Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LDX80EfO3RZtX8kjFzcTL https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1508646987567775409614683455341&mibextid=rS40aB7ScjusSuGJYhxw6v JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCAIATION 🖊️ (J.W.A) Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan kasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauk'i ✏️ Dukkan yabo da jinjina su tabbata ga ubangiji wanda yayi sammai da kassai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (S.A.W) wannan littafin mai suna RAYUWA DA MACIJIYA, PAID BOOK 📚 MALLAKIN AISHA M.B banyi wannan littafin , don naci zarafin wata, koh wani bah, Nayi shi ne don mu dau darusan dake tattare acikinta. idan wannan littafin yayi Daidai da rayuwarka toh Arashine. Ban yarda a chanza min wani Bangare koh sashi a cikin littafi nan bah, idan kuma mutum ya kuskure ya sauya min littafi na, toh na barshi da Allah, BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM 🌺 🌸RAYUWA DA MACIJIYA🐍 FREE PAGE 1⃣▶2⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY AISHA M.B🌺 (BABY ISHA) ---------------------- KAUYEN GEMBIZA🌳 Gabadaya kasar kauyen ta bushe. bishiyoyin sun kafe, gonan naki sun bushe, ruwan garin ya kafe, babu wata ciyawa dake tsirowa, saboda rashin ruwa, yayi musu tsanani. Daga dayan bangaren, jama'a garin suna a zazzaune Duk tulun su babu Ruwa koda na alwala, Duk lebu k'ansu ya bushe, yayin da kowanne su yayi tagumi, suna jiran ranar da zasu cinye wannan jaraba wa da suka tsinci kansu aciki. Daya daga cikin matan dake Zaune tace, idan tsanani yakai makurar tsanan ta, toh mafuta daya gare tah". Mai gari yace, wace mafuta kenen? Menene ba'ayi bah don kawai, musamu mu ceci rayukan mu da Kuma na y'ay'an mu, Wanda zasu taso nan gaba. Sadaukar wa, azumi, sallah, babu wacce babu yi bah, amma abun saika ra tsamari yake, shekara da shekaru kenen, rabon da ayi mana ruwan sama a wannan kauyen.mutane sai mutuwa suke, ya yinda ruwan kogin mu ta kafe, babu ruwa koh kad'an acikin ta,yara gasunan wasu sun zama marayu dalilin wannan rashin ruwan, iyayen su, sukaje suka rataye kansu, shin wane laifi koh zunubi muka aikata? Da muka cancan ci irin wannan, azabtar war!. wannan azabar ta isa, aka. Inna wuro ki taimaka kine man mana mafuta Wacce aka kira Inna wuro tace, komai yayi farko, toh zaiyi karshe, ni bansan menene mafuta bah, amma tabbas inada tabbacin cewar, Allah zai Kawo mana agaji nan bada dadewa bah, Malam liman yace, yanzu wajan shekara da shekaru kenen, kina cewa, Allah zai kawo mana agaji, sai yaushe kenen, sai yaushe ne, zamu daina zubda hawaye, akan wannan kuncin rayuwar da muke, Yanzu muna tsakanin mutuwa da rayuwa ne, saboda bayan rashin samun ruwa mah, kayan gona sun Kare, bamuda wani amfanin gona, saboda babu ruwa ko mun Shuka bata tsirowa, Gaskiya nidai inada wata Shawara, jama'an garin suka ce, Tom munaji, Allah yasa mai amfanu wa ce. Malam liman yace, mezai hana mu nemar wa kan mu mafuta , mu koma, kauyen makota, har sai komai ya lafa, an yafe mana zunuban mu, Danni dai a ganina, zunubai ne, suka mana yawa, da har za'a dunga yiwa sauran kauyuka ruwa amma banda tamu, wannan itace Shawara ta inba aka bah, mutanen mu zasu cigaba da mutuwa ne daya bayan daya, koh muje mu nemi ruwa har sai inda karfin mu ya Kare. Ard'o yace, wannan wace iriyar gurguwar Shawara ce! ta yaya, zamu bar Asalin garin kakannin mu, sannan mu koma wani kauyen daban, gaskiya wannan Shawarar tsam, bata yi bah. Malam liman yace, tabbas maganar ka gaskiya ce, amma ya muka iya, dole ne mu nemar wa kan mu mafuta koh munaso, koh Bamua so, kafun lokaci ya d'ad'a kure mana , Kuma na bada wannan Shawarar ne badan komai bah, sai don don mu ceci rayukan mu, Jama'an garin suka ce , tabbas wannan Shawara ce mai kyau, Kuma a yau bah gobe bah zamu tafi nemo wa kan mu mafuta, Tashi jama'an garin su kayi, saka Fara har'ada kayyayakin su, saida suka dau lokaci kafun su gama, sannan daya bayan daya suka Fara tafiya. "Inna wuro" cikin ranta tace, shin yaushe ne zaki bayyana domin kawo wa wannan dauk'i. Ki taimaka, ki hanzarta, muna cikin halin tsaka mai wuya, bayyanar ki itace, mafuta a garemu, :::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::: Cikin fargaba da tsoro, take bin jikin bishiyoyin dajin, gabadaya ta ranta da Kuma jaririyar dake hannunta take,. raunuka da tab'o gabadaya sun b'ata mata jiki, Daidai wani katoton bishiya wanda yafi kowane bishiya fad'i da Kuma girma acikin wannan dajin. Zama tayi, Tana saukar da ajiyan zuciya, ajiye jaririyar da bazata wuce watanni biyar zuwa shidda a haihuwa bah, wuyanta sanye yake da tsarkar lu'u lu'u (Diamond 💎) wadda tambarin masarauta ke Ajiki, da Kuma sunan yarinyar. Ajiye jaririyar matar tayi, Ta shafa bayan ta, Wanda wuka ke soke Ajiki, rintse idanuwanta tayi, hawaye nabin kan kuncin ta, ta Fara zaro wukan a hankali, har tayi nasaran zare shi baki daya, wani ihuu ta kwallah wanda ya Firgita jaririyar ta fashe da kuka. Hatake hadari bakin kirin ya taso, inda aka fara iska mai hade da guguwa, Kukan jaririyar ne ya gauraye dajin, baki daya. tsawa da walkiya ne ya wanzu, inda dabbo bin dajin suka fara guduwa suna koma wa guraren su. Inda gefe guda kuma, Macizai, kala-kala, iri -iri, daban -daban, suka Fara futowa daga cikin ramu kansu, suna nufan inda jaririya take, Daidai wajan, da jaririyar take, suka je, inda suka Fara zagaye tah, suna shafar jikin ta, Cikin fargaba da tsoro matar ta tashi, da niyyar koransu, cikin rashin sa'a daya daga cikin macizan ya sare ta, Faduwa matar tayi, kunfa yafara futa a bakinta , cikin dak'ewa tace, ya Allah, ka Kare min y'ata, kashiga lamarin ta, ya Allah ina rokan ka, da kasa ta fada hannun mutanen kirki, kada ka Bari makiya su ci galaba akanta, Duk abunda zatayi a rayuwarta ya, kasance tayi shi da kyakyawan niya. Inason ta kasance mai taimako, tausayi, da Kuma juriya. Ta kasance abun Misali ga wasu, Wanda za'a dunga Alfa'ari da itah. Tabbas nasan y'ata zata kasance Tana Tareda sa'a a rayuwar tah. Ya Allah kada ka Bari y'ata ta fada a mugun hannu, Wa enda kuma suka zalunce ta, sukayi sanadiyar kasan cewar ta Hanan, tabbas wata rana zaizo da zasu ne mi gafarar ta, sannan Kuma su dafa kafafunta. Daga hannun ta, tayi sama tace, Allah ya yi miki albarka y'ata, Tana kaiwa nan tayi Tsit, Kuka jaririyar ta kuma fashewa dashi, Dafa Malam liman" Mai gari yayi yace, shin Bakua jin kamar kukan karamin jinjiri. Inna wuro tace tabbas nima naji, Kuma Gashi yau naga, anyi hadari, gabadaya garin yayi duhu, al'alin yanzu bah lokacin Damuna bane. Ard'o yace, muje mu duba wane yaro ne, Chan cikin dajin suka nufa, suka Fara bin, inda suke jiyo kukan, jinjira. Aska dajin suka farayi da wutan iccen dake hannunsa, Chan idanuwan su ya sauka, akan jaririyar, dake yashe a k'asa, Koran macizan suka farayi, da wutan hannun su, Hajiye wutan hannun ta Inna wuro tayi, ta nufi wajan matar dake yashe a kasa. Kallon matar tayi, ta shafa kanta, Tareda rintse idanuwan ta , bude idanuwan ta tayi tace, kuzo , ku cincibi, wannan matar, ta Fada a doguwar suma, Kuma tanada bukatar taimakon gaggawa saboda, dafin macijin da ya sare ta Mai matukar, karfine. Tashi tayi ta nufi inda jaririyar take, Tareda daukan yarinyar, ta dora idanuwanta akan na jaririyar, abunda ta ganine ya matukar tsorata ta, tabbas yarinyar ruwa biyu ce, a gigice Inna wuro tace, jama'a, itace, ta bayyana, Mai cetan mu, ta karaso. Gabadaya jama'an garin suka nufi inda Inna wuro take, suka zubawa yarinyar ido, Kuka yarinyar ta fashe dashi. Hatake aka fara ruwan sama, Wanda yake hade da iska Mai ni'ima, Farin ciki ne ya lullube fuskokin su, cikin jin dadin Ganin wannan ranar, Mai gari yace, Dama zan sake Ganin anyi wa wannan kauyen ruwa, tabbas yarinyar nan yar sa'a ce, Kallon idanuwan yarinyar wanda suke Ars, Inna wuro tayi , ko kadan babu tsoro a fuskan yarinyar, Murmushi inna wuro tayi, sa'anan tace, tabbas babu abun bautawa da gaskiya sai Kai ya ubangiji, wannan yarinyar, itace zata kawo karshen zalinci a wannan karnin. COMMENT & SHARE PLS ALKALAMIN 🖊️ AISHA M.B🌺 BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM RAYUWA DA MACIJIYA FREE PAGE 2⃣➡3⃣ WRITTEN & DIRECTED BY BABY ISHA ------------------------------------- Kallon sarkar dake wuyan jaririyar Inna wuro tayi, taga an rubuta (JODA,)murmushi tayi sa'anan tace tabbas kinci sunan ki Joda, amma daga yau, sunan ki zai kasance DU'A, domin kece wacce Allah ya turo domin kawo mana agaji cikin wannan kauyen Gembiza, daga yarinyar Inna wuro tayi wacce sai kuka take ta faman yi, Inna wuro tayi tace , wannan yarinyar daga yau sunan ta zai kasance DU'A ne, Farin ciki ne ya baibaye fuskokin su, jama'an garin suka hada baki wajan fadin, barkanki da shigowa kauyen Gembiza Du'a, muna farin cikin bayyanar ki a garemu, Allah ya baki abunda kike son cimma na alkhairy nan gaba, Allah ya Kare mana ke, kuma Duk rintsi Duk wuya, bazamu taba barki bah, har sai numfashin mu na karshe. sosai jama'a kauyen, ke farin cikin sake haduwa da irin wannan ranar da ruwan sama zata zubo a yankin su. Mai gari yace tabbas wannan babbar kyauta ce daga ubangiji, shekara da shekaru kenen muna fafu tuka wajan neman ruwa, amma Zuwan wannan jaririyar Allah ya sauko mana da ruwan sama, tabbas wannan yarinyar yar sa'a ce Kuma yar baiwa, Zuwan ta wannan garin bah karamin kawo cigaba zai yi bah . Bamusan Wacece wannan jaririyar bah, kuma bamusan daga ina ta futo bah amma tabbas wanda ta haife ta, ta haifo mana da kwarin gwiwa, sa'a da Kuma kwanciyar hankali. Hamdalah gabadayansu sukayi, babu bata lokaci, suka koma cikin garin, suna shewa, Tareda fara tsalle tsalle, farin ciki lullube a fuskan kowanne su, Tara tulun su kowa yayi, suka ajiye a inda ruwa ke zubowa, Wanka sukayi wa jaririyar, sa'anan suka saka mata kayan Fulani, Wanda suka karbi jaririyar ciff kamar an auna ta. Washe garin ranar, Ard'o da Kuma makarabban sa suka futa domin yin farauta kamar yadda suka saba, Daya daga cikin su ne ya hangi, ciyawa tafara tsirowa daga cikin kasan, ihuu ya kwalla, wanda yasa mutanen yankin suka Fara futowa daga cikin mu'alinsu. Ard'o yace sani meyafaru? Sani yace ciyawa ta Fara tsirowa a gonar mu, shekara nawa kenen, rabonda muga kasar mu a jik'e ,amma yau Kalli ciyawa mah ta tsiro, acikin kasar. Hamdalah gabadayansu sukayi, suna mai godiya wa Allah, Ard'o yace, yanzu kenen zamu iya Shiga gona muyi shuka, Allah mun gode maka, shekaru kenen, da gonan nakin suke a bushe, yau Kuma ga gonar mu a jike sharkaff. Malam liman yace, inda Allah ke ikon sa kenen, babu abunda ya Kama ta muyi sai godiya ga ubangiji, Wanda yasa muka sake yin ido hudu da wannan ranar wanda ya sanya kowannen mu acikin kauyen nan farin ciki. Inna wuro yaushe wannan matar zata farfado, Kallon matar Inna wuro tayi tace, dije, sanin Yaushe zata farfado wannan bah a hannu na ya rataya bah, ki Bari Allah yayi ikon sa, wannan matar bah Lallai ta farfado nan kusa bah, saboda ta fada doguwar suma Sai dai aci gaba da kula da ita, acikin wannan bukkar, har sai lokacin da Allah yayi zata farfado. Dije tace, Tom shikenen Inna wuro, barana tafi, zanje na dora girki, Kallon yarinyar dije tayi tace, Tom Dan Allah Inna wuro a tayamu kula da Du'a. Murmushi Inna wuro tayi tace, Idan ban kula da ita bah wa kike son ya kula da ita, karki damu dije itama kamar yarmu take, kulawa da tarbiyar da zamu iya bawa y'ay'an mu, aka itama zamu bata, insha Allah bazan taba bamban ta, ta bah da sauran yaran garin nan, ba iya ni kadai bah, har mutanen kauyen nan. Tom shikenen barana jee, tashi dije tayi ta fuce daga bukkar , bayan fucewar dije, Inna wuro Ta dauki Dua, tareda dora idanuwanta akan yarinyar tace, Dua, na miki alkawarin cewar zaki ga gata iya gata, zaki samu kulawa wacce koda wacce tayi sanadin kawo ki duniya bazata iya baki bah, zan kula da rayuwarki gabadaya. Ina matukar sonki y'ata. Tana kaiwanan ta rungume yarinyar. BAYAN SHEKARU BIYAR. Mai gari wannan yarinyar tabbas tana da kokari a boko harda islamiyya, amma abunda yake yawan ziyartar ta , ya fara yawa, ana cikin karatu kawai saidai muga, tana magana ita kadai kuma idanuwanta su sauya lauli su koma Ruwa toka, Dan jimm Mai gari yayi, yana mai fadin, y'ata Dua zonan, Hatake naga yarinyar da bazata wuce shekaru biyar da haikuwa bah, ta nufa inda Mai gari yake a Zaune, kyakyawa ce makurar kyaun gaske, kana ganinta Kaga cikakkiyar Shuwa. fuskanta a hade, babu walwala a tattare da ita. Ta karasa inda Mai gari yake a Zaune. Mai gari yace, y'ata Dua menene ya faru,? Meyasa kike magana ke kadai? Motsa Dan karamin lebenta tayi cikin muryar, yara tace, Baba zuciyata yana fadamin cewar wani mummunan abu na shirin faruwa a wannan kauyen. Kuma ina iya ganin abunda Bakua gani , Inna wuro tace, mee, kike gani? Kallon ta Dua tayi tace, ina ganin Macizai. Manage page pls Comment & share ALAKALAMIN AISHA M.B (BABY ISHA) BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM 🌸RAYUWA DA MACIJIYA 🐍🐍 PAGE 3⃣➡4⃣ WRITTEN & DIRECTED 🔏 AISHA M.B (BABY ISHA) PEN🔏 IS MIGHTER THAN SWORD🗡 ----------------------------------------- Binta Inna wuro tayi da kallo, Cikeda jin mamakin kalaman ta tace, Joda me kika ce? Macizai fah kika ce, a ina kenen? Shiru sukaji tayi, cikin kankanin lokaci, jiri ya d'ibeta ta, Hatake ta fadi a wajan sumammiya. Cikin tashin hankali mutanen kauyen baki daya, su kayo kanta!, daukar ta inna wuro tayi, ta nufi dakin magani da ita Kwantar da Joda Inna wuro tayi, sa'anan ta yayyafa mata ruwa, babu bata lokaci, Joda ta tashi. Hamdalah Inna wuro tayi, Babu bata lokaci bacci yayi hawan gaba da ita. Tashi Inna wuro" tayi, Tareda fucewa daga dakin, bata nufi koh ina bah, sai fadar Mai gari, da sallama ta Shiga, yayinda yan kauyen suka bita da kallo, Damuwa bayyane a fuskokin su ganin ta yasa Mai garin hanzarin fadin ya jikin Joda"? Inna wuro ta bashi amsa da fadin, da sauk'i. Hamdala gabadayan su, sukayi. Gyaran murya Inna wuro tayi, sannan tace, Mai gari, ina da wata k'ok'an to, Mai gari yace, menene? Inna wuro ta cigaba da fadin, ina tunanin kamar yarinyar nan akwai shafar aljanu a tattare da ita, saboda ba yau aka fara dawo mana da ita bah, yau ace ta suma, gobe Kuma ace ta na sauya kammani . Wannan abunda yake faruwa da ita, ya kamata munemi mafuta, saboda kar abun nata yayi tsamari, dan naga abun nata kara harzuka yake. Dan jimmm Mai gari yayi, yana mai fadin, toh me kike so ayi Inna wuro, ke da ni da Kuma wadanan mutanen kauyen, munsan da cewar yarinyar nan, bah yar kauyen nan bane, bamusan daga wace ahali ta futo bah, bamusan sanadin dayasa ta fada a wannan mummunan halin bah. Ga mahaifiyar ta mah rai a hannun Allah, tabbas na yarda da maganar ki, amma kuma wajan wa zamuje mune mi taimako. Malam liman yace, me zai Hana muje Dajin Jarmuna, domin neman taimako. Zaro idanu gabadayan su sukayi, cikin kidima! da tsoro, Malam liman yace, me kika ce, dajin Jarmuna, wanda babu wani bil Adam dazai Shiga dajin nan ya futo, idan ya Shiga, ya Shiga kenen, saidai buzun shi, bashi bah, dajin Aljanu da mayu, dajin Macizai, wannan bazai yuhuba gsk, nidai ban shirya mutuwa bah Ard'o yace akane Malam liman Nima ban shirya bah, dajin da babu Wanda yake Shiga saboda hatsarin ta, tabbas akwai magunguna acikin dajin nan, da Kuma magani warke kowane cuta, amma babu Wanda yake da zuciyar dazai tunkari wannan dajin. Khadija wato matar Ard'o tace, wannan gaskiya ne, amma me zai hana muje wajan, Malam Ali, shine kawai zai iya Sanin abunda ke damun Joda, Mai gari yace, aba khadija, kin manta gabar dake tsakanin mu da Malam Ali, na nasan cewar bah Lallai ya taimake mu bah, Inna wuro tace, zai taimaka mana, tabbas ina da tabbacin cewar Malam Ali bazai k'i taimakon mu bah. Kallon dakaransa Mai gari yayi, sannan yace musu, suje su kira Malam Ali, Mai gari na nemansa, yanzu nan. Babu bata lokaci, dakaran nasa suka nufi gidan Malam Ali. Cikin kankanin lokaci, Malam Ali ya bayyana a wajan, Kallon Mai gari Malam Ali yayi, sa'anan yace, me Kuma ya faru, koh yau din mah, an kara makala min sharri kamar yadda aka saba. Kallon sa Mai gari yayi, sannan yace dashi, Aa Ali bah aka bane, na sa a kira ka ne don sulhu, inason wannan gabar dake tsakanin mu yazo karshe, Dan Allah, akawo karshen komai a yau .Murmushi Malam Ali yayi, yana mai fadin, aini komai ya ruga daya wuce a wajena, saidai Kuma Allah ya kiyaye gaba. Inna wuro tace, Malam Ali, abunda yasa Kaga mun taru Hanan, ba komai bane yasa akan, sai Joda, munason mu ceci rayuwar ta, muna tunanin kamar tanada Aljanu . Murmushi Malam Ali yayi, yace sun kansu Aljanu basu isa sun tunkare ta bah, shin bakusan Wacece wannan yarinyar bah, itadin daya ce tamkar dubu, yanzu yarinya ce bah Lallai kusan wane irin baiwa Allah ya bata bah, amma kijira nan da shekaru, zaku sha mamaki. Ard'o yace yanzu me zamuyi tadaina sume -sumen da takeyi, kuma wani sa'in idan tana kuka, saimu ga za aitayin ruwan sama ruwan bazai tsaya bah, harsai tadaina kuka. Menene zamuyi domin ta daina Malam Ali yace babu wani abunda zamu iya yi akai, kukan da takeyi Hana ruwan sama wannan baiwar tace daga ubangiji, babu wanda ya isa ya karbe wannan. Kuma ina gani cewar tabbas wani abun al'ajabi zai faru da yarinyar nan bayan shekaru masu zuwa. Amma kuma a halin yanzu naga rayuwar ta yana cikin hatsari, kuma dole Tana bukatar kariya, saboda Joda bah kowace mutum bace, ta bambanta da sauran mutane. Mai gari yace, Ali menene mafuta yanzu? Me zamuyi Dan kar rayuwarta yashiga hatsari? Malam Ali ya bashi amsa da fadin, mafuta daya ce, wannan yarinyar za'a ajiye tane a d'aki, wato ina nufin daga yau, ba za'a Kara barin ta, ta futa koda tsakar gida bah, karatu, ci da sha, futsari, komai, zai kasance Tana yinshi ne a d'aki, yayinda za'a yi mata ba aya a dak'in da za'a saka ta., za'a barta ne a dakin na wajan shekaru sha biyar masu zuwa, saboda ranar da zata cika shekaru ashirin a duniya, ranar abun al'ajabi zai faru wanda koda wasa, baku taba tsanmmani bah, a ranar ne asalin Wacece ita zai bayyana, ikonta, da baiwar ta, zasu habbaka a lokacin ne zata fara yin aikin da ya dawo da ita duniya, Bazata sarara wa azzalumai bah, sufarta, halittar ta, yanayin ta, zai sauya saboda lokacin zata kasance asalin DU'A dinta. Cikin rashin fahimtar magannanun shi, Inna wuro tace, bamu fahimci abunda kake nufi bah, Malam Ali, murmushi Malam Ali yayi sannan yajuya ya Kare wa kauyen kallo, yace, na tausaya muku, bazaku fahimta bah sainan gaba. Zira hannun sa yayi cikin jakar sakar sa, ya ciro kullin magani, sa'anan ya mikawa Inna wuro, karba Inna wuro tayi, Tareda jujjuya shi a hannun ta tace, wannan fah? Malam Ali yace, wannan maganin kariya ne, a Duk lokacin da kika ga tana wani irin abu, koh Kuma, ta suma, toh ki dunga bata wannan maganin insha Allahu za'a samu sauk'i. Ard'o yace, amma Malam, matan kauyen mu shekaru sha daya, sha biyu, wasu mah basua Kai wa aka, muke aurar da su, taya Kuma zamu bar Joda acikin daki na wajan tsawon shekaru sha biyar, ai kawayenta mah a lokacin suna da yara, ina ganin kamar a barta basai an rufe ta bah. Murmushin takaici Malam Ali yayi, yana mai fadin, idan babu lafiya Hana