[12/24/2019, 17:56] Takori: RAYUWAR RAYHANAH! 1 Garin TAKAI, karamar hukuma ce dake cikin birnin Kano, galibin jama’ar Takai Fulani ne da Hausawa farare da bakake, duk inda bahaushe da bafillace suke babbar sana’arsu Noma da Kiwo, manoma da makiyaya sune kashi tamanin cikin dari na jama’ar garin. Kowa ya san jama’ar Takai ya san su da hadin kai da taimakon junan su, rashin son zaman banza, sana’o’in dogaro da kai musamman saye da sayarwa na abinda suka noma da karfin su ko suka kiwata. Kowa a garin Takai kokarin neman na kansa yake babu wanda ya dogara da wani ba ga mazan kadai ba har matan manya da yara, tsofaffi, ‘yammata, da samari da wuya kasamu wanda baida sana’a, domin neman rufin asirinsa da iyayen sa ko iyalinsa. Kasuwar Takai tana ci ne ranar Talata. Don haka kamar kowacce Talatar, Malam Rashidu, yana nan bakin kasuwa ya baza hajarsa kwano-kwano cike da dankalin Hausa (Sweet Potatoe). Tun karfe goma na safe har zuwa yanzu karfe biyu na rana babu wanda ya zo inda yake balle yataya dankalinsa. Malam Rashidu yana zaune ne akan shimfidar buhun sa a tsakiyar rana shi da dankalin nasa ko lema babu, ya hada kai da gwiwa kamar zai fashe da kuka, idanuwansa duk sun zurma ciki sabida yunwa da damuwa. Babban tashin hankalin sa rashin sanin me zai baiwa diyarsa Rahane ta biya kudin makarantar da aka koro ta jiya akan bata biya ba. Rashin abin da zai basu su ci a yau bai daga hankalinsa ba kamar rashin kudin makarantar nan wanda yake janyowa tilon diyarshi a duniya koma-baya a makaranta, ba don rashin kokari ba, a’a, illa yawan fashi adalilin yawan korarta da ake yi na tsayin satittika a kan rashin biyan kudin makarantar nan. Wasa-wasa har karfe hudu yana nan zaune babu ciniki ko na kwandala. Ya mike ya fara sallar la’asar akan buhunsa da ya shimfida, dai-dai lokacin da wata mota Akori-kura ta yi fakin inda yake. Ado direban shanu ne dagaTakai zuwa kudu kuma makocin malam Rashidu ne sannan mutumin da yake zaune a gidan sa kyauta shi da iyalin sa ba haya suke biya ba, akan haka ne Malam Rashidu yake matukar girmama Ado, duk da a haife ya haife shi. Ya fito daga motar ya rufe ya bi Malam Rashidu a sallah, bayan sun idar sun yi addu’a sun shafa ya dubi himilin dankalin dake gaban Malam Rashidu yace “kamar dankalin naka baya karewa” Malam Rashidu cikin jimami yace “ya za’ayi? Yanayin kasuwar kenan, sai godiyarAllah” Ya jinjina kai ya ce, “Gaba daya na nawa ne?” Yace “na naira dari biyar ne” Ya ce, “Juye min shi a buhu duka”. Ya kaikace ya zaro kudi a aljihun wandonsa yana irgawa, cikin mamaki mara misaltuwa ya soma juye masa dankalin a buhunhunan biyu, ya daure bakin buhun sosai ya kinkima yasa mai a bayan Akori-Kurarsa. Adon ya damka masa kudinsa ya mike yana cewa, “To ni na tafi, zan kaiwa iyali, kaima ka koma gida ka huta, in kuma za ka bini ka rage wahalar tafiyar kasa sai ka bini in sauke ka”. Malam Rashidu ya yi masa godiya hawaye sun cika idonsa, ya ce, “Da keke na zo, kuma zan dan tsaya in tsintarwa su Iya dan cefane”. Ado ya kunna Akori-Kurarsa mai masifaffiyar karaji yana cewa da Malam Rashidu, “Wannan godiya haka Malam Rashidu? Ai ba kyauta na baka ba, kayan ka na siya”. Malam Rashidu ya dafa murfin motar tasa ya ce, “Duk da haka ka taimake ni, Ado Allah ya biyaka ya duba gabanka da bayanka”. Ado ya ce, “To Amin”. Ya ja motarsa mai hayagaga da buyagin karfe da salansa ya tafi. Malam Rashidu ya soma nade shimfidarsa ya tattara shirginsa da butar alwalarsa ya dora a gaban kekensa ya sanya su tsakanin hannayensa ya ja kekensa a hankali ya fita daga bakin kasuwa. Sai da ya yi gaba sosai sannan ya tsaya ya auni gero rabin tiya, dawa rabin tiya, masara tiya daya, ya sayi gwalagwajin kayan miya ya dora a kariyar keken, sauran kudin ya kulle su ya yi gaba. Ya isa gida ana kiran sallar magariba. Ya aje kekensa a jikin danga, ya soma kokarin sassauke kayan. Jin motsin shigowarsa Rahane ta yi sauri ta fito bayan danga inda kullum nan yake jingine kekensa, ta karbi kayan a nutse tana yiwa mahaifinta sannu da zuwa. Sanye take da wata kodaddiyar atamfa ‘yar wakas (wax) koriya fatau da ita kamar gudawa duk ta kode. Rahane ba ta a layin kyawawa ko munana, gata nan dai saisa-saisa, sai dai kuma ga dukkan alamu doguwa ce nan gaba kadan, kuma tana da dirin jiki na budurci mai kyau. Rahane a nutse take da wata irin nutsuwa mai ban mamaki kai baka ce bakauyiya ce ba, wadda aka Haifa kuma ta tashi akauyen tun iyayeda kakanni, komi a sanyaye take yinsa da nutsuwa da rashin kuzari. Wannan halitta ce ta Ubangiji, amma yara sa’o’inta a kauyensu tsammani suke iyayi ne da yauki ko yanga da kidifiri. To dai azahiri rashin kuzarin Rahane bai da nasaba da yanga ko iyayi, hasali ma dai bata san su ba, amma dai har da rashin samun abinci mai dauke da sinadarin calcium, protein, vitamin da mineral, sai carbohydrate kadai. Asalin Malam Rashidu mutumin garin Tsangaya ne, wani kauye a karkashin karamar hukumar Albasu. Almajiranci ya zo Takai, to kuma sai Allah ya yi abincinsa a nan yake, domin yana karatun allo yana dako a kasuwar Takai, har ya harhada ‘yan abin da yake samu yana sarin abubuwa daban-daban na fannin kayan abincin kauye masu saukin farashi yana aunawa yana sayarwa a kasuwa, irin su Gurjiya, Gyada, Yalo, Albasa da ire-irensu. A nan Allah ya hada shi da Yalwati, bafulatanar Takai ce ya aure ta ya samu ya kama musu hayar gidan kasa mai daki biyu, dan iyayenta sun ce basu yarda ya tafi da ita Tsangaya ba, don haka bayan auren shi da Yalwati (Rahane) ya je Tsangaya ya dauko mahaifiyarshi da ta rage mishi Iya (Bilki), don mahaifinshi ya dade da rasuwa, ya bata daki daya. Shi da Yalwati suna daya. Gidan ko rijiya babu, ba wuta ba ruwa sai an je tuka-tuka an debo. Babu ko daben siminti, zagaye yake da danga, babu masai sai rami ya haka da kansa ya yi mishi karamar kofa da azara, a nan suke wanka da lalurar su. Yalwati yarinya ce mai hankali, don haka zaman amana suke da surukarta Iya Bilki. Iya bata da sa-ido, ba ta shiga shirgin da ba nata ba. Don haka suke jin dadin zama da ita. Sannan ba kwance take ba, da yake da sauran karfinta tana saide-saiden kayan miya, kuka, karkashi, busasshiyar kubewa, daddawa, farin maggi, gishiri, man ja da man kuli, barkono, citta, tafarnuwa da sauransu, tana rufawa danta asiri. Ita ma Yalwati surfe take ana biyanta, don haka in Malam Rashidu ya samo wani abu wani lokacin sai su ce a zuba a asusu don tarar bukatar bazata, su kukkula su yi abinci daga aljihunsu itada Iya. Yalwati tana kiwon tumaki da kaji, zabbi, kwakwa da kunkuru, kuma Allah ya sanya mata albarka a ciki, kullum kara yawa suke, in tana da bukatar da ba za ta iya da aljihunta ba sai ta dauki daya ta sayar ta rufa asirinsu ita da mijinta da surukarta. Ba karamin so Malam Rashidu yake yiwa Yalwati ba, domin abokiyar rufin asiri ce. Ba ta taba daga masa harshe ba tunda ya aure ta, haka kuma take zaune lafiya da mahaifiyarsa. Har Allah ya bata ciki ta haifi ‘ya mace mai kama da ita, sai dai ko fuskarta ba ta gani ba, mai yanke kauna ta yanke. Mutuwar Yalwati ta wujijjiga Malam Rashidu yanda mutum ba zai taba zato ba. Ya daina wanka, ya daina walwala, ya daina shiga jama’a, ya daina zuwa kasuwa, ko ya ci, ko ya kwana da yunwa, duk daya. Hatta jam’i da makota a kofar gida ya daina zuwa, shi kadai yake sallarsa a dakinsu da Yalwati. Wannan ya daga hankalin mahaifiyarsa da abokanansa matuka. Bai taba cewa a bashi jaririyar ya gani ba, don a ganinsa ita ce ta yi silar rabuwarshi da matarsa mai sonsa. Don haka mahaifiyarshi da masu kaunarsa suka dukufa yi mishi addu’a. Iya tasa ake yi mishi rubutun dangana, aka rubuce mishi Alkur’ani ya sha, don haka a hankali ya soma warwarewa ya koma harkokin shi, amma ba kamar da ba. Iya Bilki, ta ci gaba da rainon jaririya wadda ta mayarwa da sunan mahaifiyarta na asali wato Rahane. Dangin Yalwati sun so karbar Rahane su rike a wurinsu amma Iya ta ki, ta ce da ranta ba za ayi haka ba, sai ko bayan ranta za a raba Rashidu da ‘yar Yalwati. Da taimakon madarar shanu (fresh) da waken suya, kunu da koko Rahane ta rayu a wajen kakarta. Idan da abin da Iya Bilki ke so a duniya bai wuce Rahane ba. A hankali Rahane ke rikidewa tana komawa mahaifiyarta Yalwati sak! Ta kamanni, dabi’a da halayya. A haka rayuwarsu ke garawa a hankali. Rahane na girma hankali na ratsa ta. Ba ta da kwaramniya sam, hatta muryarta sanyi gare ta. Amma fa wasan dandali baya wuce ta, ko ba za ta shiga ba ayi gadar da ita da sa’o’inta ba, za ta zauna gefe ta kunna aci-bal-bal ta tasa farantin dafaffen kwan zabo da take sayarwa a kofar gidansu tana sayarwa, wanda Iya ke dafa mata kullum da yamma. In ta sayar ta zuba a asusunta don zabbin gidan duka nata ne suke yin kwan ta diba. Cikin kasonta na gadon mahaifiyarta. Sanda Rahane ta isa shiga makaranta lokaci ne da ya zo wa Rahane da karin hankali, ta lura mahaifinta bai damu da ita ba, sai ita kuma ta dage wajen kyautata masa da yi mishi hidima, gyaran dakinsa, wankin kayansa masu datti da zuba mishi ruwan wanka, rowan alwala a buta da sauransu. Har kekensa take wankewa, sannan kullum ya dawo gida da gudu take taryo shi ta karbo kayan da ya zo dasu ta yi mishi shimfidar sallar magariba. Tun baya kula har ya gane wata Yalwatin ce Allah ya bashi a matsayin diya. A hankali zuciyarshi ta soma kaunarta, da kanshi ya dauketa ya kaita makarantar firamare, sai dai mai nisa ce sosai da gidansu. Don haka kullum yake goyata a bayan kekensa ya kaita, in sun tashi ta biyo kawayenta su dawo, don lokacin yana kasuwa. Makarantar na karbar naira dari biyu da hamsin duk bayan watanni uku daga kowanne dalibi, haka yake kukkullawa ya biya, in bai bayar ba a koro ta, ta kwashe kwanaki a gida kamin ya samu ya biya. Don lokacin Iya Bilki ta tsufa ainun ba ta sana’ar komai. Tun mutuwar Yalwati yau shekara tara kenan, Malam Rashidu ya ki yin aure, ba don komai ba sai don cewa ya san ba zai samu mai halin Yalwati ba da nagartarta. Haka nan Iya Bilki ba ta fasa takura masa ba a kan ya yi auren, yana ta ba ta uziri. Don haka ba tare da yin shawara da shi ba ta nema mishi auren Zinaru kanwar Yalwati, uwa daya uba daya, da aurenta ya mutu tana da yara hudu tare da tsohon mijinta. Shekarar Zinaru biyu tare da Malam Rashidu ta tada bala’in ba za ta zauna ba don talaucin ya isa. Ba haka ta saba a gidan tsohon mijinta ba. Dole ya sawwake mata tun da sauran mutunci, ya kuma roki Iya da ta yiwa Allah ta kyale shi da auren kowacce mace ba zai iya ba, sannan ba kowacce mace ba ce za ta iya zama da shi da talaucinsa irin Yalwati ba! Ta barshi ya raini diyar Yalwati kadai, ya inganta rayuwar ta, yayi mata aure in ta kai munzalin. Wannan ne kadai burin sa a rayuwa. Bayan wannan ba shi da wani sauran buri, sai na gamawa da duniya lafiya, da cikawa da imani. Iya ta share hawaye da habar zaninta saboda tuno Yalwati, da tijarar Zinaru, Allah daya gari bamban, kama da wane ba ta wane! Ita dama ta hada auren ne don tunanin Zinaru za ta yi halin Yalwati, ta rungumi diyar ‘yar’uwarta. To ita Zinaru ma a tsayin shekaru biyu da ta yi a gidan, baiwa ta maida Rahane, suna ji suna gani basu isa suyi magana ba saboda tsoron bala’inta. Don haka rabuwarsu da ita, sai suka ji su sakayau. Tun daga wannan lokaci Rashidu da mahaifiyarsa basu kara yin zancen ya yi aure ba. Kula da rayuwar Rahane ne a gabansu, da tarbiyyarta, lokacin shekarun Rahane goma sha daya tana firamare aji biyar. Wata irin shakuwa ce tsakanin Rahane da kakarta, tamkar ta uwa da danta. Iya Bilki na da fada sosai, kuma ba ta daukar wargi. Duk wanda ya taba mata Rahane ko ya ya take da iyayensa ba ta kyalewa. Idan samari suka aiko kiran Rahane da tabarya take korarsu, in har ka tsaya, ta rusa maka a baya. Wannan yasa duk samarin masu son Rahanen shakkarta, ba mai tare ta da zancen banza irin na sa’o’inta, don sun san karon da iyayensu za suyi da Iya Bilki. Don haka Rahane ba ta da wani saurayi, amma sa’o’inta da yawa har an ba da su, wasu an sa musu rana. Iya kan ce da Rahane, “Rabu da shashashai ki yi ta karatu, so nake ki zama malamar asibiti ki taimaki masu haihuwa a kauyen nan, kina dai ganin yadda duk auren wurin ya janyowa su Saude yoyon fitsari, ana ta fada a Radio a daina yiwa kananan yara aure amma basa ji”. Shi kuwa Malam Rashidu ba shi da buri irin ya ga ya aurar da Rahane dai-dai wannan lokacin ga managarcin miji kamar sauran tsararrakinta, amma tunda ya lura Iya ba ta ko son zancen sai ya tsahirta. Daga baya Ado direba mai gidan dasu Malam Rashidu keciki ya daina karbar kudin hayarsa, sabida wani kuduri nasa na daban. *** [12/24/2019, 17:56] Takori: Rahane ta shigo da kayan da babanta ya shigo dasu ta aje a tsakar gida, ta yi maza ta kawo mishi ruwan alwala ya karba ya ce, “Sannu Rahane kin ji? Allah ya yi miki albarka”. Ya karbi butar ya yi waje domin ya samu jam’i. Su ma Rahane da Iya alwalar suka yi, Iya na sallah a daki Rahane na yi a tsakar gida. Bayan sun idar Rahane ta karasa gaban murhu tana cire itacen dake cin wuta tana zakulo garwashin tana kashewa da ruwa, sannan ta soma kwashewa Iya tuwon, tana sakawa kowa a kwanonsa. Ta jiyo gyaran muryar babanta na kira a tsakar gida, da sauri ta mike tana amsawa ta zo ta durkusa “Ga ni Baba”. Ya zaro sauran kudin aljihunsa naira dari biyu da hamsin ya ba ta ya ce ta kai makaranta gobe ta ci gaba da zuwa makaranta. Farin ciki ya kama Rahane ta ce, “Na gode Baba, Baba Allah ya kara buda maka”. Ya ce, “Ameen Rahane, Ni dai fatana ki ci gaba da bada himma, kin ji?” Ta ce, “Insha Allah Baba”. Washegari Rahane ta koma makaranta, bayan Malam Rashidu ya sauke ta ya juya ya nufi kasuwa. Suna hanyar dawowa ita da Dije ‘yar ajinsu suka ji karar Akori-kurar Ado a bayansu, duk suka matsa gefe. Ado ya rage gudun motar yana washe katon bakinsa wai shi a wurin shi murmushi yake. Ya ce, “A’a, ‘yan makaranta an taso ne?” Jajayen idanuwanshi a kan Rahane. Ko amsa mishi ba ta yi ba ta ci gaba da tafiyarta. Dije ce ta ce da shi, “Eh, mun taso”. Ya ce, “To ku shigo in karasa daku”. Dije ta ce, “A’a, ai mun kusa”. Har yanzu idanunshi a kan Rahane ya ce, “Wai haka Rahane?” Ko juyawa ba ta yi ba ta yi banza da shi. Bai ji haushi ba ya ci gaba da washe bakinsa ya ce, “Tunda bakya magana a kan hanya Rahane, to ina nan zuwa da dare kin ji?” Bai tsammaci amsarta ba daman, ya tada Akori-kurar sa ya yi gaba, ya kasa rufe bakin. Iya na daki tana kadin auduga, Rahane ta yi sallama ta aje jakar makarantarta, ta fada jikin Iya Bilki tana fadin “Wash! Iya na gaji sosai”. Iya ta rungumeta tana cewa, “Sannu ‘yar Iya, Allah ya nuna min lokacin da za ki fara yiwa mutane allura”. Dariya ta yi ta ce, “Iya Baba fa ba zai barni in yi irin karatun nan da kike so ba, shi kullum maganarshi ta aure ce Iya. Ni kam duk abin da zai rabani da ke da gidan nan Iya bana son shi ko da karatun ne, kuma kin san ba a yin babban karatu a nan kauye sai an dangana da birni, wa muke da shi a birni? Iya ki daina sama ranki abin da ba za ki samu ba”. Jikin Iya ya yi sanyi amma ba ta karaya ba. Ta ce, “Gaskiyarki Rahane, nan Takai gaba daya ban da Ado direba ma wa yake zuwa birni? Shima da me ya tsira ban da shaye-shaye? Sai dai jikina da mafarkina suna bani ke wata ce Rahane, don haka kada ki karaya, ki sa a ranki kema kina da burin karatun da nake sonki da shi. Babu ta yadda Ubangiji baya shirya al’amarinsa”. Rahane ta gyada kai ta mike ta nufi tsakar gida ta daura alwala ta gabatar da sallar azuhur, sannan ta shiga madafi ta dauko robar abincinta a karkashin turmi. Tubani ne da mai da yaji Iya ta yi musu mai silbi, sai wucewa yake silif-silif! A makogwaronta. Ta kammala ta share kejin zabbinta da na kajinta, ta share tsakar gidansu tas, ta debi ruwa ta yi wanka ta sanya kayan makarantar allo ta yamma da take zuwa, ta dau allonta ta yiwa Iya sallama ta tafi makaranta. Wannan shine tsarin rayuwar Rahane a kullum. Yamma lis! Malam Rashidu ya dawo gida ya jingine kekensa a jikin danga, ya dauko kullin buhun da ya dawo da shi daga kasuwa ya shigo gida. Dai-dai lokacin da ita ma Rahane ta dawo daga makarantar allo, ta yiwa babanta sannu da zuwa ta cika mishi buta da ruwan alwala ta kawo mishi. Ya ce, “Sannu Rahane, Allah ya nuna min aurenki da miji na gari”. Murmushi kawai ta yi. Ya yi alwala ya shige masallaci. Rahane na cin tuwon ta bayan isha’i wani yaro ya shigo ya ce, “Wai ana sallama da Rahane”. Kafin ya rufe bakinshi Iya ta yi wuf ta sunkuto tabarya ta yi kan yaron dai-dai sanda Malam Rashidu ya sawo kai, ya yi maza ya rike tabaryar tuni yaron ya yi ta kansa. Ya ce, “Haba Iya, idan kika fasa musu kan Da me za ki ce dasu?” Ta ce, “Gafara nan tun ban sauketa a kanka ba, gobe idaan sun kara aiko shi ya yarda ya zo”. Ya ce, “Yi hakuri Iya, ba wani bane Ado ne, kuma da izinina ya zo su gana da Rahane”. A firgice Rahane ta dago ta dubi mahaifinta, kamar ba ta ji dai-dai ba. Iya ta saki tabaryar ta ce, “Wane Ado kake nufi?” Ya ce, “Ka ji Iya, Adon guda nawa ne ban da wannan makocinmu, mamallakin gidannan da muke ciki?” Iya ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta ce, “Kanka daya Baban Rahane?” Ya kama hannun Iya ya zaunar da ita ya ce, “Ki kwantar da hankalinki Iya, na riga na bawa Ado Rahane, ki bar kama jita-jitar jama’a a kan Ado domin mutumin kirki ne”. Iya ta saki baki tana mishi kallon mamaki, ta ce, “Adon da yake shan wiwi, taba da sholisho, ‘ya’ya shida kowanne uwarsa daban. Adon dake sakin aure da zarar matar ta samu ciki? Wanda yake rayuwa kudu cikin arna shi ka dauki kamilar diya kamar Rahane ka ba shi?” Malam Rashidu ya yi murmushi ya ce, “Su matan kin san me suke yi masa yake sakinsu? Amma Rahane fa? Bana jin ta, don ba ta da matsala. Ki yiwa mutumin da ake yada jita-jita a kansa kyakkyawan zato, don a karshe hakkinsa kawai ake dauka. Duk wadannan abubuwan da ake fadi game da Ado a garin nan na yi bincike a kansu. Na farko dai Ado yana shan taba amma ba abin maye ba. Na biyu ba zai tafi da Rahane kudu ba, a nan zai barta tare da matarsa ta yanzu. Na uku su matan da yake saki din laifinsu ne ba nashi ba kamar matarshi ta farko Hassu sata ta yi mishi, ita kuma.....” Kawai Iya sai ta tashi ta barshi a wurin ta shige dakinta. Rahane ta yunkura za ta bita ya balla mata harara sannan ya nuna mata hanyar kofar gida. Ta toshe bakinta ta soma kuka ta nufi kofar gida. Ado na tsaye jikin kararen da suka zagaye gidan, zai yi shekaru talatin da bakwai. Baki ne wuluk wanda idanunshi suka koma ruwan kasa suna nuna alamun shaye-shaye. Bakinsa wawakeke cike taf da jajayen hakora, bai da tsayi, don ko ita ta fishi tsayi. Ta karasa gabanshi tana kuka kawai ko uffan ba ta ce mishi ba. Ya gyara tsayuwa bakin nan a bude ya ce, “Haba Rahane? Mene ne abin kuka? Maimakon ki godewa Allah ni Ado mai shanu da mota na zo gareki na nemi aurenki ta hannun mahaifinki? Ni masoyinki ne, ba kowacce mace nake iya cewa ina so ba, sai mai sa’a kamarki. In baki yi murna da hakan ba, to ba za ki yi kuka ba”. Rahane ta ga cewa kuka ba zai mata ba, gara ta roke shi ya yiwa Allah ya rabu da ita ko kadan ba ta son shi. Ba tun yau ba, haka nan ko ganinshi ba ta son yi saboda kamanninsa. Ta ce, “Don Allah don Annabi ka yi hakuri ka nemi wata, ni makaranta nake so na yi...” Ta ci gaba da kuka. Ya ce, “In don wannan ne Rahane daina kuka, zan barki ki ci gaba da makaranta amma bayan anyi auren mu”. Ta zaro ido ta ce, “Ni ba zan yi aure ba, yoyon fitsari yake sawa”. Ya bushe da dariya ya ce, “Duk karyar nasara ce Rahane, iyayenmu da kakanninmu basu kai ki ba duk aka yi musu aure, me ya same su?” Cikin kuka ta ce, “Nifa bana sonka, ko dole ne?” Ya yi fuska sosai, sai kuma ya ce, “Ayya! Kin makaro, zamanki lafiya da matsiyacin ubanki kawai shine ki yarda ki aure ni, wanda daga ana bashi ‘yar dari biyar ya yarda ya bani aurenki. In ke baki sona, ni ina sonki, dama ba son na zo nema ba tunda baki da kunya, har ki dubi tsabar idanuna ki ce bakya sona, ba ki yi tunanin cewa ina da kamar ki a gida ba. Aure kuwa nan da sati biyu tunda kin bullo min ta nan. Makarantar ma na fasa barin ki kiyi, shashashar wofi!” Ya karkace ya zaro kudi a aljihunsa ya haska da cocilan ya ce, “Ungo nan, ki raba ke da kakarki”. Ya kuma turo mata wata katuwar leda, “Amshi nan ki sabunta tufafinki kafin a kawo lefe shashashar yarinya da ba ta san abin arziki ba”. Juyawa ta yi tana kuka sosai ta nufi cikin gidansu bata karbi kudi da ledar da yake tura mata ba. Ya bi bayanta ya kira wata yarinya dake sai da gyada a nan gefensu, ya ba ta kayan da kudin ya ce ta kai mata. Shi kuma ya saki wani matsiyacin fito ‘fiii-fiii....’ ya yi gaba yana cewa, “Kwanan nan zan farke santaleliyata, Rahane!”