru yasa tace mashi ya gane abunda take nufi har saida Maganar ta d'an bashi dariya, "baya wannan, I'm absolutely sure about that, saidai he's touching women" waro ido Fatuu tay ya d'an jinjina mata kai yaci gaba "iya ta6a mata yake am very sure akan hakan don tun muna School abroad ina mashi fad'a akan hakan yace man ya bari amman kuma daga baya sai ya cigaba, kinsan hakan yanzu wasu basu d'auke shi komai ba suna d'auka wayewa ne duk da wanda yake Muslim yasan hakan is forbidden kuma babban laifi ne kamar dai yadda akwae abubuwa da yawa da ba kyau kuma ake yi" ajiyar zuciya Fatuu ta sauke da yanayin damuwa tace "to amman kasani ko yanzu ba iya hakan yake ba yana....." Shiru tayi ta kasa idasa Maganar, da murmushi akan Fuskar shi yace mata yana da tabbacin bai yin sex don yana da ilimin Addini sosae da bazai bari yayi hakan ba shima ta6a matan da yake kawai biye ma zuciya ne kuma harda Matan da ke yawan bibiyar shi sun k'ara taimakawa wurin sashi hakan, jinjina kai Fatuu tay ya kai hannu ya shafo gaban kan shi, yar ajiyar zuciya Fatuu ta sauke, "Yanzu kana ganin hakan ba matsala bane?" Shiru ya d'an yi idon shi akan Tv kafin ya juyo kanta "a wurina hakan bazai zama problem da zai sa ak'i auren shi ba, Sameer mutumin kirki ne sai kayi mu'amala shi zakai understanding hakan duk da nasan yana da wuyar a saba da shi amman yana da Quality da mace za tayi Alfaharin samun shi as a husband" wani k'ayataccen murmushi Fatuu ta saki tare da kashe mashi ido d'aya ta furta "Kamar kai kenan" shiru yay yana kallonta da murmushi, "ina Alfaharin samun ka matsayin mijina Hubby" ta furta idanunta a d'an lumshe calmly ya furta shima hakan duk suna murmushi har lokacin kuma k'afafunta na akan jikinshi yana mammatsa mata, "in dai tana son shi ina bata shawarar tay accepting na shi, shi matsalan dana fad'a tare dashi zata iya hana shi tunda yana sonta ba kamar kuma in sun zama d'aya" d'aga gira tay tace yana tunanin hakan is possible, "yeah, ga misali nan akan mu" wani kallo tay mashi da rashin fahimta tace amman shi ai tasan bai abunda Sameer d'in yake ko, shiru yay yana mata wani kallo mai wuyar fassaruwa yanayin fuskar shi kamar zai murmushi itama murmushin take taji ya furta "ina nufin kaman yadda zaki iya hana ni abu koda ni ina so in baki so zan bari" wani kalan murmushin dad'i tayi had'i da lumshe ido tace "ai ba abunda zai maka wanda ni bazai mun ba, duk abunda kake so nima ina son shi Ya Handsome dina" yar dariya yay ya furta mata ya gode, "Amman wai shi Sameer aikin mi yake?" gyara zama ya d'an yi kafin ya fara magana "yana da aiki mai kyau, shi Aerospace engineer ne" d'an yamutsa fuska tay ta maimaita sunan aikin nashi da ta maimaita tace "mi kenan?" Ce mata yay daga sunan tay guessing tayi shiru tare da d'an k'ank'ance idanunta tana son ta canka, "Aerospace...Kaman ana nufin aeroplane ko?" ta tambaya tare da d'age baki, still da murmushi akan Fuskar shi yace "Yeah Kusan haka, shi engineer ne yana aiki da wani company a K'asar U.k, suna k'era jirgin sama ne bama shi kad'ai ba da wasu abu da suka danganci sama kaman satellites and rocket" zaro ido Fatuu tay a d'an rud'e ta furta "rocket kuma! ba itace mai kaman katuwar bindiga ba da in aka harba bullet d'inta ke fita kaman bomb ya tafi shuuuu yaje ya tarwatsa wuri??" dariya ta bashi yadda ta zaro idon yace mata eh shi wannan missile kenan shima rocket d'in ne, "Yanzu su ke had'a su?" Kai ya jinjina mata alamar eh kafin yace amman shi Sameer yafi experience sosae ta bangaren had'a jirgi don ya k'ware a kan haka shiyasa har wasu companies suna gayyatar shi aiki kaman a France da Germany, har nan US akwai wani Company da yake zuwa aiki a Washington, a nan Nigeria ma yana aiki da Ministry of aviation shiyasa akwai lokacin da yake d'an zama a Nigeria amman yafi zama a UK" jinjina kai ta shiga yi jin irin aikin da Sameer d'in yake can ta furta amman dai tasan yana samun kudi Haisam d'in yay yar dariya yace mata sosae, "To amman kai ma kana samun kud'i kaman shi" wani kallo yay mata ta waro ido da sauri tace itafa hakanan ta tambaya tunda taga shima a K'asar wajen yake aiki, kawai sai gani tay yay d'an murmushi yace "tunda ina aiki ai dole in samu kud'i ko kawai kice kina son ki ji ni da shi waya fi samun kudi right?" Ya d'age mata gira ta d'an tura baki had'i da girgiza kai, sigh yay yace "kowa da kalar aikin shi so dole salary ya bambanta amman ta wani bangaren Kusan duk damar mu d'aya ne da shi kuma aikin namu suna da alak'a tunda duk sun danganci technology ne don akwae abubuwan da company d'in mu ke yi wanda suke amfanin da shi and nima kuma ina zuwa wasu Wuraren aiki saidai shi ya riga ni fara aiki abroad Saboda ni farko dana gama first degree na anan nayi aiki shi kuma tun daga School Company d'in suka zo suka d'auke shi nima tun lokacin an so a d'auke ni amman Dad ya hana don yana jin haushin yadda duk suke d'auke Mutanen mu masu hazaka a cewar shi hakan ne ya hana tamu K'asar cigaba kuma hakan ne, bayan naje yin Master's degree d'ina nan suka matsa na fara yi masu aiki amman dana gama sai Dad yace in dawo gida nan zan yi aiki lokacin sai na nuna masa interest dina kan yin aiki da su Saboda ina son bud'e Company shine ya amince amman sai na fara aikin anan, a lokacin nayi missing Hajiya sosae don tunda na tafi Karatu na bar wurinta haka dana dawo na fara aiki a Abuja sai dai in kawo mata ziyara har na sake komawa degree na biyu a lokacin tana kewa na sosae duk da bata fad'a man amman na sani duk na kawo mata ziyara in zan tafi sai naga idanunta sun canza ga kuma rashin mijinta da a lokacin yana damunta sosae wannan dalilin ne yasa na buk'aci canza wurin aiki nazo in zauna tare da ita......." dakatawa yay yana numfashi a hankali idon shi akan Fatuu da itama nata idanun na acikin nashi, "........ashe zaman nawa wani babban Alkhairi ne zai same ni na had'uwa dake Baby, tunda kika shigo rayuwata farinciki na ya k'aru and I couldn't remember in akwae wani rana da nayi bakin ciki Saboda ke in ma akwae shi kenan, ban ta6a shiga damuwa ba sosae kaman ranar da zamu rabu zan yi aure, tun lokacin dana fahimci kin canja man na fara shiga damuwa har zuwa ranar, sosae kikai breaking heart d'ina har yanzu ina ganin image d'in wannan moment na ga Zarah a duk'e tana kuka sosae Saboda Ya Handsome d'inta gashi ni kuma ba abunda zan iya yi mata kan hakan, idanuwa na sun cika da tears a lokacin wanda bazan tuna when last naji hakan ba, koda muka shiga jirgi saidai kawae na d'age kai na na runtse ido ba komai nike ba sai tunanin halin dana baro ki a haka har muka isa Abuja...." Murmushi kawai Fatuu ke yi yayin da zuciyarta ta shiga tariyo hoton rabuwar tasu a airport, a lokacin wani irin soyuwa zuciyarta ke yi gaba daya ji tay kaman rayuwarta tazo k'arshe she felt empty, rayuwa kenan yanzu gashi komai ya zamo tarihi a gare ta duk sanadiyyar hak'uri da tawakalli, "Ranar da kika sanar man zaki abortion naji tashin hankali amman bai kai na ranar da kika fad'i ba a wurin Dinner party, that was the second day dana shiga tsananin tashin hankali a rayuwa ta, daga ranar dana rasa grandpa dina mijin Hajiya lokacin ina a Secondary school sai kuma wannan ranar ganin Zarah kwance a jikina bata numfashi , zuciyata tayi ta sak'a man abubuwa....." Labarin irin halin daya shiga lokacin da zasu kaita Asibiti harda kukan daya yi ya shiga bata yana ta murmushi har ya gama ta hau girgiza kai har saida taji idanunta sun ciko da k'walla wata irin k'aunar shi take ji na ratsa mata jinin jikinta, Sigh yay ya kalleta da murmushi yace daga bayanin aikin shi da yayi mata ta fahimci abunda take son sani na wanda yafi samun kud'i tsakanin shi da Sameer, yamutsa fuska ta shiga yi a shagwabe tace itafa wllh hakanan ta tambaya ba don wani abu ba kawae subul da baka ne, "ai dama kin cancanci kisan komai game da aikin mijin ki ko" ya fad'a yana murmushi, d'age mashi gira tay tace "to in haka ne ka fad'i man nawa ne salary en ka" tana rufe baki yay mata wani kallo mai kaman harara ta saka dariya tace to ba shi yace ta cancanci tasan komai ba, "Wannan sirri ne banda shi" ya fad'a yana yar dariya itama har lokacin Dariyar take tace mashi ita bata yarda ba sai ya fad'i mata ai shi yace, ce mata yay to zai fad'i mata amman a kunne zai rad'a mata don kar aji, har saida ta d'an Jujjuya kafin ta tsaida idonta akan shi tace to ba su kad'ai bane, hannu ya mik'a ya nuna mata cikinta yace Baby yake nufi kada ya fad'a mata ya ji wata rana in ya buk'aci ya siyo mashi/mata abu yace baida kud'i ace mashi yana dasu tunda an ji salary d'in shi daya fad'i ma Mom, dariya sosae Fatuu ke 6a66akawa tace to ita bai gudun tayi mashi hakan sai Baby yace ai ita ya gane tausayinshi take ji bata son yana kashe kud'i amman yasan k'ilan in ya fad'i mata ta daina jin tausayin nashi da sauri ta d'aga hannu tace to Allah bata son jin salary d'in tay Maganar tana dariya tare da girgiza kai shima still dariyar yake, bayan sun tsagaita gaba d'aya jingina sukai da jikin kujerar suna kallon juna kowannansu wani irin nishadi yake ji duk ya kasance da d'an uwan shi, "Na dawo daga tafiya kin hana ni in huta da tambayoyin ki" ya fad'a bayan yayi yar hamma, jin haka yasa ta sauke k'afafunta daga saman jikinshi da sauri ta fara k'ok'arin mik'ewa tana fad'in yayi hak'uri to ya tashi suje su kwanta, nuna mata bowl data sha fruit salad yay yace ta kai Kitchen bari ya kashe kayan kallon tace to, lokacin data dawo cikin parlon har ya kashe kayan kallon yana ganinta ya mik'e tsaye ta nufo shi tana murmushi, tana zuwa gaban shi kawae sai ta juya mashi bayan ta d'an rankwafa tace wai ya hau ta goya shi tunda shi bai iya goya ta Saboda ciki, dariya sosae ta bashi aikuwa tana a yadda take taji ya sunkuce ta gaba d'aya ta saka dariya, nufar hanyar Bedroom yay yana d'auke da ita ta sak'alo hannuwanta a wuyan shi tace wai bai jin nauyinta Slowly ya furta ai dama gaba d'ayan su nauyin su na a kan shi don haka bai jin shi, suna zuwa bakin kopar d'akin yasa k'afa ya tura ya shige da ita......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 91 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ ............Washe gari Asabar Misalin k'arfe sha d'aya na safe Mom na kwance ta koma bacci bayan sun yi Breakfast, tana cikin baccin ta jiyo ringing d'in wayarta kamar bazata tashi ba da k'yar dai ta bud'e idanun ta ta kai hannu gabanta ta d'aukko wayar, duba screen d'in tay taga wanda ya kira har saida tay d'an yi murmushi ganin yar uwarta ce wato Hajiya Zainab, picking tay ta kara wayar a kunne, gaisawa sukai da juna jin yanayin muryar Mom d'in yasa tace yar gayu bacci ma take ko ta tasheta, Mom na murmushi tace gayu ai sai ita kawai ta koma bacci ne Hajiya Zainab na murmushi tace to ai saida hutu ake iya komawa baccin, "Hhhh in wannan hutun ne ai kowa ma nada shi kema nasan baki so kwanciyar bane", "Uhmm wani lokacin kam ai ko kaso ba dama ka koma Saboda schedules" Mom na murmushi tace ya za'ai sai Addu'a Allah ya k'ara d'aukaka ya kuma taimaka tace Amin, "Sai kika ji Saraki ya samu Mata" shiru Mom tayi tana maimaita sunan Saraki da ta fad'a, da alamun rashin fahimta tace "mi kike son fad'i man, ba dai his Excellency ne zai aure ba?" Dariya Hajiya Zainab ta saki tace "inaaa, ai Excellency ya gama yin aure a gidan duniyar nan ya auru yadda ya kamata, Saraki wanda yay gadon Sarautar Grandpa nike nufi" shiru tay tana nazarin Maganar da tayi can tace "wai Son kike nufi?" "Eh mana, wai kina nufin baki sani ba duk da anan gidan ya samu Matar" kan Mom ne ya d'aure ba shiri ta yunk'ura ta tashi zaune jikinta sanye da kayan bacci, ce mata tayi ita bata san da wannan Maganar ba gaskiya amman wacece wadda zai auran, fad'i mata game da Fauzy ta shiga yi, sosae Mom taji mamakin Maganar har tama kasa magana saida ta nisa sannan tace, "Amman dai abun da mamaki wllh ace Saleem da kanshi yace yana son Auren yarinyar" daga d'aya bangaren Hajiya zainab tace "Wllh, it was a real surprise, kinsan farko Dad d'in shi ya tunkara da Maganar wai ya samu wadda zai aura ya tambaye shi a ina nan yake ce mashi yar Funtua ce tana karatu a Katsina koda Dad d'in nashi ya tambaye shi d'iyar waye sai cewa yay shima bai san shi ba kawai dae yasan Dad d'inta is a retired man yanzu Farmer ne, sosae shi kan shi Dad d'in nashi yay mamakin jin yarinyar da yake so ya Auran daga baya ya tuntu6e ni da Maganar ya tambayi wai ko nasan ta nace bazan iya tuna ta ba koda na ganta da bikin, amman I never thought Sameer would fall in love with such a local girl wllh, nayi mamaki ba kad'an ba duba da irin matan da ake mashi tayin auren su, kinsan ko bayan bikin Son saida muka shirya mashi had'uwa da yarinyar sarkin zazzau wadda Mom d'in ta Friend d'ina ce baki gan yarinyar ba very beautiful girl wllh gashi Kusan complexion d'inta iri d'aya da Sameer d'in don Mom d'inta balarabiyar Sudan ce bata dad'e da dawowa daga Saudiyya karatu ba shine Mom d'in nata tayi man Maganar mu gwada had'a su don tana son Sameer sosae, wllh Sis in gaya maki nasa yarinyar tazo nan ta kwana biyu wai don in yi kokarin had'a su, ranar dana kira shi don su gaisa a parlor ko kallon direction d'in da take bai yi ba saida nayi introducing nata sannan ya d'an kalleta daga baya nace bari in basu wuri su san juna sosae, na d'an jima sannan na koma parlon kawai sai na ganta zaune ita d'aya da mamaki na tambayi ina yake tace man ai ina tashi shima ya bar wurin baki ji yadda naji ba kunyar yarinyar ya kamani....." Murmushi Mom tayi ta d'an girgiza kai, "........Lokacin na iske shi a d'aki nace mashi miyasa zai baro falo bayan na tashi da bud'ar bakin shi sai cewa yay dama ba gaisawa ne zasu ba kuma sun yi hakan, sototo nayi ina kallon shi don na tabbatar ya san mi hakan dana yi ke nufi don ba yau ne na farko ai da aka had'a shi su gaisa da mace ba an yi hakan sau da dama kama daga yaran k'awayena dana Abokan Dad d'inshi har fa akwae d'iyar shugaban wurin aikin shi baturiya da shima shugaban nasu yaso had'a su amman yak'i har nan Nigeria ta ta6a biyo shi itama kyakkyawa duk da ba musulma bace, koda na nuna mashi ina son ya auri ita Raudha d'in data zo sai ce man yay bata yi mashi ba yarinyar da ko kallon Arziki bai mata ba taya zai san tayi mashi, lokacin na nuna mashi 6acin rai na kan to har sai yaushe ne zai samu wadda zata mashi yay aure kawai sai ya yi man wannan shu'umin murmushin nashi yace wai in kwantar da hankali na ya samu Mata soon zai yi aure, wllh ni duk na d'auka ya fad'a ne kawai Saboda in bar zancen Rauda ashe da gaske ne yarinyar nan yake nufi", nannauyar ajiyar zuciya Mom ta sauke ta furta "ina ruwan Son amman dai wllh it was a real surprise to hear that Sameer has chosen that girl to be his wife, duk da dai gaskiya yarinyar ba mummuna bace tana da kyaunta daidai gwargwado amman dai dole ai mamakin jin ita ya fitar a matsayin mata kinga kaman shi Habiby ba za'ai mamaki ba sosae da yarinyar da ya aura tunda ba itace ta farko ba", "Uhmm, ni kinga ma na kasa gane yarinyar yace man wai best friend d'in ita matar Son ce" "Eh hakane, amman zaki iya tuna wata yarinya da aka kira ta bada biography na ita Amaryar a wurin dinner? Kaman itace mace ta farko data yi magana a wurin" shiru Hajiya Zainab tayi da alama tana k'ok'arin tunanowa ne can tay d'an tsoki tace bata jin zata tunata Mom tace bari ta duba cikin pictures d'in bikin tasan akwae hotunan ta sai ta turo mata ta gani tace Ok, "To yanzu ya za'ai kenan? zaku amince mashi ya aure ta ne ko kuwa a'a" yar ajiyar zuciya Hajiya Zainab tayi tace "to, tunda yaji ya gani ita yake so ai Shikenan tunda bamu zamu zauna mashi da ita ba abu har ma an kira Mahaifin yarinyar kan Maganar, saidai bazan 6oye maki ba sam hakan bai kwanta man ba ba kuma don wani abu ba wai game da yarinyar kawai dai akwae wad'anda naso ya aura sosae kinga har Daughter Jahad nayi k'ok'arin had'a su saidai ban matsa mashi ba daya nuna bai so Saboda dama nayi tunanin ba lalle tayi mashi ba zai iya ganin tayi mashi k'arama to k'arshe gashi nan k'aramar ya samo zai aura" wata ajiyar zuciyar Mom ta k'ara yi cikin kwantar da murya tace "in dama Allah ya k'addaro ita ce matar tashi no matter what sai ya auretan don haka muyi mashi fatan Alkhairi kawai don kinsan in namiji na son Mace idon shi makancewa yake yanzu ga dai Son nan na fahimci ba K'aramin son Amaryar nan tashi yake ba" murmushi Hajiya Zainab tayi ta tambayi ya jikinta Mom d'in tace lafiya lou take ko laulayi bata yi tun kafin ma ta bar Abuja cikin har ya fito Hajiya Zainab d'in tace Allah sarki tayi fatan Allah ya sauketa lafiya Mom ta amsa da Amin, "Jiya mun yi waya da Ummi da Abie" Hajiya Zainab ta fad'a Mom tace "eh haka suka ce man da na kira su da daddare, wai don Allah bazaki mana k'ok'ari ba su dawo nan kusa damu kamar yadda mukai magana kwanaki" dariya Hajiya Zainab tayi tace "ai tunda nayi ma Ya Othman magana kan hakan yace muma fidda rai bazasu ta6a dawowa Nigeria ba na hakura, kuma suma basu so" Mom na dariya tace "ban ga laifin su ba wa zai so ya baro k'asa irin Qatar ya dawo Nigeria dama dai a Ethiopia suke ne" "Wllh, ai Al'amarin K'asar nan sai Addu'a kawae amman tak'i cigaba har yanzu baya muke sosae a abubuwan cigaba da dama" Mom tace "uhmm ai kune zaku taimaka mana ku farfad'o mana da ita" tana jiyo sautin dariyarta tace su a suwa suda suke k'ananu Mom tace to Allah ya dubesu ya kawo masu Shuwagabannin da zasu kawo cigaba ta amsa da Amin daga baya suka cigaba da Magana dangane da neman Auren Sameer, Misalin k'arfe ukku Fatuu ta fito daga wanka tana zaune a gaban mirror tana shiryawa yayin da Haisam ke kwance a gado yana baccin rana, shirin zuwa gidan su Fauzy take kamar yadda ta yanke zuwa yau tayi masu bayanin da Haisam yayi mata game da Sameer, bayan ta gama yin shafa ta mik'e ta nufi Wardrobe, doguwar bak'ar riga roba ta fiddo ta saka rigar d'an guntun hannu gareta ta bi jikinta cikinta ya fito sosae bayan ta gama sakata ta kai hannu ta fiddo wani lifaya lace bak'i mai adon fulawowi ja da silver, musamman dama taje Hajiya ta koya mata nad'a lifaya kwanaki Saboda tana dasu a kayanta, gaba d'aya sark'a da yan kunne silver ta saka masu kyau sai Agogo shima silver, gaban mirror ta dawo tayi d'aurin kallabi Zarah buhari da wani bakin kallabi, sosae shigar tayi mata kyau sai faman sakin murmushi take, takalma Flat ta d'aukko silver sai yar purse, gado ta nufa bayan ta gama ta zauna ta bangaren da Haisam yake tana kallon yadda yake baccin hankalin shi kwance, murmushi ta shiga saki ta matsa saitin fuskar shi ta rankwafa tay pecking kumatun shi, tana d'agowa ya bud'e idanun shi slowly suka shiga cikin nata, bin ta da kallo yay kafin a hankali taji ya furta "kin yi kyau sosae" murmura mashi ido tay tace ta gode, "Na gama shiryawa zan tafi" kai ya jinjina yace Ok bari ya kaita, da sauri tasa duka hannuwan ta akan shi alamar kada ya tashi tace ita zata je da kan ta, d'an waro ido yay cikin murya ta wanda ya tashi daga bacci yace "hannun ki fa bai fad'a sosae ba...." Da sauri ta katse shi "Wllh kau lafiya lou yanzu na iya driving d'in sosae rannan ma ba ni na kai mu School ni da Mino ba, wani kallo yay mata "amman ai ina Motan ko" tura mashi baki tay ta fara shagwa6a tana fad'in Allah lafiya lou zata je ai tana fita ita kad'ai taje gidan gwaggo ko, shiru yay kawai yana kallonta tace to bari taje sai yazo ya dawo da ita, kaman bazai ce komai ba sai kuma taga ya lumshe mata ido ta washe baki ya furta "You should be very careful pls" da sauri ta jinjina mashi kai, saida ta k'ara pecking lips d'inshi sannan ta mik'e yace bari yazo yaga fitar ta tace a'a don Allah yayi baccin shi, girgiza mata kai yay ya yunk'ura ya tashi zaune, yana ruk'e da hannunta suka fito daga cikin d'akin tace bari ta d'aukko abu a kitchen, bada Jimawa ba ta fito ruk'e da madaidaicin basket mai kyau acikin shi luxury Warmers ne guda biyu Abincin rana da tayi ne dama ta zuba zata kai ma su Fauzy, Bayan sun iso parking space d'in shi ya shiga ya fiddo mata da Motar cikin harabar, bud'e kopar driver seat d'in yay ba tare daya fito ba yace mata ta bari suje kawai ta nok'e mashi kai tana d'an yamutsa fuska tace to in ba'a bari tana fita ita kad'ai ya za'ai ta saba, shiru ya d'anyi yana kallon ta har lokacin idanun shi a d'an lumshe suke, ba yadda ya iya tunda ta nuna tana so ya fito ita kuma ta shiga ta zauna sai faman sakin murmushi take bayan ta daidaita natsuwar ta ya rufe mata kopar, sauke glass tayi ta kashe mashi ido tare da furta kada ya damu ai yasan matar shi nada saurin gane abu yay murmushi kawai tace ya shigo ta aje shi a bakin gate sai ya koma ya girgiza kai yace zai koma, yana tsaye taja Motar ta tunkari gate Officer ya taso ya zuge mata shi da zata fita ya d'aga mata hannu tare da Fad'in Allah ya tsare ta sakar mashi horn, Jama'a kuzo kuga Fatuu yar fillo na tuk'a Jeep abun na Allah ne, bata yi tunanin tsayawa ba a gidan su shagon Kawu Amadu ma a rufe yake tasan bai wuce yana ciki yana bacci ta wuce. Alhamdulillah, lafiya lou ta k'araso kopar gidan su Fauzyn, bayan ta parker ta fito kopar baya ta bud'e ta d'aukko basket d'in Abincin bayan ta rufe Motar tana niyyar nufar cikin gidan wayarta ta fara ringing tun bata ga mai kiran ba ta gane Haisam ne, d'auka tayi tana yar dariya tace ya kwantar da hankalin shi gata ta iso lafiya a hankali ya furta Alhamdulillah, tambayar shi tayi halan ma bai koma baccin ba yace mata ya kasa Saboda tunanin ta tane dariya tace to ai yanzu sai ya koma kafin ai la'asar ya furta Ok, tambayar ta yay yaushe zai zo ya dawo da ita tay d'an Jim kafin tace to asaman mi zai zo ko ya bari ta dawo da sauri yace a'a indai zata kai dare to bazata yi driving ba, k'arshe Tk tace to ya turo sai ya dawo da ita yace Ok, ba kowa a cikin parlon lokacin da ta shiga yaran Aunty Mareeya na tahfiz, sallama ta tsaya tana yi a cikin parlon jin shiru yasa tayi tunanin k'ilan bacci suke ta nufi d'akin Fauzy, tura kopar tayi ta shiga da sallama tana shiga ta hango Fauzy kwance a saman gado tana facing ceiling ta d'age k'afafun ta, saida ta isa bakin gadon sannan ta ankare da ita da sauri ta kai hannu ta cire earpiece d'in dake a kunnanta ta tashi zaune jikinta sanye da jeans da shirt, waro ido tay alamar mamaki Fatun ta zauna a bakin gadon bayan ta aje basket din, "Yaushe kika zo har ban ji shigowar ki ba?" Fauzy ta tambaya da alamun Mamaki, yar harararta Fatuu tay tace "Yaushe dama zaki ji na zo kin dad'e kunnuwa" dariya tay tayi mata sannu da zuwa Fatun ta amsa, "Ya yi kyau Amaryar Ya Haisam Mom twins in sha Allah, wannan wanka haka kinga yadda kika had'u sai kikai kaman wata shuwa Arab wllh" yar dariya Fatuun tayi "godiya nike Amaryar Sameer in sha Allah" yanayin fuskar Fauzy ne ya canza tana d'an murmushi had'i da d'an ta6e baki Fatun tace ita da zata ce Allah ya yarda tay murmushi kawai, "ina Ya Haisam d'in shi ya kawo ki?" Girgiza mata kai tay tace ita kad'ai tazo tace Napep ta hawo kenan, k'ara girgiza kai tay tace a Motar ta, da alamun mamaki Fauzy tace "inyee, kice hannun ki ya fad'a sosae" kai ta d'aga mata tana murmushi, shiru suka d'an yi duk suna d'an murmushi Fauzy na son tambayar ta yadda sukai da Haisam ta kasa can dai tay k'arfin halin ce mata ta tambayi Ya Haisam d'in tace mata eh, "to ya kukai da shi ne?" Wani kallo mai kamar harara tayi mata tace "ba ke zan fad'i mawa ba wadda ta bani sak'on zan fad'i ma yadda mukai dashi" gyad'a kai tayi tace Allah ya bata hak'uri Fatun ta saki dariya, tambayar ta tayi Aunty Mareeya tace mata tana d'aki ita da mijinta k'ilan ko bacci suke tun bayan dai da suka ci Abinci kowa ya shige d'aki itama tayi baccin ta farka ne, "ko in kira maki ita a waya ne?" Da sauri Fatuu tace a'a tunda ba yanzu zata tafi ba ta k'yale ta in ta fito sunyi Maganar tace to, kallon basket d'in data shigo dashi tay tace "k'awata mi muka samu haka?" tana murmushi tace mata alkubus d'in fulawa ne tayi, matsowa bakin gadon tayi ta kai hannu ta d'aukko basket d'in, a saman gadon ta d'aura shi kafin ta kai hannu ta bud'e babbar Warmer d'in, sosae Alkubus d'in yayi kyau ya bada shape d'in robobin da tayi amfani dasu wurin yi, bud'e d'ayar warmer d'in tay nan miya ce da ta ji had'i tayi kitif tasha ganda mai had'e da tsoka sai uban k'amshi ke tashi, jinjina kai Fauzy tayi tana murmushi tace "Abinci mai sunan Abinci dai na a Warmers d'in yan gayu" yar dariya Fatuu tay tace "su ku kenan", Fauzy tace ina ai su ba yan gayu bane, rufe Warmers d'in tay ta maido basket d'in k'asa bayan ta aje ta d'ago Fatuu tace bazata ci ba tace zata ci bari cikinta ya d'an k'ara fad'awa yadda zata yi mashi cin mutunci ta d'aga mata kai, hira suka shiga yi farko kan Sameer ne Fauzy na bayyana mata abunda take tunani game da ba sonta yake ba kawai hakanan zai aure ta in ma an amince mashi kenan ita kuma Fatun tana nuna mata bata tunanin hakan daga baya suka dawo hirar karatun su, suna haka aka fara kiran sallar la'asar bayan d'an wani lokaci Fatuu ta mik'e don tayi salla, cire nad'in lifaya d'in tayi ya rage doguwar rigar ce a jikinta Fauzy dake kallon ta tace "Ma sha Allah abu dai sai k'ara girma yake, kinsan har na k'osa inga Babyn ku don nasan dole zai yi ko zata yi ruwan kyau wllh" dariya kawai Fatuu tayi Fauzyn ta k'ara cewa Allah dai ya raba lafiya tace Amin ya Rabbi, toilet ta nufa idon Fauzy a kanta tana magana kan yadda hips d'in ta suma suka k'ara bud'ewa, bayan tayo Alwalar ta fito ganin Fauzyn bata da niyyar tashi yasa tace mata ita bazata yi sallar bane ta d'aga mata tace "tawa ta kai tuni" yar dariya Fatuu dake tsaye tayi tace yaushe rabonta da tace bata salla tun bayan da ta samu ciki Fauzy tace dama ita da period yanzu ai sai bayan ta haihu in kuma tana daga cikin Matan da basu yi ne in suna shayarwa to har sai ta yaye bayan na haihuwa ya d'auke ta d'aga mata kai, Hijab tasa Fauzyn ta bata bayan ta shimfid'a mata abun salla ta kabbara, nufar k'opa Fauzy tayi ta fita bada jimawa ba sai gata ta dawo ruk'e da plate ta duk'a a gaban basket d'in ta fara zuba alkubus d'in, komawa tay saman gado ta fara ci, "Wllh k'awata ba zancen santi ba kin bala'en iya girki, yanzu dai ji yadda wannan alkubus d'in yayi dad'i sai kace na alkama ne wllh, wai don Allah ya akai kika iya sarrafa Abinci ne Allah sau da yawa ina mamakin hakan acikin rai na" ta k'arasa tare da tura tsokar nama idonta akan Fatuu data sallame salla tana kallonta da murmushi, "wurin gwaggo da Aunty Saude na koya na kuma k'ara da tawa fasahar, in kina so ki zo in koya maki ki rink'a yi ma Angon ki Sameer yadda zaki kama mana shi da kyau" tana dariya tace wannan wane irin Abinci ne bai ci ai tasan dole yana cin masu dad'i Fatuu tace to ai itama Hubby d'inta na cin masu dad'in amman a haka yake santin nata duk in tayi hakan ai ba hujja bace da zata ce bazata k'ara koyan yadda zata rink'a yin Abinci mai dad'i ba, sosae Maganar taba Fauzy dariya tace sai kace ta ga anyi auren nasu Fatun tace ai in sha Allahu ma za'a yi Sameer bai da wata mata sai ita da yardar Allah, shiru tay don bata san mi zata ce mata ba gashi tak'i ta fad'i mata yadda sukai da Haisam, "Wai Fauziyya ko Zarah ta zo....." Kaman daga sama suka ji muryar Aunty Mareeya tana fad'in hakan, had'a idon da sukai da Fatuu data juyo tana kallon ta yasa bata k'arasa Maganar ba ta d'an waro ido alamar mamaki, k'arasa shigowa tay ta nufi bakin gado ta zauna idon ta akan Fatuu dake ta mata murmushi tace "yar gidana yaushe kika zo ban sani ba sai yanzu da Abban su Hanif ya dawo daga Masallaci yake man Maganar Motar da aka parker a waje saitin gidan nan naje na lek'o ta ina gani nace wannan ai Motar Zarah ce?" Gaishe da ita ta fara yi kafin tace mata tun d'azu tazo Fauzy tace mata tana bacci, kallon Fauzy dake ta cin Alkubus tay ta d'an harareta "maimakon kije ki fad'i man tazo" yar dariya tay tace to tana tare da mijinta ya zata je mata d'aki, "to uban me ake a d'akin da bazaki je ba ko yau kika fara zuwa" dariya suka saki harda Fatuu Fauzyn tace "uhmm nidai ai ban ce wani abu ba ko nayi tunanin ko kuna bacci ne kuma da har zan kira ki ita tace tunda ba tafiya zata yi ba in k'yale ki gata nan ki tambaye ta" tsoki ta buga still dariya Fauzy ke yi tace mata ga Alkubus nan Zarah ta kawo masu ta jinjina kai, maido idon ta kan Fatuu tay tayi mata godiya ta tambayi mijin nata ya dawo lafiya dasu Hajiya da gwaggo duk ta amsa mata, mik'ewa tayi ta cire hijab d'in tana cikin ninketa Aunty dake kallonta tace "yar gidana abun Alheri dai sai k'ara girma yake ma sha Allah, amman ya fara motsi kuwa?" tana dariya tace mata a'a ai ba fa wani girma can yayi ba ta fad'i mata watannin shi Aunty tace to amman dai gaskiya in haka ne zata yi girman ciki yadda cikin farko bai cika wani girma ba k'ilan dai da gaske yan biyun ne, ita dai murmushi kawae take yi, bayan ta aje Hijab d'in ta nufi gadon ta haye idon ta akan Aunty Mareeya tace "kiyi hak'uri jiya kinata jira na naga dare yayi shine na yanke bari sai yau in zo in fad'i maki komai baki da baki" da sauri tace ai ba komai dama itama bata san ran a jiya zata kira ta fad'i mata yadda sukai ba ba kamar data ce bai gari, "Na tambaye shi duk abunda kika ce harma da wanda baki ce ba wato aikin shi" a k'agauce Aunty tace aikuwa fa ba'a san aikin shi bama wllh to yanzu ya sukai da shi, tiryan tiryan ta shiga yi mata bayanin duk yadda sukai da Haisam gaba d'aya sun maida hankalin su akanta harda Fauzyn tayi cak tana kallon bakin Fatun, tun kafin ta rufe baki Aunty ta shiga washe baki ta fara fad'in "Alhamdulillah, Alhamdulillah dama ni wllh ban ji ina zargin shi da komai ba kawai a rai na ina jin sakayya ce ubangiji zai mata da shi" Murmushi Fauzy kawai ke saki bata ce komai ba Aunty ta kalle ta tace "to kin ji dai ai yanzu sai ki kwantar da hankalin ki tunda ga bayani nan daga bakin mai dil gashi nan kuma da kan shi yace abun kiyi Alfahari ne ma ita matsalar tashi da aka ce kada ki d'auketa a babbar matsala ke zaki zage damtse ki hana shi hakan sannan ki kore mayun kudajen matan da ke bibiyar shi wannan duk mai yuwuwa ne ba kamar in kika shige daga ciki in sha Allah za muyi k'ok'ari ya dawo bai sha'awar ta6a kowacce mace in ba ke ba" murmushi kawai Fauzy ke saki haka ma Aunty Mareeyar sai faman washe baki take gaba d'aya dad'i ya cikata farinciki ne bayyane akan fuskar ta can tace ma Fatuu to miye aikin shi data tambaya bata fad'i masu ba, bayanin aikin nashi ta shiga yi tun kafin ta gama yanayin fuskar Aunty ya fara sauyawa lokacin data gama fad'i masu gaba d'ayan su zaro ido sukai da alamun razana Aunty tace wai bata gane su ke yin rocket ba wai wadda ta sani ko kuwa, Fatuu na dariya tace mata eh, aikuwa gaba d'aya ta k'arasa zaro idanun ta kai duka hannuwanta ta dafe k'irji tace "na shiga ukku ni Mariyatu, Zarah wannan abun fa ba shine ake ce ma makamin k'are dangi ba yanzu ace su suke yin shi" sosae ta rud'e don yanayin fuskar ta ya bayyana still dariya Fatuu ke yi tace mata itama wllh farko saida hankalinta ya tashi amman ai yace shi yafi k'arfi ta bangaren had'a jirgi kuma ba kowanne rocket ne missile ba, yarfa hannu Aunty tay ta d'an cize baki tace "ki gane Zarah irin abun nan ko wanda yasan inda ake saida su dole kaji tsoron shi balle kuma wanda ya san inda ake k'era su yake kuma aiki a wurin, haba, haba kice dole ma Sameer yak'i dariya suda ke k'era wannan mugun abun tashin hankalin ta ya zai rink'a ma sakin fuska, ai wllh Fauziyya ko baki son shi yanzu yazama dole ma ne ki amince mashi in dai ba so kike ya k'arar da kaf dangin mu ba koma ya tashi garin Funtua gaba d'aya", Fatuu mi zatayi in ba dariya ba harda dafe ciki da 6ungulawa saman gadon don gaba d'aya Aunty fa ta rud'e, ita kanta Fauzy duk da ta d'an razana amman sosae Aunty ta bata dariya, bayan Fatuu ta tsagaita da yin dariyar ta taso zaune nan ta shiga kwantar ma Aunty da hankali tana nuna mata shifa ba'a ce dashi ake k'era wannan ba kuma koda dashi d'in shidai ai sana'a ce yake kuma misali don suna k'erawa hakan ba yana nufin sun iya amfani da shi ba tunda hakan ma wani ilimin ne, fuska a kwa6e Aunty ke kallonta hakan ya k'ara ba Fatuu dariya, da k'yar dai aka samu Aunty ta d'an kwantar da hankalinta Fauzy ta zuba mata alkubus ta fara ci duk in Fatuu ta kalleta sai ta saki dariya ita kuma saidai ta d'an girgiza kai ta tura Alkubus a baki, itama ta yaba alkubus d'in tana cikin ci tace ma Fauzy sai ta tsaya ta koya Abinci sosae in ba haka ba taje ta kwa6a mashi ya tarwatsa ta da rocket ita ta sani gaba d'aya suka kwashe da dariya Fauzy na fad'in ai fa sun bani da zancen rocket, bayan ta gama ci Fauzy tace yanzu sai ta kira Baban ta sanar mashi ko tana harararta tace ta sanar mashi da uban mi da ba tace bata son shi ba, Fauzy na murmushi tace to yanzu tana son shi Saboda kar a tashi Funtua suka saka dariya harda ita Auntyn, Kiran Mahaifin nasu ta shiga yi tana fara ringing ya d'aga cikin girmamawa ta gaishe dashi tare da tambayar yadda suke duk ya amsa mata, a nutse ta shiga yi mashi bayanin sun yi magana da Fauziyya kuma ta nuna tana son shi har ma sun yi bincike akan shi, nan ta kwashe komai ta sanar mashi amman banda zancen ta6a mata da aka ce yana yi, nannauyar ajiyar zuciya mahaifin nasu ya saki yay d'an jimm har saida Aunty ta tambayi Lafiya da yanayin damuwa a muryar shi yace to ai abun ne ba K'aramin Al'amari bane d'an Governor fa, Aunty tace "Don Allah kar ka wani tashi hankalin ka Baba ai Allah baya daurawa bawa abunda bazai iya ba, kuma ai shi yaron yasan ita wacece tunda ta sanar dashi har ma aiki daka ajiye da noma da kake yi yanzu duk ta sanar mashi tunda yaji ya gani to kaga ai ba abun damuwa bane kuma dama ai ance wani hanin ga Allah baiwa ne k'ilan sakayyar abunda Mujaheed yayi mata ne" jinjina kai yay ya furta hakane kafin yace yanzu ita ya take ganin za'ayi don shi wllh gaba d'aya kan shi ya d'aure ganin abun yake ma kamar wani al'mara, dariya tayi tace ba al'mara bane da gaske ne ta kuma cewa "abunda nike gani Baba shine ka kira su kamar yadda kace masu sai kace cikin weekend mai zuwa in yayi masu sai su zo" shiru yay kafin yace mata hakan bai yi kusa ba kuwa tace a'a ai tunda neman Aure ne za'a zo ba wai bikin ba gara kawai a basu dama yanzu zata yi ma Yaya Mubarak magana duk abunda ya dace za'a yi in sha Allahu itama in dai zasu zo lokacin tana tunanin zata zo, a sanyaye yace Shikenan zai kira su d'in duk kuma yadda sukai zai kira ya sanar mata tace to, fatan Alkhairi yayi ya saka masu Albarka daga haka sukai sallama, suna gamawa ta k'ara ma wayar kud'i ta bank ta kira Mahaifiyar su, kamar yadda sukai da Baban nasu haka itama tayi mata bayani, sosae itama jikinta yay sanyi daga yanayin muryarta tace mata yanzu ita tana ganin hakan mai yuwuwa ne Aunty tace in sha Allahu su yi Addu'a kawai tace Shikenan zasu yi, bayan sun gama wayar kallon Fauzy tay da tay zuru ita kanta na Baban nasu ganin abun take kamar al'mara d'in tana murmushi tace mata to ta kira Baban nasu Fauzyn ta d'an ta6e baki tace umm Fatuu ta kai hannu ta dafata da murmushi tace wannan ba abun damuwa bane abun farinciki ne k'awata tay yar dariya, "Yanzu ni abunda nike gani in sun amince zasu zo Weekend d'in kar a wani ce za'a takura kai tunda nasan maza ne masu zuwa kuma ko gidan namu suka gani zasu fahimci irin k'arfin mu, yanzu bari in je d'aki in natsu sai in kira Yaya Mubarak d'in tunda shine mai kud'in gidan yana aiki kuma dama ko ba yanzu ba kullum cikin yin hidima yake sai mu tsara abunda ya kamata duk dai a taru a had'a k'arfi da karfe, ina ganin har fenti yakamata ayi ma gidan sannan tunda a parlon Baba za'a tarbe su sai a gyara shi sosae a canza kujerun ciki da duk abunda yakamata, gaskiya dole ma in je" ta k'arasa Maganar tana jinjina kai, a sanyaye Fauzy tace to banda gadon Baban za'a canza Aunty tace tana tunanin ba sai an canza dashi ba tunda a parlor ai za'a zauna, "Amman in suka ce zasu kwana fa?" Fauzy ta fad'a fuska a d'an yamutse, shiru Aunty tayi alamar nazari can tace gaskiya bata tunanin hakan su fa manyan mutane basu kwana wuri irin haka in ma ta kama masu a Hotel suke sauka amman ko don k'ilan su buk'aci shiga yin alwala ko wani abu akwae buk'atar a canza d'in hatta toilet d'in ma a gyara shi abunda ke buk'atar canzawa a canza, kai Fauzy ta jinjina sai kuma tace ma Aunty Mareeyar akwae kud'i a account d'in ta sai a had'a dasu da sauri tace Yauwa to aikuwa zasu taimaka sosae tunda suna da d'an yawa tana rufe baki Fatuu tace itama bari ta tura mata gudunmawarta duk sai a had'a, "A'a Zarah don Allah ba sai kinyi wata dawainiya ba tunda kema ai baki rasa uzurorin kud'i ko" d'an murmushi tayi tace "ai Aunty Mareeya shine yanzu uzurin ya taso ko, ko bamu zama yan'uwa bane?" da sauri ta girgiza kai "tabbas mun zama Zarah, tun tuni ma" yar dariyar jin dad'i Fauzy tayi, nan take ta turo ma Fauzy 300k lokacin data duba alert d'in gaba d'aya ta zaro ido baki bud'e ta d'ago ta kalli Fatun sai kuma ta juya ta kalli Aunty dake niyyar tambayarta minene ta rigata ta hanyar d'aga mata wayar tana nuna mata credit alert d'in, waro ido itama tayi ta hau girgiza kai "gaskiya Zarah kud'in nan sun yi yawa a rage don Allah hidindimun rayuwar nan da yawa daga wannan fa sai wannan" girgiza kai Fatuu tay tace Allah ko an maido mata itama sai ta sake turowa, ba yarda Aunty bata yi da ita ba amman tace Allah baza'a rage ba ai don tana da su ne ta bada kuma in tasan zata k'waru ai bazata bada har haka ba inda ma tana dasu sosae fin haka zata bada to don ta tura ma Baffan ta wasu ya k'ara jari sannan kuma an siya mata shanaye, gaba d'aya fuskokin su sun nuna damuwa tana dariya tace don Allah wai ba an zama d'aya bane kuma itama ai ba wahala tayi ta same su ba nan ta shiga fadi masu da bikinta ta samu kud'i sosae don ko Mahaifiyar Sameer d'in 500k ta tura mata banda wanda k'awayen Mom suka babbata mai dubu hamsin mai dubu d'ari, daga baya godiya suka shiga yi mata Fauzy ta rungumeta ta saka kuka tana fad'in bata san da wane baki zata mata godiya ba tabbas dama tunda ta fara ganinta a school taji tana kaunarta ashe ita d'in Alkhairi ce a gareta, murmushi kawai Fatun ke yi tana ce mata haba ba komai fa, "In rungume ku to nima in yi kukan" Aunty ta fad'a ta kai hannu ta rungumo su gaba d'aya Fatuu ta saki dariya, bayan ta sake su sosae tayi ma Fatuu godiya da Addu'oi daga baya ta mik'e tace bari taje suyi magana da Yaya Mubarak d'in, har ta juya Fatuu ta kirata ta juyo fuskarta da murmushi ta tambayeta ya akai ta d'an yamutsa fuska tace Abincin data dafa take son ci, hannu Aunty ta kai ta ruk'e ha6a tace "wani aikin sharri sai ciki, yanzu ki kawo mana wannan had'addan Abincin amman namu tagajan tagajan kike son ci" gaba d'aya sukai dariya Fauzy tace wllh ta manta ne bata zubo mata ba tunda tazo ko ruwa ma bata kawo mata ba Aunty tace gaskiya bata kyauta ba wato ta dafi abincinta mai dad'i kuma ita ko ruwa bata kawo mata ba hakan ai ba Adalci bane, da sauri Fauzy ta saukko tana fad'in ayi hak'uri tasan tayi ba daidai ba bari ta kawo mata suka nufi k'opa tare da Aunty, bayan taje Bedroom d'inta nan ta hau fad'i ma mijinta Abban su Hanif yadda sukai da Fatuu game da bayanin da Haisam yayi kan Sameer da yadda sukai da Mahaifinta harda kud'in da Fatun ta bada, sosae yaji dad'in dukkan bayanan dama jiya da daddare Aunty ke fad'i mashi yadda sukai da Baban su, godiyar kud'in da Fatuu ta bada yay da Addu'ar fatan Alkhairi, kiran yayan nasu ta shiga yi bayan ya d'aga sun gaisa yace mata ai gashi ma a gida yanzu Baban su ke fad'i mashi yadda sukai yanzu ma suna niyyar kiran su Mutanen da suka kira din ne tace to duk yadda sukai dasu sai ya sanar mata, har zata mashi sallama yace mata ta dai tabbatar da duk bayanan da aka bada kan shi gaskiya ne ko don kada aga yana da nasaba ayi abunda za'a zo ayi dana sani daga baya ba fata ake ba, halin Haisam ta shiga fad'i mashi harda yadda ya auri Fatuu shima duk da ba ajin auran shi bace ta kuma tabbatar mashi da yadda yake ruk'e da ita yanzu daga baya ma sai ta mik'a ma mijin nata wayar don ya k'ara mashi bayani yana d'an murmushi ya amsa, bayan sun gaisa a nutse ya shiga yi mashi bayanin gaskiya Haisam mutumin kirki ne tun daga kan mahaifin shi da dangin shi yace yana da yak'inin bazai fad'i abun da ba haka bane akan d'an uwan nashi, hamdala Yaya Mubarak yay yace dama haka suke son ji tunda bai kamata ba ace ba ai wani bincike ba akan shi saboda aure ba abun wasa bane bayan sun k'ara tattaunawa daga baya sukai sallama ya mik'a ma Aunty wayar, cigaba da tattaunawa kan abunda yakamata ayi sukai daga baya sukai sallama. Bayan sallar Magrib Aunty ta shigo d'akin Fauzy lokacin Fatuu na zaune akan abun salla cikin washe baki ta sanar masu yanzu Yaya Mubarak ya kirata yana sanar da ita an kira wurin su Sameer din yadda aka fad'a yayi masu sun ce ranar Asabar zasu je Funtua har saida gaban Fauzy yay wani irin bugu jin abun dai da gaske ne gashi ko waya da Sameer d'in ma basu yi ba, sosae Fatuu tayi murnar jin hakan sai faman washe baki take haka Aunty Mareeya ma da alama ta manta da zancen rocket, kiran Mahaifiyar su tayi tace mata ga Zarah d'in dama suna gaisawa da ita ta wayar Fauzy, cikin girmamawa kaman ko yaushe Fatuu ta gaishe ta bayan ta amsa ta tambayi su gwaggo da mai gidan nata duk tace mata lafiyar lau nan ta hau yi mata godiya da Addu'oi Fatun na murmushi tace mata ai ba komai duk an zama d'aya tace hakane kam. Bayan sallar isha Tk ya kirata yace gashi nan kopar gida ya zo tace to dama a shirye take don sunyi waya da Haisam yace mata ga Tk d'in nan zuwa, hijab Fauzy ta saka suka fito a tare, a cikin parlon suka iske Aunty Mareeya tana serving mijinta Abinci da Hanif shida k'annan shi guda biyu sultan da iman, tana ganin su tace badai tafiya ba Fauzy tace eh ga Tk nan yazo shi zai maida ta, mik'ewa tay tana fad'in maimakon to ya shigo, gaisawa sukai da mijin Aunty d'in yana d'an murmushi ya amsa tare da yi mata godiyar abun Alkhairi daya ji itama murmushin take tace mashi ba komai, Bedroom Aunty ta nufa bada Jimawa ba ta fito ta yafo gyale Fatuu tay ma mijin nata sallama yace ta gaishe da maigidan ta, harda su Hanif suka mik'e don yi mata rakiya, har zasu fita daga parlon Aunty tace ma Fauzy to ina basket d'in Abincin da sauri tace au ta manta wllh ta koma don ta d'aukko su kuma suka fita. Bayan Fauzy ta gama komai ta kwanta ta fad'a duniyar tunanin Sameer, a yanzu ta gane tana son shi don da kafin suji bayani game dashi fargabar kada ace yana da wani mummuna hali ce ta kamata amman yanzu tunda taji bayanin da Haisam d'in yay take jin wani irin farinciki a cikin ranta sai faman yawo Sameer d'in yake mata a rai tun ma Fatuu na nan, hannu ta kai gefen filon data d'aura kanta ta d'aukko wayarta, bayan ta bud'e gallery ta shiga ta bud'o hoton shi ta k'ura ido tana kallo, zuciyar ta ce ta shiga raya mata in dai ta aure shi tabbas ba K'aramin dace da sa'a tayi ba wllh don ta ko ina Sameer yafi k'arfinta nesa ba kusa ba, shiru tayi tana cigaba da kallon hoton fuskar ta da d'an murmushi a zuciyarta ta shiga fad'in "da gaske kana sona ko kuwa matsayin taimakona zaka Aure ni" shiru tay don bata da amsar da zata ba kanta, tana ta faman zooming hoton tana k'are mashi kallo ji take kaman ta kira shi don sai taji tana son jin muryar shi, a ranta ta raya to in ma ta kira shi d'in tace mashi mi wata zuciyar tace ta gaishe dashi kamar yadda take yi, kokonton kiran nashi ta shiga yi k'arshe ta yanke bazata kira shi ba gaskiya kada yay tunanin ko don Saboda Maganar neman auren nata ne yasa ta kira, "to kuma in ba ki kiran nashi taya zai sake maki har ku saba tunda dai shi ga irin halin shi, kamata yay ki fara k'ok'arin jawo shi a jiki yadda zai sake maki har kiyi abunda Ya Haisam yace na raba shi da matan dake bibiyar shi" zuciyar tace ta raya mata hakan tay shiru tana ta d'an cizon k'umbar babban yatsanta gani take kaman hakan ba abu bane mai sauk'i can dai ta fita daga cikin gallery d'in ta koma phone bayan ta nemo number d'in shi saida tay d'an jimm kafin tay dialing nan take ta shiga, duk bugu d'aya tare yake da fad'uwar gabanta sosae fargabar kiran shi ta kamata yau ba kamar sauran lokuttan da ta kikkira shi ba a baya, har ta yanke bai d'aga ba sam bata ji komai ba don dama duk in ta kira bai d'auka sai daga baya ya biyo kiran, tun tana saka ran zai kira har ta fara fiddawa ta shiga sak'a ko bai son yin magana da ita ne ko kuma k'ilan wani uzurin yake k'arshe kuma ta yanke k'ilan ma yayi bacci ne, rufe idanunta tayi da niyyar yin bacci bayan ta gama Addu'a bata dad'e da rufe idanun ba wayarta ta fara ringing har saida gaban ta ya fad'i da sauri ta bud'e idanun, k'ura ma screen d'in ido tay bayan ta d'aukko wayar tana kallon sunan Sameer daya bayyana kaman bazata d'auka ba can dai a d'arare tay picking ta kai wayar kunnanta, shiru tayi shima kuma bai tanka ba can murya k'asa k'asa tace mashi ina wuni taji ya amsa da "lafiya" d'an murmushi ta saki jin voice d'in shi, tambayarta yay mi take bata yi bacci ba cikin daidaita natsuwa ta bashi amsa da ai ta kwanta baccin ne dai bai zo ba, bai ce komai ba suka d'an yi shiru can ya sake tambayar tana ina ne ta bashi amsa da tana gidan Sister d'inta tazo weekend k'asa k'asa taji ya furta Ok, "Kai ma kayi baccin ne?" da k'yar ta tambaya harda d'an cize baki, amsa ya bata da eh acikin baccin ne suke magana nan take ta gane Magana ya gaya mata ta saki yar dariya da har saida yaji sautin ta tace "ai ina nufin ko kayi bacci ne na tashe ka, "No, ina wurin Dad ena" d'an waro ido tay bata ce komai ba suka k'ara yin shiru, "akwae wani abu?" bayan d'an wani lokaci taji ya tambaya da sauri tace "a'a, dama na kira in gaida ka ne", "Sai kin ga dama kike wannan kenan" ba zato taji yace haka ta d'an waro ido a ranta tace kaji shi ma ba sai ya ga dama yake kirana ba a fili kuma sai tace "a'a, ba haka bane, ina son in rink'a kiran to kuma ban san ko kana cikin aiki ba kada in takura maka, "You can call whenever you want, in ina free zamu yi magana" bayan ya d'an yi shiru taji ya fad'i hakan wani irin dad'i taji tana murmushi tace mashi to, "Yaushe zaki gama School?" d'an jimm tay alamar tunani kafin tace "nan da Kusan 7 Months masu zuwa" shiru ya d'an yi sai kuma taji yace Kusan ko kuma ya kai da sauri tace eh zasu yi good 7 Months kafin su gama ya furta Ok, shiru suka k'ara yi Fauzy sai faman sakin k'ayataccen murmushi take don wani irin dad'i take ji da suna wayar duk da ba wata Magana suke ba, bayan wani lokaci taji yace mata ta kwanta yadda zata tashi da wuri tace ai gobe ba School ya furta Ok ya manta, "Yaushe zaka koma UK wurin aikin ka?" kawai sai ji tayi ta furta hakan da bud'ar bakin shi sai ce mata yay ya akai tasan a can yake aiki, waro ido tay ta bud'e baki don sai lokacin ta ankare da tayi 6aram6arama da ta fad'i hakan yanzu ya zata ce mashi yadda akai ta sanin tunda bai yuwuwa tace a wurin Haisam, tana haka taji yace yana jiran ta bashi amsa ta shiga yan kame kame can zuciyarta ta tuna mata da hoton shi data gani a Dp tare da turawa kuma akwae rubutu a k'asan dp d'in duk da bazata iya tuna mi aka rubuta ba, cikin yar rawar murya tace "d..dama a profile d'in ka ne naga hakan" tana yin Maganar gabanta ya hau fad'uwa gudun kada ace ba hakan a profile d'in, cikin ikon Allah kuwa a business profile d'in shi akwae bayani akan Company d'in nasu hakan yasa ya furta "Ok" wani sanyi taji a ranta ta d'an yi farfar da idanu alamar ta sha, ce mata yay zai koma soon, "Allah ya kaimu ya kai ka lafiya" slowly ya furta "Ameen", shiru suka d'an k'ara yi taji yace yana son yin bacci ya gaji ya za'ai da sauri tace "to, gud night" shima hakan ya furta mata ta ciro wayar ta kashe kiran, mirginawa tay ta koma kallon sama tana ta murmushi sosae abun ke bata mamaki wai ace wannan mutumin data gani a d'akin Ya Haisam taita kallon shi har ya Harare ta ne wannan kuma ma wai aure zasu yi, jinjina kai ta hau yi still da murmushi akan fuskar ta a fili ta furta "ikon Allah kenan!" komawa tay tunanin to wai bai iya soyayya bane ko mi ace wai a haka soyayya suke tayi ma tunanin zai mata Maganar neman Auren nata amman bai ce komai game da hakan ba, wata zuciyar ce ta raya mata k'ilan kuma izzar ce ta sa haka kaman yadda Aunty tace ko kuma bai sake mata ne suyi soyayyar don kada ta raina shi, yar dariya tay ta raya in hakane kuma zai aureta, tunanin to su matan da akace yana ta6awa ba soyayya suke ba can kuma ta raya koda yake ai ance yawanci sune ke lik'e mashi, yin wannan tunanin yasa taji ranta ya 6aci ta d'aure fuska a fili ta furta "zanyi iya bakin kokarina inga na hanaka aikata hakan in sha Allahu" ta kai Maganar tana d'an jinjina kai, wayarta ce tay k'ara ta juya ta kai hannu ta daukko, sak'o ne aka turo mata bayan ta bud'e bin alert d'in tay da kallo na 200k daga Sameer, d'an murmushi tayi ta fita daga wurin tasan ko ta kira ba d'auka zai yi ba hakan yasa ta shiga WhatsApp ta tura mashi sak'on godiya, tunanin ko Aunty Mareeya tayi bacci ta shiga yi sai kuma ta raya bari ta jaraba kiran ta, wayar na fara ringing ta d'auka tare da tambayar Fauzyn miye tace "ashe baki yi bacci ba, dama zan sanar maki ne yanzu muka yi waya da Sameer" tana rufe baki tace "da gaske...,ya kira kenan?" Shiru Fauzy ta d'an yi kafin tace mata a'a itace ta kira ta gaishe shi, "Ya yi kyau hakan kin kyauta dama bai kamata ki biye ma halin shi ba ta hakane zaki rink'a jawo shi jiki har ya sake maki kuma ki cire duk wani tunanin wai ko zai aure ki ne don ya taimaka maki da sauran su in bai son ki ba yadda za'ai ya aure ki tunda aure fa ba abun wasa bane da zai tsallake tarin yan mata ya za6e ki don taimako ba gama misali nan akan Zarah ba haka mukai ta nuna mata mijin nata na son ta shiyasa ya amince ya aure ta kuma sai gashi hakan ne" jinjina kai Fauzy tay tace to, "ya yi maki Maganar zuwa neman Auren naki ne" da sauri tace "a'a wllh bai ce man komai ba game da hakan kawai waya mukai nace na kira in gaishe shi ne shine har yace wai sai naga dama nike hakan nace ai don kada in rink'a takura mashi ne shine yace zan iya kiran shi duk in ina so in dai yana free zamu yi magana", Aunty ta furta da kyau ko wannan ma ai alama ce ta yana son ta, cigaba Fauzy tay tace mata ya tambayi lokacin da zata gama Makaranta ma, a d'okance Aunty tace "ina jin Saboda ranar da za'a saka maku ne ya tambayi wannan to", da sauri Fauzy tace mata eh itama tayi tunanin hakan don dama data kira bai d'auka ba sai daga baya shine yace mata yana wurin Dad d'in shi ne, "Ma sha Allah abu dai nata tabbata" Aunty ta fad'a tana washe baki, fad'i mata zancen kud'in daya turo yanzu tayi Auntyn tace "wato shi soyayyar bada kud'i ya iya bata kalamai ba kenan, hakan yayi kyau yayi ta turo su muna mashi godiya don yanzu ba zamu rink'a mamaki ba tunda mun fahimci kud'in ne har sun mashi yawa" Fauzy na dariya ta furta "kai Aunty...", "Allah kuwa Fauziyya a yadda aka fad'i aikin da yake na tabbatar ba k'ananun kud'i yake samu ba ga kuma Baban shi Governor kacokam, da ya turo maki kawai kiyi mashi godiya tunda k'arshe ma shi za'ai ma amfani dasu" murmushi kawai Fauzy tayi kafin tace mata yanzu ta turo mata su gaba d'aya ne tace a'a ta bari sai gobe zasu zauna su tsara abubuwan da za'a yi dasu don har sun gama Magana da baban su Hanif ranar Alhamis zata tafi sai ta bar su sultan d'in a gidan Maman taufiq ranar Friday in ta dawo daga School sai su dawo wurinta Fauzyn tace to, "Oh ikon Allah ikon gaske, abu dai kinga kamar wasa kuma tabbata zai yi in sha Allah, gaskiya had'uwar ki da Zarah babban Alkhairi ne yo ke wannan ai ko karatun naki ma ba lalle ki amfana da shi ba kamar yadda kika amfana da sanin Zarah kawai dai shi ya zama sila ne", "Wllh Aunty baki ji yadda nike jin ta ba a raina tamkar yar uwata uwa d'aya uba d'aya, ji yadda ta d'auki uban kud'i ta bada d'azun dama kuma tana man hidima sosae wannan ai ko wani dan'uwan naka mai hali wllh ba lalle yayi maka hakan ba, "Ai tsakanin mu da ita sai dai Addu'a kawai wllh itace zamu iya saka mata da ita amman duk da hakan ina fatan ace munyi mata wani abu da zata ji dad'i sosae a ranta......" Da sauri Fauzy ta katseta da fad'in "Yauwa Aunty nima wllh ina tunanin haka, amman tunda ga bikin Mino za'ayi mi zai hana muyi kokari muyi masu wani abu da zasu ji dad'i sosae" kai Aunty ta jinjina "tabbas kuwa kin kawo shawara duk da bansan a cikin ku bikin wa za'a fara yi ba amman koma dai nawa aka fara ba abunda zai gagara kinga in ma naki aka fara komai zai zo mana da Sauk'i don lokacin nasan Atm Card d'in Sameer ya riga ya dawo hannun ki" Dariya sosae Fauzy ta saka tana fad'in kai aunty kin jiki da wata magana, bayan sun gama tattaunawa sukai ma juna sai da safe, a ranar kowa kwanan farinciki yay tsakanin Aunty da Fauzy da kuma Fatuu. A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, ranar Alhamis tunda safe Aunty ta tafi Funtua, zuwa karfe sha d'aya ta isa gida lokacin data je har anyi ma gidan Fenti mai kyau kamar yadda sukai da Yaya Mubarak d'in su gaba d'aya gidan ya haske layin nasu dama kuma yana d'aya daga cikin gidaje masu d'an kyau a layin nasu, bayan sallar Azahar suka tafi inda za'a siyo furniture da ita da Kishiyar Maman su wadda itama suka d'auketa tamkar uwa a gare su don sam basu taso suka ga suna kishi ba da Mahaifiyarsu in ma suna yi to ba irin na tada fitina ko munafunci ba, wasu daga cikin K'annansu ma sai da suka girma ne suke gane wacece maman su, da yake Funtua akwae wuraren saida had'addun furniture da dama basu wani sha wahalar za6ar inda zasu ba don sun san inda zasu samu irin wanda suke so, bayan sun je wurin wanda katafaren bene ne sama da kasa duk kayan katakon ne iri daban daban, Manager d'in wurin suka buk'aci gani bayan anyi masu jagora wurin shi suka gaisa sannan Ya Mubarak yayi mashi bayanin dama kakara suke son suyi akwae kaya da zasu siya su kuma zasu za6i wasu sai suyi ciko cikin faran faran yace wannan ba matsala bane tunda suna yin hakan ya buk'aci ganin kayan suka sanar dashi suna gida amman akwai hoton su a waya, nuna mashi Vedio d'in kayan mahaifin nasu sukai ya gani kafin yace akwae buk'atar ya tura aje a gansu sai ayi masu kud'i sannan ayi cininkin, Yaya Mubarak ne yace to ba matsala a had'a shi da wanda zasu je d'in sai suje su dawo, ba 6ata lokaci aka had'a shi da Mutum biyu da zasu tafi Aunty Mareeya tace don Allah su kamanta ayi siyan mutunci Manager da suka fito tare da shi cikin show room d'in yana dariya yace karta damu su suna kamantawa sosae, a nan Aunty da Kishiyar Maman tasu da suke kira da gwaggo suka zauna akan kujeru don su jira su. Basu dad'e can sosae ba suka dawo ba laifi kam sun sayi kayan da mutunci don d'aki barin katako ne ba don dole tasa ba daba yadda za'ai Baban nasu ya yarda su siyar mashi da kaya Saboda yana son su ba tun yanzu bama sun so canza mashi kujerun yak'i yarda, za6ar wanda suke so suka shiga yi nan fa suka shiga ruwan idon wanda ya kamata, Manager d'in wurin ne ya basu shawarar d'aukar wasu lumbutsa lumbutsan leather chair yace tunda yaji suna d'akin mahaifin su zasu saka tunda shi Namiji ba'a san shi da k'yale k'yale ba, sosae kujerun sukai masu kyau saidai Aunty Mareeya tace ita abunda ke had'a ta dasu 6an6ara suke Manager yace ba dai irin wannan ba ai ko ita ta kalli leather d'in zata shaida ingancin ta yana mai tabbatar mata da ba abunda suke yi don ko shi irin su ne a parlon shi Aunty na dariya tace kodai abun su na yan kasuwa zai masu yace in yayi haka kuma ai kan shi ya kashe ma kasuwa ko, k'arshe dai su suka za6a harda dining table d'in su mai kujeru shidda, bayan sun gama da nan sama suka hau inda gadaje suke basu wani yi ruwan ido anan ba don sun san wanda ya dace su d'aukar mashi, bayan duk sun gama za6a Manager yace masu harda d'inkakkun labulaye suna dasu da agogunan bango in suna so Aunty tace yauwa bari su duba ya jagorance su nan ma suka za6a, bayan duk sun za6i abubuwan da suke so aka buga lissafi suka yi ciko wanda ya lillinka kud'in da aka Siya kayan nasu sosae, dama shima Ya Mubarak d'in ya bada tashi gudunmawar haka Baban su ma da yake ba K'aramin samu yake da Noma ba Saboda tsohon ma'aikacin Ktarda ne kuma ya kai babban matsayi kafin ya aje aikin banda babbar gonar da yake da ita anan garin yana da wasu k'ananu zasu kai ukku a wasu kauyuka dake kewaye da garin da alama dai Fauzy harda rud'ewa tasa tace ma Sameer mahaifin nasu bai iya biyan shi wayar data fasa mashi, a babbar Motar kamfanin aka zuba kayan su Aunty na gaba a Motar Yaya Mubarak suka tafi, bayan sun isa gidan tuni k'annansu har sun fito dana mahaifin nasu ta kopar shiga sitting room d'in shi ta waje, nan fa aka shiga sauke sabbin kayan yan unguwa suka shiga baza ido suna kallo, bayan angama aka d'aura nashi yan kamfanin suka tafi. Aiki ga mai k'are ka, aifa Aunty Mareeya bata ga ta zama ba dama ita ba mai son jiki bace bare abu kuma irin wannan nan fa suka zage ita da k'annanta maza da mata harda masu Aure guda biyu da suka zo aka shiga shirya parlon dama kuma tiles ne a k'asan kuma sam bai ji jiki ba Saboda ba yawan zirga zirga ake part d'in ba, zuwa bayan sallar La'asar sun gama komai gaba d'aya sashen ya koma kamar na Amarya sosae yay kyau yan gidan sai faman washe baki suke ba kamar yara sai tsallen murna suke, Vedio Aunty tayi ta tura ma Fauzy daga baya ta kirata ta sanar mata ta hau online ta gani, lokacin data yi arba da vedion bud'e baki tay ta waro ido nan ta shiga washe baki tana yarfa hannu sai faman fad'in Wayyo Allah take, da yamma mai gyaran Ac yazo don tuni ta lalace bata yi haka mai gyaran toilet ma, yan unguwa fa kan su ya kulle wasu da basu iya hak'uri sai tambayar ko biki ake gidan saidai ace masu a'a don Mahaifin nasu ya gargad'esu kan su ja baki suyi shiru sai komai ya tabbata. Sai da daddare Mahaifin su ya dawo gidan nan gaba d'aya aka taru a sashen nashi sai farinciki ake shima dai fuskar shi ta kasa daina murmushi Yay Addu'ar Allah ya tabbatar da Alkhairi duk suka amsa daga baya aka watse. Washe gari Friday shirye shiryen Abincin tarbar bak'i aka shiga yi da wuri su Aunty suka shiga kasuwa, a gidan Yaya Mubarak aka shirya za'a yi komai harda Warmers d'in da za'ayi amfani dasu plate duk anan za'a k'aro don Aunty Mareeya ta taho da wasu jigunannun Warmers d'inta dasu plates da sauran su. Alhamdulillah Allah yayi dare gari ya waye an shigo Asabar lafiya, tun da sassafe yan gidan suka tashi aka hau gyaran gida masu aikin Abinci duk acan gidan Yaya Mubarak d'in suka kwana, Misalin k'arfe sha biyu na rana bak'in suka iso garin, kiran Mahaifin su Fauzy sukai suka sanar dashi game da isowar tasu don aje ayo masu jagora, dama Yaya Mubarak na gidan isowar su kawai ake jira shi ya tafi don ya taho da su, bada jimawa ba suka iso layin gidan Motoci guda biyu ne d'aya jibgegiyar bakar Jeep ce wadda anan bakin suke sai k'arama wadda itama bak'a ce sai faman salk'i motocin suke anan kuma security ne cikinta gaba da baya don a cikin bak'in harda Commissioner wanda d'an uwa ne kuma abokin mahaifin Sameer d'in ne sai sauran mutum biyun d'aya k'anin Governor d'in ne uwa d'aya uba d'aya sai d'ayan cousin brother d'in Governor d'in ne matsayin Yayan shi yake, Mahaifin su Fauzy ne tare da yanuwan shi guda biyu sai Yaya Mubarak da wasu daga cikin manyan Yayan shi maza guda ukku suka tarbe su cikin girmamawa kowanne cikin bak'in na sanye da babbar riga ta alfarma mutum biyu farar shadda ce sai d'aya ash, security d'in wanda jami'an yan sanda ne guda biyu sai guda biyu na civil defence ne su basu shiga ba suna a cikin Motar amman sun bud'e kopopin sai lokacin Jama'a suka samu abun baza ido da kyau yara da Almajirai ba sosae ba duk sun tsaya cirko cirko suna kallon Motocin haka Mutanen dake wucewa kowa idon shi na akan Motocin da kuma wad'anda ke zaune a bakin shaguna sai faman tambayar juna abunda ke faruwa a gidan suke wanda kuma ba mai amsa. A mutunce aka shiga gaggaisawa parlon sai zabga uban k'amshi yake daga baya aka fara gabatar da kai, su Aunty Mareeya ne suka fara shigowa da kayan abinci suna jerawa a saman Dining duk sun yi wanka sun sa kaya masu kyau, bayan sun gama suka shigo parlon duk suka zauna a saman Carpet suna masu sannu da zuwa tare da gaishe su, haka akai ta shigowa gaishe dasu ana fita, k'anin Governor d'inne da fara'a ya tambayi harda Amaryar acikin wad'anda suka zo gaishe dasu Yaya Mubarak yace a'a ita tana Katsina acan take zaune a wurin Yayarta yayi masu kwatancen Aunty Mareeya suka ce sun gane yace to a wurinta take, bayan an gama yan gaishe gaishen Yaya Mubarak yayi masu Maganar Abinci suka ce da su fara abunda ya kawo su tukun don ba dad'ewa zasu yi ba, neman Auren Fauzy sukai aka basu sannan aka fara maganar saka rana, a yadda suka ce shi Angon so yake asa lokacin da zata gama karatu amman in hakan bai masu ba suna da damar saka duk lokacin da yayi masu, shawara suka shiga yi Yaya Mubarak ne yace yana ganin su shiga ciki sai a tattauna harda iyayen su mata duk suka amince da hakan, ce masu suka yi bari su basu wuri su ci Abinci bayan sun gama sai a k'arasa saka ranar bak'in suka ce to ba matsala duk suka mik'e suka nufi cikin gidan Yaya Mubarak ne ya tsaya don yayi serving nasu Abincin, A can cikin gidan gaba d'aya sun taru a parlon Mahaifiyar Fauzy harda Aunty Mareeya anata shawarwarin kan lokacin da za'a saka, shi mahaifin Fauzy nuna masu yake gaskiya wata bakwae kamar yayi kusa don yanzu lokaci gudu yake kaman gobe ne za'a ga yayi azo kuma ba'a gama shiryawa ba, "Ni a ganina Baba kawai a amince da lokacin da Sameer d'in ke so Maganar shiryawa kuma in sha Allahu ba abunda zai gagara watak'il ma fa suce basu son ayi mata kayan d'aki" Aunty ta fad'a, Malam Sama'ila k'anin Baban nasu ne yace "nima abunda nike tunani kenan tunda dai ai sun fi k'arfin duk wani abu da za'a yi ma Yarinyar", gwaggo ce tace "hakane, amman dai bai kamata a dogara da hakan ba in dai basu suka ce kar ayin ba yakamata ayi mata komai daidai bakin gwargwado" Baban su ne ya kalli Mahaifiyar tasu yace ita bata ce komai ba tay dan murmushi a sanyaye tace "to ita a ganinta kawai a bi yadda yaron ke so don ko ya aka sa dai lokacin zuwa zai yi kuma indai a cikin wata bakwae ba'ayi shirin daya kamata ba to ko an wuce hakan ba lalle ayi yadda ya kamatan ba" Aunty Mareeya da Baba Sama'ila ne suka ce wannan gaskiya ne, suna haka Yaya Mubarak ya shigo ya gama zuzzuba masu Abincin, bayan ya zauna ya tambayi a wace matsaya aka tsaya Aunty tayi mashi bayani, to shima dai bayan Mahaifiyar su ya bi yace abunda ta fad'a gaskiya ne kawai a amince da hakan ayi fatan Allah ya kaimu ya kuma rufa asiri ai duk ba sai an zurfafa ba tunda dai ansan wacece za'a aura duk aka ce gaskiya ne, dariya Baba Rabi'u wanda Yayan mahaifin nasu ne yayi yace Fauziyya ta giggi6o masu aiki har sai anyi meeting sannan za'a saka mata rana duk akayi dariya. Lokacin da suka koma parlon har sun gama cin Abincin sun dawo sun zauna bayan sun zauna cikin girmamawa su Baba Sama'ila suka tambayi sun dai ci sosae ko suda suka yanko hanya suna fara'a suka ce Alhamdulillah sun gode, cigaba da zancen saka ranar sukai suka ce lafiya lou a saka hakan, tambayar Date d'in da zasu gama Makarantar sukai duk basu sani ba Yaya Mubarak ne ya tashi don ya tambayo Aunty Mareeya, itama cewa tayi bata sani ba aka kirawo Fauzy a waya tace itama bata san date d'in ba kawai watan ta sani, bayan Yaya Mubarak ya koma ya sanar masu yadda sukai k'arshe aka sa bayan ta gama Makarantar da sati biyu kawai, nan kowa ya amince aka hau Addu'oi da fatan Alkhairi, kud'i suka bada miliyan d'aya na neman aure da kuma kayan saka rana don basu taho da komai ba, anan parlon suka yi jam'in sallar Azahar gaba d'aya harda security d'in bayan sun gama aka shiga yin sallama su Aunty Mareeya ma duk suka zo suka yi masu sallama da godiya da kuma Addu'oin Allah ya maida su lafiya suna fara'a suke amsawa suka ce sai Allah ya kaimu biki kuma, tare duk suka fita dasu iyayen Fauzyn maza aka shiga k'ara yin sallama daga baya suka tafi, Aunty na komawa cikin gidan ta kira Fauzy lokacin tana zaune a saman gadonta tayi zuru tun bayan da aka kirata aka tambayi date d'in da zasu gama Makaranta gaba d'aya taji jikinta yay wani irin sanyi, lokacin da kiran Auntyn ya shigo har saida gabanta ya fad'i, hannunta har d'an rawa yake ta d'aukko wayar, tana yin picking Aunty ta rangad'a wata uwar gud'a tana fad'in Allah ya yarda an saka ranarta da Sameer suna gama Makaranta da sati biyu, runtse ido Fauzy tayi ta d'an cize baki Aunty tace bazata yi magana ba ko bata farinciki kawai sai ji tayi ta fashe mata da kuka, shewa Aunty tayi tace "yi kuka Fauziyya kin cancanci ki yi kukan farinciki" fad'i mata kud'in da suka kawo tayi cikin Muryar kuka ta tambayi yaushe zata dawo tace gobe in Allah ya kaimu, sauran yan gidan ne suka shiga amsar wayar suna mata Allah yasa Alkhairi harda gwaggo da Mahaifiyar ta, bayan sun gama wayar falon Baban suka koma baki d'ayan su harda iyaye mata aka cigaba da farinciki su Aunty suka sassauko da kayan Abincin nan cikin parlon kan Carpet aka cigaba da shagali don ba laifi sunyi abubuwa da d'an yawa kuma duka kad'an bak'in nasu suka ci, To Alhamdulillah sai fatan Allah ya nuna mana Auren Fauziyya da Sameer....... 92 _ASM BY ZAINAB BATURE_ ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ .......A jiya Friday Haisam ya tafi Abuja daga can zai koma Us, lokacin da Fauzy ta kira Fatuu ta sanar mata da zancen saka ranarta tana a zaune parlon Hajiya, wata uwar k'arar murna ta saka ta hau yarfa hannu tana fad'in "Wayyo dad'i k'awata na taya ki murna wllh Allah ya sa Alkhairi ya kaimu lokacin da rai da lafiya" sai faman murna take ta kasa rufe baki, bayan ta gama wayar Hajiya ta tambayi abunda ya faru Fatun ta fad'i mata itama sosae tayi mamakin jin zancen Sameer zai auri Fauzy daga baya ta tayata murna tayi fatan Alkhairi, kiran gwaggo Fatuu tayi cike da Farinciki ta sanar mata dama tasan da Maganar itama murna ta tayata tayi fatan Alkhairi da Addu'oi, Washe gari lahadi da yamma Aunty Mareeya ta dawo gaba d'aya bakinta bai rufuwa harda kudin da zasu siya kayan da zasu raba ma mutane aka bata, a ranar da daddare Mijin Aunty ya fita dasu suka je wani shopping mall dake kusa dasu suka siyo haddadun manyan biscuits dasu sweet kala kala da chocolate dama ta taho da goro da aka Siya acan Funtua, Washe gari bayan sunje Makaranta Fauzy taba Fatuu kayan ta raba ma mutane amman tace kada ta fad'i wanda zata aura haka Aunty Mareeya tace, sai bayan da aka yi masu break sannan ta rarraba ma yan ajin tana fad'i masu kayan sa rana d'in Fauziyya Ahmad ne akai ta mata Allah yasa Alkhairi harda yan ajin kusa dasu aka rarraba mawa, bayan an gama rabon ne Zainab tazo seat d'in su ta zauna a saman desk tace ma Fatuu amman da gani itama Fauzy dai mai kud'i ne zata aura ko, dariya Fatuu tayi tace miyasa tace haka tace ai ita tunda take bata ta6a ganin an raba irin wannan kayan a saka rana ba kana cin biscuit kunnan ka na motsi har saida ta ba Fauzy dariya, magiya ta hau yi ma Fatuu kan wai ta fad'i mata waye zata aura tana murmushi tace mata d'an uwan mijinta ne, zaro ido Zainab tayi tace bayan k'anwarta da zata auri k'anin shi itama Fauzy kuma d'an uwan shi zata aura tace mata eh cousin d'in shi ne, langa6ar da kai Zainab tayi ta marairaice fuska tace "Wayyo ni Zainabu baiwar Allah ni shine ban samu ko mai aikin gidan ba duk da ba son shi zan yi ba, Don Allah Fateema Ard'o nima ku samo man d'an uwan mijin naki" tana rufe baki Fauzy dake dariya tace mata basu son bak'ar mace sai fara Fatuu kau mi zatayi in ba dariya ba Zainab d'in tace abu mai sauk'i ai hakan ba abu ne mai wuya ba sai ta koma farar, Fauzy ta sake cewa to ai basu son farin bleaching, haka tay ta tsokanar Zainab d'in. Saida aka saka ranar da kwana ukku sannan suka yi waya da Sameer shima ita ta kira shi don ta gaishe shi kuma ko Maganar saka rana d'in bai mata ba har suka gama wayar a fili ta furta lalle akwai aiki a gabanta. After a Month....... lokacin cikin Fatuu ya shiga wata na shidda sai lokacin ta fara laulayi sosae, ba komai take ci ba yanzu ga amai da take yi duk da ba sosae take yin shi ba amman data ji k'amshi ko taci abunda bai mata ba sai tayi aman ga kuma kwadayin ciki tafi son abu mai tsami ko yaji a lokacin har an tabbatar da ba d'a d'aya bane a cikin nata sosae kuma ya k'ara girma. Ranar Alhamis lokacin suna cikin Class wayar Fauzy ta fara vibration alamar ana kiranta, fiddo ta tayi daga cikin Aljihun rigarta lokacin data ga mai kiran nata d'an waro ido tayi gashi akwae malami ba damar ta d'auka, bayan kiran ya yanke sai ga wani ya sake shigowa hakan ya tabbatar mata da magana yake son su yi don in dai ya kirata sau d'aya bata kusa to bai sake kira har sai in ita ta gani ta kira sannan ya k'ara kira, d'agowa tay ta juya ta kalli Fatuu suka had'a ido ganin yanayin fuskar ta yasa k'asa k'asa tace mata ya akai ne sai da ta fakaici idon Malamin nasu sannan tace mata Sameer ne keta kira, d'an bud'a ido Fatuu tay sai kuma tace mata ta d'auki excuse sai taje suyi wayar ta d'aga mata kai, bayan ta maida wayar cikin aljihun ta mik'e ta nufi gaban ajin, tambayar malamin nasu tayi don Allah zata je ta yi fitsari da turanci ya d'aga mata kai ta juya da sauri ta fita, can k'arshen barandar ajin taje ta kai hannu ta fiddo wayar ta fara k'ok'arin kiran shi, har ta yanke bai d'aga ba tay tsaye tana jira ya sake kira aikuwa sai gashi bada dad'ewa ba ya sake kira, d'auka tayi a nutse tayi mashi sallama ya amsa tace ya kira tana cikin class ne kuma akwae malami yanzu ma excuse ta d'auka ta fito ya furta Ok, tambayar ta yayi k'arfe nawa suke tashi tace mashi k'arfe biyu saura kwata nan ma Ok ya furta daga haka taji yace ta koma Class, tsaye tayi turus a wurin a ranta ta shiga tunanin to miyasa ya tambaya, wata zuciyar ce ta raya k'ilan nufin shi ya sake kira can kuma wata zuciyar ta raya mata ko kuma zuwa zai yi, har saida gabanta yay wani dammm ta d'an zaro ido, kokonton anya zuwa zai yi ba tare daya sanar mata ko yazo garin ba ta shiga yi wani sashe na zuciyar tane ya shiga raya mata yana iya zuwan fa abunda tasan halin shi, tunanin kiran Aunty Mareeya tayi ta sanar mata, "To iya haka yace maki?" Aunty ta tambaya bayan ta kirata tace mata eh, "humm, yanzu in zuwan yay ya zamuyi kenan, ace zuwa ba sanarwa in banda abun suriki na mak'erin rocket, shiru Fauzy tay tama rasa abun cewa, "kuma fa wllh da alama zuwan yayi tunda kince sau biyu yana kiran ki gashi kuma ya tambayi k'arfe nawa kuke tashi k'ilan zuwa zai yi Makarantar kuma dai in dai yazo wurin ki nasan ai da wuya bai zo nan ba" still shiru Fauzy tayi Aunty tace wai ta wani yi shiru bazata bada shawarar abun yi ba, d'an yamutsa fuska Fauzy tay ta yarfa hannu d'aya tace to ai ita tama rasa tunanin da zata yi ne, nannauyar ajiyar zuciya ta saki tace mata to ko ta kira shi ta tambayi zuwa zai yi shiru Fauzy ta d'an yi kafin ta d'an yi guntun tsoki tace gaskiya ba sai ta kira shi ba tunda da ya so ai da ya sanar mata ko kuma ma yana iya ganin kaman wani abu ne yasa aka tambaya, cewa Aunty tayi Shikenan bari tana ganin abunda za'ai kawai ayi shirin kota kwana yanzu dai lokaci ma ya k'ure in ace a shirya lafiyayyen Abinci in zuwan yayi tana ganin bari taje tayi ma maman taufiq magana akwae wata k'awarta chef ce "In kuma ba zuwan yayi ba fa" Fauzy ta tambaya ta bata amsa da "ke zaki cinye shi kuwa" dariya Fauzy ta saka tace to ita miye laifinta tana yar dariya tace ita kuwa keda laifi tunda laifin shi nata ne don mi in baya ga yana 6aud'add'e zai zo bai sanar dasu ba, a kan hakan sukai sallama ta koma aji, sai bayan da malamin ya fita sannan suka yi magana da Fatuu itama dai zargin k'ilan zuwan zai yi tayi, gaba d'aya hankalin Fauzy ya kasu biyu tana tunanin ko zuwa Sameer zai yi tana kuma sauraren abunda ake masu a haka har aka tashi, tare suka fito da Fatuu ta rakata inda take Parking Motar ta kamar kullum, sallama suka yi tace mata k'ilan dai ba zuwan yayi ba tunda bai sake kira ba watak'il dama kiranta ne zai yi su yi magana Fauzy tace eh itama yanzu haka take tunani tayi mata Allah ya tsare sai sun had'u gobe, Bayan tafiyar Fatuu juyowa tayi ta nufo hanyar hostel bata kaiga barin Class area d'in ba wayarta ta fara ringing, hannu ta kai cikin aljihun rigarta ta curota ganin shine yasa gabanta fad'uwa saida tayi d'an jimm kafin tay picking tana karata a kunne taji yace ta same shi a parking lot na Admin nasu, waro ido Fauzy tay baki bud'e ta curo wayar tana kallon screen d'in nan take gabanta ya hau fad'uwa tamkar ana mata luguden ta6are duk da tayi zargin k'ilan zuwan zai yi sosae taji Al'ajabin zuwan nashi don ko a chat bai sanar mata ba kuma ko jiya sun gaisa, har zata tafi sai kuma ta tuna da Aunty, Da sauri ta shiga kiranta tana d'agawa ta tambayi yaya ake ciki a d'an rud'e Fauzy tace wllh zuwa yayi gashi nan ya kirata wai yana a admin, jinjina kai tayi tare da murmushi mai sauti ta furta wani aikin sai surukin ta makerin rocket, ce ma Fauzy tay kada ta damu duk abunda ya kamata za'ai mashi tace mata to, cikin mutuwar jiki ta ci gaba da tafiya dama Admin d'in wurin hostel d'in su yake, tunda ta tunkaro wurin take ta faman wurga ido tana son gano wacece Motar shi a cikin jerin motocin Malaman su dake a wurin, tana gab da isa taga an bud'e wata galleliyar bak'ar Camry sai faman shek'i take kai da gani kasan sabuwa ce, wani d'an magidancin mutum ne ya fito daga driver seat d'in Motar jikinshi sanye da k'ananun kaya wando da riga mai ma6allai, suna had'a ido yay murmushi tare da yi mata alamar tazo da kai, a d'arare ta tunkare shi tana zuwa gaban shi ya d'an rankwafa ya gaishe da ita da murmushi akan Fuskar tashi, amsa mashi tay a hankali da hannu ya nuna mata back door d'in da take tsaye a gefenta yace mata bismilla yana ciki tare da kai hannu ya bud'e mata k'opar nan take wani irin fitinannan k'amshi ya huro wajen, d'an rankwafawa tay ta kallo cikin Motar idanunta suka sauka akan Sameer dake a hakimce a bayan idanun shi a lumshe, sanye yake da shadda wheat wadda Kusan ta saje da kalar fatar jikin shi kafafun shi na sanye da bugaggun takalma half cover coffee brown haka hannun shi ma agogon hannun shi fatar ta coffee brown ce, irin d'inkin da Haisam yafi so wato Senator style ne aka yi ma shaddar hannun yasa wasu had'add'un links masu d'an adon coffee brown daga tsakiya, sumar kanshi a kwance ta kawo har tsakiyar wuyan shi haka sajen shi ma a kwance yake luff, duk da shadda ce a jikinshi hakan bai 6oye komai ba na daga suffar shi kana ganin shi zaka gane k'arfafa ne na gaske, slowly ya fara bud'e idanun suka sauka a kanta ya bita da kallo still bai bud'e idon baki d'aya ba, d'an murmushi tayi mashi gabanta na bugawa a hankali tace mashi "ina wuni, an zo lafiya" shiru bai amsa mata ba sai kallon ta yake hakan yasa ta shiga yan kame kame tana cigaba da d'an murmushi, tana haka taji yace in bazata shigo ba ta rufe mashi k'opa yana fad'in haka ya janye idanun daga kanta ya maida su ya lumshe, d'agowa tayi ta d'an waiga bayanta sannan ta shiga cikin Motar ta d'an jawo kopar ba tare data rufeta baki d'aya ba, bin shi tay da kallo gaba d'aya yau tafi ganin kwarjinin shi fiye da sauran lokuttan da ta ganshi a baya, "Ina wuni" ta sake gaishe da shi ya jinjina mata kai kawai ba tare daya kalleta ba, "an zo lafiya?" Shiru bai bata amsa ba atunaninta ko bai ji ba ne hakan yasa ta k'ara ce mashi hakan, jin shiru bai amsa ba yasa ta gane yana jinta ra'ayin amsawar ne bai da shi, tana cikin kallon shi ya juyo idanun shi suka shiga cikin nata ya shiga jefa mata wani mayen kallo nan take tasha jinin jikinta ta shiga yan kame kame tana d'an motsa baki kaman mai son fad'in abu ta kasa, "Is that how you should welcome me?" cikin husky voice d'in shi ya furta hakan tare da d'age mata gira, wani k'afaffen miyau ta had'iya ta kasa bashi amsa sai faman zare ido take don ita a ganinta ai hakan da tayi ne daidai tunda shi kanshi ba sake mata yayi ba balle ta nuna tayi murnar ganin shi, tana haka taji yace ko bata yi farincikin ganin shi bane da sauri ta hau girgiza kai murya na d'an rawa ta furta "n...nayi sosae kawae dai naji mamaki ne tunda baka fad'i man zaka zo" d'an yamutsa baki yay ya d'age mata gira yace dole ne yayi hakan ta k'ara girgiza mashi kai tace a'a, kasa jure ma kallon shi tay ta maida idonta k'asa tana kallon yatsun hannunta ba zato sai gani tay ya kawo tattausan hannun shi mai d'an fad'i da kuma dogayen yatsu masu d'auke da dogayen gyararrun k'umbuna ya kamo hannunta bata gama Al'ajabin hakan ba sai ji tay ya jawota gaban shi ya had'e ta da jikinshi ya rungumeta ta gefe, wani irin shock Fauzy taji ya ratsa dukkan jikinta gabanta ya hau wani irin mugun bugu tsoro da Al'ajabi lokaci guda suka kamata jikinta ya fara d'an rawa, kai fuskar shi yay saitin kunnanta cikin wata irin magana mai kamar rad'a ya furta mata haka yakamata tayi welcoming nashi da sauri ta runtse idanunta jin yadda Maganar ta sauka a cikin kunnanta nan take wasu abubuwa suka fara mata yawo a jiki, sam ta kasa cewa komai wani iri take jinta don a rayuwarta in ba Mujaheed ba bata ta6a had'a jiki da wani Namiji ba haka ko yan uwanta saidai ko lokacin da bata mallaki hankalinta ba shima Mujaheed sai da k'yar ta fara yarda yake ta6a ta da yayi mata dad'in bakin Auren ta zai yi, suna haka taji ya tambayi karatunta da k'yar ta iya bud'e baki tace mashi Alhamdulillah, shiru sukai gaba d'aya k'amshin jikin shi ya cika mata hanci nan take wata kasala ta fara rufar mata jikinta taji ya fara yi mata wani iri aikuwa da sauri ta d'ago tana k'ok'arin raba jikinta da nashi taji ya saketa, bin juna sukai da kallo wani irin nauyi taji idanunta sun mata hakan yasa da sauri ta juyar da fuskarta daga barin kallon shi, jin yayi shiru yasa ta d'an juyo karaf suka had'a ido da shi yana kallonta da kaifafan idanun shi, tsarguwa tay da kallon da Yake mata cikin yar in ina tace mashi Makarantar tasu akwai tsauri ne in aka ganta haka zata samu matsala ne kuma nan wurin parking d'in motocin Malamai ne ana iya ganinta, har ta gama Maganar idon shi na akanta yanayin kallon da yake mata ne ya canza zuwa harara ya d'aure fuskar tashi da sauri ta janye idanunta daga kanshi ta koma kallon k'asa, "Go and gather all your things!" Kaman daga sama taji ya fad'i haka, d'ago kai tayi da sauri ta kalle shi ya jinginar da kanshi jikin seat fuskar shi na kallon gaba ya d'an lumshe ido, da alamun rashin fahimta ta shiga bin shi da kallo ta kasa gane mi yake nufi da taje ta tattaro kayan ta, mi hakan ke nufi? shine abunda take juyawa a ranta ba dai fushi yayi da Maganar data fad'i mashi ba shiyasa yace haka, kenan ta daina karatun yake nufi ko mi, haka take ta sak'e sak'e a cikin ranta gashi yak'i ko kallonta balle ya bata amsa can da alamun rashin fahimta tace mashi bata gane abunda yake nufi ba da bud'ar bakin shi sai cewa yay bata understanding turanci ne tace a'a ta gane abunda yace amman in ta tattara kayan mi zatai da su, shiru kamar bazai bata amsa ba kafin taji yace ta daina boarding School a tak'aice yayi Maganar still idanun shi na a lumshe, kai ta jinjina kafin ta juya ta kai hannu ta bud'e kopar, Mutumin daya tuk'o shi na tsaye ya jingina da k'opar gaban suna had'a ido yay mata murmushi tare da Fad'in barka da fitowa a hankali tace Yauwa, daidai lokacin data fito akan idon su Zainab da Sa'adatu dake tahowa daga class zasu Hostel gaba d'aya idanun su na akanta har ta fito daga cikin parking space d'in ta nufi hanyar zuwa hostel aikuwa cikin d'aga murya Zainab ta k'wala mata kira, tsayawa tayi har suka k'araso ta d'an k'ak'alo murmushi tana yi masu, tambayarta Zainab d'in tayi bak'o tayi ne taga ta fito daga cikin wanccan galleliyar Motar kai ta d'aga mata alamar eh ta d'an waro ido tace "da sa ranar wani akan ki shine kuma kike saurarar wani ba kyau hakan wllh, kinga don Allah kawai ki had'a ni dashi tunda ke dai kin saida" yar dariya Fauzy tay Sa'adatu ta 6aka ma Zainab d'in bugu tana fad'in ita dai ta shiga ukku da son kudi wllh daga ganin Mota mai kyau shine zata ce a had'a su, a d'an harzuk'e tace a'a to wa zai k'i mai kud'i suma duk tasan inda mai Motar zai ce yana son su da gudu zasu yarda wllh, ganin suna 6ata mata lokaci yasa tace masu bari taje ana jiranta ne da sauri Zainab ta bita tana fad'in yanzu don Allah bak'in ciki zata mata ita tunda Allah ya bata mai kud'i ba sai ta taimake ta ba, tasan in ba fad'i mata wanene tayi ba bazata k'yaleta ba don ta cika nacin magana yasa tace mata ai wanda zata aura d'in ne yazo yanzu ma zuwa yay daukarta zata bar zama a hostel, gaba d'ayan su saida suka ji ba dad'i Zainab tace maimakon tace mashi ya barta taci gaba da zama tunda dai da sauran lokaci bikin nasu Fauzyn tace mata bai so, tare suka je d'akin nasu gaba d'aya don taya ta kwasar kayan, duk wani provisions dinta su ta raba mawa haka wasu daga cikin kayanta duk abunda wani yace mata yana so sai tace ya d'auka ba kamar Zainab duk tafi kwasar abubuwa har su bokitan ta da su robobi da plates duk su ta raba mawa iya trolley d'in kayanta sai wata yar babbar jaka ta saka sauran abubuwan da take so bata bayar ba, tare suka fito su hud'u Zainab tace to bazata yi ma mutane bankwana ba tace kawai sai gobe in Allah ya kaimu tazo har d'akin ma sai taje ta sanar ta saki, dama tunda Fatuu ta bar zama a hostel ita kad'ai take rayuwa a d'akin saidai masu zuwa taya ta zama ko kwana, a tare suka iso parking space d'in har lokacin mutumin ko ace driver d'in yana a tsaye yana ganin su da sauri ya bud'e kopar gaban ya rankwafa don ya bud'e boot d'in, bayan ya bud'e ya nufo wurin ya bud'e boot d'in suna kokarin saka kayan da sauri yace su barshi zai saka, kallon su Sa'adatu tay tana murmushi tace ta gode sai sun had'u in Allah ya kaimu suma godiyar suka yi mata har zata juya Zainab tace to 6oye masu mijin nata take da bazata had'asu su gaisa ba, d'an jimm Fauzy tay don bata san taya zata aikata hakan ba, ganin sunyi tsaye suna bin ta da ido alamar duk so suke su gaisa da shi d'in yasa tace bari tayi mashi magana, bud'e k'opar bayan tayi yana zaune a inda ta barshi yana latsa waya, rasa mi zata ce mashi tay tana a rankwafe ta bishi da ido, Slowly ya d'ago suka had'a ido tace mashi ga kayan nan ta d'aukko har an saka a boot ya d'aga mata kai kafin yace ta shigo, jimm tay tana d'an kikkafta ido ganin bata shigo ba yasa shi k'ara d'agowa tun kafin yace wani abu cikin yar in ina tace "d...dama wai k'awaye nane zasu gaida ka" shiru kaman bazai tanka mata ba sai kuma ya d'age gira yace mata yace yana son haka ne har saida ta had'iyi abu, d'an girgiza mashi kai tayi tace a'a dama sune suka taimaka mata ta tattaro kayan to sun tambayi miyasa zata bar hostel shine ta fad'a masu shine yazo daukarta, "ni wa?" taji ya jefo mata tambayar ta d'an waro ido don bata tsammaci jin tambayar ba da k'yar ta bashi amsa da wanda zata aura kawai sai gani tay ya d'an ta6e baki ya maida idon shi kan wayar dake hannun shi, tambayar shi tayi tace suzo su gaisan taga ya jinjina mata kai ba tare daya kalleta ba, d'agowa tay tace masu suzo su gaisa duk suka matso bakin Motar Fauzy taja gefe, a tare suka rankwafa suka ce mashi ina wuni a wani slow ya juyo gaba d'ayan su saida gaban su ya fad'i karma Zainab taji wani kallon k'urulla ta shiga bin shi dashi tana k'ok'arin tuna inda ta san shi, jinjina masu kai yayi kamar anyi mashi dole koda yake Kusan hakan ne yace masu ya School a tare suka had'a baki wurin amsa mashi da lafiya lou suka ce anzo lafiya anan dai kai suka samu ya jinjina masu daga haka suka ce sai anjima suka janye kan su, idanu a waje Zainab ke kallon Fauzy dake d'an murmushi tana son yi mata magana amman ba dama sai faman kallon ta take da alamun Al'ajabi, sallama ta k'ara yi masu ta shiga ciki har ta rufe k'opar sai kuma suka ga ta bude, kud'i ta mik'a ma Zainab rafar yan dubu dubu sabbi dal ta dubu d'ari tace gashi ance su raba saidai Sa'adatu ce ta amsa don gaba d'aya Zainab tayi Mutuwar tsaye, har Motar ta bar harabar Makarantar suna tsaye cirko cirko saida ta 6ace ma ganin su sannan suka juya kan Zainab nan fa suka shiga yaba irin kyaun shi har Sa'adatu na fad'in ko ina ta samo shi sai kuma tace ta tuna lokacin da aka raba kayan saka ranarta ance d'an uwan mijin Fateema Ard'o ne ba mamaki don an gan shi haka, Safiya ce tace amman dai da gani ya jik'u da Naira wllh ga mugun aji ji yadda yay masu magana ma, sai lokacin Zainab da still tsananin mamaki ke a kwance akan fuskar ta tace "to ku duk baku ma san wani abu ba, wllh wanccan mutumin da kuke ganin shi d'an Governor ne" zaro ido sukai tare da bud'e baki a tare suka furta "d'an Governor!!!" Kai ta d'aga masu cike da tabbaci tace masu da suka je bikin Fateema Ard'o Abuja a kan idonta suka zo shida Mahaifiyar shi da yan uwan shi a cikin jiniya d'an Governor d'in Nasarawa ne... Nan ta kwashe komai har yadda Sameer d'in ya fito daga cikin Mota ya shiga cikin gidan da dangantakar shi da Mijin Fatuu ta fad'i masu, nan fa duk suka shiga tsananin mamaki ba dai kamar Zainab da kanta ya gama daurewa ta yadda akai har suka san juna shida Fauzy har abun ya kai ga za'ai aure, a fili ta furta ashe shiyasa suna dawowa ta canza waya zuwa latest iPhone, gaba d'aya al'ajabi ma ya hana su yin murnar kud'in da aka basu da alama kuma gobe dole Fauzy tasha tambayoyi a wurin Zainab. Suna fitowa daga cikin Makarantar cikin girmamawa driver d'in ya d'an juyo ba tare daya kalli Sameer d'in ba ya tambayi ina zasu, kallon Fauzy yayi da tayi zuru yace ta bashi address d'in gidan Sister d'in ta tace to, basu wani d'auki lokaci ba suka karaso Unguwar don kusa take da Makarantar tasu, kallon shi tay bayan sun tsaya ya d'an d'age kanshi jikin seat idanunshi a lumshe, ce mashi tay sun iso ya d'an d'aga mata kai ta k'ara cewa suje, shiru kaman bazai tanka ba can ya juyo suka had'a ido yace taje ta sanar ta d'aga mashi kai, lokacin data fito Driver d'in na tsaye yana ganinta cikin girmamawa ya tambayi kayan boot fito da su za'ai tace mashi eh, yana k'ok'arin d'aukar mata bayan ya fito dasu tace mashi ya bashshi zata d'auka yace to bari ya kai mata ko bakin gate tayi gaba yana biye da ita a baya, lokacin data shiga cikin parlon tsaye tay tana bin shi da kallo yasha uban gyara sai uban k'amshi ke tashi har labulaye an canza haka kujerun ma da gani har goge su akai don sunyi haske a ranta ta raya lalle Aunty tayi kokari, d'akin Aunty ta nufa lokacin data shiga a zaune ta isketa gaban mirror tana yin shafa, jin sallamar Fauzyn yasa ta juyo suka had'a ido, d'an waro ido tay tace to lafiya ta ganta da kaya nik'i nik'i tana murmushi tace sabon mai iko da ita ne yace ta dawo ta gama yin boarding, k'ara waro ido Aunty tay sai kuma tayi dariya, tambayar ina yake ta yi ta bata amsa da yana waje, "Amman dai Fauziyya wani lokacin kaman d'an kai gare ki wllh ya zaki bar shi a waje maimakon ki shigo da shi" a d'an harzuk'e tayi maganar Fauzy ta bata amsa da ai shine yace ta shigo ta fad'i, da sauri Aunty ta mik'e tana fad'in don Allah taje ta shigo da shi ta nufi gaban wardrobe don ta saka kaya, a tare da shi suka shigo cikin parlon yana biye da ita, nuna mashi kujera tayi tana murmushi tace "have a sit" saida ya kalleta cikin ido sannan ya nufi kujera 2 seater ya zauna, tsaye tay ta had'e hannuwanta tana kallon shi da murmushi shi ma idon shi na kanta yana bin ta da wani kallo da sai kace yar harararta yake amman ta fahimci wani lokacin haka yake kallon shi, ganin tayi mashi kerere yasa ya furta mata bata iya neman wuri ta zauna, kujerar dake gefen tashi ta nufa ta zauna, "Aunty tana zuwa yanzu" bayan d'an wani lokaci ta fad'a ya jinjina mata kai, "Ka zo lafiya" ta tambaya still Murmushi take yay shiru sai kuma ya amsa mata da lafiya, janye idon shi yay daga kan ta ya jinginar da shi ajikin kujerar tare da lumshe ido, tana ta kallon shi can ta furta ya gaji ne yana a yadda yake ya d'an girgiza mata kai, juyar da kai tayi daga barin kallon shi a ranta tana raya magana dashi aiki ce babba, lokacin Aunty ta fito ta nufo cikin parlon tana sanye da doguwar rigar had'addan lace ta sa d'an kunnan zinari hannunta sanye da Agogo haka kanta tayi d'aurin kallabi mai kyau, tun kafin ta k'araso ta shiga washe baki idon ta akan Sameer da ya lumshe ido, saida tayi sallama sannan slowly ya bud'e idon nashi, a kujerar gefen wadda Fauzy take ta zauna tana faffad'an murmushi tace "Barka da zuwa, fatan an zo lafiya" amsa mata yay da lafiya lou ya janye idon shi daga kanta, k'ara tambayar ya ya baro Mutanen gida tayi ya amsa da lafiya ba tare daya k'ara kallon ta ba, shiru duk sukai tana murmushi idon ta akan shi can ta k'ara cewa "an gode da abubuwan Alkhairi Allah ubangiji ya k'ara girma da daukaka" slowly ya furta "Ameen" ta d'an kalli Fauzy dake d'an murmushi itama shine akan fuskar tata, shiru duk sukai parlon sai kace ba mutane Aunty Mareeya sai d'an kai idon ta take tana kallon shi acikin ranta ta shiga tuno da ranar data fara ganin shi da suka zo Abuja bata ta6a zaton akwai ranar da zasu zauna haka da shi bama balle ta kai ga zancen Auren k'anwarta, mik'ewa tay tayi ma Fauzy alamar ta biyo ta da hannu ta mik'e saida ta kalleshi tace mashi tana zuwa ya d'aga mata kai, wurin dining suka nufa Aunty ta nuna mata kayan abinci dake sama k'asa k'asa da murya tace "gashi nan sai ki mashi magana yazo ki serving nashi" kai Fauzy ta d'aga idon ta akan jigunannun Warmers d'in da aka jera a saman table d'in set biyu babba da k'arama set d'aya na Aunty ne ta san su d'ayan kuma sam bata san Aunty dasu ba a ranta ta raya k'ilan duk na chef d'inne amman sun had'u ba k'arya, bubbud'e mata su ta shiga yi babba d'aya farar shinkafa ce washarr washar gata zak'o zak'o sai k'aramar warmer d'inta tana bud'e ta wani irin kamshi mai dadi ne ya karad'e wurin vegetable soup ce gwanin kyau a ido ingredients d'inta an yanka su manya manya taji hanta, d'ayar babbar Warmer d'in kuma fried spaghetti ce tayi brown gwanin burgewa itama sai faman zuba k'amshin spices take gashi tasha vegetables su tsanwan tattasai Karas koran wake da dai sauran su gashi tasha nama ca6a ca6a, d'ayar warmer d'in ta k'arshe kuma pepper chicken ne ciki, bayan ta gama bubbud'a mata tace mata akwae coleslaw a cikin Fridge, "Amman Aunty duka order d'in nasu kikai?" Fauzy ta tambaya k'asa k'asa, "eh mana daga lokacin da kika fad'i man zai zo zuwa yanzu ina zan iya yin wani lafiyayyen Abinci har gara ma spaghetti za'a iya yi amman kuma ba komai nike da shi ba na kayan had'ata tayi kyau haka, kai Fauzy ta jinjina tace hakane, "amman ai sun yi haka ko?" da sauri Fauzy tace "ah sosae ma kin yi mana dubara naji dad'i wllh" yar dariya Aunty tay tace "jin dad'in ki your excellency shine nawa" hannu Fauzy ta kai ta gumtse dariya, "Yanzu kije ki mashi magana yazo ya ci" kai Fauzy ta d'aga sai kuma tace "Allah ma yasa ba wahalar banza akai ba ta tanadar su don yana iya k'in ci wllh" da sauri Aunty Mareeya tace "in ya ki ci ai ke zaki sashi dole yaci ko, taya zai tako yazo kuma yace bazai ci komai ba ke kuma ki bishi da ido, anya Fauziyya, gaba d'aya wani lokacin sai ki kaman ba wayyaya ba wllh na lura kaman baki iya soyayya ba ko dai kin k'arar da ita a wurin shashasha d'in can, kije ki mashi magana in ya nuna bazai ci ba kice baki yarda ba sai ya ci a cikin sigar yar shagwaba shagwaba zaki mashi magana dole fa sai kin zage damtse wllh ke ce zaki koya mashi sakin jiki da mutane bama kamar ke in ba haka ba yana a haka d'in can wllh kece Masha wuya ki ga fa yadda magana ke mashi mugun wahala ga ba sakin fuska don ma dai d'aurewar na mashi kyau tunda kyakkyawan ne....kinga an bar shi shi kad'ai jeki ki mashi magana bari in d'aukko coleslaw d'in akwai ma lemuna a cikin Fridge d'in sai ki tambayi wanda yake so in kuma sai giyar da kika ce yana sha sai kije ki nemo mashi" gwalo ido Fauzy tay jin Maganar tata ta k'arshe Auntyn ta sa dariya ta juya tana fad'in taje, komawa tayi cikin parlon Sameer d'in nata latsa waya har zata zauna a inda ta tashi sai kuma ta tuna da hud'ubar Aunty a d'arare ta nufi inda yake a hankali ta zauna daga gefen shi, idonta akan shi tace "am sorry an bar ka kai kadai naje yin abu ne" kai ya jinjina mata ba tare daya kalleta ba, "Muje ka ci Abinci" d'an jimm yay kafin ya juyo suka had'a ido tana mashi murmushi, kokarin mik'ewa ta fara taji yace mata ya k'oshi hakan yasa ta koma ta zauna, "Amman ya zaka ce ka k'oshi bayan nan kazo dole ai kaji yunwa" d'an girgiza mata kai yay yace ba nan ya fara zuwa ba so ya ci Abinci a inda ya sauka, tambayar shi tay a ina ya sauka ya bata amsa da Government House, marairaice mashi fuska tay tace "to amman dai ai nan ma yakamata kaci Abinci tunda nasan Saboda n...." Kasa k'arasa Maganar tay idon shi a kanta slowly yace yana jin ta alamar taci gaba, kikkafta idanu ta shiga yi tana motsa baki ganin irin kallon da yake mata ne yasa da k'yar ta furta "Saboda ni ka zo" kawai sai gani tay yay d'an murmushin gefe wanda tunda yazo bai yi kamar shi ba don har gefen fuskar tashi ya d'an lotsa, d'age mata gira yay yace "Who told you dat?" shiru tay tana cigaba da kikkafta ido taji ya sake cewa ba tambayar ta yayi ba, "Ba kowa, ni nayi tunanin hakan" shiru yay yana kallon ta cikin k'arfin hali ta furta "hakane?" wani kalan motsa baki yay tare da yi mata wani kallo yace in ta cancanci hakan to hakane, faffad'an murmushi tayi tace "eh nayi deserving hakan" d'an ta6e baki yay da alamun murmushi yace a matsayinta na wa ba tare da jin wani d'ar ba ta furta "Your wife to be in sha Allah" bin ta yay kawai da ido sai murmushi take tana niyyar k'ara yin magana Mijin Aunty Mareeya ya sawo kai cikin parlon da sallama su Hanif na biye da shi gaba d'aya suka kai idon su akan shi ganin shine yasa Fauzy saurin sauke kanta don sai taji kunyar zamanta a kujera d'aya da Sameer ta kamata, inda suke ya nufo yana zuwa gaban Sameer cikin sakin fuska ya bashi hannu suka gaisa yayi mashi an zo lafiya nan ma ya amsa mashi, d'an rankwafawa Hanif yayi yace mashi ina wuni ganin haka yasa su sultan ma suka yi duk ya amsa masu fuskar shi a d'an sake, juyawa Abban Hanif yay bayan sun gama gaisawar ya nufi hanyar Bedroom su Hanif na biye dashi gaba d'ayan su Uniform ne ajikinsu sun goya School bag da gani daga Makaranta ya d'aukko su , "Pls muje kaci Abincin" Fauzy ta fad'a da yar sigar shagwaba idon shi akanta yay shiru, mikewa tayi tana mashi wani kallo a kokarin ta na tayi abunda Aunty tace, shiru ya d'an yi kafin yace shi bai cin Abinci in ya riga ya koshi ya fad'a mata ya riga ya ci so ba sai yaci wannan ba, tsaye tayi tana kallon shi bayan ya gama yin Maganar shima kallon nata yake can ta nufi kujerar gefen shi ta zauna ta maida fuskarta tana kallon gefe, "Are u angry?" tana haka taji ya jefo mata tambayar, juyowa tayi suka had'a ido tay shiru bata bashi amsa ba, "I'm asking you!" Ya sake fad'a, saida ta d'an had'iya miyau kafin a sanyaye tace "a'a kawai dai naji ba dad'i ne, saboda ni kazo kuma gashi kace bazaka ci Abinci bana at least ko d'an Yaya ne sai ka ci pls" d'an murmushi yay bai ce komai ba tana ta kallon shi can taji yace Ok zai ci sai taji dad'i, washe baki tay tana yar dariya sosae taji dad'in cewa da yayi zai ci don ko ba komai hakan ya nuna zata iya sashi abu, mik'ewa tayi tace suje ya taso shima ya mik'e, bayan sunje dining area d'in da kanta taja mashi kujera ya zauna, fara serving nashi tay ta zuba mashi farar shinkafar da veg soup d'in bata sa da yawa ba don tana son sauran ma yaci, a nutse ya fara ci tana zaune daga gefen shi can ya kalleta yace ita bazata ci ba tace sai ta gama Serving nashi, da kai yay mata alamar ta zauna ta ci murmushi tayi ta mik'e don ta zuba, yana kusa gama cinye shinkafar ya aje spoon d'in tana ganin haka tay saurin mikewa ta fara zuba mashi taliyar itama yar kad'an tasa ta janye plate d'in gaban shi ta tura mashi na taliyar ganin haka yasa shi d'agowa yana mata wani kallo cikin marairaicewa ta d'an langa6ar da kai tace "pls shima bai da yawa ai" cigaba da kallon ta yay yana d'an motsa baki kokarin mikewa ya fara yana fad'in bai san a ina take son ya zuba shi ba wannan ma ya gaya mata ai a k'oshe yake kawai sai ji yay ta kawo hannu ta ruk'e nashi alamar kar ya tashi ita kanta bata san ya akai ta aikata hakan ba, dakatawa yay ya kai idon shi akan farin hannunta dake a ruk'e da nashi kafin ya d'ago ya kalleta sai d'an zare ido take gabanta na faduwa, a hankali ta saki hannun nashi tare da sadda kanta k'asa bayan d'an lokaci jin shiru yasa ta d'an d'ago idanunta ta kalle shi karaf suka had'a ido yana ta kallon ta yan kame kame ta shiga yi ta kasa tsaida idon ta cikin nashi don idanun shi nada kaifi bazata juri irin kallon ba, "Ka yi hak'uri, dama don Saboda kai ne akayi shiyasa" tana d'an kikkafta idanu ta fad'i hakan, bai ce komai ba sai gani tay ya kai hannu ya d'auki fork d'in ciki ya fara ci a nutse har bata san lokacin data saki murmushi ba ta koma ta zauna, kaman rabin wanda ta zuba mashi yaci tana ganin ya aje fork ta d'ago ya d'age mata gira yace Shikenan hakan yayi mata ya ci kai ta d'aga mashi still da d'an murmushi sai kuma tace amman da sauran wanda bai ci ba wani kallo mai kaman harara ya wurga mata tayi dariya tare da mik'ewa, pepper chicken d'in ta bud'e tasa mashi k'atuwar cinya hada tambayar shi ta k'ara yay mata shiru yana dai ta kallon ikon Allah don hakan bak'on abu ne a wurin shi yace bazai yi abu ba a matsa mashi zai iya cewa ba wanda ya ta6a mashi haka, turo plate d'in tayi gaban shi bayan ta janye na taliyar tace gashi itama ya ci don Allah ba yawa abu d'aya ne kawai, maida bayan shi yay jikin kujerar da yake zaune ba alamar zai ci sosae ta marairaice fuska tana mashi yar shagwabar ya ci daga shi shikenan, k'arshe dai saida tayi nasarar saka shi yaci cinyar rabi da kan shi ya tsiyaya ruwa a cup yasha kad'an yana k'ok'arin mik'ewa tace lemu fa ya d'an d'aga mata hannu, ganin ya tashi yasa itama ta rufe sauran abinciccikan ta biyo bayan shi, kujerar daya tashi ya koma ya zauna itama ta sake zama a gefen shi, bata dad'e da zama ba taji yace ita bata wanka ne har saida taji yar kunya tana d'an murmushi tace tana yin wanka sosae don kada ta barshi shi kad'ai ne yasa bata je ta yi ba, shiru ya d'an yi sai kuma taji yace taje tayi zasu je government House tare, har saida gaban Fauzy ya d'an fadi jin inda yace zasu je amman bata nuna komai ba tace mashi to, "Amman lafiya lou a barka kai kad'ai ko in ma Auntynah magana?" ta fad'a bayan ta mik'e da bud'ar bakin shi sai cewa yay tayi mashi mi tace wai ko ta taya shi hira, d'an yamutsa fuska yay ya fara k'ok'arin mik'ewa bayan ya tashi tsaye yace zai jira ta a Mota amman kar tay keeping nashi bai hakurin haka ta d'aga mashi kai ya nufi hanyar fita daga parlon tabi bayan shi da ido har ya fuce, wani k'ayataccen murmushi ta saki tana jin son shi na ratsa mata zuciya tabbas tasan indai ta aure shi ba k'aramar mai sa'a bace ita, da sauri ta nufi hanyar Bedroom d'inta tana zuwa direct toilet ta nufa a can ta cire Uniform d'in jikinta, after some few minutes ta fito d'aure da towel a kirji ta nufi gaban dressing mirror, shaf shaf ta d'an yi yar light makeup bayan ta gama ta nufi wurin kayanta dake a cikin Wardrobe d'in bango, bata tsaya ruwan ido ba ta yanke ta saka jallabiyar da Fatuu ta bata dama sau d'aya ta ta6a saka ta da zasu je shopping dasu Hanif, bayan ta saka gaban mirror ta koma cikin sauri ta gyara fakin din gashinta sannan ta shiga nad'a gyalen rigar, sosae tayi mata kyau dama itama tasan tana mata kyaun shiyasa ta saka ta, takalma half cover da yar karamar side bag duk bak'ak'e ta saka saida ta gama shiryawa ta tuna bata fad'i ma Aunty zancen fitar ba, wayarta ta fiddo don ta kirata sanin Abban Hanif na nan, a cikin parlor suka had'e da ita bayan ta sanar mata ta waya tana ganinta ta hau yin murmushi tana fad'in kaga Matar d'an Governor, tambayar ta tayi amman dai yaci Abincin ko tace eh kowanne saida tasa ya ci duk da bada yawa ya ci ba Auntyn tace "yayi kyau hakan ma lafiya lou tunda dai ya ci kwalliya ta biya kudin sabulu, yanzu sai government House kenan your excellency?" Yar dariya Fauzy tay tace mata eh haka yace tace Ok sai sun dawo, saida ta rakota har bakin kopar parlon tana k'ara koya mata yadda zata rink'a mashi tace ta gaida mata da iyalan Governor, yana a d'an kishingid'e idanunshi a lumshe ta shigo cikin Motar bayan driver ya bud'e mata, slowly ya bud'e idon nashi ya sauke su akanta da murmushi tayi mashi sannu tace Allah yasa dai bata bar shi yana ta jira ba shiru kaman bazai tanka mata ba can ya d'an gyara zama yace kaman haka, saida driver d'in ya tambayi umarni kafin yaja Motar, suna cikin tafiyar idon Fauzy a gefe ba zato taji ya kawo hannu ya kamo nata hannun wani irin d'umi taji ya ratsa nata hannun taushin hannun shi kuwa ba sai an fad'a ba, kallon shi tay idanun shi na akanta da kai yay mata alama ta matso, shiru tay kaman bazata matsa ba sai kuma ta d'an matsa da kanshi ya k'ara matso da ita ya rungumeta ta gefe wani iri Fauzy ta ji don tasan hakan bai dace ba tunda ba d'aura masu aure akai ba bai kamata suna had'a jiki ba, shiru tay kanta na a saman kafad'ar shi haka hannunta guda daya fara ruk'owa har lokacin yana a ruk'e dashi tay lamo ta kasa yin wani yunk'uri na raba jikinta da nashi, bayan sun isa Government House d'in baza ido Fauzy tay tana k'are ma ko ina kallo ta yadda baza'a ga k'auyancin ta ba, lokacin data ganta gata ga first lady wadda k'awar Mom d'in Sameer ce mamaki da dad'i ne suka cikata don abu ne da bata taba zaton zai faru ba a rayuwar ta, cikin faram faram ta tarbeta bayan sun gama gaisawa fuska a sake ta d'an yi mata tambayoyi da suka shafeta Fauzyn na amsa mata Sameer na zaune akan d'aya daga cikin lafiyayyun kujerun da suke zaune daga baya ya mik'e ya nufi ciki Fauzyn na kallon shi har ya 6ace ma ganinta tayin Abinci First Lady tayi mata tace gashi can a table tana murmushi tace mata wllh a koshe take ta gyad'a kai, d'akin yaranta ta kai Fauzyn wai tafi sakewa yan mata biyu ne ta gani a d'akin d'aya zata yi sa'ar ta d'ayar kuma zata d'an girme ta, gaba d'ayan su daka kallesu zaka gane hutu ya zauna masu a jikinsu ga fatar su har wani shek'i take duk da ba farare bane can amman kuma baza'a kira su da bak'ak'e ba gaba d'aya k'ananun kaya ne a jikin su, sosae suka sake ma Fauzy babbar na d'an tambayar ta game da ita da yadda suka had'u da Sameer muryarta gwanin dad'i a gayance take magana, tun dai Fauzy bata saki jiki ba har ta saki suka shiga yin hira sosae anan ita babbar take ce mata gaskiya tayi dacen miji don Sameer k'arshe ne a komai amman ita bazata iya auren shi ba har saida Fauzy ta d'an ji mamaki ta kasa hak'uri ta tambayi dalili cikin yamutsa fuska Ammah tace mata ego d'in shi yayi mata yawa dole matar shi ba k'aramar dawainiya zatayi da shi ba ita kuma hakan ke bata iyawa, shiru Fauzy tayi tana d'an murmushi tasan ba k'arya tayi ba a ranta ta raya to dama Mulki ya had'u da Mulki taya d'aya zai dawainiya da d'aya. Bayan gama sallar la'asar Sameer ya kirata yace ta same shi a parlor, tare da Ammah suka fito har yayi wanka ya canza kaya zuwa k'ananu sai baza k'amshi yake, Ammah na murmushi tace ma Sameer d'in "sannu bro" kai ya d'aga mata fuskar shi a d'an sake ta k'ara cewa ba dai tafiya zasu yi ba sai lokacin ya bud'a baki yace eh amman zata gaisa da Dad ne hakan yasa tace to suje ta raka su, parlon shi suka nufa lokacin da suka shiga yana zaune tare da First Lady da murmushi ya nuna ma Fauzy wuri yace "have a sit my Daughter" jikin Fauzy har wani tsuma yake yau itace gata ga Governor wanda saidai taga motocin su suna wucewa a hanya da jiniya sai kuma a Tv, cike da girmamawa ta gaishe da shi ya amsa ya tambayi tana lafiya da yan gidan su duk ta amsa mashi, shima dai yan tambayoyi yayi mata yadda bata 6oye ma su First Lady komai ba haka shima ta rink'a bashi amsa yana d'an jinjina kai daga baya ya saka mata Albarka da kuma fatan Allah ya nuna masu bikin, tare suka fito harda First Lady Sameer yace zai je ya dawo tace Ok su d'an jirata a parlon ta, kiran Ammah tayi tabi bayanta bada jimawa ba sosae ta dawo hannunta ruk'e da jakar kwali sai walwali take ta mik'a ma Fauzy tace gashi in ji Mom tana murmushi ta amsa tare da yin godiya sosae tace tayi mata godiya pls, har zasu tafi tace ta bata digit d'in ta zasu rink'a gaisawa Fauzyn tace to, bayan ta amsa sukai sallama ta juya ta nufi part d'in su, sosae Fauzy ta jinjina kirkin su sam basu da ji da kai har gara ma k'anwar tata itama ta fahimci bata da yawan magana ne ba wai ji da kai ba, Motar da suka zo ita suka hau saidai yanzu Sameer d'in ne zai tuk'a ta ba driver ba, bayan sun hau hanya ne taji yace tay leading nashi gidan Haisam tace to, ita ke nuna mashi hanya tana cikin haka ta tambayi bai ta6a zuwa bane farko shiru ya d'an yi idon shi akan hanya ta juya ta kalle shi suka had'a ido ta cikin mirror kafin ya kauda lokacin ya bata amsa da sau biyu ya ta6a zuwa Katsina Saboda baida business a cikinta d'an murmushi tay kawai sai kuma ta k'ara cewa amman ai ga grandmother d'in Ya Haisam a garin ya d'an d'age gira ba tare da ya kalleta ba ya bata amsa da ai shine dalilin da yasa yazo sau biyun ko. Lokacin da suka isa gidan Hajiya Fatuu na a part d'in sosae tayi farinciki ganin su tare ji take tamkar ta zuba ruwa a k'asa tasha ganin burin su dai ya tabbata, sosae Hajiya taji dad'in zuwan nashi bayan sun gaisa ta tambayi yan gidan su ya amsa mata daga baya tace wato da ya manta da ita tunda yaushe rabon da ya zo gidan tun suna karatun degree d'in su na farko da suka zo da Haisam sai yanzu dalilin zai mata kishiya ta samu ya sake ziyartar ta, murmushi yay jin abunda tace ba tare daya ce komai ba, koda tayi mashi Maganar Abinci cewa yayi ya k'oshi Hajiyar tace dama tunda Amarya ta cika shi da kayan dad'i ya zai iya cin Abincin tsohuwar mata duk suka d'an yi murmushi harda shi, kiran sallar Magrib da aka fara yasa shi mik'ewa don yaje Masallaci suma duk suka tashi don suje su yi, visitor room wanda yanzu ya koma kamar d'akin Fatun anan take komai taja Fauzy, bayan sun gama sallar cikin washe baki Fatuu ta shiga nuna ma Fauzy irin farincikin da ta ji nan ta shiga bata labarin yadda yasa ta kwaso kayanta daga hostel Fatun nata dariya tana fad'in yayi daidai, harda yadda suka samu Abincin da suka tarbe shi ta fad'i mata tace amman dai Aunty tayi dubara sosae daga baya Fauzy ta koma magana akan cikinta tana fad'in wllh tausayi take bata Fatun na yar dariya tace ai yana gab da zuwa kanta lokacin ita ta sauke sai itama ta rink'a tausaya mata ta d'an ta6e baki can kuma tace "waya ga su Fauzy da ciki alankoso kenan, ai na tabbatar sai kin fini juriya Zarah" Fatuu na dariya tace itama dole zata koyi juriyar in lokacin yayi, anan Mino ta iske Fauzy suka gaisa harda tambayar ta Angonta Nameer tana murmushi tace mata yana Makaranta, anan sukai sallar isha bayan Sameer ya dawo daga Masallaci ya kira Fauzy yace ko zai barta anan ne tace mashi a'a yace Ok ta fito yana parlor, tare suka fito su ukku Fatuu tace bari tay ma Hajiya Magana, bada jimawa ba suka shigo cikin parlon bayan sun zauna Hajiya tace wato dai tafiya zai yi bazai ci Abincin ta ba yana d'an murmushi yace wani lokacin zai ci ta gyad'a kai tace to Allah yasa tana da rabon ganin lokacin don bata sa ran nan kusa ba shi dai d'an murmushi kawai yake, su Fatuu ne suka yo mata rakiya suna zuwa bakin entrance tace mata ta koma ta girgiza mata kai tana murmushi tace suje ta raka ta ai duk cikin exercise ne, bayan sun fito cikin harabar Sameer na daga gaban su a nutse yake tafiya duk idanun su na akan shi k'asa da murya Fatuu tace wllh ganin Sameer yasa taji maraicin mijinta duk suka d'an yi dariya, bud'e Motar yayi ya shiga bayan ya k'arasa inda take suma suka karaso Fauzy tayi masu sallama tace ma Fatuu sai sun had'u School gobe, tana shiga cikin Motar ya bata rafar kud'i guda ukku yace ta ba Fatuu ta kai ma Hajiya ya k'ara bata wasu guda biyu yace ta ba Fatuu, fitowa tay har sun nufi komawa ciki ta tsaida su taje ta bata kudin, saida suka dawo tayi mashi godiya sannan suka tafi Fauzy ta shiga yaja suka tafi. Bayan sun baro gidan gari suka shiga yana driving da hannu d'aya yana latsa wayar shi da d'ayan hannun can taji ya furta Katsina K'aramin gari ne ba wurare masu kyau da mutum zai je yay having fun, ita dai shiru tayi mashi a ranta ta raya tunda dama ya saba zuwa had'add'un wurare harda su club ai dole ya fad'i haka, sai daga baya ta fahimci wayar da take latsawa yana searching wurare ne, bayan wani lokaci suka k'araso wani babban wuri kamar dai Eatery ne Kusan shine wurin cin Abinci daya fi kowanne girma da kawatuwa a garin Fauzy tasan wurin sai dae bata ta6a zuwa ba Saboda ba'a dad'e da bud'e shi ba yan Makarantar su dai na zuwa da samarin su, bayan ya parker jingina yay da kujerar ita dai Fauzy nata kallon wurin, bada jimawa ba wasu ma'aikatan wurin guda biyu suka fito hannuwan su ruk'e da ledoji suka nufo wurin parking d'in, horn Sameer d'in ya latsa hakan yasa suka nufo Motar tasu suka tsaya daga bakin kopar driver d'in slowly glass d'in ya d'an sauka ma'aikatan suka gaishe shi tare da yi mashi barka da zuwa yadda ya amsa ba lalle ma in sun ji ba yace masu su saka a seat d'in baya, bayan sun saka d'aya ya dawo gaban yace mashi ansa ya jinjina mashi kai har zai juya ya dakatar da shi, kud'i ya mik'a mashi masu yawa nan take ya hau washe baki yana godiya don ya gane kyauta ce yayi masu Saboda ya biya kud'in abubuwan da ya siya ta online d'ayan ma ya matso yayi godiyar, bayan barowar su wurin direct gida ya nufa da ita yace ta rink'a nuna mashi hanya da zata maida su tace to, a k'opar gidan ya parker bayan sun k'araso ta juya tana kallon shi, shiru sukai na d'an wani lokaci can taji yace mata gobe zai wuce in akwae wani abu ta fad'i mashi, shiru ta d'an yi kafin tace da wuri haka kaman bazai bata amsa ba yace to wani abu zai tsaya yi tay shiru kawai, "You can go, zamu yi magana" ya fad'a tare da yi mata nuni da baya yace ta d'auki abubuwan da aka je, d'an jimm tay akwae Maganar da take son yi mashi amman tana jin shakkar yinta saidai tana ganin yakamata tayi mashi ita, kaman ya lura da tana son yin magana yace mata inda wani abu yana jin ta, saida ta tattaro karfin hali sannan murya na d'an rawa ta fara magana, "D...dama akwae abunda nike son tambayar ka ne.....Ina so ka fahimce ni don Allah...." shiru tay tana jiran taji mi zai ce idonta akan shi taji yace yana sauraron ta, ci gaba tayi "dama akan aurena da zaka yi ne, nasan ba wani abu a tsakanin mu sai kawai naji Maganar aure kuma bacin bamu ta6a haka da kai ba...to shine nike son in tambaye ka miyasa zaka Aure ni tunda baka ta6a nuna kana...so na ba" da k'yar ta k'arasa Maganar da in ina tare da d'an nishi duk a lokaci guda, maida idon shi yay ya koma kallon gaban shi ta kafe shi da ido tana son gane yanayin fuskar shi da yake akwae haske sosae a layin ya d'an haska cikin Motar, sun d'an d'auki lokaci kafin taji ya furta "why did you ask me that?" Yay tambayar tare da Kallon ta, abu ta had'iya a Sanyaye tace "kawai hakanan ne inason in sani Saboda nayi mamakin hakan" tana rufe baki yace bata yarda dashi ba kenan da sauri tace "a'a wllh...kawai dai kai ne ka ta6a ce man kar in rink'a bada yarda gaba d'aya to shiyasa nike son in ji dalilin da yasa kake son aure na" kauda idon shi yay daga barin kallon ta sannan ya furta shima bai sani ba hakanan zai aure ta, tsit kake ji wani iri Fauzy take ji a cikin ranta hakan da ya fad'a, kallon ta yay daidai lokacin itama ta d'ago ido ta kalle shi calmly ya ce in tana ganin hakan bai mata ba lokaci bai k'ure ba za'a iya fasawa ai, tun kafin ya rufe baki k'irjinta ya hau bugun uku uku hannunta ya fara d'an rawa, kafeta yay da ido alamar amsarta yake jira ta fara motsa baki da k'yar cikin rashin dad'in rai ta furta "Shikenan, in hakan yayi maka nima yayi man" tana k'arasa Maganar da sauri ta sunkuyar da kanta jin k'walla sun fara tarun mata a cikin idanunta sam ba haka ta so taji daga gare shi ba a ranta ta raya Mujaheed yayi tarayya da ita don tana burgeshi shi k'ilan ma tasan koma burge shi d'in bata yi, kallon shi tay bayan tayi kokarin maida kwallar ta d'an k'ak'alo murmushi tace "Nagode Allah ya saka da Alkhairi Allah kuma ya maida ka lafiya" jinjina mata kai yayi tace mashi saida safe bin ta da ido kawai yay ya d'an yi jimm can ta juya ta kai hannu zata bud'e kopar.., "I will marry u because....i love you Fauziyyah" kaman saukan aradu haka taji Maganar ta sauka akanta, da sauri ta juyo tana kallon shi idon shi na akanta amman sai ka rantse ba shi yay Maganar ba don Kalmar k'arshe daya furta kalma ce mai matuk'ar tsada a wurin shi in ba Mom d'in shi ba ba wadda ya ta6a fad'i ma hakan duk da uban matan dake rok'on shi kan ya furta masu hakan, d'an murmushi tay ta fara motsa baki cikin yar in ina tace "are you telling the truth?" wani irin lumshe ido yay duk da acikin duhu ne ta gani ta d'an hasken cikin Motar, dad'i ne ya kama Fauzy har bata san lokacin data ce mashi don Allah ba don taji dad'i ya fad'i hakan ba, d'an ta6e baki yay yace dama mutum na auren wanda baya so ne, murmushi kawai Fauzy ke saki tace mashi ta gode in sha Allahu zata zame mashi mata ta gari wadda zata bashi Farin ciki na har abada tana ganin d'an murmushin gefen da yayi, sai faman k'ayataccen murmushi take gaba d'aya dad'i ya cikata don abunda take fata ne ya kasance yana son ta, ce mata yayi taje sai sunyi magana tace to, har zata juya taji yace haka yakamata su rabu dakatawa tayi ta maido idonta kan shi ko da bai fito ya fad'i ba ta gane yadda yake nufin yakamata su yi bankwana, shiru tayi a cikin ranta tana raya gaskiya bai kamata tana biye mashi ba tunda hakan ba kyau kuma in dai tana son ta hana shi hakan dole ta fara ta kan su, cikin yar rawar murya tace "k...kayi hak'uri naga bamu kai ga yin aure bane ina tsoron mu samu zunubi....kuma hakan na iya shafar rayuwar Auren mu don naji anata wa'azi akan hakan" shiru yay still idanun shi na akan ta sai kame kame take can taji yace ta tafi wani iri taji sai taga kaman yayi fushi ne zata so ace tayi mashi abunda zai faranta mashi ba kamar da shima yanzu yay mata abunda ya saka ta farinciki amman tasan hakan shi yafi masu Alkhairi, a sanyaye ta furta mashi "Gud nyt" kai ya d'an jinjina mata kafin yace karta manta da abun baya daga yadda ya furta Maganar bazata iya gane yanayin da yake ciki ba. Lokacin data shiga cikin gidan a parlor ta iske Aunty Mareeya da su Hanif tana yi masu Assignment, da sallama ta shiga suka taso da gudu suna mata oyoyo, amsar ledojin suka yi ta dafa Shoulder d'in iman suka nufi cikin parlon idon Aunty a kan su tana ta washe baki, a kusa da ita ta zauna tace "yan tafiya an dawo?" Fauzyn ta d'aga mata kai, "Amman wai tun da kuka fitan kuna government House d'in?" Kai ta d'an girgiza mata ta fad'i mata duk inda suka je, tambayar ina Sameer d'in tayi tace ya tafi kafin ta d'aga kai, hannu Aunty ta kai ta d'aukko jakar kwalin da ta ja hankalinta tace miye aciki Fauzy tace bata sani ba First Lady ce ta bata, bud'e ta Aunty tayi ta kai hannu ta fara fiddo abubuwan ciki, turare na guda ukku iya kwalin su abun kallo ne sai miski a yar babbar kwalba mai kyau tun ba'a fiddo turarurrukan daga cikin kwalin su ba har k'amshin su mai dad'i ya karad'e wurin, sosae Aunty ta yaba bayan ta maida su cikin jakar ta tambayi yadda suka kar6eta ta fad'i mata hakan ma taji dad'i sosae harda 6akar Fauzy a kafad'a tana fad'in ta dai zama dangin gwabnoni ita dai yar dariya tayi, tambayarta yadda Fatuu take ta k'ara yi tace halan tana nan tana ta ja tace mata eh, kallon ledojin tayi da yake akwae tambarin wurin da aka siyo kayan ciki tana dariya tace daga ziyarar chilling kenan suka wuce still Fauzy murmushi kawai tayi, fara janyo ledojin tayi su Hanif na Mik'o mata sauran ta shiga bubbud'a su, tarkacen su ice cream ne flavour daban daban dasu yoghurt sai su shawarma da pizza abubuwa dai kala kala kili guda tana cikin dubawa tace "ashe su suriki na ba iya kud'i aka iya badawa ba" tambayar Fauzy tayi cikin wurin suka shiga aka siyo tace a'a ta fad'i mata kawo masu akai tace ai dama ta d'an ji mamakin ace shiga sukai dashi aka siya, Hanif ne ya d'auki ice cream yace ma Aunty ya sha tace na Aunty Excellency ne ya tambayeta Fauzy ta d'an yamutsa fuska tace "kai Aunty don Allah" tana dariya tace tuba take, babbasu komai tayi kowa ya natsu suka fara ci itama ta d'auki shawarma tana ci, kallon Fauzy data jingina da kujera tayi shiru Aunty tayi tace "wai lafiya Fauziyya, na lura kamar akwai abunda ke damun ki tun bayan da kika shigo kin k'i sakin jiki sosae" d'an ta6e baki Fauzy tay ta furta "uhmm" dakatawa Aunty tayi da cin abun da take gaba d'aya ta maida hankalin ta kanta tace mata ya akai ne, ajiyar zuciya tayi ta fara motsa baki kafin ta shiga bata labarin yadda sukai da Sameer na tambayar da tayi mashi kan dalilin daya sa zai aure ta da amsar daya bata har zuwa yadda suka rabu, "Ni Aunty ina ganin kaman yayi fushi" shiru Aunty ta d'an yi can tayi yar ajiyar zuciya ta dafa Shoulder d'inta tace "ba lalle ba, in dai da gaske yana da ilimin Addini to bazai ji komai ba tunda yasan gaskiya kika fad'i sai ma dai yaji dad'in hakan tunda ya gane wace kalar mata zai aura, kuma fa tana iya yuwuwa ma gwada ki yake kinsan Mutane in suna abunda suka san ba daidai ba to basu son su Auri mace mai hakan don haka karma ki wani damu wllh" kai kawai Fauzy ta jinjina amman ita tasan ba wani gwadata da yayi Saboda abubuwan da yayi mata, daga baya sakin jiki tayi suka cigaba da cin abubuwan anan Aunty ta ce yakamata ta sa yazo yayi breakfast gobe Fauzyn tace anya zai zo don yace gobe zai tafi amman dai zatayi mashi magana. Bayan ta koma d'aki a bakin gado ta zauna ta shiga tunanin ko ta kira shi saidai tana jin d'ar d'ar can dai tay k'arfin halin kiran nashi, har ta yanke bai d'auka ba ta ruk'e wayar tana dakon kiran shi kamar yadda suka saba bada jimawa ba kuwa sai gashi ya kira d'in har saida tayi murmushi taji d'an sanyi a ranta, bayan ya d'auka ya ya koma tayi mashi ya amsa mata daga haka suka yi shiru can taji yace da wani abu tace mashi eh dama Aunty d'in ta ce tace tayi mashi magana yazo da safe don Allah yayi breakfast, ce mata yay bazai samu zuwa ba don Flight d'in safe zai bi tace to tayi mashi saida safe itama yayi mata, bin wayar tayi da kallo tama rasa tunanin da zata yi jikinta ya d'an yi sanyi can dai ta mik'e don tayi shirin kwanciya........... 