[12/24/2019, 21:47] Takori: RAYUWAR RAYHANAH - 2 Ji ta yi kamar an dora mata dutsen Uhudu a kanta, sabida nauyin da kalamansa yayi mata, a gigice ta dago ta dubi Khalipha jikinta na bari na rudewa da gigicewa. Ta shiga waiwaye-waiwaye kada wai ko wani ya ji abinda Yaya Khalipha ya ce. Amma ga jin dadinta kowa harkar gabanshi yake yi da iyaye da ‘yan’uwansa nesa dasu sosai, don sai da ta ware kanta can nesa da jama’a kamin ta zauna. Shi kuwa Khalipha ko a kwalar rigarshi, bajewa ya kara yi a gabanta yana gaya mata duk kalaman soyayyar dake fitowa tun daga karkashin zuciyarsa ba daga fatar baki ba. Idanunshi a lumshe, ya yi kyan da bata taba lura ashe yana da shi haka ba. Karkarwar da jikinta ke yi ya karu, don Khaliphan ya ki yin shiru. Ita kuma gaba daya a gigice take kada kannensa dake matukar ganin girmansa su zo su ga abin da yake yi, wanda ita bata sani ba. Sauran kadan ta tsuge da zawo da ta hango Jawahir ta nufosu da sassarfarta. Da karfi ta ce, “Yaya Khalipha ka cika min hannu, ga Jawahir nan”. Lokaci guda kuma tana kici-kicin kwace hannun nata daya rike cikin nasa da karfi kamar zai balla ta. Amma Khalipha ko gezau bai yi ba, juyawa kawai ya yi yana tsimayen isowar Jawahir din. Mikewa ta yi da karfi ta fizge hannunta saura kadan ta fadi. Cikin zafin nama ta zauna a kan kututturen iccenta tana kokarin dai-daita numfashinta, nutsuwarta, bugun zuciya da yanayin fuskarta kafin isowar Jawahir. To ita ma Jawahir din duk da ta ga abin da ta ganin, amma da yake wayayya ce ba ta nuna komai a fuskarta ba, a zuciyarta cewa ta yi, “Na san wata rana irin wannan na zuwa, tsakanin Raiha da Yaya Khalipha, Intimacy din ya isa, haka kulawar da suke wa junansu a gida kadai abin a digawa ayar tambaya ne. A gaban Khaliphan ta zube tana dariya. “Yaya Khalipha yau kai ne da visiting, ina Mami ina Zizah? Ina Daddy?’ Ta jefo masa tambayoyin duka a lokaci daya bakinta kamar zai tsage don fara’a da farin ciki. Ya ce, “To duk wadannan queries ni kadai Jawahir, wanne zan fara amsawa?” Dariya ta yi tana kallon Raiha ta ce, “Don Allah Rayha Yaya Khalipha bai kara kyau ba?” Ta rausayar da kai ta ce, “Ni bana yiwa mutum kallon kurilla”. Ta ba shi dariya sosai, ya ce, “Har da ni RAHANE?” Ko don albarkacin wannan suna da ya kirata da shi ya isa ya sata dariya. Ya mike yana duba agogon hannunsa, lokacin rufe makarantar ya karato. Ya ce, “Ku zo muje mota ku kwashe kayanku har na wannan shashashar (Abida)”. Suka mike suka bishi har boot din motar ya kwaso ya basu. Haka ya ware na Rahane. Wannan karon ma Jawahir ta diga ayar tambaya, amma wayewarta yasa ba ta nuna komai ba. Saboda yawan kayan sai juniors dinsu suka sa suka tayasu kai kayan hostel. Tun daga wannan ranar Rahane ta kasa samun sukunin zuciyarta. Tunanin Yaya Khalipha da al’amarinshi day a zo mata dashi kadai zuciyarta ke yi dare da rana, yini da safiya. Sai dai bata barin hakan ya shafi karatunta ko kadan saboda alkawarin da ta daukarwa ranta na farantawa Baba Dacta wannan karon da kyakkyawan sakamako. Amma fa duk sanda ta kwanta, ko ta kadaice tunanin Yaya Khalipha take yi. Ba abin da take so irin ta ganshi, ko ta ji muryar nan tasa mai sanyi yana cewa ‘RAHANE’. A haka suka zana WAEC da NECO har da JAMB, suka yi sallama da Ulul-Albab. Ya yin da Rahane ta zana (qualifying) wato jarrabawar shiga aji shidda. Sun zo gida hutu a lokacin Khalipha an tura shi kwas a kan aikinsa a Nigerian Embassy na kasar Marocco. Wanda zai yi tsayin watanni tara. Khalipha ya yi murna da wannan tafiya, ko babu komai zai yi nisa da Rayhanah na dan wani lokaci mai tsaho. Ba tare da al’amarin dake zuciyarshi ya bayyana ga kowa ba. Ya na da relief tunda ya bayyana shi gareta. Duk da bai san me ke wakana a tata zuciyar ba. Sai dai kuma ya bar ita Rahanen cikin dabaibayi mai yawa, da soyayya mai cin zuciya. Duk da ita kanta ba ta san cewa soyayyar ce ke dawainiya da ita ba. Ta san dai tunda Yaya Khalipha ya tafi ta shiga kewa, rashin kuzari a cikin gidan da makaranta duka. Tunda ya tafi ko waya basu taba yi ba, domin Baba Dacta ya hana kowaccensu rike wayar hannu, ya ce sai ya ga kamun ludayinsu a jami’a tukunna. Hakan ne yasa ko Khalipha ya yi waya da Mami ko Daddy sai dai ya a ce a gaishe su. To da haka rayuwar ke mikawa. Lokacin da Abida da Jawahir suka samu gurbi a Jami’ar Bayero, lokacin ne Rahane ta zana jarabawar barin sakandire. Cikin watanni uku ta fito, kuma Raihanah ta bai wa kowa mamaki daga ‘A’ sai ‘B’ a dukkan takardunta. Maki ne da daga Abida har Jawahir babu wadda ta same shi a kamala sakandiren ta. Wannan farin ciki da Rahane ta sanya Dr. Mansur, shi ya yi sanadin da ya fara tunanin abin da zai mata as a gift don ya kara karfafa mata gwiwa, ta kuma fahimci cewa babu maraya sai rago. Nakasa ba hujja bace ta mutuwar zuciya. Bincike suke iya bincike wajen manya-manyan likitocin kunne na gida da waje. Dr. Philips, Baturen Sikotilan ne, kuma malami ga Dr. Mansur tun zamanin yana karatu a jami’ar Trinity. Dr, Philips tsohon likitan kunne da makogwaro ne (ENT Surgeon) wanda a lokacin ya tsufa, har ya aje aiki, yana zaune a kauyensu na haihuwa (Braemar) shi da iyalansa. Tsufan Dr. Philips bai hana har zuwa lokacin ana kawo masa cases masu tsanani har gida (Braemar) ba. Idan al’amarin ya gagari manyan likitoci, haka nan manyan kasashen duniya na hayarsa domin ya yi musu aiki a fanninsa. Shine mutum na farko da Dr. Mansur da Dr. Imam suka tuno a lokacin da suka gama gwaji na karshe (hearing test) a kan lalurar Rayhanah. Ko Mami ba ta san me ake ciki ba, sai da aka zo tafiya Abuja yin visa wanda ya kama dole ita Raihan ta je. Bai yi mata bayanin komai ba sai ana i gobe tafiyarsu Abujan da daddare yake gaya mata. An ce zuciya bata da kashi, sannan Mami ‘yar Adam ce kamar kowacce mace, tunda zuciyar ta irin ta kowacce mace ce da Allah ya halitta da kishi. A lokacin da ya gaya matan ji ta yi gabanta ya yi mummunan faduwa. Me Dr. Mansur ke nufi da ita da bai yi shawara da ita ba? Bai nemi jin ra’ayinta ba? Yana nufin shi da Raihanan za su kama hanyar Abujan ko me? Yana nufin da santaleliyar budurwa za ta barshi ya sata a mota su bar gari? Ko yana nufin haka zai sa yarinyar a gaba su bar kasar? Babu dangin iya babu na baba, ita mahaukaciya ko shashashar ina ce? Wannan kauna da kulawa da Dr. Mansur ke yiwa Rayhanah fiye da ‘ya’yan cikinsa ta magani da mece ce? A take yanayin fuskarta ya sauya, kishi karara ya bayyana a kyakkyawar fuskarta. Sannan ranar da ta ga Khalipha rungume da Rayhanah a asibiti ta kara fado mata, da halin da Khalipha ya shiga a lokacin da hirar da suka yi. Tiryan-tiryan ta dinga dawo mata.......’an kasa ni! Soyayya ce Mami!!’ Nan da nan kwakwalwarta ta soma kimsa mata abubuwa daban-daban cikin ranta wadanda a zahiri ba haka suke ba. Wato uban na so, dan ma na so. Dalilin shigar Khalipha halin da ya shiga kafin ya tafi, yana nufin Daddy ya kasa shi. Tunda ya ga ba zai iya tarayya kan soyayya da mahaifinshi ba. Hankalin Mami ya tashi kwarai, wata irin firgita ta kamata. Ta mike tsaye kawai ta yi daki, ba tare da ta ce da Dacta Mansur komai ba. A lokacin ma cike form din neman visa yake yi a ipad dinsa. Jin Mamin ba ta yi magana ba ya daga ido ya dubi sashen da take, sai ya ga har ta kai kofar dakin barcinta. Ya yi dan jim yana ‘yan sake-sake. To me ya bata mata rai cikin wannan maganar? Ya aje biro ya mike ya bita dakin, sai ya ganta zaune a bakin gado ta yi tagumi da hannuwa bibbiyu, yanayin fuskarta kuwa ba zai karantu ba. Zama ya yi kawai kusa da ita kafadunsu na gugar na juna. “Asma’u Zatun-Nidakaini (ma’abociyar mayafi biyu). Mai sunanki ma’abociyar hikima da ilmi ce diya ce ga Sayyadina Abubakar As-Saddik. Lokacin da Manzo (S.A.W) ya yi Hijira zuwa Kogon Hira ita ke kai masa abinci tana rufe da mayafin..........” Sauran maganar makalewa ta yi a makogaronsa ganin Mami ta soma kuka. Hankalin Dr. Mansur ya tashi, kololuwar tashi kuwa. “Me ya faru Asma’u? Na fadi abin da ya bata ranki ne? Ina so ne kawai in gaya miki kissar mai sunanki, ba ta fushi a kan abin da ba ta da sani a kansa, ko kuwa abinda bai kai ya kawo ba”. Mami ta sharce hanci da ido da tishun dake gefen gadonta. Magana ta farko da ta furta masa tun shigowarsa ita ce, “Hausawa baku da kirki, baku da amana wallahi”. Ido ya dan bude kadan yana kallon ta, ya ce, “Mu din kuwa? To me muka yi mu Hausawa rainon Musulunci?” Ta ce, “Kuna kafa hujja da addinin Allah ku ci amanar matayenku, ku kuntata musu ku saka musu hairan da sharran. Ayi Magana ku kafa hujjah da addini bayan shi addini ne mai adalci ga kowa. Wannan na daya daga cikin abubuwan da ke tsorata masu niyyar Musulunta su ga addinin Musulunci very scary, don baku da sanin yakamata da amana, musamman aka zo maganar kara aure.”. Dr. Mansur kallonta yake sosai cikin idanunta dake ta kwararar da hawaye, ya ce, “To wane Bahaushe ne zai kara aure?” Idanunta jage-jage da hawaye ta balla masa harara ta ce, “Ba ga ka nan ba? Ka rasa da abinda za ka saka mini sai da son auren Rayhanah? Hakan ba cin amana bane? Duk taimako da karar dana yi maku?” Ya kama kanshi yana girgizawa don ma ya rasa ta cewa, ya ce, “Da shekaru hamsin da biyar din zan auri ‘yar sha bakwai? Tukunna ma, wai wace Raihanan kike nufi ne?” Gaba daya ranshi ya gama baci, Mami ta ga wani irin fushi cikin kwayar idonsa da ba ta taba gani ba. Tsigar jikinshi ta tashi gaba daya, jijiyoyin kansa sun fito rada-rada, idanunshi sun kada sunyi jawur. Ganin yanayin da ya fada yasa ta kasa bashi amsa. Ya mike tsaye zai fice daga dakin yana cewa, “Lallai kuwa duk inda mace take, komin girmanta da iliminta da shekarunta kamar dabba take”. “Nice dabba Dacta Na?” “Ai ina ga ma wata dabbar za ta fiki hankali”. Ya yi ficewarsa ya rufo mata kofar, ji kake garaam!. Kai tsaye dakin su Raihan ya shiga, dukkansu karatu suke na Alkur’ani irin (pieces) din nan mai kowanne izfi biyu. Su kan taru ne har Azizah da ta dan kara tasawa duk sati biyu suyi saukar Alkur’ani, su yiwa kansu da iyayensu addu’a da ‘ya’yan da za su haifa a gaba. Bai tsaya ba ya ce, “Rayhanatu ke da Azizah ku yi shiri zamu tafi Abuja karfe shida na safe in Allah ya kaimu”. Suka daga mishi kai ba tare da sun katse karatun nasu ba. **** Daddy na sharara gudu a kan titin Abuja da Rayhanah da Azizah, Azizah na gaba Rayha na baya. Basu jima da fara tafiya ba Azizah ta yi barci, don haka Daddy ya mika hannu ya rage mata karfin A.C. Karfe goma sha daya na rana suna Abuja. Sai da ya kaisu suka yi break fast sannan suka karasa British House dake Maitama, suka bi layin neman visa. Don haka zuwa karfe biyar na yamma sun dawo Kano. Ya sauke su, ko gida bai shiga ba ya kada kan mota ya yi asibiti. Ga mamakin Rahane sanda suka shiga falo Mami na zaune a kan carpet cikin wani yanayi da Raihanah ba ta taba ganinta a ciki ba. Tana yi mata wani irin kallo kamar ba ta san daga inda ta fito ba. Ta yi sallama, Mami ba ta amsa ba, sai juyawa ta yi kan Azizah ta soma fadin “Da izinin wa kika tafi rakiyar? Kin gaya mini?” Jikin Rahane ya yi bala’in sanyi. Azizah ta soma kyarma don ta san fushin Mami ba kyau, kamar ta saki kuka ta ce, “Mami kina barci lokacin, Daddy ya ce in shirya mu tafi”. Ta ce, “Wuce ki ban wuri ko in yi kwallo dake wallahi”. Da gudu Azizah ta karasa daki inda ta tadda na Abida na jiranta, ta harareta ta ce, “Ke yanzu don lalacewa shine kika raka wannan jakar yin visar fita waje tare da ubanki, ita ba matarsa ba, ba ‘yarsa ba, ba kowan kowa ba babu dangin iya babu na Baba?” Jawahir ta ce, “Ai ba ita za ki gayawa haka ba, wanda ya yi mata umarnin zuwa rakiyar shi ya kamata ki je ki yi mishi wannan tunasarwar ba ita ba”. Ta ballawa Jawahir din harara ta ce, “Nasa dake a ciki? Na ce na sa ki?” Yadda ta hayayyako mata sai ka rantse da Allah ita ce babba ba Jawahir din ba. Ta ce, “Sai na ji duka sannan in baki amsa”. Abida ta yi tsaki ta fice daga dakin. Mami ta juya kan Rayhanah ta kalleta da kyau, jikinta a matukar sanyaye ta kasa cira kafa daga inda take, a darare ta ce, “Mami mun dawo”. Tace “to barkanku da zuwa”. Ta shige dakin ta ta bar ta anan. Ta kwanta a gadonta amma barci ya ki zuwa. Hankalinta a masifar tashe yake. Me ya faru da Mami? Me ta yiwa Mami ta canza mata haka farat daya kamar ba ta taba saninta ba? Yadda ta kwana da wadannan damuwoyi da tambayar kai da rashin mai amsa mata, haka Dacta Asma’u ta kwana. Sai dai ita nata damuwoyin nema suke su fitar da ita daga hankalinta da tunaninta. Takun sakar da suka yi da Dr. Mansur ranar da ya kawo Rahane ke dawo mata filla-filla. Suna shiga sikeli na optical-illusion, wato tana fassarasu da abin da ta gani a fuska, ba wanda ke cikin zuciya ba. Cewa da ya yi, “Maganar aure da ‘ya’yanki kuwa, ki sa ranki a inuwa sassanya, Allah zai bawa Rayhanah miji na ban mamaki, wanda zai kaunace ta domin Allah, ya rungumeta da LALURAR ta, ba lallai ‘ya’yanki ba, masu hali da dabi’u irin naki. ‘Ya’yanki ba sune kadai MAZA a duniya ba, sannan basu fi ‘ya’yan kowa ba!!! MAZA ma tukunnah, baki gansu ba Mami.....” Wanda a yau ta fassarasu kai tsaye, yana nufin shi da kansa zai auri Rayhanah!!! Tunanin Mami ya gushe kwata-kwata, ta yadda da fassarar zuciyarta. Daman ita mace duk shekarunta da hankalinta, da iliminta in aka zo batun KISHI gushewa suke yi. Tun daga wannan ranar Rayha ba ta kara ganin hakorin Mami a gidan nan ba, ita ba ta kore ta ba, amma ta fita sabgarta. Ita da Abida take sha’aninta ko Jawahir ta san Mami ta canjawa Rahane fuska. Damuwar duniya ta yiwa Rayha yawa. To wa za ta gayamawa damuwar da take ciki ya taimaketa koda da shawara ne? Babu, Yaya Khalipha ne da Jawahir, to amma wace ce Jawahir kuma wane ne Khalipha? ‘Ya’yan Mami ne, za ta kai musu karar mahaifiyarsu ne ko ya ya? Me ta yiwa Mami? Rashin wadannan amsoshin sai su sa ta kwantar da kai cikin cinyoyinta ta yi ta kuka. A haka aka gangara har sati biyu. Daddy ya je Abuja ya karbo visa. Ko da ya dawo ko Mami bai tsaya nunawa ba balle ya bata lokacinsa wajen yi mata bayani. Gaba daya ya fita sha’aninta tun ranar da ta yi masa wannan haukan. Muraran ya gane yanzu kam bata bayan zaman yarinyar nan a gidanta. Don haka ya tattarata ya watsar ya gani ko da gadon ubanta aka cika aka saya mishi gidan? Ya tabbata da hakan ne da tuni ta koreta watakila. Ranar tashinsu ta kama Asabar, Azizah ce ‘yar rakiyar Rahane. Ta Lagos suka tashi a daren Lahadi, da shi da Dr. Imam, Rayha da Azizah. A cikin jirgin ‘boeing 709’ da suke ciki Rahane kanta ta kwantar a kujerar dake gabanta, ba ta kuka sai tunanin rayuwa da kalubalen da ke cikinta. Daddy ya juyo ya mika mata wani kyakkyawan carbi dan Madina ya ce ta yi ta maimaita “Wa-man-nasaru illa min indillahil Aliyul Azeem, Allahumma ashfiny wa afani, ya shaafee ya mu’afee”. Har suka sauka. A Aberdeen suka sauka, basu kwana ba a ranar suka wuce ‘Braemar Village’ ta Aberdeenshire. Ba kamar yadda suka tsara ba, cewa za su sauka a hotel. Dr. Philips ya ce, “A’a, yana da gidan gona a jikin gidansa inda yake kiwon kaji da tattabarun Ingila farare sol da agwagin ruwa, kifi da kangaroo (babba da jaka). A cikin wannan gidan dakuna ne falle biyu ko ko a ce hut, domin hutawarshi da iyalinsa ko sauke bakinsa na nesa. A nan ya yiwa su Daddy umarnin su sauka, har su ga abin da Allah zai yi. Amma bai dauki nauyin abincinsu ba (kun san Bature) da tsimilmila. Duk da haka ya yi umrnin Rayha da Aziza su zauna cikin iyalinsa. Matar Dr. Philips ita ma dattijuwa ce ‘yar shekaru hamsin, sunanta Mummy Regina. Amma da wuya ka bai wa Regina wadannan shekaru a zahiri za ka ba ta arba’in da uku ko da biyar ne. Baturiyar Dundee ce, kuma tsohuwar lauya mai zaman kanta. Yaranta biyu, Cynthia da Chelsea duka ‘yammata ne a jami’ar Aberdeen. Sai dai sun girmewa Rayhanah sosai, don dukkansu degree holders ne a bangarori daban-daban. Yanzu haka ita Cynthia MBA take yi (Master of Business Administration). Chelsea kuma ba ta fara masters din ba tukunna. Turawa ne ‘yan asalin Sikotilan iyaye da kakanni. Kauyen Braemar kauye ne mai tsohon tarihi a Scotland. Braemar wani dan kankanin kauye ne a tudun Grampian (Grampian High Land) wanda ke yankin Scotland. Braemar kauye ne mai kayatarwa da za ki ga gulbi na kwarara a kan duwatsu masu dadadden tarihi, ga tsaunika masu kyau tare da tsofaffin gine-gine na gargajiya, wanda suke ba da wani launi mai ban sha’awa. Kyawun kasar Scotland ya shafi wannan kauye na ‘Breamer’. Akwai wani dutse dake mahadar kogunan ‘Clunie’ da ‘Dee’ ya zama wata mahada ta shakatawa ga al’ummar kauyen, kewaye da wannan mahadar akwai kimanin tsaunuka ashirin wanda sun kai tsahon kafa 3,000. Braemar ya shahara saboda wasanni da ake gabatarwa a garin duk shekara. Wanda ake musu lakani da wasnanin tsaunuka. Shi wannan gagarumin biki ya samo asali ne tun shekarar 1832, wato zamanin sarauniyar Ingila Victoria wadda ta albarkaci wannan bukukuwa. Har zuwa yau ‘ya’yan gidan Sarautar Ingila suna halartar wadannan wasanni wanda a yanzu Sarauniya Elizabeth ita ce babbar uwa ta wadannan wasanni. Ana gabatar da wannan bikin ne a Asabar din farko ta watan Satumba, inda ake bushe-bushe da kada-kaden gargajiya masu dimbin tarihi wanda in ba a irin wannan wajen ba da wuya ka ji irinsu. Wannan wasa ya kunshi gasar busa sarewa da ganga tare da raye-raye irin na da, sannan wasannin gargajiya. Braemar cike yake da dadadden tarihi domin a nan ne aka yi boren Jacobite a shekarar (1715) wanda ya komar da ‘Stuart’ kan gadon sarautar Birtaniya. Dai-dai wajen da aka gudanar da wannan bore shine a yanzu gurbin masaukin baki na ‘Invercauds Arms Hotel’ wanda su Dr. Mansur suka so sauka a can. Wani marubuci Robert Louis Stevenson ya fara rubuta bangaren farko na tsibirin taska (treasure Island) a garin Braemar a watan Agusta na shekarar 1881. A yau guraben da suke dauke da tarihi sun zama wajen saukar baki. Fadoji biyu sun kara ma garin Breamar armashi, wato fadar ‘Kindrochit’ wadda aka gina a shekarar 1390, tana tsakiyar wannan kauyen. Sai kuma fadar Braemar wadda ke tsahon rabin mil (mile) daga garin Braemar. Wani wajen kuma mai dadadden tarihi shine cibiyar tarihi da ake wa lakabi da ‘Highland Heritage Center. Wannan cibiya tana dauke da bayanai masu kayatarwa da suka shafi tarihin garin Braemar. Bayanan sun hada da bayanin bukukuwan tuddai, da bayanin Sarauniya Victoria, da fadar Balmoral da sauraansu. Dr. Philips ke bai wa su Daddy wannan tarihi na kauyensa a kwanakin su biyu da zuwa, suna zaune cikin ‘hut’ suna shan coffee. Su Daddy suka girgiza kai cikin gamsuwa da samun karin sani. Dr. Philips ya aje dan kankanin kofinsa a dan teburin dake tsakiyarsu. Ya dubi Daddy ya ce ya yi masa karin bayani kan wanda ya turo masa ta yanar gizo kan sanadin matsalar yarinyarsu. Tiryan-tiryan Daddy ya zayyano masa komai. Ya ce, “To bayan hakan wane mataki aka dauka na gaggawa?” Dacta Imam ya mika masa komai a rubuce cikin ‘Ipad’ dinsa. Da shi da su gaba daya suka shiga Laboratory, dake cikin private asibitinsa. Bayan sun biya duka payment din duka ta yanar gizo, sunan asibitin Spire Little Aston. Dr. Philips ya shigar da Rahane ya soma gudanar da CT Scan and MRI Scan. Tsayin sati biyu kafin sakamako ya fito. A daren ranar ya sanya su gaban kwamfuta yana yi musu bayani kamar haka; Abin da ke faruwa wajen karbar sako a kunnen bil Adama shine, da farko sauti kan biyo ne wajen kunne sai ya bigi gangar kunne wanda hakan kan jawo gangar kunnen ta girgiza, inda wannan kadawar ta gangar kunne za ta isar da sakon ga kananan kasusuwan guda uku dake a tsakiyar kunne, inda su kuma za su mika wannan sauti ga can cikin kunne, wanda shine zai mai da wannan kadawar ta gangar kunne zuwa sauti, ya kuma tura shi zuwa kwakwalwa, ta haka sai mutum ya ji sauti ko magana. Yarinyarku na fama da cutar amosanin kunne wato (Otosclerosis). Shi wannan amosani ya kan kama wasu kananan kasusuwan dake a tsakiyar kunne, kuma dama sune suke taimakawa Dan Adam wajen ji tar-tar. Ita wannan cuta kan rage motsuwar wadannan kananan kasusuwan, wanda da sannu sai ya jawo mummunan lahani a kunnen mai wannan cuta. Amma a wani sa’in wannan cuta kan tsananta, inda ta kan kai har ga ta lahanta kwayoyin halittar kunne da masu kai sako wanda ke hade da kwakwalwa, in har cutar ta kai wannan matsayi to fa mai dauke da wannan cuta zai daina ji dungurungum..” Cike da fargaba Dr. Mansur ya katse Philips “To ita Rayhanatu meye matsayin nata?” [12/24/2019, 21:47] Takori: Dacta Philips ya yi murmushi ya juya yana wanke hannunshi cikin sink, ya gama ya tsane shi da dan karamin tawul, ya juyo yana kallonsu idanunsu a warwaje, Rayha kuma kanta na sunkuye cikin dan dakin da ke cike da na’urorin gwaji. Tsaurin turancin yafi karfinta