[12/27/2019, 17:59] Takori: RAYUWAR RAYHANAH 4 Duk da rashin barcin da ta samu jiya a tsayin daren baki dayansa, hakan bai hanata yin wanka karfe bakwai na safe ba, ta yi sallah ta kintsa, ta zo wajen saka kaya ta rasa wadanda ya dace ta saka. Sai ta tuna da maganar Inna jiya cewa ta yi kwalliyarta da atamfa. Idanunta duk sun tasa sunyi ja cike da nauyin barci, domin dai shi ba a cin bashinsa a zauna lafiya. A ranar ma test za ta yi, amma ko Alifun ba ta karanta ba, inda Allah ya taimaketa ma practical test ce (gwaji na aikace). Karfe goma na safe suka gama ta nufo gida. Daga informatics institute zuwa gidansu babu nisa da kafarta take takowa kullum. Atamfa ce exclusive fara tas a jikinta mai ratsin shudi da ruwan goro, ta yafa mayafi ruwan goro mai girma da ka ganta ka ga cikakkiyar Nigerian. Ganin motar su ya tabbatar mata sun shigo gidan. Sai ta rage sauri cike da jin nauyin, da wace fuska za ta dubi Daddy a yau, Ibrahim da ya haifa yana aiwatar da wadannan al’amura masu tsaurin fada a gareta? Wato sumbatar ko’ina a tareda ita? Wannan babban tashin hankaline a gareta. Ba Daddy kadai ba, shi kansa Ibraheem din ba ta jin za ta iya hada ido da shi. Don haka take tafiya sannu-sannu, kafafunta babu kwari. Da ta iso kofar shiga gidan, sai ta kasa danna bell ta yi zamanta a kan wani ginannen verse din fulawa dake bakin kofar shiga falon nata, tana tauna gefen mayafinta da fararen hakoranta. Wajen mintina ashirin da zamanta kofar ta bude. Inna ta fito da katuwar jakar kayanta za ta sanya a mota. Gaban Rayhanah ya yi mugun faduwa, kar dai Ibrahim da gaske yake rabata zai yi da Singapore? After one year and a half of dedication, struggle and endeavor? Inna ta ankara da ita a zaune ta yi salati ta yi sallallami. “Yanzu daman kin dawo tun dazu kika zauna a nan? Rahane yaushe za ki bar kauyancin ki? Ko ni tsohuwa ba zan yiwa mijina abin da kikewa Ibraheemu ba. To kai Ibrahim fito ka dauke ta ka shiga da ita gidan.... tunda bazata iya shiga ba.” Ai da jin haka ta zabura ta mike ta danna kai falon, idanunta basu sauka a ko’ina ba sai cikin lumsassun idon Ibraheem, wanda ke nutse cikin kushin, kafafunshi mike a kan tebirin glass mai garai-garai dake tsakiyar falon. Yana sanye da wasu shudayen Tommy hilfiger, masu ratsin ruwan toka da ruwan tokar safa a kafafunsa. Kallon ta ya yi na minti biyu, sai ya mai da kansa a jaridar dake hannunsa. Sai ta shige bayan labule wai tana gaida Baba Dacta shi ba ma ya jiyowa sosai. Yasa dariya ga dukkan alamu yau cikin matsanancin nishadi yake, da tabbataccen kwanciyar hankali, ya ce, “An Rahanen Inna yau sai Chicago, Inna sai TAKAI!” Ai ba ta san lokacin da ta fito daga labulen ba ta zazzaro ido. Ya girgiza kai yana dariya. “Ni dai Ibraheem ka warware wannan firraqun da ka yi min da ‘yata, tunda ka zo ban ga hakorinta ba sai razana cikin fararen idanunta. Zo nan Rayhanah, daure ki zo kada ki sa in yi fushi da zuwan Ibraheem.....’’ Ta lallabo da rarrafe ta zauna gefen kujerar da yake zaune. Ya ce, “Yaushe za ki kare test kuma yaushe zaku fara exams?” A hankali ta ce, “Mun gama test..... 1st April zamu fara exams ”. Ya ce, “Masha Allahu, mu zamu wuce gida Inna za ta Takai da Albasu ta ga dangi sannan ta dawo gidanku (Farm Center) kafin ku dawo. Za ku wuce Chicago, Ibrahim ya gama kammale-kammalen sa ya dawo gida baki daya. Kafin nan za a san yadda za a yi a kan karatun ki, ai za ki raka shi ko?” Idanunta narai-narai da hawaye ba tareda kwana ba ko sakayawa kai tsaye ta ce, “A’ah”. Hatta Inna ranta bai yi mata dadi ba da amsar Rayhanah, balle Ibraheem. Shi kuwa Dr. murmushi ya, “Why?” (Me yasa). Ba ta kalli inda Ibraheem din yake ba wanda ta tabbata idonshi na kanta, kunnensa na sauraron amsar da za ta bada. A sanyaya tace. “Na fi son na kammala karatun gaba daya mu koma gida kwata-kwata, ina son karatun Daddy, kuma na sha wahala a kansa, sannan na ci karfinsa”. Inna ta yi tsagal cikin takaici ta ce, “Amma ke kadai za ki zauna ko, ki auri karatu? Wallahi ba zan zauna ba, na gaji da zama cikin jajayen kunnen nan da basu san Allah basu san Annabi ba, ko kiran sallah babu, sai dai a duba agogo. Ban da wuyanki ya fara kauri yau Babanki ne zai yi umarni ki ce masa a’ah?” Ran Inna Juma ya baci sosai, sai fada take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Babu wanda ya ce uffan sai da Rahanen ta fara kuka. Daddy ya ce, “Inna yi hakuri, tana da ‘yar gaskiyarta.......” “Ina wata gaskiya a nan? Boko ya fi aure? To ba dani ba, kinga tafiyata, wallahi ko kwana daya ba zan kara a garin nan ba”. Ta kinkimi sauran kayan ta yi waje. Ibrahim ya mike ya ajiye jaridar a kujerar, ya shiga bed room din Rahanen ya bude cupboard ya soma diban wasu daga cikin kayanta. Karfe daya na rana za su tashi zuwa Chicago a ‘American Airlines’ daga ‘Changi Airport,’ yayin da Inna da Baba Dacta za su wuce gida Nigeria. Daddy ke lallshinta ba da fada ba, “Ki gane Rayhanatu aure yana gaba da komai, wannan karatun ma da kike yi ai na debe kewa ne kawai saboda rashin sanin ranar da Allah zai kawo mijinki. Don haka bai ma da amfani yanzu, ko da can da nake yin kan gaban kaina a kanki, a bisa rashin mijinki ne. To ga shi ya zo, ragamar al’amuran rayuwarki ta fita daga hannuna tana gareshi, shi ya ce zai tafi dake ba zai barki a nan ba, don ba shi da abin yi a nan, bai ma taba zuwa ba. Rahane ke kinga dacewar ke kina wata kasa mijinki yana wata kasa babu wani kwakkwaran dalili?” Ta girgiza kai tana share hawaye jikinta ya soma sanyi. Ya cigaba. “To kin gani. Wani hanin ga Allah baiwa ne, da kanshi in kin kwantar da hankalinki zai nema miki makaranta a duk inda kuke, Ibraheem is a nice person.... Allah ba kwarzanta shi nake yi ba. Wata rana ke da kanki za ki gaya min hakan, lokacin da zai sunkuya yana yi muku ‘doki-sukutum’ ke da yaran ku!”. Ta boye fuskarta cikin gyalenta tana dariya. Dai-dai lokacin da ya fito yana tura dirkekiyar troller dinta, kaya da yawa ya barsu duk da amfaninsu sabida ba zai iya kwasar duka ba sai wadanda suka zama dole. Haka ya wuce su bai san me sukewa dariya ba. A ransa yana fadin “Daddy ke dada sangarta yarinyar nan”. Karfe sha daya da rabi dai-dai na safe suka kullo gidan. Landlord din ya karbi mukallansa da basu kudinsu da suka ragu a hannunsa, da yake na shekara biyu cif Daddyn ya biya, yau kuma shekara daya da watanni biyu kenan, amma Daddy ya ce ba zai karba ba ya bar masa. Zuwa sha biyu da rabi suna kan layin screening. Karfe daya dai-dai jirgin ‘American-Airways’ ya soma tafiya a kan kwaltarshi. Yana wani irin kartar kasa. Rahane na share hawaye tana kallon dogayen gine-ginen kasar Singapore da suka soma kankancewa yanzun a idonta, a sabili da daidaito da jirgin ya soma a kan gajimare duk da bai keta hazo ba, tana fadi cikin ranta, “Bye-bye Singapore...... Bye-bye Informatics!!!”. Karfe biyu na cika suma su Daddy KLM ya lodosu zuwa Nigeria bayan yayi transit dasu a India. ***** RAYHANAH A CHICAGO Sanda suka sauka a babban filin jirgin saman Chicago ruwan sama ake yi kamar da bakin kwarya. Kalma wannan bata shiga tsakanin Ibraheem da Rayhanah ba. Domin dai har zuwa lokacin zuciyar Rayhanah ba ta yi sanyi ba da wannan yankan kauna da Ibraheem ya yiwa karatun ta, karatun da ta sha bakar wuya a kanshi, ta kuma ciwa buri mai yawa. Rahane ta dauki wannan karatun matsayin madafar rayuwarta ta wata rana. A kullum tana tuna maganganun Babanta ne da ya ce, ta yi kokari ta dinga tunawa a ko’ina ta tsinci kanta, ita ba kowa ba ce.... ba ‘yar kowa ba.... ba ‘yar kowan-kowa ba....face talaka ‘yar talaka. Jikar talaka. Tayi kokari ta tsaya da kafafunta. Kuma kar ta zurfafa buri. Don haka wannan karatun shikadai ne burinta a rayuwa. Tana da burin zuzzurfan ilimi domin cin gajiyarsa wata rana, tunda su ma su Daddyn alfarmar ilimin suke ta ci har su ma suka samu suka rabesu ana ci tare da su. Har yau zuciyarta ta gaza sallamawa zuwa ga karbar Ibraheem matsayin mijinta balle wani matsayi na soyayya ko akasinta a gareshi gaba daya.....domin a ganinta ya fi karfinta, ta dai yi kokari ta cire Yaya Khalipha a ranta, amma ta kasa cike gurbin da Ibraheem. Rahane ba ta gama firgita da al’amarin Ibrahim din ba sai da ya sanya mukulli ya bude wani American-Villa suka shiga har ciki da motar asibitin (Illinois) wadda ta kwaso su daga airport da chauffeur guda, mota ta alfarma da bata taba shiga irin ta ba ko a Singapore. Gajiyar dake tare da ita ba ta hanata fara yin sallah ba sannan ne ta ji ta sakayau. Ibrahim na waje da makotansa mutanen Sri Lanka suna yi mishi barka da zuwa, kafin ya sallamesu ya shigo Rayhanah ta yi barci a falon cikin kujera da kayan jikinta ba ta nemi ko da bed-room ba. Ya dade tsaye a kanta hannunshi cikin aljihun dogon wandon Armani dake jikinsa da bakar rigar sanyi mai kauri, a yadda ta yi kwanciyar, za ka fahimci sanyi take ji, ta cure ta dunkule jikinta cikin gyalenta wanda ba wani kauri ne da shi ba. Kallon ta kawai yake al’amuran da suka shude shekaru goma sha biyu a baya na dawo mai filla-filla. Yarinya mai yawan jin kan mahaifi, da nuna mishi sadaukarwa. Mai hakuri da Abida, da rashin mutuncin ta. Mai son Azizah da yin biyayya ga Mami. A saninsa Mami na son yarinyar, amma me yasa ta hana aurenta da Khalipha? Zuciyarshi ta yi saurin halarto da amsa (saboda wani baya auren matar wani). Shi mijin aure tun ranar da aka haifeka aka rubuta maka shi a allon da baya kankaruwa (Lauhul-Mahfuz). Khalipha fari sol mai kyawun da za a likashi a goshi, me yasa yake son Rayhanah? Baka..... not so much attractive...... Ba kowane namiji ne ya san darajar mata irin Rahane ba, sai su likitoci da suka san amfanin kowacce gaba da aikin kowacce halitta ta dan Adam. Wannan Rahanen, ya sha matukar wahala kamin ya manta da ita da al’amarinta bayan barowarsa gida. [12/28/2019, 12:34] Takori: ‘She’s that something which goes far beyond mere or casual assumption!’ Da ya yakice yayi fata-fata da shi daga zuciyarsa a isowar sa Chicago, wato shekaru goma sha biyu a baya kada ya zamo hindrance ko obstacle ga cigaban rayuwar sa da kyakkawan kudurin da ya fito da shi daga gida. Dadin dadawa a lokacin ya kalubalanci kansa kan damuwa da al’amarin ta da cewa tausayi ne kawai. Me take da shi da za’a so ta akan shi a lokacin banda deficiencies and inefficiencies? (Tarin nakasu). A tsarin halitta da dabi’a (personality) irinta yake burin samu. Abin nufi, baya son macen data cika kyau, baya son farar mace, baka yakeso ‘yar uwarsa, baya son mace mai kyale-kyale da artificial beauty, baya son wadda ta waye da yawa, baya son mai budadden ido, baya son wadda suka hada alakar jini, baya son yar masu kudi ko masu mulki duk da baya son ‘yar talakawa likis. Ya sani ba wanda ke samun rayuwa ko abokin rayuwa 100%da burinsa. Don haka zai iya cewa ya samu Rayhanah 80% da burin da ya dade yana ciwa abokiyar rayuwar sa. Da yake Allah ya rubuta matarshi ce ga shi ya biyoshi da ita har inda yake. Ba da yunkurin shi ba, ba da motsin sa ba, ko wani kokarin sa. Sai don kasancewar al’amarin su rubutaccen al’amari. Sai dai har yanzu ba zai iya sakin jiki da Rahane ba, ba don komai ba sai don cewa.... bai yarda da akwai soyayyarsa a zuciyarta ko da digo daya ba, kawai dai an fi karfinta ne ita kuma ta yi biyayya...... Amma Khalipha take so, tunda har maganar aure ta shiga tsakaninsu. Allah kadai ya san irin soyayyar da suka yi kafin zancen aure ya shigo ciki. In haka ne ta yi kadan ya mika mata dimbin soyayyar da ya tanadarwa matarsa alhalin ita ba son shi take yi ba. Sai dai ya yi mamakin yadda ya kasa sarrafa kansa a kanta the very first day of their encounter....