93 _ASM BY ZAINAB BATURE _ ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ .......Washe gari bayan Fauzy taje School Zainab nata son yi mata magana sai dai bata samu damar hakan ba don tana zuwa malamin su ya shigo, saida akayi break sannan tazo seat d'in su da yake yanzu basu fita break Saboda nauyin da Fatuu tayi ita ke zuwa masu da Abinci to yau itama Fauzy tazo masu da shi, zama Zainab d'in tayi a saman desk suna cikin cin Abinci ta fara jero mata tambayoyin yadda akai suka san juna da Sameer shida ko kallon mutane ba yayi, sosae ta rink'a basu dariya yarda ta hak'ik'ance tana fad'in an cuceta, har aka dawo break bata k'yale su ba k'arshe tare dasu tayi break d'in, Fauzy nata so taba Fatuu turaren data kawo mata cikin wanda aka bata amman Saboda Zainab d'in ta k'i fiddo shi don tasan tabbas sai tace a bata shi kuma ita Fatun take son tayi amfani da shi, saida aka tashi sannan ta bata, tare Tk ya d'aukesu saida aka aje Fauzy gida har Fatuu ta shiga tayo fitsari sannan ta fito Fauzy ta rakota suka tafi. Bayan sallar Juma'a wuraren k'arfe ukku na rana Fauzy tayi wanka tayi kwalliyar Juma'a lokacin tuni sunyi waya da Sameer har ya koma, tana zaune a cikin d'akinta tana chat wayarta ta fara yin ringing, bin bak'uwar lambar da aka kira tayi da kallo kafin ta d'auka a nutse tayi sallama, bayan mai kiran ya amsa cikin girmamawa ya gaishe da ita da alamun mamaki akan fuskar ta ta amsa yace dama sak'o ne ya kawo mata yana waje, d'an jimm tay kafin ta amsa da to gata nan fitowa, bin wayar tay da kallo bayan ta cire a ranta ta shiga raya to waye wannan kuma wane sak'o ne ya kawo mata, mik'ewa tay saida ta d'aukko gyale ta d'aura akan gown d'in jikinta sannan ta tafi, lokacin data shigo cikin parlon ba kowa ta nufi hanyar fita, yana tsaye a gaban bak'ar Mota yana ganinta ya shiga washe baki kallo d'aya Fauzy tayi mashi ta gane shi, k'arasawa tayi fuskar ta adan sake suka k'ara gaisawa, "Yauwa dama sako ne Yalla6ai ya bada akawo maki, Wannan Motar ce yace in kawo maki taki ce sannan ni zan rink'a kai ki Makaranta sannan yace in fara koya maki Motar in kika iya sai kici gaba da zuwa Makarantar" tunda ya fara Maganar tay sototo tana kallon shi har ya gama, ba don tasan yasanta ba da zata ce makuwa ce yayi an aike shi wurin wata duk da haka yanzu ma tunanin makuwar ce yayi tayi tana d'an murmushi tace mashi tana ganin yayi kuskure ba wurinta aka aiko shi ba, "Hajiya ba kuskure nayi ba ko baki gane ni ba, ni ne wanda nazo jiya da Yalla6ai ba har na kai ku Government House ba, tabbas ke ce aka ce in kawo mawa don yau kafin ya wuce mukai Maganar" ido kawai Fauzy ta bishi da shi don kuwa bakinta ya mutu, mik'a mata makullin Motar yayi kaman bazata amsa ba jiki a mace ta mik'a hannu ta amsa, "Yanzu yaushe za'a fara koya Motar ko zuwa gobe in yayi sai in zo tunda naga weekend ne kaman ba Makarantar" kikkafta idanu ta fara saida ta had'iyi abu kafin murya na d'an rawa tace "to...ai lambar da ka kira ni taka ce ko?" da sauri yace mata eh tace to zata yi mashi magana kan hakan yana murmushi yace to kafin ya tambayi yanzu za'a shigar da ita ciki ne ta girgiza mashi kai tace ya barta anan, sallama yayi mata ta d'aga mashi kai ya juya ya nufi hanyar barin layin da k'afa, bin bak'ar Camry d'in da akace tata ce da kallo tayi Zuciyar ta na d'an harbawa can ta maida idanunta akan makullin Motar shima ta kafe shi da ido, juyawa tayi jikinta kamar an zare mata laka ta nufi cikin gidan, tana shiga cikin parlon daidai Aunty Mareeya ta fito daga bedroom d'inta taci gayu da doguwar rigar shadda blue tasha aiki mai ratsin red takalman ta da jakar hannunta duk jajaye ne ta coge d'aurin kallabi sosae tayi kyau, tana ganin Fauzyn ta dakata tana jiranta ta k'araso, daga gefen Auntyn ta tsaya tana kallon ta, "Ke kuma daga ina yaushe kika fita?" Shiru tayi tana kallon ta kawai ganin haka yasa Aunty cewa "lafiya naga kin tsura man ido?" Hannu ta d'ago ta mik'a mata makullin ta kawo hannu ta amsa, bin shi tayi da kallo ganin na Mota ne yasa ta d'ago tace mata makullin Motar miye, a sanyaye ta shiga fad'i mata abunda mai kawo Motar yace, waro ido Aunty tay nan take ta saki jakar hannunta ta furta "Makullin Motar ki ne!!" Kai ta d'aga mata tace wai haka yace dai, washe baki Aunty tay "haka d'in ma ne wllh, kai wannan dankareriyar kyauta haka tun baki shiga daga ciki ba!" Sosae ta shiga yin murna ganin yanayin Fauzyn ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta "wai ya na ganki haka duk kin yi sanyi keda zaki murna abun farinciki ya same ki haka" d'an ta6e baki tay da alamun damuwa tace "Amman Aunty indai tawa d'in ce to ni ya zanyi da ita, Mota fa!" Wani kallo tay mata "kaji ki da wata Magana, bangane ya zaki da ita ba, ba an fad'i maki abunda zaki da itan ba" "Amman Aunty taya za'a ce kamar ni inada Mota" harara ta balla mata tace "Wllh matsalata dake wani lokacin k'auyanci komai sai kin nuna ke yar k'auye ce duk da kin shigo birni koda yake inda kika fiton ma ai ba k'auye bane kece dai haka, in banda abu irin ki mace nawa ce yanzu wadda bata kai ki ba take hawa Mota yanzu baga Zarah ba" still da alamun damuwa tace Amman ita ai matar aure ce ko, wannan karon k'ular da Aunty tayi a fusace tace "ai da yake ance mace in bata da aure bazata tuk'a Mota ba, dalla kin ma fara bani haushi in baki so ni sai ki bar man ina so, wllh ba za'a maida Motar nan ba in ma haka kike niyyar cewa, a baki abu don ki rink'a zuwa Makaranta ki tsaya kina wani fad'in k'auli da ba'adi ke da ba'a maki gwaninta" yar ajiyar zuciya tayi a sanyaye tace mata to tayi hak'uri cikin washe baki tace yauwa to ko itafa ai kawai ta kira tayi mashi godiya ita an ma yi a daidai wllh dama tana jin haushin hawa Napep, dariya Fauzy tay ita sai lokacin ma ta tuna da Aunty Mareeyar ta iya Mota, iyayensu ta kira gaba d'aya harda Yaya Mubarak d'in su ta sanar masu zancen zuwan Sameer d'in da kuma Motar da ya bata gaba d'aya sun jinjina abun sosae kafin suka sanya Alkhairi mahaifin nasu yace mata don Allah ta k'ara kulawa da ita sosae tunda yanzu a wurinta zata zauna tace in sha Allahu kar ya damu har Fauzyn ta ba duk suka yi mata Allah sa Alkhairi da Allah ya tsare itama Baban nasu saida yay mata yar nasiha kan ta k'ara kula da kanta ta guji duk wani abu data san zai ja mata dasu gaba d'aya matsala tace mashi insha Allahu zata k'ara kulawa sosae, bayan sun gama wayar Fatuu ta shiga kira lokacin Aunty ta tafi ta gano Motar, lokacin data sanar mata game da Motar wata uwar k'arar murna Fatuu ta saka cike da tsananin farinciki ta hau yi ma Fauzyn Allah sa Alkhairi cike da murna tace ikon Allah Yanzu ita tana da mota ita ma haka Fauzy tace wllh, daga baya sukai sallama tace sai tazo ganin Motar, bayan ta gama wayar hanyar wajen ta nufa a cikin harabar gidan sukai kacibus da Aunty Mareeya ta dawo sai washe baki take kamar wadda aka ma Albishir da Aljanna, tsayawa sukai cike da Farinciki ta furta "Fauziyya wannan Mota haka! da gani zata yi kud'i wllh don babba ce kuma sabuwa" dariya kawai Fauzy ke yi da sauri tace mata taje ta shirya suje yinin bikin tare a Motar Fauzy tace to ba matsala in sun hau tayi mata wani kallo tace to miye abun matsala abu tata, kai Fauzy ta d'aga tace bari taje to ta shiryo Aunty Mareeyar ma ta bi bayanta tana fad'in ai itama kaman sai ta sake shiga gaskiya sosae taba Fauzy dariya, gaba d'aya lace suka saka na Aunty bak'i ne da adon flowers pink ta saka takalma da jaka da gyale duk pink sosae tayi kyau ita kuma Fauzy nata Orange ne da torch d'in bak'i tasa takalma da jaka da mayafi bak'ak'e Wow abun sai dai ace Ma sha Allah don sosae sukai kyau, tunda suka hau hanya suke ta faman sakin murmushin farinciki gaba d'aya sun kasa rufe baki Aunty sai faman santin Motar take, suna akan hanyar ta tuna da bata fad'i ma mijinta zancen Motar ba tasa Fauzy ta fiddo mata wayarta ta kira mata shi, bayan ta sanar mashi shima sosae ya nuna ya taya Fauzy murna Aunty tace ai saima yaga Motar, tambayar shi su Hanif tayi yace daga Masallaci sun wuce gidan Hajiyar shi tace to agaishe mata da mutan gidan, daga wurin yinin bikin da yamma fitowa sukai suka d'an zaga gari daga can suka wuce gidan Hajiya don suje su nuna ma Fatuu Motar. A kwana a tashi cikin Fatuu har ya shiga wata na bakwai a lokacin tuni dama Hajiya ta hanata driving ganin yadda cikin yay girma ita kanta dama tuntuni ta fara jin rashin dad'in tuk'in, Sosae take samun kulawa don komi take so sai an mata haka ko wash tace sai Hajiya ta tambayi yaya in dai tana kusa da ita don yanzu tafi zama a part d'in, data dawo daga Makaranta nan take zuwa taci Abinci wani lokacin ma har wanka a visitor room take yi don akwai wasu daga cikin kayanta yawanci sai dare take komawa part d'inta tare da Mino, bangaren Haisam akai akai yake kiranta suna kuma yin chat sosae haka yan Abuja ma yanzu kullum sai Mom d'in Haisam d'in ta kirata ta tambayi yadda take haka Senator ma yana yawan kiranta su Jidderh wannan ba'a magana don sosae take kiranta tana tambayar Babies d'in su, bangaren gwaggo ma sosae take kulawa da autar tata kullum sai ta aiko mata da abun ci ba kamar wanda zai k'ara mata lafiya da yawan jini kamar ganyayyaki kullum sai tayi mata kwad'o mai dad'i. Ranar Monday da yamma Fatuu na zaune a part d'in Hajiya tana yin Assignment hannunta ruk'e da agwaluma tana sha sai faman tsuke baki take tana d'an runtse ido Hajiya na dariya tace to kamar dole ta hak'ura mana tana yar dariya tace wllh wannan ta cika tsami ne Hajiyar tace to ba ga wasu nan a plate ba ta duba mara tsami sosae sai tasha tace to, d'agowa tayi da niyyar ta canza watan suka ji anyi sallama a tare suka kai idanun su kan k'opa Hajiya na amsawa, lokacin da wadda ta shigo ta k'araso ciki Fatuu na ganinta ta fara murmushi ganin k'anwar haulat tace "Mami ce" kai ta d'aga mata Fatuu ta nuna mata wuri tace ta zauna, gaishe da Hajiya tayi ta amsa ta juyo kan Fatuu itama ta gaishe da ita, amsa mata tayi idon ta akan fuskar ta don ta fahimci kaman kuka tayi idanunta sunyi ja sun d'an kumbura ma, a sanyaye tace "Mami lafiya dai ko?" tana yi mata tambayar ta fashe da kuka hakan ya rud'a Fatuu ta d'ago sosae tana tambayar ta abunda ya faru ido a waje, cikin kuka Mamin tace mata dama cewa akai tazo ta fad'i mata mijin Aunty Haulat yayi had'ari jiya an kai shi Asibiti yau Allah yayi mashi rasuwa, gaba d'aya Fatuu ta zaro ido waje tare da kai hannu ta dafe k'irjinta a razane ta furta mijin Haulat ya rasu! Mami dake ta kuka tace eh, kai Hajiya ta shiga girgizawa sosae ta girgiza da jin Maganar don Haulat ma yar gidanta ce, Kuka sosae Fatuu ta saka tana zabga salati tana fad'in Wayyo Allah Haulat, rarrashinta Hajiya ta shiga yi tana fad'in ta kwantar da hankalinta ko don halin da take ciki amman ina ta kasa daina kukan hakan yasa itama Mami d'in cigaba da rusa kukan, Saude ce ta fito daga cikin kitchen jin hayaniyar kukan su, cikin Falon ta nufo ganin su Fatun nata kuka yasa a rud'e ta hau tambayar lafiya Hajiya ce ta fad'i mata abunda ya faru itama ta girgiza sosae ta shiga yin salati, had'uwa sukai suna lallashin su har Fatun ta d'an yi shiru Mami ma ta daina tana ta goge Fuskar ta da gefen Hijab dibta, waya Fatuu ta d'aukko dake ajiye a gefenta ta shiga kiran gwaggo bayan ta d'auka ko sallama bata yi mata ba cikin kuka tace taji abunda ya faru gwaggon tace mata eh yanzu Mamin ta baro nan sai hak'uri lokacin shi ne yayi, cigaba da kukan tay gwaggo ta shiga rarrashinta tana nuna mata halin da take ciki Fatun sai faman fad'in to ta daina take, bayan sun gama waya da gwaggo Haulat ta shiga kira tana cigaba da yin kuka kad'an kad'an saidai wayar tak'i shiga dama haka take wuyar samunta a waya shiyasa sun fi yin Vedio call gashi yanzu tasan ko ta hau WhatsApp ma ba ganinta zata yi ba, aje wayar tayi ta yunk'ura ta mik'e da k'yar fuskarta jage jage da k'walla tace ma Mami bari tazo su je Hajiya ta tambayi ina tace mata gidan su Haulat d'in zata tayi ma innar su gaisuwa Hajiya tace mata ta bari ayi Magrib tunda ta kawo jiki sai suje gaba d'aya tace to, komawa tay ta zauna Mami ta mik'e tace masu ta tafi Hajiya tayi mata gaisuwa tace ta yi ma innar su kafin su zo Saude ma tayi mata gaisuwar ta tafi, mik'ewa Fatuu ta k'ara yi gaba d'aya duk ta rud'e Hajiya ta k'ara tambayar ya akai cikin muryar kuka tace mata fitsari take ji tace taje tayi ta shiga k'ara bata hak'uri tana fad'in ta kwantar da hankalinta kai kawai take d'aga mata Saude tace suje ta rakata d'akin Hajiya tace yauwa, saida ta rakata har cikin d'akin sannan ta fito ta koma Kitchen jikinta gaba d'aya yayi sanyi tausayin Haulat yakamata, bayan Fatuu ta fito daga toilet bakin gado ta nufa ta zauna ta kai hannu ta d'auki wayarta da taba Saude ta aje mata bayan sun shigo, Haisam ta shiga kira bayan ya d'aga ta gaishe dashi yana jin muryar ta ya gane ba daidai take ba ko amsa gaisuwar tata baiyi ba ya shiga tambayar ta lafiya Mike damunta, cikin kuka ta sanar mashi shima yaji abun sosae yayi mashi Addu'a kafin ya shiga rarrashinta yana kwantar mata da hankali shima sai faman ce mashi to take saida ya tabbatar ta kwantar da hankalin nata kafin sukai sallama, sai bayan da akai isha sannan suka fito don su tafi gaba d'ayan su sun sa dogayen hijabai harda Saude, Tk ne zai kai su a Motar Fatuu har Hajiya na fad'in ba don dare yayi ba ai da a k'asa suka lalla6a ko Fateema tayi exercise Saude tace to suje a k'asan tunda akwai wuta Hajiyar tace tunda dai ya fiddo Motar suje kawai ko don dare, a k'opar gidan su Fatuu Hajiya tasa ya tsaya tace ma Saude taje ta tambayi Dije in bata je ba ta fito su tafi tace to lokacin shagon Kawu Amadu a rufe yake da alama tunda ya tafi salla ya kulle shi, bada jimawa ba suka fito tare da gwaggon dama Saude gaba ta shiga, baya gwaggo ta shiga inda su Hajiya suke ta gaishe da ita ta amsa tayi mata jaje da gaisuwa, kallon Fatuu tay tace har yanzu kukan take ta girgiza mata kai kafin cikin disasshiyar murya ta gaishe da ita bayan ta amsa ta shiga kara bata hak'uri, lokacin da suka je gidan akwae mutane da suka zo gaisuwa innar ta tarbe su bayan duk sun zazzauna aka shiga gaisawa da yin gaisuwa, koda Fatuu tazo yi mata gaisuwar sai kawai ta fashe da kuka nan fa innar su Haulat d'in itama ta shiga matsar k'walla haka K'annan Haulat d'in suma duk suka dasa dama kuma auren Haulat d'in na zumunci ne duk dangi ne, mutane ne suka shiga basu hak'uri suna fad'in lokacin shi ne yayi yanzu Addu'a yafi buk'ata, daga baya sai ga Kawu Amadu tare da Tk sun shigo suma sukai masu gaisuwar, suna a gidan Baban su Haulat ya dawo daga Masallaci innar tasu ta fita tayo mashi magana ya shigo daga bakin k'opar ya duk'a nan aka shiga yi mashi gaisuwar yanata amsawa tare da yin godiya. Tun bayan da suka dawo Fatuu ke ta trying kiran Haulat ba ta shiga sai bayan da suka dawo part d'in su ita da Mino lokacin sun kwanta cikin sa'a sai gashi kiran ya shiga tana d'auka Fatuu ta saka mata kuka tana fad'in ashe abunda ya faru kenan cikin disasshiyar murya ta wanda yasha kuka Haulat d'in tace mata wllh, jajanta mata ta shiga yi tare da yi mata gaisuwa ganin yadda take ta Kuka yasa Haulat d'in ta shiga rarrashinta tana fad'in don Allah ta bari bata ga halin da take ciki ba Fatun tace wllh tausayin su take ji ba kamar Umma Salma duka yarinyar ko shekara bata yi ba Haulat d'in tace mata eh amman ta kusa saura wata d'aya, jajanta mata taci gaba da yi tana Addu'oi daga baya taba Mino itama tayi mata gaisuwa. Gwaggo da Kawu Amadu ne suka shirya tafiya gaisuwa Nijar Fatuu taso ace da ita za'a saidai itama tasan bazata iya yin wannan tafiyar ba a halin da take ciki, kwana biyu da yin rasuwar suka tafi suna can akai sadakar ukku kwanan su biyu suka juyo. Bayan cikin Fatuu ya fita daga wata na bakwae ya shiga na takwas da sati d'aya Mom d'in su Haisam tazo tafiya da ita, kwananta biyu suka shirya tafiya bayan Fatuu tayi sallama da kowa Mino harda yar kwallar ta anata yi mata addu'o'in Allah ya sauketa lafiya lokacin da aka raka su Airport, Kusan gaba d'aya aka rakasu harda Hajiya dasu gwaggo Kawu Amadu da Saude da Mino su Aunty Mareeya da Fauzy kowa dai ita dai Fatuu sai d'an murmushi take zuciyarta nata saka mata abubuwa, Alhamdulillah sun sauka garin Abuja lafiya har anje an d'aukko su sai faman murnar zuwan Fatun ake karma dai Jidderh dasu twins su ji, dole Jidderh ta matsa ta sauka a d'akin ta itama Fatun hakan yayi mata dad'i, washe gari Aunty ta tafi da ita Asibitin su aka yi mata awo don samun record d'in ta. Bayan dawowar ta Abuja Kusan doubling kulawar da take samu a Katsina akai mata, sosae ake ta haba haba da ita koda yaushe cikin tambayar abunda take so ake haka safe da dare cikin zuwa dubata ake duk wanda zai fita sai yazo ya dubata harda Dad da safe kafin ya fita sai yazo ya dubata haka in ya dawo ma da daddare sauran yaran gidan ma da safe kafin su tafi school duk sai sun zo sun dubata haka da sun dawo nan suke fara sauka bayan sun dubata sannan suje suyi wanka in aka shirya ma nan za'a dawo wurinta aci Abinci kullum Jidderh cikin fad'an an 6ata mata d'aki take gashi bata isa ta hana yaran gidan zuwa d'akin ba don ta kora su Mom da kanta ta maido su tace bata isa ta hana wani zuwa ba tunda ta rik'e Fatuu in kuma tana son a daina zuwan to saidai ta bari Fatuu ta bar d'akin ta kafe tace ba inda zata anan zata zauna har ta haihu tana fatan ma Allah ya kawo haihuwar da Sauk'i suna bacci kawai suga ta haihu har saida ta ba Mom da Aunty dariya suka ce to Allah ya sa ta haihu hakan dama Aunty tana d'akin Mom ta zo maido su Yasmeen da twins da aka kora daga d'akin, duk dare su Jidderh da Yasmeen dasu twins ke rakata strolling su zagaye gidan in ta gaji ta d'an rankwafa sai suma suyi hakan kaman sun yi sahun salla in ta mik'e sai su mik'e sosae suke bata nishad'i cike da shiririta ake yin tafiyar har a zagayo, haka in tana kwance ko zaune kan gado sai su zagaye ta suna mata hira ana mata tausa in wannan suka yi suka gaji sai su ba wannan, wani lokacin in tana kwance maida cikin nata suke kaman Tv suna kallon yadda yake motsi suyi ta faman kyalkyatar dariya suna fad'in wrestling ake tsakanin Hassan da hossein ko kuma Hassana da hosaina, gaba d'aya d'akin Jidderh ya koma dining area tun tana fad'a har ma ta gaji ta daina. Satin Fatuu biyu a Abujar lokacin cikin na gab da shiga wata tara Haisam yazo, lokacin da yay arba da Fatuu wani irin tausayin ta ne ya kama shi ganin yadda Baby d'in shi ta koma, bata yi wani muni ba saidai komai nata ya k'ara girma ga cikin ma Tubarkallah yayi girma sosae, a ranar ya maidata part d'in shi aikuwa washe gari Mom ta iske shi tace ba yadda za'ai ta zauna nan gaskiya shi bai ga halin da take ciki bane ya zata rink'a hawa bene, shima saida yay wannan tunanin don a jiyan yaga da k'yar ta hau saida ma ya taimaka mata gashi shi kuma gaskiya a wurin shi yake son ta zauna, k'arshe yanke dawowa k'asa yay daga k'asan part d'in Dad dama akwae wani ciki da parlon wanda wani lokacin Dad d'in ne ke amfani dashi ba kamar in yayi bak'i, a ranar aka sa masu aiki suka gyara part d'in fes suka tare, kulawa ta musamman Haisam ke bata tun bayan da ya dawo gashi kwata kwata bai nuna mata yana son wani abu ya shiga tsakanin su sosae yake d'aga mata k'afa to dama itama bata jin abun a kanta hakan ne ma yasa tun tana gidan Hajiya daya nuna zai zo sai tace yay zaman shi kada aga yana wasa da aiki hakan yasa ya d'auki lokaci bai zo ba, duk da haka sosae yake mata abunda yasan zata ji dad'i, a kwana a tashi har cikin Fatun ya shiga wata na tara, tun ranar da ya shiga aka fara saka ran haihuwar ta dama tuni Iya ta fara bata su maganin zak'i da sauran su haka akwae wanda gwaggo ta had'a mata ta taho dasu, shiru shiru ba haihuwa kaman tasan jiranta ake ko ciwon kai Fatun bata yi a haka har Edd d'inta ya wuce hakan ya fara tada masu hankali Aunty ta shiga nuna masu hakan ba matsala bane ai dama 2 weeks before ne ko after a d'an k'ara jira a gani in ya wuce haka kawai ayi mata Cs, itama Fatun da yake tasan hakan ba matsala bane bata wani damu ba, bayan sati guda da wucewar Edd d'in ta ranar ta kama lahadi ne gaba d'aya bata wuni a part d'in nasu ba sai dare ta dawo, Haisam ne ya taimaka mata kaman ko yaushe tashiga wanka bayan sun fito yana k'ok'arin taimaka mata ta shirya tace ya bari ta shirya yaje shima yay wankan, saida ya tambayi ta tabbatar zata iya lafiya lou tana murmushi tace mashi eh, bin shi da ido tay lokacin daya nufi toilet d'in wani irin tausayi yake bata tasan ba don bai buk'atar ta ba yake k'yale ta kawai Saboda tausayinta da yake ne, hakanan taji yau tana son wani abu ya shiga tsakanin su, lokacin daya fito har ta kwanta tana kallon shi da murmushi yake shiryawa shima yana yi yana kallon ta, bayan ya gama komai yay switching wutar dakin off ya nufi gadon, saida ya kunna lamp guda d'aya sannan ya hau gadon, zama yay daga gefen k'afafunta ya fara matsa mata su dama kullum haka yake mata har tayi bacci, yana cikin yi mata tausar yaga ta fara mashi wani salo lokacin daya fahimci mi hakan ke nufi ce mata yay ba komai kada ta damu amman ta nuna mashi lafiya lou ba komai, to daman dai a buk'ace yake da ita hakan yasa ya bata goyon baya, sosae suka faranta ran junansu duk da Fatuu tana yin wani abun ne kawai don ta faranta mashi shi kuma cike da taka tsantsan yake bi da ita, bayan tayi bacci ya tashi ya nufi toilet lokacin daya dawo shiryawa yay cikin jallabiya ya kabbara sallar Nafila don rok'on Allah ya Sauketa lafiya dama Kusan duk dare yana hakan, raka'a biyu yayi bayan ya gama Addu'oi ya koma gadon, rungumota yay ta baya dama a haka suke kwanciya ya lullube su........... Around 2:00am Wani irin fitsari ne ya tashi Fatuu dama ta saba tashi fitsari cikin dare sosae, zame jikinta tayi daga nashi ta lalla6a ta saukko kafin ta nufi hanyar toilet d'in da sauri don tana saukkowa taji kaman zai zubo mata, lokacin data duk'a don yin fitsarin wani kalan discharge da bata saba gani ba taga ya zubo mata amman sanin dama tana fitar da shi yasa bata maida kai ba, bayan ta gama fitsarin tayi tsarki ta fito, komawa tayi gado ta kwanta bata fi yan mintuna ba taji cikinta yay wani irin juyawa har saida ta cize baki, wani fitsarin taji ya kamata sosae da sauri ta saukko ta nufi toilet, koda ta duk'a don tayi d'an kad'an ya zubo tare da wani irin ciwo har saida tay d'an sautin rad'ad'i, da k'yar ta yunk'ura ta fito daga cikin toilet d'in ta koma gado, gaba d'aya kwanciyar ta gagareta don ciwon k'aruwa yake mata, wasa wasa tun tana a saman gado har ta kai ta saukko ta duk'e k'asa, duk abunan bata yi tunanin tada Haisam ba don gani take kaman ciwon zai lafa, tun tana juye juye har ta kai ta fara d'an yar fa hannu tana fad'in wash, ganin abun bana k'arewa bane don sai ma cigaba da yake yasa ta gane nak'uda ce take yi a wahalce ta fara kiran sunan Haisam tun dai bata d'aga murya har takai ta d'aga tana ta kiran sunan shi tana ya taimaka mata, ganin yak'i tashi yasa ta fara bubbuga katifa can acikin baccin ya jita a hankali ya fara bud'e idanun shi, daidai ya bud'e ta k'ara kiran sunan nashi tana ya taimaka mata, wata kalar wuntsilowa yay ya sauko da sauri ya zagayo inda take a durk'ushe shima ya duk'a ya shiga tambayar mike damunta hannuwan shi rarruke da ita, cikin ciwo tace mashi tana ganin kaman nakuda ce take a rud'e ya furta Ok bari ya fad'i ma Aunty, mik'ewa yay da sauri ya nufi k'opa har ya bud'e komi ya fad'o mashi a rai sai kuma ya kulle ya dawo cikin d'akin ya nufi wurin side drawer, wayar shi ya d'aukko ya dawo saitin Fatun ya fara k'ok'arin kiran ta, lokacin da wayar ta shiga duk bugu d'aya tare yake da fad'uwar gaban shi, sai faman sintiri yake a wurin saida wayar ta kusa yankewa sannan Aunty ta d'auka cikin muryar bacci ta ambaci sunan shi tare da tambayar lafiya a d'an rud'e yace mata Baby ce ke nak'uda da sauri tace to gata nan zuwa harda ce mata don Allah tayi sauri tana cikin ciwo sosae ta furta Ok gata nan, duk'awa yay ya tallabo Fatun fuskar shi har ta fara hautsinewa cike da tausayi yake ce mata sannu, after few minutes aka turo kopar Aunty ce ta shigo tana sanye da doguwar rigar bacci yana ganin ta ya mik'e yana nuna mata Fatun ta nufo su, a gabanta ta tsaya ta duk'a tana dubata tare da yi mata sannu, d'agowa tay tace ma Haisam nakuda ce da sauri yace to yanzu ya za'ai tace tana zuwa ya taimaka su d'aurata saman gado yace to, bayan sun d'aurata d'aukar abunda ta aje a bakin gado tayi wanda disposal gloves ce ta bud'e yar jakar ta ciro su ta fara k'ok'arin sama hannuwanta, bayan ta gama ta fara duba Fatun dama itama rigar bacci ce iya gwuiwa a jikinta, Haisam na tsaye yana ta kallon abunda take mata fuskar shi a a d'an yamutse sosae yake jin tausayin Fatun, bayan ta gama ta d'ago tana cire safunan tace mashi haihuwa ce amman da d'an saura, sake tambayar ta ya za'ai yayi tace tana ganin abunda yakamata shine su tafi Asibiti yaje ya d'aukko Mota bari ta shirya yace to ya nufi bedside don ya d'aukko makullai, har zai fita Aunty ta tsaida shi ta hanyar tambayar inda kayan haihuwa suke ya dawo ya bud'e mata wardrobe d'in bangon dake cikin d'akin inda kayan suke shirgi guda don ba abunda babu da ya danganci jariri dama tun kafin Mom taje ta taho da ita tuni an gama siyan komai na haihuwar da yawa ma daga Dubai aka siyo su Haisam ma ya taho da wasu trolley guda wanda shida Fanan suka je suka siyo su had'add'un kayan jarirai ne na gaske unisex wato wanda zasu yi ma mace da namiji komai guda biyu aka siya akwae saura ma da Fanan zata taho da su , bayan ya nuna mata ya juya da sauri ya tafi ita kuma ta fara fiddo abubuwan da za'a buk'ata anan kafin ta bud'e wurin kayan Fatuu nan ma ta d'auki abunda zata d'auka, a wata jaka ta zuba komai lokacin ya dawo yace mata ga Motar nan ya kawo bakin Entry tace to, gadon ta nufa yabi bayanta ta kai hannu ta taimaka ma Fatun ta mik'e kallon Haisam tay tace ya d'aukko mata hijab ko gyale da sauri ya furta Ok tare da juyawa, bayan ya kawo Hijab d'in ta zura mata kafin ta nuna mashi jakar kayan data za6a tace ya d'aukko tana rurruke da Fatun suka nufi hanyar fita yana biye da su, sai cije cijen baki Fatuu ke da nishi Aunty nata mata sannu haka ma Haisam, bayan sun shigo cikin parlon ta tuna da itama tana buk'atar mayafi tace ma Haisam ya aje jakar ya kamata suje Mota bari ta d'aukko mayafi, bata jima ba ta fito ta d'auro after dress a saman kayan baccin jikinta bata yi tunanin fad'i ma Mom ba don tasan ba lalle in tana a d'akinta ba, saida ta d'auki jakar sannan ta nufi k'opa lokacin data fita har ya saka Fatuu a bayan Motar shima yana zaune a wurin yana ta faman yi mata sannu, fitowa yayi ya koma gaba Aunty ta shiga baya ta kwantar da Fatun a jikinta yaja Motar da gudu suka nufi hanyar Gate, Basu dad'e sosae ba Saboda gudun da yake shararawa suka iso Asibitin wanda babban private hospital ne kuma sananne, bayan sun shiga yana niyyar nufar parking space Aunty tace suje bakin entrance ya furta Ok ya nufi can, bayan ya parker a bakin kopar shiga cikin Aunty tace tana zuwa ta fito da sauri ta nufi shiga cikin Asibitin shi kuma ya fito ya koma bayan ya rungumo Fatuu a jikinshi yana cigaba da yi mata sannu kai kawai take d'aga mashi, bada dad'ewa ba Aunty ta fito Nurses guda biyu musulma da Christian na biye da ita sun turo Wheel chair Haisam na ganin su ya fito yana k'ok'arin fito da Fatun, bayan an d'aurata suka turata Aunty da Haisam suka rufa masu baya, Labour room suka nufa dama Aunty ta fad'a masu Vip zasu kaita suka nufi can da ita, gaba d'aya harda Haisam suka shiga cikin d'akin aka kwantar da Fatun saman gado bayan Aunty ta cire nata Hijab d'inta itama ta cire after dress dinta, daga gefen kanta Haisam ya zauna ya kama hannunta guda yana cigaba da yi mata sannu Fuskar shi a hautsine, ciwon kaman yasan an zo Asibiti nan ya shiga k'aruwa amman yana yi yana lafa mata in ya lafan har d'an gyangyad'i take, gaba daya Aunty da Nurses d'in biyu na a kanta suma suna ta yi mata sannu sai faman d'aga kai take tana yarfa hannu, in ciwon ya taso sosae hankalin Haisam ke tashi har sai ya lafa sannan hankalin shi ke d'an kwanciya, a haka saida aka shafe Kusan awa bata Haihun ba Haisam sai tambayar Aunty yake ya tak'i haihuwan tace mashi lokacin bai yi bane, sai bayan kamar awa d'aya da rabi sannan ciwon ya taso gaba d'aya daka kalli Fatuu kasan tana cikin Azabar ciwo don a lokacin ko anyi mata sannu bata iya amsawa gaba d'aya ta rurruke Haisam sai murkususu take tana kukan da ba hawaye cikin fitar hayyaci take fad'in "Ya Haisam bazan iya ba....kilan ma Mutuwa zan yi" sosae wannan Maganar tata ta k'ara rud'a shi tsantsar tashin hankali ne bayyane akan fuskar shi tayi wani irin ja fuskar yana ta ce ma Fadin "Pls Baby stop saying that....im here for you ba abunda zai faru in sha Allah zaki haihu lafiya" ganin abun yayi yawa a wurin shi yasa shi mik'ewa tsaye daga bakin gadon still yana ruk'e da hannunta guda, kallon Aunty dake tsaye a gefenta tana k'arfafa mata gwuiwa yayi yace "Aunty this is too much gaskiya, pls kiyi wani abu tana shan wahala da yawa" fuska a yamutse yayi Maganar, idon Aunty na akan Fatun tana mata kallon tausayi tace "bai yi yawa ba Son haka ake yi dama kuma duk abunda yakamata ayi mata an yi so sai mu jira Allah ya sauketa lafiya" wani kalan waro ido yay yace yanzu duk wannan Azabar ciwon da take sha ne da Sauk'i, kai Aunty ta jinjina mashi tace wasu suna spending whole day haka wasu ma 2 days ita kuwa bai fi awa d'aya da rabi da suka zo ba kuma in sha Allahu tana gab da haihuwan, girgiza kai yay idon shi akan Fatuu dake cigaba da murkususun azaba yace gaskiya to in haka ne ayi mata Cs kawai taya Mutum zai jure wannan wahalar, d'an guntun murmushi Aunty tay tare da d'an girgiza kai ta fahimci a wurin shi gani yake hakan sauki ne duk da tabbas in anyi nasarar yin shi lafiya lou yafi sauk'in, kara maimaita mata Maganar ayi mata Cs yayi ta kalle shi cike da jan hankali ta furta "ba sai an mata shi ba zata iya haihuwa da kanta, pls Son You should encourage her instead, wannan Maganganun da kake kana sata tana sarewa and kana anan ne don ka k'arfafa mata gwuiwa so is better if you do dat" d'an yamutsa baki yay jiki a mace yaja k'afa ya koma bakin gadon Aunty tace yayi mata Addu'a ya d'aga mata kai gaba daya rud'ewa tasa ya manta da yayi hakan, lokacin Aunty ta buk'aci amfani da wayarta ta tuna ta baro ta a gida tambayar Haisam tayi wayar shi ya girgiza mata kai alamar bai tare da ita, "Nurse Haleema pls where is your phone?" Aunty ta tambayi d'aya daga cikin nurse d'in cikin girmamawa tace mata tana a station tasa caji tace mata in ba damuwa ta d'an aro mata da sauri tace to, har ta nufi kopar fita Aunty ta dakatar da ita ta tambayi akwae karatun Qur'ani a ciki da sauri tace eh sosae tace to ta kawo mata, bada jimawa ba ta dawo lokacin Haisam nata yi ma Fatun Addu'o'i ya rurruk'e ta, bayan ta kawo wayar Aunty tasa ta kunna karatu tace to, a saman drawer din gadon Fatun aka d'aura wayar karatun ya fara tashi daga Fatiha bayan ta k'are ya shiga baqara Aunty ta tambayi Fatun ta iya surar da ake yi tun kafin ta bada amsa Haisam yace mata eh ta jinjina kai,matsowa tayi ta kai hannu ta dafa goshin Fatun tace mata ta daure su rink'a bi tare ta jinjina mata kai tana ta nishin ciwo idanunta sunyi ja luhu luhu kanta a bud'e manyan kitson da Iya tayi mata guda goma sun bayyana, sosae tayi k'arfin halin bin karatun tana yi tana tsayawa sai kuma taci gaba Aunty ma na bi haka Nurse Haleema, zuciyar Haisam ce ta raya mashi ya tashi yayi sallar Nafila tunda lokacin kar6ar Addu'a ne, yin tunanin yasa shi mik'ewa da sauri Fatuu na ganin tafiya zai yi ta k'ank'ame hannun shi ya juyo ya kalleta cikin muryar wanda ke cikin rad'ad'in ciwo ta fara fad'in "Don Allah Ya Haisam kada ka tafi ka barni....ka tsaya in ma Mutuwa zan yi in mutu a gaban ka don Allah" sosae Maganar tata ta k'aryar mashi da zuciya amman sai yay k'arfin halin komawa ya zauna yasa hannun shi guda yana shafa kanta ta sigar lallashi yace ta daina fad'in hakan ta kwantar da hankalinta in sha Allahu ba abunda zai same ta zata haihu lafiya yanzu so yake yaje yayi salla sai yayi mata Addu'a sosae he's sure in sha Allah Allah zai amsa, shiru tay tana cigaba da nishi yace bari yace ta daure taci gaba da bin karatun ta d'aga mashi kai, mik'ewa yay slowly ya zame hannun shi daga cikin nata ya juya zai tafi Aunty tace mashi yaje Office d'inta sai yayi sallar acan ya d'aga mata kai, har ya kai k'opa idanun Fatuu na akan shi yana kama handle zai bud'e ya dakata ya juyo ya kalleta idanun su suka shiga cikin na juna gaba d'aya abu iri d'aya zuciyoyin su ke ayyana masu, tunda Fatuu ta fara ciwon bata yi k'walla ba sai yanzu suka zubo mata sharr ta fara yamutsa fuska tana kuka still kallonta Haisam ke yi shima kawai sai jin k'walla yay sun zobo mashi a tashi Fuskar da sauri ya juya ya bud'e kopar ya fice, Bayan yaje Office d'in Aunty da yake babbar likita ce a Asibitin toilet ya wuce yayo Alwala, lokacin daya fito a saman kujera yaga prayer mat ya d'aukko ya shimfid'a kafin da k'yar ya samu ya daidaita natsuwar shi ya kabbara sallar, raka'a biyu ya fara yi bayan ya gama ya d'aga hannu yana ma Fatuu Addu'a k'walla na zubo mashi, k'ara tashi yay ya k'ara yin wasu raka'a biyu nan ma yayi mata Addu'a sosae a cikin sujjada bayan ya sallame zaune yayi zugudum yana tunanin ko a wane hali take ciki yanzu gaba d'aya ba cikakkar natsuwa a tare dashi don koda yana sallar halin da ya baro ta kawai yake gani a haka dai yake yi, ji yayi yana son ya koma d'akin don yaga halin da take ciki har ya mik'e wata zuciyar ta bashi ya k'ara yin raka'a biyu Shikenan sai ya koma gaba d'aya, bayan ya kai ta farko ya mik'e yana ta biyu lokacin Nurse Chioma ta fad'o cikin d'akin duk da ba saitin kofa yake kallon ba ya fahimci nurse ce ta shigo don ta gefen idonshi ya hango fararen kayanta, wani irin bugu gaban shi ya shiga yi ba kamar da yake da sauri ta shigo cikin d'akin tsoro da kuma fargabar shigowar tata ne suka cika mashi zuciya har baisan ko yana karatun sallar ma daidai ba a haka dai yaci gaba da yin sallar bai yi tunanin ya yanke ta ba, lokacin daya sallame a tsorace ya juyo ya kalleta kawai sai gani yay ta washe baki ta furta "Sir, Your Wife has deliver....." ai tun kafin ta rufe baki da sauri ya mik'e ya nufo hanyar k'opar saida ta tuna mashi da takalman shi sannan ya juyo ya dawo inda suke maimakon ya saka a k'afafun nashi kawai sai ya kwashe su a hannu ya juyo a haka ya fito daga Office d'in Nurse Chioma na biye dashi saida ta k'ara yi mashi magana tace da ya saka takalman don nan Asibiti ne akwai had'ari tafiya ba takalma sannan ya zubo su k'asa ya saka tare da furta mata thanks kafin yaci gaba da tafiya da saurin da shi bai san ma in ya ta6a yin irin shi ba a rayuwar shi, yana bud'e kopar ya shiga sai kuma yaja ya tsaya turus ido a ware yake kallon Fatuu dake faman jujjuya kai tana nishi da k'arfi tare da cize baki maida idon shi akan Aunty dake a gaban k'afafun Fatuu an lullube tun daga kan cikinta zuwa saman k'afafunta dake a d'age da blue d'in yadi, jiki a sake ya k'arasa gaban gadon cikin d'aurewar kai yace ma Aunty aka ce kuma ta haihu, d'an girgiza kai Aunty tayi tare da d'an murmushi don ta fahimci a rud'e yake kan matar tashi shiyasa har bai ji kukan jaririn daya karad'e cikin d'akin ba, da hannu tay mashi nuni da saitin da Nurse Haleema take tana goge jaririn dake ta faman tsanyara kuka sai lokacin ya dawo cikin hayyacin shi ya tuna da yan biyu ne aka ce a cikin nata, tambayar Aunty yay bata haiho d'ayan bane ba tare data kalle shi ba ta d'aga mashi kai tace gashi nan yana hanya tace yaje wurinta da sauri ya nufi wurin kan Fatun ya zauna tana ta kallon shi tana cigaba da nishi idon ta na d'an lumshewa ya kai hannu ya fara shafa kanta dayan kuma ya kamo hannunta guda yana "Sorry Baby kin kusa haihuwan d'ayan ki daina jin ciwon" kai ta jinjina mashi, bai dad'e da zama ba ta k'ara sautin nishin da take da sauri Aunty ta fara fad'in tay pushing sosae saidai da ta fara yunkurin sai kuma ta bari, hannu Aunty ta d'aga ma Haisam tace ya sata taci gaba da pushing ga Babyn nan nason fitowa aikuwa da sauri ya shiga ce mata "Push Baby..." da tayi sai ta bari tana ta jujjuya kai fuskar shi a yamutse yake ce mata don Allah ta daure tayi Ko babyn ya fito ta huta, a wahalce ta shiga fad'in "Ya Haisam k'arfi na ya k'are wllh....bazan iya ba" da k'yar take Maganar muryarta ta shak'e gaba d'aya ya k'ara rud'ewa ya juyo ya kalli Aunty ya fad'i mata abunda tace Auntyn tace mashi dole sai tayi hakan zata samu ta fito da shi don komawa yake, hannu Haisam ya kai ya ruk'e gaba d'aya shoulder d'in Fatuu yana k'ok'arin daidaita natsuwar shi cikin d'an kwantar da murya yace "listen Baby, I know you're strong so you can do it, nasan ke ba raguwa bace, pls ki daure ki pushing sosae" kai ta d'aga mashi tana nishi ta baki lokacin Aunty ta k'ara cewa tayi Haisam d'in ya hau jinjina mata kai still yana ruk'e da kafadun nata da k'arfi ya furta "push Baby...." ta daddage da iya karfinta na k'arshe tayi wani uban nishi kanta ya d'ago sama can kuma sai ta koma ta fad'a kan gadon yaraf idanunta suka shiga lumshewa a wahalce take fad'in ta gaji bazata iya ba ita dai, juyawa Haisam yay a hautsine yace "Aunty she's completely exhaust........" Bai k'arasa ba sakamakon jaririn da Aunty ta d'ago sama wani irin fari fat dashi jikinshi sam ba wata kazanta sosae Subul dashi gashi k'aton gaske, janye jaririn tay suka had'a ido da Haisam ta d'an tabe mashi baki tare da d'age gira ido waje yake kallon ta da babyn, nurse Chioma ta kira ta mik'a mata shi ta nufi inda d'ayan yake tana washe baki tare da Fad'in "What an Identical twins!" ta k'arasa inda nurse Haleema take nan suka shiga santin jarirai, ganin Aunty na niyyar maida idonta kasan Fatun yasa da sauri Haisam yace mata amman dai su kenan ko d'an girgiza kai tayi da d'an murmushi tace mashi da sauran wasu biyun ya gane wasa take hakan yasa shi yin shiru ya maida idon shi kan Fatuu da idanun ta ke a lumshe ya kai hannu ya rungumota jikinshi ta gefen shi yana mata sannu tare da fadin Shikenan ta haihu zata huta ta d'aga mashi kai, bin ta da ido yay wani irin mugun tausayinta ne ke ratsa mashi zuciya bama ita kad'ai ba gaba d'aya halittar mace tausayin su ya kama shi don yanzu yasan ainihin micece haihuwa, a hankali ya juya ya kallo inda jaririn suke cikin warming bed ana masu weighting and apgar test Aunty ce ke yi Nurse Haleema na rubuta sakamakon da take fad'i mata a jikin wani d'an white board dake a jikin bango, bayan an gama yi ma na farko komai Aunty ta kawo shi ta kwantar dashi rub da ciki a saman k'irjin Fatuu ta kalli Haisam da yayi zuru tana murmushi tace "Wato hankalin ka gaba d'aya yana akan Baby shi yasa ko tambayar abunda muka samu baka yi ba" murmushi yay cikin cool voice d'in shi ya tambayeta ta d'an harare shi tace bazata fad'a ba ya duba da kanshi, saida zata bar wurin sannan tace mashi duka Baby boys ne ya d'aga kai, gaba d'aya suka zuba ma jaririn da ta aje ido Fatuu ta bud'e idanunta sosae tana kallon jaririn da d'an murmushi wata irin k'aunar shi taji tana ratsa mata zuciya a hankali ta d'ago hannu guda ta d'aura a jikin shi ta rungume shi, zuba ma jaririn ido Haisam yay mamaki ne fal a cikin ranshi ta yadda Babyn shi ta haifo yaro haka ya shiga raya dole ta wahala ace daga jikinta ya fito kuma ta d'an wannan opening d'in ya k'ara raya iya wannan kawai ya isa mutum ya jinjina girman Ubangiji, kai jaririn ya fara d'agowa da alama yana jin k'arfi ne don tubarkallah K'ato ne, kallon Haisam yake yana yi yana rufe idon yana d'an lila kan shi Fatuu dake ta kallon shi tana sakin murmushin farinciki ta d'aga ido ta kalli Haisam cikin disasshiyar murya ta furta "He's looking at his Dad" Murmushi shima Haisam d'in yayi tace ya d'auke shi yay d'an shiru gani yake kaman in ya d'auke shi a haka ba kaya zai iya ji mashi ciwo a hankali yace ta bari a saka mashi kaya ta jinjina kai tana dai ta murmushi ita kanta tsantsar mamaki take a cikin ranta na wai wannan d'anta ne ita ta haife shi kuma tare da Haisam, k'ara kallon Haisam tayi tace "Allah ya amsa Addu'a ta kaga Babyn sak kai ne" kai ya d'aga mata don shima yaga Kamannin shi sosae yaron ya d'aukko, Nurse Chioma ce tazo zata d'aukki Babyn don a saka mashi kaya da murmushi ta kalle su ta taya su murna Haisam ne yayi mata godiya ita kuma Fatuu ta jinjina mata kai gaba d'ayan su da murmushi akan fuskokin su tana tafiya Aunty tazo da d'ayan jaririn shima ta d'aura shi a saman k'irjin Fatun tana fad'in gashi nan shima yaji dumin Mom Fatuu ta d'an fad'ad'a murmushin ta a hankali ta kai hannu ta d'ago da fuskar shi da alamun mamaki take kallon shi sai kuma ta d'aga kai ta kalli Haisam da shima fuskar jaririn yake kallo har Aunty zata wuce yace mata wannan ba shine aka d'auka ba yanzu ta d'an girgiza mashi kai tana yar dariya tace d'ayan ne identical twins ne suma sunyi k'ok'arin samun abunda za'a rink'a bambanta su sun kasa Haisam ya d'aga kai ta tafi, shima wanda aka kawon bin shi sukai da kallo suna ta murmushi gaba dayansu wani irin dad'i ne ke ratsa zukatan su ganin jariran, bada jimawa ba aka kawo Hassan d'in an shirya shi cikin set d'in fararen kayan sanyi masu kyaun gaske, Haisam aka mik'a ma shi saida ya gyara zama sannan ya amshe shi aka d'auki d'ayan shima don a shirya shi, shima kayan sanyin aka saka mashi amman nashi light blue ne anyi hakane don a iya bambanta su Aunty ce ta kawo shi tana ta murmushi tace ma Fatuu gashi itama ta d'aukka a hankali tace to ta fara k'ok'arin tashi Haisam yasa hannu guda ya taimaka mata ta zauna ta jingina da kan gadon dake a jikin bango har lokacin kuma rabin jikinta na lullube da blue yadin da aka rufa mata, sai faman washe baki suke gaba d'ayan su suna kallon yaran tsabar farinciki ma sun kasa magana sai dariya kawai suke yaran na d'an bud'e ido a hankali can na hannun Haisam ya fara kai hannu baki yana d'an tsotsa kallon Fatuu yay yace wannan k'ilan yunwa yake ji wane madara ake basu yaje ya samo bata san lokacin da tasa dariya mai d'an sauti ba tace su ai yanzu breast milk ake basu sai bayan wani lokaci ake fara basu Madara ya d'an jinjina kai a hankali yace yasan shi ake basu kawai yayi tunanin akwae wani Madara da za'a iya basu kafin ta warware sosae ta fara feeding nasu ta d'an girgiza mashi kai, dawowa wurin su Aunty tayi itama ta zauna bakin gadon daga wurin kan Fatuu ta d'ayan bangaren kallon Haisam tayi tana murmushi tace mashi yayi masu huduba ne sai lokacin ma shi ya tuna da hakan yace Ok bari yayi ta tambayi to wane suna za'a saka masu yay d'an jimm sai kuma ya juya ya kalli Fatuu da itama kallon nashi take tana son ta ji sunan da zai saka masu ganin haka yasa Aunty cewa bari ta basu wuri sai suji dad'in za6ar masu sunayen bayan ta mik'e tsaye tace ma Haisam sai yayi sauri don lokacin salla ya kusa yace to, dama tun lokacin da Fatun ta haifo na biyun akai kiran sallar farko, "Wane suna kike so a sa masu?' calmly ya tambayeta tana murmushi tace mashi ai shine Baba ko shi yakamata ya zabar masu ya d'an girgiza kai yace ita tafi cancanta ta za6a masu sunan da take so tay d'an jimm kafin tace to shi ya zaba ma d'aya itama haka jin yayi shiru ta kai idanunta da suka shishshige ta kalle shi ta furta "hakan yayi maka?" lumshe mata ido yay tace to wane suna zai za6ar mashi yay d'an shiru kafin yace sunan Dad d'in shi ta jinjina kai tace yayi, tambayar ta yay ita wane suna ta za6ar ma shi tana ta murmushi tace sunan Kakan su Mijin Hajiya yanayin kallon da yake mata ne ya sauya da d'an alamun mamaki yace ita bata so asa mashi sunan Dad d'inta ne tace "ina so, amman dai nafi son asa wanda nace Saboda Hajiya nasan zata ji dad'i sosae" shiru yay yanata kallon ta can taji yace hakan bazai zama son kai ba kuwa har saida tayi yar dariya tace to miye abun son kai ai duk d'aya ne ko kuma sunan Baffan nata ko in ta k'ara haihuwar ba sai asa ba, da mamaki ya furta "zaki k'ara kenan?" shiru tay ta kasa bashi amsa a ranta tana tuna wuyar da tasha wadda yanzu har ta zama labari don bata wani jin ciwo a jikinta saidai rashin k'arfi tana jin ta wani irin fayau daba cikin, ce mashi tayi ai dole ta k'ara tunda yanzu ta fara, "amman dai wahalan yayi yawa gaskiya I think ba sai kin k'ara ba" "Baka son Ya'ya ne?" Amsa ya bata da yana so amman tunda abun akwae wuya sai a hak'ura kawai tana yar dariya tace to ai duk haka ake haihuwan a haka ma ita nata da Sauk'i ya d'an ta6e baki yace haka wai Aunty tace, ce mashi tay yayi masu hudubar ya ce to bayan ya gama ya d'ago tace ko na hannun shi asaka mashi sunan Grandpa din tunda shine babba sai wannan asaka mashi sunan Dad ya d'aga mata kai slowly ya furta hakan yayi, mik'a mata Adam d'in yayi ya d'aukko na jikinta wato Aliyu shima ya fara yi mashi yana gamawa Aunty tazo ta tambayi an saka masu sunan yace mata eh ta tambayi wanda aka saka ya fad'i mata, jinjina kai tayi tace "Ma sha Allah, Allah ubangiji ya raya mana su ya Albarkaci rayuwarsu" Haisam ne ya amsa ita kuma Fatun a cikin rai ta amsa Auntyn ta k'ara cewa "Yakamata a kira gida a sanar masu nasan yanzu tunda Asuba tayi zasu gane bamu nan gashi duk mun taho ba wayoyi" Haisam ne yace mata bari in yayi salla sai yaje gidan ya fad'i tace to, bayan tafiyar Haisam su Nurse Haleema wurin gadon suka zo suka tsatsaya sai faman santin yaran suke gaba d'aya suma sai faman washe baki suke Nurse Chioma tace ita tunda ake haihuwar Twins a Asibitin ba'a ta6a haihuwan wanda suka matuk'ar bata sha'awa ba kaman wannan wllh ji take kaman a bata su kyauta Aunty dake dariya tace ai ga Mom d'in su nan ta tambayeta ta bata da sauri Chiomar tace ita tama fara bayan agabanta akai nak'udar su, Nurse Haleema ma Addu'ar Allah ya bata irin su tayi da sauri Chioma tace aikuwa ba bak'ar fata ba wllh bazata haife su ba ita bak'a bak'a mai d'an hanci Mijinta bak'i hancin shi mai d'an fad'i taya zasu Haifa irin su gaba d'aya aka saka dariya Haleemar ta kai hannu ta 6aketa a shoulder, mik'ewa Aunty tayi tace masu su kai babies d'in d'ayan gadon bari ta taimaka ma Mom dinsu ta tsaftace jikinta duk suka ce to, bayan ta taimaka ma Fatuu ta mik'e rigar jikinta duk ta 6aci da yake mai haske ce Aunty na ruk'e da ita suka nufi toilet wani iri take jin tafiyar ta don ma Allah ya taimake ta ko K'ari ba'a mata ba don Aunty harda Olive oil tayi mata amfani wurin fitowar na farkon. Fitowa Dad yay don tafiya Masallaci saida yaje ya taso su Affan da Mubeen kamar ko yaushe suka tafi, lokacin da suka je parking space yayi tunanin ganin Haisam acan amman sai bai gan shi ba hakan yasa shi cewa su d'an jira shi, bayan d'an wani lokaci yayi tunanin kiran shi saidai har wayar ta yanke bai d'aga ba hakan yasa shi k'ara yin tunanin ko ya riga ya tafi duk da yasan ko yaushe a tare suke tafiya, koda suka je Masallacin basu gan shi a can ba har aka gama sallar suka juyo Dad nata d'an tunanin to ko lafiya Haisam d'in bai je salla ba, lokacin daya shiga Bedroom d'in shi Mom na zaune akan prayer mat bata dad'e data gama sallar ba tana tasbih, zama yay daga gefenta a bakin gado ta juyo ta kalle shi da d'an murmushi ta gaishe shi ya amsa, ganin yayi shiru yana kallon k'asa kaman mai tunanin wani abu yasa ta tambayi Lafiya ya d'ago yace mata Son ne bai je Salla ba kuma yanata kiran layin shi yana shiga bai d'auka ba tace to ko ya makara ne shine yayi sallar a gida, girgiza mata kai yay yace ai tun da zasu je ya kira shi bai d'aga ba sai yayi tunanin ko ya tafi ne to acan ma basu iske shi ba har aka gama sallar kum bai zo ba yanzu bayan sun dawo saida ya k'ara kiran shi tana ta ringing still bai picking ba, "To ko lafiya?" Mom ta fad'a bayan ta d'an yi shiru, ce mata yay shima abunda yake ta tunani kenan, mik'ewa Mom tayi tace bari ta kira Daughter aji da sauri Dad yace yauwa, wurin side drawer ta zauna bayan ta d'auki wayarta ta fara kiran Fatuu, to itama dai har ta yanke ba'a d'aga ba da alamun mamaki ta kalli Dad yace itama bata d'auka ba ta jinjina mashi kai, sake kira tay nan ma dai shiru nan take dad ya hau girgiza kai yana fad'in anya kuwa lafiya Mom da har gabanta ya d'an fara fad'uwa ta mik'e tana fad'in bari taje part d'in nasu shima ya mik'e suka fito tare, a bakin part d'in ya tsaya ita ta shiga ba kowa a parlon ta nufi Bedroom a bakin kopar ta tsaya takai hannu ta fara knocking shiru ba'ai magana ba gashi ta lura da kopar ba'a datse take ba, d'an jimm tay zuciyarta ta fara raya mata abubuwa can dai cike da fargaba ta tura k'opar ta shiga harda yar sallama, tsaye tayi daga bakin kopar tana kallon d'akin da yake wayam ba kowa gashi tsab yake ba wani abu na alamun tashin hankali, tunanin to ina suke ta shiga yi zuciyar ta ta raya mata ta duba toilet ta raya to mi zasu zauna yi a toilet tsawon lokaci duk da haka ta nufi toilet d'in shima knocking tayi shiru ta tura kopar nan ma dai wayam ne, dawowa tayi cikin d'akin har zata nufi kopar fita idanunta suka sauka akan packet d'in gloves dake a yadde saman floor da sauri ta nufi wurin, d'aukko shi tay taga a bude yake ta lek'a tana kallon safunan dake ciki nan take ta shiga tunanin to ko Daughter nakuda ta fara ne sai lokacin ta lura da wayoyinsu d'aya na akan gadon gefen filon d'aya kuma na akan side drawer, da sauri ta fito tana ruk'e da ledar safar, Dad na ganinta ya tambayi ya akai ta nuna mashi tace tana tunanin nakuda ce ta kama Daughter d'in cikin dare k'ilan ko asibiti suka tafi da mamaki Dad yace "Asibiti kuma ba tare da sun fad'a ma kowa ba?" shiru Mom tay yanayin fuskar ta da d'an alamun damuwa can tace to ko da Aunty suka tafi da sauri Dad yace bari ya kirata su ji, to itama dai d'in Wayar har ta yanke ya k'ara kira duk ba'a d'aga ba lokacin gaba d'aya Hankulan su sun tashi da sauri Mom tace bari ta dubo ta a dakinta, lokacin data je d'akin nan ma wayam ne sai wayarta dake a gefen pillow, fitowa Mom tayi ta nufi d'akin Jidderh lokacin bata dad'e da komawa ta kwanta ba bayan tayi sallar Asuba, tura kopar tayi ta shiga ta nufi gadon Jidderh tana kiran sunanta jin kiran Mom d'in yasa ta bud'e fuskarta ta juyo tana kallon ta, tambayar ta tayi tasan ina su Daughter suke ai tana jin haka da sauri ta yunk'ura ta tashi zaune da tsananin mamaki tace "Mom basu nan ne?" Kai ta d'aga mata ta shiga fad'i mata an tashi duk ba'a gan su ba harda Aunty kuma duk wayoyin su na a gida a d'an firgice ta kai hannu ta dafe kirjinta da hannu guda baki bud'e take kallon Mom d'in da itama take ta kallonta can ta juya zata fita aikuwa da sauri ta saukko ta bi bayanta, tsaye sukai cirko cirko bayan ta sanar ma Dad d'in Auntyn ma bata nan da tashin hankali yace to in ma Asibitin suka tafi anya kuwa lafiya zasu yi irin wannan tafiyar Mom tace ita ma abunda ya tada mata hankali kenan jin haka yasa Jidderh ta fara yarfa hannu kaman zatayi kuka tace " Dad bai kamata muna wasting time ba don Allah mu bisu nasan bai wuce Asibitin su Aunty suka tafi tunda da gani suna tare" da sauri ya furta Ok dama jikinshi jallabiya ce Mom kuma akwai Hijab data yi salla Jidderh kuma kayan bacci ne riga da wando sai hula ko tunanin ta koma ta d'aukko mayafi bata yi ba suka nufi hanyar fita dama akwae makullin Motar da su Dad suka je Masallaci a aljihun shi, suna niyyar fita Haisam ya sako kai cikin parlon gaba d'ayan su kaman an latsa masu pause duk suka tsaya cak suna kallon shi atare kuma duk gaban su ya hau fad'uwa, kallon su ya shiga yi da d'an murmushi Mom ce ta fara magana tace "Habiby ina kuka je ne, ina Daughter take?" Kafin ya bata amsa Jidderh tace "Big bro ina sister Fatuu tana lafiya don Allah?" itama tana rufe baki Dad yace "Son, ya zaku fita baku sanar ma da kowa ba kuma duk kun bar phones d'in ku anan miya faru ne ina Daughter?" Yar dariya yayi jin yadda suka jera mashi tambayoyi, fad'i masu yay sunje hospital ne da sauri Mom tace nakuda Daughter d'in ta fara ne yace eh, "To kuma sai ku kama ku tafi ba tare da kun sanar da mutane ba?" Dad ne ya fad'a ya d'an d'aure fuska Haisam d'in yace mashi lokacin sunga duk suna bacci ne shiyasa yana rufe baki Dad ya dalla mashi wata uwar harara da sauri Haisam d'in ya matsa wurin shi yana zuwa ya rungumo shi jikin shi yana sakin k'ayataccen murmushi yace "We're very sorry mun yi laifi amman yanzu time en farinciki ne, guess what?" da sauri Dad d'in ya girgiza mashi kai yadda suka yi sai kace wasu abokai, "Kayi abokai..."tun kafin ya rufe baki Dad ya d'ago shi da sauri kafin yace wani abu Mom ta riga shi fad'in "ta haihu ne??" Kai ya d'aga masu kafin yace eh an samu baby boys yay maganar yana dariya gaba d'aya suka shiga washe baki Jidderh ta saki k'arar farinciki tare da daka tsalle Su Dad suka shiga fad'in Alhamdulillah, Mom ce tace su tafi ta nufi k'opa da sauri gaba d'aya bakinta yak'i rufuwa, juyawa Jidderh tayi da gudu ta nufi d'akin su Yasmeen da Affan ta fad'i masu nan fa suka shiga murna tare duk suka fito lokacin Haisam ya tuna da wayar shi yace bari ya d'aukko, Dad ne yaje ya d'aukko Jeep Mom da Jidderh suka shiga su kuma su Yasmeen da twins suka shiga ta Haisam a tare motocin suka fara tafiya bayan sun sha round suka nufi gate, Bayan Aunty ta taimaka mata ta gyara jikinta sun fito ta d'aukko mata doguwar rigar da ta sako mata cikin kayan ta saka ta d'aura gyalenta, Aunty da kanta ta shirya mata pad a jikin pant d'in da zata saka ta bata ta sa kafin ta bata turare ta fesa bayan ta gama kimtsawa ta haye saman gadon da aka canza mata acan wani bangaren d'akin, juyawa tayi tana kallon babies d'in dake kwance a gefe da murmushi Aunty ma zama tay daga bakin gadon tana kallon su bada jimawa ba Nurse Haleema ta shigo ruk'e da d'an babban tray an d'auro kayan tea da bread a leda da yake a Vip d'in har Abinci ake badawa ta d'aura akan drawer tace ma Aunty gashi nan dama ita tasata taje ta amso bayan ta ajen ta juya ta fita, Aunty ce ta had'a mata kakkauran tea ta bata ta fara sha sosae taji dad'in tea d'in biredin ne take ci kad'an tana cikin sha Aunty tace bari ta amso mata magunguna da in ta gama zata sha tace to, bayan fitar ta juyawa tay tana kallon yaran nata tana sakin k'ayataccen murmushi gaba d'aya har yanzu ganin abun take kamar wasa wai ita ta haife su ita kanta sosae take ganin kyaun yaran sai kace larabawa duk da dai akwai jinin larabawan a jikin su, lips d'in su sak kalar na Haisam wato peach saidai nasu yafi cizawa gashin girar su ma a tsare yake kwance lub gashi bak'i ne sosae komai dai nasu mai ban sha'awa ne, bada jimawa ba Aunty ta dawo lokacin ta gama shan tea din ta bata magungunan tana cikin sha Hassan d'in ya farka yana motsi can ya kai hannun shi dake cikin mitten ya fara tsotsa Aunty dake kallon shi tace "da alama dai grandpa acici ne, tun ana goge shi ya fara mamulan hannu" Fatuu dake yar dariya tace d'azun ma da ta d'aura mata shi saida ya tsotsi hannun har ta fad'i mata abunda Haisam yace na siyo mashi Madara tana dariya tace ina ruwan sabon Baba, ce ma Fatun tay ta fiddo breast d'in aga in milk d'in ya zo tace to, bayan ta fiddo tasata ta matsa ba ruwan sai yellow d'in farko tace ta bashi ya sha ruwan zai zo, koya mata yadda ake ruk'on babyn in za'ai feeding ta shiga yi Fatun nata murmushi yayin da take jin wani iri daya kama sosae yake sha Aunty na mashi tsiya tana fad'in duk da suruki ne ta wani bangaren, suna haka aka tura kopar a tare suka kai idanun su wajen Jidderh ce ta fad'o cikin d'akin da sauri su twins na biye da ita suna ganin su Fatun suka nufo su da d'an gudu gudu daga baya Mom ta shigo Dad da Haisam na biye da ita duk suka nufo gadon, tsaye duk sukai a gaban gadon da sauri Fatuu ta maida breast d'in nata ganin su Dad tuni Jidderh ta d'aukko Hussein su Yasmeen da twins duk suka mik'a ma Fatuu hannu suna yar rige rigen wanda zai amshe shi sai dariya ake ganin d'aya yak'i hak'ura a ba d'aya yasa Aunty saka baki tace su bi a hankali kowa zai d'auka, gaishe da Dad Fatuu tayi yana ta faffad'an murmushi ya amsa tare da Fad'in "Sannu, sannu da kokari Daughter" kai ta jinjina mashi tana ta murmushi Mom ma tayi mata sannu da tambayar jikinta tace lafiya lou, had'a ido sukai da Haisam suka shiga yi ma juna murmushi Mom data k'agara ta d'auki jaririn ta mik'a ma Jidderh hannu tana fad'in tunda ta gani ta kawo, "Ma sha Allah lakuwwata illa billah, Yanzu Daughter da kanki kikai wannan aiki?" Mom ta tambaya idanunta akan Fatuu tay murmushi kawai Aunty tace "ai gaskiya tayi kokari wllh" jinjina kai Mom tayi ta furta sosae kafin tace amman saida aka k'arata wannan ko Aunty tace a'a har saida fuskarta ta nuna mamaki ta shiga k'ara yi ma Fatuu sannu fuskarta d'auke da murmushin farinciki haka Dad ma sannun yake ta ma Fatuu, gaba d'aya kowa tsantsar farinciki ne akan fuskokin su kai kace ba'a ta6a yi masu haihuwa ba duk da dai an d'auki lokaci ba'ayi ba gashi wad'annan ne jikokin Farko, sai faman k'arba k'arba ake tsakanin yaran Jidderh ma sai sannu take ma Fatun, Dad ne ya tambayi an saka masu suna Aunty tace eh ta fad'i mashi har saida ya d'an waro ido alamar mamaki, "Wannan dad'in bai mana yawa ba kuwa?" Dad ya fad'a idon shi akan Haisam dake murmushi ya k'ara fad'in "Son banda son kai fa halan kai ne ka zabi sunan gaba d'aya?" Kai ya d'an girgiza calmly yace shi ne ya za6i nashi ita kuma ta za6i na grandpa, kallon Fatuu Dad yay tana murmushi ya furta "Daughter in akai haka bamu so kan mu da yawa ba kuwa karfa ayi kura da shan bugu gardi da k'wace jaka" gaba d'aya aka saka dariya a hankali tace a'a ai duk d'aya ne duk suka jinjina kai Dad harda yin godiya ya tambayi waye abokin nashi waye kuma Baban nashi duk aka nuna mashi Aunty tace sun kasa gane yadda zasu bambance su shiyasa suka bambanta masu kaya dama fin set biyu ta d'aukko wai ko zata haifi fin biyun duk akai dariya, jin haka yasa Momy ta fara k'ok'arin duba su taga ko zata samu abunda za'a rink'a Gane su, tunawa tayi da yadda ake gane ta ita da Mom d'in Sameer hakan yasa ta k'ura ma na hannun Dad wanda ta bashi wato Aliyu ido tana kallon idon shi dake a bud'e dama tunda Jidderh ta sunkuce shi yana bacci ya farka sosae ta k'ura ma idon nashi ido harda d'an bud'awa taga k'wayar bata ciza ba sosae ta d'an yi brown, juyawa tay kan d'ayan dake a hannun Affan shima ta shiga dubawa sai gashi tashi bak'a ce wuluk tana ganin haka ta d'ago tana dariya ta fad'i masu suma ga yadda za'a rink'a bambanta su duk saida suka ji mamaki ganin abu yazo d'aya suka shiga fad'in ikon Allah, Addu'oi Dad duk yayi masu bayan ya gama ya tambayi an fad'i ma su Hajiya Aunty tace a'a Saboda ba waya yace Ok bari ya sanar mata, Lokacin da kiran ya shiga bata dad'e da tashi daga kan abun salla ba ta koma ta kwanta bayan ta d'auka cikin girmamawa ya gaida ta tare da tambayar yadda take tace mashi Alhamdulillah kafin ta ce kiran sassafe mai tattare da abu biyu Alkhairi ko akasin haka tana fatan Alkhairin ne yasa aka kirata Dad dake dariyar Maganar tata yace eh Alkhairi ne dama zai sanar mata ne tayi Ya'ya yan samari amman d'aya a ciki kuma miji ne Daughter tayi mata tana jin haka ta fahimci zancen, cikin washe baki ta hau fad'in ma sha Allah Fateema Allah yayi an sauka kenan, tambayar lokacin da akai haihuwar tayi ya fad'i mata yace gasu ma a Asibitin ko sallamarta ba'a kai ga yi ba ta kara tambayar to ya jikinta nan ma yace lafiya lou take bari ya bata ya mik'a ma Fatun cikin murmushi ta gaishe da Hajiya tace "Fateema yau ai ni ya kamata in yi gaisuwa nida aka Haifa ma sabon miji, to barka, barkanmu da Arzik'i Fateema, sannu da k'ok'ari Allah ya k'ara maki lafiya ya raya mana ya kuma Albarkaci rayuwarsu" kaman bazata amsa ba sai kuma can k'asan mak'oshi ta amsa Kafin ta tambayi yaushe zata taho tace ai don yau ta riga tayi da ta taho amman gobe in sha Allahu tana nan tafe ai bata zauna ba wannan abun Arzik'in ya samu, bayan sun gama wayar tana niyyar mik'a ma Dad Jidderh tayi karaf ta amsa ko gaida Hajiyar bata yi ba ta hau zuzuta mata kyaun jariran da kuma girman su Hajiyar nata fad'in Ma sha Allah Tubarkallah kafin a k'agare tace mata tayo mata Vedion su yanzun nan ta gani da sauri tace to, bayan Hajiya ta gama wayar Gwaggo ta shiga kira lokacin itama bata dad'e da komawa ta kwanta ba wayar ta fara ringing koda ta d'aukko ganin mai kiran saida gabanta ya d'an fad'i, d'auka tayi da sallama Hajiya ta amsa tun kafin gwaggon ta k'ara cewa wani abu tace "to barkan mu da Arzuki Fateema dai Allah yayi ta sauka lafiya an samu yan samari" ba shiri gwaggo ta tashi zaune cikin washe baki take ta fad'in Alhamdulillah daga baya tayi Addu'ar Allah ya raya ya Albarkace su Hajiya ta amsa tace ai ita gobe in Allah ya kaimu ma zata tafi don harda maigida a ciki ta fad'i mata sunayen su Gwaggo tace ah lallai yakamata ta tafi da wuri ta tarbi sabon maigida tayi Maganar tana dariya, suna gama wayar ta fito ta nufi d'akin Mino har ta koma bacci tsabar farinciki ta tasheta ta fad'i mata zo kaga murna don wani kalan wuntsilowa tayi daga kan gado ta duk'a k'asa tayi sujjadar godiya ga Allah don kullum damuwarta itace yadda Adda Fatuu zata haihu, da gudu ta fito ta nufi d'akin Kawu Amadu shima har ya koma bacci ta fad'a d'akin tana faman kwad'a mashi kira aikuwa a fusace ya farka don tunda ta fara kiran nashi yana ji yayi shiru sai daga baya ya farka har zai rufeta da fad'a dama suna yawan haka duk aka aikota ta tashe shi ko kuma wata buk'ata tata kamar in tana son yayi mata Assignment, da sauri ta tari hanzarin shi cikin tsananin murna ta fad'i mashi Adda Fatuu ta haihu yan biyu duk maza nan take ya waro ido sai kuma ya washe baki, Bayan Hajiya ta kira gwaggo Hajiya Maryam ta shiga kira bayan ta d'aga ta gaishe da ita ta amsa kafin tace to tayi Ya'ya harda sabon maigida a ciki da rashin fahimta ta tambayi wani ya'ya ta fad'i mata itama ta nuna farincikinta ta yi Allah ya raya masu, lokacin da Haisam ya kira Fanan ya sanar mata Kusan suk'ewa tayi don dad'i tace miyasa da ana labour d'in bai kirata ba sunyi tare yace mata ya rud'e ne, sawa tayi ya maida kiran Vedio call lokacin da taga yaran sai kawai ta fashe da kukan dadi baiwar Allah bata da burin daya wuce ta haifi yaro mai kama da Haisam ashe ba itace mai rabon hakan ba ta raya a ranta saidai sosae take farinciki don tana da yak'inin yaran zasu zama tamkar nata, gaba d'aya saida su Dad sukai mata barka ta cikin wayar tana ta washe baki take amsawa, kan kace mi duk an kira yan'uwa da Abokan Arzik'i an sanar dasu game da haihuwar anata ba Fatuu suna mata barka a haka ma don Wayarta bata a hannun ta, lokacin da gwaggo ta kira Aunty Mareeya ta sanar mata Fauzy na cikin yin shirin Makaranta Aunty tazo d'akin nata cikin tsananin farinciki ta sanar mata har saida ta daka wani uban tsallan murna tana ta faman fad'in Wayyo Allah da Alhamdulillah, kiran layin Fatun suka shiga yi ba'a d'aga ba Aunty tace k'ilan bata tare da wayar ne gaba d'aya Fauzy a k'agare take da suyi magana Haisam ya fad'o mata a rai gashi kuma bata da lambar wayarta shi tunowa tayi da tana da Lambar Jidderh to itama data kira ba'a d'aga ba don ta bar wayarta a gida,, zuciyar ta ce ta bata ta kira Sameer sai ta tambaye shi lambar Haisam d'in, bayan ta kira saida ta yanke sannan ya kirata, gaida shi tayi kafin tace mashi don Allah lambar Haisam take so farko shiru ya d'an yi sai kuma taji ya tambayi mi zatai da shi a tunanin ta yasan da haihuwar tace mashi tanata kiran layin matar shi ne tayi mata barka to bai shiga shine take son ta kira shi sai ya bata, tambayarta yayi barkan mi zata ma wife en nashi nan ta gane bai san da haihuwar ba ta fad'i mashi yace bai sani ba Allah ya raya, karanto mata lambar yay tayi mashi godiya suna gama wayar ya kira Haisam d'in bayan ya d'aga sun gaisa Sameer d'in yace mashi tunda shi bai so yasan sun yi babies yaji wani wuri Haisam d'in na dariya ya bashi hak'uri yace baya tare da wayarshi ne bai dad'e da ya d'aukko ta daga gida ba ya tambayi ina yaje ya sanar mashi suna hospital ne yace Ok, tambayar lafiyar yaran da Mom d'in su yay Haisam d'in yace mashi duk suna cikin k'oshin lafiya bari ya maida Vedio call ya ga babies d'in nan ma Ok yace, bayan ya maida kiran Vedio nuna mashi yaran ya shiga yi Sameer na kallon shi yanayin fuskar shi da d'an murmushi daga baya yaba Fatuu suka gaisa yay mata barka, bayan Haisam ya amsa Sameer d'in na wani murmushin gefen baki yace Babies d'in sun bayyana he's very active shiyasa sukai Kamannin shi Haisam d'in yay murmushi kawai don su Mom na wurin gudun kada ya k'ara fad'in wata Maganar yasa shi saurin ce mashi ga su Mom yayi masu barka, suna gama yin wayar da Sameer kiran Fauzy na shigowa Haisam ne ya d'auka bayan sun gaisa tayi mashi barka sannan ta fad'i mashi ko wacece ya mik'a ma Fatuu, cikin tsananin farinciki suka yi mata barka harda Aunty suma harda Vedio call suka ga yaran lokacin da Fauzy ta gansu murna kamar kamar me, haka dai akaita yin waya dasu ta wayar Haisam d'in har su gwaggo suma ta nan suka kira, bayan kiraye kirayen wayar sun lafa Dad yace ma su Yasmeen su tashi ya tafi dasu suyi shirin School tun kafin ya rufe baki Mubeen da Mubeena suka tur6une fuska cikin shagwaba suka hau rok'on a k'yale su yau ba sai sunje ba suna Welcoming Babies d'in su Mom tace to ba Babies na nan ba ko sun dawo zasu gansu, da k'yar suka tashi zasu bi shi Jidderh ma ta mik'e zata bi su don akwae abunda take son yi a gidan kafin a sallamo Fatuu, bayan tafiyar su Mom tace bari ta kira Iya a d'aura ruwa Aunty tace a'a tana ganin ba sai anyi wannan ba don bp d'in Fatun ya d'an hau so bata buk'atar ruwan zafi sosae yanzu lafiya lou in sun koma zata iya amfani da na heater zuwa bp d'in ya daidai ta duk da haka ba ruwa masu zafi zata rink'a amfani dasu ba Mom tace Ok kafin cike da kulawa ta kalli Fatuu tace maijego mi take son a dafa mata ne Fatun tayi murmushi kawai gaba d'aya idanunsu na akanta harda Haisam wani irin son ta ne ke mashi yawa a jini jiki, Aunty ce tace a yanzu dai ai tasan zata fi buk'atar farfesu tace ma Fatun hakane ko Daughter ta d'aga mata kai still da murmushi a fuskar tata, masu aikin girkin gidan Mom ta kira ta basu umarnin kalolin farfesun da zasu yi.......... _Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268 94 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ ...........Wuraren k'arfe sha d'aya na safe aka sallami Fatuu saida Haisam yay ma su Nurse Haleema kyautar kowa dubu hamsin, a bayan Mota ta zauna ita da Aunty sai Mom ta zauna a gaba tana ruk'e da Adam Aunty kuma tana ruk'e da Aliyu, lokacin da suka iso gidan a bakin Entry Hall ya parker Motar duk suka bubbud'a kopopin suka fito, suna fitowa Iya ta fito daga cikin gidan ta nufo su cikin washe baki tana masu sannu da zuwa ta nufi Fatuu ta rungume ta tana fad'in "Barkan mu, Barkan mu yar gidan Iya, barka da Arzik'i" dariya Fatuu ke yi ta d'agota tana k'ara mata sannu da tambayar jikinta tace mata Alhamdulillah, juyawa tay kan Haisam daya zagayo hannun shi ruk'e da Jaka tayi mashi barka shima fuskar shi a sake ya amsa ta juya kan su Mom suma tana masu barkan duk suka amsa ta amshi jaririn hannun Aunty duk suka nufi shiga cikin gidan lokacin Dad ya fito cikin Fara'a yake masu sannu da zuwa shima ya amshi jaririn hannun Mom suka wuce, parlon tsaf dashi yasha gyara sai k'amshi ke tashi suka nufi part d'in su Fatuu, suna shiga cikin parlon Jidderh ta tarbesu cikin washe baki ta rungumo Fatuu tana k'ara mata sannu itama murmushi take mata, bayan sun shiga cikin parlon shima dai yasha gyara hatta labulaye an canza sai k'amshi yake tashi, ganin zasu zauna a cikin parlon yasa da sauri Jidderh tace ba anan zasu zauna ba pls su shiga ciki Mom ta tambayi Saboda mi tace Saboda Sis Fatuu ta kwanta ta huta suma babies d'in ta gyara masu gadon su a kwantar dasu suji d'umi duk sukai murmushi suka nufi cikin harda Dad da Haisam ta matsa mawa saida suka shiga, a tare duk sukai tsaye cakk bayan sun shiga suna k'are ma d'akin kallo daya canza suffa yasha decorations daya danganci jarirai irin su Baby photo frames da wall decals an mammanna su a wurare daban daban masu k'ayatarwa wasu hotunan bishiyu ne wasu flowers suna ta sakin k'yalli harda masu yin haske kala daban daban hatta gadon d'akin ma yasha gyara an shimfida sabon bedsheet milk a saman shi an watsa jajayen Flowers suma labulayen d'akin an canza su, daga jikin bangon da kan gadon yake wani Wall decal ne mai kaman d'an allo anyi mashi shape mai kyau jikin shi na d'auke da rubutu kamar haka _"Welcome to the world, little ones. May your life be filled with love, laughter and light. We love you"_ gaba d'aya yanayin d'akin yayi kaman nursery sai dai komai ya tsaru ba'a cika ba, gaban su Jidderh tazo tana murmushi tace ya suka ga decorations d'in gaba d'ayansu suka hau yabawa fuskokin su d'auke da faffad'an murmushi kowa ya hau yaba mata ana fad'in tayi k'ok'ari Dad yace Saboda wannan abun da tayi ko gaba da Dubai take son zuwa K'arin Karatu zai kai ta, jin haka da sauri ta nufo shi tay mashi side hug Saboda jaririn da yake ruk'e da shi tace "That's why I'm always proud of you lovely Dad, You're a Father like no other" fad'ad'a murmushin shi yay yayi pecking saman kanta tare da Fad'in shima yana Alfahari da ita a koda yaushe, sakin shi tay ta koma kan Haisam tana fad'in big brother ya kaga decorations d'in shima yaba mata yay ya jawota yay hugging nata, Aunty ce ta tambayi zasu iya zama a kan gadon ko su kwashe flowers d'in duk akai dariya Jidderh tace a'a a haka zasu hau su zauna Mom tace ma Fatuu ta hau suma duk suka zauna a baki, Addu'a Dad ya k'ara yi masu yayi ma Fatuu sannu Fuskar shi cike da annuri ya mik'a ma Mom shi kafin ya tafi Haisam kuma ya nufi kan bedside ya zauna, Iya dake ta faman washe baki ta mik'a ma Aunty na hannunta tana fad'in bari taje ta kwaso ruwan wanka dama tunda su Jidderh suka dawo taji an haihun ta d'aura tuni ma ya tafasa Aunty ta kar6i babyn tana fad'in anya wankan nan bata buk'atar ruwa masu zafi sosae Iya tace to lafiya lou sai a bari su sha iska sosae tunda akwae magunguna da zasu k'ara mata lafiya da ruwan nono a ciki yakamata tayi wankan dasu Auntyn tace mata to ta juya da sauri ta nufi hanyar fita, gaba d'aya Mom da Aunty da Jidderh idanun su na akan Babies suna ta kallon su suna sakin murmushin dadi yayin da Haisam da Fatuu keta kallon juna suna murmushi can Mom ta d'ago ta kalle shi tace "New Dad ya gajiyan labour" murmushi kawai yayi Aunty da itama ta d'ago tana murmushin tace "aikuwa kam ansha labour harda su Kuka" waro ido Mom tayi "kice labour d'in koke koke akai kenan", yar dariya Aunty tay "eh to ba sosae ba ya d'an yi hawayen tsoron kada ya rasa Babyn shi" dariya Mom ta saka haka Auntyn da Jidderh ma Haisam d'in ma ya d'an fad'ad'a murmushin shi Fatuu kuwa da sauri ta sunnar da kanta tana murmushin jin kunya, kallonta Mom tayi tana fad'in ai gaskiya tayi kokari sosae wllh angode ma Allah daya sauketa lafiya ba wata matsala gaba d'aya suka jinjina kai Mom d'in ta tambayeta bata jin wani ciwo sai lokacin ta d'ago da murmushi akan Fuskar ta tace mata eh kawai jikinne take jin shi wani iri tace mata ai wannan dama dole ne tunda yara fa har biyu suka fita daga jikin nata a hankali zata ji ta koma normal ta d'aga mata kai, masu aikin Abincin gidanne mutum biyu suka shigo kowanne na sanye da apron bayan sun gaishe da su suka yi masu barka Aunty ta nuna masu bakin gado tace su zauna, bayan sun zauna aka basu jariran nan fa suka shiga yabawa fuskar kowannen su d'auke da Murmushi, tambayar su Mom tayi sun gama aikin data sasu a tare suka amsa da eh tace Ok in sun koma sai su kawo shi nan cikin girmamawa suka amsa mata da to, Iya ce ta fara shigowa da ruwan wankan ta wuce toilet, bayan ta gama ta tambayi Mom ta fara yi ma jariran ne tace a'a bari ita tayi masu ta kawo mata ruwan tace to, bayan ta kawo tace ma Aunty ga ruwan Fatuu can ta kai toilet tace to suje sai ta taimaka mata tayi wankan ta amsa da to, tambayar dami za'ai wankan tayi Aunty tace mata towel Jidderh ta mik'e da sauri tana fad'in bari ta d'aukko mata Mom ma tace ta had'o da kayan wankan babies d'in, kallon Fatuu Iya tayi tace to suje ayi wankan tace to ta fara k'ok'arin saukkowa daga saman gadon lokacin Jidderh ta kawo towel d'in k'arami da babba Iya ta amsa suka wuce toilet. Gaba d'aya idanun su harda Haisam na akan Babyn da Mom ta fara yi ma wanka sai tsanyara kuka yake Aunty na fad'in "haba grandpa yada kukan wanka kai fa babba ne" gaba d'aya suna ta dariya kawai sai ji sukai Fatuu ta saki k'ara itama daga cikin toilet d'in da sauri suka kai idanunsu kan kopar toilet d'in dake a rufe cikin d'an d'aga murya Aunty ta k'wala ma Iya kira daga ciki ta amsa tace mata Lafiya, bud'e kopar tayi ta lek'o tana yar dariya Aunty tace badai cika mata ruwan zafin akai ba ko Iya tace "Wllh Aunty basu da wani zafi daidai daidai ne tunda kince kar a cika" kai ta jinjina mata tace Ok hakan yayi kafin ta k'ara cewa asata ta zauna ruwan sosae tace to ta koma ciki, Mom dake yar dariya tace sai a k'yale grandpa yay kukan shi tunda ga maman shi can itama tana yi duk sukai dariya, mik'ewa Haisam yayi yana murmushi yace bari yaje Aunty dake kallon shi tace shima tunda Angon jegon ne ya tsaya yay wankan, yar dariya yay har hak'oran shi suka bayyana Mom tace "gaskiya kam haka yakamata tunda ya taya nak'uda wankan ma sai ayi tayi" still dariyar yake bai dai ce komai ba yay masu sallama ya tafi, bayan angama ma Fatuu tana d'aure da Towel ta fito ta yafo gyalen rigar ta a kai duk su Aunty suka kalleta suna mata sannu tana d'an murmushi ta amsa ta nufi gadon ta zauna Jidderh ta mik'e don ta d'aukko mata kayan shafa, bayan Mom ta gama yima jariran wanka Iya ta fidda ruwan ta dawo da garwashin gashin cibiya Aunty tace ai tayi zaton za'a basu magani ne kawai Iya tace gashin yafi, bayan Fatuu ta gama shafa mai tasa Jidderh ta d'aukko mata kayan da zata saka sabuwar doguwar rigar lace ce Jidderh tace bari tayi mata makeup tunda ita amaryar jego ce duk aka yi murmushi, yar light makeup tayi mata ta d'aura mata kallabi sai gata ta fito a Amaryar jego sosae tayi kyau tana ta sakin kamshi su Mom ma duk suka yaba kwalliyar lokacin Iya ta gama gashin Aunty ta fara shirya jariran, Mom da kanta ta zuba ma Fatuu Farfesun da aka kawo Kusan kala hud'u akwae na yan ciki dana kaza sai na kifi da kuma na nama mai had'e da ganda gaba d'aya sunyi gwanin kyau a ido sai sakin kamshi suke a ido kawai kasan zasu yi dad'i, kowanne saida ta zuba mata taci ta k'oshi suma suka ci har Haisam ma aka zuba mawa Jidderh ta kai mashi, bayan sallar Azahar aka fara zuwa barka haka ta waya ma anata kiran Fatun ana mata barka har su gwaggo ma sun k'ara yin waya harda Vedio call suka ga yaran kowa sai farinciki yake. Da daddare bayan sallar isha gaba d'aya yan gidan harda Dad nan part d'in su Fatun suka zo lokacin tuni sunyi wanka tun da yamma Fatuu na sanye da doguwar rigar Atamfa haka yaran ma anshirya su cikin set na Overall ash sai hira ake kan su ana nishadi, anan falon nasu aka ci Abincin dare sai wuraren k'arfe goma sannan Mom tasa su Yasmeen suje su kwanta Saboda zuwa school da safe itama dasu Dad duk sukai ma su Fatuu saida safe ganin Jidderh bata tashi ba yasa Mom ce mata mi take jira ta tashi su tafe sai Allah ya kaimu kuma a dasa zaman jegon cikin yar shagwaba tace ita anan zata kwana, wani kallo Mom tayi mata tace to shi Habibyn ya kwana a ina da sauri tace ba ga part d'in shi can sama ba ita kuma sai ta kwana ta taya Fatuu raino Mom tace to bazata kwana ba in don raino ne shi ya tayata, "wayyo Mom don Allah ki barni in kwana wllh banson in yi nisa da y'ay'ana, kuma ai da ana da cikin su nima ba a dakina take kwana ba to nima yanzu zan rama ma k'ura aniyarta ne" dariya Mom tayi tace wannan kuma ai ita tasa kanta ko, dole Mom tasata ta mik'e tace daga baya ta kwana amman yau ta k'yale su suyi rainon babies d'in su da kan su tana tura baki ta bita bayan sunyi masu saida safe, babba babba ne wato da alama Mom ta fahimci Haisam d'in na buk'atar ke6ewa da matar shi ko kuma tasan zai so hakan don tun bayan da aka sallamo ta d'akin bai kasance ba mutane ba, bayan fitar su Mom bin juna sukai da kallo suna murmushi ita dashi yana zaune akan side drawer jikin shi sanye da farin voile, mik'ewa yay ya nufi gadon ya zauna daga baki gefen Fatun still da murmushi akan fuskokin su cikin cool voice d'in shi ya furta "Mai jego" dariya Fatun tay kafin tace "Na'am Angon jego" shima dariyar yayi ya maida idanun shi kan jariran dake a nad'e suna bacci asaman gadon itama kai idonta tayi kan su suka cigaba da kallon su a tare kowa dad'i ya cika mashi ranshi can Haisam d'in yay sigh ya furta "I'm forever grateful ya Rabbi" yana rufe baki Fatuu ta furta "We're forever grateful our perfect Rabb" jinjina mata kai kafin ya k'arasa hayewa saman gadon ya kai hannu ya jawota jikinshi ya d'aura habarshi a saman kanta sukai shiru suna ta sakin k'ayataccen murmushi, a hankali taji ya tambayi ya jikinta ta bashi amsa da ba abunda ke mata ciwo ya d'aga kai, shiru sukai kowa yana jin sabon son dan'uwan shi na ratsa zuciyoyin su can ta d'aga kai ta kalle shi ta tambayi yaushe Aunty Fanan zata zo ya bata amsa da jibi ta jinjina kai, kasa janye idonta tayi suka zuba ma juna ido breathing dinsu na had'uwa, sun d'an d'auki lokaci a haka can ta hura mashi iska a ido ya d'an kikkafta idanun ta saki dariya shima yar dariyar yayi ya k'ara matseta a jikin shi tare da furta "I Love You Baby, I don't even know how to tell you how much I love you" d'aga ido tay ta kalle shi tare da kashe mashi ido d'aya cikin wani irin salo ta furta "I can't get enough of Your love Hubby" tana rufe baki kawai sai gani tay ya had'e lips d'in su, da alama dai Fatuu har ta manta da nakudar da tayi shiyasa ta biye mashi, sun d'an d'auki lokaci a haka kukan jaririn daya karad'e d'akin ne ya dawo dasu hayyacin su da sauri suka saki juna suna dariya Fatun nata fad'in yanzu fa bashi kad'ai keda lokacin ta ba ya k'ara fad'ad'a dariyar tashi, Adam ne ya farka yana kukan tare da kai hannu baki yana tsotsa alamar yunwa yake ji, daukko shi tay ta shiga kiciniyar feeding nashi ganin haka yasa Haisam cewa ko ya taimaka mata tace eh ya kai hannu ya ruk'e mata shi, nursing pillow dake a ajiye gefe da d'azun tayi amfani dashi ta d'auko har ta iya yadda Aunty ta nuna mata bayan ta daidaita shi ta fara feeding d'in nashi sosae ya kama yana sha Haisam yay k'uri yana kallon shi can ya kalli Fatuu da alamun mamaki yace k'arami dashi yana shan abu haka ta saka dariya ta shiga bashi labarin yadda tun a Asibiti ya fara sha da tsiyar da Aunty tayi mashi, yana cikin sha d'ayan ma ya farka yana kuka Haisam ya tambayeta shima ko yunwa yake ji tace k'ilan yace to yanzu ya za'ai ga wannan na sha yadda yay Maganar har saida ya bata dariya tace ya d'auke shi wannan ya gama yace Ok ya k'arasa hayewa gadon ya d'aukko shi, yana d'aukar shi yayi shiru ya shiga mamular hannu idanunshi ya bud'e su sosae yana kallon Fuskar Haisam da shima kallon shi yake yana mashi murmushi, saida Adam d'in ya gama suka yi musaya ta amshi Aliyun, ganin yadda shima yake sha sosae yasa Haisam d'in ce mata anya zata iya shayar dasu duka kuwa, tana dariya tace mi zai hana ba ita ta haife su ba yace to amman in suna sha haka ai zata rame sosae tace a'a indai tana ci tana k'oshi lafiya lou, shima saida ya k'oshi sannan ta cire shi bayan ta goge mashi bakin shi da d'an towel mai taushi ta fara kokarin canza masu diaper d'in jikinsu kamar yadda Aunty tace kar ta bari su kwana dasu, koda ta cire basuyi komai ba dama ruwan zamzam ake basu amman duk da haka saida ta canza komai da zata buk'ata na daga gefenta cikin dresser dinsu mai kyau, bayan duk ta canza masu ta feshe su da turaren su ta maida komai, ganin ta kwantar dasu a kan gadon yasa Haisam ce mata ba ga gadonsu nan ba tace tunda dare ne gara ta kwantar dasu nan koda zasu tashi da daddare yace Ok, gaba d'aya bin yaran sukai da kallo suna masu murmushi su kuma duk sun k'ura masu ido sai kace sun san su waye su abun gwanin sha'awa, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin Haisam ya kalleta yace yasan bata rasa jin yunwa ko tace a'a bata jin wata yunwa ai taci Abinci sosae da daddaren nan kawai tea take so zata had'a tunda ga kayan nan yace Ok bari ya had'a mata ya tashi tana ta kallon shi da murmushi ta furta "You're the best husband ever" k'ayataccen murmushi ya saki tare da furta mata thanks, tea mai k'auri ya had'o mata da kanshi ya rink'a bata tana sha bayan ta gama shima ta matsa mashi saida ya had'a duk da yace mata a k'oshe yake, bayan sun gama ya tambayeta akwae abunda zai taimaka mata yana son yay wanka tace a'a yaje yayi kaya kawai zata canza, a tunaninta a nan zai wankan sai taga ya nufi k'opa yace mata bari yaje sama yayi sai ya dawo tace to, bayan fitar shi mik'ewa tayi har zata tafi ta tuna wani abu ta koma kan gadon, Addu'oi ta shiga yi masu tana tofa masu Adam har ya koma bacci sai Aliyu ne idon shi biyu tana murmushi tace mashi Mom zata je tayi shirin kwanciya ta dawo sai kace yana gane abunda ta fad'a yay mata k'uri da ido, wurin kayanta ta nufa ta fara cire kayan jikinta bayan ta gama ta d'aura towel saida ta dauki pad da pant da zata canza sannan ta nufi toilet bayan ta yafa gyale a saman kanta, bata jima sosae ba ta fito ta koma wurin kayanta, shiryawa tay cikin bakar nursing nightgown ta d'aura brown robe a sama ta saka hula akanta bayan ta gama shiryawa ta nufi gaban mirror kallon kanta ta shiga yi tana fesa turare a cikin ranta take raya wai yanzu nan ita mai jego ce tana ta murmushi har ta gama ta juya ta nufi gado shima d'ayan har ya koma baccin, hayewa tay taja duvet ta lullube su tare da kai hannu ta rungumosu su duka, bayan wasu mintuna sai gashi ya dawo shima yayi shirin kwanciya sai zuba k'amshi yake, saida ya rufe k'opar d'akin sannan ya nufi gadon ta d'ago tana kallon shi ya kunna lamp kafin ya nufi switch ya kashe hasken d'akin sannan ya nufi gadon, ta d'ayan bangaren ya hau ya fara yin Addu'a bayan ya gama ya d'an tufa bangaren su Fatun da jikinshi sannan ya kwanta yana facing Fatun ta d'an hasken da ke akwai ya hangota tana mashi murmushi shima ya fara yi mata daga baya bacci ya kwashe su. Washe gari talata bayan la'asar Hajiya ta iso, Haisam ne yaje ya d'aukko ta a Airport, bayan sun iso gidan gaba d'aya duk suna a part d'in mai jego Hajiya ta nufi can shi kuma Haisam ya nufi part d'inta don ya kai mata kayanta, suna zaune a falo harda mai jego har sunyi wankan yamma tana sanye da half gown ta sabuwar atamfa golden tayi yar kwalliyarta ta fito fess haka yaran ma duk anyi masu wanka an saka masu kaya iri daya light blue abun saidai ace Masha Allah d'aya na hannun k'awar Mom da tazo barka d'ayan kuma na a hannun d'iyarta wadda k'awar Jidderh ce dama tun d'azun aketa zuwa barka harda Abokan Dad ba'a ma dad'e da maido yaran ba daga part d'in Dad d'in harda kyautar kud'i aka yi masu, Hajiya na yin sallama gaba d'aya su twins dasu Yasmeen suka nufota da gudu suna fad'in "Oyoyo Granny" duk suka k'ank'ame ta Jidderh ma ta taso ta nufota tana mata Oyoyo, Hajiyar na dariya tace ma su Twins sai sun karyata tun bata ga sabon angon nata ba salon yace bai sonta duk suka d'ago suna dariya tace su shiga ciki, mik'ewa Mom da Aunty sukai suna mata sannu da zuwa tana amsawa ta nufi kujera ta zauna su twins d'in ma duk suka zauna a kusa da ita sun shishshige mata, zama su Aunty sukai suka shiga gaishe da ita tare da yi mata an zo lafiya K'awar Aunty ma ta gaishe da ita tare da yi mata anzo lafiya haka d'iyarta ma, Mom ce ta amso Babyn hannun Friend d'in tata ta kawo ma Hajiya Jidderh kuma ta amso na hannun d'iyar matar k'awarta ta zo gefen Hajiya dashi tana nuna mata, bin su da kallo Hajiya tay fuskarta d'auke da fara'a ta shiga fad'in Ma sha Allah, mik'ewa K'awar Mom tayi tay masu sallama tare da yi ma Hajiya barka suka tafi Mom ta rakasu, juyawa Hajiya tayi ta kalli Fatuu dake d'an murmushi tace "Sannu da kokari Fateema, sannu kin dai yi aiki ba kad'an ba wllh yara haka Tubarkallah, to Allah ubangiji ya raya mana ya Albarkaci rayuwar su kema ya k'ara maki lafiyar shayarwa" gaba d'aya harda su twins suka had'a baki wurin amsawa da Amin, "To ni bansan wanene sabon Angon ba bansan waye kuma d'an ba a cikin su a bambance man" Hajiya ta fad'a da fara'a, gaba d'aya su Jidderh suka zuba masu ido suna kokarin bambanta mata saidai duk sun kasa Saboda duk bacci jariran ke yi balle su bambance su ta ido sai faman canki canka suke abun ma sai ya zama abun nishad'i Aunty nata dariya don ita tasan kowanne Saboda tare da Mom suka kaisu wurin Dad haka lokacin da za'a maido su ita Dad ya kira taje ta amso su tare da Yasmeen lokacin Jidderh bata a d'akin tun lokacin ta ruk'e Adam aka ba k'awar Mom sai d'iyarta aka bata Aliyun, ita kanta Yasmeen da suka amso su tare duk ta rud'e ta kasa bambanta su, Hajiya sai faman dariya take tana fad'in lalle ashe aiki ne tantance su, Haisam ne ya shigo Hajiya ta d'aga kai ta kalle shi tace "to kai Baban su sai kazo ka bambanta man su tunda duk sun kasa" murmushi yay kawai ya nemi kujera ya zauna tace ya zai zauna ko shima bazai iya banbance su bane ya d'aga mata kai alamar eh kafin cikin cool voice d'in shi yace duk suna bacci dama ta ido ake gane su, jinjina kai Hajiya tayi tace shima kenan sai ta idon zai iya gane su ya d'aga mata kai, Aunty dake ta dariya tace to a tambayi Mom d'in su k'ilan ita ta gane su duk aka maida kallon kan Fatuu dake murmushi Hajiya tace tazo ta bambance mata su, mik'ewa tay ta matsa kusa dasu ta d'an sunkuya tana kallonsu, ta d'an d'auki lokaci kafin ta d'aga yatsa ta nuna na hannun Hajiya tace shine Hajiyar ta tambayi shine wa tana yar dariya tace Angonta, "To wa zai tabbatar mana in daidai ta canka" Hajiya ta tambaya tana dariya Aunty tace daidai ta canka shine Hassan d'in don ta ruk'e tunda suka kaisu wurin Dad, da sauri Jidderh tace "Sis Fatuu ya akai kike gane su don Allah?" gaba d'aya akai dariya Hajiya tace tunda koda yaushe tana tare dasu tana k'are masu kallo dama zata iya samun abunda zata rink'a banbance su, duk su Yasmeen suka hau rok'on ta nuna masu yadda suma zasu rink'a gane su, nuna masu girar Adam d'in tayi tace tanan ta gane shi don zanen tashi ya d'an fi lankwasawa kad'an aikuwa duk suka maida idanun nasu kan su harda Hajiya Aunty ma ta taso daga kujerar ta tazo don ta gani sai gashi sun ga hakanne amman sai mutum ya natsu sosae zai gane, Mom ce ta dawo d'akin tana d'auke da madaidaicin tray an d'auro ruwa da lemu da glass cup Dad na biye da ita, ganin suna ta dariya yasa ta tambayi ya akai Aunty ta bata labari Dad yay dariya yace shima in dai ba idon su biyu ba bazai gane ba, zama yay kan kujera ya d'an sunkuyar da kai ya gaishe da Hajiya tare da yi mata anzo lafiya bayan ta amsa yace bai gidanne sun fita tare da bak'i tace ba komai sai kuma tayi mashi barka, saman c-table Mom ta d'aura tray din tace ma Hajiya a kawo Abinci anan ne tace mata a'a bata jin yunwa yanzu, hira suka shiga yi cike da nishad'i ana haka jariran suka farka daga bacci nan suka k'ara tantance su ta idon su, sai da akayi sallar Magrib sannan duk suka tashi don zuwa yin salla. Washe gari wuraren k'arfe sha biyu na rana Fanan ta iso tare da Nameer suma Haisam ne yaje ya d'aukko su daga Airport tana sanye cikin brown coat dress tasa yar bak'ar himar sosae tayi kyau Nameer ma na sanye da k'ananun kaya jeans da t-shirt, gaba d'aya Fanan a k'agare take da taga jariran da suna hanyar zuwa gidan sai faman zumud'i take tana ma Haisam tambayoyi game dasu Nameer nata mata dariya, lokacin da suka isa ma'aikatan gidanne suka zo suka d'auki kayan su tare da yi masu sannu da zuwa suka nufi ciki, ba kowa parlon Fanan ta tambayi Haisam inda Fatun take ya nuna mata ta nufi part d'in da sauri shi kuma Haisam da Nameer suka tsaya don ganin an shiga da kayan nasu, lokacin da ta shiga parlon ba kowa hakan yasa ta nufi Bedroom d'in, Mom da Aunty sai Hajiya ne a ciki yaran gidan duk suna Makaranta Fatuu na a zaune tsakiyar gado tana sanye da doguwar rigar shadda tayi daurin kallabi mai kyau haka yaran ma suna sanye da fararen kaya suna bacci daga gefenta, da Sallama ta shiga duk suka kai idanun su kanta ta shiga ganin itace yasa gaba d'aya suka shiga yin murmushi harda Fatuu ta nufi gadon da sauri ta zauna a baki idonta akan yaran ta shiga sakin faffad'an Murmushin dad'i harda d'an yarfa hannu, saida ta gama kallon su sannan ta juyo tana gaishe dasu Mom Hajiya tace wato saboda zumud'in ganin yaranta sai yanzu zatai lokacin su tana yar dariya tace a'a, anzo lafiya suka yi mata ta amsa kafin duk suka yi mata barka tana ta washe baki idonta akan yaran take amsawa Fatuu ma ta gaishe da ita ta kalleta bayan ta amsa tace "Sannu sis, sannu da k'ok'ari don Allah. Look at them, very cute wllh" dariya kawai Fatun ke yi haka su Mom don gaba d'aya ta rud'e da ganin yaran, su Haisam ne suka shigo Nameer ya nufi gefen Hajiya ya zauna tare da gaishe da ita ta dafa Shoulder d'inshi tana mashi an zo lafiya bayan ya amsa ya gaishe dasu Mom suma duk suka yi mashi anzo lafiya, Hajiya ce tace mashi shi bai ga yaran nashi ba ya juya yana kallon su fuskar shi d'auke da Murmushi yace "Ma sha Allah, Allah ya raya mana su" gaba d'aya aka amsa da Amin, ganin yadda Fanan ta tsura masu ido yasa Hajiya tace to ta d'auke su mana da sauri tace "No, suna hutawa a k'yale su suyi baccin su in sun tashi na d'auke su suga Mom d'in su" Hajiyar tace to mai y'ay'a duk akai dariya, shiru Fatuu tay kamar mai tunanin wani abu idonta akan Fanan dake ta kallon yaran tana murmushi can ta kai hannu ta d'aukko Aliyu wato Hussein dake a kusa da ita hakan yasa Fanan kallonta kawai sai gani tay ta Mik'o mata shi tana d'an murmushi, kallon rashin fahimta ta bita da shi haka ma su Hajiya duk idanun su na akan su, "Aunty Fanan gashi, na baki shi ", da k'yar ta furta Maganar, d'an yamutsa fuska Fanan tay cikin d'aurewar kai tace "I..I don't understand you Sis Zarah", saida Fatuu ta had'iyi abu kafin tace "dama na fad'i ma Ya Haisam cewa in na haihu zan baki Babyn koda kuwa d'aya ne sai gashi Allah yasa na haifi biyu shine na baki d'in, Aunty Fanan wllh na baki shi har abada ga su Hajiya nan inason su zama shaida shiyasa nayi hakan a gaban su" da k'yar ta k'arasa Maganar Saboda karyewar da muryarta tayi, hannu Fanan ta kai da sauri ta rufe bakinta alamar Al'ajabin Maganar don abu ne da bata tsammaci ji ba, bin juna sukai da kallo ita da Fatun lokaci guda idanun Fanan suka ciko da k'walla cikin rawar murya ta furta "Yanzu Sis Zarah kina nufin duk wahalar da kika sha ta rainon cikin shi da kuma haifuwar shi kin bani shi ya zama nawa har abada?" Kai Fatuu ta jinjina mata itama idanunta sun ciko da k'walla kawai sai ji sukai Fanan d'in ta fashe da kuka itama Fatun k'wallan ne suka fara zubo mata gaba d'aya sun karya ma kowa zuciya can Fanan ta kai hannu ta karbe shi ta bishi da kallo tana murmushi, "Ban ta6a tunanin wani zai man irin wannan kirkin ba a rayuwata har na rasa mi zan ce ma" cikin muryar kuka tayi Maganar tana kallon su Hajiya dake mata d'an murmushi, maida idonta tayi kan Fatuu bayan ta goge k'wallan tace "All i can say to you is thank you. Thank you so much for your generosity Zarah. You have shown me a kindness that I will never forget. Never" ta k'arasa tana jujjuya kai alamar tabbatar mata da abunda ta fad'a, jinjina kai Fatuu tay tana goge kwallanta gaba d'aya sauran Mutanen cikin dakin sunyi shiru suna bin su da kallo, mik'a mata Babyn tayi bayan Fatun ta amsa tana murmushi tace "Ba sai kin bani shi ba Zarah, We're one Family so duk abunda d'aya ya mallaka tamkar na kowa ne, I'm I right?" Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai alamar eh Fanan d'in taci gaba "Gud, ko baki bani shi ba gaba d'ayan su yarana ne kuma in sha Allah zamu raine su mu basu tarbiya mai kyau tare" atare gaba d'aya aka had'a baki wurin furta "Allahu ya sha" Fanan tay d'an murmushi tace Ameen, Hajiya ce ta d'an yi gyaran murya duk suka maida idonsu kanta a nutse ta fara magana tace wannan abun daya faru babu wanda ya kai ta jin dad'i wllh, Fateema itama tayi abunda da k'yar a samu wadda zata iya yin hakan ga abokiyar zamanta kamar yadda itama Fanan d'in tayi gaba d'aya suka jinjina kai, kallon Haisam tayi tace "ina son ka sani duk Wannan sadaukarwar da suke Saboda son da suke maka ne hakan yasa duk suka fifita farincikin ka fiye da nasu don haka ina k'ara jan hankalin ka da ka k'ara jajircewa wurin ganin ka ruk'e su da amana ka kyautata masu, kaima ka fifita farincikin su fiye da naka don kuwa ba K'aramin dace kai ba wllh ka k'ara gode ma Allah, samun mata irin wannan a zamanin nan da muke ciki ba zan ce babu irin su ba amman ina mai tabbatar maka da samun su da wahala don koda mata suna son miji zaka ga basu damu da Farincikin shi ba Saboda haukan kishi kullum cikin tada mashi hankali suke a haka kuma wai don ana son shi ne, ina rok'on Allah daya k'ara had'a kan ku ya Albarkaci rayuwar ku gaba d'aya ya k'ara shirya mana ku ya kuma k'ara rufa mana asiri fiddunya Wal akhira yasa mu gama da duniya lafiya" a tare gaba d'aya suka amsa da Amin fuskokin su d'auke da Murmushi ta juya kan su Fatuu ta k'ara masu Nasiha kan su k'ara had'a kan su ta nuna masu hakan da suka za6ar ma kan su shi yafi masu Alkhairi don ko ba komai zasu kasance a cikin farinciki suma su cigaba da kyautata ma mijin su hakan shine kishin daya dace, sosae tayi masu Nasiha mai tsuma jiki duk fuskokin su d'auke da d'an murmushi suke jinjina mata kai, bayan ta gama dasu ta juyo kan Nameer dake manne da ita ta kai hannu cikin sumar shi tace "na dawo kan ka mage sarkin son jiki ko kuma in ce mazuru...." Gaba d'aya aka saka dariya, taci gaba "Allah kaima ya nuna mana bikin ka lafiya kaida yar fillon taka duk da dai ina jin ki shi" tay Maganar tare da d'an kwa6e fuska duk ta basu dariya, hira suka cigaba da yi gwanin sha'awa saida aka yi sallar Azahar duk suka tashi Fanan anan tayi sallar tun tana cikin yi yaran suka tashi suna kuka tana sallamewa ta taso ta nufo gadon tana tambayar mike damun su suke kuka Fatuu dake murmushi tace mata k'ilan yunwa suke ji tace to tay feeding nasu ta daina bari suna yin kuka pls yadda tayi Maganar har saida ta ba Fatuu dariya, ita ta taimaka mata ta fara shayar dasu saida duk suka k'oshi sannan Fanan ta d'auke su gaba d'aya tana masu wasa tana fad'in ga Mom d'in su tazo duk sukai mata k'uri da ido sai kace sun san mi take cewa sai faman saka Fatuu dariya take. Bayan Fanan ta koma d'akin Laila dama anan take sauka in tazo gidan ta shiga kiran Mom d'inta wato Hajiya Maryam, bayan tayi picking suka gaisa tayi mata anzo lafiya Fanan d'in ta amsa mata tace ai tayi zaton zata tsaya Lagos ko duk murnar sunyi Y'ay'an ce tasa bata biya ba Fanan na dariya tace mata Kusan hakane ta k'agara da ta gansu gashi tare da Nameer suke tace to, "Mom you know What?" Fanan ta fad'a Mom d'in tace mata a'a mi akai, labarin abunda ya faru tsakaninta da Fatuu ta shiga bata yadda ta d'auki d'aya daga cikin yaran ta bata kyauta, d'an ta6e baki Hajiya Maryam d'in tayi tace mata in duk cikin salon neman wurin zama ne fa da sauri Fanan tace mata Wallahi har cikin zuciyarta ta bata don a gaban kowa akayi tace kuma su zama shaida, "to ce mata akai ke bazaki haihun bane?" Kai Fanan ta girgiza fuska a d'an yamutse tace "No Mom, kawai ta bani ne saboda k'aunata da take kuma taga ita ta riga haihuwan dama na fad'a maki wllh tana zaune dani da zuciya d'aya Mom, sam bata d'auke ni a matsayin kishiya ba" still bakin Hajiya Maryam d'in na a d'an ta6e tace mata to yanzu ita ta amshi yaron kenan tace mata a'a nan ta fad'i mata yadda sukai ta k'ara da cewa "nasan ko ban amsa ba bazata ta6a man iyaka da yaran ba so nima zasu zama kamar nawa ne kinga ko ban haihu ba na samu wanda zasu kira ni da Momy, don Allah Mom ki manta komai ki so Zarah sannan ki mana fatan Alkhairi" yar dariya tayi tace ita dama ai bata ce ta tsaneta ba tana masu fatan Alkhairi Allah ya k'ara had'a kawunan su itama kuma tana mata Addu'ar Allah yabata haihuwan, cike da jin dad'i cikin washe baki Fanan d'in ta amsa da Amin tare da Fad'in shiyasa take k'aunar ta Saboda she's a Mom like no other tana jiyo dariyar Hajiya Maryam d'in, tambayar yaushe zata zo taga Babies tayi tace mata tunda ita tana nan ba sai tazo ba, a shagwabe murya kamar zata yi kuka tace"Haba Mom, yanzu fa kika nuna man komai ya wuce kuma ai ni zuwana daban naki ma daban, don Allah ki zo, haka fa da biki kika k'i zuwa pls kizo hakan zai sa aga kin manta komai kuma ma yaran nan fa grandchildren d'in ki ne" tana dariya tace mata "to sarkin tsara zance wasa nike maki zan zo in sha Allah amman gaskiya sai Ranar suna don akwae kaya na da zasu iso ranar Asabar dole zan tsaya in ga isowar su" cike da Farinciki Fanan d'in tace to ba komai ai tunda zata zo d'in Allah ya kaimu Ranar lahadin harda tambayarta a cikin kayan da tayi Order d'in akwae na jarirai tace mata eh Fanan din tace to ta za6o ma Babies d'in su Unique ones masu yawa Hajiya Maryam d'in ta amsa da tunda ita ta bata kudin da ta siyo ko Fanan ta saka dariya, hira suka cigaba da yi Fanan bata tambayi Dad d'inta ba don tasan ta baro shi a America, kafin suyi sallama ta tambaye ta Farha tace mata tana d'akin ta k'ilan ko bacci take. Bayan sun gama wayar Farha ta shiga kira lokacin da tayi picking tana jin muryarta ta gane bacci take ta bata hakurin tashin ta da tayi tace mata ba komai, tambayar ta tayi tazo ne tace mata eh gata a Abuja nan ta shiga bata labarin irin kyawun Babies d'in da aka Haifa masu fuskar Farhar da d'an murmushi take sauraronta bayan ta gama tace Allah ya raya, tambayarta tayi zata biyo Mom tazo suna ko tace mata No, cikin sigar rarrashi tace mata don Allah ta manta komai ta d'auki Zarah matsayin yar'uwarta itama don tana da kirki sosae kuma tana k'aunarta, nan ta shiga bata labarin yadda ta bata kyautar Babyn da ta haifa tace in ba don tana kaunarta ba taya zata mata haka, daga k'arshe dai saida tayi nasarar shawo kan Farhar tace mata zata biyo Mom d'in nasu zo kaga murna a wurin Fanan. Ranar Friday da rana Laila ta iso itama ta nuna farinciki sosae ganin yaran nan suka shiga shirye shiryen yin gagarumin suna, a ranar da daddare bayan sallar isha Haisam na zaune a parlon shi na saman bene yana operating laptop d'in shi jikinshi sanye da ash d'in jallabiya wayar shi tay k'ara alamar shigowar sak'o, hannu ya kai gefen shi ya d'aukko wayar ya shiga dubawa, bin sakon yayi da kallo bayan ya bud'e wanda credit alert ne na kud'i Naira miliyan d'aya da rabi daga Sameer, sam bai yi mamakin ganin kud'in ba duk da bai san na minene ba amman ba yau ya fara turo mashi kud'i ba don koda bikin shi da Fanan miliyan biyu ya bashi, fita yay daga cikin sak'on ya fara kokarin kiran Sameer d'in, saida ta kusa yankewa sannan ya d'aga suka gaisa Haisam d'in yace mashi suyi Vedio call ya furta mashi Ok, bayan ya maida kiran na gani Sameer d'in na zaune akan doguwar kujera a gidan shi dake a England wanda Company d'in su suka bashi, suma dare ne can har yayi shirin bacci yana sanye da robe da ta bayyanar da k'irjin shi wanda shima ke d'auke da kwantacciyar suma kamar dai yadda na Haisam yake, k'ara gaisawa sukai Haisam yay mashi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah, "Ya akai bakai bacci ba kai da kake gauro" Haisam ya fad'a yana murmushi Sameer d'in yay d'an guntun murmushin da iyakar shi lips d'in shi slowly yace mashi yana shan coffee ne Haisam d'in ya jinjina mashi kai suka d'an yi shiru kafin Sameer d'in ya tambayi ya Babies d'in su ya bashi amsa da suna lafiya, ce mashi yay yaga sak'on kud'i yanzu shiru Sameer din ya d'an yi kaman bazai ce mashi komai ba can yace mashi ya d'auki 1 million yaba wife en shi 500k yaran shi kuma a fad'i masu zai musu zuwa na musamman, murmushi Haisam yay yayi mashi godiya kafin ya tambayi bazai zo suna ba yace mashi yaso hakan amman aiki yayi mashi yawa amman yana nan zuwa bada dad'ewa ba Haisam yace Ok Allah ya taimaka ya amsa mashi da Amin, tambayar shi yay ina Amarya ya d'an ta6e baki ya bashi amsa da yanzu suka gama magana Haisam na murmushi yace abun nata matsowa Allah ya nuna masu can kasan mak'oshi Sameer ya amsa da Ameen suka dan k'ara yin shiru, "Ina son zaka taimaka man da abu" Sameer ya fad'a Haisam ya jinjina kai tare da dan gyara zaman shi ya tambayi miye yace mashi dama yana son zai siya ma su bride d'in tashi gida ne, kai Haisam ya d'aga kafin ya tambayi to wane taimako yake son yayi mashi yace bai san taya zai yi hakan ba tunda shi ba sanin garin su yayi ba kuma bai san kowa ba so yana son ya bashi shawarar yadda za'ai Haisam yace ya yi Maganar da Fauzy ne ya girgiza mashi kai alamar a'a kafin yace yafi tunanin yin Maganar da wani babba ba ita ba, shiru Haisam yay alamar tunani can yace mashi ya bari zasu yi Maganar da Wife d'in shi sai ta kira Yayarta tayi mata Maganar Sameer d'in yace Ok zai jira shi ya fad'i mata in tayi ma Yayar tata Maganar tace mata su duba gidan da suke so mai kyau in za'a samu Haisam yace Ok, hira suka d'an k'ara yi yawanci duk akan bikin Sameer d'in ne daga baya sukayi sallama, suna gama yin wayar ya kira Fatuu lokacin suna zaune a Bedroom d'inta da su Aunty Laila anata shirya yadda za'ai suna, bayan tayi picking tambayar ta yay tana tare da mutane ne tace mashi eh yace Ok bari zai tura mata sak'o ta WhatsApp tace to, lokacin da ta karanta sak'on daya turo matan d'an waro ido tay alamar mamaki sai kuma ta hau yin d'an murmushi, sai wuraren k'arfe goma da rabi sannan duka aka watse daga hirar da ake a d'akin Jidderh ma da anan take kwana tace ma Fatun bari taje ta dawo, suna tafiya cike da zumud'i ta shiga kiran Aunty Mareeya, saida ta kusa yankewa sannan ta d'auka bayan sun gaisa ta tambayi twins Fatun tace mata k'ilan ma har tayi bacci ta tada ita ko tace mata a'a bata kusa da wayar ne, tambayarta ina Fauzy tay tace mata tana d'akin ta bata san ko tayi bacci ba ta tambayi ita zata ba wayar ne da sauri Fatun tace a'a dama sak'o ne aka bata da alamun d'an mamaki tace mata to waye ya bada sakon tace mata Sameer har saida Aunty ta maimaita sunan Sameer d'in kafin ta tambayi sak'on miye ya bada, bayanin da yayi Fatun tayi mata bayan ta gama da tsananin mamaki Aunty Mareeya ta maimaita abunda ta fad'a tace mata eh haka yace, "Kinga Zarah wllh nama rasa mi zance maki tsabar Al'ajabi, yanzu duk uban hidiman da yake ma Fauziyya kuma harda wannan gingimemiyar dawainiyar Gida fa!" Dariya Fatuu tay jin yadda tayi Maganar tace " Wllh Aunty, yana da halin ne kuma k'ilan yana son canza gidanne Saboda bikin tunda kinga ba k'aramar hidima za'ai ba manyan mutane zasu zo" Aunty tace "hakane kam, dama muma munata shirin yin gyaran gidan don har an gama Magana ma da masu gyaran za'ai gyara sosae Saboda hakan yanzu kuma kinga ga Maganar da yayi ni bamma san to mi zan ce ba, amman abunda za'ai Zarah zan kira babban yayanmu sai muyi magana kan hakan tunda ma gobe zamu taho nan in muka zo komi mukai dashi zan fad'i maki sai ki fad'i ma Mijin naki" amsa mata da to Fatun tay tace Allah ya kawo su lafiya duk ta k'agara ta gan su wllh Auntyn na dariya tace suma bata ga yadda suka k'agara da su ganta ba amman sun fi k'agara da suka ga twins d'in su Fatun nata dariya Aunty Mareeyar ta k'ara cewa "ni kinsan abunda ma yafi damuna Zarah?" Kai Fatuu ta girgiza kafin tace mata a'a, "Wllh abunda nike gudu kada sai mun zo munyi kayan d'aki suce basu so tunda kinsan Manyan nan yadda suke" kai Fatuu ta jinjina tace hakane kuma fa, Aunty tace wllh abunda take ta tunani kenan, shiru Fatun ta d'anyi kafin can tace mata to ko tayi ma Ya Haisam magana kan hakan da sauri Aunty tace "kice mashi mi Zarah! A'a kada kiyi mashi magana kan hakan kada kuma aga kamar so muke ace kada ayin, za'a yi mata komai iya karfin mu dama mun yanke za'a siya mata kayan ne kawai Babanmu ya yanke zai siyar da gonakin shi guda biyu sai a had'a da sauran kud'in da aka tanada in sha Allahu za'ai komai yadda yakamata" Fatuu tace Allah ya bada iko ta amsa da Amin, "Ni kinsan ma abunda nafi so wllh shine in da zai yuwu da yaje Funtua sun gaisa dasu don duk fa ba wanda ya san shi in ba a hoto da aka nuna masu shi ba to kuma hakan nasan da kamar wuya tunda yanzu ma bai K'asar tun kafin ya tafi nayi ma Fauziyya Maganar kan tasa shi yazo sai ce man tayi wai ita gaskiya bata iyawa ni in yi mashi, to wai kar aga kai talaka ka zaqe yasa ban yin ba kuma ma dai nima nasan halin surukin nawa baud'add'e ne" Dariya Fatuu tasa Auntyn tace Allah kuwa yanzu dai ai sai kawai da biki sun gan shi, hira suka d'an k'ara yi kafin sukai sallama ta kira Haisam d'in tayi mashi bayanin abunda Aunty tace yace Ok Allah ya kaimu goben ya kawo su lafiya, cikin yar shagwaba ta tambayi yana ina yana murmushi yace mata gashi a part d'in shi tace mi yake ya bata amsa da yana wani aiki ne tay shiru yayin da zuciyarta ta shiga raya mata kilan ma a part d'in shi Fanan ke kwana jin tayi shiru yasa shi tambayar ta koda wani abu ne da sauri tace mashi a'a tayi mashi saida safe yana murmushi ya amsa har zata kashe taji yace tana tare da mutane ne a hankali tace mashi a'a ita kad'ai ce Jidderh taje ta dawo yace Ok bari yazo suyi bankwana da Babies tay d'an murmushi tace to, aje wayar tayi ta juya tana kallon yaran dake kwance saman gadon suna bacci sam basu da rigima da sun yi kuka yawanci yunwa suke ji, bada jimawa ba sai gashi ya shigo cikin d'akin da sallama ta d'aga kai ta kalle shi ya sakar mata murmushi itama haka, cikin d'akin ya nufo ya tsaya d'an nesa da ita yace bazatai welcoming nashi ba tunda shi bak'o ne yanzu, yar dariya tayi ta mik'e ta nufe shi tana zuwa gabanshi ta fad'a jikin shi ya rungumeta suna ta sakin murmushi ga k'amshin jikinsu ya cika ma kowa hanci, d'agowa tay tace mashi ya zauna atare suka zauna idon shi akan yaran ya tambayi ya suke itama kallon su take tace mashi lafiya lou, juyowa tay suka had'a ido ta d'an langa6ar da kai cikin lumshe ido Slowly ya furta mata "I'm missing you" dan buda ido tayi still da murmushi akan Fuskar ta k'asa k'asa tace "ba gani a kusa da kai ba" d'age gira yay yace ba shi ba itama ta d'age mashi tace wanne, wani irin kashe mata ido yay ta saki dariya shima yar dariyar yay ya jawota jikin shi, kai hannu tayi tana shafa beard cikin salo tace "na gode ma Allah dayasa na haihu lafiya naci gaba da yin rayuwa da kai" lumshe mata ido yay a hankali yace shima haka tana niyyar k'ara yin magana suka ji an shigo a tare suka kai idon su kan kopar Jidderh ce tayi shirin bacci tana ganin su ta dan waro ido tana murmushi kunya ce ta kama Fatuu ta fara k'ok'arin raba jikinta da nashi saidai yak'i bata dama ganin haka yasa Jidderh cewa ta bashi 10 minutes zata je ta dawo harda jaddada mashi da hannu duk sukai yar dariya, bayan ta fita Fatuu ta maida idonta kan shi tace tana son yi mashi wata Magana ya d'aga kai kafin yace yana ji, "Dama so nike in ce kaman yakamata Ya Sameer yaje Funtua su gaisa da iyayen Fauzy Saboda ba wanda yasan shi fa" shiru yay idon shi akanta can yace mata sun yi magana kan hakan ne da sauri tace a'a kawai itace tayi tunanin hakan, Wani kallo yay mata yace "Kai yar fillona yaushe kika iya yin wannan tunanin" dariya ta saka tace mashi tunda tay hankali ya d'age gira yace to shi miyasa bata ta6a ce mashi yakamata yaje garin su ba da sauri tace "to ai kai kaga Baffana ya sanka tun ma kafin muyi aure kuma gwaggota ma ta san ka amman shi fa ba wanda ya san shi gashi yanzu bai fi saura wata ukku ba bikin" shiru yay da alama nazarin Maganar yake can yay sigh yace mata yanzu dai bai K'asar amman yace zai zo bada dad'ewa ba in yazo zai ga abun da za'ai ta d'aga kai sai kuma tace "amman in kaga fa kaman da takura ko kawai ka bar Maganar in yaje bikin sun ganshi, kai ya girgiza mata yace ai yakamatan yaje saidai yazo, "To ni yaushe zaka je garin mu?" yana murmushi yace biyanta zai yi kenan tace eh, yace Ok zasu je sai Babies sun k'ara girma harda tambayarta hakan yayi mata tace mashi eh, dawowar Jidderh tasa yayi mata sallama ya tafi. Washe gari Misalin k'arfe ukku na rana su Gwaggo suka iso yanzu ma kamar da biki Mota biyu suka yo da Tk da Saude da Aunty Mareeya, Feenah, Kawu Amadu, Abbas, Fauzy, Mino harda Nana wannan karon ba'a zo da Zainab ba, zo kaga murna wurin Fatuu suma sai murnar ganinta suke ba kamar da suka ga yaran Mino har ta kasa rufe bakinta don dad'i gwaggo ma sai faman murmushi take haka su Aunty Mareeya da Feenah Abdul ma sam ya kasa matsawa daga kusa da yaran sai d'auka d'auka ake d'akin ya cika anata farinciki, harda uban yajin jego gwaggo ta kawo, a Ranar bayan la'asar yan Adamawa suka iso su Yadikko da Kamalu Yaya sai wata k'anwar Baban su Fatuu da d'ayar Matar Ardo wadda ba'a zo da ita biki ba wannan karon ba'a zo da innar su Altine ba duk da taso tazo kamar kamar me amman ba'a zo da itan ba don gwaggo ta fad'i ma Baffan su Fatuu kada azo da yawa tunda ba'a dad'e da aka zo biki ba, wannan karon ma harda shanu suka kawo saidai ba daga Baffan Fatuu ba daga mai girma Ard'o ya ba yan tatta6a kunnan shi saida kowa yayi mamakin yadda suka ciri tuta har ya d'au shanu sukutum ya basu don abu ne da bai ta6a yi ma wani a yaran dangin su ba, basu dad'e da zuwa ba gab da Magrib wasu yan'uwan su Haisam yan d'aura suma suka iso nan fa gida ya dauki haramar suna, wannan karon ma a part d'in baya duk aka sauke su amman su Mino da Fauzy duk a part d'in Fatuu suka ce zasu kwana, Kusan raba dare sukai suna hira gwanin nishad'i. Washe gari Lahadi suna tun bayan da akai sallar Asuba ba'a koma ba aka fara hidiman suna wannan karon ma masu aikin Abinci aka d'aukko tunda safe aka fara yanka raguna harda shanun da Ard'o ya aiko aka yanka aka kuma k'ara da kaji nan fa aka shiga soyen hanji, Misalin k'arfe goma na safe lokacin Fatuu tayi wanka tayi shigar suna ta farko da babbar atamfa da akai mata half gown da straight skirt wuyanta da hannunta tasha gold Aunty Laila tayi mata makeup da daurin kallabi mai kyau sosae tayi kyau abun sai wanda gani, lokacin