. Rahane na shigowa gida tana kuka ta yi ido hudu da Babanta a tsakar gida yana dakon shigowarta. Kofar dakinsa ya nuna mata, wato ta shiga. Shi kuma ya tashi ya bita. Ya zauna a kan tabarmar shi ta kaba dake shimfide a dakin ya dubi Rahane wadda ke ta kokarin hadiye kukanta karfi da yaji. Ya ce, “Rahane!” Ta cira kai ta dube shi idanunta jawur. Ya ce, “Ni Babanki ne, ni na haifeki, kin san kuma ba zan cuceki ba. Ko baki son auren Ado ki yi hakuri ki tusawa zuciyarki son. Na samu kaina da talauci mai yawa, kada ki manta gidan nan ma da muke ciki na Ado ne, amma yau tsayin shekara goma sha daya tun haihuwarki Ado bai kara karbar kudin haya na ba. Idan na ce zan gaya miki irin taimakon da Ado yake mini ba za ki taba yarda ba. Ya sha siye kayana don in samu abin da zan baku ku ci, ba don yana da bukatar su ba. Duk halin banzan da ake kira mishi ni na yi bincike kansu ban gani ba, zancen nan da nake miki yanzu haka ya samo min aikin kula da dawakin Hakimin Takai, na daina wahalar shan rana a kasuwa, babu wani cinikin arziki. Idan kika ki auren Ado me kike so in ce masa, ko in masa na biyashi alherin da yake yi min? Don haka ki kwantar da hankalinki, ki kwantarwa Iya. Idan har kina kaunata Rahane ki nunawa Iya kina son auren nan kin ji Rahane? Don Allah ki fitar dani kunyar Ado”. Rahane ta daga kai. Ta yarda kawai da kudi Ado ya saye Babanta. Abin da ba ta taba tsammani ba, kwadayi daga Babanta! Ya ce, “Shi kenan Rahane jeki. Allah ya yi miki albarka”. Ta mike hawaye na mata ambaliya ta fita ta samu Iya na sallah mai tsayi, sai ta hau ‘yar yaloluwar katifarsu ta kwanta. Barci ya kasa dauke Rahane, duk iya satarsa kuwa. Duk da kasancewarta karamar yarinya ‘yar shekaru goma sha daya tana da zurfin tunani da hangen nesa. Tana son Babanta fiye da yadda shi yake sonta, ta san Babanta ba shi da kwadayi, don haka ta yi matukar mamakin yadda ya yi hakan, kamar ma tsoron Adon yake ji. Ta tuno wai ya samo masa aikin kula da Dawakan Hakimi, kuma baya karbar kudin hayarsa. Wannan ne dalilin da yasa zai bashi ita. Abune da take da yakinin cewa, Iya ba za ta taba yarda ba, wato ayi mata aure yanzu, don haka ta dan samu salama a cikin ranta. Har barci ya dauke ta, kayan da Ado ya biyota dasu suna nan a gefe ko daga su Iya ba ta yi ba. Da asubahin ranar Iya ta tashe ta don ta yi sallah. Ita kuma tana hada kayan su cikin Ghana must go. Kaf ta hada kayansu bata rage komai ba. Rahane na sallah tana jin Iya da Babanta na fafatawa. Iya na cewa, “Gidan Ado ko? To daga yau bamu kara kwana cikinsa ni da Rahane, in dai a kansa ne za ka ba shi auren yarinya mai daraja irin Rahane. Sai ka san yadda za ka yi da shi da kudinsa da kake ci. Ba aikin gidan Hakimi ba, Allah yasa aikin Hajji ya samo maka. Sai ka ganmu, sannan ka yi mata auren”. Iya gigicewa Malam Rashidu ya gigice, don ya san halin Iya kwarai in ta furta abu, to wallahi ba mai iya hanata. Shi ba wani abu bane don sun tafi, bai san ya zai yi da Ado ba wanda ko mahaliccinshi baya tsoro, yadda yake tsoron Ado a kwanakin nan. Ya yi magiyar ya yi lallashin amma Iya ta yi banza da shi. Da ya gaji ya mike jiki babu kwari ya fita, ya kasa zuwa ko’ina yana zaune a dakinsa ya saka wannan ya kwance. Bai ma san sanda Iya tasa Rahane a gaba ba suka fice. Rahane dauke da dakon kayansu zuwa tashar motar Rake suka hau bayanta suka bar Takai baki dayanta. **** [12/24/2019, 17:56] Takori: Tunda suka hau titi Rahane kuka take tana tunanin Babanta da abin da ka je-ya-zo. Shi kenan yanzu ta rabu da Babanta? Shima ta raba shi da mahaifiyarsa dake matukar son shi? Ina za su? Yaushe zasu dawo? Ko dai ta hakura ta ce da Iya su koma ta auri Adon? Ita kanta Iya kuka take ranta cike da tunanika masu yawa. Ko dai su koma ne? Ta fishi iko da diyarsa ne? Ko ta fishi sonta? Ta daure mata gindi kenan ta ki yin biyayya ga mahaifinta. Ita ba aure ne ba ta son a yiwa Rahane ba, mijin ne bai yi mata ba, da shekarun Rahanen. Mummunan hatsarin ya faru ne a kwanar shiga garin Tsangaya. Inda wata motar haya peageout irin masu mugun gudun nan ta karawa Akori-kurar raken da su Rahane ke ciki ta kife. Wasu suka zubo kan titin, wasu suka fada cikin ramuka motar ta danne su. Tsirarun motocin dake gabansu da bayansu suka tsaya don kawao agaji. Ga shi babu jami’an tsaro a kan titin baki daya. **** Cikin wadanda aka kwasa zuwa asibitin koyarwa na Kano, cikin masu hatsarin da suka tsira da numfashinsu har da Rahane. Cikin gawarwakin da aka kai mutuware kuma har da Iya Bilki. A hankali Rahane ke bude idanunta tana kallon likitan da ke tsira mata allura cikin jijiyoyin hannunta. Abubuwan suka soma dawowa Rahane tar-tar a idanunta. Da sauri ta juya gefenta inda Iya Bilki ke zaune, babu kowa. Kai dakin ma da take ciki ba ta taba ganin irinshi ba. Haka mutanen da take gani suna gilmawa ba ta saba ganin irinsu ba. Wadannan fes-fes suke cikin fararen kaya masu tsabta, ba irin kalar jama’ar da ta saba gani bane. Dr. Mansur, ya manyanta sosai, shine babban likita yau a emergency, yana daga zaune yake bai wa dalibansa dake tsaitsaye lacca na taimakon da za su yiwa Rahane, wadda goshinta ya fashe ko’ina kaca-kaca da jini a jikinta, ba za ka iya tantance iyakacin raunin da ta ji ba. Dinke nan, like nan haka suka yi ta yi, yayin da kuka ya gagari Rahane saboda azabar da take ji a cikin gangar jikinta tayi azaba. Ta suma ya fi sau uku suna kakaba mata oxygen tare da bata taimakon duk da ya dace. Washegari da ta farka karfe takwas na safe da dan sauki jikin nata. Don haka ta fara kuka a hankali. Dai-dai da shigowar Dr. Mansur da tawagar kananan likitoci dake binsa a baya. Cikinsu har da photocopy na Dr. Mansur wato matashin likitan da ke (housemanship) mai amsa sunan I.M Takai, wato IBRAHIM MANSUR TAKAI. Da gani babu tambaya ka ga uba da dansa. Duk da yanayin halayyarsu a fuska ya nuna ba daya bane, domin shi Dr. Mansur mutum ne mai sakin fuska sosai, sabanin Ibraheem da yake mutum mara walwala sam-sam. Duk abin da Dr. Mansur ke yiwa Rahane suna jotting ne. Dr. Mansur ya matsa dai-dai kan Rahane ya dora hannunshi a kanta ya ce, “Daina kuka kin ji? Insha Allah za ki samu lafiya”. Ta cira idanunta da suka kada suka yi jawur a hankali ta dube shi, bakinta na motsi amma ta kasa magana. Ya dubi Ibraheem ya ce, “Dagata ta zauna”. Ya cirata ta zauna ya tusa mata filo a bayanta ta zauna sosai. Dr. Mansur ya ce, “Me sunanki?” Bin shi ta yi da ido kawai ba ta yi magana ba. Ya ce, “Ku rabu da ita ta warware a hankali”. Nurse din da suke tare ta mika mata kofin tea. Dr. Mansur ya ce, “Bata shayin ta sha Ibrahimu”. Ya yi kamar bai ji ba, ya yi baya kadan ya dan tura Eric Ipatobe abokin karatunsa dake gabansa yayi baya. Shima Dr. Mansur sai ya yi kamar bai ga abin da ya yi din ba. Cikin girgiza kai ya karbi kofin ya matsa sosai ya soma bata da kansa. Yana fadi cikin ransa, dani kake zancen, wallahi sai na kwashe maka maki (marks). Mamaki ya kama su dukkansu, Doctor Mansur da kansa! Da sauri Nurse din ta karba tana bata. Ya dan ja baya ya sarke hannun shi a kirjinsa bai kara kallon Ibrahim ba. Ya ci gaba da feso musu lacca kamar Obama ya diro Nijeriya. Kwana uku Dr. Mansur na kula da Rahane, ta ji sauki sosai amma ta ki magana. Don haka ya soma tunanin akwai wani abu. “There must be something wrong beneath!” Ya fadawa su Ibraheem. Ya girgiza kai ya juya gare su, “Tana bukatar ganin likitan kunne da makogaro yayi examining dinsu, wanda wannan ba shine darasin da muke a kanshi ba tukunna, muna neman lafiyar gangar jikinta ne gaba daya”. Cikin sati biyu Dr. Mansur ya ba da hankalin shi da kwarewar shi gaba daya a kan Rahane da shi da Dr. Imam, kwararren likitan kunnen da ake ji da shi a AKTH. Duk wani taimako da ya kamata ya bata sun bata, amma Rahane sai da aka dangana da hearing test wanda ya nuna ta gamu da very unusual hearing issue, wanda ke bukatar ayi CT Scan da MRI Scan, dake bukatar kudi na fitar hankali wanda zai nuna hakikanin menene matsalarta daga inner and outer zones na kunne da kwakwalwarta, a dalilin rashin sanin daga inda ta bullo da kuma rashin sanin kowa nata, suka samar da occasional hearing Aid gareta, sannan ta ji abin da suke cewa. Amma idan aka cire bazata ji ba. Duka daga aljihun Dr. Mansur Takai, wanda Allah ya sakawa kaunar Rahane da tausayin ta, Yau Asabar ba shine on call ba, Dr. Hashim ne, amma sai da ya shigo asibitin musamman don yaga jikin Rahane. ‘Yar shi karama AZiza na rike da hannun shi, caftan na shadda milk colour ne a jikinshi da hular da ta dace dasu ba suit da lab-coat ba. Rahane na hangoshi ta soma murmushi, shima murmushin yake mata. Ganin ta zauna ras alamun lafiya na samuwa, ya ja kujerar dake gabanta ya zauna. “Yar Doctor, lallai lafiya ta samu”. A sanyaye ta ce, “Alhamdulillah!” Lokaci na farko da ya ji furucin bakinta, tun ranar da su kai hatsarin. Shima ya ce, “Alhamdulillah ‘yata ya ya sunanki?” Ta ce, “Rahane”. Ya bushe da dariya, “RAYHANAH kenan ko?’ “A’a, RAHANE!” Ta sake gyara masa. “To na yarda Rayhanatu, ni ba zan iya fadar wancan din ba, saboda ba shi da ma’ana kwata-kwata”. Dr. Hashim na jinsu yana dariya yana auna patient din gadon kusa da ita. Lokaci guda Rahane ta soma kuka. Duka likitocin suka tsaida dariyar suka yi kanta. “Kuka Rayhanah? Daina kuka har gida zamu kai ki. Fatanmu shine Allah ya baki lafiya mu tambayeki ke da waye kuka taho? Kuma ina ne garinku?” “Ni da Iya ne, kuma ban ganta ba tun ranar”. “Za ki iya gane ta cikin kowanne hali?” Ta ce, “Eh”. “Daga ina kuke?” “Takai, zamu Tsangaya”. “Takai? Ikon Allah”. Ya yi dan shiru yana kallon ta. “Sunana Dr. Mansur Balarabe Takai....” Ta dube shi da sauri. Ya gyada mata kai yana dariya. Dr. Hashim ya juyokadan ya ce, “Dr. Takai, ashe ‘yar taka ‘yar garinku ce, dole a bata extra kulawa, kyakkyawa da ita, ina kamu Doctor”. Murmushi ya yi, ya ce da Nurse dake gefe a kawo Rahane ‘matuary”. A kujerar daukar marassa lafiya nurses biyu suka turata zuwa mutuware. Aka soma zarowa Rahane akwatunan gawarwaki abin babu kyawun gani. Rahane ba ta taba ganin gawa ba sai yau a idanunta. Iyakacin firgita ta firgita, amma da aka zaro Iya Bilki, ba ta san sanda ta fada kanta ta rungumeta ba. Kuka take na fitar hankali, domin Iya sumul take babu ko kwarzane a jikinta. Idanunta ne kurum a rufe kamar mai barci, kamar ta ce “Iya”. Ta bude ido ta amsa mata. Da kyar Dr. Mansur ya janyeta, aka hada Iya cikin motar daukar gawarwaki na asibitin. Motar Dr. Mansur na biye dauke da Rahane da I.M a gidan gaba, suka dauki hanyar Takai. Rahane na baya ta kankame jikinta tana kuka mai cin rai, sai dai daga Doctor har dansa Ibraheem babu mai jin ta sakamakon kira’ar Ahmad Sulaiman da Dr. Mansur ya saki a motar har suka isa garin Takai. Rahane ke nuna musu hanya da aka shigo Takai har kofar gidansu. Tana hango Akori-Kurar Ado a kofar gidansu gabanta ya yi mugun faduwa. Hakan bai hanata fitowa daga motar ba a lokacin da Ibraheem ya bude mata, yana ta zabga mata harara kamar ya hankadata. “Shiga ki karawo shi Rayhanah”. In ji Baba Dacta (kamar yadda take kiranshi) Da addu’a tasa kai cikin gidansu. Ta yi sallama ba a amsa ba. Sai kawai tasa kai. Caraf! Ado ya cafke ta ya danneta a dakin Iya, nan ta ga babanta a makure a gefe daga shi sai gejeran wando, ko’ina a jikinsa shatin bulala ne, jini ya bisu ya kwanta. Ado ya ce, “Munafiki! To gata ta dawo da kafafunta, auren ma na fasa a gabanka zan yi kaca-kaca da mutuncin ta in fanshe wahalata ta shekara da shekaru”. Bai yi la’akari da halin ciwuwwukan da ke jikinta ba ya hadata da bango ya keta rigar jikinta tun daga sama har kasa.......! Ihun da Rahane ta zabga ya amsa kuwwa har sauran gidajen da ke makwabtaka dasu suka jiyo. Dr. Mansur na waya, dansa Ibraheem ya yi saurin dagowa ya ce, “Daddy.....yarinyar nan ihu fa take yi”. Da sauri Dr. Mansur ya juyo, shima kunnuwansa suka jiyo masa kururuwar da Rahane ke zabgawa. Shi da Ibraheem suka runtuma cikin gidan ba tare da sunyi wata maganar ba. A lokacin Ado ya kaita kasa, dan kamfai ne kawai a jikinta. Ga Malam Rashidu a gefe dunkule wuri daya yana ta kwararar da hawaye sai tsima yakeyi ko uffan bai ce ba. Ibraheem ya danko kwalar rigarshi ya finciko shi ya hada shi da bango, ya dunkule hannu ya sauke a bakin Ado, sai ga hakora biyar sun zubo, jini ya biyo bayansu. Ya tankada shi tsakar gidan da doguwar kafarsa. A lokacin jama’a makota har sun cika gidan, shi kuma Daddy waya ya yiwa ‘yan sanda nan da nan sai gasu a (shiga-ba-biya) suka danna Ado a ciki, jama’a na ta sallallami ganin Malam Rashidu daga shi sai gajeran wando gaba daya ya fita hayyacinsa ya zama dan tsurut. Jikinsa ba masaka tsinke da tambarin bulala. Rahane na gefe ta kankame jikinta tana ta kuka. I.M Takai, ya ciro suit din dake jikinsa ya rufa mata, don ta kare tsaraicinta. Nan Malam Rashidu ya matsa gaban Rahane ya saka kuka. Cewa yake “Ina Iya Rahane?” Jama’a makota suka soma cece-kuce kan cewa yau sati biyu kenan basu sa Malam Rashidu da Rahane a idanunsu ba, sun dauka ma barin garin suka yi ba tare da sun yiwa kowa sallama ba. Dr. Mansur ya ciro malun-malun din da yake snaye da ita ya sanyawa Malam Rashidu. A nan ya soma gaya musu yau sati uku kenan Ado ya kulle shi yana azabtar da shi a kan sai ya fada masa inda ya kai Rahane don kar ya bashi aurenta. Bayan shima bai san inda suka tafi ba ita da Iya. Kowa ya ce, “Ado zai aikata fin haka. Allah ya saka masa”. Dr. Mansur ya ce, “Sunyi hatsari ne ita kadai ta sha aka kaita asibitin su, Allah ya yiwa Iya rasuwa tare suke da gawarta”. Malam Rashidu ya rikice da kuka shi yana yi Rahane na yi. Jama’a na ambaton “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Allah ya ji kan Iya Bilki, Allah ya yi mata rahama”. Kan ka ce meye wannan jama’ar Takai ma’abota kara da hadin kai sun cika kofar gidan. Tare da Dr. Mansur da I.M aka sallaci Iya Bilki, aka dauketa zuwa gidanta na gaskiya. Dacta da I.M suka wuce gidan Hakimin Takai. Dr. Mansur dan asalin garin Takai ne. Da shi da Mai-Martaba Hakimin Takai cikinsu daya, sai dai shi Mansur dan boko ne na a buga a jarida, kwata-kwata baya sha’awar sarautar tasu, ko zaman garin su sai dai ya zo da ziyara, yana Kano tare da iyalinsa. Shekararsu goma a kasar Ireland suna karatu shi da mahaifiyar su Ibraheem (Asma’u) wadda ‘ya’yanta suke kira (Mami). Mami ‘yar asalin garin Jos ce, (arnan Jos), a da, bata da addini, sunanta (Anita Shiyana). Sun hadu da Dr, Mansur a jami’ar TRINITY dake (Dublin). A hannun Mansur ta karbi musulunci ta kuma rike shi da kyau, ya sanya mata sunan mahaifiyarsa (Asma’u) wadda ta dade da rasuwa, don haka shima Mamin yake ce mata. Mami cikakkiyar likitar yara ce (paediatrician) da ta san aikinta. Duka yaransu biyar, kowane da rata sosai tsakaninsa da wanda yake bi a haihuwa. Rayuwar Mami zallanta na (Irish) wato na mutanen Ireland ne, ga masifar son ‘ya’ya. Ba ta son kowa ya rabe su, daga ita sai ‘ya’yanta sai mijinta. Sabanin mijin, Dr. Mansur mutum mai kara da kawaici, ga faram-faram da mai da kowa nasa, ga son zumunci da muhimmanta shi. Ga son mutane da saukin kai, Tunda ya shigo gidan Hakimi tunanin Rahane da Babanta yake, da yanayin ban tausayin da ya baro su a ciki. Suna hira da dan’uwansa Hakimi Abdullahi Takai, amma ya lura sam hankalin dan’uwan nasa baya tare da shi. Ya yi gyaran murya “Wani abu ya faru ne Mansur?’ Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “Wani abin tausayi nake tunani, Allah ya ja da ran Hakimi”. Ya warware masa komai. Shi Hakimi bai san su ba. Ya ce, “Yanzu da kasa kanka cikin dogon tunani irin haka me kake ganin za ka iya yi a kansu? Talakawa fa na da yawa a kasar nan, ba su kenan ba, kuma ba za su kare ba”. Dr. Mansur ya girgiza kai ya ce, “Allah shi ya hada jinina da wannan yarinya, zan tafi dasu Kano. Shi ya yi min aikin gadi, ita kuma yarinyar zan hadata da su Abida in dau nauyin iliminta, don da ganinta ba haka Allah ya yi nufin barinta ba!”. Hakimi ya girgiza kai, jin yadda yake maganar (with confidence) kuma tun daga karkashin zuciyarsa “Ka tafi da yarinyar kawai, ka bar min uban a nan za sa a kula da shi. Daman kuma sarkin Dawaki ya rasu, ina neman nitsattsen mutum wanda zai jure hidimar Dawakai na babu lalaci har na baza cikiya a cikin gari. To ka san halin talakawan namu basu yarda su rabemu saboda gudun wulakanci, na shaidi jama’ar Takai a nan”. Dr. Takai ya ce, “Hakan ya yi, na ji dadi sosai Yaya. Bari in tura Ibrahimu ya zo dasu”. Ya dauko waya ya kira I.M ya ce, “Daddy ina barga tare da Dawakan Mai Martaba”. Ya ce, “Daure ka zo maza, ko da yake ba sai ka dawo ba, ka je ka zo min da yarinyar nan da mahaifinta yanzu. Ina tare da Hakimi”. Ya rausayar da kai ya ce, “Daddy why me (me yasa sai ni)?” Doctor ya ce, “To wa ya san gidan idan ba kai ba?’ Yana daga cikin mota yana kallon yadda jama’a ‘yan zaman makokin Iya suka cika harabar gidan, yana daga cikin motar bai fito ba yana ta shan kamshi da jan numfashi. Can kuma ya yafito wani saurayi ya ce don Allah ya daure ya zo masa da Malam Rashidu da ‘yarsa, ya sanar dasu wadanda suka kawo yarinyarshi daga Kano ne suka aiko shi ya tafi dasu inda suke (gidan Hakimi). Mutumin ya juya ya doshi gidan. Shi kuma I.M ya ci gaba da zama cikin motar yana kallon rusasshiyar kofar gidan. Cikin ranshi yana kissima abubuwa daban-daban, ko neman me kuma Daddy yake wa muten nan bayan taimakon da suka yi musu, me kuma zai yi musu oho! Bai gama tunaninsa ba ya hango Malam Rashidu tafe yana rike da hannun Rahane wadda duk aka kwailewa ciwonta dake cikin bandeji jini sai zuba yake. Ji ya yi tsigar jikinshi ya tashi, don bai son ganin fitar jini daga jikin dan Adam ko kadan. Tun kan su karaso ya tada motar, ya mika hannu ya bude musu kujerar baya suka shiga ya ja motar suka tafi ko uffan bai ce musu ba. Tsakanin gidan Malam Rashidu da gidan Hakimin Takai akwai tazara sosai, Malam Rashidu bai taba zuwa gidan Hakimi ba sai yau. Tun daga soron farko ya tube takalmansa ya rungume, ita kuwa Rahane a hannu ta rike abinta, tsaf take cikin nutsuwarta. Ibraheem bai tsaya dasu a ko’ina ba sai a falon da Doctor Mansoor da Hakimi suke zaune. A nan ya tube nashi takalman suka shiga. Idon Dacta Mansoor a kan kunnen Rahane, bai ga hearing-aid din da suka makala mata ba. Ya juya ga Malam Rashidu ya ce, “Ina abin da ke makale a kunnen Rayhanatu?’ Malam Rashidu wanda ke ta kwasar gaisuwa gurin Hakimi ya juyo ga Dacta Mansoor ya ce, “Eye? Na’am?” Dacta Mansoor ya ce, “Akwai karamar na’ura makale a kunnenta sanda muka zo, ina take?” [12/24/2019, 17:56] Takori: Malam Rashidu bai wani fahimce shi ba sakamakon wani suna da ya ji ya ambata wai Rayhanah, sai ya dauka ba da shi yake ba. Haushi ya bala’in kama Doctor Mansur ganin Malam Rashidu ya saki baki yana kallonshi kawai bai ba shi amsar tambayar shi ba. Shi dai Mal. Rashidu tun dazun yake ta yiwa Rahane magana bai ji ta ba shi amsa ko daya ba, sai ya dauka duk cikin halin rasuwar Iya ne. Bai kawo wani abu daban ba. I.M ya dubi mahaifinshi ya ce, “Ina ganin sanda mutumin banzan can ya cafketa hearing-aid din ya fadi”. Dacta Mansur ya ce, “Maza ku koma ku dubo”. Malam Rashidu ya ce, “Ranka ya dade me zan dubo?” Ya dubi Ibraheem ya ce, “Ka tashi ka je ku dubo na ce”. Ibraheem ya cika fam, kiris yake jira ya fashe. Ya mike suka fito falon shi da Mal. Rashidu kamar ya shake shi don takaici. Shi bai ga dalilin da zai sa Daddy ya daura masa al’amarin talakawan nan ba, babu dangin iya babu na baba. A guje ya fizgi motar suka koma gidan Malam Rashidu, dakin Iya inda akai gumurzun Rahane da Ado suka yi ta dubawa har Allah ya bawa Mal. Rashidu sa’ar ganin dan injin a bayan randar Iya. “Wannan ne?” Ya tambayi I.M. Karba kawai ya yi ya fice bai ce da shi ko uffan ba, ya yi gaba ya bishi a baya. Suka koma gidan Hakimi. Dacta Mansur ya karba ya bude ya canza batir wanda dama yana cikin aljihunsa ya matsa ya makalwa Rahane ‘yar na’urar a bayan kunnenta. Ya ce, “RAYHANAH!” ta dago ido a hankali ta ce, “Na’am Baba Dacta”. “Za ki bini gidana in sanyaki cikin ‘ya’yana ko za ki zauna da Babanki a nan gidan Hakimi? Daga yau Babanki ya dawo nan za a ba shi aikin yi da kyakkyawan muhalli”. Ta juya ta dubi Babanta wanda ya zaro ido yana kallon su. Dacta Mansur ya dube shi ya ce, “Ka amince in rike Rayhanah har illa masha-Allahu a Kano?” Ya girgiza kai ya ce, “Aure zan yi mata!”. Gaba dayansu suka dube shi sosai har Rahanen. I.M ya mike ya fice a ranshi yana yiwa Babanshi Allah ya kara. Haka kawai don bala’i da kwashe-kwashe zai kwaso musu wasu shirgin kauye babu gaira babu dalili. Ai gara da uban nata ya gwale shi, ya yi tafiyarsa cikin gida. Hakimi ya karbi Dacta Mansur wanda ya yi mutuwar zaune ya ce, “Yar wannan yarinyar za ka yiwa auren? Wa za ka aura mata? Wa ya ce yana sonta?” Mal. Rashidu ya ce, “Ku yi hakuri don Allah, na gode da taimakon ku garemu ba wai ban gode ba, amma idan na yi mata aure hankalina zai fi kwanciya, kuma na riga na karbi sadakinta. Ado dai da kuka sa aka kama ku sako shi, don na riga na ci sadakinsa, tun kan a haifi Rahane yake hidima dani, bani da abin da zan biya shi ban da in aura masa Rahane. Ku yi hakuri don Allah, na riga na ba shi aure”. Rahane ta fashe da kuka, “Baba Dacta ku ceceni bana son sa...wallahi bana son sa…!!!”. Ta gurfana gaban Dr. Mansur tana rera kuka mai ban tausayi, ta buya a bayansa ta kankame shi. “Baba Dacta kashe ni zai yi....kana gani fa ya yaga min riga a gaban Babana… amma shine zai aura min shi?” Ran Dacta Mansur ya yi mugun baci, lallai ya yarda komai akai da matsiyaci sai ya ci kara. Wannan Mal. Rashidun a jahilan ma bai san a ajin da yake ba. Kai baka ce shi da bakinsa yake fadar rashin arzikin da Ado ya yi masa ba, wai ya boye Rahane har ya yi attempting keta mata mutunci a gabansa, wannan shine mijin da zai bawa aure. Ya ce, “Kai Malam! Ina jin dai ba lafiyarka kalau ba. Aure da wannan mutumin, mun hana, ya lissafa duk abin da ya kashe maka a biya shi, bayan ya gama zaman gidan kaso na keta haddin da yaso yi. Ba zan iya cin fuskarka ba albarkacin Rayhanah”. Ya dau waya ya ce, “Ibraheemu jeka ofishin ‘yan sandan nan ka ce su zo min da wannan mutumin da nasa aka kama yanzu-yanzun nan”. I.M Takai tsaye ya yi rike da wayar hannunshi “What’s wrong with Daddy ne?” Ya dubi wayar hannunshi sosai cike da takaici, sannan ya dubi Nabilah diyar Hakimi da suke tsaye tare, “Mts! Daddy ya samu matsala Nabilah!” Ta ce, “Matsalar me?” Ya sake hura hanci ya ce, “Jirani ina zuwa”. Ya juya ya fita. Cikin dan lokaci an kawo Ado fada. Malam Rashidu ya dube shi jikinsa yana ta rawa ya ce, “Yauwa don Allah ku sa a sake shi”. Haushi ya kama Hakimi ya ce, “Kai Malam ka nutsu ka san a inda kake bama son shirmen banza”. Malam Rashidu ya koma cikin nutsuwarsa. Dacta Mansur ya dubi Ado sosai ya ce, “Da gaske kana son auren diyar Malam Rashidu?” Ado wanda ya ci kaniyarsa sosai a hannun ‘yan sanda ya ce, “Eh”. Dacta ya ce, “Shine kuma za ka yi mata fyade a gaban ubanta?” Ya ce, “Ba nufina kenan ba”. Dacta ya ce, “To meye nufin ka na tsaraita ta?” Ya yi shiru. Dacta ya ci gaba da kallonsa a ransa yana mamakin Malam Rashidu, wai wannan mutumin mai kama da ‘yan fashi zai aurawa innocent yarinya kamar Rayhanah. Ya boye mamakinsa ya ce, “Sulhu nake nema da kai”. Ado ya dago a fusace, sai kuma suka yi mishi kwarjini ya kasa cewa komai. Dacta ya ci gaba da cewa, “Ka lissafa duk abin da ka kashewa Mal. Rashidu da ‘yarsa zan fanshe su ba ta isa aure ba!” Ado ya gallawa Mal. Rashidu harara wanda ya takure ya yi lakwam yana kallon Ado a tsorace. Ado ya bude wawulon bakinsa ya ce cikin zafin rai, “Hakorana da aka zubar min fa?” “Zamu makala maka na roba yanzu”. Ya ce, “To a rabani da ‘yan sandan nan”. Hakimi ya ce, “An raba ku”. Ado ya ce, “Naira dubu dari biyar zaku bani, kuma su tashi su bar min gidana”. Hakimi ya yi murmushi, ya jawo wata bakar akwati ya bude, ya dauko daurin kudi ‘yan dubu-dunu dauri biyar ya zube su a gaban Ado. “Gasu, gidanka kuwa ko komawa ba zasu yi ba. Duk tarkacen dake ciki ma sun bar maka. ‘Yan zaman makokin ma in kaso ka koresu ka koresu su zo nan su yi”. Ado ya gigice don dai kawai ya shaci kudin ne da gayya bai taba zaton ba za suyi musu ba. Ya kwashi kudi ya nade cikin rigarsa ya mike zai fita, cike da tsoron kada su kwace kafin ya kai kofa. Dariya ta kama Dacta Mansur ya ce, “Hakoran fa Ado?’ Ya ce, “Barsu kawai, zan je kudu a sa min”. Gaba daya suka sa dariya har Mal. Rashidu dake takure a gefe sai da ya murmusa. Karshen diramar Ado da Rahane kenan. Tunda ya hada kudin nan ya gudu ya bar Takai, ya bar ‘ya’yansa da matarsa ba a kara jin duriyarsa ba. Aka bawa Mal. Rashidu muhalli a cikin gidajen bayin Hakimi, washegari ya fara aikinsa na kula da Dawakin Hakimi. Dr. Mansur da dansa I.M suka taho Kano da Rahane, bayan ta yi sallama da babanta. RAHANE A GIDAN DR. MANSOOR Gidan Dr. Mansur Balarabe Takai babban gida ne mai tsarin gaske a unguwar Lamido Crescent, wanda ke rufe cikin bakin girgijejen get. Asalinsa Turawa ne suka zauna cikinsa shekaru masu yawa da suka gabata lokacin mulkin soja sanda suka bude kamfanin PZ da za su koma kasarsu suka sayarwa gwamnati. Lokacin da Dr. Mansur ya yi kwamishinan lafiya a Kano, lokacin Gwamna Kabiru Gaya, gwamnati ta bashi gidan ya zauna, da tenure din su ya kare ya yi kokarin da ya sayi gidan da taimakon mahaifinshi mai girma Hakimin Takai na III (Balarabe Sardauna). Haka ya ci gaba da sabunta gidan, yadda zai yi dai-dai da zamanin da ake ciki har kawo yau. Gidan farin fenti ne da shi, kana shigowa cikin get din gidan mikakkiyar kwalta ce wadda zata sadaka da rumfar adana motoci a kalla biyar, ba tare da kowacce ta gogi ‘yar’uwarta ba. Idan ka yo gaba kadan grass carpet ne wanda zai kai ka bakin kofar reception din gidan. A cikin reception din matattakalar bene take wadda za ta sadaka da falon sama da yake kunshe da dakunan barcin jama’ar gidan. Dakunan barci hudu ne a cikin falon, daya na Dr. Mansoor, daya na Mami, daya na I.M da Yayansa Khalipha, wanda a halin yanzu yake karatu a jami’ar BAZE dake Abuja, yana karantar hulda da kasashen ketare wato (International Relation). Daya dakin na Abida da Jawahir ne, sai autar su Azizah. Abida shekarunta takwas, Jawahid goma, Mami ta dade bayan haihuwar Abida kafin ta haifi Aziza wadda ke da shekaru uku a halin yanzu. Saboda tsantsenin tarbiyya irin na Dr. Mansur bai warewa I.M da Khalipha daki a wajen gidansa ba, duk da girmansu tare yake dasu yana ganin kowanne motsinsu. Idan abokai ne ga reception nan bai yarda ko baskwata su zauna ba, masu aikace-aikacen gidan ne a baskwatan. Motar Dr. Mansur ta sako kai farfajiyar gidansa. Ibraheem ne ke tukin. Dacta na gaban motar rike da jaridar This Day da ya saya a go slow din roundabout na kofar Nassarawa. Rahane na baya a makure jikin kofar motar kamar ka ce kyat! Ta bude murfin motar ta arta a na kare. Abida da Jawahid ne zaune a rumfar adana motoci tare da malamin Islamiyyarsu dake zuwa duk Alhamis da Juma’a yana koya musu karatun Alkur’ani da Hadisi, tajweed da Tawheeed, ga bakin allo (black board) an kafa musu cikin rumfar adana motocin. Ta bala’in raina malamin, don Abida ‘yar rainin wayau ce, sabanin Jawahir da ko magana ba sosai take yinta ba. Jin shigowar motar Daddy Abida ta nutsu daga mintsinin Jawahir da take yi, shi kansa Malam Umar ya lura Abida ta shiga taitayinta, don haka ya juyo don ganin abin da ya nutsar da ita. Daddy ne da Ibraheem ke fitowa daga mota, tare da wata dukun-dukun din yarinya baka wuluk! Kanta a daure cikin wani bakin tsumma da wani sidadden silifa a kafarta, ko’ina a jikinta ciwo ne, wani da plasta wani plastar ta daye. Abida ta soma zungurin Jawahir don ita ma ta juya ta ga abin da ta gani, amma Jawahir ta yi banza da ita ta ki juyawa ta ba da hankalinta sosai ga Malam Umar. Malam din ya aje Alkur’anin dake hannunsa ya isa ga Daddy ya tsugunna yana gaisuwa. Daddy ya amsa ta hanyar bashi hannu sukayi musabiha. Tuni Ibraheem ya shige gida. Daddy ya kama hannun Rahane suka doshi reception. Rahane dai taku take a tsorace, don ita tunda Allah ya halicce ta bata taba ganin waje irin wannan ba, kamar Aljanna da ake kwatantawa. “Mami! Mami!!” Daddy ke kira a falon sama. Ta fito daga laundary inda take shanyar kayan Azizah data wanke cikin injin wanki, sanye take da riga da siket na wani bakin material mai yarfin light green flowers, gashin kanta kame da hair-bound, shima light green ya sauko har kafadunta. Duk wani likita kirki ne da shi, to haka Dr. Asma’u Takai, musamman kasancewarta likitar yara. Amma a yau kam ga dukkan alamu za suyi fada da Dactan nata, don kirkin nata bai kai nan ba. Za ka rantse ba ta haifi Da kamar I.M ba, balle kuma Yayansa Khalipha. Ta fi kama da matashiya ‘yar shekaru talatin ba talatin da tara ba. Ta fito falon tana fadin “Dacta na!” Shima ya ce, “Mamina!!”. Ya juya ga Rahane, “Rayhanah matsa ki gai da Mamanku”. Sai a lokacin ta kai idonta ga Rahanen da ta zube a gabanta tana fadin “Barka da yamma Hajiya”. A firgice ta juya ga Ibraheem, sannan Daddyn ta kasa tambayar komai. Dariya ce ta kama Ibraheem ganin idanun Mami sunyi mitsi-mitsi, ya lallaba ya shige dakinsa kada dariyar da yake yi ta fito. Daddy ya yi murmushi ya isa ga Rahane yasa hannu ya cira ta daga zubewar da ta yi kamar bawa a gaban Ubangijinsa. Ya zaunar da ita a kujera yana ce da Mami “Karin ‘ya na kawo miki, sauran bayani sai anjima, yanzu ba ta abinci da ruwa tukunna mun sha tafiya”. Ta dan saki fuska ta koma kicin ta zubo abinci a plate da robar ruwan Eva mai sanyi da lemun La-casera ta kawo mata kan tebir. Amma da ta kira yarinyar ta ce ta zauna a kujera ta ci, sai ta ga ta sauke plate din kan marbles ta bararraje abinta tana ci kamar Allah ya aikota saboda yunwa. Ta bi bayan mijinta cike da mamaki. Ta same shi yana cire safar kafarshi a gefen gado, ta zauna a kasan kafafun nashi ta karbe shi. Sai da ya yi wanka ya kwanta yana hutawa, Mami ta matsa jikinsa tana cewa, “Ina ka samo yarinya bakauya haka?” Ya ce, “Garinmu Takai”. Ta ce, “Yar waye?” Ya ce, “Yar AMANA!” Ya tashi daga kishingidar da ya yi ya kama hannayenta masu taushi ya ce, “Mami batun yau ba ni da ke muke da bambancin ra’ayi a kan al’amura da dama, amma kowa ya kasa rinjayar dan’uwanshi ya bi nashi ra’ayin. Amma a yau ina neman alfarma Mami, wadda na san mai girma ce a gare ki, ita ce ki rike min Rayhanah kwatankwacin rikon da kike yiwa ‘ya’yan da kika haifa. Ko da komai bai zamo hundred parcently equal ba, ki kwatanta kara da karamci. Rayhanah da ubanta ba shegiya ba ce. Sai dai marainiya ce ba ta da uwa, ta rasu tun lokacin haihuwarta. Ta girma a hannun kakarta, ita ma yanzu babu. Na tserar da ita ne daga kaskantacciyar rayuwa da ubanta ke so ta yi, wato early and abusing marriage, sakamakon wasu extraordinary characteristics dana gani a tare da ita. Ban taba haduwa da pateint din da ya shiga raina irin ta ba. Sannan ta gamu da ‘lalura’ wadda dole a tausaya mata, a bata kwarin gwiwar da zata fuskanci rayuwa a, duk yadda ta zo mata. Ta samu hearing impairment wanda bazamu ce a sakamakon hadarin da suka yi bane, har yanzu source din, bai bayyana garemu ba, har sai anyi CT Scan and MRI Scan, wadanda bamu da injinan yin su anan Nigeria, in kin lura akwai hearing-aid a kunnenta. Mami ban taba neman alfarma kin kasa yi min ba, a yau wadda nake nema ma ba za ta gagareki ba, tunda kin saba haihuwa kin san ciwon DA. Yadda naki yake a ranki haka na kowa yake a zuciyar nashi iyayen. Ki yi min alfarma cikin dimbin alfarmominki gareni, ki rike min RAYHANAH da zuciya daya, ni kuma duk abin da kike so zan miki Mami. Wallahi-wallahi ko da bani da shi zan nemo. Kawai ina so Rayhanah ta yi rayuwa mai kyau kamar ‘ya’yanki. Ta yi ilimi, ba tare da nakasunta ya nakasta rayuwarta ba. Zan samu Mami?” Ta sauke idonta a hankali kan mijin nata, ta rasa shi wane irin mutum ne, mai maida damuwar wani tasa. Ba ta da muguwar zuciya ko kankani, sai dai ba ta son kowa ya rabi rayuwarta da mijinta da ‘ya’yanta. Ba ma wannan ne abin tsoron ba, za ta hada ‘ya’yanta ne da yarinyar da ko asalinta ba ta sani ba? Kai rigimar Daddy da yawa take. Ta ce, “Daddy zan yi maka alfarmar da kake so, amma a bisa sharadi biyu”. Kallonta ya yi, kallon ke nake sauraro. Ta ce, “Ka yi min alkawarin WATARANA ba zaka ce za ka hada aure tsakanin ‘ya’yana da wannan yarinyar ba. Sharadi na biyu shine, zan raba musu daki da su Abida, don hankalina ba zai kwanta ba idan tana tare dasu”. Dariya ta bai wa Daddy sosai. Ya ce, “Mamee!” Ta ce, “Dacta naa!!” “ki kwantar da hankalinki da Rayhanah, ba zan kawo abin da zai cuci su Abida ba. Am their Dad, remember? Baki fini son su ba!!!. Maganar aure da ‘ya’yanki kuwa kisa ranki a inuwa sassanya, Allah zai baiwa Rayhanah miji na ban mamaki wanda zai kaunaceta domin Allah ya rungumeta da lalurar ta, ba ‘ya’yanki ba, masu hali da akida irin taki, ‘ya’yanki ba sune kadai MAZA a duniya ba! MAZA ma tukunna, baki gansu ba Mami. In kin so ki aura musu ‘ya’yan Queen Elizabeth, karshenta dai kenan ko? Ki rubuta ki ajiye, babu aure tsakanin ‘ya’yanki da Rayhanah! Tunda ita baki dauketa cikakkiyar mutum ba”. “Ba haka nake nufi ba Dacta na?” “To ya ya ne?” “(A bit.......depressed). Ta ce, “Ni dai in hakan za a yi bani da matsala da yarinyar”. Dacta ya ce, “Mami, hoo!” Rahane tuni barci ya kwasheta a kan marbles din dining, inda ta ci abinci. A haka su Abida suka shigo suka sameta, Abida, Jawahir da Azizah suka sunkuya suna kallonta. Abida ta leka tafin kafarta ta ga faso da kaushi! Ta ce, “Ehoo! Yau faso zai yaga bedsheet din Jawahid, don kuwa ba dai gadona ba”. Aziza kuwa dukanta take tana cewa, “Tashi-tashi, cinnaka zai cijeki, ki hau gado”. Jawahir kuwa hannunta ta kama tana cewa, “Tashi muje daki za ki dauki sanyi a nan”. Ta bude idonta a hankali tana kallon su. Ba ta taba ganin kyawawan mutane irin wadannan yaran ba. Dacta ne da Mami suka fito tare jin hayaniyarsu, suka gansu zagaye da ita kamar sun ga wata sabuwar halitta. Mami ta ce, “Mene ne haka? Ku kaita daki mana ta yi wanka sai ta kwanta ta yi barcin”. Abida ta ce, “Ar! Mami kafarta faso! She is smelling bad!! Da soson wa za ta yi wanka?” Dacta ya dunkule hannu ya danna mata, “Da na Uwaki. Ja’ira mara hankali”. Ya matsa gabansu ya ce, “Kamata Jawahir kuje daki ki taimaka mata ta yi wanka, kin gani ba ta da lafiya”. Jawahir ta bi umarnin mahaifinta. Suka shiga daki da Rahane. Ta cika mata ruwan dumi a kwami, ta zuba dettol, ta bare sabon sabulun zest da sabon soso ta bata. Ta ce, “Ki yi wankan sosai kin ji, amma ki yi a hankali kada ki fama ciwukan ki”. Ta nuna mata hanger, “Ga towell nan, ki dauki wanda kike so. Wannan kwandon ki zuba kayan da kika cire kayan wanki ne a ciki”. Rahane ta ce, “Ai ban zo da wasu kayan da zan canza ba in na ajiye wadannan”. Ta ce, “Zan baki nawa in ji Daddy”. Ta juya ta fita tana cewa, “Ki yi wanka sosai”. Rahane ta yi tsaye tana kallon katon ramin da aka cika da ruwa aka ce wai ta shiga ciki tsulum! Ta yi wanka. To idan ta nutse fa? Ta kai hannu a hankali tana shafa gefen kwamin, santsi kamar jikin tarwada. Ga shi fari kal! Shi kansa ruwan kamshi yake. Ta fi minti ashirin ta shafa nan, ta kalli kanta a mudubi, ta kasa ko da cire kayan jikinta. Ga bayan gida tana ji amma ba ta ga masai ba, sai fararen tangaraye a rufe, da ta bude ruwa ne a kwance a cikinsu garai-garai, ta rasa inda za ta sa kanta, domin bayan gidan ya matseta. Ta kuma rasa a inda za ta yi, sai ta goce da kuka. Daga daki Abida da Jawahir suka jiyo ta, Abida ta kyalkyale da dariya ta ce, “Yanzu haka faduwa ta yi cikin soka-way”. Da sauri Jawahir ta iso bakin kofar tana buga mata tana cewa, “Lafiya?” Ta ce, “Tutu nake ji”. Ta ce, “Mene ne tutu?’ Ta ce, “Bayan gida”. Ta murda kofar ta shiga gaba-gadi, nan ta tarar ko kayan jikinta ba ta tube ba balle ta yi wankan, tana tsaye tana share ido. Tausayi ya kama Jawahir, ta bude masai ta zauna a kai. Ta ce, “Haka za ki yi ki yi bayan gidan. Sai ki murda nan ruwa zai fito ya kora shi. Nan kuma shima zama za ki yi ki danna nan zai yi miki tsarki. Ko ki fara gogewa da wannan (ta nuna mata tissue). Sai ki sa sabulu ki wanke da kanki. Kin gane?” Ta ce, “Eh”. “To maza tube ki yi sai ki yi wankan. Ko in cuda miki baya?’ Ta ce, “A’a, zan iya kada ki fama ni. Amma ba zan iya shiga wannan koramar ba ki zuba min a bokiti”. Duk dauriyar Jawahir sai da ta ji dariya. Ta ce, “Ba korama ba ce, amma tunda baki so bari in bude ruwan ya fita, sai ki kunna famfon ciki. Amma wannan famfon na zafi ne”. Ta bude rariyar ruwan ya tafi. Ta kunna mata famfon ta dauko bokitin wanki ta cika mata sannan ta fita. Abida na durkushe bisa dan gadonta rike da ciki tana ta dariya, don duk tana jinsu. Jawahid ta kai mata duka ta falla aguje ta yi falo tana bawa Mami labari. Daga daki Daddy ya jiyota shima ya yi dariya, amma ya ciro wayar charger dinsa ya fito ya yi kanta, ta yi tsalle ta boye a bayan Mami tana “Na tuba Daddy.......Daddy Allah ya huci zuciyarka”. Ya ce, “To kar in kara jin kina mata dariya in ta yi wani abun da baki sani ba, nuna mata za ku yi a hankali ba ki dinga yi mata dariya kina ba da labari ba”. Ta ce, “To Daddy”. [12/24/2019, 17:56] Takori: Haka ta yi jika-jikanta a tsaye cikin kwamin da bokiti, ta daga kafa za ta fito santsin kwamin ya kwasheta ya buga da kasa. Ta sake yunkurin fitowa ta sake shan kasa. Rahane ta ce, “Wannan bala’i da me ya yi kama?” Ta koma ta cure jikinta a cikin kwamin ta yi zamanta. Jawahir ta ji shiru wajen awanni biyu tana zaune gefen gadonta tana jiranta. Da ta tabbatar ba za ta fito ba sai ta mike tana kwankwasa mata ban dakin. Daga ciki Rahane ta ce, “Ki zo ki fiddani na kasa fitowa”. Jawahir ta murda kofar ta shiga ta kama hannayenta ta fito da ita, ta zari tawul ta daura mata suka fito. Jawahir da kanta take shafa mata vaseline a hankali kada ta fama ta. Ta ciro wasu Pakistan ruwan kwaiduwar kwai cikin kayanta ta mika mata ta sa. Sai ta ga Rahane ta kasa sakewa a cikinsu, domin dai a wurin Rahane dogon wando sutturar maza ne. Ta ce, “Don Allah ki bani zani na atampa wadannan santsi garesu”. Jawahir ta yi dan jim, sai kuma ta bude wardrove ta dauko sabuwar danyar vlisco (Holland) dinta ta bata, ta daura mata zanin, ita kuma ta sa rigar. Ta taimaka mata ta daura dan kwalin, sai ta yi kyan gani. Lokacin ne Mami da Dacta suka shigo. Dacta rike da gorar ruwan Myer da ledar magunguna fara mai tambarin AKTH. Yana tafa hannu ya ce, “Yar Dacta! Kin yi kyan gani kamar ba ke ba”. Ita dai murmushi ta yi, ta zame daga tsayuwa gaban Jawahir ta durkusa a gabansu. Da sauri Mami ta dagota ta zaunar da ita a bakin gadon Jawahir tana cewa, “Ki daina yin wannan durkuson mu mun yafe, ko da fatar baki ki gaishe mu kin ji?” Ta sunkuyar da kai kawai. Mami ta karbi gorar ruwan a hannun Baba Dacta ta murda tana juyewa a tambulan mai garai-garai, shi kuma yana ballo mata magungunan da ya kamata ta sha a lokacin. Daya bayan daya yake sa mata kwayar maganin a baki Mami na binsu da ruwa, aikinta kawai hadiyewa.. Dai-dai lokacin da aka kira sallar magariba. A ka’idar gidan duka tare suke yin sallah in har suna gida. Baba Dacta ne ke jan su. To yau ma hakan, karo na farko da Rahane ta taba yin sallar jam’i a rayuwarta. Sai ta ga banbance-banbance da yawa da irin sallah da alwalar da suke yi a kauye. Ashe su kawai dungurawa suke yi su mike, babu irin wannan karatun sallar mai dadi da Baba Dacta yake yi, basa bin ka’idoji da sharuddan da aka wajabta a kan sallar. Sannan bayan an sallame isha’i, sai an dora da shafa’i da wutiri. Sannan ayi hadaka wajen cin abinci a kan tebir. Wanda ba ta san wa ya dafa ya jera su a kan tebir din ba, ita dai kawai ta gansu, ta san kuma ba Mami ta yi ba don suna tare da ita. Daga nan kuma ta ga su Jawahir sun dauko wasu jakunkuna cike taf da litattafai har Aziza ta dauko nata, suka zube gaban iyayensu. Nan da nan suka canza harshe daga iyayen har ‘ya’yan suna ta koya musu ayyukan makaranta. Jawahir ce ke tare da Daddy, ya yin da Abida da Aziza ke tare da Mami. Turanci suke yi zallah ba irin wanda ake musu a TAKAI SPECIAL PRIMARY ba. Sha’awa ta kama Rahane, sai ta ja gefe ta tattara hankalinta a kansu, jefi-jefi Baba Dacta kan kalleta yana kuma sane da yadda ta kafa musu ido babu ko kiftawa. Karfe tara saura minti biyar duk suka rufe litattafan suka maida su jakunkunansu, suka diba suka yi dakinsu. Shi kuma Baba Dacta ya mike cikin tuma-tuman kujerun falon irin leather seats din da ko allura ba ta iya huda su, ya murdo labaran kasa na N.T.A yana sauraro. Kalar kujerun Orange and Black. To haka tattausan kilishin da aka dora akan farin marbles shima ruwan goro ne da ratsin baki, labulayen kuma light orange. Mami daki ta nufa ta yi wanka ta fito cikin shiri, lab coat dinta fara kal da farin gilashi da hand bag rike a hannayenta. Yau aikin kwana gareta a dakin yara na Isyaka Rabi’u (Paediatric-Unit). Ta russuna ta sumbaci goshin Baba Dacta, ta shafa kan Aziza dake barci a kan cinyarsa, ta dubi Rahane dake satar kallon su suna bata sha’awa ta ce, “Ni na tafi aiki Rayhana, dauki Aziza kuje ku kwanta, da wuri ake barci saboda zuwa makaranta”. Ta mike ta ce, “A dawo lafiya”. Ta dauki Aziza a cinyar Daddy ta yi dakin su Jawahir. Likitocin biyu suka bita da kallo cike da tausayi. Mamin ta fita, Dacta ya ci gaba da sauraron labaran tara cike da tunanin hanyoyin da zai bi ya inganta rayuwar Rayhana, wadda Allah ya sanya mishi kaunarta kamar, koma fiye da yadda yake kaunar su Jawahir. Tana shiga dakin karamin gado ta dora Aziza wanda ta fahimci shine nata. Abida da Jawahir sunyi wanka sun wanke baki sun sauya kaya zuwa marasa nauyi wanda a ganinta kayan maza ne (wando). Abida ta balla mata harara ta ce, “Ga (diaper) nan ki sa mata”. (Tana nufin Azizah). Ta yi sukuti tana kallon ta don ba ta san wani diaper ba. Haushi ya kashe Abida, ta tashi da kanta ta sa mata. Rahane na tsaye saboda haushin da ta bata ba ta san sanda ta hankade ta ba, saura kadan ta bugu da karfen gadon Azizah. Jawahir ta ce, “Abida mene ne haka? Wannan ai rashin mutunci ne”. Ita ma ta danna mata tata harar. Ta fiddo ido ta ce, “Sai dai in a gadonki za ta kwanta wallahi ba dai nawa ba, ta yanka min jiki da faso”. Ta dau filo ta jefa a kan marbles ta ce, “Ki kwanta a nan, wa ya sani ma ko kwarkwata ce fal kanta tunda ta zo ba ta bude shi ba.....” Sauran maganar ta makale a makoshinta da ta daga ido ta yi ido hudu da Daddy a tsaye jikin kofa yana kallonta kawai. Ta yi tsuru-tsuru ta yi shiru. Ya dubi Rahane dake sunkuye da kai ya ce, “Rayhanah!” Ta dago a hankali ta dube shi, “Hau gadon Abida ki kwanta”. Da kyar ta iya bude baki a hankali ta ce, “Baba Dacta ba zan iya kwana a kai ba fadowa zan yi, nan din ya isa”. Ya ce, “Hau ki kwanta na ce, ba za ki fado ba”. Ba za ta iya yin jayayya da shi ba, sai ta hau gadon a hankali ta takure a karshensa, duk da ba wani girma ne da shi ba, gadon silver ne karami. Ya dubi Abida da matsanancin fushi ya ce, “Ke kuma dauki filonki ki kwanta a kasan ki ji in da dadi. Abida ki kiyaye ni, ki kiyayi taba min Rayhanah. Ban ce lallai sai kin so ta ba, don ba zamanki take ba, kuma ba a kanki take zaune ba. Kin yi na biyu kada ki sake in ji na uku, karonmu dake ba zai yi miki dadi ba”. Ya ja lallausan bargonta ya rufawa Rayhanah. Ya juya ya fita bayan ya mika mata akwatin hearing aid dinta yana gaya mata yadda za ta adana shi in za ta kwanta ko wanka ko alwala, kada ruwa ya taba shi. Ya kuma nuna mata yadda za ta cire batir din da mayar da shi. Jawahir ta kasa shiru ta ce, “Daddy wannan ai hearing aid ne, me take yi da shi?” Ya dan dubeta ya ce, “Me masu amfani da shi ke yi da shi?” Ta ce, “Karin karfin ji”. Ya ce, “To ita ma Rayhanah haka”. A takaice ya gaya mata hatsarin su Rayhanah, mutuwar kakarta, auren da Babanta zai mata da yadda aka yi ya taho da ita. Jawahir ba ta san lokacin da ta taso ta dawo gadon da Rayhanah ke zaune ba ta rike hannun tad a babu ciwo tana share hawaye. Ta ce, “Daddy ni zan dinga tayata kula da shi ma”. Ya ce, “Allah ya kyautata miki kema Jawahir”. Ta ce, “Zamu kwanta gado daya, ita Abida ta hau nata”. Ya ce, “Wallahi yau a kan tayal za ta kwana, koma gadonki ki kwanta, ita ma gobe za a kawo mata nata”. Ta sauka ta koma. Ya kashe musu wuta ya fito ya jawo kofar yana gaya musu suyi addu’ar kwanciya. Washe gari Abida da ciwon baya ta tashi sakamakon kwanan dandaryar tayal, wannan ya kara fushinta da shigowar Rayhanah cikin rayuwarsu, ta tsaneta, iya kiyayyar da ba za ta iya fassarawa ba. Tunda har a kanta ne yau Daddy ya yi mata haka. Daddyn da ko tsawa mai karfi baya yi musu, sai dai ya yi musu nasiha. A haka suka bi jam’in sallar asubahi tare da Daddyn tana ta kumburi, sannan suka soma shirin wanka don tafiya makaranta. Jawahir ce ta yiwa Azizah ta shiryata cikin kayan makarantarta na play group din DARUL-ARQAM, direba ya kwashe su suka tafi, suka bar Rayhanah ita kadai a dakin ta takure can gefe a kusurwar gado,. Sai yanzu ne kewar Iya Bilki ta dawo mata sabuwa, ta shiga kuka a hankali amma mara amo, domin ta toshe bakinta da dan kwalin kanta. Karfe takwas da rabi dai-dai na safe motar Mami ta shigo farfajiyar gidan, I.M ke tukin, shima a asibiti ya kwana. Jefi-jefi suna hirarrakin da suka shafe su shi da mahaifiyarsa, ya yi parking din motar a muhallinta yana cewa, “Nifa gaskiya Mami zaman yarinyar nan da Daddy ya kwaso bai min ba, kuma ba matsayin ‘yar aiki ba, duk taimakon da ya kamata ya bata na likita da patient dinsa ai ya ba ta, hatta hearing aid din fa shi ya saya da kudi ba kadan ba. To na mene ne kuma na tahowa da ita? Shi bai san yanzu zamani ya canza ba (sunan litafin Takori mai zuwa) Kowa ta kansa yake, ka jawo mutum inuwa shi kuma da ya ji sanyinta ya turaka rana”. Mami ta ce, “To ni dai babu ruwana mun riga mun rufe wannan babin da shi. Da ai na kowa ne HIMU (sunan da take kiranshi kenan wato Ibrahimu)”. Ya kyabe baki bai sake cewa komai ba, ya dauko jakar Mami da lab-coat da sauran takardunta suka shige ta kofar kicin. Firji ta fara budewa ta dauko robar ruwan FARO mai rangwamen sanyi ta sha tambulan biyu. Al’adarta kenan a kullum da safe kafin ta sanya komi a cikinta yana da fa’ida sosai, ga lafiyar jiki da ta zuciya. Ibrahim dakinsu ya wuce don ya yi wanka, jinsa yake kamar a kwatami saboda rashin wankan. Mutum ne mai masifaffar tsaftar gaske, sannan mai baudadden hali. Abin nufi, da wuya ka gane inda Ibrahim Mansur Takai ya sa gaba, ba za ka iya gane farat daya yana da kirki ko ba shi da shi ba, mahaifinsa kadai ya san kansa, shi kuma kadai ya iya tafiyar da shi da baudadden halin nasa. Ibrahim na da kyau, wanda kallo daya za ka yi mishi ka ga hakan. Wankan tarwada, mai tsayi da rashin kauri. Yana da siririn saje a gefen fuskarsa mai laushi da sheki, da ka ganshi ka ga Mansur Takai, ta karan hancin, da manyan idanunsu. Sannan mai tattsauran ra’ayin akidun Malam Nasara. Sai dai kuma mutum ne mai riko da sallah, tabon sujjadar dake tsakiyar goshinsa kadai ya isa shaidar hakan. Ba za ka iya dorar da wani abu a kan halayyar shi ta zahiri da badani ba, wannan sai mahaifinsa, duk yadda kuke da shi kuwa. Nutsuwa irin ta Ibrahim daban take, za ka iya ganin hakan a kan ko me yake yi, kamar cin abinci, sallah, tafiya da duk wani motsi da zai yi ko a karatun likitancinsa. Dacta Mansur na son Ibrahim son da baya yiwa Yayansa Khalipha, saboda komi nashi Ibraheem ya dauko. Magana in ba mai muhimmanci ba ce Ibrahim baya yinta, ko hira ake cikin abokan karatu Ibrahim baya tofa nashi in ba mai ma’ana ba. Kasancewa ranar Lahadi ce, Dacta bai zuwa office don haka basu fito ba shi da Mami sai karfe goma na safe, cikin sassaukar shiga ta zaman gida. Mami doguwar riga ce kirar Kuwait ruwan toka a jikinta, ta kame jelunan kitsonta da ribom. Shi kuma Dacta shirt ce mara nauyi fara da shudin jeans a jikinsa. Ibrahim suka tarar bisa tebir yana kalaci, shima ya yi wanka ya yi fes da shi cikin Hilfiger Jeans ruwan bula, gashin kansa da ya yiwa saisaye yana kwance bakikkirin da shi sai sheki yake. Ga turaren shi mai sanyin kamshi na tashi a hankali a falon. A kujerar dake fuskantar shi Dacta da Mami suka zauna. Dacta ya dubi Mami ya ce, “Rayhanah ta karya ne?” Ta ce, “Anya? Bari in dubo ta”. Ta mike. Da ta shiga dakin gani ta yi kamar ba kowa, can ta jiyo shesshekar kukanta can a kusurwar gadon Jawahir. Ta shiga ta tsugunna a gabanta ta kama hannunta ta ce, “Kuka Rayhanah? Me aka yi miki?” Ta jata jikinta a hankali tana lallashinta. Dacta ma aje cokali ya yi ya nufo dakin don ya ga Mamin ta jima. Shima durkuso ya yi a gabanta ya ce, “Mene ne Rayha? Me ya same ki?” Cikin kuka ta ce, “Iya za ni”. Ya ce, “Daina kuka Rayhanah, addu’a za ki dinga yiwa Iya a duk lokacin da kika tunata. Wanda ya riga ya mutu baya dawowa, sannan baya son kuka, addu’a yake bida. Rayhanah kowa da kika gani yana yawo a doron kasa, wata rana za a wayi gari babu shi. Har mu din kuwa. Ba Iya kadai ba, duk jiran wa’adinmu muke. Duk sanda kika yi sallah ki karanta suratul Ikhlas kafa uku ki ce Allah ya kai mata ya fi ki dinga yi mata kuka. Addu’a take so kin ji”. Ta daga kai. Ya ce, “Good! To taso muje ki ci abinci”. Ya kamo hannunta har dining. Ai kuwa Ibraheem ya aje cokalinsa ya mike, don ba zai iya cin abinci tana wajen ba. She is ugly at all (mummuna ce), ga ciwuka ga dafaffiyar fatar kauye. Wannan abun haushi na Daddy da me ya yi kama? Mami dake hadawa Rayhanah tea ta cira ido ta dube shi ta ce, “Ya ka tashi? Ka koshi ne?” Tuni Daddy ya karance shi. Ya dauke fuska don baya son ganin ma inda yarinyar take kada ya yi amai, ya wuce yana cewa “Eh, Mami”. Ta turawa Rahane kofin shayin, ta zuba plantain da dankali ta tura mata “Ci maza ki sha magani”. Ta karba, amma sai ta dauko filet din da kofin ta zauna a kan marbles ta fara cin abinta. Duk suka yi mata dariya, kuma basu ce da ita ta tashi ba. A wurin Rahane su suna kan kujera ita ma ta hau kujera, ai ya zama rashin kunya. Da suka kammala Dacta ya bai wa Mami ‘master card’ dinsa na (First Bank) ya ce ko nawa ne ta cira ta sayawa Rahane sittiru da sauran kayan bukata. Ta ce, “Ni wannan kan ma na fi damuwa da a wanke. Ba zai rasa dandruff da lices ba (amosani da kwarkwata). Dubi yadda take ta sosa shi”. Haka tasa Rahane a gaba suka tafi saloon din, ita ke jan motar. Ai kuwa kwarkwata ba a magana. Haka ta yi ta biyo kumfar magani na musamman ana fidda ita. Sai da suka tabbatar babu ko daya sannan suka gyara mata gashin. Ba ta da wata suma mai yawa, sumarta ba ta fi a kama a ribbon ba, mai karfi sosai ta asalin Kanawa. Daga nan shagon (Well-Care) ta shiga ta yi mata sayayyar kayan sanyawa masu kyau da tsada. Dogayen riguna ne sai siket da riga, atamfa da les kuma ta ba da dinki a (Diallo) inda ake wa su Abida. Basu shigo gida ba sai bayan azahar. Tuni su Abida sun dawo har sunyi wanka, sai yanzu Rahane ta ga wanda yake kawo abinci ya aza a tebir. Wani kabila ne sanye da Apron fes da shi kamar ma’aikaci. Ta ji Azizah na ce masa Yohan. Da gudu Jawahir ta rungumota ta zame dan kwalinta ta ce, “Rayha kin yi kyau, yau tunda na je makaranta nake tunaninki. Don Allah Mami a kai Rayha makarantarmu”. Mami ta ce, “Ku wuce ku ci abinci ko sai Malam Umar ya zo yana jiranku?” Jawahir ta makale hannun Rahane suka zauna tare, ta ce, “In ce ko kin cire ‘Aid’ din sanda za a yi wankin kan?” Ta ce, “Eh, na cire”. Abida sai cin magani take, ta yi tsaki ta debi abin da za ta iya ci ta yi daki, don ba za ta iya cin abinci gaban wannan kazamar yarinyar ba. Azizah cinyar Rahane ta dare tana ta Alifun Ba’un da A,B.C,D tana da son mutane. Haushi bai kashe Abida ba sai da ta ga an karo musu gado, wato na Rahane ne. Ta zauna tana ta huci, da ta tuna kashedin babanta kuma sai ta fashe da kuka, don ta lura ba yadda za ta yi, kuma da gaske tare Daddy ke nufin suyi rayuwa. Karfe hudu dai-dai Malam Umar ya zo. Yana koyar dasu kira’a ne da Tajweed, sannan suyi lesson a boko. Idan yana kwararo kira’a sai ka ce Ahmad Sulyman, haka idan yana baiwa kowanne harafin Alkur’ani hukuncinsa, kamar marigayi (Malam Datti Ahmad Galadanci) Allah ya yi masa rahama. Rahane na zaune gefe tana sauraron wannan malami, ta ce a ranta ashe mu a Allo shirme muke yi. Ya ja aya ya kuma nuna Abida da ya lura hankalinta baya tare da ita tana ta sokawa Rahane tsinke, ya ce, “Abida, wane hukunci ne da wannan ta’areef?’ Ta zabura ta ce, “Eye? Na’am?” Ya sake maimaitawa. Ta yi tsit! Ya kuwa daddage ya tsula mata dorinar dake hannunsa, bulalar ta shigeta sosai, ta zabura ta sa kuka. Ya ce, “Ko ki rufe min baki ko in kara shauda miki”. Ta toshe bakin da karfi tana kuka. Ya ce, “Tun dazu ina lura dake babu karatun da kike sai tsokana, ko tausayin yarinyar nan ba kya ji. Dubi raunin dake jikinta amma kike son huda mata jiki”. Da mamaki Jawahir ta dubi Abida, don da hankalinta baya kansu. Ya ci gaba da cewa, “To zan gayawa Dacta, don ke na lura fitinanniya ce”. Tana kuka ta ce, “Don Allah Malam ka yi hakuri kada ka fadawa Daddy na daina”. Ya ce, “To kin yi na karshe”. Da haka karatun ya tashi. [12/24/2019, 17:56] Takori: A rayuwar Ibraheem, bai taba damuwa da wani abu bayan iyayensa da karatunsa ba kamar RAYHANAH! Kankanuwar yarinyar da ko kirgar dangi bata fara ba, bata kuma da wani abu attractive da zai dau hankalin namiji ta fannin sura.......bai yarda da kansa ba, don haka ya dauki duk wani motsin da zuciyarsa da gangar jikinsa ke yi a kanta da KARYA........! Jawahir ta Khalipha su suka taimakawa Rayha ta wanke kashin da Abida ta yaba mata, sannan ta yi wanka ta koma ta kudundune a bargonta ba ta ce komai ba. Sai ajiyar rai take. Khalipha ya dora hannunsa a kan goshinta, zafi rau! Ya ce, “Tun yaushe kika fara ciwon kai Rayha?’ A sanyaye ta ce, “Tun jiya”. Ya umarci Jawahir ta kawo ruwa da panadol. Ya ba ta da kansa ta koma ta kwanta. Abida na gefe tana ta kuka domin ta daku a hannun Khalipha ba kadan ba. Sai dai ko kadan hakan bai sa zuciyarta ta russuna ba daga kiyayyar da take yiwa Rayha. Zuciyarta ce ma ta kara tauri da kangarewa, don yarda da ta kara yi Rahane ta zame mata karfen-kafa. Daddy ya daina shiri da ita saboda ita, yau ga Yaya Khalipha dan’uwanta da ba ta hada soyayyarshi da ta kowa a zuciyarta ya yi mata dukan kawo wuka a kan RAYHANAH! Khalipha ya dago idonshi jajir da bacin ran da har zuwa lokacin bai ji ya ragu ba, duk da dukan da ya yiwa Abida. Ya dube ta sosai tana ta kuka ya ce, “I’m warning you Abidah.... don’t repeat it! Don’t repeat it!! Don’t repeat it!!!” Ta ce, “To Yaya Khalipha”. Ya mike ya fita ya ja musu kofar. **** A yau duk gidan shiri suke yi domin halartar bikin kammala karatun su Ibrahim, karshen kure adaka ‘ya’yan Dr. Mansur sunyi. Duka sanye suke cikin English wears kowanne da design din sa, sunyi kyau kwarai. Aziza samfurin ‘george’ Abida da Rayha ‘Mclaren’, Jawahid kuma H&M ne duka riguna da wando domin zama da madaukin kanwa yau da gobe tilas ya koyar da Rahane saka wando. Don su a wurin su (casual wear) ne da babu inda bazasu iya shiga dashi ba. Dr. Mansur baya hana su shida kansa in ya fita waje yake sayo musu saidai ya kudure ya kusan dakatar da hakan da zarar sun shiga sakandire. Kalar kayan kowanne daban, amma duka babu wadda ba yi kyau ba kamar ka lashe. Kai ka ce irin yaran nan ne dake rayuwa a Honolulu. Rahane ta kara da farin hijabi, wanda ya sauka a kan kafadunta. A zahiri duka su Abida sun fita kyau, sun fita haske. Amma idan ka dubi Rahane a wannan lokacin sai ka kara marmarin maimaitawa, saboda kalar fatar jikinta baka mai duhu amma mai sulbi kamar Somali, da dirin jikinta da ya soma bayyana da wata irin kamala da nutsuwa hadi da kwarijini bayyananne daga indallahi. Taron, wanda aka gudanar a dakin taron (Musa Abdullahi Auditorium) dake cikin sabuwar Jami’ar Bayero, ya samu halartar kusoshin ilimi na Najeriya da shuwagabanni, malamai da sarakuna. Farfesoshi da Dactoci, har da mataimakin shugaban kasa. A jawabin mai girma V.C Proffesor Attahiru Jega, ya ce yau shekaru ashirin kenan da jami’ar ta ba da shaidar MBBS mai daraja ta daya, daga nan ba ta kara samu ba sai yau a kan Dr. Ibraheem Mansur Takai. Don haka ‘chevening scholarship’ dake tallafawa hazikan ‘graduates’ na kasashe masu tasowa dake karkashin majalisar Turai ta bashi zabin duk kasar da yake so ya yi specializing a duk fannin da ya zaba. V.Cn ya kare bayanin sa da cewa “Dr. Ibraheem congratulations!” Ya fada tare da mika masa hannu suka gaisa, sannan ya mika masa kwalinsa, ya karkata masa hularsa. Sannan ya dafa kafadunsa yana girgizawa. Sai da Nabila ta san yadda ta yi ta kutsa cikin jama’a tana daukar I.M da V.C hoto duk motsin da sukayi, daga karsh Baba Dacta ya rungumo suka jero tare suna sakkowa daga kan steps din zuwa wajen Mami, wadda ke tsaye harde da hannuwa a kirji, fuskarta ta kasa rabo da kayataccen murmushin dake tattausan bakinta. Itama ta rungume shi Nabilan na ta daukar su hoto. Kwana biyu da taron Baba Dacta ya shiryawa I.M walima a nan reception din gidan. ‘yan’uwa ne na jiki, abokan arziki da abokan aiki na Baba Dacta da Mami, dangin Mami daga Jos, abokan Ibraheem da na Nabila, hatta Hakimin Takai ya zo da iyalansa. Don haka Dacta ya kama musu daki a Tahir. Don duk girman gidan nan cika ya yi da ‘yan’uwa da abokan arziki. Addu’o’i aka fara yi, sannan daya daga cikin malaman Ibraheem (Consultant Dr. Bello Sajoh) ya ba da tarihin Ya Himu, hazakarsa da determinations dinsa kan karatunsa. Sannan ya ja hankalin iyaye kan su karfafi ‘ya’yansu da karatu a fannin kiwon lafiya don taimakon kasarmu da al’ummar mu. Ba wai bamu da masu hazaka bane a Arewa kamar ‘ya’yan Kudu da sauran kasashen da suka ci gaba, a’a, determination wato (kuduri) yaran Kudu dana sauran kasashen da suka cigaba suka fi namu da jajircewa kan goal attainment, sai kuma ZUCIYA. Ya ce, “har yanzu Najeriya tana sahun underdeveloped societis, bai yarda da cewa tana shaun developing ba, saboda rashin zuciya da lalaci irin namu, muyi ta diban miliyoyinmu muna kai wa Turawa don suyi mana magani muna kara bunkasa su alhalin ba a fimu da komai ba. Maimakon masu kudinmu da shuwagabanninmu su yi amfani da miliyoyin wajen gyara asibitocinmu da kawo magunguna masu inganci da kayan aiki ko da a matsayin sadakatul jariya ne. A’a, sai suke kaiwa Turawa suna karawa mai karfi-karfi, kasarmu kuwa da marasa hali ko oho! Ka je asibitin gwamnati irin su Murtala da asibitocin koyarwar mu ka ga yadda ake wulakanta talaka da masu haihuwa. Lafiya ita ce gaba da komai, karatun kiwon lafiya bai yi tsamarin da al’umma ke duban shi da shi ba, nutsuwa kawai yake bukata da jajircewa. Masu hazakarmu sun tattare a (Social Science) maimakon (Physical Science) da Arewa ke bukata, ba don rashin kwakwalwa ba sai tsoro da muka sawa zuciyarmu a kan ilimin. Don haka ne ‘yan Kudu suka fi mu ci gaba a fannin, suka fi yawa a kasashen ketare domin neman ilimin Kimiyya. Dr. Bello ya ci gaba da cewa, “a yanzu sabuwar gwamnatin da muke ciki ta yi alkawura na daukar nauyin daliban Arewa a fannin kiwon lafiya, amma fa sai da hadin kan iyaye. Dutyn sune su ba wa ‘ya’yansu maza da mata kwarin gwiwa a kan ilimin kimiyya, musamman mata a kan (Gynaecology) wanda yake halastacce a addininmu. Ya ba da misali da Ya Himu, kwata-kwata shekarunsa ashirin da bakwai amma saboda samun kulawa da iyaye tsayayyu a kan al’amarinshi da kwarin gwiwar da ya sanyawa ransa da zuciya yau ga shi a cikakken likita (General Practioner) da zai iya duba kowacce irin cuta ta yara ko ta manya ya yi (prescribing) ya fadi maganinta, da yadda za ayi a kauce mata da kuma yadda za a shawo kanta in ta yi qamari. Me ya fi wannan amfani ga al’umma? Me ya fi wannan zama abin alfahari a zuciyar iyaye?” Jama’ar sun ji dadin tunasarwar Dr. Bello, iyaye da yawa sun dauki shawararsa. Ba irin cimar da ba a ci ba. Ibraheem ya samu kyaututtuka na alfarma. Hakimi mukullin dalleliyar mota ne. Su su Rahane yawo kawai suke cikin mutane ita ba ta ma san taron me ake yi ba sai da Jawahir ta gaya mata. Yaya Khalipha ya tafi jihar Sokoto inda aka tura shi bautar kasa. Mami na zaune a falo tana waya da Khalipha, Himu ya fito cikin shiri da alama fita zai yi. Ta yi mishi alamar ya dakata ta karasa magana da Khalipha. Ta gama ta ajiye sannan ta dube shi ta ce, “Ya za ka fita ba ka karya ba?’ Ya yi dan tsaki ya ce, “Ban jin cin abincin yanzu, heart burn ke damuna”. Ta mike ta isa ga table ta hada mishi shayi mai kauri tana firfitawa ta ce, “Atleast ka sha wannan, rashin cin abincinka ya fara damuna Ibrahim. Wai me ke damun ka ne? Na lura tunda aka yi maganar auren nan duk ka bi ka rasa kuzari. Nabilan ce ba ka so ko ya ya ne? Idan ka san ba sonta kake ba don me za ka bata mata lokaci har zuwa yanzu kana yi mata yawo da hankali? Yarinyar nan ta ki kowa sai kai, iyakar soyayya ta gaskiya ta nuna maka, ba ta cancanci rana daya ka juya mata baya ba”. Ta dauko GESTID tana girgizawa, shi kuma ya soma kurbar tean a tsaye. Sai da ya shanye ta zuba gestid din a cokali ta ba shi da hannun ta cikin bakin sa. Fuskarsa da zuciyarsa cike da jin dadin kauna da kulawar da uwarsu ke musu, kamar wasu kananan yara. Ita kwata-kwata bata ganin girman su, kullum yadda take treating su Jawahid haka take treating dinsu, wani zubin har sai Dr. Mansur ya ankarar da ita. Ya ce, “Mami nifa ba yanzu zan yi aure ba, don haka ki ajiye zancen Nabila aside. In ta samu miji ku rufawa kanku asiri ku aurar da ita. Ba zan taba auren macen da ta fara cewa tana sona ba!”. Baki Mami ta saki, ta ce, “Mai sonka kuwa ai shine masoyinka. Bakin da ya furta SO, baya dawowa ya furta kiyayya”. Murmushi ya yi, ya sumbaci goshinta ya yi gaba. “Sai na dawo Mami ba nisa zan yi ba”. Ta ce, “Nima rainin hankalin za ka yi mini Himu?” Birki ya ja, sannan ya juyo. Cikin damuwa ya ce, “Mami ya ya za ayi na raina miki hankali? Cewa nake ra’ayin da ke zuciyata kika tambaye ni? Na gaya miki gaskiyar abin da zuciyata ta yarda da shi. Bayan wannan ma ba zan yi auren zumunci ba Mami”. Ta ce, “Hujjah?” Ya ce, (cikin bude ido kadan) “Hujjoji barkatai”. “Kamar wanne da wanne?” Komawa ya yi cikin kujera ya zauna, ita ma Mamin haka, dab da shi ta zauna. “Idan ma’auratan suka samu kuskuren fahimtar juna, kowanne zai bi bayan bangarensa ne. Sai ki ga su ma’auratan har sun manta sun shirya a tsakanin su amma abin zai yi ta zama a zuciyar iyayen nasu, a dinga kallon juna da shi. Daga nan zumunci zai baci, kin ga garin hada zumunci an lalata shi. Irin zumuncin da na taso na gani tsakanin Mai martaba Hakimi da Daddy ban taba ganin irin sa ba. Bazan yardain zamo sanadin da zai yi tuntube ba ko kankani. Ina son yadda suka faro shi suna yin sada gaskiya su cigaba da yin sa har karshen rayuwar sub a tareda mun samar da tangarda a cikin sa ba. Idan na auri Nabila ko laifi tayi min bazan iya hukuntata ba, zan yi ta yi mata uzuri da Baba Hakimi, haka shima ko wacce irin cuta zan yi mata bazai tada kai ba balle ya kalla, nikuma yadda bana son a danne hakkina haka bana danne hakkin kowa. Don haka auren zumunta baya cikin tsarina, don a ganina auren mugunta ne kawai.”. Murmushi ta yi ta ce, “Hujjarka is invalid. Kai dai kawai ka ce baka ra’ayin Nabila, don in kana sonta har zuciyarka ba za ka tsaya yin la’akari da wadannan kananan abubuwan ba”. Ya ce, “To Mami maganin kada a ji, kada a yi”. Ya mike ya fice ta bishi da idanuwa. Sannan ita ma ta mike ta soma shirin tafiya ofis. **** Kwanaki ke juyawa a hankali su koma satittika, satittika su bada watanni, watanni su bada shekara. Kamar yadda rayuwa take a kullum kenan, komai ma juyawa yake. A haifa, a mutu, a girma, a tsufa. To hakan ce ta faru da Rayhanah, shekarun girma sun soma juyata daga kwaila zuwa matashiyar budurwa. Mai dauke da wasu ilhamomi da dama. A yau Rahane shekarunta goma sha hudu, sun kammala karamar sakandire a Darul-Arqam suna jiran fitowar jarrabawarsu (placement) don wucewa babbar makaranta. Shekaru biyu kenan da wucewar Ibrahim Jami’ar Chicagon Amurka, inda yake fafutukar kwalin zama cikakken (nephrologist) likitan koda. Yayin da Khalipha tuni ya kammala bautar kasa ya fara aiki da Ministry of External Affairs dake Abuja. A yanzu idan kika ga Rayhanah zai yi wuya ki shaidata farat daya. Ta saje da ‘ya’yan Baba Dacta, fari kawai suka fita, sai fatarta ta ba da wata irin kala ta wankan tarwada mai sheki, jikinta ya fara cikowa ya nuna ilimi da hutu zallah. Lokacin da jarabawarsu ta fito, kowacce makaranta daban ta ci. Amma Baba Dacta sai ya tattarasu su duka ya kai su ULUL-ALBAAB (Science Secondary) dake Katsina. Azizah ce ta ci gaba da Darul Arqam. Har zuwa inda yau ke motsi, Abida bata daina cuzgunawa Rahane ba, musamman da aka mai da su nesa da gida babu Baba Dacta balle Khalipha. Jawahir kuwa dama ta riga ta rainata kamar ita ce babbar. Haka take fadawa ‘yan ajinsu da ‘yan hostel dinsu Rayha ‘yar matsiyata ce ta zo ta makale musu, Babanta na kauye ya asirce babansu ya lika musu ita. Sannan a gaban Raihan take fada, don ba tsoron Jawahir take ba. Uffan ko daga ido Rayhanah ba ta yi balle ta yi magana. Son Abida take bilhaqqi, saboda darajar iyayenta da Yaya Khalipha. Khalipha wani irin mutum ne mai matukar tasiri da alheri cikin rayuwar Rayhanah, ko kadan baya son ya ganta cikin rashin walwala. Duk da dai dama ba mai walwalwar ba ce. Abubuwa iri-iri na gilmawa a zuciyar Khalipha a kan Rayhanah, yarinya ce da ta iya takun rayuwarta matuka, ta kuma iya tafiyar da mutum da halinsa. Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shine halayensa ba kyan sura ba. Rahane mai aji ce (classique). Duk da tushenta shine kauye. Ba kyakkyawa ba ce, sannan ba ta da wani abu mai fizgar hankalin namiji banda halayenta. A fuska kam babu kyan, amma a halittar jiki sai an tona cikin dubu kamin a samu goma irin Rayhanah. Ba ta damuwa da lallai cewa sai ta sanya hearing aid in ba lokacin daukar darasi ba. Sai ta yi kwanciyarta shiru a kan gadonta, ta yi ta tunanin makomar rayuwarta. Wato yanzu da Rahane ta kara shekaru, sai ta kara sanin ciwon kanta. Baba Dacta da Mami ba jininta bane, ba ta da kowa da za ta bugi kirji ta ce nata ne banda Babanta. Wanda ke ta fama da kansa a halin yanzu, yau ciwo gobe lafiya ba a san hakikanin abin da ke damunsa ba. Ranar da Baba Dacta da iyalinsa suka gaji da rikonta, ina za ta je? Tsufa ya soma cimma Malam Rashidu. A zahiri babbar matsalar ciwuwwukansa kenan, ta fahimci cewa ita din abin tausayi ce. Karatun nan da Baba Dacta ya tsaya mata take yi shine kadai madogararta sai Ubangijin Talikai. Duniya ba matabbata ba ce, haka komai na cikinta yana da lokaci. Ta fahimci akwai ranar da dole za ta bar hannun Baba Dacta da Mami tunda ba su suka haife ta ba. Ranar da hakan ta faru ina za ta? Takai? Ai ko gida basu da shi a Takai. Babanta babu lafiya ga tsufa, ta kowanne bangare idan ta duba sai ta ga kawai Allah ne gatanta sai yadda ya ga dama zai shirya mata rayuwa. Wani tunani ne ya fado zuciyar Rayhanah farat daya, zuciyar ta ce AURE! Rayhanah ki yi aure ki samu ki kafa naki iyalin ki yi tabbatacciyar rayuwar iyali. Ki haifi ‘ya’yan da za su rungumi rayuwarki wata rana. Amma abin tambayar a nan shine, wa za ta AURA? Wane ne zai iya aurenta da LALURAR ta? Wane miji ne zai juri cewa sai matarshi ta saka inji kafin ta ji magana? Wane ne zai ba ta kwarin gwiwa irin wadda Khalipha ke ba ta? Wane ne mai kirki irin Khalipha? A cewar Abida ita MUNAFUKA ce, son Yaya Khalipha take yi, shi yasa ta damu da shi fiye da kowa a gidan. Idan ita MUNAFUKA ce don tana son mai kyautata mata, ita kuma da take tozartata a bayan idon Khaliphan yaya sunata? They are all the same kenan ko? Kwata-kwata ma ita ba ta san wane irin so Abida ke nufi ba, don ta kan ce ya fi karfin ki.....ba ajinki bane.....me zai ci dake? Ya yi kama da mai saran kofaton Doki ne? Da sauran maganganu irin wadannan wanda inda sabo, to RAYHANA ta saba jin ire-irensu daga bakin Abida. Abida ta fi Jawahir power, ta fita baki, ga tsiwa, ga rainin wayau. In ta raina mutum ya shiga uku. ‘Abida Hukuma’. Sunanta kenan in ji Khalipa, domin duka baya karya mata zuciya sai dai ma ya kara tunzurata ga abin da ake dukan nata a kansa. Ya kara kangarar da zuciyarta a kansa. **** Wani abu da ya kara ta da ma Abida hankali a kan Rayhanah shine, kokarin da ta zo ta fita sakamakon wasa da tsokanar da ta sawa ranta. Sunyi jarrabawar shiga aji biyar, Rayhanah ta kwace 3rd position na ajin wanda Abida ke kai tun farkon shigarsu Ulul-Albaab, ita kuma ta kwaso na goma. Sun zo gida hutu ranar Asabar, a yammacin ranar ne Khalipha ya iso, sanye yake da ‘yar ciki da wando har da babbar riga na wata danyar shadda (sheraton) kalarta coffee wato ruwan kasa. Ya dora hula damanga a kan goshinsa, daman dai Khalipha ba dai iya karya karin hula ba, ita ma ruwan kasa ce. Takalmin fatar damisa ne a kafarshi budadde wanda kudinshi ya haura naira dubu ashirin, Dattijon, daure yake da agogon polo na fata a damtsen hannunsa launin kayan jikinsa. Shigarshi reception rataye da babbar rigarsa a kafudunshi da wata karamar bakar jaka mai dauke da komatsansa masu muhimmanci. Da sassarfa ya soma taka steps don cimma falon sama, sai suka yi karo garam! Da goshinsu shi da Rayhanah. Goshin nasa ya kama ya ce, “Kai-kai-kai! Rayhanah goshi za ki fasa min in rasa matar aure?” Ita ma ta kama nata goshin cikin irin muryar zolayar da ya yi mata maganar da ita ta ce, “Kai Yaya Khalipha, kai ne fa ka kara mini”. Ya bita da idanu luuuu! Wani chemistry ya yi aiki cikin ‘yan dakikai. Ba ta taba ganin irin wannan kallon da Yaya Khalipha ke mata yanzu a idon kowa ba, ji ta yi ba za ta iya jurewa kallon ba don haka ta yi saurin dauke idonta ta rabe ta gefensa za ta wuce, sai ji ta yi ya riko hannunta ba tare da ya juyo ba. Mintuna uku suka dauka a hakan, ta yi saurin zame hannunta da sassarfa ta karasa sauka daga matattakalar zuwa aiken da Mami ta yi mata wajen Mal. Dahiru maigadi. Tun daga wannan ranar Rayhanah ta samu kanta da matsananciyar kunyar Khalipha, ba ta kara bari ya ganta ba, in ta jiyo muryarsa a falo ba ta fita. Shi kuma dama tuni ya daina shiga dakinsu, tunda suka dan tasa. Balle yanzu da suka zama ‘yammata ko yau aka yi musu aure gobe za su haihu. Ya damu kwarai da ya ganta, don haka yake yawan zaman falon amma ko keyarta babu. Mami da Dacta sun je wata seminar likitoci a kan cutar Shan Inna a kasar Algeria, daga ita sai Abida ne a gidan, don Jawahir ma da Azizah suna Jos. Har ya kammala week end dinsa ya koma Rayhanah na mishi boyo. Khalipha Mansur, zaune a ofishinsa yana shigar da wasu sakonni cikin kwamfuta zuwa Nigerian Embassy Accra (Ghana). A kan zuwan Ghanain President (Rawlings of Ghana), wanda zai zo Nigeria cikin satin ya haura Philippines daga Nigeria suka samu matsalar visa za su fito daga kasar Kenya. Haka nan ya ji aikin ya gundireshi. A dan tsukin nan tunda ya dawo daga gida, ya rasa gane kansa, ya kasa gane me ke damunsa. Gaba daya ya tattaro hankalinsa da tunaninsa wuri daya. Ya zubawa tafin hannunshi ido, a hankali kuma ya kai shi hancinsa, still kamshin Escada Sentiment yana nan bai gushe ba, domin ko da ya zo wanka bai yarda ya wanke hannun ba, kada ya daina kamshin turaren RAYHANAH. Khalipha, duk da cewa yana kan gabar kuruciyarsa, kuma a kan matakin da babu macen da ba za ta so shi ba. To fa ba kowacce mace yake kallo da kima ba har ya taba yiwa kansa sha’awar aurenta, mata iri-iri kam ya yi mu’amala dasu tun zamanin yana karatu, anyi abokai cikinsu an kuma yi ‘yammata, sai dai kuma babu wacce mu’amalarsu ta kai labari tsahon shekara daya za ayi hannun riga, don shi bai yarda yana neman yarinya wani ma yana nemanta ba, daga ranar da ya gane hakan duk son da yake mata ya barta kenan har abada. Hibba kuwa da Hakimi ke son ya aura, har ta gaji da jiransa ta kama dahir, yanzu haka har an sa mata rana. Saboda tamaula da hankalin da yake mata. Da fari ya ce karatu, ta jira shi ya karasa, ya dawo ya ce Bautar Kasa. Nan ma ta jira shi. Sai kuma ya dawo ya ce sai ya fara aiki, ta jira shi har ya samu. To fa kuma tunda ya fara aikinsa, bai kara bi ta kanta ba, ita kuma ta ga ba rasa manema ta yi ba zai sa ta tsofe a gida alhalin kuma ba shi da niyyar auren ta. Don haka ta yiwa kanta ludufi ta dauki na damo, ta bar Nabilah da koshin wahala...... Yau shekara guda kenan da kammala karatunsu amma tana nan tana jiran Ya Himu, wanda tunda ya cilla kafa a Chicago ba a kara jin duriyarshi ba, ko waya ba sosai yake yi da jama’a ba, idan ya gaisa da Hakimi sai ya ce a gai da kowa. Sannan ba shi da takamaimiyar lambar waya, wani zubin ma a bakin hanya zai tsaya ya sa (credit card) dinsa a commercial ya kira wanda ya ga dama ya zare abinsa. Kowa na kokari a kan Nabilah ta yi hakuri da Ibraheem amma sai tasa musu kuka. Hajiya Karima kan ce, “Nabila ki yiwa kanki fada ki zabi daya cikin masu sonki ki aura tun tauraruwarki ba ta dishe ba. Kuruciyar ‘ya mace ta dan lokaci ce, shekarunki ashirin da bakwai ga kwalin digiri ga na master, kina tunanin idan Ibrahim ya dawo yadda yake ji da kuruciyar nan zai aure ki? Wallahi shi a lokacin ne zai fara samartakarsa, Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta”. Nabila sai dai ta hura hanci ta zumburi baki, ko me za a ce in dai a kan Himu ne ta bayan kunnenta yake wucewa. Khalipha ya yi baya da lallausar kujerarsa, ya bi jikinta ya kwanta ya lumshe ido. Abubuwa da yawa ke sawa ya so mace, amma ba kyan fuska da kyale-kyale ba, dukiya ko zuzzurfan ilimi. Yana son mace wadda ta san kanta (mai tsare gida da rashin kula maza). Kuma yana son ta kasance mai aji ba kyakkyawar da kowanne karabiti zai biyota a dalleliyar mota ya ce yana sonta ba. Yana son mace mai kunya, wadda ba ta iya hada ido da namiji in ba dole ba. Mai karancin magana, ba wadda za ta zauna cikin mutane ta yi ta zuba kamar ‘ya’yan kanya ba. Baya son mai alfahari da son nuna iyawa, baya son mai gwalli da kwarkwasa, baya son wadda za ta cika fuska da jan baki, eye shadow da su maskara da hoda. Baya son wadda za ta rambada ‘yan kunnaye da sarkoki bula-bula (Barima da hudar hanci sun isa). Baya son mai hasken kanti, sai baka mai gogaggiyar fata tunda shi fari ne sol, wadda ba mai ne ya gogeta ba, irin yanayin da take ciki ne. To amma ya hanga ya duba cikin mata bila adadin bai ga mai wadannan extraordinary characteristics din ba sai RAYHANAH, bai taba jin yana so ya yi aure ba sai yau. Ba kuma da kowa ba da ita kadai Rayhanan Baba Dacta. Hannunta kawai ya kama (by mistake) a ranar ya tuna cewa ashe shima NAMIJI ne mai bukatar mahadin rayuwa. Lokaci daya kuma lalurar Rayhah ta fado mishi a rai LOVE HAS NO BARRIER ( soyayya bata da shinge). Hasali ma Ji ya yi lalurar tace tun farko ta dasa tausayin ta a zuciyarsa, wanda yayi ta rikida har yau daya bayyana ainahin kalarsa; daga tausayi zuwa kauna. Lalurar ce kuma har ila yau, da tsantsar hakurin ta akanta da komai ma na rayuwa ta sa ya kara sonta da tausaya mata. Ya ji wani bangare na zuciyarsa na gaya masa kai kadai ne za ka aure ta ba