(rana ta farko da haduwarsu) har kuma yanzu haka abin yake, amma zuciyarshi na ta karyatawa da kalubalantar hakan da gangan. Haka ya ci gaba da tsayuwa yana kallon ta yana kissima abubuwa da yawa..... zuciyarshi na azabtar da shi a kan tunani mara tushe da makama (kishi akan abinda bai gani ba). Motsi ta yi don ta gyara rufarta, sai ta ji alamun tsayuwar mutum a kanta, ta bude idanunta a hankali sai cikin na Yayan, idanunta sunyi kalar da ba zai iya jurewa kallon cikinsu ba tare da ya kara karyata kansa ba. Don haka shi ya fara dauke idonsa da hanzari ya wuce bed room ya sakarwa kanshi shower. Sanda ya fito falon cikin shiri ne na bakaken suit da jibgegiyar rigar sanyi, kanshi babu hula, sumar nan ta yi luf a kanshi har sheki take na alamar ta kara ganin ‘ArganaVita’. Nan ya taddata inda ya barta a yadda ya barta. Haushi ya tokareshi bai san cewa ita ma haushin nasa take ji ba. Don haka yana hararar ta ita ma tana dan harararsa da karshen idanunta, ta yi kicin-kicin da fuska duk sai ta bashi dariya. Ya girgiza kai ya ce, “Ni kike harara ko Rayhanah?” Ta zumburo mishi ‘yan tausasan lebbanta gaba, abinda Ibrahim baya iya jurewa gani kenan (those luscious lips) ba tareda ya karya ta kansa ba, don haka ya yi sauri ya kawar da kansa. “Dube ki da Allah ba wanka ba sallah kina ta shirgar barci, to wallahi ba zan dau wannan ba. Nan ba Inna ba Daddy sai in yi kuli-kulin-kubra dake ba wanda zai cece ki. Mintuna ashirin na baki kafin in dawo in ganki yadda na soma ganinki, in ba haka ba, na rantse..... ni dake ne a gidan nan.......” Ya sa kai ya fita. Ta bishi da kallo tana mamaki tana harararsa. Mamakin da take yi shine, yadda duk ta zaci al’amarin ba haka ya zo ba, ta dauki Ibrahim din tuntuni a wani mutum mai raini da wulakanci. Ba za ta taba manta labarin data ji Daddy na baiwa Inna Jumah ba a (farm-center) suna hira ne inda yake gaya mata dalilina na hada auren Rayhanah da Ibrahim shine halayen Ibrahim duk irin na Rayhanah ne wato miskilanci don haka yake da tabbacin zasu ji dadin zama da juna, yana bata labarin ranar data bude idanunta daga hatsarin da sukayi ita da Iya. Daddy ya ce ya ba ta tea ta sha a AKTH ya yi baya ya buya ya tura Eric Epatobe wani abokin karatunsa baisan cewa Daddy na ganin sa ba. Tana kuma iya tuna ranar da Abida ta kifa mata pampas na kashin Aziza a fuska ya zo ya gani bai ce komi ba, bai nuna komi ba, bai wa Abida koda fada ba. Sai YAYA KHALIFA ne yayi hakan. Tun zuwanta gidansu kafin ya bar gidan, kalma wannan koda ta gaisuwa ce bata taba hadasu ba. Tun daga lokacin ta bawa Himu matsayin wani mutum mara kirki. Don haka ne fuskar da ya karbeta da ita a Singapore ta bata mamaki kwarai, ta kuma sanyata cikin shakku, akan tunaninta na baya a kansa. A ranar da ya ganta matsayin matarshi a ranar ya hada jikinsa da nata, ya yi mata sumba mai tsayawa a zuci, ba tare da ta yi wani abu don ta ja hankalinsa ba. Ba za ka taba yin hakan ga macen da kake kyankyami ko baka so ba. Wannan ya nuna cewa Ibrahim ya karbeta a matsayin mata ba don kyale-kyalenta ko wani abu special data ke da shi ba. Wannan tunanin da ta yi yanzun, sai ta ji haushin nasa da take ji na rabata da Informatics yana decreasing a hankali cikin zuciyarta. Zuciyarta ta ci gaba da yin sanyi, jikinta ya yi la’asar. Ta samu kanta da mikewa don cika umarninsa. Ba don tsoron kuli-kulin kubrar da yace zai yi da ita ba. A’ah, sai don wani kima da daraja har ma da martaba da ya kara a idaniyarta. Yanzu ma taunar gefen gyalenta take cike da tunani da bege mai yawa dake mamayar ta. Duka kofofin guda hudu dake cikin babban falo a rufe suke da mukulli, sai daki daya wanda ya fito daga cikinsa kenan, kuma can ta ga kayanta a kan gadon dakin. Cikin nauyin ido da nauyin zuciya Rayhanah ta daga ido tana karewa cikin dakin Ibrahim kallo. Daki ne sosai irin na manyan proffessionals din Amurka, babu tarkace ko kankani. Komai yana ma’adanarsa, na’urori da yawa bata san na menene ba duk da sunfi kama da computer ta san ba duka ne computer ba, sassanyan kamshi ke tashi na room fresh din rasp-berry. Dakin da dumi yake sosai, na’urar dumama daki na aiki. Tun ganin ta dashi a Singapore taji tana so ta san menene sirrin gayun Ibraheem? Don ita dai a kafatanin rayuwarta bata taba ganin mutum irinsa ba (mind blower!). Ashe amsarta tana toilet da ta rage kayan jikinta ta shiga don yin wanka. Abubuwan da ta gani a kan cabinet din bandakin tunda take a Singapore ba ta taba gani ba ko a shaguna. Hatta macleans din da yake amfani da shi daban ne, kayan aski da after shave designer din harrods, inner wears da towels a jere cikin wata cabinet din.Bath foam, bath gel da exfoliating gels kala-kala duka designers. Kayan gyaran akaifa daban, na gashi su ma daban (Argan). Rayhanah sai ta zama ‘yar kauye fitik! Ta kuma samu amsarta da wurwuri. Ba komai ne sirrin haiba da kamalar Ibrahim ba tsafta ce, amma mai tsada. Sai ta ce a ranta, “Matarshi ta more”. Zuciyarta ta jefo mata tambaya a take, “To wace ce matar tasa in ba ke ba?” Ta kyabe baki ita kadai abin dariya, a fili ta ce, “A’a, ni a suwa? Ba ya ce hudu zai auro ba? Kuma na sani ciki har da ‘yar gayun nan ‘yar’uwarshi Nabilah, ni ai ta ladan noma ce, matar shige ce, matar shige kuwa ai bata da wata daraja”. Abin da take fade kenan a fili ita kadai, tana ninkaya tana sullube jikinta da kumfar ‘Cien’ cikin jacuzzi. Ta dauki mintuna masu tsayi tana yin wankan cikin ruwan dumi mai dadi da kamshi, ta wanke gashin kanta da shampoos din Ibrahim wato Argan, sai taji sun russuna daga karfinsu (steamed) tayi brush yadda ta saba, ta dauro alwala ta dauro tawul ta fito gashin kanta na digar ruwa. Sauri ta yi ta zura Pakistan rowan Kwaiduwar kwai masu kyau a jikinta (beig), cikin Jakarta ta ciro mataji tana sharce kakkarfan gashin kanta domin bai dauko da drayer ba cikin kayan da ya kwaso mata. Da sallama ya turo kofar, ya dan kalle ta ya rausayar da kai wato ya ji dadi ta bi umarninshi, don ya dauka ba za ta yin ba. “Uwargida Rahane...... budurwar Yaya Khalipha, irin wannan daukar wanka haka?” Ko kula shi bata yi ba, don ta soma sikewa da zancen Yaya Khalipha da yake yi mata kamar bai yarda da ita ba, saboda sun so juna ita da Khalipha, wanda ita yanzu in ba ya kira sunanshi bama ba ta tuno shi. Ta ci gaba da tazar kakkarfan gashinta, sai ya iso gareta ya kai hannu yana duba gashin nata baya ko fita jikin kumb saboda karfinsa. Ibrahim shiru ya yi, amma wadannan natural features na Rayhanah na kara ribatar zuciyarsa. Ta yarda cewa ita baka ce cikakkiyar Nigerian, ba ta kokarin canza launin fata ko canza launin gashi, sai dai ta tsaftacesu. Tsoron Ibrahim da take ji a Singapore ya ragu sosai tunda bai sake attempting abin da take jiwa tsoron nasa a kai ba. Yanzu ma bai kai hannu gareta ba, gashin nata kadai ya taba, ya juya ya fita kicin ya jero masu kayan ciye ciye da ya shigo dasu a tray da kansa ya dauko, su burger da pizza da kayan McDonald’s da fresh milk ya shigo da shi har bed-room din ya aje a gefe. “Kinga malama daina tazar nan zan ci abinci, kada ki jefa min gashi a ciki”. Sai ta kame gashin ta daure da ribbon ba ta ce komi ba. Sai ya ji dan tausayi ya kama shi, saboda tunda suka zo bai yi mata magana ta dadin rai ba, alhalin ya rabota da wadanda ke sata farin ciki suna tarairayarta (Daddy da Inna). Yana kuma sane da cewa cikin bacin rai da kawa-zucin karatun ta da ya rabota da shi take. Yayi sanyi gabadaya yace a hankali, “Rayhanah idan ba za ki daina yi min abubuwan da kike yi min din nan ba, ba zamu shirya ba. Kin kama bakinki kin dinke, ina ta magana ba za ki amsa ni ba. Rayhanah ko a dawo lafiya baki ce min ba, dazu da zan fita, baki tambaye ni ina ne dakin ki ba, na dawo ko sannu da zuwa baki ce min ba. Kina jin yunwa ba za ki gaya min ba. Ba sai kin yi hakan za ki nuna min cewa Khalipha kike so ba ni ba….” Bai kai karshen maganarsa ba sai ga hawaye sun biyo kuncinta…… bai damu ba ya ci gaba da fadin. “Ba dama in fadi Khalipha sai ki sa min kuka, idan shi kika aura za ki yi mishi wannan shakulatin bangaron da ni kike mini? Ko ko don ni lika miki aka yi? Kina bakin ciki an raba ki da farin Balarabe an daura miki baki a kafa.... to dai ai gara ni sau dubu da wannan bakar fuskar taki da kike min rowarta. In don dan kiss din da nake roka ne a wajenki na bari, na zo inda zan samu a bagas, ba sai na biki ina lallashi ba. Kin ga mukulli nan, dauki ki tattara koma tsani ki kama hanyar dakin ki wancan dake kallon nawa, ranar da kika shirya karbata a mijin aurenki, sai ki zo nan inda nake….. have your way out…..!!!” Ya fadi da dan daga murya yana nuna mata kofa. Ta sulale a kan kafafunta tana kuka sosai ba ta fitan ba. Sai ya ja wani mugun tsaki ya mike ya yi fatali da abincin nasa ya suri mukullin mota ya yi waje. Tana jin tashin motarsa daga inda take, sai ta ji zuciyarta kamar ta fashe. Ta yi kukanta mai isarta, babu mai lallashi babu wanda ya san tana yi. Fitar hawayenta a ganinta shi ne hukunta zuciyarta da ta ki yin farin ciki da Ibraheem a matsayin miji. Amma kuma take KISHINSA!. Abincin da ya tankwabar ta bi ta tsittsince ta yi kokari ta ci amma ta kasa. Rabon ta da abinci tun a cikin jirgi, da ta tabbatar ba za ta iya ci din ba, tunda wanda ya sayo da kudinsa bakin cikinta yasa ya kasa ci bai ci ba, ya fita yana mai fushi da ita. Ya kasa ganeta ne, ita ba ta da yawan magana, yawancin abubuwa ma in ya fadi mata ba ta san amsar da za ta ba shi bane, shi yasa take yin shiru. Shima kuma da yana Kano ai haka yake, ba ta san yaushe ya koyi son surutu ba, abu kadan ya ce Khalipha wanda dare daya ta nemi gurbin da ta saka shi a ciki a zuciyarta ta rasa. Ya shafe kamar ba a yi shi ba (Son). Me yasa yake yi mata duka wadannan tuhume-tuhumen marasa amfani a gareshi? Abin da ya wuce, ya wuce a zuciyar Rayhanah…….. Har wata shukar ta dasu, tana so ta fidda rassa, ta yi sabuwar yabanya. Wannan bishiyar kuma ba wata ba ce illa dan tsiron da Allah ya dasa tsakanin mace da mijinta na sunna, ba irin na saurayi da budurwa ba. Idan ya ci gaba da zarginta a kan Khalipha babu shakka yana daukar alhakin ta, ina ruwansa da abin da ya gabata a wata rayuwa can da ta shude wadda ba shi da hurumi a ciki? Abin haushin ma wai a kan Yayansa ciki daya. Rayhanah ba ta san cewa da matacce ma mai sonka na kishi balle rayayye. Karfin kishin miji a kan matarsa na da nasaba da adadin soyayyarsa gareta. Don haka ita ma ta yi fushin, ta tattara inata-inata da mukullin da ya jefar mata ta yi dakin da ya batan. Ta so ne ta shirya kayanta cikin cupboard amma ta kasa. Yunwa ta ci karfinta, damuwa da fushin nasa ya fi nata fushin. Sai ta kasa hassala komai ta yi tagumi a gefen lafiyayyen gadonta ta rasa abin da ke mata dadi. Dakin kawai take kallo da kayatuwar zamanancinsa. A yau ne Rayhanah ta taba sha’awar Allah ya ba ta ‘ya’ya, ko ba komai su din sanyin zuciya ne a lokacin da ubansu ya hutsance, sannan abebaden debe kewa ne. Har agogon bango ya buga karfe goma sha biyun dare a Chicago ba ta ji shigowar motar Ibrahim ba. Sai ta fara sana’ar tata wato (kuka) har da addu’ar Allah ya sanyaya zuciyar IBRAHEEM. Har da jan Ayar “qul yaa Naaru kuuni Bardan wa Salamun alaa Ibrahimu...” Me ke faruwa da ita ne haka a kan Ya Himu? Da fushinsa ya tafi da dukkan farin cikinta? Walwalarta da bukatun rayuwarta ta dan Adam (barci da abinci). Wadannan alamu ne na wani mutum da ka damu da shi matuka. Ibrahim ya zo ya yi karan-tsaye a rayuwarta da zuciyarta. Ta yadda har bacin ransa ya tafi da sukunin zuciyarta da kuzarin gangar jikinta gaba daya. Dungurgur Rayhanah ke zaune, duk iya sata irin ta barci ya kasa sace Rayhanah. A kan idonta lokacin sallar asubahi ya yi, ta yi sai ta ci gaba da zama a inda ta yi sallar, a lokacin ne barci mai nauyi ya dauke ta. Ba ta farka ba sai a dalilin tashin kira’a daga redio dake fitowa daga falo, wannan ya tabbatar mata Ibrahim din ya dawo. Kuma da gaske yake sai ranar da ta shirya karbarshi a matsayin miji zai sauko daga fushinsa tunda ga shi bai kwana gidan ba, ya dawo kuma bai nemi inda take ba. Yaushe ce wannan ranar? Me za ta yi din ya nuna ta karbe shin? Ita tun ranar da ta san Ibrahim aka aura mata ta karbi yin Allah, babu komai cikin zuciyarta a yanzu sai so da kauna irin na mace da mijin da suka yi aure bisa tubalin soyayya. To shirin da yake nufi din ne ba ta gane ba, in dai hira ce da surutu ba ta iya su ba, ta san kuma shima din bai iya ba, banda yanzu da bakinshi ya bude. Mai zai hana suyi zamansu yadda Allah ya haliccesu? Su yi magana a inda hakan ya zamo dole, kuma mai muhimmanci? Tunanin Rayhanah kenan. ***** [12/28/2019, 19:06] Takori: Toilet din dake makale da dakinta ta shiga hajijiya na dibarta saboda yunwa wadda ta haifar mata da ciwon kai. Wanka ta yi a daddafe, ta yi brush ta kuskure da listerine, sannan ta fito. Kayan da ta dauka riga da wando ne suit na mata masu kauri da dogon hannu maroon kala, ‘yan gidan ‘george’. Ta bi ta feshe ilahirin gabobi da kusurwoyin jikinta da deo-spray din rexona, ta cakuda da turarenta na din-din-din (Makhmariyyah wa lamsa nectar), ta tausasa labbanta da vaseline din avon ta murda kofa ta fito falon. Yana kwance ruf da ciki a doguwar kujera, exercise wears ne a jikinsa. Da alama ya yi exercise din ne ya gaji yake hutawa. Ta karasa ta zauna a kujerar gefensa kanta a kasa ta yi shiru. Ya ji bude kofarta da fitowarta amma bai juyo ba, don ya san ba wani abu za ta ce masa ba, shima bai san me zai ce mata ba. Amma ga mamakinsa sai ya ji ta zauna a kasan kujerar da yake kwance muryarta na dan rawa ta ce, “Don Allah don Annabi ka yi hakuri Ya Himu, Allah ni ban san abin da zan dinga ce maka bane shi yasa nake yin shirun..” Ya yi shiru bai tanka mata ba. Sai ta sake cewa cikin damuwa ta gaske, “Ka gaya min abinda kake so in dinga gaya maka din, sai in gaya maka…” Bai juyo ba amma dariya ce ta kama shi, a kalla ta nuna ba ta da wani ra’ayi nata na kashin kanta sai nasa. Ya mike gaba daya ya zauna sosai a kujerar ya mike santala-santalan kafafunsa a kan tebirin gilashi, ga alama ya yi matukar yin sabo da irin wannan zaman. Ya dube ta a hankali ta sadda kai tana share hawaye ya ce, “Yaa Ladif! Ke kam baki da aiki sai kuka kamar matar mamaci? To ai kinga abin da bana so din kenan, kukan. Rayhanah ya za ayi na ga farin ciki da walwala a fuskarki? Bayan Daddy ya ce min kina hira har da dariya, ko duk a cikin rashin son nawa ne Rayhanah? Me zan yi ki saki jiki dani ki daina sani a gaba kina min kukan nan?” A hankali amma da alamar fusata cikin consonants and vowels din sentence din da zai fito daga bakinta tace, “Ka daina tuhumata a kan Yaya Khalipha!”