yan uwansu Mom daga Ethiopia suka iso Haisam da Nameer ne da Jidderh suka je d'aukko su, mutum biyar ne suka zo da Kakarsu sai k'annen Mom guda biyu sai kuma cousin dinta da kuma d'iyar yayan su wato Jahad da Mom taso Nameer ya aura, musamman Saboda sunan Kakarsu ta baro Qatar tazo Ethiopia shine suka taho, sosae akai farinciki da zuwansu su Aunty Mareeya sai yaba kyaun k'annen su Mom suke gaba dayansu suna yanayi da Haisam haka Jahad d'in ma kyakkyawace saidai bata da tsawo sosae kuma ba ramamma bace don zata fi Mino jiki amman Mino zata fita tsawo dukda da gani ta girmi Minon ma, nan fa hidiman suna ta kankama, zuwa sallar Azahar har an gama Abincin suna Kusan kala takwas anan gidan akai wasu wasu kuma k'awar Mom aka ba kwangilar yi haka Drink ma kala hud'u akai banda uban lemuna jibgi guda sai abunda mutum ke so zai ci ya kuma sha nama kuwa gashi nan cikin abinciccikan baje baje, ana yin salla Mai jego ta canza shiga zuwa rantsattsan leshi d'an dubu d'aruruwa anyi mata riga da skirt da suka hau jikinta sosae lokacin su Mom gaba dayansu su kuma ankon tsadaddiyar atamfa sukai ita da Aunty da Laila gaba d'aya dai yan gidan kaya iri d'aya suka saka harda Hajiya da Fanan haka Dad ma dasu Haisam suma ankon shadda sukai da sauran yara mazan gidan, kowa dai yaci gayun suna Gwaggo tasha leshi haka Mino ma lace tasa Fauzy kuma fitted gown d'in atamfa ta saka iri d'aya sukai da Aunty Mareeya, kai kowa dai yasha gayu don in natsaya bayyana kayan da kowa ya saka zamu 6ata lokaci, bayan an gama cin gayun an ci Abinci photographer da aka d'aukko ya shiga aikin d'aukar hutuna, ana cikin yin hotunan jiniya ta karad'e cikin gidan su Jidderh suka nufi kopar fita daga cikin parlon gidan da gudu suna fad'in ga Momyn Nasarawa nan ta iso jin hakan har saida gaban Fauzy yay wani irin bugu Aunty Mareeya ta kalleta tana yar dariya Fauzyn ta waro mata ido, matsawa Aunty tay wurinta tace mata tazo suje su tarbo surukarta da sauri ta girgiza mata kai Aunty ta juya tana fad'in ita bari taje, hakanan Fauzy taji gabanta na wani irin fad'uwa da sauri ta juya ta nufi baya inda suka sauka, cikin Fara'a her Excellency ke amsa barka da zuwan da ake mata tasha adon dangwatsetsen leshi da gold haka yaranta ma duk sunyi shigar alfarma Aunty Mareeya na kallon fuskar Ashraf dake a d'aure a ranta ta raya wannan da gani irin Sameer ne, bayan an gama yi mata barka da zuwa aka d'unguma ciki, suna shiga cikin parlon Aunty Mareeya ta wurga ido tana kokarin hango Fauzy saidai bata ganta ba, saida suka rakata har d'akin Mom sannan suka fito tana ta godiya, part d'in su Fatuu ta nufa don ta duba Fauzyn amman bata a ciki hakan yasa ta fito ta nufi baya, d'akin da suka sauka ta nufa tana tura kopar ta hangota zaune a bakin gado tayi zuru, k'arasa shigowa Aunty Mareeya tayi ta nufeta tana fad'in "lafiya kika zo kika k'umshe anan" d'an ta6e baki Fauzyn tayi ba tare da tace komai ba, a gefenta Aunty ta zauna ta dafa Shoulder d'inta tace mata wai lafiya, a sanyaye tace mata hakanan take jin ta wani iri zuwan Mom d'in su Sameer din gani take kaman bata yi na'am da ita ba Aunty tace "to in bata yi na'am dake ba kuma ta amince mashi ya aure ki, kar ki wani damu ni ina ganin ba wani abu don da alamun bata da wata matsala" da yanayin damuwa Fauzy tace "amman Aunty tunda aka saka Ranar mu fa bamu ta6a ko magana ta waya da ita ba yanzu har wata hud'u shiyasa dama can nike tunanin kaman bata son Auren namu kawai dai k'ilan don ya nuna yana so ta amince" d'an jimm Aunty tay don tasan da zancen basu ta6a magana da ita ba ita da kanta tana tambayar ta game da hakan, yar ajiyar zuciya ta sauke "kada ki damu Fauziyya in sha Allahu ba haka bane k'ilan dai abubuwa ne sukai mata yawa shiyasa bata nemi kuyi wayar ba kinsan Manyan Mutane yadda suke uzururruka yawa suke masu balle ita kuma da take First Lady, yanzu ki tashi muje sai kiyi mata sannu da zuwa" waro ido Fauzy tayi tace taje kuma ta d'aga mata kai tace haka yakamata, sakata tayi ta canza kaya zuwa lace mai kyau riga da skirt Aunty harda yi mata yar kwalliya ta kuma yi mata d'aurin kallabi mai kyau ta feshe ta da turare, komai dai Aunty tayi mata sai gata ta fito tayi kyau sosae dama kanta a kwance yake ta faka gashinta ya fito ta k'asan d'aurin da aka yi mata bayan ta gama shirya ta tasata ta d'aukko gyale mahad'in kayan da takalma masu d'an tsini suma sun hau da kayan ta kama mata hannu suka fito, sosae gaban Fauzy keta bugawa wata irin fargaba ce ta cikata har suka iso bakin part d'in Mom nan taja ta toge Aunty tace suje mana ba gata ba tare da ita, parlon Mom d'in cike yake da Mutane yan suna suka nufi hanyar Bedroom da anan Hajiya Zainab d'in take lokacin da suka shiga cikin d'akin nan ma dai cike yake da mutane k'awayen su Mom wasu a saman gado wasu asaman doguwar kujerar dake cikin d'akin wasu kuma zaune suke a saman Carpet sun jingina da tuma tuman tuntun d'in dake ajiye saman lallausan carpet d'in, Jidderh na zaune gefen Her Excellency tana zuba mata shagwaba da yake yar gidanta ce haka ma K'annansu da suka zo daga Ethiopia suma duk suna zagaye da ita a saman gadon su Aunty Mareeya na shigowa akan idon Jidderh cikin d'aga murya tace "Ga Bride d'in Ya Sameer nan" gaba d'aya yan d'akin suka maido idonsu kan su Fauzy yadda taji tamkar ta nutse a wurin ta kasa cigaba da tafiyar tay tsaye cak a wurin idonta a k'asa jikinta har d'an rawa yake, Jidderh ce ta taso da sauri ta nufo su tana zuwa ta kamo hannun Fauzyn ta jata ciki, kusa da Hajiya Zainab ta kai ta tace "Momy ga Daughter in-law d'in ki" Fuskarta da d'an murmushi ta kalli Fauzy data sunkuyar da kai cikin muryar ta mai dad'i ta furta "She's My Daughter not inlaw" jin haka yasa Aunty Mareeya dake a tsaye gefen Fauzyn sakin murmushin dadi ita kanta Fauzyn ta d'an ji wani sanyi a ranta da k'yar ta d'ago suka had'a ido cikin d'an rawar murya ta gaishe da ita tare da yi mata an zo lafiya tana ta murmushi ta amsa mata kafin tace ma Jidderh ta bata wuri ta zauna tace to tare da mik'ewa ta kalli Fauzyn tay mata nuni da hannu tace ta zauna, d'an can gefe da ita ta zauna har lokacin idonta na a k'asa taji tace mata ya School sai lokacin ta d'ago ta k'ara kallonta da d'an murmushi tace mata Alhamdulillah ta jinjina mata kai, kallon Aunty dake tsaye Hajiya Zainab d'in tayi tace mata ko itace Sister d'inta da take wurinta da sauri Aunty tace mata eh tana murmushi ta jinjina mata kai, Kallon k'annansu yan Ethiopia tayi da yaren su tace masu ga Wadda Sameer zai Aura su gaisa duk suka d'an d'aga ma Fauzyn hannu suka ce sunyi farincikin ganinta da turanci itama tace masu haka tay masu godiya, kallon Amal k'anwar Sameer tayi tace mata ita baza su gaisa ba tayi d'an murmushi tace ma Fauzyn ina wuni itama tana murmushin ta amsa mata daga haka suka yi shiru can kuma Her Excellency ta kalli Aunty tace mata ta zauna mana tayi tsaye ko ba wuri Aunty ta fara k'ok'arin zama akan Carpet Hajiya Zainab d'in tace ya zata zauna a k'asa ta kalli Amal tace ta bata wuri da sauri Aunty tace a'a don Allah ta k'yaleta ai ba k'asa bane tunda carpet ne tayi Maganar tare da zaunawa, ko ba komai sosae taji dad'in yadda ta mutunta su a cikin ranta, Mom ce ta shigo ta nufo gaban Hajiya Zainab tana murmushi ta kalli Fauzy tace mata suna gaisawa da Daughter ne ta d'aga mata kai sai kuma tace ita wadda Nameer zai aura bata zo bane da sauri Jidderh tace tazo bari ta kirawota ta mik'e ta nufi hanyar fita, gaba d'aya Fauzy ta takura da kallon da ake bin ta dashi ba kamar Yar'uwar su Sameer wato Jahad wani irin kallon k'urulla take bin ta dashi da alama tana tantance waya fi kyau tsakanin su don tana son Sameer sosae, ba'a dad'e ba sai gasu sun dawo tare gaba d'aya Minon rud'ewa tayi bayan sun shigo ganin yadda aka bita da kallo a harhard'e ta rink'a tafiya, gaban su Mom ta kaita sam ta kasa d'agowa ta kalli kowa kanta a k'asa ta gaishe da su, Hajiya Zainab na murmushi jin yanayin voice d'inta data gaishe su tace "to Daughter yar fillo in baki d'ago ba taya zamu san juna" duk akai murmushi da k'yar Minon ta d'ago suka had'a ido da ita a d'an dabarbarce ta k'ara gaishe da ita ta amsa, kallon yan Ethiopia ta k'ara yi tace masu ga Wadda Nameer zai aura kuma duk suka d'aga mata hannu tare da ce mata itama sunyi farincikin ganinta ta amsa masu Hajiya Zainab ta kalli Mom tace mata sunyi kama sosae da matar Son Mom d'in tace mata eh daka kalle su zaka gane yan'uwa ne, bayan sun gama gaisawar Mom tace masu su zo su gaisa da mutane gaba d'aya ji sukai kamar su nutse ba yadda zasu yi Fauzy ta mik'e suka bita ta shiga cikin d'akin dasu tana nuna ma mutane su, to duk dai yabon su suke suna fad'in suna da kyau wasu su ce gasu yara dasu, bayan sun gama gaggaisawar tace masu suje su gaisa da Ummin su wato Kakar Haisam sukai hanyar fita, mik'ewa Aunty tayi tay ma Hajiya Zainab sallama har zata juya ta tafi ta dakatar da ita tace mata anjima da daddare in an gama taro tana son zasu yi magana in ba damuwa da sauri Aunty tace to Allah ya kaimu ta k'ara yi mata sallama sannan ta tafi. Taro ya kankama Mutane sai zuwa suke suna kuma kawo abun arziki, tun Fatuu na gane yawan kayan da ake kawo mata har ta kai bata ganewa, wasu kayan daga part d'in Mom ake aikowa dasu wasu daga wurin Aunty wasu daga wurin Hajiya har daga wurin Laila wanda k'awayenta suka kawo, wasu ma yan'uwan wanda Laila zata aura sun zo suma sun kawo abun Arzik'in haka ta 6angaren Jidderh ma wasu k'awayenta da suka zo sun kawo kaya harda surukarta Maman wanda zata aura wato Matar Minister tare da k'anwar shi da kuma Yayar shi sun zo suma duk sun kawo kayan suna, haka wasu daga cikin Matan Abokan Haisam ma duk sun zo harda Saleema matar Saleem itama ya kawota da yake dama a Abujar suke zaune Sa'adiya ma k'anwar Khalid tazo tare da Mahaifiyarsu wato Hajiya Rabi'atu sosae Fatuu tayi farincikin ganinta harda sak'o khalid ya bada a kawo mata, abun Arziki dai ta ko ina Aunty Laila da Fanan suna ta kai da kawon ganin an tarbi kowa yadda yakamata sai sannu ake masu. Ana yin sallar la'asar duk suka canza shiga Fatuu ta saka shadda da tasha ubansun aiki su Mom dasu Laila gaba d'aya yan gidan suka saka lace su Fauzy ma duk suka canza shiga nan aka shiga sake yin hotuna yanzu harda su Hajiya Zainab akai, Haisam na fitowa daga Masallaci shi dasu Abbas Fanan ta kira shi ta sanar dashi Mom d'inta sun iso suna Airport yace Ok bari suje su d'aukko su, Mota biyu suka tafi da ita shida Abbas da kuma Saleem, lokacin da suka iso gidan gaba d'ayan su sunyi shiga ta Alfarma abun gwanin sha'awa ita da Farha duk tsadaddun lace ne a jikin su kowannen su na sanye da zinari sai sauran yaran ma duk suna sanye da tsadaddun kaya Fanan na ganinsu ta nufo su da gudu cike da Farinciki ta tarbe su haka ma su Mom duk sun nuna farinciki da zuwan su, tunda suka shigo falon Mino da Fauzy suka bi Farha da kallo haka ma Fatuu komai ya shiga dawo mata daya faru tsakaninsu, amsar kayan su Fanan da Laila sukai suka nufi part d'in Hajiya dasu Aunty Mareeya da bata santa ba ta tambayi Feenah wacece ta sanar mata da d'iyar Hajiya ce Mom d'in Fanan tace Ok suje su gaisa da ita, duk an gaggaisa da ita an mata sannu da zuwa harda Gwaggo ma taje ta gaidata tayi mata sannu da zuwa fuska a sake ta amsa harda yi mata barka, wurin Fatuu gwaggo tazo tace mata taje tayi mata sannu da zuwa a sanyaye tace to ta nufe su tunda ta taho Suke kallon juna ita da Farha har ta tsaya a gaban su cike da fargaba ta gaishe da Hajiya Maryam d'in itama ta sakar mata fuska ta amsa tare da yi mata barka, kallon Farha tayi da d'an murmushi tace mata sannu da zuwa ga mamakinta sai gani tayi ta maido mata da murmushin itama ta amsa mata tare da yi mata barka hakan ba K'aramin dad'i yayi ma Fatuun ba dama ita a rayuwarta bata son taga wani ya ruk'e ta yana fushi da ita, lokacin Fanan suka dawo ganinsu tare da Fatun ba karamin dad'i taji ba nan tace suzo ayi masu hotuna kafin su shiga ciki, sai gashi harda Farha anyi masu, ana gama sallar La'asar Aunty Laila ta kunna Sound system d'in cikin parlon ta k'ure volume kai kace Dj ne aka kira nan fa suka shiga tik'ar rawa harda Fanan dasu Jidderh da alama dai Aunty Laila yar casu ce don sosae ta zage tana rawa su Fauzy dai suna a cikin yan kallo Aunty Mareeya da Feenah dai sun shiga, suna cikin rawar yan uwansu yan Ethiopia suka ba Laila wak'ar yaren su ta kunna masu nan fa aka basu fili kallo ya dawo kansu dama shigar su ta al'ada suka yi gashin su ya bud'e Laila da Jidderh ma da yake sun iya rawar da suke suma sukai joining nasu abun dai sai wanda ya gani gwanin k'ayatarwa cikin yan kallo harda Mom da Hajiya Zainab yadda suke ji an tada masu tsumi kamar su shiga saidai ba dama su Laila nata ce masu wai su zo ayi dasu sai dariya suke. Alhamdulillah taro ya tashi lafiya an ci an sha anyi nishad'i ba kad'an ba an kuma raba souvenirs abubuwa iri daban daban masu d'auke da sunan jarirai amman ba hoto don Hajiya ta hana Saboda gudun bakin mutane dama shima Haisam bai so, abun dai sai san barka da fatan Allah ya raya Adam da Aliyu. Gaba d'aya Fatuu ta gaji likis haka jariran ma a daddafe tayi wanka bayan Magrib suma aka yi masu tana gama shiryawa tayi shirin kwanciya su Aunty Laila ma abun ba'a magana gaba d'aya sun gaji amman duk da haka suka shiga shirya kayan sunan da aka samu wanda suka zube a k'asa gefen gado kili guda kai kace Fatun k'aton shago zata bud'e don kaya ne aka tara ba yan kad'an ba kama daga manyan atamfofi laces materials kayan jarirai abun ba'a magana don ko Hajiya Maryam trolley guda ta kawo na kayan jarirai tsadaddun gaske da kuma manyan atamfofi guda biyu na Fatuu haka su Hajiya Zainab ma ta kawo had'add'un kaya na jarirai dana Fatun mutane da dama dai duk sun kakkawo kaya sosae harda su Baby gift set suma an tara su da yawa wasu had'addun baskets ne an nad'e su da yan flowers irin dai yadda ake ma kyauta, k'arshe dai wasu saidai nan aka barsu da safe an kimtsa su. Bayan sallar isha Aunty Mareeya na gama salla jikinta sanye da Hijab ta nufi part d'in Mom don amsa neman da Her Excellency ke mata, lokacin da ta shiga cikin Bedroom d'in da sallama ba kowa a ciki sai su biyu duk suna zaune a saman gado jikinsu sanye da dogayen riguna kowannen su ba kallabi a kan shi suna ruk'e da glass cups mai d'auke da ruwan lemu mai sanyi da gani hira suke suna sha, da murmushi gaba d'ayan su akan fuskokin su suka amsa mata Sallamarta ta nufi gadon, daga gaban gadon ta tsaya tana kallon su don kuwa sun rud'a ta bazata iya gane wacece Her Excellency d'in ba a ciki, Mom ce tace mata sannu da zuwa ta amsa ba tare data gane wacece ba tana d'an murmushi tace masu dama tazo wurin Her Excellency ne daga yanayin yadda tayi Maganar suka fahimci bata gane su ba Hajiya Zainab d'in ce tace mata "Ok, ki ganta" jin haka yasa Aunty tayi tunanin Mom ce tayi Maganar don haka sai ta juya kan Mom da tayi tunanin itace Hajiya Zainab tace "ranki ya dad'e gani na dawo kamar yadda kika ce" kasa daurewa Mom tayi ta saki dariya haka Hajiya Zainab d'in ma yar dariyar tayi ganin haka yasa Aunty Mareeya d'an waro ido tana masu kallon rashin fahimta Mom ta nuna mata Her Excellency tace mata gata nan itace tayi mata Magana, d'an bud'a baki Aunty tay sai kuma ta saki dariya don ta gane wasa da hankalinta tayi, saukkowa daga saman gadon Hajiya Zainab tayi still tana yar dariya hannunta ruk'e da cup d'in lemun tayi ma Aunty Mareeya alamar su je da hannu ta nufi doguwar kujerar cikin d'akin tana bata hakurin abunda tayi mata tace it's just for fun Auntyn ma dariya take tace ai ba komai, zama tayi kan kujerar ganin tayi tsaye tace mata ga wuri nan ta zauna, daga d'an can gefenta Aunty ta zauna ta kai cup d'in hannunta baki tay sipping lemun Aunty nata kallonta a cikin ranta tana raya sai kace ba ita ta haifi Sameer ba don sam jikinta bai nuna hakan ba, d'aura cup d'in tayi saman d'an table dake a gefen kujerar kafin ta juyo suka had'a ido da Aunty a nutse cikin girma ta fara magana "amm, dama ba wani abu bane inason muyi magana ne akan shiryen shiryen biki nasan kun fara ko?" Da sauri Aunty tace mata eh tuni anata yi, jinjina kai tayi taci gaba "Yayi kyau, game da kaya da za'ayi nike son sanar dake ba'a buk'atar komai don shi wanda zata auran ba zaune yake anan ba koda yaushe, zai tafi da ita can ne kuma yana da gida da komai haka anan ma so ko anyi su ba wani amfani da zasu yi don haka sai a barshi ba sai anyi komai ba wani abu na al'ada da komai dai duk a barshi ayi Addu'ar Allah ya tabbatar da Alkhairi" wani irin dad'i ne ya cika Aunty sai dai bata nuna ba sosae kawae dai faffad'an murmushi tayi tace "Ma sha Allah, Mun gode, mun gode kwarae your Excellency Allah ubangiji ya saka da Alkhairi ya k'ara girma da daukaka, hak'ik'a wannan ya tabbatar da ku d'in masu tausayin talakawa ne kuma duk d'aya kuka d'auke mu da ku, irin ku K'asar mu ke buk'ata ina Addu'ar Allah ubangiji yayi maku President ko mun amfana" wata irin dariya Hajiya Zainab tayi ta amsa da "Ameen ya Rabbi, in Alkhairi ne amman yanzu su Sis ne akan layi sai mu taya su da Addu'a" kai Aunty ta jinjina "Allah ya tabbatar da Alkhairi, ai your Excellency duk d'aya kuke wllh in Allah ya baku K'asar nan tamu nasan zamu more don irin ku take buk'ata bama kamar mu talakawa tabbas zamu ji dad'i, in Allah ya basu suna gamawa sai kuma ku dasa Allah ya amince" fad'ad'a dariyar ta Hajiya Zainab tayi tace mata hakan kuwa bazai zama son kai ba Aunty na dariya tace a'a wllh ai dama Ana cewa da yuyuyu gwamma d'aya kwakkwara jinjina kai Hajiya Zainab tayi tace Allah dai ya tabbatar da Alkhairi ya za6a mana Shuwagabanni nagari Aunty ta amsa da Amin, hannu ta kai ta d'aukko lemunta ta kur6a bayan ta cire Cup d'in cikin girmamawa Aunty Mareeya tace mata ko zata iya kiran Mahaifiyarsu su gaisa ta jinjina mata kai tace eh lafiya lou ai tuni ma yakamata ace sunyi hakan to ita abubuwane ke mata yawa don ko ita Daughter Fauziyya basu ta6a Magana ba sai yau, kiran Maman tasu ta shiga yi bayan ta d'auka suka gaisa ta tambayi ya Abuja da masu jego tace mata duk suna lafiya nan ta sanar mata dama zasu gaisa da Her Excellency ne, cikin alamun rashin fahimta Maman tasu ta tambayi wacece nan ta sanar mata Mahaifiyar wanda Fauziyya zata aura ai tana jin hakan ta yunk'ura dama a kwance take ta tashi zaune ta shiga daidaita zamanta Aunty Mareeya ta k'ara cewa in sun gaisa sai tayi mata godiya don tace ba sai anyi ma Fauziyya komai ba na kayan d'aki, jin hakan yasa Maman tasu kai hannu ta rufe baki alamar Al'ajabi, bayan ta ba Hajiya Zainab wayar cike da girmamawa Maman tasu ta shiga gaishe da ita duk da kuwa ta girmeta nesa ba kusa ba itama Hajiya Zainab a mutunce take gaisawa da ita, sosae Maman tasu tayi mata godiya da kuma Addu'oi fuskarta da murmushi take amsawa, bayan sun gama wayar ne tace ma Aunty Mareeya Shikenan zata iya tafiya in kuma da wani abu sai tayi magana tace mata ba komai wllh ta k'ara mata godiya har zata tashi sai kuma ta dakata cikin yar ina ina tace don Allah in ba damuwa ko zata bata lambar ta don a rink'a gaisawa tace sure bari ta bata ta amshi wayar tata ta rubuta mata daga haka sukai sallama, wurin gadon Aunty ta nufa don tayi ma Mom sallama, da murmushi Mom tace mata har an gama tattaunawar Aunty tace mata eh sai kuma tace "Don Allah Mom a k'ara taya mu godiya wurin Her Excellency tace ba sai anyi ma Fauziyya komai ba naji dad'i wllh Allah ya k'ara maku girma da d'aukaka" tana murmushi ta amsa da Amin tace mata ai ba wani abu bane duk an zama d'aya tayi Addu'ar Allah ya bar zumunci Aunty ta amsa da Amin kafin tayi mata sallama ta tafi. Tana fitowa baya ta tsaya ta shiga kiran Fauziyya, bayan ta d'aga tambayar ta tayi tana ina tace tana a inda suka sauka har ta kwanta ma tace to ta fito waje ta sameta tace to, bada jimawa ba Fauziyyar ta fito tana sanye da kayan bacci riga da wando sai hula a saman kanta, nufo Aunty tayi gabanta har d'an fad'uwa yake don tasan da Maganar cewa Hajiya Zainab na son ganin Auntyn tasan kuma bai wuce game da hakan yasa Auntyn kiranta, tana k'arasawa gabanta kawai sai gani tayi ta rungumota cike da Farinciki take fad'in "Fauziyya ki taya mu murna ance ba sai anyi maki komai ba wllh iya ke suke buk'ata, da sauri Fauzy ta d'ago daga jikinta ta waro ido da tsananin mamaki ta maimaita abunda Auntyn ta fad'a cikin washe baki tace mata Wallahi kuwa yanzun nan ta dawo daga wurin Hajiya Zainab din, nan ta shiga fad'i mata yadda suka tattauna harda gaisawar da sukai da Maman su ta shiga yabonta tana fad'in tana da kirki sosae tayi dacen suruka, shiru Fauzy tay ba baki sai murmushi kawai da take gaba d'aya ganin abubuwan take tamkar a mafarki, "Ya naga kin yi shiru ne, ko baki farinciki bane yanzu fa Shikenan Baba ba sai ya sayar da gonakin shi ba hakan kuwa ai abun murna ne" yar dariya Fauzy tay a sanyaye tace "a'a Aunty naji dad'i sosae wllh, kawai abubuwan ne keta ban mamaki wllh duka yaushe akai Maganar gida yanzu kuma ga wannan", "Ai kinsan haka abun Allah yake lokaci guda yake juya al'amurra, baki ji ana cewa dare d'aya Allah kan yi Bature ba to misalin hakan ne, ai tsakanin mu da Ubangiji wllh sai godiya Yar gidan Hajiya kin tako mana arzuki Allah yasa a wurin bikin wata ma cikin kannanmu ta samo mana wani irin Sameer d'in koma k'anin shi" dariya sosae Fauzy ta saka tana fad'in kai Aunty, "Allah kuwa ai abun fata ne ke baki ji ana cewa da arzuki a garin wasu ba gara a naku a nakun ma a cikin gidan ku duk da bansan ma ko yana da K'ani babba ba k'ilan kuma wannan da na gani lokacin da suka zo shine ke bi mashi shima dai ai lafiya lou don ya isa Aure naga kamar Nameer yake, amman wannan ma anya zai iya Auren talaka shima naga alamun kamar Sameer d'in yake, koda yake shima Sameer d'in ba gashi ya fad'a komar yar manomi ba" Dariya kawai Fauzy ke yi Aunty ta shiga yin godiya ga Allah tana fad'in wllh har ta rasa ina zata sa kanta don farinciki Allah dai ya nuna masu bikin da rai da lafiya dole taci uwar sabada har ta hango shigar da zatayi, dariya kawai Fauzy ke yi suka nufi komawa part d'in da suka sauka, bayan Fauzy ta koma d'aki zama tayi a bakin gado tayi shiru ba komai take tunani ba face Sameer don a yanzu sosae take jin son shi duk in bata ji Muryar shi ba ko sukai Vedio call bata jin dad'i duk da har yanzu d'in ba wata soyayya suke ba amman ba laifi sun fi yin magana yanzu, ji tayi bazata iya kwanciya batare da taji muryar shi ba ta d'ago wayarta ta shiga kiran shi bayan ta yanke ta zauna tana dakon ya biyo kiran...... 95 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ .............Bada jimawa ba sai gashi ya kira, bayan tayi picking a hankali ta gaishe shi da tambayar shi ya aiki, har saida ta d'an lumshe ido Jin muryar shi da ya amsa, shiru tayi tama rasa mi zata ce mashi tana hakan taji yace ya Abuja tana d'an murmushi tace lafiya lou yau anyi suna sai kuma tace mashi har ma sun gaisa da Mom d'in shi taji ya furta Ok, shiru sukai can ya k'ara cewa koda wani abu ne ta d'an tura baki shi haka yake duk ta kira shi tana jin shauk'i sai ya wani kama tambayar ta koda wani abu, Ji tayi ya k'ara cewa inda wani abu ta fad'a mashi ta d'an kara tura baki sai kuma a hankali tace "No, babu komai dama kawai na kira ne in ji mur....." Kasa k'arasawa tayi ta d'an waro ido don bata ta6a ce mashi hakan ba, "ina jin ki" taji ya fad'i hakan, abu ta had'iya kamar ta canza abunda ta fad'an wata zuciyar ta shiga k'arfafa mata gwuiwa ta fad'i mashi hakan, "Dama naji ina son jin voice en ka ne" wani kalan murmushin gefe yay taji yace mi voice en nashi gare shi, d'an Farfar tayi da ido da k'yar ta furta mashi "Yana da dad'in sauraro ne" shiru taji yayi har saida gabanta ya d'an fadi don tasan shi wani lokacin ba'a cika yi mashi gwaninta ba, tambayar ta yay tana ina ne ta bashi amsa da tana a d'akin da suka sauka ya k'ara tambayar ita da waye tace su biyu ne kuma d'ayar bata kaiga shigowa ba taji ya furta Ok suyi Vedio call tace to, lokacin daya maida kiran na gani yana kwance a saman gado yau ma robe ce a jikinshi chest d'in shi a bud'e ya tashi zaune tare da jingina da headboard, bin juna sukai da kallo Fauzy nata mashi d'an murmushi shima yanayin fuskar shi kaman zai murmushin, ganin yanayin idanun shi a lumshe kaman mai jin bacci yasa tace "ko bacci kake ne?" saida ya k'ara lumshe su sannan ya d'an girgiza mata kai, "Naga kaman har ka kwanta" ta k'ara fad'a idanunta cikin nashi yay d'an shiru can ya bata amsa da ya gaji ne yayi tafiya bai dad'e daya dawo ba ta jinjina mashi kai kafin tace "to bari in bar ka ka huta" wani kallo yay mata ya d'an shigar da lip d'in shi na k'asa kafin taji yace har ta gama sauraron muryan nashi ne, yar dariya tayi ta girgiza mashi kai alamar a'a sai kuma tace "to ai kai baka magana sosae" d'an yamutsa baki yay yace mata bai iya bane ta gyad'a kai ta k'ara cewa "in kana so sai in koya maka" murmushin gefen baki yay tare da girgiza kai yace yafi jin dad'in hakan tunda hakan ya sa6a nan ma kai ta gyad'a mashi suka k'ara yin shiru suna kallon juna, "A gida kake ne ko hotel?" shiru kaman bazai bata amsa ba taji yace da wani abu ne ta tambaya da sauri ta girgiza mashi kai "hakanan kawai na tambaya" ta bashi amsa, ce mata yay yana a gidan shi ne ta gyad'a kai sai kuma ta k'ara cewa "kuma kai kad'ai kake zaune?", "Zan zauna da wa?" Ya fad'a, tana murmushi tace "a'a dama ina nufin kai kad'ai ne ba wani wanda ke taya ka zama?" shirun dai yay yana bin ta da ido sai can yace mata yakamata ya samu abokin zama ne tace "kawai naga in kai kad'ai ne kaman kad'aici zai dame ka shiyasa nayi tunanin ko akwai wani da kuke zaune tare" lumshe ido yay tare da d'an girgiza mata kai alamar a'a sai kuma taji yace "akwai wata da zata zo" har saida gaban Fauzy ya fad'i da alamun rashin fahimta tace mashi wata zata zo nan ta zauna ya d'aga mata kai alamar eh, wani irin abu taji ya tokare mata k'irji a zuciyarta ta shiga raya kenan mata suke zuwa suna kwana tare dashi kuma a haka ace bai neman su cab, wani bangaren na zuciyar ta ya raya mata kika san wacece ko yar uwar shi ce, kasa daurewa tayi yana ta kallon ta yanayin fuskarta ya d'an canza tace mashi ita wadda zata zo d'in yar uwar shi ce kawai sai gani tayi ya girgiza mata kai alamar a'a yace kawai zata zo su zauna tare ne ya rage loneliness, abu Fauzy ta had'iya yanayin fuskar ta ya k'ara sauyawa ta koma kallon gefe tana d'an kikkafta idanu, "Any problem?" taji ya fad'i hakan ta juyo suka had'a ido wani irin abu mai zafi take ji a ranta ta bishi da kallo yanayin fuskar ta kaman zata saka kuka, d'age mata gira yay ya k'ara tambayar da matsala ne a sanyaye ta d'aga mashi kai yace miye matsalan to, ce mashi tay kawai taga ya zai kawo wata su zauna bayan ba muharramarshi bace ai yasan hakan ba kyau ko, yanayin yadda tay Maganar da yar shagwaba, d'an murmushi taga yayi yace mata ai kawai zata taya shi zama ne ba wani abu ba, yamutsa fuska Fauzy tay yadda take ji kaman ta saki kuka don tasan ko ba wani abun dole k'ilan bai rasa ta6a wadda zai kawo d'in tunda ance yana yin hakan ita yanzu ma ta fara zargin anya bai wuce hakan, ji tayi idanun ta sun ciko da k'walla kawai sai ta sadda kanta k'asa ta daina barin kallonshi shi kuma yanata kallon ta bayan d'an wani lokaci taji ya kira sunan ta shiru ta d'an yi bata amsa ba, a duniya tana jin ba wanda ya iya kiran sunanta kaman yadda yake yi don sosae yake fitar da ko wane harafi, "ba ki ji na kira ki ba?" Jin ya fad'i hakan yasa ta d'ago ta kalle shi idanunta sun d'an tara k'walla a hakan ma tayi kokarin maida wasu, "baki so tazo ne?" yana mata wani kallo ya tambayi hakan da sauri ta d'aga mashi kai, "Why?" "To ai ba kyau fa hakan kuma nasan ka sani taya wata zata zo ta taya ka zama ina laifin ko abokin ka" cikin yar karyayyar murya ta mai son yin kuka tayi Maganar, shiru yay idonshi cikin nata tana ta yan d'aure dauren fuska can taga yay wani d'an murmushi tare da ta6e baki ganin haka yasa ta maida idonta k'asa kawai sai ji tayi k'walla sun zubo mata sharr kiran sunanta ya k'ara yi ta d'ago saida yay mamakin ganin kwallan duk da bai nuna ba, ce mata yay don wata zata zo ta taya shi zama shine yasa take kuka shiru tay bata ce komai ba tana ta yan kyafcen kyafcen idanu, "In kuma wadda zata zo d'in Wife ena ce shima hakan ba kyau ne?" kaman daga sama taji ya fad'i hakan da sauri ta tsaida idanunta kan shi ya d'age mata gira alamar ta bashi amsa, shiru tayi tana juya abunda ya fad'a a cikin ranta tunanin to wacece Matar tashi ta shiga yi can zuciyarta ta raya mata ita yake nufi ko, sai lokacin ta gane kan Maganar tun daga farko tayi zuru zuru tana kallon shi yana d'an shigar da lip d'inshi na k'asa kafin ya saki yace bata bashi amsa ba, cikin jin yar kunya tace to ai bai fad'i mata hakan yake nufi bane ita tayi tunanin wata ce kawai da ba komai tsakanin su zai kawo, d'an ta6e baki yay kafin yace yar k'arama da ita tasan kishi, Maganar dariya ta bata tasa hannunta daya sha k'unshi ta d'an rufe fuskarta kafin ta cire a d'an shagwabe tace "nifa ba yarinya bace tunda na wuce 20yrs kuma baka ga ba Secondary nike ba, kuma ai ko K'aramin yaro yana kishin abunda yake so" ita kanta ji tayi kawai ta fad'i hakan, hannu ya kai ya d'an shafi beard d'in shi murmushi ya bayyana akan fuskar shi yace mata ashe tana son shi ta d'aga mashi kai yace amman ai bata ta6a fad'i mashi ba tace to ai bata san ko bai son ta fad'i mashi hakan ba yay shiru kawai yana kallonta, tattaro k'warin gwuiwa tayi idonta a cikin nashi ta furta "I love you with all my Heart" gani tayi ya d'an fad'ad'a murmushin da yake tare da d'an ta6e baki yanayin yadda yayin sai taga kaman abunda tace bata yi mashi gwaninta ba, abunda bata sani ba shine sosae yaji dad'in Maganar duk da ba bak'uwa bace a wurin shi kullum mata cikin fad'i mashi Kalmar suke don ko yau an fad'i mashi amman tata sai yaji tayi mashi dad'i shi kanshi yana mamakin kanshi sosae yadda akai Ya fad'a son ta don sosae yake jinta a ran shi (abun daga Allah ne), furta mata Thanks yayi ta d'an yi murmushi sai kuma tace to shi bai ce mata ba still da d'an murmushi a fuskar shi yace ai yayi wannan tun da yazo garin su ta d'an tura mashi baki tace wannan ai dalili ne yasa ya fad'i mata kuma yanzu bata san ya take a wurin shi ba, shiru yay kawai yana kallonta don Maganar tata ta bayyana yarintarta a wurin shi don in bai sonta Maganar auren su zata d'ore ne, d'an yamutsa mashi fuska tayi tace ita bazai fad'i mata ba d'in, "Not now" shine abunda taji ya fad'a ta gyad'a kai, cigaba da kallon juna sukai tana ta mashi murmushi shima fuskar shi a d'an sake can ya kai hannu ya shafi forehead d'in shi bayan ya ciro hannun ya d'an yi yar hamma, tambayar ta yay har yanzu jin muryar nashi bai isheta bane yana son yayi bacci yadda yay Maganar har saida ya bata dariya cikin wasa tace "ai bata isa na in ina jinta ban k'i ma mu kwana ba inata jinta" d'an wara ido yay ya tambayi is she serious ta d'aga mashi kai kafin tace ko ba zai iya kwana yana hira da ita ba , shiru ya d'an yi yana kallonta kafin yace to mi zai sa su kwana suna magana ai sai Maganan ma ta k'are tana yar dariya tace ba gashi yanzu ma sun d'auki lokaci suna hira ba kuma maganan bata k'are ba ai haka hiran love yake in ana yi ba'a gajiya, wani kalan kallo Yay mata yace waye ke yin love d'in ta nuna shi sannan ta nuna kanta wani irin kallo yay mata ya furta dama ashe bata ji ko tana dariya tace a'a ita tana ji ai ba k'arya tayi ba love d'in suke taga ya d'an girgiza kai slowly yace shi bai yin love da yarinya jin Haka yasa ta tura mashi baki kaman zatayi kuka tace Don Allah ita ya daina ce mata yarinya kawai sai gani tay ya saki yar dariya har dimple d'in shi ya d'an lotsa dama ya fahimci bata son ya kira ta da yarinya, bin shi tayi da kallo ko k'yaftawa bata yi can ta furta mashi dariya yana k'ara mashi kyau sosae kawai sai gani tayi ya d'aure fuskar yace ta fara raina shi ko ganin yadda yayi Maganar ne yasa da sauri ta girgiza mashi kai tace "taya zan raina ka bacin kai mutum ne mai girma da daraja a wurina wanda yay man alfarmar da ban ta6a zaton zan samu irinta ba a rayuwata, kullum ina son in gode maka amman na rasa taya zan hakan don Kalmar Thank you isn't enough, but I promise you I will be a devoted wife to you, I will make sure I give you all the happiness a wife can give to her husband in sha Allah, ina baka hak'uri in Maganar dana yi ka d'auka raini ce ba haka bane wllh kawai ina jin dad'in in ka sake man muna magana tunda ba cika yi kake ba" yadda ta k'arasa Maganar kamar zata saki kuka, murmushi taga yayi tare da lumshe mata ido a hankali ya furta mata thanks tare da Fad'in yana mata wasa ne kawai, sosae taji dad'i tana ta murmushi tace to yayi mata fatan Allah ya bata ikon yi mashi abunda tace ya d'aga kai kafin yace hakan itama tace mashi thanks, sigh yay ya furta "My devoted wife pls allow me to sleep na gaji sosae" Dariya Fauzy ta saka jin abunda yace shima yar dariyar yayi tace mashi to ya kwanta saida safe Allah ya tsare mata shi harda cewa yayi mafarkinta ya d'aga mata kai ta d'an d'aga hannu tana mashi bye bye daga haka yay disconnect, bayan sun gama wayar d'age kanshi yay a jikin kan gado yana d'an murmushi wani irin nishad'i yake ji tunda yake hira irin haka da mata bai ta6a jin dad'in wata ba kamar wannan lokaci guda yaji ya k'osa su zama ma'aurata don ta kasance a kusa da shi, itama bayan sun gama fad'awa tay saman gado tana murmushin jin dad'i wani kalan nishad'i na ratsa dukkan jikinta don tunda take dashi basu ta6a yin hira ba haka, lumshe ido tay suffar shi na dawo mata nan ta fara imagination d'in sun zama ma'aurata can ta bud'e idanun da sauri tana yar dariya a fili ta shiga yin godiya ga Allah da wannan babbar ni'imar da yayi mata don ko a iya haka sanin Sameer d'in da tayi tasan ni'ima ce, tana ta tunane tunanen shi a haka bacci ya kwashe ta. Washe gari Misalin k'arfe goma saura masu tafiya nata shiri, bayan Aunty Mareeya ta gama shiryawa ta nufi part d'in su Fatuu, lokacin data je har sunyi wankan safe ta koma ta kwanta saidai ba bacci take ba hira suke da Mino sai Aysha kanwarsu, da sallama ta shigo cikin Bedroom d'in Fatuu na ganinta ta yunk'ura ta tashi zaune tana fad'in sunanta ita kuma tana amsawa tana karasowa wurin gadon, a baki ta zauna Fuskar kowannen su da Murmushi su Mino suka gaishe da ita ta amsa tare da Fad'in har an shirya tace mata eh, gaishe da ita Fatuu tayi ta maido idonta kanta ta amsa tace har anyi wankan safe tace mata eh, kallon su Twins tayi dake cikin gadon su tace suma sun sha wanka suna ta bacci Fatuu tace eh sun sha wankan Kakar su Yadikko Aunty tace ah lalle dole suyi bacci ashe mata ce ta sulle su duk akai yar dariya, tunani Fatuu tay k'ilan ko Maganar da sukai ne tazo fad'i mata tunda dama tace sai tazo Abuja hakan yasa ta kalli Mino da fulatanci tace su d'an basu wuri tace to ta kamo hannun Aysha suka nufi hanyar fita, bayan fitar su ne Aunty Mareeya tace "Yauwa dama kamar kinsan magana nike son muyi duk da dai ma ba wata ta sirri bane ai kan Maganar da muka yi ta gidane, na kira Yayan mu yaje ya samu Baban mu sun tattauna, abunda ke faruwa Zarah gaskiya samun irin gidan da shi Sameer d'in zai so zai yi wuya a garin namu yawancin manyan gidaje duk masu su ne a ciki saidai za'a iya samun sabo wanda ba'a kammala ba sai a ida ginawa to amman irin wannan gaskiya sai a wajen gari haka, to yanzu dai shawarar da aka yanke itace wai ko kawai ayi renovating namu gidan tunda ba laifi d'an babba ne kuma gaskiya ginin shi mai kyau ne don da asali ginin k'asa ne irin na da d'in nan to a hankali lokacin Babanmu na aiki ya fara maida shi na bulon siminti zuwa lokacin daya aje aiki aka gama maida shi gaba d'aya na siminti kinga sai kawai a gyara a yi mashi dai irin adon zamani, kai Fatuu ta jinjina bayan ta gama tace "kuma hakan yayi Aunty Mareeya tunda kun saba da Unguwar gaskiya bazaku ji dad'in barinta ba kuma sai ma a maida shi na bene kawai" d'an zaro ido Aunty tay "na bene kuma Zarah, a'a ba sai anyi wannan uwar dawainiyar ba kar ma aga mun zaqe ki dai fad'a ma mijin naki yadda nace kar ai zancen benen nan" ta k'arasa tana yar dariya Fatun ma ita take yi tace ai da ta bari an fad'i hakan tunda dai yana da halin Aunty Mareeyar ta ce "ke dai kada ayi Maganar benen nan tawajena kinga sun duba mana sosae ban ma fad'i maki ba jiya fa Her Excellency tayi magana dani tace ba sai anyi ma Fauziyya komai ba na aure iya ita suke buk'ata" waro ido tay tace don Allah Aunty tace mata Allah kuwa, sosae Fatuu taji dad'i ta shiga washe baki tana fad'in kamar irin yadda akai mata itama ba'ayi mata komai ba Aunty tace ai yawanci Kusan duk kaddarar su daya da Fauziyya shiyasa Allah ya had'a su Fatuu tace hakane tay fatan Allah ya nuna masu bikin Aunty tace "Amin ya Rabbi, ai wllh a k'agare nike da inga anyi bikin nan ai dole ma ne muci uwar sabada bayan mun yi godiya ga ubangiji" dariya sosae Fatuu ke yi, bayan ta tsagaita tace "wai Aunty ina wannan mayaudarin daya yaudari Fauzy ya kuwa san da Maganar zata yi aure?" "Oho, wama yasan duniyar da yake nasan gaskiya bai san da Maganar ba don kinsan fa Babanmu ya hana a bud'e Maganar yace a bari sai komai ya tabbata amman yanzu nasan da an fara aikin gidan zaki ga abun ya bayyana" jinjina kai Fatuu tay tace zata so taga fuskar shi ranar daya ji Maganar Aunty tay dariya tace shegen k'ilan har ciwon zuciya sai ya kama shi, "Yauwa ina son dama in yi maki magana kan gyaran jiki kinsan fa jinin haihuwa na lalata duk wani shiri na jiki don haka dole sai kin k'ara yin sabon gyara" da sauri Fatuu tace eh dama tana son yi mata magana akan hakan, tambayar ta Aunty tay ai har yanzu jinin na zuwa ko tace mata eh ta sake tambayar ta yaushe zasu dawo Katsina ne tunda gama jarabawar su ta k'arshe ta taho tace sunyi magana da Ya Haisam kan hakan bada jimawa ba zata dawo Aunty tace "to abunda za'ai yanzu da mun koma zan tanadar maki masu kyau dama akwai wanda nasa za'a kawo ma Fauziyya daga Nijar don har yanzu ban fara bata komai ba Saboda kinsan in akwae k'ananun shekaru to ba buk'atar asha abubuwa sosae k'arshe yazo ya damu mutum shiyasa na bari sai gab da bikin amman dai ina bata nama mai romo sosae haka su fruit da fresh milk sosae nike sata tana ci Mino ma yakamata ace zuwa yanzu ana bata su sosae duk da dai bansan ko ana hakan ba amman dai zan ma gwaggo magana zuwa lokacin da za'a fara basu magungunan, shiri na musamman za'a yi masu in sha Allah", Fatuu na dariya tace "shiyasa nike son ki Auntyn mu" itama dariyar take tace "ai bani da burin daya wuce inga kun kama mazajen ku gam gam wllh kuma ta wannan hanyar ne kawai in kuma aka had'a da biyayya ai magana ta k'are" kai Fatuu ta d'aga ta k'ara cewa "in dai kinga alamun ba nan kusa zaku koma ba to ki man magana sai in aiko maki dasu nan kema kuma sai ki dage da cin abubuwan dana lissafa kinga ma har twins d'in mu sun amfana suma tunda naga kaman kina da kyaun ruwan nono don cikin sati d'aya kinga Tubarkallah sun k'ara girma wllh" amsa mata tayi da to suka d'an k'ara yin hira kafin Aunty ta mik'e tace yadda sukai da Haisam sai ta sanar mata tace to in sha Allah yanzu bada dad'ewa bama zata yi mashi Maganar. Misalin k'arfe goma da rabi duk masu tafiya suka firfito lokacin tuni su Hajiya Zainab sun tafi harda Mahaifiyar su da yan'uwanta yan Ethiopia suka tafi can Nasarawa haka su Hajiya Maryam ma Farha harda musayar lambar waya ita da Fatuu don Hajiya saida ta k'ara masu fad'a da Nasiha kan rashin shirin da suke ta nuna masu duka duniyar nawa take, dama su Yadikko driver da ya kawo su ne zai mayar dasu shi dai Kamalu Katsina zai wuce dama da shirin hakan ya taho don sun gama magana da Kawu Amadu zai koma can shima yaci gaba da karatu Saboda yanata zama ba karatun tun bayan daya gama Secondary, yan d'aura ne suka fara tafiya gaba d'aya su Mom aka fito yi ma su gwaggo rakiya driver su Yadikko nan cikin harabar gidan ya shigo Haisam yaje bayan sun gaisa ya tambayi yadda aka yi dashi zai kawo su ya kuma maida su cikin washe baki driver d'in yace ai shi Abokin Mahaifin ita mai jego d'in ne to yadda sukai ya zuba mashi mai ne zai kawo su ya koma dasu sannan sai ya Sallame shi Haisam d'in ya tambaye shi nawa ne kud'in sallamar yanata washe baki yace mashi ai ko nawa ne aka bashi lafiya lou tunda dai duk abu na gida ne, kud'i masu yawa ya bashi yana ta godiya da sa Albarka sai daga baya ma ya gane shine Mijin inna wuron suma su Yadikkon saida ya basu kud'i wai susha ruwa a hanya su Yaya ana ta washe baki ana godiya, su Gwaggo ma saida ya basu kud'in dama da zasu zo saida ya tura ma Abbas da Tk kud'in mai, Gwaggo da Aunty Mareeya suna ta ya barshi don Allah shida yay hidima yana murmushi yace masu ba wani abu, Nameer na lik'e da Mino sai shagwaba yake mata wai dama ace Shikenan tazo bazata koma ba tana ta murmushi ita kanta ji take kamar kar su rabu ba kamar yanzu da taga ya wani k'ara yin Fresh, sallama suka shiga yi ma juna su Mom da Hajiya nata masu godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci duk suka shishshige cikin Mota Abbas ne ya d'an d'aga murya yace ma Mino in sun gama shan soyayyar ta taho su tafi in kuma su barta anan to su Mom duk sukai dariya Hajiya tace ai in sun bartan daidai kenan kawai sai a d'aura aure ya wuce da ita ba shikenan ba ita kuwa Mino kunya ce ta kamata, daga baya dai duk suka shishshiga ana ta d'aga ma juna hannu a tare Motocin suka tafi sai fatan Allah ya kai su lafiya sai kuma an sake had'uwa bikin su Mino da Aunty Laila. Misalin k'arfe biyun rana lokacin Aunty ta dawo daga aiki don bata nan yan tafiya suka tafi bayan ta kimtsa ta nufi part d'in su Fatuu don duk su Aunty Laila na can harda Fanan anan ma suka ci abincin rana gaba dayansu don yaran gidan k'in zuwa School sukai wai gajiyar suna bata sake su ba, tana shiga duk suka yi mata Welcome kowa yana murmushi haka itama shi take masu ta nufi kujera tana ruk'e da wasu Manyan fararen ledoji masu d'auke da tambari ta zauna Jidderh ce ta tambayeta ta zubo mata Abinci tace eh ba da yawa ba ta d'an ci wani a wurin aiki tace to ta fita, bayan ta gama cin Abincin an saka su Yasmeen sun gyara d'akin Aunty ta d'ago jakar ta mik'a ma Fatuu tace gashi nan tayi amfani dasu ta d'ago d'ayar itama m'ika ma Fanan tace d'ayar Momyn twins itama gashi a tare duk suka bud'e, wasu had'addun laces ne kowa guda d'aya sai kuma manyan atamfofi na Fatuu guda biyu ita kuma Fanan guda d'aya, nan fa aka shiga yi ma Aunty godiya sosae Fanan taji dad'in hakan da tayi mata itama tayi mata godiya ta mik'e da sauri tana ruk'e da jaririn ta nufi hanyar fita tana fad'in bari ta je ta gwado ma Hajiya anata mata dariya don kowa ya fahimci taji dad'in kyautar, bata dad'e sosae ba ta dawo tana ruk'e da ledar cikin washe baki tace Hajiya tace ayi mata godiya sai ta shigo zata k'ara mata Aunty dake dariya tace sai kace wani abu Fanan d'in tace aikuwa wani abu ne don babbar kyauta ce nan suka cigaba da yin fira har aka yi La'asar, bayan sallar ne Fatuu tace ma Aunty Laila don Allah ta tayata su duba kayan da aka samu tace to nan aka shiga fiddo kayayyakin kili guda harda Fanan aka shiga bubbud'awa ana shirya su, Kusan raba kayan Fatuu tay wanda nata ne taba Fanan wai ta bata aikuwa tace wllh bazata amsa ba sai kace ita tayi mata nak'udar, K'arshe da k'yar ta amshi wata doguwar riga cikin wanda kakar su Haisam ta kawo mata daga Qatar tare da kayan jarirai had'add'un gaske duk da haka saida Fatuu ta k'ara mata da wata babbar atamfa ta rok'e ta kan ta amsa sannan ta amsa tayi mata godiya sosae, wasu masu yawa ta k'ara warewa tace ma Aunty Laila gashi ta kai ma Mom suyi amfani da su itama harda rok'onta Laila d'in ta d'an waro ido tace don me zata basu kaya haka ta marairaice mata, yar dariya tayi ta gyad'a kai tace tunda sak'o ne ta bata bari ta kai ma Mom d'in amman ashawarce ma da ta bar kayanta Fatuun ta girgiza mata kai tace Don Allah ta saka Mom d'in ta amsa, Bayan sun gama shirya kayan ta d'aukko jakar da kud'i suke suma ta fara kokarin fiddo su Laila dake kallonta tace mi kuma za'ai dasu tace mata wai su k'irga wani kallo tay mata tace har tama saka zata harareta tana matsayin Yayarta to shima k'irga kud'in aiki ne da bazata k'irga abunta ba, dole Laila tayi mata ta maida kud'in data fiddo bayan sun gama komai ta d'auki wanda ta basu ta tafi. Bayan Sallar la'asar Fatuu na cikin yin chat saman gado Fanan ma na daga gefenta ta tasa su twins gaba saiga Mom ta shigo Laila na biye da ita d'auke da kayan da ta kai mata tana yar dariya, a saman gado Mom ta sakata ta d'aura kayan kafin ta zauna a sanyaye Fatuu ta gaishe da ita ta masa kafin tace ga kayanta nan ta maido mata a ina ake haka kawai ta kwashi uban kaya ta basu sai kace su aka ba, marairaicewa Fatuu tay ta shiga yi mata Magiya Mom d'in tace bafa za'a amsa ba gara ma kar ta wahalar da kanta, suna haka Aunty ta shigo ganin drama d'in da suke yasa ta zauna tana dariya Mom na cema Fatuu ko tayi Kuka ba za'a amshi kayan ba, tambayar abunda ke faruwa Aunty tayi Mom ta fad'i mata tare da nuna mata kayan ta kalli Fatun tace "to daughter taya za'ai hakan ai kayan ki ne ko kiyi amfani da abun ki" murya kamar zata yi kuka tace to ai kayan da yawa ya zatayi da su Mom ce tace ba tana da yan'uwa ba sai ta babbasu suma suci albarkacin twins suyi masu Addu'a, "Amman Mom kuma ai yan'uwan nawa ne ko", tana yin Maganar k'walla suka zubo mata Mom ta d'an bud'e ido tace miye abun kuka anan, Aunty ce tace yanzu dai tunda hakane Shikenan a d'an d'auka suma suci albarkacin twins d'in tunda haka take so, ba wasu kaya masu yawa ba suka d'auka duk da haka Fatun taji dad'i hannu ta kai ta d'aukko jakar da kud'i suke Laila na ganin haka tace "Mom see, wai kud'in ma sai an gani" wani kallo mai kaman harara Mom d'in tayi mata Fatun ta marairaice fuska tana niyyar yin Magana Mom tace "Daughter yaushe muka fara wasa irin wannan ne?" abu Fatuu ta had'iya ta d'an girgiza mata kai kamar zatayi kuka ta bata hak'uri tace dama tana son nuna masu ne Mom d'in tace mata ba buk'ata komai ta gani nata ne tayi duk abunda take so da su ta d'aga mata kai, abunda Mom ta ruk'o a hannunta ta mik'a ma Fatun tace to itama ga nata tunda ta kar6i nata Fatuu tabi yan kunnan zinari da take Mik'o mata da kallo Mom tace mata ta amsa mana ta mik'a hannu ta amsa gudun kada ta k'ara cewa ta raina ta, kallon Fanan tayi itama ta mik'a mata zoben zinarin tace itama ga nata ta waro ido tare da d'an bud'e baki cike da mamaki tace itama harda ita ta d'aga mata kai kawai sai ta matso ta rungume Mom d'in tana mata godiya su Aunty ma da Fatuu sukai mata godiya, bayan Fanan ta saketa ta saukko daga saman gadon ta nufi hanyar fita tace shima bari ta nuno ma Hajiya. A Ranar da daddare duk suna a part d'in Fatun harda Hajiya da Haisam da Nameer gaba d'aya yan gidan anata hira ana cin naman suna ana korawa da lemu Aunty na ta cema su Jidderh wllh su bi a hankali ganin yadda suke ta d'irka kamar sun samu Abinci wai naman dad'i yafi wanda aka saba soya masu Hajiya tace ai haka naman suna yake, suna anan Dad ya dawo shima ya nufo nan part d'in su twins suka mik'e da gudu suna mashi oyoyo ya ruk'e su ganin bakin su jage jage da mai yace miye suke ci haka a tare suka ce naman suna ne ya d'an waro ido yace shine ko a tuna dashi suka ce ai akwai da yawa sosae ya d'aga kai suka nufo ciki, sannu da zuwa aka shiga yi mashi yana amsawa bayan ya zauna ya gaishe da Hajiya tayi mashi an dawo lafiya ya amsa Jidderh tace a zubo mashi naman shima yace anya dare ne fa suma suci a hankali in mutum yaci ya kwanta yana iya samun matsala Aunty Laila dake taunar naman tace ai zasu sha flagyl kafin su kwanta duk aka saka dariya, shima d'an kad'an yasa aka bashi ya fara ci abun gwanin sha'awa k'arshe dai saida Aunty tasa aka d'auke naman daga falon, Bayan Dad ya gama ne aka bashi tissue ya goge hannun shi ya kai hannu cikin aljihun rigar yar cikin shi dama saida yaje part d'in shi ya cire babbar rigar sannan ya nufo nan, wasu takardu ya fiddo guda biyu ya mik'a ma Mom yace taba Daughter gashi nan takardun gidaje ne guda biyu a cikin na Estate d'in shi yaba Abokanshi su daga yanzu kud'in hayar su nasu ne a bud'a masu Account a rink'a saka masu, wata irin shewar farinciki su Aunty Laila da Jidderh sukai su Mom da Aunty ma sai dariyar farinciki suke suna yi ma Dad d'in godiya da Allah ya kara girma da Arzuki, bayan an mik'a ma Fatuu takardun a sanyaye tayi mashi godiya da Addu'ar Allah ya k'ara girma da daukaka yanata amsawa, Hajiya ce tace wato salon sabon Angonta yaga bata yi farinciki da shi ba shiyasa zai masu wannan babbar kyauta haka to itama baza'a barta a baya ba ta basu d'aya daga cikin filayenta na Katsina wannan karon ihun murna Aunty Laila ta saka tana fad'in kaga yara masu k'ashin arzuki daga zuwan su duniya har sun zama masu arzuki, "Wai to sai ba yaran kyauta kuke ita Mom d'in tasu fa?" Jidderh ce ta fad'a tana tura baki idonta akan Dad d'in su yana yar dariya yace yana sane da ita in sha Allah ita da yar'uwarta zasu je Hajjin bana amman tunda da sauran lokaci zasu fara zuwa Umra gaba d'aya gidan zo kaga farinciki su twins harda rawa suna fad'in dama an dad'e ba'a je dasu ba, Mom ce tace Shikenan ma in suka je sai a biya Qatar a gaido Abie Dad yace ba matsala ya kalli Fatuu yafe ta fad'i daga nan in akwai wata k'asa da take son zuwa Albarkacin su twins sai a wuce tayi shiru tana ta murmushi tama rasa mi zata ce don gaba d'aya bakin ta ya mutu su Aunty Laila na ta fad'i don Allah, Haisam ne yace sun kusa fara Final Exams d'in su ne bai fi nan da 2 Months ba Dad na jin hakan yace to a tsaya daga Qatar d'in, kallon Hajiya Jidderh tayi tace to itama bata ba Aunty Fanan da Fatuu kyautar ba ta d'an kwa6e fuska tace dole sai ta basu suma Aunty Laila tace eh gaskiya tace to ta basu kowa kaza da zakara suyi kiwo gaba d'aya aka saka dariya Fanan tace ta gode zata tafi US dasu tayi kiwon acan Aunty Laila tace gaskiya kyautar tayi kad'an Hajiya ta d'an harareta tace to ina laifi tasan Arzikin da zasu iya janyo masu Jidderh tace duk da haka dai gaskiya sunyi kad'an, "To tunda had'in kai za'a nuna man Shikenan na basu kowa tunkiya da rago daga haka bazan k'ara ba" dariya aka fashe da ita Dad yace ai wannan ma ta basu mai yawa don tushen garke ne gaba d'aya sukai godiya, "to wai shi Angon jegon fa banga an bashi komai ba" Aunty ta fad'a Dad na dariya yace "k'yale wannan mai kud'i ne shi" tace duk da haka dai shima a bashi gaskiya Arzik'in su twins Dad d'in ya kalle shi yace yana son wani abu ne a hankali ya girgiza kai yana murmushi yace a'a an gode da wanda aka bada Allah ya k'ara lafiya da Arziki suka amsa da Amin, Dad ya kalli Aunty yace to taji dai bai son komai tana yar dariya tace to ai ba haka yakamata a yi mashi ba shima sai a bashi kawai ba ai mashi tayin rowa ba duk akayi dariya Hajiya tace to ai shima ba za'a je dashi Umra d'in ba Aunty Laila tace wannan to na Dad ne saura ita ta bashi kyautar tace Shikenan shi ta bashi kaza da zakaran da suka guda duk aka kwashe da dariya harda Haisam d'in abun gwanin nishad'i haka suka cigaba da yin firar su lokacin Dad ya tambayi Hajiya nan da 2 weeks lafiya lou za'a iya yin tafiya da yaran Saboda suje su dawo Daughter ta koma School tace mashi eh yace to sai su shirya duk aka k'ara yi mashi godiya. Bayan sati guda da yin suna yan Ethiopia suka koma lokacin saura sati d'aya su Fatuu su tafi Umra, sosae take samun kulawa gaba d'aya ita da yaran sunyi 6ul6ul dasu gwanin sha'awa, ana saura kwana ukku su tafi Hajiya tace mata in akwae kayan da za'a tafin mata dasu Katsina ta bada tunda da sun dawo zasu wuce can tace to. Lokacin da suka je Umra Fatuu harda kukanta na farinciki ganin gata ga ka'aba, sosae tayi Addu'oi daga cikin wanda tafi yi ma Addu'a akwae Mahaifiyarta da Mahaifinta sai mijinta da gwaggo, Hajiyar Sanata da kuma iyalin Sanata d'in sai sauran yan'uwanta da Abokan Arzuki harda Haulat bata manta da ita ba tayi mata Addu'ar Allah ya bata miji wanda zai kula da rayuwar ta da yarinyar ta, Satin su guda suka wuce Qatar sosae aka karramasu ba kamar Fatuu da su twins sai faman nan nan ake dasu gidan Yaya Othman d'in da suka sauka shi kan shi abun kallo ne don duniya ce mai zaman kanta ko ina walwali ke tashi kai kace da zallar gold aka yi gidan Fatuu ta girgiza da ganin gidan don bata ta6a zaton a rayuwarta zata ganta a cikin gida ba irin wannan, sun zaga garin sun sha hotuna sosae garin da suka je ya had'u Over don shine babban birnin su wato Doha, Birni ne na zamani kuma na duniya mai kyawun sararin samaniya, akwae gidajen tarihi da abubuwan jan hankali na al'adu kuma babbar cibiya ce ta kasuwanci da yawon bude ido na duniya, nan ma sati guda sukai suka juyo Abuja Haisam da Fanan kuma suka wuce US, kwanan su biyu da dawowa suka dawo Katsina, Ranar da suka dawo da daddare Fatuu ta nufi gidan su Haulat tare da Mino ta goya mata yaro guda don tana nan ta dawo anan take takaba don tun bayan rasuwar mijin nata bata jin dad'i hakan yasa aka dawo da ita nan yanzu ma har ta kusa gama takabar, lokacin da suka ga juna ita da Fatuu kuka sukai ta yi innar su na basu hakuri tana ruk'e da yaran tayi ma Fatuu barka tace taso tazo Abuja suna to Saboda yanayin da haulat take ciki yasa bata zo ba Fatun tace mata ba komai itama tana ruk'e da d'iyar Haulat, sosae tausayin Haulat ya kamata ganin yadda ta rame tana kwalla ta shiga rarrashinta kan ta rage damuwa tayi hak'uri tay d'an murmushi tace wllh ta bari ta rungumi kaddararta kawai abun ne wani lokacin in ya taso mata sai taji damuwa, k'arfafa mata gwuiwa ta shiga yi tace in sha Allahu zata samu miji wanda zai kula da ita ya ruk'e Umma Salma tamkar d'iyar shi a sanyaye Haulat d'in tace Allah yasa amman ita yanzu ma gaba d'aya auren ya fitar mata a rai Fatuu tace ta daina cewa hakan don zai zama tamkar bata yarda da kaddarar ta ba ta mik'a komai ga Allah in sha Allahu zai ji6anci lamuranta tace Allah yasa, anan ta kira Haisam ta bashi Haulat d'in ya k'ara mata gaisuwa, sosae Haulat ta yaba da su twins haka ma innar su sai faman fad'in Tubarkallah take daga baya sukai masu sallama suka tafi, Bayan komawar su gida Fatuu ta kira Aunty Mareeya ta sanar mata jini ya d'auke mata tun kafin su tafi Umra Saboda tafiyar yasa bata sanar mata ba amman ta fara amfani da wasu magungunan da Yadikko ta kawo mata tace to zata ba Fauzy sak'o ta kawo mata, washe garin da suka dawo ne Hajiya tayi ma Saude Magana akan ko za'a samo ma Fateema mai raino da zata rink'a taimaka mata Saboda zuwa Makaranta tace to za'a samu zata yi magana can gidan su, a Ranar da yamma Fatuu ta had'a uban kaya su atamfofi da lace harda dogayen riguna wasu daga cikin nata da tasan zasu yi ma Haulat da kayan shafa harda naman suna da kuma kud'i dubu hamsin taba Mino tace ta kai mata tace mata ta fara amfani dasu, lokacin da takai kayan Haulat kuka ta saka a haka cikin kukan ta kira Fatun a waya tace ya zatai mata wannan uwar dawainiyar tace mata ba komai tana dasu ne ita dai fatanta ta kwantar da hankalinta ta daina damuwa tace in sha Allahu ta daina, har gida washe gari innar su tazo tayi mata godiya harda rigunan jarirai ta kawo ma su twins taje tayi ma Hajiya barka anan take ce ma innar tasu ashe Haulat d'in gida ta dawo ta fad'i mata bata jin dad'i ne gashi ta saka damuwa a rai cike da tausayawa Hajiya tace ai dole ne don rashin miji ba K'aramin rashi bane tace ayi mata gaisuwa sai tazo innar tayi mata godiya kafin ta tafi. Kamar yadda Hajiya tace taje tayi ma Haulat d'in gaisuwa tare da Saude suka je bayan sun dawo ne tayi masu Aiken kayan abinci masu yawa, sosae Fatuu keta gyara kanta bayan Aunty ta aiko mata da magungunan Saude kuma ta samo mata mai tayata rainon su twins tare suke zuwa Makaranta da ita, sosae take missing d'in Haisam sai bayan wata d'aya da dawowar su sannan yazo suka shiga shan sabon Amarci lokacin ne yayi ma Sameer magana kan zuwa Funtua gaishe da iyayen Fauzy da yake yana a K'asar, ya amince zai je harda cewa jirgi zasu hau ko Haisam na dariya yace mashi ai ba Airport acan dole a Mota zasu anan suka tsaida Ranar da zasu Haisam ya fad'i ma Fatuu ita kuma ta kira Aunty Mareeya ta sanar mata aikuwa sosae taji dad'i tace dole zata je don a tarbesu yadda yakamata. Ana saura kwana biyu suje Haisam ya tafi Abuja don daga can zasu wuce Aunty kuma washe gari ta tafi Funtua, Ranar da zasu zo ta kama Asabar da wuri suka taho Mota biyu sukai d'aya wadda suke ciki driver na jan su sai kuma d'ayar ta security, gaba d'ayan su farar shadda ce a jikin su anyi masu kalar d'inkin da suka fi so sai baza k'amshi suke k'afafuwan su na sanye da dakakkun takalma haka agogunan hannunsu ba sai na fad'i masu tsada bane yau dai kawunan su sun samu Arzik'in huluna amman shi Sameer bai saka ba tana dai ajiye k'ilan sai sun isa zai saka, duk tafiyar ta fara gundurar Sameer don har Fuskar shi ta nuna tun yana yin shiru har takai ya fara tambayar driver ko sun kusa isa sai yace mashi da saura, Haisam daya lura ran shi ya fara 6aci yana murmushi yace mashi gara ya saba kafin Ranar d'aurin aure ai tun kafin ya rufe baki ya fara girgiza mashi kai yace bazai k'ara wannan tafiyar ba Haisam da still Murmushi yake yace to ya za'ai Ranar d'aurin auren fuska a tamke yace oho shidai bazai zo a Mota ba, lokacin da suka iso garin gaba d'aya ran Sameer ya gama 6aci Haisam ya fara bashi hak'uri yana nuna mashi ai sun iso ya yamutsa fuska yace to mi akai tunda zasu koma, Yaya Mubarak ya kira ya sanar da shi gasu sun shigo gari yace Ok yana fara mashi bayanin inda zasu nufo su had'e ya mik'a ma driver wayar yaci gaba da mashi bayani, sai faman bin garin Sameer yake da kallo haka Haisam ba laifi Sameer yaga ba k'auye bane kamar yadda ya zata, lokacin da suka had'e da Yaya Mubarak yana ganin Motocin ya gane sune yay ma driver d'in alamun ya tsaya, nufar Motocin yay da sauri aka sauke mashi glass cikin girmamawa ya gaishe dasu tare da yi masu sannu da zuwa Haisam ne ke amsawa shi kuwa Sameer tunda ya d'aga mashi kai sau d'aya bai k'ara ba balle ya tanka, bayan sun gama gaisawar yace ma driver d'in ya biyo shi a baya ya koma Motar shi suka tafi, lokacin da suka k'arasa anata aikin gyaran gidan don Kusan ma an kusa gamawa don an d'aura bene komai dai ya kusa kammaluwa, a falon Baban su aka sauke su wanda tuni an canza mashi fasali don shi yace ko angama ginin bazai hau sama ba dama kuma da k'asan aka fara gyaran, sosae aka nuna farincikin zuwan nasu duk samarin gidan da yan'uwan mahaifin nasu harda shi mahaifin nasu sun zo sun gaisa dasu sai basu girma ake ba laifi Sameer d'in ya d'an saki fuska amman kowa daya gan su yake gane shine wanda Fauziyya zata aura don sun san labarin shi, Aunty Mareeya na a falon tana gabatar masu dasu da kuma dangantakar su haka suma su Haisam d'in tana gabatar masu da dangin nasu nan aka shiga yi masu godiya yawanci dai Haisam ne ke magana, koda Aunty tayi masu Maganar Abinci cewa sukai a k'oshe suke sai da ta matsa masu sannan suka d'an ci wanda ta kawo masu kan c-table dama tasan ana iya yin hakan shiyasa basu wani yi Abinci masu yawa ba, bayan sun gama zama tayi tana k'ara yi masu sannu da zuwa da godiya ta lura da yanayin Sameer duk da tasan halin shi tana murmushi tace "K'ani na ansha gajiyar Mota ko" kallon Sameer d'in Haisam yayi yana murmushi shima ya d'an yi kad'an ba tare daya ce komai ba, basu yi awa da zuwa ba suka ce zasu tafi lokacin iyayensu sun dawo cikin parlon aka ce basu bari su k'ara hutawa Haisam yace Saboda hanya kada yamma tayi masu, godiya Haisam ya shiga yi masu na auren da aka basu sai lokacin Sameer ya bud'e baki yay godiyar shima duk suka ce ba komai ai sune da Godiya anata faman dawainiya dasu, a tare gaba d'aya aka fito yi masu rakiya harda Aunty da k'annansu mata harda masu aure da suka zo su Fareeda Mahaifiyarsu ce kawai bata fito ba amman har gwaggo ma ta fito rako su, har zasu shiga Mota Sameer ya dakata ya kira Yaya Mubarak da sauri ya nufo shi, magana yayi mashi saidai ni kaina banji mi yace mashi ba kawai dai sunga Yaya Mubarak d'in nata d'aga kai daga baya ya juya ya shige security ya rufe mashi k'opar anata d'aga masu hannu suka tafi, bayan tafiyar su cikin parlon suka koma gaba daya aka dasa hirar su Haisam d'in sai faman yaba kyaun su ake ana fad'in Fauziyya tayi dace ta ko ina Mijinta yayi k'anin mahaifin su ne yace saidai yaga kaman magana na mashi wahala ga Fauziyya da surutu ya kenan zasu yi zaman auren duk akayi dariya Aunty Mareeya tace haka yake amman in yaso yana d'an yi, Yaya Mubarak ne yayi masu bayanin kiran shi da yayi yace Maganar aikin da ake ne ya tambaye shi ko da matsala sannan ya tambaye shi anan akwae furniture masu kyau yace mashi eh to yanzu yace in aka k'arasa aikin aje a za6i wanda ake su da za'a saka a ko ina sai yayi mashi magana nan fa aka shiga fad'in Ma sha Allah wannan hidima haka abu yayi kyau saidai iyayen Fauzy sun ma kasa magana don Al'amarin ya girmi tunanin su, bayan su Aunty Mareeya da sauran yan gidan mata sun koma part d'in da aka ware masu suke zaune Saboda aikin da ake nan suka dasa hirar su Haisam kowa na fad'in wanda yafi mata wasu suce Haisam yafi burge su wasu suce dukkan su sun yi don suna kama ai sosae, "Ni wllh wannan farin yafi burge ni da yanzu zai ce yana sona da gudu zan yarda ni koma matsayin mai aikin shi ce in dai zai aure ni" wata k'anwar su ce Nusaiba tayi Maganar dama ga yanayin Maganar ta kamar ta sakarkaru aikuwa gaba d'aya aka saka dariya Aunty Mareeya tafi kowa 6a66aka dariyar ta kai hannu ta bugi shoulder d'in ta tana fad'in "Su an Nusi Nusi anga fari rainon Madara da carpet an rud'e ko, wato in zai aure ki to kima fidda rai don wanccan da kike gani ya auru zuciyar shi a gark'ame take da k'aton kwad'o da Zarah ta rufeta da shi kima fidda rai don ba samu zaki ba" tura mata baki Nusaibar tayi tace kaji Aunty Mareeya da mugun fata tasan abun Allah itama yace yana sonta kamar yadda ya faru da Yaya Fauziyya, Mahaifiyar su da tunda suke abun su bata saka masu baki ba sai murmushi kawai tace "aikuwa Nusaiba koda ace hakan ta faru bazaki aure shi ba, baki ji ana fad'in ana barin halak ko don kunya ba kar ki manta matar shi fa itace silar duk wannan Alkhairan dake samun mu" Gwaggo tace gaskiya kam, tura baki Nusaibar tayi ta juyar da kai sai kace Haisam d'in yace yana son ta yadda tayin ne duk ya k'ara basu dariya, "Ni gaskiya na Fauziyya yafi burge ni yanayin kalar fatar shi ina son Namiji haka kawai dai na lura kamar miskili ne na bugawa a Jarida" Fareeda ce tayi Maganar Aunty Mareeya tace bari mijinta ya jita tana dariya tace yo yaji mana daga ta yabi mijin k'anwarta, Ummi ce tace ita gaskiya Haisam yafi tafiya da ita don shima da gani miskili ne ga shi yafi na Fauziyya sakin fuska, ganin abun na niyyar zama gardama yasa gwaggo tace bari ta bambanta masu shi na Fauziyya gaskiya kamar yana da izza ne shine kawai Aunty ta d'aga hannu tace yauwa gwaggo kin gane, lokacin da gwaggo ke magana Yaya Mubarak ya shigo jin abunda take cewa ya sashi yin dariya yana k'ok'arin zama yace ai shi ne zai basu labarin irin izzar Sameer tunda dashi suke Maganar aikin da ake yace "wllh ba K'aramin gasa ni yake ba yasa inta faman jiran ya bani amsa sai ya mula yasha iska sannan shiyasa har nafi son muyi chat duk da shima d'in wani lokacin zai duba amman fa ba lalle in samu amsa a lokacin ba haka dai nike ta bin shi sai kace ba Yayan matar da zai aura ba kuma ko a shekaru da gani na girme mashi sosae" gaba d'aya akai dariya Abubakar Yayan Fauziyya amman Kusan tsaran juna ne da ita yace tabb lalle aiki ya samu Fauziyya kafin ya bata amsa sai ta bushe, Gwaggo dake dariya tace ai bata anan tunda yana sonta ita zai iya sakar mata baki, haka dai sukai ta hira kan su Haisam d'in daga baya Yaya Mubarak yay masu sallama zai tafi su Aunty sukai mashi godiya, lokacin da mahaifin su Fauzy ya rako yan'uwan shi zasu tafi suka tsaya suna yin bankwana yana k'ara masu godiya wani makwabcin shi ya fito daga cikin gida ganin shi yasa shi nufo shi har zai juya ya koma ciki ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunan shi "Barka Alhaji Rufa'i" dakatawa yay ya juyo ganin shi yasa shi yin murmushi yace "barka dai Alhaji Salisu" hannu ya bashi suka gaisa cikin yar in ina yaci gaba "dama Alhaji Rufa'i ina son tambayar ka ne amman ina gudun kaga kaman na saka maka ido shiyasa nayi shiru to yau dai naga ya dace in maka magana a matsayin mu na makwabta, yan kwanakin baya zuwa yanzu abubuwa na ta faruwa a gidan ka da suke ta jan hankalin mu muna ta ganin anayin bak'i wanda da gani manyan mutane ne tunda harda jami'an tsaro suke zuwa don ko na d'azun da suka zo suma naga haka ga kuma aiki da ya taso gadan gadan cikin d'an kankanin lokaci har an kusa kammalawa to gaskiya hakan yaja Hankulan mu sosae don bazan 6oye maka ba anata magana kan hakan shine na yanke in tambaya ko wani abun Alkhairin ne ya same ka bamu sani ba tunda ba alamun wani abun tashin hankali, amman dai kayi hakuri in nayi maka katsalandan don Allah" fad'ad'a murmushin shi Baban su Fauzy yayi yace mashi ko d'aya wllh dama yana niyyar ya sanar dasu to da rabon shi zai riga shi yin magana, nan ya fad'i mashi abunda ke faruwa tsabar mamaki bakin Alhaji Salisu kasa rufuwa yay yace yanzu Fauziyya dai yar wurin shi daya sani ce zata auri d'an gwamna yace mashi eh, "Yanzu Alhaji Rufa'i ana tare irin wannan abun Alkhairin ya same ka amman ace har tsawon wannan lokacin bamu sani ba, haba Alhaji ko dai baka d'auke mu yadda muka d'auke ka ba ko kuma munyi maka wani abun daya sa haka ne" ya fad'a cikin d'an kwantar da murya Baban su Fauzy nata Murmushi yace mashi ko d'aya kawai dai bai bari abun ya bayyana bane sai ya tabbata tukun tunda yasan sha'anin aure yadda yake, da sauri Alhaji Salisun yace kuma hakane hakan da yayi daidai ne saboda yan tsirku da mahassada to shidai wllh tllh ya taya shi murna sosae Allah ya tabbatar da Alkhairi ya nuna masu, Baban su Fauzy yace Amin shi bama don haka yasa ya 6oye ba kawai dai yafi son abun sai ya tabbata ne. Suna yin sallama Alhaji salisun ya nufi komawa cikin gidan shi wanda da fita ya fito zaiyi, tsaye matan shi sukai fuskar su d'auke da Al'ajabi da yana fad'a masu zancen haka ma yaran shi da suka ji zancen sai faman maimaita Fauziyya zata auri d'an gwamna suke, d'ayar matar shi ce ta buga hannu tace haba biri yayi kama da mutum ashe shiyasa abubuwa keta faruwa suke ganin dankara dankaran Motoci na zuwa gidan, d'ayar matar da bakinta ya gama mutuwa da tsananin mamaki ta tambayi maigidan nasu wai ya akai Fauziyyar ta had'u da yaron gwamna har yace yana sonta ya watsa hannu yace Allah nasani amman shima dai yaji mamakin abun ba kad'an ba, juyawa tayi zata nufi d'akinta tana fad'in bari taje gidan ya dakatar da ita yace ta bari ba yanzu ba don duk yan gidan na nan, d'aya daga cikin yaran shi ne yace ashe shiyasa d'azun yaga had'add'un motoci sun zo harda jami'ai mahaifin nasu yace eh wai shine yazo, kan kace mi matar shi daya hana zuwa har ta fita ta fara fad'a ma sauran makwabta kowa tsananin mamakin jin hakan ya yi. Bayan Yaya Mubarak ya fito saida ya biya wurin mahaifin su don yayi mashi sallama anan yasa shi ya zauna yace yana son zasu yi magana, bayan ya zauna ne a nutse ya fara mashi magana kan abunda suka tattauna da Sameer na furniture yace shi yana ganin da ya bar wad'annan tunda akwae kud'i a hannun su sai suyi kawai hidiman ta isa haka iya wannan ginin da ake masu ba K'aramin kud'i ake kashewa ba, nisawa Yaya Mubarak yayi shima a nutse yace to amman yana iya ganin ya nuna zai yi abu an hana shi don haka shi yana ganin ayi yadda yace d'in sai a fad'i mashi kud'i ba masu yawa ba in ya bada sai a had'a a zuba sababbin furniture d'in in ma ta kama sai a had'a da na gidan a sayar Alhajin nasu yar dariya yayi yace ko dai tsoron mijin Fauziyyar yake don yaga ba alamun wasa a tattare dashi shima dariyar yayi yace a'a kawai dai abunda ya sani su mutane irin su basu son a dakatar dasu kan abunda sukai niyya, mahaifin nasu ya jinjina kai yace Shikenan ayi yadda yace amman baza'a saida wasu kaya ba da niyyar a had'a in Sameer d'in ya turo shi ai mashi magana ya bada wasu sai a hada su kuma tsofaffin kayan sai a samu wasu a basu suma su dangwali arzuki ya k'are Maganar da murmushi shima Yaya Mubarak d'in murmushin yake yace to shikenan, addu'ar Allah ya k'ara mashi lafiya yayi ya amsa kafin yace mashi Shikenan zai iya tafiya sukai sallama, zuwa daren Ranar ai duk yan unguwa sun ji zancen auren Fauzyn anata mamaki wasu dai har sun zo jin kwakwaf da sunan fatan Alkhairi, Washe gari Aunty Mareeya zata baro funtuwar ta dawo Katsina. Alhamdulillah su Haisam sun koma Abuja lafiya kwanan Haisam d'aya ya dawo Katsina, bayan dawowar shine shima yaje yayi ma Haulat gaisuwa tare da Fatuu anan ya tambayi Fatuu ta amsar mashi account no d'in Haulat bayan ya fito tace to, saida suka koma gida sannan ya tura mata kud'in dubu d'ari biyar nan ma dai Haulat kuka ta saka da taga sak'on innarsu tace rayuwa kenan Allah yana had'a ka da mutum baka san moriyar da zai maka ba ta shiga tuna ma Haulat lokacin da aka kawo Fatuu da yadda in ta k'ule ta take zuwa tace ma innar tasu ita dai ta gaji da abunda take mata tace mata tayi hak'uri, tana kallon Haulat da murmushi tace mata yau ga ranar hak'urin da tayi da ita nan Haulat d'in na d'an murmushi tana d'aga mata kai a cikin ranta tana ta tuna rayuwar ta da Fatuu ta baya. Daga baya har da kaya masu yawa Fatuu ta siya ma d'iyar Haulat kullum ne sai sunyi waya wani lokacin kuma taje Haulat har Magana tayi mata kan zaryar da take tace mata in bata yi mata ba wa zata mawa, Watan Haisam guda anan sannan ya tafi lokacin Haulat har ta gama takaba su twins kuma watan su ukku amman in ka gansu sai kace sun yi wata biyar yaran Tubarkallah dasu sunyi girma duk inda aka gansu sai an tanka hakan yasa kullum Fatuu cikin yi masu Addu'oi take kamar yadda Hajiya da gwaggo ke yawan fad'i mata ta dage da yi masu Addu'a Saboda bakin mutane gwaggo har ruwan Addu'a da akayi da zam zam ta amso mata tana shafa masu, don ma yaran k'yuyar tsiya garesu iya wanda suke gani koda yaushe suke yarda dasu daga basu ba basu yadda da kowa Fauzy ma dakyar take samu suna yarda ta d'auke su. Satin Haisam guda da tafiya suka fara yin School Final sosae suka dage don daga ita sai council Shikenan, suna cikin yin jarabawar ne Hajiya Zainab ta kira Aunty Mareeya a karo na farko don tun bayan da sukai exchanging number saidai ta gaishe da ita ta chat wani lokacin sai sak'on ma ya dad'e sannan take reply ta nuna mata uzuri yayi mata yawa ne, bayan sun gaisa ne tace mata dama suna son measurements na Fauzy sannan suna neman wata alfarma game da lefen Fauzyn tunda abu bana kusa bane akwae tafiya in akace a kawo kuma sannan in aka d'aura auren sai an kwaso an maido zai zama aiki don haka abunda suke tunanin ayi shine za'a kawo wanda zata yi amfani dasu in aka kaita sai su iske sauran, da sauri Aunty tace ai ba komai duk yadda sukai yayi wllh ta hau yin godiya da Addu'oi Hajiya Zainab d'in na amsawa daga baya sukai sallama, suna gama wayar ta kira can gidan su ta sanar masu Mamar su tace ita wllh hakan yayi mata dad'i ma Allah ya saka masu dai da Alkhairi, Cikin sa'a suka gama sai kuma ta k'arshen wato council, bayan sati guda suka fara yin ta duka kwana ukku sukai suka gama, a ranar gaba d'ayansu cikin tsananin farinciki suke sun sha ankon atamfofi sun d'aura jacket mai d'auke da sunayen su a baya ta Fatuu an rubuta RN Zarah ta Fauzy kuma RN Fauzy abun gwanin k'ayatarwa nan suka shiga d'aukar hotuna mutane sai so suke suyi hoto da su twins amman sun k'i yarda, Zainab Muhammadu ce tace wllh basu isa ba ayi bikin uwar su tare da ita gari ya gari har Abuja taje amman Suk'i yarda da ita, dole da tsiya ta d'auke su suna ta kuka suna ta6e baki irin dai yadda Fatuu ke yi da k'uruciyarta in zata yi kuka suma haka suke yi don lokacin da Haisam yazo har Magana yayi akan hakan yace ita suka biyo in zasu yi kuka yadda take. Alhamdulillah shine abunda su Fatuu keta fad'a da suka kammala karatun nasu lafiya, tare da Fauzy suka dawo gida saida suka fara tsayawa a gidan gwaggo akai ta taya su murna da Addu'ar samun sakamako mai kyau daga baya suka koma gida nan ma su Hajiya da Saude kowa dai ya taya su murna Haisam ma tun bayan da suka fito daga jarabawar ya kirata ya taya ta murna da fatan sakamako mai kyau haka ma Sameer shima ya kira Fauzy ya taya ta murna. Kwana ukku da gama jarabawar su Sameer yazo Katsina Ranar ya kama Alhamis dama ya sanar ma Fauzyn zai zo ya tafi da ita Abuja can za'ai masu pre wedding pics, da yamma jirgin su ya tashi zuwa Abuja, duk da hawanta ne na farko ba laifi ta dake saidai itama taji juwa kamar yadda Fatuu tayi, gabda kiran Magrib suka sauka Aunty Laila ce taje d'aukko su don itama ta gama karatunta ta dawo dama komawar da tayi Final Exams zasu yi, gidansu suka wuce su Mom suka tarbeta hannu bibbiyu sosae Jidderh ta nuna farinciki da zuwanta shi dama Sameer ya wuce part d'in Haisam, d'akinta Aunty Laila ta wuce da ita tana zuwa salla ta fara yi bayan ta gama anan ta kawo mata Abinci da abun sha cikin fara'a tace mata ta taso taci d'an anjima zasu fita ne tace to, ba laifi ta saki jiki taci Abincin Jidderh na gefenta tana mata hira, ana gama sallar isha suka fito zasu tafi harda Jidderh tana jaye da wani madaidaicin trolley bayan sunyi sallama dasu Mom suka fito, a parking space suka had'e da Sameer yayi wanka ya canza kaya suka hau wata dankareriyar Jeep Sameer d'in ne ya shiga driver seat Fauzy na niyyar shiga baya Aunty Laila tace ta hau gaba su kuma suka shiga bayan yaja suka tafi. Wani sananne kuma tsadadden wurin hoto suka je wurin mai girman gaske ne gashi ya matuk'ar Had'uwa don iya ginin wurin abun kallo ne fitilu masu k'ayatarwa ne ta ko ina kai kace da rana ne, akwai manyan Studios d'in d'aukar hoto sai kuma na kwalliya haka akwae restaurant a wurin sannan akwai had'addan parlon hutawa ko jira, suna zuwa ba 6ata lokaci don ansan da zuwan su sunyi booking aka fara yi ma Fauzy Makeup abunka da kwararru ba'a d'au lokaci ba aka gama sosae Fauzy tayi kyau abun ba'a magana harda gashinta aka gyara, shima Sameer d'in saida aka gyara mashi fuska ya k'ara fitowa sosae, bayan sun gama ne suka nufi wurin canza kaya aka bud'e trolley d'in da suka zo da su wanda gaba d'aya sababbin kaya ne aciki wanda aka d'inka ma Fauzy tsadaddu kuma had'add'un gaske kala daban daban, hotuna daban daban aka shiga yi masu saida sukai kala goma kuma kowanne da kaya kala daban kama daga atamfa, lace, shadda, material, Abaya, English wears harda wanda aka yi masu da kayan aikin Sameer d'in irin kayan da injiniyoyi suke sakawa itama Fauzyn ta saka na mata ta saka irin hular da suke sakawa daga baya wurin wuyanta gashinta ya fito sosae tayi kyau kai kace ba bahaushiya ba, bayan sun gama ne aka yi masu wasu tare da su Aunty Laila. Aunty Mareeya bata yi niyyar fad'i ma iyayensu game da tafiyar Fauzyn Abuja tare dashi ba don tasan baban su bazai so hakan ba dole ya kalubalanci hakan saidai kuma tasan in aka yi hotunan dole suyi trending a social media kuma tabbas sai yan gidansu sun gani k'arshe Baban nasu zai iya gani shima, tunanin mafita ta shiga yi k'arshe ta yanke zata ce mashi kawai Katsina yazo akai masu. Washe gari ya sako Fauzyn jirgi ta dawo, a ranar da daddare saiga hotunan ya turo mata lokacin da ta gansu har saida tayi d'an ihun farinciki don sosae suka d'akku sunyi kyau har sun gaji gashi sun saka sutturu masu tsada haka d'inkunan da akai ma Fauzyn sun hau da jikinta sosae abundai saidai ace ma sha Allah, lokacin da Aunty ta gansu kasa rufe baki tayi tana ta faman yabawa tana fad'in Fauzyn kamar ba ita ba ta wanku iya wankuwa, kan kace mi hotunan har sun baza social media a daren Fatuu ma tun kafin Fauzy ta tura mata sai gashi ta kirata tana fad'in yayi kyau matar injiniya wannan zafafan hotuna haka, tambayar ta tayi a ina ta gansu tace gasu nan Aunty Laila ta d'aura a status harda su Jidderh har su Mom ma duk sun d'aura, sosae Fauzy tay mamakin yadda ake ta kiranta ana yaba hotunan tare da fatan Alkhairi abun har ta kasa rufe bakinta ma, gaba d'aya yan'matan Sameer sai yanzu suka san da zai yi aure ganin hotunan sosae mutane da dama sukai mamakin wadda zai aura sakamakon Comments d'in da aketa yi ana fad'in yar talakawa ce a Funtua local Government d'in Katsina take, haka aketa faman yin Comments mafi yawanci yabo ne ake tayi ana jinjina yadda d'an Governor ya auri d'iyar talakawa wasu na fad'in da ana yin haka a K'asar nan da an rage talauci sosae, wad'anda suka san Sameer d'in nata jinjina Al'amarin suna basu ta6a tunanin zai auri yarinya k'arama kuma yar talakawa ba, haka dai aketa maganganu gaba d'aya hotunansu sai trending suke ko ina ka shiga Maganar ake, ta 6angaren Sameer d'in yan matan shi sai kiran shi suke suna fad'in ya zai masu haka tare da jaddada mashi irin son da suke mashi wanda ya sani amman zai auri k'aramar yarinya kuma yar talakawa, to gaba d'aya dai amsa d'aya yake basu itace ita Allah ya k'addara mashi zata zama Matar shi kuma yana sonta, abokanan shi ma suna ta kira suna mashi Allah ya sanya Alkhairi. MUJAHEED Zaune yake a cikin parlon part d'in shi dake a cikin gidan su, dama gidan nasu Family House ne gaba d'aya shi da matar shi Rukky iyayen su anan suke dama Cousin ne shi da ita, gaba d'aya ya canza kamar ba Mujaheed d'an gayu ba yanzu sam ba wannan gayun don tun bayan daya yi aure kwanciyar hankali tayi mashi k'aranci, tashin farko matsalar daya fara fuskanta da Rukky itace bai sameta a budurwa ba bayan da suka yi auren haka dai aka yi Amarcin aka gama ba tare daya nuna mata komai ba don ita a zaton ta bai gane ba Saboda gyaran da ta sha, matsala ta biyu daya k'ara fuskanta itace k'azama ce sam bata san ta gyara muhallin da suke ciki ba ta dai iya tayi wanka tayi kwalliya amman kullum gida kaca kaca gashi sam bata iya wani girki ba, matsala ta ukku daya fuskanta a tare da ita itace sam bata bashi lokaci yadda yakamata Saboda aikin Asibiti da take dama da suka yi karatu a Malaysia ita medicine ta karanta shi kuma Business admin, a daddafe auren su yayi shekara guda don matsalolin daya ke fuskanta a tattare da ita sunyi yawa gashi har lokacin ko 6atan wata bata ta6a yi ba, Babbar Matsalar daya fuskanta a tare da ita wadda ta kusa zauta shi itace kamata da yayi red-handed tana aikata lesbian a cikin gidan shi, a lokacin yayi kuka kamar kamar me ita kanta hankalinta ya tashi sosae ta dingi bashi hak'uri tana ta tuba bazata k'ara ba amman ina dama ya gaji da auren ta hakan yasa ya tunkari iyayen su ya zayyana masu irin matsalolin da yake fuskanta a tare da ita k'arshe har lesbian daya kamata tana yi bai 6oye masu ba, suma hankalin su ya mugun tashi bama kamar Mahaifiyar shi anan tace ma Daddyn shi gaskiya a raba su amman ga mamakin su sai cewa yayi baza ayi hakan ba tunda dai abun duk na gida ne in abun ya bud'u to suma zai shafe su k'imar gidan ce zata ta6u a bari su kirata sai suyi mata fad'a insha Allahu zata bari, wani k'ululun bakin ciki ne ya tokare Mujaheed yana kuka ya shiga rok'on mahaifin nashi kan shidai a raba su kawai ya shiga girgiza mashi kai yana fad'in baza'ayi haka ba ai ba had'a su akai ba su suka fara son juna har sukai aure don haka kawai yayi hak'uri ayi mata fad'an, a lokacin Mujaheed ji yayi kamar ya mutu, bayan an kirawo ta sosae mahaifin nasu yayi mata fad'a ya nuna ta bashi mamaki yana ganinta mai hankali mai ilimi wanda a addinance da kuma a aikinta na likitanci duk tasan illolin hakan taya zata 6ata wayonta haka, sosae take kuka tana fad'in ayi hak'uri sharrin shaid'an ne amman ta bari in sha Allah zata gyara duk wasu matsalolinta da Mujaheed ya fad'a, sam Mahaifiyar shi bata so hakan ba amman ba yadda zata yi tunda Mahaifin nasu ya kafe, a haka suka ci gaba da rayuwa ba laifi a lokacin ta d'an gyara saidai sam shi hakan bai burge shi ba don ta riga ta fitar mashi a rai gaba d'aya sai lokacin ne ya gane dalilin da yasa ya sameta a ba budurwa ba ya shiga tunanin Allah kad'ai yasan tsawon lokacin da ta d'auka tana aikata hakan ashe shiyasa sam bata damu da ta bashi hakkin shi ba saboda tana bin mata yan'uwanta, yasan Rukkyn ta waye sosae amman bai ta6a tunanin zata aikata haka ba, a lokacin ne son Fauzy ya taso shi a gaba kullum cikin aikin tunanin ta yake haka cikin baccin shi yayi ta mafarkin ta saidai shi kan shi yasan samunta a lokacin abu ne mai matuk'ar wahalar gaske don yasan mahaifinta ba laifi yana da zafi hakan yasa bai ma yi tunanin zuwa gidan su ba, da yaga abun yayi mashi yawa ne ya yanke ya fara tuntu6arta in ta saurare shi sai yayi duk yadda zai yi yaga ya shawo kanta watak'il a bashi ita, Da wani yammaci ne ya shirya cikin Motar shi ya nufi gidan su Fauzy lokacin daya je a d'an nesa da gidan ya parker yana ta kallon kopar gidan yana dakon fitowar wani saida aka d'auki lokaci sannan yaga wani k'aninta da suke ce ma Abba ya dawo daga islamiyya a saman Keke yana ginin shi ya fito da sauri ya fara kiran sunan shi hakan yasa Abban tsayawa ya juyo Mujaheed d'in ya nufe shi ai koda yay arba da fuskar shi kawai sai gani yay ya tamke mashi fuska hakan yasa Mujaheed shan jinin jikin shi amman duk da hakan ya dake yana d'an murmushi yayi mashi sallama tare da ce mashi an dawo daga islamiyya ne kaman bazai amsa ba can dai cikin d'aure fuska yace mashi eh, jinjina mashi kai yayi yace yayi kyau Allah ya bada sa'a anan Abban bai amsa mashi ba sai ma ce mashi yay zai shiga gida da sauri Mujaheed ya dakatar da shi cikin yar in ina yace "a...m Fauziyya na nan?" Wani kallo mai kamar harara yayi mashi kafin yace bata nan, tambayar shi yay tana ina cikin kumbura baki yace "Oho ban sani ba nima" yana fad'in hakan ya ja keken shi ya shige, tsaye Mujaheed Yay sototo hakan da yayi mashi ba K'aramin k'aryar mashi da zuciya yay ba don bai zata yaron zai mashi hakan ba Saboda lokacin da yana tare da Fauzy suna shiri sosae da yaron don mutumina ma Mujaheed d'in ke ce mashi, da k'yar yaja k'afafun shi ya koma cikin Mota a ranshi ya shiga tunanin yaro ma yayi mashi hakan to ina ga Mahaifin kuma Fauzyn, jiki a mace ya ja Mota ya fara kokarin barin layin, yana driving yana tuna rayuwar shi da Fauzy a ranshi yana raya yasan da ita ya aura da ba K'aramin more mata zai yi ba don yarinyar na bala'en son shi kuma duk yadda yake so haka zai tafiyar da ita, haka ya dingi tuna abubuwa har ta kai yana kai ma steering Motar d'an bugu alamun takaici, tunanin yadda zai ga Fauzy ya shiga yi don tun kafin ya taho saida yayi trying layinta bai shiga, yana haka abokin shi Usman ya fad'o mashi a rai yay tunanin watak'il shi zai san inda take da sauri ya d'auki wayar shi ya kira shi bayan ya d'aga sun gaisa ne ya tambayi yana ina yace mashi gashi nan gidan shi yana shirin zuwa Masallaci yace Ok bari yazo, a tare suka tafi Masallacin bayan an gama sallar suka dawo ganin ya tsaya a bakin Motar shi Usman d'in yace mashi su shiga mana ya girgiza mashi kai, shiru yay yana kallon Mujaheed d'in don duk matsalolin da yake ciki ya sani, "Kayi hakuri ka daina saka damuwa haka sosae a ranka Mujaheed kada ka ja ma kan ka wata matsalar kuma, ka dage da Addu'a Allah kad'ai ne zai maka maganin matsalar da kake ciki" shiru yay kafin ya jinjina mashi kai tare da kai hannu ya shafi gaban kan shi can yace "Usman bazaka gane ba amman ina cikin matsala wllh" ya k'arasa tare da cize lip d'in shi na k'asa, "na sani abokina ai rashin dacen mata babbar matsala ce baka ji wak'ar nan da ake ta mace ta gari ba wllh duk abunda aka fad'a a cikinta hakanne da kaga mutum ba natsuwa duk ya firgice to da ka bincika zaka samu bai yi dacen mata bane, yanzu dai look at you kaman ba Mujaheed d'in dana sani ba duk ka fara fita hayyacin ka ko rannan saida nayi maka magana kan ka rage wannan k'asumbar taka wanda a da yaushe ma har wani zai maka magana kan haka" d'an murmushin takaici Mujaheed d'in yayi ba tare daya ce mashi komai ba, shiru suka d'an yi can Mujaheed d'in yace mashi don Allah suna magana da Fauzy har saida Usman ya d'an waro ido jin sunan wadda ya ambata tare da maimaita sunan Fauzy Mujaheed ya jinjina mashi kai, tambayar shi Usman d'in yayi mi zai da lambar tata yace mashi hakanan yana son suyi magana da ita ne zai bata hak'uri don yana tunanin duk abun nan dake faruwa dashi harda hakkinta, d'an murmushi Usaman yayi yasan ba iya dalilin daya sa yake son lambar ta ba kenan, k'ara tambayar shi Mujaheed yay in yana da lambar ta pls ya bashi Usman d'in yace gaskiya baida ita yana tunanin ta canza layi ne don ada suna gaisawa amman yanzu sun dad'e ma basu yi magana ba, tambayar shi yayi to yana ganinta cikin gari haka yace mashi a'a ai bata cika zama a nan ba yanzu Saboda ta koma Katsina wurin Yayarta acan take karatu, shiru Mujaheed yay yasan Yayar tata wato Aunty Mareeya amman bai san a ina take ba a Katsina, daga baya dai sukai sallama ya tafi Usman nata d'an girgiza kai ba yadda bai nuna mashi ba kar ya bar Fauzy don in yayi mata hakan bai kyauta ba amman ya k'i ji k'arshe ma abun ya zamar masu kamar fad'a gashi nan yanzu tun ba'a d'auki lokaci ba sosae ya fara nadama mara amfani. Tun daga wannan lokacin son Fauzy ke ta d'awainiya dashi gashi yayi duk yadda zai yi don ya had'u da ita ko kuma ya samu lambarta abun yaci tura, Wata rana ne kwatsam ya ganta a bakin titi duk yadda yaso ta tsaya ta saurare shi ta k'iya hakan yasa Ranar ya bi bayanta gida da daddare aikuwa yana zuwa suka had'e da Mahaifinta ya same shi yay mashi tatas yace Idan ya k'ara ganin shi a k'opar gidan shi to hukuma ce zata raba su nan Mujaheed d'in yayi ta bashi hak'uri yana fad'in yasan yayi kuskure bai kyauta ba amman don girman Allah ya bashi dama a yanzu zai gyara kuskuren shi ne, a lokacin wani murmushin yaro yaro ne mahaifin nasu yay kafin ya d'aga yatsa sama yace mashi "Na rantse da Allah daya hallicce ne ko bayan ba raina bazaka auri Fauziyya ba, yarinyar da kaso kashe man ita kawai don Allah yasa da sauran numfashinta a gaba shine yanzu don baka da kunya ka iya tako k'afafun ka kazo man gida, to bari kaji, ka bar kopar gidan nan tunda arzuki in ba haka ba....ka jira in shiga in fito zaka ga abun da zan sa ayi maka" cike da 6acin rai ya k'arasa maganar tare da juyawa ya shige cikin gidan, jiki a sa6ule Mujaheed ya juya ya nufi Motarshi yana k'walla ya bud'e ya tafi, duk wannan abun Fauzy bata san da an yi ba, tun daga ranar Mujaheed ya hak'ura da neman Fauzy amman fa kullum son ta da nadamar abunda yayi mata k'aruwa yake a cikin ran shi, (Allah ka kiyashe mu aikin dana sani mara amfani Amin). Yana zaunen idon shi akan Tv wayar shi dake a gefen shi ta shiga yin ruri, kai idon shi yay kanta yaga Usman ne mai kiran nashi ya kai hannu ya d'aukko ta tare da yin picking, bayan sun gaisa ne yace mashi yaga hotunan dake ta trending a social media Mujaheed d'in yace mashi a'a tun d'azun rabon shi da online Usman yace mashi Ok ya hau Facebook yanzu tambayar shi yay lafiya yace ya dai hau zai gani yace Ok, bayan ya katse Wayar kunna Data d'in shi yayi a ranshi yana ta raya to miye zai gani, yana hawa hotunan su Fauzy ya ci karo dasu farko bai ganeta ba koda ya karanta rubutun dake sama wanda aka sa d'an Governor d'in Nasarawa Sameer Bello Abdullahi zai yi Wuff da yar talakawa daga jahar Katsina a garin Funtua mai suna Fauziyya Ahmad Rufa'i, shiga yay cikin uban comments d'in mutane ya fara bi yana karantawa duk da hakan bai gane ita bace yana cikin karantawar Usman ya sake kiran shi bayan ya d'aga yace mashi yaga wadda zata auri d'an Governor d'in yace mashi eh ya gani ance yar nan Funtua ce wannan maganar yasa Usman ya gane bai ganeta ba yace "wai baka gane Amaryar bane?" Amsa ya bashi da eh da alamun mamaki Usman yace "lallai Mujaheed baka a cikin hayyacin ka wllh, yanzu Fauziyya d'in ce baka gane ba?" jin sunan Fauziyya yasa shi maimaita sunan sai lokacin hankalin shi ya koma kan sunan Amaryar da ya gani an rubuta nan take ya gane Fauzy ce, wani irin bugu gaban shi yayi da sauri ya mik'e tsaye......... 96 _ASM BY ZAINAB BATURE_ ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ ............Da tsananin Al'ajabi Mujaheed yace "U.....sman wai kana nufin Fauziyyata ce wannan Amaryar?" Amsa ya bashi da eh mana bai duba hoton bane sosae, kan Mujaheed ne ya d'aure fuska a hautsine ya shiga fad'in amman taya hakan zata faru taya za'a ce zata auri d'an Governor, Usman na murmushi yace abun Allah ai ba abun mamaki bane don wannan kad'an daga cikin ikon sane, "ka gane Usman abunda nike nufi irin wannan Mutanen had'uwa da su ba abu ne mai sauk'i ba balle kuma har ta kaiga ace zasu yi aure kuma nasan labarin mahaifin yaron ba K'aramin mai kud'i bane yana daga cikin Governors masu kud'in gaske fa taya za'a ce hakan zai faru kodai ba ita bace suna ne yazo d'aya!" hankali tashe yake Maganar, "Wannan duk ba wani abu bane Mujaheed da Allah ya so Shikenan zaka ga ya kasance cikin sauki tunda gaba d'ayan mu duk bayin sane shi yake iko da mu" yarfa hannu Mujaheed yay kaman zai saka kuka yace amman wai taya suka had'u ma, Usman yay yar dariya yace "ta yadda Allah ya had'a ku haka shima ya had'a su, ance ta dalilin karatun da take a Katsina suka had'u ni kaina nayi mamaki sosae lokacin da naga hotunan don ina gani na gane itace amman don in tabbatar sai na kira wani abokina d'an layin su shine ya tabbatar man yace suma duk basu san da abun ba kawai dai suna ganin ana yin manyan bak'i a gidan sannan kuma yanzu haka ma an canza ma gidan nasu suffa ya zama had'addan ginin benen gaske gaba d'aya dai komai cikin k'ank'anin lokaci ya faru har ma hoton gidan nasu ya turo man bari ka gan shi" yana fad'in hakan ya katse kiran don ya tura mashi hoton, komawa Mujaheed d'in yay cikin Facebook ya shiga sake kallon hotunan gaban shi na mashi wani irin bugu, sai yanzu ya tabbatar da ita d'in ce yana haka Usman ya turo mashi hoton gidan su Fauzy, Safa da Marwa ya shiga yi wayar shi ruk'e a hannunshi da k'yar yake fitar da numfashin shi da yaji yana neman k'wace mashi k'arshe ma sai yay wurgi da wayar tashi ya durk'ushe k'asa saman gwiwowin shi wasu irin k'walla masu zafi suka shiga zubo mashi.......... Washe gari Friday ya kama saura sati biyu cuf d'aurin auren Fauzy da Sameer, a ranar ne aka tura wasu daga cikin akwatunan lefen Fauzy set biyu guda goma cuf wai nan kayan da zata ci biki ne sauran sai an kaita kamar dai yadda Hajiya Zainab ta fad'a ma Aunty Mareeya harda invitation cards masu kyaun gaske aka had'o, akwatuna ne ubansu su kan su abun kallo ne kai da gani ba sai an fad'a maka ba kasan zasu yi kud'i saima da aka bud'e kayan ciki Naira ta sha kashin gaske don kaya ne na gani na fad'a kuma duk a d'inke suke a ciki harda wanda Fauzy ta saka suka yi hotuna, kowa ya gani cikin yan uwansu cewa yake yo iya wannan ma ai lefe ne na gaske, lokacin da aka tura ma su Aunty Mareeya kayan zo kaga murna ita kanta fad'i take yanzun duk wannan uban kayan har sai an k'ara wasu, itama Fauzy har ta kasa rufe bakinta don farinciki koda ta tura ma Fatuu ita kanta ta yaba sosae anan take tambayarta sai yaushe zata tafi Funtua d'in ne tace mata sai zuwa jibi Lahadi akwae shirye shiryen da Aunty take son k'arasawa, itama Fauzy ta tambayi Fatun sai yaushe zata je can tace mata sai satin bikin ana saura kwana biyu aikuwa Fauzy tace ita dai bata yarda ba gaskiya inama laifin ana saura sati d'aya ta taho, dariya Fatuu ta saka tace wannan sai kace ita ce dai Amaryar inama laifin ana saura kwana biyun Fauzy ta kafe kan ita dai yayi kad'an Fatun tace mata gaskiya daga haka bazata k'ara ba don Lokacin Hubby dinta ya dawo taya zata taho ta barshi, dariya Fauzy ta saka tace ai sai ta fito tayi mata bayani ba taita yan kame kame ba duk suka yi Dariya. Ranar Lahadi tunda safe su Aunty suka d'auki hanyar Funtua a cikin Motar Fauzy driver d'in da ya koya mata Motar ne zai kai su. Alhamdulillah sun isa lafiya anata murnar ganin su ba kamar Fauzy Amarya sai faman nan nan da ita ake, sosae sukai mamakin yadda aka canza ma gidansu fasali duk da sun gani a waya amman yanzu da suka ganshi a zahiri sai suka fi ganin kyaun shi ya zama gidan yan gayu sosae wanda kaf layin su da duk ma rukunin su ba gida tamkar shi kai a yanzu ma yana d'aya daga cikin jerin gidaje masu kyau in za'a lissafa a garin, shirye shiryen hidima sun kan kama sosae bayan zuwan nasu duk da ba wani abu da Fauzyn zata yi anan Funtua Sameer har magana yayi mata kan ko zasu yi wani event tace mashi a'a abar wanda su zasu yi kawai wato Dinner bayan an kaita sai kuma Walima wadda za'a yi matsayin bud'ar kai. Ranar Laraba Haisam ya iso yana dawowa washe gari suka tafi Abuja da Fatuu harda Hajiya acan ma dai duk shirye shiryen bikin aketa yi, Ana saura kwana biyu bikin ya kama ranar laraba kamar yadda Fatuu tace Haisam yasa driver ya tafi da ita harda Jidderh, Bayan sun isa Fauzy tayi murna da ganin su sosae haka Aunty Mareeya da sauran yan gidan sai faman nan nan ake da su anata nuna Fatuu ana cewa itace k'awar Fauzy wadda zata auri d'an uwan mijinta nan fa akai ta yi ma Fatuu godiya hatta Mahaifinsu da kanshi yazo inda suke yay masu sannu da zuwa shima saida yayi mata godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci haka yayye da k'annen Fauzy duk saida suka zo suka gaishe da ita hadda Yaya Mubarak ma fuska a sake Fatuu ke amsa masu ana ta son a d'auki twins amman sun ki yarda sai faman fad'in Tubarkallah ake dama lokacin sun k'ara girma sosae, Yaya Fareeda harda cewa Allah yasa Fauzy itama ta haifi irin su anata dariya aka amsa da Amin. Hidima ta kan kama tun a ranar Jami'an tsaro keta faman sunturi a cikin garin ana ankarar da mutane hatta gidan su Fauzy an zuba security, Washe gari Alhamis su gwaggo suka iso tare da Kawu Amadu da Mino harda Haulat da Saude bayan zuwan su kuma su Zainab Muhammadu da wasu daga cikin k'awayen su ma suka zo haka makwabtan Aunty Mareeya ma su Maman taufiq suma sunzo gida dai ya cika sai zuwa ake. FRIDAY.... Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar d'aurin aure, a ranar tunda farar safiya jiniya ta fara tashi ta ko ina wurin k'arfe sha d'aya na safe Abbas ya iso tare da Feenah, tuni Amarya Fauzy tasha had'addan k'unshi an kuma gyara mata kai haka jikinta ma yasha gyara don tun a Katsina ake ta mata gyaran jiki skin d'inta tayi wani irin sumul sai shek'i take, zuwa k'arfe sha biyu da rabi na rana garin Funtua ya cika makil da jama'a ba abunda kake ji sai jiniya ga kuma jibga jibgan motoci masu numfashi dake ta kai kawo a saman tituna da tuni an rufe su an hana mutanen garin bin su saidai suyi zagaye, kamar yadda Ango Sameer yaci alwashin bazai k'ara zuwa a Mota ba hakan ce ta faru don kuwa a helicopter suka zo harda Haisam bama su kad'ai ba wasu daga cikin manyan mutane ma a helicopter d'in suka zo daga filin da suka sauka ne Motoci na Alfarma suka daukko su, Jama'a kuzo kuga ango Sameer yasha kyau har ya gaji yana sanye da rantsattsiyar shadda light ash d'inkin yar ciki da babbar riga ba K'aramin kyau ya k'ara ba a cikin kayan ko don bai saba sakawa ba ne, su Haisam angwaye suma babbar rigar shadda duk suka saka gaba d'ayansu Abokan ango iri daya sukai suma tasu ash ce amman tafi ta Angon cizawa ba K'aramin tsaruwa sukai ba dama duk gasu yan Madara harda Abokan shi turawa da suka zo suma duk shigar suka yi abun dai sai wanda ya gani, shima Mahaifin Sameer d'in His Excellency da muk'arraban shi duk sun iso gaba d'aya jiniya ta karad'e ko ina a lokacin harabar Masallacin Juma'an da za'a d'aura auren ta cika makil da Jama'a kama daga manyan yan siyasa masu Mulki da masu Sarauta, manyan yan kasuwa da sanannun masu kudi, Manyan Mutane wanda sune Nigeria aka had'a a wurin wasu sun zo da kan su wasu sun turo wakilci taro dai yay taro malam Yan Jarida ko ta ina suna d'aukar rahoto nima dai ina daga cikin su inata rubuto maku rahoton cike da taka tsantsan gudun kada in sha na jaki a wurin jami'ai dake ta kai kawo a wurin don na lura a fusace suke duk suna ruk'e da manyan makamai gaba d'aya sun yi shirin ko ta kwana. Daga cikin wad'anda suka zo bikon Amarya harda su Mom da Aunty Laila Aunty Mareeya ta shiga gabatar dasu wurin yan uwansu tana ce masu yadda suka ga Mom haka Mahaifiyar Angon take don yan biyu ne, sosae Mom ta sakar masu fuska anata faman kawo mata gaisuwa tare da yi mata godiya da murmushi take fad'in ba komai duk an zama daya. Ana gama sallar Juma'a dubban mutane suka shaida d'aurin auren Sameer da Fauzy wanda Aminin Governor wato Senator Ali Adamu Zakee ne ya kar6a mashi akan sadaki Naira dubu d'ari biyar kamar yadda iyayen Fauzy suka buk'ata Jama'a sai fatan Alkhairi suke ma Governor mahaifin Sameer da Mahaifin Fauzy da kuma shi kanshi Angon da ba laifi ya saki fuska yana d'an murmushi haka Haisam ma sai murmushi yake shima ana mashi Allah ya sanya Alkhairi, ana gama d'aurin auren aka nufi inda aka tanada don yin reception wasu dai da yawa tafiya sukai, manyan motoci ne masu d'auke da Abinci iri iri aka bud'e a bakin Masallacin nan aka shiga rabama mutane a nutse don da mutum yay wasa yaji saukar dorina a gadon bayan shi, har gidan su Fauzyn ma Motar Abinci taje an sauke masu abun dai sai godiyar Allah, cikin wanda suka halarci sallar Juma'a aka kuma d'aura aure dasu bayan an tantance su Saboda tsaro harda Mujaheed da tun bayan daya san da Maganar auren baida cikakkar lafiya, daga nesa ya tsaya shida Usman suna hango Sameer lokacin da ake d'aura auren bayan an gama Usman yace mashi su tafi fuska kamar zai yi kuka yace mashi don Allah ya za'ai ya ga Fauziyya, waro ido Usman yay ya maimaita abunda yace Mujaheed din yace eh yana son ganinta kafin ta bar garin, ce mashi Usman yay gaskiya ganinta a yanzu abu ne mai wahala gara kawai su tafi amman ya kafe kan ya taimaka mashi yana son ya ganta ido da ido ko ya nemi yafiyar ta watak'il ya samu sauk'in abunda yake ji, nuna mashi yay Fauzy bata da matsala yasan tuni ma ta yafe mashi don haka ya hak'ura da ganinta karma suje suja ma kan su matsala, kafewa Mujaheed yay harda k'wallar shi ba yadda Usman ya iya gashi ya bashi tausayi sosae hakan yasa yace mashi suje gidan nasu amman shi yasan ganin Fauziyya a yanzu ba abu bane mai sauk'i suka nufi Motar Mujaheed bayan sun shiga yaja suka nufi gidan su Fauzy. Ana gama d'aura Aure ba 6ata lokaci aka shiga shirin tafiya da Amarya don tafiyar Mota za'ai zuwa Abuja anan za'ai Dinner in an je daga baya sai a wuce da ita Nasarawa amman an sanar ma Aunty Mareeya cewa ba mutane da yawa za'a dasu Nasarawa ba iya mutum goma suke buk'ata zuwa dai Abuja wannan ko mutum nawa suka bada lafiya lou, tun bayan da su Mujaheed suka iso kopar gidan wuri suka samu daga can gefe don kopar gidan dank'am yake da mutane ga marok'a dake ta aikin kirari da masu kad'e kad'e, rasa ta yadda zasu ga Fauzyn sukai Usman yace mashi dama saida ya fad'i mashi bafa zai iya samun ganinta ba gara su tafi daga baya shi zai mashi k'ok'arin samun lambarta sai ya kirata ya rok'eta yafiyar, Shiru Mujaheed yayi shi kad'ai yasan abunda yake ji a cikin ranshi ga tsananin mamaki da yake ganin wai duk wannan taron Fauzy akai ma shi a ranshi ya shiga raya Allah kenan sosae nadama ke dawainiya dashi. Dank'ara Dank'aran Motoci ne suka shararo cikin layin zasu kai goma sai kuma motocin Security dake a gaba da baya tare da ta yan jarida abun burgewa gaba d'aya motocin bak'ak'e ne sai k'yalli suke, cirko cirko mutane sukai suna kallon yadda ake shirya motocin, bayan an gama ne aka sanar cikin gidan cewa a fito da Amarya, rantsattsan leshi Fauzy ta saka wuyanta da hannunta na sanye da gold an d'aura mata alkyabba sai walwali take, su Aunty Mareeya iyayen hidima itama kaya ta canza daga ankon atamfar da suka yi zuwa had'add'an kuma tsadaddan lace da aka mata half gown ta coge d'aurin kallabi ya kalli gabas maso kudu harda uban glass ta k'wama, haka sauran yan gidan su ma duk sun canza shiga zuwa lace su Fatuu ma duk lace d'in ne a jikin su, ba tare da 6ata lokaci ba yan kai Amaryar suka fara fita, Akan idon Mujaheed Aunty Mareeya ta fito da ita ta rungumo kafad'arta yana ganinta ya zabura zai nufeta aikuwa da sauri Usman ya maido shi yana ce mashi bai ga Jami'ai bane a wurin, wata jibgegiyar bak'ar Jeep dake ta salk'i aka bud'e ma Aunty anan za'a saka amaryar ta kalli Fatuu dake biye da ita tace mata itama ta shigo ta zagaya ta d'aya 6angaren aka bud'e mata ta shiga itama Fauzyn aka shigar da ita tana ta yar sheshsheka da tun bayan da akayi mata fad'a take kukan, Bayan Aunty ta saka Fauzyn fitowa tayi ta rufe k'opar ta shiga nuna wanda za'ai tafiyar dasu ana bud'e masu motocin suna shiga, su gwaggo dai Motar Abbas suka shiga ita da Feenah da Saude sai Kawu Amadu Haulat kuma da Mino Mota d'aya suka shiga da Jidderh haka su Zainab k'awayen Fauzy suma Mota guda akai masu su Mom dai dama da Jeep d'insu suka zo ita suka shiga su Twins d'in Fatuu na hannunta ita da Aunty laila, saida Aunty Mareeya ta tabbatar da an shigar da kowa Mota cikin masu tafiya sannan ta dawo tasu ta bud'e ta shige ba wanda ya shiga gaban tasu don bayan driver da zai ja Motar akwae Security zaune a seat d'in gefe, wai akace ga k'oshi ga kwanan yunwa tun bayan da aka shigar da Fauzy Mota Mujaheed keta kallon Motar gaba d'aya takaici ya cika shi ji yake tamkar ya fasa ihu, da shi a haukanshi da Usman bai hana shi ba zuwa zai yi wurinta yanzu kuwa saidai sukai tsaye suka bi sahun yan kallo, sai bayan da Aunty ta koma cikin Motar ne ta natsu tana k'are mata kallo tana yi tana jinjina kai a ranta tana raya ta dai had'u ba k'arya kuma da gani sabuwa ce don seats d'in harda ledar sabuntar su ga kujerun lumtsuma lumtsuma gwanin taushi a gaban seat d'in da suke akwae screen manne da kowacce kujera da mutum zai iya yin kallo ko yayi game har internet ma zaka iya shiga ko kai connecting Bluetooth da wayar ka da dai sauran su, tsakanin su da Mutanen dake zaune a gaba akwae d'an labule na leather kalar seat d'in Motar hakan yasa basu ganin su sannan gaba d'aya glass d'in Motar tinted ne ta yadda ba'a iya hango wanda ke ciki sai dai kai kaga na waje, sosae Motar dai ta jugunu sanyin Ac nata ratsa sassan jikin su, Bayan kowa ya shiga Umarnin tafiya ake jira daga wurin Jami'an dake clearing Main titi da zasu hau su tafi, hannu Aunty Mareeya ta d'aura jikin Fauzy tace "Amarsu har yanzu kukan ake" shiru Fauzyn bata ce komai ba kuma bata d'ago ba daga sadda kan da tayi hular Alkyabbarta ta rufe mata fuska Fatuu dake latsa wayarta ta d'ago ta d'aura idonta akanta tana d'an murmushi can ta kira Sunanta k'asa k'asa ta amsa tace mata tayi hak'uri ta daina kuka don Allah, "Uhm kukan gulma ne ba wani abu ba, nan data shige daga ciki sai munci sa'a zata tuna damu" yar dariya Fatuu tay Aunty Mareeyar tace Allah kuwa Zarah, hannu Fatuu takai ta janye hular Alkyabbar ta d'an d'ago da Fuskar Fauzyn suka had'a ido idanunta sunyi jajur ta kai hannu tana goge mata k'wallan tana fad'in ya isa hakanan kada tayi ciwon kai tana Amarya Aunty tace ta fad'i mata dai, saida tasata ta daina yin Kuka ta d'ago Fuskarta sosae, a hankali ta fara bin Mutanen dake tsaye cirko cirko suna kallon Motocin nasu da kallo, tana haka idanunta suka sauka akan Mujaheed daya tsura ma saitin inda suke ido, har zata janye idanun nata sai kuma ta tsaya kamar an dakatar da ita ta k'ura mashi ido farko bata gane shi ba kawai dai sai take jin kamar tasan mutumin dake a tsaye saida ta d'an d'auki lokaci tana kallon shi ne ta fara ganin kamar shi, a ranta ta raya anya kuwa shine taya zai zo nan k'arshe ta yanke bashi bane k'ilan dai mai kama dashi ne tana janye idanunta ta d'aura su akan Usman dake gefen shi, tana ganin shi ta ganeshi a ranta ta raya Usman tana fad'in hakan da sauri ta maido idonta kan Mujaheed lokaci guda ta shaida shine da tsananin mamaki ta furta "M...UJAHEED!" har Kusan rigen kallonta su Aunty sukai da sauri tace "ina Mujaheed d'in" hannu Fauzy ta d'aga tana nuna saitinshi ta cikin glass gaba d'ayansu harda Fatuu suka zuba mashi ido shima kuma har lokacin saitin su yake kallo saidai baisan suma kallon nashi suke ba, "To uban me ya kawo shi nan kuma, koda yake nama ji dad'i daya zo ya gane ma idon shi komai" Aunty ta fad'a ta d'aure fuska tare da yamutsa baki can kuma sai cewa tayi bari ma a bud'e glass d'in don ya shaida da kyau itace Amaryar, duk yadda taso ta sauke glass d'in ta kasa har ta kai tace ma Fatuu wai ta bud'e tunda dai ita tafi ta sanin takan kayan masu arzuki Maganar har saida taba Fatuu yar dariya itama ta fara k'ok'arin sauke glass d'in amman ta kasa can Aunty tace bari ta tambaya tunda ai dai sun san Amaryar yar talakawa ce bazai zama sun yi k'auyanci ba, dariya Fatuu tasaka Aunty Mareeyar ta kai hannu ta d'an janye labulan dake tsakanin su da Driver ta d'an lek'a a Kusan tare su duka na gaban suka juyo suka kalleta yadda ta sak'a kan kamar mage, da d'an murmushi tace masu sannun su suka amsa kafin tace don Allah glass d'in baya za'a sauke masu su dai sun duba basu ga inda ake saukewa ba, suma murmushin ne akan fuskar su Security d'in dake gefen driver duk da shima driver d'in kamar security d'in ne daga yanayin shigar shi yace mata kodai basu iya bud'e glass d'in bane, da sauri tace "a'a wllh Yallabai mun iya indai yadda ake sauke glass d'in kowacce Mota ne tunda dai muma muna da yan motocin nan, kuma koda ma ace ni ban iya bane ai d'ayar da muke tare ita dole ace ta iya tunda matar Cousin d'in Angon ce d'an Senator Ali Zakee nasan baku rasa sanin shi" kai ya jinjina mata tace to har itama tayi tayi ta kasa sauke shi balle ace sun yi k'auyanci, yanayin yadda take Maganar ne ya basu dariya don sun fahimci yar barkwanci ce, driver d'inne yace mata basu yi k'auyanci ba ta nan gaba ake sauke glass d'in da sauri tace Yauwa koda taji to a sauke masu don Allah Security d'in yay mata alamun ta koma ciki ta janye kan nata ya sak'o nashi inda suke ya mik'a yatsa yana nuna mata wani wuri a jikin k'opar Motar da ita kanta abun kallo ce yace mata in tana son yin magana da su nan zata latsa sai kawai ta fad'i abunda take son ayi ba sai ta lek'a ba ta jinjina mashi kai kafin tace kenan kamar yanzu da take son a sauke glass tana latsa wurin sai tace ayi haka yace mata Yess zata ga glass d'in ya sauka ta washe baki tana fad'in Allahu Akbar shima yar dariyar yay sai kuma ya nuna mata screen yace ga system nan in suna so sai suyi kallo ya shiga nuna mata yadda zata kunna yace akwae Movies a ciki saidai ba masu yawa bane amman in tana so zata iya connecting da wayarta sai ta kalli duk abunda take so har internet zata iya hawa tayi chat d'inta anan yana bayanin yana nuna mata yadda zata yi k'arshe kuma ya nuna mata game yace ga kuma game nan in tana son yi tayi mashi wani kallo tace sai kace dai wata k'aramar yarinya yay yar dariya, duk abun nan idon Fauzy na akan Mujaheed Fatuu dai kallon abunda ake nuna ma Aunty take tana yar dariya, bayan ya gama nuna mata ya maida kan shi kawai sai jin Maganar shi sukai ta karad'e bayan ta cikin wata yar speaker yana tambayar glass d'in wane side za'a bud'e masu ta bashi amsa da na hagu tana rufe baki glass d'in ya fara sauka, bin Mujaheed da kallo Fauzy tay gabanta ya hau d'an fad'uwa ganin yadda yay wani iri kamar ba shi ba Aunty kuwa yamutsa mashi fuska ta shiga yi tana hararar shi Fatuu ma bin shi tayi da kallo a ranta ta d'an ji mamakin ganin shi haka don ba haka Fauzy ta bayyana mata shi ba tace mata d'an gayu ne yanzu kuwa duk gashi ya cika mashi fuska gashi ya zumbula wata jallabiya sai kace liman, ganin irin Kallon da Fauzyn ke mashi ne ya bashi k'warin gwuiwa ya tunkaro Motar da sauri, saida ya kusa isowa kawai Aunty ta danna wurin da aka nuna mata da sauri tace a rufe glass d'in sai gashi ya fara rufewa slowly, burki Mujaheed yaci ya zuba ma Fauzy ido yayin da glass d'in ke rufewa, kallon Aunty Fatuu tayi da sauri tace "Aunty wannan ne Mujaheed d'in?" Fuska a Yamutse ta kwa6e baki ta bata amsa da eh shine banzan ko uban me ma yazo yi nan sai kuma tace koda yake gara da yazo ya gane ma idanun shi, yanayin fuskar Fauzy kaman zata yi kuka dama kuma shi ta gama yi ta kalli Aunty tace "Aunty da baki mashi haka ba zai zama kaman kin wulak'anta shi...." Tun kafin ta rufe baki ta katseta a fusace "au wai ke nan baki ji dad'in abunda nayi ba kike nufi komai, naji dad'i in har hakan da nayi mashi zai zama wulak'anci a gare shi da akwae wulak'ancin ma da yafi wannan to shi zan mashi, ke har kin manta da irin wulakancin da yayi maki zaki wani ce an mashi wulakanci", 11abu Fauzy ta had'iya k'walla suka zubo mata cikin karyayyar murya tace "abun da yay man d'in k'aruwa nayi ko raguwa Aunty, ni wllh na yafe mashi komai yayi man tun ma ba yanzu ba" ta6e baki Aunty tayi bata ce komai ba Fauzyn ta juya tana k'ara kallon shi yana a tsaya inda ya ja ya tsaya yana kallon Motar ya marairaice Fuska tare da had'e hannuwan shi ya d'an d'aga su sama alamar rok'o, kallon Aunty Fauzy tay tace "Aunty don Allah kisa a bud'e da alama akwae abunda yake so ya fad'a man ki bari muji miye don Allah baki ga yadda ya koma ba duk yayi wani iri kamar ba shi ba" wani uban tsoki taja rai 6ace tace "Wllh baza'a bud'e ba har yana da wani abun fad'i maki, to yace maki uban me kuma Maganar canzawa ya dad'e bai lalace ba wllh ko a kwalar vest d'ita, yanzu haka hakkin ki ne ke bibiyar shi tun ba'aje ko ina ba don haka ba abunda zance in ma hakan ne sai Allah ya k'ara in ma da k'ari ya k'ara mashi, Sakaran banza sakaran wofi" tana rufe baki Fauzy ta fashe da kuka, waro ida Aunty tay da tsananin mamaki tace "ke, mi nike gani haka, wai wanccan d'in kike ma kuka Saboda Maganganun da nayi to mi kike nufi da hakan??" Girgiza kai Fauzy tayi cikin kuka tace ita wllh ba abunda take nufi kawai dai ya bata tausayi ne don da gani yana cikin matsala mutumin da yake d'an gayu d'an Kwalisa a gan shi haka" ta6e baki Aunty tay tace ita dai ta sani, magiya Fauzy ta k'ara mata kan tasa a bud'e aikuwa a fusace Aunty tace "Wallahi tallahi baza'a bud'e ba, in kuma kikai wasa yanzun nan zan buk'aci a kirawo man Mijin naki ince ke kike son ganin shi da gaggawa yana zuwa in fad'i mashi abunda ke faruwa, kindai sani ai basai na fad'i maki ba tsaff zai kakkarya shi sai muga ta tsiyar tausayi, in ba ma yana mahaukaci ba shine zai wani jawo k'afafu kamar shebur wai zai yi magana dake wato shi ga mara ta ido ko duk abunda yay maki shine har zai wani nemi yin magana dake to kuwa yanzun nan zan sa a koya mashi kunyar da bai da ita" ta k'arasa tare da yin k'wafa, wani irin kuka mai sauti Fauzy ta saka dama k'iris take jira acikin ranta ta shiga tunano tun daga farkon had'uwarta da Mujaheed d'in yadda ya rink'a mata d'awainiya da tana Makaranta, sam lokacin ba ta tuno da sharrin shi ba sai Alkhairan shi, suna haka suka ji Muryar Security d'in ta cikin speaker d'in bayan yana tambayar lafiya wake kuka ne haka mike faruwa, zaro ido Aunty Mareeya tayi da sauri ta kai hannu ta jawo Fauzy jikinta tana k'ok'arin rufe mata baki tana fad'in ta bani kuji zata ja mata sharri taja a d'aureta, duk da yanayin da Fatuu take ciki na karyewar zuciya saida tayi yar dariya, k'ara tambayar su lafiya akai koda matsala ne da sauri Aunty ta latsa wurin Maganar ta bashi amsa da a'a ba komai amaryar ce ke kukan rabuwa da gida, wannan karon sosae ta ba Fatuu dariya, rarrashin Fauzy ta shiga yi tana fad'in Shikenan tayi hak'uri itafa duk Maganganun data yi 6acin rai ne yasa tayi su kuma bata ga amfanin tayi magana da shi ba tunda ita yanzu Matar aure ce ta rabu dashi kawai, cikin muryar kuka tace ba cewa tayi zata saka a kirawo mata Sameer ba ya kakkarya shi da sauri Aunty tace wllh duk cika baki ne ita tama fara kiran shi ta fad'i mashi haka yazo duk ya tarwatsa taron da rocket, dariya Kawai Fatuu ke yi a ranta ta raya yau Aunty ta tuno da rocket, suna haka aka ba motocin izinin tafiya a Kusan tare duk suka tashi jin haka yasa Fauzy d'agowa da sauri tana kallon Mujaheed d'in Motocin suka fara tafiya a jere gaba Motar Security ce haka k'arshe ma sannan a tsakiya ma abun dai gwanin burgewa nima dai ina a cikin ta yan jarida, tun bayan da Motocin suka fara tafiya Mujaheed yaji tamkar da jinin jikin shi suke tafiya a Hankali ya fara ganin jiri ya kai hannu ya dafe goshin shi ganin haka yasa Usman nufo shi da sauri ai ko kafin ya k'araso Mujaheed d'in ya tafi gaba d'aya zai kife cikin zafin nama ya tare shi duk wannan abun akan idon Fauzy dake ta kallon su ta glass da yake Motocin a slow suke tafiya, tana ganin haka ta juyo cikin kuka take ce ma Aunty ga Mujaheed d'in can ya fad'i kawai sai ta jawota jikin ta tana fad'in zai tashi ne in kuma ya wuce daga haka Allah ya jik'an shi. Tafiya ce ake me cike da kwanciyar hankali daga baya Fauzyn ta sake bayan Fatuu ta rarrasheta Aunty ta kunna masu kallo suna ta yi abun su, lokacin da suka zo Zaria ne Aunty tace ita dai wllh k'ishi take ji yakamata ace ko wace Mota an aje lemuna da ruwa Fatuu tace ko ta tambaye su k'ilan ba'a rasawa tace to, latsa wurin tayi tace pls suna buk'atar ruwa kawai sai ji tayi an bata amsa da ta duba akwae a cikin Fridge, zaro ido Aunty tay ta d'an kakkali cikin Motar ita dai bata ga wani Fridge ba, tambayar su tayi anan bayan fridge d'in yake yace mata eh mana, "to gaskiya saidai kuyi hak'uri kun d'aukko yar k'auye nidai wllh ban ganshi ba" ta fad'a tana k'ara kallon wurin, suna jiyo d'an sautin dariyar shi kafin yace Ok bari a bud'e masu daga can yana rufe baki kawai sai gani sukai daga d'an kasan dukkan seats d'in gaban ya bud'e har saida Aunty ta d'an firgita hakan saida yaba Fauzy dariya, d'an karamin fridge ne a jikin dukkan seats d'in kowanne akwae lemuna da ruwa harda snacks a ciki, tambayar Aunty akai yanzu ta gani ko tana dariya tace masu eh sai sunyi hak'uri abun ne ya had'u da yar k'auye suna jiyo dariyar shi, gaba d'ayan su lemu da snack suka d'auka suna sha harda Fauzy Aunty nata washe baki tana fad'in ikon Allah ashe da rabon zata shiga Mota fridge da aketa fad'i, suna cikin ci ne tace to wai yanzu kuma in suka zo suna buk'atar toilet fa tunda sun ci abu, kafin wani ya bata amsa ta sake cewa koda yake k'ilan ma ai baza'a rasa toilet d'in ba acikin Motar, dariya taba Fatuu tace "kai Aunty Mareeya sai