*MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*📚🖊️ *M*. *W*. *A* _Putting smile on our readers faces._ https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp ___________________________________ *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸🌸 *Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.* *Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.* *Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_ *Free PAGE 1* "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Shine abinda matashiyar yarinya wacce ke sanye da kayan ƴan sanda take maimaitawa, alamu sun nuna cewa suma tayi aka watsa mata ruwa ta farfaɗo duba da yadda take a kwance a ƙasa idanu a rufe ga fuskarta data jiƙe da ruwan da aka watsa mata. Jin ana ƙoƙarin ɗagata a ƙasan ne yasata buɗe ido domin ganin mai taɓatan, Ammi ce wacce take matsayin ƙanwa ga mahaifinta. Kallon fuskar Ammin tayi wacce ta kumbura tayi jazir saboda kukan da tasha domin hatta idanunta sun koma can ciki ba'a ganinsu sosai saboda kumburin da fatar idon nata tayi. "Zarah kuka ba shine mafita ba a yanzu, kizo kiyi sallama dasu domin a samu damar kaisu makwancinsu da wuri." Ammin ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta. Buɗe baki tayi domin magana amma kukan data kasayi tun farko ya riga maganartata fitowa, take kuwa ta fara rera kukan mai taɓa zuciyar duk wani mai sauraro. Hannunta Ammi ta kama ta ɗagota tare da nufar inda gawarwakin mutane takwas dake sanye da suturarsu ta ƙarshe a cikin makara, koda ta iso da ita wajen sake hannunta tayi tare dayin baya domin kukane yakeson ƙara kece mata. Cikin rawar hannu ta fara yaye mayafen daya lulluɓewa gawarwakin fuska tundaga kan gawa ta farko. "Mahaifina, Mahaifiyata, Kakannina uku, ƴan biyun ƙannena sannan ƙaramar ƙanwata. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." ta ƙara fashewa da wani sabon kukan mai taɓa zuciya, lokaci ɗaya kuma ta tsagaita tare da gyara rufuwar mayafan sannan ta ɗaga hannu sama ta fara addu'a. "Ya rabbi, Ya rabbi, Ya rabbi. Ya Hayyu ya Qayyum ya Allah ina gode maka a cikin kowani yanayi dana tsinci kaina. Ya Allah kaine shaidata ban shiga aikin ƴan sanda ba saidan na taimaka gurin gyara ƙasata, Ya Allah kasani ina tsare duk wasu dokokinka bana saɓawa da gangan saidai a rashin sani. Ya ubangijina nasan ka fini son waɗannan bayi naka shiyasa ka karɓesu daga aron daka bamu, na karɓi wannan jarabawa hannu biyu sannan ina ƙara gode maka. Ya Allah ga bayinka nan zasu iso gabanka Ya Allah kayi musu gafara ka yafemusu zunubansu wanda sukasan sun aikata dama wanda basu sani ba, Allah kayi musu rahama, Ya Allah ka tsare daga duk wata fitina dake cikin kabari Allah ka karɓi shahadarsu. Ya Allah kabasu wani ɓangare a cikin Aljannarka. Ya rabbi baka aikata zalunci sannan baka barin masu aikawa, Ya Allah na kawo ƙarar duk wani wanda yake da hannu a cikin mutuwar bayinka muminai." Hatta mazan dake farfajiyar wajen saida suka zubda hawaye tare da jinjina jarumtar Zarah. Batare da ɓata lokaci ba aka sallaci gawarwakin sannan aka tafi sadasu da gidajensu na gaskiya. _Kafin faruwar wannan al'amarin_. Tsantsar abota da aminci ne a tsakanin Malam Usmanu da Malam Adamu wanda ya rikiɗe ya kuma ƴan'uwantaka hakan ya samo asaline tun daga iyayensu da sukayi zaman aminci tare, hakan kuma ya ƙarayin sanadin da yaransu suka taso cikin shaƙuwa da son juna tamkar iyayen nasu sakamakon gidajensu dake maƙotaka da juna. Asalinsu mutanen garin Deba ne a jihar Gombe kuma a nan suke da zama da iyalansu, da sana'arsu ta noma suke rufawa kansu da iyalansu asiri. Malam Usmanu yanada mata ɗaya Faɗimatu da ɗansu Abdul_Jalal wanda shi kaɗai suka haifa. Yayinda Malam Usmanu keda yara biyu Sulaiman da Rumaisa sannan matarsa Aishatu. Yaran sun taso cikin so da kulawar iyayensu, tare sukeyin komai tun yarinta har zuwa girmansu. Sulaiman shine babba cikinsu wanda a yanzu haka yake zaune a cikin garin gombe tare da yaransa biyu Muhammad Jawwad da Nusaiba dakuma matarsa Safiyat wacce yaran ke kira da Momi. Inda ya kasance ɗan kasuwane a fannin ma'adanai. Sannan Abduljalal dake zaune a garin bauchi da nashi iyalan inda yake aiki a babban asibitin tarayya dake jihar bauchi. Yanada matarshi ɗaya mai suna Zainab (Mami) sai yaransa uku Abubakar Sadiq, Rahma, sai Fatimah Zarah. Rumaisa kuwa(Ammi) a ƙasar Cairo take zaune da mijinta wanda ya kasance ɗan kasuwa da ƴan biyun ta Muhammad Adil da Muhammad Shahid. Duk da kasancewar ba guri ɗaya suke rayuwa ba, sukan ware lokuta domin zuwa ziyartar iyayensu a garin Deba. Hakan yasa yaran sukayi sabo da juna sosai in banda Muhammad Jawwad da tun bayan kammala karatunshi na firamari aka kaishi England domin ya cigaba da karatunshi a can. Haka wannan familyn suke kasancewa koda yaushe cikin so da ƙaunar juna. Mafarkin Zarah nason zama ƴar sanda ya fara tun lokuta da dama da take ganin ana zaluntar talakawa sannan ƴan sanda suƙi ɗaukan mataki, hakan yasa tasha alwashin zama ƴar sanda. Daƙyar iyayenta suka aminci da wannan buƙatarta ta domin saida ta kaita ga kwanciya a asibiti tamkar bazata rayu ba, ganin haka ne yasa suka amince tare da kafa mata sharuɗɗan kare mutuncinta dana danginta. Wani al'amari daya faru a rayuwarta wanda ta kasa mantawa shine. _Garin Bauchi_ 12:30nr Gosulo ne sosai akan titin wanda ya kasance ana yawan samun cunkuson ababen hawa duk ranar juma'a saboda tare wasu hanyoyi da akeyi sakamakon sallar juma'a da ake gabatarwa. Cikin waɗanda gosulon ya tsayar harda direban daya ɗauko Zarah daga makaranta. Saidai gabaɗaya hankalin Zarah dake cikin motar ya koma ga wata tsohuwar almajirah dake gefen hanya zaune da roba tana bara, sosai ta bata tausayi ganin babu wasu masu bata sadaka dayawa. Jakar makarantarta ta duba saidai naira ɗari biyu ne aciki.. "Baba Sule akwai kuɗi a hannunka ne". Ta tambayi direbansu dake jan motar. "Ehh baza'a rasa ba". "Zasu kai nawa ne." "Inajin zasu kai dubu biyar ko sufi haka". Ya faɗa sanda yake ƙoƙarin ƙirga kuɗin daya zaro a aljihunshi. Karɓa tayi tare da fita a motar ta nufi inda matar ke zaune. "Sannu Baba ya zaki zauna a rana ki koma inuwa mana". Cewar Zarah lokacin data ƙaraso gurin. "Ƴar nan idan kayi nesa da jama'a wasu bazasu zo inda kake su taimaka ba dole sai mutum yazo inda suke." "Allah sarki to baki da mai taimaka miki ne.? " "Da inada mai taimakamin ba zaki ganni ni ɗaya ba ƴata." "Sunana Fatimah Zarah ne, ga wannan sadaka ce babu yawa." ta miƙa mata kuɗin. "Allah ya saka da alkhairi Batula, Allah ya albarkaci rayuwarki ya kareki daga sharrin maƙiya. Allah ya bani ikon taimaka miki watarana kamar yadda kika taimakamin." Cike da jindaɗi Zarah ke amsa addu'o'in kasancewarta mutum mai son taga babba nayi mata addu'a. "Bari naje direba na jirana zan dinga tsayawa wani lokaci mu dinga gaisawa." "Toh nagode Allah ya albarkaci rayuwarki." Almajirar ta faɗa a fili amma cikin zuciyarta cewa take "Bazaki ƙara ganina ba yau ɗinma na fito ne da niyyar taimakon mai taimako ne, kuma gashi kinyi sa'ar kasancewa wacce zan taimakawa. Tun daga wannan lokacin sai ya kasance duk dare Zarah zatayi mafarkin wannan almajira sannan kullum zancen da take maimaita mata a cikin mafarkin shine. _Zaki haɗu da ƙalubale da dama a rayuwarki, ki zama mai hakuri da juriya tare da fauwalawa Allah lamuranki a duk lokacin da kika tsinci kanki cikin tsanani, sannan ki zama mai gaskiya a dukkan lamuranki. Kada kiyi zalunci kuma ki bari wasu su aikata, ki jajirce wajen bada gudumawar da za'a kauda zalunci a cikin al'umma._ Da farko abin baya damunta amma bayan tayi satikai tana neman wannan almajira a inda ta ganta sai abin yafara tsorata ta musamman da mutanen wajen ke faɗin basusan wata almajira ba, hatta Baba Sule data karɓi kuɗi a hannunshi wancan ranar yace bai san ina taje ba bayan ta fita a wannan rana. Lamarin na matuƙar damunta saidai ta kasa tunkarar kowa da lamarin. A wata ranar lahadi ne tayi mafarkin ƙarshe da almajirar wacce bata kuma zuwa mata ba saidai maganganun data gayamata a wannan rana sun tsorata ta. _Ni ba mutum bace ALJANA CE! kuma lokaci yayi dazan koma nahiyarmu, BATULA nayi miki alƙawari bazan ƙara zuwa miki a mafarki ko a zahiri ba amma kamar yadda na alƙawaranta zan taimaka miki idan lokacin taimakon yayi. Kada ki manta da nasihata a gareki domin zata taimaka miki sosai._ Tundaga wannan lokaci bata ƙara mafarkinta ba wanda ya gaskata mata cewa aljana ta taimakawa. Lokacin data fara aikin ƴan sanda sai ya kasance ta jajirce sosai wajen ganin ta ƙwaci duk wani haƙƙin talaka da ake dannewa, hakan ya jawo mata farin jini tare da ƙarin matsayi akai-akai har zuwa yanzu da take matsayin ASP. Alhaji Sulaiman, wato ɗan'uwan mahaifin Zarah nada tarin dukiya sosai da baisan adadinta ba. Babba kuma sanannen kamfaninshi shine _M.J JEWELS_. Kamfanin ya samu sunan ne daga Muhammad Jawwad wato ɗan shi na fari. Ana sarrafa duk wasu nau'ika na kayan ƙaleƙale a wannan kamfani kama daga kan ƴan kunnaye, sarƙa, awarwaro, zobuna, agogo da sauransu wanda ake sarrafasu daga ma'adanai daban daban danginsu zinari, azurfa, lu'u lu'u da dai sauransu. A shekarar data gabata ne yasamu nasarar mallakar lu'u lu'u wanda ya siya a hannun turawa da darajarshi takai dallar amurka miliyan talatin, an sakashi a wani akwatin tsaro na musamman wanda babu wani abu dazai iya fasashi koda guduma ne da bindiga dole sai mabuɗin shi wanda yake tamkar flash na jikin laptop. Kasancewar sai yayi shekaru da dama a ajiye kafin a iya sarrafashi yasa ya ɗaukeshi daga gidanshi inda yake da farko aka maida kamfaninshi saboda hare-haren ƴan fashi. Inda aka ajiyeshi a wani ɗakin sirri dake kamfaninshi, amma duk da hakan ba'a daina barazanar satar shi ba. Ganin hakan ne yasa shida ɗan'uwan shi Alhaji Abdul_Jalal suka yanke shawarar maida shi gidansa dake bauchi bayan an damƙa tsaronshi a hannun Zarah. Hatta iyayen basuda masaniyar a inda lu'u lu'un da akwatin tsaronsa suke tun bayan da aka damƙa mata ajiyarshi. *ALPHA*👽 Alpha wani taƙadirin ɗan ta'adda ne dayayi ƙaurin suna a Nigeria dama maƙotanta, ya shahara sosai wajen sace-sace da fashi gami da kisan kai. Saidai abinda yake matuƙar damun al'umma shine babu wanda ya sanshi bare inda yake zaune domin yanada yara da dama masu yimasa aiki saidai hatta wasu daga cikin masu yimai aiki basu sanshi ba. A duk lokacin da suka yi wani gagarumin laifi suna barin tambarinsu wanda yake sunan ALPHA ne haɗi da zanen bishiyar kwakwa🏝️, ta hakane ake ganewa idan sun aikata laifi saidai har yanzu ƴan sanda sun kasa kama koda ɗaya ne daga cikin masu yimasa aiki sakamakon manyan gwamnati da suke tare dashi. Tun bayan daya samu labarin wannan lu'u lu'u daga bakin wani yaronshi na sirri wanda yake aiki a _M.J JEWELS_. Yasha alwashin sace shi saidai matakan tsaron dake jikin akwatin ne ya hanashi samun damar satarshi amma yana kan shiri wajen ganin ya mallaki wannan kadara tare da ɗaiɗaita kamfanin _M.J JEWELS_. Bayan ya samu labarin inda aka maida lu'u lu'un sai yafara kiran Alhaji Abdul_Jalal tare da yimasa barazanar kashe wani nasa muddin bai sanya Zarah ta damƙa mishi akwatin da lu'u lu'un ke ciki ba, ganin bai samu nasara ba sai ya maida akalar barazanar shi ga Zarah ganin ita mace ce saidai yayi mamakin taurin kai irin nata domin akoda yaushe idan ya kira musayar maganganu marasa daɗi ne yake wakana a tsakaninsu duk da barazanar dayake mata na rasa wani daga cikin danginta. Dalilin dayasa ya yanke shawarar taɓa wani a cikin danginta ko zata saduda. _____________________________ Ciwon ciki mai tsanani ne yake damun Rahma wanda yayi sanadin harta kwanta a gadon asibiti, satinta biyu aka sallamota bayan jikinta yayi sauƙi sosai. Kasancewar lokaci ne na hutu yasa Ammi dake ƙasar Cairo ta yanke shawarar zuwa duba jikin Rahman tare da samarin ƴan biyunta, a garin Gombe jirginsu ya sauka hakan yasa dole suka ƙarasa garin Deba domin kwana washegari sai su wuce Bauchi. Bayan gaishe-gaishe da hirar yaushe gamo ne suma tsoffin suka yanke shawarar ayi tafiyar dasu domin suma dai basuje dubata ba tunda tayi rashin lafiyar, nan suka yanke cewa zasuyi sammako gabaɗaya suje domin a ranar tsoffin sukeson suje su dawo saidai tafiyar bazata yiwu da Baba Faɗimatu ba sakamakon ciwon ƙafa da take fama dashi. Da daddare Momi matar Alhaji Sulaiman ta kira Ammi tayi mata ban gajiya inda ta roƙeta akan tabar tata tafiyar sai jibi domin su tafi tare saboda gobe zataje ganin likitan ido akan matsalar ido da take fama dashi. Nan Ammi ta yanke shawarar barin tafiyar sai jibi kamar yadda ta buƙata wanda hakan zai bata daman zama da Baba Faɗimatu da za'a bari a gida ita kaɗai a ranar. Washegari kuwa kamar yadda suka tsara ƙarfe takwas suka ɗauki hanyar zuwa gari Bauchi bayan sun tsaya a cikin garin Gombe sun ɗauki Nusaiba a gidan Alhaji Sulaiman wacce itama za'ayi tafiyar tare da ita, Shahid ne ke tuƙa motar Adil na gefenshi yayinda Malam Usmanu, Malam Adamu, Baba Aisha da Nusaiba ke baya. A haka suke tafiya lokaci zuwa lokaci suna ɗan taɓa hira. Safiyar yau bayan Zarah tayi shirinta na tafiya aiki kamar koda yaushe akan kayan aikinta ta ɗaura Abaya sannan tayi rolling da mayafinta, fara ce kuma kyakkawa ce ajin ƙarshe daga kyawun fuska har na jiki, tana da tsayi amma ba sosai ba. Kyakkyawar fuskarta na ɗauke da dara-daran idanu wanda suke cike da gashin gira dana