yin aure ne? Idan babu rai zaka yi aure ne? Wannan abunda za'a yi badan aceci rayuwarta daga, mugun abunda zai tunkare ta bane, ku kuka sani, Kuyi yadda kuka gadama, nidai na ruga danayi iya bakin kokarina, an wuce gurin. Yana kaiwanan ya juya da niyan tafiya, kamar ya tuna da wani abu, sai Kuma ya juyo. Yace na manta, ban fada muku abu daya bah, Duk wani da namijin da ya fara ambatar mata Kalman soyayya, koh akasin aka, toh shine zai kasance mijin ta, na har abada. Amma sai wanda da gaskiya yake sonta bada yaudara bah, shine kawai zai aureta, kuma shi zai yi sanadin yadda zatasan Wacece ita daga wane ahalin ta futo, yana kaiwanan ya bar wajan. Barin shi keda wuya, Mai gari yasa aka rufe taro kowa ya watse. Inna wuro bata nufi ko ina bah sai cikin gidan ta, Kallon Joda Inna wuro tayi, tace Joda, mene yake faruwa dake aka, meyasa kike suma a makaranta, bayan kece dogaran wannan kauyen, ke zamu tura makaranta domin ki gyara mana kauyen mu, meyasa Kuma akan zata dunga faruwa dake. Daidai lokacin Joda ta bude idanuwan ta a hankali, Cikin rashin fahimtar maganar Inna wuro, Joda" ta Motsa karamin bakinta wanda yake ja sharkaff, cikin muryar yara tace Inna menene kike fada? Cikin Yaren fillanci ta cigaba da fadin, Inna yaushe zaki bude min kofan dakin da mama ta take, Inason zangan ta Dan Allah,. Ta karashe maganar kamar zatayi kuka. Murmushi Inna wuro tayi tace, Aa Joda har yanzu ke yarinya ce, bai kamata na bude miki dak'in nan bah, kinji zan bude miki kofan amma sai nan da shekaru masu zuwa. Kallon ta Joda tayi, tace yaushe kenen? Dago hab'ar Joda Inna wuro tayi, sannan tace, a lokacin da zaki Shiga shekaru ashirin a duniya, Kuma kinsan mene, girgiza mata Kai Joda tayi, Inna wuro tace Baba yace zai siya miki kayan wasa, daga yau a daki zaki dunga wasa, zaki zama tamkar sarauniya, Kuma idan kika zauna acikin daki, batareda kin futa bah, na wajan shekaru, kina da babbar kyauta ta mussanman, Cikeda jin dadi, Joda tace, Inna da gaske, gaskiya inason kyauta, idan na Zauna a daki saina samu kyauta koh? Murmushi Inna wuro tayi, ta bata amsa da cewar kwarai kuwa, kinga kece zaki zamo lamba ta daya, Baba zai baki kyautar doki, Yeeeeee! Joda tace tareda buga tsalle, cikeda farin ciki, tace shikenen nima zan samu doki, ga kayan wasa, gaskiya naji dadi sosai, zan zauna a daki saina samu kyauta ta. Tashi tayi tareda hawa kan gadon karar dake tsakiyan dak'in ta Fara tsalle a Kai. Hawayen ne ke shirin zubowa Inna wuro, da sauri ta share da bayan hannun ta, ta maida Kallon ta kan Joda tace, ya isa aka koh, yanzu kizo kici abinci, kiyi sallah, daga yau bake bah futa, kin ji dadin ki, malamin makarantar boko dana islamiyya, da kansu zasu dunga zuwa koyar dake. Kinga kin zama yar gatar Inna, Comments & share PLXX ALKALAMIN A'ISHA M.B (Zinariyar Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 🌸RAYUWA DA MACIJIYA 🐍 🐍 🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 2347085977298 FREE PAGE 4️⃣➡️5️⃣ WRITTEN & DIRECTED✍️ BY A'ISHA M.B (Zinariyar Jajirtattu) *______________________________________________________________________* *BAYAN SHEKARU SHA HUƊU* hankali kwance take busa sarewar nan batare da wani tsoro koh fargaba bah. yayin da karar sarewar gaba ɗaya ya karaɗe dajin. kwance take akan jibgegiyar bishiya dake tsakiyar dajin. lumshe idanuwan ta tayi waɗan da suke Ars colour masu daukan ido da hankali. Yayin da gashin ta wanda yake baki ya rufe mata fuska, akan bai bani damar ganin fuskar ta sosai bah. baje gashin ta tayi. Masha Allah baki na ya iya furta wa ganin irin tsananin kyawu da take dashi. Sanye take cikin rigar yan fulani wanda suka yi matuƙar karbar jikin ta sosai. A hankali na fara ganin macizai na fitowa daga cikin ramu kansu, suna nufar inda take, yayin da suka zagaye ta baki daya. Murmushin jin dadi tayi, ganin su firfito ga Rike ɗaya daga cikin su tayi, sannan ta motsa ɗan karamin pink lips ɗinta tace, "yau dai na kawo muku ziyara koh, yanzu kunyi farin ciki". "Shikenen toh yanzu ni zan tafi kar Inna taga bana nan, sabo da tsawon shekaru bata san ina futa bah, duk zaton ta ina cikin ɗaki, ɗan aka ni zan tafi yanzu, saimun sake haɗuwa". Dira tayi daga kan bishiyar, yayin da ta fara nannaɗe fuskar ta da mayafi, dan kar wani daga cikin kauyen ya ganta. Tafiya ta ke ƙoƙarin yi, amma sai ta ji an ririke mata ƙafafuwa. Kallon kafar ta tayi, ganin yadda macizan suka riƙe mata kafa alamin basua so ta tafi. Murmushi tayi wanda yasa asalin kyawun ta kara bayyana, sannan ta cire macizan daga jikin ta, ta kalle su tace, "Aa abokai ku bari na tafi, ku kanku kunsan da cewa bani da babban aminai sama da ku". "Idan ban tafi bah, asiri na ne zai tonu a wajan Inna, saboda ta gargade Ni cewa kada na kuskure na futa dai-dai da tsakar gida karna futa". Kuma ta dauka tsawon waɗan nan shekaru, ina cikin ɗaki ne ban taba fita ba". Zama tayi hawaye ya fara sauka kan kuncin ta, sannan tace,"Ni kadai ce a kauyen nan ba'a bari na fita, kuma ni kadai ce nayi karatu a kauyen nan". "Duk sanda na tambaye ta nace mata, yaushe ne nima zan dawo rayuwa kamar kowa, yaushe zata barni na fara fita kamar yadda suma yaran kauyen nan keyi, amma koda yaushe amsa daya take bani, shine sai nan gaba, sai kin cika shekara ashirin a duniya". Taɓa sarkar dake wuyar ta tayi, yayin da take jin zuciyar ta nayi mata kuna da radadi, tace,"Yanzu shekaru na sha tara ne, har yanzu bata bari na in futa, babu wani ɗan kauyen nan daya taɓa gani na ba". "Yanzu sau biyu kenen tsawon waɗan nan shekaru ina fita batare da sanin kowa bah, gashi mahaifiya ta har yanzu bata farfaɗo bah". Dan aka ku barni na tafi, tana kaiwa nan ta tashi tare da barin wajan. Can cikin kauyen ta nufa, saida ta tabbatar babu wanda yake kallon ta, sannan daga bisani ta haura kan gidan Inna wuro, tare da dira ciki da sauri ta shiga cikin ɗaki tare da cire tufafin dake jikin ta, sannan daga bisani ta kwanta akan gadon karar dake ɗakin. Jin takun tafiya na mutum yasa tayi saurin rufe idanuwan ta, yayin da tsoro da fargaba ya cika zuciyar ta. Sallama riƙe s baƙin ta shigo ɗakin. Amsa sallamar Dua tayi tace, "sannu da zuwa Inna". Murmushi Inna tayi tace, "yauwa ƴata shin na same ki lafiya?. Girgiza kai Dua tayi sannan tace, "eh ina lafiya kalau, ta faɗa baƙin ta na kakkarwa. Binta Inna wuro tayi da kallo ganin yadda gumi yake keto mata ta koh ina. Sannan tace, "Dua meyafaru naga kina gumi?, hanya kina da gaskiya kuwa?". Sosa kai Dua tayi tare da faɗin,"hmm babu komai fahh". Murmushi Inna wuro tayi tace, "aba Dua mara gaskiya fah koh a ruwa yake gumi yake, dan aka ki fada min menene?". Aa inna da gaske nake babu komai. tom shi kenen tunda kince babu komai cewar Inna, sannan ta ƙara da faɗin, ni yanzu zan je na kwanta sabo da gobe muna da shagali na al'adun gargajiya da za'a gabatar, dan aka ba lalle ki tashi ki tarar dani bah, dan koh yanzu mah daga gidan mai gari nake. Dani za'a shishirya abubuwa, kuma ina ganin kamar zan kai dare achan". Tashi Dua tayi sannan ta nufi inda take a zaune tace, Inna shin zan iya neman wata alfarma daga wajan ki?. Murmushi Inna tayi tace, "ki tambaye ni ko mene ne indai bazai fi karfin na bah, toh ni kuma zanyi miki. Gyara muryar ta Dua tayi tace, "dan Allah Inna nima ina son naje, tunda ake shagali a kauyen nan, dai-dai da so ɗaya ban taba zuwa bah, ki taimaka ki barni naje kinji. ta karashe maganar hawaye na sauka kan kuncin ta. Hatake naga fuskar Inna ya sauya daga walwala zuwa damuwa. Kallon ta Inna tayi tace, "nasan da cewa bai kama ta a dinga barin ki a ɗaki bah, amma sabo da babbar kyauta wacce za'a baki yasa nace ki dinga zama a ɗaki. Ke baki ga cewa ke yar gata bace, na farko ke kadai kikayi karatun boko da islamiyya a cikin yaran kauyen nan, ke kadai kika iya turanci, gashi duk faɗin kauyen nan babu wacce ta kai ki kyau. Ki cigaba da hakuri harki samu kyautar ki na doki, ance ma hakuri ci mahawadaci. Girgiza kai Dua tayi sannan tace, Ni bana so, na fasa yin gasar da aka sa, bana son kyautar doki. Abin da nake bukata yanzu shine ki dinga bari na ina futa, ina shiga cikin mutane, nima na dinga rayuwa kamar yadda kowa yake yi a cikin kauyen nan. ajiyan zuciya Inna wuro tayi tace, "maza jeki kwanta". Dua na shirin magana Inna wuro ta dakatar da ita da faɗin, ba tarbiyar dana baki kenen bah, ban baki tarbiya cewa in gaya miki abu sannan ki ƙi ji bah, ban baki tarbiyar da zaki bijire wa magana ta bah". Share hawayen ta Dua tayi, sannan tace,"kiyi hakuri Inna idan na ɓata miki rai, insha Allahu bazan sake tambayar ki komai bah". Tana kaiwa nan ta miƙe tareda shiga ɗakin da mahaifiyar ta take. Hawayen dake shirin zubo mata Inna wuro ta share. Sannan ta karkade shimfidar ta, ta kwanta... Fashe wa Dua tayi da matsanancin kuka, tare da rike hannun mahaifiyar ta tace,"nasan da cewa da idon ki biyu na tabbata ba zaki bari na dinga zama a ɗaƙa bah, na tabbata cewa ke zaki tausaya min". "Sabo da mene ne za'a ce a koda yaushe na dinga zama a ɗaki har saina kai shekaru ashirin a duniya". Share hawayen ta tayi da bayan hannun ta sannan tace, "wallahi koh mene ne zai faru, saina je wajan shagali shekara da za'a yi gobe". Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye tare da shiga cikin ɗakin ta..... Washe gari da sassafe Inna ta tafi gidan msi gari, batare da ta ɗora ƙarin kummallo kamar yadda ta saba. Ganin Inna wuro bata gidan, yasa dua fara shirye_ shiryen yadda zata fita daga gidan batareda kowa ya ganta bah. Ɗaukar mayafin data saba ɗaurawa a fuskar ta idan zata fita tayi, sannan ta nannaɗe fuskar ta da mayafin tayi rawani a kanta da wani mayafin. Sannan ta nufi tsakar gida, cikin sa'a kuwa ta tarar da babu kowa a tsakar gidan, ganin aka yasa ta saurin ficewa daga harabar gidan. Kallon hagu da damar ta tayi, yayin da take ganin mutanen kauyen na wucewa, kowannen acikin su da shigar da yayi. ɓadda kama tayi acikin su sannan ta jera dasu suka cigaba da tafiya. Gaba ɗaya babu abinda kake gani a gidan mai gari sai tarin jama'a da kayan al'adu, gefe guda kuma tukun yoyi ne a jere ba iyaka, yayin da ko wace tukunya akwai abin da ke cikin ta. Yayin da ɓangare guda kuma, ake ta kaɗe_kaɗe, hana rawa, dama al'adar kauyen kenen, ko wace shekara sai sunyi murnan zuwan ta.. . Kallon koh ina na gidan tayi, chan ta hango mutane a zazzau ne suna rera waƙoƙin gargajiya. Zuwa tayi daff dasu sannan ta samu guri a kusa da su ta zauna. Binta mutanen wajan suka yi da kallo, ganin gaba ɗaya shigar ta ya bambanta da sauran yan kauyen, gashi kuma ta rufe fuskar ta, ba damar mutum yaga wacece.. Sosai Dua ke farin cikin samu dama irin ta yau, wai ashe watarana itama zata shiga gidan mai gari. Maganar da ta shiga yi kenen. Jin karar takun kofaton doki gaba ɗaya suka yi, yayin da gaba ɗaya naga fuskar kowannen su ya sauya daga farin ciki zuwa damuwa. Sanye gaba daya kansu su yake da rawani, kallo ɗaya zaka musu kasan kasurguman kafirai ne, kuma marasa tsoron Allah. Magana ɗaya daga cikin su ya fara yi kamar aka. kowa ya bada hankalin shi nan wajan. Yanzu wata ya kare har an shigo wani watan, amma baku biya haraji bah, shin yaushe ne zaku biya. Kallon su Mai gari yayi yace, "kuyi hakuri zamu biya, abin da yasa kuka ga mun daɗe bamu biya bah shine saboda, wannan shekarar bamu samu amfanin gona bane sosai shi yasa, amma nayi muku alkawari kafin wannan watar ta ƙare zamu haɗa gaba daya mu kawo. Bamu san wannan zancen bah, cewar daya daga cikin yan jeji. Sannan ya kara da faɗin, "baza mu taɓa barin nan wajan batare da kun biya haraji ba". "Da bakuda amfanin gona, da baza ku haɗa wannan abun da kuka kira shagalin bah". Karasa inda suke Inna wuro tayi, sannan ta tsugunna cikin gwiwo win ta tare da haɗa hannayen ta guri guda, tace, "ku kara hakuri, baku taɓa zuwa karbar haraji mun hana ku bah. Tabbas abin da zai hana mu bada haraji toh babban abu ne, muna mai rokan ku da kuyi hakuri. Tsugunnawa gaba ɗaya yan kauyen suka yi, suka shiga basu hakuri yayin da Dua ke tsaye ta harde hannuwan ta a kirji. Yayin da ta bi kowannen su da kallon mamaki. Kallon Dua dake tsaye ɗaya daga cikin mutanen jeji yayi, sannan yace, "ke har wacece da zaki tsaya a tsaye bayan kowa yana a tsugunne. Murmushi Dua ta yi, sannan ta kalle shi tace, "ba'a haifi wanda zan tsugunna na bashi hakuri bah akan abin da nasan ban aikata bah, kuma koda mah zan bada hakuri bazan taba iya bawa ku kasurguman kafirai yan jeji hakuri bah". Wani wawan dariya! gaba ɗaya yan jejin suka kwashe dashi, sannan wanda yake jagoran su ya kalle ta yace, "mene ne na rufe fuska toh, ke yar wace a wannan ƙauyen, shin ba'a taɓa baki labarin mu bane, mu shika kawai muka sani da zubda jini. Kada ki sake ki fusa ta mu, idan kuwa kika fusata mu toh saimun wanke wannan ƙauyen da jinin ku. Sai dai idan babu rai a jiki na, in kuwa ina nan koh dabba baku isa kuce zaku cutar da ita bah, balle kuyi kokarin cutar da mutum cewar Dua. Bin Dua da kallo gaba ɗaya mutanen kauyen suka yi, yayin da suke jin alamun nasara a tattare da ita. Wani mahaukacin dariya ya kwashe dashi!, cike da ɓacin rai ya kalle ta yace,"zan nuna miki misali". Yana kaiwa nan ya dauki kafar sa na hagu tare da ture Inna wuro ta faɗi kasa. Wani razananniyar kara Dua ta saki!, babu bata lokaci, macizai suka fara fitowa daga cikin ramu kansu, yayin da suka fara nufar gidan mai gari. Gurnani Dua ta fara yi, babu shiri jikin shugababn nasu ya fara kakkarwa. Yayin da gefe guda Jama'an kauyen suka miƙe tare da cunku shewa guri ɗaya, gefe guda kuma tsoro da fargaba gaba daya ya baibaye zuciyoyin su. Babu zato suka ga, macizai na tunkaro inda suke, saboda yawan su mah ba zasu irgu bah, cikin kankanin lokaci suka shiga sarar mutanen jejin. Ihuu! Mutane jejin suka shiga kwalla wa, yayin da kowanne acikin su ya fara gudun ceton kansa. Gudu suka dinga yi har suka bar gidan mai gari, yayin da macizan suka bisu a baya . Murmushi Dua tayi,sannan ta karkaɗa hannun ta, ta juya da niyar tafiya. Daga sama taji muryar Inna wuro na faɗin. "Wacece ke?. 🌸RAYUWA DA MACIJIYA 🐍 🐍 🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* *2347085977298* COMMENTS & SHARE PLS ALKALAMIN A'ISHA M.B (Zinariyar Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 2347085977298 *___________________ *Dedicated this page to my fellow members of Jajirtattu writer's association,(J.W.A) Almighty Allah will continue to be guide us, protect us from the hands of devils and remember us In heaven. Muna tare har abada insha Allah🙏🏻🙏🏻*___________________ FREE PAGE 6️⃣⏩7️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B 💞 (Zinariyar 🪙Jajirtattu) *______________________________________* Murmushi Dua ta saki. sannan ta ɗora hannun ta akan ta, ta fara kunce rawanin dake kanta a hankali. Hatake gashin ta wanda yake baƙi da mugun tsantsi da tsayi ya bayyana. Daga bisani kuma ta fara kunce maya fin dake ɗaure kan fuskar ta. daga karshe tayi nasaran kunce shi baki daya. Rasss gaban Inna wuro ya faɗi!. Cikin ranta tace. "Wannan yarinyar me take shirin jawo min ne?, meya sa kuma ta fito bayan saida na fada mata cewa kada taje koh ina". Sosai mutanen ƙauyen ke yabon irin tsananin kyau na halitta da Dua keda shi. Yayin da suke ganin cewa tun da zuka zo duniya basu taɓa gamo koh mafarkin mace mai mugun jarabbaben kyau kamar Dua bah. Bin ta suka ci gaba da yi da kallo, yayin da kowa da abin da yake sawa a ransa. Motsa leɓen ta Dua tayi sannan tace. "Sunana Dua". nice nan wanda kuka kulle a ɗaki a gidan Inna wuro tsawon shekaru sha huɗu". Zabura gaba ɗaya suka yi, yayin da gaba ɗaya tsoro da fargaba ya mamaye zuciyoyin su. Kallon ta Mai gari yayi yace. "Waya baki izinin fitowa? Me yasa kika fito bayan kin san da cewa an hana ki fitowa dai-dai da tsakar gida. "Kin san dalilin da yasa aka ce miki kada ki kuskure ku fito ne?, koh kuwa kin san hatsarin da yake shirin tunkaro ki?. Amsa Joda ta bashi da cewa. "Ban san dalilin ku na hajiye ni a ɗaki bah, kuma sannan ban san wace cutarwa ce John hatsari dake tun karo inda nake bah ". "Amma abu ɗaya na sani, "Allah ne mai kare wa, kuma sannan ita kanta abin da kuke ikirarin cewa zai cutar dani bata isa ta tunkari inda nake ba, domin kuwa ina tattare da kariyar ubangiji". "Kuma sannan ina da yaƙini cewa zai kare ni". Ba zai bari na cutu ba ". Takaici ne ya ishi Inna wuro tace. "Kwarai Allah shi ne mai kare wa. "Amma bayan Allah ya kare ka, kaima saika kare kanka". "misali ki je yaƙi, sai kika ga makiyin ki ya tunkari inda kike da wuka, shin a lokacin zaki ki jira Allah ya kare ki tareda kawo miki agajin sa? Bayan kuma kinada hannun da jiki da zaki iya kare kanki". Murmushi Dua tayi tace." Har yau, har gobe abu ɗaya kawai zan ci-gaba da maimai ta wa shine. "Allah shi ne mai kare wa". Mai gari dake zaune kan kujerar sa yace. "Toh yanzu da kika fito, me kika fito yi? Kuma sannan taya lokaci ɗaya kika kwalla ƙara macizai suka fito?. Karasa wa inda yake Dua tayi tace. "Na fito ne domin zuwa shagalin shekarar da kuke yi, batun kuma macizai ban sani bah, nima kawai gani nayi sun zo, amma ban san daga ina suke bah". "Sannan kuma dan Allah ina son na nemi wata alfarma". Ta faɗa tana mai maida kallon ta ga mutanen ƙauyen. "Muna jin ki me cece alfarmar da kike nema?". Cewar mai gari. Gyaran murya Dua tayi sannan tace."ina so ku bani ƴancina dawo yin rayuwa kamar ko wace mace a wannan ƙauyen". "Bayan nan kuma, tun da yanzu na kammala karatu na a gida, ina son ku barni naje birni na fara makarantar jami'a. Tun da ai kuna so na zama likita". "Kuma nima wannan shi ne mafarki na, dan Allah kada kuce zaku hanani ". Ta karashe maganar tare da haɗa hannayen ta guri guda. Ajiyan zuciya kowa ya sauke. Yayin da Inna wuro ta nufi inda Dua take tare da jan hannun ta tace. "Ina mai bada hakuri game da abin da Dua ta aika ta, nayi alƙawarin cewa, akan ba zata sake faruwa bah ". Mai gari ya kalli Inna wuro yace. "Shikenen zaki iya tafiya da ita, kuma sannan kada ki kara barin ta tayi yinkurin futa, sabo da a halin yanzu rayuwar ta yana cikin hatsari ne". "Maganar jami'a kuma babu inda zaki je, idan kuwa kikayi yin kurin fita daga kauyen nan, toh saimun yanke miki hukunci kamar yadda dokar wannan ƙauyen ta tanadar wa waɗan da suka bar wannan kauyen ba tare da izinin kowa bah". "baza mu taɓa zuba ido muna ji muna gani wani cutarwa ya nufi inda take bah. Domin kuwa idan wani abu na cutarwa ya same ta, toh saimun fi kowa shiga baƙin ciki da damuwa. sabo da itace garkuwar da kuma jagora na wannan ƙauyen baki ɗaya". Wafce hannun ta daga riƙon da Inna wuro tayi mata Dua tayi, sannan ta kalli mutanen ƙauyen tace." Me yasa kuke wasa da rayuwa ta ne? kubar ni mana na samu yancin kaina. Shin dama na bukaci taimakon kune? Tun da nake yarinya baku taɓa barni na fita bah, shin wannan abin da kuka yi min ne kuke tunanin cewa kare ni kuke yi? Koh kuwa a ganin ku bazan iya kare kaina bane? duda cewa ni ba kowa bace, amma karfin gwiwa da rashin tsoro wanda yake tattare dani yafi naku baki ɗaya". Abin da kuke min samm ba za'a kira ta da kariya bah, domin kuwa babu wani ɗan adam daya isa sauya ƙaddara, duk abin da Allah ya rubuta cewa shi zai faru, toh babu wani dan adam koh Aljani koh kuma maye daya isa ya chanz akan". "Kuna tsoro kada wani abu ya same ni koh ya taɓa lafiya ta. "Amma abin da baku sani bah shi ne idan Allah yaso koh ina cikin ɗakin ban fita bah, abin da kuke gudun kada ya faru dani saiku ga ma idan na fita ɗin abin bai same bah. " Amma saiku ga abin yazo har gida ya same ni". "Dan aka ina roƙon kowanen ku da ya barin na tafi birni don karo karatu, duk abin da kuke ganin ina yi duk dan sabo da ƙaruwar mu ne ". Cikin ɓacin rai Mai gari yace. "Inna wuro maza_maza ki shiga da yarinyar nan ciki domin raina ya soma ɓaci". Rintse idanuwan ta Dua tayi masu kama dana mage, yayin da taji lokaci ɗaya ranta ya soma ɓaci. A fusa ce ta kalli mutanen ƙauyen sannan ta riƙe kanta da hannuwan ta guda biyu ta kwalla wani ƙara! Wanda ya sanya gaba ɗaya kowa firgita. Babu zato aka fara iska mai karfi wanda gaba ɗaya ya karaɗe kauyen. Yayin da guguwa ta soma wanzu wa, hadari baƙin ƙirin ya taso ya mamaye ƙauyen. Yayin da gaba daya ƙauyen tayi baƙin ƙirin, baka iya hango mutanen dake cikin ta sabo da mugun duhun da tayi. Ganin aka da Inna wuro tayi ya sata saurin jan hannun Dua, tare da dora sarƙar dake wuyar Dua a saitin zuciyar ta. A hankali Dua ta fara sauke numfashi, yayin da faɗi a wajan sumammiya. A hankali a hankali garin ya fara washe wa. Daga ƙarshe garin ya washe baki ɗaya. Ganin yadda suka ga Dua a kwance ya sa su firgita. Yayin Malam liman yayi karfin halin faɗin. "Abin da muke tsoro shi yake shirin faruwa, domin idan baku manta bah Malam Ali yace damu, "kada mu bari tana fito wa har saita kai shekaru ashirin a duniya". Idan kuwa bah aka bah komai zai iya faruwa". Miƙe wa Mai gari yayi yace."wannan yarinyar tana da abin al'ajabi, domin wasu baƙon abubuwa nake gani a tattare da ita". "Hanya yariynar nan mutum ce kuwa?"