kace dai wani jirgi" da sauri tace "ai wannan kaman jirgin ce mai tafiya kan titi kiga fa yadda take da abubuwa kar ki mamakin toilet d'in ma akwai nan da mun tambaya kina iya ganin sun ce akwae" Fatuu dai dariya kawai take cikin disasshiyar murya Fauzy tace don Allah sudai kada ta wani tambayi ko akwai toilet tayi mata wani kallo tace "to your Excellency kada inta bada ku ko " tura mata baki Fauzy tayi ba tare data ce komai ba ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tace "sai faman wani sha man k'amshi kike ko duk don Mujaheed ne?" Kai ta d'an girgiza mata kawai ba tare data ce komai ba, sai dai tun bayan da suka taho ya tsaya mata a rai sai tunanin halin da yake ciki take da kuma abun da ke damunshi ya hautsine haka. Alhamdulillah sun iso Kaduna Lafiya, government House d'in nan aka nufa dasu dama an shirya nan za'a tsaya a huta kafin a wuce, bayan sun huta an ci Abinci masu salla sun yi suka d'aura tafiyar. Sai bayan sallar Magrib suka iso garin Abuja, tun a gate d'in gidan da aka nufa dasu suka fara shan kallo Fauzy na ganin cikin gidan ta glass ta gane gidan da Sameer ya ta6a kawo ta ne, gaba d'aya Motocin saida aka shiga dasu cikin gidan, bayan duk an parker aka fara fitowa nan fa kowa ya shiga ba idon shi hakkin shi banda wanda suka san gidan da kuma wanda gidan ba abun kallo bane a wurin su, kowa dai cikin yan kawo Amaryar bai hana idon shi hakkin shi ba ta hanyar bin ko ina na gidan da kallo tare da jinjina ma had'uwar shi a cikin zuciya, Aunty na ruk'e da Fauzy suka nufi hanyar shiga cikin gidan kamar yadda aka basu izini suna cikin tafiyar ne k'asa k'asa da murya Aunty tace ma Fauzy nan ne gidan da Sameer ya ta6a kawo ta ko ta d'aga mata kai tace dama tana gani tayi tunanin hakan don taga yayi kaman yadda ta fasalta mata, saida suka zo bakin entrance d'in gidanne PA din Hajiya Zainab wadda da ita akaje bikon Amarya ta d'an dafa kai tace an samu matsala an manta ba'a bada card d'in da za'a bud'e gidan ba Mom ta tambayi to yanzu ya za'ai da sauri tace bari ta kira Her Excellency d'in, su dai su Aunty jugum sukai kowa na Al'ajabin jin sai da kati za'a bud'e kopar, bayan ta kirata itama nuna rashin jin dad'i tayi tace ta manta ta bada card d'in ne amman bari ta bud'e masu daga nan PA d'in tace Ok, hak'uri taba mutane na an barsu a tsaye bayan sun gama wayar tace gashi nan za'a bud'e, ba'a d'au wani lokaci ba suka ji kopar tayi wani d'an sauti PA din tace yauwa gashi nan an bud'e, ba sai na fad'i mamakin yan kawo Amarya ba, ana bud'ewa aka bada izinin a shiga PA d'in na gaba suka fara shigowa cikin passageway d'in, ita kopar falon dake anan k'asa lafiya lou ta bud'e masu ita kafin a shigar da Fauzy saida ta saci kallon hanyar benen da suka hau da Sameer, Jama'a kuzo kuyi kallon parlor mai sunan falo Aljannar duniya kenan, ashe dai yan kawo Amarya basu ga komai ba sai yanzu, wato wani irin tsararre kuma had'addan Falo ne daya jik'u da tsadaddun kayan alatu masu girgiza mutum, iya luntsuma luntsuman Sofas d'in dake cikin shi abun kallo ne ga wani musulmin Carpet dake malale a cikin shi wanda ya hau da kayan cikin Parlon, a tak'aice dai Idan nace zan tsaya bayyana had'uwar parlon to kuwa saidai in hak'ura da zuwa wurin dinner wadda za'a je da daddaren nan ni kuma gaskiya ina son ba idanuna hakkin su don haka na bar ma kowa ya fassalta had'uwar parlon a cikin zuciyar shi saidai nasan duk hasashen mutum ba lalle ya hasasho ainihin yadda yake ba tunda ba zuwa kai ba, gaba d'aya yan kai Amarya sakin baki sukai suna k'are ma falon kallo wasu na jinjina kai yayin da wasu suka kasa rufe baku nan su, ba anan aka sauke su na wani corridor aka nufa dasu sai gasu sun k'ara shigowa wani parlon, duk da bai kai had'uwar na farkon ba amman dai shima ba k'arya ya jiguna komai na cikin shi navy blue da milk ne sosae shima ya tsaru, anan aka sauke su duk suka zazzauna su Mom suka hau yi masu sannu da zuwa cikin washe baki suke amsawa, nuna masu d'akunan da zasu yi amfani dasu aka yi suna ta godiya duk suka tashi don suyi salla, bayan sun gama ne aka kawo masu lafiyayyen Abinci da lemuna aka sanar dasu in sun gama za'a tafi dinner suyi shiri lokacin Mom ta shigo tayi masu sallama tace zasu je suyi shirin dinner aka shiga k'ara yi mata godiya tanata fara'a take amsawa Fatuu ma sallama tayi masu Saboda kayan da zata saka suna can gidan tace ma Fauzy sai sun had'u wurin dinner d'in, bayan sun huta ne PA tazo da wadda zata yi ma Fauzy kwalliya harda kayan da zata saka ba 6ata lokaci aka fara. K'arfe goma saura aka zo d'aukar su ba'a bar kowa ba Amarya Fauzy ta sha kyau ba k'arya wani rantsattsan material ne golden brown aka yi mata fitted gown data hau jikinta sosae, lokacin da suka isa wurin dinner d'in shima dai ya had'u over da gani Naira ta sha kuka wurin tsara Hall d'in, tunda aka fara hidiman bikin Fauzy bata ga Sameer ba sai yanzu a wurin dinner d'in shima dai ya had'u sosae yana sanye da bugaggun Suit da suka hau da shigar Fauzyn, zuwa k'arfe goma da rabi kowa ya hallara har da uwar ango wato Hajiya Zainab tazo wurin, manyan mutane aka had'a a wurin hakan yasa ko ina ka juya jami'an tsaro ne mata da maza sosae aka zo kasantuwar wannan ce hidimar su ta farko, ba'a yi tak'amaimai anko guda ba gaba d'aya kowa da kalar wanda sukai saidae gaba d'aya lace ne aka saka kamar yan gidan su Haisam kalar lace din su d'aya haka ta bangaren su Sameer suma kalar nasu daban har kakar su ta zo da sauran dangin su yan Ethiopia haka yan Qatar ma sun zo, su Aunty Mareeya da sauran yan gidansu suma lace d'in su daban haka dai duk akayi ankon wasu kuma lace d'in su ne suka saka daban kamar su gwaggo da Aunty Feenah da Haulat dasu Zainab kowa lace d'in shi ya saka amman ita Mino irin nasu Fatuu ta saka ita ta d'inka mata Nameer dai bai samu zuwa ba don yana gab da fara yin Final Exams d'in shi, sosae kowa yayi kyau angwaye ma su Haisam duk wankan Suit sukai, ba 6ata lokaci aka shiga aiwatar da activities d'in dinner d'in abun gwanin k'ayatarwa. Gab da za'a tashi ne aka rarraba wata k'atuwar jaka mai d'auke da hoton Fauzy da Sameer cikinta uban souvenirs ne iri iri Aunty Mareeya aka ba na dangin su ta rarraba masu sauran da suka rage ta yanke aika ma Mamar su, Sai wurin k'arfe d'aya saura aka tashi abun sai godiyar Allah don an ci an sha an nishadantu yadda yakamata dinner ce da zata tsaya ma mutane a rai Aunty Mareeya dai taci uwar sabada kamar yadda ta ci alwashi kowa ka gani san barka yake dangin su Fauzy sai k'ara tayata murnar samun Sameer a matsayin miji suke ana ta fad'in ta dace ba kamar k'awayenta kowa jinjina irin rabon da take da shi suke, daga baya aka kwashe kowa aka maida su gida su Hajiya Zainab wani gidan nasu daban suka sauka wanda aka sauke su Fauzy kuma aka bar masu sai masu kula dasu. Washegari bayan sun yi lafiyayyen breakfast wurin k'arfe tara na safe aka sanar wanda za'a maida Funtua su shirya, misalin k'arfe sha d'aya na safe masu tafiyar sun gama shiryawa ciki harda su gwaggo dasu Zainab k'awayen Fauzy iya wad'anda zasu je Nasarawa mutum goma ne aka ware daga dangin Fauzyn harda Aunty Mareeya itace cikon ta goman ko k'annen su maza da mata da suka zo duk komawa za'ai dasu Fatuu dai tana cikin ayarin iyalan Senator dole taje Nasarawa, bayan anyi sallama dasu suka tafi su kuma su Aunty Mareeya suka hau shirin tafiya nasarawa, sai bayan da akayi sallar Azahar sannan aka kwashe su Amarya Fauzy ansha kwalliya tana sanye da babbar atamfa an mata half gown tasa tsadaddun takalma da jaka da kuma gyale da suka hau da kayan nata, su Aunty ma duk sun sha gayu haka ta bangaren Fatuu ma kowa dai yayi kyau. Da yake ba wani nisa ke da akwae ba tsakanin Abuja da Nasarawa basu fi awa d'aya da rabi ba suka isa garin Lafia aka nufi Government House dasu, Alhamdulillah sun isa gidan gwamnati lafiya an yi masu kyakkyawar tarba don anan suka iske su Her Excellency sun riga su isowa, komai dai na gidan mai burgewa ne a part guda aka sauke su yana da babban parlor sai kuma bedroom da zasu kai ukku ko ina an k'awata shi da lafiyayyun furniture, d'aki guda Aunty Mareeya da Fatuu da Amarya Fauzy sai Fareeda suka sauka Aunty sai washe baki take tana fad'in Allah mai iko ko yanzu ta kafa tarihi taje gidajen gwamnati har biyu na Kaduna sai kuma nan Fatuu dai sai dariya take, da yake sai da suka ci suka k'oshi a Abuja kafin su taho d'an abun sha da taunawa aka fara tarbarsu dasu daga baya duk suka kwanta suna huta gajiya, sai bayan da suka yi sallar Magrib ne aka kawo masu lafiyayyun Abinci masu saka kunnuwa su motsa harda farfesun nama da lafiyayyun gasassun kaji da abubuwan sha kai kace wata Walima zasu yi, Aunty Mareeya ce ta zuzzuba ma sauran Mutanen da suka zo tare wanda su gwaggo ne kishiyar Maman su sai Yayye da kuma k'annen mamansu da Baban su sai babbar k'awar maman tasu, bayan ta gama da kowa suma ta zuba masu duk suka zauna anan falo suna ci, suna cikin ci Hajiya Zainab tazo k'ara yi masu sannu da zuwa tana ta fara'a haka suma ta tambaye su ba wata matsala duk suka ce a'a babu komai Alhamdulillah suna godiya Allah ya k'ara d'aukaka ta amsa kafin ta kalli Fauzy data sunkuyar da kai tana murmushi tace " Daughter an sha gajiya ko?" d'an d'agowa Fauzy tayi tana murmushi ta gaishe da ita ta amsa daga baya ta tafi bayan tace ma Aunty Mareeya inda wani abu they should feel free ta kirata tayi magana, bayan tafiyarta ne suka hau yabon ta harda su Mom yadda basu d'auki duniya da zafi ba. Misalin k'arfe goma duk sunyi shirin kwanciya harma sun kwanta saidae basu yi bacci ba suna ta hira har Aunty Mareeya na tambayar Fatuu su twins tace taga tun d'azu basu wurinta tace eh suna a wurin su Aunty Laila, Aunty Mareeyar tace ba ruwan su dai basu da rigima tace mata eh gaskiya in dai suna wurin su basu wata rigima saidai ko in suna jin yunwa kuma da an basu Abinci Shikenan har kwana ma suna yi a wurin su, kallon Fauzy dake kwance jikinta sanye da kayan bacci riga da wando tayi shiru Aunty Mareeya tayi tace "Amarya ya da yin shiru ko kinata tunanin Angon naki ne" d'an murmushi tayi bata ce komai ba Fatuu ta kalleta tana murmushi Yaya Fareeda dai har tayi bacci, Aunty bata dad'e da yin Maganar ba wayar Fauzy ta fara ringing ta kai hannu ta d'aukko ta, bin screen d'in tayi da kallo ganin mai kiran Aunty Mareeya ta tambayi waye ko angon ne a hankali ta d'aga mata kai alamar eh tace to ta d'auka mana ko sai ta yanke, picking tayi ta kara a kunne a sanyaye tayi mashi sallama tana jiyo Muryar shi k'asa k'asa ya amsa suka d'an yi shiru kafin yace mata ya gajiya tayi d'an murmushi tace babu gasu nan suna hutawa yace Ok sai kuma taji yace yana son ganinta gashi nan ya turo za'ai guiding nata inda yake, shiru tayi ta kasa ce mashi komai saida yace bata ji bane sannan ta d'an had'iyi abu tace to daga haka ya katse Wayar, ganin yadda tayi tsuru bayan ta gama wayar yasa Aunty Mareeya tambayar ta ya akai ne ta d'an yi shiru tana kikkafta idanu kafin ta fad'i mata wai cewa yayi yana son ganinta zai bata sak'o, jinjina kai Aunty tayi tana murmushi tace to kuma shine tayi kwance ta tashi taje mana ta tambayi tasan inda yake ne Fauzyn na k'ok'arin tashi ta d'an girgiza mata kai alamar a'a kafin tace yace za'a zo a rakata inda yake ta d'aga mata kai still murmushi take yi haka ma Fatuu, wurin kayanta ta nufa don gaba d'aya akwatunan da aka kai mata sun taho dasu tana niyyar bude wani akwati Aunty tace mi zata dauka tace mata Hijab, ce mata tayi ta manta ba Hijabai a cikin kayan ne tace Oh ta manta wllh ta d'ago duk ta wani sha jinin jikinta, kallon Aunty Mareeya tayi tace don Allah ta ara mata Hijab d'in ta da taga tayi salla d'azun tana murmushi tace to in ta bata kuma da Asuba tana son yin salla fa ta yafa gyale mana da sauri Fauzyn tace ai zuwa zata yi ta dawo yanzu kawai abu zai fad'i mata Aunty tace Uhmm ta nuna mata jakar kayanta tace ta duba tana ciki, bayan ta d'aukko ta saka ta koma bakin gado ta zauna tana jiran mai zuwa ya tafi da ita Aunty tace mata to bazata shafa ko d'an turare ba ta tura mata baki kaman zata yi kuka tace itafa ta fad'i mata sak'o kawai zai bata Aunty tace eh duk da hakan ai yakamata a matsayin ta na Amarya aji tana zuba uban k'amshi tunda shima ta tabbatar sai taji yana sakin kamshi sosae a matsayin shi na ango, jimm tayi tana masu wani kallo ganin su duka suna mata murmushi ta yamutsa fuska tace wai miye suke ta mata murmushi da sauri Aunty tace to kuka take son taga sun yi kawai suna murmushin jin dad'i ne ganin Allah ya nufa ta zama matar aure gashi har mijin nata na kiranta, shiru tayi bata ce komai ba Aunty ta k'ara ce mata ta d'an shafa turaren tace ai ta fesa lokacin da ta saka kayan baccin duk da haka ta matsa mata kan ta k'ara fesawa, tana cikin fesawar suka ji an yi sallama a bakin kopar shigowa d'akin jin muryar mace ce yasa Aunty ta bada izinin a shigo, wata mata ce ta shigo da gani yare ce tana sanye da short skirt baki sai farar riga kanta ba kallabi sai hular gashi daga yanayin shigar ta zaka fahimci kamar uniform ne, wurin gadon ta nufo ta tsaya daga gaban shi tana murmushi ta gaishe dasu Aunty Mareeya da turanci duk suka amsa mata cikin girmamawa tace dama itace aka turo zata tafi da bride Aunty tace to ta nuna mata Fauzy tace mata gata nan, a sanyaye ta nufo matar tana zuwa gabanta ta d'an rankwafa ta gaishe da Fauzyn bayan ta amsa mata ta tambayi zasu iya tafiya ta d'aga mata kai Matar ta shige gaba Fauzy tabi bayan ta tana fara tafiya Aunty tace mata Allah ya basu Alkhairi ta juyo ta tura mata baki duk suka sa Dariya, yar tafiya sukai ta wata hanya suka iso wani Corridor Matar ta dakata ta juyo tana murmushi ta nuna ma Fauzy wata dakakkar k'opa dake kallon su tace mata nan ne part d'in shi ta shiga yana nan ciki ta d'aga mata kai Matar ta juya ta tafi, gabanta na d'an fad'uwa ta tura kopar bayan ta bud'e a d'arare sai kace mara gaskiya ta shiga, tsaye tayi daga bakin kopar tana k'are ma wurin kallo wanda madaidaicin Parlor ne mara hayaniya komai na cikin shi Fari ne da ratsin golden tsit kake ji sai Ac dake ta aiki gaba d'aya ta sanyaya cikinshi ga wani k'amshi mai dad'i dake had'e da sanyin, a ranta ta shiga raya to ko yana ina ganin parlon k'walam ba kowa, tana haka wayarta ta fara ringing har saida ta d'an tsorata da sauri ta d'agota ta kalli screen d'in, shine yake kiranta ta kai hannu tay picking tana karata a kunne kafin tace wani abu taji yace tsayuwar mi take har saida mamaki ya d'an kamata don ta fahimci yana ganinta cikin yar rawar murya tace ai bata gan shi ba, ce mata yay akwae k'opa by her left ta bud'e ta shigo ta amsa mashi da to, tana tunkarar kopar gabanta na faduwa bayan ta isa gabanta d'an jimm tay kamar bazata tura ba sai kuma ta tuna da yana kallonta hakan yasa ta tura bayan ta bud'e ta shiga, Ya Subhanallahi shine abunda na furta lokacin da nayi arba da Bedroom din, shima baida wata hayaniya amman fa ya tsaru kuma shima komai na cikin shi fari ne da golden da alama dai yana son irin had'in kalolin don ko a part d'in shi na gidan daya kaita can ma kayan haka kalar su take duk da ba design d'in su daya ba saidai na ko ina sun had'u, nan gadon round bed ne yana da table a gaban shi sai kuma nightstands da akai masu shape wanda ya hau da gadon daga can gefen gadon babbar press c ta glass ana hangen kayan dake ciki sai opposite da ita nan wani elegant dressing mirror ne suma labulayen cikin d'akin sun tsaru suna da kyau da kuma k'auri, a d'an gaban gadon golden brown d'in carpet ne an mashi ratsin fari kai da gani ba sai an fad'a ba dole zai yi laushi don wani irin gashi gashi ne dashi, daga d'an can gaban inda furniture d'in suke reading nook ne wato wurin karatu akwae yar madaidaiciyar kanta wadda itama fara ce tana d'auke da littattafai daga gabanta farin Table ne d'auke da fitilar karatu da kuma wani d'an babban jirgi kamar na wasa, gefe opposite da kantar farar leather chair ce luntsumemiya mai mazaunin mutum biyu daga gabanta kuma Ottoman ne kalar kujerar. Sauke idonta tayi akan Sameer dake kwance saman gadon yana facing sama yayin da k'afafun shi dake a bayyane suke zube k'asa suna sanye cikin flip flops jikinshi yana sanye da jar robe da gani yayi shirin kwanciya ne, fargaba ce ta kama Fauzy ba kamar data ganshi haka don ita bata yi zaton a bedroom zata same shi ba, ganin bai d'ago ba kuma tasan yasan da ta shigo yasa tayi k'arfin halin shiga ciki tana tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, daga gaban shi ta tsaya d'an nesa dashi tana kallon shi gabanta na cigaba da d'an fad'uwa, ganin bai da niyyar tashi yasa a hankali tace mashi gata yay shiru kaman bai jita ba tanata kallon fuskar shi ya lumshe ido, sai da ya d'an d'auki lokaci sannan slowly ya fara bud'e idon tana ganin haka da sauri ta maida nata idanun k'asa, bayan ya bud'e su ya yunk'ura ya tashi zaune jin motsin tashin nashi yasa ta d'an saci kallon shi karaf suka had'a ido ta shiga yan kame kame da k'yar ta k'ak'alo Kalmar ina wuni tace mashi, bai amsa ba yana dai ta kallonta da idanun shi da suke adan lumshe kaman mai jin bacci ko kuma wanda ya farka baccin bai ishe shi ba, da hannu yay mata nuni da dab da shi yace mata ta zauna, saida ta had'iyi abu sannan ta matsa don ta zauna amman ba inda ya nuna mata ba sai da ta d'an matsa sannan ta zauna, kasa kallon shi tay ta zuba ma carpet ido sosae yanzu gabanta ke fad'uwa duk da ba wannan bane karo na farko da suka samu kusanci haka tunda da akai masu hotuna ma kusancin yafi wannan sai dai a yanzu harda yanayin shigar shi ta k'ara mata fargaba don gaba d'aya chest d'in shi a bud'e yake kwantacciyar sumar da take gani wani lokacin in suna yin Vedio call da daddare yau gata tana gani a zahiri, shiru kake ji kai kace ba mutane a cikin d'akin yana ta kallonta saidai ita batasan halin da yake ciki ba amman tayi tunanin kallon nata yake, suna haka taji ya kira Sunanta da wata irin murya gabanta yay wani irin bugu da k'yar ta amsa taji ya k'ara cewa bata son kallonshi ne da turanci da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, gaba d'aya tsoron shi ne ya fara kamata ba kamar yanayin data ji yana mata magana, shiru bai k'ara cewa komai ba can kwatsam sai ji tayi ya kawo hannu ya jawota gabanshi ta yadda jikinsu ya had'u dana juna aikuwa nan take jikin ta ya fara rawa, k'ok'arin cire mata hijab d'in jikinta ya shiga yi aikuwa ta k'ank'ameta tak'i bashi dama hakan yasa shi dakatawa yana kallonta jikinta ya shiga yin 6ari sosae da k'yar ta d'aga idanunta da suka fito waje ta kalleshi taga ya d'aure fuskar tashi har saida ta had'iyi miyau Kutt da sauri ta janye idanunta daga barin kallon shi tana haka taji yaci gaba da kokarin cire Hijab d'in da sauri ta k'ara kankameta tana numfashi da d'an karfi, dakatawa ya k'ara yi cikin yar kakkausar murya yace mata miye hakan da take yi shiru bata ce komai ba ya k'ara ce mata ko yanzu ma ba kyau ne ya ta6a ta nan take ta gane Magana ya gaya mata don ta ta6a ce mashi haka lokacin daya fara zuwa wurinta a Katsina, kasa ce mashi komai tayi sosae tsoron shi ya shigeta idanunta sukai rau rau kamar zata saka kuka a lokacin ya k'ara kawo hannu zai cire Hijab din yanzu bata hana shi ba saidai yana cireta ta k'ank'ame jikinta tun ma kafin yayi mata wani abu ta fara yin k'walla cikin rawar murya ta fara ce mashi don Allah yayi hak'uri yay shiru yana bin ta da ido sai faman kerma take, d'age mata gira yay yace dame zai yi hak'urin da sauri tace kada yay mata komai don Allah, bai ce mata komai ba still bin ta yay da ido can yay yar ajiyar zuciya yace mata ta tashi taje shiru tayi don ta fahimci kaman da fushi yay Maganar amman Saboda halin tsoron shi da take yasa da sauri ta kai hannu ta d'auki hijab d'in ta maida kafin ta mik'e har zata tafi taji muryar shi yace "Su malaman da kika ce kinji suna preaching kan taba mace da ba muharrama ba baki ji suna yi akan mace data k'aurace ma mijinta ba?" dammm gabanta ya fad'i kaman an latsa mata remote ta tsaya cak zuciyarta ta hau harbawa don kuwa tun ma kafin ta mallaki hankalinta ta san kan abun a islamiyya tana jin malaman su suna fad'in duk macen data k'aurace ma mijinta Allah yana fushi da ita kuma zata kwana mala'iku suna tsine mata da ace zata mutu a wannan daren to kuwa ba makawa yar wuta ce, tuna hakan yasa da sauri ta juyo ta kalleshi idanun shi na akanta yana mata wani kallo mai tattare da 6acin rai, motsa baki ta shiga yi idanunta suka k'ara yin raurau suka cika da k'walla abu biyu suka tarun mata a cikin zuciya na farko fargabar abunda Sameer d'in zai mata sai kuma tsoron hukuncin ta in ta k'i amince mashi, jiki a mace ta koma ta zauna cikin rawar murya tace "D..don Allah kayi hakuri, d..dama ba wani abu yasa ba kawai naga kaman ba'a gama bikin bane tunda ko su Auntyna basu tafi ba yanzu ma muna cikin yin hira ka aika a taho da ni ina tsoron kada su gane wani abu in suka ga ban koma ba tunda ce masu nayi sak'o zaka bani" banza yay mata sai ma ya juyar da fuskar shi don abunda tay mashi sosae ya 6ata mashi rai ita kad'ai ce mace ta farko da take mashi abubuwa irin haka tun farko kawai don yana sonta ne yasa yake bi da ita yadda take so ta hana ya rink'a ta6ata duk da yasan hakan da tayi daidai ne amman bai yi tunanin a yanzu da aure ya shiga tsakanin su ba zata k'ara hana shi ya ta6a ta, mata da dama sun sha bashi damar ya aikata alfasha dasu wasu har rok'on shi suke amman bai ta6a kusantar wata ba koda yake ta6a mata bai ta6a aikata hakan da sunan ya biya ma kan shi buk'ata ba kawai don abun ya zame mashi jiki ne amman shi ba don yaji dad'i yake hakan ba, harda wannan dalilin yasa abunda tayi mashi ya 6ata mashi rai ganin yana da right da zai yi abunda yake so da ita amman ta hana kuma shi bai ma da niyyar aikata mata abunda ya fahimci tayi tunanin shi zai aikata mata, k'walla ne suka shiga zubo mata tana cigaba da bashi hak'uri amman yak'i ya kalleta don bai ma san mi zai ce mata ba a yadda ran shi ya 6aci yasan yana iya 6ata mata nata ran shiyasa yay banza da ita, can ba tare daya kalleta ba taji yace Shikenan taje da sauri ta girgiza mashi kai don sai taga kaman bai huce ba hakan da ya ce mata, zuciyarta ce ta raya mata tunda don ta k'i bashi damar ya ta6a ta ne yasashi yin fushin ita ta gwada yi mashi hakan k'ilan ya huce cike da k'arfin hali ta k'ara matsawa kusa dashi hannunta na rawa ta kai shi wurin nashi ta kamo hannun shi guda sai gashi a Hankali ya juyo ya kalli hannun nata dake ruk'e da nashi, ganin bai ce komai ba bai kuma janye hannun nashi ba yasa ta k'ara kai d'ayan hannunta ta kama d'ayan tana yin hakan ya d'ago ido ya kalleta cikin marairaicewa tace "Pls kayi hak'uri kada kayi fushi dani mala'iku zasu kwana suna tsine man" shiru yay yana dai ta kallonta har lokacin Fuskar shi a d'an d'aure take duk da Kusan shi koda yaushe haka fuskar tashi take amman dai yanzu tasan d'aurewar harda ta Fushi, ganin yak'i cewa komai yasa ta d'an matsa hannuwan nashi ta k'ara furta pls, jimm ya d'an yi kafin yay sigh ya furta mata is Okey duk da halin fargaba da take ciki saida ta d'an yi d'an guntun murmushi a hankali ta furta mashi ta gode ya d'an ta6e baki ganin haka yasa a d'an shagwabe tace ba yayi hak'urin ba ya d'an d'aga mata kai tace to ya saki fuskar pls kawai sai gani tayi ya d'an harareta tay d'an murmushi tare da maida idonta k'asa tana haka taji ya kawo hannu ya rungumota jikin shi duk da fargabar da take ciki saida ta d'an ji sanyi a ranta, runtse ido tay tayi lamo tana shak'ar daddad'an k'amshin da jikinshi ke saki gabanta na cigaba da fad'uwa bayan d'an lokaci taji ya kawo bakin shi saitin kunnanta cikin magana mai kaman rad'a yace mi yasa daga yin auren su ta za6i ta fara 6ata mashi rai bacin ita da kanta take cewa zata bashi happiness ko ta daina son shi ne, da sauri ta girgiza mashi kai ta d'ago tana kallon shi fuska a d'an yamutse kamar zata saka kuka tace " ba haka bane wllh kawai dai Saboda dalilin dana fad'i maka ne amman kayi hak'uri pls" yadda take Maganar da dumin numfashinta dake sauka akan face d'inshi suka k'ara turning nashi on ya tsura mata ido, a hankali tace mashi ai dai yayi hak'urin ko ya lumshe mata ido tare da kai hannu ya maidota jikinshi yay hugging nata tightly sai kace zai maida ta cikin jikinshi ita dai tay shiru tana cigaba da shak'ar daddad'an k'amshinshi, hannu ya kai ya cire Hijab d'in ya ajeta a gefe kafin ya d'aura ha6arshi a saman sumar ta yana shak'ar k'amshin da take, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin ya kai hannun shi d'aya ya fara caressing bayanta lovingly nan take gaban Fauzy yaci gaba da bugu da k'arfi amman bata yi wani yunkuri da zai sa yaga kaman zata hana shi ba ko kuma bata so, d'ago face d'in ta yay idanun su suka shiga cikin na juna ya shiga jefa mata wani irin kallo mai tada tsigar jiki ji tay bazata iya jurewa ba tana k'ok'arin janye fuskar taji ya kawo duka hannuwan shi ya tallabo fuskar aikuwa da sauri ta runtse idanunta yanayin numfashinta na fita da d'an sauri, wani irin bugu k'irjinta yay jin ya had'e face d'in su suka shiga inhaling each others breathe, sun d'an d'auki lokaci a haka jikinta nata d'an kerma ba zato kawai taji ya had'e lips d'in su and he started kissing her deeply, a wannan lokaci gigicewa tayi jikinta ya hau yin kerma sosae bayan wani d'an lokaci gaba d'aya jikinta ya saki don da wani irin salo mai rikitarwa yake mata ganin abun take kamar a mafarki yake Faruwa da ita, kwantar da ita yay saman gadon daga baya ya shiga yi mata light love affair sosae take savoring ji take tamkar zata suke sai faman sakin yar ajiyar zuciya take, bayan wani lokaci ganin he's trying to make her go nicked yasa ta fara k'ok'arin hanashi hakan ta hanyar k'ank'ame jikinta cikin wata irin murya ya furta mata "Again...." Da k'yar ta iya tattaro kalaman bakinta ta furta mashi akwae haske ba tare daya ce komai ba ya mirgina can gaban gadon, wata yar sark'a ce kawai yaja hasken ya d'auke sai kuma ya kunna standing lamb guda d'aya ta d'an haska d'akin, salon abunda yake mata ne ya canza zuwa foreplay masu zautarwa, kasa hana shi aiwatar da abunda yake son yi tayi lokacin da aka kai wannan gabar gaba d'aya Fauzy loosing mind dinta tayi she was gasping heavily for breath suna haka taji ya kai bakin shi saitin kunnanta voice d'in shi da gaba d'aya ta gama canzawa ya furta mata why is she not romantic at all, shiru tay don bazata iya ce mashi komai ba da k'yar ma ta iya fahimtar abunda yace mata, k'ara ce mata yay she should do the same to him, da k'yar ta d'an fara maida mashi martanin tun bata saki jiki ba har dai ta saki ganin yadda yake nuna mata aikuwa hakan ya taimaka wurin sashi fara rasa control k'arshe abun fin k'arfinta yay gaba d'aya ta sakar mashi idanunta a runtse gam sai k'walla ke gangaro mata, jin abun ya d'au wata hanya ta daban yasata dawowa cikin hayyacin ta aikuwa a firgice ta fara k'ok'arin k'wace jikinta sai dai ina bata samu wata damar yin hakan ba, a gigice ta hau girgiza mashi kai ta fara mashi magiya tana fad'in don Allah yayi hak'uri banda wannan ba yanzu ba, ganin baida niyyar k'yaleta ne yasata fashewa da matsanancin kuka tana yin iyakar bakin kokarinta na ta k'wace kanta aikuwa ya nuna mata k'arfi ta yadda ko kwakkwaran motsi bata iya yi a lokacin gaba d'aya tayi giving up muryarta har ta disashe Saboda magiyar da take mashi,wani irin dogon numfashi taja kamar mai neman sukewa sai kuma ta k'wala wani irin ihu...... 97 _ASM BY ZAINAB BATURE_ ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ ..........Kwance yake daga gefe yana breathing rapidly idanun shi a rufe shi kad'ai yasan yanayin da yake jinshi jikinshi har d'an rawa yake, da k'yar ya iya bud'e idanunshi da suka sauya kala ya juyar da fuskar shi ta kalli saitin Fauzy dake can gefe ta k'ank'ame jikinta sai rizgar kuka take kai da ka gani kasan tana a cikin mawuyacin hali, kiranta yay shiru bata amsa ba yay tunanin ko bata ji shi bane don muryar tashi ba sosae ta fita ba, da k'yar yaja jiki ya matsa wurin ta ya k'ara kiran sunanta nan ma shirun tayi mashi har lokacin kuma kukan take ba k'akk'autawa, hannu ya kai ya jawota jikinshi tana son ta k'wace sai dai bata iyawa don gaba d'aya jikinta yay mata wani irin nauyi ji take kamar an d'add'aureta ga wani rad'ad'in Azaba dake ratsa ko ina na jikinta k'afafunta sai faman kerma suke sosae, "Na yanka ki ne kike kuka haka?" Ya jefa mata tambayar yana nishi saidai sam bata ma sai mi yace ba kukanta take kawai, jin abun yayi yawa yasa shi janyeta daga jikin shi da k'yar ya tattaro karfi ya tashi da gwuiwowin shi ya matsa zuwa gaban gadon ya kai hannu ya ja sark'ar, lokacin da haske ya gauraye d'akin ya juyo Kusan Mutuwar tsaye yay lokaci guda gabanshi yay wani irin bugu ganin abunda ke a saman farin bedsheet d'in, aranshi ya raya ina aka samu abun da sauri ya maida idonshi kan Fauzy da duk da halin da take ciki lokacin da haske ya gauraye d'akin cike da k'arfin hali ta jawo wani abu da bata san ko minene ba ta rufa ma jikinta, komawa yay wurinta ya sa hannu ya d'agota a rud'e ya shiga tambayar ta minene, mi take ji ko yaja mata matsala ne, duk tambayoyin da yake mata bata tanka mashi ba sai kukan take cigaba da yi, gaba d'aya ya rasa ya zai yi gashi tak'i bud'e baki tayi magana balle yasan yadda take ji dama ace jirgi ce ita to da tuni yasan in ma matsala ce, sosae hankalin shi ya tashi har Fuskar shi ta nuna sai faman kallon gadon yake yana kuma kallonta, d'ago Fuskarta yayi ya tallabe ta da dukkan hannunshi cikin murya mai nuni da tsantsar tashin hankali ya shiga fad'in "Pls Wife talk to me, miye ne, akwae matsala ne, What are you feeling...? Pls tell me?" Sai faman jero mata tambayoyi yake amman bata da niyyar bashi amsar ko da d'aya ce ta runtse idanunta gam sai kuka take shar6a, jujjuya kai yay shi bai ta6a fuskantar abunda ya tada mashi hankali ba irin wannan ya rasa mike faruwa da ita da take ta faman yin kuka haka, had'e fuskar su yayi cike da damuwa yace mata don Allah tayi mashi magana yana cikin tashin hankali miya faru, da k'yar ta bud'e baki a wahalce tace mashi zafi take ji sosae duka jikinta ciwo yake k'ilan ma Mutuwa zata yi da sauri ya d'ago fuskar shi yana girgiza mata kai yace she should stop saying that pls ba abunda zai same ta zai yi mata yadda zata daina jin zafin shiru bata ce komai ba, tunanin abunda yakamata yayi ya shiga yi can wata zuciyar ta raya mashi ko yay googling k'ilan ya samu mafita sai kuma ya sake raya to mi zai fad'a shine problem d'in tunda ba sanin tak'amaimai ko miye matsalar yay ba, yanata tunanin Mafita can ya sake raya ko ya kira Mom d'in shi ya fad'i mata, karo na farko daya ji nauyin ya sanar da ita abu can Haisam ya fad'o mashi a rai, da sauri ya kwantar da ita ya jawo robe d'in shi ya maida saida yaja mata duvet sannan ya sauka daga saman gadon ya nufi wurin nightstand d'in da anan wayar shi take ajiye ya d'auka, k'ok'arin kiran Haisam ya shiga yi cikin sa'a ta fara yin ringing yana jin haka ya nufi cikin d'akin wurin inda ake karatu yayi hakan ne don in Haisam d'in ya d'auka yana iya jiyo kukanta, har ta yanke ba'a d'aga ba sai lokacin ya ga time Kusan k'arfe d'aya da rabi na dare a ranshi ya yanke yasan ko ya sake kira bama lalle Haisam d'in ya d'aga ba duk da haka ya shiga k'ok'arin sake kiran shi, har zai latsa kiran sai ga kiran Haisam d'in ya shigo dama lokacin daya kira shi yana cikin bacci yana farkawa kiran na katsewa lokacin da Haisam d'in ya ga shine mai kiran saida yay mamaki a ranshi ya ayyana ko lafiya, da sauri Sameer yay picking gaisawa sukai ya bashi hak'uri kan tashinshi da yayi yace mashi ba komai, shiru yay yama rasa ta ina zai fara Haisam na jin hakan yasan da wani abu dama tun daga kan yanayin muryarshi ya fahimci hakan, tambayar shi yay lafiya Sameer d'in yace mashi akwae wani matsala ne yana son ya taimaka mashi da sauri yace mashi Ok miya faru, bayanin halin da Fauzy ke ciki yayi mashi Haisam ya d'an yi salati kafin ya tambayi yanzu tana ina yace mashi gata can tana ta kuka da gani she's in severe pain, ajiyar zuciya Haisam ya sauke wani irin tausayin Fauzy ne ya kama shi don ya tuno da yadda hakan ta faru tsakanin shi da Fatuu gashi yasan halin Sameer sosae yasan k'ilan harda k'arfi ya nuna mata, tambayar shi Haisam yay ba akwae clinic anan ba da sauri yace mashi eh akwae yace to ya duba in akwae likita sai a dubata haka yakamata, d'an jimm Sameer d'in yay kafin yace mashi yanzu sai namiji ya dubata, d'an murmushi Haisam yayi kafin yace mashi a'a ba dole sai shi ba ya bincika in za'a samu mace sai ta dubata in kuma babu koda nurse ce sai ta dubata in taga abun babba ne a shawarce kawai ko namijin aka samu ya dubata ko kuma ya fita da ita waje ya kaita Asibiti amman a yanzu dai gaskiya tana buk'atar likita ya dubata don zai iya yuwuwa ko ta samu wound ne, kai ya jinjina mashi yayi mashi godiya Haisam d'in yay fatan Allah yasa ba babbar matsala bace a hankali yace Amin sukai sallama yace zai kira yaji halin da ake ciki, Bayan sun gama landline ya nufa da sauri idon shi akan Fauzy da ba laifi ta d'an rage sautin kukan, bayan ya kira tambaya yay ko akwae likita mace on call cikin sa'a aka ce akwae ya buk'aci a turo mashi ita, bayan ya gama wayar dawowa yayi gadon ya fara k'ok'arin maida ma Fauzy kayanta bayan ya gama bedsheet d'in ma ya yaye shi a ranshi ya shiga tunanin yadda zai yi dashi can ya juya ya nufi hanyar toilet yaje ya saka shi cikin washing machine, dawowa yayi ya zauna a bakin gadon idon shi akanta, hannu ya kai yana shafa gefen fuskar ta ya shiga jera mata sannu yace tayi hak'uri yanzu za'a zo a dubata zata daina jin zafin shiru bata tanka ba sai faman sheshsheka take, bada jimawa sosae ba akai knocking k'opar cikin d'an d'aga murya ya bada izinin a shigo, matashiyar likita ce tana sanye da lab coat kanta ta sanya farar himar idanuwanta na sanye cikin glasses yayin da hannunta ke ruk'e da d'an plastic first aid kit, da sallama ta shigo ya d'aga ido ya kalleta hakan yasa ta nufo shi, daga gefe ta tsaya fuskar ta a sake ta gaishe dashi ya amsa tace gata an buk'aci ganinta ya d'aga mata kai tare da nuna mata Fauzy a hankali yace ita zata duba ta furta Ok, aje kit d'in tayi ta kai idonta kan Fauzy data duk'unk'une tace mata sannu ko, shiru bata amsa ba hakan yasa ta rankwafa ta d'aura hannunta a jikinta ta k'ara ce mata sannu sai lokacin ta d'aga mata kai, tambayar ta tayi Mike damunta tayi shiru ta k'ara cewa ta daure ta fad'i mata hakan zai sa tasan wane treatment zata bata, da k'yar ta bud'e idanunta da sukai mata wani irin nauyi har sun d'an kumbura sunyi jajur haka lips d'inta ma sunyi ja ta shiga motsa baki amman ta rasa mi zata ce mata, tana niyyar sake tambayar ta Sameer dake kallon su ya bata amsa da she had her first night and she said she was feeling much pain, kai ta jinjina dama ta zargi hakan tunda tasan da yayi auren kawai don ta cika ka'idar aiki yasa ta tambaya, bud'e d'an akwatin tayi ta fiddo gloves bayan ta gama sakawa ta kalli Sameer tace mashi zata duba ta ya kauda kan shi tare da ce mata she should go ahead ta d'an yi murmushi tare da d'an ta6e baki ta maida idon ta kan Fauzy, saida taji tsananin tausayin Fauzy ya kamata a ranta ta yanke da gani ba tantama k'arfi ya gwada mata, sosae ta dubata tana yi tana yi mata sannu tare da d'an girgiza kai kuma har lokacin Sameer d'in na nan zaune ya had'e hannuwan shi ya d'aura Ha6arshi yana kallon gaban shi, d'agowa likitar tayi fuska a yamutse ta d'an saci kallon Sameer a ranta ta ayyana merciless, ganin bata buk'atar stitches tace mashi suna buk'atar ruwan zafi da d'an gishiri yace Ok akwai a cikin toilet gishirin kuma yace yana zuwa ya mik'e ya nufi hanyar fita, bayan fitar shi ne ta d'an zauna daga bakin gadon ta kai hannu ta d'ago da ita har lokacin sheshsheka take ta shiga rarrashinta, bada jimawa ba sai gashi ya dawo ruk'e da yar jakar gishiri ya kawo mata bayan ta amsa ta taimaka ma Fauzyn ta mik'e saidai tana yin yunk'urin tafiya ta saki yar k'ara da sauri ta fara k'ok'arin komawa ta zauna likitar tana ce mata sannu bata iya tafiyar ne tana nishi ta d'aga mata kai, Sameer ne yace bari ya kai mata ita yay mata d'aukar jarirai suka nufi toilet d'in, yana d'auke da Fauzyn har ta gama had'a ruwan ta kalleshi tace zai iya sauketa, ganin yayi masu tsaye bayan ya ajeta yasa tace Shikenan he can go kaman bazai tafi ba sai kuma ya juya ya tafin, yana komawa cikin d'akin Haisam ya kira a ranshi sosae yaji dad'in yadda ya nuna damuwa don ya gane bai koma bacci ba, bayan yayi picking tambayar shi halin da ake ciki yay ya sanar mashi da an samu Doctor din gata can tana treating nata Haisam ya furta Alhamdulillah in sha Allah zata samu sauk'i kada ya damu shima sun samu Kusan irin problem d'in da second wife en shi Sameer ya furta Ok, cike da tsokana yace mashi amman wai shi ya akai ya bari har hakan ta faru ma yana wani irin murmushi yace shi da yake da aure ma ya bari hakan ya faru balle shi da wannan ne first time en shi, yar dariya Haisam yay yace kawai dai ya fad'i mashi he lost control ya d'age gira yana murmushin gefe yace he never thought haka abun yake, dariya mai sauti Haisam yay kafin yace ai da ya tsaya yana ta cutar kanshi Sameer d'in ya furta wllh sukai dariya, kafin suyi sallama yace mashi pls ya lalla6ata sosae ya furta Ok, duk yadda likitar taso Fauzy ta zauna ruwan abun yaci tura sai faman koke koke take tana fad'in zafi bazata iya ba sai fama take da ita, jin kukanta yayi yawa ya sashi dawowa cikin toilet d'in ya tambayi ya akai likitar tayi mashi bayanin tak'i ta zauna ruwan ne yadda yakamata da bud'ar bakin shi sai cewa yay to dole sai ta zauna ne, ba don shine yayi Maganar ba daya samu amsa daidai dashi dama ya bata haushi yadda taga yayi ma Yarinyar, amsa ta bashi da eh Saboda ta samu rauni ne dole sai tana zama ruwan ne zata warke ya jinjina kai alamar gamsuwa kafin ya maida idon shi kan Fauzy da ta d'an d'osana ta zauna a bakin bathtub tana ta jan majina tare da yar sheshsheka, tambayar likitan yay daga zaman ruwan zafin sai mi tace tana buk'atar taci Abinci sai tasha pain relievers, tambayarta yay tazo da magungunan tace eh akwai wasu da zata bata yace Ok taje kawai ta aje mashi su nan zai sakata a ruwan tace Ok amman yanzu wannan tasan yasha iska akwae buk'atar a canza wani yace Ok ta canza, har ta juya ya tambayi tsawon lokacin da zata yi a ruwan ta fad'i mashi kafin tace ya bita a hankali yadda ruwan zai shigeta yadda ake so yace Ok, da biyu ta fad'i hakan don a tunaninta yana iya cewa ya gwada mata k'arfi, bayan fitar likitan rarrashin Fauzy ya shiga yi cikin kwantar da murya kai kace bai iya hakan ba, kuka taci gaba da yi tana cewa ita dai bazata iya shiga ba zafi yake k'ara mata, shiru yayi ya rasa yadda zai yi mata idon shi akanta sai faman juye juyen ciwo take, k'arshe dai dole saidai k'arfin ya gwada mata ya d'auketa cak tana ta kuka kamar za'a ma k'aramar yarinya wanka, daga baya da ruwan ya shigeta sosae ta d'an d'auki lokaci a ciki sai gashi ta fara jin dad'in shi ta saki jiki, bayan ta d'auki lokacin da aka fad'i mashi ya canza ruwan ya shiga yi mata wanka bata yi yunk'urin hana shi ba don tasan ba lalle ya k'yaleta ba gashi dama gaba d'aya ba k'arfi a jikinta saidai kawai ta runtse idanunta, bayan ya gama yi mata yace mata tayi na tsarki yana tsaye tayi ta gama ya d'aukko babban towel ya rufa mata ya sake d'aukko wani short ya lulluba mata a kai ya kara d'aukkota suka fito cikin d'akin, a saman gado ya d'aurata ya mik'e ya nufi wurin dressing mirror, mai da yake amfani dashi ya d'aukko yazo ya shafa mata yana ta kallonta har lokacin idanunta a rufe suke, bayan ya maida mai d'in wurin press d'in shi ya nufa ya bud'e yay d'an jimm yana tunanin kayan da zai d'aukko mata tasa kafin zuwa da safe, wasu riga da wando masu taushi ya d'aukko mata duk da yasan zasu yi mata yawa sosae amman zata fi jin dad'in su, shi ya saka mata kayan ganin kanta ya tsane yasa bai yi tunanin a busar dashi ba, ana gama saka kayan ta kwanta duk wannan abun bata bari ta had'a ido dashi ba, ganin yadda ta takure ya ja mata Duvet tare da mik'ewa ya nufi hanyar fita daga cikin d'akin, lamo Fauzy tay duk ta damu tunaninta yanzu taya zata je wurin su Aunty Mareeya a haka ta fara yin gyangyad'i, ya d'an d'auki lokaci sannan ya dawo yana d'auke da wani madaidaicin tray ya aje a saman table, cup d'in tea ne mai k'auri sai bread da wainar kwai Kitchen yaje yasa aka had'o mashi, wurinta ya nufa har tayi bacci kana ganin yanayin da take yin shi zaka gane shi is not alright, bai sha wahalar tashinta ba don baccin ba wani mai nauyi bane, farko nunawa tayi ta k'oshi kaman zata yi kuka da yayi mata Maganar Abincin saida ya rarrasheta sannan da kanshi ya fara bata, ba laifi ta d'an ci da yawa don wani irin fayau cikin ta yay mata, bayan ta nuna ta k'oshi tana niyyar kwanciya da sauri yace ta bari tasha magani sai ta kwanta, a saman nightstand ya d'aukko su guda biyu ne kowanne an rubuta yadda za'a sha ya 6allo mata da sauran tea din data rage ya bata tasha bayan ta gama fuska a yamutse tace ruwa zata sha da sauri ya furta Ok ya nufi hanyar fita, a hankali ta juya tana kallon bayan shi ganin shi take kamar bashi ba, a parlor ya d'aukko bottle water tare da glass cup ya kawo mata bayan ya bud'e ya zuba mata ya kai bakinta zai bata ta d'aga hannu ta amsa fuskarta na kallon gefe, kaman rabi tasha ta mik'a mashi ya amsa suma ya aje su saman table, zaune tayi bata kwanta ba yay tsaye yana kallonta ya lura da kaman fushi take dashi don tak'i ta ko kalle shi, cike da k'arfin hali ta fara kokarin mikewa yana ganin haka ya tambayeta mi take so ne tace mashi d'akin da suke zata koma da sauri ya matsa ya kamata yana fad'in taya zata koma a wannan halin ta kwanta anan ai lafiya lou zuwa da safe in ta k'ara samun sauk'i sai ta koma, shiru tay dama dai kawai ta fad'a ne amman itama ba son komawa take a wannan halin ba kuma tunda su Aunty suka ga ta dad'e tasan tuni ma sun zargi wani abu, janyewa tayi daga kamatan da yayi ta kwanta yaja mata duvet, d'auke tray d'in yay ya nufi hanyar fita, a parlor ya zauna ya idasa cinye sauran data rage don shima yunwa yake ji bayan ya gama anan ya bar kayan ya dawo cikin bedroom d'in, toilet ya wuce bayan wasu mintuna ya fito k'ugunshi d'aure da towel ya nufi press d'in shi, shima riga da wandon ya d'aukko ya fara sakawa yana yi yana kallon Fauzy bayan ya gama kimtsawa ya nufi gadon saida ya kashe wutar d'akin sannan ya daidaita kwanciyar shi, hannu ya kai zai rungumota jikinshi kawai sai ji yayi ta k'i bari yayi hakan nan ya gane idonta biyu ko kuma baccin bai d'auketa ba sosae, matsawa yay ya had'e jikinsu tana ta son k'wacewa ya kai bakin shi saitin kunnanta cikin magana mai kamar rad'a ya fara magana, "I'm very sorry Wife, I know I hurt you kiyi hak'uri pls bansan ya akai komai ya faru haka ba I don't know what came over me" sheshshekarta da yaji k'asa k'asa yasa shi gane kuka take, k'ok'arin juyo ta ya shiga yi ta dawo suna facing juna da yake a d'an kwai haske ya kai hannu yana goge mata k'wallan yana k'ara bata hak'uri yana bai san ya akai hakan ta faru ba, cikin Muryar kuka tace amman ba saida taita rok'on shi ba kan yayi hak'uri ya k'yaleta ba amman ya k'iya, a rud'e yace mata ya rasa control ne he didn't know that's how it was gaba d'aya tun farko ma baida niyyar wannan, shiru tayi bata ce komai ba ya shiga shafa gefen fuskarta yana fad'in Pls she should forgive her husband yasan yayi mata ba daidai ba, aka ce tsakanin mata da miji sai Allah ce mashi tayi shikenan tayi hak'urin, rungumeta yay sosae yana murmushi yayi mata godiya tare da Fad'in he knows he is blessed daya sameta matsayin mata shiru ta d'an yi sai kuma k'asa k'asa ta furta itama haka ya k'ara k'ank'ameta cike da jin dad'i yace "I Love You so much Babes" yay Maganar tare da pecking kumatunta, rufe ido tayi a ranta ta raya wato dama daya ta6a ce mata ba yanzu zai fad'i mata hakan ba yana nufin sai wannan lokacin kenan, shiru sukai wani irin nishad'i suke ji ba ma dai kamar Sameer ji yake yau is the happiest day of his life, jin saukar numfashinta a nutse yasa shi gane tayi bacci ya gyara masu kwanciya bada jimawa ba shima baccin ya d'auke shi. Kiran sallar Asubar farko alarm ya tashe shi, duk da bai jin k'warin jikinshi amman Saboda ya saba yin raka'atanil fajr yasa ya daure ya tashi bayan ya janye Fauzy a hankali, toilet ya nufa yayo Alwala bayan ya fito ya nufi press ya canza kaya zuwa jallabiya kafin ya nufo inda zai yi sallar, bayan ya gama zaune yay yana tasbih yana yi yana kai idon shi kan Fauzy dake ta bacci cikin Duvet fuskar shi a sake kaman zai yi murmushi, yana a wurin har lokacin sallar Asuba yayi ya tashi ya kabbara don ji yay bazai iya zuwa Masallaci ba, bayan ya gama yayi Addu'oi kafin ya mik'e ya nufi gadon, bayan ya haye yana k'ok'arin janyota jikinshi ta fara motsi a hankali ta fara bud'e idanuwan ta, tana bud'e su suka shiga cikin nashi ba laifi sun d'an k'ara washewa amman duk da haka yanayin su basu dawo daidai ba sunyi kalar na mara lafiya, bin shi da kallo tayi yay mata murmushi yace ta tashi ta d'an d'aga mashi kai, tambayarta yay ya take ji yanzu da k'yar ta bud'e baki ta bashi amsa da da sauki ya kai hannu yana shafa mata kai yace zata koma normal in sha Allah ta d'aga mashi kai, shiru suka d'an yi can yace mata ko tana jin yunwa ya samo mata abunda zata ci ta d'an girgiza mashi kai alamar a'a sai kuma ta tambaye shi gari ya waye ne yace mata eh anyi sallar Asuba ita ya gama yanzu, tana jin haka ta fara k'ok'arin tashi zaune ganin haka ya kai hannu ya taimaka mata, bayan ta zauna ya tambayi salla zata yi ta d'an yi shiru sai kuma tace mashi so take ta koma d'akin da suke in taje tayi sallar a can, ce mata yay miyasa ta damu da ta koma ne nan ba d'akin mijinta bane kuma ai ba komai don ta zo don anan ma zata zauna kafin su tafi UK, yamutsa fuska tayi kaman zatai kuka tace tafi son ta koma can in suka tafi sai ta dawo nan d'in yace Ok ta fara yin sallar, shi ya taimaka mata ta mik'e da k'yar ta fara taka k'afafun tana yin tafiya a hankali yana mata sannu k'arshe ma ganin yanayin tafiyar tata sai kawai ya d'auketa ya nufi toilet da ita, bayan anyo Alwalar Hijab d'in da tazo da ita ta saka kafin ta kabbara sallar, bayan ta gama ne ya nuna mata ya za'ai ta koma can a wannan halin ko tafiya bata iya yi sosae tace mashi gara dai ta tafi in ta zauna anan kowa zai san abunda ya faru gashi ba gama hidiman bikin akai ba ko yau ma za'a yi Walima, shi kan shi bai son abun ya bud'u hakan yasa yace suje ya rakata, farko kama mata hannu yay tana tafiya a hankali ganin bata sauri yasa shi d'aukarta tana ta fad'in don Allah ya ajeta kar a gansu yace mata ba wanda zai gansu tunda Asuba ne baza'a fito yanzu ba, suna zuwa bakin kopar Falon su tace ya ajeta shi da wai har cikin Falon zai shiga da ita ta kafe sai da ya sauketa, saida ta kalle shi sannan ta juya yay tsaye yana kallon ta har ta shige, tsaye tayi a bakin k'opar shiga Bedroom d'in da suke tana zullumin shiga can wata zuciyar ta raya mata to da tayi tsaye nan in kuma wani ya fito daga wani d'akin ya ganta fa, yin wannan tunanin yasa ta kai hannu a d'arare ta tura kopar a hankali, tana sa kai cikin d'akin suka had'a ido da Fatuu dake zaune akan abun salla bata dad'e da gamawa ba, har saida gaban Fauzy ya fad'i da suka had'a ido cikin kama kai da sauri ta janye idonta ta nufi ciki, cike da k'arfin hali take tafiya a k'ok'arinta na kada a gane saidai duk yadda taso tayi tafiyar sosae abun yaci tura dole a hankali take taka k'afafun, a bakin gado ta zauna tak'i yarda ta k'ara kallon Fatuu bayan d'an wani lokaci Fatuu ta taso ta nufo gadon itama ta zauna a gefenta tana kallonta da murmushi tace mata ta dawo, kai ta d'aga mata ba tare da tace komai ba sukai shiru can Fatuu ta dafa Shoulder d'inta tace mata ya akai ne wai sai lokacin ta d'an kalleta tana k'ok'arin k'ak'alo murmushi tace mata ba komai, Aunty Mareeya ce ta fito daga cikin toilet tana yarfe ruwa ganinta saida gaban Fauzy ya fad'i sosae tayi saurin janye idonta, nufo cikin d'akin tayi tana fad'in "Zarah kin gama sallar ki ara man Hijab d'in ita waccan mai amso sak'on ta tafin man da Hijab saida dama nace...." bata k'arasa ba sakamakon ganin Fauzy da tayi a gefen Fatuu, da sauri ta nufo inda suke ta tsaya daga gaban su tana fad'in ashe ta dawo Fatuu ta d'aga mata kai, tana kallonta tace "ke malama mai amso sak'o sai muji ki shiru kika sa munata zaman jira ko kayan dad'i ne ya siyo maki ki kawo mu tattamna muma" shiru bata ce mata komai ba bata kuma kalleta ba ganin haka yasa ta kirata "Fauziyya" shiru bata amsa ba, kallon Fatuu tay tace mata ya akai ne ta d'an rausayar da kai tace bata sani ba, tambayarta Fatun tayi yaushe ta dawo tace mata bada dad'ewa ba bayan ta gama salla itama tayi mata magana ta ganta haka, jinjina kai Aunty tay ta juya kan Fauzy ta kai hannu ta d'ago Fuskarta da d'an murmushi tace "Yar gidan Hajiya ya akai ne ko mun fara yar kunya ne" tana rufe baki Fauzyn ta fashe mata da kuka tare da kifa fuskarta a jikinta, d'an gwalo ido Aunty tay sai kuma ta fad'ad'a murmushinta ta kai hannu tana d'an bubbuga bayanta tana fad'in ya isa to miye abun kuka, jin yadda take ta kukan ne yasa ta d'ago fuskarta tana share mata hawayen tana fad'in ya isa Shikenan haka girma yake zuwa ma mutum, kukanta ne ya tashi Yaya Fareeda dake bacci da yake bata salla, tambayar Aunty tayi lafiya take kuka tana faffad'an murmushi tace mata ba komai Yaya Fareedar bata kawo komai a ranta ba don jiya tayi bacci aka tafi da Fauzyn, zama Aunty tay kusa da ita daga d'ayan 6angaren a hankali tace mata akwae abunda ke mata ciwo ne ta d'aga mata kai ta tambayi mike mata ciwon cikin muryar kuka tace duka jikinta, d'an jimm tayi tana ta kallonta can tace badai ta samu matsala ba ko tace mata likita tazo ta dubata tace wai ta rink'a zama a ruwan zafi sai magunguna da ta bata, a hankali suke Maganar amman duk su Fatuu na ji, jawota Aunty tay jikinta tana bata hak'uri tace zata daina jin ciwon bada dad'ewa ba sai faman murmushi take, tambayarta tayi yanzu ta zauna ruwan zafinne ta girgiza mata kai alamar a'a tace Ok bari tayi salla sai ta taimaka mata ta d'aga mata kai, mik'ewa tay tace ma Fatuu ta bata Hijab d'in jikinta bayan ta amsa da sauri ta nufi wurin yin sallar, bayan tafiyarta cigaba da yin sheshsheka Fauzy tay wani irin tausayinta ne ya kama Fatuu ta d'agata tana bata hak'uri tare da yi mata sannu haka ma Yaya Fareeda kai kawai take d'aga masu, bada jimawa ba Aunty ta gama sallar ta nufo su tana cire Hijab ta mik'a ma Fatuu kafin ta kalli Fauzy tace suje Toilet din, mik'ar da ita tayi har zasu tafi ta dakata tare da kai hannu tana fad'in a cire Hijab d'in ko, tana cirewa tabi kayan jikin Fauzyn da kallo kafin ta saki yar dariya tare da Fad'in "Sunan wani k'anin tsohon mu Baba Salmanu, wannan kayan fa?" tana rufe baki su Yaya Fareeda suka kwashe da dariya da sauri Fauzy ta fad'a jikinta tare da sakin wani sabon Kukan, rarrashinta ta shiga yi tana fad'in tayi hak'uri shegen bakinta ne da bai gani yayi shiru taga bada su ta tafi bane shiyasa ta tanka, da k'yar ta samu tayi shiru tayi ma su Fatuu alamar su daina yin dariyar kowa ya gumtse ta kamata har zasu tafi tace ma Fareeda ta bud'e akwatin Fauzy ta d'aukko mata towel ta kawo mata sannan suka nufi hanyar toilet tana tafiya a hankali Aunty Mareeyar tana ta mata sannu harda cewa ko ta goyata da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a, Bayan sun je toilet d'in a cikin bathtub ta tara ruwan zafin bayan ta toshe tasa Fauzy ta cire dogon wandon baccin da yake rigar ta rufeta sosae ta kawo mata har wurin gwuiwa, itama saida ta tittirje mata wurin zauna ruwan ganin yadda take yi ne yasa Aunty ce mata wai ta tabbatar bata samu matsala ba cikin nishi tace mata eh likitar ta dubata amman tace ta samu rauni, yamutsa fuska Aunty ta shiga yi tana d'an Jujjuya kai alamar tausayi kafin tace "shi kuma surukina ya da gaggawa haka, duk da dai abun farinciki ne amman banji dad'i ba d'an jakar uba ya wahalar man dake" tana rufe baki cikin yamutsa baki Fauzy tace "Aunty ki daina zagin shi shima yace bada son ranshi hakan ya faru ba" gwalo ido Aunty tay da alamun Al'ajabi tace "iyyeee, ah lallai miji dad'i, to tuba nike your Excellency ayi hak'uri su6utar baki ce" tayi Maganar tare da d'an harararta Fauzyn ta d'an tura baki tana kikkafta idanu kaman zatai kuka, sosae ta sakata ta zauna ruwan daga baya ta baro mata toilet d'in tace tayi wanka, after some minutes ta fito d'aure da towel d'in da Aunty ta kai mata su kuma kayan baccin Sameer d'in ta ninkosu lokacin Fatuu bata a d'akin taje tay feeding su twins da yake wurin su Mom suka kwana sai Yaya Fareeda itama har ta koma bacci, taimaka mata Aunty ta shiga yi ta shirya cikin doguwar jallabiya ta d'aura kallabin Aunty tace mata tasan bata rasa jin yunwa ko ta d'aga mata kai alamar eh, shiru tayi tana d'an tunani kafin tace ina wayarta ta kira shi tace tana jin yunwa, sai lokacin ta tuna da ita taje part d'in nashi hakan na nufin ta manto ta can ta fad'i mata, ce mata tayi to ta d'an kwanta aga zuwa d'an anjima k'ilan a kawo masu breakfast da wuri ta d'aga mata kai ta fara k'ok'arin hawa gado ta kwanta Auntyn na k'ara yi mata sannu sosae take jin tausayinta don tasan dole ma taji jiki, bayan ta kwanta itama Aunty Mareeyar kwanciya tayi basu dad'e ba da kwanciyar akai sallama bakin k'opa Aunty ta d'ago kai tana bada izinin a shigo, wata yar dattijuwar mata ce ta shigo tana ruke da wani had'addan basket sai k'yalli yake jikinta sanye da apron Aunty na ganinta ta mik'e zaune, nufo ta tayi da murmushi ta gaishe da ita ta amsa mata itama tana murmushin tace dama Yalla6ai Sameer ne yace ta kawo ma Amarya Aunty tace to ta tashi tsaye ta kar6a, kafin matar ta tafi ta nuna mata magunguna dake ciki basket d'in tace hada su aka ce ta kawo ta sake cewa sai kuma wannan ta Mik'o mata wayar Fauzyn, amsa tayi tay mata godiya Matar ta tambayi da wani abu Aunty tace mata a'a ta k'ara mata godiya ta juya ta tafi, nufar side drawer tayi ta d'aura kwandon kafin ta shiga bud'e had'add'un Warmers d'in dake ciki, d'aya farfesun kaza ne yaji kayan k'amshi gwanin kyau a ido, bayan ta rufe ta bud'e d'ayar soyayyen dankalin turawa ne da dafaffun k'wai sai kuma Flask wanda da gani set ne da Warmers d'in nan tea ne da yaji kayan k'amshi daga gefe akwae plates da cup sai cokulla sai Madara da milo da kwalin sugar, Murmushi Aunty ta shiga yi a fili ta furta "Su surukina kenan tunda fa an cuci yar mutane dole aita nan nan da ita" a ranta kuwa dad'i ne ya kamata don da alama komai ya kasance yadda take so, tashin Fauzy ta shiga yi bayan ta bud'e ido tace mata ta tashi ga Abinci nan Angonta ya aiko mata ta kamata ta tashi zaune, Fauzy taji dad'in Abincin dama a lokacin ta fara jin yunwar sosae, ba laifi ta ci sosae ba kamar kazar Aunty tasata tasha romon sosae, ganin tana ta ci yasa ta kalleta cikin d'an disashewar murya tace mata itama ta ci mana Aunty Mareeya tayi d'an murmushi tace ita dai ta ci ta k'oshi tukun don ta fita buk'ata, tana cikin ci sai ga kiran Sameer ya shigo Aunty ta d'auki wayar ganin shine tay d'an murmushi, picking tayi ta kara ma Fauzy a kunne shiru tay ta dakata da cin Abincin taji ya kirata da Babes d'an kallon Aunty tay data ruk'e mata wayar kafin can k'asan mak'oshi ta amsa, tambayar ta yay jikin a hankali tace mashi da Sauk'i yace ya manta bai sata ta zauna ruwan ba ta bashi amsa da tayi anan yace Ok sai kuma ya tambayi taci Abincin da aka kawo tace eh gashi nan tana ci yace Ok bari ya barta taci amman pls taci sosae sai tasha magani ta amsa da to ya katse kiran, bayan ta k'oshi ta bata magungunan tasha kafin ta koma ta kwanta sannan Aunty Mareeya itama ta zuba tana cikin ci Yaya Fareeda ta farka wai k'amshin abincin ne ya kai mata cikin bacci tama yi zaton Mafarki take Aunty tay dariya tace ango ne ya aiko ma amaryar shi shine take cin saura itama ta wanko baki tazo taci tace to. Wuraren k'arfe tara da rabi aka kawo masu breakfast lokacin Fauzy nata shan bacci tun bayan data ci Abinci, sanin ba yunwa take ji ba yasa Aunty bata tashe ta ba su Gwaggo nata tambayarta aka ce masu bacci take, bayan sun gama zama sukai anan falo suna kallo kafin zuwa k'arfe sha biyu suka fara shirin Walima don ana gama sallar Azahar za'ayi Saboda masu tafiya don gobe Monday, sosae Fauzy tasha bacci don saida Aunty ta tasheta Saboda shirin Walima kaman zata yi kuka tace ita dama an k'yaleta tayi kwanciyarta a d'aki Aunty tace ai tasan hakan bazai yuwuwa ba ta dai daure da anyi angama ai shikenan. Zuwa bayan Azahar kowa ya shirya Amarya Fauzy ansha rantsattsiyar shadda da ta sha ubansun aiki wuyanta da hannunta duk diamond ne, ba tare da 6ata lokaci ba aka shiga gudanar da Walimar data samu halartar manyan mata k'awayen su Her Excellency kowacce ka gani hamshakiyar kanta ce tsadaddun sutturu kawai kake gani kowa tayi shiga mai sunan shiga ansha gwalalai abundai sai wanda ya gani suma su Aunty ba laifi sun yi shiga mai kyau daidai k'arfin su, sai la'asar aka gama an ci an sha an kuma ba Fauzy kyaututtuka, ana gama Walimar su Mom sukai shirin tafiya harda yan Ethiopia zasu tafi can Abuja tare suma su Gwaggo suka ce tunda dai an gama mi suke jira akace Aunty tayi ma Her Excellency magana, koda tayi mata cewa tayi a'a yamma tayi su bari sai gobe da safe za'a maida su, sosae Fauzy taji dad'i da har ta shiga damuwa da suka ce zasu tafi, Fatuu ma da zata bi su Mom Aunty Mareeya ta rok'eta ta tsaya sai in zasu tafi koda ta kira Haisam ta sanar mashi cewa yay ba komai Allah ya kaimu, bayan gama Walimar ne aka kawo masu sauran akwatunan lefen Fauzy set biyu suma guda goma an narka uban kaya su Aunty suna ta jinjina yawan akwatunan har guda ashirin, bayan sun natsu ne Fauzy tace ma Aunty ta d'aukar masu kaya cikin lefen tunda dama wanda aka fara kaiwa ba'a d'auki komai ba don kayan duk a d'inke suke Fatuu ma tace mata ta d'auki abunda take so tace mata a'a ta bar shi aikuwa Fauzy tace in dai bata d'auka ba to tasan zaman da zata yi da ita wato ita ta amshi nata sai itace zata k'i amsar nata Fatuu na dariya tace to ai abun ba gasa bane ko kuma ita duka yaushe akai sunan su twins ta samu kaya sosae, duk da haka matsa mata Fauzy tayi sai ta d'auka k'arshe dai sai Aunty Mareeya ce ta d'aukar mata wasu abubuwan. Da daddare bayan sun yi shirin kwanciya Aunty tace ma Fauzy ta tafi wurin mijinta ta kwa6e fuska tace bazata je ba su Fatuu nata dariya ganin abun ya zamar masu drama Yaya Fareeda k'asa ta kwanta kan Carpet ganin gadon bazai ishe su ba don ga su twins. Washe gari bayan sunyi breakfast suka hau shirin tafiya gaba d'aya Fauzy duk tayi sukuku da ita, Misalin k'arfe sha d'aya na safe duk suka fito don tafiya Fauzy nata k'walla suna ta bata hak'uri Hajiya Zainab data rako su tana murmushi tace ma Fauzy nan ma ai gida ne ko, sha tara ta Arziki akai masu harda kud'i aka babbasu ganin da gaske tafiya zasu yi yasa Fauzy yin kuka sosae har ta karya ma Aunty Mareeya zuciya itama saida tayi k'wallan, aure kenan mai raba Y'a da uwa mai kuma raba dan'uwa da dan'uwa dole Aunty Mareeya taji kewar Fauzy don sun saba sosae, tana ji tana gani suka tafi suka barta sai fatan Allah ya kiyaye hanya ya kai su lafiya. Bayan tafiyar su Aunty part d'in Hajiya Zainab aka tafi da Fauzy anan Sameer ya sameta tana zaune a parlor ita kad'ai tana kallo saidai hankalin ta ba'a kan tv d'in yake ba damuwar tafiyar su Aunty ce a ranta yaran gidan duk sun tafi Makaranta da Amal ta zauna suna d'an yin hira jefi jefi don basu saba ba daga baya ta tashi don itama shirin barin K'asar take ta koma Makaranta dama bikin ne yasa ta zo, yana sanye cikin sabuwar farar shadda sai baza k'amshi yake ya zauna a kujerar gefenta, a sanyaye ta gaishe shi ya amsa yanata kallonta ganin yanayinta yasa a hankali ya tambayi ko har yanzu jikin nata su tafi hospital ta d'an girgiza mashi kai yace to ya ya ganta haka kaman abu na damunta tace mashi ba komai, shiru yay yana mata wani kallon ta kauda idonta can ya mik'e tare da kama hannunta yace suje, marairaice mashi tayi tace Momy ce ta taho da ita nan ya za'ai su tafi yace to sai ta zauna ita kadai tace ai tasan zata dawo sai kuma ta sameta bata nan, ce mata yay zai kirata ya sanar mata shi ya tafi da ita tana niyyar k'ara magana ya d'an d'aure fuska yace bai son gardama dole tayi shiru yana ruk'e da ita suka nufi barin falon, bayan sun fito ne ganin bata iya tafiyar sosae yasa hannu ya d'auketa gabanta sai fad'uwa yake kar wani ya gansu ahaka cikin sa'a har suka isa part d'in nashi basu had'u da kowa ba, bayan sunje a bakin gado ya d'aurata shima ya zauna ya kai hannu ya kamo nata yace ta fad'i mashi Mike damunta in ba ciwon bane, k'walla ne suka ciko mata cikin karyayyar murya tace mashi ba wani abu bane kawai ta damu da tafiyar da su Auntyn ta sukai ne tana yin Maganar k'wallan suka zubo mata sharr, jawota yay jikinshi ya sa hannu yana shafa bayanta alamar rarrashi can ya kai bakin shi saitin kunnanta yace mata ba gashi tare da ita ba miyasa zata damu, lamo tayi tana ta shak'ar daddad'an k'amshin shi mai narkar da zuciya, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin ya d'ago fuskar ta suka had'a ido nata sun d'an lumshe, tambayar ta yay jikin yana sauk'i ta d'aga mashi kai ya k'ara tambayarta ta zauna ruwan zafin yanzu tace mashi eh lokacin da tayi wanka da safe yace Ok bari a bari zuwa anjima sai ta k'ara a hankali tace to, bin juna sukai da kallo yanayin fuskar shi da d'an murmushi haka itama sun d'an d'auki lokaci haka jin bata iya jurewa yasa ta fad'a jikin shi tana d'an murmushi, kai bakin shi yay saitin kunnanta ya rad'a mata wata magana sai gashi ta d'ago da sauri tana kallon shi idanunta a d'an waje ya d'age mata gira, yamutsa fuska tayi idanunta sukai raurau alamar zata saka kuka kawai sai gani tay yay yar dariya har fararen hak'oran shi sun bayyana, maidota yay jikinshi ya rad'a mata he won't do it again until she've healed, murmushi ta shiga yi idanunta a rufe tana jin wani irin son shi na ratsa zuciyar ta. Ana gama bikin Fauzy aka tsaida lokacin da za'a yi nasu Nameer da Aunty Laila nan da wata ukku lokacin sun gama duk wani abu daya danganci karatun su, Fatuu bata koma Katsina ba dama hada karatu ke zaunar da ita can yanzu kuma ta gama k'arshe ma Haisam yanke tafiya da ita Us yay ta shiga yin shiri, ta bangaren Amarya Fauzy ma itama barin K'asar zasu yi bayan bikin da sati d'aya don har anyi mata passport, ana saura kwana biyu su tafi ranar laraba suka zo Abuja zo kaga murna wurin Fatuu su Mom ma sun yi farinciki da zuwansu suka tarbi Fauzy hannu bibbiyu, bayan sun ke6e da Fatuu a part d'in su ne ta shiga yaba canzawar da tayi cikin d'an lokaci har tana fad'in lalle Sameer ya iya tarairaiya Fauzy dai sai dariya take itama tace ma Fatun ai itace za'a ce ta canza don gaba d'aya yanzu ta koma kalar hajiyoyi haka dai sukai ta hirar nishad'i tsakanin su, anan suka wuni sai k'arfe biyar na yamma suka tafi Fauzy harda ce ma Fatuu in taje Us d'in zata sa Sameer ya kawota wurinta. Ranar Friday Jirginsu ya tashi zuwa England sai fatan a sauka lafiya. Washe gari Asabar Haisam da Fatuu suka tafi Katsina don yin sallama dasu Gwaggo ta kuma d'aukko kayan da take son tafiya dasu, har gidan Aunty Mareeya taje dama tasa tayi mata tanadin kayan gyara ta amso suka yi bankwana haka gidansu Haulat ma taje sunyi bankwana harda abun Arzik'in da ta saba tayi mata, washe gari Lahadi wuraren Azahar suka komo Abuja ta ci gaba da yin shiri don gobe in Allah ya kaimu suma jirginsu zai tashi zuwa Us, da yamma bayan anyi La'asar suka tafi inda za'a mata k'unshi da gyaran kai, Washe gari da Safe sukai bankwana wad'anda ke a gidan sukai masu rakiya zuwa Airport Jidderh kaman zata yi kuka wai zata yi missing yaranta Abie da Grandpa kaman yadda suke ce masu Mom na dariya tace koda su basu tafi ba ai itama tafiyar zata yi Dubai ta barsu ko tunda a cikin satin zata tafi itama. Tuni jirginsu Fatuu ya d'aga sai Fatan a sauka lafiya Fanan na can tana shirya masu kyakkyawar tarba sai faman farinciki take yaranta su Twins zasu zo gareta. Satin su Fauzy d'aya da zuwa lokacin tuni ta warke suna ta shan Amarci na gaske har yanzu ko ruwa bata ta6a dafawa ba bayan sunyi aure don anan d'in ma akwai mai aiki namiji da dama shi yake ma Sameer d'in Abinci da gyaran gida, koda tayi mashi magana kan ya sallame shi ta rink'a yi sai cewa yayi ba buk'atar sai tayi Abinci a marairaice ta nuna mashi ita dai tana son ta rink'a mashi girkin sai yace to ba yanzu ba, saidai ta ci ta sha ta ji da Sameer d'in, Washe gari ya kama Asabar ta kira Aunty lokacin bayan Azahar ne Sameer ya fita, Aunty na kwance tana bacci kiran ya shigo, saida ta kusa katsewa sannan ta farka ta duba tana ganin Fauzy ce ta saki murmushi tare da yin picking, bayan sun gaisa ta tambayi yadda suke ta bata amsa daga haka tay shiru, Aunty ta fahimci kaman akwae abunda take son fadi hakan yasa ta ce mata ya akai ne, ai kamar tana jira cikin murya kamar zata yi kuka tace "gaskiya Aunty wllh akwae Matsala" jin haka yasa Aunty Mareeya yunk'urin tashi zaune tana fad'in "Matsala kuma!, Allah ya rabamu da ita" bayan ta zauna sosae da alamun d'an tashin hankali tace mata wace matsala ce, Shiru tay kaman bazata yi magana ba saida Aunty ta k'ara tambayarta tace bazata fad'i mata ba ko so take hankalinta ya tashi ne sannan tace "Aunty kwanaki ba cewa kikai in dai matsalata yace yana sona ba ke zaki sa shi ya rink'a fad'i man hakan kaman cin Abincin shi safe da rana da dare ba" da sauri Aunty tace "eh hakane, bai fad'i maki hakanne?" Da sauri tace "a'a yana yi amman fa....Ke ba wai kina nufin zai rink'a ce man hakan ba?" ta canza Maganar zuwa tambaya Auntyn tace mata eh mana haka take nufi, "To nidai wllh ba ta yadda kika ce ba yake fad'i man Allah" da alamun rashin fahimta Aunty tace to taya yake fad'i mata, shiru tayi kaman bazata yi magana ba Aunty tace tana jinta taya yake fad'i mata, yar in ina ta shiga yi "n..ni Aunty bansan ya zance maki ba amman gaskiya abun yayi yawa wllh" yadda tayi Maganar kamar zata saka kuka lokaci guda Aunty ta gane mi take nufi ta shiga yin dariya jin haka yasa Fauzy ce mata yanzu dariya zata yi mata don Allah, tana yin dariyar tace mata "to Yar gidan Hajiya kece da wani abun dariya wllh, dama kawai sai ya zaune yay ta faman ce maki I love you Fauziyya kamar wani zautacce, yadda yake maki dama ta hakan nake nufi kuma wllh naji dad'i sosae k'ok'arina bai tashi a banza ba kenan kema farinciki ya kamata kiyi ba k'orafi ba" tura baki tayi tana yamutsa fuska tace to ai gaskiya abun yayi yawa bata iyawa, ta6e baki Aunty tay tana faffad'an murmushi tace "ba wani yawa, kowacce mace da kika gani da kalar mijinta haka kowa take hak'uri, bai kamata ace tun yanzu kin fara k'orafi ba yayi wuri da yawa yar gidan Aunty, kiyi hakuri a hankali zaki saba kada ki sare ko ki nuna gazawa ta wannan hanyar ake kama miji a hannu ni wllh baki ji dad'in da naji ba don hakan ya tabbatar da kwalliya ta biya kudin sabulu, ina son in ja hankalin ki dole sai kin jajirce in ba haka ba to kuwa zaki ja ma kan ki matsala ne tun ba'a je ko ina ba don yadda yanzu yasan takan abun to kuwa in baki wasa ba zai iya zarta halin shi da aka fad'i don haka kiyi hak'uri kada ki bari ki zama raguwa kawai ki dage da gyara kan ki kinji yar gidan Aunty Mareeya" kai Fauzyn ta d'aga kafin tace to don ta tsorata da Maganar Aunty da tace zai iya zarta ta6a matan da aka ce yana yi wanda shi kanshi k'ok'ari take ta saka shi ya daina kwata kwata duk da bata san ko har yanzu yana hakan ba, cigaba da kwatanta mata Aunty tay tana fad'in wannan dama ce a gareta da zata maido gaba d'aya hankalinshi a kanta Fauzyn nata fad'in to, bayan ta gama ne tace mata dama tana ta son tayi mata magana game da Motarta da suka dawo da ita nan tana ganin da aita ajiyeta mi zai hana a kai mata ita can Nasarawa in suka zo sai taci gaba da yin amfani da abunta Fauzyn tace to zata yi mashi magana kan hakan daga baya sukai sallama Aunty nata yar dariya. Sai bayan da akayi la'asar ya dawo gidan lokacin har tayi wanka ta canza kaya zuwa skinny jeans da yar top kanta tayi parking gashinta ba kallabi da yake da kanshi ya nuna mata irin kayan da yafi so tana sakawa kenan shiyasa ko da yaushe cikin k'ananun kaya take ko fita zasu yi da yake yana yawan fita da ita zaga gari a haka suke fita saidai in kaman zasu fita daga Mota ne ko siyan wani abu sai ta d'aura After dress, tana zaune a parlon su mai kyau mara hayaniya mai d'auke da lafiyayyun kujeru leathers ya shigo hannunshi ruk'e da wata yar jaka yana sanye da k'ananun kaya shima, juyawa tay ta kalle shi yana cire takalma a bakin kopa a wurin da aka tanada don yin hakan in mutum ya cire wanda ya shigo dasu sai ya saka wasu kaman slippers su kuma na shigowa cikin parlon ne, mik'ewa tay tana murmushi ta nufo shi tana zuwa daf da shi ya d'an wara mata hannuwa ta fad'a jikinshi ya rungumeta gaba dayansu sai sakin kamshi suke, d'ago kai tayi tace mashi welcome back ya d'aga mata kai fuskar shi da d'an murmushi yay sunkuyo yay pecking goshinta, nufo cikin parlon suka yi yana tallafe da ita suka nufi kujera 2 seater ya zauna tare da ita, k'ok'arin raba jikinsu ta shiga yi tana fad'in bari ta kawo mashi ruwa yak'i sakinta tare da girgiza mata kai alamar ba zai sha ba tana mashi wani kallo tace to bari ta kawo mashi lemu sai lokacin ya bud'e baki yace mata ta barshi bai jin k'ishi ya mik'a mata jakar hannun shi ta amsa tare da bud'ewa, tsadaddun kayan zak'i ne a ciki su biscuits, chocolate, Sweet da dai sauran su a ido kawai mutum ya gansu sai ya had'iyi miyau tun ma kafin yaci, d'agowa tay tana murmushi ta furta mashi "Thank you Honey, I really appreciate" wani kalar kallo yay mata tayi yar dariya don tasan dalilin kallon yace ba haka zata rink'a mashi godiya ba ita kuma kunya take ji, da k'yar ta kai bakinta tay pecking gefen fuskar shi ta d'ago tana murmushi shima shi yake yi, shiru ta d'an yi tana kallon shi slowly yace mata da wani abu ne ta d'aga mashi kai, Maganar Mota da Aunty tayi mata tay mashi, farko shiru ya d'an yi kafin ya tambayi Motar na gidansu ne tace mashi eh, ce mata yay ita Aunty d'in nata bata amfani da ita ne tace mashi eh tunda ai ba tata bace, hannu ya kai ya d'an shafi beard d'in shi tare da shigar da lip d'in shi na k'asa bayan ya sake shi yace mata ta kirata tace mata ta d'auka in tana so, waro ido tay tace yana nufin ta zama tata yace eh ita in suka koma Nigeria d'in zai siya mata wadda zata rink'a amfani da ita a can, wani irin farinciki ne ya lullubeta har fuskarta ta bayyana bata san lokacin da ta kai hannu ta tallabo fuskar shi ba tana washe baki ta furta "Thank you Honey, Allah ya kara Arzuki mai Amfani, I love you more than words can say" tana gama fad'in hakan ta kai bakinta saitin nashi ta manna mashi kiss tana d'agowa suka had'a ido kawai sai ta fad'a jikinshi tana dariya, shima yar dariyar yay don yanzu bai ma sanin yana yin ta, sosae yaji dad'in hakan da tayi mashi don bata cika yi mashi ba Saboda kunya saidai shi yayi mata da wuya ta fara mashi abu irin hakan, abunda bai sani ba shine tsoron ta tak'alo ma kanta take don yawanci daga hakan zancen yake sauyawa, kiran sunanta yay ta amsa ba tare data d'ago ba yace ta d'ago ta kalleshi, d'agowar tay tana murmushi ya bita da wani kallo can sai ji tayi ya mik'e da ita anan aka bar jakar tsarabar. Bayan sallar isha ta kira Aunty Mareeya lokacin data sanar mata zancen an bata Motar salati ta saka tace "Fauzy badai nuna mashi kikai a bani ba?" Da sauri tace mata a'a wllh ta kwashe yadda sukai ta fad'i mata, wata shewar farinciki Aunty tay tace "Sai surukina mak'erin rocket wato da alama ya fahimci ba K'aramin k'ok'ari nayi mashi ba wurin gyare ki wannan ina jin tukuici ne aka bani" dariya Fauzy tayi, godiya ta shiga yi cike da Farinciki ta tambayi yana nan tace mata a'a yaje salla amman tasan bada dad'ewa ba zai dawo tace Shikenan in ya dawo zata kira tayi godiya amman kafin nan don Allah ta fara yi mashi godiyar yadda ya kamata Fauzy na murmushi cike da Kunya tace ai tayi wannan, yar shewa Aunty tayi tace yauwa ko ita fa haka yakamata itama ta kasance da zafinta ita dai Fauzyn murmushi kawae tayi, suna cikin yin wayar ya shigo Fauzy ta nufe shi tana zuwa gabanshi ya kai hannu ya rungumota jikinshi tace mata gashi ya dawo kafin ta kanga mashi wayar a kunne k'asa da murya tace Auntynta ce, sosae Aunty tayi mashi godiya ya nuna mata ba komai. Satin su Fauzy biyu anan suka tafi Honeymoon wasu kasashen, daga cikin k'asashen da zasu je akwae, France, Germany, italy sai US kaman yadda Fauzy ta bukaci su kai ma su Fatuu ziyara sai Saudia da zasu je suyi umra daganan zasu dawo England. Bayan zuwan su Haisam Us yaso su d'an zaga wasu k'asashen tare da Fatuu suma matsayin Honeymoon da basu je ba to saidai Saboda aikin shi don yan tsakankanin nan yaje Nigeria sosae hakan yasa ya yanke bari sai bayan bikin su Nameer sai ya d'auki hutu suje duk da haka ya zagaya da ita wurare sosae a nan inda yake wato California daga baya kuma suka je wasu states na K'asar cikin wanda suka je akwai, Texas, New York, Florida, Washington sai Massachusetts. 98 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ ............Wata d'aya da rabi da zuwan Fatuu Us wata ranar Lahadi ta tashi da wani irin ciwon kai har da yar juwa take ji ranar dama Haisam a d'akinta yake su twins kuma na wurin Fanan dama haka suke yi in yana d'akin Fanan to a d'akin Fatuu zasu kwana haka in yana d'akin Fatuu to a wurin Fanan zasu kwana duk da suna da Nursery wato d'akin su wanda aka k'awata shi da abubuwan da suka danganci yara amman basu kwana a ciki, ganin yanayinta yasa yace mata su tafi Hospital amman sai tace mashi tana ganin basai sun je ba tunda ciwon ba wani tsanani yayi ba dama kuma lafiya lou ta kwanta tana ganin in tasha magani zata warke k'ilan harda gajiyar zirga zirgar da suka yi ne ya nuna gamsuwa da Maganar ta, ganin basu kaiga yin Breakfast ba yasa ta bari in taci Abinci sai tasha maganin dama suna dasu a first aid kit d'in su, Saboda yanayin da take ciki yasa bata samu zuwa Kitchen ba don had'a breakfast tare da mai aikin su wadda take baturiya, dama mafi yawancin lokutta tare suke aikin Fanan ma wani lokacin takan shiga saidai ba kowane lokaci ba Saboda aiki da take zuwa, a daddafe tayi wanka ta shirya cikin k'ananun kaya riga da skirt bayan an gama shirya masu table aka sanar dasu, gaba ɗayansu kowa yayi wanka suna sanye da k'ananun kaya lokacin da suka zauna zaman yin Breakfast d'in har su twins ma an masu gayu in ka gansu a lokacin sai kayi tunanin sunyi shekara ɗaya Koma sun fi don gaba d'aya sun yi wani irin girma sunyi 6ul6ul dasu ga bak'ar sumar su a nad'e gwanin burgewa haka idanuwansu farare tass dasu lips ɗinsu ma sun k'ara cizawa ta bangaren fata kuwa tamkar ka ta6a jini ya zubo har wani sheƙi take don mayukan fata masu tsadar gaske ake masu amfani dasu haka na gashin kan su ma, Bayan sun gaisa da juna Fanan ta kalli Little Grandpa dake hannunta da turanci tace mashi "Say Hello to Mom" kallon Fatuu yay ganin tana mashi murmushi yasa shima yay mata Fanan ta k'ara ce mashi yace mata hello ya d'aga hannu cikin Maganar shi da bata fita yace mata hello d'in itama Fatun ta d'ago mashi, kallon Abie dake hannun Haisam tayi tace mashi shima yace mata Hello ɗin yay shiru yanata kallonta ta sake maimaita mashi still baida niyyar cewa hakan yasa Fanan tace da alama shi kalar Dad d'in shi ne don tana lura bai cika yin magana ba kamar grandpa duk sukai murmushi ƙarshe saidai Haisam ya kamo hannun shi ya d'aga ma Fatun itama ta d'ago mashi sai lokacin Abie ɗin yay kaman zai yi murmushi, bayan sunyi bismilla a nutse suka fara cin Abincin baka jin komai sai k'arar cokulla Haisam na ci yana ba Abie haka Fanan ma tana ba grandpa sosae yaran suke ci, tun bayan da Fatuu ta fara ci taji kaman zuciyar ta na tashi haka dai ta daure tana cigaba, basu dad'e sosae da fara ci ba da sauri ta aje fork d'in hannunta ta dafe k'irji jin kaman amai na taho mata, Fanan ce ta fara lura ta kalleta tana tambayar ta lafiya hakan yasa Haisam kallonta shima yana niyyar yin Magana suka ga ta tashi da sauri ta nufi hanyar corridor da zai kai ta inda Bedrooms d'in su suke saidai ko kafin ta shiga corridor d'in Aman ya zubo nan ta duk'a ta shiga kwarara shi, har Kusan rigen mik'ewa ake tsakanin su suna rungume dasu twins suka nufeta, sannu gaba d'aya suka shiga yi mata Fanan ta dafata grandpa na ganin halin da Fatuu take ciki ya fashe da kuka ganin yana kuka yasa Abie shima ya saka kukan, kallon Haisam Fanan tayi da alamun damuwa akan fuskarta ta tambaye shi dama bata lafiya ne ya fad'i mata yadda sukai da ita da safen nan sam bata kawo komai a ranta ba tace mashi gaskiya yakamata su tafi Hospital a duba ta sosae da sauri yace Ok don shima halin da take cikin ya d'aga mashi hankali, saida ta gama sannan Fanan ta taimaka mata ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom da ita don ta shirya su tafi Asibiti Haisam yabi bayan su yana ruk'e da su twins da ya rarrashesu sun daina yin kukan, ba tare da 6ata lokaci ba suka fito don tafiya Fanan tayi ma mai aikin su magana kan tazo ta gyara wurin aman kafin suka tafi, Haisam ne ke driving Fanan na front seat gefen shi tana ruƙe da su twins ita kuma Fatun an bar mata baya ita kad'ai ta zame jikinta ta kwantar da kanta, akai akai suke juyowa suna mata sannu da d'an murmushi take amsa masu tace ai taji ta samu sauk'i ma da tayi aman can tace ma Fanan ta kawo yaro d'aya ta rik'e mata harda tambayarta zata iya tace mata eh ta mik'a mata Abie, Asibitin da Fanan ke aiki suka nufa bayan sun isa ya parker Motar a inda aka tanada duk suka fito, basu wani tsaya Jira ba wurin ganin likita tunda dama nan ne asibitin da suke zuwa duk da Fatun wannan ne zuwanta na farko bayan tazo ƙasar, bayan Fanan tasa anyi mata duk wani abu da ake yi kafin ganin likita aka tura sunanta, tare gaba d'aya suka shiga wurin likitan wanda Bature ne yana ganin Fanan ya washe mata baki yana mata Welcome itama murmushi ta yi mashi ta amsa mashi ya maido idonshi kan Haisam suka gaisa haka Fatuu ma, mik'a ma Fanan hannu yay alamar ta bashi Adam dake hannunta ta mik'a mashi sai gashi bai mashi ƙyuya ba ya yarda dashi, nuna ma Haisam leather sofa dake gefe Yay alamar ya zauna itama Fatuu ya nuna mata ta gaban table d'in shi Fanan ma ta zauna akan wadda take facing ta Fatuu, Fanan ce tayi mashi bayanin abunda ke damun Fatun tace tana ganin ya kamata ai mata aune aune shiyasa suka zo ya furta Ok, maida kallon shi yay kan Fatuu yace mata sannu ta amsa kafin ya shiga yi mata tambayoyi, cikin tambayoyin ne ya tambayeta yaushe rabonta da period tace mashi bayan data haihu ya dawo tayi sau d'aya daga nan bai sake dawowa ba, tambayarta watannin su twins yay ta bashi amsa da shidda da rabi, bayan ya gama yi mata tambayoyin ne yace ma Fanan ya tura tests da za'a mata ta amsa da Ok tare da mik'ewa ta kai hannu ta kamo Fatuu tace suje, kallon Haisam tay tace mashi bari suje su dawo ya d'aga mata kai, ganin zasu fita yasa Adam dake kan cinyar Doctor fashewa da kuka yana Mik'o masu hannu, dakatawa sukai Fanan ta nuna mashi saitin Haisam tana fad'in "Look at Dad he's here" juyawa yay ya kalli saitin Haisam da take nuna mashi yana ta6e baki kamar zai cigaba da yin Kukan, juyawa sukai suka tafi bayan sunje lab ɗin ba 6ata lokaci aka d'ibi jinin Fatuu don yin gwaje gwajen, bayan an d'iba dawowa sukai Office ɗin likitan Fanan tace ma Fatuu ta zauna kan kujerar da Haisam yake ita kuma ta koma kan ta gaban table d'in Doctor suka shiga tattaunawa irin tasu ta likitoci, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba aka turo results d'in Doctor ya sanar dasu gashi an turo duk suka maida idanun su kanshi, duk awon da aka mata ya nuna lafiya lou sai guda d'aya na ciki da yake nuna akwai na tsawon sati shidda wato wata d'aya da rabi kenan tunda tazo K'asar ta same shi, tsananin mamaki ne ya bayyana akan fuskokin su ba kamar Fatuu don ita a tunaninta tunda bata period bazata samu ciki ba, da mamaki Fanan tace ma Doctor ɗin is he sure about what he said cike da tabbaci yace mata haka result d'in ya gwada tare da juyo mata da computer d'in don ta gani, bayan ta tabbatar da sakamakon d'agowa tay ta kalli Fatuu da tayi zuru tana kallon su kafin ta maida idonta kan Haisam da shima mamaki ya bayyana kan fuskar shi tace mashi yaji wai Zarah is pregnant ya jinjina mata kai, Doctor d'inne yace masu ana yin hakan su kwantar da hankalin su Haisam yay sigh kafin yace ma Doctor ɗin gaskiya yayi wuri da yawa ace tana da ciki at least jikinta na buk'atar Hutu sosae tunda bata dad'e da haihuwa ba gashi kuma twins, jinjina kai Doctor din yay yace hakane yanzu ya za'ayi shiru Haisam ya d'an yi yana kallon Floor da alama yana nazarin wani abu ne can ya d'ago ya kalli Doctor ɗin yace ya yake gani in a fitar dashi, nuna mashi yay akwae risk sosae fitar da ciki amman kaman nata da yake k'arami sosae ba'a ciki samun matsala ba Magani kawai za'a bata in akai sa'a zai fita ba tare da wata matsala ba in sun amince, jinjina kai Haisam yay kafin yace a bata maganin a tare Fatuu da Fanan suka kalle shi da sauri kowa da yanayin mamakin jin Maganar, da alamun damuwa Fatuu tace "A...amma Hubby kai da kan ka zaka ce a zubar da shi bacin kasan ba kyau hakan laifi ne" shiru Fanan tayi yanayin fuskarta ya sauya kaman zatai kuka a yadda take ji inama ace cikin a jikinta yake don sai taji bata son a zubar dashi ji take kamar ta rok'e su kada a zubar dashi amman tana gudun aga ta zaƙe, shima Haisam da alamun damuwa ya shiga kwatanta mata duka yaushe ta haihu gashi tasha wuya dole jikinta na buk'atar Hutu kafin ace ta sake wahalar wani cikin ga wahalar rainon su twins suma tunda ba yaye su tayi ba, haka ya dingi kwatanta mata matsalolin yace tunda k'arami ne kuma zata iya cutuwa haka su twins ma ba laifi bane in an cire, shiru tay tana d'an tunani ita kanta bata ji tana son cikin ba amman kuma sai taji bata goyon bayan a zubar dashi, gaba ɗaya idanunsu na akan Fatuu da tayi shiru ta kasa cewa komai ganin haka yasa Doctor ce masu ko suje gida suyi shawara in still suna son a fitar dashi ko Dr Fanan zata iya d'aura su kan hakan, yana yin Maganar da sauri Fanan ta kalle shi zuciyarta ta shiga harbawa don bata jin da hannunta zata taimaka ayi abortion ga wata ma balle kuma wannan, Haisam ne yace ma Doctor ɗin a bata maganin kawai ya furta Ok yana k'ok'arin tashi a ruɗe Fatuu ta kalli Haisam tare da girgiza mashi kai tace "a'a Hubby a barshi kawai kar a cire ana iya zuwa kuma a samu matsala tunda Allah ya bamu kawai mu barshi muyi fatan ya zama Alkhairi kada mu cire kuma muzo daga baya muna so Allah yak'i bamu wasu ma da yawa suna nema basu samu ba" yanayin yadda ta k'are Maganar kamar zata yi kuka, shiru Haisam d'in yay idon shi akanta wani irin tausayinta yake ji na ratsa shi dama dalilin tausayin nata yasa yace a cire ba wai don bai son cikin ba, Maganar k'arshe da Fatuu tay ita ta ƙara karya ma Fanan zuciya har bata san idanunta sun ciko da kwalla ba saidai ji tayi sun zubo da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, duk yadda taso kar tayi kuka abun yaci tura, jin sheshshekarta a hankali yasa su kallonta da sauri ganin yanayinta yasa Fatuu kiran sunanta ta amsa cikin Muryar kuka ba tare da ta d'ago ba aikuwa zumbur ta mik'e ta nufeta, a gabanta ta tsaya tasa hannu tana k'ok'arin d'ago da fuskar ta, bin fuskar Fanan da tayi sharkaf da hawaye tay da d'an rud'ewa ta hau tambayar "Aunty Fanan what happened? Miya sa kike kuka don Allah?" Girgiza mata kai tayi kafin cikin kuka tace mata ba komai, shiru Fatuu tay tana yamutsa fuska itama kamar zata yi kuka ta shiga tunanin miya sa Fanan d'in kuka lokaci guda zuciyarta ta tariyo mata da Maganar da tayi, waro ido Fatuu tay tare da ɗan buɗa baki da sauri ta shiga faɗin "Aunty Fanan wllh ba dake nike ba da nayi Maganar kawai na bashi misali ne ban san abun zai ta6a maki zuciya ba don Allah kiyi haƙuri" idanunta har sun ciko da ƙwalla, girgiza mata kai tayi tace "No Zarah, baki man laifi ba ai abunda kika faɗa gaskiya ne kuma ni ai nasan ba dani kike ba Saboda ni inada yara ko?" Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai tare da kai hannu ta fara goge mata ƙwallan Fanan ɗin na ɗan murmushi, bayan ta gama goge mata hawayen ta tambayeta itama bata son a fitar da cikin ko farko shiru Fanan ɗin tayi kafin ta ɗan jinjina mata kai alamar eh, juyawa tayi ta kalli Haisam cikin harshen turanci tace mashi Auny Fanan ma bata so don haka koda ita bata son cikin to zata haƙura ta haife shi, murmushi yay tare da ɗan lumshe ido haka ma likitan don yanzu ya fahimci komai da bai gane abunda ke faruwa ba saboda da Hausa suke Maganar sai jefi jefi suke saka turanci, kama hannunta Fanan tay ta d'an girgiza mata kai tace duk da bata ta6a haihuwa ba tasan tun daga rainon ciki akwae wahala in dai itama taji tana son a cire d'in kada Saboda ita ta canza ra'ayi Fatun tace a'a da gaske bata son a cire har cikin ranta ta amince a bar mata suyi mata Addu'a Allah yasa kada ta sha wahala kuma ta haife shi lafiya Fanan na murmushi tace in sha Allah daga yanzu ta fara mata Addu'a kan hakan har zuwa ta haihu ta kalli Haisam dake kallon su fuskarshi a sake tace daga yanzu su fara mata Addu'a ya jinjina kai, tattaunawa Fanan ta shiga yi da Doctor kan maganin daya kamata a bata wanda zai sa ta daina amai ta rinka cin Abinci haka su twins ma suma za'a basu wanda zai k'ara inganta lafiyar su Haisam ya tambayi yanzu zata iya cigaba da breastfeeding nasu doctor din yace k'warae ba wani abu taci gaba da basu koda har zuwa ta haihu ne kuma a rinƙa basu maganin da zai basu yay mashi godiya. Bayan sun baro Asibitin tun akan hanya Fanan ta shiga kiran yan Nigeria su Hajiya da Mom ta sanar masu harda Gwaggo ma kowa yay mamakin jin samun cikin daga baya duk sukai Addu'oin Allah ya inganta ya raba lafiya. Sosae Fanan ke kulawa da Fatuu bayan da suka san da cikin haka su twins ma in dae tana gida bata je aiki ba ita ke duk wata ɗawainiya dasu dama tana kulawa dasu sosae yanzu sai ta k'ara don komai ita ke masu kama daga yin wanka shirya su basu Abinci yi masu wasa da sauransu haka Haisam ma in yana a gidan tare dashi ake masu komai koda Fatuu tayi yunƙurin yi masu wani abu sai suce ta bashshi ta huta duk da jikin nata da Sauk'i sosae iyakar ta shayar dasu sai kuma in suna zaune tare dasu ta d'auke su har tayi masu wasa, k'arshe ma Haisam cewa yay yakamata a samo masu nanny Saboda in basu nan ba sai ta rink'a wahalar kulawa dasu ba amma sai ta nuna mashi ba sai an samo ba tunda ba wani ciwo take ba zata iya wannan amman ya nuna ta bari dai a samo ganin hakan yake so yasa ta amince amman tace to ya bari tunda sun kusa tafiya biki in suka dawo sai a samu ya amince da hakan. A kwana a tashi ba wuya a wurin Ubangiji, bikin su Nameer nata matsowa har ya rage saura sati ukku lokacin watan Fatuu biyu da sati guda a Us, a yadda sukai da Haisam in ya rage saura Sati biyu zata tafi shi kuma sai ana saura sati d'aya zasu taho shi da Fanan, gudunmawar miliyan biyu ya bata yace in basu isa ba tayi mashi magana cike da nuna farinciki ta nuna mashi sun isa har ma sun yi yawa, a yadda sukai da gwaggo bayan ta kirata kan Maganar kayan ɗaki ce mata tayi tana ganin kawai za'a siya mata ne ready made har ma tayi ma Aunty Mareeya magana kan hakan tace in an tashi siya akwae inda zata kai su suna da kaya masu kyau wanda za'a siya ma Minon, Fatuu taji dad'in jin hakan gaba d'aya gudunmawar da Haisam ya bata ta tura ma gwaggo tace saura tata in tazo Gwaggon tace wannan uban kuɗi haka da ɗanta ya bada anya basu yi yawa ba Fatuu na yar dariya tace mata a haka ma cewa yay in basu isa ba tayi magana ya ƙara da sauri gwaggo tace don Allah kada ta ƙara tambayar shi ko Naira wannan ai Kusan ma shi zai mata kayan ɗakin, tambayarta Fatuu tayi kamar ya za'a mata kayan gwaggo tace wai da ita a tunaninta ayi mata saitin gado da kujeru masu kyau wanda da an gani ansan masu kud'i ne tunda Baffan su ma sunyi Magana kan kayan ɗakin ta nuna mashi ya turo kuɗi kawai a siya sai duk a haɗa a siya mata, cewa Fatuu tay gaskiya kamata yay ayi mata komai set biyu kujerun da gadon don tasan gidan da za'a kaita babba ne alabashshi ko sai a siya set ɗaya masu kuɗi sosae sai ɗayan koda wanda basu kai su kuɗi ba Gwaggon tace to hakan ma bari in aka harhaɗa kuɗin sai aga kaman ya za'a siya mata don itama tana son a yi mata kaya sosae tunda ita ba'a yi mata komai ba Fatun tace komai kenan sai tazo sai suje a siya in sha Allah ba abunda zai gagara bane, itama Gwaggon tace in sha Allah nan take faɗi mata Hajiya tayi mata magana kan inda za'a ɗaura aure sun roƙi alfarmar in ba takura a ɗaura a nan Katsina sai a haɗa da na Laila a ɗaura gaba ɗaya anan sai a tura Mota can Adamawa ta ɗaukko masu zuwa ɗaurin auren nan don in akace ayi acan sannan ayi na Laila a Abuja za'a takura mutane don zirga zirgar zata yi yawa to ta kira Baffansu kan hakan shima yayi magana da yan'uwanshi duk sun amince da hakan shi Arɗo ma ance ba lalle yazo ba don bai jin daɗi Fatuu ta tambayi abunda ke damun shi tace mata kawai harda tsufa wai jikin nashi ne bai jin daɗin shi, fatan Allah ya bashi lafiya Fatuu tayi kafin suyi sallama Gwaggo ta tambayi ina Y'ay'anta Fatun tace gasu can wurin Aunty Fanan wai tafiya take koya masu, yar dariya gwaggo tayi tace da wuri haka Fatun tace eh wai daga taga sun fara tsayuwa shine ta fara koya masu Gwaggo na dariya tace ina ruwan ɗiyarta tana dai kula da yaran sosae Fatun tace sosae don yanzu har aiki take tafiya dasu ta bada su wurin raino a can har makaranta aka so saka su amman ta hana wai ai a wurin rainon ana koya masu abunda ake koyawa a Makarantar, da alamun mamaki gwaggo tace "wace irin Makaranta kuma yaran da basu wuce wata bakwae ba" yar dariya Fatuu tayi tace mata su nan haka suke yi kamar wurin raino ne to sai a rinƙa nuna masu abubuwa don su taso sun sani gwaggon tace ta gane aikuwa bari itama tazo ta koma Makaranta ko ta ƙara sanin abubuwa kada suzo su ƙureta harda ma turanci zata koyo, Fatuu nata Dariya itama gwaggon Dariyar take daga baya ta tambayeta ya jikin nata ta bata amsa da Alhamdulillah tace badai ta laulayi sosae ko Fatun tace mata eh ai maganin da take sha kullum yana hana ta yin amai ko tashin zuciya lafiya lau take cin Abinci saidai wani lokacin tana jin kasala taita kwanciya sai kuma ciwon kai da take yi wani lokacin shima, Addu'ar Allah ya inganta ya sauketa lafiya gwaggon tayi Fatuu na murmushi tace "Amin ya rabbi, Allah ya amsa gwaggota mahaifiyata, ina tsananin son ki da dukkan zuciyata" wani irin murmushin daɗi gwaggo tayi itama tace "nima ina ƙaunar ki autata Fateema, ina roƙon Allah ya ƙara ma rayuwar ki albarka data zuriyar ki ya jiƙan Mahaifiyar ki" wani irin lumshe ido Fatuu tayi nan da nan idanunta suka ciko da kwalla don a lokacin nan koda yaushe Mahaifiyarta na a ranta sosae take jin maraicinta tana jin inama ace tana raye rayuwarta tayi albarka haka, jin tayi shiru yasa gwaggo kiran sunanta ta amsa a hankali tana jin yanayin muryar tata ta gane kuka take, itama zuciyarta karyewa tayi abubuwa suka fara mata yawo a rai tay ƙarfin halin ce ma Fatuu ta daina Kuka tayi mata Addu'a in sha Allahu ta dace a sanyaye ta amsa da Allah yasa, kafin suyi sallama gwaggon tace in kusa Fanan take ta bata su gaisa tace to, bayan ta kai ma ta a Nursery ta sanar mata ga gwaggo zasu gaisa cike da nuna jin daɗi ta amsa cikin washe baki suka gaisa gwaggo tace ai an faɗi mata tana nan tana ta aikin koya tafiya Fanan d'in tay dariya tace eh so take su iya kafin su zo biki yadda in suka zo zasu je ko ina da ƙafafun su gwaggon tace lallai kam akwae aiki yanzu nan da sati guda kenan take son su iya tafiyar tana ta dariya tace eh itama gwaggon dariyar take tace to Allah ya taimaka ya bada sa'a ta amsa da Amin kafin suyi sallama harda kara ma Adam wayar wai yace mata Hello sai gashi yace ɗin cike da jin daɗi gwaggon ta shiga yi mashi magana da hausa tana tambayar yadda suke shida ɗan'uwan shi yay zuru yana zaro ido Fanan da Fatuu sai yar dariya suke ganin yadda yay ganin sunata dariya yasa shima yin dariyar gefen kumatun shi duk suka lotsa Madarar kyau abun sai dai ace tubarkalla, amsar wayar Fanan tay gwaggo tace ko basu yi masu magana da Hausa ne tace a'a suna yi masu Momynsu ma harda Fulatanci tana masu magana haka Dad d'in su ma yana masu larabci zasu taso suna jin yare hudu Gwaggo tace Masha Allah Allah yay masu albarka da sauri ta amsa da Amin da zasu yi sallama Fanan ɗin harda cewa "We love you so much granny" gwaggo na murmushi da hausa tace "nima ina son ku Y'ayana, Allah ya ƙara ma rayuwar ku albarka ya ƙara haɗa kan ku ya kauda idon maƙiya da mahassada ya kare ku daga dukkan sharri" cike da jin daɗi Fanan ta amsa harda lumshe ido daga baya ta ba Fatuu wayar don suyi sallama. Shirye shiryen biki nata kankama a dukkan 6angarorin angwaye da amaren, Bayan sati guda Fatuu ta taho da wata babbar Mata da zata zo Kano harda iyalinta Haisam ya haɗasu don su taimaka mata da su twins dama damuwar shi kenan yadda zata yi dasu shiyasa ma bata wani kwaso kaya ba iya ɗan babban trolley ne da yar jaka sauran sai zasu zo su taho mata dasu, bayan sun iso Kano Matar tace mata in ba jirgin da zai je Katsina yanzu sai su tafi gidanta kafin lokacin tafiyar yayi Fatuu na murmushi tace mata ai da Haisam ya siya mata ticket online akwae wanda zai tashi bada daɗewa ba yaran Matar suka shiga faɗin wayyo ba haka suka so ba sun so su bisu gidansu don basu gaji da ganin su twins ba ita dai Fatuu murmushi kawai take, itama Matar da wani matashin mutum da zai tafi Katsina ta haɗa su don ya taimaka mata shima a first class zai zauna inda Fatun zata zauna, lokacin Haisam ya kira don yaji in sun sauka Fatuu taba Matar waya sukai magana sosae yayi mata godiya tana ta fara'a irin tasu ta manyan Hajiyoyi tace ai ba komai duk yima kaine tana fatan wata rana in yazo ƙasar zai kawo mata su yace in sha Allah daga baya ta sanar dashi itama ta damƙa su a hannun wani da zasu zauna tare don ta bincika bata samu mace da zata zauna anan ba yace to ba komai ya ƙara mata Godiya kafin sukai sallama, Wuraren karfe sha biyu na rana suka sauka Katsina, cike da Farinciki su Gwaggo da kawu Amadu da Amarya Mino sai Tk daya kai su suka tarbe ta basu zo da Kamalu ba shi Kawu Amadu ya baro ma shago, kowa yay mamakin ganin yadda Fatuu ta canza har sun kasa rufe bakunansu gaba ɗaya hutu ya zauna mata sosae tayi 6ul6ul da ita ga skin ɗinta ta ƙara mulkewa ta ƙara haske in tayi dariya abun gwanin burgewa ga cikinta har ya ɗan fito, su Twins kam abun ba'a magana su wannan tun a jirgi aketa santin su, sai so suke su ɗauke su amman sun ƙi yarda dama Adam ne me ɗan yarda a ɗauke shi shima sai yaga Fatun na a kusa, da ƙyar ya yarda Mino ta ɗauke shi daga wurin mutumin da ya ruƙe shi a jirgi sai faman ta6e baki yake zai yi kuka Fatuu ta shiga rarrashinshi da turanci tana ce mashi itama Minon Mom ɗin shi ce, shi dai Abie na liƙe da ita da alama ma tsoronsu yake don har fuskar shi ta nuna ya waro ido tubarkalla sai bin su da kallo yake, Sosae su gwaggo sukai ma mutumin godiya yana murmushi ya nuna masu ba komai kafin sukai sallama ya tafi, bayan sun fito wurin da aka parker Motar su ukku suka shiga baya kawu Amadu ne yanzu zai tuƙa Motar don ya iya bayan tafiyar Fatuun Tk ya koya mashi da Motar tata tare da amincewarta, yana fara driving Fatuu ta shiga yaba mashi ganin har ya iya Tk dake gefen shi yace ai yanzu ba inda bai zuwa da mota, bayan sun bar Airport ɗin suna ta hira Fatuu ke tambayar Hajiya Tk na murmushi yace tana nan lafiya tana can tana jiran isowar su, lokacin da suka iso ƙopar gidansu tsayawa Fatuu tasa akai don ta gaisa da Yayanta Kamalu yana ganinta ya hau washe baki yace bari ya rufe shago yazo su ƙarasa gidan tare, a gaban Motar Tk ya matsa mashi suka tafi suna isa gate su officer suka taso suna masu sannu da zuwa daga baya aka buɗe masu gate suka shige, a gaban entrance ya parker Motar duk suka firfito lokacin Saude ta fito cikin washe baki ta nufo Fatuu itama tana ganinta ta fara mata murmushi tana zuwa ta ɗan rungumota tana mata sannu da zuwa aikuwa Abie na ganin haka ya fashe da kuka da sauri Aunty Saude ta saketa tana faɗin ashe ba'a ta6ata ta shiga ba shi haƙuri tana faɗin ai ta saketa to yay shiru ai kamar ma tana ƙara tunzura shi sai kukan yake ƙara yi ganin haka yasa Sauden cewa to ko dai tsoron baƙaƙen Mutane yake Gwaggo tace taga alama don tun ɗazu duk ya bi ya ƙanƙame Uwar tashi, ganin Abie ɗin na kuka yasa Adam shima fashewa da kukan dama ƙiris yake jira Mino ta matso dashi wurin Fatun don ta rarrashe shi, Hajiya ce ta fito tana dogara sandarta ta alfarma idanunta sanye cikin glasses ta nufo su tana faɗin ita dai tayi gajen haƙuri ta fito, ganin su twins na kuka yasa ta tambayi mi ya faru duk suke kuka Saude ta faɗi mata ta jinjina kai tana dariya tace aikuwa aiki ya same su in dai tsoron baƙaƙen mutane suke tunda ƙasar su suka zo duk akai dariya, gaishe da ita Fatuu tay ta amsa tana ta fara'a tay mata sannu da zuwa kafin tace to a shigo ciki a zauna yadda za'a gaisa sosae suka ce so ta kalli su twins da suka bita da ido tace masu barkansu da zuwa ƙasar baƙaƙen fata, tambayar ina mai gidan nata yake tay Fatuu ta nuna mata shi a hannun Mino tace wato ita kenan don tana fara ya yarda da ita duk sukai dariya, cikin gidan duk suka nufa a parlor aka zazzauna ana ƙara gaisawa da ƙara yi masu sannu da zuwa Hajiya ta tambayi Fatuu jikinta tana ta murmushi tace Alhamdulillah tay fatan Allah ƙara ingantawa ya sauketa lafiya ta amsa tare da su Saude, sake tambayar ya ta baro su Haisam Hajiyar tay tace lafiya lou duk suna gaishe su suna nan zuwa, Saude nata kallon Fatuu don komai tayi burgeta take can ta kasa haƙuri tace mata har ta canza sosae Hajiya tace ai dole yanayin ƙasa ba ɗaya ba, Maganar Abinci Hajiya tayi ma Fatuu tace gashi can an shirya akan table in kuma a kawo nan to tace eh a kawo nan cikin parlor Saude ta amsa da to ta miƙe, sallama gwaggo tayi masu Hajiya tace ta tsaya sai sun ci Abinci sannan, lafiyayyun Abinci da abun sha aka jere akan carpet duk Saude tay serving nasu abun yay kamar yar Walima har gwaggo na faɗin to kada kuma su cinye ma baƙi abinci Hajiya tace ai dama harda yan tarbar baƙin aka yi, a nutse suka fara cin abincin harda Hajiya a kan c-table aka ɗaura mata bayan ta fara ci tace ma Mino ta kawo mata Adam, kuka ya saka bayan ta kawo mata shi yana miƙa hannu alamar Mino ta ɗauke shi Hajiya ta shiga rarrashin shi tana faɗin "Haba mai gida yada tsoron Mata inata farincikin tarbarka sai kuma kaƙi yarda dani" su Gwaggo nata murmushi Hajiya ta kalli Fatuu tace "to wai ma yana fahimtata ko sai anyi turanci" amsa ta bata da eh suna gane hausa amma sun fi fahimta in akayi turanci, komawa Hajiya tayi tana rarrashin shi da turanci har ya fara yin shiru manyan idanun shi a kanta yana ta6e baki ita kuma tana ta faɗin yayi shiru shagwa6a66an maigida, lokacin da suka gama cin Abincin an kira Azahar Kawu Amadu da Tk suka tafi Masallaci gwaggo ma tayi ma Hajiya sallama su Fatuu da Mino suma suka fito don tafiya part ɗin su wanda tuni Saude ta gyara mata shi, bayan sallar la'asar lokacin Fatuu tayi wanka ta canza kaya haka su twins ma an yi masu wanka an canza masu kaya iri ɗaya suka tafi gidan Gwaggo, a can gidan ma anyi masu abincin tarbar su Fatuu tace sai anjima sai suci tunda yanzu basu jin yunwa suka shiga tattaunawa game da shirye shiryen bikin Minon nan Gwaggo ke sanar mata Abbas ya bata gudunmawar dubu ɗari biyu Fatuu taji daɗi tay godiya da Allah ya saka da Alkhairi, anan Haulat tazo ta iske Fatuu tsaf tsaf da ita tana sanye cikin doguwar rigar material mai kyau tayi rolling veil in ka ganta baka ta6a cewa ta ta6a aure tana ruƙe da hannun ɗiyarta lokacin data zo itama tsaf da ita an sa mata kaya masu kyau haka kanta ba laifi tana da gashi ma sha Allah, gaba ɗaya sunyi farincikin ganin juna Fatuu tace ai da tana niyyar zuwa gidansu bayan Magrib shiyasa bata kirata ba ta tambayi ya akai tasan ta dawo tace mata kawu Amadu ne ya kirata ya sanar mata, nan suka shiga yin hira itama saida ta tanka kan yadda Fatun ta canza tana dariya tace ai itama ta canza taji daɗin ganinta haka don da alama ta kwantar da hankalinta Haulat ɗin tace mata eh, duk yadda Haulat taso ta ɗauki su twins sun ƙi yarda kuma sun ƙi bari Fatuu itama ta ɗauki ɗiyar Haulat ɗin da tayi yunƙurin ɗaukarta sai su fashe da kuka abun ma sai ya zama abun dariya, tana nan har aka yi sallar Magrib bayan an gama ta tafi. Washegari bayan sun gama yin breakfast ita da Mino ta shirya suka tafi gidan gwaggo don anjima zasu tafi siyayyar kayan ɗakin Mino kamar yadda suka tsara jiya da gwaggon da har tace ta bari sai gobe lokacin ta ƙara huta gajiya Fatun tace a'a gara su tafi ayi komai a gama don bikin nata matsowa, bayan sallar azahar Aunty mareeya ta iso dama ita suke jira ruƙe da babban kwali Kawu Amadu da Kamalu sun kamo mata suka shigo, a falo suka zauna aka shiga gaisawa ta ƙara yi ma Fatuu sannu da zuwa dama jiya tayi mata a waya, sai gashi ita lafiya lou su twins sun yarda da ita ta ɗauke su harda Abie su gwaggo sukai ta mamaki Aunty Mareeyar na dariya tace ai ita dama da wuya yara suyi mata ƙyuya Mino tace kuma dama itama fara ce ƙilan shiyasa suka yarda da ita da mamaki Aunty mareeya ta waro ido tace tsoron baƙaƙe suke ne aka ce mata eh aikuwa ta ƙyalƙyace da dariya tace bata ga laifin su ba wake son baƙi duk akai dariya, bayan an gama gaishe gaishen Gwaggo tasa Mino ta zubo mata abinci da sauri ta dakatar da ita tace wllh a ƙoshe take don daga kan abinci ta taso Fatuu tace to ai dai ko lemu tasha tace to a bata, bayan ta gama sha ne ta buɗe jakar ta ta fiddo kuɗi bandir biyar, miƙewa tay ta matsa daga gefen gwaggo ta aje bayan ta dawo ta zauna tace gashi nan gudunmawarta ce ita da Fauzy ga kuma wasu kayan Kitchen nan a haɗa ayi mata amfani dasu, gaba ɗayan su waro ido sukai suna kallonta da tsananin mamaki gwaggo ta kama baki kafin tace "Ƴata wannan gudunmawa haka ai tayi yawa gaskiya" tana dariya tace a'a ba wani yawan da tayi in so samu ne ma ai tafi haka tunda duk hidimarsu ce, Fatuu na niyyar yin magana Aunty Mareeyar ta dakatar da ita harda zare mata ido duk ta basu dariya, godiya sosae Gwaggo ta shiga yi mata tana addu'ar Allah ya bar zumunci haka Fatuu ma, tambayar yanayin yadda za'a siya kayan ɗakin Aunty Mareeya tayi Fatuu ta faɗi mata kowanne set biyu tace hakan yayi amman fa za'a sha kuɗi gaskiya don kaya yanzu sai Addu'a ko dai a siya set ɗin kujeru ɗaya masu kyau sai ayi gado biyu gwaggo tace ita da cewa tayi ma a yi kowanne seti ɗaya Auntyn tace a'a ayi dai gadon biyu sai kujeru ɗaya sai sauran kayan Kitchen da electronics suma nan ba ƙaramin kuɗi za'a kashe ba ga kuma labulaye, tambayar Fatuu tayi tasan yanayin gidan da za'a kaita ne don asan yawan labulayen da za'a siya tace a'a gaskiya Aunty tace yakamata kuma a sani ko akwae wanda zata iya tambaya, shiru ta ɗan yi kafin tace gashi Jidderh bata nan itace zata iya tambaya lafiya lau Aunty Mareeya tace ko ta kira Laila sai ta nuna mata labulaye ne ake son yi ai ba wani abu bane tace to, bayan ta kira Laila ɗin sun gaisa tayi ma Fatun an zo lafiya ta amsa itama tayi mata ya shirye shiryen hidima Laila tace Alhamdulillah Fatuu tay fatan Allah ya nuna masu ta amsa da Amin, tambayarta tay kamar yadda Aunty Mareeya tace Laila ta bata amsa da gidan bene ne ta fasalta mata yadda tsarin gidan yake Fatuu tayi mata godiya har zasu yi sallama Laila ta dakatar da ita tace amman fa saman benen Nameer yasa mashi kaya kar suce zasu yi kaya harda nan kuma duka gidan ma an sa labulayen ƙasa da sama sai dai kawai in zasu ƙara mata ne Fatun na murmushin jin daɗi tace to tare da yin godiya, bayan sun gama yin wayar tayi ma su Gwaggo bayani gaba ɗaya suka washe bakin farinciki Aunty Mareeya tace yauwa sunga kujeru set ɗayan sun isa tace a bata takarda da biro suyi list ɗin abubuwan da za'a siyo yadda da sun je ba tare da 6ata lokaci ba su fara yin siyayyar Fatuu ta ƙwala ma Mino kira tace ta taho da paper da biro, tare suka shiga faɗin abubuwan da za'a siya tana rubutawa, bayan ta gama suka miƙe don tafiya dama Motar Fatuu na a ƙofar gida, su ukku suka fito Aunty Mareeya na ruƙe da Adam Fatuu kuma Abie aka bar Mino a gidan, bayan sun fito ne cike da farinciki gwaggo ta sanar ma Kawu Amadu gudunmawar su Aunty Mareeya shima sosae yaji daɗi yana ta faffaɗan murmushi ya shiga yi mata godiya tana faɗin haba ba komai ai an zama ɗaya. Lokacin da suka isa wurin siyayyar babban bene ne hawa ukku gaba ɗaya manyan show rooms ne a ciki shaƙe da ƙawatattun furniture da rantsattsun kayan adon gida na gani na faɗa, cikin haba haba mai wurin wadda babbar Hajiya ce da yaranta suka tarbe su tana ta washe masu baki harda yunƙurin ɗaukar su twins suka ƙi yarda, bayan sun gama gaisawa suka yi mata bayanin kaya suke so tace gasu nan sun zo gidan kaya masu kyau da Quality ta shiga nuna masu suna jinjina kai da yabawa don ba ƙarya akwae kaya a wurin Aunty Mareeya tace ai tasan suna da kaya masu kyau shiyasa tayo masu jagora Hajiyar ta shiga yi mata godiya, ba 6ata lokaci suka shiga za6a ba tare da wani yin ruwan ido ba don kowane kaya haɗaɗaɗun kan su ne, kamar yadda suka tsara gado biyu suka za6a sai set ɗin kujeru da labulaye harda Carpet da wasu kayan ƙawata falo da ɗaki harda kitchen da kuma wasu kayan Kitchen amman banda electronics don Fatuu tace su bari suje EE inda Haisam ke zuwa gym su siya acan don suna da sauƙin kaya, kaya masu sunan kaya suka zazza6a saidai an kashe kuɗi ba kaɗan ba, bayan sun gama siyayyar suka ce ma matar ba yanzu zasu tafi dasu ba in ba matsala a cikin satin nan da za'a shiga za'a zo a ɗauka da sauri tace lafiya lou ba damuwa da ta basu receipts shikenan za'a ware masu kayan yanzu, bayan sun biya ta basu shaidar siyayyar harda ba Aunty Mareeya tukuici tana dariyar jin daɗi tayi mata godiya itama tayi masu godiyar harda cewa tana fatan suma zasu kawo mata customers suka ce in sha Allah tunda ta duba masu, bayan sun bar nan wurin siyan electronics suka wuce nan ma suka siya kayan kallo da fridge, Electric cooker harda injin wanki da sauran su, saida suka siya komai da suke buƙata sai abunda ya rage wanda sai sunje kasuwa zasu siya harda kayan gara dana abincin da za'a ci da biki, a gida suka sauke Aunty Mareeya suna ta mata godiya tana faɗin haba ba komai ta tambayi lokacin da zasu je Kasuwar Gwaggo tace ita ta fidda lokacin da take da halin zuwa, a daren ranar bayan isha Kawu Amadu ya shigo bayan ya dawo daga Masallaci nan suka shiga tattaunawa kan gyaran da za'a ma gidan Fatuu tace da da hali ma da sababbin furniture aka saka gwaggo tace a'a a gyara su kawai hidiman da yawa don ma an samu gudunmawa sosae an gode ma Allah suma kuma sunyi ƙokari ita da Kawu Amadu haka suma iyayen su Baffa da Yadikko tace ba ƙaramin ƙokari sukai ba sun bada kuɗi da yawa, suna murmushi itama gwaggon suka yaba mata tayi murmushi tare da fatan Allah ya nuna masu bikin lafiya duk suka amsa. Washe gari da safe gwaggo taje wurin Hajiya tayi mata magana game da ɗaukar kayan ɗaki tace to zata kira can Abuja tayi masu magana harda cewa tana fatan badai su takura kan su ba wurin yin kayan gwaggo na murmushi tace eh. A cikin satin suka je Kasuwa ƙarasa yin siyayyar harda wasu zinarai Fatuu ta tafi dasu tasa Aunty Mareeya ta rakata inda ake saida su ciki harda wanda aka siya mata da kuɗin da Haisam ya ta6a bata da zai yi aure lokacin da kuma zasu yi aure gwaggo ta canzo mata shi da kuɗin daya bata sai gashi sosae yayi daraja harda yan'kunnan da wata ƙawar Mom ta bata da bikin su suma ta saida gaba ɗaya kuɗin taba Gwaggo tace a haɗa ayi gara dasu tace mata don me zata saida abunta duk kuɗin data bada basu isa ba tana murmushi tace to ai ƙarin zasu yi amfani kuma dama amfanin ajiye abun kuɗin kenan Aunty Mareeya na murmushi tace naka sai naka duk suka yi murmushi gwaggo tace hakane Aunty mareeyar ta ƙara faɗin "Allah ka bar mu da yan'uwanmu ka ƙara mana ƙaunar juna da abunda zamu taimaki juna" duk suka amsa da Amin. A kwana a tashi abu nata matsowa ranar Alhamis da daddare Hajiya ta kira Fatuu ta sanar mata gobe Juma'a za'a ɗauki kayan Mino sannan jibi su Aunty zasu kawo lefenta gwaggo tace to Allah ya kaimu, washe garin wurin ƙarfe sha ɗaya na safe Motar ɗaukar kayan ta iso gwaggo ta kira Aunty Mareeya tace to su haɗu can wurin da za'a ɗauki kayan, a Motar Fatuu suka tafi harda Kawu Amadu da Tk Motar kayan tabi bayan su, bayan sun je ba 6ata lokaci aka fara fiddo kayan ana shiryawa a cikin Motar wanda zasu iya fashewa aka ware su bada su za'a tafi ba aka kai ƙaton kwalin su Motar Fatuu, bayan sun gama da nan wurin ɗaukar electronics aka wuce suma aka ɗaukko su gaba ɗaya Motar ta ɗauke kayan da yake babbace sosae, Aunty mareeya ce ta tambayi gwaggo baza'a bi su ba Saboda shirya kayan in anje tace ita sam bata ma yi tunanin hakan ba, kiran Hajiya gwaggon tayi bayan ta ɗaga sun gaisa ta sanar mata an gama shirya kayan za'a sa wani ya bisu ne saboda shirya kayan Hajiyar ta bata amsa da ba dole bane masu kai kayan na gida ne in sunje zasu shigar dasu ciki shiryawar kuma ko in an kai amaryar sai ayi wannan tace to tare da yi mata godiya, daga nan su Kawu Amadu Keke Napep suka hau suka koma gida su kuma suka wuce kasuwa don yin siyayyar kayan abincin da za'a tarbi su Aunty masu kawo lefe daga can wurin Chef Ƙawar su Aunty mareeya za'a kai su ita zata yi abincin. Washe gari Asabar anata shirye shiryen tarbar lefe, sai bayan Azahar suka iso da yake tafiyar Mota ce, a gidan Hajiya suka fara sauka su biyu suka zo Aunty da babbar Ƙawar Mom sai wata yar'uwar Senator da ta zo daga Daura ta jira su anan gidan Hajiya, saida suka huta bayan la'asar suka fito don zuwa kai lefen harda Hajiya dama ba'a fiddo akwatunan daga cikin Jeep ɗin da suka zo da ita ba, Mota biyu suka yi su Aunty driver daya kawo su ya jasu sai su Hajiya Tk ya jasu suka nufi gidan, gidan har anyi sabon fenti yay kyau lokacin da suka isa su Aunty mareeya da Feenah da inna zaliha sai ƙawar gwaggo da innar su Haulat ne suka tarbe su, falo aka nufa dasu bayan anzazzauna cikin sakin fuska aka gaggaisa dasu tare da yi masu an zo lafiya, su Tk da Kawu Amadu ne suka fara shigowa da akwatunan har suka gama set ukku ne masu guda biyar gaba ɗaya akwatunan guda goma sha biyar ne kowane set da kalar su sun haɗu sosae, Aunty mareeya ce da Feenah suka shiga duɗewa ba abunda kake ji daga bakunan mutanen wurin sai Ma sha Allah Gwaggo sai sakin murmushin farinciki take haka ma Fatuu don an zuba kaya ba ƙarya itama an ɗinka mata wasu da yawa ga uban ƙananun kaya da gani Nameer ɗin na son su haka su Aunty Mareeya suka faɗa, kaya dai sai son barka itama harda zinarai da sarƙar diamond mai kyaun gaske, sai faman yabawa ake Hajiya ta kalli Tk da Kawu Amadu dake tsaye suma suna kallo tace "ku baku da ma niyyar yin auren balle akai naku lefen" dariya sukai Tk yana ɗan sosa ƙeya yace "ai ni harda ma lefen ke ƙara man tsoron auren wllh, A.A ne ya yakamata yay niyya ya fiddo mata kwanan nan don nasan lefe ba matsala bace a wurin shi don ya daɗe yana tara kuɗin shago" duk akai yar dariya shima Amadun faffaɗan murmushi yay yace ai ba ƙananun kuɗi ke haɗa lefe ba balle kuma irin wannan shi in son samu ne ma a yafe mashi lefen yay Maganar idon shi akan Haulat, a hankali ta juyo zata saci kallon shi karaf suka haɗa ido da sauri ta janye ta koma kallon kayan Aunty Mareeya tace aikuwa ko ance an yafe dole sai ya fiddo tarin shagon da yake yi yayi shi don bazai ɗauki tsawon lokaci yana amshe ma yan unguwa kuɗi ba sannan yaƙi yin lefen yana dariya yace ai gini zai yi da wanda ya tara tace ya kawo Matar nan cikin gidan tunda ga ɗaki nan za'a bari in Mino ta tafi Auntynsu Haisam na dariya tace dole dai sai yayi lefen kenan itama Aunty Mareeyar dariyar take yi tace eh, bayan an gama ganin kayan aka yi addu'o'i kafin aka fara shigo masu da Abubuwan da aka shirya masu na ci farko cewa sukai a ƙoshe suke sun ci abinci a gidan Hajiya Gwaggo ta marairaice tana roƙon su ci Aunty mareeya ma tace yakamata na nan ma su ci tunda don su aka yi, ƙarshe dai yanke bin su akai dashi Mota tunda sun ƙi su ci aka ce in sunje gidan Hajiya sai su ci, anata masu godiya Gwaggo ta tambayi amman dai ba yau zasu koma ba ko taga yamma tayi Aunty tace eh sai gobe da safe in Allah ya kaimu, da daddare Nameer ya kira Mino aka shiga yin hira irinta masoya masu muradin juna anan tayi mashi godiyar lefe yace miye abun godiya don yayi abunda yake hakkin shi ne tana murmushi tace duk da haka dai yana murmushi yace mata in akwae abunda take so wanda babu a ciki karta ji komai tayi mashi magana zai siya ya aje mata da sauri tace babu komai yayi, tambayar ta yay taga english wears dake ciki tace mashi eh yace to su yake son ta rinƙa sakawa shiyasa ma ya siyo su daga US da ɗan alamun kunya tace to, daga yadda ta bashi amsa ya gane taji kunya yace mata yana bata shawara duk ta bar wannan kunyar a gida kafin tazo in ba haka ba shi zai cire mata ita har saida ta ɗan runtse ido kafin tace to, kafin suyi sallama ya tambayi ba wani event da zasu yi ne anan tace eh tunda za'a yi Dinner da Walima anan yace amman yakamata tayi ko don Friends ɗinta tace to bari zata yi ma Adda Fatuu magana kan hakan yace Ok in sun fidda abunda zasu yi sai ta faɗi mashi tace to, bayan sun gama wayar ta iske Fatuu a ɗakin gwaggo suna tattaunawa ganin hakan yasa ta juyo da niyyar ta fito Fatun ta kirata ta komo ciki, bayan ta zauna Fatun na murmushi tace "Amaryar mu ya akai ne" Gwaggo ma kallonta take tana murmushi, faɗi mata yadda sukai da Nameer tayi ta ɗan yi shiru kafin tace to ko tayi ko Friend's Eve ne tunda tana da yan ƙawaye anan kuma tunda ba kusa za'a kaita ba ba zuwa zasuyi ba balle ayi Dinner ɗin dasu Minon tace to bari sai ta faɗa mashi zata yi shi gwaggo tace amman kada ta bari ya turo mata kuɗi masu yawa don hidimar da yawa Fatuu tace eh ko a part ɗinta ma sai suyi abun su ba sai ance a kama wuri ba Mino tace