ido, dogon kuma matsakacin hanci ta da kuma ƙaramin bakinta suke ƙara bayyana kyawun da take tattare dashi. Kai tsaye falon Abbansu ta nufa, a zaune ta same su shida Maminsu alamun magana suke mai mahimmanci, bayan ta gaishesu ne ta sanar dasu zata wuce gurin aiki. Abban ne ya dakatar da ita daga shirin miƙewa da take sa'an nan yace "Zarah inaso na ƙara jaddada miki cewa duk rintsi kada ki maidawa Daddyn ku Sulaiman ajiyarshi kowani hali kika tsinci kanki ciki matuƙar bashi ya buƙaci ajiyarsa ba." "Toh Abbah insha Allahu zanyi yadda kace." Ta faɗa cike da ladabi "Allah ya muku albarka gabaɗayan ku ya ƙara haɗe kanku ko bayan bama nan." "Ameen Abbah." Daganan ta miƙe ta musu sallama tare da barin falon hakan takejin wani irin yanayi a tare da ita. Bayan fitarta ne Alhaji Abdul_Jalal ya kalli matarshi yace" Ina tsoron abinda taƙadirin nan zai aikata ga yarinyar." "Babu abinda zai sameta da yardar Allah." "Ameen dai amma wannan mutumi abun tsorone." Haka suka cigaba da tattaunawa game da lamarin Alpha ɗin har zuwa wani lokaci. Ƙarfe sha biyu a cikin Gombe tayi musu kai tsaye suka nufi Gwallaga Inda anan gidansu Zarah yake. Cike da farin cikin ganin juna aka tarɓesu sannan aka cika musu gaba da abubuwan motsa baki. Hira aka cigaba dayi har zuwa lokacin sallar azahar Inda mazan suka wuce masallaci matan ma suka miƙe domin gabatar da tasu. Bayan anyi sallah ne kuma aka zauna cin abincin gargajiyar da Mami ta shirya, cike da barkwancin da kakannin keyiwa jikokin nasu. Haka suka kasance cikin farin ciki har zuwa lokacin da sukayi haramar tafiya. Baba Lado mai gadi na zaune akan wani benci dake jikin gate yaji anyi horn, koda ya leƙa bai gane na cikin motar ba sai ya tsaya batare daya buɗe gate ɗin ba, wani ne ya fito daga cikin motar sanye da manyan kaya ya iso jikin ƙofar inda Baba Lado ke tsaye. "Baba dan Allah me gidan yana ciki kuwa.? " Kafin ya samu damar amsawa yaji an rufe mishi fuska da wani abu, tun daga lokacin bai kuma fahimtar komai ba. Mutumin da kanshi ya buɗe gate ɗin motar tazo ta shige sannan ya kulle. "Bari naje bayi na dawo Inna sai na baki saƙon da zaki kaiwa kishiyar tawa." Faɗin Rahmah dake ƙoƙarin shiga banɗakin dake can gefe a cikin falon. Dariya sukayi gabaɗaya domin dai Rahma akwai barkwanci dason ganin duk wanda ke tare da ita cikin farin ciki. Shigewar Rahma keda wuya aka buɗe ƙofar falon, inda wasu mutane dake sanye da baƙaƙen kaya fuska rufe suka shigo. Adadin su bakwai ne sannan kowanne a cikinsu na riƙe da bindiga. "Kada wanda ya motsa ko ya mana hargowa." Babu wanda ya motsa a ciki saidai Idan mutum ya lura da bakinsu zai gane addu'o'i sukeyi. Babbansu ne ya bada umarnin a ɗauresu gabaɗaya tare da kulle musu sannan a bincika sauran ɗakunan ko akwai wani a ciki, dukkan sashe na gidan suka duba amma ba suga kowa ba. Kasancewar sai an ɗaga labule Kafin aga ƙofar banɗakin da Rahma ke ciki yasa sam basuyi tunanin akwai wata ƙofa a falon ba sakamakon labulayen da suke a jere har gaba da ƙofar bayin, Idan ba ɗan gidan bama babu wanda zai san akwai banɗaki a wurin. Waya wani ya ciro tare da karawa a kunne. "Shugaba rayuka takwas ne cikin gidan a yanzu." Jim akayi daga ɗaya bangaren kafin akayi magana. "Su faɗa muku Inda akwatin yake da mabuɗinsa idan kuma sunyi taurin kai to ku tabbatar babu wanda ya rayu cikin takwas ɗin."..... Bayan ya kashe wayar ne ya juyo tare da maida hankalinshi inda suke, umarni ya bada aka buɗe ma Abba bakin shi dake ɗaure. "Alhaji inaso ka faɗamin inda akwatin da lu'u lu'un ke ciki da kuma mabuɗinsa, ba tashin hankali ya kawo mu ba ku bamu abinda mukeso mu tafi batare da cutar da wani ba." Ya ƙarasa faɗa yana mai saka bindiga a goshin Abban. Motsa jiki da Malam Usmanu keyi ne ya hana Abba magana ganin Ogan nasu ya nufi wajenshi tare da kunce masa ɗaurin dake bakinsa. "Abdul_Jalalu a matsayina na mahaifinka ban yarda ka faɗamusu idan ajiyar da ɗan'uwanka Sulaimanu ya baka ba, idan kayi hakan kuma bazan taɓa yafe maka ba ko bayan raina." Faɗar Malam Usmanu bayan an kunce masa ƙullin dake bakinsa. "Ba muzo nan domin jin musayar kalaman da zakuyi ba, zaka faɗa mana ne ko bazaka faɗa ba.?" Ya maida akalar tambayar shi ga Abba bayan ya ƙara ɗaure ma Malam Usmanu bakinsa. "Bazan iya faɗi inda yake ba." Abban yafaɗa "Shikenan bazamu ɓata lokaci ba zamuyi abinda ya dace." Nufar inda Nusaiba take ɗaure kusada Shahid yayi tare da tsugunawa a gabanta, hannu biyu yasa tare da jan gaban rigarta da ƙarfi hakan yayi sanadiyar yagewar rigar atamfar dake jikinta tun daga sama har ƙasa wanda ya bayyana ƙirjinta da kuma fatar cikinta. Shahid wanda ya gane abinda yakeson aikatawa ga Nusaibar ne yasa ƙafafunshi biyu dake ɗaure ya naushi fuskarsa da ƙarfin gaske, take kuwa ya kuma da baya ya faɗi. Da sauri sauran yaran suka nufi kan Shahid saidai kafin su ƙarasa inda yake Ogan ya dakatar dasu, tashi yayi tare da isa gaban Shahid ɗin batare da yayi magana ba ya zaro wuƙa a gefen cinyarshi take ya caka mishi a ciki tare da zarewa ya ƙara caka mishi. Jini ne ya ɓalle tamkar a kwata take Shahid ya sulale babu rai a jiki. Bakinsu na kulle duka amma hawayene ke bin fuskokinsu na bakin ciki. Sunaji kuma suna gani ya ketama Nusaiba haddi amma babu abinda zasu iya domin sosai aka ɗauresu bazasu iya taɓuka komai ba. Da sauri Rahma ta sake labulen jikinta na karkarwa ganin babu wanda ya ganta ne yasa tayi saurin komawa cikin banɗakin tare da kullewa. Wayarta da bata rabo da ita na hannunta, sau da dama Mami kan hanata shiga da waya banɗaki amma takasa dainawa domin wasu lokutan babu abinda zatayi a banɗaki take shiga saboda kawai kar a sakata wani aikin tana tsaka da chat. Tunawa da wayar da tayi yasa take tafara ƙoƙarin kiran Zarah domin a kawo musu taimako, kuka sosai takeyi amma na zuciya ganin kiran nata shiga ba'a ɗagawa. A ɓangaren Zarah kuwa tun ƙarfe 12:30nr kwamishina ya mata kiran gaggawa domin su gana, fiye da awa ɗaya yanata yi mata surutan da basu shafi gefen da take aiki ba amma a matsayinshi na shugabanta ta kasa tanka mishi duk da tanason komawa gida su gaisa da kakanninta da ƴan uwanta da sukazo. Wayoyinta gabaɗaya suna cikin mota hakan yasa batasan irin kiran da Rahma ke mata ba. Sai da suka tabbatar da babu wani sauran mai rai a cikinsu kafin su bar gidan. Ganin Zarah bata ɗaga kiran ne yasa Rahma danna kiran wani abokin Yayansu Mustapha dake aikin soja, bugu biyu ya ɗaga kiran yana mamakin kiranshi da tayi domin ya daɗe yana mata magiyar soyayyarshi amma tana wulaƙantashi. Yana ƙoƙarin magana ta riga shi. "Ka taimakeni Mustapha zasu kashemin iyayena dan Allah kazo da sauri". Ta faɗa da disasshiyar muryarta saboda kukan da takeyi. Jin abinda ta faɗa ne yasa shi miƙewa daga zaunen da yake. "Rahma su waye zasu kashe miki iyayen kuma a ina suke.?" "Suna cikin gidanmu yanzu haka sun ɗaure kowa da kowa nima basu ganni bane, dan Allah kazo da sau..... " kuka ne yaci ƙarfinta batare da ta ƙarasa maganarta ba. "Subhanallahi! Ki zauna a inda kike gamu nan zuwa.".. Bata iya amsawa saboda toshe bakinta da tayi tana kuka. Cikin mintuna goma sha biyar taji jiniyar sojoji wanda hakan ya tabbatar mata da Mustapha ya iso da jami'ansu na soji. A farfajiyar gidan kuwa mai gadi ne da sauran ma'aikata biyar dake musu aiki kwance basu motsi, tun daga hakan Mustapha ya gane tabbas babu lafiya hakan yasa suka tunkari ƙofar babban falon cikin shiri da ƙwarewar aiki. Jini suka fara arba dashi bayan buɗe ƙofar har zuwa cikin falon, da basu kasance sojoji ba toh tabbas sai wasu daga cikinsu sun firgice da ganin gawarwakin mutanen dake kwance domin kuwa kisa aka musu tamkar a kwata. Lungu da saƙo na gidan gabaɗaya sun duba amma babu kowa hakan ya tabbatar musu cewa masu laifin sun samu nasarar tserewa. Duk da haka sai suka raba kawunan su a ɓangarorin gidan ciki da waje. Ƙarfin hali kawai Mustapha yake yana maida hawayen dake son zubo mishi, lambar Zarah ya shiga kira saidai ba'a ɗagawa. Ganin haka ya canja akalar kiran ga wani maƙocin shi D.P.O yayi mai bayani tunda case ɗin ba wanda sojoji zasu shiga bane, taƙaitaccen bayani kawai ya iya yimishi ya kashe wayar. Cikin mintunan da basu wuce talatin ba ƴan Sanda da sojoji suka kewaye gidan ta kowanni fanni. Hayaniyar mutane da taji sosai ne yasata jarumtar buɗe ƙofar banɗakin, saida ta fara leƙowa taga taron masu kaki ne sannan ta fito gabaɗaya. Abinda ta gani ne yasata sakin ihu tare da faɗowa ƙasa sumammiya. Sai a lokacin mutanen dake falon suka ankara da ita, shikuwa Mustapha sai a lokacin ya tuna da ita tun bayan da yayi arba da mummunar ɓarnar da akayi musu. "Ya kamata a sanar da wani a cikin danginsu domin bazamu iya yin wani abu da gawarwakin batare da izinin su ba." cewar D. P. O. dake kusada Inda Rahma ke kwance. Waya Mustapha ya ciro tare da danna lambar Alhaji Sulaiman sannan ya miƙama D.P.O wayar domin baisan ta ina zai fara faɗin wannan baƙin labarin ba. Fita yayi bayan ya karɓi wayar bai jima sosai ba ya dawo sannan ya miƙawa Mustapha wayar. Ƙarfe huɗu daidai motocin Alhaji Sulaiman da tawagar shi suka iso, motar farko mutane biyar ne a ciki. Direba dake jan motar sai Alhaji Sulaiman dake gefenshi a baya koma Baaba Faɗimatu, Ammi da Momi. Sauran motoci biyun koma abokan kasuwancinshi ne a ciki daya sanar musu da rasuwar suka biyoshi domin yin jana'iza. Ganin Ƴan sanda da sojoji yasa kansu ɗaurewa domin dai Alhaji Sulaiman ɗin bai sanar dasu abinda ke faruwa ba umarni kawai yabada su shirya suzo garin Bauchi. Momi ce tayi ƙarfin halin magana lokacin da direba yayi parking. Tace" Daddyn su meke faruwa ne haka, meya kawo jami'an tsaro haka a gidan. Kodai Zarah ta karɓi masu tsaron da aka bata ne.?" "Tambayoyin sunyi min yawa ku sauka mu shiga ciki, tada Baaba daga baccin nan haka tunda mun iso." Ya faɗa gamida ficewa a cikin motar Ammi kuwa ta kasa tankawa domin zuciya da gangar jikinta sun tabbatar mata babu lafiya. "Meke faruwa ne naga ƴan'uwansu Zara'u sun cika gidan.?" Faɗin Baaba Faɗimatu da farkawarta kenan daga baccin data fara tun a hanya. "Mu shiga daga ciki dai Baaba sai muji abinda ke faruwa domin dai waƴannan jami'an tsaro akwai abinda ya kawosu ko kuma suke tsaro." Momi tafaɗa tana mai buɗe ma Baba ƙofar. Cikin rashin kuzari Ammi ta fito tabi bayansu suka nufi hanyar shiga cikin gidan. Sam Alhaji Sulaiman baiyi tunanin irin ɓarnar dazai tarar ba kenan domin D.P.O ɗin ce mishi kawai yayi ƴan fashi sun shiga gidan ɗan'uwan shi sunyi fashi haɗe da kisa. Kuka yake bil hakki ganin irin kisan wulaƙanci da akayi musu duk da kasancewar ƴan Sanda sun gyarasu daga asalin yadda suka samesu bayan likita ya tabbatar babu wani mai sauran numfashi a cikin su. Saidai tambarin *Alpha*🌴 da aka zana da jini na nan a tsakiyar falon. Da sauri ya miƙe da nufin tsayar dasu daga shigowa falon kasancewar su mata yasan dole basu da juriyar da zasu iya ganin wannan aika aikar, hatta shi dayake namiji yanajin tamkar ya ciro zuciyarshi ya aje a ƙasa saboda tarin baƙin cikin daya shige shi a lokaci ɗaya. Saidai kash!!! Kafin yakai ga ƙarasawa ƙofar fita daga falon Momi da Baba Faɗimatu sun sako kai bakinsu ɗauke da sallama, duk da haka saida ya ƙarasa inda suke cikin sassarfa ya kare fuskokinsu daga ganin cikin falon. "Baaba da kun ɗan tsaya a waje ana gudanar da bincikene anan." "Sulaimanu wani irin bincikene akeyi haka daya saka zubar da hawaye, ka matsa ka bamu guri mu ƙarasa muga abinda ake ɓoye mana. Shin ina ahalin gidan ne.?" Faɗin Baaba kenan tana mai kaucewa daga hanyar daya tare. Bayanta Su Ammi su bi domin ƙarasawa falon. Abinda ya guda shiya faru domin a tare gabaɗaya su ukun suka zube a ƙasa sumammu, shima dai hawayen ne yake zubo mishi. Wani daga cikin mutanen falon ne yayi dabarar watsa musu ruwa saidai Momi ce kawai ta farfaɗo itama ba'a cikin hayyacinta ba. "Dan Allah ku tayar dani daga wannan mummunan mafarkin ba gaskiya ban.." bata ƙarasa ba ta ƙara sulale wa. "Yallaɓai kasa hannu anan munason mu wuce da gawarwakin asibitine domin gudanar da bincike." cewar likitan da aka damƙa case ɗin binciken gawarwakin a hannunshi yana miƙawa Alhaji Sulaiman wasu takardu. "Babu wani binciken da za'a gudanar saboda a yau ɗinnan nakeson a sadasu da gidansu na gaskiya, ku taimakawa waɗannan dake sume kawai." Yafaɗa cike da rauni. Nan ya ciro waya ya fara bugawa ƴan uwa da abokan arziki, abu da zamani nan da nan anguwar ta cika maƙil da jama'a domin sallartar mamatan. Da taimakon likitoci aka samu damar kimtsa su a cikin likkafani Saidai kafin wani lokaci gabaɗaya sun rine daga kalar fari zuwa Ja saboda jinin dake zuba da jikin gawarwakin. Sau uku ana canjawa amma babu wani sauyi hakan yasa aka barsu a haka. Acan falon baƙi kuwa Limamin masallacin Juma'a na gwallaga ne tare da su Momi da aka samu suka farfaɗo dakyar, saidai har zuwa wannan lokacin Rahma bata farka ba hakan yasa aka wuce da ita asibiti. Nasiha ya musu mai ratsa jiki hakan yasa suka sassauta da koke koken da sukeyi, nan suka miƙe suka nufi falon inda baƙi suka fara cika. Nan aka fara gaisuwa da jajantawa. Kwamishina ne ya kalli Zarah dake zaune a kujerar dake fuskantar shi yace "Zarah ta wace hanya kike ganin zamu iya magance matsalar tsaro a ƙasar nan.?" Zuwa yanzu Zarah ta fara zargin akwai wani abu a ƙasa domin duk lokacin da tayi nufin tafiya sai shugaban nata ya tsayar da ita ta hanyar yi mata