......... 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 COMMENTS & SHARE PLS 🙏🏻🙏🏻🙏🏻 ALKAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 FREE PAGE 8️⃣▶️9️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) *___________________* dakatar dashi inna wuro tayi, gami da faɗin. "Mutum ce kamar kowa, amma waɗan nan kalubalen da take fuskanta ina tunanin cewa koh aljanu ne da ita ". Babu zato suka ga ɗaya daga jama'an kauyen ya faɗi kasa, yayinda ya fara shure _ shure kumfa ya fara fita daga baƙin sa. Hankalin jama'a ƙauyen ba karamin tashi yayi bah ganin yadda wannan mutumin ya fita a hayyacin shi. Da sauri suka yi kansa tareda ɗaga shi sama. Ririke shi suka yi, yayinda shi kuma yake ƙoƙarin kwace kansa daga gare su. Kallon mutanen garin malam liman yayi gami da faɗin. "Cutar sa na farfadiya ce ta tashi, kuma a halin yanzu ba muda maganin warakar ta, duk magunguna suna cikin wan nan jejin ne". Kallon sa inna wuro tayi sannan tace. Toh "Shi yasa na ke ce daku mu dinga zuwa dajin jarmuna domin samo magunguna amma kuk....... Maganar ta ne ya tsaya chak sakamakon tsawan da mai gari ya daka mata! Gami da faɗin. "Abin da ba zai taɓa yiwuwa bah kenan. Tayaya zamu je dajin da ya zama haramtacciyar wa wan nan ƙauyen. Ke kanki kin san da cewa tsawon shekaru amsin Koh sama da aka ma babu wani ɗan adam da ya isa dora kafar sa da niyar shiga dajin nan, domin kuwa duk wanda ya shiga zai mutu, kuma sannan ba za'a ga gawar sa bah domin aljanu sun yi fata _fata da naman sa. Dan aka kisa a ranki cewa babu wanda yake da zarrar shiga wan nan dajin. Dan aka Allah zai ci gaba da ƙare sa kamar yadda ya ke ƙare sa a da". Daga sama suka ji muryar Dua na cewa. "Ni zan je sannan na dawo da magani". Kallon ta gaba ɗaya mutanen ƙauyen suka yi yayinda Inna wuro tace. "Hankalin ki ɗaya kuwa? Dajin da mutum ba zai shiga kuma ya dawo da rai bah, Toh babu inda zaki je kinji na faɗa miki". Share hawayen dake shirin zubo mata Dua tayi sannan tace. "Ina son mahaifiyata ta samu lafiya. Kuma sannan shima wannan ya samu lafiya". "Nayi muku alkwari cewa zan shiga kuma na dawo lafiya ". Murmushin yaƙe Mai gari gami da cewa."indai har kika shiga sannan kuma kika fito lafiya toh na daukar miki alkawarin cewa zaki je birni karatu kamar yadda kika bukata kuma sannan mu zamu biya miki kuɗin makaranta har ki gama ". Murmushin jin dadi Dua tayi tace."insha Allah zan je na dawo. ina ne hanyar wajan? Mai gari bai kama ta ace an barta taje bah, mu mene aikin mu? Tana diya mace amma zata je wan nan dajin yayinda mu bamu je bah". "Aa ku barta taje, tana son ta nuna mana cewa ita ɗin jaruma ce kuma mu bamu san abin da muke bah, dan aka zamu barta taje". Maza taso mu kaiki har wajan. Miƙe wa Dua tayi, yayinda taga mai gari da sauran mutanen kauyen na nufan hanyar dajin. Hatake taji zuciyarta ya karaya. yayinda take ji babu sauran karfin gwiwa a tattare da ita. Mazewa tayi yayinda take ji yau koh mutuwa zata yi saita shiga wannan dajin. Kuma sannan mai gari ya cika mata alƙawarin da ya ɗaukar mata na zuwa birni karatu. Ganin sun yi nisa a tafiya ya sata saurin bin bayan su. Saida suka yi tafiya mai nisa sosai daga bisani suka isa baƙin kofan dajin. Tsayuwa gaba ɗaya suka yi yayinda suka maida kallon su kan Dua. Tsayawa Dua tayi tare da ƙarewa dajin kallo. Murmushi tayi tareda nuna dajin tace. Shin akan wannan dajin kuke jin tsoro? Ni zan shiga kuma sannan zan fito. Tana kaiwa nan ta isa baƙin dajin, batareda bata lokaci bah, ta sanya kafar ta na dama acikin dajin sannan tayi bismillah daga bisani aka neme ta aka rasa a wajan. Fargaba da tsoro ne gaba ɗaya ya mamaye zuciyoyin kowannen su. Gefe guda Inna wuro ta haɗa hannayen ta guri guda sannan ta fara addu'a. Dua bata tsinci kanta a Koh ina bah, sai chan cikin dajin wanda mutanen kauyen kewa lakabi da *Jarmuna*. Kallo koh ina na farfaɗiyar dajin tayi, yayinda idanuwan ta ya sauka akan kyawawan bishiyun masu ɗaukar hankali da ido. Gefe guda kuma furenni ne a jere babu iyaka sai sheƙi da ƙyalli suke.f Tafiya ta soma yi babu alamun tsoro a tattare da ita. Taku ɗaya, biyu tayi taji kamar hana binta a baya. Saurin waigawa tayi taga babu kowa. Hajiyan zuciya ta sauke tareda maida kallon ta gaba. Wani razannaniyar kara ta saki! Sakamakon harba da tayi da wasu munanan halittu. Fuskar su gaba ɗayan ta Baƙin kirin ne Wanda babu ido balle hanci. Baƙin su tamkar yadda kasan baƙin jakuna, wanda ke ɗauke da gantsara_gantsaran haƙora wanda suka yi matuƙar muni da abin tsoro. Babu abin da ke tsiro wa daga jikin su sai macizai ta koh ina. Yayinda kafafun su babu maraba dana doki. Babu shiri jiri ya ɗibi Dua ta faɗi a wajan sumammiya. Aljanun cikin dajin wanda yawan su bazai misaltu bah na ganin akan suka yi kanta a guje tareda malalo da harshen su waje jini na malala. hadari baƙi ne tashi, yayinda aka fara iska mai karfi. Babu abin da kake gani sabo da duhu gaba ɗaya ya karaɗe dajin. Saida suka je daff da ita da nufin cutar da ita suka ga haske ya bayyana a jikin ta wanda ya karade dajin gaba ɗaya. Hatake gaba ɗaya suka ja da baya yayinda kowane a cikin su ya faɗi kasa. A hassale ta bude idanuwan ta wanda suka kara rinewa suka yi Ars sosai. Yayinda iska ya ɗaga ta sama, ya kasance ita ba'a kasa bah kuma ba'a sama bah. Kallon su tayi yayinda gashin kanta ya baje ya tsaya a mimmike. Cikin gurnani wanda yasa fuskarta yayi jaa yayinda saɓar maciji ya fara bayyana a jikin ta. Cikin dashashiyar murya tace dasu. "Maza kuzo ku tunkari inda nake, bana tsoron mutuwa kuma sannan bana tsoron abinda mutane ke tsoro, ku tunkare ni idan kun isa". Hatake munanan halittun suka fara yowa kanta. Cike da jarumta ta tsaya batare da ta motsa bisa inda take bah. Tsalle ɗaya daga cikin Aljanun yayi tare da yin kanta cikeda mugunta. Ganin akan da Dua tayi yasata shake masa wuya. Kakari Aljanin ya fara yi. Hatake kayoyi suka fara tsiro wa daga jikin sa. Saurin sakin sa Dua tayi jin yadda kayar jikin sa ya chaki hannun ta. Rintse idonta tayi jin yadda hannun ke mata zugi. Cikin daƙewa ta ɗaga idanuwan ta. Da mamaki kuwa taga sun ɓace batt. Murmushin jin dadi tayi sannan tace. "Aka ce bakua ji, baza ku iya dani bah domin ni nafi karfin tunanin ku. Babu zato taji an ɗaga ta sama tareda naka ta da kan wani ringimemen dutsen dake tsakiyan dajin wanda suke wa lakabi da dutsen mutuwa. Wani azababiyar ƙara Dua ta sauke! Hatake jini ya fara zuba daga kanta. Jin karnin jinin ta, yasa sauran aljanun suka firfito suka fara yowa kanta. Zagaye ta gaba daya suka yi, Yayinda ta ke cikin tsakiyar su. Hatake naga jibgegen dattijo acikin su wanda haɓar sa ke dauke da farin gemu har kasa. Tare da idanuwa masu kama dana jemage. Ƙarewa Dua kallo yayi. Hatake gaban sa ya faɗi! Baki na rawa yace . "tabbas babu tantama ita ce, ta dawo daga mutuwa, macijiya mai kwanciyar ɗaukar rai. Sarauniya kuma shugaba na macizai da Aljanu harda mayu. Shekaru kenen babu ita, yanzu kuma ta bayyana, idan tazo guri bata barin wajan saita yi shiƙa domin bata jure zalunci, duk inda taga hana ba dai-dai bah saita san yadda zata yi ta kawar da abin da ake yi. Kunyi babban kuskure da kuka taɓa ta, idan har kuka bari ta tashi toh sunan mu mutattu. Domin ba zata barmu da ran mu bah". Maza_maza ku bar wajan nan dan zata iya tashi a kowane lokaci. Sarauniya kuma shugaba na gaba ki daya macizan duniya ta dawo, yanzu zata dora aikin ta a inda ta tsaya, zata ci gaba da kawar da azzalumai kamar yadda tayi lokacin baya. Wannan karan ta dawo ne da tarin karfi da kuma baiwa. Mu gudu kada ta tashi. gurnani suka jiyo daga bayan su, waigawa suka yi da sauri. hatake suka yi ido huɗu da jibgegiyar macijiya wanda girman ta ya cika dajin gaba ɗaya yayinda bakin ta ke fitar da wuta. FANS KU BIYO NI A PAGE NA GABA DON JIN YADDA ZATA KAYA TSAKANIN ALJANU DA MACIJIYA. COMMENT & SHARE PLS 🙏🏻🙏🏻🙏🏻 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 FREE PAGE 9️⃣➡️1️⃣0️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) *_______________________________* Cikin tashin hankali gaba ɗaya suka fara neman hanyar kuɓuta, yayinda suka fara gudun ceton rai. Ɓace wa gaba ɗaya suka yi yayinda suka tashi cikin sararin samania, batareda ɓata lokaci bah suka riƙe hannuwansu baƙi ɗaya tare da zagaye Dua wacce ta zama jibgegiyar macijiya. Maganganu suka fara yi cikin yaren Aljanu. Ƙaran da Dua ta saki ne yasa gaba ɗaya suka saki juna yayinda ta fara wulli da su daya bayan ɗaya. Sanin raunin ta da shugaban aljanun yayi yasa shi ya maida garin gaba ɗaya ta zama duhu, yayinda ba ka ganin komai in banda duhu. Babu zato yaga haske ya bayyana a jikin ta wanda ya cika ilahirin dajin baki ɗaya. Ganin babu sarki sai Allah ya sa gaba ɗayan su ɓace wa daga wajan. Hatake ta faɗi kasa, babu bata lokaci halittar ta na mutum ya fara dawo wa. Daga karshe ta zama mutum gaba ɗaya. Yayinda gaba ɗaya jikin ta ya mutu. Saida ta dau kusan hour tana kwance bata farfaɗo bah. Ɓangaren jama'a garin kuwa, ganin har yanzu Dua bata dawo bah yasa suka sallama cewa ta mutu, yayinda Inna wuro ta fara kuka, sosai gaba ɗaya suke dana sanin barin Dua da suka yi ta shiga wannan dajin. A hankali ta fara buɗe idanuwan ta, a wahalce ta miƙe yayinda take jin duk gaɓoɓin jikin ta nayi mata ciwo, waigawa tayi taga babu kowa. Rike kanta tayi don tuna abin da ya faru, amma ina babu abin da ta iya tunawa. Motsa leɓen ta tayi tace. "Me yake faruwa dani?, ina waɗan nan halittun suke?, waya kore su?". Tambayar data shiga yi wa kanta kenen. Basar wa tayi sannan tace. "Koh ma mene ne su suka sani, nidai na shigo dajin nan kuma sannan ina da tabbacin cewa zan fita lafiya". Tana kaiwa nan ta nufi inda bishiyoyin magunguna suke. batare da ɓata lokaci bah, ta fara tsinkar ganyayyakin. saida ta tsinki adadin yadda ranta yake so, sannan daga bisani ta nufi hanyar da take tunanin cewa ita ce hanyar futa. Saida tayi tafiya mai nisa sosai sannan daga chan nesa ta hango wani abu mai sheƙi da haske. Karasa wa tayi wajan domin cire kwarkwatar idanuwan ta. Zaro ido tayi ganin madubi ne wanda aka ƙayata shi da furenni masu kyau da daukar ido. Mamaki ta shiga yi domin ita tun da ta ke bata taɓa gani abu makamancin aka bah. Ƙoƙarin kai hannun ta take kan madubin. Ta ke taji wani zuciya yace mata kada ta taɓa. Barin wajan tayi sannan ta ci-gaba da tafiya, hango wani karamin bishiya tayi daga chan nesa, da sauri ta karasa inda bishiyar take. Rubuce_rubuce taga hanyi a jikin bishiyar. yayinda jini ke malala a jikin ganyayyakin ta. Tsoro da fargaba ne ya mamaye zuciyar Dua, yayinda ta ke ji kamar ta kawo kanta ga halaka ne. Rintse idanuwan ta tayi, cikin kwarin gwiwa ta kai hannun ta ga wannan bishiyar. Babu zato ta fara jin muryoyi mara amo da daɗin sauraro ta koh ina. Yayinda suke faɗin. "Barka da dawo wa duniyar ki sarauniyar macizai, muna miki maraba da zuwa". Cikin rashin fahimtar furucin su tace."su waye ku?, mene ne kuke nema a gare ni?, maza ku faɗa min hanyar da zan fita daga wajan nan ". An gama shugaba taji sun furta. Babu tsanmani taga anyi sama da ita sannan aka fara tafiya da ita akan iska. Saida aka yi tafiya mai nisa daga bisani suka isa baƙin wani kogi wanda launin ta ke jajir tamkar jini. Sauke ta suka yi sannan suka ce da ita. "Halitta ɗaya ce a duniyar nan zata iya bin ta wannan kogin kuma wannan halittar itace sarauniyar macizai, idan har ke ɗin ce da gaske toh zaki bi wajan nan batare da wani abu na cutar wa ya tunkari inda kike bah". "Amma kuwa indai ke ta bogi ce toh ki ƙaddara cewa kin zama gawa domin zaki yi mummunan mutuwa ne, sabo da wannan kogin halitta ɗaya ta yarda ta bi ta kanta, kuma ita ce shugaba na macizai ". 'Koh mu da muke Aljanu bamu isa mun bi ta wannan kogin bah, domin idan muka kwatanta yin akan zamu zama mutattu ne. Fatan nasara a gare ki". Suna kaiwa nan wajan yayi shiru. Bin kogin Dua tayi da kallo, yayinda take ganin kamar duk abin da suka fada karya ne. Tsugunnawa tayi ta dora idanuwanta kan ruwan kogin. Sannan daga bisani ta saka ɗan yatsarta acikin ruwan. Babu zato taga ruwan ya fara juyi, sannan ya farayin sama, saurin ja da baya tayi ganin yadda ruwan yake jujjuyawa tamkar mutum. Cikin kankanin lokaci taga ruwan ya raɓe yayinda wajan ya bada siririyar hanya. Batare da tsoro bah ta fara bin hanyar wajan da sauri. Sosai ta ke mamaki ganin baƙon al'amari irin wannan. Tana barin wajan ta kuma ganin ta a tsakiyar wani dajin daban. Namomin daji gaba ɗaya ta ke ta harba dasu. Yayinda kyawawan tsuntsaye suka fara hawa jikin ta. Cicire su ta soma yi daga jikin ta, amma a yayinda ta ke cire su wasu na zuwa. Saida tayi da gaske tukunnan suka bar jikin ta. Kowane dabba na dajin binta yake da kallo. Hatake taga namomin dajin gaba ɗaya sun tsuguna cikin gwiwo winsu tare da saukar da kai ƙasa. Mamaki ne ya kama ta. A yayinda take ganin mene ne akan da suke yi. Ci-gaba da tafiya tayi, a yayinda suke mara mata baya. Juyawa tayi da sauri gani ko wace halitta ta dajin gaba ɗaya ita suke bi. Alama ta fara yi musu da hannu dasu koma, amma ina kamar basu san tana yi bah. Ci-gaba da tafiya tayi, su kuma na biye a bayan ta. Juyawa tayi a fusa ce tare da daƙa musu tsawa! Babu shiri gaba ɗaya suka ja da baya. Cikin ɓacin rai ta nuna su tace. "Maza_maza gaba ɗaya ku koma kafin na hallaka ku baƙi ɗaya". Ta faɗa tsoro fal cikin ranta Kamar da wasa taga gaba ɗaya sun juya tare da koma wa. Baki sake tabi su da kallo, a yayinda take mamakin kanta. shafa jikin ta tayi sannan tace. "Ta yaya kuma ni na iya yi musu magana? Wacece ni? Me yasa ina ce musu su koma kuma naga sun koma?. Wani zuciyar tata tace. "Inaga sabo da tsawar da nayi ne shi yasa. Tafiya ta cigaba da yi inda a karshe ta hangi wani baƙin kofa wanda ba'a ganin ƙarshen ta sabo da girma da tsayin da ta ke dashi. Murmushin jin daɗi tayi tace. "Babu makawa wannan ita ce hanyar da zanbi domin barin wannan dajin. Batareda wani tunani bah ta nufi wajan kofar da sauri. Babu zato taji kifiyoyi na fitowa ta koh ina. Da sauri ta kwanta ƙasa, yayinda gaban ta ya tsananta faɗuwa. Cigaba da harbo kifyoyin🏹 aka yi babu kagautawa. Ganin abun bana ƙare wa bane ya sata miƙewa da sauri. Da mugun gudu ta nufi kofar da take tunanin ita ce hanyar futa. Cikin sa'a ta isa baƙin kofan batare da ta bari koh da ɗaya daga cikin kifiyan ya cake ta ba. Hajiyan zuciya ta shiga sauke wa. Saurin Daga kanta tayi tare da dora wa akan wannan kofan. Rubutu taga anyi a jiki wanda ita kanta ba tasan me aka rubuta bah. Sannan wannan kofar ba za ta taɓa bude wa bah batare da anyi kalmomin bada izinin wucewa bah. Riƙe kanta tayi alamin tana yin nazarin wani abu, da sauri ta ɗago sannan tace. "Maza buɗe". Shiru taji, taga kofa bai buɗe bah, cikin daƙewa ta cigaba da jarraba sa'ar ta,amma ina,koh gizau kofar batayi bah. Soma gajiya Dua tayi, yayinda take ganin cewa nan zata karashe rayuwar ta. Maganganun aljanun dazu ne ya fara i mata yawo a kwakwal wa. "Halitta ɗaya ce a duniyar nan zata iya bin ta wannan kogin kuma wannan halittar itace sarauniyar macizai, idan har ke ɗin ce da gaske toh zaki bi wajan nan batare da wani abu na cutar wa ya tunkari inda kike bah". Buɗe idanuwan ta tayi, sannan ta miƙar da hannun ta tare da ɗora wa akan kofar tace. "A matsayina na shugaba da kuma sarauniya na macizai da sauran halittun boye, ina bukatar wannan kofar ta buɗe yanzu kamar yadda na buƙata". Cikin kankanin lokaci kofar ta fara girgiza, hatake shima wannan dajin ya soma girgiza, faɗuwa Dua tayi ƙasa yayinda ganyayya kin hannun ta suka soma zube wa. Saurin miƙewa tayi ta kara faɗin. "Idan har niɗin ce da gaske shugabar ka, ina so ka buɗe min hanya yanzu". a hankali kofar ta fara wangale, daga karshe kofar ta buɗe gaba ɗaya. Farin ciki ne gaba ɗaya ya bayyana kan fuskarta, cike da farin ciki ta sanya kafar ta na dama tare da shi cewa cikin kofar. Shigar ta keda wuya kofar ta rufe kanta. Dua bata ganta a koh ina bah sai a cikin fadar Mai gari. Miƙewa tayi da sauri ta fara kwallah kiran Inna wuro. Ba zato bah tsammani suka jiyo muryar ta, waigawa suka yi da sauri, hatake suka ɗora idanuwan su akan ta tana riƙe da magunguna. A lokacin bah Dua suka gani bah, gobe mai haske suka gani a tattare da ita. Da gudu ta nufi wajan Inna wuro tare da rungume ta sannan ta ɗago kai ta kalle ta tace. "Dama na faɗa muku cewa zan shiga kuma na fito lafiya batareea wani abu na cutar wa ya tunkari inda nake bah, yanzu dai kun tabbatar da cewa zan iya kare kaina batare da taimakon kowa bah koh ". Kallon ta Mai gari yayi yace. "Babu wani ɗan adam da ya taɓa shiga wannan dajin ya fito a raye bah, amma ke kin shiga kuma kin tsinko magunguna sannan kuma kin fito bstareda kinji koda kwarzane bah ". "Tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari game da ke, yanzu na yarda keɗin jaruma ce, kije na baki dama kije birni domin yin karatu kamar yadda kika bukata". Kuma sannan zamu haɗa kuɗi baƙi ɗaya mu biya miki kuɗin da zaki je birni. Domin a yau ɗin nan kin sanya fuskar kowa murmushi, sannan ki mamaye zuciyoyin mu da farin ciki". Maza kije ki shirya kayan ki domin yau ɗin nan zaki je birni karatu. Tsalle Dua ta daka tare da faɗin na gode sosai Mai gari, yanzu zanje na haɗa kayana, sai wani yayi min jagora ya kaini baƙin hanyar fita daga wannan ƙauyen". Tana kaiwa nan ta shige cikin gidan su. *KANO STATE BIRNIN TARAYYA* Ƙerarriyar mota na hango kirar Mercedes Benz ta shiga makarantar