to, "Su Mino Amaryar Nameer, na lura dai ba ƙaramin ji dake angon nan yake ba sai faman nan nan da ke yake" Fatuu ta faɗa tana dariya Minon ta rufe fuska da sauri gwaggo dake dariya itama tace to ba dole yaji da ita ba, "Wllh gwaggo baki ji daɗin da nike ji ba da zata aureshi don shima Nameer ba daga baya ba na tabbatar zai kula da ita sosae" kai gwaggo ta jinjina kafin tace ai abun farincikine irin mazajen da suka samu tayi Addu'ar Allah ƙara masu fahimtar juna ya zaunar dasu lafiya yasa mutu ka raba Fatuu ce ta amsa da Amin, "Yanzu ke ya za'ai da karatun ki gashi ko Ssce ba kiyi ba" Fatuu ta tambaya idonta akan Mino, shiru ta ɗan yi tana murmushi kafin tace Nameer ɗin yace zata yi jarabawar bayan an yi, tambayarta Fatuu tayi bayan an yi mi tayi shiru tana bin ta da ido ta ƙara ce mata bayan an yi wai me zata yi jarabawar, shiru tayi tana kikkafta idanu gwaggo dai murmushi kawai take don ta fahimci mi Fatun ke so ta faɗa, ganin ta kafe sai ta faɗi mata bayan an yi mi zata yi jarabawar yasa ta tura baki tana yamutsa baki tace "Wayyo Adda Fatuu ba kin gane ba" girgiza mata kai tayi alamar bata gane ba tay shiru can ta saci kallon gwaggo ganin haka yasa Gwaggon ta juyar da fuskarta, juyawa tay ta kalli Fatuu data kafeta da ido ƙasa ƙasa da murya ta furta "Auren" tana faɗin haka ta tashi da gudu ta bar ɗakin duk suka saka dariya gwaggo tace ina ruwan Mino sarkin kunya. Washe gari da safe su Aunty suka tafi a ranar da daddare Haisam da Fanan suka iso, Washe gari Litinin Jidderh ta iso daga Dubai a ranar da yamma Haisam ya taho Katsina don gaba ɗaya a ƙagare yake da ganin Baby Fatuu ɗin sa, ko gaya mata zai zo bai yi ba saidai ta gan shi yazo sosae taji daɗi amman duk da haka saida tayi mashi shagwabar miyasa bai faɗi mata zai zo nan ba yace yana son yi mata surprise ne su twins ma sun yi murnar ganin Daddyn su, a daren ranar sun nuna yadda sukai kewar juna sosae, Washe gari aka fara program na Laila a Abuja don su zasu yi abubuwa bayan Dinner da walima da za'ayi in aka kawo Mino su zasu yi Ethiopian Night da Arabian, a ranar yan Adamawa suka iso babbar mota guda nan fa gidan gwaggo ya cika kamar yadda Yaya sukai da innar su Altine duk sun kwaso yan matan gidan a nufin su na suma su samu mazaje a dangin su Haisam, zuwa dare gidan har ya fara fita hayyacinshi don ma Yadikko na ɗan tsawatar ma yaran, har bayan isha Fatuu na gidan anata hira su twins tun bayan da aka cika gidan suka fara koke koke sun ƙi yarda a ɗauke su hakan yasa ta kai su wurin Hajiya don yanzu suna yarda da ita kuma Haisam na nan, suna hirar ne ake tambayar Fatuu inda gidan su yake ta faɗi masu ba nisa da an fita ne nan wasu suka ce wai zasu bita suga gidan sai su kwana kan ta basu amsa Gwaggo tace ai Mijinta na nan hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba don ƙarshe tasan mi zai biyo baya in suka bitan, sai wurin ƙarfe goma saura ta baro gidan ta dawo gidan su lokacin data je part ɗin Hajiya ba kowa a cikin parlon hakan yasa ta wuce Bedroom ɗinta, da sallama ta shiga Hajiyar har ta kwanta amman bata yi bacci ba jin sallamarta yasa ta ɗago Fatun ta shiga, nuna mata bakin gado tayi alamar ta zauna, bayan ta zauna ta gaidata ta amsa kafin tace ai tayi tunanin ta dawo tuni gajiya tasa bata shigo ba Fatun tace a'a yan Adamawa suka zo ta tsaya yin hira dasu ne, tambayar yaushe suka iso tayi ta bata amsa da tun ɗazun zuwan nasu ne ma yasa ta aiko dasu twins don suna ta kuka sunga mutane tace "Allah sarki, sun zo lafiya ko?" amsa mata tayi da eh lafiya lou tace to Ma sha Allah, shiru suka ɗan yi kafin Hajiyar tace mata su twins ɗin na wurin babansu ya tafi dasu can part ɗin nasu ta amsa da to, miƙewa tay tayi mata sallama har zata juya Hajiya ta dakatar da ita da faɗin to maimakon ta taho da wasu nan su kwana tunda ga ɗakuna nan ko wanda suka zo ɗin basu da yawa ne ta bata amsa da suna da yawa tace to ai data rago wasu don su samu walwala gidan, shiru tayi bata ce komai ba a ranta tace ita yaushe zata rakito su suzo suyi ba daidai ba kawai sai gani tayi Hajiyar ta kai hannu gefen pillow ta ɗaukko wayarta, kiran layin gwaggo tayi bayan ta ɗaga ta amsa gaisuwar da take mata kafin tace hidima ta fara kankama Gwaggon na murmushi tace eh wllh Hajiyar tayi fatan Allah yasa taron ya tashi lafiya da sauri gwaggo ta amsa da Amin, ce mata tayi Fateema tace waɗanda suka zo da ɗan yawa to ta turo wasu sai su kwana anan ta amsa mata da to don ba damar ta musa mata, bayan sun gama wayar tace ma Fatuu da tayi tsaye sototo shikenan taje ta ƙara yi mata sallama ta juya ta tafi, sam Gwaggo bata so hakan ba duk da za'a samu sauƙin cukowar da aka yi amman tana fargabar tura wasu su kwana can, ƙarshe Yadikko ta kira gefe ta sanar mata ta bada shawarar a tura su Yaya da Mero sai innar su Altine sai kuma in za'a ƙara wasu amman su tana ganin lafiya lou bazasu yi ba daidai ba tunda sunje Abuja sun san wasu abubuwan na yan gayu gwaggo ta ɗauki sha'awararta, bayan anyi masu magana gwaggo taja Mero gefe don tana da natsuwa ta roƙe ta kan kada ta bari ayi ma Hajiyar ba daidai ba tace to suka tafi tare da Gwaggon ta raka su. Ranar Alhamis Mino tayi Friend's Eve anan part ɗin su Fatuu akayi decoration mai kyau a cikin harabar part d'in harda kujeru, cikin kuɗin da Nameer ya turo mata ta ba Aunty mareeya aka yo abubuwan ci da sha harda wanda zata raba, ba laifi kuma ƙawayenta yan makarantar bokon su da islamiyya da na nan cikin unguwa duk sun zo an ci an sha anyi rawa anyi nishaɗi sosae, a ranar bayan Magrib iyayen su maza harda Baffan su suka iso a gidan Hajiya ɗakin Tk aka sauke su shi kuma ya koma ɗakin Kawu Amadu, yan'uwan su Hajiya mata na nan Katsina da Daura duk sun wuce Abuja mazan kuma sun tsaya ɗaurin aure yan Daura ma sai gobe da safe zasu taho nan Katsina har angwayen da dangin su duk sai gobe in Allah ya kaimu zasu taho, da daddare Hajiya ta kira gwaggo take sanar da ita game da ɗaukar Amarya ance mutum biyar ake so su bada don a jirgi za'a tafi da ita tunda tafiyar bata kusa bace sosae hakan yayi ma gwaggo daɗi Hajiya tace da fatan ba'ai masu ba daidai ba da sauri gwaggo tace a'a wllh hakan yayi ai hidiman da yawa hakan ma ba ƙaramin ƙokari akai ba, Maganar sauran kayan ɗakin Minon da akwatunan lefenta gwaggo tayi ma Hajiyar, "Wane kayan ɗaki kuma suka rage banda uwayen kayan da kuka takura kai kuka yi mata, ai dana san haka zaku yi mata kaya da bazan bari ba to bansan irin kayan da akai mata ba sai da akai kai su ake man magana abu duk ba an zama ɗaya ba sai a kama a matsa ma kai haka" da faɗa faɗa take Maganar Gwaggo na ɗan murmushi ta bata haƙuri tace ba takura ma kai akai ba an samu gudunmawa ne sosae Hajiyar tace "haka dai kika ce tunda ba sanin yadda akai akayi mata kayan nayi ba, yanzu su kayan da suka ragen su minene?" da sauri Gwaggon tace "dama kayan adon ɗaki ne da zasu iya fashewa sai akwatunan sai kuma kayan gara", fuska a tur6une Hajiyar tace "dawa yace ayi mata wata gara?" shiru gwaggon tayi Hajiyar tace to ba wata garar da za'a ɗauka zata yi Magana yanzu da Senator kan sauran kayan amman kada a sake a kai wasu kayan abinci da sunan gara in kuma ba'a ji Maganarta ba to rai kuwa zai 6aci, Gwaggo na murmushi tace in sha Allahu baza'a kai ba ta bata haƙuri Hajiyar tace ta saurareta yanzu zata yi Magana game da kayan zata kirata cike da girmamawa tace to, bada jimawa ba sai gashi ta sake kiranta ta sanar mata goben in Allah ya kaimu kafin a ɗaura auren za'a turo Mota da zata kwashe sauran kayan in ma akwae wanda zasu bi Motar lafiya lau su wanda zasu tafi ta jirgin sai su fidda su zuwa da safe zata ƙara kira su yi magana, Sosae Gwaggo tayi mata godiya da Addu'oi kafin suyi sallama saida ta jaddada mata kan kada a sake a saka kayan garar nan suyi amfani da abun su Gwaggo na murmushi tace in sha Allah baza'a saka dasu ba suka yi sallama, bayan sun gama wayar dama Gwaggon ware kanta tayi da suna wayar ta shiga tunanin to suwa za'a bada su tafi ta jirgin bata son wani yaga an yi mashi ba daidai ba, tunanin kiran Fatuu suyi shawara tayi dama tana gidan, bayan tazo ne tayi mata bayanin da Hajiya tay game da ɗaukar Minon Fatun tace "ni hakan ma wllh yayi man daɗi dama ji yadda suka kwaso uban mutane kuma nan nufin su duk gaba ɗaya za'a dasu kai Amaryar, kawai mutum biyar ɗin asa Aunty mareeya, Aunty Feenah sai ke sai kuma babbar ƙawar Mino sai cikon ta biyar ɗin asa...." shiru tay tana tunanin wadda za'a sa ta tambayi Gwaggo ko hada Yadikko za'a tace mata a'a ita da take Uwar Amarya tace to wa take ganin za'a sa na biyar ɗin gwaggon tace "sai ke ko, ai baki sa kan ki ba" Fatun tace shikenan hakan yayi da yanayin yar damuwa Gwaggo tace amman hakan baza'ai ma abun wata fahimta ba ace ba dangin Baffan su da kuma Mahaifiyarta Fatuu tace to su kawai sai a saka su a Motar da aka ce suyi gaba Gwaggon tayi ɗan shiru kafin tace ita bata son abunda zai ja rashin fahimta aga tayi ba daidai ba bari dai a kira Yadikko a faɗi mata aji mi zata ce, bayan an kira ta faɗi mata hannu ta kai ta rufe baki kafin ta cire tace mi zai ja a ɗaura yan Adamawa a jirgi ai abun kallo da magana zasu ja gara ayi yadda Fatuu tace ala bashshi su Yaya da Mero da innarta wato Kakar Mino sai Yayarta hansai su sai a ɗaura su a Motar Gwaggo tace tana ganin hakan lafiya lou tace eh in ma wani yayi tsegumi kan hakan sai ace basu da abubuwan da ake buƙata na yin tafiyar dasu a jirgi, hakan da tace yayi ma Gwaggo akan wannan matsayar suka tsaya, sai wurin ƙarfe sha ɗaya da rabi Fatuu ta koma gida direct part ɗinta ta wuce ba kowa a parlon ta wuce Bedroom, lokacin data tura ƙopar ta shiga a saman gado ta hango haisam yayi shigar bacci haka su twins ma ya saka masu kayan baccinsu da alama ma har wanka yayi masu Abie na a saman ƙirjin shi yana bacci Grandpa kuma na a ta gefen shi ya rungumo shi jikinshi da hannun shi guda gaba ɗayan su bacci suke yadda sukai kwanciyar abun gwanin burgewa, ta ɗan ɗauki lokaci tana ta kallonsu tana sakin murmushi kafin ta nufi hanyar laudary, after some minutes ta fito ɗaure da towel da ƙaramin towel tana goge jikinta kanta yasha kitso da Mero tayi mata ɗazun, press ta nufa ta fiddo kayan baccin da zata saka Nursing pajamas, bayan ta gama sawa gaban mirror ta nufa tana kallon kitson da aka mata yar yar sosae taga yayi mata kyau ko don bata saba yi bane, mai da take shafawa da daddare ta shafa harda na tafin hannu da yatsu sannan ta goga roll-on bayan ta gama ta feffeshe jikinta da turarurruka masu sanyin ƙamshi, wurin gadon ta nufa saida ta gyara ma twins nasu gadon kafin ta kai hannu a hankali don kada ta tada Haisam ta ɗauko Abie ta kai shi saman gadon shi, tana ƙoƙarin daukar Grandpa Haisam ɗin ya buɗe ido slowly suka sauka kanta ta sakar mashi murmushi tare da kashe mashi ido shima yay mata murmushin, shima Adam gadon shi ta kai shi ta juyo tana ce ma Haisam sun ci Abinci ne taga har ta kwantar dasu ba wanda ya farka ya lumshe mata ido kafin a hankali yace ya basu kafin suyi bacci yana gama Maganar ta faɗa jikin shi tana faɗin thank you Daddy wai a madadin su twins ɗin ya ƙara faɗaɗa murmushin shi, bin juna sukai da kallo kowa fuskarshi da annuri can yace yadda ta kwantan baza tayi hurting kan ta ba tace ai bata danne cikin sosae ba ya lumshe ido, tambayarta yay ya hidima tace anata yi gaba ɗaya a gajiye take don ma Gwaggo na hanata aiki sosae ya jinjina kai kafin ya kai hannu ya fara shafa kitsonta ya furta yayi kyau ta furta thanks tare da lumshe mashi ido irin yadda yake, yana ɗaya daga cikin abunda take so tattare dashi kenan duk in kayi abunda ke buƙatar yabawa sai ya ya6a sa6anin da yawan wasu mazajen basu iya yaba ma matan su in suka yi kwalliya ko wani ado wasu har sai matan sun tanka sun ce wai baka ga nayi abu kaza ba sannan in an ci sa'a yace yayi kyau wani kuwa saidai yace shi bai ma lura ba irin hakan kaman cin fuska ne ace kana tare da mace a wuri guda amman tayi abu kace wai baka lura ba shiyasa da yawan matan basu yin adon akai akai tunda wanda suke yi domin su basu yabawa sai waɗanda ya zamar ma jiki ne sun saba suke cigaba da yi koda mazan basu yabawa, Maza yakamata su gyara yaba kwalliyar mace nasa taji daɗi ta ƙara ƙaimi wurin yi akai akai sannan yana ƙara soyayya don ita mace abu kaɗan kesa a siye zuciyarta, sauketa yay daga jikin shi yace mata yana zuwa ta ɗaga mashi kai, toilet ya nufa yana shiga wayar Fatuu ta fara ringing har saida gabanta ya ɗan faɗi ta raya wake kiranta a wannan lokacin sha biyu har ta wuce, saukkowa tayi ta nufi gaban dressing mirror inda wayar take har lokacin ringing take ta kai hannu ta ɗaukko tana duba mai kiran ta saki murmushi ganin Fauziyya ce, "Ƙawata Amarya ko kun iso ne?" ta fada bayan ta ɗaga daga can ɗayan bangaren Fauzy ta bata amsa da eh yanzun nan suka sauka Abuja, cikin nuna farinciki Fatuu tayi mata anzo lafiya ta amsa ta sake tambayar Nasarawa zasu wuce tace mata a'a gidan su na Abuja zasu tsaya don gobe yana son zuwa ɗaurin aure dasu Daddyn Haisam Fatun tace suma goben zasu haɗu kenan in suka kawo amarya harda cewa ta ƙagara taga yadda ta koma Yaya Sameer ya iya kiwo Fauzyn tay yar dariya mai sauti daga baya sukai sallama, aje wayar tayi ta juya zata koma gado lokacin Haisam ya buɗe ƙopar laundry ya fito ta juya ta nufe shi suna haɗuwa ya rungumeta tana kallon fuskar shi da murmushi ta faɗi mashi Fauzy ce ta kirata ta sanar mata sun sauka Abuja yanzu ya jinjina kai kafin yace sun yi waya da Sameer kafin su taho, ɗaukarta yay ya nufi gado da ita tana ta dariya tana faɗin wai sai yaushe zai fara jin nauyin ta yay murmushi kawai, bayan ya kwantar da ita mikewa yay ya kunna lamp ta side ɗin da yake kafin ya nufi wurin Switch ya kashe hasken ɗakin ya dawo gadon ya fara mata tausa cikin salon ƙauna tana ta lumshe ido tare da yaba abunda yake matan sun ɗan ɗauki lokaci yana mata massage ɗin kafin ya fara canza salo tana ganin haka itama ta fara bashi nata salon daga haka suka lula wata duniya da ma'aurata ke zuwa. FRIDAY Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar ɗaurin aure, ana tashi aka shiga yin hidima ba kama hannun yaro, tunda safe jirgin yan ɗaurin aure ya sauka daga nan gidan su na G.R.A suka wuce kafin lokacin ɗaura auren yayi, suna isa gidan ango Nameer ya kira amaryar tashi ya sanar mata gasu sun iso yana son yaga fuskar kyakkyawar amaryarshi ta sanar mashi tana gidan Hajiya part ɗin su Adda Fatuu yace Ok gashi nan zuwa, yan Abuja basu daɗe da zuwa ba suma 6angaren angon Laila convoy ɗin su ya iso daga Kano, jerin danƙara danƙaran motoci ne masu numfarfashi tare da na security a gaba da baya da yake wanda zata auran wato bashir ɗan sanannan mai kuɗi ne a Nigeria, a Vip na haɗadɗan hotel Hillside Royal Suites suka sauka kafin lokacin ɗaura auren yayi, tunda wuri Aunty Mareeya ta taho gidan bikin saida ta biya ta ɗaukko Feenah kamar yadda sukai da ita, bayan isowarsu aka shiga yin aiki ba kama hannun yaro don ma Abincin wasu ba anan za'ai ba abunda za'ai a nan gidan kaɗan ne, ganin yadda Fatuu ke ta kujiba kujiba yasa aka fara mata magana kan ta rinƙa hutawa saboda halin da take ciki sai lokacin wasu da yawa suka san da ciki gareta har Haulat da Feenah basu gane ciki gareta ba duk an zata ƙibar da ta ƙara ne yasa ta ɗan yi tumbi, wuraren ƙarfe sha ɗaya Hajiya ta kira Gwaggo tace a fiddo da sauran kayan Minon ga wanda zai ɗauka nan yazo Gwaggo tace to ta sanar da ita akwae wanda zasu bisun sannan akwatunan na nan part ɗin su Fatuu aka maido su bari tayi mata magana sai tazo a fiddo su Hajiyar tace to ayi ma mutanen magana su fito kar a 6ata lokaci don tafiyar bata kusa bace, suna gama wayar tayi ma su Yaya da sauran wanda Yadikko tace aje dasu magana dama tun jiya ta sanar masu zasu tafi da safe, zo kaga rawar jiki wurin Yaya anji zanjen tafiya Abuja ita kuwa innarsu Altine kamar zata saka kuka tsabar takaici ita bama don yaran yan matan da suka kwaso da baza'a tafi dasu ba ita kanta da bazata ba yasa ta shiga matsananciyar damuwa sai faman roƙon a tafi da ita take Gwaggo tace ta bari aga Motar inda wuri sai ta bi su, cikin sa'a sai gashi Motar yar babba ce mai seat ukku a boot da bayan Motar aka saka akwatunan da kwalayen sauran kayan ba'asa kayan gara ko ɗaya ba tunda Hajiya ta hana, a layin tsakiya Mutum huɗu suka zauna harda innar su Altine data kasa rufe baki don murnar za'a da ita a gaba Mero ta zauna wasu harda cewa ai za'a iya ƙara mutum guda a gaban Driver ɗin yace a'a zai takura a bar mutum ɗaya yayi, Altine na tsaye bakin ƙopar Motar harda ƙwallarta tana roƙon aje da ita don Allah kofa da bikin Fatuu ba'a je dasu ba, daga cikin Motar innarsu ta wurgo mata harara tace ina za'a je da ita ra6e ra6e da Y'ay'a ko an gaya mata Abujar ruga ce Gwaggo ce ta rarrasheta tace tayi haƙuri watarana zasu je ko in Minon ta haihu fuska a yamutse tace ai ana iya ƙin zuwa da ita Gwaggon tace in sha Allahu in Allah ya kaisu lokacin ita zata sa aje da ita sannan ta ɗan kwantar da hankalinta, har Driver zai tada Motar Fatuu ta nufo Motar da yar sassarfa tana ruƙe da hannun ƙanwar su Aysha ganin tana ɗaga hannu yasa aka yi mashi magana ya dakata, bayan ta ƙaraso roƙon shi tay kan a bari ta zauna a gaban jikin inna mero da yake yasan wacece Fatun cikin kwantar da murya yace abunda yake gani Abuja ba kusa bace da za'a ce ta zauna a jikinta har suje dole su duka su gaji da alamun damuwa Fatun tace mashi to ya za'a yi don Allah ƙanwar amaryar ce gashi ta ƙwallafa rai sai Kuka take jin baza'a da ita ba, fitowa yay daga cikin motar yace bari yaga in zai iya samar mata wuri, kayan cikin boot ɗin ya gyaggyra haka akwatunan dake seat ɗin baya suma ya gyara tsarinsu ya rago guda biyu ya maido boot sai gashi an ɗan samu wuri a bayan yace ma innar su Altine tunda ita bata da jiki ta dawo nan baya sai ita yarinyar ta zauna a wurinta mutanen seat ɗin ma sun fi sakewa da sauri tace to ai ita ko a cikin boot ne indai za'a je da ita to zata shiga har saida ta ɗan ba Drivern dariya, bayan ta koma Aysha ta zauna a wurin ya rufe masu kopar kafin ya koma driver seat ya zauna saida yay Addua sannan ya tashi Motar aka shiga ɗaga masu hannu ana masu Addu'oin Allah ya tsare daga haka suka tafi. Ƙarfe sha biyu na yi sun gama ayyukan da suke su Aunty mareeya da Feenah suka tafi don su shiryo zuwa kai amarya Fatuu ma ta wuce gida don ta shirya zuwa lokacin tuni gidan ya cika da mutane ƙawayen gwaggo da yan'uwanta harda iyalin Kawu shibaɗo da shi kan shi yazo daurin auren, Jirage kawai keta kai da komowa yan ɗaurin aure sai zuwa suke zuwa lokacin Mutane sosae sun taru a gidan su Haisam na G.r.a yan uwa da abokan arzuƙi da abokan siyasa na Senator duk sun hallara har Sameer ma ya iso haka ma 6angaren Angon Laila duk sun dawo nan gidan don a tafi tare , lokacin sallar Juma'a na masallacin da za'a ɗaura auren wato Masallacin Banu Commassie na gabatowa aka shirya convoy na Motoci masu sunan Motoci aka tafi Magana ake ta harkar masu arzuƙi daya amsa sunan Arzuƙi abun sai wanda ya gani don alƙalami bazai iya zayyana ainihin ƙayatuwar ba, suma can 6angaren iyayen Mino Maza Tk da Kawu Amadu ne suka ɗaukko su a Motoci, Massallaci fa ya cika dankam da mutane ga tsaro ta ko ina don ma yana da girma da ba lalle ya isa ba, ana gama salla ɗaurin Auren su aka fara yi bayan waliyyai na kowanne 6angare sun hallara aka fara ɗaura na Dr Bashir da Dr Laila bayan an gama aka ɗaura na Engr Nameer da Ameenatu kowanne akan sadaki Naira 500 dubban mutane suka shaida, bayan angama kowa fuskar shi ɗauke take da farinciki aka shiga gaishe gaishe da fatan alkhairi ga ma'auratan yan jarida muna ta aikin ɗaukar rahoto, bayan an gama mutanen 6angaren Angon Laila Hotel ɗin da suka sauka can suka koma don yin reception bangaren su Senator kuwa G.r.a suka koma acan zasu yi nasu a Masallacin ma an raba ma mutane uban Abinci da lemuna sai Addu'oi ake ma ma'auratan da kuma Senator Ali Zakee ana faɗin Allah yayi mashi President sai murmushi yake yana gaisawa da mutane har saida jami'ai suka dakatar dasu, acan 6angaren gidan su amarya duk sun sha ankon atampa mai kyau da suka yi kowa ka gani yayi kyau cikin atampar har Hajiya da Saude duk suma ita suka saka anata hotuna da wayoyi, yan G.r.a na gama yin reception ɗin gidan Hajiya suka nufo harda Senator nan fa unguwa ta cika ango Nameer yasha babbar rigar bugaggar shadda light blue haka hular shi da agogon shi zuwa takalmanshi duk sun hau da kalar shigar da yayi sam ya kasa rufe baki hakanan ma yayi murmushi balle yanzu da dalili Allah ya mallaka mashi Babynshi yar fillo, su Kawu Amadu abokan ango duk sun sha shaddoji kowa dai yayi kyau Hajiya na ganin Nameer ta rungume shi tana faɗin duk da tana kishi tana farinciki kuma da Allah ya nuna mata wannan rana su Senator dasu Kawu Mani yan Daura nata dariya, bangaren amarya Mino kuwa tana a part ɗin Fatuu ƙwararriyar mai makeup dake a Katsina wato Munah Beauty tana tsantsara mata kwalliya, fitted gown din rantsattsan lace Navy blue da ratsin light da kuma fari mai kaman silver tasa sai net light blue an ci bakin shi da bakin lace ɗin jikinta aka yafa mata sai head ɗinta shima light blue ne clutch da takalmanta kuma silver sai sarƙarta da yan kunnanta na Diamond, Wow Ma sha Allah shine abunda aketa faɗi, bayan Munah Glam ta gama tsantsara mata kwalliya ta naɗa mata head su Aunty Mareeya suka shiga tambayar ina aka samo mai makeup ɗin nan Fatuu ta bata amsa da Babbar ƙawar Mino wato Safnah ta kawo masu ita tace da Sunan Yayarta ita tayi masu Makeup harda ma ƙunshi na zane dana salataf duk tana yi Feenah tace kenan har ƙunshin ita tayi masu Safnah dake zaune gefen Mino itama tana jira ayi mata make up ɗin ta bata amsa da eh har itama nata duk ita tayi masu, sosae suka yaba da ƙunshin shima Aunty Mareeya tace ansha da ita da ta sani itama tare dasu akai mata ya zanu raɗam haka ta ɗan harari Fatuu tace duk laifinta ne da bata sanar masu ƙwararrar mai ƙunshi zata masu ba suma ayi masu Fatuu na dariya ta bata haƙuri tace itama bata santa ba saida Safna ta kawo ta, dafa shoulder ɗin mai makeup da ƙunshin Aunty Mareeya tayi ta tambayeta irin abubuwan da take yi ta fara lissafo mata bangaren kwalliya tace suna yin ta Amare da masu Jego ko ta Birthday ko simple da za'a ma mutum don zuwa biki ko suna sannan tana koya ma mutum in yana so a bangaren ƙunshi kuma tana yin baƙi na zane da kuma ja na zane dana salataf irin wanda ke yin maroon ko kuma baƙi sannan suna yin kitso iri iri sai wanda mutum keso sannan kuma suna yin Home service wato in mutum naso a iske shi a gida ayi mashi kowanne cikin abubuwan data lissafa, tambayarta Feenah tay ya yanayin price ɗin aikin nata yake ta shiga faɗi mata ai tun kafin ta ƙarasa Aunty Mareeya ta miƙa mata waya da sauri tana faɗin yar albarka saka man lambar wayarki aikuwa su Fatuu da Aunty Feenah suka kwashe da dariya Feenah na faɗin su Maman Hanif an ji sauƙi tana dariya tace to yanzu a rayuwar nan ai sauƙin ake nema harda tsawwalawar da wasu masu makeup ɗin ke yi yasa da yawa wasu suke haƙura da yin gayun duk da suna so amman ba hali Feenah tace gaskiya kam wasu kuma sai hidima ta kama sannan suyi duk da mace da gayu aka santa amman in dai mutum zai samu Munah Glam saidai in shi ke bai son gyara kanshi, Aunty Mareeya tace ta bari kawai ai ita yanzu kakarta ta yanke saƙa gayu sai in ba'a yi yanzu ta ƙara samun tarkon da zata ƙara damƙe zuciyar Abban su hanif dama shi ɗan son gayu ne shiyasa bata wasa yanzu kuma zata ƙara ƙaimi da Munah Glam, bayan ta saka mata lambar ta miƙa mata tana cikin yin saving Feenah tace itama ta karanto mata tace to ta fara karanto mata lambar kamar haka 08169856268, Bayan an gama shirya amarya Mino Fatuu akai mawa da yake wadda za'a mata ba irin ta Mino bace hakan yasa ba'a ɗauki lokaci sosae ba aka gama aka ɗaura mata kallabi abun sai wanda ya gani Babyn Haisam itama ta fito kamar Amarya, Safnah aka shiga yi mawa bayan Fatuu ana gama mata Aunty mareeya tace itama duk da tayo kwalliyar daga gida a gyara mata ita ana cikin yi mata Haisam ya kira Fatuu yace mata ta kawo Mino part ɗin Hajiya yanzu tace to, ita da Safnah suka tafi kai Minon, lokacin da suka shiga parlon Hajiya gaba ɗaya idanu suka dawo kan su da sauri Mino ta sadda kanta ƙasa a haka suka nufi cikin parlon ango Nameer sai sakin ƙayataccen murmushi yake yaga yar fillon shi ta zama tamkar tauraruwa gashi yanayin shigarsu ta haɗu don head ɗin da aka ɗaura mata da mayafinta da kuma fulawoyin lace ɗinta sun yi kala ɗaya da shaddar shi da gani dai tsara hakan sukai, idon Haisam na akan Babyn shi Fatuu da yaga ta ƙara mashi kyau sosai wurin Hajiya suka nufa da ita tana ta murmushi ta miƙo hannu ta kamo na Mino ta zaunar da ita a gefenta tana yaba kwalliyarta harda cewa wato shine aka ƙi kawo mai yin kwalliyar tayi mata don ansan in aka yi mata sai tafi Amaryar kyau duk akai dariya su Fatuu da suka zuƙunna akan Carpet suka shiga gaishe da mutanen ciki suna ta amsawa harda Senator sukai mata ya hidima, Mino sarkin kunya gaba ɗaya ta kasa ɗagowa balle ta gaisa da mutane hakan yasa Hajiya tace ma Fatuu ta kamata ta kai ta wurin su Senator, a gaban shi suka tsugunna da ƙyar Mino ta ɗago ta gaishe shi yana ruƙe da Adam ya kai ɗayan hannun shi ya dafa shoulder ɗinta yana murmushi ya tayata murna tare dasa ma Auren nasu Albarka yace yana farinciki da shigowarta Family ɗin tare da yin Addu'o'i ya juya kan Fatuu yace ita Daughter yanzu ta zama yar gida sai dai ta tarbi wasu Fatun tay yar dariya ta ɗaga mashi kai tare da faɗin hakane saida tayi magana sannan Adam ya gane itace ya fara miƙo mata hannu yana faɗin Momy duk akai dariya don sun fahimci bai ganeta ba farko saboda Makeup da aka mata, Hotuna aka shiga yi anan cikin parlon Hajiyar lokacin da Mino ta jera da Nameer za'a yi masu har saida na furta Ma sha Allah wato kyau ya haɗu da kyau sai ya bada Madarar kyau....... 99 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ .......Har gwaggo Hajiya ta kira a waya tace tazo ayi masu hotuna ba 6ata lokaci ta zo gidan tana sanye da Atamfar anko yau dai su Gwaggo gyale aka yafa sai gashi ta fito ɗas da ita baka ta6a cewa Fatuu jikar tace tafi kama da ace ɗiyarta ce, ana gama yin hotunan Hajiya ta sanar ma Gwaggo suje su shirya ana gama sallar La'asar zasu tafi tace to, tare da Mino da Fatuu suka fito saida suka fara zuwa baya inda iyayensu Maza suke don ayi ma Mino faɗa suka kuma yi sallama dasu, to nidai bansan mi suka ce mata ba don gaba ɗaya da Fulatanci sukai mata magana naga dai tana ta ɗaga kai tana kai hannu tana goge ƙwalla, bayan sun gama da nan gidan Gwaggo suka wuce anata yabon gayunta aka kaita wurin mahaifiyarta Yadikko don tayi mata faɗa amman ta kasa ce mata komai gaba ɗayansu sun sadda kai ƙasa da alama ma Yadikkon kuka take, koda aka ƙara mata magana kan ta daure tayi mata nasiha da ƙyar murya na rawa tace ai tasan Gwaggo zata yi mata kuma acan in an kai ta iyayenta mata da suka yi gaba zasu yi mata duk akace mata duk da haka a matsayinta na Mahaifiyarta ya kamata tace mata wani abu, hannu ta kai saman kan Minon tace "Ubangiji Allah yayi maki Albarka ya Albarkaci aurenki yasa gidan zaman ki ne na har abada, ayi biyayya kuma aita haƙuri" da kyar ta kai ƙarshen Maganar a wawware saboda Kuka, ana ƙokarin miƙar da Minon da sauri ta faɗa jikin Yadikko ta saka wani irin kuka mai ta6a zuciya, da ƙyar aka raba su Aunty Mareeya ta tafi da ita don ta shiryata, bayan duk anyi salla Motoci guda biyu Jeep da ƙarama suka zo ɗaukar su tasu Hajiya da wasu yan uwansu Hajiyoyi guda biyu na biye da ita sune sukai bikon amarya aka fito da ita tana sanye da Alkyabba sai faman rizgar kuka take sai kace ba gidan masoyinta Nameer za'a kai ta ba, yan tafiya duk sun shiga Mota anata ɗaga masu hannu Fatuu taso aje da Haulat amman bai yuwuwa su Kawu Amadu suda ke abokan ango har sun wuce Airport sai fatan Allah ya kaisu lafiya. Alhamdulillah yan kawo Amarya sun isa Abuja lafiya har sun iso gidan sun samu kyakkyawar tarba daga dangin angon, biki na Abuja don gidan shaƙe yake da Mutane yan uwansu yan Ethiopia da Qatar duk sunzo haka Hajiya Maryam da iyalinta har Hajiya Zainab ma da nata iyalin harda surukarta Fauzy tuni sun hallara suma duk sun sha ankon haɗaddar atampa kowa yayi kyau, Fauzy da Fatuu suna ganin juna suka rungume juna cike da farinciki haka Jidderh ma sosae ta nuna farincikin ganin Fatuu sai kace sun shekara basu haɗu ba, Aunty Mareeya baki yaƙi rufuwa anga yar gaban goshi Fauzy, bayan an gama tarbar Amarya da gaishe gaishe part ɗin baya suka nufa dama su Yaya na can, lafiyayyun Abinci da abubuwan sha aka tarbe su dashi duk da bama wata yunwa suke ji ba, ana gama sallar Magrib aka fara shirin tafiya Dinner, ɗakin Laila aka kai Mino acan za'a shirya su tuni har an fara tsantsara ma Laila Makeup tasha ubansun ƙunshi haka jikinta sai sheƙi fatar ta ke yi kai da gani kasan ba ƙaramin gyara tasha ba haka sumar kan ta ma, bayan sallar isha duk an shirya gaba ɗaya ankon lace akai saidai na iyaye daban ne haka ƙawayen Laila ma kalar nasu daban su Fatuu dasu Jidderh nasu kala ɗaya ne duk sun sha ɗinkuna styles iri iri, tuni aka fara kwasar mutane zuwa wurin da za'ayi saida aka gama kai kowa sannan aka zo ɗaukar Amare lokacin da nayi tozali dasu har saida alƙalamina ya kusa faɗuwa to Laila ma ta tsara wani a bikin shi balle kuma nata ai sai abunda ya ture ma buzu naɗi, rantsattsan Material ne kala ɗaya suka saka ita da Mino, Material ɗin baƙi ne yana da adon golden brown sosae yay wani baza baza sai walainiya yake gaba daya fitted gown akai masu kowa daidai jikin shi sai aka ɗaura masu golden brown head wuyansu da hannuwansu sun sha gold haka takalmansu da clutch ɗin su duk golden brown Mino sai tayi kamar yar ƙanwarta saboda ba jiki don ma tana da tsawo, Uhmm wurin Dinner din abun ba'a magana don ya tsaru iya tsaruwa Naira tasha kashi, Ma sha Allah shima mijin Laila kyakkyawa dashi gashi da gani ba yaro bane don zai yi tsaran Haisam koma ya girme shi shima ba fari bane amman kuma baza'a ce mashi baƙi ba kamar dai yadda Laila ɗin take shima yana da haske gashi da ganin shi hutu ya zauna mashi sosae, shima shida Nameer kaya iri ɗaya suka saka plain yard baƙi kai da gani tsadadde ne anyi masu babbar riga aikinta kuma brown haka agogunan su ma brown ne gaba ɗaya suna sanye da dakakkun takalma baƙaƙen cover, suma dangin Mijin Laila kalar lace ɗin su daban sun sha ɗinkuna gasu duk wayayyu ne baka jin komai sai turanci gashi ba Maganar saka gyale yawanci masu ɗan gyalen duk iyaye ne haka kowane wuya da hannu ka kalla gwalagwalai ne kawae kake gani, ba 6ata lokaci aka shiga gudanar da activities ɗin dinar kowa kaga fuskar shi ɗauke take da annuri, lokacin da aka fiddo ƙawar Mino Safnah ta bada tarihinta sosae ta burge mutane gata ƙarama amman turanci a bakinta kamar zubar ruwa sosae Fatuu taji daɗin yadda tayi dama Mino ta faɗi mata tana da ƙokari gashi dama makarantar su babbar private ce da turanci ake magana shiyasa ba laifi itama Minon tana ganewa, lokacin da aka fiddo amaren da angwayen don su taka rawa kasa yin rawar Mino tayi dama gaba ɗaya a kunyace take da shigar jikinta saida Nameer ya kama mata hannuwa nan fa aka shiga zuwa yi masu liƙi ganin ana cunkushewa yasa Mc raba su yace su Nameer su koma in aka gama ma su Laila sai suma su fito sai gashi an koma yin liƙin a tsare, Su Kawu Amadu na zaune a inda aka tanadar ma abokan ango shida Kamalu da Tk gaba ɗaya ankon maza ne a jikinsu plain yard brown ɗinkin Senator style harda yar falmaran a sama sosae sukai kyau cikin kayan sumarsu duk tasha gyara in ka gansu baka cewa suma ba Ya'yan masu kuɗi bane karma Kamalu yaji don yafi kawu Amadu fari ga sumar shi a kanannaɗe take bangaren kyawun fuska kau ba'a magana dama shi Mamarsu ya biyo wato Aysha ita kuma babansu ita da kawu Amadu shi ta biyo hakan yasa Kamalun ya ɗaukko dogon hancinta ga ƙaramin baki dama ba kalar shape ɗin bakinsu ɗaya da Fatuu ba ga girarshi ta zanu raɗam ɗauke da baƙin gashi mai santsi, ganin anata zuwa ana yin liƙi yasa shi ce ma Kawu Amadu ya bashi kuɗi suma suje suyi Amadun yay yar dariya yace shi ina yaga kuɗin da zasu je suyi liƙi yana ganin uban kuɗin da ake ta liƙawa yan kuɗin da ke a jikin shi yan kaɗan ne, Tk na dariya yace ai masu yin canjin kuɗin ana masu transfer sai suba mutum Cash Kawu Amadun yace "kai rabu dasu ba wani liƙin da zanyi nima kuɗin aure nike tarawa", "Kaman gaske, kai da har yanzu baka da niyya" Tk ya faɗa yana dariya, "Serious kwanannan zan baka mamaki don mai gaba ɗaya zanyi saidai kaji Maganar aure kawai da an bani dama" Kawu Amadun ya faɗa, "to Allah yasa, in ba haka ba sai dai kaga na shige na barka don bazan biye maka ba in ƙi more rayuwata gashi har mun yi 30yrs", Amadun yace mashi yasha kurumin shi sai ma ya riga shi yi in sha Allah, hango Fatuu Tk yayi ta dawo daga wurin yin liƙi yace ma Kamalu yaje ga Hajiya Fatuu can ya amso kuɗin liƙin, kai idon shi yay kan Fatun kafin ya miƙe da sauri zai je wurinta Amadu na faɗin shima ya amso dashi ya ɗaga mashi kai, da sauri ya tunkareta don bai son ta koma wurin zaman su saboda akwae mutane, cikin rashin lura yaji ya kai ma mutum karo har abu ya faɗi ƙasa da sauri ya maido idon shi kan wadda sukai karon ta kai hannu ta dafe goshi tana sanye da irin lace ɗin su Fatuu anyi mata wasu irin style na riga da skirt kai kace a jikinta aka ɗinkasu don sun kamata sosae sun fito da suffarta wadda da gani ba ramamma bace kuma tana da shape gaba ɗaya wuyanta da kafaɗunta a bayyane suke farar fatar ta fat ta bayyana, tun daga kunnanta wuyanta zuwa hannunta data dafe goshinta gold ne, sosae hankalin Kamalu ya tashi ya wara ido yana kallonta duk da bai ga fuskarta ba ya shiga motsa baki ya rasa taya zai bata haƙuri da ƙyar yay ƙarfin halin ce mata don Allah tayi hakuri bai kula bane shiru bata ce mashi komai ba bata kuma ɗago face ɗinta ba, saida ya ƙara bata haƙurin sannan ta janye hannun idanunta suka shiga cikin nashi ta shiga kallon shi fuska a tamke, lokacin da Kamalu ya haɗa ido da ita saida gaban shi yay mugun faɗuwa tsoro ya kama shi ganin kalar ƙwayar idonta, kasa jure ma kallonta yayi ya sauke idon shi ƙasa gaban shi na ɗan faɗuwa ganin yadda ta ɗaure fuska gashi bai san wacece ita ba, "Are you blind?" kaman daga sama yaji zazzaƙar muryarta ta faɗa har saida ya haɗiyi abu kafin ya ɗago ya kalleta tunanin bata jin hausa yay da yake yayi Secondary kuma yanzu da yake shirin cigaba da karatu Kawu Amadu na koya mashi wasu abubuwan harda turanci dama kuma yana ja don duk yan ɗakin su Fatuu ba laifi kan su na rabawa, "I'm sorry please i bump into you, it was an accident my attention was elsewhere" ya faɗa da yar rawar murya sautin turancin gwanin daɗi abunka da Bafullatanin Asali, bin shi tay da ido kawai tana ƙare mashi kallo ba tare da tace komai ba shikam da ƙyar yake jure ma kallon gray eyeballs ɗinta ganin bata ce komai ba yasa shi ƙara ce mata please he's sorry sai lokacin ta motsa baki a hankali ta furta "is okey" ganin tana ƙokarin duƙawa ta ɗaukko haɗaɗdar purse ɗinta yasa shi rigata duƙawa ya ɗaukko mata ya miƙa mata still kallon shi take tayi, tana amsa sai ji yay ta furta "Nagode" daga haka ta wuce ta nufi gaban hall ɗin dama itama liƙin zata yi, saida Kamalu yay mamakin godiyar da tayi mashi gashi yay tunanin bata jin hausa ne, juyawa yay ya nufi komawa wurin zaman shi don Fatun tuni ta zauna kuma sai yaji ma yin liƙin ya fitar mashi a rai, yana komawa su Kawu Amadu suka tambayeshi miya haɗa shi da wadda suka hango su tsaye ya faɗi masu ya bugeta ne bai gani ba har jakar hannunta ta faɗi Tk yace bata yi mashi masifa ba yace a'a kawai tace mashi shi makaho ne da turanci sai ya bata hakuri ya nuna mata hankalinshi na wani wuri tace shikenan Tk ɗin yace yayi sa'a don masifaffa ce, tambayar shi yay ya santa ne yace mashi eh itama jikar Hajiyar Senator ce sunanta Farha ƙanwar kishiyar Yayar shi Fatuu Kamalun ya jinjina kai Amadu yace ya bai amso kuɗin liƙin ba ya bashi amsa da ta riga ta zauna cikin mutane a bashshi kawai, Tk na dariya yace yanzu sai ace bazasuyi ma Mino liƙi ba gaskiya da basu kyauta ba, ƙarshe dai sai tansfer ɗin Amadu yay aka basu Cash suka haɗa dana Tk sukai liƙin, Alhamdulillah an gama Dinner lafiya anci an sha an nishanɗu an zubar da galan galan na farinciki an cashe iya cashewa an raba souvenirs iri iri wasu cikin nasu Laila harda hotunansu nasu Mino dai sunan su ne kawai wasu kuma tare aka sa sunan nasu baki ɗaya dasu Laila, bayan sun koma gida kowa a gajiye yake Fatuu taso tayi fira da Fauzy amman ta gaji sosae hakan yasa tayi wanka su twins ma tayi masu suka kwanta. Washe gari ana tashi aka fara shirye shiryen Walima don da wuri za'ayi saboda ƙarfe ukku na rana za'a tafi da Laila Kano can za'a kaita itama tafiyar Jirgi za'ayi Mino kuma sai bayan Magrib za'a kaita gidanta, bayan sun gama yin Breakfast Gwaggo ta iske Hajiya bayan sun gaisa tace mata dama zata tambaya ne ko za'aje a shirya ma Mino ɗaki tunda da aka kawo kayan ba'a biyo an shirya ba Hajiyar tace ai tana tunanin kamar ma an shirya mata amma bari ta tambaya, Mom ta kira a waya bayan sun gaisa tayi mata Maganar shirya gidan Minon tace ai ansa an shirya kayan tun bayan da aka kawo su tace to, bayan sun gama wayar ta faɗi ma Gwaggo tace saidai ko in suna son zuwa ganin gidan da sauri Gwaggo tace a'a tunda za'a je kaita sun gani, ana yin salar Azahar aka fara yin Walimar Amare sun sha shaddoji da akayi ma tsantsararren ɗinki kowa kalar tata daban Walimar ma harda ankon Material voile aka yi kowa yayi kyau mutane nata zuwa itama Mino harda kyaututtuka aka rinƙa bata, Walima ta ƙayatu anci ansha anata fatan alkhairi ga ma'auratan, Misalin karfe ukku da yan mintuna duk aka fito harabar gidan rakiyar Laila da aka zo tafiya da ita, cikin wanda zasu tafi kaita harda Hajiya Maryam da Aunty da Jidderh da wasu yan uwan su yan Ethiopia sai wasu ƙawayenta da kuma wasu yan uwansu na Katsina da Daura harda Fanan Fatuu dai banda ita, anata bankwana da ita ta canza shiga zuwa jigunan lace duk yadda ta daure saida ta matse ƙwalla lokacin da Mom ɗin su ta rungumeta haka Hajiya ma, su Kawu Amadu na daga can gefe suna kallon yadda aketa bankwanan, bayan masu tafiyar sun shiga motoci anata ɗaga masu hannuwa suka tafi sai fatan Allah ya kiyaye, Fatuu na tare da Fauzy har sun juya zasu koma ciki Fatuu taji an kirata hakan yasa ta dakata ta juya don taga waye ya kirata, Kamalu ne ya nufota yana sanye da farar shadda bayan ya ƙaraso inda suke da murmushi ya gaishe da Fauzy itama tana murmushi ta amsa tay mashi ya hidima, don ta basu wuri yasa tace ma Fatuu ta isketa ciki tace to, tana murmushi tace ma Kamalun da wani abu ne yace eh wllh kuɗi yake son ta bashi zasu shiga gari ne shi kuma baida ko sisi ko jiya ma har zai zo ta bashi na yin liƙi sai Kawu Amadu ya bashi, wani kallo tayi mashi tace "Duk yadda kai kalar Ya'yan masu kuɗin nan amman kake tambayar kuɗi" dariya yay yace "to ai kinsan komai dai ba ɗan masu kuɗin bane ɗan masu shanu ne" yadda yay Maganar ne ya bata dariya tace to ai suma masu shanun suna da kudi yace uhm ayi shiru dai amman ga inda masu kuɗi suke nan, tambayar shi tay ya akai baida kuɗi yace to ai anyi hidima ya kuma yi ɗinkuna tace hakane gashi nan ai yanata saka kaya sai kace shima ɗan Senator ɗin ne ya saka dariya, ce mashi tay yaje zata tura mashi yace tunda dai ga wayar nan a hannunta ta tura mashi yanzu zasu fita bazasu ma koma cikin gidan ba, "Kodai kun yi yan mata ne zakuje siya masu ice cream" tay Maganar tare da yi mashi wani kallon tuhuma yana dariya yace waye zai so su haka basu da ko sisi tana ƙoƙarin tura mashi tace ai ba'a ganewa, duk wannan abun idon Farha na akan su tun lokacin da Kamalun ya taho wurinta, dubu asharin ta tura mashi tace gashi nan suyi maneji don a Abuja ba wani abun kirki zata siya masu ba bata da kuɗi sosae yana murmushin jin daɗi yace a hakan ma ya gode sosae Allah ya barta da Baffan su twins tana dariya tace Amin tay mashi sai sun dawo, tana niyyar juyawa ta tafi Farha ta ƙaraso wurin itama ankon Material ɗin da kayi ne a jikinta suma riga da skirt ne aka mata tayi ɗaurin kallabi Zarah Buhari dark ash ɗin sumarta ta zuba a gadon bayanta, Kamalu na ganinta gaban shi ya faɗi don ya ganeta ya bita da kallo, murmushi Fatuu tayi mata tace mata sannu itama ɗan murmushin ta mayar mata ta gaishe da ita bayan ta amsa ta maida idonta kan Kamalu suka haɗa ido a hankali yace mata sannu ta ɗaga mashi kai kafin ta maido idonta kan Fatuu tace mata brother ɗinta ne taga kaman sun yi kama tace mata eh Yayanta ne shi take bi mawa ta jinjina kai sai kuma ta ƙara cewa the same parents suke dashi kenan Fatun tace eh su biyu ne Mom ɗin su ta haifa kafin ta rasu a hankali tace Allah ya jiƙanta Fatuu ta amsa da Amin daga haka Farhar bata ƙara cewa komai ba ganin haka yasa Fatuu ce mata bari ta shiga ciki tace Ok, tana juyawa Kamalu ma ya juya zai tafi da sauri Farhar tace "Hey..." dakatawa yay ya kalleta ta bishi da ido kaman bazata tanka ba bata san daurewa kawai yake yana kallon idonta ba, sai bayan ɗan lokaci tace mashi ya bugeta jiya amman bazai iya tambayar ya take ba, sai da ya haɗiyi abu sannan cikin kama kai yace tayi haƙuri yaga wurin kaman lafiya lou, ɗan yamutsa baki tay tace dole sai wuri ya fashe ne ko yayi alama zai yi ciwo girgiza mata kai yay yace "to kiyi haƙuri fatan wurin bai yi maki zafi" ɗan murmushi tay ta ɗaga mashi kai, shiru suka ɗan yi can tace mashi a Yola suke ko yace mata eh, "kai ya baka zo Katsina ba?", ya bata amsa da ai yanzu a Katsinar yake zaune, kai ta ɗaga sai kuma tace "can i know your name?" amsa ya bata da sunan shi Kamalu ta ɗan yamutsa fuska tace suna ne haka yana murmushi ya bata amsa da eh, gyaɗa kai tayi tace bata ta6a jin sunan ba ko nasu ne na fulani yar dariya yay har haƙoranshi suka bayyana gefen kumatun shi duk ya lotsa kamar yadda na Fatuu ke yi, tambayarta yay to tasan suna Kamal ta jinjina kai alamar ta sani yace to sunan shi kenan tace amman miyasa aka maida nashi haka ya bata amsa da haka ya taso ana ce mashi shiyasa tace ya hana ana ce mashi hakan Kamal yafi, ce mata yay ai an riga an saba yanzu zai wuya a bari tace Ok, wayar shi ce ta fara yin ringing ya ɗagota yana kallon mai kiran ganin Kawu Amadu ne yasa bai ɗaga ba ya kalleta yace bari yaje ana jiran shi ta furta Ok, har zai juya tace ya bata lambar shi idan wurin da ya buge mata na mata ciwo zata kira shi yazo ya kai ta Hospital daga yadda tay Maganar ya gane wasa take yana murmushi yace to, bayan ya bata tace zata kira yanzu sai yay saving yace Ok daga haka yay mata sai anjima ya juya ta bishi da kallo hakanan bata san miyasa ba komai nashi burgeta yake, yana zuwa wurinsu Amadu yace wai mi ya tsaya yi wurin wanccan Kamalun yace mashi ba komai tazo wurin Fatuu ne to shine tayi mata bayanin shi Yayanta ne Amadun yace to kuma shine sukayi tsaye bayan Fatun ta tafi, ce mashi yay ta tambayi sunan shi ne, kafin Amadu ya sake cewa wani abu Tk na yar dariya yace to Kodai ta ƙyasa da ɗan fillo ne Amadu ya ɗan ta6e baki yace da dai wata ba waccan ba har abada bai tunanin zata yi soyayya da talaka, Tk yace "ka san abun Allah, ai dama irin su ta haka Allah ke kama su, da kuma abun ya bada kala ɗan fillo da baturiya" dariya Kamalu yay ya tambayi baturiya ce Tk yace Babanta ne bature yace ashe shiyasa yaga idanunta wani iri daga haka suka tafi, Bayan Fatuu ta koma ciki part ɗin data zauna lokacin data haifi twins ta nufa dama acan ta sauka Mino ma da Aysha da Safnah duk suna tare, a parlor ta iske Fauzy zaune dasu Safnah harda Mino ta miƙa mata hannu tace ta taso su shiga ciki, bayan sun shiga cikin Bedroom ɗin a saman gado suka zauna Fatuu na murmushi tace "Amaryar Ya Sameer bamu samu mun zauna ba inata son in tambaye ki ya amarci" ɗan ta6e baki tay tana murmushi tace ai yanzu amarci ya wuce Fatun tace duka wata ukkunne zata ce amarci ya wuce tace Uhmm kawai, hira suka cigaba da yi harda ta makaranta suna cikin yi Fauzy ta kai hannu ta ɗaukko jakarta dake a saman bedside data aje tun ɗazu ta buɗe, wata yar farar roba mai kyau ta fiddo tare da farin hanky ta maida jakar bayan ta daidaita zamanta ta latsa saman robar ya buɗe Fatuu nata kallonta a zaton ta wani abun ci zata fiddo kawai sai gani tay ta kai bakinta saitin inda ya buɗe ta zubda miyau kafin ta saki marfin ya rufe tasa hanky ɗin tana goge gefen bakinta, sakin baki Fatuu tay tana kallonta da alamun mamaki, kallonta Fauzy tay suna haɗa ido tayi murmushi tace mata ya akai ne, hannu Fatuu ta kai ta kama ha6a tace "Ke wai tsaya mi hakan da kikai ke nufi, ni nayi zaton ko Sweet ce zaki fiddo sai inga kin zubda miyau!" Dariya Fauzy tayi tace tun ɗazun yake damunta tana ta daurewa ta haɗiye saboda mutane, waro ido Fatuu tay ta buɗe baki da tsananin mamaki tace "Wai kaddai ciki gare ki Fauzy?" tana murmushi ta ɗaga mata kai alamar eh, hannu Fatuu tasa ta rufe baki sai kuma ta cire cikin washe baki tace "Ashe shiyasa naga kin ƙara haske sosae saidai kuma baki yi ƙiba ba sai ma ɗan ramewa da kikai ni na ɗauka duk amarcin ne yasa haka wllh" girgiza mata kai tay tace wahala ce don laulayi take sosae tayi mamakin ma yadda da tazo bikin ya rage sosae har abinci take ci acan ai ko abincin bata iya ci ga yawan amai har magani aka bata wanda zai sa ta daina aman in tana sha kullum to in ta sha sai ya rinƙa damunta in bata yi aman ba sai kawai wani lokacin ta ƙi sha, tambayarta Fatuu tayi watan cikin tace mata ɗaya da rabi, "Kenan ma kice da kuka je Honeymoon kika same shi" kai ta ɗaga mata tace saida yay sati ukku sannan suka san dashi ko Aunty Mareeya bata sani ba sai yanzu tana ganinta ta gane Fatun tace "Ni kinga wllh ban gane ba saboda banyi tunanin Ya Sameer ɗin zai bari ki samu ciki da wuri ba daga yanayin shi", "Aikuwa yay farinciki dana samu ni kaina saida nayi mamaki don ko Maganar haihuwa bai yi man nayi zaton bazai so cikin ba sai gashi baki ga yadda yake nan nan da ni ba, dafa wai ma bazai zo bikin nan dani ba Aikuwa nayi ta mashi kuka yace shi tsoron shi kada wani abu ya samu cikin nace mashi ai kema da cikin kika taho bikin ko shine yace to zai taho dani da yake kuma gaskiya bai son yaga damuwata yanzu kinga ya rude", yar shewar dariya Fatuu tay tace "kice dai kin damƙe ya Sameer a hannu aikin Aunty Mareeya yayi kyau", tana yar dariya tace "Aikin Aunty Mareeya ko aikin jawo ma mutum wahala ke wllh saida ta kai ina tsoron shi dana ji sallamarshi sai gabana ya faɗi har Aunty Mareeya na ta6a kira nayi mata complain taita ƙarfafa man gwuiwa daga baya dole na saba tunda naga yana son hakan sosae" Fatuu na dariya tace "kice dai Ya Sameer ya Magantu yadda Aunty Mareeya ke so" Dariya Fauzy ta saka tace wllh ita farko ma yay ta bata mamaki sai kace ba shi ba Fatuu dake ta dariya tace haka suke fa miskilan nan dama Aunty Mareeya ta faɗa ta haka ake jin bakin su, "Amman dai ba wata matsala da kike fuskanta a wurinshi ko" Fatuu ta tambaya bayan sun gama yin dariyar, girgiza mata kai Fauzy tay tace "Wllh baida wata matsala gaba ɗaya yadda nayi tunanin shi ba haka ba, sosae yake sake man yana bani kulawa dana nuna inason abu sai yayi man in kuma na nuna banso shikenan, kamar farko kinga mata na kiranshi har ya amsa wayar a gabana tunda na nuna 6acin raina shikenan ya daina lokacin harda bani haƙuri don fushi nayi dashi duk ya ruɗe tun daga lokacin bai hana ni ɗaukar wayar shi da kaina nabi na goge duk lambar wata mace da saƙonni kuma bai ce man komai ba, ko tari nayi sai ya tambaye ni lafiya haka in ina wani abun yana taya ni duk da ba wani aiki ma nike ba da nace ya sallami mai mashi girki in rinƙa yi to yanzu saboda cikin nan ma yace ba za'a sallame shi ba harda mace ma ya ƙaro man da take man aikin gida", tunda ta fara magana Fatuu keta faman sakin murmushin farinciki har ta gama tace amman taji daɗin labarin nan sosae wllh wani hanin ga Allah baiwa ne da bawa yayi haƙuri sai yaga ya kai matakin da bai ta6a zato ba, "Bari Zarah, kullum cikin gode ma Ubangiji nike wllh don yayi man ni'imar da zatona bai ta6a zata man ba, wani lokacin cikin raina sai in ta raya yanzu da nayi rashin haƙuri lokacin da aka yaudare ni na illata kai na koma na halaka kai na da shikenan nayi asara biyu gata rasa wannan babbar ni'imar ga kuma rasa ta ubangiji" girgiza kai Fatuu tay tace idan mutum yay nazari sau da yawa abubuwa masu daɗi suna samuwa ne daga marasa daɗi ita kanta ji yadda al'amarinta da Ya Haisam ya kasance data yi haƙuri gashi tanata cin ribar hakan tuni ma ta manta da irin raɗaɗin data ji a wanccan lokacin, Fauzy tace hakane haƙuri kaɗan ke haifar da jin daɗi na har abada sannan rashin haƙuri kaɗan na haifar da dana sani na har abada, nima dai mai rubutun nace wannan haka yake Allah ya ƙara mana haƙuri Amin, Hira suka cigaba da yi cike da nishaɗi har Fatuu na mata Addu'ar Allah yasa ta haifi yan biyu tana dariya tace haka ma Aunty Mareeya tace amman ita tafi son ɗayan ma. Ana gama sallar Magrib aka fara shirin kai Mino Fatuu tasa ta canza kaya bayan tayi wanka zuwa lace baiwar Allah duk tayi zuru zuru Gwaggo tazo ta tafi da ita baya wurin danginsu don ayi mata Nasiha,, bayan an kawo motoci bakin entry hall aka sanar a fito Fatuu ce ta kamo ta suka nufo cikin babban parlon gidan lokacin su gwaggo ma duk sun fito suna biye dasu, bayan sun shigo Gwaggo ta kama Minon suka nufi part ɗin Mom harda su Yaya, a falonta duk suka zazzauna bayan an gaggaisa Gwaggo tace sun kawo amarya ne suyi sallama sannan su damƙa amanarta duk da sun san ko basu bada ba za'a ruƙe masu amanarta kamar yadda aka ruƙe ta yar uwarta sannan sai anyi haƙuri don zata iya yin wani abu ba daidai ba saboda ƙarancin shekarunta in tayi kuskure a nuna mata duk da akwae yar'uwarta saidai itama ba wata babba bace kuma ba lalle su kasance tare ba gaba ɗayansu dai duk sukai ba daidai ba a kwatanta masu don su gyara Mom na murmushi tace insha Allahu kada suji komai za'a ruƙe amana yadda yakamata sannan yadda suke nuna ma yaransu in sun yi ba daidai ba suma hakan za'a yi masu tunda suma tamkar Ya'yansu ne, sosae suka ji daɗin Maganarta sukai ta godiya tare da yi masu Addu'o'i daga baya suka fito don tafiya Mom ɗin tayo masu rakiya, cikin masu zuwa harda Hajiya Zainab da Hajiya dasu Aunty Mareeya da Feenah kusan duk mutanen da suka rage zasu je Motocin da aka kawo sun kai goma, bayan duk an shishshiga harda akwatunan kayan da Minon tayi amfani dasu waɗanda su Yaya suka taho dasu kuma da sauran kayan an kai su can gidanta, a tare Motocin suka fara tafiya suka tunkari gate, ba wata tafiya mai nisa sukai ba suka iso gidan dake a Asokoro dama gidan Senator ɗin a Maitama yake basu da nisa sosae, tun a bakin gate zaka fara shaida haɗuwar shi bayan mai gadi ya buɗe masu motocin suka kutsa kai ciki, wuri daban daban akai parking don asamu duk Motocin su shiga wasu a cikin parking space ɗin gidan mai ɗaukar motoci huɗu aka shigar dasu wasu daga can gefe gefe Motar da Minon take ciki har cikin entry hall aka shigar da ita, bayan an samu duk Motocin sun shigo aka bubbuɗe kofofin motocin aka fara fitowa nan fa aka shiga bin gidan da kallo waɗanda basu san shi ba, ba laifi gidan yana da girma tunda har harabar shi ta ɗauke duka motocin hasken Fitilu ko ta ina ga shukokin fulawoyi wurare daban daban a tsare sun sha gyara, daga bakin gate akwae ɗakin mai gadi sai ɗayan bangaren nan parking space din yake sannan gaba ɗaya harabar gidan malale take da interlock daga tsakankanin su anyi adon ratsin grass carpet, bangaren ginin gidan kuwa tun daga cikin entry hall aka malala tiles ga wata babbar fitilar sama mai matukar kyau a saman daga nan zaka shiga cikin gidan ta dakakkar ƙopar da ke a wurin, kana shiga ɗan passageway ne wurin shima akwae fitila a sama da kuma flower vases sun saka ƙopar shiga falon tsakiya ana buɗeta za'a shiga cikin parlon wanda babba ne yasha manyan labulai maroon da akai ma wani irin design mai ɗaukar hankali, gaba ɗaya parlon tiles ne ruwan madara kalar fentin falon daga tsakiya aka saka kujerun Mino wanda haɗaɗɗun royal ne brown da ɗan ratsin maroon an jere throw pillows, daga tsakiyarsu lallausan carpet ne brown tsakiyarsu an aje Ottomon kalar yadin kujerun daga angles ɗin parlon an aje flower vases da suka hau da kayan ciki sai bangaren wurin kayan kallo an manna babbar plasma ɗin da aka siya mata a jikin babban Tv stand mai drawers ta kwance da kuma ta tsaye shima cikin saitin kayan yake daga baki bakin shi anyi mashi irin design na adon da aka ma kujerun daga gefe da gefen Tv stand ɗin sound systems ne, iya wurin kayan kallon abun kallo ne, daga can bayan kujerun matattakalar hawa bene take anyi mata wani irin design ta lanƙwaya ƙarafan jiki silver ne sai ɗaukar ido suke itama matattakalar anyi mata fenti ruwan madara kalar na cikin parlon sannan an shimfiɗa carpet brown yabi jikin stairs ɗin har sama, daga gefen hagun benen Dining Area ce an aje dining table da kujerun shi guda haɗu suma mahaɗin kujerun parlon ne, daga can gefen shi nan aka aje standing freezer daga gaban shi anan ƙopar shiga Kitchen take daga jikin ɗayan bangon wurin wani haɗaɗɗan console ne golden manne daga gefe da gefen shi an aje flower vases sosae wurin yay kyau daga ƙasan Dining table ɗin nan ma lallausan carpet ne maroon da ratsin brown, daga tsakiyar parlon bayan kujerun corridor ne inda bedrooms suke guda biyu suna kallon juna da toilet a tsakiya ba laifi Bedrooms ɗin suna da girma a ɗaya Royal Bed ne Milk da wardrobe ɗin shi mai guda shidda a jikinta anyi adon madubi kana ganin kanka haka a jikin bedside din ma gaba ɗaya set ɗin kayan sun haɗu ba ƙarya wani irin design akai masu mai jan hankali a ƙasa an sa carpet milk, a ɗayan ɗakin kuma Simple Modern Bed ne Coffee brown da wardrobe ɗin shi mai gida hudu sai nightstands da dressing mirror daga gaban gadon an sa carpet coffee labulayan ɗakin ma coffee ne, kowanne ɗaki akwae toilet irin na zamani irin wanda ya amsa sunan toilet ɗin masu kuɗi komai na cikin shi fari da silver ne, a 6angaren Kitchen kuwa drawers ɗin ciki L-shape ne dark ash haka cupboards ɗin sama suma L-shape ne an tsara Kitchen ɗin shima yayi kyau sosai, Bayan yan kawo Amaryar sun shigo ciki nan fa aka hau jinjina haɗuwar gidan Gwaggo sai murmushin daɗi take haka Fatuu ma su Yaya da Kakar su Minon mamaki ne shimfiɗe akan fuskokinsu ganin wai wannan Aljanar duniyar Mino zata zauna gaba ɗaya sun kasa rufe bakunansu, yadda aka shirya komai yayi ma su Gwaggo kyau sai yabawa suke, a ɗaya daga cikin ɗakunan aka kai Mino inda keda Royal Bed su Aunty Mareeya suka fito suna ƙara dudduba gidan danginsu Nameer suma suna ta yabawa suna faɗin gaskiya anyi ƙoƙari da yake sunji Hajiya na magana kan kayan da akayin tana faɗin sun kashe kuɗi sosae hakan yasa suka gane danginta sukai mata kayan ɗakin hatta Hajiya Zainab saida tace gaskiya anyi ƙoƙari, har saman bene suka hau wanda nan part ɗin Nameer ne babban falo ne an zuba luntsuma luntsuman baƙaƙen leather chairs da ƙaton carpet baƙi da ratsin ruwan toka mai duhu da kuma mai haske sai labulaye suma baƙaƙe ne da ratsin ash akwae kuma kayan kallo harda freezer falon baida hayaniya amman yayi kyau sosae, Bedroom guda ɗaya ne mai ɗauke da set ɗin gado ɗan Dubai sai toilet ko ina dai yayi kyau sai yabawa ake, har bayan gidan suka je akwae wurin yin basket ball da kuma ɗan madaidaicin Swimming pool daga gefenshi kuma akwai rumfa ta shaƙatawa mai ɗauke da tebur da folding chairs irin wanda ake linkewa, bayan sun gama zazzagaya gidan Aunty Mareeya da Fatuu suka ɗaukko kwalin kayan adon da aka kawo suka fara jera su a jikin gidajen Tv stand wasu kwalaben turaren wuta ne an masu ado wasu kuma kayan ƙawata wuri ne kowanne aka sashi a inda ya dace sosae falon ya ƙara ƙawatuwa suka jona wata jigunannar burner aka saka turaren wuta nan da nan ƙamshi mai daɗi ya fara karaɗe parlon ya haɗe da sanyin A.c, su Amadu ne suka shigo da katan katan na lemuna da abubuwan ci suka aje a saman carpet Aunty Mareeya tace sannunsu abokan ango sukai murmushi kafin suka shiga bin falon da kallo suna murmushin daɗi don ya burge su Hajiya ce tace masu to su zagaya mana su gani da kyau suka ce to, zama sukai kan kujeru suka fara cin abubuwan da aka kawo ana ɗan yin hira Hajiya tasa Fatuu ta ɗiba ta kaima Mino da ƙawarta dake a cikin Bedroom, suna cikin ci Hajiya ta kalli Gwaggo tace wato Dije kwance kwance ashe kuɗi ne daku ko shiyasa kuka zuba ma Ameenatu kaya haka duk aka yi dariya Hajiya Zainab dake cikin cin Shawarma tana murmushinta na manya tace ba Fulani bane su Hajiya tace sune na asali ma tace ai dama kuɗi garesu da an saida shanaye sai kaga uban kuɗi duk akai dariya Gwaggo dai murmushi kawai take don an kashe bakin, bayan wani lokaci suka miƙe don tafiya wasu suka fita wasu kuma suka je yin sallama da Mino harda Gwaggo da Hajiya dasu Aunty Mareeya, ai tana jin zasu tafi ta ruɗe ta saka kuka duk tabi ta ƙanƙame Gwaggo aka hau bata haƙuri Hajiya tace Ameenatu sai kace an kawo ki gidan yari, sam taƙi jin rarrashi sai fullanci take tana ce ma Gwaggo don Allah kada a barta ita kaɗai su tafi da ita Fuskarta duk tayi jage jage da hawaye har saida tasa idanun Gwaggon suka ciko da ƙwalla ita Fatuu ma har sun fara zubowa Hajiya ta tambayi Gwaggo mi Minon ke cewa ne ta faɗi mata wai su tafi da ita tay ɗan murmushi tace ina su ina tafiya da ita ai nan gidantane tazo kenan tayi haƙuri zata saba, ganin taƙi jin rarrashi yasa Hajiya ta kira Nameer a waya bayan ya ɗaga ta tambayi yana ina yace gasu nan a harabar gidan tace to ya shigo ya samesu a Bedroom yace to, bada jimawa ba sai gashi ya shigo cikin ɗakin da sallama yana sanye da riga da wando na Farar shadda fuskar nan sai annuri take ga uban ƙamshi dake tashi daga jikinshi, gaishe dasu yay bayan sun amsa mashi Hajiya ta nuna mashi Mino tace gata nan yazo ya rarrashi matar shi ta hana su tafiya wai bin su zatai, kai idon shi yay kan Minon da tabi ta ƙanƙame Gwaggo ta kifa Fuskarta a jikinta, tsaye yay kawai yana kallon su Hajiya tace yaje ya kamata ko sun tafi in kuma so yake su kwana to still bai matsa ba don kunyar yaje ya kamata yake sai ɗan murmushi yake ganin haka yasa Fatuu ta kai hannu ta ɗago da ita suka haɗa ido tace mata ya isa ta daina kukan ita zata zauna tare da ita jin hakan yasa ta faɗa jikin Fatun Hajiya tace masu su tafi, bayan duk sun fita ya rage saura Fatuu da Safnah sai Nameer da hannu Fatuu tay mashi alamar yazo ya rarrasheta, Moving yay zuwa inda suke ya tsaya a gabansu cikin kwantar da murya ya kira sunanta shiru bata amsa ba bata kuma ɗago daga jikin Fatun ba, hannu ya kai ya fara ƙoƙarin ɗago da ita ta turje su Fatuu nata bata haƙuri ganin taƙi rabuwa da jikin Fatuu yasa shi nuna mata ƙarfi ya ɗagota da ƙarfi tana barin jikin Fatun da sauri ta kamo hannun Safnah suka nufi hanyar fita daga ɗakin Minon nata rizgar kuka tana ƙoƙarin kwacewa ta bisu hakan yasa shi haɗeta da jikin shi ya rungumeta tightly ya kai bakin shi saitin kunnanta a hankali ya shiga rarrashinta yana faɗin ba gashi tare da ita ba, sukuku Fatuu ta dawo duk tausayin Mino ya kamata daga baya ta sake suka shiga yin hira da Fauzy kowa na tuna lokacin da aka kai shi ɗakin miji Safnah dai har ta kwanta don itama jikinta yayi sanyi saboda yanayin da suka baro Aminiyarta, suna cikin yin hirar Sameer ya kira Fauzy ta ɗaga kiran, tambayarta yay tana ina tace gata nan sun dawo gidansu Ya Haisam yace Ok gashi nan zuwa zai dauketa tace to, bayan sun gama wayar Fatuu na murmushi cike da tsokana tace su Fauzy ana waya da miji an wani kwantar da murya dariya tayi tace ai saida hakan, faɗi mata tay zai zo ya ɗauketa ne Fatun tace maimakon tace mashi zata kwana anan su kwana tare Fauzyn ta ɗan buɗa ido tare da jinjina kai tace ai tasan ko tace haka ba lalle ya bari ba Fatuu tace bai iya kwana ba tare da ita ba kenan, "Kusan hakan, kinsan fa koda muna London bayan mun dawo daga Honeymoon in zaije wani wuri indai kwana zai yi dani yake tafiya, ai Honey ba sauƙi sai da na samu cikin nan ne ganin ina wahala ake ɗan raga man" Fatuu na dariya tace ai hakan ake so a damu da kai sai ta dage taita gyara kanta don ma halin da take ciki ba komai zata iya sha ba Fauzyn tace eh tama daina shan wani magani Aunty ma tace a halin da take ciki ba sai tasha komai ba, bada jimawa ba Sameer ɗin ya kirata ya sanar mata gashi a gaban entry hall, tare da Fatuu suka fito tayo mata rakiya suna ƙarasowa gaban Motar ya buɗe Motar tun kafin ya idasa fitowa ƙamshin turarenshi ya karaɗe wurin, sanye yake cikin ƙananan kaya Fuskarshi tayi wani irin Fresh har yar ƙiba ya ƙara da yake wurin fayau yake da haske, bayan ya fito gaisawa sukai da Fatuu fuskarshi a sake yay mata ya hidima ta amsa da Alhamdulillah yace Allah yasa alkhairi, bayan ta amsa ya ambayi ina yaranshi tace suna wurin Mom yace a gaishe mashi dasu, maida idon shi yay kan Fauzy data jingina da Motar ta langa6ar da kai slowly yace "hope u'r Ok?" lumshe mashi ido tay ta ɗan ɗaga mashi kai yace to suje tare da yi mata alama da kai, tare suka zagaya ɗayan bangaren ya kai hannu ya buɗe mata ƙopar saida ta juyo ta kalli Fatuu dake tsaye tana ta murmushi ta ɗan ɗaga mata hannu itama ta ɗago mata sannan ta shige ya maida ƙopar ya rufe bayan ya zagayo driver side yayi ma Fatuu sallama ya buɗe ya shige, saida yaja Motar sannan ta juyo komowa cikin gidan tanata murmushin daɗi ganin yadda Sameer yake kulawa da Fauzy harda su buɗe mata ƙopa abunda bata ta6a zaton zai yi ma mace ba, bayan sun hau titi sosae ya juya ya kalli Fauzy data kwantar da kanta jikin headrest ya kai hannun shi dake gefenta ya kamo nata daga yadda take ta juyo da kan ta kalle shi yace mata ko jikin ne ta girgiza mashi kai alamar a'a ya sake cewa ko tana jin yunwa ne nan ma ta girgiza mashi kai yaci gaba da driving da hannu ɗaya ɗayan kuma yana ruƙe da nata can bayan wani ɗan lokaci ya sake juyowa ya kalleta ya tambayi ko tana son wani abu ta ɗan yi shiru kafin tace tana son ice cream yay ɗan shiru tare da maida idon shi kan hanya taji yace tana shan abu mai sanyi sosae ba ba'a son suna sha ba, ɗan yamutsa fuska tayi ta sigar shagwa6a tace to ai cikin ne yake mata zafi sai tasha abu mai sanyi take jin sauƙi ya jinjina kai, a bakin wani babban cold store ya parker tare da buɗe Motar yace mata yana zuwa ta ɗaga mashi kai, nufar shiga wurin yay tanata kallon shi ta glass wata irin ƙaunar shi na ratsata, After few minutes ya fito ruƙe da leda mai tambarin wurin ya dawo wurin Motar, bayan ya shiga ya miƙa mata ta amsa tare da furta "thank you Honey" jinjina mata kai yay ya ja suka tafi, bude ledar tayi ta fiddo roba ɗaya bayan ta buɗeta fara sha, tana cikin sha ta ɗebo ta kai bakin shi idon shi akan hanya ya buɗe ta zuba mashi bayan ya shanye ya furta mata "Love you Babes" tana murmushi tace "love you too Honey.....the best Husband ever" ɗan juyowa yay yayi mata wani kallo tana murmushi ta kashe mashi ido yay faffaɗan murmushi tare da maida idon shi kan titi bayan ɗan lokaci suka iso gidan su inda ya ta6a kawota. Bangaren Amarya Laila tuni suka isa Kano aka ɗaukko su daga Airpot a cikin jigunannun motoci masu numfashi, gidan su Angon aka nufa dasu dake a Nasarawa G.r.a, katafaren gida ne daya amsa sunan gidan masu kuɗi sosae gari guda zagaye shi a ƙafa ba ƙaramin aiki bane an narka uwar dukiya tun daga kan ginin, gidan yana da part part da yawa don matan Mahaifin Angon nata ukku surukar Laila ɗin ce ta farko hakan yasa gidan suna da ɗan yawa, a part ɗin Momyn Bashir ɗin wanda ƙarshe ne wurin haɗuwa aka saukesu sun samu kyakkyawar tarba daga danginsu, bayan sun huta aka kawo masu lafiyayyun abinci da abubuwan sha, misalin karfe biyar aka shiga shirin yin buɗar kai da za'ayi anan cikin harabar gidan har an yi haɗaɗɗan decoration gidan ya ƙara cika da Jama'a harda anko aka yi, bayan duk an shirya Amarya Laila ma ta canza shiga haka su Jidderh duk sun canza kaya ba 6ata lokaci aka shiga gabatar da buɗa kan, Sai bayan isha'i aka gama An ci an sha an yi hotuna da Vedios Sosae aka nishaɗantu, ana gama yin buɗar kan aka fara shirin kai Laila gidanta wanda shima ke anan cikin G.r.a ɗin dama duk mazan gidan masu aure anan unguwar gidajen su suke don Mahaifinsu nada gidaje a cikin unguwar sosae wasu hayar su ake, jerin motoci ne aka kawo don ɗaukar yan kai Amaryar bayan duk an shishshiga a tare motocin suka tafi, ba wata tafiya akai sosae ba aka iso gidan tun daga wajen gidan zaka shaida haɗuwarshi, gaba ɗaya motocin saida suka shige cikin harabar gidan don babbane sosae an ƙawata cikin harabar da shuke shuken fulawoyi masu kyau da tsari ga hasken fitulu sun haske ko ina, bayan duk an firfito Aunty na ruƙe da Lailar Hajiya Maryam na daga gefe suka nufi shiga cikin gidan wanda ginin bene ne, sosae su Hajiya Maryam suka yaba da tsarin gidan ita Aunty dama sun zo da aka kawo kayanta duk da basu ne suka shirya mata kayan ɗaki ba masu shirya gida aka ɗaukko suka yi aiki su kawai umarni suka rinƙa badawa, gidan Laila sai san barka an kashe naira ba ƙaɗan ba wurin yi mata kayan ɗaki sai yabawa ake, idan nace zan bayyana yadda tsarin gidan yake to kuwa ba ƙaramin lokaci zan ɗauka ba kawai dai abunda zance shine gidan Laila ƙarshe ne wurin haɗuwa Aljannar duniya ne an zuba mata kaya na gani na faɗa sai fatan Allah yasa gidan zamanta ne na har abada, tare dasu Aunty aka dawo gidansu Angon aka barota ita kaɗai anan zasu kwana gobe in Allah ya kai mu su juyo Abuja. Washe gari da Asuba Fatuu ta tashi don tayi salla su Aysha da Safnah ma da suka kwana anan ta tashesu, bayan duk sun gama komawa sukai suka kwanta don kowa a gajiye yake gashi yau su Safnah zasu tafi dasu Gwaggo amman banda Fatuu don Haisam yace nan zata tsaya, Fatuu bata daɗe da komawa ba har ta fara yin gyangyaɗi wayarta ta fara ringing ta kai hannu gefen filo ta ɗaukkota, koda taga mai kiran nata da alamun mamaki ta maimaita sunan Nameer a hankali ta furta "to lafiya???" gabanta har ɗan faɗuwa yake tay picking tare da ƙoƙarin tashi zaune, sallama tayi jin shiru bai yi magana ba bayan ta ɗaga sannan ya amsa ya gaishe da ita muryar shi ƙasa ƙasa bata ji komai ba don ya saba gaishe da ita, bayan ta amsa shiru yay bai ƙara cewa komai ba itama shirun tay tana jin fargabar abunda yasashi kiranta a wannan lokacin, jin baida niyyar magana yasa tace "Nameer lafiya kuwa ka kira kuma naji kayi shiru" tana jin sautin yar ajiyar zuciyar da yayi a hankali yace mata dama Don Allah wani taimako yake son tayi mashi da sauri tace to wane taimako taji yace zai zo ya ɗauketa yanzu in ba damuwa zasu je gidan shi, bugun da gabanta ke yi ne ya ƙaru cike da fargaba har muryarta ta bayyana tace mashi to amman lafiya kuwa shiru ya ɗan yi kafin yace mata lafiya lou ba wani abu bane Minon ce har yanzu keta kuka shine yake son taje ta rarrasheta, shiru Fatun ta ɗan yi tana juya abunda yace a ranta lokaci guda kuma zuciyarta ta raya mata wani abu da sauri tace mashi to yazo ya ɗauketan yace Ok gashi nan ma ya taho don Allah ta fito bakin entry hall da yazo sai su tafi bai son wani ya ganshi tay ɗan murmushi tace to, bayan sun gama wayar Haisam ta kira tana fara yin ringing ya ɗauka saida ta gaidashi sannan ta faɗi mashi zancen zuwa ɗaukarta da Nameer zai yi ya tambayeta lafiya tace haka yace mata lafiya lou Minon ce keta Kuka dama jiyan da ƙyar suka rabu yace Ok kafin yace ina su Abie tace bari ta kawo su nan wurin shi kafin ta dawo, Abie ta fara ɗaukkowa ta nufi part ɗin shi tana zuwa bakin benen suka haɗe da Haisam ɗin ya amshe shi ta juyo don ta ɗaukko Adam, sauri sauri ta canza kaya zuwa jallabiya tay rolling veil ta ɗauki purse bayan ta saka wayarta ta nufi ƙopar fita, tana fitowa daidai Motar Nameer ɗin na ƙarasowa yana tsayawa ta nufi gaba ta buɗe bayan ta shiga yaja suka tafi, yana sanye da brown ɗin jallabiya mai gajeran hannu gaisawa suka ƙara yi ba tare da ya kalleta ba daga haka basu ƙara cewa komai ba har suka ƙaraso gidan bayan an buɗe masu gate ya shiga a gaban entry hall ya parker Motar kusan a tare suka fito ya zagayo inda take ya ɗan kalleta tare da ce mata suje suka jera, saida yasa makulli ya buɗe kopar sannan suka shiga parlon tsaf dashi sai sanyin Ac mai haɗe da ƙamshi ke tashi, hanyar Bedroom ɗin suka nufa suna zuwa bakin corridor ɗin ya tsaya ta kalle shi yace mata ta shiga tana nan ciki, tambayar shi tayi a wane ɗaki take yace wanda suka barta jiya ta ɗaga kai tare da juyawa ta shige cikin corridor ɗin, a hankali ta tura kopar gabanta na faɗuwa ta leƙa kai, acan saman gado ta hango Mino ta takure guri guda jikinta lullu6e da duvet, a hankali tayi sallama ta shiga shiru Minon bata motsa ba ta nufi gadon, zama tayi a baki idonta a kanta har lokacin gabanta faɗuwa yake, kiran sunan Minon tayi shiru bata amsa ba hakan yasa ta ƙara ɗaga murya ta kirata lokacin Minon ta yaye duvet ɗin da sauri, koda Fatuu tay arba da fuskarta wani irin bugu da ƙarfi gabanta yay ganin yadda fuskar tay jajir ga idanuwanta duk sun kumbura haka la66anta ma sun ɗan kumbura sunyi ja kamar jini ya kwanta, yaye duvet ɗin tayi da sauri ta nufo Fatuu tana zuwa ta faɗa jikinta ta fashe da matsanancin kuka har sai da Fatuu ta ɗan runtse ido jin yadda jikin Minon yay zafi sosai, cikin fullanci take mata Magiyar don Allah ta tafi da ita gida kada ta sake barinta anan mutuwa zatayi gaba ɗaya a gigice take hakan yasa Fatuu ruɗewa ta ɗagota Fuska a yamutse take ce mata mi ya faru ta faɗi mata cikin kuka take faɗin Ya Nameer ne bai sonta mugu ne shi ashe bata ga abunda yayi mata ba so yake ya kasheta, cikin sheshsheka take Maganar jikinta sai 6ari yake Fatuu tay shiru ta bita da ido sosae take jin mamakin Maganar Mino a cikin ranta ta shiga raya badai Mino bata san miye aure ba, maidata tayi jikinta ta shiga ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi tana faɗin tayi shiru to in dai tana son ta tafi da ita ɗin aikuwa sai gashi ta daina sai ajiyar zuciya da take saukewa a jere, ɗagota Fatuu tay tana ɗan murmushi ta shiga goge mata ƙwallan fuskarta bayan ta gama bin ta tayi da kallo ta rasa ta ina ma zata fara fahimtar da ita can tace mata a Makarantar su ba'ayi masu bayani kan Aure ba, cikin disashshiyar murya Mino ta tambayeta islamiyya ko boko Fatun tace mata duka tace a islamiyya ana yi masu wa'azi kan mata ta rinƙa yima mijinta ladabi da biyayya kuma ta rinƙa nuna mashi soyayya sannan in ta haihu taba yaran tarbiyya mai kyau sannan a Boko a islamic studies anyi masu bayanin minene aure da kuma yadda ake yin shi, kai Fatuu ta jinjina kafin tace to ba'a yi masu bayanin yadda ake haihuwa ba tace anyi masu a cikin Biology a Reproduction Fatun ta tambayeta ma'anar shi ta faɗi mata harda ire iren shi, gyara zama Fatuu tayi don anzo inda take so cikin types ɗin ta tambayeta wanda ya shafi abunda take son ta sani tace tayi mata bayanin shi ta shiga yi mata tiryan tiryan, murmushi Fatuu tay tace to bata san haɗuwar da ake nufi in mace da namiji sun yi ba ake samun cikin da ta faɗa Minon tace mata ana nufin in akayi aure aka cigaba da soyayya, jinjina kai Fatuu ta shiga yi don ta fahimci da gaske Minon bata fahimci abunda ake nufi ba, "Ba daga anyi aure ana soyayya ba ake samun ciki ba tunda in hakane ai kafin kuyi auren kuna soyayya miyasa baki samu ba, abunda ya faru tsakanin ki da Nameer shi ake nufi da in mace da namiji sun haɗu don haka ba laifi yayi ba, hakan kusan shine auren ma dole sai ana hakan zaki samu ciki kuma duk lokacin da hakan ya faru tsakanin ku lada zaku samu", yamutsa Fuska Minon ta shiga yi idanunta cike da ƙwalla murya na rawa tace "amman Adda Fatuu da wuya fa sosae wllh har matuwa nayi na dawo" tana kai Maganar ta fashe da kuka kasa daurewa Fatuu tay saida tayi yar dariya tace ta suma dai ana mutuwa a dawo ne, Kuka sosae Minon keyi Fatuu ta zura mata ido bata ji mamaki sosae ba don tasan akwai ƙarancin wayewa a tattare da Mino gashi ita ba mai shiga mutane bace sosae kuma bata da shige ma ƙawaye wani lokacin kamar miskila haka take, ajiyar zuciya Fatuu ta sauke ta dafata tana faɗin to miye abun kuka ai ba ta dingi jin zafin ba kenan daga yanzu bazata ƙara ji ba, duk da haka taƙi daina yin kukan sai faɗin Allah bazata iya ba da wuya take, "Aikuwa indai kika ce bazaki bashi hakkin shi ba sallamar ki zai yi ya auro wata" Fatuu ta faɗa ta ɗan ɗaure fuska hakan yasa Minon ta ɗan tsagaita kukan Fatun ta ɗage mata gira tace hakan take so ko ya saketa da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a tace aikuwa indai tace gudunshi tace zata rinƙa yi abunda zai faru kenan tunda hakan shine auren don haka indai tana son cigaba da zama dashi dole ta daure a hankali zata saba, tana matsar ƙwalla take faɗin Allah kuwa azaba gareshi Fatun tace bata faɗi mata daga yanzu bazata ƙara jin zafin ba duk wadda take gani anyi ma aure dole hakan sai ta faru da ita taga suna baro gidajen auren nasu ne daga baya ake sabawa ko itama hakan ya faru da ita har Asibiti aka kaita da ɗinki ma za'a mata, waro idanunta da sukai luhu luhu tayi a razane tace ɗinki kuma Fatun tace eh wasu har aiki ake masu ai ɗinki in hakan ta faru dasu sai sunyi jinya kuma basu baro gidajen mazajen nasu saboda sun san dole sai hakan ta faru, wuri wuri tayi tana kifce kifcen ido ta daina yin kukan, tambayarta Fatuu tay ba'a kaita Asibiti ba da sauri ta ɗaga mata kai tace sai dae ko in da ta sume murmushi Fatuu tay tana kallon ta da sauri Minon ta sunkuyar da kanta can ta miƙe tare da kamo hannunta tace suje toilet, kokarin miƙewa ta fara Fatuu ta taimaka mata ai tana fara taka ƙafafun ta saki ƙara ta ƙanƙame Fatun ta fashe da kuka tana faɗin ƙafafuwanta sun karye Allah bazata iya tafiya ba Fatun tay yar dariya ta girgiza kai abu yazo ga su alanƙoso, duk da halin da Fatun ke ciki haka ta duƙa tace ta hau bayanta bayan ta haye ta miƙe da ita suka nufi toilet, basu daɗe da shiga ba Fatuu ta fito ta nufi wurin akwatunan Minon ta fiddo towel bata ɗaukar mata brush ba don ta ganshi a toilet ɗin, bayan ta dubata ta shiga taimaka mata sun ɗauki lokaci a cikin toilet ɗin kafin suka fito Mino na ɗaure da towel a ƙirji ta yafo short a kai ta dafo kafaɗar Fatun yanzu lafiya lou ta tako kafafun duk da a hankali take yin tafiyar, a bakin gado ta zaunar da ita ta nufi wurin kayanta tana faɗin yakamata a jera kayan nata, mai ta ɗauko da turarurruka da undies sai ta ɗauko mata doguwar riga mai kyau da gyalenta, da kanta ta shafa mata mai sannan ta bata undies ta saka bayan ta gama ta bata rigar itama tasa ta fesheta da turare harda roll on ta bata ta shafa, bayan ta gama shiryawa ta miƙe tace mata tana zuwa ta nufi ƙopar fita, parlor ta fito Nameer na zaune kan kujera duk lokacin nan yana ganin Fatuu ta fito ya miƙe da sauri ta nufo shi tana ɗan murmushi, a gaban shi ta tsaya tace mashi tayi mata abunda ya dace duk da jikin nata yayi tsami yakamata tun da wuri ta zauna ruwan ɗumi da sauri yace saida ya kira wani abokin shi likita ya faɗi mashi abunda yakamata to taƙi yarda ne data ganshi sai tayita yin ihu kamar taga Dodo har magunguna daya turo mashi yaje ya siyo amman ya rasa taya zai bata ya ƙarasa yana ɗan murmushin kunya itama yar dariya tay tace ina ruwan mino ta tambaye shi ina magungunan ya zura hannunshi cikin aljihun jallabiyarshi ya fiddo mata su, amsa tayi har zata juya sai kuma ta dakata tace mashi yakamata ta fara cin abinci don tasan bata rasa jin yunwa yace mata akwae su shawarma da kaza a cikin Fridge tace a'a mai ɗumi yakamata taci ta tambayi akwae kayan tea yace eh akwae komai a cikin store bari yaje sai ya haɗa mata, yana niyyar juyawa tace a'a bari tayi shi yaje wurin Minon yay ɗan yi jimm kafin ya tambayi lafiya lou yaje har saida yaba Fatun dariya tace ko ya fara jin tsoronta ne yay yar dariya yace kusan hakan, bayan taje Kitchen deep freezer dake ciki wadda Nameer ɗin ne ya siyeta don ba ita suka siya ma Minon ba anan dai suka ganta jiya ta buɗe, shaƙe take da vegetables da ɗanyan nama harda kaji jiya a rufe take shiyasa basu ga kayan ba, store ɗin ta nufa shima yau a buɗe yake sa6anin jiya da yake a rufe koda ta buɗe shi shima dankam yake da kayan Abinci ba abunda babu har saida Fatun ta jinjina kai tana murmushi ba 6ata lokaci ta ɗaukko abunda take buƙata ta fara yin aikin, ɗakin ya nufa gaban shi har ɗan faɗuwa yake don ba ƙaramin tada mashi hankali tayi ba, saida yay jimm a bakin ƙopar kafin ya kai hannu ya tura yasa kai tana jin an turo ƙopar ta ɗago kai ta kalli ƙopar suka haɗa ido, da yar sallama ya ƙarasa shigowa ya nufo gadon tana ganin shi ta yunƙura ta tashi zaune ta ɗan kalleshi kafin ta sadda kanta ƙasa yana ganin haka ya zauna bakin gadon idonshi a kanta ya furta "My Baby..." shiru bata amsa ba bata kuma ɗago ba saida ya ƙara kiran nata sannan ciki ciki ta amsa ya kai hannu ya kamo nata slowly yace fushi take dashi har yanzu a hankali ta ɗan girgiza mashi kai alamar a'a, ƙarasa hayewa yay saman gadon ya jawota jikinshi ya rungumeta yashiga bata haƙuri yana faɗin bai so yasa ta wahala ba amman ba yadda zai yi dole tay passing through hakan amman daga yanzu bazata ƙara shan wahala ba ta jinjina mashi kai, wani irin daɗi ne ya ratsa shi ganin ta saukko ya kwantar da kanshi saman nata tare da furta mata yana sonta sosae a hankali tace itama haka ya lumshe ido, bayan wani lokaci Fatuu ta gama haɗa masu Breakfast chips tayi masu da farfesun kaza sai ta haɗa tea, a saman babban tray ta jera komai ta ɗaukka don ta kai masu, a bakin kopar ta tsaya tayi sallama shiru ba'a amsa ba ta ƙara yi nan ma shiru hakan yasa ta aje tray ɗin tasa hannu tay knocking sai lokacin Nameer dake rugume da Mino bacci ya kwashesu yaji ya ɗago tare da cewa Yes hakan yasa ta shigo ta nufo gadon har lokacin Mino na a jikin shi tana bacci, a saman table ɗin gadon ta ɗaura ta kalleshi tana murmushi tace Ango gashi nan ta gama yace Ok bari ya tasheta sai ta bata tace shi bai iya batan yace yana son taci sosae ne in ita ta bata sai tafi ci tace to bari taje ta ɗaukko plate ta zuba mashi da tare ta zubo masu yace ba saura a Kitchen ne tace akwae yace ta bari zai je ya zuba ita sai suci tare tana dariya tace ango da zuba Abinci, shima dariyar yake yace da yaci sa'a ma daba shi ya dafa ba, bayan ya tashi Minon shi ya ɗauko table ɗin ya maido saitin da Minon take Fatuu ta zauna shi kuma ya tafi, a nutse ta shiga bata a baki tana ci can Minon tace itama ta ci tana murmushi tace zata ci ta fara ƙoshi tukun, ba laifi taci sosae itama Fatun taci bayan ta gama ta bata magunguna, cigaba da kwatanta mata rayuwar aure Fatun tay "daga yanzu kada ki ƙara gudun mijin ki kinji yar ƙanwata hakan ba kyau indai ya nemi hakkin shi kika hana Allah zai yi fushi dake mala'iku kuma su kwana suna tsine maki saidai idan baki lafiya sai ki faɗi mashi, ta hakane zaki kama zuciyar shi ya zama kullum kece a ranshi saboda hakane ma kafin auren kika ga ana baki wasu abubuwa kina sha don ki ƙara daraja a wurin shi ne ki kuma haɗa da biyayya ai Gwaggo duk ta maki bayani kan hakan, sannan ki dage da yin ado da kuma kwalliya nasan baki da matsala da wannan dama kin iya shafa jambaki da hoda to yanzun ne zasu yi maki amfani kinga dai mijinki tubarkallah ta ko ina yayi irinsu yan mata rububin su suke don haka sai kin dage ki rinƙa yi mashi abunda yake so sannan kisan irin kalar shigar da yafi so kina yi mashi...." da sauri tace mata ƙananan kaya yake so ya faɗi mata Fatun tace to ta rinƙa yawan saka su in yana gida ko kuma in tasan zai dawo amman kamar in tana sanye dasu tayi baƙi maza sai ta ɗaura after dress amman suma sauran kayan nata kada tace zata jubge su ta rinƙa sakawa akai akai tana cin gayu ba kamar ranar Juma'a Minon nata ɗaga mata kai bayan ta gama yin Maganar a hankali tace to ko ta canza kayan jikinta yanzu tasa wanda yake so ɗin fatuu tay murmushi tace a'a ta bar rigar tunda bata jin daɗi zata fi sakewa tace to, bayan sun gama yin Maganar tace mata ta kwanta ita kuma ta ɗauki tray ɗin kayan ta nufi ƙopa, lokacin data fita ba kowa a parlon ta wuce kitchen, wanke kayan da akai amfani dasu tayi tay tunanin tayi masu girki kafin ta tafi, tana cikin aikin girkin Nameer ya shigo tun yana sawo kai ƙamshin turarenshi ya karaɗe kitchen ɗin, da alama wanka yayi yana sanye da ƙananun kaya wanda da gani sababbi ne sumar shi tasha gyara sai salƙi take haka sajen shi, daga gefen ta ya tsaya ya aje tray ɗin kayan Breakfast ɗin yana murmushi yace "sannu da aiki Yayata ta kaina" wani kallo tay mashi tana murmushi tace na daɗin baki ko, "Amman kinsan ai tun da kika zama Yayata nike girmama ki ko" ɗan ta6e baki tay yana dariya yace yanzu ma zai ƙara girmamata tunda ta mashi aiki tay dariya kafin tace ai biya zai yi da sauri yace ta faɗi ko nawa ne zai bata in ma baida su zai samo tace bada kuɗi zai biya ba alƙawari zai yi na bazai ma Mino kishiya ba yana murmushi yace in don wannan ne dama baida wannan ra'ayin itace kaɗai matar shi har ya mutu ta ɗan harare shi tace ita zai ma daɗin baki, "Ba daɗin baki bane am serious mizai sa in ƙara Aure inada Ameenatu, tamkar rainonta zanyi fa lokacin da zan manyanta lokacin zata ƙara cika mace to mi zai burge ni a wurin wata" murmushi Fatuu tay tace wasa ma take mashi ita ai tana da kishiyar ko yace to shi da gaske yake daga Babynshi ya gama tace Allah ya barsu tare ya basu zaman lafiya da zuriya ɗayyiba ya amsa da Amin kafin ya tambayi mi zai tayata da shi tace ba komai duk ta cimma aikin ma sauran ƙarashe yace Ok tare da yi mata godiya ya juya ya fita, farar shinkafa da miya tayi sai coleslaw tayi farfesun yan ciki saida ta wanke komai data 6ata ta zuba abincin a cikin warmers masu kyau ta kai kan Dinning table, bedroom ɗin Minon ta nufa bata yi tunanin Nameer na ciki ba saida ta shiga ta ganshi rungume da Minon suna bacci tay murmushi ta wuce inda ta aje purse ɗinta ta ɗauka kafin ta fito, parlor ta dawo ta fiddo wayarta nan taga missed call ɗin Gwaggo har biyu, sake kiranta tayi bayan ta ɗaga sun gaisa tace ta kira bata kusa ne Gwaggon tace eh tayi tunanin hakan dama zasu tafi ne taga bata ganta ba suyi sallama saida suka fito ɗanta Haisam ke faɗi mata tana gidan Mino tace eh tare da tambayar yanzu sun tafi kenan tace mata eh gasu a Mota, fatan Allah ya tsare tay tace sai tazo, kafin suyi sallama ta tambayi ya Minon tana yar dariya tace lafiya lou dama taƙi kwantar da hankalinta ne tana ta koke koke amman yanzu ta kwantar da hankalin Gwaggo na murmushi tace ina ruwan Mino a hankali zata saba sukai sallama tace tayi ma su Yaya da Safnah Allah ya tsare tace to, bayan sun gama wayar tunanin zaman mi zata zauna yi tay hakan yasa ta shiga kiran Haisam bayan ya ɗaga tace in bai komai yazo ya ɗauketa pls yace Ok, after some minutes ya kira yace mata yana a harabar gidan ta miƙe ta nufi hanyar fita, saida ta buɗe kopar gaban Motar taga ashe harda su twins yazo da yake Motar tinted ce gaba ɗaya an yi masu wanka suna sanye da kaya iri ɗaya suna ganinta Adam ya washe mata baki Abie kuma yay mata ɗan murmushi duk suka miko mata hannu suna son ta ɗaukesu suna faɗin Momy, saida ta zauna sannan ta ruƙe su gaba ɗaya ya tashi Motar suka tafi, bayan sun hau hanya take ce mashi ashe su Gwaggo sun tafi ya ɗaga mata kai tace ta kirata har sau biyu bata kusa da wayar, shiru suka ɗanyi can ya tambayeta lafiya gidan Nameer ɗin tay faffaɗan murmushi idonta akan shi tace mashi laifi yayi ne shine aka kaita rarrashi Haisam ɗin ya ɗan buɗa ido tare da ɗage gira sai kuma yay murmushi ba tare da yace komai ba, suna cikin tafiyar take tambayar shi yaushe zata je Katsina ya bata amsa da Us zasu tafi tace bazata je sallama ba yace in tana so sai taje amman yana son zasu je Adamawa su duba jikin arɗo yaji su Dad ɗinta suna faɗi ma Dad ɗinshi bai lafiya, sosae taji daɗi jin zasu je tace mashi eh bai jin daɗi yace Ok cikin next week sai suje. Bayan sallar Azahar su Aunty yan Kano suka dawo an cika su da abubuwan arzuƙi Jidderh harda kukan baro Aunty Laila duk tayi sukuku koda ana Maganar Lailar bayan sun dawo sai ta sake saka wani sabon kukan Hajiya na faɗin itama ba Auren zata yi ta tafi ba, Bayan sallar La'asar su Hajiya Maryam suka wuce lagos su Hajiya Zainab ma lokacin suka tafi harda Fauzy. Alhamdulillah Yan Katsina sun isa lafiya sai fatan Allah ya huta gajiya, a ranar bayan sallar isha duk suna zaune a cikin parlon Gwaggo suna yin hirar bikin baka jin komai sai fullanci dake tashi su innarsu Altine sai zuzuta gidan Mino suke suna faɗin ai Aljannar duniya aka kaita, suna cikin yin firar Amadu da Kamalu suka shigo jin firar da suke ne yasashi kunna Vedio ɗin gidan Minon da yayi lokacin da suke zagayawa ya miƙa ma Yadikko ta fara gani, sakin baki tay da tsananin mamaki take kallon Vedio ɗin tana faɗin yanzu anan Minon take aka bata amsa da eh su Altine da basu je ba duk sun zagayeta sun saki baki galala suma suna kallo, ƙarshe dai kukan farinciki Yadikko ta saka ta hau gode ma Allah da kuma Gwaggo tana faɗin koda tayi aikatau a Abuja bata ta6a tunanin wani nata zai zauna a can ba balle kuma ƴarta, inna Mero matar arɗo ce tace hada halin kirkinta yaja mata yadda ta ruƙe ƴaƴan kishiyarta da Amana bata zalunce su ba ta ɗaukesu tamkar nata gashi nan hakan yayi mata rana tunda data zalunce su ba yadda za'ai Gwaggo ta ruƙa mata ɗiya har itama tayi aure gidan daula su Kakar Minon suka shiga faɗin hakane wllh Yaya kuwa duk tabi tasha jinin jikinta sai murmushin yaƙe take, suna haka wayar Kamalu ta fara ringing ya kai idon shi kan screen ɗin yaga baƙuwar lamba saida ya fito waje saboda hayaniya sannan ya ɗaga tare da yin sallama daga ɗayan bangaren zazzaƙar muryar mace ta amsa mashi tare da tambayar ya yake ya bata amsa da lafiya lou kafin ya tambayi wacece, farko shiru tayi kamar bazata tanka ba saida ya ƙara tambaya sannan tace kenan data amshi number ɗin shi tace zata kira yay saving bai yi ba kenan, jin haka yasa ya ganeta da sauri yace tayi haƙuri ya manta ne da yake lokacin jiran shi ake tace Ok kafin ta tambayi ya suka koma yace Alhamdulillah itama ya tambayeta sun koma ne ko suna Abuja tace mashi No sun koma, ɗakinsu ya nufa suka cigaba da yin wayar saidai itace ke fara yin magana sannan yayi harda tambayarshi game da karatunshi ya bata amsa da bayan ya gama Secondary acan garin su bai cigaba ba dalilin da yasa yanzu ya dawo nan kenan don ya cigaba har ma ya siya Jamb zai yi tace Ok tare da yi mashi fatan Akhairi yayi mata godiya daga baya tace mashi tana son zasu zama Friends in ba damuwa har saida ya jinjina Maganar a ran shi don baiyi zaton jin hakan daga wurinta ba jin yayi shiru tace ko bazai yi abota da ita ba, da sauri yace a'a zasu yi suka cigaba da yin wayar kafin daga baya sukai sallama ya tashi ya koma shago. Ranar Juma'a lokacin sati guda da bikinsu Nameer Jirginsu Fatuu ya tashi zuwa Yola, a yadda Haisam ya shirya masu zasu sauka a gidan wani abokin Dad ɗin shi wanda shima Senator ne mai suna Buba daga nan sai suje garin su Fatun, bayan sun sauka wurin ƙarfe goma na safe Driver ne tare da ɗan mutumin mai suna Amir wanda zai yi shekara ashirin da biyar suka je ɗaukko su, kyakkyawar tarba suka samu daga iyalan mutumin harda shi aka saukesu a part guda cikin ƙaton kuma haɗaɗɗan gidan nashi anata so a ɗauki su twins sunƙi yarda, lafiyayyun abinci da abubuwan sha aka kawo masu bayan sun ci suka huta har lokacin sallar Juma'a yayi Haisam suka tafi Masallaci tare da Senator Buba da yaran shi maza, bayan sun dawo ne ya sanar mashi zasu tafi can garin su Fatuu yace ai yayi zaton zasu kwana su ƙara hutawa ya tambayi zasu kwana acan ne Haisam ɗin yace mashi ita zai baro ta can ta kwana biyu shi zai dawo nan yace tunda hakane yana ganin kaman yanzu lokaci ya ƙure kar suyi dare ya bari gobe tunda safe sai Driver ya kaisu yadda shima zasu gaisa sosae Haisam ɗin ya amince da hakan. Washegarin wuraren ƙarfe tara da yan mintuna sukai sallama da mutanen gidan suka tafi, tafiyar Awa guda sukai suka iso tun shigowarsu bakin garin Fatuu ta fara murmushin farinciki sosae tayi kewar garin don kusan fin shekara ukku rabonta dashi da yake yanayin damuna ya fara don wasu wuraren sun fara samun ruwa ciki harda nan garin hakan yasa ganyayyaki da tsirrai sun yi kore shar shar gwanin sha'awa ga makiyaya nata koro garken shanaye da tumakai za'a tafi kiwo, Haisam dake zaune seat ɗin gaba nata kallon garin bayan sun shigo Fatuu ce ke nuna ma Driver hanya yana bi har suka ƙaraso kopar gidan tace mashi nan ne, wasu dattawan mutane da a ƙalla zasu kai biyar na zaune a ƙarƙashin ƙatuwar bishiyar dake a ƙopar gidan wasu daga cikin su yan gidan ne ciki harda Mahaifin Fatuu daya zauna yana dakon zuwan su da yake da zasu baro Yola ta kirashi ta sanar mashi sai mutum biyu a cikin su duk yayyen shi ne sauran biyun kuma abokai ne, daga can gefen su yara ne ba masu yawa ba suna ta wasa, bayan ya parker suka buɗe ƙofofin Motar suna fitowa Mutanen dake zaune suka miƙe a kusan tare suka nufo su, cikin washe baki suka shiga yi masu sannu da zuwa Baffan su Fatuu dai murmushi yake idon Fatun na akan shi itama tana murmushin farincikin ganin shi, bayan sun gama gaisawa da Haisam itama ta gaishe su suna ta fara'a suka amsa mata duk wanda yay yunƙurin ɗaukar su twins sai su ƙanƙame jikin iyayen nasu da yake kowa na ɗauke da guda ɗaya, bayan an gama yi masu sannu da zuwa Baffan tare da yayun nashi sukai ma Haisam jagora zuwa ciki, suna shiga cikin soro su Aysha suka shigo da gudu suka nufi Fatuu suka ƙanƙameta cike da farinciki suke mata sannu da zuwa da fullanci Adam dake hannunta ya fara ta6e baki zai yi kuka don sun rungumeta Aysha ta ɗago tana miƙa mashi hannu ya ƙiya sai kallonta yake kaman mai son tuna ta don da bakin su Mino ya yarda da ita Fatuu ta rinƙa faɗi mashi kowacece da fulatanci sai gashi ya tuno ta ya miƙa mata hannu cikin washe bakin jin daɗi ta ɗauke shi, ganin an amshi Adam yasa tace ma Haisam yabata Abie kafin suka idasa shiga cikin gidan mutane duk an leƙo ana masu sannu da zuwa Fatuu ke amsawa shi kuma Haisam kai yake ta jinjina masu fuskarshi a sake....... 100 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ .........Bangaren da Arɗo yake aka kaisu can gefe da inda nasu Yaya yake an kewaye wurin da yar gajeruwar kanta daga cikin wurin harda siminti a ƙasa, shiga sukai cikin ɗakin wanda yana da ɗan matsakaicin girma akwae madaidaicin gado na katako yana da wardrobe mai gida biyu samantaa an ɗaura wasu tsofaffin akwatuna na fata dana ƙarfe akwae yan durowoyi na gadon sai wata yar kanta da aka ɗaura al'quranai da wasu littafan addini daga jikin bango kuma wanda ke shafe da siminti an rataye abubuwan fulani harda takubba a cikin gidajen su daga saman ɗakin anyi ceiling irin na da da ake yi da itatuwa ƙasan ɗakin kuma gaba ɗaya a rufe yake da ledar tsakar ɗaki harda ɗan madaidaicin carpet daga tsakiya wannan duk aikin Baffan su Fatuu ne don kullum cikin yi ma mahaifin nasu hidima yake dama kuma yafi duk yan uwan shi wayewa, lokacin da suka shiga Arɗon na kwance a saman gadon jikin shi sanye da riga da wando na yadi mara nauyi sai hula ha6ar kada a saman kan shi suna shiga ya fara ƙoƙarin tashi zaune bayan Baffan su Fatuu ya sanar mashi ga su Inna wuro da maigidan nata sun iso da yake yasan da Maganar zuwan nasu duba jikin shi, saida aka taimaka mashi sannan ya zauna Haisam na niyyar zama a saman carpet da sauri cikin muryarshi data disashe yace kar ya zauna nan Haisam ɗin bai ma ji abunda yace ba ya dai gane ta hanyar hannu daya ɗaga mashi hakan yasa ya dakata Arɗon ya kalli Baffan su Fatuu da fullanci yace ya ɗaukko masu darɗuman makkan shi a cikin kayan shi, Makkan da ya shekara kusan fin talatin da zuwa wasu Ƴaƴan shi ma basu san da yaje ba balle kuma su Fatuu jikoki, bayan ya ɗaukko dardumar wadda ba laifi bata ji jiki ba saboda ji yake da ita don ta shiga cikin tarihin zuwa makkan shi tana da girma, shimfiɗa masu yay a saman carpet suka ce ma Haisam ya zauna Fatuu ma ta zauna daga gefe suma Yayun Baffan dashi duk suka zauna daga gefe nan aka shiga ƙara gaisawa ya juya suka gaisa da Arɗo tare da yi mashi ya jiki a hankali yake amsawa Fatuu ma ta gaishe shi da fullanci tayi mashi ya jiki ya amsa yayi mata sunzo lafiya da tambayar ya suka baro sauran mutane duk ta amsa masu ya kalli su twins yace wannan sune Ƴaƴan nashi da bai sani ba tana murmushi tace eh ya miƙo hannu alamar a bashi su Babban ɗanshi wanda yana cikin wanda suka shigo shima ya manyanta sosae yana murmushi yace ai basu yarda da mutane duk da haka Fatuu ta miƙe da Abie tayi ma Aysha dake daga can bakin ƙopa alamar ta kawo Adam suka kai mashi su, kamar ma tsoron Arɗon suke duk sun waro fararen idanunsu tubarkallah suna bin shi da wani irin kallo daya miƙo masu hannu sai su ƙanƙame su Fatun ƙarshe saidai a hannun nasu ya gansu ya saka masu albarka harda tofin Addu'a yayi masu yace ma Fatuu kafin su koma zai bada magungunan kariya a rinƙa basu tace to, a nutse Haisam cikin cool voice ɗin shi ya tambayi an kai shi Asibiti ne don asan abunda ke damunshi Modibbo ya bashi amsa da sun kai shi Babbar Asibiti ta Jumeta anyi mashi gwaje gwaje an tabbatar ba abunda ke damunshi kawai shekarune to sun bada wasu magunguna sannan sun ce ya rinƙa samun hutu sosae to ya gama shan magungunan kuma yana samun isashshen hutun don ko zama a fadar shi ma bai yi yanzu shiyasa ma jikin nashi da sauƙi sosae, kai Haisam ya jinjina kafin yace yana ganin yakamata a kai shi Asibitin ƙwararru dake a Yola a ƙara mashi bincike sosae suka ce to shidai Baffan su Fatuu shiru yay saidai a ranshi yaji daɗin hakan da Haisam yace don ba yarda baiyi ba a kaishi can amman yayun nashi suka ce kawai 6arnar kuɗi ne tunda an tabbatar da lafiyar shi lau, nuna ma Fatuu wata yar ƙwarya dake a rufe da faifai Arɗo yay yace mata ga fura nan taba Haisam da sauri Baffanta yace mashi ya barta tashi ce yasha suma ga ta can an haɗa masu yanzu zasu je sai su sha ya ɗaga kai Modibbo yace yakamata suje an barsu ko ruwa ba'a basu ba Baffan yace to tare da miƙewa suka ce ma Haisam suje suci Abinci duk suka miƙe harda Fatuu, Bayan sun fito bangaren su Fatuu suka nufa lokacin da suka isa Fatuu taji daɗin ganin yadda aka ƙara gyara wurin kai kace ba'a cikin gidan bane sai ma da suka shiga cikin parlor shima an ƙara gyarashi akan lokacin da tazo da za'a yi mata aure da Khalid, an sake mashi fenti na zamani haka kujerun ciki ma ba wanda ta sani bane an canza wasu manya abunda yafi burgeta shine yadda ƙasan falon aka sanya tiles daga tsakiya kuma an sa carpet haka jikin ƙopopi ma labulaye masu kyau ne harda abun maƙalesu a jikin bango ga kayan kallo harda freezer yanzu duk babu kwalliyar ƙorai da aka yi an kunna Generator fanka nata yi parlon tsaf yayi irin na yan birni, cike da farinciki Yadikko datai shiga mai kyau tana sanye da riga da zane na lace ta tarbe su tana masu maraba Fatuu ta nufeta ta ɗan rungumeta tana dariyar farincikin ganinta ta miƙo ma Abie hannu zata daukeshi yaƙi yarda Aysha ta miƙa mata Adam tana faɗin ga mai yardar nan sai gashi itama ya yarda ta ɗauke shi, bayan duk an zauna aka shiga gaisawa tare da yi masu an zo lafiya fuskar Haisam a sake yake amsawa yayi mata ya mai jiki bayan ta amsa ta tambayi mutanen gidansu duk yace mata Alhamdulillah suna gaishe su, basu daɗe da zama ba aka fara zuwa gaishe da Haisam tare da yi masu sannu da zuwa tun yana amsawa har ya koma yana ɗaga kai don sai zuwa suke Manya da yara ba alamar zasu ƙare saida Baffa yayi magana kan a bari su ci Abinci sai a zo a gaisa sosae sannan aka tsagaita da zuwa, kwanonin Abinci da ƙurai aka shiga kawo ma baƙi duk aka jere su anan tsakiyar Parlon Yadikko ta kawo masu ruwa da lemu masu sanyi da kofunan glass duk ta zuzzuba masu ta basu ta juya ta nufi cikin ƙuryar ɗaki bada jimawa ba ta dawo ruƙe da babban tray mai ɗauke da plates da cokulla da serving spoon sai Warmers guda biyu Aysha ma na biye da ita da wasu kulolin abincin Masu kyau babba da ƙarama suka aje a saman carpet bayan Yadikko ta miƙe tay ma Fatuu alamar tazo ta nufi ƙurya Fatun tabi bayanta, bayan sun shiga tace mata yanzu ya za'ai Haisam ya saba cin abinci a saman table gashi babu wai ko a ɗauki drawer ɗin gado sai a ɗaura mashi sama Maganar dariya taba Fatuu tace mata ai lafiya lou yana ci a ƙasa Yadikkon ma dariyar take tace yauwa to shikenan, "Baki tambayi Mino ba" Fatuu ta faɗa tana murmushi, ɗan yarfa hannu Yadikko tayi tace tana son ta tambaya wai kada aga tayi rashin kunya ta tambayi tana lafiya ita da mijin nata Fatuu tace eh sunyi waya ta gaya mata zasu zo harda cewa wai don Allah a taho da ita tace waye zai yi wannan haukan duka sati guda da yin aure ta marairaice mata kaman zata yi kuka tace ai ko kukan jini zata yi bazasu zo da ita ba, Yadikko dake dariya tace ai lalle kam kafin da sauri tace taje ta zuba ma Haisam Abincin tace to ta juya ta fita, miƙewa Baffansu yay yace ma Aysha taje tace ma Yadikko ta zubo ma wanda ya kawo su abinci sai ta kawo mashi waje tace to yace ma Haisam bari ya barsu suci Abinci Fatuu ta kalleshi tana mashi murmushi shima shine akan fuskarshi ya juya ya fita, a saman carpet suka zauna Fatuu tay serving nasu abincin wanda shinkafa da miya ne sai kuma burabusko sai gasassun zabbi cikin miyar abincin an cacca6a nama sai uban ƙamshi ke tashi, ba laifi Haisam yaci abincin sosae ba kamar burabuskon yayi mashi daɗi harda ce ma Fatuu bata ta6a yi masu irin shi ba tay yar dariya tace tunda yayi santi daga yanzu zata rinƙa yi yay murmushi ba tare daya ce komai ba su twins ma da alama yayi masu daɗi sai cin shi suke Aysha na daga gefe tana ba Adam ita kuma Fatuu tana ba Abie, bayan sun gama Aysha da Fatuu suka kwashe kayan suka kai Kitchen bayan sun dawo cikin parlon Yadikko ta fito masu da Fura a cikin jug dama ita take haɗawa a cikin ɗaki da kanta ta zuba ma Haisam yana ɗan murmushi yace mata ya ƙoshi yaci abinci sosae tace ya zai zo ruga bai sha fura ba yace to a bari kafin ya tafi zai sha jin haka yasa da sauri tace wai badai yau zasu koma ba cikin cool voice ɗin shi yace a'a shine zai koma Yola ita tana nan sai gobe zai dawo su tafi tace yauwa to Aysha ma ta washe bakin murna, miƙa ma Fatuu furar data zuba tayi tace ita to tasha ta amsa Aysha tace a zubo wata taba Adam, sosae Furar tayi daɗi don harda zuma aka sa ga dawon sabo ne haka nonon ma Fresh ne Fatuu nasha tana ba Abie duk ya 6ata saman bakin shi da ita harda su tanɗe baki yana yin ɗan sauti sai dariya yake basu cike da tsokana Yadikko ta kai hannu tace a bata furarta tunda bai yarda da mutane amman ya iya shanye masu abu yana ganin Fatuu ta miƙa mata cup ɗin ya fara ta6e baki zai saka kuka da sauri Yadikko ta maido mata tana dariya tace sak irin yadda take kuka da ƙuruciyarta haka suma suke yi Fatun tay murmushi ta ɗan saci kallon Haisam suka haɗa ido ya ɗan yi murmushin gefe tare da juyar da idon shi, Fatuu ce ta tambayi Yadikko ba'a samun wuta ne taga sai generator aka kunna tace wutar lantarkin ce ke yawan samun matsala daga can titi da aka jawo ta in ta lalace sai su daɗe babu ance wai ko zata daidaita sai ansa transformer anyi babban aiki ta jinjina mata kai, Baffan su Fatuu ne ya dawo yace ma Haisam ya fito yayi alwala lokacin salla ya ƙarato yace to tare da miƙewa ya kaishi ɗakin shi da shima yake tsab ga toilet a ciki ya nuna mashi yace akwae ruwa aciki zai jirashi a ƙopar ɗaki, a ƙopar gidan inda aka saba yin salla sukayi bayan angama akai ta gaisawa da Haisam ana ma mutane bayanin ko wanene daga baya suka dawo cikin gidan tare da Baffa lokacin Yaya da Mero da sauran manyan mata iyaye suka shigo gaisawa dashi Yaya nata washe baki tace ai sun bari su huta ne su twins dai sai dae a kalle su, wuraren ƙarfe ukku Haisam yace ma Fatuu yana son suje gidan Alhaji Lawal su gaisa dashi sai a maidota shi kuma ya wuce tace to, shiryawa tayi ta canza kaya su twins ma ta canza masu sannan suka tafi harda Aysha ta riƙe Adam. Lokacin da suka je Alhaji lawal ɗin na nan da yake Weekend ne sosae suka nuna farincikin ganinsu a falon Alhaji lawal aka saukesu Hajiya Rabi'atu na murmushi tace wannan zuwan bazata haka ba'a sani ba balle a shirya tarbarsu sosae suna murmushi suka ce mata ai ba komai, ruwa da lemu da Abinci aka kawo masu duk suka ce a ƙoshe suke Alhaji Lawal yace bai yarda ba ya za'ai suzo gidan shi suƙi cin abinci ƙarshe saida suka ci kaɗan, koda Alhaji Lawal yaji zancen tafiyar Haisam Yola sai yace ya bari mana su kwana gaba ɗaya anan gidan sai shi driver daya kawo su ya koma tunda nan akwae driver koda zasu buƙaci fita, da yake Haisam ɗin bai cika son kwana ba tare da Babynshi ba sai dole gashi kuma sun nuna suna son ya kwana bazai iya gardama masu ba sai ya amince da hakan, bayan anyi sallar La'asar Alhaji lawal yace ko zasu zagaya suga gari driver ya kai su Haisam ɗin yace ba sai Driver ya kaisu ba bari yay driving ɗin da kan shi, cike da zolaya Alhajin yace kada fa ya 6ace a garinsu Senator ya turo masu bataliyar sojoji Haisam ɗin yay dariya yace bazai bace ba tunda yana tare da yar gari, tare da Fatuu da Aysha suka fito Haisam ne ke tuƙa Motar suka shiga cikin garin Jumeta, bayan sun zagaya garin can da Yamma suka nufi ruga, lokacin da suka shiga garin makiyaya mata da maza cikin shiga ta fulani nata dawowa daga kiwo suna sanye da kayan fulani dabbobi ko ta ina suna ta 6ullowa, juyawa Haisam yay ya kalli Fatuu da turanci ya tambayeta itama tayi irin haka tay dariya tace ita fa yar lelen Baffanta ce duk irin wannan abun bai bari tana yi ko tallar Nono da yan matan gidansu ke yi lokacin ita bata taba yi ba, murmushi yay idon shi akan hanya yace ai ko don kada ta jawo mashi rigima ya hana tayi Fatun ta kyalkyace da dariya, ta bayan gidan su tasa su bi tace zata nuna mashi ƙoramar dake wurin, bayan sun je wurin parker Motar yay duk suka fito suka shiga zagaya wurin ruwa nata gudana ga wani irin ni'imtaccen sanyi ga bishiyun kayan itatuwa da sukai ma wurin ƙawanya duk sun nuna gasu ƙasa ƙasa Fatuu tace bari ta tsinko masu Haisam ɗin ya hana tasa Aysha ta tsinko masu itama yace ta bari kada wani abu ya cije ta tana dariya tace mashi ai suna zuwa ba abunda ke samun su sannan ya bari, basu daɗe a wurin ba harda hotuna yay masu suka tafi saboda yamma tayi sosae, wata hanya Fatuu ta nuna mashi tace su bi nan zasu 6ullo ta ɗayan gefen gidan, suna zuwa wani wuri jikin gidan nasu da sauri ta ɗaga hannu tana nuna mashi wurin tace ya ganshi ya ɗaga mata kai tace to a daidai nan ne ta ta6a yin shuka har ta jefe ma Jibo Akuya har baisan lokacin da yay dariya ba har haƙoranshi suka bayyana don ta tuna mashi ranar data bashi labarin Akuyar itama dariyar take Aysha dai bata san akan mi suke magana ba, lokacin da suka iso gidan ƙopar gidan cike yake da mutane wurin sai kace yar yara, bayan ya parker Motar suka fito cikin mutanen da ke zaune a ƙopar gidan harda Baffa da yau yaƙi zuwa ko ina saboda zuwan su suka taso suka tarbesu Fatuu da Aysha suka wuce ciki shi kuma a nan ya nuna zai tsaya shima aka bashi wurin zama bayan sun shiga ne Fatuu ke faɗi ma Yadikko zancen kwanan da zasu yi a gidan Alhaji Lawal, anan sukai isha suka ci Abinci harda wata sabuwar Fura aka dama masu mai sanyi sai gashi duk sun fi shan furar ma akan Abincin shima Haisam sosai tayi mashi daɗi su twins kau ba'a Magana hannu bibbiyu suka ruƙe cup suna sha duk sun ƙara yi ma bakin su dama dama sai tanɗan baki suke ana dariya sai gashi suma an sasu yin dariyar Yadikko har tana ce ma Fatuu kodai bata basu Fura ne tace mata eh gaskiya don lokacin da suka fara cin abinci basu ƙasar sai da suka zo bikin nan kuma lokacin da aka sha Furar a gidan Gwaggo basu gidan Yaddikon tace to gaskiya a rinƙa basu tunda dai sun gani da idon su suna so, kallon Haisam Fatuu tay ta tambaye shi a US ana samun Furar kuwa ya bata amsa da baza'a rasa ba tunda ana samun abubuwan mu na nan sosae saboda akwae mutanen mu acan shima Furar ba'a rasa masu yin shi suna saidawa in suka koma zai bincika Yadikko tace yauwa gaskiya asamo ma angwayenta Fura harda cewa don ma nesa bata maganin kusa ai da ta rinƙa yin Furar tana aika masu can don tasan koda an samu sai tata tafi daɗi duk sukai yar dariya, wurin ƙarfe takwas da rabi suka fito zasu tafi gidan Alhaji Lawal Fatuu ta ɗaukko jakar kayanta sukai sallama dasu kan sai gobe, har bakin Mota Baffan su Fatuu ya rako su har yana ce ma Haisam zai gane hanya cikin daren nan ko ya rakasu sai ya dawo yana murmushi yace mashi lafiya lou zai gane yayi mashi godiya sukai sallama, suna kan hanya ne Fatuu ke tambayar shi yanzu ya za'ai baida kayan baccin da zai saka tunda kayan shi na Yola yana murmushi yace mata sai ta bashi cikin nata yasa ta kyalkkyace da dariya tana faɗin in yana so sai ta bashi in dai zasu shigeshi, tun akan hanya su twins sukai bacci Fatuu na dariya tace Fura tayi aiki yay murmushi, bayan sun iso a harabar gidan suka iske Alhaji Lawal ɗin zaune kan kujera hannun shi ruƙe da Jarida yana ganin su ya taso ya nufo Motar bayan duk sun fito yana murmushi yay masu sannunsu da dawowa yace ai zaman dakon jiransu yake don da basu dawo ba yanzu bin sahun su zai duk sukai dariya tare da gaishe shi, tare suka shiga cikin gidan Hajiya Rabi'atu ta tarbesu, a part ɗin baƙi aka saukesu yana da parlor da kuma Bedroom an gyara masu shi tsaf sai ƙamshi da sanyin Ac ke tashi Hajiya Rabi'atu ta nuna masu kayan abinci da aka jere kan dining table tace gashi nan sai suci in sun huta harda tambayar ko a turo wadda zatai Serving nasu Fatuu tace a'a lafiya lou zatayi, duk da ba wata yunwa suke ji ba saida suka ci lafiyayyun abincin da aka yi masu saboda ɗazun da suka zo basu wani ci sosae ba, suna cikin cin Abincin Alhaji Lawal ya shigo cikin parlon hannunshi ruƙe da wata babbar farar jakar siyayya ya nufi kan kujera ya aje daga nan inda yake yace ma Haisam gashi nan yayi amfani dasu yace to tare da yi mashi godiya, bayan sun gama cin Abincin ya duba kayan ciki wanda kayan bacci ne kala biyu na maza sai kuma ɗinkakkun shaddoji suma kala biyu farare da brown kamar Alhajin yasan irin dinkin da yake so don gaba ɗaya kayan irin ɗinkin ne sai wasu yan ƙananun kwalaye guda biyu nan kuma agoguna da links ne a ciki harda biro akwae kuma kwalayen turarurruka guda biyu gaba ɗaya kayan sunyi kyau da ganin ba ƙananun kaya bane, bayan sun gama duba kayan ya kalli Fatuu cikin cool voice ɗinshi yace ba rabon yasa kayan baccinta kenan ta faɗa jikinshi tana dariya ya haɗa da ita da ledar ya sunkuceta suka nufi Bedroom. Washe gari misalin ƙarfe goma saura gaba ɗayan su sunyi wanka suna parlon Alhaji Lawal suna yin Breakfast tare Fatun na ruƙe da Abie Hajiya kuma na ruƙe da Adam ta samu yanzu ya yarda da ita dama shi in dai zaku wuni tare to zai fara yarda da kai, baka jin komai sai ƙarar cokulla sunyi nisa a cikin cin Abincin suka ji anyi sallama cikin parlon a kusan tare duk suka kalli entrance, wani irin bugu gaban Fatuu yay da tayi arba da wanda ya shigo ba kowa bane face Khalid yana sanye da ƙananun kaya idanunshi na sanye cikin farin glass irin nasu na likitoci har yanzu dai yana nan yadda yake bai yi ƙiba ba, da sauri ta kauda idonta daga barin kallonshi ya nufo dining area ɗin yana ta sakin ƙamshi, bayan ya ƙaraso a gefe ya tsaya kusa da Dad ɗinshi ya gaishe da shi ya amsa tare da ce mashi yazo lafiya da tambayar iyali duk ya amsa mashi kafin ya kai idon shi kan Hajiya yana ɗan murmushi ya furta "Mom, Good Morning" itama murmushin take ta amsa mashi tare da tambayar Matar shi da kuma ɗiyar shi Zarah ya amsa mata da suna lafiya suna gaishe ta, tace maimakon ya taho masu da Zarah still murmushi yake yace lokacin da zai taho bata tashi ba ta jinjina kai, a cikin ran Fatuu ta shiga maimaita sunan ɗiyar shi da aka faɗa tana kokonton dalilin saka sunan, Alhaji ne ya nuna mashi Haisam da idon shi na kan Abincin gabanshi kamar bai ma ji shigowar Khalid ɗin ba yace mashi "ga baƙon mu mijin ɗiyata Fateema" kai ya jinjina Alhaji ya kalli Haisam yace mashi ga babban ɗan shi Khalid su gaisa sai lokacin ya ɗago fuskar shi a sake kafin yace wani abu Khalid ya miƙa mashi hannu ya aje cokalin hannunshi shima ya bashi nashi suka gaisa yayi mashi anzo lafiya Haisam ya amsa mashi da lafiya lou, bayan sun gama gaisawar maida idon shi yay kan Fatuu da taki ɗago kai ta kalle shi ya furta "Fateema an zo lafiya" damm gabanta ya faɗi ta haɗiyi abu saida tay ƙoƙarin daidaita natsuwarta sannan ta ɗago tana yin ɗan ƙaƙalallen murmushi ta gaishe dashi da ƙyar ya amsa don saida gabanshi ya faɗi ganin yadda ta koma saidai bai bari an fahimci wani abu ba, tana gaishe dashi da sauri ta janye idonta daga kanshi, kallon Abie dake hannunta yay yace "Wannan yaran mu ne?" kafin ta bashi amsa Mom ɗin shi ta riga ce mashi eh twins ne ta nuna mashi Adam dake hannunta ya jinjina kai tare da kai hannu zai amshi Adam da yake Mom ɗin na kusa dashi Adam ɗin ya ƙanƙameta alamar bazai je ba Mom tace mashi suna yin ƙyuya ne sai sun saba da mutum suke yarda ya ɗaukeshi yana murmushi ya furta Ok, Dad ɗinshi ne ya nuna mashi seat da ba kowa yace yay joining nasu yasan ƙilan bai yi Breakfast ba tunda da wuri ya taho, gaba ɗaya Fatuu ta takura zaman Khalid a wurin da ƙyar take cin Abincin can ta saci kallon Haisam taga idon shi na kan Abincin gabanshi tana son ta gane yanayin fuskar shi amman ta kasa, Khalid bai daɗe da zama ba Haisam ya miƙe duk suka kalle shi Alhaji yace badai har ya ƙoshi ba yana murmushi yace mashi eh yace to amman ai kamar bai ci sosae ba still da yanayin murmushi ya bashi amsa da yaci da yawa Alhajin yace shikenan ya manta ma Yan gayu basu cin Abinci sosae Haisam ɗin yay yar dariya haka ma Hajiya Rabi'atu Khalid kuma murmushi yayi Fatuu kam bata ma ɗago ba balle aga yanayin fuskar ta, bayan tashin Haisam wurin duk sai taji ta ƙara takura sau biyu tana satar kallon Khalid taga ita yake kallo abunda bata sani ba dana sani kawai yake acikin ranshi don ganinta ya fama mashi babban tabon sonta dake cikin zuciyarshi sai kallon su twins yake yana raya ƙilan da yanzu su yaranshi ne, gaba ɗaya Abincin ya fice ma Fatuu arai haka shima Khalid ɗin ba don yana jin daɗin shi ba yake ci, Haisam bai daɗe ba da tashi itama ta miƙe Dad yace wato Romeo ya ƙoshi shine itama Juliet zata tashi Fatun tay yar dariya kafin tace ta ƙoshi ne, cikin parlon ta nufa inda Haisam ke zaune yana latsa waya, Bayan sun gama cin Abincin gaba ɗaya a falon aka zauna ana hira jefi jefi Haisam ke saka baki anan ma Fatuu ta lura da yadda Khalid ke fakaitar idanun mutane yana kallonta cikin sa'a bayan ɗan wani lokaci Abie yay bacci ta miƙe tace zata je ta kwantar dashi, bata daɗe da tafiya ba shima Adam yayi baccin Hajiya ta bita dashi ya rage saura Alhaji da Khalid sai Haisam suka cigaba da yin hira wadda yawanci akan aikin su ne suna cikin haka Haisam ya roƙi Khalid kan yana son ya shige ma su Baffan Fatuu gaba zasu kai Arɗo Asibitin da yake aiki a duba shi sosae yace mashi ba matsala, suna zaunen har lokacin sallar Azahar yayi Dad yace suje suyi kafin su tafi Haisam ya kira Fatuu a waya yace ta shirya da sun dawo daga salla zasu je can ruga suyi bankwana dasu sai su koma Yola ƙarfe biyar jirginsu zai tashi zuwa Abuja tace to, suna dawowa sallar ya sanar ma Dad zancen zuwa rugar yace Ok amman zasu dawo ta nan ko sai Driver ya kai su Yola ɗin Khalid na jin haka yace bari suje rugar tare sai ya duba jikin arɗon in sun dawo sai su wuce Yolar tunda shima komawa zaiyi Alhaji yace yauwa to hakan yayi, Part ɗin da aka sauke su Haisam ya wuce don ya shirya lokacin daya je Fatuu har ta gama shiryawa cikin doguwar rigar shadda ta saka sarƙa da yankunnan Diamond su twins ma ta saka masu ƙananun kaya iri ɗaya, yana shigowa ta nufeshi tana murmushi ya buɗe mata hannu yay hugging nata can ƙasan maƙoshi ya furta mata "I luv you with every single beat of My Heart Baby" lumshe ido tayi jin yadda hucin Maganar ya bugi kunnanta, shiru yay yana breathing a hankali can ta ɗago da fuskarta ta kalle shi sai taga kaman wani yanayi da bata sani ba akan fuskar shi, tambayar shi tayi ko da wani abu a hankali ya lumshe ido tare da ɗan girgiza mata kai daga haka yay pecking goshinta ya saketa yace bari yay wanka, juyawa yay ya nufi hanyar toilet tabi bayan shi da kallo can ta ɗan ɗaga murya tace "....Know dat am breathing because of you Hubby" dakatawa yay ya juyo yay mata murmushi itama shi tayi mashi kafin ya juya, zama tayi a bakin gado tay shiru kamar mai nazarin wani abu, bai daɗe ba ya fito sanin tafiya zasu yi ita ta taimaka mashi ya shirya yasa brown shaddar cikin wanda Alhaji ya kawo mashi sosae ta hau jikinshi ita ta ɗaura mashi agogo ta saka mashi links ta feshe shi da turare yanata mata murmushi, bayan sun gama shiryawa sun tattara komai suka fito kowa na ɗauke da yaro guda abun gwanin sha'awa, koda su Alhaji da Hajiya suka gansu saida suka yi santin kyaun da sukai Khalid dai murmushin karfin hali kawai yake shi kaɗai yasan mike faruwa a cikin zuciyarshi, har bakin Mota su Alhaji suka rako su sukai masu sai sun dawo, tunda suka hawo hanya Fatuu bata bari ta kalli saitin Khalid ba shi ke driving ɗin Haisam na a kujerar gefe ita kuma tana baya saitin kujerar Haisam, bai wuce sau ɗaya zuwa biyu ba sukai magana shida Haisam har suka iso, a tare gaba ɗaya suka je ɗakin Arɗon bayan sun gaishe shi Khalid ɗin ya shiga dadduba shi tare da yi mashi tambayoyi da fulatanci yana bashi amsa bayan ya gama ya faɗi ma su Baffan su Fatuu ranar da zasu kai shi asibitin suka ce to nan Haisam yayi mashi sallama da fatan Allah ya bashi lafiya ya amsa yana ta mashi godiya da saka mashi Albarka, wani ƙumshin leda yasa Baffa ya ɗaukko mashi yaba Fatuu yace ga magungunan nan ya faɗi mata yadda zata masu da yadda zata rinƙa ba su twins har itama yace tasha da Haisam sukai mashi godiya, bayan sun fito ƙopar gida Khalid ya koma su kuma suka nufi bangaren su Yadikko sai faman leƙowa ake ana kallon su, a parlor aka zazzauna suka shiga gaisawa bayan ɗan lokaci Haisam yayi ma Yadikko sallama tanata mashi godiya da saka albarka ya kai hannu aljihun rigarshi ya fiddo kuɗi masu yawa ya miƙa ma Baffa yace gashi a raba ma mutanen gidan sannan ya tambayi Account ɗin shi yace zai tura kuɗin da za'ai ma Arɗo amfani a Asibitin Baffan nata roƙonshi kan ya barshi za'a kai shi yana murmushi yace ba wani abu yayi niyya ne, kuɗi masu yawan gaske ya tura har saida Baffa ya jinjina kuɗin yace hidiman tayi yawa shidai ba komai kawae yake cewa, Godiya sosae sukai mashi ya miƙe yace ma Fatuu in ta gama