[12/24/2019, 21:48] Takori: RAYUWAR RAYHANAH! 3 Ayadda Mami ta shigo gidan, ya tabbatarwa Jawahir dake zaune tana cin abinci Mami bata cikin nutsuwa. Bata tsaya anan ba ta wuce bedroom dinta ta maida kofa ta rufe ko magana bata yiwa Jawahir din ba, wadda itama bakinta ke cike da tambayoyi fal, data ke so ta yiwa Mamin. Amman ganin babu fuskar da zata yi tambayar yasa ta like bakinta tayi shiru. Tambayoyin data ke so ta yiwa Mamin akan Rayha da Khalipha ne. Ina Yaya Khalipha ya shiga wata da watanni ta daina ganinsa? Har zuwa wannan lokacin da su Jawahir ke a matakin jami’a iyayensu basu basu iznin rike waya ba, ina kuma Rayha ta shiga? Ta wayi gari ta nemeta sama da kasa ta rasa ta? Ko kadan zuciyarta bata kawo mata wani abu game da rashin ganin Rayhanah a ranar data wayi gari bata ganta ba, ba, tayi zaton sun je Takai ne da Daddy don shi dama sammako yakeyi in zashi Takai don ya dawo akan lokaci. To amma bayan wasu yan kwanaki ta koma ganin Daddy cikin gidan bai ce mata komai game da tafiyar Rahane ba. Wasa-wasa satittika da watanni suka shiga wucewa babu Rahane a gidan. Don haka a yammacin wata ranar Lahadi Daddy yana gida sai ta tambaye shi, “ni Daddy ina Rayhanah ne?” Murmushi yayi, yace “ki kwantar da hankalinki Jawahir, nayi mata AURE!” Idanun Jawahir duka a waje kamar sa fado abin dariya, cikin kidima da gigicewa. Haka Daddy ya fice ya barta yana dariyar razanarta. Kwanaki biyu Mami tayi bata je ofis ba, tana fama da ciwon kan barin kai guda (migraine). Wannan ranar tana kwance a gadonta ta mika hannu ta lalubo wayarta ta kira Ibrahim. Don ta sanar dashi al’amuran da suka cakude mata, suke kuma gallabar rayuwarta ko ta samu sanyin zuciya duk da tasan bazai yi mata maganinsu ba, amma akalla zata ji sauki daga nauyin da zuciyarta tayi, da azabtar da ruhinta ke yi. Mace ce ta daga wayar, wadda bata tantama baturiya ce, ta sanar da ita cewa Dr. Ibrahim ya daina amfani da wannan layin. Ta nemeta data bata wadda yake amfani da ita tace babu waya hannunsa baya rike waya. Takaici ya ishi Mami tace “dauki taki wayar ki kai masa har insa yake inyi magana dashi, ni mahaifiyarsa ce”. Baturiya tace “ya shiga tiyata bazai amsa waya ba yanzu sai bayan awanni goma sha biyu”. ****** (Shekaru goma sha biyu a baya) Abinda Mamin bata sani ba shine, matsayin Dr. Ibraheem a yanzu ya zarce tunaninta a nephrology department din overall asibitin Chicago (ILLINOIS teaching hospital). Kai tsaye baka isa kayi magana dashi ba batareda appointment ba, a tun wani aiki da yayiwa shugaban kasar Brunei (sultan of Brunei) na dashen koda, wanda ya bashi damar zama consultant na nephrology department a babban asibitin ‘Illinois’ bayan wani kwas daya halarta na shekara guda a yankin‘Ohio’. Matashin likitan mai shekaru talatin da uku, mai wasu irin unique akidu da dabi’u da suka hadu suka maida shi wani mutum na daban da sauran al’ummar da yake tare da su. Suka kuma zamo silar mataki iri-iri na cigaba da yake takawa a rayuwarsa at a very young age. Manyan kasashen duniya ke daukar shi haya yayi musu aiki akan fanninsa, a kuma yi nasara ta ban mamaki. Zuwa wannan lokacin, I.M Takai, wato IBRHEEM MANSUR TAKAI, ya gama taka duk wani matsayi da Dan Adam din duk da yasan ciwon kansa ke burin samu. Matsayin da ko iyayen da suka haifeshi basu sani ba, basu zata ba basu san ya taka ba, basu kuma tsammana ba ko a mafarkinsu, kuma bai tsaya neman gaya musu ba, don ba halinsa bane yawan magana ko fadar halin da yake ciki ko abinda yake ciki ga kowa, bayan zuciyarsa, akan wanda aka tambayeshi ma balle wanda ba’a tambayeshi ba, sai ko wanda idanunsa suka gane masa, tunda bashi da halin rufe masa idon. Yaushe ma ya rike wayar bare ayi doguwar magana da shi? Shekaru uku da suka wuce Mamin ta je Chicago, tayi kwanaki bakwai tare da shi cikin gidansa dake cikin jerin gidajen malaman jami’ar ta Chicago, bayannan Baba Dacta yaje amma bai jima ba alokacin yana lecturing da part time job da asibitin lllinois, abinda suka sani kenan. To bayan dawowarsu ne al’amuran Ibraheem Takai suka ci gaba da bunkasa. Manyan kasashen duniya dai-dai ne bai jefa kafarsa ba ya yi private aiki dasu ba. Musamman Ohio, Columbia, Bruce da Brunei.To kamar yadda yake ga kowanne lafiyayyen dan Adam, kaddara da nauyin aljihu kan canza da yawa daga halayen dan Adam, duk irin tarbiyya da tsantsenin iyayen da mutum ya tashi a ciki kuwa, Ibraheem is not exempted. Da fari, wahalar karatu da kujuba-kujubarsa basu sa Ibraheem waiwaye ga al’amarin mata ba, duk da yadda suke binsa kamar kaza da ‘ya’yanta. Ina ya ga lokacin yin wata mu’amala ta soyayya ko akasinta, karatu yake ka’in da na’in kamar bai da sauran wani buri a rayuwarsa sai shi. Amma da ya hattama karatun, ya samu nutsuwa da hutu, ya kuma soma jefa kafa (outside Chicago) don aiki da samun hutu, duk tsantsenin sa sai da wasu daga cikin tarbiyyar Uwa da Uba suka canza. As a Proffesional Medical Doctor, Ibraheem bai kurba giya, baya zukar sigari balle wani abu da zai gusar da hankalinsa ko ya sa shi maye. To amma ‘yan mata fa (barin rayuwar kowanne lafiyayyen da namiji), musamman wanda bai da aure kuma jikakke kamar Ibraheem, yaro matashi mai cike da koshin lafiya da tarin ilimi da duk wata alfarma ta rayuwa. Ya dade da fita daga gidajen malamai ya sayi nasa na kansa (American – mansion) a North-Eastern Chicago bayan wata kyautar bajinta daya samu daga (Sultan of Brunei) akan aikin dashen kodar da yayi masa ya samu lafiyar da yayi shekaru yana fama, da duk wata alfarma da manyan likitocin Amurka ke tinkaho da ita. Duk da haka Ibrahim ba zaune yake wuri guda ba ko a cikin Chicago, sai ya yi watanni uku baya cikinta yana yawon (private jobs) a duk inda aka gayyace shi aiki tare da kungiyar (nephrology associate). Ita wannan kungiya ita ke tallata members din cikinta da ayyukansu da kwarewarsu ga duniya kuma ta kan turasu su wakilceta idan an bukaci likitocin koda daga cikinta. (It’s not a profit making organisation but for the benefit of its members). Abin nufi, ‘nephrology associate’ ba’a ginata don samar da riba ga kungiyar ba sai don amfanin ‘ya’yan cikinta. Haka da yawan kungiyoyin likitocin Amurka da Africa Ibraheem na cikinta, irin su AAPS (Association of American Physicians and Surgeons), NAD (National Association of Doctors), Alberta Medical Association, AMA (American Medical Association) Flying Doctors Society of Africa, AAD (African-AmericanDoctors Association), WAMA (West African Medical Association) da sauransu. Cikin shekarun da Ibrahim ya yi a lllinois-Chicago, bai wani kara jiki ba, yana nan yadda yake (Dogo mai kirar karfi). Ma’abocin zati da kamala. Kalar fatarsa ce kawai ta canza sai karin hankali da nutsuwa bayyananniya da shekaru da zurfin ilmi suka karawa fuskarsa. Baki ne shi kamar Dacta Mansur, jikinsu iri daya, tsayinsu iri daya, zubin jikinsu iri daya, amma a halin yanzu Daddy ya fishi kauri da cika ido na jikin girma. Amma idan ya juya baya yana tafiya ko yana wani abun daga tsaye tsammani zakayi Dr. Mansur ne. ***** Ya fito daga dakin tiyatar ya shiga (Doctor’s Changing Room) yana cire koren kyallen dake hancinsa da cire korayen kayan tiyatar dake jikinsa ya sanya wadanda ya zo dasu. Yana wanke hannunsa da sabulu a sink din dake cikin ofishinsa bayan ya zare ledar hannunsa, sakatariyarsa Rita ta nemi izinin shigowa, ya amsa mata, ba tare da ya juyo ba. Ta shigo cikin tarin girmamawa ta mika masa wayar dake hannunta domin ita take hada mishi appointment kuma ita yake baiwa wayarsa take amsa mishi in ya ga mai muhimmanci ce a gare shi ya amsa, in ba hakan ba, ta ce a bada sakon a fada masa, ko voicemail ya hanata sanyawa a wayar. “Your Mum has called......” Ta fada cikin tarin girmamawa tare da mika masa wayar. Ya karba ya duba ya tabbatar Mamin ce. Rita ta juya ta fita ta rufo masa kofar. Ya zauna a kujerar dake fuskantar tebirinsa, cikin nutsuwa ya kira lambar Mami. Mami dake kwance cikin zazzabi mai zafi a dalilin damuwa da matakin kauracewa da Dacta Mansur ya dora mata, da tunaninsa na cewa ita ta hana Ibraheem daukar wayarshi, bayan ita ma fiye da watanni uku kenan rabonta da jin muryar dan nata. Abin da basu sani ba shine, Ibraheem ya yi fama da matsananciyar rashin lafiya na (Ulcer). Ba komai ne mujazar rashin lafiyar Ibraheem ba, rashin Cin abinci ne, da tarawa kai aiki wanda ya fi karfin jiki da kwakwalwa su dauka (stress). Kuma ko da wasa bai gayawa Daddy ba, don a lokacin Daddyn ya rikice da murnar maganar da suka yi a waya wai ta zancen aure. Don haka bai gaya masa ba ko da wasa ya tsallake zuwa wani asibiti a ‘San – Francisco’ ya yi jinya ta lokaci mai tsaho, diyar Ambassadan Nigeria a Amurka ko-ko a ce budurwar sa, Sapna, ita ta yi jinyarsa. Cikin ‘yammatan bakar fata dake kara-kaina a kan Ibrahim musamman ‘ya’yan Jakadu da zaunannu (wadanda aka haifa a garuruwa daban-daban cikin yankin Amurka da Colombia) Sapna ce kusan a ce ta samu kallon kima daga Ibrahim, itama din a dalilin Babanta ne ya hadasu tun wani aiki da Ibrahim din ya yiwa babban dansa na dashen koda mai suna Ali. Su mutanen Sokoto ne usul, Hausarsu ce take fallasa hakan. Za’a iya cewa Ibrahim na son Sapna, kasancewarta daban da sauran ‘yammatan sa, mahaifinta ba dattijon banza bane, a’ah, Basakkwacen Dan bokone dake maintaining nationality din sa dana iyalinsa a ko’ina. Yake kuma iya kokarinsa akan tarbiyyarsu. Sapna ba ta shigar banza, ga kwakwalwa, daliba ce a jami’ar da Ibrahim ya yi (University of Chicago) gata da son addini, ga kyau kamar ita ta yi kanta. Itama baka ce (black beauty), don haka Ibrahim ke son ta. Ba ta da rawar kai da kula maza. Don haka mu’amalarsu ta yi tsayi. Ibrahim zai iya rantsewa shine namiji na farko da ya kai hannu jikin Sapna, ya sanyata cikin wata rayuwa da baza’ace bata sani ba amma bata yin ta, tayi amanna da itane alfarmar kalmar SO da tasirinta musamman ga diya mace ma’abociyar rauni da gajartar tunani, bai kuma taba keta alfarmarta ba, ba ita kadai ba ma, bai taba ba, iyakacin abin kenan (refreshing). Ya kuma dade da alkawartawa ransa duk rintsi ba zai taba keta alfarmar diya macen da ba matarsa ba, saboda fadar (S.A.W) a kan zina, idan ka yi da ‘yar wani, babu shakka za a yi da ‘yarka, kanwarka ko uwarka. Wannan yasa Ibraheem sau tari kasancewa cikin azumi, domin danne sha’awar zuka-zukan matan dake neman cinye shi danyensa, ya kuma daurawa kansa al’adar kin rike waya, wannan kwarai ya taimaka sosai wajen gyara rayuwar Ibrahim. Don haka ne da Daddy ya kawo zancen aure ya yi saurin amsawa, domin ya iso wani limit na tsananin bukatar auren, saidai ya yi zaton Daddy zai ja abin da dan nisa har ya gama da wasu ‘yan matsalolin dake gabansa, musamman zuwa San-Francisco jinya. Ya kuma fi son zaben Daddyn akan zabensa, don ya san ba zai taba zaba masa matar banza ba. Ko da nan gaba zai kara da Sapna, a kalla yana da uwargidan da ta san kimar iyayensa; Mamin nan da Daddy da babu kamarsu, za ku ma ta san cewa zaman iyayensa take, kada ta kawo masa wata fiffika idan ta san shi ya ganta ya ce yana son ta. Akwai dai abinda ya taba takura zuciyarsa a can baya, wani lokaci can da ya shude na kuruciya.....Yeeeesss... kuruciya mana..... Amma mai GIRMA!!! It goes far beyond mere or casual assumption! Wanda ya yiwa yakin zuciya da kwakwalwa, har ya samu yayi fata-fata da shi ya fatattakeshi daga rayuwarsa, domin ya fahimci ba karamin barazana bane kuma kalubale ga ci gaban rayuwarsa, da abunda ya raboshi da gida, iyaye da yan uwansa. Ya tabbata barin abin ya habaka ko ya fito sarari (a wancan lokacin) da yake determined matashi (matashi mai kuduri) zai rugurguza ginin da yake son yiwa rayuwarsa ne da burin iyayensa akansa. Kuma yanada burirrika da al’amuran da yasa gaba da suka sha gabansa (al’amarin) suka dameshi suka shanye a muhimmanci. Tun daga wancan lokacin Ibraheem bai kara takurawa zuciyarsa a kan diya mace ba. Kananan kura-kuran da yake yi ma (Lamamu), ya na rokon Allah ya yafe masa as soon as ya aikata. Domin a ganin Ibrahim da wautarsa a wancan lokacin (it’s something that a healthy human being cannot do without), ya na da kyakkyawan hope din cewa, daga ranar da Daddy ya ba shi auren da yake ikirari, babu shi babu lamamun. Abu daya ma yasa yake refreshing din (bakin Sapna), labbanta da tsagar bakinta su ke fizgar hankalinsa kamar ita ta yankawa kanta, take kuma ba shi a araha, saboda son da take masa. Shima kuma yana jin zai iya aurenta ko a nan gaba, amma ba a matsayin uwar ‘ya’ya ba. Dalilinsa shine gata ya yiwa rayuwarta yawa, ba za ta iya yiwa ‘ya’yansa irin tarbiyyar da yake so ba, irin wadda uwa da ubanshi suka dora su a kai. ***** [12/24/2019, 21:48] Takori: Hankalin Ibraheem ya yi kololuwar tashi jin Mami na kuka. Ya kara rike wayar a kunnensa da kyau, sai ya ji cikin shesshekar kuka Mamin na fadin; “Daddy no longer love me now........ a kan wani dan kuskure kalilan.... HEEMU ya zan yi???” Ta ci gaba da rusa masa kukan da bai taba ji ko ganin ta na yi ba. Abin da ya sani shine, Mami da Daddy na matukar son junansu, ta yadda har daya baya iya jure bacin ran daya na lokaci mai tsayi, ba tareda ya shiga tashin hankali ba, ba kuma ya daukar fushin dan’uwansa da sauki ba tare da ya yi exaggerating al’amarin ba fiye da kima. “Cool down Mamee....... take it easy, kukan ki na gigita ni. Ban son in ji ko& laifin na mene ne, amma zan bai wa Daddy hakuri. Nima ba cikakkiyar lafiya ce dani ba, last week akai discharging dina from bed a SanFrancisco. Zan kira Daddy yanzu........” Ai sai Mami ta manta da nata damuwar, muryarta na rawa ta ce, “Me ya sameka?” “Ai na ji sauki Mami, ulcer na ce ta motsa irin motsawar da ba ta taba yi min ba. Ban gaya muku bane don kada na tada muku hankali ku zubar da aiyukan ku ce za ku taho wajena. But am more than fine now. Luv u Mum! Kuma fa ya kamata zuwa yanzu ki dinga kiyaye lafiyar zuciyar Daddy, shekaru sun tura, yana bukatar stable family care. A abubuwa da dama kuna da ra’ayi daya amma ya ce yanzun kin canza, saboda rudin kawaye. Kin zabi bin ra’ayin kawayenki akan nasa. Kin daina bin ra’ayinsa, sai dai ke ya biki, sai abin da kawayenki suke so kike yi