bata fahimtar komi. Sai da ya huta ya nisa ya ci gaba da cewa. “Wannan cuta kan kama kunne biyu, amma in aka yi sa’a a wasu lokutan kunne daya kawai take kamawa”. Wannan karon ma Dr. Mansur tambaya ya jefo, “Mene ne kan jawo wannan cuta mai hana ji ta Otosclerosis?” “Kai tsaye ba za a iya cewa ga abin da ke kawo wannan cuta ba. Bincike ya nuna cewa a cikin mutane uku, to biyu sun gajeta ne. Amma ana samun wadanda su basu gada ba, amma suna haduwa da ita ta wani sanadin daban kamar yarinyar ku. Wasu masana na ganin akwai wasu kwayoyin cuta dake jawowa dan Adam ya kamu da wannan rashin lafiya kamar kyanda, sankarau. Ana kuma ganin cewa sinadarin fluoride na daga cikin abin da zai iya tunzura wannan cuta ta (Otosclerosis). Babba alamar cutar ita ce rashin ji, shine alamar cutar na farko. Ya kan iya kasancewa ba mai tsanani ba amma a hankali sai ya tsananta, a mafi yawan lokuta ya kan shafi kunnuwan ne guda biyu. A wasu mutane rashin jin kan dau lokaci har tsahon shekaru kafin rashin jin ya tabarbare, amma wasu kuwa dan da nan da cutar ta kama su kafin wani lokaci sai ya tsananta. A mafi yawan lokuta ya kan shafi kunnuwan ne guda biyu. A wasu mutane rashin jin kan dauki lokaci har tsahon shekaru kafin rashin jin ya tabarbare, amma wasu kuwa dan da nan da cutar ta kama su kafin wani lokaci sai su daina ji. In har ba a nemi magani da wuri ba, yana hana kunnen da ya kama ji. Bayan rashin ji mai dauke da wannan cuta kan ringa yin magana kasa-kasa, (ta yadda in har baka saurara bama ko ka saba da shi bazaka ji shi ba), sannan ga juwa da hajijiya”. Dr. Mansur ya ce, “Duk wadananan alamomi Rayhanah na fuskantarsu. Sau tari sai na saurara sosai nake jin me take cewa, to amma Dr. ta wace hanya jin Rayhanah zai dawo daidai ta daina amfani da hearing aid? Likitocinmu sunyi iya kokarinsu amma abin da suka tsaya a kai dukkaninsu shine babu wata mafita sai ta amfani da na’ura mai kara karfin ji (hearing Aid)”. Dr. Philips ya nisa ya ce, “Da farko in jin mutum ya fara raguwa, ba lallai ne sai an dau wani mataki ba, na ba da magani ko wani abu makamancin haka. Amma in cutar ta tsananta, na’urar kara ji ta kan taimaka kwarai da gaske. Amma kuma a kan kai matakin da cutar kan yi tsananin dama na’urar kara karfin ji ba za ta iya taimakawa mai matsalar ba. A wannan matakin a kan yi aikin fida. Fidar da aka fi yi ita ce wadda ake canza dodon kunnen dan Adam da wani kashi da ake yi da dafaffiyar roba ko karfe. A kan kira wannan fida a Turance ‘Stapedotomi’. A mafi yawan lokuta a kan ci nasara, inda matsalar ji kan kau. Mutum ya dinga ji rangadadau, ya kuma ba da kariya ga can cikin kunnen mutum. Amma fa wannan aikin fida yana bukatar taka-tsan-tsan, don idan aka yi rashin dace, to fa jin mutum kan dauke dungurungum a kunnen da aka yi aikin. Bugu da kari akwai hadari na lalata jijiyoyi masu kawo sako da gurbata jin sauti. Don haka kafin a yiwa mutum mai wannan lalura wannan aikin, a sanya zuciya karbar kaddarar samu ko rashi. Duk da a mafi yawan lokaci a kan dace da yin nasara a wannan aikin fidar kunne, amma akwai wahala wajen yanke hukuncin yinsa farat daya da matsalolin da ake samu idan aka yi rashin dace. Saboda haka ne yasa wasu ke gwammacewa da yin amfani da na’ura mai kara ji cikin kwanciyar hankali har jinsu ya zo ya zama ya tabarbare, inda wannaan na’uraa kan daina yi musu aiki kwata-kwata. Hakan yasa wasu kan zabi ayi musu aiki tunda wuri, wanda hakan zai sa su zama basu da bukatar wannan na’ura in an zabi yin aiki, ka ga in aiki ya yi nasara to an samu waraka kenan, in kuma an sami matsala ka ga ya zama cewa kunnen da yake da kyau sai mutum ya ci gaba da amfani da shi. Wato an jefi tsuntsu biyu da dutse daya. Masana a fannin ENT (Ear, Nose & Throat) sunyi muhawara a kan cewa ko da nan gaba a iya yiwa wancan kunnen da ya rage. Wasu daga cikin su sun yarda kan cewa gara mutum ya hakura ya ci gaba da amfani da na’urar kara ji saboda risk hatsarin dake tattare da yin aikin na samu ko karasa kashe kunnen gaba daya. Madallah da kuka kawo yarinyarku tun kafin na’urar kara karfin ji ta daina yi mata amfani, wato kafin lalurar ta tabarbare da yawa. Akwai shaida takaitacciya wadda ke da’awar cewa kwayoyin magani na flouride za su iya hana ji, kuma za su iya taimakawa wajen kyautata jin. Da ragewa mai lalurar juwa da hajijiya. Amma dai a nan Sikotilan ba’a cika amfani da kwayoyin maganin na flouride ba. Don haka zabi yana gareku, ci gaba da amfani da na’ura, fida ko kwayoyin magani. Akwai bukatar in baku lokaci zuwa gobe don ku yi tunani da kyau ku yi zabi cikin ukun don samun lafiyar Rayhanah.......” Har suna hada baki wajen katse shi da cewa, “Babu wani tunani da zamu yi mun dogara ga mahaliccinu, wanda ya saukar da kowacce irin cuta tare da maganinta. A yiwa Rayhanah fida a dukkan kunnuwan guda biyu. Sauran al’amarin (nasara ko rashin ta) mun barwa Ubangijinmu”. Murmushi Dr. Philips ya yi, yana gyada kai cike da gamsuwa, haka nan shima ya ji ya samu kwarin gwiwa. Ya tura musu takardu cikin folder suka sanya hannu. Zunzurutun kudin aikin Dr. Mansur ya tura masa cikin jakar dake gefensa (in cash) ba ta banki ba, kamar yadda Philips ya bukata. A yayin da ya dauki biro don rattaba sa-hannu cewa ya yi. “TAWAKKALTU ALAL-LAH! LA’ILAHA ILLALLAH!!!” Wato “Da Allah muka dogara! Babu sarki sai Allah!!!” Bai yi barci ba, kwana ya yi nafila, zikirin Ubangiji da neman dacewa daga Allah. Tun Dr. Imam na jan carbi a gefe, har bacci ya kwashe shi a kan sallayarsa bai san tsahon lokacin da Dr. Mansur ya dauka yana sallolinsa da ambaton Ubangijinsa ba. Yana mamaki cikin ransa, wane irin so Dr. Mansur ke yiwa patient dinsa haka? Da ba shi ya haifa ba? ‘Yan boko da yawa basu da wannan akidar. A wajen gogaggen dan Arewa a boko kowa ya yi ta kansa. Naka shine naka, basu da irin wannan zuciyar. A ganin Dr. Imam mutane irin Mansur, tsiraru ne a cikin al’ummah. Wannan haka yake (Takori) **** ALKAWARIN ALLAH YA CIKA...... Kamar daga nesa take jiyo kiran sallah, don haka ta yi hanzarin kai hannunta ta shafo na’urarta, don dai ta san bata kwanciya da ita, kuma gabanin alluran da Philips ya yi mata ta tabbata ta cire su. Da gaske babu su a tare da ita, hakan kuma bai hanata jin kiran sallar Asubar ba. Ta yi saurin juyawa don ganin ta inda sautin ke fitowa. ‘Yar rediyon Dr. Mansur ce dake kan dirowar gadonta ke fitar da sautin kiran sallar. Daga masallacin Qubah. Wata sassanyar iska kuma ta ji tana ratsawa ta cikin kunnuwanta zuwa cikin kwakwalwarta. Ba ta ko haufi jinta ne ya dawo! Rasss!! Kuma rangadadau!!!. Sai ta yunkuro da karfi daga kwancen da take, sai Daddy ya yi saurin maidata kwancen sakamakon na’urorin dake lullube da kanta. “Rayhanahtu aikin bai yi ba ko???” Dr. Mansur ya fada muryarsa na dan rawa jikinsa na dan karkarwa. Ta dago ido a hankali ta dube shi sai kwallar farin ciki ta ciko idanunta. Ta kurawa Daddy ido kawai ta kasa cewa komai. Ko uban da ya haifeta iyakar kaunar da zai yi mata kenan. Ita kuwa da me za ta sakawa Daddy a fadin duniyar nan? Babu, ba ta da shi ban da ta yi masa addu’a a bayan kowacce sallar farillah kamar yadda take yiwa iyayenta da Iya. Dr. Mansur ya gaji da kallon da Rahane ke masa babu ko kiftawa hawaye na zuba a idonta, ya karaso jikin gadonta yana tambaya “Rayhanatu........Rahane.......Rayhanah.......kina jina???” Cikin kukan farin cikin da ya kwace mata ta ce, “Ina jinka Daddy, sosai, ba tare da hearing aid ba!”. Sai ya juya baya ya yiwa Allah Sujjadah. Dai-dai lokacin da Dr. Philips da Dr. Imam suka shigo. Suka nufeta da azama suna ciccire na’urorin domin allon kwamfutar dake makale a sama ya nuna komai na Rayhanah ya dawo normal. Kwanaki bakwai suka kara bayan nan duk cikin treatments din ne, da shan magani, sai da komai ya zama dai-dai sannan suka taho. Suka sauka da asubahin safiyar Litinin mai albarka a filin jirgin Malam Aminu Kano. Daddy bai yi mamakin ganin cewa Mami ba ta zo taryarsa ba, ya san ba ta sani ba, kuma ko ta sani ba za ta zo din ba. Don ko sallamar kirki basu yi ba, wannan ne ya hanashi kiranta a waya har suka je suka dawo. Matar Dr. Imam ta zo ta dauke su, suka aje Daddy da iyalinsa a gidansa dake Lamido Crescent sannan suka wuce nasu gidan a Badawa lowcost. Malam Dahiru maigadi shi ya biyo su da kayansu. Daddy ya yi amfani da mukullin shi ya bude kofar reception suka bi matattakala zuwa sama. Jawahir da Abida na barci Zizah ta fada musu a kai tana ihun murna, “Tashi Yaya Jawahir, Yaya Abida tashi, Rayhanah na ji (with out aid), it is successful...... ku tashii ku gani....” A gigice Jawahir ta mike da gudu ta rungume Rayhanah, sai ga kwallar farin ciki. Abida kanta ta mamakantu, ta kasa komawa barcinta ta rasa cikin yanayin da take ciki, tana taya masoyan Rayhanah murna ko tana bakin ciki ne ba ta sani ba. Abin da ta sani shine jikinta ya yi sanyi, ta kasa hassala komai. Rayha wanka ta yi, ta dauro alwala ta bada faralin Asubahi, ta yi addu’o’i na godiya ga Gafurun-Rahimun, neman Rahamar Allah ga iyayenta da Baba Dacta ba don ya mutu ba. Duk hirarrakin da Azizah ke zuba musu labarin kauyen Braemar ne da basu sani ba. **** Sanda Daddy ya shiga bed room dinsa, ga mamakinsa sai ga Mami ta biyoshi fuskarta a sake kamar ba abinda ya faru. “Maraba da bakin Scotland, duk da dai tafiyar da dawowar duka babu waya..... da fatan an samu nasarar abin da aka je nema”. Ta fada tana loosing tie din wuyansa. Bai ce komi ba kawai kallon ta yake. Sai ta fada jikinshi tana kuka a hankali tana ba shi hakuri da cewa, ta zauna ta yi tunani ta ga cewa abin da ta yi bai kamata ba, kishi ne da sharrin shaidan, wanda baya so a zauna lafiya. Tsakanin mace da mijinta sai Allah. Balle Asma’u da Mansur, wadanda suka gina rayuwarsu a kan soyayya, kauna da fahimtar juna. Ya ce, “Ni me za ki ce min kuma Mamina, tunda kin daukeni dattijon banza, wannan furfurar da ta fara baibaye kaina duk ta banza ce. Ban taba zato ba Asma’u, ban taba zaton za ki iya zargina a kan komai ba balle Rayhanah! Zan dauki komai, amma ban da a taba mutuncina da gemuna da furfurata. Zan iya rabuwa da komai a kan hakan Asma’u.......... Rayhanah ‘yata ce, ki sa wannan a ranki, ina jin wani abu daban game da ita a jikina da zuciyata mai kama da kaunar jini a kanta. Allah shi ya fi kowa sani. Amma kin bani mamaki Mami, mamaki sosai, wanda ya sanya ni cikin kokonton anya ke ce? Asma’u ina hankalinki ina tunaninki? Ina yardarm da muka yiwa juna........” Ta yi saurin kai hannunta ta rufe mishi baki tana girgiza kai hawaye na zuba a idonta. “Na tuba Dactana, na tuba likitan zuciyata. Tun ranar da wannan al’amari ya faru ban kara samun nutsuwar zuciyata ba, bana isasshen barci saboda nadama. Na yarda lallai lokacin hankalina ya tafi, ka yi hakuri Dactana, don Allah ka yafe mini.......” Irin rikon da ya yi mata kadai ya isa amsar cewa ya yafe mata ko bai yafe mata ba. Tabbacin shima ya jigata da rashinta. Da safe ne yake gaya mata duk abin da ya faru a Braemar da nasarar da aka samu. Ta mamakantu kwarai, kuma a lokacin ta tafi dakin su Rahanen. Fuskarta da murmushi ta dubi Rayhanah ta ce, “Congratulation Rayhanah, Allah ya kara lafiya”. A sanyaye ta ce, “Amin”. Tana son ta yi kuka zuciyarta cike da kaunar Mami da tsoron kada ta komo irin Mamin da ta koma mata a baya. To haka rayuwar Rayhana ke tafiya a gidan Dr. Mansur, cikin dadi ko akasin sa. Dama rayuwar ta gaji haka. Watarana zuma, watarana madaci. Mami ta daina kyararta, amma fa bata shiga sha’aninta kamar da. Girman da yake bayyana a tare da Rahanen yana bata tsoro, yarinya ta koma kamar black American, kirar jikinta da yanayin tsayinta mai sa maza su kasa dauke ido a kanta ne. Ga zigar Dr. Halima wadda ta fi komai yamutsa mata lissafi. Ta kan ce idan ba ta raba yarinyar nan da gidanata ba, to kuwa ta shirya shan mamaki a gaba. Asiri kuma ko ta ina Halima bankawa Khalipha take don ya yarda da maganar Radhiyyah, shi da ma kwata-kwata babu wanda ya san halin da yake ciki. Su ba kudi ne basu da shi ba, ba kuma wani abin hannun Khalipha ko iyayensa suke hange ba, kawai tana son samawa ‘yarta abin da take so ne, don ta samu kwanciyar hankalinta. Cikin wannan tsukin Khalipha ya dawo Morocco, ya kammala kwas din da aka tura shi, ya samu karin girma a ofis dinsu. Kowa ya sha tsaraba amma ta Rayhanah (is special). Kaya ne na matan Morocco zabga-zabga, wasu lafiyayyun dogayen riguna kala-kala guda goma sha biyu, da Pakistan da Abayat suma kowanne dozen guda. Ya yin da kannensa suka tashi da guda shida-shida, doguwar riga biyu, Pakistan biyu da Abayoyi guda biyu. Wannan karon kam Mami ta kara karfafa zarginta, ta kuma sa ido sosai a mu’amalar Rahane da Khalipha. Da Khalipha ya dawo ya samu wannan labari da bai taba samun mai dadi kamar shi ba, wato warkewar Rayhanah. Daki ya shiga ya gabatar da sallar nafila raka’a biyu ya yiwa Ubangiji godiya, ya yiwa Baba Dacta addu’a, ya roki Allah ya ba shi karfin zuciyar fuskantar iyayensa a wannan lokacin a kan bukatarsa. Sai dai abin da ke bakanta mishi rai kwarai shine, sabuwar mu’amalar da Mami ta tsiri yi da Rahane, na rashin sakar mata fuska, haka ko magana take yi da Khalipha idan Rahane ta shigo wajen sai ta yi shiru. Sannan idan Rahanen ta gaisheta ko ta yi mata magana, amsawa take a ciki kamar ba ta so. A sati daya da Khalipha ya yi cikin gidan yana hutawa kamin ya koma ofis Monday ya lura da hakan. Ba ta da zancen da take yi masa sai na Radhiyyah, and he is not interested at all. Ta kasa ta tsare ta hana shi kebewa da Rahane da yake tana cikin hutu. Ko yaushe tana tare da shi, abinci tare suke ci, fita ma in ta kamata sai ta ce shi zai kaita, a haka dai har ya cinye satin shi da Rahane sai dai ya hango ta daga nesa ko in sun fito cin abinci. Ranar Lahadi da yamma ya koma Abuja ya shiga sabon ofis dinsa, wanda bai sa shi farin ciki ba ko kadan, don tunaninsa da zuciyarsa basa kai, sun yi nisa cikin zuzzurfar soyayya marar misali. Khalipha baya da zabi banda ya kara kauracewa gidan su, baya son bayyana abin da ke zuciyarshi yanzu, amma zuciyar ta ki jurewa. Ya kan kira iyayen a waya su gaisa a kai a kai ya kuma ba da uzirin rashin samun zuwa da aiki ya yi yawa. A wata Seminar likitoci na federal govt. da Dr. Mansur ya je Abuja ya yi tunanin bari ya kai ma Khalipha ziyara gida tunda Asabar ce baya zowa ofis. Gidan Khalipha da ma’aikatar su ta ba shi yana nan a (Maitama). Daddy ya yi horn maigadin ya bude mishi yana barka da zuwa. Daddy ya tambaye shi ko maigidana yana nan? Ya ce, “Eh, yana nan, amma gaskiya a tsukin nan baya ganin kowa, ya kuma yi umarni gare shi cewa ko waye ya zo neman shi ya ce baya nan ko ya same shi a ofis. Yanzun ma don ya ga Daddy ne shi yasa ya bude”. Daddy ya faka motarshi a gefe cikin rumfar adana motoci a kalla guda uku, ga ta Khalipha nan guda daya kirar (Cadillac Srx) da canzo daga Morocco, daga ita ba wata. Ya fito ya doshi (door-bell) ta falon yana dannawa. Jibril da ke wankin kayan Khaliphan a bayan gidan ya zo ya gaida shi, sannan ya ce, “Oga bai da lafiya Alhaji, kuma ya ki yarda cewa ba shi da lafiyar balle ya je asibiti, ni dai na yarda ba shi da lafiyar ko abinci ban yi zaton yana ci ba, don ya hanani yi mishi girki sai dai kullum ya yi ta aikena siyen abinci, kuma yadda na kawo haka nake fiddashi abin da ya taba ba yawa. Ba zai bude ba, da dai ka kira shi a waya”. Da sauri Daddy ya dauko wayar yana kiran Khalipha sannan ya yiwa Jibril inkiya da hannunshi alamar ya tafi. Anyi sa’a wayar Khalipha tana kunne, kuma ya sanyata a caji nesa da shi kadan, yana kwance gefen gadonshi da ruwan tokan (pjs) a jikinshi, ya tasa kwamfuta a gaba yana shigar da sakonni. Sarai ya ji kararrawar amma bai yi niyyar budewa ba, sai kuma ga kiran waya dole ya mike zuwa gareta, ga mamakinsa kiran Daddy ne. Da sauri ya amsa wayar. Daddy ya ce, “Ina kofar falonka”. Cikin rashin kuzari ya bude kofar. Daddy ya tokare hannayenshi jikin kofar falon yana kallon shi. Gaba daya ya zube ya yi jajir, idanuwansa manya masu sheki sun zurma ciki, hakan bai hana shi bayyana a kyakkyawansa ba. Yana shirin russunawa Daddy ya yi saurin kama hannunshi suka idasa shiga cikin falon, ya zaunar da shi a gefensa cikin bakaken (leather seats) din da suka yiwa falon kawanya. Kafin Khalipha ya furta gaisuwa Daddy ya katse shi da cewa........ “Me ya faru? Me ya same ka, ka kulle kanka kai kadai cikin gida? Me ya zabgar da kai haka? Mece ce damuwarka Khalipha? Gaya min maza, wannan ba Khaliphana da na sani bane”. Sai ya fada jikin mahaifinsa shi kuma ya rungume shi sosai, ba kuka yake yi ba, ajiyar zuciya yake yi. Ji ya yi zuciyar tana sanyi daga zafi da suyar da take yi. Wani bangare na zuciyarsa na karfafa shi da cewa, ka yi amfani da wannan damar da Allah ya kawo, ka fadawa Daddy abin da ke neman kwantar da kai ya salwantar da ci gaban rayuwarka. Daddy uba ne mai fahimta, da akida daban da ta Mami. Babu haufi zai fahimceka, ya mallaka maka abin da rai da zuciyarka ke so. Walwalarka da kuzarinka su dawo, ka dauko Rayhanah ku rayu tare har abada, ku haifi ‘ya’ya masu albarka har zuwa karshen rayuwarku. Duka wannan tunani Khalipha ya yi shi ne cikin ‘yan dakikan da basu wuce goma ba. Daddy bai katse shi ba, ido ya zuba masa yana sauraren amsar bakinsa. Khalipha ya dago ya kalli Daddy idanunshi sun kada sun koma brown dinsu masu sheki dake cike taf, da kwalla, wadda babu alamun za a ba ta damar zubowa saboda dauriya irin ta namiji da rashin son nuna karaya. Ya maida kai ya sunkuyar, sakamakon kwarjinin da idanun mahaifin nasa suka yi masa. Amma fa wani bangare na zuciyarsa na cewa da shi, “A kul! Ka bari wannan damar ta subuce maka...” Cikin rawar murya da sarkewar harshe ya ce, “Daddy… Rayhanah…. Rayhanah nake so ka aura mini”. Dr. Mansur bai tambaye shi wace Rayhanah ba, tunda Rayhanah daya suka sani a duniya dukkansu, basu san wata mai wannan sunan bayan ita ba. Dr. Mansur bai yi mamaki ba, shi kansa jikinshi na ba shi akwai wani boyayyen al’amari game da Rayhanah a kanshi da ‘ya’yansa tun ranar da ya fara ganinta jikinshi ya ba shi hakan. Wannan yarinyar rayuwarta cikinsu na nuna al’amura da dama wanda Allah kadai ya sani. Sai dai kuma kash! A inda ya yi fatan al’amarin ya kasance ba a can ya kasance ba. Anyway a hakan ma baya da ja, kuma yayi farin ciki, amma yadda yasan yunwar cikin sa haka yasan cewa Mami ba za ta taba amincewa ba, musamman da yake ta fishi power a kan Khalipha. Tabbas Khalipha ba wani abu ke damun shi ba sai soyayya, irin soyayyar da ya yiwa Mami mai azabtarwa, wadda ba a lokaci daya take faruwa ba, a hankali take shigar mutum ta yi masa kisan gilla batareda ya sani ba, tayi masa babakare a zuciya da gangar jiki. Ta hana shi sukuni da nutsuwa har sai ya mallaki abin da take so. Wannan shirun da Daddy ya yi ba karamin kada Khalipha ya yi ba, tsoron shi Allah, tsoron shi kada Daddy ya ce ba zai ba shi Rayhanah ba ko ba zai yi mata aure yanzu ba. At 34, yana cikin wani mataki na tsananin bukatar diya mace, amma fa Rayhanah kadai. Ga dimbin mamakinshi Daddy murmushi ya yi ya dafa kafadarsa ya ce, “Wannan shine abin damuwa Babana? Har a sanya zuciya cikin takura? Baka tsoron hypertension kake wasa da aiki da lafiyarka? Rayhanah ai ‘yata ce kamar yadda kake Da a gareni. Idan har kana so ita ma tana so me zai hana in mallaka muku juna? Ni ai abin farin ciki ne a gareni in aurar da Rayhanah a hannun da na tabbatar ko bayan raina ba za ta wulakanta ba. A da, na yi niyyar ba zan aurar da Rayha da su Abida ba sai sunyi zurfin karatu, amma tunda har haka ta faru, bani da ja da yin Allah. Abdallah jeka nemi so wajen Rayhanah, idan ta baka ni mai daura aure ko gobe ne. Alas! Babu sauran damuwa ko?” Hawayen farin ciki suka zubowa Khalipha, ya rungume Daddy yana kuka sosai. Daddyn na share masa da hankicinsa yana cewa, “Haba Babana, tsakanin uba da dansa ai ba godiya. Duty na ne as a father in tabbatar da farin cikinku in har bai sabawa addini ba. Hakkina ne in yi muku aure, saboda kun kai munzali, amma sabgogin neman duniya suka sha’afar dani ga yin hakan, har sai da ka ankarar dani. Nima na gode Babana. Ya isa kukan nan bana son shi, ya isa!” Haka ya ci gaba da share mai hawayen har kunya ta kama Khalipha. Daddy da kansa ya je kitchen ya dauki tray ya bude firij ya debo tuffah, inibi, fresh milk da cake da sandwitch ya dawo falon, ya ja tebir a tsakiyarsu ya daura tray din, ya dau tambulan mai garai-garai yana tsiyaya tatacciyar madarar Oldenburger mai sanyi yana cewa, “Ni bako ba a tareni da komai ba, to bari in yiwa kaina maraba. You donno how hungry I’m”. Dariya Khalipha ya yi, shima wata azababbiyar yunwa ya ji ta taso masa. Ya karbi tambulan din da