Northwest university da gudu, inda gaba ɗaya dalibai idonsu akan wannan motar. Tabbas sun san da cewa mutum ɗaya ne yake gudu kamar ana gasan tseren mota a wannan makaranta. Gaba ɗaya ya zamana ya cika makarantar da ƙura. Tsayuwa motar tayi . Lokaci ɗaya naga an buɗe kofan motan . Ganin wanda ke cikin motar yasa gaba ɗaya dalibai Jan jini jikin su. Sanin cewa tabbas president ɗin ɗalibai na makaranta ne wato Ahmad Yasir Bello, yasa gaba ɗaya nufan inda yake sannan suka fara kwasan gaisuwa. Kafa naga an fito dashi, wanda ke sanye da canvas blue, daga bisani ya fito daga cikin motar. dukkan yabo su tabbata ga ubangiji Wanda yayi wannan kyakyyawar halitar. Fari ne amma farin sa irin yan black Americans ne. Fuskar sa a murtuke kamar bai taɓa dariya ba. Yayinda yake ɗauke da madaidaicin hanci da baki wanda ke pink colour. Sanye yake da jeans din wando blue sai t shirt fari da facing cap blue. Wannan kaya ba karamin kyau yayi wa Ahmard bah, wanda ɗalibai ke masa lakabi da A.y the school president. Cikin lion voice ɗin sa yace. "Maza kowa ya ɓace daga nan, sannan bana son naga kowa ya wuce wani guri in bah department ɗin sa bah, understood?". Yes gaba ɗaya suka furta,cikin kankanin lokaci kowa ya nufi class ɗinsa, duda cewar ba kowane class ne suke da lecture yanzu bah, amma saida kowa ya shiga sabo da sanin halin Ahmard baya raga wa kowa. Wani mature guy na hango yana nufo inda Ahmad yaƙe. Karasa wa inda Ahmad ke tsaye yake tare da sakar masa murmushi yace. "Our president, kana aiki da kyau, chab wannan da kana shigowa makaranta jikin kowa zai fara kakkarwa kamar sunga mala'ikan mutuwa". "Gaskiya ya kama ta ka rage wannan abu da kake yi gaba ɗaya abin da kake yi is not fair". Haɗe rai Ahmad ya ƙara yi tare da kara murtuke fuska sannan yace dashi. " waya baka izinin fitowa daga class Abdul?. Kallon sa Abdul yayi, lokaci ɗaya ya ƙyalkyale da dariya, saida yayi mai isarsa sannan yace. "Nima da nake abokin ka baka barni bah, lallai kamm Ahmad wuyan ka ya isa yanka, amma ina fatan wata rana wata ta saukar maka da wannnan jiki dakai da kuma taurin kai. Murmushi gefen baki Ahmad yayi yace. "Babu ita, kuma ba zata taɓa bayyana bah, banga wacce ta isa ta saukar min da izza ta bah". Kallon sa Abdul yayi sannan yace. "Idan kuwa Allah ya bayyana ta fah? Maida kallon sa kan Abdul Ahmad yayi sannan yace. "Duk ranar da Allah ya bayyana ta, sannan kuma naja taja magana ta ba tare da tsoro kan fuskarta bah, ni kuma nayi maka alƙawarin cewa daga ranar, duk abinda kace nayi ni kuma saina yi. Wannan alkawari na ne ". *TOH FAN'S MEYE RA'AYIN KU GAME DA AHMARD, SHIN DUA ZATA ZO BIRNIN NE KOH A'a. TABBAS AKWAI KALLO GABA*. COMMENTS & SHARE PLEASE 🙏🙏🙏 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar🪙 Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 FREE PAGE 1️⃣0️⃣➡️1️⃣1️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) *_______________________________* "Uhmm Ahmard kenen sarkin rigima, toh shikenen ni kuma nace maka wannan ranar saita zo, kaje ka rubuta zaka ce na faɗa maka". "Ni abin da ma yasa kaga na fito daga class bah komai ba ne, illa kiran ka da Uncle Sharif ya ce nayi". "Mene ne mutumin nan yaƙe buƙata ne? Na faɗa masa cewa bana son takura a rayuwata, yanzu ina zuwa gaba ɗaya zai cikani da warin baki". Dariya Abdul yayi sannan yace dashi. "wallahi Ahmad kana da wuyar sha'ani, yanzu malamin naka kake wa wannan cin fuskar? Gaskiya kana buƙatar a saita ka ". Fuskar Ahmad ne ya sauya daga walwala zuwa ɓacin rai, sannan ya kalli Abdul yace. "Go back to your class Abdul". Ya faɗa tare da kauda kai gefe. "Shike nen ai zan tafi, ni na isa naja da maganar ka, kaga tafiya ta ma". Ya karashe maganar tare da barin harabar wajan. Ganin akan da Ahmad yayi yasa shima ya nufi office din Uncle Sharif. Ɓangaren Du'a kuwa, saida ta shirya tsaff ta haɗa gaba ɗaya kayan ta masu kyau sannan ta saka su a cikin jakar ta na saƙa, ta cinciɓe ta sannan ta fito da ita harabar ƙauyen. Ɗaukar wayar sa Mai gari yayi tare da kiran ƙanwar sa Sakina, sannan yayi mata bayanin zuwan da Du'a zata yi gidan ta. "Allah ya kawo ta lafiya kawai Sakina ta faɗa". Sallama Mai gari yayi mata daga bisani ya katse wayar. Kallon Du'a yayi sannan ya mai da kallon sa ga maza biyu dake tsaye yace dasu. "Kune nake so ku raka Du'a har gidan Sakina sabo da kune ƙaƙƙarfan maza a wannan ƙauye, kuma inada tabbacin za ku ƙare ta ". "In sha Allahu mah zamu kare ta duda cewar Allah ne mai karewa, amma muma zamu yi iya bakin ƙoƙarin mu wajan ganin babu wani abu na cutar wa ya nufi inda ta ke bah". Cewar ɗaya daga cikin mazan. Miƙa wa Du'a kuɗaɗe dake hannun sa Mai gari yayi, Du'a ta karɓa, tana mai cewa. "Ina matuƙar godiya da bani damar zuwa birni, kuma nayi muku alƙawari bazan taɓa baku kunya bah, baza ku taɓa dana sanin bari na da kuka yi naje birni bah". "In sha Allahu abin da ya kaini chan shi zan yi, kuma na gode da kulawar ku a gare ni ". Ta karashe maganar tare da nufa inda Inna wuro ta ke, durkusawa tayi sannan tace."inna ina son ki saka min albarka, sannan kiyi min addu'a Allah ya bani abin da naje nema ". Murmushi Inna wuro tayi tace. "Allah ya yi miki albarka ƴata, ya baki nasaran cim ma burin ki na alhkairy, yasa ki gane duk abin da aka koyar dake ". "Ameen" Du'a ta amsa. Hajiyan zuciya Inna wuro ta sauke sannan tace. "Amma wani hanzari bah gudu bah, ina so kiyi min alƙawarin cewa zaki dawo gida kafin ki cika shekaru ashirin ciff a duniya". Murmushi Du'a ta sakar mata tare da mai kallon ta kan Inna wuro tace. "Karki damu Inna in sha Allahu zan dawo kafin na cika shekaru ashirin a duniya, ai naji kuna faɗa a tsakanin ku cewa idan na cika shekaru ashirin a duniya, wani abu zai bayyana a jikina, kuma sannan rayuwata zai kasance a koda yaushe cikin hatsari ne". "Yanzu inada shekaru sha tara ne a duniya, nasan za'a yi mana hutu a makaranta kafin na cika shekaru ashirin". "Dan aka duk ku kwantar da hankulan ku baki ɗaya". Tana kaiwa nan ta cinciɓi jakarta tareda ɗora wa akan a malanke na saniya, wanda mai gari ya tanadar musamman dan suje bakin ƙauyen. Saida gaba dayansu suka hau sannan dokin ya soma tafiya, lokaci daya fuskar Du'a ya sauya daga walwala zuwa damuwa. Saurin dakatar da su tayi da faɗin. "Ku tsaya". Tsayar da a malanke ɗin suka yi tare da mai da kallon su kanta. Da sauri ta sauka daga kan amalanken sannan ta nufi cikin gida da gudu. Kai tsaye ɗaƙin magani da mahaifiyarta ta ke ta nufa. Shiga ɗaƙin tayi, sannan ta durkusa kan gwiwowin ta tace. "Mama inason ki saka min albarka, nima yanzu zan zama yar birni zan je birni karatun likitanci sannan na samo miki sunan maganin da zata farfado dake kinji". "Ina so kiyi min fatan nasara". Share hawayen ta tayi da bayan hannunta sannan ta kara da cewa. "Shike nen na tafi kuma zan so ace kafin na dawo ki farfaɗo daga wannan baccin da kike". Sannan ta ƙara da cewa. "Ya Allah ka kiyaye min mahaifiyata, kasa mata nutsuwa da kwanciyar hankali, duk wani cuta koh damuwa ka yaye mata su, ameen ya rabbil izzati". Tana kaiwa nan ta fice daga ɗaƙin tare da ficewa daga gidan ta nufi inda amalanken yake sannan ta shige ciki tare da ɗaura mayafi a fuskarta, saida ta tabbatar ba'a ganin komai na fuskarta in banda kwayar idanun ta, sannan ta yi wasu Inna sallama. Abinci kala_kala mutanen kauyen suka saka musu ganin cewar za suyi kwanaki a hanya batare da sun samu abin taɓa wa bah. Addu'a inna wuro tayi musu tare da mata fatan sauka lafiya. Sai da suka yi wa kowa sallama daga bisani suka ja amalanken suka bar harabar kauyen. Tafiya mai nisa suka yi sannan daga nan suka isa wani garin, saida suka yi kwanaki biyar a hanya kafin daga bisani suka hangi wata siririyar hanya, babu bata lokaci suka fara bin hanyar. Tafiya suke batare da wani ya kula ɗan uwansa bah, babu zato suka ji an rufa su da raga yayinda gaba dayansu suka shige cikin ragar tare da yin sama. Hatake gaba dayansu suka kwashe da dariya gami da faɗin. "Babu wanda yake bin hanyar nan ya tafi lafiya, wannan yankin mu ne babu wanda muka bawa umarnin bin wannan hanyar". Kokarin cire kanta Du'a take daga jikin ragar, amma ina akan ya cutura. Kallon su tayi a fusa ce tace. "Kune waɗan nan yan dajin masu karɓar haraji Koh?". Ƙeƙeta dariya gaba ɗaya suka yi!. Sannan daya daga cikin su yace. "Kamar naso na gane wannan muryar taki, su waɗan nan mazan da suke mara miki baya basu faɗa miki mu yan daji bane?". "Maza_maza ku kunce mu kafin raina ya ɓaci". Ta ƙarashe maganar tareda kokarin kunce kanta. "Ba za'a kunce bah mene ne za kiyi? Kin san mu su waye kuwa?, koh an gaya miki cewa bamu san abin da muke bane, mu ɗin jarumai ne na farko kin gane". "Banzaye matsorata idan har ku ɗin da gaske jarumai ne, toh ku kunce mu mana". Giegiza kai gaba ɗaya suka yi, yayinda ɗaya daga cikin su ya ɗauki wuƙa sannan ya yanka ragar, hatake gaba ɗaya suka faffaɗo daga cikin ragar. Tashi su ukun suka yi yayinda Du'a ta karkaɗa jikin ta, sannan sannu a hankali ta fara cire mayafin dake kan fuskarta, inda daga ƙarshe tayi nasaran cire shi baki ɗaya. Washe haƙora gaba ɗaya suka yi ganin yadda ta ke da matuƙar kyau na halitta. Murmushi ta sakar musu tace. "Yanzu zaku barmu mu tafi ɗin ne koh a'a?". "Sabo da me bazamu bari ki tafi bah?, mu asuwa? Ai mu bayin mata ne dan aka sai yadda kuka ce damu ". "Yauwa koh ku fa". tana kaiwa nan ta hau kan amalanken, yayinda suma mazan suka hau, a sauka lafiya yan jejin suka yi musu yayinda suka buɗe musu hanya suka tafi. Daga nesa Du'a ta hango wucewar motoci, zuru _zuru tayi da idanuwan ta ganin abinda bata saba gani bah a kauyen su. Tsayar da amalanken suka yi sannan ɗaya daga cikin su ya kalli Du'a yace."zamu dakstar da amalanken a nan sabo da ba zai yu mu tafi akan amalanke bah, motoci ne kawai ke wucewa". "Mene ne kuma motoci?" Du'a ta tambaya. Dariya gaba ɗaya suka yi sannan suka ce da ita. "Mota tans nufin abin da mutane ke hawa domin suje duk inda ransu yake so batare da sun taka da kafafin su bah ". "Auu! Kenen shi ne mota. lallai gaskiya yan birni suna jin daɗi, babu ruwan su da shan wahala saidai kawai abin ya ɗauke su babu ruwan su da takawa". Tafiya suka farayi daga bisani suka isa bakin titin. Tarar da adaidaita suka yi tare da yiwa mai napep kwatancen inda zai kai su. Shiga ciki suka yi yayinda Du'a ta tsaya tayi zuru_ zuru da idanuwa. Kallon ta suka yi suka ce da ita. "Ki shigo mana mu tafi kinga shima sauri yake, kuma inda muke ɗin nan komai zai iya faruwa". Girgiza kai Du'a ta yi tace. "Ni bazan shiga bah, tsoro nake ji gaskiya, na fasa zuwa birnin mah kawai mu koma kauyen mu". Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka. "Kamar ya mu koma ƙauye bayan mun riga mun zo birni cewar ɗaya daga cikin su, sannan ya kara da cewa. " Wallahi idan baki shigo bah akwai yan mafiya masu shan jini kuma hanan suke da zama, suna hango ki za su cinye ki, kuma gaki fara dama kuma farare suke ci". Jin aka yasa cikin Du'a ya duri ruwa, babu shiri tayi saurin shige wa cikin adaidaitan. Daga bisani mai napep yaja adaidaita yayi gaba. Kai tsaye medile aka nufa dasu, inda gefe guda Du'a ta saki baki sai kallon gidaje ta ke tana daɗa jinjina kai, taɓa ɗaya daga cikin su tayi tare da nuna gidajen tace. "Su kuma waɗan nan mene ne su? Na gansu kamar dodo". Dariya mai napep ya fashe dashi yace."gaskiya baiwar Allah kina da ban dariya, yanzu sabida Allah da Annabi gidajen ne kamar dodo, koh da yake abin ka da yar ƙauye ba lallai kisani bah ". "Toh waɗan nan gidaje ne wanda mutane ke rayuwa a ciki, dan aka ki daina ƙauyanci kada ayi miki dariya, kema da kaɗan_kaɗan zaki saba ". "kana nufin house?". Du'a ta faɗa tareda kauda kai gefe. Zaro idanu mai napep yayi yace. "Abin mamaki yar ƙauye da jin turanci, kenen kuna da makaranta achan ƙauye kenen". "Kwarai kuwa". Du'a ta faɗa. Gaskiya ne amma makarantar tana da tsada har kika san mene ne house ai kin more wallahi". Cewar mai napep. "Eh mana amma ni a cikin gida aka koyar dani". Sosai Du'a ke hira da mai adaidaita tamkar sun san juna a da. Saida suka isa bakin wani gida sannan adaidaitar ta tsagaita da tafiya tare da tsayar da napep ɗin. Fitowa suka yi daga cikin napep ɗin tare da biyan mai napep ɗin kuɗin sa. Karɓa yayi tare da yi musu godiya sannan yaja nepep ɗin shi ya bar wajan. Ƙwanƙwansa kofa suka soma yi, saida aka ɗau kusan mintuna sha biyar suna tsaye a wajan kafin daga bisani aka buɗe kofa. Sosai hajiya Sakina tayi farin ciki ganin su Du'a tare da yi musu tarɓa mai kyau. Saida su Du'a suka ci suka sha kafin daga bisani suka tashi tare da ɗauro alwala suka tada jam'i suka yi sallah tare da rama sallolin da ake binsu. Bayan sun idar da sallah mutanen Mai gari suka tashi da zimmar tafiya. Haƙuri Hajiya Sakina ta shiga basu da cewa su kwana in yaso gobe sai su koma. Amma ina suka ce mata yau suke son komawa. Ba yadda hajiya Sakina ta iya, aka tana ji tana gani suka fice daga gidan tare da tafiya. Ɗaukar ghana must go ɗin Du'a hajiya Sakina tayi tare da saka su a cikin mota ta maida kallon ta kan Du'a tace. " Masha Allah gaskiya Allah ya azurta ki da kyau, keɗin karshe ce kuma maƙura a kyau. Na tabbata maza rububin ki za su dinga yin". Murmushi kawai Du'a ta yi tace. "Na gode sosai mama". "Yauwa muje na kaiki makarantar koh domin nayi miki registration, Allah dai yasa su baki admission domin shi ne the most important thing, yanzu aka mah ƴata tana chan amma a hostel take zama, dan aka kema a hostel zaki dinga zama ". "Dan idan kika ce zaki zauna dani a nan zan gundureki ne, dan aka bana son ki takura". Tana idda magana ta shige motar sannan ta buɗe kofa yan zaman banza tace da Du'a ta shigo. Ganin Du'a bata motsa daga inda take bah yasa ta faɗin. "Du'a lafiya? Me yasa kika tsaya kuma?". Amsa Du'a ta bata da faɗin. "Ina jin tsoro nee ". Murmushi hajiya Sakina tayi tace. "Kada ki samu damuwa ki kwantar da hankalin ki babu abin da zai faru shigo mu tafi kinji ". Shiga cikin motar Du'a ta yi bsyareda ranta yaso akan bah. Tada mota hajiya Sakina tayi daga bisani ta bar harabar gudanar. Kai tsaye makarantar Northwest university ta nufa ba tare da jinkiri bah. Saida suka dau lokaci kafin su isa makarantar. Baki sake Du'a ke kallon shige da fice na daliban makarantar. Parking space direct hajiya Sakina ta nufa tare da tsayar da mota. Sannan ta cire makullin mota ta maida kallon ta kan Du'a tace. "Du'a ki zauna hanan zan je na dawo yanzu kinji". Girgiza mata kai kawai Du'a ta yi. Hajiya Sakina na kaiwa nan ta fice daga motan tare da barin Du'a kaɗai a cikin motan. Kamar kullum yauma shigowa yayi da ƙerarriyar motarsa yayinda yake gudu tamkar yana tseren mota. Gaba ɗaya ɗalibai na ganin sa kowa ya nufi department ɗinsa da sauri, yayinda mata suka fara gyare-gyare don su birge sa. Kai tsaye parking space ya nufa, ganin hanyi parking a inda ya saba ajiye motarsa yasa mamaki ya kama shi. Tabbas yasan da cewa babu wani ma'aluƙi daya isa yin parking a inda yake ajiye mota a makarantar nan. Fitowa ya yi cike da ɓacin rai ya nufi inda motar da Du'a ke ciki. COMMENTS & SHARE🙏🙏🙏 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B (Zinariyar Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 FREE PAGE ️1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) *_______________________________* Kai tsaye inda motar ta ke ya nufa, babu bata lokaci ya fara bubbuga glass ɗin motan. Du'a dake cikin mota taji hana bubbuga mota yasa tayi zaton koh hajiya Sakina ce, batare da wani tunani bah ta buɗe kofar motar. Zololo taga mutum a tsaye a kanta, tun da ga kasa har sama ta bishi da kallo sannan ta dora dara-daran idanuwan ta akan nasa. Babu zato yaji gaban shi ya yi mummunar faɗuwa, a yayinda hannunsa ya fara karkarwa. Damƙe hannunsa ya yi, tare da cije leɓen sa sannan ya watsa mata wani banza kallo cikin lion voice ɗin sa yace. "Waya baku izinin parking a nan wajan?, shin bakusan da cewa bayanni Ahmard babu wanda yake parking a wajan nan?, toh maza_maza ki ɗauke a kori kura nan. kafin na ɗauki tsatsaurar hukunci akanki". Murmushi Du'a ta yi tare da mai da kallon ta kan sa tace. "Malam nidai da muka zo wajan nan banga an rubuta cewa kai kaɗai ne aka bawa umarnin ya ajiye mota bah, sannan ai guri na kowa ne, dan aka saimun gadama zamu ɗauke motar mu daga wajan nan, kaji dai na fada maka". Ta ƙarashe maganar tare da jan dogon tsaki. Mamaki ne ya yi marukar kama Ahmard, yayinda yake ji kamar bashi bane Ahmard bah. Cikin ɓacin rai yace da ita. "Kin san waye ni?". Ya faɗa tare da nuna kansa. Dariya Du'a ta sakar masa sannan tace dashi. "Kwarai mah kuwa nayi maka farin sani, nasan waye kai sosai mah, kaiɗin mutum ne mana kamar kowa ɗan birni mai ji da kuɗin haram". Babu zato taji saukar mari a fuskarta, hatake jama'a da ɗaliban makaranta suka fara taruwa. Dafe kuncin ta tayi yayinda take jin zuciyarta na tafarfasa.Cikin huci ya kalle ta tareda nuna ta da ɗan yatsa yace. Har ke wacece da zaki faɗi aka akaina?, kina yar ƙauye kuma yar talakawa kike gaya min magana son ranki, toh wallahi ba'a ja dani ', ki kiyayi fushi na, idan kika ce zaki shiga gona ta a makarantar nan baza ki taba samun kwanciyar hankali bah, zaki sha bakar wahala ne, kuma yanzu aka fara wallahi zaman ki a wannan makarantar saina saka ya gundureki, saina saki kinji kamar ki bar duniya, muzuba mu gani". Yana kaiwa nan ya juya da zimmar tafiya, daga sama yaji tace. "Dakata". Tsaya wa ya yi batare da ya motsa koda yatsar sa bah. Takawa ta fara yi har ta isa gaban sa. Ɗora idanuwan ta tayi akan sa sannan tace. "Kwarai kuwa nida kai ɗin mu zone daga duniya biyu mabanbanta, ni yar kauye ce kai kuma ɗan birni". "Kace na kiyaye kada na shiga gonar ka Koh?, toh idan na shiga me zaka yi, wato kai kana jin kai wani ne koh, toh kasani duk zuciyarka ba zata taɓa kai tawa bah, domin mu idan aka taɓo mu bamua ragawa dan aka na riga na shigo makarantar nan, kuma babu wani ma'aluƙi daya isa ya hanani sukuni a makarantar nan, idan kuwa mutum ya kwatanta yin aka, toh ya jira yaga abin da zan yi masa ". Tana kaiwa nan ta koma jikin mota tareda shige wa ciki. Idan ran Ahmad ya kai dubu toh ya baci, tun da uwar shi ta haife shi babu wanda ya taɓa faɗa masa magana kamar aka. Girgiza kai kawai ya yi yayinda idanuwan sa suka kaɗa suka yi jajir. Kallon ɗaliban makaranta yayi, Kamar haɗin baki gaba ɗaya suka bar wajan. Hajiya Sakina da yarta Maryam ne suka fara nufa inda motar su yake, yayinda Maryam ta shiga yin mamaki ganin motar su a inda Ahmad yake parking motarsa. buɗe kofar mota hajiya Sakina tayi, tare da dora idanuwan ta kan Du'a. Murmushi tayi tana mai cewa. "Maryam ga yar uwar ki Du'a kuma ina fatan zaki ɗauke ta ramkar yar uwa a gare ki". Murmushi Maryam tayi tace. "Kuma gata kyakyawa tabarakalla, in sha Allahu umma zan riƙe ta tamkar yar uwa kuma kawa, bazan taɓa barin wani ya cutar da ita a makarantar nan bah". ganin gaba ɗaya ran Du'a a ɓace yasa Hajiya Sakina ta ce. "Du'a lafiya naga ranki a ɓace?, me aka yi muku? Koh makarantar ba tayi miki bah?. Tamƙe fuska Du'a ta yi tace. "Wallahi wani banza ba'amage ne yazo wajan nan wai shi sunan sa Ahmad, dan kawai kin hajiye motar ki shi ne wai waya bamu izinin faka mota