tareda lalurar tat a dame ka ba, ka zauna da ita cikin kowanne hali. Tana da lafiya ko bata da lafiya. Ka tallafi maraicinta, ka tallafi kanka ta hanyar samarwa zuciya abin da take so, in addition ka samawa ‘ya’yanka uwa ta gari, ka kuma mallaki ragamar rayuwarta da ita kanta Rayhanah. Ya lumshe ido a hankali ya koma ya jingina da kujera. **** Duk yadda ya so ya je gida a satin hakan bai samu ba, sai da ya gyara matsalar visar Rawlings daga Nigeria zuwa Philippines. Kawai so yake ya yi tozali da Rayha. Duka kannenshi akwai hotonsu cikin wayarsa, Raihahn ce kawai babu. Ya dokantu, ya jigatu a tsayin satin gaba daya da son ganin Rayhanah. Ranar Juma’a da daddare Mami na zaune gaban madubinta tana shafa bayan ta fito wanka. A gefen ta Rayhanah ce take jera kayan Mamin da aka kawo daga wanki a sif din Mamin. Doguwar riga ce ruwan bula a jikinta da farin Hijab mai santsi iya kafadunta, sallamar Khalipha a falo suka ji yana fadin “Mami na!” Ta ce, “Ina zuwa”. Ta karasa shafar ta sanya kaya tana ce da Rayhanah “Dan hayaniyar nan ya iso yau kunnuwanmu ba hutu”. Ai da jin haka Rayhanah ta lallaba ta shige bayin Mamin ta rufe kanta ta yi zamanta a kan kwamin wanka tana kokarin daidaita numfashinta. Khalipha ya zame mata dodo, ita kanta ba ta san dalili ba, zuciyarta na jigatuwa a duk lokacin da ta tuna shi. Wannan ya fara ne tun ranar da ya rike mata hannu, ta kan samu kanta cikin yawan tunaninsa da mafarkin sa cikin barci. Wani al’amari ne mai girma da zuciyarta ke fama da shi a kansa da ita kanta ba za ta iya fassarawa ba. Abida tana Takai, Jawahir ce da Azizah a gidan, ita ma Mamin night duty za ta tafi. Don haka a kintsenta ta shigo falon da lab-coat a hannu. Ta ce, “Muje ka sauke ni ma gaisa a hanya”. Tare suka fita. Rahane ba ta fito ba sai da ta bari suka fita ta lallaba ta koma dakinsu ta kudundune ta hau barcin dole. Tana addu’a cikin ranta Allah yasa kada Yaya Khalipha ya neme ta. Da ya dawo ba kowa a falon, Azizah ce ta fito daga dakinsu da gudu Jawahir ta biyo ta da duka. Ai tana ganin Khalipha ta yi tsalle ta dane shi, “Yaya Khalipha boye ni za ta duke ni”. Ya kuwa boye tan, ya ce da Jawahir da ta karaso, “Kina tabata zan rama mata”. Jawahir ta turo baki a shagwabe ta ce, “Don baka san me ta yi mini bane Yaya Khalipha, duk ta cike min text books dina da zane-zanen ‘yan aljanu”. Abin ya bashi dariya. Ya ce, “Wai haka Zizahna?” Ta ce, “Yi hakuri Anti Jawahir ba zan kuma ba”. Ya ce, “To kin ji ta baki hakuri, sai ki yi mata afuwa Allah yana son masu afuwa”. Ta juya ta shige daki tana kumburi. Ya ce, “Zizah ina Rayha ne?” Ta ce, “Tana wanka”. “To maza je ki gano min ko ta fito ki ce ta zo ta karbi ‘She stillborn’ din da ta bani sautu tun last month sai yau na samu”. Ta juya da gudu ta yi dakin. Lokacin da ta fito wanka kayan sallarta da hijab dinta dogo har kasa ta sanya ta tada ikama, don haka da Azizah ta ga tana sallah sai ta koma ta ce da shi tana sallah. Ta yi wucewarta harkar gabanta. [12/24/2019, 17:56] Takori: Haka Rahane ke ta hakuri da Abida, kullum da nau’in wulakancin da za ta yi mata, amma ko cira kai ba ta yi balle ta dube ta, A kwanaki talatin da suka biyo baya, Rahane ta ware sumul! Duk ciwukan jikinta sun kame sai tabo. Ta yi haske, amma ba mai yawa ba. Rahane ba kyakkyawa ba ce, amma halayenta masu kyau ne. Sai suka sayo mata kyan a idaniyar jama’ar da ta samu kanta a cikinsu. Mami ta sha gwada Rahane ta fannoni da dama amma ba ta sameta da wani hali mara kyau ba. Akwai sanda za ta kirga kudi ta aje a gefen gadonta ta kira Rahane ta ce ta dauko mata wani abun, ta dawo ta kirga kudinta dai-dai take samun su. Anyi haka ba sau daya ba. Kuma babban abin da ke burgeta da Rahanen shine, rashin son maganarta, da rashin son hayaniya, wadatar zuci, sannan duk da kasancewarta bakauya, to ba ta fiye fiddo kauyancin ba. Ga hidima da Azizah kamar kanwarta ta jini. Sun shaku sosai. An ce mai Da wawa...... to hakan ce ta faru da Mamin. Ta kai ta kawo har barci Rahane da Aziza a gado daya suke yi. Abida ba ta fasa halinta ba, sai dai in Daddy na gida ko Jawahir ta bude mata wuta. Uffan Rahane ba ta ce mata, ita har ta saba ma da rashin mutuncin Abida. Ina wuta Abida ta saka Rahane! Ranar da ta ganta shirye cikin uniform irin nasu direba zai kai su makaranta. Rahane aji hudu aka sanyata da aka yi mata gwaji, Abida da Jawahir na aji biyar. Dacta da kansa ya kaita, ya yi mata komai na zama cikakkiyar dalibar DARUL-ARQAM, sai dai Allah ya biya shi. Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a zo ba. Rahane ta samu kanta a sabuwar makarantar addinin Musulunci ta DARUL-ARQAM dake cikin tsohuwar Jami’ar Bayero. Babu laifi tana fahimtar karatun, sai dai abin ya zo mata da tsauri kwarai, a hakan dai ake kukkullawa don Malam Umar yana taimaka mata sosai, musamman da yake ya lura tana da sha’awar karatun, fahimta ce sai a hankali, musamman idan aka yi la’akari da inda ta faro karatun nata. A haka suka samu hutun karshen zango suka yi jarabawa. Kamar koyaushe ‘ya’yan Dacta Takai sun dauko na dai-daya a ajujuwansu har Azizah, Rahane ce ta dauko na ashirin cikin su arba’in. Abida ta yi ta sheka mata dariya a mota. Sai dai kamar yadda ta zata Daddy zai yi fushi da Rahane, ba ta ga hakan ba, yaba mata ya yi, ya kuma kara mata karfin gwiwa. Sanda Malam Umar ma ya basu hutu Dacta ya shirya musu tafiya Takai don ziyarar dangi, kuma Rayhanah ta ga mahaifinta za su yi kwana biyu, wato Asabar da Lahadi. Ibraheem ke jan motar wanda ta ji kannen shi na kiran shi YA HIMU wato an yanke farkon sunan an kira shi da karshe. Rayhanah ta rasa irin kiyayyar da wanan dan tahaliki ke gwada mata. Bai taba yi mata magana ba, haka bai taba daga ido ya kalle ta ba. Duk da ta lura rashin son magana halinsa ne, amma ai yana amsa gaisuwar kannensa. Wani lokacin har yana daukar Azizah su fita harabar gidan, amma ita bai daga ido ya kalle ta. Duk da dai bai fiya zaman gidan ba yana hattama karatunsa,. A cikin motar ana ta hira, Rayhanah da Ibraheem ne kadai basa magana. Daddy ya ce a ransa, “Duk halinsu daya!”. Ana sallar Azahar suka shiga Takai, kai tsaye gidan Hakimi suka zarce. Uwargidan Hakimi Haj. Karima mace ce mai kirkin gaske, kuma ita ce uwar dakin Dr. Asma’u. Tana da yara tara duk mata, duk ta aurar dasu sai autar ta Nabilah wadda ke masifar son Ibraheem, duk sanda suka zo Takai ita ce ke kula da al’amarinsa. Sai dai shi din har yanzu babu wanda ya san inda ya sa gaba a kanta, tunda har yana kula ta, suna shiri sosai. In sun je gidansu can Kano ko su sun zo Takai, kuma suna waya sau-tari, duk da shi ba kowanne lokaci yake harkar wayar nan mara kan-gado ba, a kwana ana yinta, a wuni ana yinta, babu sallah babu salati, babu amfanawa kai komai, amma ko salatin Annabi ba kowannenmu ke yi kullum ba ko da cikin carbi ne. Amma waya ita ce rayuwar al’umma a yanzu. Idan ya kashe waya sai week end yake bude ta, week end din ma idan baya komai, kowa dake tare da shi ya san hakan. Sai Hajiya Indo, ita ce uwar ‘yan mazan gidan, mai bi mata Sadiya, ta rasu wajen haihuwa, sai ta dauki ‘yar ta rike, tunda dama ita duk ‘ya’yanta maza ne sunanta Hibba, sa’ar Nabila ce, ita kuma ita ce ake wa Khalipha kamu, da ita da Nabilan duk suna karatu a Canadian Univeristy of Dubai, yanzu ma sun zo hutu ne. Sai amaryar Hakimi da ya aura bayan mutuwar Sadiya Inna Luba, tana da yara biyar maza da mata. Hajiya Karima ta dubi Rahane dake zaune gefen Mami ita da Azizah, da yake su Jawahir duk sun fice cikin sa’anninsu. Ta ce, “Ina kika samo ‘ya mai nutsuwa haka? Ko mai rainon Azizah ce?” Ta ce, “A’a, ‘yar amana ce Dacta ya bani”. Hajiya Karima ta sake juyawa tana kallon Rahane ta ce, “To ko ita ce na ji Nabilah na labarin Dacta ya tafi da ita daga nan Takai? Babanta kuma na nan tare damu?” Ta ce, “Ita ce”. Tana lallatsa wayarta. Hajiya Karima ta ce, “Allah sarki! Ai kuwa na ji Mai Martaba yana yabon Babanta, ya ce dattijon kwarai ne yana kula da Barga yadda ya kamata. Dawakansa sun kara lafiya da girma, sannan kullum fes suke, wajensu fes kuma ba ya karbar ko taro in ba ihsanin kansa ya yi masa ba”. (Not interested ga hirar) Dacta ta ce, “Allah sarki, ita ma Rayhanah ba ruwanta”. Wata baiwar Haj. Karima ta shigo, ta umarceta da ta raka Rahane wajen mahaifinta. Ta kama hannunta suka fita. Azizah ta like mata sai ta bita. Mami ta ce, “Dauke ta ku je”. Ta kuwa sungumi Azizah a bayanta suka tafi. Mahaifinta ta fara yin tozali da shi durkushe gaban wani kosasshen doki yana rage masa kofato. A gefe Ibrahim ne ke shafa gashin wata godiya sabuwar haihuwa. Ga yadda ya mai da hankalinsa a kan dawakan za ka fahimci yana son su. Da gudu ta karasa ta zube gaban Babanta tana dariya. Ibraheem ya kallo su ta gefen ido, sai suka ba shi tausayi, su wadannan wato basu da kowa sai junansu, amma wai shine yake jin haushi don mahaifinsa ya taimake su. Ya manta cewa duk wanda ya taimaki dan’uwansa Musulmi shima Allah zai taimake shi, shi yasa mahaifinsa kullum cikin nasara yake, saboda taimakon da yake yiwa al’umma. Balle maraya da Allah da kansa ya ce a taimake su. Yana kallon su kowannesu bakin shi ya ki rufo. Ta ce, “Baba kai ne ka yi kyau haka?” Shima ya ce, “Rahane ke ce?” Sai suka sa dariya. Ta ce, “Allah Baba in a hanya na ganka ba zan ganeka ba”. Ya ce, “Ni din kuma fa? Kin canza gaba daya Rahane”. “Sai mu gode Allah Baba, suma mu gode musu. Mu ci gaba da zama dasu cikin amana, Allah ya ji kan Iya”. Sai tasa habar zaninta ta share idonta. Shima kokarin mai da kwallar idanunsa yake, ya ce, “Amin ya Allah, Rahane ki yafe ni a kan tirsasawar da na yi kan cewa sai kin auri Ado shine silar da Iya ta rasa ranta don ta tserar dake daga wulakantacciyar rayuwa. Wallahi nima kaina a lokacin ban san dalilin da yasa nake tsoron Ado ba, sai yanzu na gane ba haka ya barni ba, to Allah ya fishi”. Ta ce, “Kada ka ce kai ne silar rasuwar Iya Baba lokacinta ne ya yi, ko tana dakinta ajalinta ya zo, dole za ta tafi. Baba Dacta ya ce duk sanda muka tuna ta addu’a za mu yi mata, suratul Mulk, Yasin da Ikhlas, shine soyayya ta gaskiya da zamu yi mata”. Ya ce, “Ikon Allah, Rahane har ilimi kin kara da hankali”. Ta ce, “Ai Baba makaranta muke zuwa safe da yamma, da dare ma su Baba Dacta na koya mana”. Ya ce, “Alherin Allah ya tabbata a garesu”. Himu ya bar wurin don basu ganshi ba, kuma baya so su ganshin. A soro na biyu suka ci karo da Nabila ta hado abincinsa cikin kwandon kayan abinci. Ta ce, “Ya Himu ina ka shiga ne? Ga shi ina ta kiranka ya ki shiga”. A takaice ya ce, “Ina barga”. Suka juya cikin gidan tare. Yana zaune ya mike dogayen kafafunsa a kan tattausan kilishin (sitting room) din da suke zaune, Nabila na faman zuba mishi jellop din cous-cous wadda ta ji kayan lambu, a gefe cikin dan tangaran farfesun hanta ne, ta diba a cokali ta kai bakinsa. Ya yi murmushi ya karbi cokalin daga hannunta yana ci suna ‘yar hira. Sai dai duk rabi Nabilan ce ke yin hirar tana ba shi labarin rayuwar makarantarsu. Sama-sama yake sauraronta, He is curious about something different (wani abu daban yake son sani) kan Rayhanah da Babanta. Kadan ya ci ya cika ruwa a tambulan ya sha. Ya mike yana laluben mukullansa a aljihunsa ya ce, “Am coming Nabeelah (ina zuwa)”. Ibraheem Mansur, (HEEMU ko I.M) kamar yadda kannensa da abokansa ke kiransa. Bai da shiga sharo ba shanu balle abin da bai shafe shi ba. Amma a yau, haka nan ya samu kansa da son sanin asali da tushen su Rayhanah, da rayuwarsu ta baya. Abinki da karamin gari, kowa ya san kowa. Don haka bai sha wuyar samun tarihin su Rayhanah ba. An gaya mishi uwarta ta rasu tun lokacin haihuwarta, kakarta da suka yi hatsari tare ita ta raine ta. Har makarantar su Rahane ya je ya binciko takardunta. Malamansu sun shaideta wajen kokari da son karatu. Sai ya ji hankalinsa ya kwanta da rayuwarta tare dasu. Sai dai ko a fuska bai nunawa Baba Dacta komi ba. Malam Rashidu ya samu kyakkyawar shaida daga bakin makwabtansa. Amma a da sam hankalinsa bai kwanta da zaman yarinyar tare dasu ba, saboda halin rayuwa da butulci irin na dan Adam. Sai kuma yake tambayar kansa, shin me yasa ya damu kansa kan yarinyar? Damuwa irin wadda bai taba yi a kan kowa ba??? Ya tattara zancen ya watsar ya shiga sabgoginsa. Da yammacin ranar yana barga tare da kaninsa Sha’aban dan Hakimi, kowannensu ingarman doki ya zaba Sarkin Dawaki ya aza musu sirdi suka dane suka nufi ‘yar shakatawa bayan gari. Suna tafe hira suke yi kan sabbin gine-ginen zamani da Hakimi ke yi a cikin garin da ginin gidan saukar baki mai dauke da bukkokin zamani, inda Turawa ke sauka idan sun kawo ziyara. Haka nan Hakimi na sauke bakin alfarma idan sun zo. Ibraheem ya yi sha’awar wadannan gine-ginen sosai. Yake ce da Sha’aban duk lokacin da ya tashi ginin gida zai sanya ‘Hut’ wato bukka ta gargajiya mai suffar zamani. Sanda suka dawo magariba ta gabato, suka sauka daga dawakan suka soma alwala a famfon wajen. Kamar an ce da Ibrahim ‘juya’, ya hango Rahane na yankewa Babanta akaifa da nail cut. Sai dai bai jin me suke cewa a tsakaninsu. To haka washe gari da misalin karfe goma na safe ya shigo bargar domin an kawo sababbin (Polo Horses) daga Ireland duka na Baba Dacta ne, yake ba da hayarsu ga masu sana’ar tseren Dawaki ake masa kiwon su anan bargar hakimi. Sun bambanta sosai da sauran dawakan ko daga koshinsu da shekin da suke yi da kuzari. Ya dan juya ido sai ya hango Rahane da jibgin kayan wankin Babanta da ta tattaro tana ta dirzarsu kamar Allah ya aikota. Shi kuma Baban yana gefe yana yiwa dawakin askin jelarsu da katon almakashi. Yana cewa, “Wato Rahane ba kya jin magana ko? Na ce ki bar wankin nan ya fi karfinki in na gama zan yi abina”. Ta ce, “Albarka nake nema Baba, ka barni in samu, in ban yi maka ba wa zan yiwa? Idan mun tafi ban san yaushe zamu kara dawowa ba”. Ibraheem ya jinjina kai suka kara ba shi tausayi. Washegari suka yi sallama da kowa za su tafi, Rahane har kuka ta yi saboda ba ta son barin Babanta. Amma ba ta bari Baba Dacta ya gani ba, sauri ta yi ta dauke hawayen da yatsunta. Da gudu ta koma ta sake rungume Babanta, sannan ta shiga mota tana share hawaye da sauri. Har Ibraheem ya kunna mota ya hango Mal. Rashidu tafe da sassarfarsa rike da katuwar leda, don haka ya dakata. Baba Dacta ya sauke gilashi sai ya mika masa, “Yalo ne da kashu (cashew) babu yawa a yiwa yara tsaraba”. Hannu biyu Baba Dacta yasa ya karba, ya ce, “Yara sun gode Baban Rayhanah. Allah ya kara nisan kwana”. Ya sanya hannu cikin aljihu ya zaro naira dari biyu ya mikawa Aziza, “Ungo yarinya ka sha ruwa a hanya kin ji?” Mami ce ta karba fuskarta fal fara’a ta ce, “Aziza ta gode Baba”. Ya daga musu hannu suka ja motar suka tafi. Abida ta juyar da kai gefen taga tana tsaki mara sauti. Kamar ta rufe Mamin da duka da ta karba. Su kuwa iyayen sun ji dadi har ransu. ALHERI komi kankantarsa dadi gare shi, amma ga wanda ya san mutuncin dan Adam. Kafin la’asar sun iso Kano. A harabar gidan bakuwar mota ce kankanuwa mai santsi (one door, Camero) fake a harabar adana motoci. Ai kuwa daga Jawahir, Abida har Azizah fita suka yi a guje har Azizah na faduwa, ta kuwa fashe da kuka, don har bakinta ya fashe. Da sauri Rahane ta fito ta dauke ta tana goge mata jinin dake fita daga bakinta. Mami na ta fada za su kashe mata ‘ya sai ka ce yau suka fara ganin Khalifan. Amma ko jin ta basu yi ba balle su tsaya. Sai da suka dangane ga dan’uwansu suka rungume shi. Khalipha na zaune ne a kan kujerar zaman mutum biyu, gwangwanin Maltina ne a hannunsa yana sha, amma saboda rungumar bazata da kannen suka yi masa gwangwanin ya fadi ya zube a cinyarsa. Farin kaftan nashaddah (hilton) ne sol a jikinsa dinkin Mohammed, amma haka suka wanke shi da Maltinar. Hakan bai sa ya yi fushi ba, surar Azizah ya yi daga hannun Rayhanah ya yi sama da ita ya cilla ya cafe. Ya ce, “I’m missing you.....” Ya hadasu ita da su Abidar ya rungume gaba daya yana durkushe dai-dai tsahon su. Ba tare da ya ankara da bakuwar fuskar dake gefe ba. Ita Rahane daki ta wuce don ta ga hankalinsa na kan kannenshi ko ta gaishe shi ma ba jinta zai yi ba, ta ce bari ta bari sai ya nutsu sai ta gaishe shin. Khalipha bai samu kansa daga hayaniyar su Azizah ba sai da aka kira sallar magariba. Ya mike dauke da Azizah ya kawota dakin Mami, lokacin ita Mamin tana shirin yin sallah ta wuce asibiti, don yau ma aikin kwana za ta yi. A gadonta ya dire Azizah ya ce, “Mami Dactan nan (Himu) ya bar miki mukullin daki ne?” Ta ce, “Ka duba yana jikin kofar”. Ya rungumeta ta baya ya daura kai bisa kafadunta ya ce, “You didn’t miss me Mami.....” Ta ce, “Sai in yi ta rawa ina tsalle ka dawo sannan ka yarda na yi kewarka”. Dariya ya yi ya juya ya fita. Wanka ya yi, sannan ya daura alwala, ya zuba wata shadda kaftan ruwan kasa. Khalipha Mansur baya sanya kananan kaya sam, sai shaddah, yadi ko jallabiyar Saudi ( in a gida ne). Shi yasa Mami ke kiranshi (Dattijo) a yawancin lokuta. Daga kallo na farko da ka yiwa Khalipha za ka gane mutum ne mai faram-faram da haba-haba da jama’a (sociable) sabanin Ibrahim (anti-social in nature). To haka a kamanni da sura, Khalipha Mami ne sak, fari sol da shi, ga tsayi ga zati. Kwayar idanunshi ba baka ba ce (brown) ce mai sheki. Da ka ganshi ka ga Mami. Kamar ta yi kaki ta tofar. Khalipha na da kirkin da Ibrahim bai da shi, ko daga mu’amalar kauna bayyananniya dake tsakaninsa da kannensa, wadda basa samu daga Himu ko kadan. Don haka suma basu dauke shi da wasa ba, suna bala’in kaunarsa. Ya damu dasu suma sun damu da shi sosai ba kadan ba. Daga sanda ya zo gidan Mami da Daddy sun huta da koyar da yara aikin makaranta. Ya hada digiri dinshi mai daraja ta daya daga Jami’ar (BAZE) a kan hulda da kasashen ketare, sai jiran posting din Bautar Kasa. Yadda kamanni da halayya suka sha ban-ban tsakanin Himu da Khalipha, haka dabi’u da akidu. Khalipha dattijon ne da gaske, yaro mai halin manya. Don haka shi kansa Daddyn ma sau tari kan kira shi da (Dattijo). Bayan sallar isha’i duk suna bisa tebir kamar yadda yake a al’adarsu. Rahane ta fito jaye da hannun Azizah, tana ta rigima duk hancinta ya toshe da mura. Rahane sai aikin share mata hanci take da hawaye duka, da guntun tishu dake hannunta. Ya dan juya ya dube su jin Mami na fadan a daina kunna A.C da daddare tunda ba lokacin zafi ne ba. Ya dan kara juyowa sosai ya kalli yarinyar don a da ya yi zaton idonsa ne bai gani sosai ba, ya dubi Mami ya ce, “Ina kika samo ‘ya?” Ta ce, “Allah ne ya bani”. Kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru ya ci gaba da cin abincinsa. Don ya ga bai kamata ya ci gaba da yiwa Mamin tambayar a gaban yarinyar ba. Rahane kujera ta hau kusa da Jawahir, don ko kadan ba ta zama daf da Abida, sakamakon kisan mummuken da take mata, ‘yan yatsunta take murjewa da kafar kujerarta, ko ta faki idon kowa ta takata da tsinin takalminta da take sawa musamman don muguntar. Iyakaci a ga tana kuka in sun koma daki, tambayar duniyar nan Jawahir za ta yi amma sai ta ce babu komai Iya take tunawa. Sai dai kuma ta yiwa kanta maganin abun, ta daina yarda ta zauna kusa da ita. Wanda hakan bai yiwa Abida dadi ba, don dai ita nan duniya babu wanda take jin haushi irin Rayhanah. “Zauna mana Rayhanah”. In ji Mami. Ta zauna sosai ta fara cin abincin da Mamin ta yi serving dinta. Sakwara ce da miyar alayyahu da ganda da kifi, musamman don Khalipha Mamin ta yi girkin da kanta, don nan duniya ba abincin da Khalipha ke so irin sakwara. Sunanshi na ainihi sunan mahaifin su Mami ne da ya Musulunta wato (Abdallah). Dacta Mansur da bai iya fadi a matsayin sunan na sirikin sa mai rasuwa shine yake cewa Khaliphan, to sai kowa ya kama. Abdallah ta bace bat, sai Khalipha. Da kyar Rahane ta iya cin abincin nan saboda kallon ta da Khalipha ke yi jefi-jefi. Ga kukan Azizah ya dameta, jinsa take har cikin ranta. Ko kadan ba ta son kukan yarinyar. Garin kallon nashi ne ya hango aid din dake makale bayan kunnenta. Ya zare gilashin shi a hankali yana kara kalla ya ce, “Mami bakuwar taku ba ta ji ne?” Ta bata fuska ta ce, “Wai kai Khalipha baka gani ka yi shiru ne sai ka ce dan jarida?” Ya maida gilashin sa yace, “Sorry Mum, I’m curious in cases like these….!”