a: LITTAFIN KUƊI NE, BA DANNI BA DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH. LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE, WANNAN NA KUƊI NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 A TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 AISHA ADAM JA'IZ BANK EVIDENCE OF PAYMENT TA WANNAN LAMBAR 07063065680 46_47 shiru Yusuf yayi yana kallon Widad, yayin da yaji gaba ɗaya hantar cikinsa ta kaɗa jin abunda Widad ɗin ta faɗa, ta kalleshi tace "Ya naji kayi shiru ne? Akwai matsala ne?" girgiza mata kai yayi yace "A'a babu komai" Widad tace "Shikenan, ga Abinci can, kaci seka sha magungunanka ka kwanta" Kasa motsawa yayi daga inda yake, balle ya aikata ɗaya daga cikin abunda tace, sake kallonsa tayi tace "wai ko dai jikin ne?" Girgiza mata kai yayi yace "A'a jikina ai na warke" " to ai gani nai duk ka wani koma so silent, shiyasa nayi zaton ko jikin ne, ka tashi zan kwanta " Yusuf ya miƙe, ya bata guri ta gyara shimfiɗar ta ta kwanta, yayin da ya koma gefe yayi jugum kamar wanda aka gayawa saƙon mutuwa. A ƙoƙarinsa na kaucewa zargi daga Widad, ya miƙe ya ɗakko Abincin da niyyar ya fara ci, Amma gaba ɗaya ya ya kasa, tunani burjik a zuciyar sa, ga labarin da Saleh ya gaya masa, ga kuma itama abunda ta faɗa masa yanzu, ashe dai da daru a gaba, ko wane irin hukunci zata yi masa idan ta gano shi jami'in sirrine? Gashi zuciyarsa ta riga ta gama kamuwa da tsananin ƙaunar Widad, yana matuƙar jin sonta a ransa, a yanzu haka dama yana ɗar ɗar, saboda yasan bashi da tabbacin idan suka koma gida Widad ta cigaba da zama da Auren sa, dukda a yanzu yana ƙoƙarinya jarraba Widad yaga ko tana son shi, a ƙaddara ma ta yadda da Auren, su cigaba da zama tare, waye yasan Aure suka yi, Saleh ne kawai sheda ta yaya zasu fuskanci mutane suyi musu bayanin wannan rikita rikita?.    Nan da nan wani irin gumi ya shiga tsasttsafowa Yusuf, lallai akwai ƙura a gaba, kasa cin Abincin yayi, dama gashi bakinsa babu ɗanɗano saboda zazzaɓi, dan haka ya ajiye Abincin a gefe ya nemi guri ya kwanta, sedai kamar yadda beyi tsammani ba, bacci ya ƙauracewa idonsa se tunani, yanzu meye mafita? Ta ina ze tunkari Widad yayi mata bayanin waye shi, dan kamata yayi ace shi ya gaya mata ba wani ba. Haka nan jiki a sanyaye ya cigaba da tunani, ya daɗe a zaune ba tare da ya kwanta ba, yana ta saƙawa yana warwarewa. Muryar Widad yaji tace "Tunanin Meka ke hakane wai?" Da sauri ya dawo daga tunanin da yake yace "Babu komai karki damu" "Ko kana tunanin gidane, da Ummanka?" Murmushin dole ya ƙaƙalo yace "A'a" "Nasani dole zakayi tunanin gida, nasan baka jin daɗin zaman garin nan, ko baka faɗa ba zaman garin nan ba daɗi, Amma ni ta wani ɓangaren rahama ne a gare ni, bana fargaba ko tashin hankali saboda maƙiyana, ina matuƙar jin daɗin karamcin da mutanen gidan nan suke min, dukda yadda zaman garin ke bani wahala, amma karamcin su da goyon bayanka na ƙara bani ƙwarin gwiwa, tabbas duk wani motsi da zanyi ina tunanin Daddy, ina tunanin wani hali yake ciki, me yake yi? Nasan ina ransa, sedai ina masa Addu'a zuwa lokacin da Allah ze kawo ƙarshen wannan abun in koma gida, kaima kayi haƙuri nasan duk nice silar shigar ka wannan halin" Ta ƙarasa maganar cikin damuwa. Yusuf yace "bana dana sanin kasancewa ta dake anan, saboda karamcin mahaifinki da yadda da yayi dani beci ace na bar 'yarsa ɗaya tilo ta shiga wani hali in kasa temaka mata ba, sedai dole inyi kewar Ummana, bata da kowa seni, mahaifina ya rasu, gata marainiya ni kaɗai ne a kusa da ita muke rayuwar mu tare, Allah kaɗai yasan irin damuwar da take ciki, dan tunda na tashi ban taɓa nesa da ita ba, nasan tana cikin damuwa " Cikin tausayawa Widad tace "Allah sarki, dole zukatan makusantan mu su shiga damuwa, har gara kai wataƙila bayan mamanka akwai wanda zasu damu da halin da kake ciki na ɓatan da kayi, nikam daga Daddy na se Bulama nasan sukaɗai zasu damu, duk wanda yake tare dani, yana tare dani ne dan wannan dukiyar, nasan da babu ita da bazasu nunamin so ba, kuma nasan zagina suke a bayan idona, shiyasa nake wa mutane wani kallo na daban, a da na zata duk mutane miyagu ne, kuma talakawa zasu iya komai akan kuɗi basu da kirki, sedai wani darasi da nayi shine, shi rashin kirki ba'a talaka ne ko me kuɗi ba, a mutum ne kawai, na samu misali akanka da kuma mutanen ƙauyen nan, basu san koni wace ba, amma suna ta kyautatamin" Yusuf yace "hakane kam, naga kin sake dasu sosai kamar bake ba, kamar ba kece me wannan AƘIDAR ta ƙin mutane ba, me yiwa mutane kallon miyagu ba" "Hmm ina da dalilin yin hakan, ka kwanta dare ya fara yi, kaga baka da lafiya akwai buƙatar ka samu isashen bacci" Yusuf yace "Hakane, kema ki kwanta my queen" 'ba zaka dena faɗar wannan sunan bako? " "Dama bakya son sunan ne? " "ban sani ba, ai kasan nace maka bana so" Yusuf yace "ni gaskiya daɗin sunan nake ji, My Queen, My life, I love you so much My dearest Queen" Tsaki tayi, ta canza position ɗin da take kwance ta toshe kunne ta, wai danma karta cigaba da jin meze ce" Yusuf yayi murmushi, ya kwanta sedai fa bacci yaƙi yuwuwa, saboda saƙawa da warwarewa da yayi tayi, akan ya sanar da Widad gaskiya waye shi, kokuma karya gaya mata? "Barrister Hafiz, kuyi duba a cikin lamarin nan da kyau, ku tsananta tunani kafin yanke hukunci, akwai gwagwaɓar riba da zaku samu idan akayi wannan harƙallar daku, zaku samu alheri fiye da tunaninku, zaku samu arziƙin da baku samu a harkar aiki bama" Barrister Hafiz ya gyara zama yace "Abunda nake so ku fahimta anan shine, wannan aikin fa hatsari ne dashi, mu sa hannu a siyar da kadarorin Daula, karkuyi mamaki akwai masu bibiyar al'amuran dukiyarsa bamu sani ba, idan abu yazo ya tonu sunanmu ze ɓaci, kuma mu rasa aikin mu, sannan mu fuskanci fushin hukuma" Alhaji Musa yace "Barrister, sha'anin ƙasar nan tamu yanzu kowa mafita yake nemawa kansa, da kayi ƙaramin laifi a kaika prison a banza, gara kayi gagarumi wanda zaka samu mafita a al'amuranka, kuɗi zaka samu manya ba ƙanana ba, wanda baku taɓa zaton samu ba, kuma a yanzu waye yasan inda Daula yake? Idan abubuwan nan suka samu zaku iya barin ƙasar ma gaba ɗaya, dan haka ku san dabarun da zakuyi, kuyi mana wata takarda da zata nuna yayi holan wasu daga kadarorinsa, a bisa farashi me sauƙi ". Ya kice gumi Barrister Hafiz yayi yace" Yallaɓai akwai buƙatar a ɗan bamu lokaci, zamuyi shawara tukuna " "Shikenan, amma bama buƙatar a ɓata dogon lokaci, muna sauraren ku" "Shikenan yallaɓai, sekun jimu" Hajiya Sarah ce zaune gefen Bulama, yana shan tea yana karanta jarida, tace "Yallaɓai, dan Allah ka tausayawa Hajiya Halima, kasa baki a sakar mata ɗanta, gaba ɗaya ta kasa nutsuwa, hankalin ta gaba ɗaya baya jikinta saboda damuwa" Bulama ya nisa yace "banƙi ta taki ba, amma baki fini son Halima ba, da ina da yadda zanyi da zanyi ƙoƙari in saka a fitar da shi, amma wannan case ɗin ba ƙarami bane, idan na matsa sunana ze iya ɓaci" "Hakane amma ya kamata kayi wani abu, koda ta ɓangaren kwantar mata da hankali ne, Allah kaɗai yasan halin da take ciki, ba ƙaramin abu bane uwa ta iya jure ɗanta a wani yanayi, idan ka bincika babu lallai ko Abincin kirki tana iya ci" "Eh to banƙi zancen ki ba, amma Halima mace ce me taurin kai da rashin haƙuri, maimakon tayi haƙuri a bi komai a hankali, amma se azalzala ta take, irin wannan lamarin a hankali ake binsa, amma ita ta fiye garaje, case ɗin nan ba ƙaramin case bane ba, karki manta Daula ne fa aka nema aka rasa, kuma shine yake kula dashi, gaba ɗaya ana saurarar hukuma aji me zasu ce, Amma insha Allah ze fita " Hajiya Sarah tace " shikenan, Allah yasa amma tana cikin damuwa sosai, Allah ya fitar dashi, dan yaron kirki ne sosai " Bacci be ɗauki Yusuf ba se wajen Asuba, dan haka da Asuba kasa tashi yayi, Widad ce ta fara tashi taje tayi alwala, ta dawo amma be tashi ba. Hannu tasa tana ɗan dukan ƙafarsa tace " ka tashi ka makara fa yau " A hankali Yusuf ya motsa yace "Subhanallah, kuma shine zaki dinga dukana haka da ƙarfi, sekin jimin ciwo?" "wannan ɗan dukan ne zan ji maka ciwon?" "Eh mana duba gurin kiga, har yayi ja fa, kin zage ƙarfinki kina ta faman dukana" Dagewa tayi ta ƙara masa wani dukan tace "wannan kuma se kace na karya ka ko?" Yusuf yace "kai, tabbas idan na riƙe ki se na rama, zan rama wannan dukan da kika yi min" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje domin yin alwala yazo yayi sallar Asuba. Da gari ya ƙara haske, Gwaggo ta aiko musu da koko da ƙosai, Widad ta zauna ta dinga tsintar ƙosan ta naci, tace bata shan kokon, shikam Yusuf yaji daɗin yadda ta fara sakewa, yanzu tana iya cin Abincin su, dukda a yanzun ma bakomai take iya ciba, amma tana iya cin wasu abubuwan, yanzu wanke wanke ma, ita take abunta ta wanke banɗaki, wataran kuma Hindu ce ke mata. Yusuf ya kalleta yace "meyasa ba zaki haɗa da kokon ba?" "nifa ba son wannan kokon nake ba, wataran ji nake kamar zanyi amai idan na sha" Yusuf yace "Allah yasa Baba Hari ta jiki, Kisha faɗa da baƙar magana" Dariya Widad tayi tace "Aikuwa dai, ai gaba ɗaya matar nan comedy ce, komai ta gani se tayi magana, wani abun ina sane nake yi, amma bata ganewa taita faɗa" Yusuf yace "Hmm Allah ya shiryeki to, aini ban san haka kika iya neman magana ba, ganin cewar a baya ko maganar ma bakya son yi, idan anga fara'arki to da magenki ne roux ko kuma Daddy" "Allah sarki, harka tunamin da sister roux ɗina, nasan tana missing ɗina, maybe ma yanzu sun barta ta mutu saboda yunwa, nasan bame kulamin da ita, nima haushina suke ji balle magena" Yusuf yace "Eyya Sorry, Insha Allah bata mutu ba zamu koma ki tarar da ita tana nan" "Hmm is very hard gaskiya, am missing Home Yoseef, ina tunanin dabbobina gaba ɗaya nasan suna missing ɗina" "wai me yasa kikafi son dabbobinki akan mutane, kina ƙaunar dabbobi sosai" Widad tayi ajiyar zuciya tace "labarin yana da tsayi sosai, Amma tabbas dabbobi sun fiyemin mutane, except in some circumstances, duk abu indai dabba ta shaƙu da kai, ba zata yadda a haɗa kai da ita a cutar da kai ba, amma dan adam fa yana iya manta dukkan alkhairinka a hada kai dashi a cuceka, shiyasa na zabi rayuwata a cikin dabbobi” Yusuf yace “hakane maganarki amma sedai ba duka aka zama daya ba, Amma na Allah  ai basa karewa sannan ba yadda zaai ace mutum yayi rayuwa ba mutane" Widad tace "kai ka ga haka, nikam nayi, kuma yafi kwanciyar hankali" Yusuf yace "Ai ba ƙaramin mamaki nayi ba, ranar dana ga kina sukuwa akan doki" Widad tayi murmushi tace "i miss that Moment, ko a England ina wasan polo, ina son tseren dokuna sosai" Yusuf yai murmushi yace "ko tsoro ba kya ji" Daga nan  be kuma cewa komai ba ya maida kai yayi shiru yana da  cin abincin a hankali, widad ta kalleshi tace kamar " akwai Magana abakinka da kake so ka gayamin,naga jiya tun jiya kana ta yawan kallona" Yusuf yace aini kullum cikin kallonki nake, babu wani abu da nake son gayamiki "shikenan tunda kace haka,amma gara inda akwai ka gaggauta gayamin, bazan takuraka seka gayamun ba amma nasan akwai abunda yake damunka” “kinfara samun ido kenan?” “ba ido nake samka ba, yanayinka ne ya nuna min, amma shikenan ba ina kokarin matsa maka bane, ko son sanin me kake ciki ba, ni bari in tashi in fita in dan sha iska” Yususf ya kalleta yace “bana son kifita ki barni,ina jin daɗin hirar nan da muke” Yamutsa fuska tayi tace  "ni kuma na gaji da zaman dakin, dan haka waje zan fita” Yusuf yace “shikenan tunda haka kike so,your wish is mine my queen” “ka ji dashi dai, inka gama karka manta da shan maganinka" daga nan tai waje abunta Alhaji Haruna ne shida Alhaji Munir suke cigaba da tattaunawa akan al amuransu. Alhaji Munir yace "‘anya baka ganin ayi kokari a sakarwa matar nan danta, da yasan inda Daula yake iya azabar da aka gana masa ya isa ya fadi inda yake, amma tunda be faɗa ba to tabbas besan inda yake ba, gashi ana batun tafiya kotu, karfa matar nan ta tona mana asiri” Alhaji Haruna yace “ka kwantar da hankalin ka, hakan ma duk shirine, idan sun tafi kotu, za a dauke hankalin mutane daga wasu abubuwan, da zarar hankali ya dauke ya karkata can, mukuma semu cigaba da barnar mu, kafin a farga mun kwashi abunda muka kwasa koda wancan abubuwan basu samu ba” “banƙi ta taka ba, amma ka gane wani abu guda daya, mudinga yi muna ankarewa da abunda ze biyo baya, yanzun idan aka shiga kotun nan slide mistake ze iya sakawa asrinmu ya tonu, sannan maganar  da muke har yanzu fa babu wanda yasan inda yaran nan suka shiga, tunda suka gudu har yanzu shiru babu labarinsu, babu labarin inda suka tafi, kuma har yanzu basu dawo garin nan ba, gaba daya a tsorace nake, kuma yakamta ace zuwa yanzu shi wannan yaran da muka sa su sace su me adda yake kowa?, yakamata ace basa raye bekamata abarsu suci bulus ba,suma fa hatsarine as garemu” Alhaji Haruna yayi murmushi yace “Alhaji Munir ikon Allah, kaikam wasu lokutan akwaika da tsoro, munefa masu kasar nan, ko yaya muka ga wani abu na shirin kawo mana tangarda zamuyi maganinsa, mukeda hukumar tsaro kudi da masu mulki, kai a tunnainka har akwai wani wanda ze kawo mana tarnaki ne? ka sha kuruminka, komai a tsare yake, shekara nawa mukayi ana tafiyar nan, ba tare da an samu mtsala ba? Karka manta Alhaji Bukar ma fa namune, kadai mubi komai sannu” Alhaji Munir yace “ duk nasan da wanan, amma abunda nake so ka sani shine,wannan mahaukaciyar matar fa zata iya komai idan taji za a kaimata danta prison,bafa zata zuba mana ido tana kallo danta ya tafi prison ba” “karka damu za a san yadda za ayi da ita” “shikenan, amma nifa kwanan nan na fuskanci wasu halaye da Musa yake yi, sam na kasa gane kansa fa” “ba kai kadai ba, nima kallonsa kawai nake, kar ace na fiye matsawa ne ko neman rigima shiyasa kawai nake kyleshi” Alhaji Munir yace “Banda shi mahaukaci ne, wai takara ze fito, ubanwa ze zabeshi bayan bakin tabon da Daula ya goga masa, ai mutane ba mahaukata bane” Alhaji Haruna yace “kyaleshi ai ya zata mutane basu da hamnkali, a da alokacin da yayi siyasar ma ai farin jinin Daula ne yasa aka zabeshi, ba wai dann ya cancanta ba, mu zuba masa ido ya cigaba da haukansa tunda bashi da hnakali” “aikam babu alamar hnakli, gara yaje mutane su cinye ɗan abunda ya tara ɗin ai, se sun talauta shi sannan yazo ya fadi zaben, mutum se taurin kan tsiya, baya ɗaukar shawara sam, indai 'yan siysa ne zasu ziga shine, su cinye komai idan ya fadi su gudu su barshi” Alhaji Musa yace “:ai shiyasa ban damu da in bashi shawara ba gara yaje suma suci rabon su, daga baya yayi hankali ai” ‘shikenan, ni bari in wuce se munyi waya” “shikenan,semunyi waya” Daga na sukayi sallama. Ganin wucewar Hajiya Halima ne yasa Ramlah bin bayanta zuwa dakinta, tana zuwa tace “Mummylafiya kuwa?” Zama hajiya Halima tayi tace “ina fa lafiya, wai kotu za akai Anwar kotu fa Ranlah” “mummy wane irin kotu kuma? Ba za bada belin nas ba ?” “sun hana , sunce ba zasu bada belinsa ba, kuma wadan nan banzayen sunki suyimin komai akai, sun barni se wahala nake nikadai, nikadai na haifeshi nikadai nake wahala ta, dan san abunda ze biyo baya kenan da ban barin Anwar yaje yana wannan wahalar ba, idan yaso ba zagi ba ko tsinewa ce duniiya sumun baze dameni ba,amma ina kallo akaimin da na prison baze yuwu ba, niba abun  in tona asiri ba, nima zan kwana a ciki, da sedai ayi duk wadda za ayi” Ramla tace ” mummy kiyi hakuri, ki kwantar da hankalinki, idan kika fallasa ba iya asirinsu ba hatta namu muma ze tonu ne, dan haka kiyi hakuri mubi a hankali” “wani irin mubi a hankali komai yana lalacewa, in zuba ido akaimin ɗana prison sam baze yuwu ba wallahi, ana shiga kotu nasan prion ne zasuce zasu kaimin shi” “babu me kaishi prison, kidena damun kanki, Anwar ze fito” Haka taita kwantar mata da hankali. Tunda widad ta fice tsakar gida bata sake komawa ɗaki ba, tana maƙale da Gwaggo da Hindu tana koyo aikin gida, yayinda gefe guda sunayi suna faɗa da Hari, yayinda Hanne keta jifanta da bakaken maganganu, wani abun Widad ta gane wani ba zata gane ba, dan wata hussar ina tayi tsauri bata ganewa sam, ita dai tafi maida hankali akan ta koyi aikin,Gwaggo bata hantarar ta idan tayi ba daidai ba seta gyara mata cikin ruwan sanyi. Saleh ne ya shigo gidan, ya tarar Widad zatayi tatar gasara, tanata kokowa da abun tatar Gwaggo tana gyara mata, gashi ta maida duk hankalinta so take ta koya, gwanin ban dariya da tausayi. Saleh yace "Ina kwana ranki ya dade?” Dagowa widad tayi ta kalleshi cikin basarwa tace “lafiya kalau” Saleh yace  “aiki kike ne?’ Gwaggo tace “aikam aiki muke tayi” ”madallah sannu da kokari Gwaggo, ya me jiki kuma?” Gwaggo tace “jiki da sauki Alhamdilillah” “mashaallah, bari inshiga in duba shi” Widad na jinsu tayi masa banza taki kula shi. Da sallama Saleh ya shiga dakinsu Widad, ya tarar da Yusuf a zaune yayi shiru yayi zurfi a duniyar tunani, Yusuf ya dago ya amsa. Saleh yace “ya dai ko jikin ne?” Yusuf yace “ jiki ai naji sauki Alhamdilillah” “madallah ai haka ake fata, ai can naga mutuniyar taka a tsakar gida tana ta kokawar yin tatar gasara, se barna take” Yusuf yayi dariya yace “danma baka ga yadda take tankaɗe ba, bakaga asarar garin da tayiwa Gwaggo ba, ai Gwaggo ba karamin mutunci take man aba, se fatan Allah ya sakamata da alkairi” Saleh yace “ai abunma da takaici ace yarinya kamar wanna bata iya aikin gida ba,abun da kunya ai” “yakamata kiyi mata uzuri da an koya mata da zata iya ai” Saleh yace “waye ze koya mata, ta dinga hantarar mutum tana masa wulakanci” Yusu yace “adinga kara mana matata ce fa Saleh” Sale yai murmushi yace “masu mata manya,to Allah ya bada hakuri, na manta ne, Allah yasa in an tashi komawa a tafiwa da Daula jika” Shiru Yusuf yayi bece komai ba yana tunani, Saleh yace “lafiya kuwa?” Yusuf yace “Saleh akwai matsala ina cikn damuwa sosai, har yanzu bata san waye niba, bana son taji a wani gurin tayimin kallon makaryaci, yanzu ban san ta in zan faraba bansa n ya zata kalli abunba, zata iyayimin bore ina tsoron darunta” Saleh yace “hakane amma ai kai namijine, kuma zuwa yanzu duk ta rage wasu abubuwan ai, ba lallai ta maka wulakanci tunda yanzu ba wanda ta sani se kai” “Saleh anya ba ka manta wacece Widad ba? Jiya ta gama jadaddamin bata yafiya ga wanda yayi mata karya ko yaci amanarta” Saleh yace  "ƙwarai na san wacece ita, yadda ta gaya maka hakane bata yafiya ga wanda yayi mata ƙarya ko yaci amanarta, duk yadda suke da shi kuwa, amma ai kai akwai alaƙa me matuƙar ƙarfi a tsakaninku, zata iya ɗaga maka ƙafa kuma kamata yayi ace kai da kanka ka gaya mata, karka bari taji a waje, idan kuwa ka kuskura ta samu labari a gurin wani akwai matsala, dan bata ƙi ka tafi prison ba kaima, tace an haɗa baki da kai za'a cuce ta, abun da nake ganin dai yafi shine ka sanar da ita kawai, hakan zefi " "tabbas nasan bata yafiya ga wanda yaci amanarta, nikam Saleh me kayi mata wanda yasa ta kasa duba alkhairin ka se laifukanka? " Saleh yayi murmushi yace " labari ne me tsawo Yusuf, kuma gaya maka labarin tamkar ƙara wani laifin ne akan laifi, amma ka bari idan tayi niyya zata iya gaya maka komai, nidai shawarata da kai, tun kuna nan ka gayamata waye kai" Yusuf yaja ajiyar zuciya yace " Inajin tsoro Saleh, harga Allah ni fa ina son Widad ne tsakani da Allah, yanzu idan na gaya mata zata iya ƙina, a yanzu mu tana ƙasa tana dabo ne, dan itafa bata yadda akwai so ba, dan haka bani da tabbacin tana sona, kuma inzo in gaya mata wannan magana, abun ze lalace gaba ɗaya ne fa" Saleh yace "haba namijin duniya, ai kai kana da jarumrtar da ka cancanci a sara maka, haka nan duka butulcin me butulci dole ya sarawa namijin ƙoƙarin da kayi akan Widad, ni kaina na fuskanci sonta kake, amma dole zata ɗaga maka ƙafa dan baka cancanci ta wulaƙanta ka ba, be cancanci ta manta da alkhairin da kayi maka ba, dukda yarinyar wata irin muguwar bahaguwa ce, amma kayi ƙoƙari kafin ku bar garin nan tasan abunda ake ciki " Yusuf ya dafe kai yace " Subhanallah, ban san ta ina zan fara ba Saleh, ina tsoron abunda ze biyo baya, ni kome zata yi baze dameni ba, ni fargaba ta karta rabu dani ko tayi min wata mummunar fahimta " " Yusuf kenan, da alama wannan ne karonka na farko na shiga soyayya ko?" Yusuf ya girgiza kai yace " Na taɓa soyayya Saleh, har na sawa kaina bazan sake soyayya ba, katsam Widad ta shigo cikin rayuwata ba tare da na warke daga wancan ciwon dake zuciyata ba, kuma har nake jin cewa a yanzu inawa Widad son da banyi wa waccan yarinyar ba" Saleh yace "lallai kana cikin Jarrabawa Yusuf, ina maka fatan Alkhairi tare da fatan Allah ya fitar da kai" Sallamar Widad ce a ɗakin ta katsesu, suka amsa mata gaba ɗaya, fuskarta duk bushashiyar gasara, kanta babu ɗankwali goshinta duk gumi. Ta kalli Saleh ha haɗe rai tace "Excuse us please" Saleh yace "to" ya tashi ya fita ya bar ɗakin. Ta kalli Yusuf tace "ka zauna kana ta surutu, baka san lokacin salla yayi bane, har an fara aikowa ana tuna maka, kaje kaja salla" Yusuf yace  "aini yanzu gaba ɗaya kunyar mutanen nake ji". Widad tace "me kayi musu na kunya?" Yusuf yace "tunda kika rungume ni a gabansu, indai suka ganni se inga suna wani sunkuyar da kai" Ɗan guntun tsaki Widad tayi tace "to dana rungumeka a gaban su is it an abomination? Saɓo nayi kome?" "to ai su basu saba ganin irin haka ba, is against their norms" Widad tace "to su suka sani, ni wanka zanje inyi, kaje kayi sallar" Yusuf yace "to bari inje in dawo in rama dukan da kika yi min da Asuba" "ina nan ina jiranka kuwa, kasan dai na fika ƙarfi yanzu, kai sauro ya zuƙe maka ƙarfi". "dole kice haka mana, tunda na baki jinina, dole kiyi ƙarfi ai" Ta kalle shi tace "ji wata magana, jinin naka ma da bashi da kyau, duk ba wasu sinadarai a cikinsa, shine duk ka dameni da ka bani jini, to zan biya ka abunka" Yusuf yayi dariya yace "kamar gaske" Yai waje, yana fita ta kintsa ta ɗau bokiti ta tafi taje tayi wanka. Tana zaune tana shafa man zaitun a jikinta Yusuf ya dawo, ta bawa ƙofa baya, farar fatarta se ƙyalli take da ɗaukar ido, ga baƙin gashinta ya kwanta sosai a bayan ta, ƙasansa ya jiƙe da ruwan wanka, ba taji dawowar Yusuf ba se jinsa tayi zaune a kusa da ita, numfashinsa na sauka a jikinta. Da sauri ta ɗago ta kalle shi tace "meye haka? Ya zaka zo ba ko sallama, ka zauna kana shinshinani" Seda tasa Yusuf yayi dariyar dabe shirya yinta ba, yace "niba shinshinaki nake ba, se kace wani kare" "to baga numfashinka nan inaji a jikina ba" Beyi magana ba, ya kalli hannun ta data tsiyayo zaitun, ya zura nasa hannun akan nata, zaitun ɗin wani duk ya zube, ya shiga shafa mata a jikinta. Ji tayi tsaigar jikinta na tashi, ɗan yamutse fuska tayi tace "Yoseef bana so, ka bari in shafa da kaina" "Ni kuma ina so, ki bari in shafa miki" Tsaki tayi ta ɗan ɗaga murya tace "nace maka bana so" tai maganar tana ƙoƙarin miƙewa, Amma Yusuf ya riƙeta ya hanata tashi, a hankali yace "yi haƙuri Widad, magana nake so muyi" yai maganar yana sauke numfashi. Littafin kuɗi ne, kuyi magana ta wannan lambar domin siyan littafin Nagode 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 48_49 Littafin kuɗi ne pay before you read please 🙏 🙏 🙏 Haɗe rai tayi tace "dan za muyi magana shine zaka dinga yimin wannan abun haka, ni bana so gaskiya karka sake yimin" Maimakon yayi magana Shiru yayi ya sake ƙanƙameta sosai a jikinsa, ya kwantar da kansa a jikinta, ita kuwa mutsu mustu kawai take, so take taga ta ƙwace daga jikinsa, amma abu ya gagara, ya riƙeta sosai ga ƙarfinsu ba ɗaya ba. A hasale Widad tace "Wai dan Allah Yoseef meye hakane?, ka cikani towel ɗin jikina ze kwance fa? Nace maka bana so ka cikani dan Allah, wallahi gaba ɗaya ka canza hali, kwanan nan sekai tayi min wasu abubuwa wanda bana so, kuma kana sane" A hankali ya cika ta, ya kwanta akan katifar yayi shiru tare da lumshe idonsa. Se kuma ta juya tana kallonsa tace "meye kuma?" ba tare da ya buɗe idonsa ba ya girgiza mata kai. "to me zaka gayamin?" "bakomai" ya bata amsa "wani irin bakomai bayan kace magana zamuyi?" Gabansa ne ya faɗi, yaga be kyautu yayi mata wannan zancen a wannan gaɓar ba data ɗau zafi, dan haka ya buɗe idonsa ya ɗan tsare ta da ido yace dama ba wata magana bace, ina son in sake gayamiki Ina sonki Widad " Ha ɗe rai tayi tace " kaga tasarmin daga kan katifa ta, tunda ba zaka dena wannan shirmen ba, kuma daga yau in ka san wannan shiritar zaka gayamin, karka sake cewa zakayi magana dani na gaya maka, dan bazan saurareka ba" Yusuf yace "Maganar tawace shiririta? Queen ba shirita bace i mean it, kalmar so ba abun wasa bane ko imagination ba, please my Queen ki yarda ina sonki mana" Banza tayi masa, ta ɗakko kayanta tana ƙoƙarin sakawa, ya juya mata baya don ta sa kayanta. tayi ƙasa da muryarta cikin ƙunƙuni tace 'kaji da shi dai, kai ta mun wasu abubuwa amma idan zansa kaya seka wani juya, wai kai gaka na Allah, inma baka juya ba niba abunda ya dameni sa ka yana zanyi' Bece mata komai ba se dai murmushi da yayi, se data gama sa kayan, ta yunƙura zata miƙe ya sake riƙeta, a fusace tayi niyyar yi masa rashin mutunci, amma ya rungumota ta kasa cewa komai jin ya haɗe bakin su. Gaba ɗaya Yusuf yafi ƙarfinta, ta kasa gane kansa kwata kwata, kwanan nan se wasu ɗabi'u yake mata wanda bata gane kansu, tana ji tana gani seda yayi me isarsa sannan ya cika ta, ba zata iya ƙwace kanta ba. Yana cikata bata kuma kallonsa ba, ba tace komai ba rai a matuƙar ɓace tayi waje, kallo ɗaya zaka yiwa fuskar ta kasan a fusace take, ta fita tsakar gida rana ta take, kowa yana ɗaki ta fita ta samu guri a ƙasan bishiya tayi zamanta. Hakanan Yusuf ya dinga jin be kyauta ba abunda yayi, amma ya zeyi shima bayin kansa bane, mutum ne shima kuma me cikakkiyar lafiya, shi kansa yanzu ya fara ɗar ɗar na zama da Widad a guri ɗaya, komai ze iya faruwa. Barrister Khalil kam tunda yakoma gida yake tunanin hirar da sukayi da Nurat game da mahaifinta, tabbas mahaifin Nurat ba karamin hatsabibi bane ,ze iya aikata komai muddin burinsa ze cika ,amma yayi mamakin yadda Nurat tace masa da saka hannunsa a sace Daula da akayi,abun da mamaki matuka, nan ya shiga nazarin ta ina yakamata yayi wani abu? Amm muddin ya kuskura Alhaji Musa yasan yana wani yunkuri,ko kuma ya gane ya san wani abu akan abunda yake aiktawa,to tabbas ba abunda ze hanashi daukar mataki akansa,dan bashi da Imani sam. Barrister Hafiz ma tunda ya koma gida yake tunanin batun da aka bijiro masa da shi akan dukiyar Daula,tabbas kudi abun sone,amma meze biyo baya idan suka amince akayi wann aika aika? Idan sukayi aikin nan tabbas zasu samu kudi,amma hatsarin dake cikin hakan shine abun dubawa, watakila idan shi nya amince ba lallai sauran lawyoyin su yadd ba,amm tabbas yana son kudi shima. Ya yanke shawarar zefara tuntubarsu daya bayan daya yaji opinion din sauran akan lamarin abunda suka yanke shikenan.   Ya tashi ya dau mukullin motarsa ya fice. Anwar kuwa gaba daya yayi baki,ya rame saboda zaman gurin nan babu sauki sam, ga sauro ga rahsin kula, ga azabar wahala da ake gana musu akan lallai se sun fadi inda Daula yake, amsar sa dai dayace be san inda yake ba. Yana zaune a inda suke ajiye yayi shiru yana tunani,s hi babban abunda yake damunsa shine waye ya sace Daula? Wanda ya sace shin yana iya kula dashi?maganinsa ma ko ana kula dashi a bashi oho? Yayi zurfi a duniyar tunani yaji an kira sunansa, a hankali ya daga kai, dan sandan yace “ka taso kana da bako” Anwar ya taso ya taho a hankali yana jan kafa,yabiyo bayan dan sandan. wanda aka nuna masan akace shine me nemansa sam be sanshi ba, dan ko ganinsa be taɓayi ba. Mutumin ya kalli Anwar yace “kaine Anwar?” Anwarv yace “Eh nine” Mutumin ya kalli Anwar yace “ naji ance ranar sha biyar ga wata za a kaiku kotu ko?” Anwar ya jinjina kai yacec “ eh hakane” Dukda ban gabatar maka da kaina ba baka san koni waye ba,nima turoni akayi gurinka,kuma ancemin babu bukatar seka san waye ya turoni, yanzua abunda nake so nbda kai shine ina son ka gayamin tsakani da Allah meka sani game da batan Alhaji Nasir” Anwar ya gaya masa iya abunda ya sani,Mutumin yace  "shikenan karka damu ka kwantar da hankalinka,insha Allah komai zezo da sauki” Anwar yace  “shikenan nagode sosai” Mutumin yace “sannan kuma, bana bukatar kowa yasan nazo gurinka ciki harda mahaifiyarka’ Anwar yace “shikenan,Insha Allah babu meji” Daga nana sukayi sallama mutumin yatafi. Widad na zaune a gindin bishiya, tana tunanin abunda ya shiga tsakaninta da Yusuf, tai shiru sosai tana tunani, tama rasa me yakamata tayi, haushi zataji kome?, Ganin Widad zaune ita kaɗai a gindin bishiya yasa Hindu tazo ta Zauna a gurin Widad, tace "Amarya me kike anan ke ka ɗai haka?" "ina shan iska ne kawai" Widad ta bata amsa Hindu tace "tunda ba abunda kike, ɗan koyamin turancin mana" Murmushi Widad tayi tace "to ta ina zamu fara, bansan a inda kika tsaya a turancin ba" Hindu tace "ni dai kota ina ne mu fara" Nan Widad ta shiga koya Mata daga ƙananan abubuwa wanda zata iya riƙewa. Yusuf ya fito ze tafi Sallar la'asar, ya ya kalli su Widad yace  "karatu ake ne?" Widad bata amsa ba, Hindu ce tace "eh  wallahi turanci ake koyamin" Yusuf yace "Masha Allah, Allah ya temaka" "Ameen" Hindu ta amsa banda Widad data haɗe rai. Daya dawo ma a gurin bishiyar ya tarar da ita, tana cin Abinci. Yusuf ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita yace  "Shine kike cin Abincin babu ko gayyata? Bari inzo muci tare, kin san cin Abinci tsakanin ma'aurata yana ƙara danƙon soyayya, nikuma ina son Soyayyarmu ta wuce ɗanƙo ta zama kamar ƙarfe" Banza tayi masa taƙi kula shi. Ya wanke hannu yazo yasa hannu suna cin Abincin, amma Widad taƙi ce masa komai. Se yanzu Yusuf ya fuskanci fushi take dashi. Yusuf yayi ƙasa da muryarsa yace "My Queen me nayi miki ne? Se magana nake am kin basar dani, bana jin daɗin hakan fa" Ƙara haɗe rai tayi, ba tare da tace masa komai ba. Yusuf yace "Abunda  nayi miki a ɗaki ne yasa kike fushi dani ni ko?" Cire hannunta tayi daga Abincin, taje ta wanko hannunta ta dawo tai zamanta, shiru yayi yana sake binta da kallo. Hanne ce ta fito, tana ganin Yusuf ta wangale baki tace  "Sannu" Jiki a sanyaye Yusuf yace "Yawwa Sannunki Hannatu" Ba ƙaramin daɗi Hanne taji ba jin Yusuf ya kira sunata da Hannatu. Ta ƙara wani rausayar da kai tana murmushi, ta ƙaraso inda yake zaune kusa da Widad a kan tabarma, tace "bari in ɗauke kwanon, naga kamar ka gama cin Abincin" Bece mata komai ba, taje ta ɗauke kwanon ta kai gurin wanke wanke, ta kawo masa ruwa a buta tace "ga wannan ka wanke hannu" Yusuf yace "God bless you, Nagode sosai" Ta jinjina masa kai tana murmushi, Widad ko kallon inda suke ba tayi ba, ta cigaba da kaɗa ƙafarta. Tana jin yadda Hanne keta wata kwarkwasa, Hindu  dake banɗaki ji take kamar ta fito ta shaƙe Hanne, ta wani ɓangaren kuma tana ganin baiken Widad, data zuba mata ido ta ƙyaleta. Yusuf ya tashi ya tafi ɗakin su, Hindu na fitowa daga banɗaki a fusace tace  "Hanne gaskiya abunda kike bakya kyautawa, ya zaki dinga shigewa mijin mace a gabanta, dan kawai kinga tana ɗaga miki ƙafa, haba Hanne dan Allah ki dimga tunani mana" Hanne tace "ba zanyi tunanin ba ɗin, ina ruwanki dani? Tunda ita ba zata iya kula dashi ba ai shikenan, mace ba abunda ta iya se girman kai, sam bata da tarbiyya, bata san darajar miji ba" Widad ta miƙe zata koma ɗaki, sedai babu zato Hanne taji Widad ta shaƙeta da rigar jikin ta, seda idanunta suka yo waje dan azaba, cikin zare ido da ɗaga murya Widad tace "Am tired, ban taɓa ɗagawa wani mahaluki ƙafar dana ɗaga miki ba, ina ƙyaleki ne saboda Karamcin iyayenki a gare ni, kin san wacece ni? Babu ruwana da alaƙar dake tsakaninki da Yoseef, amma karki sake sakani a irin wannan haukan naki, banda ƙaddara ko a mafarki aka ce ni Widad zan zauna a wannan ƙasƙantaccen gurin zance ƙaryane, saboda kawai ina zaune a cikin wannan jar ƙasar shine zaki dinga gayamin baƙaƙen maganganu? Kin san wace ni, idan kin san wace Widad ko hanya muka haɗa sekin kauce, banda dalilin ƙaddara babu abunda ze haɗanj da daƙiƙiyar baƙauyiya kamarki, hanyar dana sa ƙafata na wuce ma baki isa ki biyo ta ba" Hanne se kakari takeyi, Su Hari sukazo da gudu amma suka kasa ƙwatar Hanne a hannun Widad, fitowar Yusuf ne yayi daidai da shigowar Saleh, da sauri Yusuf ya ƙarasa inda dramar ke faruwa, idanun  Widad sunyi jawur, fuskarta sharkaf hawaye tana masifa. Yusuf ya ƙarasa yasa hannu ya cire hannun Widad daga wuyan Hanne, Hanne ta shiƙi iskar 'yanci, ta koma gefe tana ta haki tana zare ido, kamar an karɓeta daga hannun zaki. Saleh yace "Wallahi da ta kasheki ta kashe banza, dan babu wanda ya isa ya ɗaukarr miki mataki, kin san wacece kuwa? Kin san' yar waye ita? Ko dan kawai kin ganta a cikin gidan nan a zaune, ina lura da yadda kike mata wasu abubuwan tana ƙyaleki, tunda kika ga nima tana mun abunda taga dama ina ƙyaleta to tabbas kin san ba a banza ba, ƙaddara ce ta kawota zama daku, amma ke a gidan su ko me goge mata takalmi baza'a ɗauke ki ba" Gwaggo tana jin duk dramar da'ake yi, amma tai shiru a ɗaki bata ko fito tsakar gidan ba, saboda tasan abunda ke faruwa, tasan yadda Hanne ne ke wuce gona da iri a wasu lokutan. Shikan sa Yusuf yasan ba ƙaramin ɗaga ƙafa Widad kewa Hanne ba, a yadda Widad keda izza bata ɗauka raini, amma take sharewa idan ta mata wani abun, lallai haƙurinta ne ya ƙare. Suka shiga ɗaki, Widad se kuka take jikinta na tsuma, ga gumi data haɗa. Yusuf ya shiga share mata hawayen fuskarta  tare da faɗin "is ok, kiyi haƙuri nasan kina haƙuri, Amma ki ƙara insha Allah mun kusa mu koma gida" Kamar wadda aka mintsina, ta miƙe daga jikinsa a fusace tace  "dalla ma ni ƙyaleni, ba kaine kake mata dariya ba, yasa ta rainani takemin wani kallo na daban ba, harni wannan baƙauyiyar yarinyar zata kalla ta dinga zagina? Tunda kana mata dariya dole ta Kalleni ta dinga cewa ban iya kula da miji ba se ita, ai seka Aure ta tazo ta kula da kai, wallahi ta kuma yimin abunda bemin ba, sena ɗau mataki mafi muni a kanta, zan nuna mata wacece Widad " From no where Yusuf yaji wani farinciki yana ratsa shi, Widad ta fara kishinsa kenan? Murmushi yayi yace " Ohh yasalam, shikenan tabbas nayi laifi, dukda badan ina mata murmushi ba, da tabbas ba zata rainamin 'ya ƙwalisar mata ta ba, amma ayi haƙuri zan kiyaye insha Allah, na dena mata dariya amma ayi min afuwa". "Karma ka dena kai tayi mata, wallahi na dena ƙyaleta" "Ayi haƙuri dai, kar ayi aika aika, ki dena kuka share hawayen ki maza, mijinki baze sake kallonta yayi mata dariya ba" Shiru tayi masa ta cigaba da ajiyar zuciya. Yusuf a ransa yace  'insha Allah ko baki son meye so ba zaki sanshi a kaina, kuma ina fatan ki furta da bakinki kina son Yusuf, muje zuwa dai' Shikam Saleh a tsakar gida ya cigaba da zazzaga musu masifa, akan abubuwan da Hanne ke yiwa Widad, sun sha mamaki jin yace ko za'a tattara kaf ƙauyen da kadarorin da mutanen ƙauyen suka mallaka ba zasu sai gidan mahaifin Widad ɗaya wanda take rayuwa a ciki ba. Hari ta zaro ido tace  "Wudas ɗin?" "ke dalla ware ai kece Wudas ɗin, meye wani Wudas" Hindu ta yadda da maganar Saleh, saboda sam Widad ba tayi kalar wahala ba. Ita kuwa Hanne jinsa kawai take badan ta yadda ba, shaƙar da Widad tayi mata tafi komai bata mamaki da ɗaga mata hankali. Ramlah ce ta shiga falo, ta tarar da Amal a kwance tana kallo, amma hankalin ta sam baya kan tv tunani kawai takeyi, a ɗan gigice tace "Amal wai kinji Anwar kotu za'a kaisu next week" Da sauri Amal ta tashi zaune tace  "kamar yaya kotu?" "Yanzu Mummy ta dawo take gayamin" "Dama ana kai mutum kotu, koda ba'a  tabattar da laifin da ake tuhumarsa ba?" Ramah tace "ya za'ayi in sani? Nifa hankalina ya tashi, ashe abun nayi ne" Amal tace  "mun shiga uku Ramla, da ƙyar in aka shiga kotu kiga ba'a kai shi prison ba, yanzu meye abunyi?" "wallahi nima ban sani ba, gaba ɗaya kaina ya gama kullewa, Ga Mummy ta damu sosai, ko Abinci ma ba ta ci fa" "Subhanallah, Allah sarki Yaya Anwar, yanzu fa da sunje koti se ace se prison" Ramlah tace "wallahi nima abunda nake tunani kenan Amal, Allah sarki bawan Allah" Nan suka yi ta jimantawa juna. Har dare Widad taƙi walwala, ko kula Yusuf ta ƙiyi, yau ko harar da suke a tsakar gida dasu Hansai bata zauna ba, ta gyara shimfiɗar ta zata kwanta, Yusuf yaje kusa da ita yace "My Queen dan Allah kidena fushi dani, nasan yau gaba ɗaya ranki a ɓace yake, na farko na sake gangancin sumbatarki, ga kuma wancan laifin shima da kika ce nayi, dan Allah kiyi haƙuri bazan iya jure ganinki cikin ɓacin rai ba" Cunkusa baki tayi, ta cigaba da ƙoƙarin kwanciya. "Amma inaga dole mu koma kan shawarata ta farko, na yakamata mu raba ɗaki, kinga ni ba waliyyi bane mutum ne kamar kowa, idan muna tare a guri ɗaya akwai matsala, ina gudun wani abu yazo ya faru, kinga na fara gazawa gurin riƙe Alƙawarin yarjejeniyar dake tsakaninmu" "wallahi bazan kwana a ɗakin nan nikaɗai ba, duk inda zaka je sena bika" "to idan na kuma kissing ɗinki kika haɗemin rai se nayi abunda yafi haka, kina bani ciwon kai Widad, komai nayi laifi ne a gurinki, ki dinga sassauta min mana, a dinga jin tausayina" Kwanciya tayi ta juya masa baya, shima kuwa ya kwanta a bayanta, banza tayi masa taƙi magana, ta lumshe ido da nufin tayi bacci, a kunnenta ya dinga raɗa mata   "I love you My Queen, ina sonki Widad, and I mean it from the bottom of my heart, i love you" Cike da ƙosawa Widad tace "Naji amma dan Allah ka ƙyaleni inyi bacci" "to ba kice komai ba, kin haƙura kin dena fushin?" "eh na haƙura jeka" "kora ta fa kike Queen" "Niba korarka nayi ba, bacci nake ji" Yusuf yace "shikenan, Asuba tagari masoyiyya" "kaika santa" Yai murmushi ya koma kan shimfiɗarsa. Ana ta shirye shirye za'a kai su Anwar kotu domin fara sauraren ƙararsu, akan tuhumarsu da'ake da haɗa baki gurin sace Daula, Anwar ya duƙufa sosai da Addu'oi babu dare babu rana. Yana zaune da safe wani ɗan sanda yazo ya buɗeshi, aka tasa ƙeyarsa zuwa wani guri, wannan mutumin dai daya zo ya kuma gani, aka bawa Anwar kayansa da aka karɓa. Mutumin ya miƙawa Anwar hannu suka gaisa yace "masha Allah, you are free now malam Anwar, muje in ajiyeka a gida" Cikin mamaki Anwar ya kalle shi yace "i am free as how? An game bani da laifi kenan?" "eh baka da laifi, muje" Kamar soko haka Anwar yabi mutumin, kuma ya kasa tambayar sa waye shi, ya kai shi restaurant yaci Abinci sannan ya wuce ya kai shi har ƙofar gida. Mutumin ya kalli Anwar yace "Anwar ina maka fatan Alkhairi, ina maka murnar fitowa da kayi da kuma tsallake tarkon azzalumai, seka kula Allah ya kiyaye gaba" Anwar yace "sedai ni tunda kake zuwa gurina ban gane ka ba" Mutumin yace "nasan baka sanni ba, kuma bazaka ganeni ba, sedai nima aikoni akayi ba'a bani umarnin sanar da kai wayeni ba, babu buƙatar hakan Daula yana tare da ubangida na, shiyasa aka ɗauke shi a Asibiti, yana gurinsa dan haka ka kwantar da hankalinka" A firgice Anwar yace "dan Allah waye uban gidan naka? Daula bashi da lafiya, yana buƙatar kulawar likita" "ɗan samari kai dai ba Ruwanka, koma a wani hali yake ciki tunda dai kai ka fita, maza jeka zan tafi" Jiki a sanyaye Anwar ya sauka, yana bin motar da kallo kamar wani soko, har motar ta bara layin. Gate ɗin gjdansu ya nufa, ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, Isa ne yazo ua buɗe ƙaramar ƙofar, yana ganin Anwar ya shiga mutstsuka ido ko gizo yake masa, Isa yace "Kamar Yallaɓai Anwar nake gani" Anwar yace  "eh nine Malam Isa" Buɗe masa ƙofar yayi ya shigo, Isa yace "Yallaɓai an sakoka kenan?" Anwar yace  "Alhamdilillah Isa an sakoni" nan ma'aikatan suka dinga murna suna taya shi farinciki. Cikin gidan ya ƙarasa, yana shiga ya tarar babu kowa a falo, ɗakin mahaifiyarsa ya nufa, yasa hannu ya murɗa ƙofar ɗakin yayi Sallama, da sauri ta waigo dan mamar Muryar Anwar taji, aikuwa ba kama bane shi ɗinne, ai da hanzari ta miƙe, ta nufe shi da sauri  "Anwar kaine? Garin yaya, ya akayi aka sake ka?" Rungume ta yayi yace "Mummy ki bari in huta se in gaya miki, duk kin rame Mummy na" Kuka ta saka tace "ba dole ba Anwar, baka nan na rasa me kemin daɗi, nasan zaman gurin nan sam ba daɗi yake maka ba, nayi zarya harna gaji anƙi a sakeka, ko Abinci bana iya ci, bana baccin kirki" "shikenan, is over now, ai gani na dawo Alhamdilillah" Suna nan zaune sega su Amal, dan ta manta ma bata sanar dasu dawowar Anwar ba, nan suka dinga murna suna farinciki da dawowar Anwar, aka shiga yi masa girki, yai wanka ya huta dan ko ina na jikinsa tsami yake masa saboda wahala. Mummy tace "nikam ka gayamin, ya aka yi aka sako kame?" Anwar yace  "wallahi Mummy ikon Allah kawai, ina zaune akace in fito, wani mutum ya ɗakkoni a motarsa yace bani da laifin komai, ya kawoni har gida ya tafi" Ɗan yatsine fuska tayi tace "meye haka sekace wata almara?" "Wallahi Mummy dagaske nake miki, kiyi waya ki tambaya kiji" "ikon Allah ko wane mutumi ne wannan oho? Ta be gaya maka waye shi ba?" "nayi nayi ya gayamin, amma yaƙi sam, be gayamin ko waye shi ba" Amal tace "Mummy koma dai waye, tunda Allah yasa an sako mana shi ai shikenan, mu dama fatanmu ka dawo gida" Mummy tace  "Amma da mamaki, ina mamakin waye haka? Dan na san ba'a cikin waɗan cam tsinannun bane marasa imani" Anwar yace "Mummy suwaye kenan kkke zagi haka?" Da sauri ta wayence tace  "A'a karka damu, 'yan sanda nake nufi, ba irin zaryar da banyi ba amma suka ƙi bani belinka" "Allah sarki, ai Abincin su suke karewa suma Mummy, bekamata ki tsine musu ba" Mummy tace "hakane kam, na dena tsinemusu tunda nidai ɗana ya fito" Yau Widad har takwas na safe bata tashi ba, tunda tayi sallar Asuba, Yusuf yaje kan shimfiɗarta ya riƙe hannunta a nasa yana ɗan matsawa yace  "My heart, ki tashi baccin ya isa haka, ki tashi kici Abinci" Motsawa tayi a hankali tayi juyi tace "kaci Abincinka, ni bacci nake ji" "A'a ni gaskiya bazan iya cin Abincin babu ke ba, ki tashi please" Shiru tayi ta sake lumshe ido, "zanyi miki abunda bakya so yanzun nan fa" Murmushi tayi tace "banyi brush ba dai" ta ƙarasa tana dariya, Yusuf yace "aini bana ƙyamar ki, kece kike ƙyamata komai naki ni so nake" Widad tace "naji, ɗakkomin brush ɗin inje in wanke baki" Ya duba inda take ajiyewa, ya ɗakko ya bata, tana zaune akan katifar bata tashi ba, Yusuf yace "ya dai? Ko sena ɗauke kine?" Jinjina masa kai tayi alamar eh, aikuwa ya ƙaraso ya ɗauketa cak, dariya take tace "ajiyeni tun kan Baba Hari tamin ba'a ko ace na aikata wani babbam zunubi a koreni daga garin nan" A tare suka kwashe da dariya, Yusuf yana kallonta cike da farinciki. Tayi waje, taje tai brush ta dawo suka fara cin ɗumamen tuwo. Yusuf kallonta yake, da alama tana cikin nishaɗi, yanzu ne lokacin da ya dace ya gaya mata abunda yake son gaya mata, yai shiru yana saƙe saƙen yadda ze ɓullo da zancen yaji tace "Me kake son gayamin ne da yake razanaka har yanzu ka kasa gayamin? Ka gayamin kawai ina saurarenka" Littafin kuɗi, dan Allah a biya kafin a karanta badanniba dan girman Allah A tuntuɓeni ta wannan lambar 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 50_51 NA KUƊI NE, BOOK 1 NE FREE, DAN ALLAH A BIYA KAFIN A KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH 🙏🙏🙏 gaba ɗaya Yusuf ya ɗan ruɗe yace "ba wani abu da nake son gayamiki ba fa, kece kike ganin kamar ina son in faɗi wani abu ne" Murmushi tayi tace "Hmm Yoseef kenan, a ɗan zaman da nayi da kai daga lokacin da ka fara min aiki, na fuskanci halayenka da yawa, koba haka ba ina iya karantar abunda ke ran mutum ta hanyar fuskarsa, bana son ƙarya, karka ji wani abu, babu abunda zan maka, se abunda Allah yayi nufin ya faru da kai" Yusuf yace "dama ina son in gaya miki yau nake son na cigaba da fitane, ina son in sai mana wasu abubuwan na buƙatunmu, wasu abubuwan duk sun ƙare" Widad tace "Yaushe ka warke da har zaka fara zancen fita? Se kaje ka kuma haɗuwa da wata rashin lafiyar ko? toni babu ruwana, tunda dai ban takura maka nace seka saimin abunda baka dashi ba, ka ƙyaleni komai aka bani zanci, in wanda zan iya cine se inci, in bazan iya ciba kuma se in haƙura kawai" Sosai ta bawa Yusuf tausayi jin abunda ta faɗa, Yusuf yace " duk da haka Yakamata ace nima ina taɓuka wani abun da kaina, in sauke haƙƙinki da yake kaina, in sai miki abubuwan da kike buƙata koba duka ba" "Shikenan, amma nidai bance kayi abunda zaka cutu ba koka wahala ba, ka kula da lafiyarka" Yusuf ya gama shirinsa tsaf ze fita, Saleh ya shigo gidan ya kalli Yusuf yace "Ahh Yusuf ina zuwa haka? ' " zani cin kasuwane Saleh " Yusuf ya bashi amsa Saleh yace " Haba Yusuf, kasan fa baka da lafiya sosai " Yusuf yace " shima zaman guri ɗayan babu daɗi Saleh " Harice take a tsugune tana ta tattara ƙwan da kazarta tayi zata bayar akai kasuwa, Yusuf yace " Baba Hari, wannan ƙwan na siyarwa ne?" Hari tace " Eh za'a akaimin kasuwane" Yusuf yace "Masha Allah, inba damuwa a zuba na kaji biyar na zabi biyar, a kaiwa Queen idan na dawo insha Allah zan bada kuɗin" Hari tace "meye kuma Kun?" Yusuf yayi murmushi yace "A kaiwa Widad nake nufi" "Awo sekace min Wudas, amma kun ai bazan gane ba idan kace haka" Saleh yace "Hari baki abun magana, Queen yace ba kun ba, yana nufin sarauniya" Kwaɓe baki tayi tace "Wace sarauniyar? Sarauniyar fitsararru ba" Yusuf yace "Ayi haƙuri" Hari tace "dan dai kaine, kuma ina jin kunyar ka, amma da ita zata siya bazan sayar mata da ƙwan nan ba" Yusuf yayi dariya yace "ayi haƙuri, A temaka mana" Saleh yace  "kedai kinji kunya, ki rasa da wadda zaki dinga faɗa se wannan Yarinyar" Widad ta ƙaraso inda suke da kwanukan wanke wankenta a hannu tace "Idanma baki siyar dan Allah ba, zan buɗe gurin ƙwan ne in kwashi san raina, ko in kama kajin naki in yanka in soye muci nida Yusuf tunda bashi da lafiya dama" Dariya suka yi, Saleh ya dinga mamaki, dama Widad ta iya magana haka hadda tsokana? Hari tace tunda Yusuf ne ze sai ƙwan, ya biya kuɗin biyar, ta bashi biyar kyauta, amma bata yarda ya bawa Widad wanda ta bashi ba. Widad tace "Hari dama kina ɗan dafa ƙwan nan kici, dase kinfi haka ƙiba da kyau, ke kullum cikin neman kuɗi kamar zakiyi ƙwace, kuma na rasa inda kike kai kuɗin" Hararta Hari tayi taƙi ta kulata, aka ɗakko kwano za'a sakwa Widad ƙwai, Widad tace "kuma idan kika samun ƙanana bana so, manya za'a bani dan nima ƙatuwa ce" Haka Widad tasaka Hari a gaba, tana ta zolayarta ita kuwa Hari tunda Widad ta shaƙe Hanne take ɗan shakkarta. Yusuf yace "Queen zan tafi" Widad tace "ba zaka soyamin ƙwan ba zaka tafi?" tai maganar kamar wata ƙaramar yarinya tana sa hannu a gashin kanta. Gwaggo ta sunkuyar da kai tana jin taɓara, Yusuf yace "ki bari in dawo" Maimakon tayi magana se ta cuna baki tana kallonsa, Yusuf yace "Shikenan Muje in soyamiki, amma nasan ba iya ci zaki yi yanzu ba, dan yanzu kika gama cin Abinci" Gwaggo tace "Yusufa jeka abunka, za'a soya a bata kaji" Widad ta cunkusa baki tace "Ni gaskiya Mama nasa nake so, naga kin fi son Yoseef dani, ni kowa baya sona" Gwaggo tace "nina isa ince bana sonki, waceni niko nake sonkj, amma ina nema masa Alfarma, a ɗaga masa ƙafa tunda fita zeyi" Widad tace "shikenan Allah ya temake ka, jeka seka dawo" tai maganar tare da kashe masa ido ɗaya. Hari tace  "A'uzubullahi wannan Yarinyar idan ka zauna a inda take seta karya maka alwala" Dariya Yusuf yayi sukayi waje shida Saleh, Saleh yace "Salute to you Yusuf, babu wanda ya isa ya biyaka namijin ƙoƙarin nan da kake, kalli yarinyar da take rayuwa kamar wata halitta daban, me gudun jama'a da son rayuwar kaɗaici, amma ita ta sake a ƙauye haka take rayuwarta, cikin farin ciki fjye da wanda take a gidansu da yake da tarin arziki " " Saleh, ai dama kuɗi dukiya ba sune kwanciyar hankali ba, farinciki zama cikin wanda suka damu da kai shine farinciki, mutanen wannan zamanin muke ganin in kana da kuɗi kana da komai, ka wuce baƙin ciki " Saleh yace" tabbas hakane maganarka Yusuf, da fa tsakaninta da mutane kallon banza da hantara, amma yanzu kalli yadda ta sake da Gwaggo ta maida ta kamar wata kakarta" Yusuf yace "sosai makuwa, akwai shaƙuwa a tsakaninsu, Gwaggo nada sauƙin kai, kuma tana janta a jiki, bata hantararta idan tayi mata wauta ko wani abu, shiyasa itama take sonta" Saleh yace  "hakane, amma ya batun ciwon ta kuwa? Na taɓin hankali?" Yusuf yace "ina doubting akan wannan ciwon da take dashi, ina da question mark akai, amma lokaci nake jira" "Alhaji Musa, kaji wata maganar banza wai an saki Yaron nan Anwar"? Alhaji Musa yace "haka nima labari ya isheni, ni kaina abun ya ɗauremjn kai Munir, wane mara mutuncin ne haka, waye yayi wannan karambanin?" Alhajj Munir yace "munyi waya da Bukar, yace ze bincika nima nasa a bincikamin amma har yanzu babu wani labari, an rasa waye yasa a sake shi, wai daga sama aka bada umarni" Alhaji Musa yace "waye a saman ya bada umarni damu bamu sani ba? Ta yaya ana tuhumarsa da wannan babban laifin za'a sake shi, idan kuwa hakane to tabbas muna da abokan Adawa wanda suke mana zagon ƙasa akan lamarin nan" Alhaji Haruna da tun ɗazu bece uffan ba ya nisa yace "ni kaina gaba ɗaya ya kulle, na rasa abunyi semun toshe nan se can ya buɗe, na rasa wane banzan ne yayi wannan aikin" Alhaji Musa yace "tabbas akwai lauje cikin naɗi, yanzu abunda ze faru shine, zamu saurari Bukar muji me zece, lallai a binciki wanda yayi wannaan aika aikar, sannan a tabattar an kama yaron nan an maida shi" "haka ma za'ayi, wannan shine abunda ya dace, akama shi harse an ga Daula" Anwar yana zaune yana cin Abinci yace "Mumsy kin san wani abu kuwa?" "A'a seka faɗa" ta bashi amsa "wato bawa baya taɓa gane Allah subhanahu wata'ala yayi masa ni'ima, se yayinda wannan ni'imar ta gushe, kinga ko 'yancin kayi yawonka ɗin nan inda kaga dama, ba ƙaramar ni' ima bace, zama guri ɗaya bala'ine Mum, ga rashin gurin kwanciya me kyau, ba Abinci me kyau, wai danma nine fa wasu haka suke tagayyara a cikin gurin nan " Hajiya Halima tace " Aini duk zance ya ƙare, tunda Allah ya fito min da kak, Se fatan Allah ya kiyaye gaba" Anwar yace  "Ameen Mummy, ni yanzu fatana ubangiji Allah ya bayyana Daddy, yasa yana hannu nagari, dan na tsorata da abubuwan da suke faruwa" Mummy tace "kai kam wannan dashi ya haife ka da an shiga uku, kai har yanzu baka shiga hankalinka ba, ba kaga masifar daka shiga saboda temako ba, still kai tunaninsa ka keyi" . "Mummy ba zan taɓa iya dena tunaninsa ba, saboda gudunmuwarsa a rayuwar mu" Wayar Anwar ce ta shiga ringing, ya ajiye spoon ɗin da yake cin Abincin ya ɗaga wayar yasa a kunnensa. Lambar Bulama ce, bayan sun gaisa Bulama yace "Anwar ashe ka fito?" Cike da ladabi Anwar yace "eh Daddy na fito" "to Alhamdilillah, Allah ya kiyaye gaba inba damuwa ina son ganinka anan gida, zamuyi magana" "to shikenan, Insha Allah idan nayi sallar la'asar zanzo" Bulama yace "to babu laifi" Anwar Ya ajiye wayar, Hajiya Halima tace "waye haka?" "babansu Fahad ne, yace inaje yana son ganina" "ba zaka ba" ta faɗa kanta tsaye. "Mummy meyasa?" "saboda haka naga dama, akanme zece kaje bayan ba irin sintirim da ba ba akan yasa baki a sake ka yaƙi" Anwar yace "haba Mummy, kidinga yiwa mutane uzuri mana, a baya kinsha neman Alfarma yayi miki, dan wannan karon be miki ba be kamata ki manta baya ba, kiyi haƙuri i je i ji meze ce" "shikenan tunda kace haka, amma ba dan haka ba Wallahi da bazaka ba" "kiyi haƙuri, kar hakan yayi sanadiyyar lalacewar zumjncinku" Da yamma Hindu tayi kwalliya itada su Hanne da ƙannensu zeuje biki, Widad na ganin Hindu tace "Masha Allah, you look so beautiful Hindatu, kina da kyau masha Allah" Hindu tace "Rufani ki saya Amarya, ai daga kanku kyau ya ƙare, kina ganina baƙa kirin ina wani kyau yake?" Widad tace  "waye yace miki baki da kyau? Ke nima fa ba wata kyakkyawa bace, dan dai ina da haske ne, amma baki ganki ba, kinyi kyau Allah ya baki miji nagari ɗan birni" "hmm Amarya kenan, ni da ban taɓa zuwa birni ba, banyi boko ba ta ina ɗan birni ze ganni ya aura" Widad tace "da ina da Yaya namiji zance ya aure ki Hindu, kina da kirki kaman Mama, wai ina zakune?" "biki ne zamuje, a gangare" Widad tace "laaa shine babu gayyata, ku jirani zan biku, dama ban taɓa fita waje ba" Hindu tace "to ai Amarya baki da kaya irin Atamfa, duk kayanki ba irin namu bane, idan muka je seki zama abin kallo, kuma dama gaki ba kalarmu ba" "se in saka hijjabi" Gwaggo tace "A'a amarya bekamata ki fita ba, baki tambayi mijinki ba, se da yaddar sa sannan zaki fita" "Mama baze ce komai bafa" "dukda haka, kuda kukayi ilimi ma Amarya, ai kunfi mu sanin hukuncin hakan" Hak Widad tana ji tana gani aka tafi biki aka barta a gidan. Bata ji daɗin hanatan da Gwaggo tayi ba, sedai bata son yi mata musune. Daf da la'asar Yusuf ya dawo, ya taho da kayan da Saleh ya bayar a siyo musu, seda Gwaggo ta kalli Widad sannan ta tashi, ta taya shi kai kayan ɗaki. Ya fito ya ɗauki buta yana alwala, yace "Mama yau naga gidan shiru, ina mutan gidan ne?" Gwaggo tace  "sun tafi biki, tace zata bisu nace karta je seta tambayeka, shine taƙi kulani" Yusuf yayi dariya yace "babbar magana, faɗa tsakanin 'ya da uwa yau" Widad tace "tunda nazo fa ban taɓa fita ba, kullum ina gida" Yusuf yace  "idan kin fita Meza kiyi? Sarkin rigima" "kaikuma kaji ka, Yoseef ka kiyayeni nice sarkin rigimar?" Gwaggo tace "ɗiyar albarka a dinga saya masa sunan mana, idan daga ke se shine seki faɗa, amma a gaban mutane mu nan abun kunyane mace ta dinga faɗan sunan mijinta kai tsaye" Yusuf yace "yawwa gaya mata dai Gwaggo" Cikin Shagwaɓa tace "to me zance masa?" Gwaggo tace  "ki dai samo wani sunan mi dinga gaya masa, kafin Allah ya baku rabo, in kin haihu seki dinga cewa baban wane ko wance" Haɗa ido sukayi da Yusuf, ga mamakinsa se yaga ta kwashe da dariya tace "taɓ sedai inya Auri Hanne ta haifa masa, amma ni babu wannan Kalamin, ai Yayana ne kai ko Yoseef?" Tai maganar cikin sigar zolaya, tayi gaba ta bar tsakar gidan, Gwaggo ta zata kishine yake damunta, saboda tasan yadda basa shiri da Hanne, shi kuwa Yusuf, a wata cakwalkwalin cakwakiyar tunani ta kuma sashi, duk jikinsa yayi sanyi. Bayan yayi sallar la'asar ya koma gida, ya tarar da Widad tana gyaran Akwati, ya kalleta yace "Queen waye yace miki zan Auri Hanne? Idan kuma Gwaggo ba taji daɗin abunda kika faɗa bafa?" "Ai naga ita Hanne kaman she's having the same feelings on you, she also believes in love" "Se kuma akace miki ni Aurenta zanyi?" "to waye yasan muku? Ranar da zamu koma gida, idan ka sake ni base ka Aure ta ba, ka tafi da sabuwar Amaryarka ba" Tsaki Yusuf yayi, saboda yaji haushi sosai, ya miƙe ya bar ɗakin, bin bayansa Widad tayi da kallo, ta taɓe baki ta cigaba da aiki ta. Tunda ya fita be dawo gida ba se bayan sallar isha'i, sannan yaƙi kulata kwata kwata, dukda taji ba daɗin dena kulatan da yayi da yawan tsokanar ta da yake, yaji ba daɗi amma ta maze ta basar dashi itama, haka kowa ya kwanta be kula kowa ba. Da Asuba ma da yayi salla, suka zauna zaman karatu seda gari ya fara haske sannan ya taho gidan, tun bayan da aka idar da sallar Asuba kafin a fara karatu, Saleh ya janyo Yusuf waje yace "Nifa zan koma, sammako zanyi in tafi tunda kaji sauƙi" . Yusuf yace "da wuri haka Saleh?" Saleh yace "eh mana dole, in tafi bana son mutanen nan su farga su fara zargin wani abu" Yusuf yace "hakane, mungode Saleh Allah yasaka maka da alheri" "Ameen ya Allah, nace ka gaya mata kuwa?" Yusuf ya ɗanyi shiru sannan ya girgiza kai yace  "A'a amma zan gayamata insha Allah" Saleh yace "gara ka gaya mata, tayi duk borin da zata yi ta gama a nan, sedai Kayi haƙuri, ina son insha Allah idan na koma zanje in gaida Ummanka, in gaya mata kana cikin ƙoshin lafiya" Yusuf yayi murmushi yace  "ka gaya mata ina lafiya, kuma ina kewarta, sannan ta kwantar da hankalinta" Saleh yace  "zan gaya mata insha Allah, sena sake dawowa" Sukayi Sallama Saleh ya tafi. Widad kam wanke wanke suke ita da Hindu, Hindu tace  "Amarya ban taɓa tsammanin kin iya faɗa haka ba, ashe kina sane kike ƙyale Hanne se kace bakya kishin mijinki" Widad tace "Meye kishi?" Buɗe baki Hindu tayi tace "baki san meye kishi ba?" Widad ta jinjina mata kai tace "ni ban san wani kishi ba, banajin komai ina dai ji ana faɗa amma ban san me ake jiba" "Lallai Amarya abun mamakin ki da yawa yake, se kace wadda akayiwa Auren dole? Zakice ba kya kishinsa, Amma dai ai kina sonshi ko?" Taɓe baki Widad tayi tace  "Nifa ban san me ake ji ba a son nan, nifa kawai gani nake wannan son shirme ne, babu wani so mutanene kawai ke abunsu" Dariya Hindu tayi tace  "Yanzu dai bakya son Yusuf ɗin kenan?" "To base na yadda akwai son sannan zan iya banbance idan ina sonshi ko bana sonshi ba?" Hindu tace "ina mamakin kalar taki rayuwar Amarya, gaba ɗaya abubuwan ki wani lokacin sun saɓa da na sauran mutane, anya gidan ku akwai mutane kuwa?" Widad tayi dariya tace "eh mana, akwai mutane, sedai nikaɗai nake rayuwata" "Amma meyasa kika dinga kuka, kika kasa cin Abinci da mijinki bashi da lafiya?" Ɗan shiru Widad tayi tace "Saboda idan Yoseef ya mutu, nima tamkar matacciya nake, ban san kowa anan ba se Allah se shi, sannan ya sha wahala sosai sabodani, yana shiga damuwa idan bani da lafiya ko ina cikin damuwa, shiyasa naji rashin lafiyarsa har cikin raina, kuma kinga ni bani da wa ko ƙani, Mamana ta rasu ina Yarinya Babana kawai nasani, Yanzu Yusuf shine yaya na, shine ƙanina shine ɗan uwana, shine komai nawa anan" Hindu tace "Allah sarki Amarya, kin bani tausayi wallahi, amma Saleh yace mana ɗan uwanki ne Yusuf" Widad tace "ɗan uwana ne mana, Allah ne ya bawa Babana shi, ya zama garkuwa a gareni, Hindu kina da kirki sosai naga garin nan kun ɗau Aure da mahimmanci sosai, Allah ba yadda be iya ba, na dage ba zanyi Aure a rayuwa ta ba, babu Aure a gabana saboda wani ƙuduri da nake dashi a raina, babu zato ƙaddara tasa na Auri Yusuf, ina yiwa mazanmu na Hausawa kallon wanda basu san darajar Aure ba, gaba ɗaya ina yiwa Aure kallon rayuwar muzgunawa, Amma ina miki fatan ki Auri Namji kamar Yoseef, idan akace akwai mutum me haƙuri kamarsa zance ƙaryane, Amma yana da haƙuri sosai, nasan yana haƙuri dani, ni gaba ɗaya tausayinsa nake ji Hindu saboda..... Ta kasa ƙare maganar se Hawaye dake bin idonta, Yusuf yana tsaye a soro yana jin duk hirar da sukeyi, a hankali Yusuf yayi gyaran murya tare da yin sallama. Da sauri Widad ta basar ta share hawayenta, Yusuf yace "Sannunku da aiki" Hindu tace "Yawwa ina kwana" "lafiya ƙalau Alhamdilillah" Ya kalli Widad yace  "My Queen, let's go inside" Ta kalle shi tace  "ka gama fushin?" "ni dama nace ina fushi da ke ne?" "ni dai ka bari in gama wanke wanke na" Hindu tace "kije zan ƙarasa" Yusuf yace  "ƙyaleta, idan bata tashi ba, zan ɗauketa ne cak in kaita" Hindu ta sunkuyar da kai, dan abun nasu Yusuf wani lokacin basa jin kunya. Ɗaki suka shiga, ta kalle shi tace "gani meye?" "Ƙwanki dama zan soya miki, tunda bakya so shikenan" Murmushi tayi tace   "Au ai na manta, soyamin inci" Murmushi Yusuf yayi, ta zauna ta zuba masa ido, ya fasa ƙwan ya kaɗa yasa gishiri, dan su nan babu Seasoning. "Wai dan Allah Mamanka ce duk ta koya maka wannan aikin?" "Eh mana gashi kuwa kina gani" "taɓ gaskiya kaji daɗi, ina Baban ka, baka maganarsa  kullum se Ummanka kake faɗa" Yusuf yace "Allah yayi masa rasuwa" "Eyya Allah ya jiƙansa, yayi masa rahama" "Ameen" Ya miƙo mata ƙwan a plate, ya dafa mata tea ya haɗa mata, Widad tace "Allah sarki rayuwa, yau ni nake murna zan ci ƙwai, alhalin har kamfanine dani da'ake fitar da ƙwai har wajen Nigeria" Yusuf yace "haka lamarin ubangiji yake, sedai dama da bredi se yafi daɗi" "hakan ma nagode, zama da kai ka koyamin ci kuma da ni ba haka nake ba" "Eh mana, so nake idan muka koma gida kar aga rama a tare da ke" Dariya tayi tace  "matso muci" "A'a ci abinki, dama ke na saiwa, ni in aka ɗumama tuwo se inci" "Aikuwa ba zance kaci dole ba, cikinka ni ci zan in ƙoshi, kaita jin ƙamshinsa" Ta soma cin ƙwan nan, kawai yaga tayi murmushi tace "ban taɓa cin ƙwai mara daɗin wannan ba" Yusuf yace "to mutum ya soya wanda yafi wannan in an isa" Tai murmushi tace "Gwaggo tana koyamin ai, zakayi mamakin yadda zan iya girki, inyi girki me daɗin da baka taɓa cin irinsa ba" Ta cigaba da cin Abincinta, ƙura mata ido yayi yaga yadda take nishaɗi, tana cin Abincinta cikin nishaɗi, tunani yake ko ya gayamata yanzu? Tunda tana cikin nishaɗi, to idan kuma ya ɓata mata nishaɗin da take fa?. Ba tare da ta kalli Yusuf ba tace "gayamin abunda kake son gayamin ka dena kallona kar in ƙware" Jin maganar tata yayi a bazata, dan be zaci tana kallonsa ba, kuma yaji muryarta ta a asalin Widad ɗinta me cike da izza da jin kai. Cikin kame kame Yusuf yace "Amm. Bakomai dama.... " bana son ƙarya, kuma bana son wasa da hankali Yoseef, ina jinka ka gayamin abunda kake son faɗa " Gaban Yusuf ya faɗi, yace  " dan Allah ina son ki fahimceni dama... " "ni mutum ce kamarka, ban isa inyi maka abunda Allah be maka ba, sedai kome bakinka ze furta, karka kuskura kayi min ƙarya" "to ai ƙaryar ma nayi miki Widad, shiyasa nake fargabar ta ina zan fara miki maganar ban san yanda zaki fahimci abun ba" Wani irin sheɗanin kallo ta ɗago idonta tayi masa, me cike da tarin tuhuma, da gargaɗi gami da kashedi. LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA, BA DANNI BA DA GIRMAN ALLAH. A TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 52_53 LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH 07063065680 Gaba ɗaya Yusuf ya shiga taradaddi, gumi ya tsasttsafo masa a goshi, saboda irin kallon da take masa, dan tun a nan yaga alamar rashin nasara. Ɗauke idonta tayi daga kallonsa tace "ina jinka" tai maganar tana zuƙar tea ɗinta, Yusuf yace "Da farko zan fara da baki haƙuri dan Allah... " Katseshi tayi ta hanyar cewa "bana son wani ban haƙuri, ka tafi kai tsaye kawai ina jinka" Cikin damuwa yace "dole in baki haƙuri, saboda a karon farko da ƙarya na fara miki, tun a zuwana akan ƙarya nazo miki, saboda nima ban san ya akai hakan ta faru ba, saboda" Se kuma yayi shiru. Ba tare da ta kalle shi ba tace  "to tunda ka kasa gayamin ni bari in gaya maka abunda kake son faɗa ɗin ka kasa, na farko kai jam'in ɗan sanda ne na sirri ko ba haka ba?" Ƙuuuu  cikin Yusuf ya kaɗa, ya kalle ta a razane, ta ci gaba da cin Abincinta tace "cigaba na fara maka, ƙarasa ina jinka, saura me kuma?" Kasa magana yayi, ya dinga binta da kallo cike da ban al'ajabi, kamar yaga wata halitta daban. "yanzun ma zaka cigaba ne ko in cigaba da gaya maka"? Tai maganar tana kallonsa "Amma ya akayi kika sani?" Cikin isa da taƙama tace "An turo ka ne a matsayin jami'in sirri, da sunan wai ka bani kariya ko?" Buɗe baki Yusuf yayi yana kallonta, amma ya kasa cewa komai dama tasan waye shi? Ta kalle shi tace "shikenan ko akwai saura?" Wani irin yawu Yusuf ya haɗiye da ƙyar, kai da ka ganshi kaga mara gaskiya, yadda yake ta gumi kuma ya kasa cewa komai. "tunda ka kasa magana bari in ƙarasa maka, bayan bani kariya da kake, kuma kana yin bincike akan maƙiyan mahaifina, da wanda suke bibiya ta, ka maida hankali sosai akan aikinka, sannan kana taka tsan tsan dan kar in san ko kai waye" Ta ɗanyi shiru tana nazarinsa sannan tace  "Sannu Yoseef amma meyasa kasa hannu akan contract ɗina, bayan na gaya maka bana yafewa maƙaryaci?, saboda tsabar taurin kai, son aiki da rashin nuna gazawa ka saka hannu, dukda baka san wane irin hukunci zan ɗauka akanka ba idan na ganoka, idan ban manta ba a lokacin nace if you know you are here to spy don't sign the contract, but you feel like to sign it, saboda ba zaka iya komawa Office ba tare da kayi aikin da'aka turoka ba right? Yoseef meyasa kayimin ƙarya? " Jiki a sanyaye Yusuf yace " ai kin bawa kanki wannan amsar Widad, bazan iya komawa ince ba zanyi aikin ba, saboda Alƙawari nayi kafin in fara aiki zan kare rayuka da dukiyoyin jama'a, kuma tunda na fara aikin, dagaske har cikin zuciyata naji ina son in baki kariya, musamman ranar da mukaje gurin birthday Nurat akayi yunƙurin saceki, tun anan na fara karaya, na ƙara tabattarwa lallai rayuwarki a hatsari take, dan haka nayi ɗamarar baki kariya iya iyawata, amma dan Allah ya akayi kika san wannan abubuwan haka?" Ta ɗan jinjina kai tace " lallai biri yayi kama da mutum, ranar ba yadda banyi da kai ka gayamin meyafaru ba, amma kaƙi ka gayamin, nima nasan nayi ganganci a wannan ranar, na zuwa gidan Alhaji Musa, sedai ina ƙoƙarin cire kaina a cikin rigimarsa da mahaifina, shine dalilina na zuwa gidans, amma shima ka ɓoyemin baka gayamin meyafaru ba ranar, meyasa? " Yusuf yace " saboda muddin na gaya miki zakiyi yunƙurin ɗaukar mataki ne, da kinyi yinƙurin yin haka nikuma Asiri naa ze iya tonuwa, kuma zaki ɓata komai ne, Amma dan Allah ya akayi kika sani? " Cikin isa tace "Lallai ka raina Wacece Widad da kuma AƘIDARTA, in dai nice har yanzu bakaga komai ba, Tunda kazo gidanmu, jikina ya bani akwai something different with you, either good or bad, na kasa nutsuwa, na dinga ɓullo da abubuwa daban daban amma na kasa gane komai na cutarwa a tare da kai, ranar da 'yan sanda suka kama ka da bindiga, ni na fara ganin bindigar a jikinka kafin mu fita daga gida, kazo shiga mota ka ɗaga rigarka naga bindigar, nai shiru ban nuna na gani ba, dan ina son sanin da wacce kazo, sannan inga wani hukunci ne ya dace da kai, bayan mun fita a ranar aka kamaka da bindiga ka bawa 'yan sanda id card, sukayi ƙoƙarin saluting ɗinka amma ka hanasu, tun daga nan nabi diddigi da ƙwaƙƙwafinka na gane waye kai, har headquarter ɗinku naje aka bincikomin waye kai, sedai abu ɗaya ne ban gano ba har yanzu, waye yasa a baka aikin nan?!" Yusuf yayi ajiyar zuciya, cikin damuwa yace " Nima ban sani ba, da bani za'a bawa aikin ba, amma abokin aikina yace a bani na fishi haƙuri, ban san waye ya bada aikinba nima" Widad tace  "Abokin aikinka Sani me zuwa gurin Isa megadi ko? Wato Abbas" Gaba ɗaya Yusuf ya rasa meze ce saboda tsananin mamaki. "Ni na saka aka ɗauke shi daga kano, aka kai shi kudancin Nigeria saboda ban yadda dashi ba, yayi ruwan Azzalumai da yawa" Yusuf yace "Dama kece kika saka aka ɗauke shi? Ba mugu bane aminina ne, bani da aboki sama dashi" "Yana ɗaya daga abunda yake cutar da mutane, shine saurin yadda, waye ya gaya maka duk memaka dariya sonka yake yi? Kayi kuskure ni bemin ba, shiyasa nasa aka rabashi da garin nan, sannan ina cike da son sanin waye ya bada wannan aikin" Yusuf kam rasa bakin magana yayi, se kallonta kawai da yake yi. Widad tace "shikenan" ta miƙe tsaye ta ɗau kwanukanta, yaji taja sumar kansa tace  "matsoraci kawai, ashe haka kake da tsoro, i wish kaga idonka yadda suka sauya, kaine mutum na farko da na yafewa wanda yai min laifi mafi muni, saboda kaima hanyar da akabi aka baka aikin dan a cutar da kaine" Yusuf yace "kamar yaya?" "Bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai waje abunta tana dariya. Mamaki ya cika Yusuf tatil, yanzu dama kallon biri yake mata take masa na Ayaba, tasan waye shi tsawon lokacin nan, be taɓa zaton zata gane ba yadda ya dinga taka tsan tsan, lallai Widad ba ƙaramin wayone da ita ba, amma kuma yana da tarin tambayoyi daze mata, amma taƙi bashi damar yin hakan. Anwar ne ya shigo falon mahaifiyarsa yace  "Mummy zanje kiran da Babansu Fahad yake min ne" Ta kalle shi tace "Naji amma tare da Amal zaku tafi" Anwar yace "Amma Mummy meyasa?" "Saboda haka naga dama" ta bashi amsa, ta ɗau wayarta ta kira Amal tace tazo. Befi mintuna biyar ba sega Amal ta shigo tace  "Mummy gani" "Jeki shirya maza kizo kuje gidan Bulsma keda yayanku" Amal tace to, Hajiya Halima ta kalle shi tace "jeka mota ka jira ta" Anwar ya fita kamar yadda aka bashi umarni, Amal ta shirya ta koma ɗakin mahaifiyarta, tace  "Mummy gani na shirya" "Yawwa ki buɗe kunnenki ki jini, wannan yayan naku wani lokacin sakaraine, ba hankali ya cika ba, ina son ki saka min ido akansa, duk abunda ya faru ko abunda Bulama yace idan kun dawo ki gayamin" Amal tace "shikenan Mummy, Insha Allah zan gaya miki" Ta juya ta fita, ta samu Anwar a mota suka tafi. Suna zuwa gidan Bulama, Ramadan da Iman suka shiga murna  Ramadan yace  "Sannu Anwar, barka da Arziki Allah ya kiyaye gaba ya bayyana Daddy" Anwar yace  "Ameen Ramadan" Iman tace "Sannu Yaya Anwar, Allah ya tsare" Nan suka tsaya suna hira, Hajiya Sarah ta fito daga ɓangaren ta, itama tana ganin Anwar ta faɗaɗa murmushinta tace  "Anwar, sannu Anwar ashe ka fito da yau naso inzo har gida in maka jaje, Amma naji alamun hawan jinina ya tashi, shiyasa na fasa fitar" "Allah sarki, bakomai Mummy Allah ya baki lafiya" "Ameen Anwar, Amal sarkin zumunci ya Maman naku? ' Amal tayi murmushi tace " Mummy kenan tana lafiya " Bulama ne ya sakko daga kan benensa, bayan ya sakko Anwar cikin girmamawa ya rusina yace  " barka da Yamma Daddy " Bulama yace " Yawwa barka Anwar, ya kake ashe ka fito?" "Eh Daddy Alhamdilillah, Allah yayi na fito" Amal cike da basarwa tace "Ina wuni" Bulama yace "lafiya ƙalau Autar mamanta, ya gidan naku?" "Lafiya ƙalau" ta bashi amsa. Yazo ya zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun falon. Ya kalli Anwar yace "barka da Arziki Anwar, ba irin sintiri da shiga ficen da ba'ayi ba akan aga an samu ka kuɓuta amma Allah be nufa ba, amma ya akayi suka sakoka ne suka bar Sufyan?" Anwar yace "to nima dai wani mutum ne yazo ya taho dani, bemin wani gamshashen bayani akai ba, ya cemin shima wanine ya turoshi" "Allah sarki, haka lamarin ubangiji yake ai, kaga mu ba yadda bamuyi ba amma abu ya gagara, mahaifiyarka ta ɗaga hankalinta ta dinga ganin kamar bama wani ƙoƙari akai, se gashi Allah yayi an sako ka, to ubangiji Allah ya kiyaye gaba" "Ameen ya Allah Daddy, Daddy nace to har yanzu babu wani labari akan ɓatan Daddy, har yanzu ba'a san inda yake ba?" Bulama cikin damuwa yace  "Anwar da akwai wani labari ai da kaji, babu wani labari har yanzu, binciken ake amma kamar ba'ayi" "ubangiji Allah ya bayyana shi, ni fatana Allah yasa yana hannu nagari, tunda bashi da lafiya" Hajiya Sarah tace "sha'anin ƙasarmu ai se Addu'a, banda haka ace an sace mutum kamar Alhaji Daula, abun da mamaki kuma har yanzu ko a jita jita babu wanda yaji inda yake, bawan Allah nan ba lafiya ba, yana fama da kansa ga tashin hankalin an sace masa 'ya, Amma a bishi har gadon Asibiti a sace, ga' yar tasa har yanzu babu wanda yasan inda take, abun akwai ban tausayi, Daula yana ganin Jarrabawa " Bulama yace " tabbas, yana ganin jarrabawa, na rasa wani irin abune wannan ita kanta Widad wata na biyu zuwa uku kenan da ɓatan tal, amma babu labarin inda take, ni abun har tsoro yake bani" Anwar yace "gaskiya ne, abun da tsoro kam, kamar Widad tasan meze faru ranar da zasu tafi farm house, tana kuka tacemin ga Amanar Daddy nan in kula dashi, nace mata zanyi iya ƙoƙarina, Amma ga abunda ya faru, i don't even know how to explain this incident to her when she's back " Ramadan dake gefe yace " Allah sarki, karka damu ai duk wanda yaji abunda ya faru yasan ƙaddara ce, Amma ni wani lokacin har mamakin Widad nake, yarinyar nan 'yar baiwace akwai ta da kai" Anwar yace  "sosai makuwa, ina fatan Allah ya bayyana mana su gaba ɗaya" Suka amsa da Ameen. Haka suka cigaba da hira, sannan suka fito zasu tafi. A harabar gidan suka haɗu da Fahad, Fahad yana ganinsa cike da borin kumya ya rungume Anwar yana faɗin  "Ohh God, so you are free now, Alhamdilillah na ta yaka murna, Allah ya kiyaye gaba, nace zanje in duba ka akace ba'a bari a ganku" Anwar yace "Haba kamar kai kaje inda nake ace bazaka ganni ba, da kazo da zamu iya haɗuwa ai" Fahad yace "kasan bana son disgracing, and those people are good in that, but da naji ance court za'a kaiku ya akayi ka fito?" Anwar yace "Al'amarin ubangiji ne kawai, shiya dubeni ya fitar dani" Fahad yace "hakane, that's good ubangiji Allah ya ƙara karewa" ya kalli Amal yace  "ke bakya kula mutane ne?" Tsaki tayi tai masa wani irin kallon banza, ta buɗe mota ta shige. Anwar ya girgiza kai yace "Fahad bari inje, akwai inda nake son zuwa daga nan". "Ok, shikenan my regards to Mummy and lovely Ramla please" Anwar yayi murmushin yaƙe yace  "Fahad kenan, za suji insha Allah" Daga nan shima ya juya ya shiga motar. Suna cikin tafiya Anwar yace  "wai Amal meyasa kuke yawan faɗa da Fahad ne? Banji daɗin abun kikayi masa ba, ya yanki ne fa" Amal ta kwaɓe baki tace "nifa wallahi Yaya Anwar na tsani Fahad ɗin nan, nifa tun asali bemin ba, mugun maƙaryaci ne munafuki duk yadda kuke dashi ya kasa zuwa ya jajanta maka abunda ya same ka" Anwar yace  "to meye a ciki? Koma menene ba gashi Allah ya fito dani ba, idan kace zaka dinga biye wa mutane ranka ne kawai ze ta ɓaci" Amal tace "taɓ ai kai zuciyar ka daban Yaya, ba kowa ze iya wannan abun naka ba" Da suka je gida a waje yayi parking, ya kalli Amal yace "sauka ki shiga gida, ina son zani wani guri ne" Ba musu ta sauka daga motar ta shige gida, shi kuma Anwar ya tafi. Shiru shiru Yusuf be fito daga ɗaki ba, har Widad taje tayi wanke wanke ta dawo yana zaune a inda ta barshi, ta kalle shi tace  "wai yau bazaka fitan bane?" Jiki a sanyaye yace  "zan fita mana" "to ai naga ko wanka ba kayi ba, ko har yanzu tunanin kake ne?" Ɗan murmushin yaƙe yayi, yana sake mamakin Widad, ya miƙe yaje yayi wanka ya shirya, yana yi yana kallonta yaga ko zata canza masa, amma yaga babu wata alama ta damuwa a tare da ita. "zan tafi" "Wai naga se wani sunkuyar da kai kake, kana komai a sanyaye meyafaru ne" Cikin damuwa ya kalleta yace  "bakomai" "to seka dawo" yasa kai ya fita. A hankali Widad tana ta koyon abubuwa, dan yanzu ta fara iya saƙa mafici da Hindu ke koya mata, tana gane abubuwa duk aikin da zasuyi seta shiga cikin su tana ƙoƙari. Yanzu indai Widad zasu gaisa da Hindu da turanci suke yi, Hindu na da matuƙar ƙoƙarin riƙe abubuwa, gashi ta sawa zuciyar ta zata iya, tana son karatun sosai, Widad ta koya mata na boko sannan tana mata bayani akan litattafan addini, sega Hindu ta iya gaisuwa da turanci, tasan sunan abubuwa, Widad tana yawan yi mata magana da turanci dan wasu lokutan hausar ma wahala take mata, dan haka Hindu take kama wasu abubuwan. Nan fa Hindu ta fara birge wasu daga cikin ƙawayenta, suke cewa itama ta koya musu. Hindu suna ɗaki tana yiwa Gwaggo tsifa tace "Gwaggo, kinga laraban gidan me tabarma, da su Ishalle ne wai suma suke son a dinga koya musu karatu, nace zan tambayi Amarya amma nauyinta nake ji, kar taga kamar na takura mata" Gwaggo tace  "kunfi kusa keda ita ai, Amma na lura kamar bata son mutane fa, kina ganin ko baƙi akayi ɗaki take komawa bata son mutane, amma ki tambaye ta idan zata dinga yi muku taren" Hindu tace "to shikenan zan tambayeta insha Allah, Amma nikam Gwaggo Amarya ba ƙaramin mamaki take bani ba, wai bata son meye kishi ba, kuma wai ita gani take Soyayya ƙaryace da ɓata lokaci, na tambayeta to bata son mijin nata? Wai wallahi itama bata sani ba ko tana sonshi ko bata sonshi " Gwaggo tayi murmushi tace " Amarya 'yata ta kaina, yarinyar kam tabbas yarinta ce ke damunta, kuma kinga karta kamar shagwaɓaɓiya ce, bata san abubuwa da dama na rayuwa ba, shi kansa zaman Auren da alama bata san meye ba, Amma insha Allah ina son in zauna da ita, in dinga yi mata nasiha, naga tana jin faɗa, dan Hindu ina jin takaicin Abunda Hanne ke aikatawa a gidan nan, yadda take shigewa Yaron nan, dan ina daf da kai ƙararta gurin mahaifinku" Hindu tace  "A'a Gwaggo dan Allah kiyi hakuri, idan kika gaya masa ze ɓata mata rai sosai, ni mamakin da ta ke bani da kuɗin Aurenta a ka fa, amma take haka, ki dai cigaba da ja mata kunne zata dena" "Ai banga alamar hakan ba" Har Yusuf ya dawo a cikin damuwa yake, saboda ya fuskanci kwata kwata gane kan Widad se Allah, yanzu zaku zauna lafiya ana jimawa ta canza gaba ɗaya. Widad bata san ya dawo ba, ta fito daga wanka tana zuwa ta tarar da Yusuf ya kwanta a ƙasa, ya lumshe ido. Widad tace "ya dai harka dawo ne? Ya naga ka kwanta haka a ƙasa, ko jikinne?" Ya buɗe idonsa ya kalleta yace "Eh na dawo, na gajine sosai bayana da ƙafafuna ciwo suke min" Ajiye bokitin tayi ta zauna kusa dashi tace "me kaje kayi a wajen bayanka yake ciwo sekace tsoho?" "Faskare nayi" ya bata amsa 'meye kuma Faskare? " ta tambaye shi, kallonta yayi yace  " Faskaren ne baki sani ba? " " Wallahi ban sani ba, kaima kana ganin wani abun idam nace ban sani ba ƙarya nake ko? " " A' a ni bance ƙarya kike ba, nasan baki sani bane, kuma daɗina dake idan baki sani ba kina tambaya" Widad tace "to ai ba wani abu bane, idan mutum be sani ba gara ya tambaya, ka tashi kaci Abinci seka yi wanka mana" "bari in huta tukuna" "Shikenan bari in sa kaya" har taje ta shirya Yusuf yana kwance, a hankali yaji tana danna masa bayan tace  "wajen inane yake maka ciwon?" "duka bayan Queen" "bance bana son Queen ɗin nan ba?" "Ai sunan naki ne bana son faɗa, kuma Daddy ma Gimbiya yake ce miki, ko in koma ce miki lovely kamar yadda yake faɗa?" Dundu tayi masa tace "A'a Widad zaka dinga cemin, niba lovely kowa bace ta Daddy ce" Yusuf yace "so kike Gwaggo tayi min faɗa? Tace ina faɗar sunan ki"? Dariya Widad tayi tace "Hajiya Mama manya, tace in dena kiran sunan ka fa ko?" "Eh amma baki dena ba kuma, ga sunan nawa ma baki iya faɗa ba, ana Yusuf kina Yoseef amma fa suman yana min daɗi in kin faɗa" Murmushi tayi tana danna masa baya tace  "shikenan zan dinga cewa Yayana, kamar yadda Daddy yake ce maka" Yusuf yace "A'a nifa mijinki ne ba Yayan ki ba, call me with romantic names mana, haba ke kuwa" "Kaine romantic ɗin ai, kai ka sansu ni ban sansu ba" "Tabbas na sansu, kuma ni zan dinga kiranki dasu" Shiru tayi masa, a hankali ya juyo daga ruf da cikin da yayi yace  "Nagode sosai My wife, Allah yasa ki a Aljanna, naji daɗin tausar nan kamar karki dena, dama kin iya kula da miji haka?" "A'a zomaye na iya kulawa da, ai koma meye kaika koyamin, idan bani da lafiya kayimin ina jin daɗi, shiyasa nayi maka" Shiru ya ɗanyi sannan yace  "Widad, meyasa kika ƙyaleni dukda girman laifin da nayi miki, baki hukunta ni ba?" Widad tace "Saboda Widad ba azzaluma bace, babu zalunci a AƘIDATA, duk wanda na kasa yafewa abunda yayi min to tabbas girman laifinsa ya wuce tunani, ya wuce laifin da zan iya yafewane" "Yanzu ni laifina be kai a hukuntani ba?" ya tambayeta "tabbas laifinka ya kai girman a hukunta ka, sedai kash akwai wani dalili me ƙarfin gaske daze hana ka karɓi hukunci, akwai wata ƙaddara da ta ratsa, ita ce zata hana ka karɓi hukunci, sannan idan nace zan hukunta ka Yoseef banwa kaina adalci ba, dan ka bani kariya ka bawa rayuwata kariya sosai, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana ai, matsoraci kaga gumin da ka dingayi ɗazu kamar ba kaine Jarumin ɗan sanda ba me gwagwarmaya kamar yadda aka bani labari, amma se gashi ina baka tsoro" "Wudas babu Jarumi a soyayya, ba hukuncin da za kimin ne damuwata ba, kice zaki rabu dani shine damuwata" Haɗe rai tayi tace  "me kace?" "A ina?" "da wani sunan ka kirani?" Dariya Yusuf yayi yace  "wai Wudas"? "kaima ko? Zanyi maganinka da kai da Harin da kuke ɓatamin suna, ni ba haka aka samin ba" "niba ruwana, ɗanawa kawai nayi ai, kuma sunan naki ne na Larabawa, ba kowa ze iya faɗa ba" Jikinta ne ya ɗanyi sanyi, tai shiru, Yusuf yace  "meyafaru kuma?" "Yoseef ina missing ɗin Daddy sosai, zuciya ta na kwaɗayin in ganshi, i missed a lot from him, ina kewar babana, dashi na rayu na buɗi ido, amma yanzu muna duniya ɗaya amma munyiwa juna nisan gaske, a dalilin wasu tsirarin mutane da suka saka rayuwarmu a gaba " Hawaye ne ya fara bin idonta, janyota jikinsa yayi ya shiga share mata hawayen cikin tausayawa yace " tabbas yin nesa da wanda muke so ba abune me sauƙi ba, kin ganni nima ban taɓa nisa da mahaifiyata haka ba, amma mu ɗau wannan a matsayin wata ƙaddara ta darasin rayuwa, kiyi hakuri insha Allah zamu koma kiga Daddy, nasan zaman ƙauyen nan tamakar zaman prison ne a gurinki amma ki daure mu cinye jarrabawar mu" Ajiyar zuciya ta sauke, ta sake kwanciya a jikinsa tace  "zamana a ƙauyen nan baya damuna, na ɗau hakan tamkar wani darasine na rayuwa, Allah ya na nunamin ishara, na koyi abubuwa da dama na rayuwa wanda bam sansu ba da, kuma a nan ina zaune hankalina a kwance babu tashin hankali, babu fargabar komai saɓanin a gida, ga dukiyar ga komai hankalina kullum a tashe ina tunanin ta inda maƙiya zasu farmin, nidai tun taso wata rayuwata a cikin ƙaddara take, ina fatan Allah ya kawomin ƙarshen abun nan haka, ya kawo kwanciyar hankali a gareni da mahaifina" Tai maganar tana ci gaba da zubar da hawaye, sosai tausayinta ke ratsa ilahirin jikin Yusuf, ya dinga shfa gashin kanta cikin sigar rarrashi zuwa gefen fuskarta,  yana tunanin anya duk ƙaddarar da Widad ta tashi a ciki takai a misalta ta dashi wadda ya tashi a cikinta?...... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH NA ƊAYA KYAUTA NE, WANNAN NA SIYARWA NE ₦300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 54_55 LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 Shiri ne ya wanzu a tsakaninsu, na wani ɗan lokaci, har bacci yayi awon gaba da Widad, Yusuf ya ƙurawa fuskarta ido, yana jin wani abu na fizgarsa game da ita, wani irin sonta na ƙara ratsa ilahirin jikinsa. Wai yau Widad ce kwance a hannunsa, har take masa kuka yana rarrashinta, kamar ba itace wannan me tsawa da muzuran ba, ya kwaɗaitu da son jin meyafaru da ita a rayuwa, meyafaru a rayuwarta haka? Amma yasan idan ya takura seya sani, to tsaf ze rusa duk wata alaƙa da yadda da take tsakaninsu Anwar kuwa gidan su Nurat ya tafi, seda yaje ƙofar gidansu sannan ya ɗakko wayarsa ya kirata, tana kwance tana kallon TV sedai idonta ce kawai akan tv, yayinda zuciyar ta tana can tana fama da tunani, se da wayar ta katse ya kuma kira sannan ta faraga, tasa hannu ta ɗaga wayar sedai tayi mamakin ganin sunan wanda yake kan wayar, Sunan Anwar ne a jiki. Da hanzari ta miƙe zaune ta ɗaga wayar tasa a kunnen ta. Anwar yace  "ko bacci kike ne na tashe ki" Zumbur ta miƙe zaune tace  "muryar wa nakeji ne haka?" "Muryar Anwar mana" Cikin farin ciki Nurat tace  "innalillahi, i don't even know what to say, I pray that am not dreaming" Anwar yayi murmushi yace "you are not dreaming dear, ina harabar gidanku" "dan Allah dagaske?" ta faɗa cikin tsananin farinciki Anwar yace  "leƙo ki gani" Mayafin doguwar rigar jikinta ta ɗauka ta yafa, ta ruga da gudu tayi waje, aikuwa tana zuwa ta tarar da Anwar zaune a cikin mota, da sauri ta ƙarasa gaban motar, tana ganin Anwar ɗinne kuwa kawai ta tsaya tana murmushi a lokaci ɗaya hawayen tausayinsa da farinciki ya shiga bin fuskarta. Ya rame sosai, se dogon hanci da manyan idanunsa da suka sake yin zuru zuru, ga duhu da yaya, koba a gaya maka ba akasan inda yaje babu komai se zunzurutun wahala. Ya kalleta fuskarsa ɗauke da damuwa yace  "ya da kuka kuma?" "Yaya Anwar dole inyi kuka, baka ji ba baka gani ba daga abun alkhairi aka kama ka, kaje kasha wahala ba yadda banyi ba a ɓoye a samu a sakeka amma abu ya gagara, ƙarewa ma akace kotu za'a kaika na shiga damuwa sosai hankalina ya tashi, se gashi Allah yasa ka fito Alhamdilillah, ban taɓa zaton zaka fito ba" Anwar yayi murmushi yace  "hakane, amma yanzu dena kukan mana" Murmushi tayi tace  "ƙyaleni na farinciki ne, taso muje Mummy ma na ciki seku gaisa, amma dan Allah karka nuna muna wani abu tarene, kawai dai ka nuna ka biyo a gaisa ne please" Anwar yace  "karki damu, ba abunda zan nuna insha Allah" Ya miƙe ya bita zuwa cikin gidan, a falo ya zauna yayin da Nurat ta shiga ɗakin mahaifiyarta   "Mummy kizo ga Anwar yazo ku gaisa" Da ɗan mamaki ta kalli Nurat tace  "Wane Anwar ɗin?" "ɗan gidan Hajiya Halima mana, yazo wucewa ne yace bari ya tsaya a gaisa ai an sako shi shekaranjiya" Mummy tace "Allah sarki, yaron kirki ashe an sake shi, bari gani nan bari inzo mugaisa" Ta sako mayafi ta fito, Anwar ya risina ya gaishe ta tace  "Anwar ashe an sako ka? To Ubangiji Allah ya tsare gaba" "Ameen ya Allah Mummy nagode sosai" "bakomai Anwar, dan Allah ka gaisarmin da maman naka idan ka koma" "zataji insha Allah Mummy, nagode sosai" "Yawwa Allah ya tsare" Suka amsa da Ameen, ita kuma ta koma ɗakinta. Nurat ta jashi suka koma harabar gidan, ta kalle shi tace  "Yaya Anwar, ya akayi ka fito ne?" Ya ɗanyi ajiyar zuciya yace "kowa tambayar da yake min kenan, wallahi ban sam waye ya fito dani ba, ban san mutumin ba, na tambaye shi waye shi, yace  wai ba'a bashi damar ya sanar dani waye shi ba, amma kin san wani abu?" Tace  "A'a seka faɗa" Anwar ya ɗan ƙara ƙasa da muryarsa yace  "ya cemin Daddy yana gurinsu, shiyasa ma suka sa aka sakeni, amma ban san dalilin da yasa suka sa aka sakeni aka bar Doctor Sufyan ba" Zaro ido tayi tace "yana gurinsu kuma? To suwaye su? Meyasa suka ɗauke shi?" "Nima be bani amsa ba Nurat, abun da ya cemin kawai kenan, wallahi gaba ɗaya a cikin damuwa nake, babu Widad babu Daddynta, gashi ranar daza'a ɗauketa kamar tasan abunda ze faru tacemin Anwar ga Amanar Daddy na nan ka kulamin dashi" Cikin damuwa Nurat tace  "kayi haƙuri Yaya Anwar, Allah ya gani kayi iya ƙoƙarinka, amma ƙaddara fa ta riga fata, babu yadda muka iya, sedai muyi ta musu Addu'a Allah yasa suna hannu nagari" Anwar yace "Ameen, Amma abun da damuwa ace mace kamar Widad a hannun wanda ba'a san ko suwaye ba, akwai tashin hankali sosai Nurat, kin san ku mata kusa a cikin hatsari kuke, daɗina ɗaya tana tare da Yusuf, amma dukda haka abun ba daɗi, mussman shi ƙaddara ta faɗa masa beji ba be gani ba" Nurat ta ɗanyi shiru tace  "hakane kam, ni kaina ina tausayin Yusuf Anwar, amma dan Allah dagaske direban Widad ne?" Anwar yace  "meyasa kika tambaya?" "bakomai kawai na tambaya ne" Yace  "eh direbanta ne, me kika gani?" Ɗan girgiza kai tayi tace "yana da kirki sosai, kuma da alama ta yadda dashi sosai, na zata ɗan uwantane" "Nima na gani, kuma yana ƙoƙari sosai akanta, yana mata biyayya ne sosai, kuma yana da haƙuri shiyasa suke shiri wasu lokutan" Nurat tace  "hakane kam, amma kuwa anje gidan su Yusuf ɗin, 'yan uwansa sun san halin da yake ciki?" "Aini kinga ban daɗe da dawowa ba, wasu abubuwan duk ban san me ake ciki ba, ban san daga ina yake zuwa ba, sedai zan bincika inji ubangiji Allah ya bayyana mana su gaba ɗaya, amma ina cikin damuwa sosai Nurat, tun Widad na ƙarama nake sonta, ban taɓa furtawa ba, saboda sanin halinta, katsan bayan na dawo naji ance Fahad ɗan gidan Alhaji Bulama zata aura, naita ƙoƙarin in cireta daga raina, sedai ashe ita gaba ɗaya bata da babban maƙiyi a duniyar nan sama da Aure, tana yiwa Aure wani bahagon kallo ne, har a yanzu haka na kasa cireta daga raina, ina jin sonta a zuciyata, ko bacci bana iyayi yadda yakamata, gashi ban san inda take ba gashi na kasa riƙe amanar data barmin" Wani irin tausayin Anwar ne ya kamata, a ranta tace 'ashe kaima kana cikin damuwar da nake ta soyayya' A zahiri kuma tace "na tausaya maka Yaya Anwar, ka sawa ranka wannan ɗin Jarrabawa ce, ubangiji Allah yasa mu cinye jarrabawar nan, kasha Lemom mana" Girgiza mata kai yayi yace  "A'a tafiya zanyi nagode sosai Nurat" Ɓata rai tayi tace  "gaskiya idan baka sha ba bazan ji daɗi ba, sekace na baka wani guba, ko kaima Widad ɗinne?" Murmushi yayi yace  "wane ni in zama kamar Gimbiya" Nan ya buɗe lenon ya tsiyayya yana sha suna cigaba da hira. Mahaifin Nurat ne ya dawo suna tsaka da hira, ya shigo da motarsa gidan yayi parking, ya fito daga motar yazo ze raɓa su ya wuce, Anwar yace "barka da Rana Yallaɓai" Ɗan tsayawa yayi ya kalli Anwar yace "wa nake gani haka kamar Anwar?" "eh nine ranka ya daɗe" "Allah sarki, ashe ka fito?" "Eh wallahi Na fito Alhamdilillah" "to yayi kyau haka ake so ai, har yanzu kuma babu wani labari akan ɓatan Daula ko?" "Babu har yanzu dai muna sauraren hukuma ne dai" "Allah sarki, yanzu an fasa kaika kotun kenan?" "Eh an wankeni, ance bani da laifi shine suka ƙyaleni" Alhaji Musa yace "gaskiya ne, ai dama bekamata a tsare wanda bashi da laifi ba, hakan ba daidai bane, kuma lawyoyin naku ne suka fitar da kai?" "A'a su hana su belina akayi, daga baya ma in sunzo hana su ganina ake, wani mutum ne yazo aka fitar dani" "ikon Allah, shima lawyer ne kokuwa?" Anwar yace "a'a ban san waye ba gaskiya, dan nima be gayamin ko shi waye ba" Alhaji Musa yace  "Allah sarki, to ubangiji Allah ya tsare" "Ameen yallaɓai nagode" Alhaji Musa ya shige cikin gida. Duk a aikin gida da Widad ke koya bata taɓa attempting zuwa gaban murhu ba, saboda bata son hayaƙi sam, ko menene tana daga gefe. Tana zaune a ƙarƙashin bishiya tana gyaran wake, Hindu tace  "Amarya dan Allah ƙawayena ne suke so suma a dinga koya musu karatu, in basu dameki ba, in baza'a takura miki ba" Widad ta ɗanyi shiru sannan tace "shikenan tunda ta hanyar ki ne, aini ban isa ince a'a ba, su samo abun rubutu da littafi se mucigaba insha Allah" Gwaggo tace "Amarya idan da takura fa karkiyi kara, kice musu a'a kawai su haƙura" "A'a Mama babu takura, bana son mutane ne dai su fiye zuwa inda nake, amma ai bakomai shi ilimin 'ya mace ai abun sone, koba komai zasu amfani al' ummar da suke ciki, suzo zan koya musu Insha Allah" Gwaggo tace  "to Allah ya saka miki da Alkhairi, mu zuwanki garin nan alkhairi ne ai a wajenmu" Widad tai murmushi tace "bakomai Mama, nima haɗuwata daku alkhairi ne ai". Hindu tace "lallai su Indo zasuji daɗi, bari inyi sharar nan inje in gaya musu" Hari tace  "wudas dan Allah nima gasu abu na nan a haɗamin dasu dan Allah" Hararta Widad tayi tace  "baza'a koya musu ba ɗin, yaren yahudawan zan koya musu?" Hari ta wangale baki tace "haba Wudas, dan Allah kiyi haƙuri ki koya musu" "Anƙi a koya musun" Widad ta bata amsa tare da haɗe rai. Hari bata kuma yin magana ba, tayi shiru ganin yadda Widad ta haɗe rai, Hanne ce ta fito tana wani yatsine fuska tana harare harare, Hindu ta kalle ta tace "Hanne ke zakiyi wanke wanke fa yau, kin bari ƙudaje se bin kwanukan suke" Hanne ta galla mata harara tace  "bazan ba, inda can ke kike sani inyi, banza uwar shisshigi da sa ido" Hindu tace "ke kika sani, haka za'a miki auren kije kina ƙazanta, ki bar kwanuka ƙudaje nabi" "Eh naji gara ni inada mashinshini ma, kefa ba uban wanda yake zuwa gjrinki, aba kamar mujiya aikin banza kawai" Jikin Hindu ne yayi sanyi, tai shiru gwanin ban tausayi. Hari se cewa tayi "ni kaina ina mamakin baƙin jini irin na Hindu, ba wanda yake zuwa inda take saboda tsabar girman kanta da baƙin jini" Shiru Hindu tayi tana goge Hawaye, Gwaggo ce ta janyo Hanne ta dinga kifa mata mari a zuciye. Widad tace "wai Auren nan dolene? Meye dan mutum bashi da saurayi? Saurayin banza dana wofi, Auren dole ne, itama wannan banzar mata hankali se kace ba sister ɗinki ba, kuna uwa ɗaya kina cin zarafinta" Hansai tace  "ba uwarsu ɗaya ba, Hindu ita kaɗai babarta ta haifa ta rasu, Gwaggo ce ta Riƙeta" Widad tayi mamaki sosai, dan yadda Gwaggo ke son Hindu seka zata ita ta haife ta. Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsugune tana kuka, Widad taje ta rugumo Hindu ta dinga rarrashinta tace  "kiyi haƙuri kinji Hindu, Allah has a better plan for you kinji Hindu, kiyi haƙuri ki ƙyalesu, ai Aurem ba dole bane" Gwaggo seda tayiwa Hanne tatas da zagi, ta tsitsstinka mata mari, tazo ta kama hannun Hindu tace  "dan Allah kiyi haƙuri kinji Hinduna, muna nan insha Allah miji nagari zezo miki insha Allah" Ita dai Hindu ba tace komai ba, se goge hawayenta da yake faman yi, tana jin zafin Gorin da akan mata na cewa bata da saurayi, Widad ma abun ba ƙaramin baƙantawa Widad rai yayi ba, dan bata son taga abunda ze taɓa mata Hindu, Allah ya haɗa jininsu sosai. Widad ta kalli Hari tace  "kekam abunda kika yi baki kyauta ba Hari, ke kanki aka bibiya sadakarki aka bawa megari ba dan kina da wani abu da namiji ze kalla ya aureki ba, dan ba kyau kika fi Hindu ba, yakamata ki dinga jan girmanki kema kin haifi mata" Shiru Hari tayi da yake tasan bata da gaskiya. Gaba ɗaya ƙarashen wunin nan haka Hindu tayi shi ba walwala, hakan ya shafi Walwalar Widad itama, seta kasa sakewa sukayi jugum jugum. Nurat suka gama hirarsu da Anwar, tai masa rakiya har mota ya tafi, sannan ta dawo, tana shiga falo ta tarar da mahaifinta a tsaye yana huci, ya kalleta yace  "dan ubanki meya haɗaki da wannan yaron?" Cikin rashin fahimta Nurat tace  "Daddy Anwar nefa" "ina ruwana koma uban waye? Ke yanzu shikenan ban isa in gayamiki kiji ba? Meye haɗinki dashi nace?" Mahaifiyar Nurat ce ta fito da sauri tace  "dan Allah ka saurarawa yarinyar nan, wucewa yazo yi ya tsaya suka gaisa meye abun ɗaga hankali kuma? ' " ke dama ke kike goya mata baya take karyamin doka, ni anya ma kuwa wannan' yata ce" Cikin mamaki tace  "Meka ke nufi da anya kuwa 'yarka ce? Zargina kake kome? Kokuma dan kana abu zata kake kowama haka yake?" A fusace yace  "ni kike gayawa haka?" "na gaya maka ɗin, ashe ba daɗi nida ka gayamin" "A gaban' yata kike cewa ina biye biye?" "to kace ƙaryane mana? Ni zaka kalla kace  anya 'yarka ce?" Aikuwa cike da zuciya yayi kan mahaifiyar Nurat, sedai cikin gaggawa Nurat ta shiga tsakani tana kuka, aikuwa yasa hannu ya shaƙota yayi wurgi gefe ɗaya, bisa tsautsayi tai gware da center table, take ta zube a gurin jini ya shiga zuba a goshinta kamar an buɗe famfo, take suka yi kanta da gudu, sedai ko motsi ba tayi. Mahaifiyarta ce ta ɗagota a gigice tana kiran sunanta, Alhaji Musa yasa hannu yana ƙoƙarin karɓar Nurat a hannunta amma ta riƙeta gama taƙi sakarmasa ita, cikin kuka tace "ka ƙyalemin 'yata, ai dama kace ba' yarka bace, tunda ka kashemin ita se hankalinka ya kwanta" Be saurareta ba ya suri Nurat da sauri yayi waje da ita jini yana zuba a goshinta. Amal kuwa bayan ta shiga gida, Hajiya Halima tace "ina Anwar ɗin?" "Ya ajiueni ya tafi, wai zashi wani guri ne" "Nifa bana son yawan yawon nan da yake tafiya, se wani abun ya sameshi tukuna ko? Ze dawo ya sameni ne, ina jinki meyafaru da kukaje gurin Bulama" Amal tace "ba wani abu bane, dama kawai tambayarsa yayi ya akayi yayi free? Se kuma jaje da yayi masa" Hajiya Halima tayi tsaki tace "Aikin banza, dana san hakane wallahi ba zashi ba, mutumin banza kawai" "Mummy kenan ɗan uwankine dai" "dalla rabu dani, ɗan uwana mara amfani ba" Amal tai murmushi tace "in an jima zamuga kun jone ai, ba'a shiga faɗanku" Widad bata wani iya rarrashi ba, dan haka ta kasa saka Hindu farinciki, haka kurum idan ta tuna Gorin da'akayiwa Hindu se taji ta ƙara tsanar Hanne, sam Hanne bata ɗakko halin Gwaggo ba, Gwaggo mace ce me kirki da kawaici, ba zaka taɓa cewa ba ita ta haifi Hindu ba, saboda yadda take nunawa kamar tafi son Hindu ma aka Hanne kai kace gaba ɗaya ita ta haife su, bautar da Hindu take wa Gwaggo Hanne ba tayi, ga shegen som jikin tsiya, shiyasa basa shiri da Gwaggo. Gwaggo se jan Hindu take da hira, amma taƙi sakin jiki, saboda gaba ɗaya ranta a ɓace yake, haka suka haƙura suka ƙyaleta, sedai hakan ba ƙaramin damun Widad yayi ba. Yau shiru shiru Yusuf be dawo ba, gashi tun la'asar hadari yake haɗuwa a garin, se cida ake me ƙarfin gaske, kowa ya shige ɗaki ga iska da'ake yi, gaba ɗaya hankalin Widad yaƙi kwanciya, Yusuf be dawo ba ga hadari se cida yake, ga wani irin tsoro da ya baibayeta, lungun kan katifa ta koma tayi shiru tana ta addu'a a ranta. Har magariba Yusuf be dawo ba, daga bakin ƙofar ɗakinsu tayi alwala, ta rufe ƙofar ta dawo tayi salla, se wata irin walƙiya ake. Ana idar da la'asar aka kece da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, babu Yusuf babu labarinsa, hakan ba ƙaramin ɗagawa Widad hankali yayi ba, be taɓa yin haka ba se yau. Tun Widad na tsumayin dawowar Yusuf harta fara cire rai, ga tsoro da ya bai baye ta, take ta fashe da kuka, ta dinga kuka kamar wata ƙaramar yarinya, ga tsoro ga gefe guda tana tunanin ko wani abu ya samu Yusuf ne. Har wajen ƙarfe goma da rabi na dare, gashi babu alamar za'a tsagaita da ruwan nan, ta dunƙule guri ɗaya tana kuka, ji take tamkar ɗakin nan ze ruso a kanta, dan in akayi cida ji take tamkar ɗakin yana vibrating. Babu zato ba tsammani taga An turo ƙofar ɗakin, Yusuf ne ya shigo ya jiƙe sharkaf da ruwa se ɗiga yake, jikinsa yana rawar sanyi. Tana ganinsa maimakon ta tausayawa a halin daya dawo, kawai ta fashe da kuka ta haushi da faɗa "Ina kaje ka tsaya, kalli agogo ƙarfe nawa? Kawai ka kama ka ɗagamin hankali ga tsoro inaji, ka fita kaje kayi zamanka baka damu da halin da zan shiga ba, wannan wane irin abu ne haka?" Aikuwa Yusuf ya ƙule, akanta yaje yasha wannan uwar baƙar wahalar, ga ruwan sama yayi masa duka, bata tausaya masa ba se masifa da ta haushi da ita daga shigowarsa, aikuwa ya ajiye kayan hannunsa, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko wata leda ya jefo mata, ya juya ya shiga kokawar canza kayan jikinsa. Ledar ta ɗauka, taji an nannaɗe leda cikin leda, ga ɗumi a jikin Ledar, se ƙarnin kifi da yake tashi a jiki. Yadda ya haɗe rai ne yai mata banza yasa ta gane haushi yaji, ya canza kayan jikinsa ya ɗau abun shimfiɗarsa ya shimfiɗa a bakin ƙofa inda yake kwanciya, ga babu abun rufa ga iska da feshin ruwa a gurin. Gaba ɗaya taji tausayinsa ya kamata, ta ƙarasa kan bargon da yake kwana ta zauna tace "ka taso mu kwanta akan shimfiɗata, kaga nan ruwa yana jiƙaka" Banza yayi mata, yaƙi ko motsawa daga inda yake, balle tasa ran ze kulata. "Yoseef magana fa nake maka" still dai bece komai ba yayi mata banza. Ta Kai hannunta ta shiga ɗan girgiza shi tana faɗin "dan Allah ka tashi, muje mu kwanta nan akwai sanyi" A ɗan kausashe yace "malama ki ƙyaleni, tunda bakya tausayina komai nayi abun faɗa ne a gurinki, bana taɓa yi miki abu ki yaba, sedai ki ɓata mini rai, maimakon ki tambayi ya akayi na daɗe haka meya sameni kawai kin hauni da masifa, ni matsa ki ban guri ki dena taɓani" Se kuma taga tabbas abunda tayi bata kyauta ba. "Am sorry, ka tashi daga nan karka yi zazzabi" "ina ruwanki idan nayi, ai ba damuwa kika yi dani ba, ki rabu dani kawai" Taga dai alamar Yusuf bashi da niyyar tashi, dan haka kawai tayi kwanciyarta a bayansa, sosai ruwa yake feshi yana jiƙasu. Yusuf yace "ke ki tashi daga gurin nan, wannan ruwan da yake taɓaki ze iya saki mura ko zazzaɓi" "gara ya samu tare, tunda bazaka tashi ba" tai maganar tana sake maƙalƙaleshi ta baya, Yusuf jiya yi yana nema ya dena fushin da yake, ya maze ya kunna fitilar torchlight ya haskata yace  "malama ki cikani kije ki kwanta" Noƙe masa kafaɗa tayi, Yusuf yace "Shikenan naji, tashi muje mu kwanta a taki shimfiɗar" Tana jin haka ta miƙe suka nufi katifar, ta gyara musu ita Yusuf ya zauna yace "miƙomin ledar nan" ta juya zata ɗakko akayi wata walƙiya data haske ɗakin gaba ɗaya. Gaba ɗaya ta afko kan Yusuf, ta riƙe shi gam jikinta yana tsuma, ta runtse ido sosai tana ajiyar zuciya. Aikuwa akayi wata tsawa me ƙarfin gaske, ruwa ya sake ɓallewa, haska fuskarta yayi yaga yadda jikinta yake tsuma tayi wiƙi wiƙi da ido kamar Agola a rabon gado, yai dariya yace "wai baki iya addu'a bane, se tsoro da kuka?" Tashi tayi daga jikinsa tana cuna baki gaba, ta miƙo masa ledar kifine a ciki, ya kalle ta yace  "wani guri aka kwatantamin, nace bari inje in siyo miki kifi, gurin da nisa ga babu abun hawa a kusa, nayi tafiyar ƙafa sosai, shiyasa kiga na daɗe fa" Shiru tayi tana kallonsa kamar taga wani sabon abu, ya buɗe ledar kifin, manya manyan gashashiyar tarwaɗa ce da karfashe. Ya zauna ya dinga cire ƙayar ya ɗakko ya kai bakinta, tasa hannu zata karɓa ya girgiza mata kai yace  "karki ɓata hannunki da ƙarni" Haka ya dinga bata tana ci, can kawai yaga tana hawaye, ya kalleta yace "meyafaru kuma? Yanzu kuma me nayi miki" Girgiza masa kai tayi alamar bakomai. "kifin ne ba daɗi" ya kuma tambayarta, nan ma ta girgiza masa kai "to faɗan da nayi mikine ya saki kuka?" Nan ma ta girgiza kai, ƙarshe tace  "Nagode" Yusuf yace "da akayi me?" "Ka siyomin kifi" "Haba Queen, meye abun kukan kuma? Kukan ki yana ɗagamin hankali sosai, dan Allah kidena kinji, bakomai is my responsibility to make you happy Baby" Yai maganar yana ɗago haɓarta da hannu ɗaya. Shiru tayi tana ci gaba da share hawaye, seda ta ƙoshi sannan Yusuf yaje ya wanke hannunsa, ya dawo ya tarar da ita a zaune. Yazo ya zauna a kusa da ita yace  "oya kwanta" A hankali ta zame jikinta ta kwanta tayi shiru, kamar wadda ruwa ya cinye, shima ya kwanta sedai ko mintuna biyar ba'ayi ba aka sake ƙyallo walƙiya, aikuwa ta kuma cakumo Yusuf kamar jikinsa ya tsage ta shige. Yusuf yace "Gimbiya addu'a zaki dingayi, kidena tsoro haka" Ba tace masa komai ba se sake lafewa da tayi a jikinsa, taƙi ko motsawa. Haka aka cigaba da tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya. Shima Yusuf ya rungumeta gam a jikinsa, yana wasa da saman gashinta data ɗaure da ribbon. A hankali ya kai hannunsa kan ribbon ɗin, saitin kunneta yace  "in cire?" "inka cire min seka gyaramin" Murmushi yayi, ya zare ribbon ɗin dogon Gashin kanta ya baje akan katifar. Yusuf ya dinga wasa da gashin, yana ɗaga shi yana wasa dashi, can Widad tace  "Yoseef wai dan Allah Aure dolene? Sannan meyasa ake Aure ne?" LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 56_57 Dariya tambayar tata ta bashi yace  "Habibty wannan wace irin tambaya ce haka kuma?" "Kaima wannan wane irin sunane, ni dan Allah ka dinga faɗar sunana" "to naji Wudas" "Allah ka ƙara gayamin kaima sena samo wani sunan na sama ka mara daɗi" Dariya yayi yace  "ke baki san ina matuƙar jin nauyin faɗar sunan nan bane? Yanamin nauyi a bakina, bana iya faɗar sunanki fa" Cikin Shagwaɓa tace "to meye abun wahala a Widad ɗin?" "ƙaunar da nakewa me sunan ne yasa yake min nauyi" "kaga ni duka ba wannan ba, ka bani amsar tambaya ta" "meyasa kika tambayeni?" Widad tace  "na tambaye ka kuma kana tambayata" "to ai tambayar ta kice tazo a wata iri, nama rasa me zance miki" A waje daka ke koyarwa in sun tambayeka wace amsa kake basu? " " ƙureni zakiyi kenan? " " ba wani ƙurewa ka bani amsa kawai " Yusuf yaja ajiyar zuciya yace "Aure ba farilla bane, amma yana da fa'ida tunda Allah ya halatta yinsa, idan kika duba akwai tarin hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam da suke magana akan Aure, sannan akwai ayoyi a cikin Al'qur'ani da suke magana akan Aure, akwai wani Hadisin Annabi salallahu alaihi wassalam yace  'kuyi aure ku hayayyafa domin inyi alfahari daku ranar Alƙiyama, kinga anan yana daga amfanin Aure samun zuriya, yin aure ka haifi' ya'ya nagari babban Alkhairi ne shima duba ga hadisin manzon Allah salallahu alaihi wassalam da yace 'idan bawa ya rasu dukkanin ayyukansa suna tsayawa banda abubuwa guda huɗu, wanda ya mutu yana me imani da Allah, da sadaƙatul jariya sadaka me gudana, kamar gina rijiya makarantar islamiyya da sauransu, ko wanda ya sanar da wani ilimi wanda ko bayan ya mutu ske amfani da shi, da kuma ɗa nagari, kinga anan yana daga cikin amfanin Aure kayi shi ka samu ɗa nagari ka mutu ya dinga maka addu'a, duk ayyukan bawa suna tsayawa idan ya mutu, amma in kayi Aure Allah ya baka ɗa nagari, yana maka addu'a, kinga babbar ribace wannan, ko yayi wani aiki da ladan ze dinga iskeka. Akwai hadisin manzon Allah salallahu alaihi wassalam da yake cewa 'ya ku taron samari, wanda ya samu iko a cikinku  to yayi Aure, idan kuma bashi da halin yin Aure to yayi Azumi, kinga Aure yana da amfani domin shi katanga ne daga aikata zina, yana sanya nutsuwa a zukatan wanda suka yi shi, akwai tarin hadisan manzon Allah salallahu alaihi da ayoyi da suka yi magana akan Aure, dan haka Aure yana da mahimmanci sosai your majesty" Ajiyar zuciya Widad tayi tace  "idan mutum be Aure ba ya aikata laifi?" "A'a, kamar yadda na gayamiki Aure ba farilla bane, dan haka babu laifi ga wanda beyi ba muddin ze kiyaye iyakokin ubangiji ya tsare kansa daga aikata dukkan wani nau'i na Zina, sedai darajar wanda yake da Aure da wanda bashi da shi ba ɗaya bane, mussman mace duk abunda tayi na aiki kona ibada a cikin gidan Aurenta tana da lada, hakama namiji duba da gaba ɗaya shikansa Auren ibada ne, akwai wanda sam Aure be halatta suyi shiba, misali wanda bashi da abunda ze iya riƙe Auren, ko yake da wata nakasa da baze iya sauke haƙƙin iyalinsa na Aure ba wanda ze zamana da cutarwa a ciki" Se kuma yai shiru, be kuma cewa komai ba, Widad ta sake gyara kwanciyarta a jikinsa tace  "to amma a haka akewa mutum wani kallo dan mutum be Aure ba, yau anyi abunda ya ɓatamin rai, yau na fara ganin anawa mutum rashin mutunci akan ba shi da saurayi, baka ga Abunda aka yi wa Hindu ba, abun ya bani haushi sosai ya bani mamaki" Yusuf yace "To ai cikar mutuncin mutum shine Aure Habibty, kece kike masa wani kallo na daban" "to tunda dai Auren ba dole bane, ai bekamata a dinga takurawa mutum ba, yanzu by mistake idan tayi Auren wani abu daba a so ya faru still ita za'a ɗorawa laifi, gaba ɗaya yau wani iri ta wuni tayi kuka sosai" "Kin damu da Hindu sosai Gimbiya" Widad tace "Wallahi kuwa, ina sonta har raina tana da kirki" Yusuf yace "Ashe kin san meye son, nine kawai bakya so" "Nifa ban san irin son da kai kake faɗa ba, amma ina jin Hindu kamar 'yar uwata, inaji dama gidanmu ɗaya ace ina da sister nima, nifa da zasu yadda idan zamu koma gida in tafi da ita" Yusuf yace "Ai kina dasu, gasu Amal nan da Ramlah suma sisters ɗinki ne, amma kike musu wulaƙanci" Widad tace  "Wallahi na tsanesu, tsana mafi tsanani da ban taɓa yiwa wata halitta ba, kuma ina nan idan na koma gida se sun bar mana gida, dan ba gidan ubansu bane" "Subhanallah meyasa?" "Bakomai" ta bashi amsa tare da gyara kwanciyar ta a jikinsa. A hankali yace  "bazaki gayamin ba?" Shiru tayi masa taƙi magana, tana jin yadda yake ta jera numfashi, kamar wani mara gaskiya, zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri, ga ruwan sama da yake ƙara zuba kamar da bakin ƙwarya. A ɗan shagwaɓe Widad tace "Yoseef am scared, kuma sanyi nake ji" Yusuf yace "calm down, muna tare ba abunda ze faru insha Allah, keep praying" Ta jinjina masa kai, a hankali Yusuf ya shiga kiran sunanta, tana jinsa amma taƙi amsawa, sema wata kasala da take saukar mata. Tana jin abunda Yusuf yake yi, amma ta kasa ko motsi, duk yadda Yusuf yaso tattara nutsuwarsa ya guje faruwar wani abu a tsakaninsa da Widad abu ya gagara. Ba dan ruwan saman da'ake ta kwararawa ba kamar da bakin ƙwarya, da babu abunda ze hana mutanen ƙauyen da kewaye sanin abunda ya faru a tsakaninsu, saboda yadda Widad ta dinga kuka da neman temako, rakin tsiya da kuma Shagwaɓa. Tun tana kukan har tayi shiru, muryarta ta dena fita sosai. Seda Yusuf ya dawo hayyacinsa dafe kansa cike da dana sani, da tuhumar kansa akan wani ganganci ne ya ɗebe shi ya aikata hakan? Widad se ajiyar zuciya take, tana kuka ƙasa ƙasa, gaba ɗaya Yusuf ya bata tsoro kuma ya bata mamaki. Gaba ɗaya jikin Yusuf yayi sanyi ya kasa magana, ya rasa mema zece mata. A hankali yaja rigarsa ya saka, ya miƙe ya ɗau bokiti da tukunya ya fita tsakar gida, a cikin wannan ruwan da ake ya tafi rumfar da'ake girki, ya dinga tona cikin murhun, ya tattara gawayi da ƙyar ya tashi garwashi, ya ɗora ruwa. Haka ya zauna ya dinga fama, seda ruwan nan yayi zafi sosai ya haɗa mata, ya kai banɗaki ya ajiye. Shi kansa jikinsa a matuƙar mace yake, ya koma ɗakin ya shiga ya tarar da ita a inda ya barta a kwance tana kuka, Ya durƙusa ya ɗagota ya samata hijjabi, a hankali yace  "tashi muje ga ruwan wanka can na kai miki" Bata kula shi ba ta miƙe tsaye, ta dafa bango sedai tana zuwa bakin ƙofa ta tsaya, saboda tsoro ga tsigar jikinta dake tashi, saboda wani irin sanyi da take ji, gashi gaba ɗaya tsakar gidan ya jagwale. Kawai ji tayi yayi sama da ita, ya kaita banɗaki ya ajiye mata fitila, ya koma can tsallaken wajen rumfa ya tsaya. Ta daɗe sannan ta buɗe ƙofar banɗakin, Yusuf yaje ya ɗauke ta ya maida ita ɗaki, shi be tsaya wani dafa ruwa ba, saboda garwashin duk ya mutu, a haka ya ɗebi ruwan da sanyi da komai yaje yayi wanka. Ya dawo ya tarar da ita ta kwanta, ta duƙunƙune a cikin hijjabi, yasa bargo ya rufeta, shima ya kwanta kowa yayi shiru yana saƙe saƙe a cikin ransa. Mussman Yusuf wanda dana sani da haushin kansa suka baibayeshi. Wani private hospital aka kai Nurat, nan da nan suka karɓeta a emergency,  likitoci suka shiga ƙoƙarin ceto ran Nurat, ta hanyar tsaida jinin dake ta zuba a goshinta. Da ƙyar jinin nan ya tsaya, aka nan naɗe mata goshinta da bandeji, goshin ya kumbura suntum har gefen idonta saboda buguwar da tayi. Mahaifiyar Nurat da mahaifinta suna reception, Mahaifiyar Nurat tana ta goge Hawaye, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Likita ne ya fito ya samesu a reception, suka yo kansa gaba ɗaya suna jero masa tambayoyi. "ku kwantar da hankalinku, raunine kawai ta samu, Allah ya rufa asiri be shafi idonta ba, amma idan ta farfaɗo akwai gwaje gwajen da zamuyi muga inda yuwuwar ayi mata hoton Ƙwaƙwalwa, dan naga jini yana fita daga hancinta, karmu je ko akwai internal injury " Mahaifiyar Nurat tace " Na shiga uku, hoton Ƙwaƙwalwa kuma likita? Ba dai haukacewa tayi ba? " Tsaki Alhaji Musa yayi yace " kaga dan Allah ƙyaleta, na fahimce ka idan ta farfaɗo ɗin in akwai buƙatar hakan se ayi hoton, ni dai fatana Allah ya bata lafiya" "dole kace a rabu dani mana, tunda ka kusa kashemin 'ya, kuma yanzu kana wani nuna kamar ka damu da ita" "A nan ɗinma sekin nuna halinki ko?" "ban sani ba, kuma wallahi duk abunda ya samu' yata kaine" Likita yace  "haba dan Allah yallaɓai, da girmanku da komai, hakan be dace ba ai, akwai marasa lafiya a kwance, kamata yayi kuyi ta lafiyar 'yarku ba faɗa ba" Haka sukayi shiru likita ya wuce. Wayar Alhaji Musa ce ta shiga ringing, ya ɗanyi gefe ya ɗakko wayar yasa a kunnensa yace  "Hello ina ji" "kana inane? Akwai magana fa" "ina Asibiti, an kwantar da' yata" "Subhanallah meye ya sameta?" Alhaji Musa yace  "eh Home Accident ne, ta faɗi ne ta bige but is not that complicated" "Ok to shikenan, Allah ya ƙara afuwa, zamu shigo mu duba ta insha Allah" Alhaji Musa yace  "shikenan nagode sosai" Wata Nurse ce tazo wucewa, Maman Nurat tace  "Sister dan Allah ko zan iya shiga gurin Nurat?" Nurse ɗin tace "eh zaku iya shiga ku ganta, bacci take" Cikin rige rige suka nufi ɗakin da aka kwantar da Nurat. Nurat tana kwance tana bacci, ga drip an sa mata suka ƙarasa gaban gadon Nurat, mahaifiyar ta ta zauna a gefen gadon ta kamo hannun Nurat, jikinta ya ɗau zafi sosai Amma baccinta take ta sha. A hankali Nurat ta buɗe ido, ta kalli inda Mummynta take, a hankali ta kai hannu tta shaf goshinta inda aka nannaɗe da bandeji, ta kalli Mummynta tace "Mummy me aka samin a goshina?" "bandeji ne, aka rufe miki ciwon ki" "Mummy kaina ze tsage ciwo yake min" "kiyi haƙuri, ze dena insha Allah" Alhaji Musa ya ƙarasa gaban gadon yace  "Babyna ya jikin naki?" Kallo ɗaya tayi masa, ta ɗauke kanta tana kuka. Alhaji Musa yace  "Am sorry kinji Babyna, is just a little bit mistake, kema ki dinga jin magana ki dena taurin kai" Ita dai ba tace komai ba, kuma taƙi kallonsa. Widad se farkawa tayi ta nemi Yusuf ta rasa a ɗakin, tayi tunanin ko ya tsaya sallar Asuba ne yayi karatu, gaba ɗaya jikinta ciwo yake, ta lallaɓa taje tayi sallar Asuba. Ta koma kan katifarta ta kwanta, kanta se ciwo yake da duk ilahirin jikinta ciwo yake mata, ba ƙaramin mamaki Yusuf ya bata ba jiya, bacci ne ya sake yin awon gaba da ita. Har sha ɗaya na safe bata ga Yusuf ba  ba taga alamarsa ba, ta tashi ta lallaɓa ta gyara ɗakinta, ta ɗau bokiti taje ta karɓi ruwa tayi wanka. Ta koma ta ɗau kofi ta fita tana takawa a hankali, saboda yadda tsakar gidan ya jagwalgwale sakamakon mamakon ruwan saman da'akayi jiya da daddare, tsigar jikinta se tashi take saboda ƙyanƙyami, ga ƙarnin ruwa daya kwanta. Ƙofar ɗakin gwaggo taje tayi sallama, Gwaggo ta amsa mata, ta nemi izini sannan ta shiga. Gwaggo tace  "Amarya, yanzu nake sa ran in aiki Hindu ince ta dubamin me, yau shiru ban ganki ba ko dan anyi ruwan sama ne" Widad tace  "bana jin daɗi ne, in akwai Abinci ki bani yunwa nake ji" Da yake yau ba Gwaggo ce da girki ba, yanzu se ranar girkin Gwaggo ake basu Abinci, dan Widad bata cin Abincin kowa se nata, in dai ba ita tayi girki ba baza taci ba, sedai Yusuf ya girka mata wani abun. Gwaggo tace  "Amarya bani nayi girki ba yau, amma ina da garin kunu an karɓomin jiya daga gurin niƙa, bari in  dama miki" Widad tace "to" Ta nemi guri ta zauna tana sake ƙarewa ɗakin Gwaggo kallo, wand ke matuƙar birgeta, sedai sam abunda ya faru tsakaninta da Yusuf jiua ya kasa barin zuciyar ta. Hindu tayi Sallama da kaya a hannunta, Widad ta amsa. Hindu tayi murmushi tace "Amarya dama kin tashi? Na zata har yanzu bacci kike ai" Widad tayi murmushi tace  "A'a yazan ta bacci har I yanzu, na tashi tun ɗazu ai" "Amma ya naganki wani iri, ko baki da lafiya ne?" Widad tace  "A'a me kika gani?" "gani nayi kinyi wani iri, idonki kamar kinyi kuka, kuma kamar me zazzaɓi" Widad tace "lafiya ta ƙalau fa, yunwa kawai nake ji" Hanne ta bankaɗo ɗakin ta shigo, babu ko sallama ta kalli Widad da Hindu taja wani uban tsaki, ta ƙarasa ciki basu kulata ba Hindu ta cigaba da jerawa Widad sannu. Gwaggo ta kawowa Widad kunu, Widad tayi ta godiya ta tashi ta koma ɗakinta. Dama ba'a batun sugar acikin kunun da suke sha ko kuma koko, a haka suke sha itama kuma ta saba a haka take sha. Kunun nan da ta sha har la'asar, bata sake cin komai ba, se Dafaffiyar gyaɗar da Hindu ta bata. Shikam Yusuf nauyin Widad ne ya hana shi dawowa, be san da wani ido ze kalleta ba, besan da wani kalaman ze amfani gurin kare kansa ba, tabbas yasan yayi aika aika a daren jiya, wadda shima be yi shirin afkuwar al'amarin ba, besan ta ina ze fara haɗa ido da ita ba, besan wani mataki zata ɗauka a kansa ba. Haka nan ya tunkaro gidan yana tunanin, gabansa yana faɗuwa se Addu'a yake. Yai sallama ya tsaya suka gaisa dasu Hari, yai sallama a ƙofar ɗakin Gwaggo ma suka gaisa, da yake yau tun Asuba be dawo ba. Cike da fargaba ya nufi ɗakin su, yai sallama. Tana daga kwance a inda take ta amsa masa a ciki ciki. Ya shigo musu da 'yan kayan Abinci ya ajiye. Jiki a sanyaye ya kalle ta yace "Yama ganki a kwance"? Da harta buɗe baki za tayi masa tsiwa, kawai ta tuna abunda ya faru jiya da daddare a tsakaninsu, ba shiri ta tsuke bakinta kawai tasa kuka. Dama Yusuf yasan a rina, ya ƙarasa inda take, yasa hannu ze kama hannayenta amma ta janye hannunta. Yusuf ya ɗan ƙura mata ido, ji ba ƙwari ya fara magana yace "Widad ban san ta ina yakamata in fara ba, bani da kalaman da zanyi Amfani dasu wajen baki haƙuri, gaba ɗaya na rasa me yakamata inyi, ina me baki haƙuri sannan na shirya karɓar duk irin hukuncin da kika shirya Yimin"  yai maganar fuskarsa na fallasar da tsantsar damuwa dake kwance a zuciyarsa. Cikin kuka tace  "shine ka tafi ka barni tun safe, bayan kasan...." ta ɗanyi shiru sannan ta ɗora  "bayan kasan abunda kayi min, bani da lafiya tun Asuba baka sake dawowa ba, ga yunwa nake ji, Se gurin Gwaggo naje ta bani kokon tsamiya" ta ƙarasa maganar cikin kuka. Seda Yusuf yaji kamar yayi dariya, amma ya dake yace "subhanallah, am very sorry, na manta ne kuma ina jin nauyinki sakamakon abunda ya faru jiya, dan Allah kiyi haƙuri, i don't even know how it happens" Widad a ranta tace  'jimin ɗan rainin hankali, wai he don't even know how it happens, se kace yana maye yayi abunda yayi' Haɗe rai ta sake yi ta cigaba da kukanta, tace  "Kuma seka sake ni" Yusuf yace "Naji amma ba yanzu ba se mun koma gida, for now am very sorry please, am not able to fulfill my promises to you, dan Allah kiyi hakuri Widad" Banza tayi masa taƙi cewa komai, da haushinsa take ji kama sosai he takes away her pride, sannan yasa ƙafa yayi tafiyarsa tun safe ya barta, bata shirya faruwar haka ba sam a rayuwarta, babu Aure a gabanta, amma Yusuf ya ɓata mata komai yanzu. Hannu ya kai ze taɓa ta, aikuwa ta zabura ta miƙe zaune da sauri tana faɗin "wayyo Allah Daddy" Yusuf a rikice yace  "yi haƙuri ba wani abun zan kuma yi miki ba" "Kuma sena gayawa Daddy idan muka koma gida, idan kayi min hakane dan karka sakeni, let me tell you, we must go separated, you must divorce me na gaya maka" Yusuf yace "Widad trust me, is not intentionally shiyasa nake iya ƙoƙarina akan in kiyaye, but am human being, am not super natural" "you said i should trust you how? After you know this is arranged marriage, but you took away my pride, how can I trust you Bayan Kamin ƙarya a baya, bazan taɓa trusting ɗinka ba" Gaba ɗaya Yusuf ya rikice, ya rasa abunda yake masa daɗi, ya dafe kai yana kallon yadda take kuka, tausayinsa ne ya kamata, tace  "Nifa Yunwa nake ji, kokon tsamiya kawai na sha tun safe" Yusuf yace "to, bari in ɗora mana girki" Yai maganar tare da miƙewa, ya hau kokawar ɗora Abinci. Yana cikin gaganiyar ɗora girki taga kamar yana ɗingishi ne, bata kula ba ta share shi. Ya dawo ya ɗakko leda ya ɗakko mata pad guda goma sha biyu, da Maclean sabo da su man shafawa yace  "Kinga na siyo miki pad ɗin, kuma naga Maclean ɗinmu ya kusa ƙarewa na ɗanyi mana siyayya" Tasa hannu ta karɓa tace  "Nagode sosai Allah yasaka da alkhairi" yaji daɗin godiyar da tayi masa tace  "amma zan bawa Hindu, itama ta dinga amfani da pad instead of cloth" Yusuf yace "duk yadda kika yi" Ta tashi tayo alwala, ta dawo ɗaki Yusuf ya zauna ya tsince shinkafar hausa tsaf, ya fita yana wankewa, Hanne ma ganinsa tace  "Laa dama ka iya aikin mata haka?" Yusuf yai murmushi yace  "eh na iya mana, gashi inayi" "Kawo in wanke maka, kar ayi sallama a ga kana wanke shinkafa da kanka, bayan kana da Aure kuma akwai mata a gidan" Yusuf yace  "karki damu Hannatu, ai shinkafar kaɗance zan iya wankewa" Hanne ta ƙaraso tana faɗin gaskiya a'a, nidai bani nan in wanke maka. Widad ta gani tsaya a bakin ƙofar ɗakinta, tana watso mata wani mugun kallo, take Hanne ta tuno da shaƙar data sha, nan da nan cikinta ya kaɗa ta tsaya tayi sororo, Yusuf ya ɗaga kai ya waiga, yaga ashe Widad ta gani, bata ce musu komai ba ta shige ɗakin, tana jiran Yusuf ya shigo ta zazzage masa.   Ita mamaki ma take yi, yadda ta kasa zagewa ta ƙare masa saboda abunda ya shiga tsakaninsu, tunda ya shiga ɗakin take binsa da kallo. Be ce mata uffan ba, ya zuba shinkafar "Malam daga yanzu idan zakayi kule kulenka ka bari seka sakeni tukuna na gaya maka" Kallonta Yusuf yayi yace "Dagaske har ranki so kike ki rabu dani?" Kallonsa tayi tace "to da tare aka halicce mu? Ko kuma ka manta bisa yarjejeniya mukayi Aure ne haba? Nifa bani nace ka fara sona ba, dan baka gara tun wuri kasan abunyi" Shiru yayi ya cigaba da tunani, har ya kammala girkin ya sauke, ya ɗora mai akan wuta ya soya, sedai bisa tsautsayi saboda tunani mai ya zubar masa a hannu. Firgigit ya dawo hayyacinsa yace  "Subhanallah" Da sauri ta juyo taga abunda yake faruwa, ai nan da nan ta ƙarasa gabansa tana faɗin "Subhanallah, yoseef garin Yaya? Me kake tunani haka? Kalli yadda ka ƙone hannu, innalillahi" Ta riƙe hannun nasa, ta sa rigarta tan goge masa inda man ya zuba a hannun sa, karaf idonta ya sauka akan ƙafar wandonsa, kamar jinine a jiki, ta kai hannu ta janye wandkn, rauni me yaji a gurin, kamar an saka ƙarfe anja gurin. Ɗaga ido tayi ta kalle shi tace  "Yoseef, meye wannan?" "wannan karki damu, dama zanje cikin garine in siya miki pad ɗin nan, to kin san hanya bata da kyau, shine muka faɗi a babur, amma karki damu zan warke Insha Allah" Kallonsa tayi, wani irin tausayins ya game zuciyar ta, hawaye sharkaf a fuskar ta tace "This is serious, ya isa haka, yakamata mu koma gida kome ze faru ya gara faru, ba zamu cigaba da zama a nan lafiyarka na taɓuwa saboda ni ba" Yusuf yayi murmushi cikin jarumta yace  "wannan ai ba ciwo bane me girma, zan warke very soon insha Allah, ki kwantar da hankalinki" Cikin kuka ta shiga girgiza kai tace 'No, Yoseef se mun bar garin nan haka, wahalar da kake sha saboda ni ta isa haka, is enough ba dangin iya ba na baba se wahala kake saboda ni? Idan har lafiyarka ta cigaba da taɓuwa bazan yafewa kaina ba, gida zamu koma ba zamu ci gaba da zama anan ba kome ze faru ya faru" Tai maganar tana riƙe da ƙafar Yusuf tana kuka LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 58 _59 Ɗan ƙura mata ido Yusuf yayi yace  "haba Widad, ya zaki ce mu koma gida a wannan yanayin? Komai ze iya faruwa fa" "Koma meye yafarun, amma be kamata ratuwarka ta cigaba da cutuwa saboda ni  ba, kalli ƙaddara daga wannan se wannan yakamata inyi maka adalci bekamata in nuna son kaina da yawa ba" Yusuf ya shiga share mata hawaye yace "Karki sake  cewa ba dangin iya babu na baba tsakanina dake, koba komai koda mun rabu kin taɓa zama wani ɓangare na tarihin rayuwata wanda baze taɓa gogewa ba, dan haka kome nayi a yanzu domin farincikin ki bakomai domin kuwa haƙƙina ne inyi miki, a gurin Allah babu wani abu like arranged marriage, duk abunda abunda ze sameni saboda kare rayuwarki baze dameni ba, saboda mahimmancin da kike dashi a gurina, kidena kuka zan warke insha Allah " Girgiza kai ta shigayi, tana son yin magana amma ta kasa dan haka kawai ta faɗa jikinsa ta cigaba da kuka. Yusuf a ransa yace 'alamu sun bayyana ƙarara Widad tana sona, sedai ita bata san hakan ba' 'Amma idan harka bari Widad ta fara sonka kayi mata adalci kuwa? Kayi mata ƙarya a karo na biyu, anya ƙaddarorin rayuwarku zasu haɗu a guri guda?' wata zuciyar ta shiga gargaɗinsa. Jiki a sanyaye yake dukan bayanta cikin sigar rarrashi yace  "ni ban gaji dake ba, kuma duk abunda yake faruwa dani baze taɓa sawa in juya miki baya ba, saboda Amana ce na karɓa a gurin mahaifinki, kuma Allah ya jarabci zuciyata da sonki, babu yadda zanyi ƙaddrata kenan" A hankali ta tashi daga jikinsa, ta ɗan zuba masa ido, shi kuwa Yusuf me yake ji haka game da ita da baya iya ganin laifinta, kuma yake tarar dukkan ƙalubalen daze taso?. A hankali tace  "Muci Abinci, ina jim Yunwa" Yusuf ya haɗa musu shinkafa da mai da gishiri, suka fara ci sedai Widad da ƙyar take cakalar Abincin, ƙarshe Yusuf ne ya bata Abincin. "Kaje Asibiti kuwa da kaji ciwon?" "Naje chemist, na sai magani ciwon bayamin zafi ai, bari nayi alwala inje waje inja salla" "ba in da zaka, ka zauna ka huta" Yusuf yace "Amma.. " ba wani amma, kawai kayi salla a gida, kar kaje ka fama raunin nan" Da ƙyar ta yadda yaje yayi salla ya dawo, tazo ta zauna ta saka masa man zaitun a gurin, ta nayi tana jera masa sannu. Da kanta ta gyara masa shimfiɗarsa, ya kwanta, tana sake kallon yadda ciwon ya ɗanyi zurfi. "Allah ya baka lafiya kaji" Tai maganar tana shafa sumar kansa, yai murmushi yace  "Ameen ya Allah nagode sosai" "meye wani ka gode?" kawai se ya shagala da kallonta, ta kalle shi tace  "naga kana kallona, idan ka sake kayi abunda bana so koka tsokaneni ko, zaka ga yadda zanyi da kai" "ya akayi kika san abin da zan miki?" "Fuskarka kawai na kalla na gane hakan ' ta bashi amsa Ya shammaceta ha janyota kan shimfiɗarsa, ya mirginata aikuwa ta ware baki zata kurma ihu, cikin hanzari ya toshe mata baki yace  "sekin tara mana jama'a tukuna?" "Ka cikani ko inyi ihu Allah" "to me nayi miki da zakiyi ihu?" "Ai dole ka tambayeni me kaimin, tunda jiya... Sekuma tayi shiru," Mhmm ƙarasa mana" "dan Allah ni ka ƙyaleni bacci fa nake ji" Shiru yayi bece komai ba, ya cigaba da kwanciya a jikinta. "Masoyiyya, meyasa da muna gida kika cemin ke Karuwa ce? Alhalin ba haka bane?" Widad tace "eh ai ba ƙarya nayi ba" "Meyasa kikeyin abunda bakya so ai miki ne?" "meye maraba ta da karuwa a wannan lokacin? A shigar da nayi, da kuma inda naje harka ɓatami rai ranar, Daka san me najeyi da bakamin haka a wannan ranar ba" "Nifa tun a wannan lokacin ina matuƙar kishinki ne, tun a lokacin nake sonki shiyasa nake nuna kishina a fili, Abubuwa da yawa suna ɗauremin kai a wancan lokacin ina buƙatar warawara daga gareki" "Yoseef kenan, kaine mutum na farko da ya shigo rayuwata a hagunce kuma ya zama garkuwa a gareni, ya samu damar da da ɗunbin mutane basu samu ba, kayi nasarar canza wasu daga cikin tunanina, sedai har yanzu baka bani labarin sakamakon bincikenka da kayi ba akan maƙiyana" Yusuf yai murmushi yace "Naƙi na gaya mikin, nima ban yadda dake ba" Dariya Widad tayi, harda kai masa dukan wasa a ƙirjinsa tace  "nice baka yadda dani ba? Ai nima daliline yasa hakan, koka manta niɗin mahaukaciya ce? Haukana ne yasa bana yadda da mutane, kai kuma kaga kana da hankali" Yusuf yace "Nifa gaskiya inada question mark akan wannan ciwon naki, meya hana ciwon tashi anan?" Kasancewar a duhu suke, yasa se shseshsheƙar kukan Widad yaji, cikin sauri yace  "Am sorry, i don't mean to hurt you, ban san ze ɓata miki rai ba tambayar yi haƙuri" yai maganar da sigar rarrashi, yana shafa bayanta. Yauma Allah ne ya kiyaye, dan tana jin Yusuf ya fara zarce ƙa'ida ta narka masa cizo, ba shiri ya cikata ta miƙe ta koma kan shimfiɗar ta, tayi shiruu kamar ruwa ya cinye ta. Kwanan Nurat uku a Asibiti, anata zuwa duba ta, Allah ya temake ta da akayi hoton ƙwaƙwalwar, babu wata matsala a cikin kanta dan haka aka sallameta daga Asibitin. Suleiman ne zaune a gaban wani mutum a office, da gani mutumin babbansa ne a gurin aiki, mutumin ya kalli suleiman yace  "Nagaji da gafara sk ko ƙaho ban gani ba, har yanzu babu wani bayani akan Assignment ɗin nan da muka bayar" Suleiman ya gyara zama yace  "Yallaɓai ai akwai matsala ne" "Matsala wace iri?" "yallaɓai wanda muka bawa aikin, shine direban 'yar gidan Alhaji Nasir kuma tare aka sace su" Ɗan waro ido mutumin yayi yace  "ban fahimceka ba" Suleiman ya gyara zama yace  "ƙwarai yallaɓai, Yusuf jam'in mune, yaje da saunan aikin direba amma shine wanda muka tura muka saka aiki, kuma yanzu haka tare aka sace su ita dashi" Jinjina kai mutumin yayi yace  "Amma babu wani abu daya fara gabatarwa na sakamakon binciken da yayi?" "gaskiya Yallaɓai babu, dan a satin da nayi masa magana ya cemin zezo office yayi bayani, a satin aka sace su" Mutjmin yayi ajiyar zuciya yace  "shikenan you can leave" Suleiman ya tashi yayi saluting mutumin sannan ya fita. Susu huɗune zaune a wani matsakaicin falon Hotel, Alhaji Bukar yace "wata maganar banza da naji, wai yaron nan da'aka sacesu tare shine jami'in tsaron da aka tura yayi wannan binciken" Alhaji Musa yace  "wane yaron?" Bukar yace  "direbanta mana" Alhaji Musa yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, shikenan na kaɗe har ganyena inda wannan yaron da suke yawo tare ne" Alhaji Haruna yace "kamar yaya ka kaɗe?" "Ranar da Nurat take birthday sukazo, lokacin da nayi attempting a sacemin ita, shiya ritsa Nurat da bindiga ta gaya masa inda Yar Daula take" Alhaji Munir yace "ji wata maganar banza, to me yasa tun a lokacin baka faɗa ba se yanzu" "to ta yaya zan in sani, na tambayi Nurat tacemin itama bata san waye ba, se yanzu da akayi zancen nan sannan na gane" Alhaji Haruna yace  "gaskiya malam ka kwafsa mana, kayi mana gyɗa a gurin nan, maimakon tun a lokacin kasa ayi bincike a gano maka shi, aji dalilin da yasa ya hana a sace yarinyar, wataƙila ma da tun a lokacin munsan waye shi" Alhaji Bukar yace  "ku dakata, kuskure ne dai an riga anyi shi, sedai a kiyaye gaba kuma a sake shiri, babban abunda ya ɗagamin hankali shine, bai bada komai na shedar binciken da yake yi ba, babu wanda yasan meye sakamakon binciken nasa, amma tabbas tunda ya gano kayi yunƙurin saceta, nasan ze maida hankali da yin bincike akanka" Zufa Alhaji Musa ya shiga sharewa yace "yanzu meye abunyi? Hankalina fa ya fara tashi, gashi babu wanda yasan inda suke" Alhaji Munir yace  "kaine a ruwa ai, tunda kikayi shirme da sakaci" "Mune a ruwa dai, idan Asirina ya tonu ai naku ma gaba ɗaya ya tonu" Alhaji Haruna yace "dan Allah kuyi shiru mu nemo mafita, aikin gama ya gama ba yanzu ya kamata a nemi mafita ba, abun da ya kamata mu yi yanzu shine neman mafita" Alhaji Bukar yace  "yanzu magana ta farko dai shine, mu matsa lamba musan inda Daula yake, ɓatan Daula ma fa wani babban giɓine kuma hatsari a garemu, ga 'yarsa itama bamu san a inda take ba yanzu, ga wannan yaron da wannan maganar ta taso yanzu" Alhaji Munir yace  "Sannan wanda ya sa aka saki Yaron gurin Halima shima ba ƙaramar barazana bane a gare mu, dan bamu san waye ba, kuma banu san manufarsa ba" Alhaji Musa yace  "Aini nafi kowa shiga matsala, a hanzarta a nemo mafita gaskiya" Alhaji Bukar yace "ku kwantar da hankinku, zan san abunyi insha Allah, nasan yadda zanyi da al'amarin" Alhaji Munir yace  "Yallaɓai meye mafitar to?" Bukar yace  "when I come out with the final decision I will let you know, Musa ka kwanta da hankalinka, ba abunda ze faru zanwa tufkar hanci" Alhaji Musa yace  "to shikenan tunda kace haka yallaɓai" "Mummy karɓi wayarki, tana ta ringing kin barta a falo" Hajiya Halima tasa hannu ta karɓi wayar tace  "Salamu Alaikum" "Wa'alaikum Salam, Halima yakike ya yara?" Haɗe rai tayi tace  "Kai harkuna da bakin da zaka wani kirani kana ya Yara? Bayan rashin mutuncin da kukayi min akan belin Anwar?" Alhaji Haruna yace  "ke, ki bar wannan maganar akwai matsala ne fa" "Matsala ta ƙaremu ku acan tsakaninku banda ni, karka sake sani a cikin matsalarku tunda kowa kansa ya sani" "Aikuwa kece a wannan matsalar, dan wallahi kina ruwa" "Kamar yaya?" tai maganar cike da mamaki. "Yaron nan Yusuf yake ko Yunusa, ashe jam'in sirrine, shine wanda yake binciken" Mummy tace  "kai ɗan tsaya mana, Wai Yusuf direban Widad?" "Oho nima ban sani ba, wanda dai aka sacesu tare, ashe shine yaron da yake binciken nan, muna ganin munyi dabara ashe da kanmu muka burmawa kanmu wuƙa, yaron nan shine yake gudanar da binciken" "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, na shiga uku Haruna dan Allah yaron nan dagaske ɗan sanda ne?" "ƙwarai kuwa, ɗan sanda ne ma farin kaya, kuma shike gudanar da binciken nan" "Shikenan, wallahi idan ya dawo garin nan tabbas na kaɗe, an karɓi bayanin binciken kuwa?" "ba'a karɓa ba dan ba'a samu ba, amma Alhaji Bukar yace mu saurare shi, ze faɗa mana abunda za'ayi" Hajiya Halima tace  "ni dai dan girman Allah ku gaggauta samo mafita, wallahi akwai matsala"  tai maganar tare da ajiye wayar tana faɗin na shiga uku. Amal tace  "Mummy meyafaru ne?" Ramlah ma shigowa tayi tana faɗin "Mummy lafiya kuwa?" "Yara akwai damuwa fa, wai ashe munafukin yaron nan ɗan sanda ne?" Amal tace "wane yaron wai?" "wannan shegen direban me siffar munafukai mana" "Wai Yusuf?" "Shi, wai ashe ɗan sanda ne" Ramlah tace  "ta yaya ya zama ɗan sanda? Mummy ke waye ya gaya miki?" "Yanzu mukayi waya da Haruna yake gayamin" Ramlah tace "No wonder, sam wannan beyi kalar wanda za'ace yana cikin wahala ba, ko kuma rashin ilimi, ashe munafukine shiyasa na tsane shi, shege Azzalumi" Amal tace "shiyasa wani lokacin nake hanaki yi masa wasu abubuwan Mummy, ki saki baki kiyi ta sakin maganganu anyhow, gashi abunda ya faru ai" Ramlah tace   "dan Allah kiyiwa mutane shiru, yanzu mafita za'a nema ko surutan zaki cigaba dayi?" Amal tace "ko anemi mafita ko kar anemi mafita aikin gama ai ya gama, sedai a kiyayi gaba" Hajiya Halima tana jinsu tayi shiru, gaba ɗaya ta shiga tunani yadda take sakin magana yadda taga dama, ashe kallonsu kawai yake" Ramlah tace  "Yanzu Mummy meye abunyi ne?" Mummy tace "Nima ban sani ba, amma Bukar yace mu saurare shi, ze samo mafita" "to Ubangiji Allah yasa mafitar me ɓullewa ce, amma nikaina abun ya tsoratani" Ramlah tace  "ki kwantar da hankalinki Mummy, Insha Allah bakomai, dan ni kaina a tsure nake, kin san na taɓa zuwa nace ya samomin Password ɗin Widad, Amma tunda Alhaji Bukar yace akwai mafita, to tabbas akwaita, ki kwantar da hankalinki" Mummy ta jinjina kai, Anwar ne yai sallama a ɗakin, ya kalli fuskokinsu yace  "Ya dai na ganku kunyi jugum jugum, akwai matsala ne?" Ramlah tace  "babu wata matsala" "Ya zakice babu matsala bayan fuskokinku sun nuna hakan?" A fusace Mummy tace  'Kai fita ka barmin ɗaki, uban bin ƙwaƙwƙwafi, ance maka bakomai amma ka dage " " Allah ya baki haƙuri "  daga nan yai waje abunsa. Da Asuba tayi Yusuf ya dawo daga gurin karatu, lokacin gari yayi haske ya ɗumama musu shinkafa sukaci da safe. Ya miƙe ze fara shirin fita, ta kalle shi tace " naga kana shiri, ina zakane? " " Yau ranar kasuwa fa, zanje nema" Widad tace  "ba inda zaka se ciwon nan ya warke" "Meyasa?" "Se kaje wani abun ya kuma faruwa? Ka bari ƙafar ta warke kana ɗingisawa da ƙyar kana maganar zaka fita" Yusuf yace "Nifa lafiyata ƙalau, kawai dai.. " ba wani kawai, idan kace seka fita kana tafiya, nima zan ɗauki hijjabina in tafi " " ki tafi kije ina? " " duk inda Allah yayi " Yusuf yace " to shikenan, naji na fasa fita" Widad tace  "karma ka fasa ɗin" Ta ɗau bokiti tayi waje, suka gaisa da Gwaggo, Gwaggo tace  "Amarya ɗan miƙomin robar can me ruwan ɗorawa" Widad ta tsaya tana waige waige, tace "tana ina robar take?" Gwaggo tace  "gata can a bayanki" Widad tace  "to ai ban san meye ɗuruwar ba" Gwaggo tayi murmushi tace  "ruwan ɗorawa nace, gata can a gefen randa" Widad ta ɗakko robar, tace  "Gwaggo meye ruwan ɗaurawa"? "Kalar robar ce ruwan ɗorawa" Widad tace  "Ok Yellow kenan zaki ce Gwaggo" Gwaggo tace  "Ahh mu nan haka muke cewa" "Gwaggo dan Allah meye faskare?" Hari tace  "na shiga uku da wannan lamari, waike komai baki sani ba? Kwarankwatsa ko a birni an san waɗan nan abubuwan, amma kiyi ta rainawa mutane hankali" Kamar basuji me tace ba, Gwaggo tace  "Saran itace shine Faskare" Widad tace  "a dinga saran bishiya?" "Eh a sassara bishiya, a farfasa yadda aza'a iyayin girki dashi" Widad ta ɗanyi shiru, sannan ta jinjina kai, ta kuma cewa  "Gwaggo wai meyasa naga ruwanku seya dinga yin kala, ni wanda Yoseef yake ɗebo mana yafi wannan kyau sosai" Gwaggo tace "ban hana kiran sunansa kai tsaye ba" Widad ta toshe baki tana dariya, tace  "yi haƙuri na manta ne, wanda mijina yake ɗebowa" Hari tace "hmmhmm wa yaga kwaɗo, ba kunya wai mijinta" Widad tace  "to da mijinmu ne nida ke?" Hari tace  "A'a ni Allah ya tsareni, mijinki ne ke kaɗai" Gwaggo ta girgiza kai tace  "Inda Yusufa yake ɗebo muku ruwane, ba giri ɗaya da namu ba, shi birtsatse yake zuwa ya ɗebo muku, kuma tafiyar da yake a ƙasa kafin yaje gurin ta ɓaci, da nisa sosai ita kaɗai ce burtsatse a garin nan" "Gwaggo dan Allah meye burtsatsi?". "Ruwan famfo, amma na tuƙa tuƙa" "Nasan dai famfo, amma ban san meye tuƙa tuƙa ba" Shikan sa Yusuf da yake ɗaki yana jiyosu, seda yace  "Allah yasa kar Gwaggo ta gaji da wannan tambayoyin na Widad. Allah yasa aka zuba mata ruwan ɗumi ta tafi wankanta. Bayan ta fito daga wankanne tana shiga ɗaki, ta tarar Yusuf ya tattara kayansu na wanki ya ɗaure a guri ɗaya. Ta kalle shi tace " wannan fa?" "wanki zanje inyi mana" "A ina?" ta tambayeshi "Can wani gurine bakin ruwa, nake wankin, jira nake in ƙarasa yi miki girkin rana in tafi in wanko kayan" Widad ta ajiye bokitin, ta ƙarasa tace "gaskiya zan bika" "Ki bini ina?" "Gurin wankin mana" "No kiyi zamanki a gida inje in dawo, gurin ba kowa kuma bakin ruwane" "gaskiya ban yadda ba, tunda muka zo garin nam ban taɓa fita ba, gaskiya ka tafi dani, nima base in koyi yadda akeyi ba im dinga yi mana" "bana so Kisha wahala ne, ki bari inje inyi indai fitane, zam fita dake mu zaga gari" A hasale tace  "bana so tunda ba zaka dani ba shikenan" Ya fuskanci haushi taji, dan haka ya ƙarasa inda take yace  "Meyasa kike da saurin Fushi ne Masoyiyya, shikenan zamuje tare, kinsan bana son ɓacin ranki" Tura baki tayi taƙi magana, ya juyota ta fuskance shi yace "smile mana habibty" Tura baki ta sake yi tace  "baza ai smiling ɗinba" "In kina tura bakin nan i just feel like to kiss you" Ɗago ido tayi da sauri cikin Shagwaɓa tace  "kaga ka bari bana so" "to yi min murmushi in ƙyaleki" "to ai murmushin ne be zoba" Yadda tayi maganar ne ta bashi dariya, yace  "shikenan, ina bim bashi se anmin murmushin nan. To ko in ta yaki sa kayan?" Da sauri tace  "A'a bana so wallahi" tai maganar tsoro ƙarara  a idonta. Murmushi yayi, ya juya ya cigaba da haɗa kayan, seda ya kammala yayi musu girki, sannan yai waje. Ta tsaya ta saka hijjabinta, da silifas ɗinta ɗan madina ta fito, Hindu taga Widad ta sha hijjabi, dan bata saba gani ba idan ba salla Widad zata yi ba sunyi hannun riga da hijnabi, Hindu tace  "Amarya ina zuwa haka?" "Fita zamuyi nida Yoseef, naga kamar Gwaggo wanka take inta fito ki gayamata" Hindu tace  "shikenan zan gaya mata insha Allah, sekun dawo yau zanyi wunin kaɗaici" Widad tace  "Allah sarki Hindu, nima zanyi kewarki, semun dawo" "Shikenan Allah yasa karku daɗe" Widad tayi hanyar fita, sedai tana zuwa ta tarar an zubawa Manyan ragunan megari harawa a hanyar fita wajen, gasu da manya manyan ƙaho a murɗe, sun kai su goma sha, suna ture ture suna cin Abinci. Ƙura musu Ido Widad tayi, tana tunanin ta ina zata wuce. Jin shiru Widad bata fito ba yasa Yusuf dawowa yaga ko lafiya. Ya tarar da ita a tsaye tana kallon raguna, Yusuf yace  "Madam ke nake jira fa, kim tsaya kallon raguna" "Nifa tsoro nakeji" "Tsoron mekuma?" "kar inzo zan wuce su dakeni da wannan ƙahon nasu" Yusuf ya girgiza kai yace  "yanzu ragunan ne yasa kika tsaya kika kasa fitowa? Duk soyayyarki da dabbobin kuma yanzu tsoronsu kike ji?" "To wai so kake, su dakeni da wannan ƙahon suji min ciwo, ko ance maka ni 'yar sanda ce?" Yusuf yace "iyee au abun hadda baƙar magana, ai shikenan" Ya ratso cikin ragunan ze kama hannunta su wuce, amma taƙi wai sedai ya koresu ta wuce, amma bazata shiga ta tsakaninsu ba. Cak ya ɗagata ya ratsa ya wuce, sannan ya ajiyeta, hakan yayi dai dai da fitowar Hari taga abunda ya faru, ai take ta fara salati  "la'ilahaillalahu, yau nake ganin gardiyar lukutar baɗala a tsakar rana, wane irin abune haka goɗoɗo ba fasali bakomai?" Seda Yusuf ya ƙunshe baki yana dariya, Widad har tayi shirin ramawa, ya janyo hannunta sukayi waje. "Alhaji Haruna, nayi muku duk iya ƙoƙarin da zanyi muku, duk ayyukam da kuka sani nayi muku, yakamata ku zama masu cika Alƙawari fa" "Kai Saleh wai baka san a halinda muke ciki bane? Wai ashe yaron da aka sace 'yar gidan Daula dashi, wai ashe ɗan sanda ne" Hantar cikin Saleh ta kaɗa amma ya basar yace  "kamar ya ɗan sanda, direba dai" "to ɗan sanda ne, anyi bincike an tabattar mana da jami'in tsarone ma farin kaya" Saleh yace  "lallai biri yayi kama da mutum, amma yaya aka yi haka ta kasance?" "Kai zamu tambaya, tunda kai muka wakilta a wannan ɓangaren" Saleh yace  "to ai nima ban san komai ba, ban san shi aka saka ba sam, amma gaskiya ya iya yaudara, shine yazo a matsayin direba" Alhaji Haruna yace  "to gashi nan dai, kuma bincike ya tabattar kamar maye yake akan aikin sa, idan ya saka case a gaba se yaga bayansa, kuma bimcike ya nuna ya fara gano Alhaji Musa, sannan Hajiya Halima tayi ɓarin zance a gabansa" Saleh ya dafe kai yace  "to yanzu meye abunyi?" Alhaji Haruna yace  "abunyi kam a yanzu babu, Alhaji Bukar yace mu saurare shi, ze nemo mana mafita" Saleh yace  "lallai abubuwa sun fara lalacewa, ya zama dole a hanzarta samo mafita, tun kafin su dawo garin nan in bahaka labari fa ze canza" Haruna yace  "gaskiya ne maganar ka, muna nan dai muna sauraren Bukar" Saleh yace  "Amma ya maganar ɗan uwana kuwa? Naga bakwa wani abu akan Alƙawarinmu fa" "kai dalla ana ta kai wake ta kaya? Muna ruwa tsundum muna tsakiyar masifa kana maganar wani mutum da a yanzu bashi da wani amfani" "Alhaji Haruna, ɗan uwan nawane bashi da Amfani, dama haka mukayi daku?" "to ba dole ince bashi da amfani ba, tunda a yanzu ba ta tashi muke ba, muna tsakiyar masifa kana wani zance daban, ni kaga tafiyata, ina da appointment ƙarfe biyu da rabi" Ya tashi ya bar masa falon, Saleh ya jinjina kai yace  "lallai ashe kuwa an yanka, kuma zata tashi" Suna tafe suna hira, tana yaba kyan garin dukda rashin ababan more rayuwar dake ƙauyen. Widad ta kalli Yusuf tace  "ya naga kana ɗingisawa ne, ko in goyaka ne?" Yusuf yay murmushi yace  "wai zaki goyani, kamar ba kece kika kasa wuce raguna ba ɗazu" "to ba tsoro nakeji ba, so kake sumin illa?" "wane ni ince wani abu ya samu Gimbiyata, ai bam san idan zan sa raina ba" "Eh ai ka iya saurin kare kanka" Suka cigaba da tafiya, Widad tana ta tambaye tambaye, wata tambayar idan tayi sekace wannan tsabar rainin  hankali ne, nan ko harga Allah abubuwa da yawa bata sani ba, can tace  "Allah sarki, wai se gani a ruɓabiyar motar ice aka kawoni garin nan, Allah sarki rayuwa" Yusuf yace "hakane, Allah yasa hakan ya zama silar alkhairi" "Mhmm Ameen, amma naji jiki ranar, ji nayi kamar zan bar duniya ba dan da kai ba da ban san meze faru dani ba, Nasan idan muka koma gida kana da tukuici a gurin Daddy, ka kula da amanarsa" Yusuf yayi murmushi yace  "ni bana buƙatar komai a gurin Daddy a matsayin tukuici se abu ɗaya" "Meye abu ɗayan?" "Ya barmin Widad in cigaba da rayuwa da ita, har ƙarshen rayuwata LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 60_61 Kallonsa ta ɗanyi tace  "ina fatan Allah ya rabaka da son abunda ba zaka samu ba, na gaya maka babu Aure a tsarin rayuwata, bazan ji daɗi ba ace wani abu ya sameka saboda ni ba, amma ina fatan zumuncinmu ya ɗore nida kai" Yusuf yayi Ajiyar zuciya yace  "naga jarrabawa daban daban a rayuwata, ciki harda Jarrabawa a kan Soyayya, sam bani da sa'a a wannan ɓangaren, dukda tarin gargaɗi da kashedin da kikemin akan Sonki da nake, nakasa jin zan iya dena sonki, a kowane lokaci ina sake jin sonki a raina" Shiru tayi suka cigaba da tafiya, ba tare da sun sake cewa komai ba. Ta kalli Yusuf tace  "ko mu tsaya ka huta ne? Saboda ƙafarka" Yusuf yayi murmushin yaƙe yace  "waye yace miki nagaji ne? Ko ance miki nima ragone irinki?" "Nice ma raguwar?" "Eh kece, me tsoron rago da spider ba" Dariya tayi tace  "kaikam baka mantuwa ko? Saura mu koma gida kace ga abunda nayi ka jamin raini" "Ni na isa in faɗi abunda Gimbiya tayi, ai wannan sirrine kuma tarihi ne me matuƙar girman gaske daze zauna a zukatanmu nida ke" Widad tai murmushi tace "gaskiya ne, wannan rayuwar ba zata taɓa gogewa a zuciyata ba" Yusuf yace "dukda ragoncin nan naki, akwai inda na jinjina miki Gimbiya, ban taɓa tunanin samun jarumar mace kamarki ba, yadda kika sa hannu kika rama dukan da kidnappers ɗin nan sukayi miki, na jinjina miki ta wannan fannin" Murmushi tayi tace  "hakan ya samo asaline tun daga ƙuruciya ta, Allah Sarki, Allah ya jiƙan Ammi na da Baban Yoseef" Da sauri ya kalle ta yace  "Kaman Babana kikayi wa Addu'a" Tace  "Eh iyayenmu da muka rasa nayiwa Addu'a, ko baka so" "Ni na isa imce bana so, Ameen ya Allah, ubangiji Allah yayi musu Rahama" "Ameen" Sunyi tafiya me nisa sannan suka iso rafin, ba kowa a gurin, gurin shiru se kukan tsintsaye, da kaɗawar bishiyu. Widad tace  "Wow masha Allah, ɗan uwa gurin nan yayi kyau sosai" "enjoy yourself" Yusuf ya shiga aikin yi musu wanki, yayin da Widad keta kalle Kallen tsuntsaye. "Ɗan uwa da ruwan nan yana da kyau sosai, da swimming zanyi" "kin iya ruwane?" "Taɓ sosai ma, na iya ruwa sosai fa, ina shiga" "Ai da alama kina da rashin ji, ba wanda ze gane hakan se wanda yake zaune dake" "Wanda yake zaune da ni ɗin ma ba kowa ne ze gane hakan ba, kaima ban san yadda akayi na sake da kai haka ba, haka kurum naji kamar in yadda da kai" "Aikin gama ya gama ai, kinma yarda dani ni ɗin" Cigaba tayi da wasanninta a gurin, tayi nan tayi can ta Leƙa nan ta leƙa can, Yusuf yana ta wanki har ya kammala, yai shanya ya zura ƙafafinsa a cikin ruwan, kusa da Yusuf tazo zauna itama ta zura ƙafafunta a ruwan tana kallonsa. "Meye kuma kike kallona?" "Me zan kalla?" "Muni mana" ya bata amsa Murmushi tayi tace  "kaine mummunan? Ai baka da muni sam" Murmushi kawai yayi, yana jefa dutse a cikin ruwan. Widad tace "kasan wani abu?" "A'a sekin faɗa" "Ban taɓa sanin a duniya akwai mutane nagari kamarka ba, da ina yiwa talakawa kallon mayun kuɗi, maciya amana, amma gaba ɗaya you proves me wrong" Yusuf yace "dama bekamata ka yankewa mutane hukunci da laifin tsirari daga cikinsu ba, duk lalacewar zamani akwai na kirki" Widad tace  "Aikama nagani, dan yadda nake treating ɗinka a gida ban taɓa zaton zaka iya taimakona ba, nayi mamakin ganin hawaye a idonka lokacin da ni kaina na yanke tsammani da cigaba da rayuwa" Ta ƙarasa maganar tana kwanciya a jikin Yusuf. "Habibty, a wannan lokacin da kin mutu ban san ya zanyi ba, Nagode Allah da ya nunamin na Aure ki, dukda ba kya sona" Shiru tayi ba tace komai ba, can Yusuf yace "Widad, yanzu idan na mutu zaki damu?" Tsaki tayi tace "wace irin tambaya ce wannan?" "Tambayarki kawai nayi" "To wannan wace irin tambaya ce mara amfani, kawai muna hira ka kama wannan zancen ni bana so" Ɗagota Yusuf yayi ya kalli idonta, ƙwallace kwance a idonta, se wani tura baki take, murmushi yayi ya maida ita jikinsa ya kwantar da ita, ya shiga shafa bayanta. Ɗagowa tayi ta kalle shi tace  "Ɗan uwa" Yusuf yace "Yaushe na zama ɗan uwane, naji kin canza min suna' " Gwaggo ta hanani faɗar sunan ka, kuma kaga ni bani da ɗan uwa, se gaka ka bani jini, kaga mun zama 'yan uwa tunda an samun jininka, mun zama' yan uwa kenan" Dariya Yusuf yayi yace  "wannan philosophy ɗinfa,? Lallai kam shikenan nima nayi ƙanwa tunda bani da ƙanwa mace" Ta gyara kwanciyarta a jikinsa tace  "Yoseef, idan muka koma gida zaka dawo gidanmu ka zauna kaida ummanka?" "Ai muma muna gida" ya bata amsa "Dan Allah ka dawo gidanmu, nasan bazaka cigaba da tuƙani a mota ba, nasan maybe ma in koma ƙasar waje, amma dan Allah ka dawo gidanmu kaji" Girgiza mata kai yayi yace  "so kike Mamansu Amal ta dinga wulaƙanta Ummana? Kuma zaman me zanzo inyi a gidanku, bayan bamu da wata alaƙa, kafin nan fa mun rabu" "Dan mun rabu shine zaka ce bazaka dawo gidanmu ba, sannan idan na koma gida dole ta bar mana gida" Yusuf yace "meyasa?" "Saboda wani dalili me girman gaske, amma yanzu ba wannan maganar muke ba, dan Allah idan mun koma gida ka dawo gidanmu da zama," "Nida bakya sona, me zan zo gidanku inyi? Idan dai har ina ganinki zan cigaba da sonki ne, kuma ni bakya sona" "Nifa ba tsanarka nayi ba, kawai ni bana son soyayya ne, ban santa ba kuma ban iya ba, dan bata birgeni, ƙarya ce da tarin damuwa a cikinta, amma ni bana son ko mun koma gida kayi nesa dani, na saba da kai sosai, kana iya haƙuri da dukkanin halayena, kuma kai garkuwa ne a gareni, dan Allah Yoseef ka yadda kaji ɗan uwa" Yusuf kam murmushi yayi, a ransa yace  'sarkin taurin kai, kina sona amma kina garani' A fili ya maze yace "Idan muka koma gidanku ace munje kwaɗayi, ni nafison in zauna a gidanmu nida Ummana" "dan Allah, ba wanda zece muku haka, Dan Allah Yoseef kaji" Juyowa yayi yana kallonta, har cikin ranta take maganar. Wani abune ya dinga fizgar Yusuf game da Widad, yana jin wani irin farinciki a tare da shi, abunda bata son dai yayi mata, sedai wannan karon bata hana shi ba, sema biye masa da tayi. A hankali ya cire bakinsa daga nata ya riƙe hannunta  yace  "ina sonki Habibty" Ajiyar zuciya tayi ba tace masa komai ba. Kawai ya tsaya ya zuba mata ido, a hankali tace "yakamata muje muci Abinci" Yusuf ya cikata, suka miƙe ya shimfiɗa musu abu suka zauna, ya buɗe shinkafa da wake, da manja ya ɗakko tumatir da gurji ya yayyanka, ya juya suka fara ci. Suna ci yana kallon Widad, ta kwantar da hankalinta, ta rugumi ƙaddarar rayuwarta, da farkom zuwansu ne se yayi fama kafin taci Abincin, amma yanzu hankali kwance ta dinga cin Abincinta. "Wai meye kake kallona haka?" "Gani nayi kina loma fiye da tawa, zaki cinye Abincin ki barni" "Cigaba da kallona, cinyewa zan in barka" Ya dinga jin farinciki, ganin yadda Widad ɗinsa ke nishaɗi tana fara'a, saɓanin Widad ɗin daya sani a baya, me shegen haɗe ran tsiya da koke koke, mara afuwa da tausayi. Juyawa yayi gefensa ya tsinko wata 'yar ciwa, ya miƙo mata yana cewa "If you ask me to be your king, i will turn around and said, you mean to tell me that I can have you when ever I want, i can tell you that I love you when you love me too, no more waiting for ever our love... Kwashewa da dariya Widad tayi tace " Ai ba haka ake waƙar ba, kuma flower ake bayarwa, amma ni ka bani ciyawa sekace wata Akuya" Yusuf yayi murmushi yace  "A yanzu bani da wani abu da zan baki ai, shiyasa na baki wannan instead of flower" Hannu tasa ta karɓa, ta kalli Yusuf tana murmushi. Saleh ne a gigice ya shiga babban Ofishin dake cikin harabar gurin, Suleiman ne zaune yana danna system ɗinsa, Saleh ya shigo da sallama. Suleiman ya ɗago tare da yin murmushi yace  "Masha Allah, yau kaine a ofishin nawa? Kwana biyu" Saleh ya miƙa masa hannu suka gaisa, yace  "Suleiman ya aikin naku?" "Alhamdilillah, ya Yusuf fatan yana lafiya?" Saleh yace  "lafiya ƙalau, yana gaisheku ina sa ran zuwa gurin mahaifiyarsa, im sake kwantar mata da hankali tare da tabattar mata yana cikin ƙoshin lafiya" Suleiman ya gyara zama yace  "hakane, hakam abune me kyau nima da week ends ɗin nan, naje gidan sedai har yanzu ta kasa kwantar da hankali ta, akwai buƙatar ka ɗakko mata muryarsa, kokuma ka haɗasu a waya su gaisa" Saleh yace  "No baze yuwu ba, ai bama zuwa garin nan da waya, kai mutanen nan fa sun shallake tunanin ka, nima ina lura da duka abunda nake yi, bana shiga da waya, haka nake zuwa in fito" "to ubangiji Allah ya kuɓutar dasu, ina mamakin yadda abubuwan suke tafiya, kullum sake taɓarɓarewa sukeyi" Saleh yayi ajiyar zuciya yace  "yanzun ma matsala ce gagaruma ta taso" Suleiman ya tattara hankalinsa yace  "wace irin matsala kuma?" "mutanen nan sun gano waye Yusuf, kuma suna shirin ɗaukar mataki akan hakan?" Suleiman yace "ya akayi suka sani?" Saleh yace "niba wannan ba, babban abunda ya dameni shine, rashin sanin wani irin mataki zasu ɗauka akansa, gashi kuma yana can yana cikin zulumi akan ta yaya ze sanar da Widad gaskiyar waye shi, kasanta bata afuwa bata yafiya ga duka wanda yayi mata ƙarya, muddin suka dawo garin nan sannan ta gane waye shi akwai matsala " Suleiman yace " ai tasan waye shi? " " kamar yaya? Sannan ta yaya?" Suleiman yace '" dukda gargaɗina da tayimin, amma bari in gaya maka yadda akayi tasan waye shi, wataran da yamma na kammala abunda nake zan bar office ɗin nan, kawai sega wata mota ta shigo gurin nan a guje, kamar zata tashi sama, ma' aikatanmu sukayi kanta don son ganin wane mara ɗa'ar ne haka? Ko a jikin me tuƙin, Ta buɗe motar ta fito, wata matashiyar budurwa ce jikinta sanye da abaya, ta saka face mask, sannan ta rufe fuskarta da glass. Kai tsaye inda nake ta shiga tunkarowa, da ma'aikatanmu sunyi kanta zasu hanata ƙarasowa, nace su barta ta ƙaraso. Ko kallonsu batayi ba tazo inda nake ta tsaya ta kalleni tace "kaine Suleiman?" Nace mata "Eh nine" Tace   "ina son muyi maganane" Nace mata shikenan, nai mata jagora har office ɗina, muka shiga muka zauna, ta kalleni ta cire glashin fuskarta da face mask tace  "kasanni?" "Nace mata a'a" Tace "Amma kasan Nasir Daula?" Nace "ai duk Nigeria babu wanda be sanshi ba" tace "sunana Widad Nasir Daula, nazo me zan maka wasu tambayoyi, kuma idan ka amsamin ba dai dai ba, ka shirya karɓar abunda ze biyo baya, bana sassauci ga mutane maƙaryata, waye Yusuf?" Suleiman yayi ajiyar zuciya yace "wane Yusuf ɗin?" "Direbana" ta bashi amsa Suleiman yace "Yusuf jami'inmun ne, ɗan sanda ne na farin kaya" Suleiman ya bata amsa "danme zaku turoshi? Me yasa kuka turoshi,? wato an haɗa kai daku a cuceni" Suleiman yace  "Yusuf bashi da laifi, jajirtaccen ma'aikacine me kishin ƙasa, umarni aka bamu daga sama akan cewar, a baki kariya sannan kuma ayi bincike akan wanda suke bibiyar rayuwar ki, amma bayan haka Yusuf be san komai ba" Cikin isa da izza tace  "akan me? Sannan kuma waye ya bada umarnin hakan? Ko kuma ni nace ina buƙatar hakanne? An haɗa kai daku za'a cutar dani, in ba hakaba meyasa Yusuf yasa hannu akan takardar zeyi aiki dani, dukda na gaya masa hakan tamkar saka hannu akan kwangilar mutuwarsane? Na kama Yusuf da bindiga" Tun anan Suleiman ya jinjinawa Yusuf, ya yabawa ƙoƙarin sa na jure zama tare da yin aiki da Widad, saboda yadda take magana cike da izza da isa. Suleiman yace " kamar yadda na gaya miki, Yusuf jajirtaccen ɗan sandane, kuma ba abun mamaki bane samun ɗan sanda da bindiga, sannan Yusuf baza'a taɓa bashi aiki ya dawo dashi yace ya karaya ko baze iyaba, amma sam bashi da laifi, kuma da farko bashi mukayi niyyar bawa aikinba, abokin aikinsane yace a bashi saboda jajircewarsa da haƙurinsa" Ajiyar zuciya Widad tayi tana huci, inda Allah ya temaki Sulaiman gaskiyar data buƙata ita yake gaya mata, ta kalle shi tace  "Ina buƙatar sanin waye yasa a dinga bin diddigi na?" Suleiman yace  "kamar yadda na gaya miki ne, ban saniba nima umarni aka bani daga sama, ban san komai akai ba" Widad tace "shikenan, ni zanje in bincika da kaina, amma zan maka gargaɗi da jan kunne, Yusuf be san na ganshi da bindiga ba, kada ka kuskura Yusuf yasan nasan waye shi, idan har ka gaya masa nasan waye shi zan gane, and you know what am capable of doing" Suleiman yace "karki damu, Insha Allah baze sani ba, bazan gaya masa ba" Tace "and Mark you, bana son kowa yasan da nice nazo gurin nan, and zan cigaba da bibiyarka, duk lokacin da Yusuf yayi misbehaving ko wani abu na yunƙurin cin amana ta, to dasa hannunka a ciki" Suleiman yace "ina me tabattar miki da babu abunda zeyi na cin amanarki" Ta miƙe a gadarance, ta maida face mask ɗinta, ta saka glass ɗinta ta fito, sedai tana fitowa Abbas ya kawo kai yana shigowa, ta tsaya ta ƙura masa ido, harya shige wani office, sam Abbas be lura da kallon da take masa ba, ba tace komai ba tayi gaba da sauri ta hau motarta ta bar gurin. Bayan wasu 'yan kwanaki da yin hakan, Widad ta kira Suleiman tace tana son ya gayamata full name na Abbas da rank ɗinsa, amma Suleiman yace  hakan ya saɓa da ƙa' idar aikinsu, sedai ta gaya masa meyasa take neman hakan, bata kuma bi takansa ba bayan kwana uku, aka kawo transfer later na Abbas aka maye gurbinsa da Yusuf. Saleh ya jinjina kai yace "wato duk inda mutum yake tunanin hatsabibancin yarinyar nan ta wuce haka, yana cam yana ta zullumi akan yadda ze gayamata, ashe tuni ta sani" Sulaiman yace "tabbas tasan waye Yusuf, kallonsa kawai take sannan kamar yadda naimata Alƙawari ban gaya masa ba" Saleh yace "Allah sarki, ni gaba ɗaya tausayi yake bani wallahi, bejiba be gani ba yana ta ɗawainiya da yarinyar ta bata san kimar mutane ba, duk naga ta rage wannan zafin kan nata, ta kwantar da mai tana rayuwa a ƙauyen da babu wuta, babu ruwa babu abubuwan more rayuwa, abun gaanin ban tausayi" Suleiman yace  "Allah sarki Yusuf, samun mutum me irin zuciyarsa se an tona, ina masa fatan ubangiji Allah ya kuɓutaf dashi, daga sharrin Azzaluman nan" Saleh yace "Ameen ya Allah, amma tabbas Yusuf yana cikin jarrabawa, dan ina tunanin matakin da zasu ɗauka akansa, basu da imani sam" Suleiman yace "Allah ya fisu kam, amma indai batun sadaukarwa ne, to tabbas Yusuf yayita" Haka suka cigaba da tattaunawa a tsakanin su. Se bayan la'asar, lokacin kayansu sun bushe sannan Yusuf ya tattaresu ya ninke, suka kamo hanyar gida, suna tafe suna hira gwanin ban sha'awa, Widad nata takura masa da tambayoyi dan duk abunda ta gani bata sani ba seta tambaya. Suna zuwa gida Gwaggo tai murmushi tace "Amarya yau gidan nan ba daɗi ba kya nan, duk naji ba daɗi" Widad tai murmushi tace "nima haka naji ba daɗi yau Mama" Hindu tace  "wallahi kuwa Gwaggo, gaba ɗaya yau gidan se a hankali ba daɗi da bakya nan" Hari tace "Nikam naji daɗi, bakin mutane shiru yau ba neman magana" ' Widad tace  "in mutane na magana ki dena saka baki, danke ba mutum bace" Gwaggo tace  "Amarya yau wake muka dafa, ban sani ba ko zaki iyaci, dan haka na dama miki kunu gashi can da zafinsa" Widad tace "wayyo Allah Mamana ta kaina, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, wakenma duk zan iyaci nagode sosai Mama" Gwaggo tace  "Babu godiya a tsakaninmu ai" Yusuf kam bayan sun gama gaisawa, ɗakinsu ya wuce, ya bar Widad tana cigaba da neman maganarta. Hari tana ta ƙulla gyaɗarta ta siyarwa, Widad tazo ta cika hannu ta zuba a hijjabi tayi ɗaki, Hari ta buɗe baki tace  "Wudas yaseen sekin biyani kuɗin gyaɗar nan" Gwaggo tace  "yi haƙuri, zan baki kuɗin" Seda tayi me isarta sannan ta koma ɗakin, Yusuf tun yana mamakin halin Widad har ya dena, ta kwaso kwanukan wanke wanke tayi, gaba ɗaya yau wani irin nishaɗi take ji, taji daɗin fitar da suka yi sosai, wani irin farinciki ya dinga ratsata. Ta karɓo musu Abincin gurin Gwaggo, suka zauna suka ci, bayan sun gama ne ta ɗanyi shiru sannan tace  "Naji daɗin fitar nan sosai Yoseef, ban taɓa tunanin ana samun farinciki haka ba koda babu dukiya" Yusuf yace "aishi farinciki da jin daɗi base ka tara dukiya ba, indai zakayi tawakkali da yadda Allah ya ajiyeka, zakayi rayuwarka cikin farin ciki da jin daɗi, kuma har kafi me Dukiya walwala ma". Widad tace  "ƙwarai kuwa yau na gani, rabon da inyi farinciki haka tun Ammi na nada rai, shekara goma baya kenan" Yusuf yace "kina nufin duk tsawon wannan shekarun, bakya farinciki?" "tun bayan rasuwar Ammi, ban kuma samun farinciki haka ba, babu club ɗin da bana zuwa a waje, dan inyi nishaɗi, nice club ɗim wrestling stadiums na ball da sauran wasanni, amma babu sauyi, na kanji nishaɗi ne kawai idan nai wasan doki, kona kasance da dabbobi kuma idan ina Tare da Alhaji Nasir Daula " 'yar Wulaƙanci yau kuma saunan baban nata take faɗa gatsal" Ta cigaba da cewa "nasan Daddy zeyi murna sosai, idan ya ganni cikin walwala haka, danya fidda ran faruwar hakan a rayuwata" ta ƙarasa maganar muryarta na rawa alamun zata yi kuka. Rungumota Yusuf yayi yace  "haba Jarumata, kuma Gimbiya ta, karkiyi kuka please kiyi haƙuri kinji babyna, nifa jarumtar nan taki burgeni take yi, dan haka idan muka koma gida, zan saki a aikin ɗan sanda kema" Kwashewa tayi da dariya, tace 'kai dai kaje kaita aikin ɗan sandan, nikam a kai kasuwa " " Zaki iya kama' yan fashi fa da ɓarayi da wannan dakakkiyar zuciyar taki Baby" Shiru ta ɗanyi tace  "da wanda suka kashemin Ammi ma ko?" Yusuf yace "am just kidding, idan wanda suka kashe mahaifiyarki ne, Insha Allah ni zan ɗau nauyin yin wannan binciken" Girgiza masa kai tayi tace  "this the most dangerous case, don't take the risk of it, ni suke bibiya suke son ganin bayana, dan haka koni ko su, karka sa kanka  a ciki, a yanzu ma kalli yadda kake wahala" Yusuf yace "Amma suwaye suka kashe ta, kuma meyasa? ' Widad tace " nima ban sani ba" Yusuf yace "i have to know even a little bit of your life" "bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai maganar tana dariya. Yusuf yace "ai yadda ta ƙare, tunda muka zama abu ɗaya, har muka kasance a inuwa ɗaya" Hararsa tayi tace "wace irin inuwa ɗaya" "Inuwar Aure mana Baby na, kuma gashi.... Sekuma yayi shiru Widad tace " Kuma gashi me? Ƙarasa mana, kai ko kunyata na baka ji ko? Allah ya shiryeka, ni cikani" Ƙara rungumeta yayi yana murmushi yace "Kunyarwa zanji? Mutum da matarsa" "Matar ƙauye ba, dan iya nan ne, kafin mu koma gida zamu rabu' Murmushi kawai Yusuf yayi bece mata komai ba, a hankali yace " ki gayamin mana " " wai mai meyasa ka damu se kaji tarihin rayuwata? Ko nima binciken ake a kaina? " Yusuf yayi dariya yace " wane ni?" "idan kana son in baka labarin, kwanta in kwanta akan ƙirjinka" Yusuf yace "dan dai wannan, ai shi yafi komai sauƙi" Yusuf ya kwanta, ta kalle shi tace "kuma wallahi idan kamin wani abu, se munyi faɗa na gaya maka" Yusuf yace "idan nai miki me?" "Bansani ba" "Allah ya baki haƙuri, niba abunda zanyi miki" A hankali ta kwanta akan ƙirjinsa, tayi shiru na wani ɗan lokaci WACECE WIDAD NASIR DAULA..... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 60_61 Kallonsa ta ɗanyi tace  "ina fatan Allah ya rabaka da son abunda ba zaka samu ba, na gaya maka babu Aure a tsarin rayuwata, bazan ji daɗi ba ace wani abu ya sameka saboda ni ba, amma ina fatan zumuncinmu ya ɗore nida kai" Yusuf yayi Ajiyar zuciya yace  "naga jarrabawa daban daban a rayuwata, ciki harda Jarrabawa a kan Soyayya, sam bani da sa'a a wannan ɓangaren, dukda tarin gargaɗi da kashedin da kikemin akan Sonki da nake, nakasa jin zan iya dena sonki, a kowane lokaci ina sake jin sonki a raina" Shiru tayi suka cigaba da tafiya, ba tare da sun sake cewa komai ba. Ta kalli Yusuf tace  "ko mu tsaya ka huta ne? Saboda ƙafarka" Yusuf yayi murmushin yaƙe yace  "waye yace miki nagaji ne? Ko ance miki nima ragone irinki?" "Nice ma raguwar?" "Eh kece, me tsoron rago da spider ba" Dariya tayi tace  "kaikam baka mantuwa ko? Saura mu koma gida kace ga abunda nayi ka jamin raini" "Ni na isa in faɗi abunda Gimbiya tayi, ai wannan sirrine kuma tarihi ne me matuƙar girman gaske daze zauna a zukatanmu nida ke" Widad tai murmushi tace "gaskiya ne, wannan rayuwar ba zata taɓa gogewa a zuciyata ba" Yusuf yace "dukda ragoncin nan naki, akwai inda na jinjina miki Gimbiya, ban taɓa tunanin samun jarumar mace kamarki ba, yadda kika sa hannu kika rama dukan da kidnappers ɗin nan sukayi miki, na jinjina miki ta wannan fannin" Murmushi tayi tace  "hakan ya samo asaline tun daga ƙuruciya ta, Allah Sarki, Allah ya jiƙan Ammi na da Baban Yoseef" Da sauri ya kalle ta yace  "Kaman Babana kikayi wa Addu'a" Tace  "Eh iyayenmu da muka rasa nayiwa Addu'a, ko baka so" "Ni na isa imce bana so, Ameen ya Allah, ubangiji Allah yayi musu Rahama" "Ameen" Sunyi tafiya me nisa sannan suka iso rafin, ba kowa a gurin, gurin shiru se kukan tsintsaye, da kaɗawar bishiyu. Widad tace  "Wow masha Allah, ɗan uwa gurin nan yayi kyau sosai" "enjoy yourself" Yusuf ya shiga aikin yi musu wanki, yayin da Widad keta kalle Kallen tsuntsaye. "Ɗan uwa da ruwan nan yana da kyau sosai, da swimming zanyi" "kin iya ruwane?" "Taɓ sosai ma, na iya ruwa sosai fa, ina shiga" "Ai da alama kina da rashin ji, ba wanda ze gane hakan se wanda yake zaune dake" "Wanda yake zaune da ni ɗin ma ba kowa ne ze gane hakan ba, kaima ban san yadda akayi na sake da kai haka ba, haka kurum naji kamar in yadda da kai" "Aikin gama ya gama ai, kinma yarda dani ni ɗin" Cigaba tayi da wasanninta a gurin, tayi nan tayi can ta Leƙa nan ta leƙa can, Yusuf yana ta wanki har ya kammala, yai shanya ya zura ƙafafinsa a cikin ruwan, kusa da Yusuf tazo zauna itama ta zura ƙafafunta a ruwan tana kallonsa. "Meye kuma kike kallona?" "Me zan kalla?" "Muni mana" ya bata amsa Murmushi tayi tace  "kaine mummunan? Ai baka da muni sam" Murmushi kawai yayi, yana jefa dutse a cikin ruwan. Widad tace "kasan wani abu?" "A'a sekin faɗa" "Ban taɓa sanin a duniya akwai mutane nagari kamarka ba, da ina yiwa talakawa kallon mayun kuɗi, maciya amana, amma gaba ɗaya you proves me wrong" Yusuf yace "dama bekamata ka yankewa mutane hukunci da laifin tsirari daga cikinsu ba, duk lalacewar zamani akwai na kirki" Widad tace  "Aikama nagani, dan yadda nake treating ɗinka a gida ban taɓa zaton zaka iya taimakona ba, nayi mamakin ganin hawaye a idonka lokacin da ni kaina na yanke tsammani da cigaba da rayuwa" Ta ƙarasa maganar tana kwanciya a jikin Yusuf. "Habibty, a wannan lokacin da kin mutu ban san ya zanyi ba, Nagode Allah da ya nunamin na Aure ki, dukda ba kya sona" Shiru tayi ba tace komai ba, can Yusuf yace "Widad, yanzu idan na mutu zaki damu?" Tsaki tayi tace "wace irin tambaya ce wannan?" "Tambayarki kawai nayi" "To wannan wace irin tambaya ce mara amfani, kawai muna hira ka kama wannan zancen ni bana so" Ɗagota Yusuf yayi ya kalli idonta, ƙwallace kwance a idonta, se wani tura baki take, murmushi yayi ya maida ita jikinsa ya kwantar da ita, ya shiga shafa bayanta. Ɗagowa tayi ta kalle shi tace  "Ɗan uwa" Yusuf yace "Yaushe na zama ɗan uwane, naji kin canza min suna' " Gwaggo ta hanani faɗar sunan ka, kuma kaga ni bani da ɗan uwa, se gaka ka bani jini, kaga mun zama 'yan uwa tunda an samun jininka, mun zama' yan uwa kenan" Dariya Yusuf yayi yace  "wannan philosophy ɗinfa,? Lallai kam shikenan nima nayi ƙanwa tunda bani da ƙanwa mace" Ta gyara kwanciyarta a jikinsa tace  "Yoseef, idan muka koma gida zaka dawo gidanmu ka zauna kaida ummanka?" "Ai muma muna gida" ya bata amsa "Dan Allah ka dawo gidanmu, nasan bazaka cigaba da tuƙani a mota ba, nasan maybe ma in koma ƙasar waje, amma dan Allah ka dawo gidanmu kaji" Girgiza mata kai yayi yace  "so kike Mamansu Amal ta dinga wulaƙanta Ummana? Kuma zaman me zanzo inyi a gidanku, bayan bamu da wata alaƙa, kafin nan fa mun rabu" "Dan mun rabu shine zaka ce bazaka dawo gidanmu ba, sannan idan na koma gida dole ta bar mana gida" Yusuf yace "meyasa?" "Saboda wani dalili me girman gaske, amma yanzu ba wannan maganar muke ba, dan Allah idan mun koma gida ka dawo gidanmu da zama," "Nida bakya sona, me zan zo gidanku inyi? Idan dai har ina ganinki zan cigaba da sonki ne, kuma ni bakya sona" "Nifa ba tsanarka nayi ba, kawai ni bana son soyayya ne, ban santa ba kuma ban iya ba, dan bata birgeni, ƙarya ce da tarin damuwa a cikinta, amma ni bana son ko mun koma gida kayi nesa dani, na saba da kai sosai, kana iya haƙuri da dukkanin halayena, kuma kai garkuwa ne a gareni, dan Allah Yoseef ka yadda kaji ɗan uwa" Yusuf kam murmushi yayi, a ransa yace  'sarkin taurin kai, kina sona amma kina garani' A fili ya maze yace "Idan muka koma gidanku ace munje kwaɗayi, ni nafison in zauna a gidanmu nida Ummana" "dan Allah, ba wanda zece muku haka, Dan Allah Yoseef kaji" Juyowa yayi yana kallonta, har cikin ranta take maganar. Wani abune ya dinga fizgar Yusuf game da Widad, yana jin wani irin farinciki a tare da shi, abunda bata son dai yayi mata, sedai wannan karon bata hana shi ba, sema biye masa da tayi. A hankali ya cire bakinsa daga nata ya riƙe hannunta  yace  "ina sonki Habibty" Ajiyar zuciya tayi ba tace masa komai ba. Kawai ya tsaya ya zuba mata ido, a hankali tace "yakamata muje muci Abinci" Yusuf ya cikata, suka miƙe ya shimfiɗa musu abu suka zauna, ya buɗe shinkafa da wake, da manja ya ɗakko tumatir da gurji ya yayyanka, ya juya suka fara ci. Suna ci yana kallon Widad, ta kwantar da hankalinta, ta rugumi ƙaddarar rayuwarta, da farkom zuwansu ne se yayi fama kafin taci Abincin, amma yanzu hankali kwance ta dinga cin Abincinta. "Wai meye kake kallona haka?" "Gani nayi kina loma fiye da tawa, zaki cinye Abincin ki barni" "Cigaba da kallona, cinyewa zan in barka" Ya dinga jin farinciki, ganin yadda Widad ɗinsa ke nishaɗi tana fara'a, saɓanin Widad ɗin daya sani a baya, me shegen haɗe ran tsiya da koke koke, mara afuwa da tausayi. Juyawa yayi gefensa ya tsinko wata 'yar ciwa, ya miƙo mata yana cewa "If you ask me to be your king, i will turn around and said, you mean to tell me that I can have you when ever I want, i can tell you that I love you when you love me too, no more waiting for ever our love... Kwashewa da dariya Widad tayi tace " Ai ba haka ake waƙar ba, kuma flower ake bayarwa, amma ni ka bani ciyawa sekace wata Akuya" Yusuf yayi murmushi yace  "A yanzu bani da wani abu da zan baki ai, shiyasa na baki wannan instead of flower" Hannu tasa ta karɓa, ta kalli Yusuf tana murmushi. Saleh ne a gigice ya shiga babban Ofishin dake cikin harabar gurin, Suleiman ne zaune yana danna system ɗinsa, Saleh ya shigo da sallama. Suleiman ya ɗago tare da yin murmushi yace  "Masha Allah, yau kaine a ofishin nawa? Kwana biyu" Saleh ya miƙa masa hannu suka gaisa, yace  "Suleiman ya aikin naku?" "Alhamdilillah, ya Yusuf fatan yana lafiya?" Saleh yace  "lafiya ƙalau, yana gaisheku ina sa ran zuwa gurin mahaifiyarsa, im sake kwantar mata da hankali tare da tabattar mata yana cikin ƙoshin lafiya" Suleiman ya gyara zama yace  "hakane, hakam abune me kyau nima da week ends ɗin nan, naje gidan sedai har yanzu ta kasa kwantar da hankali ta, akwai buƙatar ka ɗakko mata muryarsa, kokuma ka haɗasu a waya su gaisa" Saleh yace  "No baze yuwu ba, ai bama zuwa garin nan da waya, kai mutanen nan fa sun shallake tunanin ka, nima ina lura da duka abunda nake yi, bana shiga da waya, haka nake zuwa in fito" "to ubangiji Allah ya kuɓutar dasu, ina mamakin yadda abubuwan suke tafiya, kullum sake taɓarɓarewa sukeyi" Saleh yayi ajiyar zuciya yace  "yanzun ma matsala ce gagaruma ta taso" Suleiman ya tattara hankalinsa yace  "wace irin matsala kuma?" "mutanen nan sun gano waye Yusuf, kuma suna shirin ɗaukar mataki akan hakan?" Suleiman yace "ya akayi suka sani?" Saleh yace "niba wannan ba, babban abunda ya dameni shine, rashin sanin wani irin mataki zasu ɗauka akansa, gashi kuma yana can yana cikin zulumi akan ta yaya ze sanar da Widad gaskiyar waye shi, kasanta bata afuwa bata yafiya ga duka wanda yayi mata ƙarya, muddin suka dawo garin nan sannan ta gane waye shi akwai matsala " Suleiman yace " ai tasan waye shi? " " kamar yaya? Sannan ta yaya?" Suleiman yace '" dukda gargaɗina da tayimin, amma bari in gaya maka yadda akayi tasan waye shi, wataran da yamma na kammala abunda nake zan bar office ɗin nan, kawai sega wata mota ta shigo gurin nan a guje, kamar zata tashi sama, ma' aikatanmu sukayi kanta don son ganin wane mara ɗa'ar ne haka? Ko a jikin me tuƙin, Ta buɗe motar ta fito, wata matashiyar budurwa ce jikinta sanye da abaya, ta saka face mask, sannan ta rufe fuskarta da glass. Kai tsaye inda nake ta shiga tunkarowa, da ma'aikatanmu sunyi kanta zasu hanata ƙarasowa, nace su barta ta ƙaraso. Ko kallonsu batayi ba tazo inda nake ta tsaya ta kalleni tace "kaine Suleiman?" Nace mata "Eh nine" Tace   "ina son muyi maganane" Nace mata shikenan, nai mata jagora har office ɗina, muka shiga muka zauna, ta kalleni ta cire glashin fuskarta da face mask tace  "kasanni?" "Nace mata a'a" Tace "Amma kasan Nasir Daula?" Nace "ai duk Nigeria babu wanda be sanshi ba" tace "sunana Widad Nasir Daula, nazo me zan maka wasu tambayoyi, kuma idan ka amsamin ba dai dai ba, ka shirya karɓar abunda ze biyo baya, bana sassauci ga mutane maƙaryata, waye Yusuf?" Suleiman yayi ajiyar zuciya yace "wane Yusuf ɗin?" "Direbana" ta bashi amsa Suleiman yace "Yusuf jami'inmun ne, ɗan sanda ne na farin kaya" Suleiman ya bata amsa "danme zaku turoshi? Me yasa kuka turoshi,? wato an haɗa kai daku a cuceni" Suleiman yace  "Yusuf bashi da laifi, jajirtaccen ma'aikacine me kishin ƙasa, umarni aka bamu daga sama akan cewar, a baki kariya sannan kuma ayi bincike akan wanda suke bibiyar rayuwar ki, amma bayan haka Yusuf be san komai ba" Cikin isa da izza tace  "akan me? Sannan kuma waye ya bada umarnin hakan? Ko kuma ni nace ina buƙatar hakanne? An haɗa kai daku za'a cutar dani, in ba hakaba meyasa Yusuf yasa hannu akan takardar zeyi aiki dani, dukda na gaya masa hakan tamkar saka hannu akan kwangilar mutuwarsane? Na kama Yusuf da bindiga" Tun anan Suleiman ya jinjinawa Yusuf, ya yabawa ƙoƙarin sa na jure zama tare da yin aiki da Widad, saboda yadda take magana cike da izza da isa. Suleiman yace " kamar yadda na gaya miki, Yusuf jajirtaccen ɗan sandane, kuma ba abun mamaki bane samun ɗan sanda da bindiga, sannan Yusuf baza'a taɓa bashi aiki ya dawo dashi yace ya karaya ko baze iyaba, amma sam bashi da laifi, kuma da farko bashi mukayi niyyar bawa aikinba, abokin aikinsane yace a bashi saboda jajircewarsa da haƙurinsa" Ajiyar zuciya Widad tayi tana huci, inda Allah ya temaki Sulaiman gaskiyar data buƙata ita yake gaya mata, ta kalle shi tace  "Ina buƙatar sanin waye yasa a dinga bin diddigi na?" Suleiman yace  "kamar yadda na gaya miki ne, ban saniba nima umarni aka bani daga sama, ban san komai akai ba" Widad tace "shikenan, ni zanje in bincika da kaina, amma zan maka gargaɗi da jan kunne, Yusuf be san na ganshi da bindiga ba, kada ka kuskura Yusuf yasan nasan waye shi, idan har ka gaya masa nasan waye shi zan gane, and you know what am capable of doing" Suleiman yace "karki damu, Insha Allah baze sani ba, bazan gaya masa ba" Tace "and Mark you, bana son kowa yasan da nice nazo gurin nan, and zan cigaba da bibiyarka, duk lokacin da Yusuf yayi misbehaving ko wani abu na yunƙurin cin amana ta, to dasa hannunka a ciki" Suleiman yace "ina me tabattar miki da babu abunda zeyi na cin amanarki" Ta miƙe a gadarance, ta maida face mask ɗinta, ta saka glass ɗinta ta fito, sedai tana fitowa Abbas ya kawo kai yana shigowa, ta tsaya ta ƙura masa ido, harya shige wani office, sam Abbas be lura da kallon da take masa ba, ba tace komai ba tayi gaba da sauri ta hau motarta ta bar gurin. Bayan wasu 'yan kwanaki da yin hakan, Widad ta kira Suleiman tace tana son ya gayamata full name na Abbas da rank ɗinsa, amma Suleiman yace  hakan ya saɓa da ƙa' idar aikinsu, sedai ta gaya masa meyasa take neman hakan, bata kuma bi takansa ba bayan kwana uku, aka kawo transfer later na Abbas aka maye gurbinsa da Yusuf. Saleh ya jinjina kai yace "wato duk inda mutum yake tunanin hatsabibancin yarinyar nan ta wuce haka, yana cam yana ta zullumi akan yadda ze gayamata, ashe tuni ta sani" Sulaiman yace "tabbas tasan waye Yusuf, kallonsa kawai take sannan kamar yadda naimata Alƙawari ban gaya masa ba" Saleh yace "Allah sarki, ni gaba ɗaya tausayi yake bani wallahi, bejiba be gani ba yana ta ɗawainiya da yarinyar ta bata san kimar mutane ba, duk naga ta rage wannan zafin kan nata, ta kwantar da mai tana rayuwa a ƙauyen da babu wuta, babu ruwa babu abubuwan more rayuwa, abun gaanin ban tausayi" Suleiman yace  "Allah sarki Yusuf, samun mutum me irin zuciyarsa se an tona, ina masa fatan ubangiji Allah ya kuɓutaf dashi, daga sharrin Azzaluman nan" Saleh yace "Ameen ya Allah, amma tabbas Yusuf yana cikin jarrabawa, dan ina tunanin matakin da zasu ɗauka akansa, basu da imani sam" Suleiman yace "Allah ya fisu kam, amma indai batun sadaukarwa ne, to tabbas Yusuf yayita" Haka suka cigaba da tattaunawa a tsakanin su. Se bayan la'asar, lokacin kayansu sun bushe sannan Yusuf ya tattaresu ya ninke, suka kamo hanyar gida, suna tafe suna hira gwanin ban sha'awa, Widad nata takura masa da tambayoyi dan duk abunda ta gani bata sani ba seta tambaya. Suna zuwa gida Gwaggo tai murmushi tace "Amarya yau gidan nan ba daɗi ba kya nan, duk naji ba daɗi" Widad tai murmushi tace "nima haka naji ba daɗi yau Mama" Hindu tace  "wallahi kuwa Gwaggo, gaba ɗaya yau gidan se a hankali ba daɗi da bakya nan" Hari tace "Nikam naji daɗi, bakin mutane shiru yau ba neman magana" ' Widad tace  "in mutane na magana ki dena saka baki, danke ba mutum bace" Gwaggo tace  "Amarya yau wake muka dafa, ban sani ba ko zaki iyaci, dan haka na dama miki kunu gashi can da zafinsa" Widad tace "wayyo Allah Mamana ta kaina, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, wakenma duk zan iyaci nagode sosai Mama" Gwaggo tace  "Babu godiya a tsakaninmu ai" Yusuf kam bayan sun gama gaisawa, ɗakinsu ya wuce, ya bar Widad tana cigaba da neman maganarta. Hari tana ta ƙulla gyaɗarta ta siyarwa, Widad tazo ta cika hannu ta zuba a hijjabi tayi ɗaki, Hari ta buɗe baki tace  "Wudas yaseen sekin biyani kuɗin gyaɗar nan" Gwaggo tace  "yi haƙuri, zan baki kuɗin" Seda tayi me isarta sannan ta koma ɗakin, Yusuf tun yana mamakin halin Widad har ya dena, ta kwaso kwanukan wanke wanke tayi, gaba ɗaya yau wani irin nishaɗi take ji, taji daɗin fitar da suka yi sosai, wani irin farinciki ya dinga ratsata. Ta karɓo musu Abincin gurin Gwaggo, suka zauna suka ci, bayan sun gama ne ta ɗanyi shiru sannan tace  "Naji daɗin fitar nan sosai Yoseef, ban taɓa tunanin ana samun farinciki haka ba koda babu dukiya" Yusuf yace "aishi farinciki da jin daɗi base ka tara dukiya ba, indai zakayi tawakkali da yadda Allah ya ajiyeka, zakayi rayuwarka cikin farin ciki da jin daɗi, kuma har kafi me Dukiya walwala ma". Widad tace  "ƙwarai kuwa yau na gani, rabon da inyi farinciki haka tun Ammi na nada rai, shekara goma baya kenan" Yusuf yace "kina nufin duk tsawon wannan shekarun, bakya farinciki?" "tun bayan rasuwar Ammi, ban kuma samun farinciki haka ba, babu club ɗin da bana zuwa a waje, dan inyi nishaɗi, nice club ɗim wrestling stadiums na ball da sauran wasanni, amma babu sauyi, na kanji nishaɗi ne kawai idan nai wasan doki, kona kasance da dabbobi kuma idan ina Tare da Alhaji Nasir Daula " 'yar Wulaƙanci yau kuma saunan baban nata take faɗa gatsal" Ta cigaba da cewa "nasan Daddy zeyi murna sosai, idan ya ganni cikin walwala haka, danya fidda ran faruwar hakan a rayuwata" ta ƙarasa maganar muryarta na rawa alamun zata yi kuka. Rungumota Yusuf yayi yace  "haba Jarumata, kuma Gimbiya ta, karkiyi kuka please kiyi haƙuri kinji babyna, nifa jarumtar nan taki burgeni take yi, dan haka idan muka koma gida, zan saki a aikin ɗan sanda kema" Kwashewa tayi da dariya, tace 'kai dai kaje kaita aikin ɗan sandan, nikam a kai kasuwa " " Zaki iya kama' yan fashi fa da ɓarayi da wannan dakakkiyar zuciyar taki Baby" Shiru ta ɗanyi tace  "da wanda suka kashemin Ammi ma ko?" Yusuf yace "am just kidding, idan wanda suka kashe mahaifiyarki ne, Insha Allah ni zan ɗau nauyin yin wannan binciken" Girgiza masa kai tayi tace  "this the most dangerous case, don't take the risk of it, ni suke bibiya suke son ganin bayana, dan haka koni ko su, karka sa kanka  a ciki, a yanzu ma kalli yadda kake wahala" Yusuf yace "Amma suwaye suka kashe ta, kuma meyasa? ' Widad tace " nima ban sani ba" Yusuf yace "i have to know even a little bit of your life" "bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai maganar tana dariya. Yusuf yace "ai yadda ta ƙare, tunda muka zama abu ɗaya, har muka kasance a inuwa ɗaya" Hararsa tayi tace "wace irin inuwa ɗaya" "Inuwar Aure mana Baby na, kuma gashi.... Sekuma yayi shiru Widad tace " Kuma gashi me? Ƙarasa mana, kai ko kunyata na baka ji ko? Allah ya shiryeka, ni cikani" Ƙara rungumeta yayi yana murmushi yace "Kunyarwa zanji? Mutum da matarsa" "Matar ƙauye ba, dan iya nan ne, kafin mu koma gida zamu rabu' Murmushi kawai Yusuf yayi bece mata komai ba, a hankali yace " ki gayamin mana " " wai mai meyasa ka damu se kaji tarihin rayuwata? Ko nima binciken ake a kaina? " Yusuf yayi dariya yace " wane ni?" "idan kana son in baka labarin, kwanta in kwanta akan ƙirjinka" Yusuf yace "dan dai wannan, ai shi yafi komai sauƙi" Yusuf ya kwanta, ta kalle shi tace "kuma wallahi idan kamin wani abu, se munyi faɗa na gaya maka" Yusuf yace "idan nai miki me?" "Bansani ba" "Allah ya baki haƙuri, niba abunda zanyi miki" A hankali ta kwanta akan ƙirjinsa, tayi shiru na wani ɗan lokaci WACECE WIDAD NASIR DAULA..... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 60_61 Mahaifin Widad Alhaji Nasir haifaffen garin Kano ne, su biyu Allah ya bawa iyayensu, Shida Yayansa me suna Yusuf. Yusuf shine babba sannan Nasir, kusan shekaru takwas Yusuf ya bawa Nasir, Nasir da Yusuf suna da matukar haƙuri da biyayya, dan har Yusuf yafi Nasir haƙuri, Yusuf yana matuƙar ƙaunar ƙaninsa, tun suna yara duk wata hidimar Nasir Yusuf ne yake yinta. Mahaifiyar su Marainiya ce, bata da wani cikakken gata, mahaifinsu Nasir kuma, shikaɗai mahaifiyarsa ta haifa, sauran duk uba ɗaya suke, hakan yasa take fuskantar ƙalubale daga ɓangaren dangin miji, tsangwamar da suke masa ta shafeta.    Ko a unguwa ana jinjina tarbiyyar Su Nasir, saboda suna da matuƙar nutsuwa, ko tarin abokan nam basu dasu, tare suke komai nasu, kansu a matuƙar haɗe yake, Nasir yana girmama Yusuf a matsayinsa na wansa, shi kuma Yusuf yana matuƙar ƙaunar Nasir da tausayinsa a matsayinsa na ƙaninsa, hakan ne yasa duk inda me sunan Yusuf yake Alhaji Nasir Daula yake girmama shi sosai.     Lokacin da suka fara tasowa, Nasir ya fara yin abokai, saboda yafi yayansa baki da son mutane, mahaifinsu yana da rufin Asiri daidai gwargwado basu nemi komai sun rasa ba. Sun fara kawo ƙarfi Allah ya karɓi rayuwar mahaifinsu, sunji mutuwar nan sosai, sun daɗe suma alhinin mutuwar nan, da ran mahaifinnasu dama dangimsa ba damuwa sukayi da su ba, balle yanzu ya bar duniya, dan haka suka sake yin watsi dasu, suka ci gaba da faɗi tashi suda mahaifiyarsu. A wannan ƙadamin wasu mutane suka tare a kusa da gidansu Nasir, sedai mutanen ba masu ƙarfi bane ba, Nasir yana matuƙar tausayin Yaran gidan, saboda rashin gata, a haka ya janyo ɗaya daga cikin 'yan gidan ya zama abokinsa, Yaron sunan kakanshi ne dashi, shine ake masa inkiya da irin inkiyar kakan nasa wato Bulama, kullum tare suke cin Abinci da Bulama, suje yawon balla tare da sauransu. Sedai halayar Bulama da Nasir tasha bamban, Bulama baya shakkar iyayensa, ga mugun rashin ji da yake fama, dan haka Yusuf ya tsani Bulama, yayi yayi ya raba Nasir da Bulama abu ya gagara. Yusuf yana jami'a, Nasir yana babbar sakandire Allah ya karɓi rayuwar mahaifiyarsu, Sunyi kuka sosai, saboda ita kaɗai ta rage musu, wadda suke kalla suji daɗi, saboda dangin mahaifinsu dasu da babu duk ɗaya, ga mahaifiyarsu itama ba wani gata ne da ita ba, dan haka koda aka share makoki babu wanda yabi ta kansu, cewar dangin mahaifinsu ai su ɗin mazane zasu iya kula da kansu, base am ɗau ɗawainiyar su ba. Nan Nasir ya ƙullaci dangin mahaifinsu, dama harda sakacinsu yayi sanadiyyar rasuwar mahaifiyarsu, tana rashin lafiya sun yi sintiri gidan ƙanin mahaifinsu ya basu kuɗi su kaita Asibiti amma ya hana, suka dinga 'yan uwan uban akan su temaka musu amma suka ƙi. Haka suka tattara ɗan abun hannunsu, suka kaita Asibiti aka rubuta musu Allurara dubu saba' in, suna cikin taradaddim yadda zasu samu kuɗin rai yayi halimsa. Tunda Allah yayi mata rasuwa, Nasir be ƙara takawa inda dangin mahaifinsu suke ba, haka Yusuf ya cigaba da buga buga da faɗi tashi, ya sai musu Abinci ya biya musu kuɗin makaranta, amma duk da haka Nasir be rabu da Bulama ba kuma be dena tamaka masa ba. A haka da ƙyar Yusuf ya kammala karatunsa, ya dinga faɗi tashi neman sana'a, ya samu aikin banki da ƙyar ta hannun wani ɗan siyasa. Cikin ikon Allah, Allah ya rufa masa Asiri har yayi Aure, dukda Nasir ya kawo ƙarfin daze fita ya nema, amma Yusuf be fasa ɗawainiya dashi ba, hatta sabulun daze wanka Yusuf seya siya ya bashi, akayi sa'a Nasir yana ɗasawa da matar Yayansa sosai, saboda bashi da ƙyuya, duk aikin data sashi yi mata yake, dukda kasancewarsa ya zama saurayi, wasu lokutan har zama suke suyi hira tare, ko suyi shawara. Ɗan zuwan da suke gidan, haka Bulama yake mata 'yan sace sace, haka take shiru saboda Nasir, Yayan Nasir ya sha dunƙule kuɗi masu kauri ya bawa Nasir da nufin yayi sana' a, amma se Bualama ya ziga shi, su kewaye kuɗin suyi bushasha, aita kashewa 'yan matan Bulama, su sai kaya su sai kayan Ball ayi shagali kuɗi su ƙare, da Yusuf yaga abunda yake faruwa seya koma yake kafawa Nasir sana' a, nan ma Bulama ya bishi su ragargaje komai. A hankali Nasir ya fara yiwa kansa faɗa, yaga asarar da yakewa Yayansa tayi yawa, gashi be taɓa nuna masa ya gaji ba, sedai yayi fushi yace baze sake bashi jari ba se yayi hankali. Ya koma ya sameshi yace ya bashi jari, in Allah ya yarda ze alkinta, Amma Yusuf yace baze bashi suje su haɗu da sakarkarun abokansa su cinye ba se yayi hankali, haka yaita sintiri amma ya hana shi. Da yaga hakan yaƙi seya koma ta gurin matar Yusuf wato Nadiya, watarana yaje ya sameta a falo, bayan sun gaisa yace  "Anty taimako nake nema fa" Tace "temakon mefa?" "Anty Yaya ya hanani Jari, nayi nayi amma yace se nayi hankali, dan Allah kisa baki, nasam yadda yake sonki da kince a bani ta zauna" Nadiya tayi murmushi tace "ai kai lamarin naka ne se a hankali, se an baka kaje ku kewaye ku cinye kai da abokai, kamar baka da wayo" "Nidai dan Allah kisa baki ya bani, Allah bazan ɓafnatar ba zan tattala" Nadiya tace "shikenan, rashin sana'a ga matashi bata da daɗi, bari ya shigo gidan inga ya za'ayi" Nasir yace "Yawwa Antyna ta kaina, Allah yasaka da alkhairi, ya kawo 'yan biyu sau biyu" (da yake tunda akayi auren bata samu rabo ba" Tai murmushi ta ce "Ameen ya Allah Nasir, Allah yasa ya baka jarin nan, daga nan ka zama babbn done" "Ameen Anty, bari in ɗau carbi inta masa lazimi kafin ya dawo" Tai dariya tace "idan ma be baka ba, ina sa ran a kawomin kuɗin gonata, se in baka" Nasir yace  "zema bani insha Allah ' Suna cikin hirar ne sega Yusuf ya dawo, Yusuf yace  " Ashe kana nan, na biya ta can gidan in baka takalmin dana siyo maka amma baka nan" Nasir yace "ai tun ɗazi ina nan, gurinka nazo" "Gurina kuma? To gani" Nadiya tace  "ka zauna kaci Abinci tukuna, idan kaci se in gaya maka saƙon nasa" Haka akayi, tare ma sukaci Abincin shida Nasir, bayan sun kammala Yusuf yace  "to Uwargida, ina jinki tunda naga kun haɗa kai, nasan wataƙila wani abu akeso na bayar ko inyi" Dariya suka yi, Nadiya tace  "Yawwa ranka ya daɗe, kaga yanzu kamar Nasir ai bekamata ace seka sai masa takalmin sawa ba, kamata yayi ace duk wannan abubuwan shiyakewa kansa, dan haka yazo neman alfarma dan Allah a temaka masa da jari" Yusuf yace "An hanashin baza'a bayar ba, in kuma bashi yake shida wancam yaron mara kunya su haɗu su cinye, gara ko meye yazo in sai masa, idan ya ƙara hankali se in bashi jarin" Nasir yace  "dan Allah Yaya, Allah nayi hankali zan tattala" Yusuf yace "Anƙi ɗin, ai tun rannan nace bazan sake baka ba" Nadiya tace  "A dai yi haƙuri ranka ya daɗe, Insha Allah baze sake ba" Yusuf yace "to naji, tunda haɗe mun kai zakuyi, naji zan bashi jari, amma rance zan bashi" Nadiya tace "haba dai rance dan Allah" "shikenan tunda bakwa so, ai bazan sake bashi kuɗi yaje yaci a banza ba, tunda besan zafinsu ba" Nasir yace "Anty na yadda, Insha Allah zan dawo masa dasj, nidai a bani jarin" Nadiya tace "dan Allah kace ya dawo maka da rabi, ya riƙe rabi mana" Yusuf yace "Nifa in bakwaso kuɗina sun huta, nasan abunda zanyi dasu" Nadiya tace  "shikenan, munji mungode Yaushe za'a bamu?" Yusuf yace "waini wace sana'ar ma zakiyi ne? Kuma nawa kake buƙata?" Nasir yace "Yaya sarƙoƙi nake son in dinga siyarwa, zan kama shago a kasuwa sannan in zuba kayan, ance dubu ɗari biyar zasu isheni". Zaro ido Yusuf yayi yace "dubu dari biyar? Kana da hankali kuwa?" Nadiya tace "kana dasu fa, kafi ƙarfinsu dan Allah ka bashi" "Gaskiya bazan bashi ba, zan dai bashi ɗari uku yaje ya nemi sauran, ɗari ukunma bashi" Nadiya tace  "Nasir karka damu, idan aka kawomin kuɗina, kazo in baka sauran, inaji a jikina wannan sana'ar ds zaka fara itace silar arzikinka, ka zama hamshaƙin Attajiri, wanda ze tara Daula ta ban mamaki" Nasir ya washe baki yace  "Allah yasa Antyna ta kaina, da duk sati sena kaiki Makka, shi kuwa yaya se shekara shekara zan dinga kai shi" Yusuf yace "kar Allah yasa ka kainin, bana insha Allah zan tafi ai, kuma kema ban yadda ki bashi kuɗi kyauta ba, rance zaki bashi kuma tare zamu je da kaina a kama shagon" Har zata yi magana, ya dakatar da ita, ya hanta magana, Nasir yaita godiya sannan ya tafi. Bayan tafiyar sa Yusuf yace  "Nadiya, ina jin daɗin yadda kike nunawa ɗan uwana ƙauna kamar ɗan uwanki, ni kaina ina tunanin wace sana'a zan sama mishi, saboda nasan bayan raina babu wanda ze iya ɗawainiya dashi kamar yadda nakeyi, ba ƙinsa nake da nace rance na bashi ba, hakan ne zesa ya maida ya tattala abunda aka bashi " Nadiya tace   " Shikenan tunda haka kace, Amma kana min kyautatawar dako nawa nakwa 'yan uwanka alheri dashi ban faɗi ba, amma tunda kace haka shikenan " Bayan kwana bakwai, aka tattara kuɗi akaje aka kamawa Nasir shago, aka zuba kayan sarƙoƙi kala kala, Nasir ya maida kai sosai a tafi da shagon nan, duk yadda Bulama yaso a kassara shagon Nasir yaƙi, sedai wataran Bulama yazo ya taya shi zama koya yayi masa shara, shi kuma ya biya shi, amma a hakan Bulama yana taɓa ƙuruciyar ɓera wato sata. Allah yasawa kasuwancin nasa albarka, nan da nan kasuwanci ya kankama, idan kuɗi suna nema su yanke masa idan ya zaga gurin Matar yayansa seta ƙara masa kuɗi, a hankali ya dinga sabawa da mutane, idan yaji labarin wani kasuwancin seya ɗibi kuɗi ya jarraba, shine ya buga nan ya buga can. Wataran aci riba, wata ran a faɗi, Yusuf yana yi yana monitoring ɗin ƙanin nasa, idan ya tambayeshi yaushe zan dawo maka da kuɗin se yace 'ba yanzu ba, idan lokacin karɓa yayi zan karɓa' Haka ya dinga faɗi tashi, da Nadiya ta ganshi seta fara tsokanarsa da seka gina Daula me ban mammaki babban don, a haka abokansa da maƙota suka fara kiransa da Daula kawai. Ana nan wani hamshaƙin attajiri a kusa da gidan Yusuf, yaje ya auro wata balarabiya 'yar maroco, akayi shagali sosai' yan uwanta na can maroco suka zo Nigeria, akayi shagalin biki sosai. Bayan wani lokaci balarabiyar nan ta haihu, aka kawo mata wata Yarinya a cikin danginta, ta zauna tare da ita saboda ta dinga tayata raino, kafin jaririn yayi ƙwari. Nasir ya kan shiga gidan mutumin, da yake akwai babban ɗan mutumin me suna Ahmad a gidan, suna gaisawa sosai da Nasir, shi ya bashi shawarar fara sana'ar kayan sarƙoƙi na mata, dan haka Nasir yana shiga gidan sosai, dan ya saba da ita Amaryar wannan mutumin Islam wato balarabiyar maroco. Duk lokacin da Nasir ya shiga gidan sukan haɗu da wannan balarabiyar Yarinyar me suna Huda 'yar uwar Islam , yana ɗan jin larabci dan haka sukan gaisa, kokuma suyi magana da turanci. Huda bata da saurin sabo, amma ta saba da Nasir, ko fita ba tayi amma Saboda Nasir har gidan Yusuf take shiga nemansa idan taga bata ganshi ba, saboda Nasir yana da barkwanci, gashi ya iya hira dan haka yakan ɗebe mata kewa sosai. A hankali mutuncinsu ya rikiɗe zuwa Soyayya, sun shaƙu da juna sosai, da farko lokacin da tazo Nigeria cewa tayi ba zata fi sati biyu ba zata koma ƙasarsu, Islam na ta fama da ita ta zauna amma fafur taƙi, amma saboda Nasir se gashi ta shafe watanni uku ba tare da ta koma maroco ba. Ya zamana Nasir ya dena karɓar Abinci a gidan yayansa Yusuf, saboda Huda zata ajiye masa idan an dafa a gidansu, idan yaje ta kawo masa su zauna yana ci suna hira. Kasancewar Nasir mutumin kirki ne daga shi har yayansa, yasa duk mutanen unguwa sun sanshi, kuma shi wannan Attajiri mijin islam yasan Nasir sosai, kuma yasan yana zuwa gidansa, shi ya fara tsokanarsa yana cewa  "Nifa Malam Nasiru ban gane wannan mutuncin haka tsakaninka da Huda ba, ko kaima marocon zaka ne?" Tun suna ɓoye ɓoye harta bayyana ga mutane, Nasir da Huda soyayya sukeyi, wasu lokutan idan aka aiketa shiyake rakata, saboda wani abun bata sanshi da hausa ba, kyautar sarƙoƙi kuwa da yake bata babu adadi. Wataran haka zata shiga gidan Yayan Nasir, gurin Nadiya ta wuni a gurinta suna hira, a haka har take sedai sam Allah be haɗa jinin Huda da Bulama ba, da tana ɓoyewa, harta kasa ɓoyewar take gayawa Nasir ita bata san ganinsa da wannan Bulaman. Nasir yace  "Hudallahi Bulama abokina ne, kuma ɗan uwanane ban san me yasa bakwa shiri ba" Huda tace "Nifa ba hanaku hulɗa nayi ba, amma idan zakazo gidan nan ka dena zuwa dashi, yaita faman kallona, ni kuma bana so" Nasir yace  "ki kwantar da hankalinki, ba abunda ze miki, dan dai kallo ai ba cinye ki zeba" Haka yaita rarraashinta, suka cigaba da soyayya ita da Nasir. Watarana Yayarta ta kirata tace  "Huda, gida fa sun matsa akan lallai ki koma, kinga kin daɗe sosai a nan" Maimakon Huda tayi magana, se tayi shiru idonta ya cika da ƙwalla, Islam tace  "kuka kuma? Me yasa ki kuka?" Huda tace  "ni bana son in koma gida" Islam tace  "meyasa, keda da ƙyar aka lallaɓoki kika yadda kika zauna" Huda ta share hawayenta tace  "bana son in koma saboda...  Sekuma tayi shiru Islam tace " Saboda Nasir ko? " Huda ta jinjina mata kai, Islam tace " Amma Huda kin san bazasu yadda su aura miki shiba? Kin san irin tashin da mukayi a gidanmu, nima dan Alhaji yana da kuɗi ne suka yadda suka Auramin shi, amma kinga Nasir bashi da kuɗin daze iya biya ya Aureki, kuma a can ga Habibullah sun masa Alƙawarin bashi Aurenki" Cikin kuka Huda tace  "ni bana son Habib, Nasir nake so, dan Allah Ukty kisa baki, wallahi ina son Nasir sosai" Islam tace  "kidena kuka ukty, Insha Allah zan tayaki da Addu'a amma nasan ko zaki Auri Nasir zaki sha wuya" Daga maroco musamman aka taso ƙanin mahaifin su Huda yazo ya tafi da ita, tayi kuka sosai saboda zata rabu da Nasir, shi kansa Nasir ya shiga damuwa sosai, ranar da zasuyi Sallama Huda ta dinga kuka, Nasir kamar ze hauka. Dan bayan sun rabu ɗaki ya koma yaje yaita nasa kukan shima, tunda Huda ta koma ya dena zuwa gidan wansa ko karɓar Abinci, ya zamana kasuwa ma ba kullum yake zuwa ba, sedai wataran Bulama yaje ya buɗe shagon ya zauna yayi wadaƙarsa san ransa da kuɗi. Mussaman Yusuf ya aika aka kira masa Nasir, Yusuf yace  "Wato Nasir saboda wannan yarinyar kake nema ka kashe kanka ko? Ko Abinci ka dena zuwa ci, kai yanzu ko Auren ne ina kaga kuɗin da zaka iya auran balarabiyar yarinyar nan? Shikansa maƙocin nawa bakaji kuɗin da ya kashe gurin auro yarta ba, me muke dashi Nasir? Kayi haƙuri ka cigaba da walwalarka, nan gaba Insha Allah ni zan maka Auren ma da kaina, a samo maka 'yar baƙa me kyau ka Aura ko ƙanina" Zumɓura baki Nasir yayi, ya haɗe rai ƙwalla ta taru a idonsa. Nadiya tace  "Shifa farar fatar nan yake so da dogon gashi ko Nasir?" Girgiza kai Nasir yayi yace "Ni wallahi kawai sonta nake, ni bana son wata inba Huda ba" Haushi ne ya kama Yusuf, da ze masa Masifa, amma ganin Nasir yana kuka yasan lallai ya kamu da yawa. Se ya koma rarrashinsa, dayi masa Nasiha da ƙyar da rarrashi da Addu'a sannan Nasir ya cigaba da zuwa shagonsa, badan ya cire Huda daga ransa ba. Ɓangaren Huda ma tunda ta koma maroco suka kasa gane kanta, bata walwala Sam, sannan taƙi saurarar wanda akeso a Aura matan, sam baya gabanta kullum cikin tunanin Nasir take da barkwancinsa, gashi lokacin waya bata yawaita a hannun mutane ba, balle ta dinga kiransa suna magana. Aka fara shirye shiryen bikin Huda da Habib, amma Huda sam bata saurarensa se aikin kuka, gaba ɗaya tabi ta rame suka kasa gane kanta. Islam ta shirya taje ganin gida, domin ayi shirye shiryen biki da ita, sedai me ganin 'yar uwatta ya razana ta gaba ɗaya ta rame, bata walwala se kuka. Gashi iyayensu sun rasu, a hannun wan mahaifinsu suke, shi kuma mutum ne me azabar tsauri kuma kaifi ɗayane baya magana biyu, dan duk wannan botsarewar da Huda take akan Auren Habib be dameshi ba sam, shirin Aurar da ita kawai yake. Seda Islam taje ta gaya masa aiga Halinda Huda take ciki, akwai wanda take so a Nigeria. Nan yai tsalle ya dire yace baze taɓa yuwuwa ba, in dai yana nan a raye ba zata Auri wani ba idan ba Habib ba. Da jin wannan batu hankalin Huda ya ƙara tashi, duk 'ya' yan wan mahaifinsu ba wanda yakewa Auren dole, sesu, yanzun ma yana son ya aurawa Habib Huda ne saboda yana da kuɗi kuma yana ci. Mijin Islam har maroco yaje, akan maganar Huda dan Islam tana ta kuka ganin tilon ƙanwarta na neman rasa ranta saboda baƙin cikin auren dole daza'ayi mata. Alhaji Abubakar yasa baki akan su ƙyale Huda da Auren nan, ko basu Aurawa Nasir ba su ƙyaleta tunda bata son Auren amma suka ƙi, har yayi barazanar ze ɗauke Huda kuma ze haɗa wan mahaifinsu da hukuma akan abunda yake yunƙurin yi. Ɓangaren Nasir ma, tunda yaji halin da Huda take ciki ya shiga matsananciyar damuwa, har kwanciya yayi a Asibiti, damuwa tayi masa yawa gashi kullum ƙara son Huda yake a cikin zuciyarsa, tun Yusuf yana jin haushin ƙanin nasa har ya dawo yana tausaya masa, saboda ya lura kamar jarabta ce wannan Soyayyar tasa da Huda. Hatta dangin su Huda da 'yan uwa suma suka sako Wan mahaifin Su Huda a gaba akan ya aura mata wanda takeso taje can ta ƙarata, indai mazan ƙabilar hausawa ne da ƙafarta zata dawo, itama Yayarta dan tana Auren me kuɗi ne, shiyasa ya iya riƙeta, itama babu tabbacin baza' a sakota nan kusa ba, dama me kuɗi itama ta samo da ɗan sauƙi amma ta ɗakko talaka, kota aureshi Auren ba inda zashi, ita dai Huda tace taji ta gani taje ƙasar Hausawa ta zauna dasu ita ba taga wani aibunsu ba, duk miyagun halayen da ake faɗa bata gani ba, kuma suna zaune da iyalansu lafiya. Ganin baki yayi yawa yasa wan mahaifinta yace  "da kuɗin Auren Huda, da kayan Aure da sadaki da komai da komai ya yanke dirham dubu ɗari takwas" Yusuf yana gida, akazo ana sallama dashi, ya fito dan ganin me sallamar hana zuwa yaga mijin Islam ne wato Alhaji Abubakar, ya fito suka gaisa da juna, Alhaji Abubakar yace  "wato dama magana ce nake tafe da ita akan ɗan uwanka Nasir, naje maroco ƙasar su matata, yarinyar nan Huda tama cikin matsanancin hali, ɗan uwan mahaifinta ma shirin yi mata Auren dole, mun kai ruwa rana sosai dashi, dan haka yace idan Nasir ya shirya nan da sati biyu ya kai kuɗin Aure, komai da komai dirham dubu ɗari takwas " Yusuf yace " Alhaji nawa kenan a kuɗin mu na Nigeria " Alhaji Abubakar ya ɗanyi shiru sannan yace " Naira miliyan uku da dubu ɗari shida kenan a kuɗinmu na nan" Shiru Yusuf yayi, ya yakice gumi sannan yace  "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, to zamuje muyi shawara inga inda yadda zamuyi, amma bamu da shi a ɗaka balle a waje, ni kaina yadda gaba ɗaya Nasir ya sukurkuce abun yana damuna, amma bakomai nagode sosai da ƙoƙarinka nagode" Alhaji Abubakar yace  "karka damu, ai ɗa na kowane kuma Nasir yaron kirkine ubangiji Allah ya yassare muku" Sukayi Sallama ya tafi, jiki a sanyaye Yusuf ya shiga cikin gida, gaba ɗaya kamar an zare masa laka, Nadiya ta kalle shi tace  "ranka ya daɗe lafiya kuwa?" Ya samu guri ya zauna yace  "Nadiya akwai matsala, baban Yarinyar nan Huda yace nan da sati biyu mu kai miliyan uku da dubu ɗari shida sannan a bashi ita, nikuma kin san bani ds ita, gashi ina tsoron wani ciwo ya kama min Nasir, gaba ɗaya yasa kansa a damuwa, duka abunda zan tsawatarwa Nasir ince ya bari yaƙi hanuwa to tabbas wannan jarrabawa ce a gareshi, Nadiya na rasa abunyi ina zan samu wannan kuɗin haka? " (A wannan lokacin kuɗi suna matuƙar daraja) Nadiya tace " yanzu meye abunyi, nikaina na fuskanci idan ba'a ɗau matakin daya dace ba, akwai yuwuwar ya faɗa mawuyacin hali " Yusuf yace  " shine abunda nake tsoro, bazan iya fitowa in nunawa Nasir gazawa taba gurin sama masa abunda yakeso ba, kinga kwanan nan kuɗin hannuna na tatike aka buɗe masa shago, idan aka saki shagon aka karɓi kuɗin idan yayi aure dame ze Riƙeta? " Nadiya tace "ai kama bar batun a saki shagon nan, muyi tunanin wata mafitar" Yusuf yace "bazan gaya masa halin da ake ciki ba, inaga zan rubutawa bankinmu su bani aron kuɗin, idan yaso a dinga cirewa a albashina, akai musu kamar yadda Nasir ne kaɗai ɗan uwana itama Islam Huda ce kaɗai 'yar uwatta, idan muka temakesu kinga mun ceci rayuka biyu kenan, amma kiyi shiru da bakinki karki gaya masa Nadiya " Nadiya tace    " Insha Allah bazan gaya masa ba, amma asaka gidana na cikin gari a kasuwa, idan aka siyar semu ragewa banki kuɗinsu ko? " Yusuf yace" A'a Nadiya, ɗawainiyar da kike da Yusuf aita isa haka, ki bari kawai ' Nadiya ta haɗe rai tace "to ainima Nasir ɗan uwanane, tunda muna zaune da kai kana kula dani, meyasa zan bar ɗan uwanka cikin damuwa?" Yusuf yace "Shikenan, ki bari in dawo se mucigaba da maganar, bari inje inyi sallar isha' i in dawo" Yai maganar yana miƙewa, sedai yana fitowa ya ci karo da Nasir a tsaye a ƙofar ɗakin...... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 64_65 Yusuf yace "yaushe ka shigo haka? Kazo ka tsaya a abakin ƙofa?" Nasir yace  "Yayana, tun ɗazu nake gurin nan naji duk hirar da kuke da Anty, sedai bazan bari ka cigaba da wahalar da kanka saboda niba, akwai buƙatar kaima ka gina rayuwar ka data iyalinka ni dai ka ƙyaleni kawai, na haƙura da Huda" Yusuf yace "ba shawararka nake nema ba, a gurin Allah nake nema, fita ka bani guri" "Yayana, ka saurareni na haƙura da zancen Huda wallahi, bazan sake zancenta bama" Yusuf be saurari Nasir ba yai waje abunsa, Nasir ya ƙarasa shiga ya tarar da Nadiya a zaune ya nemi guri ya zauna yace  "Anty dan Allah kisa baki, kar Yaya ya ciwo bashi saboda ni, ki gaya masa na haƙura da zancen Hudan nan" Nadiya tace "kai ina ruwanka, ka zuba ido kawai" "ba batun in zuba ido bane rayuwarku da cutu saboda ni, dan Allah Anty ki gaya masa na haƙura da Huda" Ƙyaleshi Anty Nadiya tayi ta shiga ayyukan ta. Bayan sallar magariba Nasir ya fita. Nasir ya tafi gidansu Bulama, ya jashi sukaje masallaci sukayi salla. Nan Nasir ya bawa Bulama labarin abunda yake faruwa, Bulama yace  "to ita kaɗaice 'ya, malam ka haƙura mana" Nasir yace "haba Bulama, ya zakace haka, kasan yadda nake son Huda kuwa?" Bulama yace  "eh mana, kai banda abun soyayya meya haɗo biri da gada dama, ina kai ina Auren balarabiya ko dan kaga kana juya kuɗi a hannunka, malam ka nemi wata me ɗan rangwamen gata in auren kake so kayi" Nasir yace  "ni bama wannan ba Bulama, kasan Yaya Nasir wai bashi ze ciyo a kai kuɗin Auren Huda, sun yanaka mana kuɗi kusan million huɗu" "Au wai dama sunce zasu baka auren nata?" "Eh mana, sunce zasu bani, amma baffanta yace kuɗin Auren million huɗu, na rasa yadda zanyi ne, ga Yayana wai ze ciyo bashi akai kuɗin auren" "bashi kuma? Kawai ka bari idan ya karɓo bashin, kazo muje 'yan mata se wadda kake so, mezesa ka wahalar da kanka akan wannan balarabiyar, hasken fatane fa kawai da gashin' Nasir yace " A'a gaskiya ni Huda nake sl, kuma bazan ma bari ya karɓo bashin nan ba gaskiya" Bulama yace  "kai meyasa baka da wayo, wallahi garin nan akwa tsula tsulan 'yan mata, duk abunda kake so zasuyi maka indai da uwar kuɗin ka" Tsaki Nasir yayi, ya tashi ya bar gurin saboda kunna shi da Bulama yayi. Be zame ko ina ba se gidan Alhaji Abubakar, ya samu Ahmad ɗan gidan Alhaji Abubakar, suka zauna suka gaisa Ahmad yace "Angon Huda ya akayine? Naga baka walwala sam" "Ahmad ina zanyi wata walwala? An yanka min sadaki fiye da tunani, gashi gaba ɗaya jarin da ribar da nake juyawa basu fi million ɗaya ba, ga Yaya Yusuf duk ya damu, har yana batun ze karɓi loan, gaba ɗaya na damu nina ma haƙura gaba ɗaya, amma yaƙi saurarata" Ahmad yace "Nasir, ita kanta Huda tana buƙatar taimako, idan ka aureta zata samu sassauci, Allah baze hanaka yadda zakayi ba, Insha Allah, in dai matarka ce seka Aureta" Nasir yace  "Ni dai na haƙura na fidda rai, nasan ina matuƙar son Huda, amma bani da halin Aurenta" "Ka dena faɗar haka, Insha Allah za'a samo kuɗin nan, kuma zaka auri Huda" Nasir yace  "to idan rabona ce Allah yasa in samu" Yusuf ya dinga faɗuwa yana tashi, ya fasa karɓar bashin banki saboda haramcin hakan, Amma ya saida abubuwansa ya tattara kuɗin hannunsa da ƙyar sukayi million ɗaya da rabi, Ahmad ya bawa Nasir gudunmuwar dubu ɗari biyu, shima ya tattara ɗan abunda yake dashi, amma kuɗi ko million biyu basu yi ba, saura kwana uku kwanakin su cika, Alhaji Abubakar yazo ya samu Yayan Nasir yace  "Malam Yusuf ya ake ciki ne? Kun haɗa kuɗin kuwa?" Yusuf yace "wallahi kuɗin nan basu kai ba, muna ta faɗi tashine, dan Allah inda hali a basu haƙuri su ɗan ƙaramana lokaci, dan Allah karsu bawa wani, Insha Allah zamu cika a samu Nasir ya aureta" Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar yayi yace  "nikam wani irin so kakewa Nasir haka?" Yusuf yayi murmushi yace  "Nasir ne kaɗai ya ragemin, kuma kaga yarone ƙarami ba wani babba bane, kuma maraya ne, yana buƙatar a jashi a jiki,  kuma iyayenmu sun mana wasiyya sosai akan muso juna, inyi haƙuri dashi in kula dashi, kaga dole in kula da marayana" Alhaji Abubakar yace  "Masha Allah, gaskiya na daɗe banga managarcin mutum kamarka ba Yusuf, Allah ya biyaka, kawo abunda ya samun, inje musu dashi inga ya zamuyi" Yusuf ya dinga murna, kamar Alhaji Abubakar yace an bawa ƙaninsa Hudan, yaje ya kawo masa kuɗin, ya duba ya ƙirga su sannan yace  "zanje can marocon, zanga yadda zamuyi, amma da ina da 'ya ko ƙanwa gaskiya dana baka, dan na yaba da amanarka da haƙuri da ɗan uwanka' Yusuf yayi murmushi yace " rufamin Asiri kar Uwargida ta jimu, kasa ta haɗemin rai yau" Sukayi dariya gaba ɗaya, daga nan suka yi sallama. Sam Nasir be san me ake ciki ba, Yusuf yana ta cigaba da fafutuka, yana haɗawa da Addu'a. Tafiyar Alhaji Abubakar da kwana biyar, ya dawo yai sallama da Yusuf ya sanar masa da an basu Huda. Yusuf ya gigice yace  "ai bamu cika kuɗin ba" "karka damu, na shawa kan wannan matsalar, nan da sati biyu za'a kawo masa ita" Yusuf yai godiya kamar ze duƙawa Alhaji Abubakar, har seda yasa Alhaji Abubakar yaji kunya. Shikam Nasir ya dawo daga kasuwa, yayi sallar isha'i yaje yayi kwanciyarsa, ko abinci be nema ba, babu abunda yake banda begen Huda. Yusuf ne ya shigo ɗakin da Nasir yake yace  "Ango kasha ƙamshi" Nasir be gane me yayansa yake nufi ba, yayi zaton zolayarsa kawai yake. Yusuf yace "gobe in Allah ya kaimu, masu aiki zasuzo suyi gyare gyare a gidan nan, ka tattare kayanka ka koma shagon gidana" Cike da rashin fahimta Nasir yace  "gyaran me kuma za'ayi?" "Amarya za'a gyarawa gida" "Aure zaka ƙara ne?" Yusuf yace "Rufamin Asiri, inani ina ƙara Aure, Nadiyata ta isheni matar rufin Asiri, 'yar aljanna insha Allah, har ƙiyama muna tare da ita" Nasir yace  "to gyaran me za' ayi?" "Huda za'a gyarawa gida" Zare ido Nasir yayi yace  "wace Hudan?" "Hudanka mana" 'Yayana, yaushe ta zama tawa? " " Sun baka, nan da sati biyu insha Allah za' a ɗaura Aure" Ai ba shiri Nasir ya rungume Yusuf ya fashe da kuka yace  "Yayana, wallahi na rasa me zance ma gaba ɗaya, yadda kake ƙoƙarin farantamin rai, Allah ya sadaka da Annabin rahama, yasaka a aljanna ma ɗaukakiya" Yusuf yace 'Ameen ya Allah, tare da kai ƙanina, farincikin ka shine nawa, nima nasan idan nine a halin da kake ciki, ba zaka zuba ido ba, ina me maka nasiha daka kula musu da' ya, ko bayan ba raina ka tuna gwagwarmayar da muka sha kafin ka sameta, ka nunawa duniya mazan hausawa Jarumai ne, kuma sun iya riƙe mace su bata kulawa " Nasir yace  " karka damu Yayana, Insha Allah zanyi iya ƙoƙarina inga na riƙe Huda da Amana" Haka Yusuf ya ci gaba da yi masa nasiha, da jan kunne akan sha'anin Aure. Nan da nan magana ta cika unguwa Nasir ze auri Huda, wani abun takaici dangin mahaifinsu sukace bada yawunsu ba, ba zasu yi jagora aje a Aurowa Nasir balarabiya ba, babu hannunsu a ciki, abun nan ya ƙara tsayawa Nasir a rai, ƙiri ƙiri se bare ne yayi jagorancin karɓa masa Auren wato Alhaji Abubakar. Haka suka tafi maroco, da Alhaji Abubakar, da ɗansa Ahmad, da Yusuf da Nasir da wasu Abokan Alhaji Abubakar suka tafi maroco, Nasir yaso a tafi da Bulama, amma Yusuf ya hana yace ba zasu je da shi ba. Huda ji take kamar ba itaba, lokacin da aka faɗa mata kuɗin da aka yankewa Nasir ta fidda rai da Aurensa, saboda tasan bashi da wannan kuɗin, ta fidda rai gaba ɗaya ta haƙura, se rashin lafiya take tana rama, babu zato babu tsammani yayarta Islam tazo mata da zancen ai megidanta ya zo da kuɗin Auren Nasir daga Nigeria, Alhaji Abubakar ne ya cika kuɗin, amma babu wanda ya gayawa hakan. Baffansu Huda be taɓa tsammanin za'a iya biyan kuɗin nan ba, duba da yadda aka gaya masa Nasir marayane, kuma bashi da ƙarfi, ganin haka yasa yace tunda ta dage se bahaushe, bahaushen ma talaka ta dage ita da 'yar uwarta to suje, gasu nan ga bahaushe, kuma ya cire hannunsa daga kansu, kome ze faru ta nemi' yar uwatta da mijinta da suka dage akan se anyi wannan Auren, karsu ƙara nemansa. Huda ta wani fannin tayi farinciki, yayinda gefe ɗaya kuma hankalinta a tashe, jin cewar jigon da suke tunƙaho da shi yace bashi basu. Alhaji Abubakar kuma yace  yaji ya gani, shi har Abada Aure albarkarsa ake nema ba wai tarin dukiya ba, idan da rabo a gaba Nasir zeyi Arziki, kuma in dai Huda ce kome ze faru ze riƙeta, balle babu abunda ze faru se alkhairi. Shikuma Habib yace se an biya shi duk abunda ya kashewa Huda, alhalin duk abunda Ake bayarwar ba bata akeyi ba, wanima bata san an bayar ɗinba. Da kuɗin Auren gurin Nasir, aka tattara abunda ya samu aka biya Habib. Kamar wasa ranar wata juma'a, bayan sallar juma'a, a masallacin Kairaouine, suka ɗanyi shagalinsu a can, da suka tashi dawowa Nigeria, Alhaji Abubakar ya kasa ya tsare ya karɓi sadakin Huda a hannun ƙanin mahaifinta, sauran 'yan uwa ma suka tattara mata sha tara ta arziki, wani aka bata wani kuma aka ƙwace, suka taho da Amarya Nigeria. 'yan unguwar su Nasir, suka haɗa kuɗi suka shirya musu walima, wani ya bada hall, wani ya bada buhun shinkafa, gaba ɗaya kai baka ce Auren maraya ne ba, abokansu suka dinga basu gudunmuwar kuɗi wasu kaya, saboda duk wanda yasan Nasir da Yusuf yasan iyayensu, yasan mutane ne masu karamci da biyayya. A lokacin maƙoci yana ganin ya isa da ɗan maƙocinsa, ana zaune lafiya kamar 'yan uwa dan haka Nasir yayi mamakin yadda bare sukayi musu wannan karar amma dangin mahaifinsu suja kasa yi musu. Duk Wanda yaji yadda akayi auren yasan kawai rabone, dama Allah ya rubuta Huda rabon Nasir ce. Huda ta tare a gidanta, musamman Yusuf yasa Nasir a gaba sukaje gaban Alhaji Abubakar sukayi masa godiya dashi da Islma amaryarsa. Nasir baze taɓa manta alherin Ahmad da mahaifinsa ba, da sauran abokansa, amma Bulama babu abunda yayi masa, sema wadaƙa da sata daya dingayiwa Nasir a shago, ganin hankalinsa ya koma kan Auren da zeyi. Sam Bulama beso Nasir ya auri zuƙeƙiyar balarabiyar yarinya ba, kullum suna tare, amma gaba ɗaya Nasir ya fishi sa'a a rayuwa. Kuɗaɗen da Nasir ya samu na gudunmuwa, da wanda aka bawa Yusuf ya ɗau abunda ze ɗauka ya bawa Nasir sauran, ya sake zuba dukiyar a harkar kasuwancinsa, duk inda yaji wata harkar samu seya ɗebi kuɗi ya tafi ya jarabba, duk lokacin da yayiwa Yusuf zancen be bashi kuɗin daya ara masa, se yace ya ajiye masa ba yanzu ba, dan gani yake idan ya karɓa hakan ze iya shafar kasuwancin ƙanin nasa, yana nan zaune da matarsa lafiya, yana sonta tana son shi, Arziki se bunƙasa yake a hankali. Ya ɗaukewa Yusuf ɗawainiyar siyan kayan Abincin gidansa, ya nuna masa baya so amma be bari ba. Huda ta ɗau kuɗinta na sadaki da abubuwan data samo a can ƙasarsu, ta bawa Nasir tace ya haɗa, da tayi ta ajiyar kuɗin babu abunda zata yi dasu gara ya dinga juya su, ya karɓa ya haɗa yana juyawa, a hankali ya dinga janyo abokansa cikin harkar kasuwancin da yake yi, wasu suzo zuciyarsu ɗaya wasu kuma suzo da niyyar mugunta. Allah maji roƙon bawa, katsam Nadiya matar Yusuf ta samu juna biyu bayan shafe shekaru uku da Aure, Nasir kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, danma yafi yayansa farinciki da wannan rabo, kullum zancensa Anty Nadiya idan kin haihu ni zanyi kaza. Tun kafin bikin Nasir ta samu cikin, sam Nasir be saniba saboda yana cikin gararin soyayya, Nadiya ta girni Huda, amma suna mutunci sosai suna ƙaunar juna, Duk inda Ahmad yaji harkar kasuwanci da samu seya janyo Nasir, shikuma Nasir seya janyo Bulama, wani abun Bulama ya ɓata lamarin. A hankali Abu ya bunƙasa, sanadiyyar Ahmad Nasir ya fara fita ƙasashen ƙetare, yana shigo da kayan ado na mata da turarruka, Ahmad ya koya masa yadda ake siyan Hannun Jari a manyan kamfanunnuka. Nan da nan Kuɗi suka fara zaunawa Nasir, duk kasuwancin daya shiga seya samu alheri, shine nan shine can. Ba ƙaramin daɗi Yusuf yaji ba, ganin dukda ƙarancin shekaru na Nasir amma ya fara nutsuwa, dan a lokacin befi shekaru Ashirin da uku ba yayi Auren, a wannan lokacin Auren wuri ba wani abu bane, indai yaro yana da sana'a. Bulama ya tsani alaƙar Ahmad da Nasir sam, da yana zuwa gidan Nasir, amma fafur Huda ta nuna bata son ya dinga zuwar mata gida. Kafin Nasir yaje Saudiyya Yayansa ya fara biyawa yaje Umara, Yusuf yace Nasir ya fara zuwa amma yaƙi yace shi yakeso ya tafi. Ba ƙaramin daɗi da farinciki Yusuf yayi ba, dan badan a wancan lokacin ya haɗa kuɗin Auren Nasir ba, da tuni yaje, aikuwa yayi farinciki sosai. Bayan dawowar Yusuf daga Saudiyya, lokacin Wata huɗu da Aurensu Nasir, matar Yusuf Nadiya ta haihu, Nasir kamar shi akayiwa haihuwar nan dan murna, kayan jariri kaf dana me jego shiya siya, hatta abun hakika shine yayi. Tunda akayi haihuwar nan, Huda take zuwa gidan mejegon nan, tana addu'ar itama ubangiji Allah ya bata nata, dan tana matuƙar son yara. Kwana bakwai da haihuwa akayi suna, yaron yaci sunan Mahaifinsu Nasir wato Umar faruk, ganin Nasir ya fara ajiye abun arziki yasa, da sunan Umar dangin Mahaifinsu suka zo suna. Anci an sha dai dai gwargwado anyi shagalin sunan daba'a taɓa makamancinsa a unguwar nan ba, nan Sunan Daula ya sake bin Nasir sosai, Suna nunawa junansu ƙauna da sadaukarwa a tsakanin shi da ɗan uwansa. Gaba ɗaya kusan Wuni Huda take yi a gidan Nadiya, ko taje gurin yayarta Islam taita musu raino saboda son yara da take yi. Kasuwancin Daula fa ya faɗaɗa, abun har mamaki yake bawa mutane, babban abunda yasa mutane ke ƙara son Nasir shine hannunsa a sake yake, bashi da rowa sam, ga jan yaransu da yake akan harkar sana'a, dukda cutar da suke masa wasu lokutan. Yusuf yana yawan yi masa faɗa akan watsi da yayi da 'yan uwan mahaifinsa, hakan be kamata ba, dan ko gaishe su baya zuwa yi. Nadiya na fama da raino, ba damar zuwa Saudiyya, Nasir ya biyawa kansa da Huda suje suyi Umara, lokacin nan Ahmad ma zashi, ana i gobe zasu tafi, suka je gidan Yayansa Yusuf suyi musu sallama. Suka zauna suka dinga hira kamar bazasu rabu ba, suka dinga tuna lokacin ƙuruciyarsu da gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa, da kuma wahalar maraici. Har Huda ta dinga kuka, Yusuf yace  "haba Huda, ai lokacin ya wuce ba gashi yanzu se labari ba?" Nadiya tace  "itafa Huda ko a labari bata son taji abunda ze taɓa wannan mijin nata, jinsa take kamar ranta, dan haka ku dena ma wannan labarim" Huda ta ƙunshe kanta tana dariya, Nasir yace  "Anty ya kika gani, kema  fa haka kike son Yayana, laifi ne dan ta so mijin ta, wallahi my Huda kidena jin kunyar Anty Nadiya, naga ta fara damun ki" Huda ita dai sedai tayi murmushi, Yusuf yace  "ɗanuwa babu abunda zan cewa Allah se godiya, kamar yadda Antynka take fata gashi ka bunƙasa kamar wasa, Allah ya ƙara yalwata maka Arzikinka, Allah yasa ku yi ibada karɓaɓiya, ya dawo daku lafiya, sannan yakamata kayi haƙuri ka manta da abunda dangin mahaifinmu sukayi mana, komai ya wuce suma ka dinga kyautata musu " Nasir yace  " Taɓɗijan, wallahi nida su har abada, bazan manta cin zarafi da wulaƙancin da suka yi mana a rayuwa ba" Yusuf yace 'A' a Nasir, abun da haƙuri be bayar ba, rashin sa baze bayar ba, ka maida komai ba komai ba, se kaga Allah ya daɗa buɗa maka, sannan ina gargaɗinka akan wannan yaron Bulama yake kowa? Ban yarda ka barshi akan kayanka ba, ko harkar kasuwancinka ba, dan bashi da kirki " Nasir yace " Nikam na rasa me Bulama yayi muku kuka tsane shi, ni tausayi yake bani kaga shima marayane, kuma basu da ƙarfi " Yusuf yace " banƙi kayi taimako ba, amma ya kamata kasan irin taimakon da zaka dingayi, Ka kiyayi yaron nan" Nasir yace "to babbn Yaya magajin babanmu, Antyna ta kaina insha Allah baɗi in Allah ya kaimu lokacin aikin hajji, seki barmin babana kema kije ki sauke farali" Nadiya tace  "Allah ya ƙara Arziki ɗan gidan Anty" Nasir yace  "Ameen, ban cika Alƙawari ba, ke nace zan fara kaiwa amma na kai Yaya, nayi son kai ko?" Nadiya tace  "ai duk wanda ya kyautatawa Mijina ni yayiwa, nan duniya in ana son farincikina to a kyautatawa mijin marainiya" Nasir yace  "imra'ati kinji ko? Tana tsokanarki kin fiye sona, amma ji abunda take cewa" Sukayi dariya, Nasir yace  "Yayana, wai yaushe zan dawo muku da kuɗinku ne? Kasan fa yanzu Alhamdilillah, zan iya biyanku hadda riba" Yusuf yayi dariya yace  "Naji, Alhamdilillah haka nake fata, ka ci gaba da juya mana, lokacin karɓar yana nan zuwa, mesu ze karɓa" Nasir yace  "waye me su ɗin dazs karɓ?" Yusuf yace "kai Baba suda sarki zance, kuje dare ya fara yi, kuje kuyi sallama dasu Antyn Huda, nima jibi in Allah ya kaimu nida su Nadiya zamu tafi Abuja, zamuje wani taro zan wakilci bankinmu, inaga daga nan idan na dawo zasu bani allowances ɗina na siyan gida da mota" Nasir yace  "masha Allah, Allah ya tabattar Yayana, Huda bani babana sanyin idaniyata, in sake ganinsa in sumbaci fararen kumatunsa" Huda ta miƙa masa Faruk, ya karɓi jaririn ya rungume shi, yana sumbatar fuskarsa. Yusuf yace "gaskiya Nasir kana ƙaunar wannan ɗan naka, Maman Faruk sekinyi dagaske karsu ƙwace mana ɗa shida matarsa" Haka suka wanzu suna zolayar juna, suna hira tare sukaci Abincin dare kamar karsu rabu, suka shiga gurin Islam sukayi mata sallama itama, nan mu sun daɗe a can, daga ƙarshe Yusuf da Nadiya seda suka kusa rakasu gida sannan suka juya suka koma. Washegari Alhaji Abubakar ya aiko da babbar mota, aka ɗauki su Nasir da Huda da matarsa, su Yusuf sukayi musu rakiya har airport, canma seda suka tsaya hira kaman karsu rabu, sannan suka tafi. Satinsu uku a can sannan suka dawo gida Nigeria, sedai dawowar tasu suka tarar da abu mafi muni a tarihin rayuwarsu, wannan rana ta zamewa Huda da Nasir rana mafi muni da a tashin hankali, tashin hankalin da bazasu taɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwarsu, ranar tazo musu da wani al'amari me taɓa zuciya da girgiza ruhi, basu kaɗai ba hatta Ahmad ɗan gidan Alhaji Abubakar wannan rana tazo masa da baƙin tarihin da baze taɓa goguwa a zuciyarsa ba LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 66_67 Mummunan labari, Islam 'yar uwar Huda, ta bawa me aikinta guga, yana cikin yi, me gidan ya dawo ya aike shi,  koda me gugan ya dawo se ya tattare kayan gugar yace da safe ya ƙarasa, ashe ya manta be kashe dutsen gugar ba, cikin tsautsayi cikin dare dutsen ya ɗau zafi wuta ta fara ci, babu wanda ya farga, har wutar ta shiga gidan Yusuf Yayan Nasir, gobara ce ta tashi sosai, daga gidan Alhaji Abubakar, har gidan Yusuf babu wanda aka iya ceta, gaba ɗaya. tsautsayin wutar nan ya ritsa dasu, suka ƙone ƙurmus a cikin wannan gobarar, 'yan unguwar sun kaɗu sun shiga cikin tashin hankali da wannan ifyila'i ya faru, se yayyafa musu ruwa akayi aka rufesu dan babu ta inda za' a iya sallatarsu. Nasir ya kaɗu da samun wannan mummunan tashin hankali, dan bashi ba hatta Huda se kwasarsu akayi zuwa Asibiti, dan babu wanda yake cikin hayyacinsa. Dukda Ahmad ma ya kaɗu ya shiga cikin tashin hankali, da labarin daya tarar na rasuwar mahaifinsa, dama shi mahaifiyarsa itace Uwargidan Alhaji Abubakar, kuma ta rasu yana da wasu matan amma ba a wannan gidan suke ba, da ya Auro Islam ne ya sakata a wannan gidan, ya dawo da Ahmad gidan, shima ya kaɗu ya shiga cikin tashin hankali, shine babba a gurin mahaifinsa gashi yana ji dashi, dukda ya sha wahalar matan uba, amma Auren Islam yasa ya samu sassauci, dan ita sam babu ruwan ta, dukda wannan masifar tashin hankali da yake ciki, amma ya tausayawa Nasir da Huda, dan duk wanda wannan mutuwar zata taɓa a bayansu yake. Seda Nasir ya kwana biyar besan inda kansa yake ba, numfashi ma baya iyayi seda taimakon Oxygen, ita kuwa Huda tunda ta farka bata magana, sedai hawaye yaita bin fuskarta, ko Abinci bata iyaci balle magana, fuskarta ta kumbura tai jawur, ga rashin 'yar uwatta, ga ɗan uwan mijinta da matarsa, ga babu mijin' yar uwatta, ga mijinta a kwance shima rai a hannun Allah. Se a kwana na Shida sannan Nasir ya farfaɗo, ya farfaɗo da kalmar la'ilahaillalah Muhammadur rasulillah salallahu alaihi wassalam " Likitoci suka rufu akansa, suna monitoring ɗin bugun zuciyarsa, salati kawai yake yana faɗin  " Yayana, ɗan uwana, shi kaɗai ne ya ragemin, Anty Nadiya da ɗansu duk babu, innalillahi wa inna ialaihi raji'un " Wani liktane yace " haba ɗan uwa kamar ba musulmi ba, kayi haƙuri kayi tawwakali, idan kaji ƙaddarar wani seka rufe baki, kayi haƙuri mu samu mu ceci rayuwar ka, an san mutuwa da ciwo amma kayi haƙuri " Nasir yace " likita, ɗan uwana ya mutu, da zan tafi umara ya muka dinga hira, ashe wasiyya ce, nayi rashi likita, banji rasuwar iyayena kamar yadda naji mutuwar Yusuf da Nadiya ba, har ɗan namu ma na rasa, innalillahi wa inna ialaihi raji'un wayyo Allah yayana" Yai maganar yana fashewa da kuka, kamar ƙaramin yaro. Likitan ya dafa kafaɗarsa yace  "Allah yasan da kai, kayi haƙuri, Allah shike da rayuwar kowane bawa, ka kwantar da hankalinka, matarka mafa tana can munata ƙoƙari akanta, karta rasa hankalin ta, idan taganka a mawiyacin hali to jikinta ze rikice" Jinina kai Nasir ya shigayi yana  "Allah sarki Hudana, Huda munyi rashi, mun rasa 'yan uwa dagani harke, Allah ka zama gatan mu, Allah kayiwa bayinka Rahama" Likitan ya amsa da Ameen, yana cigaba da kwantarwa da Nasir hankali. Nasir yace  "likita, ku kaini inga matata" Likitan yace  "A' a ka bari za'a kawo ta, har nan inda kake bama son ka dinga wahalar da jikinka" A wannan kwanaki biyar ɗin Huda tayi ɓari, amma saboda halin da suke ciki ba'a sanar musu ba, dukda alhini da Ahmad ke ciki, amma a haka yake ta sintiri a Asibitin, wata ƙawar mahaifiyar su Nasir ce take sintirin jinyar Huda, yayin da Ahmad ke kula da Nasir, 'yan unguwa nata zuwa yi musu jaje da kuma duba su. Duk Wanda yaga halin da suke ciki, sya tausaya musu, gaba ɗaya sun rame mussman Huda abun yafi mata yawa, yanzu ta rasa kowa da komai nata, se Allah da kuma mijinta Nasir, shima gashi a kwance se yadda Allah yayi dashi, ga ɗan uwan mahaifinsu ya sallamasu, dan bezo Nigeria gurin ta'aziyya ba, kuma labarin gobarar ya iskeshi, yace suje can su ƙarata ba abunda yayi masa zafi. Nasir ya takura akan yana son ganin Huda, a haka aka turo Huda a wheel chair tazo duba Nasir. Tana ganinsa a zaune ta ɗanji sanyi a ranta, ganin nasa jikin da sauƙi, ana ƙarasawa da ita suka rungume juna suna kuka, Kuka me tsuma zuciya, a hankali Huda tace  "zaujee, mun rasasu gaba ɗaya babu wanda yayi rai a cikin su ' Nasir yace " Na sani Huda, babu yadda muka iya se mu rungumi ƙaddararmu, sukuma mu cigaba da yi musu Addu'a " Nan suka dinga kuka, aka rasa me rarrashin wani, Ahmad ne ya shigo ya tarar dasu a wannan yanayi, suna ta kuka. Ahmad yaja kujera ya zauna, ya dubi su Nasir cike da rauni da karaya shima ya fara magana yace " Nasir, dama itafa duniya munzone tamkar matafiya, dole wataran mu barta, sannan dukkan ɗan Adam dole ne Allah ya jarrabe shi, Allah baya barin mumini babu jarrabawa, dan haka nida ku mu rungumi ƙaddrara mu, mu yi tawwakali mu barwa Allah komai, shi ze bamu mafita, su kuma da muka rasa muyi musu Addu'a " Ahmad ya ƙarasa maganar, ƙwalla na zuba daga idanunsa, amma ya cigaba da tausarsu yanayi musu Nasiha. Seda suka shafe sati biyu a Asibiti, saboda jikin Nasir, dan zuciyarsa ta taɓu saboda damuwa, haka likitoci suka gindaya masa sharuɗa da magunguna, sannan aka sanar dashi ɓarin da Huda tayi, sam da gashi har ita basu san da cikin ba, dan koda zasu tafi umara da aka yi gwaji babu, yanzu kuma an tabattar masa da cikin watansa uku ma, Ba laifi Bulama ma yayi zaryar Asibitin nan sosai, saboda Nasir, dan dukda rashin jituwar da yake da Yayan Nasir ya tausaya masa wannan rashin da suka yi lokaci ɗaya, shima ya dinga rarrashin Nasir, akan ya kwantar da hankalinsa ya rungumi ƙaddara. A haka aka sallamesu suka koma gida, sedai babu me iya rarrashin wani a cikinsu, idan abun ya taɓosu se su wuni kuka ita dashi, dama ga Nasir da raguwar zuciya, su wuni cikin damuwa babu me ko iya cin Abincin, saboda dukkaninsu mutuwar tana dukan su. Kusan watanni Uku, da mutuwar har ɗan gara Nasir ya fara jarumta yanzu, amma Huda kam babu wannan batun, musamman gari ya waye da ta saba ta tafi gidan Nadiya, ko Yayarta Islam taje taita musu rainon 'ya' ya kasancewar tana matuƙar som yara, amma lokaci ɗaya Allah ya karɓe su gaba ɗaya. Yanzu Nasir na iya zaman rarrashin ta, yaita bata baki yana tausarata, yace  "Huda, ni dake Allah ne gatanmu, shiya haliccemu gaba ɗaya, kuma yafi mu sonsu daya karɓesu, ni dake dole muyi kukan maraici, nasan zakiyi tunanin ya rayuwarki zata kasance a nan gaba? Huda a duniya bayan iyayena ina jin maganar Yayana fiye da tunaninki, kuma nima nasam abunda ya dace, nasan gwagwarmayar da akayi kafin in Aureki, dan haka ko sau ɗaya karki sawa zuciyarki Nasir ze juya miki baya, nida ke yanzu gaba ɗaya muna cikin maraici gaba da baya, dan haka mu rungumi ƙaddararmu mu rayu tare, mu jure duk wani ƙalubale mu kasance a tare har zuwa namu wa'adin, in dai ta ɓangare nane, Insha Allah bazaki zubda hawaye ba" Huda tayi ajiyar zuciya tace  "Zaujee, nima nasan abune mawuyaci in fuskanci ƙalubale ko juya baya daga gareka, ina da kyakkyawan yaƙini akanka, amma dole in koka, munyi rashin da ba zamu mayar da wannan gurbin ba, kamar yadda ka faɗa insha Allah, duk tsanani zan jure duk wata ƙaddara in rayu da kai, bani da kowa se Allah sekuma kai" Nasir yace "Insha Allah, bazan baki kunya ba Huda, nasan halaccin da kikamin a rayuwa, dan haka insha Allah zan kasance dake, zan kasance me baki kariya, kuma zan zame miki mijin marainiya insha Allah" Haka su dinga kwantarwa da junansu hankali, suna bawa junansu haƙuri. Amma duk da haka, Huda ta kasa sakin jiki ta haƙura gaba ɗaya, ƙarshe seda Nasir ya bar unguwar gaba ɗaya ko hankalinta ya kwanta, dan ko fita tayi tazo wucewa ta layin gidajen ƙarshenta idan ta fara kuka hadda suma. A haka Nasir ya daddafa ya cigaba da kasuwancinsa, kuɗi ko ta ina shigomasa suke, a haka har Ahmad yayi Aure, Bulama ma ya tattago maganar Aure, kusan Nasir ne yayiwa Bulama komai na Auren, dan har gidan daze zauna shiya bashi. Shikuma Nasir likkafa se ƙara cigaba take, gaba ɗaya ya zama busy man, yawo ƙasa ƙasa kasuwanci kala kala, duk ba wanda ba yayi. Shine saida kayan sarƙoƙi, motoci, kayan masarufi, ga shaguna da yake dasu a kasuwa, na siye da siyarwa, hannun jari dayake siya a manyan kamfanunnuka. Nan da nan ya zama kamar bashi ba, gashi dai matashi amma ya tara kuɗi. Nasir ya ɗauki Huda sukaje ƙasarsu can Maroco, amma baffanta yayi musu wulaƙanci, Kasancewar besan Nasir ya fara arziki ba, yayi musu fata fata yace yadda aka cinye 'yar uwatta itama haka za' a cinyeta, haka suka dawo Nigeria da ɓacin rai. Ganin Huda ta kasa samun nutsuwa har yanzu, ga tarin damuwa data sa a ranta, hakan yasa ya ɗauketa ya tafi da ita ƙasashen waje, can Dubai inda yafi harkokinsa, ya koma makaranta a can, sedai tun bayan ɓarin nan Huda bata sake samun ciki ba, kullum cikin addu'a take ubangiji Allah ya bata rabo itama. Ya zamana Huda tana Dubai, kowani abun zezo yi Nigeria, ita tana can duk dan ya samu ta rage damuwa. Seda suka shekara takwas da Aure bata sake yin ko ɓari ba, abun duniya duk ya addabeta, shikam ko a jikinsa, dukda yana addu'a sosai a ransa a bun yana damunsa, amma sam baya nuna mata, ta takura masa sukaje Asibiti akayi musu gwaje gwaje, amma akace lafiyarsu ƙalau. Se a shekara ta tara Allah yasa Huda ta samu ciki, aikuwa Nasir yayi murna babu adadi, nan suka shiga rainon cikin nan da tattalinsa, gefe guda kuma ya zama matashin ɗan kasuwa na farko, wanda sunansa yake zagawa a cikin Nigeria, a hankali yasan manyan 'yan siyasa da attajirai, saboda har harkar kwangila yake yi, nan dangin mahifinsa suka shiga ƙoƙarin nuna ai ɗansu ne, amma fafur yaƙi yadda su raɓe shi, a cikin dangi can suka haɗu da wani Musa, sun ɗan haɗa alaƙa amma ba irin ta sosai ɗin nan ba, ɗan unguwarsu ne dai, ya dinga shisshigewa Nasir, tun Nasir na basar dashi, har ya fara sakewa dashi. Musa ya nuna sha'awarsa ga harkar siyasa, Nasir ya haɗashi da manyan 'yan siyasa, ya goyi bayansa akan harkar siyasar, nan da nan mutane suka karɓi Musa, a dalilin Nasir, kasancewar Nasir mutum ne na mutane, mutane na ƙaunarshi saboda hannunsa  a sake yake, ga shaharar da yayi ganin Nasir ne ya talatta Musa da kansa, hakan yasa mutane suka karɓe shi hannu biyu biyu. Bulama kam basa jituwa da Ahmad, dan haka ya dinga shiga yana fita danya raba Ahmad da Daula, gashi kusan duk wani harkar kasuwanci Ahmad ne yake jan Daula, dan tun yana ƙarami Mahaifinsa ɗan kasuwane, dan haka yasan sirrin kasuwanci sosai, Ahmad yana yawan ankarar da Daula akan ya kiyayi Bulama, amma se Nasir yace ai Bulama ya zamani na zama shi, rabuwarmu abune me wahalar gaske. Bulama ya kunno musu wata rigima akan harkar kasuwancin da suke, ya shiga ya fita seda yasa Daula da Ahmad sukayi baran baran suka rabu, ya zamana shine ma gaban Nasir. Watan cikin Huda tara cif ta haifo sankaceciyar jariryarta mace, Daula ya  rasa inda zesa ransa dan murna, sedai haihuwar ta fama musu mutuwar mutanen da suka taka mahimmiyar rawa a rayuwar su, yau gashi kamar yadda Nadiya ke fata, Nasir ya amsa sunan Daula, ga rabo sun samu, amma babu ɗaya a mutanen nan daze taya su farinciki. Haihuwar jaririyar nan tasa sun zubda hawaye, har damuwa taso ta maye gurbin farincikin da suke ciki, wani abun mamaki jaririyar nan ta ɗakko kamanin Islam Yayar Huda, dukda Huda da Islam suna kama sosai, amma kamanin Jaririyar nan sunfi karkata ga Islam. Huda tana zaune rungume da jaririyar nan tace  "Duk wanda yake ƙaunata, ya ƙaunaci jaririyar nan, duk wanda yaƙi jaririyar nan to tabbas ni yaƙi, a duniya yanzu banda Allah, se mijina da wannan 'yar, su kaɗai Allah ya mallakamin, inajin son' yar nan  a raina, kamar yadda nake son mahaifinta, Allah yasa ta zamo me jinƙi da tausayi kamar mahaifinta " Nasir ya rungume Huda da jaririyarsu yace" tabbas nima duk me sona, to ya ƙaunaci Huda da jaririyar nan, Allah yasa mun ƙara yawa, ya azurtamu ta samun ƙaruwa, yanzu wani suna kike ganin zamu saka mata? Ko mu mayaf da Sunan Anty Islam ' Girgiza masa kai Huda tayi tace  "A' a idan ka mayar min da sunan Islam, bazan iya tsawatar mata ba, kamaninta ɗaya da Islam zan dinga ganin kamad itace, haka idan ka samun sunan Anty Nadiya, nan ma bazan iya tsawatar mata ba, saboda ina girmama Anty Nadiya, tambarin mutjwarsu baze taɓa barin zuciya ta ba, gara mu sa kamata wani sunan daban, mu sama ta Widad, wato soyayya da Abota, na zaɓi sunan ne saboda yana da kyakkyawar ma'ana, Ina sonta kuma itace babbar ƙawata" Nasir yayi murmushi yace  "muna sonta dai' Haka akayi gagarumin shagalin suna, a Nigeria, nan dangin mahaifin su Nasir suka dinga rige rigen zuwa, saboda Arziki ya samu, Bulama ya taya Nasir murnar haihuwar Widad sosai, duk da saɓanin da suka samu da Ahmad, seda yazo yayiwa Nasir barka, ya bawa Widad kyaututtuka, Bulama ne ya saiwa Widad Haikika, yayi Ƙaton Akwati da kayan jarirai, haka nan yaji yana ƙaunar yarinyar, sanadin abunda yayiwa Widad, yasa mafi yawa na ƙiyayyar da  Huda ke masa ta ragu, dan taji haushin rabuwar Nasir da Ahmad, abunka da abun masu Arziki da neman gurin zama, nan masu kuɗi suka dinga bajinta suna gwangwaje jaririyar nan da manyan kyautuka, dan kawai su birge Daula, ko ace wane ya bada kaza. Kafin su koma Dubai, kusan kullum se Bulama da matarsa sunzo, dan ya ɗauki Widad, ko kuka take ya dinga rarrashinta kenan, Yana matuƙar son yarinyar. Kwanansu Arba'in Nasir ya ɗauke Huda suka koma, Bulama ma albarkacin Nasir ya fara kama ƙasa, nan da nan ya shiga aure Auren mata, ya auri wannan ya saki, ya Auri waccan ya kora, tun Nasir yana masa faɗa harya ƙyaleshi. Kadarorin da Aka tarawa Widad na suna, Daula ya haɗa ya siyar bisa shawarar Huda, suka haɗa kuɗi suka buɗe kamfanin sarrafa ƙarafa, manyan mutane har daga ƙasashen ƙetare suka zuba hannayen jarinsu cikin kasuwancin, nan fa Sunan Daula ya ƙara shahara, ya zama babban attajiri, me sana'a goma maganin me gasa. Widad ta fara wayo a hankali tana girma, ta isa shiga makaranta se Daula ya koma England, saboda mafi akasari yanzu yafi ta'amalli dasu akan harkar kasuwancin motoci, aka saka Widad a makaranta, Huda kuma ta dage da koyar da ita na Addini, dukda akwai wani ustaz dayake koyar da yaran musulmai a ƙasar. Sedai gaba ɗaya rayuwar Widad da girmanta, ya sha ban ban dana sauran yara, sun raba gari da duk wasu ɗabi'u na yara, duk inda yaro yake an sanshi da son kallon fina finan cartoon, kona dabbobi amma banda Widad, idan za tayi kallon film, daga wrestling, se film wanda ake yaƙe yaƙe ko harbe harben bindiga, kokuma fina finan horo na ban tsoro, kona harkar fashi, suke birgeta, sam bata kallon wani film ɗin Indiya ko soyayya da tausayi, basa gabanta, Huda taita fada tana mita, amma Nasir se yace ta ƙyaleta, nan gaba zata dena. Huda taita mita tace  "yarinya kamar ba mutum ba, ke duk abunda mutane suke yi ko suke so, ke kunyi hannun riga dashi?" Widad tana da miskilanci, bata magana seta ga dama, idan har kaji ta zage tana surutu, kodai da mahaifintane ko kuma Bulama ne ya kawo musu ziyara, bata wasa da 'yan uwanta yara, sedai taita gwada tsalle tsalle, da harbin bindiga da take gani a film, shine wasanta sosai abun yake damun Huda, Nasir yace tayi haƙuri irin tata ƙuruciyar kenan. Widad tafi sakewa Da Babanta akan Amminta wato Huda, Huda tana da zafi sosai akan tarbiyyar Widad, yayinda Babanta duk abunda takeso shi yake so, amma duk da haka akwai soyayya da shaƙuwa a tsakanin Widad da Amminta, babban abunda yake haɗasu shine rashin son mutanen Widad da kuma wannan kallon da take yi. Widad ko ƙawayen kirki bata da su, saboda rashin son maganar ta, sedai tana ji da magenta, tana nuna musu soyayya, sune abokan wasanta, dasu take hirarta. Tun bayan haihuwar Widad me abun mamaki, Huda bata sake samun haihuwa ba, tana ta Addu'a tana fatan ubangiji Allah yasa ta kuma samun rabo. A wannan lokacin shaharar Daula ta wuce iya Nigeria, da taimakon Allah Daula ya goyawa Musa baya da maƙudan kuɗaɗe, ya tsaya takara a wata jam'iyar siyayasa a wannan lokacin, a dalilin son da mutane suke wa Nasir Daula suka zaɓi Musa. Tunda Musa yaci zaɓe nan ya ɓarke da bushasha, bashi da aiki se gantalin ƙasashen duniya, ya manta da al'ummar da suka zaɓeshi, da irin Alƙwarirukan daya ɗaukarwa mutane, Ya kai 'yarsa Nurat makaranta a ƙasar waje, inda Widad take karatu, Nurat tana matuƙar son Widad, Kasancewar Widad ce bahaushiya' yar uwatta a makarantar, duk sauran yaran turawa ne, tun Widad bata damuwa da Nurat harta fara kulata, a hankali suka fara sabawa suna shaƙuwa da juna. Widad sam tun haihuwarta, rayuwarta tafi a ƙasar waje, idan sunzo Nigeria to hutu sukazo ko kuma ziyara, gashi Huda ba wani Hausa takeji ba, tama jin Husa amma ba sosai ba, dan haka wasu abubuwan duk Widad bata sansu ba. Nasir ya haɗa kai da wasu 'yan china, suka buɗe wata katafariyar ma' aikatar harkar kwangila, na gine ginen tituna, da shigo da kayan gini, ya jawo matasa sosai cikin harkar, bayan wancan kamfanin ƙarafa da yake dasu, da sauran manyan kadarorinsa na mamaki, dan har rijiyar mai Daula ya mallaka, kullum Arziƙinsa gaba yake, baya baya, gashi ba wani babba ba a a wannan lokacin, amma ya tara Arziki da shahara. Shekarun Widad bakwai a duniya, har Huda sun fidda ran samun wani ɗan, kawai ta tashi da matsanancin ciwon ciki, tayi zaton ɓacin cikine kawai, amma ta wuni a kwance, hakan yasa Daula ya ɗauketa zuwa Asibiti, a nan aka tabattar masa da tama ɗauke da juna biyu. Daula ya rasa inda zesa kansa dan farinciki, sunyi murna sosai da samun wannan cikin, nan ya ƙara ririta Huda fiye da yadda yake yi a baya. Da tayi motsi se yace "me unborn ɗina yake sone, har Widad ta fara kishi tace "Daddy, wai yanzu kafin son unborn ɗin nan ne dani?" "wane ni, ga gimbiyata ince nafison wani dake, ai you are my forever Queen, babu wanda ze rusamin fadarki, kiyi yadda kike so Gimbiyar Daula' Ire iren wannan kirarin, da soyayyar da mahaifinta ke mata suke fasa mata kai, Widad bata taɓa kukan babu ba, bata san ta nemi abu ta rasa shi ba, haka ta taso cikin zunzurutun jin daɗi da dukiya ta ban mamaki. Tun Widad tana ƙarama take bada kyauta, idan Daula ya ga dama, se yace "Ran Gimbiyata ya daɗe, ga wane me kike so a bashi?" Duk abunda ta faɗa ta zauna, se an bawa mutum, Huda taita mita tama ya fiye sangarta Widad, shi kuma ya kance idan banyiwa Widad abunda takeso ba se yaushe? Idan na mutu bata mori dukiyar mahaifinta bafa?" Ya sai kadarori da sunayen Widad, kadarorin daya siya da sunanta basu da adadi, Widad komai yi mata akeyi, suna da nanny. A hankali Huda taga idan ta biyewa Daula, to Widad zata tashi a sangarce, dan haka take ɗan koya mata waus abubuwan, kamar gyaran ɗakin data kwanta, ɗauke kwanon Abinci, da shara daidai wadda zata iya. Katsam bayan tenure Musa ta farko, yana ƙoƙarin ya koma, labarin irin almundahanar da Musa yayi ta iske Daula, abun yayi masa ciwo, ya goyawa macuci baya ya jagoranci al'umma, amma ƙarshe ya zalunce su, Daula da kansa ya kai Musa EFCC yace su tuhume shi, a bincike shi ya fito da haƙƙin mutane. Abun ya bawa mutane mamaki, ganin shiya kawo Musa Siyasa, amma da kansa ya kaishi gurin hukuma, sannan yace bashi bashi, kuma duk hukuncin daya dace ayi masa. Gaba ɗaya siyasar Musa, da mutuncinsa ya zube a idon mutane, dama farin jinin saboda Daula ne, mutane suka juya masa baya. Ƙarshe da kyar ya sha a hannun EFCC, dan seda aka kaishi prison a ƙasƙance, aka ƙwace wasu daga kadarorin da ya mallaka, a wannan lokacin abubuwa basu taɓarɓare kamar yanzu ba, da ƙyara wasu daga 'yan siyasa suka dinga shiga suna fita, seda Musa yayi watanni shida a prison, sannan aka sako shi da kyar, shima se da aka ƙwace masa passport, dan gwamnatin lokacin ba tasu bace. Wannan dalilin yasa Musa ƙulattar Daula, ya manta duk alkhairin da Daula yayi masa, ya manta yadda ya tsamoshi daga ƙangin talauci da shaye2, yayi aniyar rama abunda Daula yayi masa kota halin ƙaƙa, yayi Alƙawarin tozarta shi da wulaƙa ta shi, kamar yadda yayi masa, yayi alwashin ɗanɗanawa Daula baƙin ciki mafi muni a rayuwarsa, tunda ya ɓata masa suma ya lalata masa siyasarsa..... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: .LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 68_69 Cikin Huda ya ci gaba da girma, yayin da gefe ɗaya Daula ya fara tara maƙiya da mahassada, danshi duk abunda zeyi be yadda da cuta ko ha'inci ba, komai nasa tsakani da Allah yake yinsa, ga gefe guda mutanen daya ƙwacewa kasuwar wasu abubuwan, suma suka sako shi gaba suna jin haushinsa. Wata gidan Talabijin yayi hira da Daula, akan yadda akayi ya fara kasuwanci, nasarorin daya samu da kuma ƙalubale, duk ya dinga bada amsa, gashi duk hirar da za'ayi dashi se yayi zancen Yayansa Yusuf, se yayi musu addu'a, duk inda me Suna Yusuf yake Nasir kamar ze duƙa masa saboda girmamawa, komai ƙanƙantar Yaro indai yana da wannan sunan, to tabbas yana da ƙima a idon Nasir. Babban abunda ya daɗa ja masa baƙin jini shine, yadda yakewa al'umma hidima, yake facaka da dukiyarsa gurin hidimtawa al'umma da addini, wanda sauran abikan kasuwancinsa basa yi, hakan yasa ya ƙara samun masoya ta kowane fanni. A cikin hirar da'ake dashine ya bayyanawa 'yan jarida cewar, shifa ainihin kuɗin daya fara kasuwanci dasu bashi aka bashi, kuma be biya bashin ba, ya sanar dasu cewa wanda ya bashi bashin ya gaya masa me kuɗin yana nam zuwa ya karɓi wannan kuɗi, dan haka gundarin dukiyar da yake juyawa yana samun riba akwai me ita, kuma duk sanda lokaci yayi indai me dukiyar ya bayyana to tabbas shi keda kaso bakwai cikin goma na dukiyar daya mallaka, ya ƙara da cewa a hirar nan da suke, tuni ya ware wannan dukiyar guri guda, ko bayan ransa duk wanda yasa hannu akan wasiyyar daya bari da takaddun dukiyar daya ware, to tabbas wannan dukiya tasace, ko waye yasa hannu akai tasa ce " Wannan hira da Daula yayi ba ƙaramin cecekuce ta janyo ba a cikin al'umma, wasu suna jinjinawa amanarsa, wasu suna ganin wautarsa suna inama zasuga inda tajaddun suke su saka hannu su karɓe kuɗaɗen, wanda suke da hannun jari a kamfanunnukansa suka shiga zullumi, akwai dukiyarsu a cikin kuɗaɗen Daula, kuma muddin ya janye daga kasuwancin to tabbas zasu talauce, dan haka suka shiga tunanin nemawa kansu mafita. Katsam akayiwa Huda scanning, aka tabattaf da cewa tana ɗauke da ɗa namijine a cikin ta, ana gayawa Daula ya zube yayi sujjadar godiya ga Allah, bakinsa yaƙi rufuwa, farincikinsa yakasa ɓuya. Sunyi murna sosai da wannan kyauta da Allah yayi musu, Kasancewar Daula ya daɗe yana kuma neman haihuwa yasa shi, ya shiga gayawa abokansa ai Madam ta samu rabo, kuma anyi scanning ance zata haifi namiji, zatonsa duk masuyi masa dariyar nan masoyansa ne, zasu taya shi farinciki, ashe abunda be sani ba ta ciki na cikine kawai, dan gaba ɗaya ba ƙaunarsa suke ba, dukda da yawa su, Daula shine silar Arziƙinsu. Watarana suna zaune suna hira da abokansa, suke bugun cikinsa Haruna yace  "Yanzu kai Daula, gashi ga abunda kace akan cewa akwai me kaso bakwai na dukiyarka, yanzu idan ba'a samu wanda yasa hannun bafa? Sannan meyasa me dukiyar baze zo ya karɓa ba" Daula yace  "me kuɗin, yayana ne da matarsa da Allah yayi musu rasuwa, kuma shi ya gayamin akwai wanda ze karɓi wannan kuɗin, dan haka nayi a rubuce ko bayan raina idan mesu bezoba, a rabawa al'umma su, ko kuma a gina abunda al'umma zasu amfana" Haruna yace "duk wannan uwar dukiyar, kace a rabar?" Nasir yace "eh mana, haka shine yakamata ai, har wasiyya nayi yadda na kasafta dukiyar" "to yanzu a ina suke, balle mesu ɗin yasa hannu ya karɓa?" Daula yace "idan har me dukiyar nan yazo, no matter how hard seya karɓi abarsa, babu wanda yasan inda suke, se Allah seni, nayi bayanin komai a video wasiyyar dana bari, na danƙashi a hannun 'yata Widad" Munir yace  "Widad kuma? Wannan jaririyar yarinyar?" Daula yai murmushi yace  "wannan Yarinyar, yadda kanta yake lissafi naka bayayi, a hakan tayi min alƙawarin zata adana wasiyyata kamar yadda zata adana Ranta daza ta ganshi" Haka sukayi ta bugun cikin Daula, wani abun ya gaya musu, wani abun ya waske shi duk a ganinsa an zama ɗaya, har yake labarta musu ai matarsa namiji zata haifa. Cikin Huda yana da watanni bakwai, ta dage tace ita seta koma Nigeria a can take son ta haihu, Daula ya kaɗa ya raya tace ita Nigeria takeson ta koma, yanzu zaman nan ya isheta. Haka Daula ya tattara ya dawo Nigeria, dama akwai katafaren gidansa me girman gaske, inda suke sauka idan sunzo, akwai ma'aikata a gidan saboda girmansa, dukda babu kowa a gidan akwai megadin gidan Bala, Sojane shiyake kula da shuke shuke da sauran al'amauran gidan idan basa nan, gidane har gida katafaren gaske me matuƙar girma da yalwa. Suka koma Nigeria suka sauka a wannan gidan, lokacin da cikin Huda ya shiga watanni takwas tafiya ta kama Nasir ta gaggawa, Huda haka nan taji bata son ya tafi, ta dinga masa Shagwaɓa harda kuka ita karya tafi. Widad ganin Mamanta na kuka, hadda shagwaɓa yasa tace  "da nice da yanzu Ammi kin koreni kince na fiye takura, shine kikewa Daddy kuka ko? Daddy ka ƙyale Ammi shagwaɓabiya" Nasir yayi murmushi yace "my princess gayamata dai, kalli tana kuka kaman baby" Widad suka haɗu ita da Babanta suka dinga tsokanar Huda suna dariya, akwai kyakkyawar fahimta da ƙaunar juna a tsakaninsu, haka yaita rarrashin Huda, harta haƙura ta ƙyaleshi ya tafi, ita dama tsoromta bata son ya tafi daga ita se Widad a gida ga tsohon ciki. Kwana biyu da tafiyar Daula, cikin dare sun tsaka da bacci, Widad ta tashi ta shiga kiran "Ammi, Ammi ki tashi" Cikin bacci Ammin Widad ta farka tace  "lovely lafiya kuwa?" "Ammi yunwa nakeji" "Widad yunwa cikin daren nan kuma?" Widad ta jinjina mata kai, Huda tace  "Widad kin fiye rigima, ko tausayin halin da nake ciki bakya yi, tashi muje in haɗa miki" Haka ta kama hannun Widad zuwa kitchen, ta haɗa mata Frisco ta samata madara ta bata, Widad ta zauna tana sha, yayin da Huda keta hamma saboda bacci. Widad ta kalli Amminta tace  "Ammina kije ki kwanta, idan na gama nima zanzo in kwanta" Huda tace "kin tabatta bazaki min fitina ba?" Widad tace "yes Ammi, i promise you i won't do anything bad" Huda tace "Yawwa my lovely friend, barakallahu fik" . Ta sunkuyo ta sumbaci goshin Widad, itama ta sumbaci goshin Amminta, har taje bakin ƙofar kitchen ɗin, Huda ta juyo ta kalli Widad ta ɗaga mata hannu, itama ta ɗaga mata, Huda tace  "Babyna, ki zama me riƙon Alƙawari, sannan karki zama me manta alkhairi" Widad tayi murmushi, ta jinjinawa Amminta kai. Tafiyar Ammin ɗaki ba daɗewa, Widad taji kamar ana taɓa gate ɗin gidansu, ga Ƙaton karensu yanata zabga haushi, a zatonta ko Daddynta ne ya dawo a daren nan, dan haka ta taka kujera, ta hau kan drower ɗin kitchen, ta leƙa Window, da yake gurin a saman bene ne, hakan ya bata damar ganin abunda ke faruwa a ƙasa harabar gidan. Ƙaton police dog ɗin nasu yake ta haushi yana zagaye, a harabar gidan, Bala soja ya kama karen ya maida shi ɗakinsa ya rufe, sannan yaje ya zare sakatar dake gate ɗin. Wasu mutane ne suka shigo cikin gidan, sun kai su biyar fuskarsu ɗauke da mask baƙi, baka gane fuskokin su, ga manyan bindugu a hannunsu. Tunani Widad tayi, a irin fina finan da take kallo, idan akaga mutane da irin wannan shigar musamman cikin dare, to they are dangerous, tana nan akan drower taga Bala yayi musu jagora har ƙofar da zata sadaka da cikin gidan. Ya buɗe musu ƙofar suka shiga, Widad ta sakko daga kan drower a hankali, ta leƙa ta ɗaya window, tana gani suka shigo babban falon ƙasan benen, suka shiga haurowa saman benen, komawa tayi ta ɓuya suka buɗe ƙofar ɗakin da Huda take ciki suka shiga. Suna shiga Widad ta fito daga kitchen ɗin, tana tafiya a hankali tazo ta window dake corridor ta tsaya ta Leƙa window a hankali, cikin sanɗa take komai. Tana gani ɗaya ya kunna fitila, haske ya gauraye ɗakin, Huda ta buɗe ido tana salati, nan da nan ɗayan ya janyo pillow ya danneta, ta dinga mutsu mutsu tana fizge fizge, Kasancewar ƙaramar rigar bacci ce a jikinta, kana iya ganin yadda cikin dake jikinta ya dunƙule guri ɗaya. Widad tana tsaye tana kallonsu, ta toshe bakinta da hannunta, tana ta gumi jikinta yana tsuma, ƙafafunta se rawa suke, tun Huda na iya mutsu mutsu da ƙoƙarin ƙwacewa, ɗaya ya zaga ya hau kan gadon ya riƙe hannayenta, tun tana motsa ƙafafunta, har rai yayi halinsa ta dena motsi. Widad na zuwa nan kawai ta rirriƙe Yusuf ta fashe da wani irin kuka me matuƙar ban tausayi, ba Widad ba shi kansa Yusuf seda jikinsa yai sanyi, labarin ya ratsashi sosai, tun daga rayuwar iyayenta zuwa kanta a cikin ƙaddara take, rungumeta Yusuf yayi yana shafa bayanta da sigar rarrashi, amma ya kasa magana sam se Ajiyar zuciya. Ganin Widad bata da niyyar sassauta kukan da take yasa Yusuf ya fara magana, cike da rauni da tausayawa yace  "Am very sorry dear, ubangiji Allah jiƙansu gaba ɗaya, take heart Widad, Allah ya jiƙan Ammi" "Yoseef, my Mum was killed before my eyes, a gaban idona aka kashemin ita, bayan an san bani da gata se Allah se ita da Daddy na, amma without fear, she was killed mercilessly, ga tsohon ciki, how can I forget this in my life, how?" Jikinta har tsuma yake saboda kukan da take, ga wani irin numfashi da take jerawa, Yusuf yace " tabbas an cutar da ahlinku, cutarwa mafi muni Widad, amma kiyi haƙuri ki miƙa lamarinki ga Allah, dama Allah yayi a lokacin mahaifiyarki zata rasu, bawa baya wuce lokacinsa" Widad tace "na sani, da Ammi mutuwar Allah tayi, bazan cigaba da damuwa tsawon wannan lokacin ba, nasan lokacinta ne yayi, amma aka kasheta da tsohon ciki laifin meta yi? Me tayi musu zasu kashemin ita Yoseef?" ta maganar muryarta na sarƙewa. Seda Yusuf ya zubda hawayen tausayin Widad, ya shiga share mata hawayenta yana,   " kiyi haƙuri, mucigaba da yi musu Addu'a, kidena wannan kukan, Allah yayi mata rahama, take heart " Shaƙuwa Widad ta dingayi, numfashinta yana sama yana ƙasa, gigicewa Yusuf yayi ya shiga kiran sunanta, tana jinsa amma bata iya magana  hannunsa ya ɗora akan ƙirjinta  ya shiga karanta mata duk abunda yazo bakinsa, na ayoyin alƙur'ani. A hankali ta dinga sauke ajiyar zuciya, ta dena shaƙuwar, Yusuf yace mata sannu, jinjina masa kai kawai tayi. Yace "dare yayi sosai yanzu, ma cigaba wani lokacin, ki kwanta ki huta" Ta jinjina masa kai, ya gyara mata pillow ya kwantar da ita ze miƙe, ta riƙe hannunsa, ya kalleta yace  "ya dai?" "Akwai hadari a garin, akwai yuwuwar ayi ruwan sama, ka kwanta anan kawai". Yusuf yace "to ai ba'a fara ruwan ba" "Eh bakomai ka kwanta, i need a shoulder to cry on, ka kwana a kusa dani" Har yanzun dai kuka Widad take yi, ya kwanta ya ɗora kanta a Ƙirjinsa, ya dinga sauke ajiyar zuciya, tana cigaba da zubar da hawaye. Yusuf yaja wata doguwar ajiyar zuciya yace  "Gimbiya kina son ki karyamin zuciya ne in cigaba da kukan nima?" Girgiza masa kai tayi, yace  "kinga har shaƙuwa kikeyi, kin kusa shiɗewa ɗazu saboda kuka, kiyi haƙuri dan Allah ki dena haka ya isa, yi shiru muyi musu addu'a" Widad tace  "karka damu da shiɗewar da nayi, bayan ciwon hauka inada ciwon zuciya kamar Daddy na, dan haka ba wani abu bane, nasan idan kwana na ya ƙare zanbi Ammi na ne" "Widad bakya tausayina ko? Baki damu da ki dinga gayamin zaki mutu ki barni ba ko? Babu ruwanki da halin da zan shiga idan kika mutu kika barni bako?" Ɗago kanta tayi tana kallon Yusuf, dukda a cikin duhu suke amma ta kai hannunta fuskarsa taji ɗumin hawaye a fuskarsa. Murmushi tayi tace " Ragon maza kawai, ɗan sanda yana kuka, se kace ba jarumi ba, ni meyasa ka damu dani haka baka son in mutu in barka? Dukda tarin rashin kirki na a gareka" Tai maganar cike da son bagarar da wancan zancen da suke. Mirginata yayi ya koma kanta, a hankali ya kai fuskarsa kunnenta yana mata numfashi a kunne sannan yace "saboda ni bana ganin laifinki, kuma ni bana riƙo ina sonki sosai, kuma ba kince ni ɗan uwanki bane?, kuma seki tafi ki bar ɗanuwa haka akeyi? Bakya tunanin halin da ɗan uwa ze shiga? Anya kina 'yan uwantakar dani kuwa?" Murmushi tayi tace  "wani lokacin inayi, wani lokacin kuma ba nayi" Tai maganar tana dariya, ta rungume Yusuf tace  "dare yayi sosai, muyi shiru haka mu kwanta" Yusuf ya sake gyara kwanciyarsa a jikinta, yayi shiru wani irin matsanancin tausayin ta yana ratsa ransa, daga ita har mahaifinta kowannen su yaga ƙaddarar rayuwa daban daban. A haka har bacci yayi awon gaba da dukkaninsu. Alhaji Musa yana zaune yana karyawa da safe a falonsa, wayarsa ta fara ringing, ɗaukar wayarsa yayi ya tafi bedroom, ya rufe ɗakin ya saka key sannan ya ɗaga wayar. "Ka kasa kunne yau, zakaji matakin dana ɗauka akan Yaron nan, dan haka ka kwantar da hankalinka babu abunda ze faru" Ajiyar zuciya Musa yayi yace  "Alhamdilillah, Insha Allah zan saurara inji wani irin mataki ka ɗauka akan lamarin, amma to batun Daula fa? Har yanzu fa babu wani labari a game da shi, ya muke ciki a wannan ɓangaren?" "Karka damu, shima ina nan ina tunanin mafita, sannan wannan Likitan shima masa a kau dashi, dan amfaninsa ya ƙare" Musa yace "doctor Sufyan kake nufi wai?" Bukar yace "Eh shi, na bada umarnin da ya dace akansa shima, dan haka kowa ya kwantar da hankalinsa" Alhaji Musa yace  "to shikenan, babu laifi godiya muke" Daga nan ya kashe wayarsa, yana jin wani sanyi a ransa, dan da ba ƙaramin ɗurar ruwa cikinsa yayi ba. Nura direba ne a cikin lambun Widad yana ta gyarawa, yana cire ciyayin ciki yana gyara flowers ɗin tare da sharewa, yace  "Allah sarki, lambun nan kansa yayi babban rashi, da meshi tana nan babu yadda za'ayi a barshi a haka, kai rayuwa ba tabbas" Kukan mage ya dingaji a tsakanin flowers, har ya tsorata ze ruga da gudu, sekuma yayi ta maza ya dake, leƙawa ya shigayi a hankali, yana duba ciyayin. Roux ce magen Widad a kwance, gaba ɗaya tayi wani iri abun tsoro, da ƙatuwace magen nan, gata da kyau gwanin ban sha'awa da yake bata Nigeria bace, amma yanzu kamar an jiƙata a ruwan zafi, gaba ɗaya gashin jikinta yayi wani iri, gashi duk ya zube ta koma wata iri abun tsoro. Nura yasa hannu ya ɗakkota, ya nufi bakin gate da ita, yana zuwa ya ajiye ta, Isa ya kalleshi ya yamutsa fuska yace "meye wannan haka?" Nura yace  "Magem 'yar masu gidace" Murtalah yace  "itace ta koma haka?" Nura yace "kaima dai ka faɗa, ai maraici yakama magen nan, abun tausayi" Isa yace  "wannan matsiyatan basu kula da mutum bama balle wata mage, duk halin nan da ake ciki na rashin me gidan nan da' yarsa ko a jikin su, sabgarsu kawai suke har gara ma Anwar ɗin nan, shikam akwai kirki sosai" Nura yace  "bari Isa, Allah abun tsoro duniya abun tsoro, kalli da yadda gidan nan kullum cikin shige da ficen mutane ake, amma yanzu tsit kake ji" Murtalah yace  "kai dai bari, bari in jarraba bawa magem nan Abinci ko zata ci" Isa yace "kaga fa baka da abunda zaka bata, dan Wani Abincin da fake ci kai kanka baka taɓa ciba, ka ƙyaleta kawai ta ƙarasa ta hutawa rayuwarta" Murtalah yace "A'a ba'ayi haka ba, Yanzu a dalilin taimakon dabbar nan se kaga Allah nima yaji ƙaina, kuma dame ita tana nan kasan bata yarda abar wani da yunwa a gidan nan ba, dan haka zan jarraba bata Abinci ko zata ci" Isa yace "ai se kai tayi ɗan wahala, ga hanyoyin neman lada nan ba adadi, amma ka tsaya wahalar da kanka akan abar data kusa mutuwa" Murtalah be kuma kula shi ba, yaje ya  siyo biscuit katako, da madara 'yar talatin yazo ya haɗa ya bata, ai nan da nan magen nam ta lamushe, saboda azabar Yunwa da take ji, abunka da dabba da sabo, tana jin ƙwarin jikinta ta koma ɗakin Widad, tana kuka ta hau kan gadonta ta sauka, ta fito falonta zuwa babban falo. Ramlah tace "wai dama wannan shegiyar halittar tana raye bata mutu ba?" Amal tace  "ni kaina na zata ta mutu fa" Ramlah tace "aikuwa ƙarasata zanyi, sena kasheta" Amal tace  "ke Ramlah, ina ruwanki da ita? Me tayi miki?" "ke nifa duk wani abu daya shafi waccan banzar ba sonsa nake ba, tunda Allah yasa ta bar gidan nan mukayi 'yanci, muke warwasawa son ranmu, babu tsawa balle hantara, shiyasa bana son ganin duk wani abu daya shafeta balle raina ya ɓaci" Amal tace "dukda haka dai karki huce akan magen nan danni tausayinta nake ji, itama magen wata kinibabbiya kamar uwarɗakinta, bata zuwa ko ina se tare da ita, ai gashi yanzu tana wahala" Ramlah tace  "tunda uwaɗakin nata bata nan, ai itama seta ƙara mai" Da ƙyar Yusuf ya iya tashi sallar Asuba saboda daɗewar da suka yi basu yi bacci ba jiya, hadari yana ta cida, da akama ruwan sama za'ayi. Ya tashi Widad sannan yaje yayi alwala ya fita salla, sedai harya dawo bata tashi ba, hannunsa yaje ya wanke yazo yana shafa mata ruwan a fuskarta. A hankali tayi miƙa, ta koma ta kuma lumshe idonta, ɗagota yayi daga kwanciyar gaba ɗaya ya ɗan ƙura mata ido sannan yace  "wai wani darem za'a kuma yi miki ne?" Kasa buɗe idon tayi saboda baccin da take ji, hannayenta ya shiga matsawa yace "kalli gari ya wayefa, buɗe idonki ki gani" . A hankali ta buɗe idonta, tabbas gari ya fara hasks duhun Asuba ya yaye, ta kalle shi tace  "meyasa baka tasheni ba"? "na tasheki baki tashi bane" a hankali ta zauna sosai, sannan ta miƙe taje tayi alwala tazo ta tada salla, Yusuf yana gefe yana cigaba da lazumi, ya kwaɗaitu da son jin ƙarshen labarin Widad, sedai yasan halinta da rikicin tsiya, idan bata ga dama ba haka zatai ta ja masa rai ba zata gaya masa ba, idan ya takura ta se yaji kuma suyi faɗa. Data idar da sallar ta fara lazimi ta kife a gurin, yana kallonta da alama bacci ne sosai a kanta, ya tashi a hankali ya ɗagata ya maida ita kan katifar, still yana jin tausayinta yana ratsa ruhinsa da ganganr jikinsa. Ya kwanta a bayanta cike da fargabar kar ta tashi ta kama masifa, tunda ba ita tace ya kwanta ba, sedai ta ɗanyi juyi taji shi a bayanta, a hankali ta juyo tana fuskantarsa, ba tare da ta buɗe idonta ba, ta zura hannunta ta rungumeshi, ta kwantar da kanta a jikinsa, a haka bacci ya sake yin awon gaba dasu. Har shaɗaya da rabi na Safe basu farka ba, Hari sunata aikace aikacen su a tsakar gida, ta kalli Gwaggo tace  "Yaya, har yanzu fa Wudas basu fito ba, lafiya kuwa?" Gwaggo tace "lafiya ƙalau insha Allah, ai da Asuba shi yaja salla, dan haka lafiya ƙalau" "Yaya sha ɗaya da rabi fa" Hansai tace  "A'a haba Yaya Hari, abu na mata da miji ina ruwanki? Ba suyi niyyar fitowa yanzu bane" Hanne ji tayi kamar ta faɗi ƙasa dan haushi da takaici. Widad ce ta fara farkawa, ta buɗe idonta taga yadda rana tayi, a hankali ta bar jikin Yusuf ta tashi zaune, garin ta tashin ne shima ya farka, ya kalli garin yadda rana ta buɗe, yace  "Subhanallah, rana tayi ma" Widad tace  "Aikam dai, kasan bamuyi bacci da wuri ba, shiyasa" Yusuf yace "hakane, gashi ko breakfast bakiyi ba, bari in tashi idan akwai Abinci a gurin Gwaggo shikenan, in babu se inzo in dafa" Widad tace "karka damu ni bana jin Yunwa, wanka nake son inyi amma ina son Ka temakamin in wanke kaina, gani nake kamar baha fita yana damuna sosai saboda babu gyara" Yusuf yace "to aini ban san yadda ake yi ba, ban san yadda ake wanke gashi ba" Widad ta kalleshi tace  "eh amma ka iya taɓawa ai" Yusuf yayi murmushi yace  "wannan ai me sauƙi ne, dan bana gajiya da taɓawa, amma wankewa ni ban san yadda ake yi ba" "Yau zaka koya kuwa, zan karɓo ruwa a gurin Gwaggo seka tayani mu wanke" Yusuf yace "wait, waima a ina zamu wanke kan? Ba dai banɗaki ba" "Koma a inane" ta bashi amsa Yusuf yace "kawai se aga mun shiga banɗaki tare? No banda wannan, sannan da kunya aga na taƙarƙare ina tayaki wankin kai a tsakar gida, ki bari seda daddare, muje toilet mu wanke gashin, yadda ba wanda ze ganmu" Hararar Yusuf tayi tace  "ni yanzu nake so, idan aka wanke kafin dare ya sha iska, in aka wanke daddarw na kwanta ai wari zeyi tunda babu shampoo" Yusuf yace "ni ya zanyi, kawai aga mun shiga banɗaki tare? Da kunya fa" "Au wai nan kunya kake ji, amma ai baka jin kunyata tunda.. " tunda me? " " ban sani ba" Murmushi yayi yace "Allah ya barni da abar sona, ina sonki Habibty na, kura kike ga tsoro ga ban tsoro" Suleiman ne tafe yana driving a motarsa, yana sauraren radio yana jiran ƙarfe huɗu ta cika ya saurari labaran yamma, kanin labaran ne suka ɗauki hankalinsa, hakan yasa shi maida hankali don jin cikakkun labaran. Labarin farko da aka sanarne ya ɗau hankalinsa, ya kaɗashi matuƙa ya tayar masa da hankali, be gama tsinkewa da lamarin ba, seda ya ƙarasa traffic ta tsaida hannun da yake, wani yaro yazo ya tsaya a window motarsa yana masa tallan jarida, shafin farko ya kalla yaji gabansa yayi mummunar faɗuwa. LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 MASU FITARMIN DA LITTAFI KUMA, IN DAI DAI KUKE KUN SANI IDAN AKASIN HAKANE MA KUN SANI 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 70_71 Da rawar jiki Suleiman ya sayi jaridar nan yayi parking a gefen titi, hoton Yusuf ne a bangon jaridar an rubuta wanted, ya buɗe cikin jaridar ya shiga duba shafin da labarin yake, wai 'yan sanda sun fitar da sakamakon binciken da suka yi akan ɓatan 'yar gidan Daula, bincike ya tabattar musu da direban Widad Nasir Daula wanda aka sani da Yusuf, shine ya sace Widad yayi garkuwa da ita, ba sace su akayi tare ba, dan haka jam'ian tsaro suna nan suna binciken inda suke, sannan duk wanda ya gano inda suke ya faɗa akwai kyauta me tsoka. Gaba ɗaya jikin Sulaiman yayi sanyi, akanme za'a fitar da wannan sakamakon binciken? Meye dalili? Cikin hanzari ya juya sitiyarin motarsa zuwa wani gurin, tuƙin kawai yake amma hankalinsa sam baya kan abunda yake yi, Allah ne ya kaishi inda yake son zuwa. Harabar headquarter 'yan sanda yaje yayi parking ɗin motarsa, ya fita da sauri daga cikin motar, yana shiga harabar gurin ƙananan' yan sanda sunata sara masa, cikin gaggawa ya nufi wani office, ya buɗe ya shiga suka gaisa da ma mallakin Office ɗin, Suleiman ya zauna ya miƙa masa jaridar hannunsa sannan yace  "SP waye ya fitar da sakamakon wannan binciken haka? Har aka sanar da 'yan jarida?" SP yace "kamar yaya kenan? Sakamakon binciken da akayi kenan, kuma aka bada umarni mu sanar" Suleiman yace  "haba SP, wannan yaron fa jami' inmu ne, ta yaya kake tunanin ze iya aikata wannan mummunan aikin haka, sam ba haka abun ya faru ba, ta yaya za'ace Yusuf ne yayi garkuwa da 'yar gidan Daula? Ta yaya?" "Kaga karka zo ka ɗagamin hankali mana, nima umarni aka bani inyi wannan Sanarwar kuma nayi, meye nawa a ciki?" "An gabatar maka da sakamakon binciken da akayi kafin kayi wannan Sanarwar, wannan fa tamkar ɓatawa hukumar' yan sanda sunane, ta yaya wasu tsirarin mutane zasu sa ku saɓa dokar aikinmu saboda biyan buƙatarsu?" SP ya kalli Suleiman yace  "ya akayi kasan wasu tsirarin mutane ne suka sa ayi hakan?" Nan da nan Suleiman ya dawo hayyacinsa ya daidaita nutsuwarsa yace  "to koma dai a cikinmu ne mukayi hakan ai munsan mun saɓa dokar aiki, yaron nan abokin aikinmu ne, jajirtaccen ma'aikaci ne mara ƙyuya, ga gaskiya a harkar aikinsa, ya dace ayi masa haka, zan iya rantse maka ko a wasa Yusuf baze aikata haka ba" SP yace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, kai kake zaune dashi kasan halinsa, ni babu ruwana sakamakon da aka gabatarmin shi zan bayyanawa al'umma, dan haka in baka da abunyi zaka iya bani guri, ina da baƙi" Cike da baƙin ciki da ɓacin rai, Suleiman ya baro office ɗin nan, gaba ɗaya tausayin Yusuf da mamaki suka cika zuciyarsa, tabbas idan akayiwa Yusuf haka an zalunce shi, kuma an zubar da kimar aikin ɗan sanda a idon duniya. Saleh ne yayi jifa da jaridar hannunsa yace  "Impossible, Alhaji Musa anya kanaso mu gama da duniya lafiya kuwa? Ta yaya za'ace anyi masa wannan ƙazafin haka? Abun yayi yawa, yakamata mudinga yi muna jin tsoron Allah" Alhaji Musa yace  "kai dakata! Meyasa ba zamu nemawa kanmu mafita ba? Ina ruwanmu da koma wani hali ze shiga, ai ba ƙarya akayi masa ba, in ba hakaba meyasa da suka gudu basu dawo ba, waye yasan inda suke? Dan haka shiya saceta yayi garkuwa da ita, kuma ya koma yayi garkuwa da mahaifinta, ai mafita muke nemawa kanmu, ɗan sanda nefa, yanzu idan ya dawo asirinmu ne ze tonu, dan haka gara da mukayi masa haka, idan kuma baka cikinmu ne zaka iya ƙarawa gaba" Saleh yayi shiru cike da takaici da baƙin ciki, ya rasa mema yakamata yayi, idan aka yi haka an cutar da rayuwar Yusuf ba kaɗan ba, rasa abunyi yayi kawai ya juya ya fice a matuƙar fusace. Hari tana ta fifitar Wuta, ta kuma kallon ƙofar ɗakinsu Widad tace  "taɓ amma wannan abu yayi yawa haka, ai kome suke yaci ace sun fito haka, sha biyun rana fa wane irin abune haka?" Banza Gwaggo tayi da ita, yayin da Hansai tace  "ke kuma sa idonki yayi yawa, ina ruwanki da koma me suke yi ina ruwanki? Kedai bakya rasa abun faɗa shiyasa duk tabi ta raina ki" "to naga abun magana bazan magana ba? Ai abun da damu ace garin Allah ya waye, har wannan lokaci suna ƙule a ɗaka, idan wani abun ya samesu fa" Widad ce ta fito hannunta ɗauke da bokiti, ta ƙaraso inda Gwaggo take ta gaisheta, tace  "A temakamin da ruwa, ina so da ɗan yawa zan wanke gashina ne" Gwaggo ta karɓi bokitin, taje rumfar da suke girki ta Ɗebo mata ruwan, Yusuf a kunyace ya fito suka gaisa da mutanen gidan, yaje ya Ɗebo ruwa a rijiya ya sirka ya kai banɗaki. Widad ta ɗakko abun wanka, tazo ta shige banɗaki, Yusuf ya rasa yadda zeyi ya bita toilet ɗin nan saboda kunya, leƙowa tayi tace  "Yoseef ka shigo mana, kose ruwan yayi sanyi?" Hari ta tsaya tana kallon ikon Allah, haka Yusuf ya shiga banɗakin nan, ta cire hijjabin jikinta daga ita se towel, ta cire ribbon ɗinta, ta zauna akan kujera, Nan Yusuf ya shiga tayata wanke gashin nan me matuƙar tsawo da yawa. Hansai kam burgeta sukayi, yayin da Hari ta taɓe baki tace  "ni tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin baɗalar da nake gani a gurin bayin Allah nan ba" Hansai tace "taɓ wallahi nikam birgeni sukeyi, yanzu kai anan ka isa miji ya wani ta yaka wanke kai, yadda yake ɗawainiya da ita ba ƙaramin birgeni yake ba" Hari tace "mhmm, ai ko sharar ɗaki baki isa miji anan ya tayaki ba, balle wani wanke kai, ai maza suna birni, mu nan se godiyar Allah kawai" Hansai tace  "me kike nufi to?" "Ni ba abunda nake nufi, karki ƙullamin sharri" Haka suka cigaba da maganganunsu. Yusuf dai bega wani datti da kan Widad yayi ba, ta dai damune kawai ta wanke kan nata, tunda ta saba wanke shi akai akai. Seda ta gama ya bata guri tayi wanka, duk ya jiƙa kayansa da ruwa, Widad tayi wankanta ta kammala sannan ta fito, Towel ɗin nan kawai ta ɗauro ta fito, gashin nan ya baje a bayanta se ɗigar da ruwa yake. Ai gaba ɗaya sukabi Widad da kallo, tubarkallah Allah yayi mata kyau da halitta me ɗaukar hankali, ta kama ƙasan gashinta tana yarfewa, ga towel ɗin iyakacinsa gwiwarta, fatarta se sheƙi take. Hanne tabi Widad da kallo, tana tunanin me zata yi mata ta huce wannan baƙincikin, Widad kamar da gayya take juya jikinta har ta shiga ɗakinsu. Hindu ta lura da irin kallon da Hanne ke yiwa Widad, dan haka tace  "Masha Allah, Allah me halitta duk mutumin da yake da mace kamar Amarya, wallahi babu me kama da bayan tukunyar daze kalla balle yayi sha" War Aurenta, kamar ita tayi kanta masha Allah " Hanne ta kalli Hindu, taja tsaki tayi tafiyar ta abunta. Yusuf ya kalli Widad yace  " Masoyiyya ba dai a haka kika fito ba? " " A haka na fito menene? Ai dai naga ba maza" "Anya kin san irin kyawun halittar da Allah yayi miki, koda ba maza baki abun gudu ne, dan Allah karki kuma fita a haka" "Kaga nifa na fara jin yunwa" Yusuf yace "maganar tawa ce bata da amfani ko? Shine kike sharewa" Shiru tayi masa ta nemi guri tayi zamanta. Hindu tayi sallama ƙofar ɗakinsu, ta kawo musu Abinci, Yusuf ne yaje ya karɓo ya dawo ya zauna, Widad bata da niyyar saka kaya, a haka take zaune abunta, Yusuf kam se ƙureta yake da ido, gaba ɗaya ya rasa sukuni har suka kammala cin Abincin idonsa a kanta. Bayan sun gama yace "yau kuma baza'a sa kaya bane?" "zan saka ban shafa mai bane" Yace "Kawo in shafa miki" Ɗakko zaitun tayi ta miƙa masa, ta koma ta zauna tana cin jiƙaƙiyar aya da Hindu ta koya mata ci. Yana shafa mata man yanajin fatarta kamar ze ji mata rauni idan beyi a hankali ba, Yusuf yace  "me kike cine haka?" Tace  "Hindu ce ta bani, ina son wannan abubuwan da Aya, da wata baƙar aba mulmulmulalliya, da yama sunanta wani abu baƙa cikinsa ja ƙanana me ɗan tsami tsami" Yusuf ya jinjina kai yace  sannu bagwariya, ɗinya da tsamiyar biri dai ko? " Widad tai murmushi tace " what ever dai " Haka ya kammala shafa mata mai, se sheƙi fatar take saboda man zaitun daya shafa mata, yaje ya buɗe Akwatinta ya ɗakko mata kaya, Ya kalleta yace  " bari in samiki " Tura baki tayi tace "A'a bana so" Yusuf yace "Meyasa ba kyaso? Ai tunda na shafa miki mai saura sa kaya kuma" Tace "A'a ni gaskiya bana so, ka ƙyaleni kawai in saka abuna" Kokawa suka shigayi ita da Yusuf, aikuwa ta buɗe baki ta shiga kiran sunan Gwaggo da ƙarfi, ba shiri ya cikata ya  ƙyaleta, dan a wautar Widad ba taƙi azo a tarar dasu a haka ba in be ƙyaleta ba, ta koma gefe tana harararsa hadda murguɗa baki. Yusuf yace "Ni kikewa wannan ihun Masoyiyya?" "An maka ɗin, waye yace kamin abunda zanyi ihun?" Murmushi yayi yace  "Shikenan Allah ya baki haƙuri" Zumɓura masa baki tayi, ba tare da tace komai ba. Labari ya game gari a game da Yusuf, Nurat tana kwance tana kallon labaran dare a TV aka nuno zancen Yusuf, ta kaɗu matuƙa da ganin labarin da gudu ta tafi ɗakin mahaifiyarta tana ƙwala mata kira. "Ke lafiya kike ƙwalamin kira hak?" "Mummy kinga abunda na gani kuwa?" "Ta yaya zanga abunda kika gani? Ina nan kina can" "Mummy an buga fastocin Yusuf, wai he is wanted shine yayi garkuwa da Widad sannan yayi da mahaifinta" Tace  "wai waye Yusuf ne?" Nurat tace "Mummy direban Widad ne fa" Tace "Allah sarki, dama duk abun nan shine ya sacesu aketeta nemansu?" Nurat kamar ta fashe da kuka tace "Mummy, ki gane me nake nufi mana, wannan abun duk shirin su Daddy ne, Daddy ne suke ƙulla wannan abubuwan, Yusuf bashi da laifin komai fa" Da sauri Mahaifiyarta ta riƙota, ta rufe mata baki tana waige waige, a fusace ta kalli Nurat tace  "waike yaushe zakiyi hankali ne? Kina kallo kwanan nan ya kusa halakaki, shine kike wannan maganar, maza ki bari ya jiki idan ya ƙarasaki shikenan" Cire hannun Mahaifiyarta tayi daga bakin ta ta kalle ta tace "haba Mummy, yanzu shikenan mu zuba ido babu wani abu da zamuyi, wallahi Umma Yusuf baze sace Widad ba, ina yaga yadda ze iya sace Daula a gadon Asibiti, shikenan idan baka da kuɗi baka da gata a garin nan?" "to dan ubanki kije kiyi tayi, ina gargaɗinkibakan shiga wannan sabgar tasa, akan ya hana ki fita kawai ya kusa aikaki lahira, amma se sake cusa kanki kike kina bin diddiginsa, ki cigaba karki fasa, inya kasheki ya kashe banza dukda shiya haifeki, kinfi kowa sanin takun saƙar dake tsakaninsa da Daula, kuma kin san alwashin da yayi, ki cigaba da sa kanki a lamuransa, inkin ƙiji ba zaki ƙi gani ba" "Amma Mummy......" A fusace tace "Amma me? Kije kiyi dan ubanki karki fasa, fita ki barmin ɗaki" Jiki a sanyaye ta fito daga ɗakin, tana jin wani irin jiri yana kwasarta, tana fitowa falo taci karo da mahaifinta, yana shirin fita, suka haɗa ido ya ganta kamar wata mara gaskiya, tana tafiya a hankali, ya kalle ta yace "ke lafiya kuwa?" Ba tace masa komai ba, se binsa da tayi da ido. Yace  "jeki ki kiramin mahaifiyar ki" ko kallon inda yake ba tayi ba, ta shige ɗakinta ta kulle ƙofa, ta faɗa kan gadonta ta fashe da kuka. Mamaki ne ya kama Alhaji Musa, ya nufi ɗakin Maman Nurat, yaje ya tarar da ita tana gyara kan mudubinta, ya kalleta yace  "to uwar masifa, hala wani abun kikayiwa yarinyar nan, na ganta a waje na mata magana taƙi kulani" Wata uwar harara maman Nurat tayi masa tace  "masifa harna kaika, daka kusa hallakata saboda tsabar masifarka da son zuciya, niba wani abun nayi mata ba, halayenka ne suke baƙanta mata zuciya" "Halayena kamar yaya?" Tace "Ahh gaba ɗaya ka canza mana, kana treating ɗinta kamar ba kai ka haifeta ba, dole ranta ya dinga ɓaci" A fusace yace  "ƙarya kike munafuka, kece kike zigata, idan ba haka ba ya za'ai in haifi 'ya sannan kikama kawomin ƙabali da ba' adi, babu yadda za'ayi 'yata ta dinga min wannan halin na taurin kai, in bake kike zigata ba" Ta Harare shi tace  "au har kamanta tantama kakeyi akan ko kai ka haifeta? Ai baka da tabbacin kaika haifeta ko ba kai ka haifeta ba" "Malama karki gayamin maganar banza, Nurat' ya tace nina haifeta, kuma ina son abata" Tsaki tayi ta miƙe tace  "ƙaryar banza kawai, ji wata fuffuka kake 'yarka ce, bayan da hannunka ka kusa kasheta" "Muka kusa kasheta dai, waye sila?" Banza tayi masa ta shige banɗakinta, ta rufe ƙofa ta barshi a gurin a tsaye. Juyawa yayi ya fito daga ɗakin, ya kuma kallon ƙofar Nurat, still a rufe take bata buɗe ba, girgiza kai kawai yayi ya fice abunsa. Ita kuwa Nurat tana cikin ɗakin, se rusa uban kuka take, tana jinjina zalunci irin na Mahaifinta, sun haɗa kai sun sace 'yar Daula tare da Yusuf, kuma ya koma sunsa ace shine yayi garkuwa da mahaifinta, tuna tana iya kukan hawaye na zuba, har tayi shiru se ajiyar zuciya da take yi. Da Yamma Widad suna zaune dasu Hindu, kowacce da littafinta tana koya musu karatu, cikin ikon Allah da yake sunsa kansu, suna fahimtar karatun sosai, duk me tambaya ta bashi damar ya tambaye ta, dukda idan tare da su Indo take koyawa Hindu karatu bata wani sakar musu fuska, amma a hakan girmamata sukeyi sosai, saboda bata hantararsu sam, bayan sun kammala karatun ne kuma ta shiga yi musu bayani akan tsafta da mahimmancinta, ta shiga ɗakinta ta ɗakko musu pad a cikin wadda Yusuf ya siyo mata, ta bawa kowa ɗaya, tayi musu bayanin yadda ake amfani da ita, da kuma yadda zasu dinga kula da kansu lokacin al'ada, kunya suka dingaji suna wani sinne kai, hakan seda ya kusa bawa Widad dariya, dan sam ba taga abun jin kunya a bayanin nata ba, suka karɓa suka dinga yi mata godiya, suna nan zaune suna bitar karatun da tayi musu, ita kuma tana ta faman saƙar mafici da Hindu ta koya mata. Yusuf ne yayi Sallama, suka amsa gaba ɗaya suna gaishe shi, hannunsa ɗauke da ledoji, Widad ta kalle shi ta basar tana zumɓura baki, Gwaggo ta harareta, ta gane kallon da Gwaggon take mata, taje ta karɓi kayan hannun Yusuf ne, aikuwa ta tura baki tace  "mhmm Mama kayanfa da nauyi, kuma ze iya kaiwa ɗakin" Dariya ta bawa su Indo, dan yadda take haɗe rai tana koya musu karatu, bazaka ce tana dariya ba, Gwaggo tace  "haba yarinyar kirki, aikin ladane fa duk abunda kika masa yaji daɗi lada zaki samu, ko ba kyason ladan ne?" "Ina so mana" Gwaggo tace  "Yawwa 'yar Albarka, aje a karɓi kayan hannunsa" Widad ta miƙe ta ƙarasa inda Yusuf yake yana kallonta, tana zuwa ta karɓi leda ɗaya tana harararsa, Yusuf yace  "to mara kunya, ni kike harara ko?" "Mama kinga yana cemin mara kunya ko?" Gwaggo tace  "Allah ya huci zuciyarki, tuba muke, kai kuma haka akeyi, ka samu za'a karɓi kayan naka shine za kace mata mara kunya?" Yusuf yayi dariya suka wuce ɗaki, Hari tace  "wallahi Wudas ɗin nan ba ƙaramar taɓararriya bace, gaba ɗayanta gaɓuwa ce" Hansai tace  "Allah yasa ta jiki, ta ƙare miki tatas ai" Me gari kam yana ɗaki yana jin dramarsu, koda ya fito ya kalli Gwaggo yace  "Allah ya saka miki da Alkhairi Hasana, kina ƙoƙari da wannan 'yar taki" Sukayi dariya, ya koma kan ɗaliban Widad yana cewa "masha Allah, kuna gane karatun dai ko?" Hindu tace "muna ganewa sosai" Ya kalli inda Hanne take zaune, yace  "ke ina naki littafin?" Hindu tace  "ai banda ita ake koyamana" Me gari yace "saboda me banda ita? Ke meyasa ba zaki koya ba? ' " Baffa ni bana so" Hanne ta bashi amsa. "ba kyason ƙaniyarki, kije ki samu Ila, ki gaya masa nace idan yaje kasuwa ya taho miki da kayan rubutu kema, idan na kuma zuwa na tarar ana karatu bake senaci mutuncinki" Kallon me gari tayi, ta yaya ma zata fara zama wannan mara mutuncin, 'yar wulaƙancin ta koyar da ita? Shiru tayi masa taƙi kula shi, dan ba zata taɓa zama wannan banzar ta koya mata karatu ba. Gaba ɗaya Anwar a rikice ya shigo babban falon gidan, ya tarar da Amal da Hajiya Halima na shirin fita, yayin da Ramlah ke zaune tana zuba Coca-Cola a kofi tana sha a hankali. "kai lafiya kuwa na gankaba haka? Kamar wani korarre?" "Mummy, kin saurari labarai ne yau? Ko kuma kin kalla?" "A'a ni kasan ba wani shiri nake da radio ba, dama da Daula yana nan ne, shine sarkin labarai da radio saboda kasuwanci" Anwar ya girgiza kai yace  "Mummy, na rasa mema zance miki, yanzun nan naji a labarai, wai hukumar 'yan sanda sun fitar da sakamakon binciken ɓatan Widad" Cikin Hajiya Halima yayi wata ƙara, ta dake tace  "me sukace, ni sam banji labarai ba, am ganta ne?" "Mummy wai ana zargin Yusuf ne yayi garkuwa da ita, ya nemi maƙudan kuɗaɗe da aka hana shi, shine yayi garkuwa da Daddy" Wani sanyi ne ya ratsa Hajiya Halima, dan ba ƙaramin daɗi labarin yayi mata ba, amma ta nuna kaɗuwarta a fili tace  "to yanzu ya ake ciki? An kama shi ne?" "Mummy ba'a kama shi ba, amma ance duk inda aka ganshi ko a mace ko a raye a kamo shi, Amma ni sam banji na yadda da wannan labarin ba Mummy, ya za'ayi Yusuf ya iya aikata haka? Yusuf baze wannan abunba, dukda ban daɗe tare da shiba, amma beyi siffar miyagu ba, ni ban yadda da wannan labarin ba" "to kar Allah yasa ka yadda mana, ubankane shi, ai a rayuwar nan kai dai kaga mutum kawai, yana ta shisshigi a gurin me gidan nan da Widad, ashe macuci ne Azzalumi, ai ba'a gane mugu a fuska tunda kaji an faɗi haka to tabbas ya aikata ne" Anwar ya girgiza kai yace  "gaskiya bazan taɓa yadda ba Mummy, dan yadda akayi aka sace Alhaji Nasir ba ƙaramin me hikima ne ya shirya faruwar hakan ba, kuma shida aka sace su ta yaya harya iya dawowa ya sace mahaifin Widad, nifa ina da shakku akan wannan sakamakon fa" Ramlah ta taɓe baki tace  "ni dama wannan da ganinsa ya saba aikata laifi, kuma zata iya yuwuwa da wasu ya haɗa kai bashi kaɗai yayi ba, tunda ɗansanda ne yasan duk wasu hanyoyi na aikata laifi, kuma ba abun mamaki bane dan yayi garkuwa da ita, tunda yasan da yawa daga sirrikanta, har ATM ɗinta tama bashi, ba inda be sani ba a ɗakinta, duk wani gantali da zata tare suke zuwa, Allah kaɗai yasan iya abunda suke yi kaga kuwa ba abun mamaki bane dan ya sace ta" "ƙarya kikeyi Ramlah!!! Nasani kin sani Wallahi Yusuf baze taɓa iya sace Widad ba, a gaskiya abun nan ya isa haka, haba dan Allah shikenan a dinga rayuwa babu tausayi ba imani, mutum beji ba be gani ba a ɗora masa wannan masifar, kun san hkuncin duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane kuwa? " A fusace Hajiya Halima tace " Ke Amal rufemin baki, ya isheki haka, koma meye hukuncin ina ruwan wani tunda harya iya aikata laifi mummuna irin wannan, yaje ayi masa duk hukuncin daya dace dashi, ina ruwan wani can ta Matse masa" Ƙurawa mahaifiyarta ido tayi na wani ɗan lokaci, kawai tayi ƙwafa ta juya da gudu ta koma ɓangaren su tana kuka. Kame kame Hajiya Halims ta shigayi  "Amm gaskiya Amal yarinyar nan bata da hankali, tunda ta ƙyalla ido akan yaron nan ta fara sonshi shikenan ta susuce, bata taɓa yadda ace ga abunda yayi, yaro sekace iblishi, duk yabi ya saye zuciyar mutane da halin kirki amma yana zagayewa yana cutar da mutane, me siffar munafukai. Wani irin kallo Anwar yabi mahaifiyarsa dashi, kallon data kasan tantance kallon meya ke mata, cam yace "koma meye dai, shi Allah ya haramtawa kansa zalunci sannan hmya haramtashi  a tsakanin mu, dan haka yana kallon komai, Mummy be halatta kidinga saurin yanke hukunci akan abubuwa ba, baki da tabbas akan shiya aikata dagaske ko kuma bashi bane, amma kin zauna kina ta tsine masa kin aibata shi, nan akamin ƙazafi aka ɗaureni kika kasa samun sukuni sam, bakya tunanin shima uwace ta haife shi? Bakya tunanin wani hali take ciki itama a yanzu, kefa uwace Mummy, duk abunda zakiyi you need to have that feeling as a mother, saboda kema kin haifa, kuma kome ka shuka duk daɗewa zeyi tsuro ka girbi abunka da hannunka.... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 MASU FITARMIN DA LITTAFI KUJI TSORON ALLAH, AMANACE TSAKANIN NI DAKU, IDAN KUKA FITAR BAKUMIN ADALCI BA 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 72_73 Saroro Hajiya Halima tayi tana kallon Anwar, har yayi ya gama ya juya ya bar ɗakin. Hajiya Halima tace  "ke me yaron nan yake nufi ne? Naji yana wasu maganganu, kamar jurwaye me kama da wanka" Taɓe baki Ramlah tayi tace  "dan Allah ƙyaleshi Mummy, kin sanshi da sanyin haki da kuma tausayi, shi gaba ɗaya kamar bake kika haife shi ba saboda sakalancinsa, kawai dai surutu ne irin nasa, manta da shi kawai" Hajiya Halima tayi ajiyar zuciya tace  "Saura waccan makirar, bari inje inci ubanta, tana nema ta tonamin Asiri, 'yar banza mara mutunci" Ramlah tace "A' a Mummy karki kuskura, kin san haukan Son Guy ɗin nan da take, kina matsawa ba taƙi ta ɓata komai ba, ki bita a sannu". Tai ƙwafa tace  "yarinya se kace yayi mata Asiri, duk zancen da za'ayi akan yaron nan seta kawo cikas, dani take zancen dan ƙaniyarta" "ki daibi a hankali Mummy, dan ba taƙi ta zama rival ɗinki ba, kin san halin Amal sarai" "Aikuwa da nayi maganinta, ina uwatta ta zama rival ɗina, amma nikam ba ƙaramin daɗi matakin nan yayi min ba, gaskiya mutanen nan basu da dama, kinga tunda akayi wannan sanarwar da an gano shi shikenan, a yanke masa hukunci kowama ya huta" Ramlah tace "hakane, sedai ita uwar gayyar wani mataki zaku ɗauka akanta, dan bana tunanin zata bari a rufe shi, ƙaddara ma an rufesh ta yaya za'a karɓi abun hannunta, dan ba ƙaramar gaddamamiya bace" "Allah masani, su suka san yadda za suyi da ita, nidai fatana ayi abani kasona kawai".. Suka kawashe da dariya kamar wasu ƙawaye. Widad kam suna shiga ɗakin ta ajiye ledar data karɓa a hannunsa, ya zagaya gefenta ya ajiye na hannunsa ya kalleta yace  "Sannu da gida rigimammiya, tunda baki iya cewa miji sannu da zuwa ba, se tura baki kika iya" Kallonsa tayi ba tace komai ba ta sake tura baki, ta nemi guri ta zauna, Yusuf yace "kin gama da ɗaliban naki ne? Naga kin zauna" Tace  "eh mun gama, na basu assignment ma, sannan nifa na bada kyautar pad ɗin nan, na basu suma su dinga amfani da su, zan baka kuɗi ka siyo musu brush da toothpaste, da shaver they need a lot counseling on personal hygiene, naga abubuwan nasu duk se a hankali" Yusuf yayi murmushi yace  "kaga malama ta gari me son ɗalibanta, naji daɗin hakan da kika yi dan kin temake su sosai kam, Allah ya baki lada amma a ina kika samu kuɗi?" Widad tace  "kuɗin sadakina mana, kuma yanzu na iya wannan maficin, Hindu kuma zata koyamin saƙa ksya, Mama tace idan nayi aka siyar na tara kuɗina, nikuma nace mata zomaye zan siya nima in dinga ganinsu" Murmushi kawai Yusuf yayi, Widad akwaita da Wauta wasu lokutan, yace  "Sannu sarkin son dabbobi, gashi nan Na auno mana shinkafa, na siyo mana kifi da gurji da albasa, zaki ci Abinci me daɗi yau, bari inzo in tsince shinkafar kafin magariba tayi" "Yoseef wai me kake tsinta a cikin shinkafar ne?" Yusuf yace "tsakuwa ce da sauran dattin dake ciki" Widad tace  "tsakuwa kuma? A cikin Abincin ake ganin tsakuwa kuma a ci?waye yake zubawa" Yusuf yayi murmushi yace "Eh mana, ke kinma samu me tsakuwar, idan na gaya miki a inda nake samo me tsakuwar zakiyi mamakin nisan gurin, ko kinga gidan nan ana dafa shinkafa dukda a haka wai gidan megarine?" Shiru tayi, tabbas tunda sukazo bata taɓa ganin an dafa shinkafa ba, babban abunda suka fi ci shine, dankali, rogo, kunu, se kayan rama, zogale da sauran kayan gargajiya. Amma abun ya ɗaurewa Widad kai, wai tsakuwa a cikin Abinci, ta kalli Yusuf jiki a saɓule tace  "Sannu da ƙoƙari, Allah ya saka maka da alheri, na tambayi Mama meye faskare, ta gayamin dama ina son in gaya maka, yakamata Kadena wannan aikin, kaga jikinka be saba ba" Yusuf yai murmushi yace "eh jikina yafi saba wa da tuƙa motocinki manya masu AC, sanyi na ratsani ƙamshin turarenki ya hanani sukuni, shauƙin soyayyarki yaita ɗibata, gefe kuma anamin tsiwa ana dakamin tsawa, i miss that moment fa" Dariya ya bata tace "hakama zakace?" Yace "eh mana, sedai duk da haka nauyin ciyar dake a wuyana yake, dan haka zan iya kowane aikine muddin be saɓa dokar addini ba dan in ciyar dake, bani da hujjar da zan tsaya gaban Allah in faɗa na kasa ciyar da ke alhalin inada rai da lafiya, dan haka karki damu kinji beb"  yai maganar yana kashe mata ido ɗaya. Ta ƙara tabattarwa da kanta da lallai Yusuf na daban ne, shi dai akwai sanyin hali, ta tuna labarin da Daddynta yake bata akan Yayansa, hakan yana nuna duk masu sunan haka suke kenan. Zuwa isha'i ya kammala girkin, ya haɗa shinkafa da manja da gishiri da tumatir da albasa, ga gurji ya marmasa musu kifi, ba ƙaramin daɗi Abincin nan yayiwa Widad ba, dan ko ba'a gaya mata ba tasan wannan Abincin da take ci yafi wanda take ci a gida lafiya, duk gayyar iyayi ga ba ƙoshi ake ba, ga kayan cutarwa. Suka gama ci, ya ɗakko rake a leda, yace mata  "ga tsaraba na kawo miki, ko shima baki sanshi ba" Ta kalli raken ta harareshi  tace "sugar cane ɗinne ban sani ba, amma bazan iya sha a haka ba, yayi min gjrma a baki" Yusuf yace "toni ba abun in dinga gutsuro miki ina baki ba, kar in sa yawu kiƙi sha" Hararasa tayi tace  "yawu kuma na nawa, sedai kuma kar a ƙara, ka koyamin ƙazanta kawai" "dama can kin iya a barki, bani na koyamiki ba" "wallahi ban iyaba, dan ban taɓayi ba, kaika fara Yimin" "Nayi miki me?" "Kiss mana" Yusuf yayi dariya sosai, ba ruwanta wasu lokutan sosai yake ganin ƙuruciya da kuma wautar Widad. Yusuf yace "Nima a nan na koya, ai" Tace "Kai dai ka sani" Murmushi yayi, ya samo wuƙa ya dinga sara mata raken ƙanana, tana ɗauka tana sha, seda suka gama shan rakensu tare, sunayi suna hira, Yusuf yace "gaba ɗaya kayan ƙwalamar nan na gargajiya sunfi lafiya da inganta jikin ɗan adam, saɓanin artificial ones ɗin nan, suyi ta haddasa ciwo kala kala" Widad tace "aikam dai suna da daɗi Sosai, dan bana missing chocolates da ice cream yanzu tunda ina cin waɗan nan" Suka cigaba da hira, ba tare da sun yi faɗan da suka saba ba, bayan sun kammala Yusuf ya gyara gurin, yaje yayi wanka sannan itama ta ɗau bokiti taje ta karɓi ruwan wanka, Hari taita mita wai zuwa yanzu yaci ace Widad tana wanka da ruwan sanyi, amma dan gajeren fi'ili kullum se an bata ruwan ɗumi. Widad bata saurareta ba ta tafi wankanta, bayan ta fito ta shiga ɗaki, ta ajiye bokitin ta nufi shimfiɗar ta domin sa kaya, tana hasakawa da fitila taga Yusuf kwance akan katifarta, daga shi se gajeren wando, ya lumshe ido da alama bacci nema ya ɗauke shi, da farko seda ta firgita ganin sankacecen mutum dogo kwance a gurin, daga baya kuma taga Yusuf ne. Ƙafarsa ta haska taga ciwon da yaji yana warkewa a hankali, sannan ta hasak jikinsa, tun daga kansa har fuskarsa zuwa ƙirjinsa da ƙafafunsa, lulkuɓe suje da dogayen gashi. Inda akwatinta suke a gefen Yusuf ne, gashi ya kwanta a gurin, kuma bata son ta tasheshi dan da alama a gajiye yake, ta zarwle hijjabin jikin ta ta shanya saboda a jiƙe yake da ruwan wanka, tazo ta zauna kusa da Yusuf tana son ta ɗakko Akwatin, amma se taga kamar ze tashi, ta ɗan ƙura masa ido, duk ya rame se dogon hancinsa da yake tsaye kyam, ga ƙasumba data fara fito masa wadda da bashi da ita  (kasancwarsa jam'in tsaro, basa tara gemu) . A hankali hannunta yana rawa, ta kai hannunta kan sajensa, wanda yake a kwance kamar na Fulani, a hankali ta dinga shafa gashin ta gangaro har ƙirjinsa inda gashin yafi yawa, ta dinga wasa da gashin a hankali, tana yi tana zancen zuci, yunƙurawa tayi zata ɗauke hannunta taji ya riƙe hannunta, zaro ido tayi a firgice tace "dama idonka biyu?" Gaba ɗaya ya janyo ta jikinsa, ya kwantar da ita akan katifar, yace  "me kike yi ne tun ɗazu? Duk abunda kike ina jinki fa" Haɗe rai tayi tace  "ɗagani Malam, wai baka san kana da nauyi bane?" "Ya za'ayi in sani, kin zauna tun ɗazu se taɓani kike" "jika wai se taɓaka nake, me zan taɓa wannan gashin daka tara duk abun ƙyama ma, abun amai shine ɗin zan taɓa, ni cikani in sa kaya, kar towel ɗina ya cire" Dariya yayi, ya haska fuskarta da fitila yace  "meye abun ƙyamar? Gashin jikin nawane abun ƙyama ko kume me?" Rufe idonta tayi tana tura baki, ya kama hannuta ya ɗora akan Ƙirjinsa, yace  "da abun ƙyamane dabe burgeki kin taɓa ba" Tace "meye abun burgewa anan, sakarmin hannuna ko in tsige gashin nan ɗaya bayan ɗaya" "gaki na gashi ai, yi yadda kike so dashi my Queen naki ne ai" "Sarkin daɗin baki, da zakayi politics se an zaɓeka saboda wannan daɗin bakin naka" A kunnenta yace  "ko banyi politics ba, dama ban iyaba amma ina fatan ki zaɓeni a matsayin abokin rayuwarki Weeeedaat, ina sonki masoyiyya ta, na taɓa soyayya a baya amma yanzu nake gane a baya shirme nayi, yanzu ne nake Soyayya, saboda ban san takamaimai a ina nake jin sonki a cikin zuciya ta ba" Shiru tayi ta ƙanƙame Yusuf tana saurare kalaman da yake gayamata, sedai tun ba'aje ko ina ba, al'amarin ya fara canza salo zuwa wani abu daban, da fari kamar Widad zata dake daga baya kuma tace bata san zance ba, ta tubure masa gaba ɗaya, but Yusuf he shows her the superiority of a Man. Tashi tayi zaune, ta janyo bargo ta rufe jikinta, tana neman towel ɗinta, yana daga kwance ya kai hannu ze taɓa ta Amma ta bige hnnunsa, tana ta faman zumɓura baki, zaune ya tashi shima zeyi magana, amma ta fashe da kuka. yace "Am sorry please, dan Allah kiyi haƙuri, is not intentionally kuskurene mun riga munyi shi sedai.. " Katseshi tayi ta hanyar cewa "eh dama is not intentionally mana, tunda maye kake, kullum haka kake cemin is wasn't intentionally kuma bayan kana sane, kuma karka sake cewa munyi kuskure kayi dai" Yusuf yace "jimin mara kunya, amma ina kwance kika zo inda nake ai" "kazo inda nake dai, waye yace kazo ka kwantamin akan katifata?" "Amma dana kwanta akan katifarki, shine akace ki zauna kina taɓani?" Rasa me zata ce tayi, kawai ta fashe da kuka Yusuf ya lura kukan Shagwaɓa ne kawai takeji, amma yace  "shikenan am sorry, ya isa haka kukan, ba zata sake faruwa ba, semu kiyaye gaba" Ƙwacewa tayi daga jikinsa tace  "ka kiyaye gaba dai, kawai nayi wanka na zan kwanta, kawai ka ɓatamin" Ta cigaba da ƙunƙuninta, ta miƙe ta sake zura hijjabi tayi waje, yayin da Yusuf ya koma ya kwanta yana murmushi, dan shi wasu lokutan wannan rigimar tata birge shi take. Taje bakin rumfar da ake girki ta tsaya daga baya, Hari tayi daren Abinci tana ta tankaɗe zata tuƙa tuwo, Widad tace "a zubamun ruwa zan wanka" Ta ɗago ta kalli Widad tace  "sannu Agwagwa, ko kuma ince tarwaɗa sarkin wanka, ba ɗazu Yaya ta zuba miki ruwan kikayi wanka ba?" "Eh wani zan kumayi" Widad ta bata amsa "waike sau nawa kike wanka a rana ne? Ke ko ɗan tsallaken nan bakya yi, kullum se kinyi wanka, ni a rana ma bansan sau nawa kike wankan ba, kuma yanzu ko Awa biyu ba'ayi da wankan naki ba kin kuma ɗakko bokiti kin dawo" Widad tace  "Allah ya kiyaye inyi fashin wanka, an gayamiki kowa irinki ne? Kawai mutum ya zauna be wanka ba har ya kwana ya tashi, ni ki zubamin dan Allah" Hari tace  "ko dame kike yawo bazan baki ruwan nan ba, wannan wane irin wanka ne sekace me iskokai?" "Zaki zubamin ruwan ko sena gayamiki abunda yasa zan kuma wankan?" "Ina ruwana da abunda yasa zaki sake wanka, keta shafa mace sekace wata kifi kullum cikin ta'annati da ruwa, ba dare ba rana, haba ni matsa ki bani guri" "Hari za'aji kanmu dake a daren nan fa, kin fiye samun ido da shisshigi gaskiya, zuciya ta na gaya min in faɗi wani abu" Hari tace  "aike in mutum ya biye miki yana tsaye ze bar musulunci seya sake wankan shiga musulunci" Widad ta nemi guri ta zauna a tsakar gidan, Hari ta tashi taje ɗaki ɗakko abu, dukda Widad bata san hayaƙi haka ta toshe hanci, taje gaban murhun ta ɗebi ruwanta ta ƙara gaba. Hari na fitowa taga Widad ta kwashe ruwa fiye da rabi, nan ta tsaya ta dinga zazzaga masifa, Widad ta fito ko takanta bata bi ba tai wucewarta ɗakinsu. Gwaggo ce taita bawa Hari haƙuri, saboda yadda ta wage maƙogoro tana ta zazzaga bala'i a daren nan, kuma Widad ta shareta tana ta surutu. Wani daddaɗan bacci ne yayi awon gaba da Yusuf, dan duk neman maganar data fita tayi be sani ba, kallonsa tayi taga baccinsa ma yake yi. "Tasarmin daga kan katifa, zan saka kaya in kwanta" tai maganar tana dukan filon da yake kai, a hankali ya motsa, ba tare da yace komai ba ya miƙe ya bata guri, shima ya fita dan yin wankan, ba tare da yasan me Widad ɗin taje ta aikata ba. Umman Yusuf tana zaune tana lazimi, ta kunna radio, dan gaba ɗaya ji take duniyar ta mata faɗi saboda rashin Yusuf a gidan, ba ta jin daɗin komai, ji take ta rasa wani sashi me girma, Tana ta laziminta hankalinta ya ɗauke, jin an ambaci cikakken Sunan Yusuf a radio yasa ta dawo daga tunanin da take yi, ta maida hankalinta kan radion ta ɗakkota ta ƙaro sautin. Rahoton da aka faɗane na bincike ya tabattar da Yusuf ne yai garkuwa da Widad dan ya karɓi kuɗin fansa yasa tayi jifa da radion a gigice, jikinta ya hau rawa, take ta fashe da kuka tana girgiza kai, cikin kuka tace  "baze yuwu ba, Yusuf ɗina ba haka yake ba, ni ɗana baze taɓa aikata wannan mummunan aikin ba, innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wayyo Allah ɗana, wayyo Yusuf aikin ɗan sand be maka rana ba, wannan aiki da kayi yayi silar rushewar farincikinmh, yau nayi baƙinciki fiye da wanda muka rayu a ciki ni da kai, wayyo Allah ɗana, Allah ka kuɓutarmin da Yusuf " Sosai take kuka, kamar zata shiɗe haka tayi zaman daɓaro tana ta rusa uban kuka babu me rarrashinta, gwanin ban tausayi. Amal idanunta har sun kumbura saboda kukan da tayi, Hajiya Halima ta shigo ɗakin ta tarar da ita tace " Haba Autan Mummy, kukan ne har yanzu baki dena ba, haba Amal ɗina" Tai maganar tana rungume Amal a jikinta, ta cigaba da cewa "haba Amal, meye abun kuka, dan Allah ki cire yaron nan daga ranki, kinfi son Asirin Mummy ya tonu a idon duniya? Kin san bani kaɗai ba har ku ta shafa, duk fafatukar nan da nake danku nake yi" Amal tace  "Mummy, nasani amma abun yayi yawane, haba Mummy ki duba lamarin nan fa ki gani, Abunda akayiwa Yusuf yayi yawa Mummy" Hajiya Halima tace  "ke bafa sharri akayi masa ba, tunda akace ya gudu daga hannun wancan mutanen meyasa basu dawo ba? Kina ta kuka akansa, shi kuma ba kya gabansa sam, kina kallon yadda ya dinga yanƙwanaki, yana wulaƙantaki shida waccan fitsararriyar mara mutuncin, suka dinga wulaƙantaki bama ke kaɗaiba harni ba kunya ba tsoron Allah suka dinga cin mutuncinmu, dan haka meye a ciki dan suma an musu? Ki dena kukan nan kinji, ki share hawayenki, danku nake wannan faɗi tashin, ki dena kuka kina ɗagamin hankali kinji" Amal ta jinjina kai, tana share hawayen Fuskarta. Haka nan Yusuf yaji jikinsa yayi sanyi, kamar wani abu yana faruwa, jiki a sanyaye yaje yayi wanka ya dawo ɗaki, Hari tana ganin ya shiga banɗaki da bokiti tace "la'ilahaillalah, ta tabatta Wudas bata da kunya yarinyar nan, innalillahi kai Allah yayi mana maganin wannan zamani, Taɓɗijan ashe abunda yasa ba yau gobe cikin sintirin banɗaki take yin wanka, to Allah ya maganta" Babban abun takaicin, Hari ba a hankali take magana ba, Yusuf ji yayi kamar karya fito daga banɗakin nan saboda nauyin maganganun Hari, a matuƙar kunyace ya fito ya wuce ɗakinsu, Widad ta lura kamar jikin Yusuf a sanyaye yake, kamar wani abu yana damunsa. Yazo ze ɗauki kayan shimfiɗarsa, yaji ta kira sunansa "Yoseef" Ya amsa da "Na'am" Widad ta tashi zaune tace  "meyafaru ne?" "Me kika gani?" "Naga kamar kana da damuwa ne, wani abu yana damunka" Murmushi yayi yace  "bakomai, yi kwanciyarki kawai" "Yoseef" ta kuma kiran sunansa Ya sake amsa mata kamar ɗazu. "Dan Allah ka gayamin abunda yake damunka, zaka sani a damuwa fa" Yaji daɗi a ransa, da yaga ta damu da damuwarsa, "kece kike ganin wani abu yana damuna, ni lafiya ƙalau nake" Harya juya ze tafi inda yake kwanciya, yaji ta riƙe rigarsa, tsayawa yayi ya juyo yaga ta zuba masa ido. Zama yayi akan katifar yace  "ya akayi kuma?" "Yoseef, ba yau nafara ganinka ba, ina gane fushinka ko damuwa, just recently kake walawala, suddenly kuma mood ɗinka ya canza, me nayi maka?" "Ni ba abunda kikamin banda bani joy da happiness i ever expected to get" Yai maganar yana jan hancinta, "kana son ka koma gida ko? Nima na damu mu koma dukda ina jin daɗin zaman gurin yanzu, amma ina kewar Daddy sosai" Gyara zamansa yayi yace  "Dole ne muyi kewar iyayenmu da masoya Widad, kasancewar ƙaddararki na kamanceceniya da tawa, sedai sun sha banban, Akwai dalilin da yasa Allah ya haɗamu a nan, se mucigaba da haƙuri muga hukuncin da Allah zeyi, amma ni ba abunda kika yi min kinji masoyiyya, ni farinciki kika bani ma, wanda baze taɓa gogewa a zuciyata ba, I love you so much Baby " Yai maganar yana rungumeta, ba tace komai ba se murmushi da tayi, Yusuf yana daga cikin mutanen da bazata manta dasu ba a rayuwarta, dan Ya canza mata gurɓataccen tunaninta, yayi sadaukarwar da bata taɓa tunanin wani zeyi akanta ba, yana haƙuri da dukkan halinta me kyau ko akasin haka. Ya nisa yace  "bari in baki guri ki kwanta, nasan lokacin baccinki yayi" Dukda a cikin duhu ne, amma ta niƙe kafaɗa tace  "mu kwana anan tare mana" Murmushi yayi yai ƙasa da muryarsa dai dai kunnenta yace  "haka kawai inje wani abu yafaru, kiyi ta haɗemin rai kina hararata, yanzu ma ban san yadda akayi ba naga an ƙyaleni, dukda haka ban fidda ran da safe inga an ɗauremin fuska ba" "Kai kuma abunda ke ranka kenan, nidai mu kwana tare kawai" Yusuf ya gyara kwanciyarsa yace  "as you wish your majesty, ni dama haka nakeso, saboda hakan yana ƙara danƙon soyayya a tsakanin ma'aurata" Bata kula shi ba, sedai sake shigewa da tayi jikinsa sosai tana lumshe ido. Yusuf yace "Babyna, baki ƙarasamun labarin nan bafa" "shhh, lokacin bacci yayi kayi bacci kawai, bana son in ƙara maka damuwa" "wai waye yace miki ina cikin damuwa ne?" "Hmm Yoseef kenan, tunda kaƙi yadda ai shikenan" Haka suka wanzu a haka, bacci ya ɗauke Widad yayin da Yusuf ya kasa samun nutsuwa, yana sake ji a jikinsa akwai wani abu mara daɗi dake  faruwa a wani guri, wanda hakan ya shafeshi ko kuma ya shafi Widad. LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 74_75 Yadda Uman Yusuf taga rana haka taga dare, gaba ɗaya ta rasa wanda zata kira ta gayawa halin da take ciki, unguwarsu kuwa tuni labari ya cikata, akan ga abunda Yusuf ya aikata, beji ba be gani ba an ɗaura masa mugun sharri, wasu suna ƙaryene, wasu suna ba'a shedar mutum. Mata suka dinga shiga da nufin suyi mata jaje, hadda wanda tun ɓatan Yusuf basu yi mata jaje ba, se yanzu da wannan labarin ya fasu. Saleh ne a office ɗin Suleiman, ya kai gwauro ya kai mari, ya kalli Suleiman yace "ni gaba ɗaya kaina ya rufe ruf, na rasa me yakamata inyi, gaba ɗaya mutanen nan sun shammaceni, banyi zaton ta nan zasu ɓullo ba, duk yadda nake tunanin zaluncinsu sun wuce nan, na rasa mema zanyi ko me zance" Suleiman dake zaune akan kujera yai shiru, ya nisa ya ɗago daga jinginar da yayi yace  "ni kaina bansan me zan iyayi ba, naje na samu Sp amma yaƙi saurarata, wai sakamakon da aka bashi shiya sanar, nabi duk nayi ƙoƙarin da zan iya, na tuntuɓi masu ruwa da tsaki akan abun, amma kowa ya nunamin ba ruwansa, ma'aikatan gidan nan gaba ɗaya hankalin mu a tashe yake, kuma nasan muddin mukayi wani yunƙuri, to muma baza'a barmu ba, zasu ɗau mataki akanmu ne, amma yanzu meye abunyi? " Saleh yace " Abunyi be wuce inje in ƙara tabattar da na toshe duk wata kafa, wadda zata sa a gane inda suke ba, sannan in ja masa kunne da wannan uwar taurin kan yarinyar, akan duk tsanani karsu sake su bar gurin nan, idan har bani ne naje nace su baro gurin ba" Suleiman yace "gaskiya, ka gaggauta zuwa ka same su kam, sannan ni gaba ɗaya kunyar mahaifiyar Yusuf nake ji, ban san me zance mata akan wannan al'amarin ba, ni nake bata ƙwarin gwiwa akan ɓatan nan nasa, akazo kazo da labarin sun kuɓuta, amma still hankakinta a tashe yake, ban san ya zata yi ba idan ta samu wannan Mummunan labarin " Saleh yace " dole zata damu sosai, Amma haka nan za'ayi ƙoƙari a kwantar mata da hankali, dan barinta haka babu me rareshinta shima wata babbar matsala ne" Suleiman yace  "hakane, ubangiji Allah ya shiga lamarin bayinsa, bari in tashi insha Allah zanje in gaisheta, a sake bata haƙuri da kwantar mata da hankali" Daren Yau kusan kwana su Alhaji Haruna sukayi suna meeting, sunyi farincikin da jin mafitar da Bukar ya samo musu, dan ba suyi zaton irin wannan mafitar ze kawo musu ba, dan haka yanzu kallo ze koma ga sauraren  'yan sanda aga ta inda zasu fara kamo Yusuf. Alhaji Musa yace  "yanzu idan aka gano su, yaya zamuyi da wannan shu' umar yarinyar me jarababben taurin kan bala'i" Alhaji Munir yace  "kai dai bari, yau shekaru kusan goma muna bibiyar abun nan, amma 'yar masu baƙin halin yarinyar nan ta hana, ba abun mu kashe ta ba kuma muzo muyi biyu babu" Alhaji Haruna yace  "idan muka kashe ta ai kuma zamu tashi a tutar babu ne gaba ɗaya, ya zamana duk wannan wahalar ta tashi a banza, ai yadda naji Bukar yace, shi wannan ɗan sandan yaron da an kamosu shi zamu fara kawarwa, saboda Kasancewar sa tare da ita matsala ne a gare mu, idan aka kauda shi, itakuma tunda babu wanda yasan inda ubanta yake, zamuyi poisoning ɗinta ne, a fita da ita waje neman lafiya, idan yaso kodai ta faɗi inda suke kokuma a aikata" Alhaji Munir yace  "Amma fa kun san rashin sanin inda Daula yake, itama wata babbar barazana ce me zaman kanta, muna ruwa fa idan Daula ya bayyana bamu samu abun nan ba, yakamata ace mun san inda yake a hallaka shi tunda wuri" Alhaji Musa yace  "Ai ana nan kan bincike, an duƙufa sosai gurin gano inda yake, kuma akwai alamun nasara, sannan idan aka gano shi kasheshi kawai za'ayi, karma a ɓata lokaci, tunda dama an bada sanarwar duk wannan yaron shine yayi garkuwa dasu" Alhaji Haruna yace "nifa a gurin nan kamar anyi wauta, in ba hakaba ta yaya za'ace waishi ne ya sace Daula, duk tsaron dake Asibitin nan" Alhaji Musa yace  "nima da nayi wannan tunanin, amma Bukar yace ya san abunda yasa yayi hakan, ni wai ya maganar wannan yaron da muka yi magana, Barrister Hafiz, har yanzu bece mana komai game da abunda suka yanke ba" Alhaji Munir yace  "Aishine, yau kusan sati biyu amma babu wani feedback, idan ba zasuyi ba kawai muje mu haɗo kai da banki, mu kunno wata wutar" Alhaji Haruna yace "kamar yaya kenan?" "Ahh ayi takkaddun boge mana, ace ana bin kasuwancinsa wasu mahaukatan kuɗi mana, idan yaso se muyi agreement da bankin, mu basu wani percentage" Alhaji Musa yace  "amma fa kasan Daula baya cin bashin banki?" Munir yace "Nida kai muka san wannan, sauran mutane basu sani ba, dan haka muyi tunani akai, idan can baze samu ba se mubi nan, kasan na san Ambassador Auwal Inuwa, kuma kunsan suna da banki, komai zezo da sauƙi" Haka suka cigaba da ƙulla tsiyatakunsu, kala kala babu ko tsoron Allah a ransu. Nurat a wuni ɗaya amma gaba ɗaya ta zube ta rame saboda zunzurutun damuwa da tunani, tana tunanin irin hukuncin da za'ayiwa Yusuf idan har aka gabatar da shi a gaban kotu, tana tunanin wannan zalunci ace an sace mutum, kuma a koma da baya a ɗora masa laifin da hukuncunsa daze iya sanadiyyar ɓata feature ɗinsa, tunani ta shiga yi, me za tayi wanda zesa ta samu abunda zata taimaki Yusuf dashi idan buƙatar hakan ta taso? Ta ɗakko wayarta ta kira Anwar, sedai wayarsa bata shiga sam, ta kuma jarraba layin Khalil amma shima se ace mata busy, ƙarshe dai se haƙura tayi ta ajiye wayar ta maida kai ta kwanta. Yanzu ɗaliban Widad in sunzo, suke mata wanke wanke da shara, dukda ta nuna bata so amma sesu dage se sunyi, suna matuƙar sonta, dukda bata da fuska amma tana jansu a jiki tana koya musu abubuwa da dama. Yau Habi ce ta taho mata da soyayyiyar gyɗa me ɓawo, kusan kwano guda tace babarta ce ta kawo mata, Widad tace  "Aini dan Allah nake koyar daku, ba dan ku bani wani abuba, ina dai roƙonku ku dingamin addu'a, amma ni base kun biyani ba, kuma duk wanda yake sha'awar koyar wani abu, ko abunda nake koya muku ƙofata a buɗe yake yazo ya koya" Gwaggo tace  "Amarya ba kyau maida hannun kyauta, ai basu isa sun biyaki abunda kike koyar dasu ba, jin daɗin abunda kike musu ne yasa suka baki, ki karɓa kawai" Habi tace  "yawwa Gwaggo, wallahi ba zamu biyata ba kam, amma dan Allah malama ki karɓa" Da ƙyar dan Gwaggo tasa baki sannan ta karɓa, bayan tafiyar su Gwaggo ta cigaba dayi mata nasiha, na cewar zasu ga kamar wulaƙanci ne yasa bata karɓar abu idan sun bata. Tafiyarsu keda Wuya kuma, megari ya shigo, yanzu Widad tana sakin jiki ta gaisheshi, harma wasu lokutan ya dinga tsokanar ta, ya shigo yara suka biyoshi da manyan ƙwarya, ɗaya an shaƙeta da ƙwan zabo, ɗaya kuma Nono ne a ciki, megari yasa Hindu ta kira Widad, ta fito suka gaisa yace  "Nasan Malam Yusuf be dawo ba, ga wannan inji ɗalibansa suka ce a bashi" Abun ya bawa Widad mamaki, mutanen ƙauyen nan sudai suna girmama malamai, kuma suna da rige rigen son suga sun kyautatawa mutane, saɓanin irin rayuwar da ake a birni, mutum yana ganin ɗanuwansa a matsala amma ya share, koma a haɗa kai dashi a cutar da mutum. Widad ta karɓi kayan tace  "to Baba, Yoseef ya gode sosai zan gaya masa idan ya dawo" Megari yayi murmushi yace  "bagwariyar 'yata, Yusuf ake cewa ba Yoseefa ba" Widad tayi murmushi tace  "na kasa gyarawa, kuma shima ai yafison in ce masa Yoseef ɗin, kona fara cewa Yusuf se in manta" Megari yace  "Ahh masha Allah, tunda me gidan da kansa haka yakeso gara a kira shi da hakan" Widad ta ɗau kayan zuwa ɗakinsu, Hari tace  "wai me gida duk kayan nasu ne gaba ɗaya mu kuma fa?" Yace "ke dai Allah ya shiryeki, nan har siyar da ƙwan zabo kike a gidan nan dana kaji, baki taɓa dafawa kin bawa kowa ɗaya a gidan nan ba, a gabanki dai na faɗa nace ɗalibai da yake koyar damu a masallaci sune sukace a bashi, zalamammiya kawai" Ya wuce ɗakinsa yana cigaba da mita, Widad taje ta samu guri a ɗakinta ta ɗauki gyaɗar da aka bata tana ci, Yusuf ya dawo ya tarar da ita. "Gimbiya yau kuma me aka samu haka?" "Gyaɗa aka bani" "kuma haka ake cin gyaɗar?" Raba gyaɗar take biyu da bakinta, idan ta fito shikenan, idan bata fito ba ta haɗa da ɓawaonta ta cinye kayarta. Seda Yusuf yaci dariya sannan ya nuna mata yadda ake ci, tace  "ga wannan kayan, Megari ya bani yace a baka inji ɗaliban ka" Yusuf ya kalli yawan Nonon nan da ƙwan zabi aƙall zeyi guda hamsin, yanzu ma a hanya wani ya tareshi ya bashi Albasa. Yusuf ya jinjina kai yace  "Ni wallahi kunyar karɓar kayan nan nakeji Widad, nifa saboda Allah nake koyar dasu" Widad tace "nima kaga duk yawan gyaɗar nan haka suka bani, nace bazan karɓa ba Mama taitamin faɗa" Yusuf yace "gaskiya zan mayar, abun yayi yawa ai" Widad ta Harare shi tace  "ai sedai ka maida wannan albasar, amma baza'a maida wannan ƙwan da madarar nan ba" Yusuf yace "kaga kwaɗayayyiya" "Eh naji, kawai kaje kace mungode" Yusuf yayi murmushi yace "wai yau uwa ɗakina aka bawa kyauta ta karɓa, har take baza'a mayar ba, saɓanin da kana bata abu zata ce ka rainata, ko zaka cutar da ita" Widad ta ɗan ja ajiyar zuciya tace "baka manta faɗanmu akan kayan daka bani ba ko?" Yusuf yace "ya za'ayi in manta? Sedai ya wuce a ai" "daka san faɗan da Daddy yayi min akan abun da nayi seka yi mamaki, kamar ze dakeni, shi dai Daddy a rayuwar sa kar a wulaƙanta Yusuf, kar a ɓatawa me suna Yusuf rai, ya ƙwace kayan yace shi yana so, bayan ya fita naje na ɗauke abuna, na saka rigar saboda hankalinsa ya kwanta ya dena fushi dani, sedai daya ganni a cikin kayan seda yayi kuka, kasancewar Ammi na matuƙar son irin wannan shigar tasu ta dogayen riguna" Yusuf yace "Allah sarki, ubangiji Allah yayi mata rahama" Widad tace "Ameen" "Amma yaushe zaki ƙarasamin labarin ne?" "ba rana ba wata" tai maganar tana miƙewa. Yusuf yaje yayi musu godiya da karamcin nan da suka yi masa, suka ce yafi ƙarfin haka a gurinsu, tunda yake koya musu karatu ai ya gama musu komai. Yusuf haka ya karkasa kayan nan, yayi rabonsu a cikin gidan nan, Widad kam taji daɗin ƙwan nan da Nono, dan Abinci ma seta ga dama take ci. A hankali ɗaliban Widad suka ƙara yawa, harda ƙana nan yara, ta koya musu na boko ta koya musu na Addini. Yauma wajen ƙarfe biyar na Yamma, tana ƙoƙarin sallamar ɗalibanta ƙananan yara, sega Saleh yazo, Kallo ɗaya Widad tayi masa ta ɗauke kanta, jin Sallamar wasu ne yasa ta sake ɗaga kai ta kalle su, Saleh ne shida wani mutum, da wata mace da manyan Akwatunan su. Mutan gidan ne suka ruɗe da shewa ganin mutanen da suka shigo tare da Saleh, da alama dai sun san mutanen, Maida kai Widad tayi ta cigaba da abunda take. Matar ba zata wuce shekaru Ashirin ba, ta kalli Widad tace  "Gwaggo ina muka samu balarabiya ne?" Gwaggo tace  "'yata ce itama, Allah ya bani" Wadda suka kira da Jamila tun shigowarta, yara suka karɓi jaririyar bayan ta, ta kalli Widad tace  "Sannunki"  kallonta kawai Widad tayi tai shiru. Jamila tace  "ko bata jin Hausa ne?" Hari tace  "iya shege ne, tana ji sarai kulaki ne da ba zata yi ba, haka take wannan wulaƙancin" Saleh ya kalli Widad yace  "Barka da yammaci ranki ya daɗe" Yanzu ma kallon Saleh tayi ta ɗauke kai, yai murmushi yace  "Ina Yusuf ɗin yake ne?" Ai kamar da yana magana da dutse, wanda suka shigo tare da Saleh yace  "to wannan da alama 'yar Mulki ce dai" Ƙarshe da Widad taga zasu takura mata gaba ɗaya seta bar musu tsakargidan ma, ta koma ɗaki. Baƙin nan suka shiga ɗakin Gwaggo, suka ajijiye kayansu, mutan gidan sunata farincikin ganin Jamila, da mijinta da kuma jaririyarsu. Saleh da mijin Jamila wato Sunusi, suka shiga turakar megari, bayan ya sallami baƙinsa ya shigo ya tarar dasu, megari yayi murmushi yace  "Soja marmari daga nesa, ya akayi kuka haɗu?" Saleh yace  "A tasha na gano su sunzo hutu, muka hawo akorikurar shu'aibu tare ya kawomu gida" Megari yace "Madalla, ya Jamilar ya meɗakin nawa?" Sunusi yace "duk muna lafiya, gamu munzo muyi muku hutu" "eh babu laifi, amma Nasan kun kwasarwa yarinyar nan iskar hanya, dan ko Arba'in basu rufa ba" Sunusi yace "Baffa ya za'ayi, ta matsa ita dai tazo gida, kasan can inda muke babu hausawa sosai, zaman se a hankali gaba ɗaya" Megari yace "hakane, Allah yayi mana jagora gaba ɗaya, Saleh ya ka baro binni, da mutan kanon Dabo?" "kowa lafiya ƙalau, na shigo ma ban tarar da Yusuf ba, se ita matar tasa, nayi magana kuma ta shareni" Megari yace "Malam Yusufa be dawo ba ai, aini tunda nake ban taɓa ganin Yarinya meji da isa kamarta ba, akwai mulki kam, ni kaina na daɗe bata saba dani ba, ko gaisheni ba tayi, ba ruwanta da kowa daga mijinta se Hassana (Gwaggo), se a hankali kuma ta fara sabawa dasu Hindu, se daga baya kuma na gane ɗabi'arta ce rashin yadda da saurin sabo, amma tana da kirki sosai " Saleh yace " Ai Baffa baka ga komai ba, in dai mulki da ji da kaine, ba abunda ka gani, yanzu ai ta sakko ta saki jiki daku sosai, Amma ai bata da yadda sam" Sunusi yace "to meyasa, nima daga zuwana na gani, Jamila na mata magana tayi banza da ita, kaima kayi mata ta share" Saleh yace "idan na gaya maka wacece ita, seka riƙe baki abar maganar kawai" Megari yace "waini yaushe zasu tafi ne?" "Ka gaji da zama da sune?" "Haba wane mutum, aini zuwansu garina Alkhairi ne wallahi, basu takurani ba sam, sedai ina tunanin kana ganin babu wata matsala zamansu anan ɗin, nifa matsala ce bana so" Saleh ya nisa yace  "babu wata matsala Insha Allah Baffa, amma zamansu anan shine tsira da rayuwarsu, zuwa wani ɗan lokaci insha Allah zasu bar nan, ni dai fatana a cigaba da haƙuri dasu" "Saleh aini zuwansu nan alkhairi ne, baka tarar da yara gidan nan ba? Da Asuba ko magariba shi Yusuf ya koyar da karatun Addini, gashi da ladabi, ba hantara ba cin mutunci yake gyaramana kwaɓar da mukeyi, da Yamma kuma ita ke koyar da yaranmu darussan boko, da Addini, kasan mu babu makarantu haka na muke zaune da jahilci se ɗan abunda ba'a rasa ba" Saleh ya jinjina kai yace "Yanzu, ita ke koyar da yara karatun?" "daka shigo ba kaga yara da 'yan mata a gidan nan ba, dukda gidan nan na mutane ne amma karatu take koya musu" Saleh yace "Allah sarki rayuwa" Se daf da magariba sannan Yusuf ya dawo, Yusuf be tarar da Saleh ba dan haka ya gaisa da su Hari ya wuce ɗaki, yana zuwa ya tarar da gimbiyar ta cika tayi fam, kallo ɗaya yayi mata yace  "Subhanallah, me kuma ya faru? Ko nine na miki wani abu?" Girgiza masa kai tayi tace  "A'a, Saleh ne yazo na ganshi shi da wasu, na kasa yadda hankalina yaƙi kwanciya, ban san suwaye ba" "To shine zaki ɗaga hankalin ki haka? Ki bari muji ta bakinsa mana" "A'a, nifa bana son irin wannan abun, ko dai musan suwaye, ko kuma wallahi bazan kuma kwana a garin nan ba, komai dare sena bar garin nan" Yusuf yace "yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, zan masa magana idan mun haɗu a gurin salla" Bata son tayarwa da Yusuf hankali, shiyasa ta ƙyaleshi, kamar yadda ya zata sun haɗu da Saleh a masallaci, bayan sun idar da salla, suka gaisa Yusuf yace  "kwana biyu, yau kusan watanka guda rabonka damu" Saleh yace "wallahi kuwa, abubuwa ne sun ɗanmin yawa, ai ɗazu naga gimbiyar taka, na mata magana juyin duniya taƙi kulani, a gaban mutane" Yusuf ya ɗanyi murmushi yace  "kasan dama kuna takun saƙa da ita, kuma ta ganka da baƙi bata san kosu waye ba, dole ba zata kulaka ba" Yace "hakane, amma duk da haka yakamata ko gaisawa muyi, ina gaisheta amma ko kallo ban isheta ba" Yusuf yace "Allah ya baka haƙuri, zata gyara insha Allah" 'hmmm Yusuf kenan, in dai wannan ce babu ranar gyarawa, baƙin da take magana kuma ba wasu bane, mata da miji ne, namijin shima ɗan megarine, matar ma kusan haka, ya tashi da' yan fitintunu ne baya ji, ga yawon tsiya se a shafe watanni uku huɗu, ba a ganshi ba, shine na ɗauke shi na kai shi makarantar horar da sojoji, to beyi karatun boko ba, dan haka kurtu ne yana barrack suna gadin gidan wani babban hafsin soja, shine yayi Aure ya tafi da matar, yanzuma ya samu hutun ƙarshen shekara ne, ga matar ta haihu shine muka haɗu a tasha sunzo gida, suyi hutunsu a nan amma banda haka babu wani abu, amma kai ɗan sanda ne ai, zaka iya bincikawa" Yusuf yace "A'a babu buƙatar hakan, gara ta sanine ai, kasan bata da yadda" "hakane amma ita nata yayi yawa ne" "Hakane, amma ayi haƙuri dai, yanzu meye labari? Ya ake ciki a gida?" Saleh ya ɗanyi shiru sannan yace  "Yusuf labari ba daɗi kama, sedai fatan ubangiji Allah ya shiga lamarin" "Saleh, dan Allah kamin bayani gwari gwari mana, ban gane labari babu daɗi ba, aani abune ya samu Ummana? Ko mahaifin Widad? Ko kuma wata matsalarce ka gayamin mana" Saleh yace "kwantar da hankalinka babu ɗaya, mahaifin Widad dai kamar yadda ka sani, har yanzun babu wanda yasan inda yake se Allah, ana ta bincike amma shiru, ko yana hannunsu, ko yana wani gurin Allah ne mafi sanin wannan, sannan mahaifiyarka tana lafiya, mun rabu da Suleiman akan zeje ya gaishe ta ma, sedai....... "  Se kuma yayi shiru. " Se kuma me? Dan Allah ka gayamin kana ɗagamin hankali fa" "Yusuf jin meke faruwa bashi da wani amfani a gareka, abun da nake so da kai shine, kayi taka tsantsan gurin zuwa cin kasuwar nan da kake yi, sannan ka ƙara tsananta Addu'a, kuyi haƙuri kunci gaba da zama anan, dan sun saka a nemoku duk inda kuke" Yusuf ya dafe kai yace  "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yanzu meye abunyi? Zuwa yaushe ne zamanmu ze ƙare anan, kar mu takurawa mutan gidan, sannan kuma cigaban zamana da Widad a inuwar Aure shima matsala ne babba, babu wanda yasan batun Aure mukayi se kai" Saleh yace  "batun takura, baku takura musu ba, dan munyi magana da megari, sannan Aurenku aini na san anyi, ina da sheda, kawai Allah yasa ku kawai Daula jika" "Saleh, why are you not serious about this issue? Bafa abun wasa bane, wani irin kallo mahaifinta zemin, wani suna ze kirani dashi idan har muka koma gida da ɗa?" "Ahh kallon siriki ze maka mana, karka damu Daula ba baƙon zafi bane, idan har 'yarsa tana ƙaunarka, kaje ka tabattar da irin son da take maka tukuna, nidai fatana iya wuya, idan bani nazo nace kubar gurin nan ba, kuyi zamanku anan, ka koma maza karta fara zargin wani abu " Har Yusuf ya shiga cikin gidan jikinsa a mace yake, gaba ɗaya ya easa meye yake masa daɗi, Saleh ya sake dagula masa lissafi, yanzu idan aka gano inda suke shida Widad meye sunansa? Idan ya kasance Widad ta samu juna biyu meye makomar yaron, sannan yayi mata adalci makuwa, idan har ya bari suka haɗa zuriya da ita, bayan bata san shi waye ba, ba tasan mecece tasa ƙaddarar ba balle yaji hukuncin da zata ɗauka akansa? Baya tunanin ɗorewar Alaƙa a tsakaninsu muddin taji waye shi, ba ita ba hatta mahaifinta baze farinciki ya zamo siriki a gareshi ba. LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 76_77 A haka Yusuf ya ƙarasa ɗakinsu, yana zuwa ya zauna yayi shiru ya zurafafa a cikin tunani. "Meya gaya maka haka, wanda ya jefa ka cikin wannan dogon tunanin?" yaji muryar Widad. "Bakomai" ya bata amsa "Har yanzu fa ban canza daga Widad ɗin daka sani ba, bana son ƙarya bana son ɓoye ɓoye, ka gayamin tun kafin kaima in saka a Jerin wanda nake zargi" Ya kalle ta yace  "zargin me kenan?" "zargin zaku haɗa kai ku cutar dani, in ba haka ba, meye na ɓoyemin wasu abubuwan da dole nasan sun shafi rayuwata?" Yusuf ya kalle ta yace  "har yanzu kina tunanin zan iya kasancewa cikin masu cutar dake?" "Yoseef, zuciya bata da ƙashi ya kamata kamin uzuri, musamman a irin rayuwar da na tsinci kaina, amma ya kamata in dinga sanin al'amuran da suka shafeni" "Ba wani abu bane, dama ya gayamin muƙara haƙuri da zama anan ne, saboda ana can ana nemanmu, maƙiyanki sun baza komar anemomu, tunda tuni labarin guduwarmu ya iskesu, sannan baƙon da suka zo tare, shima ɗan uwansane, soja ne sunzo hutune shida matarsa, shikenan " Ba tayi magana ba, se riƙe gashin kanta da tayi, sekuma ta shiga jan numfashi tana zazzare ido, ta dunƙule hannunta, tana girgiza kai. A Rikice Yusuf yace " Subhanallah, lafiyar ki kuwa Widad? Meyafaru? " Girgiza kai take hawaye na zuba daga idonta tace " almost ten years, good ten years ana cutar dani, bani kaɗaiba har wanda ya raɓeni, yana ɗaya daga abunda ya nesanta ni daga mutane, bana son rayuwar wani ta shiga matsala saboda ni, amma ƙaddara ta haɗa rayuwarka da tawa kana ta faman wahala, an cutar dani an kassara lafiyata, an cigaba da bin diddigina ana son ganin bayana saboda abun duniya, kuma aka jefa ƙiyayyata a zukatan jama'a suka koma gefe suna zagin AƘIDATA, Insha Allah bazan mutu ba sena ga bayan maƙiyana, ko kuma mu yi mutuwar kasko nida su, i can't tolerate it anymore " Tai maganar tana jifa da kayan gurin, sannan ta yunƙura zata miƙe, Yusuf ya riƙeta gama, fizge fizge ta dingayi tana kai masa duka tana nema ta ƙwace daga hannunsa, ya riƙeta sosai yana mata addu'a, surutai take sosai cikin ɗaga murya, idan Yusuf yasa hannu ya toshe mata baki, se taita kai masa duka, idan ya riƙe hannunta kuma seta hau surutai, yana gudun hankalin mutane ya dawo kansu, dan sam baya son wani yasan tana da larurar taɓin hankali, dan haka kawai ya haɗe bakinsa da nata. Tun tana mimmiƙewa tana son ta ƙwace, harta gaji jikinta yayi sanyi, Numfashi take saukewa a hankali, hawaye na bin gefen idonta, seda yaga ta dena fizge fizgen sannan ya cire bakinsa daga nata, ta lumshe idonta kamar me bacci, Yusuf ya rungumeta yana cigaba da karanta mata duka Addu'ar da tazo bakinsa. Widad ya kira sunanta, ɗaga masa hannu tayi alamar ya ƙyaleta, sun daɗe a haka sannan ta tashi zaune, Yusuf ya kalleta yace  "Sannu" Jinjina masa kai kawai tayi ta sunkuyar da kai, ya riƙe hannayenta yace "dan Allah kidena saka damuwa a ranki, kinga hakan yana shafar lafiyarki" "bazan iya dena damuwa ba, saboda an diga an gama kassara rayuwata, bana jin zan samu nutsuwa har se ranar da na gamsu, na ɗau fansar abunda akayimin" "Rayuwa ba zata tafi a haka ba, lafiyar ki abun dubawa ce, kalli yadda lokaci ɗaya kika fita hayyacinki fa" "Ai dama ba lafiyar ce dani ba, dan haka ba wani abu dan na ƙarasa a haka" Kawai ta rufe bakinta da hannunta tana kuka, Yusuf ya shiga share mata hawayenta, yana cewa "ke lafiyayyiya ce, kuma ina miki fatan samun lafiya me ɗorewa" Tai murmushi me ciwo tace "wai in warke daga haukan? Ko ciwon zuciya?" "Nifa ban yadda da wannan ciwon haukan ba" Widad tace  "yakamata ka yadda, ka sawa ranka kana zaune da mahaukaciyane" Yusuf ya ɗanyi shiru sannan yace "nifa akwai ranar da naga an saka miki wata ƙwaya a cikin tea, amma baki sha ba, shiyasa nake da question mark akan wannan ciwon naki" Seda tayi shiru na wasu lokuta, sannan ta gyara zamanta tace  "Bayan an kashe Ammina, ɗaya daga cikin wannan mutanen, ya ɗakko wayarsa ya fara waya, yayi wayarsa ya gama sannan ya kalli sauran yace, ku cajemin gidan nan, akwai wata yarinya, ku kawomin ita nan, Widad na tsaye tana jinsu, bata ko motsa daga inda take ba, suka fito suka shiga bincike gidan nan, amma basu ga Widad ba, suka dawo sukace "mun caje ko ina a gidan nan bamu ga yarinyar nan ba" Yace "ta yaya za kuce baku ganta ba, bayan tana cikin gidan nan?" Suka haɗu har dashi suna dubawa, sun wuce ta inda Widad take yafi sau uku, amma Allah besa sun ganta ba. Suka sauka ƙasa falo, babban ya sake kiran waya, ya sanar da wani cewar sun duba kaf basu ga Widad ba, kawai Widad ji tayi yace " An gama Oga.... " Bata iya jin cikakken sunan daya faɗa ba, kamar taji dai dai kamar kuma ba daidai ba. Babban yace  "kai mu tafi, Oga yace yasan yadda zeyi da ita, mu ɓace kafin a gane munzo" Haka suka rankaya suka fita, cikin sanɗa Widad ta sakko daga kan benen, ta sakko falo taje ta leƙa taga, taga sunyi maganganu da Bala, sannan ya buɗe musu ƙofa suka fita. Widad ta juya ta koma kan bene, ta koma ɗakin da Amminta take cikin sauri, tana zuwa ta tarar da ita a yadda ta batta. Widad ta shiga jijjigata tana kiran  "Ammi ki tashi mutanen sun tafi, baki ji ciwo bako?" Ganin Ammin nata bata motasa ba yasa tace  "Ammina bacci kikayi ne? Ko kuma sanyi kike ji?" Nanma bata samu amsa ba, dan haka ta ɗakko bargo ta lulluɓeta, itama ta shiga bargon ta rungume Ammin nata, daga nan bacci yayi awon gaba da ita. Dukda Kasancewarta yarinya ƙarama, amma da Asuba Amminta ke tashinta salla, Asuba tayi Widad ta tashi taje tayi salla, Amma Amminta bata motsa ba, ta sake zuwa ta kwanta a jikin gawar ta koma bacci, har kusan ƙarfe tara na safe Widad ta farka, ta shiga girgiza gawar Ammin tana  "Ammi ki tashi bakiyi salla ba, kuma yunwa nake ji, Ammina ki tashi ina jin yunwa, Ammi Abinci"  haka Widad ta cigaba da hayyata irin tasu ta yara, ba tare da tasan Ammin mutuwa tayi ba. Tana nan zaune, ta gaji ta shiga wasa da gashin kan Ammin nata, tana mata surutu ba tare da tasan mutuwa tayi ba. Tana nan zaune Bala ya buɗe ɗakin ya shigo, ya kalli Widad yace "ke a ina kika kwana?" Kallonsa Widad tayi ta ɗauke kai, ya kalli Gawar Huda dake kwance a gurin, ya juya ya fita. Wajen ƙarfe sha ɗaya sega Bulama da wasu abokan kasuwancin Daula, suka shigo har ɗakin, Bulama ya kalli Huda ya shiga rangaɗa salati, ya kalli Bala yace " kuma ba rashin lafiya ce ta kamata cikin dare ba?" Bala yace  "nima ban sani ba, gani nai shiru banji motsinsu ba, shine na shiga dubawa, nazo na tarar da gawa da yarinya" Bulama yayi ajiyar zuciya yace "Allah me iko, Allah yayi mata rahama amma abun da mamaki, munyi waya da Daula, lafiya ya tafi ya barsu, amma a wayi gari ta rasu, Allah kenan, yanzu dai a kira motar Asibiti aje da gawar a dubata a Asibiti, ita kuma daughter a tafi da ita gidana, zuwa muga yadda hali zeyi" Widad ta dinga bin Bala da ido, tamkar bata taɓa ganinsa ba, duk inda ya motsa seta bishi da ido. Aka ɗauketa aka tafi da ita gidan Bulama, aka tafi da gawar Huda Asibiti. Tunda aka kai Widad gidan Bulama, ba tace uffan ba se kallonsu da take kamar baƙin halitta, aka bata Abinci harta fara ci, ta ture ta shiga kuka tana kiran Ammina. Gaba ɗaya tausayinta, ya kama Hajiya Sarah, ta dinga rarrashin Widad amma fafur Widad taƙi yin shiru, Fahad yace "kai wannan wace irin jarabbabiyar yarinya ce, banza kawai ana ta magana ana rarrashin ta se wani iskanci take yi, shegiya kai me kama da Aljanu" Fahad be rufe baki ba, Widad ta ɗauki wani kofin glass ta jefa masa, gaba ɗaya ta basu mamaki, suka juyo suna kallonta, kofin ya sameshi a ƙafa ya faɗi ya fashe, sannan kuma ta koma gefe tana kallonsa tana huci, kanta yayo ze maketa a zuciye, Hajiya Sarah ta tareshi tace "yi haƙuri, marainiyar Allah ce, meyasa zaka zageta" Fizgewa yayi ze daketa, amma Widad ta shammaceshi, ta kafa masa haƙora a hannu, da ƙyar aka ɓanɓareta dan seda gurin ya fashe. Fahad ya dinga ihu yana "na shiga uku Mayya, 'yar gidan mayu zata shanye min jini" Tun daga lokacin, ko hanya basa haɗawa da Widad, dan tunda ya zageta ta tsane shi, a wunin ranar nan gaba ɗaya suka rasa yadda za suyi da Widad, suka kasa gane kanta dan bata jin rarrashi, bata sanshi ba ga kafirin taurin kan masifa, taƙi cin Abinci taƙi saurarar kowa, da Hajiya Sarah ta gaji ta kira Bulama ta gaya masa, shi kuma yace ayiwa direbansa magana Fahad ya rako su Asibitin, dan Daula ya iso. Fahad yace "Allah ya kiyaye in raka Mayya, wannan a binciki danginsu mayune, shegiya kawai" Ƙarshe direba ne ya kai Widad Asibiti,  bata tsaya jiran direban ba, ta shiga cikin Asibitin tana leƙe leƙe, ta buɗa wannan ƙofar ta buɗe waccan. A saman bene ta buɗe wani ɗaki, taga su Bulama da Bala a ciki da wasu mutane, se Mahaifinta durƙushe a gaban gado an rufe gawa, yana rusar uban kuka kamar ƙaramin yaro, Widad ta tsaya tayi sak tana binsu da kallo, Daula na ɗaga ido yaga Widad ya sake fashewa da kuka, ya miƙowa Widad hannu, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta faɗa jikinsa, cikin kuka Daula yace  "Lovely daughter, mun rasa Amminki, ta tafi ta barmu" "Daddy ina Ammina" Daula ya buɗe mata fuskar Huda, kamar kace mata tashi ta miƙe zaune. "Your Mum is dead Daughter" yai maganar cikin kuka. Zumbur Widad ta miƙe tsaye, tana kallon mahaifinta, idan bata manta ba ko a film da take kallo, when someone is dead, you won't see him again, that's mean her Ammi has gone, she won't see her again. "Noooo Daddy, she's alive, she's not death!" Wata irin ƙara tayi tana tirje tirje, ƙarshe se ɗaukarta akayi aka kaita pediatric, aka mata allurai, se bayan an kai Huda nakwancinta sannan Widad ta farka. Amma tunda ta farka ba ummm ba umm, idonta a buɗe amma sam bata magana, bayan an dawo daga kai Huda, Daula se kuka yake yana sharɓe hawaye, Asibiti ya wuce gurin Widad ya tarar ta farka, su Bulama dai yana biye dashi dasu Bala, ya zauna ya rungume Widad a jikinsa, yana kuka yayin da Widad ta tsaida idonta akan Bala megadi, bata ko ƙyaftawa. "Daddy, what exactly kills Ammi?" Tayi tambayar a bazata. Daula yace "i don't actually know daughter, likitoci sunce ta samu cardiac failure ne" "is a lie Daddy" "How?" "someone sponsored her murder, she was killed Daddy" Daula yace "what are you trying to say?" Mamaki ya cika su yadda take magana, sekace wata babba, kuma she's very serious about what she says " Alhaji Munir yace  " ranka ya daɗe, yakamata fa muje gida, mutane na jiranka. Haka suka tafi da gida, Daula na cigaba da kuka wiwi, Bulama da sauran mutane suka raka shi gida, har an kafa manyan rumfuna, manyan mutane gaba ɗaya sun hallara, anata miƙo gaisuwa. Daula na rungume da Widad a jikinsa, Widad gani take kamar ƙaryane wai Ammi ta mutu. Seda ta kwana biyu cirr ko gyangyaɗi ba tayi ba, hakan ya firgita Daula kar wani abu ya sameta, ya fara tunanin ko Asibiti ze maida ita, dan seta wuni ba tace uffan ba, sedai lokaci lokaci ta fashe da kuka. Ranar uku, gidan nan ya cika da ɗan Adam, babu masaka tsinke Kasancewar ita kanta Huda mutuniyar kirki ce ga kyauta. Ana zauna a nayiwa Daula gaisuwa, ta dubi wani babban ɗan sanda, ta tashi daga jikin Daula ta tafi gaban ɗan sandan ta zauna, ta kalle shi tace  "Are you a police?" Ya amsa mata da 'yes my dear " " Can i ask you a question? " " Yes of course " Widad tace  " idan na tambayeka, will you do your best to help me? " Yace" insha Allah " Widad tace" karka saɓa Alƙawari fa" Mamaki ya kama mutanen gurin, yadda take zaro magana haka, daki daki kamar babbar mace. Yace "insha Allah, i promise you, bazan saɓa ba" Daula yace "lovely, dawo na kusa dani, karki dameshi" Widad ta ɗagawa mahaifinta hannu, alamar ya ƙyaleta, ta kalli cikin idon ɗan sandan tace   "you promise to help me, tambayar da zan maka itace, idan aka rufe fuskar mutum da pillow ze mutu?" Yace "kamar yaya?" "misali, Daddy ya doramin pillow fuskata, inta motsi amma yaƙi ɗagani, kawai se misali Bala megadi ya dawo ya riƙemin ƙafa, in dena motsi, to zan iya mutuwa" Yace "yes of course dear, it's a murder attack, kisan kai kenan a ina kikaga anyi?" "Yanzu misali, idan na gaya maka a inda na gani, wani mataki zaka ɗauka?" Gaba ɗaya rumfar tayi shiru, ana sauraren Widad, Ɗan sandan yace  "zamuyi abunda doka tace akai, idan har muka kama mutum da laifi, zamu kashi kotu a yanke masa hukunci" "Arrest Bala! And the doctor that confirms that my Mum is dead, as a result of cardiac attack" ta faɗa kai tsaye "Why" ya tambaye ta Cikin ƙara tace  "Bala yasan suwaye suka kashe Ammina, kasheta akayi fa, i use to watch in movies, she was killed not dead as a result of cardiac attack, Ka kama Bala ko in kasheshi, he's responsible for the murder, na ganshi shine ya buɗe wa wasu ƙofa, suka rufe ammina da pillow, Arrest him i said "! Gaba ɗaya Widad ta hargitsa gurin, ihu take sosai tana nema ta fita daga hayyacinta, se kurma ihu take tana akama Bala. Alhaji Haruna yace" ya za'a biyewa yarinya ƙarama tana wa mutane shirme, watakila alhinin mutuwane ko mafarki tayi " Daula ya fashe da kuka yace " Widad mutum ce, kuma yarinya ƙarama, amma idan kaga tayi maka ƙarya ajizanci ne irin na ɗan Adam, dan haka Arrest him, ayi bincike akai " Yai maganar yana kuka, aikuwa Bala yana ihu haka aka buga masa ankwa akayi gaba dashi, nan wasu suka dinga jinjinawa kaifin basira irin na Widad da ƙarfin hali, yayin da wasubsuke ganin be kamata a kama Bala ba, tunda shirmen yarane. Nan fa 'yan sanda kuma suka shiga bincike akan Bala, Widad ta fayyace musu yadda abun ya faru, Alhaji Haruna yace "Nasir, bekamata a biyewa yarinya ƙarama ba, ta faɗi magana sannan a yadda" Daula yace "Tunda Widad ta faɗi haka ba ƙarya take ba, bata taɓa haka ba, kuma akwai ƙamshin gaskiya a lamarin nan, dan haka se abunda hukuma tace, dan nikaina bana ja da ikon Allah, amma tabbas mutuwar Huda, abar a bincika ce, lafiya muka rabu da ita, ba ta da wani ciwo, ace in dawo in tarar ta rasu, Allah na tuba " Kawai ya fashe da kuka, Bulama yace " Nasir, kayi haƙuri nasan irin mahimmancin Huda a rayuwarka, amma karkayi abunda zaka dawo kana dana sani, kar azo aji kunya " Widad na kan kujera, tana wasa da yatsunta, tunda suke maganar su bata saka baki ba, se yanzu tace "Daddy, ko nima na mutu kar ka bari a ƙyale Bala, seya faɗi wanda suka kashe Ammina, idan ba hakaba zan faɗa maka ko suwaye" Zaro ido sukayi, suka juyo da kallonsu kanta, Daula yace "Baby na, dagaske kin san suwaye? Ya akayi kika sani? Gayamin suwaye, meyafaru?" "Daddy nima ban san suwaye ba, amma nasan mutum ɗaya, naji sun faɗi sunan wani mutum, amma zanyi tunani in tuna, na manta sunan, amma zan tuna idan be faɗa ba zan faɗa" Bulama yace "Daula anya yarinyar nan bata samu matsala a ƙwaƙwalwarta ba? Ji wata irin magana da take fa, Anya baza'a kaita Asibiti ba" Alhaji Haruna yace "gaskiya kam, nima naga kamar alamun haka a tare da ita" "Niba mahaukaciya bace, karku sake cemin mahaukaciya, ni nasan abunda nake, wasune suka danne Ammina da pillow, ni ina da hankali" Daula ya rungumeta yace "Sorry my lovely, nima na sani lafiyarki ƙalau ai" Wasa wasa Widad gaba ɗaya walwalarta ta ɗauke, ta dena walwala ta dena fara'a, ko Abinci bata iya ci saboda kewa dake damunta, wasu lokutan seta wuni akan gadon nan da aka kashe Ammi, ko haka kurum taje ta buɗe wardrobe ɗin Ammin, ta watso kayan Ammin duka ta zauna a cikin kayan tana rusa uban kuka, haka Daula zezo ya na rarrashinta, wani lokacin kuma ya zauna ya tayata kukan. Sosai Widad kaɗaici yake damunta, dama gata bame son mutane ba, Babu wani dangi da suke dasu da suke zuwa gurin su, dan haka Widad abun ya ƙara nata yawa, haka kurum wani lokacin da daddare seta hau firgita tana cewa "Daddy gasu nan, ka tashi kaima karsu kasheka" ko taita ihu tana ƙoƙarin fita da gudu, se Daula ya riƙeta gam. Sosai ta dena magana, sedai ta kan zauna taita kallon magunan Ammi da take kiwo, da zomaye da tsuntsaye, da yake Huda mace ce me son dabbobi, sosai take kula dasu tana ciyar dasu, idan Widad tana kallonsu, se taga kamar Amminta tana nan, zata zo ta basu Abinci, haka zata zauna tana musu magana "Kuma kunyi missing Ammina ko? An kashe ta, amma zata zo ta baku Abinci" Bulama yace "Daula, nifa na fara jin tsoro da sha'anin yarinyar nan, karfa muna zaune ta haukace, gaba ɗaya ta canza lokaci ɗaya, ta zama wata iri" Daula yace "nima na gani, abun yana damuna, na rasa ya zanyi bana son in rasa ɗiyata, kota rasa hankalinta, gashi kullum cikin kashedi takemin akan, lallai kar in bari a saki Bala, sannan idan be faɗi waye ba ita zata faɗa, nayi nayi ta faɗa taƙi gayamin, yanzu fa ko Abincin kirki bata ci, se koke koke" Bulama yace "yanzu ajiyar da ka bata na dukiyar nan, baka tsoron ta samun taɓin Ƙwaƙwalwa, ayi asarar maƙudan kuɗaɗen nan?" Daula yace "duk me wannan dukiyar, in dai ta sace ko waye, kuma ko a ina yaje, seya karɓi kayarsa dan haka wannan ba abun damuwa bane, ni abunda ya dameni yanzu, shine lafiyar ta" Bulama yace "karka damu, akwai wani likitan ƙwaƙwalwa da Alhaji Munir ya sani, zan masa magana ya turoshi yazo ya duba ta" Haka akayi, washegari Bulama yazo da Likitan nan da Alhaji Munir, Widad na ganinsa ta miƙe da gudu ta maƙalƙale Daula, juyin duniya ta sunkuyar da kanta taƙi kallonsu. Suka gaisa da Daula, Daula yace "lovely ga likita ze dubaki, ki gaishe shi" Ƙara sunkuyar da kai tayi, taƙi kallonsu, likitan yace "Baby zomu gaisa mana, tambayarki zanyi" "Niba mahaukaciya bace" ta bashi amsa. "Ai bance mahaukaciya bace ke, tambayarki kawai zanyi" Juyin duniya Widad taƙi magana, duk tambayoyin da suke mata taƙi amsawa, likitan nan ya kaɗa ya raya, amma tayi mursisi kamar yana magana da itace. Daula yasa hannu ya janyo ta daga bayansa data shige, ta sunkuyar da kai kamar sabuwar bokanya. Ya ɗorata akan cinyarsa yace "Babyna lookup" ta ɗago ta kalli mahaifinta idonta fal hawaye. Yace "ba cutar dake za suyi ba, tambayarki za'ayi lafiyarki nake son a dubamin, kinji Gimbiyar Daddynta" "Daddy, idan Bala be faɗi wanda suka kashe Ammina ba, zan faɗi sunan da mutanen suka faɗa idan na tuna, ina kallonsu Bala ne ya rufe Alba Dog, ya buɗe musu ƙofa, shiya rako su har kan bene, ina kitchen ina kallonsu, har akace su nemoni a gidan nan" Bulama yace "ikon Allah, kalli abunda ake tambayarta daban, abun da take faɗa daban" Daula ya dafe kai yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ka rufamin Asiri kar Abunda ya ragemin ya kufcemin, Allah ka bawa 'yata lafiya". Kawai ya fashe da kuka, yana ƙanƙame Widad a ƙirjinsa, aikuwa ta kwanta a jikinsa, tana ajiyar zuciya. Alhaji Munir yace "dan Allah ka dena kukan nan" Likitan da suke kira da Hamisu yace "Alhaji ina me sake yi maka ta' aziyyar rashin matarka, sannan kayi haƙuri ka dena kukan nan, ka bani haɗin kai ka amsa tambayoyin da zan maka, saboda alamu sun nuna Ƙwaƙwalwarta ta fara taɓuwa, tana iya bacci, ya yanayin cin Abincin ta?" Daula yayi masa bayanin duk abunda Widad take yi, nan aka tabattar masa depression ne yake damunta. "zan mata wata allura guda ɗaya, idan akayi mata insha Allah zata samu sauƙi, za'a samu ƙwaƙwalwarta ta dinga karɓar abunda ake so " Widad tana zaune, aka haɗa allura aka zuƙa, tana kwance jikin Daula, likitan ya ɗaga hannunta, daidai dantsanta yayi mata allurar, sedai me ko mintuna biyar ba'ayi ba......... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 78_79 Take Widad taji duniyar tana juya mata, taga abubuwan dake ƙasa sun koma sama, na sama sun dawo ƙasa, ta kasa gane inda kanta yake, ta dinga jin kamar ta tashi ta zura da gudu, ta riƙe kanta gam, kafin can ta kurma wani uba ihu ta miƙe tsaye tana zazzare idi. Daula a gigice ya riƙeta yace  "Subhanallah, doctor meke faruwa ne? Kaga abunda take fa, meya sameta ne? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un" Likitan yace  "wannan shike tabbatar da ta samu taɓin hankali ne, badan haka ba da babu abunda allurar za tayi mata, dole a cigaba da kula da ita, idan ba hakaba kuma zata zama tuburan, amma zan sake mata wata allaurar zata samu relief tayi bacci" Widad tana ta gunji, tana fizge fizge haka aka kuma yi mata Allura, wadda seda ta ƙara birkitata ga baki ɗaya, ya zamana bata gane a duniya take ko a ina? Ga mutane tana kallonsu, amma bata gane meke faruwa, a haka har wani irin galabaitaccen bacci ya ɗauketa a wahalce. Seda bacci ya ɗauketa sannan hankalin Daula ya kwanta, ya kalli likitan yace "yanzu doctor, wannan baccin shine samun relief ɗinta? Sannan kuma ya batun yadda za'a cigaba da kula da ita" Doctor Hamisu yace "Eh shine samun sauƙinta, tunda kace baccin ma bata yinsa sosai, dan haka karka damu, ko yaushe zata kai tana wannan baccin babu wata matsala ba abun damuwa bane" Daula ya jinjina kai yace  "shikenan, ubangiji Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗunta, Allah ya baki lafiya daughter na" Alhaji Munir yace  "to tunda hakane baka ganin a cikin taɓin hankalin ne yasa tace kashe mahaifiyarta akayi? Tasa aka kama Bala? Kuma ma ai tayi ƙanƙanta ace ta bada irin wannan shedar an yarda an karɓa" Daula ya haɗe rai yace "bana yadda in zalunci kowa a rayuwa ta, ina taka tsantsan da duk abunda zan aikata da zesa in ɓatawa wani, ko in zalunci wani dukda tarin dukiyar da nake da ita, amma a wannan karon nima zan ɗana izza da amfani da ƙarfin dukiya da Allah ya bani, in dai hakan ze samarwa da 'yata farinciki, bari in gaya maka wani abu, ko nawane zan kashe a cigaba da tsare Bala, har se ya faɗi abunda yasani game da kisan matata, uwar' yata" Bulama yace  "Daula karfa soyayyar 'yarka yasa ka aikata abunda zakazo kana danasani, abi komai a sannu har a gano bakin zaren, kaga yarinyar nan ga abunda aka ce yana damunta, ga kuma ita abunda take faɗa, kar ƙaunar da kake mata yasa ka ɓata sunanka a idon duniya" Daula ya kalli Widad dake kwance a jikinsa, ya shafi gashin kanta yace  "bata taɓa aikata wani abu makamancin haka ba, 'yata ba irin sauran yara bace, Ƙwaƙwalwarta na aiki fiye da shekarunta, tunaninta ya zarta tunani irin na yara, a baya Huda na ɓacin ran irin halayen Widad, tana jin haushin irin kallace kallacen da take yi, sedai me bayan ran Huda wannan hali na Widad yayi rana, saboda ni abunda likita ya faɗa daban abunda kuma ya faru daban, abun da baku sani ba shine, har kitchen inda ta hau kan drower, har garin hawa abunda take ci ya zuba a ƙasa, seda ta nunawa 'yan sanda, kuma ta nuna musu ta ƙofar da Bala ya shiga da mutanen nan, an auna gurin anga zanen yatsunsa a jiki, dan haka bana tantama abunda ta faɗi gaskiya ne" Munir yace "Amma, baka ganin lokacin da ya shigo duba sune ya kama ƙofar ya shigo, har hoton yatsunsa ya fito" "Wannan kuma aikin hukuma ne, su zasu tabattar da gaskiyar abunda ya faru, amma wannan karon nima zan ɗana, zanyi Amfani da ƙarfin dukiyata, da kuma alfarma da sanayya da nake da ita a faɗin ƙasar nan, se an nemo wanda suka kashe matata, kuma wallahi ko Arziƙina ze ƙare se na tabattar da anbi mana haƙƙinmu" Likitan yace "Amma ranka ya daɗe kabi komai a sannu yafi, alamu sun nuna yarinyar ka tun tana ƙarama take da larurar Ƙwaƙwalwa, amma baka ɗau mataki ba" Daula yace "ni lafiyar 'yata ƙalau, babu abunda ya samu Ƙwaƙwalwarta a wancan lokacin, Allah dai ya bata kaifin basira fiye da shekarunta" yana gama maganar ya miƙe, ya saɓa Widad a kafaɗarsa ya tafi ɗakinsa da ita, yaje ya kwantar da ita, ya koma gefenta ya kwanta ya ƙura mata ido yana jin tausayinta na ratsashi, Widad ta rasa mahaifiya da ƙananan shekaru, yasan rayuwar maraici, yasan yadda take, musamman ga 'ya mace tafi shan wahala, take hawaye suka shiga zarya a fuskarsa yace  "insha Allah zanyi iyayina, ba zakiyi kukan maraici ba Widad" Wasa wasa tunda aka yiwa Widad Allurar nan bata sake farkawa ba, haka ta dinga wannan baccin kamar wata matacciya, abun ya ɗagawa Daula hankali sosai, Amma likita yace masa bakomai samun relief ɗinta kenan. Seda Widad tayi kwana biyu cir tana wannan baccin, ko motsi ba tayi rana ta biyu da yamma sannan ta farka, tunda ta fara baccin nan Daula baya matsawa ko nan da can, yana kusa da ita, har Allah yasa ta farka. Koda ta farka ta farka da wata irin matsananciyar yunwa, amma ta kasa cewa tana jin yunwa, maganar duniya Daula yayi amma taƙi bashi amsa, sedai ta bishi da ido. Ya haɗo Abinci yazo ya zauna yana bata, tana ci tana kallonsa kamar taga sabon abu a tare da shi, yana cikin cin aka zo aka sanar dashi yayi baƙi yace ayi musu iso nan inda yake baze iya tashi ya bar Widad ba. Aka musu iso suka shiga har inda Daula yake, sedai Widad na ganinsu se taga kamar wannan mutanen da suka kashe Amminta, seta dinga ganinsu da wannan mask ɗin a fuskarsu, abunda ya faru da Amminta ya shiga dawo mata fes a idonta, taga kamar a lokacin abun ke shirin faruwa, aikuwa ta kurma ihu me razanarwa, haka yasa mutanen suka tsaya suna zuba mata ido, ta riƙe Daula gam tana ihu, ta rintse idanunta alamar bata son ganin kowa gaba ɗaya. Ƙarshe mutanen nan se barin ɗakin nan sukayi gaba ɗaya, suka koma babban falo suka jira shi, abu kamar wasa sosai Widad take gudun mutane bata son kowa a inda take inba Daddynta ko Bulama ba. Watarana tana zaune a ɗakin Daddynta, tana wasa da magen Amminta data bari, Alhaji Daula yana son ya ɗan fita, amma yana tunanin yadda zeyi da Widad. Widad da a rana bata fi tayi magana sau a ƙirga ba amma tace  "Daddy kaje inda kake son zuwa, ba inda zani" "A'a lovely, ina tsoron barinki anan ke kaɗai, abubuwa sun fara bani tsoro, ina zaton zan sa a ƙara security" Widad tace  "Daddy har yanzu Bala be magana ba?" "Eh lovely, Amma a binciken 'yan sanda, security na kan babban titi sunga wucewar mota tsakar darw ta shigo hanyarmu, sedai wai sunyi zaton gurina ko wani suka zo, saboda kin san mukanyi meeting cikin dare, amma har yanzu anata bincike" Widad ta jinjina kai tace  "Daddy kaje kawai, ina nan ba inda zani" "Babyna ina tsoron barinki, kinga baki da lafiya" "Lafiyata ƙalau fa" "ko kuma mu tafi tare da ke?" "A'a Bazani ba, ka tafi kawai" Daula yace  "nayi murna daughter, yau kina magana sosai da kanki". Tayi murmushi, Daula ya shirya ya fita. Bayan fitarsa Widad ta fito ta dinga zagaye gidan, kamar bata saba ganin gidan ba. Kamar gaske ta fara dawowa daidai, amma dukda haka bata son mutane sam, daga Daddynta bata son kowa ya raɓeta, balle a yimata wani abun, haka Daula yake yawo da ita gurin taro ko harkokin kasuwanci, kamar yadda uwa ke yawo da ɗanta, sam ko makaranta bata zuwa saboda rashin son mutane, indai ba'a gida ba ko tana tare da Daddynta bata zama a ko ina. Daula Shine wankanta, Abincinta, da dukkan buƙatunta, sam baya gazawa. Wataran zeje taron kasuwanci Africa ta kudu, nanma ya ɗauki Widad ya tafi da ita, ranar da suka dawo kusan ƙarfe ɗaya na dare, direbansa yaje ya ɗakkosu daga airport suna tafe suna hira, kawai aka tare motar tasu. Widad na ganin mutanen da suka taresu ta gigice, yanayin jikinsu sak wanda suka kashe Ammi, gasu da mask a fuskarsu. "Kai buɗe motar nan"! Ɗayan yayiwa direban Daddy tsawo Widad ba zata taɓa mantawa da wannan muryar ba, tabbas sune wanda sukaje har gida suka danne Umminta da pillow, nan da nan jikin Widad ya ɗau rawa, amma ta dake taƙi nuna alamar Hakan. Suka bubbuɗe murfin motar, Daula ya rungume Widad a jikinsa yana ta nanata Hasbunalahi wani'imal wakil, suka fizgo direban Daula ƙasa suka saita masa bindiga. Ɗaya daga cikinsu Wanda Widad bazata manta dashi ba, shine wanda taji yana wayar nan ranar da suka kasje mahaifiyarta, har ya ambaci sunan wani mutum, ya kalli Daula yace  "Nasiru Daula, haƙiƙa ina me tabattar maka da zaka bi matarka inda ta tafi idan har ka mana gardama, tambaya ɗaya zan maka kuma amsa nake so ta kai tsaye, ina wannan takaddun da wasiyyar da kayi na cewar akwai wanda yake da kashi bakwai bisa goma na dukiyarka suna ina?" Daula ya kalleshi cikin mamaki yace " dama dalilin da yasa kuka taremu kenan? toni babu wannan kayan a hannuna, kamar yadda nayi bayani lokacin da nayi hira da 'yan jarida" Cikin tsawa yace " kai, karka min wata taƙama da jin kai, babu wani amfani da taurin kai ko tsaurinka ze maka a nan, zan iya fasa maka kaibda harsashen nan" Ɗauke Daula yayi, yai musu shiru. "Ina takaddun nan suke?!" sukai masa magana cikin tsawa. Ko gezau beba balle susa ran ze basu amsa, yunƙurwa sukayi zasu danƙo Daula daga cikin motar, Amma Widad ta buɗe hannayenta ta tare mahaifinta. Daula yace "lovely, ki bari kar suyi miki wani abun kinji, karsu illatamin ke" "Am not afraid of anyone, abunda suke nema yana gurina, karsu ƙara yi maka tsawa" Kallonta suka shigayi, dudu ba zata fi shekaru takwas ba, amma kalli yadda take magana kamar ba yarinya ba. Hannu babban cikinsu ya saka ze fizgo Widad, amma Daula ya riƙita gam suna janta, shi kuma ya riƙeta gam. "Idan baka saketa ba zamu fasa kanta da harsashi!" Daula yace  "idan kuka kasheta kun kasheni, kuma kun rasa abunda kuke nema, kuma koda kun barmu a raye shima duk ɗaya zaku rasa abunda kuke nema, dan wallahi kome zakuyi da kaina bazan baku amana ba, bazan baku kayan da ba nawa ba, sedai idan Widad ɗince ta yarda ta baku bani da matsala da duk wanda ta ɗauka ta bawa" Zuro hannu ya kuma yi ze danƙo Widad, sedai a wannan karon bisa sa'a, Widad ta nuna musu ita mahaukaciya ce, dan kukan kura tayi ta datse yatsan mutumin nan a bakinta, ta kafa masa haƙora kamar yadda ta yiwa Fahad. Abun mamaki sega Ƙaton da yake ɗauke da bindiga yana kurma ihu, yasa kan bindiga ya daki kan Widad, wanda hakan yasa ta ƙwala ihu ta sake shi, sega jini na zuba ta hancinta ta sume a gurin, ganin Asirinsu na ƙoƙarin tonuwa yasa suka cika wandunansu da iska suka ɓace daga gurin. Daula gaba ɗaya ya rikice, ƙarshe direban ne yayi dabarar wucewa dasu Asibiti, aka kai Widad emergency gaba ɗaya Daula ya rasa abunda yake masa daɗi, matsala daga wannan se wancan be maganin wannan ba waccan ta kunno kai. Yai shiru ya dafe kansa ya zubawa Widad ido, wadda ke kwance ruwa na shiga jikinta, ya kifa kai akan gadon da take yai kuka yai kuka, harya gaji yayi shiru, cikin dare Widad ta farka tayi juyi taji kanta yayi mata nauyi, ta juya taga mahaifinta ya kifa kansa a kan gadonta, ya riƙe hannayenta, da alamu yana cikin matsananciyar damuwa, a hankali tayi juyi ta rungumo kan Daddynta ta kwantar da kanta a kan nasa, a haka bacci ya ɗauketa. Wayewar gari labari ya cika gari, ga abunda ya sami Daula da 'yarsa nanma akayi ta tururwar zuwa Asibiti dubata. Daula ya tafi masallaci salla sega wasu mutane sun shigo ɗakin nata, wai sunzo dubata, ta dinga binsu da kallo, suka zazzauna, kallo ɗaya ta gane wanda ya buga mata bindiga jiya, wanda suka kashe Amminta ne, bata taɓa ganin fuskarsa ba se yau, bata ƙara tabattarwa ba seda ta kalli inda ta gasa masa cizo jiya, a hankali yace   "ina baban naki?" Shiru tayi ba tace masa komai ba, yazo gaban gadonta ya durƙusa sannan kalleta yace  "Baby girl, tambayarki zanyi kinji ko? Ina abubuwan da Dad ɗinki ya baki ajiya, su nake son ki gayamin inda suke kinji, nima bazan gayawa kowa ba" Widad ta tsare shi da manya manyan idanunta tana masa wani irin kallo, daya kasa gane na menene? "Baby ki gayamin kinji" Still ba amsa, ya ɗakko wata ƙaramar wuƙa yace "idan baki gayamin ba, zan gutsutsura naman jikinki da wuƙar nan, in dafa in cinye, gayamin nace" Yai maganar yana zare mata ido. Ya ɗauka Widad irin yaran dazewa barazana ne, amsar data bashi shine  "idan ka kasheni bakomai, nasan dai Daddy zeyi kuka, amma nasan wanda ya kashemin Ammina" tai maganar tana kallonsa A fusace yace "ina ruwana da wanda ya kashe ta? Kema kashe ki zanyi in kashe babanki idan baki faɗan ba" Maimakon ta bashi amsa, se tace "Na rubutawa DSP wasiƙa, zan gayamasa wanda ya kashe Ammina, yayimin Alƙawarin ze gano suwaye" "Ke dan ubanki ba wannan muke tambayarki ba, ina kayan nan suke?" Widad bata nuna ta ganesu ba, ta sake kallon hannunsa tabbas shine babu ko tantama, ga inda ta cijeshi jiya a tsintsiyar hannu, abun da ya faru ranar da aka yi kisan ya sake dawo mata ranta, gani tayi ya miƙe ya ɗakko handkerchief a aljihunsa ze saka mata a hanci, nan experience ɗinta na kallace kallacen films ya dawo mata, bata san ya akayi ba ta fasa ihu, ta ɗakko kwalbar malt zata buga masa, ai kafin tayi wani yunƙuri, sun bar ɗakin nata da sauri, nan ta cigaba da kurma ihu tana jifa da kwalabe a ɗakin. Da gudu Daula dasu Bulama, da ɗan sandan Da Widad ta saka ya kama Bala, suka ƙaraso ɗakin, dama suna kan hanyar zuwa ɗakinne, Daula yayiwa ɗansandan waya, yayi masa bayani, shine ya taho Asibitin. Tayi watsi da kwalabe tana kuka, Daula jiki  a sanyaye ya karaya, tabbas hauka ya tabatta akan Widad, ta haukace. Daula yana da matuƙar raunin zuciya, dan haka kuka baya bashi wahala, haka ze zauna idan damuwa tayi masa yawa yaita abunsa. Yazo kan gadon nata ya zauna, aikuwa nan da nan ta rungume shi, tana ta sauke numfashi kamar wadda tayi dambe. Ɗansandan yace "Alhaji, wannan harin da aka kai muku jiya, ya tabattar da maganar Widad, kashe matarka akayi muma munata tattara abunda bincike ya nuna mana, Insha Allah kamar yadda nayi Alƙawari, se naga abunda ya turewa buzu naɗi" Daula yace "nagode sosai ranka ya daɗe" Bulama yace "Nasiru kaga tashi muje a maida yarinyar nan gurin Likitan nan, ya duba ta asan halin da take ciki, abun nata gaba yake fa" Babu tunanin komai, Daula ya amince, Bulama ya saɓa Widad a kafaɗarsa, suka fito sedai tasa tafukan hannayenta ta rufe idonta, saboda bata san haske kuma bata son koda wasa ta sake ganin mutanen nan. Asibitin doctor Hamisu suka wuce, ya karɓesu hannu bibiyu, ya sake ɗurkawa Widad allurai wanda suka sake rikita ta gaba ɗaya, sannan ya ɗirka mata allurar bacci. Gaba ɗaya seda inspector ya kamu da matsanancin tausyin Widad, yarinya ƙarama amma rayuwarta a garari haka, ya kalli Daula yace "ranka ya daɗe, yakamata ace an sake tsananta matakan tsaro, a hanyar gidanka saboda kariya ga lafiyarka da kuma ta 'yarka, ina jin tausayin yarinyar nan, kuma nayi mata Alƙawari insha Allah bazan mutu ba zan cika mata, tacemin zata yi magana dani rannan, tace maganar tana da mahimmanci sosai, dan haka insha Allah zan sake zuwa, in duba ta sannan inji maganar da zata yi min" Daula yace "Nagode DSP da wannan ɗawainiya da kake, Allah yasaka maka da alheri" "Karka damu, aikina ne yin hakan ai, Allah ya bawa Baby lafiya" Kwana biyu da tafiyar DSP, lokacin Widad ta farfaɗo, a lokacin aka sanar da rasuwar Wannan DAP Na 'yan sanda da yake faɗi tashi akan case ɗin, ranar da ya bar gurin Widad, akayi masa kiran gaggawa Lagos, akan hanyarsa sukayi artabu da' yan fashi aka kashe shi. Daula ya kaɗu matuƙar gaske da jin wannan labarin, ya shiga damuwa haka kurum zuciyarsa ke raya masa, ba haka abun ya faru ba, yanzu kenan duk me niyyar taumakonsu se anga bayansa? Wannan karonma farkawar Widad yazo da sabon salo, bayan rashin magana ma, sam bata son haske sedai a rurrufe ko ina, ko yaya haske yake bata sonsa komai sedai tayi a ɗaki. Ta ƙara shiga damuwa da taji labarin mutuwar DSP, dukda ba magana take son yi ba amma tayi kuka sosai. Tace  "Daddy" Daula yace "Na'am lovely na" "Daddy dan Allah, ko duk kuɗinmu zasu ƙare, karka bari a saki Bala megadi" "Insha Allah Baby, bazan bari ba amma na fara damuwa, gashi baki da lafiya, gashi an fara kashs duk masu niyyar temakonmu" Ta kalli Daula tace "idan an kashe masu taimakon mu, Allah ze temake mu, idan kaje gaisuwa kayiwa iyalinsa alheri, ka basu haƙuri" Daga nam ta kwanta bata sake magana ba. Gaba ɗaya Daula ya ajiye batun harkar kasuwanci a gefe, ya tattara hankalinsa akan lafiyar 'yarsa. Suna zaune da Bulama a falon gidansa, Bulama yace "Daula, zamanka fa da Widad a gidan nan baze yuwu ba, zuwa yanzu ya kamata kayi Aure kodan ka samu me ta yaka kula da ita, ga harkokinka suna nema su tsaya, ni da zaka yadda dana ɗauketa, saboda ina son Yarinyar nan" Daula yace "nasan kana son 'yata Bulama, sedai koms za' ace sedai ace, zan cigaba da kula da ita, ina nema mata lafiya, yanzu abunda ya dameni ina son in samo malamai suzo su raba gadon Huda" Bulama yace "wane irin gado kuma? Naga dama idan wani abu take dashi kaika bata, tunda ta mutu ai ya zama naka" Daula ya girgiza kai yace "A'a, akwai kuɗaɗenta masu yawa da bani lokacin da mukayi Aure, ina son a ware natane a cikin dukiyata, idan aka ware zan mallakwa Widad su" "Kamar yaya? Da can ka ware kashi bakwai, yanzu kuma Allah kaɗai yasan kashi nawa zaka kuma warewa, Widad ɗin da take yarinya me zata yi da dukiya? Kuma yanzu idan duk ka kwashe kuɗaɗen nan, kasan adadin mutanen da zasu durƙushe kuwa? Mutane dayawa da Allah suka dogara, amma suna daga kwamce suke Arziki saboda kasiwancinka" "Nasani Bulama, amma hakan baya nufin zan janye kuɗaɗen ne, zan cigaba da juyasu, amma zan canza suna na dana 'yata akan abunda yake mallakinta, kuma insha Allah idan naga maganin da ake mata anan beyi ba, zamu dan gana da ƙasashen waje ne kawai" Widad fa ba zuwa makaranta, kullum se a gida banda zabure zabure da ihun da take yi cikin dare, ga ƙin mutane dan a tsorace take da mutanen nan kar su sake dawowa su cutar da su. Sedai a hakan an cigaba da yiwa Daula barazana iri iri ta waya, ace za'a kasheshi ko za'a sace Widad idan be faɗi inda takaddun nan suke ba, tun yana zarya hukumar 'yan sanda harya haƙura gaba ɗaya. Bulama ya saka Daula a gaba da yayi Aure, dan ba mutuncinsa bane babban mutum kamarshk ace bashi da Aure kuma yana zaune da gashi se ƙaramar yarinya a gida ba. Daula yace "sam baze Aure ba, yazan babu me maye gurbin Huda" Bulama yace  "idan balarabiya kake so, kana da kuɗin da zaka je kowani ƙasa ka auro mace, wadda kake so" Daula ya kan ce masa "ba balarabiya nake so ba, nagarta nake nema irin ta Huda" Bulama ya matsa, ya dage ya takurawa Daula, Daula yace "nifa ka ƙyaleni, lafiyar 'yata ta fiyemin wani Aure" Amma Bulama ya cigaba da matsawa, gefe guda kuma anata bankawa Widad allurai da ƙwayoyi da suke birkita mata lissafi, ƙiri ƙiri ta dena zancen zata faɗi wanda ya kashe Amminta, gaba ɗaya aka tsaya da zancen ma, a haka aka daddafa aka fara shari'a da Bala, anan Daula yayi amfani da tasirin dukiya, shari'a taƙi gaba taƙi baya aka tsare Bala, da rundunar sojoji sunso kawowa Bala ɗauki, Kasancewar nasu ne, sedai Daula yai amfani da kuɗinsa, hakan yaƙi tasiri. Ganin Daula bashi da niyyar yin Auren nan, gaba ɗaya ya tattara hankakinsa akan 'yarsa yasa Bulama da kansa nemawa Daula matar daze Aura, sedai me....... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 80_81 Daula yace "se Widad ta amince tukuna" abun ya bawa Bulama Haushi sosai yace "haba Nasir, kaima ka zama ƙaramin yaron kenan? Ya za'ayi kace se Widad ta amince? ita meta sani game da wannan maganar?" Daula yace "Yarinyar nan itace uwata, itace Ubana itace komaina a yanzu, dan haka duk hukuncin data yanke shikenan" Bulama yaji kamar yayiwa Daula dukan tsiya ya huce, haka ya ci gaba da cusa masa matar nan, 'yar uwace a gurin Bulama matar, sun rabu da mijinta tana da yara Uku, mijin idan ya shura takalmansa se yayi wattanni ba'asan inda yake ba, ga ba Abinci ya barta da yar taita wahala shine aka raba auren. Daula fafur yaƙi maganar sam, Ita kam Gimbiyar wato Widad ana cigaba da sake birkita mata tunani, ta hanyar ƙwayoyi da kuma allurai, gaba ɗaya ta koma wata iriya abun tausayi, wani lokacin idan ta rasa me yake damunta sedai tayi ta kuka, takasa banbance a aace duniyar take. Wani lokacin haka kurum tana zaune, sedai taji ana mata ihu ko ana kuruwa a cikin kunnuwanta, ko taga duniya tana juyawa, ko kuma taji kamar ana buɗe ƙofa za'a shigo kawai se zuciyarta ta bata mutanen nan ne zasu shigo. Abun duniya ya ishi Daula, ga surutun mutane ya fara masa yawa akan yakamata yayi Aure, bekamata ya cigaba da zama haka ba. Bulama yace  "kaga Daula, tun wuri ya kamata ka nemawa kanka mafita, kai ba dan Allah yasa kana da nasibi akan harkar kasuwanci ba, da tuni kasuwancinka yazo ƙarshe gaba ɗaya, kuma kaɗaici ze iya sawa Widad ta ƙara shiga wani hali, babu yadda za'ayi rayuwar yarinya ƙarama ta yuwu ba tare da mace me kulawa da ita ba, kai a yanzu taurin kai ba naka bane, kaje ka samu kayi Auren nan ko hankalinka yafi kwanciya " Daula yace " Bulama ba naƙi inyi Auren nan neba, bana son in Auri wadda zata zo takasa jure zama dani, wadda zata ƙarasa kassarani, yanzu duk macen da zan aura, zata aureni ne dan dukiyata, matata ta fari kuwa ta Aureni tun banda komai, shiyasa nake jin tsoron hakan, ko in Auri mace ta haihu dani in kasa daidaita adalci a tsakanin 'ya' yan, dan bazan taɓa kamanta ƙaunar abunda Huda ta bari da wani ba, Allah sarki Huda ba ita ba abunda yake cikinta, Allah ya jiƙanki Huda ya saka miki kissan gillar da akayi miki" Bulama ya dafa kafaɗarsa yace "Nasir, Kayi haƙuri, zan samo maka mace me hankali, kaga Haliman nan muyuniyar kirkice 'yar uwatace, mijin tane ta Aura Azzalumi, ƙarshe aka raba Auren, nayi imani da Allah zata zauna da kai lafiya, harta kula da Yarinyar nan tunda kaƙi bani ita, da naso ka bani ita kafin kayi Auren se in dawo maka da ita, amma kace kafi son ka kula da ita, tunda hakane gara ka lallaɓa kayi Aure, amma zaman da kake haka be dace sam, kuma kaima ka sani" Haka Bulama yaita lallaɓa Daula, harya yadda zeje su gaisa da ita matar. Duk da rashin lafiya na Widad, haka ya shiryata suka tafi tare, gidan da Halima take duk a kwararraɓe ba gyara, aka masa iso sitting room ɗin gidan, tunda sukaje Widad take kallon gidan, ita bata taɓa ganin gida a haka ba, gashi ɗan ƙarami gashi wani irin. Halima taitawa Widad magana amma taƙi kulata, Alhaji Nasir yace  "Halima kinga 'yata Widad, kuma bata da cikakkiyar lafiya tun rasuwar mahaifiyarta ta samu matsalar Ƙwaƙwalwa, bata yadda da kowa ban saniba ko zaki iya zama da ita, danni da banyi niyyar yin Aure ba, amma saboda Bulama ya matsa, kuma ke' yar uwarsa ce yasa nace to shikenan na amince, amma ya kikace? " Halima tace " insha Allah zan iya zama da ita in kula da ita, tunda kaga nima ina da yara, in Allah ya yarda baze gagara ba" Daula yace "Masha Allah, idan ba zaki damu ba, mahaifin yaran baze ce komai ba, zaki iya tarewa tare dasu, mu zauna gaba ɗaya" Nan ta rusuna tace "Masha Allah, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi Alhaji" Yarane sukayi sallama, suka amsa musu gaba ɗaya, su ukune bini in bika, sanye da uniform ɗin makarantar gwamnati, kowannensu hannusa ɗauke da jakar nan ta da wadda ake cewa Baba nagode, takalmansu Sandal wanda ake cewa ganda, duk sun tsufa sun cinye, sun tsitsinke. Yaran Biyu mata ne ɗaya namiji, suka gaida Daula, ya amsa musu cikin fara'a, Widad ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya, tana kallon suturar jikinsu, duk wani iri haka take ganinsu. Namijin ne wanda aƙalla ze kai shekaru goma sha huɗu yace  "Mama, wannan wacece?" Yai maganar yana nuna Widad, Halima tace "to sarkin surutu, aje a cire Uniform". Daula yace "A'a ba'a gwale yaro ai, Ya sunanka ne?" Yaron yace  "Anwar" Daula yace  "Masha Allah, itakuma sunanta Widad ƙanwarka ce" Anwar yai murmushi yace  "Mekyau da ita, Baby zomu gaisa" Haɗe rai Widad ta ƙarayi ta kwanta a jikin Daula, Daula yace  "ai bata da lafiya ne Yaya Anwar" Anwar yace "Allah ya bata lafiya, ina da sweet bari in baki kina so?" Yai maganar yana zura hannu a jakar makarantar sa, ya miƙo mata alewa 'yar uku biyar guda biyu, ga mamakin Daula yaga tasa hannu ta karɓa tace  "thank you" Nan Daula ya shiga murmushi, abunka dame ɗa, nan ya fara jin insha Allah a hankali Widad zata ware, ta saki jiki dasu idan ya Auri Halima, Sukam yaran matan kallon Widad kawai sukeyi, kyakkyawa da ita, ga gashi dan kanta ko ɗankwali babu, tana sanye da riga da skirt kamar 'yar turawa, tana kwance a jikin Babanta ta buɗe alawar nan tasa a bakinta, ta buɗe ɗaya tasawa Daula a baki gwanin ban sha' awa. Suka tashi tafiya Daula ya babbasu kuɗi, babu ko kara suka karɓe, sedai fafur Anwar yaƙi karɓa yace tunda an bawa Su Amal da mamansu baze karɓa ba, juyin duniya yace a'a, Widad ta zura hannu a aljihun mahaifinta ta ɗakko kuɗi taje ta miƙawa Anwar kuma ta tsatstsareshi da ido. Daula yace "Good, kuma ba'a maida kyautar Gimbiya, ni idan na baka kaƙi karɓa, ita ba'a maida mata da abu idan ta bayar" Haka Anwar yasa hannu ya karɓa ya dinga godiya. Nan Daula yaji daɗin ƙauna da karamcin da sukayi musu, dan haka ya amince da Auren Halima, amma yace baze zauna a wannan gidan ba canza gida zeyi. Ya sanar da Bulama sun amince, haka Bulama ya wuce gaba Daula ya auri Halima, sannan yace ta taho da 'ya' yanta ze riƙe mata. Suka tare a sabon gidan Daula, sedai fa wannan rashin yaddar na Widad yana nan, sam basa gabanta bata damu dasu ba, har gara Anwar shima wani lokacin take ɗan yadda dashi, amma Ramlah da Amal kam bata ɗaukesu wasu mutane bama. Part ɗinta daban a cikin gidan, dan karma wani ya takura mata. Halima kam tana Auren Daula nan da nan 'ya' yanta suka koma ce mata Mummy daga Mama, nan da nan sukayi shar, Daula ya sauya musu makaranta zuwa ta 'ya' yan masu kuɗi, ha ajiye musu direba da yake kaisu yana dawo dasu, komai shar dasu nan da nan suka fara canzawa, sedai babban abunda yake tsayewa Halima shine, Daula ya fifita 'yarsa akanta, ko magana tayi idan Widad ta rusheta ta zauna a gurin Daula, idan wani abu kake so a hannun Daula muddin Widad ta amince ka samu, wani lokacin ma itace zata baka, dan haka ta ɗorawa Widad karan tsana. Ƙwayoyi da Alluran da akewa Widad sunyi tasiri a jikinta, ya zamana ko ba abata ba, haka kurum zata fara wannan fizge fizgen da iface ifacen, idan har Daula baya nan haka zata yi ta faman wannan kuruwar, suna jinta babu me kawo mata agaji, haka wasu lokutan zata jiyawa kanta rauni, ta gama ihun harta gaji ta faɗi, Anwar ne kawai idan yana nan yake iya taimakonta, Abinci idan anyi se anga dama za'a bata, ita kuma baza tace a bata ba, amma a gaban Daula Suyita nan nan da ita suna bata kulawa da nuna mata soyayya, baya kaso komai a ransa saboda halin ko in kular da take wa su Halima, saboda yana tunanin yanayin ciwon nata ne. Tun daga nan Widad ta ƙara tsinkewa da lamarin mutanen nan, suyita nuna mata kulawa a gaban mahaifinta, amma  daga ita sesu suyi ta zaginta, suna ce mata mahaukaciya. Hakan yasa ta ƙara zame jikinta daga garesu, sam bata iya fitowa tayi karo dasu, babban abunda ya ɗaure mata kai, be wuce yadda taga mutumin da taji an ambaci sunansa ranar da aka kashe Amminta, yazo gidanba a lokacin Daddynta baya gari, abun ya ɗaure mata kai sosai, ya daɗe a gidan sannan ya tafi, kafin ya tafi zuciya ta dinga azalzalar Widad taje tai masa wani abu daze illatashi, amma ta gagara aikata komai. Jikintane ya fara tsuma, ta dinga tuna abunda ya faru, nan ta faɗi tana wannan ihun da take yi idan abun ya motsa, suna jiyo kururuwar Widad amma kota kanta basu biba, haka ta dinga gurnani ita kaɗai. Anwar ne ya shigo, yace "Mummy ina Widad ne?" "Kaje ka duba mana" Anwar  ya tafi ɓangarenta, yaje ya tarar da ita a zube a ƙasa a falonta, gaba ɗaya bata hayyacinta, a gigice Anwar ya fito falo yace  "Mummy, Widad fa ba lafiya, tana sume a ɗakinta" Halima ta lura da yadda Anwar yake nan nan da Widad, taga alamun bazata samu goyon bayansa ba, dan haka ta maze sukaje kan Widad, ya kwantar da ita akan kujera, aka kira likita, yace akaita can Asibitinsa, nan fa ya kuma ɗura mata wannan allura me kama da ta doki, wadda ke gigita Widad. Cikin tangaɗin wahalarwa da allurar ke mata, bata gane komai ga idonta a buɗe amma sam bata cikin hankalinta, Wannan mutumin da aka ambaci sunansa ne yazo kanta, ya ƙura mata ido sannan yace  "Ke ki gayamin inda kayan nan suke, takaddun nan da ubanki ya baki ayce akwai mesu, suna ina?" Kallonsa Widad take, bata gane gaskene abun yake faruwa ko kuma mafarkin ne, ta kai idonta gefe taga Halima a zaune a gurin, lumshe idonta tayi taƙi magana. Cikin tsawa yace " zakiyi magana ko sena miki azaba, irin wadda ba'a taɓa miki makamanciyarta ba"? Ko gezau ba tayi ba daga inda take, ta lumshe idonta tamkar bacci ya ɗauketa Halima tace  "bafa a hayyacinta take ba" Mutumin yace  "Aikuwa zata dawwama a haka muddin ba zata faɗa ba, semun kashe Uban nata, an dinga ɗirka mata allurar nan kenan, da ƙwayoyi seta zama mahaukaciya tuburan ta girma tana yawo tsirara tana bin bola saboda rashin gata" Widad najinsa, wani irin ƙuna ranta ya shiga yi, yasa an kashe mata mahaifiya, kuma yazo kanta yana gayamata maganar banza, sam takasa gane ko mafarki take ko a zahiri abun ya faru, ganin haka yasa hawaye ya fara bin gefen idonta, ta tabattar da ta haukace. Can bayan wasu awanni, taji an taɓata ai wani kukan kura tayi dan a zatonta wannan mutumin ne, ta kai masa wata irin mahaukaciyar shaƙa tana zazzare ido, sedai kuma se taga ashe mahaifinta ne, da farko fuskar wancan ta gani, daga baya kuma taga ashe Daddynta ne, ba ƙaramin tsorata Daula yayi ba, tunda har Widad ta fara ƙoƙarin shaƙeshi to tabbas hauka ya tabatta, a hankali ta ajiye hannunta ta kwanta a jikin Daddynta. Ko mintuna biyu ba'ayi ba kuma se bacci, amma cikin baccin banda mafarke mafarke ba abunda take yi, seta dinga ganin mafarkan kamar gaske, dan haka seta ƙwala ihu. Sosai fa Daula ya shiga damuwa, Doctor Hamisu yace  "Ranka ya daɗe, kaga ana treatment ɗin nan but her body is not responding to the treatment, dan haka she needs to be admitted to psychiatric Hospital, yadda za'afi kula da ita" Hawaye ne ya ƙwacewa Daula yace "Over my death body, in ɗau 'yata da hannuna in kai psychiatric, bazan iya ba, zan cigaba da kula da ita, idan yaso a cigaba da mata treatment" Bayan ta ɗan farfaɗo, ya ɗau' yarsa yayi gida, kwana biyu ta ɗanji sauƙi amma lokaci lokaci takan yi ihun nan na dare. Daula yana zaune da Halima da yaranta a falo suna hira, harda yaranta da jansu yake kamar 'ya' yansa, Widad ta fito tana taku ɗai ɗai tana kallonsu, Babban abunda ya ƙular da Halima be wuce yadda Daula ya miƙe tsaye ba domin tarar Widad, sekace yaga wa shugabarsa, gata gwansamemiya da ita, kusan shekara tara amma haka yake ɗorata a cinya kokuma ya goya ta a bayansa, ta zauna a cinyar Daula tace "Daddy, tunda babu me dubamin wanda ya kashe Ammina, ina son gidan nan da Ammi ta rasu ka siyomin su zomo, su mage da duk domestic Animals, ka haɗa dana Ammi in dinga ganinsu" Daula yace  "considered it done your majesty, yadda kike so haka za'ayi, kwanan nan ina son in buɗe miki Account mu dinga tara ribarmu ta kasuwanci nida ke" Murmushi kawai Widad tayi ba tace komai ba, se can tace   "Daddy wai na dena zuwa makaranta ne?" Daula yace "ina so ki warke ne tukuna, bana son a kaiki makaranta ki cigaba da rashin lafiya" Widad tace  "Daddy bana son zaman gidan nan kwata kwata" Cikin Halima ya ɗuri ruwa, ta zata Widad zata tona mata Asiri, amma se tace  "idan ina nan ina tunanin Ammine sosai" "Babyna, shiyasa muka taso daga wancan gidan fa, saboda ki dena ganin abunda ze ɗaga miki hankali" "Nan ma akwai wanda yake ɗagamin hankali, kuma ni makaranta nakeso in koma, ka maidani gidanmu na England seka kaini boarding school" Shiru Daula yayi yace "lovely, zaki tafi kibar Daddynki?" "No Daddy, kaga nan kullum kana cikin damuwa saboda ni, ni kuma ina tsorata sosai anan, dan Allah ka kaini can bana son zaman nan, please Daddy" Daula yace "Shikenan, zan duba wace makarantar yakamata in kaiki" Anwar yace  "banji Daɗi ba, bazan ji daɗi ba idan kika tafi Widad" Widad ɗin dako fara'ar kirki ba tayi amma tai murmushi, dan Anwar yana nuna mata tausayi, ko Daddy baya nan idan shi yana nan suna sassauta mata, Widad tace  "ko zaka bini ne, mu tafi tare?" Anwar yace  "Ƙwarai kuwa, daga nan har birnin sin, idan zaki dani zan biki" Murmushi tayi tace  "aini makarantar mahaukata za'a kaini, kai kuma kana da hankali ai" Sosai Anwar yaji tausayinta yace  "Ai zakiji sauƙi insha Allah, zaki warke ki dena cewa kanki mahaukaciya" Girgiza kai kawai tayi tace  "Daddy, zanje in kwanta, ka rakani" "Shikenan muje gimbiyata" Halima da tun ɗazu ba tace uffan ba, dan wani mugun haushinsu take ji, da gashi har 'yar tasa. Kwana biyu da yin wannan maganar, cikin dare suna bacci aka kuma shigowa gidan, dukda tarin security dake layin gidan, still dai wannan takaddu suka sake biyowa, aka rufe ɓangaren Halima da' ya'yanta suka shiga na Daula suka tarar dashi yana bacci, Widad na bayansa tana bacci itama. Haka suka tashesu, Amma saboda gaddama da taurin kai irin na Daula daga shi har Widad suka ƙi magana, a gabansa suka dinga solata suna bugawa da ƙasa dan tayi magana amma taƙi, ba abunda Daula ze iya saboda kashedin da suka yi masa na zasu kashe Widad idan yayi wani yunƙuri. Wani daga cikinsu yakama kumatun Widad, da suke ɓulɓul jajawur saboda hutu, yasa Ƙaton hannunsa ya matse da ƙarfi seda tayi wani uban zillo dan azaba ta saki fitsari, amma taƙi magana se kace wata itace. Ƙarshe haka suka yi jifa da ita a galabaice, suka zuba mata ido, tana kallon Daula yana kallonta yana hawaye itama tana yi. Ɗayan yace  "Wallahi ban taɓa ganin halitta me taurin kan mutumin nan da 'ya' yansa ba, ba dan ba abamu umarnin kisa ba, da wallahi sena musu kisan wulaƙanci mafi azabtarwa" Ƙarshe haka suka haƙura suka tafi, Widad ta shiga tunanin ya akayi aka kuma shigowa gidan duk da tarin security ɗin nan? Ɓangaren Daula ma yanzu ya amince dole Widad ta bar ƙasar nan dan tseratar da rayuwarta, kusan kullum cikin turo masa saƙo ake akan idan be bayarba za'a kashe shi, ko a sace 'yarsa, tun yana damuwa harya fara sabawa. Ya nemi shawarar Bulama, Bulama ya goya masa baya akan ya fita da Widad ƙasar waje, hakan tamkar tseratar da ita ne. Haka kuwa akayi, Daula ya nemawa Widad makaranta a makarantar masu fama da larura ta musamman a ƙasar England, Anwar kamar yayi kuka, Widad tace tana son ya rakata makarantar, karon farko da Anwar ya hau jirgi. Daula yace "Mummynki fa bazata rakaki ba?" Cikin harshen larabci Widad tace  "ni ba uwata bace, uwata ta mutu bani da uwa a yanzu, kuma ni mahaukaciyace, babu wanda zeso ya zama maman mahaukaci" Daddy yai shiru yana kallonta, bece komai ba suka tafi airport, da ita da Daddynta, da Bulama da Anwar suka tafi, tana tunanin irin zaman da Daddynta zeyi da wannan matar me fuska biyu, dan ko a yanzu ta lura da tana wulaƙanta mata mahaifi wani lokacin, kuma baya iyayi mata magana. Haka aka kai Widad wannan makaranta, aka danƙata a hannun likitocin can ƙasar, Daula yana kuka itama tana kuka suka rabu. Tun a hanya kewar Widad ta damu Daula, Anwar ne yaita bashi haƙuri, dan Bulama ya gaji da rarrashin Daula. Haka ya dawo gida zuciyarsa fal tunanin Tilon 'yarsa, yanzu bashi da kowa se Allah se' yar nan, yana mata son da shi kansa be san kansa ba, dan duk ƙaunar da yakewa mahaifiyarta ta koma kanta. Kamar yadda Widad ta buƙata, wannan Ƙaton gidan nasu na farko, haka ya zuba dabbobin nan a gidan nan, dukda Widad ɗin bata nan. Kullum cikin hirarta yake da begenta, abun fa ba sauƙi, dan ba'a fasa masa barazana ba iri iri, ta waya akan dukiyar nan, ƙarshe ya ware kason Widad a dukiyarsa, itama yasa mata a kasuwanci aka cigaba da juyawa, haka rayuwa ta cigaba da tafiya. Da Anwar yayi candy, Daula ya ɗauke shi dashi da Fahad ya kaisu ƙasashen waje yayi sponsoring ɗin karatunsu, da komai da komai. Amal da Ramlah kuwa manyan makaratun yaran masu kuɗi suke yi, ya mallakawa Halima kadarori da dama, taje Saudiyya ita da yaranta, duk ƙasar da suke so sunje, an kai waninta ma, amma gaba ɗaya bata gani ba, wannan dukiyar ce take hari itama, ga baƙinciki da kishin da take da Widad da Huda wadda ta riga ta rasu, jin maƙudan kuɗin da suke Asusun Widad kawai ba ƙaramin firgita ta sukayi ba. Saleh kuwa bayan an kama Bala ɗanuwansa, maƙiyan Daula sukayi amfani da shi suka sa aka kai shi gidan Daula yin aiki, dan ya zame musu CID, suka cusa masa aƙidar lallai yaɗau fansar abunda akayiwa ɗan uwansa Bala. Haka Widad ta cigaba da rayuwa, a cikin mahaukata iri iri, ana cigaba da bata kulawa a can, komai yi musu akeyi, Daula na yawan zuwa ganinta, dan wasu lokutan har gidansa na can yake tafiya da ita, suyi kwanaki su sha hira sannan in ze tafi ya maida ita, lokaci lokaci Bulama ma yakan kai mata ziyara, a bayan gidansu gidan Alhaji Musa yake, dan haka sukan haɗu da juna. Lokacin da zata shiga high school (secondary school) tace lallai se an cire ta daga makarantar mahaukata, dan ita ta warke, da yake Daula baya son ɓacin ranta haka ya cireta, da yake dama Asibiti ne haɗe da makarantar masu buƙata ta musamman. Daula ya taho da Hajiya Halima da yaranta, amma a ranar seda jikin Widad ya kusa motsawa, ta birkice masa sosai, tace "kodai su bar mata gidan nan, ko ita ta bar musu" Daula yace "daughter, Mummy cefa kuma dan su ganki suka zo" 'Daddy karka ƙara ce mata Mummy na, kuma ina neman alfarmarka, idan har ina England karsu ƙara sa ƙafa a ƙasar nan, nan gidan Ammi ne da ita muka rayu a cikinsa, dan haka bana buƙatarsu anan " Aikuwa jikin Daula yana rawa, aka maida su Hajiya Halima Hotel, abun nan ya baƙantawa Hajiya Halima rai fiye da tunani. Tun daga nan suka fara takun saƙa, duk isa da hura hancin da Halima take yi se Widad tayi abunda zata nuna mata bata isa ba. Widad ta shiga high school, itama boarding ce, amma bata mahaukata ba. Daga ƙasar da take idan taso se tayo waya, ta bada umarni a Nigeria kuma abunda tace shi za'ayi, duk azabar bin malaman Halima, amma ta kasa raba Daula da Widad. Wataran Widad tazo hutu Nigeria.... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: .LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 82_83 Lokacin da tazo Nigeria, maƙerin budurci ya fara ƙera Widad, ta fara zama budurwa me ji da kyau, zamanta a Turai sam bata san saka wata Atamfa ko makamancin kayan al'ada ba, da Amminta na da rai ma mafi yawan rayuwar su tana Turaine, dan haka sedai a saka mata blouse, yanzu kuma babu ran mahaifiyarta, gashi a tsakiyar turawa take, dan haka duk shigar da taga dama yi take ba wanda ya damu, Daula ya ɗaukar mata Nanny, idan anyi hutu tana gidansu na can, ita da Nannynta wata 'yar Nigeria ce amma bayerabiya, sedai a dafa taci, hatta gadonta da zata kwanta ta tashi sedai a gyara mata, saboda haka bata iya komai ba. Itama Nannyn Widad ba wani yadda take da ita ba, gani take duk wanda ta yadda dashi ze iya cutar ta, ba abunda Widad ta iya na aiki, duk wani abu yi mata ake, ba wata wahala data sani a rayuwar ta, komai ta nema akwai available, kuɗi ko nawa take buƙata akwai shi available. Widad tazo Nigeria, Daula ya dinga murna dan kusan shekararta Biyar bata taka Nigeria ba, sedai tunda ta dawo babu ragayya ko sassauci tsakaninta dasu Amal da babarsu, sam basa gabanta idan tana rayuwa a part ɗinta mantawa take dasu, Daula ya dinga zagayawa da ita guraren kasuwancin sa, da wanda yasa aka buɗe mata, taje har tsohon gidansu data sa aka maida shi na gona, gurin yayi mata kyau, tasa aka gyara mata wasu abubuwan aka canza mata wasu, ta cewa mahaifinta wato Daula tana son a siya mata dokuna biyu irin na wasan polo a saka mata a gidan, sannan aka kawo wani kare nasu, wanda yake a ƙasar waje, tasa aka kawo shi gidan aka ajiye. Cikin hira Daula yake gayawa Hajiya Halima batun siyan doki, yace "kinga rigima irin ta 'yarki ko? Saboda rigima wai dokin polo takeso a siyo a samata a wancan gidan namu, nasa ayo mata order su" Dama Hajiya Halima tayi tayi su koma wancan gidan, dan yafi haɗuwa da girma amma Widad tace baza"a koma ba, ƙarshe ma tasa aka zuba mata kiwon dabbobi a ciki, wani ɓangaren gida sosai, wani ɓangaren gidan gona. Hajiya Halima tace "Yanzu kai Alhaji saboda ka rasa abunda zakayi da kuɗi, seka sai wannan dokunan? Suna fa da tsada, kuma me zata yi da wasu dokuna tana mace" Daula yace "Ai babu itace damuwa, amma tunda akwai za'a sai mata, ian son abunda takeso, kin san ba wata lafiya ce sa ita ba, shiyasa nake son yi mata abunda takeso, kodan ta samu farinciki, na rasa me zanyi wanda ze dinga ɗebe mata kewa, yasa ta sake da kowa" Widad data kawo kai zata shigo falon Daddy taji wannan maganar da suka yi, da yadda Halima take kushe a sai mata abunda takeso, Widad ta maze ta shiga falon ta kalli Daula tace  "Weldone Dad" "Weldone my Queen, how are you?" "Fine Daddy" Yace "Masha Allah, Alhamdilillah, ya akayi ne, ko zuwa zanyi?" Widad tace "No but Daddy, i see over twelve cars in the parking space, what are they used for?" Daula yayi murmushi yace "na gidane, wanda muke hawa, ni nawa biyune kawai sauran na mamanki ne da Yayyaenki, tunda kinzo kema se ki sai wanda kike so" Widad ta haɗe rai cikin hura hanci tace "Niba uwata bace, bani da uwa dan haka bata haifeni ba, , and na saka a kwashe motocin a kaimin su farmhouse a ajiye, na barwa kowa mota ɗaya yayi amfani da ita ta isa, kai kuma an bar maka naka my king" ta ƙarasa maganar tana murmushi. Daula yace "to babu laifi, godiya muke gimbiyar Daula, yadda kikace ai haka za'ayi" Tayi wa Hajiya Halima wani kallon tsana na baki isa ba sannan ta fice, tana fita Halima zata fara complain, amma Daula ya dakatar da ita yace "itama dukiyarta ce, duk yadda tayi daidai ne" Halima taji kamar ta samo abu ta kashe Widad dan baƙin ciki, tun daga Nan fa suka dinga takun saƙa da Widad da matar babanta, bata ganin mutuncinsu sam, sannan bata yadda da kowa ba, sakamakon duk wanda suke cutar da Mahaifinta Yaran talakawane daya janyo a jikinsa sukayi Arziki sanadinsa, wanda ya yarda dasu sune suke cutar dashi. A wannan zuwan ma, seda akai kaiwa Widad Mummunan Hari, akaso a sace ta amma Allah ya kuɓutar da ita, daga nan ta tattara komatsanta ta koma England ta cigaba da zuwa makaranta. Daula ya bubuɗe guraren kasuwanci da kuɗinta, ciki hadda manyan gidajen gona, shagunan kasuwa da sauransu, dan haka Widad ma ta kasance 'yace me arziki a ƙashin kanta. Gaba ɗaya a rayuwarta batayi zaman shekara shida a Nigeria ba, shiyasa abubuwa da dama ita bata sansu ba, ko in anyi take mamaki. Wannan hali da ta tsinci kanta a ciki a rayuwarta yasa, ta yanke ƙauna da samun mutanen kirki, wanda ze zauna da kai a halin akwai ko babu, kuma ta yadda cewa duk talaka ze iyayin komai akan kuɗi, ta yadda idan har ka amince da mutum ya shiga jikinka, shine na farko daze fara cutar ka, ta lura mutane da yawa suna nuna mata kulawa ita da mahaifinta ne saboda wannan dukiyar da suke da ita, da babu wannan dukiyar da ba zasu dinga mutuntasu haka ba, dan haka itakuma take taka duk wanda taso. Tun data bar Nigeria a wannan lokacin bata kuma dawowa ba, seda ta cika shekaru goma sha takwas, bayan shekara huɗu kenan, lokacin ta zama cikakkiyar budurwa, yanayin tsarin rayuwarta duk na turawa ne, dukda hali na rashin sakewa da mutane da take dashi, amma tana zuwa gurin shaƙatawa da buɗe ido. Bayan gama high school ɗinta tace a Nigeria zata zo tayi karatun Jami'a, saboda kawai ta ƙallafa ran seta ta gano suwaye kuma suke da sa hannu akan kisan mahaifiyarta, suke cigaba da bibiyarta da mahaifinta akan dukiyar nan? Kuma tana son nunawa Hajiya Halima iyakarta saboda zaƙewar da take tayi yawa, da yadda take juya Daula yadda take so. A wannan dawowartata ne aka kawo mata kusan direbobi uku, amma da sun fara aiki se taga kamar an haɗa baki dasu zasu cutar da ita, dan laifi ƙalilan seta kori mutum, bata ragayya bata sassauci bata afuwa ga ƙarya ko yaudara. Dukda wannan tsawon shekaru, Magungunan nan basu dena aiki a jikin Widad ba, sakamakon ƙarfinsu ne da pressure da suke bawa jikinta yasa ta kamu da ciwon zuciya, ko kuma haka nan jikinta ya rikice ta fara wannan tsoron. Widad ta ɗanyi shiru sannan tace  "Nasan akwai abubuwa da nayi da kake buƙatar sanin dalilina na yinsu, akwai ranar da mukaje Hotel nace maka ni karuwa ce, naje wannan Hotel ɗinne, dan ganewa idona wani abu kuma na gani, wasu mutane ne da nake zargi da sa hannunsu, na gansu tare da matar Daddy, da alama sunyi meeting ne, kuma nasan akan Daddy ne, munje Club tare ranar harka hanani shiga, naje ne domin in kama Fahad red handed ta yadda maganar Aure tsakanina da shi zata rushe, haka nan tun zuwanka naji wani sashi na zuciyata nason Amincewa da kai, dukda wani ɓangaren yana gargaɗina, nace bari in jarrabaka tukuna, duk inda zanje nake tafiya da kai, sannan na maka umarnin cewa ban yadda kayi magana da kowa ba duk inda zamuje, saboda ina tsoron a haɗa baki da kai, watarana kana zaune a gidanmu inda ka saba zama, ina kan varrendar na saman bene, kawai na hango Amal taje inda kake, ka taso kuka taho tare, na fito falo inga meze faru, za kayo hanyar part ɗina, se tace maka ai bana nan ina part ɗinsu, ka bita zuwa ɓangaren su, ni kuma na bi bayanku, nasan zakayi mamaki daka fito ka ganni a tsaye a gurin amma ban ce maka komai ba, haka kurum na fara sakewa da kai bayan na gano waye kai, ganin bibiyata da ake ya fara yawa yasa na ƙara jarrabaka, na baka ATM ɗina, ka tafi dashi tsawon sati biyu, a gaban mutanen gidanmu, wanda nasan dole su bibiyeka a kai, amma ga mamakina bayan sati biyu, se gashi ka dawomin da shi, ba tare da ko ƙwandala ta ɓata ba, kuma yana daga abunda ya ƙara nesantani da mutane shine, duk wanda ya raɓeni shima cikin matsala yake shiga, an dinga bibiyarsa kenan dan a samu wannan takaddun, shiyasa nake sake yin baya baya da kowa, sedai kai ka riga ka shigo rayuwata gaba ɗaya, ban iya kareka da shiga hatsarin da nake ciki ba, seda aka ritsa da kai, sannan ƙiyayyata ga Aure kuma ya samo asaline ga yadda naga Bulama ya maida Aure da saki tamkar shan ruwa, nakan bibiyi shafukan sada zumunta na kanga irin complains akan Aure, kuma ga mahaifina yayi Aure, Amma matarsa sam baya gabanta abunda yake hannunsa shi takeso, se nake ganin muddin nayi Aure tamkar na shiga matsala ne, kuma komai ze iya faruwa dank, kuma a yadda nake jina bazan zauna ƙarƙashin wani yayi amfani da ikonsa a kaina ya wulaƙantani ba, shine abunda ya faru har zuwa ɗaukemu sa akayi tare, Yoseef wannan shine ƙarshen labarina dana mahaifina, kaga laifina akan AƘIDATA? Ban cancanci in guji mutane ba? Ko kuma rayuwar kaɗaici zata zama laifi idan har nayi hakan ne dan kaucewa tarayya da azzalumai masu biyu? Mutane dayawa basu san meyafaru dani ba, abu ɗaya kullum suke kallo shine AƘIDATA " Shiru Yusuf yayi, yasa hannayensa biyu ya dafe kansa, Widad tasa hannu ta janye nasa, tace " Kana jina kuwa?" Wata irin ajiyar zuciya yaja, wadda seda Widad ta ɗan razana, ta ɗau fitila ta haskashi, sedai taga Hawaye a Fuskar Yusuf, jijiyon kansa duk sun ɗaga ya ƙara wani kwarjini, ga ja da idanunsa sukayi, saboda labarin Widad ya kaɗashi matuƙar gaske, gaba ɗayanta abun tausayi ce, taga jalala da iftila'i me ban tausayi, a kashe maka mahaifiya a haukata maka tunani, sannan a cigaba da bibiyar rayuwarka da barazana da tsoratarwa iri iri. "Shiyasa na dinga ja maka rai fa akan baka labarin nan, kalli yadda ka ɗaga hankalinka hadda kuka, dan Allah kabari Yoseef, ni yanzu na fara mantawa da wasu abubuwan saboda sadaukarwarka a gareni, baka yi sallar isha'i bama, gashi yauma munyi dare, kayi salla kaci Abincinka seka kwanta " Bece mata komai ba ya miƙe, sosai yake jin tausayin Widad, gaba ɗaya labarin nan ya tsaye masa a ransa, Widad ta koma kan shimfiɗarta, sannan ta fara zubda nata hawayen dan bata son ta sake ɗaga masa hankali, tana kallonsa sau biyu yana sake sallame salla, yayi ya idar nan ma ya daɗe sosai akan sallayar sannan ya tashi, be ko kula Abincin ba, shimfiɗar ma beyi ba a ƙasa yaje ya kwanta a rigingine. Nanfa Ƙwaƙwalwarsa ta shiga kaiwa tana komowa akan abubuwa da dama, da irin binciken da yayi, lokaci lokaci idan ya tuna labarin Widad se yaja tsaki, dan ya rasa a inda yakamata ya ajiye wannan tsagwaron zalunci haka. Ƙarshe ma tashi yayi zaune ya sake dafe kansa, sedai Duk abun nan Widad tana kallonsa, tana tunanin yanzu akwai wanda zeji labarin abunda ya sameta ya tausaya mata haka, harya shiga wannan irin damuwar? Dukda tarin wulaƙanci da isa data dinga nuna masa, amma ya dake ya shanye har yake jin tausayinta haka, bayan ɗawainiyar da yayi da ita, da ƙoƙarin kareta daya dingayi, lokacin da akazo sace ta ba dashi sukayi niyyar ɗauka ba, ya dage ba zasu tafi da ita ba, shine suka haɗa dashi, ga wahala da azaba da ya sha gurin kuɓutarsu, gashi har yanzu a kan shan wahala yake, a rayuwar da tayi idan akace mata akwai mutum me irin zuciyar Yusuf a zamanin nan to tabbas za tace ƙaryane, ita kam me zata yiwa Yoseef, ta saka masa tasan ko duk abunda ta mallaka zata bashi bata isa ta biya shi ba. A hankali ta tashi ta tafi inda yake zaune ya rafka tagumi, ta janye hannun tace  "wai bazaka kwanta bane? Kuma ina shimfiɗar kake zaune a ƙasa haka?" "Bana jin bacci" ya bata amsa "ko Abinci ma fa baka ciba, ga yunwa ga rashin bacci? Gaskiya ban yadda ba" Yusuf yace "kije ki kwanta kawai, ni bana jin bacci" Tace "Shikenan nima bana ji, bari mu zauna kawai" "A'a, kije ki kwanta kinji nasan zaki bacci idan kika kwanta" Tace "shikenan, kwanta se in kwanta a jikinka" Yusuf yace "No jikinki ze ciwo, ki kwanta akan katifarki" Tai murmushin ƙarfin hali tace "baka san jikinka yafi katifar nan daɗin bacci ba, kwanta se in kwanta" Haka Yusuf ya kwanta, ita kuma ta kwanta a jikinsa, tasa hannu ta zare ribbon ɗin kanta, ta kamo hannunsa ta ɗora a kan gashin ta, a hankali ya rungumeta da hannu ɗaya, yasa hannu ɗaya yana wasa da gashin nata. Tana jin yadda zuciyarsa ke lugude da ƙarfin gaske, ya zamana ma taji kamar baya numfashi daidai, dukda a duhu ne amma Widad ta gane har yanzu Yusuf kuka yake, yana da matuƙar dauriya da juriya, amma wannan karon ya kasa jurewar, saboda jin Widad yake tamkar wani sashine na tsoka a zuciyarsa, haka kurum yake jin kamar shi akayiwa laifin ma ba ita ba. Ƙanƙame Yusuf tayi ta fashe da kuka, Cikin jan numfashi Yusuf yace  "Widad lafiya, kukan me kike kuma?" "Dan Allah Yoseef kamanta da labarin nan da na gaya maka, karkasa shi a ranka dan Allah, kar wani abu ya same ka ji yadda kake numfashi fa" Sosai ya sake rungumeta yace  "Never mind dear, ba abunda ze sameni insha Allah, ina tunanin meye mafita ne kawai, a shirye nake da in baki gudunmuwa kota wani ɓangare dan tina Asirin wanda suke aikata muku wannan zalunci haka, amma kafin nan nasan koba duka ba kin san wasu daga cikin mutanen nan, meyasa kika ƙyalesu baki tona musu Asiri ba? " " Yossef yadda nake shiri akansu haka suke yi a kaina, sun fini iya mugunta da zalunci, na haskawa mahaifina wasu daga cikin su, hakan yasa ya yanke hulɗar kasuwanci da wasunsu, sannan wace hujja nake dashi daze tabattar da abunda nake zarginsu? Bani da sheda se Allah" Cikin raɗa Yusuf yaje dai dai kunnenta yace "meyasa kika ƙyale Bulama, bayan ko a binciken da nake, ina sanya babbar alamar tambaya a gareshi, dan sam ban yadda da shiba, amma naga kina masa kallon uba, kuma ni shine babban suspect ɗina" Widad tace "saboda ko yana ciki ni ba ta tashi nake ba" "Meyasa?" Yusuf ya tambaye ta. "Saboda bashi nake hari ba, Bukar nake hari, na barwa zuciyata insha Allah koni ko shi, ko kuma muyi mutuwar kasko dashi, Insha Allah se Bukar yaje ƙiyama da tabon da zan masa, ya azabtar da rayuwata, yaso kassarani da mahaifina yamin zalunci mafi muni, wannan abunda akayi mana nasan da sa hannunsa, da Bukar da Baban Nurat sesun wulaƙanta a rayuwa, sun cutar dani Yoseef "  tai maganar tana fashewa da kuka, rarrashinta ya dingayi sannan yace "Waye kuma Bukar? Banji kin faɗe shi a labarin da kika bani ba" Ta gyara kwanciyarta sannan tace  "Bukar! Bukar! Alhaji Bukar! Tabbas ban faɗeshi a labarin da na baka ba, saboda labarin ma wani sashe na baka, na ɓoye maka wani, na kuma canza inda faɗa maka bashi da amfani, saboda jin wani sashin na labarina a gareka tamkar tarwatsa shirin sa nake ne, amma ina fatan ubangiji, Allah ya maida mu gida lafiya, zan baka sauran ɓangaren dana cire maka a labarin, dan se mun koma gida jin ɓangaren zeyi amfani, har in cika dukkan burikana, sannan a lokacin zan baka labarin waye Bukar " Yusuf yace  " Shikenan, ubangiji Allah ya kawo lokacin da zamu koma, Insha Allah se inda ƙarfina ya ƙare Widad, zan baki goyon baya ɗari bisa ɗari mu shiga kowane irin ƙalubale dan cikar burinki" "Thank you Yoseef, Allah ya jiƙan magabatanka, nagode sosai" Tai maganar tana Ƙanƙame shi sosai. Haka suka kwana a ƙasa shida ita, a gurin nan ga sanyi cikin dare amma basu iya tashi daga gurin ba, saboda damuwar da zukatansu suke ciki. Umman Yusuf se fama take da hawan jini saboda damuwa da tunani, ga rashin cin Abinci da bata iya ci balle bacci, gaba ɗaya ta rame tayi wani iri saboda tunanin halin da ɗanta Yusuf ke ciki, ga kuma wannan labari daya cika gari, ita dai tasan ɗanta ba mutumin banza bane, dan tasan tabbas wannan zance ƙaryace akayi masa. Tana nan kwance bayan la'asar a inda tayi salla, tana jan carbi tana ta kai kukanta ga Allah akan Allah ya kuɓutar mata da ɗanta, yasa yana cikin ƙoshin lafiya. Sallama Suleiman yayi, taja jiki da ƙyar ta tashi zaune da ƙyar ta amsa masa, ya tsorata ganin halin da take ciki, a ɗan firgice Suleiman yace  "Umma meyasameki haka?" Take ta fashe da kuka tace  "baka ga Sanarwar da akayi a kafafen yaɗa labarai bane? Wai Yusufana ake nema ido rufe wai ya sace 'ya, haɗuwar Ɗana da wannan alhali ba alheri bane, tunda ya fara aiki da yarinyar nan walwalarsa ta ragu kullum cikin tunani yake, kullum cikin damuwa yake banda sintirin fita da wuri baze dawo ba se dare amma ƙarshe abunda za'a sakamana da shi kenan, bakomai akwai Allah, Allah ya bimana haƙƙinmu" Suleiman yace "Umma kiyi haƙuri, yanzun ma abunda ya kawoni kenan, amma yanzu zan fara kaiki Asibiti tukuna, a duba ki kamar baki da lafiya" Umman Yusuf tace "Ni ba inda zani, lafiya ta ƙalau ɗana nake tunani kawai, shiyasa ake ganin kamar bani da lafiya" Da ƙyar Suleiman ya lallaɓata ta yadda ya kaita Asibiti, sukaje akayi mata gwaje gwaje, akace hawan jinine ga ulcer, aka rubuta mata magunguna sannan ya ɗauketa zuwa gida. Suna tafe tana share hawaye, bayan ya kaita gida yace  "Umma ki kula da magungunanki, kidinga shansu akan lokaci, sannan shi lamari irin wannan Addu'ar ku muke nema, idan harda Addu'ar ku, babu wani abu daze same mu insha Allah, Yusuf Addu'ar ki yake nema kiyi haƙuri, komai ze daidaita insha Allah" "Amma Suleiman, kana ganin yau watanni huɗu kenan, ban saka Yusuf a idona ba, baya nan ban san idan yake ba katsam kuma inga wannan al'amari haka, kuma naji labarin Abokinsa Abbas yazo, amma ko jaje bezo yamin ba" Suleiman yace "ki kwantar hankalinki Umma, Abbas baze dawo miki da Yusuf ba, ki manta dashi, Insha Allah muna nan muna ƙoƙari akai, sannan insha Allah zan kawo miki kayan Abinci dana buƙata, amma kisa haƙuri a ranki" Umma tace "shikenan, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, Allah yayi maka albarka ya raba ka da duniya lafiya" Suleiman yace  "Ameen" sannan ya tafi. Aka cigaba da yamaɗiɗi da zancen Yusuf, akan ya sace Widad ya gudu da ita, fastocinsa suka cigaba da yawo, dayake in Allah yasa kana zaman lafiya da kowa, baka rasa masoya, wanda suka san Yusuf suka san halinsa suka dinga ƙaryatawa, suna taya shi da Addu'a. Ramlah na kwance akan gadon ɗakin Hotel, Fahad yana tsaye yana taje kansa a gaban mudubi, Ramlah tace "Fahad, lokaci fa yana ƙurewa, zuwa yanzu yakamata ace an fara maganar aurenmu, amma naga kamar baka damu ba ko zancem baka yi" Fahad cikin salonsa na yaudara yace "Beb kin fiye garaje fa, mubi komai a hankali mana, nida nake so ayi classic wedding, so nake bikinmu ya zama the expensive wedding of the year, wasu kuɗi nake jira a hannun Dad, shiyasa amma kiyi haƙuri, soon za'ayi komai insha Allah" Ta ɗan kwaɓe baki tace "Allah yasa, danni ina ma tantama akanka, kar inje Widad ta dawo kaƙi Aurena kace se ita, dan haka kayi min wancan karon" "No karki damu, ai abunda yaaa nace zan Aureta, saboda in karɓo mana kuɗaɗen hannunta ne, in rabata da komai im azabtar da ita, sannan in sake ta, that's my plan, but unfortunately it's fails, ni yanzu wannan jakin daya gudu da ita, Allah yasa karya karɓe abun ya barmu " Ramlah tace 'kamar kuwa ka sani, dan wallahi zata iya bashi, can you imagine ATM ɗinta yayi over 1 week a gurinsa, naje masa mu haɗa kai a samu wani abu amma fafur yaƙi, munafuki se gashi yayi awon gaba da ita" Fahad yace "suje su ƙarata, ai tunda ba' a san inda Dad ɗinta yake ba, zan cigaba da kawo masu siyan kadarorim nan, a rage wani abun" Ramlah tace "hakane kam, nidai so nake ayi muyi Auren nan, kaga sau biyu ina abortion fa" "Ai kece, nace miki kije kiyi planning, amma kinƙi" "Aini kasan abun planning ɗin nan, suna da nasu matsalolin, ɗan bani tablet biyu in saka a coc, i want doze up" Ya miƙo mata magani, ta zuba a lemo ta girgiza tasha, sannan ta kwanta bacci. Ya kalleta a ransa yace "baki da hankali, uban waye ze Aureki ashe ma bani da hankali, zanta lallaɓaki ina morewa, gefe guda kuma in cigaba da damfararku" Yauma Yusuf se a ɗaki sukayi salla, dan bacci be ɗauke shi ba, se daf da Asuba. Bayan sunyi salla, suka koma suka kwanta bacci, sedai shi Yusuf baccin ya gagareshi sam, a cikin tunanin ma ya raaa wanne zeyi, se kusa ƙarfe goma sannan ya kwantar da Widad ya tashi ya shiga gyaran ɗaki, ya shaee ɗakin ya haɗo kwanukan wanke wanke ya fito tsakar gida. Da Hanne yayi karo tana shara, tana ganinsa ta zuba masa ido tana murmushi, Yusuf yace mata "Ina kwana" Cikin yashe baki tace "ina kwana" Yusuf yace "lafiya ƙalau kina lafiya" "Lafiya ƙalau, kawo in wanke maka kwanukan" Yusuf yace "A'a, yi shararki kawai" "bakomai kiyi aikinki kawai" "A'a dan Allah ka kawao" Tasa hannu ta karɓa, Yusuf ya koma ɗaki ya dafawa Widad ruwan wanka, sannan yaje ze tasheta. Zama yayi ya zuba mata ido, yana jin ƙaunarta da wani irin tausayinta yana ratsa ko ina na jikinsa Numfashin da yake mata a fuskane yasa ta buɗe ido tana kallonsa, har yanzu idon Yusuf ja, ga alamun damuwa nan ƙarara a fuskarsa. Yusuf yace "tashi ga ruwan wanka nan, kiyi wanka ki karya" Miƙa tayi tana ɗan lumshe ido, Yusuf se binta da kallo yake. "To ka matsa in tashi mana, ka danne ni kuma kana ina tashi" "Widad bana gajiya da kallon ki, nidai ina sonki Widad" Ajiyar zuciya tayi, ta shafi sajensa a hankali tace "naji ɗagani in cire kaya inje inyi wanka" Maimakon ya ɗaga ta seya sake gyara kwanciya a jikinta, yana kuma nanata mata "ina sonki Matata, ina sonki Widad" Gaba ɗaya taji wata kasala na saukar mata, batayi magana ba sedai tasa hannu ta rungumeshi itama. Hanne cw ta bankaɗo ɗakin sannan zata yi sallama..... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 84_85 Yusuf ya ɗago da sauri, yayin da jikin Hanne ya ɗau rawa, ba tare da tace uffan ba ta ajiye kwanukan da ta wanke, jikinta na rawa ta fice waje, yayin da wani abu kamar dutse yazo ya daskare mata a ƙirjinta, tana tafe amma kamar ta kifa, danko gabanta bata gani, maimakon taji haushin Yusuf, se wani tuƙuƙin tsanar Widad da taji a ranta, kamar ta janyo ta ta shaƙe haka take ji. Widad kuwa tsaki tayi, ta haɗe rai tace  "kaga malam ɗagani mana" Yusuf yace "to nikuma meye laifina da zaki wani haɗemin rai haka?" Ta ƙara haɗe rai tace "kaika sani dan Allah nika ɗagani, ina da abunyi fa" Yai ƙasa da murya yace  "My queen.. Ta katse shi ta hanyar cewa" dan Allah malam ka ɗagani nace, bana son jin komai daga bakinka, kuma karka ƙara bawa wata 'yar ƙauye kwanukana ta wanke min na gaya maka, in bahaka ba nika ajiyemin abuna zan wanke, idan kuwa ta sake wanken kwanuka na, wallahi sena zuba su gaba ɗaya a wannan rijiyar ta gidan nan, kuma idan na kuma ganinta a ɗakina duk abunda nayi mata ita ta janyowa kanta na gaya maka " Yusuf ya ƙura mata ido, yana kallon yadda take masifa fuskarta na bayyanar da matsanancin kishin dake zuciyarta, amma yanzu daze ce tana sonshi seta fara masa iyayi, tana ita bata san so ba, kawai dai danya temake ta ne. Ta ture shi daga jikinta, ta miƙe tana kumbure kumbure ta cire kayanta ta tafi wanka. Bayan fitarta ya miƙe, ya gyara mata shimfiɗarta, Gwaggo ta aiko musu da Abun karin kumallo. Koda Widad ta fita tsakar gida, tana kallon mugun Kallon da Hanne ke mata, banda Widad na ganin darajar Gwaggo, da ba abunda ze hana tayiwa Hanne rashin mutunci me wuyar mantawa, amma ta ƙyaleta taje tayi wankanta. Data dawo ɗakima Yusuf yana ta ƙoƙarin rarrashinta, amma ta basar dashi taƙi kula shi, ta barshi yaita ɓaɓatunsa shikaɗai, ta ɗakko kaya zata saka yazo ya karɓi kayan daga hannunta, amma tasa hannu fizge abunta, sosai kishi me zafi ya bayyana a fuskarta, Yusuf yace bari yayi amfani da wannan damar gurin jarraba Widad, bari yaga idan dagaske kishinsa take ko kuwa?. Ya koma gefe ya zuba mata ido, tasa kayanta, ta koma gefe tana shafa mai tai kicin kicin da fuskarta, kamar ba itace suke tare ɗazu ba cikin farin ciki. Yusuf yace "Allah sarki rayuwa, Ohh koya Amal ɗina tayi da taji an sace mata ni, Amal ta gama matowa a sona, she really loves me, ga Nurat ma light, ga fara'a ga kirki she also loves me, itama ban san ya zataji ba, ga Sakina abokiyar aikina, abunda ya hana in bawa Sakina fuska shine shigar matsatsun kaya, da yawan kule kulen maza, se gashi Allah yasa na Auri me sa matsatsun kayan, ga tsiwa gashi sam bata sona, taita bani wahala, gashi ina matuƙar sonta, kissing ɗinta in nayi ta dingamin faɗa kenan tanamin tsiwa, laifi koni nayi ko bani nayi ba taita fushi dani, bata tausayina sam, nikaɗai nake sonta, Nasan da Nurat na Aura dana huta, zan sha soyayya dan akwaita da tausayi da sanyin hali, sannan masha Allah, gata da lips masu kyau, nasan ita ba zata dinga ƙyamata ba, ko kissing ɗinta na.... Aibe ƙarasa ba yaji saukar ludayin roba a ƙeyarsa, seda ya razana ya kalli inda Widad take, kawai ta fashe da kuka harda hawaye. Yusuf yace "Ke lafiya Mena yi miki kuma? Kinƙi kulani nazo ina hirata kuma seki jefe ni, sekin jimin rauni tukuna, mu koma gida 'yan matan nawa duk su gujeni?ko kuma su kasa ganeni?" Aikuwa ta ƙara sautin kukan nata sosai, harda sheshsehseƙa, wani guntun murmushi yayi a ransa yace' yarinya kin faller ' Amma a zahiri seya miƙe, yazo inda take yace  " Widad, meyasa ki kuka ne? Kowani abun nayi miki ne?" Cikin shagwaɓa Tace" Nima ban sani ba" Yusuf yace "to meyasa kika jefeni da ludayi? Baki san naji zafi ba?" "Ni bana son zancen da kake ne, raina ɓaci yake ni karka ƙaramin zancen wata a gabana, bana so am feeling bad, ni gaba ɗaya ma zuciyata haushi nake ji" Yusuf ji yayi kamar ya ƙyalƙyale da dariya, amma yasan yana yin hakan, sabuwar rigima zata saka masa, dan haka yace "Ohhh shikenan ya isa haka, am very sorry bazan sake ba, dena kukan kinji abar sona, na dena insha Allah dena kukan haka kinji gimbiyar" Ya dinga share mata hawayen da yake ta binta fuskarta. Widad ta ture hannusa cikin zumɓira baki tace "ni rabu dani, tunda ka sani kuka" "Yi haƙuri I don't mean to hurt you Baby, ban zaci ranki ze ɓaci ba, kinga se binki nake ina magana amma kika shareni, se da ki kaji nafara lissafin 'yan matama sannan kika hau kuka" Widad tace "to waima meyasa nayi kuka ne?" Yusuf yace "Oho nima ban sani ba, aike zan tambaya" Yusuf ya bata amsa ɗan taɓa baki tayi ta ɗanyi tsaki sannan tace "wai dagaske Nurat ma budurwarka ce?" Yusuf yace "A' a naje gidansu dai, bayan mahaifinta yayi yunƙurin sawa a sace ki, ita na ritsa da bindiga ta gayamin inda kike, bayan nan na koma gidansu, dan inyi mata wasu tambayoyi, da farko ta tsorata daga baya kuma ta saki jiki, muka dinga hira a haka na samu abunda nake son ji daga gare ta, har mukayi exchange na lamba, akwai ranar da muka fita dake, nakw waya nace ina tare da matata ne, ai da ita muke waya, sedai daga baya na fuskanci Nurat ta kamu da sona ne " Widad tace "kuma kaima kana son ta"? "To waike meye naki na tambaya ne? Bayan kince bakya sona, ina ruwanki ki ƙyaleni in samo mesona, wanda bazata gujeni ba kota dinga min tsiwa ba" Ɗan guntun tsaki tayi, tare da jin haushin kanta ko meye na damuwa ma oho, ta janyo kwanon Abinci ta buɗe, kofin an zuba kunun tsamiya, kwanon kuma wainar gero ce an barbaɗeta da ƙuli ƙuli, Widad tace "wannan wane irin Abinci ne kuma, shima wani baƙi dashi??" Yusuf yace "wainar gero ce" Tace "Meye kuma wainar gero, mutanen nan suna son yin Abinci baƙi" tai maganar Tare da saka hannu ta fara yashe ƙulin kai tana lashewa, Yusuf ya kalle ta yace  "bismillahi, kwaɗayayyiya zaki cinye ƙuli ƙulin ki barmin gaya ko? Dama kin saba" Hararsa tayi ta cigaba da lasar ƙuli ƙulinta, Yusuf yace "baze fa yuwu ba, se saka yawu kike a jiki, idan muka koma gida sena gayawa Daddy yadda kike bani wahala, duk na rame kekuma ƙibarki kawai kikeyi" Duk da a fusace take amma murmushi ya suɓucemata tace 'kamar kasan akanka Daddy ze iya zaneni ma inaga, dan yana matuƙar sonka sosai" Yusuf yace "nima ina sonshi sosai" Widad ta kalle shi da sauri tace "dagaske? Kana son Daddyna?" Yusuf yace "sosai makuwa, ai bazan manta alkhairinsa a gareni ba, kuma koba komai ko bama tare, yana da matsayi a gurina saboda na taɓa Auren 'yarsa, dan haka inajinsa kamar mahaifina mussman yadda yake girmamani" Widad ta jinjina kai, har cikin ranta taji daɗin yadda Yusuf yace yana son mahaifinta harya ya beshi haka. wainar geron nan ba ƙaramin daɗi tayiwa Widad ba, ta saki jiki taci sosai, sed suka gama faɗansu da Yusuf sannan ya fita. Widad ta fito tsakar gida, amma bata ga Hindu ba, ta kalli Hansai tace "wai ina Hinduna ne yau ban ganta ba fa"? "Hindunki a ina?" Hari ta faɗa tana yatsune fuska. Banza Widad tayi mata, ta kafe Hansai da ido tana jiran amsar tambayarta, Hansai tace "Zazzaɓi take yi, tana ɗakin Gwaggo a kwance" Widad tace "subhanallah garin yaya?" Hansai tace "larura daga Allah mana" Widad ta tafi ɗakin Gwaggo, ta tsaya a bakin ƙofa tayi sallama, Aka amsa ta nemi izinin shiga, sannan ta shiga. Jamila na zaune a gefe tana shayar da jaririyarta, yayin da Hanne keta ƙoƙarin gyara ɗakin Gwaggo, Gwaggo kuma tana ta rarrashin Hindu taci Abinci amma taƙi. Gaba ɗaya damuwa ta bayyana a fuskar Widad. Jamila ta kalli Widad tace "ina kwana?" Widad ta kalli Jamila ta ɗauke kai, tazo ta nemi guri ta zauna a gaban Gwaggo tace "Mama, meyasa ba'a gayamin Hindu ba lafiya ba?" Gwaggo tace "ahh haba, ya za'ai a takura miki, amma yanzu ai gashi da kika fito kinji" Jamila taji haushin sharetan da Widad tayi a karo na biyu, kuma tana ji tana mata magana. Cike da tausayawa Widad tace "sannu Hindu, Allah ya baki lafiya" Hindu tayi murmushi tana gyɗa kai, yayin da Hanne se cika take tana batsewa, tana faman jan tsaki kamar wadda akayiwa wani abu, dan data tuna a yadda ta gansu itada Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka. Widad ta kai Hannu ta taɓa Hindu, jikinta zafi sosai Widad tace "Gwaggo, baza'a kaita Asibiti ba? A kaita a duba ta mana" Gwaggo tace "hmm Amarya kenan, da kinsan azabar tazarar dake tsakaninmu da Asibiti da baki ce a kaita ba, bamu da Asibiti a garin nan, ƙauye uku zuwa huɗune tsakaninmu da Asibitin shaka tafi, yanzu kafin a kaita ma wani wahalar ne, duk seta galabaita" Widad ta girgiza kai tace "ni wallahi ina mamakin yadda za'ace mutane suna rayuwa babu Asibiti a guri, ai wannan se mutum ya rasa ransa ma ba'a bashi wani agaji ba, haba dan Allah to yanzu ba abunda za'a bata"? "A'a na ɗan jiƙa kayan magungunanmu na gargajiya, na ɗan bata shima kuma tayi amansa" Widad tace "Mama nifa bana son wannan kayan jiƙe jiƙen, su ba ƙa'ida ne dashi ba kawai sha akeyi, kuma kayan ciki basa san wannan jiƙe jiƙen, yanzu se wani abun ya taɓu, bari Yoseef ya dawo, in da sauran nasa magungunan se a bata" Hindu tace "Nagode Amarya" "Ba godiya tsakaninmu Hindu" Jamila abun ya bata mamaki taji Widad na hira haka, kuma ta iya hausa amma tayi mata magana taƙi kulata. Bayan Widad ta gama duba Hindu, ta tashi ta fita, Gwaggo ma ta fito tsakar gida, Jamila tace "wai nikam wacece wannan? Tana ji ana mata magana amma tana wani jin kanta tana share mutane" Hanne tayi tsaki tace "bar shegiya, haka take wannan wulaƙancin dan tama ganinta a koɗe kamar an wanke karas, taita wa mutane wani iskancin banza da taƙama, se tsabar rashin kunya da rashin tarbiyya, ko magana bata iyaba ga ƙaryar masifa, komai seta dinga nuna bata sanshi ba, saboda gogewa mutane hadda " Hindu dukda jin jikin da take, ba zata iya jure jin ana cin zarafin Widad ba, Hindu taja tsaki tace " Wallahi Jamila ba bata da mutunci bane, ni baki ga yadda tamin ba, bata da wata matsala, sedai bata sakin jiki da mutane, seta daɗe tukuna, bata fiye son mutane bane, amma Hanne san zuciya ne yasa kike cewa bata da mutunci" A fusace Hanne tace "dalla malama yiwa mutane shiru, aikin banza uwar shisshigi se wani naniƙe mata kike kina cusa kai ba kwarjini, aikin banza dana wofi kawai" Jamila tace "ya isa haka, ke Hanne abun faɗa baya miki wuya yaseen, har yanzu kina nan da tijararki baki dena ba" Hanne ta riƙe ƙugu tana harare harae tace "ƙwarai kuwa, wallahi anamin nake ramawa ehee, babu 'yar masu baƙin jinin da zan saurarawa" Shiru Hindu tayi, jin Hanne na ƙoƙarin fara ci mata fuska, Jamila tace "Hanne meye hakane? Nace ya isafa" Hanne ta zumɓura baki tai waje, yinin yau Widad kanta bata da sakewa, ji take kamar itama bata da lafiya, Hindu tana matuƙar birgeta saboda biyayyarta da haƙurinta, shiyasa idan bata nan ko bata walwala Widad ma take shiga damuwa. Saleh kam kwana biyu yayi ya koma kano, yaje ya tarar abubuwa nata sake rikicewa, dan ya fara karaya ya zubawa sarautar Allah ido, saboda tarakun da'aka kafawa Yusuf, ubangiji Allah ne kaɗai ze iya fidda shi, dan babu imani babu tsoron Allah ko tausayi a tare da su Alhaji Musa. Saleh yana gidan da yake zaune, yaji ana buga ƙofa yana zuwa ya buɗe yaga Abbas, Saleh yayi murmushi yace "Ahh saukar yaushe haka? Shigo daga ciki mana" Abbas yabi bayan Saleh suka shiga, har falon Saleh, Abbas yace "ai yau sati na guda a garin nan, nazo in ɗan huta ba inda nake zuwa shiyasa baka ganni ba se yau" Saleh yace "Allah sarki, to ya Hanya?" "Hanya Alhamdilillah, dan mun shata kam" "to masha Allah" Saleh yace "wai ni kuwa nace ya ake ciki ne? Har yanzu babu wani labari ne? Tun tafiyata banji wani motsi ba har yanzu ba'a samu komai bane?" Saleh yace "haryanzu ba wani abu fa, ana ta fama ne abun duk se a hankali, shi can ya gudu ba'a san inda suke ba, shima kuma an sace shi, shi Daula babu wanda yasan inda yake haryanzu, anata fama ne" Abbas yace "Ai naga sanarwar da aka yi akan Yusuf ne ya sace Ita 'yar Daula, hakan yayi ai hakan shine zesa hankalin mutane ya ɗauke daga yin zargi, se a koma sauraren ta inda za' a gano su, ni babban abunda yake damuna ma kar muje ta bashi takaddun mu muna nan, dan wallahi ba kaga alherin da take masa ba" Saleh kallon Abbas kawai yake harya kai aya, sannan ya numfasa yace "insha Allah, babu abunda ze faru, kota bashi takaddun babu yadda zeyi dasu, su Munir su suka san kan dukiyar, su suka san yadda za'ayi lamarin ya wakana, karka damu komai ze tafi daidai, sedai kamar yadda na gaya maka kansu suma a rarrabe yake yanzu haka, karka yadda wani ɓangare yazo ya nemi wani abu a gurinka, ka yadda ka bayar, karmu ɗau side mu zama a tsakiya, tunda bamu san ɓangaren da zasu yi nasara ba" Abbas yace "dan wannan, ai karka damu tuntuni kamin wannan kashedin, kuma naji na ɗauka, dan haka ka kwantar da hankalinka, sedai muna biue dasu, zuwa lokacin daza'a samu ɗin" Saleh yace "hakanma dai dai ne" Daga nan suka cigaba da hirarrakinsu. Daga baya kuma suka yi Sallama, Abbas ya shig motarsa sega kiran Suleiman, ya ɗaga yana faɗin "Allah ya temaki Oga, barka da yamma" Suleiman yace "Yawwa barka Abbas, ya kake ya aikin?" "Alhamdilillah Oga" "Good, naji ance ka shigo garin nan, inba damuwa ina son mu haɗu gobe in Allah ya kaimu" Abbas ya ɗanyi Jim sannan yace "shikenan Oga, yadda kace kaman da ƙarfe nawa?" "Kamar goma na safe, muhaɗu a office" "Shikenan, Insha Allah zan shigo" Yana kashe wayar, Saleh yaja tsaki yace "Aikin banza munafukan banza, da kai aka haɗa baki aka canzamin gurin aiki, aka maida Yusuf kan kujerata, aiga abunda ya sameshi nan, Allah ya ƙara masa saura kaima" Ya ajiye wayar yana ƙwafa, ya kunna motarsa sannan ya tafi. Nurat ta rame tayi duhu, gaba ɗaya bata jin daɗin komai, tun mahaifiyarta tana rarrashinta harta haƙura, ita zatonta halayen mahaifinta ne suka sa tashi ga wani hali, bata san me yake damunta ba, ko Abincin kirki bata iyaci, ga wunin ɗaki data tsira, seta wuni cur bata fito ko falo ba tana ɗaki, Abinci in an kaimata ba zata ciba, sedai idan Mahaifiyar tace ta shiga ta sata a gaba shine zata ɗanci kaɗan, fuskar nan tayi fayau bakoma se dogon hancinta da idanuwa saboda damuwa. Shikuwa mahaifinta sabgar gabansa kawai yake, yana ta faɗi tashi yana kashe kuɗi gurin malamai da 'yan tsibbu, da gurin manyan' yan siyasa domin ya samu ya koma takarar ɗan majalissa da Daula ya tsaya masa yayi, gefe guda kuma sunata cigaba da ƙulle ƙullen yadda ko sun rasa wanccan kuɗin, su samu wani kason ta ɓarauniyar hanya. Yanzumu shiryawa yayi tsaf, ya tafi gidan Barrister Hafiz da kansa, domin jin inda maganarsu ta kwana akan batun ayi takaddar boge, ayi gwanjon wasu daga kadarorin Daula. Barrister Hafiz ya karɓi Alhaj Musa hannu biyu, ya masa iso har falo aka gabatar masa da Kayan ciye2, Alhaj Musa ya ture farantin fruit ɗin yace "kafin wannan, dama zuwa nayi inji inda maganar da mukayi ta kwana? Yau kimanin wata guda kenan da yin maganarmu, amma shiru ba amo ba labari bakace mana komai ba, bamu san a ina aka kwana ba" Barrister Hafiz ya ɗanyi shiru sannan yace "Yallaɓai kamar yadda a wancan lokacin muka rabu akan cewar, zan tattauna da sauran abokan aikin da muka kasance lawyoyin Alhaji Nasir Daula, na bisu ɗaya bayan ɗaya kowa naji ra'ayinsa, na zaɓe wanda nake ganin zasu iya yadda ayi harkar nan dasu, sedai me nazarin da mukayi, da binciken da muka sake yi shine, duk wata kadara da Daula ze siya muna sani, ko ince wasu daga kadarorin daze siya, a gabanmu akeyi da komai da komai, sedai fa takaddun Kadarorinsa babu ɗaya daga cikinmu daya san inda yake ajiye takaddunsa, dukda kasancewar mu lawyoyinsa, 'yar nan tasa dai ita kaɗai ce tasan inda kayansa suke, bakomai muka saniba, munyi tunanin yin takaddar boge kamar yadda kuka ce sedai babu wanda ze iya kwafar sa hannun sa, wataƙila se wannan yarinyar tasa" Alhaji Musa yai shiru sannan yace, "shikenan ba damuwa, zamuje a bincika dole za'a samu wanda ze iya kwafa, nagode sosai idan akwai buƙatar sake nemanka, zaka jimu nan gaba nagode" Ya miƙa masa hannu suka gaisa, ya tashi fita. Nurat ce zaune a bakin gadonta tana ta sharɓe hawaye, wanda ya zamar mata jiki a 'yan kwanakin nan, tayi zurfi sosai a tunani, taji sallama a hankali ta ɗaga kai domin ganin me sallamar barrister Khalil ne, bayansa kuma mahaifiyarta ce, Amsa masa tayi cikin sanyin jiki. A ɗan razane ya kalleta yace "Subhanallah Anty Sauda dama haka Nurat ta koma?" "to gata nan dai, shiyasa na kiraka ai, ban sani ba kokai idan kayi mata faɗa taji" Khalil yace "sistona, meke damunki haka kinga yadda kika rame kuwa?" Shiru Nurat tayi ba tace komai ba, Khalil yace "gayamin meke faruwa ne?" Ɗaga kai tayi ta kalli mahaifiyarta ta sunkuyar da kai, Khalil yace "Anty Sauda bamu guri muyi magana" Ba musu ta juya ta fice ta basu guri, Khalil ya rufe ƙofae, sannan ya ɗakko kujerar gaban dressing mirror ɗinta ya ajiye ya zauna, ya kalleta yace "Nurat, tsakanina dake kin san babu ɓoye ɓoye ko? Bama ɓoyewa juna komai ki gayamin meke faruwa, kin san bazan fallasa sirrinki ba, sirrinki nawane ki gayamin koda taimakon da zan iyayi miki" Aikuwa ta sake fashewa da kuka, seda tayi me isarta sannan tace "Brother meyasa wayarka bata shiga, na kira layinka babu adadi amma taƙi shiga?" Khalil yace "wayar aka sa emin a gurin ɗaurin Aure, se yau naje nayi swapping ɗin layin, amma meyasa baki kira ko Mama ba muyi magana?" Nurat ta goge hawayenta tace "bana son kowa yasan meke faruwa ne, bana son wani yaji shiyasa ban kira kowa ba". "Shikenan naji, gayamin meke faruwa na ƙagu inji meyasameki haka?" ɗakko wayarta tayi, ta buɗe labaran da ake yaɗawa akan ɓatan Widad, labarin me ɗauke da hoton Yusuf. Ta miƙa masa wayar tace "Brother kaga wannan labarin?" Khalil ya kalli wayar yace "eh naga labarin yana ta zaga gari" Nurat tace "Allah ya jarrabeni da son wannan bawan Allah brother, kuma wannan shine wanda Daddy na yasaka a gaba, wallahi brother ina tabattar maka da dasa hannun Daddy na aka sacesu, kuma yanzu anyi sanarwa wai shi ya sace Daula da 'yarsa, wallahi baze aikata haka ba brother, dan Allah ka temakeni ka temaki Yusuf " Khalil yace " yi shiru dena kukan, tsaya yanzu kin zaɓi soyayyarki akan mahaifinki"? "Brother ba soyayya na zaɓa ba, gaskiya na zaɓa na fifita, na gaya maka komai fa a baya, koka manta?" Khalil yace "ya za'ayi in manta, ban manta ba kuma indai abunda kika faɗa hakane, to tabbas mahaifinki bashi da imani, yanzu me kike ganin za'ayi? Tukuna ma waishi wannan ɗin waye? " Nurat tace "direban gidan Daula ne" "Direba kuma Nurat, to yanzu ya kike son ayi?" Nurat tace "Sonake a ɓoye, ka bincika waye Yusuf da kuma inda yake, sannan ina son a ɓoye ka cigaba da bin diddigin mahaifina ko zaka samu wani bayanin, wanda ze wanke Yusuf" Khalil yace "kin haɗani da aiki me hatsarin gaske, amma indai hakan ze sama miki farinciki to zanyi insha Allah" Ai bata san lokacin da ta faɗa jikin Khalil tana masa godiya ba, kallonta yake yi yana tunani a ransa yace "insha Allah, zan sadaukar da tawa soyayyar dan ganin kin samu taki Nurat" Zuwa yamma Hindu ta ɗanji sauƙin jikinta, dan harta fito tsakar gidama, Widad tana ta murna, Jamila na jikin ɗakin Hansai, tana wasa da jaririyarta, Widad ta ƙura mata ido kamar tace ta bata jaririyar ta ɗauka, dan ita dai da wayonta bata taɓa ɗaukar jariri ba. Yusuf yayi Sallama ya shigo, sedai abunda ya ganine yasa ya rikice cikin ɗaga murya yace "Subhanallah...... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 86_87 Wato bakomai Yusuf ya gani ba, illa Widad bata taɓa kula Jamila ba, amma taji tana son taje ta ɗau jaririyar nan dako arba'in ba tayi ba, gashi baya tunanin ta taɓa ɗaukar jaririn, Jamila na ƙoƙarin bata 'yar, idan ba'ayi wasa ba tsaf Widad inta ɗauki 'yar nan zata iya jimata rauni saboda yanayin ɗaukar da take shirin yiwa jaririyar. Yusuf ya ƙaraso da sauri yace "karki bata, bata iya ɗauka ba karta jiwa Babyn ciwo" Widad ta juyo ta kalleshi, aikuwa ta haɗe rai sosai tace  "kamar yaya ban iya ɗauka ba?" Yusuf yace "eh baki iya ɗauka ba, sekin jima ta ciwo tukuna?" "wai kai komai ban iya ba, ba a haka zan koya ba, ni gaskiya kabari a bani in ɗauka" tai maganar tana ƙoƙarin cicciɓar ƙafafuwan jaririyar" Yusuf yace "yi haƙuri tsaya kiga yadda za'ayi, bari in ɗauka ni se in baki" Yusuf ya karɓi jaririyar, dake ta bacci, yayin da Jamila kuma rigimar Yusuf da Widad suka burgeta matuƙa suka bata dariya. Yusuf yace "muje ɗaki in baki ki ɗauka" Yana tafe tana biye dashi har ɗakinsu, suna zuwa ta zauna tace  "to zauna ka bani" "Kedai akwai garaje" Yusuf ya zauna ya nuna mata yadda zata yi da hannunta, sannan ya ɗora mata Jaririyar a hannu, jaririyar dai baƙace sedai fes da ita, an mata wanka an samata riga me kyau, rigar nata ƙamshin miski, da alama Jamila tana da tsafta. Widad ta ƙurawa Jaririyar ido, ta dinga jin ina ma tatace, ace wannan 'yarta ce, a ranta tace "da ina zan sa kaina dan daɗi' " Yoseef so nake in ɗaga ta " " ki ɗaga ta ki kaita ina? " " Sonake ta buɗe ido in ganta, se kuma in mata wasa" Yusuf yace "ikon Allah, ina wannan yarinyar tasan wani wasa? Jaririya cefa dan Allah ki ƙyaleta tayi baccinta, idan kika tasheta kuma kuka za taitayi, mamanta ta karɓeta daga hannunki" Widad tace "to bazan tashe ta ba, amma sonake ta buɗe idonta" "zata buɗe ne, amma ki ƙyaleta mana tayi baccinta" "to na ƙyaleta" Widad ta cigaba da kallonta, tana ta sake ayyana ina ma ace wannan 'yarta ce. Yusuf yana canza kaya, yana yi yana kallon Widad, dan karya ɗauke ido Widad tayi wani abu daze cutar da jaririyar, Widad ta nutsu sosai danko ƙwaƙwƙwaran motsin kirki ba tayi, ta riƙe jaririyar sosai. Widad tace ' Yoseef ka samin ita a bayana, irin yadda akeyi ɗin nan" Yusuf yace "yau naga ta kaina ni Yusuf, Allah ya haɗani da rigimammiyar mace, keda kike koyon ɗaukar jaririyar ma yanzu, shine zaki wani ce a goya miki ita? Zan ƙwaceta in kaiwa mamanta, ki cigaba damin rikici" Zumɓura masa baki tayi, tana sake gyara zamanta, ya ɗakko Abincinsa ya zauna ya fara ci, Amma Widad ta hau kici kicin ɗaga jaririyar nan wai zata saka a kafaɗarta, Yusuf ya miƙe da sauri yaje ya karɓe yarinyar nan, danma jaririyar me haƙuri ce, ba tayi kuka ba se buɗe ido da tayi tana miƙa. Yusuf ya fito tsakar gida yace  "Mama ungo Jaririyar nan, bawa mamanta ita  tun kan Widad tayi aika aika" Widad kamar zata yi kuka ta biyoshi da sauri tace "Mama dan Allah ki bani, kawaifa dan nace ina son inga ta buɗe ido, shine se cewa yake ban iya ɗauka ba" Yusuf yace "karki bata, wai sena goya mata ita, ko ɗaukar jaririyar bata iya ba ta ina za'ayi goyo?" Jamila dai banda dariya ba abunda take yi, Widad tayi kicin kicin ita a dole anyi mata laifi. Megari dake ɗakin Hansai yana jinsu ya fito yana cewa "haba Malam Yusufa, yama za'ayi kace bata iya ɗaukar jariri ba, Rabu dashi yarinyar kirki Allah ya baki naki kema" Widad tace  "Ameen" Hari tace "jimin mara kunya, kikace Ameen a gaban mutane, kai Wudas baki da kunya Al'qur'an" "baza'aji kunyar ba ɗin, meye abun kunya kuma dan nace Ameen" Jamila taji daɗin yadda dukda Widad bata kula ta amma ta nuna tana son 'yarta. Bayan sun koma ɗaki Yusuf ya kalleta yace "Sannu uwar rikici" Murguɗa masa baki tayi, ta tafi kan katifarta tai zamanta. Yusuf kamar yayi dariya, haka ya dinga dariyarsa ƙasa ƙasa yana cin Abincinsa, har akayi sallar magariba bata kula Yusuf. Ta fito tsakar gida zata yi alwala, taga Gwaggo tana aikinta  a tsakar gida, Widad tace  "Mama wai nan garin ba'a samun Irish potato ne?" Gwaggo tace "meke nan?" Tace  "dankali" Gwaggo tace  "Auho, ai da kiyiwa Yusuf magana, ko kuma Ila idan sunje kasuwa su samo miki" Widad tace "bafa wannan ba Mama, dankalin nan 'yan ƙanana, ba masu zaƙin ba su nake sha' awa fa" Gwaggo tace "au dankalin turawa zakice min" Widad tace "eh shi nake nufi" Gwaggo tace  "taɓ aikuwa yana ɗan wahala, dan se anje can birni ake samu" Widad tace  "shi nake sonci fa" Gwaggo tace  "Amarya ko an gamu ne?" Widad tace "aka gamu dame?" "Ahh nasani ko addu'ar Baffa ta karɓu an samu rabo" Widad tace "wai kina nufin ina da ciki?" Gwaggo kawai tayi murmushi, ana ɗan sayewa kar a faɗa kai tsaye amma ita ta faɗa, Gwaggo ta ƙyaleta ta cigaba da aikinta, Widad taje tayi sallarta, ta zauna akan dadduma tayi shiru, kawai taji har cikin ranta tana son ta samu ciki, ace yau gata ɗauke da ɗanta na kanta a jikin ta, idan ta haihu ta samu ɗa da zata dinga gani tana jin daɗi. Tana zaune tana ta karanta wasiƙar jaki, Yusuf yayi sallama tana jinsa tai masa banza, ta miƙe ta fara shirin kwanciya. Seda ya bari ta kwanta sannan ya tafi rarrashi, tana jinsa ya hawo katifar yana lalubenta amma ta shareshi. "Kina jina amma kika shareni ko Queen, laifin me nayi miki ne?" "ni ƙyaleni bacci zanyi" "Naƙi in ƙyalekin, ni kike sharewa ko?bafa na son haka" Cikin Shagwaɓa tace "to ba kaine komai nayi kake cewa ban iya ba" "To kin iya ɗinne? Matar ƙauye kawai sarkin rigima" "Kai kuma mijin ƙauye ba" "Eh naji na yadda, ni mijin ƙauyene kuma mijin matar ƙauye, karki damu zan siyo miki teddy ki dinga wasa dashi, shima kamar baby ne seki koyi goyon a jiki" "bawani nan teddy daban, teddy mutum ne? Toni mutum nake so" Yusuf yace "Eh tunda baki da mutum, seki rainon teddy da haka zaki koyi rainon jaririn gaske" "Bana son teddyn, ni mutum nake so" Sosai Widad ke bawa Yusuf dariya wasu lokutan, Yace  "idan mutum yana yaro idan yayi wasa da dolls 'yar tsana, yana iya raino koba jariri a gidansu, amma ke baki iya ba ' Widad tace" waye ya gaya maka da ina yarinya ina wani wasa ni? Nifa kamar boss nake da ina yarinya, ba ruwana da wani wasa irin na yara" Yusuf yayi murmushi yace " Yanzun ma ai boss ɗince" Kawai tayi murmushi tace "nice boss ko, zan ramane" A haka suna taɓa hirarsu har bacci yayi awon gaba dasu gaba ɗaya. Da gari ya waye, Widad tana fitowa taga Hindu na tattare tsakar gida tana shara, Widad tace "Hindu kin warke ne kike aiki?" Hindu tace "jikina da sauƙi Amarya, gani nayi tsakar gidan yayi wani iri, duk ganyen bishiya ya faɗo, shiyasa nace bari in gyara kafin a firfito" "Kai Hindu, kina fama da kanki ki bari a share mana gaskiya bari" Widad ta ƙwace tsintsiyar ta hana Hindu sharar, ta gama abunda zata yi ita ta share, sannan ɗakinta koma ɗakinta tayi kwanciyarta. Wajejen takwas da rabi Widad ta farka, ta hangi Yusuf a zaune da gashi se gajeren wando yana buɗe kwanon Abinci, da alama har yayi wanka ma, dan jikinsa se ƙyallin mai yake. Ƙura masa ido tayi tana kallonsa, sam Yusuf bashi da makusa gashi da ƙira me kyau, gashi shikansa me kyau ne, ga kuma uwa uba zuciya me kyau. Tasowa tayi tazo inda yake ta zauna, ta kwanta a jikinsa hannunta kuma tana shafa gadon bayansa. Yace "Kin tashi kenan? Fatan kin tashi lafiya?" Maimakon tayi magana sema wani sake lafewa da tayi a jikinsa, tana sake shafa bayansa. Yusuf yayi murmushi ya cigaba da abunda yake, can yace "in kin gama shafanin seki ɗagani zanci Abinci, tunda naga kamar ke bakya jin yunwa" Yanzunma shirun ta kuma yi, ta cigaba da abunda take, janyota yayi gaba ɗaya ya ɗorata akan cinyarsa, yana ƙaremata kallo yace "ƙalau kuwa? Ko yau da son jiki kika farkane?" Murmushi tayi masa, ta kwanta sosai a jikin nasa, tana ƙare masa kallo tun daga fuskarsa har ƙirjinsa, ta kai hannu tana wasa da gashin nasa. Buge hannunta yayi yace   "mara kunya nan kika gama cewa abun ƙyamane, amma indai kika gani sekin taɓa" Murguɗa baki tayi tace "ai idan baka yi wasa ba, da fork zan maka shaving, duk in cire shi" Yai dariya yace "Kin fasa tsigeshi ɗaya bayan ɗayan?" "Duk wanda ya samu zanyi ai" Yai murmushi yana cigaba da cin Abincin sa, still kallon Yusuf take yadda yake komai a nutse, Yusuf yace "Malama karfa ki cijeni" Bata san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba, tace "aikuwa dan kasan na saba ba, da an takurani idan naga bani da mafita, se cizo kuma haƙorana dafi garesu, duk abunda na kama sena fasa shi, shiyasa Fahad ɗin Bulama yake cemin Mayya, tunda na huda shi da haƙorana" Jiki a sanyaye Yusuf yace "yanzu idan muka rabu, muka koma gida Fahad zaki aura ko?" Da sauri tace "Allah ya kiyaye, wallahi ko maza sun ƙare bazan auri wannan ba, mashayin giyane fa, ga neman mata kai zaka so in Auri wannan?" Yusuf ya girgiza mata kai, ya ɗan tsura mata ido yace   "I can't imagine my life without you Widad, ko mu koma idan zaki Auri wani bazan iya jurewa ba, ban san ya zanyi ba" "waye yace maka zanyi Aureni? Ni ba zanyi Aure ba, bani Abincin nima inci, amma a baki zaka bani yau" tai maganar cike da son da basar da wancan zancen da suke yi. Haka ya dinga bata Abincin tana karɓa, kamar 'yar yaye suka gama sannan yayi shirin fita, yau da kanta har soro ta raka shi, ta tsaya ta kalle shi tace "bana son ka fita Yoseef, kamar kazo mu koma ɗaki" "Yau kuma? To idan ma dawo me zaki ban?" "Kawai inta kallonka, kana bani nishaɗi, da jokes ɗinka da halayenka masu kyau" Yai murmushi yace "nima idan na fita, duk damuwa nake in dawo, saboda inzo inga abar sona, am missing you fa idan na fita". Tace "nima haka, keep missing me harkaje ka dawo kaji" Yusuf yace "yanzu abunda za'ayi shine, Yimin wani abu da in na fita har in dawo bazan manta ba" Tace "kamar me kenan?" Yusuf yace "just kiss me here 'yai maganar yana nuna mata kumatunsa na dama. Ganin tsakar gidan ba kowa yasa Widad, ta rungume Yusuf ta fara kissing ɗinsa a baki, he was so much surprise da abunda Widad ɗin tayi, dan haka yasa hannu biyu ya rungumeta yana murmushi. Hari ta bankaɗo labule zata fito daga ɗaki, hannunta da kofin da' aka karya, kawai tai gamo da Yusuf da Widad a bakin zaure, Yusuf ya bawa Hari baya dan haka be ganta ba sam, Widad kuwa ta ganta, amma tana sane ta basar ta ƙara maƙalƙale Yusuf ta cigaba da abunda take. Da gudu Hari ta koma ɗaki, ta bankaɗo labule ta rufo ƙofa, Widad ta zame bakinta ta hau dariya, Yusuf yace "ya dai?" Tace "bakomai, muje hanyar waje in raka ka" Yusuf yace "rana me matuƙar tarihi a gurina, ba iya yau zan cigaba da tunanin ki ba har abada zanyi tunanin ki My Queen" Murmushinta me ƙayatarwa ta cigaba dayi masa, da sukaje soronma soyayyarsu suka cigaba dayi, dukda Yusuf ne kawai ke furta mata yadda yake sonta, Widad kam ta kasa ce masa uffan. Ya riƙo ƙugunta yana kallon ƙwayar idonta, Widad tace "Idan ma makara baka fita da wuri baf ba ruwana" "Aiko ke kike da ruwa, dan ke kika hanani fita, ɗan ƙara min kiss ɗin mana kona 10 seconda ne" Tureshi ta shiga yi tana dariya, tim suka ji an saki kwano, Hanne ta taho da fantekarta cike da Albasa, tayi karo dasu Yusuf, take taji ganinta ya ɗauke ta saki fantekar albasar, Yusuf yace "Subhanallah garin yaya kika zubar? ' Yai maganar yana sakin Widad, ya yunƙura da nufin ya durƙusa ya tayata tsince albasar, amma Widad ta riƙe shi ta tsatstsare shi da ido tace " meye naka a ciki? Ko kai ka zubar mata? " Yusuf yace  "A' a amma kinga mu muka tsoratata ta zubar da albasar, yakamata a tayata kwashewa" Wani mugun kallo tayi wa Yusuf, taja tsaki ta koma cikin gida, Yusuf ya durƙusa ya taya Hanne suka tsince Albasar, yace  "ki dinga kula sosai, ki dena yawan tsorata kinji?" Hanne ta jinjina kai tace "to nagode" Ta ɗau fantekarta tai waje, tana kuka tana tunanin me zata yiwa Widad yadda zata ɗan ɗana mata taji abunda take ji. Alhaji Musane yace  "Nifa gaba ɗaya na fara gajiya da wannan wahalar, daga wannan se wannan abu sekace jaraba? Abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, shi ya ɓace ɓat kamar kuɗi an neme shi an rasa, shima wannan ɓangaren yarinyar har yanzu babu wanda ya ganosu, suma lawyoyin nasa sun kawowa mutane wasu surutansu na banza " Alhaji Haruna yace "haba Alhaji Musa, ni ban taɓa ganin ka karaya ba akan abu se yau, duk abunda aka fiye shan wuya akansa za'a samu ne, yanzu mafita yakamata mu nema amma dole mu kassara Daula, mu kassara wannan dukiyar dayake taƙama da ita" Alhaji Musa yace  "to meye mafitar, nagaji wallahi haba, ni zuwa zanyi in maida hankali akan harkar takarata kawai" Alhaji Munir yace "kaga dan Allah Kadena mana zancen wata takara please, zancen takararka kai kaɗai ta shafa, mu muyi abunda ya dame mu kawai, Alhaji Haruna meye mafita" "na saka a duba mana, wanda ze iya kwafar mana saka hannun Daula, sannan kafin a samu me saka hannun ayi fafutuka a bincika mana bankin nan, shima mu gwada muji ta ina zamu dace" Alhaji Musa yace "to ai shikenan, Allah yasa mu dace, amma ni na fara gajiya wallahi, gashi shima wancan banzan yaron har yanzu ba'a gano shi ba, nifa sonake a kamashi kafin su shigo garin nan" Haruna yace "karka damu, ai matakan da muka saka baze tsallake tarkonmu ba, ka kwantar da hankalinka komai ze tafi dai dai" Alhaji Musa yace "shikenan Allah yasa hakan, ynzu a duba mana me iya kwafar signing ɗin nan" Gidan Alhaji Daula kuwa, Hajiya Halima se shagalinsu suke da dukiya suna facaka, A ɓoye Ramlah take satar wasu abubuwan ba tare da mahaifiyarta ta sani ba ta kaiwa Fahad ya sayar ya kawo mata abunda yaga dama, sannan kuma su raba abunda ya kawo mata ɗin, Amal kam gaba ɗaya a cikin damuwa taje, dukda irin romon bakan da Mahaifiyar su take mata, akan cewar ai bakomai dan an kama Yusuf, amma hankalinta yaƙi kwanciya, sam bata da nutsuwa sosai take jin Yusuf a ranta, take tausayin halin da ze shiga idan aka kamashi da laifin ya sace Widad. Anwar kam kasuwarsa ya koma zuwa, sam baya zaman gidan nan saboda irin takaicin da yake ƙunsa a cikin gidan, a kan idonsa yana ji yana gani haka Fahad yake zuwa ya ɗauki Ramlah a mota su fita, kuma mahaifiyarsu na gani bazata ce komai ba, shikansa ya fara lura da sauyin ɗabi'a na Ramlah, ya fara zargin ko ta fara shaye shayey, amma yasan da yayi magana mahaifiyarsu zata ƙarhata shi ƙarshe ma su ƙareta babu daɗi dan haka ya zuba musu ido. Ma'aikatan gidan kuwa, su Isa se yanzu suka gane zaman Widad a gidan nan Rahama ne a garesu, saboda tsagwaron wulaƙanci da cin mutunci da suke fuskanta daga gurin Hajiya Halima da 'ya' yanta, zagi da cin zarafi gami da wulaƙanci ba irin wanda ba'a musu, Albashinsu kuma duk Hajiya Halima tabi zaftare musu, shima se sufi wata ba'a basu ba, zaman haƙuri kawai sukeyi a gidan nan, duk inda suka zauna banda tsinewa Hajiya Halima da 'ya' yanta babu abunda sukeyi, suna shiwa Widad da Alhaji Nasir Albarka, saboda kaɓakin arzikin da suke basu shida 'yarsa se yanzu suke ganin duk izzar Widad a cikin gata suke, dan gashi a yanzu an maidasu kamar bayi a gidan haka suke zaune. Saleh ma yana ji yana gani, a gidan gonar nan haka Hajiya Halima ke zuwa ta ɗau abunda takeso ta fito dashi daga gidan ta siyar, ba yadda ya iya dan idan ya zaƙe su Alhaji Musa zasu iya gano shi, balli ya tashi dan haka se dai ya zura ido. Hanne bayan ta dawo daga kai albasarta kuwa, ɓangaren Jamila ta wuce taje tayi jifa da fantekar albasar, Jamila tace "ke lafiya kuwa, ke da yayanki yana nan kikazo kika mana jifa da kwanon nan da yaci ƙaniyarki ai" Hanne tayi tsaki tace "wallahi Jamila na tsani wannan koɗaɗiyyar bayahudiyar, na rasa me zan mata in huce" Jamila tace "wace bayahudiyar?" "wannan farar banzar ta gidanmu mana" Jamila tace "dama ba musulma bace?" "Musulma ce mana, sedai shegiya ce, bata da mutunci" Jamila tace "wai meye tsakanin kune? Me tayi miki haka kuke takun saƙa" "Wai ba damar magana ta haɗani da mijin ta, seta hau gayan magana, kokuma seta ganni se ta hau wani rungumeshi" Jamila tace  "ikon Allah, toke meye naki a ciki, ba mijin ta bane ba?" "to dan mijin ta ne seta dinga min haka? Naga dai namiji na maya huɗune, shikenan kuma baza'a kula shi ba?" Jamila tace "Auho, yanzu na gane inda kika dosa, to tun wuri ki kiyayi kanki, ina ruwanki da mijin ta? Ke ke inake ina wannan bawan Allah, yana da wannan mace kamar ita tayi kanta, ki taba kanki da wahala ki lallaɓa da wanda aka sa miki rana" Ji tayi wani mugun haushi ya kuma kamata, ta ja tsaki ta ɗau fantekarta tayi waje. Saboda tsabar takaici Widad kam a ɗaki ta wuni, tunda ta fito ta gaida Gwaggo ta koma ɗakinsu, dan ta riga ta gama kawowa iya wuya akan abunda yake faruwa, so take tayiwa Hannne abunda idan ta taho suka haɗu seta canza hanya, ace yarinya 'yar ƙauye kamar wannan ta dinga shigar mata hanci, wata zuciyar tace ' me zakiytsaya tankawa waccan kucakar, shi Yusuf ɗin zaki yiwa'  haka ta wuni tana ƙunci da ɓacin rai, Abincin rana ma ta fara ci ta kasa ta ajiye, ta nemi guri ta kwanta. Koda Yusuf ya dawo gida da yamma, yama manta da abunda ya faru da Safe, ya dawo ya tarar se cika take tana bastewa, Yusuf yace "Babyna wai meya farune kike wani haɗemin rai?" Shiru tayi masa ko inda yake taƙi kallo, ƙarshema ta miƙe zata fice, Yusuf yay Wuf ya riƙota yace "haba gimbiyata, me nayi miki ne, bana jin daɗin irin wannan hukuncin da kikemin, ki hukunta ni ban san laifina ba" Ƙwacewa tayi tace "ka ƙyaleni, ka koma gurin waccan 'yar ƙauyen daƙiƙiya ka Aureta, kuma kazo ka sakeni na gaya maka, nika ƙyaleni ita kaje ka aureta ka rabu dani, tunda itace mace" Wai yau yake ganin kishi gangariyarsa, dan shaf ya manta da wani abu ya faru yau da safe, ashe abun yana ranta tun safen nan. "Widad meye ya kawo wannan maganar kuma, ni nace miki ina son watane, ni ban gayamiki haka ba, meyasa kikemin hakane,? Haba Widad ki dinga jin tausayina inje in dawo a wahale, kekuma ki ƙaramin pressure" Tsaki tayi, tai waje zata bar ɗakin, ya biyota yana cewa "naji na karɓi laifina, kiyi haƙuri dan Allah ' Amma Widad tayi fafur, fuuu tayo waje abunta. Gwaggo ta kawo kai zata fito daga banɗaki, taga suna rigima seta koma bata fito ba. Widad ta samu kujera ta zauna kawai ta fashe da kuka, tama rasa kukan me take yi ne. Yusuf kuma ya koma ɗaki, ya rasa abunda ma zeyi. Gwaggo ta fito ta kalli Widad tace  "Amarya lafiya kuwa?" Widad ta goge idonta da sauri tace  "bakomai" Gwaggo ta kamo hannunta ta janyota zuwa ɗakinta, ta zaunar da ita akan gado. Jamila na nan zaune a ɗakin, da yake da ta gama aikin da zata yi a ɓangarenta nan take tahowa. Gwaggo ta kalleta tace  "Amarya, meyasa kike haka? Meyafaru ne ba wai sa miki ido nake ba, na kawo kai naga kina rigima da mijinki, yana baki haƙuri, ba wai ina son jin lallai meya haɗaku bane, a'a yakamata ki gyara mu'amalar Aurenki 'yata, ki samu namiji ya damu dake haka, ga mijinki yaron kirki me haƙuri, amma ki dinga masa haka, anya kuwa namiji ya miki laifi ya baki haƙuri amma kiƙi saurararsa ba' a haka 'yata" Jamila dake zaune tace "Taɓɗijan lallai ke' yar gata ce, har ana baki haƙuri, lallai kinyi dace ai wani namijim shi ze miki laifi, kuma ya dinga fushi sekin bashi haƙuri, ai kekam kinyi dace" Nan suka dinga yiwa Widad faɗa, suna mata nasiha akan yadda ake kula da miji, Gwaggo tace "Amarya mahaifiyarki na da rai kuwa?" Widad ta girgiza kai alamar a'a,  "mariƙiyarki bata gayamiki yadda rayuwa take ne?" Widad tayi shiru ba tace komai ba, nan suka zage suna mata nasiha, se kuma jikin ta yayi sanyi, tabbas Yusuf yana matuƙar haƙuri da ita, sekuma taji sam bata kyauta ba abunda tayi. Jamila ta tashi ta goya 'yarta tace' zomu je ɗakina kiji wani abu"....... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 88_89 Widad ta kalli Gwaggo, ta kalli Jamila, Jamila tace "magana zamuyi" Widad ta tashi tabi Jamila, suka zaga ɓangaren Jamila, ta buɗe ɗakinta tayi mata iso, suka shiga sannan ta kalli Widad tace "dukda naga baki da sakin jiki da mutane, amma naji ina son in temakeki, kinga nima da a ƙauyen nan nake, da mijina ya aureni muka tafi can barikin sojoji, to a can nima naga abubuwa, duk banyi karatun boko ba, amma na bazama na fara nema, naga yadda mata ke kula da mijk, naga a mugun ƙauye nake bansan komai ba, a tashin da mukayi a garin nan komai iyayen mu basa iya gayamana, mussman da ya shafi ɓangaren Aure ba abunda suke iya gayamana, saboda kunya amma ita rayuwar Aure faɗine da ita, amma a ɗan zaman da nayi zuwan nan nawa na fuskanci abubuwa da dama, ta wasu ɓangaren kina ƙoƙari, amma ta wani ɓangaren kina da rauni, mijinki yana da kyau yana da kirki masha Allah, idan har kikayi sake 'yan matan ƙauyen nan zasu cigaba da bibiyar sane, kiyi ƙoƙari ki riƙeshi sosai saboda mijinki zinare ne, samunsa a cikin maza akwai wahala Dan haka shi namiji idan yana ta taka, baka wannan dogon jan ajin, ai daya miki laifi idan ya baki haƙuri kawai a wuce gurin, idan ba haka ba ze fara tunanin ko bakya sonshi ne, ya fara leƙe leƙen wasu matan, idan da ba yayi to zaki koya masa da kanki Sannan wasu lokutan kina gsyamasa baƙar magana, kuma hakan be kamata ba tunda mijin kine, ba kowace magana zaki dinga gaya maaa yadda kike so ba, a koda yaushe mune ƙasa dasu dan haka dole mi bisu, dukda ban san dalilin zamanku a garin nan ba, amm gaki sam babu abunda ya haɗa kalarki da ƙauyen nan, dan baki kama da wadda take a wahala ba, amma ke yanzu dake kaɗai aka bari ki kula da kanki a ƙauyen nan zaki iya? Babu lallai ki iya saboda haka kodan yadda yake tsaye yana kula dake, yake iya ƙoƙarinsa akanki ya cancanci ki girmamashi saboda haka. Nasan ko ban faɗa miki ba abubuwan da Hanne take kinsan son mijinki take yi, dan haka seki kula sosai bar ganin kima da wannan kyan surar, yanzu se hankalinsa ya ɗauke idan kika gaza sauke haƙƙoƙinsa dake kanki. Ki kula ki tsare haƙƙinsa, sannan rayuwar Aure duk ta haƙurice, babu yadda za'ayi ace kullum shi ze dinga baki haƙuri, tun yana ta taki zeyi watsi dake wataran, mata na rububin irin mijinki, dan haka dan Allah ki dinga haƙuri dashi, karki ƙara yi masa abunda Gwaggo ta gani ɗazu. Maza na son a girmamasu, ka basu girmansu tunda Allah ne ya basu. Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki kula da mijinki, duk abunda baki gane ba ki tambayeni zan gayamiki, dan ita Gwaggo bakomai zata gayamiki ba saboda kunya" Nan ta cigaba gayawa Widad abubuwa da dama akan sabgar Aure, wanda Widad sam bata sani ba, nan ta dinga koya mata kissa da dabarun zama da miji, wanda ita Widad sam bata taɓa sanin su bama, dan ita rayuwar Auren bata gabanta balle tasan meya ƙunsa. Abun ya dinga bawa Widad mamaki, lallai wanda ya rasa uwa yayi kuka, ita banda yanzu ma wasu abubuwan bata sansu ba game da Auren, lallai Yusuf yana haƙuri, wata zuciyar ta ta tace  'amma ai Auren bogine bana gaske ba meye na damuwa da ɗaga hankali?' Wata zuciyar kuma tace 'dukda hakan dai, ai yakamata ko yaya ki kyautata masa, ko bakomai ya cancanci hakan daga gareki, karki zama me butulci mana. Duk da Jamila ba wata babba bace, amma ta gayawa Widad abubuwa da dama da yakamata ace ta sani, game da rayuwar Aure, wanda yanayin zamansu da Yusuf ita bata saniba. Widad tayi mata godiya, sannan suka dawo ɓangaren su Gwaggo, koda ta koma Yusuf ya fita bayanan, dan haka ta shiga shagalinta. Hari na ganin Widad a tsakar gida tace  "Mhmm yau ninaga abunda yafi ƙarfina yafi ƙarfin idanuna, wai nikam dama Yaya nace mutane ma na wa junansu ɗura kamar yadda tsuntsaye keyi?" Gwaggo tace "to ikon Allah, nima ban sani ba gaskiya dan ban taɓa jiba ko gani, se yanzu a bakinki" Hari tace "hmmm, ai ina ganin tsiyataku kala daban daban, wani abunma idan na gani na dinga Tuba kenan kar inje in fita daga musulunci ban sani ba, banda jaraba ace mutum yasa bakinsa a cikin na ɗan uwansa, saboda tsabar ƙazanta, yo nidai nasam tsuntsaye ne kawai ke yin haka, amma se gashi mutane ma nayi, kai ina ganin masifa ƙuru ƙuru" Widad ta ƙura mata ido, Ba shiri Hari taja bakinta ta tsuke, tun kan Widad ta gayamata baƙar magana itama. Widad a ranta tace  "ke wannan haƙoran naki, gaftara gaftara koraye wane mijin ze sha'awar sa bakinsa a naki? ' Yusuf ya dawo amma yayi watsi da Widad, yaƙi shiga sabgarta ya cigaba da harkokin gabansa, sam yaƙi kula ta, gaba ɗaya se taji babu daɗi, ta kuma rasa yadda zata yi ya kula ta. Yusuf ya samu guri yai kwanciyarsa, ba tare da ya tsokane ta ba yau, koya mata hira, ko yazo inda take ya share ta kamar shikaɗaine a ɗakin. Bacci ma ya nemi ya gagareta, gashi 'yan kwanakin nan ta fara sabawa da kwanciya a jikinsa, amma yaƙi kulata yau, gaba ɗaya taji garin ya mata zafi. Da safe ma farkawa tayi taga yayi ficewarsa, ta rasa abunda yake mata daɗi haka nan jiki a sanyaye take komai, tayi wanka ta karya. Hindu ta tsiri yin Faten tsaki, Widad tace suyi a kan risho ɗinta, suka gyara yakuwa tare da kabewa, anan Jamila ta sake lura shikansa aikin Widad bata iya ba, danma ba tun farkon zuwanta taga kwaɓar da Widad take ba. Akayi fate aka gama, suka zuba suka fara sha, Widad da ƙyar tai spoon biyu tace "ni gaskiya wannan abun ba daɗi, tayar min da zuciya ma yake, ga tsami ga gishiri ni na kasa gane ma meye taste ɗin Abincin" Jamila ta dinga tsokanar Widad, wai kodai cikine kuma baya son faten, ita dai Widad har yanzu bata sake da Jamila ba, amma taji daɗin bayanan da tayi mata. Kuma babban abunda yake burgeta da Jamila, kullum jaririyarta tsaf da ita, kuma idan taje ɗauka bata hanata, tana bata ta ɗauka. Jamila tace "kun shirya kuwa?" Widad ta tura baki tace "baya ƙi kulani ba, me zance masa?" Jamila tace "kinga abunda nake gayamiki ko? Allah yasa ba budurwa yayi ba wadda zata dinga tarairayarsa ba" Zare ido Widad tayi ta harari Jamila tace "shi ya isa ma?" "Au haka kika ce?" "Eh haka nace" Jamila tayi murmushi tace "ai shikenan, cikin hira ta cigaba da ganar da Widad wasu al'amuran, dukda wani lokacin in anyi gabas se tayi yamma. Da yamma taga su Gwaggo suna ta shirye shirye, Widad tace" Mama ina zuku ne kuke ta shiri haka? " Gwaggo tace  " bikine zamu wani ƙauye a gabanmu, Yayar Baffa ce zata yi Auren 'ya" "Mama zan biku nima dan Allah" "Ahh haka kurum, da mijinki da komai a' a ba ruwana" Widad ta marairaice tace  "dan Allah Mama" Gwaggo tace "to ki tambayi Yusuf tukuna, danmu kwana uku zamuyi" "to ai bazece komai ba, dan Allah nidai zan biku zanje nima in haɗa kayana" "Amarya, babu yadda za'ayi muyi tafiya dake, ba tare da kin nemi izininsa ba, idan ya bari bakomai semu tafi' Widad tace  " bari yazo in tambayeshi to " Wani wahalallaen bacci ne Nurat take yinsa bayan sallar Azahar, wayarta dake ƙasan pillow ta fara vibrating, a ɗan razane ta farka, tasa hannu a ƙasan pillowa ta ɗakko wayar, ta amsa sannan ta saka a kunnenta   "Hello Brother" "Nurat, kina gida ne zan shigo yanzu?" Ta miƙe zaune da sauri tace "No karka zo dan Allah, Daddy yana gida yanzu ze iya fara zargin wani abu, kuma kasan ya hanani fita, amma me ake ciki?" Khalil yace  "Aikin da kika bani na fara, amma ko kin san cewa Yusuf ɗin nan ɗan sanda ne?" "Kamar yaya? Wai dama dagaske ne shi ɗan sanda ne? Naji a labarai na zata ƙaryane ai" Khalil yace "to gaske ne, ɗan sanda ne na farin kaya, yayi basaja yaje a matsayin direba, kuma yayi garkuwa da yarinyar" "Kahlil saboda wanke Yusuf yasa na sakoka a cikin wannan lamarin, dan Allah karka ƙara danganta Yusuf da wannan mugun aikin, baze taɓa aikata haka ba na tabatta" Khalil yace "shikenan naji, karkiyi kuka, ai ina kan yin bincike ne, ban tabattar ba, abun da ake ciki zan miki magana, amma banda kuka kinji ƙanwata" Nurat ta gyaɗa kai kamar yana ganinta. Widad da wuri ta sallami ɗalibanta yau, dan wasa wasa da yammar nan cika tsakar gidan Megari akeyi, an samo musu alli da allo na rubutu, sannan kowa da littafinsa da abun rubutu, babban abunda yake burge Widad be wuce yadda suke girmamata ba, suna girmama malami a ƙauyen nan, kuma a hankali tana jansu a jiki yanzu, musamman 'yan ƙananan yaran nan, da sunzo kwanukanta ɗakinta har tsakar gidan duk se subi su gyara, saboda tsabar girmamawa. Widad nata ɗokin Yusuf ya dawo ta tambaye shi, dan harta manta sunyi faɗa, seda ya dawo taga ba fuska, Yusuf be taɓa mata kwarjinin da yayi mata yau ba, sam ta kasa masa magana sedai kallonsa kawai da take yi. Koda yayi alwala ya fita sallar magariba, se bayan isha'i sosai sannan ya dawo, ya ɗau Abincinsa ya fara ci, ta zuba masa ido amma ta kasa magana, can dai taita maza tace "Yoseef dama, su Mama ne zasu je biki, shine tace in tambayeka idan zaka barni in bisu, inje inga yadda akeyi" Banza Yusuf yayi mata, kamar beji me tace ba, "Yoseef magana fa nake maka" "Kiyi abunda kika ga dama kawai" ya bata amsa. Jin maganar tayi wani banbarakwai ba tsari, wai tayi abunda taga dama. "Ka barni inje kenan?" "Meye na tambayata kuma ne? Nace kiyi abunda kika ga dama, ai damani baki ɗaukeni miji ba, na kan manta in wuce gona da iri wasu lokutan, waini game mata, na kan manta ashe nifa direba ne, iyakaci in miki aiki ki biyani, dan haka idan harni mininki ne, to ban yadda kije ba, sedai nasan ba lallai ki yadda da hukunci na, saboda ban kai a kirani mijinki ba, ban isa komai a gurin kiba, dan haka kiyi abunda kike so, zama ko zuwa ya rage naki" Yana gama maganar ya tashi ya bar mata ɗakin, wani malolon takaicine ya tokare mata zuciya, dama Wai Yusuf ya iya fushi haka? Har washegari be kumabi takanta ba, tana ji tana gani su Gwaggo suka shirya yaransu da manyansu suka tafi aka barsu a gida, Jamila na ɓangaren ta nata bisu ba, se abokiyar kishin Widad wato Hanne bata bisu tace bata da lafiya ita bazata ba dan haka tana gida itama. Da daddare Yusuf ya idar da sallar isha'i yana lazimi, Widad a hankali tace  "Yoseef" ta kira sunansa kusan sau uku, amma yayi shiru, can tace "Yuzarsef" Da sauri ya ɗaga ido ya kalleta jin sunan data faɗa, dukda be amsa ba amma taga damuwarsa ta ƙaru, ya kifa goshinsa akan gwiwar ƙafafuwansa daya ɗage. Sanye da zumbulelen hijjabinta tazo, tasa hannu ta ɗago fuskarsa tace "wani laifin na kuma yi maka dan na kiraka da Yuzarsef?" Girgiza mata kai yayi, alamar a'a yana ƙoƙarin maida kansa. Ta sa hannu biyu ta tallafi fuskarsa tace "Yoseef, me nayi maka ne? Dan Allah kayi haƙuri" Yusuf yace "aini baki min komai ba, sedai yau ina son in san saki nawa kike so in miki?" Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, tace  "kamar yaya? " Yace  "kamar yadda na tambayeki, saki nawa kike so?" "Yaushe nace maka haka?" Yace "kin manta abunda kika gayamin ne? Ina son in koyawa kaina rayuwa ko babu ke ne, kusan koyaushe kina maganar in sakeki, duk ƙoƙarina bakya gani, bakya tausayamin ya zanyi? Gara idan muka rabu inda wani ɗakin duk rashin kyansa a bani, in lallaɓa in fara koyawa kaina zama ko babu ke" Aikuwa ta fashe da kuka tace "nifa ban san nayi ba, ban san meyasa nake jin haushi idan naga wata ta raɓeka ba, tun jiya nake maka magana, amma kana shareni, se kulaka nake amma kaƙi ko kallona, na tambayeka abu ka hanani, kuma banyi ba, amma ka kama min faɗa, you want turn on me ko, shikenan" Ta juya zata tashi ya Riƙeta, yace "babu wani dalili da zesa in juya miki baya, sedai nine kin kasamin adalci, bakya iyayi min adalci a wasu lokutan, kiyi ta bani wahala saboda kinga ina sonki ko?" Share hawaye tayi, ba tare da tace komai ba, Yusuf yace "yanzu me kikeson ayi?" "Ka dinga kulani, ka dena ɗauremin fuska" "shikenan za'ayi yadda kike so, amma da bakinki nake son ki faɗi saki nawa kike so?" Shiru tayi batayi magana ba, sema sunkuyar da kanta da tayi tana kallon wani gurin daban. "Widad magana fa nake miki" Ɗison hawayen ta ya gani yana ɗigowa a ƙasa, taƙi ɗaga kanta kuma taƙi magana. Yace "shikenan, tashi kije ki kwanta" Ta miƙe sum sum ta tafi katifarta ta kwanta, tai shiru tana tunani, wai yanzu dagaske Yusuf yake sakinta zeyi, se taji gabanta ya faɗi, 'to meye dan ya sakeki, dama ai akan haka kuke' wani sashe na zuciyarta ya gayamata. 'Amma dukda haka nayi sabo dashi, sabo me ƙarfin gaske, yanzu idan ya rabu dani ya zanyi? Zan koma irin rayuwar kaɗaici na ta baya kenan?' Kawai ta sake fashewa da kuka, yana jinta amma yai shiru kamar be san tana yiba, se can dare bayan ya idar da sallar dare, yayi addu'oin da zeyi sannan ya tao a hankali ya hau kan katifar ya rungume ta a jikinsa, lokacin har riga tayi bacci, wannan fushin da yayi da ita na kwana biyu shikansa yaji a jikinsa, dan ba ƙaramin kewarta yayi ba, a jininsa yake jin soyayyar Widad na ratsashi, shi dai yana matuƙar sonta. Kamar yadda Suleiman ya buƙata, Abbas yaje office ɗinsa, seda ya ɗan jira ya sallami baƙi sannan ya ganshi. Bayan sun gaisa ne Suleiman yace "Abbas ashe ka shigo garin nan babu Labari, sekace wanda akayi zaman gaba aika leƙo a gaisa ' Abbas ya ɗan sosa kai yace " Ai Yallaɓai abubuwan ne dama duk se a hankali, kuma ni ɗanje ziyare ziyare ne, shiyasa amma dama can nayi niyyar in ɓullo a gaisa ai, da amana bazan watsar daku ba" Suleiman yai murmushi yace "shikenan, ya aikin ya hanya?" "Alhamdilillah, aiki can ai har yafi nan daɗi" Suleiman yace "madalla ai haka ake so, nace ka kuwa ji abunda ya faru da Yusuf?" Abbas yace "naji yallaɓai, abun ya bani mamaki, mutum a fuska mumini amma zuciyarsa ba Allah, saboda son zuciya kawai daga aiki seka yi garkuwa da 'yar mutane, gaskiya bewa kansa adalci ba, Yusuf ya bada mamaki" Suleiman yai ƙuri da ido yana sauraren Abbas, se da ya gama sannan yayi ajiyar zuciya yace "to ai koma menene Allah baya bacci, kuma muna bayan ɗan uwanmu, Insha Allah, sannan bama saka ran Yusuf ze aikata abunda ake tuhhmarsa dashi sam, yanzu ni babban abunda yaaa na kiraka shine, kaga kaine babban Abokinsa, mahaifiyarsa tana cikin damuwa ƙwarai, naje gurinta take cemin taji ance kaje amma ba kaje ka mata jajen abunda ya samu Yusuf ba, dan Allah ka daure ka zagaya kayi mata jaje ko ka ɗebe mata kewar ɗanta" Abbas yace "shikenan, dan dai wannan insha Allah daga nan ma zanje, Allah sarki insha Allah zan biya in gaisheta" Suleiman yace "ba laifi hakan yayi kyau" Abbas na fitowa yace "Aikin banza, ina ruwana uwatace ita, taje duk abunda ze sameta ya sameta, nan aka canza gurin aiki aka bawa ɗanta muƙamina, ba abunda tace se yanzu wani in mata jaje baza'ayi ba ɗin, Allah ya ƙara ' Harze wuce ya hangi Sakina ta taho da files a hannunta, yana ganinta ya fara murmushi yace "budurwar kidnapper, ashe abunda ya faru kenan? Saurayinki yaje ya sace' yar masu kuɗi gaskiya kuna ruwa" Sakina tace "haba Abbas, yazaka maida abun abun wasa? Wannan maganar be dace a jita daga bakinka ba a matsayinsa na Abokinka, kuma abokin aikin mu, kuma kasan baze aikata hakan ba" "ke dalla ware, waye yace miki baze aikata ba? Mutum nefa shi, waye baya son kuɗi a rayuwar nan? Kedai Allah ya kyauta kawai ya tona masa Asiri, dama ya daɗe yana naɗe kura da fatar Akuya ne" Sakina ta dinga bin Abbas da kallon mamaki, wai babban abokine yake faɗar maganganu akan Abokinsa haka, lallai duniyar nan ba abun yadda bace. Da Asuba Yusuf ya tashi Widad tayi salla, taji daɗi yau ya kulata ya tasheta tayi salla, bayan ta idar ta koma baccin nata na ƙa'ida. Yusuf yayi komai, har sharar tsakar gida, Hanne a ɓangaren Jamila ta kwana, da safe ta dawo ɓangaren su dan taga Yusuf, aikuwa ta tarar dashi yana shara. "Ina kwana? ' Yusuf ya kalleta ya amsa mata, ya cigaba da shara," kawo in share gidan " Yusuf yace ' A'a bakomai zanyi, ai ba wani abu bane" Duk yadda Hanne taso ko hira su ɗanyi da Yusuf yaƙi yadda, saboda ya gane Lagon Widad yanzu, kishi ne da ita matuƙa, dan haka ya fara ƙoƙarin kiyayewa. Sam Hanne bata ji daɗin yadda Yusuf yayi mata yau ba. Ya koma ya ɗora girki a ɗaki, yana yi ya kalli inda Widad ke kwance na bacci, yana zuwa beyi wata wata ba ya ɗagata sama yai waje da ita tsakar gida. Buɗe baki tayi zata yi ihu, ya rufe mata baki yace "ke nine fa" sannan tai shiru tana ajiyar zuciya tace 'shine zaka tsoratani kuma?' "Yaushe kika zama matsoraciya ne? Kedai kiyi bacci kiyi bacci, ko gajiya bakya yi? Karɓi brush ɗinki ki wanke baki, muje ki tayani girki" Yai maganar yana matsa mata toothpaste, "Yayan Daddy ka dena fushin dani ne?" "A'a har yanzu inayi" "Meyasa bazaka haƙura ba?" Yusuf yace "kona haƙura anjima ma, sekin sake abunda zanyi fushi dake" "to ai nace Kayi haƙuri, kuma ai kai baka fushi fa" Yace "waya gayamiki bana fushi? Nima mutum ne fa" "To na dena kaji" tai maganar a sigar Shagwaɓa. "Idan kika kuma, sedai ki wayi gari kiga na fece na barki" "Aikuwa inaga da haɗiyar zuciya zanyi in huta" Murmushi yayi yace "ba wani haɗiyar zuciya, ai bakya sona" Ba tace komai ba ta fara wanke bakinta, suka gama suka koma ɗaki, can Widad tace "Yoseed, meyasa da nace maka Yuzarsef naga ka shiga damuwa jiya?" Yace "karki damu ba wani abu bane, kin tunamin da babana ne" "Allah sarki, Allah yayi musu rahama gaba ɗaya" Yace "Ameen ya Allah masoyiyyata" Yai maganar tare da sumbatar kumatunta. Tayi murmushi tace "Yayan Daddy, kamin addu'a Allah yasa in samu ciki, so nake in haihu nima ace ina da baby" Da sauri Yusuf yayi mata wani irin kallo, da ita kanga bata gane ma'anar sa ba.... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 90_91 Saroro tayi tana kallonsa ta kasa gane me yake nufi da wannan kallon da yake mata, tace "ya dai naga kamar ka ɓata rai? Ko na sake faɗan wani abun na dai dai ba" Girgiza mata kai yayi yace "No bakomai" "Amma naga kamar ka ɓata rai? Da ba a haka fuskarka take ba fa" Yusuf yace "A'a ba ɓata rai nayi ba, karki damu zo kici Abincin ki, nasan kina jin yunwa yanzu, dan rana tayi baki karya ba" Ya zuba mata Abincin, Haka taci Abincin tana lura da yadda Yusuf duk yayi wani iri, kamar wani abu yana ɗan damunsa, amma babu alamar ze faɗa mata meke damun nasa. Anwar ya shirya yaje gidansu Fahad, domin yana son ganin Bulama suyi magana, sedai be sami Fahad a gida ba, dama ba gurinsa yaje ba dan haka be kula ba ya nemi idan Bulama yana nan a masa iso, Ramadan yayi masa iso zuwa gurin Bulama, Bulama na ganinsa yayi murmushi yace  "Anwar, anya in kulaka kwana biyu baka leƙowa mu gaisa" Anwar yayi murmushi yace "tuba nake, abubuwa ne suka ɗanyi yawa wlh, Daddy ya aiki ya gida? Naji amce zaka Umarah shiyasa nace bari inzo in sameka" "Alhamdilillah Anwar, eh insha Allah sati ma gaba zan tafi da yardar Allah, ya gidan naku ya babarta ka da ƙannenka?" Anwar yace "Tana lafiya ƙalau Alhamdilillah" "Masha Allah, nice to hear that haka akeso ai, naji kana son ganina meyafaru ne?" Anwar yace  "Amm Daddy, dama nazo ne akan inji wai har yanzu babu wani labari game da ɓatan Mariƙinmune? Har yanzu babu shi babu Widad gashi lokaci yana ta ƙara ja, amma shiru babu wani labari akai" Bulama ya gyara zama sannan yace  "Ahh mekuma kake sonji Anwar, bayan wanda yake ta yawo a gari? Widad garin jajibe jajibenta duk wayo da ƙin mutanenta, amma ta yayimo tsiya, wani koɗaɗɗen yaro me kama da sadakar yalla nan, direbanta ta ɗauki duk wata ragamar yaddarta ta bashi, ko gidan nan tazo duk sirrin magana sedai muyi a gabansa, ko nan da cam ba zata je ba seda shi, duk maganar da zamuyi sedai a gabansa, dan haka duk yadda take kaffa kaffa yasan wasu daga cikin sirrinta, gashi ƙarshe 'yan sanda bincikensu ya tabattar musu da cewar, shine yayi garkuwa da ita, ya nemi kuɗin fansa a gurin mahaifinta, dabe samu ba shine yabi Asibitin ya sace mahaifinta, yanzu dai' yan sanda suna nan suna binciken inda zasu gansu, amma shiru babu Labari, sedai a cigaba da Addu'a sannan mu cigaba da sauraren abunda zasu ce, amma abun da ɗaure kai fa sosai" Anwar yace "nifa Daddy har yanzu ban yadda da wannan sakamakon binciken ba da aka bayyana, babu yadda za'ayi ace shine ya saceta, Daddy kasanta da wayon tsiya, babu yadda za' ayi tana sane ta bari yasan sirrinta, sedai idan akwai wata manufa da take dashi a kanta, sannan daga rundunar 'yan sandan nan a farko an sanar da sace su akayi, har an siyar da motar da aka sace su a ciki an ganta a kasuwa, ba' a kumabi takan zancem ba, basu bincika ya akai motar taje kasuwa ba, kuma azo a sake sanar da cewa wai shine ya saceta, it doesn't make sense, kuma bayan haka ace ya kuma zuwa ya sace mahaifinta, sam beyi kama da criminals ba, ni gaba ɗaya banji ƙamshin gaskiya a lamarin nan ba, akwai wata a ƙasa dai" Bulama yace "eh to, kaima maganarka abun dubawace, amma ka sani mutum yana iya canzawa a kowane lokaci, kuma ze iya yuwuwa shine ya saida motar, tunda yasan siriikanta dan yasan abunda ban sani ba ni game da ita, sannan kuma duk abunka da ƙwaƙwƙwafinka kasan dai ba zaka gwadawa 'yan sanda aikinsu ba, tunda suka faɗi haka kasan abunda bincikensu ya nuna musu kenan, ba zasu yi ƙarya ba haka kurum, kabar mutum akan aikinsa kawai" Anwar kamar ze kuka yace "Amma Daddy babu abunda' yan sanda ba zasu iyayi akan kuɗi ba kaima ka sani, idan wasu ba zasu yi ba, wasu zasuyi tunda suma mutane ne, dan haka ba abun mamaki bane suma 'yan sanda suyi komai akan kuɗi ba, dan haka yakamata ta ɓangarenka ma, kasa a sake bincikawa a tabattar da in dagaske binciken nasu haka yake, kasan Alhaji Nasir da' yarsa suna da maƙiya, komai fa ze iya faruwa, zata iya yuwuwa su suke wannan abubuwan haka" Bulama yayi dariya irin tasu ta tsofaffin manya yace  "Yaro yarone dai, Amma kaima kace wani abu me mahimmanci fa, shikenan Anwar tunda haka kace, Insha Allah zanga ƙoƙarin da zanyi ta ɓangarena, tabbas Daula yana da maƙiya kam, kuma komai ze iya faruwa, zanga abunda zan iya, Allah ya wuce mana gaba" Anwar yace  "Ameen Daddy, nagode sosai" Kasancewar gidan babu kowa yasa Yusuf baya fita ko ina, dan baze iya fita ya barta a gida ba ita kaɗai, yasan ba zata zauna bama, suna zaune tama ta saƙa mafici Ya ɗan kalleta yace "Widad" Ta ɗago ta kalleshi Tace  "Na'am" Yace "Me kike tunani game da wannan baƙin, ɗan megari da matarsa, bakya ganin Asirinmu ze iya tonuwa zamanmu dasu? Kar muje a samu matsala fa" Widad ta ajiye abun hannunta jiki a sanyaye tace "To aini gaba ɗaya kaina ya kulle Yoseef, na rasa meye abunyi wallahi, kawai ni yanzu na fawallawa Allah lamarinsa, duk yadda yayi damu shikenan, ni dai babban fatana in cika burina kafin in mutu, nasan ko asirinmu ya tonu, ko be tonu ba dole ɗayanmu zeyi nasara, komu ko maƙiya, dan haka na miƙawa Allah lamarina, Allah ya kiyaye mu gaba ɗaya, amma nima nayi irin wannan tunanin naka, amma ba yadda na iya, in mun bar nan ina zamu?" Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "da farko ina ɗan jin shakku a raina ne, amma Saleh ya tabattar min da babu komai, ba abunda ze faru yasan matakan daya ɗauka, sedai ina fatan Allah yasa hakan, Allah ya kiyayemu da kiyayewarsa" Tace "Ameen ya Allah, Amma Yoseef nifa har yanzu baka taɓa gayamin meka gano a naka binciken ba, da kayi a lokacin muna gida" Yusuf ya ɗanyi murmushi yace  "Anƙi a faɗa ɗin, kema ai jamin rai kika dingayi, kika ƙi gayamin tarihinki" Cikin Shagwaɓa tace "please" Yusuf yace "to shagwaɓaɓiya karkimin kuka dai, bincike daga cikin gidanku na fara yi, sedai nayi mamakin ƙiyayyar da matar mahaifin ki ke miki, da farko nayi zaton tana yi ne saboda halayenki, da abunda kikeyi na wulaƙanta ta da 'ya' yanta, sedai daga baya na gane son zuciyarta ne abunda take, akwai ranar da kika rufe ƙofa kika ƙi buɗewa, nasa Amal ta kawo miki tea, sedai kika zubar da tea ɗin, nayi mamakin ganin ƙwaya a ƙasan kofin shayin" Widad tace "Kasan meyafaru a wannan daren, da na birkice?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. Tace  "samunsu nayi a falo, suna tattauna yadda zata damfari Daddy kuɗi, kasan na kanyi kwanaki a part ɗina ban fito ba, shine suka sakankance suna hirarsu, basu yi tsammani ba kawai suka ganni a ƙofar falo, shine suka shiga kame kame, bance musu komai ba, na fita dama fita zamuyi da kai ranar, bayan mun dawo cikin dare ina bacci, da yake ban rufe ƙofar ɗakina ba, kawai seji nayi cikin bacci ana lalabun hannuna, nayi yinƙuri zan ƙwaci hannuna kawai akayi min Allura, irin Allurar da'ake min a baya a birkita ni, take na fara dena gane abubuwa sosai, ban san wanda yayi min allurar ba, amma a haka bayan ya fita na tashi ina tangaɗi na rufe ƙofata, tun daga nan ban sake sanin abunda ke faruwa ba, se bayan dawowar Daddy, shiyasa a rayuwa na tsani matar nan Yoseef, na tsaneta fiye da yadda kake tunani, ji nake kamar in shaƙeta seta mutu" "a'a karki kuma cewa zaki kashe mutum, sannan kika sani ko Daddy yana son matarsa? Ki barwa Allah zakiga sakayyar daze miki, amma banda ambaton kisa" "Rabu dani bazaka gane ba Wallahi, dama muna komawa Seta barmana gida, sannan Aure zan nemawa Daddy da kaina, sannan ko banyi kisa ba idona idon Bukar a zahiri seya tafi lahira da tabom da zanyi masa" "Kibi komai a hankali Widad, Insha Allah komai zamu bishi a hankali, kuma zamuyi nasara da yardar Allah, Amma karki yinƙurim ɗaukar doka a hannu, dukda bansan waye Bukar ɗinba, kuma bansan meya yi miki ba, amma karkiyi ganganci, muyi komai a dokance" Ta girgiza kai tace "bazaka gane me nake jiba a Yoseef, idan ban kashe mutumin nan ba kona masa illar da zan nakasta shi ba, to zan mutu ne" tai maganar tana kwanciya a jikinsa. Yasa hannu ya rungumeta a jikinsa, shiru ya wanzu a tsakanin su. Yusuf idan suka gaji da zaman ɗaki sesu dawo tsakar gida, suyi shimfiɗa suyi zaman su, sannan gaba ɗaya Yusuf ya shiga kiyaye abunda yasan zai ɓata mata rai. Lokaci lokaci takan shiga ɓangaren Jamila, dan ta ɗau jaririyarta, dan har goya mata ita take yanzu, idan ta goyamata ita ta zauna guri ɗaya ta nutsu sosai kamar am goyawa yaro, Jamila tace  "Widad waike bakya saka Atamfa ne,? Kullum se ƙananan kaya, baki san yawan saka abu ɗaya yana gundurar mijinki ba?zeso yaga kin canza ai" Widad tace  "nifa ban iya saka wata atmfa ba, tun taso wata ni bana saka wata Atamfa fa ko makamancin haka" Jamila tace "Eh naga alama nima, amma Aikuwa yakamata mu bawa mijinki mamaki, ina da sabuwar atamfa na haihuwar Yusra da aka bani na barka, zan kai a ɗinka miki" Widad tace "A'a karfa Yoseef yaji haushi, ko yace ban gaya masa ba" Jamila tace "baze ce komai ba, zeyi mamaki ya ganki acikin Atamfa, karki damu ba abunda zece zeyi murna shima, kim san maza nason a basu mamaki, amma ina fatan kun shirya da shi"? Widad tace "eh mun shirya, tun jiya amma da ƙyar yayi fushi dani sosai" Jamila tayi murmushi tace  "Yawwa tawan, karki ƙara bari ya kwana yana fushi dake kinji ko, sannan ke zakiyi dabarun daze dena daɗewa yana fushi dake" Widad tace  "to ni ya zanyi?, yana daɗewa beyi ba, amma idan yayi fushi da ƙyar yake sauka fa" Tace "to kidena yin abunda ze sashi fushin mana, kuma Kinga yadda kike da kyan nan masha Allah, gaki da manyan idanu masu ɗaukar hankali masha Allah, ki dena kallonsa kamar yadda kike kallon sauran mutane, ki nuna masa Wata kissar sai mata (wanda be karanta littafin wata kissar sai mata ba na Ammar da Mufeeda, ya garzaya ya nemi nashi, akwai darasi a ciki 😍 da Nishaɗantarwa) Idan zaki masa magana, ki dinga kashe masa ido, ko ɗan shanye idanunki kamar kina maye, dama na ganki masha Allah, shagwaɓaɓiya ce duk kidinga masa, ko yayi fushinma da kansa ze sakko, saboda karya yi missing wannan kallon" Widad kawai ta kwashe da dariya, "Au dariya ma na baki? Aiko ki gwada zaki bani labari, ki dinga zuwar masa da abubuwan da bakya masa a baya, hakan zesa ya ƙara sonki, kin san mazan ne seda lallaɓawa, amma dukda haka suna mana ƙoƙari kuma suna haƙuri damu, sedai duk Allah ya bamu haƙurin zama da juna" Hanne ce ta shigo, ta dinga jiyo dariyar Widad da Jamila, ta ƙaraso ta ɗaga labule, taga Widad a zaune da goyon 'ya suna hira da Jamila, ai shigowar da ba tayi ba kenan ta koma, tana tsaki. Sunusi ne mijin Jamila ya dawo, dan haka Widad ta bawa Jamila' yarta ta fice, dama ba gaisawa suke ba da Widad, dan haka ne kulata ba bata kula shi ba ta fito ta tafi ɓangarensu, ta tarar Yusuf ya shimfiɗa tabarma a tsakar gida yayi ruf da ciki, yana karanta azkar. Tana zuwa ta cire hijjabinta, ta hau kan bayansa. Yace "ya hakane? sekin karyamin baya ne? So kike ki maidani gurgu?" "Idan na maida kai gurgu ai dai mijinane bana wata ba ko?" Yusuf yace "Allah? waye mijin naki, gayamin" Tace "Yoseef ne mana" Yace "to naji ɗagani, dan kin ƙara nauyi, matar ƙauye kawai kina ƙauye amma ƙiba kike" "kaima Mijin ƙauye, kuma bazan tashi ba, idan ka takuramin kuma ka sha cizo ba" Yusuf yace "hmm aikin taɓa cizona fa, akwai tabon a jikina" Ta zare ido tace "yaushe na cijeka?" "Ranar da aka yi ruwan sama mana da daddare" Tace  "wane ruwan saman akayi?" Yasa hannu ya janyota daga bayansa, ya kwantar da ita a jikin bango yana kallonta, sannan yace  "Ranar da kika kusa taramin jama'ar garin nan, kalli inda kika cijeni, banda duka dana sha a gurinki" Tura baki tayi tace  "Eh anyi ɗin ba kaine ka... Se tai shiru Yace " ƙarasa mana" "Anƙi a ƙarasa ɗin" tai maganar tana dariya. Yusuf ma dariya yayi ya juya yayi rigingine, ta kwanta a ƙirjinsa tace  "Yayan Daddy, a rayuwa yadda da farinciki sune gaba gurin sada mutum da walwala, kalleni a garin da babu wauti, ba ruwa, ba waya, ba system, ba motoci babu duk wani abu na more rayuwa, amma gashi kai kaɗai kana bani farincikin da duk wannan abubuwan dana rayu dasu basu bani ba, dukda na sha wahala kafin sabawa da wasu abubuwan a garin nan, amma bayan na saba sena gane ita rayuwa a bace me sauƙi, yadda ka ɗauketa haka take zuwar maka Nagode sosai Ɗan uwana, kayi rawar gani a rayuwar Yarinyar da baka haɗa komai da ita ba" Rungumeta yayi yace "ina fatan kasancewa dake har ƙarshen rayuwa ta Widad, dukda bani da tabaccin ina da mahalli a zuciyarki, kuma ban san yadda al'umma zasu karɓi Auren nan namu ba, amma nidai nasan ina sonki Widad, ban san yadda hali zeyi ba a nan gaba, ko dai mu kasance tare, kokuma mu rabu, amma ni dai nasan ina sonki, Dukda soyayya ta ta baya, banji naso wata kamarki ba, I love you Widad " Ƙanƙame Yusuf tayi, tana jin wani irin shauƙi yana ɗibarta, a koda yaushe ta kanji farinciki idan yana tare da ita, koda suna gida yana a matsayin direbanta, ko tana cikin ɓacin rai idan taga yazo se taji damuwarta ta ragu, tana jinsa sosai a ranta amma ta kasa danganta hakan da Soyayya, a duk lokacin da taji damuwa ta mata yawa, tana haɗa ƙirjinta da nasa zataji bugun zuciyarta na daidaituwa, da zarar ya fara rarrashinta  ta kan manta ɗinbin damuwarta, tayi wani irin sabo na bazata da Yusuf, wanda har take jin ya zata kasance idan ta koma gida, Yusuf ya nesanta ida?. "Yayana, zaka dawo gidanmu da zama dan Allah" "meyasa kika dage sena koma gidanku da zama?" "Saboda Halima zata bar mana gida, da kaina zan samowa Daddy mata ya aura, zaka dawo gidanmu ko?" "Meyasa kika damu sena dawo gidanku bayan bakya sona?" "Nima ban san dalili ba, sedai ina jin a jikina, rasa ka a rayuwata babban giɓine, kuma tamkar rasa garkuwa ne a gareni" "Nima rashinki a gareni babban giɓine, saboda na kamu da makauniyar soyayya cikin bazata, amma ban saniba ko zaki iya cigaba da zama dani idan kika san wani abu game da rayuwata" "Ni dai koma meye, dan Allah ka zauna a gidanmu idan mun koma kaji" Ta maganar cikin Shagwaɓa tana kallonsa,  "Babyna wannan wane irin kallone haka kikemin? You look so cute da kika juya idonki" Kamar ƙaramar yarinya ta kuma cewa "dan Allah kec zaka dawo mana" Yace "sedai in dawo im cigaba da kaiki unguwa, ni nafi son aikina" "Aikuwa demotion zan maka, ka koma gadin ɗakina" "Bakomai in dai hakan zesa in dinga ganinki" Yai maganar yana saka hancinsa a wuyanta. Ji suke tamkar suka ɗaine a duniyar, Kasancewar gidan ba kowa dan haka hankali  kwance suke soyayyarsu a tsakar gida, basu san Hanne tana ɗaki tana jiyo dariyarsu ba, dan har leƙsensu take ta taga tana share hawaye. Anwar yayi tunanin bari ya tsaya a gidansu Nurat su gaisa, kwana biyu kota waya basa haɗuwa dan bama hawa yake social media ba sosai balle su gaisa, sannan su jajantawa juna abubuwan da suke wakana, sedai a bakin gate megadi ya tareshi yace  "wa kake nema ne?" Anwar yace  "gurin Nurat nazo" Megadin yace "baka da labarin abunda ya sameta wancan zuwan naka ne? Mahaifinta seda ya kusa halakata, ni ban san hali irin na mutumin nan ba, dan haka yun wuri kabar gurin nan tun kafin kaja mata wata wahalar" Mamakine ya cika Anwar sosai da jin abunda megadin yace, amma yace "Shikenan, nagode sosai, dan Allah ka gayamata nazo mu gaisa ne kawai, kace ina gaishe ta sosai, sannan idan ta samu lokaci ta taɓani a waya se in kirata" Megadin yace "Shikenan, zan gayamata wannan karka damu kanka dan dai saƙo" Anwar ya cika da mamakin me zesa a hukunta Nurat dan yaje gurinta, alhalin mahaifinta be nuna masa komai ba har gaisawa sukayi dashi, amma ace an hukunta ta kuma bata gaya masa ga abunda ya faru ba. Haka yakama hanyar gida, yanata zancen zuci, yana danja a tsaye yana ta tunani a ransa kamar ance ya ɗaga kansa, ya hango Ramlah a farajiyar wata plaza, da Fahad da wasu maza suna ta shan shisha, kayan jikinta sun Matseta sosai kamar ba 'yar musulmi ba, abun ya ɗaure masa kai ya sake mustsustuke idonsa ya kalli gurin, babu ko tantama itace, ya dafe kai yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Mummy kina me Ramlah ta lalace haka? Kalli yadda ta koma" Motarsa ya fizga a guje yai gida, zuciyarsa na wani irin tafasa kamar ta tsaga ƙirjinsa ta fito dan baƙin ciki. Sedi yana zuwa gidan, ita kanta Mummyn bata nan gidan babu kowa se masu aiki. Ya zauna a falo yana jin zafi akan sakaci irin na mahaifiyarsu, kuma da yayi magana taji haushinsa, amma yau kome ze faru seya ɗau mataki akan Ramlah. Tun la'asar yaga Ramlah, amma har bayan isha'i babu wanda ya dawo gidan, yana nan zaune Yaji ƙararar mota ya leƙa, ya hango Ramla ta fito da ƙyar take iya buɗe idoma, saboda azabar buguwar da tayi, amma a haka ta tuƙo mota zuwa gida. Ta riƙo takalmanta a hannu da jakarta, tana tafe tana gware da bango harta shigo falon. A zafafe Anwar ya kalleta yace  "daga ina kike?" Cikin maye tace  "Ni.. Ni...... Ni....... Fa na inda naje, kawai naje cin... Cin Abinci ne a w. Wa. Wani restaurants that's all" Kwaɗamata mari yayi, wanda seda ta dawo hayyacinta na 'yan sakanni, ya zare beilt ya dinga dukanta yana ƙwallo da ita, seda yayi mata kaca kaca ya tabattar ta daku sannan yace "kaiconki Ramlah, kin biyewa wannan ɗan iskan kina lalacewa, dama Aurenki zeyi da sauƙi wataƙila ya shiryu a sanadin ki, amma kawai kin biye masa kin ɓata rayuwarki a banza a wofi kaiconki Ramlah, yanzu kin riga kin ɓata rayuwarki, ke ba aurenki zeyi ba kuma babu wani mutumin kirki daze yadda ya haɗa zuriya dake, tunda kika zaɓi rayuwar shaye shaye da lalacewa" Hajiya Halima ce ta buɗe ƙofar falon, ta shigo ita da Amal, sedai tayi tozali da Ramlah a baje a gurin fuskarta duk a kumbure, saboda dukan da ta sha, gashi a hakanma maye take yi. "Lafiya mezan gani haka Anwar?" Cikin ɓacin rai Anwar yace "Mummy ɗazu a danja, na hangeta a harabar wata plaza suna shna shishsa ita da maza, da wannan sakaran Fahad ɗin mara tarbiyya, kuma ta dawo gidan nan tana maye" "Kuma shine zaka mata wannan dukan, idan ka kashe ta kuma fa kalli yadda ka daketa, idan kaji mata rauni kace baka san yadda akayi ba?" "Mummy, amma yanzu laifin Ramlah bekai a hukunta ta ba? Shaye2 tana mace, kallifa a hakan ma maye take yi, bata san meke faruwa ba, kuma amma a haka kike cewa meyasa na daketa?" "Rufemin baki ko in tsinkeka da mari, baiwar ubankace ita da zaka mata wannan dukan? Kai duk laifin da kake yi haka nake kamaka in jibga kamar jaki? Ka ɓatawa yarinya halittun fuska, kuma kana cemin maye take, haka ake mayen zafin duka dai yasa take surutai, dalla wuce ka bani guri babban banza kawai " Anwar yace" Amma Mummy kina gani...... A fusace tace "fitarmin daga falo tun ban rama mata abunda kayi mata ba, ɗan banza me baƙin hali kamar ubansa, yadda halinka yake haka na matsiyacin ubanku yake, baƙin hali dai akwai shi hadda na masifa da jaraba ka gado shi a gurinsa, fice ka bani guri me zuciyar banza data wofi " Anwar yasha mamakin zagi da cin zarafin da mahaifiyarsu tayi masa, alhalin ga gaskiya tana gani ƙurƙuru, amma ta rintse ido ta masa wannan mummunan cin fuska haka. Hajiya Halima ta ƙarasa gaban Ramlah tana ɗagota tace " Sannu Ramlah, Allah ya haɗaku da jarababbem ɗan uwa yana nema yaga bayanki, ni na rasa wannan mummunaan hali daya kwaso a gurin ubanku, Amal kawomin ruwan sanyi a fridge in shafa mata ko zata farka daga suman da tayi, da wannan surutan da take yi" Amal tace "Mummy, maganar gaskiya fa Yaya Anwar yana da gaskiya, Ramlah fa maye take yi, kuma ba yau ta fara shan kayan maye ba" Hajiya Halima tace "kamar yaya kenan?" "Kamar yadda na gaya miki mana, wallahi tana shaye2 ne, wannan cocacolan da take sha, syrup take juyewa a ciki ta sha abunta, shine zakiga tana ta faman bacci, nayi mata magana amma kin san halinta baji take ba, wannan Fahad ɗin kuma shine silar komai" "Ke Rufemin baki, idan har dagaske ne tana shaye2 da tuni na sani, ko kuma wani abune yake damunta yasa tayi shaye2, amma idan ta tashi zamuyi magana, sannan daga nan kar in sake jin maganar nan kinji na gayamiki" Amal ta jinjina kai tace "to" Da daddare Yusuf yana kusa da Widad akan katifarta suna bacci tare, wani mummunan mafarki Widad tayi, suna tafiya ita da Yusuf a wani guri me kyau, suna sanye da kaya masu kyau sosai, yana riƙe da hannunta yana mata hira tana ta dariya, shima fuskarsa ɗauke da murmushi. Babu zato wata mata ta ɓullo a fusace, ta riƙe hannun Yusuf tana jansa, Widad ta fashe da kuka ta riƙe Yusuf gam tana "dan Allah Yoseef karka tafi ka barni, dan Allah ki ƙyalemin shi nawane ba naki bane, na fiki buƙatarsa, nafi ki kusanci dashi, dan Allah kiji tausayina ki barmin shi, dan Yoseef karka barni" Yusuf kuma ya fara ƙoƙarin bin matar nan su tafi, yana kallon Widad fuskarsa ɗauke da damuwa, da alama shima yafi son zama a gurin Widad. Hannunsa ya fara zamewa daga na Widad, ta fara dena ganin fuskar Yusuf se dishi dishi. A firgice ta farka daga baccin tana haki, tana ambaton sunan Allah, a gigice ta ɗakko fitila tana haska inda Yusuf yake sedai me...... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/15/21, 4:52 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 94_95 Haska inda Yusuf ke kwance tayi tana sauke numfashi, gani tayi ya haɗa gumi yana bacci, daga shi se dogon wando da alama zafine ya isheshi, shine ya cire rigar ya kwanta haka, ta hasakashi sosai taga kamar baya numfashi, ta kai hannunta da sauri Ƙirjinsa saitin zuciyarsa, taji zuciyarsa tana bugawa a hankali, bacci yake yi sosai sedai yayi gumi sharkaf a jikinsa. Tashi tayi a hankali ta tafi ta lalubo mafici, tazo ta zauna ta ɗaga kansa ta ɗora a kan cinyarta, ta shiga yi masa fifita, tana goge hawayen da bata san dalilinsu ba, tama jin yadda ƙirjinta ke cigaba da bugawa saboda mafarkin nan da tayi, tana kuma godewa Allah da yasa ba gaske bane mafarki ne. Yusuf ne yayi ƙoƙarin yin juyi, yaji shi a jikin mutum, ya kai hannu ya tattaɓata, ga ƙaramar fitilarsu ta kunna wadda haskenta yayi ƙasa sosai saboda rashin batir. "Widad lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh,  "to meyasa kawai zaki katse baccinki ki tashi kina min fifita?" Tace "kasa bacci nayi, kuma naga kayi gumi dayawa, ka kwanta kawai ka cigaba da baccinka" Yai murmushi yace  "Allah sarki my Widad, nagode sosai Allah yayi miki albarka, amma Kasancewar ina mijinki kina mata ta bashi ke nufin, in cutar dake ba dare lokaci ne da Allah ya bawa bayinsa, dan su huta ko suyi ibada, amma in hanaki naki baccin dan nawa no baze yuwu ba, kece yakamata in miki fifita kiyi bacci saboda nasan wata ƙila zafine ya hanaki baccin, kuma nine gaba dake akwai buƙatar in tausaya miki " Girgiza masa kai ta kuma yi tace " A'a kabari, kwanta kayi bacci kawai " Tashi zaune yayi, ya karɓe maficin hannunta sannan ya kwantar da ita, yana mata fifita yace " wai na ganki some how looking disturbed, menene meya hanaki bacci ne matar? " "Yoseef i have a bad dreams" "On what?" ya tambaye ta. Nan ta gaya masa abunda ta gani a mafarkin, ta ƙarashe zancen da kuka. Murmushi yayi yace   "Ohh My God, ya ilahil alamina Widad dreams are not true, mafarkine fa kawai meye na ɗaga hankalinki, ba gani a tare da ke ba, dena kuka haba babyna" Kukan ta sake fashewa dashi tace   "i don't want to lose you, Ina tsoron ya zama gaske mafarkin, sometimes our dreams come true, ina jin tsoro sosai, and am still having palpitation, ina jin kamar ze faru ne a gaske" Yusuf yace "No my dear, kawai dai kin tsorata ne, kuma zuciyar ki ta fara jin abunda Yusuf yake ji game dake, amma in dai nine bazan gujeki ba ko in juya miki baya, sedai in daga ɓangaren ki a samu akasi, amma nikam nasan ina son matata" Yai maganar yana saka hancinsa a wuyanta, shiru ta ɗanyi tana ƙara so ta tabbatarwa da zuciyarta kalaman Yoseef ɗin, na mafarkine kawai baze zama gaskiya ba, amma dagaske kenan Ta kamu da soyayya? Tana cikin tunanin taji Yusuf yace  "Wife, ina kika samu wannan turaren ne, tun rana yake tashi a jikinki, ina ta ƙoƙarin riƙe kaina, tauraren nan yayi daɗi a jikinki sosai" Cikin cuna baki irin na wanda ya gama kuka tace  "Jamila ce tabani" "Wow, kince mata kin gode dai ko?" Ta gyɗa masa kai, yace  "good, ki tambayeta kuɗin turaren nan, zan bayar a ƙara mana" "Dayawa fa ta bani, wai itama maƙociyarta ce a barrack ɗim da take ta bata dayawa da ta haihu, shine nima ta zubamin kuma da yawa fa ta bani" Cikin nishaɗi yace  "dukda haka i suppose to pay for it, naji daɗi Sosai, bazan manta kyautar turaren da kika bani ba, kyauta ta farko da kika bani, kyauta daga hannun masoyiyya, amma sedai naji kamar wari nake shiyasa kika bani turare" Duk da a damuwa take, amma seda tayi dariya tace  "taɓ duk wannan gayun naka, dukda basajar da kake yi amma abunda ya fara birgeni da kai ashine tsaftarka, dan wasu dan suna irin wannan aikin se suyita ƙazanta, su a dole se sun nuna talaucinsu, abun da yasa na baka turaren nan, duk lokacin da naji turare na tashi a jikinka, se naji wata kasala ta kamani, ko laifi kayi min seka rage ƙarfin fushin da nake ɗauke dashi, shiyasa nace bari in canza maka turare ko zan dena jin hakan, wataƙila daga turaren  naka ne " Yusuf yayi murmushi yace  'to daga baya mekika fuskanta?" "Nagane cewar kwarjini kakemin, kuma abun ba daga turarenka bane daga kai ɗinne" Yusuf yace "Ahse dai an daɗe ana so" Tace "Ana son me?" Yace  "bakomai, just forget, ni dai ki bari kawai in shaƙi wannan ƙamshin me daɗin gaske" Shiru tayi tana saurarensa ba tare da ta sake cewa uffan ba, aikuwa Yusuf ya wuce makaɗi da rawa, yau dai be sha cizo ba🤭🤭, sema wani farinciki mara misaltuwa da suka tsinci kansu a ciki. A hankali a kunnenta yace  "God bless you my Wife, thank you very much" Ƙin magana tayi, sema lafewa data sake yi a jikinsa, yace  "tashi in ɗora mana ruwa, naga akwai sauran kalanzir ko?" Widad tace  "eh akwai, amma shekaranjiya Hindu tayi girki a kai, idan babu se muyi dana sanyi" "No akanme? Haka kurum in baki ruwan sanyi kiyi wanka inje ki shiɗemin, abunda baki saba ba, bakomai zan dafa mana, inma babu naje in tada murhu yanzun nan" Widad tace  "Murhu kuma a daren nan?" "Eh mana, meye a ciki, muna cikin baccin mu kin tasheni kin janyo mana aiki" "Au hakama zakace ko?" "A'a tuba nake, wane ni" yai maganar cikin murmushi. Akayi sa'a da kalanzir ɗin, ya fito da rishon tsakar gida ya ɗora musu ruwa, saboda yanayi na zafi kae ɗakin ya ƙara ɗaukar zafi, kafin ruwan yayi zafi, Yusuf ya ɗakko musu gashashiyar gujjiya suka zauna suka kama cin abarsu suna hira a wannan daren, se kace aljanu. Jin ana ɓuruntu, yasa Hanne ta miƙe cikin tsoro ta leƙa taga dan ganin meke faruwa, ta hangesu zaune a cikin farin wata, suna ciue ciyensu suna hira. Ta jinjina kai tace "lallai wannan kinyi dacen miji, yana sakar mata fuska sosai saɓanin mazan garin nan, wanima murmushi baze iyayiwa mace na wai karta raina shi. Ƙarshe ma tare sukayi wankansu, Yusuf jinsa yake kamar wani sabon mutum, wani irin farinciki ya mamaye zuciyarsa, sedai duk da ɓangaren Widad ma hakan take, amma ta kasa manta mafarkin da tayi akan Yusuf, haka kurum abun ya tsaye mata a rai. Anwar gaba ɗaya abunda ya faru yau a gidansu ya tsaye masa a rai, muraran mahaifiyarsu ta tabattar maaa da tafi ƙaunar Ramlah akansa, kuma bata son ace ga laifin da tayi, balle a saka rana zata mata hukunci, ransa ya ɓaci sosai dan haka ya fara tunanin, wane mataki yakamata ya ɗauka, dan janye jikinsa daga harkokin gidanma gaba ɗaya?. Yana kwance yana tunanin meye mafita, yaji wayarsa tana ringing, da kamar baze ɗaga ba amma ya janyo wayar ya ɗaga. Jin muryar Nurat ce tayi masa sallama yasa ya ɗan saki ransa ya  amsa, Nurat tace  "Yaya Anwar, ɗazu kazo baka samu ganina ba" Anwar yace 'eh, nazo mu gaisa amma megadi yacemin zan ja miki matsala, wancan zuwan da nayi ma na jamiki matsala amma baki gayamin ba" Ajiyar zuciya Nurat tayi tace  "hmm kai dai bari kawai Yaya Anwar, abunne duk se a hankali, na kasa gane kan mahaifina gaba ɗaya, ya hanani fita zuwa ko ina, sannan ya hana kowa yazo inda nake, na kasa gane manufarsa, sam ban gane inda ya dosa ba" Anwar yace  "Amma kuma lokacin da yazo ya samemu tare be nunamin komai ba" "Ai haka yake yi, baya taɓa nunawa a gaban mutane, amma bayan tafiyar ka har dukana yayi" "Subhanallah, kiyi haƙuri wallahi ban zan zuwana ze kawo miki matsala a gurin mahaifinki ba" Nurat tace  "bakomai karka damu Yaya Anwar, ba laifinka bane, sannan kayi haƙuri rashin haɗuwar da mukayi" "A'a bakomai Nurat, ina fatan ubangiji Allah ya daidaita tsakanin ku, dama biyowa nayi mu gaisa, wallahi nima kusan a cikin damuwa nake Nurat" "Subhanallah, meyafaru?" "Wallahi Nurat abubuwan nan da suke faruwa gaba ɗaya na rasa abunyi ma, jiya Ramlah a buge ta dawo tayi mankas da ƙwaya, amma ƙiri ƙiri dan na hukuntata Mummy ta fituttuke tace ƙaryane, taita faman Yimin faɗa, ban san meyasa take haka ba, abu in dak Ramlah ce bazata taɓa ganin laifinta ba, ƙarara take nuna banbanci a tsakaninmu" Nurat tace "se haƙuri ai, lamarin iyayen nan namu sedai addu'a, ni gashi nikaɗaice a gurin iyayena, amma wasu lokutan idan Daddy yayi min wani abun, se inga kamsr bashi ya haifeni ba, yaita treating ɗina a hagunce, abun yana damuna sosai" Anwar yace  "kin san kowane bawa da irin tasa jarabbawar, kowa akwai ta ɓangaren da Allah yake jarabtarsa, sedai fatan Allah ya bamu ikon cin jarrabawa" "Ameen Yaya Anwar" "to akwai wani news ne daga gareki?" Ajiyar zuciya tayi tace  "News kam baza'a rasa ba, amma kasan wai Yusuf ɗan sanda ne ashe?" 'Eh nasani, amma da farko nima ban saniba, se daga bayan nan, da aka fitar da wannan Sanarwar" Nurat tace  "Amma Anwar meka fuskanta game da wannan Sanarwar" "To ni dai abunda nake gani, wata maƙarƙashiyar ce aka shirya domin ɓatawa Yusuf suna, turoshi akayi domin bincike akan maƙiyan Daula, amma kuma daga baya ake nema a ɗora masa sharri, ni yadda naji ma sunce wai babu wanda ya turoshi aiki gidan" Nurat tayi ajiyar zuciya tace  "Yaya Anwar, wannan abubuwan duk shirine akayi shi domin a ci mutuncin Yusuf, kuma shiryayiya ce aka shirya wannan lamarin, ni ban san yadda za'ayi Yusuf ya ƙuɓuta ba, yana cikin matsala" Anwar yace  "hakane, nima naje na samu Alhaji Bulama, tunda yana da alfarma a ƙasar nan, ayi bincike yadda yakamata" Nurat tace "Yaya Anwar, tayasu da Addu'a shine abunda yakamata, amma harkar ƙasar nan se godiyar Allah, gashi haryanzu babu labarin Mahaifin Widad" Anwar yace "wallahi kuwa, to Allah ya wuce mana gaba, Allah ya kawo mafita gaba ɗaya" "Ameen ya Allah, nagode sosai Yaya Anwar" "Bakomai, nima nagode" Washegari da safe, Widad ta riga Yusuf tashi, yau da kanta ta dafa ruwa tayi wanka, ta gyara tsakar gidan nan fes tayi wanke wanke, ta zuba shinkafa ta fara tsincewa, ta tsince shinkafar nan iya yadda zata iya, amma Yusuf be tashi daga bacci ba, Taje inda yake kwance ta zauna ya gama ƙare masa kallo, sannan ta shiga tashinsa kamar zata tashi jariri. A hankali ya buɗe ido, yanayi yana lumshewa alamar bacci be isheshi ba tace  "wai yau da Yunwa zaka barni?" Murmushi yayi ya sake lumshe idonsa, cikin Shagwaɓa tace "tashi Yunwa nakeji fa" 'Nikuma bacci nakeji " "to bari inje in dafa da kaina, tunda ba zaka tashi ba" "No sorry, bari in tashi in dafa miki' "kaga harna dafa ruwa nayi wanka, na tsince shinkafan ma" "Haba dai?" 'dagaske nake fa" Ya miƙe ya duba ta share ko ina, tayi wanka har shinkafa ta gyara ta wanke, murmushi yayi yace   "Alhamdilillah, mutuniyar ta fara zama mace" "Dama ni namijice?" "A:a ni bance ba, amma mace ai seda aikin gida, kice zamuyi surprising Daddy ' " Sosai makuwa " Ya ƙarasa musu girkin, suka zauna sukaci Abincin su. lokaci lokaci Widad se taji gabanta ya faɗi, amma ta dake da dinga ɓoyewa, dan karya gane tana cikin damuwa. Widad tace "Yoseef ina kewar su Mama sosai da Hindu, mutum rahama ne" 'Ni Aljani ne kenan? " " A' a ni ba haka nace ba, na saba ganinsu ne, ina ganin mostinsu da giftawarsu, amma kwana biyun nan shiru bana ganinsu" Yusuf yace "yanzu kin gane amfanin mutum a rayuwar ɗan adam kenan? Babu yadda za'ayi mutum yayi rayuwa shi kaɗai babu mutane kuma yace hakan yafi daɗi" 'hakane, dan ina gudun a cutar dani ne, shiyasa nake gudun mutane, amma yanzu nasan wannan mutanen da muke tare dasu bazasu cutar dani ba, shiyasa nake kewarsu" "hakane, naga taku tazo ɗaya dasu sosai, Amma naji anjima zasu dawo ai ko?" "Eh anjima zasu dawo insha Allah" "to Allah ya dawo dasu lafiya" Ta amsa da Ameen. Anwar sosai yake tunanin samawa kansa mafita, akan lamarin gidansu dan duk se yaji zaman gidan baya kansa ya fita a ransa. Shiga yayi gidan da nufin gaida mahaifiyar su da safe kamar yadda ya saba, sedai ta window ɗin ɗakinta yaji suna magana ita da Ramlah, seya tsaya be ƙarasa ba. "Ramlah wannan rayuwar da kika ɗauka ba inda zata kai miki, ki kiyayi kanki da shaye shaye nan, kinga na gwale 'yan uwanki jiya amma tabbas maye kikeyi, dan dai inajin daɗin shawara dake ne da fushi zanyi dake" 'Mummy na dena fa" "Shikenan, ai dama nasan zaki dena, nace ya kukayi da Fahad ɗinne, ina fatan dai baze tona mana asiri ko gurin babansa ba"? ' Haba Mummy, shiya fara ma tunda abun nan harda shi ake ƙaruwa " "Yawwa haka nake son ji, yanzu wannan manyan filayen nasa nake so in sa a kasuwa na GRA, dan haka kiyi masa magana, kamar yadda akayiwa Gidajen layout ɗin nan takadda, suma wannan ayi musu takaddu mu siyar, ke ni ko miliyan sha biyar biyar, a siye su" Ramlah ta ɗan zaro ido tace  "Mummy million sha biyar kima, a filayen miliyan kusan arba'in ɗin za" a siya a haka? " " Eh to seme? Da gumunmu muka tara? Nifa sonake ayi yadda za'ayi mu ɗan tara daga nan mu san nayi, dan haka ki masa magana, ke har gidan nan ma sena siyar dashi, ai in sun san wata basu san wata ba" "hakane Mummy, amma gaskiya baza'a siyar da filayen nan a haka ba se an ƙafa, in ba haka ba mume zamu ci?" "to koma dai yane, kiyi masa magana ayo takaddun daga nan musasu a kasuwa" "Shikenan zamuyi waya dashi, kokuma inaga anjima ma zezo, se muyi maganar gaba ɗaya" Hajiya Halima tace  "ainaji daɗin harkar nan da yaron nan, motocin nan na farmhouse ma ai duk shi yayi mana hanya aka siyar dasu, banda sauran abubuwa, aini wannan lamarin ma gaba ta kaimu" "Wallahi kuwa Mummy, semunci rabon mu tukuna" Anwar ji yayi kamar ƙasa ta buɗe ya nutse a ciki, dama kadarorin Daula mahaifiyar sa ke siyarwa yana wadaƙa da kuɗin? Lallai ɗan Adam butulu ne, idan ya tambayeta ina motocin gidan se tace tasa an kaisu Farm House, dama abunda take yi kenan? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un' Jiki a sanyaye yaje ya ɗau motarsa ya tafi gidan gonar Alhaji Daula wanda aka riga aka mallakawa Widad, yaje da niyyar zagaye yake ya biya dan yaga gidan, ya tarar fiye da rabin motocin nan idan ya tambaya se ace Hajiya ta turo a ɗauka, hatta dabbobin Widad tana ta musu ɗuki ɗai ɗai, dan akwai da yawa wanda bana ƙasar nan ba a ciki, dan haka ana siyansu da tsada. Abun ya bawa Anwar mamaki, ya tuna irin gwagwarmaya da ɗawainiya da Daula yayi dasu, amma mahaifiyar su ta rasa dame zata saka masa se wannan zalunci da tsantsar butulci, lallai ɗan Adam butulu. Da ƙyar ya kai kansa gida, saboda azabar ɓacin ran da yake ciki, ta haɗa kai da 'ya' yanta suna ta wadaƙa da dukiyar marainiya data mahaifinta, se yanzu yake jin Widad bata da laifi da suke iƙrarin tana Wulaƙantasu. Da yamma Widad taita zuba ido a hanya taga ta ina su Gwaggo zasu dawo, se bayan ƙarfe biyar se gasu sunyi sallama sun dawo, Widad ta dinga murna, tace  "Sannunku da zuwa na zaci ma kum fasa dawowa yau" Gwaggo tace  "aiko kowa be dawo hau ba dole in dawo saboda ke, muna can amma hankalina yana nan" Widad tace "Hindu 'yan biki, a huta azo a bani labarin abunda ya faru" Hindu tace "ni wallahi muna gurin biki, hankalina yana kan makaranta" "to aini tunda kuka tafi, nace a bari sekun dawo a cigaba' Suka baje a tsakar gida, Yusuf ya fito yayi musu sannu da zuwa sannan ya fita. Saboda ɗaurin Aure, megari ma yaje gurin bikin, da shi da Sunusi Kasancewar Yayar megari ce ta aurar da 'ya, nan ma Yusuf ya shiga yayi musu sannu da zuwa, daga nan megari yaja shi da hira suka shantake a gurin. Gwaggo ta baje kayan biki da suka zo dasu, ƙulli daban tayiwa Widad na kayan gara kuma fal da yawa, kayan zaƙin nan. Gasu wainar masa da ƙuli, Widad tana son kayan zaƙi dama, ta zauna ta cicci abunta tana lashe baki. Ana idar da sallar magariba ta tura yaro ya kira mata Yusuf a waje, Yusuf ya shigo gidan ya shiga ɗaki ya sameta yace "lafiya kika aika a kirani? Me zaki ban?" "To ai kaine kaƙi dawowa tun ɗazu" "to ai bamuyi sallar isha'i ba, kuma zamuyi karatu" Ta miƙe ta ɗakko masa kayan da Gwaggo ta bata, Yusuf yace "masha Allah, 'yar gatan Gwaggo wannan duk namu ne?" "Eh mana shiyasa nace kazo kaci naka, gashi nan kaci iya cinka, ni na tafi tsakar gida" Tana gama maganar ta miƙe ta fita. Yusuf ya zauna yana cin kayan gara, Widad tayi waje, Hindu tana ta bata labarin yadda bikin ya gudana, Hanne kuwa se cika take tana batsewa, ba wanda yabi ta kanta suka ƙyaleta da ƙuncin ran da take yi. Bayan Yusuf ya gama ya fito tsakar gida yana alwala, Widad tace "Mama waiya mutum ze gane idan yana da cikine?" Gwaggo tace "to babbar magana" Jamila tace "karki damu, ni zan gaya miki in munfi haka yawa" Widad tace "ai yanzu ma muna da yawa ki gayamin mana" Hari tace "to bahaushiya, tana nufin se daga ke se ita tukuna" Widad tace "koma yane, ni dai dan Allah Mama ki dingamin Addu'a, Allah yasa in samu ciki" Hari tace "Ai himma kawai zaki ƙara, idan kika shiga ɗaki tun magariba, se wata magaribar" Sam Widad bata gane me Hari ke nufi ba, Yusuf shi kunya cema duk ta kama shi, ya tashi ya fice waje. Jamila tace "Widad zomu je ɓangarena, in baki tawa tsarabar" Widad ta tashi ta bita, Jamila tace "Widad nace miki irin wannan tambayoyin, ni zaki dinga yiwa ba Gwaggo ba, kunyace dasu, kinga baki taɓa haihuwa ba balle ace kin san alamomin, dan haka ba lallai alamomin da zan gaya miki su zamana ciki bane, amma mafi akasari dai cikinne ke sawa, Alamomin da zaki gane kina da ciki sun haɗa da, ɗaukewar Jinin al'ada, zazzaɓi, ciwon kai, jiri, Mamanki zasu danyi miki nauyi, koma su dinga zafi, yawan tashin zuciya, koma amai, yawan san ki kasance da mijinki a shimfiɗar Aure, ko jin haushin hakan, yawan som cin wani abu ko ƙin wani kalar Abincin, da sauransu amma alamomin ba lallai kiji su duka ba" Widad tace "wanne ne babban alama to?" Jamila tace "Ɗaukewar Al'ada, ko kuma laulayi idan cikin me laulayi ne" Widad tace "shikenan nagode sosai" Jamila tace "abubuwan duk da nake gayamiki, kina ganewa kuma kina aikatawa dai ko?" Widad ta jinjina mata kai. Suka cigaba da hirarsu, tana ci gaba dayi mata lectures akan Rayuwar Aure. Da daddare Yusuf ya dawo Widad tayi masa sannu da zuwa, ya lura da ta canza akan abubuwa da dama, wanda da a baya ba tayi. Ba zato Yusuf yaji Widad tace "Yayan Daddy dan Allah meye maganin mata?" Yusuf ya kalle ta yace "ke a ina kikaji hakan?" Tace "A gurin Jamila" 'Sha kika yi kenan? Ya tambaye ta Widad tayi shiru ba tace komai ba, kawai taga Yusuf ya kwashe da dariya yace "lallai yarinya kina ruwa" Kamar zata yi kuka tace "wani abu ne ze sameni?'" "A'a ni bance wani abu ze same ki ba" Gaba ɗaya bata gane me Yusuf yake nufi ba, taga ya ɗauki kayan shimfiɗarsa yayi wajen kwanan sa. ' Yusuf meye haka wai? " Yusuf yace " A ina? " " Naga ka ɗauki kayan shimfiɗarka, yau bazaka kwana a gurina ba?' "Eh yau a gurin kwanciyata zan kwanta" Kamar zata yi kuka tace "Amma naga yaushe rabon daka kwana anan gurin, kawai se yau zaka wani ce a can zaka kwanta?'" Kamar Yusuf zeyi dariya ya maze yace "A'a ni gaskiya sha'awar kwanan kam bargona nake, kowa ya kwanta a inda ya saba kwana" Kawai ta zauna tana kuka, Yusuf ya sha dariya sosai, dan Widad ta iya gaɓunta wasu lokutan, seda yaga dagaske take sannan ya koma inda suke kwana yana mata dariya. Da gari ya waye, idan Widad ta tuna abunda tayi jiya kawai se wani irin haushi yakamata taita tsaki, Yusuf yace "uwar kwaɗayi, gobema kije a kuma baki abunda baki sani ba kici" "Bazan ƙara ba har abada" Yusuf yaita dariya yace "A'a gaskiya ki ƙara, ni zan bada kuɗi ma ki ƙara" Ya dinga mata dariya, taga idan ta biyewa dariyar da Yusuf ke mata se tayi kuka, dan haka ta biye masa suka dinga dariyar tare. Cam tace "Yoseef, dan Allah ka dinga min addu'a, Allah yasa in samu ciki, haihuwa nake so nayi nima" Maimakon yayi magana, kawai seya janye ta daga jikinsa ya bar mata ɗakin. Mamaki ne ya cika Widad ta bishi da kallo, tana tunanin me yake nufi da wannan abunda yake yi, duk lokacin da tayi zancen tana son samu ciki, seya canza mata meye Nufinsa nayin haka?...... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/15/21, 4:52 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 96_97 Widad taje ta samu guri tayi zamanta a tsakar gida tana kuka, saboda tayi mamakin abunda Yusuf yayi, idan wanine yace ze mata haka tabbas zata ƙaryata, amma se gashi Yusuf ke ƙyamar haihuwa ko meye dalilinsa oho, to koma dai wani daliline ai bashi da ƙarfin da zesa ace yana gudun haihuwa haka, idanma tunanin sa yadda zasu yi idan sun koma gida, ai suna da hujjar da zata nuna aure sukayi ba zaman kansu ba, kuma tasan Daddy zeyi farinciki da hakan, abun da yake ta buri yaga 'ya' yan Widad a rayuwarsa. Kusan kwana biyu babu Anwar, an kai har gurin 'yan sanda amma babu Labari. Hajiya Halima ta tafi gurin Alhaji Munir, yana ganinta ya ɗan ɓata rai yace "to uwar matsala, ke duk inda aka ganki ba alkhairi se tarin matsala da damuwa" Haɗe rai tayi sosai tace "nice ma kake gayawa haka? Dole kace ganina ba alkhairi bane, kuma ai ganin naku ba alkhairi bane ba, malam ɗana ya ɓata Anwar, tun jiya ban san inda yake ba, idan wata ƙulla ƙullar kuka haɗa, kowani makircin to kufito min da ɗana, dan babu ruwansa a harƙallar da mukeyi " Alhaji Munir yace " to akama ɗanki ayi masa me? Har akwai abunda za'ayi aji tsoron gayamiki ne? Kije can kineme shi, idanma a cikin namu ne toni dai bada yawuna ba, dan ban san anyi ba, sedai ko Musa kowani amma ni ban san komai ba kam" "to bari kaji in gaya maka, idan ma ka sani ka rainamin hankali wallahi duk abunda nayi maka kai ka ja, dan wallahi sena saka mutum dana sani da cizon yatsa" Alhaji Munir ya taɓe baki yace "a banza ƙiba a kunne, ƙarewa 'yar gidan Daulama duk zare idonta da hura hanci shekaru kusan Goma sha biyu ta kasa gano mu balle ta ɗau mataki, se wata ke zakizo min da wannan ƙaramar barazanar taki dan ki firgitani, kije kiyi duk abunda zakiyi karki fasa, tunda naga alama daga ke har Musa kun fara hauka" "Shikenan, zakaga hauka ganin idonka, wallahi idan da saka hannunku kika sacemin yaro wallahi se kunyi danasani, zan nuna muku masifa da kaidin mace, shima Musan zanje in kasa masa warning, tun wuri ka kiyaye ni, ku fita daga idona kallon ku kawai nake yi" Ta juya a fusace ta koma inda motarta take, Alhaji Munir ya bita da ido, yayi tsaki ya koma ciki yana jinjina hauka da rashin hankali na mata. Daga nan gurin Alhaji Musa taje a Office ɗinsa na neman zaɓe, nan ma suka fafata, sukayiwa juna kaca kaca shi da ita, sannan ta bar gurin rai a ɓace. Murtalane yake gyarawa Anwar ɗakinsa wasu lokutan, wani lokacin kuma da kansa yake gyara abunsa dan shi babu ruwansa, be ɗau duniyar da zafi ba sam kamar yadda mahaifiyarsa da' yan uwansa suka ɗauka, Nura ya shiga yana gyara ɗakin Anwar, yaga takadda a ƙarƙashin fulon Anwar ya ɗakko tajadar ya buɗe yakaranta ta tsaf sannan ya ɗauka ya nufi cikin gidan. Suna zazzaune a falo sunyi jugum jugum, suna jimami da tunanin inda za'a ga Anwar Murtalah yayi sallama. Suna kallonsa amma ba wanda ya amsa masa, a fusace Hajiya Halima tace  "dalla malami meyene, kamar baka san a halin da muke ciki ba, kazo ka samu a gaba da sallama, meyene jarababbu kawai?" Murtalah yaji haushin abunda Hajiya Halima tayi masa, koda yake imda sabo sun saba, hantara da Wulakan da cin mutunci, sun saba ganinsa dan abunda wanda ya ɗaukesu aikin baya musuma yanzu yi musu ake sedai haƙuri, amma ya dake yace "Dama ba wani abu bane, ina gyara ɗakin Anwar ne na tsinci takadda a ƙarƙashin fulonsa, shine nace bari in kawo miki" Tasa hannu ta karɓi takaddar sannan tace "to ai seka tafi ko? Ko a gabanka zan duba kaga reaction ɗina, aji daɗin gulma, munafukai kawai 'yan sa ido" Sum sum Murtalah ya fice yana ƙunƙuni, a ransa yace "Ubangiji Allah ya kawo mana ƙarshenku, jarababbiya dake da wannan matsiyatan' ya'yan naki masu kama da jakuna, da bakinsu kaman na yaran hankaka' Nurane yaji Murtala na zage zage da tsine tsine, yace   " kai kuma kai dawa? " Murtalah yace  "nida wannan balamar matar mana, daga zuwa na tsinci takadda a ɗakin ɗanta naje kaimata, ta kama zagina tana cemin munafuki, ni dana san hakane ma da wallahi ban kai mata takaddar ba, inga ta tsiya" Nura yace "kaima meya kaika? Jiya Daga Isa ya ɗanyi mata tunanin albashi, ta zage shi tsaf taci masa mutunci, hadda wai tunda ba gidan ubanmu bane, wanda ya gaji yaga baze iya ba ƙofa a bude take ya ƙara gaba, kajifa se kace ita nata gidan ubanne, ko daga gidansu tayi gammo tazo dashi, aimu tsakanin mu da wannan matar sedai Allah ya isa wallahi " Murtalah yace " Allah ya isa me 'yanci makuwa wallahi, dan koni na mata ba adadi banza tana tafiya a karkace, ita ba ɗa' a 'ya' ya babu tarbiyya, se kayan ɗuwawu kamar zata kai kayan tusa birni" Sosai Nura ya dinga dariya yace "Wallahi idan ta jika seka bar gidan nan, kaima ka sani yaseen, amma fa ka iya ba'a da cin mutunci" Murtalah yace "to takorenin mana, ai yanzu gidan Daula sunan ne kawai, amma babu komai a ciki duk a bushe muke, saboda wannan iblishiyar matar, kana gani yanzu duk tarin jama'ar dake zuwa gidan nan yanzu babu kowa saboda baƙin halinta, wannan da a aljanu tazo ba shakka se ace itace babar sheɗan" Nura yai dariya kamar cikinsa zs ciwo, ganin yadda Murtalah ya harzuƙa sosai se bala'i yake yana zage zage da rashin mutunci da gani kasan an kai shi maƙurar bangone. Nura yace "malam kar dai kayi saɓo, a gidan ubanwa ka taɓa jin ance sheɗam yana da uwa, hattara dai" "Bari Nura rainane ya ɓaci wallahi, Allah yasaka mana wallahi, Allah ya nuna mana ranar da dubunta zata cika a tarkatata a koreta da wannan iblisan 'ya' yan nata" Nura yace "Ameen dai, manyan iblisai makuwa, dan wannan babbar me soyayyen ido shaye2 take yanzu, saura ƙiris shekaranjiya tabi ta kan ƙafar Isa da tayoyin mota, Allah ya temake shi yai saurin matsawa kuma ta fito daga motar, ta zage iyayi da kakaninsa tsaf sannan tabar gurin nan tana maye " Murtalah yace  " haka zasu ƙare, saura kuma hauka da tamɓele, tunda haƙƙin mutane suka san susa a gaba suci babu imani babu tausayi " Hajiya Halima kuwa tana buɗe takaddar, taci karo da rubutun Anwar kamar haka   " *_Asslam Alaikum warahmatullah zuwa ga mahaifiyata, nasan lokacin da zaki riski saƙona nayi nisa da gida, nisam da bana tunanin zan iya waiwayar gida a kwanan nan, na bar gidane saboda faɗar ma'aiki salallahu alaihi wassalam, babu biyayya ga abun halitta gurin saɓawa Mahalicci, dan haka bazan iya jure cigaba da zama daku ba ana aiakta abunda be kamata ba, nasan idan nayi Yunƙurin yi miki nasiha ba zaki saurareni ba, kin zaɓi lalacewar 'yarki saboda tana miki hanya gurin tara dukiyar Haram, kin fifita akanmu wanda kema kin san hakan ba dai dai bane, kuma kina ɗauki ɗai ɗai ga kayan mutumin daya yayi sanadiyar fitarmu daga masifar talauci zuwa arziki, kin haɗa kai da maƙiyansa ana cutar dashi, nayi dana sani nayi kuka da bincike na ya tabattar min da dake aka haɗa baki komai yake gudana tsakaninsa da maƙiyansa, kaicon wannan butulci naki Mummy, ni bazan iya cigaba da zama daku ba dan haka na bar muku gidan, dama bana ubana bane ba, ina miki fatan Alkhairi dake da ƙannena a duk inda kuke, Allah ya sadamu da alkhairi, ɗanki me ƙaunarki har kullum ANWAR *_ Jikintane ya hau tsuma tana rarraba ido, yayin da wani irin gumi from no where ya shiga tsatsafo mata, ta dinga rarraba ido kamar shege a rabon gado. Ramlah tace "Mummy lafiya kuwa, wetin inside that later?" Miƙo mata tayi, domin idinta ya gane mata, Ramlah ta karɓa ta shiga karantowa a fili, tana zuwa ƙarshe ta yarda takaddar tace "shikenan munshiga uku Mummy, wallahi tonon asirinmu yazo, dan abune me sauƙi a gurin Anwar ya tona mana Asiri, kin san halinsa Mummy, yau munshiga uku, wayyo wallahi har cikina ya fara ciwo" Amal tace "wannan shi ake kira tashin hankali wanda ba'a samasa rana, ina muka kama tunda wannan me iƙrarin ustazancin ya san abunda ake ciki" Hajiya Halima ta goge fuskarta tace "ni tunanina a gidan ubanwa yasan wannan maganar? Waye ya gaya masa? Tsawon shekaru goma sha ɗaya ana abun nan a sirrance cikin rufin Asiri, waye ya tina min wannan Asirin haka ni Halima?" Ramlah tace "Mummy ba wannan tunanin ya kamata kiyi ba, tunanin meye mafita yakamata ayai, tunda sanin inda ya samu labarin bashi da amfani" Hajiya Halima tace "toni ta ina zan fara ne? Ta ina yakamata infara neman mafitar? Na farko ban san inda ya tafi ba, kuma tabbas abune mawuyaci ya iya ɓoye abun nan yakasa gayawa wani, ke ni gaba ɗaya na rasa abunyi wallahi, kuma ɗazun nan naje mukayi kaca kaca dasu Alhaji Munir, da Alhaji Musa na zata su suka sace shi, ni wallahi da iya tafiyar yayi da sauƙi, amma sanin wannan abubuwan yafi komai masifar ɗagamin hankali, kar Anwar ya tona min Asiri in lalace a bakin duniya" Ramlah tace "aida iya lalacewa a bakin duniya ne da sauƙi Mummy, idan Asiri ya tonufa se komai ya watse ya lalace manya manya abubuwa ne zasu tonu, wanda baki isa kici bulus ba" Cikin tashin hankali Hajiya Halima tace "Au nikaɗai ma banda ku?" Ramlah tace "Mummy koda mu koba mu, ai laifinki yafi namu yawa, duk abunda mukayi kece kika samu a hanya, yanzu mafita ɗaya ce, kije ki samu su su Alhaji Harunan, ku sake sasantawa dama kun saba faɗa ku shirya ai, kuje ku sasanta kunemi mafita, dan wallahi Asirin ki ya tonu nasu ya tonu dan se mun faɗi komai " " Kai Amma wannan yaro akwai shege me baƙin hali, kamar duk fafatukar nan ba danku nakeyi ba? " Amal tace " Mummy amma kin san halinsa, dama da kuɗin nan sun samu ban san yadda za'ayi dashi ba, dan kema kanki kin san baze cisu ba" Halima ta zauna kawai murza goshi take yi, saboda tashin hankali da damuwa. Widad fafur taƙi Yusuf, zaman ɗakinma ta ƙiyi, ya dafa Abinci da safe amma taƙici, ƙarshe ma ta koma ɗakin Gwaggo, ta hau gadon Gwaggo tayi kwanciyar ta, Yusuf ya rasa ta ina ze fara yiwa Widad bayani, ta ina ze fara nuna mata yana mata son da baze taɓa juya mata baya akan wani abu da takeso ba muddin be saɓawa ubangiji ba? Yana da dalilinsa me ƙarfi ya zeyi tagane gaba ɗaya ta fututtuke taƙi saurarensa. Haka ya shirya ya fita, se bayan ya fita ta koma ɗakin ta gyara, ta barmasa Abincinsa taƙi ci, da yamma ɗalibai suka shigo karatu gurinta, sukayi karatunsu har kusan magariba sannan ta sallamesu. Gwaggo ta fuskanci kamar sun kuma samun saɓani tsakanin ta da Yusuf, amma bata son taita mata shisshigi, dan haka ta ƙyaleta, dan gaba ɗaya walwalarta ta ragu, kusan ko san magana ma ba tayi, ko kayi maganar ma bata san abunda kake faɗa ba tana tunani. Dan mamaki yakasa barin zuciyarta wai Yusuf ne yake gudun ta haihu dashi, ita iya tunaninta babu wani dalili daze sa yayi hakan sedai son zuciyarsa kawai. Da daddare ya dawo tana kallonsa, bata kulashi ba dan ko sallamarsa ƙin Amsawa tayi, ta barmasa ɗakin gaba ɗaya ta koma tsakar gida inda aka baje tabarma ana hira. Haka ya fito kamar maraya, yayi alwala ya tafi salla, ya dawo shiru shiru taƙi komawa ɗakin, har kusan ƙarfe goma na dare, ya fito yazo inda take dayake duk hirar nan ma da ake yi, ita ba wani magana take ba, sedai in anyi abun dariya ta ɗanyi murmushi, sam hankalinta baya kan hirar ta fitone kawai dan karma Yusuf yayi mata magana. Tana jikin bango, babu haske a inda take zaune, yazo ya zauna a kusa da ita yayi ƙasa da muryarsa yace "My love, dan Allah kizo muje ɗaki mana, kin barni kamar maraya kin dawo nan kin zauna, dan Allah kiyi haƙuri kizo mu koma mana, kina da miji amma kizo zaman hira" "Yoseef bana son sake jin kalamn nan naka na yaudara, wanda naji a bayama sun isa Allah ya amfana, kaje da can ai ba tare muke hirar ba" "Widad kalaman nawane na yaudara?" "bakaji bane in sake maimaitawa, kalaman yaudara da kake yaudara ta dasu na fara amince maka zaka butulcemin mana" "Yi haƙuri dan Allah karki ɗaga murya mana, zomu je ɗaki muyi magana" Widad tace "bazani ba, nace bazanje ba, ka ƙyaleni" Yusuf ya sake marairaicewa yace "nasan haushina kikeji, a ƙule kike dani amma please and please am very sorry, kiyi haƙuri mu koma ɗaki" Ƙarshe ma juya masa baya tayi, alamar idan ya gama ze iya tashi yayi gaba. Abun duniya ya ishi Yusuf, haka ya tashi ya tafi ɗaki, jiki a sanyaye, ya dinga tunanin dama tun farko data fara zancen cikin, ba haka ya ɓullo mata ba, gashi ta birkice gaba ɗaya, tama ƙi saurararsa. SE kusan sha ɗaya da rabi, dabar hirara nan ta watse, kowa ya tashi ya tafi makwancinsa, Widad ma ɗakinsu ta nufa, sedai tana zuwa ta tarar da Yusuf a zaune be kwanta ba. Tazo ta tsallake shi ta shige abunta, tana ƙoƙarin canza kaya, Yusuf yace "Widad, akwai buƙatar ko sau ɗaya ki bani dama, in kare kaina yana da kyau kiji ta bakina kafin yanke hukunci" "baka da ta cewa fa, ai labarin zuciya a tambayi fuska babu wani abu da zaka gayamin, fuskarka ta bayyana abunda ke cikin zuciyar ka, dan haka ka ƙyaleni kawai, bana san sake jin komai kawai ka rabu dani, kuma ɗane idan Allah ya bani kace ba naka bans, ni ima so kuma bana buƙatar taimakonka a rainon ɗana, da can baka san cikin ze shiga ba kake mu'amala dani, ko in an tashi bani ciki shawara za'ayi da kai? " " Nace dai kiyi haƙuri please, zan gayamiki dalilina dan Allah, amma kiyi haƙuri ki dena wannan fushin" "Se kuma kayi, kanka ake ji" "Widad, Widad magana fa nake miki" "kaga idan ka takurani wallahi zan fita ina kwana a waje, ka ƙyaleni" Ya dinga binta da kallo harta kwanta abunta taja bargo ta rufe kanta. Amal ce zaune tayi tagumi jugum, kamar an musu mutuwa tace "Mummy, yanzu idan kinje gurinsu Alhaji Haruna me zaki ce musu? Kuma ta ina za'a fara binciken inda ya tafi?" Hajiya Halima tace " sanin gaibu se Allah Amal, zanje dai inga yadda zamuyi dasu ne kawai" Ramlah tace "to yanzu idan aka ganshi Meza kiyi masa?" Hajiya Halima tace "ubansa zanci da farko, sannan ince masa duk abunda aka gayamasa ƙaryane" "Mummy, Yaya Anwar fa isa almost 30 years, he is not kid, tayaya zaki gayamasa haka ya yadda, idan kuma ba gaya masa akayi ba wani abu ya gani fa?" "Waike Amal bakinki baya faɗar alheri se sharrine, to rufen baki tunda bazaki faɗi abun alkhairi ba" Ramlah tace "bahaka bane Mummy, yanzu idan kika je neman mafita gurinsu Alhaji Haruna, kina ganin suna ganin Asirinsu ze tonu idan suka ganshi zasu ƙyaleshi hakane? Karfa ki manta har yanzu babu wanda yake sa tabbas na Bala yana raye a kurkuku, saboda sun tsoron Asirinsu ya tonu ana cewa sunsa an kashe shi, kuma sun cigaba da aiki da Saleb, ba tare da yasan sun kashe ɗan uwansa ba, those people are evil, they are very dangerous fa" "Na shiga uku ni Halima, yanzu ya zanyi wallahi duk cikinku ina sonku, babu wanda zan iya zuba ido inga ya cutu in haƙura, duk ni na haifeku ina ƙaunar ku" Amal tace "mun sani Mummy, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki a nemo mafita mana" Isa megadi na zaune a bakin gate, riƙe da 'yar radionsa, yana ta fama ya kama stationsa amma se wani ɓurari take saboda rashin batur, ya dire radion yana zage zage da Tsinewa Hajiya Halima, ganin kuɗin batirin radio ma ya ga gareshi. Jiya yi ana bugun gate ɗin da ƙarfi kamar za' a karya ƙofar, shi dai beji horn ɗin mota ba, dan baka ya miƙe a fusace yana bala'i yana masife yana cewa "wani jakin me wannan yake mana wannan bugun se kace gidan ubansa, kokuma wani ɗan fashi, mutum se kace gidan uabansa, ko yaya kuka buga anaji, muma za'a buɗe amma komai se mutane sun yi hauka, aikin banza iyayen maula kawai" Haka ya ci gaba da surfa masifa, sannan ya buɗe gate ɗin, wani mutum ya gani a tsaye, da wani koɗaɗɗen yadinsa shara shara, hularsa ma tayi baƙi ƙirin saboda dauɗa wani zaburarre dashi kamar korarre, Isa ya ƙare masa kallo yace "mutane ba dai Jaraba ba, baka san an sace me gidan ba, dama shine yake baku, wannan mastiyaciyar me hannun jarirar ba'a ɓanɓararta jeka Allah ya baka haƙuri, an dema sadaka a gidan nan" Mutumin yace "ba Sadaka nazo nema ba, gurin Halima nazo" "au gatsal kake faɗar sunantaa? Allah yasa ta jika, tukuna ma a danginta ban taɓa ganin mutum kamarka yazo ba, daga ina ko kwatance akayi maka?" "ba kwatance akayimin ba, kaje kace mata tayi baƙo, ita tasan waye" Isa yace "shikenan, shigo daga ciki seka zauna akan benci, amma in turoka akayi a baka aikima, babu guri dan muma ba biyanmu take ba, mace ce hannu kamar kuturwa, tasan a bata amma bata san ta bayar ba" Haka Isa ya cigaba da soki burutsunsa, yaje ya sanar da Hajiya Halima zuwan baƙon nan, amma ƙarshe seda ya fito da baƙin ciki da dana sanin zuwa sanar da saƙon nan. Har kusan awa guda bata fito ba, Muratalah ne yaji tausayinsa ya bashi ruwa, dan da gani muyumin ya jigata kafin yazo, ita shaf tama manta da wani baƙo da akace tayi, ta shiryo tsaf abunta zata fita, har an ɗakko mata mota, Nura yace "Hajiya baƙonki fa" A fusace ta juya zata yi masifa "wai wane jarababbem ne haka aka dameni dashi" Muyumin yace "nine nan" Tana waiwayawa ta zare ido ta dafe ƙirji tace "Na shiga uku, Shu'aibu!!!" Abun duniya ya dami Yusuf, baccinma ya gagar ɗaukarsa, jin shiri yasa ya zata ko Widad tayi bacci, kwana biyu kenan basu kwanta manne da juna ba, duk yaji babu daɗi, a hankali ya lalaɓa yaje bayanta ya kwanta ya shiga bargon nata, ya rungumeta a jikinsa. "Malam meye hakane? Ka lallaɓone kazo ka samu abunda kake so in anjima nace Allah ya bani ciki ka haɗe rai"? Yusuf ya girgiza mata kai yace "Aa', ɗumin jikinki nake son ji, dan Allah kimin afuwa Widad, ki saurareni please" "Dan Allah nima ka ƙyaleni, wallahi bana son jin komai daga bakinka, lallaɓani zakayi in yarda da kai, in anjima kuma ka juyan baga" "babu juya baya tsakanina dakw Widad, ina son ki fahimceni ne kawai, bari in baki labarin wani yaro" Miƙewa take ƙoƙarin yi, tace "bana son ji, ka riƙe abunka" "Dan Allah ki tsaya kiji, yana da mahimmanci sannan akwai darasin rayuwa a ciki" Ganin bata da niyyar saurararsa yasa ya janyota jikinsa, ya rungumeta gam sosai yana ajiyar zuciya, a hankali taji ɓacin ran nata na raguwa, dan haka ta kwanta tayi shiru tana sauraren bugun zuciyarsa. Yusuf ya nisa sannan yace "Labarin yaron nan zaki ji daɗinsa sosai, bari in gayamiki abunda ya samu yaron..... Mun kusa ƙarƙare part 2, idan part 2 kawai kika siya karki sake ayi 3 babu ke. LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 98_99 "Akwai wani Mutum me suna  Bashir, shida matarsa me suna Jidda, wadda sukayi Auren soyayya, kusan shekara uku babu haihuwa, kin san yanayin ƙasar Hausa, abun ya kan zama abun damuwa koma gori ga matar da bata haihuwa. Aka dinga ziga mutumin nan akan yaƙara Aure tunda bata haihuwa amma yaƙi, gashi babban ɗan Sanda yana matuƙar son matar nan tasa, yana da rufin Asirinsa dai dai gwargwado, matar nan tasa tana matuƙar kyautata masa shida 'yan uwansa dukda yadda suka tsaneta suka sata gaba, suna ganin komai ya samu akanta yake ƙarewa, gata da yawan larura Kasancewar tana da Athma, kuma genotype ɗinta AS ne, dan haka kusan kullum cikin rashin lafiya take da zaryar Asibiti, shi kuma yana jin tausayinta saboda mahaifiyarta bata raye, ga mahaifinta bashi da cikakkiyar lafiya shima. Idan ciwonta ya tashi, shine yake ayyukan gidan, ko kuma yayi zaman jinyarta a gida ko a Asibiti, duk wata kulawa daya dace ya bata yana bata, katsam Allah ya bata ciki ba zato ba tsammani, ya dinga murna shida ita, sedai cikin beje ko ina ba ya zube saboda yawan rashin lafiya. Bashir mutum ne me tawakkali dan haka be taɓa gazawa ba, baya nuna mata ya ƙosa da rashin lafiyar da take yawan yi, ya kance a tausayi irin na mata da son da matarsa Jidda ke masa, idan shine yake a halin yawan larurar nan bazata guje shi ba, to shi meze sa ya gujeta, bayan ba ita tayi wa kanta ba, Allah ne ya jarabceta. Bashir Ya zama abun kwatance a dangi, mijin tace nusari da ire iren wannan miyagun sunayen haka suke kiransa, wai ya ƙare a gindin mace seta talautashi tukuna ta tsiyata shi, kullum cikin ciwo gashi bata da wata mamora tunda ba haihuwa take yi ba, ya zamana saboda irin wannan cin mutunci da ake mata ko shiga tarurrukan biki ko suna ko makamancin haka ya hanata, saboda muddin zasu haɗu da 'yan uwansa gorin nan ne se anyi shi. Idan suka fuskanci baya gari, haka zasuje har gida su zazzaga mata rashin mutunci iri iri, su ɗauki abunda suka ga dama, suce ai kayan ɗan uwansune, banda tayi Asiri ta mallake shi, ta yaya ze dinga bata abubuwa bayan juyace ba haihuwa take ba, se aikin larura dasa ɗanuwansu zaryar Asibiti, duk ta tsiya tashi saboda yawan rashin lafiyar da take yi, yayi da lafiyarsa yayi da aljihunsa, dan hatta jini idan ta buƙata shike bata. Ita kuma ba sawa ba fitarwa, haka zasuyi abunda suka ga dama idan sun tafi ta sha kukanta, kamar yadda suka saba baya gari sukaje suka mata cin kashi yadda suke so, ya dawo ya tarar da ita tasha kuka, ya tambaye ta meyasa meta? Tace masa ai bakomai, seda taga ze ɗau zafi sannan ta gaya masa, shi yayi mamaki, be taɓa sanin har gida suke biyota suyi mata ba, aikuwa yaje yayi musu tatas, kuma yace musu mutu ka raba shi da matarsa, tana da matsayi me girman gaske a zuciyar sa, dan haka komai tayi bata laifi a gurinsa, yace  larura da lafiya duk na Allah ne, me lafiya na ina komawa mara ita, mara ita ya samu, babu wanda yake sa kuɗinsa dan ya sai cuta, sedai Allah yana jarrabar komai, dan haka ya yadda rashin haihuwar Jidda, da rashin lafiyar ta jarabtace Allah ya jarrabesu dan ya gwada imaninsu. Nan ma dangi suka kuma kwaroroto, suna yamaɗiɗi dashi, waiya fifita matarsa akan danginsa, abun takaicin hadda maza ake wannan sakarcin, ba abunda yake ƙona masa rai irin hadda ƙannensa da suke uwa ɗaya uba ɗaya suke ƙin abunda yake so, ya tabattar a zuciyar tausayi da imani na mahaifiyarsu, da tana da rai duk bazata bari ayi masa haka ba, shikam Bashir ya musu banza dasu da surutun da suke yi, yayi kamar besan sunayi ba. Daga baya ma ya koma, indai zeyi tafiya ta 'yan kwanaki wani garin harkar aiki, da ita yake tafiya suje su dawo, dan karma wani daga danginsa su bita gida su ɗaga mata hankali Wataran tafiya ta kama shi, yace ta shirya su tafi Tare, haka kuwa akayi suka tafi tare, seda sukayi wata guda sannan suka shirya dawowa Kano, sedai dare yafa yi musu a hanya, Bashir yace  'Jidda, dole idan muka shiga gari mu samu Hotel mu kwana, kin san ƙasar nan ba security " Jidda tace " dama abunda nake son in gaya maka kenan, dan a tsorace nake " " to sarkin tsoro, karki damu muna samun guri zamu tsagaita da tafiyar " Da yake daga kudu suke, wani dajin idan sukabi, sesu shafe tafiyar awa guda basu ga ko giftawar me keke ba, balle abun hawa. Daga nesa suka dinga hango hayaƙi, gaba ɗaya Jidda ta tsurw tace "Anya bazamu juya ba? Nifa tsoro nakeji hayaƙin meye wancan?" ' "idan mun juya mu koma ina? Aiba inda zamu se naga meke faruwa a gurin" Jidda ta cigaba da salati, dan tunda yasa kansa seya ƙarasa, saboda Bashir Jarumi ne sosai, bashi da tsoro. Suna suka ga wata motace tayi hatsari a gurin, sun daki bishiya motar ta kama da wuta, ma'aurata ne a ciki sun kasa buɗe murfin motar su fita, se matar ta daki glass ɗin motar da yayi saura be ƙarasa rugurgujewa ba, ya fashe, tana ta ihu Wuta na cin jikinta tana Yusuf ɗana, ɗana Yusuf ta jefo jariri daga Widow, hannun ta duk ya ƙone se salati take, da alama shi mijin nata dama tuni ya mutu. Ta wurgo jaririm ta wannan tagar, sedai jikinsa lafiya ƙalau beji ciwo ba, amma gefen wuyansa ya yanke, saboda glass ɗin motar daya fashe, yaron yasha hayaƙin gobara, baya numfashi sosai ga jini na zuba a wuyansa, Jidda tai Wuf ta ɗauki kyakkyawan jaririn a towel, se ƙamshim turare da ƙaurin hayaƙi yake yi, suna ji suna gani haka Wuta ta ƙone motar da iyayen wannan jariri yake. Jidda tai kuka tai kuka, tunda take bata taɓa ganin bala'i da tashin hankali irin wannan ba, Bashir ya rarrasheta, suka shiga mota ya dinga tsala gudu, har suka fita gari suka sami Asibiti suka shiga, kasancewarsa ɗan sanda id card kawai ya nuna akayi admiting ɗin jaririn. Bashir ya ɗakko waya daga aljihunsa, Jidda tace  "wa zaka kira?" Bashir yace "zanyi wayane, in gayawa abokan aikina incident ɗin ɗaya faru, azo a san yadda za'ayi muyi mus handing ove jaririn mutafi gida" Girgiza kai ta shigayi tace  "dan Allah Yaya Bashir ina son yarom nan ka barmin shi, karma ka gayawa 'yan sanda mun samu yaro, kabarmin ina so tunda ban taɓa haihuwa ba" "to yanzu ai danginsu zasuji daɗi idan suka ga yaron ya kuɓuta" "Yaya Bashir, komai nasu fa ya ƙone, ta ina za' a fara neman dangin nasa, dan Allah ka barmin inajin ƙauna da tausayin Yaron nan a raina, dan Allah ka bsr maganar nan, zan raini yaron nan in dai kamin izinin hakan, dan Allah" Bashir yayi shiru, ganin yadda take kuka, bilhaƙƙi son ɗan nan take dagaske, yasa yace "shikenan is ok, Allah ya tayaki riƙo maman Yusuf, Allah ya raya mana Yusuf bisa tafarki madaidaici, ya bashi haƙuri da juriya irin na me sunan" Nan ta dinga murna, ta rungume Bashir tana zuba masa godiya da Addu'a, ita da Bashir sukaje yayo siyayyar kayan jarirai kala kala, da duk abunda zasu buƙata, seda suka kwana uku a Asibitin daba'a garinsu ba, dan jaririn ya samu sauƙi. Bashir kuma yayi waya, akaje aka kwashe gawarwakin nan a inda aka yi hatsarin. A kwana ukun nan madara take haɗawa ta bashi, Jaririn sam bashi da rigima, harta ɗan fara damuwa ko jikin nasa ne be gama warwarewa ba, daga baya kuma ta fuskanci haka halinsa yake, bashi da rigima sam, bayan an sallamosu suka kamo hanyar gida, amma tun a hanya ta fara tunanin me zata cewa dangin mijinta idan suka ganta da ɗa? Bashir ya lura da yadda tayi shiru, yace  "Maman Yusuf, ya kuma naga damuwa a fuskarki?" Ta ɗan yi ajiyar zuciya tace  "Yaya Bashir, ina fargabar amsar da zamu bawa mutane, idan suka ganni da jariri, mussman su Yaya Asma'u" Bashir yace "ba dai kina son ɗanki ba?" ta jinjina masa kai alamar eh. "to karka damu da abunda mutane zasu faɗa, kisa a ranki ba rainon kariri kawai zakiyi ba, harda na ƙalubale ki manta da wani ƙalubake da abunda mutane zasu faɗa, mu rungumi jaririnmu, Allah ne ya bamu" Ta kallesh tace  "dagasake kaima kana son jaririn nan?" Yace "meze hana, muda muke nema Allah ya bamu, ai ina son duk abunda kike so, ina son Yusuf nima bari kiga mu koma gida, hakika zan kuma yanka masa, muyi shagalin suna dan Jaririn naki befi watanni biyu ba, gashi me kyau masha Allah kamar ke" Jidda tayi murmushi tace  'mijina ɗan Aljanna, Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira " " Ameen tare da ke matata" Se fargabar da take ta ɗan ragu, suka nufi gida. Bayan la' asar suka isa gida, bayan sun yi salla sun huta, ta dafa ruwa ta yiwa jaririnta wanka, ta canza masa kaya, ta goya abunta tana jin ƙaunarsa a ranta. Bashir da kansa ya sai cingam, ya dinga aikawa mutane cewar za suyi taron sunan jariri, mutane suka dinga mamaki dan su dai basu san tana da ciki ba. Nan 'yan uwansa sukazo domin ganin ba' asi, aikuwa suka tarar da ita da Jariri. Wani Yayansa ya sashi a gaba da tambayoyi, akan sun san matarsa ba haihuwa take ba, ina suka samo ɗa Bashir yaƙi gayamusu, suka haɗashi da wani ƙanin babarsu, ya kira shi ya tambayeshi, Bashir yace  "gidan marayu sukaje suka ɗakko yaro, jaririn iyayensa ne suka yi hatsari suka mutu, kuma ba'a san daga inda suke ba, shine sukaje gidan suka karɓo shi. Nan ma 'yan uwa suka samu nayi, wai ya biyewa matarsa sunje gidan marayu sun ɗakko shege, babu wani iyayen yaron sun mutu, duk yaran dake gidan shegune. Jidda ta dinga kuka tana ɗanta ba shege bane, Bashir yaita rarrashinta, ya gayyaci mutane akayi sunan Yusuf, akayi shagali sosai aka watse. Jidda ta rungumi jaririmta da mijinta, sedai wani abun mamaki da iko na ubangiji, tunda Allah yasa suka fara rainon ɗan nan, Jidda ta dena wannan rashin lafiyar da take yawan yi, ta warke sarai ta dena kwanciyar Asibiti, idan ba an faɗa maka ba bazaka ce tayi fama da jinya ba a baya, sosai suke rainon Yusuf, bazaka taɓa cewa ba ɗansu bane, idan har kana son farincikin Jidda da Bashir to kaso ɗansu Yusuf. Sedai fa dangin mijinta suka kuma sata a gaba, suka tsani yaron nan ƙarara suke nuna masa ƙyama, suke ce masa shege, Sedai Jidda tayi kuka, ita dai tasan Yusuf ba shege bane da iyayensa, amma haka take sharesu ta cigaba da kulawa da shi ita da mijinta Bashir. Jidda ta kauda kai daga duk wani ƙalubale da take fuskanta, akan rainon Yusuf ta kowane ɓangare, Bashir yana iya ƙoƙrinsa akan Yusuf, daya isa shiga makaranta ya sashi a makarantar kuɗi, wanda a wannan lokacin se 'ya' yan wane da wani ake kaiwa private school, amma yasa shi a private school, yasa shi a makarantar islamiyya, ga tahfeez sannan aka ɗaukar masa malamin lesson, idan Bashir na gari shike kai Yusuf makaranta ya ɗakko shi, idan baya nan kuma Jidda ke kaishi, Yusuf ya taso cikin gata da kulawa, yayin da gefe guda dangin babansa suka sake ɗora masa karan tsana shida iyayensa, mussman Jidda waita asirce musu ɗan uwa tasa sun ɗakko shege yana masa bauta, ya taɓe a gindinta dana wannan shegen yaron. Babban abun mamakin be wuce yadda suma yana wahalta musu dai dai gwargwado yadda ze iya amma basa gani. Yusuf ya tashi da tarbiyya da ilimin addini dana zamani, gashi da matuƙar haƙuri, da wuya kaga yayi fushi, be fiye shiga faɗace faɗacen yara ba, karatunsa ya fiye masa komai. A tsakanin maƙwabta ma ana samun hassada da ƙyashi, ganin kaf tsukinsu babu me gatan Yusuf, komai ana masa sam bashi da wata damuwa, hakan yasa maƙwabta suma suka fara jin haushinsa, abun wasa duk tsadarsa zakaga Yusuf dashi, shi kaɗai amma keken hawa uku ne dashi na hawa, shekararsa takwas a duniya, amma har system yake da ita saboda karatun Al'qur'ani da sauran litattafan addini dana zamani, dan haka Ƙwaƙwalwar Yusuf na kawo wuta sosai. Nanma maƙota suka fara jin haushinsa, saboda wannan gata da tarairaya a cewarsu dama gashi shege kuma ana ƙara sangarta shi, Yusuf tunda ƙuruciyarsa yake jin kalmar shegen nandm daga bakin mutane, besan ma'anar kalmar ba, amma yasan kalmace me muni, da wasu lokutan maƙotan ko yaransu kan gaya masa, ko kuma dangin Abbansa, Yusuf yana da matuƙar haƙuri da kawaici, ko wasa ya fito cikin yara idan yaga za'ayi faɗa ko rigima, seya bar gurin ya koma gida, wasu lokutan har haushin haƙurinsa Bashir ya kanji, yaita masa faɗa ya dena yadda yara suna masa rashin mutunci yana ƙyalesu, se yace ai malaminsu yace  "Allah yace yana son bayinsa masu haƙuri" Katsam ranar suka yi faɗa da wani yaron maƙwabcinsu, akan kayan wasan Yusuf ɗin, yaron ya dinga zaginsa, uwar ɗan ta fito ta shigarwa Ɗanta, Yusuf ya juya ze koma gida, yaron ya biyo shi ya dake shi, Jidda ta fito jin Hayaniya, Jidda tace  "Maman Salim bekamata ki dinga shiga faɗan yara ba, ɗa na kowane kamata yayi ki haɗasu ki musu nasiha, in da kara ɗana da ɗanki ai duk naki ne, idan zaman tsakani da Allah akeyi, Yusuf da Salim duk namune' " Ke saurara karki ƙara haɗa ɗan sunna da shege, tsintacciyar mage wadda bata mage, akan me? Kedai da kika ɗakkoshi kikaga zaki iya se kije kiyi, kekaɗai ne ɗanki amma ni wannan yaron ba ɗana bane" Nan da nan ran Jidda ya ɓaci, kawai ta durƙusa a gurin fashe da kuka, da yake ita bata da baki sosai, Yusuf yazo ya rungumeta yai shiru yana sake juya kalmar shege a ransa. Salim ya ɗau dutse da nufin ya jefi Yusuf, amma ya samu Jidda a gadon baya, karo na farko da Yusuf ya harziƙa, beyi wata wata ba yai sama da Salim ya sake shi a kwata. Nan babar Yusuf ta gigice ta biyo Yusuf zata daka, dai dai lokacin motar Bashir ta shigo layin, take yayi parking ya fito yace  "ke lafiya zaki dakarmin ɗa? Ke kuma Umman Yusuf meya sameki haka kike kuka?" Aikuwa ba tayi nauyin baki ba ta gaya masa komai, nan ya fara sirfa bala'i, yace  "na lura mutanen nan bakwasan zaman lafiya, wallahi duk wanda ya kuma kiran ɗana da shege sena ɗaure mutum, kai kuma Yusuf duk yaran da ya kuma gayamaka haka, ko ya dakeka baka zanemin shi ba, ni zan zaneka da kaina, ba babarka zaka dinga shigarwa faɗa ba, duk wanda yayi maka ka masa duka ka lallasan mon yaro, in yaso akawomin ƙararaka zan bada haƙuri " Tun daga nan Yara suka ɗan saurarawa Yusuf, saboda babansa mutum ne me raha da barkwanci amma be iya fushi ba da tashin hankali, Yusuf ya cigaba da tasowa, tun be gane kalmar da ake gaya masa ba harya gane ma'anarta, baze manta ranar wata Juma'a ba, wadda itace ranar da ya gane mariƙansa basu suja haife shi ba, ya ɗauka ana gayamasa shegene kawai dan a zageshi, amma ya gane basu suka haife shiba. Ƙanwar Bashir, me suna Balaraba ta haihu, saboda gudun magana yasa Jidda ta shirya, ta shirya ɗanta tsaf dasu, kai kace wata matar hamshaƙin attajirice, saboda Bashir baya wasa gurin kula da gidansa, daga ci har sha da sutura, baya wasa gurin basu, shiyasa kullum iyalinsa suke tsaf dasu. Suka shirya tun safe Bashir ya tafi kaisu gidan suna, a ƙofar gidan yayi parking ya kalli Jidda yace  "kin san Allah, ba dan kin matsa ba da bazakuzo sunan nan ba, ke kin damu Yusuf yasan 'yan uwana, saboda halin Rayuwa ni kuma nasan babu wani amfani da hakan zeyi, dan haka idan kimga ba hali ki samu abun hawa kukoma gida, idan kinga zasuyi muku cin mutunci ki kirani a waya ko ku koma gida kinji ko? " Jidda ta jinjina kai, Bashir yace "ki kularmin da kanki da Yarona, ya kalli Yusuf yace   " My boy, zaka shiga cikin yara, bance ka saurarawa duk wanda ya taɓamin kai ba kaji ko? " Yusuf yayi murmushi ya sunkuyar da kai, Bashir ya sumbaci goshinsa, sannan suka shiga gidan, suna shiga basu samu wata karɓar arziki ba, sema bimta da aka dingayi da kallo a nayiwa zanin jikinta kuɗi, da kayan jikin Yusuf. Suka dinga zage zagen su, suna faɗar baƙaƙen maganganu, Jidda ta tashi da nufin ta taya su aiki, suka dinga caccakarta kamar zasu cinye ta ɗanya, suna mata gori suna zaginta. Ta tashi ta koma gefe, ta ɗau Yusuf ta ɗora akan cinyarta, tana share hawaye, Yusuf ya kwanta a jikinta yayi lamo yana jin yadda take kuka, har kusan ƙarfe ɗaya ana ta rabon Abinci, amma aka hanata ita da Yusuf, ga lokacin da shabiyu na rana tayi, take bawa Yusuf abinci, se can wata mata daga maƙotan Balaraba ce ta kawo musu Abinci, dambun shinkafa aka kawo musu, sedai Yusuf baya cin dambu, se Jidda ta aiki wani yaro tace "Dan Allah jeka gurin da ake rabon Abinci, kace a baka waina zan bawa yarone, in basu baka ba kazo ka karɓi kuɗi ka siyomin wani abun in bashi" Yaron yana zuwa yace a bashi waina, wata ta kalle shi tace "waye yace a baka"? Ya nuno Umman Yusuf yace "gata can, ita ce tace a bata zata bawa yaronta, wai baya cin dambu" Asma'u tace "iyeee ina abun yake inji Mayya, saboda samun guri har wani zaɓen Abinci yaron yake yi, lallai abunda mamaki samun guri, dama ɗan uwanmu ne ya haife shi da sauƙi, amma kin sashi a gaba anje gidan marayu an ɗakko shege se wahala yake akanku, ke gaki juya shi gashi shege ba dangin iya babu na baba an samu guri se iskanci ake, kina ci kina ƙiba kina narka kashi, gefe shegen daba'a san asalinsa ba ma yana cin nasa rabon, kin kanainaye mana ɗan uwa kin hanashi yayi mana komai " Balaraba tace " wai lafiya kike wannan kwarmaton haka? " " inafa lafiya, za'amin iyayi da feleƙe wai wannan shegen yaron sun samun an basu Abinci, hadda turowa wai a canza masa bayacin dambu, saboda samun guri wai Abincin ma seya zaɓa, dan ubanka da a gidan Marayun ka taso, naga uban da zakawa sanaben baka cin kaza, kai kaza kake ci" Jidda ta toshe baki ta fashe da kuka, a nan Yusuf ya fara fuskantar ashe ba Babansa ne ya haifeshi ba, idan be manta ba a makarantar su sun taɓa zuwa gidan marayu, akace musu wanda iyayensu suka yadda sune, kokuma wanda iyayen suka rasu, wato kenan shima yadda shi akayi, ko iyayensa na asali sun mutu. Jidda ta tashi, ta kama hannun Yusuf ta baro gidan nan, kafin ta fito ma shaddarta milk ta sha aiki, suka watsa mata dagwalon kayan miya, haka suka tafi tana tafe a hanya tana kuka, Yusuf yace "Umman Yusuf kiyi haƙuri, kidena kuka Allah yana son masu haƙuri, haka ya sayyadina yake gayamin" Amma ta kasa dena kukan nan, ta rasa wani abu tayiwa dangin Bashir suka tsaneta haka, banda hauka ina laifin Yusuf a wannan al'amarin? Me yayi musu? Shida yake yaro ƙarami, take tayi wani tunani ita yanzu daba cikakkiyar lafiya ba, idan ta mutu waye ze kular mata dashi, ita dai Allah ya jarrabeta da son Yaron nan, tasan babu matar da zata kulamata da ɗanta tsakani da Allah haka. Gaba ɗaya wunin ranar haka suka yi shi babu daɗi. Bashir na dawowa ta dake ta maze, ta ɓoye duk wata damuwa da take ciki, ta saki fuskarta, suka ci Abinci ya rungume Yusuf yana faɗin "ɗan Babansa, meyafaru ne? You look somehow disturbed, meyafaru ne gayamin" Yusuf yace "am ko Abba, ba abunda yake damuna, munje gurin suna amma ba'ani Babyn na ɗauka ba" Bashir yace "Subhanallah, to shikenan rabu dasu, da kaina zan kaika a baka ka ɗauka tunda kana so" Yusuf yace "to Abba nagode, nima Allah yasa Ummana ta haifi Baby, in dinga kular mata da ita ina goya ta" Bashir yace "Ameen ya Allah yarona, waini idan ka girma me kake son ka zama ne?" "Daddy doctor nake son zama, surgeon doctor" "Wow that's good my Boy, Allah ya bani rai da lafiya inga burinka ya cika Yusufana, kenan baza'abi sahun Abba ba a kare dukiya da rayukan al'umma ba?" "Ina so Daddy, amma bana son in dinga cin hanci, ustaz ya cemin ba kyau" Bashir yayi murmushi yace "babu aikin daba'a cin hanci Mu Son, nima na gashi police bane, kaga ina irin wannan?" Yusuf yace "A'a". "To ko duk 'yan sanda zasu lalace, amma kai ka tsaya kai da fata akan gaskiya idan wasu basu yi nasara ba, wasu zasu samu sassauci a sanadin ka, dan haka' yan sanda ba 'yan rashawa bane kaji Masoyina" Jidda tace "Abba, ko kunya ba kaji kake cewa ɗan fari masoyinka ko? Allah yasa tsofaffi su jika, kasha zazzaga" Bashir yace "sedai suyi su gaji, amma ina son masoyin nan nawa, inajinsa a zuciyata, idan na kalle shi ina samun farinciki da nutsuwa, nasan ko bayan raina akwai amfanin da zewa al'umma, ɗan waliyin Allah me halin sufaye" Jidda tace "ina ganin ikon Allah, kabari a faɗa mana kawai kasa shi a gaba kana ta koɗashi, Taso muje in maka addu'a in kwantar da kai" Bashir yace "ke yanzu me kike inba shagwaɓashi ba, baccin ma sekin kaishi, ƙyalemin yarona ya gama jin ɗumina tukuna" "Ka maida shi ciki mana ƙarewar soyayya" Sukayi dariya gaba ɗaya. Yusuf yace "Abbana ɗan aljanna, ina sonka da kai da Umman Yusuf, Allah yasa ku a Aljanna" "Ameen ya Allah, ɗa ɗaya tamkar da goma" Suka cigaba da hirarsu cikin so da ƙaunar juna, can Yusuf yayi shiru yana tunani, Bashir yace "ɗan waliyin Allah, me kake tunani ne? Kowani abun akayi maka da kuka fita, gayamin ko waye inci ƙaniyarsa" "Abba meyasa ka ɗakkoni daga gidan marayu? ....... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 100_101 Tsit sukayi gaba ɗaya suka shiga kallon kallo ita da Bashir, Bashir yace   "Yusuf, waye yace maka a gidan marayu kake? Wani mara hankalin me ya faɗi haka?" Yusuf yace "Yaya Asma'au naji tana faɗa, Mamansu Amira, kuma rannan dana tambaya ance mana a makaranta wanda suke gidan marayu basu da iyaye, tsintarsu akayi an jefar dasu" Bashir a fusace yace  "ƙarya take yi kaji ko, ba wani gidan marayu da aka ɗakkoka, ƙarya take nina haifeka" Jidda tace  "Abba ya zakace masa ƙarya take, babba ce fa ba haka yakamata ka faɗa ba, tunda yarone bekamata kace masa babba kamar wannan tana ƙaryaba, ka gaya masa wani abun dai" Bashir yace  "idan bance ƙarya take ba me zance? Ko so kike a sawa ɗana wani tunani na daban a zuciyarsa, nina haifi ɗana duk wadda ta kuma gayamaka haka kace Nine nan babanka, in ba haka su gayamaka gidan marayun dana ɗakko ka, kuma duk wanda ya kuma gayamaka haka kazo ka sameni ka gayamin, kaga yadda zan da mutum" Ran Bashir ya ɓaci sosai ya dinga faɗa yana mita, dan ba ƙaramin jin haushi yayi ba, abun yana damunsa yadda ake aibata masa yaro, yaron da yake jin sonsa a cikin jikinsa Bashir yace  "Ke yanzu a gabanki ake gayawa ɗana haka, amma ba kice komai ba, kuma ni baki gayamin ba balle in ɗau mataki, ɗana me haƙuri da hazaƙa amma a fara cusa masa tunani da ƙuruciyarsa, bazan lamunta ba Wallahi tabbas duk wanda ya kuma wannan gangancin zanyi maganinsa" Ya tashi Fuuu ya ɗau Yusuf, ya kai shi ɗakinsa ya kwantar da shi, ya zauna yaita masa addu'a yana shafa kansa me ɗauke da tarin suma me kyau, har bacci ya kwashi Yusuf, dukda zuciyarsa na cike da zullumi da tunani iri a kan maganganun da mutane ke gayamasa. Haka Rayuwa ta cigaba da gudana, Yusuf yana cikin gata da jin daɗi dai dai ɗan talaka me rufin Asiri, Yusuf akwai tsanani biyayya da haƙuri, gashi tun yana yaro yana da ilimi sosai, gashi mahaddacin Al'qur'ani ne. Bashir ɗan Sanda ne nagari, mutane sukance masa cinnaka ba ka san na gida ba, ko suce masa murmushin talaka, saboda gaskiya da riƙon Amanarsa, komarli kuɗinka da Arzikinka baze saurara maka ba idan baka da gaskiya, sannan umarni in dai na san zuciya ne, ba daga sama ba koda gurin uban waye baze karɓi umarnin san zuciya ba, aikinsa kawai yake bilhaƙƙi, ba son zuciya da cin Amanar ƙasa,shiyasa talakawa ke masa addu'a suke ƙaunarsa. Shekarar Yusuf tara a duniya, Babansa Bashir akayi masa kiran gaggawa yayi tafiya Lagos a hanya 'yan fashi suka kashe shi, shi da uban gidansa. Umman Yusuf da Yusuf sunji mutuwar nan, sun kaɗu dajin mutuwar nan, sunyi kuka, sunyi kuka dan sunsan sunyi rashin babban bangon jingina, Bashir mutum ne nagari, dukda ɗan takun saƙar dake tsakaninsa da maƙotansa akan Yusuf, amma sunji mutuwarsa, mutum ne me barkwanci da raha, ga kyauta da girmama mutane, mafi akasari in kaga anyi faɗa dashi to haƙƙin wani za'a take, shi be fiye daɗa akan kansa dan an masa wani abuba, sedai in an taɓa Yusuf ko Jidda, ko an danne haƙƙin wani, dan haka da talakawa masoyansa, da iyalansa da jama'ar unguwa sunji mutuwarsa sosai, hatta su kansu rundunar tsaron sun san sunyi rashin ma'aikaci. Bayan an gama zaman makoki maƙota suka farayi da Jidda, wai saga yadda zata yi, ta miƙe ƙafa komai sedai miji yayi mata, hatta slifas na tsakar gida Bashir be yadda ta siya ba shiyake siyan komai, yanzu tunda ya mutu a ga yadda zata yi, gata ga yaron da ba'a san wace tayi cikin shege ta yar ba, sukaje suka ɗakko, yanzu ai taje ta maida ɗan da suka ɗakko ai. Jidda bata da matemaki se Allah, rayuwa ta fara musu zafi, saboda bata da hanyar samun kuɗi, ta fara tunanin sana'ar da zata yi danta samu suci Abinci, kar ɗanta yasha wahalar rayuwa. Manyan 'yan sanda suka shiga yi mata romon baka, akan cewar zasu shiga su fita a samu haƙƙinsa ya fita, duk da jajircewar Bashir da wahalar da yayiwa Ƙasa, babu wanda ya kuma bi ta kan iyalansa, haka Umman Yusuf ta shiga faɗi tashin yadda zata yi domin ganin basu tagayyara ba, amma abun mamakin, komai ta kasa na siyarwa se maƙotanta suƙi siya, ko kuma su karɓe bashi su barta, sunaji suna gani haka ta cire Yusuf daga makarantar kuɗi ta maida shi ta gwamnati, dama ya gama primary secondary ze shiga, wasu lokutan har Abinci ma se tayi fama sannan suke iyaci, mutanen da Bashir ya dinga tallafawa babu wanda ya kuma bi takansu, dama ba'a batun danginsa tunda ba ƙaunarsu suke ba, haka Umman Yusuf ta samu Nanny a wata makaranta da ƙyar, ta kaɗa ta raya su ɗauketa aiki, tana da diploma amma suka ƙi, waisu masu degree suke ɗauka, sedai su bata Nanny, haka ta karɓi aikin Nanny take yi, tana zama ta zubda hawaye idan ta tuna Bashir, wata wahalar duk bata santa ba se daga baya, dama 'yan uwanta duk kusan matane, kuma uba ɗaya suke ba uwa ɗaya ba, kuma mahaifim nasu ya rasu, gashi dama suma duk fama suke da kansu, talakawa suke Aure, dama ita suke raɓa su samu wani abun, shima suna yi suna mata hassadar tana auren me rufin Asiri, tunda aka gama zaman makoki babu wanda ya sake ya waiwayarta. A hakan ana wannan faman, amma Umman Yusuf bata yadda Yusuf ya fita da mummunar kama ba, ko yayi mummunar cima ba, ta yadda ta zauna da yunwa, Yusuf yaci. Ga aikin Nanny ɗin nan babu wata riba, se zunzurutun wahala, ga wulaƙanci daga malamai, yaran da iyayen su dukda wannan ƙoƙarin da take yi ba'a gani. Yusuf idan yaga tayi shiru se yace "Ummana kiyi haƙuri kinji, nima bana son wannan aikin da kikeyi, nima zan duba sana'ar da zan iya in dinga temaka miki, ki bar wannan aikin" Umman Yusuf tace  "A'a ban yadda ba, yarone kai ƙarami kamata yayi ka maida hankali akan karatunka, idan kasan daɗin kuɗi bazaka maida hankali ba" Fafur ta hana shi neman kuɗi, idan bashi da littafi yana son ya siya baze tambayeta ba, sedai ɗan ashirin ɗin motar da take bashi, da kuɗin break ɗinsa haka ze tafiyar ƙafa, dan ya rage ya siya, karya tambayeta yasan bata dashi, dubu goman da'ake bata na aikin bata zuwa ko ina. Watarana Ummansa ta tashi babu lafiya, kusan sati biyu ba taje makaranta ba, gashi babu kuɗin magani, ko zuwa Asibiti tana ta fama da Asma, dan haka bata sani ba Yusuf yaje gidan Yayan Bashir, Ɗanlami yaje ya gaya masa amma yayi masa kaca kaca ya kore shi, yace baze taimaka musu ba, bayan zagi da cin mutunci da yayiwa Yusuf da gorin aishi ba ɗan ɗanuwansu bane, tun daga nan Yusuf ya ƙuduri aniyar kome ze samesu, baze ƙara neman taimako a gurin wani ba. Haka Yusuf ya samu guri a hanya ya zauna yayi kuka, yayi kuka yai me isarsa sannan ya koma gida haka ya zuba ido, Jidda tasha jiki ta rame tayi wani iri, tana ɗanji sauƙi ta koma makaranta suka bata dubu huɗu, suka ce sun koreta, dukda sun san bata da lafiya, haka suka koma gida suka tsuguna, Umman Yusuf ta rasa inda zata saka ranta, ga larura ga babu ta musu katutu, kuɗin da aka bata dubu huɗun nan baze sai musu ishashsen Abinci ba, balle ta sai magani, maƙota babu me taimakonta dako ƙwayar hatsi, sedai in ta fito aita mata habaici ana yada mata magana. Abunda bata taɓayi ba, ta shiga ɗibar zannunwanta tana siyarwa, dan a lokacin Yusuf kansa bashi da lafiya, dauriya kawai yake yi, tun yana daurewa harta koma ta kwanta babu lafiya, shima ya kwanta ba lafiya, dan komai se tayi masa saboda zafin ciwo. Haka ta kwashi flasanta da Bashir ne mafi akasari yake sauya mata, ta kai kasuwa akayi musu sayen wulaƙanci, ta karɓo kuɗin ta ɗau Yusuf zuwa Asibiti, suna zuwa aka basu gado, Ulcer ta masa mummunan kamu, ga typhoid da malaria, ita bata ta kanta ta lafiyar Yusuf take, Bill ɗinsu kusan dubu goma sha huɗu dukda Asibitin gwamnati ne, haka ta zare ta biya, taje pharmacy ta karɓo magani zata koma ward, 'yan sanda suka kawo wasu sunyi accident. Wani ya kalleta yace  "wannan kamar matar Bashir" Ta kalle shi tace  "eh nice" Yace  "Ai na sanki, ai tare mukayi aiki da Bashir, baki ganeni ba? Isyaku ne fa, amma yana ganki haka, baki da lafiya ne?" Tace  "A' a Ɗanmu ne ba lafiya, na kawo shi nan aka bamu gado, an kaantar dashi" Mutumin yace  "A'a, naga da kamar private Hospital kuke zuwa? Ya zaki kawo yaranku nan gurin? Ke kanki kamar baki da lafiya fa" Haɗe rai tayi, dan mutumin nan ya fara isarta tace  "lafiyata ƙalau ni" Yace "yi haƙuri, naga kamar kin fara hasala, amma ai naga kuɗinsa ya fito wata biyu baya, amma ya zan ganku haka, kuma kuɗin nasa dayawa" Ta kalle shi da sauri tace   "Yaushe kuɗin nasa suka fito?" "Kina nufin baki sani ba? To 'yan uwansa da wasu' yan sanda sun haɗa kai sun karɓi kuɗinsu, ai na zata an baku naku?" Da gudu ta wuce ɗakin da Yusuf yake kwance, tana kuka yanzu kuɗin mijinta sun fito amma sun karɓa sun cinye, tasan babu yadda za'ayi ko ficika su bata, ga tarin wahala da suke ciki, amma ba imani suka hanata kowani kasone a ciki, haka taje ta zaunatayi kuka kamar ba gobe. Kwanansu takwas a Asibiti aka sallami Yusuf suka koma gida, ta ƙarasa jinyarsa a gida ya koma makaranta, tayi tayi makarantar nan da take Nanny su maida ta bakin aikinta amma suka ƙi, haka ta haƙura duk yadda ta kai ga danne zuciyarta, seda tayiwa dangin mijinta Allah ya isa, akan haƙƙin mijinta da suka danne suka cinye sukaɗai. A ɓoye wani maƙocin su yaga yadda taketa wahala, yai mata hanya gurin wani ɗan siyasa a temaka mata, amma mutumin nan ya nuna mata halin bunsurai, dan haka bata kuma zuwa ba, itace wankau, itace aikatau na biki kona taro, Yusuf yana Sss1 aka tafi da shi Quiz Abuja na akan harkar lissafi, aikuwa Yusuf yazo na ɗaya aka  bashi kyautar dubu ɗari biyar, malamansu suma suka cicciri nasu dana babu gaira ba dalili, ƙarshe dubu ɗari biyu aka bashi. Umma tayi murna da samun kuɗin nan, Yusuf yace  "Umma duk an kwashe fiye da rabin kuɗin, kinga da mun samu da yawa, dubu ɗari biyar fa aka bani" Umma tace  "Yusuf ina lefi, da ina muka samu wannan ɗinma? Ai Alhamdilillah mai dai Allah yayi maka albarka, ya ƙara hasken makaranta ya jiƙan Abbanka' Yusuf yace  " Ameen Umma, ga kuɗin nan, wace sana'a kike ganin zamu fara ne? " Umma tace " Yusuf ka maida hankali a karatunka, sannan kuɗin nan ka ɗau abunda zaka ɗauka, semu yi tunanin abunyi" "haba Umma, na girma fa ki bari in fara sana'a mana, kuma ni ba abunda zan ɗauka a kuɗin nan, muyi tunanin abunyi" "A'a Yusuf, dole ka sai sutura, zan shiga kasuwa in samo maka yaduka, da takalama, dako ɗan agogone, ka fara zama saurayi, ina kallo kayanka duk sun mutu, ba yadda zanyi ne kawai" Yusuf yace "Umma karkice zaki kashemin kuɗi dayawa, ina sa ran zamu kuma zuwa wani competition ɗin, kema ki sai wani abu a ciki, nace ko injin markaɗe zamu siya, se a ajiye shi a ƙofar gida idan na dawo in dinga zama" Aikuwa Umma ta yadda da shawarar Yusuf, suka ajiye kuɗi basu taɓa ba tukuna, suna shirin siyan injin markaɗe. Yusuf ya dawo daga makaranta sukaje kasuwa suja siyo inji, akazo aka saita komai suka sai kayan Abinci da sauran buƙatu. Da safe idan Yusuf ya tafi makaranta, Ummace take markaɗen a cikin gida, idan ya dawo ya fito dashi waje yayi zuwa magariba, se maƙota suka fara surtu wai ana cika musu kunne, bayan a ƙarshen kayanma akwai babbn gurin niƙa, da suke wuni guda niƙa, amma suka zo sukace wai suna takura musu da ƙarar inji. Duk shiru na Yusuf ya dinga faɗa, yace "wallahi babu wanda ya isa ya hanamu sana'a, me kuke so muyi ƙasa zamu ci kome, yanzu da wani fitinannen na zama sekunfi kowa tsinemin, ba irin wahalar da bamu shaba, kuma mun kafa sana'a kuce semun ɗauke baze yuwuwa ba" Maƙwabcinsu Na jikin gidansu yace  "kai dalla har kana da bakin magana, banza tsintacce wanda ba'asan asalinsa ba, karuwa tayi ciki ta haife ta yar, an tsintoka an rufa maka Asiri, amma kazo kanawa mutane Iskanci a gari" Maganar nan tayiwa Yusuf ciwo, yaji haushin maganar nan, yaji kamar ya soka masa mashi a zuciyarsa, amma ya dake yace  "idanma hakan akayi, inma ba hakan bane, ba a kaina aka fara ba, kuma ba kaina za'a ƙare ba" Umma dake cikin gida, tazo ta janye hannun Yusuf tana kuka suka koma cikin gida  tace   "Yusuf mi haƙura da markaɗen nan kawai, bazan iya jure ana cimim zarafinka ba, bazan iya ba" Ya goge mata hawaye yace  "Umma idan mun dena Meza muci, kidena damuwa ni baya damuna, saboda nasan bani da wasu iyaye inba Ummana ba, da Abbana Allah ya jiƙansa, ki rabu dasu kawai, komai lokacine wataran in ance suyi min ba zasuyi ba" Haka yaita rarrashinta yana bata haƙuri, washegari ya tafi makaranta, bayan ya dawo tun daga soro ya fara jiyo kukan ummansa tana   "da ikon Allah se Allah yasakamin abunda kukayi min, yadda kukayi nufin tozartani Allah yasakamin, wallahi ɗanlami da kai da Ballo da 'yan uwanka bazan yafe muku zaluncin da kukamin ba, wallahi Allah ya isa" Yusuf ya shigavda sauri, yaje ya sameta a dirƙushe tana kuka, ga su Yaya ɗanlami da wasu mutane. Yusuf yace "Umman Yusuf, lafiya kuwa me suke mana a gida? Me kuma mukayi musu?" Yaya Bello yace  "kai dalla tafi can banza, meye naka a ciki wani wai me muke muku a gida, inane gidan naku meye haɗakinka da Bashir,? Ɗan tsintuwane fa kawai amma ko taku baka dashi a abunda ya bari, seka bazama neman karuwar da ta haifeka ta yasarka ta nuna maka ubanka" Cikin kuka Umma tace "Wallahi karka ƙara shegantamin ɗa, Yusuf ba karuwa ce ta haife shi ba, ɗana ne, kuma ɗan sunnane duk Wanda ya kuma shegantashi ban yafe ba" Yusuf bece komai ba, yaje ya durƙusa ya ɗago Umman dake kuka yace  "Umma meyafaru ne wai?" "Yusuf kaga, bayan sunje sun karɓe haƙƙin Babanka sun cinye, babu wanda ya waiwaye mu, sun saida gidan da muke ciki, an bamu notice, wai bazasu bamu gadon komai na Bashir ba, Yusuf an mana adalci kenan? Yanzu sun kyauta kenan? Yusuf ynzu kana ganin da Bashir ne a raye ze musu haka? " Yusuf ya rumgumeta ganin yadda jikinta har rawa yake tana kuka, gata ba cikakkiyar lafiya ba yace "Ummana kiyi haƙuri, ai Allah baya bacci ni idan bani da gadonsa aike matarsa ce yakamata su baki" "Yusuf gidan nanfa nawane nida kai, har rubutu Bashir yayi ya bari kafin ya rasu, kuma Bello ya sani amma shine suka saida gidan, idan na tashi daga nan mu koma ina? Me nake dashi idan na bar nan?" Ɗanlami yace "koma gidan ubanwa zaki ki tafi, ai dama ba gidan ubanki baane, seki koma gidan ƙasar da ubanki ya mutu ya bari, shi kuma ya koma gidan ajiye shegu da kuka ɗakko shi" "Wallahi se nayi shari'a daku, se an ƙwatar mana haƙƙinmu" "Haba Umman Yusuf, aishi Allah baya bacci, kuma Allah na kowane baya barin zalunci, menene gida idan sunyi haka dansu wulaƙantamu Allah baze basu dama ba, ki kwantar da hankalinki mun rasa Abba ma, kuma dangana mukayi mukai haƙuri, dan haka gida ɗazune, in da rai da lafiya insha Allah sena gina miki gida na ban mamaki, gidan a wanke hannu kafin a taɓa " Yai maganar yana goge mata hawayen fuskarta, yana murmushi dukda Shima fuskarsa sharkaf take da hawaye. Murmushi tayi na ƙarfin hali tace " na dena Yusuf, na barwa Allah nasam baze wulaƙantamu ba" Saboda keta haddi da cin mutunci, tana zaune wai za'a wuce da masu siuen gida har ɗakin baccinta a duba, Yusuf ya miƙe ya tare ƙofar yace "dul abunda zakumin zan iya jurewa, amma wallahi duk garin nan babu mecin mutuncin uwata in ƙyaleshi, ɗakin baccinta gurin sirrinta ne, dan haka babu me shiga, jibi in Allah ya kaimu zamu tashi mu bar muku gidan, ba zamuyi shari'a daku ba, amma Allah ya biwa Ummana haƙƙinta" Bello yace "kaikuma kai a wa? Gayyar tsiya arna a idi? Kama je kayi shari'ar damu mana, dalla gafara nan a duba ɗaki sirrin banza sirrin wofi" "Wallahi taku ɗaya ka ƙara daga inda kake, kai yunƙurin shiga ɗakin nan idan na ɗaga ka se nayi jifa da kai ta katangar nan wallahi" Tabbas yadda ƙirar jikin Yusuf take, dukda ba wani girma yayi ba tsaf ze iya aikatawa, haka suka haƙura suka tafi suka ƙyalesu. Umman Yusuf ta cigaba tana cewa "Yusuf Allah yasaka mana, kana gani ana cewa an kashe Abbanka, aka dawo da motarsa suka ɗauka suka siyar, banyi magana ba, kuɗinsa suka fito suka wuce gaba suka karɓe suka cinye, se a bakin jama'a naji labarin kuɗin sun fito, duk 'yan kadarorin daya bari sun siyar, kuma suna kallon wahalar da nake yi, babu tausayi babu imani a tare da su, ya suke so muyi da ranmu Yusuf, sun cutar damu" Tai maganar cikin kuka da sheshsheƙa, Yusuf yace "Umma kidena kukan nan, zanje a samo me siyan injin markaɗen nan, da ɗan cinikin da mukayi mu samu gida ko ƙaramine mu kama" Jinjina masa kai kawai tayi, tana share Hawaye, Yusuf yace "Umma wao ya akayi kika san haƙƙin Abba ya fito sun cinye?" Ta share hawayenta, ta gayamasa yadda suka yi da ɗan sandan nan, Yusuf yace "Umma tunda ya gayamiki haka, kuma beyi ƙoƙarin taimakonmu ba to tabbas dashi aka ci kuɗin nan, dan babu yadda za'ayi ba'aci kuɗi dashi ba yasan anyi, abunda nakeso dake shine kiyi haƙuri, Allah baya bacci, ki bar batun kaisu ƙara, mu barwa Allah, Insha Allah Ummana wataran zaki yi dariya zamuji daɗi, kidena kuka Umman Yusuf " Yana maganar yana goge mata hawaye. Yusuf kai inji kasuwa ya siyar, sedai babu wata daraja, saboda anga a Matse suke, suka har haɗa suka bada rabin kuɗin gida, suka wani ƙaramin gida haya, suka koma ciki suka zauna. Yusuf ya kusa shiga aji shida ma sakandire, dan haka yasan dole za'a buƙaci kuɗi a hannun su, kuma yasan Umman bata dashi, ga kuɗin hannunsu babu, ɗan Abincin da suka koma gida dashi babu, ga babu jarin sana'a, kuma kuɗin haya rabi suka bayar . Yazamana Yusuf ya fara tunanin mafita, ana idar da sallar Asuba, yake zuwa ya karɓi hayar kura yayi ga ruwa, ya tattara abunda ya samu, ya dawo gida ya saimusu abun karyawa, Umma ta matsa se taji inda ya samo kuɗi, yayi mata bayani aiko se kuka tace "Allah ya jiƙan Bashir, da yana raye nasan babu yadda za'ayi ya bar abun ƙaunarsa yayi wannan wahalar, Kayi haƙuri Yusuf nakasa baka kulawar data dace" "Haba Ummana, aini na wuce lokacin da zaki nemo ki bani, sedai in nema in baki, dan Allah kidena kukan nan, kidena wannan tunanin please" Haka rayuwa ta cigaba da ja, Yusuf sana'a iri iri, yayi wannan yayi waccan komai ƙasƙancinta kuwa, harya ɗan tarawa Ummansa jarin saida man ƙuli da manja a cikin gida, a haka suka tara cikon kuɗin haya, suka biya suka ɗan samu sassauci gurin samun Abincin da zasu ci. Dayake da suka tashi ba nisa sukayi da unguwar tasu ba, dan haka wani lokacin idan ya turo kurar ruwa, yakan haɗu da maƙotansu na da, se yaji suna "Ohh rayuwa juyi juyi, wai yau ɗangata ke tura kurar ruwa, dama shiya dace dashi tunda dai ba'a gatan aka haife shi ba" Yusuf baya tankawa, shi dai babban burinsa asirinsu ya rufu shi da Ummansa. Allah ya temake shi yaci qualifying, dan haka kuɗin Neco kawai ya biya, da na Jamb dayake Asusu sukayi shida Umman, suke jefa abunda ya samu saboda hidimar karatunsa. Yusuf ya zana jarrabawa gaba ɗaya, Waec, Neco, da kuma Jamb, dayake Allah maji roƙon bawane, kuma kullum cikin yi masa addu'a Umma take, Se Allah yasa ya tsallake gaba ɗaya jarabbawarsa, ya samj maki me kayu da ake nema, dan haka har admission ya samu a jami'a, sedai fannin daya ɗauka na medicine, kuɗinsa ya kai kusan naira dubu sittin ta wannan lokacin, wadda kuma kuɗi ce masu yawa a wannan zamanin, Nanfa murnar Umma ta koma ciki, ina zata samu wannan kuɗin? Me take dashi wanda zata yi ta cika burin ɗanta? Burin da dashi Abbansa ya rasu, Yusuf yayi karatu ya amfani al'umma...... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 102_103 Abu ya zamana ga ƙoshi ga kwanan Yunwa, ga bikin zuwa babu zanin ɗaurawa, course me wahalar samu gashi Allah yabawa Yusuf amma babu hanyar yinsa. Yusuf kam ya fidda rao, dukda ƙaunar karatun da yake a ransa, amma babu yadda iya, tunda yasan basu dashi. Allah sarki, Jidda ta damu kanta, tasan ba lallai ya kuma samun wannan damar ba, yana son karatun sosai, idan be samu ba tasan abun ze dameshi, amma baze nuna mata ba, ta duƙufa addu'a, ta nayi tana rarrashin Yusuf akan idan karatun nan be samuba, su barwa Allah, Allah ya kawo masu mafita. Sam Yusuf baya nuna mata da ya damu lallai se yayi karatun, 'yan unguwa suma ganin yadda suke fama da rayuwarsu, amma babu me tallafarsu se Allah. katsam aka kira shi a waya akace gwamnati ta bashi scholarship, an fidda gwarazan shekara na makarantun kimiyya da fasaha, kuma  Sunan Yusuf ya fito ya samu. Shi Yusuf jin abun ya dingayi kamar almara, banda iko na ubangiji wa zeyi wannan hukuncin haka? Umma kamar ta zuba ruwa a ƙaaa ta sha dan farinciki, tayi murna ta godewa Allah, babu zato babu tsammani dama tazo musu ba tare da wata wahala ba. Akayi shirye shiryen komai ya fara karatu, sedai wannan karatun karatune me wahalar gaske, ba karatun ne matsalar Yusuf ba sedai kuɗin transport, na handout excursions, practicals, field trips, kullum cikikn kawo kawo ake, gashi baya samun damar yin 'yan sana' oinsa saboda zaman makaranta. Dama a unguwa babu ruwansa da kowa, ko abokai bashi da su saboda gudun gori da wulaƙancin mutane, Amma dukda haka be tsira ba, aita surutu waiya fiue girman kai, daba'a san wayeshi bane shine ze dinga jawa mutane aji, yana wani hura hanci, shi dai shirune nasa, baya tofa komai baaa gaban sa. Karatu abu fa ya fara gagara, da ƙyar Yusuf ke iya karatun nan, saboda babu, Yusuf gashi ƙwaro na gaske saboda haddar Al'qur'ani babu karatun dake bashi wahala. Shekararsa biyu yana karatun, akayi zaɓe aka canza gwamnati, ba tausayi ba ragayya ga yaran talakawa gwamnati tace babu kuɗi, bazata iya cigaba da biyawa yaran da aka bawa scholarship kuɗin makaranta ba, wanda yake da hali ya ɗau nauyin kansa. Yusuf yanaji yana gani ya ajiye karatun medicine ya dawo gida ya zauna, Umma seda tayi kuka, shiko Yusuf akwai dakiya yaita bata haƙuri yace  "Umma da bamu san zan fara karatun bama, Allah ya bani dama, yanzu kuma ya ƙwace damarsa, mu ɗauka a ranmu Allah yayi mana wani tanadine wanda yafi wannan karki damu Ummana" Ita babbr damuwarta kar karatun ya fita daga ransa, yazo ko an samu damar ya ƙiyi takasa cika masa burinsa. Nanma 'yan unguwa suka ɗau surutu, dan Ya dena zuwa makaranta, baƙaƙen maganganu habaici da zunɗe haka yake ganinsu kala kala, Yusuf ya kan rufe kansa a ɗaki da daddare yayi kuka, yayi kuka har ya gaji ya bawa kansa haƙuri, tun tasowarsa yake fuskantar ƙubalen cin zarafin wai shi bashi da iyaye, a gidan marasa iyaye aka tsinto shi,har yanzu yi ake ba'a fasa ba. Yusuf ya dawo zaman gida, ya shiga neman yadda zasuyi su rufawa kansu asiri shida Ummansa, a haka wani mutum anan maƙotansu, dan sun ɗanfi wanda suka baro mutunci, ya samowa Yusuf Form na polytechnic, Yusuf yaji daɗi Sosai dan shi yanzu duk abunda yazo masa a rayuwa karɓarsa yake, bashi da wani zaɓi wanda ya wuce hakan, ya sake jamb ya cike Civil engineering a nan polytechnic, aikuwa ya samu ya fara zuwa, cikin ikon Allah sana'ar Ummansa ta mai ta kafu ta karɓu, ana siya sosai, ta nemawa Yusuf gurin koyon sana'a a gurin masu furniture, shima seda ta biya kusan dubu hamsin sannan aka karɓeshi. Kullum idan ya dawo daga makaranta, se yaje gurin koyon aiki, idan ya tashi ya shiga kasuwa yaga meze samu yayi, saboda baya san ɗorawa Ummansa wahala, sam Yusuf bashi da hutu, a haka ya kammala poly, Umma tace baze tsaya ba, ya nemi Form na D. E ya tafi, shi gaba ɗaya jikinsa ya fara sanyi da harkar karatun nan, ta bashi kuɗi yaje ya karɓo form yayi applying, aikuwa by luck ya samu suka bashi level 2 a university, haka nan yau akwai gobe babu haka rayuwa ta dinga tafiya, a wahalce da ƙyar Yusuf ya kammala karatun nan, aka zo maganar tafiya service, Umma taji bazata iya jure Yusuf ya bar gari ya batta ba. Haka akayi cuku cuku, Yusuf yayi service ɗinsa a kano, bayan an kammala yazo babu aikin yi, sedai kame kame, ga inda yake koyar aikin kafintan Wasu yarabawa ne, masu muguntar tsiya, ganin yana da saurin ganewa yasa suke masa mugunta, gurin koyarwar. Zaman haka ba aiki ba sana'a ya ishi Yusuf, sedai 'yan bige bige, amma a hakan idan Ummansa taji tana da kuɗi a jikinta, haka take siya masa kaya masu tsada na sawa, shiyasa bazaka ce suna fama da rayuwa ba. Rannan yana zaune yana duba wayarsa, yaga wani posting, mutane nata tofa albarkacin bakinsu akan harkar tsaro, sedai babban abunda ya bashi mamaki, be wuce yadda mafi yawa sharhin da akayi, ƙorafine akan jami'an tsaro, seya tuna hirar da suka taɓa yi da Abbansa kafin ya rasu, ya tuna yadda akayi aka haɗa kai aka cinye haƙƙin ummansa, tabbas kamar yadda Abbansa ya faɗa, koda mutum ɗayane yake nagari a cikin 'yan sanda, ko yaya wani ze amfanu dashi, dan haka se yaji yana sh' awar yayi applying shima. Sun gama cin Abinci shida Ummansa da daddare yace  "Umma" Tace  "Na'am yaron kirki" "Umma wata magana ce dama nazo da ita, so nake in gaji Abbana" "Kamar yaya kenan?" "Ɗan sanda nake son zama" "Kamar yaya Yusuf? Bana son rasaka kamar yadda na rasa Abbanka, dan Allah kabar maganar nan" "Umma, idan baki amince ba shikenan, amma Umma bakya tunanin da akwai wani tsayayyen ɗan sanda me gaskiya a gurin da an tsaya mana gurin karɓo haƙƙinki, Umma kin san mutane nawane ke shiga garari sakamakon rashin aiki yadda yakamata da wasu maciya amana sukeyi a ƙasar nan? Umma in dai zamu dinga ƙyamar aikin mu dingawa 'yan sanda kuɗin goro to tabbas za' aita cutar mutane, duk abu ba'a rasa na Allah, sedai idan suka yi ƙaranci zalunci ne yake yawaita, Umma idan kika bibiya akwai mata irin irinki wanda aka zalunta, kuma za'a cigaba da yi idan har ba'a ɗau mataki me kyau ba, ina son yin aikin ɗan sanda ne saboda in temaki al'umma, ima son zama ɗan sanda dan in ɗora daga inda mahaifina ya tsaya, dan Allah Umma ki amince, amma in bakya so na haƙura " Jikinta ne yayi sanyi, ta ɗanyi shiru taga tabbas maganganun Yusuf haka suke, kuma tana da yaƙinin cewa Yusuf mutum ne nagari, abune mawuyaci a haɗa kai dashi a cuci wani. Ta numfasa sannan tace " Shikenan Yusuf, na amince ubangiji Allah yayi maka jagora, ya goyi bayanka ya kareka a duk inda kake, Allah ya wuce maka gaba a al'amuranka, ina fatan zaka zama mutum nagari me gaskiya da riƙon Amana, Allah yasa a sanadiyar ƙudirinka ya zamana an share hawayen wanda aka zalunta, kayi gaskiya da adalci Yusuf " Yusuf yayi murmushin jin daɗi da farinciki, yace  " Insha Allah Ummana, in Allah ya yadda ba zanyi wani abu wanda ya saɓawa Alƙawarin da mukayi dake ba, Addu'ar ki nake buƙata, Allah ya kauda zuciyata daga aikata duk wani abu da ze saɓawa Allah " Umma tace "Addu'a ai kullum cikinta nake Yusuf, ina fatan Allah ya tsare, amma bana son ka sha wahala, training ɗin nan nasufa da wuya, karka je su baka wanda bazaka iya ba, Abbanka yana bani labarin wahalar abun nan" "Haba Umma, sekace wani ragon maza, kin ganina santalelen ƙato dani, se in goya maza goma in gudu dasu a bayan nan nawa" Umma tai dariya tace "eh lallai, ba shakka naga alama kam" Nanma Allah ya temake shi ya samu makarantar horar da 'yan sanda, Yusuf yasha wahala ya fuskanci ƙalubale daban daban, a haka harya kammala makarantar nan, sukayi passing out, Allah ya temake shi ya fita da babban rank, sakamakon yayi karatu yana da degree. Yusuf ya kama aiki, sedai Umma kullum cikin nasiha take, na akan yaji tsoron Allah akan wannan aiki daya fara, cikin ikon Allah yana fara samun salary yazo ya zubewa Umma kuɗin yace  "Umman Yusuf, Insha Allah inaji a jikina lokacin da zamu samu sassauci yazo, ga wahalarmu ta wannan watan, na karɓo salary" Umma tace "Alhamdilillah, dama komai yayi farko zeyi ƙarshe ai, Allah yayi albarka amma ka ɗau kuɗinka, ni duk abunda ka sanmun karɓa zanyi ince Allah yayi albarka" "Haba Umman Yusuf, wannan nakine halak malak, na bar miki, ba abunda zanyi dasu ni duk abunda kika sanmun a ciki shikenan nagode, ki fara more wahalar da muka sha Umma" Kawai seta fashe da kuka, Yusuf ya rikice gaba ɗaya yace "subhanallah, Umma laifi nayi mikine? Yi haƙuri dan Allah, ban san zan ɓata miki rai ba" Ta girgiza kai cikin kuka tace  "Tun kana ƙarami Yusuf, naso inyi duk me yuwuwa dan ganin baka gane bamu muka haifeka ba, amma hakan ya gagara, duk yadda muka kai ga ɓoyewa nida Abbanka abu ya gagara, bakin mutane yakasa yin shiru, suka dinga wulaƙantamin kai da maganganu marasa daɗin gaske masu muni, har seda suka saka kasan bani na haifeka ba, amma haka kake min biyayya kamarni na haifeka, A baya nayi kukan Gorin rashin haihuwa, an goran tamin nayi kuka nayi kuka, amma tunda Allah ya bani kai, na dena wannan kukan, nasan ba lallai ɗan dana haifa yayi min biyayyar da kake mun ba Yusuf "  ta ƙarasa maganar cikin kuka, Yusuf yaji ta fama masa ciwon dake raɗaɗi a cikin zuciyar sa, yaji kamar ya fashe da kuka, sedai be taɓa gangancin zubda hawayen rashin sanin suwaye iyayensa a gaban Jidda ba, dan idan yayi haka ya zama butulu abun Allah wadai, ya tattara nutsuwarsa ya dake, ya riƙe hannunta yace  "wayema yace ba Yusuf ba ɗan Ummansa bane, samun uwa kamar Umman Yusuf me sadaukarwa da juriya a wannan lokacin se anyi tonawar gaske, Wa Yusuf zeso in be so Ummansa ba, waze wa Biyayya idan bebi Ummansa ba, Ummana ina neman Aljannata, duk me neman Aljannarsa Annabi salallahu alaihi wassalam yace yabi Allah da ma'aiki sannan yabi uwa, shiyasa nake bin tawa mahaifiyar domin neman albarka da samun wannan Aljannah, shiyasa nake bin Ummana nasan babi da abun biyanta ladan shayarwarta da ɗawainiyarta, Allah ya haɗamu a Aljanna gaba ɗaya, amma wannan kuɗin na Umman Yusuf ne halak malak, da Yusuf da abunda Yusuf ya mallaka duk na Ummane" Ta rungume Yusuf ta fashe da kuka, a hankali Yusuf ya lumshe ido yana zubar da nasa hawayen ƙasa ƙasa, dan karta ji yana kuka, ta goge hawayenta tace  "Yusuf indai nice, nagode sosai Allah yayi Albarka, amma ka ɗauki kuɗinka, kaje kayi buƙatunka gabanka, sedai ka ɗan sai mana Abinci" Yusuf yace "Umma, nifa kuɗin nan bazan ciba, ki sanmun na mota zuwa gurin aiki kawai" "A'a Yusuf, bana son jayayya fa" Yusuf yace "ni na isa inyi Jayayya dake, tunda kin rasa abunyi dasu bari in baki shawarar yadda za'a kashe, ki rabasu biyu, rabi ki ban abunda zakimin, ki riƙe sauran, rabin idan mun samu kuɗi mudinga ƙarawa a kai, mu nemi fili a wata unguwar, mu fara gini, gara mu koma gidan kanmu " Umma tace  " na daɗe ina wannan tunanin Yusuf, yana da kyau ko fili mu siya, sedai bazan karɓe maka kuɗi duka ba, nasan kana da buƙatu kaima " Yusuf ya haɗe rai, tace  " ya dai naga ɓata rai" "Umma ni zan baki abu kiƙi karɓa ko? Allah ya jiƙan masoyina, nasan da shine baze min haka ba" Umma tace "shikenan, naji Allah yayi albarka, Allah ya kareka daga sharrin maƙiya" Shigar Yusuf aikin ɗan sanda na farin kaya, nan da nan sunansa aka fara saninsa, musamman jin laƙabin sunan mahaifinsa, Yusuf Bashir Maitama, Yusuf akwai ƙwazo akan harkar aiki, baya wasa ba ruwansa da cin hanci ko rashawa shidai aikinsa kawai. Bayan ya fara aikine ya gano irin cakwakiya da maguɗin dake cikin aikin, da irin tuggu da maƙrƙashiya dake aikin, ga me laifi ƙiri ƙiri kana gani amma saboda yana da wane ko yasan wane, se ace a ƙyaleshi, amma idan aka kamo ɗan malam wane ƙarshe 'yan sanda suna iya ajalinsa, ko ka samu case ka fara aiki a kai, daga sama se a turaka wani gurin a karɓe aikin, ko a ƙirƙiri laifi a ɗorawa wani dan a samu wani abu a hannun sa, da ire iren wannan ha' incin, A haka Yusuf yai tunanin yadda rasuwar mahaifinsa ta kasance, a nan ya gane tabbas set up ne mutuwar mahaifinsa da ubangidansa, sedai bashi da evidence dan in be manta ba, suna kan wani case ne, aka kira shi shida ubangidansa can Lagos, daga tafiyarsu se gawarsu, Yusuf baya son ɗagawa ummansa hankali dan haka be gayamata bata ba, ya bar zancen. Yusuf ya dage da aikin ginin gidansu, dukda muguntar da'ake masa a gurin koyon aiki, a haka ya iya aikin kafinta, ya kama shago ya zuba yara suke masa aikin yana biyansu. Duk yadda aka so asa Yusuf a harkar cin hanci amma yaƙi, aka dinga cewa shima tsinannen kafiya da taurin kaine dashi kamar ubansa marigayi, ko talauci ze kasheshi baya karɓar kuɗin rashawa. Yusuf ya kammal ginin gidansu, da kansa yayi furnitures ya zuba a gidan, kamar gidan wata amarya, gidan yayi kyau hatta kayan sawa seda ya canzawa ummansa kafin su koma gida, ya zuba kayan Abinci rana ɗaya yaje ya ɗakkota ya kawo ta gidan nan, umma sarkin kuka seda tayi kukan nata data saba, yaita rarrashinta, suka kwaso sauran kayan buƙatunsu suka dawo sabon gida, Yusuf ya sai Babur lifan me kyau. Alhamdilillah rayuwa ta fara yi musu sauƙi, Daidai gwargwado suna hutawa, ga salary ɗinsa ga gurin furnitures, ya hana Umma sana'ar komai, data motsa se yace "Umman Yusuf me kike so, Ummana me za'ayi miki?" Sam bata da damuwar komai, dama gata ba wani girma tayi ba dan lokacin da Suka tsinci Yusuf ba tafi sha bakwai ba, dan da ƙuruciyarta sosai akayi mata Aure, bayan mutuwar Bashir wasu sun nuna suna sha'awar Auren ta, amma taƙi Aure saboda rayuwar Yusuf, tasan ba lallai a riƙe mata ba. Babban abunda yake damun Umma da Yusuf shine ko abokan kirki bashi dasu, gashi kamar mace wani lokacin kullum yana naniƙe da ita, da girmansa da komai amma idan zata unguwa, seya bita, ya jirata a waje itakuma ta shiga, ko zata wuni yana gurin a zaune, idan kasuwa ce haka zasu tafi tare, haka idan Asibiti ne, idan ya dawo daga makaranta, idan ba masallaci ba baze je waje ya ɗanyi hira da abokai ba, tayi faɗan harta gaji amma yaƙi denawa, abun da Ummansa bata gane ba shine, shi hana gudun magana ne, ko ace anyi rigima yana gurin ko kuma wani abu ya haɗashi da wani ayi masa gori. Yanzu gashi ya kammala karatu, ga aikin yi gashi ya zama cikakken namiji amma ko budurwa bata taɓa jin Yusuf yayi ba, to mutumin da bashi da abokai mazama balle wata budurwa, ko a gurin aiki abokinsa ɗaya da yake biyo shi gida shine Abbas, banda wannan Yusuf bashi da wasu Abokai. Rannan yayi musu Abincin dare, ya zubi suna ci Umma tace "Wai nikam Yusuf, kai ko budurwa baka da ita ne, sa'aninka sun fara Aure, amma kai ko zancen budurwa baka yi, ko dai nice ake ɓoyewa" Ya ɗan tura baki yace  "Umma ni me zanyi da wata budurwa kuma, ni bani da wata budurwa" "Saboda me baka da budurwa? Se kace ba namiji ba, haka zancigaba da zama da kai gunsumeme ba Aure, sedai duk inda zani kana biye dani? Ai lokaci yayi da zaka nemi iyali kaima" "Nidai umma bana so, ki ƙyaleni a hakana kawai" "Iyeee, kai kodai baka da lafiya ne? Idan bahaka ba, amma kace baka so in ƙyaleka, idan baka da lafiya ne ka gayamin in san abunyi, amma ta yaya za ka ce baka son Aure?" Ya gane inda Umman ta dosa amma yace  "Umma wane irin rashin lafiya, niba zazzaɓi ba ba wani ciwo ba, kina ganina rasam danu, kawai ni matan ne se a hankali, bana son wadda zata zo ta damemu" "Ai ina maka addu'a, kuma nasan Allah ya amsa, Insha Allah mace tagari zaka samo mana, amma dai gaskiya anemomin sirika, ko kuma ni in nemo" Yusuf ya miƙe tsam yace   "Hajiya Umma kenan, me abun mamaki Allah ya ƙaro mana Arziki in biyamiki Makka, ni nayi nan seda safe" "Au zancen ne baka so shine ka gudu ko? Zakazo ka sameni kuwa dan ƙaniyar ka, jikoki nake son gani, na ƙagu ka ƙara gaba yara nake son gani " Yusuf yayi waje yana dariya yace "Hajiya Umma, tawa ta kaina. Yusuf ya cigaba da aikin sa, da neman kuɗinsa. Wataran ya dawo a babur ɗinsa, ze wuce gida yaji ance " Sannu da zuwa " Ya waiga yaga wata matashiyar budurwa ce, shi dai yasan yana ganinta a nan unguwarsu, amma besan daga inda take ba, kuma ba abunda yake haɗashi da ita, dan haka be kawo dashi take ba yai gaba abunsa. Aikuwa yaji haushin ƙin kulatan da yayi, haka ta wuce ta tafi nata Aiken. Da safe ya fito ze sai bredi, suka kuma haɗuwa da ita, tace masa ina kwana, ya waiga ya kuma kallonta tace "nace ina kwana" Yusuf yace "lafiya ƙalau" daga nan yai gaba. Ya zamana kusan kullum in dai ze fita kokuma ya dawo seya ganta, kuma seta kula shi, shi harta fara bashi haushi ma. Wataran Asmar Umma ta tashi ga zazzafan zazzabi, Yusuf ya kaita Asibiti aka rubuto mata ruwa da allurai, aka sama ta wasu a can ya taho da sauran gida. Da daddare za'ayi mata allura, yaje chemist ɗin bakin titi, yaje ya gayawa me chemist ɗin ko zezo yayi mata allurar a gida seya biya shi Me chemist yace "karka damu, kaje zan turo ƙanwata tayi mata" Yusuf yace "tasan gidan ne?" Yace "eh ta sani, zata zo insha Allah" Yusuf ya koma gida yana jira, yai girki ya tattara kwanukan yana wankewa, tayi sallama, ya miƙe kalleta aikuwa ya haɗe rai yace "ke lafiya?" Taya fari da ido tace "ba gurinka nazo ba kake wani haɗemin rai, ina mara lafiyar tamu?" Yusuf ya harareta yace "wace mara lafiyar? Malama ƙara gaba ba nan bane" "Kamar yaya, Yaya Sani ya cemin inzo zan mata allura fa" "Wai dama kece?" "Eh nice, ina Umman tawa take?" Yusuf a ransa yace "ji wani iyayi, wai Ummanta ummana dai ni kaɗai" Yai mata jagora gurin Ummansa, Yadda ta dinga lallaɓa Umman ne, yaji daɗi Sosai, bayan ta gama yace 'nawa ne? " Ta Harare shi tace "in mutum yayiwa mamansa abu seya biya? Ummana Allah ya ƙara sauƙi" Umma tayi murmushi tace "nagode sosai' yata, Allah yasaka da alkhairi" Yusuf ya tsaya sororo yana kallonta tace "kaje ka cigaba da wanke wankenka mana, Umma seda Safe Allah ya ƙara sauƙi, likita ya rubuta a samiki ruwa, safe da yamma na kwana biyu, zanzo in samiki insha Allah" Umma tace "to shikenan nagode Allah yayi albarka, amma baki gayamasa nawane kuɗin ba ya biya" Yarinyar tace "Abunda ze biya shine, yaje ya ƙarasa wanke wankensa, yai miki shara ya siyo miki duk abunda kike so kici, kiji ƙwarin jikin ki" Umma tace "to shikenan kana dai ji ko?" Yusuf kawai ya sosa kai, Yarinyar tace "dan Allah ka fitar dani bakin hanyar nan taku, lungunku da duhu ina jin tsoro" Umma tace "Yusuf raka ta mana" Ya kalli Umma ya kalli yarinyar, ta kashe masa ido ɗaya tayi gaba..... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 104_105 Yusuf ya bita da kallo yana hararta, Umma tace  "eh yakamata, Yusuf rakata hanya kaga dare ya fara yi, ni baki gayamin sunanki bama gashi zaki tafi" Tai murmushi tace "Sunana Salma" Umma tace "to Salma nagode, ki gaida mutan gidan" Salma tace "zasuji insha Allah" Badan Yusuf yaso ba ya biyota suka fito, Salma tace  "wai kai baka amsa gaisuwa ne?" "Eh bana amsawa" Salma tace "A'a kace dai nice baka amsa gaisuwa ta, da safe idan na ganka koda yamma idan na gaisheka seka wani basar kamar baka ji ba, kuma fa kana jina" Banza yai mata suka cigaba da tafiya,  "au kana ji ina maka magana shine kamin shiru, ga mara hankali ko?" Ko kallonta beba ya cigaba da takunsa majestically. "Shikenan kar Allah yasa ka kulani ɗin, kuma ma bana son rakiyar" Yusuf yace "to ki gaida gida" Ya juya ya koma gidansu, Salma tace "lallai ka cika ɗan rainin hankali, dani kake zancen" Washegari da Safe yakasance weekends ne ba aiki, dan haka bayan ya dawo daga salla, ya duba Umma yaga jikin nata da sauƙi, yakoma ɗaki  ya baje ya dinga bacci, saboda baya samun hutu sosai, yana tara gajiya matuƙa. Se kusan ƙarfe goma na safe ya tashi da sauri, dan ya manta shaf zeyi girki, ya tafi ɗakin Umma da sauri ya shiga da sallama ya tarar da Umma a zaune da ruwa a hannuta, Yusuf yace "Ummana dan Allah kiyi haƙuri, bacci ne ya ɗaukeni me nauyi, ashe har an samiki ruwan ban sani ba ne, bari inje in ɗora ko tea ne inje in siyo bredi" Umma tace "A'a baseka ɗora ba, ni a ƙoshe nake" "me kika ci haka, har kika ƙoshi?" Salma ce tayi sallama ɗakin, hannunta ɗauke da plate da kofi, Yusuf yana zaune a falon Umma, daga shi se gajeren wando da vest, dan haka kyakkyawar surar jikinsa ta bayyana, namijin gaske me tsabar kwarjini da kamala. Yana ganin Salama ya miƙe yace " ke meye haka zaki shigowa mutane babu sallama, baki tsaya an baki iziniba kika shigo?" Umma tace  "A'a ai tun ɗazu tana gidan nan, ita taimin shara da aikace aikace ma" Ya kalli Salma da ta tsatstsareshi da ido yace  "to waye ya sata, Da kin bari Umma idan na tashi ai zanyi, ke Malama ajiye kwanukan nan ki tafi angode, zan kaiwa yayanki kuɗinki ya ajiye miki" Hararrasa Salma tayi harda murguɗa baki, Umma tace  "jimin yaro da faɗan ba gaira ba dalili, daga taimako ita meta yi maka?" "To Umma data gama aida seta tafi, amma kalli yadda ta ganni a haka ba kaya, kuma ta wani tsareni da ido" Umma tace "to ubanwaye yace ka fito a hakan, ƙyaleshi kinji yau ban san dame ya tashi ba, naga yau rigima yake ji" Yusuf ya fice daga ɗakin yana mita. Haka aka ƙarashe kwanakin nan a haka, kullum tazo se sunyi faɗa da Yusuf, in dai tazo seta yiwa Umma 'yan aikace aikace kafin ta tafi, ko su zauna su sha hira ita da Umma, Salma tana da kyau dai dai gwargwado, gata' yar kwalliya da iya ƙwalisa, tana da hasken fata da matskaicin tsawo, sannan tana da ƙirar jiki me kyau, ta yadda ko tafiya take tana ɗaukar hankali. Mazan unguwar nan dana wajen umguwar da yawa suna rushing a kanta, amma bata da lokacin su, ba matasan samari ba har manyan masu kuɗi suna nuna tayinsu amma basu isheta kallo ba, Saboda mace ce me class, a mazan ma ba kowa ke iya tunkarar ta ba, saboda duk girmanka idan kamata abunda beyi mata ba, zata keta kane yadda take so kuma ko a gaban waye, Tayi school of Nursing, tayi midwife tana ji da kanta sosai. A bakin yayyyanta taji suna hirar Yusuf wataran da daddare, ɗayan yace  "Habu gaskiya gayen nan da yaja salla da Asuba dama ya zasu bashi limanci, jar uba kaji ƙira'a kamar a Misra" Habu yace "bari Usman, ni kaina da yaja sallar nan kamar kar ya dena karatun nan, ai rashin zuwan liman da wuri yau munga 'yan Islamiyya, anya wannan a ƙasar nan yai ilimin Addini?" Usman yace "waya san masa, gaskiya ya iya karatu inaga zanje muyi bonding kona samu hasken makaranta" "A gidan uwarwa zaka samu hasken makarantar? Bayan ko sauka Al'qur'ani ba muyi da kaiba ka fece neman kuɗi" Habu yace "eh naji, aiba sharaɗine se mutum yayi sauka za'ayi abota dashi ba" "To bari in gayamaka, kaga duk wannan ilimin nasa shegen girman kaine dashi, baha kula kowa, iyakaci in ze wuce yai muku sallama, ban da haka ko aboki bashi da shi a unguwar nan, inda gayen ya ban haushi kenan, dan kana da ilimi ubanwa zakayiwa girman kai, kai ba wani shahararraen attajiri ba, ba basarake ba amma kace bazaka kula mutane ba" Habu yace "Aikuwa ilimin baze masa amfani ba, dan girman kai rawanin tsiyane, ni harnaji ya bani haushi wallahi ' Salma tace   " Kukam Allah ya shirye ku, kawai kun zauna kuna tayi da bawan Allah kamar kun rasa abunyi " Usman yace  " ke abun da haushi fa, mutum be fika da uban komai ba amma ya dinga hura maka hanci, baze dingawa mutane magana ba, ai dole ayi dashi" Salma tace "to ka sani ko haka nature ɗinsa take, maybe jan ajinsa yake yi". Habu yace  "Nature ɗin banza da wofi, kuma jan ajin me sekace mace, jan aji ai se mata, kana namiji ubanwa zaka jawa wani aji, yana gaddi ina gaddi za'a jamin aji, wallahi mutum be isa ba" "Nikam nafison irin haka, inga mutum gentle, yafi ma wata macen jan aji amma ace duk inda mutum ya zauna dan yana namiji ya dinga sakin baki haba, ai abun ba tsari" Habu yace "wannan yarinyar kinci kai tabbas baki da hankali, namiji in ba ɗan daudu ba meye na wani jan aji" Haka suka cigaba da wannan jayayya a tsakaninsu, ya zamana kusan kullum se anyi zancen Yusuf, saboda ko minti biyar liman ya ƙara bezo ba, se kaji ana Malam Yusuf a jamu salla, saboda kawai suji ƙira'arsa me daɗin sauraro. Zuciyar Salma ta kwaɗaitu da san ganin Yusuf, saboda yadda take jin ana maganar sa, wataran da yamma taje karɓar kuɗi a chemist ɗin Usman, Yusuf yaje siyawa Umma Inhaler, tunda ya shiga daga tafiyarsa ma taga yadda yake taku cikin nutsuwa, yayi sallama suka amsa sannan ya gaishesu, ƙamshin turarensa ya gauraye shagon, Salma ta shagala da kallonsa, wanda shi sam be san ta nayi ba, ya karɓi abunda ze siya yai waje. Yana fita Salma tace  "Masha Allah, Yaya wannan ma a unguwar nan yakene? Kaga mutum nutsatse, ga ƙamshin turare, wanda seka gifta maza goma ba kaji ba, se warin hamnata mussman irinsu Yaya Habu" Usman yace "Allah yasa yaji abunda kikace ya casaki san ransa, shegiya uwar leƙe leƙe, duk tarin samarinki amma kuma kina yaba wani" Tace "kai Yayana, wallahi ko kai da kake namiji kasan gayen nan ya haɗu, kaga da yai murmushi, wasu dimples suka lotsa wayyo Allah na, gaskiya me kyau ne, kuma me ajine" Usman yace  "dalla wuce can, haka zaki ƙare ƙarshe mummuna zaki aura" Tace "Allah ya kiyaye, aini naga miji" "A ina?" "wannan wanda ya fita ɗin mana, in dai a unguwar nan yake, ina ciki" . Usman yace "aikuwa zakiyo waje daga cikin da kika shiga, dan girman kaine dashi kamar ƙaruna" Salma tace "kamar yaya kenan?" "Shine fa Yusuf ɗin da muke magana, wanda Habu yake zagi" Salma tace  "haba dai? Wayyo Allah na gaskiya ya haɗu, bashi da makusa, ga kyau ga ilimi ga nutsuwa ga tsafta, gaskiya yamin" "to 'yar wahala, wata wahalar ta ganki kenan, dan wannan banga ta inda ze kulaki ba, dukda wannan koɗaɗiyar fatar taki" "to fatar tawa ma hassada ake mata, to Allah ya shiryeka, ni na tafi ka tayani addu'a kawai" Ta juya ta fita da sauri, tun daga ranar ta gano gidansu Yusuf, take daidaitar lokacin fitarsa da dawowarsa, idan ta ganshi se tayi masa magana, farko da yake ƙin amsa gaisuwarta tayi zaton zancensu Habu haka yaje yana da girman kai, seda taje gidansu sawa Ummansa Ruwa taga yadda yake aikin gida, ga shagwaɓa kamar mace, ga tsananin biyayya ga mahaifiyarsa, anan ta gane mutane da yawa basu fahimce shi ba, bashi da son shiga mutane ne, amma mutum ne simple. Tun daga nan Salma ta liƙe masa, idan ta ganshi seta masa magana kota tsikane shi, wataran sedai ya harareta yai tafiyarsa, ta maida gidansu Yusuf gidan zuwanta, ko tayo girki ta kawowa Umma, ko tazo nan gidan ta tayata aiki. Sabo ne ƙarfi ya shiga tsakanin Umma da Salma, tana jin daɗin yadda take girmamata take tayata wasu ayyukan, dukda Yusuf haushin Salma yake ji amma a hankali, saboda soyayyar da take nunawa Ummansa da mutuntawa yasa, yake ɗan saurara mata kuma har cikin ransa yake jin daɗin kulawar da take nunawa mahaifiyarsa. Wataran Salma taje gidansu Yusuf wajen ƙarfe sha ɗaya na Safe, ta tarar da babur ɗinsa be fita ba, ta shiga cikin gidan ta tarar da Umma a tsakar gida hannunta da mayafi, Salma tace  "Umma ina zuwa haka? Kuma Yaya Yusuf be fita bane? naga babur ɗinsa" Umma tace "dama chemist ɗin yayanki zanje, kwanan sa kusan biyar yana zazzaɓi sama sama, nayi nayi yaje Asibiti yaƙi yau jikin nasa rau da zazzaɓi ko gurin aiki ya kasa fita, shine nace bari in kira yayanki, ya duba shi idan akwai abunda ze iyayi masa to, in kuma babu mutafi Asibiti, yana jin jiki, kin san shi da dauriya da taurin kai, yauma dan yaji uwar barine ya kasa fita gurin aiki" Salma tace "Ina Yaya Yusuf ɗin yake? Nima zan iya duba shi ai" Umma tace "muje yana ɗakinsa" Umma na maganar aka kirata a waya, ta tsaya ɗagawa Salma ta shiga ɗakin nasa da Sallama, ɗakin tas dashi kama r na mace, komai fes fes se ƙamshin turaren wuta da drumer ke tashi, gwanin ban sha'awa. Ta hango Yusuf kwance akan gado, ya lulluɓa da bargo, a hankali ta ƙarasa gaban gadon nasa, tasa hannu ta janye bargon tace  "to shagwaɓaɓɓe, kazo ka kwanta kaƙi zuwa Asibiti, ka tayarwa da Umma hankali" A hankali ya buɗe idonsa ya kalli Salma, cikin ƙarfin hali yace  "malama fitarmin daga ɗaki" "bazan fita ba ɗin, meke damunka ummance tace inzo in duba inga me ya kamata ayi maka" Lumshe ido yayi yaƙi magana, Umma tazo tace "Salma yaya? Za'a iya duba shi a gida" Salma tace "eh, za'a iya, zanje in karɓo ruwa da allurai in masa, amma ya rage kayan jikinsa, ki shashshafa masa ruwa ina zuwa" Haka akayi Salma ta sassaka masa ruwa, da allurai sannan Yusuf ya samu kansa. Washegari da safe da ta dawo, ta tarar da abokan aikinsa sunzo duba shi, babu wanda yasan Yusuf ɗan sanda ne a unguwar dan haka Salma tayi zaton 'yan uwansa ne suka zo duba shi, ta taho masa da Abinci daga gida. Abbas yace  "Yusuf ka samu kaci Abincin mana" Yusuf yace "bani da appetite ne, amma zanci" Sakina tace "ko in zuba naka, ka ɗanci ko kaɗanne?" Salma tace "No karki damu, zeci in kun tafi da kaina zan bashi ko Yayana" Sunkuyar da kai yayi yai mata shiru, yayin da Abbas suka shiga tsokanarsa, Sakina kuwa ta dinga harar Salma, ta dinga cika tana batsewa, saboda gaba ɗaya Haushi Salma ta bata. Bayan ya warke ya koma gurin aiki, sedai Sakina ma ta fito da manufarta na soyayyar ta ga Yusuf, sedai Yusuf ya nuna mata sam shi babu wannan, babu maganar soyayya a tsakaninsa da ita. Salma kuma ya maida ita kamar Ƙanwarsa, dan wataran shike ɗakkota ma daga inda take attachment, kusan duk ta kori samarinta saboda Yusuf, se sukai sha ɗayan dare suna waya, amma sam shi Yusuf ba wai dan yana sonta ba, dan ya ɗauketa ƙanwa ne kuma takan bashi shawarwari masu kyau. Ita kanta Umma ita duk a zatonta soyayya ce tsakanin su, tana ta jin daɗi tana murna Yusuf zeyi dacen mata, dan Salma akwai kirki sosai. Wataran Umma ta sai wata doguwar riga me kyau, ta saiwa Salma ta bawa Yusuf tace shi ze kai mata rigar. Haka Yusuf ya karɓi riga ya kai a matsayin shine ya siya, Salma ta dinga murna tana masa godiya, har ze tafi tace  "Yayana nawa nikaɗai" Yusuf yace "meye kuma? Dare fa yayi ki bari in tafi gida" Salma tace "Yusuf yaushe zamuyi Aure ne?" Yusuf yace "what? Aure kuma Salma? Ai babu batun aure a tsakanin mu, ni ƙanwa na ɗaukeki fa" "Yusuf, ƙanwa kuma? Yanzu duk abunda ke tsakaninmu ba soyayya bace? Yusuf na kori kowa a samarina, babanmu ya tambayeni, nace ni kai na tsayar yace in sallami masoyana, amma ka cemin babu soyayya a tsakanin mu?" Yusuf yace "Salma, banyi hakan da cutar dake ba, amma dan Allah kiyi haƙuri, ni gaskiya ban shirya yin aure ba" Ai bata jira me zece ba ta shige gida da gudu tana kuka, Yusuf ya dinga mamakin son da take masa. Kwana biyu Umma taga kwana biyu ba taga Salma ba, tacewa Yusuf   "kaga kwana biyu banga 'yata ba, ko zaka je anjima ka jimin ko lafiya?" Nan Yusuf ya warwarewa Umma komai, aikuwa ta sameshi ta inda ta shiga bata nan take fita ba,  "haba Yusuf, dan wulaƙanci yanzu duk sintiri da ɗawainiyar da yarinyar nan take damu, kace kai bakama san sonka take ba? Ni ina nan na saki baki zan samu Kayi Aure amma ka cemin kai bakama son sonka take ba? Idan ba sonka take ba ubanka take yi? Wani irin mutum ne kai Yusuf? Haba Yusuf haka rayuwa zata yi? Ba zakayi Aure ba haka zamuyi ta zama a cikin gidan nan, kamalar mutum ai aure, amma kai in anyi gabas seka yi yamma, duk abunda mutane ke gani daidai kai Ba haka yake a gurinka ba? Haka rayuwa zata tafi a haka? Wallahi in baka yi wasa ba haƙƙinta ze kama ka " Ganin ran Ummansa ya ɓaci, yasa ya shiga damuwa ya dinga bata haƙuri, tace idan yana son ta haƙura yaje ya rarrashi Salma sannan ya amince zw Aure ta, tunanin Farko daya fara zuwa zuciyarsa shine waye ze tsaya masa yayi Auren? Amma gudun ɓacin ranta yai shiru. Yaje gidansu Salma ya tarar bata da lafiya duk tayi wani iri saboda damuwa, Yusuf ya dinga rarrashinta, ya tabattar mata da ya amince da batun Auren, Salma ta dinga murna, take taji tama warke daga ciwon. Suka shiga soyayya shida Salma, shi dai tausayinta da yake ji yafi yawa, dan baze ce ga takamaimai feelings ɗin da yake dashi akan Salma ba, Sone da tausayi, ko kuma tausayin ne kawai. Nan aka shiga gulma a unguwa, wai Yusuf daga zuwansa yasa Salma ta kori kowa yana juyata yadda yaga dama, ya maida ita 'yar aikin babarsa, kullum cikin sintiri take  a gidansu, saboda Salma yasa ya fara kula yayyenta a hankali sukuma suke jansa cikin jama' ar unguwa dan seka zauna dashi zaka gane bashi da wani girman kai. Wataran suna sitting room ɗinsu Salma suna hira ita da Yusuf, ta sha ado se zabga ƙamshi take, suna ta taɗi ya miƙe ze tafi aka ɗauke wuta, aikuwa ta rungume shi tana kukan Shagwaɓa wai ita tsoron duhu take. Yusuf yace "Salma ki cikani, kar wani yazo ya ganmu, amana mummunar fassara" "Ni tsoro nakeji, tai maganar cikin Shagwaɓa tana sake kwanciya a jikinsa, ga wani ƙamshin turare da take yi, take jikin Yusuf ya fara tsuma, karo na farko daya rungumi mace a jikinsa, ya dinga jin wani irin yanayi yana bijiro masa, sheɗan na ƙoƙarin yi musu lalata, nan da nan yasa hannu ya raba Salma da jikinsa yai waje da saurin gaske. Ko daya koma gida, ya sauya kaya ya kwanta ya kasa manta abunda ya faru, gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idonsa, tunani iri iri, a nan ya ƙara yadda da tabbas ya kai munzalin da lallai yana buƙatar mace a tare da shi, sedai waye ze tsaya masa, tunda harkar Aure dole seda uba, ko wakilansa. Azumi ya gabato Yusuf yayi wa Salma siyayyar kayan Azumi, dana salla, Umma ba ruwanta da duk abunda ze siya ya kaiwa Salma, sema dai ta dinga yakamata ka ƙara kaza. Ya haɗa sha tara ta arziki ya kaiwa Salma, Salma ta dinga murna tana godiya, Yusuf yana kashe mata kuɗi sosai. Bayan kwana biyu mahaifinta yasa aka kira masa Yusuf, yace ya turo magabatansa ayi maganar Aure, tunda dai sun fuskanci juna, wahalar da yake ta isa haka. Sedai Yusuf ya koma gida cike da zullumi a zuciyarsa, waze turo? Wa yake dashi banda Allah da Ummansa? Bayan ya koma gida daya gayamata tayi murna, sedai itama kanta seda jikinta yayi sanyi, amma ta dake tace masa shikenan bakomai, Insha Allah za'a tura a tambayar masa, Yusuf be cikata da tambaya ba ya ƙyaleta. Umma ta shirya ta tafi gurin Yaya ɗan lami, ta gayamasa cewar dan Allah Yusuf ya samu yarinyar daze Aura ne, tana so ba dan ita ba su wuce masa gaba su tambayar masa Aure, Yaya ɗanlami yace mata ai ba matsala, bakomai dan dai wannan, zasuyi zasuje su tambayar masa Aure. Umma ta dawo gida tana ta murna tana farinciki, Yusuf ze Aure ze zama cikakken mutum shima kamar kowa. Wataran ya dawo da yamma, daga gurin harkar furnitures ɗinsa, yazo ya tarar da cincirindon mutane a ƙofar gidansu, se gabansa ya faɗi ya zaci wani abune ya samu Ummansa, dan haka a guje ya ƙarasa cikin gidan yana ture mutane, yaje ya tarar da ita a zaune tana kuka, ga kayan daya saiwa Salma na Azumi dana salla, a baje a gabanta wasu mata suna cewa "gayyar tsiya ashe bashi da uba, ya lallaɓo ze aurar mana 'ya, to Allah ya rufamana Asiri, seku koma gidan marasa iyaye inda aka ɗakkoshi, a ɗakko masa mata a can ba dai' yarmu ba, banda mutanen nan na kirki ne sunje sun gayamana, da haka zamu bawa mara uba 'ya, ai kema kin san bakiyiwa kanki adalci ba" Yusuf ransa ya ɓaci, dan yau an masa tozarci mafi muni, dama abunda yake ta gudu kenan Umma takasa ganewa, maimakon a dawo masa da kayansa salin alin, shine seda aka tara wannan gayyar mutane sannan za' aci zarafinsa haka, kuma ma dan baƙin ciki akazo akasa mahaifiyarsa a gaba da cin mutunci kuma aka cika gidan kamar wanda sukai sata ko maita, cikin tsananin ɓacin rai da juriya, Yusuf ya kalli Matan yace "mun muku laifi, Allah ya baku haƙuri, tunda kun gama abunda zakuyi, zaku iya fita" "Ai dole kace haka mana, tunda ka lallaɓo zakayi cuta, yarinya da samarinta na arziki amma zaka cuceta, yarinya 'yar dangi kyakkyawar gaske" "Wallahi idan kika kuma gayamin maganar banza sena wanka miki mari, get out from here" Yadda yayi maganar a fusace ne yasa jikinsu na rawa, sukayi waje dasu da gayyar mutanen da suka cika gidan, anata ƙananan maganganu, wai ashe duk girman kan nasa ma bashi da uba, yana taƙama da wannan kyan nasa yana hura hanci, ashe ma shegene. Yusuf be cewa Umma komai ba, ya tattare kayan yaje ya ajiye, ya wuce ɗakinsa ya kwanta, zuciyarsa na masa wani irin raɗaɗi mara misaltuwa. Umma tasan ba kowa ne yaje ya gaya musu wannan maganar ba face su ɗanlami, tayi danasanin zuwa ta samesu akan su wucewa Yusuf gaba akan harkar Aure, yanzu shikenan baza'a auri ɗanta ba saboda wannan dalilin? Dukda tarin nagarta dayake da ita. Tun daga ranar ko hanyar gidansu Salma ,Yusuf be ƙara biba, ba damar ya fita ko yazo wucewa se yaji ana yada masa da maganganu marasa daɗi, ya goge lambar Salma, da duk wani abu daya shafeta. Sedai hakan ya zame masa tamkar wani ciwo a ransa, Yana kewarta saboda sun shaƙu sosai. Wataran ya fito ze fita aiki ya ganta a ƙofar gidansu, ya ɗauke kai ze wuce amma ta sha gabansa tace "Gurinka nazo" Yusuf ya kalleta yace "meyafaru sauri nake" "Yusuf, ni kaina banji daɗin abunda akayi maka saboda ni ba, ban san haka abun yake ba, amma abun yafi ƙarfina ba yadda na iya, dan Allah kayi haƙuri, kuma ka bawa Umma haƙuri, ga katin ɗaurin Aurena nan, ina buƙatar addu'arka, kuma ina fatan ubangiji Allah ya baka wadda ta fini, komai da komai nagode da lokacin ka Yusuf " Ta zira masa katin ɗaurin Auren a gaban babur ɗinsa, ta juya tana share hawaye, shiba katin Aurenta nema ya dameshi ba, kukan da take ne ya bashi tausayi. Gaba ɗaya ya rufe babin Salma a rayuwarsa, ya koma rayuwarsa sedai mikin nan baze taɓa barin zuciyarsa ba. Yusuf yayi ajiyar zuciya sannan yace "ko wata biyu ba'ayi ba da abunda ya faru, aka bani aikin nan akanki, da farko nace ba zanyi ba, amma Abbas ya takurani, saboda wai ina da haƙuri, sedai ranar farko dana fara tozali dake, dukda isarki da izzarki, duk da jan aji da wulaƙancinki, se da naji zuciyata tayi bugun da bata taɓayin irinsa ba, ga kwarjininki yasa na kasa haɗa ido dake, ban shirya ba banyi tsammani ba na shiga kokawa da zuciyata akan Sonki da take, na nemi 'yar talakawa ma ban samu ba, saboda rashin asalina, ina ga ' ya kamarki, me Asali me dukiya gashi uwa uba naje a matsayin direba, se akanki na tabattar da Biyayya ce da shaƙuwa tasa na karɓi Salma a wancan lokacin, Amma wannan karon zuciyata ce da kanta ta zaɓi abunda take so, Widad bani da tabbas idan Dagaske Umma take na cewar, hatsari iyayena sukayi aka jefoni ta taga, nasan zata iya gayamin hakan dan hankalina ya kwanta, amma zance mafi yawa shine a gidan marayu aka ɗakkoni, Yanzu zaki yadda ki haɗa zuriya da mutum irina? Ki haihu dani alhalin bani da dangi se Allah se Ummana? Ni ba ina gudun haihuwa bane, nima ina fatan ganin jinina a duniya, amma kinji dalilina Auren nan kansa da mukayi a cikin zullumi nake Widad, ni dai nasan ina sonki amma bani da asalin da za'a nuna, nasan Ko Daddynki baze amince ba Widad, tuntuni nake zullumin gayamiki wannan labarin nawa, zaki zauna dani a haka?, ina sonki Widad, akanki na fara jin shauƙin soyayya, naji zan iya duk wata sadaukarwa saboda ke, dan Allah kar rashin iyayena yasa ki gujeni, ina sonki Widad ni kaina ina mamakin son da nake miki" Ya ƙarasa maganar yana kuka, shaɓe shaɓe da hawaye kamar mace, Widad ta ƙanƙameshi itama tana kukan, ta rungumeshi kamar jariri a ƙirjinta, ta dinga shafa sumar kansa tana "Am sorry Yoseef, am sorry kayi haƙuri please" Kamar ta ƙara tunzura Yusuf, kuka yake sosai harda sheshsheƙa, da alama abun yana cin zuciyarsa. Tana kuka take cewa "Yoseef dan Allah kayi haƙuri, ka dena kukan nan haka please" Ya girgiza mata kai yace "ki ƙyaleni inyi inji sassauci a zuciyata Widad, ban taɓa yiwa wani kukan rayuwar da nayi ko na tashi a ciki ba seke, i need a shoulder to cry on, ƙyaleni inyi matata" Widad ta rungumeshi tana kuka, tana tausayawa irin rayuwar da suka yi, dan daga ita har Yusuf kowa yaga rayuwa, kowa da irin ƙaddarar daya fuskanta a raguwarsa, amma na Yusuf ya ratsata sosai, ya bata tausayi matuƙa, ya wahala a rayuwarsa. "zan rayu da kai a duk ya kake, zan karɓi kowane ƙalubale daze taso saboda kai, ina son Aurena Yoseef, ina son zama da kai, ba ruwana da waye kai, nagartar ka da gaskiyar ka sun wadatar dani, stop crying my Husband, nima ai kana gani ba dangin ne dani ba, daga Allah se Babana, duk dangin babu, dan haka ina so mu zama ɗaya mu samar da family nida kai, ka dena kuka mijina " TAMMAT BI HAMDILLAH, NA KAMMALA KASHI NA BIYU ZAN SHIGA NA UKU, WANDA SHINE NA ƘARSHE DA YARDAR ALLAH LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 106_107 Yusuf ya sake ƙanƙame Widad yana cigaba da zubda hawaye. "Yoseef dan Allah Kadena kukan nan, zaka ɗagamin hankali, ya isa haka please kar kanka yayi ciwo kaji" "Hmm, my wife tsawon shekaru talatin da biyu, abu yana damuna a zuciya, ban samu nayi kuka yadda nake so ba, dan haka dan Allah ki barni inyi, kin ƙyaleni nika ɗai nasan what i go through, na shiga damuwa da baƙin ciki daban daban a rayuwata, i suppose to cry ko zan rage " "No Yoseef, kace Alhamdilillah daya barka da ranka da lafiyarka, kuma insha Allah daɗi yana tafe, dan bayan duk wata wuya se daɗi da yardar Allah, ka dena kuka kaji Ɗan uwana, we are now family ai ko?" Ajiyar zuciya ya dinga saukewa, yace  "Widad dagaske zaki cigaba da zama dani, koda mun koma gida?" Widad tace  "dagaske nake, Insha Allah mutu ka raba nida kai, kaine dai dai da rayuwata Yoseef, a yanzu kasanni fiye da yadda kowa ya sanni, ciki harda mahaifina, kasan abunda nake so kasan wanda bana so, you are such an amazing guy, kuma ni labarinka da naji, bazan iya rabuwa da kai ba, ƙaddarorinmu suna kamanceceniya da juna, dan haka zamanmu zeyi dai dai da yanayin rayuwar mu, zan zauna da kai Yoseef, ba ruwana da a inda aka samo ka ko makamancin haka, kuma insha Allah bazaka sake zubda hawaye saboda haka ba, ka dena kuka kaji Mijina " Tai maganar tana share masa hawaye, itakuma tana zubda hawayen, Yusuf ya ɗago kansa yana share mata hawayen fuskarta itama yace " Am sorry Baby, na saki kuka ko? Yi haƙuri yau nayi ragwanci a gaban matata, zata rainani" Ya ƙarasa maganar yana murmushin yaƙe, "kwanta muyi bacci, dare yayi kar gobe in Allah ya kaimu a barni da yunwa" Yai murmushi tare da kwanciya a jikin ta, tasa hannayenta ta zagaye bayansa dashi, tana shafa sumar kansa da hannunta ɗaya, Yusuf yana ta jan ajiyar zuciya, ta shiga ɗan duddukan bayansa alamar rarrashi. Wani irin kallo Hajiya Halima ta shiga yiwa mutumin, Mutumin yace "kina mamakin ganinane? Ai bekamata kiyi mamaki ba, butulu mara Alƙawari" Ramlah ce ta fito ita da Amal, Ramlah tace  "Mummy ya har yanzun baki tafi ba? What are you still doing their?" Suka ƙaraso inda take tsaye ita da mutumin nan, Amal ta buɗe baki tare da dafe ƙirji, Ramlah tace "Mummy wannan kuma wanene? Barar ce baza'a bari kifi ta ayimiki ba, se an biyoki har nan, mutane sun fiye zalama kamar zasuyi ƙwace dan azabar son kuɗi" Amal tace  "kai Ramlah, babanmu ne fa, baki gane shi bane?" Ramlah tace "What? Wannan ɗin kalle shi wani buguzun buguzun dashi kamar korarre" Hajiya Halima tace  "rufemin baki dan ubanki, Babanku ne" Ramlah tace "Taɓɗijan, God forbid in nuna wannan ince shine ubana, alhalin ina bearing da Sunan Nasir Daula, sannan wannan yazo yace wai shi ne babanmu, Allah ya kiyaye wallahi wannan ko riƙon jakata bazan ɗauke shi ba, ni ubana ya mutu da daɗewa, sedai babansu Anwar" Ta juya ta shige gidan tana ci gaba da maganganu, mutumin ya kalleta yace  "Halima haka mukayi dake? Saboda son zuciya irin naki haka kika mayar min da 'ya' ya, yarinyata ta kalleni tana gayamin wannan maganganun, dama haka mukayi dake?" Hajiya Halima tace  "kaga, dan Allah karka ɗagamin murya a gaban ma'aikatana, kazo mu shiga daga ciki ayi duk wacce za'ayi mana" Ya bita suka shiga cikin falo, Amal ta tafi gurin Ramlah ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta shiga, ta sameta tana zaune tana danna waya, Amal tace  "Ramlah bekamata kiyiwa mahaifinmu haka ba, ai duk lalacewarsa  shine ya haifemu" Ramlah tace  "wait, wai dan Allah dagaske wannan bagidajen shine mahaifinmu?" "Ramlah ki gyara maganarki fa, wallahi babanmu ne ya zaki manta fuskarsa, wallahi babanmu ne" "gaskiya sedai Babanku, kalli mutum a koɗe kamar baya cin Abinci, kalli suturar jikinsa yazo yace shi babanmu ne, gaskiya niba ubana bane, ai abun kunyane mu nuna wannan muce ubanmu ne, bayan duniya tasan da sunan Daula muke amfani, ai kawai babanmu ya mutu, amma wannan ai be kai mutum ba balle ace masa uba" Amal tace  "ikon Allah, wallahi Ramlah kina sane, babu yadda za'ayi kice kin manta kamanin mahaifinmu, dukda tunda muka bar gurinsa bamu kuma zuwa ba" Ramlah tace  "ke ina sane wallahi, na gane shi sarai, amma ni karan kaina kunya nakeji in kalle shi ince mahaifina ne, haba mutum a tsiyace kamar matafiyin da guzuri ya ƙare masa, kuma ya tsaya ze fara kora bayani a gaban wannan gidadawan, salon su raina mutane" Amal tace "lallai Ramlah, ke abun naki babbane ma" "Haba shu'aibu, ya zakazo a wannan lokacin da ake tsakiyar tarzoma da tashin hankali? Kazo babu aike bau Sanarwa haka akeyi, kuma ka tsaya kana neman ka tona min Asiri a gaban mutane, kai har yanzu bazaka waye ba?" Shu'aibu ya kalleta yace  "dama ina zan waye, mara mutunci dama haka mukayi dake? Nace haka mukayi dake? Akan yarjejeniya mukayi komai, amma da yake ke butulu ce, kinzo kin samu jin daɗi kin watsar dani, kinyi watsi da Yarjejeniyar da mukayi, shine nazo in miki tuni, ki cika Alƙawari sannan ki bani 'ya' yana" "wane 'ya' yan naka, malam karma ka ɗakko wannan maganar, dan ba zata yuwu ba, me ka sani na 'ya' yan naka, seda na gama wahalar? Lokacin mora yayi sannan kace in baka no, baze yuwu ba" Shu'aibu yace   "kin san Allah Halima, sekin bani 'ya' yana gaba ɗayansu bazan bar ko guda ba, kuma sekin cika Alƙawarin da mukayi daku" Tsaki tayi tace "bani account number ɗinka, zan baka dubu ɗari biyar, ka tafi ka bani guri dan Allah" "Ni zaki kalla ki bawa dubu ɗari biyar, ki riƙe kayarki amma ki saurari abunda ze biyo baya" "Kaga dan Allah karmuje ga haka, ka zauna muyi magana, Alƙawari da mukayi fa har yanzu wannan kuɗi basu samu ba, ya kake so inyi ne" Shu'aibu yace  "ƙarya kike, shakrar ki nawa a gidan nan, kima nufin duk zamanki a gidan nan baki samu komai ba, aiko duk jikina kunne ne bazan yadda ba Wallahi" "Wai kai baka san 'yarsa itace ta hana ruwa gudu ba,? dan Allah karka ɗagamin hankali ka bani account number, zan samaka million ɗaya" Shu' aibu yace  "ashema bani da hankali, kusan shekara goma sha, ko ficika bata shiga hannuna ba kice zaki ban million ɗaya, baki nemi sulhu ba tabbas, kuma abunda ze biyo baya baze miki daɗi ba na gaya miki" Hajiya Halima tace "kaga shua'aibu bazaka zo ka ɗagamin hankali ba Wallahi, yanzu ma daka zo a wani zullumin bala'in nake, ko dai ka haƙura da abunda zan baka kokuma ka haƙura, dan ban san ya kake so inyi ba, yarinyar daza'a karɓi dukiyar a hannuta ba'a san inda take ba, shi kansa me gidan ba'asan a inda yake ba, komai yana nema ya jagwalgwale min, kuma kazo kana gayamin maganar banza, dan Allah ka sauraramin" "Naji zan saurara miki, amma nima ki saurari abunda ze biyo baya, kin sanni kin sam abunda zan iya aikatawa, wallahi nima zan baki mamaki, zan ƙara miki matsala akan wadda kike ciki, sannan ki gayawa 'ya' yana ina nan zuwa in ɗauke abuna" "ka ɗauki wa? Can kaje ka nemi 'ya' yanka, karka ƙara ce mana 'ya' yanka, can ka nemi 'ya' yanka malam"  Ramlah da ta fito daga part ɗinta take faɗa. Shu'aibu yai murmushi yace "Allah sarki yaro yarone, Halima na fuskanci wannan yarinyar halina ta ɗakko, Rawar kanta da zafin kanta kamarni, amma ki gargaɗeta in ba haka ba, abunda ze biyo baya ke dasu baze muku daɗi ba Wallahi" Mummy tace "ke Ramalh, wannan fa mahaifinku ne, kidena gayamasa maganar da kika ga dama kinji ko?" "wallahi karki ƙara haɗani dashi, can ya nemi yaransa ba dai niba, uwar meya maganta  mana a rayuwar daze zo yana wani mu 'ya' yansa ne, dan Allah mu yayi ya wuce ya bamu guri, kidena ssaurarensa ki fita a samo mafita akan ɓatan Anwar, idan ba hakaba kika biyewa wannan koɗaɗɗen mutumin, komai ze iya faruwa, Anwar ze iya tona miki asiri idan wannan be tona miki ba" Zaro ido shu'aibu yayi yace  "Anwar ɗin ne ya ɓata? Halima dagaske ne abunda nakeji?" A fhaace tace "Eh gaske ne shu'aibu, duk akan a samu kuɗin nan, Anwar ya gudu ya bar gidan nan, se me ina nikaɗai naita ɗawainiya dasu ina ruwanka dasu, dan Allah ka barni inji da kaina" "zan barki kiji da kanki, zan tafi a yanzu bazan kuma dawowa ba se a lokacin daya dace, ko kuma in cigaba dayi miki aike, zan baki account number na, ina buƙata kuɗi naira million hamsin, nan da kwana bakwai idan baki turamin wallahi, wallahi abunda ze biyo baya baze miki daɗi ba" Ramlah tace "ai se kazo ka ƙwata ai, tunda kai ka tara mata" Aikuwa ya shammaci Ramlah ya wanketa da mari, jikinsa na rawa kamar wanda aka kaɗawa gangi yace  "da uwarki nake magana, ba dake ba ko ita lokacin da tana hannuna idan ina magana tana magana, tasan me yake biyo baya, idan kin manta dan lokacin kina ƙarama gara in tuna miki, Halima ki gargaɗeta ki gaya mata abunda zan iya, idan na kuma zuwa gidan nan, taimin tsinin baki sena yagalgalata a gurin nan, kuma nan ba gidana bane, zanzo in ɗauke ku, lokaci yayi da zan mori abunda na haifa nima" Ramlah ta zabura zata yi magana, amma Hajiya Halima ta dakatar da ita, ta hanata, shi kuma ya juya ya fice yana huci yana sauke numfashi. Tunda garin Allah ya waye, Widad take nan nan da Yusuf, se wani lallaɓashi take tana tarairayarsa, daya tashi da safe, idanunsa sunyi ja sosai sun ɗan kumbura, saboda kukan da yayi jiya, da ta kalli Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka, idan ta tuna labarin daya bata, da irin wahalar da ya sha shida mariƙiyarsa, sun sha wahalar rayuwa sosai. Ta ɗakko kunu, ta dinga ɗebowa tana bashi a baki, Yusuf yace "yau kuma nina koma jaririn? Se wani lallaɓani kike?" "ba dole in lallaɓaka ba, nima kana lallaɓani ai, ko baka sone?" Yace "ina so mana, ai gara kiyita lallaɓanin" Ta dinga bashi Abinci a baki, yana ci yana lumshe ido, dan dauriya kawai yake, har yanzu zuciyarsa babu daɗi, gaba ɗaya a cunkushe ransa yake, amma ya daure yana murmushi dan kar ya ɗaga mata hankali. Ta ɗago ido taga ya ƙura mata ido yana kallonta, ta miƙa masa kofin kunun bakinsa, kawai taga idonsa ya cika da ƙwalla, tasan dauriya yake kawai, amma ransa babu daɗi. Ta ajiye kofin tace  "Yoseef menene kuma?" Girgiza mata kai yayi, alamar bakomai, "da komai Yusuf menene ke kuma?" Kawai ya lumshe idonsa ya bawa hawayen daya taru a idonsa damar gangarowa, ɗaya bayan ɗaya suna zarya a fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya tallefe fuskarsa, hawaye na cigaba da bin fuskartasa. Itama hawayen ne ya shiga zubo mata, tasa hannu ta janye masa hannayen daya rufe fuskarsa, ta janyo kansa jikinta, tana son rarrashinsa amma tama rasa me zata ce masa, aikuwa ya kwanta sosai a jikinsa, yana kuka hadda sheshsheƙa, kai kace wani ɗan yaye ne. "Haba Yoseef, habe Yoseef is ok please, kana son wani ciwon ya kama min kaine? Idan ciwo ya shige ka ya zanyi, baka son kaga Lokacin da zamuyi building namu family ɗin, Allah yayi maka gata daya baka rai da lafiya Yusuf, Insha Allah zan share maka hawayen ka a rayuwa, bazan ƙara bari a maka gori ba, komai ya wuce ai, ya zama tarihi tunda ba shiri duk da kowanne mu ya fidda ran samun abokin rayuwa amma Allah ya haɗamu ya ƙaddara aurenmu, ba tare da mun shirya ba, tabbas ƙaddararmu tana kamanceceniya da juna, ni wallahi jinake dama ni na samu uwar riƙo kamar ummanka, Yoseef kana kallo ni ga gatan ga komai, amma inaji ina gani aka maidani mahaukaciyar ƙarfi da yaji, aka haɗani da larurar Ƙwaƙwalwa da zuciya, ga rashin kwanciyar hankali, ina so kamanta da wannan abun kamar be faru ba, kodai tunanin Salman kake ne? " Duk da kuka yake, seda ya ɗan murmusa sannan ya girgiza kai yace " inda ke babu macen da Yusuf ze tuna" "to ina son ya zamana in dani, babu damuwar da yuzaraef ze tuna" Yace "to Allah yasa hakan" "Ameen ya Allah, Amma ai yanzu zaka yadda mu koma gidanmu ko?" Yusuf ya girgiza kai, alamar a'a, Widad tace  "saboda me?" "Saboda ke nake so ba dukiyarki ba, ko abunda kika mallaka, dukiyarki ta kice mallakinki ce, dan haka zan sai mana gida daidai ƙarfina, in cigaba da aikina da sana'ata in riƙemu, ai zaki zauna dani da talaucina ko, duk abunda zan baki zaki karɓa ki zauna dani? " Yai maganar yana kallonta, tai murmushi tace  " na zauna da kai a ɗakin ƙasa, duk abunda ka banj na karɓa naci, kuma muke rayuwar mu a haka, ina ne zaka kaini bazan bika ba, amma gaskiya ni bana son aikin nan naka" "Saboda me?" ya tambaye ta Ta ɗanyi shiru sannan tace  "Yoseef, DSP Bashir shine Abbanka da aka kashe saboda case ɗin Ammina fa" Yusuf yace "na sani" Kallonsa tayi tace  "ya akayi ka sani"? Yusuf yace "tun lokacin ina miki aiki, na nake bincike akan statement ɗin kashe mahaifina da akace 'yan fashi sunyi, inata tunanin abun, kina bani labarin ki Nagano musababbin kisan Abba, kuma na gane dalilin da yasa da najewa Umma da batun aiki a gidanku, take cemin bata so, dukda bamu taɓa hirar da ita ba" Widad tace "Amma ya akayi baka gayamin ba?" Yai murmushi yace  "a gurinki na koya ai" "Yoseef Kayi haƙuri kaji, ka dena koke koken nan hak, kana karyamin zuciyata sosai, ka dena kuka kaji ɗan gidan Umma" Ya ɗan ja kumatunta yace  "tom insha Allah zan dena" "ka dena ko zaka dena"? "Nima ban sani ba, amma ina fatan Allah ha haɗani da wani, wanda yake yana da alaƙa da iyayena, ko 'yan uwana komai talaucinsa ina son in samu in ga wani daga dangina, koa yake is not possible, tunda babu wanda ya sanni a dangin nawa, kuma nima ba wanda na sani " Widad tace " bazaka dena kukan ba kenan? Ba gani ba,  ba nace maka zamu haɗa namu family ɗin ba, mu haifi yara ga Daddy, ga Umma gamu da 'ya' yan da zamu haifa, ba Family ya haɗu ba kenan?" Yusuf yace  " bazaki gane ba Baby, anyway nagode sosai da kulawarki, banjin wani bayan Ummana ya taɓa min rarrashin daya shigeni kamar wanda kikamin, ban taɓa zama nayi makamancin hirar nan da wani ba, duk alaƙata dashi kuwa, ko Umma bama wannan hirara da ita, balle wani saboda kar in ɗaga mata hankali, taga hawayena dan kar taga kamar ta gaza da kula dani ne, dan nasan tabbas idan na saɓamata Allah baze barni ba, ta shayar dani ta bani duk wata kulawa ta uwa da ɗa, kece kawai nayi wannan hirar dake, shiyasa I express all how I feel in my heart, kuma naji daɗin gayamikin da nayi, naji na rage kaso mafi yawa na damuwata thank you sweet heart" "Allah sarki mijina, kayi haƙuri kaji, tamu jarabatar kenan, amma ko abokinka Abbas baka taɓa yiwa zancen ba?" Yusuf ya girgiza kai yace  "A'a ban taɓa yi masa ba, amma me yasa kika tambaya?" Widad tace "saboda na tsane shi, gaba ɗaya siffar munafukai ce dashi haushi yake bani, shiyasa nasa aka rabaka dashi, aka maida shi nesa da gurin aikinka" "Amma Widad meyasa? Abokinane fa ya bani gudunmuwa sosai fa a harkar aiki da sauran mu'amalar rayuwa" Widad tace "Oho nidai na tsane shi, kuma wallahi idan ya kuma raɓarka sena ɗaureshi" Cikin mamaki ya kalleta yace  "but Baby why" "Z" ta bashi amsa tare da ƙura masa ido, alamar bata son zancen. "Yanzu za kamin Addu'ar in samu Babyn, kokuwa har yanzu baka son in haihu da kai" Ya girgiza kai yace  "Ai magana ta ƙare, tunda har kika amince dani dukda kinji labarina, Allah yabamu masu albarka Babyn Yoseef" Washe baki tayi tana murmushi, ta rasa mema zata yi dan murna, kawai ta rungume Yusuf ta haɗe bakinsa da nata tana kissing ɗinsa, Yusuf ya rungumeta shima yana kissing ɗinta suna murmushi, daga nan kuma aka shiga wani bigire daban ..... (Nikuma na fece 🚶 🚶 🚶) Bayan fitar shu'aibu Halima a fusace ta hau Ramlah da faɗa "Ramlah kinyi haukane? Koba komai mutumin nan mahaifin kune? Kin san hatsarin dayake dashi kuwa? Ko dan kuna ƙanana na bar gidansa baku san irin halayensa ba, shu'aibu da kike ganinsa bashi da imani, bashi da tausayi tsohon ɗan dabane gawurtacce makuwa kuma matsafi, idan kika zaƙe wallahi ze iya kauda ke, dan akan rigimar gonar gado har ɗanuwansa uwa ɗaya uba ɗaya ya kashe, dan haka ki kiyayi wannan tsinannen bakin naki, wanda besan yakamata ba kina zaƙewa dayawa, tynda kika ga ina binsa sannu sannu, nasan hatsarin dayake da shine, idan kinƙi ji bakyaƙi gani ba, idan kin gadama ki gyara idan bahaka ba, matakin daze ɗauka baze mana daɗi ba dagani harku" Ramlah tace  "wallahi, wallahi ba ruwana da hatsabibincinsa, tunda ya haifeni ze gane ya haifi uwarsa a hatsabibanci, harni ze ɗaga ƙazamin hannunsa duk faso ya mara? Zan nuna masa ya haifi 'yar da zata kawo ƙarshen hatsabibancin da yayi a rayuwarsa, besan wacece niba ze gani" "Ke rufemin baki, bana son cika baki kin san shi rashin jin da yayi" Ramlah tace  "shi ta shafa bani ba, but he must pay for what he did" Tai gaba fuuu tana ci gaba da masifa. Hajiya Halima ta girgiza kai tace  "Amal ɗakko mayafinki, kizo ki rakani gurin Alhaji Haruna, zan kira shi a waya yanzu, idan yana nan muje mu sameshi ayi maganin wannan matsalolin" Amal tace to, ta tafi ɗakko mayafi a ɗakin ta. Gidan Alhaji Haruna sukaje, aka musu iso part ɗinsa, yana zaune yana kallon labarai a tashar Al Jazeera. Suka samu guri suka zauna, tunda suka shigo yake bin Amal da kallo, kamar tsohon maye. Hajiya Halima tace  "gurinka nazo" Yace "yaukuma da wacce kikazo? Danke kullum cikin rigima kike" Hajiya Halima tace  "nikam duk a bar wannan maganar, yaron wajena daya ɓata ba sace shi akayi ba, guduwa yayi daga gida, kuma baun takaicin shine, ya gano abubuwan da nake aikatawa, dan hara takadda ya bari" Alhaji Haruna yace "Halima kina me haka ta faru? Garin yaya yasani, wannan yaron naki me kama da ustazai kin san ze iya tona mana asiri fa" Halima tace  "hmm wallahi ban san yadda akayi ya sani ba, shekara Goma ina ƙumbiya ƙumbiya muna wannan harƙallar tare, amma be sani ba, ban san wane munafikin ne ya gaya masa ba, kuma ma ba wannan ba ɗazu fa uban 'ya' yana yazo" Yace "Wake nan?" "Shu'aibu mana, koka manta bisa yarjejeniya da aka yi dashi ya sakeni, kuma tunda muka rabu, ba'a cika masa Alƙawarin ba, dan haka yazo yana barazanar karɓe yaransa, kuma wai sena tura masa wasu maƙudan kuɗaɗe koya tona mana Asiri" Alhaji Haruna yace "toki tura masa kuɗin mana, ko kin fi son asirin naki ya tonu?" Hajiya Halima tace  "wace irin maganace wannan, kafa san hatsarin da mutumin nan yake dashi fa" Alhaji Haruna yace "lallai akwai matsala gagaruma makuwa, amma yanzu abunda za'ayi ki saurareni, zamuyi magana dasu, yadda aka yanke zan miki magana" Hajiya Halima tace "to shikenan, amma dan Allah kuyi maganar da wuri" Yace  "shikenan, karki damu wannan ma yarinyar kice ne? Naga harta fi yayarta kyau" Hajiya Halima tace  "eh itace 'yar auta ta ai, daga Ramlah se ita" "Masha Allah, yaran naki masu kyau, sunfi kama da yayarta, Anwar ne ban san kamannin wa yayi ba" Hajiya Halima tace  "kamanin Ubansa yayi, wasu lokutan kuma dani yake kama" Alhaji Haruna yace  "A' a baya kama da shu'aibu sam, kamarsa daban shima" Hajiya Halima tace  "Amal jeki falo ki jirani kinji" Amal ta miƙe tana haɗe rai, saboda kallon da Alhaji Haruna yake mata. Tana fita Hajiya Halima tace  "Anwar fa ubansa daban shima, dana rabu da mijina na fari akwai cikinsa ko wata ɗaya beba na auri shu'aibu, na haifeshi a gidansa amma ba shine ubansa ba" Alhaji Haruna yace "ikon Allah, to waye nasa uban?" "kaga a bar maganar nan kawai, ba wanda na taɓa gayawa se kai duk yadda kukayi se muyi waya" Ta miƙe ta fito, ya biyo bayanta yana sake bin Amal da kallo, kamar wani maye. Saleh yayi 'yar siyayyar daya saba yi, ya shirya domin kaiwa su Widad ziyara, ya tafi tasha da nufin ya hau mota, da yake tafiyar dare yake yi in dai zeje garin dasu Widad suke, ya zuba kayansa a motar haya, ya zaga banɗakin tasha domin ya kama ruwa, yana fitowa yaji an shaƙa masa wani abu anyi sama dashi, daga nan be sake sanin inda kansa yake ba se...... LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" Ayimin subscribe please 🙏 🙏 🙏 11/17/21, 5:35 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 104_105 Saleh dai ne ce komai ba, yana jin yadda ake tafiya dashi a mota 'yan sanda, a galabaice yake dan haka be san inda suke tafiya ba, harabar police station akayi parking, aka fito da Saleh, yana tangaɗi haka aka tankaɗa shi cikin cell aka ƙulle. Duk da yamma ce amma sauro har ya fara shagali a gurin nan, ga zafi a gurin kamar oven, haka Saleh ya baje a ƙasa ƙirjinsa da cikinsa na masa ciwo kamar zasu tsage, saboda duk daya sha da katako. Yana jin wani ɗan sanda yayi sallama, sauram suka dinga sara masa, ɗaya daga 'yan sandan da suka ɗakko Saleh yace "Oga gashi nan a cell, munje mun ɗakko shi" Ɗan sandan yace  "ok shikenan, ku rubuta statement ɗinsa" "Yallaɓai tome zamu rubuta?" "Kai baka san me zaka rubuta ba, ku rubuta bayani akan an same shi da laifin haɗa kai da Yusuf, sun sace 'yar gidan Nasir Daula, sun ɓoye su, ka dai rubuta abunda yakamata" Ɗan sandan ya sara masa yace "ok sir, za' ayi yadda kace" "Yawwa that's very good, and a matsa shi yadda yakamata ya faɗi abunda ake nema a gurinsa" "Yes sir, za'ayi abunda kace" Yace "good" Daga nan ya wuce ya shige office ɗinsa. Hankalin Nurat ya tashi sosai, ganin cewar dagaske mahaifinta yake ze raba ta da ƙasar, itama tayi ɗamarar wannan karon zata bijire masa, kome ze faru se taga ƙwal uwar daka, se taga ƙarshen abunda mahaifinta yake yi, dan barin mutum irinsa suna cigaba da abunda suke so a doron ƙasa hatsari ne ga al'umma, wataran za'a iya wayar gari mutanen kirki su ƙare, ta ɗau wayarta ta kira Khalil, Khalil ya ɗaga yace  "Hello my dear, ya akayine any news?" Nurat tai ajiyar zuciya tace "bad news brother, Daddy ya dage akan cewar wai sena tafi imperial U. K Inyi karatau a can, me Daddy yake nufi dani ne?" "Calm down dear, make your statement clear please, kamar yaya imperial Collage, ke kaɗai zaki koma UK ɗin kiyi karatu, wanda kika yi a baya be isa ba" "Nima shi na gani brother, shifa yayi min alƙawarin zanyi school a Nigeria, a Nigeria zanyi high institution, Amma kawai yazomin da wannan maganar, da alama yana zargina ne da fara bin diddiginsa, ni kuma gaskiya i won't tolerate it dear, gaskiya zan bijire" Khalil yace "subhanallah, Nurat don't say that again, haba Nurat na sanki da biyayya da haƙuri, me zesa ki fara faɗar haka kuma? Haba Sister na" Kuka Nurat ta fashe dashi tace  "Broz Khalil, iya biyayya da haƙuri kasan nayi, nayiwa Daddy biyayya yadda yakamata, nayi ƙoƙarin kasancewa a cikin 'ya' ya nagari masu haƙuri, tun taso wata fa kullum cikin tsangwama da kyarar mahaifiyata yake, amma ban taɓa kulashi akan hakan ba, Brother babu ɗan daze dinga ganin mutuncin duk mutumin daze dinga cin zarafin mahaifiyarsa, komai kusanci da soyayyar dake tsakaninsu kuwa, amma na share na ɗauke kai, nake masa biyayya, ni da mahaifiyata mun masa biyayya, amma baya gani Khalil, baya gani kullum cikin zagi da cin zarafin mu yake, har gara ni yana ɗagamin ƙafa, akan mahaifiyata lokaci yayi da zan nuna masa nima 'yar halak ce, zan nuna masa ni ma' yace, wallahi bazan sake masa biyayya ba nagaji Khalil " Khalil yace " Calm down, calm down my dear, i feel your pain Baby, kiyi haƙuri dan Allah, nasan me kike ji a zuciyarki, amma dan Allah karki bijirewa mahaifinki, hakan ba halinki bane ba" "Yanzu na koya, kuma shine ya koyamin, kuma zega canji tabbas, na masa biyayya har akan abunda be dace ba, haka kake so in cigaba da binsa yana jan rayuwata data mahaifiyata a ƙasa?" Barrister Khalil yace  "kamar yaya ya saki abunda be dace ba?" Cikin kuka tace  "Khalil, Daddy da farko ni yasa in hilaci Widad, aka sumar da ita za'a sace ta, Yusuf ya ceceta, wani abunma baze faɗu ba ni kawai ka ƙyaleni, idan kuma ya dage sena bar ƙasar nan wallahi sena kawo masa ɗan shege ya raina a cikin gidansa na rantse da Allah " " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Nurat kin san me kike faɗa kuwa? Ko kin fara shaye2 ne ban sani ba" Ta ƙara sautin kukan ta tace "idan ma ban fara ba ina daf da farawa, dan wallahi ya takuramin zan bar masa gidansa in shiga duniya, ko in tafi England inyi irin rayuwar da yake ganin gara inyi irinta da ya kasa cinma nasa burin" Khalil ya kwantar da muryarsa yace "kina jina Nurat, am sorry kinji, nasan a irin matsala da damuwar da kike ciki, amma kin san zukata nawa ne zasu shiga garari idan kika lalace? Mummynki da kike wannan damuwar saboda ita, ya kike gank idan taga tilon 'yarta ta faɗa mummunar rayuwa? Ya kike tunanin shi masoyin naki ze kalle ki idan kika koma mutuniyar banza? Family duk zasu shiga damuwa idan suka ji labarin yarinyar da suke so, suke ji da ita ta shiga wata rayuwa daban, dan Allah kiyi haƙuri ki bar wannan maganar " " Brother idan na bar wannan maganar wacce zanyi? Am tired wallahi na gaji dayi masa biyayya, Khalil abun ba sauƙi fa, dama mutumin kirki ne da sauƙi" "Nasani Nurat, ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah zan shigo gidan naku, zanzo muyi magana amma ki dena kukan nan please, kuma karki sake faɗin wannan maganar kinji Light" gabata ne ya faɗi jin yace mata Light, sunan da Yusuf ke gayamata, ajiyar zuciya tayi tayi jifa da wayar, tana ci gaba da rushewa da kuka. A hankali hannun Amal yana warkewa, an kwance mata bandejin kanta ma, se hannun da haryanzu akayi hangin ɗinsa a wuyanta, yanzzhma ta fito daga wanka tana tsaye a gaban madubi, daga ita se towel kanta a tsefe, ta baje gashin kanta, ba laifi gashinta yana da tsawo, ga hannuta sagale a wuyanta, ga goshinta inda yayi tabon ciwon da Alhaji Haruna yaji mata, ta dinga ƙarewa kanta kallo a mudubi. A hankali tace "dubeni, mace har mace, bani da makusa sedai an gurguntamin rayuwa, an rabani da mutuncina saboda zalunci, kuma ya biyoni da wasu tarkacen banza saboda ya rainamin hankali, bayan tabo na sarari da yayi min, ya barmin na zuciya me matuƙar ɗaci da baze goge ba, me zanyiwa mutumin nan in huxe, wace irin illa zan masa daze dasa masa baƙin ciki a rayuwar sa ne? Me zanyi ne Amal kiyi tunani ƙwaƙwalwarki bata ja Sam " Ta dafe kanta ta fashe da kuka, tana tuna yadda ya suka dinga kokawa, da muguntar da yayi mata yacinma burinsa, zubewa tayi a gurin tana wani irin kuka, me tsuma zuciya " Duk laifinki ne Mummy, laifin kine, nace ba zani ba kika ce se naje, Mummy why? " Jikinta har rawa yake saboda kuka, dukda daga wanka ta fito amma ta haɗa gumi, ga hawaye ga majina se shesheƙa take. Ramlah ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune a ƙasa, idonta yai ja tana kuka. Ramlah ta ƙaraso da sauri tace " ke Amal lafiya kuwa? Meye haka? Meye ya same ki" "Bakomai" "bakomai kamar yaya? Kalle ki fa" Tsaki Amal Tayi tace  "excuse me please, dan Allah ki bani guri, ina son kaɗaicine" "wane irin kaɗaici kuma? Anya kina hayyacinki kuwa?" "Na miki kama da Widad ne, balle kice na haukace? Kawai ki fita ki bani guri" "Amma Amal" "Dan Allah ki fita ki ƙyaleni, kad in haɗiyi zuciya in mutu, dan Allah ki fita!" Tai maganar cikin kuka, Ramlah na fita taje ta dstse ƙofarta ta kwanta akan gadonta ta cigaba da rera kukanta, tana jin Ramlah ta kira Mummy, suka dinga buga ƙofar amma tayi musu banza kamar ba taji ba. Bukar ya kira Alhaji Haruna, Ya ɗaga wayar suka gaisa, Bukar yace "kunyi waya da Musa ne?" Alhaji Haruna yace "A'a gaskiya, na kwana biyu bamuyi waya ba" Alhaji Bukar yace "ok, na zaci kunyi wayane, haryanzu be ce mana komai ba akan batun wanda ze saka mana hannun, kuma yace mu saurareshi zuwa Laraba, anjima zamuyi meeting kota zoom ne, sannan ya batun takaddar da aka ce wannan yaron ya bari? Ka karɓo mana ɗinne kokuwa?" Alhaji Haruna yace  "eh na karɓo, naje har gidan da kaina naje na karɓo takaddar" Alhaji Bukar yace  "good, kasan duk wata sheda da zesa a ganemu, dole mu ɓatar da ita kar wani ya samu, dan haka ka kawomin takaddar nan" Yace "shikenan, Insha Allah zan kawo maka ita, sannan zan sanar dasu batun meeting ɗin nan da kace" Alhaji Bukar yace  "to shikenan, se kazo" Alhaji Bukar ya ajiye wayar, ya miƙe ya bar ɗakin dayake, dan ya manta da ya karɓi tajaddar yazo da ita nan gidan ko kuma a can ya barta gurin da ta bashi?. Hindu tana tsakar gida, suna ta aiki a tsakar gida, Hanne tana gefe tana gyaran wake zasuyi alala. Hari tace  "sannu da aiki Hanne, Allah ya kaimu bikinki mu kira masu kiɗan ƙwarya muyi ta juyi a gidan nan" Hanne ta taɓe baki, dan ita sama gaba ɗaya haushin Auren nan ma take ji, dan Yanzu haushin mijin da zata aura takeji, dan gani take bashi da komai idan ta kalli Yusuf, ita dai tana son Yusuf sosai, tana jin ina ma ya aure ta, da tafi kowacce mace dace a ƙauyen nan, da yana ɗan kulata amma yanzu ya dena, saboda wannan koɗaɗɗiyar matar tasa me kama da Yahudawa. Hindu tace  "Allah dai ya kaimu bikin nan ds rai da lafiya, ban san wane irin shagali zanyi ba, nima sena gyagije nayi shagali, idan kika tattara kika tafi in gaje gurin kwanciyar ki da nawa, Abinci ma zan haɗe nawa da naki ne, dama yanzu ba ƙoshi nake ba" Hindu Tayi maganar cikin sigar wasa da zolaya. Amma Hanne ta karkace ta kyaɓe baki, ta kalli Hindu tace  "aifa dama ina zaki ƙoshi tunda mayya na gidan? Ai gara in tattara in bar miki gidan ki cigaba da haɗa kafaɗunki dana iyayen mu, tunda dai ke kinfi kowa baƙin jini, babu wanda yake sonki balle kisa ran zakiyi aure ki bar gidan nan, ai se kiyi ta zaman gidan ki ƙare ki tsufa a gida, mujiyar garin nan, shikenan mutum ba zuciya balle ya samo wanda ze rufa masa Asiri ". Ai tuni idon Hindu ya ciko da hawaye, ita har ga Allah wasa tayi wa Hanne, amma harta fara yan kamata baƙaƙen maganganu da cin zarafi, Hanne na ɗagowa suka yi ido huɗu da Yusuf, da alama duk yaji abunda ta faɗa, sekuma ta shiga kame kame, dan wata irin kunyace ta kamata, bece komai ba ya sa kai ya fice, dan be fiye son shiga sabgar iyalan gidan ba. Yana fita Widad ta fito tsakar gidan nan, taga yadda Hindu ta nutsu tayi shiru, ido duk ya tara hawaye saboda zafin maganganun Hanne. Widad tace "ke Hindu, wai ita wannan banzar 'yar uwar taƙi haifarki tayi? Haifarki Tayi da zata dinga gaya miki magana kina jinta? Wai wane ɗan matsiyatan zata aura a garin nan da har take miki wannan gorin haka? Wanda zata aura ɗin ma ya kai a kira shi namiji da take miki gori a kansa "? Hanne tana hura hanci, cike da ƙauyanci da jahilci tace " Wallahi, tallahi nafi ƙarfin auren matsiyaci, niba matsiyaci zan aura ba" "wallahi kika bari nazo inda kike, na shaƙeki se na jefa ki a rijiyar nan, saboda me zaki takurawa yarinya dan bata magana, dan kinga tana da haƙuri, wallahi ki kiyayeni akan ɓata mata rai" Hanne tace "idan anƙi fa?" Wata irin zuciya ce ta kwashi Widad, sedai Hindu tai saurin riƙeta tace  "A'a Amarya yi haƙuri ƙyaleta kawai" Widad ta harzuƙa matuƙar gaske, ji take tamkar ta jefa Hanne a rijiya, mussman idan ta tuna yadda take juya manyan attajirai masu ji da kansu, amma wata kucakar 'yar ƙauye na gayamata magana, ƙwafa kawai tayi tace  "ba alfahari ba amma Wallahi da kin san wacece Widad, da baki isa ki yadda in haɗa ido dake ba, dan wallahi ko masu gyaran gadon baccina sun fiki kyan gani, ki zuba ido zakiga mijin da Hindu zata aura, Jahila kawai" Ta wuce ɗakinta tana huci, duk wannan budurin Gwaggo da Hari basa nan akayi shi, amma abun yana damun Widad taji an taɓa Hindu, setaji kamar ita aka taɓa, danma ita Hindun ce shashasha take tsayawa ana mata wulaƙanci. Amal kam wani tunani tayi a ranta, dan haka ta miƙe da ɗan sauri, ta fita falo, Mummy ta kalleta tace "kinga damar buɗewa yanzu?" Amal tace  "Mummy Ramlah ta kasa fahimta tane, wani lokacin idan ina cikin jin zafin ciwo, bana son kowa a inda nake, nafison kaɗaici amma se a takuramin, kun kasa ganewa" Mummy tace "madalla, shine nake ta magana kika ƙi buɗewa" "Am sorry, bazan sake ba insha Allah" "Hmm ai shikenan, ya hannun naki yanzu?" Tace "da sauƙi, Mummy dan Allah aramin wayarki zan transfer ɗin kuɗi, ni banki sun hanani wai ba network" Ba musu ta miƙawa Amal wayar, Amal ta karɓa ta koma gefe, ta tura lambar Alhaji Haruna wayarta, ta bata wayar tace "Mummy, ga wayar nagode" Ta koam ɗakinta, tana zuwa ta kulle ƙofa ta zauna akam gadonta ta kira Alhaji Haruna. Lokacin yana tsaka da bulayin neman takadda, ya ɗaga suka gaisa dashi, sannan tace  "Naga saƙonka, amma meyasa kwana biyu ba kazo ka dubani ba" Se ynzu ya ɗau muryar ta, yai murmushi yace  "nima naji saƙonki, ance bayan mota zakizo karɓar gids ma" Tace "eh hakane, ko idan na dawo bazan samu ba" . Yace "idan kika dawo ina?" "zuciya ta, ta fara rayamin kawai idan na warke zan bazama in nemi arziki, in more ƙuruciya ta, idan ka shirya nima a shirye naake zan dawo gareka, tunda aikim gama ya gama tunda fari" Yai wata shegiyar dariya sannan yace "ni zaki yaudara, ko har kin manta abunda kika gayamin a Asibiti, kaina yana ja sosai dan haka abune mawuyaci kiyi galaba a kaina, tabbas naji daɗin kasancewa dake sedai bazan sake amincewa dake ba, tunda kikayi wannan fueucin, ki sake shawara kinji 'yan mata, idan da gaske kike ki bazama ki kama wasu alhazan, nikam na gama muma na biya tunda na bada motar miliyoyi" Bata sanma yadda akayi ta ajiye wayar ba, tana jera ajiyar zuciya kamar wadda tai gudu, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunaninta, ashema matan suna suka tara, ba kowaccece ke iya kaidin ba, shi kansa shirya makircin ba abune me sauƙi ba, tai sharkaf da gumi tana sake tunanin wata hanyar. Yusuf na dawowa Widad ta manta da damuwar da take ciki, sedai duk da hakan seda ya gane, yace "Maman Baby, ya akayi ne naga kamar ranki a ɗan ɓace yake" Tace "A'a ni ba abunda akayi min, Ina ɗan tunani akan Hindu ne, ina ma Megari ze bani ita idan mun koma gida" Yusuf yace "gaskiya abune me wahala, ya ɗau 'ya ya bamu alhalin bamu da wata dangantaka a tsakaninmu" Ta jinjina kai tace "hakane, Gaskiya nifa na damu Saleh yazo ayi wacce za' ayi, na fara gajiya hankalina yayi gida sosai fa" Yusuf yace "ki kwantar da hankalinki, nima shi nake jira yazo, muji abunda yakamata ayi" Tace "shikenan, Allah ya kawo shi" Yace  "Ameen" A gurin 'yan sandan ma babu sassauci, baƙar wahala Saleh yake sha, dan yana kyautata zaton an masa illa saboda duka, dan a nan ɗinma' yan sanda ke sa kulki, suyi ta dukansa izaya daban daban wai lallai seya faɗi inda su Yusuf suke, ga rashin Abinci gashi ko Najasa ne sedai yayi a nan, nan da nan Saleh ya fita daga hayyacinsa, ya canza kamanni fuska duk ta kumbura, ko ina rauni me yake zubda jini, sun doddoke masa ƙafafuwa da ƙyar yake iya miƙewa. Da Safe Yusuf yana kwance akan cinyar Widad, ta samu comb se jagwalgwala masa sumar kansa take yi, shi kuma yana lumshe ido, can yace  "gaskiya ki ƙyalemin gashina mana, haba se izaya kikemin a kaina" Ta ɗan tura baki tace  "kitso fa zan koya" "To aini na gaji se jagwalgwala min suma ake, ga zafi banda ma tsabar rigima irin taki ta ina za'a kitsa sumata?" "Ni dai ka ƙyaleni" Yace "shikenan, Allah sarki ni, gaskiya idan na kuma jin zafi sena rama, sena aske wannan gashin naki da akewa mutane iyayi dashi" Tai murmushi tace "daka temakeni, dan ba dan babu kyau ba sena rage shi, kuma idan ka aske ai kanka kayiwa, kaine kake wasa dashi ai" Yai murmushi yace "kuma fa hakane, to na fasa askewar" "A'a gara dai ka aske ɗin" Hindu Tayi sallama kawo musu Abincin Safe, akayi mata izinin shiga tana shiga ta tarar da Yusuf kwance akan cinyar Widad. Ta sunkuyar da kai cikin matuƙar jin kunya, Widad tace  "sarkin kunya, idan na aura miki ɗan birnin haka zaki dingayi masa?" Hindu ta juya da sauri tana murmushi, ta bar ɗakin, Widad tace  "Yuzarsef, wallahi da ina da Yaya, ko wani ɗan uwa da babu abunda ze hana in roƙi ya auri Hindu, she's very kind and innocent" Yusuf yace "hakane tana da kirki kam, ga nutsuwa" Yusuf yaga abun na Widad ba na ƙarewa bane, dan haka ya tashi daga cinyarta yace  "ke nagaji, kaina se zafi yake duk kin jagwalgwala min suma" "ni kayiwa haka ko? In ƙara ganin ka taɓamin gashi ni da kaine, kuma ma insha Allah ta mace zan haifa, saboda in dinga mata kitso ta zama ƙawata kuma" Yusuf yace "sannu sarkin shirirta, da shirme, ga tsabar ƙuruciya mutum baze gane hakan ba, se ya zauna dake, to ni bame yiwa 'yata kitso balle a jagwalgwala mata kai, idan kin haifi namiji nakine, mace kuma ta wace" "A' a ban yadda ba, gaba ɗaya nawane, bayan kace baka son Baby" Yusuf yace "Nina ce miki bana so? So kai amma ki bari ki samu cikin tukuna, sekimin iyayi da tsari" "wai dan Allah dagaske bani da ciki?" Yace "zan miki ƙarya ne? Kin manta shekarata biyu ina medicine, baki da komai madam" Ta kwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "insha Allah ina da shi" "Seki zauna kiyi ta imagination ai, miƙomin abincin nan inci" Ta ɗakko kwananon Abinci ta miƙo masa, suka ci tare suna hira. Yusuf yace "idan na dawo da daddare, kwaɗon gurji da zogale zan mana, zaki ci?" Widad tace "Sosai ma, ranar Gwaggo tayi naci da daɗi Sosai" Yusuf murmushi yace "to kwaɗayayyiya" "Eh anji ɗin" A haka suka yi sallama, yana ta tsokanarta, kamar karsu rabu. Duk iya dubawar da Saleh zeyi, yayi amma ya rasa takaddar nan, ya duba ya duba amma takadda tace ɗaukeni inda ka'a ajiyeni, gashi yacewa Bukar ya karɓo takaddar nan. Ya koma guest House ɗinsa, inda suka dinga kokawa da Amal, ya dinga duba takaddar nan, yai tsai gana dubawa ya birkita komai, ya hango ta a ƙasan gado. Hamdala yayi, ya durƙusa ya ɗakko takaddar, yana ajiyar zuciya ya buɗe takaddar, sedai me ba takaddar bace form ne na koyon kwalliya na Amal, tsaki yayi yai jifa da takaddar yana tunanin ina yasa waccan takadda data bashi, amma kuma lokacin da ta bashi takaddar ai be buɗa ba, balle yasan me ta bashi, hankalinsa na kan yai mata akuyanci kawai, ya birkita ko ina amma babu wata takaddar se wannan, nan take gumi ya shiga tsasttsafo masa. Widad taita jiran Yusuf ya dawo, dan se nishaɗi take ji ze kawo gurji yayi musu kwaɗo, bayan ya dawo da kayan gurjin da yamma, ta zauna ta cire ɓawon tsaf, ta gyara zogalen suka ɗora zogalen akan wuta, suna zaune suna hira a ƙofar ɗakinsu suna aikin su, hankali kwance yayin da zamantakewarsu kan burge wasu daga mutanen gidan. Ya gama suka haɗa Kwaɗon nan a roba, Suka bawa wanda zasu bawa, Widad se haɗiyar yawu take, ta zauna zata saka hannu ta fara ci Yusuf yace "tsaya waye yace ki fara ci, salon ki fini loma ki fini ci ko?" Ai ba ta saurareshi ba, danji take kamar hanjinta ze fito idan bata ci ba, jiki na rawa ta sa hannu ta fara cin Abunta, Yusuf yana kallonta yana nazarinta, tunda ta fara ci bata saurareshi ba seda taji ta ƙoshi tukuna, ta miƙe taje ta wanke hannunta ta sha ruwa ta dawo ɗaki sannan tace  " Yawwa ina jinka, mema kace ɗazu?" Yace "cewa nayi, sannu da aiki acici" "Yawwa mijin acici, kai dai ubangiji Allah yayi maka albarka, ya saka maka da alheri nagode sosai" Yace "Ameen, amma a dena cinye Abinci ana barina" Kawai ta kwashe da dariya tace  "ba ruwana cin abuna zanyi ehe" Yace "ai shikenan poor me" Tace "shagwaɓaɓe kawai, me sexy eyes" Yace "what, sexy eyes kuma sekace wani mace" "baka sani ba, you are having sexy eyes fa" "Mhmm Malam kawai kice abunda yake ranki kenan" Tace "What? Wai Yoseef meye haka? Kawai ba damar inyi magana seka canza mata ma'ana" Tai maganar tana kai masa duka, ya kwanta yana dariya yasa pillow yana karewa. "Kuma ma kai mummuna ne" tace tana harararsa. "Eh naji bakomai, a haka 'yan mata suke rububina, saboda munina a haka suke sona" Widad tace "Wallahi idan muka koma gida,  duk wadda tayi gangancin raɓarka zata ga matakin da zan ɗauka wallahi" Tai maganar very serious, dan kamar ma haushi taji. Yace  "haka akeyi, shikenan duk suna kallo se kice baza'a kulani ba, bayan kin sanni da farinjini, cewa fa kika yi in Auri Hanne" Tsaki tayi zata tashi, ya fizgota jikinsa, yasa fitila ya haske mata fuska. "Ni ka dena haskani, bana so" Yusuf yai ƙasa da murya yace "An taɓa gayamiki ke kyakkyawa ce kuwa My wife?" "Ai ko ba'a faɗa ba, nasan ni me kyauce sakeni" "in sake ki kuma?" Da sauri tace "No, i don't mean you should divorce me, ka cikani i mean" Yai murmushi yace "nima na sani ai, ni dake ai mutu ka raba Babayna me kama da teddy" Tace "Yoseef me yake damunka ne yau? Duk ka takuramin nice kuma me kama da teddy?" "Eh ramawa nayi, ko kin manta haka kika cemin cartoon jiya" Yai maganar yana dariya, itama dariyar ce ta kamata, ta buɗe baki kamar zata cije shi, amma ta fara kissing ɗinsa. Kamar ranar suka fara kasancewa da juna, sunyi nishaɗi mara misaltuwa, sun farantawa junansu rai sosai, kowanne yana sake jin ɗan uwansa a ransa. Haka suka wayi gari cikin farin ciki, sedai dukda wannan farincikin Yusuf se fama yake da fargaba, ya rasa dalilin hakan. Yana ta shiri ze fita, yaji kamar harbin bindiga, gabansa ya faɗi yace  "Lovely, kamar harbi fa nake ji" Widad tace "A'a ko dai tunanin gurin aiki kake, amma wane irin harbin bindiga ana zaune ƙalau? Bari inyi walha, idan na idar seka tafi" Ta juya ta tada salla, tayi raka'ar farko zata yi ta biyu suka ji Hayaniya, aka sake harba bindiga a ƙofar gidan mutane nata guje guje. Yusuf yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un" Daga tsakar gida suka ji ana "duk wanda ya motsa, zamu fasa kansa da bindiga, kowa ya tsaya a inda yake" Gaba ɗaya jikinsu se tsuma yake, Hari ta samu wani lungu a bayan randa ta shige, se zare ido take saboda tsoro. Nan da nan sega jiniyar motar' yan sanda ta ƙaraso Da gudu Widad ta fito tsakar gidan, amma taga 'yan sanda tare da Saleh hannunsa duk ankwa a cikin mawuyacin hali. Tace "me zan gani haka? Meye haka?" Wani ɗan sanda yace "Yusuf, ina Yusuf yake?" Widad tace "ban sani ba, bazan faɗi inda yaken ba" Hari daga inda ta laɓe tace "Wudas ki dena magana karsu kashe ki fa" "Ina Yusuf yake!" a kai mata magana cikin tsawa. Itama cikin tsawar tace "ban sani ba nace" Yusuf ya fito daga ɗakinsu, jikinsa sanye da jallabiya, ya ƙarasa gabansu ya miƙa musu hannunsa cikin surrender . Widad ta fashe da kuka tace  "No! This is impossible, me yayi muku? Laifin me yayi mijinane fa, ku cire masa wannan cuff ɗin" Su kai mata banza suka tasa ƙeyar Yusuf, itama suka sata  a gaba ihu take tana kururuwa akan su sake shi amma sukayi burus da ita. Aka sashi a bayan motar 'yan sanda, idonsa yayi ja ya kasa magana, se kallonta da yake gaba ɗaya ta birkice se ihu take tana kuka, muryarta harta fara dashewa. "Ina sonka, Yusuf ina sonka, I love you Yusuf, dan Allah ku sakarmin mijina, beyi laifi ba, beyi laifin komai ba" Yusuf ya ƙura mata ido, ya lumshe idonsa a hankali, yayin da Widad ke zubda wani irin hawaye tana kuka, me sauti. Aka sakata a motar gida seinna, shikuma a bayan motar 'yan sanda gashi ga Saleh, kowanne hannu da sarƙa!!! (Rayuwa ƙaddarace kowa da irin tasa......... 🎶 ) LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 11/17/21, 5:35 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 106_107 Sosai Widad ta cigaba da gunjin kuka, yayin da mutanen ƙauyen suka fito suka yi duru duru suna kallo, ɗaliban Widad se kuka suke, haka Hindu gaba ɗaya ta birkice banda kuka ba abunda take yi, ba Hindu ba kawai hatta Megari, da su Hari hankalinsu ya tashi sosai, ga Sunusi mijin Jamila baya nan akazo aka kama su Widad. Ana tafe a hanya amma bakin Widad yaƙi mutuwa, kuka kawai take akan a sakar mata mijin ta, tun Yusuf yana iya juyo muryarta da kukanta, har muryar tata ta dashe ba ajin me take faɗa sosai, haka sukaita tafiya har suka fito daga wannan kwazazzaban, da ramukan dake hanyar garin, suka hau kan kwalta ɗoɗar suka kama hanyar Kano. Alhaji Haruna fa ya haɗa uban gumi, saboda ya tabattar da babu wannan takadda, takaddar form ɗin koyon kwalliya ta bashi, ba shiri ya ɗau wayarsa ya kirata da lambar da ta kirashi ɗazu, tana ganin kiran nasa Amal ta tashi da sauri, ta duba har zata ɗaga kawai ta fasa, ta ajiye wayar yai mata kira yafi Ashirin, ƙarshema ta saka wayar a silent tai kwanciyarta. Yai wujiga wujiga, saboda takaddar nan saboda yasan Bukar ba kyau, gashi ya riga yace aiya karɓo, tunda takaddar zata iya zama sheda a kansu, wannan wasiƙar zata nuna akwai halin rashin gaskiya da mahaifiyar Anwar take aikatawa wanda yasa ya bar gida, idan tuhuma tayi tuhuma kuma za'a gano su. Ya tura mata saƙo kusan kala shida amma babu reply, can dai ta ɗau wayar ta duba saƙon daya turo, magiya yake mata akan dan Allah ta ɗaga wayarsa, mahimmiyar magana yake son suyi. Tana cikin karantawa kuwa ya kuma kira, seda taja aji sannan ta ɗaga, yai ajiyar zuciya yace  "habba kyakkyawa, tun ɗazu naake kiran waya, amma anyi biris dani?" Tace "to me kake so in maka? Ko in ɗaga in ce maka?" "A'a kwantar da hankalinki, ai duk abun bana zafi bame ko ɗaga hankali, magana zamuyi" Tace "ina jinka" Yace "Yawwa, dama cewa nayi wannan takaddar da kika kawomin, kinyi mistake ba wasiƙar kika bani ba, form ɗinki ne na koyon kwalliya, kinyi mistake gurin bani" Tace "se akayi yaya?" "A'a dama ba wani abu bane ba, cewa nai zanzo in karɓa in an jima, saboda takaddar tana da mahimmanci sosai" "Karka sake ka soma zuwa inda nake, bazan bayarba ka riƙe wadda na baka a matsayin ta" Alhaji Haruna yai gyaran murya yace "haba beautiful Baby, ai abun duk bekamata ya kaimu ga haka ba, meye na ɗaukar zafi haka? Ai abun bana zafi bane ba, ki gayamin me kike so ayi yanzu in karɓi takaddar nan? Ko nawane zan baki" Amal ta janyo Jakarta, wadda yace tayi accident da ita, ta duba amma itama taga babu takaddar a ciki, amma tai ajiyar zuciya tace  "nima nazo maka da buƙata ta, amma kaƙi amincewa, dan haka kowa ha riƙe buƙatarsa, bazan bayarba gara asirin kowa ma ya tonu a huta" Yace "Subhanallah, hadda mamanki fa"   Tace "har ita ɗin" Yace "dan Allah kar muyi haka dake, ki bani takaddar nan na riga na cewa Bukar na karɓo takardar yace in kai masa, kuma yanzu inzo ince bahaka ba, baze sauraramin ba" Amal tace "Ai gara karya saurara makan, kamar yadda nima baka sauraramin ba, kuma baka karɓi buƙata ta ba" Yace "dakata, yanzu idan na karɓi buƙatar taki shikenan?" Am tace "A'a ai kuma mun wuce wannan maganar yanzu, zan baka takadda bisa sharuɗa, yanzu abu na farko zan gaya maka Account Number ɗina, ina son inji wasu kuɗi masu nauyi, domin inci kaji in warke da wuri daga raunin daka min" "Shikenan zan turomiki, yaushe zanzo in karɓa"? Tace "turo ɗin tukuna in gani mana" Yace "shikenan naji" Ta kashe wayarta, lumshe ido tare da faɗin "Alhamdilillah, cikin sauƙi Allah ya kawomin hanyar da zan rama cin zarafin da kayi min, tabbas inaga yadda takkadar nan nayi, dan babu ita a jakata, amma a haka zan maka rashin mutunci in rama" Alert ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta duba 500k ne, ta jinjina kai tace yanzu aka fara wasan Seda yayi mata kira biyar, sannan ta ɗaga a fusace tace "wai meye ne?" "dama cewa zanyi, kinga alert ɗin?" Tace "na gani, amma sunmin kaɗan, na kuma raina" Ta katse kiran tare da kashe wayarta gaba ɗaya, ta kulle ɗakinta da key, tai kwanciyarta. Tunda suka taho Yusuf bece uffan ba, yai shiru yana saƙawa yana kwancewa a zuciyarsa, tabbas duk sunan da za'a kira shi dashi, ko a tuhume shi dashi, bashi da abunda ze kare kansa dashi, tabbas shi dai tunda ya tashi a rayuwarsa a siraɗin ƙaddara yake, daga wannan ya faɗa waccan, daga waccan ya faɗo wannan, haka ya sunkuyar da kansa yana ta tsabihi ga Allah, akan ya sauƙaƙa masa wannan lamarin. Sun shigowa cikin garin kano, akayi hanyar babbar headquarter hukumar 'yan sanda dake garin kano, motarsu Widad kuma tayi wani gurin, ai tana ganin haka ta kuma fashewa da ihu, tana bori tana kuka tana   "ina zaku kaishi? Ina zaku kaimin mijina? Beyi laifin komai ba, babu abunda yayi muku, ku ƙyalemin mijina wayyo Allah na Yoseef duk nice sila, saboda ni ka shiga wannan tashin hankalin, Dan Allah ka yafemin Yoseef, Allah ka fitar da mijina daga sharrin Azzaluman nan, Allah ga bawanka ka fitarmin da mijina" Ta ƙarasa maganar, tana wani irin kuka me taɓa zuciya babu wanda ya kula ta a cikin 'yan sandan suka cigaba da tafiya. Wani ofishin' yan sandan aka tafi da ita, suka fito da ita daga mota zuwa gurin 'yan sanda, idanunta sun kumbura sunyi ja saboda kuka. Wani ɗan sanda yace  "gata yallaɓai, yanzu muka shigo gari, shi an wuce dashi headquarter, ita kuma gata" Ɗan sandan ya kalleta yace  "Good, Madam congratulations, you are now free, mun cetoki daga hannun wanda sukayi garkuwa dake" "Niba garkuwa yayi dani ba, wanda sukayi garkuwa dani daban, Yoseef ceto na yayi, shine ya temakeni beyi garkuwa dani ba, ka gaya musu suje su sakarmin mijina" Ɗan sandan yace "koma dai ya akayi, wannan ku ta shafa ke dashi, muba abunda ya dame mu, zamu rubuta sannan mu sanar da duniya cewar, munyi namijin ƙoƙari gurin bincike mun gano wanda yayi garkuwa da Widad Nasir Daula, kuma ba wani bane face direbanta, wanda ya kasance ɗansanda, yaje gidansu yai basaja dan yayi garkuwa da ita, nasan hakan ze sake ɗaga darajar rundunar mu a ga namijin ƙoƙarin da muke, ba dare ba rana gurin kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma " " Shut up!!! " Ta faɗa cikin ƙaraji, tace " idan har ina raye ina numfashi, ko komai nawa ze ƙare se Yusuf ya fita, babu wanda ze cutarmin dashi, baku isa ba azzalumai ma cuta, lokacin da aka yi garkuwa damu muna buƙatar taimakk, babu wanda ya taimakemu na kusa rasa rayuwa ta, se yanzu da yayi komai ya gama, Allah yasa ya kare rayuwata, shine za'a masa sharri wallahi bazan lamunta ba, he's my Husband " Ɗan sandan nan yace  " ku ɗaukemin wannan mahaukaciyar daga gabana, a tafi da ita Asibiti a duba lafiyarta, sannan ku kiramin Ubanta Bulama tunda babu wanda yasan inda wancan yake " Widad bata gane meyake nufi ba ta cigaba da kukanta, haka suka kawo Ambulance dan iya makirci, aka sheƙa mata wani abu ta sume a gurin, aka kira 'yan jaridu suka cika gurin, aka ɗauki Widad aka saka ta a motar Agajin gaggawa wato Ambulance suka tafi da ita. Jaridu kuwa da sassafe shafin farko, hotunan Yusuf ne da Saleh, musamman na Yusuf ɗaure a cikin sarƙa ya sunkuyar da kai, gefe ga hoton Widad da aka ɗauka an fito da ita daga ofishin 'yan sanda an sata a ambulance, daka kunna gidan radio, labarai ko talabijin babu abunda zaka fara ji se   "Me dokar bacci ya ɓige da gyangyɗi, kuma ƙarshen tika tiki tik inji hausawa A yaune  jami' am tasaro sukayi nasarar cafke jami'in ɗan sandan nan na farin kaya wato Yusuf Bashir Maitama, wanda yayi garkuwa da 'yar gidan fitaccen me Arziki nan a gida da wajen Nigeria wato Nasir Daula,' yan sandan sunyi nasarar gano shi ya sace ta tare da ɓoyeta a wani ƙasurgumin ƙauye dake garin Bauchi, 'yan sandan sun ceto Widad Nasir Daula, wadda ke cikin mawuyacin hali, da zauwansu basu yi wata wata ba aka kira motar Asibiti aka tafi da ita domin duba lafiyarta, zamu ci gaba da bibiya da kasa kunne domin jin wani mataki hukuma zata ɗauka akan wannan ɗan sanda, wanda ake tunanin har shi Nasir Daula ɗin shine yai garkuwa dashi, mu dai anan se muce Allah ya kyauta, yai mana tsari da irin wannan jam'ian tsaro a cikin al'ummar mu" Nan fa gari ya ɗau ɗumi, aka dinga cece kuce, wasu na Allah wadai suna Tsinewa Yusuf, yayin da wasu ke a bari a ga abunda bincike zeyi tukuna. Widad kam bata sake sanin inda kanta yake ba, inda har a gadon Asibiti aka bita aka dinga ɗaukar hotunan ta, ga fuskarta tayi ja saboda kuka, da gajiyar tafiyar hanya, amma aka dinga ɗauka ana watsawa duniya wai tana cikin mawuyacin hali, hannunta ɗauke da drip. Alhaji Haruna ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba a taɓa raina masa hankali kamar yadda akayi yau ba, ya kira layin Hajiya Halima, Ramlah na zaune a falo wayar ta fara ringing, Mummy tana ciki tana amsa wata wayar dan haka ta ɗaga wayar tasa a kunnenta tace "Hello" Yace "Yawwa Amal ce?" "No Ramlah ce" "Dan Allah idan Amal tana kusa ɗan bata wayar muyi magana" Tace "tana ɗakinta, bari in kai mata" Ta miƙe ta tafi ɗakin Amal, amma ɗakin a rufe harta kashe fitila ma " Ramlah tace " gaskiya tayi bacci, dan ta rufe ɗakinta ma ta kashe fitila" Yace "Yasalam" Ramlah tace "ya dai? Akwai matsala ne?" "A'a babu wata matsala, ina son muyi magana ne kawai" "to ka gayamin saƙon in bata mana" Yace "A'a karki damu, idan ta tashi na sake kira" Ya kashe wayar yace "Amma dai Allah ya Tsinewa yarinyar nan, kaga min shegiyar yarinya mara albarka" ya ciji yatsa yai ƙwafa yace "dani kike zancen wallahi, kema sema wulaƙantaki," Amal ta ɗau wayarta ta tura masa saƙo tace "ka cigaba da kiran Mummy, kana cewa kana son Magana dani, wallahi idan baka yi wasa ba sena gayamata abunda kayi min, kuma kasan halinta sarai, kasan buyaginta zata maka abunda kai kanka zaka kasa gane kansa, dan haka muddin ba zaka cika sharaɗina ba, wallahi ba zan baka ba na gaya maka, kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan, nima a account dina ina da wanda suka fisu" Ta kashe wayarta ta sake kwanciya, ya duba message ɗin, yaja wata ajiyar zuciya yana cije leɓe, totally ta riga ta gama raina masa hankali, yama rasa me zeyi ko me zece. Yana nan tsaye yana tunanin mafita kiran wayar Bukar ya shigo wayarsa, ya ɗaga jiki na tsuma, yace "Hello" "Haruna, yau muna da zama na gaggawa, cikin dare dan haka duk ku tattaru" Yace "harda Halima?" "banda ita, sannan kazo min da wannan takaddar, zamuyi magana a kai itama" Daga nan ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya yakice gumi, yana huci Amal ta masa rashin mutunci, dan kawai abu ya shiga tsakaninsu se tayi masa haka?. Mutan ƙauyen da Widad suka zauna suka dinga taradaddi, kowa da abunda yake faɗa wasu suna dama megari yayi wauta, wataƙila dama can 'yan fashi ne ko wasu masu laifin ne, amma daga zuwansu ya karɓesu, be san daga inda suke ba. Hindu kam kuka, kamar wadda aka kama uwarta, ita kanta Hari gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, wunin ranar gidan daga masu koke koke, se masu salallami, Hanne kuwa ko a jikinta. Koda Sunusi ya dawo, Jamika ta gaya masa abunda ya faru, dan haka yace dole gobe insha Allah ya tafi kank, yaje yaji ba'asin abunda ya faru. Jamila tace "dan Allah karkaje, kar kaima a kama ka, dan na san da kana nan wataƙila da kai zasu haɗa" Sunusi yace "da nayi musu me? Kince an kama Saleh, kuma Saleh shiya kawo su nan, meyasa aka kama shi, dole zanje inji" Daddare megari ya tara iyalansa yace "to wannan bayin Allah dai, ni dai a ɗan zaman da mukayi dasu, ban tunanin mutane ne marasa gaskiya, ko makamancin haka, zamanmu da su ma mu alkhairi ya zame mana a garin nan, dan haka dan Allah ina roƙonku da kuyi haƙuri ku dena kuka, kukan ya isa haka, Hasana nasanki da son 'ya' ya kuma zamanmu dasu jin shaƙu dasu sosai, dan Allah kidena kuka kiyi musu Addu'a, Hindu Baffa kema kukan ya isa haka, muyi musu Addu'a, Allah ya basu mafita sannan Hari a samo makulli a rufe musu ɗakinsu, kar wanda ya sake shiga tunda da kayansu a ciki " Hari ta tashi ta shiga ɗakinta ta samo mukulli, tana ƙoƙarin rufewa taga bokitinsu a tsakar gida, ta tafi ta ɗakko bokitin, kawai ta fashe da kuka tace " Allah sarki Wudas, da yanzu muna faɗa akan ruwan zafin da zata yi wanka, tace sena bata na bawa mijin ta, ban taɓa ganin abun tausayi kamar yau ba, yadda ta rikice tana kuka, Allah sarki Allah ya fitar dasu" A kaita bata haƙuri, aka kulle ɗakinsu aka bawa Megari mukullin, ya kai ɗakinsa ya ɓoye. Yusuf yana kwance a cikin cell, an raba masa cell shida Saleh, sauro yana ta masa buduri a ka, yai rigingine yana tunanin ya Umma zataji idan wannan mummunan labari ya isheta?. Aka buɗe ƙofar cell ɗin, wasu 'yan sanda suka shigo su biyu, ya tashi zaune yana kallon su. Ɗaya ya kalleshi yace "munafuki, kalleshi kamar na Allah, amma ƙasurgumin Azzalumi ne, kai garkuwa da' ya ka koma kayi da Ubanta, saboda kai Azzalumi ne, kuma a haka wai kai ɗansanda ne" Yusuf yai shiru be ko ɗaga kai ba, ɗayan yace "rabu dashi corporal Sani, zuwa gobe in Allah ya kaimu semun sauya halittun fuskarsa, kafin 'yan jarida suzo, a buga shi a nunawa duniya shi, azzalumin banza dana wofi kawai" Yusuf dai yai shiru bece komai ba, suka gama zage zagensu suka fita, suka sake rufe shi, tun Abincin safe Yusuf be kuma cin komai ba, ga doguwar tafiyar da suka yi, amma sam baya jin yunwa tunanin makaomarsa kawai yake a wannan hali da yake ciki. Nurat na kwance cikin dare, taji Mahaifinta yana waya ƙasa ƙasa, ya fito daga ɗakinsa da alama dai fita zeyi, ta kalli agogo ƙarfe biyu da rabi na dare, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito falo, aikuwa yana fitowa ya ganta a falo, ya ɗan haɗe rai yace "ke me kike yi a falo a wannan tsohon daren haka?" Tace "ruwa na fito sha" "ina ma fridge ɗin dakinki?" "yayi sanyi da yawa, duk ya zama ƙanƙara shiyasa na fito" Yace "to kin sha ɗin ne kokuwa?" Tace "A'a yanzu dai zan sha" "maza jeki sha, kizo ki wuce ki kwanta" Ta nufi hanyar kitchen, tana tunanin ina zashi a wannan tsohon daren, ta fito ta tarar da shi a falon a tsaye, yace "kinsha ruwan?" Tace "eh na sha" "to maza ki wuce, ki tafi ɗakinki ki kwanta" Harta juya ta tafi, ta waigo taga yana tsaye yana kallon ta, tace "Amma naga kamar fita zakayi, ina zaka yanzu dare yayi sosai" "Yaushe na fara wasa dake? Ko kuma kika zama uwata da zaki dinga tuhuma ta haka?" "hmm Daddy kenan, ai kaine kake abun tuhumar, wani irin abune wannan da ba'ayi ido ma ganin ido ba se yanzu a tsakiyar dare haka hmmm Allah dai ya kyauta?" Ta buɗe ɗakinta ta shige, ta barshi tsaye yana binta da kallo, yarinyar da idan ta ganshi jikinta ke rawa, itace take gaya masa magama haka, tabbas uwarta ce ke zigata kuma zeyi maganinsu gaba ɗaya. Kamar yadda suka saba haɗuwa yauma sun hallara gabaɗayansu, suna zazzaune a ɗakin Hotel ɗin da ya zamana babu ma me kama shi sesu. Bukar yace "kyakkyawan labari" Alhaji Musa yace "muna jinka" Alhaji Bukar yace "yaron nan yazo hannu" Sukace wane yaron? Alhaji Bukar yace "ku duk baku sani ba, dukda yadda da labarin ya yaɗu a daren nan? To ina nufin Yaron nan Yusuf, direbanta wanda aka yi garkuwa dasu tare" Sukace "Alhamdilillah, abu yayi kyau" Alhaji Bukar yace "An kamosu a wani ƙauye a Bauchi, inda Saleh ya basu mafaka, yanzu haka yana hannun 'yan sanda, za' a tattare duk wata sheda da ta kamata daga nam za'a kaishi kotu, zamu saki kuɗi ayi masa shari'a da hukuncin daya dace da shi, saboda babu wanda ya ta:a kawo mana cikas da tangarɗa a harkar nan kamar shi, kunga daga nan babu wanda ya isa yace mune muka sa akayi garkuwa dasu" Alhaji Munir yace "good, wannan abu yayi kyawuuu sosai, kuma ya tafi yadda ake so, dan haka semu hanzarta, mu kuma samu hanyar da zamu ɓalli namu kason tun kan Daula ya bayyana, dan shi har yanzu bamu san fa inda yake ba, kar muje wasu su rigamu karɓa abun nan fa" Bukar yace "na toshe duk wata hanya da zata saka wani ya mallaki abun nan bamu ba, sannan dole nasa a matsa yaron nan, idan ma abun yana hannunsa ya faɗi inda suke" Alhaji Musa yace "kai amma abu yayi kyau wallahi, komai ya tafi yadda yakamata" Alhaji Bukar yace "Haruna ina takaddar da wancan yaron ya bari, ɗan gurin Halima? Shima nasa a nemo shi, duk inda aka ganshi kawai a kawar dashi, bama san duk wani abu da zesa a samu sheda a kanmu" Alhaji Haruna yai tsilli tsilli da ido yace "Amm.. Mm.. Wallahi an ɗan samu akasine, na rasa inda takaddar ta faɗa amma ina ta ƙoƙarin dubawa" Alhaji Bukar yace "Amma kasan bana son akasi ko?" Yace "Ayimin afuwa dan Allah, Insha Allah za'a nemota in kawo" Alhaji Bukar yace "shikenan, nan da kwana bakwai, na baka isashen lokaci, nan kusa nake so a fara shari'ar yaron nan, ba da nisa ba, kuma ina son a rufe duk wata hujja da zata bayyana mu" Alhaji Haruna yace "insha Allah, zan kawo takaddar nan ba da jimawa ba" Haka suka gama tattaunawa sannan suka watse. Widad ce ke ƙoƙarin farkawa, se jujjuya wuyanta take tana kuka cikin bacci, "Wayyo Allah na, yuzarsef yunwa nake ji, zuciya ta ciwo take, Yoseef dan Allah, dan Allah ka dawo please! Ta farka a gigice tana kiran Yoseef! Yoseef kana inane?" Bulama ne da Matarsa Hajiya Sarah a gigice suka yi kanta gaba ɗaya, Bulama yace "Sannu daughter, sannu ki kwantar da hankalinki, kin ganni a tare da ke, ga Maman Iman ma, an kuɓutar dake ki kwantar da hankalinki" "Ni bazan kwantar da hankalina ba, ina mijina yake? Ina Yoseef kace su sakarmin shi, ni ba saceni yayi ba, wallahi idan basu sake shi ba mutuwa zanyi, laifina ne, duk saboda ya ceceni haka ta faru dashi, beyi laifi ba, tun farko seda na gaya masa death contract ne amma ya amince, kaga abunda nake nufi Yoseef, dan Allah ku ƙyaleshi idan wani abu ya sameshi bazan yafewa kaina ba, dan Allah ka cewa Bukar na dawo, ni yazo ya kamani yasa a sakarmin mijina dan Allah " Tai maganar wasu irin hawaye na ambaliya daga idonta, idanun da suka rine zuwa kalar ja jawur suka kumbure. Bulama yace "toni ina na san wani Bukar, balle in nemo miki shi? Ke kaɗai kika sanshi, ni ban san a inda yake ba" Kafin ya rufe baki... Ayi subscribing YouTube channel ɗina please 🙏 🙏 🙏 🙏 Ayshercool 11/18/21, 7:47 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 108_109 Kafin ya rufe baki ta cire drip ɗin hannunta tayi jifa dashi tace  "ni na sanshi, kuma zan nemo shi insha Allah, dole a sakarmin Yoseef ɗina" Hajiya Sarah tace "haba Widad, baji da lafiya fa, drip ne a jikinki, ya zaki cire ki yar?" "ni lafiyata ƙalau, ba abunda yake damuna se son inga an sakarmin mijina" Bulama yace "wai waye mijin naki ne?" Tace "Yoseef, mijina ne, Aure mukayi dashi" Hajiya Sarah tace "wane irin aure ba tare da izinin magamabatnki ba? Anya ba ciwon nakine ya tashi ba?" "Karka ƙara dangantani da hauka, na gaya maka in bahaka ba zan maka haaukan ganin idonka" Ta diro daga kan gadon zata yi waje, aka Riƙeta da ƙyar tana fizge fizge seta ƙwace ta fita. Da Alhaji Musa ya koma gida a harabar gidan ya tarar da Nurat a zaune yai parking ya fito ze wuce ta kalle shi ta dauke kai, ya kalleta yace  "can't you greet your Dad?" "I don't think my Dad still loves me" Yace "why" "saboda yadda kake treating ɗina kamar ba 'yarka ba" ta ƙarasa maganar tana tashi ta bar gurin ya bita da kallo. Harta shiga ɗaki taji ta gaji da zaman, ga Khalil yace zezo amma shiru bezo ba, fitowa tayi daga ɗakinta ta haɗo tea, ta dawo falo ta zauna ta kunna TV ta nayi tana ɗan shan tea ɗinta a hankali. Ta tarar har angama title ɗin news ɗin an fara labaran, sedai ana fara gabatar da labarin su Yusuf jikinta ya hau shaking, gabanta ya shiga dukan uku uku, ai ba'a gama labaran ba ta saki kofin tea ɗin dake hannunta, da ibu zata saka amma ta toshe bakinta, ta shiga ɗakinta da sauri ta kulle ƙofa, zubewa tayi a gurin ta shiga rusar kuka kamar wadda babanta ya mutu, ta dinga kuka tabbas babu ko tantama wannan ƙulle ƙullen mahaifinta ne, wataƙila shine ma dalilin kwanansa a waje jiya, wannan labarin sam babu ƙamshin gaskiya a cikinsa, ta yaya za'ayi garkuwa da mutane kuma an gano su ace Yusuf ne ya saceta baze yuwu ba. Ta ɗakko wayarta ta shige toilet, ta nemo lambar Khalil, tana kuka Khalil ya ɗaga, yana ɗagawa ta fashe da kuka yace 'Nurat lafiya kuwa, meyafaru ne? " "bakaga News ba na yau, wanda akayi da safen nan?" Yai ajiyar zuciya yace "Na gani sister" "Amma meyasa baka gayamin ba? Kaga abunda ya faru kaga abunda akace Yusuf yayi ko?" Khalil yace "nagani, bana son in ɗaga miki hankaline, amma tun jiya da daddare na gani, gefw guda kuma Anwar ɗan gidan Hajiya Halima shima ba'asan inda yake ba, duk na ɓoye ne, dan gudun tayar miki da hankali" Nurat ta share hawayenta tace "Yaya Khalil, ka dena min ɓoye ɓoye, lokaci yayi da zaka temakeni, Khalil mahaifina azzalumi ne wallahi, jiya be kwana a gida ba, nasan saboda wannan dalilin ne, Wallahi idan ba'ayi wani abu a kai ba, rayuwar Yusuf zata shiga garari" "Nasani Nurat, but am doing my best kinji, bari kinga yanzu zan shigo gidan naku kafin in wuce office" Nurat tace "No karkazo, ka san shi da zargi, zefara zargin wani abune dan Allah karka zo ka bari kawai, mu dinga communicating ta waya ya isa, bana son ya gane komai" Khalil yace "shikenan, naji ki kwantar da hankalinki, komai zezo da sauƙi zancigaba da bibiya inga yadda zata kaya" "Shikenan brother nagode sosai, dan Allah ka ƙara ƙoƙari" "karki damu sister, Insha Allah i will do my best for you" Ta jinjina kai ta ajiye wayar, tana ci gaba da jujjuya kai tana tausayawa Yusuf. Ma'aikatan gidan Alhaji Daula suka rikice jin kabarin abunda ya faru da Yusuf, sun kadu matuƙar gaske dukda wasun su suna jin haushinsa amma a zaman da suka yi dashi sun sanshi da sanyin hali, basa tunanin ze aikata wannan aiki haka. Ɓangaren Suleiman makuwa ya kaɗu Matuƙa da jin wannan labarin, hankalinsa ya tashi sosai ya tafi headquarter da kansa dan ganin Yusuf, amma fafur aka hanashi ganinsa, dukda shima babban jami'ine amma a kace baze ganshi ba, ana kan gudanar da bincike akansu ne. Yusuf kam yaci duka da kulki a hannun kuratan 'yan sanda, yama rasa dukan me suke masa? Me suke yai musu su ƙyaleshi, ya daku iya dakuwa ƙafafunsa da bayansa ya gaya masa saboda duka, yana nan gurin a duƙe wani ɗan sanda ya shigo aka ajiye ɗan sandan kujera ya zauna, ya sallami kowa daga gurin, ya ɗan ƙurawa Yusuf ido sannan yace   "Malam Yusuf" Yusuf yai shiru be ɗagoba, yana nan zaune ya durƙusar da kansa. "Ina so karka bamu wahala, kuma karka bawa kanka wahala, yana da kyau ka amsa laifinka tun a nan dan muyi gaggawar kaika kotu a yanke maka hukuncin daya dace, sannan abu na gaba shine, Widad ta baka bayanin inda dukiyar da mahaifinata ya ware take?" Ɗago kai Yusuf yayi, ya kalli ɗan sandan, se yanzu ya ƙara tabattar da cewa wannan abun set up ne kawai, an shirya wulaƙant shi ne kawai. Ya maida kansa ya sunkuyar, yaƙi magana. Cikin shouting ɗan sandan yace" ba magana nake maka ba? Ta gaya maka ko kuwa, ka sauƙaƙawa kanka ka gayamin suna ina? " Cikin dakiya da juriya irin na Yusuf, ya sake gyra zamansa ya ƙi kallon ɗan sandan, ai kuwa ɗan sandan nan ya harzuƙa, yasa aka kawo masa kulki, ya ding bugawa Yusuf, Yusuf ya dinga juyi a gurin saboda azabar wahala dayake sha, dan dukan kulkin nan ba ƙaramin shigarsa yake ba, amma sukayi sukayi, Yusuf yaƙi cewa uffan. Widad kam aka hana 'yan jarida ganinta, aka gama bata magunguna da gwaje gwaje, Bulama ya ɗauketa zuwa gidan sa, Widad sam bata iya ma magana yanzu, haka aka tafi da ita gidan Bulama. Likitoci suka bada rahoton, wai ta samu raunuka a jikinta, kuma ta galabaita saboda rashin Abinci da azabtarwar da ta sha  hannun Yusuf da yayi garkuwa da ita. Bulama ya tafi da ita gidansa, sedai banda sharar hawaye babu abunda take yi, ƙarshe ma maganar ta gagara, aka bata ɗaki, suna shiga ɗakin ta zube a ƙasa tana maida numfashi, saboda nauyin da taji ƙirjinta yayi mata, ta kalli Bulama tace  "meyasa ka kawoni nan?" Yace "A'a, daughter nanma ai gidanku ne, meye na damuwa kuma?" "Nan ba gidanmu bane, ina Daddy yake tunda nazo ban ganshi ba, yana ina?" Hajiya Sarah ta kalli Bulama, shima ya kalleta yace "Amm daughter kin gane, ki kwantar da hankalinki kinji, Daddyn ki yana nan lafiya, kuma yana nan zuwa insha Allah, kedai ki kwantar da hankalinki kawai saboda lafiyarki" Widad tace "ni babu abunda ya sameni, ka gayamin ina mahaifina yake? Ina Daddy na" Hajiya Sarah tace  "Kaga, Ka gayamata gaskiya kawai, tunda har Allah yasa an gano ta bashi da wani amfani a cigaba da yi mata ɓoye ɓoye, dan haka kawai ka fito ka faɗa mata gaskiya" Bulama yace "Sarah meyasa kike hakane? Kina ganin halin da take ciki amma kina wani zance daban meyasa kike hakane?" Hajiya Sarah tace "dan meyasa ba zanyi haka ba, ka gayamata gaskiya mana da wuri, kasan halinta sarai ba baka sani ba, idan ta sani daga baya duk seta ɗaga mana hankali gaba ɗaya gidan nan, ni a yanzu hakama a tsorace nake, kafi kowa sanin halinta" Bulama yace "koma meye halin nata ba haƙuri zakiyi ba, da  'yar kice haka zaki ce? Kiyi haƙuri mana muga yadda hali zeyi" Sunata jayayya a tsakanin su, Widad ta zame jiki ta zauna a gurin, tai musu shiru ta lumshe idonta tana jin sautin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri kamar zata tsaga ƙirjinta ta fito. Bulama ya durƙuso gabanta yace  "ki kwantar da hanlinki kinji daughter, babu wata matsala Daddynki yana nan lafiya, zezo inda kike, amma sekin kwantar da hankalinki, kin san baki da cikakkiyar lafiya, mubi komai a sannu" Idonta a lumshe bata buɗe ba tace  "Daddy" Yace  "Na'am daughter" "kasa a sakarmin Yusuf" "saboda me? Meyasa zakice a sake shi, mutumin da yayi garkuwa dake, aka samoki da ƙyar a wani ƙungurmin ƙauye, sannan kice a sake shi, baki duba abunda yayi miki bane?" "Yoseef beyi garkuwa dani ba sam, anyi garkuwa damune ni da shi, ba wahalar da beyi ba saboda in tsira da rayuwata, meyasa yanzu za'ace shine ya saceni? Anyi masa adalci kenan kasa a sake shi please, dan Allah a saki Yoseef bashi da laifin komai fa" ta ƙarasa maganar tana kuka. Bulama yace "Ni yanzu ta yaya zan fara sakawa a sake shi? 'yan sanda sun fitar da rahoto akan abunda ya faru kawai ace nasa a sake shi, bafa a ko ina ake alfarma ba, yanzu gaba ɗaya case na hannun hukuma, babu abunda zan iya ni" "Shikenan tunda babu abunda zaka iya, ni zanyi ko zan ƙarar da dukiyar Daula sena fitar da Yoseef, saboda ni ba butulu bace ba, Yoseef yayi min halacci" Ta miƙe ta kwanta a gurin, tana ta kera gwaron numfashi, wani na bin wani. Suleiman gidan su Yusuf ya tafi, yana zuwa ya tarar da Umman Yusuf a kwance, an kewaye ta ana yayyafa mata ruwa, sam bata san inda kanta yake ba, ga Asmarta ta tashi tana jan numfashi da ƙyar, an sheƙa mata inhaler amma a banza. Suleiman yace "Subhanallah, ya ba'a kaita Asibiti ba? Meye ya faru da ita haka?" Wata maƙociyarsu tace  "wallahi yau da Asuba bayan ta idar da sallar Asuba, ya kunna radio taji ance an kama ɗanta Yusuf, shikenan muka jiyo kukanta, muna shigowa harta fara fita daga hayyacinta, numfashi yaƙi tsayawa a ƙirjinta. Suleiman yace" da ba seku kaita Asibiti ba, koda kuwa na gwamnati ne ba, zata iya rasa ranta fa a haka, maza ku ɗakkota ga mota can, a sata a ciki mu tafi Asibiti " Haka kuwa akayi, aka sa Umman Yusuf a mota, da wasu maƙotanta suka Tafi Kaita Asibiti. Suna zuwa aka karɓeta a emergency, aka shiga da ita, likitoci sukayi gwaje gwajen da zasuyi suka ga jininta ya hau fiye da kima, dama tana zuwa shan magani ana duba jinin, tun lokacin da Yusuf ya ɓata ta haɗu da hawan jini. Yanzu jinin ya hau fiye da kima, ga Asma ta tashi saboda kukan da take yi, gaba ɗaya bata a hayyacinta, a nata ƙoƙarin ganin jinin ya sauka amma abu ya gagara, ƙarshe seda aka haɗa mata da oxygen, da allurai da drip, Suleiman duk ya biya charges ɗin. Da Safe Amal bata tashi ba se wajen sha ɗaya na safe, ta tashi daga bacci ta tashi da wata irin yunwa, ta tashi ta shiga toilet tayi wanka, ta canza kayan jikinta daga na bacci, har zata fita tace "bari dai in kunna wayata, inga me wannan jakin kuma ya kuma turowa" ta zauna ta kunna wayarta, ta buɗe data messages nata shigowa, amma babu na Alhaji Haruna, ta taɓe baki ta tashi zata fita, sega kiran wayarsa ya shigo wayarta. Ta koma ta zauna sannan ta ɗaga, Alhaji Haruna yace "yaushe zanzo in karɓi takaddar nan ne?" "ba rana ba wata, muddin ba zaka cika sharuɗan dana sama ka ba" "Waike ynzu 500k ne suka miki kaɗan? Haba ke kuwa dan Allah" Amal tace  "kaga sauraramin, meye wani 500k,duk kuɗin da kake sata na haram kakeci, seni zaka rainawa hankali, wallahi bazan baka takaddar nan a 500k ba" Aikuwa ya fusata yace  "ke wai wace irin yarinya ce, kwana bakwai fa kawai aka bani in kai takaddar nan, ya zakice bazaki bank ba haka akeyi?" "Kai bari kaji in gaya maka wani abu, wallahi idan baka yi wasa ba sena sa takaddar nan ta zama hujja akanku gaba ɗaya" "har babar taki?" "Eh har ita, duk zaka ja muku ne, bari in maka magana ta ƙarshe, wallahi bazan baka takaddar nan ba har se ka bani kuɗin da zaka fanshi budurcina da ka karɓa ta ƙarfi" "Ke, ni kike gayawa haka? Wace irin magana ce wannan?" "ai kace min ka ga kaidi iri iri na mata a bariki, to zan nuna maka nawa na dabanne, zan kawo ƙarshen bunsurancinka, wallahi ko inje in haɗa maka masifa da tashin hankali a gurin Alhaji Bukar ɗin, baka san kalar nawa kaidin ba zan gwada maka Akuya kawai" Ai kasa magana yayi, se bin wayar yayi da kallo, lallai yarinyar nan bata da mutunci sam. Ta ajiye wayar tace za kaga tsiya ganin idonka, tai tsaki ta saka wayar a caji ta fito falo, Dariyar Mummy taji da Ramlah, Ramlah tace  "dara taci gida, sunzo hannu Alhamdilillah, naji ance a ƙungurmin ƙauye aka gano su, koya akayi ta iya zaman wannan ƙauyen oho" Mummy tace "su suka sani, ni dai tunda an kamo su na fara jin ƙamshin samun kuɗin nan" Ramlah tace "Ance yana can hannun 'yan sanda ido ya raina fata, tun jiya ya fara cin ƙaniyarsa a hannunsu, ai gara yaji jiki, kafin a shiga kotu ya raina kansa" Mummy tace "eh Bulama ya cemin idan aka gama bincike kotu za' a kaishi, dan haka ni yanzu ba ta tashi nake ba, ta Anwar nakeyi har yanzu shiru, tunda Amal ta kai musu takaddar basu sake cemin komai ba" Ramlah tace "zasuyi miki magana ne, bari mu kunna TV mu sake ganin idon munafukin nan, dan ban manta lokacin da ake wulaƙantamu ana cin zarafin mu saboda shi ba" Ajiyar zuciya Amal tayi, wanda yasa suka juya gaba ɗaya suka kalleta, wucewa tayi kitchen dan Samarwa kanta abunda zata ci. Mummy tace  "Auta ya jiki?" Ta kalli Mummy ta ɗauke kai, ta wuce kitchen, ta fito daga kitchen tazo ta zauna tace "Mummy, hira naji kuna yi kamar an kama Yusuf ko?" Ramlah tai farat tace  "Eh an kama shi, seme ne kuma? Ko zaki fara wa mutane shirmen naki ne?" Amal ta girgiza kai tace  "No akanme? Ina Ita Widad ɗin take?" "Tana gidan Bulama, dan shi ze iya wannan haukan nata" Amal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi ɗakimta, tana jinjina kai, da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga social media, aikuwa taga yadda labarin ya cika social media, yadda aka haɗa ƙarya da gaskiya. Ta ajiye wayar tayi shiru tana tunani, kasa shan tea ɗin nan tayi, se tunani daya dabai baye zuciyarta, gaba ɗaya tausayin Yusuf ya mamaye zuciyarta, tama jin tsohuwar soyayyar sa na taso mata. "Nurat" Alhaji Musa ya kira sunanta, ta amsa masa da "Na'am Daddy" "ya maganar shirye shiryen tafiyarki ne, you should preparing for it fa, lokaci yana gabatowa" "but Daddy, i thought we have discussed this issue since" Ya kalleta yace "muka ce mene?" "Daddy na gaya maka ni bana son tafiyar nan, ni ba inda zanje a gida Nigeria zanyi karatun" "ba zakiyi a nan ɗin ba, ƙasar nan zaki bari, waike yaushe muka fara sainsa dake ne? Ni zance ga yadda za'ayi amma ki bijiremin? To baki isa ba nina haifeki bake kika haifeni ba" Ya dinga banbamin bala'insa, yayi ya gama tsaf bata sake cewa komai ba, seda ya gama tukuna sannan ta miƙe ta bar masa ɗakinsa, tana zuwa ɗakinta tace 'wallahi ba inda zanje, bazan bar ƙasar nan ana wannan halin ba, se naga abunda ya turewa buzu naɗi" Yusuf kam ya daku a gurin jami' an tsaro, akan lallai seya amsa shine ya sace Widad, amma Yusuf ƙemem yaƙi magana, dama shi Saleh ba'a maganarsa saboda ya galabaita fiye da Yusuf ko magana baya iyayi, bama shi da lafiya. Juyin duniya Yusuf ya amsa shine ya sace Widad yaƙi, yaƙi ko ɗaga kansa ma balle yayi magana. Mutumin da yake jibgarsa yace "ga 'yan jarida cam suka cika harabar gidan nan, zamu basu lokaci suyi magana da kai, ka furta kaine ka sace yarinyar nan koka samj sassauci, idan kuma kaƙi to haka zamu ci gaba da casaka a gurin nan, gara ka nemawa kanka mafita, ka amsa kai ka sace ta" Yusuf dai beyi magana ba, aka taso ƙeyarsa a gaba aka saka masa handcuffs hannu da ƙafa, aka fito da shi harabar headquarter na 'yan sanda, fuskarsa duk ta kumbur saboda duka. ' yan jarida sun cika gurin nan, suka kewaye Yusuf da abun magana, kowa yana yanko masa tambaya, wasu ta gaske wasu ta cin mutunci, amma Yusuf yai shiru, sukayi sukayi har suka gaji, har ya juya za'a maida shi ya tsaya ya waigo, ya kalli' yan jaridar nan yace "Bani na sace ta ba" Kawai ya juya, ds ƙyar 'yan sanda suka dakatar da' yan jaridar nan aka mayar da Yusuf inda aka ɗakko shi. Nurat gaba ɗaya ta tayarwa da Khalil hankali akan maganar Yusuf, ga koke koken da take akan batun komawarta karatu, tana ta saƙawa da warwar akan ta gudu ta bar gidan gaba ɗaya, amma sedai tasan idan tayi hakan ba zata sake daraja a idon mutane ba. Alhaji Haruna duk ya shiga damuwa da tashin hankali, akan takaddar nan da Amal keta rainamasa hankali akan ta, ya shiga part ɗin Amaryarsa ya tarar da ita ta ƙurawa TV ido cike da damuwa, ya zauna kusa da ita yace "Baby kallo ake ne?" Ta ɗan ɓata fuska tace "ina kallon wani abune daya tsayamin a zuciya, wannan bawan Allah da aka kama akan 'yar gidan Daula ya tsayemin, i can't imagine ze aikata wani abu makamancin haka, ƙarya ce kawai akayi masa" Yace "ke ya akayi kika san ƙarya akayi masa? Wannan shine abunda ya dace dashi, kuma zamu tsaya kai da fata se an hukunta shi anyi maganin irinsa a cikin al'umma" Ta kalle shi tace "Nasan Yusuf, fiye da yadda kake tunani, inaga mahaufiyarsa ce kawai zata fini sanin waye shi, wallahi wannan maganar ƙarya ake masa, mutumin da yake kamar waliyyi dan haƙuri, wannan maganar ƙaryane wallahi" Alhaji Haruna yace "Salma meye haɗinki dashi da kike wannan zaƙewar, meye haka kike yi akansa, kuma a gabana?" Ta Harare shi tace "Yusuf unguwar mu ɗaya, kuma tsohon saurayi nane, wanda aka hanani Aurensa aka ƙaƙabamin kai" Kawai ya kwashe da dariya yace "lallai baki da hankali, aikuwa kina ji kina gani ze tafi prison Salmata, sedai haƙuri" Ya tashi ya barta a gurin, tausayin Yusuf ya kamata, tasan Yusuf baze taɓa aikata abunda akace yayi ba. Widad tana zaune kamad wata mahaukaciya, tun jiya da safe rabonta da Abinci, tana jin yadda zuciyarta take bugawa ba daidai ba, tai shiru tunani da tausayin Yusuf ne yake ta ratsa zuciyarta. Iman ta shigowa da Widad da Abinci tace "ga Abinci, ki daure kici dan Allah" Widad tace "kiramin Bulama, zamuyi magana" Iman tace to, befi mintuna biyar da fitarta ba sega Bulama ya shigo ɗakin, yana shigowa ya kalleta yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Widad har yanzu bakya cin Abincin, subhanallah ko mota za'a ɗakko mu tafi Asibiti ne?" Tace "wani hali Mijina yake ciki?" Bulama yace "waye mijinki kuma?" "Yoseef" ta bashi amsa "yaushe kikayi Aure bamu sani ba?" Cikin tsawa tace "ka dena amsamin tambayata da tambaya, ina Yoseef yake?" Bulama yace "yana hannun hukuma har yanzun" Ta miƙe tsaye tace "har yanzu baka yi komai a kai ba ko? Ni ka maidani gidan mu gurin Daddy na, shiyasan ranar da Yusuf yayi masa, baze bari ya cutu ba akan laifin da beyi ba" Bulama yace "kinga ki kwantar da hankalinki". "Karka ƙara cewa in kwantar da hankalina, ina Alhaji Nasir Daula yake? Ina babana Daddyna nake maka magana, yana ina? Ta yaya za'ace tun jiya har yanzu babu shi babu dalilinsa bezo inda nake ba"? Tai maganar a jere bako haɗiyar yawu, tare da ɗaga murya sosai. Bulama yace "kinga zauna kici Abinci tukuna" Ai be rufe baki ba tasa ƙafa tai ball da kayan breakfast ɗin, ta riƙe gaban rigar Bulama tace "ka gayamin gaskiya, ina Daula yake? Idan an kashemin shine ka gayamin, yana ina? Ina yake ina Daddyna?!" Jin Hayaniya yasa tuni mutan gidan suka fara taruwa a ɗakin, Hajiya Sarah tace "babanki Nasir Daula, tun bayan ɓatanki ya kwanta rashin lafiya, aka bishi har gadon Asibiti aka sace shi, har yau babu wanda yasan inda yake" A hankali Widad ta saki rigar Bulama, tana kallon Hajiya Sarah "Annn. An sace Daddyn Widad a gadon Asibiti, this serious, Daddyn how comes? Ta yaya za'a sace shi ba wanda ya sani, shikenan na rasa Yoseef ɗina, Daddyna ma ace ba'a ganshi ba, Noooooo! This impossible!!! Tana maganar ta silale ta faɗi ta ruf da ciki, ko numfashi ba tayi. Ayi haƙuri ba editing Ayi subscribing YouTube channel ɗina dan Allah, me suna Cool Arewa TV 11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 110_111 Me Adda ya kawowa mutumin kujera ya zauna, ya kalli Saleh yace "ka dena mamaki mana, ai bekamata kayi mamaki ba, a zatonka kai kaɗaine me wayo, ko kuma kafi kowa wayo? Kifi na ganinka me jar koma, kallonka kawai nakeyi" Saleh yace  "hmm Bukar kenan, kaima kuka karya Alƙawari balle ni, haka mukayi daku? Ashe kun kashe min ɗan uwana, banma sani ba balle kua bamu gawar muyi masa sitira, dama haka akeyi, kunyi amfani dani ne dan cinma burinku?" "ƙwarai kuwa, muna amfani da kaine dan cinma burinmu, kai bari in gayamaka wani abu, ku duka wanda nake aikin harƙallar nam daku, ina amfani da kune dan cinma burina nikaɗai, na ɗaukeku karnukan farauta tane kawai " " Amma wallahi Bukar baka da imani, baka da adalci " Me Adda ya yunƙura ze kaiwa Saleh duka amma Bukar ya hana shi yace "ƙyaleshi, ai baaka ga komai a cikin ƙudrina da AƘIDATA ba, kuma dama tuntuni kowannen ku nayi masa tanadin makomarsa idan deal ɗinmu ya kammala, sedai kai kayi gaggawa gurin riskar taka makomar, tunda ka yaudareni kaci amanata zaka riski makomarka a nan kusa, ina Widad take? " Saleh yai masa wani irin mugun kallo yace "ni ka bawa ajiyarsu kokuwa? Kaje ka tambayi wanda aka sa su sacesu gasu nan a gabanka" 'bana son in wahalar da kai kafin ka mutu Saleh, ko dan irin wahalar da kayimin, amma gaddama da taurin kai zesa in maka uƙuba wadda zata yi ajalinka, Saleh kaine ka bawa Widad da direbanta mafaka, kasan inda suke kaine ka kuɓutar dasu, dan haka karka wahalar dani, ko ka wahalar da kanka kafin ka mutu, ka gayamin ina ka kaisu"? "Ni bani na ɗauke su ba, ban san inda suke ba, dan haka karka ƙara tambaya ta na gaya maka" Bukar yace  "Shikenan, tunda baka san rarrashi ba, bari a biyo maka ta inda ya dace, Me Addda ku gasamim shi tsawon kwana uku, muga iya juriyarsa a mtsayinsa na kurtun soja" Daga nan Bukar ya tashi ya fita daga ɗakin suka rufa masa baya. Amal tana ta sauri taje ta kai takaddun nan, daga nan ta kai wadda aka bata ta kaiwa Alhaji Haruna, yamma ta fara yi sosai kuma bata son Mummy ta kama faɗan nata akan bataje aiken da tayi mata da wuri ba, dan haka a harabar gidan gurin shiga mota ta ƙarasa saka takaddun a jakarta, da wasiƙar gurin Anwar, da takaddar form ɗinta, ta buɗe mota ta shiga ta fice. Unguwar da guest House ɗin Alhaji Haruna take shiru babu mutane a unguwar, duk se kangwaye da sababbin gidaje, bata kawo komai a ranta ba tace bari taje ta fara kai masa tasa takaddar, daga nan kuma seta je gurin nata kai takaddar. Tana zuwa megadi ya buɗe mata gate ta shiga, tace  "yana nan kuwa?" Megadi yace "Eh yana ciki" Ta fito daga motar ta shiga, ta murɗa ƙofar falon tare da yin sallama, sedai babu kowa a falon, ta nemi guri tayi zamanta a falon, shiru shiru babu wanda ya fito, ta tashi ta koma gurin megadi tace  "Anya kuwa yana nan? Naje nayi sallama amma shiru ba'a amsa ba" Megadi yace "ai be fiye zama a falon ba, ki shiga yana ciki" Tace "Cikin ina? Kaga ungo bari in baka takaddar ka ajiye masa" Megadin yace "rufani ki saya, ai be yadda in karɓi kowane saƙo ba idan bashi yace ba, ki buɗe ƙofar dake cikin falon wasu falukan ne a ciki fa" "kaga muje ka rakani da kanka, ni bazan shiga ni kaɗai ba" Yace "shikenan muje" Ya rakata, yana gaba tana bin bayansa, suka dinga ratsa faluka, sukaje wata ƙofa yace "yawwa a nan yake ganin baƙi, ki shiga ki bashi" "kazo dai mi shiga tare, danni bazan iya maida kaina waje ba, wannan gida duk lunguna kamar gidan matsafa" Yace "A'a shiga dai ki fito, ina nan ina jiranki" Tace "to shikenan" Ta buɗe ɗakin ta shiga da sallama ashe bedroom ne, ya amsa mata yana zaune akan gado yana danna system, yana ganinta ya faɗaɗa murmushinsa yace  "Ashe kinzo, ai tun ɗazu nake jiranki" yai maganar yana binta da kallo. Haɗe rai tayi tace  "eh nazo, ina falo ne ga takaddar tace akawo maka" Alhaji Haruna yace  "ok kawomin nan" Ta ƙaraso tana zumɓura baki, ta sa hannu a jakarta ta ɗakko takaddar, ta ƙarasa inda yake ta miƙa masa takaddar, sedai me se ya haɗa da hannunta, ya riƙe. A fusace ta kalle shi tace  "meye haka kuma? Dalla malam sakeni" Yace "haba Baby, gaki kamar wayayyiya amma kina wani kidahumanci, ki kwantar da hankalinki karki ji komai kinji" "Dalla ka sakeni ko in maka ihu wallahi" Yai murmushi yace "to idan kinyi ihu kina tunanin akwai wanda ze kawo miki ɗauki ne? Ba wani abu fa rainane ya biya kawai, ki kwantar da hankalinki kici Arziki ki barshi" Kici kicin ƙwacewa ta shiga yi amma ya riƙeta gama, yana wani lashe baki kamar kare yace "'yar uwarki ta fiki wayewa, ke kamar ba' yar birni ba" Ya fara ƙoƙarin rabata da kayan jikinta, sosai Amal take ihu tana ƙwacewa, tana rirriƙe jikinta tana kururuwa, amma tsohon najadun nan ko a jikinsa, burinsa kawai ya cimma burinsa, Amal ta dunƙule hannu ta dinga kai masa naushi kota ko ina, wani naushi data kai masa a ido a gigice ya sake ta, yaja da baya, ta durƙusa tana ƙoƙarin mayar da kayanta, kuma taso mata yayi haiƙan yana kuma riƙeta, sosai kokawa ta ka came a tsakanin su, ya hankaɗata ƙasa ta faɗi akan hannunta, ta kurma wani uban ihu, saboda azababben zafin da taji ya ratsa hannunta, haka ta kuma yunƙurawa ta miƙe sedai ta kasa ɗaga hannun nata, ganin zata hana shi rawar gaban hantsi, be tausayawa halin da take ciki ba, ya shammaceta ya buga mata kwalba a goshi, ta kuma kurma ihu ta baje a gurin a sume. Yusuf seda ya kwana biyu sannan ya iya cigaba da fita, sedai wata irin shaƙuwa da kusanci ne ke ƙara shiga tsakaninsa da Widad, wata irin kulawa take bashi ta musamman wadda bata masa a baya, ga Jamila dake ƙara sata a hanya yadda zata dinga kula da mijin ta, gefe guda kuma ta tara ɗalibai sosai, idan yamma tayi cika gidan megari ake yara da manya tana koyar dasu ilimin addini dana zamani. Yau Widad ta haɗa kayanta dana Yusuf ta wanke su tsaf, gwanin ban sha'awa. Yusuf ya dawo a gajiye, yana dawowa ya tarar da Widad harta dafa ruwan wanka ta ajiye masa. Yusuf yayi murmushi yace "Waini wannan kulawar da ake bani fa, nifa abun yana mamaki, an maida ni wani ɗan gata meye sirrin ne?" Widad tai masa fari da ido tace  "tukuici kawai zaka bayar, if you really appreciate" "to me akeso in bayar?" Ba tace masa koma ba se murmushi da tayi, tana sake kashe masa ido, Yusuf yace "Ohh my God, wannan kallon da kikemin se in rasa ina zan sa kaina, gaba ɗaya narkamin zuciyata yake Baby" Widad tai dariya tace "shagwaɓaɓɓe kawai, ji yadda yake magana kamar wani Baby" "Baby ne mana, tunda na auri Baby nima na zama baby ai" "Naji, je kayi wanka kazo in baka Abinci a baki zaka ci?" "zan mana, dayawa ma zanci sosai tunda Baby ce zata bani a baki" Yai murmushi ya fice daga ɗakin, yaje yayo wanka ya dawo ɗakin, sedai ya tarar bata ɗakin tana tsakar gida, yana zuwa yaga babu kayansa, ya duba Akwatin Widad yaga kayansa a wanke, ya ɗadɗaga ya haska yagansu a wanke fes, mamkine ya kama shi, ya fito ya ƙwala mata kira, ta taso taje Yusuf yace "My Wife, gani nayi kamar an wanke min kaya, ya haka?" Widad tace "to meye yafaru? Ko laifi ne?" "Amma waye ya wanke min? Nidai nasan baki iya wanki ba, ni nake mana to yaya akayi aka wanke su?" "Shikenan kuma a haka zan zauna ban iya komai ba,? To in gaya maka na iya aiki sosai yanzu, nice nan na wanke mana su ɗazu" Yusuf yace "abun mamaki, yanzu ke kika wanke mana kayan nan duka? Ina mamaki fa" "wallahi nina wanke mana, ko basu fita bane?" "Ni na isa ince basu fita ba, sun fita fes, amma baki saba ba karki sake wankewa, zan wanke mana da kaina kinji matar Yusuf" "A'a gaskiya, ni dai sena wanke" Yace "bafa na son gaddama, kawai ka bari nagode Allah yayi albarka, amma ni zan dinga wanke mana kinji beautyna" "A'a ai kai ba bawana bane, dan haka nima yakamata in dinga ƙoƙartawa, tunda ina iyawa ai bakomai kai ba murna zakayi ba ina koya ba" Yusuf yace "naji amma ki bari mu dingayi tare, kinji Babyn Yusuf" Tace "to naji" "Yawwa Babyna I love you" yai maganar yana kissing din goshinta, bata bashi amsa ba se murmushi da tayi, tana lumshe ido, babban abunda yake bawa Yusuf mamaki da ita be wuce yadda idan har yace yana sonta, sedai tayi murmushi amma ita ta kasa gayamasa hakan, har yanzu yakasa gane haƙiƙanin abunda yake ranta, sedai yana ganin kishinsa da tausayinsa muraran a idonta, sedai tausayi da kishi suna cikin alama na soyayya. Widad tace "zauna inzo in baka abincin, naga kwana biyu ba kaci kana ƙoshi, bana son mu koma gida a ganka a rame, bazanji daɗi ba, aga nayi ƙiba mijina kuma a rame ba'" Yusuf yace "inyee kaga masu miji, kamar ba mutum ne yake cewa shi be yadda da Aure ba, baze aura ya zauna a ƙarƙashin wani ba, kawai se naji mutum yana cewa ina son Aurena Yoseef, Zan zauna da kai a yadda kake, ya akayi mutum ya canza ra'ayi ne haka da sauri?" Murguɗa baki tayi tace 'bana son tsokana fa" Yusuf yayi dariya yace "gayamin meyasa kike son Aurennaki ne? Gayamin mana" Widad tace "nima ban san yadda akayi haka ba, a baya ina da dalilin da yasa nace bazan yi aure ba, amma yanzu na samu mijin marainiya, wanda yake lallaɓani ban yaɓa zaton akwai miji irinsa ba, ka bani farinciki mara misaltuwa, shiyasa nake jin kamar bazan iya bari kayi nesa dani ba, shiyasa nake son Aurena " Yusuf yayi murmushi yace "Mutum ma ya faɗi gaskiya ma, se wani kauce kauce kike, zama ki faɗi gaskiya ne ai" Widad ta buɗe baki tace "ba ruwana, Allah ya shiryeka, a haka kaman salihi amma mutum yaita sakin magana" "Kyaji dashi dai, ni dai azo a bani Abincina inci yunwa nakeji" Ta zauna tana bawa Yusuf Abincin sa a baki, suna hirarsu cikin nishaɗi da jin daɗi. Amal kawai farakwa tayi ta ganta akan gadon Asibiti, taga kanta nannaɗe da bandeji, hannunta ma data faɗi akai haka, mamkine ya kamata ta juya ta ganta a ɗakin Asibiti a kwance, ga wani irin raɗaɗi da yake ratsata daga tsakanin ƙafafunta. Shiru tayi taga Mummy ta shigo ɗakin hannunta da ledar magani, ta ƙaraso da sauri tana Autana sannu, ya jikin naki ne?" Amal tace "Mummy meya sameni ne?" Mummy tace "hatsari kika yi mana Baby, ina zaune a gida Alhaji Haruna yayi min waya yacemin bayan kin kai masa takaddar, kika samu hatsari a titin unguwarsu" Wani uban ihu ta saki, da tuno abunda ya faru tsakaninta da Alhaji Haruna, ya mata fyaɗe kenan, kuma yake gayawa mahaifiyarta hatsari tayi. Ta fashe da kuka, tana jujjuya kanta, wani irin baƙin ciki ne da takaici ya mamaye mata zuciya. Mummy tace " Haba Amal, kiyi haƙuri dan Allah, ai abun be tsawwala ba Autana, karaya kika samu a hannu se kwalba daya fasa miki goshi, Ai Alhaji Haruna yayi mana mutunci, shiya kawoki Asibitin nan" Kawai Amal ta dinga kuka, ji tayi kamar ta shaƙe mahaifiyarta jin maganar da take, ya cuceta ya kassara rayuwarta, ya raba ta da mutuncinta, kuma ya kawota Asibiti yace hatsari tayi, ji tayi kamar zuciyarta ta tsaga ƙirjinta ta fito saboda azabar baƙinciki da takaici, tama rasa me zata yi, kawai ta fasa ihu ta fizge ruwan dake jikinta tayi jifa dashi, ta dinga wani uban ihu, da ƙyar aka kira likitoci, aka daddanneta akayi mata allurar bacci. Mummy ta kalli likitan cike da damuwa tace "Doctor, wai dan Allah meyasa meta ne? Naga kamar ta haukace" Likitan yace "A'a ba haukacewa tayi ba, stress ne da damuwa suka ɗan dameta amma insha Allah komai zezo da sauƙi, zamu sake mata hoton hannun, idan hali yayi a goben ma insha Allah zamu iyayi mata aikin, tunda Alhaji Haruna ya gama biyan komai, dama anan yake da family file " Hajiya Halima tace "shikenan, mungode nidai Alhamdilillah tunda ba wani abunne ya sameta ba" Bayan sallar isha'i Yusuf ya shigo, ya tarar da Widad a kwance ta kunna fitila, tana ta saƙa maficinta daga nan inda take kwance, yai sallama ta amsa, yana zuwa ya kwanta a kanta. Cikin Shagwaɓa tace "wayyo Allah na, Yuzarsef meye haka? Kana fa da nauyi seka danne min kan Babyna" Yusuf yace "wainine nake da nauyi, ina wani Baby yake anan?" Tace 'ba a nan mana" tai maganar tana nuna masa cikinta. Yusuf yasa hannu ya danna cikin nata yace "Malama bakomai anan hanji, waye yace miki a nan ɗa yake zama" "wayyo Allah na, Yoseef yau cinzali kake ji, dan Allah ka dena danna min cikina, kar kasa in haifi ɗa da lotsatsen ƙeya mana" Yace "Madam wannan cikin naki bakomai a ciki, inma akwai be zama mutum ba, amma duk kin ishi mutane, ke wannan idan cikin ya samu na shigesu, da langwai da Shagwaɓa" Widad ta tura baki tace "Yuzarsef, da nace zan sakawa jaririna sunanka, amma na fasa tunda kana adawa da baybn nan nawa" "Au da bazaki saka sunan Daddy ba, se sunana?" "Eh mana sunanka zan samasa mana" Yusuf yace "salon Daddy yace kinfi son mijinki akansa" Tace "to ai dai ɗana ne naga, ko ɗan Daddyn ne?" "Iyee, ba kara ba kunya Baby, Allah ya shiryeki wallahi za'aga uwa mara kunya gaskiya" Tace "eh naji ɗin, ni ɗagani karka samin ɗa kuka" Yusuf yace "iko se Allah, wai yanzu ke kin haƙiƙance ɗane a cikinki? Kwana nawa kika ƙara baki period ba?, ina shekaranjiya kika cemin mararki na ciwo baki period ɗinba?" "Ai bezo ba tukuna, kwana biyar ya ƙara fa, Insha Allah ina da ciki" Yusuf yace "mara kunya kawai" yai maganar tare da danna gefen mararta ɗaya, wani irin ihu tayi haɗi da zillo, se hawaye, Yusuf ya bita da kallo yana nazarinta. Cikin hawaye tace "Yusuf meye haka? Da zafi fa wallahi" Yusuf yace "yi haƙuri, am sorry kinji babyna, yi haƙuri bazan sake ba insha Allah, abu nake son ji" "Ni ƙyaleni, kawai se cin zalina kake, kuma bazan kwana da kai ba a katifata ba, tunda haka ka koma" "Ke kin isa ki koreni daga kan katifar nan, ina nan tare zamu kwana semun samo Babyn Baby" "Ni na samu Babyna in gaya maka, kuma sena rama abunda kayi min, ni wanka zanje inyi" Yusuf yace "ina nan ina jiranki, kije kiyi wankan kizo kimin tausa inyi bacci" "bazan ba" tai maganar tana hararasa, sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin tana murmushi. Haka suka kwana tare abunsu, cike da soyayya da ƙaunar juna, tana sake jin Yusuf a zuciyarta, bata jin zata iya rabuwa dashi. Saleh kam iya azaba ya shata, su ciko bokiti su danna kansa a ciki, seya suma, banda wutar lantarki da suka dinga jona masa, ga ba Abinci babu ruwan sha, ya galabaita fiye da tunani, banda duka da suke masa da katakwaye, sun masa laga laga gaba ɗaya Saleh ya zama abun tausayi, ya galabaita ya lalace saboda azaba, suyita buga masa itace a ciki, kai da ƙirjinsa, ya dinga fidda jini ta baki da hancinsa, gaba ɗaya ya suma baya hayyacinsa a haka se da aka kwana uku, sannan suka yi waya suka sanar da Bukar, yace musu yana nan tafe zezo gidan da ake ajiye da Saleh yaji idan yayi laushi zuwa yanzu. "Alhaji Bukar, kana sane da cewar mahaifinmu yazo har gidanmu ya saka hannu ya mareni?" "Eh, naji na samu labarin zuwansa, amma ni sam ban san da zancen ya dakeki ba" Ramlah tace "to ya saka hannu ya dakeni, bayan tsawon shekaru be san cina shana ko suturata ba, an gayamin cewar hatsabibine, dan haka sonake in nuna masa ya haifi wadda ta fishi hatsabiban ci" Alhaji Bukar yace "Anya zakifi mahaifinku hatsabibanci kuwa? Amma me kike so ayi masa?" "Sonake a nemo shi duk inda yake, a sauke masa hannun da ya mareni dashi" "Amma fa naga mahaifinkine, idan kikayi haka baki kyauta ba" "Naga dai shima ba mutumin kirki bane, koda bama tare dashi, labarin aika aikar dayayi duk na sani, dan haka rama cuta ga macuci ibadane, zan kawo ƙarshen iya shegensa, a sauke masa hannu nake buƙata" Alhaju Bukar yace "kin samu yarinya, kije kin kwantar da hankalinki, za'ayi abunda ya dace, yadda kike so haka za'ayi ai". Koda Amal ta sake farkawa ta ganta a Asibiti ta tabattar ba mafarki take ba, ta sake fashewa da kuka, ta tuna yadda suka yi da Alhaji Haruna, shikenan Ya kassara mata rayuwa, ya cuce ta, ya gama da ita, tinƙahon kowace mace shine budurcinta amma a banza wani tsohon najadu dabba ya kassara mata rayuwa, ya tarwatsa mata rayuwa ya cuceta, wasu irin zafafan Hawaye suka shiga yi mata sintiri a fuskar ta, tana tunanin me zata yiwa Alhaji Haruna ta huce, me zata yi masa wanda zesa ta huce, ita gaba ɗaya Yusuf ta tanadar wa kanta, saboda babu komai a zuciyar ta inba shiba, dole tayi wani abu wanda zaya rama abunda Alhaji Haruna yayi mata. Ramlah ta kalleta tace "Amal wai wannan wani irin kukane haka? Ki saurarawa kanki mana, Allah ya taƙaita miki wahala baki mutu ba, kuma hannun be cire gaba ɗaya ba, amma se kuka kikeyi, ki kwantar da hankalinki dan Allah kiyi haƙuri. Mummy da ta idar da salla tace " tayani gaya mata dai Ko zataji, tunda abun nan ya faru take kuka, na rasa kukan ubanme take haka? Ni kin kai masa takadda makuwa kafin abun ya faru?" Banza tayi mata, ta ɗauke kanta ta cigaba da kukanta, Alhaji Haruna ne yai sallama, ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, hannunsa ɗauke da manyan ledoji, ya shigo suka gaisa da Mummy, yace " Ya jikin Auta kuwa? " Mummy tace "Jiki da sauƙi, sedai se kuka take, taƙi yin shiru, kuma ga abun be tsawwala da yawa ba, karayace kuma ance yau za'a mata ɗori" Alhaji Haruna ya zauna a gefen gadon yace "Auta ya jikin naki?" Lallai mutumin nan ya cika gardin ɗan iska, ya mata wannan aika aika, sannan yazo wai yazo dubata, shiru tayi taƙi magana. Hajiya Halima tace "Amal ba magana ake miki ba kika yi shiru? ' Alhaji Haruna yace "Halima ku ɗan bamu guri dan Allah, zan mata magana" Ba musu suka fice, sedai kallo Ramlah ta dinga binsa dashi na tuhuma. Yace "Haba Baby, daga abu ya faru shikenan seki ɗaga hankalinki, haba Baby Amal, kiyi haƙuri kinji ai is not that painful, zaki warke kuma karayar nan is just an accident, zaki warke insha Allah, amma kidena kukan haka kinji" Ji tayi kamar ya kunna wuta a zuciyarta, tabbas ds da makami seta kasheshi kome za'ayi mata ayi, ga mahaifiyarta sam batayi hankalin gane abunda ya faru ba. Ganin tayi shiru, yasa ya janyo ya jikinsa yana faɗin "you make my day jiya, na daɗe ban samu mace kamarki ba, ki kwantar da hankalinki mucigaba da rayuwar mu babu wanda ze gane kinji" Amal tai shiru, taƙi buɗe ido zuciyarta ta dinga tafasa, ganin tayi shiru batayi magana ba, yasa seda yayi shagalinsa sannan ya dunƙulo bandir ɗin kuɗi ya zube mata. Seda yaje bakin ƙofa ze fita tace "idan ba'a gaɓa gwada maka kaidin mace ba, ka fara ƙirgawa daga yau zaka fara gani, wallahi Haruna sena maka abunda bazaka manta ba har abada, sena maka Baƙin tabon da yafi wanda kayi min, wallahi sena ƙulla maka makirin da duniya basu isa su kwance maka ba, zaka gane baka da wayo daga maina bazaka sake gwada akuyanci akan wata 'ya ba, ka saurareni....' . LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 112_113 Alhaji Haruna yai murmushi irin na tsofaffin 'yan duniya sannan yace "hmm Yaro man kaza, wato shi dai yaro yarone kam, ke a gwagwarmayar da nayi, babu kalar karuwar da ban gani ba, babu kalar barazana da kaidin matan da ban gani ba, nayi Aure Aure, nayi biye biye ba irin matan da ban gani ba, dan haka' yar ƙaramar barazanar ki bazata tsoratani ba, you better calm yourself down, ba'a kanki aka fara ba kuma ba'a kanki za'a ƙare ba, karki ƙarawa kanki ciwo akan ciwo, ki kwantar da hankalinki ki more ƙuruciyarki ki tara abun duniya" Wani gululun baƙin ciki ne yazo ya tokare maƙogwaron Amal, wanda yasa ta jan numfashi da kyar, ta rasa me zata yiwa Alhaji Haruna wanda zesa taji ta rage azabar da zuciyarta ke mata, ga karaya data samu ga rauni a kanta, ga uwa uba fyaɗe da yayi mata, kuma yazo ya tsaya yana gayamata maganar banza, ta lumshe idonta wasu irin hawaye na takaici da baƙin ciki suna bin gefen idonta. Tana jinsa ya buɗe ƙofar yai waje abunsa hankalinsa kwance wani nishaɗi yana ratsashi, dan ba abunda yake ji na damuwa ko tashin hankali a tare da shi dangane da abunda ya aikata. Kusan mintuna ashirin da fitarsa, Ramlah tai sallama ta dawo ɗakin, ta janyo kujera ta zauna a gaban gadon Amal, Amal tace  "Ina Mummy ne?" "Taje gida zata yi wanka ne, ta canza kaya" Amal ta jinjina kai, tana sake jin wani irin zafi a hannuta da ƙasanta, ta ɗan rintse ido tana girgiza kai, an mata illar da bazai taɓa gyaruwa ba ta gyara kwanciyarta tana ajiyar zuciya . Ramlah ta kalleta tace  "Amal meye tsakanin ki da wannan mutumin ne, naga fa kamar akwai damuwa a tare da ke? Meyafaru ne" Girgiza mata kai tayi tace "bakomai" Ramlah tace "ki gayamin gaskiya, ko akwai taimakon da zan iyayi miki, naga kamar akwai wani ɓoyaayyen al'amari a tsakaninku ke da shi, naji yana yiwa Mummy wasu maganganu ne marasa kan gafo, wai ai shi ya gani yana so, wai idan zata bashi ke yana so, ni ina tunanin ma wannan hatsarin da akace kinyi, gaba ɗaya na kasa yadda abun kamar wani shirin film ko tatsuniya fa" Amal taji kamar ta gayawa Ramlah gaskiya, se taga yin hakan tamkar tonawa kanta asiri ne, kuma idan harta nemi taimakon wani, to bata cika mace ba, yakamata ta nunawa Haruna tsantsar kaidi da makirci irin na 'ya mace. Amal ta dake tace  "Idan ma yana nufin sona yake, gaskiya ni bazan auri tsoho kamarshi ba, amma in dai zan fizgi rabona a jikinsa ai shikenan, zan iya biye masa nima in tatsi arziki som raina, Amma dan Allah ki temakamin da ruwan zafi mana, zan gasa jikina, dan duk ciwo yake min" Ramlah ta jinjina kai, taje samo mata ruwa me zafi ta rakata banɗaki, da ƙyar ta iya kintsa jikinta, saboda karayar hannunta, ga ciwo da kanta keyi, haka ta tsaya tai kuka me isarta a toilet sannan ta fito. Saleh ya jigata sosai, Alhaji Bukar yaje yaga halin da Saleh yake ciki seda ya ɗan tsorata, dan kar Saleh ya mutu, dan muddin Saleh ya mutu shikenan, abubuwa sun lalace, dan haka yasa aka kira likitansa, ya duba shi yai masa allaurai ya samasa ruwa, da ƙyar Saleh ya farfaɗo koda ya farfaɗo ruwan leda ɗayane se garau garau na shinkafa da aka kawo masa, mutumin daya kwana uku babu abinci, amma ya faraka a bashi bushshsiyar shinkafa da wake, abunka da me jin yunwa ya kama Abincin nan ya dinga turawa, sedai ba'aje ko ina ba yaji kamar yana cin duwatsu ne, dan haka ya dinga aman abincin nan, Saleh ya galabaita sosy, dan kwanakin nan gaba ɗaya a ɗaure yake a igiya kamar rago, dan haka kowace gaɓa tasa ciwo take masa, ga shedar igiya ta fito raɗa raɗa a jikinsa duk fatarsa tayi jajawur, ga ciwon ƙirji saboda dukan da yake sha da katako kamar Ɓarawo. Bukar ya kalli Saleh yace "wuya koda magani ba daɗi, ina fatan zuwa yanzu ka ɗanɗana kuɗarka kuma zaka bani haɗin kai, ka gayamin abunda na buƙata, ko kuma in sa a ninka maka wannan azabtarwar da ake maka. Shiru Saleh yayi beyi magana ba, se suka numfashi dayake na wahala, yayi zuru zuri dashi kamar wanda yayi amai da gudawa, maganar duniya Amma Saleh yaƙi cewa uffan. Me Adda yace "wai ba zakayi magana ba, semun ƙarasa sauke maka allon ƙirjinka?" Bukar yace "saurara tukuna, wannan idan aka yi ƙwaƙwaran yunƙuri ze iya mutuwa, kuma idan ya mutu ze jamin gagarumar asarane a yanzu haka, dan haka ƙyaleshi tukuna, zuwa anjima idan be faɗa ba, a kamashi kusamin kansa a ƙasa, ƙafafunsa a sama a samo ruwan zafi ku saɓulemin fatarsa dashi, ku barshi anan gurin " Saleh yabi Bukar da kallo, yana jinjina mugunta da zalunci irin na Bukar, haka Alhaji Bukar ya fice ya barshi a hannun su me Adda yayi tafiyarsa. Akayiwa Amal aiki a hannunta, aiki yayi kyau an ɗorata, mutane nata tururwar zuwa dubata a Asibiti, kullum a can Hajiya Halima take kwana, kwana uku da yin ɗorin likita ya sallameta, yace su dinga zuwa duk bayan sati biyu ana dubawa harya gama warkewa gaba ɗaya. Aka basu magunguna da sauran abun buƙata suka tafi gida, ma'aikatan gidan su Nura su Murtalah duk suka shiga suka dubata, suna fitowa Nura yace  "Allah ya ƙara, Allah yasa karta warke da wuri hannunma ya ruɓe, jakar matar nan da yake 'yarta ce ta samu matsala, ji yadda ta dinga zarya a Asibiti, amma lokacin da megida yana kwance a Asibiti, sefa ta ga dama take zuwa, ɗantane kawai yaita wahalar jinya, shiba ubansa ba ba komai ba" Isa yace "karkiya wa Amal wannan muguwar addu'ar, da dai waccan me ƙaton bakin ce Ramlah, ai gara Amal sau dubu da Ramla, dukda itama Amal ɗin ta iya rashin mutunci" Murtalah dake gefe yace  "hakane kam, Allah sarki, Allah ne kaɗai yasan inda megida yake, kaga kaman ma sum rufe babinsa, basa neman inda yake Yusuf kawai suke nema" Nura yace "Allah sarki, wallahi tsayinsa nakeji, koba komai ba ruwansa wallahi" Isa yace "kai dai bari, aiko ni da nake jin haushinsa da addua nake masa yanzu, na dinga duba yadda wasu abubuwan suk dinga faruwa amma baya magana, nan ze zauna in ta gayamasa baƙaƙen magana amma ko kallo bam isheshi ba, ima dana sanin wasu abubuwan da nayi masa wallahi " Nura yace " nima inayi, amma ka fini zaƙewa sosai, kaga nifa da ace wani ne wallahi ko dagaske sace yarinyar nan yayi, wallahi sena hana a kama shi, yasha wahalrta sosai wallahi, ta gara shi san ranta " Isa yace " Ai wannan akwai sa'a, duk garawar da take masa basu rabu ba, ya dinga mata biyayya, nifa wallahi ban yadda shiya sace ta ba, makirci ne kawai " Murtalah yace " makairci kamar yaya kenan? " "Nan Hajiya ta kirani falonta tace min, duk yadda zanyi inyi in nemo mata inda adireshin gidansu Yusuf yake, nayi nayi ya gayamin yaƙi, in ba makirci na Meza tayi da adireshin sa, kuma kun san wani abu, babu ma'aikacin da ake ɗagawa ƙafa a gidan nan kamarsa saboda 'yar masu gida" Murtalah yace "ƙwarai kuwa, dan ba ƙaramin ci musu mutunci take ba saboda shi, amma dagaske an saka nemo inda yake?" Isa yace "wallahi dagaske nake, sedai sam kamar yasan an sani fafur yaƙi gayamin, shegen wayone dashi kamar dila" Nura yace "ba ɗan sanda bane, kai ka isa ka masa wayo nan da nan, ai kaima kasan baka isa ba" Isa yace "kamar ya ɗan sanda wai?" "Au kai a labaran da aka sanar ba gani bane, to ɗan sandan farin kaya ne, aikin bincike yake a gidan nan" Isa yace "la'ilahaillalah illalah, dagaske? Yo aini ban sani ba" Murtalah yace "to an barka a baya, baka san kanun Labaran ba kam, ɗan sanda ne ai shiyasa hankalin mutan gidan ya sake tashi" Isa yace  "tir ƙashi, amma wannan anyi munafuki, shine be taɓa gayamana ba, muka zauma dashi muyi ta sakin baki" Nura yace "to mutan gidan ma basu sani ba, balle kai ance maka jami'in sirrine kawai seya zo ya fara gayamaka ai shi ɗansanda ne? Saboda be san aikinsa ba kobe san ciwon kansa ba? Kai dai Isa naga ranar sa zaka waye" Haka suka cigaba da surutansu dai. Ita kam Amal ta tsunduma a kogin tunanin me yakamata tayiwa Alhaji Haruna ta huce, da wani makami yakamata ta yaƙeshi ta ɗau fansar budurcinta daya rabata dashi? Sam ta kasa ko da cin Abinci, se uban tunani da koke koke, idan ta kulle kanta a ɗaki se tayi me isar ta, dan sam bata san me yakamata tayi masa bama, ta gama barazanar da zata yi masa amma bata san meye zata yi masan ba ta huce, gashi ta kasa gayawa kowa wannan labarin balle ta samu shawara, gani take zata tinawa kanta asiri ne a banza a wofi, tazo ta kasa samun mafita kuma, ta kalli hannunta dake nan naɗe da bandeji ga goshinta ma, ta lumshe idanunta tana jin zafi a zuciyarta. Ramlah ta shigo ɗakin tace  "Amal kizo ga matan Alhaji Harun nan sunzo dubaki" Kallon Ramlah tayi kamar bata gane me tace ba, Ramlah tace "ko bakiji bane?" Amal tace "Ai abunne naji wani iri, sun sanni ne daza suzo dubani? Ramlah tace "oho muku, sun san Mummy ai, idan ke basu sanki ba" Amal tayi tsaki tace "ba inda zani" Ramlah tace "meyasa?" "haka kawai, bazan zo ba, ki koma ki san abunda zaki gaya musu" Tai maganar tare da kwanciya, Ramlah ta ɗan taɓe baki ta juya ta fice. Amal ta sake jinjina rashin kunya, da iskanci irin na Alhaji Haruna, saboda ya gawurta har matansa ya turo su dubata, to suce mata me? Ji tayi kamar taje ta tona masa Asiri a gurinsu, amma meye shedarta? Taja tsaki tai shiru tana ci gaba da tunani. Kamar wadda aka mintsina ta miƙe da sauri, dan seda ta kusa fama hannunta, ta tako a hankali ta fito, a hanya suka haɗu da Mummy, dan Ramlah ta gaya mata saƙon Amal, Mummy tace  "da meyasa kikace bazaki fito ba?" Amal tace  "gaba ɗaya jikina ciwo yake, bana son hayaniya ne, sedai kuma naga babu daɗi, shiyasa nace kawai bari inzo mu gaisa" Mummy tace "da dai yafi" Suka fito gaba ɗaya falon, uwargidansace se Amaryarsa wadda take yarinya sosai, Amal ta ƙaraso suka gaisa, sukayi mata ya jiki, Amal ta amsa tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Da zasu tafi uwargidan tace  "ga mukullin mota yace a baki, gata can yace a baki tunda taki ta lalace, Allah ya ƙara sauƙi" Amal tai murmushin takaici tace  "Amma fa nagode sosai, ai masa godiya ace masa naji daɗin motar nan fa, sannan ina nan tafe karɓar mukullin gida kuma" Basu kawo komai ba, tunda ce musu yayi 'yace a gurinsa tunda sun san Hajiya Halima, Amal ta karɓi lambar wayarsu, tace sa dinga gaisawa. Nurat tana zaune suna hira da Mummynta, ta gwada layin Anwar harta gaji amma shiru bata shiga, tun abun baya damunta har ya fara damunta, ta kalli mahaifiyarta tace "Mummy fita nake son yi fa" "Kije ina?" "Mummy duk inda ta kama, tunda aka samin doka yau kwana nawa ban fita ko ina ba, gashi ina buƙatar in ɗan fita ɗin in rage zafi, kullum ina cikin gida kamar wata mara gaskiya" Mummy tace "nidai babu duwana, duk abunda kika jawa ka ki shikenan ba ruwana, kin san yadda kuka ƙareta dashi wancan karon dai" "Mummy gidan Daula nake son zuwa, ina sin jin ko lafiya, layin Yaya Anwar baya shiga fa Sam" "gidan Daula ko? Sekin dawo tunda baki da hankali" "Mummy ba haka bane, ai gaida me gaishe ka ko baze amsa ba, amma tunda hakane, bari in jida zuwan bdk Khalil, idan yazo ya biya ya dubamin ko lafiya" "Ke wani Khalil ɗin, baki san ranar da yazo ya tarar dashi ba kirana yayi yana masifa ba, wai zaryar me Khalil yake masa a cikin gida ba? Wai in dakatar da shi da zuwa ba" Nurat tace  "to Mummy ke kuma baki ce masa komai ba, sannan me Khalil yayi masa?" "Oho kin san halinsa na rashin gaskiya ai, shi duk wani motsi seya zata bin diddiginsa ake, shiyasa kullum bashi da nutsuwa ai, shima dole zanyi masa waya, ya rage yawan sintir a gidan nan, ya bari se an kwana biyu yazo" Nurat ta dafe kai tace  "Ohh my God, ba dai gudun tinon Asiri yake ba, Insha Allah ya gamu da shi kenan, in Allah ya yadda se asirinsa ya tonu" "Ke rufemin baki, kar yazo ya tarar dske kina wannan maganaganun, ya zata wani abun muke shiryawa" A fusace Nurat ta miƙe ta e  "to ya zata iɗn mana Mummy, na gajiya walilahi, am tired" Ta juya ta bar falon ranta a ɓace, zuciyarta na wani irin tafasa tana tururi. Yusuf na zaune yana zaune, Widad na kwance akan cin yarsa, yana ta wasa da gashin kanta, tana masa hira sedai gaba ɗaya hankalinsa baya kanta, ya tafi can duniyar tunani, ƙirjinsa nata bugawa haka kurum, yaka sa gank dalikin bugawar ƙirjin nasa, "Yoseef" ta kira sunansa, da sauri ya dawo hayyacinsa yace "Na'am" "Me kake tunani ne?" Yace mata 'bakomai " Ta gyara kwanciyarta tace "Yuzarsef, kwana biyu Saleh bezo na, nifa hankalina yayi gida, gaba ɗaya na ɗan fara damuwa tunda yake zuwa be taɓa cemin komai akan mahaifina ba, zuciyata na son ganin mahaifina, ina yawan mafarkinsa ina son jin abunda ke faruwa gaskiya" Seda gaban Yusuf ya faɗi, dan Saleh ha tabbatar masa babu wani sahihin kabadi har yanzu akan ɓatan mahaifinta, gashi ita bata sani bama, ya dake yace "tabbas nima ina ta fama da kokwanto a raina, ina son sanin meke faruwa a gida, gashi naga kwana biyu Saleh bezo ba" Tace "hakane, dukda ni ba shiga sabgarsa nake ba, amma dole zan tambaye shi ya Daddyna yake, in dai lafiya ƙalau ne, baze jure tsawon wannan lokacin be gannj ba, dase yazo har nan kota halin yayane, amma tunda naji shiru something is going wrong somewhere, gidanmu nake son komawa " " Insha Allah nothing is wrong anywhere, komai yana tafiya dai dai, am yakamata mu koma gida haka kam" Tace "Allah yasa hakan" Yace "Ameen, but Baby ta yaya zamu tabattarwa da al'umma Aurenmu, meye shedarmu?" Widad tace  "Allah" Yace "hakane Allah sheda ne, amma baze yuwu mu gayawa mutane haka ba, dole mu nuna shedar aure mukayi, tunda au can babu wansa yasan hakan" Widad tace  "karka damu, Saleh ya sani, ga al'ummar garin nan da muka zauna tare dasu, suma sun isa sheda ai" "Hakane, Allah yayi mana jagora" Tace "Ameen" Alhaji Musa yana zaune a ɗakinsa yana cin Abinci, ya ɗau waya ya kira Nurat yace yana son ganinta a ɗakinsa, Mamanta ta kalle shi tace  "lafiya kuwa? Ina fatan dai ba wani laifin tayi maka ba?" "ina ruwanki ne? Nida 'yata bazan kirata ba, ki zuba ido kawai" Tace "Ai gara in dingayi ina bin ba' asai, saboda naga kai abun naka se a hankali gaba ɗaya" Nurat tayi sallama ta shigo da dogon hijjabinta  a jikinta, yace "Bacci kike ne?" Ta girgiza masa kai tace "A'a salla nayi" Yace "madalla fatan a nayiwa Daddy addu'a" Ta jinjina masa kai yace "yawwa 'yar gidan Daddy, dama ba wani abune yasa na kiraki ba, zan sanar dake jn the next couple of weeks zaki koma Karatu" Nurat tace "A ina kenan?" Yace "can inda kika baro mana abroad, na nema miki imperial College London, kije kiyi business administration ɗin da kike so a can" Girgiza masa kai tayi tace "Amma Daddy ai ba haka mukayi da kaiba, ka tambayeni nace maka ni a Nigeria nake son in cigaba, ka amincemin kuma yanzu kace ba haka ba" Yace "look Nurat, ina nema miki sauƙi ne da kuma safe environment, inda zakije kiyi karatun ki cikin nutsuwa da kwanciyar hankali" Tace "Nan ma akwai nutsuwa da kwanciyar hankali ai, ni dai kawai ka ƙyaleni a nan, bana son zuwa" Aikuwa ya harzuƙa yace "ke, nine zance ga yadda za'ayi kice ke ba hakaba? Waye ya haifi wani tsakanin nida ke?" Nurat tace  "kai ka haifeni, amma kaima ka cika Alƙawari mana Daddy, baka gudun yadda tarbiyyata zata kasance, ni ina can ku kuna nan ni gaskiya bazanje ba" Ya kalli Maman Nurat dake gefe tana jinsu yace  "wato ke kike ziga yarinyar nan take rashin mutuncin da taga dama ko? Idan ba hakaba ya za'ayi ina magana tana magana?" "Malam babu ruwana ni, 'yarka ce yau da gobe ai tafi ƙarfin wasa, ka fiye son kanka da yawa, shiyasa tun yarinyar nan na maka biyayya harta zo ta dena yi maka saboda son zuciyarka, kuma nima gaskiya ban yadda inyi nesa da ita ba, tunda mun baro ƙasar ma meye kuma ita za' a maida ita" Alhaji Musa yace "lallai ba shakka, na ƙara tabattar da cewa ke kike ziga yarinyar nan, in faɗa ki faɗa tana gani ai dole itama ta fara, to bari kijin in gayamiki tafiya daram, seta tafi dole ta bar ƙasar nan taje inda na nema mata karatu" Nurat ta fashe da kuka tace  "ni gaskiya bazani ba, kuma idan aka takura sena je, wallahi barin gidan nan zanyi, dama naga yanzu ba'a ƙauna ta, tunda har yunƙurin rabani da rayuwata akayi" tai maganar tana ficewa daga falon, tana ji yana ƙwala mata kira amma tai banza dashi tai tafiyarta ko waigowa ba tayi ba. Yusuf yana kwance har wajen shaɗayan safe, idonsa a lumshe yayi rigingine yana jin yadda gabansa ke cigaba da faɗuwa akai akai, Widad ta shigo ɗakin ta fito daga wanka tace "Yoseef, wai ba zaka tashi bane haryanzu shaɗayan rana, seka sa Hari tazo tana gayamin magana ko? Ina jinta shekaranjiya wai na fiye jaraba goma na safiya ina rufe ƙofa saboda shegen sa ido irin nata" Yusuf ya kwashe da dariya yace  "Ai gaskiya ta faɗa ba ƙarya ba, hakane abunda ta faɗa waike dole sekin samo Baby ba" Widad ta buɗe baki tace  "lallai Yoseef sannu, hakama zakace ko? Kaifa kace in rufe ƙofa sanyi kake ji, shine zakamin sharri"? "Ba wani sharri malama, ni bance ki rufe ƙofa ba" Widad tace "Ikon Allah, ni nama rasa me zance maka" "dole ki rasa mana, kuma yau bazan kwana akan katifarki ba, a ƙasa zan kwana" "Kaje kaita kwanan mana ina ruwana?" "A'a dai karkizo kina min kuka, wai kai Yoseef meye haka? Dan Allah kazo ka kwanta" yai maganar yana kwaikwayon muryarta. Tace "Nikam na shigesu a gurinka, Allah ya shiryeka" "to kice ba'ayi haka ba mana" "Aini bazan sake magana ba, nayi shiru" Yai murmushi ya maida idonsa ya lumshe, ta ɗan ƙura masa ido, ya ɗan faɗa sedai masha Allah Yusuf ba dai kyau ba. Tai murmushi tace "Mutum da hanci kamar an zana cartoon" Yace "Kyau yai miki yarinya, shiyasa kike min ba'a" "Ba wani kyau a nan gurin, wannan zanƙalelen hancin kaman cartoon" "Kyaji dashi dai, yabawa kika yi" Tazo tasa hannu ta matse masa hanci, Yusuf yace "ko ki sakarmin hanci, ko kuma yanzu in ɓaro ɗan dake cikin ki" Da sauri ta cika shi tace 'yi haƙuri " Yai dariya yace " Yarinya baki da komai a wannan cikin naki " Ta murguɗa masa baki tace "aini nasan akwai" Tai maganar tana tura baki, yayin da ya bita da kallo yana jin sonta na ƙara ninkuwa a  zuciyarsa, idan ya tuna lokacin da take garashi da izza da rashin mutunci, ga gefe guda azabtuwa da soyayyarta daya dingayi ba tare da ta sani ba, idan akace masa akwai rana da zata zo su kasance a haka baze yadda ba, amma shine zaune da ita a ƙarƙashin inuwa ɗaya ta Aure, suke zaune ba tare da ya ɗaga masa hankali ba, wani farinciki ne ke ratsa zuciyarsa, tabbas da Widad ta rayu da masoya na gaskiya, mussman tare da mahaifiyar ta ba zata yi wannan izzar da jin kai ba, sedai rashin masoya, da kuma tsantstsar zalunci da butulci da aka gwada mata yasa tayi wa mutane gaba ɗaya kuɗin goro mussman talakawa. Saleh gaba ɗaya ya sadaƙar, jira yake kawai suzo su fara gana masa azabar da Bukar yayi umarni, sedai basu yi masa komai ba sedai ɗaɗɗaureshi da suka kuma yi. Yana zaune a inda yake aka buɗe ƙofar ɗakin da yake kwance a ciki, ya ɗaga kai seya ga 'yan sanda sun shigo, tare da Alhaji Bukar, ya nuna musu shi yace "gashi nan, ku tuhume shi yasan inda suke, kuyi masa duk wata izaya da duk wani abubda zesa ya faɗi gaskiya, karku saurara masa dan Allah" Ɗaya ɗan sandan yace "karka wani damu, zamuyi abunda ya dace"  suka kwancewa Saleh wannan igiyoyin suka ɗauke shi suka sashi a mota suka tafi dashi. LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 114_115 Saleh dai ne ce komai ba, yana jin yadda ake tafiya dashi a mota 'yan sanda, a galabaice yake dan haka be san inda suke tafiya ba, harabar police station akayi parking, aka fito da Saleh, yana tangaɗi haka aka tankaɗa shi cikin cell aka ƙulle. Duk da yamma ce amma sauro har ya fara shagali a gurin nan, ga zafi a gurin kamar oven, haka Saleh ya baje a ƙasa ƙirjinsa da cikinsa na masa ciwo kamar zasu tsage, saboda duk daya sha da katako. Yana jin wani ɗan sanda yayi sallama, sauram suka dinga sara masa, ɗaya daga 'yan sandan da suka ɗakko Saleh yace "Oga gashi nan a cell, munje mun ɗakko shi" Ɗan sandan yace  "ok shikenan, ku rubuta statement ɗinsa" "Yallaɓai tome zamu rubuta?" "Kai baka san me zaka rubuta ba, ku rubuta bayani akan an same shi da laifin haɗa kai da Yusuf, sun sace 'yar gidan Nasir Daula, sun ɓoye su, ka dai rubuta abunda yakamata" Ɗan sandan ya sara masa yace "ok sir, za' ayi yadda kace" "Yawwa that's very good, and a matsa shi yadda yakamata ya faɗi abunda ake nema a gurinsa" "Yes sir, za'ayi abunda kace" Yace "good" Daga nan ya wuce ya shige office ɗinsa. Hankalin Nurat ya tashi sosai, ganin cewar dagaske mahaifinta yake ze raba ta da ƙasar, itama tayi ɗamarar wannan karon zata bijire masa, kome ze faru se taga ƙwal uwar daka, se taga ƙarshen abunda mahaifinta yake yi, dan barin mutum irinsa suna cigaba da abunda suke so a doron ƙasa hatsari ne ga al'umma, wataran za'a iya wayar gari mutanen kirki su ƙare, ta ɗau wayarta ta kira Khalil, Khalil ya ɗaga yace  "Hello my dear, ya akayine any news?" Nurat tai ajiyar zuciya tace "bad news brother, Daddy ya dage akan cewar wai sena tafi imperial U. K Inyi karatau a can, me Daddy yake nufi dani ne?" "Calm down dear, make your statement clear please, kamar yaya imperial Collage, ke kaɗai zaki koma UK ɗin kiyi karatu, wanda kika yi a baya be isa ba" "Nima shi na gani brother, shifa yayi min alƙawarin zanyi school a Nigeria, a Nigeria zanyi high institution, Amma kawai yazomin da wannan maganar, da alama yana zargina ne da fara bin diddiginsa, ni kuma gaskiya i won't tolerate it dear, gaskiya zan bijire" Khalil yace "subhanallah, Nurat don't say that again, haba Nurat na sanki da biyayya da haƙuri, me zesa ki fara faɗar haka kuma? Haba Sister na" Kuka Nurat ta fashe dashi tace  "Broz Khalil, iya biyayya da haƙuri kasan nayi, nayiwa Daddy biyayya yadda yakamata, nayi ƙoƙarin kasancewa a cikin 'ya' ya nagari masu haƙuri, tun taso wata fa kullum cikin tsangwama da kyarar mahaifiyata yake, amma ban taɓa kulashi akan hakan ba, Brother babu ɗan daze dinga ganin mutuncin duk mutumin daze dinga cin zarafin mahaifiyarsa, komai kusanci da soyayyar dake tsakaninsu kuwa, amma na share na ɗauke kai, nake masa biyayya, ni da mahaifiyata mun masa biyayya, amma baya gani Khalil, baya gani kullum cikin zagi da cin zarafin mu yake, har gara ni yana ɗagamin ƙafa, akan mahaifiyata lokaci yayi da zan nuna masa nima 'yar halak ce, zan nuna masa ni ma' yace, wallahi bazan sake masa biyayya ba nagaji Khalil " Khalil yace " Calm down, calm down my dear, i feel your pain Baby, kiyi haƙuri dan Allah, nasan me kike ji a zuciyarki, amma dan Allah karki bijirewa mahaifinki, hakan ba halinki bane ba" "Yanzu na koya, kuma shine ya koyamin, kuma zega canji tabbas, na masa biyayya har akan abunda be dace ba, haka kake so in cigaba da binsa yana jan rayuwata data mahaifiyata a ƙasa?" Barrister Khalil yace  "kamar yaya ya saki abunda be dace ba?" Cikin kuka tace  "Khalil, Daddy da farko ni yasa in hilaci Widad, aka sumar da ita za'a sace ta, Yusuf ya ceceta, wani abunma baze faɗu ba ni kawai ka ƙyaleni, idan kuma ya dage sena bar ƙasar nan wallahi sena kawo masa ɗan shege ya raina a cikin gidansa na rantse da Allah " " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Nurat kin san me kike faɗa kuwa? Ko kin fara shaye2 ne ban sani ba" Ta ƙara sautin kukan ta tace "idan ma ban fara ba ina daf da farawa, dan wallahi ya takuramin zan bar masa gidansa in shiga duniya, ko in tafi England inyi irin rayuwar da yake ganin gara inyi irinta da ya kasa cinma nasa burin" Khalil ya kwantar da muryarsa yace "kina jina Nurat, am sorry kinji, nasan a irin matsala da damuwar da kike ciki, amma kin san zukata nawa ne zasu shiga garari idan kika lalace? Mummynki da kike wannan damuwar saboda ita, ya kike gank idan taga tilon 'yarta ta faɗa mummunar rayuwa? Ya kike tunanin shi masoyin naki ze kalle ki idan kika koma mutuniyar banza? Family duk zasu shiga damuwa idan suka ji labarin yarinyar da suke so, suke ji da ita ta shiga wata rayuwa daban, dan Allah kiyi haƙuri ki bar wannan maganar " " Brother idan na bar wannan maganar wacce zanyi? Am tired wallahi na gaji dayi masa biyayya, Khalil abun ba sauƙi fa, dama mutumin kirki ne da sauƙi" "Nasani Nurat, ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah zan shigo gidan naku, zanzo muyi magana amma ki dena kukan nan please, kuma karki sake faɗin wannan maganar kinji Light" gabata ne ya faɗi jin yace mata Light, sunan da Yusuf ke gayamata, ajiyar zuciya tayi tayi jifa da wayar, tana ci gaba da rushewa da kuka. A hankali hannun Amal yana warkewa, an kwance mata bandejin kanta ma, se hannun da haryanzu akayi hangin ɗinsa a wuyanta, yanzzhma ta fito daga wanka tana tsaye a gaban madubi, daga ita se towel kanta a tsefe, ta baje gashin kanta, ba laifi gashinta yana da tsawo, ga hannuta sagale a wuyanta, ga goshinta inda yayi tabon ciwon da Alhaji Haruna yaji mata, ta dinga ƙarewa kanta kallo a mudubi. A hankali tace "dubeni, mace har mace, bani da makusa sedai an gurguntamin rayuwa, an rabani da mutuncina saboda zalunci, kuma ya biyoni da wasu tarkacen banza saboda ya rainamin hankali, bayan tabo na sarari da yayi min, ya barmin na zuciya me matuƙar ɗaci da baze goge ba, me zanyiwa mutumin nan in huxe, wace irin illa zan masa daze dasa masa baƙin ciki a rayuwar sa ne? Me zanyi ne Amal kiyi tunani ƙwaƙwalwarki bata ja Sam " Ta dafe kanta ta fashe da kuka, tana tuna yadda ya suka dinga kokawa, da muguntar da yayi mata yacinma burinsa, zubewa tayi a gurin tana wani irin kuka, me tsuma zuciya " Duk laifinki ne Mummy, laifin kine, nace ba zani ba kika ce se naje, Mummy why? " Jikinta har rawa yake saboda kuka, dukda daga wanka ta fito amma ta haɗa gumi, ga hawaye ga majina se shesheƙa take. Ramlah ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune a ƙasa, idonta yai ja tana kuka. Ramlah ta ƙaraso da sauri tace " ke Amal lafiya kuwa? Meye haka? Meye ya same ki" "Bakomai" "bakomai kamar yaya? Kalle ki fa" Tsaki Amal Tayi tace  "excuse me please, dan Allah ki bani guri, ina son kaɗaicine" "wane irin kaɗaici kuma? Anya kina hayyacinki kuwa?" "Na miki kama da Widad ne, balle kice na haukace? Kawai ki fita ki bani guri" "Amma Amal" "Dan Allah ki fita ki ƙyaleni, kad in haɗiyi zuciya in mutu, dan Allah ki fita!" Tai maganar cikin kuka, Ramlah na fita taje ta dstse ƙofarta ta kwanta akan gadonta ta cigaba da rera kukanta, tana jin Ramlah ta kira Mummy, suka dinga buga ƙofar amma tayi musu banza kamar ba taji ba. Bukar ya kira Alhaji Haruna, Ya ɗaga wayar suka gaisa, Bukar yace "kunyi waya da Musa ne?" Alhaji Haruna yace "A'a gaskiya, na kwana biyu bamuyi waya ba" Alhaji Bukar yace "ok, na zaci kunyi wayane, haryanzu be ce mana komai ba akan batun wanda ze saka mana hannun, kuma yace mu saurareshi zuwa Laraba, anjima zamuyi meeting kota zoom ne, sannan ya batun takaddar da aka ce wannan yaron ya bari? Ka karɓo mana ɗinne kokuwa?" Alhaji Haruna yace  "eh na karɓo, naje har gidan da kaina naje na karɓo takaddar" Alhaji Bukar yace  "good, kasan duk wata sheda da zesa a ganemu, dole mu ɓatar da ita kar wani ya samu, dan haka ka kawomin takaddar nan" Yace "shikenan, Insha Allah zan kawo maka ita, sannan zan sanar dasu batun meeting ɗin nan da kace" Alhaji Bukar yace  "to shikenan, se kazo" Alhaji Bukar ya ajiye wayar, ya miƙe ya bar ɗakin dayake, dan ya manta da ya karɓi tajaddar yazo da ita nan gidan ko kuma a can ya barta gurin da ta bashi?. Hindu tana tsakar gida, suna ta aiki a tsakar gida, Hanne tana gefe tana gyaran wake zasuyi alala. Hari tace  "sannu da aiki Hanne, Allah ya kaimu bikinki mu kira masu kiɗan ƙwarya muyi ta juyi a gidan nan" Hanne ta taɓe baki, dan ita sama gaba ɗaya haushin Auren nan ma take ji, dan Yanzu haushin mijin da zata aura takeji, dan gani take bashi da komai idan ta kalli Yusuf, ita dai tana son Yusuf sosai, tana jin ina ma ya aure ta, da tafi kowacce mace dace a ƙauyen nan, da yana ɗan kulata amma yanzu ya dena, saboda wannan koɗaɗɗiyar matar tasa me kama da Yahudawa. Hindu tace  "Allah dai ya kaimu bikin nan ds rai da lafiya, ban san wane irin shagali zanyi ba, nima sena gyagije nayi shagali, idan kika tattara kika tafi in gaje gurin kwanciyar ki da nawa, Abinci ma zan haɗe nawa da naki ne, dama yanzu ba ƙoshi nake ba" Hindu Tayi maganar cikin sigar wasa da zolaya. Amma Hanne ta karkace ta kyaɓe baki, ta kalli Hindu tace  "aifa dama ina zaki ƙoshi tunda mayya na gidan? Ai gara in tattara in bar miki gidan ki cigaba da haɗa kafaɗunki dana iyayen mu, tunda dai ke kinfi kowa baƙin jini, babu wanda yake sonki balle kisa ran zakiyi aure ki bar gidan nan, ai se kiyi ta zaman gidan ki ƙare ki tsufa a gida, mujiyar garin nan, shikenan mutum ba zuciya balle ya samo wanda ze rufa masa Asiri ". Ai tuni idon Hindu ya ciko da hawaye, ita har ga Allah wasa tayi wa Hanne, amma harta fara yan kamata baƙaƙen maganganu da cin zarafi, Hanne na ɗagowa suka yi ido huɗu da Yusuf, da alama duk yaji abunda ta faɗa, sekuma ta shiga kame kame, dan wata irin kunyace ta kamata, bece komai ba ya sa kai ya fice, dan be fiye son shiga sabgar iyalan gidan ba. Yana fita Widad ta fito tsakar gidan nan, taga yadda Hindu ta nutsu tayi shiru, ido duk ya tara hawaye saboda zafin maganganun Hanne. Widad tace "ke Hindu, wai ita wannan banzar 'yar uwar taƙi haifarki tayi? Haifarki Tayi da zata dinga gaya miki magana kina jinta? Wai wane ɗan matsiyatan zata aura a garin nan da har take miki wannan gorin haka? Wanda zata aura ɗin ma ya kai a kira shi namiji da take miki gori a kansa "? Hanne tana hura hanci, cike da ƙauyanci da jahilci tace " Wallahi, tallahi nafi ƙarfin auren matsiyaci, niba matsiyaci zan aura ba" "wallahi kika bari nazo inda kike, na shaƙeki se na jefa ki a rijiyar nan, saboda me zaki takurawa yarinya dan bata magana, dan kinga tana da haƙuri, wallahi ki kiyayeni akan ɓata mata rai" Hanne tace "idan anƙi fa?" Wata irin zuciya ce ta kwashi Widad, sedai Hindu tai saurin riƙeta tace  "A'a Amarya yi haƙuri ƙyaleta kawai" Widad ta harzuƙa matuƙar gaske, ji take tamkar ta jefa Hanne a rijiya, mussman idan ta tuna yadda take juya manyan attajirai masu ji da kansu, amma wata kucakar 'yar ƙauye na gayamata magana, ƙwafa kawai tayi tace  "ba alfahari ba amma Wallahi da kin san wacece Widad, da baki isa ki yadda in haɗa ido dake ba, dan wallahi ko masu gyaran gadon baccina sun fiki kyan gani, ki zuba ido zakiga mijin da Hindu zata aura, Jahila kawai" Ta wuce ɗakinta tana huci, duk wannan budurin Gwaggo da Hari basa nan akayi shi, amma abun yana damun Widad taji an taɓa Hindu, setaji kamar ita aka taɓa, danma ita Hindun ce shashasha take tsayawa ana mata wulaƙanci. Amal kam wani tunani tayi a ranta, dan haka ta miƙe da ɗan sauri, ta fita falo, Mummy ta kalleta tace "kinga damar buɗewa yanzu?" Amal tace  "Mummy Ramlah ta kasa fahimta tane, wani lokacin idan ina cikin jin zafin ciwo, bana son kowa a inda nake, nafison kaɗaici amma se a takuramin, kun kasa ganewa" Mummy tace "madalla, shine nake ta magana kika ƙi buɗewa" "Am sorry, bazan sake ba insha Allah" "Hmm ai shikenan, ya hannun naki yanzu?" Tace "da sauƙi, Mummy dan Allah aramin wayarki zan transfer ɗin kuɗi, ni banki sun hanani wai ba network" Ba musu ta miƙawa Amal wayar, Amal ta karɓa ta koma gefe, ta tura lambar Alhaji Haruna wayarta, ta bata wayar tace "Mummy, ga wayar nagode" Ta koam ɗakinta, tana zuwa ta kulle ƙofa ta zauna akam gadonta ta kira Alhaji Haruna. Lokacin yana tsaka da bulayin neman takadda, ya ɗaga suka gaisa dashi, sannan tace  "Naga saƙonka, amma meyasa kwana biyu ba kazo ka dubani ba" Se ynzu ya ɗau muryar ta, yai murmushi yace  "nima naji saƙonki, ance bayan mota zakizo karɓar gids ma" Tace "eh hakane, ko idan na dawo bazan samu ba" . Yace "idan kika dawo ina?" "zuciya ta, ta fara rayamin kawai idan na warke zan bazama in nemi arziki, in more ƙuruciya ta, idan ka shirya nima a shirye naake zan dawo gareka, tunda aikim gama ya gama tunda fari" Yai wata shegiyar dariya sannan yace "ni zaki yaudara, ko har kin manta abunda kika gayamin a Asibiti, kaina yana ja sosai dan haka abune mawuyaci kiyi galaba a kaina, tabbas naji daɗin kasancewa dake sedai bazan sake amincewa dake ba, tunda kikayi wannan fueucin, ki sake shawara kinji 'yan mata, idan da gaske kike ki bazama ki kama wasu alhazan, nikam na gama muma na biya tunda na bada motar miliyoyi" Bata sanma yadda akayi ta ajiye wayar ba, tana jera ajiyar zuciya kamar wadda tai gudu, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunaninta, ashema matan suna suka tara, ba kowaccece ke iya kaidin ba, shi kansa shirya makircin ba abune me sauƙi ba, tai sharkaf da gumi tana sake tunanin wata hanyar. Yusuf na dawowa Widad ta manta da damuwar da take ciki, sedai duk da hakan seda ya gane, yace "Maman Baby, ya akayi ne naga kamar ranki a ɗan ɓace yake" Tace "A'a ni ba abunda akayi min, Ina ɗan tunani akan Hindu ne, ina ma Megari ze bani ita idan mun koma gida" Yusuf yace "gaskiya abune me wahala, ya ɗau 'ya ya bamu alhalin bamu da wata dangantaka a tsakaninmu" Ta jinjina kai tace "hakane, Gaskiya nifa na damu Saleh yazo ayi wacce za' ayi, na fara gajiya hankalina yayi gida sosai fa" Yusuf yace "ki kwantar da hankalinki, nima shi nake jira yazo, muji abunda yakamata ayi" Tace "shikenan, Allah ya kawo shi" Yace  "Ameen" A gurin 'yan sandan ma babu sassauci, baƙar wahala Saleh yake sha, dan yana kyautata zaton an masa illa saboda duka, dan a nan ɗinma' yan sanda ke sa kulki, suyi ta dukansa izaya daban daban wai lallai seya faɗi inda su Yusuf suke, ga rashin Abinci gashi ko Najasa ne sedai yayi a nan, nan da nan Saleh ya fita daga hayyacinsa, ya canza kamanni fuska duk ta kumbura, ko ina rauni me yake zubda jini, sun doddoke masa ƙafafuwa da ƙyar yake iya miƙewa. Da Safe Yusuf yana kwance akan cinyar Widad, ta samu comb se jagwalgwala masa sumar kansa take yi, shi kuma yana lumshe ido, can yace  "gaskiya ki ƙyalemin gashina mana, haba se izaya kikemin a kaina" Ta ɗan tura baki tace  "kitso fa zan koya" "To aini na gaji se jagwalgwala min suma ake, ga zafi banda ma tsabar rigima irin taki ta ina za'a kitsa sumata?" "Ni dai ka ƙyaleni" Yace "shikenan, Allah sarki ni, gaskiya idan na kuma jin zafi sena rama, sena aske wannan gashin naki da akewa mutane iyayi dashi" Tai murmushi tace "daka temakeni, dan ba dan babu kyau ba sena rage shi, kuma idan ka aske ai kanka kayiwa, kaine kake wasa dashi ai" Yai murmushi yace "kuma fa hakane, to na fasa askewar" "A'a gara dai ka aske ɗin" Hindu Tayi sallama kawo musu Abincin Safe, akayi mata izinin shiga tana shiga ta tarar da Yusuf kwance akan cinyar Widad. Ta sunkuyar da kai cikin matuƙar jin kunya, Widad tace  "sarkin kunya, idan na aura miki ɗan birnin haka zaki dingayi masa?" Hindu ta juya da sauri tana murmushi, ta bar ɗakin, Widad tace  "Yuzarsef, wallahi da ina da Yaya, ko wani ɗan uwa da babu abunda ze hana in roƙi ya auri Hindu, she's very kind and innocent" Yusuf yace "hakane tana da kirki kam, ga nutsuwa" Yusuf yaga abun na Widad ba na ƙarewa bane, dan haka ya tashi daga cinyarta yace  "ke nagaji, kaina se zafi yake duk kin jagwalgwala min suma" "ni kayiwa haka ko? In ƙara ganin ka taɓamin gashi ni da kaine, kuma ma insha Allah ta mace zan haifa, saboda in dinga mata kitso ta zama ƙawata kuma" Yusuf yace "sannu sarkin shirirta, da shirme, ga tsabar ƙuruciya mutum baze gane hakan ba, se ya zauna dake, to ni bame yiwa 'yata kitso balle a jagwalgwala mata kai, idan kin haifi namiji nakine, mace kuma ta wace" "A' a ban yadda ba, gaba ɗaya nawane, bayan kace baka son Baby" Yusuf yace "Nina ce miki bana so? So kai amma ki bari ki samu cikin tukuna, sekimin iyayi da tsari" "wai dan Allah dagaske bani da ciki?" Yace "zan miki ƙarya ne? Kin manta shekarata biyu ina medicine, baki da komai madam" Ta kwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "insha Allah ina da shi" "Seki zauna kiyi ta imagination ai, miƙomin abincin nan inci" Ta ɗakko kwananon Abinci ta miƙo masa, suka ci tare suna hira. Yusuf yace "idan na dawo da daddare, kwaɗon gurji da zogale zan mana, zaki ci?" Widad tace "Sosai ma, ranar Gwaggo tayi naci da daɗi Sosai" Yusuf murmushi yace "to kwaɗayayyiya" "Eh anji ɗin" A haka suka yi sallama, yana ta tsokanarta, kamar karsu rabu. Duk iya dubawar da Saleh zeyi, yayi amma ya rasa takaddar nan, ya duba ya duba amma takadda tace ɗaukeni inda ka'a ajiyeni, gashi yacewa Bukar ya karɓo takaddar nan. Ya koma guest House ɗinsa, inda suka dinga kokawa da Amal, ya dinga duba takaddar nan, yai tsai gana dubawa ya birkita komai, ya hango ta a ƙasan gado. Hamdala yayi, ya durƙusa ya ɗakko takaddar, yana ajiyar zuciya ya buɗe takaddar, sedai me ba takaddar bace form ne na koyon kwalliya na Amal, tsaki yayi yai jifa da takaddar yana tunanin ina yasa waccan takadda data bashi, amma kuma lokacin da ta bashi takaddar ai be buɗa ba, balle yasan me ta bashi, hankalinsa na kan yai mata akuyanci kawai, ya birkita ko ina amma babu wata takaddar se wannan, nan take gumi ya shiga tsasttsafo masa. Widad taita jiran Yusuf ya dawo, dan se nishaɗi take ji ze kawo gurji yayi musu kwaɗo, bayan ya dawo da kayan gurjin da yamma, ta zauna ta cire ɓawon tsaf, ta gyara zogalen suka ɗora zogalen akan wuta, suna zaune suna hira a ƙofar ɗakinsu suna aikin su, hankali kwance yayin da zamantakewarsu kan burge wasu daga mutanen gidan. Ya gama suka haɗa Kwaɗon nan a roba, Suka bawa wanda zasu bawa, Widad se haɗiyar yawu take, ta zauna zata saka hannu ta fara ci Yusuf yace "tsaya waye yace ki fara ci, salon ki fini loma ki fini ci ko?" Ai ba ta saurareshi ba, danji take kamar hanjinta ze fito idan bata ci ba, jiki na rawa ta sa hannu ta fara cin Abunta, Yusuf yana kallonta yana nazarinta, tunda ta fara ci bata saurareshi ba seda taji ta ƙoshi tukuna, ta miƙe taje ta wanke hannunta ta sha ruwa ta dawo ɗaki sannan tace  " Yawwa ina jinka, mema kace ɗazu?" Yace "cewa nayi, sannu da aiki acici" "Yawwa mijin acici, kai dai ubangiji Allah yayi maka albarka, ya saka maka da alheri nagode sosai" Yace "Ameen, amma a dena cinye Abinci ana barina" Kawai ta kwashe da dariya tace  "ba ruwana cin abuna zanyi ehe" Yace "ai shikenan poor me" Tace "shagwaɓaɓe kawai, me sexy eyes" Yace "what, sexy eyes kuma sekace wani mace" "baka sani ba, you are having  sexy eyes fa" "Mhmm Malam kawai kice abunda yake ranki kenan" Tace "What? Wai Yoseef meye haka? Kawai ba damar inyi magana seka canza mata ma'ana" Tai maganar tana kai masa duka, ya kwanta yana dariya yasa pillow yana karewa. "Kuma ma kai mummuna ne" tace tana harararsa. "Eh naji bakomai, a haka 'yan mata suke rububina, saboda munina a haka suke sona" Widad tace "Wallahi idan muka koma gida,  duk wadda tayi gangancin raɓarka zata ga matakin da zan ɗauka wallahi" Tai maganar very serious, dan kamar ma haushi taji. Yace  "haka akeyi, shikenan duk suna kallo se kice baza'a kulani ba, bayan kin sanni da farinjini, cewa fa kika yi in Auri Hanne" Tsaki tayi zata tashi, ya fizgota jikinsa, yasa fitila ya haske mata fuska. "Ni ka dena haskani, bana so" Yusuf yai ƙasa da murya yace "An taɓa gayamiki ke kyakkyawa ce kuwa My wife?" "Ai ko ba'a faɗa ba, nasan ni me kyauce sakeni" "in sake ki kuma?" Da sauri tace "No, i don't mean you should divorce me, ka cikani i mean" Yai murmushi yace "nima na sani ai, ni dake ai mutu ka raba Babayna me kama da teddy" Tace "Yoseef me yake damunka ne yau? Duk ka takuramin nice kuma me kama da teddy?" "Eh ramawa nayi, ko kin manta haka kika cemin cartoon jiya" Yai maganar yana dariya, itama dariyar ce ta kamata, ta buɗe baki kamar zata cije shi, amma ta fara kissing ɗinsa. Kamar ranar suka fara kasancewa da juna, sunyi nishaɗi mara misaltuwa, sun farantawa junansu rai sosai, kowanne yana sake jin ɗan uwansa a ransa. Haka suka wayi gari cikin farin ciki, sedai dukda wannan farincikin Yusuf se fama yake da fargaba, ya rasa dalilin hakan. Yana ta shiri ze fita, yaji kamar harbin bindiga, gabansa ya faɗi yace  "Lovely, kamar harbi fa nake ji" Widad tace "A'a ko dai tunanin gurin aiki kake, amma wane irin harbin bindiga ana zaune ƙalau? Bari inyi walha, idan na idar seka tafi" Ta juya ta tada salla, tayi raka'ar farko zata yi ta biyu suka ji Hayaniya, aka sake harba bindiga a ƙofar gidan mutane nata guje guje. Yusuf yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un" Daga tsakar gida suka ji ana "duk wanda ya motsa, zamu fasa kansa da bindiga, kowa ya tsaya a inda yake" Gaba ɗaya jikinsu se tsuma yake, Hari ta samu wani lungu a bayan randa ta shige, se zare ido take saboda tsoro. Nan da nan sega jiniyar motar' yan sanda ta ƙaraso Da gudu Widad ta fito tsakar gidan, amma taga 'yan sanda tare da Saleh hannunsa duk ankwa a cikin mawuyacin hali. Tace "me zan gani haka? Meye haka?" Wani ɗan sanda yace "Yusuf, ina Yusuf yake?" Widad tace "ban sani ba, bazan faɗi inda yaken ba" Hari daga inda ta laɓe tace "Wudas ki dena magana karsu kashe ki fa" "Ina Yusuf yake!" a kai mata magana cikin tsawa. Itama cikin tsawar tace "ban sani ba nace" Yusuf ya fito daga ɗakinsu, jikinsa sanye da jallabiya, ya ƙarasa gabansu ya miƙa musu hannunsa cikin surrender . Widad ta fashe da kuka tace  "No! This is impossible, me yayi muku? Laifin me yayi mijinane fa, ku cire masa wannan cuff ɗin" Su kai mata banza suka tasa ƙeyar Yusuf, itama suka sata  a gaba ihu take tana kururuwa akan su sake shi amma sukayi burus da ita. Aka sashi a bayan motar 'yan sanda, idonsa yayi ja ya kasa magana, se kallonta da yake gaba ɗaya ta birkice se ihu take tana kuka, muryarta harta fara dashewa. "Ina sonka, Yusuf ina sonka, I love you Yusuf, dan Allah ku sakarmin mijina, beyi laifi ba, beyi laifin komai ba" Yusuf ya ƙura mata ido, ya lumshe idonsa a hankali, yayin da Widad ke zubda wani irin hawaye tana kuka, me sauti. Aka sakata a motar gida seinna, shikuma a bayan motar 'yan sanda gashi ga Saleh, kowanne hannu da sarƙa!!! (Rayuwa ƙaddarace kowa da irin tasa......... 