a nan wajan, da yake ubansa ne ya gina makarantar". "Nashi ga uku!". Suka ji Maryam ta faɗa. Sannan ta kara da faɗin. "Tabbas kin aikata babban kuskure Du'a, kin san waye shi kuwa? Shi ne fa shugaban ɗalibai na makarantar nan, Gaba ɗaya ɗaliban makarantar nan sha yin sa suke, hatta ƴan cultism na makarantar nan da malamai tsoron sa suke. Me yasa bakiyi shiru bah sanda yake magana?". "Wallahi na tabbata ba zai kyale ki bah, saiya muzguna miki harkiji makarantar nan ya fara gunduranki, mata da dama sabo da shi suka bar wannan makarantar domin ba za su iya jure wulakancin da yake musu bah". Bin Maryam Du'a tayi da kallo tace."wallahi bai isa yasa wannan makarantar ta gundureni bah, bai isa ya koreni daga makarantar nan bah, shi ɗin banza shi ɗin wofi, wallahi dana san aka birni yake da ban wahalar da kaina nazo bah". "Kuma yanzu tun da na shigo na shigo kenen babu fita saidai wani ikon Allah Wallahi". Ajiyan zuciya hajiya Sakina ta sauke tace. "A'a Du'a wannan duniyar da kike gani karama ce, kuma duniya makaranta ce fah, rayuwar nan bata da tabbas". "Kada kice dan yayi miki ba dai-dai bah kice saikin dau fansa koh akasarin akan, kamar yadda Maryam ta faɗa kuje yanzu ki bashi haƙuri, sabo da ki zauna cikin salama a makarantar nan, bana so ace daga zuwan ki kina faɗa kunshi?'". "Akan me zan bashi haƙuri, shin dukan sa nayi koh me?, shin ubansa na zaga koh mamarsa, taya za'a ce mace ce zata je ta bawa namiji haƙuri bayan kuma shi ne da laifi ". "Dana bashi haƙuri na gwammace na haƙura da karatun". Du'a ta ƙarashe maganar tareda kauda kanta gefe. Murmushi hajiya Sakina tayi tace. "Wallahi Du'a da a ƴar sarakuna kika fito da anga izza, daga gani ba zaki so raini bah". "Koma dai mene ne ki same shi ki bashi haƙuri, dan bakisan me zai iya aikata bah, kada kice zakiyi sa'insa da ɗa namiji domin akan ba abu bane mai kyau". Yanzu dai ki tashi ki Maryam ta tayaki ɗaukar kayanki, saiku tafi hostel, dan yanzu na gama yi miki komai, inda department ɗin ki yake ne bansani bah ". Ɗaukar ɗaya daga cikin jakarta Du'a ta yi, yayinda Maryam ta daukar mata ɗayan jakan. "Yauwa Maryam na tura miki wasu ƴan kuɗaɗe wanda zai isheku yin duk abin da kuke so kafin month ya kare,kuma sannan inason ki siyawa Du'a duk abin da ta ke buƙata Please and please ". "In sha Allah umma zan siya mata duk abin da take so kamar yadda kika buƙata ". "Toh shi kenen Allah ubangiji ya yi wa rayuwar ku albarka, Allah yasa Du'a ki fara makarantar nan a sa'a, ki samu ki taimakawa ƴan ƙauyen ku da ilimin ki ". "Ameen" gaba ɗaya suka furta, daga bisani suka nufi hanyar hostel. Saida hajiya Sakina ta tabbatar dasun tafi sannan ta tayar da mota tabar harabar makarantar. Tun da suka fara tafiya Du'a ke kalle_kalle, yayinda maza da mata na makarantar suka bita da kallo ganin irin tsananin kyau da Allah ya bata. Babu zato suka ga an sha gabansu. Gaba ɗaya su ukun babu wacce shigarta yayi kama da ƴa musulma bah, a yayinda baƙin kowannen su ke ɗauke da ke cewgum, yadda suke tauna cewgum ɗin kai ka ɗauka karuwai ne. Rai a ɓace Du'a ta kalle su ukun tace. "Mene aka zaku zo ku wani sha gaban mu, ku matsa zamu wuce dan Allah". Wacce ke gaba a cikin su ukun ce ta matso daff da su Du'a, da alama ita ce shugabar su. Kallon Du'a tayi a kaskance tare da hura mata iskar baƙin ta a fuska sannan ta saki wani murmushin mugunta tare da nuna ta da ɗan yatsa tace. "Kada ki kuskure ki shiga gonar da ba ta ki bah, idan kuwa kika ce zaki shiga gonar da ba taki bah toh wallahi ba zaki taɓa jin daɗin abin da zai biyo baya bah. Ahmad na ni Jennifer kaɗai ne, babu wacce ta isa ta faɗa masa magana mara daɗi na kyale ta, idan har ƴar talakawa zata ji kanta tamkar wata, Toh mu kuma yan masu kuɗi fah?". Murmushi Du'a tayi tace. "Kafin komai maza_maza sauke wannan kazamin hannun nan naki, kafin raina ya ɓaci". Rai a matuƙar ɓace Jennifer tace. "What will you do idan ban ajiye hannun nawa bah? Eh nace me zaki yi idan ban ajiye hannu na bah ". Ganin abin nasu bana zuba wa ido bane yasa Maryam ta fara jan Du'a. Wafce hannunta Du'a tayi daga na Maryam tace. "Martam ki rabu dani, bana son ki shiga wannan maganar". Maida kallon ta Du'a tayi kan Jennifer ta ce. "Babu abin da zan yi miki, amma kisani idan baki ɗauke hannunki bah, jikin ki ne zai gaya miki ". Ɗariyar mugunta Jennifer ta sakar wa Du'a sannan ta ce. "Toh barana yi mai gaba ɗaya saina ga mene ne zaki iya yi". Tana kaiwa nan ta saka hannunta na dama tsreda dungure wa Du'a kai. Hatake Du'a ta saki wani irin razannaniyar ƙara! Wanda yasa gaba ɗaya ɗalibai da malamai fitowa daga aji. Jikin Du'a ne ya fara kakkarwa, yayinda haƙoranta na sama da kasa na dukan juna, take idanuwan ta suka kara rinewa suka yi arsh sosai, yayinda ta zaro gaba ɗaya idanuwan ta tamkar za su fito waje. Saurin ja da baya jennifer da sauran wanda suke mara mata baya suka yi, yayinda tsoron Du'a fal ya cika zuciyoyin su. A hassale Du'a tayi kan Jennifer tare da shaƙe mata wuya. Hatake daya daga cikin ɗaliban makarantar ta kwallah ƙara! Yayinda ta faɗi ta fara birgima a kasa, tare da kanka kwashe kasusuwan ta. Juyawa Du'a tayi ta sauke idonta akan wannan ɗalibar. Sakin Jennifer tayi, yayinda Jennifer ta fara tari. Babu bata lokaci Du'a ta nufi inda ɗalibar ta ke wacce aljanun ta suka tashi. Hatare suka haɗa ido da dalibar, saurin ja da baya ɗalibar tayi tare da haɗe hannayen ta guri guda baki na rawa tace. "Dan Allah kada ki kashe ni zan fita, nayi miki alƙawarin zan fita bazan sake shiga jikin ta bah, bana so ki karaso inda nake". Ta faɗa tana daɗa jada baya. Mamaki lulluɓe a fuskar Du'a ta ce." Mene kike faɗa ne aka? me ya same ki? Ni bana cutarwa kuma sannan Ni mutum ce kamar kowa, meyasa kuma zaki ji tsoro na?. "Karya kike ke ba mutum bace, babu abin da kika sani sai shiƙa, kece nan bazan taɓa manta wannan fuskar taki bah". @@@@@@@@@@@@@@@@@@@ *TUNATAR WA......, Free page dai ya kusan kare wa, fan's a fara tara kuɗi don biyan kuɗin wannan littafin Naira ₦400 complt babu tsada, ki siya ki mori karatun ki cikin kwanciyar hankali*. COMMENT & SHARE PLS 🙏🙏🙏 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B (Zinariyar🪙 Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 FREE PAGE ️1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) *_______________________________* "Nifa ban fahimci abin da kike magana akai bah" cewar Du'a. A ta ke budurwar ta faɗi ƙasa sumammiya. Ganin akan da Maryam ta yi ya sa ta saurin jan hannun Du'a sannan ta nufi hostel da ita. Barin su keda wuya Ahmad ya kalli ɗaliban ya ce. "Me kuka tsaya kallo? Kafin na irga uku gaba ɗaya ku ɓace min daga gani, koh ba ku san da cewa kuna da aji bane?". Kamar haɗin baki gaba ɗaya ɗaliban suka bar wajan, a yayin da suka cinciɓi wacce ta tada aljanu. Ganin gaba ɗaya sun wuce classes ɗin su ya sashi shima barin wajan. "Me yasa kika janyo ni nan Maryam?, ina da tambayoyi wanda nake so wacce ta tayar da aljanu ta amsa min, gaskiya banji daɗin abin da kika yi bah samm". Cewar Du'a. "Aba Du'a ke baki ga shugaban ɗalibai na makarantar nan ya zo wajan bah? Na san idan ban riƙe ki mun tafi bah komai zai iya faruwa. sabo da kin ruga da kin ɓata masa rai tun farko, muda muke so mu ba shi haƙuri kuma kije ki kara aikata wani abin da zai sa ya kara tsanar ki". Murmushin takaici Du'a ta saki sannan ta kalli Maryam ta ce. "Wallahi kina ban mamaki, wai shin wannan shugaban ɗalibai mala'ika ne Koh me? Me yasa a koda yaushe baki da wata magana sai nasa. Ni na *TUNATAR WA......, Free page dai ya kusan kare wa, fan's a fara tara kuɗi don biyan kuɗin wannan littafin Naira ₦400 complt babu tsada, ki siya ki mori karatun ki cikin kwanciyar hankali*. gaji da jin wannan maganar". "Allah na tuba dan kawai an bashi shugaban ɗalibai shi ne zai dinga wani jijida kai, toh wallahi duk taurin kansa bai kaini bah, duk wannan izza da yake takama da shi duk saina sauke masa su". "Da na san inda office ɗin principal ɗin makarantar nan ya ke wallahi da saina kaishi ƙara. kawai mu fuskanci abin da ke gabanmu bawai mu tsaya muna tuannin wani mahaluƙi wai shi Ahmad bah". "Shi kenen yanzu dai ki tashi kiyi wanka sannan na ɗora mana girki mu ci mu gabatar da sallah, saina zo na nunnuna miki ɓangare-ɓangare na makarantar nan". Girgiza kai kawai Du'a ta yi sannan ta ce. "Dan Allah na tambaye ki mana?". Kallonta Maryam ta yi tare da faɗin. "Allah ya sa na sani " Du'a ta ce da ita. "Shin ba ki san inda macizai suke bah a makarantar nan dan Allah?". Kallon Du'a maryam ta yi mamaki lulluɓe kan fuskarta ta ce. "Kamar ya bansan inda macizai suke bah?, ban fahimci maganar ki bah, ina so ki ganar dani". Du'a ta ce. "Eh abin da de kika ji na faɗa, nace kinsan inda macizai suke da zama a wannan makarantar?". Wani kallon baki da hankali Maryam ta bi Du'a da shi sannan ta ce. "Kin manta har girki da wanka nake musu. Wato sabo da rainin hankali irin naki kike wani tambaya na nasan inda macizai suke". "Shin ni jinsin su ce da zan san inda suke da zama? Hanya Du'a kalau kike kuwa? Ta ya ya zaki tsare ni ki dinga yi min wannan tamabayar, duk wanda ya jiki ma sai ya ɗauka koh kina da mental problem wallahi". "Aba Maryam, ni fah nasan me yasa nayi miki wannan tamabayar. Su ɗin da kike gani abokai na ne sosai, na shaƙu dasu tun ina ƙaramar yarinya. kuma sannan har yanzu muna abota dasu ". "Abin da ma yasa kika ga na tambaya shi ne, sabo da na fara kewar su ne. Kin san ya nake dasu kuwa? Su kaɗai ne idan ina kuka suke rarrashi na, su suke ɗebe min kewa idan ina cikin kaɗaici". "Basua so su ganni cikin kunci, damuwar su ke sani ɗimuwa, murmushin su kuma ke sani dariya. Idan har ban gansu bah, banajin cewa zan iya bacci yau". "Tabbas kina buƙatar ganin likita Du'a". Cewar Maryam. Sannan ta ƙara da faɗin. "Hanya Du'a bakida shafar aljanu kuwa? Ta ya ya za'a ce mutum yana abota da macizai wanda suke da illa wa lafiyar mu? Ni wallahi kin fara bani tsoro ma, karna je kema macijiya ce". Ɓata rai Du'a ta yi ta ce. "Kada ki ƙara ce min macijiya bana so ". Maryam ta ce. "Toh kema in banda abinki ta ya ya nima bazan yi tunanin koh kema macijiya bace, kin san yadda nake matuƙar tsoron macizai kuwa? Na tsani macizai a rayuwata. Ke bama ni kaɗai bah, kowane ɗan adam a duniya bazai so dabbar da zata cutar da lafiyarsa bah". "Ni dan Allah abar ma wannan maganar, ki tashi muje mu yi abin da zai finshe mu". Cewar Maryam. Miƙe wa Du'a ta yi tsaye ta ce. "Shi kenen kada kiji tsoro in sha Allahu daga yau bazan sake ambatar sunan maciji bah kinji?". "Shi kenen". Kawai Maryam ta furta, daga bisani ta ja hannun Du'a suka fita don neman ruwan da za su gabatar da alwala. "Saina saka ta gane kuskuren ta, tun da har ta sake ta yi sa'insa dani toh saina sa ta gane Allah ɗaya ne. Ba'a min na ƙyale .saina saka wannan makarantar ya gagare ta da zama". "Aba Ahmad this is not fear, bai kamata a ce ka dinga faɗan kalamai marasa daɗi haka bah, koh ba komai duk ƙanƙantar mace uwa ce ". "Kuma sannan kaima mace ce ta kawo ka wannan duni..... Maganar sace ta dakata sakamakon tsawana da Ahmad ya daka masa. Zumbur Ahmad ya miƙe daga kan kujerar da yake tare da nuna Abdul da ɗan yatsarsa sannan ya ce. "Idan har ban gasa magana da kai bah, toh bana so ka saka min baki ". "Dame take takama a wannan garin?, shin kasan maganganu marasa daɗi da ta faɗa min, idan da kana wajan ba zaka tsaya kana faɗa min story bah, kasan cewa na tsani na ja magana a ja ". "Tun da ta ruga ta ta yi musayar yawu dani, toh walwala da farin ciki sun ƙare mata, don saina gallazawa rayuwarta a makarantar nan ". Yana kaiwa nan ya shige cikin mota tare da tada motan sannan ya bar cikin makarantar. Baki sake Abdul ya bishi da kallo, sannan ya ce. "Ahmad ina fatan Allah ya shirye ka idan mai shiryuwa ne". *9: o'clock na dare* Mata wajan kusan biyar zuwa shida na hango kwance akan bonch ɗin kwanciya. Kowacce tanada wajan kwanciyar ta. Gefe guda kuma su Du'a ne kwance akan gado wanda mafi yawanci student ke amfani da shi wajan kwanciya. Gaba ɗaya idanuwan matan ɗaƙin akan Du'a ya ke, duk inda Du'a ta juya sai ta ga suna kallonta.yayin da suke ganin irin tsananin kyau na halitta da Du'a ta ke da shi. Juyarda da kanta Du'a ta yi tare da mai da kallonta kan Maryam ta ce. "Me yasa matan nan suke kallo na ne? Shin na aikata musu wani abu ne?". Murmushi Maryam ta yi sannan ta ce. "Kema in banda abinki ta ya ya ba zasu kalle ki bah, farko kina da kyau, ga gashi har baya, kina da idanuwa da matsakaicin hanci masu ɗaukar hankali, gaba ɗayanki ma baki yi zubin yan Nigeria bah". "Toh faɗa min ta ya ya ba za su kalle ki bah? Nida bani da kyau gashi nan babu ma wanda ta ke kallona sabo da bana gaban ta, kawai ki kwanta kiyi bacci ki daina waɗan nan saƙe-saƙen a ranki". "Na ji shi kenan zan kwanta" cewar Du'a. Sai da Maryam ta rabbatar kowa ya gama uzurin sa sannan ta kai hannunta kan fitila domin kashe hasken ɗaƙin. Ganin aka da Du'a ta yi ya sa ta saurin riƙe hannun Maryam damuwa lulluɓe kan fuskarta. Mai da kallonta Maryam ta yi kan Du'a sannan ta ce. "Mene ne haka kuma Du'a? Me yasa kika riƙe min hannu lokaci ɗaya?". Girgiza kai Du'a ta yi sannan ta ce. "Dan Allah Maryam kada ki kashe fitilan nan, wallahi ina matukar tsoron duhu, idan kika kashe zan iya shiga wani hali wanda ke kanki saikin zo kina da na sani ". "Bana son duhu maryam ki bar wutan a kunne dan Allah". Ɗaya daga cikin yan ɗaƙin ne ta kalli Du'a ta ce. "Aba baiwar Allah, ta ya ya zaki ce kada a kashe hasken wuta. Toh mudai sabo da ke ba zamu iya kwana cikin haske bah gaskiya". "Haka ne Du'a, maganarta gaskiya ne, bai kamata a ce mun kwana cikin haske bah gaskiya, sabo da babu ma kyau kwana da haske, sai dai fa kiyi haƙuri, ki lallaɓa ki kwanta a aka". Maryam ta ƙarashe maganar tare da kashe fitilan ɗaƙin. Cun kushewa waje guda Du'a ta yi yayin da zuciyarta ya tsananta faɗuwa. Ƙaƙƙarwa jikin ta ya soma yi, yayin da haƙoranta na dukan na sama da ƙasa. A ta ke hawaye suka fara zarya akan fuskarta, babu zato ƴan ɗaƙin suka ji ƙaran tsawa da walkiya. Mamaki ne ya kama su sabo da a sanin su dai wannan lokaci bana damuna bane, amma kuma alamu sun nuna kamar za'a yi ruwan sama ne. gurnanin Du'a Maryam ta faraji ƙasa-ƙasa, saurin kunna fitila Maryam ta yi tsreda mai da kallonta kan Du'a. Rass ta ji gabanta ya faɗi! Cikin tashin hankali ta nufi inda Du'a ta ke ganin yadda gaba ɗaya ta rikice numfashinta na neman sarƙewa. Tashi suma sauran ƴan ɗaƙin suka yi tare da tallafawa Maryam ta ɗago Du'a. Ganin tadda idanuwan Du'a ke jujjuyawa yasa gaba ɗaya tsoro ya baibaye zuciyoyin su. Saurin miƙe wa ɗaya daga cikin matan ɗaƙin ta yi, sannan ta nufi inda bokitin ruwa ya ke. Ɗaukar kofi ta yi sannan ta ɗebi ruwa kaɗan a cikin kofi ta nufi inda su Du'a suke. A hankali ta fara shafa mata fuskarta da ruwan koh Allah zai sa ta dawo dai-dai, amma kamar ma abin da ɗa ƙaruwa ya ke. "Na shiga uku ni Maryam!, dama na sani ban kashe fitilan nan bah, yanzu mai zamu yi ta dawo dai-dai?". "Ɗaya daga cikin ƴan ɗaƙin ne ta kalli Maryam ta ce. "Ki kwantar da hankalin ki wannan abin da ke damunta nasan ba zai wuce shafar aljanu bane, dan aka kawai mafita ɗaya ce, shi ne muyi mata ruƙiya koh Allah zai sa su lafa". "A'a ƴar uwata bata da aljanu koh kaɗan, bana so ki kara ce mata tanada aljanu ". Tana kaiwa nan ta miƙe da zimmar fita don neman wa kansu mafita. Ji ta yi an riƙe mata hannu, waigawa ta yi tare da ɗora idanuwan ta kan nata. Baki na rawa Du'a ta ce. "Kada ku tayar da hankulan ku a kaina, wannan bah sabon abu bane, bah yau ne karo na farko dana fara shiga irin wanann halin bah, zan dawo dai-dai nan bada jimawa, kudai kawai ku kwanta kuyi bacci nasan ta yadda nake dawo da kaina dai-dai". "Kin tabbatar zaki dawo dai-dai ba sai mun nemi mafita bah?". Cewar Maryam. "Kwarai ina da tabbaci akan maganar dana faɗa, kawai kuyi abin da nace". Jin hakan da suka yi ya sa gaba ɗayansu kwanciya cike da fargaban kada wani abu ya samu Du'a. "Mene ne ya faru Inna wuro? Ya naga hankalin ki a tashe?". Cewar mai gari . Amsa Inna wuro ta bashi da cewa. "Gaba ɗaya hankali na ya'ƙi kwanciya zuwa birnin da Du'a ta yi, tun ɗazu gabana yake ta faɗuwa, kuma bansan dalilin akan bah". "Kuma jikina yana bani cewa Du'a na cikin halin tsaka mai wuya wanda babu wanda zai iya taimaka mata bayan mu da muka san duk matsalolin da ke damunta, ina tsoron kada wani abu ya faru da ita". Murmushi Mai gari ya yi sannan ya ce. "Babu abin da zai faru in banda alhkairy, dan Allah ki daina irin wannan saƙe_saƙen a ranki, Allah shi ne mai karewa, kuma ina da tabbacin cewa Allah zai kare ta domin tana tareda albarkar iyaye da kuma albarkar mutanen kauyen nan". "Maza kije ki kwanta dare ya yi, in sha Allahu ma babu abin da zai same ta ƙunshi?. "Na ji shi kenan Mai gari na gode, ni yanzu zan koma ciki, da safe zamu ci gaba da yiwa mahaifiyarta magani sabo da na fara ganin sauyi a tattare da jikinta, alamu na nuna cewa nan kusa zata tashi". "Masha Allah". Mai gari ya faɗa sannan ya ce. "Allah yasa akan, ubangiji ya saka ta farfaɗo nan kusa, domin yarta na matuƙar buƙatar ta". Washe gari sa sassafe jikin Du'a ya yi sauƙi, harta shirya zata tafi aji domin daukar darasi. Kallonta Maryam ta yi ta ce. "Du'a kamar ba keba wallahi, kinga yadda kika bamu tsoro a jiyan nan". Mai da kallonta Du'a ta yi kan Maryam ta ce. "Kinga dan Allah abar wannan maganar, ki tawo muyi sauri mu tafi aji sabo da kada mu makara". Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Ke in banda abinki wazai yi miki lecture ƙarfe shida na safe, koh mune ƴan hallazi boko ai sai akan, gaggawan me kike? Ki bari bakwai ta yi tukun nan sai mu tafi ". Ɗaukar jakarta na saƙa Du'a ta yi sannan ta ce. "Kinga tafiyata, ni bazan iya jiran har ƙarfe bakwai ya yi bah, sabo da ina so naje na kofi rubutun da aka yi bana nan". Dakatar da ita Maryam ta yi da faɗin toh idan ma za kije, sai ki tafi da wannan jakar dan Allah, ai saiki sa a raina mu. Kalli fah jakar gaba ɗaya ta yi muni da yawa gashi kuma saƙa ta aka yi, kawai ki ɗau ɗaya daga cikin jakunkuna na ki tafi dashi". Girgiza kai kawai Du'a ta yi sannan ta ce. "Babu wanda ya ajiye ni a makarantar nan, ni karatu nazo yi bah gayu bah, duk abin da nake dashi toh shi zan saka, idan kuwa bani dashi toh bazan takura wa kaina don mallakar abin da banda shi bah ". "Idan ma kallona za suyi koh zagi koh akasin aka toh sun daɗe basu yi bah. Ni kinga tafiyata sai kin tawo". Tana kaiwa nan ta fice daga ɗaƙin. Ɗaukar jakarta Maryam ta yi tare da bin bayanta da sauri. Tafiya mai nisa suka yi kafin daga bisani suka isa wajan department ɗin su. Shiga ciki suka yi suka tarar babu kowa a cikin ajin. chan sama Du'a ta nufa tare da ajiye jakarta akan kujera sannan ita ma ta zauna akan kujerar da ta ke ganin shi yafi cancan ta ta zauna. Zuwa Maryam ta yi kusa da ita sannan ta ce. "Du'a me zai hana ki samu wani kujeran ki zauna, wannan kujerar da kika zauna akai, na su Jennifer ne kuma babu wanda ya ke zama in banda Jennifer". "Dan Allah ki nemi wani ki zauna". Murmushin takaici Du'a ta saki sannan ta kalleta ta ce. "Ni dai dana zo wajan nan banga inda aka rubuta cewa iya Jennifer ce kawai ke da ikon zama akan wannan kujerar bah, shin kujerar daga gidan su ta tawo dashi koh me? Koh an rubuta a jikin kujerar cewa kada wanda ya zauna a kan wannwn kujeran, dan aka dan Allah ki rabu dani ". Shiru Maryam ta yi mata sannan itama ta samu guri ta zauna. A hankali ɗalibai suka fara shigowa cikin aji, babu bata lokaci ajin gaba ɗaya ya cika, yayin da suka dinga bin Du'a da kallo. Chan Maryam ta hango tawowar su Jennifer daga windon ajin. Da sauri ta taɓa Du'a Tare da faɗin. "Du'a ki tashi gatanan zuwa fah, dan Allah ki tashi kada tazo ta tarar dake a kan kujerar zamanta". "Murmushi Du'a ta yi wanda ya sanya dimple ɗinta lotsawa, sannan ta ce. "Allah ya kawo ta lafiya, wallahi daɗi na dake Maryam bakida jarumta, samm bakisan darajar ki ta mace bah, ta ya ya wata ɗaliba zata zo tana tsorata ki, kuma ke..... Maganar ta ne ya tsaya chak jin muryar Jennifer na faɗin. "Waya baki izinin zama a waje na, kinsan kuwa wace ce ni a makarantar nan, toh maza- maza ki tashi kafin na nuna miki ɗanyen kaina". Miƙe wa Du'a ta yi murmushi ɗauke kan fuskarta ta ce. "Keda wannan bahamagen wanda kuke kira shugaban ɗalibai baku da maraba, shima aka ya ke kuri amma banga har yanzu ya aiwatar da abin da ya ce bah". "Kuma kema aka, dan aka ki samu wani gurin ki zauna, dan kuwa wannan gurin karfi ya cinye". Ƙoƙarin magana Jennifer ke yi suka ji shigowar lectura, harara Jennifer ta watsa mata sannan ta samu wani kujerar ta zauna akai. Gaishe sa gaba ɗaya ɗaliban suka yi, daga bisani kuma lecturan ya fara koyar dasu darasi. Sosai Du'a ke fahimtar darasin da ake koyarwa, duda cewar bah duka abubuwan ta ke fahimta. A hankali ya sanya kafufawansa a cikin ajin. Ɗaliban ajin na ganin sa gaba ɗaya suka mimmiƙe, tare da gaishe sa. Banda Du'a wacce ke zaune kamar bata san da shigowar sa bah. Ran Ahmad ne ya soma ɓaci, ganin gaba ɗaya ta yi kamar bata san da shigowar sa ajin bah. Gyaran murya ya yi sannan ya ce. Wace ce Du'a a wannan ajin? Jin ya ambaci sunan ta yasata ɗago da kanta ta ce. "Nice nan fatan dai komai lafiya?". "Kallonta lecturan ajin ya yi, mamaki ɗauke akan fuskarsa ya ce. "Ke baki ga shugaban ɗalibai bane, ba zaki iya tashi ki gaida shi bah, baki ga kowa ya tashi bane?". "Eh na gani, naga ɗalibai sun tashi, ni kuma bai kai matsayin wanda zan tashi na gaida bah, idan ma mafarki ya ke toh ya farka, dan bazan taɓa gaishe shi bah saidai duk abin da zai faru ya faru". A hassale Ahmad ya fara tunkaran inda ta ke, babu tsammani Du'a taji saukar maruka kam fuskarta, yana sauke hannunsa ita ma ta ɗaga nata hannun. *TUNATAR WA......, Free page ya kusan kare wa, fan's ina fatan Allah(SWA) ya hore muku ya baku ikon biyan kuɗin wannan littafin Naira ₦400 complt babu tsada, ki siya ki mori karatun ki cikin kwanciyar hankali*. COMMENTS & SHARE PLS 🙏 🙏 🙏 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar 🪙Jajirtattu) https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 FREE PAGE ️️1️⃣2️⃣➡️1️⃣3️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) *_______________________________* Chak Du'a ta tsaya sakamakon riƙe mata hannu da jennifer ta yi. Murmushi Jennifer ta sakar ma Du'a, sannan ta ce. "Mene kike shirin aikata wa? Wai da niyarki ki ɗaga hannu sannan ki maresa? Toh ki sani duk wanda ya yi yinkurin akan sai ya fuskanci hukunci, dan aka kema dole ki fuskanci hukunci". Cike da ɓacin rai Ahmard ya kalli Du'a ya ce. "Da tunanin ki ki ɗaga hannu ki mare ni? Har yanzu baki san waye ni bah Koh? Toh ki jira kiga abin da zan aikata yanzu a wajan nan". Yana kaiwa nan ya ja mayafin ta sannan ya riƙe hannunta ya fara jan ta. Ƙoƙarin kwace kanta ta ke amma akan ya cutura. Ganin dai da gaske waje zai kai ta ya sata fara bashi haƙuri. Shiko Ahmad kamar ma bai san tana yi bah. Sai da ya kaita tsakiyar makarantar ya yin da dalibai daga kowane department suka fara fitowa daga classes ɗin su. Zama ya yi akan mota, ya yin da ita Du'a ke tsugunne a kasan wajan. Ganin dalibai sun zagaye su ya sashi sakar mata murmushi. Ganin jama'a sun taru waje ɗaya tare da kewaye wajan ya sanya su Abdul suka karasa wajan. Kallon ɗalibai makarantar Ahmard ya yi ya ce. "Wannan da kuke gani ta raina muku shugaba sannan ta daga hannunta da zimmar mari na". Shin wane mataki ya kamata na ɗauka akan ta? Na hukunta ta ne ko na barta taci bulus?". Hatare gaba ɗaya ɗaliban suka haɗa baki wajan cewa . "A hukunta ta". Ku kan da Du'a ke riƙe wa ne ya subuce mata. Ya yin da ta fara ku ka hawaye na zarya kan fuskarta. Babu zato suka ga gaba ɗaya garin ya yi duhu, ya yin da hadari ya ta shi a sararin samania tare da iska mai karfin gaske. Da mamaki gaba ɗaya suka kalli sama ya yin da suka yi matuƙar mamaki ganin lokaci ɗaya hadari ya ta shi. Babu zato suka ga an zuge da ruwan sama mai matukar yawan gaske. A ta ke ɗalibai suka fara komawa aji da sauri. Ganin aka ya sa Ahmard sauƙowa daga kan motar da ya ke kai sannan ya shige cikin mota sannan ya figi motar tare da barin wajan. Da sauri Maryam ta isa inda Du'a ta ke sannan ta ja hannunta da zimmar ɗaga ta sama. Fizge hannunta Du'a ta yi sannan ta ce. "Bana so ki rabu dani, harni zai ci wa mutunci, ni zai tarawa jama'a sai kace wacce ta yi sata a kasuwa, tun da har ya kuskure ya yi min wannan cin mutuncin wallahi saina nuna masa cewa Allah ɗaya ne" "Zan nuna masa bambancin ƙauye da birni. Ki tafi kawai ki barni a nan wajan". "Ta ya ya zan tafi na barki a nan Du'a? Kema kin san ba zan iya tafiya na barki ke kaɗai a nan wajan bah, kizo mu koma class, kada ki bari professor's su zo su gan mu a nan wajan". Maryam ta ƙarashe maganar tare da jan hannunta. "Ki rabu dani!". Du'a ta faɗa cikin daka tsawa. "Shi kenen Du'a zan barki kamar yadda kika buƙata". Maryam na kaiwa nan ta shige cikin class. Ruff da ciki Du'a ta yi sannan ta ci gaba da rusa ku ka. Daga sama ta ji muryar mutum a kan ta yana faɗin. "Barkan ki dai kyakkyawar sura, mene ne ki ke yi a cikin ruwan sama kuma? Bai kamata a ce kyakyawa irin ki tana cikin ruwa bah, ki ta shi kada ki bari zazzaɓi ya kama ki". Saurin ɗago da kan ta Du'a ta yi sannan ta ɗora a kan sa. Motsa leɓenta ta yi sannan ta ce."wane ne kai? Mene kake bukata daga waje na? Shin waya turo ka domin ka cutar dani?". Tambayar da ta shiga yi masa kenen. Murmushi ya yi sannan ya kalle ta ya ce. "Babu wanda ya turo ni kuma bawai na zo ne don cutar da lafiyar ki bah". Koda ma zuwa ka yi don cutar da lafiyata toh akan ma ba zata faru bah, don ka ma cire a ranka cewa zaka cutar dani domin babu wanda ya isa kwatanta akan". Cewar Du'a. "By the way ni sunana Umar habib harun ne, kuma ni ɗin ba kowan kowa ba ne, nima ɗan makarantar nan ne kamar ke ɗin nan, jiya na ga lokacin da shugaban ɗalibai na miki magana kina mayar masa, akan yasa naji tabbas tun da har ki ka iya yi wa shugaban ɗaliban makaranta magana ba tare da wani tsoro koh fargaba bah, ya sa naji cewa koma waye ba zaki kyale ba". "Shi ya sa nake so kiyi min wani taimako". Kallonsa Du'a ta yi ta ce. "Mene ne?". Amsa Umar ya bata da cewa. "Ina so na zama abokin ki, mu kasance tare koh ina duk abin da baki gane bah a boko zan fahimtar da ke, kuma ina so ki yarda dani cewa bah cutar da ke na zo yi bah". "Shi kenen na ji amma da sharaɗi". Kallonta Umar ya yi sa'annan ya ce. "Faɗa min mene ne sharaɗin? In sha Allahu zan bi kuma zan kiyaye". Tashi Du'a ta yi sannan ta nufi garden ɗin makarantar. Ganin akan da Umar ya yi ya sa shi saurin bin bayanta. Zama Du'a ta yi daga cikin kujerun da ke wajan ya yin da shi ma ya zauna ba tare da tsoron abin da zai biyo baya bah. Kallonsa Du'a ta yi ta ce. "Kace sunanka Umar koh"? Amsa umar ya bata da cewa. "Eh". "Shi kenen sharaɗin dama shi ne abota ni da kai ta tsaya a iya abota kawai banda soyayya, domin babu abin da na tsana a duniyar nan sama na ji an furta kalman soyayya a kusa da ni bana sonta dan aka a tsaya a iya abota". Murmushi Umar ya yi sannan ya ce. "In sha Allahu ma a iya abota zamu tsaya, nida na ke da tawa budurwar me kuma zan yi da guda biyu". "Karki damu nayi miki alƙawari iya abota ce kawai zata haɗa mu da ke banda soyayya, amma dan Allah ina so tun da yanzu kin ɗauke ni a matsayin aboki kuma ɗan uwa, kuma a matsayin aboki nake so na faɗa miki wannan magana. Kuma maganar ita ce ina so kije ki bawa Ahmard haƙuri dan Allah". A ta ke fuskar Du'a ya koma daga walwala zuwa ɓacin rai. Lokaci ɗaya ta tuna da irin cin mutuncin da ya yi mata ɗa zu, cikin jin aushin maganarsa ta ce. "Bazan je bah, Allah ya kiyaye na je na basa haƙuri sabo da shi ɗin autar maza ne zai sani na je na basa haƙuri, ai koh da me ya ke yawo a makarantar nan bai isa na je na basa haƙuri bah shi ɗin banza shi ɗin wofi". Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Du'a ina da dalilin da ya sa ki ka ji na ce aka, wallahi Ahmard bah kunya ce ta ishe shi bah, a makarantar nan kusan ɗalibai amsin ya sa aka kora, kuma ɗaliban yawancin su mata ne kuma sabo da sun ce suna sonsa ne ya sa aka kore su daga makaranta". "Shi ya sa ma babu wacce ta ke tanka masa a makarantar nan, indai ya yi magana ba'a ja hatta malamai sha yinsa su ke, indai har bakyason ki kunyatar da kanki da kuma iyayen ki toh dan Allah ki je ki ba shi haƙuri, in ba aka bah zaki sha baƙar wahala". Ajiyan zuciya Du'a ta sauke ta ce. "Gaskiya wannan anyi shedani kuma mara tunani, aka kawai dan mata sun ce suna sonsa sai ya fara koransu sai kace ubansa ne ya gina makarantar, shi kenen in ba dan nayi wa yan ƙauyen mu alƙawarin cewa zan zamo musu garkuwa wacce zata dinga yi musu magani idan na zama likita bah koh, da Allah ba zan ba shi hakuri bah sai dai duk abin da zai faru ya faru". Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye tare da nufar inda department ɗin su ya ke. Bin ta Umar ya yi da kallo sannan ya saki murmushi. Ciro wayar sa ya yi daga aljihu sannan ya yi dialling ɗin number wacce gaba ɗaya number bata yi kama da ta Nigeria ba. Kira ɗaya biyu aka ɗaga, lankwasa kafa ya yi ya ce. "Yallabai na fara aikin kamar yadda ka umarta, ta ruga da ta bani haɗin kai yanzu shiga jikin ta zan yi sannan na sace ta tare da kawo maka ita fada". Daga ɗayan ɓangaren aka ce. "Shi kenen abin da nake so kenen, amma ka tabbata baka cutar da ita bah, bana so koh kwarzane ta ji, idan har kayi mata wani abin toh ka tabbata ba zan kyale ka bah saina hukunta ka, domin ita ce goben wannan masarautar". "Sannan ka binciko min mahaifiyarta naji ance tana wani kauye kuma sannan na ji an ce tana raye har yanzu. duk inda ta ke ka saka yaranka su bazu koh ina su nemo ta, domin ta dawo inda tushen ta ya ke ". Umar ya ce. "In sha Allah ranka shi daɗe zan bi abin dalla-dalla, ta yadda babu wanda zai gane ni ɗin ɗan basaja ne ba". "Shi kenen ka bi komai a sannu sannan ka kula da kanka". mutumin na kaiwa nan ya katse wayan. Ganin a kan ya sa Umar buɗe bayan wayan sannan ya cire sms ɗin wayar gaba ɗaya tare da saka wa a aljihu. Miƙe wa ya yi tare da karkaɗe jikin sa sannan ya nufi office ɗin head of department. "Hello sir, har yanzu ina kan mission ɗin ne, na saka sauran wanda suke tare dani su karaɗe koh ina su nemo shi duk inda ya ke. Kuma na tabbata duk inda ya ke zasu zaƙulo shi". "What! Mutumin ya faɗa. Sannan ya kara da faɗin. "This is not the first time da ka ke faɗa min aka? yanzu fah kusan four good year's kenen baka samo makashin da ake nema bah, wannan mutumin fah is a big criminal, gaba ɗaya police da su soldier's aka bawa aiki domin a nemo sa, kasan nawa za'a bawa duk wanda ya samo sa kuwa?". "Koda ya ke kai bah lallai kuɗin su dame ka bah, sabo da already kana da kuɗi kana da dukiya kana da duk abin da ɗan adam ya ke so na more rayuwa dole ba zaka damu bah". "Ni ina wanann aikin ne dan kawai muyi nasara mu samu wannan kuɗin, but kai naga alamun kuɗin ba su ne a gaban ka bah. Ni banga ma amfanin aikin da ka ke yi bah, dan da ni ne Allah ya ɗora a matsayin da ka ke wallahi da babu wani aiki da zan yi a duniyar nan, domin Allah ya ruga daya wadata ni da komai na rayuwa, kawai zan baka shawara ka ajiye aiki". Murmushi ya yi ya ce. "Ni ba dan kuɗi nake aiki na ba, ina yi ne domin kare al'ummar kasa ta, ina yin aikin nan ne sabo da shi ne buri da fatan marigayi Bello, dan aka shi ya sa kawai na shiga wannan aikin ". "Kuma wanda ake nema nayi maka alƙawarin cewa nan bada daɗewa bah zan nemo sa duk inda ya ke wannan alƙawari na ne". Yana kaiwa nan ya kashe wayar sannan ya fito daga cikin mota tare da cire hular da ta rufe fuskarsa tare da buɗe gate ɗin gidan. Wow! Na ce sakamakon harba dana yi da gidan. Tabbas wannan gidan tafi ƙarfin a ce na talaka ne, domin kana ganin gidan kasan kuɗaɗe sun yi ku ka wajan gina gidan, sai ka rantse cewa gidan ba'a Nigeria ta ke bah, koh kuma ba ƴan Nigeria ne suka gina ta bah, gaba ɗaya motoci ne a jere wajan parking space kowacce da kalar jikinta. Gaba ɗaya kasan interlock na gidan grass carpet ne, gefe guda kuma swimmin pool ne a chan nesa kusa da garden. Sosai gidan ya yi matuƙar tsaruwa dan tsayawa faɗa muku yadda gidan ya haɗu ɓata lokaci ne. Taka wa ya soma ya yi, saida ya isa baƙin kofa sannan ya dauki remote tare da danna remote din sannan ya saka babbar yatsar sa tare da fuskar sa a jikin kofar. Sai da kofar ta yi scanning ɗin fuskarsa sosai sannan kofar ta wangale. Saurin ja da baya nayi sabo da harba dana yi da cikin parlourn, gaba ɗaya kayan furniture's din parlourn gold ne, ya yin da babu abin da parlourn ke yi sai sheƙi da kamshi, ya yin da ƙaran Ac ya cika parlourn, gaba ɗaya babu abin da ka ke gabi sai kayan halatu da na more rayuwa. Zama ya yi kan ɗaya daga cikin kujerun sannan ya girgiza kai tareda furzar da iska mai zafi ya ce. "har ni wata zata ci wa mutunci, saina nuna mata ɗanyen kaina, ba ta san koh ni waye bah, kuma sannan ba ta san me zan iya aikata bah, mun din ina wannan makarantar toh farin ciki da walwala sun ƙare miki". Murmushin gefen baki ya yi ya ce. " Mene ne zan yi domin sa yarinyar nan ɗanɗana kuɗar ta?". A ta ke ya ji wani dabara ya faɗo masa. Babu zato ya ji wayarsa ta fara ringing kallon wayar ya yi ya ga baƙuwar number. Katse wayar ya yi sanann ya kwanta a kan kujera. Sai da aka kira ku san ten missed call bai ɗaga bah, ya yin da aka ci gaba da kira ba tare da wani gajiya wa bah. Ganin abin ya ƙi ƙarewa ya sa shi ɗaukar wayar sannan ya ce. "Who is on the line?". Daga ɗayan ɓangaren aka ce"ni ce nan". COMMENTS & SHARE PLEASE 🙏 🙏 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B (Zinariyar Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 FREE PAGE 1️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) *_______________________________* "Kece wa?". Gyara muryan ta Maryam ta yi sannan ta ce. "Maryam ce ke magana. ina ɗaya daga cikin ɗaliban northwest university". Tsaki Ahmard ya ja sanann ya ce. "Wane taimako zan iya miki? Fatan dai komai lafiya?". "Komai lafiya lau, dama na kira ka ne akan abin da kawa ta ta yi maka wanda samm akan bai dace bah. Shi ya sa ta ce min dan Allah idan babu damuwa tana so ta baka haƙurin abin da ta aikata maka". Maryam ta ƙarashe maganar gabanta na faɗuwa. Murmushin gefen baki Ahmard ya yi sannan ya ce. "Shi kenen na ji babu damuwa gobe ku jira ni a laboratory room idan na zo makaranta gobe da kanta na ke so ta bani haƙuri a wajan. kuma sannan akwai abubuwan da za ta yi min domin wanke kanta sannan na yafe mata". Yana kaiwa nan ya kashe wayan. Ajiyan zuciya Maryam ta sauke. Du'a da ke ta kai kawo acikin ɗaƙin ce ta juyo ta kalli Maryam. Kallo ɗaya za ka mata kasan cewa hankalin ta a matuƙar tashe ya ke. Da sauri ta nufi inda maryam ta ke ta ce. "Maryam me ya ce? Shin ya ce ya yafe min koh A'a?". Furzar da iska Maryam ta yi sannan ta ce. "Gaskiya Du'a bai kama ta a ce daga zuwan ki makaranta kin fara faɗa da mutane bah, samm akan mai bai dace bah". "Kin san kuwa bah ƙaramin halin Ahmard bane ya sa a kore ki daga makarantar nan? Wallahi ni na san tun da ya ce sai kin yi masa wani abun tukun nan zai ƙyale ki toh abin da ki ka masa bai wuce a zuciyarsa bah". "Wallahi Maryam ban san da cewa aka za ta faru bah, da na san aka za ta faru da ban kula shi a wan can ranar bah". "Idan na koma ƙauye da wane ido zan kalli mutanen ƙauyen na ce musu an kore ni? Bayan ni ce na ce ina buƙatar zuwa jami'a, yanzu idan suka ga an kore ni na tabbata ransu zai yi matukar ɓaci sosai". "Ni na yarda koma mene zai yi ya yi, indai har zan ci gaba da kasan cewa a wannan makarantar toh alhamdulillah". Du'a ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka. "Ki kwantar da hankalin ki Du'a, ba ya ce mu haɗu a laboratory room bah gobe? toh Allah ya kai mu lafiya sai ki bashi haƙuri, dama sai da na fada miki kada ki samu yi takun saƙa da Ahmard. Kin san mene abin mamaki a tattare da shi kuwa?" Amsa Du'a ta ba ta da cewa. "A'a sai kin faɗa". Maryam ta ce. "A makarantar nan har yau har gobe ba'a san waye shi bah, ba bu wanda ya san daga ina ya fito, an dai san da cewa shi ɗin ɗan attajirin mai kuɗi ne amma ba'a san daga wane jaha ya ke bah". "Kuma kwata-kwata bai yi kama da student bah, ya fi kama da irin sojojin nan koh jami'in boye, shi ya sa yan matan makarantar nan ke mutuwar sonsa ni kai na da ki ke gani sai da nayi daƙon sonsa amma daga baya na cire sonsa a raina sabo da koda na ci gaba da daƙon sonsa toh wahalar da kai na kawai zan yi. Shi ya sa na fauwala wa Allah ko mai". Ɗan jimm Du'a ta yi ta ce. "Gwanda ma da ki ka cire sonsa a ranki, ni Allah na tuba kwata-kwata bana son namiji ya fiye kyau da yawa, sabo da idan na je na aure sa hankali na a koda yaushe zai kasance a tashe ne. Dan aka ki gode wa Allah da ya cire miki son wan can jarabbaben a ranki". Nannauyan ajiyan zuciya Maryam ta sauke sannan ta ce. "Wallahi har yanzu ina jin sonsa a raina, ban taɓa jin dai-dai da rana ɗaya sonsa ya ragu a zuciyata bah, kawai dai ina danne zuciyata ne akansa sabo da ire-iren abubuwan da ya ke yi wa mata Waɗan da suka ce suna sonsa". Kwanciya Du'a ta yi akan gado tare da yin mi ƙa sannan ta kalli Maryam ta ce. "Kinga kizo mu kwanta gobe muna da darasi karfe tara bana so na maƙara". "A'a ki kwanta kawai ni ba yanzu bah sabo da bana jin bacci". Cewar Maryam. Girgiza kai Du'a kawai ta yi ta ce. "Allah ya ya ye miki yar uwa". Tana kai wa nan ta ja pillow tare da kwanciya a kai sannan ta fara lumshe idanuwanta alamun bacci na san ɗibanta. Babu ɓata lokaci barcin barawo ya sace ta. Ƙarfe ukun dare. Ganinta ta yi a tsakiyar daji mai matuƙar abin tsoro, a ya yin da ta fara waige-waige tana neman hanyar kuɓuta, chan ta hangi wani ƙaramin halitta a gaban ta. Ba ta re da jinkiri bah ta nufi inda halittar ya ke. Gaba ɗaya wajan zagaye ya ke da macizai kala-kala masu matuƙar girma. Ya yin da ta ke tafiya macizai na mara mata baya. Sai da ta je gaban wannan halittar sannan ta tsuguna tare da fuskantar sa. Kallon sa ta yi ido cikin ido a ta ke ta yi wani irin muguwar zabura ganin yadda sufar sa ya ke da matukar munin gaske. Cikin daƙe wa ta kara kallon sa a karo na biyu sannan ta ce. "Wane ne kai? Me ya sa ku ka kawo ni cikin wannan baƙar dajin?" Amsa ƙaramin halittar ya bata da cewa. "Mun kawo ki ne sabo da ki na da halaƙa da wannan dajin. ke ɗin jinin mu ce kuma kece sarauniyar wannan dajin gaba ɗaya, me ya sa ba za ki dawo ki ci gaba da mulkar dajin ki kamar yadda ki ka saba yi a da bah? bai kama ta a ce ki ci gaba da kasancewa cikin mutane wanda ke kan ki kin san da cewa ke bah jinsin su bace". "Har yanzu ke mu ke jira don ga kujerar ki na sarauta chan yana jira ki dawo gare sa. Koda yaushe wannan kujerar ku ka ta ke yi. dan aka yanzu ba ki da wani zabi da ya wuce ki dawo duniyar ki, domin shi ne zai zamo alhkairy a ga re ki". A fusa ce Du'a ta miƙe tsaye sannan ta kalle shi cikin ɓaccin rai ta ce. "Karya ka ke makaryacin banza kawai, Ni ɗin mutum ce ba macijiya bah, har kai waye da za ka ce Ni ba mutum bace" "Idan har ni ɗin macijiya ce da gaske toh me ya sa bana sauya kammani? Na ga ji da jin ire-iren waɗan nan tatsuniyoyin da ku ke yawan faɗa, wannan ya zamo na farko kuma na karshe da za ku ƙara cewa ni macijiya ce". "Kuma shin kana da hujja akan abin da ka ke faɗa?". Amsa aljanin ya bata da cewa. "Ba za ki san da cewa ke macijiya bace sai lokacin bayyanar baiwar ki ya yi tukun nan, kuma ba za ki ji komai a baki na bah, aka zalika hujja ma ba za ki ji daga waje na bah, amma ita asalin mahaifyar ki ta san ko mai, ita za ki je ki tambaya domin ita keda cikakkun bayanai ga me da rayuwarki". A fusa ce Du'a ta shaƙe masa wuya tana mai cewa. "Makaryancin banza wato kana so ka shiga tsakanina da mahafiyata koh, yau bah gobe bah zan ga bayanka. Babu zato ta ga macizai sun fara hawa jikin ta, a ta ke ta saki wani irin razannaniyar ƙara!. Ihuuu! Maryam ta yi ganin yadda Du'a ta maƙure ta ta re da shaƙe mata wuya. Zabura gaba ɗaya ƴan ɗaƙin suka yi, ganin yadda Du'a ta shaƙe wuyan Maryam tana surutai. Babu ɓata lokaci kowannen su ya kai wa Maryam ɗauki. A firgice Du'a ta farka daga mafarkin da ta ke. Da sauri ta cire hannunta daga wuyan Maryam ganin yadda ta shaƙe ta. Tari Maryam ta soma yi babu sassauci. Ganin akan da Du'a da ƴan ɗaƙin su ka yi ya sa hankali su ya ƙara tashi!. Da sauri Du'a ta tashi tare da nufan inda ruwa ya ke. ɗebo ruwan ta yi a cikin kofi sannan ta nufi kan Maryam da shi. Ɗaya daga cikin matan ɗaƙin wato Khadija ce ta wafce kofin da ke hannun Du'a sannan ta yi magana cikin ɓacin rai ta ce. "Baki da hankali za ki shaƙe mata wuya? sabo da me za ki aika ta mata aka? Ki dubi yadda ki ka sa ta gigice duk sabo da ke". "Naga alamu tun da ki ka shi go cikin makarantar nan abubuwa mara sa kyau suke faruwa. Farkon shigowa ki makarantar nan wata ta tayar da aljanu, kin ce bakya iya kwana cikin duhu sabo da kina jin tsoro, aka muka haƙura muke kwana cikin haske, yanzu kuma kin zo kin maƙure ta kina son ki kashe ta Koh? Nan gaba ma abin ba'a iya nan zai tsaya bah harda mu za ki haɗa". Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. "Ni samm bada sane na aikata mata akan bah, mafarki na ke yi shi ya sa ban san na shaƙe mata wuya bah". "Ka ji munafuka algunguma, wato mafarki ki ke shi ne aka ce ki shaƙe mata wuya koh?". Cewar habiba. Sannan ta kara da cewa. "Wallahi babu tantama yarinyar nan mayya ce, in bah mayya bah mene na shaƙe mata wuya wato so ki ke ki zuƙi jininta Koh? Toh ki sa ni jinin mu ɗaci ne da shi babu wata mayya da ta isa ta ce za ta sha mana jini". Girgiza kai Du'a ta fara yi ta ce. "Na rantse ni ba mayya bace kuma ni bana shan jini, kawai kun yi min gurguwar fahimta ne shi ya sa, amma ni samm bah mayya bace". Ture ta khadija ta yi ta ce. "Dalla ware dangin mayu kawai mai fara ƙafa, daga yau kada mu sa ke ganin kin kusanci inda Maryam ta ke, in kuma ba aka bah, sai kin gane kuranki. Tana kaiwa nan ta bangaje Du'a. A ta ke Du'a ta faɗi a wajan a yayin da hawaye suka fara zarya a kan ƙun cin ta. Da sauri ta ta shi tare da yin hanyar waje da gudu. Gudu ta ke yi babu ƙagautawa sai da ta yi tafiya mai nisan gaske ba tare da tana ganin gaban ta bah, bakin bishiya ta samu ta zauna sannan ta fara ku ka. Ku ka ta ke tamkar ranta zai futa. Ɗago idanuwanta ta yi wanda su ka yi jajir ta ce. "Me ya sa akan ta ke faruwa dani? Mene ne tsakani na da macizai, me ya sa na ke irin waɗan nan munanan mafarkan? Shin ko dai da gaske ina da halaƙa da macizai?". "Me ya sa ma banyi zama na a kauye bah? Da nasani ban zo birni bah na yi zama na a ƙauye domin nafi samun farin ciki a chan". Miƙe wa tsaye ta yi tare da share hawayen ta ta ce. "Ni wace ce? Me ya sa nake iya mu'amala da macizai bayan kuma ni ɗin mutum ce? Tabbas maganar su khadija gaskiya ne. kenen da gaske ni mayya ce? me ya sa zan kasance mayya bayan a dangi na babu mayu, toh kodai mamata mayya ce?". Ji ta yi gaba ɗaya ku kan tsuntsaye ya gauraye wajan yayin da aka fara iska mai ƙarfi wanda ya ke haɗe da guguwa. a ta ke ta fara kalle-kalle, tare da juya wa. Juyawar ta ke da wuya ta ga wani jibgegen baƙi maciji wanda ya zalalo da harshen sa wanda ke a tsage gida uku. Zaro ido ta yi waje sannan ta sa ki wani irin ihuu da sauri ta fara ja da baya-baya, sannan ta fara ƙoƙarin guduwa, kafin ta yi wani yunkuri, macijin ya nannaɗe ta tare da ɗaga ta sama. Ƙoƙarin kwace kan ta ta ke amma akan ya cutura. Rintse idanuwan ta ta yi don ta gama sallame wa cewa yau ne ranar mutuwar ta. Jin shiru babu abin da ya same ta, ya sa ta buɗe idanuwanta a hankali tare da ɗorawa akan na macijin. Sauke ta macijin ya yi sannan ya shafa gashin kan ta da jelar sa na macijin daga bisani ya yi tafiyar sa. Baki sa ke Du'a ta bi macijin da kallo sai da ta tabbatar idanuwanta sun daina ganin sa sannan ta ce. "Shi kuma wannan macijin daga ina ya fito? Me ya sa kuma zai zo waje na? Sannan fuskarsa ya nuna shiɗin ba ya da cutarwa". Babu zato ta ji an dafa mata kafaɗa. A firgice ta juya da sauri ta ɗora idanuwanta akan na ta. COMMENTS & SHARE PLS 🙏 🙏 🙏 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️ Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 *DA nayi niyar bar muku free page a aka, amma insha Allah zan kai muku shi twenty free page 🙏🙏🙏* FREE PAGE ️1️⃣4️⃣➡️1️⃣5️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) *_______________________________* Rass gabanta ya faɗi! Yayin da jiri mai karfi ya fara ɗibanta, ta saki wani iriyar razannaniyar ƙara!. Da sauri ta fara ja da baya-baya sakamakon harba da ta yi da wata mai kama da ita sakk. Riƙe kanta ta yi sannan ta nuna ta da ɗan yatsa a tsorace ta ce. "Wace ce ke? Me ya sa ki ke matuƙar kama da ni? Dan Allah na roƙe ki kada ki cutar da ni". Murmushi aljanar ta yi sannan ta ce. "Ni bah cutar da ke na zo yi bah, ai idan na kwatanta taɓa lafiyar ki ni ce zan mutu bake bah. Dan aka ki tsaya ki saurari abin da zan faɗa miki". Ta faɗa tana nufar inda Du'a ta ke. "Kada ki matso kusa da ni, bana so ki rabu dani dan Allah kada ki cutar da ni". Cewar Du'a. Girgiza kai aljanar ta yi ta ce. "Na faɗa miki bah cutar da ke zan yi bah, ina so ne na sanar miki da wata muhimmiyar magana wacce za ta sa ki iya kare kanki a Koh ina, wanda koh mutum koh aljan bai isa ya tunkari inda ki ke da mugun nufi bah". Kuka Du'a ta soma yi sannan ta ce. Yayin da hadari ya tashi aka fara yayyafi. "Ni bana so, ki rabu da ni dan Allah". Ta ƙarashe maganar tare da juya wa da niyar tafiya. Babu zato taji ta yi tuntuɓe da dutse. Luuu ta tafi tare da faɗuwa a kasan wajan. Jin takun takalmin mutun yasa aljanar ta ɓace daga farfajiyan wajan. Karasawa wajan Maryam ta yi tare da kwallah kiran sunan Du'a. Jin shiru da ta yi ya sa hankalin ta ya yi matuƙar tashi. Da sauri ta fara waige-waige koh Allah zai sa ta ci karo da Du'a. Can ta hango ta a yashe a kasa. Babu jinkiri ta yi saurin karasawa wajan. Saurin ɗaga Du'a Maryam ta yi. Yayin da ta fara jijigata tana mai kiran sunanta. A hankali Du'a ta fara buɗe idanuwan ta yayin da ta dora su hakan na Maryam. Saurin miƙe wa ta yi sannan ta fara waige-waige. Kallonta Maryam ta yi cike da mamaki ta ce. "Meyafaru Du'a? Me yasa na ganki a yashe a wajan nan. Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. "Babu abin da ya same ni, ina cikin ƙoshin lafiya sannan ta ce. "Maryam kin samu lafiya, babu abin da ya same ki Koh?". Du'a ta ƙarashe maganar tare da tattaɓa wuyan Maryam. Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Kada ki damu ba bu abin da ya same ni, yanzu ina cikin ƙoshi lafiya kin ji. Amma me ya sa na ganki a nan ke ɗaya?, keda waye ku ke a nan?". Amsa Du'a ta ba ta da cewa. "Ba bu kowa Ni kaɗai ce hanan wajan". Tana kaiwa nan ta ja hannun maryam sannan ta nufi kujerun da ke garden ɗin da ita. sai da suka isa wajan sannan Du'a ta zaunar da Maryam ta ce. "Maryam ina so na yi miki wata tambaya. Shin mutum yana iya zama maciji koh kuwa karya ne?". "Mamaki ne ya kama Maryam jin abin da Du'a ta furta. Amsa Maryam ta bawa Du'a da faɗin. "Kin taɓa ji koh koh ganin inda mutum ya zama maciji? Duk wacce ma ta fada miki cewa mutum yana iya rikiɗa ya koma maciji toh karya ta ke domin tatsuniya ce kawai bah wani abu bah. sai dai na taɓa jin wani labari da ummata ta taɓa bani akan wata macijiya". Da sauri Du'a ta kalle ta sannan ta ce. "faɗa min dan Allah ina so na ji". Kallon ta Maryam ta yi ta ce. "Me ya sa na ga kin bi kin damu? Ki bari bah yanzu bah , kinga yanzu asuba ce, kuma kinga ya kama ta muje mu ɗauro alwala domin gabatar da sallah". Riƙe mata hannu Du'a ta yi hawaye na sauka kan kun cinta ta ce. "Inaso ki fada min dan Allah, wannan abin abu ne da ya shafi rayuwata gaba ɗaya, ina so na san ko mai ga me da macizai dan Allah". Ta faɗa tare da haɗa hannayen ta guri guda. "Ni wallahi ban san ta ina zan fara baki labari bah Du'a. kiyi haƙuri nan gaba za ki san ko mai ga me da macizai tun da aka ki ke so". Cewar Maryam. "Shi kenen Maryam tun da baza ki faɗa min bah, zan samu masana wanda suka sani na san za su faɗa min". "Kuma sannan dan Allah da ga yanzu mu daina tafiya tare, saboda ƴan ɗaƙin mu gaba ɗaya aushi na suke ji akan abin da ya faru da ke ɗazu". Murmushi Maryam ta yi sannan ta ce. "Duniya kyakyawan guri ne, guri ne mai matuƙar kyau mutanen ciki masu kyawawan zuciyoyi ne, dan aka ki dunga kai zuciyar ki nesa kada ki bari sheɗan ya ci galaba a kanki". Kallon ta Du'a ta yi tare da faɗin. "Ta ya ya gaba ɗaya mutanen ciki suka zama gaba ga masu kyawawan zuciyoyi? Duda cewa koh wane ƙarni sai an samu azzalumi koh sheɗani, shi ne kuma ki ke cewa masu kyawawan zuciyoyi ne, dan Allah kiyi shiru ki rabu rani". "Da ace kowa addini ɗaya ya ke yi a wannan duniyar, da ba za'a samu kafirai bah, da kowa sai ya fi samun ƴancin kansa". Amma yanzu aikata zunubai da alfasha sun yawaita, Sheɗanci yanzu sune suka zama ruwan dare a cikin zukatan mu". Murmushi Du'a ta yi tana mai cewa. A duk lokacin da Sheɗanci ya kai makurar tsananta, adalci ne kaɗai ke iya yin maganin sa, kamar yadda idan duhu ya mamaye rayuwar ɗan adam toh haske ne ke iya yin maganin wannan duhun". "Duda cewar a makarantar nan ina ji kamar akwai sheɗanu, amma ni samm bazan yi wani abu a kai bah domin bah abin da ya shafe ni bane, amma da ina da halin dakatar da su da kuwa ba bu tantama sai na kawar da su". Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Koda ya shafe ki ma ba za ki iya bah, keda bah kowan kowa bah shi ne za ki ce wai za ki dakatar da sheɗanu makarantar nan, kuma bara kiji na faɗa miki, a makarantar nan ba bu sheɗanu. dan aka ki dinga kiyaye harshen ki dan Allah domin ba bu wanda ya san me zai zo ya biyo baya". Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. "Koh kare ya zama sarki, toh kura ta fi karfin haraji. Idan na faɗi abu toh ki yarda cewa sai na yi, a ƙauye mu har dajin da ba bu wanda ya ke iya shiga ta fito a raye na shiga kuma na fito batare da na ji koda kwarzane ne". "Ƙauye da birni Du'a suna da banbamci, ke ƙauye ki ka sani bakisan birni bah, abin da ki ke gani a kauye bah lallai ki zo birni ki tarar da shi bah, aka zalika abin da ki ke gani a birni babu tabbacin ki iya gani sa a ƙauye". "Ni Allah na tuba ma daji nawa ne ban shiga bah, koda yaushe a makarantar nan muna cikin zuwa excusion, kuma ba bu inda muke zuwa sai daji, domin samo magani cututtuka. Amma bah gashi bah ba bu abin da ya same ni". "Shi kenen" Du'a ta faɗa. Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye tare da nufar cikin hostel. Bin bayan ta Maryam ta yi da kallo tare da sakin murmushi ta ce. "Allah ya yaye miki Du'a". Tana kaiwa nan ita ma ta miƙe tsaye tare da bin bayan Du'a. Ƙarfe takwas ya yi musu a cikin hostel, kafin daga bisani suka fito cikin shigar su ta alfarma. Sanye Du'a ta ke cikin abaya milk colour wanda umma ta aiko a ba ta. Kayan bah ƙaramin kyau ya yi mata bah. Gaba ɗaya ɗalibai idanuwansu akanta. Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Du'a kinga yadda ɗalibai maza da mata suke binki da kallo?". Amsa Du'a ta bata da cewa. "Wannan su ya dama, sun daɗe basu kalle ni bah, ni buri Na yanzu shi ne muyi sauri mu isa inda Ahmad ya ce mu haɗu dan wallahi bana son koma wa ƙauye" ta faɗa tare da fito da sarƙar ta daga cikin kayan ta. Zaro idanu Maryam ta yi ganin sarƙar da ke wuyan Du'a. Baki na rawa ta ce. "Du'a ina ki ka samu wannan sarƙar? Na tabbata wannan sarƙar lu'ulu'u ne kuma zai kai makudan kuɗaɗe kuma naga kamar harda tambarin masarauta a jiki. Du'a a ina ki ka samo shi?" Kallon sarƙar wuyarta Du'a ta yi sannan ta saki murmushi ta ce. "Wai kinq nufin wannan sarƙar? Toh ai wannan sarƙar ta daɗe sosai. Inna ta fe min mamata ce ta bani kyautar sarƙar, nima tashi nayi naga sarƙar a wuyana". Bin ta Maryam ta yi da kallo sannan ta ce. "Du'a kuma kin tabbata ke yar ƙauyen gembiza ce? Dan idai har wannan sarkar naki ne kuma mamanki ce ta baki, Toh bani da tantama kin haɗa jini da sarauta, tabbas kina da halaƙa da jinin sarauta". Kallon baki da hankali Du'a ta bita dashi ta ce. "Kinsan me ki ke faɗa kuwa Maryam? Ni da aka haife Ni can cikin ƙauye shi ne za ki ce na haɗa jini da sarauta, sai dai inaga kece ki ka haɗa jini da sarauta bani bah". Taɓa ta taji Maryam ta yi. Saurin kallonta Du'a ta yi ta ce. "Mene ne?". Nuni Maryam ta yi mata da ɗan yatsarta. Bin ɗan yatsar Maryam Du'a ta yi da kallo, zaro ido ta yi ganin yadda jama'a suka taru guri guda, gefe ɗaya kuma HOD da sauran lectures ɗin makarantar ne zazzau ne. Provost kuma na zaune gede ɗaya, yayin da kowanensu ya ƙagu ya ji mai zai fito daga bakin Ahmad. Gaban Du'a ne ya bada wani sauti. Cikin ɗimauce wa ta ce. " Na shiga uku Maryam, kardai Ahmad ya tara su ne don a kore ni daga makaranta? In kuwa aka ne na tabbata tawa ta kare". Ta faɗa yayin da idanuwanta suka cicciki da hawaye. Jan hannunta Maryam ta yi ta ce. "Dan Allah Du'a ki daina saka ire-iren waɗan nan abubuwan a ranki, in sha Allahu ma ba abin da ki ke tunani bane zai faru kizo muje mu kashe kwarkwatar idanun mu". Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. A'a ni bazan je bah, bana so naje naji abin da zai tayar min da hankali, ke kije kawai ni zan tsaya a nan wajan". "Dallah can Du'a ki tawo muje ba bu ko mai fah kawai dai kina sawa ranki abin da bashi bane bah, kuma akan bah abu bane mai kyau, kawai ki tawo mu tafi". Ta faɗa tare da jan hannunta, ba bu musu Du'a ta bita. Sai da suka isa wajan sannan suka tsaya, yayin da Du'a ta ƙagu taji abin da ya sa Ahmad ya tara ɗalibai da malamai a wajan. Gyara muryarsa Ahmad ya yi sannan ya ce. “Barka da safiya fitattun malamai da sauran mahalarta taron nan. Abin da ya sa ku ka ga na tara ku a nan shi ne saboda, ina so na sanar muku da wata muhimmiyar magana ne. "Kwarai da gaske ni ne shugaba dake kula da ƙoƙarin ƙungiyarsa akan abubuwan ayyukan ɗalibi da tsarawa, tallafin manufofin makaranta daga dalibai, kasafi kasafin kudi, tsara kasafin kudi, sanin abubuwan da suka shafi ci gaba da suka shafi dalibai, da sadarwa tsakanin malamai / ma'aikata da ƙungiyar dalibai, kuma ni ɗaya nake fafutuka wajan kula da fanin ɗalibai". "Shi ya sa nake neman alfarma da a bani wanda zai dinga taimaka min a makarantar nan domin aikin ni kaɗai ya yi yawa". Ɗaya daga cikin lectures ɗin ne ya ce. "Haka ne ne Ahmad maganar ka gaskiya ne, amma naga ko za'a kowa to wacce ta cancanta ita ce Jennifer koh kuma Amina, kuma sannan sai sun cika ka'idoji da kuma ɗaukar alƙawarin cewa za suyi duk abin da ya kamata ba za su taɓa tauye haƙkƙin wani bah". Ɗan jimm Ahmad ya yi sannan ya fara waige-waige. can ya hango Du'a wacce ta yi zuru -zuru tana kallonsa, murmushin mugunta ya saki sannan ya ce. "Akwai wacce nake so ta zama assistant ɗina, kuma wacce kane magana akai bah kowa bace illa Du'a". Zaro idanuwa gaba ɗaya ɗalibai da su Du'a suka yi. Ɗaya daga cikin malamai ne ya ce. "Ta ya ya zamu bata assitan bayan ita new comer ce, wa enda suka yi shekaru a makar nan ba'a basu bah sai ita za'a kalla ace za'a bawa. Ita me ta sani a fanin kula da karatun ɗalibai? Ba zai mau yiwu a ce mu bata bah, saboda har yanzu bata gama sanin dokokin makarantar nan bah, kuma kasan dole sai an yi voting kafin a bata assistant". Kallonsa Ahmad ya yi ya ce. "Ita nake bukata in bah aka bah zan yi withdraw daga makarantar nan. Sai ku zaba koh a saka ta a cikin waɗan da za'a yi voting ɗinsu Koh kuma na bar makarantar nan baki ɗaya". Shugaban makarantar ne ya miƙe tsaye sannan ya ce. "Shi kenen toh Indai har aka yi exam na zaɓe sannan dalibai suka zaɓe ta toh za'a bata mataimakiyar ka, amma kuma indai ba ita taci ba toh sai dai kayi haƙuri, ƙa'ida kuma shi ne". "Zama jami'ar ƙungiyar ɗalibai yana ba ku damar kawo canjin da ku ke son gani a makarantarku. Haka nan yana da ban sha'awa akan CV ɗinku". "Dan aka dole tun da ita ka ke so ta ci sai ka kasance koda yaushe kana bata shawarwari kuma sannan saika dage ka nuna mata hanyoyin da za ta bi. Dan aka Amina jafar, Jennifer David and Du'a Muna so gaba ɗaya ku kasance cikin shiri, in sha Allah next month za'a fara voting, ta yadda kowa zai zabi kuri'ar sa". "Yanzu muna so kowa ya kowa ya koma department ɗin sa". Babu bata lokaci dalibai suka fara watse wa. Sauko wa Ahmad ya yi daga wajan sannan ya riƙe hannun Du'a tare da nufan cikin laboratory room da ita. Ganin akan da Maryam ta yi ya sa ta yi saurin bin bayan su. Shiga cikin wajan suka yi, ganin Maryam na ƙoƙarin shigowa ya sa ya dakatar da ita da faɗin. "Kada ki kuskure ki shigo wajan nan. Babu jayayya Maryam ta bar wajan. Zaunar da Du'a ya yi. Jikin Du'a na kakkarwa ta ce. "Me yasa ka kawo ni wajan nan? Koh kayi tuannin ni yar iska ce kamar..... Bata inda karasa maganar bah taji ya ja mata leɓenta da mugun karfi. Ƙara ta saki! Yayin da taji bakin ta na mata raɗaɗi. Sai da yaga ta jigata sannan ya saki leɓen ya ce. "Waya ce ke yar iska ce, ke wallahi ki kiyaye ni, ni bah kamar sauran mazaje ba ne da zaki min abu na kyale ki ni tattaka ki zan yi a banza a wofi". "Yanzu dai na kawo ki nan ne badan komai bah sai dan na faɗa miki abubuwa game da voting, dan aka ki nutsu ki saurare ni". "Lokacin shirya jawabi don zaɓen Shugaba Koh assistant, yana da mahimmanci ki mayar da hankali kan nuna halayen jagoranci, hangen nesa ga makaranta". "da ikon ki na wakiltar ƙungiyar ɗalibai yadda ya kamata. Anan akwai wasu shawarwari zan faɗa miki abubuwan da za ki iya yi don haɓaka damar ki na cin nasara". "Farko dai, Gabatar da Kanki. Fara da gabatar da kanki da kuma raba kaɗan game da tarihin ki, abubuwan da ki ke so, da kuma dalilin