*ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 1 Mota ƙirar ƙasar (South Korea) ce ta tsaya a dai-dai ƙofar wani kanti, wanda zamu iya kiranshi da suna na tailoli, ma'ana shagon ɗinki kenan,Mai suna Almansir Tailoring and Fashion Design Company. Mutumin ƙofar shagon shi ya nuna mana cewa mata da maza na iya kai ɗinki a shagon. Ruwan toka ash colour shi ne fentin motar, wanda zamu iya kiran motar da suna KIA Saloon. Farar yarinya ce,za mu ce ko budurwa, ita ce matuƙiyar motar, wacce ta fito sanye da riga da wando zubin (Suits) irin na ƙasashen tsallake (Abroad) amma na mata, kenan mai shimi mai babban maƙwancin hannun kafaɗa, sai doguwar riga ƙwat ta ɗora a sama, wacce ta kai mata har wucewar gwiwa. Maɓallin tsakiyar doguwar rigar ƙwat ɗin ne kawai ke maƙale da rigar, ruwan toka ne ash colour kalar kayan nata. Takamin ƙafarta kuwa baƙi ne, tare da farin gilashi manne a saman dogon hancinta, wanda mafiya yawan likitoci ke sanya irin shi. Babu komai a hannun ta sai kan wayar zamani ta Ipad,gashin kanta kuwa a sake yake wanda za mu iya cewa ya kai tsakiyar bayanta,babu wani alamar ɗanƙwali balle mayafi a saman kanta, kallo ɗaya za ka yi mata sai ka maimaita goma a lokaci ɗaya baka sani ba. Tabbas yanayin yanda take kulle motar ta kawai zai iya nuna mana mace ce mai taƙama da ƙyan da Allah ya bata, zan iya cewa kuma ita kanta ta san duk inda ta gifta sai ta tsayar da ayyukan mutane, shi yasa na fahimce ta mai jiji da kai. Doguwa ce, amma ba shal ba, yanayin kiran zubin jikinta kuwa,za mu iya kamanta shi da na Pretty Zeeta, ƴar ƙasar India. Kai kallo ɗaya ma ka yi mata za ka iya ce mata ba ƴar ƙasar Najeriya ba ce, saboda yanayin zubinta ya fi kama da na ƴan (Miss World),Sarauniyar ƙyau ta duniya. Yatsun hannunta kuwa zara-zara suke, waɗanda suka sha fentin ƙwalba (Lamp paint) a saman faratanta, shi ma ruwan toka, faratanta sunyi tsayi kamar ƴan kanti, ta saka a yatsun ta. Sai da ta ɗan ɗauki sakan biyar, sannan ta sa makulli ta rufe motarta. Ɗagowar da zata yi kuwa, sai da ta rausaya da gashin saman kanta da ya zubo mata a fuskarta,a lokacin da take kulle motarta, sai da ta duba hagu da damarta, sannan ta tsallaka titin da ke a gaban,MONAK STORE, shi ta shiga. Tsayin minti talatin da baƙwai na yi ina dudduba kayan ƙwadayin da ke kaini duk wata (Super store), cakulet (chocolate) dasu Chingam (Chewing gum) sannan biskit (Biscuits), irin waɗanda na mayar abinci na,kayan ƙwalliya kuwa sai dai in dinga ɗaukar kala-kalar jam baki da man leɓe (Wetlips). Leda ce a hannuna wacce aka cika ta da rubutun sunan kantin da na fito,ƙarar wayar dake hannuna, ita ta ɗan ɗauke mini hankali,a bisa tafiyar da nake yi. "Ka san dai bana magana a titi, sai dai kayi haƙuri bayan mintuna arba'in ka bugo,a wannan lokaci na isa gidan Aunty,okey, thank bye." Maganar da nayi a waya kenan da (Proposed) ɗin da na tsayar a matsayin wanda zan aura nan da ɗan lokaci ƙanƙani, don ma ina ja masa rai, saboda tunanin barin gida, wannan yake ɗan tayar mini da hankali. Zamu iya cewa yanayin da muke ciki na sanyi duk da dama mun san Garin Jos gari ne mai ni'imar gaske, dalilin haka ne ma Turawa da sauran fararan fata,sun fi yawa a can, saboda sabo da suka yi na jin sanyi a ƙasashensu. Wannan yanayi na yau ya sha bamban da na kullum,tun da yau sanyin da sauƙi, sai dai iska da ake hurawa a hankali mai ratsa jiki, wadda za ta iya saka nishaɗi. Na ɗaga kaina sama ina kallon giza-gizan sanyi na tafiya cikin natsuwa,gashin kaina kuwa iska ke yi mini wasan ball da shi, ina faman buɗe fuskata. Tabbas na hango motoci a tafe, amma ganin nesa suke da ni yasa na kalli ɗaya gefen nawa, na tsallaka titi, iska ta watsar mini da gashin kaina wanda ya watsu a fuskata, ina ƙoƙarin buɗe fuskata ne na ji mota ta kai mini zungura, take na faɗi zaune a ƙasa tsakiyar titi. Ƙarar jan birki ita ta sa na ɗora hannayena a saman kaina, ina jiran ƙarfen Nasara ya bi ta saman kaina. Tsawa na ji an daka mini da ƙarfin gaske, wannan yasa na yi saurin ɗago kaina, haushi ya kama ni a take da na ga ashe daga motar baya ce ma ake yi mini wannan tsawar, ta gabana kuwa mai zubin (Cardillale Lemousine) wacce ta banke ni kenan doguwa mai ƙofa uku. Baƙin gilashi ne daɗe da ita,babu alamar zugewa, balle in samu tabbarakin ganin ko naji ciwo, wannan ya ƙara tunzura mini zuciya,na miƙe da sauri na sa hannuna na daki gaban motar, daga sama suka faɗo,ko ko ta ƙarƙashin ƙasa? Oho ƙartin mutane ne masu kaya layi-layi, wanda na ga layin ya ƙunshi kala biyu. Dogarawa kenan, waɗanda aka fi saninsu a gidajen masarautu. Ko gama gane su banyi ba, cikin dishi-dishin idanuna na ga wani ƙato daga cikin su ya ɗaga hannu zai kai mini mari,cikin zafin nama na riƙe hannunsa, duk da sai da hannuna ya yi kamar zai karye biyu,tsayawar shi kuwa kusa da cinyata, saboda yafi ƙarfina. Ƙwanƙwasa baƙin gilashin muka ji anyi daga cikin motar nan ta gabanmu, shi yasa gaba ɗayanmu hankalinmu ya koma ga gilashin da yake sauka a hankali. Ƙyakkyawan mutum ne,sanye da manyan kaya na alfarma,ƙwance a kusurwar mota (Owner's Corner) zan iya ganin gashin bakin fuskarsa mai suna ƙwata miliyon (Quater Million) farin gilashi ne manne a fuskarshi, duk cikin sakan ɗin da bai wuce uku ba na karanto hakan. Sai da ya yatsina tamkar mace, sannan ya motsa jikinsa da ƙyar, ya ƙara gyara ƙwanciyarsa a kusurwar motar, da ƙyar ya ɗaga hannunsa ya cire gilashin fuskarsa. A tunanina magana zai yi, amma sai naga ya yi masu alama da kai, ma'ana ya girgiza kai,hannunsa mai gilashin nan ya ɗan ɗaga ya yi masu alamar su koma cikin motocinsu. Daga wannan kuwa sai dai na ga baƙin gilashin motar nan na komawa sama mazaunin sa a hankali, har gilashin ya kusan rufewa, sai na ga an cillo bandir ɗin ƴan ɗari biyar-biyar ƙwaya ɗaya,an ja motar an tafi. Ban san lokacin da na kaiwa bayan zumɓutun motar nan duka ba da ƙarfina, amma ko tsayawa ma bata yi niyyar yi ba. Wucewarsu ke da wuya mutane suka taru a kaina suna yi mini sannu, a cikin su ne wata mata,ɗaure da zani da riga masu buɗaɗɗen hannu ta kama ni, da ganin ta kaga yare, da harshen Turanci ta yi mini maganar sannunta. "Sorry wooo!" A nan ne take gaya mini wai na ci arziƙi, saboda ina da ƙyau, da yau sai an ɗaure ni nasha dukan ƙarti,ban san ko waye ba a cikin motar,wai ɗan Egwe ne mai jiran gado a hausarmu kenan Yarima,yaren da ta faɗa kuma He is the Prince,ta dinga rawarsu ta yare cewa take. "You Are very luck woman." Wai in yi sauri in ɓace daga nan kada a aiko a ɗauke ni. Wani mugun haushi da baƙin ciki ya kama ni a take. Su kuwa sai miƙa mini kuɗin nan sukeyi, sai cewa suke Allah na sona, na waiga na kalli mutanen da ke zagaye da ni dukkansu ba mai rigar da ta wuce dubu ɗaya, na kalli matar nan, sannan na karɓi kuɗin a hannun wani namiji wanda ke ta faman miƙo mini su,na miƙawa matar nan, sannan na ce. "Madam go and share it. Na ɗauki ledata na isa ga motata,ni kaina sai fadanci suke yi mini wai Allah ya taimake ni. "Good bless you." Gidanmu na nufa kai tsaye, saboda haushi na fasa isa gidan Auntynmu. Get ɗin gidan da motata ta tsaya ina yin horn mai ruwan jinin kare ne (Maroon colour) fentin gidan kuwa fari ne da ratsin ruwan Maroon colour. Maigadin gidan bai wuce ɗan shekara arba'in da biyar ba,ƙaton yare maji ƙarfi da shi, shi ya leƙo sannan ya buɗe mini ƙofa da rawar jikinsa. Da gudu ya iso ga motata, kamar yanda ya saba, amma yau ban tsaya saurarenshi ba,ko rufe murfin motar ma ni ban tsaya yi ba, balle ledar kayana ko wata waya can. Da gudu na haye matattakalar,benen da ke ƙofar shiga gidanmu, wacce zata kai biyar. Ƙofar gilashi ce mai ƙwarin gaske, amma da hannu ɗaya na tura ta na shiga,ban tsaya ko'ina ba sai (Set room) ɗin Babana,ɗakin shaƙatawa, da ƙyar na iya yin sallama, na shiga yana kishingiɗe a saman lallausan kafet ɗin tsakiyar falo, wanda musamman aka saka shi a gefe ɗaya na falon, wanda ƙasan shi katifa ce mai laushin gaske, inda yake ɗora hannu kuma tuntaye ne na fatar damisa har guda huɗu a zagaye da shi. Kujeru ne ƙwaya uku kacal, masu zubin irin na teburin cin abinci,a gefenshi zagaye, wanda in kazo gaishe shi,ko ya yi baƙi,yana wajen za su zauna a kai su gaisa,ko wacce kujera da ɗan tebir a kusa da ita da jarida (magazine), a saman shi,in za a kawo ruwa ko lemu,a sama za a ɗorawa kowa. Ya fi yin wannan kishingiɗa daga bayan sallar la'asar zuwa ta magriba, daga nan kuma sai wajen ƙarfe taƙwas da rabi na dare idan har yana gida. Ina shiga na zauna ɗaya daga cikin kujerun alfarmar da suke a tsakiyar falon, cikin sigar shagwaɓa nake kukana. Babana ya saba da shagwaɓata, saboda haka sai ya yi dariyarsu ta manya. "A'a Yasmin yaya? Ko wani ne ya ɓata miki rai ne? Taso in ji,taso inji autar Daddy. Come and tell me my dear." Na tashi na isa na durƙusa a gabanshi, kafin in yi magana Mamata wacce muke kira da Mamee ta shigo, Babanmu kuwa muna kiranshi Dad. Tana shigowa ta fara faɗa, "wallahi My Dear,kai ke ƙara shagwaɓa yarinyar nan, shi yasa kullum take ganin ta kamar ƙaramar yarinya, ta ƙi tsayawa ma ta ƙwantar da hankalinta ta fito da miji a yi mata aure ma mu huta, ina dalilin sakarci irin wannan? Wallahi na kusan gajiya zan haɗa kanki in auna da ke Syria in huta,ko bakina ma ya gajarce." "Dad kaga Mamee ko bata so na, yanzu da Aunty ce dakaga sun shige ɗaki sun koro ni waje, amma ni kullum ta dinga yi mini faɗa." "Ki yi aure ki gani in na ƙara yi miki haka." "Dad..." "Ke sorry ƙyale ta,ban ma san wanda ya kira ta ba, fita My Dear kada in taso miki nan." "Allah ya huci zuciyarka duk dai son da ake mata,ni dai wajena ba shi da amfani, tunda an ƙi yi mata aure shekara ashirin da uku. Ni kuwa tawa ɗiyar tun da sha taƙwas nayi mata auranta." "Fita na ce ko!" Ya faɗa har da ɗan tashi daga kishingiɗar da ya yi. "Na yi shiru sorry." "Nayi nima, dawo nan to ki zauna." Ya nuna kusa da shi kaɗan ta taso ta zauna, sannan ya ce, "Okey, talk my daughter." *Dad,dama da na fita ne wani ya bankeni da mota." "What?" Ya faɗa har da tashi zaune. "Wa ye shi?" "Nima ban san shi ba na faɗi kuma wai sai yasa wasu za su dake ni." "How is that senseless man?" Ya tashi zaune sosai. "Okey, tell me." "Dad,kuma ya ja motarshi ya yi tafiyarsa,wai don raini ma har da jifa na da kuɗi. Dad ko magana fa ba ya yi, da kai da hannu yake ba su duka (Instruction)." "To waye ubanshi a garin nan?" "Oho,ni dai na ji mutanen da suka zagaye ni bayan ya tafi suna cewa wai ko ɗan waye ma, oho,fa don haushi ban tsaya tambayarsu ba. Dad da ƙyar fa yake motsi,ƙwance yake a bayan mota." "Zaki iya gane shi in kin ganshi yanzu?" "Eh Dad." "To duk lokacin da ki ka ganshi ki ɗauko mini lambar motarsa da sunanshi kawai ma sun isa, zan haɗa shi da hukuma tunda haka sukeyi wa mutane sakarci a gari." "Haba My Dear, ya za ka biyewa zancen yara ka je kaji kunya." "A'a zan sa a koya masa hankali, ba wai don ya taɓa ƴata ba, illa saboda nan gaba, tunda da gani haka suke yi wa mutane,don suna taƙama da iyayensu na da kuɗi." "Wallahi Daddy da gaske ne,ka ga ma kayana yanda suka koma,ƙafata ma sai ciwo take yi." "To anji Allah ya bada sauƙi, tashi ki je ki sha (Panadol) fanadol.)" "Dad ka ga Mamee ko?" "Ke ƙyaleta,je ki abin ki ke dai ki yi mini aikin da na saka ki kinji ko?" Na ce, "To." Na tashi na tafi. Ina isa falo na samu Katung a tsaye. Katung mutum ne mai ban dariya, ga iya bin hanyoyin da zai saka ka cikin farin ciki,ko da ranka a ɓace yake. Ai kuwa nan ya dinga bin hanyoyin shi da ya saba, har sai da ya saka ni dariya a dole. A nan ne har ya samu damar tambayata, na ƙwashe duk abin da ya faru na gaya masa. A nan ya ce in har na gane ko waye, to shima fa zai bayar da gudummawarsa, ya ɗan ba ni ƙwarin gwiwa, sannan ya miƙo mini kayana,har da makullin motata, waɗanda na manta da su ƙwata-ƙwata, sannan na haye ɗakina, na jefa kayana saman gado na wuce banɗaki kawai, saboda in shiga ɗan ruwan ɗumi ko naji ɗan daɗin jikina. **** **** **** Plateau State,wacce jama'a suka fi kira da suna Jos. Jos gari ne wanda Allah ya yi masa ni'imar sanyi da duwatsu kala-kala, ga wajen ƙwanciyar ruwa yana dashi. In kayi la'akari da Jos,za kaga yanayinta ya fi kama da ƴan ƙasashen tsallake (Abroad), ire-iren wannan ne ya sa garin kullum tamkar ana damina. In kuwa lokacin sanyi ya zo,.... *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 2 In kuwa lokacin sanyi ya zo, sai ka ga har ƙananan dusar ƙanƙara ke zuba wasu lokutan (Snow), amma saboda sabo wannan duk baya hana mutanen garin yawonsu da hidimomin su. Wannan kuma yasa yawancin Turawa da sauran ƴan ƙasashen duniya ke zama a Jos. Asali ma ƴan garuruwa da ƴan ƙasashe daban-daban sun fi yawa a garin. Sai dai mutanen garin Jos, yawancinsu sun fi baiwa (English wears) mahimmanci, ƙananan kayan turawa. Wannan dalili ne ma yasa ko a tarihin Jos, shi ne garin da aka fara kawo kayan gwanjo daga ƙasashen duniya, shi yasa har yau kuwa ita ce kasuwar duniyar Gwanjo ga wuraren da shagunan siyar da sababbin kayan turawa (Boutiques) sun yi yawa. Jos gari ne wanda ya saba da jama'a kala-kala, wasu in ka samu tarihinsu sun daɗe sosai a garin, wasu ma ba su san asalin inda garin iyayensu da kakanninsu yake ba. Wannan dalilin ma ya haddasa samun harshen yare da dama a garin, wanda a iya ɗan ƙiyastawa za a iya samun harshen yare ya kai kusan ɗari biyu a garin, wannan yasa suka ɗauki Hausa Central Language ɗinsu. Sai dai sun ɗan fi amincewa da Turanci,ko da kuwa irin turancin da aka fi sanin ƴan Legas ko kuma mutanen Ibo,wato (Broken English). Yanzu haka sana'o'in masu kuɗin ba su wuce shigo da motoci, da kayan sawar turawa da Gwanjo, amma za a ga masu kuɗinsu na yawo da ƴar ƙaramar sanda mai lankwasashen masa. Ni kam garin na burge ni, saboda wuraren shaƙatawarsa, amma fa sunayen Hausawansu duk irin sunayenmu ne. Wannan kuma bai hana su yin karatun zamani ba, wato makarantun boko, ga shi akwai Islamiyoyi a garin, kamar yanda aƙwai wajen bautar yawancin wasu yare Choci. Mahaifina kuwa ɗan asalin ƙasar Najeriya ne,a jahar Adamawa, wacce take kusa da jahar Taraba. Suna wani ƙauye wai shi Gembo. Iyayenshi duk ƴan asalin can ne, amma duk Allah ya yi musu rasuwa, tun yana ɗan yaro,a hannun Yayan Babansa ya girma. Mahaifinmu bai yi karatun boko ba, a lokacin da yana garin Gembo. Saboda a lokacin ba a waye sosai da karatun ba. Asali ma abin da ya hanashi karatun mariƙinshi talaka ne sosai, sai dai sun yi karatun allo, wanda har sun yi sauka. An taɓa yi masa aure a ƙauyen Gembo wanda dalilin auran ne suka yanke shawara shi da abokanshi su fita neman kuɗi. A lokacin yana shekara sha takwas kaɗai. Sun fara tsayawa Kano tsawon shekara ɗaya,a inda ya fara sana'ar siyar da rake a ƴar kura (baro), shi ma ta haya ce ɗaya daga cikin abokansa,ko in ce abokin wasanshi, saboda ɗan mace da ɗan namiji suke, shi ne ya kama sana'ar Gwanjo a kasuwar Ƙofar Wambai. Tun yana tsaro ana biyanshi, har ya fara ɗan sarar nasa yana yawo da su a hannu, ganin yana samu yasa ya janyo hankalin mahaifina da ya daina sana'ar rake ya koma ta Gwanjo, da ƙyar ya amince. Ganin sun ɗan bunƙasa kaɗan yasa suka yanke hukuncin zuwa Jos su dinga sarowa. Zuwansu uku,ana huɗu ya yi shawara da yayan Babanshi ya amince suka koma Jos da zama, shi da kanshi bai san ya bar matarsa da ciki ba,sai dai haihuwa aka aiko masa. Saboda ya ce mana sukan yi wata baƙwai,taƙwas ba su je gida ba. A ranar da ya isa gida, a daren matarshi mai suna Huraira ta rasu, lokacin ƙwananta uku da haihuwa,ana gobe sunan yarinyar da ta samu, ita ma ta ce ga garinku nan. Shi ne tun da ya baro Gembo bayan an gama makoki da sati uku, daga shekara sai shekara yake komawa garin, domin gaishe da wan Babanshi Alhaji Tsalha. Har yau kuwa yana nan da rai, sai dai ya tsufa. Ikon Allah yasa suka shiga makarantar yaƙi da jahilci,su wai don saboda su iya maganar ciniki da yaran garin,a haka kuwa suka yi fice wajen iya komai, aka sa su, suka zama zakaru a ajin. Wannan yasa aka tura su Sakandire ta garin da suka gama, aka dinga bin su da aiki. A lokacin neman masu karatun ake ba kamar yanzu ba. Cikin ikon Allah Daddy na har digiri ya yi inda ya haɗu da mahaifiyata kenan ita ma tana digiri ɗin ta a kan Education, shekararta ta farko. Shi kuwa yana shekarar ƙarshe ta kammala digiri ɗinsa,a lokacin yana ɗan shekara talatin da biyar kenan. A shekara sha ɗaya ya je Jos, ya yi shekara ɗaya ashirin kenan, suka yi yaƙi da jahilci shekara biyu, Sakandire shekara shida, shekara biyu sharar fagen shiga jami'a, Diploma kenan, sai haɗa digiri shekara uku, sai kuma kammalawa da bautar ƙasa ya ɗauke shi shekara biyu. Tunda Allah ya haɗa Momeena da Dad ɗina, Mahaifinta ya nema masa aiki a ma'aikatar (NNPC) ta Jos, ya kama masu wajen zama. Mameena gidan Dad ta kammala karatunta na digiri, da tana aiki a ma'aikatar Ilimi (Ministry of Education), amma daga baya Dad ya hana, saboda maza da suka dame ta. A hankali har Allah yasa komai nasa ya bunƙasa, amma har yanzu sana'ar shigo da kayan Gwanjo tana nan Dad na yin ta,irin tasu ta manya-manyan ƴan kasuwa. Saboda yanzun haka, ba ya aikin gwamnati, sai dai siyar da motoci da harkar Gwanjo da ta safarar kayayyaki ƙasashen duniya. Amininsa abokinsa ɗan uwansa, wanda suka fara harkar tare shi ne Alhaji Kabir babansu Aminiyata ƴar uwata Fatima Kabir. Mahaiyata Mamee, wacce sunanta na gaskiya Sharifat,iyayenta ƴan asalin Syria ne,mahaifinta ne yazo aikin wakilcin Syria a Nijeriya (Ambassador) ya zo da su Mamee suna ƴan mata,a inda Mamee ta gama makarantar gaba da Secondary a Najeriya ta fara karatun digiri ɗin ta a jami'ar Jos. Mahaifin Mamee ya zo Najeriya tun shekara ta 1973, a lokacin mulkin Gen.Gawon, a inda ya ji daɗin zaman Najeriya, ya yanke hukuncin zama a cikinta,a lokacin da ya kammala aikinshi. Su Mamee su biyu ne a wajen iyayen