*ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 1 buloga.com.ng Ƙwana na yi ina juyi gudun kada ya je ya sanar a gidanmu, saboda na ga alama ba shi da kunyar kai ƙara, tun da ya kai ƙara ta ga Aunty. Ganin an wayi gari lafiya, shi ne na yi wanka na saka kayana doguwar riga ce mai ruɓi biyu, ƴar Saudiyya za mu iya kiranta ko Dubai. Na fito daga gidan ko ɗankwali babu kaina na nufi bakin dutsen da nake hutawa na yi tsaye. Lokacin kuwa ya nuna ƙarfe taƙwas na safe kawai wanda na ce na yafewa su Mansura rakiyata,ko kalaci ban tsaya yi ba. Ina tsaye nan ina ta saƙa abubuwan da na san ba zan samu ba,wato Yarima ya ji haushin maganar jiya ya ce ya sauwaƙe mini inje in auri Anwar, na ɗaga kaina jikin barandar ɗakinsa, sai na hango shi zaune a kujera ya ɗora ƙafafunsa a saman tebir ɗin gabansa. Na juya abina, sai ma na tattaka na haye dutsen, tsayin minti sha biyar na yi sai na ji ina sha'awar shiga ƙoramar nan,ta hanyar tattaka duwatsun da aka jera layi da su, waɗanda suka yi cikin ɗan dajin inda ruwa nan ke nufa,su kuwa duwatsun babu ruwanka da taɓa ruwa idan dai har ka sa ƙafarka a kansu. Nan take na saɓule takalman da ke ƙafata, na sulala cikin ruwan inda na dinga taka duwatsun a hankali, na yi tsaye a wurin ina ta waiwaigawa sai na hango barandar Faysal,ai kuwa juyawar da zan yi ina tsaki, sai na ga wani ƙaton miciji ya nufo inda nake tsaye, ta cikin ruwan nan kanshi a buɗe yana ta huci ban san lokacin da na yi baya da sauri ba ina ƙwalla ihu. Cikin ƙanƙanin lokaci ya tari gabana babu zancan iya motsi a yanda na ga yana hucin. Runtse idanuwana na yi na dinga ƙara,tun ina ƙarar har ya kaini ga kiran Yarima. Saman ƙafata ya kai wa sara, sai dai naji gab,na yi wata irin ƙara, na buɗe idanuwana, sai kuwa na hango Yarima Faysal a guje shi da wasu a bayansa. Sai na dinga cewa, "Maciji! Maciji!! Bai wani tsaya tattaka duwatsun nan ba sai dai kawai na ganshi da gudu a cikin ruwan, wanda ganin da nake masa dishi-dishi ne, daga nan kuwa sai dai na dinga jin maganganun mutane sama-sama, sai kuwa ji na yi ana jijjiga ni da kiran sunana da nake jin ana yi. Ina jin ƙasa na juyawa da ni, sannan ina ji sama-sama Yarima na daka masu tsawa zan iya cewa ɗaukata ya yi cak ya koma gudu, amma daga nan ban ƙara sanin komai ba. A hankali na dinga motsa idanuwana,alamar ina son buɗe su, ina cikin haka na ji Yarima na kiran sunana. "Yasmin! Yasmin!!" Sai na ji yana dafa goshina. "Ta motsa?" Na ji an tambaya. "Eh,tana motsa idanuwanta." Na samu tsayin minti biyar a haka, amma na kasa buɗe idanuwana, amma ina jin abin da ake faɗa. Jin abu mai sanyi a goshina, shi ya ƙara taimaka mini na ji hular idanuwana ta saki daga nauyin da ta yi mini, idanuwana Faysal suka fara gani zaune gefen gado,yana ɗora mini abin nan mai sanyi da nake ji, sai na ga ya yi saurin jefar da shi ya ɗago kaina ya rungume a ƙirjinsa, ya yi wata irin ajiyar zuciya. Sannan na ji ya ce, "Ta tashi." Ya mayar da ni ya ƙara gyara mini ƙwanciya,sannan ya sumbaci goshina, bayan nan kuwa mutane suka dinga leƙowa suna yi mini sannu, idanuwansu kuwa jajir kamar suna ciwon idon Afolo. Da ɗaiɗaya duk na fara gane fuskokinsu, amma matan,mazan ban san kowa ba,gwara ma ƴan na kusa da shi da ba su fi Biyar ba, ƴaƴan ɗakina kuwa har wannan lokacin kuka sukeyi. Bayan kamar minti sha biyar duk suka fita,a inda Yarima ya miƙe shi ma ya ɗauki wayar hannu, ya fara daddannawa. "Barka da yamma,eh, yanzun za ta yi minti ashirin, Eh, tana gane mutane, a'a ban duba ba, to yanzun zan duba. To sai kun zo,Mama da wuri don Allah yanzun ko, to zataji." Ya juyo ya yi mini murmushi. Sannan na ga ya cigaba, "Barka da yamma, eh, Yarima ne. Eh,Mamee, yanzu ta yi minti ashirin da ɗaya,a cewa Daddy ya zo yanzun ta gan shi. To Mamee ai kamawa ta yi,to, to zataji, to sai kun iso, to a huta lafiya, eh tana ƙasa, eh, na san yanzun zata hayo,kin san ƙwana biyu bacci ina jin bacci ne ya ɗauke ta,a ɗakin ƙasa, to za'a taso ta, mungode." Ya dawo ya zauna gefena ya matso kusa da ni sosai, sannan yasa hannunsa ya shafa gashin kaina, ya ƙara gyara mini gashina zuwa gefe, "Sannu." Ya ga dai ban amsa ba, sai na ga ya juyo sosai. "Yasmin,kina jina? Yasmin?" Sai na ɗaga masa kai, sai na ga ya ɗan mayar da numfashi tare da lumshe idanuwa, ya yi saurin kai min sumbata a kumatuna. Ya tashi a hankali sai na ga ya buɗe bargon da yake lulluɓe da ƙafa ta, sai a lokacin na tuna da cewa fa Maciji ya sare ni, nayi ƙoƙarin motsa ƙafar, na ji ta kamar dutse, ina kallo ya ɗaga ƙafar tawa a hankali, yasa hannu ya ɗan shafe ta. "Ƙafar ta mutu ko Yarima?" Na faɗa da muryata irin ta marasa lafiya. Ya rufe ya zagayo ya kama hannuna tare da zaunawa a gefena, wanda ƙafarshi ɗaya ya ɗago ta duka ya lanƙwashe ta har sai da gwiwarsa ma ta ɗan hau saman cikina. "Bata mutu ba,za ki warke sosai ma." Ya sumbaci hannun nawa,a take sai na ji tausayinsa ya kama ni. "A kawo miki abinci za ki iya ci?" Na girgiza kai. "A'a,zaki ɗan ci ko yaya ne,ko abu mai ruwa ne." Ya miƙe. "Bari inyi miki burush(Brush)." Da saurinsa ya fito daga banɗaki da burushi na a hannunsa wanda saman shi ke cike da makilin, da ruwa a ƙaton kofi da wata silba a hannunsa, ya ajiye su gefen gado, sannan ya hayo gadon gaba ɗayansa, ya ɗaga ni ya jera filallika guda uku a bayana, na ɗago sosai, ya janye bargon jikina ya mayar da shi iya ƙuguna, ya gyara shi sosai, sannan ya sauka ya ɗauko kayan ya ɗora silbar a cinyata. Ya kanga mini kofin a bakina, "Kuskure bakin tukunna." Na kurɓa, ya yi saurin ajiye ruwan a durowar gefen gadon, sannan ya ɗago silbar. "Zuba a nan." Na zuba sai na ga jajawur yawun bakina, ga ɗoyi yana yi, kunya ta kamani, amma na ga shi bai nuna alamar ƙyanƙyamina ba, ya ƙara bani ruwan na kurɓa, na ƙara kuskurewa ya ɗago na juye. Ya ɗauko burushin na ɗago hannuna na riƙe, "Zan iya." "A'a, kada ki wahala fa." Bazan wahala ba." Ya ƙura mini idanuwa,sai ya lumshe su tare da yin murmushinsa, ya buɗe idanuwan tare da girgiza kai. "No Yasmin, jikinki ba ƙarfi, ki yi haƙuri in kula da ke har ki warke,kina ga ya dace in bar yaran can su dinga kula da ke, alhalin ƙasa suke da ni, amma su ga wani ɓangare na sirrin matata? No,no,is not possible." "Wallahi zan iya." Ya miƙo mini burushin. "Na amince da ke." A hankali na dinga gogawa, saboda jikina babu ƙarfi sosai, amma duk da haka sai da naji na gaji sai da na ɗan tsaya hutawa, ya yi murmushi ya karɓa ya ƙarasa mini. "Ya sunan ɗaya daga cikin yaran gidanki?" "Mansura ko Muslum." Ya miƙe da hanzari ya ajiye kayan a ƙasa ya leƙa barandar cikin falo, ya kira Mansura, da gudu ta hayo,a inda shi kuma ya dawo ya zauna. Ya umarce ta da ta ɗauko masa mango juice a firji,ta tafi cikin saurinta, shi kuma ya shiga banɗaki da kayan ƙazantar wanke bakina a hannunsa. Ko fitowa bai yi ba, sai ga Aunty ta ce, "Lah! Ina Yarima, bari in gaya masa kin tashi." Sai ga shi ya fito. "Ta tashi?" "Ta ɗan jima, abin da yasa ban ce a taso ki ba,ganin kin samu bacci shi yasa." Ta iso ta zauna gefen gado. "Ya jiki Yasmin?" "Da sauƙi." Nan suka ci gaba da zama ita da Yarima, har sai da ya ga nasha mango juice ɗin nan sannan Aunty ta matsanta masa da ya je ya yi koda wanka ne, da ƙyar ya amince. Bai fi mintuna goma da tafiya ba, sai ga Mama ta iso, cewa take, "Barkanmu, barkanmu Yasmin,tare da Sarki muke yana ƙasa,kin san abun mata, shi ne na hayo in ga yanda ku ke tukunna." Ta juya ta yi baya, sai ga su sun shigo tare da Sarki tun da ya shigo na ga fuskarsa cike da walwala. Sarki ne har gefen gadona,yana ta jinjina abin da ya faru, Mama ta ɗaga bargon da suka lulluɓe ƙafata, suka kalli ƙafar. "She will be alright." Sai ga yarima da saurinsa. Doguwar riga ce a jikinsa har ƙasa ta ƴan Saudiyya, wacce ta sha aiki tun daga samanta har ƙasa da wandonta da hula kalar ruwan madara da takalman ƙafarshi kalar hular. Yana shigowa ya zauna har ƙasa ya gaishe da Sarki, da mahaifiyarsa,yana sunkuyar da kai irin na girmamawa, amma sai na ga Sarki ya ɗan ɗaure fuska,Yarima na ɗagowa, sai na ga ya yi mini ƙyau,wanda ban taɓa gani ba a fuskarshi, na ƙara kallonsa, sai na ga fuskarshi tana ƙara sheƙi. Na juyar da fuskata gefe, saboda tunanin ko shaiɗan ne ya ƙara ƙayata mini fuskarsa. Ranar kam naga jama'a, sai yiwa Yarima barka ake yi, madadin a yi mini. Su Mamee ma da aka zo,ai ta Yarima ake yi bata ni ba,ni kuwa madadin inji yana ba ni haushi kamar baya, sai na ji ina jin daɗi yadda yake nuna ai ya shiga tashin hankali, a inda yake baiwa masu zuwa labarin ƙwanana biyu kenan da suma haka ban farfaɗo ba sai yau. Anan na samu labarin ashe har ƙwanaki na yi a ƙwance,lallai dole bakina ya yi ɗoyi. Ƙwanana huɗu a ƙwancan nan, amma duk wata kulawa da ake nema, tabbas Yarima na ba ni ita, har ma wacce ta fita,a inda tunda ƙwana biyu ya ce Aunty ta tafi gidanta ta ƙwana ta ji da yaranta. Tun ban ɗaukar abin da Yarima ke mini da sunan so, har zuciyata ta amince lallai ya kamu da ciwon sona, ciwon da na lura ya riga ya yi masa katanga a zuciya,ni dai bana cewa ina son Yarima, amma tsanar da nake nuna masa a baya, yanzun bana iya yi masa ita. Da la'asar wacce ta cika ƙwana huɗun sai ga Mama, bayan gaisawarmu ne, na ga sun fita falon sama da yake labulan shara-shara ne tsakanin ƙofata da falon, shi ya bani damar ganin abin da ke faruwa a tsakanin Yarima da Mama. Shi ne na ga ya durƙusa ƙasa yana yi mata magana, amma bana jin maganar, sun ɗan ɗauki mintuna sha biyar sannan ya shigo. "Yasmin can gida zan tafi da ke domin yi miki magani sosai,kin ga can an fi samun magani,a yanzun haka ma Sarki ya tura a ɗauko wani mai magani a ƙauyen Bukuru." Na washe baki alamar na ji daɗin maganar da ta faɗa, amma sai na ji jikina kamar bai amince ba, sai dai kuma ba zancen gardama a tsakaninmu,ɗaga kaina da nayi na hango Yarima jingine a jikin bangon shigowa ɗakina, shi yasa na ji tausayinsa ya kama ni. Ya iso wajen Mama jiki a sanyaye, ya durƙusa ƙasa ya kama hannuwanta. "Mama, wallahi ina kulawa da ita,ki tambaye ta ki ji, Yasmin ba ina kulawa da ke ba? Mama a nan fa nake ƙwana a wajenta, Mama ki bar ta wallahi zan kula da ita sosai, zan fi dama." "Wai kai meye na damun kanka ne a kanta, kai ka ce mini baka son...." "Mama kada ki faɗa, wannan a da ne,shin ba cewa na yi ƙwata-ƙwata ba." "Ka ga an gama magana, sai dai ka yi haƙuri." Ta juya ta kalleni. "Zan tafi da ke yanzun,su wa za'a kira su shirya miki kayanki?" "Mansura." Na bata amsa. Ta kalleshi, "Kirawo Mansura a falo babba." Ya ce to, ya miƙe ya tafi. Saman kujera doguwa yake zaune a babban falo, ya ƙwanta jikinta sosai, da gani ka san cikin damuwa yake, ya ɗago ya kalleni a daidai lokacin da ake saukowa da ni sai na ga ya yi murmushi. "Ina nan zuwa anjima." Haka kawai ya faɗa,mu kuwa muka wuce. **** **** ***" Lallai kam na ga gata, na tabbatar da cewa iyayen mijina na ƙaunar ɗan su, shi yasa ƙaunar ta shafe ni,a nan na ƙara yarda da cewa sarauta abin ƙauna ce, ga wanda bai shige ta ba ne yake ganin tamkar aikin bauta ake a cikinta. Yanzun kam ni da kaina zuciyata da sauran jikina suna ƙaunar sarauta, saboda ganin yanda take tafiya cikin tsari da nunawa jama'a ƙauna ta gaske. A wannan zaman ne ma na san wa ye Yarima da iyayensa. **** **** **** Yarima fari ne,ƙyakƙyawan gaske wanda dirin jikinsa na cikakken namijin da ya amsa sunansa, wanda gashin bakin fuskarsa ya ƙara ƙawata fuskar tasa, amma shi farin shi ja ne, tamkar na Turawa, idanuwansa kuwa sun ɗan yi girma kaɗan, tamkar na Salman Khan ɗan ƙasar Indiya. Sai dai shi zamu iya kiran ƙirar jikinsa irin ta Turawa, da ganinsa dai ka ga (Handsome). Tabbas ya cancanci sunansa, wato FAYSAL. Su biyar ne kaɗai ƴaƴan Sarki. Yarima shi ne babba, sai ƙannansa huɗu, amma mace ke bi masa Salimat, ita ce matar ɗan Sarkin Wasai, wato ƙaramar hukuma ce a Jos,sunan mai bi mata Idris,saurayi ne yana karatu a London, sai Sauda wacce take aure a Mina,sai autansu Ahmad. Yarima za a iya kiransa ɗan shekara talatin da biyar, ya yi karatunsa ne a Greece tun yana ɗan Sakandire aka kai shi ya karanci hulɗa da jama'a Public Relations. Ba wai domin ya yi aiki ba, a'a don dai ya iya zama da jama'a da riƙe gari, idan ya zamana ya hau mulki. Matan Sarki biyu ne, amma mahaifiyarsu Yarima Hajiya Mariya, ita ta haifesu su uku, shi da ƙannansa, da Idris da Salimat, amma Sauda ƴar ɗakin Hajiya Khilishi ce ita da Ahmad wanda yanzu yake makarantar gaba da Primary. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 2 Ko a ido ka ga yanda ake wa Yarima,ka san ana ji da shi, sannan kuma sam ba ka gane cewa ba ɗakinsu ɗaya da ragowar ƙannansa ba,ni kaina sai da na zauna gidan sannan na gane da kaina. Amma Mama ta ce mini, Yarima ba shi ne ɗan Sarki na farko ba,yana da yayyansa biyu mace ce babbar gidan ƙwata-ƙwata Hajiya Asabe, sai ƙannanta Abdul Rahman, amma tun kafin sarki ya hau sarauta ya auri uwarsu Hajiya Hadiza, sun rabu tun shekaru da dama. Yanda ta ba ni labari ba ta san abin da ya haɗa su ba, amma Sarki baya son ko sunan yaran a ambata, ba ma uwarsu ba, wannan dalili ne ma yasa jama'a da dama sun yi zaton Yarima ne babban ɗan Sarki Jafar. Uwarsu Abdul Rahman tafiya ta yi da su hannunta tun suna ƙanana, sai dai in sun ga dama suna zuwa gaishe shi, shi ma sai a yi shekaru basu zo ba, yanda ta bani labarin, yanzun haka Hajiya Asabe tana Ibadan tana auran wani mai kuɗi Alhaji Alabi. Shi kuwa Abdul Rahman yana Scotland zaune da matarsa baturiya (Vivian), yanda Mama take nuna mini kamar Sarki ya yafe su ƙwata-ƙwata, kenan ya barwa uwarsu su, sai dai ta ce ya kan aika masu da kuɗin makaranta da na abinci da suna yara, yanzun kuwa ko maganarsu ma baya son a tayar. Asalinsu Mama kuma iyayenta ƴan barikin Ladi ta nan Jahar Plateau,tun da daɗewa a garin Jos,ƴan ƙauyukan garin ke zuwa karatu, wato Makarantar ƙwana ta gaba da Primary,anan suka haɗe da Sarki a lokacin bai ma hau gadon sarauta ba, daga baya ne ma da ya hau mulki ya ƙara auran Hajiya Kilishi. Yanzun haka iyayen Mama suna nan da ransu a garin Aboko, da sauran danginta. Yarima kuwa shi ne ɗan ta na farko, sai Salimat, sannan Idris, daga su kuwa ba ta ƙara ba. Hajiya Kilishi kuwa anan Jos ya aure ta,ɗiyar hakimin Bukuro ce ta nan ƙaramar hukumar Plateau. Saboda rashin ganin hanya a ranar da muka zo gaishe da iyayen Yarima, shi yasa ban gane cikin gari suke zaune ba,a unguwar Dogon Agogo,wai wannan rukunin da nake gani har wajen baƙwai a gidan Yarima,wai na farko fada ce in Sarki ya zo kenan dai gidansa ne na hutawa,ko kawo baƙi na musamman. Sai masallaci a liƙe da shi, ragowar rukunin kuwa kamar namu ne,gidana da na Yarima, sai na su Idris da Ahmad,wai in sun yi aure, amma kowanne da kalar yanda aka tsara nasa ginin, amma tsananin kowanne gida zuwa wani gida, sai an shiga mota,in ba motsa jini za'a yi ba, saboda ko da Asuba ko ragowar sallolin nan an kai Yarima a mota. *** **** **** Tsugunne muke gaban Sarki ni da Yarima a ƙaton falonsa, na cikin gida,kawunanmu kuwa a sunkuye suke da gani ka san gaban manya muke. "Yau ne matarka za ta koma gidanta wacce ta samu tsayin ƙwanaki arba'in da biyu a hannunmu, dalilin da sakacin da ka yi da ita har ta faɗa haɗarin saran maciji. Bayani ya same ni na irin zaman da ka yi da ita a baya, zaman ko in kula da banzatar da ita. Wannan dalili ne ma ya janyo mata faɗawa rayuwa ƙuntatacciya, na gode,ka yi mini daidai ashe ni ina taƙama da ina da ɗa mai biyayya, ashe ban sani ba,ƙarya zuciyata ke gaya mini. Ka bani mamaki,a ce ita mace na je na nemo auranta ga iyayenta, suka amince suka ba ka ita, alhalin ba ta san ka ba, kuma suna da wanda ke jiransu su aura masa ƴarsu, ita ma tana da wanda zuciyarta ke so, amma ta haƙura ta yi biyayya ga iyayenta, kai kuwa ban isa ba." "Baba...." Yarima ya faɗa cikin sanyin murya. "Kada ka ce mini komai, kai ne da bakin ka ka gaya mini da ka amince in zaɓa maka wacce na ga ta dace da kai, tun daga ranar na baza mutane a kan su gano mini matar da ta dace da ɗana wanda nake mugun ƙauna a zuciyata, Allah ya ba ni ya kuma ba da sa'ar aka samu ƴar gidan manyan mutane masu mutunci. Ka tuna,bakina da naka muka yi wannan maganar ba fa aike na yi maka ba,ka tuna,kiranka na yi ka faɗa mini wacce yarinya ka gani ta ƙwanta maka a yi maganar auranku,ka tuna, kai da bakinka ka ce mini babu. Yanzun na yanke hukunci zan raba auranku, amma na baka tsayin ƙwanaki biyar ka zo mini da rubutacciyar takardar sakinta...." "Baba...." "Bana son jin komai daga gare ka,ka bani haushi,ka ɓata mini raina matuƙa." Ya miƙe tsaye, "Ɗiyata ina ƙaunarki da ɗana, amma ki je kiyi haƙuri, sannan ki yafe ni da na sa aka raba ki da wanda ke son ki,saboda son kai irin nawa. Zan aiko a yi kiranki." Ya juya ya tafi. Yana ƙulewa a inda har ya ƙule, Yarima na Baba,Baba cikin girmamawa, amma bai ko juyo ba,ni kuwa na waigo a sanyaye na kalli Yarima inda ya koma ya ƙarasa zama a ƙasa. "Tashi mu tafi." Na faɗa cikin muryar da zata ƙara karyar da zuciya. "Kin ji abin da Sarki ya ce fa Yasmin." Na ɗan yi murmushin da ƙago shi kawai na yi. "Kana da magani?" Ya girgiza kai. Na miƙe na bar shi a wajen zaune,gudun kada ya karyar mini da zuciyata. Ina jiyo su daga falo,suna cikin ɗakin Mama yana gaya mata, amsar da ta bashi ce nima ta ɗan firgita ni. "Gara haka,ai ni har naji daɗi, tun da baka son ƴar mutane a dinga ajiyarta a gidanka,ƙwanaki nawa kuka ɗauka da ita ba ka ji kana son ta ba,sai yanzu....?" "Mama zan iya yi miki rantsuwa da Alƙur'ani akan ina son ta, Mama duk laifinta ne...." "Laifintan wa? Kusan kullum sai mun yi waya in har baka zo ba,in dinga ƙwatanta maka cewa don tana mace,kai ya kamata ka dinga shishshige mata,yau da gobe za ta saki jiki da kai." "Wallahi Mama, ina yi mata, ita da wanda take so,wai shi ANWAR." "Shi kenan ka ga yanzu ka yi wa kanka, ita kuwa tana da wani." "Mama yanzu ya zan yi? Wallahi ina son Yasmin,ni dama can ina son ta." "Ƙarya ka ke yi, da kana son ta da baka tsaya yi mata mulki da kuma ƘASAITA ba, haka ka ga muna zaune da mahaifinka? Mulkinsa da ƙasaitarsa