Daddy ke mika masa cike da madara mai sanyi ya shanye, ya sake cika masa ya kwankwade. Zai karo masa yana dariya ya daga masa hannu. Sai shi ya cika ya shanye. Khalipha ya mike ya je kicin din, ya debo dambun nama mai yawa da Mami ke ba shi in zai taho da coconut-cake mai yawa da ta ke sawa ayi mishi da kwalin Exotic ya zo ya kara musu a kan tray din, suka yi shiru dukkansu sai ci suke, da alama kowannen su tsohuwar yunwa ce a jikinsa. Daddy na bai wa Khalipha labarin zuwansu (Braemar Village), da yadda komai ya wakana, a lokacin shi Khalipha yana Morocco. A nan ne Khalipha yake gayawa Daddy shima ya taba yin wannan tunanin, amma sai ya ga cewa tafiyarsu shi da ita ba za ta yiwu ba. Shi yasa ya bari a ransa sai sunyi aure. Daddy murmushi ya yi yana tuno artabunshi da Mami a kan tafiyar, amma bai gayawa Khalipha ba kada mutuncin mahaifiyarsa ya zube a idonsa. Shima ya dade yana mamakin wai Mami ce ta yi masa haka? Zargi a kan shirme? To dai ya yi mata uziri da matantaka. Ai mace ce ita ma. Tunaninsu ragagge ne. A wani fannin kuma yana cikin damuwar yadda za su karke da ita a karo na biyu idan ta ji bukatar Khalipha, sannan in ya tuna alkawarin da ya yi mata kafin ta yarda ta karbi yarinyar. Amma ai ba ta fi karfin addu’a ba, Allah ya sanyaya zuciyarta don ya san ba ta iya fushi ba, shima bai iya ba. Musamman a kan Rayhanah. Khalipha wanda ke cikin farin cikin da Daddy bai taba ganinsa cikin kwatankwacinsa ba ya katse tunanin shi da cewa, “Daddy zan iya kiran Rayhanah a waya da amincewar ka? Daddy zan iya ba ta waya?” A sanda ya fadi hakan kansa na sunkuye ne. Daddy sai ya mika masa hannu ya ce, “Bani in kai mata. Amma da wajewar cewa za a bani salalar kaiwar, ka san ba a aikin banza a Kano”. Dariya Khalipha ya yi, ya zaro wayarsa ya cire layin (MTN) wanda kowa ya san shi da shi ya sanya sabo na Etisalat ya mikawa Daddy. Daddy ya karba ya zura a aljihun coat dinsa, ya sake mika masa hannu ya ce, “To bani salalar”. Ba yadda Khalipha ya iya don tsananin farin cikin da yake ciki ya fi gaban biro ya rubuta, ya dauko credit card na layin da Daddy ke amfani da shi na naira dubu daya ya dauki wayar Daddy ya loda a ciki. Daddyn ya karba ya mike yana cewa, “To ai kaga haka ya fi, yanzu zan san na zama dan aiken soyayyah da hujjah”. **** [12/24/2019, 21:47] Takori: Daddy na gudu a kan titi zuciyarsa kamar takarda don haske, Allah yana cika masa burirrika tun gabanin ya yi furuci a kansu. Addu’ar da yake yiwa Rayhanah a kullum shine, Allah ya ba ta miji na gari, bai taba yin zabi ba sai kiyasi. Wato dama a ce..... sai ga shi kiyasin ya fada a inda bai zata ba. Baya tsoron Mami da rigimarta godiya yake yiwa Allah da ya ba wa Rayhana miji irin wanda yake yi mata addu’ar samu dare da rana, fiye ma da kintacensa. Daddy bai iso Kano ba sai karfe goma sha daya na dare. Sai dai tun kafin ya yi parking wayarsa ta hau tsuwwa, da ya daga sai ya ga Dr. Abubakar ne wani likita dake karkashinsa. “Dr. it is urgent......a fatal accident at emergency.....” Abin da ya fada kawai kenan. Bai yi la’akari da gajiyarsa ba da baccin dake cin idanunsa ya karya kan motar Mal. Dahiru ya kara bude mishi ya fita aguje don ba abin da ya fi ceton rai muhimmanci a wurin Dr. Mansur. Shine on-call ko ba shine ba, muddin aka samu mummunan hatsari sai ya tsaya a kai muddin an gaya masa. Don haka bai samu dawowa gida cikin iyalinsa ba sai da Asubahi. Zuciyarsa cike da wani irin sabon Imani. Bai taba ganin mummunan accident irin wannan ba, kafa ta fita, hannu daya ya fita, ‘yan yatsu sun gutsire. Don haka he is not in the mood ko Mami bai nema ba yana dakinsa, ya yi wanka ya sha coffee ya koma ni’imtaccen gadonsa ya nade bayan ya karo karfin na’urar sanyaya daki don ya samu nutsuwa. Mami ba ta san Dr. na cikin gidan ba ma sai da ta shigo dakinsa don ta gyara, wannan aikinta ne ba ta sanya kowa. Nan ta ganshi yana ta barci, sai ta hakura da gyaran don kada ta tada shi, ta koma kicin don ta hado masa karin kumallo mai kyau, don ga dukkan alamu a jigace yake. Dr. bai fito ba sai karfe daya na rana ya fito a kintse, lokacin Mami na shirin fita ita kuma har ta ratayo (handbag), sai suka yiwa juna murmushi. Ta ce, “Dactana.......” Ya ce, “Maminaah!” Su Abida duk suka fito, Rayhanah na bayansu suna gaida Daddyn don tun shekaran jiya basu sa shi a idonsu ba. Fuskarshi da fara’a sosai yake amsawa, idonshi a kan Rahane ya ce, “Yammatan Mami duk za su tafi makaranta su barki ke kadai, don ke sai shekara mai zuwa, don haka maimakon zaman kadaicin gara a ribaci lokacin, na nema miki gurbi a Informatics dake Kazaure za ki yi International Diploma a Cyber Security (Computing) tsayin watanni takwas”. Har kasa ta zube tana yiwa Daddy godiya. Abida na huci da zumbura baki, don dai tun farko ita ta kawo zancen shiga Informatics kafin result dinsu ya fito, amma Daddy ya ki amincewa da barinta ta tafin, a cewarsa rawar kanta ya yi yawa ba zai yarda ta je inda babu mai sa ido a kanta ba. Ita kuma ta so tafiyar ne saboda kawayenta da yawa ‘ya’yan manyan gwamnati suna Informatics. Amma ga shi ya ce makiyarta ce za ta je. Duk duniya Rahane ba ta da burin da ya wuce karantar na’ura mai kwakwalwa, tana sha’awar taganta da ita tana sarrafa ta, me za ta ce da Daddy a duniya ban da ta yi mishi biyayya da addu’a? Mami ko a kwalarta hankalinta ya yi gaba, domin kauye za su je da Dr. Halima a kan maganar Khalipha da Radhiyyah. Ta daina nuna adawa da Rahane a kan idon Daddy da ita Rahanen. Dr. Halima ta ce ta yi hakan, ta ruwan sanyi za ta raba iyalinta da Raihar da ta zo ta zame mata karfen kafa, saboda take-taken Khalipha a kanta. Jawahir ta taya Rayhanah godiya a wajen Daddy. Ya ce babu komai su je su fara shiri. Abida da Jawahir duk sun samu gurbi ne a Jami’ar Bayero. Abida a Zoology, Jawahir a Microbiology, Azizah an samu wucewa SS I a Nigerian Turkish dake Tarauni (Boarding). Abida bata son kwas din da aka bata don ba shi ta zaba ba, amma da aka yi post UME suka cillata can saboda makinta bai kai ba, medicine ta zaba. Wannan ya bakanta ran Abida ba kadan ba, ta yi kuka har ta gode Allah, ta ce ba za ta yi ba, za ta jira shekara ta zagayo ta kara nema. Daddy ya ce sai ta yi, ba za ta zauna a gida kowa yana makaranta ba. Don haka ne ta kawo masa zancen Informatics ya ga ba ta dace da kowa ba sai Rayhanah. Ita kuma a bisa dole ta hakura za ta yi Zoology din don Mami ta tausheta da cewa ta yi din, ta kuma sake neman Medicine din shekara mai zuwa. Litinin, Jawahir da Abida suka fara registration a Bayero, Azizah aka kaita Turkish, Rahane Dr. da kansa ya sata a gaban mota ya kaita Kazaure. Duk wasu cike-ciken takardu da ya kamata ya yi mata, aka ba ta daki da sauransu. Rahane ta kudire a ranta da yardar Ubangiji ba za ta bawa Baba Dacta kunya ba. Da ya karya kan mota zai tafi, hawaye ne suka zubo mata. Ba na bakin cikin an kawota inda za ta zauna ita kadai ba, a’a, na kauna ne da farin ciki. Ganin tana kuka sai ya yi ribas ya dawo dai-dai inda take tsaye ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro dalleliyar wayar (sony xperia) yana cewa, “Af! Kinga Rayhanatu na sha’afa, ungo wannan taki ce, zan dinga kiranki, Yayanki zai dinga kiranki, kema in kina cikin matsala za ki iya kiranmu na zuba miki duk lambobinmu, maimakon duk sati ki zo gida, ki yi hakuri sai bayan wata-wata zan ke zuwa da kaina in tafi dake a duk Asabar din karshen wata”. Tana share ido da gefen gyalenta ta ce, “To Daddy”. Ya ce, “Kukan na mene ne?” Da sauri ta ce, “Ba na komai bane Daddy....... is just that I will miss my Daddy so much....” Murmushi ya yi ya ce, “Daddy will miss you too. Sai dai hakan ba zai hana neman ilimi ba, duk matakin da muke a yau, albarkacin ilimin ne, wanda iyayenmu suka tsaya mana muka yi. Don haka dole ki yi hakuri da komai ki mai da hankali a kan abin da na kawo ki ki yi, ki manta da komai da kowa! Ki kawo min sakamakon da nake tsammani daga gareki”. Da sassarfa ta daga kafa ta nufi hanyar hostel. Shi kuma ya ja motar a hankali ya fita daga harabar makarantar yana yi mata addu’a kala-kala cikin zuciyarsa. **** RAYHANAH A KAZAURE Rayuwar Rayhanah a Informatics, have brought new insights a kowanne fanni na ci gaban rayuwarta. Malaman duk Asians ne, mostly Indians da Singaporeans. Ba neman kawaye ya kaita ba, don haka ba ta tsaya neman sabo da kowa ba. Tsakaninta da ‘yan hostel da ‘yan ajinsu gaisuwa ce ta Musulunci ta hanyar sallama da musabaha. Rahane ba ta wasa da addininta, ba ta wasa da sallolinta guda biyar a kan lokaci, duk sanyi, duk zafi, duk ruwan sama basa hanata yinsu tare da liman a masallaci. Da farko ta samu kanta cikin rikicewa da rudanin ganin kamar karatun ya fi karfinta. Amma a hankali da taimakon malamanta, ta soma gane kan karatun nasu, har ta hada da wayar da kan wadanda basu gane ba cikin ‘yan ajin nasu a lokacin da babu darasi (Tutorial). Satinta biyu a Kazaure ba ta taba kunna wayar da Daddy ya bata ba, sai wata ranar Lahadi da yamma bayan ta gama duk abin da za ta yi. Tana ninke kayanta ne wayar ta fado daga inda ta tusa ta, domin a wurin Rahane ai sai da matsala ko lalura waya take da amfani. Haka nan ta samu kanta da son sanyata a caji. Bayan awa daya ta cika ta kwanta a rigingine a gefen gadonta, kyan wayar ya isa, ba ta taba ganin waya mai kyan wannan ba. Tana kunnawa sakonni hudu suka shigo, na farko daga Daddy ne, lafiyarta yake tambaya da yanayin karatun nasu, a karshe ya kare da yi mata addu’a da fatan alheri. Sako na biyu babu suna, sai dai anyi saving lambar da ‘husband’. Wane ne husband? Ba ta sani ba. Ga abin da ke rubuce. “Idanuwana sun makance a laluben neman uwar ‘ya’yana. Shekara da shekaru zuciya na fada min ba za ka sameta nan kusa ba. Sai dai kuma Allah ya yanke min wahalar a lokacin da ban zata ba. To amma Rayhanah wife din ba ta san ina yi ba”. Ba ta fahimci komai ba, amma da ta ji an ambaci sunanta ta tabbata sakon nata ne. To wane ne ya turo? Lambar ba iri daya ce da ta Daddy ba. Sai ta matsa ga sako na gaba. “Wani lokacin idan na yi yunkurin in bayyana kaina gareta, sai kwarjininta da fargabar yadda zata karbi al’amarin ya hanani, saboda matsayin da ta bani ba matsayi ne na uban ‘ya’yanta ba. Mai yiwuwa kuma ba zan zama irin zabin mijin da take so ba, sai ta yi amfani da karamci da halarci ta karbe ni, wanda nikuma bana son hakan. Rayhanah soyayyarta nake nema, ba halacci da karamci ba”. Sako na gaba. “Bude zuciyarki ki sanya mata wani hoto na wani mutum da kika yiwa farin sani. Kin bashi matsayi kala-kala a rayuwarki, amma cikin kwayar idonki bai taba ganin SO ba! Rayhanah sai girmamawa da sadaukarwa! When he decided to turn the relationship to a more complex one, more important, more valued, ya zamo ya shigo cikin rayuwarki ta kowanne bangare right, left and central........ would it be accepted?” Ba ta san sanda ta yi murmushi ba, haka nan ta samu kanta da yin replying a gajarce. “Who is he???” “Someone that love u unconditionally Rayhanah!!!y”. A dai-dai lokacin ne kuma kiran waya ya shigo daga wata lambar daban wadda babu ita cikin wadanda Baba Dacta ya yi saving. Hakan bai hanata dagawa ba, Yaya Khalipha ne. Yadda ya ji muryarta tana rawa sanda take gaisheshi sai ya ji babu dadi, bai so ya yi hakan ba, da ya san zai sata cikin damuwa. To amma bai da mafita sai hakan, don baya son ya yi mata fin karfi. Ya sani ya kuma tabbata ba ta taba yin mu’amala da wani namiji ba a rayuwarta, balle ya yi tunanin tana son wani. A shekarunta na yanzun (goma sha takwas) a ganinsa ta isa ta tantance abin da take so da wanda ba ta so. “Ya na ji muryarki kamar tana rawa?” Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Wasu sakonni aka turo min Yaya Khalipha, na kasa gane musu”. “Wa ya turo?” “I don’t know!” Ta fada a hankali. Domin a wurin Rahane rashin tarbiya ne a ce maka (I love you) har da unconditionally. Khalipha sai ya yi murmushi, ya sake kwanciya sosai cikin sofa din bed room dinsa. “Me ya ce cikin sakon?” Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Something like rashin kunya Yaya Khalipha”. Dariya ya yi mara sauti. Ya lumshe ido cikin murya kasa-kasa ya ce, “Ya ce miki I love you ne?” Sai da ta rufe fuska sannan ta ce, “Eh mana”. Ya ce, “To ke baki son shi?” Ta girgiza kai ta ce, “Yaya Khalipha a bar maganar nan, ni bana son irin wannan maganar”. “Why Rayhanah? Kin girma fa, amma ki kasa sanin abin da duk mai shekaru kamar naki ya kamata ya sani?” Shiru ta yi, wanda ya ba shi damar ya fallasa kansa kawai komai ta fanjama-fanjam. Ya ce, “Idan kuma nine fah?” Ta zaro ido sannan ta rufe da karfi, ta kasa cewa da shi komai. Shiru ta ratsa na wani ‘yan dakikai, zuciyoyinsu da gangar jikinsu ke aiki iri daya. Rahane ta dade tana son Yaya Khalipha, sai dai ita kanta ba ta san cewa son nashi take yi ba. Ta dauka kawai shakuwa ce da kauna a dalilin kulawar da ya nuna cikin rayuwarta. Sai dai ba ta taba kawo wani abu da ya wuce wannan cikin zuciyarta ba. A yau da Khalipha ya yi mata wannan misalign, sai ya zamanto kamar yayi fami ne akan tsohon gyambo, sai kaunar da kwantacciyar soyayyar suka taso gaba daya. Soyayyar da Khalipha ke yiwa Rayhanah yana jinyarta shekara da shekaru unexpressable ce. Don haka a yau daga Khalipha har Rayhanah babu wanda ya yi barcin kirki, tunda ya ji ta yi shiru ba ta da niyyar tankawa ya kashe wayar. Bai kuma kara kiranta ba sai bayan kwana biyar. Kwanaki biyar din nan tamkar shekaru biyar ne a wurin Khalipha. Duk da haka ya daure bai kira Rayhanah ba, yana so ya ba ta sarari ne ta karbi soyayyarsa a hankali. Ita kuma Rahane sai ta ji dadi da bai kara kiran nata ba, don in da wanda take jin nauyi yanzu a duniya, to Yaya Khalipha ne. Sai dai ita ma kwanakin sun dafa ta, har ta dafu lugub. Sai dai wani mafarki da ta yi a kan Khalipha ya tsaya mata a rai matuka, a rana ta hudu da yin wayarsu. A al’adarta idan ta yi mafarki ta tashi ba ta kara tunawa da shi, amma ta rasa dalilin da yasa ta kasa manta wannan mafarkin. Cikin wata gona ce mai cike da korran gangayyaki, ga kayan itatuwa nunannu irin su goba, kashu, inibi, tuffah, mangoro har da fasa-dabur da roman, yara goma kyawawa lafiyayyu na ta tsinkowa suna kawo mata inda take zaune cikin wani gado na alfarma. “Momi ga kashu......Momi ga roman...... Mommy ga Inab.....” Sai ta ce musu, “To ku raba su biyu, ku kai wa Daddy rabi ga shi can”. Ta nuna musu managarcin mutum da ke tsaye yana yiwa fulawoyi ban ruwa. Ya juya bayansa, wanda take da tabbacin Khalipha ne. Da gudu yaran suka doshe shi ko wanne irke da kayan marmari nunanne na karshe. “Take it Daddy..... Momy ta ce mu kawo maka, she said she love you much...... and we love u either...... do you love us, Dad?” Sai ya juyo da murmushi yana karba yana gutsira yana basu, ya janyo su duka ya rungume yana cewa, “Daddy love you too...... and he love mummy as well, a kiss plzzzz???” Ya tura musu kumatunshi, ko juyowar da ya yi ne ta bata damar ganin fuskarsa. Ba Khalipha bane….. IBRAHEEM NE!. Wannan mafarki ya tsaya a zuciyar Rayhana, mene ne hadinta da Ibraheem da har take mafarkinsa? Mutum na farko da ta tsana saboda girman kansa. Duk da ba ta da shekaru masu yawa sanda Ibraheem ya bar Nigeria, ta yi mishi farin sani, ba ta kuma manta halayensa ba. Idan za ta fassara mafarkinta, yana nufin Ibraheem shine uban ‘ya’yanta? “Noooo!!!” Ta fada a fili. Mafarki ne kawai ba gaskiya bane, kuma ba duka mafarki ne yake gaske ba. Don tasa abin a ranta ne kawai. Ko da kiran Khalipha ya shigo a rana ta biyar, Rahane kasa dagawa ta yi saboda jin nauyi da nauyin zuciya hadi da rashin abin ce masa. Bai yi fushi ba ya ci gaba da kira a kai a kai amma ta kasa dagawa. Zuciyarta bugawa take yi a duk lokacin da sunan Yaya Khalipha ya bayyana a screen din wayar. Da ya kira a karo na bakwai sai ta yi shahada ta daga a hankali wayar na neman subucewa saboda rawar da hannunta ke yi. Khalipha ya yi ajiyar zuciya a galabaice ya ce, “Rayhanah sabauta ni kike so ki yi? Laifin me na yi miki haka da kika zabi ki azabtar dani ta wannan hanyar?’ Shiru ta yi. Da ya tabbatar bata da amsar ba shi sai ya ce, “Alright, maybe am not good enough to be your husband. Bari in barki ki huta. Good night”. Ya kashe wayar. Shi kansa ya san ya fada ne don ya yi causing damuwa a zuciyarta, amma ya san nauyi ne da rashin sabo ya hanata daga wayar. Ai kuwa ya kunnata, da sauri ta kira lambarsa ta sake kira ta ci gaba da kira amma ya share ya ki dagawa. Rahane sai ta soma kuka, Allah ya sota ita kadai ce dakin lokacin. Hawayenta na zuba a kan wayar ta yi typing text ta tura masa. “Ka yi hakuri Yaya Khalipha ba haka bane, ban san me zan ce maka bane”. Shima shiru makatau ya ki replying. Sai ta rufe wayar gaba daya tana tsane hawayen idonta da gefen hijabin sallarta. Wahaltaccen barci Rahane ta yi, da mafarkai barkatai wadanda babu Khalipha a cikinsu sai IBRAHEEM!!!. Wannan al’amari ya fara tsorata Rahane, wanda take so yake sonta daban, wanda take gani cikin mafarkinta daban. Ya Allah! Meye gaminta da Ibraheem? Da ta manta shekaru takwas? Ba ta kara tuno shi ba, balle wani abu da ya shafe shi, sai yanzu da Khalipha da soyayyarsa suka shigo cikin rayuwarta? Washe gari ranar Juma’a kenan, tana masallaci tana Azkar bayan an sakko daga sallar Juma’a, tana yi tana share hawaye saboda damuwa, ta yi alkawarin ba za ta sake kunna waya ba tunda ita tasa Yaya Khalipha ya yi fushi da ita. Gobe ne Asabar din karshen wata, kuma gobe Baba Dact zai zo ya dauke ta. Yau watanta guda kenan a Informatics Kazaure. Zaituna classmate dinta ce, ita ce ta shigo cikin masallacin tana dube-dube, ta hangota a can lungu ta dukunkune cikin farin hijabin sallar ta ko jan carbi take ko karatu take ita kadai ta sani. Ta nufeta da hanzari ta ce, “Tun dazu ake nemanki Yayanki ya zo za ku tafi”. Cikin mamaki ta ce a ranta, “Wane Yayan nawa?” Haka dai ta mike ta bi bayan Zaitunan. Daga nesa ta hango wata dalleliyar Cadillac srx ruwan makuba, gilasanta masu duhu ne (tintics), don haka ba ta gane ko waye a ciki ba. Don haka ta ja gefe ta tsaya, Zaituna ta wuce hanyar hostel. Hannuwanta a kirji tana harare-harare da jiran ko ta kwana don ta yi zaton irin lalatattun ‘ya’yan masu kudin nan ne da suka cika Informatics suna diban ‘yammata su fita dasu. Ta yi tsaki ta juya za ta tafi, sai ya sauke gilasan motar gaba daya ya ce, “Rayhanah!: Da sauri ta juyo, Yaya Khalipha ne. Ya fito daga cikin motar ya yi tattaki har inda take. ‘Yar ciki da wando na farin yadin filtex ne a jikinshi, da alama babbar rigar na cikin motar da hula ruwan kasa a kanshi. A yau ne ta taba yiwa Yaya Khalipha kallo na sosi, na cikin ido da ido. Ta gano ba karamin kyakkyawa bane, sannan kamanninshi da Mami a sarari suke bai da digon Baba Dacta ko kadan, fari ne shi sol kamar Mami, bai da digon bakar fatar Baba Dacta. Sannan fatarshi ta nuna alamun ba cikakken dan Nigerian bane ya fi kama da mutanen Middle East. Idan ta hada da kanta ta yi judging za ta fidda tambayoyi da dama, me Khalipha ya gani a tare da ita da har ya zabe ta ta zame masa uwargida kuma uwar ‘ya’yanshi? Ita dai ta san ita ba kyau ne da ita ba, ba ‘yar kowa ba ce, bata da abin da za ta ja hankalinsa dashi. Babu wanda zai ba ta amsar wannan tambayar sai shi Khaliphan kansa. To sai take tambayar kanta ita din ai ta san da hakan amma take sonshi, kuma kyawun sura ba shine dalili ba. Tana son Khalipha ne saboda halayensa kawai da yadda yake mutunta ta yake martabata tun tana nakasasshiya. Kaskantaccen asalinta ba abin juyawa a kalla bane a wajen Khalipha. For him, (Inna akramakum indallahi atqakum). Da idanun dake cike da wadannan maganganu Rayhanah ta daga ido tana duban Khalipha. “Idan ni munafuka ce don ina son Yaya Khalipha kamar yadda Abida ta ce, na yarda a rada min sarautar munafukai”. Rahane ta ce a zuciyarta. Bata san ina zata saka kanta da fushin da khalifa keyi da ita ba, bata san da wace kalma zata roke shi ya daina fushin da yakeyi da ita ba, da ace zata iya data gaya masa cewa zuciyarta mai rauni ce a kansa ba za ta iya jurewa ba. Sai hawaye suka balle a idonta, ta yi saurin juya masa baya tana sharewa da gefen hijabinta. Hannunta Khalipha ya kama ya janyota har seat din mai zaman banza na motarsa, kansa ya daura a kan sitiyari ya lumshe idonsa, ya jima kafin ya bude (but she is still wiping tears). Khalipha bai tausaya mata ba duk da ya karanci dalilin tashin hankalinta, ya kuma san duk wani motion na zuciyarta a kansa. Sai cewa ya yi, “Sorry for the uninvited visit, na kasa jurewa ne Rayhanah! Ban zo don in saki kuka ba, ki yi hakuri. Insha Allah ba zan kuma zuwa ba da izininki ba. Now go to your hostel tunda na saki kuka......” Da karfi take kokarin kafar da hawayen, sannan cikin karkarwar murya ta ce, “Ni Yaya Khalipha kana misjudging dina, kana yanke min hukunci da abin da ba shine a raina ba”. Da sauri ya ce, “To mene ne a ran naki?” Ta sunkuyar da kai, hawayen na son kara gocewa ta ce, “Daban ne da abin da kake tsammani.....” Sai a nan ne ya tausaya mata, ya yi murmushi ya ce, “Is it opposite?” Ta daga mishi kai a hankali ba tare da ta bari fuskarta ta kalle shi ba. Sai Khalipha yasa gefen babbar rigarsa yana share mata hawaye yana cewa, “Kin karbe ni a matsayin uban ‘ya’yanki Rayhanah ba tare da hakan ya zamo karamci, sakayya ko tursasawa kai ba?” Wannan karon ma girgiza kai ta yi sama wato eh, wata zuciyar na gaya mata cewa, “Ki bude baki ki gaya masa kema ba yau kika fara son nasa ba”. Amma kawaici da mutunta kai a matsayin ta na diya mace ya danne komai. Sai ya rankwafo ya leka fuskarta, tana ta fyace hanci. Duk kokarinsa na son ta kalle shi cikin ido ba ta yi hakan ba, ta runtse idonta da karfi. Sai ya zakuda kadan ya ce, “Rahane, haba Rahanena, dube ni mana”. Ba ta san sanda ta yi dariya ba ga hawaye a idonta, ta ce, “Idan na ce maka Audu ai na rama”. Khalipha ya kama baki, “A ina kika san real name dina Rahane?” Ta juya masa keya ta ce, “A idon matambayi”. Khalipha ya rikice gaba daya, ya kasa controling effect din (tasirin) wannan acting na Rayhanah. Hular ma cireta ya yi a hankali ya dora mata a kan cinyarta. “Dama kina da baki Rayhanah?” Turo mai siraran lebbanta ta yi gaba tareda juya masa keya ta ce, “Shafa ka ji”. Ya ce, “A shafa labari-shuni???” Dariya ta yi wadda ta fiddo fararen lafiyayyun hakoranta masu sheki, ta ce, “Ko a Jakar-Magori idan ka shafa za ka ji”. “Shake my hands RAYHAH......” Ya fada a wahalce tare da mika mata hannun damansa wanda ke daure da ruwan kasar agogon ‘Swatch’. Ba ta mika mishin ba, sai ta bude kofar motar tana fadin “An kira sallah Yaya K....... can I go?” Ya shafo sumar kansa ahankali daga goshinsa har zuwa keyarsa idanunshi a lumshe, sun kada sun zama brown dinsu ya ce a wahalce, “Go to Masjid Rayhah........! tun kafin ki kashe ni da raina!!”