wadanda kin kasa gane ba masoyanki bane, anya Mami??? Ina nan tahowa Nigeria nan da wata daya”. Dr. Asma’u ta kawo doguwar ajiyar zuciya. Wane irin zurfin ciki ke da Dacta Mansur da babu mai jin zuciyarsa sai Ibraheem? Hatta ita MATARSA Asma’unsa!!! Ita ko a fuska bai taba nuna mata tana yi mishi ba dai-dai ba, duk da ita akan sanin kanta tasan ta yi mishi ba daidai din ba, kawai ya daina yarda ya kadaice da ita, ya daina zaman gidan sam-sam. Abinci ko ta mance yaushe rabon ya zauna su ci shi tare da ‘ya’yansu, wanda a da yake da kakkarfar akida a kan hakan. Domin ya kan ce, hakan na kara kauna a zuciyar ‘ya’ya da iyayensu. Yana hana yaro ya zama mai kwadayi, yana kara jin kai da hadin kai tsakanin ‘ya’ya da iyayensu. Abin da Mami ba ta sani ba shine, can a (Farm-Center) yake cin abinci in yana da bukata wajen Inna Juma da suruka, ayi hira ayi raha, ya cikasu da shopping sannan ya dawo (Lamido Crescent) ya nemi gadon barcinsa ya kulle da mukulli, duk don ya hora Asma’un, a bisa sababbin halayen da ta tsiro masa dasu wadanda ba zai dauka ba ko daya. An ce kukan kurciya jawabi ne, in tana da hankali sai ta gane. Ba ta gane din ba, sai yanzu da dan cikinta ya ankarar da ita. Ita kanta ta san mai laifi-kan-laifi ce a wajen Dr. Mansur, bai taba tambayarta ina Rayhanah ba, tun ranar da ta kore ta. Wanda a yanzu take cikin fargabar ina yarinyar ta shiga babu ko duriyarta, amma Dacta bai tambaya ba, bai tambaye ta ina Khalipha ba, ina kuma zancen aurensa da ta hana ya kwana? Ina wadda ta aura masan? Me take ci? Me take bata tunda Khaliphan baya nan? Ita kanta ta fi son kada ya tambayetan, don ba ta da amsar ba shi. Sosai yake sakar mata fuska a falo in sun hadu gaban ‘ya’yansu, sai dare ya yi ya garkame kofarsa. Wannan ya fi komi tada hankalin Dr. Asma’u wadda ke son gyara kuskurenta, amma Dacta ya ki bata dama. Babu fuska ma bashi da lokacinta. Ba don yana kwana a gidan ba ma (if he is not on-call) da sai ta ce wata ce ta janye shi, kasancewarsa mai farin jinin mata a wajen aiki, manya da yara, masu aure da marasa aure, duk da ya manyanta saboda yadda Allah ya suranta shi, ya kuma yi masa ado da kirki da tausayi har ma da nuna kulawa ta musamman ga marasa lafiyansa da kananan likitoci da ma’aikatan dake karkashinsu. Wadatar zuci da rikon addininsa sun shafe shekarunsa a jiki da fuska, sun ba shi shekaru arba’in da biyar na magidanci mai kananan ‘ya’ya. Ajiyar zuciya ta sake yi ta kasa ce da Ibraheem komai, la shakka ta yi kuskure, anya ma ita ce? Ta maida kanta jahila haka? Ina zurfin tunaninta ina kwalayen iliminta? Ta maida kanta irin matan bakin- kasuwa? Nadama ce take shigarta sosai, a kasalce ta ce da Himun. “Komai ya canza daga yau insha Allahu, tunda na yi maganin matsalar. Kai min addu’a ka ba shi hakuri..... Himu don Allah.......” Tausayi da kaunar Mamin suka kara kama shi. A take ya ce, “Mami komi ya wuce, na ari bakin Daddyn na ci masa albasa, komi ya wuce, sai na iso”. Ya kashe wayar da sauri don zuciyarsa ba za ta iya jurar sauraron kukan mahaifiyar ba. Wanda ke tada tsigar jikinsa har ya sanyawa jikinsa tsuma. Ibraheem kenan, shi da Khalipha ban san wa ya fi kaunar Mamin nan ba (Takori). Allah ka barmu da iyayenmu, mu rayu tare har karshen rayuwarmu. Ka bamu iko da karfin zuciyar yi musu biyayya, albarkarsu ta zama mayafinmu kuma bango abar jinginarmu. Sannan abin tinkahonmu gobe kiyama. ****** A FARM CENTRE “Halan waken nan sai da aka barza shi aka fidda dusar, kafin ayi faten nan?” Dr. Mansur kenan, ke tambayar Inna Juma. Rahane ta dau pillow na kujera ta tura bayan Daddy. Bai lura da shakiyancin da ta yi masa ba ya sake tambayar Juma. “Kuma kifin nika shi kika yi a blander kafin ki zuba?” Ai sai Rayha ta kwashe da dariya. Inna Juma ta zuba mata duka a cinyarta ta ce, “Uban naki kikewa shakiyanci ko ya yi kama da Malam Hudu? (Kakanta wanda ya haifi Yalwati). Sai a lokacin Dr. Mansur ya ankara da abinda ke faruwa, ya karashe lomarsa ta karshe ya mike ya kora da lemun safari cikin tambulan, ya dauki mukullin motarsa ya yi hanyar kofa yana murmushi ya ce, “kyaleta Inna Juma, ta mai dani kakan nata ya fiye min da ta rikeni a matsayin siriki ta dinga nuku-nuku dani, ta kasa gaya mun damuwarta. Bayan nine uwarta, nine ubanta, nine abokinta, kuma kawarta. Ke kuma kakarta. Bari in wuce gida yamma ta yi, yanzu zan yi tuki da kuzari tunda hanjina ya warware. Go-slow ne dai na san sai ya kai ni magariba a titin nan idan ma na yi sauri kenan, Kano is full, alhamdulillah Kanon Dabo ta yi zarrah a jihohin Nigeria gaba daya, wajen albarkar Al’ umma”. Rayhanah ce ta bude masa kofar motar ya shiga ta rufe, “Sleep well Daddy.....” Ta fada tana daga masa hannu har ya bar get dinsu yana daga mata shima. Maigadi ya kulle, ita kuma ta koma cikin gida. Nan ta ga wayar Daddyn a nan inda ya tashi santin faten waken Inna Juma ya mantar da shi. Ta ce, “Lah! Inna kinga Daddy ya manta wayarsa”. Inna ta ce, “Sai ki adana gobe ya karba”. Ta ce, “Ba lallai ya zo gobe ba, karshen wata ne zai je Takai. Bari dai na ajiye din”. Ta yi dakinta da ita ta sanya a kan lokar gadonta, ta fada bayan gida don ta yi alwalar sallar magariba. Kafin lokacin magariba ya cika, Rayhanah na zaune kan sallaya da carbinta a hannu cikin kyakkyawar shiga da ta ware musamman don yin ibada, doguwar Abaya ce kirar Kuwait da farin Hijab wanda ya tsaya iya gwiwoyinta, tana yiwa Ubangiji tazbihi. Har aka kira magariba ta tada sallah, a lokacin da wayar Daddy dake kan lokar gadonta ta soma dan kida ba mai cika kunnuwa da gigita mutum ba. Don haka a nutse ta ci gaba da sallarta har ta idar, mai kiran bai hakura ya daina kiran ba sai kira yake akai-akai-akai. Yana yi yana karawa. Ta mike ta kwanta a gefen gadonta ta dauki wayar Daddy don ta kashe, a ranta tana kunkuni cikin fadin “these so-called AKTH emergency unit, will not leave my Dad to live in peace ........haba! Ko inji ai yana son (service) kafin ya ci gaba da aiki balle mutum dan-Adam. Amma shi Daddyn baya gajiya, ko ya kwana da an kira shi komin dare zai tafi. Ni gara ma da ya bar wayar, yau daya dai ya huta”. Amma ga mamakinta sai ta kasa kashewa, ta zubawa lambar ido, domin ba ta yi kama da normal lambobin da ta saba gani ba. Lambobi ne rankacau (International). Haka nan ta samu kanta da faduwar gaba, mutuwar jiki da sanyin gwiwa, wanda suka dage da cewa lallai suna son amsa wannan wayar, ta gayawa mai su Daddy baya tare da wayar, don ganin yawan kiran mai nuna mai ita a matse yake da son magana da Daddyn daga kololuwar duniya ba kiran asibiti bane. A dai-dai lokacin da kiran ya kara shigowa, sai ta kishingida ta amsa. “Dacta baya tare da wayar fa! Be patient mana!!”. Wata irin sassanyar murya ce mara amo da karsashi, sannan kuma mai taushi, yarinyar ta yi amfani da ita wajen yi masa wannan kalamin, wadda ta tsirga har cikin kwakwalwarsa, ta haifar masa da macewar jiki, at the same time, ta tada tsigogin jikinsa. Da ta ji anyi shiru kawai sai ta katse wayar ta ajiye. Ta dau remote ta kunna A.C ta soma addu’ar kwanciya barci. Ibraheem ya yi shiru yana kallon wayar hannunsa, tsaye yake a balcony din gidansa (terrace) a saman bene yana kallon yadda ruwa ke tsiri, yana zuba cikin furanninsa korra sharr. Akwai wani abu extraordinary cikin muryar yarinyar da bai taba ji a muryar wata diya mace ba, mai sanya sanyin jiki da kasala. Me ya hada Daddy da budurwa har wayarsa ta je hannunta? Yana da kyakkyawan zato a kan mahaifinsa, amma wannan ba Abida ba ce ba Jawahir ba, ba kuma Azizah ba. Idan ma sune ba yadda za ai wayar Daddy ta zo hannunsu. Don haka ya ji yana so ya tambayeta ita wace ce? Me ya hadata da wayar mahaifinsa? Don haka ya sake kira, ta kuwa sake amsawa don yau cikin nishadi take, don Daddy ya ce za ta tafi Singapore jibi in Allah ya kaimu ta dora karatunta kafin Ibraheem ya nemi gida..... “Wace ce ke?” Abinda ya tambaya kenan a gintse, da makalalliyar hausarsa mai fita a doron harshe, cikin tsananin takaitawa. Ita ma a takaicen ta samu kanta da amsawa. “Sunana Juma”. “Juma? What kind of name is this?” Ta amsa da cewa, “Sunan da iyayena suka rada min kenan”. A muryarta kamar ta ji zafin tambayar da ya yi mata, shi kuma a rayuwarsa bai iya muzanta dan adam ba. Sai ya yi saurin cewa, “Ki gafarce ni plz, ina so in san yadda akai wayar Dr. Mansur ta zo hannunki ne?” “Am the Nurse on duty, and he left it at the ward”. Ibraheem ya gamsu da bayaninta har ga Allah, ita kuma kawai cikin nishadi take kan wannan albishir mai dadi da Daddy yayi mata na tafiya Singapore (Informatics-Singapore) ta rasa da wanda za ta yi sharing nishadin nata, sai ya fada a kan Ibraheem. Ya ce, “Alright, zan kira zuwa gobe. Thank you” “Don’t mind”. In ji ta. Karfe biyar na Asubahi tana tsaka da barci sai ga kira again, ta yi dan tsaki ta mika hannu ta dauko wayar tana ganin laifin kanta da ba ta kashe wayar ba tun jiya, ga shi an katse mata barci mai dadi da take yi bilhakki. Sai dai ita kanta ta san ba laifinta bane, laifin yatsunta ne, sun kasa kashe wayar kada mai Turanci mai dadi ya bugo bata dauka ta sake gillara masa karya ba. Ai tana ganin lambar ce sai ta nemi barcin da ya cika mata ido ta rasa. Ta amsa da sallama cikin muryar barci, wannan karon tasirin da muryar ta yi a jikin Ibrahim Mansur, Allah ya yi yawa da shi, ta yadda biro na bazai iya rubutawa ba. Har ta kai ga Ibraheem ya fada cikin wani yanayi na daban. Muryarshi can kasan makoshinsa ya ce, “Ki yi hakuri na tashe ki daga barci”. “Don’t mind”. Ta sake cewa. “Jumah!” Ya kira sunanta da murya (which is deeply suffering).... Sai ta ji jikinta ya kama rawa, ta yi magana cikin sarkewar harshe. “Doctor is not yet at office!”. Ta kashe wayar hannunta yana rawa, gangar jikinta ma gabadayana yi. Irin wadannan mazan sune masu yin zinar murya, me yasa zai rika yi mata magana da irin wannan sauti mai kassara gabban jiki kamar wata matarsa ko budurwarsa? Ba za ta kuma amsa wayarsa ba. Batasan cewa murya ce da Ubangiji Subhana ya halicce shi da ita ba. Sai kuma ta baiwa kanta dariya, sanda wani bari na zuciyarta ya tambayeta, “Wa ya gaya miki haka miji ko saurayi ke yin magana da budurwarsa ko matarsa Rayhah?Tunda ke baki da saurayin ko mijin? Babu kuma wanda ya taba yi miki magana hakan including Yaya Khalipha?” Oho!” Ta fada tana kyabe baki tareda shigewa cikin lallausan bargonta tana cewa, “A to, haka dai na ga Daddy na yiwa Mami magana, ita ma in ya yi tafiya tana waya da shi ai haka take yi mishi magana”. Barci ne mai karfi ya dauke ta. Hasken rana da ya hudo ta farin labulen da ya zagaye dakin barcin nata shi ya ratso ya dallare mata fuska. Ba shiri ta tashi tana mittsike ido ta fada toilet ta yi wanka ta yi brush da yake ta yi sallar Asubahi ta fito falo. A kicin ta jiyo motsin Inna, don haka ta tasarma kicindin. Can ta iske Inna Juma tana kwabin Alkubus, ta ce, “Allah ya ja da ran Inna ta, yau Alkubus zamu ci haka?” Tana buga fulawar ba tare da ta juyo ba ta ce, “Ni ba ke nake yiwa ba, Baba Likita nake yiwa don jiya ya gaya min yana son shi”. “Ba kya jin magana Jumah.......! (ta fada da sauti irin na Ibraheem) wanda ita kanta ba ta san sanda muryarta ta karye ta canza ta koma haka ba. Na gaya miki yau ba zai zo ba zai je Takai Asabar din karshen wata ce”. Inna ta yi dan jim, sannan ta juyo ta dubeta. Abubuwa biyu ne suka sa Innar yin shirun da juyowar. Na farko kiran sunanta da Rayhanah ta yi da wani irin amo (tune) da ba nata ba, na biyu kuma ba ta ce mata Inna ba kamar yadda ta saba. Gani ta yi Rayhanah na rawar dari, ta kankame hannunta a kirjinta, murya na rawa idanunta na lumshewa, suna budewa ta ce, “Inna sanyi nake ji”. Sai ta tsame hannunta daga cikin fulawar ta rufe ta don ta tashi, ta wanke hannunta ta kama Raihanan, ta soma tofa mata duk addu’ar da ta zo bakinta, domin a tsammanin Inna aljanu ne suka shiga jikin jikar tata yanzu-yanzun nan. Tabbas muryar da ta yi mata magana da ita, ba tata ba ce. Daki ta maida ita ta ce ta kwanta, bari ta je asibiti ta kira Dacta (da yake ta san ofishinsa ya taba kaisu). Rahane ta ce, “Wai Jumah........! (ta kara yin magana da irin sautin dazu) sau nawa zan gaya miki Daddy baya nan ne?” Inna ta ci gaba da tofa mata addu’a. Haushi ya kama Rahane, don ta ga Inna ta mai da ita mai aljanu kawai don ta ce da ita tana jin sanyi. “Kinga Jumah..... (ta kara fada da sautin Ibrahim da tune dinsa na yin magana) jeki ki yi Alkubus dinki, ki rabu dani don Allah bana son wannan tofe-tofen da kike mini, fever ne kawai ke son shiga na, rufa min bargo, jeki don Allah”. Inna ta ce, “Ba zan tafi din ba, aljani ke son auren ki. Bari Baba Likita ya zo a daddale magana, idan dan American nan baya sonki, to ya sahale miki ki yi rayuwar ‘yanci ki samu wani mai sonki ki aura. Wannan ba aure bane, watanni goma fa! Ana shirin shiga na sha daya. Babu miji ba dalilin sa”. Inna babatu take ba ta san cewa Rayhanah ba jinta take ba. Zazzabi mai zafi ya rufeta ruf. Ina ma ba ta kashe wayar nan dazun ba, da watakila ta ji sunan mai wannan poisonous murya wadda ta dura mata virus ta cikin kunnuwanta ta haifar mata da zazzabi mai zafi. Ita dai fatanta Inna ta fita ta ji da abinda ya sameta, amma Innar ta ki. Sai da ta hada da magiya sannan Inna ta fita tana ta mita, ita wannan aure ya isheta, ba ta san irinsa ba. Bata taba gani ba! Bayan fitar Inna kira ya sake shigowa, Rayhanah ta daga, duk da ta ce ba za ta kara dagawa ba, zuciyar da gangar jikin sun ki amincewa, cewa suke; “........ ba zamu samu sauki ba in bamu ji shi ba, ba zamu barki ki zauna lafiya ba sai mun ji ko shine IBRAHEEM!!! [12/25/2019, 15:42] Takori: Ya tabbata ta amsa kiran, amma ba ta yi magana ba. Ya dade shima bai ce komin ba, sai da ya saisaita kansa ta hanyar yin ajiyar zuciya akai-akai, sannan a sanyaye ya ce, “Am now not to ask for Doctor, (yanzun ba Dr. Zan tambaya ba) don haka don Allah kar ki kashe min waya. I want to know more about you..., Concerning you. ...” Ta ce, “You can ask me anything (za ka iya yi min kowacce tambaya) insha Allahu ba zan kashe ba”. Ta fada da muryar da ta kara kassara Ibraheem. Ya ce, “Meye alakarki da Doctor Mansur?” “Likita da mai taimaka masa”. Ta amsa kai tsaye. “Wannan matsayin da kike ikirari bai yi isar da zai sa ya baki wayarsa ba. Don Allah!Ke wace ce dinsa???” Tunda ya ce ALLAH! Sai ta ji ba za ta iya yi mishi karya ba. Kuma jikinta yayi wani irin sanyi, da wata muryar again da Ibrahim ba zai taba mantawa ba, ta ce, “Kafin in amsa maka, nima ina so in tambayeka don ALLAH! Ko kai ne IBRAHIM.....???” Shiruuuu! Ya bakunci kunnenta. Da ta duba sai ta ga cajin wayar ne ya mutu. Don haushi sai raunanniyar zuciyarta ta ce da ita, “Ki rushe da kuka........” Shi din kuwa ta shiga yi mai yawa, sai da ta yi ya isheta. Wannan mutumin da take waya da shi, da matsayin da zuciya da gangar jikinta suka baiwa muryarsa, suka kuma karbeta, da tasirin muryar cikin gangar jikinta da kwakwalwarta, da wata tsoka guda daya dake tsakiyar kirjinta (zuciya) ya fi gaban na wani mutum kawai, wanda yin waya da shi kawai zai haifar da wadannan emotions. He must be the HUSBAND. Ba ta tantama ko shakkar cewa shine mijinta IBRAHEEM MANSUR TAKAI.... Zazzabin na karuwa, sanyin da take ji na daduwa. Har Azahar ba ta fito ba kuma ta ki bude kofarta kada Inna Juma ta dameta sai ta ci alkubus. Ita yau ko naman Dawisu (Peacock) aka gasa aka kyafe mata aka ce ta ci da gida da mota (in return), baza ta iya ci ba. Muryar Ibraheem kawai take son sake ji, da son ganinsa a zahiri. Wata murya data haifar da wasu bakin abubuwa agareta da bata taba ji ba a rayuwarta, ba kuma zata iya fassarasu ko fasaltasu ba da kowacce irin siga don wani ya gane ko ya fahimta. Zazzabin kuma sai ta ji yana sauka a hankali, a saboda lallashin da zuciyarta ke mata da cewa, “Watakila shine angon Rayhanah! Amma anya Rayhanah baki kamfato da yawa ba? Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki? Idan kuma ba shi bane hatta wannan tunanin da kike da bari da kike muryarshi na tasiri a gangar jikinki da zuciyarki, kina aikata haramun ne fa, a matsayinki na matar aure!!! “Astagfirullah!” Rayhah ta fada a hankali. Ta debo kuzari da karfi ta zubawa jikinta, ta mike cikin zafin nama, ta bude bed-side fridge dinta ta dauko gorar ruwan FARO mara sanyi ta soma kwankwanda. Sai da ta sha rabin doguwar robar sannan ta ajiye. Ba ta mantawa wannan horon Mami ne, ba ta bari su karya kumallo sai sun sha fresh water sun koshi. Sannan ta adanawa Daddy wayarsa, ta bude kofa ta nufi falo wajen Inna. Ba ta falon, don haka ta wuce dakin da ya zan mallakin Innar a kasan benenta. Sanda ta shiga Inna na sallar Azahar, sai ta shiga bayin Innar ita ma ta yi alwalar ta fito ta tada sallah. Ko da Inna ta idar ba ta kulata ba laziminta ta ci gaba da yi kasancewarta mai son ibada, ba ta zama haka kawai, inda abokin hira ayi hira ayi dariya, in babu a yiwa Ubangiji tazbihi ayiwa Annabi salati. Ta gane lamarin na Inna yau har da fushi a cikinsa. Ko don ta rufe kofa ne ko don ta ki cin Alkubus ita ba ta sani ba. Sai ta ji ranta ba dadi, ta gurgusa ta kwantar da kai a cinyoyinta, cikin murya mai ban tausayi ta ce, “Inna idan laifi na yi miki don Allah ki yi hakuri”. Girgiza kai Inna ta yi alamar a’a. Sai da ta kai laziminta ta ja addu’a ta shafa ta shafawa Raihanan, sannan ta ce, “Ni baki yi min laifin komai ba, auren nan ne dai nake so a kawo karshensa in ba mai nasara bane”. Rayhanah ba ta gane abinda Inna ke nufi ba, cikin mamaki ta ce, “Inna kamar ya ya idan ba mai nasara bane?” Inna ta ce, “Eh, idan ba mai nasara bane, abin nufi idan yaron baya so, ba zan zuba ido ki kare kuruciyarki a haka ba har jinnu su soma kokarin auren ki. Daga yau daki daya zamu dinga kwana. Bari Baba Likita ya zo, wannan zaman jiran tsammanin warabbuka ya ishe ni”. Fushi ne sosai ya bayyana cikin idanun Rayhanah, ba ta san sanda ta dagawa Inna sauti ba. “Ko zaman shekaru ashirin ne Daddy ya ce in yi zaman auren dansa, kuma dan baya sona, ba jinnu ba, ko ifritai ne za su aure ni ba zan taba ce da shi ya kawo karshen auren ba. Tunda daurawa ce tashi, amma igiyar aure ba a hannunsa take ba balle ya tsinka ta. Sama da wannan ni abin ikonsa ce sai yadda ya ga dama dani, don na san ba zai taba yin abu don ya cutar dani ba. Shi ya mai dani -MUTUM....... Wani kwayar halitta guda daya da ya tsaya ya maidani MUTUM!!! (Cewar Rahma Abdulmajid ). Ba don shi ba ban san ya ya rayuwata ta baya za ta kasance ba, a lokacin da na budi ido babu kowa nawa a duniya. Don haka Inna don Allah kada ki yi masa wannan maganar hankalinsa zai tashi, ni na ce na-ji-na-gani INA SON IBRAHEEM.......!!! Ina darajja igiyoyin aurensa da suke kaina, ko da baya sona. Koda har abada bazan ganshi ba, balle mu zauna tare. Baku sani bane, baku san rawar da Daddy ya taka a rayuwata ba. Kun budi ido ne kawai kun ganmu tare. He is someone I cherish and respect most! Ko me zan yi masa ba zan iya biyansa hidimar da ya yi dani da rayuwata ba. Inna gaya miki ne ban taba yi ba, amma har nakasa nayi; babu ji dungurungum!” Ta yi shiru tana share hawaye cikin TUNA BAYA. .....sannan ta ci gaba da cewa, “Shi ya nema min magani na warke, da lafiyarsa, da iliminsa da lokacinsa da aljihunsa. Shi ya bani ilimi irin wanda ya baiwa ‘ya’yan da ya haifa dama wanda bai basu ba. Duk wannan bai isa ba, ya dauke ni ya aurawa dan da ya fi so cikin ‘ya’yansa. A lokacin da aka so rayuwata ta tozarta Don na fito daga karamin asali, na taba yin cuta. Sai kawai don yaron ban yi masa ba ya ki zuwa sai ki ce Daddy ya raba ni da auren dansa? A’a, Inna kada ki fara, na zabi in mutu, in kare kuruciyata da rayuwata gaba daya da igiyar auren Ibraheem, ina mai darajjata da kare martabarta. Don haka don Allah Inna kada ki kara tada wannan magana za ta tada hankalin Daddy”. “Sai na yi!” Abin da Inna ta ce kenan. “Fito fili kawai ki yi mana gori, bamu tallafi rayuwarki ba kina karama, a nan kam bani da bakin musa miki. Amma ina da shi a wajen Allah, wannan kyautayi da alherin da ya yi ai sakayyarsa na gurin Allah. Ba zai zama hujjar cewa sai kin biyashi da tauye kuruciya ba, babu inda musulunci ya yarda da wannan, sai in dama ya yi ne ba don Allah ba sai don ya aurawa dansa wanda baya so. Mene ne dole? Babu dole!” Amsar Rayhanah cikin rurin kuka ta bata mamaki. “Inna in dai kin gaji da tayani zaman jiran Ibrahim ne..... kina iya komawa Takai ni in zauna ni kadai. Babu abinda zai cinyeni cikin gidannan da yardar Ubangiji....,In har ba za ki taimaka min in yiwa Daddyna biyayya ba.......!’’ Sai Inna ta mike a hasale tana fadin “Haka kika ce ko? To shi kenan”. Ta soma ciro kayanta daga cikin kwaba tana dannawa a (Ghana Must Go) din da suka zo a ciki. Kan ta gama kukan tuni Inna ta gama cika jakarta ta yi lullubi ta kinkima ta daura a kanta ta yi waje. Kamar an yiwa Rayha allura haka ta bita da gudu, ba ta cimmata ba sai a kofar fita daga falon, ta kama jakar ta kankame tana kuka kamar na fitar rai. Inna na ja Rahane na ja, a haka Allah ya kawo Dr. Mansur, saboda bacin ran junansu ko karar shigowar motarshi basu ji ba. “Subhanallahi-Subhanallahi!” Abin da yake fada kawai kenan. Inna Juma ba ta ko kalli kwayar idanunsa ba don ita kanta ya yi mata kwarjini. Sai ta kasa cewa komai ta sunkuyar da kanta kasa, ya yin da Rayha ta dauki jakar da kyar sabida nauyin ta, ta maida ita ciki. Tana ji yana bai wa Inna hakuri da lallami da lallashi cikin girmamawa, sai haushin Inna Juma ya kara kamata, da kyar ya lallabata suka koma falo. Ya zauna a kan kujera yana fuskantar tsohuwa Juma, wadda ke zaune kasa kan kilishi ta rasa daga inda za ta dauko masa zaren bayanin da ya bukata, wanda ya sata yin fushi haka, har za ta iya tafiya ba tare da ta neme shi ba,. Ko me Rayhanah ta yi mata ai yarinya ce, shi ya kamata ta jira ya zo in na fada ne ya yiwa Raihan, in na tsawatarwa ne ya tsawatar mata. Yara yanzu ai ka haifesu ne kawai amma ba ka biye musu sai ku taru ku zama yaran dukkanninku. Inna ta yi shiru dai-dai lokacin da Rayha ta iso da tray shake da jus da ‘ya’yan inibi, peach da pear ta ja karamin tebur din dake gefen kujerar da Daddy ke zaune ta dora ta matsar dasu gabansa. Hankalinsa kwance ya soma cin kayan marmarin yana sa mata albarka kamar ba shi ya sayo da kudinsa ba. Ta koma daki ta dauko masa wayarsa ita ma ta dora a kan tebir din. Ya shiga hamdala yana cewa, “Ashe a nan na barta, kai! Batan waya babu dadi, ba wayar ce abin ji ba, al’amuran da suke ciki. Ke Rayhanatu jeki daki zan yi magana da Inna”. Ta ce, “To Daddy”. Ta mike ta nufi bed room dinta. Ya sha tambulan din ruwa mai sanyi, ya gyara zama ya ce, “To Inna ke nake sauraro, laifin me mutuniyar taki ta yi miki haka har kika yi tunanin tafiya ki barta?” Inna ta share ido da gefen zaninta saboda tausayin Rayhanah, in iyayenta suna raye ai dole za su yi wani abu a kan wannan zaman mara kan gado. Ta ce, “Ita ce ta ce na tafi”. “Raihan?” Ya tambaya da mamaki. “To a kan me?” Ya sake dorawa ba tare da ya jira amsar ta farko ba. Inna ta kwaso zance tiryan-tiryan ta shiga gaya masa yadda suka yi da Rayha da abubuwan da ta fada akansa da aurenta da Ibrahim. Sai ga Dr. Mansur yana kuka amma ba mai sauti ba, danshin idonsa kawai yake daukewa da hankicinsa. Kaunar Rayhanah ce da kimarta suka karu a idanunsa,at the same time, Inna ta burge shi, ta nuna masa a duniya akwai masu kaunar Rayhanah bayan shi. Kauna ba ta abin hannunta ba ko don a rabi inuwar da take ciki, ingantacciyar rayuwa take nema mata, ba kwadayi da son duniya ba. Muryar Dacta Mansur na rawa ya ce, “Don Allah don Annabi Inna ki kara hakuri komai ya zo karshe insha Allahu. Ni na daura kuma ni zan kwance da yardar Ubangiji, zan bi Ibraheem har inda yake in karbowa Rayha takardar ‘yanci. Amma kafin nan..........” Ya zaro passport guda biyu ya mika mata. “Kamar yadda na yi miki bayani shekaranjiya gobe zaku wuce kasar Singapore, Rayhanah za ta dora karatunta ni kuma in wuce Chicago. Ba zan baroku ba sai na tabbatar Rayhanah ta samu ‘yancin kanta, aure ko saki ayi karatu. Abin da yasa har yanzu ban dau mataki ba akwai wsu matsaloli ne da nake warwarewa na cikin gida, kuma alhamdulillahi na fara shawo kansu, ku kara hakuri Inna”. Ta ce, “Ai shi kenan, Allah ya zaba abin da ya fi alkhairi. Sai dai ni kam ba zan iya zuwa kasar da babu Allah babu Annabi ba idan ba Makka da Madina ba, don haka ni dai don Allah Alhaji Likita ka cire ni daga wannan lamari naku na nasara ko na samu in cika da imani. Yaya mace da igiyar aure a kanta za ta tsallake mijin ta cilla wata duniya daban wai karatu? Kuma ba da izinin mijinta ba, ka duba lamarin nan da kyau Alhaji”. Dariya ce ta kama Dr. Mansur ganin yadda Inna ta takarkare tana bayani tsakaninta da Allah. Ya ce, “Inna zamani ya canza. Mata da miji duka fafutukar neman ilimi suke tunda Allah bai iyakance ba, su taru su rufawa juna asiri. Don haka kada ki tauyi Rayhanah..... ba ki san tarin baiwar da Allah ya yi mata ba. Ni na gaya miki RAYHANAH na da future akwai wani nasibi da Allah ya yi mata wanda bai yiwa sauran ‘ya’ya ba, wannan nasibi shine kwakwalwa, wanda jikina yake bani ba za ta kare rayuwarta haka ba. Hakan kuma ba zai faru ba sai da zuzzurfan ilimi wanda duniya ke damawa da shi, musamman irin nata (computer). Abin da za ki yiwa Rayhanah a yanzu shine addu’a da bata kauna da kwarin gwiwa irin wanda Iya Bilki ta ba ta. Wannan shine abin da za ki yi mata yanzu har Allah ya daidaita al’amarinta, nima ban tsaurara ba, in Ibraheem ba shi da hujjar yanke sadarwa dani, ya yi ne don ba ya son zabina, wallahi sai na raba auren ko a kotu ne. Ki kwantar da hankalin ki Inna”. Inna ta ji dadi har cikin ranta. Ya kara da cewa, “Yanzu kada ki nuna mata kin gaya min musabbabin fadanku, ki lallameta ki ce da ita baki kyauta ba, kuma kin gane ke kika yi laifi. Ni zan wuce gida ku hada kayan da za ku bukata tun yanzu, gobe da daddare zamu tashi, ni zan raka ku har Singapore, ba zan tafi ba sai Rayhanah ta soma shiga aji. Daga nan sai in wuce neman Ibraheem, ki kwantar da hankalinki Inna, Allah yana ko’ina kuma ko’ina kika yi ibada ko a birnin Sin ne ba Asiya ba (Asia) Allah zai karba. Idan babu ke wane ne zai debewa Rayhanah kewar mijin? Wa zai dafa mata abinci kamin ta dawo? Waye zai sadaukar da lokacinsa da rayuwarsa gareta idan ba ke ba? Kindly observe it........” Murmushi ta yi ba don ta ji Turancin ba, sai don ya nuna mata ita mutum ce mai kima da wani amfani ko yaya yake a RAYUWAR RAYHANAH duk da ba ta da abin da za ta bata ta wanke dattinsu da su Zinaru suka goga a idon yarinyar ban da kauna ta fisabilillahi wanda shine tsakaninta da Rayha a yanzu. Ita ta soma ciro kaya a kwabar Rayhan tana shiryawa cikin akwatunan lefenta (jakunkuna), wadanda har yau ko rabi-rabinsu ba ta sanya a jikinta ba. Da yawa ma suna cikin jakar ko taba su ba ta taba yi ba tsayin shekara guda ba kadan. Duk kuma yadda Dacta ya ce ta yiwa Rayhanan haka Inna ta yi. Karfe tara na dare suka rurrufe ko’ina na gidan suka nufi airport. Jirginsu ya daga Singapore karfe goma na dare, wanda Ibraheem ya biyo daga Chicago ya sauka karfe 12 na dare a garin Abuja-Nigeria. ****** RAYHANAH A SINGAPORE Sun sauka a tsohon filin jirgin saman nan mai tsohon tarihi na Singapore (Changi Airport) da asubahin washe gari. A matsayin Rayhanah na dalibar Informatics wadda suka san da zuwanta, motar makaranta ce ta zo ta debe su zuwa gidan da Dr. Mansur ya kama musu a kusa da Institute din, bai yarda Rayhanah ta zauna cikin dalibai ‘yan’uwanta ba sai bisa kulawa da sa-idon babba wato Innarta Juma. Shi a Hotel ya sauka. A wunin ranar baki dayanta dukkansu basu tsinana komai ba sai barcin gajiya. Sai wajejen magariba Dacta ya zo a motar Hotel din da ya sauka ya kawo musu take away na Ji Hao (abincin mutanan Asia ne) da Inna Juma ta gagara hadiyewa duk dauriyarta sai da ta kwararo shi waje. Dacta da Rayhanah suka ce me za su yiwa Inna ba dariya ba, dama tun a cikin jirgi ake dirama da ita, komai sai ta ce sun yi mata ba dai-dai ba. Haka abokan tafiyar tata da ma’aikatan jirgin mata da maza suka yi ta lallabata har Allah ya sauke su lafiya. Yanzun ma danja ta bude ita a nemo mata ko samanbita ne ta tuka tuwo ta ci in ba so ake yunwa ta yi mata lahani ba, yini biyu kenan ba ta sa kwakkwaran abinci cikin hanjinta ba sai kayan tashin zuciya. Cikin