wasu maganganun da ba ita ya dace a faɗawa, cike da ƙosawa tace " Yallaɓai a tunani na wannan matsala ce da zamu taro mu samu mafitar ta, matsala ce data shafi jaharmu da ƙasa baki ɗaya don haka muna buƙatar mu tattauna da sauran manyan jami'ai domin samun mafita.?" Kafin ya samu damar amsa mata wayarsa dake gefe tayi ƙara, hannu yasa ya ɗauku wayar tare da karawa a kunnenshi batare da yayi magana ba. "Zaka iya bata damar tafiya yanzu mun gama aikinmu sannan ka duba wayarka akwai saƙon kuɗi dana turama a asusun bankin ka." Abinda aka faɗa kenan daga ɗaya ɓangaren sannan aka kashe wayar batare da jiran amsar da kwamishinan zai bada ba. Kallon shi ya maida kan Zarah yace" ASP zaki iya tafiya. " Cike da mamaki ta miƙe tare da sara mishi sannan tafice a ofishin, jikinta taji ya mata wani iri ga zuciyarta dake bugawa da ƙarfi tamkar zata faso ƙirjinta. Shigarta cikin mota yayi daidai da katsewar kiran wayarta dake ringing kafin shigowarta, sai da ta zauna kafin ta sa hannu ta ɗauki wayar. Ido da zaro ganin anyi mata kira har 66, take ta duba domin ganin masu kiran, 35 missed calls daga Rahma, 6 missed calls daga Mustapha, 15 missed calls daga Daddy sai sauran kira 10 daga mutane daban daban. Da sauri ta shiga danna kiran Rahma saidai har ta gama ringing ba'a ɗaga, haka tayi ta kira ba'a ɗagawa kafin ya danna kiran Daddy sai dai wayarsa bata shiga. Ganin haka yasa ta canja akalar kiran ga wayar Mustapha. Bugu biyo ya ɗaga tare da faɗin" Zarah kina inane haka ake ta kiran wayarki bakya ɗagawa." "Na shiga ganawar sirri ne da kwamishina kuma wayar na cikin mota, meke faruwa ne.?" tafaɗa cike da zaƙuwar son jin abinda ke faruwa domin a lokacin bugawar da zuciyarta keyi ya ƙaru. "Babu komai ki taho gida anason ganinki." yafaɗa gami da kashe wayar baki ɗaya. Cikin sauri ta taɗa motar tare da harbawa kan titi bakinta ɗauke da kalmar hasbunallahu wa ni'imal wakil saboda yanayin da take jinta a ciki. Tun daga farkon shigowar anguwansu take ganin jerin motoci har zuwa gaban gidansu data tara cike da jama'a, nan zuciyarta ta ƙara tsinkewa gami da tabbatar mata lallai wani abu ya faru, horn ta danna a ƙofar gidan saidai a maimakon taga mai gadinsu sai taga Alhaji Sulaima na buɗe mata ƙofar. Bata ko gama parking ɗin motar ba ta fito da sauri, hannunta taji an riƙo hakan yasata tsaya wa daga tafiyar data fara tare da waigowa Daddy ta gani a tsaye. Kallo ɗaya ta mishi taga alamun kuka a fuskarshi. "Daddy meke faruwane dan Allah ka faɗamin." Batare da yayi magana ba yaja hannunta suka koma jikin motar, ƙofar baya ya buɗe mata tare da gyaɗa mata kai alamun ta shiga sannan shima ya shiga ya zauna. "Zarah." ya faɗa bayan ya zauna Cike da rauni ta amsa da" Na'am Daddy". "Nasan kinyi karatun islamiyya har zuwa matakin da kika sauke alqur'ani koh.?" Kai kawai ta iya gyaɗa mishi. "Inaso ki nutsu wasu tambayoyi zan miki." "Toh Daddy." "Inaso ki gayamin abinda Allah yace a cikin suratul Baqara a ƙarshen aya ta ɗari da hamsin da biyar zuwa aya ta ɗari da hamsin da shida(2:155-156) tare da ma'anar shi." Kai ta jinjina sanna tace" Allah maɗaukakin Sarki yana cewa و بشر الصبر ين(155) لَّذِينَ إِذَآ أَصَٰبَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوٓا۟ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيْهِ رَٰجِعُون(156) Fassarar shine "Kuma kayi bishara ga masu haƙuri(155) Waɗanda suka kasance idan wata masifa ta same su sai su ce _Lallai ne mu ga Allah muke, kuma lallai ne mu, zuwa gare Shi muke komawa._ A taƙaice ayar na nufin idan Allah ya jarabci bawa da wanu abu na baƙin ciki sai ya kasance mai yawan furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Murmushi yayi wanda iyakar shi fuska sannan yace" Masha Allah, to me Allah ya sake cewa a cikin suratul Ankabut aya ta hamsin dashi.?" Allah yace" كُلُّ نَفْسٍ ذَآئِقَةُ ٱلْمَوْتِۖ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ Fassarar ayar "Kowani rai mai ɗanɗanar mutuwane, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar daku."(Q29:57). "Alhamdulillahi tunda kin kasance mai ilimi, kinga kenan duk abinda yasamu bawa to ƙaddararre ne sannan da mutuwa da rayuwa duk na Allah koh.?". Daddy yafaɗa yana mai yimata kallo irin na tausayawa. "Ehh hakane Daddy." "Toh Zarah inaso ki kasance mai haƙuri tare da rungumar ƙaddarar data same mu duka, kiyi haƙuri ƴan fashi sun shigo gidannan sannan sunyi kisan kai kafin su tafi." A ruɗe ta kalli Daddy tanason gane inda maganarshi ta dosa. Tace" Ƴan fashi, kisan kai.? Wa suka kashe mana.?" Ganin tana shirin ficewa a hayyacinta ne yasa ya riƙo hannayenta biyu tare da faɗin" Ki nutsu Zarah sannan ki cigaba da faɗin kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Haka yayi ta maimaita mata har zuwa lokacin da ta ɗan nutsu kafin ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofar motar ta fito sannan yajata zuwa inda aka ajiye gawarwakin kafin a fita dasu a sallace su domin farfajiyar gidan bazata ɗauki mutanen da sukazo jana'izar ba. Dangin mamatan ne a gurin kowa yana karantu musu addu'a tare da kallon ƙarshe. Abinda ta hangone ya sata sulalewa a ƙasa batare da sun ƙarasa ba, da sauri Ammi data hango lokacin faɗowarta ta nufi inda butar Baba me gadi take ta ɗauko tare da watsa mata ruwan ciki a fuska. Shidai Daddy yana tsaye yakasa koda motsawa domin zuwa yanzu shima ya fara rasa jarumtar shi. Tsiyaya mata ruwan Ammi ta farayi ganin bata farfaɗo ba. Cikin sa'a kuwa taja numfashi mai ƙarfi. _Cigaban labari_. Zuwa ƙarfe bakwai na dare gidan ya ƙara cika sosai saboda ƴan uwa da abokan arziki na nesa da suka ƙaraso, domin hatta dangin Babansu Shahid dake Taraba duk sunzo kasancewar dayawa daga cikinsu jirgi suka bi. Haka akayi ta koke koke kafinan suka saurara aka cigaba da karɓan gaisuwa. A daren ranar dai babu wani daga cikin wannan ahalin daya samu damar runtsawa, kwana sukayi suna raya wannan dare da yiwa matattun addu'o'i tare da fatan Allah ya basu juriyar rashin da sukayi. Daddy ne ya hana a sanar da Sadiq dake ƙasar Singapore yana rubuta jarabawarshi ta ƙarshe na zama cikakken likitan zuciya wato *Cardiologist Consultant* sakamakon asarar shekaru da zaiyi inhar baici jarrabawar. Muhammad Jawwad kuwa sai ranar da akayi sadakar uku Daddy ya sanar dashi, shima dai kuka yayi tayi saida Daddy ya rarrashe shi. Nan yace ma Daddyn zai nemi biza ya taho bayan yayi ƙorafin rashin faɗa mishi da ba'ayi da wuri ba. Bayan kwanaki ukun ne baƙi suka rago a gida amma kullum wuni suke karɓar gaisuwa daga mutane daban daban, masu kwana ne dai babu. A cikin kwana ukun nan duk wanda yaga halin da suke ciki saiya kuka, Baaba kawai mai ƙarfin hali a cikin su. Ga Rahma da har yanzu bata farfaɗo ba. Gabaɗaya suna zaune a falo a daren ranar ukun harda Daddy da Mustapha da shima kullum baya rabo da gidan. Zarah na kwance saman dogowar kujera yayinda tayi filo da ƙafar Baaba. Lokaci ɗaya ta miƙe a firgice. Kallonta Daddy yayi tare da faɗin" Lafiya kuwa Zarah.?" "Daddy CCTV , na jona CCTV a duka falon dake gidan nan." Ta faɗa lokacin da ta miƙe sannan da gudu ta nufi hanyar ɗakinta...... Da gudu ta nufi cikin ɗakin tare da nufar inda ƙaramar na'urarta take ajiye, sashin abubuwan da suka faru a cikin satin ta shiga tare da playing daga ranar farko. Daddy da sauran mutanen gidan ne suka shigo ɗakin, gabaɗaya suka zauna domin kallon abinda ke wakana a cikin na'urar. Saidai gabaɗaya babu abubuwan da suka faro a kwanaki uku da suka wuce wanda hakan ya tabbatar mata da cewa akwai wani wanda ya shaidama Alpha na'urar da ta saka. Cike da takaici ta rufe na'urar tare da kwanciya akan gadonta. Babu wanda ya tanka duk suka fice a ɗakin. Babu daɗewa kira ya shigo wayar Zarah, hannu ta kai ta janyo wayar tare da kallon fuskar wayar domin ganin mai kira. Ɓoyayyiyar number ce ke kira, tamkar bazata ɗaga kiran ba saida ta kusa yankewa kafin ta ɗaga tare da karawa a kunnenta batare da tayi magana ba. "Na tabbatar yanzu kin fara gaskata abinda Alpha yake da damar yi ga duk wanda ya shiga gonarsa." Daga ɗaya ɓangaren aka faɗa Zaune ta miƙe batare da tayi magana domin ta gane wanda yake maganar. Magana ya cigaba dayi ta hanyar faɗin "Kada kiyi saurin karaya ta hanyar ajiye aikinki Zarah domin kin riga kin shiga wasan da baki da damar fita, ba'ayi komai ba tukun. Kin shirya bada kadarar ko baki shirya.?" Mamaki ne ya cikata jin abinda ya faɗa, tabbas Alpha ba ƙaramin shiri yayi akanta ba domin da Daddy kaɗai tayi maganar ajiye aiki kuma shiɗin ma bai goyi bayan hakan ba sannan tanada tabbacin cewa ba wajen Daddy yaji wannan batun ba. Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye kafin tace "Bana zuwa akan lokaci amma tabbas idan na iso waje ina jan ragamar kowani wasa tare da kasancewa mai nasara, ka faɗama kowaye ya sanar dakai cewa Zarah zata ajiye aiki da yaje ofishinta a gobe ranar litinin domin ya samu maka cikakken bayani." Bata jira mai zaice ba ta kashe wayar gabaɗaya. Takalmi ta zura tare da fita zuwa falo, dukkan su suna zaune kamar yadda suke da farko. Zama tayi kusada ƙafafun Daddy tare da faɗin "Daddy inaso gobe zan koma bakin aiki." "Zara'u wace irin magana kikeyi haka, kodai kema ƙwaƙwalwarki ta taɓo ne kamar yadda ƴar uwarki ta samu.?" Faɗin Baaba wacce maganar da Zarah tayi ya tadata Zaune daga kishingiɗen da take. Sunkuyar da kai tayi batare da tayi magana ba. Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa. "Baaba ina ganin mu barta ta koma bakin aikinta ƙila akwai wani muhimmin abu da zata gudanar ne bayan haka kuma zamanta a gida bashine zai dawo mana da waƴanda muka rasa ba. Hasalima aikin nata zai taimaka wajen binciko da masu hannu akan wannan lamarin." Jinjina kai Baaba tayi cikin gamsuwa da maganganun Daddyn sa'an nan tace. "Toh yaya batun Rahmatu kuma.?" "Ehh Amminsu zata wuce da ita can Cairo a cigaba da duba lafiyarta tunda maigidan nata ya amince, Zarah kuma zata zauna anan saboda binciken da zata cigaba da gudanarw. Sannan ina neman alfarmarki Baaba da ki cigaba da zama anan tare da ita, kasancewar mace bai kamata ta zauna ita kaɗai ba saboda kare mutuncinta. Insha Allahu kuma zamuyi ƙoƙarin ziyartar ku lokaci lokaci kamar yadda muka saba." Cewar Daddy "Babu damuwa Sulaimanu Allah yayi albarka ya albarkaci zuri'a." Da Ameen sika amsa gabaɗaya kafin kowa ya miƙe domin zuwa kwanciyar bacci wanda a zahiri ba haka bane domin raba dare suke gaban mahalicci suna kai mishi kukansu. Washegari tun ƙarfe bakwai Zarah ta fito cikin shirinta sanye da kakinsu na ƴan sanda, baƙin wando da shuɗiyar riga, inda ta ɗora baƙar Abaya mai ratsin shuɗi a saman kayan sannan tayi rolling da gelen rigar. Ammi kaɗai ta tarar zaune a falo tana jan carbi, ƙarasawa tayi tare da zaunawa a ƙasan kujerar da Ammin ke zaune. "Barka da safiya Ammi." Kanta Ammin ta kwantar akan cinyarta tare da shafawa a hankali. "Ina fatan kintashi lafiya.?" "Lafiya lau Ammi, zan wuce aiki ina barar addu'a." cewar Zarah lokacin da take gyara kanta a cinyar Ammin. "Allah ya kareki daga dukkan sharrin masu sharri, Allah ya nesanta zuciyarki da aikata abinda ba daidai ba, Ina roƙon Allah ya baki nasara ga duk abinda kikasa a gaba. Allah ya albarkaci rayuwarki." Cike da jindaɗin addu'o'in Ammin take amsawa da Ameen kafin ta miƙe tare da mata sallama ta nufi hanyar fita daga cikin falon. Gurin motarta da yaran Mustapha suka wanke mata ta nufa domin masu yi musu aiki tun bayan faruwar wannan lamarin suka aje aiki saboda tsoron kada a ƙara kawo wani harin a haɗa dasu tunda na farko dai hodar saka bacci aka shaƙa musu basusanai zai iya faruwa ba nan gaba. Cikin mintuna ƙalilan ta isa ofishin nasu, tun kafin ta ƙarasa parking sergent Bala ya iso inda motar take ya buɗe mata ƙofa bayan ta gyara tsayuwar motar. Ƙamewa yayi har saida ta fito sannan ya kulle motar. "Ranki ya daɗe barka da safiya. Ya ƙarin haƙurin mu." "Barka dai Bala, haƙuri mungode Allah." ta faɗa tana mai fara tafiya domin isa ofishinta. Karbar jakarta yayi bayan yace" Allah ya gafarta musu." "Ameen." tace a taƙaice. Haka ƙananun jami'an suka jigaba da mata gaisuwa harta ƙarasa cikin ofishin ta. Tana ƙoƙarin ajiye wayarta akan tebirinta kira ya shigo, ganin mai kiran ne yasata sakin wani kyakkyawan murmushi. "Assalamu alaiki ya habibaty." abinda aka faɗa kenan bayan ta kara wayar a kunnenta "Wa'alaiki salam Dr. Jiddah amaryar Bar. Saleem." Zarah ta faɗa tanamai zama a kujerarta ''Ki faɗawa wanda bai sani ba, naga alama tsokanar da bakiyi kwana biyu ba kikeson yi kuma ba kulaki zanyi ba. Dafatan kin tashi lafiya yasu Ammi." "Lafiya lau suke duka." "Ya ƙarin haƙuri kuma." "Alhamdulillah." "Allah ya musu Rahama." "Ameen Ameen. Ina kika baro maƙalematan naki banji motsinsa ba." Zarah ta faɗa cike da barkwanci. "Ke dai bari habibaty, jiya kwana nayi ina mishi kukan nagaji da zama a cikin masu jajayen kunnuwa shine yau ba shiri ya fita domin fara haɗa tarkacensa." Jidda kenan take maganar cikin sanyi murya. "Babu kyau abinda kike aikatawa fa, ki dinga damun bawan Allah yana miki abinda kikeso koda shi bayaso ɗin." "Auren kenan ai kema kiyi kigani ko baza'a miki abinda kikeso ba." Kafin tayi magana aka kwankwasa ƙofar ofishin nata da haka tace. "Zamuyi magana anjima SA.JID zan fara aiki a ofis." "Innalillahi! Yanzu Zarah tun ba'a sadakar bakwai bama har kin fara fita wannan ƙaddararren aikin, so kike ki jama kanki zance