. **** [12/24/2019, 21:47] Takori: Wannan shine dan mabudin da ya bude kofar soyayyar Rayhah da Khalipha. Alkunyarta, rashin son magana, saukin kai da kawaici, rikon addininta sune manyan halayen ta da suka jawo Khalipha gaba daya ya afka a rijiyar soyayya ruwan ya sha shi har wuyansa. Duk yadda ya yi tsammanin Rayhanah ta wuce nan a qualities din da yake hasashen tana dasu, wadanda yake so a matar aurensa. Washe garin ranar Daddy ya zo ya dauketa suka wuce Kano, ta kwana biyu ya maidota Talata saboda Monday aiki bai barshi ya samu sukuni ba, ba kuma zai sata a motar haya ba. Yadda Rayha ta ga Mami cikin kwanaki biyun nan da ta yi abin ya tsoratata. Completely Mami ta canza kamar wahainiya, muraran take nuna ba ta son zaman Rayhanah a gidanta yanzu, duk da Baba Dacta bai fito fili ya gaya mata Khalipha son ta yake ba. Amma ya ce da ita aure zai mata ba za ta shiga B.U.K ba. Ta tambaye shi waye mijin? Ya ce da ita, “Time will tell you!” sai tasa mishi ido tana cewa a ranta, “Kai ma lokacin zai gaya maka ko wace ce Anita Shiyana, tunda Asma’u ka sani. Lallai gaskiyar Dr. Halima ta yi sakaci da yawa da Dr. Mansur, tana ganin cewa wai yana sonta, ba za ta taba bin malamai a kansa ba. Yanzu kam ta yarda cewa ta yi sakacin, tunda ya fara munafuntarta ya soma boye mata wasu al’amura da ya lura ba za ta yi na’am dasu ba. Shi kuma har ga Allah zuciyarsa daya, bai ki gaya mata don munafurci ba sai don baya son bacin ranta ko nasa cikin al’amarin, ya fi son sai komi ya kankama tukunna sannan ya zauna ya yi mata bayani ya ba ta hakurin karya alkawarin da ya yi mata, a dalilin ajizanci irin na dan Adam. Bai yi da niyya ba, bai hadasu ba su suka hada kansu. Shi dan bin umarnin Allah ne kawai da sunnar ma’aiki da ya ce idan ‘ya’yanku sun nuna suna son aure, to ku yi musu cikin umarnin Ubangiji. Ban da haka shi bai taba hasaso Khalipha zai taba cewa yana son Rayhanah ba, yana dai da nashi burin a kan Rayhanan amma tunda Khalipha ya riga ya furta to ya kashe waccan kudirin nasa ya karbi wanda Allah ya bayyana. Duk sati Khalipha na tafe, baya Abuja baya Kano, baya Kazaure. Wata muguwar shakuwa da fahimtar juna ta wanzu tsakaninsa da Rayhanah. Duk da cewa kullum shine mai nuna son, kalamanta tsada suke masa saboda kunyarta, in yana so ya ji furucin bakinta, to sai ya kirata da Rahane, ko ya ce matar Audu, a nan kam ba ta jurewa sai ta bayyana masa kyawawan hakoranta guda talatin da biyu. Ba soyayya ce kadai tsakanin Khalipha da Rahane ba, akwai wani abu wai shi yarda da juna, kusancin zuciya da zuciya da amincin da ya zarta soyayya. Ko Baba Dacta bai san Rahane yadda Khalipha ya yi mata kyakkyawan sani ba ciki da bai dinta. Ya san halinta, ya san abin da take so da wanda ba ta so. Ba ta da yawan ado, kuma ba ta cika kwalliya a jikinta, she is smart, and simple. Yana son Rayhanah har yadda ba zai iya kwatantawa ba. Yana son Rayhanah yadda shi kansa bai san adadin ba. Yadda kwanaki ke gudu suna juyawa tamkar gare-gare abin wasan yara a wannan zamanin, don haka bai zamo abin mamaki ba idan aka ce har ga watanni takwas sun cika. Rahane ta fito da kwalin (International Diploma in Cyber Security) tare da admission na daukar ta degree a babban reshensu dake kasar Singapore, a matsayinta na (overall student). Fadin irin farin cikin da Baba Dacta ya yi ba zai fadu ba, a take ya yiwa Khalipha waya yake sanar masa ita ma Mami ya sanar da ita tun kafin su iso Kano daga Kazaure. Mami ta dade zaune a bakin gadonta tana mamaki, don dai akwai ‘ya’yan kawayenta da dama a Informatics fin shekaru uku sun kasa fita daga makarantar. A karshe sai bari suka yi aka yi asarar dubunnai. Da gaske Dr. Halima take idan har ba ta raba yarinyar nan da gidanta ba, ba ta gama shan mamaki ba. A take ta bugawa Dr. Halima take sanar mata. Ta ce da ita kada ta damu komai ya zo karshe, amma ta shirya gobe su wuce Plateau (Jos) tushen Mami kenan, komai ya kammala karbowa kawai za suyi. Don haka da suka iso ba ta yi wani action negatively a kan nasarar Rayhanan ba. Sai dai shi a can Khalipha ya shiga damuwa, yana tsoron kada Daddy ya yarda da batun tafiya yin digirin ba tare da anyi aurensu ba. Don haka ranar Juma’a ya baro dukkan ayyyukansa ya taho Kano, abin haushin Daddy baya gari ya je Ireland wani taron karawa juna sani a kan cutar Otosclerosis a matsayinsa na ganau ba jiyau ba a kan fidarta, da aka yi aka kuma ci nasara a yankin Braemar. Khalipha ya yi sallama a bedroom din Mami ba ta ji ba tana waya, kuma da yake ta bai wa kofa baya ba ta ga shigowar shi ba. Hirar da take yi a wayar bai fahimceta ba, amma kawai jikinshi ya ji ya yi sanyi da ya ji Mami na cewa, “Ko zan yi yawo tsirara haihuwar uwa da uba na Khalipha ba zai auri yarinyar nan ba”. Ta ajiye wayar tana huci, a lokacin ne ta ankara da shigowarsa. Ta kasa saisaita fushinta ta kasa boye anger din da ta taso mata. Don haka kallon sa kawai ta yi ba ta ce masa komai ba. A salube ya zauna a kusa da ita gwiwoyinsa babu kwari, duk da bai san wace yarinyar ake nufi ba tunda Allah bai nufe shi da jin an kama suna ba. Khalipha ya san iya rayuwar Mami ba ta da makiyi, ba ta da mugun hali. To a kan wa take cin mugun alwashi haka? Ta dago idanunta jajir ta dube shi. Cikin kakkausar murya ta ce, “ABDALLAH!” A firgice ya dubeta saboda shi dai tsawon rayuwarsa bai taba ji ko da kuskure ta ambaci sunansa na ainihi ba, sai ko ranar da ta je gidansa a Abuja ta kama shi da babban laifi. Fargaba bata barshi ya amsa ba. Ta ci gaba da cewa, “Duk abin da kuke ciki kai da ubanka na sani, tunda ban yi kama da wadda ba ta je makarantar boko ba. Amma ina so in ji sahihiyar amsa daga bakin ka, tunda Allah ya hana hukunci a kan zargi”. Ya girgiza mata kai alamar yana sauraronta. Kafin ta jefo masa tambayar tata da ta shafe taraddadinsa. “Wace ce yarinyar da kake so ka aura?” Ba tare da nuku-nuku ba kai tsaye ya ce, “Rayhanah!’ Ta sake cewa, “Wane ne mijin da Dacta yake so ya aura mata?” Ya nuna kirjinshi ba tare da ya yi magana ba wato “Shine”. Mami ta girgiza kai, “Kai tsaye abin da zan iya cewa shine, ban amince ba! Watakila bai gaya maka alkawarin da muka yi da shi ba kamin in yarda da zaman yarinyar nan tare da mu. Kai kuma da fari ka munafunce ni, tunda har Abuja na taka na je saboda kai da damuwa da halin da kake ciki, amma ka ninke ni a bai-bai, saboda ka raina min hankali. Me ka gani a jikin wannan yarinyar Khalipha ban da son zubar mana da kima da mutunci? Kaskantaccen asali, ragowar cuta, babu iyaye babu dangi, an ce ‘yar Takai ce uwarta da ubanta da kakarta sun rasu, to su daga sama suka fado kenan tunda basu da dangi?” Ta fidda manyan idanunta. Khalipha tun daga kansa har yatsar kafarsa gumi yake, duk da sanyin split dake neman daskarar da mutanen dakin. Tunda ta fara magana bai ce mata komai ba, haka da ta dire tana sauraron jin ta bakinsa amma ya gaza ce mata komai. Ta nuna shi da dan-alinta cikin matsanancin fushi ta ci gaba da magana, “Idan kana son zaman lafiya dani, to ka bar maganar nan, ka kai wa ubanka maganar Radhiyyah, idan fa har ni na haifeka na yi nakudarka bayan daukar ka cikin mahaifata har tsayin watanni tara cikin halin kaka-nikayi. Ba ta yi isar da zan hada jini da ita ba. Wannan kawai ita ce magana. Idan ma ka je ka ce masa ka fasa kai masa zancen Radhiyya, idan ka ki kuma kada ka ga laifina a kan duk abin da ya biyo baya. Kwanaki biyu kacal na baka ka je ka warware kullin naku kai da uban naka, in ba haka ba wallahi za ku sha mamaki, na shirya karbar kowanne bacin rai na Dacta, na shirya masa kana iya tafiya, wannan shine”. **** Saboda gigicewa Khalipha bai tsaya kara ko mintuna biyar cikin gidan ba, ya juya kan motarshi ya dauki hanyar Abuja. Karfin zuciya irin ta namiji da karfin imani da tasirin addu’a su suka kawo Khalipha Abuja lafiya, amma ba nutsuwar tuki ba. Maganar a ce ya hakura da Rayha ma ba mai dadin ji ba ce a kunnensa, gara a soka mai allurai dari ba daya da wannan furucin na Mami, wai ya ce da Baba Dacta ya fasa auren Rayhanah. Ta ya ya? Ta ina? Ta wace hanya? Da wane bakin da wace fuskar zai je ya fadi hakan?” Sai dai fa wani bangare na zuciyarsa na gaya masa, wannan fa umarni ne na MAHAIFIYA, wanda bai isa ya musunta shi ba. Don haka Khalipha ya shiga wani irin tashin hankali da bai taba shiga irinsa ba. Har kullum Mami da Daddy abin da suke so suke musu, don haka ba duka kalubalen rayuwa suka sani ba. Basu san su so abu ko yaya su rasa ba balle soyayyar zuciyarsa ga Rayhanah! Wadda yakeda yaqinin an halicci zuciyarsa ne tare da sonta, kowanne bugunta kuma ke tafiya tareda kaunarta. Don haka haqiqatan baima san takamaman inda son Rayhana yake ba specifically azuciyarsa, balle yasa wuka ya yanko mata shi, tunda ya mamaye zuciyar duka, sai dai Mami ta tsigeta gabadaya (zuciyar) daga shi har ita kowa ya huta. Bayan kaduwa da tsorata, yana cikin mamakin ashe halin mutum yana canzawa haka farat daya daga mai kirki da sanin ciwon kai zuwa mara kirki da tunani? Iyaka hangensa bai ga hujjar Mami kwakkwara guda ta haramta masa abin da yake so shekaru har takwas da doriya ba, bayan kuma ya riga ya sanar da mahaifinsa ya yi na’am, me Mami take so Daddy ya dauke shi? Idan ya je ya ce ya fasa auren Rayhanah? Fiye da wannan ma, ya ya rayuwar za ta kasance idan babu Rahane a ciki? Mene ne hujjar Mami na cewa lallai sai ya auri ‘yar kawarta? Ita ba kwadayi ba, su ba kwadayi ba, me Mami take nufi ne? Ka taba auren wadda baka taba jin kana so ba? To ta yaya za ku rayu? Shi fa ba wai so kawai yake yiwa Rayhanah ba, har da son ya tallafi rayuwarta ya ingantata, idan bai aure ta ba wani ne can da bai san darajarta ba bai san mutuncinta ba zai aure ta. A yadda mazan yanzu suka mayar da aure kamar sanya riga da tube ta ga ‘ya’yan gata ma ba marayu marasa madafa irin Rayhanah ba, wane ne zai aure ta ya daraja ta? Ya rike musu ita irin yadda sukeso shida Daddy??? Bai yi aune ba sai ji ya yi wani ruwa mai dumi yana fita daga idonsa. Da ya kai hannu ya sharesu, wasu ne suka kara shimfidowa aguje. Wannan karon bai yi wata hobbasa ta hanasu zubowar ba, kyalesu ya yi suka yi ta shatata, fitarsu na rage masa suyar da kirjinsa ke yi. A gida ko ofis, cikin kwanaki biyun nan Khalipha ya gama fita daga hayyacinsa. Ya rufe waya, ya kasa aiki a ofis, ga shi ya yiwa Mami alkawarin barin shan Marlboro balle ya sha ta wanke mai zuciya. Maimakon hakan ya yanke shawarar fara shan zam-zam ya zamo masa ruwan sha. A hankali sai ya ji tunanin da yai yawa da katutu cikin kwakwalwarsa da zuciyarsa na raguwa, nutsuwa ta zo mishi, addu’a kawai yake da nafilfili Allah ya sauko da zuciyar Mami, don dai ya kasa aiwatar da umarninta har yau. An debi kwanaki har hudu, Khalipha bai cika umarnin Mami ba, ya kashe waya tun dawowarsa. Itama Rahanen baya kiranta, don baya son ya zamo heart breaker a gareta. Ko da yake dai-dai da second daya bai taba tunanin wai zai iya hakurin da ita ba. Mami ta neme shi a waya har ta gaji, domin tana son aiwatar da kudirinta a kan Rayha da Khalipha kamin Daddy ya dawo ne kada ya bata mata lamari. A yau saura kwanaki biyu Dr. Mansur ya dawo Najeriya. Cikin daren Khalipha ya kasa barci ya kuma kasa kunna waya. Ya lura Mami so take ta zurma shi cikin laifin shi kadai wajen Daddy ba tare da sunanta ya fito ba. “Ya Allah me ya samu mahaifiyata ne haka? Ya Allah me na yiwa Mami da a yau ta gwammace in sarayar da farin cikin rayuwata a banza? Saboda Rayha ta fito daga tsattson talakawa, ta yi cuta shine kawai hujjar a ki aurenta? Mami ta manta ita ma tana da ‘ya’ya mata? Abin da ya faru da Rayha zai iya faruwa ga ‘ya’yanta, sai a ce kada a aure su? Ita ‘yar masu kudin me za ta yi mata? Kudi za ta ba ta ko Makka za ta kaita? A iya sanin Khalipha Mami ta fi uwarta albashi mai tsoka, ubanta ne dan siyasa (arzikinku na dan wani lokaci) balle ya ce wani abu Mami ke hange a kan lamarin. Yadda take daukar al’amarin Dr. Halima da muhimmanci ba ta daukar na mijinta haka yanzu. Ta zama wata irin masifaffiya, ya tabbata muddin ya gayawa Daddy cewa ita ta ce ya yi kaza ya yi kaza Daddy zai sa mata katanga ma ba birki ba. Ya kuma lura ita ma ta shirya daukar kowanne hukunci daga Daddyn idan ya tuno da kalamanta. Wanda ba zai so haka ba, a kan nasa auren ya raba na iyayensa. Kuma ta ce duk abin da ya biyo baya idan ya ki bin umarninta kada a ga laifinta. Wato za ta iya korar Rayhanah daga gidanta, ta fada wani hannu da basu sani ba tunda su ba mazauna bane daga shi har Daddy. Wannan tunani da Khalipha ya yi ya razana shi ba dan kadan ba. Bai san sanda ya mika hannu ya dauko wayarsa daga kan center table ya kunnata ba. Bai tsaya karanta sakonnin dake ta tuttudowa cikin wayar ba, ya yiwa Mami text ya tura mata ya sake rufe wayar da sauri a lokacin da kiran Rayhanah ya shigo. Kuwa riris Khalipha yake yi wanda bai taba yin irinsa a rayuwarsa ba. **** A lokacin da sakon Khalipha ya shiga wayar Dr. Asma’u tana ofis dinta tare da Dr. Halima suna ci gaba da kulle-kullensu na tsiya, a kan mutanen da basu ji ba basu gani ba, son zuciya kawai da raina talaka. “Ya rufe wayar har yau na kasa samun shi, fargabata gobe Dr. zai dawo, so nake mu gama kafin ya dawo kada ya bata al’amarin don na rantse zai iya yin komai don ya nuna min bacin ransa, mafi kankantar ciki shine SAKI, ni kuma na shirya masa”. Dr. Halima ta ce, “Wallahi kuwa, ko yau kasuwar ta watse dan koli ya ci riba. Wa zai dube ki ya ce kin haifi Jawahir ma balle Ibrahim da Khalipha? Wallahi za ki yi mamakin yadda consultants za su yo rubdugu a kanki. Dr. Mansur ya raina ki, ki yarda da abin da na ce, ya raina ki”. Fuskar Dr. Asma’u ta muzanta kwarai, ba abin da ta tsana a rayuwarta irin raini. Babbar hujjarta ta kin Rahane kenan, ta fito daga tsatson raini, abin kunya cikin kawayenta da tsararrakin yin ta. Shigowar sakon cikin wayarta yasa ta sassauta bacin fuskarta, ta dauki wayar ta bude. “Uwata da na sani a baya farin cikina shine nata, babban tashin hankalinta shine shigata cikin damuwa, ko wani hali na kaka- nikayi. Mami would never lose her temper to such an extent....... shi yasa har yau na kasa yanke hukuncin yarda da abinda idanuwa da kunnuwa na suka jiye mini daga Mami. Ina cikin tantamar, anya Mamina ce??? A cikin kwanakin da ban yanke hukunci ba, so nake idan mafarki nake Allah ya farkar dani. Mamina ta asali za ta iya kadar da duk abin da ta mallaka saboda farin cikinmu. Sai nake tambayar manazarta halayyar dan Adam cewa, shin dama halin mutum yana canzawa a lokaci daya? Tunda dai na yarda cewa ba mafarkin nake yi ba, cikin biyayyarki da umarninki na hakura da Rayhanah..... Allah ya ba ta wanda ya fini......ki ce Amin Mami ba don ni ba sai don kasancewarta Musulma ‘yar musulmai ‘yan’uwanmu. Ni kuma ki aura min duk wadda ta yi miki Mami........ na yi miki alkawarin zama da ita har karshen rayuwata! Amma kada ki yi yunkurin raba gidan nan da Rahane Mami, ko don ki ceto mana aurenki da kwanciyar hankalin Daddy. Idan akwai biyayyar da ta fi wannan Mami ina rokon Allah ya bani ikon yi miki. A yau zan gayawa Daddy na hakura da RAYHANAH......na karbi zabin ki Mami. Ina neman albarkarki. Dan ki. -Khalipha. Ta dade tana maimaita karanta sakon dake neman karya mata zuciya, Dr. Halima na ta magana amma ba ta jinta. Sai ta kwace wayar ta soma karantawa. Farin cikinta ya kasa boyuwa a fuskarta. Ta ce, “Ki ji yaro da lauya magana, wallahi sai ta tafi in ba haka ba ba’a rabu da Bukar ba an haifi Habu muddin tana cikin gidan yana ganinta. Ta ruwan sanyi za ta tafi babu duka babu zagi balle bakar magana”. A nan ne Mamin ta yi magana, “Ina ganin mu kyale yarinyar nan Halima tunda dai an samu ya yi kokarin da ba’a zata haka cikin sauri ba. Baki san Khalipha ba a kan abin da yake so, kamar kuma yadda ya ce din ne AURENA zai yi tangal-tangal idan ya dawo ba ta gidan, babu kuma wata kwakkwarar magana kan inda ta shiga”. Dr. Halima a fusace ta ce, “To shi kenan, na rantse kuwa za ta zama kishiyarki idan Khalipha bai aura ba. Kuma ai ba korarta za ayi ba, kiranye za ayi mata ta koma mahaifarta ko za a kasheta ba za ta yarda ta dawo ba. Ai muma Musulmai ne, ba cutarta zamu yi ba”. Ta yadda da maganar Dr. Halima dari bisa dari har cikin ranta. ** ** “Daddy yaushe za ka dawo?” Khalipha ya tambayi Baba Dacta a raunane, bayan sun gaisa ta waya. Maimakon ya ba shi amsar tambayarshi sai ya ce, “Ya ya na ji maganarka so cool, wani abu ya faru ne?’ Ya girgiza kai cikin karin hawaye ya ce, “Eh to, magana nake so muyi ta fahimta.....” Sai kuma ya yi shiru. “Ba za a iya barin maganar har sai na dawo ayi ta face-to-face ba? Tunda na lura mai nauyi ce?” “To shi kenan Daddy, yaushe za a dawo?’ “Yanzu haka na taho on transit nake a Germany. Zuwa asubahin gobe ina Kano insha Allahu”. ** ** Dawowar Daddy gida lafiya, da kuma ganin yanayin fuskarsa bai canza ba ko kankani, yasa Dr. Asma’u cikin kokonton anya Khalipha ya yi abin da ya ce zai yi bisa umarninta? Irin kayan da ake shigowa dasu ana jibgewa a (store) ya kara tabbatar mata da lallai Khalipha ya rainata. Kayan furnitures ne ‘yan ubansu-ubansu da manyan jakunkunan zamani shake da duk wani nau’in suttura ta kwalliyar mata da suka fi kama da kayan lefe. Dr. cikin walwala yake matuka, a lokacin da yake nuna mata kayan, yana yi mata bayanin lefen Khalipha ne. Ya kaikaice ya zaro warawarai guda shida na farin zinare daga aljihunsa, ya ce ga shi ta adana, shine sadaki. A wannan lokacin ya kwantar da harshe ya ce, “Asma’u na san bani da kalaman wanke kaina daga daudar mai laifi a gareki, amma ina baki hakuri, bani kuma da hannu a ciki. Kamar yadda na ce ba zan hada ba ban hada ba, su suka hada kansu, ni kuma na ture komi, na zabi in cika umrnin Ubangiji in ya so in yi kaffara a kan alkawarin da na yi miki. Tsakanin ‘ya’yanki da ‘yar amanar da Allah ya bamu. Zan iya cewa ban karya alkawari ba, tunda kuwa ban hada soyayya tsakanin Khalipha da Rayhanatu ba. Ki sa fahimta a cikin lamarin nan, ki sa albarka, ki dauki duniya da sauki. Khalipha ke son auren Rayhanah, ni kuma na ba shi da na tabbatar da amincewarta. Ga wannan.....” Ya tura mata bandir din bugaggen (invitation card) na daurin aure da yasa aka buga masa a Dublin.. Ya kare da cewa, “Jibi Lahadi insha Allahu za a daura auren a gida Takai, Hakimi shine waliyyinta. Don haka ga wannan”. (Ya tura mata ATM Card dinsa na bakin (Gruaranteed Trust). Ya ce, “Ki dauki abin da zai isheki, daga naira dari har zuwa miliyan biyu na lamince miki ki fara shirye-shiryenki. Na taho da komai na kawata gida, kayan kithcen ne sai ku mata. Da sauran abubuwan da babu sai ki karasa. Duk wasu activities da kike ganin za a yi ayi, amma ban da wanda za a hada mata da maza. Kin yi hakurin Mamina kin fahimceni?” Sakatoto! Ta yi tana mishi kallon takaici, kamar ta amayo zuciyarta ta huta. Ta so yin kissa ta karya, amma ba halinta bane, don ba ta iya ba. Wadanda take yi a baya ma duk Dr. Halima ke koya mata, ga shi kuma ba ta zaci haka ba, ba ta koyo yadda za ta karbi zancen ba. Sai kawai ta aje warawaran da ya dora mata a cinya da katinan daurin auren a nan gabanshi ta mike ta yi dakinta ba tare da ta ce da shi komi ba. Ta zauna a gefen gadonta jikinta yana bari ta kira Khalipha. Bugu biyu ya amsa cikin nutsuwa, domin yana bisa sallaya ne yana mikawa Ubangiji bukatunsa, bayan sallame nafila raka’a hudu, wadda a kowacce raka’a ya karanto suratul Ikhlas kafa bakwai. Sallah ce ta neman zabin Allah ita ma, amma ba Istikhara ba. Tuni Khalipha ya dade da samun nutsuwar zuciyarsa albarkacin ruwan zam-zam mai sanyi da ya mayar ruwan shan sa. Ko ya ya rayuwar ta zo, ya shirya karbarta, in dai zai wanye lafiya da mahaifiyarsa, kuma mahaifinshi kada ya ga laifinta. Ya manta shima uba yana da nashi hakkin amma Khalipha ji yake ya gwammace bacin ran Daddy a kan na Mami. Daddy mai saukin hali ne ba ya daukar al’amuran rayuwa da zafi. Duk da haka ya san idan sunan Mami bai fito ba, duka laifin kanshi zai kare, domin Daddy baya son karanta kuma baya shiri da mai magana biyu, balle a kan ‘yar da ta fi nashi ‘ya’yan a zuciyarsa. Zai karbi duka laifin in dai hakan shine farin cikin Mami, wadda yake wa wani irin so na UWA wanda ya zarta wanda yake yiwa ubansa Dr. Mansur. Tana huci kamar mesa ta ce, “Abdallah!” Ya amsa “Na’am Mami”. “Ni ka yaudara ka wulakanta ko?” Ta fada tana nishi kamar wadda ta yi tsaren ceton rai. Ya ce, “Subhanallah! Kada Allah ya nuna min ranar da zan yi miki dayan biyun hakan, ya dauki raina kafin in yi hakan....” “Rufe min baki”. Ta fada cikin tsawar da bai taba ji ta yi ba. “Ka ce za ka kira Dacta ka fada mishi cewa ka fasa auren matsiyaciyar yarinyar nan Radhiyya kake so, shine baka kirashin ba kuke shirye-shiryen biki ta waya har I.v an bugo jibi daurin aure. Wane irin tozarci kake so ka yi mini? Na ce ban yarda ba, ba ta isa ba, ba ta isa ba wallahi in yi suruka da ita. Zan la’ance ka Khalipha…….. muddin ka yarda aka daura ma aure da yarinyar nan jibi.....” Ta kashe wayarta, ba ta saurari uzurinshi ba, ta barshi a wani hali da ya kasa tantance wane iri ne. Wayyo! Allah sarki Daddy...... ashe shi yana can yana yi min gata ban sani ba...... ashe shi yana can yana so ya yi surprizing dina a kan alherin da ban taba son wani abu kamarsa ba. Amma sakamakon sa shine in karya masa zuciya in zubar da mutuncina a idanunsa. Kullum cikin hirarsa sai ya ce, “Karamin mutum shine mai saka hairan da wulakanci, yau zan zama mayaudari, a RAYUWAR RAYHANAH! Zan ceci auren uwata, ni in tsira da hakan, Allah ya baki hakuri Rayhana, ya baki wanda ya fini......” Ya kifa kai jikin gadonsa yana kuka da sauti. **** [12/24/2019, 21:47] Takori: Daddy na kan hanyar Takai bayan motarsa shake da goro da alawa lokacin da wayar Khalipha ta shigo masa. Don haka bai daga ba domin baya amsa call yana tuki, shi kuma Khaliphan bai fasa kira ba. Kira a kai a kai wanda ya tabbatarwa Dr. Mansur cewa wannan kira ba na lafiya bane, domin Khalipha baya takurawa mutum da kira, kusan kullum ma shi wayarsa a (voicemail) take. Sai ya ratse kan hanya ya parker motar ya amsa kiran Khalipha. A nutse suka gaisa shi da Daddyn, sai dai yadda Daddy ya ji muryar Khalipha babu amo (a dushe) kuma sanyinta ya yi yawa ya tabbatar Khalipha ba shi da lafiyar zuciya da kuzari cikin gangar jikinsa. He is always very energetic a murya da zuciya, kuma a muryarsa yake karantar halin da zuciyarsa ke ciki. Bayan sun gaisa ya ce, “Ina kan hanyar Takai ne zan kai wa Hakimi goro da alawar daurin auren ka, gobe insha Allahu za a daura karfe goma sha daya na rana. So ka bar kome kake yi ka taho Takai a yau, abin ne ya zo a kurace, don haka a kuracen za ayi, duk wata gayyata na gamata a jiya sai ko ‘yan office din ku su ma ka yi text kawai ka turawa kowa. Na jika ba a yadda na saba jinka ba, wani abu?” Hawaye suka ziraro daga idanun Khalipha, sharrrrr..........suke zuba kamar an sunce famfo. Ya ce cikin rishin kuka, “Daddy na gode da kaunarka da kulawarka gareni, da kyakkyawar zuciyarka mai son faranta min a kullum. Abin da zan fada yanzu don Allah Daddy kada ka yi masa wata fassara daban, ko ka yi tunanin na yi ne don in mai da kai abokin wasana, ko kuma na yi don in tozarta in wulakanta ka, ko don ban gode maka ba, ko don in karya maka zuciya. Na yi hakan ne domin neman masalaha tsakanina da Ubangijina. Na fasa auren RAYHANAH a daura da Radhiyyah ‘yar Dr. Halima. Ita kuma Rayhanah Allah ya huci zuciyarta ya ba ta wanda ya fini”. Kawai sai yasa masa kuka. Dr. Mansur ya dade bai yi magana ba, zuciyarsa ke wani irin tukuki na fushi da Mami mai tsanani, fushi irin wanda bai taba yi ba a rayuwarshi ta duniya. Tabbas Asma’u ce ta yiwa Khalipha barazana da matsayinta na (uwa) domin dankafar da Rayhanah da martaba nata Dan. “To ai shi kenan”. Bai san sanda ya gayawa Khalipha hakan ba. “Ta nuna power dinta a kanka, nima zan nuna tawa da wanda na haifa nake da iko da shi. Dadin haihuwa kenan. Yau da ban haihu ba da Asma’u ta nuna min iyakata ta nunawa duniya BA NI NA HAIFE KA BA! Babu komai, daina kuka Khalipha, zan mata yadda take so, nima zan yi yadda nake so. All the best Khalipha, yi biyayya ga mahaifiyarka domin samun tsira a gidan duniya da lahira baki daya. Kada ka damu da bacin raina, wallahi ko kadan baka bata min ba, ban kalleka da matsayoyin da ka lissafa a baya ba, face na yi maka kallon DA MAI NEMAN ALJANNAH a diga-digan mahaifiyarsa.........” Ihu Khalipha ya saka masa. “Daddy ba kai ka haifeni ba? To wane ne? Shege ne ni?” Kara yake saki da ihu mai gigitarwa saida shi kansa Dr. Mansur ya razana. Da tsoron kada Khalipha yayiwa kansa wani lahani. Bai san sanda ya soma kuka ba shima ya soma kira cikin lallashi da nadamar bacin ran da ya kai shi ga furta abinda yayiwa kansa alqawarin har abada bazai furta ba, “Cool down Khalipha!!! Ba shege kake ba, da ubanka, ita ta haifi abinta da mijinta na fari, tun auren saurayi da budurwa, bayan haihuwarka suka rabu, kana da shekara biyu ya rasu. Ni da ita mun hadu ne a jami’ar Trinity din Ireland (Dublin) ta zo karatu nima na zo, tana zaune da Uncle din ta da matarshi tare da kai, Nanny na kula da kai ita kuma tana karatu. Da muka yi aure ne na karbeka muka karasa karatu muka dawo, da shekaru hudu da auren mu ta haifa min Ibraheem. To ka ji, kwantar da hankalinka har gobe kai Dana ne Khalipha, ba wanda ya isa, ba abin da ya isa ya kankare wannan sunan Abdullahi Mansur Takai, sai wanda ya halicce ni ya halicceka. Mahaifinka Balaraben Hurghada ne (Egyptian) ya zo Jos kasuwanci ne ya zauna a cikinta tsayin lokaci har ake kiransa (Ba Hurgade Mukhlis), ya kuma bar maka tarin arziki mai yawa wanda iyayensa suka zo suka kwashe, suka kuma ki karbarka, a cewarsu basu san da zancen auren ba tunda bai gaya musu ba, duk da fata ta nuna amma kamanninka da ita ne sak. Tun daga lokacin na mai da kai Da na Khalipha, kuma har gobe matsayinka kenan. Share hawayen nan Khalipha bana son su and I’ll stand by you..... ina a bayan ka yiwa mahaifiyarka biyayya domin ta sha wahala da kai yadda baka zato a Dublin. Ga karatun medicine ga rashin lafiyar ka ta ciwon hanta har Allah ya baka lafiya. Tunda ba ta so to ba ta so din ne, ko anyi abin ba zai yi albarka ba, ba kuma za ta bari a zauna lafiya ba. Kyale Asma’u da kafiya a kan abin da bata so, in fa ba ta son abu ba za ta taba son sa ba. Tana da hakki mai girma a kanka wanda ni bani da shi. Zan kuma nuna mata nima na haifa, kowa ya yi iko da nasa”. Ya ci gaba da lallashin Khalipha wanda ke kuka mai keta zuciyar duk mai imani, har suka aje wayar Khalipha bai daina kuka ba. Shima Dr. Mansur hawayen yake ta sharewa da hankicinsa. Ya tada motar ya hau kan titi ya karasa Takai. A kofar gidan Hakimi ake ta sauke huhun goro da alawa da Dr. Mansur ya zo dasu shake a boot din motarsa. Wajen matan gidan ya fara shiga aka gaggaisa da su Haj. Karima, sannan suka kule a falon Hakimi shi da dan’uwansa suna tattauna mai yiwuwa. A take aka soma gayyatar daurin auren da za ayi a gobe Lahadi. Bayan Khalipha ya yi kukansa har ya gaji, idanunshi sun soma yi mai zafi da wannan sabon al’amari da ya tunkaro shi. Ya girgiza zuciya da ilahirin gangar jikinsa. Wai Baba Dacta ba shi ya haife shi ba. To shi din wane irin mutum ne mai karamci da kyautatawa ga al’umma? Mutane irinsa tsiraru ne a cikin al’umma. Mami ya kira, muryarsa sak kamar babu komi a cikinta. “Alright Mami. It’s done, sai ki sanar da Dr. Haliman Daddy ya ce in gaya miki gobe in sun dawo daga daurin auren da za suyi a Takai za su zarto nan Kano a daura na Radhiyyah. Mami kisa min albarka! Albarkarki kawai nake nema Mami, bayan wannan babu wani abu. Zan samu Mami???” Hawaye ne suka sake zubo masa, wanda bai damu da ya sharesu ba, suna ta zuba a kan cinyarsa. Maimakon Mamin tasa mishi albarka kamar yadda ya roka, sai ma ta hau tambayarshi wai daurin auren wa su Daddyn za su yi a Takai? Khalipha don bakin ciki sai ya sanya kansa cikin gwiwoyinsa kamar karamin yaro ya ci gaba da kokawa kansa-da-kansa. Ita kuma Mamin a can ta gaza sukuni. Ga dai Khalipha ya haifu ya yi mata yadda take so, ya hakura da farin cikin rayuwarsa domin ya faranta mata, ya samu albarkarta amma zuciyarta ta gaza nutsuwa da son sanin auren wa za a daura a Takai? Kada zancen Dr. Halima fa ya tabbata, Rayhanah ta zama kishiyarta Dr Mansur ya yi auren huce haushi da ita. Tasan zuciya irin tasa idan ransa yayi mummunan baci bahagon hukunci yake yankewa. Ai sai ta mike ta zari makullin mota ta nufi gidan Dr. Halima a gigice domin maganar ta fi karfin ayita a waya. Dr. Mansur macijin sari ka noke ne, shirunsa a kan al’amari na nufin daukar mataki wanda ba zai yiwa victim dadi ba. Tana tafe da gudu tayar motarta ta gaba ta fice, motar ta gangara ta bugawa wata katuwar mota duk fitilunta suka kwankwatse, Allah ya sota ba abin da ya sameta, sai buguwa da kanta ya yi a jikin sitiyari, sai dan gilashin da ya yanki goshinta. A take jami’an tsaro suka cika wajen suka jawo mata bacin lokaci da biyan cin hanci. Ba ta isa gidan Dr. Halima ba sai da magariba. Dr. Haliman ta ganta afujajan ga jini na zuba duk ya bata tsadadden swiss lace yellow dake jikinta. Ita ta yi mata dressing din wajen ta rufe da plasta, sannan Mamin ta koro mata bayani. Maimakon Dr. Halima ta tayata jimamin abin da take wa gigita da tsoro a kai, sai guda ta je ta sakarwa Radhiyya a ka, ta kira Babanta a take ta sanar da shi. To dama shi Alh. Kabir shanyayye ne, take babu bin ba’asin wannan kagararren aure ya soma gayyatar jama’arsa ta waya. Radhiyya ta kunna (Nancy Agram) tana taka rawa a gaban Mamin har ta ji wani bangare na zuciyarta ya yi mata ba dadi, amma ta kasa nunawa ko a fusaka sai dariyar yake take taya Radhiyyah. Ta kuma ce, “To Radhiyyah kinga dai kokari da fadi-tashin da muka sha ni da mahaifiyarki don samun farin cikinki, kin kuma san Khalipha ba shi ya ce yana ra’ayinki ba. Don haka (handle him with care Radhiyyah), ki kular min da shi don Allah shima ki yi hakuri da shi sai a hankali, insha Allahu komi zai daidaita”. Radhiyya ta rungume Mami har da hawayen farin ciki a idanunta. Haka Mami ta dawo gida a salube gwiwa babu nauyi. Don ko cikakkiyar sallama basu yi da Dr. Halima ba, ba ta tofa wani abu a kan damuwarta ba, she is busy calling her people su zo daurin auren Radhiyya da Khalipha gobe. Idan Mami ta ce ta yi barci a daren yau ita kanta ta san karya ne. Ga azabar ciwon kai, ga radadin ciwo, ga tunani, fargaba da damuwa. Har sha biyun dare Dr. Mansur bai shigo gidan ba, tana falo tana dakon shigowarsa amma har karfe biyun dare babu ko inuwarsa, wannan ya tabbatar mata a Takai zai kwana. Ta soma kiran wayarsa ana cewa a rufe. Sai ta koma kiran Khalipha shima a rufe. Tamkar wadda aka yiwa allura ta zabura ta yo dakin ‘ya’yanta mata, kwayar idanunta sun zurma ciki sosai tashin hankali da zullumi. Abida da Jawahir kowacce na barci a gadonta, sai Azizah a kan sofa take nata barcin. Daga can kusurwar karshe ta dakin ta hango Rahane tana kan sallaya da hijabin da ya rufe dukkan jikinta sai fuska da tafin hannu, amma ko kafafunta ba a gani, tana rike da Alkur’ani bugun Misra tana karantawa amma ba a fili ba. Dai-dai lokacin da ladanin wani masallaci dake makwabtaka dasu ya kwalla kiran sallar Asubahi. A yadda Mami ta nufota a fusace kamar kurar dake jin yunwa ya sata rufe Alkur’anin da sauri ta aje gefe, tana karanto duk addu’ar da ta zo bakinta, don ta yi zaton Mami rufeta da duka za ta yi. Bayan ita dinma bata da lafiya, adalilin duk wasu hanyoyin sadarwa tsakaninta da Khalipha sun yanke. Baya neman ta, ita kuma idan abu ya dameta, bata iya gayawa kowa, kawai tasa a ranta Khalipha ya gama yayinta ne dama ba aurenta zai yi ba, yaudara ce kawai irin tasu ta ‘ya’yan gata. Ya samu wata dai-dai da shi, ita kuma ya rufe duniyarta. Wannan ciwon da Khalipha ya ji mata a zuciya, shi ya kassara ta, ciwo take a tsaitsaye duk da bata kwanta ba. Wani bangare na zuciyar tata kuma sai ya ce, “To ai Khalipha ba shi da laifi, bai yaudareki ba, ke kika yaudari kanki, da kika dauki dukkan amana da soyayyar duniya kika bashi, da saninki kan cewa kina zaman ‘yar karo ne a gidansu amma kika zarme kika wuce gona da iri, wai shine life-mate dinki......” Wannan tunanin din dai, bai rage komi daga son da takewa Khalipha ba, sai beken kanta da take gani. Ba ta gama tunane-tunanenta ba da mamakin abin da ya kawo Mami dakinsu yanzu da asubahi haka kamar Damisa, ta ji Mamin ta finciko ta babu ko takalmi a kafarta. Figarta kawai take har a kan step din bene wanda zai sadata da reception din gidan, tana buguwa tana komai amma Mami ba ta fasa janta ba sai da ta dangana da gate. Ta bude kofar wucewar mutum ta cillata wajen gidan tana cewa, “Ki tafi gidan ubanki! In ya mutu ne ki nemi danginki. Ba nufina in wulakanta ki ba, amma ke kin dauko hanyar wargaza min rayuwar iyali, kin rabani da mijina da ‘ya’yana da kwanciyar hankalina. Taimako ba hauka bane, Allah ya gani na yi iya wanda zan iya. Ina rokonki Rayhanah kada ki sake waiwayen inda muke, ki je kauyenku ki yi aure ya fiye miki da ci gaba da zama cikin iyalina kin ji na gaya miki”. Garammm! Ta rufe kofar. Karar kofar kenan da ta razana Malam Dahiru dake sallah ya fito da gudu ya ga shigewar Mami da kulle kofofin reception dinta da ta yi. Sai kuma ya ji shesshekar kukan mace a wajen get dinsa. Da azama ya bude ya fita yana haskatata da tocilan dinsa. “Wace ce a nan?” Ya tambaya cikin barazana, a lokacin da kwayar idonsa suka shaida wadda ke tsugunne a gefe tana kuka..... “Rayhanatu?” Ya ambaci sunanta cikin kokwanto. Hawaye kadai ke zuba ta ce, “Taimakamin da kudin Motar da zai kai ni Takai Malam Dahiru......... don Allah ba don ni ba......” Ta ci gaba da kuka mai matukar ban tausayi. A kidime ya ce, “Rayhanatu ba inda za ki, shigo daga nan, sai Dacta ya dawo koma mene ne ba zan barki ki tafi ba don kin yi ma Mami laifi. Ki yi hakuri ki daina kukan ya dawo”. Tana kuka sosai ta ce, “Malam Dahiru za ka iya bani ko ba za ka bani ba?” Yadda ta fiddo masa manyan idanunta dake jike jagab da hawaye sun kuma kada sunyi jawur, sai jikinsa ya hau bari. Ya ce, “Zan shiga matsala ne Rayhanatu idan na barki kika tafi....... ki ceci hanyar cin abincina ni da iyalina kada ki yi sanadin rabuwata da karimin mutum irin Babanku. Ita ma dai Hajiya wane irin laifi danka zai yi maka ka kore shi? Korar ma cikin duhun Asubahi?” Da ta ga Malam Dahiru ya tsaya ya tsinke mata da surutu mai ban haushi a gareta, ba kuma shi da niyyar taimakon nata. Bakin ciki ya yi bakin ciki a zuciyar Rayhanah, sai kawai ta tattare doguwar jallabiyyar dake jikinta ta yanka da gudu, gudun da ba ta taba zaton ta iya ba kamar filfilwa a lokacin gari ya soma haske. Ko kabarin iyayenta ne ta yarda ta koma da ta kara kallon ko da get din gidan su Khalipha, Abida da Mami, da suka yiwa zuciyarta rauni mai zurfi da ba zai taba warkewa ba. Malam Dahiru dai girma ya soma cimmasa, ba zai iya wannan gudun da Rahane ta fyalla ba balle ya kamata. Sai ya dau wayarsa ya kira Dacta ya gaya mishi iya abin da ya gani. Ga mamakin Mal. Dahiru, Dacta bai wani razana ba, bai yi mamaki ko fadan da ya yi tsammani ba, cewa ya yi da shi, “Don me baka ba ta kudin motar ba? Hau babur dinka maza ka bita ka ba ta kudin ka yi tafiyarka”. Ya jefa waya a aljihunsa ya tashi babur aguje shima ya bi hanyar da ta bi wadda za ta sadata da bakin titi. Unguwar Lamido Crescent unguwa ce a Kano ta wadanda suka san muhimmancin BIRO (‘yan boko). Babu ruwan kowa da kowa, ba cinkoso ba sa-ido kamar kana Abuja. Don haka ko gilmawar motoci babu a dai wannan lokacin. Sanda Mal. Dahiru ya hawo kan titi ya hangota can gaba da shi tana bin gefen titi sauri-sauri gudu-gudu kamar mai yin Safah da Marwah. Ita kanta ba ta san ina take jefa kafarta ba, fatanta kawai ta ganta a Takai, koda akan iska ne, kuma hawaye basu bar tsere a kan kundukukinta ba tana ta sharewa da zurmemen hijabinta. Da ta ji karar babur a bayanta ai sai ta kara artawa a guje, shima kuma ya nuna mata mutum da inji ba daya bane, ya sha gabanta har ya dan bugeta ta fadi a kan titin. Ya taimaka mata ta tashi ya rike hannunta gam-gam domin kiciniyar kwacewa take tana rokonsa kada ya maidata gidan Dr. Mansur, ya tafi ya kyaleta tunda ba zai taimaka mata ba. Mal. Dahiru ya ce, “Na rantse da mahaliccina ba zan mai da ki ba. Hau bayana in kai ki tashar Mariri in sa ki a motar Takai”. Kukan dai bai tsaya ba, amma ta ji sa’ida a ranta. Ta dane bayan babur ya ja suka tafi. Lokacin gari ya fara haske misalin karfe shida na safiyar Lahadi kenan. A tasha Mal. Dahiru ya sata a motar Tsangaya, ya sanar dasu a Takai za su sauke ta. Ya kirgo kudin da suka bukata ya basu ta shiga gefen taga daga baya ta zauna. Tana share idonta tana dagawa Mal. Dahiru hannu da godiya. Ya zagayo tagar da take ya mika mata naira dari biyu da kunshin kosai mai zafi. Hannu biyu tasa ta karba, tana gode masa. Ta share hawaye ta ce, “Sai wata rana...... Malam Dahiru na gode a gai da Sahura”. (Matarsa). Bai bar tashar ba sai da ya ga tashinsu, bayan motar ta cika. Shima sai ya ji danshi a kan fuskarsa, yarinya-yarinyar kirki, me ya raba ta da mutanen kirki irin wadannan? A fuskarta da yanayinta dai ya nuna ko yatsa kasa mata a baki ba za ta ciza ba, in baka yi mata izini ba. To me ya hadata da Dr. Asma’u haka? Ita ma ai mutuniyar kirki ce”. Haka ya yi ta sake-sakensa shi kadai har ya koma gida ya jingine babur dinsa ya ci gaba da harkokin gabansa. **** [12/24/2019, 21:47] Takori: Haj. Karima wadda ta amsa sunanta (Mai Karamci) kuma uwargida abun alfahari ga miji da iyalanta, ta yi sallama dakin da amaryar take a lokacin Inna Juma na faman yi mata fadan ta ki shan jarkar tsumin da Haj. Karima ta kawo tun jiya. A sanyaye Rahane ta ce, “Inna zaki ne da shi mai yawa, bama shan sukari. Baba Dacta ya ce yana sanya Diabetes (ciwon suga), kuma yana lahani cikin hakora”. Inna Juma ta ce, “Ciwon sukarin ya ci uwatar, mu da muka shanye fiye da jarkoki dubu ai kin gammu a asibiti”. Ta tsiyayo a kofi. “Ungo kwankwade ki bani kofin, don kushewar Ubanki.........” Ita Hajiya Karima sai dariya take da jin muhawarar tasu. Ta idasa shigowa cikin dakin tana ce da Inna Juma. “Kyaleta Inna, da kanta za ta ce ki bata idan ta san amfaninsa, sanda za ta kwankwade jarka goma ma ba za ta sani ba”. Rahane ta kyabe baki ta zumbaro shi ga Inna Juma, ta ce, “Don Allah Maman Anty Nabilah mene ne amfaninsa a lafiyar dan-adam? Zaki yana sa basir da….......” Ai buge bakinta Inna ta yi da mafici har leben kasan ya kumbura. Da sauri Haj. Karima ta kwace maficin Inna na shirin kara mata, ta ce “Rufa mata asiri Inna kada angon ya ganta da kumburarren baki ya ce ya fi son ki. Rayhanah sha kawai rabu da Inna, ki sa a ranki kawai Inna ba za ta dage ki ci abu ba, alhalin ta san zai cutar dake ba”. Inna ta ce, “Sanabe a gun Rahane har da na tsiya, komai ta ce yana sa kaza yana sa kaza, komai ka yi baka yi dai-dai ba sai ta kwakulo ma illah”. Hajiya Karima na dariya ta ce, “Inna rainon likitoci ce fa, ‘yar likita (uwa da uba) matar likita, kinga kuwa ko ba ta shiga aji don ta koyo likitanci ba za ta iya yi miki allura ta baki maganin kowacce cuta, ai ke gaba ta kai ki, wai gobarar titi a Jos, babu ke babu hawa layin ganin likita a asibiti”. Haka dai