. “Saboda kada in taso miki da son da kike masa?” “Ka ga abin da bana so din kenan”. “Sai in yi shiru, ni ina aurenki kina tunanin wani can?” “Ni na ce maka ina tunanin sa?” Ta fada muryar na kara yin rawa. “Kada ki yi min kukan saurara….. dago ido ki dube ni…..” Ta kasa dagowar sai da ya sake maimaitawa a dan zafafe. Cike da nauyi, da tsoro da firgita ta daga idanunta a hankali ta dube shi. Abin da ta gani cikin idanun Ibraheem din suna da yawa, ga kishi, ga rikici, ga neman rigima, ga neman tada zaune tsaye….. sannan ga so da kauna mai yawa….. so yake ayi ta rikici kada a daina ba shi da alamun saukowa idan ba a fadi yadda yake so ba. Sai ta mike ta yi dakinta da sauri-sauri da gudu-gudu don zuciyarta da gangar jikinta ba za su iya jure rikicin nasa ba. Shine bai son a zauna lafiya sai dai ya yi ta tone-tone kamar kaza, to ita ina yake so ta jefa ranta? Eh, da gaske ta so Khalipha domin mutum ne mai kyautata mata, mai son ganin walwala da farin ciki a fuskarta da zuciyarta…. Mai son inganta rayuwarta, mai darajata a duk lokacin da Abida ta wulakantata. Mai nuna mata cewa nakasa ba hujjaba ga jera kafada da sauran mutane! Yaya Khalipha yace da ita a lokuta da dama “You are only disabled if you truely believed you are .........!! He’ll stand by her even when the whole world turns its back on her..... he's indeed her pace-setter!!! To mai yi maka wannan ya za ayi ba za ka so shi ba? Tunda ita zuciya an halicceta ne da son mai kyautata mata??? To Allah mai juya al’amura bai nufi za su yi aure ba, ya canza mata da shi, kuma ta karbi canjin, ta gane abubuwa da yawa wadanda a da ba haka suke ba. Wato sai da Ibrahim ya zo ne da ‘yar mu’amalarsu ta tsahon lokacin nan ta soma rarrabe abubuwa. Ta fahimci ta so Khalipha so ba irin wannan da take yi a yanzu ba. So ne na rama halacci ga wanda ya yi maka alheri. So ne wanda ba ta taba jin tana sha’awar hada jiki da Khalipha ba, zuciyarta ba ta taba rikicewa don ta ga Khalipha ba, ko don ya kalle ta. Amma shi wannan (Ya Himu) ….... ??? Ta girgiza kai. Ba za ta iya fassara abubuwan da take ji a zuciya da gangar jikinta a kansa ba. Shine ke gigitata, shine ko magana ya yi mata ko ina a jikinta sai ya amsa. Shine bacin ransa ke kassarata ya sanyata kasa yin komai including barci da cin abinci dolen dan adam. Shine mutum na farko da ya rungumeta ya hada da jikinsa da nata ya zuba mata wasu chemicals cikin bakinta da sassan jikinta gaba daya, da suka karkashe kwayoyin son Khalipha da birbishinsu daga kowane sako da kowanne lungu da kusurwa na jiki da zuciyarta. Suka dasa wata bishiyar, wadda ta yi sauri ta fidda rassa da korran ganyayyaki suka yi girman da suka rufe kofar zuciyarta ruf, daga tunanin kowanne Da namiji cikin dan lokaci kadan, suka shimfida tasu katuwar dardumar suka zauna suka baje, suka yi kane-kane suka kankane ko ina, suka yi babakere a kowanne angle. (Kusurwa). Wannan shine matsayin Ya Himun a yanzu da ba za ta iya fassara masa ba. Ba ta san kuma wata hanya da za ta bi ta nuna masa hakan ba. Ta yarda ya ci gaba da zargin nata da tone-tonen nasa in sha Allahu ta daina damuwa, in ba haka ba Himun so yake ya tarwatsa mata zuciya. Sai ta soma nemawa kanta abin debe kewa don ta raba kanta da damuwa da fitinar Ibrahim, kawai sai ta dauko biro da exercise book ta ce “Bari in fara RUBUTU!” Sunan farko da ya fado mata a zuciyarta shine, bari in sawa littafin suna RAYUWAR RAYHANAH! Bari in rubuta labarin rayuwata tun daga kauye zuwa birni. Bari in bawa ‘yan’uwana mata da masu irin lalurata labarina ko sa sanyawa zuciyarsu hope da salama… (kada su fidda rai da rahamar Ubangiji (waraka) domin shine mai sanya cuta mai kuma yayeta a sanda ya so. Babu wata cuta da aka saukar a bayan kasa ba tareda an saukar da ita tareda maganinta ba. Cuta lokaci daya take shiga, amma waraka sai lokacin da Allah YA so. Duk kudin ka duk mulkin ka, lafiya ta Allah ce. Rai dai, baya rabuwa da rabo, saidai idan ya kare! Cikin littafin nan ba zan manta da mutum biyu masu muhimmanci ga rayuwata ba. (DADDY) Dacta Mansur Balarabe Takai da Abdullahi Mansur Takai (YAYA KHALIPHA…..) ba zan manta da IYA BILKI ba, da ADO da ya yi sanadiyyar da na fito daga kauye har a yau na samu alfarmar zamantowa barin rayuwar YA HIMU na mallakeshi a matsayin MIJI NA. Really it’s a blessing….. a mysterious miracle ba isa ta ce ba dabara ta ba......!!! Watakila idan na rubuta yadda nake son YA HIMU zai fi fahimta ya yarda dani ya daina zargina a kan Yaya Khalipha........ Ya daina azabtar dani da fushinsa, wanda ya fi zafin bulala a dukkan jikina…....... Ba zan manta da Jawahir ba…. Ita ma MAMI ba zan taba mantawa da ita ba. Na yi mata uzuri sau (70) a bisa yadda rabuwar mu ta kasance, domin a da, ba haka take ba…. “ Haka ta yi ta rubutu tana tsiyayar da ruwan biro. Sallah da wanka, shan tea, cake da juice dake cikin firij a kicin dinsu kadai ke tada ita tsawon kwana uku. Ta tattara Ibrahim da iyayen cefanensa ta watsar, ko tattasai daya ba ta taba ba. Daga baya ta fahimci ya samu kuku da mai gyaran gida duka Turawan Ohio ne. Taji yana kiransa Benjamin. Idan ya gama girkin yana aje mata a dining ya kuma danna mata intercom ya sanar da ita, ‘to’ kawai take cewa, amma yadda ya aje haka yake daukar abinsa. Ibrahim ya soma damuwa, me yarinyar nan take yi a daki tsayin kwana hudu ba ci ba sha? Kada fa yaje wani abu ya sameta, ga shi ta garkame kofa da mukulli ta ki cire shi daga jikin kofar. Wai ita ma nan fushi ta yi kenan? Ban da ya damu da rashin cin abincin ta Allah sai dai ta yi ta gaji ta fito ko sati daya ne. Dawowarsa kenan daga asibitinsu ko farar rigar likitocin dake jikinsa da abin wuyan sa bai cire ba ya doso dakin nata, da karfi yake bugawa sosai yana fadin "Ba za ki bude ba Rayhanah?" Banza ta yi da shi ta ci gaba da rubutunta. Tana fadi cikin ranta, "Idan ka balla kofar ai taka ce ni ina ruwana?". Bugun duniya Ibrahim ya yi amaryar ta ki budewa, har hannayensa sun fara zafi. sai ya juya ya nemo sikundireba da wuka ya zo yana kwance kofar. Ita dai ta ji dan sukur-sukur amma ba ta kawowa ranta kofar yake kwancewa ba. Ibraheem so ya yi ya bata bahagon mari hagu da dama, amma a yadda ya risketan bisa study table tana ta rubutu sanye da belted- waist –shirt din da ya fara ganinta da ita a singapore, ta yiwa gashin kanta tufka mai kauri guda biyu ta makalesu da farin dutse (bead) ta zama kamar wani fure da mutum zai so daukewa ya gudu ko ba’a bashi ba, sai ya daskare a tsaye. Rayhanah ta ji ya kwance kofar ya kuma shigo, amma juyowa wannan ba ta yi ba. Ya tabbatar ba za ta kalle shi ba, ba za ta yi mishi magana ba. Sai ya tabbatar lallai fushin nata na gaske ne. Wace irin miskilar mata Allah ya hada shi da ita haka! Allah sarki Doctor I.M Takai, komi nasa kwancewa ya yi ya kasa marin da ya shigo da niyyar yi, ya jingina da kofar sakamakon kafafunsa da suka ce; ba za su iya daukar nauyin gangar jikinsa ba. "Rayhanah!" Ya fada a hankali cikin kwantaccen sauti da tausasawa mai nuna amsar laifi. Amma ba ta juyo ba. Rubutu kawai take ta yi kamar SUMAYYAH TAKORI. A lokacin ne kuma hawayen da suka cika mata ido suka mirgino a kan takardunta..... ta zari tissue guda daya tana tsane su da hannun dama tana ci gaba da rubutunta da hannun hagun (lefter) ce. Ya sake kira, wannan karon da rawar murya "Rayhanah….. Rayhanah...... Rayhanah, am your husband…… kin zabi azabar Allah ta tabbata a kanki ta hanyar wulakantani………..???” Da sauri ta dago fuskarta jike da hawaye ta dube shi. Sun dade suna kallon juna kafin Ibrahim yayo tattaki ya zo dan tebirin nata ya rungumeta gabadaya ta baya, ya rufe idonsa sosai yana ajiyar zuciya kafin ya bude idonsa a kan takardun nata. Hawayen da suka jika mata fuska, da kuma saukar su a kan katoton exercise book din, suna jika shi, da kuma rungumar da Ibrahim yayi mata daga bayanta bai hanata ci gaba da yin rubutun da take yi ba, don gudun kada ta manta. Duk da cewa ya dora mata nauyinsa kadan. Idona akan takardun nata. Dai-dai sanda take rubuta; “.......he didn’t trust me anymore........ Yana referring kowanne motion na zuciyata a kansa da KARYA… Bayan kuma sau tari tsoron kar ya ce na yi KARYAR yake kidima ni in yi masa shiru. Idan ni munafuka ce don ina son YAYA KHALIPHA, nayi zaton an halicci zuciya ne da soyayyar mai kyautata mata? Shi da yake sanya zargi a cikin AURE ya ya sunan sa.......??????? Fizge littafin ya yi ya keta shi gida biyu…. Bude baki ta yi cikin takaici, haushi da tsoro duka a lokaci daya, ta kuma mike tsaye da nufin fita ta bar mishi dakin tun da wuri, sabida ganin wani irin temper da ya samu kansa a ciki, sai ya fizgo hannunta da azama ta fado jikinsa. Shima bashi da kwarin, don haka gadon suka fada baki daya kamar jikakkun tsummokara. Sai da ya tabbatar ya kanainayeta ya boyeta sosai ajikinsa, ya hanata yin koda kwakkwaran motsi don ta kwaci kanta, ya hanata yin kukan ta hanyar rufe bakinsa da nata. Kissing din da yake gudanarwa ga RAYHANAH zazzafa ne sosai, shi kansa bai san zai iya yinsu ba in real life ga kowacce diya mace a duniya saidai cikin kintace (imaginations). Domin sumbace dake wanzuwa kadai a bisa umarnin zuciya da jagorancin so da kauna da kuma bukatar gangar jiki na miji ga matar da yake mutuwar so..... dying for her......!!! Rayhanah ta rasa inda za ta sa kanta da sabon al’amarin da ya tunkaro ta a yau. Har sai da GIRMA ya risketa. Girman da take zaton shekaru sune shi, ashe basu bane. Girman diya mace daban ne. A yau ta tabbatar ta bi sahun sauran mata, sai dai nata GIRMAN da wahalar da ta ci kafin ta same shi daban ne da na sauran mata. Domin nata mijin ko a cikin MAZA sunansa MAZAJE….. ya kuma nuna mata bambancin sa da sauran maza….. ta hanyar sauke mata gaba dayan kauna da soyayyar shekara da shekaru da ya adanawa matarsa. Da shi kansa baisan wacece ba. Wanda ke nufin, ita din, ita tayi nasarar mallakar gurbin UWAR IYALIN. Ko da za a karo wata daga baya, to ba za ta samu komai ba, sai burbushi ko ragowar IBRAHEEM MANSUR TAKAI (leftover). In ma akwai burbushin da ragowar kenan. Tayi amanna da cewa Ibraheem ya mallaka mata zuciya da gangar jikinsa gaba daya. Ko da ya samu nutsuwa bai rabata da katafaren kirjinsa ba, domin shi kansa ya san ba karamar azaba ya gana mata ba. Sannan ya ki bada damar ta yi kuka, a doke ka a hanaka kuka! Shi kansa ya san bai bi a hankali ba don shima al’amarin sabo ne a gareshi. Wanda ya jima yana tsimayen ranar zuwansa, ya sha kissima a yadda zai zo, da wadda zata amsheshi, would she be fresh on it kamar shi? Wani abu ne da ya fi karfinsa, ya fi karfin duk yadda ya zace shi. Ya tabbata Rayhanah is his first luv..… ya so ta tun tana ‘yar Takai…. Ya so ta a sanda Daddy ya maida ta ‘yarsa….. ya so ta a sanda Abida ke wulakantata ta yadda har yau babu alaka mai dadi tsakaninsa da Abida… Haka ya so ta a ‘yar Baba Dacta mai hearing-aid da har yau bai san ina ya tafi ba. Ya so ta son da ya tabbata Khalipha bai yi mata shi ba, domin daga dukkan alamu tausayi, jihadi da imani sune jigon soyayyar Khalipha. Shi tashi babu wannan a cikinta, bai taba jin tausayinta ba daidai da rana daya, wai don ta rasa wani sashe na halittar dan Adam. Ya yarda babu nakasashshe sai kasashshe. You are only disabled if you truely believed you are....kuma da lalurar da Allah Ya dora matan ta kwarara zuciyarta ta kowanne bangare bata kasa ba. As a medical student as he is a lokacin, ya kan fada a ransa dole ta gode Allah ma tana using hearing aid din yayi mata rana, wani duk gatansa, duk kudin sa bai samu alfarmar da (hearing aid) din da zai yi masa amfani ba. [12/29/2019, 13:31] Takori: Otosclerosis muguwar cuta ce da sai mai tsananin sa’a zai samu kubuta daga gareta. Don haka ya yi hasashen, Rayhanah na daga cikin ‘ya’ya masu sa’a a rayuwarsu, kuma masu baiwa ta daban. Gaba daya halayenta da dabi’unta ba irin na sauran mata bane. Cikin kwanakin da suka yi tare ne ya tantance hakan, sannan masani ne a ilimin psychology matuka. Cikin kwanakin da ya yi tare da ita zai iya dorar da wasu halayen ta wadanda suka taimaka kwarai wajen ribato zuciyarsa da ilahirin gangar jikinsa zuwa gareta, kadan daga ciki sune. Ba ta yin kwalliya ko kyale-kyale wai don ta burge shi. Tana da tsaftarta a kan kashin kanta. Tsaftarta ta kulli-yaumin ce; ba don shi takeyi ba don haka ta riga tazame mata jiki ta kama jikinta ko tayi ko bata yi ba she's luscious and sexy.... Tsaftarta kuma ba ta fuska da shafe-shafe ba ce ko tsadaddun sittiru, a’a, inner tsafta ce. Manyan halayen da ya karanta daga gareta sune ‘pure heart’ wato tsaftar zuciya, da amsar kuskurenta daka nusashsheta, mai saurin yin afuwa da rashin kullaci ga kowanne bil adama, ko da kuwa ya bata mata uziri take yi masa da…. “Ai a baya ya yi min kaza….. ya yi min kaza…. Don yanzu ranshi ya baci ya yi min wannan ba zan kullace shi ba.” Sannan da rashin manta wanda duk ya yi mata alheri ko da za a yi mata mummunar fassara a kansa. A misali, Yaya Khalipha. Idan ta bika ta lallami don ka fahimceta ka ki, to za ta kangare maka ka kasa sarrafata. Sannan rashin yawan maganarta na da alaka da kasa fitowa fili ta fadi hakikanin abin da ke ranta. Ita kuma inner tsafta, abin da Ibraheem ke nufi da ita shine, ma’abota wannan tsaftar a bandakin su take (toilet), a nan ne za ki gane abin da yake nufi ba a kan mudubinsu ko cikin kwabar kayansu ba. Sannan they live a moderate life, yet a modest. Basu yarda suyi ta narkar da kudinsu wajen sayen lesussuka masu tsada da atamfofi masu tsada don su kece raini, da mayukan sauya launin fata masu tsadar tashin hankali don su zama kyawawan dole ba. Sun yarda da yadda Allah ya halicce su and they will be beautifull as such......amma za su kashe ko nawa wajen sayen kayan tsaftar jikinsu da bandaki (toiletries) da turaren da za su shafa a jikinsu da wanda za su fesa a tufafinsu da muhallinsu. Kayan wankan da take amfani da shi mai alfarma ne sannan wanda ta tabbatar (dermatologically tested) ne will in no way or the other change her skin colour. Sabulan wanke bakinta (maclean) shima na daban ne mai lasar manyan kudi, haka (mouth wash) da