a gari." Shiru Zarah tayi na wani lokaci kafin tace" Jiddah ya zanyi to, *Alpha* kinsani Idan ban kasance a ofis ba na wani lokaci mutane da dama zasu rasa abubuwa masu mahimmanci sanadin wannan mutumin." "Shikenan Allah ya taimaka, nima dai Insha Allah zuwa wani watan zamu dawo." Jiddah ta taɗa cike da tausayin Zarah. Sallama sukayi sannan suka katse kiran lokaci guda. Umarni ta bada a shigo lokacin da take ajiye wayar a kan teburinta. Sergent Bala ne ya kuma shigowa hannunshi ɗauke da farar takarda, saida ya sara mata kafin ya fara magana. "Ranki ya daɗe wannan saƙo ne daga ofishin mai girma kwamishina, jiya da yamma ya aiko tare da bada umarnin lallai akai miki saboda abune mai mahimmanci. Dama yau nakeson kawo miki idan na tashi a aiki sai kuma gaki kinzo." Kaɗa kai Zarah tayi kafin tace" Sau sa dama Bala ina gayamaka ka koyi saka maganganu a cikin kalma ɗaya, basai kayita dogon sharhi ba a matsayinka na ɗan sanda. Anaso maganar jami'i ta banbanta dana sauran mutane, anfiso idan kayi magana sai mutane sunyi nazari sosai kafin su gane ainahin abinda kake nufi ba kamar yadda kake magana yanzu ba." Ƙamewa ya kuma yi kafin yace. "Ayimin afuwa ranki ya daɗe zan gyara." Bata kula da maganarshi ba tace. "Me takardar ta ƙunsa." "Ranki ya daɗe bani da damar buɗewa saboda a kulle take cikin envelop." Hannu tasa ta karɓi takardar tare da buɗe envelop ɗin ta cirota. Mintuna biyu ta ɓata wajen nazartar abinda ke cikinta. Ɗagowa tayi daga kallon takardar tare da maida kallonta ga Sergent Bala sa'an nan tace. "Taron ƙarawa juna sani a harkar aiki ne ake umartana naje wanda za'a gudanar a garin Abuja. Cikin sati ɗaya za'a gama gudanar da taron wanda zai fara ranar alhamis, sannan kaida Jennifer ne zamu kasance tare." Bata jira mai zaice ba ta bashi umarnin tafiya. Jingina kanta tayi da jikin kujerar sannan ta lumshe idanuwa. Haka ta wuni a ofishin sam takasa taɓuka komai bayan kuma da shirin yin aiki ta fito saidai ta danganta hakan da saƙon kwamishina daya risketa. Cikin kwana ukun ta kammala duk wasu shirye shiryen ta na tafiyar. A gefe guda kuma su Ammi na shirye shiryen tarban Muhammad Jawwad da shima zai iso ƙasar ranar Alhamis wanda rabonshi da ita tun yana ɗan shekara 14. Jirgin ƙarfe tara Zarah zatabi zuwa garin Abuja yayinda jirginsu Muhammad Jawwad zai sauka ƙarfe takwas da rabi. "Daddy ina jin ku wuce kawai zanbj ta ofishin kwamishina kafin mu wuce." Zarah kenan ke faɗi bayan ta gama amsa wayar da Sergent Bala ya bugo mata. "Babu rabon zaku haɗu da ɗan'uwan naki kenan saboda shima kwanaki biyar zaiyi ya koma saboda inaso ya dawo ƙasarshi ya cigaba da aiki." cewar Daddy "Banji daɗin haka ba gaskiya amma tunda zai dawo ƙasar gabaɗaya zamu ga juna." "Shikenan Allah ya kiyaye hanya." "Ameen Daddy." Sauran iyayenata ma addu'ar sauka lafiya suka mata kafin ta shige motarta ta fice a gidan. Daddy, Momi da Ammi sune sukaje airport tarbar ɗan nasu domin Baaba batada damar fita saboda halin takaba da take ciki. Basu jima da isa ba jirgin ya sauka, dubawa suke domin ganin ta inda zai ɓullo amma basu ganshi ba. Wani kyakkyawan bature ne suka ga ya nufo inda suke tsaye, basu ankara ba suga ya rungume Daddy tare da faɗin" Nayi kewarka Daddyna." Salati Ammi ta shiga rafkawa tana faɗin. "Jawwad kaine haka.? Shikenan masu jajayen kunnuwa sun canja ka, ka koma jinsinsu." Dariya sukayi gabaɗaya sannan suka nufi gurin da motarsu take, ita kuwa Momi kunyar fulani da kawaicin ɗan fari ne ya hanata magana. Mota suka shiga tare da nufar gida. A ɓangaren Zarah kuwa koda kwamishina ya gama zayyana mata tsarin yadda taron zai kasance saita miƙe domin tafiya, har ta kama hannun ƙofar da nufin buɗewa ta fasa tare da waiwayowa ta kalli kwamishinan da hankalin shi ya koma kan takardun dake saman teburinsa tace. "Yallaɓai nace ba." Kallonta yayi batare da yace komai ba. Murmushi tayi mai cike da ma'anoni kafin tace. "Yallaɓai idan ba damuwa ka faɗawa wanda ya baka umarnin wakiltani a matsayin wacce zata halarci wannan taron cewa _Babu ma'ajiyar CCTV a ofishin ASP Zarah sannan baya buƙatar na'ura mai ɗaukan sauti domin sanin abubuwan da nake gudanarwa a cikin ofishina._ Bata jira mai zaice ba ta buɗe ƙofar tare da ficewa a ofishin........ ✍🏼 *Jasmine*🌸🌸 *TALLA*! *TALLA*!! *TALLA* *Uwargida!!! Shin ko kinsan zaki iya magance matsalolin da suka daɗe suna ci miki tuwo a kwarya cikin gidan aurenki.???* *Uhmm riƙe sirri sai mai sirri, shin kinada labarin shahararriyar matar nan wacce ta shahara wajen ganin cewa mata basu wulaƙanta a gidan mazajensu ba.!? Wacce ta kware wajen gyara amarya har ma da uwargida.? Ita ɗin dai dake siyar da kayan gyara na musamman masu sauƙin kuɗi amma akwai aiki, mai kawo muku sirrika da dabarun gamsar da miji ta kowani fanni.*😍 *Kardai na cika uwar gida da surutu, nice dai HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA. A wannan karon nazo ne da zafafan darussa da zan gabatarwa mata tare da kayan gyara na musamman. Bari dai na lasa muku zuma a baki, kaɗan daga cikin darussan da zan gabatar a wannan karon:* *Sirrin TomTom* _Shidai tom tom da kika sani uwargida, matsalar ki ta wajen kasa gamsar da mai gida ta ƙarw idan kika riƙe wannan sirri._ *Zuba ki lashe* _Bazance komai ba a wannan fannin idan kinason sani to ki kasance tareda ni a cikin sati ukun dazan gabatar da darussa_. *Kayan gyara na musamman zai iso ki har garin da kike idan kinyi odarsu, domin sanin kalar su da amfaninsu to ki kasance dani cikin zazzafan darussa na sati uku da zan gabatar a Special Group na ASP ZARAH FANS.* *Kada ki bari ƙaramin kuɗi ya saki zama mara gata gidan mijinki.* *Ki tuntuɓi wannan number 07048961623 domin samun damar shiga ASP ZARAH SPECIAL FANS GROUP, Inda ni HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA zan kasance daku.* *Kada ki bari ƴar uwarki ta baki labari*. *SAI KUNZO* Ya kasa koda motsa yatsa ne saboda kaɗuwa da yayi da zancenta, yanzu kam ya fara zargin ko Zarah tana da aljanu masu faɗa matan idan anyi maganarta. Kiran wayar sirri sukayi da Alpha lokacin da yake shaida mishi ya tura Zarah garin Abuja domin halarta taron ƙarin ilimi a fannin aiki, hatta da wayar da yayi amfani da ita tana killace a ɗakin barcinshi na gida. Duk tunanin dayayi bai samar mishi da amsar inda Zarah taji labarin za'a sanya CCTV a ofishinta ba, yanke shawara yayi na kiran Alpha domin shaida mishi abinda ya faru. Saida ya kira sau biyu kafin aka ɗaga kiran. Cike da jimami kwamishina ya karanto mishi abinda ya faru a ofishin nashi kusan mintuna goma da suka wuce. "Ya akayi tasan da batun CCTV.?" Alpha ya faɗa cike da masifa "Kayi haƙuri Alpha nima bansan ina ta samu labarin ba." Ya faɗa kai a sunkuye tamkar yana gabanshi. Shiru ya biyo baya na wani lokaci kafin Alpha yace. "Ku bar batun saka camera ɗin tukunnan zanji da lamarinta a garin Abujan." Ya kashe wayar batare da yayi magana ba. Ƙayataccen ɗaki ne wanda yaji kayan alatu masu matuƙar kyau da tsada, tsaruwar ɗakin kaɗai zaisa mutum yayi tunanin na wani hamshaƙin shugaban ƙasa ne amma idan aka ƙurewa fitilun dake kawowa da ɗaukewa idon za'a gane mamallakin ɗakin sakamakon sunan Alpha da suke rubutawa a kowani kawowa da suke yi. A tsakiyar ɗakin wani haɗaɗɗen gilashi ɗauke da kyawawan kifaye a saman shi cikin ruwa suna ta shawagi yayinda ƙasan gilashin ke ɗauke da wasu kyawawan halittun ruwa da bazan iya tantance sunayensu ba. Maganganun ke tashi a cikin falon saidai banga alamun ta inda nake jiyo maganar ba, muryar namiji ne ke maganar inda yake cewa. "A matsayin marainiya mai neman aiki domin tallafawa mahaifiyarki zakije gidan, sannan ki tabbatar bata cikin gidan yayinda zakije neman aikin saboda kaucewa matsala." Har zuwa wannan lokaci mai maganar bai bayyana ba illa wata matashiyar yarinya da tafito daga wata kusurwa a cikin falon, kyakkyawa ce daidai gwargwado sannan fatarta ta kasance kalar chocolate. Kallo ɗaya mutum zaiyi mata ta gane tana cikin damuwa sosai sakamakon idanunta da sukayi jazir saboda kukan da tasha. Ƙofar dazata sadata da farfajiyar gidan ta buɗe tare da fita a falon, babban fili ne sosai dake ɗauke da gine gine a wani gefe sannan shukoki kala daban daban da suka ƙawata wajen ciki harda manyan bishoyin kwakwa wanda su sukafi yawa a wajen. Sai ƙananun shukoki da aka tsarasu tamkar a ƙasar turai, a ƙasa kuwa wasu kyawawan duwatsu ne masu haske da sheƙi waɗanda ke ƙara bayyana kyawu da tsarin farfajiyar wannan gida da ya kasance tamkar na sarauta. Jefi-jefi mutane na shawagi a farfajiyar inda yawancinsu suka kasance mata sa'an masu ƙananun shekaru. Tafiya tayi sosai kafin ta iso wani keɓaɓɓen guri da ruwa ke gudana tsakanin waɗansu matsakaitan duwatsu, wasu mata ne ke zaune su uku suna ɓare kwakwa. Ta farko keyin hanya a jikin kwakwar, ta biyu kuma ke ƙarasa barewa yayinda ta ukun cikinsu ke ɗauraye jikin kwakwar bayan a ɓare tare da jerasu cikin wani kyawawan kwando. Zama matashiyar yarinyar tayi a gefe tare da jingina kanta a jikin wata ƙaramar bishiya. Gabaɗaya suka maida hankalinsu kanta, kafin wacce ke wanke kwakwar tace. "Meke faruwa ne Raliya, wani abinda ya miki ne.?" Ɗago kanta tayi tare da maida kallonta garesu tace. "Zanso ace wani abu ne ya shiga tsakanina dashi saidai babu abinda yamin illa aiki dazai turani a gidan da waƴannan lu'u lu'un suke." "Raliya wani lokacin kina saka mana shakku akanki, dukkan mu anan fata muke mubar cikin wannan azzalumin gida ke a lokacin ne keki fatan kasancewa da mai gidan ki dinga aikata haramtaccen abu dashi." Fadin ɗaya daga cikinsu bayan ta maida hankali kan ɓarar kwakwar da takeyi bayan jin furucin Raliyan. "A yanzu bana fatan barin wannan wajen saboda waƴanda nayi fatan ƙara kasance dasu basa duniyar zan fiso na cigaba da kasance anan saboda ko bana nan ɗin zaiyi wuya na tserewa *ALPHA* tunda na rigada nasan wasu sirrika nashi, bazai taɓa barina a raye ba tunani zaiyi asirin shi zan tona." Faɗin Raliya Ɗayar da tun fara maganar bata tofa ba tace. "Ki dinga yiwa kanki kyakkyawan fata Raliya idan ba haka ba zuciyarki zata iya rikeɗewa ta koma irin tasa na marasa imani." "Hauwa kenan ai yanzu haka banajin akwai abinda zuciya da gangar jikina zasu kasayi indai umarnin Alpha ne. Ku da iyayenku kawai ya rabaku ya kawoku nan amma nifa? Da hannayena guda biyu yasa na kashe iyayena, zuciyata ta gama bushewa tun a waccan ranar. Zan iya raba kowaye da jindaɗin sa kamar yadda akasa na raba kaina da nawa jindaɗin." Ta faɗa tana mai maida kanta ga kishingiɗar da tayi a jikin bishiyar. Babu wanda ya kuma tankawa a cikinsu domin dai sun saba da jin kwatankwacin wannan furuci a bakin Raliyan tin bayan da tasamu kusanci da Alpha lokacin da tayi nasarar ganin yatsun hannunshi, mutum ne shi mai matuƙar taka tsantsan kasancewar shi wanda jami'ai ke nema ido rufe shiyasa baya taɓa bada damar a ga wani sashi na jikinshi koda kuwa farce ne. Idan kuwa kayi nasarar ganin wani abu nashi to daga wannan lokaci zaka zama makusancin shi bayan an shiga dakai wani ɗaki mai taken _Kusanci da Alpha_, wata ɗaya cur ake kwashewa ga duk wanda ya samu nasarar shiga wannan ɗakin saidai mutum yakan fito ne a galabaice. Idan mai tsawon kwana ne zaiyi dogowar jinya, idan yazo da ƙarar kwana kuma saidai a wuce da mutum kabari. Babu wanda yasan abinda akeyiwa mutum a cikin wannan ɗakin domin hatta Raliya da aka shigar da ita tace bazata iya tuna komai da ya faru ba. Ko bayan mutum ya samu kusanci dashi bazai ƙara samun damar ganin wani sashi na jikinshi ba saidai zai kasance yana kasa saɓa umarnin Alpha ɗin koda kuwa umartarka yayi da kashe kanka. *Abuja* Cikin kwanciyar hankali da tsari ake gudanar da taron na ƙarawa juna sani a harkar aiki inda Zarah tayi zarra kwarai wajen baiyana dabaru da koma salon aiki da kowani jami'i ya kamata yayi amfani dasu, a cikin kwana huɗun da tayi a gari Abuja an samo nasarar zaƙolo manyan masu laifi da aka daɗe ana nema, hakan yasa aka shirya karramata a ranar ƙarshe da za'a kammala taron a matsayinta na jajirtacciyar ƴar Sanda da hukuma ke son irinta. Kasancewarta mace kuma kyakkyawa yasa manyan masu muƙami a rundunar Ƴan Sanda ke ƙoƙarin janta a jiki amma taƙi bada damar hakan, domin hatta ɗakin da aka kama mata a hotel ɗin da aka sauki baƙi irinta wanda sukazo daga wani gari taƙi karɓa. Gidan wata abokiyar karatunta na sakandire dake zaune da mijinta a cikin garin Abujan nan ta sauka. *Bauchi* A yau ne akayi addu'ar kwana bakwai na rayukan da aka rasa a farfajiyar gidan marigayi Alhaji Abdul_Jalal, inda akayi saukar alqur'ani mai girma tare da yiwa mamatan addu'o'i. Ƙarfe biyu jirginsu Ammi ya ɗaga zuwa Cairo ita da maigidanta da kuma Rahma da suka wuce da ita domin cigaba da duba lafiyar saboda har zuwa wannan lokacin bata magana tun bayan farfaɗowarta. Daddy da Momi ma bayan sallar la'asar suka ɗauki hanyar tafiya Bauchi. Sai gidan ya ragw daga Baaba sai Muhammad Jawwad da wata tsohuwa da Daddy ya samu domin tayasu zama sannan jami'an tsaron da Mustapha ys ɗauki nauyin ajiye musu guda biyar. Shima Muhammad Jawwad a washegarin ranar zai wuce Abuja ya ziyarci wani abokinshi dake aiki acan, sa'an nan daga can ya wuce ƙasar England domin haɗo takardunshi tare da takardar shaidar aiki da yakeyi acan saboda samun sauƙin cigaba da aikinshi a Nigeria. Washegarin kuwa shima ya wuce garin Abuja, kasancewar su Daddy basuyi mishi batun Zarah ba shiyasa baisan tana garin ba. Ƙarfe 12:30nr ya isa garin Abujan inda abokin nashi yazo ta taryeshi a airport ɗin, daga nan kai tsaye gidanshi suka nufa. Bayan yaci abinci ya huta ne ya buƙaci su fita domin zaga gari. Ta fito da nufin tafiya gurin da suke ƙaddamar da taron kiran wata abokiyar aikinta Toyin wacce suka haɗu wajen taron ya shigo wayarta inda ta buƙaci ta biyo ta hotel ɗin da take domin su wuce tare. Agogon hannunta ta kalla taga akwai sauran mintuna 45 kafin a fara taron hakan yasa ta yanke shawarar tsayawa a wani resturant da tagani domin siyan burger da ta tashi da marmarin ci a yau. Suna ƙoƙarin fitowa daga *Koise Delicies* ita kuma tana ƙoƙarin shiga waya kare a kunnenta, karo sukayi da Abdallah wanda ke gaba yayinda Muhammad Jawwad ke bayan shi. "Sannu dan Allah." shine abinda ta furta sannan ta cigaba da tafiya tana mai magana a waya inda takw cewa. "Jirani a reception na hotel ɗin bansan ɗakin ba." Dogon tsaki Muhammad Jawwad ya saki bayan sun shiga mota kafin yace. "Suna fakewa da aikin ƴan sanda suna abinda suka ga dama, yanzu menene abin burgewa ga mace a aikin ƴan sanda kuma musulma.?" Dariya Abdallah yayi sannan yace. "Nikam naga abin burgewa sosai, ka dubi yadda tayi shiga cikin kamala ba kamar wasu matan dake irin aikinta ba, sannan maganar hotel da kaji tanayi ƙila wani aikim zai kaita can kasan su aikinsu babu inda bayakai mutum." Baki kawai ya taɓe batare da ya kuma magana ba.... *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸🌸 *Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.