suka yi ta barkwanci, Inna da Haj. Karima, Rahane ba ta tsoma musu baki ba. Cewa take cikin ranta; Haj. Karima daban ce cikin matan gidan nan wajen saukin kai da karamci, dole mijinta ya sota fiye da su Haj. Indo. Don ta kama girmanta, ta iya zama da kowa dake samanta ko karkashinta da zuciya daya. Kusa da Rahanen ta dawo ta zauna, ta ciro wasu tablet din na Indonesia tana cewa, “Rahane maza kora wadannan da ruwa, kinga yanzu za a kai ki gidanki a Kano kafin sati mai zuwa Daddy ya danka ki hannun angonki. A sannan ne wadannan magunguna da muke takura miki ki sha za suyi miki amfani. Ki daina mai da kanki yarinya mana, kin girma fa, aure GIRMA ne, ko shekaru basu kai ba”. Rahane murmushi ta yi har fararen hakoranta suka bayyana, kanta ya kumbura, don tana son GIRMA. Tana so a ce ta girma, she’s no more a kid now!!! Ta karbi magungunan daga hannun Haj. Karima tana dubawa, ta kasa karanta rubutun chinese dake jiki. Ta ce cikin ranta, “How can I take drugs without Doctor’s order?” Ta karba ta hambuda su a baki, ta boye su a kasan harshenta ta kora da ruwa. Haj. Karima na ba da baya domin ta je ta dawo ta yi toilet da gudu ta tofo su cikin masai ta yi flushing ta wanke bakinta. Inna Juma da ta fahimceta ta hau salati da sallallami. Rahane ta rungumeta tana rokonta kada ta gayawa Hajiya har da ‘yar kwallarta. Ta ce, “Inna ni ba zan sha maganin da ban san na mene ne ba, ba zan sha tablet din da ba likita ne ya yi Prescribing din ta gareni ba”. Inna Juma ta tureta daga jikinta tace, “Ni da Allah daga ni, ai shi kenan ke kika sani. Ana miki gata kina iyayi. Sai ki je wa mijin salam! Ina ruwan wani”. Da dan mamaki a fuskarta ta ce, “Inna da da gishiri kike so in je masa?” Inna Juma ta ce, “Eh mana, ai gara ki je da dandano ko ya so ki, tunda ba kiyo kyawun Yalwati ba, kin dauko bakar fuskar ubanki. Ko da yake yanzu kin dan fara washewa ba kamar sanda kina yarinya ba”. Rahane na dariya ta ce, “Inna har da cin fuska?” Inna ta ce, “Har da cin kafafuwa kuwa, idan kika yi wasa in kwace mijin idan ya yi mini. In ta tsuma kaina yadda zai ji ni cau!” Wadannan languages na Inna Rahane ta kasa gane musu, kuma Innar ta ki fitowa fili ta yi mata bayani sai dukunkune maganar take. Ta je da dandano? Ta yi cau? Sai ka ce wata abinci. May be Inna Juma bata iya Hausa ba. Barorin gidan Hakimi ke ta shigowa da manyan jakunkuna. Haj. Karima ta biyo bayansu ta zauna sosai tana bude jakunkunan tana fadawa Rayhanah cewa lefenta ne a dinke. Ta dinga daga atamfofin super da swiss lace kamar debo su akai a kasuwa ba kudi aka sa masu yawa aka saya ba. Takalma da jakunkuna ‘yan Italy abin sai wanda ya gani. Kayan shafe-shafe, turaruka, gyaluluwa, sabulai abin ba’a magana. Ta gaya mata cewa duk nata ne. To abin ya fi karfin Rayhanah ta yi magana sai ido, kuma shi ta zuba mata. **** RAHANE A GIDAN AURENTA! A al’adar babban gida musamman irin na sarauta, lokacin bikin aure an saba gwangwajewa a cashe ayi almubazzaranci da dukiya. Amma wannan auren na ‘ya’yan Dr. Mansur biyu (Khalipha da Ibraheem) ya zo da sabon sauyi, ko algaita ba a busa ba, ko kwarya ba a buga ba, haka ko guda babu wanda ya rangada. Wannan kuma ya samo asali ne da yadda auren ya zo ba cikin shiri ba, ga kuma duka angwayen babu ko daya. Gidan bangaren daya amaryar kam sun cashe sun gwangwaje yadda ransu yake so, an wulakanta naira. Amarya ta daura sittiru na kece raini, anyi hotuna da sauransu. Amma a bangaren daya amaryar ba ta da wannan gatan, ba ta ma sa-aka ba, ba ta ma kuma da wanda za ta gayyato a duniya idan ba Jawahir ba, ga shi kuma watakila har abada ba za ta koma inda Jawahir din take ba, da aminiyarta Azizah. Sannan ‘ya’yan Hakimi da yawa da sauran matansa basa farin ciki da aurenta da Ibraheem saboda Nabilah. Don haka ko taron wuni ba kowacce ce ta zo ba, wannan bai damu amaryar ba, balle danginta da suka zo rakata gidan mijinta daga Albasu, Takai da Tsangaya dukun-dukun da su, bayan su a wurinsu sun kure adaka. Hakimi da kansa yana gaban motar Dr. Mansur wanda ya zo daukar amaryar da kansa, a bayan motar Haj. Karima ce, Inna Juma (wadda za ta zauna tare da ita) da Zinaru da babbar ‘yarta Hansai. Bai tsaya ba sai farfajiyar wani matsakaicin mansion mai rufi ruwan kasa da fenti ruwan madara. Guda biyu ne a jere amma cikin get daban-daban a unguwar ‘Farm Center’ dake bayan shagon Kasa (Country Mall). Babu yawaitar jama’a a unguwar babu cinkoso, yawanci ma duk gidajen ma’aikatan gwamnati ne da sababbin gine-gine da aka fara ba a karasa ba. Sai kamfanoni da shaguna sababbi wadanda ba a fi shekara da bubbude su ba. Hannun Rahane cikin na Baba Dacta har dakin barcinta, cewa yake “Da a Takai gidanki yake, a kan doki zan kai ki Rahane. Shiga gidanki kina mai neman aminci daga Ubangijinki, ta hanyar cewa “Assalamu Alaikum”. Shiga gidanki cikin neman dukkan alkhairan dake cikinsa, ki nemi tsari daga sharrinsa. Ta hanyar shiga da kafar dama. Ina rokon Allah yasa mutuwa ce kadai za ta fitar dake din-din-din daga gidan mijinki, ita ma din ina fatan ta dauke ku tare. Amma fa bayan kun bar min jikoki, tattaba kunne da uhm-hm-hm”. Hakimi murmushi ya yi ya ce, “Har da uhm-hm-hm Mansur? Anya baka zarmewa duniyar ba? Kana da hamsin da bakwai yanzu, amma kana neman wasu sittin a nan gaba?” Dr. Mansur ya ce, “Yaya Abdulkadir ina son tsufa mai tsaho, tsufan dake da sanyin idaniya (‘ya’ya da jikoki da tattaba kunne) dadi ne da shi, musamman idan suka baibaye ka suna jan farin gemunka......... Hurry Rahane....... yearly! (wato tayi sauri duk shekara ta kawo jika)”. Kowa dariya yake banda Rahanen, wadda take jin ina ma kasar ta tsage ta shige cikinta da kunyar wannan magana da Baba Dacta ya yi. Ta sake kudundunewa cikin mayalwacin mayafinta. Doguwar addu’a Hakimi Abdulkadir Balarabe Sardauna ya ja aka shafa. Rahane ba ta tashi tsinkewa da kuka ba sai da suka sa kafa suna fita daga dakin, bayan sun gama yi mata tofin albarka. Da gudu ta mike ta bi bayan Baba Dacta ta kama kafafunsa tana kuka sosai ta ce, “Allah ya fini sanin alherin da ka yi mini. Don haka shi nake roko ya saka maka da fiye da shi. Ina rokon ku idan na taba bata muku a shekarun da muka yi tare Baba Dacta kana gina rayuwata positively… ka dubi Allah ka yafe mini, ka daina fushi da Mami a kaina don Allah Daddy.......” Ta ci gaba da kuka mai keta zuciyar duk wani mai birbishin imani a zuciyarsa. Hannu biyu yasa ya dagata, “Bari kukan nan haka Rayhanatu bana son shi, in ma kin min laifin ai afuwa ce har kullum tsakanin Uba da dansa. Guda dai-dai har dubu malala gashin tunkiya, na yi miki ita Rayhanah, na yiwa Mamin ki, ban taba riketa da komai ba a kanki, sai ajizanci irin na dan Adam. Ni na gaya miki WATARANA na zuwa da Asmau da kanta za ta goya ‘ya’yanki, MADALLAH! Da zuciya mai tsafta irin taki Rayhanah!!!” Da sassarfa ya wuce ya bi bayan Hakimi. Don baya so taga kwallar data sauko daga idaniyarsa. Inna Juma ta bisu ta rufe kofofin gidan suka gaisa da maigadin Buzun Nijar ne. Ta dawo ta kama hannunta suka koma dakin barcinta tana lallashinta. Ta ce, “Gani ni dake zamu yi zaman mu, zama mai dadi cikin kwanciyar hankali har Allah ya kawo mana angonmu lafiya. In kika yi sakwa-sakwa sai in kwace shi”. Ta ce, “Daga ido Rahanen Yalwati, mai sunan Yalwati ki sha kallon gidan mijin da Allah ya baki”. Ta yaye mata lullubin gaba daya ta nuna mata wani dan karamin hoto cikin dan ‘frame’ din dake kan durowar gadonta. Ibraheem ne rungume jikin Baba Dacta ranar ‘graduation’ dinsa daga MBBS. Kin kallon hoton ta yi, ta yi maza ta kunshe idonta cikin kafafunta. Sai Juma ta yi dariya a ranta ta ce, “Kunya kamar Yalwati, ga rayuwar birni ba ta sa kin yi watsi da ita ba. Ta soma tunano kuruciyar mahaifiyar Rayhanah, haka take da kunya da rashin wayo. **** ASALINSU Su ‘yan asalin Takai ne gaba da baya, basu da wata daukaka ko wani mulki ko suna (reputation) kawai bayin Allah ne da suka fi karfin abin da za su ci, da wanda za su daura. Da ita da Gwaggo Jummai kakar su Rahane uwarsu daya ubansu daya. Lokacin da Malam Rashidu ya fito neman auren Rahane (Yalwati) dukkansu babu wanda ya marawa al’amarin baya, ba don komi ba kuwa sai don cewa ba haifaffen Takai bane bakon haure ne daga Tsangaya, wani kauye cikin karamar hukumar Albasu. Amma ba don karancin samunsa ba. Ko da Rashidu ya yi alkawarin ba zai raba ‘yarsu da mahaifarta ba basu yarda ba, Babanta ne ya yi musu bazata ya karbi sadakin Rahane daga Mal. Rashidu, ya ce ko bangon duniya ne ya kaita, ba inda aure baya kai mace, balle ina Tsangaya ina Takai? Ban da neman zance irin na mata? Sai kuma Rashidun ya basu mamaki da soyayyar da yake yiwa Yalwati. Ya je ya tattaro komi nasa daga mahaifarsa, bai bar ko allura ba. Dama gaida mahaifiyarshi Iya Bilki ke kai shi Tsangaya sai ya je ya dauko abarsa ya ajiyeta kusa da shi, uba ya jima da rasuwa, dangi sun kare, ita kadai ta rage mishi. Ya kawo ta ya ba ta daki a gidan mahaifin Ado da yake haya a ciki. Bayan mahaifin Ado ya rasu, Ado ya gaji gidan. Zamane suka yi mai dadi shi da Rahane da mahaifiyarsa, domin Iya Bilki ba tsohuwar banza ba ce ta san abin da take yi. Ashe zaman nasu na dan takaitaccen lokaci ne (shekara biyu) Allah ya karbi ranta wajen haihuwar Rayhanah. Don haka iyayen Yalwati (Rahane) basu ji ko dar wajen ba shi Zinaru ba, a lokacin da Iya Bilki ta nemi hakan. Ta je ta zuba musu rashin mutuncinta ta fito ta koma gidan tsohon mijinta a Albasu. A lokacin da Iya Bilki ta rasu Inna Juma ba ta Takai tana birni tana wanke-wanke tsayin wasu shekaru masu yawa tun bayan rasuwar mijinta Malam Saleh, ba ta kara jin duriyar Rahane ba sai da ta dawo birni take tambayar al’ummar kauyen, su ma suka ce basu sani ba, amma dai kowa ya san sunyi rikici da Ado, wanda shima ya dade baya kauyen sai da cutar zamani ta dawo da shi jinyar dole gida. A bakin Ado ne ya ce ta bincika gidan Hakimi shi can ya barosu. Inna Juma ba ta yi kasa a gwiwa ba ta ci gaba da binciken Rahane da Zinaru har Allah ya hada su. Ta kawo gwauron numfashi ta daga ido tana duban Rahane, wadda barci ya yi awon gaba da ita. Ta mike ta kashe mata fitila ta kunna mata na’urar sanyaya daki, da yake ta yi rayuwar Birni ba ta da duhun kai sam. Ta jawo kofar dakin ta nufi wanda aka ce shine nata. **** Rahane ba ta kara tsinkewa da irin kaunar da Baba Dacta ke mata ba sai a washe garin ranar da safe. Safiya ta farko a gidan miji, wacce ke cike da sauyin rayuwa a gareta. Ta tashi ne ta jita cikin wata irin nutsuwa da ba ta taba ji ba a kafatanin rayuwarta, ta daga kai tana kallon dakin barcin nata. Fentin dakin fari tas, haka marbles din tsakar dakin. Ga wasu ubansu English-Furnished Funiture bakake da ratsin silba, labulen ma silba ne da ratsin baki, split na aiki. Katifar gadon ta ruwa ce kamar kana kan gajimare. Ba ta kara tsinkewa ba sai da ta shiga bandaki domin dauro alwala da wanka, inda ta ga bakonta ya iso (period). Don haka wankan ta yi, cikin lokokin saman da aka yi a bandakin ta samu pad da pantis ta gyara kanta, bayan ta yi wanka. Ba ta da yawan ado, Pakistan ruwan toka kawai ta zura, ta fesa spray ko lotion ba ta shafa ba kasancewar zafi ake yi. Ta yi tattaki ta fito falo. Duniyar Turawan da Daddy ya shirya mata ko ‘yar gwamna sai haka, komai cool ba harbatsiya, abin kayatarwa a ido, kujerun kansu yatsu ta kai tana latsasu, domin kyansu da santsinsu ya isa (Leather Francaise) maroon da ratsin makuba, haka labulayen ma kalarsu kenan. Dakunan barci uku ne a falon, na Inna Juma yana falon kasa, shigifar duk da ta shiga kalar kayan dakin daban ne. Musamman Baba Dacta ya taho da decorators din da suka gina gidan daga Ireland, sune kuma suka shirya gidan. Ta shiga nan ta fita can har ta jefa kanta dakin da Gwaggo Juma take, tana kan darduma tana lazimi da carbinta mai ‘ya’ya dubu cunkus a gabanta. Ba ta katseta ba bayan sallamar da ta yi, Juma ta daga kai alamar amsawa, sai ta fada gadon Juman kawai ba ta san sanda barcin gajiya ya sake yina won gaba da ita ba. Tunda aka fara al’amarin nan ba ta samu isasshen barci irin wanda ta samu yau ba. Da Juma ta gama laziminta, kicin ta fada tana yi musu abin da za su karya da shi. Duk na’urori ne fal da yawa ba ta san amfanin su ba. Amma ta san yadda ake amfani da Gass Cooker. Nan ta bude store babu abin da ba a zuba ba ta fannin kayan abinci. Haka firij babu nau’in nama ko kifin da babu dankare cikin kankara a freezer. Ta debi dankali (potatoes) ta soya musu da kwai, ta dafa musu shayi a filas, kayan shayin ma duk gasu nan a cikin irin kwandon nan mai tayoyi, ta hado komai ta dawo dakin nata. Har zuwa lokacin Rahane na barci. Sai ta ci gaba da ‘yan kintse-kintsen tsummokaranta cikin kwabar jikin bango. Ba ita ta tashi ba sai karfe goma da rabi, ta koma dakinta ta yi brush ta dawo suka fara karyawa. Haka suka ci gaba da zamansu cikin kwanciyar hankali. Alal hakika Rahane ba ta iya komai da ya shafi girki ba, domin Mami ba ta sa su girki, ita take yi in tana gida ko kuku. Haka Iya Bilki Allah ya ji kan rai ba ta bata tukin tuwo sai kwashewa da rabawa. Don haka Juma ta fuskanci hakan, sai ta dage wajen koya mata girki, mafi yawa na gargajiya don ita ma ba ta iya na zamani ba. Ta koya mata kunun tsamiya, na kanwa da na gyada dana farar shinkafa. Ta koya mata tuwo na alkama, na semo da na shinkafa. Ta koya mata sinasir da miyar ganye, waina da taushe, fankaso, dambun shinkafa, moi-moi (Alala), gashin kaza cikin oven da soya ta, dambun nama and much more. Yau ga shi har sun kwashi wajen watanni uku. Daddy kan zo wani zubin in ya taso aiki su gaisa, ya ji ko suna da damuwa ta kudi ko ta cefane, kuma ka’ida ne muddin ya zo sai ya ba ta kudi ko tana bukata ko ba ta bukata, bai taba yi mata zancen angon ba, ita ma ba ta tambaya ba, sai dai ta fuskanci Daddy cikin damuwa yake yana dai yin kokari ne na boyewa amma har ya rame shi bai san ya rame din ba. Kamar dai yau da ya zo ya kawo mata computers sabbi gal har guda biyu, laptop da Ipad, da conecction dinsu da komai, tana ta godiya duk da bai bata waya ba. Tata a can gidan Mami ta barota ba ta dauko ba tun ranar da Mamin ta kore ta. Ba ta damu ba, farin cikin wadannan computers yasa ta manta da komai. Haka ya tafi babu kuzari a jikinshi. Damuwar Dr. Mansur kuwa shine, Ibraheem na neman ba shi kunya. Tun maganar farko da suka yi, inda ya ce mishi ya zaba masa matar aure ba tare da ya gaya mishi ko wace ce ba, ya ce dai wadda hankalinsa ya kwanta da ita. Ya tattaro ya dawo gida Najeriya haka, ya bar aikin da yake yi a Chicago kasarmu ta fisu bukatar Nephrologists, Jami’ar ta rike shi yana part-time lecturing, haka yana aiki a babban asibitin koyarwa na Chicago (Illinois Teaching Hospital). Abinda Ibraheem ya cewa Daddy shine, kowacece ya zaba mishi din ya karba, in dai ba auren zumunci bane. Zai duba bukatar mahaifin nasa ta dawowa gida cikin satin ko da bai dawo gaba daya ba. Tun daga wannan maganar da suka yi, bai kara samun wayar Ibraheem ba. Idan ya kira ba ta shiga, babu shi a social network don shi dama baya sanya kansa cikin wannan abubuwan na asarar lokaci. Daddy ya buga ya buga ya kasa samun Ibraheem wata da watanni. Ga yarinya ya ajiye babu future plan na ci gabanta. Mami da ta gaji da ajiyar amaryar Khalipha sai tasa ta a gaban mota ta bishi da ita Abuja. Anyi sa’a ya dawo daga Hurghada inda ya yi sa’ar samun kakanshi mahaifin Mukhlis da ‘yan’uwanshi. An tafka shari’a a kotun Muslunci ta Hurghada tsakanin Khalipha da dangin mahaifinsa, inda ya yi kararsu a kan sun sheganta shi, ba dukiyar da suka lamushe ba ce a gabansa, a’a, tabbatuwar identity dinsa. Madaura auren Mukhlis da Asma’u a Jos duk sun bayyana a babbar kotun Hurghada, inda sarkin Jos ya ba da shaidar komai, hotunan da aka yi da Mukhlis ranar daurin aurensa da Asma’u, har (vedio casette) da aka yi a lokacin da Mukhlis an kunna a kotun kowa ya gani. Likitoci sun debi jini sun tabbatar. Shima Abu-Arab kakan Khalipha ya bada diary na marigayin wanda ke rubuce da bayanin aurensa da Asma’u da niyyarshi ta kawota Hurghada cikin shekarar. Ga hotunansu nan kala-kala shi da Asma’u da zungureren cikinta, dole dangin suka yi saranda suka karbi diyaucin Khalipha. Amma sun nemi da ya yafe musu dukiya kam babu, sama ko kasa sun lamusheta. To dama haka cin dukiyar maraya yake kamar cin wutar auduga. Allah ka kara mana imani da arziki na halali ameen. Khalipha ya yafe musu, ya kuma tabbatar musu shi ba dalilin neman shi dasu kenan ba. Abu-Arab ya hana shi tahowa sam-sam sai da ma’aikatar Foreign Affairs ta tsoma baki sannan kakan ya yarda ya koma bakin aikinsa. Sai dai kuma tare da santaleliyar Balarabiyar amarya (Mimtaaz) ‘yar kanin mahaifinsa. Khalipha yaso ya turje, suka ce bai isa ba. Ya gaya musu Mamanshi ta yi mishi wani auren ko tarewa ba ayi ba, suka ce ai al’adarshi ta yarda ya zauna da mata hudu ma ba biyu ba, duk bayanin da ya yi kokarin yi musu mai nuni da cewa zai shiga matsala da mahaifiyarshi kakansa ya ki yi masa uziri. A karshe ma kuka yasa masa, ya ce a yanzu shi yake gani kamar Mukhlis, zamanshi tare da ‘yar’uwarshi Mimtaz shine kawai alfarmar da yake so ya yi mishi kafin Allah ya dau ransa, ya tsufa sosai, amma hakan bai hanashi hada kan iyalinsa ba, ta hanyar kulla auratayya a tsakanin matasan jikokinsa. Don haka Khalipha ya yi tubus, ya kara neman alfarmar Mimtaaz din ta zauna a Hurghada ya je ya yiwa mahaifiyarshi bayani tukunna ya dawo ya tafi da ita, zai dauki nauyinta. Nan ma tsoho ya ki yarda, ya ce kafarshi-kafarta in yaso uwar tasa ta yi gunduwa-gunduwa da ita tasa a miya. Rigimar wannan tsoho da yawa take...... in ji Khalipha. Sai ya sako sullubebiyar matarshi a gaba suka sauka a gidan shi na Abuja. Rayuwar Khalipha da Mimtaaz ta watanni biyu kacal sai ta zamo abar alfahari a zuciyar kowannensu. Mimtaaz ta ci sunanta Mimtaaz wato (excellent). Kaunar jini mai karfi ta haifar da tasirin da ya fi soyayya karfi. Yarinya danya shataf mai tarin baiwarwaki da falaloli da yawa daga indallahi. Sai ga Khalipha yasa Mimtaz dinsa a barin damansa sun cilla Birnin Manzo yin umarah, daga nan suka wuce Sweden suka kwashi sati biyu suna (honey-mooning). Sai ga bakin cikin dake zuciyar Khalipha yana yayewa, haske ya cika shi farin ciki ya maye gurbin bakin ciki. Sai dai kullum ya kan tuna Rayha, ko wane hali take ciki? Addu’a yake mata ba dare ba rana Allah ya zama gatanta kamar yadda ya yi mishi gata ba don ba shi da shi ba. Sai don ya dubi zuciyarsa mai kyau ce a kan kowa, mai son farantawa uwa mahaifiya don gamawa da duniya lafiya. Haka yake kyautata zato a kan ita ma Rayhanah. Kwanansu biyu kenan da dawowa daga Sweden Mami ta iso da amarya Radhiyyah a gaban motar ta, maigadi bai hana Mami shiga ba don ya santa. Ma’auratan na falo Khalipha na karantawa Mimtaz wani novel mai suna (Surgeon’s Wife) na Azizah Idris Gombe, kasancewarta mai son labaru. Haka yake bata lokaci ya yi ta karanta mata in ya dawo ofis, da yake tana jin Turanci sosai don a jami’ar Coventry take karatu aka tsigeta aka yi mata auren. Witness to Tears ma na Abubakar Gimba duk ya karanta mata tun a Sweden, The Burden of Memory na Wole Soyinka da wasu daga cikin na Babansu William Shakespear da yake Literature take karanta, ita kuma tana kusa da shi tana fifita masa shayin da yaji suga da na’a-na’a, daga shi sai singlet da wando short-nicker Mami ta yi sallama a falon, hannun Radhiyyah cikin nata. Sai ta tsaya kawai kamar an dasa ta ana kallon-kallo tsakaninta da Mimtaaz, ba fuskar kowa take gani a fuskar Mimtaaz ba face fuskar Mukhlis (mijinta na fari), Balaraben Hurghada Mukhlis Abu-Arab. Don haka ta tsaya stand still ta kasa gaba ta kasa baya, amma bakinta ya mutu ta kasa yin ihun da da farko taso ta yi na ganin Khalipha da macen da ba tashi ba. Duk da haka ba komai bane kuma ba abin mamaki ba a wurin matasan yanzu, musamman wadanda ke jike cikin naira suke kuma jan ragamar rayuwarsu irin su Khalipha. Sai dai tana da yaqinin nata dan, ba zai taba yin hakan ba tunda ita dai bata taba yin zina ba a rayuwarta ko kafin ta Musulunta. Shekaru talatin da biyar a baya suka shiga dawowa suna giftawa a idanunnta tamkar majigi. **** [12/24/2019, 21:47] Takori: RESHE YA JUYE DA MUJIYA! “Anzo Takai, ina na Takai ku sakko!” Kwandastan yake ta fadi, yana bubbuga kofar motar. Rahane ta daga ido tana kallon mahaifarta wadda har gobe ba ta canza a idanunta ba, duk da dadewar da ta yi ba ta zo ba tun rasuwar Babanta. Ga tafasa ta nuna, gero da masara sunyi yabanya kore sharr dasu, da yake lokacin na damuna ne. Da kyar ta cira kafa da ta yi mata tsamin gaske ta fito daga motar. To gata ta dawo gida, amma wajen wa za ta a Takai? Ba uwa, ba uba balle dangi. Ko gidan