daren Baba Dacta sai da ya san inda ya je ya nemo mata shinkafa da kaza sannan aka zauna lafiya. Shi da suruka sai cin kayan dadinsu suke yi irin su kayanfulawar ‘McDonalds, KFC (Kentucky Fried Chicken), Cendol, Hainanese da Rojak (Asian snacks). Sai bayan isha’i ya yi musu sallama ya koma masaukinsa. Washe gari da safe suka shiga Informatics Arena karfe takwas na safe shi da Rayhanah, a (admin office) duk wasu cike-ciken takardu da suka kama Dr. Mansur ya yi su, Rayhanah tasa hannu, kudaden da suka nema duk ya biyasu ta banki. A take ba bata lokaci Rayhanah ta shiga aji, inda ta fara daukar lacca, ta tadda dalibai ‘yan’uwanta daga Nationality daban-daban maza da mata. Tun a ranar ta soma kwankwadar ilimin na’ura mai kwakwalwa wanda a iya dan iliminta a Kazaure ba ta san da shi ba, kwakwalwar a wanke take, zuciyar a sake take babu damuwar komai a ciki sai godiya ga Allah da wanda ya zamo silar haskaka rayuwarta. Don haka ta mai da hankali don bai wa mara Da kunya da fita kunyar Baba Dacta. Kwanan Baba Dacta uku kacal a Singapore ya wuce Chicago, bayan ya tabbatar basu da matsala, ya shake musu store da kicin da duk wani nau’in kayan abinci da kayan amfani da za su bukata, da katin daukar kudi a ko’inacikin duniya (mastercard) a duk lokacin da suke bukata bayan ya koyawa Rayhanah komai. A asibitin Illinois Baba Dacta ya doki babban gurbi na tahowar Dr. Ibraheem gida Nigeria very last week. Amma a satin suke zuba idon dawowarsa. Kwanansa daya kacal ya juyo gida Nigeria. A nan ma gurbin ya doka, Ibraheem ya tafi wajen dan’uwansa Khalipha a Abuja da yake ta can ya sauka. Don haka ba yadda zai yi, ya zauna karbar lallashi da ban bakin Mami masu nuna nadama, da alkawarin rashin maimaitawa. To tsakanin Mansur da Asma’u sai Allah, shi kadai ya san soyayyar dake tsakaninsu. Dole shima ya sauke nasa kan, domin ya fita jigata. Suka koma suka dinke kamar super glue, sai dai duk da haka bai kara yi mata zancen Rayhanah ba. Ita ce dai abin ke cin ranta tana kuma tsoron tambaya, idan ta tuna korar karen da ta yi mata. Cike take da fargabar ina yarinyar ta fada? Har Khalipha ta tambaya ya ce wallahi Allah bai sani ba, Daddy bai kara yi masa zancenta ba. Cikin Mami ya kara durar ruwaa lokacin.Cike da alhininzuwan ranar da Baba Dacta zai gama miskilancinsa ya tsuye ta ta fito masa da Rayhanahr da ya bata amana, me zata ce masa? Shi Khalipha yanzu shirin taren Babynsu suke yi Mimtaz haihuwa yau ko gobe. Zuwan Ibraheem Abuja unexpected haka ya gigita Khalipha, wata irin runguma suka yiwa juna har saida suka kai kasa, dukkanninsu babu wanda bai zubar da hawaye ba, inda Mimtaz ta cika da mamakin to kukan me suke yi? Na farin ciki ne ko na mene ne? Su kansu basu sani ba Shi dai Ibraheem kewar da ya yi ta shekara goma ta Khalipha ita tasa shi kukan, duk da cewa Khaliphan ya sha kai wa Ibraheem din ziyara wajen sau hudu, sai kuma farin cikin ganin kyakkyawar rayuwar da Khalipha ke ciki da matarsa ‘yar’uwarsa Mimtaz har ga albarkar aure na shirin fara zuwa. Duk yawancin hirarsu a kan dangin Khalipha ne na Hurghada da yadda ta kwaranye tsakaninsu da yake Ibrahim ya san Khalipha step-brother dinsa ne tuntuni. Shima ba Mami ce ta gaya masa ba Uncle Yohan ne, amma bai taba nunawa Khaliphan ya sani ba, don ya san Khalipha bai sani ba. Sun hana shi kwana a otel yana dakin saukar bakin gidan Khaliphan. Mimtaz duk da nauyin da ta yi ba ta kwanta ba, girke-girken Egyptians kala-kala take shiryawa Ibrahim, irin su Kushari, Mulukhiyah, Ful-Medames, Fatta, Feseekh da Tarokolacasia Soup da sauransu. Kuma Ibrahim din is appreciating ya samu canjin yanayi, canjin abinci da canjin atmosphere. Ya rabo da kankara da dusar ta. Haka kawai cikin ransa ya ji ba zai iya komawa Chicago ba, weather din kasar Nigeria ta yi mishi dadi. Sanyin is not too much da an sa rigar sanyi ko an rufa da bargo shi kenan, zafin idan kana da A.C a gidanka da motarka da ofishinka, to ba za ka san ana yin shi ba ma. Rayuwar Khalipha da iyalinshi ta burge shi, ta kuma kara kwadaitar da shi son aure. Goyo ne kawai Khalipha baya yiwa Mimtaz, ko abu zai bata sai ya russuna, ko faranti ta dauko sai ya mike da sauri ya amsheta ya hau fada kamar zai ari baki shi meye amfaninsa? Girkin ma da take yi kusan shine ginshikin aikin, illa tana instructing din sa tana zaune daga kujerar da ya kafa mata a kicin..... zuba kaza adadi kaza yanka kaza..... fere kaza ka zuba....... to motsa shi sosai ya hade jikinsa...... cakuda shi da wannan, markada wannan ka juye a ciki..... haka dai har a gama. Ibraheem na jiyowa daga falo yana ta dariya, duk da bai fiya yinta da tsayi ba. Lallai soyayya ta yi, don dai shi bai taba ganin kafar Khalipha a kicin ba tun tasowarsu, don Mami ba ta saka su. Amma yau ga Khalipha ya zama kwararren Egyptian-chef (kukun-Masar) saboda iyalinsa, ya sha Apron da zungureriyar hular Larabawa ta girki, Apron din ma fari ne tas irin nasu suka taho da abinsu daga Hurghada. Ko ofis Khalipha ya tafi baya barin kunnuwan Ibraheem su huta da waya, wai ya leka ya gano Mimtaz kada nakuda ta zo basu sani ba. Haka zai yi ta zarya daga dakin baki zuwa falon Mimtaz don cika umarnin babban yaya, ya ganta tana waya da carkwadeden Larabcinta ko tana cin abinci ko tana kallo ya koma ya gaya masa. Ranar da zai koma Kano wato ranar da ya cika sati guda a Abuja, ko da yake zaman shi a Abuja da dadewarsa cikin ta, ba wai kawai saboda Khalipha bane, transferring komai nashi yake yi daga Chicago zuwa Nigeria. A ranar da ya samu wayar Mami wato ranar da ya cika sati guda inda take sanar da shi Daddy ya dawo, a ranar ne Mimtaz ta haihu, yaro namiji kamar Mami ta yi kaki ta tofar ko farin iyayen bai debo ba, lafiyayye katoto sai suma mai yawa da ta cika kansa. Ibraheem ne ya karbi haihuwar har dinki shi ya yi mata. Ko asibiti sai daga baya suka je aka duba lafiyarsu itada jaririn komi normal, suka sallamo su gida bayan an yiwa yaro takardar haihuwa. A daren ranar su Khaliphan ma tareda su gaba daya suka kamo hanyar Kano duk da magariba ta yi. Gudu yake shararawa dasu a kan titin da zai kawo su Kano daga Abuja cikin lafiyayyar motar Khalipha‘Ferrari has come....., shi ya zama direba domin Khalipha na kankame da jaririnshi a baya ya hana Mimtaz da jaririn sakat wai lallai sai ta yarda jininsa ya fi nata karfi, da kamar Mami ce ta haife shi Ita dai Mimtaz murmushi take saboda tana kunyar Ibraheem,saboda bata saba da shi ba, har rokon Khaliphan take yicikin Larabci don Allah ya matsa gefe Uncle Ibrahim na jinsa. Ya ce, “An ki a matsa din”. Da turanci yadda Ibrahim din zai ji sosai. “Idan ya yi zuciya ya kwato matarsa daga duk inda Daddy ya boye ta shekara mai zuwa su haifi nasu babyn, in yaso ya matsa gefen daga jikin matarsa”. Shi dai Ibraheem murmushi yake yana jinsu yana tukinsa cikin nutsuwa, cikin ransa yana cewa, “Au boye matar tasa Daddy ya yi? To shi ina ruwansa in ya ga dama ya ba shi in ya ga dama ya hana baya cikin matsuwa a kan wannan auren da Daddy ya yi masa da bai san da sunan da zai fassara shi da shi ba, left or right (hagu ko dama) duk ta inda Daddy ya bullo dashi ta nan zai karbe shi. Sai dai Allah yasa ba mai ragunta bace irin Mimtaz, ihu da kururuwar da ta rika yi lokacin haihuwa ya rika tunawa. Da ya dauko allura ya zarga zaren dinki ta tabbatar dinketa zai yi kamar kwarya, ai sai ta gyagije ta daka tsalle ta fado daga gadon kamar ba ita ce katoton Da ya fado daga jikinta ba yanzunnan. Tayi bayan Khalipha tana kururuwa sai da suka hadu shi da Khaliphansuka sa mata karfi tukunna. Tunnin da yake ta yi kenan yana murmushi shikadai yana jin shakiyancin da Khalipha ke masa. “Ya daina cika miki ido kina daukar shi maigida sama dani, duk wannan tsare gidan nasa za ki yi mamaki ranar da za ki je gidansa ki ganshi yana wanke-wanke da canzawa baby diaper. Hura hancinsa ya daina razanaki irin su in sun tashi tasu soyayyar Alkur’an mata suke komawa”. Mimtaz ta rufe baki cikin kidima ta toshe masa baki da lallausar tafin hannunta, “Ka yiwa Allah ka yi shiru Yaya Khalipha, akwai girma da kimar Dacta Ibraheem da yawa a idaniyata”. Khalipha da Ibraheem basu san sanda suka sa dariya ba saboda yadda ta yi maganar tsakaninta da Allah da darajjawa mai yawa cikin murya da idanunta. Sun shigo Zaria take tambayar Khalipha cikin rada, “Matarsa baka ce ko fara?” Allah ya yiwa Ibraheem ji mai karfi, saboda cin gasasshen nama, don haka Mimtaz ba ta san ya jita ba. [12/25/2019, 19:13] Takori: Khalipha da ba a sirri da shi ya kara rungume wankan tarwadan jaririnsa ya ce da karfi yadda Ibraheem zai ji, “Yadda yake baki, haka take baka sidik. Aradun Allah nawa jaririn zai washe kwana biyu idan ya fara shan nonon farar mace, amma ‘ya’yan IBRAHEEM da RAYHANAH sai an rufe ido don muni. Ni wannan yaron ma ba don ina son mai da shi little Mansur ba, ai Ibrahim zan sa masa tunda ya nuna min da shi yake uban ba dani ba”. Ibraheem bai tofa musu ba.......ya yi nisa a cikin tunanin kalmar da Khalifa ya ambata...... RAYHANAH! RAYHANAH!! RAYHANAH!!! A ina ya taba jin wannan sunan???????? So Khalipha na nufin sunan matarsa Rayhanah.... kamar ya san sunan..... tabbas ya taba jinsa.....amma a ina? Ba zai iya tunawa ba. Shekaru masu yawa sun shude, abubuwa da yawa sun shude, wasu kuma da yawa sun shigo in one’s life journey of struggle toward achievements........ ya takurawa kwakwalwarsa da umarnin ta tuno din, amman ga dukkan alamu ta kasa! Sabida yawan sababbin abubuwa da al’amuran da aka dura mata cikin shekarun da suka gabata din. A dai-dai garin Tiga sitiyari ya kwace masa motar ta yi jeji....... cikin wani mugun zafin nama ya kama akalarta ya maida ta kan titi. Dukkanninsu sai da suka jirkito don ma Allah yasa da belt a jikinsu. Sannan yadda Khalipha ya kankame jaririnsa bai kankame Mimtaz haka ba. Wuta ta daukewa Khalipha da matarsa, tabbas yau sun ga mutuwa kusa. Sai Khalipha ya sassauta murya ya ce “Man! Am not ready to die now. Life began at fourty....” Murmushi ya yi, wani irin murmushi mai nufin amsoshi da dama ga statement din Yayansa Khalipha. Shi kansa ai bai son mutuwar yanzu, gara Khalipha tunda shi har ya ajiye mai yi masa addu’a. Shi me ya cimma a rayuwar? Just his proffession...... Akwai sauran bukatun sa masu muhimmanci bayan wannan..... SOYAYYA..... AURE.... ‘YA’YA.... TARBIYYAR ‘YA’YA..... son binciko hakikanin ko wace ce JUMAH!. A kalla ko ya karbi auren da Daddy ya ke ikirarin yayi masa, yayi alfarmacikin dimbin alfarmominsa da basa karewa agareshi, ya kara masa da ita. Muryarta kawai ya ji.... amma ta tabo wani al’amari mai girma a can tsakiyar zuciyarsa. Zai iya hakura da son bakin Sapna, ya kara da JUMAH NURSE. Wata bakuwar halittar da bai taba gani ba data shigo cikin rayuwarsa in an era of global communication...... (waya), ga auren iyaye mai albarka, ga kuma na son rai, wanda zai karairaya akidar nasara ta zama da mace daya dake zuciyarsa zuwa karbar na sunnah (polygamy) na Musulmi, musamman Bahaushe. “To an taba son mace ba a ganta ba Ibraheem?” Zuciyarsa ta jefo tambaya. “Eh.....” Shima ya ba ta amsa. Akwai wani abu “Soyayyar zuciya” da ba ido ne yake gani ba. Ita wannan soyayyar Allah ne yake yin dalilinta ba ido ba, wanda ke gina tashi soyayyar akan kyawu ko (personality). Wato kyan mace da yadda Allah ya suranta ta ko halinta da dabi’unta. Shi soyayyar zuciya kuma, zuciya ce take so da gangar jiki gaba daya. Wasu daga cikin physical parts (bangarorin jikin dan adam wadanda Allah ya halicceshi dasu) su suke so ba ido ba........ sune..... - ZUCIYA (tana son kullum ta yi ta tunanin wannan mace). - KUNNE (yana so kullum ya ji muryarta). - HANNAYE (suna so su kai kansu gareta). - BAKI (yana so ya sumbace ta) - KWIBI (pelvic girdle) zuwa kafafu (suna so suyi exceptional tarayya ta har abada da ita (sexual need). -Dr. Norman Vincent Peale (American Psychologist) -SegmundFreud (Sociologist/Psycho-Sexual Analyst....) Wannan shine tunanin Ibraheem, tunanin da ya kusa shekawa dasu jeji su karairaye da dan kyakkyawan jaririn da Allah ya basu. Suka dauki buri mai yawa suka dora a kansa, musamman hope din ya gaji suna da halin mutum mai daraja da martaba a garesu (Muhd. Mansur). Karfe tara na dare suka shigo Kano suka doshi Lamido Crescent. Malam Dahiru ya wangale musu kofa suka shiga. Daddy, Mami, Jawahir, Abida (babu Azizah) suke cin abincin dare tare bisa tebir cikin raha da annashuwa mai yawa wadda su kansu sun mance tun yaushe rabonsu da hakan, a kalla za su iya cewa, tun kafin Khalipha ya ce yana son Rayhanah, soyayyar da ta wargaza musu gida da duk wani farin cikin dake cikinsa. Ibrahim Mansur da Khalipha Abdullahi Mansur Takai, Matasan Maza masu wata irin baiwa ta zati da kamala da wani kwarjini na daban daga Indallahi, suka yi sallama cikin muryoyinsu na kasaita, Balarabiyar surukar na biye dasu, Ibraheem rungume da jariri. Gabadaya daga ‘ya’yan har iyayen mikewa tsaye suka yi, suka gigice suka rikice da murna. Yau ga Yaya Khalipha ga Ya Himu......... ga baby da rabon da su same shi cikin gidansu shekara a kalla goma. Rige-rigen karbar baby ake tsakanin ‘ya’yan da iyayen, ba wanda ya bi ta kan bakuwar fuskar sai Jawahir, ita ta nemota ta rungume, ta yi mata jagora zuwa tebir dinsu tana zuba mata lemo. Sai da kowa ya dau baby sannan hankali ya dawo kanta. Daddy da Mami “Sannu Mimtaz”. Suke jera mata ba kakkautawa, kanta a sunkuye tana dan murmushi. Ai a take Mami ta mike ta soma shirin jego, abincin da ba ta ci ba kenan. Su gidansu basu gina shi da safayan daki ba, don basu bukatar bakin kwana. Don haka Mami a dakinta ta sauki Mimtaz. Nan da nan ta yiwa kuku waya ya zo, ta lissafo abubuwa masu yawa na fannin kayan abincin da mai haihuwa take bukata. Ta hada mata ruwan dumi da dettol ta sanyata a ciki, ta dauki baby ta soma wanke shi sai da ta yi sabi uku tana canza ruwa. Ta shafe shi da olive oil ta sunke shi cikin kayan sanyi farare kal masu kamshin turaren baby mara karfi. A sannan ne bawan Allah ya soma atishawa. Mami ta hau fada, “Hala A.C kuka kunna a motar ko tagogi kuka bubbude?” Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba a kan Himu da Khalipha. A.C din gidan ma kashe su ta yi duka kowa ya hakura, ayi jegon tare da shi. Daddy na ta yi mata dariya da zolaya. “Ba saban ba! Ni Asma’u na zama kaka”. Ai kowa sai da ya dara. Da Ibraheem ya ji gumi ya fara jika shi sai ya hakura da cin abincin ya yi ta kansa (ya shige dakinsu tun na kuruciya da samartaka ya kure A.C) ya yi kwanciyarshi yana hutawa, zuciyarshi babu sukuni ko kadan, ta cunkushe da tunani. To wai ina matar da aka aura masan? So ake sai ya tsaga billensa ya tambaya? Ai da nauyi, Daddy na son ja masa rai ne kawai ya wahalar da shi. Shikuma wallahi tunda haka ne ko za’a shekara bazai tambaya ba. Shima fa yana so ya ga irin wannan farin cikin da tarairayar a fuskar Daddy da Mami a kan nashi iyalin. Da ya ga tunanin na damunsa sai ya kira Sapna suka shiga hirarsu, tana gaya masa kewarsa da take ciki, yaushe zai dawo? Kai tsaye ya ce, “Sapna na dawo gida kenan mahaifina ya yi min aure!” Wannan ita ce kalma mafi muni da Sapna ta taba ji a rayuwarta. Ji ta yi kamar ya caka mata mashi a kahon zuci. Sai ta fara yi masa kuka mai girgiza zuciya, ya yi saurin kashe wayar, domin ji ya yi banda ya rungumeta ya rarrasheta ba abin da yake so ya yi. Ya soma tambayar kansa anya Allah ba zai tuhume shi da hakkin Sapna ba? Ya riga ya mai da ita emotionally disturbed zai yi wuya ta iya fiddashi daga rayuwarta farat daya. Shima zai dade bai mantata ba a sabuwar rayuwar da ya bude yanzu. Yana rokon Allah ya yafe masa itama ta yafe masa a kan turbar da yasa Sapna, ya gudo ya barta. Duk da ya san bai taba keta mutuncinta ba, amma yana rage zafi da ita. Ita kuma tana ba da kai ne saboda son da take masa, da kuma tabbacin da take da shi na zai aure ta. ‘Yan’uwana mata musamman ‘yammata ku gane, ku hankaltu kusan irin sarrafawar da za ku yiwa soyayyar saurayi a zuciyoyinku, don maza, musamman yara irin Ibraheem masu tashen naira da kuruciya da zurfin ilimi, wallahi ba kowacce mace suke aura ba, sai innocent. Za su yi soyayyar wucin-gadi dake ne kawai don amfanin kansu a dan lokacin da suke bukata, in sun gama abinda ya kusanta sure dake su tsallake su barki su nemi ‘yar mutunci mara kyale-kyalen duniya da budadden ido su aura. Yarinya danya jagab wadda ba ta kai shekaru ashirin ba ke kuma (used and dumped)Sunanki. “Bye-Bye Sapna........!” Ibrahim ya fada a hankali, wasu hawayen tausayi da sabo cike da idanunsa. “Ni da Illinois (Chicago) watakila sai da yawo”. Abin da yake fada cikin zuciyarsa kenan. ***** Jego sosai Dr. Asma’u ke wa Mimtaz, tana gasa mata jiki da tawul kullum sau hudu a rana, ta sanyata a ruwan dumi sau uku. Har edcuse ta dauka a wajen aiki don an maida ta Murtala Mohammed Specialist Hospital kamar yadda ta bukata, domin raba kanta da duk wata alaka da Dr. Halima. Tana jin yadda ake fadin irin zagin da Haliman ke mata da tonon silili daga bakin Nurses din da suka yi zaman aminci da ita, da mugun alwashin da ta dauka a kanta na sai ta rabata da Dr. Mansur ta aure shi. Wai ita tsohuwar arniyar Jos ce tubabba kuma ba a budurwa Dacta Mansur ya aure ta ba har da dan shege da ta so ta yi kuskuren lakabawa ‘yarta Allah ya cece su. Ire-iren abubuwan da suka tsorata Dr. Asma’u kenan ta bar AKTH don ba ta iya tashin hankali a rayuwarta ba. Ta soma nemawa kanta tsarin Allah daga sharrin mutum da aljan. Ta rage barci kullum sai tsayuwar dare duk da dai hidimar baby Mansur ba ta barinsu suyi barcin kirki daga ita har Mimtaz din, ga shi da kukan dare, ya wuni sur lafiya lau yana barci dare na yi ya bude musu murya ya gigitasu, nonon ma ya ki sha sai kuka, har su Jawahir kwana suke a kansa suna miko wannan suna miko wancan. Dr. Asma’u ta soma bincikensa da kyau, inda ta gano kashi ne baya iya yi da daren saboda tsutsar ciki, sai ta fara treating dinsa da antibiotics masu sa cin abinci, don ko nono da ruwa in dare ya yi baya amsa da sauran magunguna masu kashe tsutsar ciki da narkar da abinci da taimakawa digestive system. Sati bai zagayo ba yaro ya yi ras, cikin koshin lafiya. Tuni Khalipha ya koma bakin aiki ya barsu a gidan karkashin kulawar likitoci har uku, uwa da uba da brother. Ai kuwa cikin wata daya baby Mansur ya zama garjeje dagawa da kyar, goyawa da dan banzan nishi, domin Azizah da ta zo hutu daga Turkish kasa daga shi ta yi. Ita ma mai jegon ta zama sambaleliya mul-mul da ita, sai ka ganta cikin su Jawahir ta takarkare wai tana koyon Hausa za ka ci dariya, sun saba sosai, ta soma koyon amma namiji shine mace, mace ita ce namiji a bakin Mimtaz. Sai ta cewa Jawahir “Dauko Mohd Mansur ki canza mata audugar nan (Pampas).....” Sai su kwashe mata da dariya sai da Mami ta tsawatar. Ibraheem a nashi bangaren, ya zubawa Daddy ido kamar yadda Mami ta zuba masa a kan aurensa. Tunda ya zo ko da subutar baki Daddy bai yi masa zancen matarsa ba, amma fa yana ta janshi a jiki cikin kauna da kulawa. Ya kuma dauke shi a yau ya sada shi da gidan da ya mallaka masa shi da Khalipha a Farm Center, ya bar dakinsu na gidansu ya koma gidansa, shi Daddyn bai zauna ba har yau ya kwashi takardun Ibrahim ne ya mikasu federal. Abin da bai sani ba, kuma miskilin dan nasa bai gaya masa ba, shine cewa ‘nephrology associates’ da sauran ‘medical associations’ da yake ciki suna ko’ina a duniya za kuma su ba shi aiki dai-dai da matsayinshi a (Illinois Teaching Hospital) Chicago sai inda ya zaba. To zaben ne har yanzu bai yi ba, saboda basu zauna da Daddy ba har yau ko ko ya ce Daddy bai ba shi fuskar ya furta masa damuwar tashi ba. Babu zancen da yake masa sai na aiki kamar wani inji babu hutu babu mata babu budurwa saboda shi karfe ne, kullum ya yi ta hada shi da voluntary jobs wato aikin sa kai na neman lada ga marasa karfi masu cutar koda a Najeriya da basu da karfin fita waje kamar wani inji. To ya daina zuwa AKTH, Abdullahi Wase, Murtala Mohammed daga yau zai yi kwanciyarsa a gida ya huta, Daddy ya yi ta boye matar zai koma ya auro Sapna. Wani abin dariya Ibrahim ya tambayi Daddy rannan suna kan hanyar zuwa Abuja. “Plz Daddy wace ce Juma da ta amsa wayata lokacin da ka bar wayarka a office ta amsa kirana?” Daddy ya ce, “Au Juma? Ai ba a ofis bane na bar wayar a gidanka ne. Ita ta amsa ma wayar?” Ya ce, “Eh”. Cikin fargaba ya ce da Daddy, “Don Allah Daddy zan iya ganin hoton ta?” Fuska a sake Dacta Mansur ya ce, “Why not?” Ya yi parking a gefen titi ya fiddo dalleliyar wayarsa yabude gallery ya fiddo hoton Inna Juma da ya taba daukanta ita kadai lokacin da za a yi mata passport din tafiya Singapore ya nuna masa. Ibrahim hannu na kyarma jiki na tsuma ya karbi wayar ya duba. Me Ibrahim zai gani? Wata bakar tsohuwa ce da a kalla ta ba saba’in baya, ta sha dauri da Adiko ta kawata idonta da farin kwalli ta yi ras!. Haba! Ai ba shiri Ibrahim ya jefa wayar Daddy a kan titi yana haki kamar wanda ya tiki gudun cetar rai. Ya ja bakinsa ya yi shiru kirjinsa na ta bugawa.. Daddy ya bude murfin motar ya dauko wayarsa har ta tsage tawargajeakan titi, ya kuwa ce da wa Allah ya hada shi ba da Ibrahim ba. Fadi yake, “Wane irin wulakanci da iskanci ne wannan? Ba kai ka ce in nuna maka hotonta ba? Don ka ganta talaka sai ka wulakanta hotonta har ka fasa min waya? Ka ci gidanku, ka ci kaniyarka.Wannan tsohuwar mai daraja ce a wajena.....” Shi dai ya yi gum da bakinsa ya rasa inda zai sa kansa da mamaki da takaici. Tsohuwa ce da muryar danyar yarinya har da Turanci? Saboda bakin ciki har suka zo Abuja bai kara yin magana ba. A lokacin Khalipha da iyalinsa sun tafi Hurghada har da Azizah da Jawahir da Abida za a kai wa dangi Muhd Mansur su ganshi. Ya iya zama har da kokarin mikewa bul-bul da shi a lokacin watanninsa hudu. Kamanninsa da Mami da duhun fatarsa basu canza ba da ka ganshi ka ga half caste, very cute da shi. Yau kwanan Ibrahim Mansur goma a gidansa na ( Farm Center ) wanda ya yi dai-dai da cikar sa watanni na hudu a Nigeria, bai taba damuwa da wai ya shiga daki-dakin dake a kulle ya ga yadda suke ba, iyakancinsa ya shigo ya wuce bed room dinsa ko ya zauna a falo ya kalli labaran tara ko CNN. Amma a yau Asabar kulle wayarsa ya yi ya kuma kulle kansa a gidan kada Daddy ya neme shi ya hadashi da aikin dashen kodar nan. Shima tashi ba ta da lafiya it's now weak and delicate to such an extent that it fails to perform its normal functions properly, in zasu dasa mishi mai kwari shima yana so. Daddy yana wujijjiga shi, ba don ubanshi ne ma ba cewa zai yi rainin hankalin ya isa. “I need a life partner, ina sha’awar rayuwar Khalipha, ina bukatar mace, I’m at the Zenith of my thirty (30)”. Abin da yake fada kenan cikin zuciyarsa, yana daga kwance ciki sofa din dake gefe guda a mayalwacin dakin barcinsa, pjamas ne kawai a jikinsa ruwan toka, wadanda basu rufe faffadan kirjinsa ba. Lallausan gashi ne baki sidik kwance luf a kirjinsa. A wannan lokacin Ibrahim rufe idonsa ya yi, muryar yarinyar da ta kira kanta da (Jumah) ta soma amsa kuwwa a kwanyarsa. “Dacta ba ya tare da wayar fah..... Dacta is not yet at office.......” Ya Allah! Wannan wane irin bala’i ne ya same ni? Dana sani da ban yi maka waya ba....... watakila aljana ce ta yi min magana ta dasa min wannan bala’in. Bari kawai na mai da kaina busy na yi sanitary ko na samu sa’eedah. Da nashi dakin ya soma, ya canza bedsheet ya hada kayan wankinsa cikin kwando ya turasu laundary ya goge ko ina ya fesa insecticide ya kullo dakin. Yasa injin shara yana zuke kurar (center carpet) dake tsakiyar wawakeken falon. Yasa duster ya karkade kujerun da plasma da sauran tarkacen kayan lantarkin dake dakin. Sai ya koma daya dakin dake bude wani bedroom din ne shake da kayan wasan yara da gadajensu da study table na yara da katifu, kekuna, babur, toys, teddies da ‘yan tsanoni masu aiki da batir. Sai ya samu kansa da yin dariya, dariya mai yawa da ya dade bai yi ba, ya kara kaunar mahaifinsa. Komai ma sabo ne ba a fiddashi daga kwalinsa da ledarsa ba, don haka dakin baya bukatar wani gyara amma duk da haka sai da ya sharo yana ya fesa Rambo. Daki na karshe wanda shine a kulle da mukulli sai da ya yi ta gwada bounch of keys sannan ya samu guda ya bude. A nan ne Ibraheem ya daskare cikin mamaki. Ibrahim na da masaniyar cewa, wannan gidan da Dacta ya mallaka musu, gina shi ya yi ba sayen shi ya yi a gine ba, don kafin a fara ginin ma sai da ya nemi Ibraheem din da ya turo sample na irin ginin da yake so. Shi ya turo samfur daga San Francisco da Daddyn ya yi amfani da shi, don haka bai sa ‘yan haya ba. Zai rantse shine mutum na farko da ya fara kwana a gidan, amma wannan dakin ya karyata haka. Daki ne yalwatacce mai dauke da fararen Italian furnitures, ga bargo ba a ninke ba, ga kayan kwalliya da turarukan mace da su deo-spray a jere a kan mudubi, a gefe ma wasu jakunkuna ne shake da kayan ado na mata sababbi da alama ko sa su ba ayi ba, ga braziya da pantis farare kal an wanke an shanya a bayi (toilet) ba’a kwashe ba, ga su brush da maclean da turarukan wanka har da audugar mata (pad), da alama an cira ne an aje ragowa ba sabuwa ba ce. Ibraheem kidimewa ya yi da tsoro, firgici da mamaki don ya tabbatar kam ba shi kadai yake kwana cikin gidan nan ba, duk da bai taba jin motsin dan adam a cikin gidan ba. Tabbas akwai aljana a tare da shi, amma fa yana son kamshin dakin aljanar nan idan ma aljanar ce. Sai ya zauna a bakin kyakkyawan gadon ya dauki bargon yana sunsunawa, kamshin is cool..... sai ka sunsuna za ka ji. Ji ya yi tsoron ya fice daga zuciyarsa, ya samu kansa da kwanciya sosai a gadon ya ci gaba da shakar kamshin yana kara nazarin dakin. Kaya baja-baja a warwatse ga takalma flat da masu tsini masu kyau da jakunkunansu ‘yan gidan Micheal Kors, Nordstrom, Replica, Cloe da Harrods cikin wata jaka ko sa su ba a yi ba. Ya ce a ransa, “Cikin aljanun ita wannan ‘yar gaye ce, tunda har irin kayan Sapna take amfani dasu”. Nan Ibraheem ya lalace a dakin ya kwana, a dakin ya wuni, sallah ke ta da shi da shaye-shayen lemuna da madarar dake dankare cikin firjin dake gefen gadon. Sai da suka nemi karewa yaje store da zummar karo wasu. Tunda ya zo gidan ma bai leka kicin ba, don a koshe yake shigowa barci kawai ke kawo shi sai ruwa da jus da madara yake sha a nashi dakin. A kicin din ma ya kara tsinkewa da lamarin aljanar gidansa. Tukwane a wanke kal-kal an kife su komi tsaf, amma fa ga potatoe ya rube har ya yi tsutsotsi yana ta wari har ya soma busar da kansa. Da ya bude firij sai ya ja da baya cikin dan tsoro yana fadin “Subhanallahi.....!” Kifi ne, nama ne, markade ne, kaji ne duk gasu nan sunyi kankara sun kankare kamar duwatsu. Ai da azama ya fito ya bude kofofin da ya kukkule ya zari mukullin mota ya yi asibitin da yake gudu don ya gayawa Daddy ba zai zauna gida daya da mutanen boye ba. In ba zai barshi ya zauna kusa da uwarsa ba to zai koma inda ya fito. Daddy yana seminar-room da likitocin bangarensa gaba daya wadanda suke karkashinsa, meeting suke yi mai muhimmanci a kan sabuwar cutar da ta iso Nigeria ‘Ebola’. Ibraheem ya fado dakin tattaunawar babu ko sallama, kwarai a firgice yake kira yake “Daddy-Daddy.....” Gaba daya likitocin sama da talatin suka maida hankalinsu da idanunsu gare shi. Ba ta tasu yake ba sai da ya isa jikin mahaifinsa ya rungumeshi jikinsa yana kyarma yana fadin “Wallahi ba zan koma gidan nan ba, in ba auren za ka bani ba to zan koma Chicago, I’m exetremely perplexed.......” [12/26/2019, 13:19] Takori: Hannunsa Dr. Mansur ya kama sannan ya manna shi a jikinsa ya dauki excuse suka fito yana jaye da hannunsa yana yi masa magana cikin lallashi. “Kwantar da hankalinka gaya min me ya faru?Ka ji Ibrahimu?” Ya rungume shi sosai a jikinsa don ya samu nutsuwa, yana jin yadda yake sauke numfashi da sauri. Sai da ya nutsu ya ce, “Muje kawai Daddy ka gani da idonka”. Daddy ya ce, “Ba zai yiwu ba, baka ganin meeting muke yi”. Ya ce, “To bari in jiraka a ofis dinka ka je ku gama”. Ya ce, “Alright”. Mintuna arba’in Dr. Mansur ya yi kamin ya dawo. Shi ya karbi tukin suka nufo Farm Center, Ibraheem ya kame bakinsa ya yi shiru. Daddy ne ya bude gidan da kansa don Ibraheem baya-baya yake yi. Ya kama hannun Daddy zuwa bedroom din ya shiga nuna masa. “Ka gani, ka gani....... akwai spirit a cikin gidan nan”. Yana nuna masa kan mudubin, ya kuma ja shi ya kai shi toilet yana nuna masa su (Pad) har da guntun sabulu dasu maclean din da aka yi amfani da rabi. Ga jakunkuna da takalma ga su brazier, sannan ya ja shi kicin ya kai shi ya yi ta nuna masa, da gaske a rikice yake kamar yadda ya ce dinne...... “He is perplexed.....” Sai a lokacin Daddy ya soma fahimtar me ke faruwa, me Ibraheem ke son ganar da shi? Dariya ce ta kulle masa ciki yana ta kokarin hadiyeta a cikinsa. Ibraheem ya ce, “Na taba tambayarka wace ce Jumah, ka nuna min wata tsohuwa. Ni kuma tabbas na yi magana da wata yarinya mai suna Juma duk da na san sunan tsofaffi ne, amma wallahi Daddy ni da (fresh girl) na yi magana. Ina jin aljana ke son aure na. I cannot live in this house anymore...... sai ranar da Allah ya bani iyali........” Yadda yake maganar ya bala’in baiwa Dr. Mansur tausayi. Ya ji wani abu ya motsa a zuciyarsa, ya kamo Ibrahim ya jingina a jikinsa. “Wace ce ita Juma din?” “Nurse din ofishinka”. “Ce maka ta yi a ofishina take? Yaushe akai hakan?” Ibraheem ya ce, “Wayarka na kira ta dauka, bayan nan ma mun kara magana, har ta tambaye ni wai don Allah nine Ibraheem? Kafin in ba ta amsa wayarta ta mutu. Kuma wallahi da layinka Daddy”. Sai a nan Daddy ya gano komai, ya tuna randa ya manta wayarsa a gidan. Ya gane Rayhanah ce ta amsa mishi waya ta ce sunanta Juma, kuma ya ga received calls na Ibrahim amma bai bi ta kansu ba. Sai ya ce da Ibraheem, “One minute...”