* *Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.* *Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍ Free Page Alhamdulillahi taro yayi kyau an watse lafiya bayan kyaututtuka da aka rarrabawa jami'ai tare da karrama wasu daga ciki inda Zarah ta kasance cikin waɗanda aka karrama. Saida ta ƙara kwana biyu cikin garin Abuja sakamakon jirginsu Jiddah dazai sauka ta garin bayan ya taso daga ƙasar Malasia. *_Jiddah ƙawace ga Zarah tun zamanin ƙuruciya, tare sukayi makarantar firamari da sakandire inda bayan sun kammala Jidda ta wuce jami'a yayinda itakuma Zarah ta wuce makarantar bada horo na ƴan sanda. Duk wasu sirrika na Zarah Jidda tasansu kamar yadda yake a ɓangaren Zarah itama._ _A shekarar data gabata ne Jiddah tayi aure inda mijin data aura ya kasance Barrister wanda yake aiki a ƙasar Malasia wato Bar. Saleem, dakyar aka rarrashi Jiddah tabi Saleem ƙasar a waccan lokacin bayan tayi iƙirarin ita bazata iya tafiya wata ƙasa batare da Zarah ba, shima dai Saleem ɗin bawai yana ƙaunar aiki a wata ƙasa bane illa dai kawai yanason ƙarasa yarjejeniyar aiki da sukayi da ƙasar. Tun bayan tafiyarsu kuma basuzo gida ba sai wannan karon da suka tattaro gabaɗaya suka dawo ƙasarsu ta gado._" Sallama tayi da ƙawarta ta tare da yimata godiya sannan ta wuce filin jirgi inda tanan zasubi wani jirgin zuwa Bauchi. Tana tsaye jirgin ya sauko daga sararin samaniya, bayan wadu mintuna kuma matafiya suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya, sam bata kula ba sai ji tayi an rungumeta gam tamkar za'a tsaga ta. "Nayi kewarki sosai sahibaty.'' Jiddah wacce ita ke da alhakin rungumar ta faɗa cike da farin ciki, kana ta saketa tare da ƙamewa ta sara mata kana tace. "Na gaida ASP da kanta." Murmushi kawai tayi tare da maida hankalinta ga Saleem dake cewa. "Zan shigar dake ƙara fa Zarah, ganinki kawai yasa ta mance dani ma gabaɗaya." Dariya sukayi duka sannan suka nufi gurin da aka tana da domin zaman ma tafiya. Mintuna kaɗan jirgin dazai sadasu da garin Bauchi ya keta hazo. *England* Tsaki yaja a karo na ba adadi cike da takaici, tashinsa kenan daga bacci sannan kamar koda yaushe yau ma mafarkinta ya ƙarayi wanda ya haddasa wajabcin wanka ya hau kanshi. Ya rasa dalilin dayasa tun ranar daya ganta kullum dare sai yayi mafarkin yana wani abu da ita wanda hakan ke silar dole idan ya tashi sai yayi wankan tsarki. Wannan shine dalilin dayasa yake jin wata muguwar tsanarta a cikin ranshi. Miƙewa yayi tare da shiga banɗaki, bai jima sosai ba ya fito cikin shirinsa na farar riga da baƙin wando. Wayoyinshi ya ɗauka da niyar ficewa a ɗakin, saidai missed calls din Ammi daya gani a cikin wayar ne yasa shi dakatawa tare da zama a gefen gadonshi yana ƙoƙarin kiranta. Bugu biyu ta ɗauka tana mai sallama, amsawa yayi tare da gaisheta. "Har yanzu banga wani alert ba fa Jawwad." Ammi ta faɗa. Cikin son gane mai take nufi yace. "Ammi wani irin alert kuma na mene ne." "Zan saɓa maka fa, ka maidani sa'ar wasan kace. Ko ba dakai mukayi magana zaka turo kuɗi a fara haɗa lefen ba.?" Ta ƙarasa magana cikin hassala. Dafe kai yayi saboda tunawa da abinda take nufi, gaba ɗaya ya manta da batun aurenshi da Daddy yace zai haɗa da ƴar marigayi wacce bai ma santa a fuska. Shi a tunanin shi girman kai ne ya hanata zuwa ta gaidashi ko tabari su haɗu lokacin da yaje Nigeria, shiyasa yaji baya ƙaunar yin auren duk da matsalar da yake fama da ita na ƙarfin sha'awa. "Ayi haƙuri Ammi zan turo insha Allah." Ya faɗa cike da biyayya. "Toh ina jira kada ka sake na ƙara kiranka akan wannan batun idan ba haka ba kuma ranka ɓaci zaiyi." Ta faɗa gami da kashe wayar. Dafe kai yayi cikin damuwa, shifa yana da ra'ayin irin matar da yakeson aura, amma gashi yanzu Daddy ya ruguza mai duk wasu tsarin shi. Miƙewa yayi jiki babu laka ya fita domin yana a farkon sabuwar wata da za'a yakeson komawa gida gaba ɗaya, shi da ƙasar turawa kuma sai ziyara ko hutu ko kuma wani abu mai mahimmanci. ....................... A bakin gate su Zarah suka tarar da wasu mutane biyu da alama dai miji da mata ne sannan marasa ƙarfi. Ganin motar ne yasa su miƙewa daga durƙusun da suke a gefen gidan. Tsayar da motar Saleem yayi kamar yadda Zarah ta buƙata, buɗe ƙofar baya ta fito ta nufi inda suke tsaye. Da sassafar matar ta ƙaraso tare da durƙusawa akan gwiwoyinta tace. "Ranki ya daɗe ki taimake mu, kwana uku kenan muna zuwa gidan nan amma anƙi bamu damar shiga. Hatta ofishinku ma an hanamu ganinki dan Allah ranki ya daɗe ki sauraremu." Ɗagota Zarah tayi kana tace. "Kada ki bani kunya ta hanyar durƙusawa a gabana domin neman wata alfarma, hakan zai sa nayi tunanin ko baki ɗaukeni a matsayin ƴa ba. Ku tashi mu shiga daga ciki muyi magana a nutse." Ta ƙaramar ƙofa suka shige bayan su Saleem sun shige da motar tuni. Falon saukar baƙi ta kaisu kana taje kicin da kanta ta kawo musu ruwa da lemo. "Bismillah ga ruwa ku sha sai muyi maganar abinda ke tafe daku." Fadin Zarah bayan ta aje tiren dake dauke da gorar ruwa da lemu a kan ƙaramin teburin dake tsakiyar falon. "Ranki ya daɗe ba zamu iya shan komai ba ahalin da muke ciki." Faɗin mijin "Meke faruwa ne.?" Zarah ta faɗa tana mai zama a kujerar dake fuskantarsu. "Ranki ya daɗe ƴar mu akayi wa fyaɗe, sannan mun tabbatar da wanda ya aikata laifin. Yaron wani ɗan majalisa ne dake maƙobtaka damu amma bayan mun sami mahaifin yaron da batun ya ƙaryata lamarin tare da faɗin zaiyi shari'a damu duk sanda muka nemi ɓata masa suna ko ɗan shi. Yanzu haka yarinyar na gadon asibiti ana neman kuɗin aiki sannan bamu da halin biya." Ya faɗa yana mai fashewa da kuka inda matar ke taya shi. Sosai zuciyarta ta tsinke da lamarin musamman da taga manyan mutanen da suka haifeta a shekaru suna zubar da hawaye. "Amma meyasa baku kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa ba.?" Zarah ta tambaya a raunane. "Tun faruwa lamarin muka kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa damu, saidai bayan sun gana da mahaifin yaron suka fatattake mu tare da faɗin sharri mukeson ƙullawa ɗan sa. Wannan dalilin yasa muka garzaya ofishinki bayan wani maƙocin ya bamu shawarar yin hakan, tun kwanaki uku da suka wuce muke zirya a ofishin an hana mu shiga shine mai gadin wajen ya bamu adireshin ki." Matar ke wannan bayanin. Kai kawai ta jinjina tare faɗin. "Ina zuwa." kana ta miƙe ta fita. Bata daɗe ba ta shigo tare da Saleem da Jidda, zama sukayi tare da gaisa. "Wannan shine Bar. Saleem tare da matarsa Dr. Jidda, za muje asibitin tare domin ganin halin da yarinyar take ciki kafin shigar da ƙara a kotu." faɗin Zarah bayan tayi nuni da kujerar da Saleem ke zaune shida Jidda. Godiya su kayi sosai kana suka miƙe gaba ɗaya suka nufi waje. Motar Zarah suka shiga duka inda Saleem ke tuƙin. Mintuna kaɗan suka iso asibitin, kasancewar Zarah ƴar sanda shiyasa basu wani sha wuya ba wajen isa ɗakin da yarinyar take. Ita kaɗai ke kwance a gadon jikinta rufe da zani yayinda acan kusurwar dakin wata ke zaune kan dadduma da alama dai itace mai jinyar. Bayan sun mata ya jiki ne suka zazzauna inda Saleem ya ciro ƙaramar sound recorder tare da jan kujera ya ƙarasa bakin gadon yace. "Baiwar Allah da farko dai ina ƙara jajanta miki akan wannan lamari da ya afku dake sannan inason sanin ko ke wacece.?" "Da farko dai ni suna na Fahima ina zaune ne tare da iyayena a anguwar bakin kura dake nan jihar Bauchi. Sannan mahaifina mai ƙaramin ƙarfi ne." magana take a hankali alamum dai tana jin jiki. "Meya jawo afkuwar wannan lamarin a gareki." "Ina aikine a gidan wani ɗn majalisa dake nan anguwar mu wato Alhaji Nura Mai Riga. Tun lokacin da nafara aiki a gidan ɗan sa Kabeer ke yawan shigemin tare da nuna alamun yanaso muyi sabo sosai saidai ban bada damar hakan ba. To a ranar larabar data gabata ne bayan na kai masa abincinsa na rana kamar yadda na saba kowani lokaci bayan na gama girki ina kai masa nashi bangarensa. Bayan na ajiye abincin ne ya miƙomin kofin dake hannunshi wanda ke ɗauke da lemu ya umarceni da na shanye, naso nayi jayayya saidai yace idan ban sha ba bazai barni na tafi ba shiyasa na karɓa na shanye tare da miƙewa da nufin tafiya sai ya kuma cewa na share mai falon shi yayi ƙura. Tunda nafara sharar nakejin bacci na fizgata kafin nagama kuma bansan inda kaina yake ba sai farkawa nayj na ganni akan gadonshi ya ketamin haddi..." Ta ƙarasa faɗa tana mai fashewa da wani marayan kuka wanda ke nuni da ciwon abin da takeji. Kashe recorder ɗin Saleem yayi kana ya miƙe ya fita yana musu alama da ido. Zarah da Jidda ma miƙewa sukayi kana Zarah tace. "Insha Allahu za'a bi miki haƙƙinki sannan kafin mu tafi za'a sa hannu a shigar dake aikin da za'a miki na matsalar yoyon fitsari da kika samu." Godiya suka ƙara yi musu sosai. Sanna su Jiddan suka bar ɗakin. Saida suka biya kuɗin aikin da za'ayi wa Fahima sannan suka bar cikin asibitin. A hanyarsh da zuwa gida ne Jidda dake gaban motar ta waiwayo ta kalli Zarah data jingina kanta a jikin kujerar bayan motar tace. "Zarah kina ganin ba muyi ganganci ba wajen shiga cikin wannan case ɗin daya shafi Alhaji Nura Mai Riga.?" "Banason halinki na saurin karaya Jidda, kada ki manta Allah yana tare da msi mai gaskiya." Ta faɗa tana mai ɗagowa daga jinginawar da tayi jikin kujerar. "Waye ne Alhaji Nura Mai Riga.?" Saleem ya tambaya hankalinshi na kan hanya. *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸🌸 *Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ ... Jidda ce ta gyara zama tare da fara magana. "Wani sanannen ɗan siyasa a ciki da wajen Bauchi, anyi mishi shaidar rashin arziki da wulaƙanci gami da cin zarafin na ƙasa dashi, baya ragama kowa kasancewar yana da muƙami ga dukiya kuma daya tara, shiyasa yake taka kowa ya zauna lafiya daga shi har ɗan nashi. Ana faɗin cewa zai iyayin komai akan yaronshi ko da kuwa kisa ne. Shiyasa nake tsoron kar wani abu ya haɗa su da Zarah saboda baza'a haifar da ɗa mai ido ba." Kai Saleem ya girgiza kana yace. "Gaki a haka kamar Jaruma amma zuciyarki fal take da tsoro, ni a gani na wannan ba wani abu bane da za'a tsorata har ayi shakkun yin shari'a dashi. Insha Allah zamu zauna anan har sai munga an kwatar ma yarinyar nan hakkinta. Kuma ni zan zame mata lauya." "A zahiri bakai bane zaka zame mata lauyan amma a baɗini kai ne." Zarah ta faɗa idonta a lumshe kamar ba ita tayi maganar ba. Ɗan juyuwa Saleen yayi yana son fahimtar abinda take nufi. "Wani lauyan zamu nema yanzu a matsayin wanda zai kareta, saboda zai iya siye duk wani lauya da zamu ɗauka da kuɗi. Bayan mun gama yarda muna da lauya sai ranar da za'a shiga kotu mu rasa mafita. Shiyasa a yanzu dole mu ɗau wani lauyan na ganin ido, amma a baɗini zamu cigaba da gudanar da bincike tare da haɗa shaidun da zamu gabatar a kotu." Cewar Zarah Sosai suka ƙara mamakin fasahar ta wajen yin tunani abinda masu laifi zasu aikata. "Sam banyi tunanin haka ba da farko, kuma tabbas nasan Alhaji Mai Riga zai aikata haka." Faɗin Jidda tana mai haɗe hannayenta alamun jinjina ga Jidda. Haka suka cigaba da tafiya suna hira jefi-jefi har suka ƙaraso gidan. Ɗakinta ta wuce kai tsaye tare da shigewa banɗaki, wanka tayi sannan ta fito ɗaure da towel a jikinta. Zama tayi da nufin yin shafa amma ta kasa illa kwakwalwarta dake tariyo mata irin matsalolin da take dasu a gabanta, riƙe kanta tayi da hannu biyu bayan ta kifashi a jikin mirro ɗin. Saitin zuciyarta ta kuma dafewa da hannu ɗaya tanajin yadda take bugawa da sauri, tabbas tasan watarana matsalolin ƙasar nan zata haddasa mata bugawar zuciya saboda yadda ta ɗau matsalolin tamkar yadda take ɗaukan duk wani abu da ya shafeta ko danginta. Miƙewa take shirin yi ta nufin saka kaya batare data shafa man ba, turo ƙofar da akayi ne yasata dakatawa tare da maida kallonta ga Baaba dake