gado ba ta da shi, balle ta je ta share ta zauna. Wata zuciyar ta ce, “Ki tafi gidan Hakimi”. Wata kuma ta kalubalance ta da cewa, “A sanadin wa kika san Hakimi da iyalansa? In kika je gidan Hakimi kin je rokon a mayar dake gidan Dr. Mansur ne, a hada Mami da Daddy fada a kan gaskiyarta, ba ta yi isar da za ta hada mu’amalar jini da ita ba. Don haka ba ta ga laifin Mami ba don ta raba danta da ita, sai ma laifin ita kanta da ta gani, da ta bari zuciya ta rudeta ta mance da reality na rayuwa na dai-dai ruwa dai-dai tsaki ta amince da soyayyar Khalipha. Har zuwa yanzun kuma babu abin da ya canza daga soyayyar da take yiwa Khalipha, domin soyayyar ba shigar sauri ta yi mata ba, balle ta fita fit! Farat daya. Circulating ta yi a hankali cikin jini da tsoka har ta huda kashi ta shiga cikin bargonta. Sai dai ta amincewa kanta ko soyayyar za ta kasheta, har abada ita da Yaya Khalipha. Ta kai gefen hijabinta ta share hawayen da suka zubo mata a wannan lokacin. Ba wanda ta tuna a wannan lokacin sai Zinaru kanwar mahaifiyarta Yalwati da Malam Rashidu ya aura ya saki, rabonta da Zinaru tun ranar da ta bar gidansu. Ta sani cewa duka kakanninta na wajen uwa sun rasu, amma Zinaru tana raye, za kuma ta iya sadata da wasu daga cikin dangin Yalwati in akwai, idan ita ba za ta zauna da ita ba har zuwa lokacin da Allah zai ba ta miji a nan Takai dai-dai da rayuwarta, wanda ba zai kalli tushenta, asalinta da tsohuwar lalurarta ababen kyama ba, tunda tushe da asalinsu daya. To yanzu ina za ta nufa neman Zinaru? Shekarun da yawa, Takai da girma. Abin da ya kara ruruta wutar kukan da take yi kenan. Ta bi gefen titi ta soma tafiya tana kukan, amma ta toshe bakinta da hijabin. Tafiya take cikin zafin nama ba tare da ta san inda take jefa kafafunta ba. Horn din mota ta ji a bayanta ba kakkautawa, amma ba ta juyo ba ta ci gaba da tafiyarta, tunda ta san ita dai ba a tsakiyar titi take tafiya ba balle a ce ta matsa. Sai ma ta kara azama ta soma shigewa cikin gonakin masara. Fakin din motar aka yi a gefe aka biyota da kafafu. Muryar da ta ji na kiran sunanta da karfi ya sata juyowa cikin razana da firgici. Baba Dacta ne da Sha’aban dan wajen Hakimi. Ya fi karfin ta kalle shi ta wuce, yana da kimar da babu mai ita a idanunta a duniya idan ka dauke iyayenta. Don haka ta ja ta tsaya idonta cike da hawayen da suka kasa tsagaitawa. Har Baba Dacta ya iso inda take ya kama hannunta idanunsa shima sun kada sunyi jawur, amma ba hawaye a cikinsu. Sha’aban ya koma ya matso da motar har inda suke. Baba Dacta ya bude kofar baya ya shigar da ita ya rufe, shi kuma ya zauna wajen mai zaman banza, Sha’aban ya ja motar suka hau titi. Cikowar da ta ga kofar gidan Hakimi ta yi da bil-adama bai zamo bako a gareta ba, domin an saba yin bukukuwa da daurin aure a gidan Hakimin. Sha’aban ya yi parking, wannan karon ma hannunta cikin na Baban suka shiga gidan. A dakin Hajiya Karima ta tadda Hakimi da kansa da sauran ‘ya’yansa wadanda suke kusa ba na nesa irin su Hibbah ba, har da Nabilah, da sauran iyayensu mata. Ga Nabilah na suma ana yayyafa mata ruwa kamar mai iskokai, idan ta farfado ta yi surutai sai ta kara sumewa. Fuskar marikiyarta Inna Indo kamar hadari ta dubi Rahanen da Dacta ya shigo da ita shekeke!. Sai Haj. Karima Maman Nabilan ta asali ce ta nuna mata wajen zama, ta zauna a darare tana ta kuka. Dacta yake gayawa dan’uwansa a bakin titi suka ganta dama ya kintaci lokacin tahowarsu ne da awoyin da za su dauka kamin su iso, ya je tashar ya daukota sai ya hangota bisa titi. Hakimi ya ce, “Sannu Rayhanatu kin ji, insha Allahu kin yi sallama da rayuwar maraici, tunda kin samu uba irin MANSUR da nagartaccen miji irin IBRAHEEM da kuma ni surukinki Abdulkadir. Share hawayen nan Rahane, daga yau na tabbatar miki haka kawai ba za su kara zuba ba. Sai ko a kan wata kaddarar daban ba ta maraici da rashin dangi ba. Muna yi miki barka da zuwa cikin zuri’armu ta alfarma wadda kudurinta shine kiyaye martaba da mutuncin talakawanta. Sannan muna farin cikin shaida miki cewa, mun samu kanwar mahaifiyarki Zinaru wadda ta hanyarta aka samu dangin mahaifiyarki. Sha’aban jeka shigo dasu”. Ya mike da kansa ya iso har gabanta, ya dora mata warawaren farin zinare (bangles) a kan cinyarta. “Ga sadakinki, mun daura aurenki da IBRAHEEM MANSUR TAKAI. Babanki ya karbi waliccin ki, na karbi na Da na Ibraheemu. Shaidar da Babanki Mansur ya yi miki ta kyawawan halaye, tarbiyya, biyayya da hakuri, ina fatan ta dore har a gidan aurenki. Yadda Ibraheem ya karbi zabin da mahaifinsa ya yi masa hannu bibbiyu, muke fatan kema ki karba. Ki yarda cewa baka auren mijin da ba naka ba, kamar yadda baka auren macen da ba taka ba. Komai na rayuwar Dan Adam tun fil’azal rubutacce ne a (Lauhul-Mahfouz). Muna son jin ta bakinki Rayhanah, shin kin amince da zabin Babanki ko kina da uzirin da zai hana ki yin hakan?” Girgiza kai take cikin kidima da gigicewa. Wannan fa shi ake kira reshe ya juye da mujiya…. Ana bikin duniya ake na kiyama….. Abinda ta samu harshenta na fadi ba tareda ta shirya kalaman daga kwakwalwarta ba kawai shine, “Idan ni din ban yi biyayya ga zabin Baba Dacta ba…., idan shi bai ji kyamar hadani da Dan da ya fito daga jikinsa ba, duk da kauyancin da talaucin nawa, da lalurar dana samu kaina ciki a baya…. ai ni ba zan ki karbar zabinsa ba ko da tura kaina cikin dakin Zakuna ne. Yadda Allah zai tambayeni idan ban yiwa iyayen da suka tsugunna suka haifeni biyayya ba, na tabbata haka zai tambaye ni idan ban yiwa Baba Dacta ba.......!” Ta ci gaba da kukan da bata san dalilinsa ba. Ta barsu suna juya tasirin kalamanta a zukatan su. Daidai lokacin da ta ji sallamar jama’a, ta daga kai a hankali tana kallon su. Wasu harbatsattsun kauyawa ne babu wadda za a ce “gara ita”. Da kyar ta gane Zinaru a cikinsu saboda cindon dake gefen hancinta. Ji ta yi kamar anyi mata gafara ta mike tsaye tana kallon su idanu a warwaje. Zinaru ta karaso ta rungumeta, wani hamami na baki da hammata ya nausheta, mugun naushi kuwa, rokonta take ta yafe mata, alhakinsu ya sanya ta wulakanta a rayuwarta. Abinki da ‘yar likitoci, da dai ta samu Zinaru ta saketa ai sa ta yi toilet din Haj. Karima da gudu ta rika kelaya amai cikin sink kamar ta amayar da ‘yan hanjinta. Su sun dauka kuka ta je tana yi, don haka ba wanda ya bi ta. Da ta wanko fuskarta ta dawo ne Zinaru take mata bayanin sauran matan su hudu, biyu tsofaffi biyu za suyi shekaru arba’in haka, amma wahalar rayuwar karkara tasa sun fi kama da tsofaffin. Akwai mai fara’a sosai cikin dattijan mai amsa sunan Inna Juma, Zinaru ta ce, “Juma kanwar kakarki ce wadda ta haifi ubanmu, Inna Hanne Yayar mahaifinmu ce, don haka uwa ce a gareni ke kuma kaka a gareki. Ta-sidi da Kubra kannen mahaifiyarmu ne gasu duk a Albasu suke aure, ni kuma a Jahun. An nemo ni Takai ta hanyar Inna Juma da yake ita tana nan Takai ko bayan mutuwar mijinta Malam Saleh, bata taba haihuwa ba, mu kam akwai tarin iyali. Ina yi miki ta’aziyyar Iya Bilki da Malam Rashidu, ki dubi Allah Rahane ki yafe mini..........” Kuka sosai Zinaru take yi har Rahane ta ji zuciyarta ta girgiza. Ba ta son kukan babba ko kadan balle Zinaru da take jin ta kamar mahaifiyarta. Duk da bata kasance mai kyautayi a gareta ba. Ta yi saurin rike hannunta, “Na yafe miki Inna Zinaru, wallahi na yafe muku baki daya Allah ya yafe mana”. Juma ta ce, “Bar ‘yar banza da kukan munafurci, sai yanzu da kika ganta a matsayin mutum mai daraja da kyawun gani kika san ta yafe miki? Kin taba zuwa kin ganta ko sau daya bayan barinki gidansu? A matsayinta na diyar shakikiyarki? Al’umma ban san bolar da muka kai zumunci a wannan zamanin ba, na cikin ka kawai shine naka. Sau nawa ina tambayarki inda take kina cewa ba za ki rike ta ba? Duk ma inda take ta je kowa ya yi ta kansa? Sai da na bi diddigi ta wajen marigayi Ado ya gaya min inda ta fada? Kauce daga nan kada in maganre ki........” “Inna komai ya wuce”. In ji Haj. Karima. “Rayuwar duka ‘yar afuwa ce, kema ki yi hakuri. Mun godewa Allah da ya hada ku cikin sauki, a taru duka a yafewa juna komai na duniya dan afuwa ne. Da Ubangijinmu baya yin afuwa a garemu da bamu kawo yanzu ba”. (In ji Hakimi). Duk cikinsu Rahane ji ta yi Inna Juma ta fi kwanta mata. Ita ce tsohuwar ciki, amma ta fi su kwari da kyan gani, da alamun tsafta a tattare da ita kuma da jin cewa tana sane da ita, har tana neman ta. Bayyanar dangin Yalwati mahaifiyarta shi ya shafe firgicin da rudanin da zuciyarta ta shiga na auren mutumin da rabonta da shi shekaru goma cif, wadanda tsayinsu da shudewar su basu mantar da ita waye shi ba; Dan Mami! Wanda ta fi so fiye da kowa da komai a rayuwarta (YA HEEMU). “An gudu ba a tsira ba, an rabu da Bukar an haifi Habu!!!”. In ji masu iya magana. Har gara-gara ma Khalipha a kan son da Mami ke yiwa HEEMU da burirrikan da ta ci a kanshi. Wadannan tunane-tunane basu bar zuciyar Rahane ta huta ba a wannan dare, basu bar idanuwanta sun runtsa ba. Jin al’amarin take kamar almara. Wane irin aure ne irin haka? An taba yin aure irin nata a duniya kuwa? Babu shiri? Babu zato babu tsammani? Babu so babu kauna daga kowanne bangare? Babu shakuwa babu alaqa? HIMU? I.M? IBRAHEEM MANSUR? Wai shine mijinta? Ya ALLAH! Idan mafarki nake kayi gaggawar farkar dani kafin na zama zautacciya!!! Rayhanah ta fada a fili tana mai kaiwa da komowa kamar mai yin safah da marwah a dakin data ke ciki. Wane irin matsayi Baba Dacta ya bata ne a zuciyarsa haka? Me take das hi day a bata wannnan matsayin? Ba ta cancance shi ba, matsayinta bai kai nan ba! Hadin bai yi matching ba sam..... Ibrahim ya fi karfin ta!! Sau dubu gara Khalipha. Shi wannan ko babu komai akwai shakuwa da fahimtar juna akwai kuma shimfidar fuska idan babu ta tabarma ba wannan zundumemen dan bokon ba. Ta daga hannunta na dama a hankali ta kalli warawaran farin zinare da Haj. Karima ta zura mata, wadanda Hakimi ya ce Sadakinta kenan. Sai walainiya suke a hannunta cikin rangwamen hasken lantarkin dake dakin da take kwance (bedroom din Haj. Karima). Wadanda karbarsu da ta yi sun tabbatar da cewa ta zama matar IBRHEEM, ba Khalipha ba. Mafarke-mafarken da ta rinka yi a Informatics farkon kulluwar soyayyarsu da Khalipha a kan Ibraheem suka shiga dawo mata filla-filla, wadanda a yau ta fassarasu da cewa, Allah ne yake nuna mata Ibrahim shine uban ‘ya’yanta ba Khalipha ba. To ya za ta yi da son Yaya Khaliphan? A wannan sabon matsayin nata na matar kaninsa? Daddy na nufin ta haka rami ta binne soyayyar Khalipha wanda har zuwa yanzu zuciyarta ta ki yarda da cewa ya ki aurenta ne don yaudara, sai ko don wani muhimmin al’amari beyond his ability. Haka nan zuciyarta ta yi masa wannan uzurin duba da tsayin lokacin da Khalipha ya diba cikin soyayyarta tun tana kankanuwa, wannan ba yaudara ba ce. Laifinsa daya ya ki su magantu balle ta san daga ina matsalar take? Sai dai kaso tamanin cikin dari na zuciyarta ce mata yake “Daga Mami ne”. To in daga Mami ne ya ya akai ta amince ayi da wanda ta fi so ta fi ciwa buri fiye da Khalipha? Da ta ga wadannan lissafe-lissafe da saka da warwara da tunane-tunane na neman tarwatsa mata kwakwalwa da wargaza kwanyar kanta, ba kuma zasu samar mata da amsoshin data ke son sani ba, haka bazasu zamo solution ga halin da take ciki a yanzu ba, sai ta tattarasu duka ta mikawa Allah! Wahidun Qahharun!! Mai tsarawa bawa rayuwa ta inda bai zata ba. Minsharin Inna Juma ya dameta, wadda suke kwance tare a dakin anyi mata shimfida a kan kilishi da filo sai kwasar rabar A.C take tana kwararo minshari mai sauti. Kallonta Rahane ke yi cikin shudiyar fitilar barci dake kunne tana jin wani sanyi a zuciyarta. Kafin wata sabuwar fargabar ta zo ta lullube mata zuciya........ yaushe za su hadu da Ibrahim? Yaushe zai zo? Da wace fuska zai karbi al’amarin? Wace irin karba zai yiwa auren nasu? Maganar so ma ta san babu ita in aka yi la’akari da irin yanayin rayuwarshi wadda ta sha bambam da ta Khalipha ta kowanne bangare. Ita dai kam a yanzu zuciyarta neutral. Wato ba ta bayan kowanne bangare (neither tana son sa nor ba ta son sa). Lamarin zai kasance ne da fuskar da ya zo mata, da ita za ta karbe shi. Babu soyayya cikin zuciyarta kuma babu kiyayya, kai ita duk jinin Dr. Mansur ma abin so ne da girmamawa a gareta. Ba don komi ba sai don cewa, su suka rufa mata asiri a lokacin da ta bude ido ta tsinci kanta tare dasu, babu kowa nata. Ba ta taba kullatar Mami ba ko ta sawa ranta Mami ba ta sonta. Rikon shekara goma shag Dan da ba kai ka Haifa ba ba karamin sadaukarwa bane. Ta yarda da abin da Mami ke ikirari na cewa ba kinta take ba, asalinta ne da tsohuwar lalurar ta ya sanya bata isa ta hada zuri’a da ita ba. Ita ma kuma ta yarda da cewa asalin nata (idan aka hada da nasu) kaskantacce ne. Sannan lalurar ta abin gudu ce ko don tsoron genetic wato gado. Sai dai kuma Mami ta mantacewa ba’a yiwa Allah wayo itama bata gada ba iftila’I ne na Ubangiji. Hakan baya nufin suma ba mutane ne da Ubangiji ya halitta don baya son su ba,kowa da kaddarar rayuwarsa in one way or the other! Dukkanmu masu nakasu ne idan bata nan ba ta can. Maganar asali kuwa Ubangiji guda ne ya halicce mu yana kuma son bayinsa bakidaya. Ba don baya son su bane ya hana su ilimin, mulkin da arzikin, sai don cewa ko ‘yan yatsu bai yi mana su kai daya ba. There is always hierarchy...... a tsakanin bani-Adam. Abin da ta yarda da shi shine, “Inna akramakum indallahi atqakum”. Wato mafi girmanku a wajen Ubangiji shine wanda yafi tsoron sa. Don haka zamu iya cewa, a wannan daren baki dayansa, idanuwan Rahane basu runtsa ba. A kan kunnenta aka kira Asubahi, sai ta yi amfani da damar don gusarwa da kanta damuwar da ta gallabeta ta addabeta, ba kuma za ta amfanata da komai ba. Ta yo alwala ta fito ta tashi Inna Juma. Yayin da ta nabba’a a gaban mahaliccinta don nemawa zuciya, kwakwalwa da rayuwarta sauki a wajen Mai duka. Tana rokon sa ya cire mata firgici da faduwar gaban da take samun kanta a ciki, a duk lokacin da ta tuno ranar da zata yi arba da IBRAHEEM MANSUR TAKAI. Har yanzu tana tantama tana kuma shakkun kasancewar wai Ibraheem ne mijinta ba Khalipha ba. A hankali ta kai duba ga warawaran hannun ta masu kara tabbatar mata da hakan, ta hanyar fidda dan sauti kas-kas da walainiyar da sukeyi a duk kankanin motsin da ta yi. Abubuwan ban mamakin rayuwa yawa garesu, wasu ma basu zo ba tukunna….. wasu ba’a fara su bama RAYHANAAAAH!!! **** Washe gari ya kasance litinin, su Daddy tun jiya bayan daurin aure suka wuce Kano aka daura na Khalipha da Radhiyyah. Daddy shi ya biya sadaki da wara-waran zinare kamar yadda ya biya na Rayhanah. A take kuma gidan su amarya suka zarce da biki na tsere ma sa’a. Ita dai Mami har zuwa lokacin ta gaza nutsuwa da samun kwanciyar hankali, don har zuwa lokacin Daddy bai bude baki ya ce mata komai game da Rayhanah ba, bai tambayeta ina Rayhanah ba, bai gaya mata auren wa aka daura a Takai ba. Ba ta kara ganin Khalipha ba har zuwa lokacin, ya wuce Abuja ya mai da kansa kamar inji saboda aiki, ya ki yarda zuciyarsa ta kadaice ko kadan balle ta samu filin saka mishi damuwa, tashin hankalin jin cewa shi ba dan Baba Dacta bane ya shafe komi, wato ya fi karfin soyayyar Rayhanah wadda ya kira da sunan bygone issue. Sawun Giwa ya take na Rakumi kuma gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta………. Daddy ya gama masa komai tunda bai bar Rayhanah ta wulakanta ba, wanda shine babbar damuwarsa kuma babban abinda ke kara ingizashi cikin son ya aure ta ya tallafi rayuwarta bayan Kalmar SO, ya zaba mata miji na garari na likawa a goshi in ana likawa, wanda zurfin tunaninsa bai taba bashi kasancewar hakan ba. Damuwarsa daya, wace irin tarba Ibraheem zai yiwa Rahane ‘as a wife??? Yana yi mata fatan alheri. Shi yanzu haka ma shirin zuwa Jos yake wajen dangin Mami na can don ya fara bincike a kan al’amarin mahaifin nasa, ya dangana da Hurghada. Ya mance da wata aba can wai amarya Radhiyyah. Lafiya sumul Daddy ya tarbi Dr. Asma’u da fara’a da komai a sanda ya shigo gidan daga ofis ranar da ya dawo daga Takai, ta yi mishi barka da zuwa. Rungumeta ma yayi, ya ce, “Mami naaa.....” Ita ma ta ce, “Dacta naaah....” Tana loosing tie din wuyan shi. “Ya aka baro su Hakimi?” “Kowa lafiya”. Ya zagayeta da hannayenshi.kanshi cikin wuyanta yana sunsunar ta yake fadin; “Gashin ba saloon..... Mami na tsami ba wanka, kayan jikinta yau kwana uku ba ta canja su ba. Lebenta a bushe kyamas, kamar tayi sati bata sha ruwa ba! Allah ya isa........ tsakanina da duk mai canza min Asma’u na zuwa Ta-ma’ule!”. Ya dan ture ta ta yi taga-taga ta fada kan gado ya wuce toilet ya hada ruwa mai zafi ya zuba dettol da sabulun ASDA, ya dauko Mami ya wanketa tas, ya wanke gashinta da kumfar shampoo (pert-plus) ya nado ta cikin shawul ya jona dryer yana busar da gashin kanta. Ya dauko doguwar riga ruwan madara mai kyau dinkin Dammam ya sanya mata, ya juyota ya rungumeta. Runguma mai karfi da tsanani. Kamar zai tsaga kirjinsa ya sanyata. Mami don tausayin Dacta, sai tasa kuka. Kyaleta ya yi ta yi kukanta mai isarta bai katse ta ba, tana rungume a kirjinsa. “Ni kaina na rasa me ke damuna Dacta, na zama rikitacciya, abu kadan sai ya ruda ni, ya tsorata ni. Kaina na gaya min abubuwa wadanda na kasa gane musu........” Hannu ya kai ya toshe mata baki. “Ba komai bane, sakaci da ibada ne, da rashin tsai da salloli biyar a kan lokaci. Mami ki nutsu ki koma Asma’unki, you are not my precious Asma’u, Dacta guda da warin hammata???” Ya fada yana dariya yana fesa mata ‘Carolina Herrera’ sai ta rungume shi kam’kam, da haka al’amarin ya sauya. Ko bayan da suka koma cikin nutsuwarsu suka yi wanka suka yi sallah bai gaya mata ya aurawa Ibrahim Rayhanah ba. Sai batun dauko amaryar Khalipha. Gidan da Daddy ya ginawa Ibrahim da Khalipha na nan a (Farm Center). European Flat zallah, mai dakin barci uku, falo, katon kitchen da bandaki, can ya ce a kai kayan Radhiyyah, har da Mami a ‘yan jere da Dacta Haliman kanta. Naira kam ta sha kuka, aure na GIRMA da KASAITA irin wanda Mami ke so. Washe gari aka kai amarya dakinta, sai dai babu ango babu alamarshi. Wayoyinsa duk a kulle, basu sani ba shi a lokacin kwanansa biyu a Hurghada tare da Uncle Yohan Yayan Mami suna binciken dangin Mukhlis Imran a birnin Hurghada. Haka suka hakura suka baro amaryar ita kadai da ‘yan aiki a gidanta ta ci gaba da jiran ango, a karbe shi da soyayya marar misali, da aka tanadar masa. **** A TAKAI A Takai, Rayhanah ta wayi gari a gidan Hakimi matsayin daya daga cikin surukan gidan, yadda Haj. Karima da Hakimi ke kula da tarairayarta basa yiwa ‘ya’yan da suka haifa su Nabilah. Ga wani girma na musamman da barorin gidan ke bata. Su Zinaru sun koma gidajensu. Juma kawai aka bar mata, Hakimi ya ce ta rufo gidanta kwata-kwata ta zauna da jikarta a duk inda Allah ya kaita zaman aure. Tunda bata da miji, ba Da, ba jika. Don dadi Rayhanah kuka ta saki ta rungume Inna Juma tana yiwa Hakimi godiya. Ya ce, “Babu komai Rayhanah, yadda zamu kula da ‘ya’yan cikinmu, haka muke kula da surukanmu. A kalla kina bukatar budar ido ki ga jininki ko yaushe a kusa dake. Allah ya ji kan Malam Rashidu, na zauna da shi cikin amana don haka Rayhanah ke amanar Allah ce a hannunmu”. Tunda aka daura auren nan Nabilah ke ta kuka, ta hana uwarta sakat da jama’ar gidan baki daya. Kowa na da masaniyar cewa ta zauna ta kai shekaru talatin a gida ne cikin jiran dawowar Ya Himu, ta kori duk masoyanta amma ba a duba hakan ba, mahaifinta da mahaifiyarta sune ja-gaba wajen aurawa Ibraheem din da ta kallafawa rai wata bare ‘yar talakawa ba ita ba. Duk mai tausayi dole ya tausayawa Nabilah a bisa yadda ta mai da kanta kamar matar mamaci, balle kuma iyayen da suka haifeta. Haj. Karima mutum ce mai tsananin kawaici da zuciyar mai da nata ba nata bane, da kuma biyayya ga mijinta. Tabbas tana tausayin Nabilah amma ita a ganinta gara haka, gara da hakan ta faru da Nabilah ta yi auren da ba za a ga kimar ta ba, tunda ita ce mai son, wanda ake son bai san tana yi ba. Tabbas kulluwar aure a tsakaninsu zai iya kawo babbar baraka cikin zumuncin iyayensu da suka budi ido suka gansu tare ba a taba jin kansu ba (Dr. Mansur da Hakimin Takai Abdulkadir Balarabe Sardauna). Ta kuma yi la’akari da cewa, Dr. Mansur ya san da zaman Nabilah, amma ya kawo baren ya ce ita ya zabawa dansa. To nacin na mene ne? Dama ita ta maida kanta tsohuwa, amma manema wane iri ne Nabilah bata gani ba? ‘Yan boko, attajirai, masarauta babu irin wadanda basu nemi auren ta ba amma ta ki. Yanzu da hakan ta faru a ganin Haj. Karima, sai ta nutsu, ta san tudun dafawa (in fa har tana da hankali). Ibrahim ba shine autan maza