su, ita da ƙaninta Saifullah. Shekarar iyayenta goma sha ɗaya kenan da komawarsu Syria,a lokacin kuwa ina da wayona sosai, saboda ina ƴar shekara sha biyu a inda suka tafi da Yaya Habib can ƙasar,a wata jaha wacce take mai albarkar noma da kiwo. Kenan zan iya cewa kakannina Fulanin Larabawa ne, yanzun haka su kan zo lokaci-lokaci,mu ma mukan je masu ziyara. Mu uku ne kacal su Mamee suka haifa,Aunty Salwa ita ce yayarmu, shekara biyar ta baiwa Yaya Habib. Ni kuma shekara biyar Yaya Habib ya bani, kenan Aunty Salwa shekararta talatin da uku,Yaya Habib ashirin da taƙwas, sai ni ƴar auta ashirin da uku. Dukkanmu mun yi digiri, amma Aunty Salwa a gidan mijinta ta yi shi,tana ƴar shekara sha takwas aka yi mata aure, ta gama makaranta da shekara ɗaya kenan, yanzun haka ƴaƴanta uku. Shekarar ta sha biyar da auran Uncle Abdulƙadir,amma suna zamansu lafiya. Ɗan ta na farko shekararsa shida, sai ƴar yarinyarta mai shekara biyu Haulatu, har yanzun kuma shiru, amma Uncle ya hana ta yin aiki, sai dai tana yin kasuwancin siyar da injinan saƙa da na keken ɗinki, da na hawa, kuma mijinta Uncle yana da abin hannunsa sosai. Yaya Habib yanzun yake digirinsa na biyu a jami'ar Syria,wanda ya yi karatunsa ne gaba ɗaya a can ƙasar,wajen iyayen Mamee. Yana karantar (Agronomy) karatun fitar da tsiro daga cikin ƙasa. Alhaji Fahat shi ya zaɓa masa wannan fannin,wato mahaifin Mamee kenan. Yaya ba mazaunin gida ba ne, sai dai in yazo hutu. Ni kuwa na yi primary ɗi ta a Al-Imam School of Science nan Jos,na yi Sakandire ɗina a Minna,amma nan Jos na kammala makaranta ta, inda a can ne na haɗu da Anwar tsawon shekara huɗu muna tare da shi. Mahaifinmu Alhaji Sani Sa'id, yana nuna mana ƙauna fiye da tunanin kowa, shi yasa mu ma muke ƙoƙarin yi masa abin da zai ji daɗi, balle ga girma ya tunkaro shi, saboda mutum ɗan shekara sittin da takwas a duniya,ai mun san dattijo ne, sai dai jin daɗi yasa ba'a gane tsufan jikinsa. Ina da ƙyau,ko ni na sani, sai dai farina irin na Larabawa ne wato fari mai haske. Structure ɗin jikina kuwa na burge ni,ga manan ƙirjina daidai ne, yawancin ƙawayena suna cewa ina yanayi da ƴar ƙasar Indiyar nan wato Pretty Zeenta,sai dai wai na fita fari mai ƙyau, kuma gashinmu ba iri ɗaya ba ne,ni irin mai laushi ne irin na Larabawa, ita kuwa nata mai tauri ne,ko kuwa a ce bazar yake. A unguwar Refin Rizont gidan iyayena yake,gani ƴar gata gaba da baya, saboda ƙauna da ake nuna mini,balle kuma ni ce auta. **** **** **** Hidima kamar ta yi mini yawa, balle yau ne ranar walimar iyaye da abokan arziki (Dinner party). Rana ce wacce da iyaye da ƴaƴa da abokanan arziƙi ke haɗuwa, to balle hidima irin ta manya haka. Yau ne mahaifin Fatima, wanda yake abokin wasa ga Dad yake yin party ɗin ɗiyarshi ta uku, wacce take ƴar'uwata, Aminiyata ga ta ƙawata. Biki kuwa irin na manya, kowa ya san shuwagabannin kasashe ke taruwa ban da Sarakunan duniya. Tabbas sun taru a yau. A hotel ɗin jero wanda shi ne Hotel na biyu a Jos a duk faɗin Jos. Ƴan gidajen rediyo da talabijin kuwa ba zan iya ƙirga yawansu ba, ballantana kuma dama kowanne shugaba in zai zo da tawagarshi, zai taho ne da ƴan ɗaukar hotansa, ban da ƴan ɗaukar hotan kaset (Camera man) da ƴan gidan rediyo na garinshi. Shi hall ɗin kuwa,an jera masa kujeru na alfarma, amma za a iya cewa duk tebir ɗaya mutum uku ne zagaye da shi, suna kallon saman ɗakin taron, manyan sarakuna da shuwagaban ƙasashe kuwa su ne irin lafiyayyun kujerun nan da ake keɓewa (VIP Cushion). Kowa ya san in an haɗo irin wannan taro a kan ɗauki lokaci ana gabatar da shirye-shirye tun da akan gayyato mawaƙa kala-kala, da ƴan wasan ƙwaiƙwayo na Turanci, da na yare, sai an gama irin wannan shaƙatawa sannan ma ake buɗa fili da ƴan surutai, da kuma sannu da zuwan baƙi wanda uban ango da na amarya ke yi. Da waɗanda aka ɗora a matsayin baƙin taro,a kan ba ango da abokinshi fili su yi godiya. Ango kenan abokin ango ya gabatar da halayen ango masu ƙyau, haka ƙawar amarya ma takan yabi ƙawarta. Amarya kuwa godiya kawai take yi da nuna murnarta. Yau ne duk ranar yin haka, wanda tuni ɗakin taro ya cika maƙil da jama'a, kafin komai ya fara bayyana kaset ɗin kiɗa mai fitar sauti a hankali (Slow music) a lokacin kuma ƴan mata masu rabon abinci ke ratsa mutane suna ajiye masu ƴan kayan lasawa, kafin a gama a fara kawo abinci. A cikin ƴan matan kuwa har da mu ƙawayen amarya, wanda muka dinga yawo da ƴan farantai a hannu muna raba madara mai ƙanƙara da lemun ƙwali da ruwan doguwar roba (Ice Cream,Lemon juice, and Swan water). Ni kaina na san duk ɗakin taron nan mutum ɗai ɗai ne wanda hankalinsa ba ya kaina, shi ma sai dai in bai hangoni ba, saboda ƙyau da Allah ya yi mini. Riga da wando ne a jikina, amma ruwan baƙaƙe, sannan kuma masu ɗauke idanuwa, saboda yadin mai sheƙi ne tamkar madubi. Wando ne har ƙasa, amma daga ƙasa a buɗe yake, sai rigar kuwa ƴar iya ƙuguna, wanda hannunta kuwa na shimi ne, ɗan siririn gaske, amma doguwar riga mai buɗaɗɗan gaba da dogon hannu ita ce a saman shimin nan, wanda ɗan abin ɓalle doguwar rigar dai dai saman cibiyata yake. Gashina ya sha gyaran kanti, wato (salon), amma na taje shi gaba ɗaya ya bi bayana, sai sheƙi yake,dama Tubarakallah! Ga shi baƙiƙƙirin, tamkar izgar baƙin doki,dama asali ni ba mai ɗaura ɗanƙwali ba ce ba, saboda haka ma baya cikin tunanina, sai dai na ɗan yanko ƙalilan daga cikin gashina ya sauko gefen fuskata, wanda yake ɗan saka ni aikin gyara shi idan na duƙa ajiye ƴan kayan lasawa a gaban mutane....... *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 3 Fararan takalma ne a ƙafata, sannan sarƙa da ƴan kunne ne a wuyana, amma na (Diamond), wanda duk sun ƙunshi agogon hannuna da zobunan hannuna guda huɗu, baƙin fenti ke liƙe a farcina na (Lamp paint), haka baƙin jam baki ne manne a leɓɓuna na, wanda ke sheƙi. Lallai ni kaina na san na yi ƙyau, wannan ƙyau nawa kuwa ina taƙama da shi,ga takalma na masu tsinin gaske ko'ina na kai (Ice Cream) ɗin nan sai sun yi mini magana,ni kuwa dama ba mace ba ce mai son magana, wannan yasa sai dai in yi musu murmushi wanda ƴar lotsawar gefen kumatuna ke bayyana (Dimple). Ina cikin rarrabawa ne kuwa har na kawo wani tebir a tsakiyar ɗakin taron, na ajiyewa na gabana,na ajiyewa ɗayan na kusa da shi, sai na ji mutanen nan biyu na cewa. "Allah ya ja da ran Gimbiya,Yarima na gaishe ki." Na samu na gyara gashin da ya rufe mini fuska. Gabana ne naji ya yi mummunan faɗuwa a daidai lokacin da na ɗago kaina na ga mutumin da motarshi ta bige ni,a tsakiyar titin unguwar Ahmadu Bello way,wanda tamkar ya banke akuya shi ne kishingiɗe a cikin kujera ko motsi ma ya kasa yi don mulki zan ce ko ƘASAITA. Na yi masa kallo wanda ya kai na minti uku, a inda na ƙara karantar fuskarshi,a cikin kallon da nake yi masa ne naga da ƙyar yasa hannu ya cire farin gilashin da ke manne a saman idanuwanshi, sannan na ga ya lumshe idanuwansa duka biyu, sannan ya buɗe. Da hannunsa mai gilashin nan ya ɗan yi masu nuni kaɗan, sai naji sun ce, "Yarima na amsa gaisuwar ki." Nayi murmushi da ke bayyanar mini da asirtaccen ƙyauna, wanda na yi shi ne don haushi da takaici da nuna masa cewa nima fa na isa,ƙyau yake taƙama da shi, nima aƙwai wanda ya fi nasa a jikina. Na rausayar da gashin kaina, ya shafi fuskarshi, sannan na sunkuya na ɗauke kayan lasawata,ice cream da lemuna har ruwana, na mayar a gaban na kusa da shi, sannan na miƙe na yi gaba abina,a zuciyata na ce, sai dai wata ta kawo maka ba dai ni ba, nima nan da ka ke ganina sarauniyar kaina ce, iyayena kawai nake wa shagwaɓa sai kuwa yayyena. Tsakanina da Dad da aƙwai nisa, sannan ga shi cikin jama'a yake, waɗanda suke manyan mutane ne. Wannan ne ya hanani in isa wajen Dad in nuna masa azzalumin mutumin da ya kaɗe ni, sannan ga tsoro ina ji, kada in tafi wajen tsurkun nunawa Daddy shi, wani ya ce yana sona a cikin mutanen da yake tare da su,ni kuwa sai angona Anwar. Bayan ɗakin taro ya nutsu ne aka bayar da umarnin cewa amarya da ango su shigo ɗakin taron, cikin mintina goma (Martina Desginer) jikina da ƙwalliyar dark blue les mai dige-ɗigen fari, musamman domin ta gyarawa ƴan matan amarya jiki aka ɗauko mana ita. Gwaggwarona kalar fari, haka takalmana, da jaka ƴar sagale a hannuna,ƴar siririyar sarƙa ce mai kalar fari a wuyana, wacce zamu iya kiranta da suna Diamond, gashin kaina kuwa nannaɗe shi na yi waje ɗaya, tamkar naɗin da Indiyawa ke yi wa gashinsu. Wetlips ne kawai a laɓɓana, sai dai zagayan saman laɓɓan nasa masu jagira mai kalar fara. Kowa ya hango ni, sai ya yi zaton ni ce amaryar, sai dai don ita amarya ta sha bamban a duk inda take, gefen amarya nake, shi ma abokin ango a gefen angon yake, kenan mun jera layi a kan mutane huɗu-huɗu, maza biyu mata biyu. Dole ɗakin taron ya kaure da surutai don ma dai taron manya ne har ihu ma sai anyi, saboda ni kaina nasan mun yi ƙyan da za a iya ɗaukarmu a matsayin (Magazine) Ɗinkunan zamani ne a jikinmu in ka ganmu tamkar an shirya mu ne domin a sa a Magazine ɗin (Ovation Magazine). Fitowarmu ke da wuya, sautin kiɗa ya canja a hankali ya soma tashi, wanda har muka isa wajen zamanmu,saman ɗakin taron daga gefe ɗaya, saboda gefe ɗaya an bar shi ne saboda ƴan wasa. Abin ka ga garin da ya tara yarurruka kala-kala, wannan yasa kusan yare ashirin suka yi raye-rayensu da waƙoƙin su, sannan aka koma wasan ƙwaiƙwayo, inda ƴan Legas suka yi nasu a kan zamantakewar auratayya da tarbiyyar yara. Ƴan wasa kuwa shahararru ne, irin su Pate Odochi,Sam Loco,Ramsy Noah,Geneve Nneji,Liz Benson,Mama G. Gaskiya wasan ya yi ƙyau, dole ne ma fili ya ɗauki tafi,abin ka ga mutanen da ba su da Addini duk da ita ma Jos da sauƙin Addinin, amma yanda suka shirya shi ne kamar da gaske, shi ya burge ni. A nan take na ji ina son yin auren, saboda rayuwar da suka nuna. Kamar an ce in ɗaga kaina, sai na hango wannan sakaran mutumin wanda ya kaɗe ni ya wani ƙwanta a kujera sai fizgar kai yake yi, kowa ya kewa, Oho. A zuciyata na ce yau ka faɗa, da Dad zan haɗa ka,kasha dukan tsiya. Bayan fitarsu ne sai fili ya ɗan ruɗe kaɗan da hayaniya,in ɗan kalla sosai sai na ga ashe shahararrun ƴan wasan Hausa ne na jahar Kano waɗanda muke gani a cikin talabijin yau ga su a fili, kamar su Iyaye Alhaji Ibrahim Mandawari, Alhaji Hamisu Iyantama,Kabiru Na Ƙwango, Shehu Hassan Kano,Usaini Sule Ƙoƙi,Kabir Mai Kaba. Tare suke da ƴan fim ɗin su maza da mata. Sai iyayen fim din su mata na biye da su kamar su Hajara Usman salihar mace,Saratu Giɗaɗo macen da kowa ke so, Jamila Haruna kin fi kama da matar Gwamna da dai sauransu. In na tsaya lissafawa ba zamu gama ba,sun yi wasan ƙwaiƙwayonsu a kan samu da rashi sannan da mutuwa da kuma ƙaunar iyaye da ƴaƴansu, wasan kuma ya sanyayar da zukatan mutane, wanda a take kowa ka kalla ya yi la'asar, tamkar yana jiran Mala'ikun mutuwa su iso kanshi. Bayan nan kuma ɗaya bayan ɗaya aka dinga tashi ana magana da ƙoƙon fitar da sautin magana da ƙarfi (Microphone), iyaye,abokan arziƙi, shuwagabanni,a inda har wani shugaba a nan Jos ya baiwa ƴan wasan Kano ƙyauta ta motoci guda biyu, saboda yawon wasa da suke yi. Wannan ne ya buɗe fili aka dinga yi musu ƙyaututtuka. A ƙarshe abokin ango ya fara faɗin halayyar abokinsa, ya kuranta shi, inda ni ma na tashi na yi, duk fa da harshen Turanci,dama su ni an iya turancin hanci (Slang) shi nayi a wajen. Ni kuma na san duk wanda ya ganni a tsaye ya ji turancina kuma ba zai taɓa ɗaukar ni bahausa ba ce ba, sai dai ƴar ƙasar tsallake. Ango ya yi godiya, amarya ma haka, daga nan sai aka dinga rarraba abinci wanda duk ka ke so, sai ma an tambaye ka wanda nan kuma masu raba abincin Hotel ɗin ne ke aikinsu (Waiters). Ƙarfe biyu da rabi na dare aka tashi ba wai watsewa ba, saboda in na tashi ne ake samun damar gaisawa da jama'a na nesa da na kusa. A lokacin ɗakin taron da wajen ya baje da jama'a ana ta gaisawa tare da yin hira da su a gidan talabijin. Da ƙyar na samu na je na gayawa Dad cewa na ga mutumin da ya kaɗe ni, kafin in waiga in nuna masa shi ya ɓace mini,wannan yasa na yi saurin jan ɗaya daga cikin ƙawayenmu na fita wajen Hotel ɗin, domin in samu damar ɗaukar lambar motarshi. Cikin ɗan sauri-sauri muke tafiya, a inda na ci karo da wani, wanda har sai da muka haɗu da juna sosai, turaren da ke jikinsa kuwa, irin mai sanyaya zuciya ne, ina jin ƙarar faɗuwar jakata da wani abu a ƙasanmu, duk wannan bai fi cikin sakan uku ba, maimakon in kalli ko waye sai na duƙa don ɗauko masa wayar hannunsa, wacce ta faɗi tare da jakata. Ɗagowa ta kuwa ta yi daidai da duƙawarsa ya ɗauko mini jakata yana ɗagowa ina shirin ba shi haƙuri, saboda a zatona ya yi tsaran iyayenmu, sai kawai haushi ya kama ni a take kamar yanda na lura al'ajabi ya kama shi mutumin da nake faman nema in nunawa Dad ɗina,shi ne muka yi karo da juna. Na rasa me zan ce masa, na yi tsaye da wayarsa a hannuna, shi ma da jakata, ganin shi ba shi da niyyar yi mini magana, saboda tsananin girman kai, yasa nima na ƙi tanka masa, sai dai na fizge jakata da ke hannunsa ta ƙarfin tsiya, sannan na jefe shi da wayar da ke hannuna, ta faɗi ƙasa ta tarwatse. Wannan ta yi daidai da tahowar wasu gungun shuwagabanni, za su wuce gamu mun tsare hanya,ƙawata Uwani ita ta janye ni cikin sauri sannan na ga ta sunkuya ƙasa tana tsince masa tarwatsatstsiyar wayarsa, wanda ta bi shi da sauri don ta bashi, saboda gungun mutanen sun yi gaba da shi. Wai sai da na ɗauki mintuna biyar a tsaye sannan na yi saurin tunowa da lambarshi fa zan ɗauka ta mota. Na fita cikin zafin nama ina ta waige-waige, amma ko kalar mai rigar sa ban hango ba. Na gaji da waigena har na juya zan koma ciki, sai na ji Uwani na ƙwala mini kira na yi saurin waigawa domin in gano inda take, saboda na ma san na gane mutumin nan, amma sai na ganta ita kaɗai, na yi saurin taryar ta, ina tambayarta. "Ina yake, ina yake?" Wai tambaya take wa? Na ce mata wanda ki ka kaiwa waya. Sannan ta nuna mini motar da yake ciki wacce ta kusan fita daga hotel ɗin, ba kuma za a iya hangen lambar jikin motar ba, balle a ɗauka. Haushi ya kama ni na dinga yi mata faɗan masifa a taron nan,a haka har aka tashi wannan taro, ina cikin ɓacin ran rashin ɗaukar lambar motar nan. Bayan mun je gida na sanar da Dad abin da ya faru,nan ya ce inyi ƙoƙarin ɗaukar masa lambar in na yi haka, to shi kenan in sa ido, na amsa masa tare da ƙudirin sai na ɗauke ta in Allah ya yarda, amma har muka gama biki ban ƙara ganin ko mai kama da shi ba. Wannan kuwa ba ƙaramin takura ni ya yi ba. **** **** **** Bayan ƙwanaki arba'in da huɗu da gama bikin Fatima da mijinta Ibrahim, wacce take da mahaifinta da Dad abokan wasa suke. Ni kuwa bayan bikin ban ƙara zuwa inda take ba, sai yau ranar Asabar saboda in samu Ibrahim a gida shi yasa na bari sai Asabar. Cikin isa nake jan motata zuwa unguwar Ring Road,domin kai wa Fatima ziyara, daidai wajen bada hannu ne wajen unguwar Ahmad Bello way,na tsaya bai fi mintuna biyu da tsayawa ta ba ina jiran a ba ƴan layinmu hannu, sai kawai na ga ƙato ya buɗe murfin motata a gaba ya shigo, ina ƙoƙarin yi masa magana na ji buɗewar baya,waigawar da zan yi sai naga ƙarti uku zaune a cikinta, sun nuna mini bindiga, wanda na gaba ya ce mini. "Kiyi shiru,ki ja mota kawai muke so!" Ban tsaya gardama da su ba na mayar da hankalina ga tuƙina inda aka ba mu hannu. "Titin hannun ki na dama za ki bi." Haka ɗayan ya ce mini. Ni dai na san ba zan ɓata ba a garin nan sai dai in kashe ni za su yi, saboda haka ban razana ba. Duk inda suka ce in nufa,nan nake bi da motata, har zuwa wani mahaukacin gida, wanda yake ɗauke da yawan fitilu, duk da safe ne ba kunna su aka yi ba, amma ganin su a tsaye shi ya nuna mini yawansu. Titin get ɗin gidan muka miƙe, tamkar za mu wani garin, bayan mun shiga get ɗin gidan waɗanda yake ɗauke da sojoji sun kai goma sha biyar,ni kuwa ganin sojojin ma ya ƙara mini ƙwarin giwar in sakin jikina ma, sai da muka dinga wuce gidaje zan ce ko gine-gine, sun kai baƙwai sannan suka ce in tsaya a ƙofar wani gida mai bene,wanda saman shi yake zagaye da barandar sama. Da gani zagaye yake kamar ƙwano kenan circle ta can sama na hango ƙyallin wani mutum ta labule ya ɗan ɗago masu hannu, daga nan sai suka ce in yi gaba na ja mota muka nausa cikin wani daji, duk fa a cikin harabar wannan gine-gine. Bayan tafiya ta kai ta kilomita uku, sannan na ga mun iso wani gida mai dogon gini kamar ginin Choci. Nan aka umarce ni da in tsaya in fito daga motar, ba wanda ya taɓa ni cikin su, suka nuna mini hanya har cikin gidan nan. Mun wuce wurare da dama, sannan na dinga ganin ragar ƙarfe da mutane a ciki, wannan ya nuna mini gidan yari ne aka kawo ni,abin da ban gane ba,shin ziyara aka kawo ni inyi ko kuwa ganin wani,ni dai na san ban yi laifin komai ba...... *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 4 Abin tausayi na gidan (Yarin) gidan maza, saboda duk sun bi sun rame, sun ƙare,ga su nan da ƙyar suke magana, masu ɗan ƙarfi ne ke miƙewa su zo su kama ƙarfen suna yi mana magana wadda bana ganewa. Matattakalar bene muka haye ni da su, wanda nan naga mata birjik a ɗaure a zuciyata na ce laifin me suka yi waɗannan bayin Allah, har da masu tsohon ciki da masu ƴaƴa, ga su nan a kukkulle,ni dai ƴar kallo ce har aka kai wani ɗaki na ga an buɗe shi wai in shiga,ban musu gardama ba muka shiga tare da su. Gado ne ƙarami irin na ƴan makaranta amma wanda bashi da sama, sai ɗaya a kusa da shi da wata ƙwance tana bacci. Ba su yi mini magana ba ɗaya daga ciki ya buɗe wata ƙofa,nan na ga ashe banɗaki ne, ɗaya ya buɗe famfo a kusa da ni, na ga ruwa ya zo, duk dai ban yi magana ba. Sai da na ga duk sun fita suna shirin kulle ni a ciki, sannan na yi masu magana da harshen Turanci. "Baku gaya mini komai ba har za ku tafi." Ɗaya daga cikinsu ne ya