. Ta ce, “Iftila’i na rana daya, sun samu accident ne shine sanadi”. Yace “ta yaya accident zai zamo cause to hearing impairment? Ku dai kara bincikawa, haka kawai ma ji kan dauke, mostly as a result of typhoid fever ko meningitis, ko kuma hereditary factor (gado) na amosanin kunne (otesclerosis)”. Mami tace “to Dr. Khalipha, babu daya kanwar biyu, professionals basu ga hakan ba har sai sun gudanar da CT Scan and MRI Scan wanda abune dake neman naira miliyan biyu cash. Kuma ba’ayin shi a Nigeria. Mahaifinta kuma ya tabbatar lafiyar ta kalau ta baro gida kamin suyi hadarin kuma bata gada daga ko’ina ba (uwa ko uba)”. Ya mikawa Rahane hannu wadda ta sunkuyar da kai...... “Shake my hands, Rayha.....” Murmushi ta yi amma bata bashi hannun ba. Ya ce, “To shi kenan tunda bakya abotar dani”. Ya fada cikin launin shagwaba da langabar da kai. Ba ta san sanda ta yi dariya ba, fararen hakoranta yiri-yiri farare sol suka bayyana. Babba dashi yana shagwaba a gaban mamarsa. Ya ce, “Do not your problem slow down, you will achieve a lot in life!” Ita bata ma ji mai ya ce ba saboda yadda harshensa ke harde da Turanci gangariya, sai gwani a harshen ne kadai zai iya fahimtarsa. Wannan ya samo asali ne da haihuwar Khalipha da Himu da Mami ta yi a Ireland (Dublin). Inda Khalipha ya yi karatun shi har zuwa aji biyar na sakandire kamin su tattaro su dawo Nigeria. A haka aka kare cin abincin. Koyarwar Yaya Khalipha daban take, ko yaro shine jaki wajen dakikanci dole ya gane koyarwar Yaya Khalipha. Da ya zo kan littafin Rahane, ya gane Rahanen na da rauni a lissafi (Mathematics) don haka ya tabbatar ta yi a gabansa dai-dai sannan ya kyaleta. A daren ne Mami take ba shi labarin Rahane, ya saurara da nutsuwa. Yana tsaye jikin balcony na dakinsu yana kokarin kunna Marlboro da lighter ya hango Abida ta fizge hearing aid din Rayha ta yi cilli da shi tana cewa. “Banza ‘yar kauye, wadda bata ji said a inji, ai sai ki ji mu gani”. Da gudu Rahane ta bishi inda ta yar ta dauka, sai ta ga ya fashe. Abida ta gudu tana kyalkyala mata dariya. Durkushewa ta yi a nan tana kuka don ba ta san me za ta ce da Baba Dacta ba, domin ya yi mata gargadi sosai a kan takula da shi, ita kuma ba za ta iya ce da shi ga laifin Abida ba. Da hanzari ya ajiye abin da ke hannunsa ya fito zuwa harabar gidan, tsugunawa ya yi gaban Rahane ya karba yana gyarawa. Ido ta dago ta dube shi sai ta hau share hawaye da hanzari, don bata so ya ganta tana kukan ba. Da ya gyara sai ya mayar mata ya ce, “Tafi gida”. Tun daga ranar Khalipha ya sa ido a kan mu’amalar Rayha da Abida, Jawahir da kuma Azizah. Ya gane Abida bata son Rayhanah sam-sam, komi ta yi sai ta kushe ta gwale, ta wulakantata. Ya ci gaba da bibiyarsu da hankali, nan ya gane kaunar da Jawahir ke wa Rahane, suna son junansu sosai, da kaunar da Rahane kewa Azizah wadda ta sayo mata kauna a zuciyar Mami. Tara Abida yake yi, bai yi kuma niyyar sanarwa Daddy ba shi zai yi maganin abin. Yau suna zaune shi da Malam Dahiru maigadinsu a kan benci suna hira, su kuma yaran suna can wajen shukokin grass-carpet suna wasanninsu ya hango Abida ta janyo mesar da ake bai wa shukoki ruwa ta saki ruwan a kan Rayhanah, tun daga kanta har kafafunta ta jikata sharkaf, amma ko uffan yarinyar nan bata ce ba. Ta ja mesar ta gudu da ta hango Jawahir na tahowa. Tun daga ranar ya lura Rayhanah ta daina shiga cikinsu. Ba ma ya ganinta kwata-kwata. Daga baya ya lura kullum tana daki ne kwance a gadonta lullube da bargo. Sai ta ji Mami ko Baba Dacta a falo sannan take fitowa, amma ko abinci in basa nan ba ta ci. Ganin haka shi kuma duk sanda zai ci abinci sai ya tura Azizah ta kirata, ya cika mata filet ya ce sai ta cinye a gabansa. Ya soma janta a jiki ta hanyar labarai da son jin damuwarta, da kuma ba ta misalan rayuwa kala-kala a kan kaddarar da Ubangiji ya yi nufi ga bayinsa, sai su karbeta su kasance masu godiya a gare shi, don in ya baka wannan, sai ya hana maka wancan, ya ga cewa za ka gode masa ne ko za ka butulce a kan wannan jarrabawar kankanuwa da ya yi maka? Kwarai Rahane ke jin dadin hira da Yaya Khalipha, halinsa ba daya ne da na dan’uwansa ba, komai nasu opposite. Ita Rahane yadda Yaya Khalipha ya damu da lalurarta ita ba ta damu kanta haka ba. Ita fa ko babu injin nan za ta iya zamanta lafiya, tunda tana da lafiya falil-lahil hamdu. Rannan da yamma kuma Jawahir tana falo, Abida ta ja Azizah daki ta cire mata pampers. Ta yi kashi fal! Rahane na kwance a gadonta cikin bargo kanta ke ciwo sosai ga zazzabi-zazzabi na neman kama ta. Ba ta son wannan na’ura mai mayar da daki kamar firinji. Duk da Mami ta ce a daina kunnawa sai lokacin zafi su kam basa iyawa sai sun kunna in za su kwanta in ba haka ba ba za su iya barci ba. Abida ta kunso kashin pampers ta dawo dakin kamar abin arziki ta ce, “RAYHA!’ Ta dan janye bargon ta fiddo fuskarta idanunta duk sun kankance sunyi jawur alamun ciwon kai mai zafi. Ba ta yi wata-wata ba ta kifa mata kashin a fuska. Dai-dai lokacin da Jawahir ta shigo. Cikin karaji ta ce, “Abidaaaa!” Wannan ya janyo hankalin Himu da Khalipha wadanda ke zaune a falo suka yo dakin aguje saboda yadda ta yi maganar da karfi da kururuwa, tsammani suka yi Abidar mutuwa ta yi. Ta ce, “Ku duba ku gani, kashin Azizah ta kifa mata a fuska”. Ai kuwa Khalipa ya kama Abida da duka don dama bai iya fushi ba, kuma tarata yake yau ta kai shi bango. Shi kuwa Ibraheem juyawa ya yi ya fita ya ma bar gidan zuciyarsa na wani irin harbawa, tsigar jikinsa na tashi, don baya son ya yi kowanne action a kan Rayhanah balle har ya fassara reaction din sa a kanta. Yana referring kowane motion dinsa a kanta da KARYA....... Bayan kuma sau tari tsoron kar zuciyarsa ta ce ya yi KARYAR yake kidima shi ya yi mata KARYAR. Ya damu da RAYHANAH fiye da kowa da komi a duniya, amma yana KARYATAWA da kalubalantar kansa a kullum. Wani gini ne ke tsiro na TAUSAYI da KAUNA tun ranad da suka baro Takai. [12/24/2019, 17:56] Takori: Khalipha ya ci gaba da kallon labaran CNN da Mu’azzam Kanti ke kwararowa (Alkawari Bayan Rai). Lokaci-lokaci ya kan duba agogon (RADO) baki dake daure a hannunsa, sai kuma ya dan dubi kofar dakin nasu. Amma ko keyar Rayhana babu har karfe goma. Tuni Azizah ta yi barci a dakin Mami. Yana jin sanda Jawahir ta yi musu light off (wato ta kashe wutar dakin). Sai ya mike a hankali jikinshi babu kwari ya nufi dakinsa ya sunce ya daura tawul ya sakarwa kanshi shower, amma zuciyarshi ta ki yin sanyi. A azabce take matuka da zazzafar soyayya, wadda shi kansa bai san ya zai yi ya amayar da ita ba ga kankanuwar yarinya kamar Raihanah mai shekaru goma sha biyar wadda kuma ke matukar ganin girmansa. Ya daura Pjs ya kwanta a sofa, ya janyo kwalin Marlboro ya soma tada karamin hadari da hayakinta, duk don ya samu sassauci a zuciyarsa, ya danne wannan al’amari da ya kutso cikin rayuwarsa ba da tsammaninsa ba, zuwa sanda Rahane za ta kara girma ta mallaki cikakken hankali yadda za ta fahimci al’amarin, at least ko sakandire ne ta gama. Ya san Daddy ba zai hana shi ba idan ya ce yana so. To balle kuma Mami da ta mai da Rayhan diyar cikinta. Barci a wannan daren rabi-da-rabi Khalipha ya yi shi. Karshe shida dai-dai ya ji Daddy na buga mishi kofa, abinda bai taba yi ba. Idanunshi jajir kuma mitsi-mitsi cikin mugun barci mai dadi ya bude kofar. Kafin ya gaida Daddyn ya ce, “In ce ko ka yi sallah Khalipha Ya amsa “Eh, Daddy na yi”. To ka canzo kayan jikinka mu tafi Takai”. Tuni ya nemi barcin ya rasa, ya ce, “Lafiya Daddy?” Ya ce, “Shiryo dai mu yi sauri kamin yaran nan su farka”. Saboda zullumi Khalipha a bai-bai yasa rigarsa, ya suro hula da takalmi ya bi bayan Daddy. Sai da suka hau titi dodar, sannan ne yake gaya mishi Hakimi ne ya kirashi a waya ya ce da shi Malam Rashidu ya fadi a bayi (toilet) rabin jikinshi ya mutu (Pralysed) jiya da daddare. Khalipha ya ce, “Subhanallah! To ai Daddy da mun taho da Rayha”. Ya ce, “Zamu taho dashi asibiti ne ai, idan na ga yanayin jikin nasa. Ba zan so ta ganshi in a bad condition ba, ka san damuwarta da mahaifinta”. Khalipha dai shiru ya yi, amma kar ki so ki tona zuciyarshi da damuwa ta yiwa yawa. Har ya fi Daddy damuwa. Har suka shigo garin Takai bai kara yin magana ba. Da hantsi suka isa Takai. A kofar gidan Hakimi suka yi parking. A dakin Hajiya Karima suka karya kumallo, kafin su shiga wajen da aka warewa Mal. Rashidu. Yana kwance bai san wanda yake kanshi ba, har Baba Dacta ya gama dube-dube da aune-aunenshi a kansa bai san ana yi ba. Bakinsa a karkace rabin fuskarshi ya mutu. Duk wani taimakon gaggawa da ake yiwa masu lalurar Dr. Mansur ya ba shi, sannan ya gayawa Hakimi za su tafi da shi asibiti, kwararru a fanninsa su duba shi. La’asar lis suna cikin asibitin koyarwa na Kano. A take aka ba shi gado a (aminity) aka soma bincikarsa tare da gwaje-gwaje da dora shi a kan tretment din da ya dace da shi a (physiothearapy department). Sai magariba suka koma gida a gajiye likis. Suka yi sallah suka ci abinci suka samu nutsuwa. Bayan sunyi sallar isha’i suka koma asibitin, zuwa lokacin ya bude idonsa amma baya magana, sai dai duk abin da suke cewa yana jinsu. Yana ta motsi da bakin yana son gaya musu wani abin amma ya kasa. Albarkacin Baba Dacta duka likitocin dake kula da shi basu dauke shi da wasa ba, kula suke da shi sosai ba dare ba rana. Khalipha shi ya kwana da shi. Washe gari da safe Dacta ya zo da Mami don ita kwanan asibitin ta yi, suka duba jikin nasa yana samun sauki ba laifi ba kamar jiya ba. Har ya yiwa Khalipha murmushi, Khalipha ya matsa gare shi shima ya yi murmushin. Ya ce, “Sannu Baba, Allah zai baka lafiya ka ji?” Ga mamakinsa sai ya ga ya yi masa alamar ya daga kai. Khalipha ya ce, “Zan je in yi wanka in dawo Baba”. Sai ya rike hannunsa da hannunsa mai lafiyar ya ki saki, yana ta kakarin magana. Da Khalipha ya nutsu ya fahimci cewa yake “Ka zo da RAHANE”. Ya ce, “To Baba Rayhanah za ta zo”. Da yake Asabar ce duk suna gida, Khalipha ya dube su daya bayan daya, Jawahir ce kewa Azizah kitso, Rahane na shafa mata lallen Rani a kan yatsunta. Abida dama ba ta dawo ba. Basu ankara da shigowar shi ba saboda karar t.v don haka shima ya wuce dakinsa a hankali, babu wacce ta ankara da shigowarsa. Sai da ya yi wanka ya shirya ya fito dining nan suka san ma yana cikin gidan. Kowacce gaishe shi take don tunda suka dan kara tasawa suka daina damukarsa sai dai gaisuwa ta ladabi. Ya dubi Rayhanah kadan ya ce, “Ki shirya asibiti zamu yanzu Rayhanah”. A hankali ta juyo ta dube shi tana son ta tambaye shi waye ba lafiya? Amma ta kasa sakamakon kwayar idanunshi dake sanya mata wani al’amari da ke taba zuciyarta da ilahirin gangar jikinta. Tsam ta mike ta dauko hijabi irin dogon nan mai hannuwa ta saka ba tare da ta tsaya ko duba madubi ba, da takalmi flat. Ta bi bayan Yaya Khalipha wanda har ya tada mota. Karo na farko a rayuwarta da ta shiga motar Khalipha. Wani ni’imtaccen sanyin A.C wanda ya cakude da kamshin (car fresh) din citrus da turaren da Khalipha ya yi amfani Azzaro Chrome (Legend) shi ya soma bakuntarta a sanda ta shiga gefen Khalipha ta zauna. Ya dan juya kadan ya dube ta suka hada ido, inda ya gano alamomin tambaya fal cikin idanunta amma ta kasa furtawa. Ya fi minti uku bai yi magana ba kuma bai ja motar ba. Rahane ta gaza hakuri ta ce, “Don Allah Yaya Khalifa waye ba lafiya?” Ya kunna motar a hankali ya fara yin reverse, sannan ya ce da ita, “Ki yi hakuri Rayhanah, Baba Rashidu ne ba lafiya amma mun taho da shi nan asibiti har ya fara samun sauki”. Kwalla fal idonta ta ce, “Tun yaushe ne?” Khalipha ya ce, “Tun jiya, ai sammakon da muka yi ni da Daddy Takai muka tafi”. Ta jinjina kai sai ga hawaye ya balle a ka kundukukinta. Ta yi saurin juyawa tana kallon titi kada Yaya Khalipha ya gani. Yana gaba tana binshi a baya har dakin aminity na male-ward din inda Malam Rashidu ke kwance. Da sauri Rahane ta karasa gaban Baban ta kama hannunsa, wannan lokacin kuka ne sosai ya kwace mata da ta fahimci halin da Babanta ke ciki. Khalipha (cikin bugun zuciya) da hawayen da Raiha ke fitarwa ya ce, “To kuwa zan maida ke gida Rayha, ciwo ba mutuwa bane, ke da za ki ba shi karfin gwiwa da kalamai masu dadi sai ki yi masa kuka?” Ta soma share hawayen da gefen hijabinta. Dai-dai lokacin da Khalipha ya matso kusa da Baban, don ganin kamar ya bude ido. Ya ce, “Baba ga Rayhanah ta zo, Baba Allah ya baka lafiya”. Sai ya mika mata hannunshi mai lafiyar ta kama, jikinta har rawa yake yi. Kamar wanda ya warke a take ya bude ido garau yana kallon diyar tasa, tausayinta yake ji sosai, don ya san ba ta da kowa a duniya da za ta bugi kirji ta ce nata ne sai shi sai Ubangijin da ya halicceta. Yana ji a jikinsa wannan rashin lafiyar tasa ba ta tashi ba ce. Bayin Allah na gari (Saliheen) Allah kan nuna musu karshen rayuwarsu. Duk da haka ya daure ya tattara kuzarin da Allah ya ba shi a lokacin muryarshi da sanyi kwarai ya ce, “Rahanen-Iya diyar Yalwati-na!!!”. Sai ta yi murmushi idonta fal da hawaye. Ya ci gaba da cewa, “Idan Allah yasa na tashi abin da zan fara yi miki Rahane shine AURE. Bana son in kwanta dama ban ganki a dakin mijinki ba. Sai dai kuma da na yi wani tunani sai na ga cewa kina da Uba makwafina, wato Likita Mansur. Na yarda shi mai kaunarki ne saboda Allah ba don wani bayyananne ko boyayyen dalili ba. Don haka Rahane na horeki da yi masa biyayya kwatankwacin yadda kike mini. In ya saki ki yi, in ya hanaki ki hanu. Rayuwar dan Adam Rahane gajeriya ce, don da ta shigo saba’in shi kenan ta kare komin jin dadi kuwa, kada ki shagala da dadin duniya ki manta da Allah. Duk rintsi ki yarda cewa mutum bai isa ya tsarawa kansa rayuwa yadda yake so ba sai yadda Ubangijinsa ya ga dama. Rahane ban bar miki gadon komai ba sai na tarbiyyar da na yi miki, wadda na tabbata za ta yi miki jagora har karshen rayuwarki. Kada dadin duniya yasa ki shagala ki manta ko ke wace ce; talaka, diyar talaka, jikar talakawa. Talakawan ma na kauye. Don haka ki taimaki talaka a duk inda kika samu dama kema Allah zai taimaka miki kamar yadda likita Mansur ya taimakeki. Ki zabi miji dai-dai ke, abin da nake nufi a nan shine, ki auri talaka dan’uwanki wanda zai daraja ki ya mutunta tushenki, in har zai ci dake ya shayar, ya tufatar, kada ki kai kanki inda Allah bai kai ki ba.........” Kuka take sosai tare da katse shi da cewa, “Baba don Allah ka daina wadannan maganganun, masu kamadawasiyya, ni ba wani aure yanzu a gabana neman ilimi zan yi, shine sutturar mara galihu. Kuma Baba ni wa zai min auren idan babu kai? Baba me yasa kake yanke kauna da rayuwa a dalilin zafin ciwo? Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar, wato ranar da zan wayi gari babu kai.....” Ta ci gaba da wani irin kuka, ta kifa kanta jikin karfen gadon da Baban ke kwance. Rahane dai ba ta sani ba, ba ta san abin da Khalipha ya ankara da shi ba. Ji ta yi an dafa kafadarta da wasu yatsu masu bala’in taushi. Ba sai ta juyo ba ta san Khalipha ne tunda su uku ne kawai a cikin dakin, ba ta kuma ji wani ya murda kofa ya shigo ba. Ta dago a hankali ta dubi Khalipha idanunta kamar an gumbuda musu barkono. Shima nashin sun canja launi, ya kasa jarumtakar da zai rarrasheta bai san lokacin da hannayenshi suka yi motsi ba suka sarrafa kansu suka kai ga rungume Raihanah. Sannan ya rufewa Malam Rashidu ido, ya ja zanin gado ya rufe shi har kansa. Dai-dai lokacin da Mami da Baba Dacta da wasu daga cikin Phyisothearapists na ward din suka shigo. Idanun Mami a kan Khalipha dake rungume kam-kam da Rayhanah, ya kasa sakinta don kar ta fahimci abinda ya faru, ya rasa inda zai sa kansa, rikon da yayi mata mai karfi ne don kar ta juya, gaban Mami ya yi wani irin mugun faduwa ta tsaya turus! A bakin kofa. Da gudu su Baba Dacta suka karasa suka bude rufar da Khalipha ya yi masa, gaba daya suka ce, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!”. Baba Dacta ya juya yana share idonsa da hankici. Da karfin gaske Rayhanah ta zame daga jikin Khalipha ta juyo da gudu ga Babanta, ta bude rufar ta ga abin da kowa ya gani. Dora haannu ta yi a kan kirjinsa wai ta ji bugun zuciyarsa, ba ta san alamun mutuwa ba, amma ta tabbatar Babanta ya mutu. Tunda ga shi ta ji ba ya numfashi. Zuciyar shi bata bugawa ko alama. Bayan wannan ba ta kara sanin me ke faruwa a duniyar ba, bayan gilmawar wasu taurari a idanunta. Da gudu Khalipha ya yi kanta shi da Baba Dacta, suka hanata kaiwa kasa, yayin da su Mami ke rufe Mal. Rashidun, likitocinsa na ta rubuce-rubuce cikin file din sa. **** A gidan Hakimi aka yi jana’izar Mal. Rashidu. Ya kuwa samu jama’a na ban mamaki, kwana uku ana karbar gaisuwa, har zuwa lokacin Rahane na gadon asibiti jininta ya hau sosai, ta ki ci ta ki sha, sai ruwa ake ta kara mata leda-leda. Ba kuka take yi ba, don ta nemi hawayen a idanunta ta rasa. Kwance kawai take ba ta umh ba ta uhm-uhm sai kallon gilmawar mutane da shige da ficen likitoci. Wato shi kansa kukan (wuri shi ka samu), wani tashin hankalin ya fi karfin ka yi masa kuka. Kuka rahama ne a lokacin da zuciya ke ciwo, ciwo irin wanda babu irinsa a rayuwa. Rahane ta kasa kuka sai addu’a take cikin zuciyarta ita ma Allah ya dau ranta ta bi iyayenta da Iya ta huta. Yanzu kam ta tabbata ta zama marainiyar gaba da baya. Da dai-dai da dai-dai Allah ya yi ikonsa a kan wadanda ya bata su zame mata garkuwa a rayuwa, kuma bango abin jingina. Shi kenan kuma ita yanzu ba ta da kowa! Idan Baba Dacta da iyalinshi suka gaji da rikonta ina za ta je? ...........