yana waje Baffan ma ya miƙe suka fita tare, bayan fitar shi ne Yadikko ke mata tsegumin Khalid don taji dashi suka zo Fatuu ta faɗi mata yadda akai suka taho tare tace kuma Haisam bai nuna komai ba tace mata a'a, itama Fatun saida taba Yadikko kuɗi harda Baffanta ta bada ta bashi dasu Aysha sukaita Godiya ta ɗaukko mata wasu magunguna da zasu inganta lafiyar ta data cikin jikinta da kuma wanda zata samu sauƙin haihuwa ta faɗi mata yadda zatayi amfani dasu, tare da Yadikko suka zazzagaya yi ma sauran mutane sallama nan fa aka shiga ba su twins kyautar abubuwa su kaji, zabbi harda akuyoyi cikin wanda suka basu akoyoyi harda Yaya, duk Yadikko ta amsa tace zata kiwata masu kafin daga baya a aika masu tunda ba'a Mota zasu koma ba, bangaren su Yadikkon ƙwai masu yawa suka basu da uban dawon fura da Nono harda zuma mai yawa da man shanu duk akai masu dubara yadda ƙwan bazasu fashe ba haka Nonon ma harda ƙanƙara aka saka mashi yadda zai tsaya da sanyin shi gaba ɗaya cikin wata jaka aka saka su a haka ma kayan sunyi ma Yadikko kaɗan tace inda da Mota suka zo sai an cika boot ɗinta da fura da Nono saboda su twins Fatuu nata dariya tace a haka ma ai da yawa, kusan gaba ɗaya gidan aka fito rakiyar su waje anata masu Allah ya tsare hanya, bayan sun baro rugar gidan su Khalid suka koma anan suka ci abincin rana kafin sukai masu sallama Hajiya Rabi'atu taba Fatuu kyautar atampopi masu kyau guda biyu da lace harda humra masu ƙamshi da turarurrukan wuta su twins ma ta basu kaya sosae tayi mata godiya harda Haisam, har bakin Mota suka rako su lokacin da suka baro gidan ƙarfe ukku na rana zuwa karfe huɗu da wasu mintuna suka iso Yola, har gidan Senator Buba Khalid ya kai su da har yace bari ya jira su sai ya kai su Airport Haisam yace mashi ya bashshi kawai kar su 6ata mashi lokaci akwae Driver da zai kai su yayi mashi godiya kafin ya amshi lambar shi yace zai kira yaji yadda ake ciki dangane da jikin Arɗo Khalid ɗin yace Ok, harda kuɗi yaba su twins Fatuu tace ya barshi yana murmushi yace ai ba ita yaba ba yaranshi yaba ta amsa tayi mashi godiya tare da cewa ya gaishe da iyali yace zasu ji daga haka ya tafi, da suka shiga cikin gidan basu daɗe ba salla kawai sukai koda aka basu abinci cewa sukai a ƙoshe suke sukai masu sallama nan ma saida aka ba Fatuu da twins kaya Senator Buba ma ya basu kyautar kuɗi masu yawa zumunci mai daɗi, a wata jibgegiyar Jeep aka tafi kai su Airport harda Senator Buba yay masu rakiya, suna akan hanyar ne Fatuu taji ƙarar shigowar saƙo a wayarta, lokacin data duba saƙon har saida gabanta yay bugu da ƙarfi don ta gane Khalid ne ya turo duk da bata da lambarshi amman daga yanayin saƙon ta gane nashi ne, da turanci ya rubuto mata yana mai bata haƙuri da kuma neman yafiyarta akan abunda ya faru a tsakaninsu a baya yayi nadama da kuma danasanin da yasan har ya mutu bazai daina yi ba sai dai ta wani bangaren yayi farincikin shigowarta rayuwarshi don ta dalilinta Allah yasa ya daina duk wani abu mara kyau a ƙarshe yana son ta sani ta zamo wani bangare na rayuwarshi wanda hakan ne ma yasa shi saka ma ɗiyarshi sunanta, tana gama karantawa ta ɗan saci kallon Haisam dake gefenta taga idon shi na a gaba suna yar hira da Senator Buba dake a seat ɗin gaba, kamar ta share Khalid ɗin ba sai ta mayar mashi da amsa ba sai kuma wata zuciyar ta raya mata yana iya cewa zai ƙara turo mata wani saƙon saboda rashin jin amsarta hakan yasa ta maida mashi da amsa, itama da turanci tace komai ya rigada ya wuce don har tama manta kuma tun bayan da aka fasa aurensu ta yafe mashi don haka tana fatan shima ya manta sannan ta gode da karar da yayi mata ya gaida mata da Zarah da Mamanta, tana tura saƙon ta goge duka nashi daya turo mata da nata data tura mashi sannan tayi blocking ɗin lambar tashi yadda bazai iya sake turo mata saƙo ba ko ya kirata tay shiru zuciyarta ta shiga tariyo mata da abubuwan da suka faru tsakaninsu yadda ya rinƙa yi mata a cikin Mota da gidan gonarsu da ya kaita, idanunta ne suka fara tara ƙwalla da sauri ta fara ƙoƙarin mayar dasu tare da kawar da tunanin daga ranta. Bayan sun dawo Abuja Washe gari Fatuu taje gidan Mino kai mata tsaraba Haisam ne ya kawota su twins a gida ta barsu, taji daɗin ganin yadda Mino ta saki jiki suna ta shan amarci da Nameer ta sha kananun kaya riga da wando, bayan data je ne Nameer ɗin ya fita, sosae Mino taji daɗin tsarabar data kai mata tace itama bada daɗewa ba zata je Yola Fatuu ta ɗan harareta tace ba yanzu ba sai ta shekara Minon ta noƙe kai tace "kai Adda Fatuu shekara yayi yawa ni dai gaskiya nan bada daɗewa ba zanje nasan dana nuna ma My Love ina son zuwa zai bar ni ƙilan ma tare zamu je" ɗan buɗa ido Fatuu tay ta ruƙe haba ta maimaita My Love ɗin da ta faɗa Mino ta saka dariya tare da rufe fuska alamar kunya, hira suka cigaba da yi anan Fatuu ke mata zancen Karatunta tace kar ta bari soyayya tasa ta shashantar dashi koda SSCE ne tayi ta samu result ɗin gama Secondary Minon tace eh rannan sunyi magana yace zata zana jarabawar sannan in zai tafi yin Master's Degree ɗin shi US zasu tafi tare sai taci gaba da Karatu a can, sosae Fatuu taji dadin jin hakan anan take sanar mata zancen komawarsu Us Mino ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace yanzu shikenan tafiya zatayi ta zama bata da kowa a nan Fatun tace mata kada ta damu tasan bazata yi maraicin rashinta ba tunda ga yan gidan su Nameer nan tasan zasu zame mata tamkar yan'uwa, tare suka shiga Kitchen yin abinci suna cikin yin aikin ne Mino ke faɗi mata wai Nameer yace in tana so a samo mata mai aiki da sauri Fatuu tace to ya tace mashi Minon tace cewa tayi ba sai an samo ba tunda ba wani aiki sosae sai yace wai ko gyaran gida ne a rinƙa yi mata, girgiza kai Fatuu tay tace kada a samo mata wata mai aiki ai gyaran gidan ma zata iya tunda ba wani datti yake yi ba inda take amfani dashi kullum kamar Bedroom, toilet da Kitchen su ta rinƙa gyara su kullum shi kuma falon tunda yana da girma in kamar taga bai 6aci ba tana iya bari sai bayan kwana biyu ta rinƙa sharewa amman zata iya kullum tasa towel ta goge kayan kallo da kujeru sai ta rinƙa saka turaren wuta akai akai koda zata yi mai aiki a bari ba yanzu ba sai kamar in ta samu ciki tayi nauyi kuma mai aikin ma kada ta bari a samo mata yarinya ko budurwa in ba haka ba a kwace mata My Love tana gani, dariya Mino tayi tace ita so take ma Aysha ta dawo wurinta shikenan ma ba sai tayi wata mai aiki ba Fatun tayi ɗan jimm alamar nazari kafin tace mata hakan ma yayi amman ta bari ba yanzu zata ɗaukkota ba tace to, bayan sun gama girkin saida suka gyara ko ina sannan suka zauna suka ci tare, Sai bayan Magrib Haisam yazo ɗaukarta lokacin Nameer ya dawo ya shigo cikin parlon suka gaisa Mino ta kawo mashi abun ta6awa da lemu daga baya sukai sallama. A ranar da daddare Haisam ke faɗi mata nan da sati guda zasu tafi Us, ana saura kwana ukku su tafi taje Katsina yin bankwana, har gidan Aunty mareeya da Feenah taje sannan taje gidansu Aminiyarta Haulat harda abun arziƙin data saba tayi mata taba Kawu Amadu makullin Motarta tace yaci gaba da yin amfani da ita, kwananta biyu ta dawo Abuja Washe gari wurin ƙarfe sha ɗaya suka tafi harda Mino amarya akai masu rakiya Airport daga nan Lagos zasu je wurin Fanan sai da daddare zasu tashi zuwa Us. Fauzy taso zuwa Funtua bayan zuwan su amman Sameer yace tayi haƙuri ba yanzu ba don tana iya samun matsala in tayi wannan tafiyar a mota dole ta haƙura anan Nasarawa suka tsaya don zasu ɗan kwana biyu kafin su koma London, Bayan bikin Mino da kamar wata ɗaya lokacin satin su Fatuu biyu da komawa da daddare bayan sallar isha Gwaggo na zaune kan abun salla tun bayan data gama sallar take zaune a wurin kamar mai tunanin wani abu can ta kai hannu ta ɗaukko wayarta dake ajiye gefen abun salla ta shiga kiran Amadu, bayan ya ɗaga ta tambayi sun dawo daga masallaci ne yace mata eh ta ƙara tambayar ina Kamalu yace gasu nan tare a shago tace to shi ya shigo tana son ganin shi yace to, bada daɗewa ba ya shigo ɗakin da sallama ta ɗaga kai ta kalleshi tana amsawa ya nufi kan kujera ya zauna, gaishe da ita yayi ta amsa yace gashi ta ɗaga kai, shiru ta ɗan yi yanata kallonta can tace "Dama so nike in tambayeka wai kai baka son yin Aure ne?" ɗan waro ido yay sai kuma yayi yar dariya yace yana so mana amman miyasa tace haka ta ɗan ta6e baki tace taga baida niyya ne gashi yanata girma yanzu har ya fita daga shekara talatin amman bata ta6a jin yayi zancen yana da budurwa ba, yana dariya yace kawai shi soyayyarce ya ɗauketa 6ata lokaci don da yawa sai yaga an daɗe ana soyayya amman sai kaga anzo ba'a yi aure ba shiyasa Amman daya samu wadda suka fahimci juna zai yi auren, kai Gwaggo ta jinjina ta ɗan yi shiru tana kallon ƙasa ya fahimci kamar akwae wani abu a ranta hakan yasa shi tambayarta koda wani abu ta ɗago tana murmushi tace "Dama wata shawara ce nike son baka nace mi zai hana ka auri Haulatu duk da ba budurwa bace amman bata da wani aibu ina son yarinyar don tanada halin kirki kuma abunda aka fi buƙata kenan a wurin macen aure na tabbatar duk wanda ya aureta sai yaji daɗin zama da ita saboda tana da haƙuri sosae, ka duba yadda aka kasa yin ƙawance da Fatuu saboda halinta lokacin kuruciyarta amman haka Haulat ta jure duk da halinta na cika mutum haka taita haƙuri sa ita sukayi ƙawance har suka zama tamkar yan'uwa", Shiru Kawu Amadu yay idonshi a ƙasa ganin haka yasa Gwaggon tace ita shawara ce ta bashi ba dole take mashi ba in bata yi mashi ba shikenan tana mashi Addu'ar Allah ya bashi wadda zasu daidaita mai halin kirki, ɗagowa yay yana murmushi yace a'a bawai bata yi mashi bane kawai yana mamakin yadda tunaninsu yazo daya ne don tun bayan dawowarta yaji yana son aurenta saida ya bari ta gama takaba sannan kwanaki yaje mata da Maganar amman sai bata yi na'am ba tace wai tursasa mashi akai kan ya aureta kuma tasan bai wuce Fatuu ce tasa saboda tausayinta da take amman in akace ya aureta ai an ƙware shi tunda ita yanzu ba budurwa bace, lokacin ya nuna mata shi ba wanda yasa shi shiya kawo kanshi to sai tace wai ya bata lokaci zata yi shawara to har yanzu zaman jiran amsarta yake ko bayan bikin su Mino saida yayi mata maganar amman sai ta ƙara cewa ya dai ƙara mata lokaci, Murmushi Gwaggo tayi tace ina ruwan Haulatu, duba agogon wayarta tayi taga lokaci kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa tana faɗin bari taje gidan su, miƙewa yay shima yace suje ya rakata, bayan sun fito Amadu ya kwala ma Kamalu kira ya leƙo yace mashi zasu je su dawo yace to ya gaishe da gwaggo ta amsa tana murmushi, suna tafe suna hira gwanin sha'awa har kama Gwaggon yake lokacin da suka iso gidan a waje ya tsaya ita ta shiga, lokacin da tayi sallama innarsu Haulatun na a tsakar gida ta tarbeta da fara'a tana mata sannu da zuwa suka nufi ɗaki, bakin gado ta nuna mata Gwaggon tace bari ta zauna a kan tabarma dake shimfiɗe innar tace ya zata zauna a ƙasa don Allah, Gwaggo tana murmushi tace to ai ita ba baƙuwa bace ko kuma ai ba'a ƙasa bane tunda kan tabarma ne, itama innar zama tayi gefen gwaggon suka shiga gaisawa ta tambayi wurin su Fatuu da Amarya Mino duk tace mata suna nan lafiya, bayan sun gama gaisawa Gwaggo tace mata ina Haulat ne ta bata amsa da tana ɗakin ta ko ta kirata Gwaggon tace a'a tukunna, tambayar innar tayi ko sunyi magana data danganci Amadu da itane da alamun rashin fahimta ta bata amsa da a'a gaskiya, Gwaggo na murmushi a nutse ta shiga yi ma innar bayanin abunda ke faruwa tsakaninsu da Amadu sosae tayi mamaki har fuskarta ta bayyana tana murmushi tace wllh sam bata san da Maganar ba, "To ko dai tana da wanda take so ta aura ne?" Gwaggo ta tambaya innar ta ɗan yi jimm kafin tace gaskiya bata tunani don har yanzu bata ga ta tsaya ma da wani ba tun bayan data gama takaba amman dai bari a kirata sai aji, Haulat na kwance a saman gado tun bayan data gama yin salla ta kwanta don tasa ummasalma bacci, tuni ma yarinyar tayi baccin ita kuma ta faɗa duniyar tunani wanda a yanzu ya zamar mata jiki ciki harda na Kawu Amadu don idan tace bata son auren shi to tayi ƙarya saidai gani take shi ba don yana sonta bane zai aure ta, innarsu ce ta shigo da sallama ta ɗago kai ta kalleta tare da amsa mata, tambayarta tay ko har ta fara bacci ne tace mata a'a ta kwantar da salma ne tace mata to tazo ɗakinta yanzu da sauri ta tambayeta lafiya innar tay ɗan murmushi tace in tazo taga ko menene ta juya, innar na shiga ɗakin itama ta shigo tana sanye da doguwar rigar bacci ta yafo gyale a kanta, koda taga Gwaggo bata kawo komai ba a ranta ta ɗauka an kirata ne su gaisa ta duƙa a gabanta tana ɗan murmushi ta gaishe da ita itama fuska a sake ta amsa ta tambayi Salma tace mata tayi bacci, shiru ta ɗan biyo baya can Gwaggo ta sauke yar ajiyar zuciya ta kalleta tace mata dama taji abunda ke faruwa tsakaninta da Amadu sai dai yadda tayi tunani ba haka bane ba wanda ya saka shi ya nemeta tsakanin ita da Fatuu basu ma san da yayi mata Maganar ba in ba yanzu daya faɗi mata ba kuma ita a ganinta koda sashi akai ya nemi Aurenta ai don an yaba da kyawawan halayenta ne, "Ko akwai wanda kike so ne?" innar su ta jefa mata tambaya ta girgiza mata kai ba tare data ɗago ba Gwaggo tace to in dai har taji tana son Amadun ta bashi dama tunda ba haramun bane wai don yana saurayi sau nawa akai ga misali nan ma akan Manzon Rahama, shiru suka ɗanyi kafin Gwaggo tace mata ta tashi taje ita dama tazo ne don ta Warware mata abunda take tunani in Allah yasa sun daidaita to suna Farinciki, miƙewa tay ƙasa ƙasa da murya tace ma Gwaggon saida safe ta amsa mata, bayan fitar Haulat yar hira sukai da innar tasu kafin Gwaggo tayi mata Sallama suka miƙe tare, har bakin zaure ta rakota tayi mata Godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci sukai ma juna saida safe, lokacin da ta fito Amadu na zaune bisa ɗan dandamalin gaban gidan dake kallon nasu Haulat yana latsa waya, yana ganinta ya miƙe ya nufo ta, a gabanta ya tsaya yace har ta fito tana murmushi tace eh suje ya ɗan sosa ƙeya yace to ya ake ciki tay mashi wani kallo mai kaman harara tace yadda ake waje yay yar dariya ta ƙara ce mashi suje in sunje gida yaji yadda akai, ɗan ƙara sosa ƙeya yay yace ko taje ya taho daga baya tayi murmushi tare da ɗan girgiza kai tace dama ba rakota yay ba kenan abun shi ya kawo shi, daga haka ta juya yana dariya yace mata a'a yanzu zai taho ƙilan ma ya sameta a hanya, bayan tafiyarta wayar shi ya ɗago ya shiga kiran Haulat bayan tayi ringing ta ɗaga tayi mashi sallama ya amsa ta gaishe dashi nan ma ya amsa daga haka tayi shiru yace mata in ba damuwa yana son ganinta a ƙopar gida tay ɗan jimm jin haka yasa yace mata in bazata samu fitowa ba ba damuwa bari ya tafi, a hankali tace mashi a'a gata nan zuwa, shiru tayi tana tunanin yadda zata fita hakanan sai taji wata irin kunyar shi ta kamata can dai ta miƙe ta nufi wurin kayanta ta curo doguwar Hijab ta daura saman rigar jikinta, tsaye tayi bakin kopar ɗakin tana jin nauyin zuwa ta tambayi innarsu can dai ta nufi ɗakin saida ta ƙara yin jimm kafin ta kai hannu ta ɗaga labulan ta shiga da yar Sallama, innar tasu har ta kwanta ta amsa mata tare da ɗago kanta tana kallonta Haulat ɗin ta sadda kanta ƙasa da ƙyar tace mata dama wai Kawu Amadu ne ke son ganinta a waje, murmushi innar tayi tace mata to taje, har ta juya taji ta kirata ta juyo ta kalleta, "So nike in tambaye ki kina son Amadun ne ko kuwa?" maida idonta tayi ƙasa sannan ta ɗan jinjina mata kai alamar eh, "To idan kinje yay maki Maganar Aure ki bashi dama a turo kawai" ɗagowa tay ta kalli innar cikin sanyin murya tace ita gani take kamar yayi wuri da yawa kada aita yin surutu, innar na murmushi tace to miye abun surutu abu kusan shekara da rasuwar Mijin nata wasu ma suna gama takaba da sun samu miji suke yin auren su tunda rashin yin auren ai ba abunda zai canza ko to duk miye na jinkiri tunda Allah ya kawo mai sonta kuma ma Mutum kamar Amadu ta amince mashi kawai ta amsa da to ta juya, yana tsaye gefen ƙopar gidan ta fito ta tsaya a jikin kopar ya juyo yana kallonta da murmushi da yake akwae haske itama ɗan murmushin take mashi ta gaishe shi ya amsa tare da tambayar ina ɗiyar shi tace mashi tayi bacci, "Allah yasa dai kema ba baccin kike ba na tado ki" a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a suka ɗanyi shiru suna kallon juna can yace "na cika naci ko, kiyi haƙuri kinsan abunda rai ke so ba kamar kuma ga baƙon abun gaba ɗaya na kasa samun natsuwa da aka ƙi amince man" Murmushi tayi kawai bata ce komai ba ya sake cewa "Gwaggota tazo kun yi magana ne?" kai ta daga mashi alamar eh, "To yanzu kin yarda ba tursasa man akai in aure ki ba ni ke son hakan?" kai ta ƙara ɗaga mashi, "To yanzu an yanke shawara game da buƙatar tawa ko sai na ƙara jira?" shiru tayi tana ɗan yi murmushi kafin a hankali tace an yanke yace to yana saurarenta Allah yasa yaji Alkhairi ya tsareta da ido yana mata wani kallo gaba ɗaya duk sai taji nauyin shi take ji ganin abun take kamar a Mafarki wai ita da Kawu Amadu ne suke soyayya har ma da zancen aure abunda bata ta6a kawo wa a ranta ba, cikin kwantar da murya yace mata pls a tausaya mashi kada aja mashi aji, kallon shi tayi tana murmushi a hankali ta furta "an amince maka" ɗan buɗa ido yay yace "You Mean kin amince zaki aure ni?" kai ta ɗaga mashi ya wani lumshe ido tare da kai hannu ya dafe saitin zuciyarshi ya furta "Alhamdulillah, har bansan yadda zan bayyana daɗin dana ji ba yau dai ɗan Gwaggo zai yi bacci hada munshari da ana niyyar a zautar mata da yaro" Dariya Haulat tayi har haƙoranta suka bayyana tace "Kai Kawu Amadu" buɗe idon shi yay sosae yace "Allah kuwa kullum da tunanin amsar da zaki ban nike kwana kinsan ni ba sanin kan abun nayi ba gaba ɗaya na zurma har na fara tunanin ko ban shiga fagen Soyayyar ba a sa'a da naga kamar ba'a so na", "Ai kai da wuya ace ba'a son ka kawai don baka cewa kana son ne" ɗage gira yay yace Why ta faɗi Hakan, "Saboda kana da duk wani abu da mace zata so a wurin Namiji" da ƙyar ta ƙarasa Maganar yana murmushi yace a hakan shi da baida kuɗi abunda yanzu kusan mata saboda su suke son Mutum, "Ai Kawu Amadu banda kuɗi Kyau ma nasa a so mutum kuma kana dashi" ɗan juya ido yay yace mata kenan ita don kyau take son shi tana dariya tace "a'a, don ka cancanci in so ka Kawu Amadu saboda kana da halin kirki" wani kalan murmushin daɗi yay yace "To nagode Allah ya tabbatar mana da Alkhairi ya ƙara mana ƙaunar junanmu, amman pls ina neman wata alfarma wannan Kawu Amadun da ake ce man a aje shi a gefe a rinƙa kirana da sunan da zansan nima na fara soyayya da aketa man gori da surutu ashe ma ni tuni Allah ya za6a man mata lokaci ne kawae baiba yanzu gashi lokacin yayi ta bayyana" gaba ɗayansu kallon juna suke cikin ido suna sakar ma juna ƙayataccen murmushi cikin kwantar da murya ta furta "Ok My Dear an canza maka in ma wannan bai yi ba sai a canza wani" wani farfar yay da ido yace "yayi sosae Sweetie nah" da sauri ta kai duka hannuwanta ta rufe fuska alamar kunya Amadun ya sa dariya, suna haka Mahaifinta ya dawo yabi su da kallo Amadu ya sunkuyar da kai ya gaishe dashi bayan ya amsa yace "kamar Amadu ko" kai ya ɗaga mashi yace eh shine Mahaifin nata yay ɗan murmushi tare da furta Ma sha Allah, daga haka ya juya zai shiga da sauri Haulat taja gefe tana mashi sannu da zuwa ya amsa kafin ya shige, kallonta Amadu yay yace Allah yasa data koma gidan Baban yace mata ace ya turo tana murmushi tace da wuri haka yace eh mana mi zasu tsaya yi gara suyi auren alabashshi sunyi soyayyar a gidansu tayi dariya, Mahaifinta na shiga ɗakin innarsu ya wuce tana kwancen har ta fara yin bacci saidai bai yi nisa ba, yana yin sallama ta buɗe ido ganin shine ta fara ƙoƙarin tashi zaune tana mashi sannu da zuwa ya nufi wurin gadon yana amsa mata, a bakin gadon ya zauna ta fara ƙoƙarin saukkowa tana faɗin bari a kawo Abinci ya dakatar da ita ta hanyar faɗin tukunna ta koma ta zauna, tambayarta yay mike tsakanin Haulatu da Yaron can Amadu ne ya gansu tsaye a ƙopar gida, murmushi tayi nan ta kwashe komai game da zuwan gwaggo ta faɗa mashi tun kafin ta ida ya hau jinjina kai tare da yin murmushi bayan ta gama faɗi mashi yace amman dai yayi farincikin jin zancen wllh don Amadu ba dai hankali ba ga ƙoƙarin neman na kai itama tace sosae taji dadin al'amarin don tana son Amadu, Mahaifin nasu yay fatan Allah ya tabbatar masu da Alkhairi ta amsa da Amin, bayan shigar Mahaifin Haulat basu jima ba sosae suka yi sallama harda kuɗi ya bata yace da safe ta siya ma Salma abunda takeso tace mashi don Allah ya barsu yay mata wani kallo yace badai iko zata nuna mashi da ɗiyar tashi ba, da sauri ta bashi haƙuri tana murmushi shima shi yake yi ta amsa tare da yi mashi godiya sukai bankwana cike da nuna ƙauna, kamo hanyar gida yayi sai faman sakin murmushi yake sai kace zautacce yana isowa ciki ya shige ya nufi ɗakin Gwaggo lokacin har ta kwanta ya shiga da sallama ta ɗago tana amsa mashi tare da kunna wayarta haske ya kawo tace mashi ya kunna wutar ɗakin, bayan ya kunna kujera ya nufa ya zauna sai faman murmushi yake Gwaggo ta tashi zaune tana kallonshi tace mashi ya akai ya bata amsa da Haulat ɗin ta amince mashi yanzu sai kawai a saka rana, ɗan buɗa baki Gwaggo tayi ta kai hannu ta ruƙe ha6a tace ko kunyarta bai ji da sauri ya sunkuyar da kai yana yar dariya yace yaga kamar tana son yayi auren ne shiyasa ta ɗan ta6e baki tace shikenan Allah ya tabbatar masu da Alkhairi zata yi ma dangin Baban shi magana kan hakan ya ɗago yace to, har zai miƙe yaji tace to yana da kuɗin yin Auren ko ya kalleta tare da ɗan sosa kai yace bazasu gagara ba tayi yar dariya tace yaje Allah ya taimaka yayi mata saida safe ya juya tabi shi da kallo tana murmushin daɗi don yana ɗaya daga cikin burinta a yanzu taga auren autan nata, yana fitowa wayar shi ta fara yin ringing ya duba ganin Haulat ce yasa shi nufar ɗakin shi da sauri saida yaje bakin kopar shiga ya ɗaga tare da ƙarasa shigewa, ce mashi tay dama ta kira ne taji ya ya koma gida jama'a zo kuga washe bakin daɗi wurin Amadu yace haka ta damu dashi wannan in sukai aure yasan ba ƙaramar kulawa zata bashi ba tana murmushi tace mashi in sha Allah fatan itama zai kula da ita da sauri yace tamkar ƙwai in sha Allah duk sukai dariya, a saman ƙatuwar katifar shi daya canza tuni ya kwanta suka cigaba da shan soyayya, sun ɗan ɗauki lokaci kafin sukai bankwana, bayan ya gama kiran Kamalu yayi ta wayar yace mashi ya kullo shagon ya shigo shi gashi nan har ya kwanta, a ranar kwanan farinciki yan gidan su Amadu da Haulat sukai karma dai su Masoyan. Washe gari wurin misalin ƙarfe goma na Safe Gwaggo ta kira Fatuu bayan tayi ringing Fatun ta yanke ita ta kira dama haka take duk suka kirata, gaisawa sukai ta tambayi jikinta dasu twins da Babansu da Fanan duk ta amsa mata da suna lafiya, "Dama na kira in maki Albishir ne duk da bansan ko wani yayi maki ba" da sauri Fatun tace mata a'a basu yi waya da kowa ba a ƙagauce ta tambayeta wane Albishir ne nan Gwaggon ta faɗi mata game da Amadu da Haulat, wata uwar ƙarar farinciki Fatuu ta saka ta hau fadin Alhamdulillah ya Allah Gwaggo nata dariya, bayan ta tsagaita da yin murnar da alamun mamaki ta tambayi Gwaggon ita tasa shi ya nemi auren Haulat ɗin ne tace mata a'a ta faɗi mata yadda sukai dashi, "Kai amma naji dadi wllh, kinsan Gwaggo tun kwanaki nike raya inama Kawu Amadu ya auri Haulat, sai dai gani nike kamar bazai amince ba tunda ba budurwa bace abun Allah ashe har ya furta mata kuma ni bata yi man maganar ba ma" daga jin yadda take Magana zaka fahimci ba ƙaramin farinciki take ciki ba, Maganar saka rana Fatun tayi mata gwaggon tace yau take niyyar kiran dangin babanshi ta faɗa masu sai suzo nema mashi auren daga nan a saka rana gaba ɗaya, da sauri Fatuu tace "Gwaggo don Allah a saka sai bayan na haihu Ya Haisam yace bazan ƙara zuwa ba har sai na haihu kuma yanzu saura wata biyar tunda yayi wata haɗu" a marairaice tayi Maganar Gwaggon na dariya tace ai itama bata son a saka da wurin don tana son ayi ma gidan gyara sosae don anan take son su zauna tare, cike da murna Fatun tace yauwa hakan yayi ta tambayi kamar wata nawa za'a saka Gwaggon tace ko shidda ko bakwai Fatun tace a bari bakwai ɗin lokacin har wanka ta gama tace hakane to sai a barshi bakwai ɗin daga baya sukai sallama, suna gama wayar parlor ta nufa da sauri don taje ta faɗi ma Haisam da yake Weekend ne yana gida, yana kishingiɗe kan doguwar kujera su twins na kwance a kan ƙafafun shi suna yin kallo ta nufo su cikin Washe baki Haisam ya juya yana kallon ta, ganin farinciki akan fuskarta yasashi yi mata murmushi a kan hannun kujerar da ya jingina ta zauna ta kai hannu cikin sumar shi ta fara ɗan sosai mashi, ɗago fuskarshi yay ya kalleta idanunshi a ɗan lumshe ya tambayi ya akai yaga tana farinciki ta kashe mashi ido tace tana Bedroom ta tuno da shine mijinta shine take farincikin, wani kalan murmushin gefen baki yay yace ai kullum tasan shine mijinta yasan bata mantawa da hakan tana murmushi tace hakane in ma ta manta to kuwa bata cikin hayyacinta, faɗi mashi tayi Gwaggo ce ta kirata ta sanar mata da Kawu Amadu zai auri ƙawarta Haulat" sosae shima ya nuna farincikin shi yace Amadun ya kyauta ya tambayi yaushe za'a sa rana ɗin ta faɗi mashi yadda sukai da Gwaggo na sai nan da wata bakwai saboda za'a gyara gidan tana son su zauna anan ya jinjina kai yace Allah ya kaimu ta amsa kafin ta maida idonta kan su twins daketa kallon su kamar suna fahimtar abunda ake a Tv da fulatanci tace basu ga Mom bane Adam ne ya kalleta yana mata dariya shi kuwa miskili Abie ko kallon nata bai yi ba, saukkowa Adam yay da yake sun fara iya tafiya ya nufota yana zuwa ta ɗaukeshi ya kai hannu yana ta6a ƙirjinta alamar yana son tayi feeding nashi saida ta gyara zama sannan ta fara bashi Abie na ganin haka shima ya saukko daga kan kujerar zai nufota ta ɗan harare shi yaja ya tsaya yana kallonta da idanunshi tubarkallah Haisam nata kallon su yana murmushi, ganin kallon da take mashi yasa ya fara ta6e baki zai yi kuka da turanci Fatun tace mashi tunda bai damu da ita ba itama bata ƙara bashi abunta kawai sai ya kife fuskarshi a jikin Haisam ya fashe da kuka, suna haka Fanan ta fito tana sanye da skinny jeans da yar top ta nufo su da sauri tana faɗin waya ta6a mata Little Abie yanzu suyi faɗa, daukar shi tayi tana tambayar waye ya saka shi kuka da hannu ya nuna mata Fatuu ta juya tana kallonta ta ɗan ɗaure fuska tace miyasa zata saka shi kuka kafin ta bata amsa Adam ya saki breast ɗin ta dago yana gwaranci shi ala dole magana yake duk ya basu dariya, tambayar Haisam tayi abunda ya haɗa su yana murmushi ya faɗi mata ta nufi gefen Fatuu tana faɗin ayi haƙuri dasu haka halin su yake ba shareta sukai ba ta zauna kusa da ita tace ma Abie din yace mata Sorry saida ta maimaita mashi kusan sau ukku sannan ya faɗi Sorry ɗin, bayan ta gama ba Adam ɗin ta amshe shi shima ta fara bashi anan take faɗi mata zancen auren Amadu da Haulat itama Fanan ɗin ta nuna farinciki sosae tayi fatan Alkhairi. A ranar Gwaggo taje ta sanar ma Hajiya itama tayi farinciki sosae tace Amadu ya kyauta Saude ma ta nuna farinciki, Tk na jin zancen Auren Amadun yace aikuwa bazai riga shi yin aure ba shima zaisa aje a nema mashi aure, da yamma Amadu na shago Haisam ya kira shi a waya cikin girmamawa ya gaishe dashi bayan ya ɗaga Haisam ɗin yace mashi yaji abun farinciki Allah yasa Alkhairi Amadun na murmushi ya amsa tare da yi mashi godiya, tambayarshi Haisam ɗin yay akwae gida na kusa da gidan su yana son sanin wanda ke ciki haya suke ko kuwa nasu ne da alamun rashin fahimta Amadun ya tambayi wanne ciki yace duka na left da right ya bashi amsa da na bangaren dama gidan kansu ne sai na hagu wato gidan su Umar su haya suke Haisam ɗin yace mashi yasan mai gidan yace mashi eh wani Alhaji Isah ne shima anan unguwar yake daga can ƙasa yace mashi yana da lambarshi Amadun yace a'a gaskiya, tambayar shi yay zai iya samo mashi lambar tashi da sauri Amadun yace eh yace Ok ya samo mashi harda ta shi wanda yake hayar gidan Amadun yace ita yana da ita yace to ya fara turo mashi ita kafin ya samo mashi ta mai gidan yace to zai tura mashi yanzu sukai sallama. Da yamma bayan sallar la'asar sai ga Baban su Umar yazo shagon Amadu cikin fara'a suka gaisa kafin cike da farinciki yake sanar dashi ɗazun mijin yar'uwar shi ya kira shi yake ce mashi yana buƙatar siyan gidan da yake ciki ne shine yace zai siya mashi gida da zai zauna har ma yace mashi ya nemi gidan da yake so in ya samu sai yayi mashi magana, sam Amadu bai kawo komai a ranshi ba ya nuna ya taya shi murna sosae, Bayan sallar isha Tk ya samu Hajiya a parlonta daga gefenta ya zauna ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa, shiru yay ya maida kan shi ƙasa yana wasa da yatsun hannunshi Hajiya ta lura da Magana yake son yi tace "Ya akai ɗan gidan Hajiyar Sanata mi ake son faɗi man ne?" ɗagowa yay yana murmushi ya kasa mata magana tace mashi ko sun fara yar kunya ne still murmushin yake bai ce mata komai ba tace kar yaji komai ya fadi mata abunda yake son fadi mata da ƙyar yana yar in ina yace dama so yake a je a nemo mashi Aure, ɗan buɗa ido tay tana kallonshi tace "Wato ashe dama kana da wadda kake so shine tuntuni kaƙi yin niyya sai yanzu da kaji abokin ka zaiyi kana gudun yayi ya barka ko" yana ɗan sosa kai yace a'a yaga bai fara aiki ba shiyasa bai yi niyya ba tace to yanzu aikin ya fara ne yay shiru yana murmushi, "Ai ganin baka da niyya yasa banyi Maganar a nema maka aikin ba tunda mi zakai da aiki ba iyali amman yanzu tunda kayi niyya zanyi magana sai a nema maka sai kayi Addu'a Allah yasa a dace, Maganar zuwa nema maka aure kuma zan yi ma mahaifinka magana amman tukunna sai ansan wacece kake so tunda ba'a kama nema maka aure ba tare da anyi bincike ba" dakatawa tayi kafin ta tambaye shi sunan yarinyar da kuma yar gidan waye ya faɗi mata sunanta Asma'u tare suka yi karatu har ya kwantanta mata ita yace sun ta6a zuwa ta gaishe da ita Hajiyar tace ta ganeta yanzu zata sa ai bincike sosae kafin tayi ma Mahaifin nashi magana sai a turo mutum ɗaya ko biyu itama zata kira Kawu Mani sai su haɗu suje, Godiya yayi mata tare da Addu'o'i tana murmushi tace Allah ya nuna mata bikin Tukur ɗan autanta yana murmushi ƙasa ƙasa yace Amin kafin yayi mata sallama ya tafi. Washe gari bayan sallar La'asar sai ga Abbas yazo tare da wasu Mutane bayan sun gaisa da Amadu ya tambayeshi Gwaggo na nan ne yace mashi eh, juyawa yay wurin Motar mutanen da suka zo tare su biyu yace masu yana zuwa suka furta Ok ya juyo ya nufi gidan, a bakin ƙopar zauren ciki ya tsaya yana sallama Gwaggo ta leƙo daga cikin falo tana amsawa tana ganin shine ta washe baki tana faɗin "ɗana Abbas ashe kai ne ka shigo mana" yana murmushi ya nufo falon Gwaggon ta koma ciki, bayan ya shiga a kujera ya zauna suka gaisa ta tambayi su Abdul yace mata duk suna lafiya kafin yace mata yaji abun murna na auren Amadu Allah ya sanya alkhairi tana fara'a ta amsa da Amin, ce mata yay dama yazo tare da injiniyoyi zasu duba gidan da alamun rashin fahimta Gwaggon tace gida kuma ganin yadda tayi Maganar yasa yace mata basu yi Magana da Haisam bane akan aikin da za'ayi a gidan da sauri ta girgiza kai tace gaskiya basu yi Magana ba sai dai ko Amadu, yar dariya Abbas yayi yace ina ruwan H,Zakee nan ya shiga yi mata bayanin aiki za'a ma gidan don har ma anyi cinikin gidan dake makwabtaka dasu Haisam ɗin ya siya za'a haɗe da wannan ayi sabon gini, zaro ido Gwaggo tayi baki buɗe take kallon shi a ɗan ruɗe tace "anya dai ɗana Abbas haka maganar nan take" yana dariya yace mata tabbas haka take ƙilan da Amadu sukai maganar, cike da mamaki tace anya ai daya faɗi mata amman bari ta kira shi taji, wayarta ta ɗaukko ta shiga kiran nashi bayan ya ɗaga tace mashi ya shigo yanzun tana son ganinshi, bada daɗewa ba ya shigo da sallama ya nufi kujera ya zauna yace mata gashi, tambayar shi tayi ko sunyi maganar za'ayi aikin gidanan da ɗanta Haisam da alamun rashin fahimta ya girgiza mata kai alamar a'a kafin ya faɗi mata yadda sukai dashi game da gidansu Umar da lambobin daya tura mashi sai kuma zuwan da Babansu Umar yayi cike da farinciki ya bayyana mashi sunyi waya da shi yace yana buƙatar siyan gidan da yake ciki shi kuma zai siya mashi wani ya zauna, Abbas na murmushi yace to ai su ya siya ma gidan za'a haɗe da wannan a maida shi babban gini shi ya ɗaura ma kan aikin shine ma yazo da injiniyoyi don su fara duba gidajen, gaba ɗaya Gwaggo da Amadu idanunsu a waje suke kawu Amadu ya kai hannu ya rufe baki alamar Al'ajabi da alama mamaki ya kashe masu bakuna can da tsananin mamaki kawu Amadu yace "Wai Yaya Abbas yanzu kana nufin saboda mu ya siya gidan su Umar ɗin kuma har ya siya masu suma gida?" kai Abbas ya ɗaga mashi yace eh a yadda sukai za'a haɗe sai ai babban Flat a fidda ma Gwaggo part ɗinta sai shima Amadun a fidda mashi nashi da zai zauna da iyalinshi harda ma 6angaren baƙi, nannauyar ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke ta shiga girgiza kai da alamun damuwa tace "Amman gaskiya ɗana Abbas wannan hidiman tayi yawa sosae ace ya siya masu gida sannan ya siya wanda suke ciki kuma a haɗe da wannan a fara sabon gini yadda gini kede cin kuɗi ai gaskiya abun yayi yawa nidai da za'a bi ta tawa don Allah ya barshi in ma dole so yake yayi to a gyara wannan namun kawai ni sai in koma can ɗayan ɗakin shi kuma Amadun sai su ɗauki dakina da nan falon za'a ma iya ƙara girman falon tunda ga ɗan sauran wuri nan daga gefe har banɗaki ma za'a iya yi masu a ƙuryar lafiya lau wannan ma zai ishe mu" fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar Abbas na dariya yace "to Gwaggon mu waya ƙi cigaba tunda shi yayi niyya yana da halin yi ne karki wani damu tunda daya san zai takura da bazai fara cewa zai yi ba, a yadda ma ya faɗi man dama yana ta son a canza ginin gidan to yadda yake son a maida gidan bazai isa ba kuma yasan kun riga kun saba da unguwar bazaku ji daɗi ba in ya yi maku ginin wani wuri Hajiya ma yasan bazata so ku rabu ba shine yanzu yay tunanin yin hakan harma anyi cinikin gidan ya biya shi kuma wanda aka siya ma gidan dama can yanada rabo a wurin shi ne, yanzu dai na bar mutane a waje zan iya masu magana su shigo?" duk tayi sukuku da ita ta ɗaga mashi kai alamar eh ya miƙe yana dariya yana faɗin karta wani damu abun farinciki ne don haka tayi farinciki kawai ta ɗan yi murmushi ya juya kan Amadu da yayi duruduru yace ya taso yaje gidan su Umar ɗin yaga in mai gidan na nan yace za'a shigo a duba yace to tare da miƙewa suka fita, Gwaggo dai tayi zuru tana ta jinjina abun a ranta tasan dole gidan su Umar ɗin yayi kuɗi don yafi nasu girma ga gida kuma da aka siyan masu sannan azo a dasa gini, Bayan duk sun gama dubawa Abbas yace ma Gwaggo za'a kawo hotunan gidaje sai su za6a tace to kawai sukai sallama, zaune sukai falon Gwaggo ta kasa yin magana sai Amadu dake ta faman jinjina abun yana faɗin to wai hakanan ya yanke yi masu ginin ko kuwa dai yaji batun gyaran gidan saboda aurenshi shine zai yi masu, wannan Maganar da yayi yasa Gwaggo ta ɗaukko wayarta ta shiga kiran Fatuu, bayan ta yanke Fatun ta kira suka gaisa nan take tambayar ta wai sunyi maganar gyaran gida da tace mata tana son ayi kafin bikin Amadu da Haisam ne tace mata a'a kawae dai ta sanar mashi zancen shine ya tambayi yaushe za'a saka rana ta fadi mashi yadda sukai da ita na ba yanzu ba sai an yi gyaran gidan Gwaggon ta sauke ajiyar zuciya, da sauri ta tambayeta miya faru ne nan ta kwashe komai ta faɗi mata ita kanta Fatun tayi mamaki sosae ido waje ta shiga jinjina Maganar aikin tace gaskiya hidiman tayi yawa sosae Gwaggon tace wllh itama duk ta damu Fatun tace bari tayi mashi magana gaskiya in ma aikin yake son yi masu to a gyara gidan nasu kawai Gwaggo tace itama abunda tace kenan to Abbas yace ai har ya riga ya siya gidan kuma shi Baban su Umar yanzu in aka hana yana iya ganin anyi mashi baƙin ciki, tana cikin yin Maganar Amadu ya miƙa hannu ta bashi wayar bayan sun gaisa da Fatun yace mata kawai a kyaleshi ai mashi godiya yanzu ko anyi mashi magana kan ya bari sun san dai ba fasawa zai yi ba, a sanyaye tace shikenan sukai sallama, Bayan sun gama yin wayar Haisam ta shiga kira da yake su safiya ce yana wurin aiki, bayan yayi picking tace mashi tana son suyi vedio call ya furta Ok, yana zaune a Office ɗin shi jikinshi sanye da baƙaƙen suit fuskar shi sai annuri take, fuska a tur6une ta gaishe dashi yana ɗan murmushi ya amsa ya gane laifi yayi mata daga yanayin face ɗinta, daga gaisuwar tayi shiru tana ta tura baki, lumshe mata ido yay ya furta "ya akai ne My Baby?" wani kallo tayi mashi a marairaice tace taji abunda yayi amman gaskiya hidiman yayi yawa in aikin za'ayi to ayi iya gidansu basai ya kashe uban kuɗi ba haka, murmushi kawai yake ganin har yanzu halinta na rashin son ya kashe kuɗi sosae na nan, ganin bai ce komai ba ta tura baki tace bazai yi magana ba, "Yanzu nayi laifi don zan ma Family ena abu?" ya tambaya tare da ɗage mata gira, kaman zatayi kuka tace "a'a ni bance kayi laifi ba Amman gaskiya kashe kuɗin zai yi yawa" sigh yay still murmushi yake yace "bazai yi yawa ba akwae kuɗin Baby so don't worry" yamutsa fuska tayi tace to in suka ƙare fa har saida yayi yar dariya ganin taƙi ta girma har yanzu tana behaving kamar da yarintarta duk da yasan yanzun ma ba wani girma tayi ba tunda yanzu take 20yrs, yana yar dariya yace mata bazasu ƙare ba saboda yana dasu da yawa akwae Dollars ya tara cike da tsokana yayi Maganar ta zaro ido ya ɗage mata gira, murmushi tay tace "baka tsoron insa ai kidnapping ɗinka kana faɗi man ka tara Dollars" dariya yay har haƙoranshi suka bayyana yace ai tuntuni ta riga tayi kidnapping ɗin Heart ɗinshi yanzu ko duka kuɗin dake gareshi tace ya bata zai tattara ya bata, wani kallo tayi mashi tace is he serious ya jinjina mata kai yace amman zai fidda na aikin gidan da za'ai don kar aga yayi magana biyu sai kuma wanda zai ciyar dasu kafin ya sake tara wasu kada Allah ya kama shi ya barsu da yunwa, wani irin kallon ƙauna ta shiga bin shi da shi shima kallon nata yake idanu a ɗan lumshe cikin sanyin murya ta furta mashi "Thank you for loving me unconditionally Hubby. You have shown me what true love is, and I am forever grateful for that. I couldn't imagine my life without you" tana gama Maganar kwalla suka zubo mata sharrr, lumshe ido yay tare da ɗan murmushi yasa yatsa saman screen ɗin yana yin alamar goge mata ƙwallan hakan yasa ta yi yar dariya, Godiya ta shiga yi mashi sosae da Addu'o'i a hankali yake amsa mata daga baya sukai sallama cike da nuna ƙauna, a ranar haɗaɗɗun abinciccika suka haɗa mashi ita da mai aikin su da daddare kuwa duk da halin da take ciki saida ta tabbatar tayi mashi godiya ta hanyar gigitashi ta yadda har saida suka zubda hawaye su duka.......... 101 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ .......Ranar Alhamis Hajiya ta kira kawu Mani na Daura ta tambaye shi gobe Juma'a zai shigo Katsina ne yace mata a'a amman in tanason ganin shi sai yazo tace mashi in bazata takura shi ba tana son ganin shi yace to ba damuwa zai shigo. Washe gari kafin ayi salla ya iso Ya yi shigar manyan kaya ya fito a dattijo mai kamala anan gidan yayi sallar Juma'a suka ci Abinci tare da Hajiya a dining, bayan sun gama cin abincin ne suka dawo falo yana zaune a kujerar dake gefen ta Hajiya yace "Hajjaju gani na amsa kira Allah yasa na lafiya ne" tana murmushi ta bashi amsa da lafiya lou sai alkhairi ya furta Alhamdulillah shi suke fata a koda yaushe, Maganar zuwa neman auren Tk tayi mashi tace tana son ya shige gaba tasa anyi mata bincike akan gidansu yarinyar an tabbatar mata da basu da matsala shi mahaifin nata asali mutumin Gombe ne aikin custom ya kawo shi Katsina daga nan zaman ya ɗore don yanzu har ma yayi retired to tana son ya tuntube shi kan su bada lokacin da za'aje neman auren, jinjina kai yayi yace to ba matsala a yau ma kafin ya tafi sai ya tuntube shin a bashi Address ko kuma lambar wayar shi tace to dama ta amshi lambar a wurin tukur ɗin, bashi lambar Baban Asma'un tayi yayi saving ya ɗago yana murmushi yace ashe sun kusa shan bikin ɗan gidan Hajiya itama murmushin take tace aikuwa yay fatan Allah ya sanya alkhairi ya nuna masu, bayan ta amsa da Amin tace "Kai ma in kana son ƙara Auren akwae mata a ƙasa zan baka" waro ido yay ya ɗan buɗa baki sai kuma yayi dariya yace yasan ai wasa take, ɗan ta6e baki tayi tace dama ana wasa da Maganar aure, yana dariya ya tambayeta wacece matar, tace "Kana so ne?" "To Hajjaju taya zansan ko ina so ba tare dana ganta ba" yana ta dariya yay Maganar, "To ai in kai baka santa ba ni na santa kuma na yaba da ita ne shiyasa nayi maka maganarta tuntuni ma nake kwaɗayin wani cikin Family ya aureta saboda kyawun halinta Allah bai nufa nayi ma wani maganarta ba sai kai da nayi mawa yanzu", "To ai Hajjaju kyau dai in ganta" still dariyar yake itama haka tace "ai ina ganin ma kasan wacece Kakar matan su Haisam da Nameer ce, ba wani tsufa tayi ba kawai don anyi mata auren wuri ne da yake asalin Fulanin daji ce in ba don haka ba bazata aje ma jikoki kamar su ba don ina ganin ka girmeta kaga kai baka dade daka samu Yan jikokin ba" shiru yay yana ƙoƙarin tuna ko yasanta can yace gaskiya ya kasa ganeta koda ya santa Hajiyar tace bari taga ai kaman akwai hotonta da akayi da bikin su Nameer anan falonta kuma shima ranar yana nan dashi akai hotunan, hoton gwaggo da tayi tare da Mino a ranar ta buɗo mashi ta miƙa mashi ya amsa ya bi hoton da kallo yana ɗan murmushi can ya ɗago ya tambayi Hajiyar bata da aure ne tace inda tana dashi zatayi mashi tayin auren nata ne ya sake tambayar abunda ya rabata da mijin nata ta faɗi mashi aurenta biyu na farko na dole ne akai mata da yake ta taso marainiya shine kawunta da ya riƙeta ya aura mata abokin shi to hardai zaman ya ƙare basu haihu ba bayan ta dawo wurin kawun nata Daura tana zuwa tallan nono a kasuwar mashi Allah ya haɗa ta da mijinta na biyu data aura shine suka haifi yara biyu kafin ya rasu sanadiyyar haɗarin mota tun daga nan kuma bata ƙara yin aure ba kusan shekara ashirin da biyar duk da tana da masu son auren nata itace bata so cikin dangin mijinta daya rasu wani ya samo mata aikin asibiti tana yi farko ma a gidan shi ta fara zama daga baya saboda rashin jituwar da suke samu da matarshi ta baro mashi gidan tazo ta gina wannan da take ciki a filin da suka gada, nan ta bashi labarin yadda mahaifiyar Fatuu tayi aure ta haifesu su biyu da yadda Gwaggon ta ɗaukko su ta riƙe ta kuma shiga nuna mashi kyawawan halayenta, ajiyar zuciya Kawu Mani ya sauke ya sake kallon hoton gwaggon kafin ya miƙa ma Hajiya wayar ta amsa tare da tambayar tayi mashi ko kuwa yana yar dariya yace tunda tayi mata tana son ya aureta in dai zata amince zai auretan, "A'a ba wani tunda tayi man inason ka aureta salon kaja man matanka su ƙullace ni, kawai in kaji kana son ta zaka aureta to in kuma bata yi maka ba lafiya lau ka fito ka faɗi man ai ba wani abu bane dama don naga kana da ra'ayin mata fiye da ɗaya ne tunda yanzu haka biyu gareka shiyasa nayi maka Maganarta" sosae yake dariya jin abunda tace bayan ya tsagaita yace to yanzu koda tayi mashin in ita taƙi amincewa dashi fa tunda tace tana da masu son aurenta itace bata so Hajiyar tace ai sai suma su jaraba sa'ar su ƙilan Allah yasa ta amince dashi, gyaɗa kai yay yace to yanzu ya za'ai tasan dashi, "Wannan mai sauƙi ne in ka shirya haɗuwa da ita kuyi magana sai in kirata in mata magana", yar ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi yace abunda za'ai yanzu zai kira mahaifin ita wadda tukur ke so yayi mashi maganar haɗuwarsu in ya bashi dama da yayi sallar la'asar sai ya tafi yanzu abunda za'ai tayi ma ita Matar magana in ya fita sai ya fara tsayawa wurinta su gaisa kafin ya wuce, wani kallo Hajiya tayi mashi tace "Humm, su Mani anga farar fata har an zurma da anaso ai man bariki" Dariya ya 6a66ake da ita harda buga ƙafa yace "Sai Hajjaju mai dalilin aure, saboda dai kina so ne kawai" "To tunda hakane a barshi kawai na janye....." da sauri ya katseta "a'a Hajjaju ba'a yi haka ba tunda dai kinyi niyyar haɗawa kada kima kan ki buƙulun lada ki kiratan kawai sai inje mu gwada sa'ar" wani kallo mai kaman harara tayi mashi ya saka dariya, ce mashi tay ya bari ayi sallar la'asar ɗin zata kirata Kawu Manin harda ce mata to ai kada ta fita unguwa Hajiyar na dariya tace ya dawo wani lokacin, "gara dai ayi komai yau hajjaju kinsan ance da zafi zafi ake dukan ƙarfe" Dariya Hajiya tay tare da girgiza kai, bada daɗewa ba aka kira sallar la'asar ya miƙe don yaje masallaci itama Hajiya ta tashi tana ruƙe da sandarta ta nufi hanyar Bedroom don taje tayi sallar, bayan ta gama ne ta kira layin Gwaggo wayar na fara yin ringing ta ɗaga cikin girmamawa ta gaishe da ita tare da yi mata barka da juma'a bayan Hajiyar ta amsa ta tambayi tana gida tace mata eh bata daɗe data dawo bama daga wurin aiki, an dawo lafiya tayi mata Gwaggon ta amsa da lafiya lau Alhamdulillah, "to ga baƙo nan na turo zai zo ku gaisa" ɗan jimm Gwaggo tay a ranta ta maimaita abunda Hajiyar tace kafin ta amsa mata da to sukai sallama, zugudum Gwaggo tay ruƙe da wayar tana ta nanata zancen zuwan baƙon don abun sai taji shi wani iri saboda basu ta6a haka da Hajiyar ba wai tace mata ga wani nan zai zo su gaisa, Bayan sun gama yin wayar fitowa Hajiya tayi cikin falon kusan a tare suka dawo da Kawu Manin, bayan sun zauna ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa tace yayi na yara duk sukai salla sai sun gaishe da mutum shima murmushin Yay yace ai haka yakamata kafin yace mata yanzu bayan ya fito ya kira Mahaifin yarinyar har ya bashi Address zai je ya same shi daga can zai wuce Daura duk yadda sukai dashi zai sanar mata ta amsa da to tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya, shiru suka ɗan yi bai miƙe ba can yace mata bata kirata bane tay dariya tace ai ta zata ya manta yaje ta kirata a waya, tambayar inda gidan yake yayi ta kwatanta mashi da shagon Amadu tace in yaje yaronta ne mai shagon sai yasa shi yaje yayi mata magana ya amsa da to tare da miƙewa tana murmushi tace Allah yasa taji Alkhairi ya amsa da Amin ta ƙara cewa zata turo mashi kuɗi yanzu sai ya zuba mai yayi mata godiya itama tayi mashi da fatan Allah ya kiyaye hanya tace ya gaida iyali daga aka ya fito, A daidai shagon Amadu ya parker Motar shi lokacin basu daɗe da dawowa daga Masallaci ba, fitowa yay bayan ya kulle ƙopar Motar ya tunkari shagon, a gaban shagon ya tsaya fuskarshi ɗauke da murmushi yayi masu Sallama tunda ya fito Amadun ke kallon shi yana ganin kaman ya sanshi saida ya ƙaraso gaban shagon ya gane shi shima Amadun murmushin ya mayar mashi bayan ya amsa sallamar cikin girmamawa ya gaishe dashi Kamalu ma dake zaune kan plastic chair yana latsa waya ya ɗago kai ya gaishe dashi shima da murmushi ya amsa mashi, tambayar waye Amadu a cikin su yayi Kawu Amadu yace shine ya nuna Kamalu yace to shi kuma wannan fa ya bashi amsa da ɗan Yayarshi ne, "Kenan ɗanka ne" Amadu na murmushi ya bashi amsa da eh, "Ko shine Yayan Matar Haisam" da sauri Amadun yace mashi eh, "Allah sarki, Allah yayi maku Albarka ya jiƙan Mahaifiyarsu da Mahaifin ka" a tare duk suka amsa mashi da Amin, "Yauwa ka shiga ciki kace ga baƙon ya iso" ya faɗa still da murmushi akan fuskarshi, da alamun rashin Fahimta Amadun yace wa zai faɗi ma hakan Kawu Manin yace mashi ita mai gidan zaije yace ma ga baƙon da Hajiya tayi mata magana yazo da sauri ya amsa da to ya juyo ya buɗe shagon ya fito, lokacin daya shigo gidan Gwaggon na cikin ɗakinta tun bayan data yi waya da Hajiya dama tana kan abun salla ne bata tashi ba, da sallama ya shigo ta amsa tare da juyowa ta kalleshi ya sanar mata zancen zuwan baƙon tay ɗan jimm kafin a hankali tace mashi ya shigo dashi falo yace to ya juya, shiru tayi a ranta ta shiga tunanin to wane baƙo ne kuma wace irin gaisawa zasu yi kaman yadda Hajia tace, tana jin lokacin da suka shigo Kawu Manin yay sallama, bayan ya shigar dashi yazo ɗakin ya sanar mata gashi can a falo kai kawai ta ɗaga mashi ya juya ya tafi, miƙewa tayi duk tayi sukuku ganin Hijab ɗin jikinta lafiya lou dama gogagga ce ta ɗaukko tayi sallar da ita ta nufi ƙopar fita, lokacin data tunkari falon gabanta har ɗan faɗuwa yake, da sallama ta saka kai cikin falon ƙamshin turaren shi ya bugi hancinta yana zaune akan 2 seater ya ɗago yana kallonta da murmushi ya amsa mata sallamar suna haɗa ido ta gane shi ta nufi kujera mai mazaunin mutum ɗaya daga can gefen tashi ta zauna idon shi akanta yace mata "Barka da Fitowa", ɗan murmushi tayi ta amsa tare da gaishe dashi yana ta murmushi ya amsa, kanta ne ya ɗaure ganin shine don bata ta6a zaton shi zata gani ba matsayin baƙon don tunda tasan Hajiya tasan shi yana zuwa gidan matsayin ƙanin Hajiya tsawon lokacin kuma bai ta6a zuwa nan gidan ba sai yau, miƙewa tayi ta nufi Fridge ya bita da kallo bayan ta buɗe ta ɗaukko lemu da robar ruwa tare da glass cup bayan ta rufe tana juyowa suka haɗa ido ta maida nata ƙasa ta nufo inda ɗan table yake ta ɗaura sannan ta ɗaukeshi ta matsar dashi gabanshi, buɗe lemun tayi ta zuba a cikin cup ɗin ba tare data kalleshi ba tace gashi yasha yana murmushi ya furta "Shukran" ɗan murmushi tayi ta koma inda ta taso, ɗaukar cup ɗin yayi ya kai baki saida ya kur6a kamar sau uku sannan ya aje tare da furta Alhamdulillah ya ɗaura idon shi kan Gwaggo dake kallon Carpet yace "Fatan na same ki lafiya, ya gida ya yara ya aiki kuma" ɗago ido tayi ta kalleshi da ɗan murmushi ta amsa mashi da lafiya lau Alhamdulillah shima ta tambayi ya nashi iyalin da aiki yana sakin ƙayataccen murmushi ya amsa mata, shiru suka yi can ta miƙe tace bari a kawo mashi abinci da sauri ya dakatar da ita yace lemun ma ya isa a ƙoshe yake ta koma ta zauna, "Yauwa, kamar yadda Hajjaju ta sanar maki ita ta turo ni don mu gaisa da juna kuma tunda mu ba yara bane nasan kin gane wace irin gaisawa ake nufi, ni dai na gan ki kuma kin mani don haka in an amince man Aure nike son muyi tunda duk naji duk wani abu dangane dake nima kuma in kina son sanin abunda ya dangance ni zaki iya yi ma ita Hajjaju magana da fatan za'a amince man" tunda ya fara Maganar ta sunkuyar da kanta har ya gama ta kasa ɗagowa balle tace mashi wani abu, ganin taƙi yin magana yasashi ce mata ita yake saurare ta taimaka ta bashi amsa, gaba ɗaya ya ɗaureta ta rasa amsar da zata bashi don sai taji bata iya ƙin amince ma buƙatar daya zo da ita kodan Hajiya gashi ita ta cire sake yin aure a ranta, a hankali ta ɗago suka haɗa ido tayi saurin kawar da nata kafin tace mashi tana buƙatar yin shawara ya ɗan bata lokaci, yana murmushi yace "Har sai anyi shawara kuma, to kodai ban samu kar6uwa bane?" kallon shi tayi da ɗan murmushi tace a'a kawai tana buƙatar yin shawara ne tunda tana da babban yaro, ɗan buɗa ido yay yace "dashi za'ai shawarar kenan karfa yasa aƙi amince man don kinsan wasu yaran sukan taya iyayensu maza kishi" yar dariya tayi kawai, "Yanzu har tsawon wane lokaci zan jira Hajiya" yay Maganar yana mata wani kallo da gani shima za'a dashi ta bangaren soyayya, tana murmushi tace malama dai ya wani ɗage gira yace "Ni Hajiya na gani" shiru tay kawai tana murmushi ganin ya kafeta da ido tace mashi ko mi kenan zata sanar mashi ya furta Ok bari ya bata lambar shi amman don Allah kada a ɗauki lokaci asa ya kasa samun natsuwa tace uhmm kawai, wayarta ya tambaya yasa mata lambar tashi ta miƙe tace bari ta ɗaukko tana ɗaki, bada jimawa ba ta dawo ta miƙa mashi wayar ya amsa yana murmushi ya ɗan jujjuyata yace "amman Hajiya sai naga kamar kinfi ƙarfin wannan wayar" murmushi tayi tace tafi jin daɗin amfani da irinta ne yace to amman ga na zamani ai sai a haƙura da tsohon yayi gaskiya yakamata a canza ta tace mashi tuntuni yara keson canza mata ita ce bata so, "To ai yanzu sai aba maigida dama ya canza" da sauri ta kalleshi ganin kallon da yake mata yasa ta kauda fuskarta yace "na cika azar6a6i ko tun ba'a sanar dani matsayi na ba har na yanke hukunci, ayi haƙuri abunda rai ke muradi ne" juyowa tay ta kalleshi tana ɗan murmushi, lambar tashi ya saka a tata ya kira kafin yayi mata saving tashi ya miƙa mata yace gashinan ya saka mata Alhaji Mani ya tambayi ita kuma Hajiya wa zai saka mata tace Dije ya ɗan yamutsa fuska yace "Wannan na zamanin da ne bari in saka na zamanin yanzu Khadija ko kuma Khadijatul Khubra" Gwaggo bata san lokacin da tayi yar dariya ba shima ita yake yi bayan ya gama saving ɗin ya ɗago ya kalleta yace "to Hajiya Khadija ni bari in zo in wuce inada wani uzuri da zan aiwatar kafin na hau hanya sai naji daga gareki ina fata kuma za'a duba man inji abunda nike fatan ji" murmushi kawai take, miƙewa yay ya zura hannu cikin yan cikin babbar rigar shi ya fiddo kuɗi masu ɗan yawa ya ɗaura akan table ɗin yace gashi nan a ba ɗan shi da jikanshi, da sauri ta kalleshi tace don Allah ya barshi yana mata wani kallo yace bata ji waɗanda yace taba bane dole tayi shiru, tafiya ya fara yi zai fita daga cikin falon ta ɗan juya tana kallonshi har ya kusa ƙopa ya tsaya ganin zai juyo yasa da sauri ta kauda idonta tana haka taji muryarshi yana faɗin bazata raka baƙon nata bane tay ɗan jimm kafin ta kalleshi suka haɗa ido yana mata murmushi, jiki a sanyaye ta miƙe ya furta yauwa ko ita fa ya juya tana biye dashi, saida suka kusa ƙopar fita ya juyo yace to ya gode ta koma kada ya wahalar da Hajiya ta ɗan yi murmushi tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya ya amsa, falo ta dawo ta zauna kan kujera tayi jugum ta rasa ma tunanin da zata yi ganin abun take kamar ba'a gaske ba duk da ba yau aka fara zuwa neman aurenta ba wannan sai taji yayi mata girma sosae ba kamar daya haɗa da Hajiya, tana haka Amadu ya shigo da sallama ta ɗaga ido ta kalleshi ta amsa a hankali, nufo inda take yayi ya zauna a kujerar dake gefen tata ya ɗan yi shiru yana kallonta kamar mai nazarin wani abu ita kuma ta kauda idonta daga barin kallonshi, "Gwaggota lafiya kuwa?" taji muryarshi yana tambaya, kallonshi tayi da ɗan guntun murmushi tace mashi lafiya lou yace amman to ya ya ganta kamar wani abu na damunta ta ɗan yi shiru kafin tace mashi ba komai, shiru ya ɗanyi yanata kallonta can ya sake tambayarta to lafiya Kawu Mani yazo gidansu yaga bai ta6a zuwa ba tunda suke a gidan, shiru Gwaggo tayi tana tunanin mi zata ce mashi ya kawo shin tunda gashi yasan bai ta6a zuwa gidan ba can zuciyarta ta bata kawai ta faɗi mashi abunda ya kawo shi tunda dama ko ba yanzu ba dole zata faɗi mashi, ajiyar zuciya ta sauke tare da kallonshi kaman mai zullumin faɗi mashi shi kuma ya ƙura mata ido alamar ita yake jira tayi magana can dai tayi ƙarfin halin faɗi mashi Hajiya ce ta turo shi wai ya nemi aurenta, ɗan waro ido Amadun yay kafin da sauri yace "to kin amince mashi zaki aure shin???" a hankali ta girgiza kai kafin tace ce mashi tayi sai tayi shawara amman ita....kafin ta ƙarasa abunda take son faɗin kawai sai gani tayi ya kamo hannunta yace "Don Allah Gwaggota ki amince mashi kada ki ƙi kamar yadda kike yi a baya na roƙe ki, wllh ba wuce kiyi aure kikai ba tsofaffi tukuf ma zaki ga suna da aure tunda shi ibada ne, kinga in kika amince mashi muma a ƙalla zai zama muna da Baba a cikin gidan nan" shiru tayi tana kallon shi ta wani bangaren ta ɗan ji mamaki don bai ta6a nuna mata ya damu da tayi aure ba irin yanzu yawanci da anzo neman aurenta ta nuna bata so sai yace shikenan tunda haka take so, tana haka sai gani tayi ya saukko daga saman kujerar ya duƙa a saman guiwowinshi cikin marairaicewa yace "Don Allah Gwaggota ko don ni ki amince mashi nima dai ace inada wanda zan kira da sunan BABA ba tare dana haɗa da sunan shi ba, tun tasowa ta ba wanda nike kira da sunan Baba ba tare da nace Baba wane ba kamar Baba shehu, Baba musa da sauransu kinga yanzu in kika aure shi Baba zan rinƙa kiranshi ba yadda za'ai in haɗa da sunan shi nima a ƙalla in muna hira da wasu zance Babanmu ka za...." kasa ƙarasawa yay saboda ƙwallan da suka tarun mashi suna niyyar zubowa, wani irin tausayinshi ne Gwaggo taji ya kamata tun yana ɗan shekara shidda ya rasa mahaifinshi, girgiza hannunta yay ya furta "Don Allah Gwaggota..." ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi tace "baka tunanin ba lalle ya zama kamar uba a garekan ba kamar yadda yake faruwa sau da yawa wasu ma sai kaga sun raba uwa da ɗanta..." da sauri ya tari hanzarinta, "A'a Gwaggo ina da yaƙinin bazai yi hakan ba tunda kika ga Hajiya ta turo shi to tasan baida matsala ne, na tabbatar mutumin kirki ne ai ina ganin shi a gidan Hajiyar muna gaisawa, don Allah ki amince?" shiru tay tana kallon shi ƙwallan idon shi har sun zubo mashi can tace shikenan tunda haka yake so zata amince mashi, da sauri ya miƙe ya zauna gefenta tare da ƙanƙameta cikin tsananin farinciki ya shiga yi mata godiya harda su Kiss ya manna mata a gefen fuskarta ita dae sai dariya take zata iya cewa bata ta6a ganinshi cikin farinciki irin wannan ba in ma ta ta6a gani to ta manta, sakinta yay sai faman washe baki yake ya shiga laluban wayarshi yana faɗin bari ya sanar ma Fatuu wannan abun Farinciki, da sauri Gwaggo tace kada ya sanar mata yace a'a yakamata ta sani da zafi zafi, ƙoƙarin amshe wayar Gwaggon tayi ya miƙe yana dariya ya shiga yin safa da marwa a tsakar falon cikin harshen fullanci Gwaggon ke faɗin tana wasa dashi wai sai dariya yake itama yar dariyar take, tana fara yin ringing Fatun ta yanke sai gashi ta kira yana ɗauka ko gaisawa basu yi ba da sauri yace mata Albishirinta a ƙagauce ta amsa da goro fari ƙal yace banda shi ango sun ƙara samun Amarya a gidansu nan ya shiga faɗi mata zancen auren Gwaggo aikuwa wata uwar ƙarar murna ta saki tana faɗin Alhamdulillah abubuwan farinciki sai faruwa suke dasu Amadun yace Wllh kuwa da sauri tace mashi ina Gwaggon ya bata wayar bari ta maida Vedio call taga fuskar amarya yace to, duk Gwaggo na jin su da yake a speaker yasa kiran sai girgiza kai take tana ɗan murmushi, bayan an maida kiran na gani ya miƙa ma Gwaggon saida ta ɗan harareshi sannan ta amsa Fatuu na ganinta ta daddage ta rangaɗa guɗa duk da bama ta wani iya ba sosae Gwaggon tayi yar dariya, cikin washe baki ta gaishe da ita kafin ta shiga yi mata shaƙiyanci tana faɗin ashe dai da rabon za'a mata makeup na amare a ɗaura mata gwaggaro nan take Gwaggon ta tuna da lokacin da Fatun ta faɗi haka can shekarun baya kafin ta girma ta shiga yin dariya, da sauri Amadu ya fita ya kirawo Kamalu suka dawo falon nan suka haɗu suna ta mata iya shege har saida tace in suka isheta zata fasa Allah sannan suka shafa mata lafiya. Washe gari sai ga Kawu Mani ya kirawota wai ya kira yaji yadda suke nan take sanar mashi ta amince ma buƙatar shi, sosae ya nuna jin daɗin shi harda ce mata shi dama yasan zata amince don su jinin sa'a ne tayi murmushi kawai kafin tace mashi amman ko za'a ɗaura masu aure sai anyi na Amadu yace mata amman mi zai hana a riga yin nasu yadda zasu aurar dashi tare tace mashi ita dai tafi son a riga nashi kuma gidan nasu ma Haisam yasa za'a mashi gyara ne tunda anan zata zauna yace duk yadda take so haka za'ayi tunda anan take son zama lafiya lou ya rinƙa zuwa dama yana yawan zuwa katsinar ko can baya saida yayi tunanin yin mata anan yace alabashshi sai ya rinƙa biyanta kuɗin hayar zaman da take, da sauri tace mashi a'a ba sai yayi hakan ba yana murmushi yace to ai saboda ya fita hakkinsu tunda gidan gado ne tace mashi ai itama tana da kaso a ciki lafiya lou kawai dae fatan ta ya ruƙe su amana kada tayi dana sanin yin auren bayan tsawon lokaci, yar dariya mai sauti yayi yace "Kada ki damu Amaryata, Hajjaju tasan zan ruƙe amanarki shiyasa tayi man maganar ki ni kuma ina ganin ki mashin son ki ya soke man zuciya ba shiri na faɗa tarko" Yadda yayi Maganar har saida tayi dariya don ta fahimci ɗan barkwanci ne sai ga Gwaggo an saki jiki ana shan Love😍 Bayan wata guda aka fara aikin gidan nasu gadan gadan lokacin har Baban su Umar ya samu gida an siya mashi sun tashi Tk ma an saka ranar aurenshi daidai dana Amadu wato rana ɗaya za'a ɗaura masu aure, 6angare guda aka ware masu suke zaune kafin aikin yazo inda suke. Cikin sa'a Kamalu ya rubuta Jamb ya samu point da ake buƙata don yin karatu a Jami'ar daya cike wato Umaru Musa Yar'adua University Katsina (Umyuk), bayan sun yi post Utme cikin sa'a ya samu Admission don fara karatu inda zai yi Degree akan Computer Science, a lokacin sosae suke waya da Farha sun shaƙu da juna ta kai har kuɗi ta turo mashi don ya canza waya saboda in suna yin Vedio call wani lokacin wayar shi na basu matsala, lokacin daya yi ma kawu Amadu magana kan ya rakashi su sayi wayar jin itace ta turo mashi kuɗin saida ya tambayeshi mike tsakaninsu wai dama yana lura da yawan wayar da suke, Kamalun bai 6oye mashi yadda sukai da ita ba na cewa da tayi tana son su zamo abokai, sosae kawu Amadu yayi mamakin jin hakan, bayan an siyo wayar ne suka je nuna ma Gwaggo itama dai tayi mamakin jin Farha ce ta turo mashi kuɗi ya siya saida ta tambayi yadda akai suka san juna ya faɗi mata, sam Gwaggo bata kawo komai ba a ranta tayi tunanin jinin su ne ya haɗu tayi mashi Allah ya sanya Alkhairi, lokacin daya fara karatu ita kuma ta gama Degree ɗinta a Jami'ar Lagos ta nemi da a turo ta Katsina bautar ƙasa da yake suna da hanya sai gashi an turo ta Katsinar har saida Hajiya tayi mamaki lokacin da Hajiya Maryam ta sanar da ita zancen zuwan Farhar wurinta ta zauna don yin service kuma ita ta za6i hakan, lokacin da za ta zo harda uban sababbin kayan sawa da takalma da jakuna irin wanda samari ke amfani dasu a Makaranta ta kawo ma Kamalu, ranar data zo ta kama Friday da rana tunda Tk ya ɗaukkota daga Airport tasha gayun ƙananun kaya ta tambayeshi Kamal yace bai san ko yana nan ba amman bari in sunje bakin shagonsu sai su duba, lokacin da suka iso Kawu Amadu ne kawai a ciki Tk ya tambayeshi Kamalu yace bai nan yana School Farhar harda gaishe da kawu Amadun ba laifi ya ɗan saki fuska ya amsa mata tare da yi mata sannu da zuwa, bayan ta amsa ne ta tambayi kaman zuwa ƙarfe nawa zai dawo yace mata sai anyi La'asar daga haka suka wuce, suna zuwa parlon Hajiya lokacin tana zaune Farhar ta nufeta da gudu taje ta rungumeta Hajiya ta nuna farincikin zuwan ta sosae Tk ya tambayi ina zai kai kayanta Hajiya tace ya kai su Visitor room, bayan sun gama gaisawa Hajiya tayi mata Maganar abinci tace mata bata jin yunwa sai anjima tace to taje ta huta ko, koda taje ɗakin wanda tuni an gyara mata shi ta kwanta a gado kasa yin baccin tayi don ba wanda take son gani irin Kamal ƙarshe sai ta ɗauki wayarta ta shiga lallatsawa, tana haka akayi la'asar ta miƙe ta nufi toilet tayo wanka, shiryawa tayi da atampa mai kyau anyi mata straight gown ta kamata sosae tayi ɗaurin kallabin Zarah Buhari a wurin Fanan taga tana yawan yin shi kuma yana mata kyau shine itama take yi kuma yana mata kyau sosae harda yar kwalliya tayi duk da ita bata cika son yin kwalliya a fuskarta ba kamar Fanan, tana cikin shiryawa Hajiya ta shigo cikin ɗakin da sallama ta juyo tana kallonta da murmushi Hajiyar tace "au ni nayi zaton ma kina nan kinata bacci naga anyi La'asar gashi baki ci komai ba nace bari in zo in tashe ki ashe ke kina nan kina ta rangaɗa kwalliya", still murmushin take yi bata ce komai ba, "To wannan kwalliyar ta mecece daga zuwa kodai angon nawa anan yake shine zai zo yin sannu da zuwa?" dariya Farhar tayi tace mata No kawai tayi ne kuma tana son ta fita jikinta ya ɗan saki Hajiyar tace to ita ina ta sani da zata je, ɗan jimm tay kafin tace ko gidan su Zarah sai ta gaishe da Granny ɗinta, sosae Hajiya taji daɗin jin hakan don ya tabbatar mata da Farhar ta canza da gaske tace mata to tazo ta fara cin abinci kafin ta tafi suka nufi ƙopar fita harda kama Hajiyar tace wai bari ta taimaka mata taga bata yin tafiyar sosae Hajiya na dariya tace da wannan sandar tata sai tayi tafiyar da ita bata iya yi, lokacin da suka fito daga cikin corridor Saude na niyyar shiga Kitchen ganin su yasa ta dakata tana murmushi tana niyyar gaishe da Farha sai ji tayi ta rigata gaishe da ita Sauden ta amsa tare da yi mata anzo lafiya da tambayar yan'uwanta da Momynsu duk tace mata suna lafiya Hajiya ta tambayi Farhar a dining zata ci abincin tace a'a a kawo mata a parlor yadda tana ci suna hira Saude ta juya da sauri tana faɗin to bari ta kawo mata can suma suka nufo cikin parlon, a saman c-table aka shirya mata kayan abincin bayan tayi serving nata tace mata aci lafiya Farhar na ɗan murmushi tayi mata godiya, lokacin da Saude ta nufi hanyar Kitchen sosae take mamakin canzawar Farhar a ranta, ba wani sosae taci ba tace ta ƙoshi Hajiya dake yin kallo ta kalleta tace dama wannan ɗamammiyar rigar ai bazata bari taci wani abinci sosae ba basu son suna ɗinka wadatattun kaya suyi ta faman takura kai, murmushi kawai Farhar tayi itama ta maida idonta kan Tv tana kallon abunda Hajiya ke kallo can bayan wani ɗan lokaci ta miƙe ta nufi hanyar bedroom, bada daɗewa ba ta fito tana ruƙe da ƙatuwar leda mai tambarin Shopping Mall ɗin Mamanta, cikin parlon ta dawo daga bakin kujeru ta tsaya tace ma Hajiya zata je ta dawo ta ɗaga mata kai har zata juya tace mata to ina mayafi kuma ta kalleta tana ɗan yamutsa fuska tace takura mata yake gashi sai yayi ta faɗuwa saboda bata saba sakawa ba Hajiya tace mata amman bai kyautu kuma ai ta fita haka ba tana yar musulma kuma ma ba kyau fita hakan ai ta sani tunda tana zuwa islamiyya su kan su waɗannan kayan bai kamata tana saka su ba ta fita indai ba lullu6e jikinta zatayi ba komi mutum zai yi ya rinƙa tuna lahirar shi, ɗan murmushi tayi tace Ok zata gyara ta aje ledar ta juya don ta ɗaukko mayafi Hajiya ta bita da kallo tana murmushi sosae take jin daɗin yadda ta canza don inda da ne tayi mata Maganar shigar da tayi yamutsa fuska zatayi kuma bazata canza ba, gyale ta yafo daya shiga da atamfar saman kafaɗa duk da baida wani girma yadda ta yafan ya rufe mata bayanta bayan ta ɗauki ledar tayi ma Hajiya sai ta dawo, ko a bakin gate saida su Officer sukai Maganar canzawarta bayan ta gaishe su ta wuce, tana zuwa saitin shagon kallo ɗaya tayi ma na ciki ta gane Kamalun ne duk da ya juya baya yana sanye da riga da wando na light blue shadda, tsayawa tayi tana murmushi cikin zazzaƙar muryata tace a bata Sweet yace wane iri saida ta wurga idonta saitin ledojin Sweet ɗin taga wani ansa mango da sauri tace mashi shi yace Ok guda nawa tana yar dariya tace pack guda, ɗaukko jakar Sweet ɗin yayi yana juyowa idanunshi suka shiga cikin nata har saida yay alamun tsorata Farhar ta saka dariya, da tsananin mamaki yace da gaske itace tana murmushi ta ɗaga mashi gira tare da furta yes, "Amman yaushe kika zo?" still da mamaki ya tambaya tace mashi ɗazun ai tazo nan ta tambaye shi Uncle nashi yace bai dawo ba bai faɗi mashi bane yace mata lokacin daya dawo daga School ɗin shi kuma ya tafi kasuwa to basu haɗu ba shiyasa bai san data zo ba, "Amman ko fa yau da safe munyi waya baki faɗi man yau zaki zo ba" ɗan farfar tayi da ido tace "i want to give you a surprise" yana murmushi yace aikuwa gashi ta bashi shi har tsoro ma yaji daya ganta tana yar dariya tace ai ta gani, shiru sukai ta shiga jefa mashi wani kallo shi kuma yana ɗan murmushi can tace "Ka ƙara kyau" yar dariya yay duk dimples ɗinshi suka lotsa yace "ina wani kyau kullum ina zaryar School rana yana buguna" tace duk da haka ita taga ya ƙara kyau kodai saboda ya fara zuwa University yana haɗuwa da yan'mata shiyasa yake gyara masu kanshi, tayi Maganar tana mashi wani kallo yay yar dariya yace shida bai daɗe da fara zuwa ba kuma shi karatunshi ya saka a gaba ba ruwan shi da wasu yan'mata ta ɗan yamutsa fuska tace Allah yasa gaskiya yake faɗa mata, rantse mata yay kan shi ba ruwan shi da wasu yan'mata ta ɗan yi murmushi ta furta Better gara ya maida hankali yayi karatu ya bar duk wani shiriritar yin yan'mata ya furta mata in sha Allah, "Ka bar ni a tsaye haka ake welcoming baƙo" ta faɗa ta ɗan tura baki da sauri ya bata haƙuri yace ko zata shigo cikin shagon ga kujera ta girgiza mashi kai tace ciki zai shigar da ita zata gaisa da Grandma ɗin shi yace to, fitowa yay ya kulle ƙopar shago ta zagayo wurin shi yanata mata murmushi ganinta da kaya yace ta kawo ya ruƙe ta sakar mashi hannu guda suka kama tare suka nufi cikin gidan, faran faran Gwaggo ta tarbeta cikin sakin fuska a falo suka zauna ta gaishe da Gwaggon tana murmushi ta amsa mata tare da yi mata anzo lafiya da tambayar yan gidansu tace mata duk suna nan lafiya Kamalu yace ma Gwaggo tazo yin bautar ƙasa ne nan cikin fara'a tayi mata fatan alkhairi da fatan Allah ya bada sa'a yasa a gama lafiya ta amsa da Amin, miƙewa Gwaggo tayi ta fita daga cikin falon lokacin Farhar tace mashi kayan shi ne a cikin ledar akwae ma saura a gida bata iya ɗaukkowa sai dai in zata koma sai su je tare ya daukko, da mamaki ya buɗe ledar ya shiga duba kayan kafin da tsananin mamaki ya ɗago ya kalleta yace ya zata yi wannan hidiman haka sosae ta yamutsa mashi fuska tare da yi mashi wani kallo tace What are Friends for abunta nashi ne so bata son yana yi mata irin haka kawai inta bashi abu ya amsa shikenan, yana murmushi yace to tayi haƙuri yayi mata godiya tare da faɗin Allah shima ya bashi ikon kyautata mata haka tace bata buƙata iya haka da ya saki jiki da ita ya wadatar, ruƙe da tray mai ɗauke da kayan abinci Gwaggo ta dawo ta daura akan table ta matsar dashi gaban Farhar tana niyyar buɗe Warmer ɗin Farhar tace wllh ta ƙoshi yanzu taci abinci Gwaggon tace ai abun marmari ne taci ko ba yawa tunda ita baƙuwar su ce, Waina ce da miya taji alaiyahu da nama sai ƙamshi take Gwaggo ta kalleta tana murmushi tace ta dai iya cin waina ko tay yar dariya tace eh ana masu shi, bada yawa tasa ta zuba mata ba ta nufi Fridge ta ɗaukko mata ruwa da lemu ta kawo mata, bayan ta koma ta zauna Kamalu ya taso da kayan ya dawo wurin Gwaggo ya nuna mata yace ita ta kawo mashi tace ma akwae saura zasu je ya ɗaukko, duba kayan gwaggo ta shiga yi kafin ta ɗago da mamaki ta kalli Farha dake cin waina a nutse tace harda hidima haka banda wadda akai ai da ta bassu kada ɗawainiyar tayi yawa idonta a ƙasa tana ɗan murmushi tace mata a'a ba komai, godiya Gwaggon tayi mata da Addu'ar Allah ya saka da alkhairi, bayan ta gama ci harda ɗaukar tray ɗin zata fitar da sauri Kamalu ya miƙe ya kar6a yaje ya kai Kitchen bayan ya dawo tashi Gwaggo tayi ta fita, tambayoyi ta shiga yi mashi kan karatun shi yana bata amsa suna haka aka shigo siyan abu sai lokacin ya tuna da ya baro shago a buɗe yace mata zai koma shago zata zauna anan tace a'a bari su fita tare, bayan sun fito Kamalun yayi ma Gwaggo magana ta leƙo sukai sallama sannan suka fito shi ya shiga cikin shagon ita kuma ta tsaya daga gaba tana kallon yadda yake sallamar yaron da yazo siyayyar tana ta murmushi, bayan ya sallami yaron ya tafi tace mashi gaskiya irin wannan business ɗin bai dace dashi ba kamata yay ace a Haɗaɗɗan Office yake A.c na hura shi har saida yayi dariyar da haƙoran shi suka fito yace shi ina zai samu irin wannan aikin abunda ma duka yanzu ya fara karatun yace ai gara ma wannan sana'ar a cikin shago yake kuma akwae fanka a garinsu kafin yazo nan rake yake saidawa akan table wani lokacin cikin rana ma ta ɗan buɗa ido alamar mamaki, ganin tana ta tsayuwa yace mata ko zata shigo tace a'a bari ta wuce yaushe zai zo amsar sauran kayan yace ko in anyi Magrib daga masallaci sai ya shigo tace ok tare da ce mashi Bye, tana niyyar tafiya ya tsaidata ya miƙo mata ledar Sweet ɗin ta ɗan girgiza mashi kai alamar a'a ya ɗan mariraice mata fuska yace please wannan ce kyauta ta farko daya ta6a mata duk da ba wata mai yawa bace ta amsa zai ji daɗi in kuma bata son irin shi sai ya canza mata wani, murmushi tayi tace ba kowane Sweet take sha bane yace ok ta faɗi mashi wadda take sha sai ya kira Uncle ɗinshi tunda yana kasuwa ya taho mata da ita tace No ba sai yayi haka ba tunda wannan ya bata zata sha ta miƙa mashi hannu ya bata tayi mashi godiya kafin ta ɗaga farin hannunta fatt tana mashi bye bye shima yayi mata ta tafi ya leƙo kai yana kallonta itama tana yi tana waiwayen shi tana mashi murmushi har saida ta kusa gida sannan ya maida kan shi, sai gab da Magrib Amadu ya dawo lokacin daya ga kayan da Farha ta kawo ma Kamalun shima ya jinjina abun har yana faɗin Allah yasa dai kar yazama wata matsala Gwaggo tace Amin, bayan sun gama sallar Magrib Kamalu yace mashi zai je ya amso sauran kayan kamar yadda yace mata Amadun ya tafi shi kuma ya wuce part ɗin Hajiya, a parlor ya iske Farhar tana kallo da yake ba salla take yi ba Hajiya kuma na bedroom ɗinta, sosae ta nuna jin daɗin zuwan nashi ya zauna nan suka shiga yin hira, har aka kira sallar isha suna zaune tace mashi yaje yayi salla in ya dawo sai ta ɗaukko mashi yace to, koda aka gama yin sallar ya dawo hirar suka cigaba da yi har Hajiya ta fito ta iske su suka gaisa dashi cikin fara'a ta tambayi ya karatunshi yana dai maida hankali ko yace mata sosae, ita kanta Hajiya saida ta ɗan yi mamakin ganin yadda suka saba da juna ƙarshe saida Farhar ta matsa mashi suka ci abinci tare bayan sun gama yace mata zai tafi harda ce mashi ai gobe ba School ko yace ya baro Uncle ɗin shi yana jiranshi ne sannan taje ta ɗaukko mashi tace ma Hajiya zata rakashi ta dawo tace to, tare suka kama ledar kayan suna tafe suna hira har suka iso bakin shagon yayi mata godiya ta gaishe da Amadu ya amsa mata ya ɗan saki fuska kafin tayi ma Kamalun saida safe ta tafi yana shiga cikin shagon Amadu ya wurga mashi harara tun ma kafin yayi magana yana murmushi ya bashi haƙuri yace itace ta ruƙe shi da hira, a ɗan fusace Amadun yace shi kuma da yake tsoronta yake ji da bazai ce mata zai tafi ba Kamalun nata ɗan murmushi ya ƙara bashi haƙuri yace bazai sake ba, Bayan Farha ta koma saida Hajiya ta tambayeta yadda akai tasan Kamalu har suka saba haka tace mata a Abuja wurin bikin Yaya Nameer suka san juna itama Hajiyar bata kawo komai ba a ranta tayi tunanin jininsu ne ya haɗu don shima Kamal ɗin kamar Fatuu yake yana da farin jini dama kuma yawanci Mutum mai kyau haka yake da shiga rai, bayan sun tashi daga shagon sun shiga gidane Kamalu ya haɗa duka kayan yace ma Amadun ya ɗauki wanda yake so da sauri yace mashi a'a yayi amfani da kayanshi, marairaice mashi yayi yana mashi magiya da ƙyar ya ɗauki wasu jeans da t-shirt yace sun isa ya gode duk da haka saida ya ƙara mashi da agogo da takalma, Washe gari Gwaggo ta kira Fatuu anan take sanar mata game da abubuwan da Farha ta kawo ma Kamalu sosae tayi mamaki tace banda kuɗin da akace ta turo mashi ya canza waya Gwaggon tace mata wllh kuwa kaya sosae ta kawo mashi Fatun tace ita gaskiya abubuwan da take mashi basu kwanta mata a rai ba tunda ansan halinta duk da ta canza kada daga baya abu yazo ya zama wata matsala ko tace zata yi mashi gori, Gwaggo na murmushi tace to ai dai ba roƙonta akayi ba ita taji ta gani duk da dai tana kyautata mata zaton da zuciya ɗaya take mashi Fatun tace to Allah yasa amma dai duk da haka a daina amsar mata kaya zata kira Kamalun ma tayi mashi magana Gwaggon tace gashi can ɗaki bari ta bashi tace to, bayan sun gaisa ta tambayi ya karatu ya amsa mata tambayar shi tayi wai mike tsakaninshi da Farha ne yace mata shi wllh ba komai daga dai abotar data ce mashi tana son suyi shikenan Fatuu tace to ita bata son yana amsar mata abubuwa ko yace zai tambayeta wani abu don zai iya zama matsala duk abunda yake so ita ya kirata in sha Allahu indai baifi ƙarfinta ba zata mashi yace mata to tare da yi mata godiya daga baya sukai sallama. Bayan su Farha sun shiga Camp sosae take kiran Kamalun a waya su kuma yi Vedio call a lokacin aikin da ake yazo kan inda suke zaune aka buƙaci sai sun tashi Gwaggo ta yanke kama masu hayar inda zasu zauna kafin a gama anan unguwar, a bakin Kawu Mani Hajiya taji zancen hayar da Gwaggo zata kama ta kirata tace ba sai ta kama wata haya ba tunda ga wurin zama a gidanta su dawo nan kawai zuwa a gama aikin, ba dama ta musa mata tayi godiya sosae, a ɗakin Tk Amadu da Kamalu suka koma sai ita kuma Gwaggo Hajiya ta bata ɗakin dake kusa da nata, tun gwaggo bata saki jiki ba har dai ta saki in dai tana gida tare suke aikin gidan da Saude har Hajiya saida tayi mata magana kan waya sakata ta rinƙa yin aiki tana dariya tace mata ta saba ne in bata yi ba jikinta bai mata daɗi Hajiyar tace to kar dai taja mata sharri tunda ita dae bata sakata ta rinƙa yin aiki ba Maganar har saida taba Gwaggon da Saude dariya, zaman su a gidan gwanin daɗi tare suke cin Abinci da Hajiyar wani lokacin harda su Amadu in suna gida, ana haka su Farha suka fito daga Camp lokacin data dawo ta iskesu a gidan sosae ta nuna jin daɗin hakan shaƙuwa sosae taci gaba da shiga tsakaninsu da Kamalu koda yaushe in tana gida zaka gansu tare in kuma suna shago ta bishi can har Assignment in an ba Kamalun take taya shi suyi harda lesson suke yi ta koya mashi turanci da yake tana yawan yi mashi magana da turanci ya ta6a ce mata shi ba sosae ya iya ba shine take koya mashi ita kuma sai tace ya koya mata fullanci yadda suke abun gwanin sha'awa in suna yi a gaban su Hajiya da Gwaggo suyi ta burge su shidai Kawu Amadu yanzu ya zura masu ido kawai har abinci wani lokacin tare suke ci su biyu. A kwana a tashi cikin Fatuu nata ƙara girma yana gab da shiga wata tara, ta bangaren Arɗo kuwa tuni an kai shi Asibitin da taimakon Khalid anyi mashi duk abunda ya dace ba'a samu wata babbar lalura ba a tattare dashi ba kawai tsufa ne da gajiya sai yan ƙananun cututtuka an bashi magunguna da abubuwan da zai kiyaye ba laifi yanzu ya ƙara samun lafiya duk harkokin shi na mulki kuma Baffan su Fatuu ya ɗaura akai masu tsegumi nata yi. Lokacin da cikin Fatuu ya kai wata tara har an kammala aikin gidansu Gwaggo gida ya zama na yan gayu wanda yana ɗaya daga cikin gidaje masu kyaun gaske a unguwar abun sai wanda ya gani yanzu ta gate ake shiga gaba ɗaya harabar gidan interlock ne duk da bata da girma sosae don ginin ya cinye filin amman Mota biyu zata iya shiga daga jikin gidan gefen gate aka fitar ma da kawu Amadu babban shago wanda yana da ƙopa da zai rinƙa shiga gidan ta ciki, gidan part biyu ne na Gwaggo da kuma na Amadu sai akwai ɗaki da falo daban matsayin na baƙi, a kowane bangare na Gwaggo da Amadu akwae ɗan babban falo sai Bedroom guda biyu da toilet a tsakiyar su sai kuma Kitchen daya sha cabinet sai akwae toilet na waje cikin haraba, iya fentin gidan da yadda aka tsara ginin da ƙopopi zuwa winduna da fitilun da aka saka abun kallo ne kana ganin ginin zaka san ba ƙaramin kuɗi aka kashe ba su Gwaggo baki yaƙi rufuwa sai farinciki ake mutane yan'uwa da abokan arziƙi nata zuwa yin Allah ya sanya Alkhairi har Hajiya ma tazo taga gida itama ta yaba sosai ta kuma yi Addu'o'i, lokacin da Fatuu taga Vedion gidan zo kaga murna harda cewa ba don cikin jikinta yayi girma sosae ba da sai tayi tsallan murna Gwaggo nata dariya haka Mino ma data gani ita harda tsallan tayi tace bada daɗewa ba zata zo ta gani Gwaggo tace ta bari tunda ga bikin Amadu ya matso sai tazo tace ita dai tana son zuwa kusan wata biyar fa yanzu rabonta da Katsina in bikin yazo ta ƙara zuwa, Bayan gama ginin kuma sai ga kuɗi Haisam ya turo ma Kawu Amadu wai a siya furniture Gwaggo harda ƙwalla tayi ma Haisam da tasa aka kira mata shi Vedio call tace hidiman nan tayi yawa shima yaji da nashi hidindimun yace mata ba wani abu ai duk ɗaya ne, godiya sosae suka yi mashi harda Baffan su Fatuu ya yi mashi godiyar, Kawu mani ma yazo yaga gida ya yaba ya kuma yi Allah a sanya Alkhairi sannan shima ya bada gudunmawar shi ta siyan furniture har Baffan su Fatuu da Hajiya duk saida suka bada gudunmawar kuɗin siyan furniture daɗi har yayi ma Gwaggo yawa sai godiya take ga Allah, cikin sati guda aka zuba furniture ɗin gaba ɗaya Bedrooms ɗin part ɗin gwaggo an saka set na gadaje sai falon ma an saka kujeru masu kyau da carpet harda kayan kallo da labulaye komai dai na ƙawata wuri an saka kai kace part ɗin yarinyar mace ne, haka part ɗin Amadu a bedroom guda ɗaya an saka set ɗin gado sai falon an saka carpet da labulaye sai ɗayan ɗakin mai falo wanda yake matsayin na baƙi a bedroom ɗin irin ƙatuwar katifa da bata hawa gado aka saka da carpet da labulaye sai falon kujerun falon gwaggo na da aka gyara suka koma sababbi aka saka ko ina dai ya fito yayi kyau daidai daidai. Cikin Fatuu har yayi wata tara da yan kwanaki lokacin su twins shekararsu guda da wata biyu har sun yaye kan su don da kansu suka daina shan Nono, Ranar wata laraba da safe gidan ba kowa sai ita kaɗai da mai aikin su Fanan da Haisam na wurin aiki haka su twins ma suna makaranta tana cikin baccin safen data koma wani irin ciwon mara ya tasheta, jin tana jin fitsari yasa ta lalla6a ta tafi toilet don tayi, tana duƙawa don yin fitsarin taga discharge irin wanda ta gani da haihuwar su twins tana gani ta gane haihuwa ce ba arziƙi ta fito daga cikin toilet ɗin ta nufi wayarta dake a gefen filo ta shiga kiran Fanan dama kullum sai tace mata data ɗan ji ciwo ko yaya ne in bata gida tayi sauri ta kira ta, tana fara yin ringing Fanan ɗin ta ɗaga kafin Fatun tace wani abu ta rigata tambayar haihuwan yazo ne cikin nishi tace mata eh gata nan mararta ta fara mata ciwo da sauri tace Ok gata nan zuwa ta katse kiran, tana katse kiran mai aikin su ta shiga kira wadda babbar mace ce baturiya bayan ta ɗaga ko amsa gaisuwar da take mata bata yi ba cikin sauri ta bata umarnin taje part ɗin Fatuu ta fara labour ta taimaka mata ta shirya gata nan zuwa da sauri mai aikin ta amsa mata tana katse kiran ta nufi part ɗin Fatuu, bayan wasu mintuna Fanan ɗin ta iso a Motar asibitinsu tare da wasu nurses guda biyu lokacin da suka shiga bedroom ɗin da Fatuu take ta shirya da taimakon mai aikin nasu ciwon kuma ya ɗan ƙara tsananta ba 6ata lokaci suka ɗaurata akan wheelchair da nurses ɗin suka shigo da ita Fanan kuma cikin sauri ta ɗauki abubuwan da za'a buƙata dama ashirye suke, saida suka hau hanya sannan ta kira Haisam ta sanar mashi nan take hankalinshi ya tashi jin Babyn shi na naƙuda don bai manta yadda aka sha wanccan gumurzon ba da sauri yace ma Fanan gashi nan zuwa asibitin don Allah kada ta bari ta wahala sosae tace mashi to suyi mata addu'a, suna isa asibitin aka nufi labour room da ita aka shiga yi mata duk abunda ya dace kan kace mi naƙudar ta ida kankama gaba ɗaya Fanan ta ruɗe sai faman yi mata sannu da Addu'o'i take kaman zata mata kuka, cikin ikon Allah basu fi minti talatin da zuwa ba ta haiho san6aleliyar jaririya dama tun wurin scanning an faɗi masu mace ce sai gashi hasashen su ya tabbata zo kaga murna a wurin Fanan sam ta kasa rufe baki sai faman faɗin Alhamdulillah take, koda Haisam ya iso ai saidai ya taras da Baby shima har fuskarshi ta kasa 6oye farincikin sosae yaji daɗin yadda bata sha wahala ba kamar tasu twins, lokacin da aka bashi Babyn zuba mata ido yay yana kallonta da murmushi sak fuskar Fatuu ta ɗaukko in akwae abunda za'a ce ta ɗaukko nashi to ƙilan saidai ko farinshi don jajir take da gani zata fi Fatuu fari amman komai na fuskarta na Fatuu ne Fanan ma saida tace Zarah ta biyo, tun a asibitin bayan yayi mata huɗuba ya raɗa mata suna AISHA wato sunan Mahaifiyar Fatun, yan Nigeria sai farincikin jin haihuwar ake kowa daya ga Babyn a Vedio sai ya faɗi kamanninta da Fatuu, Sosae itama Fatun tayi farinciki ganin Babyn data haifa koda Fanan ta faɗi mata sunan da aka saka mata saida tayi ƙwalla wata irin ƙaunar yarinyar ta mamaye mata zuciya. Bayan sati biyu da Haihuwar suka iso Nigeria nan aka Shiga shirin yin suna wanda na iya yan Family ɗin su ne, sati guda da dawowarsu akayi sunan duk yan'uwa sun zo su Gwaggo da Hajiya har Aunty Mareeya ma tazo Farha dai na Katsina bata biyo Hajiya ba, su Hajia Zainab ma sun zo Fauzy dai ba'a zo da ita ba a Nasarawa aka barta don tayi nauyi sosae haihuwa ko yau ko gobe gashi itama an tabbatar da yan biyu ne, Aunty Laila ma ciki ne da ita har ya fito sosae don zaiyi wata biyar, Mino na ganin cikin Lailan ta ƙara shiga damuwa dama tana ta zura ido taga ta samu ciki amman shiru har yanzu kusan wata bakwai da yin aure, bayan an gama yin shagalin sunan da daddare Mino ta samu Fatuu a Bedroom ɗinta cikin sa'a ita kaɗai ce sai Baby Esha kamar yadda aka yanke za'a ringa kiranta, a bakin gado ta zauna Fatuu na kallonta ta gane akwae abunda ke damunta cike da kulawa tace "Amaryarmu ya akai kamar akwai abunda ke damun ki ko?" kai Minon ta ɗaga mata Fatun ta tattara hankalinta gaba ɗaya a kanta tace ta faɗi mata miye kaman zata yi kuka tace dama ce mata zata yi ita taga har yanzu bata samu ciki ba kuma ga Aunty Laila nan da aka yi bikinsu tare har ta samu nata harma ya girma Fatun tay kasaƙe tana kallonta tama rasa mi zata ce mata can ta tambayeta tana period lafiya lou da sauri tace mata eh tana yi kamar yadda ta saba kuma shina abunda tace mata sai anayi ake samun cikin sosae suke yi, kunya ce ta kama Fatun ta juyar da kanta gefe a ranta ta raya bata san ranar da Mino zata rabu da wauta ba, juyowa tayi Minon ta ƙura mata ido a nutse tace mata ta kwantar da hankalinta tunda ba wata matsala zata samu dama ba daga anyi aure ake samu ba kowa da yadda yake har ta bata misali da Fanan tace mata bata ga har yanzu itama bata samu ba kuma ga Auntyn su Nameer ma itama har yanzu bata haihu ba....katseta Minon tayi idanunta sun cika da ƙwalla tace yanzu itama bazata haihun ba kenan da sauri Fatuu tace "ni bance bazaki haihu ba, kawai na baki misali ne don haka ki kwantar da hankalinki don shi in ka tada hankalinka to baka samu, sannan kada ki sake kiyi ma wani irin wannan Maganar da kikai man za'a ɗauke ki mara kunya ne in dae kina da wata matsala game da gidan auren ki ni zaki rinƙa sanar mawa kamar yadda kikai yanzu" da sauri ta ɗaga mata kai Fatuu tace ta saki ranta in sha Allahu kwanan nan zata samu Minon tayi ɗan murmushi kawai, miƙewa tay zata tafi Fatuu ta tambayeta anan zata kwana ne tace mata eh tace to ta kwanta anan mana tunda ita kaɗai zata kwana su twins ba anan zasu kwana ba Minon tay ɗan jim kafin da ƙyar tace mata Ya Nameer yace a part ɗinshi zasu kwana Fatun tay ɗan murmushi tare da ɗaga mata kai tace taje saida safe ta juya ta tafi Fatuu nata kallonta har ta fice ta ɗan girgiza kai a ranta ta raya ta zata haihuwar sauƙi ne da ita, dasu Gwaggo zasu tafi Fatuu ta bata akwatuna set guda data siyo ma Amadu acan na lefe tace mata da set biyu ma taso ta siyo to kayan zasu yi yawa ne Gwaggon tace ai dama sun siya set guda, da shi Amadun ma set biyu yaso a siya tace mashi tunda Fatun tace zata taho da wasu a barsu haka. Bayan sati biyu da yin sunan Fatuu Fauzy ta haiho twins duk mata saidai ita Cs aka mata, yaran saidai ace Tubarkallah masha Allah sak Sameer suka biyo gasu identical ne suma kamar na Fatuu amman su ta gashinsu ake banbanta su Hassanar nata baƙi ne wuluk hussainar kuma kalar na sameer ne baida baƙi sosae kowa yaga yaran sai ya yaba zo kaga murna wurin dangin Fauzy karma Aunty Mareeya taji sam bakinta ya kasa rufuwa sai kiranta ake itama ana mata barka, saboda aikin da aka mata akace baza'ai taron suna ba saidai duk akaje Nasarawa aka yi masu barka aka kuma yi ma maijego alheri sabon Baba Sameer sai nan nan yake da Babies ɗin da kuma mamansu ko kunyar mutane bai ji yaran sun ci sunan Mahaifiyar Sameer data Fauzy wato Zainab da Haleema. Sati guda da haihuwar Fauzy Fatuu ta tafi Katsina dama haihuwar ta tsaidata lokacin saura sati ukku bikin Amadu da Tk, saida taje ta ƙara jinjina yadda gidan nasu ya haɗu, tana zuwa Washe gari suka tafi kasuwa da gwaggon don ƙarasa siyayyar kayan lefen daga can wurin K.b tailor suka wuce dama Fatuu tasa Kawu Amadu ya kai mashi wasu kaya ya ɗinka lokacin da suka je har ya gama su suka bashi wasu cikin wanda suka siyo Fatuu tace don Allah nan da sati ɗaya suke son su kai lefen za'ai, yana dariya yace ai tasan bai mata wasa ko don kada ya 6ata ran Maigidanshi Haisam itama saida tayi dariya don ta fahimci da biyu yayi Maganar saboda tun farkon fara kawo mashi ɗinkinta da akai, bayan zuwan Fatun tayi ma Aunty Mareeya magana kan tana son magunguna masu kyau da Haulat zata yi amfani dasu ta can bangaren Haulat ɗin ma tana amfani da wasu da aka kawo mata daga Nijar, kwana biyu da zuwan Fatuu aka kai lefen Tk akwatuna set ukku masu guda huɗu guda sha biyu kenan kuma bako ƙwandalar Tk a ciki komai Hajiya tayi mashi sai su Senator da Hajiya Maryam da suka bada gudunmawa, a yadda Hajiya ta tsara a nan part ɗinta zai zauna Senator har Maganar siya mashi gida yayi amman tace a kusa da ita take son ya zauna, sam hakan baima Hajiya Maryam daɗi ba tace ma Hajiyar ba gwara ta bari a siya mashi gida ba yanzu nan part ɗinta a ina zai wani zauna Hajiyar tace lafiya lau tunda falonta yana da girma sosae zata sa a maida shi bangare biyu sai suyi amfani da ɗaya bedrooms kuma tunda guda huɗu ne biyu ita ke amfani dasu biyu kuma na baƙi sai su zauna a ɗaya in kuma biyu suke buƙata sai ta basu na baƙin sai ɗayan nata ya koma na baƙi Hajiya Maryam ɗin ta nuna yanzu kuma idan wata hidima ta kama ko suka zo taya bedroom ɗaya zai ishe su in ta basu biyu Hajiyar tace to ba ga Bedroom ɗinta ba sannan ga wangamemen gidan Yayanta can a G.r.a sai a tafi can, duk da haka ta nuna hakan bai mata ba ƙarshe Hajiya tace shikenan in taga da takura daga baya zata sa a ƙara wasu Bedrooms ɗin a can ɗayan bangaren falon wurin Dining Area tunda akwae fili sai a barsu matsayin na baƙi amman tare zata zauna da Tukur don matsayin ɗa yake a wurinta yaron da tun yana ɗan ƙarami aka bata shi miye don ta zauna tare da iyalinshi dole Hajiya Maryam ta haƙura, har kiran Tk Hajiya tayi ta faɗi mashi yadda ta yanke game da zaman su tare tace bata san ko hakan zai takura mashi ba amman in yafi son zama daban lafiya lou sai a siya mashi gidan bawan Allah harda kukan daɗin shi yace mata Wllh dama damuwarshi kenan yadda zai rabu da ita yana kuka yake mata godiya da Addu'o'i, har iyayenshi ya kira yana kuka ya faɗi masu irin gatan da Hajiya tayi mashi Mahaifinshi har saida yazo yayi mata godiya shima harda kukan nashi, to Kamar yadda Hajiyar tace haka akayi ma falon nata ba raba shi akai ba kawai anyi wani ɗan gini mai kamar ado ta yadda falon ya koma bangare biyu sai Kitchen ma da yake yana da faɗi da tsawo shima aka maida shi bangare biyu sannan gaba ɗaya gidan aka yi mashi Fenti mai kyau don ba wani gyara da yake buƙata komai lafiya lou don gini ne bana wasa ba. Ana saura sati biyu bikin aka kai lefen Haulat akwatuna takwas harda babbar ghana must go, ba laifi an zuba manyan kaya kai kace lefen budurwa ne budurwar ma wadda tayi sa'a sai faman yabo ake farinciki ya cika iyayenta ita kanta Haulat ɗin harda kukan daɗinta don ko a aurenta na farko bata samu kaya haka ba duk da shima dai anyi mata kayan ba laifi, bukukuwa nata matsowa ana ta shirye shirye bangaren Amadu ba wani shagali da za'ai don Haulat ta nuna bata so dama shima Amadun ba damunshi sukai ba kawai dai zata yi Wa'azi sai Walima bayan an kawota, bangaren Tk kuma shi za'ayi kamu ana gobe ɗaurin aure sai Walima bayan an kawo Amarya amman can bangaren Amaryar zata yi wasu abubuwan, ana saura sati guda Hajiya ta kira Gwaggo a waya tace mata mi zai hana ta bada dama a ɗaura auranta tare dana Amadun lokacin duk mutane sun haɗu don kowa ya shaida tana ganin hakan zai fi dole Gwaggon tace to duk da ita a yadda taso su Kawu Manin suje can wurin kawunta shibaɗo a ɗaura auren nasu acan Daura, ana saura kwana biyar bikin Amarya Mino ta iso Fatuu ce taje Airport ta ɗaukko ta, ana sauran kwana ukku su Yadikko suka iso shi Baffan su Fatuu sai daren ɗaurin aure zai zo, sosae sukai Al'ajabin ganin yadda aka maida gidan sunata yabawa, a ranar akayi ma Amaryar Tk jere Bedroom biyu wanda Saude ke amfani dashi da kuma na kusa dashi Hajiya ta basu don gado biyu aka mata sai haɗaɗɗun kujeru dasu kayan kallo haka Kitchen ma an zuba mata kaya sosae daga yanayin kayan zaka fahimci suna da hali, washe gari lokacin saura kwana biyu akayi ma Haulat itama jeren an mata tsadaddun saitin gado da kujeru harda kayan kallo amman su Amadu ne ya siya mata da freezer sai Kitchen ma anyi mata kaya ba laifi harda su cooker gas da sauran kayan amfani na zamani. Alhamdulillah Ranar Asabar da Misalin ƙarfe sha biyu da rabi na rana Jama'a suka shaida ɗaurin auren Amadu da Haulat sai Khadija (Gwaggo) da Kawu Mani a masallacin gidan Hajiya su ango Kawu Amadu ansha babbar rigar farar shadda sai washe baki yake ganin abun yake kamar a mafarki, sosae mutane suka halarci ɗaurin auren har Nameer yazo da kuma Senator, misalin ƙarfe biyu bayan anyi sallar Azahar aka ɗaura auren Tukur da Asma'u wadda ake cema Husna a Masallacin G.r.a dake layout Senator ne ya kar6ar mashi auren sai fatan Allah yasa alkhairi yaba ma'auratan zaman Lafiya, Gidan Gwaggo ya cika da yan biki duk an sha anko baka jin bakin kowa sai Aunty Mareeya sai shegantaka suke ma Gwaggo har saida suka matsa mata ita da Fatuu sukai mata kwalliya sai ga amarya Gwaggo ta fito fess kai kace ba ita ba tasha leshi mai kyau gaba ɗaya duk sun cikata da kunya, bayan sallar La'asar jerin Motoci suka je daukko Amaryar Tk bayan an kawota aka ɗaukko Haulat abun sai san barka komai ya tafi daidai dangin Hajiya sun yi ma Tk kara tun daga kan yan Daura da yan nan Katsina duk sunzo har Hajiya Maryam ma tazo haka Fanan dasu Mom ɗin Haisam duk sun zo, ta bangaren Tk ɗinma danginshi duk sun zo, Washe gari da wuri akai Walima saboda masu tafiya su Hajiya Maryam da Mom har Nameer ranar zai koma Mino dai ta roƙi ya barta ta ƙara kwana biyu ya amince, a ranar da daddare angwaye suka shiga ɗakunan Amaren nasu sai fatan Allah yasa Albarka ya bada zuriya ɗayyiba. Bayan sati guda da yin bikin su Fatuu suka koma lokacin Esha ta fara girma tubarkallah washe garin tafiyar su ranar Lahadi ango Kawu Mani yazo gidan harda akwatunan shi guda biyar na kaya da yayi ma Gwaggon da Kayan abinci sosae ta nuna jin daɗinta tayi mashi godiya, ta ɗauka zai tafi ne sai taga ba haka ba ashe zuwa yay shima wurin Amaryar tashi duk da ba haka taso ba taso ace sai bayan kaman wata guda da bikin su Amadu saidai ba yadda zatayi dole ta bashi haɗin kai suma suka shiga shan amarci sauƙin ta ma kowa da bangaren shi bawan Allah Kamalu an bar shi da tsaron shago sauƙin shi ma Farha na nan kuma yana zuwa Makaranta. Bayan wata guda da bikin su Amadu aka ɗaura auren Ashiru wato gaye da Amaryarshi Jamila mai awara dama itace Hajiya ta haɗasu yanzu ta zama babbar budurwa har ma ta gama karatunta a Health technology Haisam ne ya ɗauki nauyin karatun da bikin ma shida Hajiya suka yi mata kayan ɗaki shima gayen sun bashi gudunmawa sosae Fatuu ma ta aiko mashi da tata gudunmawar kuɗin ta wurin Gwaggo sai fatan Allah yasa Albarka a cikin auren Amin....... 102 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ .......Zaman su Hajiya da Husnah matar Tk gwanin daɗi, sosae take mata biyayya dama kuma Tk ya jaddada mata irin muhimmancinta a wajen shi, haka ma Saude suna shiri da ita kusan tare ma suke yin aiyukan gidan Abinci ma wasu lokuttan tare suke ci da Hajiyar har Farha ma ba laifi tana shiri da ita da yake Husnar wayayya ce gata fara tana da kyau ba laifi da yake fulanin Gombe ce, ba don Tk ya shigo birni ba da wannan ta wuce ajin auren shi, A bangaren Haulat ma wannan ko ban faɗa ba ansan zata yi ma Gwaggo biyayya tamkar uwa da ɗiya suke zamansu haka aiyukan gidan ma tare suke da yake tun kafin a ɗaura Auranta da Kawu Mani ya nuna bai son taci gaba da aikin da take yi to tun bayan ma da aka ɗaura auran bata je wurin aikin ba yanzu ma shirin ajewa take, Haulat har ce mata tayi ta bari ta rinƙa gyara mata part ɗinta tana yin Abinci Gwaggon tace to ita ta zauna tayi mi, Auransu na yin wata biyu upper ɗin aikinsu Tk da Amadu ta fito gaba ɗaya sun samu aiki a bangaren Lab na Teaching hospital kowa yayi farinciki har gida Gwaggo da Haulat suka je yi ma Hajiya Godiya don ita tasa aka samar masu aikin. Za6e ya taho wanda kuma na canza shuwagabanni ne ma'ana waɗanda ke akan mulki tenure ɗin su ce ta ƙarshe, daga cikin masu sauka harda mahaifin su Sameer sannan cikin yan takarar neman shugabancin ƙasar nan da suka fito a ƙarƙashin Jam'iya mai mulki harda Mahaifinsu Haisam wato Senator Ali Adamu wanda mutane suka tursasa mashi dole ya fito don shi ba so yake ba ciki harda shugaban ƙasan da zai sauka shi ya fidda matsayin ɗan takararshi, Bayan ansha gwagwarmayar zaben fidda gwani na jam'iyar mai mulki cikin sa'a Senator Ali ne ya lashe saura Babban za6e nan da wata ukku, cikin lokacin aka shiga gudanar da Campaign saƙo da lunguna na ƙasar nan, A Katsina gidan Hajiya na cikin wuraren da ake raba kayan Campaign su Tk da Amadu na cikin masu gudanar da Campaign saƙo da lunguna tun ma kafin ayi za6en mutane keta hasashen Senator Ali ne zai lashe don sosae yay farinjini wurin al'umma a kudu da arewa ko ina ya samu kar6uwa dama shugaban da zai sauka ba musulmi bane kuma sai ya fiddo Senator Alin matsayin ɗan takarar shi, a Masallatai ma ana ta mashi Addu'o'i kan in Alkairi ne Allah ya bashi ko ina sai faɗin kyawawan halayenshi ake ana cewa ba don kuɗi yake takara ba don da nashi kuɗin ma aiki yake ma Al'umma yana taimakon su talakaw, ana gab da yin Babban za6e su Fatuu suka zo don yin za6en suma anan Abuja suka sauka. Alhamdulillah ranar za6e tazo cikin lumana aka fara gudanar da zaben an zuba matakan tsaro ko ta ina, bayan an kammala aka shiga zaman jiran sakamako wanda sai dare aka bayyana, Allah dai ya amince Senator Ali ne wanda ya lashe kujerar shugabancin ƙasa zo kaga murna wurin mutane gaba ɗaya Social Media ta ɗauka cikin gari aka fara celebrations wani abun sai ma a Katsina ban tunanin Mutane zasu yi bacci ranar saboda tsabar murna, Bayan an bayyana sakamakon Hajiya ta kira shi don ta taya shi murna da fatan Alkhairi yana ɗaukar wayar kawai sai ya saka mata kuka wanda har cikin ranta taji shi ita kanta tasan ba son mulkin yake ba, rarrashin shi ta shiga yi tace yayi haƙuri ya rungumi mulkin tunda Allah ya bashi cikin muryar kuka ya amsa mata tare da roƙonta kan a tayashi da Addu'a tana murmushi tace wannan koda yaushe cikin yi mashi take yanzun kuma zata ƙara zage damtse yayi mata godiya ta shiga yi mashi Addu'o'in Allah ya dafa mashi ya kare shi yanata amsawa da Amin daga baya sukai sallama, haka akaita kiraye kirayen wayoyi ana taya yan'uwa murna. Bayan wasu watanni aka gabatar da inauguration Ceremony a Eagle Square dake Abuja wuri ya cika maƙil da Jama'a an sha anko mai tambarin jam'iya da hoton President Ali da Vice ɗin shi wanda christian ne su Mom da Aunty an sha gwaggwaro suna gefen mai girma shugaban ƙasa harda Hajiya ma tana a wurin dasu Hajiya Maryam harda Hajiya Zainab da maigidanta dasu Sameer da iyalan sabon shugaban ƙasan su Haisam harda su Fatuu da Mino duk suna a wurin Laila ma tazo da Mijinta tare da kyakkyawar Babynta data haifa wadda taci sunan surukarta wato Safeeya suna ce mata Mimi, su Gwaggo dai suna a gida suna kallo a Tv, bayan Senator Ali yayi rantsuwar karbar office aka tabbatar dashi a matsayin cikakken shugaban ƙasa, daga nan rakiyar tsohon shugaban ƙasa aka tafi bakin city gate ana dawowa aka raka President Ali Adamu Aso rock presidential Villa abun na Allah ne sai ga su Fatuu da Mino yan fillo a Villa, daga cikin waɗanda suka lashe kujerun yan Majalissar tarayya harda Alhaji Lawal mahaifin Khalid, bayan sati ɗaya da komawar su Mom Villa su Haisam suka tafi wannan karon harda Nameer da Mino don zaici gaba da karatun shi itama Mino har ya samar mata makaranta zata yi Nursing a can, Bayan tafiyarsu Fatuu da sati biyu matar Tk ta haiho san6aleliyar budurwa mai kama da mamanta Hajiya na jin Haihuwar ta dawo don tunda aka rantsar da shugaban ƙasa sun ƙi bari ta dawo, zo kaga murna a wurin Tk an zama baba tun a ranar ya raɗa mata sunan Hajiya wato Hauwa'u suka yanke zasu rinƙa kiranta da Jiddah Hajiya tace a rinƙa kiranta da sunanta kada a wani 6oye mata suna shikenan ita ta samu ƙawa kuma takwara, Haulat ma a lokacin ciki ne da ita wurin wata shidda da yake Husnar ta rigata samu, tunda Mino taji batun Haihuwar matar Tk gaba ɗaya ta ƙara shiga damuwa da rashin Haihuwarta har Asibiti Nameer ɗin yasa suka je ganin yadda ta damu aka tabbatar masu da lafiyar su lou nan ya shiga rarrashinta yana nuna mata lokacin haihuwar ne bai yi ba kuma shi koda bata haihu ba bazai damu ba zasu yi zaman su a haka ko kuma su amshi yaro a wurin Adda Fatunta tunda ita tana haihuwa akai akai yasan bazata hana su ba wannan Maganar tashi tasa ta ɗan kwantar da hankalinta ta maida hankali kan karatunta, ganin Mino na karatu yasa Fatuu tayi ma Haisam magana kan in zai yuwu itama tana son taci gaba da karatun Medicine yace mata shima yana son hakan saidai matsalan shekarun suna da yawa gashi kuma suna gab da komawa Nigeria amman in tana so ita sai ta zauna anan taci gaba da Karatun ko kuma ta bari in suka koma Nigeria sai tayi Karatun a India inda Fanan tayi shekarun karatun basu kai na nan America ba ta amince da hakan, tuni Farha ta gama bautar ƙasanta amman taƙi komawa gida tay zaune abunta gidan Hajiya kuma ba saboda kowa bane face Kamalu. Bayan President Ali ya hau mulki da wasu watanni ya za6i Ministocin da zasu yi aiki tare ciki harda Hajiya Maryam ita ya za6a matsayin Minister of Industry, Trade and Investment wato Ministan Masana'antu, Kasuwanci da Zuba jari wanda babban muƙami ne acikin ministoci kuma ya bi cancanta ne shiyasa ya bata saboda kasuwanci ta karanta gata babbar yar kasuwa, Haisam ma yaso ya bashi Minister of Communication and Digital Economy lokacin daya tuntu6eshi kan yana son bashi muƙamin Haisam ɗin ya nuna mashi hakan zai iya zama wani abun magana ace yaba ɗan shi Minister Daddyn nashi yace shi ba ruwan shi tunda cancanta ya bi ba son rai ba amman Haisam ɗin ya bashi haƙuri yace yaba wani wanda ya cancanta saboda shi yafi son ya maida hankali akan Companyn shi da ake cikin ginawa anan Abuja, ƙarshe sai dai wani ɗin aka ba dama kujerar sonta ake, Mahaifin Sameer ma ya bashi Minister of Foreign affairs wato Ministan harkokin waje haka Kawunsu Mani mijin Gwaggo ya bashi P.A ɗin shi haka dai akaita rarraba muƙamai saidai duk cancanta ya bi bayan an tantance su a National Assembly suka shiga gudanar da aiyukansu su Hajiya Maryam an samu dalilin soke kallabi da hujja, Bayan shigar su Hajiya Maryam Office tace ma Farha ta dawo Lagos don ta kula da ƙannanta saboda ita yanzu bata cika zama a Lagos ba, gaba ɗaya ita da Kamal sun shiga damuwar rabuwa da juna don sun shaƙu sosae haka dai suka rabun ta tafi Abuja don Hajiya Maryam ɗin na can Villa a apartment ɗin da Ministoci ke zama daga baya Farhar tare da Dad ɗin su da ƙannan nata suka koma Lagos saboda karatun su da kuma aikin Dad ɗin su, su Gwaggo Matar P.A Duniya sabuwa jin daɗi na musamman ake tuni har ta fara canzawa gashi wani ikon Allah sosae Kawu Mani ke ji da ita duk da tafi sauran matanshi manyan taka, cikin Haulat na cika wata tara ta haiho ƙaton saurayi mai kama da Kawu Amadu sak kowa yayi murna karma Fatuu taji Lokacin data ga Vedio ɗin jaririn ji tayi Kamar tayi tsuntsuwa ta taho yaron yaci sunan mahaifin Amadu wato Abdullahi, Tun bayan da Farha ta koma gida ta rasa mike mata daɗi don gaba ɗaya kewar Kamal ta addabeta duk da suna yin waya sosae suna kuma yin Vedio call duk hakan bai mata ba so take kawai ta gan su a tare hakan yasa ta gane ta kamu da son shi ta shiga tunanin yadda zata sanar mashi, ana haka Cousin brother ɗinta wato ɗan Yayan Mahaifinta mai suna Emran shima Bature ne ɗan America da suke soyayya dashi duk iyayensu sun san da Maganar yayi mata Maganar aure tunda ta gama karatu, yana mata zancen aure taji gaba ɗaya ya fitar mata a rai bata son auren shi hakan yasa tace mashi ba yanzu zata yi aure ba don zata cigaba da Karatu ne ya nuna mata ai lafiya lou zasu iya yin auren sai taci gaba da karatun a America, ganin ya takura mata da Maganar ita kuma sai kauce kauce take mashi yaƙi ya k Ƙyaleta ƙarshe ma sai cewa yayi zai ma Dad ɗin shi Maganar suyi Magana da Dad ɗinta sai kawai ta fito mashi a mutum tace mashi itafa ta daina son shi don haka bazata aure shi ba, sosae hankalinshi ya tashi da yake Vedio call suke ta faɗi mashi hakan harda ƙwallan shi yana faɗin ya zata yi mashi haka bayan suna son junansu duk an sani yanata zaman jiranta har ta gama karatu kuma sai yanzu tace bata son shi, magiya ya shiga yi mata kan in laifi yayi mata tayi haƙuri ta faɗi mashi zai gyara in kuma wani abu take so ko minene ko nawa yake ta faɗi mashi zai siya mata amman don Allah kar ta guje shi don itace rayuwar shi bazai iya rayuwa ba tare da ita ba, duk yadda yay da ita taƙi canza ra'ayi ƙarshe ma sai ta faɗi mashi ta samu wani ne shi take son ta aura aukuwa wannan Maganar ba ƙaramin dugunzuma ran shi tayi ba, bayan sun gama yin wayar zugudum tayi ta rasa mike mata daɗi don tabbas tasan Emran na masifar sonta sosae yake mata ɗawainiya kullum cikin turo mata kuɗi yake kuma itama tana son shi amman yanzu gaba ɗaya taji ya fitar mata a rai ba wanda ke mata yawo a cikin zuciya sai Kamal, sanin tabbas Emran ɗin zai faɗi ma iyayenta abunda ya faru kuma za'a iya kiranta a tambayeta waye wanda tace yanzu shi take so yasa ta yanke faɗi ma Kamal cewa tana son shi, Vedio call ta kira shi lokacin da yamma ne bai daɗe da dawowa daga Makaranta ba yayi wanka ya ɗan kwanta yana hutawa kafin a kira Magrib, yana murmushi suka gaisa daga haka tayi shiru tana ta kallonshi ya lura kaman tana cikin damuwa hakan yasa ya tambayeta wani abu na damunta ne ta ɗaga mashi kai alamar eh, jin haka yasa shi tashi zaune da sauri cikin nuna kulawa ya tambayi mike damunta ne, shiru ta ɗan yi kafin tace mashi in yaji damuwarta zai mata magani ne da sauri yace in yana da ikon yin hakan zai yi tace yayi alƙawari yace mata eh, "Kamal ina son ka, kuma so nike muyi Aure ni da kai" Kamar saukar aradu haka yaji Maganar gaba ɗaya ya zaro idanun shi yana kallonta cikin rawar murya yace amma dai tana mashi wasa ne ko ta girgiza mashi kai kafin tace da gaske take bayan ta dawo ne ta gane ta kamu da son shi, gaban shi ne ya shiga faɗuwa don bai ta6a zaton zatayi mashi irin wannan Maganar ba koda suke shiri da juna, gaba ɗaya rasa amsar da zai bata yayi sai kallonta kawai yake itama haka can tace mashi yayi shiru bai ce komai ba gashi yayi mata alƙawarin maganin damuwarta da ƙyar ya buɗe baki yace mata shi ai baisan wannan ce damuwarta ba, da ɗan alamun tashin hankali tace kenan bai amince da soyayyarta ba, "No Farha, kawai dai ina ganin Soyayya tsakaninmu bazata yuwu ba tunda kinga muna da bambanci sosae kuma kince so kike muyi aure ni kuma yanzu ba yadda za'ai in yi aure saboda ban daɗe da fara yin karatu ba kinga ba aiki nike ba da zan iya auren ki" da yanayin damuwa yayi Maganar itama fuskarta a yamutse tace mashi ba wani bambancin dake tsakanin su tunda ai duk ɗaya suke a wurin Allah kuma ai ba dole sai ana aiki za'ayi aure ba tunda yana yin business lafiya lou zasu iya yin aure sai a faɗaɗa business ɗin, ganin dai da gaske take yasa shi bata haƙuri yace gara su ci gaba da ƙawancensu su bar Maganar soyayya da aure don abu ne da shi yasan ba mai yuwuwa bane a tsakanin su ba lalle gaba ɗaya a amince masu ba ba kamar shi za'a ga yayi ƙarami da yin aure, idanunta ne suka ciko da ƙwalla cikin karyayyar murya tace yanzu duk da yana da ikon cire mata damuwa shine zai watsa mata ƙasa a ido tunda take dashi tana jin wannan ce buƙata ta farko data zo mashi da ita amman shine bazai taimaketa ba ya amince mata kuma da yake cewa baza'a amince masu ba sai dai in basu nuna suna son junansu ba sannan Maganar yayi ƙarami ai tasan shekarunshi yana da shekaru 26 ɗin ne zai ce bai isa aure ba wasu ma basu kai shekarun shi ba suke yin aure wani ma Matar ta girme shi suke yin auren balle su da ya girmeta, duk tabi ta ruɗa shi ganin yadda take magana tana yin ƙwalla sai bata haƙuri yake tace ita ba wannan take so ba kawae ya amince mata don in yaƙi za'a mata auren dole ne kuma ita shi take so in bai aureta ba to zata mutu kowa ya huta, zo kaga ido a wurin ɗan fillo yaji zancen za'a mutu saboda shi a razane ya shiga roƙonta kan ta daina cewa haka yanzu ta ɗan bashi lokaci zai yi shawara tunda yanzu tazo mashi da Maganar yana buƙatar yayi shawara idanunta sharkaf da ƙwalla tace har tsawon wane lokaci zai yi shawarar yace bada daɗewa ba zai kirata tace shikenan tana jiran shi, tana yanke kiran hannun shi har rawa yake wurin kiran Fatuu saida ta yanke sai gashi ta kira suka gaisa ta tambayi mutanen gidan da karatun shi ya amsa mata tana jin yanayin muryarshi ta tambayeshi ya akai ne da damuwa yace mata akwae matsala ne da sauri ta tambayi miya faru nan ya shiga faɗi mata yadda sukai da Farha ita kanta ta jinjina abun tace mashi to ita dae a shawarce ya rabu da ita don ta tabbatar ba abu bane mai yuwuwa ƙarshenta rayuka ne zasu 6aci ba kamar yanzu da Mamanta take babba a da ma ba son talaka suke ba balle yanzu ita kanta Farhar don ta nuna ta canza ne amman ba ƙaunar talaka take ba, nan ta kwashe komai daya ta6a shiga tsakanin su ta faɗi mashi tace koda ace auren ya yuwu a tsakaninsu to bata tunanin zata mutunta yan'uwansu don ance mai hali baya barin halin shi don haka ya bata haƙuri kawae kada wani tsara kalamenta su ruɗe shi gara taga bai mata daidai ba akan abunda zai je ya dawo ya amsa mata da to sukai sallama, zaune yay jugum bayan sun gama yin wayar gaba ɗaya ya rasa mike mashi daɗi Maganar Fatuu ta kashe mashi jiki sosae, suna gama yin wayar Gwaggo Fatuu ta kira bayan sun gaisa ta kwashe komai ta faɗi mata itama sosae ta jinjina abun ta kuma goyi bayan abunda Fatun tace mashi tace gara haka zama lafiya yafi zama ɗan sarki, Kamalu na zaunen har aka kira Magrib ya tashi don yaje masallaci jikinshi duk yayi sanyi lakwas, tun akan hanyarsu ta zuwa Kawu Amadu ya lura da kamar akwae abunda ke damunshi ya tambayeshi amman sai yace mashi ba komai ya gaji ne Amadun yace mashi halan kuma yayi baccin yamma ya bashi amsa da eh yace shi yasa, bayan an gama sallar sun dawo suna niyyar tsayawa shago Gwaggo ta kira Amadu ta tambayi sun dawo daga salla ne yace mata eh gasu nan sun tsaya shago tace to su shigo shida Kamalun tana son ganin su yace to, a falonta suka isketa zaune suma duk suka nemi wuri suka zauna cikin kwantar da murya ta fara magana idonta akan Kamalu tace taji yadda sukai da Farha a wurin Fatuu tana son ya sani ba wai ana ƙoƙarin hana shi yin soyayya da ita bane kawae ana gudun matsala ne don duk abunda Fatun ta faɗa mashi gaskiya ne ya faru don haka kamar yadda sukai da ita ya bata haƙuri shi ya fi don ko ya amince mata mawuyacin abu ne a barta ta aure shi, kai Kamalun ya jinjina a sanyaye yace to zai yi yadda suka ce da alamun rashin fahimta kawu Amadu ya tambayi mike faruwa ne tsakaninshi da Farhar Gwaggo ta kwashe komai ta faɗi mashi, shima jinjina abun yay yace ina ai ba abu bane mai yuwuwa ma shi dama tunda yaga take takenta yasan da wuya bata ce tana son shi ba to gara ya bata haƙuri kawae don ko kowa ya amince mamarta yasan bazata ta6a yarda wai ta aure shi ba an auri mijin ɗiyarta tayi ma mutane tijara ina ga kuma yanzu ace ɗiyar tata za'a aura ai sai yaƙi tsakaninsu balle yanzu da ta zama wata a ƙasa ita kanta Farhar ai ba kanwar lasa bace kawai dai don suna shiri ne yasa yake ganin kamar bata da matsala, ɗan murmushi Gwaggo tayi tace ƙilan da gaske ta canza tunda tun kafin tasan Kamalun ta canza sai ai mata kyakkyawan zato Amadun yace to ko dai ita lafiya lou wannan Maman tata ba lafiya lou ba, haka suka dingi tattaunawa daga baya suka fito suka koma shago, bayan sallar isha yana shago sai ga kiran Farha saida ya fito daga shagon ya nufi gate ɗin shiga gida sannan yay picking, bayan ya ɗauka tace yay keeping nata tana ta jira kuma yace bada daɗewa ba zai kirata, haƙuri ya bata yace dama yana niyyar kiran nata bai gidane amman gashi nan zai je ɗaki sai suyi magana tace Ok, bayan ya shiga cikin ɗakin da yake zaune ya nufi katifa ya zauna saida yay ƙoƙarin daidaita natsuwarshi sannan ya fara mata magana ya nuna mata yayi magana da yan'uwan shi kanta gaskiya duk sun nuna ba abu bane da zai yuwu don haka yana bata haƙuri ba wai don bai sonta ba sai don ba'a goyi baya ba, "Nasan saboda abubuwan da suka ta6a faruwa tsakani na da Sister ɗinka ne yasa zasu ƙi goyon bayan ka aure ne amman ai i'm a changed person now, na canza tun ba yanzu ba kuma nayi dana sanin komai bazan sake ba, yanzu nasan da mai kuɗi da wanda baya dashi duk ɗaya ne at least they should give us chance zan tabbatar masu da na canza gaba ɗaya bazan basu matsala ba" cikin breaking voice take Maganar gaba ɗaya tausayinta ya kama shi don daga yadda take yin Maganar ya tabbatar da gaske tana son shi kuma yaji ya amince da cewa ta canza ɗin, jin yayi shiru tace mashi in shi bai son tane to zata haƙura amman ya sani tana ƙaunarshi kuma ta fara son shi ne tunda ta fara ganinshi wannan dalilin ne yasa suka shaƙu bata gane hakan bane sai yanzu da sauri yace mata a'a wllh shima yanzu yaji yana son ta to amman kowa gani yake hakan ba mai yuwuwa bane za'a iya samun matsala don ba lalle iyayenta su Amince ba, katse shi tayi tace ita buƙatarta itace shima ya sota ya kuma amince zai aureta Maganar iyayenta zata yi duk yadda zata yi in ma basu amince ba tasa su amince yace mata shikenan shima yana sonta kuma zai je yanzu suyi magana da gwaggon shi zai nuna mata ta canza yasan zata amince tunda tana da sauƙin kai tace Ok tare da yi mashi godiya yana murmushi yace to ta daina yin kuka bai jin daɗin hakan ace tana kuka saboda shi, a hankali tace ai ba kuka take ba yace shida ya santa sosae ai daya ji muryarta zai gane tace to ta bari sai kuma ta ƙara cewa ai duk laifin shi ne da son shi yay mata babban kamu yay yar dariya yace to ai shidai yasan abota suke bai san ya akai abun ya koma haka ba nan ta shiga bashi labarin bayan ta dawo gida gaba ɗaya ta shiga damuwar rashin shi a kusa da ita kullum cikin tunaninshi take nan ta gane son shi take yace to ai shima duk hakan ya faru dashi bayan tafiyarta ko abinci bai mashi daɗi duk sai ya rinƙa jin shi kamar mara lafiya har