ce, "ki zauna za a neme ki." Ya juya ya tafi ban ce masu komai ba,nima na ɗan kalli gidan nan na zauna. Tsayin awa ɗaya, sai na ga matar nan ta tashi, tana ganina ta taso a hankali ta iso wajena ta zauna. "Yaushe aka kawo ki?" Naji ta faɗa da Hausa. Na kalleta sosai. "Ko baƙya jin Hausa?" "Ina ji,ɗazun aka kawo ni." "Me ki kayi?" "Ba komai" "To Allah ya taimake mu" "Musulma ce ke?" "Eh." Daga nan muka dinga hira da ita. Ina nan har ƙarfe tara na dare, sannan naga waɗannan mutanen sun buɗe in da muke sun shigo, ɗaya daga ciki ne ya ce in taso, na yi wa wacce muke tare sallama mai suna Mabaruka. Tana kuka na bar ta tausayinta ya kama ni. A motata muka kuma shiga na ja har gaban gidan da muka tsaya da rana. Muna tsayawa na ɗaga kaina sama sai na hango mutum zaune a barandar saman bene ya miƙe tsaye sosai ya juyo tare da dafa majinginin barandar, cewa suka yi in fito, na fito na kalleshi sosai, cikin sakan uku na gane mutumin da ya kaɗe ni watanni huɗu da suka wuce. Me zan ce masa ni kuma yanzu bai yi magana ba, nima ban yi masa ba. Na girgiza kaina na juya na koma motata har na tashe ta ɗaya daga cikin ƙartin nan masu sanye da fararan T.shirt, ya sunkuyo ta gilashin da nake tuƙi ya ce. "An baki last warning saboda haka yana gargaɗinki da kada ki ƙara shiga layin gonar shi, balle har ganganci ya kai ki kice za ki ratsa tsakiyar ta, ina fatan kin fahimta?" Na ɗaga masa kai kawai, na ja motata har na yi nisa na tsaya na leƙo da kaina na ɗaga masa babban ɗan yatsana ma'anata a nan za mu haɗu wata rana. A mota ne na yi tunanin ba zan gayawa Dad kome ya faru da ni ba, amma ni da kaina zan ɗauki mataki wanda ko a hanya ya hango ni sai ya ce a sake wata. Har na isa gida ina tunanin hanyoyin da zan bi, amma na rasa su, saboda haka na ajiye lamarin, na dangana shi da ba aikin gaggawa ba ne. Sai da Mamee ta ɗan yi mini faɗa a kan nayi dare, goma saura kaɗan, na san banida gaskiya na dinga ba ta haƙuri,gudun kada ta gayawa Dad shi kuwa ba wasa a lamarin sa, idan har ka taɓo shi. Kun san iyaye dai. Bayan na yi wanka na shirya jikina ne na gabatar da sallolin da ake bina, daga nan ban iya yin bacci ba, saboda tunanin hanyar ramuwar gayyar da nake son haɗawa Yarima. Wannan dalili ne yasa na tunano da litattafan novel na Turanci na shahararren marubucin nan (James H. Chase). Na san a cikin litattafan sa akwai idea zan iya samun wata hikima a ciki. Daɗi, murmushi, dariya, suka saukar mini a lokaci ɗaya, wannan ya sa na kashe fitilar gefen gadona na koma na ƙwanta, tare da tabbacin yanzu bacci zai zo mini. Haka aka yi kuwa,sallar Asubahi ma Mamee ce ta tashe ni. Da ƙyar na shawo kan Mamee ta amince na fita, shima don na ba ta tabbacin iyakata Bookshop na nufa domin neman wasu littattafai, cikin saurin da bai fi na mintuna talatin ba na dawo,lode da litattafan James, sun kai goma sha biyar. Tun da na haye sama ɗakina ko motsi na kirki ma bana son yi, abincin rana kuwa sai da la'asar na samu na ci shi. Sai da na ɗauki ƙwanaki goma ina nazarin litattafan nan da birona da zungureran littafina a gefe,in ta kama in rubuta in kuwa tawa muguntar ta faɗo in rubuta. Wani lokaci a falon Dad,nake shigewa saboda kada a dameni, sai na ji dawowarshi, sannan in koma ɗakina, na gama karantawa saura haɗa ayyuka. To yaya kenan?. Ƙarfe taƙwas saura na safiyar Litinin wacce ta yi daidai da ƙwanana biyu da gamawa, na je na samu Katung Maigadi nan na zauna na gaya masa buƙatata, a take ya ce ai wannan duk abu mai sauƙi ne, tunda da akwai shi, sannan akwai abokanansa,in zan tura da kuɗi kawai su zasu kawo mini aikin da suka shirya. Na yi murna ƙwarai da gaske, sannan na ce ya bani ƙwana ɗaya. Saboda na jima ban fita ba, shi ne na tambayi Mamee zan je gidan Aunty,ta amince mini. Ina isa gidan na ce mata kuɗi nake so, na dinga narke mata kamar zan yi kuka, har sai da ta bani dubu goma, na bugawa Yaya Habib waya na ce masa kuɗi nake so ya ce zai turo ta account ɗina wato banki. Sai da na haɗo dubu talatin, sannan na ɗauki ashirin a nawa (account) ɗin na haɗa, na zo wajen Dad kuma na dinga fadanci cewa litattafai zan siyo, ya bani, saboda ganin da yake ina yawan karanta su, ya bani talatin. To saura Mamee, na girka mata kuka tun da ita ba wasa. Ganin duk ranar kuka kawai nake, shi ne ta tausaya mini ta dinga lallashina, har tana tambayar me nake so, shi ne na gaya mata cewa account ɗina ba komai a ciki, shi ne nake son kuɗi in siyi litattafai, shi ne Dad ya bani kaɗan ,nan ta ce nawa ne? Na ce ashirin, ta ƙirgo ta ba ni. Bayan ƙwanaki tara, ya zo ya ce mini komai ya haɗu, amma aikin farko kenan,yau wajen ƙarfe biyar na yamma in bi ta hanyar Bank Road saboda ruwan da ake yi na san yanzu zai kai har nan da tsayin lokaci a yanda (weather forecast) ta nuna. Cikin ruwan sama mai tsanani na bi hanyar Bank Road,hanyar da bata cika mutane sosai ba, sannan tana da haɗarin bi a lokacin ruwa, ga shi yau garin na Jos shugaban ƙasa ne ya kawo mana ziyara, saboda ganewa idanunshi tabbacin zaman lafiyar da aka samu yanzu a Jos, madadin rikicin da aka samu tsawon lokaci ana yi a baya. A cikin shekara ta ɗari biyu da uku (2003). Wannan yasa sai motoci ɗaiɗai ke yawo a garin,na laɓe da motata a gindin wata babbar mota na ga motocin Yarima sun wuce cikin gudu sai da suka yi nisa, sannan na ji sun bugo mini waya da in tafi,nima in bi hanyar, cikin natsuwa na dinga tuƙina, balle kuma yanda ake tafka ruwan sama. Ban fi tsayin tafiyar kilomita ɗaya ba, sai ga shi na same su motocin su sun tsaya, ga ruwa ana yi balle su samu damar ɗauko wasu,ga ba motoci masu giftawa, saboda ruwa da ake yi kamar da bakin ƙwarya. Tun daga ɗan nesa na ga mutum a tsaye da lema yana ɗaga mini hannu, daidai motarshi Yariman, na tsaya na zuge gilashina,nan wannan yake mini bayanin zan bayar da motata za a mayar da Yarima gida. "A'a ka ce masa sai dai ya fito in rage masa hanya,me ma ya samu motocin naku?" "Kawai gani muka yi motarmu ta tsaya,mun ɗan tsaya gyarawa sai ta bayanmu ta kama hayaƙi, ba mu lura da ta Yarima tayoyin sun sace ba sai da muka ta da ita da sunan shi a isa dashi gida." "Ka gaya masa in ya amince, amma gaskiya bana bayar da aron motata ni in tsaya nan har sai an kaishi an dawo ba,ka tuna ni macece." "To Hajiya." Mayar da gilashina na yi na zuge, ina kallonsu sun ɗan jima, sannan na ga sun zagayo da sauri dukkansu sun kara masa lema tare da baza babbar riga,wai gudun kada ruwa ya jiƙa shi,a haka suka kawo shi har motata, inda aka buɗe masa baya ya shiga. Ya koma ya ƙwanta yanda yake yi, kafin wani ya zagayo ya buɗe gaba,ni har na ja motata, amma don ƘASAITA ko motsi bai yi ba, balle magana. A Hill Station Hotel na yi fakin da motata a wajen harabar ajiye motoci, ina fita suna isowa da baƙaƙen kaya dogaye suka nuna masa bindigogi a cikin motar, mutane ne sun kai goma. "Fito!" Haka ɗaya daga cikinsu ya ce, cikin taƙama ya fito a daidai lokacin da ni kuma na cire baƙin gilashin da ke manne a fuskata. Tabbas ko ban faɗa ba na san mamaki ya dirar masa a lokaci ɗaya don dai namiji ne mai ji da mulki, shi yasa bai nuna razanarsa a fili ba. Duk fuskokinsu manne suke da safar fuska baƙa, wanda gilashi baƙi ne ke manne da fuskarsu. "Alhaji doka ta ɗaya" wani daga cikinsu ya faɗa da harshen Turanci. "Na farko za ka bi Madam zuwa sama, ba na buƙatar ka nunawa wani cewa kana tare da mu,in kuwa ka ƙi." Ya ɗago hoto duk dogarawansa ne tsare da bindigogi. "Zamu ɗauki rayukansu a yanzu, sannan mu ɗauki naka." Sai a yanzu ya samu ya yatsina fuska ya yi magana cikin isa a hankali. "Okey,no problem." Na yi gaba yana biye da ni, na waiga na ce masa. "Ka je ka biya kuɗin ɗaki ni nayi gaba." Bai ko kalleni ba, ya yi wajen biyan kuɗi ni kuwa na haye sama. Tsayin minti sha biyar sai ga shi ya miƙo mini makullin da aka rubuta No.120, ɗaki na ɗari da ashirin, ina tafe yana biye da ni har ɗakin. Na buɗe na shiga ya biyo bayana, sannan na juyo na fito na mayar da ƙofar na kulle. Na sauko na bawa Katung makullin. "Ku ƙarasa sauran aikinku, amma kada ku yi masa komai, kuyi komai cikin mutunci,kun san babba ne ku ƙarasa haɗa komai, ina fatan kun gane?" Suka amsa eh. Na miƙa masa dubu talatin a biya a ɗan ci abinci. Bayan ƙwana uku na dira a hotel ɗin da ƙarfe goma na dare, wanda su Mamee ma basu san na fito ba, na sa makulli na buɗe shi yana kishingiɗe a gado yana karatun mujalla ta Turanci (Tell) da ido ɗaya ya ɗago ya kalleni. "Za ka iya tasowa mu tafi yanzu." Bai ce komai ba ya miƙe ya zura babbar rigarshi da ke gefe ɗaya ya biyo bayana. A motata har wannan gidan da yasa aka kai ni, amma inda yake da alama dai gidansa ne,kafin in shiga sai da na rufe fuskata da wata baƙar fuska mai tafe da kitso, sannan na ɗaga wata ƙatuwar ambulan na ce masa. "Ko baƙar magana ka gaya mini sai na kai wa Sarki wannan ambulan ɗin da ba zaka san ko meye a ciki ba, sai nan da ɗan wani lokaci." Ya buɗe murfin motar ya fita ba tare da ya ce mini ƙala ba,ya juya ya tafi abin sa, nima na ja motata sai gida. Duk da na yi masa haka, amma ban ga alamar razana ba a jikinsa, wannan ta sani kaina na ce lallai wannan ya cancanci ya hau gadon mulki, saboda ba a san matsoracin Sarki, ga shi kuma da iya ƘASAITA, na yi dariya ni kaɗai, nayi murmushi kuma sannan na haye gadona na ƙwanta. Bayan ƙwana biyu ne na taka da kaina har get ɗin gidan sarautar nan, wajen sojojin nan muka gaisa amma a cikin ɓatacciyar fuskar nan, sannan na kawo ƙatuwar ambulan (envelope), na miƙa masu na ce. "Saƙon Yarima ne daga ƙasar Sudan." Suka ɗan dudduba ni da motata, sannan suka ce sai na zazzage kayan ciki, na ce masu ba zai yiwu ba, amma su buga masa waya su sanar da shi cewa yana da baƙuwa ta kawo masa saƙo amma kun ce sai na buɗe.... *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 5 Nan take suka buga masa, sai ya ce a karɓi saƙon kawai a kawo masa, ya san da shi,ni kuwa na juya na yi tafiyata gidan Auntyna. Ɓangaren wajen Yarima kuwa,kaset ne aka kai masa da hoto ƙwaya ɗaya. Ya sanya kaset ɗin,lallai ya san na isa, hoton ƙwance yake ba riga a jikinsa da bargo lulluɓe daga ƙafafunsa zuwa ƙugunshi, sannan ƙirjinsa yarinya ce ƙwance a daidai lokacin da yake rungume da ita, ya kai bakin shi ya sumbaci goshinta nan aka ɗauki hoton. Kaset kuwa daga inda ya ɗauki yarinyar ne har zuwa hotel ɗin da shiga ɗakin hotel ɗin duk dai yarinyar ɗaya ce, da takarda wacce na gaya masa, idan har ya ƙara sawa aka kama ni ko ya yi ƙoƙarin sawa a yi mini wani abu zan kai wa Sarki kaset ɗin da hotunan da kaina, na yi sallama. Tabbas ni kaina na san na gama da Yarima, saboda yanzu ba shi da wata hanyar yi mini wulaƙanci,sai dai ni inyi yanda nake so a garin nan, da ya nemi takura mini da na tona masa asiri da ƙundin kaset ɗin da na ɗauka a matsayin ɓata masa suna. In kuwa haka ta faru, sarauta kuwa shi da ita har abada. **** **** Yamma ce yanzu wacce ta nuna ƙarfe biyar har da wasu mintuna goma, yanayin sanyin daminar garin sun haɗa sun mayar da garin tamkar dare ya yi, sanyi kuwa mai shiga cikin tsokar jiki. Motocin da na gani a harabar gidanmu a lokacin da na shigo da motata, shi yasa na ɗaga hannuna na kalli agogon da ke maƙale a tsintsiyar hannuna, tabbas waɗannan koma su waye baƙin Daddy ne, da gani ka san manya ne na gaskiya, saboda ganin manya-manyan (Jeep) da na yi har wajen biyar,ban da ƙananan (Pegeout 406) ga zungureriyar motar nan irin ta Yarima Limousine Cadillae. Don dai kalarsu ce ba ɗaya ba, kuma wannan mai murfin ƙofa huɗu ce, kenan babbar ta Yarima ce,na samu na raɓa tawa motar daga gefe ɗaya, sannan da Katung ya iso nake tambayarsa su waye? Nan ya nuna mini bai san ko su waye ba, amma manyan mutane ne (Big Men). Mamee na falo ita ma da wasu mata har biyar, ina isowa na sunkuya har ƙasa na gaishe su, sannan na isa ga Mamee, na sumbaci kumatunta alamar na dawo kenan har zan wuce sai na ji Mamee na cewa. "Ai itace wannan." Wata mata wacce take zaune ita kaɗai a doguwar kujera wacce da ƙyar take motsi, ita ta yi ƴar dariya ta ce mini in zo. Ina zuwa na zauna ƙasa kusa da ita, sai na ga ta shafi gashin kaina wanda yake a buɗe ta ce. "She is beautiful, she deserves to be the Prince's wife,amma daga yau ki dinga kula da rufe gashin kan ki, saboda yanzun kin zama babba." Ta faɗa da harshen Hausa, sannan ta ce in tafi. Ina tashi na kalli Mamee kallo mai alamar tambaya, amma sai na ga ta kawar da kanta, na taɓe bakina na haye sama, zuwa ɗakina. Bayan kamar mintuna goma sha biyar, sai ga Mamee ta shigo ɗakin da nake ta miƙo mini wasu riga da zani na ɗanyan ƙwatin less (Cotton less) mai launin kore wanda ya chiza wato ruwan kayan sojoji (Amry colour) da takalma ruwansa, amma mai haske (light green) da file ɗanƙwalin saƙi, da abin sagalawa a wuya, duk ruwan takalman. Da wani irin English Gold wai duk in saka a jikina. Tambayar Mamee nake, amma ta ƙi ba ni amsa, sai dai faman shirya ni take yi hatta shimi da siket ɗin duk kalar kayan ne,ni kaina na san nayi ƙyau, balle raba gashina biyu da Mamee ta yi ta sakko mini su a gaban ƙirjina, wanda ya sauko mini har kusan rabin cikina. Fuskata kuwa ta sha gyara,ni kaina ban san Mamee ta iya ƙwalliyar kece raini ba, sai yau, tun da ita Mamee ba ta ƙwalliya,iyakacinta ta murza hoda kawai da ɗan ƙwalli a idanuwanta. Ta umarce ni da in biyo ta,na bi bayanta a hankali wanda take ce mini taku ɗaiɗai zan dinga yi. Dama ni sarkin iya ƘASAITA, shi na dinga yi. Mun isa falo na ga matan da ke zaune duk sun ruɗe, na yi zaton iya nan kawai za mu tsaya, amma sai na ga an nufi sashen (Sitting room) ɗin Dad,ɗakin shaƙatawarshi da ni. Muna kai wa ƙofar ɗakin na ga Mamee ta ƙara fesa mini wani Desginer ɗin turare, sannan ta ce. "In kin shiga da kin kai tsakiyar falon ki durƙusa ki gaishe su, amma da harshen Turanci, ban da sakarci, ban da shagwaɓar da ki ka saba yi wa My dear,kina ji na?" Na ce, "To Mamee,wai su waye,me suka zo yi?" "Baki da amsa yanzun sai sun tafi." Na ɗan kaɗa kai na shiga. "Tafiyar nutsuwa." Haka na ji Mamee ta ce. Yawan mutanen falon Dad su suka sa na fara rikicewa wajen tafiya, amma tunanin kada in kunyata iyayena,shi yasa na yi saurin sanyawa jikina nutsuwa a take, hankalina kam ya tashi, sai dai ban yarda na nuna ba, saboda ganin dattijon mutum da na yi a hakimce a saman kujerar kishingiɗewa, har da sa masa darduma mai laushin gaske a saman kujerar. Ban da mutane biyu da ke tsaye a kan shi, suna sama da ƙasa da wani ƙaton abu mai gashi, faɗin shi kamar ƙaton faifan bakacan masara, sai dai bazar gashin jikinsa da kalar ja da yalo da ke jikinsa da mariƙin da suka fito da shi, zai nuna maka mafici ne. Amma na fi ganin shi a cikin talabijin, shi ma sai in an nuno wani sarki. A zuciyata na ce dan kinibibi duk A.C ɗin da ke falon Dadyna, amma sai an yi masa fifita. Yanda Mamee ta ce inyi haka na yi,bacin duk dama hankalinsu ya dawo kaina tun da na shigo. Dad ɗina ne ya iso ya kama ni ya tashe ni tsaye, sannan ya fara magana. "Your Highness this is My daughter Yasmin." Ya tafi da ni har gaban wannan mutumin,ya tsugunnar da ni. "Ɗiyata ɗago da kanki." Na ɗago. "Very fine lady,na tabbatar ɗana zai yaba da ita." "Haka ne, haka ne, ai ba ja."waɗannan mutane na tsaye bayansa suka faɗa. Sannan ya kama hannuna muka miƙe tare da shi, shi wannan mutumin ya juyar da ni na kalli ragowar mutanen da ke baje a ƙasa, sai dai wasu uku da ke zaune a kujera daban-daban. "Wannan ita ce matar da na zaɓawa ɗana Faisal, ina fatan ta yi?" "Ta yi, tayi." "Waziri ta yi?" Ta yi,ta yi." Sai na ji wazirin ya ƙwala kira, amma ban ji yanda ya kira sunan ba, sai na ga wasu mata su huɗu sun shigo ɗauke da farantai lulluɓe da kaya a ciki, da wani farin gyale sun ajiye gabana. "Ƙyauta daga waziri." Inji wani ya faɗa. Aka dinga shigowa da kaya kala-kala,ni dai ina daga tsaye, daga a ce ƙyauta daga wa ne, sai daga wane, bayan kamar minti ashirin aka sallame ni na tafi. Raina a ɓace na shiga falon Mamee baƙin da na gani da waɗannan mata, shi yasa na ɗan saki fuskata, sannan na sunkuya na yi masu sallama na haye sama. Komai cillar da shi nayi daga tsaye, takalma,tuntun saman kaina,sarƙar,awarwaron, na faɗa a gado. "Me ye wannan?" Na tambayi kaina. "Me su Dad ke nufi da ni,ƙyautar da ni suka yi ko kuwa siyarwa? Yanzun manufarsu in rabu da Anwar Proposed ɗina? Mutumin da nake ƙauna. Mamee fa ta san yanda nake son shi, shine zata je ta yadda a haɗa ni da wanda ban taɓa gani ba, hawaye suka gangaro mini,shi kenan rayuwata ta raunana, tun da za'a aura mini wanda ba na so, yanzun ba za'a barni in zaɓa ba kamar yanda Aunty Salwa ta zaɓa?. Kenan an nuna mini a gidan nan an fi son Aunty Salwa da ni, yanzu duk ƙaunar da na ga ana nuna mini,ashe duk ƙarya ne, ashe iyaye ma na yaudarar ƴaƴansu,anya kuwa ma su suka haife ni? Ban yarda ba,ƙila dai ruƙona suke yi, shi yasa za su haɗa ni da ɗan gidan sarauta ko sarautar wane gari ce ma? Oho. Ko dai cikin dangin Mamee ne waɗanda ba su Musulunta ba, na ga suma ƙyansu ya yi yawa irin nata. Tashin motocin da na ji, shi yasa na rarrafa daga gadona na ɗaga labule ina leƙensu. Suna wucewa na sauko ina dire-dire na kuka, na shige banɗaki,dama na sani da ban tafi da wayata ba, duk ita ta janyo mini, da bata nan ai da ba za'a kira ni in zo ba. A banɗaki nake wannan tunanin da kuka mai fitar da sauti, to an fa tuno da Allah duk da dama muna kiyayewa mu a gidan nan. Nan take na yi alwala na fito,ai sai sallah, kafin a kira sallar magriba na yi nafila ta kai goma, ina ji Mamee ta leƙo ɗakina ta koma,ganin ina sallah. Ƙarfe taƙwas saura minti huɗu,Mamee ta shigo ta ce in je inji Dad. Na ɗago kaina, na kalle ta kawai, na mayar. "Ba ki ji ni bane?" "Na ji Mamee yanzun zan je." Tana fita,nima na bi bayanta. Bayan kamar minti biyar. Yana kishingiɗe a inda ya saba hutawa, duk bayan sallar isha'i, Mamee na daga