da ya sa kike takarar assistant of head of students". Miƙe wa Du'a ta yi cikin ɓaci rai ta ce. "Mene ne akan? Shin ni na bukaci a bani takara ne a makarantar nan? Kuma ma wai mataimakiyar ka, na rasa wanda zan yi wa bauta sai kai, shin kana cikin hayyacin ka kuwa?. Toh yanzu a ta ke a wajan nan ka yi maza ka koma ka sanar da waɗan da ka faɗa wa zan shiga takara cewa, bakaso bani ka ke nufi ba in bah aka bah..... Tasss taji ya tsinka mata maruka har guda biyu. Cike da ɓacin rai ya shaƙe mata wuya sannan ya ce. In bah aka bah mene zai faru? Shin kashe ni zakiyi koh kuwa za ki dake ni ne?, kin san da wa ki ke ja kuwa? Kin san waye ni? A yanzu da ina so zan iya sa a batar min dake daga kasar nan baki ɗaya". "Ki kiyaye ni in bah aka bah zaki sha bakar wahala". Yana kaiwa nan ya ture ta ta faɗi a kasa. Tari Du'a ta fara yi yayin da idanuwanta suka fara sauya launi, yayin da hawaye ya fara sauka kan kunci ta. Ba bu bata lokaci aka fara yayyafi mai haɗe da iska mai karfi. Saurin dafa kanta ta yi yayin da ta rintse idanuwan ta cikin kunan zuciya ta saki wani irin razannaniyar ƙara". COMMENTS & SHARE PLS 🙏 🙏 🙏 ALKALAMIN ✍️ A'ISHA M.B💞💞💞 (Zinariyar🧝‍♀️Jajirtattu) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5 https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹 *🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍 *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 *LAST FREE PAGE* ️️1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣ WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🪙 Jajirtattu) *___________________________________* Babu zato ya ji jikinsa ya fara kakkarwa, yayin da idanuwansa su ka daina gani gaba ɗaya.ja da baya ya fara yi yayin da ya gigice tamkar wanda ya sha maye. Ganin akan da Du'a ta yi ya sa hankalin ta ya yi matukar tashi. Tattaro nutsuwar ta ta yi sannan ta nufi inda ya ke cikin halin tsaka mai wuya. Ganin tana tunkaro inda ya ke ya sa ya yi saurin dakatar da ita sannan ya ce. "Kada ki kuskure ki karaso inda na ke, in bah aka bah duk abin da ya biyo baya ke ki ka ja". Tsaya wa Du'a ta yi tana kallonsa cike da tsoro da fargaba ta ce. "Ka yi haƙuri da nasan aka ne za ta biyo baya da ban ja da maganar ka bah, ka yi haƙuri ba zan sake bah". "Maza-maza ki fita kafin kija wa kanki masifar da zai yi miki wahala kafin ki fita daga ciki". Ya faɗa yana mai ƙara ja da baya. "Shi kenen zan fita amma dan Allah kasa a janye maganar zaɓen dan nidai ba zan shiga wani zaɓe bah". Cewar Du'a. Rintse idanuwansa ya yi sannan ya buɗe su a hankali ya ɗora su akanta ya ce. "Wannan shi ne zai zama na farko da na ƙarshe da zan gaya miki cewa ki fita daga wannan wuri. Idan ba haka ba za ki sha wahalar da har numfashin ki na ƙarshe ba za ki taɓa mantawa da ni ba. Wannan shawara ce ba gargaɗi bah". "Kuma daga yanzu bana son sake ganin fuskarki har abada, yanzu ki fita daga wurin nan in ba haka ba, zan ba ki mamaki da har ki mutu ba za ki taɓa mantawa da ni bah". Cikin rashin tsoron abin da zai biyo baya, Du'a ta nufi inda ya ke sannan ta tsaya ta kalle shi ido cikin ido sannan ta yi murmushi ta ce. "Har yanzu bakasan wace ce ni bah Koh?, domin naga alamin kana jin ka wani jan wuya a makarantar nan. Toh ka sani cewa ba zan taɓa mika wuya bah domin naga alamin kwata-kwata baka daraja ƴa mace kuma bakasan mahimmancin da ta ke dashi bah a rayuwar ɗan adam". "Ka sani cewa, Wasu raunuka ba sa warkewa, komai nawa lokaci ya wuce. Yadda nake ganin ka ɗin nan, Zuciyata na ji kamar na wargaje ka zuwa gida miliyan". Tana kaiwa nan ta fice ta barsa a cikin ɗaƙin gwaje-gwaje na makarantar. Mamakin kan sa ya soma yi, gsnin mace ta faɗa masa magana bah tare da ya tanka mata bah. Girgiza kai ya yi sannan ya ce "dole ne na gyara mata zama". Takun takalmin da ya ji ne, ya sa shi saurin juyawa. Mamaki ne bayyane kan fuskarsa ganin wanda bai yi zaton ganin bah. A ta ke ta ƙara turnuƙe fuska sannan ya kalle ta a kasƙance ya ce. "Wai ke Amina sai kace mayya, aba dan Allah shin soyayyar nan dole ce koh me, na ce bana son ki amma kin wani na ce min kamar ƙuda". Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Amina ta yi sannan ta ce. "Me ya sa kullun ka ke watsi da bukatuna? Da alama kana kula da kanka ne kawai kuma batare da ka yi la'akari da yadda nake ji". "Na cancanci zama fifiko a rayuwar ka Ahmad, baka taɓa tunanin wane irin hali zan shiga idan na rasa ka. Koda ya ke yanzu ka yi budurwa koh wancan yarinyar sabuwar zuwa, shi ya sa gaba ɗaya ka ƙi karbar soyayya ta Koh? Tsawon shekaru uku kenen ina daƙon sonka amma baka taɓa bani dama dai-dai da rana ɗaya na bayyana maka abin da ke raina bah". "Akan ka, na zama tamkar wacce bata da gata koh kaɗan, duk girman kai na na sauke su duk dan na samu soyayyar ka Ahmad, kayi haƙuri kah bani koh da dama ɗaya ce kawai. Ni kuma ina mai tabbatar maka cewa zan........ Bata inda maganar ta bah ta ji ya ce. "Kina hauka ne? Akwai wani abu da ke damun kwakwalwar ki ne ban sani bah? ban faɗa miki cewa kada ki taɓa kusantar inda nake ba? Na yi kama da mutumin da bai san abin da ya ke yi ba? Na gaya miki sau da yawa Cewa ba zan taɓa soyayya da jahila mara hankali irin ki bah". Kuka Amina ta fashe dashi sannan ta ce. "Toh naji koh da ba za ka karɓi soyayya ta bah, kawai ka amince mu zama abokai nida kai". Takaici ne ya kama Ahmad ya ce. "Shin ke kurma ce bakya jin magana ne? Na ce miki ba zan iya bah koh. Ke sai na ma tsaya yi miki dogon zance? Maza zo ki fita kafin na ɓata miki rai yanzu". "Ka sani duk daren daɗe wa saika soni kuma saina sa ka faɗa a soyayya ta". Tana kaiwa nan ta fice da mugun gudu. Su Jennifer wanda su ka maƙala kunne jikin gini ne su ka gano tawowar ta. Sai da Amina ta isa inda su Jennifer su ke sannan ta fashe da wani irin matsanancin kuka. Rarrashin ta jennifer ta fara yi sannan ta tambaye ta meyafaru?. Duk abin da ya faru tun daga farko har karshe Amina ta zayyane musu. Cikin ɓacin rai Jennifer ta ce. Sai yau nasan da cewa Amina bakida hankali, kema in banda abinki kin san da cewa koh mutuwa za ki yi Ahmad Ba zai saurare ki bah. Kuma kina so ki zama budurwarsa amma ki ke tambayar sa ko zaku iya zama abokai kawai. Me ya sa zai zama abokin ki kawai? Kuma ki faɗa masa aka sannan ki sa ran zai yarda?". Daga sama suka ji muryar Du'a na faɗin. "Kin fara tuntuɓar wani ɗan makarantar nan halinsa? Dana son wancan banzan mutumi, na gwammace in shaƙe da gwada hakan. Idan ni ma ina son ki kuma na sarrafa na nuna miki ƙaramin kore haske kuma ba ki da wayo, kawai na yi watsi da kasancewar ki budurwa ta ya za ki yi, kawai ki manta da shi ki fara sabuwar rayuwa". Cikin huci Amina ta ce. "Ina ruwan ki dani? Shin an gasa magana da ke ne da za ki zo ki wani saka mana baki?". Murmushi Du'a ta yi ta ce. "Baku gasa dani bah, amma kawai na faɗa muku magana ne a kaikaice amma idan na fassara muku abin da nake nufi toh ba za ku ji daɗi bah". Sannan ta ƙara da cewa. " Ƙaunar namijin da ba ya son ka yana da wuyar gaske, amma ba sabon abu ba ne - wannan yanayin ya haifar da yawancin fasaha a duniya, Abin takaici, idan wani ba ya son ka, ba za ka iya canza ra'ayinsa bah". "Samun kan wanda ba ya son ka yana yiwuwa gaba ɗaya, Ba yana nufin keda shi ba ku cancanta ba, ko kuma ba ku isa ba. yana nufin gaba ɗaya jininki bai zo ɗaya da nasa bane koh wani abu mai kyau tsakanin ku biyun. Wasu zan basua son mace mara kamun kai koda kuwa ita ce maƙurar kyau a duniya". "don aka inaga ki dage koh Allah zai sa ya fara sonki". Tana kaiwa nan ta bar wajan. Tsaki gaba ɗayansu suka ja, yayin da Amina ta ce. "Nasan da cewa saboda ita ne ya ƙi ƙarbar soyyayata, amma mudin nasa aka kawar min da ita daga doron duniya toh komai zai dawo dai-dai.". Murmushi Jennifer ta yi ta ce. "Rabu da ita kawata, za ta san duk wanda ya ci tuwo damu miya yasha. Sai mun nuna mata matsayin ta a makarantar nan". "Ke Du'a ina ki ka je tun ɗazu na ke ta neman ki? Shin Ahmad ɗin ne ya tsayar da ke aka kome?". Amsa Du'a ta ba ta da cewa. "rabu da shi zai san dani ya ke, ba'a min na ƙyale wallahi, saina nuna masa bambancin da ke tsakani na dashi". Ɗan jimm Maryam ta yi sannan ta ce. "Aa Du'a ki bi komai a sannu, kinga next week muna da exam wanda kuma kowa sai ya biya kuɗi kafin ya rubuta, kamata ai a ce ki fara neman kuɗaɗen da za ki rubuta jarabawa, bawai ki tsaya ki biye wa Ahmad bah". "Kuma fah Maryam kin kawo magana mai kyau, in sha Allahu ma mi ba zan ƙara shiga harkar sa bah. Kum... Maganar ta ne ya dakata sakamakon jin sallamar Umar daga bayan ta. Juyawa ta yi da sauri sannan ta kalle shi ta ce. "Me kuma ya kawo ka nan wajan?". Kallon mamaki Maryam ta bi Du'a da shi sannan ta ɗaga mata gira ɗaya ta ce. "Shi ɗin wane ne?". Amsa Du'a ta bata da cewa. " Shiɗin sabon aboki na ne, jiya muka haɗu da shi ya ce yana son mu zama abokai". "Ohhh masha Allah akan ma ya yi Toh ya ka ke abokin mu". Maryam ta faɗa. Dariya Umar ya yi sannan ya ce. "Wallahi lafiya kalau alhamdulillah, ya karatu da fatan dai hana mai da hankali kan karatu sosai Koh". Amsa Maryam ta bashi da faɗin. "Eh wallahi karatu sai abin da ya yi gaba, dan alhamdulillah muna mai da hankali sosai". "Masha Allah aka akeso. Dama na zo ne na yi wa Du'a sallama na tafi. Shi kenen Ni zan tafi sai gobe. kuma ku tabbata cewa kun fara karatun exams yau domin ku tsallake sharrin carry over". "In sha Allahu zamu yi karatu". Cewar Du'a. Shi kenan Toh sai goben. Yana kaiwa nan ya shige cikin motarshi sannan ya fice daga makarantar. Duk abin da suke akan idanuwan Ahmad wanda ya jingina jikin motarsa yana hayyana wane irin azabtar wa zai yi wa Du'a ya ji sauƙin abin da ta yi masa. Abdul ne ya karaso inda Ahmad ya ke yana mai cewa. "Babban president bada kanka a sare, me aka yi maka naga ranka a bace?". Kawar da kansa Ahmad ya yi ya ce. "Bana son takura Abdul, ka rabu dani ka yi abin da zai finshe ka, bawai ka tsaya ka dinga tsegumi bah". Kallonsa Abdul ya yi ya ce. "Ahmad ni ka ke cewa ina maka tsegumi,Ahmad ni". Ya faɗa tare da nuna kan sa. Sannan ya kara da cewa. "Shi kenan Ahmad in sha Allah ba zan sake tambayar ka wani abu wanda ya shafi rayuwar ka bah". Yana kaiwa nan ya bar wajan. Tsaki Ahmad ya ja sannan ya ce. "Ka ji dashi, shashancin banza kawai". Wayarsa ya ji ta fara Ringing, dauka ya yi sannan ya shige cikin mota tare da jan motar ya bar makarantar gaba ɗaya. "Ke Du'a gaskiya Umar ɗin nan yana da mutunci sosai, har namiji ya zo ya ce yana son ku zama abokai bana soyayya bah kinga mutumin kwarai ne. Gashi kyawawa amma fah bai kai Ahmad bah". Takaici ne ya kama Du'a ta ce. "Ni fa idan muna tare da ke bana son ki dinga ambatar sunan wannan mutumin a inda na ke. Kuma shi Umar ɗin da ki ke magana akai ma ni ban yarda da shi bah wallahi , gaba ɗaya fuskarsa baiyi kalan mutanen kirki bah. Kin san ance, Kada ka yanke hukunci da littafin da murfinsa (don't judge book by it cover)". "Haka ne Du'a ban musan dame ya zo mana dashi bah, koma mene ne aniyarsa ta bishi". Yanzu muje kawai mu fara shirye-shiryen exam na first semester, Na riga dana faɗa wa umma komai kuma ta ce in sha Allah za ta tura mana da kuɗin". "Shi kenen" kawai Du'a ta furta. Yayin da kai tsaye suka nufi cikin hostel. Bah dare bah rana su Du'a suke fafutuka wajan karatun exam. Yayin da suma sauran ɗalibai na course ɗinsu suke karatu sosai. Gefe ɗaya kuma tsakanin Du'a da Ahmad ba bu wanda ya sa ke haɗa ido da wani. Gefe ɗaya kuma ƴan ƙauyen su sun yi fafutuka wajan neman kuɗin da Du'a za ta rubuta jarabawa, aka suka dinga siyar da amfanin gonar su don cika muradin ƴa ɗaya tilo wacce za ta zamo jagoran ƙauyen. Inda a karshe da ƙyar da wahala suka samu suka haɗa dubu amsin kuɗin jarabawa. Ya Inna wuro ce ta kira Du'a a wayar mai gari sosai suka gaisa da Du'a yayin da Inna wuro ta ce wa Du'a. "Ƴata kiyi min alƙawarin cewa ba za ki faɗi wannan jarabawar bah, idan ki ka faɗi toh ki sani cewa ba zamu kara baki kuɗin karatu bah sai dai kije ki nemi wanda zai dinga biya miki kuɗin jarabawa. Dan aka ki dage sosai dan bakisan irin wahalar da muka sha bah wajan ganin mu fidda wannan kuɗin". Murmushi Du'a ta yi ta ce. "In sha Allah Inna ba zan taɓa yin rashin nasara bah, a koda yaushe zan kasance cikin yin nasara ne. Dan aka ku kwantar da hankulanku wannan jarabawar kamar naci ne". Ranar Monday su Du'a suka rubuta jarrabawar su da kwarin gwiwar cewar za su yi nasara a wannan jarabawa. Yau ne ta kama ranar Friday, wato ranar da jarabawar su ta fito. Du'a na hango ita da Maryam sun ci hijabi onion colour wanda bah karamin kyau ya yi musu bah, bare ma Du'a wacce hijabin ya yi matuƙar karbarta. Dafa Maryam Du'a ta yi ta ce. "Maryam ba zan iya karasa wa wajan da ake duba wa bah jarabawa bah, baki ga yadda ɗalibai suka cika wajan bah?. Kuma ni ina tsoro kada naje naga na faɗi, don zuciyata tana raya min cewa banci wannan exams ɗin bah". "Aba Du'a an ce fah faɗi alhkairy ko ka yi shiru, in sha Allahu ma babu abin da zamu je mu tarar sai alhkairy dan aka tawo muje". Tana kaiwa nan ta ja hannunta suka nufi wajan. Tsaya wa suka yi ganin sun isa wajan. Dubbuba sunanta Maryam ta fara yi yayin da ita ma Du'a ba ta yi jinkiri bah wajan duba na ta". Ihuun! jin daɗi Maryam ta yi tans mai faɗin. "Du'a na aye alhamdulillah naci jarabawata duka bani da carry over". Murna sosai Du'a ta taya ta, yayin da ita ma Maryam ta taya ta neman sunanta a jerin daliban da suka ci jarabawa. Amma ina sunyi neman duniya basu ga sunanta bah. Hankalin Du'a bah ƙaramin tashi ya yi bah ganin ba bu sunanta. Kallonta Maryam ta yi ta ce. "Kiyi haƙuri Du'a". Kallonta Du'a ta yi ta ce. "Me ya sa ki ke bani haƙuri kuma?". Amsa Maryam ta ba ta da cewa indai bski ga sunanki bah toh akan yans nufin baki ci wannan jarabawar bah, kin faɗi Du'a". "Ƙarya ne! Du'a ta faɗa da mugun ƙarfi. Sannan ta ce. "Duk karatun da nake yi bah dare bah rana kenen akan yana nufin ya tafi a banza kenen, wallahi ba zan yarda bah". Tana kaiwa nan ta nufi office ɗin HOD ɗinsu. Ganin akan da Maryam ta yi ya sa ta yi saurin bin bayan Du'a. Da sallama ta shiga office ɗin hawaye shaɓe-shaɓe kan fuskarta. Kallonta HOD ya yi ya ce. "Lafiya? Me aka miki ki ke kuka? Shin baki ci exam bane?". Tambayar da ya shiga yi mata kenen. Cikin sheshekar kuka Du'a ta ce. "Na faɗi jarabawa ta kuma ina da tabbacin wani ne ya sa aka faɗar dani a exam saboda naji ance kuna karɓar cin anci a makarantar nan, dan aka ina son sanin wanda ya sa aka faɗar da ni a jarabawa". Kallonta HOD ya yi sannan ya ce. "Me ki ke nufi da cews muna karɓar cin anci, shin ke bakya daraja manya ne, wato ni ne nake karɓar cin anci koh, Ni ɗan sanda ne kenen mai karɓar kuɗin mutane". Haƙuri Maryam ta fara bashi tare da jan hannun Du'a. Wafce hannunta Du'a ta yi daga na Maryam sannan ta nuna Maryam ta ce. "Kada ki kuskure ki kara taba ni, dan wallahi komai zai iya faruwa. Maida kallonta ta yi kan HOD ɗin ta ce tambaya na karshe waye ta baka kuɗi ka saka na faɗi a jarabawa bayan maƙudan kuɗaɗen da muka biya". Amsa HOD ya bata da cewa. Ahmad ne. Shi ya faɗa min gaba ɗaya halayen ki marasa kyau. Ashe dama satar amsa ki ke yi bah ƙoƙarin ki bane, sannan kina google amsa a cikin wayar ki bayan an hana shiga da waya cikin exam hall. Dan aka ɗauki exams ɗin ki, ki fice min daga office". Jikin Du'a ne ya mutu jin kalaman HOD. Rintse idanuwan ta ta yi cikin kunan zuciya ta ce. "Ahmad me ya sa za ka min aka? Me nayi maka da ka nemi gurɓata min suna a idon duniya, tabbas bazan kyale ka bah, a yau komai zai ƙare". Tana kaiwa nan ta ɗauki takaddun tare da bangaje Maryam ta wuce. Da sauri Maryam da HOD suka bi bayanta yayin da suka dinga kiran sunanta. Can ta hango shi kan motarsa yana latsa waya. Ba bu jinkirtawa ta karasa inda ya ke. Hango ta da ya yi ya sa shi sakin murmushi sannan ya sauko daga motar. Du'a na kaiwa inda ya ke, bata yi wata- wata bah ta watsa masa takaddun a fuska. Ba bu ɓata lokaci gaba ɗaya ɗaliban makarantar suka taru suka zagaye su. Cikin ɓaci rai da kunan zuciya ta ce"Gasu nan ka je ka cinye. Yanzu ai burin ka ya cika kasa na faɗi a jarabawa. Maza jeka haɗa shagali kayi murna". Ta karasa maganar tare da fashe wa da matsanancin kuka mai ratsa zuciya. Cikin sheshekar kuka ta ce. "Kasan ta yadda aka samu aka biya min kuɗin wannan jarabawar? Kasan irin wahalar da ƴan ƙauyen mu suka sha kafin su fitar da wannan kuɗin, me ya sa ba za ka rama fansar ka akaina bah sai akan jarabawa da na dora rayuwata akai". "Da a ce baka sa na faɗi jarabawa bah da yanzu nasan na riga dana faɗa wa ƴan ƙauyen mu, amma yanzu banida fuska koh kwarin gwiwa da zan iya fuskantar su nace musu na faɗi jarabawa". "Da badan kai bah da yanzu ina cikin farin ciki da annashuwa. Shi kenan yanzu ka rusa min babban mafarki na, saboda ba zan iya ci-gaba da karatu a makarantar nan bah, tafiya zan yi na bar wannan makarantar". "Na tsane ka, bana son sake haɗuwa da wannan fuskar ta ka wacce gaba ɗaya zuciyarta bushashiya ce. Ka sani cewa zan ɗauke ka ne a matsayin wanda ya taɓa tsayar min da farin ciki na". Tana kaiwa nan ta juya da niyar tafiya. Cikin rashin sa'a ta ji ya fizgo ta jikin sa. A fusa ce ta ture shi yayin da ta saki wani irin ƙara tare da buga kafarta na dama a kasa da mugum ƙarfi. Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara wata ieiyar iska da guguwa wacce ta karaɗe gaba ki ɗaya makarantar, wanda hatta kai ga bishiyoyin makarantar suna karyewa. Ba bu ɓata lokaci suka ga macizai suka fara fitowa ta koh ina. Ihuuun ɗalibai ne gaba ɗaya ya karaɗe makarantar, yayin da kowa ya fara yin ta kansa. Banda Ahmad wanda koh gizau bai yi daga inda ya ke, saima ƙara gyara tsayuwar sa da ya yi. Yayin da idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir. Gaba ɗaya ɗaliban ne suka ja da baya inda suka bar iya Ahmad da Du'a a tsakiyar makarantar yayin da kowanensu na fuskarta ɗan uwansa. A ta ke macizai suka fara zagaye Du'a da Ahmad. Babu shiri jikin Du'a ya fara kakkarwa, yayin da fatarta ya fara saɓulewa. Duk abin da ya ke faruwa akan idanuwan ɗalibai da kuma malamai na makarantar. Ganin akan da shugaban makarantar ya yi, ya sa shi saurin kiran jami'an tsaro. Kallon Ahmad Du'a ta yi ta ce. "Jarumtar ka ba zai taɓa burgeni bah, domin a yau bah gobe bah za ka mutu, domin kuwa kashe ka za suyi. Murmushi Ahmad ya yi sannan ya ce. "Kwarai kuwa ba bu tantama kece wacce na daɗe na ke nema kuma yau gani ga ki a gabana. a yau za ki san koh ni wane ne. 🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍 YANZU WASAN YA FARA🏹🔪🗡️. SHIN AHMAD WANENE? ME YASA YA DAƊE YANA NEMAN DU'A, SHIN DAMA A CAN DA YA SAN DA ZAMANTA NE KOH Aa. KODAI SHIMA BAH MUTUM BA NE. TOH KAWAI KUDAI KU BIYO NI DAN JIN YADDA ZA'A KAYA. *END OF FREE PAGE* COMMENTS & SHARE PLS 🙏 🙏 *MASU SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN RAYUWA DA MACIJIYA SAI KU BIYA KUƊI DOMIN A SAKA KU A ƊAYAN GROUP DIN WANDA ZAN CI-GABA DA KAWO MUKU RAYUWA DA MACIJIYA.* IDAN KIN SHIRYA BIYA SAI KI BIYA DOMIN A SAKA KI A DAYAN GROUP NA PAID. *PAID BOOK ₦400 complt* kacal babu tsada *9043687746 Hassana Aliyu Opay bank* *Evidence of payment* 09130398321 KADA KU BARI A BAKU LABARI. ALKALAMIN ✍️ BY A'ISHA M.B💞 (Zinariyar 🧝‍♀️ Jajirtattu)