Uncle ɗin shi saida ya gane saboda tafiyarta ne ya shiga damuwa haka a School ma Friends ɗinshi suna ta tambayarshi mike damunshi koda ya faɗi masu saboda tafiyarta ne sai suka ce sonta yake shi kuma ya ƙaryata su yace kawai abota suke, tana murmushi tace duk sun faɗa son juna ba tare da sun sani ba yace hakane, daga haka suka shiga shan soyayya Farha ba wasa dama gata ruwa biyu ta wani bangaren a wurinta ba abun kunya bane don ta riga cewa tana son shi nan fa ta shiga yi mashi kalamai harda faɗi mashi irin soyayyar da zasu sha in suka zama married couple, shima Kamalun ba laifi ya shigo birni ya iya kalaman soyayya masu daɗi, sun ɗan ɗauki lokaci suna wayar kafin Farhar tace mashi ga Brother ɗinta yazo zata taimaka mashi yayi wani Assignment Kamalun yace Ok sukai sallama cike da nuna ƙaunar juna, bayan gama wayar zaune Kamal yay yanata sakin murmushi wani irin nashaɗi yake ji sai yanzu yake jin son Farhar sosae na shigarshi amman ada bai ta6a tunanin jin yana sonta ba don gani yake tafi ƙarfin shi ta ko ina, yana haka ya tuna da kalaman su Gwaggo zuciyar shi ta bashi yaje ya faɗi ma Gwaggon yadda sukai da ita da sauri ya miƙe ya nufi hanyar fita, bayan ya fito part ɗin Gwaggon ya nufa lokacin daya shiga a parlor ya isketa zaune tana kallo ruƙe da Abdallah yaron Amadu yana bacci, ciki ya shiga gabanshi na ɗan faɗuwa saboda fargabar kada ta ƙi amincewa da zancen Farhar, bayan ya zauna yay mata sannu da fulatanci idonta akan shi ta amsa mashi daga haka ya sunkuyar da kai ya rasa ta yadda zai sanar mata, tana ɗan murmushi da fullanci tace mashi ya akai ne ya ɗago cikin kama kai yace dama sunyi magana da Farhar ne Gwaggon tace to ya sukai da ita nan ya faɗi mata abunda tace na ta canza yanzu tasan mai kuɗi da talaka duk ɗaya ne bazata bada matsala ba in aka bata dama za'a tabbatar da haka, yar dariya Gwaggo tay tana kallon shi tace to ai su dama ba matsalarta suke hange ba ta iyayenta da za'a iya samu ba kamar Mahaifiyarta, da sauri ya tari numfashin Gwaggon yace suma tace ita tasan yadda zata sa su amince Gwaggon tay shiru kamar mai nazarin wani abu can ta tambayeshi yana Son Farhar ne da sauri ya sunkuyar da kai alamar kunya tace ita ya bata amsa ba wani sunkuyar da kai ba a yadda yake ya ɗaga mata kai alamar eh yana sonta tay ɗan jimm tanata kallon shi bayan ɗan wani lokaci tace ya tashi yaje zuwa da safe zata neme shi yace to tare da miƙewa yay mata saida safe ta amsa da Allah ya basu Alkhairi, bayan tafiyar shi tunani ta shiga yi a cikin ranta ita dai sam bata son Al'amarin ya haifar da fitina ƙarshe ta yanke zuwa ta sanar ma Hajiya kawai. Washe gari ya kama Juma'a da safe wurin ƙarfe sha ɗaya da rabi Gwaggo ta nufi gidan Hajiya sai da ta tsaya a bakin gate suka gaisa da Securities wanda yanzu sun kai su Biyar don bayan Senator ya zama shugaban ƙasa an ƙaro wasu, bayan ta shiga a parlor bangaren Hajiyar ta isketa zaune tana ruƙe da ɗiyar Tk tana mata wasa da abubuwan wasa, da murmushi Gwaggo ta ƙarasa cikin parlon Hajiya ta ɗago tana mata maraba bayan ta zauna kan kujera suka gaisa, "Ana wasa da ƙawa ne" Gwaggo ta faɗa tana yar dariya Hajiyar tace wai ta hana uwar yin aiki ne shine ta riƙe mata ita take mata wayo duk su kai yar dariya, shiru Gwaggo tayi ta rasa ta ina zata fara yi mata Maganar data kawo ta don sai kuma taji tana jin nauyi, "Ya akai Amaryar Mani kinyi shiru koda wani abune?" Hajiya ta faɗa idonta akan Gwaggon tana murmushi itama murmushin take mata tace eh, "sai kuma ki kama kiyi shiru koda yake mufa yanzu surukai ne ko, to ina jin ki ya akai ne Allah yasa in ji Alkhairi" yar dariya Gwaggo tayi jin abunda Hajiyar tace na su surukai ne, a nutse ta fara faɗi mata tiryan tiryan yadda Kamal yay da Farha Hajiya ta ɗan ta6e baki tana murmushi take sauraronta har ta gama, "To Ke Dije Matar Mani ina ruwan ki da shiga harkar yara irin haka, ta bayyana mashi tana son shi in shima yana sonta sai kiyi masu fatan alkhairi ba shikenan ba" shiru Gwaggo ta ɗanyi kafin tace "Dama ni kawai ina gudun abunda zaije ya dawo ne shiyasa", "Mi zai je ya dawon?" ta tambaya ta kafeta da ido da ƙyar Gwaggon tace mata can bangaren iyayen Farhar kar azo hakan bai masu daɗi ba ƙarshe abun yazo ya haifar da bacin rai, "Uhm, to ke kin isa ki hana faruwar wani abun ne, yaran yanzu ana hanasu abunda suke so ne, kina iya kiga ai kin hanashi yin tarayya da ita su zagaye can suna soyayyarsu ƙarshe kuma abunda kike gudun yazo ya faru don haka ki rabu dasu ayi masu fatan alkhairi ba abunda zai faru face abunda Ubangiji ya ƙaddaro zai faru", kai Gwaggo ta jinjina tace hakane Allah ya tabbatar da alkhairi Hajiyar ta amsa da Amin tace shikenan, Gwaggo har taji ta ɗan samu natsuwa bayan wani lokaci tayi mata sallama ta tafi. A ranar Minister Hajiya Maryam ta sauka Lagos dama duk Friday take dawowa sai ranar Lahadi da yamma ta koma a yadda suka tsara da maigidan nata wani lokacin shi zaije can Abujar tare da yara, sosae sukai murnar zuwan Momyn nasu tayi shiga ta alfarma ada ma tayi ado balle yanzu da suke da ƙasa, bayan an gama murnar zuwan nata Bedroom ɗin Daddyn su ta wuce dama shiya ɗaukkota daga Airport, da daddare tare suka ci abinci cikin nishaɗi bayan sun gama suka koma falo nan ta shiga tambayar yaran nata buƙatunsu kowa na faɗi da aka zo kan Farha yamutsa fuska tay tace ita bata da wata buƙata kawai so take su kasance tare koda yaushe don kula da yaran nan na bata wahala Hajiya Maryam ɗin na dariya tace to wace wahala take sha abunda akwae masu aiki ba girki take masu ba ba wanki da guga take masu ba haka ba shara take ba Farhar tace duk da haka basu barin kunnuwanta su huta Hajiya Maryam ɗin tace to ta ɗan ƙara haƙuri bada jimawa ba zasu koma Abuja baki ɗaya sai suci gaba da yin School acan nan kuma da Weekend ko lokacin hutu sai su rinƙa zuwa nan fa su Abraham suka shiga yin murna, sun ɗan dauki lokaci a falon kafin sukai ma juna saida safe kowa ya wuce part ɗin shi itama suka wuce tare da Dr Mohammad part ɗin shi suna saƙale da hannun juna, Washe gari Asabar tun da wuri aka kai yaran gidan islamiyya ya rage sai Farha don ita tunda tayi sauka ta daina zuwa, wuraren ƙarfe goma suka zauna yin breakfast duk sunyi wanka sai ƙamshi suke, Farha ce ta fara tashi daga kujerarta alamar ta ƙoshi Dad ɗinta yace ta jira shi a parlor zasu yi magana tace Ok, a tare suka gama da Hajiya Maryam ɗin suka nufi parlon duk suka zazzauna tun ma kafin Dad ɗin yayi magana ta yanke a ranta Maganar Emran zai mata, bayan sun zauna a nutse da turanci Dad ɗin nata ya fara mata magana yace mike faruwa ne tsakaninsu da Emran ya kirashi cikin tashin hankali yace tace bazata aure shi ba gaba ɗaya ya tada ma iyayen shi hankali suma sun kira shi kan Maganar, da alamun mamaki Hajiya Maryam ta maimaita bazata aure shi ba Dad ɗin yace haka Emran ɗin yace mashi tace, kallon Farha tayi tace miya faru tsakanin su ne da zata ce haka ta fara yamutsa fuska ta kasa yin magana Dad ɗinta yace kar taji komai ta faɗi masu in wani ƙwaƙƙwaran dalili ne zasu goya mata baya, muryarta kaman zata yi kuka tace ita ta daina son shi gaskiya ta samu wani wanda take so shi zata aura, a tare iyayen nata suka kalli juna alamar mamaki, "Yaushe kika samu wanin da mu bamu sani ba?" Hajiya Maryam ta tambaya Farhar ta shiga motsa baki kafin tace sun ɗan daɗe tare sun fi shekara, tambayarta Dad ɗinsu yay waye shi kuma a ina yake saida cikinta ya ɗan kaɗa fargabar faɗin ko waye ta kamata ba kowa take tsoron yaji ko waye ba face Hajiya Maryam don inda Dad ɗinta ne kaɗai bazata ji komai ba zata faɗi mashi, Mom ɗin su ce ta ɗan ɗaga murya tace ita suke saurare suna da abun yi, da ƙyar ta tattaro ƙwarin gwuiwa idonta akan Dad ɗinsu tace a Katsina y ake Yayan abokiyar zaman Sis Fanan ne, ɗan waro ido Hajiya Maryam tay tace wace abokiyar zaman Fanan ɗin badai wannan dangin shanun take nufi ba cikin tura baki Farhar tace ita, wata gigitacciyar tsawa data daka mata sai da suka tsorata su duka hada Dad ɗin a fusace tace "tsabar kin raina mu yasa kike dubar idanun mu kina faɗin Mutumin daji zaki kawo mana mu aura maki!!!!" idanun Farhar ne suka ciko da ƙwalla tana tura baki tace ai ba a daji yake ba ko yana nan gidan kakar shi a Katsina kuma yanzu haka yana cikin yin Degree ɗin shi a Umyuk, "Over my dead body.....!!! Wllh bazaki auri wannan dangin ƙarnin ba, anya ma kuwa kina cikin hankali ki...Not at all, Farha dana sani bazata ta6a son wani ɗan wannan Family ɗin ba so kuma na aure there must to be something behind all this..." har huci take tana Maganar cikin kuka Farhar tace ita Wllh itace kuma shi take so ai talaka da mai kuɗi duk ɗaya ne a wurin Allah aikuwa tun kafin ta rufe baki Hajiya Maryam ɗin ta yunƙura tare da kai hannu zata maketa da sauri ta goce tare da miƙewa ta nufi Dad ɗinsu ta faɗa jikinshi tare da ƙanƙame shi tana kuka tana faɗin ita Allah she will not marry Emran don bata son shi Kamal take so shi zata aura, aikuwa Mom ɗin ta ƙara yin kukan kura zata kai mata bugu Dad ɗin ya tare ta yana girgiza mata kai yace abi komai a hankali kada ta ji mata ciwo a fusace tace ai gara ta lahanta ta tunda ta raina mutane bata da hankali har su zata zo ma da wannan Maganar to in ma bata cikin hankalinta ne gara tun wuri ta dawo cikin shi don matuƙar tana raye bazata ta6a auren shi ba har taya ma aure zai yuwu tsakaninsu ai kalar zaren ba kalar yadin bane, ɗago kan Farhar Dad ɗin su yay yana kallon fuskarta da tayi jage jage da hawaye ta sigar lallashi yace mata ba gara ta auri Emran ba shida ya gina rayuwar shi yana da komai wannan da take so tace yanzu yake cikin yin karatu yaushe ya gama har ya samu aiki tunda ba yadda za'ai suyi auri bai da hanyar samun kuɗi, cikin muryar kuka tace ai yana yin business Dad ɗin ya tambayi wani irin Business tace suna da provision store a jikin gidansu tun kafin ta rufe baki cike da takaici Hajiya maryam ta kai hannu ta ciro hular kanta ta jefa mata a fuska Farha ta fashe da kuka tare da miƙewa ta nufi hanyar Bedroom tana tafiya tana bubbuga ƙafa tana faɗin ita Wllh shi zata aura itama Sis Fanan ba wanda take so aka bata ba cikin zafin nama Hajiya Maryam ta yunkura zata bi bayanta da sauri Dr ya riƙo hannunta ta juyo ta kalleshi tana huci kamar zakanya ya girgiza mata kai tare da yi mata alamar ta zauna, bayan ta koma ta zauna cikin kwantar da murya ya fara lallashinta tare da nuna mata komai a hankali yakamata a bi shi yaro ɗan lallashi ne in ta kwantar da hankalinta cikin rarrashi da kalamai sai taga tayi nasara akanta, haka ya dingi kwatanta mata har ta ɗan saukko ta miƙe tace bari ta sameta shima ya miƙe suka nufi ɗakin Farhar, lokacin da suka shiga tana saman gado ta kife fuskarta sai rizgar kuka take kai kace an faɗi mata saƙon uwarta ta mutu ne, a bakin gado duk suka zauna cikin kwantar da murya Hajiya Maryam ɗin ta kira sunanta shiru bata amsa ba saida ta ƙara sannan cikin kuka ta amsa tace ta tashi zasu yi magana ta fara ƙoƙarin ɗagowa idanunta har sunyi ja, zama tayi tana cigaba da yin kukan Mom ɗin tasu ta kai hannu tana goge mata tana faɗin ya isa, bayan ta ɗan tsagaita ne ta tambayeta yadda akai suka haɗu da Kamal ɗin cikin disashshiyar murya tace mata a wurin bikin Ya Nameer ne ta taho zata je yin liƙi shine ya bugeta bai gani ba har purse ɗinta ta faɗi ya bata haƙuri ya ɗaukko mata to tun daga nan taji ya burgeta daga baya ne tasan shi Yayan Fatuu ne har suka yi exchanging phone number suka fara gaisawa daga haka suka shaƙu shine ma dalilin daya sa taje bautar ƙasa Katsina, wani murmushin takaici Mom ɗin tayi tace "i know, wannan ba yin kan ki bane asiri ne" wani kallo Farhar tayi mata Hajiya Maryam ɗin ta ɗaga mata gira cike da tabbatarwa tace yess asiri ne ke ɗawainiya da ita Farhar tace amman shi ai bai santa ba ko sai ranar suka fara haɗuwa taya zata ce asiri yay mata tana murmushi tace mata ai su dama mutanen daji irinsu da an haifi yaro ake tsafe jikinshi don ya kasance yadda ake so to su tana jin na asirin nasara akai masu wannan dalilin ne yasa har Ƙanwarshi tayi nasarar auran Haisam ba don ta kai matsayin ya aureta ba kuma ya kasa sakinta haka Nameer ma shima abun ya faɗa kanshi yana ganin ƙanwarsu yaji yana sonta to itama kusan hakan ne, shiru Farha tay da alamun maganar ta ɗan yi tasiri a zuciyarta ta shiga tunanin ko shiyasa lokacin daya bugeta ta kasa yi mashi faɗa sai ma ji tay ya burgeta ko asirin ne ya shigeta can kuma wani bangare na zuciyarta ya shiga raya mata amman da asirin ne miyasa tunda suka haɗun bata ji tana son shi ba sai daga baya kuma koda ta furta mashi tana son shi farko bai amince ba kuma yan gidan su ma basu amince ba, koda ta faɗi ma Hajiya Maryam cewa itace fa ta fara cewa tana son shi kuma yangidan su da suka ji basu amince ba cewa sukai su haƙura gudun matsala sai cewa tay ai duk dubara ce sun san cewa sun riga sun asirce ta dole bazata iya haƙura dashi ba, shiru Farha tayi tana nazarin maganar a cikin ranta wani bangare na zuciyarta ya ƙi gasgata zancen asirin wani bangare kuma na son gasgatawa, lokaci guda ta fara ganin fuskar Kamalu ɗauke da ƙayataccen murmushin shi da maganarshi mai daɗi wata zuciyar ta raya mata yanzu shikenan sai ta haƙura dashi ƙilan ma Mom ɗin nata duk daɗin baki ne tayi mata ba wani abu ba, kamo hannunta Hajiya Maryam tay tace kada ta bari asirinsu yay tasiri akanta tazo taƙi mai sonta da gaskiya wanda zai treating ɗinta kamar Queen wanda zai mata duk abunda take so wannan kuma ƙarshe zata yi dana sani ne don ba iya ruƙeta zai yi ba kawai zai yi auren jari ne da ita don haka ta cire shi a ranta, shiru Farhar tayi tana kallonta yayin da zuciyarta ke ƙara tabbatar mata da wayau ne Mom ɗin nasu ke mata in ta rabu da Kamal kanta tayi mawa dama danginshi ba so suke ba dama, wani irin son Kamal ɗin ne taji ya taso mata cikin yamutsa fuska tace ma Mom ɗin ita ta tabbatar ba Asiri bane Allah ne ya saka mata son shi ita dai shi take so Wllh yanzu bata jin son Emran, wata uwar harara Mom ɗin ta wurga mata tare da sakin hannunta a fusace tace to tunda ita keda kanta ai sai ta aureshi ta gani daga haka ta tashi fuuu ta nufi hanyar barin ɗakin Farhar ta fashe da sabon kuka tana buga katifa Dad ɗinta ya matsa tare da jawota jikinshi ya rungumeta yana faɗin shikenan tayi shiru kada taja ma kanta ciwo cikin kuka take faɗin "Dad i love him, help me marry him pls" shiru yay yana shafa bayanta shi in don tashi ne indai har yaron yana da hali mai kyau to zai amince ta aure shi don mutum ne mai tsananin son yaranshi dama kuma haka turawa suke da son yara gashi suna ba yaran su yanci sam bai son abunda zai tada masu hankali ko ya 6ata masu rai shiyasa duk abunda suke so to yana son shi, jin ta ɗan lafa da yin kuka yasashi ɗagota yace ta kwantar da hankalinta indai har yaron baida matsala to yana tare da ita zai yi bakin ƙoƙarinshi ya ga ya taimaka mata ta samu abunda take so da sauri tace mashi wllh baida matsala ya kira Hajiya ya tambayeta yana da ilimin addini kuma yana da ƙokari gashi yana da ƙoƙarin neman na kan shi sam baida kwaɗayi don ko abu tayi mashi da ƙyar yake amsa, murmushi Dad ɗin yayi yace yayi kyau ya tambayi tana da hoton shi ya gani da sauri tace eh ta juya tana laluban wayarta, bayan ta ɗaukko ta shiga gallery ta dawo jikin Dad ɗin ta shiga nuna mashi hotunan Kamal wasu tare sukai wasu kuma shi kaɗai yana murmushi yace yana da kyau ta ɗaga kai ya sake cewa amman kamar ta girmeshi a shekaru tace a'a ya ɗan girmeta yace Ok yana son ta kwantar da hankalinta duk abunda Allah ya ƙaddaro shine zai faru ta ɗaga mashi kai, Hajiya Maryam na fita ɗakinta ta nufa a zuciye tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna ta shiga cize baki abun ya matuƙar daure mata kai wai ace Farha data sani itace zata ce tana son yaron wannan dangin tabbas bata tunanin yin kanta ne, a fusace ta kai hannu ta rarumo wayarta ta shiga kiran Hajiya bayan tayi ringing Hajiyar ta ɗauka murya ciki ciki ta gaishe da ita ta amsa daga haka tayi shiru Hajiyar tace ya akai ne taji muryarta wani iri ai kaman tana jira ta miƙe tsaye yadda zata ji daɗin kora bayani ta shiga faɗin wai Farha ce tazo masu da wani banzan zance na bata son wanda ke sonta ɗan dangin shanun nan take so ashe ma dalilin zuwan ta wurinta kenan yin service duk saboda shi ne, Murmushi Hajiya tayi tace ai tasan da Maganar suna son junansu, da tsananin mamaki Hajiya Maryam ɗin tace amman shine kuma ta ƙyale su bata hana abun ba, "To akan mi zan hana Maryam, yara suna son junansu", "Saboda bai kai yayi soyayya da ita ba Hajjaju", yar dariya Hajiya tayi "saboda shi ba mutum bane ko mi?", "Mutum ne amman wanda bai kai yayi soyayya da ita ba" ɗan ta6e baki Hajiya tayi tace "to ni a wurina ya akai shiyasa ban dakatar da abun ba" yarfa hannu Hajiya Maryam tayi muryarta har tana sarƙewa wurin faɗin "Wai Hajjaju miyasa a koda yaushe kike goyon bayan bare ne taya za'ace wai kamar Farha ta auri wannan dangin ƙarnin" faɗaɗa dariya Hajiya tayi tace "A'a Maryam banda sharri, anan ai ba bare na goyi baya ba tamun na goya ma baya tunda ita ta fara nuna tana son shi hasali ma su dangin yaron ba so suke ba don kakarshi har nan ta same ni tayi man magana kan hakan kinga da bare na goya ma baya to zan ƙi abun ne", cikin huci tace ai duk wannan munafurci ne don sun san sun asirce Farhar Hajiya ta shiga girgiza kai tace "anya Maryam, taya akai wai kike neman barin imanin ki yay rauni ne, komai kice anyi asiri", Murya kamar zata yi kuka tace to in ba asirin ba taya Farha zata kamu da son wannan yaron Hajiyar tace ta in Allah ya ƙaddaro hakan don haka tana bata shawara tabi komai a hankali in har Allah ya ƙaddaro aure tsakanin su to dole zasu yi, ai kamar Hajiyar ta watsa mata garwashin wuta a cikin zuciya cike da cin alwashi tace Wllh bazata bari Farha ta auri wannan yaron ba Hajiya tace ai shikenan ɗiyarta ce tayi duk abunda take ganin yayi mata Hajiya Maryam ɗin tace zatayi kuma ta faɗi ma kakar yaron in ma wani abu sukai ma ɗiyarta suyi gaggawar warware shi in ba haka ba duk abunda ya faru dasu to su suka siya ma kansu Hajiya tace tsakaninsu ne tazo da kanta sai ta faɗi masu, tana niyyar kashe wayar Hajiya tace "Maryam ina son ki sani yadda kike uwar zamani haka Farha take ɗiyar zamani sannan yin jayyaya da ikon Allah tamkar ɗaukar dutsen Dala ba gammo ne don haka ina mai baki shawara da ki bi komai a hankali sannan kibar ikon Allah yay aikin shi, ki gaida man da kowa" daga haka ta yanke wayar, komawa Hajiya Maryam tay ta zauna da6as saman gado ta shiga juya Maganar Hajiya ta ƙarshe nan take ta yanke wani abu a ranta, gaba ɗaya yinin ranar a cikin ɗaki Farha ta wuni koda lokacin cin abinci yay aka aiko kiranta ƙin fita tayi ƙarshe saidai Dad ɗin su yazo ya fito da ita suna zuwa Dining ɗin Hajiya Maryam ta miƙe ta bar wurin hakan yasa Farhar fashewa da kuka Dad ɗinta ya shiga rarrashinta, ganin abunda ya faru yasa da daddare Dad ɗin bai matsa ma Farhar ta fito ba bayan sun gama cin abincin ya ɗauki nata ya kai mata ɗaki saida ya zauna taci sannan ya baro ɗakin, a daren ta kira Fanan tana kuka ta faɗi mata abunda ke faruwa itama rarrashinta ta shiga yi tace tunda Dad ya nuna zai taimaka mata ta kwantar da hankalinta tasan Momynsu nada zuciya dole bazata goyi bayan abun ba ta cikin sauƙi amman itama tana goyon bayan abunda take so don haka zata tayata da Addu'a itama ta dage da yi tace to tare da yi mata godiya, suna gama yin wayar Fanan ta kira Mom ɗin nasu ko daga yanayin muryarta ta fahimci tana cikin 6acin rai, bayan sun gaisa cikin kwantar da murya Fanan ɗin ta fara lallashinta tana nuna mata ba aibu bane don Farha ta auri Kamal tasan kawai don basu da arzuƙi ne matsalansu kuma shi na Allah ne a duk lokacin daya so sai ya azurta bawa haka mai kuɗin ma duk yawan kuɗinshi cikin few seconds sai ya maida mutum talaka don haka suyi fatan alkhairi a gare su kawai, har ta gama maganarta Mom ɗin bata katseta ba saida ta gama tace mata ta gama Fanan ɗin tace eh kawai sai ta kashe wayar tare da buga uban tsoki, gaba ɗaya Farha ta koma rayuwar ɗaki washe gari lahadi da yamma Hajiya Maryam ta shirya komawa Abuja taci gayu cikin jigunannan lace ta soke kallabi bayan ta fito ne ta nufi ɗakin Farha lokacin data shiga tana kwance kan gado kamar mara lafiya tana ganin Mom ɗin nasu ta shigo ta yunƙura ta tashi zaune tana kallonta can ta gaishe da ita a hankali Mom ɗin ta ta6e baki tace ta ruƙe gaisuwarta bata so ai yanzu bata da daraja a wurinta saboda dangin shanu shiyasa bata iya zuwa ta gaishe da ita, idanun Farhar ne suka ciko da ƙwalla tace mata tayi haƙuri Hajiya Maryam ɗin ta ƙara ta6e baki tace ita ai zata ba haƙuri don tazo ne ta sanar mata nan da sati biyu za'a ɗaura auranta da Emran don haka gara ta tsaida hankalinta wuri ɗaya tana gama faɗin hakan ta juya ta tafi Farhar tasa wani irin kuka tana faɗin Wllh bazata aure shi ba Kamal zata aura in ba haka ba mutuwa zatai, daidai Hajiya Maryam ta kai bakin ƙopa ta watsa mata hannu daga haka ta fuce. Gaba ɗaya hankalin Dr ya tashi ganin halin da Farhar take ciki kullum cikin kuka ta daina cin abinci sai ya rarrasheta dole hankalinshi ya kasu biyu wurin aiki da kuma gida a haka har sati ya ƙare Hajiya Maryam ɗin ta dawo ya sameta don suyi magana ya nuna mata gara a bar Farhar ta auri wanda take so don tana niyyar lahanta kanta Hajiya Maryam ɗin tace ya rabu da ita duk tana yi ne don a saduda a goyi bayanta da an ɗaura masu aure da Emran ya tafi da ita America zata koma daidai, bayan ta gama Weekend ta koma an shiga wani satin ganin yana niyyar rasa ɗiyarshi yasa ya kirawo Hajiya ya sanar mata halin da Farhar ke ciki da hukuncin da Hajiya Maryam ta yanke na ɗaura masu aure da Emran a satin Hajiya na jin haka ta saka salati tace Maryam badai taurin kai ba ai ita bata san da ta yanke wannan hukuncin ba tace ma Dr ɗin abunda za'ai yasa Farha ta rubuta takarda cewa tunda an hanata wanda take so to ta shiga duniya kuma kada a nemeta don baza'a sameta ba in ta rubuta sai ya turo mata ita amman kada ta hawo jirgin Katsina ta hawo na Kano in ta sauka sai ta hau Motar haya ta ƙaraso Katsina sannan kada ya bari kowa yasan da wannan plan ɗin daga shi sai Farhar kuma ya siya mata sabon layin waya sannan itama wayar ya siya mata ƙarama tata ta baro ta nan gida, bayan sun gama wayar tasa ya kai ma Farha wayarshi ta sanar da ita yadda sukai da Mahaifinta tace mata ta kwantar da hankalinta ta samu niƙab in ta isa kano ta saka shi a fuskarta har ta iso Katsina sannan kuma tayi dubara ta saka dogon Hijab a park ɗin data iso Katsina sai ta kirata ta sanar mata zata sa azo a ɗauketa da sauri tace to, kamar yadda suka tsara haka sukai ya sakata ta siya ticket ta online washe gari ya kama talata lokacin duk ƙannanta sun tafi School shima Dad ɗin ya fito daga gidan matsayin ya tafi aiki bayan wani lokaci ya kirata ta sabon layinta yace ta fito daga gidan koda wani zai tambayi ina zata tace zata je Abuja ne wurin Mom ɗinta, tana janye da madaidaicin trolley ta fito cikin sa'a har ta fito daga gidan ba wanda ya ganta sai Security dake gadin gate da suka gaisa suka tambayi unguwa zata je ne tace eh zata Abuja wurin Mom ɗinta har wani yace to ina driver ta fito ita kaɗai tace bai dawo daga kai su Noor School ba tana sauri zata hau taxi kawai sukai mata Allah ya kiyaye, bayan sun haɗu da Dad ɗin nata inda ya tsaya tace ya bari ta hau taxi tunda in ya kaita Airport za'a iya gane plan ne tunda akwae cctv yace ta bari in suka kusa isa sai ta hau taxi ɗin, tun a cikin Motar ta naɗa gyalenta tayi kamar niƙab a cikin Motar suka yi bankwana da Dad ɗin nata duk ya damu, bayan ta fito saida ta samu taxi ta hau sannan Dad ɗin nata ya tafi har suka isa Airport bata buɗe fuskarta ba sai bayan data shiga tana janye da trolley da zasu tafi sannan ta buɗe, bayan sun iso Kano fuskarta a rufe ta bar Airport ɗin ta hau keke napep don ya kaita tasha, wuraren azahar ta iso Katsina ta kira Hajiya ta sanar mata ta tambayi inda take bayan ta faɗi mata ta kira Tk ta sanar dashi ya ɗauki Mota tinted yaje ya taho da Farhar tace kada ya ɗaukkota a tashar in ya kusa isa ya kirata ta fito sai su haɗu kan hanya ya ɗaukkota, duk yadda Hajiya ta tsara haka akayi lokacin da suka iso gidan Hajiya na Bedroom bata daɗe da gama yin sallar Azahar ba Farhar ta shigo tana hangota ta nufota da sauri tana zuwa ta faɗa jikinta tana kuka Hajiyar na murmushi tace mata ya isa miye abun kuka, gaba ɗaya su Saude da Husnah harda Tk saida Hajiya taja kunnansu kan kar wanda ya sake ya bayyana Farhar na gidan koda za'a tambaye su nan gaba har su Gwaggo tace kar a bari su san da zuwanta gidan duk suka ce to, itama Farhar tace mata kada ta bari kowa yasan tana gidan har Kamalun tace to. Lokacin da Dr ya kira Hajiya Maryam da alamun tashin hankali ya sanar mata zancen barin Farha gida da takardar data bari harda wayarta zo kaga rawar jiki da tsananin tashin hankali ta shiga tambayar ina taje ya akai har ta bar gida ba wanda ya sani yace to shi dai ya tafi wurin aiki yara kuma an tafi kai su School koda ya dawo dubata kamar yadda yake yi sai dai takarda ya gani kuma ya tambayi security sun tabbatar mashi da fita tayi kuma cewa tayi wurinta zata zo Abuja, a fusace tace to ubanwa yace su bari ta fita Dr yace sunce ba'a basu umarnin su hana wani ya fita ba sai lokacin ta tuna da haka gaba ɗaya ta gama ruɗewa tace mashi a bibbincika inda ake tunanin zata iya zuwa pls yace mata bai tunanin zata tsaya kusa don da gani ta shirya ma abun bazata tsaya inda za'a ganota ba shi dama abunda yaketa kwatanta mata kenan tace yanzu ba lokacin wannan bane duk da haka adai bincika ko ina itama zata kira wasu wuraren taji ko taje can, abu kamar wasa har zuwa yamma ba'a ji taje wani wuri ba, lokacin da ta kira Hajiya ta tambayi ko Farha tazo da alamun mamaki ta tambayi ina Farhar taje farko shiru Hajiya Maryam ɗin tayi saida Hajiya ta ɗaga mata murya tace bazata faɗi mata ba sannan tace aje takarda tayi wai tunda baza'a bata wanda take so ba ta shiga duniya, wani salati da Hajiya ta saka baka ta6a cewa tasan inda Farhar take da alamun tashin hankali tace yanzu duk Maganar data yi mata shine bata ji ba saida tayi sanadin barin ta gida kamar Hajiya Maryam ɗin zatai kuka tace yanzu dai don Allah ta bar Maganar a taya su bincikawa inda ake tunanin zata iya zuwa, zuwa dare har zancen 6atan Farhar ya fara baza wurare har Mai girma shugaban ƙasa yaji sosae hankalinshi ya tashi ba kamar da yaji cewa takarda ta aje ta tafi shima da kan shi ya shiga kiran yan'uwa na jiki yana tambayar ko taje in aka ce bata je ba sai yace to a taya su bincikawa, lokacin da ya kira Hajiya nan ta warware mashi komai tace su kwantar da hankalinsu Farhar na wurinta amman kada a bari Hajiya Maryam ɗin taji in ba haka aka yi mata ba bazata saduda ta ƙyale yarinyar ba hakan kuma na iya haifar da abunda za'ayi dana sani tunda yaran zamani ba'a cewa za'a yi masu dole yace ya fahimta, Washe gari tunda safe Hajiya Maryam ta koma Lagos nan fa aka hau bincike wurare daban daban har gidajen radio da Tv aka kai cigiya ko wani ya ganta har binciken lambar wayarta akayi aka tabbatar wayar da tayi ta ƙarshe anan Lagos ne, kan kace mi zancen 6atan ya karaɗe social media ana ta faɗin ɗiyar ƙanwar shugaban ƙasa kuma Minister Maryam Adamu Zakee ta 6ace sai dai ba wanda yasan dalilin 6atan nata don ba'a bayyana ba da yawan mutane sun tafi akan ƙilan kidnapping ɗinta akai, har su Fanan sun samu labarin sosae hankalin Fanan ya tashi har ta fara shirin tahowa Nigeria Haisam ya kira Hajiya kan 6acewar Farha ɗin nan ta bayyana mashi komai tace su kwantar da hankalinsu amman kada wanda ya sanar ma Hajiya Maryam ɗin saida Fanan taji haka sannan hankalinta ya kwanta har waya sukai da Farhar amman ita Hajiya Maryam duk sai suka nuna mata hankulansu ya tashi, da yake abun na masu ƙasa ne an zurfafa bincike sai gashi zuwa yamma an tabbatar da ta siya ticket online kuma ta hau jirgin Kano a jiya nan da nan bincike ya koma Kano, bayan an tabbatar da taje kano Hajiya Maryam ta kira Hajiya ta sanar mata ta tambayi ko ta ƙaraso nan Katsina Hajiya tace a'a bata zo ba ai in nan zata zo mi zai sa ta hau jirgin Kano, cike da nuna Al'ajabi Hajiyar tace "to amman wai mi zaisa Farha taje kano, ko kinada mutanen da kike tunanin zata iya zuwa can wurinsu??" cike da damuwa Hajiya Maryam tace tana da abokan kasuwancinta acan saidai Farhar bata san su ba sai kuma abokanta da sukayi karatu tare suma ba kowanne Farha ta sani ba sai wata ƙawarta guda Hajiya Turai kuma ta kirata ta tambayi ko Farhar taje wurinta ta tabbatar mata da bata je ba, "Oh ya Allah, shiyasa aka ce maganin kada ayi to kada a fara yanzu ina amfanin haka ace budurwa kamar Farha ta 6ace ai dole a shiga dumuwa da tashin hankalin halin da take ciki, yanzu da ta tafi Kano mi taje yi can in ma acan ɗin ta tsaya, to ko dai yin Film ta tafi ne don naji ance dama wasu yan wasan hausan sanadin auren dole suke tafiyar su su shiga, to in ma dai Film ɗin taje yi ai da sauƙi don tana farawa za'a ganta tsorona ace ba a Kanon ta tsaya ba ta haɗu da wata yar Kano to Jidda ta hure mata kunne kan ta gudo wurinta ta fitar da ita waje....." da sauri Hajiya Maryam ta katseta da faɗin "Don Allah Hajjaju ki daina yin wannan fatan", "To Maryam na bari Hankalina ne ya tashi na rasa tunanin da zanyi kan inda ta dosa amman in sha Allahu tana a hannu nagari Allah zai tsareta" da sauri Hajiya Maryam ta amsa da Allah yasa kafin a zuciye tace "In dai ba'a ganta ba zuwa gobe ina nan zuwa Katsina zan sa a kama yaron nan da kaf danginshi a tuhume su na tabbatar basu rasa sanin inda take don haka sai sun nemo man yarinyata", da sauri Hajiya tace "akan me, ke waya faɗi maki su suka ɗauketa, yarinyar da daga gani ita ta shirya ma kanta hakan tunda har da takarda ta aje to ina ruwan yaro da dangin shi anan?" a fusace tace ai zai iya yuwuwa shiya tsara mata, "Ba wani tsara matan da yayi yaron da tun farko ita ta bayyana mashi so nan fa Kakarshi tazo cikin damuwa kan bata son al'amarin gudun matsala sai kuma suja ma kan su matsalar, don haka ni ban amince kisa ayi masu wani abu ba don na tabbatar basu da sa hannu a 6atan ta in kuma kika ƙi jin maganata kika sa akai ma yaron mutane wani abun ita mai guduwar ta samu labari al'amarin ya ƙara kwa6ewa to ba ruwana kar ma kice zaki kirani dama yanzu ai harda ƙin jin maganata yasa hakan ta faru don haka na dai gaya maki ban amince kisa ayi masu wani abu ba muci gaba da Addu'ar bayyanarta da kasancewarta cikin ƙoshin lafiya" a sanyaye ta amsa mata da Amin kafin sukai sallama, bincike ya tsananta a Kano a gidajen radio da tv da social Media harda Airport anata cigiya harda hotunan Farhar da ranar data zo kano harda kayan jikinta, duk abun nan su Gwaggo basu sani ba kawai dai Kamalu nata kiran layinta bai shiga har ya fara shiga damuwa dama lokacin da tana gida cikin halin damuwa sunyi waya har yake mata magana kan jin muryarta ta canza tace mashi bata jin daɗi ne duk sai tunanin shi ya tafi akan ko ciwon ne yay tsanani yasa ba'a samunta a waya, sai ranar juma'a lokacin kwana ukku da 6acewarta Kamalu yaje School wani abokin shi da suke tare ya nuna mashi hoton Farhar a Facebook yace mashi wai wannan ba itace wannan ɗiyar Minister ɗin ba ƙawarshi da yake ganin hotunanta a wayarshi da sauri Kamalun yace mashi eh itace miya faru nan yake ce mashi wai nemanta ake ta 6ace ai da sauri ya warci wayar yana dubawa nan ya tabbatar da hakan yana bashi wayar ya miƙe sai gida, Lokacin daya dawo a falon Gwaggo ya isketa tare da Amadu da Haulat duk sunyi jugum tun bayan da Amadu ya shigo masu da labarin 6atan Farhar suke haka kowa ya kasa yin ƙwaƙƙwaran motsi, shima zama yay cikin tashin hankali yace masu ko sun samu labarin daya samu yanzu a School wai Farha ta 6ace duk suka ɗaga mashi kai ai shima sai ya nemi wuri ya zauna, bayan wani lokaci Gwaggo ta sauke nannauyar ajiyar zuciya cike da damuwa tace ita dai fatan ta Allah yasa ba dalilin abunda tazo dashi bane tunda dama tace ma Kamalu ita tasan yadda zata sa iyayenta su amince in ko har hakan ne to kuwa akwae babbar matsala, jin Maganar Gwaggo yasa cikin Kamalu juyawa Amadu yace mashi suna waya da ita ne nan ya faɗi masu rabon shi da ita a waya Haulat tace Allah yasa dai ba dalilin hakan yasa ta 6ace ba Allah kuma yasa a ganta duk suka amsa da Amin, Amadu ne yace bari ya kira Fatuu yasan ta bakinta zasu iya jin dalilin 6acewar tata, bayan ta kira sun gaisa yake mata zancen Farhar yace da gaske wai ta 6ace tace mashi eh ya tambayi tasan dalilin 6acewar tata nan ta faɗi mashi guduwa tayi don harda takarda ta aje Mom ɗin su taƙi yarda da Kamalu shine ta yanke yi mata auren dole da Cousin ɗinta da suke yin soyayya a satin data gudun, salati Gwaggo ta saka tare da rufe ido ta dafe goshi shi kuwa Kamalu zumbur ya miƙe yay hanyar ɗakin shi yana zuwa sai toilet, Fatun bata fito ta bayyana masu inda Farhar take ba duk da ta sani saboda Hajiya tace kar a faɗi ma kowa sai dai ta shiga kwantar masu da hankali tace in sha Allahu za'a ganta tunda har an gano ta hau jirgi taje kano Amadu yace to Allah yasa ta amsa tace ina Gwaggo yace gata nan tayi jugum duk tsoro ya kamata tace Kamalu fa yana yar dariya yace shi wannan yana tunanin yana toilet don yana jin bayanin data yi ya miƙe yay hanyar ɗaki Fatun tay yar dariya tace su kwantar da hankalinsu tasa aka ba Gwaggo suka gaisa nan ta shiga kwantar mata da hankali ita dae sai uhmm da to kawai take cewa, suna gama yin wayar Gwaggo ta miƙe tace bari taje tayi ma Hajiya jaje Haulat ma ta miƙe tace bari ta sako Hijab suje, lokacin da suka je Hajiyar na bedroom Farha kuma tana a ɗayan bedroom ɗin Husnah tanata shan bacci abunta dama nan Hajiya tasa ta zauna gudun kada Momynta tayi zuwan bazata, Saude ce ta kirawo masu Hajiyar bayan ta shigo cikin falon tana ɗan murmushi tayi masu sannu da zuwa tare da yi masu barka da Juma'a duk suka amsa suka gaisheta, Gwaggo ce ta fara mata jajen tace su wllh basu san abunda ke faruwa ba sai yau da su Amadu suka ga ana cigiyarta a waya Hajiya na ɗan murmushi tace tsakaninta ne da uwarta taƙi goyon bayan wanda take so ƙarshe ma sai ta yanke yi mata auren dole to dama yaran zamani ana masu dole ne shine ta kaɗa kai tayi gaba abunta, cike da damuwa Gwaggo tace wllh tun farko irin haka take ta gudu don tasan abu ne mai wuya iyayenta su amince Hajiya tace shi mahaifinta ma ya amince uwarce taƙi da yake taurin kai ne da ita sai kuma ta samu yarinya irinta sai suyi ta cakusawa, itama Haulat jajen tayi mata da Addu'ar Allah ya bayyanata ta amsa da Amin ganin yadda Gwaggo tayi gwalau duk ta shiga damuwa yasa Hajiyar yin yar dariya tace "Amaryar Mani ya ya, ko kina tsoron hukuncin da Minister zata yi maku na kun yi silar 6acewar ɗiyarta" ɗan motsa baki Gwaggon tayi kafin tace a'a kawai dai 6acewar mutum bata da daɗi ba'a san a wane hali take ciki ba, Hajiyar tace mata kar su damu za'a ganta ne suka ce Allah ya sa, bayan sun mata sallama sun fito ne Haulat tace ma Gwaggo ita sai taga kamar Hajiya tasan inda Farhar take don taga kamar bata damu ba Gwaggo tace itama ta lura ƙilan kuma kawai ƙarfin zuciya ne Haulat ɗin ta ƙara cewa ko kuma shiri ne akai don Hajiya Maryam ɗin ta saduda Gwaggo tayi shiru tana nazarin Maganar, har aka shiga Weekend shiru Farha bata bayyana ba Kamalu kuwa yana can yana zazza6in zullumi, ranar Lahadi Dr mijin Hajiya Maryam ya kira Hajiya anan yake sanar mata ba ƙaramin tashi hankalin Hajiya Maryam yayi ba ko isasshshen bacci bata yi taita kuka tana faɗin tayi sanadin 6acewar ɗiyarta waya sani ma ko ta mutu shi yanzu tausayi take bashi sosae gashi sai zuba kuɗi take ana cigiya a gidajen tv da radio yanzu har kuɗi tasa masu yawa na duk wanda ya kawo ta ko ya faɗi inda take zata bashi, murmushi Hajiya tayi tare da ɗan ta6e baki tace mashi ya ƙyaleta ta ɗan ƙara jin jiki tukun su kuma kuɗi da take 6atarwa na cigiya ai tana dasu ne don haka suma kafafen sadarwar ta fitar masu da zakka Dr ya ɗan yi shiru kafin yace shi abunda yake gudu kada wani ciwon kuma ya haye mata Hajiyar tay murmushi mai ɗan sauti jin yanzu kuma ta matar shi yake tace mashi kada ya damu ba ciwon da zai haye mata in ba hakan aka yi mata ba bazata daina taurin kai ba, bayan sun gama yin wayar shiru Hajiya tayi ta ɗan ta6e baki a ranta ta shiga raya in ba don ta kama ba ita kanta ai bazata so ta tada ma ɗiyarta hankali ba, damuwa tasa Hajiya Maryam ƙin komawa Abuja har wata rama tayi daka ganta kasan tana cikin damuwa bayan Hajiya ta warware ma President komai ya kira Hajiya Maryam ɗin sosae yayi mata faɗa yace al'amarin irin wannan ai a hankali ake bi da ta saurari Hajiya duk da hakan bata faru ba yakamata ta daina saurin fushi ta rinƙa bin komai a hankali tana ƙwalla tace mashi in sha Allahu zata rinƙa bin komai a hankali su Mom ma duk sun kirata sunyi mata jaje har suna cewa zasu zo Lagos ɗin suyi mata jaje tace ba sai sun zo ba kawai dai don Allah a tayasu bincikawa ba kamar wurin mutanensu dake Kano suka ce dama duk sunsa anata cigitawa in sha Allahu za'a ganta, Fanan ma ce mata tayi tana son tazo Nigeria ɗin amman ta ɗan ƙara saurarawa ne ko Farhar zata taho wurinta daga Kanon Hajiya Maryam ɗin tace hakan yayi kada ta taho, a ranar Monday da daddare Hajiya ta kira Hajiya Maryam tace mata gobe tazo tana son ganinta tana jin haka da sauri tace mata ko Farhar tazo wurinta ne tace mata a'a tana son yin magana da ita ne........... 103 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ ........Washe gari da safe jirgin su ya sauka tare da security detail ɗinta aka ɗaukkosu zuwa gidan Hajiya motocin escort gaba da baya sai Jeep ɗin da take ciki a tsakiya, koda Hajiya ta ganta saida ta jinjina yadda ta rame, a bedroom ɗinta suka zauna tana kallonta tace ashe ta damu da Farha har haka amman shine taƙi goyon bayan abunda take so Hajiya Maryam ɗin ta ɗan yamutsa fuska kafin cikin karyayyar murya tace ai dole ta damu ace yarinyarka budurwa tabar gida ita damuwarta a wane hali take ciki ina taje, tana yin Maganar ƙwalla suka zubo mata sharr Hajiya tace "in sha Allahu tana cikin ƙoshin lafiya kuma a hannu nagari" a hankali ta amsa da Allah yasa, "Yanzu in aka ganta zaki goyi bayan abunda take so ko?" Hajiya ta tambaya tana kallonta tay ɗan jimm kafin tace "Hajjaju ni a ganina ba kowanne abu yaro ke zuwa dashi a goya mashi baya ba, komai da nike yi saboda rayuwarta ta inganta ne taya za'a ce Farha ta auri yaro kamar wannan bacin ga wanda ya gina rayuwarshi wanda zai ruƙeta da kyau muna gani sai mu barta taje ta jefa rayuwarta a wahala" ɗan murmushi Hajiya tayi tace "idan abunda yaron yazo dashi baida wani aibu lafiya lou sai a goya mashi baya mana, sannan Maganar gina rayuwa ai shima baki san abunda Allah zai yi ma tashi rayuwar ba tunda yanzu yake kan gina ta, sannan Maganar jefa rayuwa a wahala shi wanda kike hangen zai ruƙeta da kyau saboda kuɗi ke a tunaninki mai kuɗi ne ke ruƙe mata da kyau, Matan masu kuɗi nawa ne suke cikin damuwa a gidajen auransu har suna ganin dama talaka suka aura wanda zai basu farinciki, ko kuwa don ke kin dace sai kike ganin kowace mace ma hakan take a wurinta to kije ki bincika na tabbatar zaki samu mata da dama wanda kuɗaɗen mazajensu basu sa sun kasance a cikin farinciki ba face damuwa", ɗan yamutsa fuska tay da yanayin damuwa tace "Yanzu dai fatana Farhar ta bayyana shine kawai, gani kince kina son ganina", Hajiya na ɗan murmushi tace ta dameta ko shiyasa take son a canza Maganar, da sauri tace mata a'a kawai dai taga ba abunda yakamata su maida kai akai bane tunda wadda ake Maganar don ita ba'a san inda take ba Hajiyar tace hakane Allah ya bayyana masu ita ta amsa da Amin, "Kinzo na tsare ki da surutu ban baki abinci ba kuma halan ko breakfast baki yi ba" Hajiya ta faɗa idonta a kanta, warware gyalen haɗaɗɗar doguwar rigar dake jikinta data laga tayi ta kwanta a saman gadon tana faɗin tasha ɗan tea Abincin ne kwata kwata bai mata daɗi gashi duk in tazo ci sai tayi ta tunanin ko Farha taci abinci, yadda ta ƙarasa Maganar kamar zata saka kuka Hajiya na murmushi tace in sha Allahu taci mai kyau ma, "Yanzu tea ɗin za'a ƙara haɗo maki sai a haɗa da wainar ƙwai muna da farfesun kaza ma, in kuma duk baki son su sai ki faɗi abunda kike so a haɗa maki" shiru ta ɗan yi kamar bazata yi magana ba can ƙasa ƙasa tace rana tayi abar tea ɗin a kawo mata farfesun taga in zata iya sha Hajiya tace to ko a soya doya sai ta haɗa da sauri ta girgiza mata kai tace abu mai ruwa ruwa kawai take ɗan iya ci Hajiya tayi murmushi tace to bari tasa a kawo mata anan, wayarta ta ɗaukko ta shiga yin kira bayan an ɗaga umarnin kawo ma Hajiya Maryam farfesu ta bayar tare da lemu da ruwa daga haka ta kashe wayar idanunta akan Hajiya Maryam data rufe ido kamar mai yin bacci, ba'a jima ba aka turo ƙopar ɗakin Farha ta shigo tana sanye da ƙananun kaya kaman ko yaushe kanta ba kallabi sai dark ash ɗin sumarta dake a fake ta lanƙwasa ta, bata yi sallama ba Hajiya tay mata nuni da gaban gadon saitin inda Hajiya Maryam ke kwance tace taje ta aje anan kan carpet, har ta aje Hajiya Maryam bata buɗe ido ba Farhar ta ɗago tana kallonta wata irin kewar Mahaifiyar tata taji ita kanta taga canzawar da tayi bata ta6a tunanin za'a samu ranar da zasu samu sa6ani da Mom ɗin tata ba don sun shaƙu kamar abokai haka suke dalilin shaƙuwarsu ne ma yasa Farhar bata fita ƙasar waje yin karatu ba tayi a nan, da hannu Hajiya tayi mata alamun ta gaishe da ita cikin ɗan rawar murya tace mata ina kwana still bata buɗe idon ba da alama ma bata ji ba, saida Hajiya tace mata ana gaisheta sannan ta ɗan ɗaga hannu alamar ta amsa, tsaye Farhar tayi tana ta kallonta a hankali ƙamshin turarenta ya fara kurɗaɗawa cikin hancin Hajiya Maryam lokacin data shaƙe shi sosae da mamaki ta ayyana ƙamshin kamar na Farha, zuciyarta na raya mata hakan da sauri ta buɗe idanun nata suka shiga cikin na Farha dake tsaye ai a sukwane ta tashi zaune tana kallonta idanu waje, muryarta har tana sarƙewa wurin faɗin "Wannan kamar Farha a gabana Hajjaju kodai gizon data saba yi man ne dama sai inta ganinta koda yaushe" Hajiya na murmushi tace itama kamar ita take gani, maido idonta tayi kan Farha dake ta kallonta sai kuma ta maida kan Hajiya, murmushin da taga tana yi ne yasa ta gane Farhar ce aikuwa da sauri ta miƙe tsaye cikin rawar murya ta furta "F...Farha, it's You...???" shiru ta ɗan yi kafin a hankali ta furta "Yes, Mom" zaro ido Hajiya Maryam tayi gaba ɗaya ta juya kan Hajiya cike da al'ajabi tace "Amman Hajjaju ya akai kika samota ko nan tazo?" ɗan ta6e baki Hajiya tayi tare da ɗan girgiza kai tace dama tana nan, cikin ɗaurewar kai ta maimaita abunda Hajiya ta faɗa ta ɗaga mata kai alamar tabbatar wa, "Yanzu Hajjaju kina nufin duk abun nan Farha na wurin ki?" Hajiya tace mata eh ita ta tsara mata komai tasa ta taho wurin ta, wani kalan yarfa hannu Hajiya Maryam tayi tare da yamutsa fuska ta koma gado ta zauna yaraf kamar zata yi kuka tace "But Why, Hajjaju, miyasa don Allah zaki tada mana hankali har haka kika sa anata cigiya mutane nata kashe kuɗi suna zuwa jaje amman ashe tana wurinki kuma kina sane da dole hakan zai tada mana hankali ba kaɗan ba" wani irin ɗaure fuska Hajiya tayi da hannu tayi ma Farha alamar ta zauna a kan carpet, bayan ta zauna ta maida idonta kan Hajiya Maryam fuska a ɗaure ta fara magana, "Nasani hankalin wanda bai san da tana wurina ba zai tashi kamar ke sannan Maganar kashe kuɗi da zuwa jaje duk nasan za'ai hakan saidai ina son ki sani na za6i yin hakan ne don in baki misalin irin tashin hankalin da kike niyyar janyo mana kenan koma wanda yafi wannan, saboda taurin kan ki kina ƙoƙarin ki saka mu a damuwa da danasanin da har mu mutu bazamu daina ba to aka me zamu zura ido muna kallo ki jefa mu a hakan, kina sane da illolin da auren dole ke tattare dashi amman shine kika rufe ido saboda wani kurman ra'ayin ki zaki jefa rayuwar yarinya a halaka, baki tunanin zata iya kassara rayuwarta ba ko kuma ta ƙyaleki ki ɗaura mata auren shi mijin ta illata shi ba, in hakan ya faru wane irin tashin hankali kike tunanin hakan zai haifar mana, so kike mu zama abun misali a idon duniya ki jaza mana tambarin da bazai ta6a goguwa ba har ƙarshen rayuwar mu?"" a fusace take yin Maganar, jin tayi shiru ne yasa Hajiya Maryam ɗin cewa "amman Hajjaju wannan ai ba auren dole bane tunda akwae soyayya tsakaninsu ta tsawon lokaci kuma su duka suna son junansu kwatsam kuma sai ta dawo tace wai bata son shi....." Katseta Hajiya tayi taci gaba "tace bata son shin ai ba laifi tayi ba dama yana faruwa yau kaji kana son mutum gobe ka dawo kaji baka son shi dama ana samun haka wanda aka ɗauki lokaci ana soyayya sai kiga bashi Allah ya ƙaddaro za'a aura ba sai daga baya mijin ya 6ullo ta inda ba'ai zato ba yasha faruwa koma yana kan faruwa ma shiyasa wasu suke gudun 6ata lokaci wurin yin soyayya suke bari sai sun shirya ma aure sannan su fara wasu kuma suna yin soyayya da shirin kota kwana, shiyasa ba'a so ana soyayya ai ta ma juna ƙaryayyaki da alƙawura tunda mutum bashi keda kan shi ba ta yuwu wanda kake hasashen aura bashi Allah ya ƙaddaro zai zama abokin rayuwarka ba shiyasa yana da kyau a gina soyayya kan wannan turbar kowa yasa hakan a zuciyarshi sai kiga koda rabuwar tazo baza'a ji ciwo sosai ba, don haka ki rabu da yarinya ta auri wanda take so wataƙil dama wannan shine wanda Allah ya ƙaddaro zai zama abokin rayuwarta" ba alamun wasa Hajiya ke yin Maganar, "Naji Hajjaju, in bata son Emran ɗin shikenan amman nidai gaskiya ban goyon bayan ta auri yaron don haka ta nemi wani" fuska a yamutse tay maganar aikuwa a fusace Hajiya tace "bata neman wanin wanda take son shi zata aura matuƙar Allah ya ƙaddara hakan, ke waya hana ki auren wanda kike so, wato yanzu kin kawo ƙarfi ke ga uwa shine zaki nemi ɗaga ma mutane hankali ke wa yay maki haka, inace lokacin da kika haɗu da Mahaifinsu kina da samarin da kuke soyayya lokacin in ban mance ba yaron nan soja ɗan wurin abokin Mahaifinku gashi nan da suna.....Nasir yauwa ba wanda bai yi tunanin shi zaki aura ba daga haɗuwa da mahaifunsu duk kika ruɗe ke kinga mai jan kunne rana ɗaya kika zo mana da zancen ke shi zaki aura, a lokacin Allah ya jiƙan rai mahaifin ku shine ma yaso ya ƙi abun don shi mutum ne mai kishin ƙasar shi da al'ummarshi ni na rarrashe shi kan ya ƙyale ki har Allah yasa kukai aure, in ma kin manta ne to gashi nan na tuna maki don haka yadda ba wanda ya hana ki auren wanda kike so haka itama ba wanda zai hanata auren wanda take so" idanun Hajiya Maryam ne suka ciko da ƙwalla suka zubo mata sharr cikin 6acin rai ta shiga faɗin amman ita ko a lokacin data kawo mahaifin su ai ya gina rayuwar shi ko shikenan sai ace an taru anata auren dangin su kowa su Haisam da Nameer sun auresu ga Kakar tasu ma kan su za'a ƙare, "Zancen gina rayuwa ko ɗazun nayi maki maganar saurin mi kike ki jira shima kiga baki san yadda Allah zai da tashi rayuwar ba sai kiga ya zamo abunda baki ta6a zato ba ai shi arzuƙi na Allah ne Maryam kema ai ba wayon ki ne ya baki ba ko, sannan Maganar anata auren su alamar suna da nagarta ne ai ko a kasuwa zaki ga ana rububin abu mai nagarta, wasu Familyn ma zaki ga basu auren bare sai yasu yasu ma don haka don anata auren su ai ba aibu bane" shiru Hajiya Maryam ɗin tayi tana goge ƙwalla, "Ina son jan hankalin ki Maryam al'amari in dai akace na Allah ne ki daina kafiya irin haka, wannan abun daya faru yanzu tamkar ishara ne Allah ya nuna maki, nan yarinyar nan Fateema daga ta auri mijin ɗiyar ki kika ɗaga masu hankali kikai ta kumfar bakin ke ɗiyarki bazata zauna da ita matsayin kishiya ba don bata kai matsayin tayi kishi da ita ba waye waye, to yanzu ga ɗiyar ki nan ta cikin ki Allah ya ɗaura mata son Yayanta so mai tsanani itama yar jakar ubar nan harda ita aka hana Fateema zaman lafiya amma kinga soyayya ta rufe mata ido ko kunya bata ji ba tazo tace tana son Yayanta..." ta juya tana kallon Farha tare da ɗan harararta Farhar ta ɗan tura baki a hankali tace "pls Hajiya let bygones be bygones, ba kinsa mun shirya tuntuni ba", ta6e baki Hajiya tay tace "da yake fa abunsu kike so kyace haka, shiyasa ita fitina bata da daɗi sam, yanzu da baku shirya ba kina tunani shi wanda kike son zai saurareki ne alhali kina tsangwamar yar'uwar shi, to da ya zaki da son ko sai kije ki faɗa rijiya mai kwala6e?" yar dariya Farhar tay ta sunnar da kai, maida idonta tay kan Hajiya Maryam da 6acin rai ya bayyana akan fuskarta cikin kwantar da murya tace "Wato shi Ubangiji yana yin abubuwa cikin hikima, daya halicci bayinsa sai ya kasasu wasu yayi su masu wadata wasu masu rufin asiri wasu kuma wanda basu dashi gaba ɗaya hikimar yin hakan shine don kowa ya amfana da kowa don inda yaso zai ba kowa arzuƙi amman sai bai yi hakan ba, duk wanda kika ga Allah ya ba arzuki bai bashi don ya amfana shi kaɗai ba face don ya taimaki wanda bashi dashi wanda ta silar haka zaka samu ɗunbin lada har kasamu shiga aljanna haka wanda bashi dashi in yayi haƙuri da yadda Allah yayi shi ya rungumi ƙaddarar shi bai sa6i Allah ta dalilin hakan ba shima sai kiga ya cinye jarabawar shi ta hanyar hakan har ya shiga aljanna, wasu da yawa Allah na saka arzuƙin su a hannun wasu shine zaki ga ta silar taimakon da kayi ma wani in ma aiki ka sama mashi ko kuɗi ka bashi ko auren shi kai da sauransu sai kiga hakan yayi silar arzuƙin mutumin, to dana yi nazari sai na gano kusan hakan ce Allah ya ƙaddaro tsakaninmu dasu Dije shiyasa har ya haɗamu maƙwabtaka kuma in kikai la'akari da ai basu kaɗai bane makwabtana akwae wanda muke tare tun kan suzo zaki shaida hakan, Allah yasa rabon wadatuwar su a hannun mu don haka bamu da ikon hana hakan koda kuwa ace bamu so to wllh sai rabonsu dake tattare damu ya isa gare su, don haka inason ki kwantar da hankalinki ki ɗauka mu dasu yanzu mun zama Family duk abunda ya taso tsakanin mu dasu in dai mai kyau ne to mu rungume shi hannu bibbiyu muyi fatan alkairi" shiru Hajiya Maryam tayi ta maida idonta ƙasa, "Yanzu kin amince mata kan abunda take son?" Hajiya ta tambaya idonta akanta, ba tare data ɗago ba tace "taje Allah ya taimaka", "Ba haka yakamata kice ba Maryam fatan alkairi zaki yi mata matsayinki na mahaifiyarta sannan ki yaƙi zuciyar ki ta rinƙa kallon abun a alkhairin" shiru tayi duk idanunsu na akanta can ta ɗago ta kalli Hajiyar tace Allah ya tabbatar da alkhairi, murmushi Hajiya tayi ta amsa da Amin Farha ta shiga yin murmushin farinciki tana washe baki tace "Thank you so much Mom, I love u" wata uwar harara ta wurga mata Hajiya tay yar dariya tace "in kina harararta fa zata ƙara 6acewa" ɗan gutsirin murmushi Hajiya Maryam ɗin tayi bata ce komai ba da sauri Farhar ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin, tana fitowa ɗakin Husnah ta nufa tana niyyar shiga Husnar ta fito daga ɗayan bedroom ɗin nata cike da farinciki Farhar ta sanar mata Mom ɗinta ta amince ma soyayyarsu da Kamal ta ɗan buɗa ido kafin tana murmushi tace ta tayata murna Allah ya tabbatar da alkhairi ta amsa da Amin ta ƙarasa shigewa cikin ɗakin, gyale ta yafo saman kanta tana fitowa falo ta nufi hanyar fita, gidan Gwaggo ta nufa bayan ta fito koda tazo shagon Amadu a rufe yake ta shige gate, tana niyyar shiga entrance Amadu na sako kai dama wanka ya shigo yi yana ganinta yaja ya tsaya yana ƙare mata kallo ita kuma tana ɗan murmushi ta gaishe shi bai amsa ba da tsananin mamaki yace mata an ganta kenan tay yar dariya tace dama ba 6acewa tayi ba tana nan gidan Hajiya, da alamun rashin fahimta yace kuma shine aketa cigiyarta, nan ta kwashe komai ta faɗi mashi sosae ya jinjina abun yace lallai Hajiya ta iya shirya abu kamar Film, tare suka shiga ya nufi part ɗin Gwaggo da ita lokacin Haulat ma na can sun fara aikin abincin rana, a falo suka tsaya Amadun ya shiga ƙwala ma Gwaggo kira yana ta fito taga wani abu, tana fitowa tayi arba da Farha itama zaro ido tay cike da al'ajabi tace kamar Farha take gani Amadu na murmushi yace itace da sauri ta tambayi ina aka ganta nan Amadun ya faɗi mata ashe wai tana gidan Hajiya Gwaggon ta washe bakin farinciki tace dama sai da Haulat ta zargi hakan da suka je jaje nan ta shiga ƙwala ma Haulat kira, bayan ta fito daga cikin Kichen ɗin itama saida ta nuna mamakin ganin Farha cikin washe baki Gwaggo ta shiga faɗin zarginta ya tabbata ashe wai tana wurin Hajiya Haulat ɗin tace ita dama tunda suka je ta lura da sam Hajiyar bata cikin damuwar 6acewar tata, zama sukai kan kujeru Amadu yace ma Farhar yaga mamanta ma tazo ɗazun ta gano tana nan kenan tace mashi a'a sai bayan data zo, nan take faɗi masu ai yanzu ta amince da tarayyarsu da Kamal ɗin cike da tsokana Amadu yace ai da ta haƙura da Kamalun tabi abunda Mom ɗin nata ke so ta wani tura mashi baki tare da ɗaure fuska duk sukai dariya, tambayar shi tayi Kamal ɗin tace ko yana School yace mata ai rabon shi da School tunda yaji labarin ta gudu saboda shi yanzu haka yana ɗaki bai jin daɗi, ai tana jin haka zumbur ta miƙe ta nufi hanyar ɗakinshi tana faɗin bari taje ta faɗi mashi ba guduwa tayi ba duk suka bita da kallo, juyowa Amadu yay ya kalli Gwaggo dake murmushi yace Allah ya haɗata da suruka ƙwara ba kunya duk sukai dariya, lokacin data shiga cikin ɗakin yana kwance kan katifa idanunshi a rufe tay tsaye daga gaban ƙopa tana kallonshi da murmushi can ta kira sunan shi "Kamal" a hankali ya fara motsa idanun shi masu ɗauke da zarazaran gashin ido kafin ya buɗesu ya ƙura ma gabanshi ido duk ɗaukar shi muryarta ce ke mashi gizo, saida ta ƙara kiran nashi sannan da sauri ya ɗago kai ai koda yay arba da ita a firgice ya ƙarasa tashi zaune yana kallonta ita kuma sai murmushi take mashi ya murje idanun shi ya buɗe ganin still tana nan yasa shi nunata tare da kiran sunanta ta ɗage mashi gira tare da amsa mashi da Yes, zumbur yay ya miƙe tsaye da alamun al'ajabi yace don Allah da gaske itace yadda yay tambayar ne ya bata dariya don duk alamun tsoro ya bayyana a tattare da shi tace mashi itace mana amman tunda taga bai yi farincikin ganinta ba bari ta koma da sauri yace a'a ta tsaya pls ya nufeta, a ɗan gabanta ya tsaya har fuskar shi ta faɗa da tsananin mamaki yace mata yaushe aka ganta ne kuma miyasa zatai haka, saida ta matso gaban shi sannan tace mashi itafa ba 6acewa tayi ba dama duk shiri ne nan ta shiga faɗi mashi yadda akai, shima sosae yayi mamaki cike da farinciki ta kai duka hannuwanta ta kamo nashi tace "guess what?" da sauri ya girgiza mata kai ta sanar dashi yanzu babu wata matsala zasu yi soyayyarsu hankali kwance don Mom ɗinta ta amince masu ya ɗan buɗa ido yace don Allah da gaske tace eh mana yanzu haka Mom ɗin nasu na gidan Hajiya, ƙayataccen murmushin daɗi ya shiga saki tace yayi haƙuri ta saka shi ciwo in ba hakan akayi ba Mom ɗin nasu daba lalle ta amince masu ba, da sauri yace ba komai ai yanzu ma yaji ya warke shi dama abunda yafi damunshi shine a wane hali take ciki hakan har kuka yake saka shi, bin juna sukai da wani irin kallo mai nuni da tsantsar ƙaunar da suke ma juna can Farhar ta furta "I love so much Kamal, pls dont turn your back on me", "I will never do that to you, My Love, i'm very grateful for accepting me for who i am, ban ta6a tunanin zaki so ni haka ba saboda tazarar dake tsakanin mu ajin ki ya wuce na ki soni shiyasa koda kika nemi da muyi ƙawance saida na jinjina abun sosae yanzu gashi kin za6i ma in zama abokin rayuwarki, i can't thank you enough, but, i give you all my heart in return" wani kalan murmushin daɗi tay ta faɗa jikinshi tare da lumshe ido yay shiru ƙirjin shi na bugawa don hakan abu ne da bai ta6a faruwa dashi ba ya haɗa jikin shi da mace koda kuwa yar'uwarshi tun bayan daya balaga duk da su a al'adarsu hakan ba wani abu bane amman su da yake suna da ilimin addini sun san hakan haramun ne shiyasa bai ta6a kowacce mace, hannu ya kai ya ɗagota suka haɗa ido tana ɗan murmushi ta furta yayi haƙuri taji daɗin Maganarshi ne, dama tun ba yanzu ba da suna ƙawance tana yawan ta6a shi tun yana sharewa ganin abun na yin yawa yace mata ta bar ta6a shi ba kyau kada su rinƙa samun zunubi, ce mashi tayi yazo suje ya gaida Mom ɗin ta ya ɗan waro ido tare da buɗa baki yace ba matsala kuwa tay yar dariya tace mashi he should be a man ba abund zai faru shima yay dariya yace to ko ta jirashi a falon Gwaggo ko Aunty Haulat ya shirya tace Ok ta juya tana faɗin yayi kyau sosae yace to, shiryawa yay cikin ƙananun kaya baƙin jeans da jar t-shirt anyi bakin rubutu a gabanta ƙafafunshi yasa baƙaƙen takalma sai agogo itama baƙa sumar nan tashi tubarkalla dama koda yaushe a kwance take ya ƙara gyarata sai salƙi take ya feshe jikinshi da turare ko maƙiyinshi sai dai don ƙiyayya yace bai yi kyau ba, lokacin da suka fito Amadu na shago yaje yace mashi zai je gaida surukarshi yay mashi Addu'a yay Maganar yana dariya shima Amadun dariyar yayi yace to Allah yasa a wanye lafiya in sun ji shiru kuma zasu zo beli Kamal ɗin yay dariya, tunda suka shigo harabar gidan gabanshi ke ɗan faɗuwa hakanan ya daure, lokacin da suka shigo cikin parlon ba kowa su Husnarh na Kitchen don rana tayi ta nufi bedroom ɗin Hajiya tare dashi, ita ta fara shiga shi kuma yay tsaye saida ta kalli cikin ɗakin taga yadda suke sannan ta juyo tace mashi ya shigo mana, ƙasa ƙasa da murya yace ta fara faɗi masu mana Hajiya dake kishingiɗe akan lallausan carpet ɗin gaban gado ta tada kai da tuntun ta ɗan ɗaga murya tace ita da waye anan ta maido kanta cikin ɗakin tana murmushi tace Kamal ne, tashi zaune sosae Hajiyar tayi tana faɗin to ya shigo mana shida ɗakin matarshi, tare suka shiga yay sallama ta amsa tana murmushi lokacin da idanunshi suka sauka akan Hajiya Maryam dake kwance saman gado ta rufe odo ƙananun kitson kanta sun bayyana sai da gabanshi ya buga sosae da sauri ya kauda idon, nuna mashi wuri Hajiya tay gefenta tace ya zauna Farha ma ta zauna cikin muryarshi mai daɗi ta bafullatanin daya ji hausa ya gaishe da Hajiya ta amsa tare da yi mashi ya jiki tace ai tukur ya faɗi mata yana can yana zazza6i Masoyiyarshi ta 6ace, da sauri ya sunnar da kan shi don wata irin kunya ce ta rufe shi data yi maganar Farha dake murmushi tace ko School baya zuwa, "To ai yanzu sai kaci gaba da zuwa tunda gata ta bayyana" ta faɗa tana yar dariya shima murmushi yake bai ce komai ba, juyawa tay kan Hajiya Maryam tace tayi bacci ne ga ɗanta yazo su gaisa shiru bata motsa ba Hajiyar tace ƙilan tayi bacci dama bayan ta gama cin abinci tace bacci take ji, miƙewa Farha tay ta rankwafa saman gadon ta shiga ɗan bubbugata, buɗe ido tay da alamu baccin ne ya ɗauketa fuska a yamutse tace lafiya ta tashe ta nuna mata saitin Kamal tayi tace dama shine yazo gaidata ta wurga mata wani kallo mai kamar harara, har zata faɗi wata magana sai kuma tayi shiru ta maida idonta kan Kamal Farha tace mashi su gaisa ya ɗago ido ya kalli Hajiya Maryam ɗin cikin faɗuwar gaba yace mata ina wuni kamar bazata amsa ba sai kuma ta ɗaga mashi kai ya ƙara cewa an zo lafiya kamar wadda akai ma dole tace lafiya daga haka ta maida idanunta ta rufe, cigaba da jan shi da magana Hajiya tayi har tana tambayar yanayin karatunshi yana dai maida hankali ko yace mata eh, bayan wani ɗan lokaci yay mata sallama ya miƙe Farha ma ta miƙe Hajiya ta kalleta tana murmushi tace Juliet za'a raka Romeo tayi dariya, buɗe ido Hajiya Maryam tayi tabi Kamal ɗin da kallo har suka fita Hajiya data lura da tana kallon Kamal ɗin bayan fitar su tana murmushi tace to ya taga surukin nata tayi shiru bata ce komai ba, "Inda zaki ɗauki shawarata kija yaron nan a jiki ki gina rayuwar shi sai yafi ma ruƙe maki ɗiyar taki da daraja" shiru Hajiya Maryam ɗin tay saida Hajiya tace bata jita bane sannan ta ɗan ta6e baki tace nawa akai ma haka amman suka butulce da sauri Hajiya tace sai dai dama can in butulun ne amman tana da yaƙinin zuri'ar Dije ba butulu bane Hajiya Maryam ɗin tay shiru bata ce komai ba can Hajiyar ta ƙara cewa "bari in maku da yaren daku yan siyasa kuka fi ganewa, yanzu aji kinja shi a jiki kin ginashi sannan kin ɗauki ɗiyarki kin bashi wane irin farin jini kike tunanin zaki a wurin mutane ta yadda koda nan gaba kin fito takara hakan zai iya saka mutane su za6e ki don ansan baki ƙyamar talaka kuma su naki ne, yanzu kamar yaron nan Sameer yadda ya auri ƙawar ita Fateema akai ta jinjina abun yanzu bashi ba ko mahaifinshi ya fito wata takara mutane da dama sai sun za6e shi dalilin haka, amman kawai misali ne na baki kan amfanin taimakon talaka a wurin ku yan siyasa nafi son komai zaki mashi kiyi mashi don Allah, ɗan jimm tayi kamar bazata tanka ba can ta tambayi Hajiyar mi yake karanta ta ɗan yi shiru alamar tunani kafin ta faɗi mata, "Yanzu kenan ita Farhar zatayi ta zaman jiranshi har ya gama karatun?" ta tambaya idonta akan Hajiya tace mata to yanzu duka ba saura shekara ukku ba ganin lokacin ne mai wuya ai amman yadda yanzu shekara ta zama kamar wata ai kaman gobe ne zai gama in kuma zasu bashi yana karatun to sai a kawota nan Katsina shi yana karatunshi Hajiya Maryam ɗin ta ɗan ta6e baki bata ce komai ba, tambayarta Hajiya tayi yaushe zata koma tace tana tunanin ko zuwa anjima Hajiyar tace ta bari sai gobe mana tana kallonta tace to dama ba dalilin Farhar yasa ta kirata ba Hajiya tana murmushi tace "Eh, amman ban gaji da ganin yar autar tawa ba" ba shiri Hajia Maryam ɗin tayi murmushi, "Kina yarinya Haƙuri ne dake sosae ba wanda zai ce in kin girma zaki zama rigimamma" tana murmushin tace mata ita ai bata rigima sai akan abunda take ganin shine daidai Hajiya na dariya tace haka dai tace, "Yanzu da Farhar zaki tafi ne?" Hajiya ta tambaya tace mata eh saboda su Abraham suna zaune gida su kaɗai Hajiya ta jinjina kai kafin tace yakamata ma su koma gabanta can Abujar tace eh tana shirin yin hakan sai kuma Hajiya ta sake cewa to shi Dr ɗin sai a barshi a Lagos shi kaɗai Hajiya Maryam tace to tunda can yake aiki dole can zai zauna sai su rinƙa zuwa mashi Weekend ko kuma shi yaje Abujar in anyi hutun School ma sai yaran suje mashi hutu, "To ki bashshi kawai ya ƙara aure mana" wani kallo tay ma Hajiyar sai kuma tayi ɗan murmushi tace ashe bata sonta har haka Hajiyar tayi dariya tace miye abun rashin so daga ta bata shawara yadda zata yi ma Dr adalci tace ai bata mashi rashin adalci tana kamantawa kuma itama ai bata rayu da kishiya ba ko, Hajiyar tace ai ita shine ke tafiya can aikin sojan shi ya barta ba itace ke barin shi ba kamar ita, Hajiya Maryam ɗin tace ai koda take barin shi bai zarta ƙa'ida ba da har zai sashi ƙara wani aure, ruƙe ha6a Hajiya tayi tace oh kowa gudun kishiya ita ko da ba'a yi mata ba General ɗin ne bai ra'ayi ba wai ita ta hanashi ba, Hajiya Maryam dake ɗan murmushi tace ai ba abun daɗi bace ita ko sunanta ma bata son ana faɗa, "anya Maryam, adai rage zafin kishi tunda ba'asan abunda Allah ya ƙaddaro ba" da sauri tace "in dai ta wannan bangaren ne ba abunda ya ƙaddaro in sha Allah auren zobe mukai da shi" dariya Hajiya tayi tace banda wanda aka ɗaura masu a Masallaci kenan wani suka ƙara ɗaurawa tsakaninsu Hajiya Maryam ɗin na murmushi tace mata eh, haka suka cigaba da yin hira sama sama har baccin ya sake ɗaukar Hajiya Maryam. Washe gari da safe ta koma tare da Farhar, sosae Dr Mahaifin Farha yay farincikin amincewar da Hajiya Maryam ɗin tayi, bayan dawowarta ne Dr ɗin yasa suka zauna don yin shawara game da Kamal yadda zasu inganta rayuwar shi nan ya bada shawarar su fitar dashi ƙasar waje yayi karatu a can ita kuma Farha sai taci gaba da yin Master's degree ɗinta ta amince da hakan, Hajiya ta kira ta sanar da ita suna son fitar da Kamalun waje tace ta sanar da dangin shi, Gwaggo ta kira ta sanar mawa koda Amadu yaji zancen bai goyi baya ba haka da aka sanar ma Fatuu cewa tayi gaskiya kada a amince a ƙyale shi yaci gaba da karatun shi anan salon nan gaba ayi mashi gorin an ɗauki nauyin karatun shi Gwaggo tace to ai ba roƙonsu akai ba su suka yanke hakan Fatun tace ita dai gaskiya bata goyon bayan hakan tunda ai karatun nan ma lafiya lou zai yi ya kuma samu aiki mai kyau, Gwaggo tace itama in son samu ne tafi son a ƙyale shi tunda ma har ya fara yin nisa saidai kuma bata son Hajiya taga anyi masu ba daidai ba, Amadu yace ai Maganar bata Hajiya bace ita da saƙo aka bata yasan zata fahimce su in aka nuna mata tunda ya riga ya fara anan har ya shiga shekara ta biyu a barshi ya ƙarasa, Gwaggo da kanta taje wurin Hajiyar cikin fahimta tayi mata bayanin da Amadun yayi tace itama saida tayi tunanin hakan to amman tunda saƙo ne aka bata shiyasa ta isar, kamar yadda sukai da Gwaggon haka Hajiya ta sanar ma Hajiya Maryam hakan yasa ta fara tabbatar da su bama su Kwaɗayi bane sanin da wuya ai ma wani tayin karatu a ƙasar waje amman ya maida, Soyayya sosae su Farhar suke sha ita da Kamalu don sun samu yanci daga baya ta fara shirye shiryen fara cigaba da karatunta. Bayan sabuwar Gwamnati ta fara ayyuka sosae Haisam ya tuntubi Alhaji lawal kan buƙatar ayi ma garin su Fatuu hanya a kuma gyara masu wutar lantarki kasantuwar shine ɗan majalissarsu na tarayya ya bashi tabbacin za'ayi masu, tuni aikin ginin Kamfanin Haisam wanda ƙwararran kuma sanannen Companyn gini anan Abujar keyi ya kankama, a yadda aka tsara zuwa nan da shekara guda za'a gama, tuni Al'umma sun fara sheda cewa sabuwar Gwamnati data hau ta aiki ce don kuwa anfara gudanar da ayyuka gadan gadan a faɗin ƙasa bayan hawan ta mulki ciki harda shirye shiryen da zasu tallafa ma talaka ya dogara da kan shi da yake ba laifi mai girma shugaban ƙasa ya samu abokan tafiya da shawara na ƙwarae masu tausayin talakawa, Kawu Mani har Abuja ya fara zuwa da Gwaggo acan ya samu inda ya kaita aka fara koya mata turanci don ta iya karatu, kan kace mi Gwaggo ta canza ta ƙara murmurewa duk alamun tsofanta daya bayyana yanzu babu sosae farinta ya ƙara fitowa tayi dumurmur abunta dama gata doguwar mace abun dai saidai ace tubarkallah, a bangaren First Lady kuwa wato Mahaifiyar su Haisam abun ba'a magana yanzu jin daɗi ya ninninku ta ƙara wani irin kyau Jama'a kowa yabon kyaunta da kuma kirkinta ake don mace ce mai sauƙin kai wadda kowa nata ne mutane har so suke a nunota tana jawabi don ta iya magana ba ƙaɗan ba, a yadda mutane keta faɗa ba'a ta6a First Lady kamarta ba wadda ta ko ina tayi, su Fatuu da Mino ana can America Mino ta maida hankali tanata karatu haka Nameer ma. Lokacin da za'ayi bikin cikar President shekara ɗaya a kan kujerar mulki aka shirya buɗe Companyn Haisam, da lokacin Hajji yayi gaba ɗayansu suka je harda shi shugaban ƙasan da Hajiya dasu Mom suma su Fatuu da Mino da Fanan da Haisam da Nameer nan Nigeria suka zo suka tafi tare harda Aunty Laila da Mijinta harda Jidderh ma duk wanda suka isa aikin Hajji a Familyn shugaban ƙasan saida suka je haka bangaren Minister Hajiya Maryam taje ita da Mijinta da Farha, sosae sukai ma shugaban ƙasa Addu'oi kan Allah ya tallafa mashi ya taya shi sauke nauyin dake kan shi kamar yadda ya roƙesu kan suyi mashi Addu'oin, Haisam ma sunyi mashi Addu'oin Allah yasa ya buɗe Companyn shi a sa'a, bayan gama aikin Hajjin suka dawo gida Nigeria, abun na Allah ne su Fatuu an zama Hajiya harda haƙorin Makka tasa haka ma Mino kuma sosae yay masu kyau, bayan dawowar su sun ɗan zauna a Nigeria Haisam ya duba ginin nashi wanda tuni yayi nisa lokacin Fatuu da Mino suka tafi Katsina Hajiya dai President ya ruƙeta kan sai ta ƙara hutawa sosae ita Hajiya Maryam ma cewa tayi kada ta koma Katsina ta dawo nan da zama kawai shima President ɗin dasu Mom suka nuna goyon bayan hakan Hajiyar ta nuna tafi son zama a can don ta saba da mutane kuma bai kamata ace duk sun baro can ba tunda nan ne tushen su, bayan zuwan su Fatuu Katsina har gidan Aunty Mareeya da Feenah taje ta kai masu tsaraba harda Abdul ɗan gidanta shima yasha tsaraba haka Aminiyarta ma Haulat tayo mata tsaraba kullum tana a gidan Gwaggo anan ma take kwana tunda shi Haisam na Abuja, bayan sati biyu suka koma America, bayan komawarsu ne Haisam yaba Fatuu da Fanan damar za6a ma Companyn suna yace yana son duk sunayen su ya fito a ciki nan suka shiga haɗa sunaye ita Fatuu tace ko asa HAIFAN ita kuma Fanan tace HAIFAT zai fi, ƙarshe dai HAIFAT TechWorld aka yanke saka ma Companyn. A kwana a tashi ba wuya har gashi shekara guda da hawan su President Ali Washegarin da akayi bikin murnar cika shekarar aka buɗe katafaren Companyn Haisam wato HAIFAT TechWorld, Kamfani ne da zai rinƙa ƙera kwanfutoci da saida bangarorinta da building softwares products da kuma Internet services daban daban da Online Services tare da kuma Consulting Services, sosae ginin kamfanin ya ƙeru yana da bangarori daban daban harda elevator ke akwae da zai kai mutum can sama abun sai dai ace Ma sha Allah, Mutane da dama ne suka halarci bikin buɗe shi ciki harda Mahaifin Haisam ɗin da manyan ƙososhin Gwamnati harda na wasu ƙasashen makwabta sannan ta bangaren danginsu kowa yazo har su Gwaggo harda Baffan Fatuu da Yadikko haka yan uwansu yan Ethiopia su Hajiya Zainab da Sameer harda Fauzy tare da twins ɗinsu da suka girma abun sai dai ace tubarkallah, abokan aikin Haisam ma turawa duk sun zo ciki harda waɗanda ya ɗauka zasu yi aiki tare gaba ɗaya duk wani masoyin Haisam da Abokan shi suna a wurin harda su Abbas da Najeeb da Saleem, ba ƙaramin mutane aka haɗa ba kowa yayi shiga ta alfarma kar ma su Mom suji su Fatuu ma ansha rantsattsan leshi iri ɗaya ita da Fanan wuya da hannu sun sha danƙararrun gold Haisam ma yasha bugaggun fararen suit sai necktie baƙi haka ƙafafunshi na sanye da dakakkun baƙaƙen cover suma abokan aikin nashi duk suit ne a jikinsu, yaran su gwanin burgewa duk sun girma su Twins yanzu shekararsu ukku da watanni amman sai kace sun fi hakan don suna da tsawo da kuma kauri suma suna sanye da suit na yara Esha kuma shekarunta biyu itama tana sanye da ƙananun kaya riga da wando an raba mata baƙar sumarta biyu ta saukko har ta wuce kafaɗarta kunnanta na sanye da barimar diamond da yan hannu ba ƙaramin kyau yaran sukai ba duk wanda ya kallesu sai ya ƙara yan jarida duk sun zagaye wurin suna ta aikin ɗaukar rahoto, bayan jin bayanai da suka danganci sabon kamfanin daga bakunan wasu masu ruwa da tsaki a kamfanin ciki harda Chief Executive Officer (CEO) wato Haisam da Mr President da wasu turawa a tare Haisam ɗin da Fatuu da Fanan suka yanka ribbon ɗin da aka zagaye ƙopar shiga cikin kamfanin mutane suka sa tafi ji kake "raf...raf...raf...) wasu suka shiga faɗin "Behind every Sucessiful Man there is woman or women" duk akasa dariya kafin akai bismillah suka sa kai, ginin bene ne hawa ukku akwae Ofisoshi daban daban da bangarorin gudanar da aikin kamfanin ko ina an zuba nagartattun furniture da suka dace da wurin wani abun ma sai Office ɗin Haisam wata daula ce guda akwae kuma ɗakin taro wanda aka sa haɗaɗɗan zunguren tebur aka kewaye shi da kujeru mahaɗin shi, haka akai ta zagayawa wurare ana ɗaukar hotuna da Vedios Mutane sai yabo da sa Albarka suke yan jarida nata yi ma mutanen tambayoyi ciki harda su Fatuu aka tambayesu irin farincikin da suke ciki, bayan an gama duba ko ina saida akayi addu'o'i sannan aka fita daga nan kuma Villa aka nufa don yin lunch event, komai dai ya ƙayatar an ci an sha anyi hani'an sai fatan Allah ubangiji yasa ma kamfanin albarka ake, a ranar kusan kowacce tashar Tv saida aka nuna bikin buɗewar haka Social media Maganar sabon kamfanin kawai ake da gidajen radio ana tallata irin ayyukan da kamfanin zai rinƙa yi har da tashoshin wasu ƙasashen an nuna dasu bbc, a ranar da daddare Khalid na zaune a falon gidanshi yana kallon bikin buɗewar a NTA, lokacin da aka nuno Fatuu na magana da turanci tana murmushi shima ɗan murmushin yayi saidai nashi yafi kama dana takaici don kuwa shi yasan yayi babban rashi kuma har abada bazata fita a ranshi ba, matarshi Hafsat ce ta dawo cikin falon daga kwantar da ɗiyarsu Zarah bayan ta zauna ya nuna mata Fatuu cikin Tv ɗin yace mata wannan itace Fateema, kallon Tv ɗin tayi kafin ta juyo ta kalleshi da alamun rashin fahimta tace mashi wace Fateema yay shiru kawai tana ta kallonshi can yace mata ta garinsu yana faɗin hakan ta gane don tasan labarin da ita zai aura aka fasa saidai bata san dalilin fasawar ba, maida idonta tayi kan Tv ɗin lokaci guda taji Fatun ta burgeta ta juya da ɗan murmushi tace mashi tana da kyau sosae yay ɗan guntun murmushi kawai bai ce komai ba can sai ya miƙe ma ya nufi hanyar Bedroom ta bishi da kallo. Bayan buɗe kamfanin ranar Monday aka fara aiki a cikin shi, a yadda Haisam ya shirya zasu ɗan daɗe anan daga baya sai su koma America suyo parking ɗin dawowa Nigeria gaba ɗaya dama ya aje aikin kamfanin da yake acan saidai ba kwata kwata ya daina aiki dasu ba akwae wanda zai cigaba da yi masu sannan shima akwae aikin da daga can za'a rinƙa yi mashi a Companyn shi, bayan wata biyu akayi bikin Jidderh da Saurayinta Sadeeq ɗan Minister wanda bayan hawan Senator Ali kujerar shugabanci ya sake ba Mahaifin nashi muƙamin Minister, ba ƙaramin shagali aka sha ba auran ɗiyar shugaban ƙasa da kuma ɗan Minister wanda anan Abuja aka ɗaura ya kuma samu halarta manyan mutane daga ko ina ciki da wajen ƙasar nan sai fatan Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Tuni aiki ya kankama a kamfanin Haisam anata neman aiki bayan wata ukku da buɗeshi lokacin wata guda da yin bikin Jidderh suka koma America, sati biyu sukai suka dawo acan aka baro Nameer da Mino sai sun gama karatunsu nan da shekara ɗaya da wasu watanni suma zasu baro can, Bayan dawowarsu Haisam Nigeria a yadda ya tsara zasu zauna a gidanshi ne, dama duk mazan gidansu kowa yana da gida da Dad ɗinsu ya mallaka masu saboda ba zaune suke ba dundundun yasa basu zauna acan ba suke zama a gidansu in sunzo Abuja, shi Nameer wanda yake zaune inda aka kai Mino shine nashi shima Haisam nada nashi shima a Asokoro saidai bayan dawowar tasu Dad ɗinsu yace mashi su fara zama anan gidanshi inda suka baro suka koma Villa don kar a bar gidan hakanan in aka ƙara wasu shekaru sai su koma nasu, hakan aka yi anan gidan suka zauna duk da yayi masu girma sosae, bayan dawowar su bada daɗewa ba Fanan ta samu aiki a National Hospital Fatuu kuma Haisam yay mata magana kan tafiyarta ƙasar india yin karatun Medicine amman sai tace mashi tunda anayi anan kawai ya bari sai tayi nan ba sai ta tafi wata ƙasa ba, ta yanke hakan ne don bata son yin nisa dashi yace mata amman karatun nan zai iya mata wahala tace lafiya lou in dai za'a koya mata to zata iya ya amince da hakan dama shima kawai don ya cika mata burinta ne zai barta taje India amman ba don yana son yin nisa da ita ba, cikin sa'a ta rubuta Jamb kuma points ɗinta ya kai yadda ake so don karatun likitancin, ba tare da wata wahala ba ta samu Admission a ABU Zaria Haisam ya kama mata gida mai kyau a zariar harda Security aka aje mata sannan tasa Iya ta samo mata mai aiki yar'uwarsu wadda dattijuwa ce daga can Daura suka zauna tare, lokacin data fara karatun tayi ma Haisam magana kan yasa akawo mata motarta daga Katsina amman sai yace tunda Amadu ke amfani da ita ta bari za'a kawo mata wata daga Kaduna hakan kuwa akai, Gidan Haisam ya zama biyu Abuja da Zaria, duk Weekend yake zuwa Zaria wani lokacin a mota ko kuma ya hau jirgi zuwa Kaduna daga nan ya wuto Zaria idan kuma bai samu zuwa da Weekend ba cikin ranakun aiki yake ware rana yazo ya kwana sai ya koma wani lokacin kuma Fatun ce ke zuwa can Abujar akwae driver musamman dake kai ta, su Twins da Esha dai duk suna a Villa wurin Mom sai Weekend Fanan ke ɗaukkosu nan wurinta, sosae Fatuu ke jinjina ƙokarin da Haisam ke yi na zaryar zuwa wurinta ta san duk don ƙaunarta da yake yi ne, duk in yazo haka zatai ta mashi godiya da Addu'o'i, bayan wasu watanni da fara karatun nata suka ji Yadikko ta haihu abun yazo masu a bazata don basu san da tana da ciki ba aikuwa sunyi murna karma Fatuu da Mino suji don ta daɗe bata haihu ba sun ma ɗauka ta gama ne duk da Yadikkon bata wani manyanta ba haka shima Baffan nasu ba wani manyanta yayi ba haihuwa ta biyar ce tayi gashi namiji ta haifa dama bata da ɗa namiji Fatuu taji daɗi data haihu cikin Weekend, da satin suna ya zagayo ranar Friday tana gama lectures ta wuce Abuja washe gari Asabar suna da safe suka bi jirgi zuwa Yola ita da Esha harda Fanan, daga gidan gwamnatin Yola aka tura Motar da zata ɗaukesu harda ta Security suka wuce garin nasu, lokacin da suka isa tayi mamakin ganin yadda aikin hanyar da ake masu yayi nisa harda rijiyoyin burtsatse aka yi masu Fanan sai yaba garin take tana faɗin ya burgeta, anan ta iske Gwaggo da Haulat su jiya suka zo sosae kowa ya nuna farincikin zuwan nasu sai nan nan ake dasu ba kamar Fanan, Yadikko ma sosae tayi murnar zuwansu nan Fatuu ta bata saƙon su Mom harda Aunty kayane masu kyau da tsada atamfofi da laces sai kayan baby wanda yaci sunan Arɗo wato Ibrahim, Fatuu sai santin Babyn take harda ce ma Yadikko ta bata shi tana dariya tace ta ɗauka Fanan da tunda suka zo tana ruƙe dashi tace a'a ita za'a ba sai dariya ake masu, lokacin da Fatuu ta kira Mino Vedio call harda ƙwalla tayi ganin an haɗu banda ita, washe gari da wuri suka fara shirin tafiya saboda bayan sun koma Abuja a ranar kuma Fatuu zata wuce Zaria, tunda Aysha taga suna shirin tafiya ta shiga roƙon Fatuu ta tafi da ita harda ƙwallanta Gwaggo tace da kuma tace ita zata bi Ayshar tace a'a yanzu Adda Fatuu take son bi, to itama Fatun taji tana son tafiya da ita dama Mino na niyyar ɗaukarta tace mata ta shirya kayanta su tafi, Yadikko najin hakan tace ya za'ai ta kama ta tafi da ita ba tare da izinin mijinta ba ai bai kamata kawai ace ta ɗauketa taje masu da ita ba Gwaggo tace hakane kamata yay ace sai ta ambayi izinin shi duk da tasan bazai ƙi ba amman dai yana da kyau ta tambaye shi izni tace to, lokacin data kira Haisam ta faɗi mashi tana son tahowa da Aysha don ta nuna tana son biyota Murmushi yay yace yanzu don zatayi hakan shine sai ta faɗi mashi kada ta manta shi da ita abu ɗaya ne duk abunda yayi mata to shima yayi mashi tana murmushin jin daɗi tayi mashi godiya, wurin ƙarfe sha ɗaya na safe aka zo ɗaukar su suka yi sallama da kowa sai Godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci ake ma Fanan, harda uban naman suna aka basu dana su Mom dama saboda su aka fara aikin naman tunda wuri, kamar kar a rabu haka aka rakosu tare da Aysha dake ta faman washe baki harda su Gwaggo da Haulat su sai gobe zasu tafi suma ta jirgi suka zo kuma tashi zasu koma. Tare da Aysha Fatuu ta koma Zaria Asabe mai aikin Fatun ke kula da ita in ta tafi Makaranta daga baya itama Ayshar Haisam ya sakata a wata private dake anan layout unguwar da suke aka sata aji ukku na Secondary. Cikin ɗan lokaci HAIFAT TechWorld ya samu kar6uwa a faɗin ƙasar nan, bama nan kaɗai ba harda wasu ƙasashen don kamfani ne da babu kamar sa a yankin Africa ta bangaren technology dama kuma yanzu harkar fasaha ba ƙaramin ci take ba, akwae abubuwa da dama da kamfanin ke samarwa wanda ada sai an dangana da ƙasashen turai yanzu kam nesa tazo kusa a kowacce rana ba ƙaramar riba Kamfanin ke samu ba. A kwana a tashi ba wuya a wurin Ubangiji gashi har kamfanin yayi shekara ɗaya da buɗewa anyi Addu'o'i da bikin murnar cika shekarar inda aka bayyana irin nasarorin da companyn ya samu da kuma irin ayyukan cigaba da ya kawo ma ƙasar nan aka ƙara samun masu son saka hannun jari, an ci an sha an ba ma'aikatan kamfanin masu ƙwazo kyaututtuka shima Haisam ya samu lambobin yabo abun saidai ace Alhamdulillah, bayan cikar kamfanin shekara ɗaya da wasu watanni su Nameer suka dawo Nigeria gaba ɗaya don duk sun gama karatun su, bayan dawowar su Nameer ya fara aiki shima a kamfanin a matsayin Software engineer, ganin Fatuu na karatu a Zaria kuma tana zaune a can Nameer ya yanke nemawa Mino Admission don ta yi degree kan abunda ta karanta a America wato Nursing dama matsayin diploma ce tayi, ba tare da wata wahala ba aka samar mata itama ta fara karatu a can ta zauna a gidan Fatuu, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Fatun ba dama gidan babban gida ne kowacce da part ɗinta in mazajen su suka zo amman in suka tafi gaba ɗaya harda Aysha a part ɗin Fatuu suke zama rayuwar karatun nasu gwanin daɗi sam basu da wata matsala. A bangaren Kamalu har ya shiga shekara ta ukku itama Farha tana cikin yin Master's Degree ɗinta a jami'ir Lagos, a bangaren soyayyarsu suna cigaba da gudanar da ita sosae saidai matsalar da Kamalun ke fuskanta a wurinta shine ta cika kishin tsiya ba dama ta kirashi taji yana waya ko bai ɗauka ba sai ta fara zargin ko da wata yake waya ko kuma ya rage sonta haka dai yake ta haƙuri don yasan saboda son da take mashi ne yasa take mashi hakan kuma shima yana son ta sosae. Kwance tashi har Kamalun ya gama karatun shi na Degree, cikin sa'a result ɗinshi yayi kyau sosae saura kuma yin Nysc, result ɗin nashi na fitowa Fatuu tayi ma Haisam magana kan in zai yuwu ya ɗauke shi aiki a company ɗinshi tunda abunda ya karanta ya danganci aikin kamfanin yace mata lafiya lou zasu ɗauke shi daya gama Service sosae taji daɗi dama ita abunda bata so shine ace Hajiya Maryam ce ta samar mashi aiki gudun wata rana a goranta mashi, Abuja Haisam yasa aka kawo shi yin bautar ƙasan a kamfanin shi ya zauna a gidan su kullum in Haisam ɗin zai tafi aiki tare suke tafiya hakan kuma ba ƙaramin daɗi yayi ma Fatuu ba, tun ma kafin Kamalun ya zama ma'aikacin kamfanin Haisam ya yaba da ƙwazon shi cikin ɗan lokaci Kamalun ya ƙara murmurewa ya zama kalar samarin Abuja, gab da Kamalu zai kammala bautar ƙasar aka fara shirye shiryen yin za6e yayin da waɗanda ke akan mulki duk suka bayyana muradinsu na yin tazarce ciki harda Dad ɗinsu Haisam wanda shi tun kafin ma ayi za6en mutane har sun za6e shi kawai don ya zama dole sai anyi zaben amman Al'umma basu ƙi kawai yaci gaba ba don a mulkinshi sun shar6i romon demokaraɗiyya ba kaɗan ba, a cikin shekaru huɗun da yayi abubuwa da dama sun inganta kama daga ilimi, lafiya, harkar tsaro, wutar lantarki, ruwan sha hanyoyi da dai sauransu gashi an tallafa ma talakawa ta yadda da yawa sun samu abun yi yanzu tun a makaranta ake koya ma yaro sana'a don ya tashi yana da sana'ar yi haka manoma ma harkar abinci ta inganta sosae ake amfani da abincin nan gida gashi da yawan mutanen mu masu ƙwazo dake aiki a ƙasashen waje yayi yadda yay suka dawo suna ma ƙasa aiki hakan ba ƙaramin inganta bangarorin da suke aiki yayi ba ciki harda Asibitoci yanzu saidai don ra'ayin mutum yaje asibitin ƙuɗi ko ya kai ƴaƴanshi makarantun kuɗi ba wai don rashin ingancin na gwamnati ba don komai ya gyaru haka tsofaffin masana'antu da suka daɗe da daina yin aiki duk an farfaɗo dasu abun dai sai son barka (Allah ka bamu shuwagabani irin haka Alfarmar Annabin rahama (S.A.W), Amin ya Hayyu ya ƙayyum). Bayan gudanar da za6e tuni President Ali Adamu Zakee ya koma kan kujerar shi aka ci gaba daga inda aka tsaya, bayan yin za6en Kamfanin Haisam ya cika shekara ukku batun nasarorin da ya samu ko yake samu abun ba'a magana, a yadda suke yi duk ƙarshen shekara ake raba ribar da aka samu kuma duk in suka raba sai yaba Fatuu da Fanan wani kaso mai tsoka zuwa shekaru ukkun sai gashi Fatuu ta tara kuɗi masu ɗan yawa a yadda ta tsara in suka kai kuɗin zuwa Hajjin mutum biyu sai ta biya ma Baffanta da Gwaggo. Kamalu na gama bautar ƙasar shi aka fara shirye shiryen auren shi da Farha lokacin itama ta kammala karatunta, ba ƙaramin shagali aka sha ba bikin ɗiyar Minister ɗiyar shugaban ƙasa, gaba ɗaya hidimar bikin a Abuja aka yi ta gashi wata gwaninta da Hajiya Maryam tayi ta ban mamaki itace gaba ɗaya Amaryar da Angon ta haɗa tayi masu lefe dama tunda bikin ya taho ta sanar ma Hajiya a faɗi ma su Gwaggo kada ayi ma Farhar lefe lokacin har wasu sukai tunanin ko don tasan ba lalle Kamalun yayi lefen daya dace bane sai gashi ta bada mamaki ai kuwa gaba ɗaya ƙasa ta ɗaukka sai zancen ake na ta ba talaka ɗiyarta kuma tayi masu lefe gaba ɗaya, tun kafin bikin Haisam ya roƙi Dad dinshi kan yaba Kamalun gidan da zai zauna kafin ya mallaki nashi tunda zasu fara aiki tare, ɗaya daga cikin gidajen shi na Sabuwar Estate ɗin shi dake a Gwarinpa ya ba Kamalun, ganin babban gidane yasa Haisam ɗin yace mashi ya faɗi mashi yadda zai rinƙa biyan haya Dad ɗin nashi yace dama ɗa yana haya a gidan babanshi ne ai Kamalun kamar ɗan shi yake don haka bashi yay ya zauna kafin Allah yasa ya mallaki nashi, sosae Haisam yaji daɗin hakan yay mashi godiya da Addu'oi, lokacin har Hajiya Maryam tayi niyyar basu gidan da zasu zauna aikuwa hakan da Haisam yayi ba ƙaramin daɗi yayi ma Fatuu da Amadu ba dama sune masu gudun ayi ma Kamalun abun da za'a iya goranta mashi, ko ban faɗa ba kunsan ba ƙananun kayan ɗaki akai ma Farhar ba wanda in nace zan bayyana to ni kaina wasu abubuwan bansan ya zan faɗe su ba gida dai yayi kyau! yayi kyau!! abun saidai ace Ma sha Allah Kamalu anyi auren gata abun na Allah ne, ƙarshe dai Farha ta zama matar Kamalu ɗan fillo duk wanda yaga hotonunsu da sukai na pre wedding sai ya sake kallo wasu mutanen ma har ƙaryata cewa Kamalun ɗan talakawa ne suke domin ba kama ba alama, sai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba Amin, bayan bikin Hajiya Maryam ta basu kyautar motoci masu kyau Kamalun ya fara yin aiki a Kamfanin Haisam ita kuma Farhar Mom ɗinta ta samo mata aiki a Federal Inland Revenue. A cikin shekarar lokacin da zuwa aikin Hajji yayi Kawu Mani ya biya ma Gwaggo bayan duk Matan shi ya biya masu sunje aikuwa sosae su Fatuu sukai Farinciki itama Gwaggon tayi farincikishi sai hamdala take, bayan gama murnar biya ma Gwaggon Haisam da Nameer sukai ma su wata irin bazata Haisam ya biya ma Baffansu shi kuma Nameer ya biya ma Yadikko wayyo daɗi! farincikin yayi yawa saida aka dangana da yan koke koke, bayan tafiyarsu ne ciwo ya tasar ma Arɗo sosae har saida su Fatuu da Haisam da Nameer suka je dubashi kafin su baro saida su Haisam ɗin suka kai shi Yola asibiti aka kwantar dashi ya miƙa kulawar shi a hannun Khalid, bayan kwana biyar aka sallame shi ba laifi ya ɗan samu sauƙi suka koma gida, gaba ɗaya hankalin Baffansu Fatuu a tashe yake da jin zancen ciwon sosae yake ma mahaifin nashi Addu'a acan Makka kan Allah ya bashi lafiya, Alhamdulillah Mahajjata sun dawo gida lafiya su Gwaggo an zama Hajiya ma sha Allah, kwana ukku da dawowar su Baffa Allah yay ma Arɗo cikawa, akace mahaifi mahaifi ne duk da dama arɗon ya tsufa sosae Baffansu Fatuu yaji mutuwar tashi harda kukan shi don yasan mahaifin nashi ba ƙaramin son shi yake ba ko kafin ya rasu saida ya bar wasiyyar cewa shi zai gaji mulkin shi na arɗo kuma ya roƙe shi kan ya haɗa kan iyalin kada ya bari a samu 6araka, lokacin da Fatuu taji labarin rasuwar sosae ta damu harda kukanta sa6anin lokacin da tana yarinya bata da burin daya wuce arɗon ya rasu duk da harda ƙuruciya, washe gari suka tafi gaisuwa suna can Mom da Aunty suka je dasu Fanan da Jidderh har Aunty Laila ma tazo Lokacin Fauzy basu ƙasar shiyasa bata zo ba amman Hajiya Zainab tazo, sosae suka yi ma su Fatun kara har mai girma shugaban ƙasa ya turo wakilci an zo anyi masu gaisuwa, duk a ranar dasu Mom suka zo suka koma amman su Fatuu sai da akayi sadakar uku washe gari suka dawo. Ƙarshe dai kuɗin da Fatuu ke tarawa canza ra'ayi tayi tunda an kai Baffan nata makka ta yanke buɗe Foundation da zata fara tallafa ma talakawa a Katsina, koda Fanan taji niyyarta nan tace itama tana so su buɗe tare Haisam daya ji ya basu goyon baya harda gudunmawa, haka su Mom harda Hajiya Maryam da President duk suma sun basu gudunmawa, daga baya aka buɗe Foundation ɗin mai suna HAIFAT FOUNDATION, bayan buɗe shi a hannun Gwaggo suka damƙa kula da shi su kawu Amadu da Tk da matansu su Haulat da Husnah suka zama masu taimaka mata wurin gudanar da ayyukanshi harda Aunty Mareeya da Feenah duk sun shiga cikin masu gudanar da ayyukan shi sai fatan Allah ya sanya albarka, Bayan komawar President Ali kan mulki da shekara ɗaya da wasu watanni ne Hajiya ta kwanta rashin lafiya, farko daga zazza6i ranar wata lahadi ta tashi da shi bayan tasha magani ta ji ta samu sauƙi, da daddare bayan ta kwanta ciwo ya dawo mata zuwa wayewar gari jikinta yayi zafi sosae lokacin da Tk ya dawo daga Masallaci ya je gaisheta kamar yadda yake yi kullum da ƙyar ta amsa mashi sallama, bayan ya shiga a kwance ya isketa saman carpet tana sanye da Hijab da ƙyar tayi ƙarfin hali tayi Salla, jin yadda ta amsa mashi gaisuwar tana nishi dama gashi ya ganta a kwance ƙasa yasa shi tambayarta kamar bata lafiya tace mashi tun jiya take jin zazza6i sama sama tasha magani to da daddare ya idasa rufeta yanzu ma da ƙyar tayi salla yana jin haka da alamun tashin hankali yace bari ya fiddo Mota su tafi asibiti, batare daya jira jin mi zata ce ba ya miƙe da sauri ya nufi ƙopar fita, bayan ya fito saida ya shiga yayi ma Husnah magana kan taje ta taimaka ma Hajiyar ta shirya sai su tafi asibitin tare, itama hankalinta ya ɗan tashi jin Hajiya ba lafiya don da wuya kaji ciwo ya kwantar da ita kaji dai tana cewa bata jin daɗi, bayan zuwan su Asibitin wanda suke zuwa ba 6ata lokaci aka dubata tare da yi mata aune aune bayan an turo result likita ya yi masu bayanin zazza6in malaria da typhoid ne ke damunta har saida Hajiya ta ɗan yi mamakin jin harda typhoid, da likitan yace ko a bata gado don a dubata sosae ta kuma huta tace a'a adai yi mata abunda ya dace yanzu ta koma gida sai taci gaban da shan magani, bayan anyi mata allura an bata maguguna suka tafi, sai bayan da suka dawo Saude tasan da rashin lafiyar nata nan fa suka shiga bata kulawa kowa ya damu Hajiya ba lafiya Tk yace ko ya kira Haisam ya sanar mashi Hajiyar tace a'a kada a tada masu hankali zata samu sauƙi in sha Allah, Amadu ne ya kira Tk kan ya fito su wuce wurin aiki yaga lokaci na niyyar ƙurewa ya sanar mashi da Hajiya ce ba lafiya, Gwaggo na jin Hajiya ba lafiya suka taho harda Haulat da Amadun, gaba ɗaya duk kowa ya shiga damuwa gashi bata cin abinci sai ɗan abu mai ruwa shima daga baya aman abunda tasha ta fara yi ganin haka yasa tk yace ko su koma asibitin tace mashi a'a dama haka zazza6i yake da naci ai zata samu sauki, wasa wasa saiga ciwo nata gaba maimakon a samu sauƙi cikin kwana biyu sai gashi ya kai komai sai su Saude sun yi mata lokacin da Gwaggo tazo taga halin da take ciki ta tambayi Tk yan Abuja sun san bata lafiyar cikin damuwa yace Hajiyar ta hana a sanar masu Gwaggon tace ai ba biye mata za'ai ba, nan take ta buga ma Haisam waya ta sanar dashi da alamun tashin hankali ya tambayi abunda ke damunta ganin ko jiya sunyi waya da ita amman bai gane bata lafiya ba tayi mashi bayani, ana gama sallar Magrib sai ga Haisam ɗin ya iso Tk ne yaje ya ɗaukko shi tun suna kan hanyar zuwa gidan Dad ɗin shi da Hajiya Maryam suka kira suna tambayar ya isa ya jikin Hajiyar yace masu yana hanyar zuwa gidan, lokacin da yaga yanayin jikin Hajiyar bayan ya iso hankalinshi ya ƙara tashi don duk ta faɗa da gani tana jin jiki Haisam ɗin yace ma Tk tun yashe ne bata lafiya cike da damuwa yace kwananta biyu nan ya sanar mashi yadda sukai da likita harda kwantar da itan da akace za'a yi taƙi, bayan Dad ɗinshi ya kirashi ya sanar mashi gaskiya tana ɗan jin jiki Hajiya Maryam harda Vedio call suka yi taga Hajiyar nan fa hankalinta ya ƙara tashi tace ma Haisam gobe da safe zata zo ta ɗauketa, a daren ranar mutanen da suka ji zancen ciwon duk da zullumi suka kwana, washe gari wurin ƙarfe bakwai Hajiya Maryam ta iso nan ta hau su Tk da faɗan ya tana rashin lafiya zasu ƙi kira su sanar tunda ta fara ciwon, bawan Allah harda yar ƙwallan shi yace mata Hajiyar ce ta hana don kada a tada masu hankali aikuwa ta ƙara balbale shi da faɗa harda cewa ko don ba Mahaifiyarshi bace, wannan kalma ta saka shi fashewa da kuka, cikin halin ciwo Hajiya tace mata don me zata faɗi mashi haka bata ji yace ita ta hana ba ko so take yay mata rashin biyayya yaƙi jin Maganarta ganin ran Hajiyar ya 6aci ga kuma halin da take ciki yasa ta ba Tk ɗin haƙuri kan Maganar da tayi, wuraren ƙarfe sha ɗaya suka tafi da Hajiyar Abuja aka bar su Tk da kewa da damuwa sai Addu'ar Allah ya tashi kafaɗun Hajiyar suke, su Gwaggo ma duk sun damu haka yan'unguwa da yawanci duk basu san da Hajiyar bata lafiya ba sai yau da aka tafi da ita duk an damu yara da manya anata mata Addu'o'i. Bayan zuwa da Hajiya Abuja a babban private hospital ɗin likitansu na Germany wanda yana ɗaya daga cikin likitocin da Shugaban ƙasa ya maido nan wanda yana aiki a Asibitin Gwamnati sannan kuma ya buɗe private hospital ya zuba ƙwararrun ma'aikata wanda wasu abokan aikinshi ne a can, bayan anyi mata aune aune aka tabbatar da abunda akace yana damunta a Katsina suke damunta kuma ma da sauƙi sosae nan aka tabbatar da jikinta yana buƙatar hutu sosae wataƙil bata hutawa sosae ko tana yawan yin zurga zurga, ran Hajiya Maryam ne ya 6aci tace ita dama ba son zamanta take a Katsina ba kawai don ta nuna hakan take so tunda basu a kusa da ita dama ai abunda taga dama zatai tayi ba mai hanata ko aikin NGO da take da ƙyar aka samu ta daina, ita dai Hajiya jin abunda likitan yace kawai tayi don tasan ita ba wata zurga zurgar da take yi, a ɗaki na musamman aka kwantar da ita sosae ake bata kulawa hatta zuwa dubata an ware lokacin da za'a rinƙa zuwa don kada a dameta, bayan sati ɗaya sai gashi jikin nata ya fara yin kyau lokacin har massaging jikin ake mata ana kuma bata lafiyayyun abinci da zasu ƙara mata ƙarfi da kuzari, bayan tayi satin su Tk da Gwaggo suka zo dubata harda Amadu gaba ɗaya sunji daɗi ganin yadda ta fara samun sauƙi ba kamar Tk kullum da zullumin ciwon nata yake kwana duk ya damu kwanansu biyu suka koma, bayan sati biyu aka sallameta suka wuce Villa da ita, zo kaga murna Hajiya ta warke kowa sai farinciki yake duk sun haɗu harda su Fatuu, a can Katsina ma sai murnar jin Hajiya ta samu lafiya ake, anan Villa aka cigaba da kula da ita tana shan magunguna, bayan tayi sati biyu ya kama watan ta guda a Abuja lokacin ta warke sosae har ɗan ƙara jiki tayi da haske tace ma President tana son komawa Katsina nan fa ya shiga roƙonta kan ta haƙura da zaman Katsina taci gaba da zama nan amman ta nuna mashi ita tafi son zaman can, koda Hajiya Maryam taji itama zuwa tayi suka haɗu da President ɗin suna roƙonta kan ta zauna nan Hajiya Maryam harda yin ƙwalla tana faɗin su basu son su rasata ne yanzu da basu yi gaggawar ɗaukkota nan ba da Allah kaɗai yasan mi zai faru Hajiyar na murmushi tace abunda Allah ya ƙadarro shi zai faru da lokacinta yayi sai ta tafi kuma a tunaninta su suka sa ta warke ne, Hajiya Maryam ɗin tace eh duk da hakan dai gara ta zauna anan tafi samun kulawa, ƙarshe dai saida suka yi nasarar tursasa mata ta dawo nan amman tace masu dole zata koma tayo sallama da mutane Hajiya Maryam harda cewa in don wannan ne ai sai suje rana ɗaya tayo su dawo tace a'a tana buƙatar lokaci ba wai daga taje zata dawo ba don haka aƙalla zata yi wata guda Hajiya Maryam tasa rigimar gaskiya yayi yawa da ƙyar aka tsaya kan sati biyu shima saida Hajiyar ta kafe kafin ta amince, kafin su tafi ne tace tana son bar masu wasiyya ko ba yanzu ba in ajali ya risketa tana son kada su tada Tk daga gidanta koda zasu yi amfani da gidan to a ware mashi isasshshen wurin da zai zauna ta bashi halak malak sannan su Saude ma a barsu suci gaba da zama har sai in su suka buƙaci tashi ko kuma su in suna buƙatar su tashi to sai su siya ma Sauden gida, gaba ɗaya suka haɗa baki wurin cewa in sha Allahu zasu yi kamar yadda tace Hajiya Maryam tace amman ta daina faɗin wasiyyar nan tana tada masu hankali, Hajiyar tayi yar dariya tace to miye abun tashin hankali abunda ya zama dole da lokacinta yayi kuma su ai yan gata ne tunda sun rayu da ita tsawon lokaci wasu da yawa ma basu san Mahaifiyarsu ba, Hajiya Maryam ɗin tace duk da hakan dai suna roƙon Allah ya yasa su cigaba da rayuwa da ita tsawon lokaci tana murmushi ta amsa da Amin, bayan kwana biyu ta dawo Katsina harda First Lady da Aunty suka rakota, zo kaga murna Hajiyar Sanata ta dawo kar ma su Tk gaba ɗaya bakunansu sun ƙi rufuwa dama Tk kusan yafi kowa shiga damuwar ciwon nata zuciyarshi tay ta raya mashi kodai mutuwa Hajiyar zata yi shi bama damuwar shi makomarshi ba a'a yadda zai rayu babu ita shine yafi tada mashi hankali don ba ƙaramin shaƙuwa yayi da ita ba ko Mahaifiyar shi bai jinta a ranshi kamar yadda yake jin Hajiya, Mutane sai so suke su shigo gidan suga Hajiya amman ba dama don ƙopar gidan dankam take da Security wasu kuma sun zagaye gidan wanda babu wasa a tattare dasu gasu da manyan makamai, su Gwaggo dai sun shiga har sun gaisa da Mom da Aunty sun masu ya maijiki, haka manyan mutane mata da maza da yan siyasa sun zo duk an barsu sun shiga sun gaisa da su Mom tare da yi masu ya mai jiki har Governor da First Lady ɗin Katsina sun zo unguwa fa ta ɗinke ba abunda kake gani sai motoci masu numfashi da jiniya, Washe gari su Mom suka tafi bayan tafiyarsu ne Tk ya faɗi ma Hajiyar mutane yan unguwa nata son su shigo su gaishe ta an hana su, tana jin hakan ta bada iznin duk wanda yazo a barshi ya shigo nan fa yan unguwa sukai ta shigowa dubiya manya da yara da dattawa Hajiya tayi amfani da wannan damar duk wanda yazo gaidata sai tayi mashi bankwana ta nemi yafiya, gaba ɗaya gwuiwar mutane sai tayi sanyi kuma jin Hajiyar zata bar Katsina harda masu yin ƙwalla tun ma ranar tafiyar bata yi ba, kowa ya nuna rashin jin daɗin tafiyar da zata yi tana ta ce masu kada su damu ai ba shikenan an rabu ba indai da sauran rayuwa za'a cigaba da zumunci kuma ga Tukur nan zai cigaba da zama a gidan don haka ba abunda zai fasu tsakaninsu, tunda su Tk da Saude da Husnah suka ji zancen komawar Hajiyar Abuja gaba ɗaya suka shiga damuwa kowa jikin shi yay sanyi, bayan dawowarta da sati ɗaya ne ranar Friday da daddare ta kira Tukur da Saude a cikin Bedroom ɗinta, a kan carpet suka zauna ita kuma tana zaune a bakin gado idanunta sanye a cikin gilashi, sun ɗan ɗauki lokaci shiru tana ta kallonsu su kuma duk sun sunnar da kai yayin da ƙirjinsu ke bugawa tamkar ana masu luguden ta6are can Hajiyar ta nisa kafin a nutse ta fara magana, "Na buƙaci ganin ku ne don yin maganar da nasan bazaku ta6a jin daɗin ta ba kamar yadda nima ba don daɗin yasa zanyi maku ita ba, da farko dai ina mai matuƙar godiya a gare ku godiya mara iyaka, gaba ɗayan mu bamu da wata dangantaka ta jini face ta kasancewar mu musulmai amman Allah ya haɗamu muka zauna tare tsawon lokaci har muka zama tamkar dangin juna, ina son ku sani, ku mutane ne masu matuƙar muhimmanci a gare ni wanda wasu ma da yawa da nike da alaƙa ta jini dasu basu da irin muhimmancin a wurina, Tukur, kai tamkar ɗan dana haifa kake a wurina duk da kafi kama da jikana amman kallon ɗana na jini nake maka, haka kema Saudatu ina matuƙar jin ki a rai na ba kuma don hidimar da kike man ba sai don ƙaunar ki a gare ni wadda nasan ita tasa kika zauna tsawon lokaci kina hidimta man ba tare da gajiyawa ba kuma daidai da rana ɗaya bazan iya cewa ga lokacin da kika sa6a man ta hanyar yi man rashin biyayya ko makamancin hakan......to, gaba ɗaya dai ba abunda zance sai dai ince maku Nagode, Nagode Allah ubangiji ya saka maku da mafificin Alkhairinsa ya ji6anci al'amuranku, ina kuma roƙon shi da yadda ya haɗa mu a gidan duniyar nan ya haɗa mu a gidan aljanna muci gaba da yin rayuwa tare, nasan bazaku rasa jin zancen komawata Abuja ba duk da bamuyi maganar da ku ba kafin yanzu, nasan dole kuji ba daɗi amman ina mai baku haƙuri dama haka rayuwa ta gada in har aka haɗu to tabbas wata rana sai an rabu koda kuwa ba mutuwa ba, don haka inason ku kwantar da hankalinku dan na tafi ba yana nufin an rabu ba kenan indai da rayuwa dole aci gaba da zumunci, kai Tukur zaka cigaba da zama a gidan nan koda kuwa bayan bani a duniya kana da kaso a cikin sa so nike Hajiyar Sanata taci gaba da wanzuwa ta dalilin ka, haka kema Saudatu zaku cigaba da zama keda mijinki har zuwa lokacin da kuke so ke bazance ki zauna dundundun ba saboda yanayin aikin mijinki a koda yaushe za'a iya canza mashi wuri dama ni na roƙa aka bar man shi tsawon lokaci muna tare ba'a ɗauke shi ba saboda ina jin daɗin zaman shi sai kuma yazo ya aure ki aka ƙara zama ɗaya...., akwae gida da nike son siya maki koda bani ba na faɗa za'a siya maki in kun buƙaci barin nan, A ƙarshe ina mai ƙara godiya a gareku sannan ina roƙon yafiyarku saboda ance zo mu zauna zo mu sa6a indai nayi maku ba daidai ba da sani na ko akasin hakan ina mai roƙon ku da ku yafe man ni dai na yafe ma kowa sannan ina mai roƙon ku da kuci gaba da kyautata ma abokan zaman ku", Saida ta gama Magana ta fahimci gaba ɗaya kuka suke jin sheshshekarsu tay shiru tana kallon su dama itama ƙarfin hali kawai take, bayan wani lokaci tace "To duk kun tasani a gaba kunata kuka ko nima so kuke ɗan ƙarfin halin da nike in karaya in sa kukan ne?" a tare suka haɗa baki cikin muryar kuka suka ce "a'a......" tace to su daina suyi haƙuri don Allah tun farko tasan dama dole suji ba daɗi to amman sai ayi haƙuri wataƙil dama Allah ya ƙaddaro zamanta Abujan ne tunda tuntuni suke son ta koma taƙi hardai yanzu sukai galabar sata ta koma suyi haƙuri ai ba'a rabu ba kenan kamata yay ma su gode ma Allah daya sa ta miƙe, nasiha sosae tayi masu suna ta sharar ƙwalla daga ƙarshe tace suje, har zasu miƙe tace to su basu yafe matan ba wannan magana ba ƙaramin ta6a masu zuciya tayi ba duk suka ce mata su wllh ba abunda ta ta6a yi masu ba daidai ba tace duk da haka dai su yafe mata, a tare suka haɗa baki suka ce sun yafe mata tare da yi mata Addu'o'i, bin su tayi da ido lokacin da suka nufi ƙopa, bayan fitar su ta maido idonta tana kallon gabanta can ta sa hannu ta ɗaga gilashin idanunta ta goge ƙwallan da suka gangaro mata........... 104 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ .........Suna fitowa Tk ya wuce ɗakin su Saude kuma ta nufi baya inda ɗakinta yake, a bakin gado ya zauna yaci gaba da yin kukan mai cin rai yana haka Husnah ta shigo ciki ma gareta har ya girma, zama tayi a kusa dashi fuskarta ɗauke da damuwa ta shiga bashi haƙuri kai kawai yake ɗaga mata, da yake tasan wurin Hajiya suka je cike da damuwa ta tambayeshi tafiyar dai zata yi da gaske ya ɗaga mata kai alamar eh ta ɗan girgiza kai itama duk wani iri take ji can ta kai hannu ta fara goge mashi ƙwallan tana bashi haƙuri, Saude ma tana komawa ɗakinta ta faɗa gado ta saka kuka mai sauti gwanin ban tausayi, ta ɗan ɗauki lokaci kafin Officer ya shigo ya isketa a haka, da alamun tashin hankali ya nufi bakin gadon ya zauna ya kai hannu yana ta6ata tare da kiran sunanta yana tambayarta lafiya miya faru, cikin kuka tace mashi da gaske Hajiya tafiya zata yi, cikin sanyin jiki yace mata eh yasani nan da sati guda ya shiga bata haƙuri yana nuna mata ai ba an rabu ba kenan za'a cigaba da zumunci yanzu ma daga wurinta yake tace ma zasu iya cigaba da zama a gidan, haƙuri yaci gaba da bata can ta ɗago idanunta sunyi jajir ta saukko daga saman gadon a tunanin shi wani wuri zata ko toilet kawai sai gani yay ta duƙa a gabanshi cikin kuka a marairaice tace mashi don Allah tana neman alfarma a wurin shi tana rokon ya dubi girman Allah yayi mata, gaban shi ne ya fara faɗuwa yace mata in sha Allah in bata fi ƙarfin shi ba zai yi mata, a marairaice tace mashi tunda dama a nan gidan suka haɗu har sukai aure kuma Allah bai sa sun samu rabon haihuwa ba don Allah tana roƙon shi ya sawaƙe mata Allah ne shaidarta tana jin Hajiya har cikin ranta bata jin zata iya cigaba da zama a gidan nan ba tare da ita ba, shiru yay yana kallonta duk da yaji ba daɗi data yi Maganar amman ta bashi tausayi yace mata yanzu in ya sawaƙe matan garinsu zata koma kenan tace a'a zata roƙi Hajiyar ne ta tafi da ita, shiru yay yana kallonta ta langa6ar da kai tana mashi magiya can yay yar ajiyar zuciya yace mata shikenan ta bari sai da safe zasu yi Maganar tunda yanzu dare yayi ya kama hannunta ya miƙar da ita yace suje ta wanke fuskarta. A wannan daren baccin su gaba ɗaya harda Tk ragagge ne, Washe gari Officer na dawowa daga sallar Asuba part ɗin Hajiya ya wuce, bayan ya ƙwankwasa ƙopar daga ciki ya jiyo muryarta tana bashi izinin ya shigo, zaune take kan darduma hannunta ruƙe da cazbaha, da hannu tayi mashi alamar ya shigo ya nufi inda take ya duƙa a kan carpet, bayan ta shafa Addu'a ta kalleshi da ɗan murmushi da sauri ya gaishe da ita ta amsa tayi mashi ya suka tashi ya amsa da Alhamdulillah daga haka yay shiru idon shi akan carpet, daga yanayin shi ta fahimci da wani abu tana ɗan murmushi tace mashi tana fatan dai lafiya ko da wani abu, dagowa yay a nutse yace mata dama Saudatu ce jiya da daddare ta roƙeshi kan yay mata wata alfarma to yace ta bari sai zuwa da safe shine yaga ya dace ya fara tuntu6arta gudun yay mata ba daidai ba, kai Hajiya ta jinjina ta tambayi wace alfarma take son ya yi mata ne nan ya faɗi mata duk yadda sukai da Sauden, "Humm, Saudatu Kenan, to yanzu kai ka amince zaka sawaƙe matan ne?" Hajiya ta faɗa tana ɗan murmushi idonta akan shi, ɗan shiru yay farko kafin yace tunda ta nuna hakan take so zai mata Hajiyar tace bai son auren ne ko kuwa, da sauri da alamun damuwa yace wllh yana son zamanshi da ita Allah ya sani kawai dai ya fahimci in bai yi mata yadda take so ba ba lalle zaman nasu yaci gaba da yin daɗi ba don ta nuna bazata iya cigaba da zama ba tare da ita ba, yar ajiyar zuciya Hajiya ta sauke ta juya ta kai hannu ta ɗaukko wayarta ta shiga kiran layin Saude bayan ta ɗaga tace mata tazo dakinta tana son ganinta, ba'a ɗau lokaci ba Sauden ta shigo cikin ɗakin da sallama tana sanye da doguwar Hijabi duk suka amsa mata ta nufo ciki, gefen Officer Hajiya ta nuna mata alamar ta zauna, bayan ta zauna ta gaishe da Hajiyar tare da yi mata an tashi lafiya da tambayar ƙarfin jikinta duk ta amsa mata daga haka Sauden ta sunkuyar da kanta idon Hajiya a kanta tana ɗan murmushi, a nutse cikin dattako ta fara magana tace taji yadda sukai da maigidanta saidai sam bata jin daɗin jin hakan ya fito daga bakinta ba a matsayinta na wadda take gani mai hankali taya zata tunkari mijinta da zancen ya saketa kenan ta za6i bauta a ƙarƙashin wani fiye da ubangijinta, da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a, "Aure shine mutuncin kowace mace Saudatu, nasan saboda kauna da sabo yasa kika za6i hakan saidai ni a wurina zaman ki a ɗakin mijinki shine abun alfaharina ba kamar in na tuna a gidana kuka haɗu har akai auren, kiyi haƙuri don na tafi ba yana nufin shikenan an rabu ba in sha Allahu za'a cigaba da yin zumunci in dai da rayuwar" ɗagowa Sauden tayi idanunta sharkaf da ƙwalla ta ɗaga mata kai kafin cikin disashshiyar murya tace mata to zata koma Daura, "To auren fa Saudatu, taya zaki koma can bacin ga mijin ki anan?", shiru ta ɗan yi idonta a ƙasa kafin tace "Hajiya don Allah ki bari in koma Allah ne shaidata bazan iya cigaba da zama ba a gidan nan in baki nan" shiru Hajiya tayi tana ɗan murmushi idonta a kan ta, cikin sigar rarrashi tace mata ta dai yi haƙuri ta zauna saboda aurenta Sauden tayi shiru tana matsar kwalla can Officer yace in hakan take so lafiya lou shi ya amince ta koma Daura din Hajiya tace to ya za'ai hakan yace ba komai indai hankalinta zai fi kwanciya sai ya rinƙa zuwa, ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace shikenan bari ta gani in zata iya neman alfarma sai a maida shi Daura da aiki dama tuntuni abunda yasa ya daɗe anan gidan ita ta roƙi alfarmar abar mata shi yanzu abunda za'ayi tunda dama zata siya ma Sauden gida in ta amince sai a siya mata acan Daurar sai su zauna a cikin shi, da sauri Sauden ta ɗaga kai alamar ta amince Hajiyar tayi murmushi tace to wurin ina take son a siya mata gidan tasa a bincika mata Sauden ta ɗago ta faɗi mata tace shikenan, kallon Officer tay tace ya jirata Maganar canjin wurin aiki ya yi kuma Addu'a Allah yasa a maida shi can yace Amin ta ƙara ce mashi zata turo mashi saƙon kuɗi sai ya juya ya haɗa da aikin nashi Allah ya ƙara rufa asiri ya amsa da Amin tare da yi mata godiya da addu'o'i ta amsa tare da cewa shikenan zasu iya tafiya. Tun bayan da Hajiya tayi magana dasu Tk game da tafiyarta gaba ɗaya duk sun shiga damuwa gidan ya koma shiru sam basu da wata walwala a haka har ranar tafiyar tata tazo, ranar ta kama Juma'a da safe jirgin Hajiya Maryam ya iso tazo tafiya da ita, bayan zuwan nata nan da nan gidan Hajiyar ya cika da manyan mutane musamman yan siyasa sun zo yi ma Minister sannu da zuwa da kuma yin sallama da Hajiya, da lokacin sallar Juma'a yayi gaba ɗaya a Masallacin gidan duk sukai salla, misalin ƙarfe huɗu na yamma ana gama sallar La'asar aka firfito don raka Hajiya Airport tuni an fito da akwatunan kayanta an saka a Mota don iya su kawai zata tafi dasu ba'a dauki komai na gidan ba, a gaban entrance aka jere motocin lokacin da Hajiya ta fito sanye da rantsatstsiyar lifaya tana dogara sandarta ta alfarma Tk na daga can gefe a tsaye idanunshi sunyi ja don tun da safe yake matsar ƙwalla, har su Gwaggo sun zo suma zasuyi rakiya Amadu ne zai kai su a Motar Fatuu, bayan an fara shiga cikin motoci Amadu ya nufi wurin Tk ya dafa kafaɗarshi yana bashi haƙuri yace mashi yazo suje suyi mata rakiya idanunshi cike da ƙwalla ya girgiza mashi kai yace su je kawai, ganin yanayin shi yana cikin matsananciyar damuwa yasa Amadun ƙyale shi ya juya, a tare Convoy ɗin motocin suka tashi gaba da baya motocin security ne idanun Hajiya na akan Tk dake tsaye har suka isa gate suka ta ɗan girgiza kai tare da rufe idonta, lokacin da suka fito kopar gidan cike yake da mutane yan unguwa tun dazu suke son shiga yin bankwana da Hajiya amman Security sun hana, motocin na fitowa suka shiga daga masu hannu suna faɗin sunan Hajiyar Sanata ganin haka yasa Hajiya tasa a dakata, bayan Jeep ɗin da take ciki ta tsaya ta sauke glass aikuwa mutane na ganinta suka nufo ta da sauri nan fa aka shiga tutsetseniyar kama hannun nata ana kiran sunanta harda masu yin kuka daga baya ma sai ta buɗe Motar ta fito aikuwa matan unguwa da yara aka shiga rungumeta ana kuka cike da ƙarfin hali take basu haƙuri tana kwantar masu da hankali tace ai ba an rabu ba kenan in sha Allahu za'a cigaba da zumunci kuma duk abunda take yi baza'a bari ba tunda ga Tk nan, ganin suna 6ata lokaci yasa Hajiya Maryam tayi ma security magana suka sallami mutanen Hajiyar ta koma cikin Mota, duk yadda ta daure saida ta matse ƙwalla motocin suka tafi anata cigaba da ɗaga ma Hajiyar hannu, mutane rahama ko iya haka za'a iya cewa Hajiya ta dace. Hajiya ta tafi ta bar mutane da kewa ba kamar su Tk don tun bayan tafiyarta yake ta zazza6i bawan Allah don ma Allah yasa yana da mata tanata aikin rarrashin shi duk da itama sosae take kewar Hajiya don ba ƙaramin shaƙuwa sukai ba ita kanta ɗiyar su Hauwa'u duk ta damu ko yaushe cikin tambayar yaushe Hajiyarsu zata dawo take sai an kira mata ita ta waya sunyi magana ko Vedio call take kwantar da hankalinta, ta bangaren Saude ma taso tafiya Daura bayan tafiyar Hajiya Officer ya rarrasheta kan tayi haƙuri tunda Hajiya tace zata nema mashi transfer sai su koma can baki ɗaya da haka ya samu ta haƙura, su Gwaggo ma duk sun yi kewar Hajiyar duk da su bama gida daya suke da ita ba amman da sun zauna suna hira sai sun yi maganarta, sai bayan wani lokaci Tk ya warware amman ko yaushe cikin jin kewar Hajiyar shi yake. Bayan komawar Hajiya Abuja da yan watanni Allah ya sauki Farha ta haiho san6aleliyar ɗiyarta mace kai kace ɗiyar aljanu ce don kyau gaba ɗaya mamanta da babanta ta biyo, a fuska da Kamalu take kama amman farinta na Farha ne sannan ƙwayar idonta ma ta Farha ce gashin kanta kuma baƙi ne wuluk kalar na babanta, cikin sa'a lokacin da akai haihuwar su Fatuu na hutu hakan ba ƙaramin daɗi yay masu ba, kowa ya ga Babyn sai ya furta ma sha Allah ana ta farinciki Hajiya Maryam ma lokacin data ga Babyn sam kasa rufe bakinta tay sai farin ciki take, bayan sun koma gida daga asibiti da daddare Lokacin da Kamal ya shiga wurin maijegon yana ruƙe da babyn yake sanar mata da sunan da yake son sakamata wato sunan Hajiya Maryam Farhar tace mashi ba gara yasa sunan late Mom ɗin shi ba yace mata tunda Fatuu tasa su bari in ta ƙara haihuwa sai su saka sunan Mom ɗin nashi, harda yar harararshi tayi tace ita wannan wahalar da tasha ta gama haihuwa yana murmushi tare da yi mata kallo mai cike da tsantsar ƙauna yace tayi haƙuri pls ta ƙara mashi yana son su haifi yara tare, itama murmushin tayi ta kai idonta kanshi tana mashi kallon love tace indai irin yaran nan zata rinƙa haifa tare dashi to zata ƙara wasu Amman sai ta huta sosae yay murmushin shi mai burgewa tare da jinjina mata kai alamar amincewa da zancenta tana murmushi ta kwantar da kanta a kan shoulder dinshi tana kallon Kyakkyawar Babyn su tana haka taji ya furta "Thank you my lovely wife for loving me for who i am" ɗago kai tayi ta kalle shi ta kashe mashi ido tare da furta "i will always love u Babe" yadda tayi maganar har sai da ɗumin bakin ta ya bugi fuskarshi saboda kusancin da fuskokin nasu suke dashi, shiru sukai suna kallon juna wani lokacin har mamaki Kamal yake a cikin ranshi irin yadda take nuna mashi ƙauna bata ƙi a ce koda yaushe suna manne da juna ba, a iya zaman da sukai matsayin ma'aurata ba ƙaramar zazzafar soyayya ta nuna mashi ba hakan yasa shima yake ƙokari wurin faranta mata a koda yaushe bai ta6a yin wani abu da zai nuna ta takura mashi ba zaman su suke lafiya sam baida matsala da ita kawai dai tana da zafin kishi wannan kuma tun kafin suyi auren ya sani shiyasa yake taka tsantsan da duk abunda yasan zai haifar masu da matsala, lokacin da Hajiya Maryam taji sunanta aka saka ma jaririyar murnarta ninkuwa tayi jin anyi mata takwara, bayan kwana biyar da yin haihuwar aka maida maijegon Villa don acan za'ayi suna, saida Hajiya Maryam tayi ma jaririyar saitin akwatuna ukku masu guda huɗu haɗaɗɗun gaske shaƙe da kayan jarirai na gani na faɗa da sauran kuma abubuwan da suka danganci jarirai ita kanta mai jegon ita tayi mata kayan da zata fita suna harda shi ma Baban jaririyar tayi mashi ɗinkuna na alfarma abun dai gwanin daɗi, ranar suna ta kama Juma'a suna na gani na faɗa akayi a Villa maijego ta samu iyayen kaya ita da Baby, mai girma shugaban ƙasa kyautar ƙaton fili yay ma jaririyar haka dai aka cika su da abubuwan arzuƙi kowa yayi bajinta su Gwaggo da Haulat harda Kawu Amadu da Tk da matarshi duk sun zo suna, zo kaga farincikin ganin juna wurin Hajiya