burshinta duka masu karfin kashe plaque ne accepted and approved by dentists. Mai inner tsafta, har ila yau ba ta barin tsiron gashi ko kadan a jikinta, banda na kai da gira, domin akwai shower shave da wanka kawai za ta yi da shi kowanne tsiron gashi dake jikinta ya bi rariya. Rayhanah hakoranta kamar kankara suke don haske, domin a kalla tana wanke su sau uku a rana, kafin karin kumallo, bayan lunch da lokacin kwanciya barci. Tana kurkure su da mouthwashes (cavity fighters) masu karfi. In bata da halinsu, to bata wasa da yin siwaak da shan lipton data dafashi ya jiku da kanimfari. Mai inner tsafta ba ta jin wahalar sayen turare mai kyau mai sanyin kamshi ba lallai sai mai tsada ba a’ah, daidai karfinta, domin mace wadda ta amsa sunan mace sai da turare, a jiki da muhalli, ba kawai na fesawa a suttura tana barbada kamshi don za ta fita ba, mala’ikun Rahma na rubuta mata zunubin yin zina. Ita ko yaushe ka rabeta ma in har ba ka sunsunata ba, ko ta kusance ka sosai ba za ka ji tashin kamshin ba, sannan ya fi yawa a kayan barcinta. Duk sanda maigidanta ya kusanceta baya iya jurewa sai ya raba jikinshi da nata, domin ya samu nasa kason na ni’imar kamshin fatar jikinta da kamshin bakinta, ya haska idonshi da hasken hakoranta. Ya fahimci Rayhanah tana amfani da fararen kayan ciki ne (inner wears) kuma kulawar da take basu kullum ba ta bari su canja launi, domin ba sai sun nuna datti take wanke su ba, in har ta san ta saka, ta wuni ta kwana dasu, to lokacin wankanta da safe za ta wanke su da omo da bleach ta shanyasu. Inda duk Ibrahim ya sa kai a jikinta baya iya mai da numfashinsa dai-dai ba tare da ya rabi ni’imar da Allah ya zuba a jikinta ba. Ba ta ciye-ciyen kayan mata na shirme da lakatawa da mannawa da turawa, sai dai ta ci wadanda za su kara mata lafiya. Wadanda addini ya yarda su, kimiyyar lafiya ta yi amanna dasu. A fannin sittiru ba irin atamfar da ba ta daurawa in dai kalarta za ta amshi bakar fatarta ta haskakata, ba sai ta dubunnan nairori ba. Ta nairorin ma sau dubu sai ta zabi mai rangwamen kudi ta barta, in dai kalarta ta amshi fatar jikin ta, saboda sanin sirrin atamfa ajikin matar bahaushe, atamfa ko wacce iri ce kyau take indai a jikin Rahane ne. Kuma ita ce favourite regular attire dinta. Wannan ita ce, RAYHANAH MATAR IBRAHEEM!!! Wadda ba kyale-kyale ne ke fizgar hankalin mijinta a kanta ba. Tsafta ce, da gyara. Don ko jambaki, bai taba gani a lebban Rayhanah ba, sai Avon lip Gloss. A tsayin mintunan da Ibrahim ya diba yana bambance kamanni, halaye da dabi’un matar tasa, sai ya yardarwa kansa cewa wannan ita ce MATAR DA YA KE MAFARKI; mai kyakkyawa kuma sassaukan gayu na hankali da tunani, kuma ‘yar bokon data yiwa boko kyakkyawar fassara, though she's not wealthy but she has a great mind! Ba kamar yadda mata da yawa suka jahilci kalmomin guda biyu ba. Turawa da larabawa da yawa kudinsu suke sanyawa suna sayen (Zaitun) don su rage hasken fatarsu. Black is beauty! And there's nothing worth respecting like naturalism!!! Fari ba shine kadai kyau ba, balle wanda akasa kudi aka sayo. Mata da yawa sun gama amincewa cewa yin shampoo (kona gashi) da karin gashi, sanya tsadaddar suttura ta almubazzaranci ko mai zahirantar da tsiraici a wuce ana barbadawa duniya kamshi. A sanya dankwala-dankwalan ‘yan kunnaye, a lambata jambaki shine kwalliya ta wayewa da burgewa…. To ba shi bane a ra’ayin RAYHANAH RASHID TAKAI. ****** Da wannan Ibrahim ya sauke idonshi a kan Rayhanah, sai ya ga ta yi barci tana numfashi cikin nutsuwa, baccin da ba na komai bane face na wahala da azabar da ya gana mata. Shima da ya duba aika-aikar da ya yi mata sai ya ji kwalla ta ciko idanunsa. Ya kasa sakinta, ya kasa aikata komai a kanshi ko a kanta, yana jarumtakar maida hawayensa amma sun ki hakan, sai da suka mirgina cikin gashin Rayhanah. Ya kankameta sosai. Sauran abubuwan da yake tattaunawa cikin zuciyarsa na auratayyar da yayi a yau da Rayhanah, kuma al’amari na farko a tsayin rayuwarsa, da matsayin da hakan ya karamata a zuciyar sa, daga shi sai Ubangijinsa suka sani. Shi da kansa ya fiddo kayan aiki da baka rasa likita da su a gida, don ya tabbata sai ya yi mata stitches, ya ji mata rauni sosai da hakan ya sa shi challenging (kalubalantar) kansa da selfishness (son kai) da rashin tausayi. Bai san kuma ya zai yi ya yi mata ba tareda ta tashi daga barcin hutun da baya son ya rabata da shi ba. Sai ya maida ta kan sofa dake gefe ya yi mata allurar da ta karawa barcinta nauyi, sannan ne ya yi, ya gyara komai ya canza shimfidar gadon. Ya yi wanka ya fita dining don ganin abin da Benjamin ya girka. Ya kai hannu ya bubbude dishes din yana gani; Lemon Ricotta, Pancakes with syrup, Quinoa, Poached-eggs, Sliced bacon, Sliced bread with jam. Abinda Benjamin ya shirya musu a dining kenan matsayin karin kumallo. Yasa murya ya ce, “Benjamin!” Daga can kicin Benjamin ya amsa ya fito da hanzarinsa hannunsa rike da wuka da farar albasa katuwa. Ya ce, “Jeka maza ka yo min farfesun salmon (kifi) easy chicken recipe da omelets ya isa, ina son su in ten minutes”. Benjamin ya amsa cike da girmamawa ya koma ya fara aikin. Minti uku ya kara akai daga mintunan da ubangidansa ya ba shi, ya jero a tray cikin ‘yan kananan bowls din karau (tangaran) zai soma jerawa a dining bayan ya kwashe wadancan maigidan nasa ya fito daga corridor din da zai sadaka da dakinsa yana sanye da farar shirt DKNY an rubuta DKNY din da ruwan kasar zare da dogon (brown jeans) ya debi wanka ya sharce gashin nan nasa da kumfar Arganavita. Shaidar sujjadarsa ta fito sosai a karshen goshinsa. Ga mamakin Benjamin isowa ya yi gareshi da kansa ya karbi katon tray din ya sallame shi. Har sanda ya shiga bedroom din nata da abincin ba ta tashi daga nannauyan barcin da ya tsikara mata allura don ta yi ta yin shi ba. Shima bai bi ta kan abincin ba computer ya kunna yana ci gaba da hidimar da ta kawo shi ta yanar gizo. Ba wani abu ne ya kawo shi ba face tattara ajiyarsa da ke manyan bankunan Amurka daban-daban irin su J.P Morgan Chase, HSBC, U.S Bancorp, Morgan Stenly, Wells Fargo Don komawa gida kwata-kwata. Gidan da yake ciki wanda mallakinsa ne kadai zai bari a Amurka ba zai sayar ba. Jefi-jefi ya kan daga kai ya kallo Rayhanah wadda ta soma gyara kwanciya, sai ya sunkuya ya ci gaba da abin da yake yi. Yau jin kansa yake sakayau, kamar an sake haifo shi duniyar ne, new IBRHEEM! Babu nauyin komai cikin jikinsa da kwakwalwarsa har ma da zuciyarsa, sai abubuwan da zai loda musu yanzu. Duk wasu tensions sun fita. Wanda ya tabbatarwa kansa ba komai ne ya haifar masa da wannan nutsuwar ba face rahamar dake cikin aure, da tarin lada da gafarar da Ubangiji ya sanya a cikinsa. Daga lokacin da ka daura hannu a jikin matarka ta sunnah dukkan alhakin da ka dauka a rayuwarka na zina ko makamancin hakan Ubangiji ya juya shi zuwa abundant reward wanda shi kadai ya san adadinsa. Juyi ta yi cikin gyara kwanciya kafin ta soma magana cikin gigin barci ne ko na allurar barci ne bai sani ba….. “Ya Himu….. Ya Himu .... don Allah ka yi hakuri, na tuba na bi Allah na bika….Baba Dacta ka ceceni zai kasheni....!”. Kalaman da take furtawa kenan wadanda a jiya ya hanata furtawa, sai yanzu suka samu sarari suke sakin kansu cikin magagin barci. Wadanda suka sa Ibrahim Takai, cikin wani hali mai kama da nadama, bai so al’amarin ya zo masa all of a sudden haka ba, amma ba regretting yake yi ba, tunda in a wajen Ubangiji ne baida wani laifi. Shi Ya ce ku zowa matanku a duk lokacin da kuka so ko da suna a halin nakuda. Matanku gonakinku ne, ku zo musu a duk lokacin da kuka ga dama idan ba haila, ko nifasi suke yi ba. Yadda bai yi tunanin cutuwarta ba sai na shi biyan bukatar shine abinda yake regretting, to shi kansa bai san yadda zai yi da kansa ba, samartakar, tashen balagar da tuzurancin ya hada duka ya saukewa Rayhanah a lokaci daya. Adadin kaunarka ga matarka, adadin karfin sha’awarka a kanta. Sai dai ya yarda ya yi laifi, dole ya yi lallashi harma da banbadanci, in ma bai iya ba yanzun nan zai shiga makarantar soyayyah ya koyo. Ture laptop din ya yi, ya mike ya shige cikin bargon nata, ya mika hannu ya janyota gareshi. Ai sai ta soma kokarin kwacewa tana rokonsa tana magiya cikin kuka, gabadaya ta gama tsorata da shi. Ko ganinsa bata son yi. Karfi yasa sosai ya riketa. Har tasoma gajiya da kokawar ta, jikinta yayi sanyi lakwas. “Ka taba kashe abin da ka fi so a duniya RAYHANAH???” Yadda ya yi maganar cikin sanyi, tarin so da kauna da kulawa, sai ta daina kokawar kwatar kan nata. “Rayhanah idan ka kashe shi kai da wa za ka zauna? Wajen wa za ka je ka sauke son nashi da ya yi maka babakare a zuciya? Ina rokon Allah ya kasheni ya barki, ki yiwa ‘ya’yana tarbiyya irin taki. Madallah….. da shigowarki cikin rayuwata….. Maadallah... da Uba irin Babanki Dr. MANSUR. Mai so na da ALHERI..... da dimbin kauna mai yawa agareni. INA SONKI RAYHANAH! INA SONKI RAYHAH!! RAYHANAH I so much love you!!!.” [12/29/2019, 19:10] Takori: Sai ta daga kai a hankali don ganin daga bakin da wadannan zakakan kalmomin ke fitowa, da babu wanda ya taba gaya mata kwatankwacinsu a zaki da gardi? Tana tababar ya zamo cewa daga bakin Ya Himu ne…. wanda in ya ganta bai iya cin abinci. Fuskar da ta gani cikin hasken safiyar da ya keto fararen curtains din dakin barcin, ya fi gaban a kirashi Ya Himu. Cikakken likitan Koda ne Dr. Ibrahim Mansur Balarabe Sardauna, mai matsayin (Nephrology Consultant) a babban asibitin Illinois, ba dan matashin dalibin nan mai girman kai da kwalisa a AKTH da gidan Dacta Mansur ba. Wannan fuskarsa cike take da gargasa lallausa, da tarin hankalin da shekaru suka taimaka wajen karuwarsa. Idan aka kira shi Dr. Ibrahim Mansur Takai, zai fi dacewa da shi fiye da a kira shi Ya Himu. Duk da cewa halayen basu canza ba, zuciyarshi ta yi laushin da bata da shi a baya, mijin da ko kyakkyawar surar jikinsa ta kalla kullum, ya ishi zuciyarta ta kasance cike da wadatar zuci, da godiyar Ubangiji. Ta kuma yi alfahari da zamantowarsa barin rayuwarta, kuma uban ‘ya’yanta. Wadda ta fi kowacce mace a duniya samun alfarmarsa, har kuwa da uwar da ta haife shi sai dai a ba ta matsayinta na UWA a bar neman albarka, amma ba za ta taka wannan matsayin ba. In haka ne bai kamata ta ji haushi, tsoro ko nuna gazawa a kan hakkinsa da Allah ya rataya a wuyanta ba. Har ta yi sake da wannan damar da Allah ya bata, wasu ‘yan iska a waje su kwace. Masu iya magana suka ce, wai tsalle daya shi ke jefa mutum rijiya, abin nufi a nan, tun a lokaci na farko ta nuna gazawa wanda hakan zai sa ya yi baya-baya da ita don gudun bacin ranta ko bacin zuciyarta. Ya soma tunanin hanyar da zai bi ya dinke barakar ta, wadda ba komai ba ce illa ya nemo wata, wadda za ta jurewa jarumtakarsa a auratayya. Wannan tunanin da Rayhanah ta yi, ba wani ne ya koya mata ba, ba karantawa ta yi ba. Tsinkayen hankali ne kawai (foresight ). An ce wai idan baka iya kuka ba, to iyayenka ne ba su mutu ba. Baki iya goyo ba saboda yana da wahala kuma zubewar aji ne, to baki haihu bane. Ko kece ‘yar Karuna in dai Bahaushiya ce ke, kuma cikakkiyar ‘yar kasar Nigeria. Shirun da Rayhanah ta yi, da kukan da ta daina lokaci daya kamar daukewar ruwan sama, shi ya ba Doctor Takai, damar kara mamayarta (Needing for more…....). Amma ga mamakinsa wannan karon bata nuna razana ba, shi din ne ya tuna da dinkin da ya yi mata ya hakura, amma fa ya kasa hakura da abin da ya fi so daga wadannan ‘luscious lips’ na Rayhanah, shi din ya ci gaba da yi cikin wani irin salo da Rahane ta kasa juyawa baya, lallashi da banbadanci har da hawayen neman afuwa, abinda ya gigita Rayhanah…. Ya Himu ne? (She is still doubting). Alkawarirrikan da yake daukar mata ta san ba a hayyacinsa yake fadarsu ba, don haka ba ta kama ko daya ba. Ba ta san lokacin da hannuwanta suka yi fitar bazata ba suka rungume Ibraheem, rungumar da bata taba yiwa wani abu a rayuwarta ba, bayan gawar mahaifinta. Ga mamakin Ibrahim Rayhanah ta soma taya shi sumbar cikin nata salon mai bin umarnin zuciya da odar gangar jiki. Ta sakar mishi komai, ta yarda in mutuwa za ta yi ta mutun, in dai a kan farin cikin Ibrahim ne. Shi din ne ya yi jarumtakar cewa, “A’ah…Rayhanah ” Yana yin baya-baya da ita kada cin zalin ya yi yawa. Ita kuma cikin kara iza shi take da tana fadin…. “Ba sai a kara dinkewa ba???” Duk da halin da Ibraheem ke ciki bai fasa yin dariya ba saboda farin cikin da ya lullube shi. A kalla yau ya tabbatar Rayhanah na son sa, son da ba ta yiwa Khalipha. Kalami ta yi cikin jin kan mace ga mijinta ba bisa tursasawa ba ko son fita hakkinsa, a’a, don tana sonsa. Tana son farin cikinsa fiyeda nata. Sai ya kwaikwayi ‘yar muryarta cikin dariya ya ce, “A sake dinkewa don kin zama kwarya??????” ***** Cikin wannan rayuwar da ta fi kowacce dadi da gardi ga kowanne dan Adam, Ibraheem da Rayhanah suka ci gaba da rayuwa a Chicago. Suna waya da Daddy da Inna Juma a kai a kai, shima Ibrahim yana gaisawa da mahaifiyarsa da Yaya Khalipha, sai dai bai taba yi mata zancen aurensa ko zancen Rayhanah ba, don Daddy ya gargade shi da kakkausan harshe da yin hakan. An debi watanni biyar, duk abin da ya kawo shi ya kammala shi, ya auna komai da ya mallaka a Chicago bankunan gida Nigeria, wasu kuma daga ciki shipping dinsu yayi kamar motoci da furnitures da yake son kawata gidansa dasu. Gidansa kawai ya bari bai kadar ba. A zuciyarsa ya ajiye shi ne ga first born din da duk Allah