a waje suke, sai kuwa idan ya shigo gida ya ga barorinsa, wannan dole ya yi,kana kallo wata rana da kansa zai leƙo ya kira wacce yake son yin magana da ita a cikinmu. Ko an ce maka jakadiyar da aka sa a tsakaninku, Addini ne ya shinfiɗa ta?" "Mama matsalar, Mama, Yasmin ba ta sona ƙwata-ƙwata,ni kawai ke sonta." "A yanzu ko kai ma?" "Mama ki tuna ranar da na fara ganinta daga can sai nan fa nazo na gaya miki na ga yarinyar da nake so,amma ban san ko ƴar waye ba, har ki ka ce sai in je in ta nema, wallahi Mama ita ce nake gaya miki, don dai haɗuwarmu ta zo ne da saɓani shi ya sanya...." "Saɓani ko dai ka nuna mata kai ka isa, dole ne ta ji tsoron zama da kai yanzun." "Mama duk ki bar wannan maganar,a yanzu na ajiye duk wata ƘASAITA in dai ina tare da Yasmin kamar yanda nake miki Mama." "Yanzun ko?" "Mama,ki taimaka,in Sarki ya haƙura ma zamu Greece Honeymoon da ita." "In tana son ka ko, na san zai sa a tambaye ta,in ta nuna a'a, to kai ka sani." "Mama zan yi ƙoƙarin da Yasmin zata so ni, wallahi na yi miki rantsuwa da Allah." "To na ji kayi ta addu'a ka san halin Sarki, baya tayar da magana in dai har ya furta ta da bakinsa,ka san dai ba sabon abu ba ne ba wannan. Yanzun da ƙafar ƴar mutane ta lalace ya za mu cewa iyayenta?" "Mama shi kenan mu zamu tafi, zan dinga zuwa." Ta yi dariya, "Dama ni ce Yasmin in ce sai Anwar " Ta cigaba da dariya. Suka fito,ni kuwa sai ma na nuna ban san abin da suke yi ba. "Ƴan gidan tun daga nesa na hango su tsaye ana ta murna,kai har da mazajen sashen gidan Yarima, Allah Sarki, Mansura har da kuka,yarinyar nan ta shiga raina nima,ko don yadda take nuna mini ƙauna,wai sai da muka kusan wajen sannan aka ƙara sakin labulan nan baƙi, duk da dama gilashin motar ma baƙi ne, sai dai ka ga mutum amma shi baya ganin ka. Ya juyo sosai ya riƙe hannuna, "A tanadar mini abinci,yau gidanki zan yi hira, saboda in taya ki zama." Na rausayar da idanuwana na yi murmushin da na san gefen kumatuna suna lotsawa. "Ka fi ƙarfina." Ya yi saurin matsowa. "Kada ki ƙara faɗar haka, har kin janyo ma ba zan iya wucewa gidana ba,naki gidan zan sauka." Ka rufa mini asiri." Sai na ga ya yi saurin sakin hannuna ya matsa baya, wacce ta yi daidai da buɗe ƙofar motar da muke ciki. Mun gaisa da jama'a da dama, sannan muka haye sama ɗakina, sai na ji na kasa komai. Wannan yasa na dinga haɗa shi da Allah ya tafi ɗakinsa,an jima da dare ya dawo hirar sannan ya amince. Ƙwana uku yana zuwa taya ni hira, sai sha biyun dare yake tafiya, a ranar na huɗun da goma na dare na ji wayar hannuna ta yi ƙara, na ɗauka a tunanina Aunty ce, sai na ji muryar Yariman da na gaji da jira, na yi ƙwalliyata mai ƙyau, saboda shi amma shiru, wanda na kasa zaune na kasa tsaye saboda rashin zuwansa,ni kuma na kasa zuwa inda yake in dubo ko lafiya. A hankali yake magana cikin muryar da zata iya tayar maka da hankali, idan ka ji ta, saboda tafi yanayi da ta marasa lafiya,a take kuwa na ji hankalina ya tashi. "Yasmin na kasa zuwa wajanki." Cikin yanayin tashin hankali na tambaye shi, "Ba ka da lafiya ne?" "Eh, to ni ya zan ce miki, zaki iya zuwa gare ni yanzu? Yasmin forget the fast please." "Zan yi tunani." "Please Yasmin." "Okey,na ji." Ya kashe wayar, na miƙe tsaye daga zaunawar da na yi a gado, na nufi madubina, na ƙara feshe jikina da turare, na kalli kaina irin kayan da ke jikina, riga da siket ne na Turawa amma buɗaɗɗen siket ne, ga shi da tsayi har zuwa ƙwaurina,bulu ne mai haske (light blue). Sai ruwan ja amma mai haske light pink mai dogon hannuwa ce, amma daga ƙarshen hannun buɗaɗɗu ne, sai buɗaɗɗan wuya, wanda ya nuna sashen bayana a buɗe yake, haka gaban rigar (roundneck) , zagayayyen wuya ne, da wasu zarirrika biyu a gaban rigar waɗanda an yi su don ƙwalliya kawai. Takalmin ƙafata masu ɗan tsini ne,kalar rigar jikina, amma ɗan mayafin da aka sakowa kayan irinsu ɗaya da siket ɗin,bulu mai haske kenan, sai da na feshe gashin kaina da turaran shi, sannan na mayar da mayafi na yafa kalar rigar jikina,alkyabbar da na rufa a sama, ita ma pink ce, sai da na kuskura man ƙamshin baki mai ƙamshin (mouth wash,rinse), sannan na rataye wayata mai ruwan alkyabbar a hannuna. Na murɗa ƙofa na shiga,ƙasan ba kowa sai fitilar nan ɗaya da aka saba bari duk dare na Ubangiji, na haye matattakalar bene,domin in isa ɗakinsa. Falon sama na same shi ƙwance cikin kujerar hutawa farar shirt ce da wando a jikinsa, amma ya ɓalle maɓallan gaban rigar, sai farar singilet ce ta rufe fatar naman jikinsa. Wayar hannu ita ce a saman ƙirjinsa, wacce kalar jikinta fari ne daga ƙwancen ya juyo ya kalleni. "Yasmin." Shi kaɗai ya faɗa, amma bai tashi ba, na iso na tsugunna gabansa. "Ba ka da lafiya ne?" Na dafa saman goshinsa, ya lumshe idanuwansa. "A'a." "Yana ga jikinka ya yi laushi?" "Ke ce." "Me ya faru kuma?" "Gobe ne fa Sarki ya yanka mini." Ya yi shiru nima sai na ji gabana ya faɗi. "Na yi waya da Mama yanzun kafin in yi miki, amma ta ce Sarki yana nan a kan abin da ya faɗa." *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 3 "To me ye na damuwa?" "Na san halin Sarki ba tayar da magana." "Shi ne na ce me ye na damuwa? Iyaka ka auro wacce ka ke so,dama ni ma takura ka aka yi ka au...." Ya tashi zaune tamkar tashin wanda ba shi da lafiya. "Me ye abin damuwa Yasmin? Ni ke ce abin damuwata." Na miƙe tsaye na ja baya tare da dafa goshina, na juya kamar zan tafi. "Yasmin,No! No!! No!!! I love you. Na juyo da kaina na gan shi a tsaye yana kallona, na girgiza kaina na juya zan tafi. "Please, Yasmin." Na tsaya cak a lokacin da na ji wani abu yana yi mini yawo a cikin jikina, wanda ba zan iya faɗar yanda yake ba, na mayar da idanuwana na lumshe tare da fitar da numfashi sama-sama,shin me ye wannan? Ban kai ga tunanin amsar ba, na ji an rungume ni ta baya. Ajiyar zuciya uku ce ta fito gaba ɗaya a cikin sakan ɗaya, kafin in yi tunanin ya zan yi in ƙwace jikina daga Yarima, sai na ji ya zame alkyabbar da ke sanye a jikina zuwa bayana, madadin buɗe bakin da na yi inyi magana, sai dai bakin ne ya tsaya a buɗe sakamakon sumbata da ya kai a buɗaɗɗan bayana, wanda riga ba ta ƙarasa rufe shi ba. Madadin inji ya sake ni, sai na ji ya cigaba da sumbatar wuyana zuwa bayana. Me ye wannan ke yi mini yawo a jikina? Lallai ba zan iya gano ko me ye ba,saboda ya fi ƙarfin in iya faɗarsa, jin alkyabbata ta faɗi ƙasa, ita ta dawo da hankalina a jikina, wanda na ji sam ba shi da ƙarfin komai. Ba zan iya wata magana ba, sai dai na yi ɗan ƙoƙarin da bai wuce na mirginawar marar lafiya ba, na zame jikina, ina girgiza kaina, idanuwansa a lumshe suke inda yake saukar da numfashi sama-sama kamar mai asma farkon tashi. Numfashin haɗe yake da faɗar, "No! No!! No!!!" Wacce ba zan iya ƙirga ko nawa ce take fita daga bakinsa ba, wannan ne ya ba ni damar jan jikina in tafi gidana, wanda ko alkyabbar ban tsaya ɗauka ba. Sai da na tsaya jikin ƙarfen matattakalar bene na ɗan huta,don ƙarfi ya samu a jikina, sannan na samu na iya gangarewa ƙasa, har na kai ƙofa na murɗa na juyo muryarshi. "Yasmin." Na waigo na kalleshi tsaye yake a ƙofar benen riƙe da alkyabbata a hannunsa, na mayar da kaina na sunkuya a inda ya iso, ya tsaya gabana tare da miƙo mini alkyabbata,na karɓa muna kallon-kallo da shi. Sannan na murɗa ƙofa zan fita, ya juyar da kai tare da ɗan asirtaccen murmushi, wanda da gani tare yake da takaici, saboda fitowar da ya yi tare da numfashi, sai da ya yi irinsa ya kai sau baƙwai, sannan ya ja baya na buɗe ƙofar, ya yi saurin riƙo hannuna. "Yasmin stay with me." Na girgiza kai, na saɓula hannuna na yi gaba, sai dai na jiyo shi yana kiran. No! No!! No!!!" Ɗinsa da ya saba kira,ko waigowa ban yi ba. Da gudu na haye saman ɗakina, ina zuwa na faɗa gadona, sai da na mayar da numfashi ya fi talatin kamar wacce asma ta taso mata, ga idanuwana a lumshe, sannan na ji tunani ya zo mini. Shin ko wannan shi ne SO? Na girgiza kai,ba zan so Yarima ba. To me ye wannan? Oho, abin da zuciyata ke faɗa kenan,nan take ta juya linzamin tunaninta ga abin da ya faru ƴan mintuna da ba su wuce goma ba da suka wuce. Jikina na ji ya kama rawa shi kaɗai, na yi sauri na miƙe tsaye, sai na ji kamar jiri na shirin kada ni, na yi saurin zama, na cire mayafin kaina na jefar da shi ƙasa, na juyar da kaina, kamar wacce ta rasa abin da ke yi mata ciwo a jikinta, na sunkuyar da kaina, gashin kaina ya zubo a fuskata,a inda na tura hannuwana duk biyun cikin gashina. Na samu mintuna goma sha biyu a haka, sannan na ji kamar an sumbaci bayana, na yi saurin ɗagowa, amma ban ga kowa ba, na yi murmushi na miƙe na nufi banɗaki. A banɗaki na cire kayana duka na shiga ruwan wanka mai ɗumin gaske,wai ko abin da nake ji ya sake ni. Tsayin mintuna biyar na yi kawai na miƙe da sauri, saboda tunanin da ya faɗo mini a lokaci ɗaya. Na ɗaura tawul na fito da saurina,wai ji nayi kamar an bugo mini waya,ba abin da ya faɗo mini kuwa sai maganar Sarki. "Zan turo a kira mini ke kin ji." Hankalina ya tashi matuƙa, gobe, gobe lallai zan shiga damuwa kenan in an rabani da Yarima. Na yi saurin tunano Anwar a zuciyata, take sai na ji bana son tunaninsa,na fi son tunanin Yarima,shin ina son Yarima? Ba amsa, na ɗauki rigar bacci ta da su Mansura suka ajiye mini na zura a jikina, da ƙyar na iya ɗaga ƙafata na zura ɗan diras ɗin da ke kusa da ita, na isa ga madubi na taje kaina tare da ƙara gyare shi. Rigar baccin doguwar shimi ce har ƙasa, orange colour da ƴan hannuwanta guda bibbiyu a kowanne ɓangare sai ɗan leshi da ya ratsa saman ƙirjinta, ruwan lemo ce mai santsin gaske. Na feshe jikina da turare madadin in haye gadona sai na ji na kasa, buɗe ƙofar barandar gaban gidan na yi na fita. Kamar yanda na saba a kullum yau ma haka na yi, shi ne in ware hannayena duk biyun,yau ma kuwa na samu sa'ar garin yana fitar da iska mai sanyin gaske, wadda ta taimaka da wasa da gashin kaina, idanuwana kuwa a lumshe suke, amma na kasa tunanin komai a yau. Cikin wani sanyin jiki da sanyin zuciya, na ji tunanin Yarima ya faɗo mini a zuciyata a iya nawa tunanin, sai na ji dama Yarima ya iso yanzu,can ɗayan gefen na zuciyata kuwa, sai ya dinga karanto ni a jikin Yarima,a cikin tunanina ne na ji kamar an bi nawa hannayen a hankali, wani daɗi ya dirar mini a zuciya. Cikin tunanin kuwa na ji an haɗe ƴan yatsun hannuna da nashi waje ɗaya an runtse su, cikin ƙwanciyar hankali ya rungume bayana a ƙirjinsa, sumbatar da ya kaiwa wuyana shi yasa na saukar da ajiyar zuciya mai fitar da sauti. Hankalina gaba ɗaya na ji ya ɗauke har ya zamo na manta mai nake ji a jikina, ƙwaƙwalwata ta fara karanto mini da in buɗe idanuwana da suka yi nauyi in ga ko zan ga Yarima a barandarsa. Cikin sakan biyar na ji hankalina ya dawo a jikina, madadin in jini ni kaɗai ina tunanina, sai kawai na tsinci kaina da jin ɗumin mutum a jikina, gaske ne,ko dai har yanzun mafarkin tunanin ne nake yi,jin sautin numfashi na tashi a kunnuwana yasa na buɗe idanuwana da sauri. Na razana, na tsorata, duk a lokaci ɗaya da na ji bakina ana Yarima, na yi ɗan gaggawar fizge jikina na ja baya, kenan mafarkin tunanin da nake yi da gaske ne, na girgiza kai tare da ɓata fuska. "Me ke damun ka haka? Bana son abin da ka ke yi mini,ba na..." "Yasmin ya isa haka nan,don Allah, na san na yi miki laifi a baya, ya kamata ki zamo mai yafe mini." Ya matso ya tallabo fuskata Wacce gashi ya rufe ta, yasa hunnunsa ya gyara gashin zuwa baya. "Yasmin." "Ni fa ba zan..." "Yasmin kada ki faɗi abin da zai ƙara tayar mini da hankali." "Ka manta gobe ne ranar ƙarshena da kai,ka ga ba zancen wani gyara a nan." "Na sani Yasmin,ki yi tunani kada kiyi tunanin ko yaudara ce tsakanina da ke, wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Tun a ranar da na gan ki a titin Ahmadu Bello Waya, har zuwa yau ban taɓa daina tunaninki ba, matsalar da na samu shi ne ban san gidanku ba, ina shirin in bincika Allah ya haɗa ni da ke a wajen fati,a ranar na so mu daidaita sai ma ta ƙarasa ƙwaɓe mana." Ya ɗan tsaya ya mayar da numfashi, ya saki fuskata, ya durƙusa a gabana. "Please Yasmin ki taimakeni,ki zauna da ni." Na tsugunno nima na fara magana a hankali, kamar yanda yake yin tasa. "Ba zai yiwu ba Yarima,ba zan iya zama da kai a wannan matsayin naka na mulki ba,ko tari na yi duk gidan nan an sani, har zuwa gidanku." Na miƙe na koma ɗaki na zauna gefen gadona. Mintuna baƙwai da zamana ya shigo ɗakin shi ma ya iso gaban gadon ya tsaya. "Ba zan taɓa cewa na haƙura da ke ba, ba kuma zan gaji da baki haƙuri ba, ba zan taɓa mantawa da cewa ina son ki ba, Allah ya gani, na yi miki abubuwa ne domin ki so ni, nima amma na yi kuskure." Ya juya ya tafi ya ja mini ƙofar da har sai da na ɗan tsorata. Na koma na ƙwanta a rigingine, na dafe kaina da hannayena na yi tsaki, na juya na tashi zaune, na mayar da numfashi na tashi na je na rufe ƙofar gaba, na koma na kulle ƙofar ɗakina, na zare makullin na kashe dukkan fitilun ɗakin, na ɗaga filo na saka makullan, na koma na shige bargona, kaina ne kawai a waje, inda idanuwana ke kallon duhuwar ɗakina, duk da hasken da ke shigowa ta kafar labulaye ya ɗan taimakawa ɗakin da rage duhu sosai. "Yarima!" Shi na faɗa a fili, na tuna da maganar Sarki, na tunano Mama da ta ce Sarki ba ya magana ya tayar da ita, hawaye na ji sun gangaro mini,wata zuciya ta tambaye ni, "Shin ko ina son Yarima Faysal ne?" Anwar shi ne mutumin da ya fara saka ni hanyar soyayya, mutumin da ya shayar da ni ɗanɗanonta. Anwar Mutum ne wanda ya rigaya ya karanci halayyata, har ta zamo ba ta ɓata masa rai. Anwar ba wai ƙyakkyawa ba ne, sai dai sam ba ya layin munana,kalar fatar jikinsa kuwa mai ɗan duhu ce, amma da ganinsa ka san yana cikin hutu. Anwar babban ma'aikaci ne shi, wanda har ya kai matsayin babba a ofishin da yake (Cooporate Affairs Commission). Mahaifinshi ya tsufa, mahaifiyarshi ce mai ɗan jini a jika, wanda gidansu su huɗu ne kacal,yayyansa biyu, mace da namiji, sai kuwa ƙaninsa namiji ɗaya. Ni kaina na san ina son Anwar, Mutumin da muka shekara uku da shi muna (Friending), amma rashin auranmu da shi tun a baya, na san laifina ne, tare da ƙaddarar auran Yarima Faysal. Iyayensa ƴan asalin Kano ne, aiki ya kawo mahaifinsa na Likitan dabbobi, suna da arziƙinsu daidai gwargwado, ga shi mutum ne mai tausayin gaske ni kaina na san Anwar na matuƙar ƙaunata. **** **** **** Wazirin Sarki,Galadima,Tafida, Talba da Durɓi,su ne a tebirin shawarar Sarki, wanda Sarki Jafar Sada ya tarasu ne a kan hukuncin da ya yanke a raba auran Yarima Faysal da Gimbiya Yasmin,saboda su ne mutanen da suka fi kowa kasanci da shi fiye da kowa. An ɗauki ɗan tsayin lokacin da za'a iya ba shi sa'a ɗaya (awa ɗaya), ana mahawara a kan maganar, wanda a ƙarshe magana ta koma ta basuyi na'am da hukuncin da Sarki ya yanke ba, saboda dalilai da suka kawo irin nasu na manya, kamar dalilin waziri. Ya Kawo dalilinsa ne a kan nan gaba idan suka nemi aure za'a iya hana su, saboda za'a ga ba sa riƙe aure da daraja, dalilinsa na biyu kuwa shi ne,a bar yaran da kansu su zo su ce basa son junansu,in sun zo da zancen haka, ina ga in an raba su ba za'ayi laifi ba wajen kowa. Galadima kuwa cewa ya yi a kan samu haka a tsakanin ma'auratan da aka haɗa aure, ma'ana waɗanda ba su suka zaɓi junansu ba. Shi kuwa Tafida cewa ya yi abin kunya ne a garesu a ce sun yi wa ɗansu aure wanda suka tara jama'a ba iyaka daga garuruwa, jahohi, ƙasashe, amma a ce ƙwanakin da ba su wuce arba'in ba aure ya rabu, alhalin muna taƙama da cewa shi ne magajin Sarkinmu a nan gaba. Shi kuwa Durɓi cewa ya yi anyi daidai da aka ja masu kunne aka tsorata su, amma maganar rabuwa ma bata taso ba,a kira su dai a ƙara ba su lokaci, idan har ba su sasanta kansu ba, to sai a haɗu da iyayen yarinya a ƙara tattaunawa, daga nan sai a nemi shawarar da ta fi cancanta, sannan yana mai baiwa Sarki shawarar ya je ya samu iyalinsa ya lalubi wani abu daga gare su na game da yaran, saboda su mata ne za su fi mu samun labarinsu. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 4 A nan dai suka tashi saboda ganin juma'a ce za'a fita Masallaci da wuri. Sarki ya shiga ya kira iyalansa,Mama Mariya ita ce mahaifiyar Yarima, sai kuwa Hajiya Kilishi wacce take mahaifiyarsu Ahmad ga ta amarya. Ya gaya masu shawarar da ya yanke a kansu Yarima, amma yana mai tambayarsu shawarar ya suka gani. Hajiya Kilishi ita ta fara magana,haba Shugaba ya za'a yi a ji irin wannan maganar daga bakinka, alhalin ku ne manyan da ku ke yankewa ƙanana hukunci,haba mai girma,ai ka san auran haɗi dama ya gaji haka kafin ma'auratan su saba. Ka tuna kanka mana,watana nawa a gidan nan ban saba ba, yanzu fa ka ga a sai mutuwa kawai ta rage mini a cikin gidanka. Ni a shawarata mai girma a sa masu ido, tun da an ɗan tsorata su, balle ma yanda naga shi Yarima na yawan zuwa gidan nan,a lokacin da aka dawo da Yasmin nan gidan,kai a taƙaice sai na kore shi gida yake tafiya in dare ya yi. In kuwa suka shige ƙuryar Mama sai su ƙwashi awanni, sallah kawai ke fito da shi,don ma yarinyar na da kunya,waya kuwa in dai har ba ya cikin gidan nan har gajiya muke yi da ɗauka, sai na cewa yarinyar ta taimaka ta ɗauka, sannan zai bar mana kunnuwa su huta. A fahimtata dai Yarima ya sauko, ita ce dai ke da saura, kuma ka san dan tana mace, akwai kunya irin ta mata,ko Mama kin yi shiru?" "Me zan ce ai kin gama faɗa, ƴaƴanki ne fa, shawarata ɗaya in har da ragowar zamansu tare,to ki kira ɗanki ki ja masa kunne, saboda laifin na wajensa,ai ya ba ni labarin duk abin da ya haɗa su tun farko." "Allah ya huci zuciyar Sarki,a ƙara dai duba wannan magana." Inji Hajiya Kilishi. Ya miƙe, "Zan je in huta kafin tafiya masallaci, zan duba maganar insha Allahu." "Godiya muke,a huta lafiya, sai ka fito." Inji su gaba ɗaya. **** **** **** Sarki Jafar Sada ne zaune a doguwar kujerar mulkinsa, amma ta fadar cikin gida, kenan ɗakin shaƙatawar da yake ganawa da iyalinsa. Ni da Yarima kuma muna zaune a tsakiyar fadar,kowannan mu kanshi a sunkuye a ƙasa,ko ban faɗa ba kuwa na san daga ni har Yarima gabanmu faɗuwa yake yi, saboda na kalle shi ta wutsiyar ido ko motsi ma baya iya yi, saboda sanyi da jikinsa ya yi. Cikin ɗan satar kallo ta wutsiyar ido na kallo fuskar Sarki, gumi ne ya fara tsiyayo mini a fuskata,tun kafin in dawo da kallon gabana, saboda ganin fuskarsa da na yi ba wani annuri cikinta, ballantana alamar wasa. Na ƙara mayar da satar wutsiyar idon nawa ga yarima, na gan shi yana mayar da ajiyar zuciya, duk bayan sakan biyu, ban da gumin da na hango yana yi wa kansa magangara a jikinsa. Take kawai sai na ji tamkar in sa haɓar mayafina in dinga goge masa, wannan ne ma yasa na ji kamar zuciyata na ɗan kiɗan da ba sauti, balle ta samu ƴan rawa, hakan kuwa shi ya tunano mini daran jiya yanda muka ƙwana. A daran jiya ni na yi imanin babu wanda ya samu runtsawa ni da Yarima, dalilin da yasa na gane hakan kuwa shi ne,ganin saman ɗakinsa da fitila duk da ba mai haske ba ce ba,a tunanina ta gefen gado ce ma ya bari a kunne. Na gane hakan ne a sakamakon leƙen da na kusan ƙwana ina yi ta labulayen taga ta,wai ko na ga Yarima a ƴar barandarsa, yanda ya saba. Amma har na gaji na haye gadona ban ga ko da ƙyallin kayansa ba, wannan ya ba ni tabbacin bai samu yin bacci ba,ƙila gara ma ni tunda na samu na shiga bargona na yi lamo. Inji Malam bahaushe ya ce, "wacce ta fi barci daɗi." To ni dai jiya, wacce ta fi barci ciwo na yi. Saboda har yatsun hannuna sai da suka yi mini ciwo, saboda jan carbi,wai ko ya suɓuce daga hannuna in samu bacci ya ɗan ɗauke ni, amma sai dai na gaji na ajiye na cigaba da lazimin cikin zuciya, sai dai wani abin al'ajabi zan ce ko abin haushi? Wai har a wannan lokacin sai na ji zuciyata har gangar jikina sun ƙi amincewa da suna iya zama da Yarima Faysal, mutumin da yake taƙama da mulkin ƘASAITA,shin ko dai ni ce ban san son ba, ban kuma san makarai da makangan so ba? Tambayar tawa babu mai amsa mini ita. Ganin har ƙarfe uku na dare ta yi yasa na miƙe na yi alwala domin in ragewa kaina da zuciyata zafin da suka ɗauka, sannan in roƙi Allah da ya zaɓa mini abokin zama wanda yake mafi alheri a gareni, Anwar ko Yarima, saboda ni na kasa gane wa nake so a cikinsu. Ƙarfe goma na safiyar yau juma'a sai ga ɗan aike daga fadar Sarki,magatakarda ya kawo mini saƙon zungureriyar takardar da ta ƙara tayar mini da hankalina,dama daga wanka na fito, cikin nauyin jiki don ma na samu na ɗan gyara fuskata, da ɗan mutstsuka mai ina shirin saka kayana saƙo ya iso mini. Tun da na zauna a gefen kujerar tsakiyar ɗakina ban iya ma buɗe takardar ba, saboda ji nayi kamar kaina ba a wuyana yake ba,ni kaina ban san iya mintunan da na ɗauka ba a nan zaune, sai da Mansura ta shigo sannan na ji tana tambaya ta wai lafiya? Duk maganar da take mini a farko na ɗauka mafarki nake, sai da na ji an dafa mini yatsun ƙafafuna, sannan na ɗaga na gan ta a durƙushe gabana. Ban san hawaye nake fitarwa ba sai da na dawo hankalina ga shi duk tafiyar nan da na yi ban ji na je kowacce duniyar tunani ba,ni dai cewa na yi ko kuwa don haukan minti biyar ɗin da aka ce duk ɗan adam na yin shi duk rana kenan dai shi na yi a zaune. Miƙawa Mansura takardar na yi na ce karanta mini da ƙarfi. Da ta karanta sai na ji ba wata takardar tafiya gida ba ce,ko ince takardar rabuwa da Yarima ba, ashe ta saƙon in je Sarki na kirana ce,in an sauko daga masallaci,tana gamawa na ce mata je ki waje ga ni nan zuwa, to ina za ni? Wa zan gayawa? Tunanin da na cigaba da yi kenan. Cikin mintuna baƙwai sai na ji Aunty Salwa ta faɗo mini a raina, na yi sauri na miƙe na ɗauko wayata na daddana nambobin, minti ɗaya aka ɗauka, ina fara gaya mata abin da ke faruwa. Ya isa haka ta ce mini,in je tana son ganina,ba zancen waya ba ne ba, saboda haka in tambayi Yarima in fito da wuri,in biya ta gidanta. Wannan fa ya bani ƙwarin gwiwar in shirya in isa gidan Yarima,a yanzun ɗin nan. Baƙar shadda ce Galila, wacce aka yi wa aikin hannu, duk ta sha ɗigon farin aiki, ƙasan zanin kuwa aiki ne mai yanka-yanka, iya kusurwar cinya yake, sai hannu iya rariyar hannuna, duk ya sha tsagun irin na jikin zanan. Turare na ɗauka hannuna ina shirin fesa shi a jikina, sai na ji murɗawar ƙofar ɗakina a hankali, ban yi tunanin juyawa in ga kowa ke shigowa ba, saboda ganin ina tsaye a jikin madubi kenan ko wa ye zan gan shi ta cikin madubina. Gabana na ji ya yi wani abu wanda ya ratsa mini naman jikina ya bi ta cikin jinina har ya fito ga saman fatata. In da gashin da ke saman fatar duk ya miƙe tsaye, wannan ne na ji ana cewa tsigar jiki. "Me ya kawo mini? Ganin Yarima da na yi ta cikin madubina ya shigo da doguwar rigar bacci jikinsa mai wani irin aikin sarauta, amma iyakacinsa bakin ƙofa, ya jingina da ƙofar ya mayar da hannayensa ya goya a saman ƙirjinsa ya harɗe ƙafafunsa da juna, tare da mayar da kai ya jingina shi a jikin bakin ƙofa sannan ya ɗan ɗaga kansa sama da turaran a hannuna na ɗan wayance na iso wajen da yake a tsaye. "Yarima barka da asuba." Ya juyo da kanshi ya kalleni, sannan ya amsa da laɓɓansa ne kawai na ga sun motsa, har da lumshe idanuwa da buɗewa. "Lafiya?" Ya juyo ya kalleni,a take na ga idanuwansa sun yi jajir. "Da ki kaga me?" Ya faɗa cikin maganar raɗa-raɗa. "Idanuwanka na ga sun yi ja.” Sai na ga ya yi murmushin da ya dinga fitar da sauti, sai na ga ya wuce ni ya shiga cikin ɗakin ya samu kujerar da ke tsakar ɗakin ya zauna, sannan ya ɗago hannu ya yafito ni, ya nuna kusa da shi, ma'ana in zo in Zauna. Ban wani nuna damuwa ta ba na iso amma sai na ji na kasa zama saman kujerar na koma gefe ɗaya na zauna a ƙasa, madadin ya yi magana shi ma sai na ga ya zamo ƙasa ya zauna kusa da ni, na yi alamar zan matsa, gaba ɗayan shi ma ya juyo gare ni tare da kaikansa wuyana. Cikin maganar raɗa na ji ya yi magana. "You hate me.” Ya ƙara yin sama da kan shi zuwa daidai kumatuna. "Sarki ya aiko in je." Na yi saurin faɗa ina mai alamar tashi, yasa hannuwansa duk biyu ya rungumo ni jikinsa ta gefena. "Yarima." "Yasmin, Yasmin, Yasmin,jiya na ƙwana ina roƙon Allah ya cire mini ke daga zuciyata but still... Na lura ke har yanzu zuciyarki ba ta son zama da ni." Ya yi murmushi. "Nayi tunanin in zo in yi sallama da ke, Idan har na fahimci ke har yanzu you don't want to stay with me,saboda ni na san halin Sarki, ba ya sauraran komai idan ya riga ya faɗi magana.” Duk wannan maganar da yake yi a cikin raɗa yake yin ta, irin ta marar lafiya, sannan ga shi ya matse ni a jikinsa, sai shinshinar min wuya yake,yana ƙara tura kansa cikin wuyana,ni kuwa idanuwana a lumshe suke ban da numfashina da ke neman ɗaukewa. "Ba zan iya tsallake duk hukuncin da Sarki ya yanke min ba, amma zan ɗan yi iya ƙoƙarina in ga ko na samu nasara.” Ya yi shiru a daidai lokacin da ya juyo da fuskata a tasa. "Amma na yanke hukuncin barin ƙasar.” "Saboda me?" Na faɗa a sanyaye nima. "Saboda ke.” "Kai da baka so...” yasa yatsunsa biyu a laɓɓana yana zagaya su, wannan yasa ban iya ƙarasa magana ta ba. Na yi ɗan hanzari kaɗan na miƙe, saboda jikina da na ji ya fara rawa. "Wai me ye haka Yarima?” Na yi irin maganar nan wacce da ji na da ƙyar na ƙwato ta daga bakina, ya mayar da numfashi ya kai sau baƙwai, sannan ya miƙe tsaye. "Sorry.” ya juya ya tafi, har ya kai ƙofa na tuno da maganar zuwa gidan Aunty Salwa,na yi masa magana. "Yarima,ni zan je gidan Aunty Salwa yanzu, bayan masallaci nima zan wuce Sarki ya aiko in je." "Ki gaishe ta.” Kawai ya ce ya juya ya fita,a inda nake tsaye a nan na durƙushe na yi wajen minti talatin sannan na samu da ƙyar na miƙe na ƙarasa shiryawa. Ban ƙara ganin Yarima ba sai da na shiga ɗakin Hajiya a nan ne take ce min Yarima na cikin ƙuryar ɗakinta a ƙwance, ban iya tambayarta ba ko lafiya sai na ji zuciyata tana son ta ganshi, na san kuwa ba zan taɓa iya wuce Hajiya in nufi ƙofar dakinta ba, har na zauna na ji ta ce, "Shiga ciki mana ki zauna man baƙi sun yi yawa, balle ma yau juma'a." Na ce to, tare da saurin tashina. Amma ina shiga sai na ga Yarima ya juyo da kansa ya kalleni ya mayar gefe ɗaya, na isa bakin gadon a daidai lokacin da nake zaro takardar da Aunty Salwa ta bayar in kawo masa. "Gashi in ji Aunty." Ya juyo ya kalleni ya lumshe idanuwansa kamar wanda ake ƙoƙarin ƙara masa ruwan ledar asibiti, domin ceto ransa daga ciwon amai da gudawa da ya yi masa mummunan kamu. To haka na ga Yarima na buɗe idanuwa da ƙyar. Ya zaro hannu tamkar hannun ya yi masa nauyin ɗagawa ni kuwa na ɗora masa takardar a kai, madadin in zauna sai na dawo falo na biyun Hajiya na zauna saboda ba zan iya zama a wajensa ba...... Maganar da Sarki ya fara ita ta katse mini tunanin da na tafi, wanda a cikin mintuna biyar kacal na yi shi. "Yau ne ranar da muka yi alƙawari da kai zaka zo mini da abin da na umarce ka, ina jiranka." Yanda na ji cikin naman jikina na rawa haka kuwa na tabbatar Yarima na cikin halin da ya fi nawa, da jin maganar da Yarima yake yi,ka san a tsorace,a firgice,a nadamance da kuma karfin hali irin na maza yake yin ta. Bayan ya miƙe da ƙyar ya koma can kusa da Sarki. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 5 "Baba ka yi mini afuwa a kan abin da na aikata maka na rashin ƙyautatawa,a baya na yi alƙawarin ba za ka ƙara kama ni da wani laifi ba na rashin ƙyautatawa ba." Sai na ji ya rage sautin maganar ta juya izuwa sanyi da rawar murya. "Ba..ba yan...zun ina son abin da ka ke so, zan iya zama na har abada da abin da ka ke so." Ya yi shiru. "Yanzun me ka ke son inyi maka kuma? Bacin ka kunyata ni ka tozarta ni a idon jama'a." Ina kallo ta wutsiyar idanuwana ya ja jikinsa ya matsa sosai kusa da ƙafafuwan Sarki. "Baba ka yi mini hukuncin duk da ka ga ya dace da ni, wallahi zan ɗauka matsawar dai yin hakan zai huce zuciyarka zai saka ka yafe mini. "Ka zaɓi ɗaya cikin abu biyun nan,auranka ko sarauta." "Baba duk wanda ka zaɓar mini ina so." "In zaɓa maka ka ƙara yi mini yanda ka ga dama." "Baba ka yi haƙuri, wallahi kuskure ne,ba zan ƙara ba har abada." "Koma ka zauna, zan yi tunani a kan ka, ke kuma ki gaya mini gaskiya zaki iya zama da shi ko kuwa?" "Duk hukuncin da ka yanke ya yi mini nima." "Tashi je ki ciki." "Na gode." Na miƙe a sanyaye na nufi ciki. Tsayin mintuna arba'in Yarima ya yi shi da Mai Martaba, amma ni ina ƙwance saman lanƙwasashshiyar kujerar Mama, na yi lamo alamar bacci nake yi, ina ji ya shigo suka shiga ƙuryar ɗaki da Mama sun ɗauki mintuna sun kai ashirin sannan suka fito, ina jin shi ya yi sallama ya fita. Bayan sallar la'asar ne,Mai Martaba Sarki yasa aka kira ni zuwa fadarsa ta cikin gida, zan iya kiran lokacin da huɗu da rabi na yamma,ni da Mama muka shiga fadar wacce ita ƴar rakiya ce, wani sanyin daɗi na ji ya sauka a zuciyata,a lokacin da Mai Martaba ya ce Mama ta zauna ita ma. Ba mu fi minti biyu da zama ba sai ga Hajiya Kilishi ta shigo. A nan Sarki ya umurce ta da ta zauna, wanda dama alamar da ta nuna Sarkin ne ya aika a kira ta. Maganganu, misalai,nasihun da suka yi mini yasa a take na ji zuciyata ta karaya a kan duk wani abu da na ƙudura a kan Yarima na game da wahalar da shi. Lallai Yarima ya samu yabo a wajen mahaifansa, da kishiyar Mama, Hajiya Kilishi, ta faɗi irin halayyarsa da suke ji, ita ma, sai na dinga jinsa a zuciyata a take kuma na tunano kalaman Aunty Salwa waɗanda ta karantar da ni tsantsar so kuma me ye shi da tafiyar da wanda ake so. Na dawo hayyacina lokacin da na ji Mai Martaba ya ce, "Ƴata ina fatan za ki gafartawa mijinkin abubuwan da ya yi miki a baya, na rashin ƙyautatawa, saboda ya yi nadama ya nuna ba zai sake ƙwatanta miki su ba, ya nuna mini yana son matarsa." Yabo, nasiha da maganganun da Mai Martaba da iyalansa suka yi mini shi ya sanyayar mini da jikina, sannan Sarki ya yi mini alƙawarin yi wa Yarima hukunci, matsawar bai gyara halayyarsa ba, ya tabbatar mini da sati ɗaya ya bani idan har na ga ba daidai ba,in sanar da shi. Irin maganganun mutane da suka yi mini sun sa na ji alamar ɗan ɗigon wani abu a zuciyata, wanda na tuno da Aunty ta ce wai shi ne alamomin so. Ƙarfe shida saura mintuna goma sha baƙwai motocin ayarina suka shiga get ɗin gidan Yarima,wai sai na ji na tsinci kaina cikin wani irin nishaɗin farin ciki. Mu ma muka sauka inda ake ajiye motocin gidana. Yarima na hango a tsaye ya jingina da ɗaya daga cikin ragowar motocin da ke ajiye a rumfar ajiye motocin. Dukkan hannayensa ya saka su a aljihunsa ƙafafuwansa kuwa ya harɗe su a waje ɗaya, tabbas sai na ga ya ƙara yi mini ƙyau,ko kuwa don baƙar T.Shirt ɗin da ke jikinsa ce ta ƙara haska shi dama abu ga farar fata. Amma yanayinsa ya nuna mini da ganinsa cikin ɗan ruɗani yake, saboda yana hango motocina sai na ga ya yi saurin miƙewa tsaye sosai. Murmushin da nake yi kuwa,ni na san ya shiga har zuciyata, motocin na tsayawa shi ma na ga ya ɗan taho alamar zai iso ga motata, ganin an buɗe mini na fito shi ya sa naga yayi tsaye cak, tare da mayar da ajiyar zuciyar da ta fito fili, wanda ya yi ta cikin lumshe idanuwansa duk biyu. A hankali na ga ya zaro hannu ɗaya daga cikin aljihunsa ya shafi gashin kansa da shi, sannan na ga ya buɗe idanuwansa ya ɗan ɗaga su kaɗan ya kallo ni. Ni kuwa tuni har na kusa zuwa inda yake a tsaye, saboda ita ce hanyar da zan bi in shiga cikin gidana,ni kaina na san na canja tafiya, amma wani abin ban mamakin da na yi shi ne ina isa inda yake tsaye sai na ji ba zan iya yi masa magana ba balle har ta kai ni ga tsayawa wajensa. Sai dai kawai na yi murmushi na raɓa ta gefensa na wuce. "Kin tayar mini da hankalina,kin daɗe sosai." Maganar da na ji ya yi daidai lokacin da na zo zan wuce ta kusa da shi, na ɗan juyo da kaina na ɗan kaɗa idanuwana tare da yin murmushin da na san ya ƙara bayyanar mini da ƙyan fuskata,ƴar lotsawar gefen kumatuna ta bayyana a fili (Dimple), wacce na tabbatar ita ce sirrin fuskata. Na juya na nufi gidana a inda ina shiga falo wayar hannuna na yin ƙara, Yarima na ga an rubuta tare da lambarsa na yi murmushi na kanga wayar a kunnena. "Hey!" Na faɗa. "Muryarki ta yi mini daɗi a zuciyata, ita kaɗai dama nake son ji ko hankalina ya daɗa ƙwanciya." "Wa ke magana ne ban gane ba?" "Yasmin mijinki ne." Na yi murmushi na kashe wayar. Ina aje wayar ƴan matan suka yi mini sannu da dawowa na amsa masu tare da ɗan ɓata mintuna biyar a wajensu, domin in basu nasu haƙƙin, na lura kuwa hakan na yi masu daɗi matuƙa. Ina hawa ban tsaya komai ba sai hidimar wanka, saboda ganin magriba ta kawo jiki sosai. Yau kam addu'ata ta sha bamban da ta kullum, tunda yau na yi ta ne a kan Allah yasa Yarima ya ci gaba da sona har abada,ni kuma Allah yasa inji ina son shi,in gane son in aikata shi nima, Allah yasa in dinga yi wa Yarima biyayya a kan duk abin da ya umurce ni da shi. Ƙarar wayata ita ta ɗan sa na waiga na kallo ta saman gadona, har na kawar da kaina manufata ba zan ɗauka ba, sai na yi tunanin ko Aunty ce, wannan tunanin ne yasa na miƙe cikin ɗan hanzarina na isa ga wayar tawa. Yarima na ga an ƙara rubutawa. Na yi murmushi na kanga a kunnena. "Don't say hello to me. Saboda muryarki na rikita ni, ina gayyatarki cin abinci ƙarfe taƙwas na daren yau." Kafin in yi magana har ya kashe. Na koma da baya na ƙwanta saman gadona na lumshe idanuwana haɗe da murmushin daɗi,nan take na tambayi kaina shin ko dai ina son Yarima ne? A take na ji ƙwayar idanuwana na karanto mini fuskarshi,shin ko wannan shi ne son? Na yi saurin tashi ina girgiza kaina,kai a'a,ni na san ba na son Yarima. Na yi tsaki na miƙe na nufi ƙasa wajen ƴan matan gidana. A hankali suka dinga ba ni labari,a nan har na dinga zolayarsu da cewa ko wacce sai ta gaya mini sunan saurayinta. Muna cikin haka wayar da ke falo ta ɗauki ƙara, tana nuna mana alamun an bugo waya kenan. Mansura ce ta yi saurin zuwa ta ɗauka, cikin sakan ɗaya da kanga kan wayar a kunnenta na ga ta yi saurin durƙushewa ƙasa, sannan na ji tana gaishe da mai maganar. Yanda take yi tamkar tsaye take a gabansa, sai dai na ji ta ce, "To." Da sauri da sauri na ga ta iso gabana bayan ta ajiye kan wayar ta tsugunna tamkar tana neman in gafarta mata daga wani laifin da ta yi mini sannan ta yi magana. "Allah ya taimaki Gimbiya, Yarima ne ya ce ki ɗauki wayar hannunki." A take na ji gabana ya faɗi, wanda ya yi daidai da kallon agogon da ke manne a kusurwar falon. Ƙarfe tara saura mintuna sha takwas,nan na tunano gayyatar da aka yi mini ta zuwa cin abinci ƙarfe taƙwas na daren yau. Cikin ɗan gaggawa na nufi sama tun kafin na isa falon sama na ji wayar tana ta kukan kirana, na yi saurin gudu na isa, tare da saurin kanga wayar a kunnena. "Hey." Na faɗa cikin muryar da tafi kama da ta marar lafiya. "Na san kin gane na samu kaina cikin son ganin ki,shi yasa ki ke wahalar da ni." Shi ma tamkar ba shi da lafiya yake mayar mini da amsa. "Sorry." "Ina jiran ki." Bai jira na mayar da amsa ba na ji ya kashe. Na ƙurawa kan wayar ido, tamkar zan ga hoton Yarima a ciki, na yi murmushin da ya ratsa jijiyoyin jikina, sannan na miƙe. Ƙarfe tara daidai ina gaban madubina ina kallon jikina, riga da siket ne na atamfar Super Holland, ɗinkin wanda ya bi jikina ne, shi ne mai (shape) babu wani ƙwalliya a gaban ɗinkin sai dai buɗaɗɗan wuya ne mai zagaye. Sai kawai dogon zib tun daga saman wuya har izuwa bakin ƙugu, wanda makamin zuge shi,zamu iya cewa ya yi kama da ɗan ƙaramin zobe, shi kuwa siket ɗin irin ɗinkin nan wanda ƙarshensa buɗaɗɗe ne sosai. Takalman dana saka, basu da wani tsini sosai, mayafin jikina kuwa kalar takalman ne, wanda suka yi shige da ɗaya daga cikin ƙwalliyar atamfar wato ja, turaren (Glorious Lonkoom) shi na feshe jikina da shi, wanda wayar G.S.M ce mai kalar ja a hannuna. Na yi murmushi sannan na tambayi kaina, shin me yasa nake jin farin ciki a zuciyata? Na lumshe idanuwana haɗe da tunanin wai ga Yarima nan zai rungume ni ta bayana. Na buɗe ido da ɗan saurina har da ƴar ƙara haɗe da ɗan tsallena, tamkar da gaske, na yi dariyar da na ji tamkar yau ne ranar da aka yi mini wahayi da farin ciki, sannan na nufi gidan Yarima. Falon ƙasa na yi sallama na shiga, kafin in rufe baki mutane sun kai baƙwai suka zube a gabana suna kirari da gaisuwa a gare ni, na amsa masu cikin nuna nima fa ƴar mulki ce, kafin in ƙarasa wajensa,tuni an malala mini wata lallausar darduma a wata kujerar da ke kusa da shi da alama ta mulkinsa ce. Yarima kuwa yana ƙwance a gadon mulkinsa mai kama da katifa,ko in ce kujera mai hannuwa, amma mai faɗin gaske, ban da fitilu da ke zagaye da ita, ita kanta katifar mulkin sai ka tattaka hawa biyu sannan ka same shi ana uku ƙwance,ke nan kamar kana hawan matattakalar bene. Yanda yake a ƙwanciyar rigingine nan wayoyin hannu da na gida sun zagaye shi sun kai baƙwai, amma kai da ganinsa ka san hankalinsa ba ya a wajen mutanen da ke zagaye da shi, suna ta fadancinsu,su ma za su kai taƙwas, daga ƙwancen da yake kawai ya waigo da kansa ya kalleni. Hararar lumshe idanuwa ya yi mini,wacce zan iya cewa ta bayar da ma'anoni da dama, gaisuwa,kin mini laifi,ƙauna,son ganin ki nake,na ji daɗin zuwan ki. Cikin nuna ban fahimci mai yake ciki ba na ɗan ɓata fuska alamar na ji haushi,nan take na ga yana girgiza kansa, sannan ya juyo ya kalli mutanen da suka kasu gida biyu. Wasu a wajensa suna yi masa firfita da gyara shi, ban da kirari da suke yi masa. Wasu kuwa suna a kaina ni ma ana yi mini nawa,kallonsu kawai ya yi sai na ji suna cewa. "Mun bar ku lafiya, ƴaƴan mulki, waɗanda suka gaje shi, godiya muke." Kafin su ce sun yi gaisuwar nan da suke,ko in ce sallama,tuni wani dogari ya iso gabana da faranti a hannunsa lulluɓe da farin yanki,a take na fahimci komai wai in ina so inyi musu ƙyauta. Na ɗan sunkuyo kaɗan na ɗauki bandir uku na miƙawa na kusa da ni da hannu na yi masu inkiya da su raba. Ai kuwa na sha godiya da kirari irin na ƙwararrun dogarawa. Cikin mintuna uku falon ya koma shiru, daga ni sai Yarima da ke ƙwance, kamar mai jiran motar asibiti (Ambulance),ta zo ɗaukar shi. Mun samu mintuna biyu a haka, sannan na yi murmushi na ce a zuciyata, mulki sai mai shi, sai kuwa ɗan da ya gaje shi. ƘASAITA, sai Sarki, sai kuwa jinin da ya fito ta sarauta. Na girgiza kaina sannan na yi murmushi na miƙe tsaye na nufi inda yake ƙwance. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 6 Dole,in zamo ƙasanshi, ta wani ɓangaren kamar yanda Aunty ta faɗa, matattakala biyu na hau, sannan na zauna gefe ɗaya. "Sorry." Na faɗa cikin sanyin murya. Ya juyo da fuska ya kalleni,kunyarsa tasa na sunkuyar da kaina, ina jin motsawarsa ashe matsowa ya yi ya kama yatsun hannuna ɗaya. "Yasmin kin firgita ni sosai,kin tayar mini da hankali,kin saka mini rashin walwala a jikina." Ya sumbaci tafin hannuna na ɗan yi saurin janyewa nuna alamar kunya, na ɗan juya kansa jin a daidai nan yana magana. "Yunwa nake ji, ki taimaka mini da abinci." Na sa tafin hannuna na ɗan ture shi. "Ba ƙya so?" "Tashi mu je ka ci abincin." Na faɗa cikin muryar sassarƙewa. Ina jinsa ya koma da baya ya ƙwanta da ƙarfi tare da ajiyar zuciya, na juya na kalleshi yana mayar da numfashi a hankali, ya juyo muka haɗa ido na yi saurin miƙewa, sai na ga ya yi murmushin kunya ta kama shi, shi ma sai ya miƙe. Alkyabbar da ke jikinsa ya ƙara gyarawa, sannan muka nufi wajen cin abinci, sai da muka isa sannan ya cire alkyabbar ya miƙo mini,na karɓa sannan na tafi ga ɗan ƙarfen da ake ajiyewa na rataye ta, ina juyowa na gan shi tsaye sai kallona yake,muna haɗa ido muka yi murmushi gaba ɗayanmu. "Zan tafi idan kana yawan kallona." "Dole ne in kalle ki Yasmin,saboda kin canja mini rayuwata gaba ɗaya,kin mayar da ni tamkar ba ni da jini a jikina." "Ka gani...." "Ki yi haƙuri ba zan daina ba fa." Na juya alamar zan tafi. "Zo, na daina." Ya ɗauke fuska ya zauna sosai na iso na tsugunna a gabansa domin in zuba masa abinci. Tuwon niƙaƙƙiyar shinkafa ne,miyar dagwargwajajjan naman kaza, wacce aka yi ta da agushi, ya yi kalar kore-kore da gani ya sha kori (curry),shi kuwa tuwon ya sha naɗi a leda tamkar a hotel, na zuba masa, sannan na buɗe ɗaya ƙwanon, farfesun dagwargwajajjiyar hanta ne, shi kuwa ɗayan farfesun kifi ne, wanda hausawa kan ce masa ragon ruwa, ga shi ya sha albasa mai lawashi a cikinsa, da gani an saka shi a injin ɗin zare ƙayar kifi,ko kuwa in ce injin ɗin sa ƙaya ta yi laushi. "Ke fa?" "Ni naci a gidana." Ya yi murmushi. "Sam ban amince ba,ni dai na san kunyata ki ke ji, amma tsaya ki ga yanda za'ayi." Ya miƙe tsaye a inda ni kuma dama a tsayen nake ya isa makunnan fitila ya kashe ta, dawowar da zai yi sai ya rungume ni a jikinsa, ya yi ajiyar zuciya. "Sorry, ban lura da ke ba." Ya faɗa cikin raɗa, sannan ni kuma na zame na zauna. Zaunawar da na yi tayi daidai da kamawar wata ƴar fitila mai duhuwa wacce haskenta kawai za ka gani, amma ba zakaga mutum ba sosai, yanda nake zaune nan haka ya zo ya zauna kusa da ni a hankali ya dinga lalubo bakina yana saka mini tuwon nan, shi ma a haka ya ci nasa. Idan na girgiza kaina, shi ma sai ya ce ya ƙoshi,ni kuwa na san Yarima yana tare da yunwa sosai, saboda tashin hankalin da ya saka kansa, na ganin zai rasa ni. Cin abincin da ya kamata ayi shi cikin mintuna sha biyar, sai ga mu mun ƙwashi awa ɗaya. Na gane haka ne a lokacin da na iso kicin domin ajiye ƙwanukan abincin da muka ci,ni kuwa na yi tsaye a kicin ɗin na rasa me ke damun jikina, saboda wasu abubuwa da nake jin suna yi mini yawo tamkar kiyashi na bi mini jiki,shin ko son kenan? Shin ko na kamu da ciwon son Yarima ne nima? Kamar yanda na ga duk ya yi laushi a kan ciwon da ya kama zuciyarsa da gangar jikinsa,wai shi ciwon so na. Motsin da naji yasa na yi saurin ci gaba da harhaɗa ƙwanuka tamkar dama aiki nake tun da na shigo. "Sannu da aiki." Na juyo na kalle shi ya jingina da gefen ƙofa, ya rungume hannayensa a ƙirjinsa, murmushi kawai na yi masa,a zuciyata na ce lallai Yarima yana son ƙananan kaya, saboda riga mai dogon hannu da take jikinsa wacce ya ɓallewa maɓallan gaba na rigar. "Ki bar shi, da akwai masu gyarawa." Na sunkuya wajen famfo na wanke hannuwana, sannan na iso inda yake tsaye ni ma na tsaya saboda ba hanyar wucewa, maimakon ya gafara in wuce sai na ga ya rakuɓe gefen ƙofa sosai, ma'ana in zo in wuce, wanda ya yi mini alamar da hannunsa ɗaya, duk da dama idanuwansa tsaye suke a kaina suna yi mini kallon kamun barewar damisa a jeji, ma'ana tamkar idanuwansa za su lumshe gaba ɗaya. A hankali na zo na raɓa zan wuce, sai da na shiga tsakiyarsa sai ya sa hannuwansa ya kare ni, wato ya saka ni tsakiya sai da ya lumshe ido ya buɗe ya ɗan girgiza kai alamar kana son faɗar wata magana, sannan ya yi magana. "Ina za ki?" "Kina da gidan da ya wuce nan?" "Eh." "Wanne kenan?" "Wanda iyayena suka saka ni a ciki." Ya ɗan juyar da kansa ya kai sau huɗu, sannan ya dawo da kallonsa gare ni. "Ina son da kiyi mini wani aiki." "Na me kuma?" "Mu je sama ki gan shi." "Dare fa ya yi, goma ta wuce." "Ƙuya kenan fa." Nayi murmushin kunya. "Na isa,mu je in yi maka ko na tafi kada inyi dare." "Matata na ce mini za tayi dare a wajena,Yasmin kenan." Ya faɗa a daidai lokacin da ya sauke hannuwansa na wuce. Sama na isa, wanda shi dama yana biye a bayana, kujerar da ke kusa da gado ita na zauna shi kuwa a zagayen gadon da ke tsakiyar ɗakinsa, ina kallo ya janyo durowar kusa da gadonsa ya ɗauko wata babbar ambulan mai fulawoyi ja, wanda ita kuma bulu ce mai haske (light blue), ya ɗago ya kalleni,ni kuwa dama shi nake kallo. "Zo ki gani." Na yi murmushin zuci na miƙe, saboda tunanin me Yarima ya mayar da ni,yarinya ko me? Na iso na zauna gefe ɗan nesa da shi ya miƙo mini na karɓa ina mai mayar da hankali a kan ambulan ɗin. "Buɗe mana." Ban ce komai ba na buɗe ta, litattafai ne guda biyu wanda yanayin hotan da ke jikinsu da sunansu ya nuna mini cewa su Nobel (Novel) ne, na ɗora su a cinyata, saboda jin da sauran wani a ciki,alawoyin chakuleti na ji a ciki (Chocolate), ina zarowa na ga an rubuta Bounty a jiki. Na ɗago na kalleshi wanda kallon yana nuna alamar tambaya. "Taimaka mini za ki yi ki karanta mini su, amma yau mu fara da ɗayan duk da na san da wuya mu yi ƙwata a yau, amma ƙila ma yi sati muna karantashi, chakulet kuwa matata na siyawa, saboda na san zata taya ta hira." Ya haye can ƙarshen gado ya ƙwanta irin ƙwanciyarsa da ya saba,wato rigingine, sannan ya yi filo da tafukan hannayensa, ya mayar da idanuwansa ya lumshe. Na girgiza kaina sannan nima na gyara sosai nasa fulalluka na tare bayana, sannan na soma karantawa. Ni kaina na san muryata ta yi daɗi a wajen karatun, na san kuma duk mai sauraren karatun zai ji daɗinsa, saboda dallah-dallah nake yinsa, cikin cikakkiyar nutsuwa. A ƙalla ni na san na ɗauki mintuna talatin zuwa talatin da ƴan mintuna ina karantawa, sannan na ɗago kaina na kalli Yarima wanda na ji ya yi shiru,ni a tunanina ya yi bacci, amma sai na ga ya ɓalle maɓallin gaban rigarsa gaba ɗaya. Ni kaina na san Yarima na da gashin da ya ƙwanta a ƙirjinsa, dalilin ganin kuwa,ɗakinsa da na taɓa shiga na same shi yana bacci, amma abin mamaki sai na ga na yau yafi na ranar yawa,baƙi,ƙwantacce tamkar sumar jariri. Na yi saurin mayar da kaina ga littafin da ke hannuna, amma kuma sai na ji na samu kaina da son kallonsa duk bayan ƴan mintuna. Ɗagowar da zan yi in kalleshi sai naga ya ware duk biyun gaba ɗayan rigar jikinsa ta sauka saman gado, cikinsa, cibiyarshi,ƙirjinsa da kafaɗunsa duk a waje suke, take na ji jikina na neman kama rawa,me ye wannan? Ni dai na san har yanzun ba na son Yarima, sai dai na san ina jin kunyarsa. Na mayar da kaina ga karatuna, amma ni kaina sai na ji muryata ta canja,lumfashina kuwa ma nema yake ya tsaya,a zuciyata nake rayawa cewa in ajiye littafin in tafi gidana, madadin in ji ƙwarin gwiwa sai na ji tamkar an sare mini gwaiwoyina,cikin hakan da nake kawai sai na ji Yarima na kiran sunana a hankali. Jin kiran sunana ma sai na ji ya ƙara sani na dake, na dawo dai-dai saboda tunanin ko Yarima ya fahimci na shiga wata matsala da na san ba zan iya faɗarta ba,kiran sunana ya kamata a ce ɗaya ne ko biyu, amma tun da Yarima ya fara shi ban ji ya tsaya ba, tun ina ci gaba da karatun har ya zama ina saukar littafin hannuna a hankali izuwa ƙirjina. Kallona sai ya koma ga yarima da yake kirana, wanda idona ya hango ƙirjinsa na fitar da numfashi da sauri da sauri, wani mashi ne na ji ya dirar mini ta tsakiyar kaina, jikina na ji har ya ɗauki rawa cikin sakan ɗaya, saboda kiran da Yarima yake mini ya fi ƙarfin a tsaya ƙirgawa. Littafin saman ƙirjina wanda hannuwana suka taimaka masa ya zauna a ƙirjin nawa, sai na ji ya faɗo saman cinyata saboda hannuwan nawa sun kasa ɗaukarsa,jiri ne ya ɗauke ni ko kuwa suman sakan biyu na yi? Ni dai ji na nayi na sulale na ƙwanta saman gado sosai a riginginan da nake da ƙyar na ja filo ɗaya ya tallaɓe mini kaina. Amma duk wannan bai hana Yarima kiran sunana ba, idanuwana, kaina,jikina sun yi mini nauyin da ba za su iya motsawa ba, balle har ƙwayar idona ta samu ganin halin da Yarima yake ciki,ko ni kaina,shin me ye wannan? Ni na san ƙwaƙwalwata ta daina aiki balle in tunano amsar abubuwan da suka tarar mini a cikin mintunan da ba su wuce uku ba. Mai nake ji a jikina? Kamar numfashin mutum a hancina, ƙwaƙwalwata na ji na karanto mini Yarima na bin jikina, hannayena da ke ware ya bi da hannayensa a hankali har izuwa tafukan hannayena ya haɗa da nashi ya runtse gam, sumbatar wuyana na ji ya yi, ya dawo hancina,bakina,buɗaɗɗan gaban ƙirjina da riga ba ta ƙarasa rufe shi ba. Ni na san ina ji, amma ba zan iya motsa ɗan yatsana ba, balle har ya kai ni ga iya magana,ko ƙwatar jikina ba, sai dai na san numfashina yana fita sama-sama, ina jin shi kanshi ya ruɗe ya rasa ina zai kai sumbatar nasa,ko ina ya yi ina jin sa yasa haƙoransa ya zuge zib ɗin da ke gaban riga ta, wai nan na yi ƙarfin hali zan yi magana, amma madadin bakin da na samu da ƙyar na buɗe in yi magana sai gani na tsaya da wani irin numfashin da ya kasa wucewa cikina, ya tsaya mini cak a maƙoshina,saboda jin harshen Yarima na lasar fatar cikina, sai a lokacin na ji kamar na tunano ban sa shimi ba,rigar mama ce kawai na saka da zan taho. Jin ya nutsa hannayensa a gashin kaina yasa na samu da ƙyar lumfashina ya isa cikin cikina tare da faɗar "Hasbunallahu wani'imal wakil" sai na ji kamar ɗan jinin jikina ya dawo, na samu na yi ɗan ƙoƙarin miƙewa zaune, amma ina sam na kasa, saboda Yarima da ya samu ƙaramin taɓin hankali a jikina. Da ƙyar na buɗe idanuwana sannan na ɗaga kan Yarima na tallabo kumatunsa na girgiza kaina, wanda fuskata ke fitar da hawaye da ban fahimci ta ina suke fitowa ba, yasa hannuwansa duk biyun ya ɗago kaina ya girgiza kanshi shi ma, sai a nan na lura da hawayen da suka wanke fuskarshi shi ma, da ƙyar na ji ya ce, "Yasmin!" Yana mayar da numfashi ɗaya bayan ɗaya. Na girgiza kaina da ƙarfi, sannan na samu na miƙe na zauna, ya koma gefe ya ƙwanta rigingine yana wani irin numfashi. Na miƙe tsaye, tafiya na fara nayi luuu zan faɗi, na yi saurin zaunawa, na nutsa hannuwana a gashin kaina, jin ya rarrafo ya zo ya rungume ni yasa na ɗan samu ƙarfin cire hannuwansa daga jikina na miƙe. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 7 Na mayar da zib ɗin rigata na zuge, na samu na ja mayafina da ke saman gado ba zancen tsayawa yafawa, sai da na je ƙofa, sannan na tsugunna na ɗauki takalmana a lokacin idanuwana suka sauya kallo izuwa saman gadon da Yarima ke durƙushe yana kallona ya ware hannayensa yana ɗan girgiza kansa kada in tafi. Ganin ina kallon shi yasa na ji yana kiran, "Please Yasmin come to me." Wannan ma yasa na juya na tafi, sai kuwa da na je ƙofar fita, sannan na samu na yafa mayafina, amma takalma sai da na je ƙofar gida, sannan na iya sa su, ina buɗe ƙofa kuwa taku uku na yi na tuɓe su na riƙe a hannuna ina isa ɗakina na wurgar da su. Fitilu kawai na kashe na faɗa saman gadona ban tsaya neman wata rigar bacci ba,fulalluka na haɗa na rungume a ƙirjina,ni kaina ban san me zan tunano ba saboda ƙwaƙwalwata ma ta daina aiki, sai dai numfashina kam ya dawo, amma da ɗan sauri nake fitar da shi tamkar na yi gudu na gaji. Ban fi mintuna biyar ba na ji an murɗa ƙofata an shigo, da ƙyar na samu na lalubo wayar makunnan fitilar ɗakina ina kunnawa sai na ga Yarima a tsaye, yanda rigarsa take haka take ma yanzu, na lumshe idanuwana na mayar da kaina na ƙwantar alamar mamaki,jin an mayar da ƙofa an rufe yasa na ɗaga na kalleshi, ban yi wani ƙoƙarin tashi ba. Ganin ya nufo gadona yasa na fara tunanin me zan yi yanzu ban tunano komai ba na ji ƙarar faɗuwa, kallon da zan yi sai na ga yarima a ƙasa na yi wata doguwar wuntsulawar da ban san ma ina da ƙarfin yin ta ba,ni dai gani na nayi kawai a gabansa na ɗago shi na girgiza shi, cikin wani yanayin muryar tashin hankali na kira sunansa. Cikin sakan uku na ga ya buɗe idanuwansa yana murmushi,ni kuwa har na fara fita daga hayyacina a cikin ƴan sakannin nan, sai na ji kawai na yi ƴar dariya, shi ma sai ya ƙara yin murmushi, sannan ya tashi ya zauna ya kishingiɗa a cinyata da take durƙushe, sai a lokacin ne ma hankalinmu ya kai ga abin da ya kada shi. Takalmana ne da na yi jifa da su muka gani a gefe ɗaya, yasa hannu ya ɗaga takalman ya kalleni sai kuwa muka yi dariya gaba ɗaya, amma irin mai kama da murmushin dariya,yana cikin haka ne ya juyo ya haɗa goshina da nasa, sannan ya rataye hannayensa bayan wuyana. Cikin yanayin dariya ne ƴan hawayen da suka fito a lokacin da nake faman son in ga ya tashi suka gangaro, sai na ji ya saki takalmin ya ɗago fuskata yasa hannayensa duk biyun ya lalubo kumatuna, sannan yasa manyan ƴan yatsunsa yana goge mini hawayena tare da girgiza kansa alamar a'a. Sai kuwa na jina lumshe idanuwana ina yin ƴar wata dariyar kuka-kuka, murna-murna, sannan na sunkuyar da kaina sosai na ci gaba da ɗan kukan murna,gashin kaina kuwa ya zubo ya rufe mana fuskokinmu. Ina jinsa ya sa hannayensa ya tattare gashina, sannan ya ɗago kaina da hannayensa, kallon da ya yi mini yasa a take na ji na nutsu, saboda haɗa ido huɗu da muka yi da shi,kafin in yi wani motsi tuni ya kai bakinsa ga nawa, kafin inyi wani tunani har ya lalubo harshena ya riƙe. Wasu tsutsotsi na ji suna yawo a kaina na yi sauri na ƙwace bakina, amma sai na ji kuma na faɗa ƙirjinsa na ƙwanta,jin ya mayar da ni ya rungume tare da sumbatar gefen wuyana cikin nutsuwa na ji ya ɗagoni yana sumbatar ko'ina na jikina, wata zuciya ta dinga karanta mini maganar da Aunty ta yi mini amma wajen da ta ce. "Muddin jikinku ya fara haɗuwa, to dole ne so ya shiga mai tsanani, ba zai iya rabuwa da son taɓa jikinki ba, har sai ya tabbatar da kin zama tasa, wannan kuma shi ne zaman aure mai haifar da so,ƙauna,kulawa da juna,ki yi haƙuri idan hakan ta iso gare ki, wannan shi ne auren." Kafin in dawo daga tunanin sakan uku sai dai na ji kamar jikina ba riga, kafin in yi wani abu sai na ji har hannuwan rigar mamana sun dawo cinyar hannuwana, kafin in ƙarasa tuna me nake ciki, sai na ji laɓɓansa a saman ƙirjina. Tabbas ajiyar zuciyar da ya fitar mai ƙarfin gaske ba ta hana ni ɗago kansa ba, na girgiza kaina, wanda idanuwana ke a rufe,jin ya ambaci sunana cikin wata ɓoyayyiyar murya yasa na yi saurin miƙewa tsaye,a tangal-tangal na isa bakin gadona na zauna,a lokacin ne na samu damar gyara rigunan jikina, na ɗago na kalli Yarima Faysal da ke durƙushe a inda na bar shi. An ɗauki mintuna biyar kowa na haka, sannan na ji ya zo ya zauna kusa dani, ya ɗauki wata minti biyun kafin ya yi komai ko in ce yayi magana, ya ɗan ja numfashi a hankali, sannan na ji ya fara magana. "Ya kamata a ce komai ya wuce a tsakaninmu,ya kamata a ce yanzun mun amince da junanmu ko ma samu rayuwar aure mai ƙyau,ni na san laifina ne tun farko, amma yanzu ni na san dole in zama ƙasa gare ki, na yi tunanin shi mulki ko ina ma yinsa ka ke yi ashe ba zai yiwu ba ga iyalinka ba waɗanda ka ke ƙauna, waɗanda su ne rayuwarka gaba ɗaya." Kada ki ji haushina ko kiyi mamakina, wallahi Yasmin ban san aure ba, ban san so ba ban taɓa tsayawa na kalli ƴa mace ba balle har in ji ta a