“Sai dai kuma da na yi wani tunani sai na ga cewa kina da Uba makwafi na, wato Likita Mansur.....” Ta tuno kalaman Mal. Rashidu masu kama da wasiyya. Ashe hirar karshe ce Baba, kaicona da na katseka!!! A wannan lokacin ne ta samu hawaye suka zubo, ba tare da ta san suna kwarara ba sai ta ji an sa tissue ana share mata. Ta juyo kadan sai ta ga Jawahir, ita ma kukan take tayata. Ta ce, “Rayha ki yi hakuri, Baba kwananshi ne ya kare, kin sani ko muma zamu iya mutuwa a kowanne lokaci. Addu’a za ki yi mishi. Rayuwa yanzu kika fara ta Rayhanah, ko ba iyaye za ka rayu idan haka Allah ya tsara maka. Belle ke kin rayu da Baba, ya yi miki tarbiyya, ya baki ilimi dai-dai karfinsa. Sannan bai barki a hannun da za ki wulakanta ba. Rayha ki daure ki tashi mu ci gaba da fafutukar rayuwa, darussa za su wuce ki, alhalin Allah bai nufa rayuwarki ta zo karshe ba. Ina miki ta’aziyyah Raihanah, Allah ya ji kan Baba, ya ji kansa ya yi masa rahama, yasa Aljannah ce makomarsa, ya sanya mana dangana”. Kwanaki bakwai da suka biyo baya, aka yi sadakar bakwan Mal. Rashidu. A cikin wadannan kwanakin, kwana biyu kacal ta yi a gida, ragowar a gadon asibiti. Tuni Khalipha ya koma bakin aikinshi cike da alhinin RAYUWAR RAYHANAH!. Ga nakasa ga hawan jini, sannan ga maraiaci na uwa da uba da rashin dangi. Tausayi ba zai barshi ya ci gaba da ganin Rayha cikin wannan halin ba. Ta rame kwarai, ita dama shiru-shiru jiki ba jiki ba, yanzu abin ya koma daga eh, sai a’a. Sai da Baba Dacta yasa aka soma rubuce mata Alkur’ani tana sha tsayin sati biyu. Hatta Abida ta rage rashin mutuncin ta don ganin Rayhan, a yanzu kam wani dan Adam bai da abin da zai bata mata rai da shi, ko yankata za ta yi ba za ta daga ido ta kalleta ba balle ta san tana yi. Tunda ta jure rabuwa da Iya da Baba, to mene ne ma ba za ta iya jure shi a rayuwar duniya ba? Duniya ta fita a kanta sai fatan cikawa da imani. Sati biyu bayan nan suka koma makaranta suka soma shirin zana jarrabawar shiga aji shida. Rahane kam ba fus, sakamako bai yi kyau ba. Sun ba ta maimaicin shekara guda (repeating), yayin da su Abida suka shige aji shida suka barta a aji biyar. Amma maimakon Baba Dacta ya yi fada kamar yadda suka zata, sai ya ce “Rayhanatu a hakan ma kin yi kokari, Allah ya yi miki mai kyau a duniya, mai kyau a lahira a dalilin juriyar ki kan kaddarorin ki da kyawawan halayenki”. Sati biyu Khalipha bai zo gida ba, ba don komi ba sai don baya son abin da ke zuciyarshi a kan Rayhanah ya fito sarari. Ya zo wani limit da ba zai iya boye soyayyarta ba zuciyar ba za ta iya basarwa ba. In kuma har ya yi kokari ya boye din, to za ka iya karantar hakan cikin kwayar idanunsa cewa yana so.........kuma yana tausayin Rayhanah. Haka nan ya samu kansa da wani sabon tunani, wato ya kai Rahane waje, masu jajayen kunnuwa su duba lalurarta. Babu cutar da ba ta da magani. Likitocinmu ba finsu kwarewa aka yi ba, kayan aiki ne bamu dasu kamar sauran kasashen da suka ci gaba. Daga fara aikin shi zuwa yanzu yasan yanada account mai nauyi don bashi da almubazzaranci kuma babu nauyin kowa a kansa. In ma ya kakare ya tabbata Baba Dacta zai agaza masa in ya gaya masa kudurin sa. To amma Rayhah ta balaga, shekarunta goma sha shida ya za ayi Baba Dacta ya yarda su tafi wata uwa duniya tare? Duk da neman magani ne? Wata zuciyar ta ce, “To ka fito fili mana ka sanar da Daddy kana sonta ya aura maka ka tallafi rayuwarta da taka? In ta zama matarka shikenan babu sauran shinge. To amma anya ba ta yi kankanta ba? Ya tabbata ko Daddy giyar wake ya sha ba zai aurar da Rayha a wadannan kananun shekarun ba. Don haka furtawar ma bata da amfani. Da ya kwashi wata daya bai zo gida ba, kewarshi ta damu al’ummar gidan, kada Azizh ta ji labari. Duk sanda Mami ta kira wayarshi sai ta jita a kashe, haka in ta yi amfani da social network baya responding. Zuciyar UWA! Ba irin tunanin da ba ta yi ba. A yau dai ta kasa daurewa ta samu Daddy da zancen. Ya ce, “Lafiya ita ke buya Asma’u, amma ba rashinta ba”. Duk da haka ta kasa sukuni, a ranar Alhamis Daddy ya daga kasar Ireland domin halartar taron “Old Students Alumni of Trinity University”. Kwananshi daya da tafiya ta dauki hanyar Abuja ita kadai a motarta, tana tafe tana zancen zuci. Khalipha na kwance cikin leather seat din falonsa bakake, a gabansa ash-tray ne na silver wanda ke cike taf da guntattakin Marlboro, a wannan lokacin ma abin da yake ta yi kenan, wato gajimare da hayaki. Ya yi baki ya bar kasumba ta cika masa fuska, wannan kwantaccen gashin nasa duk ya kanannade saboda rashin gyara. Falon kaca-kaca ga kuma kura da kayan wuta suka yi, don ya hana yaronsa Jibril shigo masa daki balle ya gyara masa sai idan shi ya kira shi a waya ya sayo masa abinci. Kararrawar shigowa falon ta yi kara, ta yi ta sake yi yana kwance bai motsa ba. A zatonsa Jibril ne alhalin ya san ya hana shi zuwa inda yake in ba shi ya kira shi ba. Farar singilet ce a jikinshi da dogon bakin wandon DKNY. A fusace ya mike ya bude don ya yi masa marin da uwarsa bata taba yi masa ba. Amma sai ya yi tozali da tashi uwar wacce ko cikin mafarkinsa bai zaci ganinta a nan ba. Kallon shi kawai Mami ke yi, bayan mintuna uku ta bi gefenshi ta shige falon ba tare da ya bata damar hakan ba. Sai ta fara kiran ‘Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un....... smoking ABDALLAH???” Sai ta zube cikin kujera ta saka mishi kuka. Jikinsa ya yi bala’in yin sanyi, ya zube a gabanta ya kwantar da kai a cinyoyinta cikin matsanancin tashin hankali; mahaifiyarsa na zub da hawaye a dalilinsa. Ta kara dago ido ta dube shi, “Ashe addicted ka zama? Shi yasa baka nemanmu? Abdallah tun yaushe kake shaye-shaye ban sani ba? Me ya kawo ni ganin wannan bakin cikin? Me ya kawo ni, ni Asma’u???” Sai ta mike za ta fice idanunta jage-jage da hawaye. Da hanzarin gaske ya cimmata ya rungume kafafunta. “Wallahi Mami ki yarda dani, ban taba shan abin da zai fitar dani daga hankalina ba. Mami damuwa ce bana cikin sukunin da zan iya sarrafa kaina. Ina sha ne kurum don ta rage min damuwa. Marlboro ce kawai, wallahi Mami idan na taba shan wani abu bayan ita, Allah ya yi miki sakayya a kan tarbiyyar da kika bani”. Ta tsaya da kukan, ta shiga nazarin falon baki dayansa cikin bakin-ciki marar misali, ta ce, “Mene ne haka? Me zan gani haka? Kazami kuma ka koma? Me kake yi yau a gida ranar aiki baka je office ba?” Bai bata amsa ba, don bai san me zai ce mata ba. Ta girgiza kai ta ce “ai Shi kenan, ni zan tafi, dama na zo in duba lafiyarka ne. Don na san haka kawai ba za ka ki gaishemu ba. To na gani lafiyarka kalau bamu isa bane kawai mu ji damuwar taka ka gwammace ka lalata rayuwarka”. Da hanzari ta fita, bata barshi ya yi wani furuci ba. Kayan dake jikinsa kuwa ba za su barshi ya bita ba. Ko hutawa bata yi ba, ko ruwa ba ta sha ba ta dauko hanyar Kano. Allah ne kawai ya kawo Mami gida, amma ba nutsuwar zuciya ba. Wai Dan da ta haifa ne yake shan taba bata taba sani ba. Ko tun tsahon yaushe yake sha? Duk tsantseninta a kan ‘ya’yanta, duk jansu da take a jikinta don su zama abokan rayuwarta, a yau Khalipha ya nuna mata aikin banza take, ya nuna mata yana da wata damuwar da ba ta isa ya gaya mata ba, ya gwammace ya mutu a cikinta. Da asubahin ranar ta ji Malam Dahiru ya bude get, ta daga labulen dakinta tana kallon shigowar motarshi, wannan ya tabbatar mata tafiyar dare yayo, sai ta ji tausayi ya tsirga a zuciyarta. Har ya fito daga motar ya rufe ya ratayo bakar jakarshi ya shigo reception tana kallon shi. Ta koma bakin gadonta ta zauna, ko minti biyu ba ta yi da zama ba ta tsinkayi sassanyar sallamar sa a kofar dakinta. Babu kuzari sam a jikinta ta ce, “Yes, come in”. A yadda ya shigo din cikin kayan da ta baro shi ne, bakar rigar sanyi kawai ya dora a kai wadda ta iso har gwiwarsa, bakin glass da bakin cover takalmi. Sai ta nuna mishi toilet dinta, tana daga zaune “Go take a wudu’ (alwala), a brush, a shave and a shower, then come to me….”. (Shiga ka yi wanka, ka yi brush, ka yi alwala, ka yi aski sannan ka zo gareni). Maimakon ya shiga nata toilet din sai ya juya nashi dakin ya bi umarninta. Ya idar da sallah ya yi addu’o’i masu yawa, yana rokon Allah yasa Mami ta fahimci ba shi ya dorawa kanshi damuwar ba, Allah ne ya dora mishi. Sannan ba shi da karfin zuciyar da zai sarrafata ko ya boyeta. Su kuma ba za su iya yi masa maganinta a wannan lokacin ba. Don haka ba zai iya fada mata ba, don fadar bazata yi wani amfani ba. Mami ta ji shiru-shiru Khalipha bai fito ba. Ta kasa hakuri ta biyo bayanshi har dakin nasu. A lokacin shi yana shirya abin da zai gaya mata ne don ba zai iya gaya mata gaskiya yanzu ba. Ya san Mami da boko kamar Ibraheem, cewa za suyi Rayhanah ba ta isa aure ba ko su kushe zabin nasa. Ko suce ‘child abuse’. Don haka tuni ya tattara abin da zai gaya mata. Dai-dai lokacin da ta zauna gefen ‘sofa’ dinsa. Ya shafa addu’a ya ce, “Mami kin zo lafiya?” Ta ce, “Da ban zo lafiyar ba za ka ganni ne har dakinka da kafafuna eyi?” Ya yi murmushi, “Mami kin tayar min da hankali Allah, da baki tsaya kin ji uzirina ba balle damuwar dake damun nawa. Mami in kika yi fushi dani ina zan sa raina? Jahannama fa Mami, babu ni babu jin kamshin Aljannah. Mami don Allah kar ki kara yin fushi dani, kin ji Mami?” Jikinta ya yi sanyi kalau, ta ce, “Mene ne ke damun naka?” Ya ce, “Mami SOYAYYAH!” Sai ta yi murmushi ta ce, “Alhakin Hibba ne, wace mai tsautsayin ce again?” Ya ce, “Mami ban sameta ba, an kasa ni”. Ta kara yin murmushin ta ce, “Ba ita kadai ce diya mace a duniya ba, Allah yasa hakan ya zama mafi alkhairi. Wani zubin in Allah ya tsara abu, sai ka ga na gaban ya fiye maka amfani. Ni tuni ai na yi maka mata Khalipha, jira nake ka zamo settled tukunna kafin in gabatar maka da zancen”. Cikin Halifa ya karta ya bala’in kadawa. Da sauri ya ce, “Um-um Mami, bar zuciya da abin da take so. Har yau din dai da nake gaya miki ban fidda rai da samunta ba. Wani sanadi zai iya zuwa idan har matata ce Allah ya bani in aureta. Tunda an ce matar mutum kabarinsa”. “Ya ya sunanta? A ina take Dattijo? Su waye iyayenta?” Ya ce, “Mami tunda a yanzun bani da damar aurenta sanin wadannan amsoshin ba zai amfaneki da komai ba”. Cikin rashin damuwa da lamarin ta mike tana fadin, “Toh! Allah ya maganta maka, ni na dauka wani muhimmin al’amari ne, zancen Radhiyyah kuwa na baka sati har biyu ka yi tunani a kai”. A cunkushe da zancen ya ce, “Radhiyyah kuma? Gaskiya Mami bana son ki sa ranki ga abin da ba zai yiwu ba. Matakin iliminta ya wuce wanda nake so a macen da zan aura kafin in aure ta. Nafison duk wani ilmi da mace zata yi bayan sakandire tayi shi a gida na. Kuma da kadan na girmeta, in zan iya tunawa shekara uku na bata. Haba Mami, ai an dena irin wannan hadin auren yanzu a kauye ma ba a birni ba, gaskiya ta min tsufa. A perception dinki ban zaci akwai irin wannan tunanin ba, na abubuwan da aka yi a can wani karni can da ya shude. Na soyayyar ma yaya aka kare da shi balle na hadi? Ki barni kawai in na samu wadda za ta maye min gurbinta da kaina zan gaya miki. Amma don Allah Mami kada ki kara daga maganar nan, kada zumuncin da ke tsakaninku da Mamanta ya lalace a kan abin da ba zai yiwu ba”. Cikin mamaki Mami ta ce, “Ni kake cewa haka Dattijo?” Da sauri ya gyara kuskurensa da cewa, “Ba nufina baki da iko a kai bane Mami, kawai ina gaya miki abin da zuciyata ke gaya min a kan maganar. Ki yi hakuri idan kalamaina sun bata miki rai, I’m sorry Mamee! Ki yi hakuri don Allah”. Ta yi ajiyar zuciya sannan ta fita. Allah kadai ya san abin da take sakawa da warwarewa a zuciyar nan tata. Mami na son ‘ya’yanta matuka, tana kishinsu irin kishin nan mara amfani, wanda ya kimsa mata tunanin cewa da akidar cewa ba za ta bari su auri wadanda suke mutuwar so ba, sai wadanda ke son su, don kar su rabata da su. Irin ‘yan’uwansu su Hibbah, Nabila da Radhiyyah diyar aminiyarta Dacta Halima wadda ta ki auren minister saboda mahaukaciyar soyayyar da take yiwa Khalipha. Mami na da wannan kudurin cikin ranta tuni, wanda kuma take da yakinin ko za ta yi yawo tsirara ne sai ta cika shi. Saboda masifar son da take wa ‘ya’yanta. **** ASabar, biyar ga watan Yuli, rana ce ta ziyarar ‘yan makarantar kwana. Khalipha na tsaka da aiki a Office kiran Mami ya shigo wayarsa. Ya dakatar da komai ya daga ya fara gaisheta. A gurguje ta amsa tare da cewa, “An zabe ni zuwa karbar (Award of the best paediatrician of Africa) a kasar Djbouti zamu tafi har Daddy gobe insha Allahu, so ba zamu samu zuwa ma yara visiting Katsina ba, shine na ce ko za ka samu sararin lekasu can Katsina tunda ba ranar aiki ba ce?” Khalipha ji ya yi kamar yana yawo a kan gajimare dan dadi. Ga dama ta samu ta ganin Rayhanah wadda yau sati shida kenan bai dora ido a kanta ba, ba da tsimi ko dabararsa ba. Domin dai Mami ba ta taba cewa yaje musu visiting ba, shi bama ya sanin yaushe ake yi sai dai Mamin ta ba shi labarin cewa yara suna gaishe shi. Amma sai ya dan danne farin cikinsa ya ce, “O,k, to ba matsala Mami zan yi kokari in gani ko zan samu zuwan in b azan je gida ba, Congratulations Mami! Safe journey........” Suna murmushi dukkansu suka aje wayar lokaci guda. Aikin da ke gabansa kasa karasashi ya yi, ya hada komai ya rufe ya aje ya mike ya nufi gida. Washe gari ranar ta kama Juma’a, bayan ya fito daga sallar Juma’a ya nufi Sahad ya soma shopping. Ba kayan ci kadai ba, har da na amfani. Wani irin Shopping yake yi kamar ba sai ya yi losing energy dinsa da lokacinsa ake ba shi kudin ba. Sai dai kuma kayan abinci ne ya sayi komai na mutum uku, sauran kayan amfani kuwa sitturu nena sanyawa a gida ko makaranta designers ‘yan gidan versace da channel hade da dogayen riguna kala-kala da tafi amfani dasu. Kayan shafa na Avon da coesmetics, deo-sprays duka ‘yan gidan Avon. Ya ma manta a makaranta take. Shi kansa bai san adadin kudin da yake kashewa ba, burinsa kawai Rahane ta koma irin yadda yake son ganin matarsa. Filin makarantar ya cika ya batse da motoci da jama’a. Ba tun yau ba, tsarin Ulul-Abaab ke burge Khalipha ba. Jama’a makil kowa nasa yake nema, sai manya-manyan coolers kawai ake saukewa da katan-katan na kayan abinci da abin sha. Lokacin da Khalipha ya iso karfe goma sha biyu dai-dai, tunanin Khalipha shine cikin wannan bataliyar al’umma ina zai je ya nemo ‘yan kannen nashi? Don haka ne kawai ya fito daga mota ya jingina jikin kofar direba ya harde hannayenshi a kirji, don bai san ma wa zai tambaya ya nemo mishi su ba. Sanye yake da shaddah getzner baka kar da bakar hula kalar shaddar dinkin Mohammed. Khalipha fari ne sol mai wata irin fata jawur da ta fi kama da ta mutanen Hurghada (Middle East). Hasken fatarshi ne kadai yasa ake danganta shi da Mami amma ba kamanni ba, domin ya fita kyau nesa ba kusa ba, musamman kanannadaddiyar sumar kanshi. Haka yake kamar ruwa biyu. Kamar an ce da Khalipha juya, ya karyar da kai ya juya wani sashe daban. Rayhanah ce zaune a gindin wata bishiyar lemon tsami mai karancin jama’a ta yi tagumi da hannuwanta biyu, ko me take tunani? Allah masani. Sanye take cikin uniform dinsu na daliban Ulul-Albaab da gajeren farin hijabi iya kafadunta. A idanun Khalipha har tsayi da zati ta kara. Duk wasu alamu na cikar budurci sun bayyana a jikinta. Kirar jiki dirarre wanda bai da alaka da kiba, cin kitse (cholestrol) ko over-eating duka babu su a jikinta. Da ganinta ka ga rainon likitoci wadda ke cin komai moderately kuma cikin tsarin balance diet na Bature. Ya kai kallonshi ga fuskarta, kalarta choculate (wankan tarwada), fatarta fresh kamar ta yaran goye. Ba ta da dogon karan hanci gashi nan dai dan matsakaici sai manyan idanu dake lumshewa da kansu. Mai gazar-gazar din gashin gira dana ido bakake wul. Rayhanah na da lebba masu dan kauri da sulbi kuma zagayayyu (kissable). Bayan wannan, Rayhanah ba ta da wani mugun kyan da za a dorar. Wannan ita ce irin matar da yake so, ya dade yana nema, yana lalube bai samu ba. Ashe tana nan cikin gidansu. Duka wadannan nazarce-nazarce da ya yi, ya yi su ne cikin dan lokaci da bai gaza mintuna biyar ba. Zuciyarshi na bugu da sauri da sauri ya rintse idanunsa, kafin ya yi tattaki zuwa inda take zaune. A lokacin ta sadda kanta kasa ne don haka ba ta ga tahowarshi ba, har ya tsugunna a gabanta. Sassanyan kamshin Chrome Legend ya tsirga har cikin kanta. Da sauri ta dago ido ta dube shi, “Yaya Khalipha!” Ta fada cike da al’ajabi da farin cikin da ta gagara boyewa. Murmushi ya yi, “Yaya Rahane”. Dariya ya bata sosai, don rabon da ta ji wani ya kira ta da wanann sunan, tun ranar da Babanta ya bar duniya. A rayuwarta kuma ba sunan da take so irin Rahanen. Suna ne na mahaifiyarta da bata taba gani a duniya ba. Suna ne da Babanta ya zabar mata don kar ya manta da Yalwatinsa. Suna ne da ake kiranta da shi a Takai da intonation daban-daban. Muskutawa ta yi ta soma share masa kura da dan hankicin dake hannunta kan dan kututturen itacen bishiyar da ta ke zaune. “Sannu da zuwa Yaya Khalipha, yi maneji da nan ka ga duk an kwashe kujerun”. Murmushi yake sosai, ya kwaikwayi ‘yar muryarta “Yi maneji da nan Yaya Khalipha”. Kunya ce ta kama ta, ta rufe fuskarta da zara-zaran yatsunta. “Ka sha hanya”. Ta fada ba tare da ta daina murmushin da ke like a tattausar fatar bakinta ba. “To ya za ayi? Ai ko bangon duniya Rahane ke karatu ba zan yi kasa a gwiwa wajen zuwa ziyararta ba, balle Katsina”. A zuci yake fadi, bai san a fili yake yi ba saboda azabar son da ke kara ruruwa a zuciyarsa. Sai ta yi dan jim tana nazarin kalamansa don sun dan yi mata tsaurin fahimta. Ya ankara da katobarar da ya yi, ya yi saurin gyarawa da cewa, “Ina su Abida kike zaune a nan ke daya?” Ta sadda kai ta ce, “Ni tun safe yau ban ga Abida ba, Jawahir muna zaune nan tare kawarta Teemoh ta zo ta yi kiranta su gaisa da ‘yan gidansu”. Ta fadi haka ne don ta kare Abida, a zahiri kuma Abidar mari ta zabga mata cikin (domitory) a bainar jama’a, kan wai ta shafa vasiline dinta don nata ya kare. Jawahir kuma ba ta shafa vasilne sai lotion, abin da ya kaita ga shafa na Abida kenan. Wannan wulakancin da Abida ta yi mata shine dalilinta na kadaicewa, tana tunanin rayuwa, canje-canjenta da juyinta, kamar rawar ‘yammata wai na gaba ya koma baya, da abebaden ban tsoro dake faruwa a cikinta. Abin nufi, kowa baya tunanin gaba, wato me gobe za ta haifar? Mutuwa na iya zuwar wa bawa kowanne lokaci amma ta kasa gane me mutane masu irin halin Abida ke daukar duniya. Da suke tozarta dan Adam don baya da shi, shi ba kowa ne ba. Sun manta da darajar da Allah ya yiwa dan Adam, har ya fadi da kansa cikin Alkur’ani mai girma cewa, ‘Ya karrama dan Adam…..’. Da wannan tunanin da ta yi ne cikin ‘yan mintuna a gaban Khalipha idanuwanta suka kawo ruwa, suka kada suka yi jajir. Tunda ta sunkuyar da kanta ba ta kara dagowa ta dubi Khalipha ba kada ya gane bacin ranta. Shi kuma Khalipha har zuwa lokacin kallon ta kawai yake cike da matsananciyar kauna cikin kwayar idanunsa, zuciyarshi harbawa take da gudun gaske sakamakon ganewa da ya yi Rahane kuka take. Bai san sanda ya baje shaddarshi a kas, ya zauna dirshan agabanta ba, kiris ya rage su dunkule waje daya. Gaba daya ya manta a inda suke. Da murya mai sanyi yake fadin. “Daina tunanin komai cikin rayuwar nan Rayha, tunda ga ni, zan zame miki uwa, uba, kawa, yar uwa, dan uwa, aminiya, masoyi, sannan MIJIN AURE. Insha Allahu, daga ranar da aka daura mana aure (idan har kin amince) kin gama zubar da hawaye a kan kalubalen rayuwa. Ina sonki Rayhanah, Rayhanah za ki aure ni???” Mu biyo Rayhanah da Yaya Khalipha a littafi na biyu. Don jin amsar ta. Tare suke. Sumayyah Abdulkadir ce Manan SAFAH da MARWAH. ke yi muku fatan alkhairi.