da Tk harda rungume shi tayi, suna yayi suna abun sai son barka bayan gama sunan anan Villa apartment ɗin da Hajiya Maryam take Farha ta zauna sai ta gama wanka zata koma. A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji gashi President Ali har yayi shekara biyu da komawa kujerar mulki lokacin yaran Fatuu duk sun girma su Twins nada shekara takwas Esha kuma nada shekara bakwai, tun bayan da Esha ta fara girma gaba ɗaya halayenta sak na Fatuu da tana da ƙuruciya ne don sam bata jin magana ga masifa sannan tana da ƙarfi sosae don abu kaɗan sai ta kai bugu ko su twins bata ƙyalesu ba da ɗan abu ya haɗa su sai ta kama bugun su duk da suna maza bugunsu take har ta saka su kuka kuma duk sun fita tsawo amman tana da jiki bulbul take, kullum cikin rabata faɗa ake da yara a gida da kuma makaranta gashi saboda ansan ko ita wacece yasa ba'a ta6a kai ƙorafin halinta ba ga iyayenta har sai watarana data fasa ma wata yar ajin su baki daga ta taka mata colour bata gani ba ta karye tana bata haƙuri amman duk da haka saida ta kai mata bugu saitin bakinta aikuwa bakin ya fashe yay ta jini lokacin Class Aunty ɗin su ta yanke yin magana da Dad ɗinta don ai mata faɗa ta rage faɗa da yara da yake suna da lambobin wayoyin iyayensu, bayan ta kira Haisam cike da girmamawa tayi mashi bayanin dalilin kiran nashi harda bashi haƙuri kan hakan da tayi tace taga abun yana yin yawa ne kada wata rana ta illata wani student sosae, Haisam ɗin yace mata ba wani abu ya gode da sanar mashi da tayi, a ranar da daddare bayan ya dawo daga sallar isha ya zauna a main parlor dama duk dare in ya dawo daga salla nan yake zama su Twins da Esha din su kawo mashi Assignment ɗin su ya taya su bayan sun gama sai ya rakasu ɗakunansu su kwanta, su Twins ɗakin su ɗaya sai ita kuma Esha a Bedroom ɗin Fanan take kwana, bai daɗe da zama ba sai gasu sun fito duk suna sanye da ƙananun kaya su Twins Jeans da t-shirt sai Esha tana sanye da blouse da ɗan gajeran skirt duka kalar pink gashinta na fake a tsakiya ya sauka har kusan tsakiyar bayanta dama kusan koda yaushe sai dai ka ganta da gyaran gashi don bata son kitso, kowannensu ya ɗaukko ƙatuwar jakar Makarantarshi, suna ƙarasowa inda Haisam yake zaune Esha ta saki jakarta ƙasa ta washe baki duk gefen kumatunta suka lotsa sosae ta nufi Haisam da yar sassarfa tana faɗin "My Daddy.." dama ita yar gidan Daddy ce sosae suke shiri kowa ma ya sani daddie's pet ma ake ce mata ko rashin ji take da ance in ya dawo sai an faɗi mashi take cewa ta bari kada a faɗi mashi don Allah, haka in ya dawo gidan in suna nan haka zata nufeshi da gudu tana mashi welcome ya ɗagata sama yana faɗin His little Angel tun bata girma ba yake mata haka har kuma yanzu data girman a haka suke tarbar juna, haka in yana zaune ma tana zuwa zata faɗa jikinshi tana mashi dariya shima yayi mata har gyaran gashi yake mata da wanka cikin Weekend da yake yana ƙoƙarin basu lokaci sosae a ƙarshen sati har fita yake dasu outing wani lokacin kuma anan cikin gidan zaije dasu Field suyi wasanni harda Fanan in Fatuu ma tazo Weekend da ita ake yi, Esha ɗin na zuwa zata faɗa jikin Daddy ɗin nata yay saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu fuskarshi a ɗan ɗaure hakan yasa ta ja ta tsaya a gaban shi tana kallon shi da manyan idanunta masu ɗauke da zarazaran gashin ido, da alamun ɗan mamaki take kallonshi don ta gane ya ɗaure mata fuska su Twins ma tsaye sukai suna kallonshi can yace masu su zauna dukansu suka zauna akan carpet dama anan suke zama in za'ayi Assignment ɗin shima Haisam ɗin sai ya saukko ya zauna akan carpet ya fara nuna masu yadda zasuyi koda sun iya ƙa'ida sai tare da Haisam ɗin zasu yi don haka suka saba, yawanci ma duk Assignment ɗin da aka basu suna iya fiddawa dama gasu da ƙoƙarin tsiya sune gaba gaba a cikin ɗalibai masu ƙwazo a Makarantarsu, bayan duk sun zauna harda Esha ɗin zuru sukai suna kallonshi duk sun fahimci ya canza masu fuska, Adam ne cikin shan jinin jiki ya gaishe dashi da turanci Haisam din ya jinjina mashi kai ganin haka yasa Abie ma gaishe dashi ya amsa a hankali da sauri itama Esha tace "Good Evening My Daddy" wani kallo yay mata mai kaman harara ba tare daya amsa ba nan take ta gane da ita yake fushi ta shiga kikkafta idanu tana motsa baki, ba tare daya saukko daga saman kujerar ba still fuskar shi a ɗaure take ya fara magana cikin cool voice ɗinshi da har yanzu bata canza ba idon shi akan Esha yace dama duk faɗan da ake mata kan ta daina rashin ji bata ɗauka, da sauri tace mashi ta bari Allah, "Kin bari shine kika fasa ma classmate ɗinki baki?" ya faɗa tare da ƙara ɗaure fuska ta ɗan waro ido jin abunda yace don tunda take rashin ji a School ba'a ta6a yi mata maganar ba a gida, cikin ɗan tura baki tare da yamutsa fuska tace ai itace ta karya mata colour ko, aikuwa a ɗan fusace Haisam yace miye colour da don ta karya zata kama bugunta har ta fasa mata baki kuma ai ba shine rashin ji na farko ba da take a School ɗin dama ance ta saba bugun students kan ƙaramin abu kuma wani lokacin ita take fara jan su sannan tana ma malamai rashin kunya, tana jin abunda yace ta fara ta6e baki tana ɗan nishi idanunta suka ciko da ƙwalla cikin muryar kuka ta fara faɗin Allah karya ake mata ita bata rashin ji kuma duk wanda ta buga shi ya fara jan ta kawai dai teachers ɗin nasu sun tsaneta shiyasa za'a yi mata sharri, shiru Haisam yayi yana kallonta kawai don komai take yi ƙuruciyar Fatuu take tuna mashi yasan gaba ɗaya halinta ne na yarinta ta gado shiyasa bai cika damuwa da rashin jin ta ba don yasan zata daina, sai faman rantse rantse take tana faɗin karya malaman ke mata Haisam ɗin dai bai ce mata komai ba idon shi na kanta, yadda take faɗin malaman su ƙarya suke mata sun tsaneta sai ta tuna mashi da can baya lokacin ƙuruciyar Fatuu ta ta6a faɗi mashi magana makamanciyar wannan, ba tare daya saki fuskar shi ba ya katseta ta hanyar faɗin Teachers ɗin nasu take ce ma suna ƙarya idanunta sharkaf da ƙwalla tace to ai ita bata rashin jin da aka faɗi mashi, juyawa yay ya kalli su Twins dake ta bin su da ido sai kace an aje photocopy ɗin Haisam don sak fuskar su irin tashi ce komai da komai, tambayar su yay abunda aka faɗa game da Esha ɗin gaskiya ne Abie yay shiru don shi magana wuya take mashi Adam ne yace eh gaskiya ne bata jin magana taita bugun Students kuma tana ma Teachers rashin kunya har suma da suke Yayyenta ta raina su tana masu rashin kunya kuma har bugunsu take aikuwa yana rufe baki tai kukan kura ta nufe shi, da sauri Adam ɗin yace ma Haisam ya gani ko gashi nan zata bugeshin aikuwa a fusace ya daka mata tsawa ta hanyar kiran sunanta yace in ta sake ta buge shi sai ya 6ata mata rai, wani irin kuka mai sautin gaske ta fashe dashi ta shiga faɗin ita kowa yayi hating nata shiyasa sai ai ta mata sharri, kukanta ne yasa Fanan fitowa tana sanye da wando skin tight da yar top kayan sun bi shape dinta kanta a buɗe brown sumarta ta saketa ta zubo gefe da gefen wuyanta, tana nan yadda take bata canza ba saidai hutu ya ƙara zauna ma jikinta ta ƙara wani irin fayau da ita sannan ta ɗan ƙara jiki kaɗan, da sauri ta nufo cikin parlon tana faɗin "What's Happening Sweetheart....." Esha na jin muryarta ta miƙe daga durƙuson data yi ta nufeta da gudu suna haɗuwa ta faɗa jikinta, ɗago kanta Fanan ɗin tayi ta sake tambayarta mike faruwa waya sakata kuka ne, "Momy, they made Dad angry with me" Esha ɗin ta faɗa fuskarta jage jage da hawaye ita damuwarta fushin da Haisam yayi da ita, ɗan buɗa ido Fanan tayi tace mata su waye suka sa Dad ɗin yayi fushi da ita cikin kuka tace Teachers ɗin su kuma harda su Twins, kama hannunta tayi suka nufi inda su Haisam suke, a kusa da Haisam ɗin Fanan ta zauna da yake akan kujera mai mazaunin mutum biyu yake ta zaunar da Esha ɗin akan cinyoyinta sai kallon Haisam ɗin take tana sheshsheka shi kuma yaƙi kallon su, hannu Fanan ta kai ta kamo hannunshi tana murmushi ta furta "Babe, What happened?" shiru kaman bazai magana ba sai kuma ba tare daya kalleta ba ya shiga faɗi mata abunda aka kirashi daga School ɗin su aka fadi mashi, zaro ido Fana tayi tana kallon Esha dake yan kifce kifcen idanun rashin gaskiya, "Sweetheart, Why? Miyasa zaki hakan duk nasihar da nike maki kan ki daina faɗa kina bugun mutane ki natsu ashe baki ji" Fanan ta faɗa da turanci ta ɗan daure fuska cikin kuka Esha tace "Momy ba itane ta karya man colour ba" Fanan ɗin tace mata amman ai tasan ba tana sani tayi mata hakan ba ko, da sauri Adam yace eh zata wuce ne ita kuma Esha tazo sakawa a cikin locker ɗin seat dinta shine color ɗin ya faɗo ƙasa ya gangara ita kuma tazo wucewa shine ta taka mata Esha ɗin ta juya ta wurga mashi harara tare da kumburo baki, nasiha Fanan ta shiga yi mata tana nuna mata ba komai ake fushi ba ta rinƙa haƙuri pls ta hakane zata zama Good Girl, Cikin yamutsa fuska Esha ɗin tace "Momy, am i not a Good Girl?" da sauri Fanan ɗin ta kai hannu tana shafa kumatunta tace "Oh no, Sweetheart you are a Good Girl, kawai dai in kina haƙuri da abubuwa shine zaki ƙara zama yarinyan kirki ki rinƙa jan Friends ɗin ki a jiki da yan'uwanki kuyi wasa ba tare da kunyi faɗa ba amman yanzu kowa bai jin daɗin yin wasa dake saboda yawan faɗan ki, We are not happy yadda kowa ke maganan baki ji pls ki bari yadda za'a rinƙa cewa Esha Good Girl ce tana da haƙuri da kirki" kai Esha ɗin ta ɗaga mata tace to zata rinƙa yin haƙurin, Fanan ta tambayi ta yi promise ta bari da sauri ta ɗaga mata kai alamar eh tace yauwa haka take so amman in ta ƙara ji ta bugi wani har tayi mashi rauni itama zata 6ata da ita, da sauri Esha ɗin ta girgiza mata kai tace Allah bazata ƙara ba, kallon Haisam Fanan tayi da duk abun nan bai kallesu ba tayi ɗan murmushi kafin ta maido idonta kan Esha ta kai hannu ta matso da kanta ta raɗa mata ta sauka ta duƙa gabanshi ta bashi haƙuri da sauri ta ɗaga mata kai don sosae ta damu da fushin da yayi da ita, saukkowa tayi a ɗarare ta matsa saitin shi tayi kneel down cikin karyayyar murya ta furta "i'm Sorry Daddy, i won't do it again i promise you" shiru bai ce komai ba bai kuma kalleta ba har lokacin fuskar shi a ɗaure take, cikin mutuwar jiki Esha ɗin ta juya ta kalli Fanan tana ta6e baki da kai tayi mata alamun ta ƙara matsawa kusa dashi ta bashi haƙurin, sanin tunda suke dashi bai ta6a bugunsu ba yasa bata ji tsoron matsawa dab dashi ba ta ƙara maimaita haƙurin data bashi sai lokacin ya maido idanun shi kanta ganin haka yasa ta marairaice mashi fuska tana dan motsa baki, ganin baice komai ba yasa ta kalli Fanan ta ƙara yi mata alamun ta kama hannun shi ta bashi haƙurin, hannunta har ɗan rawa yake ta kai ta ɗan kama hannun Haisam guda ganin bai janye ba yasa ta kai ɗayan ta kama duka hannuwan shi tace "pls My Daddy, am Sorry..." tana faɗin haka su Twins suka haɗa baki suka ce please Dad Sorry, hannu Fanan ta kai ta dafa kafaɗarshi tace "Sorry Babe, please forgive her, tayi alƙawarin bazata ƙara ba" Sigh yay cikin muryarshi mai cike da natsuwa idanun shi akan Esha ɗin yace mata kada ta ƙara aikata abu irin haka in ba haka ba zai ɗauki mataki akan ta kuma ba ruwanshi da ita, da sauri ta jinjina mashi kai ya saki fuska tare da ɗago da ita aikuwa da sauri ta faɗa jikin shi tana murmushin farinciki haka su Twins ma murmushin suke harda yi masu gwalo Fanan ma dariyar take ta furta "Esha, Daddy's pet", harda Fanan aka zauna yin Assignment ɗin abun gwanin burgewa, Washe gari Haisam ɗinne ya kai su Makarantar yayi shigar zuwa aiki yana sanye cikin suit, har class ɗinsu yaje yasa aka kira mashi yarinyar data buga ya bata haƙuri itama Esha yasa ta bata haƙurin yace ma Esha daga yanzu su abokai ne su rinƙa yin wasa tare kada ya ƙara jin tayi faɗa da wani tace mashi to, harda kyautar kuɗi masu yawa yaba class Aunty ɗinsu kafin ya tafi, ba laifi a lokacin ta rage rashin jin saidai ance wai mai hali baya barin halin shi koda ya barin wani lokacin bata cikin sauƙi ba. Cikin sa'a Mino ta kammala karatunta na nursing saida Fatuu taji ba daɗi zata koma Abuja ta barta sauƙinta ma Aysha na nan lokacin itama Aysha ajinta shidda suna gabda yin jarabawar gama Makaranta, bayan result ɗin Mino ya fito wanda yayi kyau sosae ta fara shirin fara yin bautar ƙasa, a wani Weekend da Haisam zaije Zaria ne ya tafi tare da abokinshi Na'eem yayi mashi rakiya daga nan shima zai gaido danginshi don ɗan Zaria ɗinne amman iyayenshi a Abuja suke zaune, bayan sallar Juma'a suka iso Zaria lokacin da suka isa gidan Fatuu bata dawo daga makaranta ba sai Aysha kawai da mai aikinsu, tana sanye cikin riga da skirt na atampa ta zama budurwa sak irin jikin Mino gareta itama doguwa ce kuma bata da jiki gashi tana da kyawun Fuska saidai bata kama dasu Fatuu sosae kamar yadda Mino ke kama da ita, ita ta tarbesu cikin fara'a tana masu sannu da zuwa gaba ɗayansu fuskokinsu a sake suna mata murmushi suka amsa mata, a parlor suka zauna ta kawo masu ruwa da lemu tace bari ta shirya masu table Haisam yace ta bari ba yanzu zasu ci abincin ba sun ci a Kaduna sai ko zuwa ɗan anjima tace to, har zata tafi taji ya tambayi ya karatunta ta tsaya tana murmushi ta amsa mashi da Alhamdulillah suna ta shirin yin jarabawa yay mata fatan sa'a haka ma Na'eem daketa kallonta yana murmushi shima yay mata fatan sa'a ta kalleshi tay mashi godiya kafin ta juya ta tafi, bayan tafiyarta ne Na'eem ya maida idonshi kan Haisam yace mashi amma daga ganin wannan sister ɗin Madam ce ko ya ɗaga mashi kai, tambayar shi yay zuwa tayi Haisam din ya bashi amsa da anan take wurinta tana tayata zama itama tana karatu, jinjina kai Na'eem ya ɗan yi yay shiru can kuma sai yace mashi zasu bashi ita don ya ganta kuma tayi mashi, "Ita kuma wife en naka fa?" Haisam ya tambaya yana murmushi shima Na'eem din murmushin yake yace zai ƙara ne kamar yadda shima yake da biyu, murmushi kawai Haisam yay bai ce komai ba ganin haka yasa Na'eem yace shi yake saurare Haisam ya tambayi wai is he serious ya ɗaga mashi kai yace Allah tayi mashi da gaske yaji yana sonta da aure, murmushin gefe Haisam yay yace mashi ai ƙarama ce yanzu zata gama Secondary Na'eem din yace ai abun ba'a nan yake ba tunda dai ta balaga lafiya lou za'a iya yi mata aure tunda ta isa, shiru ya ɗan yi kafin ya gyaɗa kai yace in da gaske yake sai ya nemi soyayyar yarinyar Na'eem ɗin ya gyaɗa kai ya tambayi sunanta ya faɗi mashi, anan falo suka zauna suna kallo har akayi sallar La'asar suka tafi Masallaci, bayan dawowarsu Haisam yace suje ciki ya huta yace a'a yana son zai yi magana da Aysha Haisam yace Ok shi zai shiga ciki Na'eem ɗin yace Ok pls ya turo mashi ita, a saman doguwar kujera ya zauna bada daɗewa ba sai ga Ayshar ta fito ta nufo cikin falon, daga gabanshi ta tsaya tana murmushi shima shi yake mata tace gata Yaya Haisam yace yana kiranta yace mata eh tare da nuna mata gefen shi yace tazo ta zauna, saida tayi ɗan jim kafin ta nufi inda ya nuna matan ta zauna daga can ƙarshe ya gyara zaman shi ya dawo yana kallonta, "Aysha ya School?" ya tambaya da muryarshi ta yan gayu, tanata murmushi tace mashi lafiya lou ya sake tambayar tana dai maida hankali ko tace mashi eh ya tambayi wane department take tace mashi Science, "Ko kema kina son zama Doctor ne?" kai ta ɗaga mashi alamar eh yace ashe da future Doctor yake zaune tayi yar dariya, "To za'a rinƙa duba ni in an zama Doctor en?" kai ta ɗaga mashi kafin cikin yar muryarta tace in yana so yay yar dariya yace in mutum bashi da lafiya har sai yana so likita zai duba shi murmushi tayi bata ce komai ba, ta lura da irin kallon da yake mata hakan yasa ta fara yin wasa da yatsunta tana yi tana ɗan kallonshi tana murmushi, "Yanzu in kiga gama karatun zaki aure ne sai kici gaba da karatun ko?" da sauri ta kalleshi tare da ɗan waro ido tace "Aure kuma!" kai ya ɗaga mata ta ɗan girgiza mashi nata tace ba aure zata yi ba Karatun zata cigaba, "Why bazaki aure ba, ai ana karatu koda aure ba kiga sister en ki ba itama tana da aure harda yara ma kuma tana karatunta", "To ai ni ko Saurayi ban dashi" ta faɗa tana ta murmushi, wani kallo yayi mata yace wasa dai take mashi amman kamar ita ya za'ai tace bata da saurayi, da sauri tace "Allah da gaske nake maka ni ko ance ana sona ban yarda saboda Karatu nike son yi" yadda take mashi magana sosae yake burgeshi gashi daga yanayin Maganarta zaka gane yarintar ta, "Yanzu ace ki samu wanda yake son ki kuma kema kina son shi bazaki yarda kuyi auren ba sai kici gaba da karatun?" da alamun rashin fahimta tace "wa?" yace mata misali ne ya bata tay ɗan shiru alamar tunani yana ta kallonta can tana murmushi tace to in su Adda Fatuu sun amince sai tayi, "Ai ba su zasu zauna maki ba ko Aysha, in kina so nasan bazasu hana kiyi auren ba" kai ta ɗaga mashi alamar eh yace in ta samu wanda take son kenan zata yi auren ta sake ɗaga mashi kai kafin ta sunnar da kanta alamar kunya, "Ok, dama wani ne ya ganki kin yi mashi yaji yana son auren ki da Kin gama School, to har nayi ma Yayan ki Haisam Maganar yace ya nemi amincewar ki shiyasa nace to bari in maki magana" ba shiri ta ɗago tana kallon shi da alamun mamaki har ya gama ta waro idanunta tubarkalla tace mashi "ni kuma!" kai ya ɗaga mata ta sake cewa "a ina ya sanni"? Yadda tayi ne ya sashi yin yar dariya kafin yace yaga hoton ta ne tay shiru tana kallon shi, "Aysha baki ce komai ba game da wanda na faɗa maki yana son ki" dan yamutsa fuska tay ta ɗan yarfa hannu alamar bata san mi zata ce ba, ganin ya kafeta da ido yasa tace to ai ita bata san shi ba, "In kin ganshi yayi maki zaki amince?" shiru tayi tana ta kikkafta idanu, ɗage mata gira yay yace ita yake sauraro a sanyaye ta ɗaga mashi kai alamar eh, bin ta yay da wani irin kallo ta ƙara maida kanta tana wasa da yatsunta, tana haka taji muryarshi yace "Aysha ni ne na ganki naji ina son ki kuma auren ki nike son yi in kin gama School amman sai in nayi maki nima" da sauri ta ɗago ta kalleshi idanunta a ware fuskarta ta nuna tsananin mamakin Maganar shi yana murmushi ya ɗan lumshe mata ido, ƙirjinta ne ya fara bugu da sauri da sauri ta maida idonta ƙasa, "Sunana Na'eem, ni abokin Yayinki Haisam ne, inada mata da yara biyu sannan ina aiki da Central Bank, ban san ko na ta6a ganinki ba kafin yanzu tunda muna yawan kasancewa da Haisam duk wata hidima data danganci Family ɗin su ina zuwa saidai a wurina yau na fara ganinki zuwan mu nan, kuma cikin ikon Allah ina ganinki naji na kamu da son ki abunda bature ke cewa, Love at first sight, nayi ma shi yayan naki magana kan haka shine yace to in nemi soyayyar ki idan Allah yasa kinga nayi maki to zan aure ki da kin gama School sannan zan barki kici gaba da Karatun ki in sha Allahu" shiru bata ce komai ba bata kuma ɗago ba abun ya ɗaure mata kai sosae don bata yi tunanin zai mata wannan Maganar ba, ganin taƙi tace komai yasa shi kiran sunanta ta amsa ba tare data ɗago ba yace tayi shiru bata ce komai ba still taƙi cewa komai ɗin, "Ayshat" amsa mashi tayi ba tare data ɗago ba yace "Look at me" saida tay ɗan jimm kafin a hankali ta ɗago idanunta suka sauka akan kyakkyawar doguwar fuskarshi mai ɗauke da kwantaccen saje, yanayin fatarshi ba za'a ce mashi fari ba kuma ba baƙi bane yafi kama da a kira shi da wankan tarwaɗa, sosae yanayin hutu ya bayyana a jikin fatar ta shi yana da kyawun fuska wadda take a cike ɗauke da dogon hanci da kuma madaidaicin baki mai dauke da jerarrun fararen haƙora harda yar wushirya, a bangaren yanayin jiki sam ba gajere bane don da kaɗan Haisam ya ɗara shi tsawo sannan kuma ba siriri bane yana da cikar jiki, ganin tanata kallonshi yasa shi ce mata kada taji komai in taji bata son shi ta faɗi mashi bazai ji komai ba kuma ko Yayanta bazai faɗi ma yadda sukai da ita ba, motsa baki ta fara da ƙyar tace mashi shikenan idan Yaya Haisam ya amince to ta yarda, ɗan girgiza mata kai yayi yace mata aure ba abu bane da wani zai amince maka tunda bashine zai zauna maka ba sannan aure ana yin shi in ana son juna don haka ita zata amince mashi in taji tana son shi, shiru tayi tana yi tana maida idonta ƙasa ya ɗan ɗage mata gira yana murmushi, sai faman yan kame kame take don taji itama yayi mata don Na'eem ba irin mazan da suke furta ma mace so taƙi amincewa bane kawai dai abun ne taji yayi mata girma ba kamar da yake wannan ne karo na farko da tayi Magana irin haka da Namiji, "Amman...ita Matarka to zata amince ka aure ni ne?" da ƙyar ta furta mashi hakan, gyara zama yay kafin yace "Ayshat ba kowace mace bace ke son a ƙara mata abokiyar zama ba saidai inada kyakkyawar fahimta da mata na nasan zata amince koda hakan bai mata dadi ba amman tasan inada ikon ƙara wata matar kuma dama ban ta6a mata alƙawarin zan kasance da ita kaɗai ba don haka nasan bazata bani matsala ba in kin amince zaki aure ni" kai ta ɗaga mashi kafin tace shikenan, "Kin amince zaki aure ni kenan?" kai ta ƙara ɗaga mashi ya sake cewa "ina fata dai ba saboda wani dalili ko don ni abokin yayanki bane yasa kika amince man, nafi son ki amince man don kema kinji kina sona" kai ta jinjina mashi yana mata wani kallo yace "nayi maki kina so na?" kan dai ta sake ɗaga mashi, "Ok in dai da gaske kike kema kamata yay ki faɗi man da bakinki kamar yadda na faɗa maki" ɗan murmushi ta shiga yi tana motsa baki ya ɗage mata gira alamar ta bashi amsa, da kyar ta furta "nima ina son...ka" tana yin Maganar da sauri tasa duka hannuwanta masu ɗauke da dogayen yatsu ta rufe fuskarta Na'eem ɗin ya shiga yin yar dariya, da yake wayayye ne sai gashi yasa ta saki dashi sun shiga yin firar soyayya, suna haka Hajiya Fatuu ta shigo cikin falon tana sanye da riga da skirt na lace da suka amshi jikinta tare da gyale mahadinsu, tana nan yadda take bata ƙara ƙiba ba saidai ta ƙara cikowa tay dumdum fatar nan tata har wani sheki take hutu ya zauna mata sosae, ƙafafunta na sanye da wasu takalma masu tsini mai ɗan gwa6i har yanzu halinta nason takalma masu tudu nan, ta bangaren hips dinta kuwa abun saidai ace tubarkalla don suna nan sai ma ƙara cika da sukai duk da gyalen jikinta babba ne amman kana kallonta zaka san tana dasu, hannunta na hagu na rataye da yar babbar jaka da take ɗauke da kayan karatunta sai kuma ɗayan hannunta na hagu ta ruƙo Lab coat dashi, tana ganin Na'eem ta fara yin murmushi hakan ya bayyanar sa fararen haƙoranta kamar auduga masu ɗauke da haƙorin makka daya ƙara ƙawata fuskar tata, cikin falon ta nufa sam bata yi mamakin ganin Na'eem ɗin ba don da sukayi waya da Haisam ya sanar mata tare suka zo, a saman kujera dake gefen wadda suke ta zauna Na'eem daya maido idonshi kanta yana murmushi shima yay mata sannu da dawowa ta amsa tare da gaishe dashi da yi mashi anzo lafiya, bayan ya amsa ya tambayi karatunta tace mashi Alhamdulillah itama ta tambayi matar shi Fadeela da yaransu duk yace mata lafiya lou suke, saida suka gama gaisawa sannan Aysha tayi mata sannu da zuwa ta maida idonta kanta tana murmushi ta amsa ta tambayi ya School tace mata lafiya lou, yar hira sukai da Na'eem kafin ta miƙe tace bari ta ɗan shiga ciki yace Ok. Sai bayan sallar Magrib sun dawo daga masallaci suka zauna cin abinci gaba ɗayan su Na'eem da Aysha sai satar kallon juna suke suna murmushi, bayan sun dawo daga sallar isha gaba daya a falo suka zauna suna kallo, wuraren ƙarfe tara Haisam ya miƙe yace ma Na'eem bacci yake ji ya taso suje ya kai shi ɗakin da zai kwanta yana murmushi yace shi da Aysha basu gama yin kallon ba yace Ok yazo suje ya nuna mashi in ya gama sai yaje ya kwanta ya miƙe, bayan tafiyar su ne Fatuu ma ta miƙe tayi ma Ayshar saida safe dama duk in Haisam yazo a ɗayan bedroom ɗin dake part ɗin Fatuu take kwana tare da mai aikin su Asabe, bada jimawa ba Na'eem ya dawo a saman kujera mai mazaunin mutum ukku ya zauna yace ma Aysha ta dawo nan, a can gefe kamar ɗazu ta zauna ya jingina kanshi da jikin kujerar ya shiga sakar mata kallon love da alama dai shima gwani ne ta bangaren soyayya, hirar soyayyarsu suka shiga yi ba laifi ta saki jiki sun ɗan ɗauki lokaci wurin ƙarfe goma saura yace bari ya barta taje tayi bacci kadda ya gajiyar da amaryarshi tayi dariya suka miƙe a tare. Washe gari bayan Haisam ya dawo daga sallar Asuba itama Fatun tayi sun koma sun kwanta ta tada kanta a saman jikinshi yake mata zancen son auren Aysha da Na'eem keyi ya faɗi mata yace mashi ya nemi amincewarta to har sunyi magana kuma ta amince, sosae Fatuu ta jinjina abun don ita koda ta gansu tare bata kawo komai a ranta ba saboda tasan Ayshar nada saurin sakin jiki da mutane ba kamar Mino ba, da alamun damuwa tace mashi amman bai ganin hakan zai iya haifar da matsala tsakaninsu da matar shi taga anyi mata ba daidai ba tunda sun san juna suna gaisawa, yana ɗan murmushi yace itama ba sun san juna ba da Fanan kuma ta aureshi, juyawa tay tayi mashi wani kallo tare da ɗan tura mashi baki tace to ai ita bata san da Auren ba ko ya ɗage mata gira yace data sani bazata amince ba kenan tay shiru tana kallon shi yace ta bashi amsa, yamutsa fuska tay ta sigar shagwa6a tace to tunda dai an riga anyi ya wuce miye na maido maganar, yana murmushi yace Ok tunda itama ya aureta kuma sun san juna da Fanan itama Ayshar ba wani abu bane don ta auri Na'eem, shiru Fatuu ta ɗan yi kafin tace ya sani fa Aunty Fanan daban take a cikin mata don da wuya a samu wadda zata iya jarumtar da tayi, shiru yay yana sakin murmushi yayin da zuciyarshi ta shiga dawo mashi da fuskar Fanan. Wuraren ƙarfe goma na safe suka zauna yin breakfast, kowa cikinsu yayi wanka Haisam da Na'eem na sanye da ƙananun kaya wando da riga Fatuu kuma da Aysha suna sanye da dogayen riguna masu taushi suna da gajerun hannuwa kowa ya saka hula a kanshi daga bayan hular yay tudu sosae saboda gashin su, bayan sun zauna a kujerun dining ɗin suka shiga gaishe da juna kafin Fatuu ta shiga yin serving nasu, bayan ta gama a nutse suka fara ci baka jin komai sai ƙarar cokulla sai kuma Ac dake a wurin tana ta aiki, bayan sun gama gaba ɗaya a falo suka zazzauna suna yin hira wadda Haisam da Na'eem sai Fatuu ne ke yi ita dai Aysha tayi shiru tana saurararsu akai akai kuma suke haɗa ido da Na'eem su sakar ma juna murmushi, suna cikin yin firar Na'eem yace ma Fatuu "Madam ko in ce Yayata, ina fatan Yalla6ai ya isar maki da saƙona na naga ƙanwarmu tayi man ina neman iri pls, yace man in nemi amincewarta da yake mu indai ta wannan bangaren ne bamu failing tuni har an amince man ance ana sona" ya kai idon shi kan Aysha yace "Ayshanah hakane ko, kin amince zaki aure ni ai ko?" ai tana jin abunda ya faɗa tay zumbur ta miƙe da gudu ta nufi hanyar bedroom duk suka bita da ido suna yar dariya, bayan barinta wurin ne Fatuu tace mashi sunyi Maganar da Hubby taji daɗi saidai tana gudun hakan ya haifar da matsala tsakaninsu da Fadeela tana iya ganin an yi mata ba daidai ba, yana murmushi yace mata kar ta damu zai faɗi mata shi yaga Aysha yaji yana sonta kuma akai sa'a itama tana son shi ba wanda ya haɗa su in sha Allah ba wata matsala da zata faru tsakaninsu Fatun tace Allah yasa, tambayar ta yay lokacin da zata gama School Fatun ta faɗi mashi yace Ok nan da sati ɗaya in sha Allah zaije Yola ya gaida Parents ɗin su Haisam yay mashi wani kallo kafin slowly yace mashi saurin mi yake ne tunda ta amince mashi yabi komai a hankali da sauri Na'eem ɗin yace ai ba mata irinsu ake bi a hankali ba wurin neman aurensu nan tana gama Secondary zaiga masu son ta suna ta kunno kai ƙarshe asamu wani yayi mashi overtaking shiyasa yake son tana gama School ɗin yayi wuff da ita duk sukai yar dariya, hira suka cigaba da yi bayan wani lokaci Haisam ya tambaye shi yaushe zai je gaida relatives ɗin nashi Na'eem ɗin ya duba agogon hannunshi kafin ya bashi amsa da zuwa ƙarfe sha biyu zai tafi Haisam yace Ok in lokacin ya ƙarasa sai suje ya raka shi, "No, kai zaman ka kaida kazo Weekend Madam na buƙatar ka a kusa da ita koda yaushe ka ƙyale ni in je ni kaɗai, ko kuma tunda nima ga Amaryata sai ta rakani kawai kaga ma sai inyi amfani da daman in fara introducing nata ga Family na" Na'eem ya faɗa yana murmushi suma duk murmushin sukai basu ce komai ba, ganin lokacin fitar nashi ya ƙarato yasashi ce ma Fatuu pls yana neman alfarmar fita da Aysha tana murmushi tace an mashi yay mata godiya kafin yace to ta taimaka tayi ma Amaryar tashi mai kunya magana ta shirya tace to tana dariya tare da miƙewa shima Na'eem ɗin ya miƙe yace ma Haisam bari ya shirya ya ɗaga mashi kai, a bedroom ta iske Aysha kwance saman gado ta nufeta tana faɗin kwanciya tayi kenan Ayshar ta ɗago tana kallonta, a bakin gadon ta zauna tana kallonta da murmushi tace mata Amaryar Na'eem Ayshar tayi murmushi kawai, shiru Fatun ta ɗan yi kafin tace mata ta tabbatar da yayi mata tana son shi don shi da gaske yake aurenta zaiyi tana gama School, shiru Ayshar tayi tana kifce kifcen idanu Fatuu tace mata ta buɗe baki tayi mata magana, a hankali tace mata eh in dai baida wata matsala Fatun tace gaskiya Na'eem bata tunanin yanada wata matsala a yadda ita ta sanshi mutumin kirki ne kuma tasan da yanada matsala ma tun Farko Haisam bazai bashi damar ya nemi soyayyarta ba kawai inda take tunanin matsala wurin matarshi ne duk da itama tana da kirki to amman wata baka gane rashin kirkinta sai za'a mata kishiya kawai dai suyi addu'a Allah yasa ta fahimta ta kuma kar6i abun kamar yadda Aunty Fanan tayi Ayshar ta amsa da Amin kafin tace "amman fa Adda Fatuu wllh Aunty Fanan ta daban ce" murmushi Fatun tay tace ta sani samun irinta cikin mata da wuya in ma akwae duk da tasan akwai mata da yawa wanda in mijinsu yaje masu da zancen ƙara aure duk da basu so amman suna karbar abun a matsayin ƙaddararsu tunda sun san Allah ne ya halarta masu yin jayayya da hakan kuma wahalar da kai ne ƙarshe mutum ya jefa kan shi a halaka, faɗi ma Ayshar tayi zasu fita da Na'eem ɗin yana son zuwa da ita wurin danginshi ya gabatar masu da ita, tana jin haka ta ɗan zaro ido kafin tace amman da wuri haka, miƙewa Fatuu tay tana yar dariya tace shifa da gaske yake yace ma nan da sati ɗaya zaije Yola gaishe dasu Baffa don haka ta fara shiri don ita amarya ce, "Amman Adda Fatuu ban yi ƙarama ba da yin aure" Aysha ta faɗa da yar damuwa, Fatuu dake tsaye a gaban wardrobe ɗin bango tana ƙoƙarin za6o mata kaya ta bata amsa da "ba wata ƙarama da kikai Aysha, ke ai gara kema akan Mino, ita fa ko gama Secondary bata yi ba akayi mata aure gashi ko a jiki ma kin ɗan fita kauri lokacin" ta ƙarasa Maganar tana dawowa wurin gadon hannunta ruƙe da riga da skirt na lace kalar blue da ratsin golden brown, ita ta taimaka ma Ayshar ta shirya cikin kayan ta saka mata yan kunnan zinari da zobe sai kuma agogo golden mai kyau, yar light make up tayi mata ta ɗaura mata kallabi sai gashi ta fito tayi wani irin kyau, bayan an gama saka kayan ta yafa gyale mahadinsu haka jaka da takalmanta suma duk kalar kwalliyar lace ɗinne takalman masu dan tudu ne kadan don tana da tsawo don bata cika saka takalma masu tsini ba, lokacin da suka fito falon Na'eem din har ya gama shiryawa ya dawo suna zaune da Haisam, shima shadda ce ya saka brown wadda ta hau da kwalliyar lace ɗin jikin Ayshar sai baza ƙamshi yake, Na'eem na ganin shigarta yana murmushi yace ko daga yanayin shigar su hakan ya tabbatar da sun dace da juna duk akayi yar dariya Aysha ta sunnar da kai, har bakin galleliyar baƙar Motar Haisam da suka zo da ita suka rako su bayan sun shiga sukai masu sai sun dawo, yana driving suna hira irin ta masoya haka suka shiga zaga gidajen yan'uwan su Na'eem wanda duk mawadata ne, duk inda suka je sai ya gabatar da ita matsayin matar shi ta biyu da zai aura nan bada jimawa ba anata yabata tare da fatan alkhairi, lokacin da suka je gidan Kakarshi wadda ta haifi Mom ɗinshi shima haɗaɗɗan gidane mai girma don yana da parts da yan'uwan mahaifiyarshi maza ke zaune da matansu haka itama kakar 6angarenta daban an ƙawata shi ai kace ba sashen tsohuwa ba, lokacin daya gabatar mata da Aysha matsayin wadda zai ƙara mata cike da zolaya irinta Kaka ta yamutsa fuska tace in baya ga rigima irinta namiji mi zai ci da wannan yar ƙaramar bafullatanar bayan yana da mata ƙaƙƙarfa kamar ita, ita dai Aysha murmushi kawai take kanta a ƙasa haka shima Na'eem ɗin yar dariya yake yace ina wani ƙarfi a tare da ita, sosae ta sake ma Aysha tana ta mata tambayoyi game da ita tana bata amsa da yake tasan Haisam sosae ta yaba da al'amarin tayi Addu'ar Allah ya sanya alkhairi, duk sauran parts ɗin gidan saida ya kai ta ko ina an yi mata tarba mai kyau, daga baya bangaren Kakar suka koma sai bayan sallar La'asar ya dawo daga Masallaci yace mata zasu tafi tace ma Aysha tunda a garin take zaune ta rinƙa zuwa gaishe da ita tana kama ƙafa in tana son ta amince ta aurar mata miji in ba haka ba ita dashi saidai kallo, tana murmushi tace mata in sha Allahu zata riƙa zuwa sukai mata sallama cike da tsokana Na'eem yace tunda ita mai ƙarfi ce sai ta taso ta raka su bakin mota ko, wurga mashi harara tayi tace Allah ya kyauta tayi ma kishiyarta rakiya duk sukai dariya, bayan sun baro gidan Shopping ya wuce da ita, koda yace mata ta ɗauki duk abunda take so cikin marairaicewa tace mashi ai ita tana da komai yana mata wani kallo yace duk da haka ta ƙara so yake daga yau ta fara amfani da kayan mijinta, ba yadda ta iya haka ta fara ɗaukar yan abubuwa tana sakawa a cart da ya ɗaukko mata, ganin bata ɗaukar kayan sosae yasa shi fara za6ar mata da kanshi yana yi yana tambayar wanda take amfani dasu, bayan sun gama da wurin kayan shafa wurin dogayen riguna suka nufa tana ta roƙon ya barsu tana da su da yawa amman duk da haka saida ya daukar mata guda biyar da takalma guda ukku bayan sun gama da nan bangaren undies suka nufa duk yadda take jin kunya saida ya sakata ta ɗauka, abunda bata sani ba yana amfani da hakan ne wurin sanin size ɗinta saboda in zai yi mata lefe, saida ya cika Shopping cart ɗin taff da kaya sannan suka nufi wurin biya aka saka masu kayan a ledoji bayan an saka a Mota suka tafi. Kamar yadda Na'eem yace wani ƙarshen satin na zagayowa suka shirya zuwa Yola da Haisam, ranar asabar da safe suka bi jirgi zuwa Yola bayan sun isa aka tura Mota ta ɗauke su zuwa garin su Fatuu, bayan sun isa sun samu kyakkyawar tarba daga mutan gidan aka sauke su a part ɗin su Yadikko nan aka shiga zuwa gaishe da su kan kace mi an jere masu kwanonin abinci iri iri koda Yadikko tayi masu Maganar cin abinci cewa sukai a ƙoshe suke Baffa dake zaune yana murmushi yace duk da haka yakamata su ci tunda tafiya suka yo, ba wani mai yawa suka ci ba saidai sun sha fura ba laifi, bayan sun gama ne Haisam ya gabatar masu da Na'eem matsayin shine mai son auren Aysha in ta gama School, dama an riga an sanar masu game da zuwansu, sosae suka nuna farinciki da Addu'ar Allah ya sanya alkhairi bayan sun amsa Haisam ya sake cewa yana son a faɗi mashi lokacin da zasu turo a saka rana Baffa na murmushi cikin Maganar shi mai tattare da natsuwa yace ai tunda ga shi Haisam ɗin shima matsayin Mahaifi yake wurin Aysha don haka a nemi aurenta a wurinshi duk yadda ya yanke yayi lafiya lou tunda ba abu bane na kusa kada aita wahalar yin zarya, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Na'eem ba shima Haisam yaji daɗin yadda ya girmamashi yay mashi godiya da Addu'ar Allah ya ƙara girma da lafiya yana murmushi ya amsa shima yay mashi godiyar abubuwan alkhairi da ake ta masu da Addu'ar Allah ya ƙara girma da arzuki duk suka amsa da Amin, shiru falon ya ɗan yi kafin Baffan yace masu bari ya kai su bangaren shi sai su huta Haisam yace ai ba daɗewa zasu yi ba zasu koma Yola anjima zasu koma Abuja Baffan yace amman zasu kai azahar ko yana son bayan an gama sallar azahar lokacin duk yan uwanshi sun haɗu sai su gaisa dasu yace to, bangarenshi ya tafi dasu don su hutan kafin ayi sallar, bayan gama yin sallar azahar a ƙopar gida a fadar dake a cikin soro inda arɗo ke zama kafin ya rasu wadda yanzu Baffa ne ke zama don shine arɗon suka shiga harda sauran yan'uwan nashi, bayan sun gaggaisa Baffa ya gabatar masu da Na'eem, duk sun nuna farinciki kan al'amarin tare da Addu'ar Allah ya sanya alkhairi, da fulatanci Baffa yay masu bayanin lokacin da Aysha zata gama Makaranta yake son ayi auren ya kuma bada izinin a nemi auren a wurin shi mijin inna wuro kada zaryar tayi yawa, gaba ɗaya dai sun nuna hakan yayi Baban altine harda cewa ai Haisam ɗin yanzu shima na gida ne kuma ga abun alkhairi da yake ta kawo masu, bayan sun gama gaisuwar kuɗi masu yawa Na'eem ya aje masu yace suyi amfani nan fa suka shiga yin godiya Haisam ma ya ƙara aje masu wasu bandir bandir ɗin zo kaga godiya da addu'o'i, bayan sun fito bangaren su Baffa suka koma yasa Yadikko ta kaisu su gaisa dasu Yaya, cikin faram faram Yaya ta tarbesu akayi masu shimfiɗa suka zauna Yadikko taje tayo ma su Mairo Magana duk suka zo nan ɗakin aka shiga gaisawa dasu da tambayar Haisam yadda su Fatuu suke fuska a sake yake amsa masu daga baya ya gabatar masu da Na'eem, duk sun nuna farincikin su suma sunyi Addu'ar Allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna masu, nan ma saida suka aje masu kuɗi masu yawa kafin su taso, basu daɗe ba bayan sun koma falon Yadikko sukai masu sallama suma saida suka aje masu kuɗi Baffa yace don Allah su bar shi kada hidiman tayi yawa wanda suka bada sun isa Yadikko tace mashi ko can wurin su Yaya ma saida suka bada masu yawa, duk yadda sukai dasu kan su barshi basu ɗauka ba dole sukai masu godiya, har bakin mota duk aka rakosu su suka yi bankwana dasu kafin suka tafi, a kan hanya ne Na'eem ke yabon Baffan su Fatuu yace ya burge shi wllh sosae kai kace ba mutumin ruga ba yana da natsuwa da wayewa in ba don haka ba bazai sake masu ba matsayin su na surukai Haisam yay murmushi yace haka yake ya fita daban a cikin su. Gab da sallar Magrib suka dawo Abuja sosae Na'eem yayi ma Haisam godiya da zasu rabu, saboda tafiyar da su Haisam ɗin sukai yasa wannan Weekend ɗin Fatuu ce tazo Abuja, da daddare bayan sun kwanta ne Haisam ke ce mata mi zai hana Baffansu ya baro ƙauye ya dawo ko Katsina tunda gasu Gwaggo sai ya siya mashi gida su zauna, itama Fatuu ta nuna tana son hakan tace zata tuntu6eshi kan hakan, Washe gari da safe ta kira Baffan bayan sun gaisa ne take mashi Maganar, farko shiru yayi kafin yace mata zai so hakan saidai barin ruga yanzu ba abu bane mai yuwuwa a wurinshi don arɗo ya bar mashi amanar gidan yace kada ya bari kan iyalin ya tarwatse yanzu in yace ya tafi yasan za'a iya samun 6araka kuma shi kan shi yafi sabawa da nan tunda anan ya taso yace taba Haisam haƙuri kuma tayi mashi godiya kan kudirin nashi tace to, koda ta sanar ma Haisam ɗin ya fahimci Baffan ya nuna mata bakomai, da yamma ta shirya komawa Zaria ta jirgi Esha ta saka rigimar sai ta bita Fanan ta shiga rarrashinta tace ta bari in akayi hutun School sai suje mata hutu kamar yadda suke yi sannan ta haƙura suka yi mata rakiya gaba ɗayansu harda Haisam Airport tabi charter flight zuwa Kaduna daga can driver zai wuce da ita Zaria. Cikin sa'a Mino ta fara yin bautar ƙasarta a Asibiti, wata biyu da farawa kwatsam sai ga ciki ta samu, zo kuga farinciki a wurin Mino duk yadda take da kunya saida ta kasa 6oye murnarta haka kowa ma yayi farincikin samun cikin karma dai Fatuu sosae tayi murnar samun cikin na Mino, ta bangaren Nameer shima yayi farinciki don duk yadda yake nuna bai damu ba yana son yaga ɗanshi na cikin shi, bayan samun cikin sai kuma ta fara yin laulayi sosae ta yadda har saida ta daina zuwa Asibitin da take bautar ƙasan nata ƙarshe ma saida ta kai Nameer ya maidata wurin Mom ɗin su don bata iya cin komai duk abunda kuma ta samu ta ɗan ci sai ta amayar dashi tun lokacin ta gane ciki ba wasa bane, saida tayi wata biyu a Villa kafin ta dawo gidanta lokacin cikin ya kai wata ukku kuma ba laifi ta ɗan rage yawan laulayin amman bautar ƙasan da take yi saidai aka tsaida shi daga baya tayi, cikin na wata biyar akayi bikin Aysha da Na'eem anan Abuja, a gidansu Haisam akayi hidiman bikin don Haisam su Baffa suka amince mawa ya bada aurenta, yan Katsina da yan Adamawa duk nan suka zo ranar ɗaurin auren ya kama Juma'a kafin lokacin yin salla su Baffa suka iso, ana gama salla aka ɗaura masu auren akan sadaki naira dubu ɗari ukku sai fatan Allah ya sanya alkhairi ya basu zuri'a ɗayyiba, ana gama sallar Magrib jerin motoci suka zo ɗaukar yan kai Amarya zuwa gidanta dake a Garki, ba'a gida ɗaya zasu zauna da kishiyarta ba ita tana a gidajen manyan ma'aikatan bankin da yake aiki wato CBN, gidan da aka kai Ayshar babban Flat ne mai kyau, ba laifi anyi mata kaya daidai gwargwado wanda da yawa Haisam ne yayi mata su Fatuu ma da Kamalu dasu Gwaggo sun taka rawa wurin yin kayan ɗakin, shi kanshi angon Na'eem ya siya wasu abubuwan na gidan kafin a kawota kamar labulaye dasu carpets sannan part ɗin shi ya zuba komai, tun kafin ayi bikin Fatuu ta fahimtar da ita komai game da aure gudun kada a maimaita na Mino sai gashi a yadda ta fahimta Ayshar tasan miye auren wanda bata yi mamakin hakan ba don tafi Mino wayewar kai lokacin da aka yi mata aure, an kai amarya ɗakinta lafiya tana ta kuka aka barota sai fatan Allah ya basu lafiya. Ana gama yin bikin Aysha su Haisam suka fara shirye shiryen komawa gidanshi na Asokoro, ƙara sawa a gyara gidan Haisam yayi duk da sabo ne ba'a ta6a shigar shi ba amman za'a ƙara ƙawata shi, Jidderh na jin zancen shirin komawar tasu ta roƙi Haisam kan ya bata kwangilar shirya gidan in an gama gyaran sai gashi ya bata aikuwa sosae taji daɗi dama yanzu ta ƙware ta fannin shirya wuri har ta buɗe Company Hajiya Maryam ma na taimaka mata wurin gudanar da kamfanin harda hannun jari ta zuba kuma da yake ita babbar yar kasuwa ce tana yo mata Order ɗin kaya daga wasu ƙasashen, kafin tayi Odar kayan gidan saida ta fara zuwa ta gano shi don bata ta6a zuwa ba ta dai san da Haisam nada gida, bayan ta gano gidan ta tuntu6i Fatuu da Fanan don taji irin kalar kayan ɗakin da suke so duk suka faɗi mata sannan ta fara ƙoƙarin yo Order ɗin kayan da taimakon Hajiya Maryam. Saida aka ɗauki wata ukku wurin ƙara gyara gidan da kuma shirya shi kafin aka gama, ranar da zasu koma ya kama Friday bayan an gama sallar Juma'a akai convoy harda President da Mom da sauran yan uwa da abokan arzuƙi aka raka su lokacin Fatuu na kan Hanyar dawowa daga Zaria, lokacin da suka iso tun daga bakin gate ɗin gidan abun kallo ya fara, dakakken electric gate ne wanda ake amfani da remote wurin buɗe shi idan kuma ba wuta akwai inda ake dannawa sannan a zuge shi saidai sai mutum ya iya sannan zai iya buɗewa haka saman katangar gidan da aka tsarata nan ma zagaye take da electric fence, daga bakin gate din akwae Security guda ukku ruƙe da bindigu, bayan an buɗe masu gate ɗin duk suka kutsa Motocin cikin harabar gidan wadda take mai girman gaske, to Salamu alaikum mun shigo daular su Fatuu, tsaye nan ina kallon ƙasan harabar gidan wadda na kasa gane glass ne a ƙasanta ko kuwa wani kalar tiles ne da ban sani ba don gaba ɗaya harabar wani irin salƙi take kai kace in Mota ta taka ƙasan zai fashe saidai abun mamaki ko gezo bata yi ba, bayan duk an parker motocin wasu a parking space ɗin gidan guda biyu dake a 6angaren hagu da dama da zasu ɗauki motoci shidda shidda wasu kuma a gaban danƙareren ginin gidan duk aka parker su, akwae shukokin fulawoyi masu ban sha'awa su kansu an tsara su ta yadda sun ƙara ƙawata farfajiyar gidan, bayan duk an firfito harabar aka fara tsayawa ana kallo kafin aka nufi shiga cikin ginin wanda yake ƙaton ginin bene ne, koda nayi arba da ƙopar shiga shiru nayi na shiga tunanin ta yadda za'a buɗeta ban gama tunanin ba naga Haisam ya nufi ƙopar a wani ɗan rami mai glass ya ɗaura saman babban yatsan shi sai gashi ta buɗe ashe ƙopar mai fingerprint sensor ce, ganin yadda ya buɗe yasa Hajiya dake bayan shi tace yanzu wannan in mutum na gaggawa sai ya tsaya yan ta6e ta6e kuma su yara in tsawon su bai kai ba taya zasu ta6a har ta buɗe duk akai murmushi Haisam ya bata amsa da ana cire fingerprint ɗin a buɗe lafiya lou ko kuma in cajin ƙopar ya ƙare Hajiyar ta jinjina kai, bayan ƙopar ta buɗe aka fara shiga ciki, wata yar hanya ce zaka fara shigowa tun anan zaka ji wani ni'imtaccen sanyi ya ratsa sassan jikin ka, saman wurin na ɗauke da wata irin babbar fitila mai sarƙoƙi da suka zubo ni dai har saida na ɗaura hannuwana a saman kai don sai naga kamar zata faɗo man, ta cikin wurin matattakalar bene take ta wani lanƙwaya daga bangon dake kallon mutum kuma nan ma wata dakakkar ƙopa ce ita Haisam ya buɗe aka bi bayan shi nima na saka kai, a wani irin haɗaɗɗan falo mai sunan falon masu arziki na tsinci kaina, gaba ɗaya na ruɗe na rasa ma ta ina zan fara, falon nada girma ba laifi gaba daya fentin cikinshi fari ne sai walwali yake haka ƙasan shi malale yake da tiles, akwae set na jajayen kujeru royal masu ratsin golden brown haka lallausan carpet ɗin dake tsakiyan kujerun shima kalar kujerun ne, komai na falon mai daukar hankali ne tun daga kan inda kayan kallo suke da sound systems haka Dining area ɗin dake a can gefe nan ma abun mutum ya tsaya kallo ne akwae dining table da kujeru suma royal kalar na falon da gani mahaɗinsu ne akwae glass door deep freezer wadda marfinta na gilas ne kana hango abubuwan dake a cikinta sannan akwae display Carbinet ta glass mai ɗauke da cups da dishes da wasu kayan ƙawa dake ta walainiya, sosae wurin ya ƙawatu harda flower vases masu ɗauke da fulawoyi masu ban sha'awa a jikin bangon wurin daga gefe ƙatuwar ƙopar shiga Kitchen take, babban Kitchen ne U-shape gaba ɗaya kayan cikinshi kalar ja da fari ne hatta cabinet ɗin sama da ƙasa katakon fentin ja da fari ne sosae Kitchen ɗin ya tsaru ya sha tsadaddun kayan amfani kama daga masu amfani da wuta zuwa wanda basu amfani da wuta a cikin shi ƙopar store take shima shaƙe yake da kayan abinci, a jikin bangon falon ba'a liƙa komai ba don irin tsarin bangon ba'a fasa shi sai daga wurin adon gidajen da aka saka kayan kallo ne aka aje manyan hotunan masu gidan dana sauran Family ɗinsu su Dad da Mom da Hajiya da dai sauran su, daga wurin bangaren cin abinci wato dining area akwae wata matattakalar benen da itama zata kai ka sama wato daga nan falon zaka iya bi ka hau sama ka sauka ta ɗayan matattakalar dake a waje ko kuma daga ta wajen ka hawo ka saukko ta cikin falon, daga bangaren dama na falon part ɗin Fanan yake sai na Fatuu na a bangaren hagu, a kowane part ɗin nasu akwae madaidaicin falo sai ɗakuna guda biyu, a falon Fanan komai na ciki blue ne kama daga lumbutsa lumbutsan kujerun ciki wadda suke na fata wato leather chairs zuwa carpet da labulaye duk suma kalar kujerun ne akwae kayan kallo da kuma kayan ƙawata falo harda wani haɗaɗdan console wato madubin falo mai hade da table ɗin shi anyi masu design masu ban sha'awa, sosae falon ya haɗu ba kamar da fentin cikinshi ya kasance fari sai ya ƙara mashi kyau sosae, a Bedroom ɗaya gadon ciki italian royal ne shima blue da Wardrobe ɗinshi bango guda sai side drawers da dressing mirror, a ɗayan bedroom ɗin shima gadon italian ne amman mara hayaniya katakon irin mai salƙi ne komai na cikin shi fari da ratsin baƙi ne, a cikin kowanne ɗaki akwae toilet kalar na zamani komai na cikinshi fari da silver ne, a cikin toilet ɗin da Royal bed yake har da laundary room wato wurin yin wanki mai ɗauke da injin wanki da kuma cabinet mai marfin glass anan tawul suke da rigunan wanka, in muka koma bangaren Hajiya Fatuu itama kamar yadda bangaren Fanan yake haka nata yake wato falo da kuma ɗakuna biyu, a falonta itama leather chairs ne maroon sai dai nata L-shape ne, tun daga kan Carpet da labulayen ɗakin suma duk marron ne akwae tabur ɗin tsakiyar falo wato center table na glass haka daga can ƙarshen kujerar akwae wani madaidaici an ɗaura ɗan madaidaicin abun saka fulawa shima kalar maroon cikinshi ɗauke da fulawoyi green da ja wanda ya ciza yay kamar maroon sai kuma farare, itama akwae kayan kallo kamar na falon Fanan, a Bedroom ɗin farko itama italian royal bed ne kalar maroon da sauran mahaɗinshi sai dayan ɗakin simple modern italian ne wato itama mara hayaniya kamar na Fanan amman nata kalar ruwan toka ne suma sai salƙi suke jikinsu nada sul6i, a kowane ɗaki akwae toilet itama komai na ciki fari ne da silver sosae aka kashe mashi kuɗi ba abunda babu na banɗakin masu kuɗi da suka amsa sunan masu kuɗi harda shower cubicle wato ke6antaccen wurin yin wanka na glass, bayan an gama da ƙasan benen sama aka hau saidai Hajiya bata hau ba tace suyo mata Vedio Haisam harda cewa bari ya ɗauketa ta watsa mashi harara, Mino ma an hanata hawa don cikinta ya tsufa ya shiga wata na takwas itama a falon ƙasa ta zauna tare da Hajiya, saman benen 6angaren Oga Haisam ne akwae ɗan babban falo mai ɗauke da kujeru leathers kalar ruwan madara suma L-shape ne haka carpet da labulayen duk ruwan madara ne akwae kayan kallo daga inda suke anyi adon gidaje an saka hotuna haka daga gefen kujerar an aje ɗan tebur na glass an ɗaura fitila mai kyau haka a tsakiya ma an aje wani tebur ɗin, akwae bedroom guda biyu a bangaren dama da hagu, a bangaren dama Bedroom ɗin Haisam yake yana ɗauke da saitin italian bed shima mara hayaniya ruwan madara a ciki akwae laundary room da kuma toilet, ɗayan ɗakin ake kusa dashi nan kuma ɗakin daya danganci aikin Haisam ne duk kayan aikin fasaha ne a ciki, daga ɗayan bangaren falon nan ma wasu ɗakunan ne ɗaya nasu Twins ne yana da ɗan girma an saka yan gadajen katako guda biyu iri ɗaya harda drawers ɗinsu sannan akwai wardrobe ɗin bango daga can gefe kuma wurin karatu ne aka ware masu akwae ɗan babban tebur da kujerunshi guda biyu sai kuma daga gefe yar kanta ce mai ɗauke da littattafai harda toilet ke akwae a cikin ɗakin, a ɗayan ɗakin kuma nan ma akwae gado kalar coffe brown da drawers ɗinshi da madubi sai wardrobe ɗin bango itama kalar coffe brown nan kuma matsayin ɗakin baƙin Haisam ne, abun saidai ace Masha Allah kawai komai yayi an narka dukiya ba kaɗan ba a wannan gida gashi akwae free internet access wato damar hawa yanar gizo da mutum ya buɗe wi-fi shikenan sai yay ta browsing da chat basai kana da Data ba, bayan an gama da ciki bayan gidan aka nufa wanda gaba ɗayan shi malale yake da grass carpet, akwae swimming pool wanda aka ƙawata tsarin shi gwanin burgewa ruwa har ta sama yake zubowa sannan ta ƙasa ma akwae wasu haɗaɗɗun kan famfuna dake zubo da wani ruwan, daga gaban shi wani wuri ne da aka zagaye da waya ciki kayan wasan yara ne kamar dai park, akwae wurin wasanni guda biyu na ƙwallon kwando wato basketball da kuma ƙwallon raga wato Volley ball sai wasu rumfuna biyu na shaƙatawa ne sai ɗayar wadda ta gini ce ita kuma anyi tane don yi ma yara lesson, daga jikin gidan ta baya akwae ƙopar fitowa sannan akwai wani ɗaki mai babbar ƙopa cikinshi ma yana da girma nan kuma Gym ne wato ɗakin motsa jiki mai ɗauke da kayan motsa jikin iri iri harda treadmill irin wanda Fatuu ta ta6a hawa ya wujijjigata har ta suma... 105 ~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~ ......... Alhamdulillah Allah yayi mun gama zagaya ko ina sai yaba gidan ake ana an dai kashe kuɗi, cike da tsokana Dad ɗin su Haisam wato Mr President yace mashi anya bazai sa EFCC su bincike shi ba don an kashe ma gidan kuɗi da yawa duk akai dariya Hajiya tace in an tashi bincikar tashi sai a haɗa dashi tunda ai shine ƙarfin nashi, Dad ɗin na yar dariya yace shi ai gida kawai yasan ya bashi amman ba hannunshi a wannan uban kayan daya zuba ma gidan Hajiyar tace aikuwa shike da hannu tunda ai shiya biya mashi yaje yayi karatun fasahar da yake samun kuɗi duk akayi dariya harda Security dake biye dasu, itama Mom yaba ma Jidderh tayi tace bata san kamfaninta sun ƙware haka ba sai yanzu gaba ɗayan kayan da aka zuba ma gidan sun hau kuma sunyi kyau nan fa duk aka shiga yaba mata tanata dariyar jin daɗi haka mijinta Sadeeq shima yaji daɗin yabon nata da ake Dad ɗin su har yana cewa zai bata kwangilar zuba ma gidan su kaya in ya sauka zasu koma, cike da jin daɗi tayi mashi godiya Aunty ma tace zata rinƙa samo mata kwangila kuwa tunda sun ƙware haka Hajiya Zainab ma itama tace zata rinƙa samo mata dama harda ita aka zo don yanzu sunfi zama a Abuja bayan an ba Dad ɗinsu Sameer Minister, Fauzy dai basu ƙasar kuma har yanzu bata sake haihuwa ba itama don Sameer yace sai ta huta sosae ba kamar daya ga Cs aka yi mata, ganin Dad ɗinsu na niyyar tafiya yasa Haisam ce mashi please ya bari suci abinci ya ɗan buɗa mashi ido kafin yace ai baya jin yunwa Jidderh dake murmushi tace ai na murnar sabon gida ne ya kamata yaci yana murmushi yace to tunda hakane a bashi ya tafi da abunshi duk akayi dariya dama ya iya barkwanci, Fanan ce ta nufi cikin gidan da sauri dama sunyi Order ɗin abinciccika saboda masu rako su sabon gidan, bada jimawa ba ta fito ruƙe da manyan ledoji guda biyu ta nufo shi dasu, har rige rigen amsa muƙarrabanshi daya zo dasu suke amman sai yace masu su bari shi zai ruƙe abunshi don kada wani ya cinye mashi aikuwa mi za'ai ba dariya ba kuma shi ɗin ya kar6i abun shi anata ya kawo don Allah a ruƙe ya ƙi badawa, Addu'o'i yayi masu na Allah ya sanya alkhairi yasa sun dawo a sa'a ya karesu daga dukkan sharri anata amsawa daga baya sukai sallama aka buɗe mashi mota duk sauran abokan tafiyar nashi suma suka shiga motocin saida aka ga tafiyar su sannan suka koma cikin gidan harda su Mom, a falo aka zazzauna zaman cin abincin abun gwanin sha'awa su Mom sai kace ba First lady ba sun saki jiki cikin yan uwa ana ta cin abinci ana hirar nishaɗi. Sai gab da Magrib Fatuu ta iso Haisam yaje ɗaukkota tasha gayun doguwar rigar shadda, tun a bakin gate ɗin gidan ta fara sakin baki don itama ba sanin gidan tayi ba ta dai san shi a hoto, lokacin su Mom duk sun tafi sai su Mino da Aysha da kuma Jidderh da suka tsaya su tarbeta, sosae aka nuna farincikin dawowarta bama kamar su twins, Esha tana ganinta ta ƙanƙameta tana mata welcome tare da nuna mata sabon gidan su, sam Fatuu ta kasa 6oye al'ajabinta da kuma farincikin gidan sai faman bin gidan take da kallo idanu waje tana kuma sakin murmushi duk a lokaci guda, zagayawa suka shiga yi da ita harda Fanan Haisam kuma ya tafi Masallaci, bayan sun gama ganin ko ina ciki suka dawo don yin salla, sosae Fatuu tayi godiya ga Allah da yadda yake ta mata ni'imomi da bata ta6a zaton samu ba a rayuwarta, harda kukan daɗinta sannan tayi ma Mijinta Addu'o'i sosae shima, bayan sallar isha aka zo ɗaukar su Mino anata mata Addu'ar Allah ya raba ta da cikinta lafiya haka Aysha amarya ma ba'a daɗe da ɗaukar Mino ba itama angonta Na'eem yazo ya ɗauketa, Jidderh ce ta ƙarshe da aka ɗauka duk saida mazajen nasu sukai ma Fatuu Allah ya sanya alkhairi kafin su tafi don ɗazun da suka zo bata nan, bayan Haisam ya dawo a tare gaba ɗaya suka zauna cin abinci a dining area fuskokin kowannensu cike take da annuri, bayan sun gama cin abincin ne Haisam yace suyi alwala suyi Nafila duk suka ce to harda yaran, anan babban falon sukayi sallar raka'a biyu ta godiya ga Allah bayan sun gama kowa yayi addu'a Esha tana yi tana dariya tana leƙen fuskokin su twins, a falo suka zauna nan Fatuu tayi ma Haisam ɗin godiya da Addu'oin Allah ya ƙara mashi lafiya da arzuƙi mai amfani harda su Fanan dasu Esha ake amsawa, kallo suka yi zuwa ƙarfe tara da rabi Haisam yace ma su twins suje ya rakasu su kwanta aikuwa Esha na jin haka ta fara tura baki tana ƙunƙunin ita ba'a yi mata ɗaki ba a saka mata ɗan gadonta itama duk sukai dariya Fatuu tace ita dake da ma ɗakuna har biyu ga ɗayan na part ɗinta ga kuma na Momynta sai inda take so zata kwana ta tura baki tace ai duk gadon sun mata ƙato ita kalar nasu twins take so, Haisam dake a tsaye yana murmushi yace mata tayi haƙuri in ta samu sister sai ayi masu ɗakinsu suma su biyu ta wani yarfa hannu tace to ba Aunty da Momyn suƙi su haihu ba tayi ƙanwa duk sukai dariya, jawota Fanan tayi jikinta tana bata haƙuri tace bada daɗewa ba zata yi ƙanwa da Aunty ta gama karatu, "To Momy ke ki haihun man younger sister tunda ita sai ta gama karatun" ta faɗa a shagwa6e, murmushi Fanan ɗin ta shiga yi tana ɗan kikkifta ido ta kasa ce mata komai, hannu Fatuu ta kai ta dafa kafaɗar Esha ɗin tace "Momy zata haifar maki sister in sha Allahu, daga yanzu duk kikai salla pray for her, kuma su twins ku rinƙa yi ma Momynku Addu'ar Allah yasa ta haiho mana Baby mai kyau" ta ƙarasa tana murmushi duk suka ce to Haisam nata murmushi bai ce komai ba ya kama hannuwansu bayan sun yi masu saida safe suka tafi yadda ya ruƙe su abun gwanin sha'awa, bayan sun haye bene Fanan ta miƙe tana ruƙe da hannun Esha tace suje itama ta kwanta ta ɗaga hannu tana ce ma Fatuu "Good night, Aunty" itama hannun ta ɗaga mata tace "Goodnight, Esha Darling" ta saki dariyarta mai kyau suka tafi, bin su da ido Fatuu tay har suka shige ta ɗan girgiza kai wani irin tausayin Fanan take ji game da rashin haihuwarta don ta san dole tana tsananin son ta haihun, lokacin da su twins suka fara girma duk sun ɗauka Fanan ɗin ce ta haife su saboda yawan jan su a jiki da take, koda ta fahimci hakan don sun fi sakewa da ita da kanta ta sanar masu da cewa Fatuu ce ta haife su Adam har saida yaje ya tambayi Fatun wai da gaske ba Momy bace ta haife su ta tambayeshi waya faɗi mashi hakan yace ita, jin haka yasa taje tayi mata magana kan miyasa zata yi masu wannan Maganar tana murmushi tace yakamata su sani ne don uwa ba wasa bace in bata faɗi masu ba zasu iya ƙin bata muhimmancin daya kamata lokacin har saida su duka sukai ƙwalla, daga baya ne Fatun tace masu suci gaba da ɗaukar Fanan matsayin Momyn su ita kuma su rinƙa ce mata Aunty, miƙewa tayi ta nufi Bedroom ɗinta inda keda royal bed, bayan ta shiga shirin yin wanka tayi dama duk kayan sawarsu an riga an kawo su tun kafin su dawo har ta ware wasu masu yawa zata aika ma Gwaggo a bada su sadaka a Foundation ɗinsu wanda yanzu sosae ya cigaba ana tallafa ma marasa ƙarfi ba kamar yan gudun hijira da akwae su sosae a yankin Katsina, su twins ma da Esha duk an ware kayan su da yawa za'a bada Fanan ma haka, a cikin laundary ta cire kayan jikinta ta ɗaukko rigar wanka ta saka tana ta kallon kanta ta cikin ƙaton madubin wurin, gaba ɗaya ganin komai take kamar a mafarki gashi sai take ganin komai ya faru da wuri wato dai ashe cin ribar haƙuri haka yake da daɗi, lafiyayyan wanka tayi lokacin data fito sai faman sakin wani irin ƙamshi take, Bedroom ta shiga ta zauna akan kujerar gaban madubi tana kallon kanta tana goge lemar ruwan jikinta data kanta, tana haka Haisam ya shigo cikin ɗakin da sallama ta juya tana kallonshi suna haɗa ido ta fara sakar mashi ƙayataccen murmushi shima ya shiga maido mata, tun kafin ya ƙaraso gareta ƙamshin turarenshi ya rigashi isowa yana sanye da kayan bacci riga da wando farare masu taushi wanda da gani sababbi ne, wurinta ya nufo yana zuwa ya tsaya yana kallonta suna sakar ma juna murmushi can ya miƙa hannu ya amshi towel ɗin da take goge jikin ya cigaba da goge mata sai dai nashi da wani irin salo mai tsuma zuciya yake yi suna yi suna kallon juna ta cikin madubin suna cigaba da sakin ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar ƙaunar juna, bayan ya gama goge mata da kanshi ya shafa mata man da yasan tana amfani dashi da daddare, gaba ɗaya shi yayi mata shafe shafe da goge gogen da take yi da daddare da yake gashinta bai jiƙe ba sosae iya baki baki ne hakan yasa bai busar mata dashi ba, bayan ya gama miƙewa tayi da niyyar taje ta saka kaya kawai sai ji tayi ya janyota ya haɗe jikinsu kafin ya haɗe fuskokinsu suka shiga shaƙar numfashi da ƙamshin juna, slowly ya kai lips ɗinshi ya haɗe da nata ya shiga bata deep and hot french kiss, tun ƙafafunta na ɗaukarta har suka kasa gaba ɗaya ta ƙanƙame shi, ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya saketa ai da ƙyar take iya kallonshi hakan yasa shi yin ɗan murmushi mai sauti ya kai hannu ya ɗauketa gaba ɗaya, yana ɗauke da ita ya nufi switch ya kashe hasken ɗakin kafin ya nufi haɗaɗɗan royal bed ɗinta daya sha lafiyayyan zanin gadon da ko mutum bai yi niyyar bacci ba ya kwanta sai ya ɗauke shi, sosae Fatuu tayi ma Haisam godiya ta hanyar faranta mashi daren ranar ya shiga cikin tarihinta, Washe gari da safe ita da Fanan suka shiga Kitchen don yin Breakfast sai mai aikinsu ta wancen gidan da suka taho da ita ita kuma tana gyara gidan duk da bai wani 6aci ba, suna cikin aiki ne Fanan take ce ma Fatuu yakamata a ƙara masu aiki don yanzu aikin dole zai yi yawa ba kamar wanccan gidan ba tunda shi iya inda suke amfani ake gyarawa Fatun tace mata tana ganin a ƙara guda ɗaya tunda in ta gama karatunta zata dawo da Asabe mai aikinta ta can Zaria nan, "Allah sarki, har na tuna da Aunty Saude mace mai kirki gashi sam bata da son jiki, in mutum ya samu mai aiki kamarta ya more don tana da amana" Fatuu dake juya dankalin turawa cikin mai ta faɗa, Fanan na jin abunda tace itama tace gashi ta iya girki kamar me Fatuu tace wllh, "To ko ayi mata magana in tana da wadda zata turo mana, dama ni ban cika son irin wanda agent ke turowa ba don baka san mutum ba wasu mutanen are evil" kai Fatuu ta jinjina tace to zata mata magana dama basu daɗe da sukai waya ba tayi mata barka don ta haihu, ɗan buɗa ido Fanan tayi "Don Allah fa!" Fatuu tace mata wllh, "Amman ban samu labari ba ai da nayi mata barka kuwa, ikon Allah, itama tunda tayi aure bata haihu ba sai yanzu duk da bansan ko tana Family planning bane tunda ance tana da wasu yara" Fatuu tace mata eh tana da yara da tsohon mijinta kafin ta ƙara cewa "kema in sha Allahu Aunty Fanan zaki haihu" tana murmushi tace to Amin in tana da rabo in kuma bata da rabo already Allah ya bata ta wata hanyar Fatuu tay murmushi, "Amman fa in kin mata Maganar mai aiki kada a samo yarinya ko budurwa babba kamarta zaki ce" Fanan ta faɗa tana motsa farfesu, cikin rashin fahimta Fatuu tace to dama aikin gidan nan babbar zata fi, yar dariya Fanan tayi don ta fahimci bata gane dalilin da yasa ta faɗi haka ba tace mata ita saboda kada a ƙwace masu miji ta faɗi haka don tana jin labarun faruwar irin haka, dariya sosae Fatuu tay harda ɗage kai Fanan dake dariya itama tace Allah, bayan Fatuu ta tsagaita da yin dariyar tace ai Hubby bazai yi hakan ba, "Uhmm, wani lokacin suna ba mutum mamaki fa ba kamar shi da ya cika tausayi hakan na iya saka shi ya auri mai aiki", shiru Fatuu ta ɗan yi tana ɗan murmushi, jin tayi shiru yasa Fanan ɗin kallonta nan take ta fahimci yanayin fuskarta ya canza da sauri ta kai hannu ta dafata tace "Zarah bafa nayi Maganar saboda ke bane wllh, i just said it as an example, Babe wani irin mutum ne shi yana da kirki sosae, inda kirki yana yin yawa to zance kirkin shi har yayi yawa abunda baka tunanin zai iya yi sai kiga ya yi, kamar yadda ya aure ki da niyyar taimako nima haka ne, gara ke ma don na tabbatar yana son ki kawai bai sani bane, amman ni na tabbatar baya sona lokacin daya aure ni kawai yayi ne don ya faranta man ganin na shiga mawuyacin hali saboda shi, amman saboda kirkin shi tunda nike dashi bai ta6a wulaƙanta ni ba daidai da rana ɗaya gashi ko haihuwa bana yi, Babe na musamman ne" ta ƙarasa idonta a sama tana murmushi, itama Fatuu murmushin ta shiga yi tana tunano tun daga farkon haɗuwar su, "Amman Aunty Fanan nace mi zai hana mu ɗan hada mashi surprised party matsayin godiya da wannan sabon gidan" Fatuu ta faɗa tana kallon ta, da sauri Fanan tace wannan shawara ce mai kyau ya take gani za'ai Fatun tace ayi mashi cake sai ai decorating falonta, Jidderh suka yanke zasu kira kan tazo ta shirya falon Fanan ɗin in zasu yi mashi partyn bazatar, waya Fatuu ta ɗauka bayan ta kira Jidderh ta ɗauka sun gaisa take faɗi mata abunda suke son yi, tambayar ta tayi yaushe suke son yin partyn Fatuu ta kalli Fanan ta tambayeta tay ɗan jimm alamar tunani kafin tace ko gobe ko Fatun tace to ai kuma ita gobe zata koma, ce ma Jidderh sukai in zai yuwuwa zuwa da yamma kamar wurin ƙarfe biyar tace Ok lafiya lau zata masu ƙoƙarin hakan, Misalin ƙarfe huɗu Jidderh ta iso gidan a Motarta, saida ta fara kiran Fatuu ta tambayi in Haisam bai a babban falo tace mata eh yana Masallaci, tare da wata abokiyar aikinta yare suka zo, bayan sun fito daga cikin Motar suka fara kwasar kayan da suka zo suna shiga dasu, bayan sun kai wasu Fanan da Fatuu suka biyo su suma suka taya su ɗaukar wasu, ba 6ata lokaci Jidderh da abokiyar aikinta suka fara shirya falon, bayan sunyi nisa ne Fanan da Fatuu suka tafi su shirya, wuraren ƙarfe biyar Fanan ta kira Haisam a waya ta tambayi yana ina ya bata amsa da yana a sama suna yin lesson dasu twins tace pls in ba damuwa ya zo part ɗinta tana son ganin shi ya furta Ok, ba'a ɗau lokaci ba ya turo ƙopar yana sanye da ƙananun kaya da suka amshi jikinshi, yana niyyar yin sallama ya dakata sakamakon wani ƙyalƙyali daya zubo mashi har saida ya ɗan runtse ido, bayan ya tsagaita da zubo mashi yasa hannu yana kakka6e wanda ya maƙale mashi a jiki da saman sumar shi, yana ɗagowa ya kalli gaban shi idanunshi suka sauka akan wata yar banner da aka yi rubutu mai walwali an rubuta _"Thank you for our new home, We really love you our Husband"_ ƙayataccen murmushi ya saki ganin rubutun kafin ya juya ya kalli cikin falon wanda aka ƙawata shi da baloons wato balo kala kala sannan an aje manyan hotunan bikinsu shida Fanan da kuma wanda akayi mashi da Fatuu a Dinner ɗin su da akai a Abuja sannan an aje wanda sukai su duka da yaran su harda babban cake mai hawa biyu anyi decoration da hotunan Haisam da zasu kai biyar sannan an yi rubutu in icing an rubuta "Home sweet home" sannan daga saman baki bakin cake ɗin anyi topping da fresh fruit da suka ƙara ƙawata shi, nufo shi Fatuu da Fanan sukayi sun sha gayun ƙananun kaya riga da wando da suka bayyanar da dirin su gashin kan su gaba ɗaya sun sake shi kai kace hausa bazata fito daga bakunansu ba, ko a iya matan da Allah ya ba Haisam za'a iya cewa ba ƙaramin dacewa yay ba don mata ne da suka amsa sunan mata uwa uba gasu da hali na gari, a gabanshi suka tsaya suna sakin murmushi tare da ƙara yi mashi godiyar yanata murmushi ya ware masu hannuwanshi a tare suka faɗa jikinshi suna ta yar dariya Jidderh da abokiyar aikinta ma dariyar suke ta shiga yi masu Vedio, bayan sun ɗago daga jikinshi kamo hannuwansu yayi suka nufo ciki, a saman doguwar kujera suka zauna dama a gabanta aka aje cake ɗin, bayan zaman su Jidderh tace yakamata a kira su twins suzo a yanka cake tare dasu Fanan ta miƙe ta nufi inda wayar landline take ta kira part ɗin Haisam, Esha ce ta ɗauka cikin zazzaƙar muryarta tace waye ne ke kiran Dad to bayanan da turanci tayi Maganar Fanan na murmushi tace to Momynsu ce, waro ido Eshar tayi sai kuma tayi dariya ta kira sunanta ta amsa tare da tambayarta ina su twins tace mata gasu nan tace to suzo part ɗinta yanzun nan akwae surprise da sauri Esha ta maimaita abunda tace tare da waro ido Fanan ɗin tace mata eh, kife kan telephone ɗin tayi cike da zumuɗi ta faɗi ma su twins abunda Momy tace ta nufi hanyar fita da gudu, Esha ce ta fara shigowa da gudu tana sanye da ɗan skirt na jeans da farar t-shart bayan ta shigo su twins suka biyo bayanta suma ƙananun kaya ne a jikinsu, koda Esha taga yadda akai ma Falon da tsananin mamaki taja ta tsaya a gabansu ido waje ta furta "Wow! what a surprised!!" hannu Fanan ta miƙo mata ta nufesu tana washe baki, a saman jikinta ta ɗaurata gaba ɗaya ta ruɗe sai faman tambayar su Dad ake ma Birthday take, saida Adam ya nuna mata rubutun jikin cake ɗin sannan ta fahimci mi ake, a tare gaba ɗaya suka kama ma Haisam ɗin hannu suka yanka cake Jidderh nata masu Video, bayan an yanka kowa ya ɗauka ya bashi a baki kafin shima ya basu har shafa mashi icing ɗin jiki sukai a fuska suna ta dariyar farinciki daga baya Fanan ta kama hannunshi da turanci tayi mashi kalami masu tsuma zuciya kan muhimmancin shi a wajenta da kuma yadda take son shi ƙarshe tayi mashi godiya da Addu'oi, bayan ta gama Fatuu ma tayi suma su Esha saida sukai mashi abun dai gwanin burgewa daga baya aka shiga yin hotuna, harda music Fanan ta kunna aikuwa Esha ba ƙaramin cashewa tayi ba sosae taba mutane dariya, sosae Haisam ya yaba da abunda sukai mashi shima saidai yay masu kalamai kan yadda suke a wurinshi saida aka kira sallar Magrib suka gama. A cikin satin akaita zuwa ganin sabon gidan da yi masu Allah yasa Alkhairi har Laila ma tazo daga Kano ita da mijinta da yaranta biyu don ta ƙara haihuwa, ranar Friday su Gwaggo suka zo da Kawu Amadu da Tk da kuma matansu sai yaransu don dukkansu sun ƙara haihuwa ita matar Tk mace ta ƙara haihuwa itama Haulat mace ce mai sunan Gwaggo wato Khadija, zuwan nasu yasa Fatuu ta ƙara zuwa Abujar kowa saida ya jinjina haɗuwar gidan akai masu Allah yasa Alkhairi da Addu'oi, a yadda suka shirya zasu bi Gwaggo ne apartment ɗin da take zama in tazo amman Fatuu ta hana tace anan zasu kwana harda gwaggon tunda ai don su suka zo, ƙarshe dai anan suka kwana don Haisam da Fanan duk sun saka baki kan su kwana anan, Washe gari Asabar bayan sunyi lafiyayyan breakfast suka shirya fita harda su Fanan da Fatuu sukai Mota ukku data Fatuu dasu Gwaggo suka zo da ita sai kuma ta Fanan sai wadda Haisam zai hau, Villa suka fara zuwa duk an nuna farincikin zuwansu karma Hajiya sosae tayi murnar ganin su akai masu tarba mai kyau, daga Villa gidan Mino suka wuce zo kaga murna har tana ce ma Gwaggo amman dai bazata koma ba har ta haihu ko Gwaggon na dariya tace a'a abunda da saura amman zata kwana biyu in ta haihun ta dawo, da ƙyar ta barsu suka tafi harda roƙonsu kan su dawo su kwana anan suka ce to ƙilan su dawo, daga nan gidan Aysha aka wuce itama taji daɗin ganinsu har ta kasa rufe baki gashi tayi masu lafiyayyan abinci don tasan da zuwan nasu, bayan gidan Aysha gidan Kamalu aka nufa nan ma dai sun nuna farincikin zuwan nasu hannu bibbiyu Farha ta kar6e su Babynsu har ta girma tubarkallah, gaba ɗaya ko ina roƙonsu ake kan su kwana ƙarshe saidai rabawa sukai Haulat da Husnah suka koma gidan Mino Tk da Amadu kuma gidan Kamalu zasu kwana Gwaggo kuma gidan Aysha sai dare su Fatuu suka koma gida, Washe gari gaba ɗaya suka koma gidansu Fatuu a yadda suka shirya tare da ita zasu tafi Zaria su kwana washe gari Monday da safe sai su wuce Gwaggo dai anan zata tsaya sai ta kwana biyu, Kwance tashi cikin Mino ya shiga wata na tara lokacin watan su Fatuu ɗaya da komawa sabon gida kuma Fatun na gida don sun samu hutu, tun ranar litinin ta fara yin naƙuda tsaitsaye zuwa washegari talata ciwo ya kankama amman koda aka kaita asibiti sai aka ce da saura su dawo gida taita yin exercise, kan kace mi duk ta fita hayyacinta dama abu ga sabon shiga tuni ido ya raina fata sai murƙususun azaba take har zuwa Fatuu tay ta dubata itama taga da saura ɗin haka tay ta ƙarfafa mata gwuiwa har tana ce mata kodai dama bata yin exercise da cikin ya tsufa cikin ciwo tace wllh tana yi, sai dare Fatuu ta koma gida Nameer ya dasa yin jinyar, wuraren ƙarfe sha biyu ba arziƙi ya kwasheta suka koma asibitin, wannan karon an kwantar da ita a vip wato ɗaki na musamman ita kaɗai ce aciki duk da haka an faɗi ma Nameer cewa da sauran lokaci, koda Fatuu ta kira taji ya jikinta Nameer ne ya sanar mata sun dawo asibiti an kwantar da ita amman ance still da saura tana jin haka tace gata nan zuwa, bayan zuwanta Asibitin Auntynsu Nameer ma tazo, shiru shiru ba haihuwa gashi ga dukkan alamu tana cikin azaba wasa wasa sai gashi har asuba bata haihu ba lokacin ta gama jigata ƙarfinta ya ƙare, gari na wayewa Aunty ta bada umarnin ayi mata Cs, sosae hankalin Nameer ya tashi jin zancen aikin amman ba yadda ya iya haka ya saka hannu, Wuraren ƙarfe tara na safe aka shiga da ita ɗakin tiyatar lokacin duk yan uwa sun zo harda Mom, Aysha ma tazo sai kuka take ana ce mata tayi mata Addu'a, ita kanta Fatuu hankalinta a tashe yake ƙarfin hali kawai take tana ta yi mata Addu'oi, bayan kamar minti ashirin da shiga da ita sai ga likitan ya fito yana ta murmushi ya sanar dasu tama haihu da kanta ba'a riga anyi aikin ba, zo kaga murna Aysha har da tsalle sai ga mai kuka ta koma yin dariya Fatuu da Nameer harda sujjadar godiya ga Allah sukai, lokacin da aka fito da Babyn wanda namiji ne baka jin komai daga bakunansu sai tubarkallah ma sha Allah Babyn kyakkyawan gaske gashi ƙato, daga baya itama Mino aka fito da ita saman gado baiwar Allah har an saka mata rigar aiki, bayan an canza mata ɗaki duk aka shiga ana mata ya jiki da barka, su Mino an ɗanɗana tun a asibitin ta rinƙa faɗin ta gama haihuwa aikuwa mi Fatuu zatayi in ba dariya ba tace wasa take ai yanzu ma ta fara sai gata harda kukanta sha6e sha6e tana ta rantsuwar ita Allah ta gama, da yamma aka sallameta ganin lafiyarta lau suka koma gidanta aka cigaba da zaman jego har ranar suna tazo yaro yaci sunan mahaifinsu Fatuu wato Muhammad aikuwa ba ƙaramin farinciki su Fatuu sukai ba, bayan suna da kwana ukku ta koma Yola acan zatayi wanka kamar yadda ta buƙata a wurin Nameer. Bayan sati biyu da haihuwar Mino ranar Alhamis lokacin hutun su Fatuu na gab da ƙarewa tana kwance saman gado da safe wurin ƙarfe sha biyu na rana jikinta sanye da turkish dress riga da wando kalar Yellow gyalen kayan na daga can gefe hakan ya bayyanar da kanta da akai ma kitson sunan Mino sati ɗaya daya wuce, tana cikin yin baccin Esha ta shigo ɗakin da gudu koda ta hangota kwance sai ta nufi gadon, hayewa tay ta fara bubbuga jikin Fatuu tana faɗin "Aunty, wake up!, wake up pls!! ki tashi" yanayin yadda take Maganar kamar zata saka kuka, buɗe ido Fatun tayi ganin Esha ce ke tashinta yasa ta tamke fuska da alamun 6acin rai ta furta "Esha! Why do you always disturb my sleep for God's sake! Banda dama in kwanta sai kin tashe ni kuma bada wani dalili ba kawai baki so ki ganni a kwance!" yamutsa fuska Esha ɗin ta shiga yi idanunta suka ciko da ƙwalla, a fusace Fatun ta ƙara cewa "yanzu da kika zo kina buguna haka miye zan maki??" cikin karyayyar murya Esha ɗin tace "Ba Momy ne bata lafiya ba kuma tayi amai da kuka" waro ido Fatun tay ta maimaita "amai da kuka!" da sauri ta jinjina mata kai aikuwa ba shiri ta wuntsilo daga saman gadon ko ta kan gyalen kayan bata bi ba ta nufi hanyar ƙopa Esha data saukko itama tabi bayanta da sauri, lokacin data shiga Bedroom ɗin Fanan kwance ta sameta a saman gado rabin jikinta lullu6e da duvet sai nishi take su twins sun sakata tsakiya fuskokinsu duk ƙwalla, a ruɗe Fatuu ta nufi bakin gadon ta zauna tare da kai hannu ta ta6a fuskarta tana tambayarta mike damunta haka, cikin nishi tace mata tunda ta tashi bata jin daɗin jikinta haka ta rinƙa daurewa har sukai breakfast to bayan sun gama ta dawo ɗaki taji zuciyanta ta fara tashi daga baya kuma sai amai yazo mata bayan tayi ne zazza6i da ciwon kai suka rufeta tana haka su twins suka zo yanzu ma bata daɗe data ƙara yin aman ba gashi harda juwa take ji shiyasa tasa a kira mata ita ganin ciwon na gaba, cike da damuwa Fatuu tace ai da tun da taji bata lafiya tasa aka kirata, wayar Fanan ɗin ta ɗauka ta kira Haisam bayan ya ɗauka cikin tashin hankali ta sanar mashi da halin da Fanan take ciki Shima hankalinshi ya tashi ba kamar daya ga lafiya lou suka yi breakfast, ce mata yay ko ta kaita Asibitin Villa tunda yafi Kusa zai iskesu yayi wasu baƙi ne daga Lagos amman bada jimawa ba zai sallamesu yazo duk yadda ake ciki pls ta sanar mashi da sauri tace to, suna gama wayar Mom ɗin shi ya kira ya sanar mata tace bari ta kirasu, bayan ta kira wayar Fanan ɗin Fatuu ta ɗauka ta tambayi yanayin jikin Fanan ɗin da damuwa Fatun tace to gata nan da gani dai tana jin jiki tana tunanin fever ce ke damunta Mom ɗin tace Ok su taho nan sai a dubata, dama Fanan ɗin a shirye take don duk sunyi wankan safe gyale Fatuu ta ɗaukko mata itama ta ɗauki wani cikin nata ta yafa, a tare harda su twins suka kamo Fanan ɗin yaran duk sun shiga damuwa gwanin tausayi, a Motar Fanan suka tafi, bayan sun isa Mom ta tarbesu aka wuce da ita Asibitin, suna zuwa kwantar da ita akai a ɗaya daga cikin lafiyayyun dakunan da ake kwantar da marasa lafiya da suka danganci gidan gwamnatin tarayyar, tambayoyi likitan daya kar6eta ya shiga yi mata tana bashi amsa ciki harda rabonta da period ta bashi amsa da tayi last Month sai wannan watan ne bata kaiga yi ba amman dama wani lokacin tana fita daga wata sannan har tsallaken wata ma tana yi nan tayi mashi bayanin lalurar data yi a baya amman tace mashi ta samu sauƙi, lokacin da ake mata tambayoyin Mom ta kira Hajiya Maryam ta sanar mata ga Fanan an kawo ba lafiya nan take hankalinta ya tashi ta shiga tambayar abunda ya sameta Mom ɗin tace ba'asan taƙamaimai ba amman gashi nan likita na bincikawa tace to gata nan zuwa, jininta aka ɗiba aka tafi yi mata gwaje gwaje, ba'a jima ba Hajiya Maryam ta ƙaraso tana ganin yanayin jikin Fanan ɗin a ruɗe ta hau tambayarta abunda ke damunta Fatuu dake zaune a wurin kanta tayi mata bayanin yadda ciwon ya fara sam ba wanda ya kawo komai a ranshi Mom tace su jira likita yazo ya faɗi sakamakon gwaje gwajen, bayan wani ɗan lokaci Hajiya Maryam ɗin ta miƙe tace bari dai tabi bayan likitan don ta ƙagara taji mike damunta haka, tana niyyar fita likitan ya sako kai da sallama taja gefe, yana shigowa ta hau tambayar shi mike damunta ne fuskarshi ɗauke da murmushi yace ta kwantar da hankalinta abun farinciki ne, su Mom na jin haka duk suka miƙe suka nufo shi, tambayarshi Hajiya Maryam ta sake yi miye abun farincikin yace sakamakon gwajin ciki da akai mata ya bayyana tana ɗauke da ciki na tsawon sati ukku, yadda kasan wutar jikinsu ta ɗauke gaba ɗaya bin shi sukai da ido ba mai ko ƙwakkwaran motsi shi kuma likitan sai murmushi yake, "Wait Dr, wai abunda kake son faɗi mana shine kana nufin ita Fanan ɗin ke ɗauke da ciki?" da tsananin mamaki Hajiya Maryam ta tambaya cikin girmamawa yace mata eh haka sakamakon ya nuna tana dashi na sati ukku yay maganar tare da miƙo mata wata farar takarda da aka naɗe, har saura kaɗan ta saki wayarta dake a hannunta wurin rawar hannun ta amsa, bayan ta buɗe Mom da Fatuu suma suka shiga dubawa nan idonsu ya tabbatar masu, da tsananin farinciki suka shiga washe baki Fatuu harda sa hannu guda ta rufe bakinta alamar mamaki, nan fa aka shiga yin murna su Esha harda tsalle suna faɗin Momy is pregnant zata haifa masu baby Allah ya amshi addu'ar su, nan fa aka fara kiraye kirayen waya ana ma yan'uwa albishir, ko ban faɗa ba ansan dole ai tsananin farincikin samun cikin, Mom ce ta kira Haisam lokacin ma yana kan hanyar zuwa tayi mashi albishir to shima dai ba ƙaramin mamaki da murna yay ba , kan kace mi ɗakin ya cika har Hajiya tazo da Farha anata farinciki, kyautar miliyan guda Hajiya Maryam tayi ma likitan daya faɗi masu zancen cikin Haisam ma ya ƙara mashi wata miliyan guda ɗin kakar likita ta yanke saƙa har ya rasa irin godiyar da zai yi, Mom na dariya tace to ai itama yakamata a bata kyautar tunda ita ta kirata ta sanar mata zancen ciwon duk akai dariya Hajiya Maryam ɗin tana dariya tace to ta bata kyautar Mota duk akai shewar murna, Mom nata dariya tace ita ta yafe Doughter yakamata a ba kyautar tunda ita ta kawota asibitin Hajiya Maryam ɗin tace to ta ba Fatun Motar, da sauri Fatuu tace a'a ta barta ai duk abun farincikin nasu ne Hajiya Maryam ɗin tace ta riga ta bata in bata so sai ta bayar, Esha na jin haka ta ruƙe ƙugu tace to ai suma tare dasu aka kawo Momyn a basu kyautar, hannu Hajiya maryam ta kai ta ɗan ja kumatunta tace ta faɗi abunda duk take so da sauri tace stroller take so da zata rinƙa tura baby aikuwa mi za'ai in ba dariya ba Hajiya Maryam ɗin tace an gama in ma guda goma take so zata siya mata ta juya kam Adam tace shi mi yake so yace kayan wasa da zai rinƙa yima Baby wasa harda Mota da zasu rinƙa shiga tare suna zagaye gida tace to shima za'a siya mashi, juyawa tay kan Abie da yayi shiru kai kace babu shi a wurin tana dariya tace "kai kuma miskilin mu mi kake so?" shiru yay yana bin ta da idanunshi da suke a ɗan lumshe duk da idanun nasu manya ne amman wani lokacin sai su lumshesu kamar dai yadda na Haisam ke yi, shiru yay bai tanka mata ba duk idanunsu na akan shi ana son aji mi zai ce don Magana mugun wuya take mashi wannan da alama ma sai yafi Haisam miskilanci dama ance wai kyawun magaji ya zarta, ganin baida niyyar magana yasa tace mashi in fa bai faɗi mi yake so ba to in aka haiho Babyn saidai ya rinƙa kallonshi do n baza'a bashi ba ya ɗauka balle har ya yi mashi wasa, ana jin abunda tace su Mom suka ce mashi ya faɗi mata ko so yake su Esha su rinƙa ɗaukar baby suna mashi wasa banda shi, a hankali ya fara motsa baki kafin da ƙyar cikin sanyayyar muryarshi ya furta Water Bottle yake so da zai rinƙa ba Babyn ruwa aikuwa mi za'ai in ba dariya ba har Haisam saida yayi dariyar Hajiya dake zaune tace ai shine Water Bottle ɗin aka ƙara yin dariyar, Fatuu dake zaune gefen Fanan ta lura da ita kamar bata farincikin samun cikin don ko uffan bata ce ba duk abun nan tana kwance sai ɗan murmushi da take in anyi abun dariya hakan yasa ta dafata tace "Aunty Fanan ya naga kamar baki farincikin samun cikin ko jikinne?" wannan Maganar da tayi ce ta maido hankulan yan ɗakin kan su Hajiya Maryam tace itama ta lura don ta ɗauka jin zancen cikin zai sa ma ta wartsake, ganin duk sun zuba mata ido yasa tayi ɗan faffaɗan murmushi tace tana farinciki mana saidai ita a wurinta already tana da yara so bata jin wannan kamar a cikinta na farko, gaba ɗaya Maganar tayi masu daɗi Hajiya dake murmushi tace gaskiya ne Maganarta, Auntyn su Haisam ce tace ya kamata a barta ta huta sun zo suna ta surutu a kanta Mom tace abun farinciki ne ya samu dole ayi murna, tambayar likita Aunty tay in ba wata matsala zasu tafi da ita ta huta sosae yace eh lafiya lou zai bata magunguna saboda zazza6i da ciwon kan sai kuma na amai da take, bayan sun koma cikin Villa a ɗaki daban ta kwanta aka kawo mata abinci da ƙyar ta ɗan ci bayan ta gama Fatuu ta bata magunguna tasha ta buƙaci yin wanka Fatuu ta taimaka mata, bayan tayi wanka kwanciya tayi nan da nan bacci ya ɗauketa, a ranar iyalan cikin farinciki suka kasance koda aka sanar da Laila itama tayi murna har tana cewa wannan dole tazo ta dubata, Fatuu nata so ta sanar ma Gwaggo saidai ta baro wayarta a gida, anan suka wuni sai bayan Magrib suka shirya komawa gida Hajiya Maryam tace ma Fanan ita mi zai hana ta tsaya ta ɗan kwana biyu tunda ba sanin irin yanayin tayi ba zata fi samun kulawa anan tana murmushi tace ai sister Fatuu ta sani zata kula da ita tunda tana cikin hutu dole tayi shiru amman ba don taso Fanan ɗin ta tafi ba a lokacin, bayan sunyi sallama da kowa Haisam ya ɗaukko su a jigunannar Jeep ɗin shi da bai daɗe da siyanta ba ita kuma Motar Fanan aka barta anan, saida Hajiya Maryam ta rakasu bayan sun isa gidan haka tay ta faman faɗi ma Fanan ɗin abubuwan da zata kiyaye gudun kada cikin ya samu matsala tace ma Haisam aiki ma ta daina zuwa ta ɗauki hutu har zuwa ta ƙara warwarewa yace Ok, ta ƙara cewa abinci ma asata ta rinƙa ci akai akai koda tana amayar dashi wani zai tsaya nan ma yace mata to kafin ya sake cewa likita ma yace maganin daya bata zai sa ta daina yin aman ta rinƙa cin abinci sosae in ma baiyi mata ba akwae wanda Zarah tayi amfani dashi a Us yana da kyau sosae sai yasa akawo mata cikin nuna jin daɗi tace to daga baya tayi masu sallama kamar kar ta baro Fanan ɗin don gani take kaman cikin zai iya samun matsala haka dai ta taho Fatuu da Haisam suka yo mata rakiya ta tafi, bayan sun koma ciki gaba ɗayansu a bedroom ɗin Fanan suka zauna tana kwance su Esha sun zagaye ta, hira suka shiga yi cike da farinciki daga baya Fatuu ta tambayi ko tana son wani abu ta haɗa mata da sauri ta girgiza mata kai tace ai bata daɗe data ci abinci ba a Villa Fatun tace to bari ta kawo mata fruit ba tare data jira cewarta ba ta saukko daga gadon ta nufi ƙopa, bayan fitarta bin juna sukai da kallo ita da Haisam suna sakar ma juna ƙayaaccen murmushi, saida Fanan ɗin tayi bacci sannan Fatuu ta koma ɗakinta lokacin ta kira Gwaggo ta sanar mata samun cikin ai tana ji ta shiga yin hamdala cikin tsananin farinciki ta tambayi ina Fanan ɗin ta tayata murna da sannu da jiki tace tayi bacci Gwaggon tace to in Allah ya kaimu zata kira, bayan ta gama wayar da Gwaggo Aunty Mareeya da Feenah ta kira suma ta sanar masu kowa yayi farincikin jin zancen samun cikin suna ta addu'oin Allah ya inganta, daren ranar gaba ɗaya Fatuu da Haisam saida suka yi nafila tsakar dare suka gode ma Allah tare da Addu'ar Allah ya inganta masu cikin ya sauketa lafiya. Kulawa sosae suke ba Fanan ɗin ba laifi kuma maganin da take amfani dashi yana mata aiki don tana cin abinci, bayan hutun Fatuu ya ƙare tace ma Haisam ko yayi ma Mom magana a turo Iya ta dawo nan gidan tunda ita dattijuwa ce zata taimaka ma Fanan ɗin sosae yace Ok, koda akai ma Mom magana cewa tayi lafiya lou sai ta dawo nan ɗin, ana washe gari Fatuu zata tafi Iya ɗin ta dawo nan gidan hakan ya ƙara kwantar ma da Fatuu hankali da tana ta zullumin tafiya ta barta duk da suna da masu aiki har biyu amman tafi son ace akwae wani babba na jiki a tare da ita hakanne ma yasa tayi tunanin a maido Iya ɗin nan. Kwance tashi cikin Fanan ɗin har ya fito kuma bata wani laulayi sosae don har ta koma aiki, lokacin da cikin ya kai wata takwas ne aka tabbatar da in aka bari ta haihu da kanta zata iya samun matsala don haka aka yanke yi mata Cs in ya kai wata tara, Hajiya Maryam na jin haka tace zata fitar da ita waje kawai ta haihu a can amman Fanan ɗin taƙi amincewa tace ko taje can duk abu ɗaya ne don anyi mata bayanin matsalar da ake hasashe ta kuma gamsu da hakan don saida aka yi mata duk binciken daya dace kafin a tabbatar kuma likitan da yayi mata binciken ƙwararre ne kuma shima da a ƙasar wajen yake aiki wato likitansu mai aiki Germany dole Hajiya Maryam ta ƙyale ta, bayan cikin ya shiga wata na tara kafin zuwa ranar da za'ayi su Fatuu duk cikin zullumi suke duk da Fanan ɗin lafiyarta lou, ana gobe za'ayi aikin ranar ta kama lahadi amman Fatuu bata iya ta koma Zaria ba, gaba ɗaya duk sun shiga damuwa suna ta Addu'oi a ranar kusan raba dare Fatuu da Haisam sukai suna nafilfilin roƙon Allah yasa ayi aikin lafiya itama Fanan ɗin ta yi ma kanta Addu'oin, har su twins Fatuu ta tada sukai Nafila suma sukai mata Addu'a, Washe gari Monday su Esha ƙin zuwa Makaranta sukai saboda aikin da za'ayi ma Mommynsu, misalin ƙarfe goma na safe aka shiga da ita aikin Fatuu harda ƙwallarta haka su Esha sauran yan'uwa ma duk suna a asibitin anata fatan nasara, Hajiya Maryam dai har bata iya magana saboda fargaba sai Addu'o'i take a cikin ranta, bayan an shiga da ita a Office ɗin Doctor ɗin wanda yake mai girma ne akwae kuma kujeru suka zazzauna kowa yayi jigum, bayan kamar minti arba'in da biyar da shiga aikin Doctor Taj wanda shine likitansu na Germany kuma shine yayi aikin ya shigo cikin office ɗin ai suna ganinshi duk suka mimmiƙe kusan gaba ɗaya suka haɗa baki wurin tambayarshi yadda ake ciki yana murmushi yace anyi aikin cikin nasara an fiddo mata da Baby Boy, zo kaga murna Haisam da Fatuu da Hajiya Maryam a tare suka duƙa sukai sujjada su Esha na ganin sun yi suma duk suka yi haka ma Farha da Jidderh, tura baki Esha tayi bayan ta gama yin sujjadar tace miyasa Momy ta haiho Baby Boy ita Baby Girl take so ta samu ƙanwa duk akai dariya akace tayi haƙuri in zata ƙara haihuwa in sha Allah zata haiho mata Baby Girl ɗin, Aunty ce ta kawo masu Babyn wanda ina gani na furta Ma sha Allah saboda tsananin kyaun shi sak Haisam ya biyo hakan yasa yay kama da yan biyun Fatuu sosae, sam bakunansu sun kasa rufuwa sai faman kar6a kar6ar Babyn ake, a ɗaki na musamman dake Amenity aka kwantar da Fanan din duk yan uwa sun cika shi itama Fanan ɗin idonta biyu tana amsa ya jiki da barkar da ake mata fuskarta ɗauke da murmushi, zuwa yamma duk yan'uwan da abokan arzuƙi anata zuwa dubata sai yaba Babyn ake, wuraren ƙarfe biyar Dad ɗinsu Haisam yazo tare da muƙarrabanshi suka dubata tare da yi ma Baby addu'a, kwananta biyu a Asibitin kafin aka sallameta suka koma gida, a ranar da suka koma da daddare lokacin su Esha sunyi bacci Fatuu ma ta koma part ɗinta sai Fanan ɗin tare da Iya babyn kuma na kwance cikin net yana bacci Haisam ya shigo jikinshi sanye da jallabiya, bayan sun gaisa da Iya ta miƙe don ta basu wuri, murmushi suka shiga sakar ma juna ya tambayi ya jikinta tace da sauki sosae ya jinjina kai kafin yace Allah ya ƙara mata lafiya ta amsa da Amin tay mashi godiya, juyawa yay yana kallon babyn ta cikin net ganin haka tace ko ta fiddo mashi shi ya girgiza mata kai alamar a'a, kallonta yay ya tambayi wane suna take son a saka mashi ne tace ai tayi zaton ma ya riga ya saka mashi suna ya ɗan girgiza mata kai kafin yace ya bari a sallameta sai ta za6ar mashi sunan da take so, shiru ta ɗanyi tana murmushi can tace mashi sunanshi take son a saka mashi wato Haisam, ɗan buɗa ido yay yana murmushi yace yayi tunanin zata saka mashi sunan Dad ɗinta ne tay shiru kafin tace "nafi son a saka mashi sunan ka Babe" ɗage mata gira yay ya tambayi saboda mi, "Saboda ni a wurina sunan yafi kowane suna muhimmaci kuma shine sunan da ya cancanta a saka mashi, kayi man abubuwan alkhairi da yawa Babe, ka aure ni don ka faranta man sannan ka zauna dani tsawon lokaci ba tare dana haihu ba kuma daidai da rana ɗaya baka ta6a nuna man damuwarka ba ko kayi man wulaƙanci kaine ma kake ƙarfafa man gwuiwa kan hakan, kuma nasan ba don Allah ya ƙaddaro aure tsakaninka da Zarah ba na tabbatar zaka iya rayuwa dani a haka ba tare da ka ƙara aure ba kawai don farinciki na, kai na daban ne Babe, I know I can never repay you for everything you have done for me, amman ina son ka sani Babe ina son ka da kowanne bugun zuciyana sannan ina mai godiya a gareka mara iyaka Allah ya bar mu tare har abada, ina roƙon Allah ubangiji ya ƙara inganta rayuwar ka Babe ya dawwamar da kai a cikin farinciki ya saka maka da gidan aljanna maɗaukakiya..." ƙwallan da suka tarun mata a idanu ne suka fara zubowa tasa hannu tana gogewa, matsawa yay gabanta da yake a kishingiɗe take saboda aikin da aka mata ya kai hannu yana goge mata ƙwallan cikin cool voice ɗinshi yace mata ya isa haka shima yana matuƙar alfahari da ita sannan yana farinciki da Allah ya bata lafiya har ta haihu yayi Addu'ar Allah ya raya masu shi da sauran yaransu ta amsa da Amin ya Rabbi. Saboda aikin da aka mata yasa aka ɗaga yin taron suna sai bayan sati biyu ita Fanan ɗin ma cewa tayi a bar taron ba sai anyi ba amman kowa ya nuna yana so, gaba ɗaya satin Fatuu bata samu komawa Zaria ba tana gida sunata zaman jego sai ranar lahadi ta tafi, hidima ba yar kaɗan ba Hajiya Maryam tayi ma jaririn don shima saida tayi mashi dozin ɗin akwatunan kaya sannan tayi ma Fanan kayan fitar suna ciki harda wata danƙareriyar sarƙar zinari ta miliyoyin kuɗi hatta Haisam da Fatuu ma saida tayi masu kayan fitar suna haka su twins ma tayi masu kayan fitar sunan sannan kowannen su ta siya mashi abunda yace yana so a Asibiti hatta Abie ta siyo mashi robobin ba yaro ruwa masu tsananin kyau yan ƙasar waje da zasu kai goma sannan Fatuu ma tasa an kawo mata Motar data bata itama mai jegon ta canza mata tsadaddiyar Mota, kowa yaji daɗin abunda tayi duk da haka kuma Haisam ma saida yayi masu kayan fitar sunan shima, waɗannan kayan fitar sunan dai ban tunanin za'a iya saka su gaba ɗaya ranar sunan don sunyi masu yawa, Ranar Alhamis Fatuu ta dawo nan suka shiga hidiman sunan da za'a yi ran Asabar a maimakon ranar litinin saboda ranar ta kama ta aiki duk mutane suna zuwa wurin aiki, Washe gari Juma'a su Gwaggo suka iso da Haulat da Husnah harda Aunty Mareeya da Feenah sosae Fanan da Fatuu suka ji daɗin zuwan nasu, a daren ranar sunan aka kira Haisam a waya cewa saƙon shanu daga Yola ya iso wanda Baffan Fatuu ne ya aiko mashi dashi a yanka ma yaro, har Fatuu bata san da aiken ba saida Haisam ya kirata a waya ya sanar mata aiko taji daɗin hakan da yayi sosae, Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar suna hidima ta kankama ba kama hannun yaro, a ranar da safe sai ga su Yadikko da Yaya da Mairo sun iso harda dawon furarsu mai uban yawa da kuma Nono sai zuma da ƙwai masu yawan gaske, zo kaga murna wurin su Aysha da Mino anga Mahaifiya, bayan sallar azahar gida ya fara cika da yan suna mai jego da Fatuu da kuma yaransu suna ta cin uban gayu, zuwa sallar la'asar taro yayi taro malam hidima data amsa hidiman manyan masu kuɗi ake har bansan ma ta yadda zan bayyana yadda hidiman ke wakana ba don abun na neman fin ƙarfin al'ƙalamina kawai sai na koma yar kallo, ina cikin kallon manyan Hajiyoyin Abuja dake ta zuwa kwatsam sai ga Hajiya Kubra wato Momy ta iso a Motarta harda iyalanta suma sun zo suna, ina hangota cikin Washe baki na nufeta muka gaisa nace ashe zata zo sunan cikin fara'ar ta tace man ai ita tana yin Fanan sosae dama tana cikin wanda suka damu da halin rashin haihuwarta lokacin data ji labarin haihuwar sosae tayi farinciki ta kuma yi godiya ga Allah dama ance shi maharƙuci tabbas mawadaci ne nace wannan gaskiya ne Momy Allah ya ƙara mana haƙuri da kuma dangana ta amsa da Amin kafin suka shiga ciki ni kuma naci gaba da baza idanu ina ganin danƙara ɗanƙaran, jibga jibgan Motoci masu numfashi dake ta sawo kai cikin harabar yayin da wasu kuma ke tafiya, a taƙaice dai Abuja ce ta haɗu a gidan Haisam don First lady na nan da sauran matan muƙarraban shugaban ƙasa. Alhamdulillah taro ya tashi lafiya yaro yaci sunan Haisam suna ce mashi Junior, an ci an sha anyi wadaƙa da nishaɗi sannan an raba kayan suna masu ɗauke da sunan Baby kawai ba'a saka hoton shi ba, a bangaren maijego Fanan ta samu kayan suna kai kace zata buɗe ƙaton shago ne ita kanta saida tayi mamakin kayan da aka tara mata, a daren ranar su Fatuu da Farha harda Aunty Mareeya suka shirya kayan kafin su kwanta, Washe gari Lahadi yan Katsina da Yola suka koma duk an cikasu da abubuwan arzuƙi, haka sauran yan'uwan su Haisam yan Katsina da Daura da suka sauka a Villa duk suma sun tafi, Fatuu ma taso tafiya Zaria a ranar saidai da sauran abubuwan da zatayi a gidan dole ta bari sai gobe da sassafe sai ta koma, kusan raba kayan da Fanan ta samu nata tayi taba Fatuu duk yadda taso taƙi kar6a Fanan ɗin ta kafe, har rage kayan tayi ta maida mata wasu amman taƙi kar6a ƙarshe ma sai ta nuna mata 6acin ranta sosae hakan yasa dole ta amsa tayi mata godiya da kuma Addu'oi. *BAYAN SHEKARU BIYAR* Abubuwa da yawa sun faru a cikin waɗannan shekarun daga ciki abu na farko daya faru shine saukar President Ali Adamu daga kujerar mulki tuni kuma wata sabuwar gwamnatin ta hau, a lokacin daya sauka al'umma sunyi kukan rashin jajirtacce kuma nagartaccen shugaban ƙasa, bayan saukar shi Katsina suka koma da zama a gidansu dake G.r.a a lokacin tsohuwa mai ran ƙarfe wato Hajiyar sanata ta koma gidanta da zama saidai bana dundun dundun bane zo kaga murna a wurin yan unguwa karma Tk yaji, Saude da har zata dawo Hajiyar ta hana tace ai ba daɗewa zatayi ba tunda ga matar tukur nan lafiya lou tayi zamanta a ɗakin mijinta, shekara guda sukai a Katsina kafin suka koma Abuja. Bayan saukar shi da shekara ɗaya Fatuu kuma ta gama karatunta cikin nasara har ta fara aiki bayan shekaru biyu da fara yin aikin nata ne ta ƙara haihuwar yan biyu duk mata an saka masu Khadija da kuma Fateema wato sunan Gwaggo da kuma Mom ɗin su Haisam, Esha tayi murna kamar kamar me da samun ƙanne mata, a lokacin wasu sun ƙara haihu wasu kuma nada ciki, a cikin wanda suka ƙara haihuwa harda Jidderh da kuma Fauzy ta ƙara haihuwar Namiji an saka mashi sunan mahaifin Sameer wato Bello, Aysha ma ƙanwar Mino a lokacin tayi haihuwarta ta farko ta haiho Baby girl an saka mata sunan Yadikko wato Jameela, Mino dai har lokacin bata ƙara haihuwa ba don tace ba yanzu ba bata manta kwakwar data ci ba ansamu dai ta amince zata ƙara yaronta yanzu shekararshi shidda, Farha ma ta ƙara haiho Namiji an saka mashi sunan Mahaifinsu wato Muhammad, Haulat ma ta ƙara haihuwar Namiji an saka mashi sunan mahaifinta wato ishaq, a bangaren Fanan kuwa ita bata ƙara samun cikin ba tun bayan Haisam Junior wanda yanzu shekararshi biyar da yan watanni, duk a cikin lokacin akai ma wasu aure ciki harda Yasmeen ƙanwarsu Haisam ta auri yaron Yayan Mahaifiyarta na Qatar mai suna Abdurrahman suna zaune a can ƙasar haka ƙanin Sameer wato Ashraf shi kuma ya auri Jahad itama ɗiyar yayansu ɗin na Qatar suna a Abuja zaune burin su Mom ya cika na son haɗa yaransu auren zumunci. A bangaren Haisam kuwa tuni Kamfaninshi ya ƙara ha6aka sosae yanzu ana ƙera wasu abubuwan ba iya kwamfutoci ba yanzu harda su Tv da kuma wayoyi, a lokacin arzuƙin shi ya ƙaru sosae don har ya ƙara buɗe wasu rassa na Kamfaninshi a Lagos, PortHarcourt, Kano da kuma Sokoto yana da kuma burin ƙara buɗewa a wasu States ɗin in Allah ya yarda, a yanzu Haisam ya zama Billionaire wanda yana ɗaya daga cikin Manyan masu kuɗin ƙasa don har private jet ya mallaka wato jirgin kanshi wanda ake hidimar iyalinshi da kuma Kamfanoninshi, daga baya aka fara yin hayar jirgin ganin akwae riba yasa Haisam ɗin yayi ma Dad dinshi Magana kan su haɗa su sayi wani jirgin na haya ya amince da hakan koda Sameer yaji zancen siyan jirgin hayar shima sai ya nuna yana ra'ayin saka hannun jari haka Hajiya Maryam ma dama duk suna da hannayen jari a Kamfanin shi na Technology, daga baya suka buɗe kamfanin sufurin jirage mai suna HaiFat Air wanda a yanzu suke da jirage guda ukku biyu manya wanda har yan Hajji ake kaiwa dasu sai ɗaya ƙarami wato private jet suma jiragen suna niyyar ƙara wasu da yardar Allah, A cikin shekaru biyar ɗin nan a duk shekara Haisam sai ya kai wasu a cikin dangi Makka, a shekarar farko daya fara kai mutane makka ne yace ma Fatuu ta bada mutum biyu cikin danginta ta bada sunan Gwaggo da kuma Kawu Amadu su Gwaggo za'a sake sauke farali sosae tayi farinciki, Hajiya na jin zancen tafiyar Amadu Hajji itama ta biya ma Tukur wato Tk Har Haisam yace ta bari shekara mai zuwa zai biya mashi tace ai shida Amadu kamar yan biyu suke bai ga ko aure tare sukai ba ya bari ta biya mashi ai duk ɗaya ne, da wata shekara ta zagayo ya sake cewa ta bada mutum biyu sai ta bada Yaya da kuma kishiyarta Mairo sannan ita kuma da kuɗinta ta biya ma Aminiyarta Haulat, da rabon dai Fatuu ita zata kai Yaya Makka a lokacin ƙurucyarta ta ta6a ce ma Haisam in ta girma tayi kuɗi zata kai kowa Makka amman banda Yaya saboda ta tsaneta har yayi mata Nasiha kan muhimmancin yafiya, Sosae su Mero sukai farincikin biya masu Makka saidai ita Yaya akwae abunda ke damunta a cikin rai shine hakkin Mahaifiyar Baffan su Fatuu dake a kanta don tun Maganar da Mero ta ta6a yi mata a Abuja kan hakan bata manta ba, ƙarshe samun Mairo tayi ɗakinta cike da damuwa tace mata ita tana tsoron taje tayi aikin Hajjin Allah yaƙi kar6a saboda hakkin A'isha dake kanta, shawara Mairo ta bata kan taje ta samu Baffansu Fatuu ta roƙe shi yafiya ta roƙeta kan ta rakata, tare suka iske Mahaifinsu Fatuu a bangarenshi wanda yanzu ya koma babban falo da Bedroom da suka sha kayan alatu don Haisam ya bashi kuɗi masu yawa Fatuu ma ta ƙara mashi an gyara part ɗin nasu ya koma babban Flat saida aka ƙara faɗaɗa shi, sauran bangarorin ma anyi gyare gyare don yanzu gaba ɗayan tsakar gidan siminti ne ko ina sannan an zagaye gidan da katangar bulon siminti haka gaban gidan ma ya koma irin na yan birni harda gate, fadar da Baffa ke zama itama ta koma irin ta zamani, bayan sun zauna anyi gaishe gaishe shiru Yaya tayi ta rasa ta ina zata fara sai Mairo ce ta fara magana tace mashi dama Yaya ce tazo neman yafiya a wurinshi kan abubuwan da suka faru a baya ta juya kan Yaya tace tayi magana, cikin karyayyar murya ta shiga roƙonshi akan abubuwan data yi masu a baya ta bayyana mashi ta zalunci mahaifiyarshi don ita tayi mata asiri duk gidan aka tsaneta harda arɗo wannan ne yay silar ta kamu da ciwon zuciya har ta mutu haka shima tay ta zaluntar shi bayan rasuwarta ganin arɗo ya damu dashi shima tayi mashi asiri ya daina ji da shi sai bayan daya girma ne da yake shi mai yawan ibada ne sosae sai ya zama ko tayi asirin bai kamashi hakan yasa soyyyarshi ta dawo ma arɗo sai kuma ta rinƙa yi mashi makirci haka iyalinshi ma ta ɗauki karan tsana ta ɗaura masu, shiru Baffa yayi kan shi a ƙasa yayinda ƙwaƙwalwarshi ta shiga dawo mashi da lokacin don bazai ta6a mantawa da irin rayuwar ƙuncin da mahaifiyarshi tayi ba a gidan lokacin yanada ƙuruciya har zuwa mutuwarta lokacin haka ya rinƙa kuka yana roƙon shima Allah yasa ya mutu ya bita, kawai saboda yana da haƙuri sosae da kuma kawaici irin na fulani yasa bai nuna masu komai amman ba wai don ya manta ba, saukkowa Yaya tayi kan carpet ta duƙa cikin kuka ta shiga bashi haƙuri tana mashi magiyar ya yafe mata, Mairo ce da idanunta suka ciko da ƙwalla cikin kwantar da murya ta shiga roƙonshi ya yafe mata Don Allah duk irin abunda tayi mashi gashi nan bai hana rayuwarshi yin albarka ba ƙarshe ma gaba ɗayansu sun koma karkashin kulawarshi yayi koyi da mai sunan shi wato manzon Allah (S.A.W) wanda haƙuri da yafiya halin shi ne, ɗagowa yay idanunshi sun yi ja sun cika da ƙwalla cikin karyayyar murya yace shikenan ya yafe mata sai taita istigfari ta roƙi Allah ya yafe mata abunda tayi ma Mahaifiyar shi, godiya sosae ta shiga yi mashi fuska jage jage harda su majina ta shiga yi ma Mahaifiyar tashi Addu'o'i a hankali yake amsawa daga baya suka tafi, bayan tafiyarsu kuka sosae ya shiga yi yana tunawa da mahaifiyarshi tare da yi mata Addu'a, bayan Yaya ta koma ɗaki saida ta kira Fatuu a waya itama ta roƙeta yafiya kan abubuwan da tayi mata na tsanarta da tayi tana murmushi tace mata ba komai ai ya riga ya wuce ta yafe mata taita mata godiya da Addu'oi, sai lokacin Yaya taji hankalinta ya ɗan kwanta da tafiya Hajjin da zatayi tun daga ranar kullum da cazhaba zaka ganta tana ta istigfari. Ta dalilin Fatuu yanzu yan ƙauyansu suna karatun boko sosae, a gidansu ma an daina yi ma mata auren wuri sai sunyi boko har Abuja yan'uwan nasu suke zuwa hutu wurinsu inda rabo ƙilan wasu su ƙara samun mazaje a can. A can Katsina yanzu Foundation ɗin su Fatuu ya ha6aka sosae anata taimakon mutane yanzu a unguwarsu Gwaggo ita ta koma matsayin Hajiyar Sanata sosae take taimakon Makwabtanta, rayuwa dai ta inganta ga dukkan bangarorin. Ta dalilin Addu'oin da wanda Haisam ke kaiwa Hajji ke mashi sosae hakan yake ƙara ha6aka arzukin shi wanda yanzu shi kanshi Haisam ɗin bai sai iya adadin dukiyarshi ba har gida ya gina ma Abbas ya kuma kaishi Makka harda Feenah sannan ya ɗauki nauyin karatun Abdul wanda yanzu ya girma, a bangaren Aunty Mareeya itama Sameer ya gina masu babban gida har sun koma kuma duk sunje Hajji suma. Bayan wani lokaci Haisam yasa aka fara gina ma su Fatuu Asibiti anan Abuja wato private Hospital ita da Fanan wanda aka yanke saka mashi HAIFAT SPECIALISTS HOSPITAL sai fatan Allah yasa a gama lafiya a kuma buɗeshi lafiya yasa kuma mutane su amfana, Amin. Fatuu zaune a gaban madubi da daddare tana yin shafa bayan ta fito daga wanka yayin da Haisam ke zaune a saman gadonta ya ɗaura Laptop a saman table ɗin gaban gado yana daddanawa da alama wani aikin yake jikinshi sanye da robe haka idanunshi na sanye cikin glass ya ƙara manyanta saidai duk da haka ba sosae jikinshi ya nuna ba saboda har yanzu yana motsa jiki sosae, kamar an jefo Esha ta faɗo cikin ɗakin tana ƙwala ma Fatuu kira tana faɗin "Auntyyy!" itama yanzu ta ƙara girma don tana shekara ta sha huɗu duk da bata da tsawo sosae sak irin jikin Fatuu tana yarinya gareta, "Esha! Wai sai yaushe zaki hankali ne, didn't i warn you to always say salaam before entering into a place???" a fusace Fatuu tay mata Maganar ta ɗaure fuska, tura baki Esha ɗin tayi tana ɗan murmushi tare da noƙe kai tace "to Sorry Aunty mantawa nike bari inje inyi salaam ɗin" tayi maganar tare da juyawa ta nufi kopa, bayan ta fita daddagewa tayi ta kwaɗa wata uwar sallama har saida Haisam ya ɗan yamutsa fuska Fatuu kuma ta girgiza kai kafin tace wani abu Esha ɗin ta ƙara kware baki ta rafko wato sallamar tare da faɗin "Aunty in shigo???" ba arzuƙi gudun ta sake yin wata da sauri Fatun tace mata ta shigo, shigowa tayi tana dariya Fatuu ta wurga mata harara, bayan tazo gabanta tace mata miya kawota ɗakinta yanzu cikin zazzaƙar muryarta tace "Momy ce tace ki bata charger ɗin phone en ki in baki using dashi mun shanye mata caji zata saka nata ya ƙiya kafin tomorrow Dad ya kawo mata wani" yadda kasan abun faɗa yadda tayi Maganar, maida kanta tayi kan madubi tana cigaba da shafar ta tace mata gata can jikin socket wurin bedside drawer taje ta ɗauka, maimakon taje ta ɗaukan sai ta tsaya tana kallon fuskar Fatun ta cikin madubi tana wani murmushi tace "Aunty Daddy kike ma makeup?" dakatawa Fatuu tay ta watsa mata harara, dariya Esha ɗin tayi tace "ai nasan Dad kike mawa don ke Babynshi ce....." tsawa Fatun ta daka mata "Esha! Will you go and take the charger ko zaki tsaya kina surutun banza ne!!" da sauri ta wuce tana dariya, tana zuwa saitin Haisam ta furta "My lovely Dad" dagowa yay ya kalleta yay mata murmushi tare da miƙa mata hannu suka kashe yace taje ta ɗauki charger din ana jiranta tace to, bayan ta ɗauko cazar ta nufi hanyar fita, har ta kusa fita ta tsaya da ƙarfi ta furta "Babyn Daddy kin yi kyau...." robar mai Fatuu ta wawuro Esha na ganin haka ta fice da gudu tana dariya, tsoki Fatuu tayi tare da girgiza kai idonta akan madubi ta furta "i think Aisha needs to see a psychiatrist gaskiya" murmushi Haisam yay ba tare daya kalleta ba can idonshi akan screen ɗin kwamfuta yace mata saboda mi, juyawa tay da sauri ta kalleshi tace "baka ga yadda take behaving abnormal bane, wataƙil in aka kaita aka binciki ƙwalwarta aga tana da problem", "An yi maki hakan ne?" Haisam daya ɗago yana kallonta ya furta, da alamun rashin fahimta tace to ita akan mi za'a kaita wurin likitan kwakwalwa, yana murmushi yace saboda da tana kamarta itama tana buƙatar hakan amman ba'a kaita ba to don haka itama ba sai an kaita ba zata bari ne kuma in ma tana tunanin tana da matsalar kwakwalwa to ita tata matsalar da tana yarinya ta linka tata tunda ita Esha har yanzu bata fasa ma wani glass ɗin Mota ba, waro ido Fatuu tay jin abunda yace ta bishi da kallon mamaki bakinta a ɗan buɗe shi kuma sai murmushi yake, da alamun mamaki ta furta "kana son kace nayi hauka lokacin?" ɗan ƙanƙance ido yay cike da tsokana ya furta kusan hakane, ƙara zaro ido tay ya shiga yi mata faffaɗan murmushi can ta miƙe a fusace ta nufe shi, lokacin data tashi har saida alƙalamina ya kusa su6ucewa ganin irin haɗaɗɗar rigar baccin dake jikinta gaba ɗaya ta fito da dirinta na babbar mace yar 30s tana tafiya ko ina na jikinta na amsawa abun saidai ace tubarkalla, tana zuwa gaba ɗaya ta faɗa jikinshi har saida yay ɗan sautin zafi batai wata wata ba ta hau bugunshi saidai bugun yafi kama da a kirashi dana soyayya, haƙuri ya fara bata yanata dariya har haƙuranshi sun bayyana cike da shagwa6a data riga ta zame mata jiki ta shiga faɗin Allah bata yin haƙurin tunda ya kirata da mahaukaciya yana ta dariya yace shifa bai ce mata haka ba itace ta kira kanta da haka, cigaba da bugun nashi tayi tana faɗin ai haka yake nufi ko yace to tayi haƙuri taga ƙopa a buɗe take amman taƙi bari aikuwa ya nuna mata ƙarfi ya burkice da ita ta yadda ko ƙwaƙkwaran motsi bata iya yi, ɗaure mata fuska yay yace tunda abun yar haka ce ya bata haƙuri taƙi to shima ya warware yarjejeniyar dake tsakaninsu ta glass, tana ɗan nishin nauyi tayi murmushi tace ai yanzu ba wannan yarjejeniyar tunda tayi abunda yace a lokacin, fuskarshi a daure yace shi ba ruwan shi sai ta biya shi, ɗage mashi gira tayi tace in don dai miliyan goma yanzun nan zata biya shi ya ɗaga ta, girgiza mata kai yay yace ba kuɗi yake so ba ta kanne mashi ido tace to mi yake so, ce mata yay yara zata haifa mashi yawan hakan yanzu tayi biyar saura biyar kuma a lokaci ɗaya yake son ta haiho mashi yan biyar, bata san lokacin data ƙyalƙyace da dariya ba tace kawai yace mata ya gaji da ita so yake ta mutu in ba haka ba taya zata haifi yara har biyar, still fuskar shi a ɗaure take yace ai ana haihuwan har ma fin hakan tana dariya tace ta sani amman ita dai bata iyawa yayi haƙuri yace bazai yi ba sai ta ƙara mashi yara biyar lokaci guda, lumshe mashi ido tay tace yafi ƙarfin hakan a wurinta don haka indai ya bata yara biyar ɗin to zatayi ƙoƙari ta haifa mashi, jin abunda tace yasashi sakin murmushi itama shi take mashi ya mirgina gefenta suka shiga bin juna da wani irin azababben kallo mai cike da tsagwaron ƙauna can Fatun ta saki yar ajiyar zuciya ta fara magana, "Thank you Hubby, Thank you for your support and guidance. You didn't just change my life, you became a part of it and loved me unconditionally. You have shown me what true is.Thank you for choosing me to be your life partner. You are truly my best friend and my soulmate, and I couldn't imagine my life without you. Thank you from the bottom of my heart for everything that you have done for me......" ( Nagode Hubby, Nagode da taimakon ka da jagorancinka a gare ni, ba wai kawai ka canza rayuwata ba, ka zama wani bangare a cikinta kuma ka so ni so mara iyaka, ka nuna man mene ne soyayya ta gaskiya. Na gode da za6ata a matsayin abokiyar rayuwarka. Haƙika kai ne babban abokina kuma abokin ruhina sannan bana iya tunanin rayuwa ba tare da kai ba, Ina mai matuƙar godiya a gareka daga can ƙasan zuciyata akan duk abin da ka yi min....." muryarta ce ta karye hawaye suka shiga gangaro mata, matsar da fuskarshi yay saitin tata ya shiga kissing hawayen kafin can ƙasan maƙoshi yace shima yana godiya a gareta sosae data saka shi yake jin yafi kowane namiji sa'ar mata a duniya, haɗe fuskokinsu yay inhaling each others breathe, ganin yana ƙoƙarin hade lips ɗinsu da sauri ta ankarar dashi ƙopa a buɗe take hakan ya sashi dakatawa, saukkowa yay don yaje ya rufe a lokacin nima naga ya dace na bar masu cikin ɗakin. *Alhamdulillah!* *Alhamdulillah!!* *Alhamdulillah!!!💃💃💃💃💃💃💃* *A nan na kawo karshen littafin A Sanadin Makwabtaka wanda na ɗau lokaci ina rubutawa😍* _Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala, the Most Compassionate, the Most Omnipotent and the Most Omniscient da ya bani ikon kammalawa cikin ƙoshin lpy kamar yadda na fara, to him be all the glory🙏, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi muhammad(S.A.W) da Ahalinsa da Sahabbansa baki ɗaya😍, Darussan dake ciki Allah ubangiji yasa mu amfana dasu🙏 ya sadar da ladan gareni da mahaifana da zuri'ata, yan'uwana da malamai na, kura kuren ciki ina roƙon Allah ubangiji ya yafe man Alfamar Annabin rahama (S.A.W)🙏_ _Gaisuwar ban girma ga Mahaifiyata Hajiya Rabi'atu Yahaya, she is my first luv and my everything💘,Allah ya ja da rai ya ƙara maki lafiya my sweetheart😘, My beloved Siblings💞waɗanda littafin nan Sadaukarwa ne a garesu, Nafisat, Aisha, Khadija, Maimunatu, Hafsat, Abdul'azeez, Fatima, Maryam, Ameenatu, I luv you so so much, kune ni, in baku bani, I really appreaciate ur Encouragement💪,prayers and all-round support👍, Allah ya kara haɗa kawunanmu ya jiƙan Mahaifinmu, Ameen_ _Gratitude To my Sweetheart😍, who is ever glad at every inch of my progress, I really appreaciate ur Support, Encouragement and prayers, Allah ya bar mu tare ya ƙara daukaka, Amin_. _Special thanks to My lovely Sis Hafsat Bature Writer Of Abban Sojoji and Kurkukun Ƙaddara na gode da ƙarfafa man Gwuiwa Allah ya baki ikon Kammala naki cikin ƙoshin Lafiya yasa ya amfani al'umma Amin, Abubakar Sadeeq AlQuramy, Uncle Isma'il ina matuƙar godiya a gareku da taimakon da kuka bani Allah ya ƙara taimakon ku a dukkan Al'amuran rayuwar ku🙏, My P.A Munah Bature sannu da ƙokari Allah ya ƙara ma rayuwar ki Albarka ya kawo miji nagari Amin, ina matuƙar godiya agareki😘_ *To My Novel's Fans* *Ina matuƙar godiya a gareku musamman waɗanda suka saka kuɗin su suka sayi littafin nan ina roƙon Allah ya ƙara arzuƙi yasa ku amfana da littafin, Members Of Comment Section na gode da ƙaunarku da uzurinku a gareni kamar su, Asma'u sani, Asma'u Kebbi, Bajatu, Bahillot, Dr Hamida Gandi, Mrs Mu'utassim, Sofix, Minat Sgy, Shafa Adill, Zeefakhad Collecion, MaryamSalisu, Rababs222, Angel love, A'isha Abdurrahman, Fadeelamande, Queen, Shafar Dauran, Aunty wasee, Amina Sulaiman, Habibty, Aunty Hadiza, Aunty Sa'adatu, Salma Nijar, Fatima Fannami, Hauwaabubakar, First Lady, Maman Amir, Ummulkhairi Nijar, Satheyer, Maman Naeem, Deejarh da sauran waɗanda bansamu na lissafo sunayensu ba, ina sane daku, ina matuƙar godiya a gareku ur comment means a lot to me, bansan da wane kalmomi zanyi amfani wurin gode maku ba, sai dae ince Allah ya barmu tare don ku ɗin kun wuce fans kun zama yan'uwa agareni,* *Ina Gwanar wata ga tawa💃😍 Jinjina a gareki Hajiya Kubrah (Momy) Mace mai irin halin Hajiyar Sanata, Allah ya ƙaro mana irin ku acikin al'umma, har bansan da wane irin kalmomi zanyi godiya a gareki ba sai dai kawai ince Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya raya maki zuriya ya ƙara danƙon kauna keda Oga yasa afi haka ya kuma sa a gama da Duniyar nan lafiya, ya bar mana zumunci daga nan har Aljanna, Amin ya Hayyu ya Ƙayyum🙏* *Ban mance da irin gudunmawar da kika bani ba Miss Walida Ɗanwaire Fulanin Yola ina matuƙar Godiya a gareki Allah ya barki da Oga ya raya Baby Maryam, Maman Afra kema ban mance da irin taki gudunmawar ba ina miƙo godiya lodi lodi Allah ya raya zuri'a ya bar ƙauna keda Oga, ya jiƙan Habiba (Ummy), Amin ya Rabbi, haka ban mance da taki gudunmawar ba wato Nabila Yar Gata Fulanin Daura kema Allah ya bar ƙauna keda Oga ya baku zuriya ɗayyiba* *Allah Ya bar mana zumunci daga nan har Gidan Aljanna, Allah Yabiya maku dukkan buƙatunku, Allah ya baku ikon Yin amfani da darussan dake acikin Labarin nan, Ina matuƙar godiya Da irin haƙurin da kuka yi da kuma uzirin da kukayi mun har Allah ya bani Ikon Kammala Littafin nan, Yanzu gashi komai Ya wuce no more kiran ayi man uzuri, lols😂* *Littafin nan Ya ƙunshi darussa daban daban Na rayuwa,Ya ilmantar,Ya faɗakar,Ya kuma nishaɗantar, Manyan darussan cikin shi sune Muhimmacin Haƙuri da kuma Taimako wanda gaba ɗaya labarin ya ginu ne akan hakan💃💃💃*    *Taku Mai ƙaunarku da zuciya ɗaya, ZAINAB BATURE (Zee Laluh/Oum Imam).* *Ga mai buƙatar wannan littafin Complete tun daga na ɗaya har zuwa na ukku sai ya tuntu6i ɗaya daga cikin waɗannan lambobin wayar, 09013804524 ko 08169856268.