jinin jikina. Yasmin sai ke,ki ture auren haɗi a tsakaninmu,ki mayar da shi mu ne muka ga juna muna so,in ke ba haka ba ne a zuciyarki wallahi ni,ni na ganki na ji ina son ki tun ranar farko. A lokacin da na zo gidanku ganin ke ce ki ka fito matsayin matar da aka zaɓa mini na ji daɗi,sanyi a zuciyata, amma tsananin mulkin da yake a kaina ya hana ni nuna miki. Ke wallahi na ma nuna, tunda da ba ke bace ba,ba kowacce ta isa in tako in bata haƙuri har in bi ta gidan Yayarta. Yasmin na baki rayuwata gaba ɗaya, wallahi ba zan iya rabuwa da ke ba, har sai na ga kin zama jinina, na zama naki. Yasmin ke ce wacce ta taɓa sace zuciyata gaba ɗaya. Ki tausaya ki so ni,ko ƙya dawo mini da zuciyata ta cigaba da tunanin rayuwa da ke. Na san za kiyi shakkun zama da ni, wallahi ki cire duk wani shakku,ki ɗauka kin samu mijin da sai abin da ki ke so za'ayi miki, matsawar bai saɓawa shari'a ba,na karanta takardar Aunty na ji matsalolinki,ki yi haƙuri, zan ɗauki mataki mai ƙarfi a kan abubuwan da ba ƙya so a cikin gidana. Ki yi tunanin yanzun kunnuwa da idanuwan Sarki da jama'a da dama yana kanmu ya kamata mu kuma mu basu mamaki." Ya sauko ya zo saitina ya durƙusa a gabana. "Yasmin ki rufa mini asiri kada ki sa a raba ni da ke, wallahi mutuwa zan yi idan..." Na yi sauri na sauko na rufe bakinsa da tafin hannuna,ni na kasa gane kaina, ina son Yarima ko kuwa tausaya masa nake yi? Ya kamo hannuna ya sumbaci bayan hannun, sannan ya juyo da tafin hannunsa ya miƙo mini. "Na fi son ki amince da kanki,ki ɗora mini amanarki a tafin hannunki ki saka mini ita a nawa tafin hannun,in kuma har yanzu ba ƙya sona ki bani amanar ni zan yi miki abubuwan da zasu sa ki so ni." Na kalli tafin hannun sannan na juyar da kaina. "Please, Yasmin,kada ki guje ni don Allah." Na tashi na koma na zauna a gadona, ya ƙara matsowa ya ɗora hannunsa a cinyata. Na tunano yanda Sarki ya ce mini da irin ƙaunar da ya nuna mini,na tuno Mamee tare da Dadyna, na tunano Aunty Salwa,na ga ita ma kamar yanda aka kawo ni haka aka kai ta, amma yanzu ƴaƴanta uku,shin ko shi ne son? Ko shi ne auran? Na juya na kalli Yarima da ya ƙura mini idanuwa,na tuno irin mulkin da ke gare shi, ban da dukiya da barori,ƙarti da ƴanmata, da tsofaffi, amma yau ga shi yana yi mini magiya da in so shi. Zuciyata a take ta amince da in so shi, na juyo tafin farin hannuna na kalla, wanda na ga tsagu guda uku manya, amma na tsakiyar ya shiga cikin babban ɗaya, ke nan ni da Yarima, sai son da Yarima ke mini ne ya shiga cikin jikina, na matsa, hannuna na ɗora a saman hannunsa sai na ji ya yi ajiyar zuciya ya riƙe hannun nawa sosai. Na samu na karɓe hannuna sannan na koma gadona na ƙwanta a gicciye, ina jin Yarima ya taso ya zauna a gadona, wanda ya lalubi makunnin fitila ya kashe, sai dai na ga duhu a cikin runtsatstsan idanuwana, ina ji ya juyar da ni nayi rigingine ya zuge zib ɗin da na lura ya tsone masa ido, idanuwana na ƙara runtsewa da ƙarfin gaske a lokacin da na ji ya juyar da ni yana saɓule rigar jikina. Na yi saurin ƙanƙame jikina da na ji hannayensa na ƙoƙarin ɓalle ɗan masankallin da yake riƙe da rigar mamata, na runtse hannuwan gam da na ji ya kai wa tsakiyar bayana sumbata, ban dawo daga tafiyar balaguron da na yi ba sai naji ya haɗani ya rungume a ƙirjinsa ta bayana, gashin da ke ƙwance a ƙirjinsa ya tsirar mini fatar bayana, tabbas na fitar da numfashi wajen kala goma a lokaci ɗaya, amma har a yanzun na kasa gane me ye so da ƙauna. **** **** **** Motsin da na dinga ji yana tashi sama-sama cikin hankalin, shi ya farkar da ni daga baccin da nake yi, na buɗe idanuwana da ƙyar sai na ga hasken fitilar gefen gadona, amma ta ɓangare ɗaya, na ɗan juyar da kaina a hankali gudun kada inyi motsi da ƙarfi. Yarima na gani tsaye gaban durowata ɗaure da tawul a jikinsa. Kunya ta saukar mini tare da wani ɗan saurayin murmushi, duk da na san hankalinsa ba kaina yake ba, ina kallo har na ga ya janyo wasu kayan daba zan iya shaidasu ba, saboda ɗakin babu haske sosai, ina kallonsa ya iso wajen gado ya ajiye su a inda na yi saurin runtse idanuwana ganin yana shirin cire tawul ɗin jikinsa. Cikin dabara na mayar da kaina inda yake da farko,bai fi minti ɗaya ba na ga ya nufi gaban madubina ya ɗauki turarena ya fesa, wata wauta irin ta Yarima har da sumbatar ƙwalbar turaran nawa sannan ya ajiye kai tsaye ya nufo inda nake ya zauna kusa da ni sosai. Na yi saurin lumshe idanuwana tamkar bacci nake, ina ji ya dinga shafa kumatuna, ya shafi gashin kaina, ya sunkuyo ya sumbaci kumatuna, yasa hannu ya dinga zagaya laɓɓana. "Beautiful,Ina roƙon Allah ya taimakawa rayuwarki, yasa ke ce matata har in mutu, ya sa ki haifa mini ƴaƴa masu tarbiyya kamar ki. I love You." Ya ɗaga hannuwana da suke waje ya janyo bargo a hankali ya lulluɓe ni, sannan ya sumbaci kafaɗa ta. Ina jin motsin janyo durowa a hankali, bayan ƴan mintuna kuma sai na ji an rufe ta, ina jin tashinsa can kuma na ji ya dawo ya sumbaci bakina. "I miss You." Ya zaro hannuna ya tura a ƙirjinsa. "Kin ji yanda ƙirjina ke bugawa don zai rabu da ke." Ya miƙe ya tafi. A hankali na buɗe idanuwana sosai amma zuciyata ta cika da tunanin ina Yarima za shi a cikin daran nan? Na ɗauki wajen minti uku ina tunani tare da al'ajabin fitar Yarima da dare kamar haka,ban kai ga tunani ko baiwa kaina amsa ba, sai kawai na ji ƙarar tashin mota, hankalina na ji ya tashi matuƙa, wannan ne yasa na yi saurin ƙwaye bargon da ke lulluɓe da ni cikin sauri na miƙe saboda kawai in ga inda motar za ta tafi a tsohon daran nan. Cikin lokaci ɗaya abubuwa uku suka saukar mini shi ne mayar da ni baya da aka yi aka ƙwantar da ƙarfi, al'ajabi alamar tambaya. Al'ajabi shi ne ganin jikina ba kaya. Tambaya kuwa,me ya sameni naji jikina ba ƙarfi? Mayar da ni baya kuwa shi ne jikina na ji ya riƙe gam, ga mugun ciwo da na ji yana yi. To me ye kuma? Kafin in karanto amsa kuwa, sai gani ina kokawar jan bargo da lulluɓe kaina saboda firgita da nayi jin wata ƙara na tashi kusa da ni, cikin rawar jiki na samu na lalubo makunnan da ke ƙarƙashin filona tare da karanta Ayatul kursiyu na daure na kunna fitilar ɗakina. Hasken da ya gauraye ɗakina ya yi sakan uku kenan da kamawa amma sai ta cikin bargo na iya leƙo idona ɗaya, da ido ɗayan nan na dinga bin ɗakina da kallo,in ga ta inda ƙarar nan ke fitowa,saman ƙaramar ƴar durowar da ke kusa da gadona (side bed) na ga ɗan ƙaramin agogon tsugunno, sai a lokacin na ji ɗan kuzarin miƙa hannu in ɗauko shi domin kashewa. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 8 Lokacin da agogon ya nuna kuwa biyar saura ƙwata na asuba. Me ya fitar da Yarima ƙarfe biyar saura? Ko dai suna da wani abu ne na sarauta wanda suke yi daidai wannan lokacin? Ni kaɗai ke tunanina, da agogo a hannuna, na ɗan ɓata raina, na girgiza kaina, shi kenan rayuwata ta ƙare, sai da na amince da Yarima, sannan wani sabon halinsa ya bayyana. Cikin sanyin jiki da cikowar hawaye a idanuwana na mayar da agogon na ajiye saman durowar,farar takarda mai rubutun baƙin biro mai ruwan (ink pen) idona ya gani a gefen durowar, na yi ɗan saurin miƙa hannuna na ɗauka, cikin ɗan rawar jiki na kai idanuwana a jikinta. _Barka da Asuba_ _Mace tagari,macen da kowanne namiji na duniya yake son ya mallaki irin ta,kin zama abin alfahari a gare ni._ Na gode. _Na je masallaci, amma komai zai biyo baya, ina neman afuwarki, saboda ni kaina bana son al'adar nan da zata biyo baya yanzun ba da daɗewa ba, ba wai naƙi tsayawa in taimaka miki ba, na kasa tsayawa ne saboda abubuwa guda uku,kunyarki,girmanki, wanda ba za su bar ni haɗa ido da ke ba,sai kuwa masallaci saboda ba a tayar da sallah sai na isa._ _Rashin ganina a masallaci zai iya haifar da ɗan ƙaramin tashin hankali, saboda za su yi zaton ko banida lafiya ne, godiyata ba zata iya samun ki ta baki ba, saboda ban san wane bakin ne ya cancanci ya yi miki godiya ba,ni dai na yanke hukuncin yi miki addu'a da Allah yasaka miki da aljanna firdausi mani'imciya._ _Husband._ Na jefar da takardar na sa tafukan hannayena na rufe fuskata, saboda kunyar da na ji,a hakan ma sai na ga kamar yana tsaye yana kallona, wannan yasa na yi sauri na lalubo makashin fitila na kashe,bargo na ja na rufe har kaina, ba wani tunani da ya faɗo mini sai na ya zanyi in haɗa ido da iyayena da shi kansa Yarima? Tunani ya faɗo mini,na inyi sauri in shirya in ɓuya kafin Yarima ya dawo, amma kuma abu ɗaya yana neman gagara ta, shi ne tashi tsaye, amma duk da haka na samu na yi ƙarfin hali na tashi zaune, na yi shiru ina sauraran ko zan ji motsin Yarima,wai ni gudun kada in tashi ban sani ba ko yana laɓe yana kallona. Tsayin minti biyu na ɗauka sannan na ɗan janyo jikina na kunna fitilar gefen gadona, haske ya gauraye ɗakin nawa,a nan ne na hango rigar wankan da Yarima ya ɗora a saman gefen gadona, na ja jikina zuwa inda take, nasa hannu kenan na ɗauka sai na ji motsin murɗa ƙofa, na yi sauri na janyo rigar na dawo na kashe fitila na koma na ƙwanta. Muryar da na ji tana kirana, "Gimbiya, Allah ya taimaki Gimbiya." Da naji na gane ta mace ce, a cikin rufar da nake na ce, "Wace ce?" "Allah ya taimaki Gimbiya uwar kowa, jakadiya ce, mai girma Yarima ya ce in zo kina kirana,wai zan taimaka miki da wasu ayyukan." Nan take na ji hankalina ya tashi, me Yarima yake nufi? Zuwa ya yi ya gaya mata abin da ya faru da ni? Nan take haushi ya kama ni, da nayi tunanin korar ta amma sai na yi tunani sai fa an taimaka mini, da su Mansura su taimaka mini kuwa ai gara jakadiya, tun da ko banza ta haife ni. "Shigo mana, ba na jin daɗi ne." Na laluba makunnin fitila na ajiye kusa da ni, sai da na zauna nasa rigar wankan sannan na kunna, da rawar jikinta ta iso gaban gadona ta zube ƙasa,tana ɗan sussunkuyar da kai, yanda na ga tana yi shi ya sa nake tambayar kaina da cewa ko Yarima ya gaya mata ne? Kamar ta san tambayar da nayi, sai na ji tana wasu ƴan surutai, "Ai dama duk ƴa tagari shi ne ta cika ɗakinta,a yanzu ba ke ba koni na zama abin girmamawa, tunda matar ɗana ta cika ɗakinta,yau kam shagali ya same mu,ai mu yau sai yanda hali ya yi." "Bana son magana ki tashi ki yi aikinki." "To, to ai komai ki ka ce shi za'ayi." Ta miƙe da rawar jiki, sai na ga ta ajiye wasu ƙwalabe, sun kai huɗu ban dai tsaya tambayar ta ba ta shige banɗaki. "Ai ya tara mana ruwan ɗumin,a gaishe da ɗana,ai fa na raine shi tun ranar da aka haife shi,dama ai in ka raini yaro a gidan sarauta, to kai za kayi masa jakadiya a al'adance, saboda kun shaƙu da junanku, yanzu ne dai ake son rai, sai wasu su dinga ɗaukar wata,kin ga ai ta nan za'a iya haɗa kai da ita a cutar da shi, ke kuwa da kika raine shi tamkar ɗa yake a gareki, ba ke ba cutarwa a tsakaninku. Bari dai ki gani in yi sauri, kada a fara taruwa,ai ni murna ce ma ta hana ni yin komai,kin ga yanzun wallahi duk abin da ki ka faɗa ta zauna, komai ki ke so kuwa shi za'ayi miki,ai daga yau kin zama shalelen Sarki. Duk maganganun da take kuwa cikin rawar jikin ɗaukar ƙwalaban da ta ajiye ne, da rawar jiki ta nufi banɗakin. Kafin ta fito na yi ƙoƙari na miƙe, wanda cikin sauri na na mayar da bargo na rufe zanin gadon da na tashi a kai,dama abu ga zanin gado fari ƙal, cikin dabara na dinga jan zanin gadon, amma ya ƙi fita, ina haka sai ga jakadiya ta fito. "Dama na tanadi kayayyakina,ai ina sai kin juya Yarima kamar waina,na dinga gyara ki kenan, yanzun haka waɗannan sai da na je ƙasar Sanigal na siyo su wajen jika ashirin da biyar,dama burina ɗana ya samu mace tagari." Ni kuwa kamar an kulle bakina, ita kaɗai ke surutanta tana rawar jiki, can sai ta lura da ɗan jan zanin gadon da nake yi. "Ina,ai sai wanda ya zaunu gidan sarauta ya san yanda ake shimfiɗa zanin gadon nan ranki ya daɗe." Tun ta ɓangaranta na ga tana ɓalle wasu abubuwa, ɗora su da tayi a gado sai na ga dogayen abu tamkar ƴar fill ɗin ɓalle kaya (fila) ta ɓalle har ta zo inda nake, tana gamawa na janye zanin gadon na ƙudundune shi. "Don Allah jakadiya kada ki bar kowa ya gani,ki ɓoye mini shi, zan tambaye ki anjima,ko da yake ba ni shi nan ma in shiga da shi in wanke." "A'a Gimbiya me ye amfanina." "A'a bai dace ba, ba ni." "To,ai..ai...ai.....dashi ake... ake...imm...im ki dai shiga wankan in ɓoye miki,ai...ai...ɗana ya kamata dai ya wanke ke dai shiga Gimbiya." Ban dai fahimci abin da take nufi ba, haka nan dai na shige banɗakin na ƙyale ta a tsaye tana ƴan soshe-soshe, ina shiga na ji wani irin mugun ƙamshi, wanda dole idan ya shiga hancin mutum sai ya lumshe idanuwa, daga nan ma zai iya tafiya mafarkin tsaye. Na buɗe idanuwana, na ce lallai jakadiya tana son Yarima zan ce,ko kuwa ni take so? Har na ɗaga ƙafa zan shiga cikin ruwan da ke cike da bahon wankan wanda kalarshi ta koma ja-ja ja-ja, sai na tuno cikin surutan jakadiya na ji tana cewa lallai sai an fara yin wankan sabulu sai ayi wanka, kuma na tsarkake jiki, daga baya sai a shiga ruwan bahon, ana ɗaukar minti talatin har fi a ciki, saboda komai na sinadarin ƙamshin ya ratsa jiki. Na girgiza kaina,lallai harka da irin su jakadiya akwai ilimantarwa, zan kuwa ja ta a jikina ta dinga koya mini sirrikan zama da miji da jama'a,lallai sarauta sai ɗanta,sai kuwa wanda ya gaje ta, wannan turare kullum kana wanka da shi,ai sai ka hana mijinka fita ƙofar gida. Bayan kamar mintuna hamsin da uku na fito daga banɗaki, wani al'ajabi ya dirar mini a take, tawul ɗin da ke hannuna ina tsane kaina na saki ƙasa,shin me ye haka kuma? Ɗakina na ga ya canja gaba ɗaya, wajen zaman gadon da zanin gadon sababbin wasu zagayayyun filalluka sun kai goma sha biyu aka zuba a saman gadon, kowanne an yi masa mazauninsa, shi kansa labulan gadon ya koma kalar zannuwan gadon, haka labulayen da ke zagaye a ɗakin nawa, na ƙara zagayawa sai na ga wata irin lafiyayyiyar kujera zan ce ko gado ƙarama daga gefe, ta sha dardumai, daidai da kafet ɗin gaban gadon an canja mini shi, da komai ruwan fari ne a ɗakin, yanzu kuwa ruwan bulu ne mai haske, ma'ana tamkar fararan kayan da suka sha bula. Mata ne su uku zaune a ƙasa, ban da jakadiya ta huɗu, wani ƙamshi ɗakin ke yi wanda kuma ya sha bambam da na banɗakin da ya ruɗani, saboda mamaki har ma na kasa tunawa da komai,maganar da suka ɗauki yi gaba ɗayansu ita ta dawo mini da hankalina a jikina. Irin kirarin nan da ake wa ƴaƴan sarauta shi na ji suna yi mini,wanda ba zan iya riƙe komai daga cikin abinda suke faɗa ba, na isa wajen abin sallata tare da saka rigar sallata, na sa hijabin sallah, waɗanda na tarar duk an canja mini su, hatta da mazauninsu ma sai da aka canja. Sai a lokacin na ɗago kai na kalli jakadiya cikin ɗan jan kai irin na masu mulki na yi masu magana. Jakadiya ku ɗan bani waje in shirya ko?" "Ki dai kimtsa Gimbiya, amma ai masu shirya ki sun iso suna ƙasa." Wannan maganar ta jakadiya tana yi tana tafiya, wacce a lokacin da ta kai ƙofa ta gama yin ta, wannan ne ni kuma bai bani damar mayar mata da amsa ba,ko kuwa in ce tambayarta ba, da cewa su wa zasu shirya ni, wanda ya wuce ni kaina?. Kafin in gama sallah da lazimin da na kan taɓa bayan kowacce sallar farillah tawa, jakadiya ta leƙo ya kai sau taƙwas a inda daga ƙarshe ta ga na kammala na miƙe tsaye ina ninke hijabin sallah ta. Wannan kuwa ya yi daidai da shidda da ƙwata na safiyar asabar. Ko mai ban ƙarasa shafawa ba na ga jakadiya ta shigo tana cewa, "Ku shigo ku shigo mana." "Me zasu yi miki in sun shigo?" "Dama masu shirin ne." "Shirin me?" "Jikinki,daga gidan Mai Martaba aka turo su." "Ba na so kina jina,ku fita." "Allah ya huce ran Gimbiya ai.." Wayar da ke kan ƴar durowar gefen gadona ta ɗauki ƙara. Cikin gaggawa jakadiya ta isa ta yi saurin ɗauka ta kanga a kunnanta,ganin cikin saurin da bai wuce na sakan ba ta durƙusa ƙasa yasa na gane, Yarima ne ko kuwa shi kansa Mai Martaba Sarki ne. "Eh,to,to." Ta ce kawai,ta cakumo kan wayar ta nufe ni. "Allah ya ja da rai gata." Sannan ta miƙa mini. Kafin inyi magana tuni na gane muryarsa, duk da ji ta ƙara zame mini baƙuwa,saboda ta koma ƴar ƙarama mai zaƙin gaske. "Good morning, I hope you are recovering?" "Darling what happening?" "Oh, darling sorry, honey say hello to me please,ko na samu nutsuwa." Ni na san dama ba zan iya amsa masa duk maganar da zai yi ba saboda abu biyu kunya da haushin tonan asirin da ya yi mini,saboda haka na kife kan wayar ba tare da nayi magana ba,bai fi minti ɗaya da ajiye wayar ba na ga Hajiya Kilishi ta yi sallama ta shigo. Subhanahi! Shi kenan ƙaryata ta ƙare, wannan tonan asirin na san ya je kunnan Sarki. Hawaye ma na ji kawai sun tarar mini a cikin ƙwayoyin idanuwana,mata biyar ne biye da ita, da ganinsu ka san matan masu faɗa a ji ne, wato matan masu kuɗi, saboda biyu daga cikinsu na san su suna zuwa duba ni da na zauna zaman jinyar saran maciji a gidan Sarki. Kaya ne lodi-lodi a hannunsu, irin farantan da jakadiya ta taɓa kawo mini kayan siyan baki,a ranar da aka bar ni ni ɗaya. Da ƙyar na samu na gaishe su saboda kunya. A nan jakadiya ta gayawa Hajiya na ƙi yarda a yi mini komai, da lallashi da ban magana ta shawo kaina, shi ma dan ina jin kunya da nauyinta, ga shi kuma tana da girma a idanuwana. Ta tabbatar mini da cewa ita ma haka aka yi mata, sannan duk ɗan hakimi a kan haɗa masa ƴar ƙwarya-ƙwaryar irin wannan bikin idan dai har matarsa takai, to balle ni wai da nake matar ɗan Sarki gaba ɗaya. Dole dai ta sa na tsaya,nan fa naga hidima, ƙunshi mai zane, hannuwa da ƙafafuwa, wani irin naɗin kitso ƙwaya shida kacal, wanda na ga ya fi yi mini kama da kalba, amma bambancinsu shi naɗinsa kamar ana murɗa igiyar shanya. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 9 Ni gyaran da ake yi mini ko ina amarya Ni ban same shi ba, saboda sai da Hajiya Kilishi ta sa na tsugunna ga turarurruka kala-kala shida, dukkansu kuma na garwashin wuta, sai a lokacin da suka gama ne ma aka buɗe kayan da suka shigo da su. Wata ƙwarya ce ta sha zanan baƙi ƴar ƙarama aka miƙo mini,wai in shanye abin da ke cikinta, ban yi gardama ba na kafa bakina sai naji kamar ruwan inibi da madara, kamar kuma madara da ruwan ƙwaƙwa, ni dai na shanye. A taƙaice dai hidima ta tashi sabuwa tamkar ana wani ƙasaitaccen biki. Ƙarfe goma na safe kuwa ai gida ba inda zaka zauna, saboda jama'a. Hajiya Kilishi ta gaya mini cewa za'a tambaye ni me nake so, saboda mutane da kunya da wuya in iya magana, amma in rubuta a takarda,in an tambaya in bai wa jakadiya,kar in yarda wai a ga fuskata sosai,in zamo mai kunya. Da za'a fita da ni inda zan zauna, sai da aka sa nayi tsaye na ware ƙafafuwana a saman wani kaskon wuta mai fitar da hayaƙin ƙamshi, shiga ta kuwa ba zan iya faɗar ko meye a jikina ba,ni dai kiran shi da yadi mai laushin gaske,ko kuwa les ne? Oho,ni dai na san sai dai kalar sa ce ruwan hoda, takalma da alkyabbar jikina kuwa ruwan madara ne, tare da mayafin da na zizara a saman kafaɗa ta. Wannan al'ada ina amfaninta, na faɗa a zuciyata. A lokacin da na isa kujerar zamana inda muka zauna ina amarya,yau ma anan muke,ni da Yarima, sai dai kujerun da shimfiɗun kafet ɗin sun sha bamban da na baya,sam ban sani ba, ashe kowa ya hallara ni kawai ake jira, hatta da sarki ya iso yana nashi rukunin, ango Yarima kuwa nan na sameshi a zaune. Ba zan iya gane ko su wa da su waye ba ne a bayana, saboda gilashin da ke manne a idanuwana, ban da wani mayani da Hajiya Kilishi tasa ta ɗan lulluɓe min rabin fuskata, filin kasan ƙasan kuwa daga can gefe ɗaya raguna ne kawai ake gasawa a ƙarƙashin wuta, tamkar dai waɗanda zasu yi fati. Aka buɗe fili da addu'a da sauran bayanan manyan mutane, wanda a ƙarshe Sarki ne da kansa ya miƙe yana bayani da godiya ga waɗanda suka zo,ni kuwa da ɗansa Yarima mun sha albarka, a lokacin ne naji Yarima ya zuro hannu ta alkyabbarsa ya kama hannuna. Ban da dama tun da na zauna yake ta zunguran mini ƙafa da tashi ƙafar, ta ƙarƙashin kujerarmu,ni na san ba mai gani, tunda alkyabbun jikinmu sun rufe har ƙafafunmu, na ji kalma ɗaya da ya faɗa ita ce, "You Are cheerful Yasmin." Na samu na sulale hannuna ba tare da na kalleshi ba. Ƙyaututtuka kam na sha su, shi kansa Sarki ƙyautar gidan gonarsa na ƙauyan Bukuru ya ba ni, ya kuma ce zan ziyarci ƙasa huɗu, sai wacce na zaɓa, sannan ya baiwa iyayena sababbin motoci guda biyu, ban da wani dunƙulin abu a cikin jar jaka da naga ya ce tasu ce, sai dai ban san komai ke ciki ba. Waziri ya bani bayi huɗu da dokuna uku,doki biyu goɗiya, ɗaya namiji, da sabuwar mota ƙirar KIA (Optima). Ni wata ƙyautar ma in an faɗeta sai inji kamar ma ƙarya sukeyi, magana kuwa cikin nutsuwa yanda ba mai ji, Yarima ya dinga yi mini ita sau ɗaya na yi murmushi, na ji ya ce, "Thank God." Kaina na ji ya sara tare da juyawa wani amai mai zafin gaske da na ji ya taso mini,wannan kuwa ya sameni a daidai lokacin da na ga wasu fadawa biyu sun miƙe tsaye da wani farin abu a hannunsu,sam da ban gane ko meye ba, sai lokacin da naji sun ce, "wannan farin zanin da kuke gani, shi ne zanin shaidar cewa ƴarmu ta kai ɗakinta, wato Gimbiya Yasmin." A take na gane zanin gadon ɗakina ne wanda na baiwa jakadiya amanarshi, shi ne fa hankalina ya yi matuƙar tashi, a take na tallabe ƙirjina alamar amai, Yarima ya yi saurin dafa ni. "Yasmin meye?" Wata tambayar raini ma na faɗa a zuciyata, kafin ya ƙara yin wata magana sai dai na hango an ware zanin gadon nan kowa ya kama gefe ɗaya, kenan dai an yi masa buɗewar zanin da za'a shanya. Cikin sakan biyu sai dai na ji amai ya wanke mini jiki dama ni gani ban iya ganin abin tashin hankali ba, sai inji ni ina ta amai, kamar wata mai yaron ciki,ko kunya ma Yarima bai ji ba naga ya miƙe da sauri ya kama ni,kafin sakan uku sai dai na ga wani koran labule ya sauka a gabanmu da bayanmu dama gefenmu ba kowa kujerunmu ne kawai. Cikin ƙanƙanin lokaci Yarima ya ɗaga ni na miƙe tsaye,da amai ya yi tsalle sai jikin Yarima amma sai na ga ko a jikinsa shi dai buƙatarsa in taka,gyaran murya na ji ya yi sai dai na ga hannu ya zuro ta wata ƙofa ya miƙo masa wani yanki ja, mai kama da yankin bargon jariri, har ya fara goge mini,ganin ina layi yasa na ga ya ɗauke ni cak sai dai na ji ya yi gyaran murya. A take na ga kawai yana tafiya labulan nan na binmu ba mai ganin kowa ba mai ganinmu, shi kuwa ɗan yankin nan ya shinfiɗa shi saman ƙirjina wanda amai ke ta zuba a jikinsa,ni dai dole ta sa na koma saman ƙirjin Yarima na ƙwanta, idanuwana kuwa tuni a lumshe suke. Jin an ajiye ni wani abu mai laushi yasa na buɗe idanuwana,gani na a ɗakina saman lallausar katifar mulkin nan zan ce ko kujera? Wacce ta sha dardumai na alfarma, da rawar jiki na ga ya cire alkyabbar jikinsa da ta sha feshin amai, sannan ya duƙo wajena yana ƙoƙarin cire mini tawa,na ɗaya masa hannu alamar ya tsaya. "Don't touch me." Na faɗa. "Yasmin ki yi haƙuri in taimaka miki." "Bana so,ni ka kira mini Aunty Salwa." Na saka kuka, yayin da na ci gaba da cewa "ka cuceni,ka tona mini asiri,ka yaudare ni, Allah ya saka mini, yanzun kuma gidanmu zan tafi, ba zan ƙara zaman dabbanci ba a gidanka,ƙiri-ƙiri ku mayar da al'ada addini." Yasmin ni kaina ba na so, ya zan yi dama na san sai kin zarge ni." "Zargi ne ma?" Ya zauna jikin gadon zai kama ni. "Kada ka taɓa ni,wa ya sani ko yanzun ma ka fita ka faɗawa jama'a cewa ka rungume ni." "Oh! My Darling....." Dagewa na yi nasa kuka mai ƙarfi, sai na ji ya tashi ina jin takun fitarsa,bai fi minti biyar ba sai na ji an shigo. Aunty Salwa ce ta shigo da saurin ta. "Aunty kin ga Yarima ko, ya cuceni, ya wulaƙanta ni a gaban jama'a." Na ƙara sa da kuka. Ta iso ta zauna kusa da ni tare da dafa kafaɗata. "Haba Yasmin bai dace ba a ce kin zargi mijinki ba a kan abin da ya faru,in har za kiyi la'akari da taron da aka yi a yanzu, wannan zai nuna miki cewa tun kafin a san za'a haifi shi kanshi Sarkin haka akeyi, na fahimci al'ada ce su wacce take muhimmiya a wajensu. Saboda muhimmancinta fa Sarki da kansa yau tun da baƙwai na safe ya je ya gayawa Daddy,kin ga irin murnar da Sarki ke yi kuwa,ni a ɗan tunanina da na yi, wannan shi ne mataki na ƙarshe da za'a gane wa ye Sarki na gaba,in ka dace da mace tagari, to daga lokacin ma za'a iya kiranka Sarki mai jiran gado,in kuwa da sauƙi, to ko mutuwa sarki ya yi an san ɗansa wanda ya cancanci a baiwa sarauta. Ki yi tunani ki gani,ni tunanin abin da za ki yi ƙoƙarin ki hana a nan gaba, shi ne yin taron,ko nunawa jama'a zanin gadon yanzun ki tashi ki canja kayan jikinki, kamata ya yi ma ki ɗan shiga ruwan ɗumi." Aunty ce ta taimaka mini na shirya jikina na ƙara narka wasu kayan, duk da cikin waɗanda Mama ta aiko mini da su ne, shi ma wani irin yadi ne na alfarma mai ruwan jinin kare mai duhuwa (Coffee colour), Ina niyyar in koma in da ake taron, amma ina sai na ji zazzaɓi ya rufe ni. Aunty ta ɗauko magani ta bani na sha, amma duk da haka, sai na ji ƙwanciya kawai nake so. Ƙarfe ɗaya da ƙwata limamin masallacin gidan Yarima ya ƙwallah kiran sallar azahar,jin mata na ta ƴar hayaniya yasa na gane an tashi, amma sai na ƙara yin lamo saboda kunya da ta hanani haɗa ido da kowa, ina jin su Hajiya Kilishi da sauran mutane aka shiga ana yi wa Aunty ya mai jiki. Yanda na ji Aunty nata hira da mutane yasa na gane lallai da ƴan'uwanmu suke hira,shin wa ya gaya musu? Haushi da takaici suka ƙara dirar mini a zuciyata. Yanda na ji ana yi masa sannu da zuwa da tambayarsa ya mai jiki shi ya tabbatar mini da Yarima ne ya shigo, ƙara lamo na yi tamkar ma yanzun na fara barcin, ina jin shi yana tambayar na yi sallah? Aka bashi amsa a'a, sai na ji ya ce lallai a tashe ni inyi sallah. Bayan sallar isha'i ne ya shigo ɗakina ni kuwa a wannan lokacin na samu sauƙi sosai kamar ma ban yi wani zazzaɓi ba, asali ma ina zaune a kan abin sallah ta da alƙur'ani mai tsarki a hannuna ina karantawa, ba don komai ba saboda godiya ga Allah da ya taimakeni na riƙe mutuncina, sannan na yi godiya ta musamman ga iyayena da suka yi mini tarbiyya tagari. Maimakon ya yi mini magana sai na ga ya zauna gefen gadona, ina jin gani ya yi ba ni da niyyar dainawa, saboda ya yi kusan mintuna ashirin da biyu, amma sai in buɗe wani fejin in cigaba, ganin haka na san yasa shi ya taso ya zo ya zauna bayana, madadin inji ya yi magana sai na ji ya ɗaga hijabin da ke jikina ya shiga ciki, daga nan kuwa sai dai na ji ya sa hannayensa ya rungume ni ta bayana, kenan hannayensa suna saman ruwan cikina, sai a lokacin na ji ya yi magana. "Ya isa haka nan Yasayyada, ya kamata a zo a kula da baƙo ko shima ya zo ya yi wa matarsa sannu. Madadin in tashi ko in mayar masa sai dai na ajiye Alƙur'anin na mayar da kaina na matse a tsakanin gwaiwoyina saboda dalilin abu biyu. Na farko na san ni ba zan iya haɗa ido da shi ba, saboda kunya. Na biyu kuma saboda ɗan haushinsa da yake a zuciyata. Ganin ya samu sama da mintuna sha biyar yana fama da ni in ma yi masa magana na ƙiya, ya sa naga ya sake ni ya miƙe tsaye,dama tuni ya cire hijabin jikina ya mayar da ni ya ƙwantar a cinyarsa,yana ta ɗan kokawar cire tafukan hannayena waɗanda ke rufe da fuskata, wanda ko ya cire zan runtse idanuwana da ƙarfi. Sai dai na ji yana cewa, "Mama ta ƙi yi mini magana, Mama ki zo,wai haushina take ji,ni ma na gaya mata ba laifina ba ne ba,kona ba ta ba zata karɓa ba." "Kai! Ni na ce." Na faɗa cikin sauri. Ya juyo muka haɗa ido na harare shi. "Dama na ce miki cewa ta yi ni ɗin me." Na taso zan karɓi wayar ya juya na bi shi ya juya na riƙe hannunsa,wai ni in karɓe wayar, amma saboda ƙarfi irin na namiji ya riƙe hannun gam. "Mama ban yi mata ƙarya ba, cewa ta yi ban isa in sa ta karɓa ba." Na yi tsalle na fige wayar. "Mama wallahi ba da gaske ba ne ba sai na kashe wayar nasa kuka. Bacin ka gama wulaƙanta ni a gaban jama'a yanzun kuma so ka ke mahaifayarka ta tsane Ni?" Na tafi na faɗa gado. Kusan mintuna arba'in kenan da zuwan Mama,ni kuwa tsugunne a falo jikina ya sha naɗi da hijabi, hankalina ya nutsu da abin da Mama ke faɗi, kamar yanda ta fara da farko. "Ba wata kalmar da zan yi amfani da ita inyi miki godiya, sai dai inyi amfani da ƙarfina in yi miki addu'ar Allah ya saka miki da ƴaƴa nagari, kamar yanda iyayenki suka yi dace da ke ƴa tagari. Ki yi haƙuri ki zauna da mijinki lafiya, duk abubuwan da suka faru a baya ya kamata a ce kun haƙura kun ajiye su gefe,kun mayar da su yarinta, wannan abu kuma da ya faru abu ne na al'adar sarautar gidan nan tun iyaye da kakanni. Hikimar yin shi kuwa shi ne hana rigima idan Allah ya ɗauki ran Sarki,a wancan zamanin,kin san kowacce masarauta a wancan zamanin da irin hikimar da ake amfani domin fitar da Magaji,wato wanda zai gaji sarauta. A zamanin da zaki ga wata masarautar su kan sa yaransu su yi tafiya mai nisa domin ɗauko wani abu ko samo wani abu. To su kuwa wannan masarautar ta haka suke ganewa. Ina son ki yi murna kuma ki godewa Allah da yasa ki ka samu kanki a wannan matsayi. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 10 Tsaya in baki wani labarin da ba wanda ya san shi daga ni sai Mai Martaba, sai kuwa ita wacce abin ya sama sai kuwa Allah. Kin ga wannan abin da ya faru da ke a yau, to shi ne ya haddasa tsana mai tsanani tsakanin Sarki da matarsa ta farko, Hajiya uwarsu Abdulrahman, da na taɓa ba ki labarinta. Mai martaba ya bani labari cewa, lokacin da aka kawo ta tana amarya ita ce ta dinga nuna masa ya zo gareta,kin san yanda auran sarauta yake da wuya a bar ka ka auri wacce ka ke so, sai dai a zaɓa maka. To wannan ne yasa ba so a tsakaninsu, lokacin wata ƴar barga yake so, wato irin ƴaƴan masu aikin gidansu, aka hana shi auranta aka aura masa Hajiya Asabe. Ranar da Allah yasa za su haɗu da ita a matsayin miji da mata, sai ga shi ya sameta ba yanda ake so ba, wato ta taɓa sanin wani bayan shi. Tun a daren ya kira jakadiya ya sanar da ita, jakadiya ita ta kawo shawarar a samo kaza a yanka ta,jininta a zuba shi a shinfiɗarsu, wannan dabara ita aka yi, balle a wancan lokacin jakadiyarsa mai himma ce da wayo, ita ta yi masa wannan dabarar har ya samu ya haye a matsayin zai gaji sarauta. Tun daga wannan lokacin ya tsani Hajiya Asabe, har ya zama yana zarginta da fita waje in ta fita unguwa. Ke a ƙarshe dai sai da suka rabu hankalinsa ya ƙwanta. Ke ki godewa Allah ko in ce mu godewa Allah, wallahi ni ma nan da ki ka gani sai da aka yi mini wannan taron,ki yi haƙuri ki zauna da mijinki lafiya. Mu dama tuni abin da muke son ji kenan, saboda duk wani masoyin Yarima zai so a ce ya ji wannan ranar, ta zo kuma yanda ake son ta. To ni zan koma sai kun zo mana sallama ko, Allah ya yi muku albarka, kira shi ki ce ni zan koma." Abin ka da falon sama muke dama sai kawai na shiga ɗaki, ina shiga ya ɗago kai ya kalleni daga inda yake ƙwance,bai tashi ba har na iso gabansa. "Mama na kira." Na samu na faɗa,a inda na juya na koma wajenta. Sallama kawai ta yi da mu ta yi tafiyarta,iyakata bakin ƙofar falo, Yarima kuwa shi ne ɗan doguwar rakiya. Kafin Yarima ya dawo ni kuwa har na saka rigar baccina na haye gadona, saboda ba zan iya cigaba da haɗa ido da Yarima ba. Ina kallon shigowarsa, ta ƙyallin idona ɗaya, ya zo ya tsaya a gabana kallona kawai ya dinga yi yana murmushi. Ya yi tsayin mintuna biyu a haka, sannan ya shige ciki, kenan ya koma ta bayana,ni ga shi babu damar in juya in kalli me zai yi ba. Ina jin shi ya shigo cikin bargon da nake ƙudundune sannan ya hayo ta saman jikina ya ɗauki makunnin kashe fitilar ɗakin. Me ya manta? Na faɗa a zuciyata, saboda jin ya sauka daga saman gadona,ƙyallin idona ɗaya na ƙara buɗewa a nan ne na ga ya isa ga ƙofa yasa makullintaa ya kulle, cikin bargon ya koma tare da kashe fitilar ɗakin gaba ɗayanta, ina jin shi ya zare ɗan abun ɗane gashin da na sa na ɗaure gashina (band) cikin ruwan sanyi na saukar da ajiyar zuciya jin ya sumbaci bayana, tare da rungume ni jikinsa ta bayana. "Na san kina ji na ki kayi shiru, because you hate me Yasmin,har abada ba zan taɓa yaudarar ki ba,sona,ƙaunata, mulkina,ƘASAITA, duk naki ne,in har babu ke a tare da ni na san zan iya zama ba ko ɗaya a cikin abubuwan da na lissafa,ni na san ƘASAITa ta biya ni, tunda ta hana mata da yawa yi wa rayuwata katsalandan. Ki yi tunani, da ni mutum ne mai sakin fuska da mata nawa ne zasu dinga neman cin fuskarki, saboda suna kishi da ke. Ke kaɗai na fara sakarwa fuskata, da jikina baki ɗaya, kuma na yi imanin ke ce ƙarshe. Please Yasmin ki saki jiki da ni saboda ke special ce a gare ni, kamar yanda sunanki ya ke special a wajen jama'a. Ki so ni,zaki sameni mai sauƙin kai, komai ki kaga na yi na mulki a baya, saboda tsare mutuncin kaina ne." Ya kama ni ya juyo ni a jikinsa sosai kumatuna ne ya ƙwanta a ƙirjinsa ya yi ɗan saurin ɗago kaina na san dalilin ɗaga ni haka. "What? What? Yasmin, still you hate me." Na koma na ƙwanta a ƙirjinsa mai ni'imtaccen gashi, ina jinsa ya yi ajiyar zuciya ya ƙara rungume ni gam a jikinsa. Gashin kaina yasa hannu yana ɗan shafa shi a fuskata, ban iya buɗe idanuwana ba, amma nasa hannuna na riƙo gashin tare da yin murmushina. "Zan je sallah ne masallaci ki tashi ki yi taki sallar, saboda yau zamu ɗan fita zuwa wani ɗan lokaci, amma ƙasar Greece za mu fara zuwa,a can nayi karatuna, sai in nuna miki wuraren dana sani, ragowar ƙasashe uku ke ce za ki zaɓa." "Ni ba zan je ba." Ya sa haƙoranshi ya cije laɓɓana duk biyun, har sai da na ɗan yi ƙara kaɗan, na samu na ƙwace na cusa fuskata a ƙirjinsa. "Zane ki zan yi da tsintsiyar ƙwaƙwa na ga alama." Nasa yatsuna na ɗan ja gashin da ke ƙwance a ƙirjinsa, yasa ƙara kaɗan tare da ƴar kokawar ƙwace jikinsa ya mirgina ya tashi yana dariya ya sunkuyo ya sumbaci kumatuna. "Zan rama ne, gudu nake kada na makara da kin faɗa." Ni kuwa na ƙudundune kaina a filo, ina ƴar dariyar murmushi ina jin shi har ya kammala alwalla ya fito daga banɗaki, saboda jan faɗa har da buɗe ƙafata ya yayyafa mini ruwa. "Tashi." Na yi saurin jan ƙafata shi kuwa ina jin dariyarsa a hankali har ya fice daga ɗakin. Fitarsa zan iya cewa jinkirin minti ɗaya na yi na miƙe da tsallen murna, na sauka daga gadona, jin ƙuguna ya ɗan amsa, shi ya tuna mini ashe fa ba na jin daɗin jikina, na yi murmushi na shige banɗaki tare da tunanin na zama ta Yarima Faisal. **** **** ***** Ƙasar Greece,nan muka sauka FIVE STAR HOTEL,shi ne masaukinmu, wanda ɗakinmu shi ne ɗaki na ɗari da goma sha biyu (112) , ya kama kuma hawa na uku kenan. Bai fi mintuna biyar ba da shigowar mu ɗakin ba wata ƴar ƙararrawa ta kaɗa cikin sauri na ga Yarima ya fita falon da muka baro,mu kuwa muna ɗaki Yarima na ɗan shirya mana kayanmu. Jin an ɗauki ƴan mintuna yasa na fito falon da ɗan saurina, fararan mutane ne biyu Turawa, sanye da farar rigar shirt da bulu ɗin wando, sai baƙaƙen takalma a ƙafarsu, wannan ne ya nuna mini alamun su ne ma'aikatan hotel ɗin da muka sauka. Baki ɗayan hankalinsu ya dawo gare ni,ni kaina sai na ji kunya ta kama ni kallon da na ga suna yi mini, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci Yarima ya nufo inda nake. "Shiga ciki." Ya faɗa a daidai lokacin da ya iso gareni. Na shiga ciki ina ɗan murmushina na mamakin yanda Yarima ya nuna kishinsa a fili. Wajen yammarsu, wacce a tamu yamman za mu iya kiranta ƙarfe biyar da wasu mintuna na yamma. A lokacin ne muka gama komai muna zaune a falonmu mu dai ga mu nan, ba ka cewa ƙiyayya ba kuma za ka kira mu masoya ba, tunda kowa a kujerarsa yake a zaune,ni zan iya cewa kishingiɗe nake a tawa kujerar duk maganar da ya yi idan ta amsa ce in bashi amsarta,in naji zan iya. Ana cikin haka hankalina ya kai ga talabijin ɗin da ke ta aiki ita kaɗai, na yi saurin tashi zaune har da ɗan salatina. "Me ye?" Ya tambaye ni. Har sai na ji na ɗan ji kunya, "Wa ye wannan? Ɗan uwanku ne?" "A'a. Ya naga kina ta murnar ganinsa?" "Ɗan wasa ne na finafinan Indiya." Ya gyara zama sosai. "Ya sunansa?" Na ce, "Sharukhan." "Haka nan ki ke son ganinsa?" "Ina bala'in son shi ne, ya iya acting." "Me kika ce?" "Cewa na yi ina son shi." Ya yi murmushi mai fitar da sauti. "Ko wajensa za ki koma?" Nan take na juyo na kalli fuskarshi,ko kallona ma bai yi ba, balle ya bani wata amsa, na miƙe na nufi cikin