. Ya shigatoilet din Rayhana ya yi dariya ya koshi sannan ya fito. Ibraheem ya kulu ya kumbura, don ya gane Daddy abin dariya ya dauki abin. Ganin yanayin da yaron ke ciki sai ya zama serious. “Kwantar da hankalinka Ibraheem...... ba wata ba ce mai suna Juman, RAYHANAH ce MATARKA!!!” ****** Ya dago fararen idanunshi da sauri ya dubi mahaifinsa. Babu alamar wasa a tare da shi. Ya ci gaba da cewa, “Ko da yake a da ne take matarka, amma na dade da yanke shawarar raba auren zan yi, tunda baka yi na’am da zabina ba, ka mai dani ba komai ba a idanun Rayhanah da kakarta Juma”. Wannan karon da firgici ya dubi Daddy....... “Kakar tata ce Juman?” Daddy ya daga kai. “Wannan kuma dakin da ta zauna ne shakara guda tana dakon auren ka”. Ya kara kallon Daddyn sosai, “Me yasa ka yanke shawarar raba auren Daddy? Da bakina ban ce maka bana so ba”. “Kana so ka wulakanta ni? Rimi-rimi muka yi magana, ka ce da amincewarka in aura maka wadda zuciyata ta amince da ita, baka da zabi a auren fari. Cikin girma da mutunci da bacin ran mutane masu yawa aka yi auren nan, na dauko yarinya na kawo ta gidanka ni da Yaya Abdulkadir cikin mutunci da mutuntawa. Tun daga ranar Ibraheem baka kara nemana ba, idan na neme ka baka amfani da layin. Yarinya na ta hakuri har kakarta ta damu, ta nemi da a raba auren. Amma Rayhanah ta zabi ta rabu da kakarta har abada ta ci gaba da dakon aurenka har karshen rayuwarta. Koda har abada bazata ganka ba. Ba don kai ba, ba don ta sanka ba, ba don tana sonka ba sai saboda darajata. Karewa ma da Khalipha ne zai aure ta uwarku ta wargaza lamarin. Wai ni mai DA, wanda nake da yakinin na isa da shi, kuma shi mai share min hawaye ne a kowane lokaci na bukata, na baka auren Rayhanah don dama can kai na fi yiwa sha’awarta saboda na san za ku zauna lafiya tunda halayya da dabi’unku daya. Ibraheem da me na tsira a wannan gatan da na yi maka? Sai kunya da na sha da yake da neman yadda zan yi in rage mata rayuwar kadaicin duk da bai dameta ba sai kakarta. Don haka me ya yi zafi? Rayhanah ba rasa mijin aure ta yi ba. Ban ba ta wannan damar bane, da ka ga dama ka zo ko sau daya baka taba tambayata lafiyar matarka ba, kana jira sai na tallata maka ita. Na kasa ta a fai-fai na ce Ibraheem dauki? To ka yi kadan, uwarku ta yi kadan. Ungo wannan.......” Ya ciro takarda a gaban kwat dinsa ya zaro biron dake makale jikinsa ya mika masa, “Yankewa Rayhanah igiyar auren nan ko guda daya ce ta huta”. Idanun Ibraheem suka cicciko da kwallah. “Daddy kada mu yi haka...... kada mu yi haka...... saurareni ka ji uzirina tukunnah....” “Zan saurare ka kadai bayan ka rubutawa Rayhanah saki ko guda daya. Wane uziri ke gareka? Ni ka ga tafiyata, kada ka sake ka zo min gida in ba takardar Rayha ka kawo min ba, babu gardin da zai zauna min a gida, ‘ya’yana sun girma kuma duk mata ne. A toh! Allah ya bamu alkhairi”. Ya juya ya fita yana kara fadin, “In ma aljanar ce za ta aure ka ku yi ta auren, kai ta ga ka yi mata, tunda tuzuru ne, sama da shekara talatin babu mai kiranka saurayi, ba Khalipha mai iyali abin burgewa ba”. ****** Juyi yake a matsakaicin gadon, lullube cikin zanin atamfar Rayhanah. Sai yanzu ya gane turaren ba wani bane ‘Makhmariyyah wa lamsa nectar’ ne wanda ake durawa a wani kanti a Jiddah. Shima Sapna ce ta gaya masa wata rana yana rungume da ita yake tambayarta wane irin turare ne mai sanyi da kwantar da hankali ta shafa a tufafinta haka? Me yasa take amfani da abubuwa irin na Sapna?Is it a coincidence or what? (Arashi ne ko minene?) Ta san abubuwan da yasa yake son Sapna har da ire-iren wadannan abubuwan? Gayun Sapna cool ne and cooly ba na tashin hankali ba. She's a designer baby. Tukunna ma, wace ce Rayhanah? Shi fa ya san wannan sunan, amma ya manta inda ya san shi. Ko Daddy zai tsire shi, ba zai taba yin sakin nan ba, ko ba don ji da ya yi ita ce Juman da ya so a murya ba, sai wannan furuci da ta yi na cewa za ta jira shi da aurensa har abada saboda Daddy. Koda har abada bazata ganshi ba. Ba don komai ba sai don cewa duk mai darajja Daddy abin so ne da girmamawa a gare shi. Shima zai koyawa zuciyarsa bajinta, zai sota zai zauna da ita har abada saboda Daddy ko da a fili (a zahiri) ba ta yi masa ba. In yaso nan gaba sai ya je ya auro Sapna ya kara idan tana da rakin da ba za ta iya dauke shi a shimfidarta ba. Ya tara bukata mai yawa ga duk macen da tai kasadar aurensa, shekarunsa talatin da uku bai taba sanin ‘ya mace ba. Ya killace kansa ne (insha Allahu) only ga matar aurensa, wadda yake fatan ta zama itace tubalin iyalinsa. Ya kuma yarda ya baiwa Rayhanah da bai sani ba wannan babban matsayin tunda zabin Daddy ce. Addu’a yake har a fili Allah yasa RAYHANAH ba irin wadannan ‘yan lagwai-lagwai din bane kamar tsada irin matar Yaya Khalipha. Bakar mace yake so ‘yar’uwarsa fully Nigerian. Ba kyale-kyalen gashi da farar fata ba. Shi kadai kuma ya koma yiwa kansa dariya duk da yana cikin tension din da Daddy ya hada masa wai ya rubuta saki. Abin da ya ba shi dariyar shine tambayar da zuciyarsa ta yi masa. “Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki? Tun ba a ga matar ba an ga kyau ko muninta, an ga yankan bakinta har an fara kissima yadda ake son ta a shimfida? Man! Kwanciyar aure ba ita ce kawai abin kissimawa a cikin aure ba, akwai wasu abubuwa masu muhimmanci ko da a ce basu kaita muhimmanci ba, to suma suna da nasu. Shakuwa da juna, kusancin zuciya da zuciya, soyayya, tausayi da jin kai a tsakanin ma’aurata, fahimtar juna, nuna kulawa da bakin cikin ko farin cikin juna, planning a kan tarbiyyar ‘ya’ya da yanayin yadda ta dauki addininta da yadda take gudanar da ibadarta. Idan ta dauki nauyinka yadda kake so a shimfida, ta kuma rasa wadannan qualities din she’s not enough wallahi auren ba zai dore ba. Ga kuma kasancewar dan adam tara yake bai cika goma ba, da wuya a samu wadda ta hada dukkan wadannan din, a wurin Ibraheem idan irin haka ta faru to saki ba shine solution ba. Dubo wata wadda ba ta da wancan take da wannan ka hadasu, sai rayuwa ta fahimta da soyayya ta dore. Tunanin Himu kenan har barci mai karfi ya dauke shi, mafarkin yadda zai ga Rayhanah yake, saboda yasa abin a ransa. ******* Da asubah bayan ya yi sallah a masallacin dake kusa da gidansa wajejen karfe shida na safe, ya zauna ya shiryawa Daddy (text msg) na ban hakuri da neman afuwa. A ciki yace da Daddyn “Aurensa da Rayhanah na har ranar busa kaho ne. Ya yi hakuri ya yafe masa ba zai iya ko da kwatanta abin da ya umarce shi ba, ya ba shi RAYHANAH....... akwai uzurin da ya janyo bai neme shi a waya ba shima ya kasa samunsa. Ya rufe wayar ne kwata-kwata a dalilin jinya mai tsaho da ya yi a SanFrancisco, ya tambayi Mami ita ai ya gaya mata. Ya kare da cewa, “Daddy I’m sorry........ Luv u Dad!” Shima fitowar shi kenan daga masallacin asibitin wayar dake aljihunsa ta sanar da shi shigowar sakon. Ya dauko ya karanta, sai jikinsa ya yi sanyi. Amma bai ba shi amsa ba. Mota ya dauka ya nufo gida da yake aikin kwana ya yi. A farfajiyar gidan ya cimma motar Ibraheem, jikinsa ya kara yin sanyi da ya shigo falo ya ganshi zaune cikin kujera yatsunshi goma cikin sumar kanshi kansa a sunkuye. Kayan jikinsa na barci ne. Duk sallamar da Daddyn ya yi bai ji ba, ya yi nisa cikin tunani mai zurfi, kawai so yake ya ga wannan Rayhanah da ta tokare masa a kahon zuci. Yasa hannu ya mikar da dansa tsaye, sannan ya rungume shi. “Jeka dauko passport ayi biza in sadaka ga Rayhaanah, amma don Allah Ibraheem ka rike min Rayhana amana, domin amanar Allah ce a hannuna. Idan ba ta yi maka ba, ka bani ‘yata kar ka wulakanta min ita yadda uwarku ta wulakantata......!!!” Hannu ya kai ya toshe bakin Daddyn don ganin yana so ya tuno tsohon bacin ran da Mami ta dasa mishi. “Past is past Daddy........ just the present!” Dacta Mansur ya girgiza kai, wato ya yarda da shi. Ibraheem a dan nauyaye da nauyin harshe ya ce, “A ina Rayhanah take?” Daddy ya ce, “Informatics - Singapore”. Fiddo idon da Ibrahim ya yi ya baiwa Dr. Mansur dariya. “Ita da wa Daddy? Da aurena?” Daddy ya ce, “Ita da budurwarka Juma, da kuke soyayya a waya”. “Kasa tsage in shige!”. In ji Ibraheem........ sai ya rufe fuskarsa da tafukansa. Wai ya ji kunya kenan. Dacta ya wuce ciki yana dariyar Ibraheem. Idan yana tare da Dr. Mansur (mahaifinsa) bai san sanda yake mai da kansa kamar yaron goye ba. And the Dad likes it..... shi har gobe Ibrahim da Khalipha hangosu yake suna ‘yan digwui-digwui a Al-Muntada da Al-Falah (Children Islamic Schools) a Birtaniya. Sanda yake kama hannun daya, Asma’u ta kama daya su tsallaka titi. Su shigar dasu makaranta. Don haka shi har gobe yaran goye ne a idanunsa baya sakar musu ragamar rayuwarsu sai a bisa hanya madaidaiciya, ba kuma takura musu yake ba, tsaka-tsaki. Ayi raha lokacin raha, ayi discipline in sun karkace, sannan ayi musu abin da suke so [12/26/2019, 21:08] Takori: ***** HADUWAR AMARYAR DA ANGON! Cikin jirgin ‘Turkish Airlines’ da sukeciki, bairin tunanin da Ibraheem Mansur Takai bai yi ba, ya gaza ko da kurbar dan jusin dake cike da kananan kankara da suka mishi a dan kofin su dan kankani dake hannunshi. Wace ce wannan Rayhanan? Ya take? Wace irin tarba za ta yi masa? Shima wace iri ya dace ya yi mata? Zai so ta? Zai iya ba ta matsayin mata a gare shi? Zai iya hada rayuwarsa har abada da yarinyar da bai sani ba bai taba gani ba? Bai taba yin wata mu’amala da ita ba balle ya san kamanninta ko halayenta? Tunaninnikan da suka addabi kwakwalwar Ibraheem kenan, yayin da a bangaren mahaifinsa Dr. Mansur Takai, babu abin da ya dame shi, daga ya sha jus sai ya bude shafukan jaridar ‘Daily Tribune’ dake hannunsa, in yaso ya yafito ma’aikatan jirgin su zo su ba shi abinda yake bukata da yake a first class seats suke. Lokaci-lokaci ya kan saci kallon Ibrahim ta gefen idonsa, sarai ya san tunaninnikan da ke damunsa, amma bai ce masa komai ba, bai ma nuna ya san halin da yake ciki ba. A lokacin da aka ba da order a daura belt jirgi zai sauka a ‘Changi-Airport’, Ibrahim bai ji ba. Sai ji ya yi Baban yana makala masa, bayan ya makala nasa. A lokacin ne Ibrahim ya gane ‘he is lost...... (ya yi nisa a tunani). Ya kalli uban, shima ya kalle shi, sai suka yi ‘yar dariya a tare. Bayan sun sauka motar hotel din da Daddy ya yi booking tun kafin su taho (Mandarin Orchard Singapore) already tana jiransu, ta kwashesu da ‘yan jakunkunansu marasa nauyi zuwa otel din. Tun a hanya Daddy ke kiran wayar Rayhanah ana gaya masa a kashe take. A lokacin ita Rayhanah tana aji suna wata jarrabawar gwaji (test) domin gab suke da fara jarrabawar karshen shekara. Kuma dama karatun na shekaru biyu ne kacal, da yake tana da diploma tare dasu. Karfe shidda na yamma ta baro cikin institute din nasu ta kamo hanyar gida, ta tsaya ta sayawa Inna roasted KFC, ita kuma ta sayawa kanta ‘wantanmee’ ko ‘wonton’ (yadda suka fi kiransa), ‘chili crab’ da ‘fried hokkien mee,’ duka suna daga cikin (40 Singapore foods Singaporeans cannot live without) abincin mutanen kasar Singapore guda arba’in da baza su iya rayuwa basu ba, saboda ta ce da Innar yau kada ta yi musu girki za ta yo take away don ta wayi gari ba ta jin dadi, sauri ma take ta isa gida don ta kaita clinic a duba ta. Haka nan ta tsinci kanta da faduwar gaba a lokacin da ta doso gida. Sai da ta tsaya a kan wani dan tudu ta zauna ta zube ledodin hannunta a kasa tana dan hutawa tana hango kofar gidan nasu da bakuwar motar otel din (Mandarin Orchard) fara sol. Ta san hotel din da Daddy ke sauka kenan, don haka jikinta ya ba ta Daddy ne ya zo. To amma wannan faduwar gaban da ta samu kanta a ciki ta mece ce? Ta so ta kunna wayarta, sai ta tuna a gidan ta barota. Sai kawai ta mike da dan kuzari tana cewa a ranta bari in karasa gidan, daman dai kuma ta kwan biyu basu yi waya da Daddyn ba, har Inna kan tambayeta kwana biyu Baba Likita bai kira ba, lafiya? Ta kan ce lafiya sumul insha Allahu, kin manta Baban nawa busy doctor ne?’ Inna ta ce, “Allah yasa buzu ne ba busy ba, ki kira min shi kawai”. Ta yi dariya ta ce, “To ai ni yanzu bani da lokacin kunna waya idan ban gama tsarge tests din nan da suka sako ni a gaba ba, na yi na yi ki koyi operating din waya da kanki kin ki saidai ki dameni in kira miki wannan in kira miki wancan, yanzu sai ki yi zuciya ki koya”. Duka Inna ta kai mata ta fice da gudu tana dariyarta. A haka suka rabu yau. Ta mike ta ci gaba da tafiya a gefen titi a hankali don yunwa take ji sosai, ledodi da hand bag dinta kamar ta watsar dasu don nauyin da su kai mata, musamman kwalin kazar Inna kaji biyu ne a ciki. A haka ta daure ta ci gaba da tafiya at the same time, faduwar gabanta na kara tsananta. Ba wata kwalliya ba ce a jikinta, amma da ka ganta kai tsaye za ka kirata black-American. Shigar jikinta usul shiga ce ta matan Singapore (Belted-Waist-Shirt) dark blue mai dogon hannu. As a Muslim, sai ta sanya bakin dogon wando a ciki, ta kuma sanya karamin hijab na Larabawa a kanta wanda ya tsaya iya kafadunta. Also kayan jikin nata are not expensive.....kuma basu nuna komai na jikinta ba, daka ganta kasan Musulma ce cikakkiya. Singapore is very modern but dressing very sexily will not be acceptable in certain places.... don haka matan kasar musamman musulmin can basu fiya yin shiga ta tsiraici ba balle ita Rayhanah. Kafafunta rufe cikin bakin cover kuma flat takalmi Melissa (brand din ZALORA). Rahane ba zuwa take ta sayo kayan nan ba, Dr. Mansur ke zuwa ya sayo da kansa a shaguna duk zuwan da ya yi ya zo ya zube mata su, illa dai yana karbar size dinta har ya rike. Zamanta cikin dalibai ‘yan’uwanta musamman haifaffun Singapore shi yasa yau da gobe ta iya shigarsu. Fuskarta ko powder (hoda) babu, haka lebbanta babu danshin mai, but they are soft and supple kamar tana basu wani extra care ne, amma babu ko daya. Babu gumi a fuskarta, fuskarta tas fresh and choculate. Ba ta da dogon hanci, gashin nan dai dan madaidaici a tsakanin idanunta. Gashin kanta a tsefe yake, baki mai karfi amma ta matse karshensa da ribbon, hakan bai hana ya yi dan tudu ba, da yake ba ta taba sanya masa relaxer ba, haka yake da karfi kamar reza na asalin Hausawan Kano jikokin barbushe da tsimbirbira. Da wannan shiga, da wannan fuska, da wannan yanayi Rayhanah ta danna kararrawar shiga falonta. ***** Wanda ya bude kofar wani matashi ne baki mai tsayi sambal, mai wasu irin idanu masu lumshewa da kansu, da budewa cikin nutsuwa cikin umartar kansu da yin hakan, cikin kwayar idonshi akwai wani abu mai sheki kuma ba farare ne tas ba, ga dogon hanci kamar Dacta Mansur, fatarshi ta nuna haifaffen Nigeria ne, gashi nan kamar Dr. Mansur (choculate in complexion), duk da Dr. Mansur ya fishi haske. Ya tara suma mai dan tudu a kanshi, ba kuma nannadaddiya ba ce ta ‘yan asalin Northwest-Nigeria ce wato mai karfi, amma ta sha taza ta sha mai mai tausasa gashi (ArganaVita) da ba a samun shi sai a kasashen ketare. Sanye yake da farar shadda kal hilton dinkin Mohammed, rigar ta kusa kasa sai wandon a ciki, kanshi babu hula, daure a damtsen hannunsa agogon ‘Calibre de Cartier’ ne da ya kwanta cikin tattausar fatar hannunsa wadda lallausar bakin gashi ya kwanta a ciki. Babban abin jan hankali a halittarsa, wannan tsagar bakin nasa ne da bakaken lebbansa marasa kauri, sai kuma lallausar sajen da ya kwanta a gefen kunnuwansa bai iso habarsa ba, wadda dan lotsawar nan na tsakiyar haba (cleft) ya bayyana a fili ko da bai motsa bakin don cin abinci, dariya ko yin magana ba. Kallon-kallo ake tsakanin Rayhanah Rashid Takai da matashin da ya amsa sunan Ibraheem Mansur. Kallon da bai da ma’ana at all. Kallon da kai tsaye za ka fassara shi da kallon zakuwa a tantance juna kawai, ba na so ba, na kauna, ko akasin haka ba, kawai ‘eager to see each other,’ kuma ba tare da sun bar kallon ya tsawaita ba tunda ko da kalma ba ta shiga tsakani ba kowa ya gane kowa, kuma kowa ya yi ‘quenching’eager dinsa. Don haka Rayha ta yi saurin sadda kai wani abu yammmm! Na bin ilahirin jikinta, wanda ya fi karfin tashin tsigar jiki sai circulating din jini abnormally da yadda ya saba aiki, domin bukatarsa nason ya isar da sako ta kowanne hali (by all means) daga zuciya zuwa cikin gangar jiki da kwakwalwa. Duk wadannan mintunan da suka kwashe a tsaye, Dr. Mansur da Inna na kallon su, addu’a kowannensu ke yi cikin zuciyarsa Allah ya daidaita. Cikin Dr. Mansur ya fi na Inna Juma durar ruwa, idan Ibraheem ya ce Rayhanah ba ta yi masa ba ina zai sa kansa? Amma ga HIMUN, abin ba haka yake ba. Kallon da ya yi mata na farko, eager look ne na neman tantancewa da kauda curiosity. Amma as his eyes enter her’s much more deeply..., (da kwayar idanunshi ta shiga cikin tata sosai), kokari kwakwalwarsa ta shiga yi wajen farfado masa da shekaru goma sha daya a baya. Tabbas ya san fuskar, yasan wadannan idanun masu rauni da sanya kasala, ya san ‘yar yarinyar nan ce RAHANE, data shigo cikin rayuwarsu daga asibitin Malsm Aminu Kano, mai kula da ubanta a bargar dawakin Hakimi, mai yiwa ubanta wanki, yanke farce da taya shi feeding horses (baiwa dawakin Hakimi Abdulqadir abinci). ‘Yar yarinyar nan ce da Daddy ya dauko daga Takai..... wadda ta rasa jinta dungurungum, ‘yar yarinyar nan ce mai amfani da HEARING AID....... wadda ta sa shi barin gida ba don ya so ba, sai don ya ceci kansa ya ceci zuciyarsa daga fadawa soyayyah a inda bai dace ba, a kuma lokacin da bai kamata ba. Yana ‘referring’ kowanne ‘motion’ na zuciyarsa a kanta da KARYA........ bayan kuma sau tari tsoron kar zuciyarsa ta ce ya yi karyar yake kidima shi ya yi mata KARYAR...... Ya bar gida saboda kar zuciyarshi ta wulakantashi da kauna da soyayyar kwaila ‘yar kauye mai lalurar JI, hade da wasu ‘extraordinary charismatic features’ (baiwarwaki da karama) da ake kira ‘Rahane.’ A girl with a great mind! To yaushe ta koma RAYHANAH? (Daddy ne ya canza mata suna), zuciyarsa ta yi saurin tuno masa........ “Mene ne sunanki......?” “Rahane”. “Rayhanatu kenan ko?” “A’a, Rahane.......” “To ni ba zan iya kiranki Rahanen ba, don baida ma’ana at all sam-sam....... Rayhanah....!!!” Ya tuno tattaunawar farko da mahaifinsa ya yi da ita a ranar da ta fara samun kanta daga hatsarin da suka yi, a kuma ranar da Baban da abokinsa Dr. Imam suka makala mata ‘hearing aid’. As soon as da suka fahimci she's hearing impaired! Kafin Rayhanah ta ankara Ibraheem ya kai hannu gareta ya cire hijabinta yana duba kunnenta da bayan kunnen, babu komai sai dan karamin dan kunne mai barima na farin dutse. Ta saki ledodi da jakar hannunta kasa saboda razana. “Where's your hearing aid?”. Abin da ya tambayeta kenan da wata murya mai sanyi, harshensa da accent dinsa (American), wato na Amurka ba na Birtaniya da ya fi saukin furtawa ba. Hannuwanta biyu ta kai kan nata tana son rufe gashinta da ya tsiraita. Sai ya russuna yana kwashe mata ledodin ta da jakarta da ta zubar ya bata hanya tareda yi mata alamar ta wuce, sai ta rabe ta gefensa ta shige ciki. Babu kowa a falon, Inna da Baba Dacta sun shige kicin tun sanda Ibraheem ya cizge hijabin Rahane. Ai ganin ba kowa a falon sai ta kara da gudu ta yi dakin barcinta ta rufo kofar ta jingina da ita tana numfarfashi kamar wadda ta yi gudun mita duba. Idanunta ta lumshe tana ambaton “Yaa Wahhabu......... Yaa jamilal munzarrr (Ya mafi kyawun masu gani)!” Ya Himu ne, tabbas shine....Daddy ya kinkimo ya kawo mata tana zaman-zamanta lafiya, ita ina ruwanta da wani Ibraheem. Tun can bai son ta, kyankyaminta yake, kalma wannan ba ta taba shiga tsakaninsu ba tun saninta da shi a gidan Dacta Mansur, kawo barinsa gidan don ba ta ishe shi ko da kallo ba. Ita fa wannan auren kawai ta dauke shi suna ne, biyan bukatar ran Daddy bata taba tunanin zai zama reality ba. Ta yi zaton haka za ta kare rayuwarta cikin kwanciyar hankali da neman ilmi da taimakon Babanta Mansur da Innarta Juma. Ba ta taba kawowa ranta Ibraheem din zai shigo cikin rayuwarta ba....... Ta shiga uku....... wannan gundamemen Ba-amurken ne mijin nata da har Inna da Baba Dacta za su fita su barta da shi a gida akan saninsu? To tace masa me? Ko tayi masa me? Tayi yaya da shi? Watakila ma dubawa ya yi in da hearing aid ya ce baya son ta. Duk Khalipha shi ya janyo mata....... da sunyi aurensu na so da kauna da ganin mutunci da kimar juna ai da Daddy bai yi mata AUREN HUCE HAUSHI da Ibrahim ba. Sai ji ta yi hawaye na bin fuskarta. Bokon nashi har ya zarta misali, tsoro yake bata, kwarjinin shi razanata yake, ba ta san inda Daddy ke nufi ta kai shi a matsayin life-partner ba. Wannan gandamemen baqin bature haka wanda zai iya hadiyeta baki dayanta? Ya yi biyun Yaya Khalipha a girma da tsayi, ba wai kiba ce da shi ba (physique). Kuma ita bata taba yiwa kanta sha’awar rayuwa da wani Da namiji ba bayan Khalipha, shine dai-dai ita, domin ta kowanne bangare bai tsaurara ba...... ga boko ga addini, ga simplicity bai dauki kansa a bakin komai ba. Rana daya wannan iftila’i ya ratsa, ta karbi zabin Daddy don biyayya da yakinin da take da shi na cewa a haka za su kare rayuwar tasu ita da Innarta da Daddy Ibrahim ba zai zo ba. Yau gata ga IBRAHIM MANSUR TAKAI. Kokarin bude kofar ake, kofar da take jingine a jikinta. Ai da ta yi wata zabura guda daya sai ganinta ta yi a toilet dinta na bedroom ta kulle kanta. Inna ta shigo tana cewa, “Yau na ga abin da ya isheni ni Juma, mijin kike gudu haka? Lallai kin hada kanki da aiki. Fito ki ci abincin da kika siyo shi Ibraheemu ma ya dade da fita a gidan nan.......” Ai kuwa ta bude kofar ta fito idanunta sun ci kuka sunyi jawur. Haka Inna ta yi ta lallamin ta don ta ci abincin, amma ta kasa cin abin kirki duk soyayyarta da ‘wontonmee’ da ‘chili crab’. Ga Inna ba ta iya cin wannan cakudedeniyar ba, barta dai a KFC (Kentucky Fried Chicken). Sai ta tattara ta zuba mata a firij tana ta mita....... [12/27/2019, 11:51] Takori: “Kuma shi kenan don Allah ya amsa addu’armu Ibraheem ya zo, sai ki kuntatawa kanki? Tun safe baki yi karin kumallon kirki ba kika fita, na kuma tabbata a can baki ci ba, kin sayo abin dadin ki rimi-rimi sai ki ki ci Rahane? Haba Rahane, an Rahane na! ‘yar gidan BABANTA!! Kina son Uba kina gudun Dan sa, anya an taba yin haka?!!!” Hawaye suka fitowa Rahane surrrrr...! Har daga cikin hanci, cikin dakushewar murya mai cike da kuka ta ce, “Inna ni dai na fi son Yaya Khalipha.......” Sai bammm! Inna ta buge bakinta da hannun ta, “Kina auren wani kina cewa wani kike so? Maza-maza ki yi istigfari. Wanene Yaya Khalipha kuma? Shashashar banza, irin wannan zabgegen miji haka na likawa a goshi? To ni ina son sa ki bar mini, ki ga yadda zan killace abina a daki kada wata ta tayi min kwace...... idan baki godewa Allah kin godewa Baba Likita ba, to za ki ga ba dai-dai ba a rayuwarki wallahi Allah ki dawo cikin nutsuwarki. Haba an Rahane na? Ibraheem mai kyau da shi? Mai tarin ilmi. Daga yi min allura ya bani kwayoyi na sha na nemi ciwon bayan dake damuna na rasa. Ubangiji ya ce idan bamu godewa rahamarsa ba, la-shakka zamu godewa azabarsa. Ki nutsu, ki manta da wani Khalipha Rahane ki karbi mijin da Allah ya baki. Shi bai ce baya son ki ba, bai kamata ke ki fadi hakan ba. SO na Allah ne, shi ke sanya shi a tsakanin bayinSa. Je ki ki yi wanka Rahane, ki yi kwalliya ki tarbi mijinki, ki yi kwalliyarki ta ‘ya’yan Hausawa ya san cewa tushensa ya aura. Tashi maza ki cire shirmen nan na jikinki ki yi wanka.....” Rahane ta katseta cikin kuka, “Ni wallahi babu wankan da zan yi, da can bana wanka sai don ya zo? Kuma ai gidan nan babu dakin da zai sauka in ba naki za a ba shi ba ina zai je?” Inna dai lallami take don haka ta gintse dariyar da ta cika mata ciki, ta ce, “Na ji na ba shi nawan ni zan kwana a falo, ai ko wadannan lausasan kujerun sun isheni in yi barcina har da saleba. To canza kayan tunda ba za ki yi wankan ba.......” Ai kuwa ta rantse ba abin da za ta yi a ciki. Ran Inna ya soma baci, ta tashi ta rabu da ita ta shiga kicin don yin abincin da Daddy ya ce ta yi musu kafin su dawo, ta barta nan ta sanya kai cikin kafafu tana ta kuka. Ta gama kular da Inna, don haka ta fita sha’anin ta har ta gama girkinta ta jera a dining dan karami na mutum biyu (mai kujeru biyu kacal) dake can gefe a falon. Duk shiga da ficen da take sai ta ganta yadda ta barta, zuwa lokacin kuma ta gaji da kukan ta yi shiru, sai ajiyar rai take. Kararrawar kofa ta soma kara, ai kuwa ta yi fit, ta yi dakinta kamar filfilwa. Inna ta bude kofa, Ibaheem ne a gaba Daddy na bayansa, dukkansu rike da manyan ledojin cefanen da suka yiwowa Inna na African-Food. Da hanzari Inna ta amshe su tana musu sannu da dawowa. Sai a lokacin Ibraheem ya dube ta sosai, sai ya gane ita ce Juman da Daddy ya nuna mishi hotonta. Sai ya yi murmushi. Ya ce a ransa, “Lallai yarinyar nan ja’ira ce, wato ita ce Juman”. Da yake sun yi sallar isha’i kan su shigo a wani masallaci, dining suka hau suka soma cin funkason Inna da miyar ganye da aka yi da manja da kaji zuku-zuku a ciki. Loma biyar Baba Dacta ya kai ya dakata ya soma kwalawa Rayhanah kira. Ai ji ta yi hanjin cikinta ya nannade waje guda ta kara kudundunewa a cikin bargon ta. Kira har sau uku ta ki amsawa. Sai ya ce, “Ibraheem je ka zo min da amaryar nan taka. Na lura yau surukuta take yi dani, ko gaisheni ba ta yi ba”. Ya fada yana nuna masa dakin. Kamar ba zai je ba, ko tunanin me yayi sai kuma ya tsame hannunsa daga plate dinsa ya ciri tissue ya goge, ya sha ruwa sosai sannan ya mike ya nufi dakin. Murda kofar ya yi ya shiga dakin, tana can karshen gadon ta kudundune cikin blanket mai bala’in taushi kamar curin alkaki, dariya ta kama Ibrahim, gata a Singapore amma ashe bagidajiya ce. Abin da bai sani ba, Rayhanah ko a ina ta tsinci kanta ba abin da zai canza mata akida ko dabi’a, ko al’ada ta kasar haihuwarta. Ita Rayhanah ba ta yarda da wani abu wai shi wayewa ba, abin da ta sani shine ita musulma ce kuma Bahaushiya, amma tana karatun boko don fita daga duhun jahilci, ba abinda zai canza mata wannan perception (belief). Ba za ta aro wata dabi’a ba wai don ta burge ko a ce mata wayayya, masu yin hakan ma a Informatics Institute mahaukata take kallon su. Bargon ya kama ya zare shi ta karfin tsiya tana rikewa yana fizgewa ya cillar. Ya zauna a gefen gado ya ce, “Toh ke Rayhanah kuma haka zamu yi dake? Haka ake tarbar miji? Ko gaisheni baki yi ba Rayhanaah, ga dukkan alamu ma bakin ciki kike da zuwana zan takura miki......” Shiru kake ji, ta juya bayanta ta cure jikinta. “Juyo nan, Allah-wallahi kada ki sa in kai hannu jikinki da sunan duka, ko in dauke ki a hannu in kai wa Daddyn ke......” Nan ma shiru ta yi masa. Bugun zuciyarta na kara tsananta..... tabbas shine suke magana a waya, wanda muryarsa kadai ta yi tasirori masu yawa a zuciya da gangar jikinta. Ya ce, “Wato wai ke Jumah ko? To Allah yasa Jummai ce yau gani-gaki, ki kara yi min karya ki gani in ban cinye bakinki ba. Wai ke ga wadda ta matsu miji ya zo har kike tambaya nine Ibrahim??? In ma Ibro ne ga ni, me za ki yi min? Me za ki bani kike nemana???” Haushi ya kama Rahane, ba ta juyo ba ta ce (cikin kunkuni) “Ni ban ce ka zo ba, ban ce ina nemanka ba. Tambayarka kawai na yi don in san da wa nake magana ba don wai wani Ibraheem ya zo ba. Da za ka koma in da ka fito ka sakar min mara in yi karatuna yadda na faro shi ba tare da an takura min ba da na fi farin ciki.......” Kama baki ya yi da mamaki mai yawa, dariya kuma ta kama shi da yadda take tura baki gaba tana zumbura shi tana cunoshi yana girgiza kai yana dariyar ya mika hannu ya janyo tafin kafarta keeey.... zuwa inda ya ke zaune, ya kama hannayenta biyu ya rike cikin tafin hannunsa na dama ya soma dalle mata baki da yatsunsa na hagu. Ya ce, “Say it again, ashe baki da ta ido? Watch your words mijinki ne ni ba saurayinki ba....’’ Azaba ta ishi Rahane har leben ta na sama ya dan kumbura..... wasu matsiyatan hawayen azaba suka feso, kamin kuma ta yi aune Ibraheem ya rungumeta gaba dayanta cikin kirjinsa, runguma so calm har baka hango ‘yar Rayhanah cikin physique chest din Ibrahim. Sannan ya kai bakinsa cikin nata ya soma yin abin da ya fi so a rayuwarsa, wato mouth to mouth kissing. Rikon da ya yi mata mai karfi ne da ta kasa kwatar kanta. Rayhanah ta tsinci kanta a wata duniya ta daban da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba. Abubuwa da yawa ke yawo a kwanya da zuciya da jikin Ibrahim a wannan lokacin. Wadanda shi kansa ya kasa fassarasu, ya kasa daina sumbar kuma ya kasa rabata da jikinsa. A lokacin ta fara kuka na ido, wato zubar hawaye, tunda kamar yadda ya ce din ne zai cinye bakin, ta yarda tareda yin amanna da gaske yake cinyewar zai yi, in tayi la’akari da yanayin yadda yake tafiyar dashi din. Ya ki sakin bakin balle ta koma magiya. Hawayen da ke fita a idonta su suka sanyayar da jikinsa, ya daina abinda yake yi din ba don ya gaji ko ya gamsu ba, he don’t actually know what he’s deriving in it but it’s something pleasurable ever in his entire life...., amma hakan bai sa ya rabata da jikinsa ba. Data samu hakan sai ta soma ba shi hakuri cikin kuka dole ya karaya ya cikata. Shi da kansa ya dauko ribbon din daya fadi ya tattara kakkarfan gashin da bai taba ganin relaxer ba ya daure mata...... a ranshi yana ta mamakin yadda mace zata bar gashin kanta in its naturality haka. Shi kuma ya koma da baya ya kwantar da bayansa a gadon kafafunsa na kasa. Ya nuna mata hanyar kofa....... “Ki je Daddy na kiranki”. Ya fada da wani sauti kamar ba nasa ba. Ta kokarta ta mike amma cira kafa ya gagara. Sai ya yunkura ya mike gaba dayansa yana binta da kallo sosai, ya mika hannu ya kunna fitilar data fi kowacce haske a dakin (ressaince) ta jikin ceiling, wadda haskenta yasa Rayhanah kai tafukan hannunta ta rufe fuskarta. Doguwa ce sosai amma ya fita, siririya ce amma kirjinta da kugunta a cike suke. Har yanzu sanye take da suturarta ta dazu (belted -waist -shirt) da dogon bakin wandon jeans. Ta zargo belt din tsakiyar rigar ta daure. Sai ya kamo hannunta suka fito suka tadda Daddy da Inna suna hira a falo, tuni ya gama cin abincin. Rayhanah ba ta taba jin kunyar Daddy a duniya irin yau ba. Ga kanta babu kallabi, sai ta cure a gefe daga can bayan Inna wai gaishe shi take, shi sam ma baya jiyota, balle ya San magana take ya amsa mata. Abin da ya ce shine, “Rayhanatu yau Allah ya yanke mana komai ga Ibrahimu ko?” Daga mishi kai ta yi ba tare da ta dago ta kalle shi ba. Ya yi murmushi na jin dadi da samun kwanciyar hankali cikin kulawa yace “Babu wata damuwa ko?” Ta sake daga mishi kai again. Da hanzari ya ce, “Ki bari Rayhanah, kada ki bullo da wannan sabuwar mu’amalar tsakaninmu, wai saboda Ibrahim ya zo. Ni ban san shi ba ke na sani a matsayin ‘yata, in kuma kin canza min matsayi daga uba zuwa suruki ne, ehh to ki gaya min?”. Nan ma girgiza kai ta yi. Ya dai tabbatar yau Rayhanah surukuta ta musamman take yi da shi ba zai samu matsayin baya da yake so ba. Sai ya hakura ya mike a lokacin Ibrahim yana wajen socket ya kunna wayar Rayhanah a inda tasa chaji ya dau lambarta ya zuba nashi lambobin a ciki na layin da ya saka anan Singapore, amma bai sa suna ba. Daddy ya ce, “To Ibrahim mu tafi masauki, tunda ka yi min firraqu ni da ‘yata, kaima ba zan barka a gidan ba, wuce muje”. Shi Ibraheem murmushi kawai ya yi ko Rayhan bai kara kallo ba ya yi gaba, ka rantse da Allah ba shine wancan mai deep kisses din ba. Shi yake tukasu zuwa otel din su, sai dai ya karanta hira tsakaninsu, ya fi mai da hankali ga tukin. Daddy ne kadai yake ta zuba yana gaya masa don Allah ya rike masa ‘ya amana, ya ji kanta ya tausaya mata, ya tausayawa maraicin ta da raunin ta, ba ta da uwa ba ta da uba sai shi a yanzu. Duk abin da ta nuna ba ta so don Allah kada ka takura mata. Ibraheem ya ce a ransa, “Saboda ni ba Da bane, tsinto ni ka yi a bola?” ***** [12/27/2019, 17:59] Takori: Sabon dare a wajen Rayhanah! Bayan fitarsu ta dade ba ta motsa daga inda take ba, wato bayan Inna Juma. Ita Juman kicin ta shiga ta ci gaba da ‘yan kaye-kayenta da su wanke-wanke, tana yi tana ‘yan wakokinta..... Wai “duk wayon amarya sai an sha manta....... na zama dauko riga, na zama dauko wando, na zama dauko hula.... shekara mai zuwa war haka zan fara goyo da wankin kashi da share tumbidi........” Abin da Inna ba ta sani ba shine, ita Rahane ba jinta take ba don ta yi nisa cikin tunani mai zurfi. Da ta gaji da zaman falon sai ta lallaba ta shige daki. Kwanciya ta yi a gadonta don ta samu barci, amma idanun sun ce basu san wannan ba. Duk motsin da ta yi, duk juyin da ta yi, jinta take a kirjin Ibraheem. Gaba dayanta ma in fact, kamshin Ibrahim take, wani irin kamshi da ba ta taba jin mai sanyi da dadinsa a duniya ba, ba ta kuma iya tantance kowanne turare ne ba. Ta kasa barci sai juyi a kan gado. Jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta ke karbar wani sabon sako mai kassara gabban jiki. Cikin wannan halin, wayarta da Ibraheem ya aje a bed-side ta soma kira. Ba ta yi niyyar dagawa ba, domin dare ya mika sosai, amma da kiran ya isheta sai ta mika hannu ta daga. Sabuwar lamba ce, amma ta nan Singapore. Daddy ba zai kirata a irin wannan lokacin ba sai dai in ba lafiya ba. Wannan tunanin da ta yin shi yasa ta daukar wayar ta amsa cikin sanyi. Wajen minti biyu ba a yi magana ba, za ta kashe ya ce, “Rayhanah kada ki kashe min waya, zamu bata”. Da muryar da ta kasa amincewa cewa ta Ibraheem ce. A hankali ta ji idanunta sun lumshe da kansu. Ya kara cewa, “Hira nake so muyi, Rayhaanah za ki yi min?” Ta girgiza kai kamar yana ganinta. Amma ba tayi magana ba. “Ba za ki amsa ni ba Rayhanahhh?” Ya fada tun daga karkashin zuciyar sa in a subdued. Ji tayi sunan yafi dadi a bakin sa fiyeda bakin kowa, fiyeda bakin duk wani Dan Adam data taba jin ya furta sunan a kunnenta, tun bayan da Allah ya yayemata lalurar ta, jama’a suke ambaton RAIHANAH!!! “Ni fa barci nake yi, hirar me zan maka da tsakiyar dare haka Ya Himu?” “Karya kike idonki biyu!”. Ya fada kai tsaye. Kamin ta ce wani abu ya ce. “Hira irin wadda mata take wa mijinta, kamin yayi barci”. Ji ta yi kamar ya kinkimo katon dutse ya dora mata aka. Don haka ba ta amsa mishi ba ma wannan karon. A sanyaye ya ce, “Rayhanah haka zamu yi da ke ko?” Da likitan zai tsaga jikinta a wannan lokacin da ya ga yadda jininta ya daina ratsawa a jikinta. Mene ne haka? Yau wane irin dare ne a rayuwarta? Me ke shirin faruwa da ita? Shirun nata ya matukar tuke Ibrahim, ya ce a dan zafafe..... “Allah idan ba za ki bude baki ki yi min magana ba zan zo yanzu Rayhanah mu kwana tare, cikin bargo daya. Kin san kuma Inna ba za ta ki bude min kofa ba”. Hawaye ya cicciko idanunta, wannan shine abin da ta fi tsoro a rayuwarta kenan yanzu (sake kadaicewa da Ibrahim). Cikin ‘yar rawar murya da karkarwar jiki ta ce, “To me..... me zan ce maka Ya Himu?’ “Labarin rayuwarki ta baya, da saurayinki Yaya Khalipha.......” Hannu ta kai ta toshe bakinta.... ta fidda ido alama razana. “Ka daina irin wannan maganar don Allah..... babu kyau Ya Himu”. Ibraheem ya lumshe idonsa a hankali ya ce, “Na bari, to amma samarinki nawa a Kazaure?” Da sauri ta ce, “Allah mu bamu da saurayi, Daddy baya bari”. Dariya ya yi, domin yadda ta yi maganar kuruciyarta ta fito sosai. Sai ya kara tausasa murya, “Ai an gaya min ne wai da Yaya Khalipha ne zai aure ki......” “To Allah bai yarda ba”. Ta fada da sauri. Ta ce a ranta “ko da yake son nawa nima nake son sa, ai kai nake gani a matsayin miji cikin mafarkaina, don haka ban mika masa soyayyar zuciyata gaba daya ba”. Ba ta san cewa a fili ta fada ba. Ibrahim ya runtse ido, cikin mamaki da hardewar harshe da nauyin American-accent dinsa ya rinjaya ya ce, “Har mafarkina kike yi Rayhanahhh?” Sai a lokacin ta ankara da subutar bakinta, ta ce, “Lah! Ni fa ba da kai nake ba”. Ya ce, “To na yarda ba da ni kike ba, tadin zuci ne ko? Amma ya ya kike ganina cikin mafarkin? Da ‘ya’ya, da jikoki ko Rayhahhh?” Muryarta na rawa cikin kidima da daburcewa ta ce, “Don Allah zan kwanta, gobe (8 am) ina da test”. “Da izinin wa za ki je yin test din? Da kam kina bisa umarnin Daddy albarkacin cewa bana nan, amma yanzu na dawo, babu inda za ki kuma zuwa ba da amincewa ta ba, goben barin kasar ma zamu yi gobe insha Allahu......” Ai dama kiris take jira, sai ta soma magana cikin son kecewa da kuka....,, “Idan ka yi min hakan ka zalunce ni Ya Himu, na wahala a kan karatun nan, ga shi na ci karfinsa watanni tara suka rage min...”.Sai kuka. Kyaleta ya yi ta yi ta yin abinta, bai kashe ba ita ma ba ta kashe ba. Gidan waya na ta kwasar kudi. Saida ta yi shiru don kanta, sannan ya sassauta murya. “Na ce zan rabaki da karatunki ne?” “Eh, ba haka ka ce ba?” Ya ce cikin ‘yar dariya, “Ni ban ce haka ba, barin Singapore na ce”. “Eh mana, am not a kid, barin kasar na nufin barin karatun!”. Murmushi ya yi mai sauti. “Rayhanah bani da wannan amsar yanzu, muyi hirar da na ce muyi”. Jikinta ya yi sanyi kamar ta soma rokonsa amma kawai sai ta fasa, muryarta abin tausayi ta ce, “Tohh”. “Has he ever held your hand?” Da sauri kuma a razane ta ce, “Wa?” “Yaya Khalipha!”. Wuta ta daukewa Rayhanah, ta rasa abin da za ta ce masa. Ba ta san sanda ta ce, “Kai ka taba rike hannun Aunty Nabilah? Saboda kai ne ba ta so na!!!”. Very shocked Ibrahim ya zama, ya dauke wuta dif! Ashe da wayonta take yin abu irin na yara, gidadawa. Kuma ashe har tayi masa farin sanin da har ta fahimci akwai wani abu tun tana karama tsakanin sa da Nabilah Abdulqadir. Yayi ta maza Ya ce, “Ai ni namiji ne mijin mace hudu ne, ko na rike hannunta bani da laifi, tunda zan iya karawa da ita. Ke kuwa tare kuka balaga da Khalipha gida daya, ga soyayya da kusanci mai nisa a tsakaninku, INA KIIISHIIII Rayhanah.......!!! Has he ever did it???” Duk da amsarsa ta farko ta bugi kirjinta, amma yadda ya yi sentence din karshe ya gigitata...... tana kokarin kashe wayar ya fadi da karfi. “Kada ki kuskura ki kashe min waya Rayhanah..... zamu yi mummunar sabawa. Na ce Khalipha ya taba rike hannunki ko wani abu makamancin haka?” Cikin rawar murya ta ce, “Eh”. “Sau nawa?” “Sau daya ne Allah”. “A ina?’ “A kafar benen gida”. “Sai kuma me?” “Wallahi Allah shi kenan”. Sai ta fara kuka tun karfinta. Bata taba ganin irin wannan mutumin ba mai neman kada a zauna lafiya da titsiye no rhym no reason (babu gara babu dalili). Sai kawai ta ji ya kashe wayar. Ba a jima ba ta ji shigowar mota harabar gidan, wayarta ta yi kara, shi din ne. Ta sake dagawa hannunta da jikinta duk suna rawa. “Zo ki bude min kofa, bazan danna‘doorbell’ ba, kada in tada Inna”. Ba karamin razana ta yi ba, da ta mike tsaye don cika umarninsa ji ta yi hajijiya na dibar ta. A haka ta bi bango ta fita daga dakin ta ratsa ta falo ta bude mishi kofar. Kayan barci ne farare sol a jikinsa masu dan kauri. Ta ba shi hanya ya wuce cikin falon, amma ita ba ta matsa daga inda take ba, ta rabe a jikin kofar. Ibraheem zama ya yi cikin tausasan kujerun falon ya nutsa hannuwansa cikin tarin sumar kansa, ya sunkuyar da kai ya yi shiru. Shudewar mintina goma a hakan sannan ya dago idanunsa jajir ya dube ta. Tana rabe a jikin kofar kamar mai jiran ya gama abin da zai yi ya fita ta rufe kofarta. A zafafe ya ce, “Ki daina yi min wannan kauyancin da gidadancin da kike mini, a Turai na ganki kina rayuwa cikin Singaporeans, har shigarsu kin iya, ba a Takai na dauko ki ba. Am not here for what you think, o.k?” Ta sadda kai kasa. Hannunshi na dama ya mika mata...... “Zo mu yi hira!” Jikinta na makyarkyata ta ce, “Ni barci nake ji”. “Tunda na kasa kema ba za ki iya ba”. “Ya Himu don Allah ka zo ka tafi, Inna na fitowa alwalar asubahi, don Allah ka rufa min asiri, cewa za ta yi ni na kirawo ka.....” Halin da yake ciki bai hana shi yin dariya ba, gaba daya ta gama firgicewa kamar mai fargabar kada mijinta ya kamata da kwarto. A tausashe ya ce, “Zan tafi, but on one condition....” Ido ta zazzaro masa tana jiran jin condition din. Hannu ya kara miko mata. “I only want to kiss you again! Rayhaanah don Allah.....!! Zan miki addu’a Allah ya saki a aljanna!!!”. Ba ta motsa daga inda take ba, sai shi din ne ya taso ya tako a hankali ya tadda ita har inda take. Irin rikon da ya yi mata da amsar da yayiwa bakin nata, ya tabbatar mata he will go far beyond abinda ya roka din, za ta gayawa aya zakinta idan ta sake ta bashi dama. A lokacin ne Inna ta fito don yin alwala, ta kuwa yi kyakkyawan gani, sai ta juya a hankali da baya da baya har ta buge keyarta da kofa. Sai karfe shida Ibrahim ya bar gidan. Jikinta babu sauran kuzari ta zauna a kujerar falon tana nemo consciousness din ta da diminishing gigicewarta. Sai da Inna ta tabbatar ya tafi sannan ta fito ta yi alwalarta ta wuce daki ko uffan bata ce mata ba. A ranta addu’a take musu tana kuma roqon Allah da ya bawa Rahane soyayyar Ibrahim cikin sauki. Ba kamar yadda suke tararrabi ba itada Baba Dacta. Yasa abinda ta ganewa idonta yanzun haka yake har zuciyar Ibrahim!!! Littafi Na 4 na dauke da karashen labarin kuma tare suke da Dan uwansa. Taku har abada; Sumayyah Abdulqadir ( TAKORI).