ba, ta yiwa kanta suttura kamar yadda Hibbah ta yi, gata can da ‘ya’yanta dugwi-dugwi dasu har uku. Soyayya daban, aure daban. Aure ana yin shi ne don Ibada, ba don son zuciya ba, soyayya ba ita ce aure ba. Sai ayi soyayya kamar a cinye juna shekaru aru-aru, amma idan Allah ya kawo aure, sai a yi shi cikin kwana uku. Masana a ilmin halayyar dan Adam sunyi ‘analysis’ a kan soyayya sun gano cewa, majority (akasari) long-dating (doguwar soyayya) ba a yin nasarar yin aure da ita, iska take bi, kamar ba a yi ta ba. Sai ayi aure ba a san juna ba kuma a zauna lafiya, a hankali sai so ya shiga. Shi wannan son ba irin na soyayyar iska bane, so ne na halitta wanda gamayyar jiki (physical relationship) ke haifar da shi. Yana da karfin da soyayya bata da shi, yana da tasirin da soyayya bata da shi, yana da tubalin da dan Adam bai iya hako tushensa wanda shine tsakanin Adamu da Hauwa’u, sune kuma suka haifemu, Allah ne ke sanya shi ba long-dating ba. Don haka ita Haj. Karima addu’a take yiwa autarta Allah ya yi mata zabin miji mafi alheri, wanda zai so ta fiye da yadda take son shi, amma ba bahaguwar soyayyar da take yiwa Ibraheem ba. Gara ka auri wanda ke sonka a kan ka auri wanda kake so!!! **** [12/24/2019, 21:48] Takori: Mukhlis Abu-Arab, shi ya musuluntar da ita a Jos, ba da sanin yayanta Yohan ba, wanda yake rike da ita a lokacin bayan mutuwar iyayensu. Mukhlis abokin cinikin Yohan ne, yana kawo kaya daga Egypt su Yohan na saye su zuba a shagunansu a babbar kasuwar Jos. Galibi gayan yara ne (Children wears and accessories) a lokacin duniya na kwance, kasuwanci yanada albarka. Sai Allah ya hada Yohan da Mukhlis duk da bambancin addini sakamakon son da yake yiwa tilon kanwarshi. Shi Yohan bai taba haihuwa ba da matarshi Marye, shi yasa yake son kanwarshi Anita kamar shi ya haifeta, gata da hazaka a makaranta, ita ma Marye tana son Anita saboda yarinya ce kyakkyawa mai shiga rai. Har yau Yohan bai musulunta ba, sai dai ya bar Anita (Asma’u) ta yi addinin da ta zaba shi kam banda shi. Kuma fa Hausawa ne, Hausa rangadadau a bakinsu kamar jakan Kano, amma basu yarda da addini ba, Neither Islam nor Christianity, Budduism, Hinduism, Jainism, Sikhism Paganism, Rastafari, Taosim ko kowanne ma. Ta wannan kasuwancin Mukhlis da Yohan suka yi kudi na ban mamaki. Mukhlis ya sayi gida a Jos, kawai don Yohan ya yarda ya aura masa Anita. Suka ci gaba da kasuwancinsu Anita na girma. Mukhlis ya sayi kadarori da yawa a Jos don a nan yake son kafa tubalin iyalinsa. A lokacin kasar Egypt na fama da matsin durkushewar tattalin arziki kamar Sudan. Larabawan Egypt da yawa sun warwatsu a duniya don neman halalinsu. Garin Hurghada a can matsin yafi yawa. A Larabce ana kiran Hurghada da El-Ghardaqah). Da yawa sun shigo cikin Cairo suna leburanci masu ilimi sun tsallaka kasashe irin Saudiyyah, Dubai, Bahrain, Kuwait, Taiwan, Dammam Qatar da sauransu. Wasu sunyo Africa irin su Mukhlis kenan. Duk dimbin iliminsa a kan Geography ya fi ganewa kasuwanci, kuma Allah ya sanya mishi albarka a ciki. Har ya soma tsallakawa kasashen da suka ci gaba yana kawo kayan daga can, musamman Saudiyyah, akwai wani shago a Madina wai shi Majma’al Qimmah da ya shahara wajen kayan yara, Mukhlis na daya daga cikin manyan dilolinsu. Sanda Anita ta shiga aji shida na sakandire shekarunta goma sha biyar, sai tsahon kafa kawai. A lokacin ne ya nemi Yohan da bukatarsa na neman iri a wajensa. A lokacin shi Yohan yana shirye-shiryen komawa kasar Ireland shi da Marye, inda harkokinsa suka fi yawa. Shi abin ma dariya ya bashi, wai Mukhlis ya yiwa Anita tsufa duk da bai taba aure ba. Sai dai shi kansa ya san bai isa ya hana Mukhlis Anita ba, ba don su basu da addini ba su, sai don shakuwar da ke tsakaninsu ta tsayin shekaru masu yawa. Tun Anita na ‘yar shekara biyar Mukhlis yake kula da ita da daukar nauyoyin rayuwarta. Da dora ta a kan hanyar tarbiyya kamar diyar Musulmi. Ya dora Asma’u a kan turbar yin shigar da ba ta fidda tsaraici ba, sun sha yin sallah shi da ita a boye. Haka ya taka rawa wajen kara mata karfin gwiwa a kan ilimin zamani. Har abada Asma’u ba za ta manta da Mukhlis ba, har abada hoton wannan ranar ba zai taba gushewa daga zuciyarta ba. Wato ranar da Mukhlis ya danka sadakinta a hannun Yayanta Yohan, ‘yan’uwa da abokan arziki suka shaida. Bai kuma taba ta a ranar ba sai da ya lakana mata LA’ILAHA ILALLAHU, MUHAMMADUR-RASULULLAHI a bisa ra’ayi da yardarta. Don zuwa lokacin Anita ta yarda su dabbobi ne kawai sakamakon cakudo da musulmi a makarantu da take yi da kuma tarayyarta da Mukhlis, tana ganin yadda yake tafiyar da ibadar addininshi yana burgeta, su haka nan suke kara zube, kamar katakwaye da duwatsu. Babu direction. Mukhlis shi ya sanya mata suna Asma’u, sunan mahaifiyarsa bayan yin shahadarta. Wata da watanni Mukhlis na koyar da Asma’u hukunce-hukuncen addinin gaskiya. A karatun Alkur’ani da yake koya mata sun zo izfi ashirin ya kuma dauketa ya sanya a Islamiyya, kasancewar shi ba mazauni ba. Sai da ya tabbatar ta ilmantu ta zama cikakkiyar Musulma sannan ya fara mu’amalar aure da ita. Rayuwar auren Asma’u da Mukhlis rayuwa ce mai dadi amma takaitacciya. A lokacin Yohan da Marye suna Ireland sun tafi sun barta da mijinta, wanda ke tattara komai nasa a Nigeria cikin nutsuwa domin ya koma gida tare da matarsa. Allah ya aiko da mummunan hatsarin jirgin ‘Egypt Air’ wanda ya taso daga Cairo zuwa Nigeria har da Mukhlis a ciki. Asma’u dai sakamakon wannan labari sai nakuda ta tashi, ciki wata takwas sai fedeta aka yi don ta kasa haihuwa. Aka fidda yaro namiji mai kama da ita, amma kalar mahaifinsa. Bayan takaba da zuwan dangin Mukhlis suka sai da duk wata kadara tasa suka auna suka yi gaba, sun ki sauraren kowa a kan matar da Dan. A lokacin Yohan na Ireland kuma babu hanyoyin sadarwa irin na yanzu. Asma’u gidan Yohan ta koma ita kadai ta ci gaba da rainon yaronta wanda take yiwa wani irin masifaffen so kamar yadda take son Mukhlis Abu-Arab, tana amfani da ajiyarta ta banki da Mukhlis ke zuba mata duk wata tun aurensu da sunan asusun ajiyar ko-ta-kwana. Yau da gobe ba ta bar komai ba, kudin banki suka kare. Ko kudin da za a saiwa yaro madara babu, saboda tana da karancin ruwan nono. Haka nan ta yi ta fadi-tashi har da wanke-wanke da shara gidan masu akwai don kawai ta samu abin da za ta sanyawa Abdullahi a baki. Ba ta damu da kanta ba, she only want to save his life..... Asma’u har kosai da fanke ta sayar, a kofar gidansu take soyawa safe da yamma da kuruciyarta da komai, duk saboda Khalipha. Khalipha na da shekara daya Allah ya jefo Yohan gida. Kuka na duniya Yohan ya yi shi da ganin yadda tilon kanwarsa wanke-hannu ka taba ta koma rufe hannunka sannan ka taba. Amma fa yaronta bul-bul very energetic, diety. Ita dai ce cikin tsummokara, amma danta tsaf cikin napkin mai tsafta da riga mai kyau har kamshi yake. Rasuwar Mukhlis da abin da danginsa suka yiwa Asma’u da danta ya taba zuciyar Yohan. Abin da ya kai shi ga yin alkawarin har Khalipha ya mutu ba zai kai musu shi ba, zai rike. A satin suka daga Dublin. Abin da Yohan ya fara yi domin inganta rayuwar Asma’u da danta shine samar mata gurbi a Jami’ar Trinity, ta fara karatun medicine cikin himma. Ba ta yi nisa da karatu ba Khalipha ya soma wani rashin lafiya, sai hankalinta ya rabu biyu, don ma Marye tana taimaka mata da hidimarsa. Zama a Turai bai sa Asma’u ta canza daga addinin da ta karba da zuciya daya ba, ba ta son barin danta hannun Marye don ta san ba ta da tsarki. Ta fi so ta kula da danta da kanta, ko ina zata tura shi take cikin keken zaman yara, sai dai dole lokutan daukar darasi take barinsa da Marye. Likitoci sun sha bincike a kan dalilin da ya hana yaro Khalipha barci kullum cikin dare sai kuka, inda suka gano cewa ciwon hanta ne (Hypertitis B). Allah ne ya yi kawai Khalipha rayayye ne ba maganin asibiti da kwakule-kwakulen likitoci ba. Asma’u ta ji jiki ta sha wahala da danta Khalipha, Yohan da Marye sun taimaka. Ta yi ta yi su Musulunta sun ki. Rashin lafiyar Khalipha ne yasa ta dauki bangaren likitancin yara paedatric don kawai ta kula da lafiyar Khaliphanta. Haduwarta da Mansur Balarabe Sardauna, ta samo asali ne a matsayinsa na daya daga cikin malamansu, a lokacin shi ya yi graduating yana aikin da ya zamewa duk wani foreigner dole bayan kammala karatu kamin ya koma kasarsu. Ya lura in ana darasi tana yawan fita ta je ta shayar da baby a hannun wata dattijiyar Balarabiya da take aikin leburanci a Jami’ar, take rike mata dan saboda Allah, don ta lura Asma’u ce kadai Musulma a bangaren da take kula da shi. Amma abinda yake daukar hankalin Mansur da Khalisah (dattijuwar), basu taba ganin uban dan ba, ga shi Balarabe ziryan ita kuma da ganinta ka ga ‘yar Nigeria. A al’ada irin ta Bature, mace mai aure kusan koyaushe tare take da mijinta duk inda za su je, balle idan akwai karamin yaro kusan uban ne ke da wannan alhaki na kula da yaron a lokacin zirga-zirga, shi zai tura shi zai dauka, basa barin matansu su sha wahala. Hazakarta a karatu na ba shi mamaki yadda take yin zarra da manyan maki (marks) a cikin Turawa. Ya damu da al’amarin ta, gata yarinya karama da ko ashirin ba ta rufa ba. Idan yana lacca kusan rabin hankalinsa a kanta yake, idan tambaya ce ita yake jefawa, ba ta yin kasa a gwiwa wajen farke masa zare da abawa. Tafi-tafi Mansur ya kasa sukuni da tunanin Asma’u da begenta dare da rana. Uncle Yohan shi yake daukar nauyin karatun Asma’u, ba yadda bai yi ba don ya samo mata Nanny din da za ta dinga kula mata da Khalipha a gida ta je ta dawo tunda ba ta son shi a hannun Marye. Asma’u ta ki. Ya ce, zai dinga kai shi gidan raino na Turawa shima ta ki. Don haka ya yi fushi ya rabu da ita kamar akan ta aka soma haihuwa. Ga shi Allah ya jarrabi zuciyarsa da son Khalipha kasancewar shi Allah bai ba shi haihuwa ba. Daga shi har Marye kyamarsu take, ko abincinsu ba kowanne take ci ba. Don a Jos Marye murde kan kaza take da ranta ta cizge ta cillar ta fige ta dafa. Ire-iren wadannan yasa Asma’u ta gwammace Yohan ya ba ta kudi ta sayi ‘halaal’ ta dafa da kanta ko ta yi take away daga makaranta a wajen larabawa musulmi ko Pakistani mazauna turai. Asma’u bata takurawa Yohan da cewa lallai sai ya Musulunta ba, don ta lura tana tufka ne Marye na warware mata, ko yaso ya saduda zigar Marye ke hana shi. Tana nuna masa cewa addinin Musulunci addini ne na takurawa kawai, sannan Musulmin da ya zama kasurgumin Musulmi shine yake zama terrorist (dan ta-adda). To Allah shi ke hukunta al’amura yadda yaso, idan ya so bawanshi da shiriya ruwa da iska basu isa su hana ba. Marye ta yi mutuwar wulakanci a Dublin inda wani ginin bene ya rubza da ita da jama’a masu dimbin yawa, ko gawarta sai part-part aka tattara, sauran namanta ya zama na ungulu da tsuntsaye. Asma’u ta ja dan’uwanta a jiki, dare da rana, yini da safiya tana kwadaita masa dadin addini musamman na Islam. Ta kan ce, “Shi Musulunci haske ne kuma guidance ne, wanda zai sada dan Adam ga nutsuwa da kwanciyar hankali, hanya ce kawai dake nuna maka yadda za ka rayu a kan tafarki madaidaici. Tsani ne mai mika mutum kusa da Ubangijinsa yaje ya iske sakamakon abin da ya shuka a rayuwarsa ta duniya. Ba abin da addinin musulunci bai koya mana ba, hatta shiga bandaki, tsarki, wanka, cin abinci duk Islam ya kawo su a kan hanya sahihiya (to the heaven)” Haka dai, yau da gobe har Allah ya taimaketa ta yi galaba a kan Yohan, ta kai shi wajen Limamai suka musuluntar da shi ya mai da sunanshi Yahya. Hakan bai hana har yau jama’ar da suka san shi kiranshi da Yohan ba. Yohan (Yahya) ya shiga Islam ne da zuciya daya. A wannan lokacin Yohan ya yi karfi na ban mamaki cikin kasuwancin da yake yi tsakanin Ireland da Nigeria. Ta hanyar Asma’u ya auri wata mutuniyar Somali zaunannun Dublin wai ita Aasiya. Ba ta taba yin aure ba amma ta manyanta domin cikakkiyar likitar mata ce. Shekara ba ta kai ga fita ba Dr. Aasiya ta haihu da namiji. Ashe matsalar daga Marye ne ita din ta sani likitoci sun gaya mata, wannan ne yasa ta san duk hanyar da ta bi ta hana Yohan zuwa asibiti a bincike su sai karyar bari (miscarriage) take masa. Har lokacin Asma’u na jinyar Khalipha dake fama da hypertitis B. Zuwan Aasiya gidansu ya kawo sauki mai yawa cikin rayuwarta duk da ita ma Aasiyar ma’aikaciya ce a babban asibitin kasa amma tana taimaka mata sosai wajen rainon Khalipha har Allah ya raya shi, ta kai shi wata Islamic school a London (Al-Muntada Islamic Pri. Sch.) boarding, ita kuma ta koma Dublin. Duka cikin aljihun Uncle Yohan. A shekarar Dr. Aasiya ta kara haihuwar diya mace, a wannan lokacin shekarun da Mansur zai yi yana aikin wucin-gadi da jami’ar Trinity sun kusa cika, zuwa lokacin ya yi duk binciken da zai iya a kan Asma’u, ya tadda komai, wato ba ta da aure, uban dan ya rasu. A matsayinshi na Bahaushe Ba-Kano kuma wanda ya fito daga jinin sarautar Takai abin ya zo a karkace, saurayi da auren bazawara mai da. Duk da addininmu bai hana ba, karewa ma hakan sunnah ce, kuma ya san yayansa Abdulkadir ba zai taba ki ba. Shi a kaunar da yakewa Asma’u ma, ko kantin kwari ta haife zai rike mata, kuma in ta amince zai aureta. Kai tsaye bai doshi Asma’u ba, domin ba fuska, kullum suturce take cikin yalwatacciyar suttura da karamin hijabi iya kafadunta. Sai ya bi ta hanyar da kowacce UWA ba za ta iya kaucewa ba. Wato yaje ya yi kawance da dattijuwar lebura Khalisa, yake tayata hidimar Khalipha kafin Mamanshi ta kai shi makarantar kwana. In ba shi da lacca wajen Khalipha da Khalisa yake lalacewa. Siyo wannan, siyo wancan duk na Khalipha. Har Asma’u ta fara mamaki saboda ta san ko shi wane ne a Trinity da tarin iliminsa. A hankali suka soma gaisawa, tunda an ce mai Da wawa. Wani irin so Mansur kewa Khalipha wanda ko shi ya haife shi sai haka, ba kuma don komi ba sai don kamanninsa da mahaifiyarsa. So na hakika shine ka so uwa tare da dan ta. Sai ga Asma’u na gayar da Mansur Takai kullum, har in ba ta ganshi ba ta hau tambayar Khalisa yau Baban Khalipha bai zo bane? Khalisa kan ce, ya zo ya sumbace shi ya ba shi chaculates ya tafi. Sai Asma’u ta yi murmushi har ta kai Khalipha London a bisa shawarar Mansur a haka suke. Mansur shi ya lalubo mata makarantar kasancewar ya zauna England kafin Ireland inda ya yi karatun share fagen shiga jami’a. Ya fita sanin UK da Islamic Schools masu yawa dake cikin ta. Sai kuma aka koma kawance har cin abinci take gayyatarsa gidansu wajen Uncle da Dr. Aasiya. Ta kai ta kawo duk wani wanda ya rabi Asma’u, to ya saba da Mansur mai yi mata son kan-uwa-da-wabi, wato sonta yake tare da dukkan ahalinta da duk wanda take tare da shi. Tare suke zuwa London dubo Khalipha duk wata. Lokacin komawar Mansur gida ya cika, amma ya kara neman visar aiki ya shantake ya ki tafiya saboda Asma’u. Su kuwa gwamnatin Dublin ai gaba ta kai su don dama irin Mansur din suke so su suke gudunsu domin kishin kasa (Patriotism). Irin na ‘yan bokon nijeriyar jiya ba na yau ba. Sai suka shiga jika shi da kudi, gida cikin gidajen malaman Jami’ar Trinity da Insurance, accommodation and allowances. Da Hakimi ya bi ba’asin fasa dawowar tasa bai boye masa ba, “He cannot live without Asma’uuuuu!!!” “Wace ce ita?” Hakimi ya tambaya. Bai boye komai ba ya warware masa zare da abawa. Satin bai cinye ba, sai ga Hakimi Abdulkadir Balarabe Sardauna da mai dakinsa Kareema a Dublin. Suka karbi auren Asma’u da amincewarta hannun Yohan, suka danganata da dakin mijinta da alkawarin suma din su koma gida. Suka yi musu alkawarin hakan, wato da zarar ita Asma’un ta kare Khalipha ya gama primary. Mansur da Asma’u cinye junansu ne kawai basu yi ba, saboda so da kauna, a shekararsu ta biyu da aure ne ta haifi IBRAHEEM. Ba ta kara haihuwa ba, ba kuma dalilin tsarin iyali ba, Allah ne bai bata ba, don in ta Asma’u da Mansur ne, duk shekara su haife, suna da halin da za su kula da abinsu, kuma suna so, kamar su hadiye su. Sanda Khalipha ya gama primary, Ibraheem na primary 3 a Al-Falah Islamic Children School in London. Asma’u ta karbi kwalinta suka tattaro suka dawo gida Nigeria da ‘ya’yansu biyu maza, baki da fari duk kyawawa, kowanne da irin kyan shi mai daukar hankali. Tun kan su zauna sosai su huta federal ta karbesu aka cillasu asibitin koyarwa na UNILAG Dr. Mansur na aiki yana kuma koyar da medical student. Basu kara haihuwa ba har aka mai dasu Ibadan Teaching Hospital duka tare suke aikin shi da Asma’u. A can ne Allah ya basu Jawahir, aka mai dasu Jos suka haifi Abida a can bayan shekaru uku. Daga nan haihuwa ta kara dauke mata dif! Har suka dawo Kano, lokacin Gwamna Kabiru Gaya, shi ya dauki kujerar kwamishinan lafiya ya baiwa Dr. Mansur a dalilin wani aiki na koyarwar sa-kai (voluntary) da ya yiwa jami’ar Abdullahi Bayero, wanda shi gwamnan ya neme shi da ya yi. Wannan ne mafarin zamansu a gidan da suke ciki yanzu a Lamido Crescent, Gwamnatin ce ta bashi ya zauna har ya yi kokarin da ya mallake shi bayan barinsu Gwamnati da komawarsu bakin aiki. A nan ne kuma ta haifi auta Azizah. Shima Uncle Yohan ya baro Dublin tuni da iyalinsa suna zaune a Jos. Shakuwar dake tsakanin Khalipha da Uncle Yohan ta wuce tunani, don haka yau abin da ta gani ya tabbatar mata da sanya hannun Yohan Khalipha ya nemo dangin ubansa har ya auro jininsa ba da izininta ba. Ta riga ta yi fushi mai tsanani da dangin Mukhlis shi yasa ko da wasa ba ta taba gaya masa cewa ba Dacta Mansur ne ya haife shi ba kada ya ce zai je ya nemo su. Da ta kawo nan a tunanin da take yi a tsaye a bakin kofa sai hawaye suka tsinke mata. Yohan da Baba Dacta basu kyauta mata ba, ta fassara hakan da cewa Baba Dacta ya yi hakan ne don ya rama abinda ta yi masa na hana Khalipha auren gallafirar ‘yarsa, me ta yi da zafi, da ta cancanci hakan???! **** MURFIN LITTAFI NA BIYU! Tana shirin juyawa ta fita ta ji hannayensu sun rungumeta, sun hanata fitar. Khalipha da Mimtaaz, ke hawayen suma, suna rokonta ta shigo gidansu, ta sa musu albarka, in sun bata mata ne abisa rashin sani ta yafe musu. Domin dukkansu sun tsorata da dogon tunanin da ta afka a tsaye a bakin kofa. Mimtaaz hannun Radhiyyah ta kamo suka shigo dasu cikin falon.. Ita dai Radhiyyah jikinta ya yi sanyi, musamman da Mimtaz ta soma hidimar kawo wannan kawo wancan tana lallaminsu su ci. Tambayar kanta take mececedin Khalipha wannan? Khalipha bedroom ya shiga ya sako cikakkiyar suttura a jikinshi ya dawo. A baki yake baiwa Mami abinci. Mimtaz na hidimar zuzzubawa. Sai ta ji tausayinsu dukkansu su biyun ya kamata. Hawaye sosai take yi da ta tuna Mukhlis haka yake wannan hidimar da ita wajen cin abinci yadda Mimtaaz ke yi yanzu. Kawai sai ta rungume Khalipha tana bashi hakuri tana yiwa Mukhlis addu’a. Sai ya jawo Mimtaaz ya kara mata ita cikin hannuwanta. Sun dau lokaci a hakan kafin Mami ta ce, “Ga Radhiyyah, amma wallahi na daina shishshigi a al’amarin Ubangiji. Na baka zabi ka zauna da ita ko ka sahale mata in baka so tun iddah ba ta hau kanta ba. Babu ruwana, kana naka Allah na nashi, kuma nashin shine gaskiya”. Ta kai gefen mayafinta tana share ido. Tambayar kanta take tana mamaki wa ya nunawa Khalipha danginsa har suka yi masa aure? Ita kanta duk dadewarta a duniya in za’a kashe ta bata san hanyar Hurghadah ba. Ya ce, “Na sake ta Mami, Mimtaaz ‘yar uwata kuma kanwata ta isheni, Allah ya bata miji na gari, ba zan iya yin adalci ba.”. A daren Mami da Radhiyyah suka juyo Kano ko gidanta ba ta shiga ba, sai da ta kai Radhiyyah gaban iyayenta. Ta kawo takardar saki da Khalipha ya rubuta ta bayar. Babu tsoro babu shakka ta gayawa Dr. Halima aure ya kare, Khalipha baya so. Sai abin ya zama fadi-in-fada a tsakaninsu, aka soma maidawa juna magana ana tonawa juna asiri. Mami ta ce, “Ai na gane kokari kike ki tarwatsa min gida, ki aure min miji, ko kin dauka ban san kuna neman Dacta har ofishinsa ba tunda naki mijin hoto ne baya amfanuwa, in takurawa Da na ya tsane ni, in kuntata masa ke ki farantawa taki? Ko kin dauka ban san asirin da kike jifana da shi ba? Ba Rayhanah ba, ko uwarta ce yaje ya auro min zan zauna lafiya da ita, so kike ki fiddani daga addinina kina tura min shaidanu cikin kaina, to ta Allah ba taki ba. Ga ‘yarki nan Umma ta gai da Assha, gobe kuje ku kwashe tarkacenku Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi, amin”. Ta mike ta nufi kofa Dr. Halima na gyada kai tana fadin “Za ki gani, in dai Dr. Mansur ne da kike takama da shi haka za ki barshi wutsiya a zage. Tsohuwar arniya tubabba”. Mami ta ce, a sanda ta murda kofar falon zata fita batareda ta juyo ba “Na fi wadanda aka haifa cikin Musuluncin, tunda bana zina balle kwartanci”. Da haka ta fice. Mu Hadu a RAYUWAR RAYHANAH 3&4.