ya ba shi, mace ko namiji. Su zo su zauna ciki suyi karatu, in sunyi aure su zauna da iyalinsu. Idan asibiti zai shiga, tare suke shiga, idan University of Chicago zai shiga yi lecturing, zama take cikin daliban ayi laccar da ita. Ko tsura masa ido wata a cikin daliban ta yi, ta fara auna mata harara kenen. Ta hanashi motsin kirki ko doguwar hira yake yi a waya sai ta ce zance yake yi. Haka suke yawo cikin Illinois hannayensu sarke da juna. Idan theatre za su shiga, Rayhanah na ofishinsa tana jiransa, shi Ibrahim maimakon ya ji haushi kamar yadda sauran maza ke ji in matansu na musu hakan, shi dadi yake ji. Domin ta rabashi da karnukan dake farautarsa, ko wata mu’amala ce ta hada shi da matan asibitin ko dalibansa, tana gefe sarke da hannu a kirji kafafu a sarke, tana dakon mai kawo wargi. Ga Turawa da shegen tsoro basa son tashin hankali, ta fi ganin maita a kan Ibrahim daga mutanenmu mazauna can. Mutum daya ta tsaya mata a rai dake yawan yi masa waya kuma su dade suna hira wai ita Sapna, bai taba ignoring kiranta ba, amma a cewarsa dalibarsa ce. Kuma duk sanda ta binciki wayarsa babu hoto. Don haka take addu’ar Allah yasa wata rana idonta ya ga idon wannan Sapnar, sai yau Litinin a wani marece Allah ya amsa addu’arta. ****** Ibrahim na dakin ganawa da (Chief Medical Director) na Illinois TH, tare da manyan likitocin koda na duniya, tattaunawa ake yi a kan cutar (sars) tare da wakilan kungiyoyin AAPS, NAD, AMA, da Alberta. Ibrahim ya mike yana magana ta cikin ‘yar na’urar daukaka sauti dake makale jikin farar rigarsa ta likitoci, can karkashin rigar bakaken suit ne wuyanshi daure da bakin tie din da Rahane ta daura masa. A lokacin ita Rayhanah tana can ofishinsa tana tsimayinsa, ya hadata da typing din wani record da yake son fitarwa a kan cutar ta sars, ba tare da sallama ba ko neman izinin sakatariya ko danna knocking na neman izini, wata farar yarinya kyakkyawa (ko da yake ba za a kira ta yarinya ba, domin a kalla tana da ashirin da takwas), ta murdo kofar ofishin ta shigo. Kallon-Kallo ake tsakanin Rayhanah diyar Malam Rashidu Takai da diyar Ambasada Kabiru Abubakar Dogon-Daji. Rahanen, glasses ne prada a idanunta mai duhu wanda ya boye kwayar idonta. Tana sanye cikin traditional attire dinta atamfa ‘yar Holland koriya shar, yafe da mayafin da ya shiga da adon atamfar wato yellow, a kafafunta takalmi ne mai tsayin dunduniya sosai (heel shoe) shima yellow, babu kwalliyar komai a fuskarta sai ruwan hodar mary-kay sai lebbanta dake kyallin lip-balm mai danko. Ita ma Sapnan ba wata kwalliya ta yi ba amma kallo daya za ka yi mata ka kirata da sunaye uku; ‘yar gata, ‘yar hutu, yar gayu. Shadda ce getzner dinkin Senegal a jikinta dark pink wadda ba a cika zare da yawa wajen yin sirfaninta ba, wanda aka yi shi da zare light pink, haka dan shara-shara gyalen da ta zarga a wuyanta shima light pink din ne, sai babbar jaka ta mata baka mahadin takalmi flat baki da ke kafarta samfurin (gucci). Haka suka ci gaba da kallon juna kowacce ba ta yi magana ba, amma ta soma huci, hancina sun bubbude kowanne tsiron gashi ya mike sai Allah ya jeho Ibrahim gabanin a fara baiwa hammata iska. Mara gaskiya an ce ko a ruwa jibi yake, Ibrahim rikicewa ya yi. Amma da yake namiji ne lab-coat din jikinshi ya soma kokarin cirewa yana fadin “A’a, Sapna, wata sabon gani”. Ta mai da budadden hancin nata a kansa kamar ta feso shi daga cikin hancin don takaici. Me wannan bakar yarinyar ta fita da har ya zabeta a kanta? Tsakaninta da Ibraheem sai ALLAH YA ISA! Domin ya gama wulakantata…… Rahane ta mike tsaye wanda ya baiwa Sapna damar ganin matashin cikin dake jikinta har ya soma turowa gaba sosai. Sai Sapna ta cire takalminta ta rufe Ibrahim da duka da hannu da kuma takalmanta….. “Mugu….. azzalumi…. maci amana, tsakanina da kai sai ALLAH YA ISA! Na gode Allah da ban taba baka budurcina ba balle in yi nadamar haduwa da kai….. I hate you Ibraheem….!!!” Ta zubar da takalman ta fashe da kuka ta durkushe a gabansa tana ta yi. Daga karshe ta mike ta yi kofa da gudu ta fita, ga mamakin Rayhanah sai Ibrahim ya bita, amma ba da gudu ba sai sassarfa. Rayhanah ba ta iya tukin mota ba, wannan dalilin ne yasa ta tsimayen Ibrahim, banda haka da tuni ta ja motar ta tafi in ya so ya debo da sayyadarsa ko masoyiyar tashi ta kai shi gida. Daga inda take tsaye jikin motar mijin nata tana hangosu ta cikin gilashinta, Sapna ta bude mota ta shige shi kuma ya zauna a gefen mai zaman banza ya danne totur din motar da kafafunsa yadda ba za ta iya jan motar ba, ya kuma dafe sitiyarin da hannayensa yana yi mata magana, da alama cikin lallashi. Sai ta ji wani bakin ciki ya turnike mata zuciya ba ta ankara ba sai da hawaye suka zubo. Sai kawai ta hau tafiya ta fita daga harabar Illinois TH tana bin gefen titi a hankali ba ta san inda take jefa kafarta ba. Da gudu motar Sapna ta zo ta wuce ta, tabbas ba don a kasar da ba’a laifi a kwana lafiya bane da ta kwasheta da motar. Jin tahowar motar Ibraheem ta yi a bayanta yana ta horn yana binta sannu-sannu, amma ko kallon shi ta ki yi, ba ta ko son ganinsa ya yi duhu a zuciyarta, ya yi muni a idanunta. Maimakon ta tsaya ma hanzari ta kara yi, dole ya kashe motar a gefen titi ya kara da gudu ya cimmata ya rike hannunta a lokacin da ita kuma ta rufe idonta gam, sai kawai ya daddage ya sureta tana fiffizgewa tana komai ya sata a motar ya rufe kofofinta da lock, glasan motar dama ko guduma aka rotsa musu ba za su fashe ba saboda ingancinta. A haka ya ja motar suka nufi gida. ***** Lallashin duniya Ibrahim ya yi, ban bakin duniya ya yi shi, Rayhanah ta ki saukowa. Ta yanke duk wata kyakkyawar mu’amala dake tsakaninsu, ta kaurace masa a shimfida, ta kaurace masa a ido biyu. Ko falo ta daina fitowa balle ta rakashi wani wuri. Cikin ma dake like jikinta da za ta iya da ta ciro masa abinsa ta bashi, in yaso ya kaiwa Sapnar. To ba ta da ikon wannan, wanda take da iko da shi, ta hana. Duk da ta san cewa zai iya jure komai amma ban da wannan Hausar (a raba daki). Ba ta yi karya ba, idan ta ce Ibraheem ya rame, ya rage fita. Wani sashi na zuciyar da soyayya ta mamaya na neman fizgarta su sako mata tausayi, musamman da ta soma saukowa. Ba ta da saurin fushi amma idan ta yin, ba ta sauka da wuri. Ibrahim a falo yake kwana tsayin kwanaki goma sha hudu (sati biyu). Ba rufe daki take yi ba, cewa ta yi muddin ya shigo mata daki wallahi zai nemeta ya rasa a Chicago. “Idan wannan shine kishi Rayhanah, ashe kuwa dole a cika jahannama da mata. To ni wannan ai lasisi kika bani idan ni dan iskan ne ma in je in ci gaba da iskanci na. Kina tunanin wannan rashin hankali da rashin zurfafa tunanin naki, shi zai raba namiji mai kuruciya kamana da mata a America? Kin yi kuskure. Idan kin manta ne bari in tuna miki, ba ni kika fara so ba, Khalipha ne. Kaddarar Allah ce ta wanzar da aurenmu ba tare da mun san juna ba. Ni kuwa Rayhanah na so ki ne tun kina RAHANE.....Na so ki ba tare da na ganki a fili ba, na so ki again daga jin muryarki zuciyata ta gaya min uwar ‘ya’yana ce wannan duk da ban ganta ba. Da na ganki a fili a matsayin matata babu abin da ya canza daga soyayyar da nake yimiki, sai ma abin da ya karu. Duk da nasan ke din ba ni kika fara so ba. Rayhanah duk baki duba wannan ba, sai don wata ta ce tana sona, alhalin na barta ne saboda ke? Ai idan baki gode min ba, to a kalla ki cire takunkumin da kika sanya a tsakaninmu. Hakurina ya gaza ba zan iya jurewa ba….!!!” Tsaye yake a bakin kofarta a sanda yake yi mata wannan maganar. Ya tokare hannunsa da kofar. Tana kwance ta yi shiru tana jinsa amma ba ta ce komai ba, ba ta juyo ba ma balle ya ga fuskarta. Har ya san cewa maganganun sa sunyi tasiri a gareta ko basu yi ba. Sai ya girgiza kai, ya fita ya bar mata dakin. Abu daya yake tattali yanzu a duniyar nan (cikin Rayhanah). Wannan ne dalilin da yasa bai fiya takura mata ba, don sau biyu tana yin barin ciki dan sati uku. Wannan ne aka samu ya zauna da taimako da dabarun likitoci. Ibraheem ya rasa yadda zai yi da ita ta birkice ta hautsine masa gaba daya. Bai taba ganin kishi irin na Rayhanah ba. Tun yana binta yana lallami har ya gaji ya rabu da ita, ya kuma koma zagayawa wajen Sapna ta bayan fage. A sabuwar tarbar da Sapna ta yiwa Ibraheem cikin rayuwarta, a shirye take da ta mallaka masa kanta in dai zai aure ta. Bai yi hakan ba, cewa yake da ita a yawancin lokuta. “Idan kin bani kan naki yanzun Sapna, idan muka yi auren kuma me za ki bani???” Rayhanah da kanta ta soma noticing Ibraheem ya canza, ya daina zama a gidan sam-sam, in kuma da dare ne to cinye daren yake yana waya, kamar yadda ya ce ta ba shi lasisin iskanci, iskancin sa kuwa yake ta yi abinsa har a office kullum suna tare da Sapna kamar tip da taya. Idan ta saurari hirar da yake yi da dare duka da Sapna ne. Wata irin hira marar dadin ji da tada hankali agareta. Sai fushin ya sauka, hankalinta ya yi mugun tashi, ta soma kokarin repenting gundumemen kuskurenta. Amma duk ta inda tayi tunanin bullowa Ibraheem baya bata fuska. Mata da yawa muna wannan kuskuren, a lokacinda miji yake binmu da lallashi da kokarin amsa laifinsa, a lokacin ne shekarar girman kanmu ke kamawa. ***** [12/30/2019, 14:40] Takori: BAYAN WATA DAYA 1/Sha’aban Wannan rana bakar rana ce ga Sapna da shi kansa Ibraheem din watakila. A yau ne za su bar kasar Amurka a dalilin sauyin aiki da aka yiwa mahaifinta Ambasada Kabiru Abubakar Dogon-Daji zuwa kasar Djibouti. Kuma da yake ta kammala karatunta mahaifinta ya sata a gaba suka tafi yana gaya mata wannan Dr. Ibrahim din da ta likewa ba karamin raina mata wayo ya yi ba, dan taking advantage ne ba aurenta zai yi ba. So ba hauka bane, ko lambarta ta kasar Djibouti ta ba shi sai ya tsine mata albarka. Addu’ar Rayhanah ce kawai Allah ya amsa amma ba isarta ba. Tashi take cikin dare ta yi sallar nafila raka’a biyu, cikin sujjadarta ta karanta “Ya hibbu na hum ka-hibbullahi (kafa bakwai). Qad shagafahaa hubbah (sau bakwai). Sai ta ce, “Yaa Allah ka mallaka min soyayyar Ibrahim dan Mansur da Asma’u. Ka kare min shi daga zina da neman maza, da duk ayyukan sabo dake da alaka dasu. Ka juyo da hankalinsa gareni ka ragemin kishin da nake da shi a kansa. Yaa Allah ka bani soyayya da kaunar dake cikin zuciyarsa baki dayanta, ka dora shi a kan hanya madaidaiciya ta neman halali, ka cire haramun daga aljihunsa. Yaa Allah ka ba shi ikon ciyar damu (ni da abin da ke cikina) da tufatar damu da shayar damu da halal. Ya Allah ka zama jagoran sa, ka rabani da abinda ke ciki na lafiya.” Wannan ita ce adduar da Rayhanah ta dukufa tana yi dare da rana a cikin satittika hudun da suka biyo baya, wadanda suka yi dai-dai da cikar cikin jikinta watanni shida. Kasancewarta doguwa kuma cikin fari, kallon farko ba za ka ga cikin ba, musamman in riga da zani ne a jikinta, sai in ta sanya doguwar riga. Yau kwanan su Sapna uku da barin America. Idan ya ce bai yi kewarta ba ya yi karya. Ya rage gantalin, dama wuraren shakatawa suke zuwa, ko bakin ruwa (beaches) su ci su sha, suyi kazamiyar soyayyarsu. Don haka yau da ya kasance a gida wuni guda zur, ko kofar gida bai leka ba, ita kanta Rayhanah haushinta yake ji. Yana ta tsimayen wayar Sapna amma har ta cika sati da komawa Djibouti ba ta kira shi ko sau daya ba. Ita kuma wannan muguwar ta cikin gida ga yadda take, ba ta da niyyar ko ranar daina muguntar ta. Iyaka tunanin da ta yi na hanyar da za ta bi ta nuna ta karbi laifinta ba ta samu ba. Sai ta hau zirga-zirga daga kicin zuwa bed room, ta yi kyau cikin (Layered-mini-Dress) duk da cikin ya turo sosai, amma ko kallon ta ya ki yi. Ya yi rigingine da waya a hannu yana faman hira da wata daban, tunda ba Sapna. Rayhanah ta ga idan ta bari Ibraheem ya ci gaba da cusa mata bakin ciki a kan ‘yammatan kan titi ta fadi babu nauyi, kuma zuciyarta za ta buga. Sai ta yi zaman ‘yan bori a gabansa ta daddage ta fasa masa kuka mai gigitarwa. Iyakar tsorata Ibraheem ya tsorata, wayar hannunsa bai san inda ya jefa ta ba. Don ya dauka nakuda ce ta zo mata da ciki wata shida. Ya kama ta ya kankame yana kira. “Mene ne Rayhanah? Haihuwar ce?” Ture shi ta dinga yi da iya karfinta.. “Ka rabu dani, in ma mutuwa zan yi in mutum mana ina ruwanka? Tunda ‘yan iska sun sa ka juya min baya, to ka mai dani inda ka dauko ni…..” Dariya ce sosai ta kama Ibraheem da ya fahimci musabbabin wannan ihun da ya kada masa ‘ya’yan hanji, yasa shi cikin tashin hankalin, kada a haife masa bakwaini a tsakar daki. Ya ce, “To ga bayan na dawo miki da shi, zo ki hau!” Ya juyo mata bayan, ya yi durkuso a gabanta….. “Zo ki hau Rayhanah, na daina juya miki shi. Zo ki hau ki riga baby hawa, don ban tashi juya miki baya ba ma sai ranar da Allah ya fito da Da na ko ‘yata duniya Rayhanah, muddin baki daina kokarin azabtar dani da kishinki na shirme ba, wanda ba irin na su Nana Aisha ba. Kishi ne na halaka da daukar hakki Rayhanah, duk abinda zai munana lahirar ki bana sonki da shi Rayhanah, kuma ba zan zama sanadi ba. A da, na san Rahane mai yiwa mutane uziri ce, uzri sau saba’in, kafin ta kama su da yi mata laifi, tunda ‘no body is perfect, except our Almighty…..!!!” Jikin Rahane ya yi matukar nauyi, idonta ta dago a hankali ta kalli mijin nata, shima idonsa a kanta. Sai dai gab yake da ya fidda hawaye. “Zo ki hau…..” Ya zube a kasa ya bata bayan. Da gudu ta runtuma ta rungume shi ta bayan, tana fadi cikin kuka, “Ka yafe min Yaa Himu? Zan kasance cikin tababbu, butulu masu manta alkhairi da rashin godiyar Ubangiji idan baka yafe min ba IBRAHEEM…....” Juyowa ya yi ya kama ta, fuskar mai cike da kwarjini da kamala, kunshe da murmushi mai kayatarwa yana kada kai. “Zan yafe miki only in kin hau bayan nan na goya ki, kafin na goya ‘ya’yan Ibrahim!!!”