shigowa bakinta ɗauke da sallama. Amsa wa tayi tare da faɗin. "Wannan tsohuwa me zakiyi min a ɗaki ne haka daya saki haurowa sama, dan wannan zuwan naki kam akwai abinda ta kawoki tunda nasan ba haurowa sama kikeyi ba." "Yo idan ba wani abu ba mai zanzo nayi a bene nikam salon watarana na faɗi a garin sauka." Baaba ta faɗa tana mai zama a gefen gadon Zarah. Sai da suka gama barkwancin jika da kaka sannan Baaba tayi gyaran murya tace. "Zara'u." Ɗagowa tayi ta kalleta, gani yanayin fuskarta ne yasa tagane magana ce mai mahimmanci zasuyi. "Na'am Baaba." "Kin sani Zara'u kin kai mun zalin daya kamata ace kema kinyi aure kamar ƴar uwarki Jidda, aure shine darajar duk wata ƴa mace koda kuwa tana da tarin dukiya, kyau, muƙami ko nasaba. Ba mu da yawan zuri'a Zara'u kune muke fatan ku hayayyafa ku sama mana masu yi mana addu'a damu daku gaba ɗaya koda bama a raye, shekarunki na haihuwa fa yanzu 23 yakamata ace kinyi aure kin sama kanki daraja musamman a irin yanayin aikin da kikeyi da ake tunanin duk wata mace da takeyin shi bata da kamun kai. Dan Allah ki siya mana mutunci da kanki kar a fara maganar a gari ana cewa mun barki sakaka." Shiru Zarah tayi batare da tayi magana ba, Baaba ce ta kuma cewa. "Munyi magana da babanku Sulaiman yace nagaya miki ki turo mishi wanda kika tsayar domin manya su shiga maganar." "Baaba bawai auren ne banaso ba, akwai burika na da nakeson cikawa wanda nasan va kowani namiji dazan aura bane zai bani damar cikasu, shiyasa ma bana saka auren cikin lissafina a yanzu amma idan lokaci yayi zanyi insha Allahu." Ta faɗa alamun maganar Baaba bata wani dame ta ba. "Toh akwai wani wanda kuka sasanta ne ko kuma kukeson ku sasanta tsakaninku dashi.?" "Dan Allah Baaba ki barni ni babu wani da nakeso ko muke soyayya, aikina shine a gabana yanzu." Cewar Zarah da ta miƙe ta nufi gaban durowar kayanta. "Nima ai ina fatan ki kasance tare da aikinki kodan kawo ƙarshen waɗanda azzaluman mutanen, amma ki dawo ki zauna muyi magana domin bankai ga faɗin sakon da aka aikoni na isar ba." "Waye kuma ya aikoki.?" "Toh da farko dai mai saƙon yace bazai zo da kanshi bane gudun kada kiji nauyin shi kiyi abinda bashi ranki ke so ba, alfarma ce yake nema a gurin ki nason haɗa zuri'a dake, ma'ana dai yana neman alfarmar ki akan yanason ya haɗaki da ɗansa ku raya sunnar manzo S. A. W a ƙarƙashin inuwa ɗaya. Kuma yana fatan ace wani bai riga shi ba sannan yace a barki kiyi shawara kafin ki bada amsa." Wani kallo Zarah ta mata kafin tace. "Waye da wannan doguwar wasiƙa kuma Baaba." Miƙewa tayi kana tace. "Doddon ku mana Sulaimanu yace yana neman alfarmar ki amince da auren ɗan sa Muhammad Jawwad." Dariya sosai Zarah tayi jin yadda Baaba ta kira Daddy wai Doddo kana ta tsagaita ganin har Baaba takai kusa da ƙofa, ƙarasa wa tayi inda take sannan tace. "Ban fahimce ki sosai ba Baaba." "Ke dai ba kurma bace sannan kuma ke ba mahaukaciya bace bare nace bakya fahimta, abinda dai kikaji shi nake nufi idan kuma kina tantama ne to ki ɗau waya ki kirashi ya miki ƙarin bayani." ta faɗa tana mai ficewa a ɗakin. Ta daɗe tsaye a inda Baaba ta barta tana sakawa da kuncewa akan maganganun Baaban, lokaci ɗaya kuma ta watsar da zance daga tunaninta sannan ta nufi durowar ta ɗauko wata doguwar rigar atamfa super ta zura. Mai kawai ta shafa a leɓanta kana ta zura takalmi ta fice zuwa falo inda tasan Jidda na jiranta. A zaune ta same su ita da Saleem sun tasa laptop a gaba da alama abu suke gani a ciki mai mahimmanci. Jidda ce ta ɗago ta kalleta tace. "Madam ASP tun ɗazu muke jiranki anan munkawo ƙara.'' Kyaɓe baki tayi kana ta gaishe da Saleem sannan ta kalli Jidda ta kuma cewa. "Ace mutum shi kullum cikin zolaya kamar mara damuwa." "Wace damuwa ne dani nikam, ga mijina a gefe ai sai farin ciki ko da yaushe." Jidda ta fada. Bata kulata ba sakamakon abinda Saleem yake nuna mata a cikin laptop ɗin, shiru sukayi gaba ɗaya suna mai maida hankalinsu kan laptop ɗin. "Na rigada na gama bincike kuma na tabbatar shi ne mai laifin shaidune kawai suka rage mana, sannan nayi magana da babban likitan asibitin da yarinyar take akan Jidda zataje ta gudanar da duk wasu bincike da rahoton likita da za'a buƙata a kotu, yanzu binciken ya rage na ɓangarenki daga nan kuma a shigar da ƙara kotu." Cewar Saleem "Abun zaizo da sauƙi ai, nima yanzu nake so na fita na gudanar da wasu bincike na saboda gobe nakeson a shigar da ƙara kotu." Faɗin Zarah. "Yanzu baiyi yamma ba Zarah.?" Cewar Jidda. Kaɗa kai tayi kana tace. "Inason zuwa ofishin ƴan sanda da suka fara kai ƙara ne domin haɗuwa da Inspector ɗin wajen, na samu labarin yafi zama a office a irin wannan lokaci." "Ki tsare shi ya faɗa miki gaskiya fa Zarah kuma ya gayamiki nawa a bashi ya danne gaskiya." Jidda ta faɗa cike da takaicin abinda aka aikatawa Fahima. Dariya Zarah tayi sannan ta maida kallonta ga Saleem tace. "Gaskiya Sa.Jid ina tunanin kwanan nan zan shigar da matar ka aikin ƴan sanda ita ma, naga alama ta fini zaƙewa akan aikin nan." "A'a ki rufamin asiri, ai aikin ƴan sanda sai irinkj jajirtattu bana su Jidda bane." Faɗin Saleem cike da zolaya. Dariya suka yi duka kafin Zarah ta miƙe ta koma ɗakinta inda ta ɗauko mayafi da jaga, sallama ta musu sa'an nan ta fice domin zuwa inda ta faɗa musu. A hankali take driving har ta iso bakin ofishin, kallon gurin tayi wanda ke tsabtace sosai sai ƴan sanda da mutane dake shawagi ɗaɗɗaya. Kasancewae gilashin motar mai duhu ne yasa jami'an basu gane wacce ke ciki ba har saida ta fito, nan tsirarun da suke farfajiyar wajen suka ƙaraso gabanta da hanzari suka sara mata. Kai kawai ta jinjina sannan ta fara tafiya a hankali inda suke take mata baya har zuwa ofishin Inspector ɗin. Miƙewa yayi da sauri daga kishingiɗen da yake tare da miƙewa...... *MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*📚🖊️ *M*. *W*. *A* _Putting smile on our readers face_ https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp ___________________________________ *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸🌸 *Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.* *Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.* *Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_ *Free Page 7* ... "Barka da zuwa ranki ya daɗe." ya faɗa cike da ladabi. Zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun office ɗin sannan ta umarce shi ya zauna shi ma. "Ina son sanin gaskiyar binciken da kayi game da case ɗin fyaɗe da aka kawo maka kwanaki biyar da suka wuce." Zarah ta faɗa tana mai zuba mishi idanu. Daburcewa yayi alamun rashin gaskiya, take kuma zufa ta keto mishi duk da iskar fanka dake kaɗawa a ofishin. Kana yace. "Dama ranki ya daɗe ƙazafi ne ake yiwa yaron amma bai aikata laifin ba." Bata ce komai ba ta ciro wata paper daga cikin jakarta ta miƙa mai tana mai cewa. "Ka cire mana hular mu da belt ɗin mu, sauran kayan kuma idan kaje gida ka aiko mana dasu. Sannan duk wani abu daya kasance mallakin hukumar mu ka dawo mana dashi, karɓi wannan takardar korarka daga hukumar mu ta ƴan sanda ne." Durƙosawa yayi akan gwiwan shi tare da faɗin. "Ki rufamin asiri ranki ya daɗe wallahi zan faɗi gaskiya, wannan aikin dashi nake ci da iyali na da mahaifiyata idan kika rabank dashi bansan ya zanyi ba. Sharrin shaiɗan ne yasa ni karɓa kuɗin toshiyar bakin daya bani." Shiru tayi batare da tace komai ba, hakan ya bashi damar cigaba da magana inda yace. "Bayan an kawo case ɗin ni da kaina naje har gidansu wanda ake zargin, bayan mun zauna da mahaifinsa ne yake gayamin cewatabbas ɗan sa ya aikata abinda ake zarginsa dashi amma yana so a kori case ɗin inda ya bani kyautar kuɗi naira dubu ɗari uku, dalilin dayasa na kori case ɗin kenan. Dan Allah ranki ya daɗe ayimin afuwa bazan ƙara ba, nayi alƙawari." Tsaye ta miƙe kana ta mayar da takardar cikin jakarta sannan tace. "Ka shirya zama shaida a kotu." "Nagode ranki ya daɗe insha Allah zan kasance mai faɗar gaskiya." Nan ya rakota har bakin motarta yana mai ƙara yimata godiya. Gida ta wuce kai tsaye tana mai tuƙi cikin nutsuwa. "Har kin dawo." cewar Jidda dake tsaye a dinning tana shirya kulolin abinci bayan Zarah ta shigo cikin falon. "Ehh sannu da aiki fa Madam." Hararar wasa ta aika mata sannan tace. "Yauwa ASP." Tsayawa tayi a bakin bene da zai sadata da ɗakinta jin maganar Jidda dake cewa. "Jirani mu haura tare." Hannunta ta riƙe kana suka haura sama inda suka shige ɗakin Zarah wanda yake farko a jerin ɗakunan dake saman. Tsalle Jidda tayi ta faɗa kan gado tare da yin juyi sannan ta fuskanci Zarah dake ƙoƙorin rage kayan jikinta. "Ɗazu Baaba ke tsegunta min wani zance." "Wani zance kenan." "Zancen auren ki da Muhammad Jawwad mana." "Uhmm." "Meyasa ba zaki amince ba Zarah, babu wani fa da zaki aura ya riƙe ki da daraja kamar shi. Idan ma aikin ki kike tunani ai shi ɗan uwanki ne dole zai barki ki cigaba aikin ki batare da tsauwalawa ba, nikam bana tunanin akwai aibu a cikin wannan haɗin." "Kema kinsan dai Daddy uba ne a gare ni ko da ace Abba na yana raye shi mai zaɓa min miji ne, bazan iya cewa a'a ba kawai dai zaɓin Allah nake nema a cikin al'amura na." "Toh Allah ya shige mana gaba baki ɗaya ya kuma zaɓa mana abinda yake mafi alkairi." "Ameen" Zarah ta faɗa tana mai shigewa banɗaki. Duk wasu bincike daya kamata a gudanar sun gama haɗa shi, zuwa yanzu mai laifin ya daɗe da kasancewa a bayan kanta a kulle sai jiran ranar shiga kotu duk da yaƙi amsa laifin nashi. Har zuwa yanzu kuma Zarah bataje office ba tun bayan ranar sa takaiwa C. P rahoton abubuwan da suka faru. Yau dai ta shirya domin zuwa ofishin nata bayan tayi sallama da jama'ar gidan. Kyawawan motoci guda uku ta gani a harabar ofishin nasu wanda ya tabbatar mata da sunyi baƙin manyan mutane. Tun kafin ta ƙarasa ta hango Alhaji Mai Riga zaune a inda suka tanada domin zaman baƙi. Bata ko kalle inda yake ba lokacin da ta ƙaraso kusan shi saima shigewa ofishin ta da Sergent Bala ya buɗe mata ƙofar. Saida ta zauna kafin Sergent din yace. "Ranki ya daɗe wannan mutumin shine wanda yake ta ziryar son ganinki a kwana biyun nan, yau ma tun ƙarfe bakwai yazo saboda na faɗa mai zaki zo office yau." Kai ta gyaɗa sannan tace. "Ka shigo dashi." Fita yayi bada jimawa ba kuma ya ƙara shigowa inda a bayan shi Alhaji Mai Riga ne da wasu body guards dinsa da suka sha baƙaƙen kaya guda biyu. Kujerar da Sergent Bala ya nuna mai ya zauna. Shikuwa Bala sara mata yayi tare da ficewa a office ɗin. "Alhaji a tunani na kaine wanda keson zantawa dani." Faɗin Zarah Washe baki yayi tare da faɗin. "Ehh nine ranki ya daɗe." "Toh tsayuwar me waɗannan keyi anan." Umarni ya basu da su fita waje, nan suka nufi ƙofar fita bayan daya ys ajiye wata brief case a kan teburin........ ✍🏼 *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Daga Alƙalamin_✍🏻 _Asmau Bint Abubakar_ _Jasmine_🌸 *Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*. *Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ . 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ 👩‍✈️ .. "Na kwana biyu ina zuwa nan ranki ya daɗe bana samun ki." cewar Alhaji Mai Riga. "Ayya." ta faɗa a hankali. Zama ya gyara sannan yace. "Dama nazo ne akan maganar case ɗin yaron waje na da aka ce ke kike riƙe dashi, duk da naga wannan case ɗin na ƙananun jami'ai ne ba manya irin ku ba." "Akwai kundin tsarin daya ce babban jami'i kar ya karɓi case ne.?" "Ba haka nake nufi ba ranki ya daɗe, nazo ne kawai muyi magana akan case ɗin ne." "Ka samo mana wata shaidar ne.?" "Ba shaida ba dai ranki shi daɗe, kawai inason ayi wani abu akai ne." "Bangane wani abu ba." "Ehhm nace dama ko za'a bar maganar shiga kotun a sasanta a gida kawai." "Bai aikata abinda ake zarginsa dashi bane.?" "Ranki ya daɗe kinsan halin yara basa tunani kafin su aikata wani abin." "Tambaya ce kawai nayi bai aikata bane." "Ehh toh gaskiya yace min ya aikata amma...'' Hannu ta ɗaga mai alamun batason jin sauran zancen sannan tace. "Toh Alhaji ya aikata ya kakeson ayi kenan." "Yauwa nace a sasanta kawai anan inyaso sai abiya kuɗin da mahaifan yarinyar suka kashe akan nema mata lafiya." "Baka gudun ya kuma aikatawa." "Toh kinsan halin yaran zamani su komai sukayi gani suke daidai ne." "Yanzu kana nufin a janye ƙarar kenan.?" "Ehh haka nakeso ranki ya daɗe, ni ɗan siyasa ne hakan zai iya jawomin cece kuce a tsakanin jam'iyun adawa. Yanzu ga wannan." Ya ƙarasa faɗa yana mai buɗe jakar da body guard ɗin ya ajiye, kuɗi ne maƙil a cikin jakar rafar dubu ɗaɗɗaya an jere su. Murmushi tayi har saida dimple ɗinta ya lotsa sosai kana ta sa hannu ta taɓa kuɗi tare da ɗaga rafa ɗaya ta jujjuya sannan ta aje. Cikin ƙwarin gwiwa alamun nasara Alhaji Mai Riga yace. "Shiyasa ban turo kowa ba nace bari nazo da kaina ayi maganar zamu fi fahimtar juna." Gyaɗa kai tayi kana tace. "Zan iya tambayan ka idan babu damuwa." "Bakomai ranki ya daɗe yi tambayarki." "Kana da ƴa mace.?" "A'a babu yarona ɗaya ne dai wannan da muke magana akan shi." "Ohk to kana da Yaya ko Ƙanwa mace." "Gaskiya babu dake dukkan mu maza ne iyayen mu suka haifa. Amma lafiya kike min irin tambayar nan ranki ya daɗe." "Ban kai ga ƙarasa tambayata ba idan na gama zan amsa taka tambayar. mahaifiyar yaron nan yakake jinta a ranka a matsayinta na waccw nake tunanin tun auren ƙuruciya shine har yanzu." "Gaskiya bazan iya misalta miki yadda nake jinta a raina ba, wannan