🎶 ) LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 11/22/21, 4:49 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 116_117 Sosai Widad ta cigaba da gunjin kuka, yayin da mutanen ƙauyen suka fito suka yi duru duru suna kallo, ɗaliban Widad se kuka suke, haka Hindu gaba ɗaya ta birkice banda kuka ba abunda take yi, ba Hindu ba kawai hatta Megari, da su Hari hankalinsu ya tashi sosai, ga Sunusi mijin Jamila baya nan akazo aka kama su Widad. Ana tafe a hanya amma bakin Widad yaƙi mutuwa, kuka kawai take akan a sakar mata mijin ta, tun Yusuf yana iya juyo muryarta da kukanta, har muryar tata ta dashe ba ajin me take faɗa sosai, haka sukaita tafiya har suka fito daga wannan kwazazzaban, da ramukan dake hanyar garin, suka hau kan kwalta ɗoɗar suka kama hanyar Kano. Alhaji Haruna fa ya haɗa uban gumi, saboda ya tabattar da babu wannan takadda, takaddar form ɗin koyon kwalliya ta bashi, ba shiri ya ɗau wayarsa ya kirata da lambar da ta kirashi ɗazu, tana ganin kiran nasa Amal ta tashi da sauri, ta duba har zata ɗaga kawai ta fasa, ta ajiye wayar yai mata kira yafi Ashirin, ƙarshema ta saka wayar a silent tai kwanciyarta. Yai wujiga wujiga, saboda takaddar nan saboda yasan Bukar ba kyau, gashi ya riga yace aiya karɓo, tunda takaddar zata iya zama sheda a kansu, wannan wasiƙar zata nuna akwai halin rashin gaskiya da mahaifiyar Anwar take aikatawa wanda yasa ya bar gida, idan tuhuma tayi tuhuma kuma za'a gano su. Ya tura mata saƙo kusan kala shida amma babu reply, can dai ta ɗau wayar ta duba saƙon daya turo, magiya yake mata akan dan Allah ta ɗaga wayarsa, mahimmiyar magana yake son suyi. Tana cikin karantawa kuwa ya kuma kira, seda taja aji sannan ta ɗaga, yai ajiyar zuciya yace  "habba kyakkyawa, tun ɗazu naake kiran waya, amma anyi biris dani?" Tace "to me kake so in maka? Ko in ɗaga in ce maka?" "A'a kwantar da hankalinki, ai duk abun bana zafi bame ko ɗaga hankali, magana zamuyi" Tace "ina jinka" Yace "Yawwa, dama cewa nayi wannan takaddar da kika kawomin, kinyi mistake ba wasiƙar kika bani ba, form ɗinki ne na koyon kwalliya, kinyi mistake gurin bani" Tace "se akayi yaya?" "A'a dama ba wani abu bane ba, cewa nai zanzo in karɓa in an jima, saboda takaddar tana da mahimmanci sosai" "Karka sake ka soma zuwa inda nake, bazan bayarba ka riƙe wadda na baka a matsayin ta" Alhaji Haruna yai gyaran murya yace "haba beautiful Baby, ai abun duk bekamata ya kaimu ga haka ba, meye na ɗaukar zafi haka? Ai abun bana zafi bane ba, ki gayamin me kike so ayi yanzu in karɓi takaddar nan? Ko nawane zan baki" Amal ta janyo Jakarta, wadda yace tayi accident da ita, ta duba amma itama taga babu takaddar a ciki, amma tai ajiyar zuciya tace  "nima nazo maka da buƙata ta, amma kaƙi amincewa, dan haka kowa ha riƙe buƙatarsa, bazan bayarba gara asirin kowa ma ya tonu a huta" Yace "Subhanallah, hadda mamanki fa"   Tace "har ita ɗin" Yace "dan Allah kar muyi haka dake, ki bani takaddar nan na riga na cewa Bukar na karɓo takardar yace in kai masa, kuma yanzu inzo ince bahaka ba, baze sauraramin ba" Amal tace "Ai gara karya saurara makan, kamar yadda nima baka sauraramin ba, kuma baka karɓi buƙata ta ba" Yace "dakata, yanzu idan na karɓi buƙatar taki shikenan?" Am tace "A'a ai kuma mun wuce wannan maganar yanzu, zan baka takadda bisa sharuɗa, yanzu abu na farko zan gaya maka Account Number ɗina, ina son inji wasu kuɗi masu nauyi, domin inci kaji in warke da wuri daga raunin daka min" "Shikenan zan turomiki, yaushe zanzo in karɓa"? Tace "turo ɗin tukuna in gani mana" Yace "shikenan naji" Ta kashe wayarta, lumshe ido tare da faɗin "Alhamdilillah, cikin sauƙi Allah ya kawomin hanyar da zan rama cin zarafin da kayi min, tabbas inaga yadda takkadar nan nayi, dan babu ita a jakata, amma a haka zan maka rashin mutunci in rama" Alert ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta duba 500k ne, ta jinjina kai tace yanzu aka fara wasan Seda yayi mata kira biyar, sannan ta ɗaga a fusace tace "wai meye ne?" "dama cewa zanyi, kinga alert ɗin?" Tace "na gani, amma sunmin kaɗan, na kuma raina" Ta katse kiran tare da kashe wayarta gaba ɗaya, ta kulle ɗakinta da key, tai kwanciyarta. Tunda suka taho Yusuf bece uffan ba, yai shiru yana saƙawa yana kwancewa a zuciyarsa, tabbas duk sunan da za'a kira shi dashi, ko a tuhume shi dashi, bashi da abunda ze kare kansa dashi, tabbas shi dai tunda ya tashi a rayuwarsa a siraɗin ƙaddara yake, daga wannan ya faɗa waccan, daga waccan ya faɗo wannan, haka ya sunkuyar da kansa yana ta tsabihi ga Allah, akan ya sauƙaƙa masa wannan lamarin. Sun shigowa cikin garin kano, akayi hanyar babbar headquarter hukumar 'yan sanda dake garin kano, motarsu Widad kuma tayi wani gurin, ai tana ganin haka ta kuma fashewa da ihu, tana bori tana kuka tana   "ina zaku kaishi? Ina zaku kaimin mijina? Beyi laifin komai ba, babu abunda yayi muku, ku ƙyalemin mijina wayyo Allah na Yoseef duk nice sila, saboda ni ka shiga wannan tashin hankalin, Dan Allah ka yafemin Yoseef, Allah ka fitar da mijina daga sharrin Azzaluman nan, Allah ga bawanka ka fitarmin da mijina" Ta ƙarasa maganar, tana wani irin kuka me taɓa zuciya babu wanda ya kula ta a cikin 'yan sandan suka cigaba da tafiya. Wani ofishin' yan sandan aka tafi da ita, suka fito da ita daga mota zuwa gurin 'yan sanda, idanunta sun kumbura sunyi ja saboda kuka. Wani ɗan sanda yace  "gata yallaɓai, yanzu muka shigo gari, shi an wuce dashi headquarter, ita kuma gata" Ɗan sandan ya kalleta yace  "Good, Madam congratulations, you are now free, mun cetoki daga hannun wanda sukayi garkuwa dake" "Niba garkuwa yayi dani ba, wanda sukayi garkuwa dani daban, Yoseef ceto na yayi, shine ya temakeni beyi garkuwa dani ba, ka gaya musu suje su sakarmin mijina" Ɗan sandan yace "koma dai ya akayi, wannan ku ta shafa ke dashi, muba abunda ya dame mu, zamu rubuta sannan mu sanar da duniya cewar, munyi namijin ƙoƙari gurin bincike mun gano wanda yayi garkuwa da Widad Nasir Daula, kuma ba wani bane face direbanta, wanda ya kasance ɗansanda, yaje gidansu yai basaja dan yayi garkuwa da ita, nasan hakan ze sake ɗaga darajar rundunar mu a ga namijin ƙoƙarin da muke, ba dare ba rana gurin kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma " " Shut up!!! " Ta faɗa cikin ƙaraji, tace " idan har ina raye ina numfashi, ko komai nawa ze ƙare se Yusuf ya fita, babu wanda ze cutarmin dashi, baku isa ba azzalumai ma cuta, lokacin da aka yi garkuwa damu muna buƙatar taimakk, babu wanda ya taimakemu na kusa rasa rayuwa ta, se yanzu da yayi komai ya gama, Allah yasa ya kare rayuwata, shine za'a masa sharri wallahi bazan lamunta ba, he's my Husband " Ɗan sandan nan yace  " ku ɗaukemin wannan mahaukaciyar daga gabana, a tafi da ita Asibiti a duba lafiyarta, sannan ku kiramin Ubanta Bulama tunda babu wanda yasan inda wancan yake " Widad bata gane meyake nufi ba ta cigaba da kukanta, haka suka kawo Ambulance dan iya makirci, aka sheƙa mata wani abu ta sume a gurin, aka kira 'yan jaridu suka cika gurin, aka ɗauki Widad aka saka ta a motar Agajin gaggawa wato Ambulance suka tafi da ita. Jaridu kuwa da sassafe shafin farko, hotunan Yusuf ne da Saleh, musamman na Yusuf ɗaure a cikin sarƙa ya sunkuyar da kai, gefe ga hoton Widad da aka ɗauka an fito da ita daga ofishin 'yan sanda an sata a ambulance, daka kunna gidan radio, labarai ko talabijin babu abunda zaka fara ji se   "Me dokar bacci ya ɓige da gyangyɗi, kuma ƙarshen tika tiki tik inji hausawa A yaune  jami' am tasaro sukayi nasarar cafke jami'in ɗan sandan nan na farin kaya wato Yusuf Bashir Maitama, wanda yayi garkuwa da 'yar gidan fitaccen me Arziki nan a gida da wajen Nigeria wato Nasir Daula,' yan sandan sunyi nasarar gano shi ya sace ta tare da ɓoyeta a wani ƙasurgumin ƙauye dake garin Bauchi, 'yan sandan sun ceto Widad Nasir Daula, wadda ke cikin mawuyacin hali, da zauwansu basu yi wata wata ba aka kira motar Asibiti aka tafi da ita domin duba lafiyarta, zamu ci gaba da bibiya da kasa kunne domin jin wani mataki hukuma zata ɗauka akan wannan ɗan sanda, wanda ake tunanin har shi Nasir Daula ɗin shine yai garkuwa dashi, mu dai anan se muce Allah ya kyauta, yai mana tsari da irin wannan jam'ian tsaro a cikin al'ummar mu" Nan fa gari ya ɗau ɗumi, aka dinga cece kuce, wasu na Allah wadai suna Tsinewa Yusuf, yayin da wasu ke a bari a ga abunda bincike zeyi tukuna. Widad kam bata sake sanin inda kanta yake ba, inda har a gadon Asibiti aka bita aka dinga ɗaukar hotunan ta, ga fuskarta tayi ja saboda kuka, da gajiyar tafiyar hanya, amma aka dinga ɗauka ana watsawa duniya wai tana cikin mawuyacin hali, hannunta ɗauke da drip. Alhaji Haruna ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba a taɓa raina masa hankali kamar yadda akayi yau ba, ya kira layin Hajiya Halima, Ramlah na zaune a falo wayar ta fara ringing, Mummy tana ciki tana amsa wata wayar dan haka ta ɗaga wayar tasa a kunnenta tace "Hello" Yace "Yawwa Amal ce?" "No Ramlah ce" "Dan Allah idan Amal tana kusa ɗan bata wayar muyi magana" Tace "tana ɗakinta, bari in kai mata" Ta miƙe ta tafi ɗakin Amal, amma ɗakin a rufe harta kashe fitila ma " Ramlah tace " gaskiya tayi bacci, dan ta rufe ɗakinta ma ta kashe fitila" Yace "Yasalam" Ramlah tace "ya dai? Akwai matsala ne?" "A'a babu wata matsala, ina son muyi magana ne kawai" "to ka gayamin saƙon in bata mana" Yace "A'a karki damu, idan ta tashi na sake kira" Ya kashe wayar yace "Amma dai Allah ya Tsinewa yarinyar nan, kaga min shegiyar yarinya mara albarka" ya ciji yatsa yai ƙwafa yace  "dani kike zancen wallahi, kema sema wulaƙantaki," Amal ta ɗau wayarta ta tura masa saƙo tace "ka cigaba da kiran Mummy, kana cewa kana son Magana dani, wallahi idan baka yi wasa ba sena gayamata abunda kayi min, kuma kasan halinta sarai, kasan buyaginta zata maka abunda kai kanka zaka kasa gane kansa, dan haka muddin ba zaka cika sharaɗina ba, wallahi ba zan baka ba na gaya maka, kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan, nima a account dina ina da wanda suka fisu" Ta kashe wayarta ta sake kwanciya, ya duba message ɗin, yaja wata ajiyar zuciya yana cije leɓe, totally ta riga ta gama raina masa hankali, yama rasa me zeyi ko me zece. Yana nan tsaye yana tunanin mafita kiran wayar Bukar ya shigo wayarsa, ya ɗaga jiki na tsuma, yace "Hello" "Haruna, yau muna da zama na gaggawa, cikin dare dan haka duk ku tattaru" Yace "harda Halima?" "banda ita, sannan kazo min da wannan takaddar, zamuyi magana a kai itama" Daga nan ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya yakice gumi, yana huci Amal ta masa rashin mutunci, dan kawai abu ya shiga tsakaninsu se tayi masa haka?. Mutan ƙauyen da Widad suka zauna suka dinga taradaddi, kowa da abunda yake faɗa wasu suna dama megari yayi wauta, wataƙila dama can 'yan fashi ne ko wasu masu laifin ne, amma daga zuwansu ya karɓesu, be san daga inda suke ba. Hindu kam kuka, kamar wadda aka kama uwarta, ita kanta Hari gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, wunin ranar gidan daga masu koke koke, se masu salallami, Hanne kuwa ko a jikinta. Koda Sunusi ya dawo, Jamika ta gaya masa abunda ya faru, dan haka yace dole gobe insha Allah ya tafi kank, yaje yaji ba'asin abunda ya faru. Jamila tace "dan Allah karkaje, kar kaima a kama ka, dan na san da kana nan wataƙila da kai zasu haɗa" Sunusi yace "da nayi musu me? Kince an kama Saleh, kuma Saleh shiya kawo su nan, meyasa aka kama shi, dole zanje inji" Daddare megari ya tara iyalansa yace  "to wannan bayin Allah dai, ni dai a ɗan zaman da mukayi dasu, ban tunanin mutane ne marasa gaskiya, ko makamancin haka, zamanmu da su ma mu alkhairi ya zame mana a garin nan, dan haka dan Allah ina roƙonku da kuyi haƙuri ku dena kuka, kukan ya isa haka, Hasana nasanki da son 'ya' ya kuma zamanmu dasu jin shaƙu dasu sosai, dan Allah kidena kuka kiyi musu Addu'a, Hindu Baffa kema kukan ya isa haka, muyi musu Addu'a, Allah ya basu mafita sannan Hari a samo makulli a rufe musu ɗakinsu, kar wanda ya sake shiga tunda da kayansu a ciki " Hari ta tashi ta shiga ɗakinta ta samo mukulli, tana ƙoƙarin rufewa taga bokitinsu a tsakar gida, ta tafi ta ɗakko bokitin, kawai ta fashe da kuka tace " Allah sarki Wudas, da yanzu muna faɗa akan ruwan zafin da zata yi wanka, tace sena bata na bawa mijin ta, ban taɓa ganin abun tausayi kamar yau ba, yadda ta rikice tana kuka, Allah sarki Allah ya fitar dasu" A kaita bata haƙuri, aka kulle ɗakinsu aka bawa Megari mukullin, ya kai ɗakinsa ya ɓoye. Yusuf yana kwance a cikin cell, an raba masa cell shida Saleh, sauro yana ta masa buduri a ka, yai rigingine yana tunanin ya Umma zataji idan wannan mummunan labari ya isheta?. Aka buɗe ƙofar cell ɗin, wasu 'yan sanda suka shigo su biyu, ya tashi zaune yana kallon su. Ɗaya ya kalleshi yace  "munafuki, kalleshi kamar na Allah, amma ƙasurgumin Azzalumi ne, kai garkuwa da' ya ka koma kayi da Ubanta, saboda kai Azzalumi ne, kuma a haka wai kai ɗansanda ne" Yusuf yai shiru be ko ɗaga kai ba, ɗayan yace "rabu dashi corporal Sani, zuwa gobe in Allah ya kaimu semun sauya halittun fuskarsa, kafin 'yan jarida suzo, a buga shi a nunawa duniya shi, azzalumin banza dana wofi kawai" Yusuf dai yai shiru bece komai ba, suka gama zage zagensu suka fita, suka sake rufe shi, tun Abincin safe Yusuf be kuma cin komai ba, ga doguwar tafiyar da suka yi, amma sam baya jin yunwa tunanin makaomarsa kawai yake a wannan hali da yake ciki. Nurat na kwance cikin dare, taji Mahaifinta yana waya ƙasa ƙasa, ya fito daga ɗakinsa da alama dai fita zeyi, ta kalli agogo ƙarfe biyu da rabi na dare, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito falo, aikuwa yana fitowa ya ganta a falo, ya ɗan haɗe rai yace "ke me kike yi a falo a wannan tsohon daren haka?" Tace "ruwa na fito sha" "ina ma fridge ɗin dakinki?" "yayi sanyi da yawa, duk ya zama ƙanƙara shiyasa na fito" Yace "to kin sha ɗin ne kokuwa?" Tace "A'a yanzu dai zan sha" "maza jeki sha, kizo ki wuce ki kwanta" Ta nufi hanyar kitchen, tana tunanin ina zashi a wannan tsohon daren, ta fito ta tarar da shi a falon a tsaye, yace "kinsha ruwan?" Tace "eh na sha" "to maza ki wuce, ki tafi ɗakinki ki kwanta" Harta juya ta tafi, ta waigo taga yana tsaye yana kallon ta, tace  "Amma naga kamar fita zakayi, ina zaka yanzu dare yayi sosai" "Yaushe na fara wasa dake? Ko kuma kika zama uwata da zaki dinga tuhuma ta haka?" "hmm Daddy kenan, ai kaine kake abun tuhumar, wani irin abune wannan da ba'ayi ido ma ganin ido ba se yanzu a tsakiyar dare haka hmmm Allah dai ya kyauta?" Ta buɗe ɗakinta ta shige, ta barshi tsaye yana binta da kallo, yarinyar da idan ta ganshi jikinta ke rawa, itace take gaya masa magama haka, tabbas uwarta ce ke zigata kuma zeyi maganinsu gaba ɗaya. Kamar yadda suka saba haɗuwa yauma sun hallara gabaɗayansu, suna zazzaune a ɗakin Hotel ɗin da ya zamana babu ma me kama shi sesu. Bukar yace "kyakkyawan labari" Alhaji Musa yace "muna jinka" Alhaji Bukar yace "yaron nan yazo hannu" Sukace wane yaron? Alhaji Bukar yace "ku duk baku sani ba, dukda yadda da labarin ya yaɗu a daren nan? To ina nufin Yaron nan Yusuf, direbanta wanda aka yi garkuwa dasu tare" Sukace "Alhamdilillah, abu yayi kyau" Alhaji Bukar yace  "An kamosu a wani ƙauye a Bauchi, inda Saleh ya basu mafaka, yanzu haka yana hannun 'yan sanda, za' a tattare duk wata sheda da ta kamata daga nam za'a kaishi kotu, zamu saki kuɗi ayi masa shari'a da hukuncin daya dace da shi, saboda babu wanda ya ta:a kawo mana cikas da tangarɗa a harkar nan kamar shi, kunga daga nan babu wanda ya isa yace mune muka sa akayi garkuwa dasu" Alhaji Munir yace "good, wannan abu yayi kyawuuu sosai, kuma ya tafi yadda ake so, dan haka semu hanzarta, mu kuma samu hanyar da zamu ɓalli namu kason tun kan Daula ya bayyana, dan shi har yanzu bamu san fa inda yake ba, kar muje wasu su rigamu karɓa abun nan fa" Bukar yace "na toshe duk wata hanya da zata saka wani ya mallaki abun nan bamu ba, sannan dole nasa a matsa yaron nan, idan ma abun yana hannunsa ya faɗi inda suke" Alhaji Musa yace "kai amma abu yayi kyau wallahi, komai ya tafi yadda yakamata" Alhaji Bukar yace "Haruna ina takaddar da wancan yaron ya bari, ɗan gurin Halima? Shima nasa a nemo shi, duk inda aka ganshi kawai a kawar dashi, bama san duk wani abu da zesa a samu sheda a kanmu" Alhaji Haruna yai tsilli tsilli da ido yace "Amm.. Mm.. Wallahi an ɗan samu akasine, na rasa inda takaddar ta faɗa amma ina ta ƙoƙarin dubawa" Alhaji Bukar yace "Amma kasan bana son akasi ko?" Yace "Ayimin afuwa dan Allah, Insha Allah za'a nemota in kawo" Alhaji Bukar yace "shikenan, nan da kwana bakwai, na baka isashen lokaci, nan kusa nake so a fara shari'ar yaron nan, ba da nisa ba, kuma ina son a rufe duk wata hujja da zata bayyana mu" Alhaji Haruna yace  "insha Allah, zan kawo takaddar nan ba da jimawa ba" Haka suka gama tattaunawa sannan suka watse. Widad ce ke ƙoƙarin farkawa, se jujjuya wuyanta take tana kuka cikin bacci, "Wayyo Allah na, yuzarsef yunwa nake ji, zuciya ta ciwo take, Yoseef dan Allah, dan Allah ka dawo please! Ta farka a gigice tana kiran Yoseef! Yoseef kana inane?" Bulama ne da Matarsa Hajiya Sarah a gigice suka yi kanta gaba ɗaya, Bulama yace  "Sannu daughter, sannu ki kwantar da hankalinki, kin ganni a tare da ke, ga Maman Iman ma, an kuɓutar dake ki kwantar da hankalinki" "Ni bazan kwantar da hankalina ba, ina mijina yake? Ina Yoseef kace su sakarmin shi, ni ba saceni yayi ba, wallahi idan basu sake shi ba mutuwa zanyi, laifina ne, duk saboda ya ceceni haka ta faru dashi, beyi laifi ba, tun farko seda na gaya masa death contract ne amma ya amince, kaga abunda nake nufi Yoseef, dan Allah ku ƙyaleshi idan wani abu ya sameshi bazan yafewa kaina ba, dan Allah ka cewa Bukar na dawo, ni yazo ya kamani yasa a sakarmin mijina dan Allah " Tai maganar wasu irin hawaye na ambaliya daga idonta, idanun da suka rine zuwa kalar ja jawur suka kumbure. Bulama yace "toni ina na san wani Bukar, balle in nemo miki shi? Ke kaɗai kika sanshi, ni ban san a inda yake ba" Kafin ya rufe baki... Ayi subscribing YouTube channel ɗina please 🙏 🙏 🙏 🙏 Ayshercool 11/23/21, 8:06 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 118_119 Alhaji Haruna kam juyi yayi ya farka ya ganshi kwance a gurin daya sha lemon nan, shi dai yasan da magariba Amal tazo, amma yanzu yaga kamar yammace, nan da nan ya tashi da sauri yana dube dube, ya kalli agogo yaga ƙarfe biyar na yamma, ya duba yaga wayarsa a gefensa a kashe, me yarinyar nan tayi masa haka? Ko kuma meye ya faru da shine? Yai yai ya tuna wani abu amma ya kasa, ya gagara tuna komai daga inda ya sha lemon nan baya iya tuna komai, ya tashi ya fito falonsa amma komai yana nan yadda yake, babu abunda ya canza. Duk ya lalleƙa babu wani canji daya gani, amma ya akayi yayi wannan baccin haka? Ya tambayi kansa, tabbas wannan yarinyar ce tayi masa wani abu, sedai ya kasa gane meyafaru dashi. Sunusi duk yadda yake tunanin lamarin ya wuce nan, dan daya zo Kano ya samu labarin inda su Saleh suke tsare, sedai tun daga bakin gate wani yace masa tun wuri yayi takansa, karma a san daga imda yazo ko kuma shi wanene a gurin Saleh, idan ba haka ba tabbas shima kamshi zasuyi su rufe har dashi. Haka Sale ya koma babu wani daddaɗan labari, su kuma su megari suna can suna jiran sa yazo ya gaya musu yabake ciki, sedai yanayin fuskarsa kawai ya nuna musu babu nasara. Me gari yace "Sunusi, kayi mana bayani, da kaje kanon menene ya faru? Ya kukayi dasu?kaga su Yusuf ɗin da Saleh fatan suna lafiya?" megari ya jero masa tambayoyin. Sunusi yace "Baffa, lamarin nan fa ya wuce inda kake tunani fa, duk abun ba yadda muke tunani bane, ita wannan yarinyar daka gani, matar wannan Yusuf ɗin Wato Widad, 'yar gidan Alhaji Nasir Daula ce, wai ance Yusuf ɗin ne suka haɗa kai da Saleh sukayi garkuwa da ita, dan su karɓi kuɗin fansa, shine sukazo suka ɓoyeta a garin nan" Hansai tace " wai Daula dai shahararren attajirin nan da ake labarinsa? Wanda ake yawan faɗansa ɗin nan" Sunusi yace" to da daulan guda nawane? Shi dai 'yarsa ce" Gwaggo tace 'biri yayi kama da mutum, kwata kwata yarinyar nan ba kalar wahala bace, yanayin yadda take rayuwarta da yadda bata iya wasu abubuwan ba ze tabattar maka da bata tashi cikin wahala ba, sedai gaskiya bazan taɓa yadda wai satota sukayi ba, nan fa suka zo da ita babu lafiya Yusuf ne ya goyota a bayan sa, bata yadda da kowa seshi farkon zuwa su, kuma da satota yayi da tabbas tayi yunƙurin guduwa wataran " Hari tace " Akwai dai wani abu a ƙasa, amma yadda take ji da Yusuf ɗin nan ƙaryane a ce satota yayi, komai shi, kullum tana liƙe dashi, sannan ace satota yayi gaskiya ban yadda ba sam " Sunusi yace  " to kai Baffa da baka san daga inda suke ba, ka karɓe su?" Megari yace " Saleh ne ya kawomin su, yace garinsu faɗa akeyi, babu kwanciyar hankali an kashe iyayensu, shida ita 'yan uwane, amma ba ciki ɗaya ba, na wuce gaba aka ɗaura musu Aure saboda dai ai baka ƙi taimakon mutum ba, amma ni dai gaskiya ban yadda ace wai satota sukayi ba, dan lokacin da suka zo gidan nan, shi kamsa Yusuf ɗin kamar a galabaice yake bashi da lafiya, zaka ce daga gurin da ake yaƙi suke ' Sunusi yace "Amma abun da mamaki gaskiya" Hindu tace  "kuma da kaje babu wanda ka gani a cikinsu, daga Amarya har mijin nata?" Sunusi yace "ke, case ɗinfa babba ne, yafi gaban yadda kike tunani, kedai kiyi ta addu'a kawai" Hindu tace "Allah sarki' yar uwata, gaskiya na tausaya mata, ashe 'yar gidan attajirai ce amma tazo tai rayuwa a wannan ƙauyen namu? Kuma taita binmu tana lallaɓamu mu koya mata abu, kuma da alama mijinta kawai ake nema, da akazo kamasu tambayarta suke yana ina" Megari yace "koma dai yane, ubangiji Allah ya kuɓutar dasu" Haka suka cigaba da tattaunawa suna salallami. Aka buɗe ƙofar ɗakin da Widad ke ciki aka shigo, ko ba'a faɗa ba tasan waye ya shigo ɗakin, dan haka ko ɗaga kai batayi ta kalleshi ba, ta maida hankalinta ga wani gurin, ya ƙaraso ya zauna a gabanta yana ƙare mata kallo, still bata motsa ba balle ta ɗaga kanta ta kalleshi. "koki kalli inda nake, ko karki kalla yin biyayya ga dukkanin umarnina ya zame miki dole a yanzu, tunda shine last option ɗinki, tunda kika riga kika gano waye Bukar, zan gwada miki aikinsa a aikace, ranar Litinin za'a kai wancan sakaram da kike iƙrarin mijinki ns kotu, kuma na ɗau dukkan wasu matakai dana san zasuyi amfani sena tura shi gidan yari ya ƙare rayuwarsa a can, babanki kuwa koma ina ya tafi ya tafi kenan, har Abada har gaba da Abada baze dawo ba, dama burina kenan in ɗaiɗai ta farincikin sa" Widad dai bata motsa ba balle tayi magana, tai shiru ta cigaba da kallon waje ɗaya. Ya cigaba da cewa "ki temaki kanki tun baki makara ba, ki bani takaddun da ubanki ya ware, yace wai dukiyar akwai me ita, duk wanda yasa hannu akan takaddun nasane suna ina?" "Idan ubaka ne ya tara masa seka sa in baka, bazan bayar ba nayu Alƙawarin me ita zan bawa, kuma na riga na miƙasu ga masu ita" "Niki ke gayawa haka?" "Na gaya maka ɗin, tsakanin wuta da aljanna wacce kake da ita, balle ka sani? An faɗa maka ɗin kayi abunda zakayi karka fasa" "Ina binki sannu sannu ne, saboda har yanzu akwai ɓurɓushin imani a raina, mahaifinki yamin ranar dabe yiwa wani a rayuwa ba, sannan dukiyar ki ce dalilin tsayawar kasuwancina da ƙafafunsa shiyasa nake son in kamanta miki adalci, ina takaddun suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi tun ban saɓa miki ba, kokuma na gwada miki" "Ban sani ba!" ta faɗa cikin shouting, "Idan kana so ka kashe ni hankalinka ya kwanta, kuma zalunci indai nakane wanne ne ban gani ba, ai babu irin wanda baka gwadamin ba, ko zaka gutststura naman jikina, bazan baka ba" ai kuwa ya kifa mata mari, abun da ba'a taɓa yi mata ba a rayuwar ta, dan seda bakinta ya fashe. "Wallahi ko kina so, koba kya so sekin bani kuma ba kimin wannan raunin a banza ba se na ɗau mataki a kanki" "bazan bayarba, Amana ce kuma na danƙata a hannun masu ita suna rayuwarsu, me kake so inyi maka? Ko me zance maka?" "ƙarya ki keyi, baki danƙata a hannun kowa ba, ki gayamin ina suke" yai maganar cikin tsawa. Banza tayi masa, taƙi magana ta shiga goge jinin da bakinta yake yi, ai kuwa taji saukar tio a jikinta, tunda Widad take ba'a taɓa dukanta da abu me zafim wannan ba, bayan wanda aka mata da bakin bindiga, ta banƙare ta ƙwala ihu, take fatar jikinta ta tashi tai jawur kamar an ƙonata. Tana zubar da hawaye tana girgiza kai, ji take kamar an saka mata wuta a bayanta, saboda azabar bala'i, ya sake zage ƙarfinsa ya shiga zuba mata, tun tana iya ihu harta kasa, se nishi da take yi yasa ƙafarsa da babu ciwon yai ball da ita, ai dukan da yayi mata be mata ciwo ba, kamar yadda yai ball da ita da ƙafarsa, ya ƙaraso inda take yana huci yace     "zaki gayamin ko bazaki faɗaba" Ta ɗaga jajayen idanunta tana kallansa, ta shammaceshi ta kafa masa faratanta a inda aka masa ɗinkin nan a cinya, dayake naɗe ƙafar wandon yake, saboda karya sosai masa ciwon yaƙi warkewa. Aikuwa haka ya buɗe baki ya ƙwala ihu shima, dan har jini gurin ya fara, ta janyo wuƙar nan da ta ji masa ciwo da ita akan taga, tace "wallahi idan baka fita daga gurin nan ba kashe ka zanyi, sena kashe ka wallahi ' Tuna yadda ya sha yanka da wuƙa ne wancan lokacin yasa shi fita da sauri yana faɗin  " dawowata ta biyu bazata miki daɗi ba, zaya kasance dawowa me muni a gare ki " Ya fita hannun sa riƙe da cinyarsa, tana masa wani irin zugi, har yanzu Widad ba tayi laushi ba, halinta be canza ba na baƙar zuciya da taurin kai na jaraba, gashi dukda dukan databsha da rashin lafiyar da take ciki, be hana ta fama masa ciwon nan ba, dan gashi har ya fara tstatsafo da jini, ta fama masa yai ƙwafa ya fita yana tunanin yadda zewa Widad izaya irin wadda ba'a taɓa yi mata ba, wadda zata tirsasata yin abunda yake so. Ita kuwa Widad zama tayi tana kuka, saboda azabar raɗaɗin da jikinta ke mata saboda dukan da ta sha da tio, jikinta duk yayi tsami, tai kuka tai kuka harta fara tari daga nan kuma se Amai, gashi ba komai a cikin nata, dan baka ta dinga yunƙuri amma babu abunda yake fita, se miyau ga ɗaci da maƙogwaronta yake, se kuma ta shiga aman jini, haka ta dinga kakarin aman nan gwanin ban tausayi, abun da bata saba ba ya sameta, taji ba abunda take so banda ta samu ƙanƙara ta matsa lemon tsami ta sha ba. Tan nan ta kwanta akan tiles, tana jin yadda sanyin ke ratsata, jikinta kuma yana ɗaukar zafi. A hankali aka turo ƙofar ɗakin nata, ta tashi zumbur dan zatonta Bulama ne, wannan me aikince ta shigo cikin sanɗa, taga Widad a mawiyacin hali, dan tana jiyo kakarinta tun ɗazu. Widad zata yi magana tai sauri ta girgiza mata kai, cikin ƙasa da murya tace  "karki ɗaga murya mana, kinga Alhaji Bukar yace kar a kuma baki Abinci se sau ɗaya a rana, ya gindaya mugayen sharuɗa akanki, ni kuma ina jin tausayinki zan ɗan temaka mikine, ga Abinci na kawo miki kici" Widad tace "bana ci, ki bani ruwa me sanyi sosai, ki bani in sha" "A'a, kici Abinci mana, cikinki bakomai ga jikinki ya ɗau zafi sosai ki daure" Ta tirsasa Widad yaci Abincin kaɗan, ta bata ruwan sanyi kamar yadda ta buƙata, sannan tai mata sallama ta fita. Widad ta koma kan tiles ɗin nan tayi kwanciyarta, fatar jikinta duk jini ya kwanta akan fatar ta, ta lumshe idonta ga sanyin A. C gana tiles haka tai kwanciyar ta abunta. Umma jikinta sauƙi an sallameta daga Asibiti, sedai jikin nata ya kasa ƙwari, saboda tsabar damuwa da tashin hankali da take ciki, ta rame sosai tayi zuru zuru duk ta fita daga hayyacinta, bata iya cin Abinci sam sedai abunda ba'a rasa ba, kullum tana cikin Addu'a ne, dan da kanta taje ganin Yusuf amma aka hanata ganinsa, haka ta dawo gwiwa a saɓule. Tana zaune ta idar da sallar la'asar, tana lazimi idonta duk yayi ja saboda rashin bacci, sallama taji anyi ta amsa sedai kafin ta bada izinin shigowa Suka shigo ɗakin gaba ɗaya, ta ɗaga kai ta kallesu tace "Sannunku da zuwa Anty Asma'u" "A'a riƙe sannu da zuwanki, zuwa mukayi muyi kallo sannan mu jajanta, yau dai kinga maganar da muke tayi tun shekarun baya, tsintacciyar mage bata mage, yau dai shege ya ɗakko miki magana, dama ina shege zeyi wani abun arziki, kina ta wahala kika saka ɗan uwanmu yaita wahala daku, ke juya shi kuma shege yau dak gashi ƙarshen Alawa ƙasa, ya zama gagarumin ɗan ta'adda ya sace 'ya yaje yai mata fyaɗe yana neman kuɗin fansa, Allah wadaran naka ya lalace " Balaraba tace " Ameen dai Anty, alhakinmu ne ya kama su, da tasa ɗan uwanmu ya dinga wahala dasu, yana wulaƙantamu yau gashi kina kuka da idonki, kuka kam yanzu kika farashi, saura ke se sunzo sun haɗa ke dashi tukuna, tunda idan ya samo tare kuke ci" Suka dinga zazzage mata rashin mutunci iri iri, ta inda suka shiha ba ta nan suke fita ba, Umma ba tace musu komai ba ta sunkuyar da kai kawai, ta cigaba da jan carbinta na tare da ta kulasu ba. Suka yi suka gama san ransu, sannan suka tafi Umma ta girgiza kai kawai, tana share hawaye. "Khalil ya ake cikine? Ka samu ganin Widad ɗin kuwa?" Khalil yace "Nurat, ban samu ganin Widad ba, bata gidan Alhaji Bulama ance wai bata da lafiya an kaita Asibiti, amma ɗan nasa be gayamin ina take ba, wai shima be sani ba, nace masa zan kuma komawa inji abunda ake ciki" Nurat tace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Yaya Khalil an kusa shiga kotu fa, Allah yasa dai a gano ta, na damu sosai dan Allah ka koma da wuri kaji" "Shikenan insha Allah, karki damu zan koma inga yadda zamu yi dashi" Alhaji Haruna ya kira layin Amal ba adadi amma taƙi shiga, ya rasa me yarinyar nan tayi masa ranar da tazo, ta barshi a yashe, yana ta tunanin ne kiran Alhaji Musa ya shigo wayarsa ji a sanyaye ya ɗaga. Alhaji Musa yace "Haruna ina ka shiga ne? An kira layin ka ba adadi amma taƙi shiga, gashi baka bawa Bukar takaddar nan ba gashi za'a shiga kotu, kasan fa idan wani ya ɗau takaddar nan tsaf zamu shiga matsala, har saƙo aka turo maka na zamuyi taro amma baka ɗaga ba" Alhaji Haruna yace  "bani da lafiya ne, banga saƙon ba" Alhaji Musa yace "ban yadda ba, akwai wani abu a ƙasa, ka gayamin ko menene mana? Kasan halin Bukar wallahi ze iyayi maka Akuya kasani sarai" Alhaji Haruna yace "a bar zancen kawai, zanzo in same ka zamuyi magana" "Shikenan, seka zo amma kasan yarinyar nan ta gano Bukar kuwa" "Ahh haba dai garin yaya kuma?" "oho masa dai, wallahi tayi masa sheda da wuƙa, ta yanke shiba fuskarsa da cinyarsa, kai baka ga yadda ya sha ɗinki ba, gaba ɗaya halittun fuskarsa sun sauya" Alhaji Haruna yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Taɓɗijan dara taci gida kenan, to wani mataki ya ɗauka" Alhaji Musa yace  "eh to, yace tunda ga riga ta gano shi yasan yadda ze da ita, sedai kawai idan mun haɗu da kai tukuna, mayi magana mu tattauna maganar bazata yi ta waya ba, zan shiga meeting ne yanzu" "Shikenan, sena zo tukuna" Ramadan ne yai sallama ya shiga falon mahaifinsa, yana zaune yana kallon labarai, Ramadan yace "Daddy barka da hutawa" Bulama yace "Yawwa barka, sannunka wai ni ina ɗan uwanka Fahad ne, yaushe rabon da in sashi a idona" Ramadan yace "Daddy kasan halinsa fa, wallahi yau kwanansa huɗu baya gidan nan, nima ban san inda yake ba, babu wanda yayiwa sallama, dama hana yin haka fa, yakan kwana biyu ma baya gidan nan" Bulama yace "da kyau, ze gauraya dani kuwa, dan ubansa" Ramadan yace "Yawwa Daddy, nace a wane Asibitin Widad take ne, Nurat ta aiko a gayamata imsa take, tana son ganin tane kasan ƙawarta ce" Bulama yai shiru yana nazarim Ramadan sannan yace  "wata aiko?" "Wani ne, nima ban sanshi ba, wai ko Khalil ne kowaye, ya cemin ɗan uwanta ne shi, yana so zeyi magana da Widad ne, Nurat na son sanin halin da take ciki" Bulama ya jinjina kai yace  "rabu dasu kawai" "Daddy saboda me? Aikowa yasan tana hannunka, yakamata ka faɗi Asibitin da take, saboda masu dubiya sannan wataƙila 'yan sanda zasu samu wani rahoton daga gareta" "Kai Ramadan ka kiyaayeni, ka fiye shisshigin tsiya wallahi, to ban saniba tunda nace maka tana Asibiti amma kama cigaba damin tambaya" "Allah ya baka haƙuri, amma Daddy wannan yakan fa dake fuskarka da ƙafarka? Tun shekaranjiya nake son in tambayeka amma se inga kana bacci, na tambayi Mummy tace itama bata sani ba" Bulama yace "Accident ne na samu, tashi ka bani guri tafi maza ka bani guri in huta" Haka ya fatattaki Ramadan, ya kulle ƙofarsa ya ɗakko wayarsa ya kira Alhaji Musa, ya ɗaga yace  "Allah ya temaki Bukar Bulama" Alhaji Bulama yace "Musa kasan da ana shirin samun ɓaraka daga gidanka kuwa?" "kamar yaya kenan?" Bulama yace  "Waye Khalil a family ɗinka kona matarka?" Alhaji Musa yace  "ɗan yayar Babar Nurat ne, cousins ne shida ita" "Shine ta turoshi gidana wai azo agane mata ya Widad take? Wai aga halin da take ciki, da sanin ka akayi haka?" Alhaji Musa yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wallahi ban sani ba saboda haka fa na kirsheta a gida, ko nan da cam bata zuwa, na hanata zuwa ko ina Sam, ban san yadda akayi tayi hakan ba, amma ka ƙyaleta zanyi maganin ta, zan ƙwace wayoyinta sannan in turata ƙasar waje, bakomai zan ɗau mataki a kai, hakan bazata sake faruwa ba" "gara dai kayiwa tufkar hanci tun kafin inyi abunda yakamata da kaina, karka ƙara turomin wani yazo yana neman Widad, ka jawa 'yarka kunne" "Insha Allah, hakan bazata sake faruwa ba, zanyi abunda ya dace base ka ɗau mataki da kanka ba" Bulama yace "da dai yafi" Litinin, tushen aiki kotu ta cika maƙil, domin ji da ganin yadda shari'a zata kaya, musamman shari'ar da mutane suke cike da sonji da ganin yadda zata kaya, wato shari'ar Yusuf Bashir Maitama, ɗaga jajirtaccen ɗansanda wato Bashir Maitama. Umma ya halarci zaman kotun nan, dan shine kaɗai hanyar da zata ga Ɗanta Yusuf, 'ya' yan Bulama su Alhaji Munir, da Hajiya Halima da 'ya' yanta duk sun halarra a kotun. Umma tana nan zune tana waige waige aka shigo da Yusuf, hannunsa ɗauke da sarƙa, 'yan sanda sun taso shi a gaba, yadda yake jan ƙafa da ƙyara da yadda jaabiyarsa tai baƙiƙirin saboda datti, ga fuskarsa duk a kumbure, kai da gani base an faɗa ba kasan Yusuf a wahala yake, Umma ta ƙunshe fuskarta a mayafinta ta fashe da kuka. Haka akaje aka tsayar da Yusuf, 'yan sanda suka kewaye inda yake, Yusuf ya ɗaga kai yaga yadda kotu ta cika maƙil, masu masa kallon banza nayu, masu na tausayi suna yi, idonsa ya sauka akan ummansa wadda idonta yayi fururu saboda kuka, ya sunkuyar da kansa yana danne hawayen dake shirin zubo masa Allah kaɗai yasan me Umma takeji a rantava yanzu haka. Aka karantowa Yusuf ƙunshin tuhumar da ake masa, amma Yusuf ya musanta yace "shi bashi ya sace Widad ba" Barrister Saminu ya miƙe, ya gabatar da kansa a matsayin lawyoyin gwamnati masu gabatar da ƙara sannan yace "duba da yadda wanda ake zargi ya musanta abunda ake tubumarsa dashi, muna neman wannan kotu me Alfarma data bamu dama muje mu tattara hujjojinmu da zamu gabatar a gabanta, wanda zs tabattar da abunda ake zargin wanda ake ƙara ya aikata" Me shari'a Justice Abdallah A dutse yace "duba da yadda lawayan gwamnati ya nemi a basu dama domin kawo shedunsu, wannan kotu ta ɗage sauraran wannan ƙara zuwa goma ga wata me kamawa, sannan wannan kotu tayi umarni da akai wanda ake zargi gidan gyaran hali zuwa lokacin da za'a sake wannan zama" Haka aka tashi a shria'r yau, aka taho da Yusuf za'a sashi a motar 'yan sanda,' yan jarida sukayi dandazo amma aka hansu magana da shi, Umma ta taho da gudu Suleiman ma cikin hanzari ya nufi inda su Yusuf suke, Umma tana kuka tana "dan Allah ku barni in ganshi ko sau ɗayane, ɗana ne watana kusan biyar rabona dashi, ganinsa kawai zanyi Suleiman dan Allah kace su bari in ganshi" Suleiman yace "Dan girman Allah ku bar baiwar Allah nan taga ɗanta, ko sau ɗayane uwace kunsan ba zata iya jurewa ba, dan Allah ku bari ta ganshi" "Ba a bamu wannan damar ba, seta bari idan mun kaishi prison taje can idan sun batta seta ganshi" Ayshercool 07063065680 11/23/21, 8:06 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 130_131 Haka aka ja mota aka tafi da Yusuf, umma tana ta zabga kuka, Yusuf ma ya sunkuyar da kansa yana kuka a cikin motar nan, shiba kaishi gidan yarin bane damuwarsa, kukan da Ummansa take shine ya tsaya masa a ransa. Dan abun takaici, 'yan jarida sukazo suka kangawa Umman Abubuwan magana sun antaya mata tambayoyi, Suleiman ya janyeta suka hau mota suka tafi, ba tare da tace uffan ba, amma a haka suka naɗi muryarta tana kuka tana ambaton Allah dan suji daɗin yayatawa a duniya. Haka aka watse a zaman kotu, kowa da abunda yake faɗa, wasu su faɗi alkhairi wasu kuma su faɗi som zuciyarsu. Aka wuce da Yusuf gidan gyaran hali, aka bashi kayan fursunoni, aka shigar da bayanan sa, sannan aka kaishi ɗakin daze zauna, mutane masu laifi sunyi su sittin a ɗaki ɗaya, ga rashin isashshen vantilation, ga cunkoso ga tsamin dauɗa da wasu suke yi, gaba ɗaya abun se godiyar Allah haka akaje aka gwamutsa Yusuf a cikinsu. Bayan an tashi daga zaman kotune, Bulama yabi Justice Abdullah gidansa, aka masa iso ya shiga, yana ganinsa A dutse ya faɗaɗa murmushinsa yace  "kaine da kanka haka baa aike ba?" Bulama yace  "Ai saƙonne, yafi da cewa in isar dashi da kaine ba aike ba" "to barka sa zuwa, ya kaga zaman shari'ar tamu na yau?" "To Aini dutse banyi zaton haka ba, muda muke da shedu tuni mun tanada, na gaskiya dana boge amma kace wai ka ɗage sauraren ƙarara, ina laifin a fara gabatar da shedun, nifa da wuri nake son ayita ta ƙare fa, ayi a yanke masa hukunci in rufe babainsa, saboda in dai yana nan ze hanani rawar gaban hantsi, dan gaba ɗayansa matsalane a gare ni wallahi " A dutse yayi murmushi sannan yace " hmmm Bukar Bulama, ai ita shari'a saɓanin hankkalice, bar ganin ka saye ni ka saye lawyoyi da hukunar 'yan sanda, karka manta akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu, na kare haƙƙin ɗan Adam, akwai lawyoyi masu zaman kansu, dukda wasu abubuwa da akayi da suke fito da laifin shi yaron ƙarara, amma duk da haka zasu saka ido akan shari'ar, za' a samu wanda zasu bibiyi shari'ar, dan haka muje a sannu, ina sane nayi hakan komai a sannu akeyinsa cikin hikima da ƙwarewa irin ta aiki " Bulama yace " Aini gaba ɗaya hankalina baze kwanta ba muddin ba a gama shari'ar nan ba, yaron nan fa ba ƙaramin bincike yayi akaina ba, kuma bana son Daula ya bayyana ba'a gama shari'ar nan ba" "Calm down mana, waini haryanzu babu labarinsa, babu wanda yasan inda yake ne? Abunfa da mamaki" "to waye ya sani, anneme shi am rasa kamar wani kuɗi, duk iya bincike na saka anyi amma babu labarinsa, ni dai kayi kayi ayi gaggawa a ƙarƙarw shari'ar nan da wuri, ka yanke masa hukunci, kuma hukunima me tsanani wanda ze ƙare a prison" Justice Abdullah yai murmushi yace  "Bukar Bulama, ai komai akan doka akeyinsa, dukda munawa dokar karen tsaye wasu lokutan, saboda irinku da mukewa alfarma, amma karka damu insha Allah zanyi duk yadda zanyi in ƙarƙare shari'ar nan, ba da daɗewa ba yanzu se Allah ya kaimu bayan sati uku zamu sake zama " "Gara dai ayi a sake zaman, dan Allah karka zake jan lokaci dayawa, bazan iya jira ba, sonake a ƙare komai" "Shikenan, kaje ka kwantar da hankalinka, nan kusa zan ƙarƙare shari'ar hankalinka ya kwanta" Bulama yace "da dai yafi ai" A dutse yace  "Amma, wai ya akayi kaji wannan raunin haka? Gaba ɗaya kamaninka sun sauya kayi wani iri, fuskarka ko ina ɗinki" Bulama ya miƙe yace "karka damu da wannan, ƙyaleni kawai daga nan wani guri zanje, ina nan ina sauraren yadda zata kaya" A dutse yace "shikenan, nagode sosai ka gaida gida" Sukayi musabaha sannan Bulama ya tafi. Nurat! Nurat!! Alhaji Musa ya shigo yana ƙwalawa Nurat kira, ta fito falo tace "Gani" "Ubanwaye yace ki aika wai aje a duba miki Widad?" Ta kalle shi tai shiru, ba tace komai ba. "Ba magana nake miki ba? Ubanwaye yace ki aika wai a dubo miki ita babarkice ita meye haɗinki da ita?" Yai maganar yana zazzaro ido kamar ze daketa. Nurat ta girgiza kai tace  "A'a Daddy nifa ba da wani abu na aika ba, kawai naga ƙawata ce kuma ga abunda ya sameta, ni kuma ka hanani figa, shine nace aje a dubamin" "Ƙawarki ɗin banza da ta wofi, kuma wallahi ki kiyayeni da wannan yaron Khalil, idan kika bari na sake ganinsa a gidan nan sena ci mutumcinsa, sannan kije ki kwaso min wayoyinki ki kawomin su nan, kuma ko kina so ko bakya so sati me zuwa zaki bar ƙasar nan " Mahaifiyar Nurta ta fito tana cewa," Kwanan nsm bam san meyasa kake wannan abubuwan haka ba, meye laifi dan kawai tace aje a duba mata ya take? " " Idan ina magana kika ƙara sakamin baki wallahi sena ci mutuncinki, na gayamiki kin sani sarai abunda ke tsakanina da uban yarinyar, amma take shisshige mata" "Amma larura ai tafi ƙarfim wasa, abun jaje ya samu mutum kace baza'a jajanta masa ba?" Yace  "eh baza'a jajanta ɗin ba, wuce kije ki kawomin wayoyinki, daga yau har ranar da zaki bar ƙasar nan, bake ba fita ko ina, kuma kar wani ya sake yazomin gida, ɗakkomin wayoyinki gabaɗaya, har System ɗinki" Nurat ta shiga ɗakinta, ta ɗauki wayarta ta ɓoye, ta ɗakko sauran ya kai masa, ya karɓi wayoyin da system ɗin yace  "ina ɗaya wayar taki take"? Yai maganar yana kallon ta, Nurat tace  "Na bawa Khalil ya kaimin gurin gyara" "to ki gaya masa maza maza ya kawota, ki aika direba maza ya karɓomin wayar nan, maza fice daga nan ki bani guri" Nurat ta wuce ɗakinta, tana tunanin meye abunyi, koda tsiya koda tsiya tsiya dai bazata bar ƙasar nan ba, se taga abunda ya turewa buzu naɗi" Wasa wasa fa fiye da wata guda babu Anwar babu labarinsa, duk neman dazaa'yi anyi amma ba'a samu Anwar ba, hankalin Hajiya Halima gaba ɗaya a tashe yake, da tana iya basarwa amma yanzu ta kasa jurewa, ga Shu'aibu ya sata gaba yana ta tatsarta kota ko ina, ta zauna tayi shiru a falo ta rasa abunda yake mata daɗi. Sallamar Alhaji Haruna ce tasa ta ɗaga kai ta kalle shi, mamakine yakamata ganinsa da tai kamar korarre, tace  "lafiya kuwa?" "Ina fa lafiya, ina' yarki take?" "wace 'yar tawa kake nufi?" "Yarinyar da kika aiko ta kawon takadda" "Wai Amal kake nufi?" "Eh ita, wadda ta karye" Hajiya Halima tace  "to meye yasa kake nemanta? Wani abun tayi makane ko kuwa?" "Eh nemanta nake" Amal tace "gani nan, lafiya kake nemana haka? Ko kuma naci ban biys bane?" Suka juya, suka bita da kallo, tace  "meye kake nemana?" Sekuma ya diririce, ya rasa me zece ganin ga Hajiya Halima ta tsatstsare shi da ido. Amal tace  "faɗi mana, ina jinka" Hajiya Halima tace "nifa gaba ɗaya kaina ya kulle, kumin bayanin abunda yake faruwa" Amal tace  "Mummy, ki kwantar da hankalinki babu wani abu fa, Alhaji muje farfajiya muyi magana" Amal ta janye shi zuwa farfajiyar gidan ta kalle shi tace "lallai kaci ksi, baka da hankali da nasani nz tona maka Asirin abunda kayimin a gabanta, tunda kanka baya js yadda yakamata" "wace maganar banza kikeyi hakane? Me kika aikatamin?" "ba wani abu na aikata maka ba, illa na saka maye na ɗauki wayarka na bayar anyi abunda yakamata na turi kuɗi daga Account ɗinka, na raba kuɗin gida biyu na ɗau rabi, shine fansar budurcina daka ɗauka, kuma bari in gaya maka wani abu, akwai mahimmin saƙo da na ajiye na rarrabawa mutane, wallahi duk abunda ya sameni kaine, seka ƙara wannan akan kaidim mata da kace mim ba wanda baka sani ba, wawa kawai kuma wallahi ka kuma zuwa gidan nan duk abunda nayi maka kaika siya da kuɗinka ba wani ya sai maka ba, kuma a taƙaice takadda dai babu ita dan nima ban san inda take ba" Ta ƙarasa maganar tana masa wani irin mugun kallo, ta shigevta barshi a gurin kaman gunkin mutanen farko. Har ta shiga zata wuce ɗakinta, Hajiya Halima ta kira sunanta   "Amal" Ba tare da ta juyo ba ta tsaya cak , "meye haɗinki da wannan mutumin?" "Babu komai" "Karkimin ƙarya, meye haɗinki dashi?" Yace "yana so nane, nikuma nace bana sonshi, ya takuramin nikuma na zage shi, shine zezo ya ɗagamin hankali" "to dan ba kya sonsa meye na zagin masa kuma? Ai bekamata ki zage shi ba" "to Mummy ni kalarsa ce? Ko da ƙuriciyata zan Auri wannan dattijon mutumin ne? Ai uba na ɗauke shi, amma tunda bega hakan ba shine nai masa abunda ya dace dashi" "koma dai meye karki kuma zaginsa, dan ya haifeki kuma koba komaiakwai mutunci, da alaƙa tsakanina dashi" "karki ji komai Mummy, hakan bazata sake faruwa ba"  ta wuce ɗakinta. Bulama ya fito ze fita, yaga motar Fahad a harabar gidan, dan haka ya fasa fitar ya nufi BQ inda suke, a falo ya tarar da Fahad, yana ƙoƙarin kunna TV, ya kalli Fahad yace  "kai daga ina kake? Na samu labarin seka kwanaki baka gidan nan, gidan ubanwa kake zuwa haka?" Fahad ya sosa kai yace  "Daddy gurin abokaina nake zuwa, shiyasa" "wasu irin abokaine zakaje ka kwana huɗu a gurin su? Kai baku da gidane?" "muna dashi" "to ya akayi kake zuwa kwana wani guri?" Fahad yai shiru, Bulama yace  "Shikenan ka kiyaye idan na sake ji sena hukunta ka na gaya maka" Fahad yace 'to, amma Dad what's wrong with you in your face, naga ɗinki a fuskarka" "Da ka damu dani ai da baka fita ba, kaje kayi kwanaki haka ba, ban sani ba" "Sweet heart, wai har yanzu me kake a falon ne?" Wata yarinya ce ta fito da Towel ɗaure a ƙirjinta daga bedroom ɗin Fahad, Fahad ya shiga zazzare ido, Bulama yace  what, mezam gani haka? Fahad wacece wannan? " Fahad ya sunkuyara da kai yana sosa kai," ba magana nake maka ba? Wacece wannan ɗin me take a nan ". " Daddy dan Allah kayi haƙuri " " Sallameta tazo ta barmin gida maza maza " " wallahi ka bani kunya Fahad, neman mata? Akanme kuma a cikin gida na dan asara" Fahad yace "wallahi Daddy ni Aure nakeso, kuma har yanzu kaƙi ka auramin Widad shiyasa, ni gaskiya shiyasa kawai nake bi ta ɓarauniyar hanya" Bulama ya dinga masa bala'i, ya kori karuwar nan, ya taho cikin gida yana zazzaga bala'i,  "Sarah, kina gidan nan amma yaron nan yake neman mata, kai Ramadan ga ɗakinka ga nasa, amma yake kawo mata gidan nan baka taɓa faɗa ba?" Ramadan yace "ai Daddy kafi sonsa, kuma kona faɗa ba yadda zakayi ba Shiyasa" "Nika ke gayawa haka Ramadan?ke Sarah kina kallo amma baki ɗau mataki ba, ko ki gayamin ba?" "Barewa bata gudu, ɗanta yai rarrafe"  shine amsar kawai data bashi, ya tsaya sororo yana kallonta. Nurat taje ta ɗauki wayarta, ta ɓoye ta shiga tunanin yadda zata bawa Khalil wayar nan, ba tare da mahaifinta ya sani ba, tunda an hanata fita, kuma Mahaifiyarta na ja maata kunne sosai akan shisshigi akan lamarin mahaifinta. A hankali ta lallaɓa ta sato wayar Mum ɗinta, ta dawo ɗakinta ta kira Khalil, yana ɗagawa tace "Brother a gurguje, dan Allah karka sake zuwa gidan Bulama neman Widad, akwai wata ƙulallaiya a ƙasa, akwai wani abu ds suke ƙullawa shi da Daddy na, ya gaya masa kaje gidansa neman Widad, amma Daddy yazo yana ta faman min faɗa, ya ksrɓs wayoyina saura ɗaya kawai, ya za'ayi kazo ka karɓa? " " Nima na fuskanci akwai wani abu a ƙasa a tsakanin mahaifinki da Bulaman nan, ina da wani plan ne a ƙasa, amma karki damu zanzo in karɓi wayar " " karka soma zuwa Brother, akwai matsala, zan san yadda zanyi idan ina so muyi magana zan kiraka a wayar Mum, se anjima " Tai sauri ta kashe wayar, ta lallaɓa ta mayar mata da wayar. Bulama ya kalli Fahad dake zaune ya sunkuyar da kai yace " kai dama Aure kake so amma ka tsaya kana bin wannan sakarkarun matan? Bayan zan aura maka cikakkiyar mace " " Daddy wane cikakkiyar mace, bayan har ciki gareta?" "ina ruwanka da cikinta? Nayi wani planning akanta, yanzu haka tama gidana na can hanyar ƙuyukan nan ma bayan gari, in da nake noman albasa, wannan gidan can na kaita na ajiye, kuma ko tana so ko bata so, za'a zubar da cikin nan ka Aureta, amma wannan da kake kawowa aiba mata bsne, idan aka kamanta su da ita " Fahad ya washe baki yace " to Daddy nagode sosai, wallahi idan na Aureta sema rama dukan da tayi min, bazan manta marin nan ba" Bulama yace "kai dai ka bari, aure kamar anyi an gama ne ai" Fahad ya dinga washe baki, kamar wani sakarai. Widad duk ta ƙare saboda larura da rashin kula, gashi cikin nan ya sakata gaba da Amai komai taci baya zama in dai ba Ruwan sanyin nan ba da lemon tsami, a ɓoye take zuwa ta turasasa Widad taci Abinci, sam bata kwanan kan katifar nan sedai kan tiles, duk ƙibarta seda ta ƙare ta rame sosai, duk tayi wani iri. Yauma meaikin me suna Sabuwa tazo tana bata ƙosai da kunu, tana ci ds kyar, can Widad tace "Dan Allah ina labarin mijina kuwa? An fara shari'arsa ko?" Sabuwa tace "gaskiya an fara, dan har Alƙali ya kaishi prison se bayan sati uku za'a cigaba da shari'ar" Widad ta girgiza kai cikin ƙunar zuciya tace "Allah sarki mijina, Allah ya kawo maka mafita ta inda baka zata ba, babu abunda zan iya yi a kai, Allah ya fitarmin da kai Yoseef" Sabuwa tace "Addu'ar dai da kike masa ita yakamata ki cigaba amma ba wannan kukan ba" Widad dai nata shiru ba tace komai ba, dan tayi nisa bata jin kira, can tace "zan kwanta, ina son inyi bacci" Sabuwa tace "to shikenan" Ta tashi ta bawa Widad guri, ta rufe mata ƙofa, Widad yau taji bata san kwanciyar tiles ɗin ta koma kan ƙatuwar katifar dake baje a ɗakin, ta rage kayan jikinta ta kwanta tayi shiru, ko yaya Yusuf zeyi a prison, tana kwance akan katifa, amma bata ds tabbacin a inda Yusuf yake kwance a prison, ta tashi da sauri, taje ta leƙa tagar dake ɗakin. Ko ina da haske, ga wasu ƙarti ne ke sintiri a harabar gidan, babu hanyar guduwa, gashi dama hanyar gurin gaba ɗaya babu gidaje, se kangwaye da gonaki, da manya manyan filaye fetal a gurin, dan haka babu hanyar guduwa. Ta koma kan katifar nan, ta kwanta wani irin ƙaunar Yusuf da tausayinsa na ratsa jinin jikinta, ga wani irin mugun kewarsa da take yi, tana buƙatarsa a kusa da ita, ta tabattar da yana kusa da ita yasan da cikin nan, zata sha kulawa sosai. Ta ƙanƙame filon nan a ƙirjinta, tana hawaye, a hankali tace "i miss you Yoseef, ina kewarka sosai, Allah yasa abunda ya faru karyasa ka dena sona, ina sonka Yoseef ka yafemin please, dalilina ka shiga wannan halin Yoseef, ina sonka Yoseef dan Allah ka dawo gare ni" a hankali take furta maganar tana zubar da hawaye. Kwana uku da kai Yusuf prison Umma ta damu ta ɗaga hankalinta, akan lallai seta je ta ganshi, dan haka Suleiman yaje har gida ya ɗakko ta suka tafi gidan yarin tare. Kasancewar Suleman ɗansanda ne yasa har gurin shugabn gandirobobi na gidan suka shiga, suka gaisa Suleiman yace  "wannan mahaifiyar Yusuf ce, da aka kawo gidan nan, dan Allah munzo a bamu dama dan Allah muganshi" Shugaban gandirobobin yace "a gaskiya ba'a bamu wannan damar ba, daga sama akace karmu bar kowa ya kawo masa ziyara" Suleiman yace "saboda shi ba mutum bane? Ko kuma ba ɗan ƙasa bane ba? Haba dan Allah, wallahi kwata kwata babu adalci a shria'r da za'ayiwa Yusuf, dan Allah ka dubi girman Allah ka bari mu ganshi" Umma cikin kuka tace  "dan Allah dan Annabi ɗan nan kabari in ganshi, kusan watanni biyar zuwa shida, tynda akayi garkuwa dashi, ban sashiba idona ba ka temakamin" "Wannan ce mahaifiyarsa?" Suleiman yace "eh mahaifiyarsa ce" Yace "kaman ba ita ta haife shi ba, kamar yayarsa, anyway gaskiya na lura da yanayinsa, tunda aka kawo mana shi gidan nan, ba sawa ba fitarwa, ko magana ba ruwansa da kowa, bashi da Hayaniya sam hakan yasa na fara tausayinsa, kuma nake jin ina shakku akan laifin da akace yayi, sedai baya iya cin Abincin gidan nan kunsan yanayin yadda Abincin namu yake, kuma gashi ance ba'a yadda kowa yazo gurinsa ba, nayi nayi inyi interview dashi amma yaƙi magana Sam " Sulaiman yace " ai ba lallai yai maka ba, kaima Allah ya saka maka da alkhairi, shima abokin aikinmune ɗan sanda sakamakon wannan abunda ya faru, naji an sanar da an kore shi daga aikin, amma ita gaskiya ai zata yi halinta, nidai fatana ka mana wannan alfarmar dan Allah, ka bari mu ganshi" Yace " Shikenan, kuyi zamanku bari aje azo dashi" Suna nan zaune yai umarnin, aje azo da Yusuf suka cigaba da tattaunawa da gandiroban nan. Aka shigo da Yusuf sanye da kayan prison, yana jan ƙafarsa da ƙyar da alama ƙafar ciwo take masa, da Gudu Umma ta tashi taje ta rungume shi tana kuka, Yusuf yasa hannayensa ya rungumeta shima, hawaye na gangarowa daga idonsa. Tana so tayi masa magana amma takasa, se kuka da take Yusuf ya share nasa hawayen sannan ya ɗago Umman ya kalleta ya ƙaƙalo murmushi yace  "Umman Yusuf, baki da lafiya ne? Kinyi baƙi kin rame sosai" Girgiza kai take tace  "Yusuf ka ganka kuwa? Gaba ɗaya ka fita hayyacinka kamsr ba kai ba, fuskarka duk ciwo Yusuf garin yaya haka ta faru?" Yusuf bece komai ba, se cigaba da share mata hawaye da yayi, ya samu guri ya zauna, suka gaisa da Suleiman, Suleiman yace "nayi iya ƙoƙarin da zanyi, akan a barni inzo inda kake amma abu ya gagara, se yanzu da aka mana alfarma" Yusuf yace "Aini bani data cewa, na barwa Allah shine ze fidda ni" Suleiman yace  "waini ina Saleh nema, Saleh yasan komai fa" Yusuf yace "Anyiwa Saleh illafa saboda duka, inaga wani abu ya taɓu a cikin sa, yana kwance a Asibiti" Umma tace  "Yusuf wai ya akayi haka ta faru ne? Ya akayi aka kamaka kaida ita? Ance kai kayi garkuwa da ita harda fyaɗe, garin Yaya Yusuf" "Umma kin yadda zanyi haka?" "Kasan bazan taɓa yadda ba ai, ina son jin dahir ne" "Umma, na shiga wannan halin ne dan kawai na temki Widad, ita kaɗai zata iya bada sheda akan abunda ya faru, se kuma Saleh, kinga bansan ma inda Widad ɗin take ba" Suleiman yace "tana hannun abokin babanta Bulama" Yusuf yace "Bulama kuma?" "Eh tana hannunsa" Yusuf yai ajiyar zuciya, Umma tace  "wai ya akayi aka kamaka da ita a ƙauye? Garin yaya Yusuf?" "Umma Aure mukayi da Widad" Ta kalle shi tace  "Aure kamar yaya?" Gandiroban nan yace  "Hajiya lokaci yayi, yakamata ku tafi haka" Umma tace  "to hakanma nagode sosai Allah yasaka da alkhairi" Suleiman ya bawa Yusuf siyayar da suka yi masa, suka tafi yakasa waigawa ya kuma kallon Umma saboda yasan kuka take. Suka juya suka bar Yusuf a gidan yari. Bayan tafiyar su Umma, wannan gandiroban yasa aka canzawa Yusuf ɗaki, zuwa me mutum Ashirin, yana nsn kwance yana tunanin rayuwa, mussman Widad ya damu da yaji Widad wai tana hannun Bulama, shifa tun farkon saninta da yayi ya tsani Bulama, mussman da yayi bincike a kansa, sosai yake kewar matarsa, yana son sanin halin da take ciki, yana missing ɗinta sosai, kawai Fahad ya faɗo masa a rai, take yaji gabansa ya faɗi ya miƙe tsaye da sauri. Cikin dare bacci da ƙyar ya ɗauki Widad, baccin beje ko ina b taji an motsa ƙofar ɗakin da take kwance, a hankali an buɗe ƙofar. Banyi editing ba amin afuwa A siya kafin a karanta dan Allah Ayshercool 0009450228 11/23/21, 8:45 AM - Buhainat: Ki tura document din nan anjima takwara🙏🏻🙏🏻 11/23/21, 8:48 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 132_133 Widad ta buɗe idonta a hankali, tana son ganin waye wannan ya shigo mata haka a wannan daren, Kasancewar ɗakin da duhu shi baya ganinta se ita ke ganinsa, ya ɗakko ƙaramar wayarsa ya kunna ya haskata, tana kwance ta lumshe ido kamar me bacci, ya tako ya ƙaraso a hankali inda take, ya ƙara hasketa da fitila ya kai hannu a hankali ze taɓata ta miƙe zaune da sauri. Tace "waye wannan? Ɗan dena haskani mana, waye wannan zaka shigomin ɗaki babu izini ko baka san ni matar Aure bace"? "Aurenki na banza dana wofi, nazo in rama marin da kikamin ne, yadda gobe in ance ki kuma yiwa wani abunda kikamin, bazaki ba" Se yanzu ta ɗau muryarsa, Fahad ne ba wani ba dan haka tai zumbur ta miƙe tsaye, shima kuwa ya miƙe, ya kai hannu ya riƙota ze gwada mata ƙarfi, sedai tarihi ya maimaita kansa, kamar yadda ta taɓayi masa shekarun baya, ta saka masa haƙora a hannunsa, wata irin azaba yaji ta ratsa shi tun daga yatsunsa har kansa, ya danƙi kanta yai jifa da ita a ƙasa, ai kuwa kanta ya gwaru da bango, hancinta ya fashe, ta saki wani marayan kuka, saboda zafi da taji, ya kuma yo kanta amma cikin sauri da zafin nama, ta tashi tai waje da gudu tana ihu, sedai duk wannan ihun da take babu wanda yayi yunƙurin kawo mata ɗauki, nan suka shiga guje guje dashi, Allah ya bata sa'a ta samu wani ƙarfe ta buga masa ya gigice, ta koma ɗakinta da sauri ta rufe ƙofa, gigicewar da yayi tasa yakasa komai ya shiga tangaɗi a gurin, duk ta bashi wahala sosai. Ta shige banɗakin dake ɗakin ta rufe, ta dinga rusa kuka, gaba ɗaya ta rasa mema zata yi? Ta ding kuka me sauti. Haka nan Yusuf ya dinga jin faɗuwar gaba a wannan daren, yakasa bacci sam, ƙirjinsa ya dinga bugawa da sauri, yakasa zaune ya kasa tsaye kawai yake jin kamar wani abu yana faruwa da Widad ɗin, ya dinga addu'a a haka har gari ya waye ba tare da ya rintsa ba. Alhaji Haruna ya rasa me zeyi wa Amal ya huce, kuɗin data kwasa a account ɗinsa ba ƙananan kuɗaɗe bane, ya rasa meze mata wanda ze huce. Yana zaune yana wannan tunanin Salma ta shigo ɗakinsa a fusace, ya ɗaga kai ya kalleta yace "lafiya kuwa?" "dole ka tambayeni lafiya mana, munafuki macuci, to bari kaji in gaya maka, barin gidanka zanyi bazan zauna ba da kai ba Wallahi, dama can ba sonka nake ba aka ƙaƙabamin kai" "Ni se wasu maganganu kike wanda ban gane inda kika dosa ba, kimin bayani yadda zan gane mana" Jefo masa wayarta tayi, ya ɗauka ya duba, message ne aka turo mata da wata baƙuwar lamba  "Ki saka ido akan mijinki, in bahaka ba watarn ze shafa muku ciwo, dan yana ta'amalli da mata a guest house ɗinsa, idan kin musa ina da sheda, zan iya turomiki idan kina da buƙata" Wani gumine ya fara tstatsafo masa, ya dake yace "wannan wane irin shirme ne za'a turomiki ki yadda, kawai a turomiki magana ki yadda, wataƙila ma bake za'a turowa ba" "ɗan saurara karka rainamin hankali mana, idan ƙarya ake maka saƙon ya rasa wayar waze faɗo se tawa? Kuma yawan fitar cikin dare da kake wataran bako sallama ina kake zuwa?" "wannan kuma harkar aikine ke fitar dani" "harkar banza dai, wans irin aiakine baza'ayi shi da rana ido na ganin ido ba se a takatainin dare, wallahi kaji tsoron Allah, kome kake aikatawa Allah yana kallonka, kuma wallahi idan na tabattar da abunda naake zargi seka sakeni wallahi, kuma sena tona maka Asiri a idon duniya, bani wayata ni" Ta saka hannu ta ɗauke wayarta, tai waje ranta a matuƙar ɓace, ya dafe jansa kallai wanna kafon ya ɗebo ruwan dafa kansa, ga ya haɗu da mskira 'yar damfara. Kiran Bukar ne ya shigo wayarasa, jiki na rawa ya ɗaga suka gaisa  yace "Haruna na gaji da wannan zagaye zagaye da raini hankamin da kakemin, ka fito ka gayamin gaskiya mske faruwa, ina takaddar nan take? Idan kuma wata manufar ce da kai kuma seka ajiye agurinka" Alhaji Haruna yace "Babu yadda za'ayi takaddar nana tana gurina inƙi kawowa, wata 'yara matsala aka samune, kuma ba da daɗewa ba zan warwarwta a ɗan ƙara ɗagamin ƙafa" "Bana alfarma a karo biyu, daga ta farko bana ta biyu, Amma ka sani daga wannan shikenan, idan wani ya samu takaddar nan Asirinmu ya tonu, ze zama hujja akanmu, gara idan ɓataraa kayi ka nemota tun wuri, idan kuma ɓoyewa kayi kaje ka cigaba da ajiyar ta karka fito da ita " Ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya rasa abunda zeyi, aka kuma kiransa da ovt number, kamar kar ya ɗaga amma ya ɗaga," ɗan duba what's app ɗinka akwai saƙo" Be ɗauki muryara waye ba, amma dai muraya mr mace ce, ya kunna data ya shiga what's app ɗinsa, messages suka gama shigowa sannan ya shiga dubawa. Video ɗin tsiraicinsa ne da wata wadda besan kowacce ba a guest house ɗinsa, daga ƙasa aka rubuta  "dukda wannan abubuwan da na maka banji na fanshi mutuncina daka keta ba, wallahi idan baka biniba sannu ba sena yaɗawa duniya, kuma yanzu a haka akwai video ɗin nan a wayar mutum huɗu, isan har wani abu ya faru dani zasu watsa a duniya" Ko ba'a gayamasa ba yasan message ɗin Amal ne, yace  "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, be taɓa gamuwa da masifa a rayuwar sa irin wannan ba, ya ɗebo ruwan dafa kansa over. Widad kam seda gari ya waye yayi haske sannan tai alwala ta fito tayi sallar Asuba, ta dinga kai kukanta ga Allah, kuka kama dama ya zame mata jiki, dan inda sabo ta riga ta gama sabawa. Tana cikin kukan ne Sabuwa ta shigo mata da abun karyawa, Widad ta kalleta tace "yanzu dan Allah jiya baki ji ihuna ba cikin dare?" Sabuwa tace "idan nace vamji ba nayi ƙarya, sedai kona fito ba abunda zan iya yi miki, saboda Kinsan nima aiki aka ɗaukeni inyi, idan na shiga hurumin da ba nawa ba, zasu kasheni ne, seda akamin wannan sharaɗin sannan na fara aikin kula dake ɗin nan" Widad ta jinjina kai tace "ɗauke wannan Abincin bana ci" "Saboda me?" Widad tace "kawai bana ci" Haka Sabuwa ta kwashe kayan Abincin nan ta fita dasu. Widad tana nan zaune sega Bulama ya shigo ɗakinta, shida wasu ƙarti su biyu, aka kawo masa kujera aka ajiye, ya hau kai ya zauna ya kalli Widad yace  "karo na ƙarshe, ki gayamin inda takaddun nan suke" Widad ta kalle shi tace  "gargaɗi na farko kuma na ƙarshe, ka jawa ɗanka kunne, idan ya sake zuwa inda nake, wallahi sena kasheshi har lahira" "ina miki magana kina gayamin wani shirme daban? Ki kasheshi ɗin karki fasa, ina takaddu suke su nake tambayar ki" "Na miƙasu ga masu shi" Bulama yace "zan azabtar dake, azaba irin wadda ba'a taɓa yi miki ba, ina suke?" "Duk Azabarka a duniya ne kawai, kuma babu wanda yake da ikon yin azaba se Allah, na gaya maka na bawa masu dukiyar nan dukiyarsu, ka ƙyaleni ka rabu da rayuwata haka" Bece mata uffan ba, taga na jona wani abu a jikin socket, an miƙawa Bulama ya karɓi abun yayo kanta gadan gadan, bata motsaba ta tsaya tana kallonsa, kawai ya jona mata abun a hannunta, ji tayi kamar ba a duniya take ba, ta rasa meke mata daɗi gaba ɗaya ta fita hayyacinta. "zaki faɗa ko bzaki faɗa ba?" Girgiza kai ta dingayi tana kuka, amma taƙi magana, yasa ƙafa ya take yatsunta yana murzawa ciki mugunta, amma dayake Indai taurin kaine Widad ta iya shi taƙi magana. Ba azabtarwar da basu mata ba amma taƙi faɗa, haka suka gaji Bulama ji yake kamar yasa wuƙa ya yanka ta, amma yaga idan ya kashe ta beyi Achieving komai ba, haka suka tashi suka fita, suka barta  a galabaice. sedai fitar sa babu daɗewa wani irin ciwon kai ya kama Widad, ko iya gani ba tayi sosai,  ga ƙirjinfa daya riƙe gam, nan ta kwanta tun tana kwnace, harta fara juyi ya zamana bata iya ganin komai, se dishi dishi daga baya kuma ta dena gani gaba ɗaya. Daga nana bata sake farkawa ba se a gadon Asibiti, taji anayiwa Bulama bayanin zuciyartace ta kumbura kuma ga jininta ya hau, Ba tausayi ba imani Bualama yayiwa doctor Hamisu umarnin ya cire ɗan cikin Widad koda tsiya ne. Ta buɗe idonta fes a kansu, amma hakan besa Bulama yai shiru ba, ya bada umarnin a cire cikin. Haka doctor Hamisu yaje ya ɗakko allurai, yazo ya haɗasu yayi mata duk tana kallonsa, sedai ta kasa motsa koda ɗan yatsanta ne, gaba ɗaya tama rasa inane yake mata ciwo, haka ya kwance cannula yai mata wata allura, sannan yasa wata a ruwa, ya gama ya fice tana kallonsa. Sosai Yusuf yake jinsa a damuwa, hankalinsa yaƙi kwanciya sam, yake jin jikinsa ba daɗi, tunanin Widad ya cika masa zuciya. "To wai kai Haruna ya akayi ka bari haka ta farune? Ta yaya yarinya ƙarama zata dinga wasa da hankalinka haka?" Alhaji Haruna yace "kai dai bari kawai Alhaji Musa, wallahi nikaina ban san abun ze kai haka ba, ganin irin kuɗaɗen dana bata, ni nama rasa abunyi wallahi, babban abun tsorona shine video na data ɗauka, karta saki a duniya mutuncina ya zube" Alhaji Musa yace "rabu da ita, duka barazanar banzace ba zata saki ba ƙarya take" "Ya zakace ƙarya take? Bayan har Salma ta turawa message a kaina?" "ni nace maka ka ƙyaleta ai, to ka ƙyaleta ba zata iya yaɗawa ba, sannan batun takadda ka gayawa Bulama gaskiya kawai, ai da tun farko ka faɗa masa ma da tuni an wuce gurin, ƙilma yai maka maganinta" Alhaji Haruna dai yai ajiyar zuciya yai shiru kawai. Bacci ne ya ɗauki Widad me nauyi, sedai wani irin gigitaccen ciwon mara yasa ta farka babu shiri, ji tayi wani irin ciwo yana ratsata, tun daga mararta zuwa bayanta da ƙafafuwanta, wani irin ƙarfine yazo mata, ta zabura ta fizge cannula, aikuwa take jini ya shiga zuba daga inda ta cire cannulan. Ta faɗo daga kan gadon, Nurses ne suka shigo da sauri, suka ga yadda Widad ta faɗo ƙasa, ta riƙe mararta hawaye na zuba daga idonta, alamar tana jin jiki, ɗayar ta kalli ɗaya tace  "Sister, ki kira likita da sauri yazo ya dubata" Tace "shikenan bari inje" Tana zuwa ta sami doctor Hamisu a Office tace "doctor, patient ɗin Alhaji Bulama ta Amenity she's unconscious fa, harta faɗo daga kan gadon" "Ku kaita labor room kuyi mata abunda yakamata, Abortion ne cikin jikintane ze faɗi" "doctor, amma naga kaman ba case ɗin Abotion aka kawota ba, cardiac failure ne, da hypertension kawai, ya za'ayi within a minutes ace kuma Abotion yai occurring" "Are you going to teach me my job? Wace makarantar kika yi ne, baki san cardiac failure na uwar ze iya shafar abunda ke cikinta bane? Get out from here kije kuyi abunda nace" Jiki a saluɓe Nurse ɗin ta fita daga Office ɗin ta koma ɗakin Widad, ta tarar da ɗaya Nurse ɗin rungume da Widad tana mata sannu. "Sister ina doctor ɗin?" "naje yamin wulaƙanci, wai mukai ta labor room abortion ne, muyi mata abunda yakamata, shikenan babu wani taimako da za'a bata se a bari cikin ya fita?" 'haka yace miki? " " Gashi kuwa ina gayamiki, zan masa ƙaryane? " Widad kam banda aikin gumi babu abunda take yi, fuskar nan tayi jawur saboda azabar wahala, haka taita wannan wahalar tana addu'a tana ambaton Allah, tana roƙon Allah ya bar mata cikin nan. Ɗayar taje ta samo wata allura a pharmacy tayi wa Widad, cikin ikon Allah se bacci ya ɗauketa, can sega doctor Hamisu ya shigo yana cewa "Yaya? Cikin ya fita dai ko?" Ɗayar tace "ta samu relief bacci take yi" "Ya faɗin dai ko?" Nurse ɗin tace "Eh ya faɗi, mun gyarata ne ta samu hutu, amma babu wani wanda suka zo tare da ita ne?" "Ba ruwan ku da wannan, tunda mun samu ya faɗi Alhamdilillah, a bata medication ɗinta na dare" "To insha Allah, za'a bata" Bayan fitarsa ɗaya ta kalli ɗayar tace  "Sister Habiba, kijimin ikon Allah, ni anya ba doctor ne yai mata wani abuba akan cikin nan ba kuwa?" Sister Habiba tace "ya za'ayi in sani, amma nima ina zargin hakan wallahi, Allah sarki tana murƙusus amma fatanta Allah ya bar mata cikin ta, Insha Allah be zube ba, ko akanme ze damu cikinta ya zube oho" "Hmm kedai bari, shida wannan Bulaman dama basu fiye ƙulla abun Arziki ba, naga shiya kawota kika bibiya karuwarsa ce, ko kuma dai cutarta sukayi suke so su rabata da cikin, kin san ɗan Bulaman Fahad ya saba kawo mata nan a cire musu ciki" Sister Safiyya tace  "ai kedai bar masu kuɗin nan kawai, Allah dai ya shirya naga ta samu bacci, gashi babu kowa a gurinta, balle idan ta farka a bata Abinci" Sister Habiba tace "ai kamar yadda kika faɗa ɗinne, kika bibiya dai ba ta hanyar Allah aka samu cikin ba, shine suke son su zubar mata ta ƙarfin tsiya" Baiwar Allah, ita Widad sam bata san meke faruwa ba, wani galabaitaccen baccine ya ɗauketa, wanda fal yake da mafarkin Yusuf cike da bege da shauƙin son ganinsa, se kuma mafarkin daddy da take yi. Ɓangaren Ramlah kuwa, taga kwata kwata kusan Fahad yayi dumping ɗinta aside, kwata kwata baya ta tata yanzu, dan haka ta shirya da kanta ta tafi Hotel ɗin da yake zuwa, tana zuwa kuwa ta sameshi da wata mace a ɗakin, Ranta ya ɓaci matuƙa ta dube shi tace  "Lallai Fahad, ka cika tantirin butulalle, a wani postion ka ajiyeni ma tukuna?" Fahad yai murmushi yace "postion ɗinki dai na farko, a nan ns ajiye ki, me kike tunani" "dalla saurara, karka gayamin maganar banza mana, ban gane postion ɗina na farko ba, ina maganar Auren mu da kai?" Fahad ya kwashe da dariya yace "haba tawan, meye muma na ɗaga jijiyoyin wuya haka? Maganar Aure tana nan mana, ki bari idan na Auri Widad kema se inzo daga baya in Aure ki" Ta kalle shi tace  "Fahad, yau wace irin giya ka Shane haka? Data gaya maka ƙarya wadda harta saka ka kalli idona kake gayamin maganar banza da iska?" "irin wadda na saba sha ce dai, sedai ban sani ba ko nasha expired ne" "Lallai Fahad kana wasa, baka san abunda ka aikata me ze haifar ba ko? Ds kyau wallahi ka ɗebo ruwan dafa janka in dai Ramlah ce, zakaga tsiya" Ta juya buguzun buguzun tai waje, bata zame ko 'ina ba se ofishin Bulama, tana zuwa ta tarar yana aiki a Office, sedai tayi mamaki ganin ɗinki haka a fuskarsa, koda yake ba wannan yakawo ta ba. Ya ɗago ya dubeta yace "Ramlah lafiya kuwa? Ya kika shigomin Office haka?" "Kamawa tayi na shigo a haka, ina maganar ds mukayi da kai?" "wace maganar kenan?" "Maganar da mukayi akan wannan mutumin, da yake iƙrarim shi mahaifin mu ne, kace zaka ɗau mataki akansa, amma har yanzu bani da tabbas na ka ɗauka kokuwa?" "Banda abunki Ramlah, nima fa ban san takamaimai inda yake zaune ba, ta yaya zan ɗaukar miki matakin? Nasa aje inda nasan shi, amma baya nan baya zama a guri ɗaya sam" Tai tsaki sannan tace  "waima ni wane irin hatsari ne dashi haka, wanda yasa Mummy ke tsoronsa?" Bulama yace "wannan tambayar ai ita zakiyiwa bani ba, kije ki tambaye ta zata gayamiki komai" Tai ajiyar zuciya, tare da jinjina kai tace "idan kai baka ɗau mataki ba, nika gayamin inda yake in ɗau matakin daya dace dashi mana" "Haba Ramlah, kema kin san da nasan inda mutumin man yake aida da kaina zam ɗauksr miki mataki akansa" Kallon Bulama kawai take, ba wai dan ta gamsu da abunda yake faɗa ba, ta suri jakarta tai waje tana ƙwafa. Fafur Nurat ta dena fitowa ko falo, saboda karma su haɗu da mahaifinata yai mata zancen komawa ƙasar waje. Dayake yau Weekend ne sam be fita ba, yana gida amma still bega gilmawar Nurat ba, ya tafi ɗakin matarsa ya tarar tana kwance tana chatting, yace  "wai ina yarinyar nan ne? Wunin yau banga gilamawarta ba" Ta tashi zaune tace "tana ɗakinta mana, kasan halimta wasu lokutan bata san shiga mutane, tafi son zaman kaɗaici a ɗakinta, balle kuma ka ƙwace wayoyin ta" "Ina fatan dai tana nan tana shirin tafiya?" "tafiya ina? Ai wannan maganar kuce kai da ita" "kamar yaya kenan?" "kamar yadda nake gayamaka mana, kai ds ita kukayi magana, dan haka babu ruwana ka tambaye ta idan tana shirin da kanka" Ya jinina kai, kwanan nan yaga zam iyalin nasa sun dena tsoronsa kamar yadda suke tskronsa a baya, ya rasa dalili. Yana shiga ɗakin Nurat, ya tarar tana tilawar Al'qur'ani mai girma, ya jira ta kai aya ta ɗago ta kalle shi, dan taga magana yake son suyi. Yace "dama zuwa nayi in ji ko kina shirin tafiyar nan kuwa? Jirginku ze tashi jibi in Allah ya kaimu fa" Nurat ta miƙe taje ta ajiye Al'qur'anin ta sannan tace "nifa ba inda zanje Daddy, tsawon shekaru ina maka biyayya, dukda yi maka biyayya umarnin Allah ne, amma nima kayimin adalci mana, wallahi idan na tafi karatun nan bashi zanyi ba, rayuwata kawai zanyi" A fusace  yace "ni kike gayawa haka?" "wallahi Daddy kace sena tafi guduwa zanyi daga gidan nan, ni bana son tafiyar" Ya ƙura mata ido na wasu mintuna, sannan yai ƙwafa ya tashi ya fita. Widad tana gadon Asibitin nan, ko iya miƙesa ba tayi, amma a haka aka sakata a wheel chair, Aka kaita mota aka maida ita wannan gidan da ake ɓoye ta. Haka aka maida Ita, yau s bsta wannan maganin gobe a ɗurma mata wannan Allurar, haka take ta fama ga ciwo yaƙici yaƙi cinyewa, banda izayar da Bulama ke mata akan ta bada takaddun nan. Kwanci tashi asarar rai, Yusuf ya cika sati uku cif a gidan yari, rana ta zagayo aka koma dashi kotu domin ci gaban shari'arsa..... IDAN KIN SAI LITTAFIN NAN KE KAƊAI KIKA SIYA, KUMA AMANACE TSAKANINA DAKU, IDAN KUKA FITAR BAKUMIN ADALCI BA, TUNDA BAMUYI DAKU ZAKU FITARMIN BA. AYSHERCOOL 07063065680 11/23/21, 10:26 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 134_135 Yauma kotun a cike take maƙil da ɗan Adam, 'yan jarida kota ko' ina, ga 'yan sanda da sauran mutane domin sauraren cigaban ƙararar, seda akayi kusan shari'a uku sannan aka gabatar da ƙarar Yusuf, Barrister Sadik ya fito ya sake gabatar da kansa a gaban kotu, sannan yace ze fara gabatar da shedun su akan Yusuf. Barrister Sadik yace  "zan fara gabatarwa da kotu shedarmu ta farko akan cewar Yusuf shine yayi garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula" Nan Barrister ya kira wani mutum, mutumin ya fito ya tsaya ya fuskanci kotu, Barrister ya taka gaban sa yace  "ko zaka iya faɗawa kotu sunanka?" Mutumin yace  "Sunana Sada" "Kasan wannan" yai mavanar yana nuna masa Yusuf. Sada yace "eh nasan shi" "Meye a tsakaninka dashi?" Sada yace  "Eh nasan shi, sunanshi Yusuf, yana kawomin gyaran motoci" Barrister Sadik yace  "yaushene ganinka na ƙarshe dashi?" "Eh ganina dashi na ƙarshe shine, ranar daya kawomin wata mota yace in siya, nace masa gaskiya ni bana siyan mota sedai zan haɗashi da masu saida mota, bayan na haɗashi dasu se aka kawon lambar motar da na kawo maka, wadda ta kasance lambar motocin gidan Daula ne " Aikuwa aka kawo lambar mota aka nuna a kotu, wannan lambar ita ce lambar dake jikin motar da Yusuf suka fita aka sace su a cikinta, tunda Yusuf yake be taɓa ganin wannan mutumin ba me suna Sada, amma yau an samoshi an masa sharri. Yusuf yai shiru ya dafe kai, ya kasa cewa komai. Barrister Khalil yace  "Sheda na gaba da zan gabatarwa da wannan kotu shine wanda ake zargin tare suka haɗa kai da Yusuf suka sace 'yar gidan Nasir Daula wato Saleh" Aka shigo da Saleh, yana takawa da kyar wanda gaba ɗaya ya fita a hayyacinsa, kallo ɗaya zakayi masa kasan bashi da lafiya aka rakitoshi. Akaje aka tsaida Saleh, Barrister Sadik yace  "Malam Saleh, ko zaka iya gayamana waye kai a gidan Daula?" Cikin murya ƙasa ƙasa yace  "Ni tsohon sojane, kuma hadimi a katafaren gidan Daula" "Waye wannan?" ya nuna masa Yusuf. "Shine direban 'yar gidan Daula, shi yake kaita duk inda zata je" Barrister Sadik yace  "ya akayi kuka haɗa baki kuka sace ta, harka basu mafaka?" Saleh ya kalli Yusuf, ya sunkuyar da kai yace  "Bayan Yusuf yayi duk shirin daze, ya nemi da ina nema masa inda ze zauna ya ɓuya, ba tare da an gano inda suke ba, yayi Alƙawarin ze bani kuɗi, ni kuma na yadda na amince, daya sato ta na gaya masa inda zamu haɗu, shine na kaisu wannan ƙauyen daga baya ya je ya saida motar, muka raba kuɗin " Yusuf ya ƙurawa Saleh ido, amma Saleh ya kasa ɗaga kai ya kalli Yusuf, ya sunkuyar da kai yai shiru, yakasa kallon Yusuf, shima Yusuf bashi da zaɓin daya wuce ya sunkuyar da nasa kan, Umma se kuka take tana mamakin, ya za'ayi ace ɗantane yai wannan abubuwan haka? " Barrister Khalil yace 'idan kotu ta bani dama, zan gayyato Malam Audi, wanda shine Saleh ya nemo ya ɗauki Yusuf da' yar gidan Daula, a ƙurƙurarsa zuwa cikin ƙauyen da akayi garkuwa da ita" Malam Audi ya fito shima, Barrister Khalil yai masa tambayoyin duk daya dace yai masa, shima ya bada amsa, kamar yadda aka buƙata. Barrister Khalil, ya kira doctor Mustapha wanda shine Likitan daya duba Widad lokacin da aka harbeta, shima ya fito ya tsaya ya bayyana sunansa a gaban kotu. Barrister Sadik yace  "Doctor Almustapha, kaine Likitan daya karɓi 'yar gidan Daula, lokacin da Wannan bayin Allah suka kaita Asibitinka ha akayi?" Doctor Mustapha yace  "eh hakane, Wataran da safs ina aiki, suka shigo cikin Asibiti na, ɗauke da wata matashiyar budurwa wadda take a galabaice, jini nata zuba daga jikinta, suka shiga da ita Office ɗina, sukace patient suka kawo in duba musu, nace musu bazan karɓi case ɗinba, saboda harbine a hannunta, amma Saleh ya ciro bindiga yace idan banba ze kasheni, haka na cire mata bullet daga jikinta, ko gama watstsakewa ba tayi ba suka ɗauketa suka gudu" Justice Abdullah A dutse yace  "wanda ake ƙara ko kana da abunda zaka ce?" Yusuf ya girgiza kansa alamar A'a, ya juya ga Barrister Sadik yace  "muna saurarenka Barrister" Barrister Sadik yace  "ya me girma me shari'a, wannan sune ƙwararan shedunmu da zamu gabatarwa wannan kotu, sannan in Allah ya yarda a zaman kotu na gaba zamu ƙarasa kawo shedunmu da tarin hujjojunmu, wanda zasu tabattar da wanda ake zargi shine ya sace 'yar gidan Alhaji Daula" A dutse yace  "duba da yadda barrister ya gabatarwa da kotu shedunsa, kuma aka tambayi wanda ake ƙara be musa ba, da kuma yadda Barrister ya nema, wannan kotu tayi umarni da' a maida wanda ake zargi gidan gyaran hali, zuwa sha biyar ga wata me kamawa" Daga nan ya buga gavel, wato gudumar kotu. Yusuf ko ɗaga kai baya yi, saboda bashi da idon daze kalli al'umma dashi mussman masoyansa, wani abun idan ba'ayi ba anyi wank, ga tarin hujjoji da shedu da aka gabatar, shi kuma gashi ba masanin fannin shari'a ba, to idan ya musa ma yace me? Bashi da zaɓin daya wuce ya amsa, haka aka kuma zura shi a motar gidan yari, ba'a bari 'yan jarida sunyi magana da shi ba, kowa wani yayi magana da shi ba aka tafi da shi. Koda Nurat taga yadda kanun shari'ar ya gudana yau gaba ɗaya ta ɗimauce, ta rasa inda zata saka ranta yanzu shikenan babu wanda ze tsayawa Yusuf kenan? Dukda wannan shedun da aka gabatar har yanzu zuciyarta bata saduda ba, tana jin sharri ne kawai akewa Yusuf ɗin. Ta fita taje ɗakin Mummynta, ta tarar tana salla, ta ɗauki wayarta akan gado tai waje, bata tsaya ko ina ba se ɗakinta, ta shiga ga kulle ƙofa ta ciki ta kira Khalil. Yana ɗagawa ta fashe masa da kuka, yace  "subhanallah, Nurat ya haka?" "Khalil kana gani an gabatar da shedun ƙarya akan Yusuf, shikenan haka za'a bari a kulle shi, ba zaka iya komai ba?" Khalil yace  "Nurat, abun ya wuce tunanin ki, ke yarinya ce kuma kina gida a zaune baki san meke wakana ba, wallahi ana nan ana barazana ga duk wanda yai yunƙurin shiga shari'ar nan da nufin kare Yusuf, kedai ki cigaba da Addu'a, Allah zeyi ikonsa, kuma.. Ai bata jira meze ƙarasa faɗa ba, ta ajiye wayar tai shiru ta dafe kai, ta rasa abunyi dan yanzu kukanma bata iyawa, gaba ɗaya taji kamar jiri na kamata, ta buɗe ƙofa ta fito tana dafa bango, sedai tama zuwa falo kawai ta faɗi a gurin, hakan yai dai dai da shigowar Alhaji Musa, ya ƙaraso kanta da sauri yana kiran sunanta, sedai bata san meke cewa ba. Ya ɗakko ruwa me sanyi yana shafa mata, a hankali ta dinga sauke numfashi, Mummynta ta fito falo kawai ta tarar da Alhaji Musa rungumen da Nurat yana shafa mata ruwa. Tace "subhanallah, Daddy meye ya sameta?" Alhaji Musa yace "nima ina shigowa na tarar ta faɗi ƙasa" Tace "subhanallah, ko Asibiti zamu tafi?" Yace "A'a, ɗan tsaya muga naga kamar ta farfaɗo" Yace "Nurat" Ta buɗe idonta ta kalle shi tace "Na'am Daddy" Yace "meke damun ki ne haka? Ina shigowa naga kin faɗi, meke damun ki?" Ta girgiza masa kai alamar bakomai. "Kyace fa bakomai? Gata nan ko Abincin kirki bataci, na rasa meke damunta, bayan tea ko biscuit, bayan nan bata cin komai, haka yake wuni duk tabi ta ƙare ta bushe" Ya kalleta cikin kulawa yace  "meke damunki ne Nurat, meyasa bakya cin Abinci? Duk kin rame" "Daddy ni bana son tafiya karatun nan dan Allah ka ƙyaleni" Yace "shiyasa bakya cin Abincin?" Ta jinjina masa kai, yace  "zanyi shawara, fitinarki da rawar kanki ce tai yawa, shiyasa nake son turaki can, zanyi shawara amma kidena ƙin cin Abinci" Ya ƙura masa ido, yana sonta dukda halinsa dayake ita 'yarsa ce yana sonta, amma meyasa ze jefa rayuwar' ya'yan wasu cikin damuwa? Adalci kenan hakan? " Hawaye ya shiga gangarowa gefen idonta, ya dinga share mata yana ya isa haka, tashi muje ki kwanta ki huta anjima zan kira likita yazo ya dubamin ke. Ya kama hannunta, ya kaita ɗakin ta ta kwanta, sannan ya fito ya rufe mata ɗakin. Yauma Widad na zaune, ta ari wayar sabuwa ta duba yadda shari'ar ta kasance, sedai babu wata hanyar mafita ko nasara akan lamarin, babu wata hanya da zata bi ta temaki Yusuf, gashi bata da tabbacin da wace manufar wannan matar ke nuna mata kulawa da tausayi, saboda Bulama makirine, babu abunda baze iya ba, haka ta bata wayarta ta, ta koma ta kwanta, tare da lumshe idonta. Har yanzu tana jin alamun cikin ta na nan, dan babu abunda ya sauya na daga abunda takeji, na laulayi shikuma Doctor Hamisu ya tabattarwa da Bulama cikin Widad ya fita, gaba ɗaya ta koɗe kamar ba Widad 'yar ƙwalisan mam ba, matashiyar' yar hamshaƙin attajiri, 'yar gayu me cin zamaninta ba, duk tayi wani iri, ga tashin hankali da tunani ha pressure ciki, abunda bata saba ba bata san yadda yake ba, ga kuma sauran ciwukan da suke damunta, banda uban duka da take sha a hannun Bulama, da sauran mugunta da yake mata. Yusuf yana zaune a gidan yari, akace yazo yayi baƙi, shi dai yasan an dena barin kowa yazo inda yake, Umma ma sau ɗaya aka bari ta ganshi, ko saƙo aka kawo masa ba bashi ake ba, haka yake zamansa a wahale, Yusuf ɗan gayu daya saba da tsafta, rayuwar gidan nan ba ƙaramin wahala take masa ba. Aka fito da shi zuwa ofishin gandirobobi, yaga wannan ɗan sandan me kula da sashin manyan laifuka, daya zauna a sashensa lokacin da yana hannun 'yan sanda, wanda ya dinga azabtar dashi, Yusuf na ganinsa ya sake haɗe rai ya ƙaraso ya zauna. Ya kalli Yusuf yai murmushi yace  "haba Yusuf, ba faɗa meya kawo gaba kuma? Meye na haɗe rai dan ka ganni, ashe an fara shari'arka?" Yusuf yai masa banza yaƙi magana, yace "shikenan, tunda bazakamin magana ba, na fuskanci kai dai halinka ne a haka, miskilanci da taurin kai, zamanka a hannunmu be sa ka canza ba, kai dai haka Allah yayi ka kenan?" "mekazo yi gurina? Bayan an hana kowa yazo gurina kai meyasa aka barka kazo gurina, me zan maka?" "kwantar da hankalinka, ai dole zan gaya maka ms zakamin". Yasa hannu a aljihunsa, ya ɗakko biro da farar takadda a cikin wani file, ya miƙawa Yusuf yace  "ɗan Yimin signing ɗinka a nan in gani" Yusuf ya kalli takaddar ya kalli ɗan sandan yace "na menene wannan?" "kai meye naka na tambaya? Ka saka hannu nace" "bazan saka ba" ya bada amsa kai tsaye. "Ni kake cewa bazaka saka ba, kai idanma tinƙahonka kaima ɗan sandane, aiko a aiki na girmeka, haka a shekaru ni zaka gwadawa taurin Kai?" Yusuf yace "eh bazan saka hannunbau, bazan saka hannu akan abunda ban san meye ba" Aikuwa ɗan sandan ya kashe Yusuf da mari, Yusuf kuma ya rama, kafin kace kwabo gandirobobin nan sunyo kan Yusuf da duka, kota ina suka haɗu suka masa lilis, ko motsi baya iyayi, sannan aka sureshi aka maida shi, a galabice. Ɗaurarrun gidan dayawa sun sanshi, baya magana ba ruwansa da kowa, kamun kansa yasa suke girmama shi, musamman da suka jiya ana masa laƙabi da maitama, akace musu ɗan gidan marigayi Bashir maitama ne, su suka karɓeshi, suna mamakin wane laifin yayi aka kama shi aka dake shi haka? Suka samo ruwan zafi a kitchen aka dinga gasa masa inda ha farfashe a jikinsa. Duk takurar da akayiwa Yusuf akan ya gwada yin signing ɗinsa, su sake gwadawa dana Bulama su gani ƙi yayi, aka ƙara tsananta masa a gidan kurkun nan, hantara cin mutunci zagi, ayyuka ma wahala amma Yusuf yaƙi sakawa fafur, danma wani abun fursunoni sukan shigar masa saboda suna ganin salihancinsa da haƙurinsa be kamata a dinga cuzguna masa ba. Ranaku gudu suke, lokaci na ƙara sauri, kamar ƙyaftawar ido, lokacin komawar Yusuf kotu yayi, suka sake shiga kotu domin cigaban shari'arsa. A wannan karon kuma Barrister Saminune ya fito dan gabatar da shedu da hujjoji akan Yusuf. Barrister Saminu ya gabatar da kansa, sannan yace  "kamar yadda wanda aka yi ƙara yayi da'awa a hannun 'yan sanda cewar a hukumance aka bashi umarnin yayi aiki a gidan Daula, domin bawa' yarsa kariya, sedai a iya binciken 'yan sanda babu wanda ya sashi wannan aikin, sannan hukumar' yan sanda tayi Allah wadai da abunda yayi sun sallameshi daga aikinsa gaba ɗaya, kuma abokin aikinsa me suna Abbas Habib, wanda wanda ake ƙara yace shine shedarsa akan an sashi aiki a gidan Daula, ya tabattarwa da kotu cewa, Babu wanda yasaka Yusuf wannan aiki, Yusuf ƙarya yake masa dan haka Yusuf yayi basaja ne a gidan Daula, yaje da suffar mutanen kirki danya sace 'yarsa " Babu abunda ya bawa Yusuf mamaki se jin sunan Abbas, da kuma abunda akace yace a game dashi, ya jinjina kai ya tuna yadda Widad take nuna tsanarta ga Abbas, ashe Abbas ze iya yi masa haka? Sekuma yai tunanin Amma Suleiman yana kotun nan, kenan shima baze iya taimakonsa ba? Yusuf yai shiru kawai yana sauraren ikon Allah. Babban Abun mamaki, harda su Ramlah aka kira a matsayin wanda zasu bada sheda akan Yusuf ne ya sace Widad. Barrister Saminu ya kalli Ramlah yace "ko zaki iya shedawa kotu wacece ke?" Ramlah tace  "Sunana Ramlah, kuma Widad 'yar uwatace" "ko zaki shedawa kotu abunda kika sani game da Yusuf, alaƙar dake tsakaninsa da Widad yarinyar daya sace?" Ramlah tace "eh to, lokacin da aka kawo shi zeyi aikin direba, da bata aminta dadhi ba ita Widad, saboda halinta na rashin yadda, ganin mahaifinta ya yadda dashi, shiyasa itama ta haƙura da hakan ta yadda dashi a matsayin direban nata, Daya ke mukan ɗan gaisa da shi, wataran yake tambayata wai dan Allah nasan Password ɗin Widad na banki, dayake daga baya ta ɗan yadda dashi har ɗakinta yana shiga, nace masa me zeyi da password ɗinta na banki, se yace min bakomai tambayata kawai yayi, se nace masa nima ban sani ba, to haka dai Widad ta kan yi complaining akan ana mata sace sace bayan babu wanda yake shiga ɗakinta seshi, har wataran sukayi sa'insa ta kusa korarsa, mahaifinta ya hanata, sedai ba daɗewa wannan lamarin ya faru aka neme ta aka rasa " Barrister yace " Shikenan, mungode Malama Ramlah zaki iya komawa kije ki zauna " Yusuf yabi Ramlah da ido, har taje ta zauna, me shari'a yace " ko wanda ake ƙara, yana da abun cewa? " Yusuf ya girgiza kai, ya maida kai ya sunkuya, Umma ta tashi da sauri ta fice daga kotun, tana kuka. Barrister Saminu yace "idan wannan kotu ta bani dama, zan sake gabatar da sheda akan wanda ake zargi" Wani ma'aikacine daga gidan gonar Daula ya fito, aka gabatar da shi a matsayin Iliya. Barrister Saminu yace "ranar da abun ya faru, ance kana nan da daddare kana aiki a gidan meyafaru?" Iliya yace  "eh to, a ranar sunzo gidan dashi da Ita, da Alhaji Nasir Daula, cikin dare suka fito shida ita kamar ze nuna mata wani abu a wajen mota, kawai ya buɗe motar ya dannata ta ƙarfi, lokacin ina saman benen dake kusa da inda suke, kafin in sakko wasu mutane sun ɓullo daga gurin fulawoyi a laɓe, da alama dama suna laɓe ne gidan a ɓoye suka buɗe masa gate, Jin motsi yasa Daula ya fito a guje, yace lafiya? Se Saleh yace ai wasu mutane ne suka shigo suka fita da Widad, shine Daula ya faɗi a gurin " Suleiman ya sunkuyar da kai kawai, dan kowa yaji yadda ake gudanar da wannan shari'a, tsantsar son zuciya ne kawai da rashin imani, wata irin bahaguwar shari'a ake ba fasali babu komai, kuma duk wanda ya bada sheda babu wani bin diddigi a masa tambayoyi dan tabattar da abunda yake faɗa, kawai se a karɓi wannan shedar. Barrister Saminu yace "idan kotu ta bani dama, zan gabatar da sheda ta ƙarshe wadda itace me ɗungurungum, wadda zata tabattar da Wanda ake zargi shine yai garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula. Yusuf ya ƙura ido yaga waye ze shigo, me ze gani Widad ce aka shigo da ita, tayi haske amma da gani kasan hasken cutane, ta rame tayi wani iri, duk wanda yasan ta a baya, idan ya ganta baze ganeta ba se mutum yayi dagaske, saboda tsabar rama da fita hayyacinta da tayi. Yusuf yabi Widad da ido, yadda ta koma yana tunani daban daban a ranta. Akaje aka tsaida Widad, amma ta gaza kallon Yusuf, yayin da Yusuf ya kafe ta da idanuwa, Barrister Khalil yace "ko zaki iya bayyanawa kotu wacece ke?" "Widad Nasir Daula" ta bashi amsa, ba tare da ta kalle shi ba, ya nuna mata Yusuf yace "kin san wannan?" Ya nuna mata Yusuf, ta jinjina masa kai, waye shi? Meye alaƙarki dashi? " Bata kalli inda Yusuf yake ba tace "da farko direbana ne, yayi aiki tare dani a gidanmu" "Lokacin da yayi aiki dake, kin san cewar ɗan sanda ne?" Ta girgiza kai, "Ana zargin shine ya sace ki, yai garkuwa dake, me zakice akan haka?" "Eh Yusuf yayi garkuwa dani, na zauna a hannunsa tsawon watanni biyar, sedai babu wani abu na cutawarwa ko tsoratarwa da yayimin" "Ya isa haka Malama Widad, zaki iya tafiya" Barrister Khalil ya katseta, ganin hawaye ya cika idonta tana neman ta saki layi, aka fito da ita zasu tafi, se a lokacin ta ɗaga kai ta kalli Yusuf, taga yadda yake binta da kallon da bata gane na menene ba? Hawayene ke shirin gangarowa a idonta, ta girgiza masa kai, ta fita daga cikin kotun. Tana fitowa tai karo da Umman Yusuf, cikin kuka Umma tace "Wallahi keda Allah, Allah ya sakawa ɗana, wallahi Allah ze bi mana haƙƙinmu, saboda rayuwarki ta ɗana ta kassara, a sanadiyarki aka kashemin miji, yanzu gashi sanadinki za'a kullemin ɗa, bayan danke duk ya shiga wannan halin, Allah yana kallonki fa, kiji tsoron Allah " Umma na zubda hawaye, Widad na zubda hawaye, tana son tayi magana amma ta gimtse maganarta saboda abunda hakan ka iya haifarwa, ta shige mota ba tare da ta cewa da Umma Uffan ba. Alƙali ya sanya sati biyu, domin yanke hukunci na ƙarshe akan Yusuf, kotu ta watse ana Yusuf bashi da sauran mafita, tunda ita da bakinta ta tabattar da ya sace ta. Gaba ɗaya hope ɗin Yusuf ya ƙare, tunda Widad ta tabattar da hakan ba shakka bashi da mafita sam. Abun duniya ya ishi Widad, aka maida ita inda ake tsareta a gidan Bulama, ta ɗora hannu a kanta tana wani irin kuka, jikinta har rawa yake, zuwa yanzu tana jin yadda abunda ke cikinta yake ɗan motsawa kaɗan kaɗan. Bulama ya shigo ɗakin da Widad take, yana kallonta ya kwashe da dariya yace "ban taɓa tunanin zaki so wani abu a rayuwarki bayan mahaifinki, kamar wannan shashashan Yaron ba, kamar ma kinfi sonshi akan Daula, sedai na ƙarar da soyayyar a nan, na saka mata aya, tunda gidan yari za'a kaishi" Widad ta kalli Bukar tace "Kayi kuskure, kai Yusuf gidan yari baze taɓa kawo ƙarshen soyayyar da nake masa ba, dukda kai ba mutum ne me cika Alƙawari ba, nasan ba lallai ka cika Alƙawarin da kamin akan Yusuf ba, ni dai fatana kamar yadda mukayi da kai kar kuyi sanadiyyar rayuwarsa dan Allah " Tai maganar tana kuka a gaban Bulama, yai dariya yace " wannan kaɗai be isa in bar yaron nam a raye ba, harse kin gayamin inda kayan nan suke " Widad ta kalle shi tace " A zatonka kafini wayo da dabara ne, to bari in gaya maka abunda baka sani ba tsayin shekaru, Daula ba dukiyar ya ɗauka ya danƙamin ba, ya naɗi video akan yadda takaddun suke, da yadda dukiyar take da kuma a inda take, ni kuma dana tashi na bawa Amintacce na ya ajiyemin, nasan ko bayan raina, idan ya gano ajiyar dana bashi ze danƙa amana ga masu ita " Tai maganar tana tsura masa ido, nata cikin nasa. " me kike nufi, suna gurinwa? " " Gurin masoyina mana, da kake so ya ƙare rayuwarsa a prison, seka bari ranar daya fito seya baka " Ya wanketa da mari da wannan Ƙaton hannun nasa, idan ya mareta har wani jirine yake kwasarta, amma ta dake tace "idan ka kasheni, ka kashe dukiyar da kake nema, ka huta, shedar tana gurinsa, mabuɗin yana gurina, dan haka dabara ta rage game shiga rijiya" IDAN KIN SIYA AMANACE, IDAN KIKA FITAR KUMA KINCI AMANA!!! Ayshercool 07063065680 11/24/21, 10:26 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 136_137 Bulama ji yayi kamar ya shaƙeta ya huta da wannan baƙincikin, daga wannan se wannan, daga wancan se wancan se wasa take masa da hankali, ya miƙe kamar ze fita ya juyo ya kalleta, yasa ƙafarsa ya dinga dukanta yana taka ta, tasa hannu tana tare cikinta saboda karya dakar mata ciki, danshi ya sakankance cikin nan babu shi ya fita tuni. Haka ya dinga Takata da ƙafarsa, ko kukan bata iyawa sedai hawaye dake zuba kawai kamar an kunna famfo, yai me isarsa ya dinga zaginta ita da Daula, yai ya gama yasa kai ya fice. Widad tai kuka har hawayen suka gagara zuba se ƙunar rai da take, tana jin abunda ke cikinta yana motsawa kaɗan kaɗan, ta tuna yadda Yusuf ya dinga binta da kallo, kana ganinsa kasan a tsatsanr wahala yake, fuskarsa duk tabo da raunuka na ciwo. idanunta sukayi jawur, kamar wadda aka zubawa barkono saboda kuka, ta sunkuyar da kanta ta shafi cikin ta, da take jin motsinsa kaɗan kaɗan a can ƙasar mararta, cikin zubda hawaye tace "wace amsa zan bawa abunda yake cikina, idan har ya girma ya samu labarin mahaifiyarsa taje kotu ta bada sheda akan mahaifinsa an kai shi prison? Shedarma ta ƙarya, nasan duniya zata zageni ga duka wanda yasan ainihin abunda ya faru, sedai ba yadda na iya, nayi hakanne da ceton rayuwarsa, kaicona haɗuwa ta da Yusuf ta zame masa babbar ƙaddara a rayuwarsa, ya sadaukar da rayuwarsa don inganta tawa, amma maƙiyana suna ƙoƙarin cin galaba akanmu, abun da basu sani ba shine, tun ran gini tun ran zane, ita gaskiya duk daren daɗewa zata yi halinta" Tai maganar ranat yana mata wani irin zafi da raɗaɗi. Yusuf kam ya sha mamaki da Widad taje ta bada sheda a kotu, akan cewar saceta yayi sedai yanayin daya gantabya tabattar masa akwai lauje cikin naɗi, akwai abunda yake damunta, da gani duk inda take ba'a kwanciyar hankali take ba, amma duk da haka ya zaci zuwanta kotu ze zama sassauci a gareshi, sedai zuwanta kotu ya zama ƙarin tsanani a gareshi, yanzu kam ya haƙura yasan idan ba ikon Allah ba, bashi da wata hanyar kuɓuta sam. Alhaji Haruna kwana biyu ya samu sauƙi, Amal ta dena bibiyar sa, sedai ba ƙaramar kassarawa tayi masa ba, kwashe masa kuɗin Account da tayi, gashi ba damar kai rahoto yaje ya ɗaure kansa da kansa, gashi gaba ɗaya yanzu wanda zs nemi shawarar tasu hankinsu na kan wannan shari'a da'ake fafatawa. Bulama gaba ɗaya yakasa nutsuwa, dukda wannan shirin da wannan shirin da yake yi, slide mistake Asirinsa ze iya tonuwa, kuma yasan koda tsiya, koda Arziki Yusuf baze bada abun nan ba, yayi signing ma a tabattar wannan signing ɗin nasane, me shige dana Daula amma yaƙi, babu irin dukan da baa'yi masa a gidan yarin nan ba amma fafur Yusuf yaƙi sakawa, wane ma tabbaci yake dashi akan cewar Recording ɗin yana gurin Yusuf, dan rainin hankali ba wani abun wahala bane a gurin Widad, zata iya raina masa hankali tace yana gurin Yusuf amma baya gurin nasa, nan ya dinga takura Ƙwaƙwalwarsa, akan lallai seya gano mafita. Umma kuwa tun daga ranar da Widad ta bada wannan shedar taji ta tsane ta, bata sonta duk wannan halin wahalar sanadiyyarta ya shiga amma taje ta bada shedar zirr, gashi a maganar da Yusuf yai mata ranar da sukaje ganinsa a prison ya gayamata wai Widad ɗin matarsa ce, ko ta yaya oho? Umma gaba ɗaya tunaninta ya tsaya, bata da yadda zata yi wanda zata temaki Yusuf dashi. Ta kira Suleman tace "dan Allah idan baya komai yaje tana son ganinsa" Bayan awa ɗaya da rabi, sega Suleiman yazo suka gaisa sannan tace  "Suleiman, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi da ƙoƙarin da kake ta min, amma ina neman wata alfarma ne a gurinka" Suleiman yace "To Umma ina jinki" Tace "dama cewa nayi, ko zaka samo me siyan gidan nan, ai masa kuɗi a siyar, a saida Babur ɗin Yusuf, da gurin furnitures ɗinsa, a ɗauki lawyer me zaman kansa yaje kotu ya tsayawa Yusuf , ko Allah zesa a dace" Suleiman yace "Umma da hakan ze yuwu, da tuni nayi wallahi base an siyar da gidan nan ba, har Office akamin aike daga sama, akace muddin nace zan saka kaina a cikin case ɗin nan, to tabbas zan rasa aikina, kuma nima za'ace dani aka haɗa baki, sannan a hanya aka kuma tsareni, akace idan nai involving kaina a case ɗin nan, to za'a kasheni da iyalina, kuma irin wannan barazana akewa duk wanda yai yunƙurin taimakon Yusuf, shiyasa kikaga an kasa komai a kai, bakiga inaji ina gani akace wai ba hukumar 'yan sanda ce ta bashi aiki ba, bayan kuma nasan ƙaryane ba, da hannuna na bawa Yusuf aikin nan, amma ina yunƙurin yin wani abu, komai ze kwaɓe " Umma tai ajiyar zuciya tace" babu wanda ya bani mamaki irin Abbas, har gida yake zuwa ya ɗaukeshi su tafi gidansu yarinyar nan, amma saboda rashin imani, yace wai be san zancen ba" Suleiman yace "kiyi haƙuri, ki dena kuka haka, dama ai si mutane kullum ƙara koya maka hankali suke, amma ina tabattar miki Yusuf baze zauna a gidan yari ba, gaskiya zata yi halin ta" Umma tace "Allah yasa, ina fatan haka nima" Nurat kam kamar ta ɗora hannu aka tai ihu, ta rasa abunda yake mata daɗi, wai ace Widad ya bada wannan shedar aka Yusuf, dukda irin yaddar da tayi dashi, tabbas da Yusuf yana neman wani abu a gurin Widad dabe dinga bata kariya ba, yanzu shikenan saboda shedar Widad, ta tabatta Yusuf yayi abunda ake zarginsa dashi, kamar wadda mintsina, ta tashi da sauri don taje ta sato wayar Mummy tai waya, sedai tana fitowa falo ta tarar daddynta yana kallon labarai, 'yan jarida na bayyana abunda ya faru a kotu, Alhaji Musa yace  "Maman Nurat, kinga shari'ar yaron nan ko? Dama na faɗa miki, irinsa ba abun tausayi bane, gashi nan ita kanta yarinyar ta tabattar da abunda ake zarginsa dashi, bari in kira Bulama" Ya ɗakko wayarsa ya kira Bulama, "Allah ya baka yawan rai, ai yau naga yadda shari'ar nan ta kasance, komai ya tafi daidai, kayi ƙoƙari gaskiya, haka ake son Amini, gashi baya nan amma ka tsaya tsayin daka akan sha'anin iyalinsa, gaskiya kayi namijin ƙoƙari, Allah dai yasaka da alkhairi" Nurat bata iya jin abunda ake cewa daga ɗaya ɓangaren, amma tana ganin yadda Daddynta ke ƙyaƙyata dariyar mugunta a waya. A hankali ta juya ta koma ɗakinta, tana hawaye tace "Allah sarki Yusuf, ya za'ayi in fita in gayawa duniya cewar ba kai kayi garkuwa da Widad ba, da saka hannun mahaifina a sace su Yusuf? Ta yaya? Tabbas idan aka rufe Yusuf ba'a masa adalci ba, definitely tasan akwai yadda akayi har suka kuɓuta aka kamasu a ƙauye, amma Yusuf baze garkuwa da Widad ba, ta zauna tai shiru tana tunani, bata san ta ina zata fara temakawa Yusuf ba, amma tabbas ƙarshen zalunci an masa. Ramlah ce tsaye akan Fahad tana zazzaga masa masifa, "Wallahi Amal baka isa ba, tun wuri ka maida hankalinka, nafi ƙarfin ka wulaƙantani, wato ka gama dani ka kama wasu, to baka isa ba tun wuri kaje ka turo azo ayi maganar Auren nan" Fahad yai wata irin dariya sannan yace "Ramlah kenan, waye yake yaudarar wani tsakanin nida ke, dama a rashin wannan yarinyar ne, tuntuni tun ina ƙasar waje kin san ita zan aura, kuma gata ta dawo, dan haka me kike so inyi miki kuma? Kawai ki rungumi sorry, in kin samu wani wanda zaku daidaita se ku haɗe, dukda dai bance ke mummuna bacd but gaskiya ga balarabiya ina kallo bazan aureki ba, sorry kawai " " Ni kake kallo kake gayawa haka? Lallai baka san Ramlah ba, kai ƙaramin ɗan isaka ne, wallahi baka isa ba, zaka ga abunda zan maka " Fahad ya busa hayaƙin shisha sama sannan yai murmushi yace " Hmm keme baki san waye Fahad ba, karki bari ki gane waye Fahad tabbas " " Ni kake gayawa haka ko? " "Na gayamiki ɗin, dama haka bariki ta gada, kuma ki shiga hankalinki tunda wuri, tun ban saɓa miki ba" Ramlah ta kalleshi tai ƙwafa, tai waje a matuƙar fusace, tana fitowa tai karo da Hajiya Sarah ta fito zata fita, mamaki yakamata ganin Ramlah daga part ɗin Fahad, ta tsaya Ramlah ta ƙaraso, tana ƙoƙarin buɗe motarta, Hajiya Sarah tace "Ramlah, lafiya kuwa? Me kika je yi ɗakin Fahad? Ina fatan lafiya?" Ramlah ta kalleta tace "ba lafiya ba, kuma wallahi ki gayawa ɗanki ya saurari abunda ze biyo baya" Hajiya Sarah tace "lafiya kuwa? Meya haɗaki da Fahad ɗinne? Me yayi miki ne?" "Ki tambaye shi, shi yasan me yayi, kuma ya jira sakamakon abunda yayi min" Ta bankaɗa ƙofar motarta ta shige ta jata a guje, mamakine ya cika Hajiya Sarah, ta shiga part ɗin Fahad, tana zuwa ta tarar yana shan shisha ta kalle shi tace "Fahad, wato har yanzu baka dena shaye shayen banzan nan bako, kana kawo mana matan banza har cikin gidan nan, kasa ubanka yazo ya kamani da faɗa da masifa, wallahi kaji tsoron Allah, ita kuma Ramlah meye ya haɗaka da ita?" "wani abun tace miki na mata?" "Ban sani ba, me take a part ɗinka? Ko itama shashancin kuke yi?" "Mum dan Allah ki bar wannan maganar, kawai wasu suratanta ne na banza, marasa tushe balle makama, tazo ta nawa mutane Hayaniya a ka" "wane irin Hayaniya ce? Gayamin kasan halin uwatta sarai, daga ita har yaranta ba mutunci suka cika ba, har gara Anwar ma, amma wannan me soyayyen idon, idan ka sake wani abu mara daɗi ya haɗaku dasu, wallahi duk abunda suka maka kai ka janyowa kanka, kaje ka ƙarata kai da uwarsu, idan yaso ubanka yasan yadda zeyi dasu, tunda 'yan uwansa ne, na gaya maka, tunda wannan rayuwar ka zaɓawa kanka Fahad, gaka nam ga duniyar kaje kayi Allah ya temaka " Ba ce mata komai ba, ta fito ta baro ɗakin nasa, zuciyarta sam babu daɗi, ace yaronta na farine ke irin wannan mummunar rayuwa haka, ranat baya mata daɗi Sam. Amal ta rasa yadda zata yi da uban kuɗin data damfari Alhaji Haruna, gashi sam Mummy bata san abunda ya faru da ita ba, balle tasan da wannan uban kuɗin data damfari Alhaji Haruna, sedai Amal ta kasa gane abunda yake damunta, gaba ɗaya yanzu kullum cikin ciwo take, nan ciwo can ciwo, abun ya fara damunta, ta yanke shawarar zata je ganin likita zata je taji meye yake damunta haka. Ramlah kuwa data bar gidan Bulama kamfaninsa ta tafi, yana tsaka da aiki yana shirin shiga meeting se gata, babu sallama babu komai ta tsaya ta tstsareshi da ido. "Ke lafiya kuwa? Ni na rasa waye yafi hanki tsakanin ke da babarki, ya zaki zo ki tsaya a kaina haka kina ƙaremin kallo babu ko sallama" "kaga suararamin kawai, tsason shekaru kana juya mahaifiyarmu, muna abunda kake so, wancan satin har kotu kasa naje na bada sheda akan wannan sharia'r, to nazo da buƙatata guda ɗaya tam, da nake so kamin" "wace irin buƙatace haka? Bayan seda aka baki wani percentage kema, kuma idan kuɗin nan suka samu hadda ke za'a ci" "Niba kuɗi zaka bani ba, shekaruna sun na ina zaune a gida na gama karatu bana aimin fari, balle na baƙi, kuma ɗanka Fahad ya taɓa min Alƙawarin Aure, dan haka tunda wuri azo ayi maganar da za'ayi a wuce gurin" "Nifa ban gane maganar da kike ba" "Kamar yaya baka gane me nake nufi ba? Wane yaren nakeyi maka? Ɗanka Fahad ya Aureni" "Haba Ramlah, wacs irin kwaɗon magana ce wannan haka mara daɗin ji? Baki san Widad ze aura ba?" "ban saniba, kuma matsalar kuce ba ta Ramlah ba, kawai ayi maganar da za'ayi" Bulama yace "ni kike wa magana a haka? Ƙwarai kuwa waye kai a gudina da bazan maka magana a haka ba, ina ƙarewa 'yar gidan Daula shekaru ta kwashe tana maka wulaƙancin data ga dama, balle kuma ni da kake wa kallon biri ina maka ta ayaba, kawai kayi abunda ya dace, ko kuma komai ya faru " Bulama yace " Ramlah, ban san meyasa kike haka ba? Kema kin san aurenki da Fahad ba abune me yuwuwa ba ko? " " Aurena da Fahad, ba abune me yuwuwa ba, ka gayamin shima ya gayamin, nagode nima ku jira matakin da zan iya ɗauka " Ta bar office ɗin Bulama, zuciyarta na ƙuna da raɗaɗin abunda sukayi mata, Amal na zaune a falo tana kallo, cikinta ss ciwo yake mata, ga wani irin ciwon baya da take fama dashi, gashi lokaci lokaci inda ta karye yana motsa mata. Ramlah tana parking ta fito, ta buga ƙofar motar da ƙarfin gaske, tai ciki fuuuuu, kamar guguwa, Nura yace "Allah dai ya kwashe ma wannan baiwa Albarka, da ita da duk wanda suka je kotu suka bada shedar ƙarya akan Yusuf" Murtalah yace "bari Nura, wallahi abun ya bani mamaki sosai, Amma nan aka zo aka taramu aka mana kashedi akan duk wanda yai wani yunƙuri, ze fallasa wani abu se an kasheshi, wayaga ta bakin magana, amma da tabbas nima sena bada sheda" Isa yace "dan Allah Murtalah kaje ka bada shedar nan a saki Yusuf, wallahi zaluntarsa kawai ake yi" Nura yace "Allah sarki duniya, kalli Isa wai kaine ke cewa ayi abunda za'a temaki Yusuf, abun da mamaki" Isa yace "bari Nura, wallahi duk baƙin cikin mutum da iya ƙiyayyarsa, idan dai har mutum ya zauna da wannan bawan Allah, wallahi idan kaji za'a masa haka dole ka tausaya masa, kalli duk irin abunda muka dinga masa baya tanka mana, se azabar miskilancin tsiya a cikinsa kamar Uwarɗakinsa" Nura yace "kai dai bari Isa" Isa yace "kun san abunda ya ɗauremin kai kuwa?" Sukace A'a "Wai ashe Sani me yankan farce shima ɗan sanda ne, shine fa ya haɗani da Yusuf yace ɗan uwansa ne, dana gayamasa ana neman direba, amma naji wannan lawyern yace wai Abbas be san zancen ba, Amma duniya babu gaskiya, tabbas yanzu nake ganin gimbiyar Daula bata da laifi na ƙin mutane, ka yadda da mutum ya cuce ka a banza, yanzu duk wanda suke jikin Daula suna morarsa sune suke zalintarsa, kalli matar gidan nan ko sau ɗaya ba taje kotun nan ba" Murtalah yace "iko se Allah, wallahi Isa da zamu samu dama ko iya wannan shedun muka riƙa, aka shiga kotu dasu zasu temakawa Yusuf, amma wallahi ina jin tsoro, kuma wallahi dani akan matar gidan nan zan bada shedata" Nura yace "kai ita ta dameka, a samu a Yusuf ya kuɓuta, wallahi dukda nima inajin haushinsa yadda ƙirƙiri ya samu fada fiye damu a gidan nan, musamman ni daya nemi ya ƙwacemin aiki na, Amma gaskiya Yusuf baze aikata haka ba, kalli fa ko magana ake, idan aka sakota ko aka zageta seya haɗe rai yana ɓata fuska yana kare ta, wallahi da yayi niyyar sace ta da tuni ya saceta, akwai dai yadda akayi " Nan suka cigaba da tattaaunawa suna hirar a tsakaninsu. Ramlah kuwa tana shiga falo, Amal ta kira sunanta, Ramlah ta waigo a fusace tace " lafiya kuwa? " " Ashe kema kim bada sheda a kotu akan Yusuf "? " Eh na bayar se yaya? " " Yakamata kiyiwa kanki adalci Ramlah, a bar bawan Allah nan da wahalar da aka jefa shi a ciki, bakya ganin saboda Alhakinsa ne muma namu ɗan uwan yana nan kwana da kwanaki ba'a ganshi ba, ga mahaifiyarmu se fama take da marurar hawan jini saboda damuwane da ɓacin rai? " 'Ke dalla sauraramin, an bada shedad kiyi abunda zakiyi, da aga Anwar da kar a ganshi be dameni ba, abunda yake gabana shi zanyi, kuma karki ƙara yimin wannan maganar" Ta nufi ɗakinta, tana jin yadda zuciyarta take tafasa. Tana zuwa ta jefar da Jakarta akan gado, ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗakko kwalaben syrup, kawai ta kafa kai ta kama tittilawa cikin ta, Hakan yai dai dai da buɗe ƙofar ɗakin da Hajiya Halima tayi, ta tarar Ramlah ya shanye kwalaben syrup ta faɗi a gurin, cikin fitar hayyaci. "Na shiga uku, Ramlah me zan gani haka? Ramlah dama dagaske shaye2 kike? Me yasa zaki cuci kanki" Sam Ramlah bata san me ake ba, tuni ta fara maye ta lula gajimare. "Amal! Amal!" ta shiga ƙwalawa Amal kira. Amal tazo tace "gani" "Amal kinga, shaye2 Ramlah take yi, meke damunta haka zata faɗa wannan mummunar hanyar haka?" Amal ta ɗan taɓe baki, tare da naɗe hannunta tace "Allah ya jiƙan Yaya Anwar, ba dan ya mutu ba, nan ya hukunta ta ya gayamiki ga abunda take yi, amma baki yadda ba, tuntuni take shaye shayenta, kuma wannan Fahad ɗinne ya koyamata, amma ba yau ta fara ba" Hajiya Halima tace "Na shiga uku ni Halima, wannan wace irin masifa ce haka, Ramlah dama baki dena wannan halin ba, Kisha kwalba huɗu a cikin ki?" Amal kam taɓe baki tayi tai nata guri ta barsu. Kamar koda yaushe, yauma zaune suke suna tattaunawa, Bukar yai gyaran murya yace 'ga samu ga rashi, labaran kala biyune, masu daɗi da kuma akasin hakan, wannan yaron munyi magana da A dutse, ya tabbatar min a zama na gaba ze ƙarƙare shari'ar yaron nan, sedai wani hanzari ba gudu ba, ita wannan yarinyar da yake ita uwar Daula ce a jarabar taurin kai, taƙi bayar da abun nan, ba irin azabtarwar da banyi mata ba, amma taƙi ƙarshe ma se cewa tayi ai "Recording ɗin inda dukiyar take Daula yayi, ya bata itama bata san inda dukiyar take ba, kuma wai recoding ɗin yana hannun Wannan yaron Yusuf" What! Cewar Alhaji Munir "to yanzu meye abunyi?" Alhaji Musa yace "kawai aje kurkuku ta ƙarfin tsiya ace ya bayar" Bukar yace "Mhmm, baku san azabar taurin kan mutanen nan ba, ya saka hannu kawai mugani a tabattar idan wannan signing ɗin nasa ne, me kama dana Daula, amma wallahi fafur yaƙi, shima an azabtar dashi kamar kamar me a gidan yarin nan amma yaƙi, na rasa abunyi" Alhaji Haruna yace "a sake azabtar dashi mana, ya faɗi inda recording ɗin yake, ko kuma aje a ɗauke mahaifiyarsa, ai naga tana zuwa kotun" Bukar yace "ai abun ya wuce tunaninku, idan mukayi wani yunƙuri zamu iya barin ɓarakar da za'a ganomu, komai a sannu ake samun sa, zan cigaba da bibiyar yadda za'ayi a samu" Suka gama tattaaunawa suka watse, dama a office ɗin Bukar sukayi meeting ɗin. Bayan fitowarsu Alhaji Haruna yacewa Alhaji Musa "Waini anya ba raina mana hankali Bujar keyi ba, yarinyar nan tana hannunsa fa, babu wanda yasan inda take, ta yaya za'ace ko yaya bata gaya masa wanj abun ba, nifa kamar mutumin nan raina mana hankali yake" Alhaji Musa yace "kai dai bari kawai, kallonsa kawai nake yi, gaba ɗaya kuɗaɗenmu sun tafi akan wannan harkar, amma Har yanzu babu wata riba" "ba gara kaiba akaina, ni kamanta wannan yarinyar ta damfareni, rabin kuɗin account ɗina ta kwashe fa" "kasa a sato maka ita, kaci ubanta ta mayar maka da kuɗinka, ni yanzu kallon Bukar kawai nake idan be wasa ba, zan ɓallo ruwa... LITTAFIN KUƊI NE, IDAN KIN SIYA AMANANE, IDAN KIKA FITARMIN KINCI AMANA, KIMIN ADALCI KIYIWA KANKI AYSHERCOOL 07063065680 11/29/21, 8:55 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 138_139 Alhaji Haruna yace "kamar yaya zaka ɓallo ruwa?" "Eh zan ɓallo ruwa mana, muddin naga za'a cuceni, zan tads husuma ne, daga fara harƙallar nan zuwa yanzu zunzurutun kuɗi nawa muka kashe? Haka abun yayi yawa, mutumin nan ba imani ne dashi ba, ze iyayin komai dan haka gara mu saka ido yadda yakamata" Alhaji Haruna yace "hakane kam, shikenan se anjima se yadda ta yuwu" Daga nan suka watse. Ramlah har gari ya waye, tana tangaɗi bata san me takeyi ba zabo maye, kwalba huɗu ta shanye babu sirki da komai, tayiwa kanta caji na sosai, yayin da Hajiya Halima ta dinga kuka, ganin yadda shaye2 ya ratsa Ramlah haka, ga ɓatan Anwar yana cin zuciyarta, gashi duk 'yan kuɗaɗen data tara Shu' aibu ya karɓesu, ta rasa inda zata saka kanta. Amal kam bata tasu takeyi ba, gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta, ta rasa takamaimai meke damunta, tana zaune tana danna wayarta taga wani business, wanda idan kayi investing kuɗinka, zasu nunnuku a lokaci kaɗan, nan da nan ta gyara zama tana sake duba yadda bayanin abun yake, ta shiga link ɗin group ɗin da aka bayar, taga yadda mutane keta comments wai sun sak kuɗinsu an riɓanya musu an basu. Nan wani tunani yazo mata, dan wannan maƙudan kuɗin da suke account ɗinta bata san ya zata yi dasu ba, dan haka ta jarraba saka naira dubu hamsin, bayan awannin biyar aka turo mata dubu ɗari da biyu, abun ya bata mamaki, nan ta dinga murna akan ta samu sana'a daga kwance zata dinga samun kuɗi. Widad se kaffakaffa take da Cikinta, kar Bulama ya gane cikin nan yana nan be fita ba, dan ya fara ɗagawa sosai tana jin motsinsa, wasu lokutan yaji yana motsi sosai, wani lokacin kuma yayi dankam motsinma se kaɗan kaɗan, mussman idan bata da lafiya, duk lokacin da taji ya daɗe be motsa ba se tai taɓa cikin tana addu'a Allah yasa ba wani abunne ya sami abunda take ɗauke dashi ɗin ba. Cuta kuwa kullum a cikinta take, gashi babu me gayamata yi kaza bar kaza, ita dai Sabuwa ta kan tirsasata ne taci Abinci, amma babu magani ga kwanciyar ƙasa da take, da shan abu me sanyi duk se tabi ta kukkumbura, babu hanyar zuwa Asibiti, ga Fahad dayake yawan kawo mata farmaki wasu lokutan, dan haka baccinma ba iya shi take cikin kwanciyar hankali ba, sedai tana yi tama farkawa, gani take da nannauyan bacci ya ɗauketa Fahad ze shigo yai mata wani abun. Haka rayuwar Widad ke tafiya a wannan gurin da take, gashi dai yafi ɗakinta na ƙauye nesa ba kusa ba, amma ɗakinta na ƙauye ya fiye mata daɗi da kwanciyar hankali akan wannan ɗakin da take ciki haka a cike da wannan damuwar da tashin hanaklin. Se wajen laa'sar sannan Ramlah ta dawo hayyacinta, daga wannan muguwar buguwar da tayi, taje tayi wanka ta canza kaya, ta nemi abunda zata saka a cikinta, ba tare da ta kula kowa ba, Hajiya Halima ce ta bita ɗakinta, ta sameta tana ƙoƙarin fara cin Abinci. Ta ƙare mata kallo sannan tace  "Ramlah, wannan rayuwar ita kika zaɓawa kanki ko? Rayuwar shaye2, Ramlah kwalba huuɗ fa kika shanye a cikinmi, ke ko tsoron lafiyarki bakya yi, bakya tausayin halin da nake ciki ko? Ban san inda ɗan uwanku yake ba, ga wannan uban naku yana ta min barazana akan ze tonamin Asiri, amma a haka kike ƙara gayyato mana wata matsalar, meyasa haka Ramlah? " " Dan Allah Mummy ki ƙyaleni injibds abunda ya dameni, ni Fahad ze kalla yace baze Aureni ba, bayan tuntuni yasan zaman jiran sa nakeyi, amma zemin haka" "to yanzu dan yace naze aureki ba shine zaki kashe kanki? Shine zaki sha wannan maganin haka? Haba Ramlah shikaɗai me namiji ko shine autan maza, kina gani kuɗaɗen hannuna duka babu sun ƙare, shine yake kawo mana wanda suke siyan kadarorin nan fa a ɓoye, ki lallaɓashi ku rabu lafiya mu samu mu sake wawurarar abunda ya samu mu siyar, idan muka siyar seki ƙyaleshi, Allah ya baki wani ki aura" "Mummy, ni gaba ɗaya ma nakasa gane kan maganganun nan da kikeyi fa, kamar yaya babu kuɗi a hannunki, ina duk kuɗaɗen da kika saida filayen nan? Duk suna ina, kuma ga wannan kuɗaɗen da ake saka rai na gurin Bulama daze samo a hannunta suma basu samu ba, abun yazo da rainin hankali fa" "wai bana gayamiki ubanku ke tamin barazana ba, kin sam maƙudan kuɗaɗen daya karɓa kuwa  hannu na?" Ramlah tace "wai wannan jakin da yazo harya mareni kike nufi?" "Eh, shu'aibu dai" "to meyasa kike bashi?" "Ramlah idan shu'aibu ya tinamin Asiri na kaɗe, dan na gama yawo, mutumin nan hatsabibin gaske ne, baku da wayo lokacin da muka rabu ai" "Lallai Mummy, wallahi dana san hakane baza'a bashi ko kobo ba, sedai yaje ya tina karya fasa, yanzu shikenan mun tashi a tutar babu? Duk wannan baƙar wahalar da mukayi? Yana gefe kika dinga tura masa kuɗi, baze yuwu ba Wallahi" "bazs yuwu ba kamar yaya? Ai tuni ya yuwu, bashi kuɗin nam sune rufin asirinmu, kuma karki kuskura kice zakiyi wani abu, kinji ma gayamiki sannan Ramlaj ki shiga hankalin ki, akan wannan mummunar ɗabi'ar, babu inda zata kaiki shaye2 ba abunyi bame, kuma ba cinyewa bane " 'mhmm Mummy kenan, yadda raina yake a ɓace idan har ba caji nayiwa kaina ba bana jin daɗi, kawai ki ƙyaleni idan kuma kina buƙatar in dema shaye2 to tabbas Fahad ya aureni, idan bahaka ba bakiga komai ba har yanzu" "Ramlah ni kike gayawa haka?" "Ai gaskiya na gayamiki ba wani abu bz, idan harya Aureni shikenan an wuce gurin saɓanin haka kuma, komai ma zaki iya gani" Ta ƙarasa magana, tare da fara cin Abimcinta, bata sake bi ta kan mahaifiyarta dake kallomta da mamaki ba. Jiki a saɓule Hajiya Halima ta tashi ta fita ta bar ɗakin Ramlah, ranta sam babu daɗi, wai yanzu Ramlah ce a wannan mummunar hanyar. Alhaji Musa sosai yake jin zuciyarsa tana ɗarsa masa wani abiua ransa, yana zargin Bulama kawai ƙoƙarin kifesu yake yi, yana can yana zare zaren, dan haka dole zeyi wani abu a akai, ta ƙarƙashin ƙasa ze bincika ya hani ko Bulama na karɓar wani abu basi sani ba. Yauma akazo akace ana son ganin Yusuf, ya zata ma ko Ummace ko Suleiman wani ya kawo masa ziyara, sedai still wannan ɗan sandan ya gani, se wasu gandirobobi, aka saka Yusuf a wani tsukakkaken ɗaki, da gashi sesu a ciki, aka zaunar da Yusuf ɗan sandan ya kalleshi yace  "Hmm Nasan kayi mamaki, ganin yarinyar daka ceta ta juya maka baya taje kotu ta bada sheda akanka ko? Dama haka mata suke basu da tabbas, gashi tana can tana hutawa, ranar da za'a yanke maka hukunci, a satin za'a ɗaura mata Aure da Fahad Bukar Bulama. A razane Yusuf ya kalleshi yace  "Bukar Bulama kuma?" "Au kana mamakine? Ƙwarai Ɗan gidan Bukar Bulama, wato Fahad, yanzu haka ta aiko mune gurinka, akam cewar akwai ajiyar wani recording data baka, ka gaya mana inda recorder ɗin take, zamu je mu ɗauka ' Hankalin Yusuf sam baya kan Ɗan sandan, sedai nanata Bukar Bulama day keyi a zuciyarsa, wato abu biyune ya haɗar masa, ga mamakin Jin an Ambaci Bulama da Bukar, to kenam shine Bukar ɗin da Widad take magana kokuwa? Idan shine ya akayi gake zaune a hannun sa? Idan ya cutar da ita fa? Sannan wani irin azababben kishi ya taso masa, dagaske Widad ɗinsa ce zata Auri Fahad? 'to idan bata aure shi ba me kake so tayi? Kaida rayuwarka zata ƙare a kurkuku, kuma taje har kotu ta bada sheda akan ka' wata zuciyar ta tunasar dashi, amma dukda wannan abun ya kasa jin tsanar Widad a ransa, shi wani irin tausayinta ne yake kama shi ma, kuma gefe guda zuciyarsa ma cigaba da begen sake kasancewa da ita. "Kai Malam magana nake maka fa!" Ɗan sandam yai maganar cikin tsawa, Yusuf be razana ba ya kalleshi yace "ita Widad ɗince tace maka ta bani wani abu ajiya?" "zan maka ƙaryane?" Yusuf yace "to meze hana kayi ƙarya, tunda mutum ne kai ba mala'ika ba, kamar yadda tace muku ta bani ajiya, tazo da kanta ta Karɓa, ta gayamin lokacin data bani, sannan ta karɓa" Ɗan sandan yai ƙasa da murya yace  "ka bani tunda wuri, ko kuma a ran mahaifiyarka" Yusuf yace "Ran mahaifiyata yana hannun Allah, babu wanda ze iyayi mata abunda Allah be rubuta ze sameta ba, Magana ɗayace, ni bata bani komai ba, idan kuma ta bani ku kawota ta gayamin lokacin data bani ajiyar recording ɗin" Ɗan sandan nan ya jinjinawa azababben baƙin taurin kai irin na Yusuf, ya kalli gandirobobi yace  "ku tambayeshi" Yusuf be motsa daga inda yake ba, suka dinga buga masa kulki kota ina, sedai yana ƙoƙarin karewa, babu wata gaɓa ta jikinsa da bata masa ciwo saboda azabar dukan da yake sha a kowane lokaci. Suka farfasa masa jikinsa, banda targaɗe dake yatsunsa saboda duka. 'zaka bamu ko bazaka bamu ba"? Yusuf yace "ni bata bani komai ba na gaya maka, karka ƙara tambaya ta" Ya ɗaga hannu ze wanke Yusuf da mari, Amma jarumin ya riƙe hannunsa yace "karka kuskura ka mareni, kuyita dukana har lokacin da zaku ga na dena numfashi, tunda haka kuke so, amma karka kuskura ka sake ɗaga hannu kace zaka mareni" Suka kum sashi gaba da duka, seda suka ga baya motsi, sannan hankalinsu ya kwanta, suka tafi suka barshi a gurin. Widad na zaune kawai taji gabanta ya faɗi, hakan yasa kawai ta fashe da kuka, domin ta fuskanci kamar idan Yusuf yana cikin mawuyacin hali se taji wannan faɗuwar gaban, ai kuwa ta hau aikin kuka, tayi ta gaji ta haƙura, ta cigaba da yi masa addu'a, tans tuno irin haƙurin daya dingayi da ita, ga rarrashinta da yake yawan yi, da yadda ta koyi abubuwa da dama a sanadin zama dashi Yusuf mutum ne, wani irin shauƙin soyayarsa ne ke taso mata, ta rintse ido ko zata samu sassauci a zuciyarta, tana jin inama tana buɗe idonta ta ganata a kusa da Yusuf, lallai so ba ƙarya ne ba. "Allah ya fitomin da kai Yoseef, ka dawo muyi rayuwa tare, mu rainin cikin nan tare da kai, nasan da muna tare zan samu kulawarka" tai maganar tana hawaye. Can kuma tayi wani tunani a ranta, wani irin kallo Yusuf zeyi mata idan Allah yasa ya fito, bayan taje ta tsaya a gaban mutane ta tabattar da Yusuf saceta yayi. Cikin kuka tace "wayyo Allah na, Yoseef kayi haƙuri ba laifina bane, nayi hakan ne dan in ceci rayuwarka, karsu kashemin kai, ban manta halaccinka a gareni ba Yoseef, ba yadda zanyi ne" Sabuwace ta shigo da sauri tana faɗin "lafiya kike kuwa? Kinga ki dinga ramgwatawa kanki wannan kukan da kike yi haka, naji ance kina da ciwon zuciya gashi ba ganin likita ake kaiki ba, karki kashe kanki a banza mana" "Ni ki ƙyaleni inyi kukana, baki san abunda yake damuna ba, ki rabu dani dan Allah ki ƙyaleni" Sabuwa tace "A'a Allah ya baki haƙuri, na ƙyeki yi abunki som ranki" Widad ta cigaba da gunjin kukanta. "Allah ya isa tsakanina da kai Bulama, Insha Allah se gawar jaki tafi taka daraja, Azzalumi macuci" Bulama yace  "yi addu'arki da kyau, ai ina kusa ba nisa nayi ba, duk abunda zaki faɗa ki faɗa" "me Yoseef yayi maka? Meye laifin da yayi maka da kake azabtar dashi haka, kake neman cutar da rayuwar sa Kasashi a garari?" Bulama yace "saboda ya raɓeku, ni kuma duk wanda ze raɓeku, in dai ba dani ze haɗa kai ba in mallaki abunda nakeso to tabbas bashi da wani amfani, shiyasa nake kawar da du wani makusanta a gareku, ko wanda ke shirin sama muku farinciki, kum ɗaukake shi da matsayi me girma, dukda baki yadda da mutane amma naga ya zama wani abun yadda a gareki, nasa an jarabbashi koze aminta damu, ya karɓo abun hannunki ya bamu, sena fuskanci shima irinki ne, me taurin kan tsiya, kuma ya dasa hasashensa da bincikensa a kaina, Allah yasa na farga da suri, da yanzu ya kassarani, dan haka dole in koya masa darasi " Widad ta ƙure shi da ido tace" Shikenan, ayi dai mu gani, na yadda da rayuwata da Yoseef da Babana jarrabawa ce Allah yake mana, kuma ina fatan muyi nasara, Allah ya nunamin ranar da zata zo ka wulaƙanta, ka tozarta a idon duniya " Bukar yace  " daha baya kenan, bayan ns mallaki wannan dukiyar, sannan Wannan uban masu koɗaɗɗen idon, yaƙi bada recording ɗin, yace shi baki bashi komai ba, dan haka a wannan karonma dole ki san yadda zaki yi, kodai ya bayar kodai yaita shan wahala harya mutu a kurkuku, kamar Yadda nasa a ka kashe Bala a gidan yari " Widad tai murmushi tace  " Yoseef be san na bashi ajiyar nan ba, dan haka Kadena yaudarar kanka da tunanin ko zaka samu abun nan cikin sauƙi " Bukama ya ƙure ta ido, ta ɗauke kanta daga kallon inda yake, yama rasa me ze mata saboda tsabar wasa da hankali da raina masa hankali da take yi. Ya kalleta yace " shikenan, a bakin ran mahaifiyar Yoseef " " itakuma me tayi maka? " " zaki fanshe ta ne idan kika bada abunda ake nema, dan haka ki zaɓa ko ki bani abunda na nema, ko kuma a bakin ranta" "Abunda ka nema yana hannun Yoseef, kuma shima besan meye na bashi ba, sedai ka kaini gurinsa in karɓa maka, amma karka cutar da ita dan Allah" "Se kuma kiyi, ba dai taken ki rainin hankali da iya wasa ba, to zaki gane kurenki" Widad ta bishi da kallo harya fice, ta kwanta a nan inda take, ta lumshe idonta tana tunani. Mutane nata sauraren lokaci yayi, suji yadda za'a ƙarƙare shari'ar Yusuf, kullum Gidajen radio da dandalin sada zumunta zancen kawai ake yi, kowa yana tofa albarkacin bakinsa, wani ya tofa na alkhairi wani kuma ya tofa akasin haka. Suleiman yaje kaiwa Umma ziyara shida matarsa Surayya, sedai kallo ɗaya zakayi mata kasan bayan damuwa harda rashin lafiya take fama. Surayyah ce ta fara cewa "Umma kodai jikinne ya motsa? Naga kinyi wani iri" Suleiman yace "nima nagani, ko gurin likita zamu koma ne?" Umma tace "A'a Suleiman, ɗawainiyar nan tayi yawa, lafiyata ƙalau ai" Suleiman yace "wace irin ɗawainiya kuma Umma, ai in dai da amana nine yakamata in kula dake, Umma ban san haka abun nan ze kasance ba, Abbas ne yace a bawa Yusuf aikin nam ze iya, na goyi bayan hakan na bashi aikin, dana san haka zata faru da ban bashi ba, kuma ace wannan abu ya faru dashi, in kasa kulawa da mahaifiyarsa, ai da banyi wa kaina adalci ba, ni dai ina baki haƙuri Umma" Umma tace  "haba Suleiman, ai duk wani mumina dole ya yadda da ƙaddara, ba kai ka kama Yusuf ba, kuma ba kai kasa aka kamashi ba, ƙaddararsa ce a haka, duk imani da girma irin na Annabawan Allah, seda ya jarrabesu to waye Yusuf da Allah baze jarrabeshi ba, nasani Allah yana jarrabar bayinsa ne wanda yake so, dan haka inawa Yarona Addu'a, Allah ya bashi mafita ta idan bamu zata ba, sedai babu wanda ya bani mamaki kamar Abbas, ba ƙaramin mamaki ya bani ba, irin yadda yake nunawa Yusuf soyayya, Yusuf bashi da abokin daya wuce shi, da kansa yazo ya ɗau Yusuf ya kai shi gidansu yarinyar nan, amma yace be san zancen ba" Suleiman yace "Umma kiyi haƙuri, ki dena tunawa kawai, mu barwa Allah mucigaba da Addu'a" Umma tace  "Addu'a kam, na duƙufa ina nan inayi, kuma na saka anata saukar Al'qur'ani, na miƙawa Allah ya isar mana" Surayyah tace "insha Allah, addu'arki bazata faɗi ƙasa ba Umma, amma Umma akwai Abinci a gidan nan?" Umma tace "eh ina da Abinci" Surayyah tace "dafaffe fa" Umma tace "Aa', sedai in yanzu za'a girka miki, kina jin yunwa ne?" Surayyah tace "hakan ya nuna bakya cin Abinci Umma, ƙarfe biyu yaci ace ai anyi girkin rana" Umma tai murmushi tace "wayo kikayi min kenan?" Surayyah tace "ai ramar taki tayi yawa, dama munyi magana da Abban Nihal ne, muna so ki koma gidanmu zuwa muga yadda hali zeyi" Umma tace "A'a, hakanma nagode ku barni a nan, bazan ɗora muku wahala ba" Surayyah tace "Umma ba wahala bace bafa, kinga kaɗaici yana damunki sosai, ga rashin cin Abinci, ga larurar rashin lafiya kina tare da ita" Umma ta dage ba zata bar gidan nan ba, Suka dinga mata magiya sukace bazat wuce sati ɗaya ba, so suke jikinta ya warware. Da ƙyar Umma ta yarda, Surayyah ta haɗa mata kayan ta, suka tafi da ita gidan Suleiman. Yusuf duk iya azabtarwar daya sha, basu samu abunda suke so ba, ƙarshe ma Yusuf ya koma kurman ƙarfi da yaji, juyin duniya baya magana, itama Widad bata da maraba da 'yar prison ɗin itama, tayi wujuga wujuga itama, kamar korarriya ga Duka ga azabtarwa da take sha a hannun Bulama, duk ta fita hayyacinta. Nurat ma bata da kwanciyar hankali, se fama take da damuwa da tunani, sedai ta rufe ɗakinta tasha kuka, gashi yanzu ta dena samun magana Da Khalil sam. Haka gidan Hajiya Halima ya rincaɓe, Ramlah shaye2 ba kama hannun yaro, bata ganin kimar Mahaifiyarsu sam, yayin da Amal kuma gaba ɗaya haushinsu takeji, dan haka tai dumping ɗinsu gaba ɗaya a side, ta dena shiga sabgar su, ta kama wayarta take shiga wata caca a online da kuɗin data damfari Alhaji Haruna, sabgar ta kawai take ta dena shiga harkar mamanta da 'yar uwatta, idan taga Mummya zata dameta da koke koke ma, ko zancen Ramlah, se tai waje ta bar musu gidan, ko kuma ta shige ɗaki ta rufe taita danna wayarta, saboda tun kan Ramlah tai nisa da shaye2 Anwar yaso ɗaukar mataki akan lamarin, amma ta nuna bata so taci masa mutunci, dan haka na meye zata takura kanta akansu yanzu?. Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, yau kotu tafi kullum cika, da mutane daban daban, duk ana jiran jin yadda zata kaya a wannan shari'ar, yadda aka rirriƙo Yusuf aka shigo da shi cikin sarƙa, yana jan ƙafa da ƙyar, saboda wahala. Aka kammala wasu shari'ar da take kafinta su Yusuf, sannan akazo kan Tasu Yusuf. Justice Abdullah A Dutse ya gama rubuce rubucensa sannan yace "duba da yadda muka fara wannan shari'ar, da irin shedu da hujjoji a gaban wannan kotu, kuma wanda ake ƙara ya gaza musanta abunda ake tuhumarsa dashi, an samu wanda ake zargi da laifin yin garkuwa da mutum, duba sashi na 273 na kundin penal court, wannan kotu ta yanke wa wanda ake ƙara hukuncin shekaru goma a gidan yari, ba tare da zaɓin tara ba, sekuma laifi na biyu da ake tuhumarsa dashi shine laifin fyaɗe ga ita wadda akai garkuwa da ita, duba da sashin manyan laifuka, ƙarƙashin sashe na 221 wannan kotu ta yanke wa wanda ake zargi hukuncin shekaru goma sha huɗu a gidan yari, tare da aiki me tsanani, sekuma laifi na gaba laifin sata da siyar da abunda ba mallakinsa ba, saida motar ita wannan yarinya wadda kuɗinta yayi naira miliyan talatin, wannan kotu ta yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari, da tarar Naira million biyar, wanda ake ƙara idan hukuncin nan be masa ba, yana da damar ɗaukaka ƙara nan da kwanaki talatin masu zuwa " Alƙali ya buga gudumarsa ta kotu, aka sake taso Yusuf a gaba, sarƙa hannu da ƙafa akayo waje dashi, kamar kullum duk yadda 'yan jarida suka so jin ta bakinsa, yaƙi cewa uffan. Suleiman kuwa dama hana Umman Yusuf yayi zuwa ganin shari'ar gaba ɗaya. Ramlah kuwa ta sake bin Fahad ɗakin Hotel, tana ta zazzaga masa bala' i akan lallai seya aure ta, Fahad yace "asje ke ƙwayar da kike sha, hauka ta saka miki ban sani ba, ko matan duniya sun ƙare bazan aure ki ba, kin zama second hand, kije ki samu wani ajawon daze iya rufamiki asiri". Cikin ɓacin rai tace "ita wadda kake harin, itama ba second hand ɗin bace?" 