. Sai ta dane shi, ya mike kamar bai dauki komai ba sabida rashin nauyinta, ya nufi master bedroom dinsu. Tana tuno kalaman Daddy ne a wannan lokacin….. “Ibraheem is a nice person… Allah ba kwarzantashi nake yi ba Rayhanatu… wata rana ke da kanki za ki gaya min hakan…. Lokacin da zai sunkuya yana yi muku doki sukutum ke da yaranku…..” “Ba ka yi karya ba Daddy… bayan kasancewarsa nice, honest ne, kind ne, brave ne, sweet ne, jarumi ne kuma sadauki a fannin nuna soyayyah!!!” ***** Tun daga wannan ranar da Ibrahim ya nunawa Rayhanah, ita wani bangare ce na rayuwarsa da ba zai iya rayuwa ba ita ba, fushinta a kansa zai iya gurbata rayuwarsa. Rayhanah ba ta sake yin irin wautar da ta yi a baya ba, ba ta sake takurawa Ibrahim a kan ‘yammata ko wayarsa da mutane ba. Ita duk mai son Ibrahim ma duk kyanta da matsayin da take takama da shi ko na iyayenta tausayi take ba ta. Annabi (S.A.W) ya ce, “Imanin dayan ku baya cika har sai ya sowa dan’uwansa Musulmi abin da yake sowa kansa”. Ta yarda ta amince Ibraheem abin so ne, ba kowacce mace mara aure ce za ta iya dauke ido a kansa ba, don haka ta kama addu’a ta kama Ibrahim, ta kuma hada da kau da kai daga mu’amalarsa da kowa. Illa kullum tunaninta shine hanyoyin da za ta bi ta kara kyautata aurenta, ta kara martabarta a idanunsa. Tunda ita din dai da ba kyakkyawar ba, ba ‘yar kowan-kowa ba, ita Allah ya kashe ya baiwa. Already Ibrahim ya gama duk abin da zai yi a Chicago, amma ganin cikin Rayhanah ya shiga wata tara sai ya bari sai ta haihu don su jewa Daddy da tsarabar da za ta gigita shi, don ko kusa bai taba gaya masa Rayhanah na da ciki ba. Shi Daddyn ne dai yake faman tambaya sai ya yi dariya ya ce, “A ci gaba da addu’a Daddy”. A dai-dai lokacin EDD dinta ya cika, don haka bai cika yin nisa da gida ba, haka ko tafiya yake on the street waya suke, sai idan driving yake. Shima din earpiece na jikinsa, da ta yi kira zai sauka gefen titi ya amsa. Ranar litinin, bayan gajeruwar nakuda ta haifi diyarta mace mai kyau, abin mamaki mai matukar kama da Mami, duk da cewa kalar iyayenta ce (choculate) har sun fi ta haske. A labour - room na asibitin (Illinois). Ibrahim da shi aka karbi haihuwar, kuma sai da aka sake dinketa kamar kwarya (kamar yadda yake fadi). Shi da kansa ya goge jaririyar da olive oil (Zaitun), ya nadeta cikin shawul ya rungume yana yi mata huduba da kalmar shahada cikin kunnuwanta, ya dura mata zam-zam, ya tauna dabino (ajwa) ya sa mata a baki, sannan ne ya bari Nurses suka karbeta suka yi ta wanke ta. Ashe har da dattin ciki ya kara mata baki, da aka gama wanke ta sai ta koma kamar Abida. Rayhanah da ta dubi yarinyar da Ibrahim ya dora mata a kan cinyarta sai da ta tsorata….. Yarinya kamar Abida ce ta haife ta, cleft din Ibrahim a kasan habarta, ga beauty point din Mami. Sai ta ji hawaye na diga daga idanunta suna sauka a fuskar jaririyar da ta tabbatar Mami da Abida ba za su karbeta a matsayin jininsu ba, duk da cewa dasu take kama, saboda daga jikinta da suke gani kaskantacciya sauran cuta ta fito. Sai ta yi wani tunanin da ya sanyaya mata zuciya, tunanin cewa, “ Jawahir za ta goya ta, Aziza za ta dauke ta.” Rayhanah ji ta yi hankalinta ya dugunzuma ya yi gida Nigeria, gara ayi wacce za ayi tsakaninta da Mami wannan boyayyen aure ya isheta, ba za ta yarda Mami ta sheganta mata ‘ya ba, tunda ba ta san da auren ba. Babban takaicinta a kullum idan ta tuno tozarcin da Mami ta yi mata sanda take zargin Daddy da nemanta. A wancan lokacin ba ta dau al’amarin da zafi ba saboda rayuwarta dake reto a gidan iyayen rikon nata, amma yanzu da ta samu nutsuwa da karin hankali ta yadda ba karamin tozarci da wulakanci Mami ta yi mata ba. Mutumin da yake makwafin mahaifi agareta. Ta dauki ‘yar sosai a jikinta, tana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ta ji hanci da ido, da dan bakinta mai kyau kamar Dr. Asma’u Mansur Takai…. Sai ji ta yi Ibraheem ya rungumesu ta baya. Dukkansu rufe idanunsu suka yi ruf, daga su har jaririyar, a sakamakon shigowar wata sabuwar kauna da soyayya mai girman da baya misaltuwa da ta kara shigewa cikin zukatan kowannensu. Tsayin minti biyar sannan Ibrahim ya karbi Babyn daga hannunta yana kallo yana murmushi, ya ce, “Mami na ce….. sunanta NANA ASMA’U!’ Cikin karaji Rayhanah ta ce, “Ban yarda ba, sai in ita da kanta ta amince a kira ta Asma’un…..” Idanun Ibrahim suka yi mici-mici yana kallon ta da mamakin dalilin wannan ANGER haka a kan sunan mahaifiyarsa. To sunan Mamin ne ba ta so ko Mamin ce ba ta so? Ko kuma me take nufi da sai idan ita da kanta ta yarda a kira yarinyar Asma’u? Bai gama tunanin da yake yi ba sai gani ya yi Rayhanah ta goye ‘yarta da tawul din da take kunshe ciki, ta yi lullubinta yadda ta saba ba tare da tunanin cewa a asibiti take ba, kuma likitanta bai sallameta ba ta doshi kofa. Ibraheem tsayawa ya yi yana kallon ta ya daskare a tsaye kamar statue (mutum-mutumi). Bai ankara ba har ta kai kofa, sai ya yi azama da sassarfa ya cimmata ya damko hannunta. A rikice ya ce, “Rayhanah ina za ki je? Tafiya za ki yi ki barni Rayhanah? Me na yi miki? Ko ko ba ki yi farin ciki da kyautar da Allah ya bamu bane? Ko don na ce zan sawa ‘yata sunan mahaifiyata? Above all ma ina za ki je ne?” Hawaye na kwarara a kan fuskarta ta ce, ‘TAKAI!” “Takai???” Ya fada cikin sigar tambaya. “To wajen wa?” Ya sake fadi a gigice. Ba tareda ya jira amsar farko ba. Ta kai tafukanta ta rufe fuskarta ta soma shesshekar kuka kafin ta ce, “Wajen Inna Juma da Inna Zinaru”. Wannan lokacin Ibrahim ya fara fusata. “Saboda na ce zan sawa ‘yata suna Asma’u? Ko don tsuntsun soyayyata ya tashi don kin haihu dani?” Ba ta ce komai ba, sai girgiza kai take tana kuka. “Zinarun ta ci uwata….. ta ci ubanta! Ke idan kina da hankali har za ki sakota cikin wadanda za ki yi tinkaho da su? To amma ba da wannan jaririyar da ke bayan ki ba ko?” Ta fiddo ido jike da hawaye ta ce, “Ai ita zan kai can, sai ni in dawo”. “........Da yake kutumar uban Zinaru ne ya yi cikinta ko? Sakko min ‘yata!” Ya mika mata hannu. Shi kansa baisan sanda wannan ashariyar da bai taba yi ba koda wasa ta sulmiyo daga bakin sa ba. Cikin kuka mai fitowa tun daga karkashin zuciya ta ce, “Idan sama da kasa za ta hadu, ba zan baka ‘yata ba ka kaiwa Mami....….” Ai ba ta idasa rufe bakinta ba ta ji saukar marin da ya tafi da jinta da ganinta na wucin gadi, har sai da ta ga wuta da gilmawar taurari, kafin ta farfado ya sake shimfida mata wani, ya fizgo yarinyar dake bayanta, wadda a take ta soma canyara kukan da ya ratsa har cikin kwakwalwar Ibrahim….. Rayhanah na durkushe tana regaining consciousness. Ta rasa a duniya take ko a lahira. Ibrahim ya kara da cewa, “Idan don lasisin da na baki na soyayyata a gareki ne yasa za ki wulakanta min UWA, to kin yi kadan Rayhanah! Son ya ci uwatar! Soyayyar ta ci abu kazan.....ubanta. Ki gaida mutanen TAKAI”. Ya raba ta gefenta ya wuce rungume da ‘yarsa, wadda har zuwa lokacin ba ta daina tsala ihu ba. Wata Nurse ce dake bangaren Nursery, wai ita Regina ta karbi jaririyar daga hannunsa ta sanya mata kan feeding bottle a bakinta (nipple), sai ta yi shiru. Ta mika masa ita tana tambaya. “Where is her Mum?” Sai ya wuceta zuwa motarsa bai bata amsa ba. Ya bude motar ya shiga ya zauna ya bude tawul din ya rufeta sosai ya kwantar da ita a kusurwar kujerar baya, ya dinga jan motar a hankali kamar mai tafiya akan kwai kada ya jijjigata. In ka kalle su shi da jaririyar sai sunyi bala’in baka tausayi. Idanun shi sun kada sunyi jawur amma ba hawaye yake ba. Bakin ciki ne da fushi mai tsanani, yana mamakin halayen mata. Kai ka so su, ka kaunace su da zuciyarka daya, ka so nasu har fiye da yadda kake son naka, amma ba za su saka maka da komai ba sai raini ga mahaifiyarka, wadda itace silar komai na zamowarka in existence har kayi girma da balagar da suka samu suka aura suke mora, ba don komai ba sai don saboda sun sameka a hannu. To Allah wadaran soyayya! Shi ya sanya bai taba yiwa kansa sha’awar auren soyayya ba da farko saboda gudun irin wannan fiffikar. Ga wadda yake murna da halayenta, dabi’unta da ginin da suka soma yiwa rayuwarsu, ta nuna masa itama bata da bambanci da sauran mata. Har ya iso gida tunanin da yake ta yi kenan. ***** [12/30/2019, 20:24] Takori: Sanda Rayhanah ta samu dawowa hayyacinta daga gigitattun marin Ibrahim sai ta mike tsaye hajijiya na dibarta. Dai-dai lokacin likitanta da Nurse suka shigo, cikin mamakin abinda ya kawo ta bakin kofa haka ko hutawa ba ta gama yi ba. Haka suka sata gaba da lallami da ban baki har ta hakura ta koma gadonta ta kwanta. Suka ci gaba da abin da ya kawo su, suka bata magungunanta ta sha suka sanyata ruwan zafi suna ci gaba da kula da ita, kulawa ta musamman albarkacin Dr. Ibraheem. Likitan ya tambayi babyn, tana kuka ta ce Babanta ya tafi da ita. Cikin mamaki suka ce “Ina?” Ta ce, “Ba ta sani ba”. Sai kuka. A take Dr. Aziz, Musulmin Lebanon ya kira wayar Dr. Ibraheem, magana suka yi mai kama da jayayya. A karshe ta tsinci maganar Dr. Aziz inda yake cewa. “Wannan Issue dinku ne kai da iyalinka babu ruwan baiwar Allah, kada ka kwareta ka kawo ta uwarta ta shayar da ita ko in kai maganar kotu wallahi”. A wajen Bature yaro ya fi komai muhimmanci, kuma gwamnati na da ikon raba Da da iyayensa idan irin haka ta faru, ko in an ga za su cutar da rayuwar yaron musamman kasar Amurka da Ingila. Ba ta dai ji me Ibrahim din ya ce ba, Dr. Aziz ya ci gaba da bincikar lafiyarta. Ya yi rubuce-rubuce cikin file dinta, sannan ya iso gabanta a hankali ya ce, “Ko mene ne ya hadaki da Dr. Ibrahim ki kwantar da kai ki amshi laifin, ki karbi jaririyarki ki shayar da ita kin ji? Babu abin da take bukata a halin yanzu sai ke da dumin jikinki, idan fa har kina son soyayyar uwa da Da ta kasance tsakaninku, kar ki bari a rabaku, kin ji?” Tana share hawaye ta daga masa kai. Ya ce ta zo ya kaita gida in ji Ibraheem. Ba ta da zabi in ba komawa gidan ba, jiki ba karfi babu passport ina za ta je? Sai dai ita ma ta yi fushi da Ibrahim a kan marin da ya yi mata, fushi irin wanda ba ta taba yinsa a kan kowa ba, including MAMI. Shine ya danna bell a flat dinsu, Ibraheem ya bude daga shi sai farar singilet da wandon wanka gajere, ya bata hanya ta wuce inda ta jiyo babyn nata tsala kuka. Tsikar jikinta ta tashi gaba daya ta saurara don jin daga inda kukan ke fitowa, master bed room ne. Ba ta bi ta kan wani Ibraheem ba ta je ta sunkuto ‘yarta ta fito. Dr. Aziz na nan falo tare da Ibraheem suna ta ragargazar Turanci kamar an bude CNN. Da alama mukabala suke yi, Dr. Aziz na tausarsa. Ta zo za ta wuce dakinta ya ce, “Come here Rayhanah”. Tana matukar ganin kimarsa kasancewarsa consultant na gynecology din Illinois baki daya, kuma aboki ne na jiki ga Ibrahim, domin tare suka yi karatu duk da suna fanni daban-daban. Ya mika hannu ya ce, “Bani ita”. Tana share hawaye ta mika masa, Ibrahim ya yi kicin-kicin ko kallon ta ya ki yi. Dr. Aziz ya ce, “Durkusa ki ba shi hakuri”. Sai ba ta yi musu ba ta durkusa din. “Ka yi hakuri Ya Himu, bai kamata ka yi hanzarin yanke hukunci a kaina ba, ba tare da ka tambayeni dalilina ba. Na san abinda baka sani ba. Mami ba ta sona, shi yasa Daddy yake boye mata aurenmu. To kuma ga zuri’a ta soma taruwa ina so Mami ta sani…. ina tsoron..,. ina tsoron… kada ta ce ba za ta amshe ta a matsayin jika ba…. tunda ba ta san da aurenmu ba”. Cikin harshen Hausa take yin maganar cikin kuka da karkarwar murya, kada Dr. Aziz ya fahimta. “Wannan statement da kika fada wai bata son ki, kamar ya ya ba ta son ki, ban gane mata ba? Wane irin so kike so ta yi miki bayan wanda ta yi miki tun kina Rahanen ki? Da bakina mun yi fada da Mami a kanki, da na ce ban yarda da zamanku tare da su Abida ba. Cewa ta yi ita babu ruwanta, Da na kowa ne, za ta rike ki tsakaninta da Allah. Sannan don yanzu na ce zan sawa ‘yata sunanta ki nemi wulakanta min ita Rayhanah? Sam, ba zan dauka ba wallahi. Ki yi mana duk zabin da kika gama dama, a shirye nake da karbar duk hukuncin da kika yanke. Sunan ‘yata Asma’u, Rayhanah ki yi duk abin da za ki yi….” Ganin cewa ba ta da hujjar da za ta kare kanta a kan wannan bayani na Ibrahim a kan mahaifiyarsa, sai ta bi shawarar Dr. Aziz wanda ke ta daga mata kai da kada mata ido alamar ta dauki laifin, sai ta kama kafarsa…. “Na yi kuskure Ya Himu, don Allah ka yi hakuri….” Ta ci gaba da rera masa kuka mai nuna MARAICIN ta. “Ba ni da uwa, bani da uba, bani da komai sai kai da Baba Dacta, sai ‘yar da Allah ya bamu yau din nan. Idan ka rabani da ita ka ki ni saboda kuskurena ina za ni? Ibrahim ina zan sa kaina???”