ƙafarshi zaune tana yi masa matsar yatsun ƙafa. "Yauwa,autar Daddy zo nan." Na isa na zauna ƙasa ɗan nesa da shi. Ya ɗaure fuska, irin alamar in babba zai yi maka maganar da yake ganin so yake yaro ya ɗauke ta da muhimmanci na gaskiya, sannan ya kira sunana. "Yasmin." Sai na ga Mamee ta tashi ta fita, sannan ya ci gaba. "Yasmin,kin san kowanne uba yana son ya ga ƴaƴanshi sun fi na kowa ɗaukaka,ƙyau, asali, tarbiyya, miji nagari, idan mata ne,in maza ne mata nagari. To balle ku ƴaƴana da ku ke a zuciyata tun ranar da na haife ku har izuwa yau. Ku kanku kun san ba wanda nake so a duniya in har suka wuce iyayena sai kuwa ku da mahaifiyarku, kamar yanda nake ƙaunar Manzon Allah (S.A.W) haka na koya muku sonshi da ƙaunarsa,a matsayinku na ƴaƴana, na horar da ku tarbiyyar bautawa Allah da bin sunnar Manzon Allah (S.A.W). Kamar yanda ku ka san ba wanda zai ba ka ladan bautar Allah,sai shi Allah, haka ba ɗan da ya isa ya biya iyayenshi ladan tarbiyya da haihuwarshi da suka yi sai shi Allah, amma ana son a yi masu biyayya, ga duk abin da aka ga suna so da wanda suka umarta idan dai har an tabbatar bai saɓawa shari'ar Muslunci ba, da abin da Manzon Allah (S.A.W), ya zo mana da shi. Ko da kuwa sun zama suna masu tsanar abin da suka umarce su, da ƙiyayya mai tsanani to yin biyayya ga abin da suka faɗa ɗin nan, shi zai sa su sadu da rahamar Ubangiji, wata rana kuma su ƙaunaci abin,su yi wa iyayen godiya ta musamman da addu'a idan sun riga sun rasu. Yasmin,kin san dai duk cikin ku ukun nan,ba wacce nake ƙauna da so, sai ke. Ke ce ƴar da take ƙwance a cikin zuciyata a koda yaushe,ke ce ƴar da nake ganin nan gaba za ki ƙaunace ni, ki kula da rayuwata. Ki tuna na haife ki, nayi miki tarbiyya tagari, na baki ilmi, na wadata ki da abinci mai ƙyau, na kawo gida mai ƙyau na gina na saka ku,ya na same su, wacce wahala na yi? Oho,ni dai ku ji daɗi,yau rana ta zo ta ki nuna mini ɗaya daga cikin son da ki ke yi mini,ki nuna mini iri-irin biyayyar da zaki iya yi mini ko da bayan raina ne. Ki sani Addini ya yarjewa iyaye su zaɓawa ƴaƴansu mazaje na gari, idan har ƴan mata ne, ko samari, amma in sun zama aure ne na biyu, bazawara,ko bazawari, shari'ah ta ce a bashi dama ya zaɓa, ba wai don ba zai iya zaɓa da farko ba, a'a saboda Allah kaɗai ya san hikimar da yake nufi a nan. Yasmin yau na zauna a ƙasanki ina roƙonki wata alfarma ƙwaya ɗaya, amma girmanta ya fi ƙarfin Najeriya gaba ɗayanta, nauyinta kuwa ya fi ƙarfin teku, amma a gare ki in kin yi,abu ne mai sauƙi da rashin nauyi....... *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 6 Kada kiyi tunanin na yi miki haka ne don in cutawa rayuwarki,a'a na yi ne domin ina ganin na isa a gare ki, kuma na san ke yarinya ce mai biyayya, mai ƙaunata, na yi ne domin in sakaki jin daɗi da annashuwa a nan gaba, ranar da hankali ya huda miki jiki. Ke kin san dai yanzu nafi ƙarfin a kalleni ace zan je ƙwaɗayin wani abin duniya,ko zan kai ƴaƴana domin ƙwaɗayin wani samu na duniya ke kanki kin san nafi ƙarfin haka, sannan kin san na mallaki abin da zan iya ciyar da ku har ƙarshen rayuwarmu,ko na riga ku mutuwa, zan yi alfahari da cewa na bar muku abin da za ku tafiyar da rayuwarku har ku bini inda na tafi. Yasmin na san kina son Anwar,na san zakiyi farin ciki yau a ce shi zan aura miki a matsayin miji a gareki, amma ki sani yawancin abin da ka fi so,in har ba ka same shi ba, to ba alheri ba ne a gareka, ta yiwu alherin na ga wanda ba ka son nan. Yasmin ni mahaifinki nake son baki haƙuri a kan hana ki auran wanda ki ke so Anwar,Ina neman alfarma a gareki da ki yi mini biyayya zan haɗa ki aure da ɗan Sarki Jafar,ki yi haƙuri na san da takurawa. Yasmin ki taimaka ki fitar da ni kunya, sannan ki sani,ni ba irin iyayen da suke kai tallan ƴaƴansu ba ne ba, na fi ƙarfin haka nan. Ko kuwa kuna da yawa a gabana, balle ku biyu ne, da kansu suka zo har gidan nan neman wannan alfarmar, ban sani ba, sai yau, ban taɓa jin labari ba, sai dai ganin su nayi sun zo, ban san abin da ke tafe da su ba, sai da suka faɗa,ban san wanda ya ba su labarin ina da ɗiya ba, sai da suka faɗa cewa wajen taron bikin gidan Alhaji Kabir suka ganki. Shi ne Sarkin yasa aka dinga cigiyar ke ƴar gidan waye, ba su samu ba sai wannan satin, shi ne Sarkin ya zo da kansa wai gudun kada in ga da wasa ake yi. Ban san ko waye ba a cikin ƴaƴansa ba, sai dai ya ce zai turo shi cikin satin nan ya zo ku gaisa,ku daidaita kafin nan da lokacin bikin. Wannan da ki ke gani shine Sarkin nan garin na musulmi." Gabana ya faɗi shi kenan gidan cin mutane ma za'a kai ni, saboda waɗannan mutane na gidan yarin in ba cin su ake ba,ai ya isa a sake su su koma gidajensu, da gani ma sai an shanye jininsu, sannan a cinye tsokar a yanda na ga sun bushe a tsaye. Nan take na yi dana sanin kin gayawa Daddy abin da Yarima ya yi mini wata uku da suka wuce, da na sani wata ɗaya da wani abu da ya wuce da ban ɗauki fansa da kaina ba, da na faɗa an ɗaukar mini,na san da yanzu Dad ba zai yarda ya aurawa wani ɗan gidan ba ni ba. Shi yasa aka ce ta yaro ƙyau take, amma ba ta ƙarko, ga shi dai ni yanzu ba damar in faɗa Daddy ya ga kamar zan tozarta shi ne a idon duniya. "Yasmin na ji kin yi shiru." "Dad ai na san ba zaka zaɓa mini abin da ka san zai cutar da ni ba, saboda haka na amince da zaɓinka matsawar in ka amince da in naga abin cutarwa zan zo in sanar da kai, kuma zakayi saurin ɗaukar matakin gaggawa a gareni,ka ba ni gudummawar ka ta uba." "Na yi miki wannan alƙawari, sannan ni ma kin tunasar da ni zan faɗa masu da wuri tun kafin akai ki, na gode Allah ya yi miki albarka, ya baki ke ma ƴaƴan da za su yi biyayya a gareki,ki yi haƙuri na san na takura miki." Na ce, "Ba komai." Na miƙe na koma cikin gida. **** **** **** Shi kenan,Rayuwata ta raunana, tun daga ranar da Daddy ya gaya mini maganar aurena, har zuwa yau,ƙwanaki tara kenan, ba ni da wata walwala,in ma naɗan yi ta, to gabansu iyayena ne,gudun kada su yi wani tunani na daban. Amma ni a ɗakina,ko motsin kirki ma bana son yi saboda tsananin tunani da kuma rabuwa da masoyina Anwar,wanda muka rabu muna kuka ga junanmu. Ƙwanaki huɗu da suka wuce, amma har yanzu ɗin nan sai da ya bugo mini waya, kullum kuwa riƙe nake da kan wayata ina kallon hotanshi wanda shi ne (Screen Saver) ɗin wayata,hoton fuskar wayata. Na kasa fita ko ina yawon da na saba, balle in isa gidan Aunty in gaya mata halin da nake ciki,ko gidan Fatima amarya da na yi niyyar buga musu waya kuwa, sai in ga matsalar tafi ƙarfin faɗa a waya. Ƙarfe huɗu da rabi ina zaune a kan abin sallah ta, sai na ji ƙwanƙwasawar ƙofa, da ƙyar na ce a shigo. Yaya Habib, na yi tsalle na ruga na rungume shi, ina yi masa oyoyo, madadin mu koma ƙasa, sai na janyo shi cikin ɗakina na mayar da makulli na kulle ƙofata. "Yaya zauna tambayoyi zan yi maka,dama ina neman ka, saboda ina cikin tashin hankali, amma kada ka gayawa su Mamee, ba na nunawa a gabansu." "To ina jin ki." Nayi saurin tsugunnawa a gabanshi, shi kuwa yana saman gado zaune. "Yaya su Mamee kuwa su suka haifeni ko riƙona suke yi?" "Kina da hankali kuwa, da tambayar taki kenan ta mahaukata?" "Yaya don Allah ka da ka juya mini baya, kai dai ka amsa mini,zan gaya maka dalili." "Eh,su suka haife ki." "Kana da wayo sosai a lokacin da Mamee ta haife ni ina jaririya,kana ganin tana ba ni nono a gabanka?" "Wai ke yau ko kin yi gamo da aljanu ne?" "Wallahi Yaya da hankalina,kai dai ka amsa mini don Allah." "Zan iya tuna lokacin da take shayar da ke, har ma nake cewa ki sam mini nono in sha, ana yi mini dariya, har in je in kai ƙararsu ga Daddinmu." "Kuma ka ga suna so na?" Ya miƙe tsaye, "bana son sakarcin banza, zan yi miki duka yanzun nan." "Don Allah Yaya ka yi haƙuri." Sai nasa kuka. "Wai Yaya wai ɗan Sarki Jafar za'a aura mini,ban san ko waye ba a cikin ƴaƴan nasa, shi ma Dad wai ya amsa shi zan aura,ni kuma bana son shi, koma waye a cikin su, duk azzalumai ne fa." Na saka kuka na miƙe na cakume shi.ina ji ya saukar da ajiyar zuciya, ya ɗago kaina. "Haba Yasmin ƴar ƙanwata,ki yi tunanin irin son da Dad yake nuna miki yanzun haka in za ki buɗe zuciyar Dad shima baya so, Amma,zan je in tabbatar da me yake faruwa." "Kada ka gaya masa cewa na ce bana so." "Ba zan faɗa ba,kin ji ƙanwata." Ya goge mini hawayen fuskata,sannan ya juya ya fita. Bayan mintuna hamsin ne Yaya ya shigo, ya yin da ya nuna mini sai dai in ta addu'a kawai, saboda aurena ba fashi, yanda yake gaya mini ma har sun tsayar da ranar ɗaurin aure, da sarki Jafar,nan da wata biyu shi ma domin mu samu shaƙuwa da juna. Iya bayanin da Yaya ya yi mini kenan, ya fita shi ma jikinsa a sanyaye, ban taɓa shiga tashin hankali ba tun da nayi wayo sai a cikin ƙwanakin nan tara, ban taɓa tunanin za'a samu abin da zai girgiza min zuciya ba, amma yanzu ga shi na samu wanda Yake neman kawar mini da tunanina. Yau ƙwana goma sha bakwai da zuwan sarki Jafar kenan ya rage saura ƙwanaki arba'in da uku yinin bikina, sai yau ne aka ce ai ga Faysal wanda zai zama angona, duk da sanyin da ake yi, amma sai da na ji tamkar an watsa mini ruwan zafi. Mamee ta shigo ta umarce ni da in shirya in isa falon Daddy na yi baƙo, lallashi, nasihohi,Mamee ta dinga yi mini na kada in nuna masa halayyar sakarcina. Ni kuwa ba ta san gani nake ma ba ta ƙaunata. Dogon siket da riga ne,ƙirar ƙasar Japan nasa a jikina, dogayen hannu gare su har idon hannuwana,buɗaɗɗan wuya gare su tamkar irin ɗinkunan da ake ya yi yanzu a Najeriyarmu, sai dai tare yake da ɗan ziririn mayafinsu wanda za mu iya cewa iya wuya kawai ya tsaya. Mamee ta lulluɓa mini shi, ta sako leɓe ɗaya a gaban ƙirjina,ɗayan kuwa ya nufi bayana, gashin kaina kuwa yana can baya aka tattara shi, sai ƴan ƙwayoyi da ta ɗan gyara mini su ta sako su gefen fuskata, wanda ya bi ƙirjina ya ƙwanta. Na sha turare da gyaran fuska, abin ka da kalar ruwan ƙasa mai cizawa ne,siket ɗin sai ya yi mini ƙyau,rigar kuwa baƙa ce mai ƙyalƙali a gabanta, ɗan mayafin kuwa kalar siket ɗin ne,baƙaƙen takalma na saka a ƙafata, waɗanda suka yi daidai da rigar, na ɗauki baƙar wayar hannu na riƙe a hannuna. Kafin in yi sallama in shiga, sai da na leƙa ta kafar labule,jiri ne yasa na koma baya da ƙarfina, na sulale ƙasa na zauna, wanda na samu da ƙyar na isa ga bango na jingina,gumi ne ke ta tsatstsafowa daga jikina,a take na ji yunƙurin amai a lokacin da cikina ya juya. Cikin zafin nama na yi gudu zuwa ɗakin Dad ɗina,na shige banɗakinsa,amai kam tamkar in zazzago kayan dake cikina, na samu da ƙyar na ƙwaye shantalin matsatstsan siket ɗin jikina na gabatar da fitsari mai yawan gaske, daidai lokacin da aman ya ɗan tsagaita mini. A saman tudun da ake tsugunnin lalurar bahaya anan na zauna, tsayin mintuna goma, sannan na samu da ƙyar na ɗauraye jikina na miƙe, isa na yi ga madubin da ke manne a jikin (Wardrobe) ɗin Dad na kalli jikina yanda na faɗa a lokaci ƙanƙani, sannan na zauna saman wata ƴar kujera mai ɗan tebir a gefenta na kunna ƴar ƙaramar fankar da take a samanta, wacce zan iya cewa daidai fuskata kawai da wuyana take baiwa iska. Shi ma domin in samu gumin da ke fitowa a jikina ya tsaya, ɗan wanda ya fito kuma ya tsotse. A take kuma dabara ta faɗo mini na in dinga karanta "Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un!" Cikin ƙanƙanin lokaci na ji na samu nutsuwa, na isa ga gefen gadon Dad,na ɗauki farar butar da Mamee ke ajiyewa, domin gyarawa Dad fuska, na ƙara gyara tawa fuskar na fice, sai falon Daddy,inda baƙo ke jirana wanda ganin shi ya tayar mini da hankali,wai shi Yarima Faisal. Na yi sallama na shiga,a lokacin da wasu mutum biyu ke zaune a ƙasa a kowanne gefensa, biyu kuma na tsaye saman kan shi gefe-gefe, biyu na bakin ƙofa a tsaye, sun saka ƙofar a tsakiya ɗaya ne ke tsaye tsakiyar kanshi ta baya yana firfita shi da wannan ƙaton maficin nasu. Da ƙyar ya ɗago ido ɗaya ta gilashi ya kalleni, maimakon in ga ya nuna razana da mamaki,sai dai na ga ya ɗan yatsina fuska, ya ƙara gyara ƙwanciya a kusurwar kujera ya kishingiɗa, sannan na ga ya ɗan ɗaga hannu kaɗan. Sai na ji sun ɗauki magana gaba ɗayansu na tsaye duk sun yi saurin zubewa suna cewa. "Takawarki lafiya,ƴar manya, Gimbiya taka a hankali ƴar ƘASAITA,matar ƘASAITA,Yarima na gaishe ki,yana yi miki sannu da isowa." Ɗaya daga cikinsu ya yi saurin isa kujerar da zan zauna yasa wani abu mai kyau kamar abin sallah ya shinfiɗa mini, ɗaya kuwa ya yi saurin isowa bayana da ƙaton maficin nasu ya fara yi mini fifitar tun Ina tsaye. A take nima na fara nuna irin tamu isar ta mata, na zauna tsakiyar kujera na mayar da ƙafa ɗaya a kan ɗaya na ɗora, ina ɗan juya jikina a hankali. Yarima Faisal mutumin da muke takun saƙar ƙiyayya da shi,mutumin da ya kaɗe ni da mota, kamar ya banke akuya, shi ne yau ya zo wajena a matsayin mijin da zan aura mu yi zaman aure mai tsayi, na gani. An ɗauki mintuna goma, gaba ɗayan falon shiru yake, sai masu gadin ke cewa ana gaishe ni, can sai ɗaya daga cikin waɗanda ke ƙasa zaune ya fara magana. "Allah ya taimaki Sayyada, Gimbiya, ɗan Sarkin Sarakuna,Yarima na gaishe ki, kuma mun zo nan ne domin amsa gayyatar da ki ka yi mana ta alheri, wannan da ki ke gani dai shi ne Sadukul ummati." "Eh,Yarima kenan wanda yake jiran gado,yau ko gobe ko anjima ma." "Haka yake, gaskiyarka ne, Sarkin dogarawan zamani." "To shi ne muka zo a kan...." Na ɗago masa hannu, ya yi saurin cewa,"Dole ne in bi umarni,shiru ma hankali ne, godiya nake." *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 7 Sai da na yi yatsina nima na ɗaga baki da ƙyar na yi masu magana. "Ku fita gaba ɗayanku ina son yin magana da shugabanku." "Godiya muke, Allah ya daɗa girma, umarninki ne abin bi." Suka sunkuya gaba ɗayansu gabanshi. "Mun barka lafiya." "Eh, Gimbiya ce ta bayar da umarni." Ya ɗaga kai yana ɗan jingina shi,wato ya amsa kenan,wai! ƘASAITA. Ya amsa,eh, ya ce ya amsa godiya muke. Suka bi layi suka fice ƙofar waje. "Yau fa ake yin ta!" Na faɗa a zuciyata, saboda na ga yanda za'a yi a yi magana tsakanin ni da shi. Mun ɗauki minti goma sha biyu kenan, ba wanda ya yi cikakken motsi a cikinmu, na ga ina ɓatawa kaina rai da lokaci, sai na miƙe na isa ga ɗan ma'ajin takardun Dad na ɗauko biro da takarda. "Me ya kawo ka ne?" Shi kawai na rubuta na miƙe na isa na miƙa masa, sai da ya ɗauki mintuna biyu, sannan ya miƙo hannu ya karɓa. "Cewa aka yi in zo in gani in kinyi mini." Na karanta,a lokacin da ya taso shi ma ya miƙo mini. "Ka koma ka gayawa wanda ya turo ka na ganka, cewa ba ka yi mini ba,ni Yasmin a ƙara gaba." Na miƙa masa. Sai a lokacin ya ɗago kai ya kalleni, sai na ga ya yi murmushi, irin na isa ya mayar da kan shi. "Dole ma in yi miki, tunda mu ba ma saɓa maganar iyayenmu,ki sani, ba ki tsarin cikin matan da zan iya aure, darajar Sarki kawai za ki ci." Ya miƙo mini. "Ka tuna,ni ce wacce zan zame maka masifa, idan kuma ka kuskura ka tsallake ɗaya daga cikin dokokin da zan dinga gindaya maka, zan bayyanar da boyayyen sirrinka a gaban Sarki!" "Na gama da ke, tun da zan zamo mijinki." "Ba ni da lokacinka, ina kuma gargaɗinka." Na miƙa masa, na koma cikin gida. Ina laɓe ta labule na ga ya rubuta wani abu ya ajiye, sannan ya yi gyaran murya, sai ga su sun shigo a guje, ina kallo ya yi wa ɗaya daga ciki magana, amma ko shi wanda ake wa maganar sai da ya sunkuyo kusa da shi sosai, sannan ya ji abin da ake cewa, to balle ni da ke laɓe a bayan labule. Cikin rawar jiki na ga ya sa hannu a aljihu ya fito da wasu dogayen takardu da biro ya miƙa masa da sauri ya sunkuya bayanshi, sai na ga ya ɗora a kai yana rubutu, ya ajiye. Sorry,kin ji." Na ɗaga kaina. "Thank you." "Je ki ciki kiyi hidimar ki zan zo miki da labari mai daɗi, nima dama ba san auran nake ba,ke tashi ma mu tafi tare,in ajiye ki gidan Salwa da dare na aiko a ɗauke ki kin ji?" Na ce to. Na miƙe na shiga gida na ɗauko ɗan guntun mayafi na rufe kaina da shi, wanda riga da siket ne na atamfar Super Holland ce a jikina wacce ake kira da suna A daidaita Sahu, inji mutanen Kano,mu kuwa muke ce mata Open Neck. Da kuka na shiga gidan Aunty Salwa. Aunty Salwa ta Zauna ta dinga lallashina ina gaya mata abin da ke damuna, da ƙyar na ƙwashe labari na gaya mata, tun farkon haɗuwata da shi da irin fansar da ya ɗauka a kaina,Ni kuma da ramuwar da nayi na ba ta takardar zancen da muka yi da shi yau da ƙarfe uku. Ta yi shiru na tsaya kusan mintuna taƙwas, sannan na ga ta juyo da hankalinta gare ni. "Haba Yasmin,kada ki bayar da kanki fa, kada ki zubar da ajinki,ki tuna ke ce macen da ya kamata a ce kin tsunduma kanki gidan sarauta, saboda ƙyawun da Allah ya yi miki. Ki kalleni ki gani,ƙyawuna fa ya sani auran ɗan manyan mutane,ki sani dama fa ajinmu ya wuce na ƙananan yara, balle ƴaƴan talakawa." "Gaskiya Aunty ni dai ina son Anwar,ko da kuwa zai dinga yin dako yana ba ni abinci ni shi nake so, balle fa da aikinsa." "To yanzu Yasmin ya ki ke so ayi miki? Mu haɗa kai mu kunyata mahaifinmu,ko kuwa? What do you want?" Ta matso ta ƙara dafa ni. *Haba ƙanwata me yasa ba zaki haƙura ki bi umurnin iyayenmu ba, alhalin su suna yi mana abin da duk muke so,in na tambaye ki zaki iya ba ni amsa tsakaninki da Allah?" Na ɗaga mata kai, saboda kuka ya hana ni magana. "Ba shi da ƙyau ne?" Nan take na karanto fuskarshi a idanuwana, tabbas ƙyakyƙyawa ne, wanda ba zan iya misalto ƙyansa ba, na tuno ƙwayar idaniyarsa da ta kalleni fara ƙal, kamar kullum a ruwa take ajiye,ƙwata miliyan ɗin gashin bakinsa kuwa daidai fuskarshi. Na ɗan nutsu ina tunano mai irin gashin bakin a take na tunano (Craig David), shahararren mawaƙin turanci, sai dai na san Faisal ya fi shi ƙyau nesa ma ba kusa ba, sannan shi Faisal fari ne, irin farin da za mu iya cewa yalo-yalo. "To me ye baƙya so ne a tare da shi, wanda har yasa ki ka tsane shi?" Maganar Aunty