dalilin ne ma yasa har yanzu banyi mata kishiya ba." "Masha Allah, yanzu Alhaji misali wani ya shiga gidanka yayi wa matar ka fyaɗe sannan da akayi bincike aka gano mai laifin, wani irin mataki zaka ɗauka.?" "Wallahi da hannu na zan kashe shi, idan ban samu damuwar haka ba kuma zan tsaya da dukiya da ƙarfina har sai naga an yanke mishi mummunan hukunci akan laifin daya aikata min." Dariya Zarah tayi sosai sannan lokaci ɗaya ta gimtse kana ta jawo jakar kuɗin gabanta ta zuge zip ɗin kamar yadda yake tare da tura jakar gaban Alhaji Mai Riga kana tace. "Kamar yadda kakejin zaka tsaya da ƙarfi kuma da dukiyarka ni idan akayi qa matarka fyaɗe, toh ni inajin fiye da hakan wajen ganin na tsayawa kowace mace da aka ketawa haddi domin abi mata haƙƙinta. Wannan kuɗin da ka kawo bazai taɓa canzamin ra'ayi domin na saba riƙe fiye da irinsu, cin hanci koh? Toh kasani cewa bakayi kuɗin da zaka iya bawa Zarah cin hanci ba, wannan kuɗin ko albashin ma'aikatana na wata ɗaya bazai iya biya ba. Shin kasan girman laifin da ka aikata na baiwa ƴar sanda cin hanci.? Tabbas zan baka mamaki kuma dole a yankewa yaron ka hukunci daidai laifin daya aikata. Banason na ƙara jin ko da kalma ɗaya ce ta fito daga bakin ka idan kuma ba haka ba, hmm kulle ka ba wani abu mai girma bane a wajena sannan babu wani jami'in dayasa isa ya saka ni buɗeka idan nayi hakan. Dan haka kaɗau tarkacen kuɗinka ka ficemin daga office." taƙarasa faɗi tana mai buga teburin, wanda hakan ya ƙara ɗarsa tsoro a zuciyar Alhaji Mai Riga domin dai dama ƙarfin hali kawai yakeyi yake iya mata magana amma ba ƙaramin kwarjini take masa ba. Batare da tanka ba kamar yadda tace yaɗau jakar tare da ficewa daga office ɗin yana mai banko ƙofar da ƙarfi. Murmushi Zarah tayi sannan tace. "Mai Riga kenan, ba shirin wasa nayi a kanka ba duk wani motsin ka yanzu a tafin hannu na yake.". Kiran wayar daya shigo ne yasa ta saka hannu ta jawo wayar daga inda take, numbar Daddy da tagani ne yasa bata ɗaga ba har saida ta yanke sannan ta maida kiran. "Assalamu alaikum." "Wa'alaikumus salam daughter barka da safiya." "Daddy ina kwana." "Lafiya lau kun tashi lafiya koh.?" "Lafiya kalau Daddy ya Momi." "Gata nan lafiya lau, yasu Baaban dai da mutanen turai." "Duk suna lafiya Daddy." "Kin fita aiki ne yau.?" "Ehh ina office." "A'a toh bari na bari ki koma gida kar na katse miki aiki, dama nayi tunanin kina gida ne shiyasa na kira muyi magana." "Bakomai Daddy ba aiki nakeyi ba dama, zamu iya magana babu damuwa." "Toh Masha Allah, nace ko Baaba ta isar miki da saƙo na.?" "Ehh Daddy ta gayamin kuma na amince." "A'a Zarah idan kina da wani ki faɗa kar na tauye miki." "Babu kowa Daddy." "Toh nagode kwarai Allah yayi albarka." "Ameen Daddy." "Sai anjima ki gaishe da su Baaban." "Zasuji insha Allah." Nan suka yi sallama ta aje wayar a gefenta tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. "Oh ni Fatimaj Zarah, aure da mijin da bansan shi ba." Sai kuma tayi murmushi ita kaɗai tare da kaɗa kai. ......... Shi kuwa Alhaji Mai Riga bayan fitarsa daga office ɗin Zarah cike da takaicin rashi haɗin kai da bata bashi ba, kai tsaye gidan alƙalin kotun da aka shigar da ƙarar ya nufa. Bai wani sha wahala ba aka shigar dashi cikin gidan, bayan sun gaisa da alƙalin ne yake faɗa mishi abinda ke tafe dashi nason kar a yankewa yaronshi hukunci tare da korar ƙarar gabaɗaya. Toh ƙasar tamu dai ta ɓaci kowa son kuɗi kawai, babu ɓata lokaci alƙalin ya amince gani irin maƙuda kuɗin da aka aje a gabansa. Sallama sukayi zuciyar Alhaji Mai Riga fal da farin ciki. *By* *Jasmine*🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Paid book_. _Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki._Za'a turo kuɗi ta wannan asusun 0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623._ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Page 9* *ALPHA VILLA*👽 Kamar koda yaushe ba'a taɓa ganin daga inda yake magana saidai a jiyo sautin muryar sa. "Raliya ki kula sosai banaso a samu wata matsala, yanzu idan kuka bar nan za'a kaiki filin jirgi inda daga can zaki wuce Gombe, kiyi amfani da adireshin dana baki ki isa zuwa gidan kamar yadda na tsara miki, ki tafiyar da komai cikin tsari kada ki bari a gano ki. Gobe da safe ne zaki isa zuwa gidan bayan ta fita zuwa gurin aiki. Kin fahimce ni." "Na fahimta Oga zanyj komai yadda kace." Raliya dake rakuɓe a gefen ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ta faɗa kanta a sunkuye. "Banason rawar kai Raliya, samo masaniyar inda lu'u lu'un yake shine kawai aikinki, ban baki damar kiyi yunƙurin sacewa ba wannan aikin ba naki bane. Ina ƙara jaddada mi ki." "Ba za'a samu matsala ba Oga." "Ki tashi kije ki gama kintsawa ƙarfe biyar za ku wuce." "Toh na barka lafiya yallaɓai." ta faɗa tana mai miƙewa daga durƙushen da ta ke sa'an nan ta nufi ƙofar da zata fidda ta daga cikin falon. ........................................ Haka Alhaji Mai Riga yayi ta zagawa yana siye bakin waɗanda ke da masaniya akan case ɗin hatta lauyan bogi da Zarah ta ɗauka saida ya bashi maƙudan kuɗi akan ranar da za'a shiga kotu yayi tawaye yace shi lauya ne mai kare wanda ake zargi. Yau ta kama ranar lahadi inda gobe ranar litinin za'a shiga kotu, dukkan su suna zaune a falo suna hira jefi- jefi wanda akasarin hirar tsakanin Jidda ne da Baaba domin Saleem da Jidda suna gaban na'ura mai kwakwalwa suna gudanar da aiki. Baaba ce ta kalli gefen da su Zarah suke kana tace. "Zara'u ince dai mahaifin naku ya faɗa miki matsayar da ya yanke game da bikin ku." Kallonta Zarah tayi batare da ta tanka ba ta maida hankali kan abinda ta keyi, Jidda ce ta maida hankalinta wurin Baaba tace. "Wace matsaya kuma Baaba tunda ta rigada ta amince.?" "Ai uban nasu yace nan da watanni biyu za'ayi bikin, shima Muhammadun ya kusa dawowa gida domin fara hidimar bikin." inji Baaba "Lallai kice mu ma mu fara shiri kenan Baaba mun kusa zama amare." Jidda ta faɗa cike da zolaya. "Sosai ma kuwa." Faɗin Baaba. "Amma Yaya Sadiq zai dawo bikin koh.?" "Ehh naji Sulaimanu na cewa sun gama karatun zaije da kanshi ya taho dashi, kinsan tunda yaji labarin rasuwar nan shima yake ta noƙe noƙen son cigaba da zama a cikin turawa." "Gaskiya kam ya dawo bikin ƙanwa babu babban Yaya ai ba zaiyi armashi ba." "A toh su daɗi su keji ganin kansu a tsakiyar arna suna shawagi." "Kai Baaba bafa duka bane arna akwai musulmai sosai." "Duk jirgi ɗaya ya kwaso ku ai." "Baaba watarana dai zamu kaiki ƙasar turawan nan kiji yadda akeji idan ana can." "Allah ya tsareni ni Faɗimatu, bana fatan gani ko a mafarki na. Zara'u wani irin aiki ne kuke yi haka da baza ki bari kizo kiyi karin kumallo ba, ina fa lura dake kwana biyun nan sam bakyason cin abinci, shiyasa kike ta ƙarewa kamar kazar mayu." Ta ƙarashe maganar hankalinta na kan Zarah. "Baaba ko kece kika tsinci kanki halin da take ciki baza ki samu nutsuwa ba sai kin kai ga ci." Faɗin Jidda "Yoo wani hali ne take ciki banda na sama kanta damuwa sai an daina cin hanci a ƙasar nan, waɗanda suka fita ma sun gwada sun ƙyale." "A'a fa Baaba case ɗin fyaɗe ne a hannunta kuma gobe za'a shiga kotu, shiyasa take ƙoƙarin tara duk wasu hujjoji gudun kada aka dasu, gashi dama iyayen yarinyar ba masu hali bane." Salati Baaba ta shiga dokawa harda ƴar guntuwar kwalla kafin tace. "Ashe har yanzu ana wannan rashin imanin a ƙasar nan, shikenan dai shi talaka bazai taɓa hutawa ba. Yanzu mene ne ribar yiwa mace fyaɗe, kawai saboda tsantar zalunci da son rugujewa mutum rayuwa. Insha Allahu duk asirin su saiya tuno an hukunta su, shiyasa nake son aikin Zara'u saboda gaskiyar ta. Nayi ma Muhammadu magana ma dole zai barta ta cigaba da aikinta saboda rashin ta zai iya saka al'umma cikin wani hali." "Baaba ƙasar tamu yanzu ai sai dak kawai mu cigaba da addu'ar samun gyara, amma kullum lamura ƙara taɓarɓarewa suke yi." "Kullum cikin addu'a muke kuma bazamu taɓa gajiya wa ba." Nan suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin dake addabar ƙasar ta mu har zuwa lokacin da su Saleem suka gama aikin suka dawo cikin falon aka cigaba da hirar da su. Washe gari da wuri Zarah ta bar gidan bayan tayi sallama da su Jidda da zasu haɗu acan kotun. Kotun ta cika maƙil saboda ba shari'a ɗaya ake gudanarwa ba, baya ga haka kuma abokan hamayyar Alhaji Mai Riga su ma sunzo dan ganin yadda zata kasance. Shari'a biyu aka gudanar kafin azo kan case ɗin Fahima. Kamar kowace shari'a, lauyoyin sun hallara a inda aka tanadar musu domin zama. Nan aka umarci su gabatar da kansu. "Suna na Bar. Labaran Ahmad tare da abokin aiki na Bar. Gideon Wangson mu ne masu kare wanda ake tuhuma." Faɗin ɗaya daga cikin lauyoyi biyu dake zaune a inda aka tanadar musu. "Shin Bar. Labaran bakai bane lauyan masu ƙara." Faɗin Alƙalin. "Bani bane my lord." Inji Labaran. Jinjina kai kawai alƙalin yayi kana yace. "Ina lauyan masu ƙara." Shiru babu amsa. Alhaji Mai Riga ne ya kalli inda Zarah take tare da yin wani shu'umin murmushi mai cike da ma'anoni, ita ma murmushin ta maida masa mai alamar bakasan me kake yi ba. Kafin ya gama mamakin murmushin daya gani a fuskar ta ya jiyo sautin magana. "Suna na Barrister Saleem Sa'ad ni ne lauyan masu ƙara, my lord ayimin haƙurin lattin da nayi hakan ya faru ne a sanadin cunkoson ababen hawa da na samu a hanya." cewar Saleem wanda shigowarsa kenan ya nufi gurin zaman lauyoyin. "Bar. Saleem a kiyaye na gaba." cewar alƙalin. Ba iya Alhaji Mai Riga bane ya shiga mamaki da ruɗun jin abinda ya fito daga bakin Saleem, hatta Labaran saida ya ruɗe domin dai ko kafin a fara gabatar da zaman kotun na yau sun tattauna da Zarah a matsayin shi na wanda zai tsayawa Fahima. Lallai ya tabbatar ta samu labarin zaiyi tawaye shiyasa ta tanadi wani lauyan. Zufa ce ta fara keto masa ta kowani sashi ba jikinshi, ɗagowa yayi jin alƙali ya buƙaci su gabatar da shaidar su ta farko, sai dai me...............✍🏼 *BY* *Jasmine*🌸🌸 07048961623. *ASSALAMU ALAIKUM* *Uwargida da amarya har yanzu fa ƙofa buɗe take, zaki iya samun damar kasancewa da ni HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA a cikin zafafan darussan da nake gabatarwa a ASP ZARAH SPECIAL FANS GROUP, domin samun dabarun zama da miji, ɓoyayyun sirrikan da zakiyi amfani da su wajen mallake mijinki cikin sauƙi, tare da sahihan kayan gyara na musamman sha yanzu magani yanzu. Kada ki bari ƴar uwarki ta labarta miki.* *Cikin ikon Allah a ƙanƙanin lokaci group ɗin mu na farko ya cika kuma yanzu haka mun buɗe wani sabon group ɗin ga masu buƙatar su shiga a baje wannan kolin dasu. Kada kumanta dai zaku iya samun damar shiga wannan group ta hanyar tuntuɓar wannan number 07048961623. Ina jiran zuwanku, ni ce dai takun da bani da tamka HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA*. *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Paid book_. _Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Za'a turo kuɗi ta wannan asusun 0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623. *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Zarah ya gani ta kafe shi da idanunta masu rikitarwa, nan take ya ruɗe har saida yaji Gideon na gabatar da tambayoyi ga Kabeer kafin ya maida hankali. Mintuna talatin ana fafatawa tsakanin ɓangare biyun inda Saleem ke gabatar da zafafan shaidun daya tada hankalin Alhaji Mai Riga da muƙarrabansa, domin hatta inda yake cewa Zarah tabbas ɗan shi ya aikata laifin da ake zargin shi saida aka gabatar a gaban kotu. Nan fa kotu ta rikice kowa na faɗin albarkacin bakinsa musamman ƴan adawan Alhaji Mai Riga. Hutun rabin lokaci aka alkali ya bayar, gaba ɗaya jama'a aka fita waje. Duk yadda Mai Riga yaso ganin alkalin a wannan lokacin abu ya gagara, hankalin shi ne yaji ya tashi amma tunawa dayayi da irin maƙudan kuɗin da ya bawa alkalin sai ya ɗan samj nutsuwa tare da tabbatarwa kanshi samun nasara. A daidai wannan lokacin kuwa Baaba tana zaune a falo tana kallon wa'azi a sunna TV, ɗaya daga cikin masu tsaron ne ya shigo tare da shaida mata cewa tana da baƙuwa, batare da dogon tunani ba tace ya shigo da ita. Jim kaɗan ya dawo tare da Raliya wacce ta ɓadda kama sosai tamkar ba ita ba, wasu tsofaffin kayane a jikinta wanda a kowani lokaci zasu iya yagewa sai wata ƙaramar Ghana-Must-Go itama ta tsofa sosai. Da sallama ta ƙarasa cikin falon sannan ta zauna ƙasa nesa da inda Baaba take. "Ki hau saman kujerar mana baiwar Allah." Inji Baaba. "A'a nan ma yayi Hajiya, ina wuni." Faɗin Raliya. "Lafiya lau sannu da zuwa, sai dai ban shaida fuskar taki ba kodai gurin Zara'u kika zo ne." "A'a Hajiya dama nazo neman aiki ne." "Wane irin aiki kuma daga ina kike.?" "Ni marainiya ce a garin Tilden Fulani nake, iyayena sun mutu ne sanadiyyar gobara da ta cinye gidan mu tun daga lokacin kuma na rasa masu taimakamin. Toh akwai wata Mata a can gurin namu da take shigowa birni tana aiki shine ta bani shawarar na shigo na zaga gidan masu hali na nemi aikin yi saboda nasamu abinda zan dinga rufawa kaina asiri dashi." "Duniya ta lalace mutane basason taimako, ai shi maraya idan ka taimaka mi shi tamkar ka zuba adashe ne da zaka kwashe ranar lahira. Kada ki damu insha Allahu za'a baki aiki koda na goge-goge ne." "Nagode Hajiya Allah ya saka da alkhairi." "Amin babu komai ai hakkin maraya ne mukeson saukewa."Inji Baaba. Sun ɗan jima suna taɓa hira kafin Baaba ta miƙe ta shige ɗaki