. Ta kwantar da kai a kan gwiwoyinsa tana sauke ajiyar zuciya. Ga mamakinta sai Ibrahim ya mika hannu ya dago habarta yana share mata hawayen da ‘yan yatsunsa zara-zara guda biyu. Sai Dr. Aziz ya yi gyaran murya don su san da zamansa a falon, domin ga dukkan alamu suna bukatar fiye da hakan wajen lallashin junansu. Rayhanah ta mike ta zauna kusa da Ibrahim, ya mika hannu ya sarkafo kugunta. Dr. Aziz ya ce, “Kin iya breast feeding?” Ta girgiza kai cikin jin kunya wato “A’ah”. Sai ya hau nuna mata, “Haka za ki rike ta, ki dago ta haka…. Ki sanya nipple din a tsakanin yatsunki biyu, sai ki sa mata a baki. Amma ki dinga yi da lura kada ki toshe mata hanci. Idan ta sha da yawa sai ki dagata ki dora a nan…. (ya nuna mata) har sai ta yi gyatsa”. Rayhanah ta daga kai. To ungota yi in gani. Ta karbi ‘yar, amma don kunya sai ta yi dakinta, ba za ta iya wannan rashin kunyar ta likitoci ba. Ba Dr. Aziz kadai ba, Ibrahim ma ya yi dariya. Ya raka Dr. Aziz har motarsa ya dawo ya rufe gidan bayan ya sallami Benjamin. A yadda ya shigo ya same su, ta takarkare tana aikata yadda Dr. Aziz ya koya mata ne, har ‘yar ta kama hungrily tana ta tsotso. Sai suka ba shi sha’awa da tausayi, duk da har lokacin bai gama warewa sosai ba. Itama din kuma a shake take, bata huce ba daga marin barin makauniyar da yayi mata. Kawa-zucin ‘yar dama shi ya fi damun ta, tunda ga abarta a hannu, to babu laifi ko Ibraheem ya ci gaba da dukanta. Sai ga hawaye sur-sur! Suna tittidowa. Ibrahim ya zauna a kusa da ita a hankali, ya turmutsa yatsunsa cikin kwantacciyar sumar kanshi ya lumshe ido a hankali, sannan ya bude yana kallon yadda ‘yarshi ke zukar nonon uwarta, ya tabbatar ya dau alhaki, ya san Rayhanah kuka take, amma bai yi yunkurin komai a kai ba. Wata irin soyayya ce mai yawa ta tsakanin uba da Da ke ratsa shi. A lokaci guda kuma tausayin Rayhanah, yana tuna kalaman da ta gaya mishi dazu. Wannan shine a doke ka a hanaka kuka. Shi kansa ya san Abida ba ta son Rayhanah, amma bai san da Mami ba. Haka nan ya yi mamakin dalilin da yasa Daddy ya hana shi gayawa Mami aurensa da Rayhanah, in haka ne akwai ayar tambaya a tsakanin mu’amalar Rayhanah da Mami. Ya tuna cikin kalamanta tace “nasan abinda baka sani ba!” Har kuma zuwa inda yau ke motsi, daga Daddy har ita babu wanda ya yarda koda cikin raha ko subutar baki ya gayamasa dalilin fasa auren Rayha da Khalipha. Saidai su ce “Allah bai yi ba!”. Eh, gaskiya ne komai sai Allah ya yarda, amma babu abinda ke faruwa a duniya babu dalili. Sai ya ji jikinshi ya yi sanyi, mai daki shi ya san inda yake masa yoyo. Zuciyar Rayhanah mai kyau ce, ba za ta fadi sharri ko batanci haka kawai a kan kowa ba, balle a kan uwar da ta haife shi. Tukunna ma, shi shekarunsa nawa baya tare da su? Ya san irin rayuwar da suka yi cikin tsayin shekarun ne? Da wannan tunanin ya mika hannu ya rungumo matarsa, ya kwantar da kai a kafadunta, zuciyarshi cike da nadamar saurin kai hannunshi ga lafiyar jikin wadda ta ba shi farin cikin rayuwar da bai taba tsintar kansa a ciki ba. A kuma ranar da ta ba shi farin cikin ko hutawa ba ta yi ba. Jinta gaba daya jikin Ibrahim kamshin jikinsa na ratsata sai ta idasa narkewa, hawayen suka kara shimfidowa a kan kundukukinta. “Ki yafe ni Rayhanah, kin yafe min Rayhanah?” Ta daga kai…. “A’a, wannan bai gamsar dani ba, bude bakinki ki gaya mini….” Ya fada a lokacin da ya dago habarta. Sai ya soma dauke hawayen da harshensa. Runtse ido ta yi, amma jin Ibrahim na neman zafafa al’amarin sai ta kwace. “Malam yi a hankali, dinkin likita ce”. Ibrahim yasa dariya ya sake kamo ta. “Ba sai a sake dinkewa ba???” Ya fada da muryar da ta gaya mishi hakan shekaru biyu a baya. A take ta tuno da first night dinsu. Ta juya masa keya cikin jin kunya tana jijjiga babyn. Ibrahim ya sake binta ya ce, “Ko kwaryar ba masaka tsinke ne inda za a sake soka allurar?” ‘Yar ta aje cikin ‘yar katifarta, ta dau filo ta danne shi tana bugu. Sai ya hantsilota ya koma samanta ya mamayeta yadda ko motsi ba za ta iya ba. Cikin dariya da shaukin bege mai yawa ya ce, “Wallahi ki bini a hankali, in ba haka ba wannan dinkin farkashi zan yi yanzu”. Ganin ya soma zarce Zaria ta soma lallashi, wanda ba ta san yaushe ta iya ba, har da su dadin baki, kirari da bambadanci. “Haba dan Ibro na…. angon Rayhanah Baban Asma’u….. dan gaban goshin Baba Dacta.....likitan likitocin kodar Rayhanah......” Ibrahim dariya yayi yace “har kin tunomin da Ado, oh su Rahane da yanzu fa anada ‘ya’ya goma” ta shaka tayi fus, kamar alkubus. A ranta tace “yanzunnan zan rama”. “Ai dai duk da kaki bani shayin da Baba Dacta yace ka bani, ka turo inyamuri ya bani, kuma arzikin kalma ko ta sannu ce ban taba samu ba, na ganka kana mazari kana tsuma kana gwada ‘yar kashi da Adon don yana kokarin shimfidar ni.....” Inda abin da ya tsana a tayar ko a tuna masa a duniya to wannan zancen ne. Ai kuwa a take ya koma serious. Fuskarsa tayi kicin-kicin kamar ba shi yake rahar da yake yi yanzun ba. “Rayhanah zamu bata, uwar Asma’u zamu bata……” “Na tuba….. na bi Allah na bika Baban Asma’u. I’m in nostalgia (ina cikin begen gida)”. “Nima gidan nake so Rayhanah, amma bari Mamina ta yi dan kwari zuwa watanni biyar haka”. Har cikin ranta ta gamsu da hakan. ****** WELCOME TO THE WORLD ASMA’U IBRAHEEM MANSUR Rubutun da za ka fara cin karo da shi kenan a kasan tangamemen hoton da za ka fara cin karo da shi da zarar ka shigo falon nasu, mai kama da fadar wani gwamnan a Nigeria. Uwar da Uban ne cikin ‘Native Hausa Attire (shadda da Atamfa) shi dinkin Mohammed na shudiyar shadda sheraton da hula Damanga shudiya mai duhu, sun sa buleliyar ‘yar tasu a tsakaninsu kowa ya rungumo bari daya, wadda ta washe ta yi haske ta zama kamar ‘yar Sudanese, dukkansu bakinsu a washe, fararen hakoransu a warwaje kamar masu tallan colgate. Itama ‘yar bakinta kamar ya tsage da dariya, cleft da beauty point din Mami da Ibrahim duk sun lotsa. Hoto ne wanda Ibrahim ya turawa Baba Dacta copy dinsa cikin wayarsa, ta hanyar BlackBerry Messenger. A lokacin yana kan hanyar komawa gida daga wajen aiki. Ya ji shigowar hoton amma bai bude ba, sai da ya shiga get Mal. Dahiru ya rufe ya adana motar a rumfar adana motocinsu. Ya dauko kwat dinsa da bakar jakarsa tukunna ya bude. Sai da ya jingina da motar kada kafafunshi su kada shi. Kwallar farin ciki ta tsiyayo daga idanun Dr. Mansur. Ya tsura musu ido dukkansu ukun kamar ya hadiyesu don kauna. Wannan rana yake jira, ya maidawa Asma’u martanin bakin cikin da ta kunsa masa shekaru uku da suka wuce. Ai bai shiga gidan ba, mota ya koma duk da gajiyar dake jikinsa ya sake fitowa ya nufi Arewa Studio dake Tarauni ya basu suyi mishi window size guda biyar zai dawo gobe ya amsa, bayan ya biyasu. Wani abin mamaki a washegari bayan ya karbo hoton sai ya dasa a falonsu, daya a bed-room dinsa, daya a dakin su Abida, a lokacin duk basa nan. Jawahir tana Hurghada, Mimtaz ta sake haihuwar da namiji again. Mami na office, Abida da Aziza suna makaranta. Bayan ya kakkafa enlargements din ya yi tafiyarsa office dinsa da nasa copy din da zai sa a office dinsa, zuciyarsa kal kamar madara. Duk inda ya gitta cikin ward din su an san Dr. Takai yau yana cikin farin ciki. Sai raha yake yi da likitocin da ke karkashinsa da marasa lafiyansa. Dr. Kofar Mata ya kasa shiru ya ce, “Wai Dr. Mansur hala amarya ka yiwa Dr. Ma’u?” Bakin Dr. Mansur har kunne ya ce, “Eh, kamar ka sani kuwa wallahi Dr. K/Mata, gata”. Ya mika masa hoton da ya yi saving a fuskar wayarsa. “Zo muje office ka ga amaryar tawa sosai”. Ai kuwa ya mike ya bishi office ya nuna masa tangamemen hoton. Dr. K/Mata kamar yau bai ci abinci ba, haka ya bude baki yana ta kallon hoton. Ya ce, “Wannan kamar Ibraheem, ‘yar kamar Asma’u, matar ce ban sani ba”. Murmushi ya yi ya ce, “Ita ma ‘yata ce, ni nake rikon ta”. Dr. K/Mata ya ce, “Masha Allahu, Allah ya albarkaci little Asma’u ya rayata cikin tafarkin Islama, amma ban san sanda Ibraheem ya yi aure ba”. “Auren ne ya zo a kurace, amma abu wajen shekara uku”. Haka suka yi ta zancen Ibrahim da iyalinsa, suka manta da patients dinsu. A take Daddy ya turawa Hakimi da Haj. Karima da Inna Juma, wadda ba ta yarda ta zauna a Farm Center ita kadai ba, tana gidan Hakimi, can aka ba ta daki take zaune. A take kuwa suka hau kiran wayar Dacta suna neman karin bayani, baki har kunne Daddyn ke amsa musu. Tafi-tafi zance ya yadu cikin gidan Hakimi da wajensa Ibrahim matarshi ta haihu, ‘ya kamar Asma’u. Wannan kadai ya isheta aya, idan fa har tana da hankalin tsinkayen hakan kenan. Abida da Aziza ne suka fara dawowa gidan a gajiye tubis, suka baje a falo suka kure A.C. Kamar an ce da Aziza daga kanki ta yi arba da tangamemen hoton, ta hau zubawa Abida duka a cinya. “Yaya Abida….. Yaya Abida ....sister…. Sister kin ga… kin ga”. Abida ta juyo a fusace domin har ta samu barcin gajiya ya sureta Aziza ta katse mata. Tana niyyar mangare Azizah sai ta ji tana fadin. “Kamar Ya Himu da RAYHANAH da ‘Cute Baby!”. Abida ta daga ido ta kalli side din. Ai da sauri suka mike dukkaninsu suka runtuma ga hoton suna kallo sosai. Iyakar rikicewa da firgita Abida ta yi. A take ta ja waya ta kira Mami. “Mami ki taho gida maza – maza yanzu ki ga wani abin mamaki”. “Mene ne?” Ta fada da dan karfi. “Ke dai ki taho Mami za ki sha mamaki, idan fa har baki suma ba”. Ta kashe wayar ta kyale Mami. Dr. Asma’u ta dade tana juya kan wayarta a hannunta. Ita ba ta son irin wannan sam, a ce ta yi abu, amma ba a gaya mata dalilin yin shi ba. Tana da ayyuka masu yawa a gabanta amma dole ta ture ta mike don Abida ba ta taba yi mata haka ba. Abida jikinta bari yake, saboda kaduwa da razana. Azizah tsalle take, tsallen murna tana fadin “A perfect match! Miskila, sai miskili dan’uwanta. Daddy the matchmaker! What a beautiful daughter I’ve….. wayyo ni dadi kashe ni. Come soon baby Asma’u in goya ki in miki rawa in cillaki in café ki”. Ta isa ga hoton ta sumbaci yarinyar daidai lokacin da Mamin ta fado falon. Abida ta janyota ta isar da ita ga hoton tana fadin “Mami dubi rainin hankalin da aka miki, har aure Ya Himu ya yi da tsintacciyar yarinyar nan har sun haihu baki sani ba saboda an raina ki…..” Ba ta kai ga rufe bakinta ba Daddy ya fito daga dakinshi yana ba ta amsa da cewa. “An raina ta ko ta raina kanta annamimiya? Ba tun yau na kwana da sanin mugun halinki ba, to ki sani, ita wannan da kike kira tsintacciyar mage ta zama jininki, dolenki, uwar ‘ya’yanki ko ki mutu, ko ki yi rai ba abin da zai sameta da ikon Allah, wai don kun wulakanta ta. Babu yadda za ku yi da ita, sai dai ku ci gaba da raina kanku, domin KAINUWA ce dashen Allah, kuma murucin kan dutse baka fito ba sai da ka shirya!!! Idan kuna da hankali wannan ya isheku ishara. An gaya muku ana yiwa Allah shisshigi ne cikin al’amarinsa?” Ya juya ya shige dakinsa. Abida ta yi tsumu-tsumu, ita kuwa Dr. Asma’u sai ta zube a doguwar kujerar falon tana kuka, kukan da dukkansu basu san dalilin da yasa take yinsa ba, na bakin ciki ne ko na nadama? Allah kadai ya san me ke a zuciyar bayinsa. Cikin zuciyarta Allah ya isa take wa Dr. Halima da ta goga mata bakin fenti a idanuwan wanda ya fi kowa sonta a duniya, ya yarda da ita, ya ba ta amanar gidansa. Ya yi mata kyakkyawar shaida a zuciya da bakinsa na uwargida ta gari. Yanzu wane bayani za ta yiwa Daddy ya saurare ta? Babban bakin cikin Mami kullacin da Dacta Mansur ya yi mata a kan ikon da ta nuna a kan Khalipha da cewa da ya yi ta nuna masa yau ba shi ya haifi Khalipha ba….. tabbas ta dade da manta wannan tunda shi din bai taba nuna wata kafa da za a bambance ko a tuno hakan tsakanin Himu da Khalipha ba. Kenan in da halacci bai cancanci butulci da rashin biyayyar da ta saka masa dasu ba. A lokacin da babban mutum irin Dr. Mansur yake cikin fushi, dosar shi da ba da hakuri da karbar kuskure kamar izawa wuta fetir ne. don haka Mami tasa mishi ido har tsayin kwana uku. Sai dai fa kullum cikin dare sai ta fito falo ta kurawa hoton ido tana shafa fuskar yarinyar, wadda Allah ya kinkimo wata gundumemiyar kaunar yarinyar ya saka mata a zuci. Ta kan dade tana kallon Rayhanah wadda babu abin da ya sauya a halittarta sai santsin fata. Da ka ganta ka ga matashiyar Bahaushiya ‘yar kimanin shekaru ashirin da shida, amma yanayin jikinta da canzawar fatar ta sai ka yi zaton daga kwai aka barota. Ta yi sumul ta yi mulmul har da wata ‘yar kiba ta samun perfection and contentment in life. Shi kuma angon nata da ganinshi ka ga bakin Bature, kamanninshi da mahaifinshi sun sake fitowa sarari, da ka gansu za ka fahimci cewa komai na rayuwa ya yi musu dai-dai kamar yadda kowanne dan Adam ke burin samu. Lallai Dacta Mansur ta yarda ba karamin hatsabibin dan boko bane. Wato ta hana da Khalipha tunda ta nuna ba nashi bane, sai ya yi mata lambo ta gama shuka tsiyarta, sannan ya fito mata ta bayan gida. Ta inda bata taba zata ba. Ta tabbata ba ta isa in Ibrahim ne ta yi masa abin da ta yiwa Khalipha ba, don shi ba shi da hakuri ko kankani. Idan yana son abu fa kawai yana son shi, haka in bai so, jan ido da lallashi basu isa su sanya ya so abin nan ba. Yau dai ga Rayhanah da take kora don tayi nisa da zuri’arta ta zama barin rayuwar Ibraheem. Da mafi soyawa a zuciyarta, ta hada zuri’ar da ba ta so din da ita, kuma Allah ya sanya mata so da kaunar zuri’ar, kamar ko ma fiye da yadda take son Ibrahim. Dama an ce wai abin cikin kwai ya fi kwan dadi. Gaskiyar Dr. Mansur ne da ya ce ba a yiwa Allah shisshigi cikin al’amarinsa. Dr. Asma’u ta yi nadama matuka, nadama irin wadda Ubangiji (S.W.T) ya yi alkawarin karbarta, wato nadama da tabbacin da bawa ya yi da zuciyarsa na cewa ba zaya kuma komawa izuwa zunubin ba. ***** [1/1, 10:27] Takori: Karfe goma dai dai na safiyar litinin jirgin KLM ya sauke Dr. Ibrahim Mansur da iyalansa a filin jirgin saman Abuja, Khalipha ne yaje ya taho dasu daga filin jirgi, duk da cewa suma dawowarsu kenan a daren jiya daga Hurghada inda yaje ya taho da Mimtaz da Jawahir, wadanda suka kwashe watanni biyu a Egypt