ta dawo da ni daga karanto fuskar Yarima da nake yi,ni taƙamar shi ce take ba ni haushi, kamar fa shi ne Sarkin fa, yanda mutane ke yi masa, Aunty ga shi azzalumi ne,kin ga gidan yarin da ya kai ni kuwa, wallahi sai kin yiwa mutanen ciki kuka,in kuwa kina da saurin jin tsoro,ke da bacci sai an dage da yi miki addu'a." "To shi kenan ma,kin ga yanzu aikin samun lada ma ya zo gare ki, sai ki yi haƙuri,ki aure shi ko don taimakawa waɗanda ke gidan yarin a sannu kuma duk ki san yadda za ki yi ki raba shi da halayyar da ba ƙya so,miji fa Yasmin dole ne fa ki juya shi. Yasmin kin ma bani dariya ko da yake dole ne,ki ruɗe tunda har yanzu yarinya ki ke,ko me sanin ki da namiji miji ya fi shi. Tunda shi namijin waje zance ne kawai da kalaman so, amma fa kuma ki sani duk inda sarauta take, aƙwai ƘASAITA, ta musamman a wajen, ba kuma za ki iya raba jinin sarauta da ita ba ke duk sarautar da ba ƘASAITA,ai zaki ga ma ba ta da ƙarfi, saboda haka, kema fa sai kin koya." Hankalina ne naji ya ƙara tashi, kenan ni ba ni da mai goya mini baya? A nan take na yi tunanin ko in gudu zuwa Adamawa su ma in gaya masu,wataƙilan na samu a raba ni da wannan auran. A take na yi tunanin ban ƙyauta ba, tunda ban cewa Dad ba na so ba,bai kuma sani ba, balle in ce ya tilasta mini. Ba ni da wata hanyar fita, maigadin gidan Aunty ne ya shigo da rawar jiki wai an yi baƙi, Aunty ta tambaye shi maza ne ko mata? Ya bata amsar maza ne. Ta miƙe ta shiga ɗakin mijinta Uncle Abdulƙadir ta gaya masa, doguwar riga ce ta shan iskar maza ce a jikinsa ya fita. Cikin mintuna baƙwai sai ga shi ya shigo a nan ne yake gaya mana,Yarima ne yake nema na, saboda haka mu bayar da falon zai shigo. Takaici zan ce ko baƙin ciki,ko haushi,ni dai zan iya haɗa su gaba ɗaya in ce su ne a zuciyata, amma sai na ga Aunty har da turaren Humra ɗan Maiduguri shafa mini, ban da wanda ta fesa mini ta ja ni da tsiya sai na yi ƙwalliya kada ya fahimci na yi kuka. Amma na ƙiya, na ce gara ya san ba na son shi tun yanzu kada ma ya yi tunanin son shi nake yi. Bayan ƴan mintuna ne na fita falon a inda yake da gayyar jama'ar nan tasa da ke bin shi ko'ina, haushi ya ƙara kama ni. Kafin in Zauna ma na yi masu alama da hannu su fita da rawar jiki da kirarin nan nasu suka yi waje, sannan na zauna fuska a ɗaure, cikin sakan uku ma na jini ba na ma son ganin shi, na mayar da kaina na kifa a cinyata. Ban ɗago kaina ba, amma daga ƙwancen da kaina yake na karkato na kalle shi, bayan mintuna kamar goma da zamanmu falon wanda ya yi tsit, shi ma maganar da naji ya yi ita ta bani mamaki wacce ya yi cikin sanyin murya. "Sorry about what happened last time Sarki ne ya yi mini faɗa sosai, ya ce inzo in ba ki haƙuri." Ina kallonshi daga ƙwanciyar cinyar nan da na yi,yasa hannu ya cire gilas ɗin fuskarshi ya ajiye shi gefe ɗaya, sannan ya miƙe tsaye ya iso inda nake zaune, ban ko motsa ba, ya miƙo mini ambulan ƙatuwa mai ruwan (pink) na sa hannu na karɓa,bai ce komai baya ya juya ya tafi. Ina kallo ya mayar da gilashin fuskarshi ya juya ya ƙara kallona, sannan ya yi gaba. Na miƙe na shiga ɗakin Aunty,tana ƙwance a gadonta, na miƙa mata ambulan ɗin. Aunty ta buɗa, sai ga katin ban haƙuri ƙato,dana nuna ana son ka,I love You, Greeting Card,sai takarda inda muka buɗe muka karanta. "Ni ma ba da son zuciyata zan aure ki ba, saboda ba zan iya yi wa mahaifina gardama ba, na san abin da ke damun ki, shi ne baƙya sona, kamar yanda nima zuciyata take ƙuna in na tuna ba ni ne na zaɓi matar da zan aura ba. A matsayinki na mace kuwa, na san ke taki zuciyar tafi tawa ciwo da ƙuna, da tsana ta, amma ki yi haƙuri, rayuwar da muka tsinci kanmu kenan." Husband Na ƙara narkewa da kuka. "Aunty bana son shi, Aunty guduwa zan yi." "Ai kuwa da kin yi wayon banza,a ce kin wulaƙanta naki uban a idon duniya, namiji ma ya yi haƙuri ya bi doka da umarnin iyayensa, sai ke mace. Haba My sister don't be a silly girl mana." Ta taso ta iso inda nake ƙwance, ta ɗago ni ta rungume. "Ki tuna Yasmin mu uku kaɗai mahaifinmu ya haifa,ki tuna gaba ɗayan duniyar nan mu ya sawa ido, ya ga mun zama ƴaƴa nagari,ki tuna cikinmu ba wacce yafi so da ƙauna sai ke,mu ƴan uwanki mun sani, duk wanda yake tare da Dad ya san ke yafi ƙauna. Ki tuna ba shi da iyaye sai mu kawai gare shi. Amma a ce kece za ki ci mutumcinsa a idon duniya. Haba Sister, kada ki yi mana haka mana,haƙuri shi ne naki,kin san halin sarauta, yanzu haka an gama aikawa duniya da katikan gayyatar bikinku,ko kin manta,ki duba ki gani fa yanzu, duk iya sarautar Sarki, amma Dad ya je ya tunkare shi da maganar da ki ka gaya masa ta game da ɗansa,kina kallo ko awa ɗaya ba, sai da ɗanshi ya dangane da inda ki ke ya ƙasƙantar da kansa ya ba ki haƙuri. Haba Yasmin ya ki keso Daddy ya yi, ya goya ki ko kuwa ya saki Mamee ya aure ki? Iya kacin so kenan. Ke ma Yasmin kin san Dad ya nuna miki shi a fili,ni dai shawara ta a nan shi ne, ki yi haƙuri a yi auranki lafiya,ki nuna murna da farin cikinki a fili duniya ta gani, amma da an gama biki,ki ja matsayinki na mace. Wato ki zauna matsugunin ɗakinki har nan da lokacin da ya kawo kan shi gare ki, ya ajiye duk wata taƙama da ƘASAITA gefe ɗaya, ya zo ya roƙi arziƙin kanki da kanki, amma da me? Kin san gidan sarauta da akwai girma, balle na Sarki Jafar, saboda haka sai kin ajiye komai kin dinga fita shan iska, cikin ƙwalliya mai jan hankali da sauran hidimomin da za su iya janyo miki shi. Ki tuna Yasmin,ke mace ce fa, wacce ko tsoho ya hango ki sai ya yarda sandar hannunsa dan ƙyau,dirin jiki, gashi Yasmin ba inda Allah rage ki, balle ki ce,ni nasan dole ne ma ya so ki. Ki tuna ke mace ce,son ɗa namiji baya wuyar shiga zuciyarki,ki tuna mu mata haka Allah ya halicce mu, balle ma kin ce shi ma ƙyakƙyawa ne." Aunty ta samu wajen awa ɗaya tana ta lallashina, har muka koma falo,mun buɗe talabijin, gidan talabijin na kasa N.T.A ya ƙyallo sanarwar auranmu da harshen Turanci. _His Highness, the Emir of Plateau, wishe to invite the general public, to the wedding ceremony of his son,Prince Faysal,on 27th June, 2005, at Emir's place at Jos._ Hankalina ya ƙara tashi, na miƙe na canja tasha na mayar gidan talabijin ɗin jaha na dawo na rabka tagumi. Aunty dai ba ta ce komai. Ƙarfe taƙwas da rabi na dare su Aunty suka mayar da ni gida ita da mijinta Uncle Abdulƙadir. Na samu Dad shi ma da Mamee a falonmu na gida suna ta hirarsu. Mamee kuwa ƴan bautar aure ana ta yiwa Dad susa a kai, har ma sai na ji kunyarsu ta kama ni, abin da ban taɓa ji ba ko don an ce za'a yi mini aure ne? Oho. Ya zaunar da ni ya ƙara yi mini nasihohi da ban haƙuri da sa mini albarka. Kalaman da ya yi amfani da su,su suka ƙara ƙwantar mini da zuciya na ji na haƙura. Haka ma Mamee kullum sai ta yi mini huɗubar da zata ƙara ba ni ƙwarin gwiwa. *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 8 Yau ne ranar juma'a, wanda ya kama ashirin da bakwai ga watan Yuni, wacce ta zo daidai da ranar ɗaurin aurena da Yarima Faysal mutumin da sai a wajen harkar biki muka haɗu da shi, tun a ranar da ya je gidan Aunty rabona da shi. Gaskiya ni kaina na san na gaji da hidima kala-kala, wanda tun saura ƙwana goma ɗaurin aure ake ta yin ta. Garin Jos kuwa,ba masaka tsinke, wanda a wajen hidimomin nan na dinga ganin manyan mutanen da sai a talabijin nake ganinsu. Tsayawa ambatan fatikan da hidimomin da makaɗan da suka halarci wannan hidimar aure namu,ɓata lokaci ne saboda Allah ya yi yawa da su. Abu ɗaya ne ba zan manta ba, shi ne ƴan wa'azin da suka kai mana ziyara,a matsayin gudummawar su, wanda suka yi a babban masallaci na Jos washegari da aka kai ni gidan Yarima kenan, ranar Lahadi a kan biyayyar aure suka yi shi. Tabbas a ranar jikina ya yi laushi, amma ragowar hidimar sai dai in ce Alhamdulillahi. Riƙe nake da Daddy gam,ina ihu zan ce ba kuka ba,a lokacin da ya gama yi mini nasihohi wanda zan iya cewa uba ke yi kafin a kai ƴarsa gidan miji, wanda suka haɗu da ragowar ƴan'uwansa aka yi mini,fita da ni daga falon Dad ita ce ta zamo tashin hankali. Da ƙyar mata suka ɓanbare ni daga jikinsa. Ganin yanda nake yi ne yasa Daddy ya ce su tafi, zai kai ni da kanshi daga baya. Hakan yasa sai dai aka lulluɓa wata abokiyar wasata aka fita da ita a matsayin amarya. Ni kuwa har goma da rabi na dare,Daddy nata lallashina da ƙyar na amince, shi ma sai da ya yi mini alƙawarin gobe tun da safe zai je gidan,in ya ga ban haƙura ba zai dawo da ni, kai ni kaina na san dai wayo kawai ya yi mini. Duk da na san dai shi kanshi dole ta sa zai rabu da ni,kari da ganin hankalin Dad ya yi mugun tashi har yana zubar da hawaye ganin yanda nake kuka, har da neman shiɗewa. Da lallashi da ban magana,Daddy ya kaini har gidan Faysal, shi da kanshi ya rakani har cikin ɗakin da yake nawa bayan nan ma sai da ya ɗan zauna ya ƙara yi mini ƴan maganganun da za su ƙwantar mini da hankali, wanda sai da jama'a suka ɗan ba mu fili, saboda yawa, amma duk da haka da zai tafi sai da na ji hankalina ya yi mugun tashi. Abu ɗaya ya hana in bi shi, ƴan'uwa da ƙawayena da sauran waɗanda suka isa a kaina, kamar ƙannan Dad da na Mamee,da suka riƙe ni suna lallashi, dole dai ta sa na haƙura. A wannan rana sai da aka bar mini mutane daga gidanmu suka ƙwana, har da ƙawayena,ganin Aunty Salwa ta ƙwana,shi ma ya ƙara taimaka mini. Sabuwar hidima ce ta ɓalle da gari ya waye,taro a cikin ariyar (area) gidan Sarki tamkar yau aka fara bikin, tun daga get kuwa har izuwa cikin gidana, wani sabon biki ma ni zan ce ake yi. Yamma na yi kuwa, sai hawan Daba ya tashi ranar Litinin kenan. A al'adarsu,wai amarya da ango ke fitowa saman gidan Sarki, Sarki da tawagarsa a gefe ɗaya, ango da amarya a gefe ɗaya a sama. To sai a dinga kawo gaisuwa, dole ta sa na shirya, saboda Aunty na nan, ban da sauran dangin iyayena,ƴan Syria,kuwa suna can wajen Mamee suna taya ta zama. Sai da muka kai gaisuwa wajen Sarki, sannan muka wuce ni da Yarima muka zauna, baya ga ƴan bi baya da muka samu, tun daga fitowata, kafin ma in iso inda Yarima ke jira na,a nan zaune har sai da aka yi kiran Magriba, tsakani da Allah na ga girmamawa da ƙauna a wajen jama'a. Wannan tasa ma na saki jikina. Ranar Talata kuma amarya da ango ke zuwa gidan Sarki na cikin gari, amma iyakacinmu fadarshi aka gabatar da mu ga manya-manyan hakiman Sarki. Daga nan kuma sai zuwa gaishe da iyayensa, shi Sarkin wanda dangin amarya ne ke raka ta, kuɗi,ƙyaututtuka kuwa,wai na sha su,ni kaina na sake da irin ƙaunar da ake nunawa Faysal, na san kuwa iyayenshi suka fara nuna masa ita. Ranar Laraba,a ranar ango ke yin tashi walimar da abokanansa, saboda gabatar da amaryarsa a gare su, ita ma ta san su, sannan da ƴan ƙawayenta ko su goma ne,a wani babban wajen taro na manya. Iyakaci na da Faysal wajen hidimar auranmu, da mun iso gida, kowa hanyarshi yake nufa,dama kuma ba mota ɗaya muke shiga ba,ni da motocina, shi ma da nasa. Ranar Alhamis ita ce ranar da na ga kowa na tafiya, wasu da safe, wasu kuwa sai yamma, amma ni ƴan'uwana, sai da dare suka tafi, cikinsu kuwa har da Aunty da Fatima amarya, zan ma iya cewa su ne na ƙarshen tafiya, wajen taƙwas da rabi na dare, saboda sai da suka gyara gidan duk inda aka ɓata,turaran wuta da sauran kimtsa amarya da ake yi kafin ango ya shigo ɗaki, shi da abokanansa, wanda ake kiranshi siyan baki, sai da suka sa na sake wani wankan na sake kaya, sannan suka umarce ni da in sauka ƙasa,in zauna ga wata kujera ta nan ita ɗaya, idan sun tafi. Huɗuba, ba wacce ban sha ba a wajen Aunty,daga nan muka yi sallama suka tafi, da sunan ba zata dawo da wuri ba, saboda gidan sarauta ba a yi masa zirga-zirga,ganin na narke zan yi mata kuka ta ce wai jibi za ta dawo,ni dai na san tsarani kawai ta yi. Na sauko daga sama a daidai lokacin da agogon bango ya buga ƙarfe tara na dare, na shigo falo na yi tsaye a inda nake tunanin an bar ni ni kaɗai kamar mayya, na tuna irin jama'a da suka taru a gidan nan,yau gashi rana ɗaya kamar an ƙwashe su. Na samu ƙwanar kujerar kishingiɗa na ƙwanta gefe, ita kaɗai ta sha shimfiɗun sarauta,ƙasan ta ma zagayayyan kafet ne (Circle) mai taushin gaske, da gani ka san ita ce kujerar zama idan mulki ya taso. A hankali na dinga bin ɗakin shaƙatawar da kallo, ba inda idona ya kai, sai ga ƙaton hoton Faysal wanda zan iya cewa ya fi ƙarfin taga, sai dai ƙofar mutan da. **** **** **** Ban ce ƙala ba, har ta gama, ina kallonta suka jera layi ita da ragowar ƴan matanta suka yi waje sai guda biyun nan su ne suka yi saurin dawowa gefena suka zauna a ƙasa, na yi murmushi na juyar da kaina gefe, sai na ji hawaye sun gangaro mini,saboda tunanin tausayawa yara ƙanana da aka jera mini su,ni ina aure su suna bauta, Allah ya kiyaye. Na ɗan motsa na tashi zaune, amma na ɗan kishingiɗa, cikin sauri duk suka miƙe tsaye ɗaya ta ɗauki ƙafata ta gyara mata mazauni, na kalle su, ba laifi duk suna da ƙyawunsu. "Ku zauna na gode." Suka yi saurin zama, na kalle su. "Ya sunayenku?" Ɗayar ƴar wacce ta fi ƙyan ta ce mini, "Mansura." Ɗayar kuma Musulum. "A wane gari ku ke?" "Nan gidan Sarki." "Na sani,iyayenku nake cewa." "Can cikin gidan Sarki, babban gidan kenan." Nayi shiru, ina tunanin me suke nufi da haka, ban kammala tunani ba, sai na ji sallama, na juyo a hankali na kalli masu shigowa. Jakadiya Dela ce da wasu mata biyar ɗauke da wasu abubuwa a rufe suna biye da bayanta, tana zuwa kusa da ni, ta ƙara zubewa a ƙasa,su kuwa suka matso gaban kujerar suka ajiye kayan, suka ja da baya, suka zube ƙasa, sannan suka ce. "Gaisuwa muke, gaisuwa muke." Na ɗago masu hannu. "Gimbiya ta amsa." Na ji jakadiya ta ce. "Gimbiya ayi mana afuwa,muna damun ki da zirga-zirga." "Ba komai." "Abin da ki ka ce ba ƙarya." Inji ɗaya daga cikin matan da suka shigo tare da jakadiya. Ta miƙe tsaye ta iso gaban abubuwan da suka shigo da su, sannan ta tsugunna. "Allah ya ja da ran Gimbiya wannan saƙo ne daga Yarima, ya ce in kawo gaisuwa a gare ki." Na miƙe zaune, inda su Mansura suka miƙe da sauri za su kama ni, na yi saurin ɗaga masu hannu, ina zama sosai, sai na ga jakadiya ta fara buɗe kayan ɗaya bayan ɗaya. Faranti ne ɗan dogo, mai ruwan zuma (golden color) kayan marmari ne a ciki,lemon zai kai goma,ayaba nono ɗaya, sai tuffa (apple) da dabino a tsakiya, amma fa na alfarma, dole ne ma su ba ka sha'awa, saboda ƙyawunsu, daga saman dabinon wani ɗan faranti ne shi ma mai zagayewa. A warwaraye ne cikinshi, tsakiyarsu da sauran kaya rakwacam, na sunkuyo na ɗauki ɗan farantin na ɗaga awarwarayen (ƴan hannu) sai na ga su shida ne, da sarƙa ƙatuwar gaske, zobuna huɗu da ɗan kunnayensu na zinare ne ƴan Dubai ɗin asalin (Daham). Na miƙawa Mansura ta yi saurin karɓa ta ɗora a kai, sannan aka buɗe ɗayan,Faranti ne shi ma kamar tsayin na farko, sai dai shi kalar ruwan silba (Silver colour) kayan sawa ne a ciki, amma da gani na bacci ne, da faranti ƙaramin sama. "Mansura miƙo mini." Na faɗa. Awarwaraye ne ƙwaya huɗu da sarƙa da ɗan kunne, da zobuna biyu kacal, amma Diamond,sun bala'in burge ni, ta dinga ɗagawa,sama rigunan bacci ne a ƙwalinsu guda bakwai, kala-kala, sai tawul ƙasa da silifas, amma masu ƙyan gaske, dukkansu a ƙwalaye suke irin ƙwalayen ƙasashen tsallake,su kansu ƙwalayen abin kallo ne. Na miƙa mata ɗan farantin hannuna ta karɓa, sannan aka buɗe ɗayan duk fa kalar faranti kalar ɗan yankin da ke rufe da shi, leshi na gani na faɗa, da takalmansa,jakarshi,mayafinshi,a samansu aƙwatina ne masu ƙyau guda huɗu sai ɗan ƙarami a sama. Aka miƙo mini ɗan akwatin na buɗa, ɗan zobe ne, mai ƙyau na Diamond da ɗan ƙaramin zanen abin sarauta a jikinsa, ya yi mini ƙyau sosai, na ajiye shi gefe, aka dinga miƙo mini ƴan aƙwatinan duk turarurruka ne a cikinsu desginer na miƙa musu, sannan aka buɗe na cikon na huɗun,kaji ne gasassu har guda huɗu masu rai da lafiya,ko a ido ka gansu sai ka yaba. Sai ƙamshi ke tashi sai sheƙi suke yi, da wuƙaƙe biyu ƙanana a gefe ɗaya,ɗayan gefen kuma cokula masu yatsu ne (Knife and fork) nayi murmushi na koma sosai na jingina. "Gimbiya Allah ya ja da rai, waɗannan kayan siyen baki ne inji Yarima." Sannan ta buɗa na biyar ɗin bandiran kuɗi ne ƴan ɗari biyar biyar sun kai guda goma. "Allah ya ja da ran Gimbiya idan har baki ya siyo wannan leshin Gimbiya zata saka, sai mu tafi tare can gidan shi Yarima ɗin, tare da dukkan farantan nan, saboda ko za'a buƙata a can." Na miƙe tsaye, a daidai lokacin da jakadiya ta gama tata maganar cikin ƘASAITA na haye matattakalar bene zuwa ɗaki inda na ce su Musulum su zo. Na basu umarnin da su ɗauki kayan da ke saman gadona su ma lulluɓe da fararan yanki, ina isowa falo, sai da naga na daidaita wajen zamana, sannan na ce da jakadiya. "Ga waɗannan ki kai masa,ki faɗa masa baki ya siyu, amma Gimbiya hutawa take yi sai nan ƙila da sati biyu." Na umarci Mansura da ta ɗauko mini faranti a kicin,ta miƙe da sauri. Faranti ɗaya kayan sawa ne, riga da wando da babbar riga, waɗanda aka ɗinko su daga ƙasar Sinigal,aƙwalinsu, sai dogayen riguna guda huɗu, sai gajerun wanduna huɗu, duk a ƙwalayensu da silifas, da turarurruka huɗu da tuwal ɗaya a samansu ne ke da zobe ƙwaya ɗaya na azurfa. Ɗaya farantin kuma alƙur'ani ne da abin ɗora shi, ɗan katakon nan da dardumar sallah mai beza mai ƙyan gaske, da carbi da littafin ibada da hukunci ƙwaya ɗaya. Farantin da Mansura ta ɗauko mini kuwa, na sa hannu na ɗauki kaza ɗaya, na ɗora a saman shi, cokali mai yatsu ɗaya, gefe ɗaya na sa tufa biyu,lemo biyu,ayaba biyu, na ɗauki dabino huɗu na zuba, na bayar da umarnin a ɗauki yanki ɗaya a rufe. *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 9 Sannan na ɗauki kaza ɗaya na baiwa ƴan kawowa, tare da bandir ɗin kuɗi. "Jakadiya ku je ku raba,ke da abokan rakiyar ki, waɗannan kuma na gaya miki ki kai masa,ki ce Gimbiya na gaishe shi baki ya siyu, amma tana hutawa har nan