ɗakina na ƙwanta,bai fi mintuna sha biyar ba sai gashi ya shigo, ya iso ya zauna gefena. "Ban fahimci abin da ki ke nufi da tasowa ki ƙwanta ba, daga na yi miki maganar mutumin da ba muharramin ki ba?" Ya juyo sosai ya sumbaci kumatuna. "Ki yi haƙuri in kin ji ba daɗi." Na ɗan yi murmushi. "Ban ji komai ba, na dai zo na ƙwanta ne kawai." "To taso mu sauka ƙasa ki ga mutane kafin gobe in kai ki wurare da dama waɗanda na sani." Na yi murmushi na tashi zaune, da niyyar in tashi mu tafi, ya riƙe hannuna. "Kisa doguwar suit ɗinki,saboda jama'a." Yau ƙwananmu huɗu a ƙasar Greece,a ƙwanakin ukun da muka fara fita ba inda Yarima bai kai ni ba, wuraren wasansu na yara, amma su manya ma na zuwa,a nan ma ya ga na fara sakin jiki da shi, balle da aka ɗora ni wata mota mai sa jiri ina saukowa na kasa tafiya, sai dai Yarima ne ya ƙwantar da ni saman kafaɗarsa muka samu wajen zama yana yi mini dariya. Wani abin burgewa irin na ƙasar Turawa, shi ne ba wanda ya damu da abin da ka ke ciki, balle a tsaya kallonka, shi kansa Yarima sai yanzun na ƙara gane cewa dogarawan da ke bin shi a baya suke ƙara masa girman kai, amma yanzun ba ki gane shi ko ɗan waye. A ƙwanakin nan huɗu kuwa ba wata alama da Yarima ya nuna mini sai ma ɗan tilasta ni in yawaita shiga ruwan ɗumi cikin hikima irin tasa. Tabbas Yarima na sona,ni kaina na amince da hakan,ni kuwa zuciyata har yanzun tana baƙunta da shi, shi ne ta kasa tsayawa ta saki jikinta da shi, har ta gano irin son da take yi masa. Yanda nake ƙwance a gadon da ke bakin ramin wanka,in ka hango ni ba ni da maraba da Turawa, saboda kayan jikina,siket ne baƙi da farar riga a jikina, wanda gilashi ne manne a idanuwana, irin ɗaurin ɗanƙwalin Turawa nima shi na yi, shi ne ka ɗaure gefe-gefe amma tsakiya a baje saman baya. Kaina ƙwance yake gefe, ina kallon cikin ramin wankan,babu inda idanuwana suke sai kan Yarima da ke ta wasan wanka a cikin ruwan, duk da duk ɗan lokaci ya zo bakin ruwan ya ɗan watso mini shi kaɗan,in ɗan yi ƴar ƙarar ƙissa, shi kuwa ya yi ƴar dariya ya ƙara komawa sosai cikin ruwan. Ganin inda ya nutsa kansa ya tsaya cak ruwan baya motsi irin ana wanka da shi, shi yasa na ɗan ɗaga kaina sosai ko zan ƙara hango shi, amma ba na ganin sa ko kaɗan, cikin sakan ɗaya sai na ji kamar kaina ya sara, irin na tashin hankalin nan, ban san lokacin da na miƙe tsaye ba, isowa na yi bakin ruwan na tsugunna duk gwiwa biyu ina jira,in ga ɗagowar Yarima. Tun ina ganin kamar wasa, har na ga ya ƙwashe mintuna,nan take na ji kamar kaina ya fara juyawa, na waiga ban hango wani wanda ya yi kama da ɗan Afrika ba, ballantana in kirawo shi, abin ka ga ƙasar Turawa, kowa da tashi hidimar ba ma wanda hankalinsa yake a kaina. Juyowar da zan yi sai na hango Yarima ƙwance saman ruwa, amma ta bayansa kenan kanshi da cikinsa duk a ruwan suke, na miƙe tsaye na yi kamar in yi ihu, to wa zan yi wa,ni kuwa dalilina na ƙara ruɗewa a irin ƴan fina-finan da nake kallo na san in an ga mutum a saman ruwa to ya mutu kenan. Ganin ba zan iya zuwa cikin hotel ɗin ba in kira ma'aikatan yasa na ji wani ƙarfi ya zo mini ban san lokacin da na shiga cikin ruwan nan ba sai dai gani na nayi ina kokawa da gangar jikin Yarima,manufata in juyo fuskarshi ta kalleni ta hakan zan gane ko yana da rai. Duk cikin mintin da bai wuce ɗaya ba na yi haka,babu wani alamar rai a jikin Yarima a lokacin da na juyo shi nan take na ji zazzafan gumi na tsiyayo mini ta saman gashina, ban da mugayen hawayen da ke shatata ba tare da an rera masu waƙar kuka ba. Ƙarfi na ji ya ƙara zo mini cikin rawar jiki na ji na janyo shi zuwa bakin ruwan, sannan na yi ta maza na ɗora shi saman gefen ruwan, da rawar jikina na zagaya na fita daga ruwan. Sannan na janyo shi. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 11 Amma ina namiji ba mace ba sai ma ya ƙara komawa cikin ruwan nan, take na sa ƙara mai tsanani, na ruga a guje ina cewa a taimaka mini da harshen Turanci, ma'ana. "Please help me! Help me!!” Nan da nan aka zagaye shi ni kuwa gani nake duk ba su isa ba, tunda ba ma'aikatan hotel ɗin, da gudu na isa falon da ake fara karɓar baƙi (Reception) da harshen Turanci na yi masu bayani, kafin minti biyu har sun riga ni isa inda yake, ina isa na cakume shi, cewa nake, "Yarima ka tashi! Tashi!!...” har sai da suka ɗan riƙe ni, sannan aka danna ƙirjinsa da cikinsa sai ruwa ya ɗan fito ta bakinsa. Na fizge na zo na ƙara kama shi,a taƙaice dai ban ƙara sanin abubuwan da na dinga faɗa ba har aka kawo ɗan wani gado aka ɗora shi, sannan aka tambaye ni lambar ɗakinmu da ƙyar na iya faɗa,saman gado aka ƙwantar da shi na warware bargo na rufa masa, sannan na ga an yi masa wata allura a jijiya, cikin sakan biyu na ji ya yi wani tari, na ƙara riƙe hannunsa gam, cewa nake. "Tashi! Tashi!! Tashi!!! Yarima kada ka mutu." Sun gaya mini da harshen Turanci, zai tashi amma in dinga murza tafin hannunsa, da ƙyar na amsa da to. Sannan duk suka fita na kuwa dage goga hannuwansa duk biyun in na yi wa ɗaya in saki in kama ɗaya,kai sai gani har da busa bakinsa,ni sam na ma manta da wani haɗa baki muke yi da shi, wani ihu bayan hari zan ce, saboda wai sai a yanzun na ji ina mugun son Yarima, amma kuma ga shi a saman gado ya zame min ƙila wa ƙala. Na samu wajen minti talatin a haka, wanda hakan yasa na ji na karaya, sai kawai na ƙwanta saman ƙirjinsa na dinga kuka. Kuka mai tsananin gaske, amma ba wanda ake ihu ba, wanda gangar jikinka duka ke motsawa. Sama da mintuna ashirin ina haka wanda tuni har tunanina ya bani in bugawa Aunty waya in ce a zo a tafi da mu. Hannu na ji an sa an shafi gashin kaina ɗan motsi da numfashi su suka sa na yi saurin ɗaga kaina saboda in ga mai taɓa mini gashina. Yarima ne ke kallona yana murmushi, na yi wata sassanyar ajiyar zuciya na dinga murmushin daɗi don ma ina jin kunyarsa da tuni na yi tsalle. Na tashi da sauri na dawo saman gadon na faɗa jikinsa ya mayar da hannuwansa ya rungume ni ina jin shi yana ta shafa gashin kaina, alamar lallashi ina jinsa yana ƙoƙarin ya ɗago ni amma na rungume shi tamau, ina jinsa ya faɗi kalmomin nan da harshen Turanci. "Yasmin do you love me now? Zaki iya sakin jiki da ni?" Na ɗaga kaina wanda ke ƙwance a tsokar naman kafaɗarsa. Tabbas murnar Yarima ta fito fili,dana amsa masa ina son shi, ya ɗauke ni baki ɗaya ya ɗora ni a gadon da yake ƙwance, ya mayar da ni ya ƙwantar a ƙirjinsa ya janyo bargo ya lulluɓe mu a ciki, fuskokinmu kawai ke waje, na ɗago na ce masa. "Ka samu sauƙi?" Ya yi murmushin da yasa na ji sabuwar kunyarsa ta dirar mini sannan ya ɗaga kai alamar eh, wanda jin ɗaga kan kawai nayi saboda ni tuni na mayar da kaina a ƙirjinsa na ƙwantar. Lallai yanzu zuciyata da gangar jikina sun amince mini da ina son Yarima,su ma kansu son Yarima ya cika su dama. Na yi sauri na ɗan yi alamar zan tashi ya ruƙo gashina ta bayana, na juyo da sauri har da ƴar ƙara da ido da kai ya tambaye ni ina zani? Na sunkuyar da kaina ina murmushin da yake fita tare da ƴan ragowar hawayen idanuwana. "Magani zan ɗauko maka, likita ne ya ce da ka tashi na baka." Da kai ya nuna mini cewa inje na ɗauko, ina murmushin mamaki na cikin zuciya kenan bai fito fili ba, saboda mamakin yanda Yarima ya ƙware da maganar kai ko da yake ba mamaki idan na yi la'akari da farkon haɗuwata da shi yanda ya yi wa dogarawansa magana da gilashin hannunsa. Bayan na kama shi ya tashi zaune na taimaka masa na jingina shi jikin kan gado wanda nasa filo a bayansa sannan na zauna kusa da shi na miƙa masa maganin da ruwa a kofi, maganin ƙwaya ɗaya ne ɗan ƙarami, sannan na ƙara janyo kujerar da na ɗora ɗan farantin da kofin maganin na ajiye kofin sannan na miƙa masa kofin ruwan madara ya shanye. Saboda magriba ta kawo jiki,in na yi la'akari kamar a ce ƙarfe shida na Nigeriya kenan, wannan yasa na ce ya yi ƙoƙari ya je ya shiga ruwan ɗumi a banɗaki ko ya samu ƙarfin jikinsa sosai,bai yi mini gardama ba ya miƙe abinka ga namiji sai na ga baya ko irin ɗan tangaɗin nan na marasa lafiya. Ina zaune ni kuwa na rabka uban tagumi a gefen gado ina jiran ya fito, wanda tuni na tafi duniyar tunanina, na da Yarima ya mutu da ya zan yi? Ba don komai ba sai don yanda zuciyata ta fara nutsuwa wajen son zama da shi a matsayin mijin aurena,wai don shirme sai na ji hawaye sun taho na samu na lumshe idanuwana su kuwa suka ci gaba da gangarowa. Ban ji fitowarsa ba, saboda idanuwana a lumshe suke, kuma linzamin tunanina ya canja salo ya koma tunanin abubuwan son da Yarima ya nuna min a fili, na tuna ranar da ya mallake ni a matsayin matarsa irin nuna so da ƙaunar da ya yi mini a wannan daren ƙwaya ɗaya cal. Jin an sumbaci laɓɓan bakina shi yasa na dawo daga duniyar tunanin da na tafi, na buɗe lumsassun idanuwana sai na ga Yarima tsaye a kaina, na yi saurin ƙwantar da kaina a cinyata na ce, "Kai Yarima." Cikin kunnena ya ce, "Ke Yasmin me ye.?" Na ɗaga ɗanyatsa na nuna shi, "Me ye,tawul, Yasmin sai in ƙi ɗauro tawul ni da matata ni ne fa kawai a ɗakin" Da jin yanda sautin maganar ke fita ka san Yarima bai saba da yawan magana ba, saboda cikin nutsuwa yake yin ta. "Ki ɗago Yasmin na zama naki fa." Na girgiza kaina. "Sai kasa riga." Ina jin sa ya zauna dab da ni tabbas na ji sunkuyowarsa daidai da kunnena, saboda jin hucin numfashinsa, madadin ya yi magana sai dai kawai na ji ya hura kunnena,tsigar naman jikina na ji ta yamutsa, na rasa ya zan yi sai dai kawai na koma gado na ƙwanta a ƙudundune. Haɗani ya yi ya rungume a ƙirjinsa, amma ta bayana, kalaman da suke fita daga bakinsa su suka sakani na ji ɗakin na juyawa da gadon da nake ƙwance, jin ya ƙara hura mini saitin ƙofar kunnena yasa na mirgina ɗaya kusa da shi na samu na miƙe na gudu, na shiga banɗaki, saboda na san nan kaɗai ne in na shiga na tsira, shi ma idan na kulle saboda ƙaton falo ne da ɗaki ɗaya kawai su ne ɗakunan hotel ɗin. Na kulle ƙofar, amma sai na ji na jingina da ita tare da sulalewa ƙasa na zauna, kai sai na ji ina jin kunya ni kaɗai a banɗaki, na ƙudundune kaina jikin cinyata, na dinga murmushin da zan iya kiranshi na daɗi,wai don tsananin shirme irin nawa da na ɗaga fuskata sai in mayar wai kunya nake ji. Sai da na ƙwashi wajen mintuna sha uku a haka, sannan na yi sauri na miƙe tsaye saboda tunanin da na ji ya faɗo mini a take,shi ne sallah na san bai fi sauran mintuna a kira sallah ba,ko kuwa in ce lokacin sallah ya yi tun da garin arnaku muke balle mu samu kunnuwanmu da jin kiran Sallah. Na saɓule kayan dukkansu a gaban ƙaton madubinsu na banɗaki na kalli kaina tas na yi murmushi ganin ba ni da ko ƙwantalan ƙurji a dukkan jikina ballantana tabo, sannan ko'ina na jikina farinsu ɗaya,in an ɗauke saman tsokar ƙirjina. Na shige ƙwami na zauna dirshen sannan na saki famfunan dukkan biyun ɗaya na zubo da ruwan zafi ɗayan kuwa na sanyi yake ƙwararo min, cikin ɗan gaggawa na gama wankana,gudun kada Yarima ya jira ni da yawa, saboda na san shi mutum ne mai son jam'i. Ina fita sanye da rigar wanka,shi kuma yana sallame sallah. A zuciyata na ce har ya ƙagara. Na ɗauki kayana riga da wando,wandon ruwan baƙi ne rigar kuwa mai dogon hannu ce ruwan madara, sannan rigar ba ta wuce ƙugu ba, na fito na zauna gaban madubi na yi gaggawar shafa ɗan Wetlips kawai nasa a laɓɓana, na taje gashin kaina na ɗaure shi na sakeshi a baya, sai kuwa turaran da na feshe jikina da shi. Alkyabbata na zura domin gabatar da sallah, ina isa wajen da na keɓe mana domin sallah na ga Yarima ya miƙe, sannan ya ce mini "Bismillah." Sai wannan lokacin tunani ya faɗo mini cewa nafila ce Yarima ya yi irin waɗannan halayyar ta son Addininsa yana ba ni mamaki, saboda ban taɓa tunanin yana ma sallah ba, ballantana ya iya riƙe Addininsa da hannu bibbiyu, balle da na je gidan yari na ga irin yanda yake baiwa jama'a wahala, ga mulki har na fitar hankali. Bayan mun gama ne na ji ya ɗaga hannu sama yana jero sunayen Allah gaba ɗayansu daga nan kuwa na ji ya faɗa ga addu'ar Allahumma izzal Islama wal Muslimin har ƙarshenta, sannan ya rufe da wata addu'a wacce tun ina yarinya na ji ana yi mana ita, abin da ya bani mamaki kuma sai na ji ya rufe da ɗayar ma wacce zan ce kowa tun yana yaro ma ya iya ta. _Rabbana atina fidduniya hasanatan wafil alkhirati hasanatan waƙina azaban nari._ _Rabbana latuziƙ ƙulubana ba ada izhadaitana wahablana min ladin ka rahamatan innaka antal wahab._ A take na tuna da malamin islamiyyarmu da yake ce mana ana son duk sallah a dinga karanta ta,falalarta Allah kaɗai ya san yawansa, sai dai yawan yin ta na kawo arziƙi duniya da lahira. Hankalina na ji ya ƙara nutsuwa a kan Yarima,ganinsa yanda yake kula da Addininsa. Muna kammalawa ya miƙe ya gabatar mana da sallar isha'i ni dai gaskiya na ji mamaki matuƙa a kan yanda na ga Yarima na tafiyar da rayuwarsa,in na yi la'akari da yanda yake a baya, mutumin da ko motsi ma baya iya yi sai dai a yi masa. Bayan kammala addu'armu ne na ga ya tashi ya buɗe aƙwatinsa ni kuwa sai bin shi nake da kallon mamaki, wasu kaya na ga ya ɗauko da alama dai na mata ne, ya zauna saman gado sannan na ji ya kira ni na tashi na je inda yake, nima na zauna a gefensa. "Waɗannan kayan nake son ki saka mini su yanzu,zamu fita mu ci abinci a can." Riga ce doguwa har ƙasa take, amma sai ɗan siririn hannunta, sai kuwa ƴar samanta mai dogon hannu har izuwa wuyan hannunta, dole ta sa na tattare su na matse a tsakanin cinyata,gudun kada su ja ƙasa,a cikin banɗaki na isa gaban madubin banɗakin na tare gashin kaina na ɗaure shi da ɗan mayafin da na gani maƙale a jikin kayan, na yi murmushi ganin na yi mugun ƙyau, abin ka ga kalar jinin kare, sai kuwa dogayen hannuwan rigar, amma ragowar jikinsu kuwa duk jinin kare ne (Maroon colour). Na fito ina murmushi, sannan na yi saurin sakin rigar sai na ga take ta saman tsakanina da ɗan leɓunta zai kai taku biyu ta cikin ce kawai ke ƙwance a daidai ƙafafuna. Na isa bakin madubi na zauna domin gyara fuskata, na gyare ta da wata irin hodar da take fitowa da ainihin kalar fatar jikinka,jan baki kuwa kalar kayana na saka, jinin kare kenan,dan in ƙarasa zama su turawan har ma gashin ido na saka, gashin ya yi tsaye abin gwanin ban sha'awa. Girata kuwa sai na goga mata ƙarin baƙin jagira, domin ta ƙara fitowa, na ɗauki turare zan fesa, sai na ji ya riƙe hannuna har na ɗan ji tsoro saboda ban ga isowarsa ba, ɗan firgitar tsoron da na yi sai ma naga ta burge shi ya kamo hannuna ya miƙar da ni tsaye sai na ga ya sumbaci goshina, kunya ta sa na sunkuyar da kaina ya tallabo haɓata da hannunsa ɗaya. "Your beauty make you to be the Prince's wife. Yasmin ya za'ayi in samu kamar ki in yi sakaci in rabu da ke,ai ya zama dole in ajiye mulkina in zama bawa a gare ki, saboda in samu in mallake ki da zuciyarki su zamo sun gauraya da jinina." Idona a nashi amma sai na ji kamar idanunsa sun fi ƙarfin nawa, saboda wasu kunamun haske da suka fito daga cikinsa suka shiga nawa idon, wannan yasa na yi fari da idanuwana tare da lumshe su, wanda ɗan guntun murmushin da na yi, ya nutsar da gefunan kumatuna, abin da na san yana ƙara fito mini da ƙyauna a fili. *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 12 "Sorry,ina baki kunya ko? Tashi na daina." Ya kamo ni na miƙe tsaye, sannan ya fesa mini turaren da ke hannunsa. "Komai ya yi sai dai abu ɗaya da ki ka manta." Na ɗan yi ƴan dube-dubena, na ga jikina ba abin da ya rasa, na tambaye shi amma irin tambayar nan ta ido. Ya warware ɗan mayafin da na ɗaure gashin kaina ya lulluɓa mini shi irin lulluɓin nan na ƴan gayun boko shi ne a nannaɗe kai kawai a saki leɓe ɗaya a baya, ɗaya kuwa gaba, wanda ya bazashi ya rufe ƙirjina da shi, sannan ya zagaya ya fito da gashina ya ƙwanta baya, ya zagayo. "Tsaya ina zuwa." Har da ɗan gudun saurinsa ya isa ga aƙwati ya buɗa sai ga ɗan aƙwati ya fito da shi ya iso ya ɗora saman madubi, sannan ya buɗe sai ga sarƙa da ƴan kunne da zobe da agogo, duk shi ya saka mini su,ni kuwa ina tsaye ina kallon ikon Allah. "Kin san dalilin gyara miki mayafi?" Na girgiza kaina. "Saboda You are full house wife." Na yi murmushi. "To an gama, sai in ce miki yau zan miki wani abin mamaki, amma sai mun sauka ƙasa, sannan zan ɗaure miki idanuwanki da wannan ɗan hankicin sai mun isa." "Gaya min tun a nan." "No,sai kin gani da idonki." Riƙe yake da hannuna muna tafiya har sai da muka iso ƙafar bene,sannan ya rungume ni jikinsa wai kada in faɗi,balle wani irin takalmi mai tsini ya saka ni sawa,ni dai na san mun daɗe muna sauka ƙafar benen,don na ji ya ce in tsaya ya dawo. Na yi tsaye tare da riƙe katakon da ke kare mai tafiya. Ɗan tsayin mintuna biyu sai ga shi ya dawo, ya kama ni ina ji muka ci gaba da tafiya,ƙafata ta gane an zo irin ɗan filin nan na tsakanin wani hawa da wani sai na ji ya tsayar da ni ya zagayo ta bayana sai na ji ya ce. "Zan ƙwance miki, amma kada ki buɗe ido sai na ce ki buɗe." Sai da ya samu minti ɗaya da ƙwance mini,sannan na ji ya ce, "Open your eyes." Ina buɗewa sai na ga wasu abubuwa masu ƙyalli sun zubo da yawa, waɗanda suka hana ni kallon abin da ke gabana, can cikin mamakin da nake yi sai na ji tafi ya cika mini kunnuwana tare da kiran. "Happy birthday to you! Happy birthday to you Yasmin, Happy birthday to you." Can sai na ga kamar an yi sama da wani farin yanki sai kawai na ga hall (ɗakin taro), cike da mutane sun saka cake ɗin murna a gaba (Birthday cake) Na juyo na kalli Yarima irin kallon murna da mamaki, sannan na ce, "Thank you." A kunya ce. "Kin fi ƙarfin haka a gare ni." Sannan muka jero muka sauko ana ta tafin waƙar da suke yi tun farko. Kai tsaye wajen dogon cake mai hawa wajen shida muka tsaya a gabansa, sannan na ji waje ya yi shiru, can daga sama na ji ana cewa. "Muslim prayers." Sai na ji an karanta Fatiha, can kuma sai na ji an ce, "Christian prayers." Sai na ji suna yin addu'arsu da harshen Turanci, duk da ita kanta fatihar da harshen Turancin aka karanta ta. Ana shafawa ɗakin taron ya ɗauki ɗan ihun waƙar yanka cake ɗin murna, amma ta waƙar kiɗan Bature, sannan