a dalilin haihuwar da Mimtaz ta yi ya kai su can suka yi biki. Khalipha bai yi kasa a gwiwa ba wajen radawa second born dinsa suna Ibrahim Khaleel. Yau sai ga Rayhana da Yaya Khalipha, bayan gushewar a kalla shekaru uku da doriya. Ta kasa hada ido da Yaya Khalipha wanda ke rungume da Asma’u a kirjinsa. Shima Ibrahim rungume da takwaransa, kowanne ya kasa ajiye dan ya yi tukin motar. Dukkansu suna gaba, ita da Mimtaz suna baya. Jefi-jefi Rayhanah kan saci kallon Yaya Khalipha, ya yi kiba ‘yar kadan ta hutu, ya kara murjewa. Da ganinshi za ka fahimci cikin kwanciyar hankalinsa yake, sannan likkafa ta yi gaba ko daga irin motar da ya dauko su a ciki da Balarabiyar da ya aje mai neman kashewa mutum ido don haske da hasken idanu. Mimtaz ba ta da bakunta ko kadan, sai jan Rayhanah take da hira ta ji Hausa zau kamar (vedan) a dalilin rayuwa da su Jawahir, in ka ji tana Larabci to ita da iyayenta da danginta ne, amma ko Khalipha da Hausa suke magana. Ta ce, “Yaya Khalipha aniyarka ta bika, ka ce ‘yar Dr. Ibrahim da Rayhanah muni za ta yi, gata nan ta fi duk iyayen kyau da haske”. Ya ce, “Ai albarkacin sunan Mami ne shi yasa ta dan washe”. Ya kara duban yarinyar cike da kauna yana fadin, “Lallai Muhd. Mansur ya yi mata, zuki!” Ya sumbaci ‘yar. Sai a lokacin ya juya ga Rayhana yana murmushi ya ce, “Madam kinsha aiki, mun gode fah”. Tana murmushi ta ce, “Aikin me Yaya Khalipha?” Ya mikawa Mimtaz Asma’u ya tada motar ya ce, “Aikin haifo mana UWA, ba ta barota a komai ba”. A ranta ta ce, “Allah yasa kada ta yo halinta”. Don dai ita har yanzu fargabar haduwa da Mami take, don ba ta san irin tarbar da za ta yi musu ba ita da ‘yarta. Tunda ita ba ‘ya ba ce annoba ce da ake neman guje mata, Allah ya kara manna musu. Khalipha ya so suyi sati a Abuja su huta ya dan zazzaga dasu su ga sauye-sauyen ci gaba da Nigeria ta samu a Abuja, amma Ibraheem ya ki, ya ce a gobe za su wuce ya matsu da ya ga Mami don ya dade bai jita a waya ba, shi kuma in ya kira a ce da shi a kashe take. Jawahir ta dawo daga asibiti cikin motar Mimtaz, ta kai Muhd Mansur asibiti ne yana fama da zazzabin sauyin yanayi, domin sun dade a Hurghada sosai har watanni biyu. Tun daga kofar falonsu ta fahimci lallai suna da baki. Don haka ta shiga bakinta da sallama rike da hannun Muhd Mansur. Rayhanah ta dago ido don jin muryar Jawahir, suka kuwa yi ido hudu da juna. Ai Jawahir cillar da jakar hannunta ta yi ta saki Mansur ta sheka da gudu ta rungume Rayhanah, ita ma ta rungumeta hawaye na zuba daga idon su. Hawayen kauna da TUNA BAYA…… (TUNA BAYA SHINE ROKO!) Inji Sumayyah Abdulkadir Takori. Ita sam Jawahir ba ta lura da Ya Himu ba, balle karin ‘yar da falon ya samu. A lokacin ne Asma’u ta soma kuka tana zillo daga hannun Yaya Khalipha tana mikawa uwarta hannu, don ganin an shake mata ita. Ibrahim ya ce, “Kinga malama sakar min mata ta baiwa ‘yarta nono…..” A firgice Jawahir ta juya don ta ji wata murya ne kamar ta Ya Himu, ta tabbatar shi din ne, ta kuma juya ga Yaya Khalipha wanda ya mikowa Rayhanah ‘yar, ta mika hannu ta karbeta. Baki Jawahir ta bude tana kallon wani salon ba da nono na mutum biyu (uwa da uban). ‘Yar na shan nono amma uban ne ke rike da ita kamar shi zai yi breast feeding din, yana fadin, “Kuma shi kenan don ta iya kamawa da kanta sai ki sakar mata? Salon ta yi katon baki irin na Jawahir? Hangangam!” Jawahir ta bude baki (hangangam din kamar yadda yace) ta kuma kasa rufe shi. Sai ta kalli Rayhanah ta juya ta kalli Yayan nata, sannan ta maida idonta kan kyakkyawar jaririyar. “Ki kwantar da hankalinki Jawahir na yi mata AURE!” Ta tuna da kalaman Daddynsu a kan tambayar Rayhanah da ta yi. Shekaru uku da doriya a baya, ranar data wayi gari bata kara ganin Rayha a gidansu ba. Tun daga ranar kuma Daddy bai sake ba ta wata kofar da za ta yi masa zancen Rayhanah ba. Wato Ya Himu ya aurawa! Sai ta zube a kasa tana yiwa Ubangiji Sujjada, dama da mayafinta a kanta. Jawahir ta fadi a ranta “What a genius and examplary father they have?!” “Bravo Daddy!” Ta fada a hankali, idanunta na lumshewa. Kaunar mahaifinsu da mamakin kyakkyawar zuciya irin tasa ya cika mata zuciya. Irin su Daddy, V.C Baba Sa’idu (GIRMA YA FADI), Brigadier Bello Makarfi (SIRADIN RAYUWA), Alhaji Aliyu Dambatta (ALHERI), Tahir Usman Karaye (TUNA BAYA....), tsiraru ne a cikin al’umma. ‘Yan boko ne da basu fassara boko da defination din da sauran al’umma da dama suka fassara shi da shi ba, sun ba shi kyakkyawar fassara da ma’ana wadda ta yi dai-dai da addininsu wajen jin kan TALAKA da daukaka darajarsa ya tadda kafadar masu gata. Sun kuma amince da ayar Ubangiji (SWT) ta “inna akramakum indallahi atqaakum....”. Suna kuma aiki da ita. A cikin dukkan al’amuransu na rayuwar yau da kullum. Jawahir tace “How she wish za ta iya rubutu? Da ta bawa al’ummar Annabi labarinsu. Domin suyi koyi da kyawawan halayensu. Ta mika hannu tana hawaye ta ce, “Ku bani ita na dauke ta…..” Rayhanah ta fizgeta daga nonon tana fadin “Jeki wajen uwarki Asma’u…..” Ai kuwa yarinya ta fasa kara, don bata koshi ba. A haka Rayhanah ta mannata a jikin Jawahir. Jawahir na daga cikin dai-daikun mutanen da ba za ta taba mantawa dasu ba cikin tarihin rahuwarta. Ibraheem ya so ya yi bala’in an fizge masa ‘ya daga nono, amma ganin irin maternal rungumar da Jawahir ta yi mata tana shafa bayanta a hankali har ta yi shiru, ta ci gaba da dubanta cikin kauna, kwatankwacin kaunarta da dan’uwanta Ibraheem. Sai ya fasa, ya dauke ido a kansu ya mayar ga amsa call din Daddy yana gaya masa sun sauka lafiya suna Abuja, sai gobe za su taho. A ranar dai Baby Ma’u a jikin Jawahir ta kwana, kuma da yake ta fara cin abinci, ba ta farkawar dare. Da ta farka sau daya ta ba ta ruwa ba ta kara farkawa ba. A daren ta hada kayanta ta ce ita ma da ita za a Kanon, ba za ta iya barin ‘yarta ba. Washegari basu bar Abuja da wuri ba sai da suka karya kumallo suka kintsa a tsanake, sannan suka dunguma dukkansu har Khalipha da nasa iyalin suka yo Kanon a jibgegiyar ‘BMW’ din Yaya Khalipha. ****** RAHANE A GIDAN DR. MANSUR (Karo na Biyu) Wannan karon, ta shiga ne da kafa mai kwari irin wadda Mimtaz ta shiga da ita. Ta samu karfin gwiwar hakan ne sakamakon hannunta da Ibrahim ya rike kam-kam cikin nasa har da matsa mata yatsun da karfi. Asma’u na goye a bayan Jawahir ta yi barci tun a hanya. Shigar yamma suka yiwa Kanon, don basu taso da wuri ba. Ga tsaye-tsayen da Khalipha ya yi ta yi yana yiwa Mami cefane kamar yadda ya saba kullum zai je Kano. (Dankalin Turawa, Doya, Albasa, Kayan Miya, Manja da Plantain). Sanda suka shigo gidan, Daddy baya nan ma, amma sunyi waya ya ce yana kan hanyar dawowa ya samu emergency call ne. Mami da Abida ido muzai-muzai abin tausayi, duk babu kintsi tare dasu, don Dacta Mansur ya dawo da bara bana, ya fita harkarsu da Aziza kawai yake harkokinsa, ita ta jagoranci kukunsu wajen girka abin da za a taryi bakin dasu. Cikin Sallama a falon Mamin, wanda ke saman bene, bayan sun wuce falon kasa suka shiga falon, mazan da babbar murya suka yi sallama, matan har Jawahir mai goyo da karamar murya sukai sallamar. Dr. Asma’u ta mike tsaye idonta cikin na Rayhanah wadda ke barin kafadun Ibrahim, hangawa kawai take don ta hango ‘yar. Can ta hango ta bayan Jawahir. Ibrahim da Khalipha suka saki hannun matayensu suka hadu suka rungumeta, daya ta gaba daya ta baya. Don farin ciki sai tasa kuka tana fadin. “Ka yafe mini Khalipha, ku roka min Rayhanah ta yafe mini. Na yi kuskure bisa son zuciya da ingiza mai kantun kawayen banza, don Allah ku roketa ta yafe mini, ina jin kunyar sake hada ido da ita a matsayin sirikata bayan na yi mata korar kare. Ko cikin ‘ya’yana ban taba samun wadda ta yi min biyayyar da Rayhanah ta yi min ba…… ga shi Allah ya nuna min kuskure na a fili tun ban mutu ba, na kuma karba na yarda babu mai yi sai Allah….!!!” Rayhanah ce ta je ta zube a gabanta tana fadin. “Ba ki yi min komai ba Mami, ni ban taba rikeki a raina ba. Butulallen bawa shine mai manta baya idan gaba ta canza. Mami na san baki taba kina ba, sai dan kuskuren fahimta da ya gifta a tsakaninmu, da kuma uzurin da na yi amanna da cewa, wani bai isa ya tsarawa wani dan Adam rayuwa ba, face Ubangijin da ya halicce shi. Ban zata ba Mami, nima ban taba zaton al’amuran za su juye haka ba. In da na kuskuro nima ina baki hakuri…..” Suka rungume juna sosai hawaye sharrr! A idon kowaccensu. A haka Dr. Mansur ya cimmasu, ko da yake ya jima a bakin kofa yana kallonsu yana sauraronsu, sune dai basu ganshi ba. Sai da suka samu nutsuwa ne ta kama hannunsu ita da Mimtaz ta zaunar dasu gefe da gefenta, wato suka sakata a tsakiya a kan doguwar seater. Mami ta mikawa Jawahir hannu ta ce, “To sauko min ita sarkin iyayi da kankanba, ke kadai kin goye Asma’un, ko ta yi kama da mai suna Jawahir mummuna ne oho?’ Dr. Mansur ya karaso falon yana fadin, “Basu ‘yarsu Jawahir dita. Jeki dauki dan Balaraben danki”. Ya nuna Khaleel dake ta kuka a cinyar Ibraheem. Ta ce, “Wallahi kuwa Daddy, dadin haihuwa sama da daya kenan”. Ta sauko Asma’u ta dorawa Mami a cinya. Ta dade tana kallon buleliyar jikar tata, mai cike da tarin suma akanta da tsafta da koshin lafiya. Sai ta mike ta sanyata a bayanta ta goye da zanin Jawahir. Rayhanah ta lumshe ido, hawayen farin ciki suka zubo mata. Muhd. Mansur yasa rigima shima sai Mami ta goya shi. Ta ce, “Katoto da kai haka Daddy?” Sai ta sure shi shima duk girmansa ta dora a kafadarta tana fadin, “Miji na yin kishi ne dama da matarsa Mansur?”. Ya ce, “A’a, Ni kece matata ba wannan Asma’un ba ta yi nauyi da yawa bana iya daukan ta”. Kowa yasa dariya. Abida da duk ta bi ta muzanta a falon, ba don komi ba sai don ba mai kallon ta a falon, ba wanda yabi ta kanta kamar basu san tana wajen ba. Ta rungume Yaya Khalipha tana kuka tana fadin ya roka mata afuwar Rayhanah. Ya ce, “A’a, ni a suwa kuma? Ga mijinta gata da kanta”. Ko giyar wake ta sha ta san itama ba ta isa ta doshi Ibrahim ba, wanda tunda ya shigo falon yake jefa mata harara. Ta kara kama kafar Yaya Khalipha tana kuka. Dole ya dago ta ya zaunar a gefensa, dan’uwa rabin jiki. Ya ce, “Rahane, an Rahane na! Ga Abida da kokon bararta ko Daddy da Himu sa daina kyarar ta”. Ta murguda baki ta ce, “Idan na ce maka Audu ai na rama…..!” Tuno lokacin yasa Khalipha yin dariya. Dariya mai yawan gaske da ya manta rabon da yayi irinta. Ibrahim ma da ba kallon su yake ba hankalinshi na kan wayarsa sai da ya murmusa. Ta ce, “Abida ai ni ban taba kin ki ba, ban taba kullatar ki ba daidai da rana daya. Allah ya yi mana afuwa baki dayanmu”. Nan dai aka yafi juna. Dacta Mansur ya yafewa Maminsa, wadda dai-dai da rana daya son da yake mata bai taba canzawa da komai ba, illa dai ya yi kokarin nuna bacin ransa gareta don ta gane kuskurenta. Ta kuma gane hanyar data dauko rana tsaka ba mai billewa bace. Aziza tuntuni tana makale jikin Rayhanah. Nan Daddy ya ja doguwar addu’a suka shafa, suka yi dinner tare cikin farin ciki marar misaltuwa. Sai da suka share kwana uku a gidan (with nostalgia)cike da begen gida, sannan iyayen suka rakasu gidajensu da ke unguwar (Farm Center). Washegari sun je Takai gaida dangi da Hakimi, inda suka tarar ana shagalin sunan Nabilah, ta haihu danta namiji tasa mishi suna IBRAHEEM…. Sai da kwalla ta fito daga idanun Rahane saboda tausayin Nabilah, wadda har yau kwayar idonta bata daina yiwa Himu kallon da take mishi tun farko ba, duk da auren nata a Lagos, inda ta auri wani ma’aikacin Custom Kabiru Dalhatu. Sun sha gata wajen Hakimi da Haj. Kareema, daga nan suka tafi da Inna Juma, suka je Albasu wajen sauran dangi bayan motarsu shake da sittiru da kayan abinci. Sai da Zinaru ta yi ta kuka kamar ranta zai fita. Bayan sun dawo daga Takai sunyi settling Dr. Ibraheem ya shiga sabon ofishinsa matsayin nephrology consultant cikin asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano. Har ila yau, malami a (Faculty of medicine) na jami’ar Bayero ta Kano. MURFI Likkafa ta ci gaba ga iyalin Dr. Mansur Takai, ta kowanne fanni daukaka ke binsu a gindi -a-gindi. Rayhanah ta samu komawa Jami’ar Bayero ta dora degree a (Computer Sceince), ta kuma fara koyarwa a bangaren nata (lecturing) matsayin (assistant-lecturer) albarkacin darajar kwali mai matsayi na farko data fito da shi, cikin nasara mai dimbin yawa. Tun daga kai Asma’u yaye Mami ta kwace ta hanasu. Wai ita ma tana so ta ga dan karami yana gilmawa a gabanta. Daga ita sai Azizah wadda ke shekarar farko a Jami’a. Jawahir da Abida duk an aurar dasu shekaru biyu a baya. Jawahir ta haihu. Abida na da karamin ciki. A shekarar da Rayhanah ta sake haihuwar Bilkisu, wadda ta sanyawa sunan Iya Bilki, a shekarar ne aka rantsar da Dr. Mansur a matsayin Ministan lafiya na kasa baki daya, saboda dimbin taimakon da yake bayarwa a fannin kiwon lafiyar al’ummar Nigeria, daga federal posting din ya fito. Shekara na zagayowa ta sake haifo ‘yarta Jawahir, sai da ta jera mata biyar sannan Allah ya ba ta Da namiji, Ibrahim ya saka mishi sunan Hakimi Abdulkadir, tunda Khalipha ya yiwa Dacta Mansur takwara. Suna kiranshi Abdul. Babu diya mace a idon Ibrahim duk duniya bayan RAYHANAH! Babu uwargida sarautar mata bayan RAYHANAH!! Babu sanyin idaniya a rayuwar Ibrahim sai RAYHANAH da ‘ya’yanta. Wannan shine labarin RAYUWAR RAYHANAH. Masha Allahu la’quwwata illa billah. Allahumma salli ala Dayyibil-mudayyibi. Wa ala ahlihi wa sahbihi wa sallim tasliman katheera!!! -Maman Khazraji.