da sati biyu." "Maganar ki ita za'a bi, godiya muke." Na koma na ƙwanta jikin kujerar da nake zaune, ina kallonsu suka bi layi suka fita kamar yanda suka shigo, bayan nan kuma na umarci su Mansura da su ƙwashe kayan su ɗan ɗibar mini kayan marmarin,su ɗauki ragowar, haka kajin na ce su ɗauki ɗaya. Cikin girmamawa da biyayya suka aikata yanda na faɗa, tun daga lokacin kuwa sai na koma sama,a inda na umarci su Mansura da su ɗauki daki ɗaya a ƙasa su ƙwanta,ni sai da safensu. Baƙin ciki, takaici, suka saukar mini a daidai lokacin da na tuno da Anwar,na yi tunanin da shi na aura,muna can ya shigo ɗaki a sunanshi na ango, ina can yana tarairayata da nuna mini kulawa ɗari bisa ɗari, wannan tunanin yasa na sha kayan baccina, na buɗe ƙofar da za ta fitar da kai barandar da take a gaban gidan. Na dafa ƙarfen barandar, wanda na mayar da idanuwana na lumshe,a daidai lokacin da wani ni'imtacciyar iska ta kaɗa, iska ta dinga ɗaukar gashin kaina tana juya shi a hankali, hawaye masu sanyi suka tsiyayo mini a kumatuna, a lokacin da tunanin rayuwata ta raunana ya faɗo mini,anya kuwa zan amince in dinga irin wannan zaman jakadancin? Komai ke tsakaninka da mijinka sai wata ta sani. Na buɗe idanuwana tare da ware hannayena tamkar ina jiran wani ya rungume ni, kamar an ce in kalli barandar sama wacce take kallon tawa barandar,sai kawai na hango mutum a tsaye, shi ma ya dafa ƙarfen barandar ya sunkuyo yana kallona. Da ɗan nisa, shi ya hana ni in gane ko waye, kuma ga iska tana kaɗawa, natsuwa na yi sosai na ƙura masa ido, ba abin da idanuwana suka karanta mini sai angona Faysal. Tsanarshi na ji ta ƙaru a zuciyata a take ban san lokacin da na juya na shige cikin ɗakina ba, na mayar da ƙofa na kulle, na wuce na faɗa gadona a inda na kasa tunano komai sai Dad wanda da ya san rayuwar da ya jefa ni ciki, na san da bai fara ba. Ni ce har ƙarfe biyun dare zaune a abin sallah ta, ina roƙon Allah ya kawo mini canjin rayuwar da ta fi alheri a gareni,ni kam na san ba zan iya wannan auran ba, na yi tunanin wai yau ne daren farko (first night) ɗina,amma gani nan a zaune ko kalar ango ma ban gani ba. Ƙarfe shida na safe na farka, hakan yasa na yi saurin saukowa daga gadona, domin gabatar da sallar Asubahi ɗin da na makara ban samu yi ba. Ƙarfe tara na safe har na gama komai na sauka ƙasa domin nemawa cikina abin da zan ci. Wani abin mamaki da na gani, shi ne yanda har an gama gyara ko'ina na falon, sai ƙamshi ke tashi, sannan kuma gaba ɗayan gayyar ƴan matan nan sun hallara waje ɗaya ni kawai ake jiran fitowata. Tausayinsu ya kama ni,a zuciyata na ce bayin Allah, insha Allahu sai na raba ku da wannan ƙangin na bauta,a take na ji ina ƙaunarsu, sannan ya zama dole ma in ɗan saki jikina da su, saboda su ji daɗi su ma. A take na yi murmushin dariya, "A'a Mansura har kun tashi?" Cikin sakan ɗaya har sun gama isowa bakin matattakalar benan da nake saukowa sun zube ƙasa. "Haba, abokaina, ya zaku dinga yi mini haka, tamkar wata wacce ku ke bautawa, na san dole ne ku ba ni girma, amma irin wanda nima zan ji daɗinshi ba irin wannan ba. Sai na ga wannan ya kalli waccan, waccan ta kalli ƴar uwarta, na sauko na dinga dafa kafaɗar na kusa da ni. "Ku zo muje." Suka biyo bayana. Ina zama gaba ɗaya suka zube ƙasa. "Gimbiya mun gaishe ki. Barka da ƙwana?" Na amsa masu da lafiya ƙalau. A nan na dinga tambayarsu sunayensu, ɗaya bayan ɗaya, wani abun in yi ƙoƙarin ba su dariya, amma bayin Allah nan sai na ga sun kasa yin dariya, ga ta kuma suna son yi. Na waiga na kalli Mansura. "Mansura, har yanzu ban fahimci waɗanda ke kicin ba." "Allah ya ja da ran Gimbiya ga mu nan." A take na ga ƴan mata masu ƙyau suma. "Yaya abinci?" "An gama shirya shi a wajen cin abinci, na Yarima fa?" "Ai can ake haɗa masa shi ma." "Su wa ke haɗa masa?" "Yana da masu yi masa." *Maza ko mata?" "Maza ne." Na taɓe baki, sannan na miƙe na bada umurnin a kai ni wajen cin abincin. Kai wata duniyar ma in ka shige ta, sai ka ga tamkar yau aka haife ka, saboda ganin sabon yanayi da sabon tsari. Duk a cikin falon muke, amma da muka bi ta wata hanyar sai na ga tamkar mun fita ƙasashen turawa, wani ɗan rukuni ne mai kama da ɗan ƙaramin wajen shaƙatawa an saka masa wasu labulaye masu kama da rumen kitso, da ka buɗa sai ka ji sun yi kankacakau, madadin tebirin cin abinci da muka baro a falo. Sai na samu shi kuma wajen shafe yake da kafet, mai ƙyan gaske ga wani tsakiya mai zagayewa, sannan na ga an shinfiɗa wani yanki mai ƙyan gaske,fari mai zanen jajayen fulawoyi, shi ma zagayayye ne,saman shi aka jera kayan abincin,ga tuntayen alfarma guda uku gefunansa. Ina zama jakadiya na isowa, ta zube gabana ta kai gaisuwa. "Allah ya ja da ran kilishin Gimbiyoyi jakadiya na yi miki barka da Asuba." Na yi murmushi, "Gimbiya na amsawa jakadiya,kin ƙwana lafiya?" Sai na ga tana sussunne kai. "Jakadiya ba a amsa mini." "Lafiya lau, Kilishin Gimbiyoyi." "Dama Yarima ne, ya aiko ni ya ce a gaya miki yana jiran gaisuwarki, sannan yana gayyatarki karya kumallon safiyar nan,zuwana na huɗu kenan a lokacin dai baki fito ba." "Ki gaya masa ina amsawa, amma ki ce kin same ni har na Zauna saman in da zan karya nawa kumallon,sai dai ya jira wata safiyar sai ya ƙara aikowa." "An gaishe ki." Ta miƙe da hanzari ta yi gaba,ni kuwa na buɗe kayan cin abincina, amma a cikin sauri ƴan matan nan masu girki suka karɓe ni. Farfesun naman kai ne da sinasir a gefe ɗaya, sai soyayyan dankali mai ƙwai a ciki, ga kunun gyaɗa a gefe ɗaya, ban da ruwan shayi da yake a gefe, da cinyoyin kaji zalla an soya su. Bayan na gama ne na umarci su Mansura su zo su raka ni in zagaye gidan, har waje saboda sanin yanda yake duk da ƙwanana biyar kenan a gidan, amma a tare nake da jama'a ƴan biki. Samana dai falo ne babban gaske, wanda ya sha kujerun alfarma har kala biyu, kowanne rukuni,kalar kujerun su daban, amma irin na gidan sarauta, sai ɗakuna ƙwaya biyu kacal, wani gado ne ƙwaya ɗaya a tsakiyar ɗakin zagayayye mai kama da ƙwano (Circle), ƙaton gaske,an zagaye shi da wasu labulaye farare, wanda sai dare ya yi ake danna wata na'ura wato remote sannan sai ya sauko. Gaba ɗayansa shinfiɗe yake da zanin gadon da ya bazu ƙasan shi, wanda kafet mai laushin gaske ne ƙasan shi, shi ma a zagaye yake, sai daga can gefensa kujeru ne masu zagaye aka yi masu rukuninsu daban, har ɗan tebirin tsakiyarsu (Centre table), sai daga kusurwa tebirin rubutu ne har da kujerunsa biyu. Daga ɗan nesa da gadon kuma kujerar kushin ce doguwa, ƙwaya ɗaya, wacce ta sha shinfiɗar dardumar sarauta da filillikan ta biyu. Gefe ɗaya kuwa wani irin kafet ne, amma ba wai irin wanda ni kaina na sani ba, tabbas wannan ya fi kafet ɗin tsakiya laushin gaske. Bangon gidan kuwa ɗaukar ido kawai yake yi, wanda na yi imani da Allah ba tayal ba ne ba saboda yanda yake ɗaukar ido. Ɗaya ɗakin kuwa, shi ma an zuba masa wani irin gado, wanda kan shi kawai ma abin kallo ne, sai kujeru ƙwaya uku da ke gefe, sai kuwa rukunin tebir ɗin kayan Na'ura mai ƙwaƙwalwa (Computer). Banɗakin ɗakunan kuwa shi ma wani sabon gida ne, saboda shiga ka ke yi ƙwamin wanka tamkar ka shiga ramin wanka (Swimming pool) saboda ƙasa ya shafe, kuma sam ba ka ganin mai ke ƙasan ƙwamin ne,ko kuwa irin abin da ke manne a bangon gidan ne? Oho, sai dai zaka ga yana ta gudu, tamkar ka shiga ƙorama. Sannan an rubuta zafi da sanyi a jikin wani bango da yake tsaye shi kaɗai a can tsakiyar kusa da ramin wanka, shi kan shi ramin wankan ka tattaka matattakalar bene,amma shi sai mu ce kamar za ka gidan ƙasa, sannan ka shiga ciki. Wasu green da blue ɗin abubuwa ne liƙe da ɗan dandamalin inda za ka ajiye hannuwanka in ka shiga, wanda aka rubuta sabulu da soso, ma'ana su za ka danna su fito da kansu,in ka gama ma su koma da kansu. Ƙaton madubi ne wanda za mu iya cewa ya kai rabin bangon banɗakin, shi ne ke kallon ka in ka shiga, da in ka fito. Tsayawa ƙarasa bayanin ma na san abu ne mai ɗaukar lokaci. Da ka buɗe ƙofar da ke cikin ɗakin,za ka ga gaban gidan, wanda yake kallon gaban wani gida wanda na ga Faysal tsaye jiya da daddare,da ka gangaro matattakalar benen,sai ƙaton falo, wanda zan iya cewa tsayawa fassara shi ɓata lokaci ne, sai dai aƙwai ɗakuna biyu shi ma a ƙasan da banɗakinsu. In ka fita cikin gidan,za ka samu bene ne zagaye da shi kamar ƙwabo, sai filin tsakiyar,in ka fita ƙofar shigowa kuwa za ka samu ragowar rariyar gidan, waje kenan inda ke da lambu in ka dawo ta gaban gidan kuma doguwar baranda ce kamar ta asibiti, amma wannan yanayinta kamar ƙaton fayif ɗin ruwa. Tun da zagaye take da shukokin fulawoyi,in kana ciki kamar kana cikin inuwa, ita za ta ɗauke ka har ka shiga gidan Faysal, wacce kamar nan naɗe take da wayoyi, sai dai akwai ƙofa biyu in ka zo tsakiyar ta. Ɗaya ƙofar za ta fitar da kai filayen wasa na gidan, wanda gaba ɗayan zagayen gidan ciyawar nan ce ƙwantacciya mai kama da kafet ɗin ƙasa, filayen wasa ne kala-kala, akwai na ƙwallon ƙafa, ƙwallon raga, ƙwallon ƙwando, ƙwallon hannu,ƴar ƙwallon rami da sauran wasanni kala-kala. Daga can nesa da wajen kuma wani dutse ne wanda ƙasanshi duk ƙananan duwatsu ne, ga ruwa mai ƙyau yana gudanya a ƙasansa, wanda za mu iya cewa wajen shaƙatawa, wajen ya yi mini daɗi da sanyi-sanyi. Ƙaton dutsen kuwa malale yake, tamkar an shinfiɗa a kai wanda sai ka taka kamar ƙananan duwatsu uku, sannan ka haye shi. Ba zan iya cewa ga inda wannan ruwan ke nufa ba, saboda gabanshi duk daji ne,wato dogayen itatuwa ne, masu kama da iccen turare,ko ko iccen fulwaya za mu ce, shi kuwa ruwan kana hango ƙasanshi garai-garai, wanda ƙananan duwatsu ne ke aiki. Muna isa wajen kuwa, na tattaka na haye saman dutsen nan,a nan take sai na ji ai ni na samu wajen zama in dinga hutawa, duk da an keɓe wajen hutawa a cikin wajen filin wasan. Ɗaya hanyar kuwa, ɓangaren lambu ne,babu abin da babu,a cikin wajen, wanda sai da muka zagaya shi sosai, sannan muka fita, shi ma a cikin shi akwai duwatsu, sannan an tanadi wata rumfar gargajiya a ciki, wacce ta sha shimfiɗu a inda daga nesa da ita akwai wani ɗan ƙaramin gida mai ƙyan gaske, sai dai sun ce gidan hutawar Yarima ne. Saman dutsen nan mai ruwa shi ne ƙarshen zagayen gidana, tunda ni ba abin da zai kai ni gidan Yarima. A nan na umarce su da su ɗan kawo mini darduma,zan zauna a saman dutsen,dama ni ba gwanar ɗan ƙwali ba, sannan ga ni da son ƙananan kaya (English wears) duk da dama ƴan Jos haka muke,mun fi baiwa ƙananan kaya muhimmanci a kan kayan gargajiya. Doguwar riga ce kuwa jikina, wacce take ɓalalliya daga ƙasa, ba ta wuce ƙwaurina ba, sai dai ƙaramin hannu gare ta, iya cinyar hannuna, na sa suka ɗebo mini ƴan ƙananan duwatsu don kawai in dinga jefawa a cikin ruwan. Na samu tsayin awa ɗaya a wajen nan,ni da Mansura da Muslima, sai ga jakadiya cikin hanzari ta zube a can ƙasa, sannan ta nemi iznin hayowa, na bata,a inda ni kuma na kishingiɗa a ɗan tuntun da suka kawo mini. *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 10 "Allah ya taimaki Gimbiya,Yarima ya ce a ce miki yau ƙarfe huɗu na yamma ki same shi gidanshi,za ku gaishe da Sarki, da mahaifiyar shi,dama haka al'adar take, domin su ga ya ku ka ƙwana." Na yi shiru, sannan na nisa na fara magana. "Ki ce masa ina da ƴar hidima a gidana, amma shi in ya shirya yazo ta gidana mu tafi in kuma ba damuwa ma iya haɗewa a can, ina da ƴar rakiya." Sai na ga tana rausayar da kai. "Shikenan jakadiya." "To,to,to, Gimbiya ai ba gardama, abin da ki ka ce shine." Ta miƙe ta gangara ta tafi,ni kuma na cigaba da harkokina, wanda suke yi mini daɗi, ga ba rana ko kaɗan a ganina sai ma iska da ke ratsa jikina, irin ta sanyin damuna. Ƙarfe biyar na yamma na farka daga baccin da ya ƙwashe ni a kan abin sallah ta wanda na tashi da mamakin jikina ba hijabin da na saka na yi sallah, sannan an ɗora mini kaina a saman filo. Cikin ɗan hanzari da faɗuwar gaba na miƙe, saboda tunawa da na yi cewa mun yi da Yarima za mu gidansu. Banɗaki na shige na watsa ruwa da saurina, ina fitowa ɗaure da tawul na leƙo ta barandar sama, ta cikin falo, na kira Mansura,wai dama in tambaye ta cewa Yarima ya aiko,ko ya zo? Ai sai kawai muka yi ido huɗu da shi. Ya yi tsaye a maimakon in kira Mansura, ganin ya cire gilashin da ke manne a fuskarshi, ya ƙara ɗago idanuwanshi a kaina, ya tuna mini cewa jikina ba riga, na yi saurin shigewa cikin ɗakina, tare da ƙwallawa Mansura kira. Ta shigo da sauri, "Ya daɗe da zuwa?" Tambayar da nayi mata kenan. "Eh, ya daɗe." "Tun yaushe ya zo?" "Tun ƙarfe huɗu, na zo gaya miki sai na same ki kina bacci, shi ne na gaya masa,ni dai na ga ya hayo saman da kanshi, sai ya sauko ya zauna a nan,mun kawo masa kayan marmari da lemu, amma bai ko kalle su ba." Na yi tsaki, "maimakon ki ce masa ya tafi zan zo daga baya?" Na ga ta zaro idanuwa da sauri. "Allah ya huci zuciya,ai ba a mayarwa da Yarima magana, yanzun ka ƙwana a yari." Nan take sai na tuno yarin nan,nima na taɓa zuwanta, ta tsawon awa goma. "Ke ki ka cire mini hijabin jikina ki ka sa mini fulo a kaina?" "A'a" Haushi ya kama ni, "wa ya ce ki ka barshi ya shigar mini ɗaki?" Ta yi saurin sunkuyar dakai, ba ta ce komai ba, "fita ki bani waje ki turo mini masu kula da kayana!" "Ai sun ajiye Gimbiya, Allah ya huci zuciya,ga su nan sun fito da su." Ta nuna saman kujera da ɗan yatsa, sannan ta yi waje. Boyal ne mai ruwan makuba (Coffee Color) wanda ya amsa sunansa, wanda ya sha aikin surfani a wuyansa da hannayensa, amma hannun bai wuce cinyar hannuwana ba, sai rigar kuwa da kaɗan ta wuce ƙuguna, amma buɗaɗɗiya ce, wacce ake kira da Stella Style. Zanin kuwa ya sha ado, wanda zai ɗaukewa jama'a hankali,ni kaina mai kayan sai da na ji sun birge ni, na zauna a jikin madubin da ke kusa da gadona, na gyare fuskata. Takalmi da jaka ruwan ƙasa ne nasa a ƙafata, wacce jakar iya silin hannu kawai ake rataya ta, da gani ka san desginer ce,wata siririyar diamond na saka a wuyana,inda zobunan hannuwana da ɗan kunnan duk kalar sarƙarce, zobe ƙwaya biyu kacal ne a hannun nawa. Ɗan ƙwalin Boyal ɗin ne aka naɗo shi, tamkar naɗin gwaggwaro, amma a matsayin ɗaurin ɗankwalin yake. Turaren (Network) na zuba a jikina, ban tsaya wani make-up ba a fuskata,saboda gaishe da sirikan dole zan je, sai dai na san dole ta sha farar hoda da Wetlips mai sheƙi,farcena kuwa sun sha fenti ruwan ƙasa suma. Taku ɗaiɗai nake yi na sauko daga ƙafar bene inda takalmin ƙafata ke fitar da sauti cikin nutsuwa, saboda malalen kafet da ya baje gidan, shi ya hana su ƙara mai fitar da sauti da ƙarfi. Babu kowa a falon sai Faysal shi kaɗai da jarida a hannunsa,jin takuna yasa ya ajiye jaridar, amma ba tare da ya kalli inda nake ba, har sai da na iso daidai da shi, sannan na ga ya ɗaga kai ta gefe ɗaya ya kalleni,mayar da kan da ya yi ya sunkuyar ya yi daidai da fitar maganarshi a hankali. "Something is missing." Na ƙara kallon jikina sosai, ban ga abin da na manta ba. "What?" Na faɗa cikin jan aji. "Mayafi,ko kin manta yanzu ke matar aure ce?" Na tsaya na ƙare masa kallo, amma shi ko motsi bai yi ba,a hankali na nufi inda na san zan ga su Mansura, sannan na yafito ta, ta iso da gudun saurinta, sannan na umarce ta da ta ɗauko mini mayafi wanda yake iri ɗaya da takalman da jakata, cikin rawar jiki ta ce to. Ko kallon inda yake ban yi ba, na wuce zuwa waje abina,bai ce ƙala ba, shi ma na ga ya taso ya biyo bayana. Wani abun al'ajabin kuma shi ne dakarun tsaron shi suna nan tsaye ƙam suna jiran shi, a zuciyata na ce lallai wannan mutumin da mulkin masifa yake. Limousine motar nan mai ƙofa uku, wacce ta bugeni a titin Ahmad Bello Waya, ita aka buɗe mini na shiga cikin takaicinta, ta gefe ɗaya na ga ya shigo shi ma,a inda bai fi sakan biyu da zama ba, na ga labulaye baƙaƙe sun sauka da kansu, kenan an rufe mu,ko direban ma bana gani. Kujerar gefenmu ba kowa, sai tsakiyarta naga ƙaramar talabijin na aiki,sanyi na ji ya sauka a lokaci ɗaya, tare da wata fitila mai kalar duhuwa ita ma a zuciyata na ce lallai dole a dinga kaɗe ƴaƴan talakawa ba a sani ba. Yanda ya shige ƙwanar kujerar da yake,ni ma haka na ƙwanta linkif a cikinta,tsawon mintuna goma sannan na ga ya cire gilashin fuskarsa da ƙyar, sai ga wani ɗan tebir ya ɓullo daga ƙasa da ƙwalaban lemu amma ba irinsu fanta ba,da kofunansu, wasu ƙwalaben ne abin kallo, don ma ina ƴar gidan masu da shi, da sai in ce giyoyi ne ba lemo ba. Ya ɗora gilashinsa a sama, sannan yasa hannu ya janyo gaban tebirin, sai na ga ashe ɗan firji ne ya zaro robar Ice Cream da Chukulat, ya ajiye a gabana, sannan ya ɗaga ƙwalba ya tsiyaya lemo a kofi, ya ajiye a gabana, sai na ga shi ma ya tsiyaya. Sai da ya kurɓa sau biyu, sannan ya ajiye ni kuwa sai bin shi nake da kallo ta wutsiyar idanuwana. "Na aiko da gaisuwata ɗazu, amma ban ji gamsasshiyar amsa ba, wanda ke ce mace a ƙarƙashina ki ke,ke ya cancanci ki aika mini da ita,ko kizo ki gaishe ni." Ya yi shiru ya ƙara ɗaukar kofin ya kurɓa lemun. "Ki sha mana,sarkin shan zaƙi." Na ɗago na kalleshi a zuciyata na ce wa ya gaya masa ina son waɗannan kayayyakin, ban amsa masa ba sai naga ya ɗan sunkuyo kaɗan ya ɗauki Ice Cream ɗin ya buɗa ya miƙo mini. "Karɓi." Na girgiza kaina alamar a'a, saboda mamaki da al'ajabi ya hana ni motsi, ashe ya iya magana mai sanyin gaske ko don bai cika yin magana ba. "Yasmin!" Na juyo sosai na kalle shi domin mamakin yanda aka yi yasan sunana, ya ɗan yi murmushin ƘASAITA, ya ƙara miƙo mini,na sa hannu zan karɓa, sai na ga yasa ɗayan hannunsa ya riƙe hannuna, ya kama ƴan yatsuna, sannan na ji ya yi magana. "Daga yau don Allah kada ki ƙara shafa irin wannan fentin, ina son kisa a yanke miki faratan gaba ɗayansu,ni ba na so, Allah ma baya so." Na zame hannuna, "Dole ne ki bi umurnina, saboda ina mijinki, ba ki da wata hanyar rabuwa da ni, tunda kin zo hannuna." Na yatsina