aka zo aka zagaye mu. Wani Bature ya tsaya gefenmu sai na ji ya ce, "Wannan ɗan Sarki ne a Nijeriya, wannan kuma matarsa ce." Haka na ji ya faɗa da harshen Turanci. Sai ya ɗauki wuƙa ya baiwa Yarima, sannan na ji ya ce, "Prince Faysal Jafar from Nigeria,zai yanka cake ya baiwa matarsa." Ya faɗa da harshen turanci, sai ya fara ƴar ƙirga, bayan Faysal ya saita wuƙar a jikin cake ɗin sai ya ce, "One, two, three." Yana faɗar muka fara hure wutar (Candle) ɗin da suke cin wuta a saman cake ɗin har izuwa biyu,yana cewa uku Yarima na Kamo hannuna muka datsa cake ɗin waje ya ɗauki tafi. Sannan Yarima ya yanko yasa mini a baki, a kunya ce na gutsura ni ma na yanko na sa masa shi ma ya gutsura sai ɗan tafi ihu ya tashi, shi kuwa Yarima har da saurin rungume ni. Kai rayuwar Turawa na bani sha'awa, amma iyakacinta kenan sha'awar, tunda ba Addini a tare da su,daga nan sai na ji kiɗa ya canja, cikin ƙanƙanin lokaci na ga suna kama junansu namiji da mace suna rawa suna bin kiɗan a hankali. Yarima ya miƙo min hannu ni dai na san ban iya ba, na girgiza kaina, "No,taho." Na ɗan maƙale ya janyo ni jikinsa. "Kalli ƙafafunsu." Ya raɗa mini a kunne na tsaya na kalla. "Ke ma haka za ki dinga yi." Ni dai na san kunya zan ba shi sai na ce kunya nake ji, ya dinga sani dole ni kuwa na ƙiya, ƙarshe wata Baturiya ta miƙo masa hannu sai ya sake ni ya kamata ya ci gaba da rawarsu. Ni kuwa ina tsaye ina kallonsu ganin ta ƙwanta a kafaɗarsa yasa na ji wani ɗan abu ya dakar mini zuciya,wai a take sai na ji nayi tunanin ko dai irin ƴan matan da yake tare da su ne a nan,nan take na ji raina ya ɓaci, idona kuwa ya kasa ɗaukewa daga wajensu. Can na ga ya ɗago yana ɗan waigen nema na, ya ɗago mini hannu sai kawai na ji na harare shi na juya, sai na ji na rasa inda zan nufa ina tunanin in tafi ɗaki sai na ji ya ruƙo hannuna ta baya ya rungume ni, tare da turo haɓarsa a jikin kafaɗata, sai na ji ya cigaba da rawa da ni tamkar muna rawar tare. "Sorry my darling,kin san su al'adarsu ce." "Kai kuma Addininka ne.?" "Kai, to fa,ki yi haƙuri na yi kuskure babba,ƙato." Sai kawai muka ji kiɗa ya tsaya wajen ya ɗan ɗauki tafi. Daga nan sai na ga wannan dai Baturan ya ɗauki bututun magana (Macrophone) yana cewa duk su tsaya inda suke za'a gabatar da kowa, ɗaya bayan ɗaya ya dinga gaya mini sunayensu,su al'adarsu shi ne a gaisa ko a ɗan rungumi juna, amma mai jawabi ya gaya musu mu haramun ne tun farko ma saboda haka sai dai a ɗaga hannu in wuce. Sannan suka ƙara gabatar da ni,nima da bada ɗan guntun tarihina ga shi duk wanda na zo kanshi sai ya ba ni ƙyauta dama wata mace na biye a bayana da irin kayan ma'aikatan hotel ɗin in aka ba ni in miƙa mata. Wasu har da ƴar guntuwar fulawa wasu doguwar fulawa, wasu mai yawa, wacce take naɗe a cikin leda, wasu ƙwalaye nannaɗe da ledar naɗe ƙyauta (Wrapping sheet), daga nan kuma aka bayar da umarnin a tafi ɗakin cin abinci, gaba ɗaya muka nufi can. Waje ne shi ma ƙaton gaske, amma gaba ɗayansa wani tebiri ne zagaye da shi mai kamar an ajiye doguwar gwanda, wato ba zagaye yake ba kamar ƙarfen kuɗi zagaye yake amma kamar Oval shape. Kowa ya ja kujera ya zauna,mu kuwa muka zauna ƙarshen tsinin tebirin kenan kowa mu yake kallo, duk yawan mutanen nan kuwa kamar an ƙirga su kowa ya samu wajan zama,dama kafin mu isa an gama shirya komai kowa an ɗiga masa lemun ruwan nan nasu,rabin kofi,mukaɗai aka ajiyewa wata doguwar ƙwalba an rubuta concentrated sof drinks. Ana ci ana yiwa juna tsiya, daga wannan ya ce mini shi ya koyawa Yarima magana a ƙwashe da dariya, sai wancan ya ce shi ya koya masa cin abincinsu, suka dinga hirar makaranta, tsiya dai kala-kala sun yi wa juna,anan kuma suke yaba masa da iya zaɓen mata,wai har cewa suke aƙwai mata masu ƙyau a Nijeriya?. Nan na ga ashe idan aka yi Birthday yanka cake ɗin ake ashe a baiwa kowa, saboda na gan shi a ɗan faranti gaban kowa, da gani kuma yanka shi aka yi, tabbas na ga yanda turawa ke rayuwa, dole Yarima ya zama ɗan rayuwa,ni har kunya na dinga ji idan na hango wasu na tsotsar bakin juna,ko ƴar soyayyarsu, ga shi a gaban kowa ma yi suke ba wanda ya damu da wani, wani lokacin ma Yarima ke taɓo ni in gani sai in sha masa kunu. Ba mu tashi ba sai wajen ƙarfe uku na darensu wanda sai da muka zo ɗaki ma na ga dare ya yi, kafin a gama shigowa da kayan da aka ba ni ƙyaututtuka na cewa Yarima zan ɗan shiga ruwan ɗumi saboda na gaji da yawa, shi kuwa har da yi mini kashedin in na fito shi zai zaɓa mini kayan baccin da zan saka, na bishi da to. Ya koma falo saboda tsayawa ya ga masu aikin hotel ɗin sun gama shigo da kayan duka. Ban wani daɗe ba ganin dare ya yi, ga shi idanuwana cike suke da bacci, saboda haka ban fi mintuna biyar ba, ina fitowa tun daga ɗaki na ɗan ji tashin muryar Yarima kaɗan kaɗan, duk da dama shi ba mai sakin murya ba ne ba,ko waya yake yi za kaga kamar ba a jin abin da yake cewa, amma yau nayi mamakin jiyo muryarsa. Na buɗe durowa na ƙwaso rigunan bacci uku, na taho da su domin nuna masa ya zaɓa mini,me zan jiyo. "Mama wallahi lafiya lau muke,tana wanka." Har na washe baki na taho in karɓi waya mu gaisa da Mama, sai na ji maganarsa ta canja salo, na yi tsaye cak saboda jikina da na ji ya yi nauyi,gudun kada in yi taku da ƙarfi ya jiyo ni. "Mama ai dabara na yi mata, to gajiya na yi,yau nayi mata ciwon ƙarya a ruwan wankan nunawa na yi na mutu na taso sama,kin ga ɗiyarki na ihu a zo a taimake ta,miji zai mutu. A'a Mama, wallahi dama don in gane tana so na ko har yanzu zaman dole take yi da ni. Eh, na gane,kin ga yanda ta ruɗe dama na haɗa baki da ƴan hotel ɗin. Mama ai hotel ɗin da Mai Martaba Sarki ke sauka ne,mun saba da su sosai,su na haɗa baki da su na ce su yi mini allurar (B. Complex), kin ga ai na ɗan ci in ƙoshi na ƙwana biyu." Sai na ji ya sa dariya. A'a Mama, ina zan yarda ta yi kukan da za ta haɗu da wani ciwon, ai ni ma da na kama ciwon gaskiya wallahi Mama lafiya ƙalau,ni yanzu ma na ji ta ƙara shiga raina, saboda hankalinta, wallahi ina son ta,so sosai, Mama ki daina koƙwanto, yanzu mu duka muna son juna. Mama kenan, na so insa a ɗauki hotan ɗiyarki in aiko miki ki ga yanda take kuka. To na daina za ta ji, ta shiga wanka daga ma ƙasa muke yanzu, abokaina na nan suka haɗa mata fatin murnar auranmu, amma kin san Turawa suna kiran shi da Birthday,amma fa duk sun ruɗe wai na iya zaɓen mata, zan daina, sai anjima. Ki gaishe da Baba Sarki da Hajiya, kowa ma. Ita ma a aika a ce tana gaishe su, to to,bye Mama I love you,I miss you great Mama." Sai na ga ya kashe yana ƴar dariya har da sumbatar wayar, sannan ya tashi tsaye ina jin da niyyar ya zo ɗaki sai kawai ya juyo ya ganni a tsaye juyowarshi nima tasa na saki kayan da ke hannuwana wannan kuwa na lura da ta firgita shi,dan kuwa ya gane na ji duk abin da yake faɗa. Ya yi saurin nufo inda nake tsaye, kafin ya iso na shige ɗaki da saurina na faɗa gado, ya iso ya yi saurin ɗago ni. "Yasa..."kafin ya ƙarasa kiran har na ji wasu zafafan hawaye sun zubo mini,wannan ne ya hana shi ƙarasa kiran. "Me za kace mini yanzun kuma?" Na faɗa cikin sanyin murya. "Yasmin sorry,wallahi har a zuciyata na yi haka ne domin na gane kina sona kamar yanda ni ma na daɗe da sonki,in za ki tuna ma haka na cewa Mama." "Ni dai ba zan iya auran ku ba,komai muke ciki kowa sai ya sani." "Haba My love, ya zaki ce mini haka, alhalin kin san yanda zuciyata take ƙaunarki." Na sauka ƙasan gado ya durƙusa, "Yasmin ki yi haƙuri ki so ni nima." *ƘASAITA BOOK 2* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 13 Kansa a sunkuye yana ɗagowa muna haɗa ido na yi saurin sunkuyar da kaina. "Ka daina yi mini haka,bai dace ba,ka durƙusa mini ina matsayin matarka." "Kin amince ke matata ce?" Na koma da sauri na kife kaina jikin katifa, sannan na ɗaga kaina. Ya hawo a hankali ya tura kai a cikin wuyana ya sumbace ni. "Na gode, to tashi in zaɓa miki rigar baccin." Ya ɗago ni na tashi zaune ya yi saurin tafiya ya ƙwaso kayan ya iso ya zube su a gado har ya zaɓa mini ɗaya daga ciki ya miƙe tsaye. "Kafin in fito daga wanka kin saka mini ita, kada ki lulluɓe ta na san ki da kunya." Yana yi yana cire coat ɗin da ke jikinsa da shet (suit) shigar nasa kayan (wedding Anniversary) ɗin kenan. Ina jin motsin fitowarsa na yi saurin miƙewa tsaye tare da sunkuyar da kaina ina faman murza ƴan yatsun hannuna,ni kaina na san rigar baccin ta yi mini ƙyau. Doguwa ce iya wucewar gwiwata amma matsatstsan ƙugu gare ta,siririn hannu gare ta kamar ɗan mariƙin hular sanyin yara, kuma a murɗan yake tamkar ɗan abin ɗaurin hular yara. Amma tafe take da ƙoƙunan rigar Mama daga cikinta wanda za su iya tallabo maka ƙirjinka ya ɗan bayyana a waje, ya kuma fitar da tsakiyarsu, sai dai sakata ake yi kamar ana saka wando, saboda haɗe take da ɗan diras ɗinta, jikinta gashi-gashi ne kamar gashin jikin jaririyar mage, kenan laushi, amma ba ya tsirar mutum. Ƙasanta kuwa kamar ƙarshen jelar mage an daddasa sannan kuma sai ka maƙala ɗan siririn maƙallamin rigar mama sannan za ka zuge wani zib da ke cikin bayan rigar, wanda ba a gane shi, sai an laluba saboda gashin jikin rigar ya ɓoyeshi. Ɗan wani guntun mayafi gare ta,ko na ce ɗan abin da zaka rataya a wuyanka, shi kuwa kamar ƙatuwar jelar mage, saboda duk ta rufe mini wuyana. Kunya ce ta hanani ɗaga idanuwana daga tsayuwar murza ƴan yatsun da na yi, jin shigowarsa ɗakin ta sa na ɗan ɗaga idanuwana na kalleshi, cikin sauri na sunkuyar da kaina saboda ganinsa nayi ɗaure da tawul mamadin ya sako rigar wankan shi, ɗan tsayin mintuna biyu ya yi ban ji motsin shi ba, gyaran muryar da ya yi ita ta kawar da tsit ɗin da ɗakin ya yi. Jin sautin maganarsa na yi yana yi mini magana cikin sarƙaƙƙiyar murya. "Miƙo mini rigar wanka ga ta nan a kan gado." "Tawa ce wannan taka na ciki." "Na sani taki nake son sakawa a yau,ko ba za'a ba ni aro ba?" "Za'a baka." Na faɗa a daidai lokacin da na juya domin ɗauko masa. Kaina kuwa a sunkuye nake tafiya har na iso inda yake tsaye, cikin ɗan yanayi na kunyar gaske na miƙa masa rigar ba tare da na ɗaga kaina ba, juyawar da zan yi na koma ta yi daidai da ruƙo hannuna da ya yi ta bayana ba zan iya ƙwatanta yanda jikina ya amsa girgizar da ya yi ba, juyo ni ya yi ya haɗa ni da ƙirjinsa rigar da ke hannunsa kuwa ina ji ta sulale a tsakaninmu ta faɗi ƙasa. Bai yi magana ba, amma sai na ji ya sa ɗan yatsansa yana zana mini cinyar hannuwana,wanda har ya dire a yatsun hannuna,ɗago tafin hannuna ya yi ya ɗora a saman ƙirjinsa,gashin ƙirjinsa wanda yake cike da lemar ruwa ya haɗu da ɗan sanyin ruwa ya tsirar mini tafin hannuna,na yi saurin lumshe idanuwana tare da kiran sunansa "Yarima." Cikin kunnena na ji ya yi magana, "Faysal dai, ke ya kamata na kira da Gimbiya, Sarauniya,Yarimiya,kin san kuwa kin cancanci sunayan nan, saboda kin riga kin siye zuciyar Yarima, wanda yake taƙama da mulki. Wanda bai taɓa tunanin da macen da za tasa zuciyarsa ta koma tamkar ba tashi ba, Yasmin ke zuciyata kawai take tunani,ni a yanzu ma ji na nake ƙarya ne ni ba nine Yariman da kike faɗa ba." Sai na ji ya yi murmushi mai fitar da sauti tare da ɗago fuskata,"Open your eyes, kalleni." Da ƙyar na iya kallonsa na sakan ɗaya. "Yanzun ni naki ne Yasmin,ki daina jin shakkun komai,ki daina jin kunyata,ki fitar da tsorona daga zuciyarki, kin canja mini rayuwata gaba ɗaya." Ina jin shi yasa hannu ya janye ɗan dogon gashin da na rufe jikina da shi. Ya sunkuyo ya sumbaci ƙirjina na yi saurin ƙwantawa ƙirjinsa ya tallabe kumatuna. "Yasmin you love me sure?" Na ɗaga kaina alamar eh, ya ɗauke ni cak ni kuwa na koma na ƙwanta a ƙirjinsa ya hau gadon sosai, sannan ya ƙwantar da ni ya janyo filo ya ɗaga ni ya gyara mini ƙwanciyata sosai, ya juya ya janyo bargon da ke maƙale jikin gado ya lulluɓa mini har izuwa ƙirjina,sannan ya sunkuyo ya sumbaci goshina da laɓɓana yasa hannu ya gyara mini gashin da ya sauko mini a saman fuska. Ni kuwa cikin lumsashshen ido nake kallonsa sannan ya ce, "ina zuwa." A cikin raɗa sai na ga ya sauka na buɗe idanuwana sosai na bishi da kallo a take sai na ji na tsorata saboda ganin shi ɗaure da tawul haka ya nuna min ashe Yarima na da tsokar jiki,ganin wasu cinyoyin tsoka a cinyar hannunsa duk sun yi kusurwoyi kamar ta ƴan kokawa (Wrestling). Ga wata tsoka ta ƙwanta a gefunan wuyansa, ban da tsokar da na hango a cinyar ƙafarshi, ya buɗe durowa ina kallonsa sai na ganshi ya juyo yana fesa wani abu a hannunsa, ganin dogon gwangwani ne yasa na gane abun sa ƙamshin ɗaki ne (Room Freshner) duk da ban ga sunansa ba, cikin sakan uku ɗaki ya kaure da ƙamshi mai sanyin gaske, ban da laushin shaƙa da hancina ya yi. Ya ɗauko wata ƴar ƙwalba bayan ya ajiye wancan sai na ga yana ɗan ɗigata yana shafawa a gashin ƙirjinsa,a zuciyata na ce ashe maza ma suna ƴan gyara irin na mata. Ina kallo ya ɗauko turare ya fesawa jikinsa ya mayar da durowa ya rufe, juyowar da zai yi sai na ga idanuwansa sun ƙara fitowa sun yi ja,dama abu (Barakallah), manya da su, sai ya juye mini kamar na ƙwatanta shi da ɗan fim ɗin nan na ƙasar Indiya (Salman Khan), har da faɗin ƙirjin ga tsokar curi-curi a cinyoyin hannunsa. Na ɗan yi saurin kawar da kaina gudun kada ya gane kallonsa nake yi,jin bai hayo gado ba yasa na ƙara waigowa sai na ga ya kunna mana hitar gasa ɗaki (Room heater), sannan ya isa ga makunnin fitila ya kashe ta sai fitila ɗaya ke ci, ta gefen gadonmu, tun da ya hayo gadon ya ƙwanta tare da kashe fitilar gefen gadonmu ban ji ya yi motsi ba, ga shi kusan mintuna ashirin kenan. Zuciyata ba abin da bata saƙa mini ba,na ko lafiya ko kuwa ya yi bacci? Hakan ya sa na juya nima na cigaba da addu'o'in ƙwanciya baccina, na yi ƙwanciyata, jin ya ce, "Alhamdulillah." A bayyane yasa na ce ashe idonsa biyu. Madadin na ji ya yi magana sai kawai na ji ya ɗan cizar mini bayana na ɗan firgita kaɗan saboda a bazatan da cizon ya zo min tare da faɗar. "Kai Yarima!" Kafin in ƙarasa ya kuma cije leɓatun kunnena, daidai wajensa ɗan kunne, kafin na yi magana ya kurɗa ya ciji wuyana, kumatuna, na yi saurin juyowa na fuskance shi, sai kawai na ji ya cije laɓɓana. "Kai...." Yasa tafin hannu ya rufe bakina. "Don't talk." Numfashina na ji ya yi sama wanda ya ɗauki mintuna uku kenan bai dawo mini ba, ba wani abu ya janyo mini haka ba shi ne salon yanda Yarima ke tsotsar ƴan yatsun hannayena. Shin Yarima ne kuwa? Tambayar da zuciyata ta yi mini kenan,a daidai lokacin da numfashina ya dawo dai-dai kunya ta kama ni da na ji ya amsa mini da "Yasmin ni ne." A nan take na tabbatar wa kaina maganar da ke cikin zuciyata ce ta fito fili. Idanuwana kuwa na ƙara runtsewa,runtsewar da ta kai ni har wayewar gari ban ƙara buɗa su ba. Ji na cikin ruwan ɗumi yasa na san mafarki nake,a cikin mafarkin na dinga cewa, "Yarima mafarki nake na shiga ruwa." A kunnena na ji ya ce "Buɗe idanuwanki ba mafarki ba ne ba." Na firgita sai na ji ni rungume a ƙirjin Yariman a cikin ruwa, na waiga na kalle shi ƙwance cikin ruwan kumfa sai ƙamshi kawai ke tashi, na juyo na kalli kaina nima cikin ruwan kumfa. Na sa hannu na dinga laluba jikina, na ji zargin da nake ya tabbata na rashin kayan jikina, na juyo na ƙara kallonsa sosai sai na ga ya lumshe mini ido na juya a sanyaye na ƙwantar da kaina jikin gefen bahon wankan, sai na ji hawaye, saboda tunanin gane ni ba kaya. "Why! Why!! Why!!! Yarima? Me yasa ba ka tashe ni ba? Me yasa ka kalle mini jiki?" Ya ƙwanta bayana, "Yasmin,don kina matata kin manta mun amince da junanmu." Ya sumbaci bayan wuyana, "kada ki yi da na sani ko ki ji haushin abin da na yi,me yasa ba ki da yarda Yasmin? Nifa na amince da ke ce matata, ke me yasa ki ke kokwanto ne har yanzu?" Ya yi saurin dawowa gabana jin ina fitar da ƴar jaririyar kukan ƙissa, wanda Aunty ta ce mini ana yi, ya dago kumatuna ya tallabe da hannuwansa masu kumfa. "Ba ki son abin da na yi miki? Na ɗaga kaina. "To shi kenan ki yi haƙuri tsaya na baki haƙuri sosai." Sai na ga ya ɗebo kumfa yasa a saman kansa ya ɗiga a goshi, hanci a kunnuwa, sannan ya riƙe kunnuwa ya gwale idanuwa,dama abu (Tubarakallah) inji Malam bahaushe. Sannan ya ce, "Sorry." Dole ne ma na yi dariya, na yi murmushi kuwa sai ya yi saurin rungume ni. Ya ɗago kaina ya goge hawayen fuskata. "Kin yi haƙuri?" Na ɗaga kaina. "Ban yarda ba, sai kin ce eheee." Yanda ya tale baki ya ce eh, dole ta sa ka dariya, na sa dariya na daki ƙirjinsa da dukkan hannayena, ya girgiza kansa alamar jin daɗi sai ya rungume ni tare da faɗar "I love You too." Nima na amsa masa da "I love You too much." Amma a zuciyata,na koma na ƙara lafewa a ƙirjinsa. **** **** **** Satinmu huɗu a Greece,amma wurare ɗai-ɗai ne ban sani ba, balle ma da muka shirya sosai da shi. Ƙasar London,Rum(Italy) da kuma Turkey,duk su ma satinmu bibbiyu, wanda idan na haɗa su waje ɗaya mun ƙwashe watanmu biyu da sati biyu. Yau kuwa ranar Asabar ce, wacce ta yi daidai da ita ce ranar da muka iso Nijeriya, sai da ma Yarima ya tashe ni daga bacci ya sanar da ni an zo Nijeriya, wanda tun da muka shiga jirgi ya janyo ni ya ƙwantar a ƙirjinsa, ɗan wasannin shafa mini baya ya kama yi, wannan ne ma yasa har bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba. Maƙale nake a kafaɗar Yarima har muka iso bakin ƙofar fitowa daga jirgi cikin ɗan ƙaramin lokaci na yi saurin janye jikina daga gare shi, saboda hango mutanenmu da na yi sun zo taryarmu. Dogarawa kenan. Ya janyo ni jikinsa. "Me ye haka,mun iso Nijeriya za ki fara gasa ni, wallahi sai mu koma." "Kalli gabanka." Na faɗa a lokacin da muke sauka matattakalar benen jirgin. Waziri ne da sauran manyan fada a tsaye suna jiran saukowarmu, ban da dogarawa waɗanda sun kai ashirin, motoci kuwa sun cika filin jirgin Jos International Airport,da gani ka san na taryar mu ne. Cikin sakan ɗaya na ga Yarima har ya rikiɗe ya koma Yarima na da dana sani, da na juyo na kalleshi ta wutsiyar idanuwana ni kaina sai na ji tsoronsa ya sauko min. Alhamdulillah! Mu haɗu a littafi na uku. Daga Mai ƙaunarku. Aunty Maryam Kabir Mashi.