'ai gara ita dake, koba komai ko second hand ce ai akwai kyau, dujda kema ba munine dake ba, amma ai kowa yana son canji, kuma itama da manufa zan aure ta " " wallahi baka isa ba, kayi kaɗan Fahad, zan gwada maka Rashin mutunci, jaki macuci kawai wallahi bazan yafe maka ba" "Ai babarki ce macuciya, itace babbar macuciya, kuma ina baki shawarar kije Asibiti a tabattar da lafiyarki, saboda akwai matsala a lafiya ta" Maimakon hankalin Ramlah ya tashi, kawai se yaga ta ƙyalƙyale da dariya irin ta mugwayen nan..... AMANA! AMANA!! AMANA!!! Ayshercool 07063065680 11/29/21, 8:55 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 140_141 Seda Ramlah tai dariya me isarta, yayimda Fahad ya bita da kallon mamaki irin dariyar da take ƙyaƙyatawa, tace  "Fahad ai duk yadda kake tunanina na wuce nan in gaya maka, shiyasa nake ta binka Allah ma'aiki ka aureni, ban nuna maka nasan kana ɗauke da cutar HiV ba harka samin ba, nake ta lallaɓaka amma baka gane ba, to na ɗau matakin daya dace, dan haka zan maka Albishir, Danni agurin Albishir ne, ina me farincikin sanar da kai cewa Ubanka Bulama ma yana ɗauke da wannan ƙwayar cuta " Ai a razane besan ya miƙe tsaye ba akan ƙafafunsa, ya dinga binta da wani ƙasƙantaccen kallo, yace " mekike nufi? " " Kurma ne kai? Ko yaren da nayi magana dashi ne baka ji, nace ubanka mahaifi wato Bulama, shima yana da cutar, na saka masa dan haka seka hanzarta kaje kasa shi ya fara shan magani akan lokaci, tun kan ciwon ya huda shi sosai, sannan yama da kyau ka binciki babarkama, ko itama ta rabauat seku duƙufa shan magani, kaga rabajau daku idan wannan ya manta lokacin sham magani yayi, se wannan ya tuna muku " Kamar Fahad ze fashe da kuka yace" kina nufin, Dad ɗina yana ɗauke da wannan cutar ne? " " babu ko shakka " ta bashi amsa " Amma wace irin tinkiyace ke Ramlah, yanzu sekiyi mu'amala dani ki koma kiyi da mahaifina saboda mugun abu? " Ramlah tace " duk cikin iya takune, da farko shiya fara ɓatamin rayuwa, na rufa masa Asiri, har na fara sonka, tun a wancan lokacin ya fara take taken baya goyon bayan soyayyar, kaima kazo ka nemeni na bada ksi bori ya hau ina zaton zaka Aureni, amma kaƙi kuma na kasa rabuwa da kai, duk da yadda Anwar ya dinga nusar dani, kawai naga magani a jakarka, na tambayeka na mene kace min na gyaran jiki ne, nai nai ka bani ka hanani, shine nai snapping nace a samomin maganin, aka gayamin na meye, nayi kuka na shiga damuwa amma nakasa gayawa mowa damuwata, na cigaba da shaye2 daka koyamin dan ragewa kaina tension, naga babu hanyar da zanbi in huce takaicin nan daka ƙunsami , seta hanyar sanyawa Ubanka wannan ciwon, se duk muyi jinyar tare, nake ta binka ka aureni kana rainamin hankali kana ganin ka cuceni, kuma ina me tabattar maka da cewa dukda kamilewa irin ta ƙaninka Ramadan, shima zan iya bashi nasa rabon, dan haka seka san abunyi tun dare be maka ba ". Ta ƙarasa maganar tana hararasa, ta bar ɗakin. Ya dafe kai ya zauna yana faɗin" Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ya isa tsakanina dake, kin cuceni, ba kowa aka cuta ba se Mother, tana gefe ta kawamme kanta ta riƙe Aurenta an kwasa mata masifa, Daddy why? " (dama ita zina haka take, idan ka yi da ɗan wani za'ai da naka, idan ba ayi da naka ba in one way or another, dole se wannan illar zinar ya shafi wani naka, zina bata da wata riba sam, ga zunubi, ga cuta ga ɗaukar alhakin wanda basuji ba basu gani ba, Allah ya shirya al'ummar musulmi baki ɗaya) Fahad ya cigaba da kuka yana tunanin, ta yaya ze fara gayawa Mummy abunda ya faru, wama ze tunkara da wannan Mummunan labari haka? Babu wanda aka cuta sama da Mummyn mu, dama har yanzu Daddy yana biye biyen mata? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un. "Ramlah kin cuceni, tsakanina dake Allah ya isa kawai ban yafe ba Wallahi, wayyo Allah na, ban taɓa dana sanin irin rayuwar da nayi ba se yau, ubangiji Allah yasa Mummy bata ɗauka ba, saboda abun kunya da Allah wadai, ace inbi yarinya mahaifina ma yayi, wace irin rayuwa ce haka? Ta yaya zan tun kari Mummy in sanar da ita ta binciki lafiyarta? Fahad ya zauna zaman dirshan a ƙasa yana kuka, sekace ɗan yaye kuka harda majina, ya rasa inda ze saka kansa dan baƙin ciki da takaici, yau a dalilinsa za'a sakawa mahaifiyarsa wannan larura, koma an riga an saka mata, yanzu ta yaya ze tun kare ta da wannan maganar? Seda aka watse daga kotu sannan Bulama yabi Justice A duste chamber, A dutse yai murmushi yace "ya kaga shari'ar tamu? Naga tunda muka fa fara shari'ar baka zuwa" Bulama yace "ya za'ayi inzo, sannan shari'a tayi dan yi, shekaru talatin ai kan nan komai yayi dai dai , amma abunda ya bani mamaki shine meyasa zaka ce wai yana da damar daze ɗaukaka ƙara, ɗaukaka ƙarar na mene kuma? Tunda ka yanke hukunci, meye kuma na wani ze iya ɗaukaka ƙara kuma? " " Bulama kenan, har yanzu baka san meye shari'a ba, babu yadda za'ayi aiwa mutum hukunci a irin kotunanmu sannan ka hanashi ɗaukaka ƙara idan hukuncin be masa ba, ba'ai haka ba haka ƙa'idar aikin take ba, nan da kwanaki talatin yana da damar daze je ya ɗaukaka ƙara " Bulama ya ɗanyi ƙaramin tsaki yace " to yanzu meye abunyi? " " Eh to, iyakaci kuyi ƙoƙarin toshe duk wata dama da zata saka ya ɗaukaka ƙararar, idan kuma ya ɗaukaka ƙararar, to se ka faɗi ka tashi suma ka siye su " Bulama yai tsaki yace " Aini daya ɗaukaka ƙarar da kar ya ɗaukaka idan na samu abunda nakeso, can ta matse musu, ni yanzu zanje in maida hankali in samu abunda nake so " A dutse yace "Shikenan, as you wish" Bulama yace "Nagode sosai da gudunmuwar ka" Suka musabaha, ya bar chamber. Bulama kai tsaye gidan da Widad take ya nufa, yana zuwa ya tarar da ita a zaune cikin zumbulelen hijjabinta, ta ƙara zabgewa, duk babu ƙibar nan, Widad lazumi kawai take a zuciyarta, dan tasan yaune ranar daza'a yankewa Yusuf hukunci a kotu, sedai zuwa yanzu bata san wani hukuncin za'a yanke masa ba. Bulama yazo ya sakata a gaba yana ƙare mata kallo, shikansa yaga yadda duk ta rame ta fita hayyacinta, mutum baya ce ita ce Widad Nasir Daula ba. Tunda ya shigo bata motsa ba, balle ta ɗaga kai ta kalle shi, ta zuba guri ɗaya ido ko motsi ba tayi. "Ina fatan kinji hukuncin da aka yankewa wannan sakaran xa kike iƙrarin mijinki ne? Koda yake ba lallai ki sani ba, amma shekarun babu yawa, shekaru talatin da ɗaya ne, se tarar miliyan biyar, sakamakon kama shi da laifin garkuwa da mutum, laifin fyaɗe da kuma sata, ina fatan yanzu kin san me Bulama ze iya aikatawa? Koda yake tun ba yau ba kin san irin abunda nake iya aikatawa idan ina buƙatar abu" Widad bata motsa ba bata kalle shi ba, tai shiru abunta tana cigabs da ƙurawa guri ɗaya ido. "Yanzu kin shirya gayamin inda abubuwan nan suke ko sena je nasa an kashe Uwar Yusuf"? A hankali ta ɗaga kai ta dube shi, tace "kai a tunanin ka zan bar mijina ya shekara talatin da ɗaya a gidan yarine? Lallai baka da hankali, kuma ga dukkanin alamu ka manta wacece Widad ko? Zan baka mamaki kuwa, Yoseef baze zaman gidan yari ba, kuma bazaka samu abunda kake so ba" "Kin zaɓi mahaifiyarsa ta mutu kenan?" "Ba zata mutu ba se lokacinta yayi" "Shikenan, tunda haka kika zaɓa, zaki gani kuwa" Widad tace "meye ban gani ba Bukar, zalunci da mugunta wanne ne bakamana ba? Kasa aka kashe mahaifiyata, kasa aka haukatani, kai kutungwila ka aurawa mahaifina matar da ta dinga azabtar da shi tsawon lokaci, yana bauta ita da 'ya' yanta amma suna azabtar dashi, hakan be isheka ba kasa aka dinga kaimin farmaki dan a kasheni akan dukiyar nan, banda message na razanarwa da tashin hankali da kake turomana, ƙiri ƙiri ka rabani da ƙasata ta haihuwa saboda mugun zaluncinka, kasa nayi rayuwa kamar matacciya, babu me raɓata ka jefa tsoron mutane a zuciyata, kasa aka dinga farautata kamar dabbar daji, Allah ya kawo Yoseef na fara samun sassauci, nan ma akasa akayi garkuwa damu, muka kuɓuta ya dinga wahala dani, amma a ƙarshe kalli sanadin zaluncinka abunda aka masa, nida abun a kaina ya ƙare da sauƙi, shi meye nasa a cikin lamarin nan? Wallahi wata shari'ar se a lahira shi kaɗai ze sakamin wannan zalunci da kamin " Bulama ya ƙyaƙyace da dariya yace " ke yanzu da duk kin san ni nake shirya wannan abubuwan amma kika ƙyaleni nake cin karena ba babbaka? Lallai kin iya wauta, meyasa kika ƙyaleni kikemin kallon uba bayan kin san ni maƙiyinki ne " Widad tace " talala na maka, tun ranar da aka kashe mahaifiyata aka ambaci sunanka, bazan taɓa manatawa ba, sedai na ƙyaleka ne saboda muddin nai wani yunƙuri zaka kashe min mahaifi, shiyasa na ƙyeleka, amma a yanzu inaji a jikina kana daf da yin faɗuwar baƙar tasa" "Hmm, lallai yarinya dole a sarawa ƙoƙarinki, da iya takunki tun kina ƙarama kanki yake kawo wuta sosai, kin iya lissafi sosai, Amma ki sani ni tsohon hannune a duniyanci, tunda hukuncin da akayiwa mijinki be zama izina a gareki ba, zan sa a kamo min uwarsa, inzo in yankata a gabanki tunda ke taurin kai baze barki ki ƙwaci kanki ba" Wani mugun kallo tayi masa, ya tashi ya fita daga ɗakin nata, bayan tafiyarsa Sabuwa ta shigo ɗakin Widad tana dube dube tace "dan Allah ban yarda memory ɗina a ɗakin nan ba, tun jiya nake nemansa ban ganshi ba sam" Widad tace "nima ban ganshi ba gaskiya, dan Allah Al'ada ne yazomin, tunda aka ciremin cikin nan ban ƙarayi ba se yanzu, dan Allah ki aramin dubu ɗaya, in rubuta miki irin wadda nakeso ki kai kowane shago a baki, idan Allah ya fitar dani zan bi yaki" Sabuwa tace "to shikenan" taje ta samo biro da takadda ta bawa Widad ta raba takaddar biyu, Widad tai rubutu akan kowacce takaddar, da yake Sabuwa bata iya karatu ba, Widad ta rubuta ta bata ta ɗakko wata leda tace "dan Allah karki gayawa kowa na aike ki, ki kai shago kice a bani abunda na rubuta a jiki, ki haɗa musu da wannan ledar ki basu" Sabuwa ta karɓa tace "shikenan, zan sawo maki insha Allah" Widad tace "nagode sosai" Mum Nurat taga sam bata ga gilmawar 'yarta ba, dan haka ta tafi ɗakin Nurat ɗin, tana zuwa ta tarar tayi wujuga wujuga saboda kuka, se rusa uban kuka take kamar ubanta ya mutu. A ɗan gigice tace "ke lafiya kuwa? Meye ya faru dake haka? Me akayi miki ne?" Maimakon ta bata amsa, sema sake rushewa da kukada tayi, "ke bana son sakarci fa, menene haka? Meya sameki kike rusa wannan uban kukan haka?" "Mummy baki ga hukuncin da aka yankewa Yusuf bane?" "To idanma na gani me zanyi, ko kuma me zance? Allah ya bayyana gaskiya kawai, amma shine zakizo kina wannan uban kukan haka? Ai koni na mutu iyakar wannan kukan kenan" "Mummy wai meyasa kike basarwa ne, baki san menene yake wakana ba? Kin san fa komai Mummy? Daga gidan nan fa ake shirya maƙarƙashiya fa kin sani fa" Da sauri Mummy ta ƙarasa, ta tishe mata baki tace "dan ubanki yana cikin gidan nan, so kike ya jiyo yazo yai miki wani abun?" Nurat ta fizge tace "Haba Mummy, meyasa zamu ɗauke ido akan gaskiya Mummy? Wallahi ranar lahira muma harda mu a cikin wannan zaluncin da akayi, Mummy da saka hannun Daddy fa aka sace su Widad, Mummy da kunnena fa naji shi" Maman Nurat na juyawa taga Alhaji Musa a ƙofar ɗakin, yana kallon su. Nurat taƙi yin shiru tace "gaskiya Mummy idan mukayi shiru bamu da adalci, wallahi da saka hannun Daddy akan abunda ya faru, kuma kema kin sani, Wallahi da Daddy ake shirya komai, Mummy ya zakiji idan ɗankibaka yankewa hukuncin shekaru talatin da ɗaya a gidan yari? Kefa uwa ce Umma, bakya tunanin me mahaifiyarsa zataji a ranta a yanzu haka? Ancd shikaɗaine ɗanta amma an yanke masa hukuncin shekaru talatin da ɗaya a gidan yari " Cikin tsawa Mummy tace " dan ubanki bazaki min shiru ba, seya miki wani abun tukuna? " Nurat tace" Mummy nifa gaskiya nake faɗa, kuma ni zanje in bayar da shedar abunda ya faru, mahaifina yasan komai fa" Alhaji Musa ya tako a hankali, yana zuwa bece komai ba ya danƙi hannun Nurat ya fara jan ta, a gigice Mummy tace "ya haka? Ina zaka kaimin 'yata? Ina zaka kaita? Karka cutarmin da ita dan Allah, ita kaɗaice' yata karka cutar da ita na gaya maka" Be tankamata ba, ya dinga jan Nurat, Nurat tana faɗin "Daddy kaji tsoron Allah, a wannan shekarun naka me kakae nema a duniya haka, wanda zesa kasa hannu a zalunci wani, da Alhaji Nasir kake da matsala bada 'yarsa ko wanda beji ba be gani ba, dan Allah Daddy ku ƙyale Daula ya huta, da kunnena naji kana magana kune kuka saka aka sace Widad da direbanta, kuma yanzu kun sauya maganar kuna gabi aka kaishi kotu aka yanke masa hukunci akan abunda bejiba be gani ba" Yana jan Nurat, tana biye dashi yayin da mahaifiyarta ke binsu tana masa magiya, wani ɗaki yaja Nurat can bayan ɗakinsa a ƙarshen bene, ya jefa ta ciki yasa mukulli ya kulle ta, ya juya ze tafi, Maman Nurat ta sha gabansa tace "meyasa zaka kullemin yarinya a wannan ɗakin ita kaɗai? Me yasa haka? Dan Allah ka buɗe mata ƙofar nan ta fito, karta cutu dan Allah" Alhaji Musa yace "wallahi bazan buɗe ta ba, ashe kune manyan maƙiyanaba gidan nan? Dole ta bar ƙasar nan ko tana so ko bata so, kuma kema daga yau, bake ba fita ko ina, kuma duk sena karɓe wayoyin ki, munafukar banza da ta wofi" "Niba munafuka bace, karka ƙara kirana da munafuka, halin rashin gaskiya 'yarka ce ta fara gano kana yi, dan haka babu laifina a cikin wannan batun? Dan Allah ka buɗemin' yata dan Allah ka barta ta fito, wallahi bazan bari tayi komai ba, dan Allah kayi haƙuri " Tsaki yayi, ya raɓa ze wuce ta, amma ta sha gabansa tana kuka akan ya buɗe Nurat, aikuwa ya Tureta ze wuce bisa ga tsautsayi ta gangaro daga kan benen nan, ta ƙwala ihu da ƙarfin gaske, tun daga ƙafar farko har ƙasa, da sauri ya bita sedai kan ya ƙaraso tuni ta ƙarasa, ta faɗa da fuska aikuwa tuni jini ya wanke gurin, jikinsa yana rawa yazo ya ɗagota, fuskarta ta wanke tsaf da jini, gashi ko motsi ba tayi, akan idon me gadinsa ta faɗo daga kan benen. Nurat ta jiyo ihun mahaifiyarta, amma bata san meyafaru ba, dan haka hankakinta ya tashi, ta shiga dukan ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske tans kuka, tana kiran sunan Mummy. Aka ɗauki Maman Nurat, zuwa Asibiti cikin gaggawa, ana zuwa aka karɓeta a Asibitin, da gaggawa aka shiga da ita emergency. Sabuwa ta dawo gidan da Widad take, ta shiga gurin Widad tace "Nifa naje na kai musu, amma basu bani komai ba, sun karɓi takardar sun karanta, sun bani wata takardar, sun karɓi ledar sunce in tafi kawai, hadda tambayata wai waye ya aikoni?" Widad tayi murmushi tace "inaga basu da ita ne, bani takardar da suka baki" Ta miƙawa Widad takardar da suka bata, ta karɓa ta karanta, tai ajiyar zuciya tace "nagode sosai Sabuwa, sunce basu da irin wadda nake so, se Allah ya kaimu jibi kije ki karɓa" Sabuwa tace "to yanzu ya zakiyi? Ga jini na zuba?" "no karki damu, zan iya maleji zuwa lokacin da zasu kawo ɗin, bana iya amfani da kowacce se ita ne" Sabuwa tace "to shikenan, Allah sarki ashe cikin ya fita dagaske?" Widad tace "eh ya fita, ina son zan ɗan kwanta" Sabuwa tace "to shikenan, se anjima" Fahad fa ya rasa inda zesa kansa, da yaga mamansa, se yaji tausayinta ya kama shi, se yaji ƙwalla ta tarar masa, maimakon yaji haushin kansa, haushin mahaifinsa ya dinga ji, dan dabe nemi mata ba da babu abunda zesa mahaifiyarsa ta samu, gashi ya rasa ta inda ze mata wannan baƙin bayanin mara daɗin ji. Gidansu Amal ma gidan sam babu daɗi, idan Ramlah taga dama a falo, haka take zuwa ta kama shan shisharta, kota kunna sigari tana busawa, ta baje kayan coadine ɗinta taita yiwa kanta caji, Hajiya Halima yanzu kam tsaro Ramlah take bata, sam bata iyayi mata magana, tana kallon ta, tana yi amma bazata iya cenata bari ba, Amal kuwa dama tuni ta fita daga harkar su. Hajiya Halima na ɗakinta, ko izininta bata tambaya ba ta fice ta tafi Asibiti dan a dubata, sedai ta razana da sakamako ya fito aka tabattar mata da tana ɗauke da juna biyu, ta shiga ɗimuwa da tashin hankali, tun a Asibitin ta lalubi lambar Alhaji Haruna ta sanar masa da tana ɗauke da juna biyu, kuma ko yasan yadda zeyi da ita ko kuma tayiwa duniya Albishir da tana ɗauke da cikinsa. Abubuwa fa suka rincaɓe sosai, Wata Nurse inyamuda ta jata gefe tace mata tasan inda zata kaita a zubar da cikin, in dai bata son cikin, ba musu ko tunanin komai Amal ta amince da a zubar da cikin. Yusuf yana cikin fursunoni, yana zaund shiru kamar yadda ya saba zama, akace yayi baƙi ya kalli gandiroban ya ɗauke kai kamar beji ba, "Malam da kaifa neka" gandiroban yai maganar a ɗan hasale" Yusuf yace "bazani ba" "Kamar yaya bazaka ba?" 'me zanje inyi? An riga an yanke min hukunci, burinku ya cika kuda iyayen gidanku, me kuke nema a gurina kuma? Ko waye bazani ba" Gandiroban yace "koda mahaifiyarka ce kuwa?" Da jin haka Yusuf ya miƙe da sauri, se kuma yaji bashi da karsashin tunkararta ya kalleta, dan yasan abune mawuyaci sukuma rayuwa da Ummansa kamar da. Yusuf yabi bayan gandiroban jiki a saɓule, yana dogara ƙarafarsa da kyar saboda ciwo da take masa. Yana zuwa yaga wasu mutane a zazzaune, wanda be sansu ba sam, aka bashi guri ya zauna yana ƙare musu kallo. Ɗayan ya kalle shi yace "sannu Malam Yusuf, sunana Barrister Hafiz wannan abokan aikinane" yai maganar yana miƙawa Yusuf hannu. Amma Yusuf ya ƙeƙashe ƙasa yaƙi bashi hannu, ya kalle shi yace "me kuke nema a gurina? Bayan shari'a tazo ƙarshe an yankemin hukunci, me yayi saura kuma me kuke so inyu muku" Yai maganar cike da karaya, ƙwalla na taruwa a idon sa. Hafiz jiya yi kamar yayi kuka shima, ya maze yace "haba Yusuf, ai ka tsaya kaji meke tafe damu ai, Barrister miƙo takaddar nan" Barristern dake gefensa ya ɗakko takadda ya miƙawa Hafiz, Hafiz ya karɓa ya miƙa masa yace "ga saƙo inji matarka" Jikin Yusuf na tsuma ya karɓi takaddar yana buɗewa yaga rubutun Widad " _Bani da abunda zan iyayi maka a halin da nake ciki I love you My Yoseef, but I will do my best to see what I can do for you, please pray for me, is either we should meet again or the time you will be free i pass away_ Yusuf yace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un" AMANA! AMANA!! AMANA!!! AYSHERCOOL 07063065680 11/30/21, 8:20 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" _(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_) IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _ Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)       Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji   Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219 Chat 08063114606 144_145 Ai zumbur ta miƙe zaune tace "ban gane a kasheshi ba? Anwar ɗin nawa za'a kashe? Me yayi masa haka?" Alhaji Musa yace "ke nifa tuni na dawo daga rakiyar mutumin nan, Azzalumi ne kawai, kansa ya sani bashi da imani sam, ni kaina yanzu haka muna Asibiti nida su Nurat, amma gaba ɗaya ko yamin jaje se masifa da tashin hankali da yake min, shiyasa na kwashi kuɗina na saka a siyasa, in samu su bani takara in huta da wannan mulkin mallakar da yake mana, ga uwar dukiyarmu da muke narkawa amma har ynzu babu wani bayani " Hajiya Halima ta fashe da kuka tace " ni Bulama zeyi wa haka? Anwar kamar ɗa yake a gurinsa amma shine zece a kashemin shi? Baze yuwu ba kuwa " Ta ajiye wayar, ta miƙe ta shiga ɗakinta ta zura doguwar riga, kusan ƙarfe goma saura na dare, amma tayi waje ta ɗau mota ta fita ta tafi gidan Bulama a daren. Shikuma Bulama yana zaune yana ta nazari akan yadda ze ɓullowa al'amura da suke neman damalmale masa, ya dinga kiran layin su Me Adda amma shiru babu Labari, waya taƙi shiga sam. Masu gadi kansu sunyi mamakin ganinta a wannan daren, kamar wata mahaukaciya ko gabanta bata gani sosai saboda tashin hankali, kai tsaye ya shiga falon dake ƙasa tana bala'i  "Ina Bulama yake? Ina Bulaman?" Iman ce zaune a falon tana kallon zee world tace "Mummy lafiya kuwa?" "ban sani ba, ina uban naku yake tsohon macuci azzalumi?" Iman ta kalleta da mamaki jin irin furcin da take akan mahaifinsu wanda ya kasance ɗan uwa a gareta, Iman tace "Mummy ya riga ya hau sama, inaga ma ya kwanta fa" Ai bata tsaya jiran me Imana zata kuma ce mata ba ta haura saman da kanta, ba zato ba tsammani ya ɗaga kai yaci karo da Hajiya Halima a tsaye a kansa. Ya kalleta yace "Halima, lafiya kuwa zaki zo a daren nan? Bakya jira ayi miki iso kawai ki hauromin ɗaki haka?" "Dalla rufemin baki, me zaka gayamin har wani iso zan jira ayimin, munafuki azzalumin banza dana wofi, tsawon shekaru ina maka aiki, kana sani duk abunda kaga dama ina maka, dan ka cinma burinka ba tare da na nuna gazawata ba, shine halin naka na baƙin kumurci zaka gwadamin, shine kayi umarni da idan anga Anwar a kasheshi, ɗan nawa za'a kashe? Wallahi baka da imani ba kada Alƙawari tun wuri ka dakatar da wannan maganar idan ba haka ba Wallahi ran ɗana baze tafi a banza ba" Zazzaro ido Bulama yayi ya dinga ƙifta mata ido akan tayi shiru, amma tace "bazan shirun ba, wallahi babu inda zani se an dawo min da ɗana" "Halima wai wace irin magana kike hakane? Kamar yaya nace idan anga Anwar a kasheshi? Me Anwar yayi min wanda zesa ince a kashe shi, ni da na kaiwa jam'ian tsaro maganar dan ayi bincike akansa a gano inda yake ya zakice nace a kasheshi? Wani munafukin ne ke neman haɗani da 'yar uwata?" " Kaga bana son kame kame da ƙaryar banza, wanda ya gayamin baze maka ƙarya ba, macucin banza da na wofi kuma wallahi idan ɗana ya mutu you must pay for it, wallahi aka kashemin Anwar seka fanshi ransa, nima kasan halina ka san abunda zan iya aikatawa " Gaba ɗaya Bulama ya dirirce ya rasa abunyi, ya shiga tsuma yana fatan Allah yasa wani beji abunda ta faɗa ba. Ya biyo bayanta ya leƙa, yaga ba kowa a falon ƙasa dukda ɗakin a rufe yake babu wanda ze iya jiyo me sukayi, ya koma bedroom ɗinsa ya tarar da Hajiya Sarah tana ta baccinta hankali kwance, yai ajiyar zuciya tare da tunanin bata jiba, amma ya zauna yai shiru akan gadon yana tunani, tabbas babu wanda ze gayawa Halima wannan maganar idan ba Alhaji Musa ba, tabbas dole yayi maganin Alhaji Musa. Cikinsa ne ya murɗa ya tashi ya tafi banɗaki, kusan kwana huɗu kenan yana fama da gudawa taƙi tsayawa, dan haka ya sa ransa idan ya gama da wannan matter ɗin zeja yaga likita. Yusuf se sake juya takaddar nan yake, yana tunanin wani hali Widad ɗin ke ciki, tabbas yasan da  tana da dama bazata barshi a gurin nan ba, dole akwai wani abu da yake gudana a ɓoye, idan ya kalli sentence ɗinta na ƙarshe na ba lallai su sake haɗuwa ba se yaji gabansa ya faɗi, lallai ko a ina take tana cikin mawuyacin hali, "Allah ya ƙara haɗa fuskokinmu my wife, Allah yasa kina hannu na gari, i love you too" yai maganar a hankali tare da lumshe idonsa. Rayuwar da suka yi tare a ƙauye ta dinga dawo masa, koba komai zamansa da ita ba ƙaramin farinciki ya samu ba, zamansu a ƙauye yasa Ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ta samu hutu na wani ɗan lokaci, ya daɗe beji cin zarafi da gorin rashin iyaye daga mutane ba, sedai matukar kewar Ummansa da yayi, be sake zaton ze samu wadda zata aureshi ba saboda rashin nasaba ba, sedai cikin hukuncin Allah ya auri yarinyar da zuciyarsa ta mato a sonta, dukda nisa da ratar dake tsakanin su, yarinyar da manyan wanda suka isa ma basa gabanta, soyayyar ma bata yadda da ita ba, amma Allah ya ƙaddara Aurensu, har suka yi zama cikin farin ciki, ya dinga tuna irin Shagwaɓarta wauta da yarinta wasu lokutan, ya tuna lokacin da take koyar tankaɗe, da sanda take wa Abincin garin kallon banza, da yadda ta dage ita seta samu ciki, da irin kallon da take masa idan ya tsokane ta. A hankali ya sake lumshe ido yana murmushi, sekuma ya tuna yadda ta shiga damuwa daya bata labarinsa, da yadda ta dinga kururuwa tana kuka tana gaya masa tana sonsa lokacin da aka kama shi a garin, da yadda taje kotu ta bada sheda akansa, ga shekarun da aka yanke masa a gidan yari, ga abunda ta rubuta masa kawai se yaji ya karaya hawaye ya shiga bin gefen idonsa, baya tunanin ze sake wata rayuwa me daɗi a nan gaba, mussman kasancewa da Widad a inuwar Aure. Da ƙyar likitoci suka samu Nurat ta dawo hayyacinta ta samu bacci, aka sa mata ruwa, sedai harta farfaɗo ɗin numfashinta da vital signs ɗinta suka daidaita bata gane mutane sosai, saboda ta galabaita an samu dai bacci ya ɗauketa cike da fatan idan ta tashi zata iya dawowa hayyacinta gaba ɗaya, mahaifiyarta kuwa gaba ɗaya har yanzu ba'a gano kanta ba, tana kwance ne kawai, numfashi ne kawai a ƙijinta, banda haka babu abunda yake aiki a jikinta, sam bata san abunda ke faruwa ba, shi kansa numfashin nata da ƙyar take yinsa wasu lokutan, saboda ta zubar da jini sosai, kuma ana kyautata zaton ta samu rauni a cikin kanta, sakamakon buguwa da tayi, likitoci sun rubuta mata hoton Ƙwaƙwalwa dan tabattar da abunda yake damunta. Abu kamar wasa, jini yaƙi tsayawa Amal, se aikin zaryar banɗaki take, jini se zuba yake babu ƙaƙƙautawa, ta rarrafa ta haɗa Abinci tana ci kota samu sauƙin wannan wahalar haka, zuciyarta tana ƙuna akan yadda Alhaji Haruna ya cuce ta, Hajiya Halima ta fito falon ta zauna ta dafe kai ta kalli Amal tace "wai kuwa lafiyarki ƙalau kuwa? Gaba ɗaya kin wani ɗashe kinyi fari ƙal, kamar baki da jini a jiki, ko baki da lafiya ne?" Amal tace "lafiyata ƙalau, period kawai nake shiyasa" Hajiya Halima tai ajiyar zuciya tace "Amal kin kuwa san abunda Bulama yaimin?" "A'a sekin faɗa" "wai an gano inda Anwar yake, amma yace wai a kasheshi saboda karya tona Asiri" Da sauri Amal ta kalleta tace "A kasheshi kuma? Me me kikace masa?" "Naje har gidansa jiya da daddare, na ƙare masa tatas, nace wallahi aka kashe min ɗana seya fanshi ransa da nasa ran kona 'ya' yansa" Amal tabi mahaifiyarsu da kallo, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, duk mahaifiyarsu ta ɗaiɗaita rayuwarsu da kanta, kowa yana karɓar nasa kason ɗaya bayan ɗaya. Ramlah ce ta fito tana tangaɗi, tana magana cike da maye ta tsaya a tsakiyar falon tace  "Wai ni.... Waini Fahad baze Aureni bane... Bazaki ce ya aureni ba ko? Wa.. W.. Wallahi kuwa bazan dena shaye2 ba tunda ya lalatani, ku.... Kuma... Kumaaa ai shikenan tunda nasan Na sakawa Bulama cutar tunda shima ya sakamin... Wallahi idan baka Aureni ba sena sakawa Wannan yaron Ramadan ma, idan yaso kow... Ko..... Kowama ya samu ni za'ayiwa hauka? Ya.. Ya ɗauka bani da wayo hmm baka san Rmalha bane"  kawai ta faɗi a gurin tana juyi tana ci gaba da sambatu marasa kan gado sam. Hajiya Halima ta kalleta tace "Ramlah wai wace cutar kike magana akai ne? Wace irin cuta?" Ramlah bata san me take ba, juyi kawai take yi tana wasu surutan irin na marasa kan gado, Amal kam tasan babu mamaki idan akace Fahad yana ɗauke da wannan cutar me karya garkuwar jiki, amma sedai dagaske Ramlah take tana mu'amala da Bulama ma kenan, gaban Amal ne ya faɗi kardai ace itama tana da wannan cutar, miƙewa tayi da sauri zata tafi ɗakinta, Hajiya Halima tace  "Amal ina zaki? Kina jin maganar da gake faɗa? Ko dai duk a cikin maye take ne?" Amal tace "tunda ki kaji ta faɗa a maye, to ko ba'a mayen bama ya faru, sedai fatan Allah ya kyauta" Amal ta tafi ɗakinta, dan itama fama take da kanta, wannan azabar ciwon marar da zubar jinin sun isheta haka. Anty Saddiƙa ƙanwar Maman Nurat itace a gurin Nurat, itakuma maman Nurat ba'a barin kowa ya shiga inda take in ba likitoci ba, saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman, Anty Saddiƙa taje salla Khalil na zaune a gurin Nurat, ai kuwa ta farka ta zaci zata ganta a ɗakin Dad ɗinta ya kulle ta, sedai tana buɗe ido tai arba da wani gurin daban, ta yunƙura zata tashi zaune, Khalil ya taho da sauri ya riƙeta yace  "yi haƙuri, ki kwanta kinji, karki gaggawa jikinki babu ƙwari" A Shagwaɓe Nurat tace  "Brother ruwa zan sha" Yace "ok bari in baki" Ya ɗakko ruwam roba, ya buɗe ya bata ta sha, har ze gyara mata kwanciyarta ta kwanta, ta riƙe shi gam tana kallonsa, tana ƙoƙarin tuna meyafaru ihun Mummynta ta tuna, nan da nan ta razana tace masa "Mummy, Khalil Mummy na tana ina?" Khalil yace "kwantar da hankalinki tana nan lafiya" "A'a ban yadda ba, naji ihunta fa ranar, ban san meye ya sameta ba, tunda Daddy ya kulleni ban sake ganinta ba, waini ya akayi ma nazo nan ne?" Khalil ya kalleta yace "kamar yaya ya kulle ki? Ya kulleki a ina?" Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta gaya masa, yai shiru yana nazarin maganganun Nurat, cikin kuka tace  "ina Mummy take? Dan Allah ka kaini in ganta dan Allah" Khalil yace "ki kwantar da hankalinki, likitoci na can na kula da ita, idan ta farka zata zo ki ganta" "to wai meyasa meta ne?" "Bakomai, ta faɗi ne kawai saboda Dad ɗinki ya rufeki, bari Anty Saddiƙa tazo ta temaka miki kiyi wanka" Bayan Saddiƙa ta shigone, Khalil ya tashi ya fita, a reception yaje ya samu Alhaji Musa a zaune, dan idan yazo Asibitin ya duba su Nurat nan yake dawowa ya zauna, dan gaba ɗaya haushinsa suke ji. Ya zauna kusa da Alhaji Musa ya kalle shi yace  "garin yaya ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene?" Alhaji Musa yace  "wace irin magana ce wannan? Ba a gabanka nayi wannan bayanin ba?" Khalil ya kalle shi yace  "to ya akayi ka kulle Nurat? Laifin me tayi maka" Da sauri Alhaji Musa yace  "tana ina? Nurat ɗin ta farkane?" Yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma Khalil ya tareshi yace "na tambayeka kana ƙoƙarin tashi ina zaka?" Yace  "wai ita Nurat ɗince tace maka kulleta nayi?" Khalil yace "labari na samu, daga majiya me ƙarfin gaske, dan haka nake tambayarka garin yaya ka kulleta" "wai Khalil yaushe ka koma haka? Yaushe ka koma mara kunyane?" "ba rashin kunya bane, gaskiya ce dama ina da ayar tambaya akanka, wallahi muddin na ganoka da wani abu ba dai dai ba, naga wani abun kayiwa ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene, wallahi se nayi shari'a da kai, yanzun ma ba ƙyaleka zan ba, dan ba ƙaramin haushinka nakeji ba" Alhaji Musa zeyi magana, amma Khalil ya dakatar dashi yace "ba abunda zaka gayamin, bana buƙatar jin komai daga gareka, amma tabbas ina nan ina bincike akanka, kuma wallahi ina daf da tsayawa a kotu a gaban alƙali da kai" "Da nayi maka me?" "in mun haɗu a kotu kaji" Ya miƙe ya bar gurin, Alhaji Musa ya bi shi da kallo, yana tunanin me Khalil yake nufine? Bayan Ramlah ta tashi daga mayen da take ne, Hajiya Halima tazo ta sata a gaba tana tambayarta   "Ramlah wata magana naji kina yi ɗazu cikin maye, wai Fahad yasa miki cuta, kekuma kin sakawa Bulama, wacce magana ce haka?" Ramlah tace  "Eh to, dukda kince a maye nayi maganar kamar yadda kiji maganar haka take, Bulama shiya fara lalatamin rayuwa ta, na kamu da son ɗansa wanda hakan yasa na biye masa, sedai Bulama yaƙi goyon bayan ya aureni, yake ta cusa masa 'yar Daula ya aura saboda ya cika burinsa, soyayyar da nakewa ɗansa tasa na dinga biye masa ya koyamin shaye2, ya koyamin rayuwar banza nida shi ba abunda bama yi, nace ya Aureni amma yaƙi, kuma na gano yana da cuta me karya garkuwar jiki, dan haka na ƙuduri aniyar ramawa na komawa mahaifinsa, kuma da yake ɗan Akuyane ya karɓeni, ba tare da yasan ina mu'amala da ɗansa ba, dan haka shima ya kwasa, zuwa yanzu nasan uwarsa ma ta ɗauka, hakan yasa na ɗan rage abunda ke zuciyata gara muyi jinyar tare hadda ubansa" Hajiya Halima ta ɗora hannu a ka tace "yanzu Ramlah abunda kikayi kenan? Ramlah gaba ɗaya kika biyewa namiji kika barbaɗar da rayuwarki da mutuncinki? Kin kyautawa kanki kenan?" Ramlah tace "Mummy, bafa laifina bane wannan lamarin, duk wanda yazo neman Aurena se ki nunamin ai shi ba sa'an aurena bane, ina gidan Attajiri kamar Daula bekamata in Auri wane ba, ƙarewa ɗan uwanki ya biyoni ya lalata, na kamu da son ɗansa amma yai biris dani, kuma akan idinki nake fita ai, kin taɓa tuhumata ina muke zuwa nida Fahad idan mun fita? Me yasa? saboda idonki ya rufe ke burinki ya kawo miki masu siyan kadarori ki tara kuɗi, don't blame me for this please " Ta tashi tai tafiyar ta ɗaki ta bar mata falon, Hajiya Halima ta dafe kai ta fashe da kuka, Bulama ya riga ya gama cutarta a rayuwa, ba ta san mema za tace a game da shi ba, ya lalata mata rayuwar 'ya, kuma wai yanzu Ramlah na ɗuke da cuta me karya garkuwar jiki, wanda ta samune a sanadin ɗansa, kuma ya dawo yace a kashe mata ɗa, ta rushe da kuka harda sheshsheƙa, gaba ɗaya komai ya rikice mata, tama rasa meye abunyi, wannan wace irin masiface haka take bibiyar ta? Daga wannan se waccan gaba ɗaya 'ya' yanta sun barbaɗe, haka ta dinga gunjin kuka ita ɗaya a falo, Amal ta ƙarawa ƙofar ɗakinta key, dan bata son tashin hankali. Da safe Fahad ya shiga cikin gida, domin gaida iyayensa, sedai yan zaune a falon Iman nata masa surutu amma sam hankalinsa baya kanta, yayi zurfi a tunani can ya ɗago kai yace "ke wai ina Mummy ne?" Iman tace "tana sama ɗakin Daddy" Ji yayi kamar ta watsa masa wuta, ta ina ze fara gayamata hakinda ake ciki? Koma ya gayamata ai yasan aikin gama ya riga ya gana zuwa yanzu. Yana nan zaune Sega Bulama yana Sakkowa, hannunsa ɗauke da jakarsa, Mummy sanye da doguwar rigar baccinta, ta riƙo masa wayarsa suna hira, Fahad yaji kamar yaje ya make Bulama saboda tsabar baƙin ciki da takaici, ga wani irin tausayin mahaifiyarsa ya kama shi. Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace  "yau Allah ya nufe ka da shigowa cikin gidan kenan? Yaushe rabonka da shigowa" Bulama yace "wai gidan ubanwa kake shigewa ne? Ko haryanzu yawon kake baka kwana a gida?" ga mamakinsa seya ga Fahad ya maka masa wata uwar harara, abun da be taɓa yi masa ba, ya kalli mahaifiyarsa yace  "Mummy ina kwana?" "Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?" "Lafiya ƙalau, dama na shigo mu gaisa ne zan karya" Tace "shi Daddyn naka bazaka gaishe shi ba?" "Ai na gama gaidashi, ni da sake gaisheshi har abada" Kallonsa sukayi gaba ɗaya, Hajiya Sarah tace  "Fahad, daga kan kayan shaye2 naka ka taso ka shigomin falo ko? Shine har kake gayawa mahaifinka wannan maganar?" Alhaji Bukar yace "ƙyaleshi, ina daf da maganinsa akan wannan mummunar ɗabi'a ta shaye2, dank yake zancen, ban agogona zan fita ina da ayyuka da yawa a Office " Yasa hannu ya karɓi agogonsa, yai waje bayan fitarsa Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace " Fahad, meyasa ka gayawa mahaifinka wannan maganar haka? Kai lalacewar taka harta kai kayiaa mahaifinka haka? Me yayi maka? " Yace " bakomai " " Bakomai amma ka faɗa masa wannan maganar? Abunda kayi ya dace kenan?" Ya girgiza kai alamar a'a "to meyasa kayi, salon mutane suji suce ni nake saku a turbar banza, na ku Wulaƙanta mahaifinku?" "Nifa Mummy bakomai, kema da kin san me yayi da baki faɗi wannan maganar ba, kawai dai Allah ya kyauta" Ya mike a fusace ya baf falon, tabi bayansa da kallo, Iman tace  "Mummy" "Na'am" "wai kuwa idonki biyu, jiya da Maman su Amal tazo gidan nan?" "haba dai? Gidan nan tazo? Ai ban sani ba" Iman tace "wallahi tazo, bayan ƙarfe goma se bala'i take tana neman Daddy" "subhanallah, Allah yasa ba'a akan Ramlah tazo ba, saboda kin san halin ɗan uwanku sarai, ina kyautata zaton akwai alaƙar banza a tsakanin sa da Ramlah" . "Mummy ya akayi kika sani?" "last week na ganta ta fito daga sashinsa, na tambaye ta amma bata gayamin komai ba, sema baƙar magana da tayi min" Iman tace "Umma kiyi ta haƙuri, Yaya Fahad se Addu'a gaba ɗaya zamansa a ƙasar waje ba abunda yasa masa se koyar mugayen halaye" Hajiya Sarah tace  "idan da zaman ƙasar waje dai to harda halinsa, meyasa shi Anwar be lalace ba se shi? Bani da abunyi se dai yi masa addu'a, baya jin faɗa baya jin rarrashi, babu wanda banyi ba, amma duk baya ɗauka" "Mummy kiyi haƙuri, wataran se labari ze dena insha Allah" "Mhmm Iman kenan, yaushene watarn ɗin? Mutum ya girma amma kullum ba hankali, Allah ya kyauta dai kawai". Yanzu ma Bulama yana zaune a Office, kiran wayar Me Adda kawai yaje amma taƙi shiga, yai shiru can wayar ta fara ringing, cikin hanzari ya ɗauka ya zata me Adda ne, sedai yaga baƙuwar lambace, ya ɗaga yai sallama "justice A dutse ne ke magana ' Bulama yace " ok nagane, ya kake ya aiki? " " Alhamdilillah, dama na bugo in sanar makane da cewar tawagar lawyoyi da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ɗaukaka ƙarar shari'ar Yusuf da nayi, kuma ina kyautata zaton ƙarƙashin jagorancin shahararren lawayrn nan ɗan gwagwarmaya wato Barrister Adam A Adam, dan haka tun wuri kasan abunyi!!! (Alhamdilillah masha Allah, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, da addu'oinku da na samu bisa rashin da akayi mana, nagode sosai Allah ya bar zumunci) AMANA! AMANA! AMANACE!!! AYSHERCOOL 07063065680 11/30/21, 8:20 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" _(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_) IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _ 142_143 Yusuf ya dinga jujjuya takardar nan, ya kalli Barrister Hafiz yace  "Ya akayi ta rubuta takadda a bani?" Barrister Hafiz ya matso daf da Yusuf, ya shiga yi masa magana ƙasa ƙasa  (ni kaina da nake ɗakko rahoton banji me yace masa ba) Yusuf ya sunkuyar da kai yana sauraren Hafiz, Hafiz ya gama gaya masa abunda ze gaya masa, Yusuf ya dinga jinjina kai, Hafiz yace "ka sairaremu nan da wani ɗan lokaci, mungode sosai" Sukayi musabiha da Yusuf, suka miƙe suk tafi, Yusuf kuma aka maida shi inda yake, hannunsa ɗauke da takaddar da'akace Widad ce ta bayar a bashi, yaje ya samu guri ya zauna yana jujjuya takaddar da'aka bashi yana sake karantawa. A hankali ya furta  "Allah yasa kina lafiya Widad, koba wane hali kike Allah ya kuɓutar dake, ya sake ƙaddara saduwarmu dake" Widad tana nan a tunanin Allah yasa saƙonta ya isa inda ta aika shi, dan zuwa yanzu ta sare da zata bar gurin nan, dan bata ga hanyar barin gidan nan ba, Amma Allah yasa kafin ta mutu Yusuf ya yafe mata, karta mutu yama ɗauke da pain ɗin bada shedar ƙarya da tayi akansa. Da ta lumshe ido se hawaye, wani na bin wani, tana tunanin anya zata samu sassauci game da wannan halin ni 'yasu da take ciki? Ita dai fatan ta Allah ya haɗa ta da Yusuf ta nemi afuwarsa. Ganin Widad dagaske ba zata bashi inda dukiyar take ba, tana ta faman raina masa hankali, ya ƙudurce tabbas ze ɗakko mahaifiyar Yusuf yayi garkuwa da ita, ko ta bashi, ko kuma ya illata ta a gabanta, tunda ya fuskanci bata son duk wani abu daze saka Yusuf da ahalinsa su shiga damuwa. Dan haka ya ɗakko wayarsa, ya kira me Adda  "Allah ya temaki Oga, in ba kai waza mu duƙawa muci?" Bulama yace "kai kana inane? Kana  cikin garin nan ne?" "A'a, na ɗan baza yin wata harƙalla, duk cikin iya taku da ɓoyewa masu saka na mujiya" "ina son ganinka a yau ba se gobe ba, a cikin daren yau nake so kaje ka ɗakkomin tsohuwar wancan sakaram yaron" Me Adda yace "sa hankalinka a inuwa, turo adreshinta, zamuyi ram da ita mu kawo maka" Bulama yace "Good, zan turo maka adreshin, a daren yau nake son a gama komai, ku ɗakkota ka kawomin ita" "An gama yallaɓai" me Adda yai maganar kamar yana maye. Likitoci suka yi iya abunda zasu iya akan Mahaifiyar Nurat, amma babu wani cigaba, ta gaza farfaɗowa gashi jini yaƙi tsayawa, numfashi kawai take amma sam zuciyarta bata harbawa yadda yakamata, tuni danginta da 'yan uwanta suka cika Asibitin, Alhaji Musa yayi mamakin yadda akayi suka ji, bayan shi dai be kira kowa ya gaya masa ba. Nan suka shiga tambayar ba'asi, akan yadda akayi' yar uwarsu ta faɗo daga kan bene? Alhaji Musa yace  "Wallahi ta fito ne daga ɗaƙi, zata sakko daga kan bene kawai ta zamo ta gangaro, dama tun safe take cemin tana jiri, nace mata ko  Asibiti zamuje tace in bari seda yamma, ina ga harda jirine ma ya ɗebe ta yasa ta faɗo" Barrister Khalil kallon Alhaji Musa kawai yake, ji yake tamkar ya danƙo wiyansa ya rufe shi da duka, dan sam beji ya gamsu da maganar da ya faɗa ba. Amal ta shirya tsaf, dan taje a zubar mata da ciji ba tare da mahaifiyarta ta san halin da take ciki ba, gaba ɗaya ta tattara ta zuba musu ido, dan itama fama take da kanta, ko gani bata iyayi sosai sedai dususu saboda tsabar ɓacin rai da damuwa da yake ta'azzara mata hawan jini, gaba ɗaya ta koma kamar wata zararriya, yauma ta tashi tana ta fama da kanta, jiri da ciwon kai jininta ya hau, tana kwance a falo tana fama da kanta, Amal tazo zata fice. "Amal ina Ramlah ne?" Amal tace "tana ɗakinta, inaga yauma tayi shaye2 tana can tana bacci" . Hajiya Halima tai ajiyar zuciya, tace "kekuma ina zaki? Naga kamar fita zakiyi" "Eh zan ɗan fitane, ba nisa zanyi ba" "Amma kina kallon yadda nake fama, ina kwance ina fama da kaina, amma zaki saka kai ki fice ki barni a haka?" Amal tace  "Mummy, na matsu in fitane ina da wani uzuri na gaggawa, ba daɗewa zanyi ba, ga Ramlah can kuma tana nan ai, ba daɗewa zanyi ba" Tai maganar tana tafiya, a haka harta bar falon ta fice abunta. Tana zaune a mota ta kira Alhaji Haruna, ya ɗaga ba tare da yasan wanda ya kira shi ba, "na gaya maka ina ɗauke da juna biyu, Amma kaƙi ɗaukar kowane mataki ko? To ka saurareni wallahi zan tona maka Asiri, duniya taji abunda ka aikata" "wai ke ni dan Allah ya kike son inyi ne? Har yanzu baki fanshe bane? Me kike so inyi miki?" 'haka ma zaka ce? To shikenan, ciki dai nakane, kai kayi shi, wallahi ba zanyi abun kunya ni kaɗai ba, na gaya maka' Ta ajiye wayar, tare da yin ajiyar zuciya, ta kunna motar ta ta fita. Suka yi waya da wannan Nurse ɗin, wadda tace zata taimaka mata ta zubar da cikin nan, ta gaya mata a dai dai inda zasu haɗu. Aikuwa tana zuwa suka haɗu, ta ɗau Nurse ɗin a motarta, ta fara nunawa Amal hanyar zuwa Gurin, Amal tace "nifa gaskiya tsoro nakeji, wallahi ji nake kamar wani abu ze faru" Nurse ɗin tace "haba ke kuwa, amma dai wannan ne karon farko da zakiyi abortion ko?" Amal ta jinjina kai alamar eh, Nurse ɗin tace "karki damu mana, ai ke naki cikinma ƙaramine, nan da nan za'a cire shi babu wani tashin hankali, ɗan pain ɗin kaɗanne, ke ciki koya kai 9 months Doctor Hamisu ze jajjageshi ya cire shi tsaf, dan haka ki kwantar da hankalinki, komai ze tafi normal" Sukaje Asibitin, Nurse ɗin ta jata har office ɗin doctor Hamisu, suka tarar yana aiki a system, Nurse ɗin ta gaisheshi tace  "Doctor, ga customer fa cikine take son a cire mata" Ya ɗago ya kalli Amal sannan yace "cikin wata nawane?" Amal tace "nima ban sani ba, amma naji da akamin test ance watansa ɗaya be cika biyu ba" Doctor Hamisu yace "ai wannan ba abun damuwa bane ba, za'a cire shi ba wata wahala, an gayamiki kuɗin aikin?" Tace "eh an gayamin, zanyi transfer ɗin kuɗin". Ya ɗago ya sake kallon ta yace "you look familiar to me, is like I know you somewhere" Amal tace "eh nima ina ganin kamar na sanka fa, kamar likitan dake duba Widad shekarun baya" Yace "exactly, that's where I know you, ya maman naki?" "tana lafiya ƙalau" "masha Allah, amma ya akayi ke kuwa wannan abun ya faru haka?" Amal ta ɗan ɓata fuska tace "wallahi wanine yamin Akuya, daga zuwa kai masa saƙo, shiyasa nake son inyi acire kafin ta gane" "ba matsala, karki damu kinji yanzu za'a cireshi insha Allah, Nurse maza kaita ɗakin da ake aiki ta kwanta ta jirani". Aka kai Amal ɗakin, ta kwanta tana jiransa, gabatan se faɗuwa yake, tana tunanin kar wani abu ya faru, bayan an cire cikin " Tana nan kwance, yazo ya ɗaura mata ruwa, ya bata wani magani ta sha, ko mintuna goma ba'ayi ba da saka mata ruwan, da bata maganin ta fara wani irin ciwon mara kamar zata mutu, ta dinga murƙususu, kafin kace meye wannan tuni jini ya fara malala daga jikinta, bayanta kamar ze ɓalle da ƙugunta, ta dinga antayar da jini, Nurse ɗin nan ta dinga temaka mata, yazo ya sake mata wasu allauran, yace "Sister, maza idan ta ɗan huta ki kaita gida ta samu rest, jinin ze tsaya insha Allah" Haka kuwa akayi, Ta kai Amal har gida, Amal ta shiga da motar, a dudduƙe ta tafi ɗakinta ba tare da kowa ya ganta ba, taje ta baje akan gadonta, dan wani irin sanyi take ji da jiri a lokaci ɗaya. Duk yadda Suleiman yaso ɓoyewa Umma yadda shari'ar Yusuf ta kaya seda taji a radio, kasancewarta mace ms son jin radio, da farko zamanta a gidan tare da Surayyah ta ɗanji daɗi, dan koba komai motsin mutum rahama ne, tana ɗebe mata kewa ita da yaran ta, kuma ta kan sakata a gaba lallai se taci Abinci, ta sha magani amma tunda taji hukuncin da akayiwa Yusuf ta kasa zaune ta kasa tsaye, se kuka nan da nan jikinta ya nemi ya rikice saboda tashin hankali da damuwa. Suleiman yaje ya sameta a ɗakin da take, yace "Umma, babu yadda za'ayi Yusuf yayi wannan shekarun haka a gidan yari, ai kowa yaga irin shari'ar da akai, ana nan ana wani ƙoƙari, sedai cikin sirri ake komai, ki kwantar da hankalinki, nina gayamiki da yardar ubangiji se Yusuf ya kuɓuta, amma kidena wannan kukan haka da damuwa dan Allah " Umma tace " Haba Suleiman, kaifa ka cemin duk wanda yai yunƙurin taimakonsa barazana ake masa, taya ya za'a samu wanda zasu taimaka masa alhalin kowa yana kallon yadda akai shari'ar, kuma babu wani taimako da aka masa? Ni na karaya kawai, haka Allah ya ƙaddara masa rayuwarsa, ƙaddara babi babi, daga wannan se waccan " tai maganar tana kuka me taɓa zuciya. Sulaiman yace" Umma, kece fa kike bani misali da Annabawan Allah, da irin jarabtar da Allah yayi masa, dan haka mu ɗauka jarrabawar sa ce a haka, kuma Allah yasa sanadin ɗaukakarsa ne yazo a haka, duk yadda Allah ya kai ga jarabtar bawansa, se kinga ta wani ɓangaren Allah ya masa wata ni'ima wadda ba kowa yayi wa ba, ki kwantar da hankinki Umma, shirye shirye sunyi nisa ta ƙarƙashin ƙasa, kuma insha Allah zamu bawa maƙiya kunya " Umma ta gyɗa kai tace " to Allah yasa" "Ameen ya Allah, ki cigaba da Addu'a Umma, ubangiji Allah ya bamu nasara" "Addu'a ina nan ina yi, Allah yayi maka albarka da kai da iyalanka, ubangiji Allah ya jiƙan magabatanka ya rahamshesu, ubangiji Allah ya raya maka zuriyar ka akan tafarki madaidaici, yasa su zamo masu jin ƙai kamar kai, Matarka Allah yayi mata albarka ya sake haɗa kanku, tunda abun nan ya samu ɗana kake tsaye a kaina, kana bani gudunmuwa iyayinka, kaine dana ganka nake jin daɗi, nake jin daɗin yadda kake tausata nagode nagode " Suleiman yace " bakomai umman Yusuf, karki damu duk yiwa kaine, ni ban rayu da mahaiyata ba, marayane ni tun ina yaro ƙarami, ina jinjina soyayyar uwa ga ɗanta, shiyasa nasan kina cikin damuwa rashin Yusuf da dole kina buƙatar a tausasa miki, ga Ɗanki mutum ne nagari kamili, wani abu da Yusuf ya taɓa yimin da bazan manta ba, lokacin mahaifina yana ciwon ajali sunje duba shi, baya iya cin Abinci sam, Yusuf ya kai masa dafaffen ƙwai da kayan marmari, naje siyo masa magani Yusuf ya zauna yana bashi ƙwan nan a baki, bayan ya gama bashi Baba yayi amai, ya ɓatawa Yusuf jiki, kayansa masu kyau a jikinsa suka ɓaci, amma be nuna damuwarsa ba ya ɗaga shi ya gyara masa jiki, kullum aka tashi daga gurin aiki se yaje ya duba mahaifina, har suyi hira, alhalin ni a lokacin ko kulani bayayi sosai, dukda ina shugabansa a gurin aiki, duk ranar da beje ba Baba ya dinga tambayar ina yaron nan me fararen idanuwa kuwa? Ranar da Baba ze bar duniya seda yayi masa addu'a sosai, bazan manta ba, naji daɗin yadda ya nuna damuwa akan mahaifina fiye da tunani, dukda wannan abun alkhairi da yayi min ba fiye shiga sabgata ba sedai in sha'anin aiki ya haɗamu, hakan ya tabattar min halinsa ne a haka, halin taimako da tausayi ga mutane, shiyasa bazan taɓa bari inga wani mummunan abu ya samu iyayen Yusuf ba" Umma tai ajiyar zuciya tace  "Kaga ni be taɓamin wannan hirar ba" Suleiman yace   "Ai Umma wannan ɗan naki halinsa se shi, miskiline ajin farko sedai akwai tausayi da jin ƙai, ni dai fatana kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki" (Wato shi alkhairi a rayuwa, idan har zaka aikata shi ko bayan ranka waninka ze mora, Kayi ƙoƙari kayi abunda mutane zasu dinga tunaka da alkhairin ka, ba da mugun aiki ba) Nan Sulaiman yaita kwantarwa da Umman Yusuf hankali, shida matarsa. Kamar yadda Bulama yai umarni, cikin dare su me Adda suka bazama gidansu Yusuf, inda suke kyautata zaton Umman Yusuf tana nan. Amal har dare yayi tana fama da matsanancin ciwon mara kamar zata yi hauka, gashi ta kasa cin komai, se uban amai da take faman yi, ga jini se zuba yake yaƙi tsayawa ita kaɗai a ɗaki babu wanda yasan halin da take ciki sam. Gaba ɗaya babu wanda hankalinsa ya kai kan cewar Nurat bata nan se bayan kwana ɗaya, tai ihun tayi bugun ƙofar babu wanda ya ji balle ya buɗe ta, gashi bata san halin da mahaifiyarta ke ciki ba, sakamakon taji ihutmnta amma bata da tabbas ɗin abunda ya faru da ita. Khalil ne ya kalli Alhaji Musa yace  "wai ina Nurat ne? Tunda mu kazo Asibitin nan ban ganta ba fa" Cikin inda inda Alhaji Musa yace "Amm da yake itama bata da lafiyar ne, ban san ya nata jikin ba, bana son hankalin ta ya tashi ne, bari inje gidan in taho da ita" Khalil yace "kace duk gidan ma basu da lafiya?" "wallahi kuwa, Nurat ɗince ma ta fara sannan uwar" "Amma an kaita Asibiti kuwa? Meke damun Nurat ɗin" . "A'a ba wani abu bane dama, dama nace zata koma karatu ne itakuma bata so, shiyasa take ta damun kanta dai, kusan damuwace ta saka take rashin lafiya"    "Amma meyasa baka ƙyaleta ba, tunda bata so ba? Ka takura se taje kaga gashi ta shiga wani hali" Maman Khalil tace "kai Khalil, wai nan a kotu muke ne? Jimin ja'irin yaro ka tasa mutum a gaba da tambayoyi". Khalil yace "Allah ya bada haƙuri, muje semu taho nida Nurat ɗin kai seka huta kawai". Alhaji Musa yace "No, bakomai ai ka bari zan kawota da kaina" Maman Khalil tace "kuje tare mana, ai bakomai se su taho taho shida ita" Khalil ya saka Alhaji Musa a gaba, da wani irin kallo wanda ya kasa tantance na menene. Haka suka tafi kowa a motar Alhaji Musa, koda sukaje gidan Alhaji Musa yace "bari in kirata tana saman bene" Khalil yace "shikenan babu laifi, bari in jira a nan" ya zauna a falo. Alhaji Musa ya hau sama da sauri, danshi gaba ɗaya ya manta daya kulle Nurat a ɗaki, yana zuwa ya buɗe ya tarar da ita a baje a sume a ɗakin, a gigice ya ƙarasa yana kiran sunanta amma bata motsi, da sauri ya ɗakkota ya sakko daga benen, hannunsa riƙe da ita. Khalil ya miƙe tsaye yace "lafiya kuwa?" Alhaji Musa yace "a sume na tarar da ita" Basu tsaya ba sukayi waje gurin mota, aka saka Nurat a ciki suka nufi Asibiti cikin gaggawa. Itama a emergency ɗin aka karɓeta, aka rufu akanta don ceto rayuwarta itama, rufetan da yayi dama bata karya ba, ga kuka ga damuwa ga tashin hankalin da ta shiga jin ihun mahaifiyarta, hakan yasa ta shiga tashin hankali, garin kuka tai shaƙuwa numfashinta ya sarƙe ta faɗi, ga yunwa dan haka abun ya tarar mata, daya buɗe ɗakinma ya ɗakkota numfashinta iya ƙirjinta ne kawai, babu inda yake motsi a jikinta. Alhaji Musa ya koma reception ya zauna ya dafe kai, yana tunanin wannan wace irin masifa ce haka kashi kashi? Ze kashe iyalansa ɗaya bayan ɗaya da kansa, da hannunsa duk a dalilin aikin banza, dalilin neman kare a Karofi, Bulama nata musu gafara sa amma babu ƙaho tsayin shekaru. Bulama yana ta jiran yaji su me Adda sun bashi feedback akan aikin daya sa kasu, amma shiru ba suyi magana ba, ya kira layin me Adda babu adadi amma tun tana shiga ta dawo bata shiga, sema ace masa line busy, daga ƙarshema aka kashe wayar gaba ɗaya. Alhaji Musa yana nan zaune, aka kira shi a waya aka sanar masa da an gano inda Anwar yake, yayiwa Bulama magana, akan me yakamata ayi? An kira wayarsa bata shiga se ace busy. Kamar ya share ya basar, amma dai ya kira Bulama, Bulama ya ɗaga yace "ya naji muryarka a hakane? Baka da lafiya ne?" "A'a lafiyata ƙalau, amma ina Asibiti" "me kake a Asibiti kuma?" "Wallahi abubuwa sun damalmalemin gaba ɗaya, bisa tsautsayi daga zan ture Maman Nurat daga bene in sakko, bisa tsautsayi ta faɗo kwananta biyu a Asibiti har yanzu bata hayyacinta, na rufe Nurat a ɗaki saboda ta gano halin da ake ciki, ta gano da saka hannuna a abunda ke faruwa a gidan Daula, itama gata can a emergency bata san wake kanta ba, gaba ɗaya na rasa abunyi ma" Maimakon Bulama ya tausayawa Alhaji Musa halin da yake ciki, seya haushi da faɗa  "wai kai wand irin mutum ne haka Musa? Ya za'ayi kabari yarinyar ka ta gano? Gaskiya baze yuwu ba sam, wancan karon dana maka magana ashe baka ɗau mataki ba? To dole kasan yadda zakayi tun wuri dole a ɗau matakin daya dace akanta, bazs yuwu ta tona mana Asiri ba" Ran Alhaji Musa yai matuƙar ɓaci da jin Kalaman Bulama, bs tausaya masa halin dayake ciki ba, amma ya haushi da faɗa, dan haka a hasale yace  "kaga ya isa  naji, ance in gaya maka an gano inda Anwar yake, ɗan gidan Hajiya Halima" Bulama yace 'to me kace musu? " " me kuwa zance musu? Umarninka suke jira" "Aina riga na gama bada umarni, a kasheshi kawai dan baze yuwu a ƙyaleshi ba" Alhaji Musa yace "seka kirasu ka gaya musu, ni yanzu ina cikin wata matsalar ne" Yana gama faɗin hakan ya katse kiran, tunani ya fara yi, Hajiya Halima tana da Alaƙa da Bulama 'ya' yanta kamar nasane, amma yace a kashe ɗanta dan kar Asirinsa ya tonu, dan haka babu shakka idan ya gama da Anwar kan Nurat ze dawo. Ai nan da nan ya ɗau wayarsa ya kira Hajiya Halima, ta ɗaga wayar da ƙyar alamar tana jin jiki, tai sallama a hankali Alhaji Musa yace "malama idan zaki ware muryar ki ki ware, an gano inda ɗanki yake Anwar, amma Bulama yace A kasheshi dan karya tona masa Asiri.... AMANA! AMANA!! AMANACE!!! AYSHERCOOL 07063065680 12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" _(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_) IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _ Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)       Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji   Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219 Chat 08063114606 144_145 Ai zumbur ta miƙe zaune tace "ban gane a kasheshi ba? Anwar ɗin nawa za'a kashe? Me yayi masa haka?" Alhaji Musa yace "ke nifa tuni na dawo daga rakiyar mutumin nan, Azzalumi ne kawai, kansa ya sani bashi da imani sam, ni kaina yanzu haka muna Asibiti nida su Nurat, amma gaba ɗaya ko yamin jaje se masifa da tashin hankali da yake min, shiyasa na kwashi kuɗina na saka a siyasa, in samu su bani takara in huta da wannan mulkin mallakar da yake mana, ga uwar dukiyarmu da muke narkawa amma har ynzu babu wani bayani " Hajiya Halima ta fashe da kuka tace " ni Bulama zeyi wa haka? Anwar kamar ɗa yake a gurinsa amma shine zece a kashemin shi? Baze yuwu ba kuwa " Ta ajiye wayar, ta miƙe ta shiga ɗakinta ta zura doguwar riga, kusan ƙarfe goma saura na dare, amma tayi waje ta ɗau mota ta fita ta tafi gidan Bulama a daren. Shikuma Bulama yana zaune yana ta nazari akan yadda ze ɓullowa al'amura da suke neman damalmale masa, ya dinga kiran layin su Me Adda amma shiru babu Labari, waya taƙi shiga sam. Masu gadi kansu sunyi mamakin ganinta a wannan daren, kamar wata mahaukaciya ko gabanta bata gani sosai saboda tashin hankali, kai tsaye ya shiga falon dake ƙasa tana bala'i  "Ina Bulama yake? Ina Bulaman?" Iman ce zaune a falon tana kallon zee world tace "Mummy lafiya kuwa?" "ban sani ba, ina uban naku yake tsohon macuci azzalumi?" Iman ta kalleta da mamaki jin irin furcin da take akan mahaifinsu wanda ya kasance ɗan uwa a gareta, Iman tace "Mummy ya riga ya hau sama, inaga ma ya kwanta fa" Ai bata tsaya jiran me Imana zata kuma ce mata ba ta haura saman da kanta, ba zato ba tsammani ya ɗaga kai yaci karo da Hajiya Halima a tsaye a kansa. Ya kalleta yace "Halima, lafiya kuwa zaki zo a daren nan? Bakya jira ayi miki iso kawai ki hauromin ɗaki haka?" "Dalla rufemin baki, me zaka gayamin har wani iso zan jira ayimin, munafuki azzalumin banza dana wofi, tsawon shekaru ina maka aiki, kana sani duk abunda kaga dama ina maka, dan ka cinma burinka ba tare da na nuna gazawata ba, shine halin naka na baƙin kumurci zaka gwadamin, shine kayi umarni da idan anga Anwar a kasheshi, ɗan nawa za'a kashe? Wallahi baka da imani ba kada Alƙawari tun wuri ka dakatar da wannan maganar idan ba haka ba Wallahi ran ɗana baze tafi a banza ba" Zazzaro ido Bulama yayi ya dinga ƙifta mata ido akan tayi shiru, amma tace "bazan shirun ba, wallahi babu inda zani se an dawo min da ɗana" "Halima wai wace irin magana kike hakane? Kamar yaya nace idan anga Anwar a kasheshi? Me Anwar yayi min wanda zesa ince a kashe shi, ni da na kaiwa jam'ian tsaro maganar dan ayi bincike akansa a gano inda yake ya zakice nace a kasheshi? Wani munafukin ne ke neman haɗani da 'yar uwata?" " Kaga bana son kame kame da ƙaryar banza, wanda ya gayamin baze maka ƙarya ba, macucin banza da na wofi kuma wallahi idan ɗana ya mutu you must pay for it, wallahi aka kashemin Anwar seka fanshi ransa, nima kasan halina ka san abunda zan iya aikatawa " Gaba ɗaya Bulama ya dirirce ya rasa abunyi, ya shiga tsuma yana fatan Allah yasa wani beji abunda ta faɗa ba. Ya biyo bayanta ya leƙa, yaga ba kowa a falon ƙasa dukda ɗakin a rufe yake babu wanda ze iya jiyo me sukayi, ya koma bedroom ɗinsa ya tarar da Hajiya Sarah tana ta baccinta hankali kwance, yai ajiyar zuciya tare da tunanin bata jiba, amma ya zauna yai shiru akan gadon yana tunani, tabbas babu wanda ze gayawa Halima wannan maganar idan ba Alhaji Musa ba, tabbas dole yayi maganin Alhaji Musa. Cikinsa ne ya murɗa ya tashi ya tafi banɗaki, kusan kwana huɗu kenan yana fama da gudawa taƙi tsayawa, dan haka ya sa ransa idan ya gama da wannan matter ɗin zeja yaga likita. Yusuf se sake juya takaddar nan yake, yana tunanin wani hali Widad ɗin ke ciki, tabbas yasan da  tana da dama bazata barshi a gurin nan ba, dole akwai wani abu da yake gudana a ɓoye, idan ya kalli sentence ɗinta na ƙarshe na ba lallai su sake haɗuwa ba se yaji gabansa ya faɗi, lallai ko a ina take tana cikin mawuyacin hali, "Allah ya ƙara haɗa fuskokinmu my wife, Allah yasa kina hannu na gari, i love you too" yai maganar a hankali tare da lumshe idonsa. Rayuwar da suka yi tare a ƙauye ta dinga dawo masa, koba komai zamansa da ita ba ƙaramin farinciki ya samu ba, zamansu a ƙauye yasa Ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ta samu hutu na wani ɗan lokaci, ya daɗe beji cin zarafi da gorin rashin iyaye daga mutane ba, sedai matukar kewar Ummansa da yayi, be sake zaton ze samu wadda zata aureshi ba saboda rashin nasaba ba, sedai cikin hukuncin Allah ya auri yarinyar da zuciyarsa ta mato a sonta, dukda nisa da ratar dake tsakanin su, yarinyar da manyan wanda suka isa ma basa gabanta, soyayyar ma bata yadda da ita ba, amma Allah ya ƙaddara Aurensu, har suka yi zama cikin farin ciki, ya dinga tuna irin Shagwaɓarta wauta da yarinta wasu lokutan, ya tuna lokacin da take koyar tankaɗe, da sanda take wa Abincin garin kallon banza, da yadda ta dage ita seta samu ciki, da irin kallon da take masa idan ya tsokane ta. A hankali ya sake lumshe ido yana murmushi, sekuma ya tuna yadda ta shiga damuwa daya bata labarinsa, da yadda ta dinga kururuwa tana kuka tana gaya masa tana sonsa lokacin da aka kama shi a garin, da yadda taje kotu ta bada sheda akansa, ga shekarun da aka yanke masa a gidan yari, ga abunda ta rubuta masa kawai se yaji ya karaya hawaye ya shiga bin gefen idonsa, baya tunanin ze sake wata rayuwa me daɗi a nan gaba, mussman kasancewa da Widad a inuwar Aure. Da ƙyar likitoci suka samu Nurat ta dawo hayyacinta ta samu bacci, aka sa mata ruwa, sedai harta farfaɗo ɗin numfashinta da vital signs ɗinta suka daidaita bata gane mutane sosai, saboda ta galabaita an samu dai bacci ya ɗauketa cike da fatan idan ta tashi zata iya dawowa hayyacinta gaba ɗaya, mahaifiyarta kuwa gaba ɗaya har yanzu ba'a gano kanta ba, tana kwance ne kawai, numfashi ne kawai a ƙijinta, banda haka babu abunda yake aiki a jikinta, sam bata san abunda ke faruwa ba, shi kansa numfashin nata da ƙyar take yinsa wasu lokutan, saboda ta zubar da jini sosai, kuma ana kyautata zaton ta samu rauni a cikin kanta, sakamakon buguwa da tayi, likitoci sun rubuta mata hoton Ƙwaƙwalwa dan tabattar da abunda yake damunta. Abu kamar wasa, jini yaƙi tsayawa Amal, se aikin zaryar banɗaki take, jini se zuba yake babu ƙaƙƙautawa, ta rarrafa ta haɗa Abinci tana ci kota samu sauƙin wannan wahalar haka, zuciyarta tana ƙuna akan yadda Alhaji Haruna ya cuce ta, Hajiya Halima ta fito falon ta zauna ta dafe kai ta kalli Amal tace "wai kuwa lafiyarki ƙalau kuwa? Gaba ɗaya kin wani ɗashe kinyi fari ƙal, kamar baki da jini a jiki, ko baki da lafiya ne?" Amal tace "lafiyata ƙalau, period kawai nake shiyasa" Hajiya Halima tai ajiyar zuciya tace "Amal kin kuwa san abunda Bulama yaimin?" "A'a sekin faɗa" "wai an gano inda Anwar yake, amma yace wai a kasheshi saboda karya tona Asiri" Da sauri Amal ta kalleta tace "A kasheshi kuma? Me me kikace masa?" "Naje har gidansa jiya da daddare, na ƙare masa tatas, nace wallahi aka kashe min ɗana seya fanshi ransa da nasa ran kona 'ya' yansa" Amal tabi mahaifiyarsu da kallo, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, duk mahaifiyarsu ta ɗaiɗaita rayuwarsu da kanta, kowa yana karɓar nasa kason ɗaya bayan ɗaya. Ramlah ce ta fito tana tangaɗi, tana magana cike da maye ta tsaya a tsakiyar falon tace  "Wai ni.... Waini Fahad baze Aureni bane... Bazaki ce ya aureni ba ko? Wa.. W.. Wallahi kuwa bazan dena shaye2 ba tunda ya lalatani, ku.... Kuma... Kumaaa ai shikenan tunda nasan Na sakawa Bulama cutar tunda shima ya sakamin... Wallahi idan baka Aureni ba sena sakawa Wannan yaron Ramadan ma, idan yaso kow... Ko..... Kowama ya samu ni za'ayiwa hauka? Ya.. Ya ɗauka bani da wayo hmm baka san Rmalha bane"  kawai ta faɗi a gurin tana juyi tana ci gaba da sambatu marasa kan gado sam. Hajiya Halima ta kalleta tace "Ramlah wai wace cutar kike magana akai ne? Wace irin cuta?" Ramlah bata san me take ba, juyi kawai take yi tana wasu surutan irin na marasa kan gado, Amal kam tasan babu mamaki idan akace Fahad yana ɗauke da wannan cutar me karya garkuwar jiki, amma sedai dagaske Ramlah take tana mu'amala da Bulama ma kenan, gaban Amal ne ya faɗi kardai ace itama tana da wannan cutar, miƙewa tayi da sauri zata tafi ɗakinta, Hajiya Halima tace  "Amal ina zaki? Kina jin maganar da gake faɗa? Ko dai duk a cikin maye take ne?" Amal tace "tunda ki kaji ta faɗa a maye, to ko ba'a mayen bama ya faru, sedai fatan Allah ya kyauta" Amal ta tafi ɗakinta, dan itama fama take da kanta, wannan azabar ciwon marar da zubar jinin sun isheta haka. Anty Saddiƙa ƙanwar Maman Nurat itace a gurin Nurat, itakuma maman Nurat ba'a barin kowa ya shiga inda take in ba likitoci ba, saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman, Anty Saddiƙa taje salla Khalil na zaune a gurin Nurat, ai kuwa ta farka ta zaci zata ganta a ɗakin Dad ɗinta ya kulle ta, sedai tana buɗe ido tai arba da wani gurin daban, ta yunƙura zata tashi zaune, Khalil ya taho da sauri ya riƙeta yace  "yi haƙuri, ki kwanta kinji, karki gaggawa jikinki babu ƙwari" A Shagwaɓe Nurat tace  "Brother ruwa zan sha" Yace "ok bari in baki" Ya ɗakko ruwam roba, ya buɗe ya bata ta sha, har ze gyara mata kwanciyarta ta kwanta, ta riƙe shi gam tana kallonsa, tana ƙoƙarin tuna meyafaru ihun Mummynta ta tuna, nan da nan ta razana tace masa "Mummy, Khalil Mummy na tana ina?" Khalil yace "kwantar da hankalinki tana nan lafiya" "A'a ban yadda ba, naji ihunta fa ranar, ban san meye ya sameta ba, tunda Daddy ya kulleni ban sake ganinta ba, waini ya akayi ma nazo nan ne?" Khalil ya kalleta yace "kamar yaya ya kulle ki? Ya kulleki a ina?" Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta gaya masa, yai shiru yana nazarin maganganun Nurat, cikin kuka tace  "ina Mummy take? Dan Allah ka kaini in ganta dan Allah" Khalil yace "ki kwantar da hankalinki, likitoci na can na kula da ita, idan ta farka zata zo ki ganta" "to wai meyasa meta ne?" "Bakomai, ta faɗi ne kawai saboda Dad ɗinki ya rufeki, bari Anty Saddiƙa tazo ta temaka miki kiyi wanka" Bayan Saddiƙa ta shigone, Khalil ya tashi ya fita, a reception yaje ya samu Alhaji Musa a zaune, dan idan yazo Asibitin ya duba su Nurat nan yake dawowa ya zauna, dan gaba ɗaya haushinsa suke ji. Ya zauna kusa da Alhaji Musa ya kalle shi yace  "garin yaya ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene?" Alhaji Musa yace  "wace irin magana ce wannan? Ba a gabanka nayi wannan bayanin ba?" Khalil ya kalle shi yace  "to ya akayi ka kulle Nurat? Laifin me tayi maka" Da sauri Alhaji Musa yace  "tana ina? Nurat ɗin ta farkane?" Yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma Khalil ya tareshi yace "na tambayeka kana ƙoƙarin tashi ina zaka?" Yace  "wai ita Nurat ɗince tace maka kulleta nayi?" Khalil yace "labari na samu, daga majiya me ƙarfin gaske, dan haka nake tambayarka garin yaya ka kulleta" "wai Khalil yaushe ka koma haka? Yaushe ka koma mara kunyane?" "ba rashin kunya bane, gaskiya ce dama ina da ayar tambaya akanka, wallahi muddin na ganoka da wani abu ba dai dai ba, naga wani abun kayiwa ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene, wallahi se nayi shari'a da kai, yanzun ma ba ƙyaleka zan ba, dan ba ƙaramin haushinka nakeji ba" Alhaji Musa zeyi magana, amma Khalil ya dakatar dashi yace "ba abunda zaka gayamin, bana buƙatar jin komai daga gareka, amma tabbas ina nan ina bincike akanka, kuma wallahi ina daf da tsayawa a kotu a gaban alƙali da kai" "Da nayi maka me?" "in mun haɗu a kotu kaji" Ya miƙe ya bar gurin, Alhaji Musa ya bi shi da kallo, yana tunanin me Khalil yake nufine? Bayan Ramlah ta tashi daga mayen da take ne, Hajiya Halima tazo ta sata a gaba tana tambayarta   "Ramlah wata magana naji kina yi ɗazu cikin maye, wai Fahad yasa miki cuta, kekuma kin sakawa Bulama, wacce magana ce haka?" Ramlah tace  "Eh to, dukda kince a maye nayi maganar kamar yadda kiji maganar haka take, Bulama shiya fara lalatamin rayuwa ta, na kamu da son ɗansa wanda hakan yasa na biye masa, sedai Bulama yaƙi goyon bayan ya aureni, yake ta cusa masa 'yar Daula ya aura saboda ya cika burinsa, soyayyar da nakewa ɗansa tasa na dinga biye masa ya koyamin shaye2, ya koyamin rayuwar banza nida shi ba abunda bama yi, nace ya Aureni amma yaƙi, kuma na gano yana da cuta me karya garkuwar jiki, dan haka na ƙuduri aniyar ramawa na komawa mahaifinsa, kuma da yake ɗan Akuyane ya karɓeni, ba tare da yasan ina mu'amala da ɗansa ba, dan haka shima ya kwasa, zuwa yanzu nasan uwarsa ma ta ɗauka, hakan yasa na ɗan rage abunda ke zuciyata gara muyi jinyar tare hadda ubansa" Hajiya Halima ta ɗora hannu a ka tace "yanzu Ramlah abunda kikayi kenan? Ramlah gaba ɗaya kika biyewa namiji kika barbaɗar da rayuwarki da mutuncinki? Kin kyautawa kanki kenan?" Ramlah tace "Mummy, bafa laifina bane wannan lamarin, duk wanda yazo neman Aurena se ki nunamin ai shi ba sa'an aurena bane, ina gidan Attajiri kamar Daula bekamata in Auri wane ba, ƙarewa ɗan uwanki ya biyoni ya lalata, na kamu da son ɗansa amma yai biris dani, kuma akan idinki nake fita ai, kin taɓa tuhumata ina muke zuwa nida Fahad idan mun fita? Me yasa? saboda idonki ya rufe ke burinki ya kawo miki masu siyan kadarori ki tara kuɗi, don't blame me for this please " Ta tashi tai tafiyar ta ɗaki ta bar mata falon, Hajiya Halima ta dafe kai ta fashe da kuka, Bulama ya riga ya gama cutarta a rayuwa, ba ta san mema za tace a game da shi ba, ya lalata mata rayuwar 'ya, kuma wai yanzu Ramlah na ɗuke da cuta me karya garkuwar jiki, wanda ta samune a sanadin ɗansa, kuma ya dawo yace a kashe mata ɗa, ta rushe da kuka harda sheshsheƙa, gaba ɗaya komai ya rikice mata, tama rasa meye abunyi, wannan wace irin masiface haka take bibiyar ta? Daga wannan se waccan gaba ɗaya 'ya' yanta sun barbaɗe, haka ta dinga gunjin kuka ita ɗaya a falo, Amal ta ƙarawa ƙofar ɗakinta key, dan bata son tashin hankali. Da safe Fahad ya shiga cikin gida, domin gaida iyayensa, sedai yan zaune a falon Iman nata masa surutu amma sam hankalinsa baya kanta, yayi zurfi a tunani can ya ɗago kai yace "ke wai ina Mummy ne?" Iman tace "tana sama ɗakin Daddy" Ji yayi kamar ta watsa masa wuta, ta ina ze fara gayamata hakinda ake ciki? Koma ya gayamata ai yasan aikin gama ya riga ya gana zuwa yanzu. Yana nan zaune Sega Bulama yana Sakkowa, hannunsa ɗauke da jakarsa, Mummy sanye da doguwar rigar baccinta, ta riƙo masa wayarsa suna hira, Fahad yaji kamar yaje ya make Bulama saboda tsabar baƙin ciki da takaici, ga wani irin tausayin mahaifiyarsa ya kama shi. Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace  "yau Allah ya nufe ka da shigowa cikin gidan kenan? Yaushe rabonka da shigowa" Bulama yace "wai gidan ubanwa kake shigewa ne? Ko haryanzu yawon kake baka kwana a gida?" ga mamakinsa seya ga Fahad ya maka masa wata uwar harara, abun da be taɓa yi masa ba, ya kalli mahaifiyarsa yace  "Mummy ina kwana?" "Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?" "Lafiya ƙalau, dama na shigo mu gaisa ne zan karya" Tace "shi Daddyn naka bazaka gaishe shi ba?" "Ai na gama gaidashi, ni da sake gaisheshi har abada" Kallonsa sukayi gaba ɗaya, Hajiya Sarah tace  "Fahad, daga kan kayan shaye2 naka ka taso ka shigomin falo ko? Shine har kake gayawa mahaifinka wannan maganar?" Alhaji Bukar yace "ƙyaleshi, ina daf da maganinsa akan wannan mummunar ɗabi'a ta shaye2, dank yake zancen, ban agogona zan fita ina da ayyuka da yawa a Office " Yasa hannu ya karɓi agogonsa, yai waje bayan fitarsa Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace " Fahad, meyasa ka gayawa mahaifinka wannan maganar haka? Kai lalacewar taka harta kai kayiaa mahaifinka haka? Me yayi maka? " Yace " bakomai " " Bakomai amma ka faɗa masa wannan maganar? Abunda kayi ya dace kenan?" Ya girgiza kai alamar a'a "to meyasa kayi, salon mutane suji suce ni nake saku a turbar banza, na ku Wulaƙanta mahaifinku?" "Nifa Mummy bakomai, kema da kin san me yayi da baki faɗi wannan maganar ba, kawai dai Allah ya kyauta" Ya mike a fusace ya baf falon, tabi bayansa da kallo, Iman tace  "Mummy" "Na'am" "wai kuwa idonki biyu, jiya da Maman su Amal tazo gidan nan?" "haba dai? Gidan nan tazo? Ai ban sani ba" Iman tace "wallahi tazo, bayan ƙarfe goma se bala'i take tana neman Daddy" "subhanallah, Allah yasa ba'a akan Ramlah tazo ba, saboda kin san halin ɗan uwanku sarai, ina kyautata zaton akwai alaƙar banza a tsakanin sa da Ramlah" . "Mummy ya akayi kika sani?" "last week na ganta ta fito daga sashinsa, na tambaye ta amma bata gayamin komai ba, sema baƙar magana da tayi min" Iman tace "Umma kiyi ta haƙuri, Yaya Fahad se Addu'a gaba ɗaya zamansa a ƙasar waje ba abunda yasa masa se koyar mugayen halaye" Hajiya Sarah tace  "idan da zaman ƙasar waje dai to harda halinsa, meyasa shi Anwar be lalace ba se shi? Bani da abunyi se dai yi masa addu'a, baya jin faɗa baya jin rarrashi, babu wanda banyi ba, amma duk baya ɗauka" "Mummy kiyi haƙuri, wataran se labari ze dena insha Allah" "Mhmm Iman kenan, yaushene watarn ɗin? Mutum ya girma amma kullum ba hankali, Allah ya kyauta dai kawai". Yanzu ma Bulama yana zaune a Office, kiran wayar Me Adda kawai yaje amma taƙi shiga, yai shiru can wayar ta fara ringing, cikin hanzari ya ɗauka ya zata me Adda ne, sedai yaga baƙuwar lambace, ya ɗaga yai sallama "justice A dutse ne ke magana ' Bulama yace " ok nagane, ya kake ya aiki? " " Alhamdilillah, dama na bugo in sanar makane da cewar tawagar lawyoyi da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ɗaukaka ƙarar shari'ar Yusuf da nayi, kuma ina kyautata zaton ƙarƙashin jagorancin shahararren lawayrn nan ɗan gwagwarmaya wato Barrister Adam A Adam, dan haka tun wuri kasan abunyi!!! (Alhamdilillah masha Allah, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, da addu'oinku da na samu bisa rashin da akayi mana, nagode sosai Allah ya bar zumunci) AMANA! AMANA! AMANACE!!! AYSHERCOOL 07063065680 12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" _(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_) IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _ 146_147 Cikin Bulama yai wata irin ƙara yace  "A dutse garin yaya haka ta faru? Ina tarin kuɗin dana baka kaida lawyoyi, ya za'amin haka?" 'Aini kuɗin daka bani, nayi aikin daya dace da su, na rufe yaron nam amma doka ta bashi damar ɗaukaka ƙara, kuma ya ɗaukaka ni yanzu shawara ɗaya zan baka, karka sake a gane kana da hannu cikin wannan badaƙala dake faruwa, idan da hali ma ka halarci zaman kotu da za'ayi, karka bari wani ya gane da saka hannunka" Bulama yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, ko dai ƙasar zan bari gaba ɗaya ne? ' " baza' a gane da saka hannunka ba, tunda manyan ƙasar nan da 'aya siyasa dama jam'ian tsaro suna tare da kai, karkaji komai I will give you the necessary support i can, ka kwantar da hankalinka fa" Bulama kawai ya ajiye wayar, ya dafe kansa Fahad ne ya bankaɗo office ɗin kamar wanda aka jefo, Bulama ya ɗaga kai ya kalleshi, ya mayar ya sunkuyar, Fahad ya ƙaraso gabansa ya tsaya yace "wallahi Daddy ka bani kunya, ka zubar mana da mutunci a idom duniya, ka cucemu ka zaluncemu kuma se Allah ya sakawa Mummy" Kasa vane inda maganganun Fahad ɗin suka dosa yayi, dan haka yace "kai me kame faɗane haka? Meye hakan?" "dole ka tambayeni mana, dama Daddy kana alaƙar banza tsakaninka da Ramlah?" "kai wace irin maganar banzace wannan? Ƙwayar taka bata sakeka a gidan ba shine ka biyoni har nan za kamin hauka? Wacece kuma Ramlah" Cikin shouting Fahad yace "niba hauka nake ba, dagaske nake, akwai haramtacciyar alaƙa a tsakaninka da Fahad, kuma Asirinka ya tonu" "wane banzan ne ya gaya maka wannan maganar banzar, mara tushe balle makama? Waye wannan waima wace Ramlah kake nufi ne?" "Ramlah dai, 'yar gidan Hajiya Halima kumabita ta gayamin, da bakinta ta gayamin" A fusace Bulama yace "zaka fitarmin daga Office ko sena ci ubanka na tattaka ka, dama akan tsini nake, saboda mahaukaci ne kai kamar ni, ni zan nemi wannan yarinyar? Inyi uwarme da ita? Fitarmin daga Office kobin saka security su casamin kai, kai ko kunya bakajiba, ina ubanka ka tunkareni da wannan maganar ba kai ba ma'ana, kai data gayamaka meyasa baka yi bincike a kai ba? Kawai ta gayamaka maganar banza ka hau kai ka yadda, fitarmin daga Office shashasha kawai " Sekuma Jikin Fahad yai sanyi, dan ƙarya batawa Ramlab wahala, a ransa ya dinga fatan Allah yasa ƙarya takeyi, yana fita Bulama ya share gumi ya zauna yace " Jimin tsinanniyar yarinya, ni zata kwaɓawa aiki haka? Waini garin yaya abubuwa suke ta cakuɗewa ne babu mafita sam a cikin lamuran, daga wannan se wancan? Kai baze yuwu ba da sake gaskiya" Mahaifiyar Nurat fa babu sauƙi a lamarin nata, dan a kwanaki ukun nan ko yatsan ƙafarta bata motsa ba, yadda take a kwance a haka take, sedai a juya ta nan a juyata can, babu wani cigaba kuma a wannan kwanaki ukun still, lokaci lokaci jini na fita ta hancinta da bakinta.      Nurat ta ɗaga hankalinta akan san sanin Halinda mahaifiyarat ke ciki, amma se dai ace mata tana ƙarƙashin kulawa ta musamman ta likitoci, dan haka bazata ganta ba, Bata da aiki se kuka, danta fara zargin ko ta mutune ake ɓoye mata, Khalil neke aikin rarrashi kullum cikin rarrashinta yake akan ta kwantar da hankalinta, Mum ɗinta zata tashi zata warke da yardar Allah. Sam bata son ganin mahaifinta yazo inda take, data ganshi se taji ranta babu daɗi, mussman idan ta tuna irin muguntarsa da zalumcinsa, da rashin afuwarsa. Bulama mussman ya shirya ya tafi gidan Justice A dutse da yamma, lokacin yasan ya dawo daga gurin aiki. Bulama yace "Nifa A dutse na kasa gane bayanin ka, ji naifa kace wai harda wannan barrister me shegen bakin tsiya za'ayi shari'ar nan, yanzu meye abunyi kenan?" A dutse yace  "eh to, kaga dai ko ana hauka kasan A Adam baze karɓi bribe ba, ni dai shawarata da kai shine karka yi wani Yunƙuri da zesa a ganoka, dan ba kaiba harni zamu shiga cikin matsala, saboda irin shari'ar da nayi, musamman idan aka gano na karɓi cin hanci daga hannuka, abun baze mana kyau ba" Bulama ya dafe kai yace "yanzu shikenan, babu wata mafita kenan?" "Karfa ka damu, ka kwantar da hankalinka ai su Barrister Sadik suna nan, za suyi iya yinsu akan shari'ar, suma jajirtaccune karka damu koka ɗaga hankalinka, babu abunda ze faru fa" Bulama yace "to shikenan, dan Allah idan da wani information ka dinga sanar dani" A Dutse yace "Insha Allah, kar kaji komai, ba zasu yi Nasara ba" Fahad kuwa yana zuwa gida, ya ɗau waya ya kira Ramlah, yana kira ta ɗaga. Aikuwa tana ɗagawa yace  "munafukar banza da ta wofi, ashe ƙarya kikewa Mahaifina zaki haɗani faɗa da ubana, mara mutunci ƙaramar karuwa" "Lallai Fahad, Bulama ya maida kai gaula, gashi ka ka raineni ka bani training a harkar karuwanci, amma kuma na shallake tunanink, dan na kai inda baka kaiba, to idan uban naka ya isa, ya kirani a waya a gabanka yace ƙaryane abunda na faɗa mana, ko kuma yaje a binciki lafiyarsa ko yazo har gida ya sameni yace ƙarya nayi mana, ai baka isa ka cuceni a banza ba, gidanku ma kun ƙara yawa masu ciwon, seku dage da shan magani tare " Ta katse kiran wayar gaba ɗaya, Fahad ya jinjina kai tabbas tunda ta dage babu ko shakka mahaifinsa ya aikata abin da Ramlah ta faɗa, kuma da wuya idan ba'a sameshi da cita me karya garkuwar jiki ba, dan tunda ya iya neman Ramlah to yana biye biyen mata. A hankali ya furta wayyo Allah Mummyna, ya nufi gida da sauri, yana zuwa ya tarar da mahaifiyarsu Hajiya Sarah ta shirya ta sha gayu zata fita, dama gata mace me iyayi da son kwalliya. Ya ƙura mata ido, yana jin tausayinta a ransa, "kai lafiya kuwa? Wannan kallon ƙurillar da kakemin fa? ' Fahad yai murmushin ƙarfin hali yace" kyau kikamin Mummy " Tai murmushi tace "Allah ya shiryeka, sarkin zolaya" Tai maganar tare da murmushi, ta shige motarta taja ta fita. Jiki a sanyaye Fahad ya tafi part ɗinsa, yana zuwa ɗakinsa ya zube akan akan gadonsa yana rusa kuka kamar ransa ze fita  "wayyo Allah na, kaicona da irin wannan rayuwar da nayi, a sanadina rayuwar mahaifiyata zata shiga garari, Daddy bakamana Adalci ba, wayyo Allah kaicona" Jin hargowar kukan Fahad ne yasa Ramadan farkawa daga bacccin da yake yi, ya fito daga ɗakinsa ya shiga ɗakin Fahad, ya tarar da shi a zaune zaman dirshen yana ta gursheƙen kuka. Jiki a sanyaye Ramadan yace  "Fahad lafiya kuwa? Waye ya mutu?" Fahad ya ɗago ya kalli Ramadan, ya goge hawayensa tare da daidaita nutsuwarsa yace  "ba kowa" "Amma kake wannan kukan? Idan ba mutuwa akayi ba meyafaru? Kukan kane fa ya tasheni daga bacci" Fahad ya share hawayensa yace  "Ramadan Daddy be mana adalci ba, wai ashe Daddy yana da mummunar alaƙa tsakaninsa da Ramlah" Ramadan yace "wace Ramlan?" "Ramlah dai, Ƙanwar Anwar" Ramadan yace "subhanallah, wai kana nufin da Daddynmu take mummunar mu'amala" Fahad yace "ba wai bane Ramadan, gaskiya ne ita ta gayamin da bakinta" Ramadan yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, meyasa Daddy ze mana haka? Fahad abunda kake aikatawa ga 'ya' yan wasu ne muma yazo mana har cikin gida, kai kayi Daddy yayi alhalin muna da uwa muna da ƙanwa mace wannan abun dame yai kama?" Fahad yace "wallahi Ramadan nayi nadama, nadamar da bata da amfani sam, a yanzu haka maganar da nake maka da ƙyar idan Daddy bashi da cuta me karya garkuwar jiki, saboda Ramlah ta tabattar min tana da ita" A razane Ramadan ya kalli Fahad, "HiV kake nufi fa?" Fahad ya jinina masa kai alamar eh. "La'ilahaillalah Muhammadu rasulillah salallahu alaihi wassalam, Fahad HIV? Mummy kenan itama ta ɗauka a jikinsa? Subhanallah kun jawa wadda bata ji ba baya gani ba Fahad, ka ga illar zina da nake ta nuna maka ka kasa ganewa, Anwar ma ya nuna maka ka toshe kunnenka, gashi sanadin zina Daddy ya kwaso mana masifa, illar zina kenan idan kayi kai kaɗai illarta seta shafi al'umma da dama, Daddy be kyauta mana ba" Fahad a ransa yace  "Ramadan idan na gaya maka ni na sakawa Ramlah ciwo ta sakawa mahaifina ban san wani kallo zakamin ba" Ramadan ya zauna yana share hawaye, tare da baƙincikin abunda mahaifinsu ya aikata, tausayin mahaifiyarsu ya mamayeshi, ya kalli ɗan uwansa yace  "yanzu Fahad yaya zamuyi mu gayawa Mummy wannan maganar? Itama taje a binciki lafiyarta tunda wuri?" Fahad yace "Ramadan abunda nake ta tunani kenan, na rasa abunyi gaba ɗaya, ban san ta inda zan ɓullowa wannan maganar ba, da ƙyar idan Mummy bata ɗauka ba, dan babu wanda yasan tun yaushe yake tare da ita, suke mu'amala" Ramadan ya dafe kansa, ya dinga jujjuya kansa cike da ƙunar rai, ya fice jiki a sanyaye daga ɗakin Fahad, zuciyarsa na masa wani irin zugi da takaici, gami da tausayin mahaifiyarsu. Shirye shirye sukayi nisa, akan ɗaukaka ƙarar Yusuf, manyan lawyoyi da masu kare haƙƙin ɗan Adam suka shiga lamarin, suna ta tattar hujjoji da shedu wanda suma zasu gabatar, a sake sharia'r Yusuf. Yayinda Widad ke zaune a inda take ɓoye, inda Bulama yake ɓoye da ita, take communicating da mutane a waje, ta hanyar Sabuwa me aiki, taita aikenta da takadda ba tare da Sabuwa tasan ma'anar hakan ba, ga cikinta ya ɗan ɗaga sosai ya fito, dan sosai yake motsi yanzu, sedai duk lokacin da cikin ya shiga wani watan, se wata matsala ta taso, kodai yawan amai, ko ciwon kai, ko rashin son Abinci, haka Widad keta wahala tana ƙumbiya ƙumbiya da cikin a hijjabi kar wani ya gani, ga Bulama ya shafe kwanaki bezo ba, tunda yayi mata barazanar kama mahaifiyar Yusuf bata sake ganinsa ba. Bulama kuma yaga canji a tattare da yaransa, abun da ya bashi mamaki be wuce yadda Ramadan ɗin dayake nutsatse yabi sahun Fahad ba, sam basa gaisheshi ko kallon inda yake basayi, balle ya saka ran wani abu na kirki ya shiga tsakaninsu dashi, suka dena shiga cikin gidan ma sam. Bulama yace "Sarah, kin lura da yadda yaran nan suka canza gaba ɗaya a gidan nan? Na rasa me nayi musu, sam basa shiga harkata sun dena ko gaishesni, ko wani abun sukace nayi musune?" Hajiya Sarah tace   "ni dai bani da masaniya akan komai, ni Ramadan yafi bani mamaki ma, nasan ba haka yake ba, amma ban san yadda akayi shima ya ɗauki wannan mummunan halin ba, amma dan Allah kayi haƙuri, zanyi magana dasu insha Allah" Bulama yace "shikenan, yakamata kam" Daga nan ya kintsa ya fita, bayan fitarsa Hajiya Sarah taje har BQ ta samesu, 'Fahad, wani abu nake gani wanda na kasa gane kansa, meye dalikinku na dena kula mahaifinku ne?' Fahad yace "babu komai" "ƙarya kuke yi, akwai dalili idan ba haka ba, meye na wannan shareshin da kuke yi?" Ramadan zeyi magana, Fahad ya girgiza masa kai yace "Mummy, kin san daddy da yawan faɗa, komai ya gani se yayi magana, se yayi mita da faɗa, shiyasa muke ɗan janyewa kawai" Tace "Ai ba yanayi ne dan ya takuda muku ba, dole idan kukayi ba daidai ba a tsawatar muku, dan haka bana son wannan abun da kuke, a gyara dan ya fara zargin koni nake saku kuke masa haka" Fahad yace "to insha Allah, zamu gyara" Bayan fitarata, Ramadan yace "Fahad meyasa ka hana a gayamata?" Fahad yace  "Ramadan, ba'akowane irin yanayi ake gayawa mutum magana ba, ka bari zamu gayamata ' " Aikuwa bashi da amfani ko mun gaya mata, nasan aikin gama ya gama, ya riga ya cutar da ita " Fahad yai shiru be kuma cewa komai ba. Jini fa yaƙi tsayawa Amal, gaba ɗaya ta ɗashe tayi fari, ta kira doctor Hamisu a waya, ya rubuta mata magani, taje ta siya amma idan ta sha wuni take a kwance tana jiri, gaba ɗaya tayi wani iri, tambayar duniya taƙi gayawa Hajiya Halima abunda ke faruwa. Tana kwance ta lallaɓa, zataje Asibitin da aka cire mata cikin ganin Likitan, se taga message nata shigowa wayarta, tana dubawa me zata gani? Kuɗinta na Account ake ta kwashewa, ta tashi a gigice sedai ba wani abu data iyayi an kwashe kuɗin nan tsaf, sakamakon wani website data shiga, akace ta saka BVN Number ɗinta, kuma ta saka akayi amfani da shi aka kwashe kuɗin nata. Ta fito falo a gigice tana kuka, Hajiya Halima tace "ke lafiya kuwa?" "Mummy kuɗina, an kwashemin kuɗina a Account" Ramlah tace "ke kuwa kina me? Garin yaya?" "Wani website ne, na shiga na saka BVN ina ga ta nan aka kwashemin kuiɗn, gashi nayi investing kusan million biyar a wani business shima an kwashe ma shiga uku" Hajiya Halima tace "million goma kuma? A kna kika samu million goma?" Sekuma ta dawo hayyacinta, ta shiag inda inda, cikin tsawa Hajiya Halima tace  "magana nake miki, a ina kika samu million goma?" Tai shiru tana tura baki, "zakiyi magana ne? Ko kuma sena tashi na tattaka ki?" "Alhaji Haruna me yamin fyaɗe, ni kuma na sace masa kuɗi a account" Ramlah ta buɗe baki, Hajiya Halima ta miƙe tsaye  "ya miki fyaɗe kamar yaya?" Nan Amal ya kwashe komai ta gayamata, har jinin da take ta zubarwa tunda aka cire cikin. Nan da nan jikin Hajiya Halima ya ɗau rawa, ta kasa magana ma gaba ɗaya, ta dinga bin Amal da Ramlah da kallo. Tunda mutane suka ji batun Yusuf zeyi appeal, suke ta ɗokin sake zaman ganin shari'ar nan, ranar da za'a fara sauraren ƙarar kotu ta cika maƙil, musamman jin labarin a ƙarƙashin jagorancin gogaggaun Matasan lawyoyi dodannin Azzalumai za'ayi shari'ar, kotu tayi maƙil assurance ɗin da Bulama ya samu a gurin Justice A dutse, da kuma su Barrister Sadik yasa ya je kotun da ƙwarin gwiwarsa, sedai duk da haka bashi da wani karsashi, saboda Alƙalin koyun bashi da wasa, balle ka tunkareshi da wata maganar cin hanci Justice Muhammad Mustapha. Shikansa Yusuf yayi mamakin ganin, manyan lawyoyin da sukazo dan tsaya masa, da yawa a radio yake jin sunayen su, sekuma a dandalin sada zumunta, amma yau gashi gasu wai zasu tsaya masa, a iya saninsa ba kowa ke iya ɗaukarsu shari'a ba, saboda lawyoyine masu tsadar gasme, kuma basa tsayawa shari'ar Azzalumai, to ta yaya akai shi suke son tsaya masa? Bayan ta bayyana ƙarara shi me laifine?. Barrister Adam A Adam ya fito gaban alƙali ya gabatar da kansa a gaban alƙali, sannan ya kalli kotu yace  "sunana Barrister Adam A Adam, ni lawyer ne me zaman kansa, ina daga cikin tawagar lawyoyin da zasu tsayawa wanda ake ƙara, don bashi kariya, a tare dani akwai hujjoji da shedu da zasu tabattarwa da alƙali cewar wanda ake tuhuma, be aijata ɗaya daga laifukan da ake zarginsa dasu ba, idan kotu ta bani dama ina buƙatar ganin Sada, wanda yace Yusuf ya kai masa mota ya siya " Sada ya fito yana rarraba ido, dan kallo ɗaya zakayiwa Barrister Adam A Adam kasan babu wasa a tare da shi, sannan abune mawuyaci a kada shi a shari'a, saboda gogaggen lawyer ne, kuma ɗan gwagwarmaya. Barrister ya kalli Sada yace " ko zaka iya gayawa kotu sunanka, da abunda ka sani akan wanda ake zargi?" Sada ya maimaita abunda ya faɗa a kotun baya, Barrister Adam yace  "wow, ko zaka iya gayawa kotu wame irin motoci Yusuf ke kai maka gyara daga gidan Daula?" Sada yace "motocine dai, kamar su jeep su Honda da sauransu" Barrister yace "wace irin mota ce Yusuf ya kai maka ta gidan Daula ka siya?" "Prado ce" ya bada amsa "wow, kasan irin wannan motocin se gidan attajirai irinsu daula kam, amma ya akayi ka siyi motar da kuɗinta ya haura naira million talatin a matsayinka na bakanike?" "Amm ai, ai, ai dama bani nake... Objection ya me shari'a cewar Barrister Sadik, " Barrister Adam yana ƙoƙarin jefa tsoro da razani a zuciyar sheda, kuma ai shi arziki sirrine, dan mutum yana ƙaramar sana'a shikenan baze mallaki dukiya ba? " Justice Mustapha yace  "tambayoyin da Barrister Adam yakewa Sheda, zam basu kauce ba dan haka wannan ƙorafin be karɓu ba, cigaba da aikinka" "Nagode ya mai girma me shari'a" cewar Adam A Adam. "Sada, waye megidanka da ya sai motar?" "Amm, wa.. Wani oganane ubangidanane" "Amma meyasa kuka sai motar, bayan kun san Yusuf bashi da arzikin daze mallaki wannan motar?" "Amm, ai, ai dama bece min satota yayi ba, kawai yace in siya nace masa bana siyan mota, na haɗashi da me siya na zata ko bashi motar Alhaji Nasir yayi, kasamcewarsa mutum me kyauta" Barrister Adam yace "hakane, ina neman alfarma da kotu ta bani dama dan gabatar da wata ƙwaƙwarar sheda da zata tabattar da abunda Sada ya faɗa ba gaskiya bane" Aka bawa Adam dama, aka shigo da Nura, aka tsayar da Nura a gurin Tsayuwa, Barrister Adam yace  "ko zaka gayawa kotu sunanka" "Sunana Nura Idris" "Kasan wannan" aka nuna masa Yusuf, Nura ya jinjina kai alamar eh, "wannan fa?" aka nuna masa Sada, Nura yace "A'a" "toko zaka iya shedawa Kotu, abun da ka sani game da abunda ake tuhumar Yusuf dashi?" Nura yace "kamar yadda na faɗa sunana Nura, kuma nine direban Alhaji Nasir Daula, kafin zuwan Yusuf ya fifita Yusuf sama da kowane ma'aikaci a gidan, na shekara a ƙalla tara ina aiki a gidansa, a haƙiƙanin gaskiya idan mota ta lalace a gidan Alhaji Nasir, Har gida ake zuwa a gyara ta, kuma Yusuf baya kai gyaran mota iya abunda nasan yanayi, shine tuƙa 'yaf gidan Alhaji Nasir Daula, sekuma shikansa Alhaj Daulan wasu lokutan, kuma idan mota ta lalace ma ba' a fiye barinta a gidan ba, gyara ta ake a bayar da ita, dan haka gaskiya ni ban san wannan bawan Allah ba, kuma a gidan Alhaji Nasir Daula, babu irin motocin daya faɗa, manyan motoci na alfarma su ake hawa a gidan Alhaji Nasir" Barrister Adam yace "Malam Nura muna godiya, ban sani ba ko Sada yana da abun faɗa?" Sada ya soma inda inda, yana kallon inda Su Bulama suke, akace ko su Barrister Sadik suna da abun faɗa? Sukace babu. Barrister Adam yace  "sheda ta gaba da zan gabatarwa da kotu itace, shedar da aka bawa Yusuf a hukumance, daga hukumar 'yan sanda, na cewar yaje gidan Alhaji Daula yai bincike sannan ya bawa' yarsa kariya a ɓoye, a matsayinsa na ɗan sandan farin kaya, wanda hukumar ta musanta hakan, Amma akwai takadda da aka samu, wadda da saka hannun hukumar da stamp ɗinta, wanda babu wanda ya isa ya samu wannan stamp ɗin, idan har ba daga ofishin manyan cikin jam'ian tsaron ba "  Barrister Adam ya fito da takadda aka karɓa ka miƙawa alƙali, shi dai Yusuf yana tsaye, yana tunanin waye ya masa wannan ƙoƙarin haka?" "dan haka muna neman jin cikakken bayani daga bakin 'yan sanda, idan har bata hannunsu wannan takadda ta fito ba, ta yaya akayi stamp ɗinsu ya fito a takaddar, idan kuma da saninsu yaje yin aikin, meyasa suka musanta sune suka bashi aikin?" Nan fa sa'insa ta kaure tsakanin lawyoyin, su Barrister Sadik suna da'awar ai ƙarewa Wadda abun ya faru akanta da kanta ta bada sheda, seda alƙali ya buga guduma, yace ya ɗage shari'ar zuwa sati biyu gaba. AMANA! AMAA!! AMANACE!!! AYSHERCOOL 07063065680 12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" _(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_) IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _ 150_151 Zare ido Bulama yayi jin an ambace shi haka, abun da be taɓa kawowa ba, yaga dai duk shedun da aka gabatar babu wanda yai wata magana da ta shafe shi, amma yaji an ambaci sunansa. Ya tsaya yana zazzare ido, ya miƙe cikin fargaba ya fito ya tsaya a inda ake tsayawa, Barrister Khalil yace   "Alhaji Bukar Bulama, duniya tasan kaine babban abokin mahaifin Widad, wato Alhaji Nasir Daula, ko zaka iya gayamana abunda kasani game da ɓatanta?" Bulama yace  "Eh to, kafin ɓatan nata dai, kamar yadda ka faɗa ni ubane a gurinta, dukda rashin yaddarta ga mutane akwai kyakkyawar alaƙa tsakani na da ita, Daula da 'yarsa sun bada amanna sosai ga wannan bawan Allah, sun yadda dashi sosai. Har nake ja masa kunne akan yayi taka tsan tsan, da wannan yaron saboda be kamata ace yana shishigemasa haka ba, saboda duniya babu gaskiya, wata rana ina bacci cikin dare, sega wayar Daula ina ɗagawa a gigice yake gayamin ai Widad direbanta ya gudu da ita, a daren na tafi gidan gonarsa, yake gayamin ya kira Yusuf akan ze kai Widad Abuja, yana son ya kwana a nan gidan gonar dan suyi tafiyar Asuba suje da wuri, amma cikin dare Yusuf ya sace ta ya gudu da ita" Barrister Khalil yace  "duk ina ma'aikatan gidan, da har ya gudu da ita a mota babu wanda ya sani?" "Nima ban saniba, tunda seda abun ya faru sannan ya kirani" Khalil yace "Kasancewar ka Uba ga wannan yarinya, bayan an gano inda take, an karɓota daga hannun masu garkuwa, an kaita Asibiti an gama mata dukkanin wasu gwaje gwaje da yakamata, tana hannunka a zaune kenan?" "Eh tana gurina" Bulama ya bada amsa, Khalil yace  "tana gurinka, amma ba'a gidanka da kake zaune da iyalinka ba?" Bulama yace  "Eh, tana wani gidan daban sakamakon rashin jituwa dake tsakaninta da ɗana Fahad, da kuma ta samu hutu" "Amma me yakawo rashin jituwa tsakaninsu, dukda cewar kusan uba kake a gurinsu duka"? Bulama ya rasa yadda zeyi da tambayoyin Khalil, yace  "Eh, nima ban san dalili ba, amma basa jituwa ' Khalil yace "bekamata ace baka sani ba kuwa, sannan duk wanda yasan Alhaji Bukar Bulama a baya bashi da wannan tabon ɗinki a fuskarsa haka? Ko ya akayi ya samu wannan tabon? " Barrister Saminu yai suka akan abunda Khalil yake yi, amma Justice Mustapha yaƙi saurarrasa, yace Khalil ya cigaba. Bulama yace  "'yan dabane suka yankeni a fuskar" "meya haɗaka da' yan daba kana babban mutum har suka maka wannan yankan a fuska haka?" Bulama yace  'kuɗi suka nemi in basu ban bayar ba, shine suka yankeni a fuska da cinya ta " " ka kai rahoton faruwar hakan ga hukuma? " ' A'a" Khalil yace "saboda me?" Bulama kawai yai shiru, yama rasa meze cewa Khalil, saboda yadda ya titsiyeshi da tambayoyi, tabbas da tun a shari'ar farko irin wannan shari' ar akayiwa Yusuf, da baze je prison ba, Umma dake zaune na kallon shari'ar banda tasbihi da hamdala ba abunda take yi a ranta. Barrister Khalil yace  "bayan kai akwai wanda Yasan inda gidan daka ajiye Widad Nasir Daula yake?" Yace "Eh" Khalil yace  "wakenan?" "'ya' yana duk sun sani" 'ka bawa' yan jarida damar ganawa da ita? Ko kuma jam'ian tsaro sun san inda take? , ko kuma meyasa iya kaida 'ya' yanka ne suka san inda take, alhalin ana kan shari'a, dole za'a so bincike se anji wani abun ta bakin ta, ka kaita ka ɓoye ta, ka tirsasata ta bada shedar ƙarya a kotu, kai yunƙurin cutar da ita, tai maka rauni da wuƙa, Bulama kaike da alhakin daukkanin abunda ke faruwa a gidan Alhaji Nasir daula, saboda babu wanda yasan sirrinsa sama da kai" "Objection yame shari'a, wani irin abu Barrister Khalil yakeyi haka? Yana ƙoƙarin liƙa laifi ga wanda be jiba be gani ba, ba tare da wata hujja ko sheda ba, yana ta ƙoƙarin ƙirƙirar labari da hanyar da ze jingina laifi akan wanda bashi da laifi" cewar barrister Sadik. Alƙaki yace  "Barrister Khalil, ko kana da shedar abunda kake faɗa?" "Ina da ita yame girma me shari'a" Khalil ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko wata waya, yazo gaban Yusuf ya nuna masa wayar yace  "ko za ka iya tuna wannan wayar?". Yusuf ya karɓa ya jujjuya wayar yace "eh na gane wayar" "wayar waye?" Yusuf yace "Wayar Nurat ce, 'yar gidan Alhaji Musa" Khalil yace "meyasa baka gabatar da wannan wayar a matsayin shedarka ba lokacin da ake maka sharia' ar farko?" Yusuf yace "saboda an hanani duk wata dama da zan kare kaina" Khalil yace "ina son ka karɓi wannan wayar, kayiwa kotu bayanin abunda ke ciki" Yusuf shi gaba ɗaya ya manta ma da batun wayar Nurat, ko ya akayi Khalil ya gano da wani abu a wayar harya ksrɓota oho, saboda Yusuf besan akwai alaƙa a tsakanin Nurat da Khalil ba. Yusuf ya riƙe wayar yace  "Kamar yadda nake gudanar da bincike na a ɓoye, a gidan Alhaji Nasir Daula, katsam watarana nayi dare a gidan na fito zan tafi gida wasu mutane suka tareni, sunamin kashedi akan lallai suna daga cikin masu bibiyar Alhaji Nasir da 'yarsa, kuma nima zasu dinga bibiyata akan lallai sena samo musu wani abu a hannun Widad, har mukayi sa' insa dasu suka dakeni, still bayan wani lokaci suka sake biyoni, nan ma suka dakeni sedai na ɗau lambar motar tasu, naje na kai Office muka bibiyi lambar, a nan na gano lambar motar gidan Alhaji Musa ce, wato mahaifin Nurat. sannan na taɓa kai Widad wani hotel, na jirata a waje, ta shiga ta fito tana kuka, bayan mun koma gida, na maida ita naji lallai ina son sanin me taje yi a Hotel ɗin nan, bayan na koma na kasa gane komai, sena nemi manager nace ina buƙatar ya bani record na wanda suka kama ɗaki a hotel ɗinsu, mun kai ruwa rana kafin ya bani, dan seda na biya shi, aka bani Jerin record na wanda suka kama ɗaki na kusan watanni huɗu, a nan naga Alhaji Bulama yafi kowa kama ɗaki, dan yakan kama na wata guda, kuma da na ƙara bincike sena gano suna yawan zama dashi Alhaji Bulama, da Alhaji Musa, da Alhaji Munir da kuma matar Alhaji Nasir Daula, yanayin yadda Widad ke matuƙar tsoron mutane da kuma nima yadda akace za'a dinga bibiyata, yasa naji cewar lallai ya kamata inyiwa binciken da nake kyakkyawan ɓoyo, bayan na system ɗina na wayata, da wanda nake haɗa report a takadda, dan haka na yanke shawarar zuwa gidan Alhaji Musa, Na samu Nurat, na samu bayanai daga bakinta na yadda rashin jituwar mahaifinta da Alhaji Nasir ya samo Asali. nai amfani da wannan damar, na karɓi wayarta na buɗe wani website nai hiding ɗinsa, na tura mata duk wani sakamakon binciken da nayi, sannan nai linking ɗinsa da wayata duka lokacin dana tura wani abu website ɗin ze shiga wayarta, kuma ze zauna akan wayata, nasan babu wanda zeyi tunanin da wani abu a wayarta, ko da na rasa na gurina" Aiba Khalil ba hatta jama'ar kotun, sun jinjinawa Yusuf wannan basira tasa, Khalil yace "Amma ya akayi kai garkuwa da 'yar Alhaji Nasir Daula?" Yusuf yace "banyi garkuwa da itaba, Alhaji Nasir ya nemi da inje gidan gonarsa in kwana, zan kai Widad Abuja dan ganin wani likitan Ƙwaƙwalwa, cikin dare aka turo masa saƙo a wayarsa, ina kwance ina bacci yazo tasoni nida Widad, ya nunamin saƙon yace maza maza in ɗau Widad mu bar gidan, na tsaya ina tambayarsa ina zamuje, yace maza maza in bar gidan da Widad, saboda saƙon da aka tura masa ana barazana ne ga kodai ya bada abunda akeso, ko kuma a hallaka 'yarsa, nace masa mu kira' yan sanda amma yace aa', in kula da Widad, na ɗauketa muka fita ba tare da nasan inda zamuba, munyi tafiya me nisa ga dare, kawai aka zagaye motarmu, da Widad kawai suka so su ɗauka, ta riƙeni tana kuka na hana su tafi da ita, shune suka haɗa dani, kwananmu biyar a hannunsu, Saleh ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan gonar Alhaji Nasir, yaje ya kuɓutar damu, an harbi Widad a hannu ya kaimu Asibiti, aka cire mata bullet, sannan ya bamu mafaka a wannan ƙauyen, ya cemin idan har muka dawo za'a hallaka Widad dani kaina, dan haka mu zauna zuwa lokacin da komai ze lafa, amma bani na sace ta ba" Barrister Saminu ya mike yace  "meyasa baku shigar da ƙara ga hukumar 'yan sanda ba? Ka cigaba da zama da ita a inda babu wanda yasani tsawon lokaci?" Yusuf zeyi magana Barrister Khalil yace  "zan gabatarwa da kotu, wata shedar wadda take nuna wanda ake zargi bashi da laifi a zaman kotu na gaba" Nan kotu ta hargitse da Hayaniya, kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Alƙali ya buga gudumarsa, akayi shiru, yai rubuce rubuce sannan yace Duba da yadda lawyoyi suka gabatar da shedu da hujjoji, wannan kotu me albarka zata ɗage cigaban wannan sharia'r zuwa nan da sati biyu masu zuwa, dan yin zama na ƙarshe da yanke hukuncin daya dace akan wannan shari'a, sannan kotu tana umarni da hukumar 'yan sanda su binciki Alhaji Bulama da tawagarsa" Kotu ta ɗau hargowa da sowa, 'yan sanda suka tafi da Yusuf gidan yari, Umma ta kalli Suleiman tace " Suleiman ya haka? Naga za' a maida shi" Suleiman yace "ki kwantar da hankalinki, kin san shari'a komai a hankali a binsa ki kwantar da hankalinki" Suleiman yaita kwantar mata da hankali, yana bata baki. Hajiya Halima ganin ba'a kama da ita ba, yasa ta silale tai gida, zuciyarta cike da fargaba da kuma tsoro, tana tunanin meye mafitarta ta ƙarshe? Tasan tunda Bulama yaje hannu itama tata ta ƙare, sedai tana zuwa gidan ta tarar da gate ɗin gidan hanhai a buɗe, ga motar 'yansanda, ga mutane sun cika gidan, kamar ta juya ta gudu, amma ta fasa ta ƙarasa, tana zuwa me zata gani, an rufe mutum da zani alamar ya mutu, Ramlah se uban kuka take, ga Amal a sume a gefe ana ta mata fifita, jiki na rawa ta ƙarasa gaban gawar, tasa hannu ta yaye zanin, Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!!! Gawar Anwar ce ɗanta, gawar se zubar da jini take, idonsa a rufe kamar me bacci, kamar kace tashi ya tashi a nutsensa yake, amma ya mutu. Ta ɗora hannu a ka tana kurma ihu  "Wayyo Allah na shiga uku ni Halima, Bulama ka cuceni ka tarwatsa rayuwata, Allah ya isa tsakanina da kai Bulama, Bulama seda kasa aka kashemin Anwar? Nayi dana sanin saninka, da farko ka rabani da gidan uban Anwar, na Auri Shu'aibu shima ka kashemin Auren, ka haɗa kai da Shu'aibu kuka kashe matarsa ya sakeni dan Daula ya aureni, duk biyayyar da na maka, amma ka kashemin ɗana Me ƙaunata da gayamin gaskiya, wayyo Allah Anwar ɗina, wayyo Anwar ka tashi dan Allah, na shiga uku " Tana wannan ihun, tana maganganun nan ana mata video, ita dai Ramlah kasa cewa komai tayi, se bin mahaifiyarsu da ido, ga Amal wadda babu tabaccin tana da rai itama, dan abun yazo mata akan gaɓa, dama ta gama galabaita babu jini a jikinta, kuma ga wannan mutuwar ta Anwar, ƙarseh wannan kururwar da Hajiya Halima keyi, se rufeta akayi a ɗaki akayiwa Anwar sutura. Khalil kuwa yana ta rawar jiki yaje ya bawa Nurat labarin yadda shari'a ta kaya, akwai alamun nasara akan shari'ar Yusuf sedai yana zuwa gida ya tarar da fuskaokinsu wani iri, Nurat a zube a ƙasa ana ta fama numfashinta ya tsaya. Khalil yace "lafiya kuwa?" "Allah yayiwa mahaifiyar Nurat rasuwa, yanzun nan an tafi ɗakko gawarta daga Asibiti"  Anty Saddiƙa tai maganar tana kuka. Khalil yace "la'ilahaillalah Muhammadu rasulillah salallahu alaihi wassalam, Antyna ta rasu kenan?wallahi Musane ya kasheta, shine ya kasheta" Yai maganar yana zubar da hawaye. Haka itama akayi mata sutura aka sallaceta, aka kaita makwancinta na gaskiya, Nurat kam tasha kuka kamar ranta ze fita, gaba ɗaya ta birkice an kasa gane kanta ma gaba ɗaya, se da aka samo likita yai mata alluarar bacci dan ta samu relief. Amal kuwa har aka kai Anwar bata dawo hayyacinta ba, gawar Anwar ya tara mutane sosai kasancewarsa mutum ne na mutane, ga sauƙin kai da girmama jama'a. Fahad ya kaɗu da jin labarin an kama mahaifinsa, da kuma harƙallar da suka ƙulla da shi da Hajiya Halima, suka dinga siyar da dukiyarsa ba bisa ƙa'ida ba, ga mutuwar Anwar data dake shi, ya kaɗu matuƙa da jin Anwar ya mutu, ya lallaɓa komtsan sa ya ɗau mota ya gudu. Haka Bulama ya kasance a hannun 'yan sanda shima, Aka kama Alhaji Musa, shi laifuka biyuma aka kama shi dasu, ga laifin hankaɗo matarsa daga bene, gana wanda suka aikata da Bulama. Tunda Amal ta farka ta farka ba a daidai ba, tunda ta buɗe idonta bata magana kwata kwata, sedai taita bin mutane da kallo, kamar bata sansu ba, Hajiya Halima kuwa kamar wadda ta shekara a daji, tai wujiga wujiga ko tayi shiru idan aka jima se surutai, taita tonawa kansu Asiri ita da su Bulama, itama ƙarshe ana cikin makoki 'yan sanda suka zo suka yi gaba da ita. Nurat tana cikin tashin hankali, na rashin mahaifiyarta, ga kama mahaifinta anyi da wannan manya manyan laifuka haka, dukda tarin abunda yai mata na laifuka, amma ya haifeta, gaba ɗaya ta rame tai wani iri, ga labarin mutuwar Anwar ya risketa, mutuwar ta girgiza ta ƙwarai, ba zata manta halacci da kara irin na Anwar ba, Anwar mutum ne nagari me haƙuri da nagarta gaske. Bulama a hannun Hukumar 'yasanda ɓangaren SWAT aka danƙasu, domin tuhumarsu, dama kuwa masu fushi da fushin wani, dan haka ba'a ragawa su Bulama ba sam, kamar yadda suke sawa a azabtar da wasu, haka suma suka shiga hannu aka dinga azabtar dasu. Ana wannan halin, a haka sati biyu ta cika, aka koma kotu ranar da aka koma kotu kallo ɗaya zakayiwa Khalil kasan yana cikin alhini sosai. Kamar kullum an cika kotun nan maƙil, haka aka shigo dasu Bulama, wujiga wujiga. Khalil ya fito gaban kotu, ya gabatar da shedarsa da suke dashi akan Bulama. Babban abunda ya bawa Yusuf mamaki, be wuce yadda yaga Sunusi ya shigo ba, ya buɗe baki yana kallon Sunusi. Sunusi yazo ya tsaya, Khalil ya masa umarni ya gabatar da kansa, Sunusi ya gabatar da kansa sannan yace  "tabbas wanda ake zargi bashi da laifi, Saleh ɗan uwanane, kuma akwai Bala Yayansa, Saleh ya haɗa kai da Alhaji Bulama da niyyar ya ɗau fansa akan Alhaji Daula na sakawa da 'yarsa tayi aka tsare ɗanuwansa, dan tana zargin da hannunsa a kashe mahaifinta, sedai Bulama ya gaza cika Alƙawarin da yaiwa Saleh ma ze saka a saki ɗan uwansa, su ɗau fansa akan Daula, ganin haka yasa ya koma taimakon' yar gidan Daula, ya kuɓitar dasu daga hannun masu garkuwar, sannan ya kaisu ƙauyenmu gurin mahaaifina, saboda muddin suka dawo za'a kashe yarinyar, kuma shima Saleh ze shiga matsala, lokacin da sukaje ƙauyen bata yadda da kowa se Yusuf, ga jikinta duk rauni se anyi jinyarta, shi kuma yace ita ba muharramarsa bace, babu yadda zeyi jinyarta wannan dalilin ne yasa Saleh ya shige gaba aka ɗaura musu Aure bisa amincewarta, shedar da aka saka ya bayar a kotu shedar ƙarya ce, tursasashi akayi kuma aka masa rauni a cikinsa saboda duka, akace za'a kasheshi in be bada shedar ba, shine aka kawo shi kotu ya faɗi wannan shedar, sannan lokacin da suke ƙauye ya gayamin idan har aka kama Yusuf za'a kasheshi dashi da Widad baki ɗaya, tunda Daula ma ba'asan inda yake ba, nace masa ya gayawa 'yan sanda, amma yace a"a akwai haɗaka me ƙarfin gaske tsakanin Alhaji Bulama da Hukumomin tsaro, dan haka yana da ɗaurin gindi, idan ya faɗa tamkar ya sake jefasu a garari ne" Nan kotu ta ɗau salallami, Barrister Khalil yace " Alhaji Bukar Bulama, kaine mutum na farko da Alhaji Nasir ya kira bayan an sace 'yarsa, ya akayi wanda suke turo masa saƙo suka san inda suka tafi idan ba kai ka gaya musu ba? " Bulama yace " ni.. Ni bani bane ba, ya za' ayi in saka a sace yarinyar da takemin kallon uba? " Khalil yace " Akwai sheda, ina son kotu ta bani dama, in gabatar da sheda ta ta ƙarshe wanda zata tabattar da Alhaji Bulama shike da alhakin dukkan wannan abubuwan da suke faruwa, yasa akayi garkuwa da 'yar Amininsa, kuma yake bibiyar yadda ze mallake dukiyar Aminin nasa" Aka bashi dama, wa Bulama ze gani? Su me Adda aka jero a layi, akaje aka tsaidasu, nan da nan Bulama ya sadaƙar yasan ƙarshensa yazo. Aka tsaida me Adda, Khalil yace  "gayawa kotu sunanka" "Sunana Hashimu, amma ana cemin me Adda" "meka sani game da garkuwar da akayi da 'yar Nasir Daula?" Me Adda ya kalli Bulama yace  "eh, Alhaji Musane da farko ubangidana, dashi da Alhaji Musa da Haruna da Munir suke sa kamu aiki, nine na dinga bibiyar Yusuf nida yarana, Bulama ne ya kiramu a waya, yace mana ga inda zamuje, motar gidan Daula zata zo da Widad a ciki da direbanta, mu kama Widad, muka je kamata amma shi Yusuf yai ƙoƙarin hanamu, yace mu haɗa dashi, kwananmu biyar muna basu wahala, akan ta faɗi inda dukiyar nan take, amma taƙi, shine yace mu kasheta, dan har mun harbeta ma a hannu, kuma mun musu horon Yunwa da duka, bayan yace a kashesu muna zuwa muka tarar sun gudu, tsawon watanni ba'a gansu ba, seya gano Saleh yana mufuntarsa, shine yace mu kamo Saleh, bayan mun kamk Saleh ne shima muka dinga dukansa muna bashi wahala, daga baya ya bawa 'yansanda shi yace a tuhumeshi ya faɗi inda ya ɓoyesu, bayan wannan kuma yace muje gidansu Yusuf da daddre mu ɗakko masa babarsa, ashe akwai' yan sanda a kewaye da gidan bamu sani ba, muna zuwa suka kama mu " Khalil yace " tsawon wane lokaci ka ɗauka kana masa aiki? " Me Adda yace " gaskiya an daɗe, muna masa aiki yana biyan mu, yana bamu kuɗi sosai, a haƙiƙanin gaskiya mune mukayi garkuwa dasu, 'yan sanda sun tambayemu kuma mun faɗa musu gaskiya" Barrister Khalil yace  "Ya me girma me shari'a, duba da tarin hujjoji da shedu da kuma sakamakon' yan sanda, da muka gabatarwa wannan kotu, muna neman wannan kotu me albarka ta wanke wanda ake ƙara daga wannan tuhuma da 'ake masa Justice Mustapha Yace " duba ga yadda shari'a ta kasance, da tarin hujjoji da shedu da aka gabatar, wannan kotu da dogon Nazari da duba ga kudin shari'a wannan kotu ta wanke wanda ake zargi, wato Yusuf Bashir Maitama, sannan wannan kotu me albarka tayi umarni da hukumar 'yan sanda su  kama Alhaji Bukar Bulama, da muƙarabbansa don zurafafa bincike a sake gurfanar dasu, sannan hukumar' yan sanda zata biya wanda ake ƙara Wato Yusuf Naira million goma, sakamakon ɓata masa suna, da tauye masa haƙƙinsa a matsayinsa na ɗan ƙasa dukda dama da kundin tsarin mulki ya bashi, sannan kotu tana umarni a maida shi bakin aikin sa " Yusuf yana jin haka ya fashe da Kuka, ya zube a gurin yana sujudu shukur ga ubangiji subhanahu wata'ala, kuka sosai kamar wani ƙaramin yaro, Umma ta taho da gudu, ta rungume shi itama tana zubar da hawaye, tawagar 'yan sanda suka rako Yusuf wajen kotu, yayin da akayi Ram da Bulama da Alhaji Haruna dake gurin, sannan aka bazama nemo sauran. Yusuf na fitowa jama'a suka baibaiyeshi, sedai ya kasa magana se hawaye, Suleiman ya rungume Yusuf yana faɗin "barka da Arziki abokin aiki, barka da Arziki Yusuf" Yusuf ya rungume Sulaiman shima, sedai ba bakin magana se hawaye dake fita daga idonsa, tawagar lawyoyin nan suka zo gaban Yusuf suka dinga miƙa masa hannu suna gaisawa, Cikin kuka Yusuf yake faɗin  "Nagode, Nagode, Nagode" yana maganar yana kuka dan yama rasa meze ce musu. Umma ta rirriƙe Yusuf, kamar za'a sake ƙwace mata shi, itama kuka kawai take yi. Khalil yace  "yau na sauke babban nauyin dana ɗauka, na Alƙawari ga Nurat, da nace zanyi iyayina inga ka kuɓuta" Yusuf yace "Nurat kuma?" Khalil ya jinjina kai, yace  "Eh Nurat, sannan Yakamata a wuce dashi Asibiti, a duba lafiyarsa. Bulama kuwa aka fito da shi, da Alhaji Haruna, dasu Musa a ƙasƙance, mutane nata tsine musu, 'yan jarida suka sa kasu a gaba, amma sukaƙi magana sam, suka duƙufar da kai kamar munafukai. Bisa rakiyar' yan sanda, aka tafi da Yusuf Asibiti. Yusuf kuwa ya galabaita, dan admitting ɗinsa akayi, yana buƙatar agajin gaggawa, saboda tarin raunuka dake jikinsa, gashi ya kasa dena kukan da yake yi, Suleiman cewa yake  "Yusuf, kukan nan ya isa haka, ka godewa Allah, dan shine ya dubi halin da kake ciki ya fitar mana da kai, amma mun shiga cikin damuwa muma lokacin da ka shiga mawuyacin hali" Cikin kuka Yusuf yace "Yallaɓai, yanzu kenan harda Abbas aka haɗa kai dan cutar dani? Yace be san da an bani aikin nan ba? Abbas fa? Aminina Abbas fa?" Suleiman yace "koma dai menene, ba gashi kai ka kuɓuta ba, kuma nasan shima dole kotu ta neme shi ai" Wayar Suleiman ta fara ringing, ya ɗakkota a aljihunsa ya saka a kunnensa, "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, ubangiji Allah yai musu rahama, Allah ya jiƙan su" Umma tace "Sulaiman waye ya mutu?" Suleiman yace  "Ina Barrister Khalil? Lawyern daya dinga magana daga ƙarshe" Umma tace "eh nagane meya sameshi?" "Ai ɗan uwan Nurat ne, kuma itace ta tsaya kai da fata akan ganin an kuɓutar da Yusuf, Mahaifiyarta ce ta rasu, kuma  mahaifintane ya turo uwar daga kan bene, dan ta masa magana ya kulle Nurat ɗin, ashe duk saboda shari'ar kane akan ta dage ayi maka adalci, ya gano ta san sirrinsa shine yai dalilin rasuwar mahaifiyarta" Umma ta dafe ƙirji tace "subhanallah" , Yusuf ya girgiza kai hawaye na bin idonsa yace  "Allah sarki Nurat, Allah ya jiƙan Mummynki, nayi silar shigarki matsala kema Allah sarki Nurat" (INA JIRAN TUKUCINA NA WANNAN OAGE ƊIN, TUNDA AN SAKAR MUKU YUSUF 😎😂😂) Ayshercool 07063065680 12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" _(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_) IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _ 148_149 Gaba ɗaya Bulama bega alamar Nasara a tattare da wannan shari'ar ba, wata zuciyar ta dinga rayamasa kawai yaje ya kashe Widad ya huta, wani sashin ya gargaɗeshi akan aikata hakan. Haka ya koma gida jikinsa a sanyaye, babu alamar Nasara sam, yana zuwa ya tarar da Hajiya Sarah da Ramadan suna hira a falo, sedai da yayi sallama maimakon Ramadan ya amsa sema tsaki daya ja, suka kalleshi gaba ɗaya tace   "Ramadan, are you out of your sense? Mahaifin naka kakewa haka? Ina yabo ka salla zaka kasa alwala?" Nan da nan Ramadan ya shiga hawaye, "Mummy nayi dana sanin kasamcewarsa mahaifina wallahi, baki san halin mutumin nan ba mugune azzalumi macuci" Buɗe baki sukayi suna kallon Ramadan, Yace "Mummy ina abun kunya ina abunda Daddy ya aikata? Saboda tsabar abun kunya wai 'yar' yar uwarsa, wadda take kamar a gareshi yake bi, Mummy Ramlah fa kuma ta tabattarwa da Fahad tana ɗauke da cuta me garkuwar jiki" Gab ɗaya suka kalleshi a razane, Bulama yace "waye ya gaya maka wannan maganar banzar?" "Karka ƙara kiran ta da maganar banza, dan ba ƙarya akayi maka ba, ko basu sani ba dama yau nayi niyyar zuwa in fayyace musu komai, ɗanka Fahad shine ya shafamin wannan ciwon, ni kuma nai alwashin shafa maka, dan haka ka bimciki lafiyarka, daga kai har matarka, daga yau kaida ɗanka seku shiga taitayinku ku kiyayi yaran mutane" Kuka Hajiya Sarah ke ƙoƙarin yi, amma ta kasa ta dinga binsu da kallo, yayinda Ramadan ya daskare dan mamaki, Bulama yace  "wallahi ƙarya kikemin, ni ban aikata haka ba, wallahi ƙaryane" Ramlah tace "wannan kuma ya rage naka Bulama, nayi hakane dama dan tarwatsa kan iyalinka kamar yadda a sanadinka duk mun ɗaiɗaice babu wanda be abun kunya ba, gara a raba ai, ace kowama yayi" Ta kalli Hajiya Sarah tace  "Hajiya Sarah kece abar tausayi, Kasancewar kin zauna da baƙin kumurci tsayin shekaru baki san waye ba, ki gaggauta bincika lafiyarki, idan baki kamu ba shikenan, idan kuma kin kamu se ince  Allah ya bamu lafiya baki ɗaya" Ta juya ta bar musu falonsj, ta fics tana fita kuwa Hajiya Sarah ta yanke jiki ta faɗi cike da ɗimuwa Ramadan da Bulama sukayi kanta, sedai Ramadan yace "karka sake ka taɓamin uwa, Kuma insha Allah zaka ga sakamakonka tun a nan duniya, macuci mara imani kawai" Ramadan ya shiga kiciniyar ɗagota, Fahad kuwa yana ta bayan ɗakin, yana laɓe yaji komai ya zame ƙasa ya zauna yana kuka, tabbas Ramlah ta rusa musu farinciki gaba ɗaya, farinciki na har Abada makuwa, ya shiga tunanin me zeyi wanda ze fanshe wannan cin mutunci da tayi musu?. Hajiya Halima ma gidan Alhaji Haruna ta tafi, bayan jin irin katoɓarar da yayi mata akan Amal, taje ta sameshi shida Salma da uwargidansa a falo, da gani wata matsalar ce na family issues suke solving, taje musu afujajan kamar wadda tayi gobara a ka, tana zuwa ba sallama ba gaisuwa bakomai ta haushi da bala'i. "Wallahi Haruna ka bani mamaki, nayi mamakin abunda ka aikatamin, ashe fyaɗe kayiwa Amal? Daga aikota ta kawo maka takadda dan baƙin zalunci, wallahi baka isa ba zakaga matakin da zan ɗauka akanka" Uwargidansa ta bisu da ido, dan ita bata da wani baki sosai, Salma kuwa tace "ba shakka, biri yayi kama da mutum, shiyasa yarinyar nan ta dinga bibiyar ka? Tana turon saƙonni da ɓoyayyiyar lamba ashe dagaske ne abuika aikata? Ko kunya ba kaji ba gaka da yara mata, amma kayiwa wata fyaɗe?" Cikin inda inda Alhaji Haruna yace "Ni, Ni wallahi ƙarya takemin ita ta kawo kanta" Salma tace  "kai ko kunya bakaji ba kake cewa ifa ga kawo maka kanta? Allah wadaran halinka nayi dana sanin Aurenk, Wallahi da in Auenka gara ace Yusuf ɗina na Aura dukda rashin asalinsa, dan nasan baze taɓa wannan akuyancin ba" Hajiya Halima tace  "Haruna ka bani kunya, ka bani mamaki ka cutar min da yarinya, gaba ɗaya kun kassaramin rayuwata data yarana, wancan ya ɓata kunce a kasheshi, wannan kai ka lalata ta, waccan kuma Bulama ya lalata ta ɗansa ma yayi, sun saka mata HIV, na rasa dame ma zan kiraku, kun cuceni kai da Bulama dukda kasancewarsa ɗan uwana Allah ya isa wallahi " Tai maganar tana kuka, Alhaji Haruna ya saki tumbi yana kallonta, duk damfara da satar da 'yarta tayi masa bata gani ba se shi zata kalli abunda yayi mata. Ya kalleta sama da ƙasa yace "Malama ki fita ki barmin gidana, kije can ku ƙarata, ita bata gayamiki abunda tayimin ba, se wanda nai mata, kije kiyi duk abunda zakiyi, kinzo kin ɗagamin hankali a cikin iyalina" Hajiya Sarah ta kalleshi tace "ni kakewa haka? Ni kake kora daga gidanka? Kamin wannan mummunan abu sannan ka Kalleni kace in bar maka gida?" fice daga gidan, zuciyarta na ƙuna gaba ɗaya yaranta sun lalace gaba ɗaya. Salma taje gabansa ta tsaya tace "wallahi banga amfanin zama da fasiƙin mutum irinka ba, dan haka ka sakeni malam" Alhaji Haruna yace "Ai Aurena dake har abada tunda iyayenki kwaɗayayyune, sunga kuɗi sun auramin ke wallahi bazan sakeki ba dan ina sonki" "karka sake ka zagarmin iyaye, kuma wallahi seka sakeni tunda ba tare aka haifemu ba, macuci me abun kunya kawai" Ya tureta yai wucewarsa yace "kanki ake ji, wadda taga zata zauna shikenan, wadda bzata iya ba ta ƙara gaba, amma saki kam babu shi" Cikin kuka Salma tace "wallahi ƙarya kake seka sakeni, wallahi bazan cigaba da zama sa fasiƙi ba" Uwargidan kam bata iya magana, sedai kuka dayake irin ta da ɗin nan ce, tun auren ƙuruciya gashi babu wani isashen ilimi a tare da ita. Lamarin mahaifiyar Nurat fa sam babu sauƙi a lamarin, dan sati guda kenan babu wani cigaba, gaba ɗaya Nurat ta ɗaga hankalinta akan halinda mahaifiyarta ke ciki, jin mahaifintane yai sanadiyar faɗowar mahaifiyarta daga bene yasa taji gaba ɗaya ya fita daga ranta, ko san ganinsa ma batayi, gashi idan yazo Asibiti dubata 'yan uwanta suyi ta haɗe masa rai, ko sabgarsa basa shiga, Nurat kam an sallameta tuni amma taƙi barin Asibitin, idan tana buƙatar wani abuma gidan su Khalil take tafiya, gidan yayar mahaifiyarata kenan. Ramadan kam Asibiti ya kai mahaifiyarsu, ya kira Iman dake makaranta suka zauna a gurinta dan kula da ita, dan ta samu shock ne a wannan lokacin. Bulama kuwa bayan tafiyar Ramlah ya bita har gida, yana zuwa lokacin Hajiya Halima ta dawo da baƙincikin gidan Alhaji Haruna, yazo yana wani muzurai yace  "Ina Ramlah take?" Hajiya Halima ta kalleshi tace  'ban sani na, azzalumi ma cuci burinka ya cika, gaba ɗaya yaran sun watse Bukar saboda muguntarka da rashin imani" Bukar yace "saboda son zuciyarki dai, da son Abun duniya" "Ni kake gayawa haka?" "Na gayamiki ɗin, ai ba ƙarya nayi miki ba, mugun son Abun duniyarkine ya janyo miki da kwaɗayi" "Lallai Bulama ka cika butulu azzalumi, to wallahi zan taka bakin faranti komai ya watse" "kar Allah yasa ki fasa takawar, kije kiyi duk abunda zakiyi, ai idan ta tashi watsewa tare zata watse mana, kuma ki sani idona idon Ramlah sena saka an kashe ta" "ka daɗe baka sa an kasheta ba, kayi maza karka fasa" Ramlah ta fito daga sashensu tana tauna cingan, kallo ɗaya za kamata kasan 'yar wisi ce, ta kalli Bulama tace  "kai ka isa kasa a kasheni, ai base kunyi barazanar taka bakim faranti ba, kuji da abunda ke tunakaroku, Asirinku na daf da tonuwa a kotu, a nan yakamata ku maida kai mussman ma kai, ba wai zaka kasheni ba, dan ni na diha na kasheka da ranka tuni" Ta ƙarasa maganar tana ɗura ruwan roba a cikinta, ta juya ta wuce dining dan cin Abinci, Hajiya Halima ji take tamkar tayi hauka, komai ya dagule mata, ta rasa meke mata daɗi. Bulama ya fita da sacacciyar gwiwa jiki ba ƙwari, yanzu duk wannan barazanar da kwarinin dayake ana tsoronsa duk babu. Tunda Ramadan ya ɗau mahaifiyarsa daga gidan basu sake komawa ba, har Allah yasa ta farfaɗo, aka ɗibi jininta aka gwada amma ba'aga ƙwayar cutar ba, akace bayan watanni uku zasu dawo sake yi, se kuka take tana tunanin wans irin lamarine wannan, ɗa ya nemi mace ta bashi kanta, kuma ta koma tabi mahaifinsa saboda Taɓarɓarewar ƙarshen zamani. Daga Asibiti kai tsaye, Adamawa Ramadan ya tafi da Mummyn, saboda can ne ainihin garinsu. Bulama yaje Asibiti aka ɗibi jininsa, da niyyar yasan a wani mataki yake, yana da cutar ko babu? Amma yakasa tsayawa a gaya masa sakamakon saboda fargaba ya gudu. Haka abubuwa suka cigaba da damalmalewa azzalumai, basu fargaba lokacin komawa kotu yayi, ga kawunansu a rarrabe, kowa yana kallon kowa a banza, ga yadda suka dinga zaluntar  junansu. Yau kuma Barrister Hafiz ne ya fito ya gabatar da kansa, tunda Bulama ya ga Barrister Hafiz cikinsa ya ɗuri ruwa ya zuba ido yaga meze faru. Barrister Hafiz ya fito ya gabatar da kansa, yace  "Sunana Barrister Hafiz, lawyer me zaman kansa, ina ɗaya daga cikin lawyoyi gidan Alhaji Nasir Daula, kuma ina ɗaya daga cikin lawyoyin da zasu bawa wanda ake ƙara kariya, kimanin shekaru goma sha biyu baya, tun bayan da ayyana cewar kaso bakwai na dukiyarsa akwai me ita, yasa aka dinga bibiyarsa da 'yarsa akan lallai a karɓi wannan dukiya, har kawo ga kashe matarsa da akayi, wanda ba' a ƙarabi ta kan case ɗinba tsawon shekaru, a tare dani akwai shedu da hujjoji da zasu tabattarwa da kotu wanda ake ƙara bashi da hannu gurin yin garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula, ko kuma shi Daula kansa " Ya ƙarasa inda Yusuf yake tsaye, ya kalli Yusuf yace " Malam Yusuf, ko zaka iya gayamana yadda akayi ka fara aiki a gidan Alhaji Nasir Daula? " Yusuf ya ɗanyi shiru yana kallon Barrister Hafiz, Barrister Hafiz ya jinjina masa kai alamar ƙwarin gwiwa. Yusuf yace  "Abokin aikina Abbas, shine yazo ya sameni da maganar ga aikin da ake so inyi, shugabanmu yace a bani umarnin yin wannan bincike, da farko naƙi amsawa, daga baya naga tunda aikinane bazan iya cewa a'a ba, tunda ni na ɗau alƙawarin aiki, Abbas shine ya kaini gidan Alhaji Nasir Daula da kansa, yana zuwar musu gidan a matsayin Sani me yankan farce, kuma yana mutunci dame gadin gidan " " waye me gadin gidan? " cewar Barrister Hafiz. Yusuf yace " Isa ne" "muje kotu na saurarenka" "Bayan an kaini gurin 'yar gidan Daula, tace min sena saka hannu akan wata takadda kafin in fara aiki da ita, na karɓa na saka, tace min saka hannun da nayi tamkar na saka hannu a contract ɗin mutuwana ne, da farko naji tsoro se ban nuna ba saboda tunda aiki najeyi, bazan janye ba saboda abunda ta faɗa " Barrister Hafiz ya jinjina kai yace " ko Isa megadi yana gurin nan? " Isa megadi ya miƙe, aka masa umarni daya fito, ai kuwa ya fito yazo ya tsaya. Barrister ya kalle shi yace " me zaki iya cewa akan abunda Yusuf ya faɗa " Isa megadi yace" tabbas lokacin da ake neman direban da ze dinga jan 'yar Alhaji Daula a mota, Sani me yankan farce, wanda se da aka fara shari'a naji sunansa Abbas kuma ɗan sandane, shine ya kawo Yusuf gidan nan, kuma daya kawo shi me gidan yana matuƙar ƙaunarsa saboda haƙurinsa, kuma duk rashin yaddarta ita uwarɗakin nasa tana yadda dashi sosai" Barrister Hafiz yace  "Isa megadi zaka iya komawa" Kafin Barrister Hafiz ya kuma gabatar da sheda, Barrister Sadik yace yana da tambayoyin da zewa Yusuf, Alƙali ya bashi dama, yaje gaban Yusuf ya tsaya yace  "Kamar yadda ka bayyanawa kotu cewa, 'yar gidan Nasir Daula tace maka aiki da ita tamkar signing ne akan contract ɗin mutuwarka, meyasa ka amince kayi aiki da ita, ko duk cikin shirinka ne na saceta"? "Objection ya megirma me shari'a, Barrister yana ƙoƙarin saka wanda ake zargi yayi confessing ne ko kuma tambayarsa yake?" Alƙali ya buga guduma yace "Order, Barrister Sadik cigaba da tambayoyinka" Yusuf yace "Ni ɗan sanda ne, kuma dama rayuwar ɗan sanda na tsakanin rayuwa da mutuwane dan kare rayuwa da dukiyar wasu, shiyasa ban razana na janye ba, saboda aiki nake" Barrister Sadik yace "kace bincike kaje yi gidan Alhaji Nasir da kuma bawa 'yarsa kariya, wane irin bincike?" "Kamar yadda Barrister ya faɗa ɗazu, ana kai musu farmaki, saboda dukiyar da yace batasa bace, an bani aikinne dan gano suwaye da kuma bawa Widad kariya" Barrister Sadik yaga idan ya cigaba da tambayoyin nan, tabbas Yusuf ze ɓallo ruwa, dan haka ya koma ya zauna. Barrister Khalil ne ya shigo cikin kotun da hanzari, fuskarsa babu annuri idonsa jajawur, ya tsaya yace  "ina me neman afuwar kotu, na gaza halartar kotu da wuri, hakan ya biyo bayan neman wata sheda da bata zo hannunmu akan lokaci ba, sunana Barrister Ibrahim Khalil, lawyer me zaman kansa ina cikin tawagar lawyoyi dake bawa wanda ake tuhuma kariya, idan kotu ta bani dama, zan fara gabatar da shedu da hujjoji, amma kafin nan ina son yiwa wanda ake ƙara tambayoyi" Aka bawa Khalil dama, Khalil yaje gaban Yusuf ya kalleshi, dukda Yusuf a wahale yake amma hakan be hana Khalil ganin kyau da Yusuf yake dashi ba, yace  "Malam Yusuf, kamar yadda kayi iƙrarin bincike kaje yi gidan Alhaji Nasir Daula, kotu zata so ta san wane sakamako ka samu na binciken? Sannan ina kudin binciken da kayi?" Yusuf ya ɗaga ido yai ido huɗu da Hajiya Halima, ya kalli inda Bulama ke zaune, ya ɗauke kai yace "An karɓi kundin binciken, lokacin da aka kamoni ina hannun 'yan sanda, sannan a bincikema na farko, akwai yunƙuri da akayi na sace' yar gidan Daula, a gidan wani tsohon ɗan majalisa da taje taya 'yarsa murnar zagayowar haihuwarta" Khalil yace "ko kana da sheda?" Yusuf ya girgiza kai, alamar a' a. Khalil yace "cigaba ina jinka" "Matar Alhaji Nasir, tana da wani ɓoyayyen nufi akan Widad, suna bata maganin gusar da hankali, sannan suna da wani nufi akan dukiyar Alhaji Nasir, dan akwai babbar 'yarta data taɓa cemin in bata password ɗin Banki na' yar Alhaji Nasir" "ya akayi kasan password ɗin nata kai?" "Saboda tana aikena, Na kanyi kwanaki da ATM ɗinta a hannuna" Barrister Saminu ya mike yace "Objections sir, wannan tambayoyin da Barrister kewa wanda ake ƙara, basu da tushe balle makama kame kame ne kawai sukeyi, dan haka ina Roƙon wannan kotu me Alfarma, da tayi watsi da wannan magana da wanda ake ƙara yake faɗa" Cikin zafi Khalil yace  "ina da tabacci da ƙwararan shedu akan abunda wanda ake ƙara gaskiya yake faɗa, idan kotu ta bani dama ina son ganin Hajiya Halima, matar Alhaji Nasir Daula, don gabatar mata da wasu tambayoyi" Aka bashi dama, Hajiya Halima ta fito, gaba ɗaya ta tsoste tsufanta ya fito jikinta se rawa take yi, bayan ta tsaya Barrister Khalil ya nemi ta gabatar da kanta, ta gabatar da kanta a gaban kotu, Khalil yaje gabanta ya ɗakko wata takadda a aljihunsa, ya ajiye a gabanta yace "kin san rubutun waye wannan?" Jikinta ne ya hau rawa, wasiƙar da Anwar ya bari ce, ta kalli Khalil a razane ta girgiza kai tace  "A'a ban sani ba" Yace  "waye Anwar a gurinki? ' Tace " ɗana ne" "kina nufin bashi ya rubuta wannan takaddar ba?" Ta jinjina kai alamar eh, Khalil ya juya ya kira Murtalah, Murtalah ya fito ya tsaya, Khalil yace   "kotu na buƙatar ka gabatar da kanka, sannan ka faɗi abunda ka sani" Murtalah yace  "Sunana Murtalah, kuma ɗaya daga masu aiki a gidan Alhaji Nasir Daula, wata ɗaya zuwa biyu baya, naje ɗakin Anwar zan gyara masa, na ga ya bar wannan takaddar, na ɗauka na karanta na kaiwa mahaifiyarsa ba tare da na nuna mata na karanta ba, bayan na kai mata da yamma 'yarta Amal tazo zata fita tana ga sauri, bata sani ba seta yarda takaddar, nikuma na tsinta, kamar yadda ya rubuta a takaddar, tun daga wannan lokacin ba' a ƙara ganin inda yake ba ya bar gidan gaba ɗaya " Barrister Khalil yace "zaka iya komawa ka zauna" Yaje ya dudduba cikin takaddunsa ya ɗakko wani littafi, ya dawo gaban Hajiya Halima ya miƙa mata littafin yace  "wannan kamar littafin ɗanki me Anwar, na Jami'a ko?" Ta karɓa ta duba, ta jinjina kai, Khalil yace  "ki dubamin ko akwai bambanci tsakanin rubutun cikin wannan littafin dana takaddar gabanki?" Take ƙafafunta suka hau rawa, taji tana numfashi sama sama, ta tsaya tana rarraba ido. Khalil ya ɗau takaddar da littafin da takaddar, ya miƙawa Alƙali. Alƙali ya karɓi takadda da littafi, Khalil ya kalli Hajiya Halima yace " wane irin rashin gaskiya ne haka ɗanki yake tuhumarki dashi? Wanda yasa har ya bar gida?" Hajiya Halima tace "Ni babu wani rashin gaskiya da nake aikatawa fa, kawai maganace tsakaninsa da 'yar uwarsa akan abunda take aikatawa, da kuma zargin nafi fifita' yan uwansa akansa" Barrister Khalil ya jinjina kai yace  "shikenan zamu gani" Akace taje ta zauna, ta koma inda ta taso tana godewa Allah. Barrister Khalil yace  "ina neman wannan kotu ta bani dama, domin yiwa Babban Amini ga Alhaji Nasir wasu tambayoyi wato Alhaji Bukar Bulama!!!" Ayshercool 07063065680 12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 152_153 Suleiman yace "Yusuf ka kwantar da hankalinka, dama Allah ya ƙaddara hakan seta faru, ta wannan dalili naka, mudai fatanmu Allah ya baka lafiya ka warware" Yusuf yace "Ameen, nagode sosai Yallaɓai" Suleiman yace "bakomai Yusuf, Allah dai ya baka lafiya ya ƙara wanke mana kai daga sharrin maƙiya" Yusuf yace "Ameen ya Allah, to su lawyoyin da suka tsayamin sun sanni ne? Meyasa suka tsaya min, kuma meyasa basu taimakeni da farko ba?" "Yusuf, lokacin da ake maka shari'a ta farko, su Bulama sunyi mamaya ga wannan shari'a fiye da tunaninka, ta ƙarƙashin ƙasa aka bi aka dinga samo shedun nan fa, a yadda Khalil yake gayamin, Nurat ce ta takurashi akan lallai ya tsaya a fitar da kai, saboda tasan wasu daga abubuwan da mahaifinta ke aikatawa, to yazo dai ya kawomin ziyara, muka tattauna na gaya masa abunda nasani daga abunda Saleh yake zuwa yana gayamin, yayi duk binciken su daya dace na tallafa masa da abunda nasani, to su dai sauran lawyoyin bansan yadda akai ya samosu ba, nidai ya sanarmin zasu ɗaukaka ƙara, shikenan se ranar shari'a nima na gansu " Yusuf ya jinjina kai  yace " Alhamdilillah, Allah nagode maka " Suleiman yace" An gode Allah kam, ka kwantar da hankalinka, komai ze wuce insha Allah " Umma tace " dan Allah ka kwantar da hankalinka, sannan kai shiru da wannan surutun ka samu isashen bacci " Yusuf yace " to Umma " Har Yusuf yayi shiru, ya kuma cewa " Yallaɓai ya Widad fa? A wani hali take ciki? " Umma tace " Meka ce? " Yusuf yace   " cewa nayi a wani hali Widad take ciki? " A fusace Umma tace " waya san mata, baka da zuciya Yusuf, yarinyar tazo ta bada sheda akanka, bayan a dalilinta ka shiga halin da kake ciki, amma kana wani maganar tana ina, in sake jin kayi maganarta sena saɓa maka" Yusuf yai shiru, Amma yana tunanin shiya kuɓuta, to matarsa fa?. Widad kuwa tuni 'yan sanda sukaje suka ɗakko ta a gidan nan bayan an kama Bulama yaji matsa ya faɗi inda take, tana zaune a ɗakin da take, taji ana guje guje, ba inda ta iya motsawa daga inda take zaune, Sega' yan sanda sun shigo, suka ɗakko ta suka tafi da ita Asibiti, tayi baƙi duk ta kukkumbura, haka suka ɗakkota a gakabaice ga babu isashen Abinci da kulawa. 'yan sanda suka kama har wannan Sabuwar, wadda take kuka da Widad a gidan. Da aka kaita Asibiti ma, a emergency aka ajiye ta, saboda ciwon zuciya da jininta daya hau fiye da kima, ga dislocation data samu a hannunta saboda ball da Bulama yake da ita. Likitoci sun fara tunanin ko a cire mata cikin, saboda kar yai sanadiyyar rasa ranta, Amma Widad a wahal ce tace  "likita, dan Allah ka barmin cikina, gara in mutu dashi a jikina, dan Allah a bawa Yoseef haƙuri, na bada sheda ne dan in ceci rayuwarsa, amma nasan ya bani gudunmuwa, dan Allah ya yafemin, nagode Allah tunda ya kuɓuta" Haka taita surutai, seda aka mata Allura sannan bacci ya ɗauketa, ta ɗau tsawon lokaci tana wannan baccin, kafin ta farka sedai ga mamakin su, bayan ta farko jininta ya sauka ba kamar da ba, suna yi suna monitoring ɗin yanayin jikinta, da kuma probability na surviving ɗinta da wannan cikin.    Sedai babu kowa a gurin Widad, musamman mace wadda zata dinga kula da ita, Nurses ne suke mata komai, nan ta sake kukan rashin dangi, da tana da dangi da an samu me kula da ita.     