fuska. "Ka manta da ina da abin da zan iya tona maka asiri da shi?" Ya yi murmushi, "Ai yanzun kan ki zaki tonawa asiri, tunda duniya za ta kira ni da mijin Yasmin ne ɗan iska mai bin mata. Amma duk da haka ina roƙon ki ƙonasu,bana so mu ɓata ran mahaifanmu." Na yi murmushi na juyar da kaina gefe ɗaya. "Zan ƙona su, amma sai ka bi dokokina." "Bama za ki same su ba,ki yi shiru kawai." Bai yi wata magana ba, na ga ya koma ƙwana ya ƙara gyara ƙwanciyarsa. Ni dai ƴar bi ce kawai, saboda ban san ko'ina ba a gidan, har muka iso wani falo. Wata ƙyakƙyawar mata ce kishingiɗe a saman wani tudu kamar na katifa, wanda ya sha shinfiɗun dardumai wanda kalolinsu ba sa ƙirguwa. Sai da muka isa kusa da matar, sannan na ga na ma taɓa ganin ta. Ƙasa na ga Yarima ya zauna cikin ladabi, nima sai na yi yanda ya yi. Cikin ɗan lokaci ƙanƙani, na ga matan da ke zagaye da ita suna kawo mana gaisuwa,suna ficewa waje. "Barka da yamma Mama." "Barka ka dai yarona." Nima sai na faɗi yadda ya ce, "Barka da yamma Mama." "Ɗiyata barka da yau, ya baƙunta, ina fata baya ɓata miki rai?" "A'a Mama, lafiya ƙalau." Sai na ga ya tashi ya haye shinfiɗar ya zauna, ya fara wata magana irin ta shagwaɓa, mamaki ya kama ni,nan take na ce lallai iyaye, iyaye ne ashe da wanda Faysal ke wa magana lafiya ƙalau ba taƙama. "Mama ni har yanzun Sarki ya hana ni zuwa Malesiya,Mama don Allah ki sa baki ya bar ni in tafi gobe." "Ba fa zai yiwu ba,in dai ka tashi zuwa Honey Moon ne to na san ba zai hana ka ba." "Mama don Allah." Ya ƙara matsawa kusa da ita har da riƙe mata hannu. "Kana da naci Yarima a kan abin da ka san ba zai taɓa yiwuwa ba. Yanzun ka tashi ka je ku gaisa da Sarki naji an ce ya shigo, kuma na san saboda kai kawai ya shigo. Baby Yasmin ku je ku gaishe da Babanku, ga shi can ya shigo gida,ki ƙyale wannan shagwaɓaɓɓan mijin naki,kin gan shi nan kullum bai girma ji yake kamar a mayar da shi ciki ma." "Mama, kada ta raina ni,ni bana yi mata wasa." "A'a,lallai ni tashi ka wuce ka ba ni waje,marar kunya." "Mama." Ya faɗa a daidai lokacin da shi kuma ya sauko muka tafi. Tabbas sarauta sai ɗanta, Sarki kam yana mugun ƙaunar Faysal, saboda yanda ya nuna lokacin da muka shiga. Mun shiga Faysal ya sunkuya har ƙasa ya gaishe da Sarki,a inda ni ma na yi yanda na ga ya yi, sannan muka zauna gabansa. "Faysal na ji aikenka har karo biyu, amma na bayar da amsa ɗaya, ita ce a'a, yanzun ma a gabanka na ce a'a, ba wai don in ɓata maka rai ba, a'a saboda yanzun ba da bane ba, yanzun kana da nauyin iyali a kanka, ya kamata a ce ka tsaya ka kula da su na tsawon lokaci kafin ka yi wata tafiya. Faysal ban haɗa ku aure da sunan in zalunce ku ba,mu iyayenku mun haɗa ku aure ne, saboda muna ganin ku ƴaƴa ne nagari masu tarbiyya, hakan yasa ni nayi tunanin wacce ta dace da kai ta ɓangaren ko'ina rayuwar duniya nan, har izuwa lahira, na ga ba wacce ta dace sai wannan yarinya. Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Ɓacin ranta zai iya shafar tsakaninmu da kai,ko da kuwa labari na samu,ka riƙe ta tsakaninka da Allah, shi so da ka ke gani, a hankali yake shiga cikin zuciya, har ya ratsa gangar jiki,in kuka yi haƙuri da juna, wata rana sai kun yi murna. Saboda mu ma duk haka aka yi mana,ga shi yanzun ya zame mana alheri." Daga nan ya ci gaba da yi mana nasihohi, sannan ya sallame mu. Muna fitowa daga ƙaton falon Sarki,Yarima ya yi gaba ya bar ni a baya,a zuciyata na ce ni dama cewa ka yi in tafi gidanmu,ni ya fiye mini alheri, tunda nima saboda mahaifina kawai nake zaune a gidanka. Ina isa falon mahaifiyarsa na ga ban gansu ba, sai na nufi wata ƙofa nima in nemi inda suka shiga sai na jiyo muryar Yarima. *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 11 "Mama wallahi yarinyar nan ba ta sona ƙwata-ƙwata, nima har yanzu ban ji ta ƙwanta mini ba sosai. Mama taƙama gareta ga jiji da kai." "Kai ka fara yi mata,ka manta labarin da ka ba ni a baya cewa yi fa tana burge ka,tun ranar da ka fara ganinta." "To Mama ai burgewa ba so bane ba." "To yanzun me ka ke so inyi maka?" "Mama ki yi mata faɗa, ita ma ta rage jiji da kai." "Kai ka yi mata." "Wallahi Mama tun da ki ka ce kada in yi mata wallahi ba na yi mata." "Haba Faysal na san ka fa." "Mama ko yanzun fa da zamu zo nan ni na je har ɗakinta, sai da ma na jira ta tashi daga bacci. Mama ai kuwa na yi." "Shin wai waya gaya maka rana ɗaya so ke shiga,a hankali in kuna tare zaka ji kana sonta, amma na gaya maka dole kai ne za ka yi ƙasa ka dinga lallashinta,ƙiyayyar mace ba ta da tsanani." "Mama ni wallahi da an bar ni nayi tafiyata kawai." "Bana son haukan nan naka fa,kullum ana koya maka hankali, amma ka ƙi ka koya." Jin kamar ta yi ɗan shiru yasa na yi saurin yin baya na samu ƙasa na zauna. "Haba Yasmin!" "Na ji an faɗa, na yi saurin ɗaga kaina. Mama ce, "Nan fa ya zama gidanku,ki saki jikinki." "Na yi murmushi, ta zo ta zauna kujerar kusa da ni, sannan ta kama hannuna ta sa mini awarwaraye da zobe. "Na gode Yasmin,ki je kuyi ta haƙuri kin ji ko, balle ma na san za ki samu kulawa sai na kawo muku ziyara." Nayi godiya, sannan muka yi sallama. Ai tunda muka shiga mota ban kalli inda ma yake zaune ba, saboda baƙin ciki,wai ni Yasmin ce yau ake tambulan da ni ga ɗa namijin da ba na ƙauna,wai har ba shi baki ake yi da lallashi a kaina dole ne in zo in tayi masa abin da zai ji haushi, har ya haƙura da ni,a raba auran don dole. Safiya na yi na sa aka kira mini jakadiya,na tambaye ta wa ke tsaran gidan yari? Ta amsa mini da Sarkin tsaron gida, na ce ta sa a kira mini shi, shi da mai kula da basu abinci, wanda ta ce mini sunanshi Ma'aji. Suna zuwa na umarce su da su shiga dafa abinci mai ƙyau kamar wanda suka san ana ci su dinga ba ƴan gidan yarin, kuma sau huɗu a rana. Da wadataccen ruwan sha, sabulun wanka,wanki,kayan sakawa, na tabbatar zan yi masu ƙyautar da ba su taɓa kawowa zuciyarsu ba, sannan tabbas zan iya kai masu ziyarar bazata,a duk lokacin da na so. A take na ce masu idan Yarima ya tambaya suna iya ce masa ni na saka su, na ɗaga filon ɗin da yake kusa da ni, na ɗauko bandir ɗin ƴan ɗari biyar guda huɗu na basu na ce su raba. Na kawo guda shida na basu na ce a siyi duk abinda aka san babu. Nan Ma'aji ya tabbatar mini aƙwai komai, ya ba ni labarin irin kayan abincin da ke gidan nan,ya tabbatar mini za su iya ciyar da mutanen Jos da ƙauyukansu har na tsawon shekaru goma, mai ƙyau mai daɗi. Bayan sati biyu ta cika ne,a daren ranar sai ga jakadiya da mace ɗaya tana biye da bayanta,a inda ta tsugunna ta gaishe ni. Ni kuwa ina kishingiɗe saman kafet ina hutawa su Mansura na gefena, ana ta ba ni labarurrukan ban dariya da nishaɗantarwa. Na ba ta iznin ta faɗi abin da ya kawo ta, shi ne ta ce Yarima ne ya turo ta tunasar mini na lokacin da na ɗiba ya cika, ta ajiye mini farantin hannun matar nan ɗaya,tana buɗewa sai na ga manya-manyan kaji ne har guda uku, na ɗan yi shiru na tsayin mintuna biyu, sannan na nisa. "Ki koma ki sanar da shi cewa ni ma na san lokaci ya cika, amma ko a wancan lokacin na baya, cewa na yi ƙila, saboda haka ki mayar masa da waɗannan kaya ki ce na ji saƙon shi, amma idan ya samu dama ina son ganin shi yanzun, anjima, gobe,ko duk lokacin da ya samu damar zuwa,ki gaishe shi." Ta ɗan ɗauki lokaci, sannan ta miƙe, shi ma kamar ba za ta tafi ba, na juyo na kalle ta. "Shi kenan." Ta tafi tana kiran,"To, to,ai ba gardama." Mun samu sama da awa uku muna hira ni da ƴan matan gidana,ganin sha ɗaya na dare ta yi yasa na sallame su,ni ma na nufi ɗakina, domin kayar da kafaɗata saman gado. Al'adata ce yin Sallar nafila kafin in ƙwanta bacci, sannan in kawo wutirina, wanda nake ƙin yi dama sai dare ya yi. Sam ban wani tsaya tunanin zuwan wani Yarima ba na haye gadona. Ƙarfe goma na safiyar juma'a na shirya tsab na fita,a inda na samu motocin da na bayar da umarnin a shirya mini su tun jiya. Motoci ne guda huɗu, ɗaya ta maza ce ƴan rakiyata, ragowar kuwa ƴan matana ne, ba wani waje za mu ba,illa gidan yari zan kai masu ziyara in ga ko ana yi masu yanda na umarta. Bayan na shiga mota ne, na hango Yarima saman barandar ɗakinsa yana kallona, tare da al'ajabin ganin yanda na danna kaina a mota, amma abin ka da sarauta,ko ya nuna alamar ya yi mini magana, balle ya tambaye ni ina zani. Na ji daɗi ƙwarai da gaske, yanda na ga mutanen gidan yarin nan duk sun fara ƙyan gani, duk da akwai rama a jikinsu, amma ni kaina na san ta ragu sosai, gaba ɗayansu aka tara mini su,a inda na yi masu ƴan nasihohi, sannan na ƙwantar masu da hankali da maganganu masu daɗi. Da ganin yanda suke nunawa ka san sun ji daɗi sosai,nan take na yi masu alƙawarin kawo masu ƙwararrun likitoci, domin a duba marasa lafiyarsu, da su kansu masu lafiyar, domin tabbatar da tasu lafiyar. Na ƙara jadadda masu cewa abinci mai ƙyau kuwa yanzun ma aka fara ba su. Sannan na ce masu za'a dinga fitar da su wajen wasanni, amma sai sun yi mini alƙawarin ba za su dinga guduwa ba,in kuma na same su da cika alƙawari,nima na yi masu alƙawarin wani abu, amma ba zan faɗeshi ba, sai idan lokacin ya yi. Bayan gama jawabina, na umarce su da su ja layi za'a raba masu wasu kayan da na zo dasu. Tun bayan goma na safe nake cikin gidan yarin nan, amma ban fito ba sai ƙarfe uku na yamma. Ina isa gida kuwa sai wanka, ban fi minti sha biyar da fitowa ba sai ga jakadiya ta russuna ta yi gaisuwa, sannan ta ce Yarima na son ganina,na bata amsa da cewa in ya shirya gani, ina nan a gida zaune. Ƙwana uku tsakani, amma ba Yarima ba dalilinsa, wannan ba ƙaramin tayar mini da hankali ya yi ba,shin wai haka za mu yi zaman auran? Tambayar da nake wa kaina kenan daga ƙwance cikin gadona, wanda tun da na yi sallar Asubahi nake cikinsa, har ƙarfe ɗaya na rana. Kuka kawai nake yi daga ƙwancan nan, Mansura suka shigo na sanar masu cewa ba na jin daɗi, ƙarfe biyu saura ƙwata na rana sai ga Yarima ya shigo har ɗakina, ina ƙudundune cikin bargo, amma ba ƙudundunar rashin lafiya ba, duk baƙin ciki ne yasa na kasa tashi in yi komai. Tsaye ya yi a bakin gadona, sai da ya ɗan ɗauki minti ɗaya, sannan ya cire gilashin fuskarsa,ni kuwa ina kallon shi da idanuwana masu fitar da hawaye. "Ni ban san ba ki da lafiya ba, sai yanzun, sannu da jikin naki." Ya ɗan yi shiru. "Da zaki daure ki ɗan saka kayanki saboda zan turo miki likita yanzu." "Ka barshi ma, na sha magani, zan samu sauƙi." Ya janyo kujerar tebirin rubutu a gaban gado, ya zauna, ya kalleni ina kukana, amma bai iya yi mini magana ba. Wannan zama kuwa ya ɗauke shi har wajen awa ɗaya, sai dai ya ce mini sannu sau ɗaya kawai. Bayan nan ya miƙe ya zo ya ɗan dafa goshina, wanda jijiyoyin kuka suka tashi a saman shi, ina kallo yasa ɗan ƙaramin hankici ya goge mini hawayena,amma fa ba tare da ya yi mini magana ba. "Zan dawo anjima." Ita kawai ya faɗa ya juya ya tafi abinsa. Haushi da takaici suka saukar mini a lokaci ɗaya, tare da tunano masoyina Anwar na san da shi ne, da naga ruɗewa a yau, amma shi ko a tsokar naman jikinsa ma. Sallamar da aka yi ta kai uku, sannan na amsa na bayar da umarnin a shigo,a inda nake ƙwancen nan. Na ga Aunty Salwa ta shigo, ban san lokacin da na miƙe da ihu ba na duro daga gado na taryeta,sai dariya take yi ita kuwa, bayan mun zauna ne take yi mini ya jiki. A inda ni kuma na tabbatar mata lafiya ta ƙalau,baƙin ciki ne ya yi mini yawa a zuciyata,amma yanzun tunda ta iso na warke, na ƙara gyara zama, na kalle ta sosai tare da riƙe hannuwanta, kafin bakina ya motsa har hawayen da ke cikin ƙwayar idanuwana sun gangaro a kumatuna. "Aunty gaskiya ni ba zan iya wannan zaman ba,ki gayawa Dad, ya zo ya raba ni da wannan rayuwar ƙiri-ƙiri mutum ya ce baya sona,ni ma bana son shi, amma an tursasa mu, sai mun yi zaman dole." Na ƙwashe labarin duk irin zaman da na yi na tsawon ƙwanaki ashirin da uku a gidan nan amma ba ruwansa da harkata. "A'a ba ruwanki da harkarsa dai,ai shi ba laifi,yana daurewa yana kula ki,ke ce mai matsalar,ni ba ma ruwana da wannan, tsaya in dawo ga haƙƙinsa. Shin kin san ba abin da yake ci ko sha?" Na girgiza kai. "Kin san a inda yake ƙwana,ma'ana a nan tsabtar muhallin shi?" Na kuma girgiza kaina. "Kin taɓa shiga ɓangaren sa ki gaishe shi ya nuna miki baya so?" "A'a, amma Aunty ai duk yana da masu yi masa." "Ba ruwana da masu yi masa,ai ke dai haƙƙin ki zaki sauke." "Ni wallahi Anti..." "Ke wallahi da me? Haba Yasmin ya ki ke so iyayenmu suyi da ransu,so ki ke su kashe kansu a kanmu?" "Aunty ki yi haƙuri abin ba na faɗa ba ne." "In baƙya son faɗa, to ki tashi ki yi wanka ki shirya jikinki,muje ki raka ni wajen Yariman mu gaisa." "Kai Aunty in je gidansa,ai Kamar na ma zubar da ajina ne, na dai aika a kirawo shi." "Sannu mai makaranta, saboda ai yanda ki ka ɗauki kan ki ma naga alama ya wuce aji, sai dai makaranta kawai. Wallahi idan ba ki ɗauki kanki da sauƙi ba, zaki sha wahalar rayuwar duniya,su waɗannan mutanen babu abin da Allah bai basu ba, sannan ina ki ka taɓa jin auran gidan sarauta na rabuwa? Da wahalar gaske. Sai dai su auro wata su ƙara,kina kallo ya auro wata ya yi zamanshi lafiya da ita." "Ni dai Aunty da zai sallame ni,ni ya auro huɗu ma a lokaci ɗaya, har ya haɗo da ƙwarƙwara ma." Nan take na ga ta daddanna wayar da ke hannunta. "Zan gayawa Daddy halin da ki ke ciki,in ya so shi sai ya san matakin ɗauka." Na yi saurin fizge wayar daga hannunta, na kashe. "Aunty ke daga wasa." "To tashi ki shirya." Dole ta sa na tashi gudun kada ran iyayena ya ɓaci a kaina. Riga da zani ne na wani yadi three in one mai ƙyan gaske, ruwan madara ne da dishi-dishin ruwan ƙasa mai duhu a jikinsa,zanan ya sha ado, kamar dai yanda ake yayi ( Wrapper Skirt ) yanzu,takalman da na sa a ƙafata kuwa masu kamar silifas ne (Flat) ruwan madara ne, sai mayafi kawai da na yafa a kaina, ban wani tsaya neman ɗankwalinsu ba, na feshe jikina da turare, amma ba wata ƙwalliya a fuskata, saboda sanyi ma da ake da ko mai ba zan shafa ba. Farar hoda kawai na gogawa fuskata, sai kuwa man leɓe da na sakawa laɓɓana. Jere muke da Aunty a inda na cewa su Mansura su jira in dawo. Muna isa ƙofar gidansa, mutane ne sun kai goma a zazzaune, suka yi saurin miƙewa suka kawo gaisuwa, muka amsa sannan muka wace ciki. Mutane ne su huɗu zaune a ƙasa suna ta hirarsu,falo ne shi ma ƙaton gaske, wanda ba zan iya cewa ga abin da ya ƙunsa ba, saboda farkon shigowa ta kenan, mutanen nan suka kawo mana gaisuwa, waɗanda zan iya kiran su dogarawa. Bayan mun zauna da minti ɗaya sai nake ce musu su yi mana magana da Yarima. *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 12 A take ɗaya daga cikinsu ya ce ai ba a hawa idan har yana sama, sai dai ni ina iya hawa. Na nuna a barshi in ya sauko ma dawo. Amma Aunty ta ce sai na hau saman nan, kamar wacce zata hadu da abin tsoro, haka nake tattaka matattakalar benen, saboda na fahimci yanayin zubinsu ɗaya da gidana. Duk inda na duba baya nan, har sai da na kai ga ɗakinsa. A hankali na murɗa hannun ƙofar gudun kada ya ji ƙara, na tura ta cikin sanɗa, sannan na yi sallama, amma shiru ba wanda ya amsa mini,sai da na kai tsakiyar ɗakin manufata in isa barandar gidan inda na fahimci ya fi zama. Kamar an ce in kalli gefen ɗakin, sai na ganshi ƙwance a ƙasa, ya yi rigingine yana bacci ba riga a jikinsa, sai dogon wando, na matso na tsugunna a hankali a gabanshi inda na ƙurawa halittar Allah idanuwa. Ƙyau kam gashi nan a ƙwance, a take sai na ji dama Anwar ne na samu a ƙwance nan, amma matsala ɗaya ita ce hannuwanshi waje ɗaya ya yi filo da su, da gani kuma ka san abu ne wanda zai iya wahalar da shi. Wai sai na tsinci kaina da son gyara masa, na miƙe zuwa gado na ɗauko filo, na iso na zauna dirshen, na zare hannuwansa a hankali, abin ka da gefe nake zaune, sai kawai na ga ya yi juyin da ya iso saman cinyata, ya sa hannuwa duk biyun ya zagaye ni. Kenan ya koma rub da ciki,a zuciyata na ce Allah ya ƙara mini,cikin ƴar dabara na samu na zame jikina nasa masa fili,wai sai na ji ina son taɓa gashin kan shi inji kowanne iri ne, a hannuna na ji wani irin laushi,dama na san hakan za ta iya faruwa, saboda baƙin gashin ya yi yawa, sai dai ba shi da yawa. Na miƙe a hankali na juya na tafi,a inda na samu Aunty na sanar da ita bacci yake yi,baccin kuma ya yi nisa, haka muka koma sashena muka ci gaba da hirarmu. Ƙarfe biyar na yamma na dinga haɗa Aunty da Allah a kan ta sa kayan wasa mu je muyi tennis a filin wasa. Siket da riga iya gwiwa na saka,farare ƙal, da ganinsu ka ga kayan wasa, saboda wuyan T.Shirt ɗin kore ne zagaye da ita, haka hannuwanta ma, sai bal ɗin matse gashi wanda na roba ne,koriyar safa ce amma farin kambos ne a ƙafata. Ita kuwa Aunty Siket ɗin ta har ƙasa yake, sannan ta ɗaura ɗanƙwalin wasa sai dai ita ma farare ne na wasa, na umarci su Mansura da su je su duba mana lafiyar filin wasan, sannan su isa da ruwa da lemo kafin mu isa, wanda tuni nasa an yi gaba da kayan wasan. Shigar da nayi ita tasa na ji ni tamkar an yi mini albishir da Aljanna, saboda samun kaina da na yi cikin farin ciki da nishaɗi,hakan yasa ma da guduna na isa filin wasan, saboda motsa jikina. Aunty kuwa ta biye mini ne kawai na san don dai ta ja ra'ayina in yi haƙuri in ci gaba da zama. Wasa kam ya yi daɗi, amma har yanzu ba wanda ya ci wani. Ikon Allah kuwa Allah ya ba ni Sa'a na ci Aunty,ban san lokacin da na dinga ihun murna ba, har da su tsalle. Kamar an ce in kai idona ga barandar Yarima, sai na gan shi a sunkuye ya dafa ƙarfe yana kallonmu, kallon da nayi masa ya kai na minti ɗaya sannan na juyo na yi tsaki,a inda ya ɗago mini babban ɗan yatsa,alamar yabawa da cin da na yi. Na kira Mansura na ce ta je ta kirawo min jakadiya ta amsa tare da tafiya da saurinta. Ban fasa wasan ba wai saboda ganin Yarima, sai dai jikina na bani kallona yake yi. Tsawon mintunan da ba su wuce taƙwas ba, sai ga jakadiya da saurinta tana zuwa ta zube gefena a inda ina wasana ina gaya mata saƙo. Saƙon kuwa bai wuce ta je ta cewa Yarima ga Antina ta zo in yana da dama za su gaisa. Gudu nake kada in ce yazo Aunty ta yi mini faɗa,ni kuwa ba na fatan ƙara zuwa sashinsa,lallai zance,ko kuwa tabɗijan! Ganin Yarima a filin da muke wasa, shi kaɗai da silifas a ƙafarshi,shin ina aka ajiye girman kan da ƘASAITAR, koda yake na lura a cikin gidan shi sauƙin kai ne da shi, tunda har yana ƙwanciya ƙasa saman kafet,ko filo babu. Cikin rawar jiki ƴan matan nan suka sunkuya suka gaishe shi. A idona cikin mintuna biyu na ga an kafa rumfar lema da kujerunta uku amma na (Cane) irin kan Nan mai lanƙwaso da tebir a tsakiya, wannan duk aikin wasu maza ne, waɗanda ban ga isowarsu ba, sai dai aikinsu kawai na gani. Mulki, na ce a zuciyata saboda ganin ga rumfar da aka tanada don hutawa, amma har sai da aka kafa masa wata. Mamaki yasa na yi tsaye na riƙe ƙugu da hannuwana duk biyun, ganin yanda ya gaishe da Aunty har da ɗan russunawa alamar girmamawa, yasa na dinga tunanin anya kuwa Yarima Faysal ne kuwa? Tambayar da nayi wa kaina kenan a daidai lokacin da na ga sun jera da Aunty suna tafiya zuwa ƙarƙashin inuwar lemar nan. Har sai da suka zauna, sannan Aunty ta yi mini maganar wai in zo,a lokacin ne ma hankalina ya dawo a jikina, na iso na zauna a tawa kujerar, wacce ke gefe ɗaya,hakan kuwa ya yi ɗaya da lokacin da wani mutum ya iso da farantin kayan sha,su lemo kenan, wanda gefensu kuma tufa ce (Apple) Hira sosai shi da Aunty. A cikin hirar na ji tana cewa, "Wai ranar da ku ka je gida Mamee ta gaya mini,cewa kun biya ta gidana ba ku same ni ba." A zuciyata na ce, Au! Ashe har gidanmu ake zuwa ba a gaya mini ba,neman shiga. Iska ta taso mai ƙarfin gaske, wanda zan iya kiranta da guguwa,jin yanayin wasu addu'o'i a bayyane yasa na yi mamaki, a inda ni kuma gashin kaina ya kaiwa gefen fuskarshi ziyara, yasa hannu ya cire shi a hankali,a inda ya ci gaba da magana da Aunty. "Aunty ki yi mata faɗa, ba ta son ɗaura ɗanƙwali ƙwata-ƙwata, tunda ta zo gidan nan ni dai sau ɗaya na ganta da ɗankwali, shi ma na san don gidanmu za'a." Ta juyo gare ni, "kin ji ki daina." "Aunty ba fa kowa a inda nake sai yaran nan su Mansura fa." "A yanda ki ke gani ba,ni ko jiya na ji cikin dogarawana wasu na yin fasalin ƙyan gashinki,kin ga kenan suna kallonki in kin fito." Maganar da yake yi mini kuwa tana nuna cikin jin haushi yake yin ta, na kalli Aunty, "Sai kin shigo Aunty." Na miƙe a fusace. "Yasmin zauna." Na ji ya faɗa. Na juyo na kalle shi sannan na kalli Aunty. Aunty ta daka mini harara na koma na zauna, amma sai na kawar da fuskata ɗayan gefen. "Aunty kin ga matsalar da muke ciki kenan ni da Yasmin ba yanda za'ayi in ce tayi abu ta yi shi, alhalin ta hakan za mu samu jituwa, amma na yi iya ƙoƙarina ina ƙasƙantar da kaina ina bin abin da ta umarce ni, yanzun kin ga an kusa ƙwana ashirin da ce mata ta yanke farcinan hannunta, amma ban isa ba." Aunty ta juyo ta kalleni, "Yasmin tashi ki shiga ciki ina zuwa." Na tashi cikin fushi na yi gaba, har sai da na yi wanka na shirya sannan Aunty ta shigo a inda ta same ni falon sama. "Yasmin,duk na fahimci matsalarku, ba ta wuce jiji da kai duk ya gaya mini irin yanda ku ke tafiyar da rayuwarku. Na ba shi haƙuri. Yasmin ya ce baki girmama shi,in ya aiko ki je, sai ki mayar da ɗan aiken da cewa ba ki zuwa. Ya nuna mini kina kunyatashi a gaban barorinsa,a nan ma kuma na gaya masa kin gaya mini aiken jakadiya ne baƙya so, ya ce yayi alƙawarin ya daina, sai dai ko aike na hidimar gida, yanda yake nuna mini ke ce mai matsalar kin rigaya kin sanya tsanar shi a zuciyarki. Haba ƴar ƙanwata, yanzun daɗinmu ne a ce mu dinga ɓatawa iyayenmu rai, kiyi tunani mana, wallahi na san Dad na kuma fiki sanin halayyarsa,kin ga saboda wannan matsalar,za ku iya mugun ɓatawa. Ba na mantawa akwai wata rana muka yi rigima ni da Abdulƙadir lokacin ina goyan Tahir kin ga bai fi shekara ɗaya da ƴan watanni ba kenan, rigima ta kai mu har gida,kin ga yanda Dad ya yi mini kuwa. Ke a takaice sai da na shekara uku Daddy baya amsa gaisuwata sosai,in ma na samu ya amsa, balle faɗan ni ce banida gaskiya. Kinga kuwa a nan ke ce ba ki da gaskiya, duk da nasan ba ƙya son shi, amma ai shi Dad gabansa kin nuna za ki zauna da mijinki lafiya." Nasihohi da faɗa su Aunty ta dinga yi mini,a inda ni kuma ba ni da wata maganar mayar mata sai kuka. Kai a ƙarshe na ce mata. "Aunty ba na son shi,bana son shi, shi ma fa baya sona, jiki na kawai yake wa ƙwadayin ya samu Aunty." Cikin kukana da mayar da kaina saman kujera na ƙwanta, Aunty ta ɗago ni ta rungume a inda ta gaya mini maganganu masu ƙwantar da hankali, sai da taga na ɗan samu kaina sannan ta tashi ta shiga wanka,a inda sallar magriba ta kawo jiki. Bayan sallar magriba ne, sai ga Uncle ya zo ɗaukar ta, sai dai kawai muka gansu sun shigo tare da Yarima,mu kanmu mun yi mamaki, sai dai kuma tunanin gidan da ake tsaron shi kamar wannan gida, dole ne a san mai shiga da fita, har mota muka raka su Aunty Salwa,ni da Yarima muna tsaye dakarunsa guda biyu suka buɗe but ɗinsu Aunty suka sa musu wasu kaya, ban san ko su meye ba. A daren ba a ƙwana ba, na ga masu aiki na ta haɗa wata waya a cikin gidana, wacce na ga an liƙa wani ƙaramin jan abu a falon ƙasa, haka a falon sama. Ni dai iyakaci na idanuwa, sai da ma suka gama, ana gwadawa a ga in ya yi,jin ƙarar shi yasa na gane Inner caller abin da ake kiran mutum idan yana nesa. Ƙarfe sha ɗaya saura ƙwata na dare na ji ƙararrawar nan ta yi ƙara, doguwar rigar bacci ce a jikina tare da ƴar samanta, mai ƙyan gaske, har na kallu ba zani ba, saboda na rigaya na yi shirin ƙwanciya, amma tunanin abin da muka yi da Aunty yasa na ɗauki doguwar alkyabba na ɗora ta sama, sai ɗanƙwalinta na rufa a kaina. Gaskiya aƙwai tsoro fita a wannan lokacin, don dai ma ko'ina gidan fitila ce tamkar da rana ne, ƙasan falonshi ba kowa, sannan fitilu duk a kashe suke, sai ƙwaya ɗaya, wacce ta bayar da kalar duhuwar haske na mayar da ƙofa na rufe kamar yadda na ganta. Falonshi na sama ba kowa, sai duhu ne a tare da shi, ba wata fitila ko ɗaya, cikin jin haushi na tura ɗakinsa na shiga, tare da sallamata. Fitilar gefen gado ce kawai a kunne, amma ban ga kowa ba a cikin ɗakin,sanin zuwan da nayi da rana na same shi ƙasa ƙwance, yasa na dinga kallon ƙasan ɗakin, amma ban ga kowa ba. Wucewa na yi barandar shi inda na san ya cika zama, shi ma baya nan, na leƙa kaina ƙasan barandar, amma ban ga kowa ba, sai ma na ji tsoro ya kama ni da baya da baya na dinga tafiya,wai ni gudun kada in juya wani abu ya kama ni,banyi aune ba sai kawai na ji nayi karo da wani abu ta bayana, kafin in yi ƙoƙarin juyowa sai na ji an rungume ni gam,an sa gefen fuska a tawa fuskar. "Yasmin gani nan." Ya faɗa cikin muryar raɗa a hankali na bi na zame jikina,a inda na bi ta gefensa na wuce na zauna kujerar kusa da ni, wucewa ya yi saman gado ya zauna, sannan na ga hasken fitila ya gauraye ɗakin. Maganarsa a hankali take fita, "Dama kirawo ki na yi saboda ina jin yunwa, don Allah ki sama mini wani abu in ci, ko da shayi ne." "Ina kicin ɗin?" "Yana ƙasa." Na miƙe na nufi ƙasa, lokacin da na ji jikina ya yi mini sanyi. Firji na gani, ina buɗashi na ga cike yake da kayan kicin,alayyahu ne,nama,salat,tumatirin gwangwani,kai tarkace na kicin dai gasu nan birjik. A nan take na yi tunanin haɗa masa salat, na kuwa cire mayafin da na yafa a kaina na ajiye gefe ɗaya, haka alkyabbar saman kayan baccina, cikin ƙanƙanin lokaci na gama yanka salat ɗin,ƙwai kawai nake jira ya dafu, madadin in tsaya haka nan sai na yi tunanin haɗa masa matsatstsan lemo da abarba. Miser ta matse lemo nasa na matse shi, abin ka ga na'urar bature, haka kuma injin ɗin markaɗe na bature ya markaɗe mini abarba (Blander), rashin sabo da dogayen kaya yasa na ji rigar saman na damuna, amma dole haka na haƙura da ita. Bayan na tace su ne, na samo ƙanƙara na jefa a cikin ɗan siririn dogon kofin da na gani mai murfi yalo (jug), shuga ɗan kaɗan na saka masa na ga ƙatuwar ƙwalbar fulebo, ta sitirober (Strawberry). "Sannu da aiki." Na ji an ce daga bayana. *ƘASAITA BOOK 1* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 13 Na yi saurin firgita na nufi inda alkyabbata take na ɗauka na saka ta. Farar singilet ce a jikinsa da dogon wando, wannan yasa ban ƙara juyawa na kalle shi ba, duk da dama jingine yake a jikin ƙofar shigowa ya harɗe hannayensa saman ƙirjinsa. "In kin gama ina sama." Ban amsa ba ni dai na ƙagu in gama in koma in ƙwanta. Ƙarfe sha biyu da mintuna goma na kammala komai, cikin tangarayen nan nasu na sarauta a ciki na haɗa masa haɗin salat ɗin, na jera a wani ƙyakƙyawan faranti. Ina shiga ɗakin nasa yana ƙwance a ƙasa kamar yanda na same shi da rana, na iso kusa da shi na ajiye kayan, ya tashi zaune. "Za ki ci?" Na girgiza kaina. "To na gode, shi kenan dama,mu je in rakaki." Na miƙe na fara yin gaba, zuciyata ta cika dam da daɗi. Ina tafe yana biye da ni har ƙofar gida ta ƙasa, na juya na kalle shi. "Mu je in kai ki gida ko,ko baƙya jin tsoro?" Ban dai samu yin magana ba. Yana bakin ƙofata ya dafa ta,ni kuwa ina daga cikin gida na riƙe ƙofar alamar zan rufe, ganin yana murmushi yasa na tsaya ina kallonsa. "Na gode Yasmin,sai da safe kin kawo mini karin kumallo (Break fast)." "Nima ba ni nake yin karin kumallo ba, yi mini ake yi." "Ina son ci haka nan." Sai naga yana leƙen bayana, na ga ya ƙara zare idanuwansa. "Me ye?" Na tambaye shi da sauri. "Kamar wani abu ne tafe a bayanki." Sai na yi saurin sakin ƙofa na fito da niyyar in waiga in ga ko meye, sai na ga ya yi ƴar dariya. "Ba komai zolayarki nake yi, saboda kin ƙi yin fara'a." Na ɗan yi murmushin dole, na koma cikin gida, sannan ya juya ya tafi,ni kuwa na kasa rufe ƙofar da take riƙe a hannuna, ina ta bin shi da kallon mamaki. Har sai da ya juyo ya ɗago mini hannu, sannan na mayar da ƙofa na kulle da gudu na haye sama saboda tsoro. Ina isa madadin in ƙwanta sai na cire kayan saman rigar baccina, na buɗe ƙofar gaban gidan na fita baranda na runtse idanuwana na ware hannayena duk biyun iska na ɗaukan gashina a hankali. Babu wanda ke zuciyata sai Anwar,son shi da ƙaunarshi suka dawo mini sabo a wannan daren,shin ko dai dama yaudara ce Yarima ya yi mini yanzu gashi nan ya tunasar da ni masoyina. Na tuna wata rana da Anwar ya zo gidanmu zai tafi, na yi masa rakiya, har ya zauna kujerar motarsa sai na ga ya miƙe tsaye, mamadin ya yi magana, sai na ga ya matso kusa da ni sosai. A hankali ya ce, "Kalli ki ga yanda bishiyoyin nan ke rausayar jin daɗi, saboda sun samu ni'imtaccen wajen ƙwanciya." Ya kawo hancinsa gab da nawa, sai na ji ya ce, "Haka muma wani daren za mu samu ni'imtaccen maƙwanci." Idanuwana a lumshe ina ji ya sumbaci wuyana, yanda tsigar jikina ta tashi a wancan lokacin, haka na ji ni a yanzu. Mamadin inji farin ciki, sai na ji lemar hawaye na gangaro mini,saboda tunaninmu ya zama mafarki,ko a wane hali yake ciki yanzu? Tunanin da nake so in kawar a zuciyata,amma sai nema yake ya haye mini,wai tunanin Yariman da yake babban maƙiyina na yi tsaki a daidai lokacin da na tuno ni bayana ƙwance a ƙirjinsa. "Allah ya saka mini." Na faɗa tare da buɗe idanuwana, na shige cikin gida, har na kama ƙofar gidan zan rufe, sai na hango Yarima a barandarsa yasa hannuwa a aljihu yana kallon sama, na yi saurin mayar da ƙofata na kulle. Abin ka ga ƙofa mai gilashi ce, sai na ɗaga labulan na leƙo yanda na barshi haka yake, na yi tsaki na wuce na yi ƙwanciyata. Bacci zo mana, amma kamar an busar mini da idanuwana,ko me ye dalili? Oho, na mutstsuke idanuwana tare da runtse su na yi lamo, amma babu alamar bacci a idanuwana. Ni kuma na kasa sanin me ya hana ni yin sa,a zuciyata na ji ina so na ƙara leƙawa in ga yarima ya shiga ɗakinsa ko kuwa yana nan a tsaye. Shin dama haka yake yi ko kuwa yau ne kawai? Na miƙe na je na ɗaga labulan ƙofata,yana nan a tsaye, amma yanzu ya ɗan sunkuya ya dafa ɗan abin barandar wato gilashi mai zagayen nan. Taɓe baki na yi na koma, meye dalilinsa na ƙurawa dakina idanuwa,ko yana nufin nima irin sa ce mai tsayuwar dare, haka na faɗa gadona na tura kaina a ƙarƙashin filo, sannan na ɗan samu nutsuwa. Ƙarfe goma na safiya na samu na farka daga saman gadona. Baccin bayan sallar Asubahi da na samu na yi ta da ƙyar, shi ma na san saboda kiran sallar masallacin cikin gidan shi yasa, wanda ake yin shi tamkar a ƙofar taga ta. Na samu tsayin awa ɗaya, sannan na fito falon ƙasa,wayata da ke rataye a hannuna ita ce ta ɗauki ƙara, ina karawa a kunnena, sai na ji an ce. "Ina jiran Gimbiya in ta tashi,abincina nake son ci." Sai a lokacin na tuna da ya ce yana cin abincin gidan na safe, na taɓe baki a lokacin da na isa ɓangaren da nake yin karin kumallo. Su Musulma na zazzaune suna jirana, da sauri suka miƙe suka miƙa gaisuwarsu,a inda na zauna na bubbuɗe abin da su Asiya suka girka mini,kunun gyaɗa ne mai ɗauke da lafiyayyar madara, tare da farfesun dagwargwajajjan naman kaza, wanda babu ƙashi ko ɗaya a jikinsa, gefe ɗaya kuma biredi ne wanda aka yi shi da faɗi, tamkar an yayyankashi. Ban da kunun aya wanda mutumina ne,ni na ce kullum ina buƙatar a dinga yi mini shi, amma mai kaurin gaske, cikin wata tangaran doguwa kuma tsire ne ya sha kayan haɗinsa sai ɗaukan ido da hanci yake, gefe ɗaya kuwa sinasir ne shishshimfiɗe a ƙwanan tangaran. Na umarci su Mansura da su samo farantai su shirya su,su kai gidan Yarima su ce ga ni nan zuwa, haka aka yi. Ina shiga na same shi a sashen cin abinci ya kishingiɗa,siket da riga ne na atamfa ƴar Holand a jikina, ɗinkin mai shaf ne (fitted), amma buɗaɗɗan wuya da dogon hannu ne, sai mayafi ƙarami da na lulluɓe kaina da shi. Atamfar Koriya ce da ɗishi-ɗishin zane baki a jikinta, wanda takalma masu tsini ne a ƙafata,su kuma baƙaƙe, haka mayafin saman kaina. Daga kishingiɗan nan da yake bai tashi ba, har sai da na zauna tukunna ya tashi ya zauna. "Barka da Asuba." Na ce masa. "Kin tashi lafiya?" Na yi murmushi, "ga ni kuwa kaga alama." "Ya jikin naki?" "Ya warware." Na ɗan yi shiru, "Ka yi haƙuri don Allah na manta ne da tuni an kawo maka,ni kuma ban tashi da wuri ba." "Ba damuwa,ni ma ban daɗe da tashi ba,yau da ƙyar na je masallaci sallah saboda bacci, throughout jiya ban samu bacci ba na rasa abin da ya hana ni bacci. "Jin daɗi." Na bashi amsa. Ya yi ɗan murmushi, "ina fa jin daɗi ga wanda ba shi da mata." Ya faɗa a daidai lokacin da ya rage sautin muryarsa, na ɗago kai muka haɗa ido da shi, sai na ga ya yi murmushi tare da lumshe idanuwansa tare da buɗe su. "Ko zaki amince ki zama matata,ki kawo mini jin daɗin?" Na girgiza kaina tare da miƙewa tsaye. "Zan tafi ni." Na faɗa, amma sai na tsinci kaina da canjawar murya. "Kayan abincin jiya na ɗaki,ko za ki fito da su,dama ni mai gata ne, da an gyara mini ɗakin nawa yau ɗaya dai." Ban ce masa komai ba na wuce abina. "Ɗinkin ya yi miki ƙyau." Na ji ya faɗa a lokacin da na juya na tafi,a zuciyata na ce ka ƙari kinibibinka ni dai ba zan taɓa zama tare da kai ba,mayaudari,in ji da kunnena ka ce ba ka sona, sai yanzun don an hana ka zuwa wajen ƴaƴan turawa, shi ne za ka dinga kashe mini muryar kinibibi. Na gangaro na ajiye kayan kicin na yi gaba, zuwa gidana. An samu ƙwanaki shida kenan yanayi mini ire-iren waɗannan tsirfar, ban da kallo da yake bina da shi, idan ina zaune a saman dutsen da nake hutawa, amma ko da wasa ban damu da abubuwan da yake yi ba, wani lokacin ma haushinsa nake ji, sai dai kuma abu ɗaya da ban gane shi ba, shi ne idan ina tare da shi duk jikina sai ya yi sanyi,ko magana ba na son yi. Kuma idan na san yana waje a zaune, zan ga ina yawaitar kallon wajen,ko me ye haka kuma? Ni dai na san ina yawan tunanin Anwar wanda nake ta mafarkin ya zama angona,shekaru huɗu kenan, amma yau rana ɗaya mafarkina ya zama dirama. Na wayi gari da safe, ranar cikon kwanaki taƙwas, wanda ya zamo daran jiya muna tare da Yarima har ƙarfe ɗaya na dare,wai dole sai na tayashi hira,a irin zaman da muke yi ne a falo talabijin na ta aikin yin hidimominta, wanda hasken da ke fitowa ta jikinta shi ne kawai hasken falon saman da muke zaune. Cikin mintuna biyar hankalinmu ya koma ga wani fim da suke yi wanda yaro da yarinyar fim ɗin suke zaune suna hirarsu, kamar dai mu sai naga yaron ya miƙe ya iso inda take zaune ya tsugunna daga nan ya yi mata wata magana wacce ta ƙunshi aure. "Za ki aure ni, Please." Sai na ga yarinyar ta ɗaga kanta tare da riƙe hannunsa ta tashi tsaye da sauri. Abin ka ga marasa kunya sai suka kama tsotsan bakin juna, ta wutsiyar ido na ga Yarima ya ƙura mini ido. Ɗan minti ɗayan nan da na yi ina kallon Yarima ta wutsiyar ido, sai kawai na ji takun kiɗan talabijin ɗin ya canja kallon farko ban ƙara maimaitawa ba, na miƙe jikina na rawa ko sallama babu na sauko da saurina, sai gidana. Ina isa gadona na faɗa sai kuka. Anwar na dinga kira da ƙarfi, saboda shi ne mutumin da yake ƙwance a zuciyata. Ko da wasa ban yi zaton Yarima zai biyo bayana ba, asali ma ban ji ya shigo ɗakina ba, sai dai jin an zauna gefen gadona na ji anyi, na ɗago da sauri,dama fitilar gefen gadona ƙwaya ɗaya ita ke kunne,ido muka haɗa da shi. "Wa ye Anwar Yasmin? Ina ƙoƙarin in ga na mallaki zuciyarki da gangar jikinki gaba ki ɗaya, ashe duk ban sani ba da wanda zuciyarki ke ƙauna, na yi da na sani a yanzun da nine na fara sakar miki jikina, saboda samun ƙwanciyar hankalin junanmu." Ya miƙe tsaye yasa hannuwansa a aljihun wandonshi, wanda dama T.shirt ce a jikinsa, tsayuwar da ya yi zata kai ta mintuna taƙwas, sannan ya juya ya tafi. Tabbas ban ji daɗi ba, ban kuma so a ce yajini ina ambaton sunan masoyina ba. _To masu karatu sai mun hadu a littafi na biyu, wanda tare suka fito._ _Taku har kullum: Maryam Kabir Mashi_