Ramlah gaba ɗaya itama a zabure take, mutuwar Anwar ta da keta, bata taɓa zaton dagaske Bulama yasaka a kashe Anwar ba, gashi 'yan sanda suna kama mahaifiyarsu, ga Amal ita bame hankali ba ita ba mara hankali ba, haka suke zaune gaba ɗaya rayuwa ta juya musu baya. Seda Yusuf ya kwan tara a Asibiti, ana masa screening daban daban dan tabattar da ingancin lafiyarsa, Yusuf ya ɗan murmure sakamakon Abinci da kulawa da yake samu, kullum se an dafo Abinci daga gidan Suleiman an kawowa Yusuf, ya ɗan farfaɗo sedai uwar rama da yayi. Aka sallameshi daga Asibiti, tare da magunguna zuwa gida, tunda suka koma gida 'yan jaje ke sintirin zuwa gidan nan, wasu dan suyi jaje wasu dan suyi kallo, sedai Yusuf ko tsakar gida baya fitowa saboda baya san Hayaniya. Abokan Aikinsa suka yi tawaga guda sukazo duba Yusuf, seda wasu suka yi kukan farinciki, dukda miskilancin Yusuf, amma akwai kirki da girmama mutane, duk wanda ya ganshi se yayi mamakin ramar da yayi. Ɓangare guda kuma, hankalin Yusuf yana kan ta ina zega Widad, a wani hali take ciki? Seda Widad tai sati biyu a Asibiti, cikin ikon Allah ta murmure, jininta ya sauka amma an kafa mata sharaɗin idan ta tashi haihuwa ta taho Asibiti, saboda tana cikin hatsari karta ce zata haihu a gida, dama tunda aka kai Widad Asibitin kullum 'yan sanda cikin patrol suke a Asibitin, har zuwa sallamarta da akayi. Da aka sallameta ma headquarter na' yan sanda aka tafi da ita, domin amsa wasu tambayoyi da za'a mata, gaba ɗaya saboda yadda akayi shari'ar Yusuf da yadda abubuwa suka wakana, an sauya manyan shugabbani dake riƙe da manyan muƙamai a hukumar, duk an canza wanda Bulama ya siye da wasu. Widad ta faɗi yadda komai ya faru, tun daga kan kisan mahaifiyarta, da irin Abubuwan da Bulama ya dingayi, ba tare da yasan tasan shine Bukar ba, har sace ta da akayi tare da Yusuf, ta nuna musu inda aka harbeta a hannu, da yadda Yusuf ya dinga wahala da ita, ƙarshe seda aka kamo doctor Hamisu wanda yake mata allurar hauka, da sauran wanda suke da hannu a miyagun laifukan ta'addanci da aka dinga aikatawa Daula da iyslinsa, Shima Saleh can aka samoshi a wani Asibitin gwamnati babu kulawa, saboda garin dukan daya dinga sha ya samu rauni a hantarsa. Widad bata da gurin wanda zata ta zauna, Akace a kaita gidan gwamnati fa zauna, kafin Allah ya bayyana mahaifinta, tace ita gidan gonar nan zata je ta zauna, akace baze yuwu ta zauna ita kaɗai ba, Amma Widad ta dage ita babu gidan wanda zata ta zauna, aka ajiye jami'an tsaro a layi da kuma cikin gidan dan tsaron lafiyarta aka barta ta zauna ɗi . Widad Ta dinga tunanin ya akayi Yusuf be nemeta ba, dukda yayi free yanzu, sedai tayi tunani babu lallai Yusuf ya sake karɓarta, bayan ta gaza taimakonsa a lokacin da yake buƙatar hakan. Gaba ɗaya gidan ya canza, babu manyan dawakan nan nata, da wasu daga dabbobinta duk babu su, haka manyan motocin dake gidan duk babu, an kwakwance wasu abubuwan masu mahimmanci daga gidan, taga gidan ya mata faɗi, babu Daddy babu kowa a tare da ita yanzu. Ta zauna tai shiru tana tunani, ta fito harabar gidan tana zagaye, ma'aikatan se zuwa suke suna mata fadanci, suna mata jaje tare da barka da Arziki, ta kira wani daga cikin ma'aikatan gidan Imrana, yazo gabanta ya durƙusa tace  "naga gaba ɗaya gidan nan ya canza, ina wasu daga cikin dabbobina da motocin duk da suke cikin gidan nan?" Imrana yace  "ranki ya daɗe, Hajiya ce take turowa a ɗiba a fita dasu, kuma bamu da ta cewa" Widad ta jinjina kai tace  "shikenan jeka" Haka ta dinga zaga gidan, tana tuna abubuwa da suke shuɗe, da abubuwan da suka faru daren da akayi garkuwa dasu, ta shiga ɗakin data kwanta a ranar, tana dube dube, can ta hango wayarta guda ɗaya a ƙasan gado, Da daddy yazo ya azalzaleta ta tashi ta fito wayar ta faɗa ƙasan gado, ta ɗau waya ɗaya ta fita, waya ɗayan da yanzu bata san a inda take ba, ta ɗakko wayar ta ganta a kashe, ta jona a jikin caji aikuwa ta kama. Ta jona wayar ta koma ta zauna, a hankali tace  "Yoseef am missing you, i have no one, help me to relay on you, ka yafeni ka dawo gare ni mana" Ta yanke shawarar komawa tayi zamanta ita kaɗai, ta cigaba da Addu'a Allah ya bayyana mata mahaifinta, kota rage wata damuwar, amma da kunya a gareta ta tinkari Yusuf a yanzu. Gaba ɗaya damuwa da kaɗaici suka baibayeta, ta fito ta ɗau mota zata fita ɗaya daga cikin 'yan sandan dame gadinta yazo yace  "ranki ya daɗe, ina zakije ne haka?" "Fita zanyi" ta bashi amsa Yace "ranki ya daɗe har yanzu kina ƙarƙashin kulawar' yan sanda ne, idan kika fita ke kaɗai hakan ze iya zame mana laifi a sama" Widad tace "shikenan, dan kuna gadina bazan fita ba? Da can wake kula dani idan ba Allah ba? Ina kuna garin nan da saninku aka siye wasu daga cikinku akaci zarafin mijina, aka sacemu babu wanda yai yunƙurin kawo mana ɗauki, se yanzu zaka zo kana gayamin zancen banza? Ban fidda ran a sake dawowa a haɗa baki daku a cuceni ba" Ɗan sandan yace " Allah ya temakeki, kiyi haƙuri kin san duk yadda kaso ga kamanta gaskiya, se an baka umarnin aimata wani abun daga sama kafin kayi, amma dan Allah kiyi haƙuri karki fita ke kaɗai, dan Allah ki rufamana Asiri, za'a iya ladabatar damu idan mukayi sakaci wani abun ya same ki, har yanzu kina ƙarƙashin kulawar jami'an tsaro ne" Ta jefa masa key ɗin mota tace  "kaini gidanmu, inda muke zaune" Ɗan sandan ya ɗauki key ɗin, yana mamakin wannan izza ta Widad, ta shiga bayan mota ta zauna, ta tuna idan Yusuf ze fita da ita, a gaban mota take zama, suna tafe wataran tana zazzaga masa masifa, ko kuma yana wani abun da ze bata haushi suyita faɗa. Ta lumshe idonta tana jin yadda sonsa ke ƙara ratsa ilahirin gaɓoɓin jikinta, se yanzu ta yadda so babbar cutane, bata taɓa tunanin haka yake ba, bata zaci tayi sabo da Yusuf haka ba, tana jin ya zama wani ɓangare na rayuwarta gaba ɗaya, kobe nemeta ba doke ita ta nemeshi. Suna zuwa ƙofar gidan, tace ya tsaya yayi horn, yai horn aikuwa Isa yaeƙo yaga waye, kawai ya hangi Widad a bayan motar, aikuwa ya gigice ya tafi da gudu ze buɗe Gate, ya dawo ya kuma komawa ya rasa mema zeyi. Widad ta sauke gkass ɗin motarta tai masa nuni da yazo, ya taho da sauri jiki na ɓari yazo ya durƙusa yana faɗin  "Allah ya temakeki, Allah ya tsare ki sharrin maƙiya" kawai ya fashe da kuka ya kasa cigaba da maganar. Widad tace  "Lafiya kuwa? Me yasaka kuka kuma?" "ranki ya daɗe dole inyi kuka, tunda kika tafi babu ke babu Yallaɓai, gaba ɗaya gidan annurinsa ya ɗauke, muka shiga mummunan yanayi, katsam kuma se gashi kun dawo amma ba'a yadda akeso ba, a wani yanayi na daban abubuwa sun faru marasa daɗi ranki ya daɗe Alhamdilillah tunda dai kin dawo kuma kin kuɓuta " Widad tace " Isa dukda mugayen halayena da kuke faɗa, dama zaku iya shiga damuwa dan na bar gida? " Isa yace " A'a a'aha, ai ranki ya daɗe Hausawa sukace kada Allah ya kawo ranar yabo, amma wallahi zamanki a gidan nan ba ƙaramin haske bane, mungode Allah" Widad tace "shikenan, kiramin su Nura da Murtalah" Yace "ranki ya daɗe, bazaki shiga gidan bane?" Tace "Eh, kiramin su" Isa ya zabura da sauri hadda gudu, ya shiga gidan yana ƙwalawa Su Nura kira. Aikuwa gaba ɗaya suka rankayo suka biyo shi, suna zuwa suka ga Widad bakinsu yaƙi rufuwa, suka zube a gabanta suna surutai kowa da abunda yake faɗa. Haka nan Widad taji ƙwalla ta rasa ta mecece? Tai murmushi tace  "Nagode Allah, tunda duk kun tsallake tarko da sharri na Bulama, naji daɗi Sosai da gudunmuwar da kuka bayar a kotu, gurin kuɓutar da mijina, nagode muku sosai Allah yasaka da alkhairi" Murtalah yace  "wai dagaske ranki ya daɗe Yusuf mijinki ne?" Abun mamaki wai yau Widad na hira da maa'ikatan gidansu, matar da ko murmushinta ba'a gani idan ba na mugunta ba, ko tana gaban mahaifinta ba. Widad tace  "Eh mijina ne, ko akwai magana ne?" Murtalah yace  "A'a, abunne da mamaki sosai ranki ya daɗe" Widad tace  "IKone na Allah kawai, naji daɗi Sosai da kuka temaka da sheda a kotu" Murtalah yace  "Ai bakomai ranki ya daɗe, Yusuf mutum ne ya cancanci a temaka masa, tunda na tsinci takaddar nan na rasa ina zan kaita, saboda barazana da akewa duk wanda yai yunƙurin temakawa Yusuf, katsam sega lawyern Yallaɓai, ya gayyacemu gidansa a ɓoye yai tattaunawar sirri damu, a nan na bada wannan takaddar " Widad ta jinjina kai tace " Masha Allah, ina godiya sosai da gudunmuwar ka, kuma insha Allah kuna da tukuici akan wannan gudunmuwar da kuka bamu " Nura yace " Allah ya temakeki, wai yanzu dama duk abubuwan nan Alhaji Bulama ke shirya su, tabbas banga laifinki ba na ƙin mutane da kike, amma abun ya bamu mamaki sosai " Widad tai murmushin takaici, har bata son yuna irin azabar da suka sha, tace " ya ake cikine? Me gidan namu yake ciki dan bazan shiga ba" Nura yace  "ranki ya daɗe, gida babu daɗi dan ya watse gaba ɗaya, bayan ɓatanku, Yallaɓai ya faɗi yai wata rashin lafiya, babu me zuwa gurinsa ko kula dashi se Anwar, shine yake masa komai yake jinyarsa, da aka sace Yallaɓai a gadon Asibiti ma aka kama shi, akace  da saka hannunsa ya sha wahala sosai, Amma ya kula da Yallaɓai " Jiki a sanyaye Widad tace " Allah sarki Anwar, yana gidan ne yanzu haka? " Su Isa suka kalli Juna, jin bata san meyafaru ba. Isa yace " ranki ya daɗe, Amma kin san an kama Hajiya ko? " Tace" Eh na sani " Yace" to dama ya bar gida ai tuntuni, takaddar daya bari ai ita Murtalah ya tsinta, ranar da aka yi zaman ƙarshe a kotu, muna nan 'yan sanda suka zo a motoci suna ta jini ya, na buɗe musu gate sukazo suka shimfiɗe Anwar, an gano shi a wani gida yake rayuwarsa yana kasuwanci a can cikin Jos, aka kawo shi an kasheshi ta hanyar caka masa makami a gefen cikinsa, sedai babu wanda yasan wanda ya kasheshi, amma a ranar kukan da Hajiya Halima take kamar dasa hannun shi Bulaman dai a kisan" Ai tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta dinga jujjuya kai tana maimaita innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Ya Allah, Yaya Anwar ubangiji Allah ya jiƙanka, naso na sameka a raye in maka godiya riƙemin amana da kai, amma zan dawwama yi maka Addu'ar samun salama a kabarinka, kana daga cikin mutanen da bazan manta dasu ba a rayuwata, Allah ya yafe maka Yaya Anwar" Kuka yaci ƙarfin Widad, yayin da suma duka jikinsu yayi sanyi sukaji mutuwar tamkar yanzu akayi ta. Widad cikin kuka tace   "Murtalah ka sameni a farm House gobe in Allah ya kaimu da yamma, nagode muku Allah yasaka da alkhairi nagode sosai" Ta kasa ko rufe ƙofar motar, se kuka da take yi, Isa ya rufe mata ƙofar motar, ɗan sandan nan ya ja suka tafi, suna tafe tana kuka, dan Mutuwar Anwar ta da keta fiye da tunani. Yusuf ya ɗan warware, Suleiman ya kwashe su a mota domin sujewa Nurat gaisuwa, da yake an kwana biyu da rasuwar mutane duk sun watse se tsilla tsilla. Kahlil yai musu iso har wani katafaren falo, aka kira Nurat, Nurat ta fito cikin Ƙaton hijjabi, tana ganin Yusuf ta kasa magana se hawaye haɗe da murmushi daya ƙwace mata. Ta durƙusa har ƙasa ta gaida Umman Yusuf, Yusuf yace "Nurat ya ƙarin haƙuri kuma?" Nurat tace "Alhamdilillah" "Allah ya jiƙanta yasa ta huta" Nurat tace "Ameen" Nan duk sukayi mata gaisuwa, Umma tace  "dama munzo muyi miki gaisuwa ne, kuma zamuyi zuwa na mussman muyi miki godiya ' Yusuf yace  " Nurat, ban san me zance miki ba, wanda ze nuna irin tarin godiyar dake bakina ba, a sanadiyata ga abubuwa marasa daɗi sun faru dake, Nurat dan Allah kiyi haƙuri, ban san mema zance ba" Khalil yace "karka damu Yusuf, dama haka Allah ya ƙaddara seya faru, ba kaine sila ba, Allah ya riga ya rubuta hakan dama, sedai kam tabbas tayi faɗi tashi a kanka sosai, tun daga ɓatanku har wannan lokacin" Umma tace  "mungode, mungode Allah ya saka miki da alkhairi, Allah yayi miki Albarka ya jiƙan mahaifiyarki" Nurat ta dinga jinjina kai, tana tuno Mummynta, ta kalli Yusuf tace  "Kasan kuwa an kashe Yaya Anwar?" A razane Yusuf ya kalleta yace  "wane Anwar ɗin wai?" Ta goge Hawaye tace  "Bayan ɓatanku, Daddyn Widad faɗuwa yayi, ya fara rashin lafiya babu kowa a gurinsa babu me zuwa gurinsa , Anwar ne kawai yake gurinsa, ya dinga jinyarsa tsawon lokaci, bayan wani lokaci aka sace Daddyn Widad a Asibiti, aka kama Anwar ya daɗe a tsare ya sha wahala sosai kafin ya kuɓuta, to kwanan nan dai Brother ya cemin ai Ya bar letter a gida, ya bar gidan gaba ɗaya ba'asan inda yake ba, ranar da aka gama shari'arka akace an kashe shi kuma ana zargin Bulama ne yasaka " . Umma ta dafe kai tana faɗin innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yayin da Nurat ta sake fashewa da kuka. Khalil yace  "se haƙuri, da kuma mu taya su da Addu'a, Wannan me aikin gidan ne Murtalah, ya tsinto takaddar, ban san ya'akayi yai kyan kai ya kaiwa Barrister Hafiz ba, dan abun zamana yayi duk wanda yai wani yinƙuri na temakawa a gano gaskiyar lamarin, se an bishi da mummunar barazana, mutumin nan maƙurane gurin zalunci" Umma tai shiru tana hawaye, tana jinjinawa zaluncin Bukar, musamman Da taji wai ashe Anwar ɗane a gurinsa. Nurat ta kira Yayar mahaifiyarta suka gaisa da Umma, sun daɗe suna hira suna jajantawa juna, yayin da Suleiman da Khalil ke hira. Nurat tai shiru a gefe, tana kuka Yusuf yai ƙasa da muryarsa cike da tausayinta yace  "Light am very sorry, kiyi haƙuri da ƙaddarar data same ki a sanadina dan Allah" 'Nifa ba kaine silar faruwar haka a gareni ba, dama Allah ya ƙaddaramin haka zata faru dani ne " " Bazaki dinga kallona da abunda ya faru ba, koki zargi saboda ni haka ta sameki ba? " Ta jinjina masa kai alamar eh, Yusuf yace " Nagode sosai, Allah ya jiƙan Mummy ". Nurat tace " Ameen, naji ance an kaika Asibiti ya jiki kuma? " Yusuf yace " jiki Alhamdilillah, mungode Allah " " Allah ya kiyaye gaba, se nazo maka jaje " Yusuf yace "A'a ni yakamata in sake dawowa in dubaki in sake miki ta'aziyya, Allah ya baki haƙurin jure rashin Mahaifiyarki" Ta jinjina masa kai tana kuka, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi sosai, ya cigaba da rarrashinta, Umma ta fito ta tarar dasu tace  "mu tafi ne ka taho kokuwa?" Yusuf yace "A'a tare zamu tafi" Ya miƙe Nurat ta rakosu har bakin mota, Yusuf yana ta sake bata haƙuri yana mata gaisuwa. Suna tafe a motar, Yusuf yayi shiru yana tausayin Nurat, ga mutuwar Anwar data gigita shi, ga yana son ganin Widad. Can yaji Umma tace  "gaskiya Yarinyar nan tana da nutsuwa da tarbiyya, na yaba da hankalinta gashi ta bani tausayi Yusuf, nikam ko zaka nemi Aurenta idan zasu baka?" AMANA! AMANA! AMANACE!!! IDAN KIN FITAR ALLAH NA KALLONKI AYSHERCOOL 07063065680 12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 154_155 Gaban Yusuf yai mummunar faɗuwa jin abunda Umma tace, ya kalli Ummansa ta Mirror, amma yai shiru yaƙi cewa komai sema ɗauke kansa da yayi yana kallon waje. Umma tace  "ya Kay shiru ba kace komai ba?" Ƙin magana yayi, dan bayama son zancen, Umma tace  "Suleiman, dan Allah baka yaba da hankalin Nurat ba? Yarinyar tana da nutsuwa da kuma kirki sosai" Suleiman yace "tabbas hakane Umma, ni kaina na yaba da nutsuwar ta, kuma da alama dai Yusuf akwai dalilin da yasa ta dage ta temake ka" Umma tace  "jimin yaro da wulaƙanci, ana masa magana yayi shiru, kamar ba dashi ake ba" Yusuf yace "Umma me zance ne? Nifa ina da Aure ya zanyi da Widad kuma?" "Karka ƙaramin zancen wannan yarinyar, wadda bata san halcci ba bata san abun alkhairi ba, kai ko zuciya baka da ita, duk wannan abunda ya sameka sanadinka baze zame maka darasi ba Yusuf, irin wahalar da ka sha, ba kai kaɗai ba harni kaina da sauran mutane, amma kake ƙara nanata wai kana da Aure, toni ban san da wannan Auren ba, ba wani Aure da kake da shi, ni dai ga yarinyar da ta kwantamin" Yusuf yace "Umma, Widad bazata bada sheda haka kurum ba, akwai wani dal..... " Rufemin baki, bana son jin zancen yarinyar nan gaba ɗaya, na gaya maka " Yusuf yai shiru, ya maida idonsa wajen window, yana tunanin yaze da Umma akan Widad, gashi yana son ya haɗu da ita yana son su gana, amma Umma tana nema ta ɓata komai, kuma yaga alamar idan ya matsa, ze ɓata mata rai, shi kuma babban abunda baya so kenan, ɓacin ranta. Haka Umma da Suleiman suka cigaba da hira har sukaje gida, ba tare da Yusuf ya tofa ta bakinsa ba, yai shiru dan bema san me suke cewa ba. Suna zuwa gida Yusuf yaiwa Suleiman sallama ya shige gida abunsa, Umma kuma seda tayi sallama da Suleiman sannan ta shiga gida. Widad kam sosai take jin mutuwar Anwar, ji take kamar mutuwar Anwar wani babban giɓine a gareta, dukda ba ɗan uwanta ne na jini ba, amma Anwar zuciyarsa ba irin ta mahaifiyarsa bace ba. Tai kuka, tai kuka ƙarshe taje tai alwala ta tada salla mussman dan taiwa wanda ta rasa addu'a, ƙarshe ta ɗaga hannu zata yi Addu'a, ta kasa roƙar komai kawai ta fashe da kuka, "Allah ka yafemin laifukana, Allah na tuba ka yafeni, Ba Ammina, ba Daddyna, Ba Yaya Anwar, wanda nake sa ran zeji ƙaina maƙiya sun sa na masa abunda bazan sake kima a idonsa ba, ban san dangin mahaifina ba ban san na mahaifiyata ba, bani da wanda zan kalla a rayuwata inji sanyi, babu me raɓata babu wanda zan raɓa, Allah ka kawomin ɗauki " Ta ƙarasa maganar tana rirriƙe gado da gefenta tana wani irin kuka me raunata zuciya, idanunta sukayi jawur ta fita hayyacin ta, ta rasa abunda yake mata daɗi, gashi har yanzu da tsoron mutane a ranta, tana jin tsoron raɓar wani, bata san meza'a kuma yi mata na cutarwa ba, ta fara tunanin ko ƙauye zata koma gurin Gwaggo? Wata zuciya tace "suwaye a gareki? Suba danginki ba, wane karɓa zasuyi miki bayan suna zaune an tayar musu da hankali, hadda 'yan sanda ta yaya zasu sake karɓarki? Idanma zasu karɓekin kin san hanyar da za' abi aje a garin? ' Lumshe idinta tayi, hawaye na zuba daga idonta, tana jin yadda take sauke numfashi da ƙyar, alamun zuciyarta bata aiki yadda yakamata. Ta takure a jikin bango, ta haɗa kai da gwiwarta, tana ci gaba da kuka, sanyin AC dake ratsata taji sanyin da take ji yayi mata yawa, nan da nan jikinta ya ɗau rawa, ta dinga rawar sanyi, kanta na wani irin sarawa amma ta kasa motsawa daga inda takey, ƙarshe ma ta haka ta kwanta a gurin, tana jin cikinta na motsawa, ta tuna Yusuf be san da cikin bama, ta shafa cikin a hankali tana tausayawa abunda ke cikin nata. Amal ta ɗan farfaɗo, sedai befi tayi magana kaɗan a rana ba, bata magana sam seda ƙyar, gaba ɗaya ta ɗashe ta bushe saboda azabar bleeding da tayi, ga fargaba da tashin hankali da take ciki na kama Mummynsu, ga mutuwar Anwar da damfarar ta kuɗin nan da akayi, gashi har yanzu raɗaɗin fyaɗen da Alhaji Haruna ya mata yakasa barin Ƙwaƙwalwarta, dan haka abun ya mata yawa, ta samu depression, Ramlah ce ke kula da Ita take jinyarta, taga abun nata bana ƙare bane, ta ɗauketa ta kaita Asibiti. Likita ya dubata, ya rubuta musu teses, ta kaita lap akayimata, suka kaiwa Likitan, ya karɓa ya duba ya kalli Amal yace  "ƙanwata, gayamin tsakaninki da Allah ƙanwata meyasameki kike bleeding haka?" Amal ta kalli Likitan, ta sunkuyar da kai se hawaye, Ramlah tace  "doctor, ba lallai tayi maka magana ba, saboda tunda akayi mana rasuwa batavda sukuni, bata magana se kaɗan kaɗan, Fyaɗe akayi mata, harta samu ciki, shine taje ta zubar da cikin jini ya ɓalle mata yaƙi tsayawa" Likitan yace "waye yayi mata fyaɗen?" "Wani mutum ne" Ramlaj ta bashi amsa. Yace "kuma an kai shi gaban hukuma da yayi mata fyaɗen?" Ramlah tace  "doctor, bamu da wannan lokacin yanzu ma baka san da yadda na kawota ba, kawai ai mata abunda ya dace" "Amma kun san illar dake tattare da ayiwa mace fyaɗe aja baki ayi shiru ba tare da ɗaukaf mataki ba, ba hujja bace a ɓoye irin wannan lamarin dan gudun jin kunyar mutane, ki tsaya ki ƙwaci haƙƙinki shine yakamata, yanzu yaushe abun ya faru? Kuma da ya faru an kaita Asibiti an mata gwaje gwaje ne? " Ramlah tace " dan Allah ke dena wannan tambayoyin, kawai ka rubuta mata magani a wuce gurin " Ya ɗan taɓe baki yace " Any way, tunda haka kuka zaɓa zan miki bayanin sakamakon gwaje gwajen da mukayi, wannan abortion ɗin da tayi, an mata amfani da pills me ƙarfi wanda yafi ƙarfinta sosai, musamman duba da yanayin rukunin jininta, hakan ya samar da gagarumin rauni a mahaifarta, wanda yasa take ta zubar da jini, mahaifarta tayi raunin xa abune mawuyaci ta sake ɗaukar ciki, sedai idan an kaita India anyi mata aiki, akwai wani ƙwararren gynecologist dayake aikin, sannan a shawarce yana da kyau a dinga kaita tana ganin Likitan Ƙwaƙwalwa, saboda wannan depression ɗin ze iya zame mata hauka tuburan, duba da yadda matakin depression ɗin nata yayi worst " Ramlah tace  " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yanzu nawane kuɗin aikin zeci? " Ya kashingiɗa a kan kujerarsa yace " idan kun shirya kumin magana, baya cin fiye da naira miliyan uku haka, ko yanzu idan a shirye kuke, za'a iya booking na jirgi ku tafi" Ramlah ta dafe kai, dan babu inda zata samo wannan kuɗaɗen, komai ya ƙare musu, basu da komai yanzu a kangon gidan kawai suke, gashi taji labarin Widad na Farm House dan haka a tsorace take, kar Widad tazo ta fatattake su koma tace a kamasu. Ramlah tace "thank you very much doctor, when we are ready, we will let you know" Likitan yace "shikenan, ba damuwa Allah ya bata lafiya" Ramlah ta kama hannun Widad, suka fito suka hau motar da ta rage musu zuwa gida, haka suka koma Ramlah ta saka Amal a gaba tana kallonta, yanzu ita kaɗai ta rage mata, ba Mummy, ba Anwar, ita kanta bata da tabbacin zata tsira, har gara Amal ita ba lallai a sameta da wani laifi ba, gashi itama Amal ɗin ta zama shiri shiri, Ramlah ta rasa abunyi, taje ta ɗakko kayan shaye2 ta ɗurawa cikinta, seda taji tayi dam sannan ta baje tana bacci a gurin. Kamar yadda Widad tace wa Murtalah tana son ganinsa, haka akayi yaje gidan gona dan ya sameta, amma 'yan sandan da suke gadinta suka hanashi shiga, seda sukaje suka sameta suka gayamata zuwansa, sannan tace a barshi ya shigo tasan da zuwansa. Har falon ya shiga ya zauna, ta fito cikin dogon hijjabinta, Murtalah a ransa yace  "iko se Allah, wai yanzu Widad uwar tsiwa, gadara ganioda izza itace a haka? Itace yanzu take komai sanyi sanyi, harda shigar zumbulelen hijjabi haka, lallai tayi darasi na rayuwa a makarantar duny, me cike da ƙalubale da tarin matsaloli, ya ga yadda ta sake ramewa, se kumburi a fuskarta, duk ƙibar nan babu da da aukinta, amma yanzu kamar sillen kara haka ta koma. Ta ƙaraso ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon, gaba ɗaya a takude take saboda zazzaɓine ma a jikinta, ga jira dake kwasarta dan tun safe tea ne kawai a cikinta se biscuit, bata da appetite na cin komai sam.. Murtalah ya zube a ƙasa yana  "barka da yamma ranki ya daɗe" Tace "yawwa kana lafiya?" "lafiya ƙalau Alhamdilillah ranki ya daɗe" Widad tace "masha Allah, na kiraka ne nan dan muyi magana, zan saka wani aiki ne, amma kafin nan bani labari, wane hali gidan mahaifina ke ciki?" Murtalah yace "eh to, kamar dai yadda kika sani, an kama matar gidan saboda da haɗin bakinta Alhaji Bulama yake gudanar da wasu abubuwan, ita kuma Amal mamar hankalinta ya gushe, tunda aka kawo gawar Anwar, aka kama mahaifiyarsu ta faɗi shikenan, ko magana bata son yi, kamar dai ta samu matsala a Ƙwaƙwalwarta ne, ita kuma babbar dama tun bayan ɓacewarki take bin wannan ɗan gidan Bulaman, to a yadda muke ganin abubuwa na gudana ma dai, shaye2 take yi dan wataran mankas haka take dawo mana gidan nan, yanzu dai su biyune kawai a gidan ba kowa " Widad ta jinjina kai tace " Allah sarki, Allah me yadda yaso, anyi ƙoƙarin ƙaƙabamin hauka tuburan ga haauka ya fara bibiyar 'ya' yanta, an haɗa kai an kashemin mahaifiyata, se gashi itama an sa an kashe ɗanta, shi kuma wancan ya kashe matarsa da hannunsa, haƙƙinmu baze taɓa barinsu jin daɗin duniya ba" Widad tai maganar tana share hawaye, Murtalah yace  "ayi haƙuri ranki ya daɗe, ai an gode Allah an auna Arziki sosai, Amma dama ita tasa aka kashe mahaifiyarki?" "karka shiga hurumin da ba naka ba, ka tsaya iya matsayinka, ina son in dinga sanin duk wani motsinsu, da duk wani abu dayake kaiwa yana komowa a gidan ka dinga sanarmin, tashi ka tafi" Murtalah ya miƙe yana godiya, harze fita tace  "ya batun salary ɗinku? Ana biyanku kuwa?" Yace "ranki ya daɗe, ai se muyi wata biyu kafin a bamu albashin ma, kuma duk anbi an rarrage mana albashin" "Kuyi lissafin abunda kuke bi na bashi, zan biya ku ruɓinsu biyu insha Allah" Murtalah ya zube a gurin yana   "Allah ya temakeki, Allah ya baki yawan rai yasa kifi ƙarfin maƙiyanki" Widad tace  "Ameen" Yana fita itama ta fito, ta kira ɗan sandan nan daya kaita gidansu jiya, ya taho jikinsa na tsuma ya gurfana a gabanta, ta kalleshi tace  "kasan gidansu Yoseef?" Yace "A'a ranki ya daɗe" Tace  "ina son saka ka aikine, kaje ka bincikamin inane gidansu, ina son in dinga sanin duk wani moves ɗinsa ne, ina son dinga sanin halin dayake ciki" Yace "to ranki ya daɗe, zan ƙoƙari in gano gidan nasu, amma kin san bani da damar da zan bari gidan nan, in koma unguwarsu saboda a nan aka ajiyeni inyi aiki" "karka damu, akwai tukuici me kyau, sannan babu wanda ze zargeka akan hakan, zan baka kariya ince nine na saka aikin" Yace "shikenan ranki ya daɗe, amma ki sanar da shugaban mu" "baka da matsala" Yusuf jikinsa yayi kyau sosai, ya farfaɗo daga wannan uban baƙin da yayi kamar bashi ba, saboda samun sassauci da yayi daga ƙangin zaman gidan kurkuku, sedai Umma na cigaba da damunsa akan lallai yaje ya nemi Auren Nurat, yace  "Umma, kina cewa inje in nemi Auren Nurat, idan fa na nemi Aurenta dole za'azo bincike wataran, bana son abunda ya faru dani akan Salma ya sake faruwa, ga kuma abunda ya faru da iyayenta saboda ni, ina jin tsoro Umma, amma kinga Widad tasan koni wayey, tasan Halinda nake ciki amma muka zauna tare a haka, ba tare da ta nuna ƙyamarta a gareni ba" Umma tace  "kaga sauraramin, Itama Nurat ɗin zata iya aurenka ai, yarinyar bata da matsala kuma banga alamar wulaƙanci a tare da danginsu ba, nifa wannan Widad ɗince bana so, abun da ya samemu saboda ita bazan taɓa mantawa ba, duk wannan baƙar azabar ka shata ne saboda ita fa, amma baka gani " Yusuf yace " Umma, Widad abun tausayi ce, baki san abunda ya faru da ita bane, ni kaina nasa.... Umma ta katseshi ta hanyar cewa "ban san abunda ya faru da ita ba, kuma bana buƙatar in sani, tun wuri ka kiyayeni akan wannan yarinyar, ita 'yar masu kuɗice ka barta taje, taimakon daka mata Allah ya amfana, kaima ka rungumi talaucinka, kuma idan ka sake ka taka kaje inda take zakaga yadda zanyi da kai, kalli dukda kayi free ai yakamata ko dubaka tazo tayi amma ba ita babu dalilinta" Yusuf ya rasa yazewa Umma ta fuskance shi, Yasan dole Umma zataji babu daɗi saboda yadda take ƙaunarsa, amma Widad taje ta bada wannan shedar, amma taƙi bari ya gayamata abunda yake faruwa, wanda ita bata sani ba. Babban abunda ya bawa Umma mamaki, be wuce yadda Yusuf ya ɓata rai ba, duk laifin da zeyi tai masa faɗa baya fushi, amma ƙarara a fusakrsa wannan karon, ya nuna beji daɗin hukuncin data yanke ba, ta dinga binsa da kallo, yai shiru bece komai ba. Umma tace  "yakamata kuma kaje ka sake yiwa Nurat gaisuwa" Yusuf yace 'to, zanje insha Allah " Ramadan yaji takaici jin labarin mahaifinsi ne ya dinga shirya duk wata manaƙisa akan Daula, dukda tarin alkhairansa a gareshi, babban abunda ya daɗaɗa masa rai kuma shine ba' a samu mahaifiyarsu da cutar HIV ba, amma yana ta sake zullumi akan ance su koma bayan watanni uku a sake yi. Ramadan yace  "Umma, yanzu shikenan Daddy ya lalata rayuwarsa, mu kuma ya bar mana abh mafi muni da abun kunya, ban taɓa jin labarin mutum me butulci kamar mahaifinmu ba" Hajiya Sarah tace  "bari kawai Ramadan, ni kaina nayi haƙuri da shi tsawo shekaru na masa biyayya iyayi na, amma ban taɓa zaton yanawa Daula zagon ƙasa haka ba, dukda wasu lokutan inajin haushin Widad, amma tabbas mahaifinku ya zalunceta, zalunci me muni ina fatan Allah yasa bani da wannan cutar, shi kuma yaje can yaƙarata, ya girbi abunda ya shuka ' Iman tace "waini Mummy, Yaya Fahad baze zo ya duba ki bane? Tunda muka taho Adamawa be neme mu ba, kuma a waya ba wanda ya kira fa" Hajiya Sarah tace "ƙyaleshi kawai, ki rabu da shi, aini Na zubawa sarautar Allah ido kawai, nasan zaluncin da mahaifinku ya aikata muma se hakkin ya shafemu" Ramadan yace "karkice haka Mummy, ai Allah baya kama wani da laifin wani, dan haka kiyi hakuri Allah ya yafe mana kurakuranmu" Suka amsa da Ameen gaba ɗaya. Ramlah ta farka daga uban baccin da take n shaye2 da tayi, lokaci ya ƙure tana wannan baccin, amma still damuwar dake tattare da ita bata sake ta ba, ji tayi ma kamar an ƙara mata wata damuwarne, akan wadda take ciki. Ta miƙe a hankali amma bata ga Amal ba, tayi zaton ko tana ɗakinta ne, ta tafi ɗakin nata, ta duba amma nan ma bata ciki sam, ta sakko ta fito harabar gidan ta tarar masu aiki suna wa Amal fifita. Ta taho da sauri tace  "lafiya kuwa?" Isa yace  "wuƙa ta ɗakko ta fito da ita, tana yunƙurin kashe kanta, da ƙyar muka ƙwace wuƙar, shine ta faɗi ta suma" Ramlah ta ƙarasa ta ɗago Amal tace  "why Amal Why? Why will you attempt to kill yourself, why do you attempt to murder yourself? Haba Amal" Ta kalli Nura tace ya kawo mata ruwa, ya kawo ruwa aka dinga shafawa Amal ɗin, can taja ajiyar zuciya ta buɗe ido, Ramlah tace  "Amal meyasa zaki yunƙurin kashe kanki? Komai yai zafi maganinsa Allah" Cikin kuka Amal tace   "Mummy, Mummy na, Yaya Anwar, dan a kainin inga Mummy i love hery, she's my Mum, dan Allah kice ayi haƙuri bazata sake ba, ina son in ganta" Ramlah ta rungumeta tana rarrashinta, tace  "kiyi haƙy, za'a kaiki ki ganta insha Allah, amma karki ƙara yunƙurin kashe kanki, kinji ko?" Amal ta jinjina mata, ta kama hannunta zuwa cikin gidan, yayin da masu aikknysuka shiga gulmarsu. Gabaɗaya walwalar Yusuf ta ɗauke, ko Abinci baya iya ci, idan ya kwanta tunanin Widad kawai yake yi, yana son ya ganta sosai, Amma Umma taƙi. Ya zauna yai shiru a tsakar gida, Umma ta fito da gyalenta a hannu tace  "Yusuf bari zan ɗan shiga kasuwa, ba daɗeaayzan ba yanzu zan dawo" Yusuf yace "to A dawo lafiya" Tace  "Allah yasa" ta sa kai ta fice. Widad tana zaune ta tasa 'ya' yan itatuwa a gabanta, ta kasa ci ta zuba musu ido, tana kallonsu kamar ranar ta fara ganinsu, kamar an tsunkuleta ta tashi da hanzari, tai waje ta samu ɗaya daga 'yan sanda dake bata tsaro, ta tambayeshi ina wannan ɗan sandan da suka fita tare, yace mata "Ai ya tafi aikin da kika sashi ranki ya daɗe" Tace "maza kiramin shi a waya" Ba musu, ya kira shi a waya, aikuwa ya ɗaga ya miƙa mata wayar, Widad tace  "ka gano min gidan nasu?" Yace "eh na gano, naje na tambayi abokan aikina da suka kaishi Asibiti" "a cikin ƙasa da mintuna uku, ka hanzarta ka turomin Adress ɗin" Yace an gama ranki ya daɗe, aikuwa ya tura mata, ta karɓa ta duba ta shiga cikin gidan da sauri, taje ta shirya tsaf ta fito, bata sairari kowa ba, ta buɗe wata mota ta shiga, 'yan sandan suka taho kanta suna tambayar ina zata? Babu wanda ta saurara a cikin su, ta fafari motar tana wani irin mahaukacin horn, wanda ya tilastawa masu gadin buɗe mata, saboda gudun ɓacin ranta, tai waje da motar a guje. Nan da nan' yan sandan suka ɗau mota suka rufa mata baya. Yusuf yana nan zaune, ya gaji da zaman tsakar gidan, ya tashi ya koma ɗaki, Sallama yaji a tsakar gida, ya amsa Sallamar daga ɗaki yace  "Umman bata nan" Me Sallamar tace  "dan Allah zan sha ruwa" Haushine ya kama Yusuf, shi ga abunda ya dameshi amma baƙuwa zata addabeshi, ya fito ransa a ɓace kawai yaci karo da Nurat, tai masa murmushi, gaba ɗaya ya ɗan ruɗe yace "dama kece?" Nurat tace  "Nice ko in koma ne?" "Ni na isa ince ki koma, ɗazu Umma ta fita nasan zuwa yanzu tana hanya, shigo bismillah" Nurat tace  "Yaya Khalil yana waje, tare muka zo" Yace "bari inje mu gaisa da shi" Yusuf ya bata gurin zama a falo, shikuma ya fita waje, yana fita suka gaisa da Khalil, Yusuf yace "shigo daga ciki mana, ka tsaya a waje" Khalil yace   "A'a bazan shiga ba, Naga ta gaji da zaman kaɗaicine damuwa tana damunta, nace bari mu fito tazo ta dubaka ta gaida Umman kota samu relief" Jiki a sanyaye Yusuf yace  "Barrister ina matuƙar jin tausayin Nurat, ga kunyarta nakeji gani nake duk nine sanadin shigarta matsala" "ka dena faɗar haka Yusuf, ai duk mumini dole ze yadda da ƙaddara me kyau ko mara kyau" Yusuf yace "hakane, shigo mana" Khalil yace  "zan shigo, bari inje in ga abokina a nan ƙasan layin ku" Yusuf yace "to shikenan" ya koma cikin gidan. Nurat tana zaune a guri ɗaya, tai shiru Yusuf ya shigo ta ɗaga kai ta kalle shi tana wannan murmushin nata daya zama nature ɗinta. Yusuf mabya mayar mata da murmushin, yaje ya ɗakko mata ruwa a fridge da lemo ya kawo mata, yace " Sannu da zuwa light, ga ruwa Kisha umma tana daf da shigowa" Shiru tai tana sunkuyar da kai yace  "ikon Allah, kunyata kuma kike ji? Ko kuma ba kya shan irin wannan?" Ta girgiza kai tace  "ni kowanne ina sha" "Na gidanmu ne bazaki sha ba kenan" Ta girgiza masa kai tana murmushi yace  "idan Umma ta dawo kuwa sekin sha, Umma ba'a zuwa gidanta a ƙi karɓar abunda ta bawa mutum" Ita dai sedai murmushin, amma ta kasa cewa komai. Can Yusuf yace  "light, wai nikam dan Allah ya akayi kika san da abunda na ajiye a wayarki?" Cikin sanyin muryarta tace "ai ka taɓa cemin kayi ajiya a wayata, amma baka gayamin meye ba, lokacin da aka kama ka sena gayawa brother, harda ajiyar da kace kayi a wayar, shine yace in bashi wayar, ya dinga bincike a kai, daga nan ya kaiwa wani Abokinsa, ban san yadda akayi suka gano ba " Yusuf yace " Aini bani da bakin da zan miki godiya Nurat, Allah jiƙan Mummy, Allah yasaka da alkhairi " Tace " Ameen " Can kuma tace " dan Allah dagaske kana da Aure? " Yusuf yai murmushi yace " Waye ya gayamiki? " " Kai ka taɓa gayamin, da na kiraka a waya, ka cemin kana tare da matarka " Yusuf yace " A lokacin tsokanar ki nakeyi, bani da Aure amma a yanzu ina da Aure, Widad mata tace " Ƙirjin Nurat ya buga da wani irin ƙarfi, take annurin fuskarta ya ɗauke gaba ɗaya. Yusuf yace " ya dai? Ko kina sona ne, kamar kishi fa nake gani a fuskarki" Ta ɗago manyan idanunta farare ƙal, ta sauke akan Yusuf, take taji ta karaya gaba ɗaya ƙwalla na neman cika mata ido. "Yoseef!!!" Yaji an kira sunansa, kuma babu me ambatar sunansa a haka idan ba gimbiyar Daula ba. AMANA! AMANA! AMANACE!!! LITTAFIN KUƊI NE. AYSHERCOOL 07063065680 12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 156_157 Yusuf da Nurat duk suka ɗaga kai suna kallon inda Widad ke tsaye a bakin ƙofa, seda ƙirjin Yusuf ya buga da ƙarfi ganinta a tsaye, fuskarta babu Annuri sam, dan kwata kwata be taɓa zatan ganinta ba a wannan lokacin, ba Yusuf kawai ba hatta Nurat seda hanjin cikinta ya kaɗa, ta shiga fargaba saboda yadda Widad ɗin tai kicin kicin da rai. Yusuf ya tattaro dukkan jarumtarsa, ya dake ya kauda fargabar dake zuciyarsa ya kalli Nurat yace  "Light, gaskiya ki sha ko ruwane kafin umma ta dawo, bazanji daɗi kizo gidanmu ki tafi baki ci komai ba" Fargaba ce lulluɓe a fuskar Nurat, jikinta se tsuma yake kamar taga zakanya. Yusuf ya ɗakko ruwan roba, ya buɗe ya zuba a cup ya miƙawa Nurat, amma Nurat ta kasa karɓa se kallon Widad kawai da take yi, Widad ɗin dake tsaye tana huci. Nurat tace  "Amm.. Am naga kamar gurinka tazo bari in baku guri" Yusuf yace "yi zaman ki kawai, idan wani abunne ya kawota ta faɗa a nan ina jinta" Widad ta kalli Yusuf, taiwa Nurat wani mugun kallo, ai ba shiri Nurat ta miƙe, a ɗarare ta raɓa ta jikin Widad ta fice daga ɗakin, tana fargabar kar Widad ɗin tayi mata wani abun Yusuf ya yunƙura daga kan kujerar da yake, ze bar mata ɗakin amma ta sha gabansa ta kalle shi tace  "Yoseef, Anya kamin adalci kuwa? Na cancanci haka daga gareka? Bani da kowa se Allah, ba uwa, ba uwa, ba dangi ba kowa kasan bani da kowa se Allah, se kuma kai da nake sa rai, amma kamin haka? Yoseef tunda Allah yasa ka kuɓuta baka nemi inda nake ba, ina ta faman wahala da rayuwata babu me temakona se Allah, bani da wani jigo da zan jingina dashi inji farinciki, kawai se inzo in ganka da wata, bayan kasan zuciyata bazata iya jure hakan ba"  tai maganar idonta taf ƙwalla. Yusuf yace "ni bance ba kimin adalci ba seke zaki gayamin haka? Duk tarin wahalar dana sha saboda ke, amma kika kalli duniya kika bada shedar ƙarya a kaina Widad, baki tausayawa halin dana shiga ba, seni zakiwa kallon ban kyauta miki ba?" "Yoseef, a tunanina ko kowa be fahimceni ba kai zaka fahimceni, na gaya maka komai, kasan komai game dani fiye da kowa, na baka dukkanin yarda wanda har hakan yasa na gaya maka waceceni, da abunda ya faru da rayuwata, kasan bazan taɓa yin haka dan in tozarta ka ba, dukda na ɓoye maka waye Bukar, ba nayi hakan ne dan komai ba se dan tseratar da rayuwarka, da kuɓutar da kai daga sharrinsu, na ɓoye maka Bukar shine Bulama saboda na bar hakan a zuciyata har ranar da zan kama shi red handed, sedai ƙaddara ta riga fata, amma shikenan tunda baka buƙata ta yanzu a rayuwarka, zan rungumi ƙaddara da irin rayuwar da Allah ya ƙaddara zanyi, amma kafin nan " Ta saka hannu ta cire dogin hijjabin jikinta, wanda ya kasance har ƙasa, ta cire doguwar rigar abayar dake jikinta, ya rage daga ita se gajeran wando, da kuma half vest. Tozalin da Yusuf yayi da cikin dake jikin Widad ne yasa shi ya ɗan rikice, tabbas idonsa ba gizo yake masa ba, cikine a jikin Widad gashi nan yayi girma sosai ya fito. Ta ƙaraso gabansa ta kama hannunsa, ta ɗora a kan cikin nata tace  "dan Allah Yoseef, koka watsar dani karka watsar da ɗanka, yau idan na mutu bashi da kowa se kai, dan Allah karka bari yayi irin rayuwar dani ko kai mukayi, Yoseef ka tausayamin ko dan ɗanka da nake ɗauke dashi. Yusuf ya kalli Widad ya kalli cikin jikinta yace  "You are pregnant Widad" Ta jinjina masa kai,  Yusuf yai murmushi yace  "'yar baiwa, ashe Allah ya amsa Addu'ar ki, ya baki abunda kike nema, hankalinki ya kwanta" yai maganar cikin farin ciki fuskarsa ɗauke da murmushi. Ya rungumeta a jikinsa hawaye na zuba daga idonsa, Widad ta rirriƙeshi itama tana kukan tana faɗin  "We miss you Daddy me and your unborn, munyi missing ɗinka sosai, we really suffered, banyi zaton zan sake ganinka ba, bam zaci zanyi rai zuwa wannan lokacin ba" Ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka, Yusuf ya sake manneta a jikinsa shima yana zubar da hawaye yace  "i miss you too Babyna, i miss you my Queen, I love you" "I love you too my Husband" Sosai suke kuka daga shi har ita kamsr ƙananan yara, ya sake ɗagota ya kalli cikin nata, ya rungumota jikinsa ya haɗe bakinsu yana kissing ɗinta, hawayen tausayawa kansu na zuba a idonsa, yayin da itama kukan take. Ya cire bakinsa daga nata, yana share mata hawaye ya kalleta  yace "ɗan sake maimaita min abunda kikace yanzu mana" Murmushi tai ta miƙa hannunta itama fuskarsa, tana share masa hawaye  "tace me kake so in sake faɗa?" "kin san koda ina prison, kalmomin nan da kika dinga faɗamin ranar da aka kamani sun tsaya a zuciyata sosai my wife" Fashewa ta sake yi da kuka tace  "dan Allah Yoseef ka dena tunamin kayi zaman prison please, zuciyata zata tarwatse, am sorry Yoseef duk sanadina ne ka shiga mummunan yanayi" Yusuf yace "ni dai a sake cewa ana sona please" yai maganar a Shagwaɓe. Ta noƙe kafaɗa tace  "Anƙi ɗin" "Ya akayi kika fara so nane?" "Nima ban sani ba ai, Yoseef dan Allah ka dawo gareni, akwai maganganu dayawa da nakeso muyi, kuma kaga nikaɗai nake rayuwa ina farmhouse, kalli jikina duk ya kumbura, Yoseef zuciyata ciwo take, likitoci sunce idan nazo haihuwa ko dai muyi surviving, ko mu mutu gaba ɗaya ko ɗaya ya mutu ya bar ɗaya" "Shhhhh hakan baze faru ba insha Allah, zaki haihu lafiya, kinga a yanzu haka ina ta fama da Umma saboda ke, kin san a rayuwa Umma bata son abunda ze taɓani, dan haka abune mawuyaci ta fuskanceni, saboda tana cikin kotu kika bada sheda a kaina, dan haka sena fara shawo kanta tukuna" "Yoseef, umma bata sona kenan?" "A'a ba haka nake nufi ba, taji ba daɗine abunda kikayi" "Dan Allah kayi mata bayani Yoseef, nasan kaika fahimceni kasan komai fa" "Na sani my wife, kiyi haƙuri, zanyi ƙoƙari inzo har farmhouse ɗin in ganki, yanzu maida rigarki in rakaki mota, nasan Umma na daf da shigowa" Ai gaba ɗaya sun manga da batun Nurat, dan Widad ta manta ma da taga Nurat tare da Yusuf. Ta tura baki tace  "Nika ɗakko ka samin" Ya harareta yace  "zaki fara sani aiki ko?" "Eh mana, tunda ka haɗani da aiki ai dole Kayi aiki" Yusuf yai dariya yace  "lallai kinyi baki, mara kunya kawai" "Ai kaika koyamin rashin kunyar" "Allah yasa Hari ta jiki, Kisha baƙar magana" Widad tace  "Allah sarki Hari mutuniyata, ina jin bayin Allah nan sosai a raina, ina kewarsu mussman Hinduna da Gwaggo, in komai ya daidaita zamuje insha Allah" Yusuf yace "kin san kuwa wannan Sunusin, mijin Jamila yaje ya bada sheda a kotu?" Widad tace  "Nasani" "Ya akayi kika sani?" Widad tai ajiyar zuciya tace "shiyasa nace maka ina son mu haɗu, ina da magana da kai sosai" Tai maganar cikin Shagwaɓa tana tura baki. Yusuf yace "Malama karki sa mu saki layi, matso in saka miki rigarki" Murmushi tai masa ta ƙara matsowa daf dashi, sedai yaga abu kamar kwanciyar bulala yai duhu akan fatarta, wajen damtsenta. "Baby meye wannan?" Yai maganar yana kallon hannun nata. "Bakomai, samin rigata in tafi" Shiru yai yana nazarinta, idonsa ya kuma sauka akan gefen fuskarta, nan ma wani tabon ne a gurin, ya sake kallonta zeyi magana tace "waiya kake ƙaremin kallo hakane kamar yauka fara ganina? Bani rigata in saka tunda kallona zakai ba samin ba" Yusuf ya riƙe rigar yace  "bazan taɓa gajiya da kallonki ba" yai maganar yana sake janyota jikinsa, yana sa fuskarsa a wuyanta. "Naji, amma ka ƙyaleni in tafi, hankalina ya kwanta tunda na ganka" Haka ya saka mata rigar, ta ɗau hijjabin zata saka, ya dakatar da ita ya ɗaga rigar jikinta, ya sake kallon cikim nata, ya sumbaci cikin ta yace  "I love you my unborn, karka waharmin da Mum ɗinka kaji Babyna, i love both of you" Widad ta dinga masa dariya, wai yana surutu shi kaɗai, kamar zasu cinye juna, ko sababbin masoya. Nurat kam tana fita daga ɗakin, waje tayi amma bata ga Khalila ba, se motocin 'yan sanda dake gurin, dan haka ta koma tsakar gidan, can nesa da ɗakin da su Yusuf suke, ta zauna akan kujerar tsakar gida. Sedai tana jiyo dariyar su, ta sunkuyar da kanta a tsakanin cinyoyinta, tai shiru tana tunani, tana son Yusuf so na haƙiƙa, tana sonshi saboda Allah, amma tasan tunda ya auri Widad abune me wahala ya saurareta, kuma ga dukkan Alamu Widad ma tana matuƙar sonshi itama, dan haka Yusuf babu lallai ya saurare ta. A hankali ta fara hawaye, tana gogewa a hankali, tana addu'a a zuciyarta  "Allah ka yaye min son Yusuf, Allah ka zaɓamin abunda yafi Alkhairi a rayuwa ta" Jin abun nasu bana ƙare bane, yasa ta sake miƙewa ta fita waje, tana fitavtarar da Khalil ya dawo, ya kalleta yace  "Ta Yusuf harkin fito ne? Ai bamu gaisa da Umman ba" Nurat tace  "Brother mutafi gida" Yace "meyasa? Kefa kika damu in kawoki" Nurat tace "ni dai mutafi gida kawai" Tai maganar hawaye na ƙoƙarin tona asirin dake zuciyarta, a ɗan dirirce yace  "ko wani abun Yusuf ɗin yayi mkki?" Ta girgiza masa kai ta buɗe mota ta shige, cike da mamaki Khalil ya bita da kallo. Umma ceta shigo layin hannunta ɗauke da ledoji, sedai ganin motar 'yan sanda a ƙofar gidan yasa gabanta ya faɗi, ta dinga nanata innalillahi wa inna ialaihi raji'un, hankalinta ya ɗan kwanta data hangi Khalil. Ta ƙaraso inda Khalil ke tsaye, tace  "Khalil lafiya kuwa? Naga motar' yan Sanda?" Khalil yace "lafiya ƙalau Umma, sunce min wani aiki sukeyi, Nurat na kawo ku gaisa kuma bakya nanma ashe" Umma tace  "Ai da kun shiga Yusuf yana nan ai" Yace "Ai ita ta shiga ɗinma, amma ta fito" Umma tace  "A'a ban yadda ba, Nuratu fitowa zaki mu shiga mu gaisa" Nurat tace  "Umma yamma tayi ai" Umma tace "a'a, ai ga Khalil nan Tare kuke kuma ga mota fito maza" Nurat bata son tayi sanadin da zata gusar da farincikin dake zuciyar masoyinta, amma babu yadda ta iya, Umma ta haifeta bekamata ta bijirewa umarninta ba. Nurat ta fito daga motar, tabi bayan Umma suka shiga gidan, sedai suna shiga suka tarar Yusuf da Widad sun fito, yana riƙe da ƙugun Widad suna murmushi cike da kulawa da juna. Suna yin tozali da Umma, Yusuf ya saki Widad da sauri, ita kanta seda Widad ta tsorata ganin kallon da Umman take musu. Umma ta kalli Widad tace  "kinzo ki sake kulle shin ne kokuwa? Ko prison ɗin kike son ya koma?" Widad ta kalli Yusuf, ta sunkuyar da kai. Umma tace  "ya kikayi shiru baki bani amsa ba? Kinzo ki sake maida shi prison ne, bayan duk wahalar da ya sha saboda ke, ki kaje kotu kika bada sheda akansa, banda Allah yasa wannan yarinyar Nurat da ɗan uwanta sunyi masa ƙoƙari suma da yanzu shekaru talatin zeyi a kurkuku " Widad ta ɗaga ido ta jefi Nurat dake bayan Umma da wani matsiyacin kallo, wanda yasa Nurat jin kayan cikinta kamar sun koma bayan ta, a hankali ta silale ta fice ba tare da Umma ta lura ba. Umma ta kalli Yusuf tace " kai kuma na dawo kanka, mara zuciya kai har abunda yai saura tsakaninka da wannan yarinyar, saboda rashin zuciya tana mace amma ta biyoka har gida? Idan na ƙara ganinta a gidan nan duk abunda nayi mata ita siya, yakamata ma hukuma tai mana tsakani da ita, tunda Allah yasa dai an gane baka da laifi meye kuma na cigaba da bibiyarka, kowa se yayi hanyarsa Allah ya bada lada " Yusuf yace 'Umma dan Allah kiyi haƙuri, Widad aurenta nayi mata tace, amma.. Umma ta katse shi tace " kai kasan wannan, ni ban san da haka ba, iya sanin da nayi baka da wata mata, Ni Nuratu nake fatan ka Aura, dan se tafi wannan yarinyar sauƙin kai " Widad ji tayi zuciyarta ta buga da ƙargi, tankar Umma ta soka mata mashi, take taji ta tsani Nurat, dama ga abunda mahaifinta yai mata, gashi kuma yanzu tana bibiyar mijinta, hawaye ya fara zarya a fuskar Widad, a hankali ta sanya takalmanta tai waje. Yusuf kamar ya ɗora hannu a ka ya kurma ihu haka yake ji, baya son kukan Widad yana matuƙar ƙaunarta, amma Umma na son datse igiyar farincikin dake tsakanin su. Umma ta kalle shi tace  "wato da Nuratun tazo gidan nan wulaƙanci kai mata saboda wannan yarinyar ko? Farar fatarta na ɗaukar maka ido kana nema ka gayamin magana saboda ita ko Yusuf?" Yusuf ya girgiza kai, Umma tace  "duk abun kaga nayi bazanyi dan in citar da kai ba, wannan yarinyar idan ta ƙara raɓarka za'a iya samun matsala, ka manta da ita kawai ka nemi wannan yarinyar Nurat, dan se tafi waccan tausayi, kuma dama kaga Auren naku mutane na shakku a kai, tunda ba kowane yasan da wani kunyi Aure ba, kayi haƙuri ka rabu da yarinyar nan, Allah ya zaɓa maka mafi Alkhairi kaji yaron kirki, bana son abunda ze sake ɗaga mana hankali tashin hankalin da muka shiga ma ubangiji Allah ya yaye mana ya kiyaye gaba, Allah yabaka mace tagari mafi Alkhairi a rayuwar ka " Ta miƙa masa wata ƙatuwar leda tace " yawwa ga wannan, yadine guda uku masu kyau da shadda biyu, idan anyi sallar magariba dare yayi ka kaiwa magaji ya ɗinka maka, ga takalma nan ma, hadda sabon agogo na siyo maka, ka ƙara akan kayanka, sonake nan kusa ka koma gurin aikinka" Jiki a sanyaye yasa hannu ya karɓa yace  "Nagode Umma" Ya juya ya shiga ɗakinsa, yana zuwa ya ajiye kayan ya zauna ya dafe kansa yace "ua zanyi da umarnin Ummana, matar da ta dimga ɗawainiya dani tun a zanin goyo harna zama mutum, bani da uwar data fita, sannan ya zanyi da matatat wadda a yanzu haka nauyin kula da ita a kaina yake, haba Umma ki fuskanceni mana" Yai maganar yana sake dafe kansa dake sara masa. Nurat kuwa har sukaje gida, bata ce komai ba, juyin duniya Khalil yai yai ta gaya masa abunda ke faruwa amma fafur taƙi, suna zuwa gida ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa ta shiga aikin kuka, tana jin yadda soyayyar Yusuf ke ƙafa tsuma mata zuciya, tana shiga dukkan wani sashe na jikinta, amma tasan ssamun Yusuf idan ba wani iko na Allah ba, abune da baze taɓa yuwuwa ba, ya riga ya mata nisa tunda ya zama miji ga Widad, ko ba'a gayamata ba Tasan Widad bazata zauna da kishiya ba, kishiyarma ita wadda mahaifinta ke da Mummunan tabo a gurin Widad ɗin.   Khalil duk ya shiga damuwa ganin Halin da Nurat ke ciki, a nan falo mahaifiyarsa ta fito ta sameshi tace  "Khalil har kun dawo ne? Ina Autar tawa take ne?" Khalil yace "Ta shiga ɗakinta" Tace "yaya, da kuka fitan ta ɗam saki jikinta kuwa? Na fuskanci har yanzu Nurat tana cikin damuwa da alhini, bana son rashin walwalrata, gashi ni bani da 'ya mace balle ta samu' yar uwa, ni kuma ba son yawan hira take dani ba, na rasa ya zanyi, Abbanku ma ya faramin magana akan rashin walwalarta wai kowani abu nake mata? Nace masa ya za'ayi in takuramata tana 'yar ƙanwata? " Khalil yai ajiyar zuciya yace " Mama akwai abunda yake damunta, kuma baze rasa nasaba da halin data tsinci kanta a ciki ba, dole se an bita  a hankali " Mama tace " to shikenan, naga kai taku tazo ɗaya sosai, dan Allah ka dinga kwantar mata da hankali, kana rarrashinta" "to Mama Insha Allah, bari in shiga inyi alwala magariba tayi ' Ya tashi ya baf falon, uana jin inama ze iya ɗaukewa Nurat damuwar da take ciki. Widad kam tasha kuka data koma gida, taji ta tsani Nurat bata ƙaunarta sam, ta barwa ranta sedai ayi duk wadda za' ayi, amma bazata bari Yusuf ya auri Nurat ba. Yusuf ya fita yai sallar magariba ya kai ɗinkin kayansa, ya dawo yana daf da shiga gida wani yai masa sallama, ya tsaya ya amsa suka gaisa. Mutumin yace "matarka ce ta aikoni, tace ga wannan in baka" Yusuf ya karɓi ledar daya bashi, mutumin ya tafi, Yusuf ya shiga gida ya wuce ɗakinsa, yana zuwa ya buɗe ledar, sabuwar wayace kar a ciki da layi, tai rubutu a jikin kwalin wayar" "switch on the phone, and call me Baby, Your wife" Murmushi yayi cikin rawar jiki ya kunna wayar, ya duba yaga lamba ɗayace a ciki, maimakon ya kirata da wayar, seya kwafa a ƙaramar wayar dake hannunsa ya kirata. Tana kwance akan gado, tayi rigingine wayar ta fara ringing, ai da sauri ta ɗakko wayar ta ɗaga. "Hello My Queen" "meyasa baka kirani da layin dana baka ba?" "so kike Umma ta tambayeni ina na samo waya?" "Shikenan, ya kake?" Yace "lafiya ƙalau, ya ki kaje gida?" Tai ajiyar zuciya sannan tace  "Alhamdilillah" Yace  "Widad dan Allah kiyi haƙuri da abunda ya faru yau kin san" "I understand, just forget sonake kawai muyi hira da kai, inji daɗi a raina, kaɗaici ya dameni ko Abinci bana iyaci Yoseef, ga bani da lafiya I need you Yoseef, i need your help" Jiki a sanyaye Yusuf yace 'ki kwantar da hankalinki my wife, Insha Allah inaji a jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe insha Allah, kiyi haƙuri karki cutarmin da kanki da Babyna, ki dinga cin Abinci please, karki mana illa " " toni ya zanyi inci, babu me rarrashina ya bani a baki? Gashi bana samin irin Abincin da nake so, Yoseef dan Allah ka bawa Umma haƙuri ka dawo gare ni please " " karki damu, Umma zata soki tana da sauƙin kai sosai, Insha Allah zam sam abunyi, amma dan Allah kici Abinci kinji Wudas ɗina " " Wudas ko? " tai maganar a Shagwaɓe. Yusuf yai dariya yace " ba haka Hari take ce miki ba? " " to kai ita ne? Kasan meze faru kashe wayar, zanje inyi wanka video call nake son muyi in ganka " Yace" shikenan, as you wish Babyna" Yusuf ya rungume wayar nan. Ko takan Abincin dare Yusuf bebi ba, Widad ta sake kiransa video call, ta saki dogon gashin nan nata, tana shafa mai. Yusuf yace "Cikin nan ba ƙaramin kyau ya miki ba fa" "Allah ne yayi cikin nan baze fita ba, amma allurar zubar da ciki Bulama yasa ayimin" "cikin nawa aka so zubarwa?" "Eh mana, sun kusa kasheni fa, akwai labari idan mun haɗu fa" Yusuf yace "Allah sarki babyna, mun sha wuya sosai, ko da kikazo kotu kallo ɗaya nai miki na gane ba'a kwanciyar hankali kike ba" Widad tace  "bar wannan zancen kawai, kar ka ɓatamin rai ka rusa mana farinciki" Yai murmushi yace  "to shikenan, kina min ƙwalele da gashin nan fa" Tai murmushi tana masa gwalo ta waya, tace "ziro hannu ka taɓa mana" "Inama in rufe idona in buɗe in ganni a kusa dake, in tayaki shafa man nan" "Harka tunamin lokacin da muna ƙauye, gaskiya Yoseef kana da haƙuri kayi haƙuri dani sosai, shiyasa ka taka wani gagarumin matsayi a zuciyata my love" Har tagama shirin kwanciya, ta kwanga video call suke, ba tare da sun sam dare yayi ba. Ƙarfe biyu da rabi lokacin ne Umma take sallar dare, ta fita alwala ta dinga jin maganar Yusuf ƙasa ƙasa, ta leƙa tagarsa ta hangoshi akan gadonsa ya tasa screen ɗin waya a gaba yana murmushi. "Ki kwantar da hankalinki, Insha Allah zuwa jibi zanzo in ganki masoyiyata" "Allah ya kawo ka lafiya, zaman kaɗaici ya isheni Yoseef, babu kowa a kusa dani fa" "Ai mace miki zanzo insha Allah, inzo in ganki inji labarin da kike son gayamin, inji yadda akayi kika samu wannan tabon haka a jikin ki, ki kwanta kiyi bacci dare yayi fa" Tace  "ok come closer, hug me and kiss me, then we sleep together" Yusuf yai murmushi yace  "nayi missing ɗinki Widad, yai kissing ɗin screen ɗin wayar yana lumshe ido, ƙarshe ya kashe wayar ya ajiye, ya rungume pillow sosai a jikinsa yana lumshe ido. Umma ta jinjina kai ga wuce banɗaki domin yin alwala. Da safe Yusuf ya tashi yana ta nishaɗi kamar bashi ba, Umma tana kallonsa amma ba tace masa komai ba. Ranar da yayiwa Widad alƙawarin ze je yana ta kallon agogo, yana zaune Umma ta sashi a gaba yaci Abinci, ya gama ci wayarsa ta fara ringing, sedai ba suna amma yaƙi ɗagawa, Umma tana kallonsa. Can yace  "Umma bari inje ɗaki zan kwanta bacci" Umma tace  "ɗakko pillow ka kwanta a nan" Ba haka yaso ba, amma haka nan ya haƙura, ya ɗakko pillow ya kwanta a ɗakin Umman. Aikuwa babu daɗewa bacci ya ɗaukeshi, saboda dama dare yake rabawa yana soyayya. Umma ta ɗakko mafici tana masa fifita, Kasancewar an ɗauke wuta gashi ya fara gumi. Sedai tun ba'aje ko'ina ba Yusuf ya fara surutan bacci. "My Wife, kiyi murmushi mana yarinya fushi baya miki kyau fa" Umma ta juya tana kallonsa, iya saninta dashi tun yana yaro ƙarami, baya surutan bacci, amma yau da ranar Allah yana bacci yana surutu akan wata. Bata gama mamakin ba ya cigaba "Baby ki dena kuka, bana so fa, kinga baki da lafiya, kuma Gwaggo yau zata kawo mana kunun tsamiya, ai zaki sha ko?" Suleiman ne yai sallama a gidan, Umma ta amsa masa, ya shigo ya zauna yana faɗin  "Lallai ɗan gata, yana bacci Umma na masa fifita, tashi c Yai maganar yana taɓa Yusuf, Umma tace " ze tashi kuwa, yana mafarkin soyayya " Suleiman yace " Soyayya kuma? " " Eh mana, se surutai yake shikaɗai" Suleiman ya daddaki Yusuf, Yusuf ya buɗe ido a hankali, ya tashi zaune yace  "Yallaɓai dama kaine?" "Eh nine, ka tashi ka shirya mutafi" Yusuf yace "mutafi ina?" Umma tace  "gidansu Nurat zaka je, Munyi waya da Khalil bata da lafiya!!!" Wayat Yusuf ta shiga ringing, ya kalli wayar lambar Widad ce, tana can tana jiransa AMANA! AMANA! AMANACE!!! DUK WANDA YACI AMANA, AMANA ZATA CISHI AYSHERCOOL 07063065680 12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 158_159 Yusuf yace "Amma Umma, da wani guri nake son zuwa" "zaka bijirewa umarnina ne?" Yusuf ya girgiza kai, Umma tace "to tashi maza, jeka kintsa kazo ku tafi" Jikin Yusuf babu daɗi, ransa sam ba daɗi yaje yai wanka ya shirya ya fito. Umma tace "Suleiman, dan Allah ga Shi nan, ka tabattar yaje dan Allah ga kuɗi ku sai mata ko kayan marmari ne, aje a duba ta, gaida mai gaisheka ko baze amsa ba" Yusuf dai bece komai ba yai waje, wayarsa na cigaba da ringing. Suleiman ya fito ya shiga motar suka tafi, Umma ta maida Suleiman kamar ɗanta Yaya a gurin Yusuf, dan shima tana masa hidima shida iyalinsa, tunda yaita faɗi tashi akan case ɗin Yusuf. Yusuf be kula Suleiman ba, gaba ɗaya ransa a ɓace yake, ya ɗakko wayarsa ya kira Widad, tana ɗagwa ta fara mita "Haba Yoseef, inata kiran wayarka kaƙi ɗagawa, na shirya ina ta jiranka fa" Tai maganar cikin Shagwaɓa. Yusuf yace "Am sorry, wata fitace ta gaggawa ta kama ni, amma idan na kammala zanzo insha Allah, ki kwantar da hankalin ki kinji my Wife" Tace "to naji, ka siyomin abu me daɗi, ina jin kwaɗayi" "To shikenan, zanje ƙauye in Hari tayi girki ta zubo in kawo miki" A tare sukayi dariya, yace "shikenan sena zo" Ya maida wayarsa ya ajiye, Suleiman yace "Yusuf zaka karya maganar Ummanka kaje inda Widad take kenan?" Yusuf yace "yallaɓi, yakamata ka fahimceni Widad fa ita kaɗai take zaune a gidan nan, babu kowa kuma ina tare da Aurenta, duk haƙƙoƙinta suna kaina, Umma taƙi bani dama in mata bayani, bayan haka Widad tana buƙatar kulawa, duk ta kumbura saboda ciwon zuciya da hawan jini, kuma.. Kuma tana ɗauke da tsohon ciki fa" Yusuf ya ƙarasa magaanar cike da jin kunya da kuma damuwa. Suleiman yace "hakane, yakamata ace Umma ta fuskance ka, amma tanaa gudun abunda ze sake kawo barazana ga rayuwarka ne, amma kabi a hankali, zata fahimta Insha Allah" Yusuf yace "Allah yasa, amma ni batun Auren nam da Umma ta bijiro dashi, dan Allah Yallaɓi kasa baki, idan har nace zan Auri Nurat Widad zata rabu dani, kuma ina matuƙar son mata ta" "Shikenan nagane halinda kake ciki, amma Nurat ma abun tausayi ce" Yusuf yace "Nasani, badan kishi irin na Widad ba da zan iya auren Nurat, saboda tana sona sannan bata da wani aibu, sema nine nake da aibun da za'a gujeni saboda shi" Suleiman yace " aibun me kenan?" Yusuf yace "bakomai, manta kawai" Suka cigaba da hirarsu, har zuwa gidan su Nurat. Koda dukaje Khalil baya gida, megadi yaje ya sanar da zuwansu, aka musu iso. Sedai Suleiman yace baze shiga ba sedai Yusuf yaje, haka kuwa akayi aka masa jagora har falon da aka saukesu wancan zuwa. Yayar maman Nurat ce ta fara zuwa, Yusuf ya gaisheta cikin girmamawa, sannan ta koma ta turo masa Nurat. Yusuf yana nan zaune yana sake kallon wayarsa, yana addu'a Allah yasa kar Widad tayi fushi, yaji ƙamshin turaren Nurat, ya ɗaga kai ya kalli Nurat, duk ta rame kallo ɗaya zaka mata kasan bata da lafiya, a hankali take tafiya tana ɗan lumshe ido irin na marasa lafiya, ta ƙaraso ta zauna a kan carfet. Yusuf ya dawo kujerar da Nurat ke zaune a ƙasa, ya kalleta yace  "Light Dama baki da lafiya?" Maimakon ta bashi amsa se cewa tayi  "ina wuni" Yusuf yace  "lafiya ƙalau, ya jiki ɗazu Umma ke gayamin ban sani bane" "Jiki da sauƙi Alhamdilillah" ta faɗa tana rausayar da kanta ƙasa. "Amma kin daɗe kina rashin lafiyar nan, meke damunki haka?" Girgiza masa kai tayi tace  "bakomai" "ban yadda bakomai ba, ki gayamin meke faruwa ne?" Kasa magana tayi, se hawaye da suka shiga zarya a fuskarta, ba tare da ta shirya zubarsu ba, dan tayi duk me yuwuwa ganin basu zuba ba, amma abun ya gagara. Yusuf ya sakko daga kan kujerar, ya zauna a kan carfet ɗin yana kallonta, a hankali yace "Nurat, dan Allah kiyi magana mana, meyafaru?" Shiru tayi ta ɗauke kai daga kallon inda yake, dan data kalle shi sonshi ƙara shigarta yake, da kuma kishinsa. "Nur ko nine nayi miki laifi?" Ta ɗago idanunta ta kalleshi na wani ɗan lokaci, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta, a hankali tace  "Nagode sosai kazo ka dubani, nagode ka gaida Umma" Ta yunƙura ta miƙe zata tafi, cikin zafin nama Yusuf ya miƙe ya riƙo hannunta, ta juyo tana fuskantarsa, ta kalli inda ya riƙe hannunta ta kalli Fuskarsa taji tamkar ta rungumeshi tayi kuka, ita dai a rayuwarta maza dayawa sun nuna suna sonta, amma bata taɓa jin ƙauna da soyayyar wani a ranta kamar Yusuf ba, zata iya cewa akansa ta fara Soyayya. Yusuf yace  "Nurat bana so in zama butulu, bana son zama ɗaya daga cikin masu butulci, ki gayamin me kike so? Meke saki kuka haka?" Cikin sassanyar muryarta, me cike da karaya tace  "bazan samu abunda nake so ɗin ba ai, dan haka babu buƙatar cigaba da ɓata lokaci gurin faɗa" Yusuf yace  "gayamin, ko mene ki faɗamin, me kike so?" "Yusuf kai nake so, kaine Yusuf, ban taɓa so ba se akanka, ban san haka ake ji ba, sedai nasan bazan sameka ba, kamin nisa na har abada, nasan ko a mafarki Widad bazata yadda ka auri wata bayan ita ba, bayan haka ta fini komai, sannan ga abunda ke tsakaninta da mahaifina, ina ganin ƙiyayyata ƙarara a idonta, ga kuma bazan so ka dinga samun saɓani da mahaifiyarka saboda ni ba, dan haka ina muku fatan Alkhairi a rayuwar Aurenku me cike da alkhairi, Allah ya ƙara tsareku daga sharrin maƙiya, da mahassada nagode sosai Yusuf " Gaba ɗaya jikinsa yai sanyi, sosai ta bawa Yusuf tausayi, tabbas Nurat ta cancanci a tausaya mata, da tausayi halin da take ciki a yanzu, amma yasan ko wace kalar wiwi yake sha, baze haɗa Widad da wata ba, saboda yasan azabar kishi irin na Widad, Nurat ta zare hannunta daga nasa ta koma ciki da sauri. Jiki ba ƙwari Yusuf ya fito daga falon, ya nufi waje, Suleiman ya kalleshi yace  "lafiya kuwa?" Yusuf yace  "Yallaɓai akwai damuwa" "meyafaru"? "Nurat sona take dagaske fa" Suleiman yace  "Au kaida baka san son naka take ba?" Yusuf ya dafe kai yace  "Yallaɓai, dan Allah kamin alfarma ka kaini in ga Widad, dan Allah bazan daɗe ba insha Allah" Sulaiman yace  "Shikenan, bakomai mije ina ne?" Yusuf yai masa kwatance suka tafi, a bakin gate wani ɗan sanda ya taresu yace  "ya akayi?" Yusuf yace  "a gayawa Widad Yusuf ne" Ɗan sandan yai murmushi yace "Ohhh ashe megidane, ai tun ɗazu take jiranka" Aka buɗe musu gate, Suleiman ya shiga da motar yana mamakin haɗuwa da tsaruwa gami da girman gidan. Yai parking Yusuf ya fito daga motar, yace  "Yallaɓai zo mu shiga mana" Suleiman yace  "Gurin budurwa ma ban bika ba se gurin matarka, a'a ina nan" Yusuf kawai yai murmushi ya girgiza kai, ya shiga ya dinga duba falukan dake gidan, Kasancewar ya kirata bata ɗaga ba, can ya hangota a wani falo, tana zaune akan 3 seater, ta haɗe rai sosai, sanye take da dogon wando, da 'yar riga ƙarama, ta gyara gashin kanta ta saka ribbon saki ƙarshensa   a bayan ta, hakan ya bawa cikinta damar fitowa sosai, abun mamaki ta saka jambaki da kwalli a idonta, abun da Yusuf be taɓa gani ba, sedai ta haɗe rai. Yusuf ya ƙaraso inda take yana murmushi yace  "farar mace alkyabbar mata, why are you sad? Ba gani nazo ba" Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta mayar ta sunkuyar da kanta tana danna wayarta. Yusuf ya ƙaraso ya zauna kusa da ita yace  "bazaki ɗago in ƙare miki kallo ba?" Matsawa tayi daga kusa dashi, ya kalleta cike da mamaki yace  "lafiya kuwa?" Ta ɗago tace  "Daga ina kake?" Yusuf yace  "naje wani gurine shiyasa.. " Yoseef kasan bana son ƙarya fa, ina kaje? " Maimakon yai mata magana, seya ƙura mata ido, ta saka idonta a nasa tace " Yoseef gurin Nurat kaje " " waye ya gayamiki gurinta naje? " " tunda ka cemin zaka wani guri, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, naji a jikina gurinta zaka je, kuma kana shigowa naji kana ƙamshin turarenta, Yoseef wallahi gurinta kaje" Yusuf yace  "lallai zuciyarki tana tare dani, dan ba tayi miki ƙarya ba, tabbas naje gurin Nurat bisa ga Umarnin Umma, naje na duba Nurat bata da lafiya, Widad, Nurat bata cancanci wulaƙanci ko banzatarwata ba, dukda abunda mahaifinta yayi, amma ta taka mshimmiyar rawa a gurin kuɓutata, kalli ta rasa mahaifiyarta, mahaifinta ya tafi prison, kuma a yau take gayamin tana sona, be cancanci in wulaƙatanta ba" "Yanzu me kake so ka gayamin? Zaka Auri Nurat ne kokuwa?" Tai maganar tana tsststare shi da ido, Yusuf yace  "ni bahaka nske nufi ba, itama tasan hakan bame yuwuwa bane, amma yakamata itama a dubata, a tausaya mata, ta rasa kowa Widad ko ban Aureta ba bata cancanci wulaƙanci ba, ta temakeni kuma kin..... Cikin faɗa Widad ta dakatar da shi, ta hanyar cewa  " ni ka cikamin kunne da ta temakeka, ni wulaƙanta ka nayi? Ko kana zaton Nurat tana da abunda zata ja da Bukar Bulama ne? Kasan waye Bulama kuwa? Aiko mahaifinta da suke tare da Bulama, wallahi bashi da ƙarfin ja da shi, yana da arziki kuma goyon bayan manyan mutane a duniya ba ƙasa ba kawai, Yoseef Bukar yamin barazana ko inje kotu in bada sheda ko ya kashe Ummanka, ko kasan ba Nurat ce tai sanadin kuɓitarka ba Allah ne ya kuɓutar da kai, amma se da na bada kadarorina na miliyoyin nairori, aka siye mutanen Da Bulama ya siye, nasa aka ninka musu abunda ya basu, na ɗaukar maka babban lawyer wanda shine ya tsara komai? " Ta ɗanyi shiru sannan ta kalli Yusuf, daya zuba mata ido tace "inda Bulama ya kaini ya ɓoye, akwai wata mata da take kula dani a gidan, wayarta nake karɓa inyi browsing inga yadda shari'arka ke gudana, katsam ta bar wayar a hannuna, ta tafi aikace aikacenta, ni kuma nayi recording a wayar, na cire memory card ɗin bata sani ba, na bata wayarta, na rubuta takadda na bata na nannaɗe memory card ɗin a leda, a cikin takadda, nace ta aramin dubu ɗaya taje ta samu shagon masu saida abubuwa ta basu, na bata ina addu'a Allah yasa saƙona yaje inda na tura shi. Nayi rubutu ne, nace 'zuwa ga wannan takaddar taje gareshi, dan Allah ina neman Alfarma, ina son duk yadda za' ayi ledar dana aiko da ita, da abunda ke cikin ledar, a kaiwa Barrister Hafiz Mubi, ace masa inji Widad, sannan a karɓi dubu ɗayan hannun matar a bawa wanda ze kai yayi kuɗin mota, itakuma ace maya babu abunda na aikota ta saimin. Shine aka karɓi saƙon, akace mata babu aiken da na mata, ta dawo ba tare da tasan mena aiketa ba. Barrister Hafiz, ɗahane daga cikin lawyoyin Daddy, saƙon ya isheshi ya duba, shima na rubuta masa wasiƙa, nace ya duba cikin memory card ɗin, akwai saƙo ya duba. A cikin audio na gaya masa yadda ze saida wasu daga kadarorina, ya ɗaukar maka lawyer, Kasancewarsa abokin Khalil ɗan uwan Nurat, a nan ya samu dama shima suka haɗu da wasu lawyoyin aka tsaya maka a shari'ar, badan kuɗin da na saki ba, da har yanzu ba'a ƙare shari'ar a haka ba, da kotu bazata wanke ka ba, harse an kammala shari'a dasu Bulama, sedai a bada belinka, amma daka motsa sekace Nurat ta maka halacci, kaje ka ƙarat kai da ita, kaje ka Auri Nurat" Ta ƙarasa maganar tana kuka, ta tashi zata tafi, Yusuf ya riƙeta gam ya zuba mata idanunsa, taƙi kallonsa ta cigaba da kukanta, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa. "Kinji nace miki zan auri Nurat ne?" "Idan ma baka faɗa ba alamu sun nuna ai" "kina so in saɓawa Umma, dukda tarin alkhairinta a gareni saboda ke? Idan nayi haka na kyauta? Kina ganin raguwar auren namu zata yi albarka ne?" Widad ta girgiza kai alamar a'a. Yusuf yace  "ki bani lokaci, ina son in daidiata komai ne, amma sekin dena wannan koke koken, da tayarmin da hankalin sonake mubi komai a sannu, kinga ni duk ban san wannan ba se yanzu da kika gayamin, kiyi haƙuri kinji" Ta zumɓura baki taƙi magana, hawaye na cigaba da fita daga idonta. "bazaki dena kukan bane?" "Nika ƙyaleni inyi dan haushinka nake ji" tai maganar tana basarwa Yusuf yace "to shikenan, bari in tashi in tafi" Sauri tayi ta riƙe shi tace  "wallahi ka tafi sena bika" "to goge hawayen nan maza" Bata goge hawayen ba, ta kwanta a jikinsa tana sake tura baki gaba, kamar yarinya ƙarama. Ya shafa gashin kanta yace  "dama haka kike sona? Bani da bakin yi miki godiya, nagode sosai Babyna, Allah ya bani abunda zan mayar miki da kadarorinki bazan so ace kin rasa wani abu da kika mallaka saboda ni ba" Widad tace "Dukiya ɗazu ce, ni kai ne a gabana Yoseef, bana kallon dukiya ni kai nake kallo kawai, zuciyata kai kawai take kallo, ni kai nake so fa, ni banyi dan ka biyani ba, ni tukucin zuciyarka nakeso kawai" Tai maganar tana sake kwanciya a jikinsa tana kuka. Ya rungumeta sosai a jikinsa yace "is ok my love, ki dena kuka na fahimce ki, in dai zuciyata ce kin samu I love you my wife" Tace "I love you too Yoseef" Ta maƙalƙaleshi tana lumshe ido, tana shaƙar ƙamshin turarensa daya kashe mata jiki sosai. Yusuf ya shafa gashin kanta yace "kinyi kyau sosai masoyiyata, kamar in sace ki in gudu haka nakeji" Widad tace "dan Allah mijina ka fahimtar da Umma, mu samu ta yadda mu rayu tare, Yoseef na yadda in rasa komai nawa in kasance da kai har abada, you are my world and happiness Yoseef" Yusuf kasa magana yayi, se ajiyar zuciya da yake tayi, saboda yadda jikinsa ya mutu gaba ɗaya, ya dinga sauke ajiyar zuciya, can yace "My love ya babyna yake? Fatan baya wahalar min dake dai?" Ta tura baki tace "gaskiya yana bani wahala, yaita kicking cikina, ko ya hanani cin Abinci" "ki kwantar da hankalinki, lokacine ze dena insha Allah, zan masa faɗa ya dena wahalar min da babyna, ke dashi duk ina sonku sosai" Widad ta tashi daga jikin Yusuf, ta kalli cikinta tana murmushi tace "kaji dai Abunda Dad ɗinka yace ko? Ka dena takuramin" Yusuf ya ƙura mata ido sosai, ta ɗago ta kalle shi tace "lafiya kuwa? Wannan kallon fa? Ga fruit can a dining tashi muje ka bani abaki, nima in baka" Yusuf ya girgiza mata kai alamar a'a, tace masa "why?" Yace "that's not what I want" 'So what do you want? " tai maganar tana kallonsa. " I want to kiss you, lips ɗinki sunyi kyau sosai da kika sa jambaki " Murmushi kawai tayi ta ɗauke kai daga kallonsa, a hankali ya sunkuyo da fuskarsa dai dai tata yana mata wani irin kallo me wuyar fassara, a hankali yake mata numfashi a fuska, Widad kamar an sassaƙata ta kasa ko motsi daga inda take zaune, tana jin saukar numfashinsa a fuskar ta. Rungumeta yayi yana kissing ɗinta, to show her how he misses her, and she responds to his message to show him that she also miss him, wayar Yusuf data fara ringing ce ta dakatar dashi daga abunda yake yunƙurin yi. Sunan Umma ya gani akan screen ɗinsa, yaiwa Widad alama da tayi shiru, ya daidaita nutsuwar sa ya ɗaga wayar yace "hello Umman Yusuf" Umma tace "kuna inane?" "muna gidansu Nurat ne" "bata wayar mu gaisa" "Umma ai ta koma cikin gida, kin ganni a harabar gidansu, yanzu zamu taho da Yallaɓai" Umma tace "to shikenan, ka hanzarta ka dawo, bana son ka dinga nisa sosai" Yusuf yace "to Umma, Insha Allah gani nan dawowa" Ya kashe wayar yasa a aljihunsa, ya kalli Widad dake kwance, ta ɗauke daga kallonsa yace "sweetheart am sorry, kiyi haƙuri zan tafi kar Umma ta gane nazo gurinki kinji" Bata ce masa komai ba se binsa da kallo da tayi, ya saita nutsuwarsa ya miƙe ze fita, ya waigo ya kalleta yaga tana hawaye, ya dawo ya durƙusa ya riƙe hannayenta yace "kiyi haƙuri matata, Insha Allah na kusa dawowa gareki kinji, karki damu dan Allah kidena kukan nan haka, nafi ki buƙatar ganinki a kusa dani" Ya share mata hawayen fuskarta, ya sunkuya ya sumbaci goshinta, sannan ya bar falon cikin hanzari. Suleiman na ganinsa yace "kai haka mukayi da kai, daga zuwa ka ganta seka shige kayi zamanka kana soyayya ka shanyani, har Umma ta kirani a waya, na mata ƙarya ai muna tare a gidansu Nurat" Yusuf yace "muje kawai, nima ta kirani karta gane naje gurin Widad" Sulaiman yace "shikenan muje" Tunda suka tafi Yusuf hankalinsa baya jikinsa, ya baro shi can a tare da matarsa, gashi yayi mamakin jin itace tayi me yuwuwa, da dukiyarta dan ganin shiya kuɓuta daga halin daya shiga. Tunani kawai yake yi, Suleiman ya fuskanci hakan, dan haka yaita masa nasiha yana kwantar masa da hankali, amma sam Yusuf baya gane me Suleiman ke cewa. A waje Suleiman ya ajiye Yusuf, shi kuma ya tafi, Yusuf ya shiga cikin gidan. Ya shiga tare da sallama, Umma ta amsa masa tace "Yusuf kun daɗe fa, ya jikin Nuratun"? Yusuf yace "da sauƙi, suna gaisheki?" Umma tace "to Allah ya ƙara afuwa, amma ya na ganka wani iri? Akwai matsala ne?" "A'a Umma, bakomai fa" Umma tace "shikenan, ana daf da shiga sallar magariba, kai alwala ka tafi masallaci" Yusuf yace "to Umma" Ya shiga ɗakinsa, cike da tunani fal a zuciyarsa. Dan kar Umma ta gane yana cikin damuwa, yasa yaje ya ɗauki Abincin dare yaci, Umma nata masa hira amma baya ganewa, se amsa mata yake da ummmm. Ya tashi ya tafi ɗakinsa, yana zuwa beyi wata wata ba ya ɗakko waya ya kira Widad, sedai muryarta ƙasa ƙasa kamar bata da lafiya. Yusuf yace "lafiya kuwa wife?" "bakomai" ta bashi amsa "Kiranki nayi muyi hira, kuma naji kamar ba lafiya" "hirar da zata fi kowacce a gurina, itace ganinka a kusa dani, amma kamin nisa, ina ji ina gani ba yadda na iya, dukda son da nake maka" Nan Yusuf ya kwantar da murya ya shiga aikin rarrashi, harta saki jikinta dashi, ta dena fushin suka koma soyayya, yauma seda suka sha soyayyar su, seda dare yayi sosai sannan suka kwanta bacci cike da begen junansu. Umma tana monitoring ɗin Yusuf, ya dena zaman tsakar gida ko kuma hira da ita, kullum yana ɗaki riƙe da waya, da tayi zancen Nurat seya dinga basarwa, saboda haka ta zuba masa ido, sedai ta toshe duk wata hanya daze fita yaje yaga Widad, dan bata son ya kuma raɓar Widad yaja musu matsala. Sosai fa Suke kewar juna shida matarsa, gashi baze iya bijirewa Umma ba, yana matuƙar tausayin Widad sosai, dan yadda suka yi waya yau ya gane bata da lafiya tana jin jiki sosai, ga babu hanyar fita, dan idan harze fita se Umma ta tambayi ina zashi. Da Yamma Umma ta hanshi zaune yayi jugum, yayi shiru kamar wanda akayiwa mutuwa. Ta kalle shi tace "Yusuf zo kaje ka siyo kayan miya, zanyi girki naga yamma tayi" Yace "to" Ta bashi kuɗi ta lissafa masa abunda ze siyo mata, sannan ta bashi dubu biyu tace "ga wannan ka riƙe a hannunka, kafin ka koma gurin aikin" Yusuf ya karɓa yace ya gode, ya fita yin cefanen. Umma tana ta aikinta a tsakar gida, taji anyi sallama, ta amsa tare da waigowa wanda ta gani ne yasata sakin tsintsiyar hannuta ta saki baki, tana kallonsa.. AMANA! AMANA!! AMANACE!!! IDAN KIKA FITAR BADA IZININA BA, ALLAH YANA KALLONKI, KUMA KINCI AMANA AYSHERCOOL 07063065680 12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 160_161 Umma ta bi mutumin da kallo kamar taga baƙuwar halitta, mutumin yace  "Madam a bamu guri mu zauna mana, an tsaya ana bina da ido" Jin yace a basu gurin zamane yasa Umma leƙa bayansa, taga mutumin tare da Widad a bayansa, take Umma ta ɗan tsuke rai. Mutumin yace  "Jidda wannan kallon fa? Ki bamu gurin zama mana" Umma tai musu jagora zuwa falonta, taje fridge ta kawo musu ruwa da lemo, Widad tace  "Umma ina wuni" Umma ta amsa sama sama, Mutumin yace  "Jidda dama rai kanga rai? Rabona dake tun kina budurwa, ban sake sanin inda kike ba, se kwanan nan naji ashe Bashir Maitama ne mijinki, Allah ya jiƙansa da Rahama" Umma tace  "Ameen ya Allah, kwana ba adadi Alhaji Ahmad, dan yanzu sedai ince Alhaji ka ƙara ƙiba, kamar ba kaiba kamaninka sun canza saboda kuɗi sun zauna" Alhaji Ahmad yace "bari Jidda, abubuwa duk se godiyar Allah kawai" Ya juya ya kalli Widad yace  "daughter na, wannan ce sirikar taki" Widad ta jinjina kai, Ya kalli Umma yace   "dama kece sirikar tamu kike wahalar min da 'ya?" Umma tace  "kamar yaya kenan?" Alhaji Ahmad yace  "to a al' adar Hausawa dai, namiji ke zuwa biko, to hula taja ɗankwali, munzo muyi bikone, dan Allah a temake mu a bamu mijin mu mana, ayi mana afuwa" Umma tace  "wai ya akayi ta zama 'yarka kuma? Kuma ni gaskiya ina tsoron abunda ze biyo bayane, ni inajin tsoron ɗana ya sake shiga matsala gaskiya" Alhaji Ahmad yace "labarin dogone, amma dan Allah ayi haƙuri a bamu mijinmu, zamuyi miki bayanin komai, amma waini ina sirikin nawa yake nema? A nunamin shi in ganshi, inga ya yake a yanƙwanamu akansa haka?" Umma tace  "A'a ba wani na musamman bane, kawai ni bana son ɗana ya sake shiga matsala saboda itane, ya wahala fiye da tunaninka, duk saboda ita, wahalar da akayi a baya Allah ya amfana" Yusuf ne yayi sallama, hannunsa ɗauke da ledar aiken da Umma tayi masa, ya shigo falon cikin nutsuwa da sallama, sedai yana ganin Widad a zaune gabansa ya faɗi, ya ɗan tsaya yana kallonta, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta. Yusuf ya durƙusa ya gaida Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad ya amsa yana ƙarewa Yusuf kallo, yace  "iko se Allah, lallai dole a mana jan aji akan wannan zuƙeƙen matashin, Widad banga laifinki ba da kikabi kika ɗaga hankalinki akan mijinki, dan an ganshi kyakkyawa shine ake wani jamana Aji" Yusuf ya ɗanyi murmushi, yana son sanin waye wannan mutumin da suka zo tare da Widad? Yusuf ya maida kallonsa ga Widad, ya ɗan kashe mata ido, amma ta haɗe rai tana ƙoƙarin maida ƙwallar idonta, girgiza mata kai Yusuf yayi, ya ɗakko handkerchief ɗinsa, ya faki idon Umma, ya miƙawa Widad, Alhaji Ahmad suna magana da Umma, amma hankalinsa yana kansu Yusuf. Yusuf ya miƙe ze bar falon, Widad tabi Yusuf da kallo, kamar zata cinye shi. Alhaji Ahmad ya kalleta yace  "Widad ɗan bamu guri, maza tashi ki bishi, ai tunda Allah yasa munzo se Jidda ta bamu mijinmu, an dena wahalar min da 'ya dan anga yana da kyau, nasan dai' yata tafi shi kyau" Umma tayi murmushi, Widad kam cikin hanzari ba kara ba kunya, ta miƙe yabi bayan Yusuf, yayin da Umma ta jinjina rashin ta ido irin na Widad " Suna fita Yusuf ya janyota gefe yace " sweetheart, waye wannan mutumin ne? " " Nima ban sanshi ba" "Are you serious?" "dagaske nake" ta bashi amsa "Amma ya akayi kuka zo tare?" "Nifa ban sanshi ba, ya cemin yasan Ummane, nazo mu bada haƙuri" Yai murmushi yace  "shikenan naji, zomuje ɗakina muyi hira kafin su gama maganar" Widad ta zaro ido tace  "haka kurum, Umma tace bani da kunya, ni a nan zan zauna" Ya shimfiɗa musu dadduma, suka zauna hirarsu suke kawai kamar babu abunda yake damunsu, Umma ta fito ita da Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad yace "Widad taso mutafi, se Allah ya kaimu weekends ɗin" Widad ta tsaya tana kallonsa, kamar bata gane me yake faɗa ba. Ya sake maimaita masa maganar, amma Widad taƙi motsawa. Yusuf yace  "ki tashi ku tafi mana" Aiba kunya Widad ta noƙe kafaɗa, alamar ba inda zata je. Alhaji Ahmad yace  "iko se Allah, kiyi haƙuri kizo mutafi, idan Allah ya kaimu Weekend zamuyi tafiyar nan, kuma ina lallaɓa sirikata mu, dan haka kiyi haƙuri za'a baki mijinki" Widad tace  "dan Allah ni ka ƙyaleni a nan, wallahi bana son zaman gidan nan nika ɗai, damuwa damuna take, dan Allah ka barni a nan zuwa weekends ɗin mu tafi ta nan gaba ɗaya" Alhaji Ahmad yace "Ikon Allah to sirkarmu kinji abunda tace, bakomai ta zauna ɗin a nan, zuwa Allah ya kaimu weekends ɗin?" Umma tace  "toni me zance, in dai gidane gashi nan ta zauna, sedai mu bamu da Arziki ba lallai muna da abubuwan da take buƙata ba" Yusuf a ransa yace  "Umma da kin san a ƙungurmin ƙauyen da muka zauna, da baki faɗi haka ba" Widad kam cewa tayi  "Ni dai zan zauna a nan" Alhaji Ahmad yace  "toke yanzu gashi baki ɗakko kayanki ba, a haka zaki zauna ɗin?" Widad tace  "zamuje da Yoseef in ɗakko" Alhaji Ahmad yace  "ina ganin ƙauna, ikon Allah dan Allah Jidda ayi haƙuri idan muka dawo daga tafiya Yusuf ya koma ɗakinsa" Seda Umma tayi dariya, jin abunda Alhaji Ahmad ya faɗa, gaba ɗaya suka raka shi har bakin mota ya tafi, sedai tafiyarsa babu wuya aka girke 'yan sanda a bakin layin su Yusuf dan basu tsaro. Mutanen layin sunata gulma dan sunga an kawo' yan sanda layin, wataƙila Yusuf aka kuma zuwa kamawa, tunda yai wannan laifin unguwarsu bata rabo da 'yan sanda. Yusuf yana son ya keɓe da Widad suyi hira sosai, amma kunyar Umma yake ji sosai, Umma kam basar dasu tayi kamar bata san da zamansu ba, sabgogin gabanta kawai take yi. Bayan sallar magariba Yusuf ya dawo daga masallaci, Widad tace  "Yoseef nayi waya gida, Nura zezo da mota muje farm House mu ɗakko kayan. Yusuf ya kalli Umma, amma yaga basu take kallo ba. Ba daɗewa sega Nura direban Daddy ya ƙaraso, Yusuf yaje ya samu Umma yace " Umma zan raka Widad ta ɗakko kayan ta " Umma tace  "sekun dawo" Sam Yusuf baya jin daɗin yadda Umman keyi, duk se yaji ya damu ya tsargu sosai, baya jin daɗin hakan sam. Widad ta saka takalmanta tayi waje, Yusuf yabi bayan ta, suna zuwa Nura ya buɗe mota ya fito yana, jinjinawa Yusuf hadda duƙawa yana   "Allah ya temaki me gida, Allah ya tsare gabanka da bayanka mijin Hajiya Widad, siriki ga Alhaji Nasir Daula" Yusuf yai murmushi yace  "Nura karka bani kunya mana dan Allah, ni nayi laifi ma, tunda aka sakeni, ban samu nazo mun gaisa na muku godiya ba, saboda bana son sake zuwa gidan nan ne, amma ina godiya Nura" Yai maganar yana miƙawa Nura hannu su gaisa, Nura ya zare ido yace  "wane talaka haɗa hannu da kai yanzu? Ai sedai ai muku gaisuwa irin taku ta manya" Yusuf yace  "dan Allah Nura ka bari, bazanji daɗin haka ba, ka barni a Yusuf direba na kawai" Widad tace  "aikuwa naga wanda ze kiramin miji da direba, yaga yadda zanyi dashi, koda yake ni kaɗai zan dinga ce masa direbana" Sukayi dariya gaba ɗaya, Widad ta ɗakko ƙaramar jakarta, ta ɗebo kuɗi ta miƙawa Nura tace  "gashi nan, ka hau mota ka koma gida, bawa Direbana mukullin, zamuje yawo tare" Yusuf yai murmushi yace  "Yarinya ki cigaba da cemin direba, idan na kaiki bazan dawo dake ba" "kai ka isa"? Tai maganar tana kaimasa dukan wasa a ƙirjinsa, Yusuf ya karɓi mukullin motar suka shiga suka tafi. Nura kuma yai ram da kuɗin da Widad ta bashi, dan kuɗin yafi ƙarfin dubu Ashirin, yana tafe yana mamakin yadda Widad ta canza gaba ɗaya, ga kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin so takewa Yusuf ba. Haka ya isa gida yana wannan mamakin da tunani, Isa yace  "ha na ganka kao kaɗai? Ina motar da kuma gimbiyar Daula?" Nura yace  "barni inyi mamaki Isa, gaskiya gimbiyar Daula ta canza, kaga wasa da dariya?" Isa yace  "na gani ranar data zo nan kam" Nura yace  "mhmmm, na yadda dare ɗaya Allah kanyi bature, nikam dama can Gimbiya bata son Yusuf kuwa, tunani nake yadda ko a baya da yana direbanta, tana masa wulaƙanci son ranta amma bata yadda wani ya taɓashi ba, kai kaga soyayya, motar suka karɓa wai zasu unguwa, Allah sarki dafa a cikinmu yake, amma Allah ya tsame shi ya auri 'yar masu gida, shikenan Allah ya masa sitirar arziki, dan ynzu yayi hannun riga shida talauci, da Daula yana da wata' yar nima se ince inama inama" Isa yace  "Inama me? Kana ganin baƙar azabar da ya sha, kafin ya kuɓuta, ni mamakin da nake ya akayi sukayi auren ne?" Nura yace "kanaji ana gayamaka, Saleh ne ya kuɓutara dasu, ya kaisu wani ƙauye aka ɓoyesu, kasan ta bata da yadda sam, taƙi yadda da kowa seshi, kuma ance lokacin bata da lafiya sosai, tace bame kula da ita seshi, shine fa sukayi Aure a can, daga nan kuma abu ya zame masa silar Arziki, dan nasan yanzu ita da abunda ta mallaka yana da iko dasu, dama ka santa ga kyauta, gaskiya ze warwasa, inama inama nima ace in samu dama haka ko bata kai kamar tasa ba" Isa yace  "ga Amal, ka lallaɓa da ita mana"   Nura ya haɗe rai yace  "Agolar? Uwar me taci balle ta bani, suma yanzu suna fama da kansu, sun saida koma, komai ya ƙare musu, an kashe babban ɗa, uwa ta tafi hannun hukuma, ita wannan ga rashin lafiya, waccan ga shaye2, komai ya ƙare, ni nayi mamaki ma da Gimbiya ta ƙyalesu har yanzu zaune a cikin gidan nan, ai dama shi ramin mugunta idan zaka ginashi, seka gina shi gajere, dan wataƙila kai zaka faɗa " Isa yace " babu wanda yafi bani mamaki, se Alhaji Bulama ubangiji Allah yayi mana tsari da azzalumai kamarsa, yanzu duk yada yake da Daula, da soyayyar da yake nunawa Daula, ashe azzalumi ne mufuki, na ƙaryane zagon ƙasa yake masa, gaskiya mun shiga haƙƙin Widad na ganin aibunta, ashe tana da dalili akan ƙin mutane, ji wannan asara fisabilillahi " Nura yace " bari kawai Isa, duniya babu gaskiya, mutane mun lalace se fatan shiriya, amma tabbas gaba ɗaya mutanen nan sunyi tarayya a cikin ƙaddarorinsu, Alhaji Daula, 'yarsa da kuma Yusuf daya shiga rayuwarsu daga baya, sedai fatan Allah yasa bakin wahalrsu kenan, kuma Allah ya bayyana Alhaji Daula " Isa yace " Ameen ya Allah " Yusuf da Widad kuwa, seda suka sha yawonsu a gari, sannan ya kaita suka ɗakko kayanta suka dawo gida. Ɗakin Umma ya kai akwatin kayan nata ya ajiye, ita dai UMMA bata tanka musu ba, tana ganin Yadda suke rawar kai akan junansu, da nan nan da juna cike da tsantsar kulawa da soyayya. Yusuf yace  "Umma kinci Abincin dare ne?" Umma tace  "eh naci, ga naku can a flask" Yusuf ya ɗakko flask ɗinAbinci ya kawo, tuwon Alkama ne miyar kuɓewa Umma dafa, Yusuf yana zubawa Widad kamar zata shiga cikin kwanon, saboda yadda yawunta ya tsinke. "Yoseef dan Allah ka zuba da sauri mana, kana yi a hankali fa, kuma ni sonake inci" Tai maganar a ɗan Shagwaɓe, Yusuf ya kalli Umma, amma yaga hankalinta baya kansu, kuma tana jin taɓarar da Widad ɗin keyi. Yusuf a hankali yace  "bazanyi saurin ba" Ta harari Yusuf tana tura baki, ya zuba mata tuwon nan, miyar ta sha kifi, ya samat man shanu, yadda Widad ta duƙa tana zuba tuwon nan yafi komai bawa Yusuf mamaki, ci take kawai ko magana ba tayi. Yusuf yace  "wai baki ƙoshi bane har yanzu?" Widad tace  "wallahi ban ƙoshi ba, rabona da Abinci inci cikakken Abinci cikin kwanciyar hankali, tun ranar da muka baro ƙauyen nan, bana samun Abinci inci, ga Abincin yayi daɗi Sosai" Yusuf yace "ikon Allah, yanzu ke tunda kike gurin Bulaman bakya cin Abinci?" Widad tai murmushi me ciwo tace "Yoseef, bana son tuna abunda ya riga ya wuce, ban zaci zan kuɓuta ba, na sha wahala fiye da tunaninka, banda duka da baƙar azabtarwa ba abunda nake sha a hannunsa, ga ɗansa kuma Fahad, daya dinga nema yaci zarafina, bana samun abunda nake so inci, komai bayamin daɗi, shiyasa na masa wannan tabon da wuƙa a fuskarsa, ko zan rage raɗaɗin abunda yayi min" Gaba ɗaya jikin Widad yai sanyi tace "ƙaramin tuwon nan, yunwa nakeji ban ƙoshi ba" Ya sake zuba mata, ta dinga cin abunta, ba wata kunya ko kara seda taji tayi ƙyat babu sauran gurin zubawa sannan ta haƙura, ta tashi taje fridge ta samo ruwa me sanyin gaske, ta zauna ta sha abunta ta wanko hannunta tazo ta zauna tana hutawa. Yusuf yace "Sannu da aiki" Widad tai murmushi ba tace komai ba. Abincin data cine ya fara taso mata, tai shiru ta kasa magana, Yusuf ya zuba abunda ta rage yana ci. Cikin hanzari Widad ta tashi ta fita, ta dinga amai, seda ta amayar da duk abunda taci, Yusuf yabi bayan ta da sauri. Tayi amai sosai, Yusuf ya temaka mata, ta gyara jikinta ta kuskure bakinta. Umma ta fito daga ɗaki tace "garin yaya take amai haka? Ko bata da lafiya ne?" Widad tace "A'a Umma, lafiyata ƙalau" Yusuf yace "inaga ko over feeding ne da tayi" Umma tace "in ba hali, ko Asibiti zaka kaita saboda dare" Widad tace "A'a, base munje Asibiti ba, ya lafamin ma" Umma tace "shikenan, kije kwanta ki huta" Widad taje ta canza kayanta, zuwa na bacci ta sake burma ƙaton hijjabinta, ta nemi guri ta kwanta a ƙasan carfet. Umma ta shigo ɗakin ta ga Widad a kwance a ƙasa tace "tashi ki hau kan gadon mana" Widad tace "A'a Umma, bana jin daɗin kwanciyar kan katifa, bayana ciwo yake nafison kwanan ƙasa" Umma tace "shikenan" Widad dukda basar da ita da Umma take, amma taji daɗin ganin yadda Umman, ta nuna mata kulawa. Umma taje ɗakin Yusuf tace "bani bargonka guda ɗaya, a shimfiɗa nata tace bata son kwanciyar kan gado" Yusuf yace "yawwa Umma, naji ana cewa za" ayi tafiya da weekend, amma ina za'aje ne? " " ban sani ba, meya hana ka tambayi matarka? Bani bargo ni" Yusuf ya miƙa mata bargon, ya ja bakinsa ya tsuke. Umma ta gyarwa Widad gurin kwanciya, ta kwanta. Nurat kam gaba ɗaya damuwa ta addabeta sosai da sosai, bata jin daɗin zaman gidan gaba ɗaya, gashi ta saka duk mutan gidan a damuwa, ganin yadda taƙi sakin jikinta, Nurat tai tunani taga damuwa bazata maganta mata abunda ke damunta ba, ta tashi ta fito falon gidan. Ba kowa a gidan, duk ma'aikata ne sun tafi gurin aiki, ƙannen Khalil kuma duk suna kudancin Nigeria suna karatu. Nurat ta gyara ko'ina na gidan, tayi girki yaje tai wanka ta dawo falo tana kallo, duk a ƙoƙarin ta na kauda damuwar dake ranta. Wajen ƙarfe biyu Khalil ya dawo gida, ganin Nurat a falo tana kallo yasa yaji daɗi, ba kamar da ba da kullum tana ɗaki, ya ƙaraso yana mata murmushi yace "Sisyna, masha Allah, wannan kyau haka" Tai murmushi taje ta karɓo kayan hannunsa, tana masa sannu da zuwa tana masa murmushin nan nata me ɗaukar hankali. Yaji inama ace matarsa ce. Nurat tace "Sannu da zuwa, kaje kai wanka kazo yau nina yi girki kaci Abinci" Khalil yace "ashe yau da shagali, zanci Abincin 'yar auta" Nurat tai murmushi, taje ta kai masa kayan ɗakinsa, dake kusa da falon. Bayan yayi wanka yai salla, ya fito ya zauna a falo yana jiranta, ta shigo da sallama hannunta ɗauke da kulolin Abinci, ta tarar da Khalil ya zubawa wayarsa ido. Nurat tace "inyee, da alama wannan matashin barrister ya shiga soyayya, hoton wa ake kallo haka?" Ya ɗago ya kalleta yace "kalleki, wai hoton wa nake kallo, niwa zan kalla" "Nifa dama baka taɓa nunamin budurwarka ba, gaskiya yakamata kayi aure haka, haba seka zama tuzuru tukuna, dan kaga Mama ta shagwaɓaka ne, da Abincin ta, ta koraka bakin gate a maka ɗaki, sannan a dena baka abinci zakayi aure" Khalil yace "kice azabtar dani za'ayi kenan? Hmm ni tsoron matan yanzu nake Nurat, soyayyar gaskiya tana wahala, shiyasa ni ban taɓa budurwa ba" Nurat tace "No akwai soyayyar gaskiya mana, kai dai kawai kace tsoron 'yan mata kake yi, you can't toast a lady" Tai maganar tana dariya, Khalil ya girgiza kai yace "Eh naji ɗin, yanzu dai in kin matsu inyi Aure ki samo min budurwa, sannan ki dinga rakani zance" Nurat tai murmushi, seda fararen haƙoranta suka bayyana tace "ba budurwar da zata aureka kuwa a haka, in dai sena raka ka zance" Ta zuba masa Abinci, yanaci yana kallonta, yana jin kamar ya gayamata yana Sonta, sedai yasan zuciyarta tana tare da Yusuf. Da Safe Widad ta tashi, Umma tana bacci ta tafi ɗakin Yusuf, yana kwance yayi ɗai ɗai akan gado, yana baccinsa. Ta kalli ɗakinsa, ɗakin tsaf dashi, kamar ɗakin wata matar ga Mirror, da gado wardrobe komai tsaf dashi. Ta ƙarasa kan gadon nasa, ta zauna ta ƙura masa ido, Wani murmushi take ganin yadda yake baccinsa hankali kwance, kamar wani jariri ya ɗan ciko daga ramar da yayi, sedai shima jikinsa duk tabon duka daya sha a prison. Hannu ta kai tana shafa gefen fuskarsa, tai ƙasa sa muryarta tace "Hubbyna ka tashi muna jin yunwa fa" A hankali ya buɗe ido ya kalleta yace "ke kin fiye takura, haba Babyna wace irin yunwa ƙarfe shida na safe?" Cikin shagwaɓa tace "ni dagaske yunwa nakeji, ka tashi yunwa nakeji" Yusuf ya noƙe kafaɗa, yana ɗora kansa akan cinyarta yana lumshe ido. "Wallahi idan baka tashi ba, zan zauna se Umma tazo ta gamu a nan tare" Ba shiri Yusuf ya miƙe zaune, yace "rufamin Asiri, tashi muje" Widad ta dinga dariya, har sunje bakin ƙofa, ya juyo ya kalleta ya rungumota jikinsa yai kissing ɗinta yace "good morning" "Morning, ka tashi lafiya?" "Alhamdilillah, ya babyna?" Tace "yana nan yana jinka" Yai murmushi, suka fito tare suka shiga kitchen. Suka feraye dankalin hausa tare, suka dafa tea, suka shiga suya Tare, hirarsu kawai suke kamar suka ɗaine a gidan. Yusuf so yake ya saki layi, amma Widad na kakkarewa tana hanashi. Umma kuwa tuni motsinsu ya tashe ta, amma bata fito ba karta takurasu, suka gama sukayi wanke wanke suka gyara komai tsaf. Widad na shiga ɗakin ta tarar Umma ta tashi, Widad tace "Umma ina kwana" Umma tace "lafiya ƙalau, ya jikin naki?" Widad tace "naji sauƙi" Umma tace "Allah ya ƙara sauƙi" Duk yadda Umma take basar da Widad, Widad bata nuna mata taji haushi ba sam, tana girmamata sosai, sedai bata iya kara ta ɓoye soyayyarta ga Yusuf ko a gaban Umma ne Wajen ƙarfe goma na safe, ciwon ciki ya kama Widad, tun tana mazewa seds Umma ta gane. Lokacin Umma ta aiki Yusuf, baya gidan amma ganin Yadda Widad ke murƙusus yasa Umma ta kira shi a waya. Da hanzari ya dawo gida, ya tarar Da Widad ta durƙusa tana kuka, se numfashi take da ƙyar. Yusuf ya ɗagota yace "Widad, lafiya kuwa?" "Yoseef cikina, ciwo yakemin" "Wai anya ma kina zuwa Asibiti awo?" Umma tace "Awon me kuma?" Ɗan dirircewa Yusuf yayi, dan Umma bata san da ciki a jikin Widad ba, saboda kullum cikin zumbulelen hijjabi take. Yusuf yace "ina nufin, taje likita ya ganta" Umma ta tashi, taje ta ɗaga Widad daga jikin Yusuf, ta kwantar da ita akan pillow, tace "naga da mota a hannun ka, jeka ɗakko kazo a kaita Asibiti ko ɓarine" Yusuf yace "Umma ba ɓari bane" Umma tace "kamar yaya?" Widad cikin kuka take cewa "Umma cikina, zan mutu" Widad ta haɗa gumi sosai Umma tace "kiyi ta ambaton Allah, kidena kuka" Widad ta kwanta rigingine, tana jujjuya kai, hakan ya bawa cikin nata damar fitowa sosai, Umma tayi mamakin ganin cikn nan, kenan dama da cikin aka kamosu? Umma tace "to ko haihuwa ce?" Widad ta girgiza kai tace "beyi wata shida ba, Allah yasa ba zubewa zeyi ba" Yusuf dai haka ya ɗakko mota, suka sa Widad a ciki zuwa Asibiti. Ta sha wahala sosai, seda suka wuni a Asibiti, likita ya tabattar musu da cewa allurar zubar da ciki da aka dinga mata ce take bata wahala haka. Yusuf yace "Widad meye ya haɗaki da allurar zubar da ciki?" Widad tace "Bulama, shine yasa aka dingayi min tunda akace masa ina da ciki, Amma dai cikin yana nan ko likita? Bana son in rasa shi dan Allah" Likitan yace "ki kwantar da hankalinki, bakomai cikinki yana nan lafiya" Haka nan Umma taji Widad tana bata tausayi sosai, mussman da taji tace allurar zubar da ciki aka dinga mata. Se bayan ƙarfe goma na dare suka koma gida. Bulama yasha matsa sosai, dan gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, a hankali yake ta faɗar da wanda yake haɗa baki ana cutar Daula, ga HIV ta fara nunawa a jikinsa, gudawa yake ba ƙaƙƙautawa, ga zazzaɓi me zafin gaske da yake fama. Ya kalli 'yan sandan dayake hannunsu yace "Ranka ya daɗe, yakamata fa ace an barni naga lawayerna, dan har yanzu ba' a tabattar da laifin da ake zargina dashi ba" Ɗan sandan yace "ka makara, dan baka da wannan damar kaima, kamar yadda ka siye wasu daga cikin hukumomin tsaro akayi maka yadda kake so a wancan karon, to yanzu an siyesu, ninkin yadda ka siyesu, kuma anace kar a sake a baka duk wata dama ko kwatankwacin ƙofar Allura ce, dan haka karka yi zaton zakayi free, kaida 'yanci har abada daga kai har muƙarrabanka!!! AMANA! AMANA!! AMANACE!!! DUK WANDA YA FITARMIN YACI AMANA AYSHERCOOL 07063065680 12/9/21, 2:40 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 166__167 Gaba ɗaya a razane suka kalli Bulama, ya cigaba da cewa  "bayan ya kashe Huda, shine ya ambaci sunana har Widad taji, da niyyata har ita a kashe, bayan ya kasheta ne, a gurin zaman makoki Widad ta tonawa Bala asiri a gaban Wannan ɗan sandan, shima na faɗi na tashi na saka aka kashe shi!" Yusuf ya rintse ido, yana jin kamar Bulama yana rura wuta a zuciyarsa. Bulama ya cigaba da cewa," daga nan na lallaɓ Saleh, akan ya saki Halima, akwai kaso me tsoka daze samu idan harya sake ta ta aureka, dama ba iya kula dasu yake ba, dan haka ya amince dan yaji batun kuɗi, ya sake ta ko idda batayi ba, na dinga tura ta a gurinka, har seda ka amince da Aurenta, ka kuma ɗauki ɗawainiyar yaranta, ta aureka dan ta dinga tatsar mana kuɗi a gurinka. Da kuma saka ido, domin mu samu ta karɓo mana wannan dukiyar daga hannunka, na saka aka dingayi wa 'yarka Allurar mahaaukata, saboda kar ta tona min Asiri, kuma inyi amfani da damar idan ta haukace ko Allah zesa in samu inda dumiyar nan taje, amma a banza, na dinga tura maka saƙonni kala kala, na razanarwa akan dukiyar nan, na dinga farmakar ka kaida' yarka da barazanar kisan kai, sannan duk wanda yai yunƙurin raɓarku koku raɓeshi, se shime in farmake shi, na taka rawar gani akan AƘIDAR 'yarka, dana ga hakan bzata yuwu ba, na koma ma baka shawarar ka aurar da ita ga ɗana Fahad, hakan zesa ta canza halaye, amma a zuciyata ina son ta auri Fahad ne dan idan bamu samu waccan dukiyarba, mu gane zunzurutun dukiyar da ka malllaka mata, duk wani meeting da yadda za'a karɓi dukiyarka da matarka mukeyi, watarnma se cikin dare a hotel haka muke meetings ɗin, bazan ɓoye maka ba Daula, tunda komai yazo ƙarshe wallahi ban taɓa sonka ba, na tsaneka ko ganinka nayi cikin walwala se inji kamar in kasheka in huta, kafini komai bana appreciating duk wani goodness ɗinka, burina kawai inga bayanka hankalina ya kwanta, saboda ganinka a raye ma bana ƙaunar yi " Daula ya sunkuyar da kai, hawaye na bin idonsa, Alhaji Ahmad yace" kaiconka Bulama, kayi asara Nasir da dukiyarsa, da ƙarfinsa haka ya dinga maka wahala kai da iyalinka, ka kawo wasu ma cin arziki, kuma ya musu, amma ƙarshe ga inda ciwon hassada ya kawoka, to ina maka Albishir dukiyar da kake hari, ga me ita nan" Ya nuna Yusuf, sannan ya ci gaba da cewa "dukiyarsa ce, shine ɗan Yusuf yayan Nasir, wanda kasa rai akan lallai seka karɓi dukiyar, ka azabtar dashi da ahalinsa saboda abun duniya, yadda kazo a banza haka zaka koma a wofi, sannan duk wata kadara indai ta Nasir ce, zamu karɓeta har gidan da kake ciki da motoci, da kamfanin daya ɗora kka akai ka maida shi naka, sannan kema Halima da kika dinga siyar da kadarorinsa, bayan wanda kika ci a baya, da wanda kika dinga sata, duk wanda kika siyarwa da wani abu ya sai aikin banza, zasu iya yin shari'a daku ku biyasu dukiyarsu, sannan bisa ga adalci na Nasir, yace  "ze baku duk wata dama a shari'a, baze amfani da dukiya ba ai muku hukuncin daya dace daku akan kisan kai na matarsa, da kuma garkuwa da kuka yi masa da yaransa" Widad fuskarta sharkaf hawaye tace  "Nikuma zanyi Amfani da ƙarfin dukiya, ayi masa irin shari'ar da yai amfani da kuɗi akayiwa mijina, kaiconka Bulama daga kai har 'yar uwarka da sauran mutanen da suka zaluncemu, kuda Allah" Ana cikin haka aka tankaɗo Abbas ma, Ya kalli Yusuf, Yusuf ya kalle shi, Abbas ya fashe da kuka yana faɗin "dan Allah Yusuf ka yafemin, na biyewa Zuciya da son abun duniya na aka haɗa kai dani aka cutar da kai, dan Allah Yusuf ka yafemin" Yusuf ko kallonsa beyi ba, yai waje da sauri, yana tuna shima irin yadda ya amince da Abbas, be taɓa aboki kamarsa ba, amma yai masa wannan muguntar. Su Alhaji Ahmad ma sukayi waje, daga gurin, su Alhaji Musa suna ta salalami dan sun san tasu ta ƙare, ga jikin girma dama kuɗine yasa ba'a gane tsufan nasu sosai, yanzu kuwa kam se cituttukane ke kunno musu kai kala kala. Wani ɗan sanda ya biyo bayansu Daula yana musu bayani "To yallaɓai har yanzu muna nan munata tattara bayanai, da bincike akan wannan baƙin azzalumi da duk wanda ya haɗa kai dasu, kama daga yadda suka haɗa baki da megadinka, wani Bala zuwa yadda yasa aka kashe shi a gidan yari, da duk wani wanda yake da hannu muna ta kama mutane ɗaya bayan ɗaya, kuma ba da daɗewa ba zamu gurfanar dasu a gaban kotu insha Allah " Alhaji Ahmad yace " Masha Allah, yayi kyau sosai wannan shine wanda aka bawa aikin dana bayar, Bulama sukayi amfani da wannan damar wajen cinma burinsu" Widad ta kalli Alhaji Ahmad tace "wane aiki kenan?" Alhaji Ahmad yace  "Aini koda bama tare da Daula, ina bibiyar al'amarunsa, kuma haka nan nake zargin Bulama zata iya kasancewa da hannunsa a masu yiwa Daula barazana, dan tuni ns gane dukiyarsa yakewa, sedai a lokacin son Bulama ya rufewa Daula ido, baya ganewa, ina jin duk labarin yadda kike bakya sakewa da mutane, da larurar taɓin hankali da kuma bibiyarki da ake akan wannan dukiyar, ni kuma na saka ayi bincike akan me bibiyar taku, sannan a baki tsaro ba tare dake ko mahaifinki wani ya sani ba, sedai ban san yadda akayi Bulama yasan an bada wannan aikin ba, har ya shiga ƙoƙarin karɓar file ɗin idan an gama binciken, dan ɓatar da duk wata hujja da zata saka a gane shi " Widad ta sauke ajiyar zuciya tace " kowa yayi nagari kansa, a duniya babu abunda za ayiwa Bulama wanda zesa mu huce takaicin abunda yai mana, sedai ai masa hukuncin daya dace duniya sauran a barshi se a lahira " Haka suka shiga mota suka tafi gida, suna jinjinawa azabara zalunci da baƙar mugunta na Bulama, tunda ya kashe ɗan 'yar uwarsa waye baze kashe ba, duk saboda abun duniya. Da suka koma gida, fuskonkinsu kawai Umma ta kalla tasan wani abun takaicin suka kuma zuwa suka jiyo, a gurin' yan sanda shiyasa tun farko tace bazata bisu ba. Umma tai musu sannu da zuwa, Daula ya wuce ɗakin hutawarsa, saboda yana buƙatar ya ɗan huta yayi tunani. Widad ma ta janye mijinta, zuwa wani ɗakin daban, Alhaji Ahmad ya zauna a kujerar dake kusa da ta Umma yace  "Hajiya Jidda" Umma tace "Jiddan dai banda Hajiyar" "Dole ace miki Hajiya mana, tunda kika riƙe ɗan Daula, kika riƙe babban attajiri haka" Umma tace 'mhmm, ni tsoro nake ma kar yace ze ƙwacemin ɗana, bana son sunana ya canza daga Umman Yusuf, dan bana tunanin ko da Allah ya bani haihuwa, zanso ɗan nan kamar yadda nake son Yusuf' 'tabbas nima nagani, kuma Wallahi Daula ua jinjinawa ƙoƙarin ki, yace idan ya kalli abunda Bulama ya masa, se yace "Anya kuwa akwai ragowar mutanen kirki a duniya? Idan ya duba irin riƙo da wahalar da kika sha da Yusuf se yace duk lalacewar zamani akwai na Allah, wallahi kin ciri tuta Jidda, kuma abunda kikayi Jihadi ne, riƙon maraya da zuciya ɗaya tamkar ɗan da kika haifa " Jidda tace " gashi nan ina morarsa, wataƙila da ban riƙe Yusuf ba haka tsufa ze riskeni babu me jin ƙaina, 'yan uwana bama su ƙarfi bane, hasalima a gurina suke nema, bani da wanda muke uwa ɗaya uba ɗaya sedai' yan uba, amma Yusuf ya riƙeni Uwa, yanamin biyayya fiye da yadda kake zato, ƙare magana ko ɗan dana haifa banajin zemin biyayyar da Yusuf yayi min, koda ban taɓa haihuwa ba, amma ni riƙon Yusuf yamin rana, ko be zama komai ba, tausayinsa da jin ƙansa ya gamamin komai " Alhaji Ahmad yace" hakane, tabbas yana da haƙuri da biyayya, kuma bayan wannan dukiyar dai Allah yayi tasa ce, da ba lallai ya iya jure wannan tsananin da wahlar ba, amma da yake tasace kuma Jininsa ne Daula, kinga ya jure duk gwagwarmaya, an gaisheki Jidda kin cika Uwa tagari " Jidda tai murmushi tace  'Nikam Ahmad, ina naka iyalin ne?" "Meyasa kike tambayata?" "gani nayi tunda mu kazo banga ka koma gidanka ba, ko ka yi zancen su ba" Yai murmushi yace "iyali suna nan a kano, da ina nan zaune tare dasu ne a nan Abuja, tace ita dai tafison zaman kano, shine suka koma suka barni sedai in dinga zuwar musu" Umma tace "Allah sarki, Allah ya raya zuriya" Yace "ameen ya Allah, Jidda nayi mamaki har yanzu kina nan da kyanki baki canza ba gs gayu" "kajika da wani zance, ina wani kyau da gayu bayan na tsufa" "wallahi baki tsufa ba, kalleki fa ras dske, amma meyasa baki sake aure ba bayan mijinki ya rasu?" Umma tai ajiyar zuciya tace "saboda ina son in kula da yarona, idan na auri wani waze yadda ya riƙemin shi, mussman da bani na haife shi ba, shiyasa na zaɓi in zauna ba Aure in riƙeshi" Alhaji Ahmad yace "to amma ai yanzu ya girma, shima me riƙe wasu ne mussman wannan sitira da Allah yayi masa yanzu, saboda haka yakamata kiyi aure ai" Umma tace "tsofaitsofai dani se in kama yin wani aure, a'a ai na girma Aure mun barwa yara" "kece kika tsufan kokuma wa?" "Eh mana, na tsufa" "yanzu fa da wanine ya gaya miki seki ji haushi ko?" Umma tace "akanme zanji haushi, ai nasan na tsufan ne" Alhaji Ahmad yace "ba wani nan, ni dai ina zawarci har yanzu, ina so" Umma ta kalli Alhaji Ahmad tace "dan Allah ka dena wannan zamcen haka, haba Ahmad" "kinga dole inyi wannan zancen, haba Jidda me zesa ki haramtawa kanki Abunda Allah ya halatta, haka zaki cigaba da zama babu Aure kenan?" Tace "eh mana, har zuwa lokacin da Allah ze karɓi rayuwata" Alhaji Ahmad yace "No, gaskiya bazaki zauna haka ba, kawai ki tsaya mu sasanta" Umma ta miƙe tace "kai dai bazaka canza hali ba, ka girma kana abun yara" Yai murmushi yace "Au hakama zakice? Aini bazaki girman a idona ba, tunda.. Bari dai in shiru" Umma ta bar falon tana dariya. Yusuf kam salla yayi a ɗakin da suke, Widad tasa aka kawo fruit da madara me sanyi, amma Yusuf yaƙi sha. Widad tace "haba my Fluid of life, wai baka murna da kasancewat ƙanwa a gareka ne? Naga baka walwala sam duk kana cikin damuwa" Yusuf yai murmushin ƙarfin hali yace "yama za'ayi ince bana farinciki da Kasancewar ki ƙanwata, na daɗe ina miki so mai tsanani da takurawa ruhi, se yanzu na tabattar da ashe son ne ya haɗemin dana 'yan uwantaka, tsabar farinciki ne yasa na rasa ta ina zan nuna tsantsan farinciki danake ciki, ashe tun tuni da' yar uwata nake tare, shiyasa nake jin zan iya yin komai ko in bada komai nawa, gurin baki kariya koda kuwa raina ne, nayi farinciki da haka, kuma gefe guda ina jimanta irin wahalar da muka sha, da mamakin cin amanar yadda na mutanen wannan zamani, dukda abunda akayimin be kai na Daddy ba, Amma Widad ko a tatsuniya akacemin Abbas zemin haka bazan yadda ba, ashe haɗa baki akayi dashi akamin gadar zare, yazo ya lallaɓani aka bani aiki, shi yayi dan cutar dani, ashe hakan Silar taradda farinciki nane, kai Widad mutane abun tsorone, banga laifin AƘIDARKI ba baby, kaso mutum dan Allah shikuma bashi da maƙiyi kamarka" Ya ƙarasa maganar muryarsa na rawa, alamun karaya Widad ta rungume Yusuf tana shafa sumar kansa ta sigar rarrashi tace "tabbas haɗuwarmu da wasu mutanen a rayuwarmu darasi yake bamu, da mutane sunyiwa AƘIDATA mummunara fahimta, amma ba haka kurum nake abubuwan da nake ba a baya, dukda daga baya na gane a AƘIDATA akwai wadda bata kamaceni ba, amma a hankali duniya ta ladabtar dani ns gane rayuwa sosai, sannan nayi farinciki na kasancewarka ɗaya daga ahalina managarcin mutum me matuƙar kamala, ina sonka Yusuf " Yusuf ya kalleta dukda gefen idonsa hawayene ke zuba, amma yai murmushi har seda haƙoransa suka fito yace " waye ya koya miki yadda ake faɗar sunana? In kikace Yoseef yafimin daɗi, saboda nasan ba wanda yake faɗar sunana a haka se Gimbiyar Yusuf " Widad tai murmushi tana sake rungume Yusuf a jikinta, Widad tace "Alhaji Yoseef Nasir Daula, seka dena bearing wancan sunan, tunda har gida akazo ama kashedi akan ka dena amfani da sunan saboda tsabar jaraba irin ta mutanen nan" Yusuf yace "am sorry to say, Baby bazan iya dena amfani da sunan Bashir maitama ba, saboda shina saniba ubana, shina buɗe ido dashi yana ɗawainiya dani" Widad tace "hakane, babu laifi Mijina" Yace "Amma ni gaskiya, wannan kuɗin da ake shirin bani, nifa ban san yadda zanyi dasu ba" "Yoseef, wannan kuɗinfa na mahaifinka ne da mahaifiyarka, wakake so a bawa idan ba kaai ba?" Yusuf yai shiru yana zancen zuci, Widad tace "mu bar maganar nan, zamuje ƙauye a satin nan yaushe zamu tare ne, nina gaji gaskiya" "to mara kunya, kije ki tambayi Daddy, wace tarewa kike nema, banda wannan tarewar na cikinki" Sosai Yusuf ya bata dariya tace "ai shikenan, bama semun wani tare ba, ɗaki ɗaya zamu koma kwana, ai akwai ɗakuna dayawa a gidan nan" Yusuf yace "Allah ya baki haƙuri, kiyi haƙuri mu koma kano kinji ƙanwata" Tai murmushi tace "naji, tashi muci Abinci ko?" Haka suka wanzu suna farinciki da annashuwa a tsakaninsu. Nuray kama tunda ta gano Khalil sonta yake, take jin tausayinsa, be taɓa gayamata ba, amma idan tana tuna kyautatawarsa, da kulawarsa a gareta, tabbas idan ba so babu abunda ze kawo hakan. Tana kitchen tana aikace aikace tana tunanin yai sallama ya shigo, ta amsa masa tana binsa da kallo. Yace "Nurun, me kike soya mana ne?" Tai murmushi tace "kwaɗayi nake ji, ma rasa me zanci na tsiri yin cake" "kwaɗayayyiya kawai, amma dai ɗan sanmun" Tai dariya tace "mun zama kwaɗayayyu kenan" Ya ɗauka yana ci yana faɗin, "kai Komai naki na dabanne, ban taɓa cin Abinci me daɗin wannan ba fa, Allah ya bani mace tagari wadda ta iya girki kamarki" Nurat ta kasa ce masa komai se kallonsa kawai da take yi, jiki a sanyaye yace "lafiya kuwa?" "Lafiya ƙalau Yayana" "to ai gani nai kamar jikinka ba ƙwari fa, ko akwai matsala ne?" Ta girgiza masa kai alamar aa' "ko Yusuf ɗinne dai ya kuma yi miki wani abu?" "Brother, Yusuf yafi ƙarfina na haƙura dashi" Cikin damuwa yace "saboda me? Ya da karaya haka Nurat" "Khalil, Ka sani an tabattar da Widad matarsa ce, aure sukayi Dan harda tsohon ciki ma, kasan a ynzu na shiga sahun maƙiyan Widad, nasan bata ƙaunata yanzu haka, Yusuf yana son matarsa sosai cigaba da musu shisshigi a rayuwar su ze iya basu matsala, musamman da Ummansa da take son lallai ya aureni, Yusuf mutum ne me nagarta da haƙuri ba dan Widad ba ze iya aurena, amma ga laifin da mahaifina yai musu, ga Widad nasan dukda a baya bata soyayya amma yanzu na fuskanci akan Yusuf ba abunda bazata iya ba, gara in ƙyalesu bana som zama silar rasa farincikin kowa a rayuwa, ina wa Widad murnar samin nagartaccen abokin rayuwa, nima Allah ya bani miji nagari wanda ze soni, me kyawawan halaye kamar Yusuf " Ta ƙarasa maganar, tana zubar da hawaye sosai, Khalil ya ƙarasa gabanat, wani irin matsanancin tausayinta ya kama shi, he feels her pain, yasan yadda raɗaɗin son maso wani yake, Nurat ta so Yusuf sosai yana zuwa inda take tsaye, ta faɗa jikinsa tana kuka, ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, da alama abun yana cim zuciyarta bata samu damar yin kukan bane ba. "kiyi haƙuri, Allah ze miki musaya mafi Alkhairi, kin san da yawa a rayuwa, mu kanso abunda ba alkhairi bane a rayuwarmu, Allah ya zaɓa miki mafi Alkhairi Ƙanwata" Ta dinga jinjina masa kai, amma ta kasa magana, saitin kunneta yace "koda kuwa nine, idan Allah ya musanya miki kina so?" Tashi tayi daga jikinsa ta goge hawauenta tace "cake ɗina ze ƙone, bani guri in duba" Tai maganar tana basar da abunda yace kamar bata ji ba, ya dinga bimta da kallo yana tunanin she didn't accept his proposals. Su Widad sun shirya tsaf, domin zuwa ƙauye, Widad se murna take, Amma daga baya se jikinta yai sanyi tace "Daddy, wai ina Saleh ne? Zamuje garin su gurin 'yan uwansa, me zamuce musu idan suka tambayemu shi?" Daula yace "ai kema kin san Daula baya manta alkhairi, Saleh yayi sintiri a Asibiti saboda ni, kuma shiyafara gayamin kuna hannunsa, sannan kunyi Aure, saboda alkhairin da yayi muku nakejin zan iya yafe masa, na karɓeshi a hannun 'yan sanda, an kai shi Egypt saboda anma rauni da duka a hantarsa, za' a masa aiki " Widad tace" Daddy hanta kuma? " Daula yace "Eh, saboda dukansa da aka dingayi a ciki ya samu matsala" Widad tace "Allah ya bashi lafiya, amma yayi ɗawainiya damu sosai" Yusuf ne ya fito Umma da Alhaji Ahmad suna bayansa, seda suka fara shirin shiga motar sannan Yusuf yace "nifa Umma har yanzu banji yadda akayi kika san Alhaji Ahmad ba?" Daula yai murmushi yace "Budurwarsa ce ta farko tun zamanin ƙuruciya, a gidansu akaga be shirya ba Abbanka ya aureta ya barshi' Kunya ta kama Umma, kamar ta nitse a ƙasa dan kunya, Widad da Yusuf suka shiga yimata dariya. Alhaji Ahmad yace" kuma har yanzu ina so ba, amma tace min se ɗanta ya yadda, dan haka Yusuf nidai ina so har yanzu " Yusuf yai dariya ya buɗe mota yana faɗin, ni dai ba ruwana". Suka shiga mota suka ɗau hanyar garin Bauchi, bisa rakiyar 'yan sanda. Tun su Alhaji Daula suna sa ran ƙarewar tafiyar, har suka zuba ido nausawa kawai ake cikin ƙauyuka, sannan aka bar kan titi aka saki hanya aka nausa wani surƙuƙin ƙaiye, tun daga nan Daula yake tasibihi, da mamakin azabar surƙuƙin gurin nan. Nanam sukayi tafiya me nisa akan burji, babu kwalta ba zaka taɓa cewa zaka tarar da gida ba, se sama da ƙasa sukeyi danma a manyan motoci suke, amma hakan be hanasu jin jiki ba, idan aka shiga wani ramin, se Yusuf ya riƙe Widad gam saboda kar abunda ke cikinta ya wahala, a haka suka ƙaraso ƙauyen nan. Suka fir fito yayinda 'yan garin sukayi dandazo suna kallon motocin, yayin da wasu suke gudu saboda ganin motar' yan sanda. Daula ya kalli ƙauyen, ya sake kallo yace "yanzu Baby, a nan kuka rayu?" Widad tace "ƙwarai kuwa Daddy" Ita kanta Umma daba wani kuɗine da itaba, tunani take ta yadda zata yi rayuwa a wannan ƙauyen. Widad ta raɗawa Yusuf a kunne "Allah sarki, yau zanje inga ɗakin amarcinmu" Suka ƙunshe baki suna dariya Tuni labari yajewa megari, ga wasu nan sunzo a jibga jibgan motoci irin na masi sace mutane, da 'yan sanda, ya fito a ruɗe, dan baya son abunda ze tayarwa da mutanensa hankali. Sam be gane Yusuf ba balle Widad, Yusuf ya ƙarasa gaban sa ya zube yana gaisheshi, seda ya tsurawa Yusuf ido sannan ya gane shi, yace "innalillahi, Malam Yusuf kaine? Dama zan sake ganinka Yusufa?" Yusuf yace "Alhamdilillah, gani ai tare muke da iyayen namu ai" Widad ta ƙaraso itama tana gaida megari, yace "Allahu Akbar, Amarya 'yar gwaggonta" Widad tace "aikam bari in ƙarasa in ganta kuwa" Ta shiga da sallama, Hindu na zaune tana tankaɗen garin dawa, taji wani irin ƙamshin turare ya gaauraye gidan, ta ɗaga kai zata amsa sallama tayi tozali da Widad, aiba shiri tayi wani uban tsalle tai fatali da ƙwaryar garin, tai gurin Widad tace "Allah yasa ba mafarki nake ba?" Widad tace "idonki biyu Hindu, nice Widad ce" Suka rungume juna suna kuka, Gwaggo ta fito da sauri jin kamar muryar Widad, aikuwa itace ba wata ba, nan gida ya hargitse da murna da koke koke, Widad tace "ina aminiyata abikiyar faɗana Hari" Hansai tace "taje barka bayan layi ita da Hanne, amma yanzu zasu shigo" Tana gama rufe bakinta, sega Hari da gudu kamar ƙaramar yarinya "wayyo Allah na, jama'a dagaske Wudas ce? Wai Wudas ce tazo garin nan?" Widad tace "nice Hari" Widad ta rungume Hari, Hari ta shiga kuka tace "ban taɓa zaton na saba dake haka ba, seda kuka bar garin nan" Umma tai sallama itama ta shigo, nan aka shimfiɗa musu tabarma, suka karɓsu hannu bibbiyu Widad tace "Mama ga Wannan itace Umma mamanmu nida Yoseef" Hari tace "kamar yaya kenan? Ya za'ayi ku zama uwa ɗaya? ' Widad tace " zaki fara ko? Tunda na gayamiki ki barshi a haka mana" Hari tace "naji an barshi a hakan" Hanne tai sallama ta shigo, ta kalli inda Widad take, ta ganta a balarabiyarta, fatarta ta sake ja tayi kyau sosai, Kallo ɗaya Widad tayi mata ta ɗauke kai daga kanta. Tuni aka fara kiciniyar ɗora girki, Widad tace base an ɗora komai ba, sunabda abinci a mota, amma ita dai idan an gama tuwo a bata zata ci. Aka karɓo mukulli aka buɗe ɗakinsu da suka zauna, Widad cikin hawaye tace Allah sarki ɗakin mijina, wayyo rayuwa, a lokacin da nake shan baƙar azaba a hannun Bulama ji nake tamkar in dawo ƙauyen nan da zama in huta" Ita kanta Umma tayi mamakin yadda suka rayu a gurin nan, megari yayiwa Su Daddy jagora har ɗakinsu Widad, nan suka tsaya suma suna mamaki. Hindu har ƙasa ta durƙusa ta gaishesu, Yusuf yace "Hindu amma dake zamu tafi kano ko?" Hindu tai murmushi tace "waceni" "yakamata, kinga yayartaki ta kusa haihuwa, seki tayata zama" Hindu tai murmushi tace "Allah ya sauketa lafiya" Yace "Ameen" Daddy ya kalli ɗakin nan nasu yace "yanzu Widad ce ta rayu a ɗakin nan? Allah me yadda yaso sannu Yusuf nasan ka sha gwagwarmaya" Yusuf sedai yai murmushi. Hari yazo kusa da Widad ta zauna tace "abun mamaki, Wudas da ciki ana shan taɓara nasan" Widad tace "ko in kira miki Yusuf ki tambaye shi idan ina taɓarar ko ba nayi?" "kefa matsala ce dake, baki san wasa ba" Hari ta shiga halin nata na ɓare ɓaren zance, aka shiga shigo da kayan Abinci gidan nan kamar ba gobe, wanima basu san meye ba. Nan jikinsu ya hau rawa, suka tabattar da lallai Widad 'yaf ga tace gaba da baya. Widad taja hannun Hindu gefe, tace "Hindu kinga babana?" Tace "Na ganshi mana" Widad tace "tsoho ne sosai ko?" "A' a wallahi ba tshoho bane, gashi me kyau wallahi yana kama da mijinki sosai, dake dashi da Yusuf duk kuna kama, irin idanunku ɗaya sak" Widad tai murmushi tace "zaki iya auren Babana?" A razane Hindu ta kalleta tace "Kamar yaya, ta yaya babanki ze auri 'yar ƙauye kamarni, gashi babban mutum" "Hindu ki dena duba wannan, dan Allah ki aure shi, nasan zaki kulamin dashi dan Allah Hindu ki auri babana" Jikin Hindu ya hau rawa, zata yi magana amma Widad tace "yi shiru, karkice komai ina zuwa, kuma karki gayawa kowa wannan maganar" Widad taje ɗakinsu, inda su Daddy ke zazzaune tace "Daddy, i want to talk to you" Ba musu ya miƙe ya biyo bayan ta, ta ja shi can waje a wani soro tace "Daddy nifa nayi maka mata a garin nan" "mata kuma kamar yaya?" "Daddy, matar Aure dai nayi maka, dan Allah karka bani kunya kaji Daddy" "Widad, nifa na haƙura da Auren nan" "A'a Daddy, dan Allah ka tsaya ka ganta mana" Yace "shikenan" Ta shiga cikin gidan da sauri, ta tarar da Hindu a inda ta barta, jikinta a sanyaye tace "saka hijjabinki kizo muje" Hindu ta saka hijjabi, ta biyo bayan Widad, ta mata jagora zuwa inda Daddy yake zaune, gaba ɗaya yaiwa Hindu wani irin kwarjini, da bata taɓa gani a gurin wani ba. Suka ƙarasa Widad tace "Daddy, ga amaryar da nayi maka, ina fatan bazaka ƙi karɓa ba" Daddy ya kalli Hindj, yarinya ce ƙarama, yace "Amma daughter, naganta yarinya ce sosai fa, kamar zaki girme mata ma" Cikin harshen larabci Widad tace "Daddy aiba haramun bane, wallahi yarinyace tagari me nutsuwa, zakayi alfahari da ita" Yace "to ita kin tabatta tana sona? Karki ƙwareta dan son kai kinga na girma dayawa" "Daddy Hindu bazata ƙika bafa" tai magana kamar zata yi kuka. Daddy ya kalli Hindu yace "ya sunan ki ne?" Hindu dake gefe ta takure kamar bokanya tace "Sunana Hindu" "masha Allah, Hindu kinji rigimar da wannan matar ta tattago, ban miki tsufa ba?" Hindu ta kasa cewa komai, se jikinta dake ta tsuma, tana rarraba ido. Widad tace "Daddy ai mun gama magana da ita, yanzu megari zakayi wa magana, kaga se a bada kuɗin aure ma kafin mutafi. AMANACE!!! Ayshercool 07063065680 12/10/21, 1:36 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 168_169 Daula yace 'Widad mubi komai a sannu, ki bari muji ta bakinta, karki mata dole mana, kuma maganar aure ai ba' a gaggawa " Widad tace " Daddy, nasan irin zaɓen da na maka ne, ni dai ka amince kawai please " Daula ya lura da yadda jikin Hindu keta tsuma, ko idonta bata iya ɗagawa ta kalle shi, ta sunkuyar da kai tanata cimimiyewa a hijjabinta. Daula yace " Hindatu, tashi ki koma gida, Widad zata sa ki auri tsoho " Cikin hanzari Hindu ta miƙe, ta shige cikin gida tana haɗa hanya, Daula ya kalli Widad yace  "Widad, wannan haɗin naki beyi ba, kowa zega kamar an ƙwareta ne, tayi yarinta dayawa kuma kinga ba ita tace miki tana sona ba, gashi ni na riga na fidda rai da Aure" Widad tace "Daddy, na zauna a garin nan na zauna dasu, nasan halin yarinyar nan, Daddy karka duba ƙauyanci ko ƙuruciyarta, ni dai tukuicin dazakamin shine ka Auri Hindu, sannan akawo musu cigaba a garin nan, shine zaka biyani ɗawainiyar sa sukayi damu, dan Allah Daddyna " Daula yace " Naji, zanyi shawara kafin mutafi " Da ƙyar ya lallaɓa Widad ta tafi, ta koma gurin Alhaji Ahmad da Yusuf ta dinga musu magiya akan lallai su saka baki, Daddynta ya auri Hindu, Alhaji Ahmad yace "to muyi musaay, kice mijinki ya bani ummansa nima" Widad tai dariya tace  "ka samu, nidai fatana Daddy ya amince da Auren Hindu, sonake kafin mutafi ya bada kuɗin Aurenta" Umma tace "Widad, ba'a gaggawa a harkar Aure, karki takuramasa ko ita yarinyar ki takura ta fa" Yusuf yace "Umma Hindu bata da matsala, and she deserves to marry a descent person like him, idan harya yarda ya aureta ze sha biyayya" Widad tace  "Yoseef, dan Allah zomuje ka gayawa Megari, bana son Daddy yayi missing wannan opportunity ɗin" Daula yai shiru yana tunanin maganar da Widad tazo masa da ita, yadda yaga suna nan nan da su Widad, da yadda suka sake dasu, suma hira ama wasa ana dariya, da yadda mutane keta shiga suna fita a gidan, ya tabattar masa da cewa sun riƙe su Yusuf da Amana, dan haka duk wanda ya shigo gidan seya fita da kuɗi ko Abinci, Daula ya dinga basu kyautar kuɗi da Abinci, da wannan ya shigo se Widad tace Daddy ga wane a bashi kaza, ko kuma ai masa kyautar kaza. Widad sun sha hira da Gwaggo, seda aka tuƙa tuwon nan taci, suna ta faɗa ita Hari, Hari tace  "Ohh ni Hari, wai Wudas ce sa ciki, ranar haihuwa akwai kallo" Widad tace "me za'a kalla?" "raki da rashin haƙuri mana" "Hari kema fa Allah kaɗai yasan abunda kika yi haihuwar fari" Umma sunyi hira sosai da Gwaggo, ta dinga bata labarin yanayin zaman da suka yi dasu Yusuf a gidan, Hanne kam ta kasa yadda ace wannan ne mahaifin Widad, iya motocin da suka cika ƙofar gidansu ma 'yan rakiya kawai abun kallone, banda rakiyar motar' yan sanda, wai ashe dagaske dai Daula ne baban Widad, lallai yaci sunansa Daula. Ɗaliban Widad suka dinga zarya suma, suma zuwa gaishe ta da ɗaliban Yusuf, magidantan da yai ta koyarwa, sedai dukda wannan tarin kaɓakin kayan Abincin da aka rarrabawa 'yan ƙauyen, wannan yazo ya bawa Widad kyautar kuka, wannan ya kawo tsintsiya, wannan ya kawo Nono, ƙwan zabi zuma, haka suka dinga kawo musu wai suyi tsaraba, Daddy yai farinciki da karamcin mutanen garin, da yadda suka riƙe' ya'yansa suka zauna lafiya, gefe guda kuma ya tausaya musu yadda suke rayuwa ba makaranta, ba wutar lantarki ba kwalta bare Asibiti. Kafin su bar garin, Daddy ya sanar da me gari cewa za'azo a gina musu makaranta ta boko da islamiyya a saka gwamnati ta kawo musu malamai, Widad kuma tace zata gina musu Asibiti, a kawo musu ma'aikatan lafiya, Daddy yace  "Alhaji Yusuf baka yi magana ba" Yusuf yai murmushi yace  "Aini tunda aka musu makaranta da Asibiti, an gama min komai, fatana kuma ai musu boreholes na ruwan sha, saboda babu ruwa a garin nan, a saka gwamnati ta samar musu da wutar lantarki, saboda Asibiti baze yuwu babu wuta ba. Nan jama'ar suka dinga murna suna Allah ya Sanya alkhairi, suna saka musu albarka. Hindu kam ta ƙuke a ɗaki, tana tunanin abunda Widad ke shirin yi, banda abun Widad ina ita ina wannan hamshaƙin attajiri, ɗan gayu me ilimi ga kyau da dukiya, ita kuwa ga ƙauyanci da rashin wayewa, amma ta dage seta aure shi, ita gani take kawai ze aureta ne saboda 'yarsa, amma tabbas ba sa' ar Aurensa bace. Tana cikin tunanin taji ana guɗa da shela a tsakar gida "Alhaji Daula, yaga 'yarmu yana so, kuma harya bada kuɗin Aurenta naira dubu ɗari biyar, mudai zaman Yusuf da matarsa a garin nan namu alkhairi ne, yace ya gani yana so, kuma me gari ya amsa, yace ya bashi, watan arzikinmu a ƙauyen nan ya tsaya,' yarmu zata auri attajiri, ko iya Asibiti da makarnta da akace za' a mana aimu am biyamu, 'yarmu Hindu Tayi goshi, zungureren goshima kuwa " Gaban Hindu ya faɗi, kenan dagaske dai ta tabatta Widad za tayiwa Babanta Auren dole da' yar ƙauye? Hanne kuwa gigicewa tayi, dan a ganinta tafi Hindu komai, dan meyasa ba'ace itaba se wata Hindu, Hindun daba wani kyaune da ita ba ga baƙin jimi, amma ace zata auri attajiri haka. Da zasu tafi Widad ji tayi kamar karsu tafi, dan sosai takejin kewa da ƙaunar mutanen garin, saboda karamcinsu da girmamawa, Ta shiga ɗakin Gwaggo ta sami Hindu a ƙarshen gado  tayi shiru tana tunani. Widad tace  "Hindu, karki ɗaga hankalin ki, babana bashi da matsala ko damuwa, mutumin kirki ne zaku zauna lafiya ƙalau dashi, sannan an saka wata biyu, saboda kafin ɗaurin Aure a kawo muku cigaba garin nan, saboda manyan mutane ne zasu garin nan, munyi magana za'a aiko da mota tun saura sati biyu biki a ɗauke ki a kaimin ke can kano, mu fara shirye shirye " Hindu kawai jinjina mata kai tayi, daga nan suka yi sallama suka tafi, a hanya sunata jinjina karamci da mutuntawa na wannan al'ummar gari. Gaba ɗaya ƙauyen nan ya ɗauka, Daula ze auri Hindu, ga kuma kaɓakin arzikin da aka sauke musj, sunata rawa da murna ga alƙawarurrukan da aka musu na kawo musu cigaba a garin. Su Widad kuwa garin kanon dabo suka wuce kai tsaye, suka sauka a farmhouse, Bayan sun huta Alhaji Ahmad ya wuce gidansa, Umma tace ba zata zauna a nan gidan ba, gidanta zata tafi, shi kuma Yusuf nauyi yake ji, koba komai Daddy sirikinsa ne, ace suna gida ɗaya su kwana ɗaki ɗaya da Widad, haka ya basar Widad kuma ta dage se Umma ta kwana a gidan ba zata tafi can gidanta ba, da ƙyar Umma ta yadda ta amince. Wasa2 Seda suka kwana biyu da dawowa, amma suna farmhouse tare da Umma, kullum se Alhaji Ahmad yazo, Umma ta takura akan cewa lallai seta bar gidan, dan ita gaba ɗaya jinta take a takure. Daddy yace zasu rakata gida, kafin nan ze kaisu gidan daya saiwa su Yusuf, kuma ranar nan da sati biyu Yusuf ze tafi Lagos, inda babban kamfanin shige da ficen ƙarafa yake, wanda yake mallakinsane, shi dai Yusuf jin abun yake banbarakwai, kamar bashi ba. Koda suka fita seda suka fara zuwa ainihin gidansu da suke zaune, suna zuwa ma'aikatan nan suka dinga rige rige zuwa gurin Daula, ganin ya bayyana ashe yana raye, sedai gidan kamar kango, ba shige da ficen mutane, ba manyan motocim dake harabar gidan, abun duk se  a hankali. Nan su Murtalah, Nura da sauran ma'aikatan gidan suka dinga tururuwar zuwa gaban Daula, masu kuka nayi masu murna nayi, ai nan da nan labarin bayyanar Daula ya karaɗa gari, da jaridu Widad kam cikin gidan ta wuce, tana ganin gidan ya koma kamar wani kango. Alhaji Daula yace "ina sauran mutanen gidan?" Nura yace "ai ranka ya daɗe ai an kama Hajiyar" Daula yace "nasani" Nura yace "to yanzu dai, 'yan sanda sunzo sun kama Ramlah jiya, se Amal ce kawai a cikin gidan" Daddy ya jinjina kai, ya shiga cikin gidan, yana shiga ya tarar Widad ta wuce ɗakinta, Amal tana zaune a falon tana ta kuka kamar an mata mutuwa, ta rame sosai kamar wadda aka zuƙewa jini, tayi baƙi sosai duk ta canza kamanni gwanin ban tausayi. Maimakon Daddy yaji haushinta sema wani tausayinta daya kama shi, kafin yai magana Widad ta fito, Umma tace "Yusuf wannan kuma wacece?" Yusuf yace "Umma wannan itace Amal, 'yar matar gidan nan ce" "Amma ya naganta kamar mara lafiya?" Yusuf yace "nima ban san abunda ya sameta ba" Widad ta kalli Amal tace  "Malama You have to leave this house, within some minutes, azzalumai kawai marasa tsoron Allah, masu butulci" Amal ta shiga girgiza kai tana cigaba da kuka, dan idan ta fita bata san ina zata ba, dan bayan mamansu ta auri Daula, a dangima ba kowa take gani da gashi ba, yanzu idan ta fita ina zata? Cikin tsawa Widad tace "Am talking to you" Daddy yace "No Widad, ɗan dakata tukuna" Ya ƙarasa gaban Amal ya durƙusa, yace  "Amal ɗin Daddy, baki da lafiya ne? Kikayi wannan ramar haka?" Amal cikin kuka tace  "Dan Allah kuyi haƙuri, kuyafemin, dan Allah, dan Allah kuyi haƙuri" Tai maganar tana haɗa hannayenta alamar neman afuwa  🙏 "Daddy, waiya kake wani lallaɓatane? Do you want give them another chance to finish us?" Daddy ya girgiza mata kai, ya sake kallon Amal yace  "yanzu meke damunki kika rame haka?" Nan ta gaya musu yadda akayi mata fyaɗe, Alhaji Haruna ya keta mata mutunci da abunda likita yace, a maganartata zaka fuskanci ta samu taɓin hankali. Yusuf kansa seda tausayinta ya kama shi, duk rashin mutuncinsu, Amal ta ɗanfi sauƙin kai, dama Ramlah tafi zaƙewa da wulaƙanci. Daddy yace "ki kwantar da hankalinki, nasan yanzu dole zaki shiga damuwa sosai, saboda gaba ɗaya 'yan uwanki da iyayenki suna hannu, ina fatan ze zame miki izina akan abunda ya faru, ban miki Alƙawarin saka baki akan taimakon mahaifiyarki da yayarki ba, saboda sun cutar dani a rayuwa, amma daga nan ko zuwa wace ƙasane, daga naira ɗaya zuwa miliyoyi, zan kashe a nema miki lafiya, kidena kuka kiyi musu fatan Allah ya shiryesu, sannan ki dimga musu Addu'a " Aikuwa a hasale Widad tace " Daddy, why? Me yasa zakayi wannan hukuncin, dukda tarin laifukan da suka aikata mana? " Yusuf ma cikin tsawa yace " Widad, Daddy kikewa magana fa, talk to him with respect " " Haba Yoseef, a gabanka akace Mahaifimsu aka saka ya kashe min Ammina, yanzu meze sa Daddy ya temake ta? Bayan yadda suka so ganin bayana, da ganin ma zama mahaukaciya tuburan?" Daula yace  "Widad, ɗan halak baya manta alkhairi, ko bakomai ɗan uwanta yamin wahala, yayi ɗawainiya dani a Asibiti, yamin biyayya, kuma itama ba laifi tana girmamani, albarkacin Anwar nakeso Amal taci, ba ita tayi miki laifin ba, dan haka kiyi haƙuri, kiyi haƙuri ba danni ba dan Allah " Daddy ya riga ya ɗaureta da jijiyoyinta, dan haka dole tayi shiru. Daga gidan suka wuce inda nan ne gidan da Daddy yace nasu Yusuf ne, a unguwar lamiɗo crescent, gida ne hargida ya haɗu ya tsaru iya tsaruwa, kamar ba'a Nigeria ba, Widad nata murna yayinda Yusuf ke jinjina abun, waishine da wannan gidan haka? Amma Babban abunda Widad bata ji daɗinsa ba, be wuce yadda Daddy yace " wai anyi bookin ɗin jirgi shida Yusuf a ranar zasu tafi lagos da yamma, dan canne inda kamfanin Yusuf yake, zeje a nuna masa abubuwa tun yanzu, Widad taji haushi sosai, dan harga Allah tana kewar mijinta sosai, kusan watanni shida ana neman na bakwai basa tare, amma haryanzu sun kasa samun dama su kasance tare, shikansa Yusuf mazewa yake dan yana da kunya sosai amma yana kewar matarsa sosai, Widad ce dai wani lokacin se a hankali bata fiye jin kunya sosai ba, duna da yanayin rayuwarta. Amal kuwa a ranar Daula yasa aka ɗauketa aka kaita Asibiti, dan a dubata a ga idan aikin ze yuwu a nan Nigeria. Haka Widad tana ji tana gani, da yamma su Yusuf suka tafi Lagos, ta koma gidan Umma tai zamanta, kwana ɗaya da tafiyarsu Lagos, Daula yai hira a kafafen watsa labarai a can Lagos, ya sake bayyana kansa, ya bayyana dukiya ta Yusuf ce, da irin wahala da azabtarwar da Bulama yayi masa, ƙarshe yai jan hankali da nasiha me ratsa jiki, akan mutane su lura da suwaye masoyansu na gaskiya. Umma da Widad basu san anyi hirar ba, se gani sukai mutane na zuwa gidan, wai sunzo yiwa Umma murna,ashe Yusuf ɗan Daula ne, babu kunya ciki hardasu Yaya ɗanllami masu yi masa gori, Sunga Arziki ya sameshi, Widad ta dinga mamaki wato a rayuwa idan kaga ana nan nan da kai, wata damace Allah ya baka, ko kuma kuɗine da kai. Garin su Hindu kuwa, tuni aka kai kayan aiki dan cika alƙawarin da Daddy ya ɗauka, da yake akwai kuɗi, nan da nan aka fara aiki, kuma yace a ɗau leburori a garin dan su samu wani abu suma, gefe guda sunata shiri suma murna akan Hindu zata Auri Daula, yayin da ita Hindu gaba ɗaya yake mata kwarjini, take tunanin taya zatai zaman aure dashi, mutumin daya girmeta nesa ba kusa ba, yama haifeta? " Nurat kam ta riga ta haƙura da batun Yusuf, tayi murna sosai jin labarin ashe yana da alƙa da Widad, itama in akabi nasaba ɗan uwantane. Ta samu Khalil a falo tace masa" brother, kaga wani iko na Allah ko? Duk wannan wahalar ashe dai ɗan uwan Widad ne Yusuf, kuma akan dukiyarsa aketa wannan abun " Khalil yace " hakane kam, Allah babu yadda be iya ba, Sakamakon haƙuri da juriya ga abunda Allah yayi masa, haƙuri me tadda rabo, kema Allah ya baki miji nagari wanda yake sonki" Nurat tace  "Aima ya bani" "A ina yake? Baki gayamin ba" "Sunanshi Barrister Ibrahim Khalil gora" Da sauri ya kalleta yace  "Are you serious?" Ta jinjina masa kai tana murmushi, "yanzu kin yarda kima sona zaki aureni Nur?" Ta jinjina masa kai alamar eh, murmushi ya shiga yi yana faɗin Alhamdilillah, Alhaji na dawowa zan sanar masa " " Haba brother, meye na gaggawa kuma? " " kar inje wani yayi min ba daidai ba, gara in hanzarta inyi wuf dake" Nurat ta rufe fuskarta tana murmushi. Wasa wasa, seda Yusuf sukayi Sati biyu sannan suka dawo Kano, kuma da suka dawo ɗinma seda Daula yaje har gidansu Nurat domin yi mata ta'aziyyar mahaifiyarta, abunda bata taɓa zaton Daula zeyi ba, tana ganinsa ta tsaya tana mamaki. Daula yace  "Nurat, ƙaraso mana" Ta ƙarasa ta zibe ƙasa tana gaishe shi" Ua amsa tare da faɗin "ya ƙarin haƙuri kuma?" "Alhamdilillah Daddy" "ubangiji Allah ya jiƙan ummanki, yai mata rahama" Nurat tace "Ameen" Nanma Yusuf ya sake yi mata gaisuwa, Daula yace  "Nurat, idan akabi nasaba ina da alaƙa ta jini da mahaifinki, dan haka ki ɗaukeni Uba, duk abunda ya taso miki kike buƙatarsa, ki nemeni ko menene insha Allah, zanyi iya ƙoƙarina imga na miki, am your father now, kinji Nurat" Nurat tace "to Daddy nagode sosai" Seda Daula ya tsaya suka gaisa da mariƙin nata, sannan suka tafi. Yallaɓai Suleiman kansa, seda ya samu tagomashin katafaren gida, da kuma kuɗi masu yawa a gurin Yusuf, saboda irin jajircewa da taimakon da yayi masa. Kwanansu Uku da dawowa suka tare shida Widad a sabon gidansu, ya samu rakiyar abokan aikinsa gidan, Kasancewar bashi da wasu abokan kirki, Widad kamar tayi tsalle dan murna da farinciki. Bayan kowa ya watse, gajiya duk ta damu Yusuf, saboda hada hada da mutane, dan har walima akayi na tariyar a event center, Daddy ya gayyato manyan abokansa, Yusuf duk ya gaji dan be saba da hada hadar mutane haka ba, ya shiga yai wanka, lokacin tuni Widad ta shiga ɗaya ɗakim tayi nata wankan, dan itama a gajiue take sosai, ta fito cikin riga da wando na bacci masu jikin bargo pink, ta kashe fitilar ɗakin ta bar dump side lamp, ta ƙaraso inda Yusuf ke zaune yana taje sumar kansa, Yusuf yace  "malama ce miki akayi na gama kika kashemin fitila?" Tace "kai ba mace na amma se ƙaƙale, da mace ne Allah kaɗai yasan me zakayi" "Shi namiji baze gyara ba kenan, se kincemin ƙazami?" Widad tace "kuma mayukana zaka dimga shafawa, na bleaching ne dai ba ruwana in ka zama fari" Yusuf yai dariya yace  "dan dai bleaching ai ba damuwa ranki ya daɗe, ince mata tace takemin" Sukayi dariya tare, ta ƙaraso ta rumgumeshi ta bayansa, tana numfashi a hankali, kwararar hawayenta yaji a Ƙirjinsa da sauri yace  "lafiya kuwa Widad?" Kasa magana tayi, ta cigaba da kukan, ya janyota gabansa yana sake tambayarta, amma sema ƙara saugin kukan da tayi, yace  "haba Babyna, mena yi miki kuma? Kodai shagwaɓarce?" Still bata amsa masa ba, dan haka ya jata zuwa kan katafaren gadon su, ƙato ya zaunar da ita sannan ya zauna yace "gayamin, menene? Ko laifi nayi miki" Rumgumeshi tayi tana kuka take faɗin "thank you very much Yoseef, thank you very much for your love, caring the sacrifice and all you have done for me, you change my life Yoseef, i love you" "I love you too my wife, you also done a lot of things for me, bani da bakin godiya se dai zuciyata taki ce mata ta" Haka suka cigaba da gayawa jinansu kalamai masu daɗi, masu cike da nuna kewar juna, daga nan kuma suka wula wani gurin. 🚶 🚶 🚶 🚶 Ji suke tankar lokacin suka yi aure, dan a wannan lokacin suke cin nasu amarcin a nutse, ba inda Yusuf yake fita, kullum yana gida tare da Widad, yana bata kulawa ta musamman. Alhaji Ahmad ma ya nemi Auren Umman Yusuf, akasaka lokacin daidai lokacin bikin Daula, ayi biki gaba ɗaya Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, tun saura sati biyu biki, Widad taje ƙauye ta ɗakko Hindu daga ƙauye zuwa kano domin shirin biki sosai, motar da aka kawo Hindu Tint glass ne da ita, dan haka bata samu damar ƙarewa garin kallo ba, seda suka shiga gidan Widad, data fito daga motar cak ta tsaya tana ƙarewa harabar gidan kawai kallo. Widad ce ta fito tana murmushi ta ƙaraso tana faɗin "oyoyo amaryar mu, sannu da zuwa Anty Hindu" Hindu ta sunkuyar da kai cikin jin kunya. Widad taja Hindu zuwa cikin gidan, yayin da Hindu ta kasa magana saboda tsantsar mamaki, ace a duniya akwai irin wannan gidan lallai jin daɗi yana birni, suna shiga falon Widad taji wani irin sanyi ya ratsata wanda babu shi a waje, tun Hindu na mamaki harta zubawa sarautar Allah ido, dan abun ya shallake hankalinta. Widad ta dinga koyamata yadda ake amfani da wasu abubuwan, ta dinga kaita gurin gyaran jiki kafin lokacin biki. Hindu tayi shar da ita, tayi kyau sosai sedai tana jin kunyar Widad sosai, saura kwana huɗu biki sannan Widad ta kira Daddynta a waya tace masa yazo ga amaryarsa a gidan ta. Ba musu kuwa sega Daddyn a gidan, Hindu na jinjina rashin girman kai na mutumin nan, yana da matukar sauƙin kai da sanyin hali, dukda kuɗin da yake dashi, da kuma shekarunsa. Yana zaune a falo, Hindu suka fito ita da Widad tayi kyau sosai, Widad tana ja da kyar saboda nauyin cikinta, Widad tace "Daddy ga amaryarka nan, bari in kawo muku abin sha" ta juya ta koma ciki. Ƙafar Hindu na rawa ta ƙarasa gaban Dula, ta tsuguna tace "ina wuni" Daddy yace "lafiya ƙalau Hindatu, ya baƙunta? Ina fatan dai Widad bata takuramiki?" Hindu ta girgiza kai alamar a'a, yace "to in dai tana matsa miki, ki gayamin nida ita ne" yai maganar yana murmushi ƙarshe shikaɗai yai taɗin ya gama bata iya cewa komai, saboda kunya da kwarjinin sa. Lokacin biki Aka aika da motoci ƙauyen su Hindu, aka kwaso su zuwa birni dan bikin 'yarsu, a tsohon gidansu Widad aka sauke su, sedai Hari tafi kowa rikicewa da ganin gidan nan, tun daga gate motocin dake harabar gidan suka rikita ta, suka shiga katafaren falon gidan, Hari ta rasa a ina zata zauna, tace "ohh ni Hari, yanzu wannan ko' a aljanna ka samu wannan ai ka more" Hansai tace "ke Hari, ance talaka a gidan aljanna shine gidansa kamar girman duniya, kike cewa ki samu kamar wannan" "Ke bari Hansai, ke kina tunanin kin aikata abin da da zaki samu wannan ne? Ai ni indai irin wannan ne yaseen ya isheni, kai jama'a kun lura da wani abun mamaki kuwa? Waje lafiya ƙalau amma ɗakin nan hunturu Aradu, sanyi ake sosai a cikin ɗaki ikon Allah" Widad tasa aka dinga sauke musu Abinci, Abinci kala kala Gwaggo tace "Amarya wai ina 'yar tawa ne?" Widad tace "wace' yar bayan nikuma?" Gwaggo tai murmushi, Widad tace "zasu taho tare da Daddy, da kuma Umma" Gida ya ɗau harama, aka kawo Hindu, suka dinga zuba guɗa, gaba ɗaya Hindu ta canza a sati biyun nan, tayi kyau sosai kamar ba ita ba. Aka dinga ɗorawa ana sauke musu Abinci, aka ɗakko masu aiki da an ɓata guri su gyara, Da Yamma aka ɗauki Hindu aka tafi reception, na Daddy da abokansa da kuma Ahmad, dama umma cewa tayi ba zata ba. Hanne kam ji take kamar tayi kuka, tafi Hindu kyau da haske amma zata auri wannan haɗaɗɗen mutum a birni, amma ita zata auri ɗan ƙauye, tunda suka zo Widad ko kallon inda Hanne take ba tayi balle tayi mata magana. Washegari juma'a, aka ɗaura Auren Umma, da kuma na Hindu da Daula, anyi shagali sosai a gidan nan, dukda ba wani gagarumin taro suka yi ba, amma anci an sha sosai kowa yasan anyi biki, akaita yiwa Hindu Nasiha, akam haƙuri da tsoron Allah, Widad tace Gwaggo, da Hari suzo a raka Hindu gidan ta " Hari tace" au wai dama nan ba'a gidanta muke ba? " " Gidan Amaryar za'a sauke ku? Sannu Hajiya Hari me taɓargaza" Haka suka cigaba da faɗansu da suka saba ita da Hari, Farm House aka sake gyarawa, aka canza furnitures wanda ya tattaka gidan da aka sauki su Hari, Hari se salati take da salallami  wai "Nidai Hindu, idan ana neman 'yar wanke wanke dan Allah zanyi" Widad tace "Kina uwatta zaki zo wanke2"? "eh wallahi zanyi" Tun Widad na biyewa ƙauyancin Hari harta ƙyaleta, saboda abun nata bana ƙare bane. Bayan sun rakata, sun mata addu'a Gwaggo tace "to Hindu, mu daga nan gobe in Allah ya kaimu zamu wuce gida, ki zauna lafiya da mijinki da kowa ma, nasan dai baki da matsala amma dai ayi haƙuri" Hindu ta rirriƙe Gwaggo tana kuka, da ƙyar ta cikata suka tafi, suna tafiya tsoro ya cika Hindu, saboda ita girman gidan ma abun tsorone, gashi tana jiyo kukan dabbobi kaɗan kaɗan  a falon, tana cikin zare idone sega Daula ya shigo da abokansa. Ta cukuikuye a cikin lifaya taƙi ɗago kanta balle ta kalli wanima, nan suka musu fatan Alkhairi sannan suka tafi. Ayshercool 07063065680 12/22/21, 11:07 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE NORMAL GROUP ₦300 VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0009450228 JA'IZ BANK AISHA ADAM SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 07063065680 (Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni" 170 Bayan fitarsu Daula ya kalleta yace "taso mu tafi" Ta ɗago a hankali ta kalleshi, sannan ta miƙe tana waige waige, ya miƙe yai gaba tana binsa a baya, wani gurin seta tsaya kallo, seta ɗago taga ya tsaya jiranta setai maza ta taho, ya dinga ratsawa da ita faluka, wai nan duk dan zaman mutum ɗaya akayi shi, suka zo ƙafar bene ya fara hawa tana binsa, sedai ta zame ta faɗi, saboda matattakalr benen kanta wata iri take ganinta, ga ƙananan fitilu a jiki, gata kamar ta glass ta tsaya kallo shine ta faɗi, a ɗan gigice ya waigo yna faɗin "subhanallah, garin yaya? Kodai ɗaukarki zanyi ne?" Da sauri ta girgiza kai yace "sannu, miƙomin hannunki in riƙeki" Ta miƙa masa hannu, ya riƙe hannunsa kamar bana namiji ba saboda laushi. Haka suka ƙarasa saman bene, cikin katafaren falonsa, ji tayi sanyin data keji ya ƙaru, hartana nema ta fara rawar sanyi, yaje ya rage AC suka shiga bedroom, ai a jikin ƙofa ta tsaya tana kallon ikon Allah, lallai gaskiyar Saleh, da yace ko za'a saida duk kadarar da 'yan ƙauyensu suka mallaka baza su siyi ko da motar hawan Widad ba, balle wannan uban gidaje haka. Ya bata gurin zama, ta zauna already kaji da kayan shaye2 suna ɗakin da plate da komai, amma juyin duniya Hindu taƙi ci, ba yadda beyi da ita ba, amma taƙi ci, se ƙyaleta yayi, sukayi alwala sukayi salla, bisa ga koyi ga sunnar ma'aiki salallahu alaihi wassalam, tare da yin addu'oi, ya miƙe yace mata ga gado cam taje ta kwanta, shi kansa gadon abun kallo ne, lallai Su Widad sun tara abun duniya. Shima da ƙyar ta hau ta kwanta, ta dunƙule a guri ɗaya, ya ɗakko ƙaton bargo ya lulluɓa mata, ya cire babbar rigarsa taga ya sake tada salla, sannan hankalinta ya kwanta ta shiga baccin ta. Wani irin laushine da katifar, ga bargon ma laushi se ƙamshine ke tashi a jikin bargon, cikin dare ta tashi a firgice saboda tsoro, Daula yace "lafiya kuwa?" "tsoro nakeji" Yai murmushi yace "aiba abunda ze sameki, ki rage yawan tsoro dan wataran ke kaɗai zaki kwana a gidan nan, ki kwanta kiyi addu'a, ba abin da ze sameki" Haka ta kwanta tana cigaba da rarraba ido. Sedai a yau ɗinne dai Hindu ta zama cikakkiyar matar aure, dukda tsoro da razanin data tsinci kanta a ciki. Su Hari kuwa haka suka koma ƙauye, suna zuzuta haɗuwar gidajen da suka je, Abinci kam wannan duk azabar cin mugunta da suka yi seda suka barshi, akayi musu rakiya da sha tara ta arziki, yayin da ayyukan da ake musu sunyi nisa sosai, dan har an kai musu wutar lantarki ma. Washegari Widad ta aika direba da Abinci ya kai gidansu, sedai ita amaryar ce taƙi sakin jiki sam, lokaci lokaci se Daula ya kalleta yayi murmushi, yarinya ce sosai sedai akwai kunya sosai. Yace "ga Abinci Widad ta aiko, kizo kici ko in kirata in gayamata kinƙi cin komai" "Aa' dan Allah karka gayamata" "to zokici Abincin nan" Ta sakko ta zauna, ya zuba abincin a plate, ya haɗa mata da tea ya bata, sedai kunyar ci take a gabansa, ta ɗan dinga cakala, ya karɓi plate ɗin, ya ɗebo a spoon ya kai bakin ta, kunya takeji sosai, ta sunkuyar da kai yace  "haka zamuyi dake? In gayamata kina gaddama ko?" Ta girgiza kai, yace "in bakya so in gayamata, maza karɓi kici" Abun har mamaki yake bata, babban mutum haka amma ya zauna yana lallaɓata, seda taci ta ƙoshi ya jata zuwa wani ɗaki ya nuna mata kayan lefenta. Banda wanda aka shirya mata a drower. Umman Yusuf, kwana uku da ɗaurin Aure ta tare a babban birnin tarayya, Widad taso zuwa sedai tana daf da shiga watan haihuwarta, dan haka akace ta haƙura. Bulama kuma tuni aka shiga zaman kotu, aka dinga shari'a ana warware duk wata ƙulalliya da makirci daya aikata, laifukan nasa da yawa danshi ƙarshe se hukuncin rai da rai aka masa, sauran kuma daga me shekaru Ashirin da wani abu seme talatin, Hajiya Halima kuma shekaru Ashirin da takwas itama, Ramlah kuwa hauka ta dingayi tuburan saboda azabar shaye2, ƙarshe se gidan mahaukata aka maida ita. Bulama kuma ya dinga larura, ciwo bayan na ƙanjamau ya din rashin lafiya, aka kai shi Asibitin gidan yari ashe cancer ce ta kama masa hanji zuwa duburarsa, ga kotu dukata ƙwace kadsrorinsa ta mayarwa da Daula, bashi da komai ba shi da kuɗin daza'a masa aiki, ƙarshe haka gurin bayan gidansa ya dinga tsutsa, ga wani irin wari yanayi, shima Fahad ya samu shekaru sha biyu a gidan yari, gashi ga ubansa Alhaji Musa kuwa shima rai da rai ne hukuncinsa, saboda hadda laifin kashe matarsa, ga sugar ya fito masa a ƙafa, shima ƙafa ta dinga ruɓewa kamar bata ɗan Adam ba. A hankali Hindu take ɗan sakin jiki da Daula, babban abunda yake burgeshi da ita shine, tsananin biyayya kamar zata shige cikinsa, ko magana yake mata kanta a ƙasa, wanda rabonsa da samun farinciki tunda Huda ta rasu. Satinta biyu yasa ta a makaranta, ya ɗaukar mata me zuwa gida yai mata lesson, na ilimin addini dana zamani, kuma gata da saurin ganewa. Yanzuma yana zaune ta ɗora kanta akan cinyar sa, yana nuna mata hotunan maman Widad daya ɗauka a wayarsa, Hindu ta zuba musu ido tace  "masha Allah, tana da kyau sosai gata kamarta ɗaya da Widad" Sam bata nuna masa kishi ba, sema addu'a data dinga yi mata. Daula ya bata wani littafin turanci, yace ta karanta yaji, aikuwa ta dinga karanta masa, gashi makarantar da yasa ta, malaman su turawa ne, tana yi yana tafa mata yana murmushi. Jin sallamar su Widad a falon, yasa cikin hanzari ta tashi daga kan cinyar Daula, tana neman ɗankwali, wai kar Widad taga kamar ta raina shi. Widad tai murmushi tace  "kekam Allah ya shiryeki, ni idan nice ba kunyarki zanji ba, mijin nakima da yake tsoho" Hindu ta duƙunƙune fuska tana jin kunya. Yusuf dai sedai ya kallesu yayi murmushi, sun daɗe a gidan se bayan goma sannan suka tafi gida. A satin Saleh ya dawo, an masa aiki ya warke tsaf dashi, yayi murna da jin Daula ya Auri Hindu, shima an masa halacci sosai, sannan Daula ya canza masa aiki, aka maida shi Lagos. Amal ma a nan Nigeria aka mata aiki, sedai taji sauƙi sosai anata ƙoƙari karta rasa hankalinta, likitan da yayi mata aiki ya nuna yana sonta ze Aure ta, Daula be ɓoye masa ba ya gaya masa komai game da Amal yace "Amma itama 'ya tace, idan kasan zaka aure ta ka wulaƙantata ka ƙyalemin' yata" Yace "shi tsakani da Allah yake sonta" Daula ya shige gaba ya karɓi kuɗin Aurenta, sedai ita tana Asibiti har yanzu. Wataran da Safe, Hindu ta tashi daga bacci, sega kiran Widad, ta ɗaga wayar tana cewa "Maman biyu kin haihune?" Widad tace "kedai bari, ina nan ina ja, ima wannan dattijon yake? Zanyi magana da shi" "Hindu tace " waye kuma dattijon? " " Mijinki mana " " gaskiya kidena ce masa dattijo " Widad ta dinga dariya tace" lallai Hindu, Allah ya baki haƙuri yana ina? " Hindu tace "bacci yake yi" "idan ya tashi kice masa, zan tafi Asibiti na fara jin ciwo, yayi min addu'a zanje inji abunda zasu ce, zan iya haihuwa ko kuma aikin za'ayi" Jikiua sanyaye Hindu tace "insha Allah zaki haihu lafiya, ki kwantar da hankalinki" Widad tace 'to Allah yasa" Hindu ta ajiye wayar tai shiru, Daula ya tashi zaune yana cewa matar dattijo ha dai.? Kallonsa tai tayi murmushi tace "lafiya, Widad ce tace zata Asibiti a duba, idan zata iya haihuwa ko kuma aiki za' a mata" Da sauri ya karɓi wayar, ya sake kira Yusuf ya ɗaga yace "Daddy mina Asibiti, daga zuwanmu suka riƙe ta sukace haihuwa zata yi" Daddy yace 'wani Asibitin ne? Gani nan zuwa " Ya gayamasa, aikuwa anan da nan suka shirya shida Hindu suka tafi Asibitin. Ansha daru da Widad kafin ta haihu, Allah ya temake ta ta haihu da kanta, sedai Yusuf ya sha kira sosai da Daddy. Aka fito aka miƙo musu, santalelen jariri me kama da Yusuf sak, Daula ya karɓi Jaririn yana faɗin masha Allah, Alhamdilillah. Nan ya shiga bige bigen waya, yana sanar da haihuwar ta Widad, nan da nan aka cika Asibitin 'yan barka, se bayan awanni huɗu sannan aka sallameta, suka tafi gida. Daddy ya rasa inda ze saka ransa da murna, a ranar Umma ta dawo kano, Umma kamar ita akayiwa haihuwar, ta dinga murna tana farinciki ta ɗau jika. Saura kwana biyu Suna su Hari suka zo daga ƙauye, da abun arzikinsu, megari yabada raguna biyu manya yace a yankawa jaririn nan, Yusuf yai masa huɗuba da Muhammad Bashir sunan mariƙinsa, anyi shagali sosai a sunan nan, jariri ya samu kyaututtuka daban daban daga gurin mutane. Ana zaune a falon Widad, bayan an dawo daga event ɗin da akayi sunan, ba zato ba tsammani Widad tace "wai yaushe ne bikin Hanne" Hari tace "to ai mijin natane har ynzu be shirya ba, lega yake tafiya neman kuɗi, amma dai abun dai duk se a hankali ba wata Ƙwaƙwaƙwarar sana'a da yake yi" Widad tace "aiga 'yar uwatta nan Hindu, ta tambayar mata mijinta a sama masa abunyi shima" Hindu ta kalli Widad, dan ita harga Allah bata iya tambayar Daula komai, to mema zata tambayeshi bayan komai ya ajiye mata. Hindu tayi fuska ba tace komai ba, da daddare Daddy da kansa yaje ya ɗakko Hindu, bayan sunje gida har sun kwanta yace "Hindatu Widad tacemin zakiyi magana dani ko?" Hindu ta girgiza kai tace "A'a" "gayamin, nasan bazata miki ƙarya ba" "Bafa nice ba, cewa tai wai ince maka a samawa wanda ze auri Hanne aiki" Yai murmushi yace 'ta gayamin, ina son ji daga bakinki ne, daga yau kome kike buƙata kowa kike so ayiwa alfarma ki faɗa kanki tsaye zan masa, ance ya iya tuƙin mota, zamu bashi jan manyan motocinmu, sannan zan basu gida a nan garin, itama ta dawo ta zauna a nan ta shiga makaranta " Hindu harda kukan murna, ta durƙusa har ƙasa tana masa godiya, ya girgiza kai yace" meye abun damuwa haka kuma? Karki damu kinji" Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, lokaci ɗaya akayi bikin Nurat da kuma Amal, kuma duk Daulane yayi musu walicci, da kayan ɗaki da manyan kyautuka ga kowaccensu. Muhammad Bashir wanda suke cewa Aryan yayi wayo, kusan koda yaushe Daula ya kan je gidan Widad saboda Aryan, yana matuƙar ƙaunar Yaron. Wataran da daddare Daula ya shigo yace "Hindatu, kisa hijjabinki zamuje muyiwa su Widad sallama, gobe in Allah ya kaimu zamuje Abuja, daga nan zamuje Dubai ki rakani taron kasuwanci" Hindu tace "sekaje dani taron kasuwanci har wata ƙasar, abokanka za suyi maka dariya ka auri 'yar ƙauye" "Ni matata ba' yar ƙauye bace, kuma ba inda zanji shakkar shiga da ita, in nunata ince wannan matata ce, saboda ina sonta a haka" Hindu ta rufe fuska tana murmushi. A daren suka tafi gidansu Widad, Hindu ta kama Aryan ta rungume tana ta masa wasa, Widad ta karɓi Aryan ta bawa Daddy, taja Hindu ɗakinta, ta bata wata riga tace ta gwada, Hindu ta cire hijjabinta ta gwada rigar, abun da Widad ke son gani, kuma ta gani ciki ne a jikin Hindu. Widad tai kamar bata gani ba, ta bata kyautar riga, a ranta tace "shine Daddy bemin Albishir ba. Widad tana jin daɗin yadda mahaifinta ya samu nutsuwa, Dan ita kanta ta lura da yadda Daddy ya samu nutsuwa, da biyayya da take masa, daga ita har Daddy sunyi tsaf dasu sunyi ƙiba, watan Aryan biyar Widad tabi Yusuf Lagos, ya kama harkar kasuwancinsa sosai. Watannin cikin Hindu tara ta haihu, amma seda aka mata CS aka cire yaron daga cikinta, saboda yai girma da yawa, kwana biyu tana labor, sannan aka mata cs ɗin aka cire yaron. Widad kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna, an yi mata ƙani, yaron kamarsa ɗaya da Yusuf sak, kamar shiya haife shi, kuma kusan duk kamaninsu ɗayane dai da Daula. Daula be taɓa saka ran ze sake haihuwa ba, lokacin da aka gayamasa Hindu na da ciki ma, shiru yayi da bakinsa yaita Addu'a, da cikin ya fara girma kuma ya dena zuwa ko ina da ita, saboda kar itama ayi mata yadda akayiwa Huda, se yanzu data haihu sannan kowa yaji, an taya Daula murna sosai, da kyautar da Allah ya bashi na ɗa namiji. Widad anyi ƙani, ga kuma ɗa da miji, murna ba kama hannun yaro, se bayan sati biyu akayi gagarumin shagalin suna, a garin kano, har Nurat da 'yan gidsnsu sunje barka, sedai Widad sam bata shiga sabgar Nurat sosai, seda Daddy ya zauna ya sata a gaba, yaita mata faɗa da Nasiha, sannan take ɗan sakin jiki da ita kaɗan. Duniya ta dawo sabuwa ga wannan ahali, suka dinga tara zuriya, dukda Daddy ya manyanta amma seda Hindu ta haifi yara huɗu dashi, Widad ma ya haifawa Yusuf yara uku. Bulama kuwa bayan shekara shida a haka ya mutu a gidan yari, yana wannan tsutsar da zubar da ruwan, babu wanda yake iya zuwa inda yake saboda wari da ɗoyi, haka aka yasar dashi a gadon Asibiti, harya mutu babu wata cikakkiyar kulawa haka ya mutu a wulaƙance. Lokaci lokaci Amal ta kanje ta kaiwa mahaifiyarta ziyara a gidan yari, sannan tana zuwa gidan masu rangwamen hankali, Ramlah ta zama mahaukaciya tuburan, se an ɗaɗɗaureta haka zatai ta ihu tana fizgar gashin kanta, idan bayan gidane a nan za tayi, komai a gurin take yi, ta zama mahaukaciya tuburan, abun da Hajiya Halima taso Widad tayi, shine ya faru a kanta. Duk wanda ya zamana da sa hannunsa a badaƙalar da Bulama yayi, seda aka masa hukunci daidai da shi, daya mutu ma ds ƙyar aka samu masu masa jana'iza, sedai kowa yana toshe hanci saboda yadda jikinsa ya dinga ruɓewa tun yana raye, ga kowa baya faɗan alkhairi akansa, sedai sharrinsa da Allah wadaran. Daula baya ƙasar lokacin daya samu labarin rasuwar Bulama, amma seda ya zubda hawaye jin irin mutuwar da Abokin nasa yayi, tabbas da yana Nigeria dashi za'a sallaci Bulama, ya dinga kuka yana "Allah ya jiƙanka Abubakar, Allah ya maka rahama ya yafe maka, yasa jinyar da kayi kaffara ce, ni dai na yafe maka abubuwan da kamin, Allah ya yafe maka" Seda Widad taji haushin yadda Daddy ya damu saboda mutuwar Bulama. Daula a haka ya  dinga sawa ana kai kayan Abinci gidan yari, da gidan mahaukata, Arziki ya cigaba da bunƙasa, Hindu ta zama hamshaƙiyar mace itama, Daula ya ɗau nauyinta taita karatu na addini dana zamani. Umma dai Allah be bata haihuwa ba, amma bata sa hakan a ranta, saboda tana da Yusuf ga sirikata ta ɗaiketa uwa, ga yara sun haifa suna da jikoki, gashi tana zaune da mijinta da matarsa lafiya, yaransa suna matuƙar girmama ta. Yusuf ma suka samu kyakkyawar rayuwa, suna zaune abunsu a garin Lagos da yaransu, ƙauyen su Hindu kuwa, banda wanda yasan ƙauyen ƙayaune a baya ba zakace shine a yanzu ba, saboda cigaban da suka samu ta kowane fanni, bazasu taɓa mantawa dasu Widad ba, saboda a sanadinsu ne Allah yasa suka samu wannan cigaban wanda basu samu ba a baya. TAMMAT BI HAMDILLAH 9/12/2021 ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN, ALLAH YA NUFA NA KAMMALA WANNAN LITTAFIN NA AƘIDATA, INA FATAN DARUSSAN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU LADA, AKASIN HAKA UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA. A TARA NAN GABA KAƊAN DOMIN JIM LITTAFIN DA ZANZO MUKU DASHI, AKWAI LITATTAAFAI JINGIM A TASKAR COOL, WASU NA KUƊI WASU NA KYAUTA, INA FATAN DUK WANDA NAZO MUKU DASHI, ZAKU KARƁA HANNU BIYU, NAGODE SOSAI DA KULAWARKU DA KUMA ƘAUNARKU A GARENI SANNAN INA SON JIN RA'AYOYINKU AKAN WANNAN LABARIN DA KUKA KARANTA NAGODE SOSAI, A KODA YAUSHE INA MATUKAR ALFAHARI DAKU MASOYA. ƘOFATA A BUƊE TAKE, DAN GYARA, SHARHI KOKUMA SHAWARA AYSHERCOOL 07063065680