bayan tabar Raliya a falo tana kallo, da sanɗa tabi bayan Baaba dan ganin mai zatayi a ɗakin, ganin shigewarta banɗaki ne yasa tayi saurin komawa falo tare da buɗe jakarta ta ciro wani abu kamar bead na kitson yara ta nufi saman bene. Bata sha wuyar gane ɗakin Zarah ba saboda taswirar gidan da ta haddace a kanta, ɗakin a buɗe yake dan haka tana shiga ta nufi gaban durowar kayan Zarah, wannan abun ta ajiye acan saman durowar ta yadda babu wani mahaluƙin dazai iya cewa akwai wani abu a gurin idan ba anfaɗa ba. Komawa falon tayi cikin sanɗa tamkar ɓeran dayayi sata yana tsoron a kamashi. A can kotu kuwa bayan mintuna talatin sun cika aka koma aka cigaba da fafatawa tsakanin ɓangarorin guda biyu, domin dai da alama shari'ar ta kwana ɗaya ce. Shiru ya ratsa cikin kotun bayan shuɗewar wasu mintuna, duk wannan abu dake faruwa Alhaji Mai Riga lokaci zuwa lokaci yake ɗagowa ya kalli ɓangaren da Zarah take yana yi mata murmushin ƙeta domin dai zuwa yanzu ya gama tabbatarwa kanshi cewa shi ɗin mai nasara ne sannan baza a yankewa ɗansa hukunci ba. Ita kuwa Zarah zancen zuci take a duk lokacin daya kalletan sai tace. "Shi dai mutum mara basira ko ina yake ana ganewa." Alƙali ne ya fara magana kamar haka. "Bayan sauraron shaidu da ɓangare biyu suka gabatar tare da hujjoji wanda suka gamsar da kotu da kuma kundin tsarin shari'a na ƙasa, kotu ta yankewa Kabeer hukuncin zama a gidan kaso na shekaru goma tare da aiki mai tsanani sa'an nan zai biya tarar miliyan biyar domin nemawa Fahima lafiya, Alhaji Nuhu Mai Riga kotu ta kama shi da laifin yunƙurin baiwa ɗan sanda cin hanci, dan haka kotu ta yanke mishi hukuncin zama gidan horo na wata biyar ko kuma tarar miliyan ɗaya." yana gama faɗin haka ya buga gudumarsa wanda ke nuna alamar ya gama aikin shi na wannan rana. Kotu fa ta rikice inda Alhaji Mai Riga keta zage-zage tamkar mai taɓin hankali ana riƙeshi, nan fa ƴan jam'iyun adawa da ƴan jaridu suka samu inda sukayi ta ɗaukan hotonan shi, wasu harda yi mashi video. Haka yana ji yana gani aka wuce da ɗanshi ɗaya tilo tamkar rai zuwa gidan kaso, take kuma ya zube a ƙasa tare da sakin kuka mai tsanani. "Jidda mu wuce gida kawai ki rabu da Saleem ɗinki da ƴan Jaridun nan." cewar Zarah bayan ta janyo hannu Jidda zuwa wani keɓeɓɓen waje a bayan kotun. "Mene ne haka wai Zarah ki barni mana a haskani a jarida tare da hubby na." "Mtssww mu wuce Jidda banason dogon zance, jikina na bani wani yanayi da ban gamsu dashi ba." ta faɗa tana tura Jiddan cikin motar ta, wuta ta baiwa motar bayan ta shiga itama, nan suka bar farfajiyar kotun zuwa gida...... ✍🏼 *By* *Jasmine*🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Second to the last free pages._ _Paid book._ _Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Ku tuntuɓeni a 07048961623 domin biya._ *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *M*. *W*. *A*. Gudu takeyi tamkar zata tashi sama, yayinda Jidda ke mata ƙorafin karfa tayi sanadin tafiyarta lahira bata shirya. Ko kulata batayi ba har suka iso bakin gate ɗin gidan, horn tayi aka buɗe mata ta shigar da motar ciki, sai a lokacin ta samu nutsuwa amma duk da haka tanajin wani irin yanayi a tattare da ita. ''Haka kawai kin rabo ni da mijina, toh wallahi garin ma zamu bar miki tunda mun gama yin abinda ya tsaida mu." Inji Jidda. "Ba iya garin nake so ku bari ba, dan Allah ku bar ƙasar ma baki ɗaya." Zarah ta faɗa cike da tsokana lokacin da take fita a cikin motar. Da gudu Jidda ta bita suka nufi hanyar babban falo tamkar wasu ƙananan yara. "Allah ya shirye ku, wannan ai sai kusa nima na ruga da gudu, manya daku kuna wasan guje-guje, ke Hauwa idan ita bata rigada ta gama girma ba ai ke kam kin girma saiki daina biye mata." Faɗin Baaba wacce ke zaune a falo lokacin da suka shigo da gudu. "Kai Baaba kin manta wai nafi Jidda shekaru ne.?" Inji Zarah. "Yo idan kin fita shekaru ai yanzu kam ta fiki tunda a ɗakin mijinta take." "Saboda kawai tayi auren.?" "Ehh mana ai ko ƴar shekara 14 tayi aure yanzu dole za'a kirata da yayarki." "Faɗa mata dai Baaba ko zata daina raina ni." Jidda kenan ta faɗi. "Nima dai auren nan na kusa yinshi na huta." Ta faɗa tana zama a kujerar da Baaba take kai. "Ahh lallai da bamu yi shawarar aurar dake ba gaba bamu san abinda zaki dinga furtawa a gaban mu ba." Faɗin Baaba tana tafa hannayenta. Bata kulata ba saima plate ɗin dake gaban Baaban data janyo wanda ke ɗauke da lafiyayyen dambun shinkafa da yaji haɗi. "Baaba yau kin tuna da gargajiya ne haka, shiyasa kika kasa jira mu dawo muyi girkin." Zarah ta faɗa tana ɗebo dambun a cokali da nufin kaiwa baki. "Allah sarki bama nina dafa ba, baƙuwa mukayi shine nace ta shiga kicin ta girka mana gudun kada ku dawo a gajiye, kin ganshi nan yanzu aka gama shine na ɗebo naci." Harta buɗe baki da nufin cin dambun da ta ɗebo, amma jin abinda Baaba ta faɗa yasata dawo da cokalin tare da maidawa kan plate ɗin. "Wacce baƙuwa kuma.?" Ta tambaya fuska a yamutse. "Ƴar aiki na samu mana, tunda Iya Delu dai bamusan ranar dawowarta ba." "Ƴar aiki kuma.?" "Ehh ko banyi daidai bane uwata.?" "A'a kawai nayi mamakin inda kika samo ƴar aikin ne bayan ba fita kikeyi ba." "Nan tazo neman aikin, toh ganin muna buƙata yasa na ɗauketa, kuma naga tana da hankali da nutsuwa shiyasa bayan haka kuma marainiya ce." "Ana ɗaukan aiki batare da bincike bane Baaba.?" Harara Baaba ta wurga mata kana tace. "Nasan ki ai da shigen bin ƙwaƙƙwafi shiyasa ma na nemi wacce ta kawo ta birnin muka zanta, bayan haka kuma ga lambar ta nan na karɓa idan kinason jin ƙarin bayani, mtsww." "Me yayi zafi Baaba tunda ke zata dinga taimakawa, nikam ai bani da matsala tunda ba gidan nake wuni ba." "Yo ai nayi tunanin koh kulle ni zakayi tunda nayi abu batare da izinin ki ba." Ita dai Jidda bata saka baki ba, tana zaune a kujera ta kurɓar fresh milk ɗin da ta ɗauko, saboda surutunta ne ma yasa bata saka baki ba domin dai Baaba batasan a fara magana a bari ta daɗi ba, shiyasa ta barta da Zarah sanin da tayi cewa Zarah bata da magana sosai, tasan zancen bazai yi nisa ba za'a ƙarƙareshi. "Kin ci dambun ne Baaba.?" Zarah ta tambaya fuska babu walwala. "Na ɗebo kenan zanci ai kuka shigomin a birkice." Batace komai ba ta ɗau plate ɗin dambun ta nufi hanyar kicin. "Ina zaki kaimin abincin kuma.?'' "Yau ba dambu na tsara zamu ci a gidan nan ba, dan haka babu mai ci. Habibaty taso mu dafa wani abu mai sauƙi kafin SaJid ɗin naki da baya jurar yunwa ya dawo." ta faɗa tana mai shigewa corridor ɗin dazai sada ta da kitchen. Jidda ma tashi tayi da sauri ta bita tun kafin Baaba tayi magana. "Ki kiyayeni fa Zara'u wallahi zan saɓa miki, ki kawomim abincin nan tun kafin na iso gurin na sameki." Faɗin Baaba dake ƙoƙarin tashi ta nufi kitchen ɗin. "Kulle ƙofar nan SaJid karta zo ta dame mu." "Toh ke wai meye dalilinki na hanata cin dambun ne, nima wallahi ya bani sha'awa so nake naci." "Kawai naji ban yarda da girkin bane, dan haka babu mai ci." "Kamar ya baki yarda da girkin ba? tsabtar shi ko me.?" "A'a bansan hanyoyin da aka bi aka sarrafa shi ba ne shiyasa, da ace ina gida ma babu wata ƴar aiki da zamu ɗauka saidai mu jira har zuwa lokacin da Iya delu zata dawo." "Ƙyanƙyami ne kawai irin naki amma kina ganin dambun nan ai kinsan an tsabtace shi, nikam banga ƴar aiki da ake magana akanta ba ma." "Ƙila tana ɗakin da Iya Delu ta zauna. Mu haɗa Jallof ɗin cous-cous kawai nima yunwar nakeji sosai." Cikin ƙanƙanin lokaci suka haɗa lafiyayyen cous-cous da yaji kayan haɗi da nama, sai lemun citta da fruit salat da suka yi. A faranti suka jere komai, inda Jidda ta ɗauka domin zuwa ta jere a dinning, ita kuwa Zarah fruit salad ta ɗeba a plate ta nufi cikin falon. Baaba na nan zaune inda ta barta, saɓanin ɗazu da take ita kaɗai yanzu tare suke da wata da bata ga fuskarta ba, remote ta ɗauka tare da canja tasha daga Sunnah TV zuwa TVC News kana ta zauna a kujerar dake fuskantar Raliya dake zaune a ƙasa rakuɓe a jikin kujera. "Ya zaki canja mana tasha muna kallon wa'azi zuwa tashar arna." Faɗin Baaba a hassale. "Kiyu haƙuri Baaba ta ki daina wannan fushin da ni kinji, labarai kawai zan kalla na tashi." Sai a wannan lokacin Raliya da tayi nisa a cikin tunani ta lura da shigowar Zarah, kallonta tayi ta ƙasan ido, ai nan dake ta ɗauke kanta daga kanta saboda wani irin kwarjinin Zarah da ta hango. Cikin dakiya da dauriya tace. "Ina wuni ranki ya daɗe." Kafeta da ido Zarah tayi tana son gano wani ɓoyayyen abu a tattare da ita. Ita kuwa Raliya kai ta sunkuyar cikin ruɗu tare da tunanin ko Zarah ta gane ta ne. "Banason haka fa Zara'u kin kafe baiwar Allah da ido tamkar mai laifi a bayan kanta." "Marabar kaɗan ne." cewar Zarah a cikin ranta duk da batada wani tabbaci akan yanayin rashin gaskiya da zuciyarta ke gayamata akan Raliyan. "Lafiya." ta faɗa a taƙaice tana mai cigaba da cin fruit salad ɗin. Sunanan a zaune a falon har lokacin da Saleem ya dawo, Baaba ce take tambayar Saleem ɗin yadda shari'ar ta kasance, baki ya buɗe da nufin labarta mana amma saidai kallon da Zarah ta mishi ne yasa shi cewa. "Baaba munyi nasara." yafaɗa a takaice domin ya gane ma'anar kallon Zarah a gareshi, nufinta karya faɗi yadda shari'ar ta kasance. "Hubby kai muke jira tun ɗazu, mu ƙarasa dinning yunwa mukeji." Su uku suka miƙe suka nufi dinning ɗin, Jidda ce tayi serving ɗinsu, nan suka fara cin abincin. Kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinta batare da ta amsa tambayar da Jidda ke mata ba...... *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Paid book._ _Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP kuma N500. A tuntuɓeni a 07048961623 domin biya._ *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️ *M*. *W*. *A* ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *Free Page* Haka nan taji tamkar ana umartarta ta zuwa ɗakin, da sallama a bakinta ta shiga duk da tasan babu kowa a cikin ɗakin, maida ƙofar tayi ta rufe kana ta jingina jikinta a jikin ƙofar tana mai ƙarewa yanayin ɗakin, yana nan kamar yadda ta barshi. Gaban durowar kayanta ta isa tare da tsayawa tana kallon gurin, tabbas wani ɓangare na umartarta da bincikar gurin saidai ɗaya ɓangare na hanata ƙoƙarin haka. Ƙarar wayar ta ne ya fargar da ita, kallon fuskar wayar tayi taga Ammi ce mai kiran, saida ta zauna a bakin gadon tukun kafin ta ɗaga wayar. "Ammi na." ta faɗa a hankali.. "Na'am daughter ya kuke." "Lafiya lau Ammi ya jikin Rahma." "Alhamdulullahi jiki ya fara samuwa, yanzu tana iya yin magana wasu lokutan amma ba sosai ba." "Allah ya ƙara lafiya." "Kin fara gyaran jiki kuwa Zarah." cewar Ammi Cikin son gane mai take nufi Zarah tace. "Wani irin gyara jiki kuma Ammi.?" "Zan saɓa miki fa, kina nufin baki fara amfani da kayan da Momin ku ta turo miki ba." cewar Ammin. Dafe kai Zarah tayi, sam ta manta batun kayan da Momi ta aiko mata dasu. Jin shiru ne yasa Ammi cewa. "Kina nufin haka zakije gidan mijin kamar almajira." "Ni fa Ammi.." "Ke fa me, toh wallahi ki fara amfani da kayan nan tun wuri, nima ina nan tafe zuwa wani watan domin mu fara shirye shirye da wuri." "Toh Ammi, Allah ya kawo lafiya." "Amin ki gaidamin da Baaba, su Jidda sun wuce Bauchi ne.?" "A'a sai zuwa jibi tukun, akwai wani case da muka gudanar da Saleem ne shiyasa basu tafi ba." "Ya batun binciken nan Zarah." Ammi ta tambaya cike da rauni. "Ammi batun bincike ai babu shi tunda an riga da ansan mai laifin." "Allah ya saka mana wannan zaluncin da ya aikata mana." cewar Ammi cikin rawar murya. Sallama Zarah tayi mata gudun kada itama ta fara hawayen kamar yadda take da tabbacin kuka Ammi keson farawa. Miƙewa tayi ta shiga toilet domin yin wanka, jim kaɗan ta fito ɗaure da ƙaramin towel. A gaban madubi ta tsaya, goge jikinta tayi kana ta murza lotion a jikinta sama-sama, hoda ta shafa a fuskarta kaɗan tare da goga lipbalm. Cikin sauri ta saka doguwar rigar atamfa tare da yana ƙaramin mayafi akanta, wayarta ta ɗauka tare da nufar falon. Baaba da Jidda ne ke zaune a kujera, yayinda Raliya take can gefe a rakuɓe. Zama tayi a kusa da kujerar da Jidda take kana tace. "Barka da yamma Baab." Kauda kai tayi daga kallo ta kamar ba da ita take magana ba. Murmushi mai sauti Zarah tayi sannan tace. "Har yanzu baki gama fushin bane Baaba ta." Jidda ce ta fashe da dariya ganin yadda Baaba take yatsina tamkar taga abin ƙazanta. "Ina ganin mu bar yin alkubus din nan sai gobe ko.? Ta faɗa tana ƙoƙarin maida dariyar dake taso mata, tana sane tayi maganar saboda tasan Baaba na matuƙar son alkubus. "Haba ƴaƴan albarka, kuyi mana shi da dare, na daɗe banci ba nima." cewar Baaba fuska a sake. Dariya sukayi gabaɗaya kana Zarah tace. "Sa.Jid ki kwaɓa mana a saka shi a rana kafin anjima." "Mene ne ma'anar wannan sojut ɗin da kike kiranta dashi." Inji Baaba. Dariya Zarah da Jidda keyi sosai har saida Jidda tabar kan kujerar ta dawo ƙasa, tsagaitawa da dariyar tayi tace. "Ke dai Baaba kowani suna saikin ɓata shi, Sa.Jid fa aka ce ba Sojut ba." "Mene ne ma'anar hakan.?" "Yauwa kinga Sa. farkon sunan Saleem ne sai Jid kuma farkon Jidda, shine aka haɗa kalmomin biyu ake faɗin Sa.Jid." Taɓe baki Baaba tayi tace. "Boko dai baiyi muku rana ba." Miƙewa sukayi su biyun suka nufi hanyar kitchen batare da sun kuma magana ba. ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ Kiran wayar dake shigowa wayarsa ne akai akai ne yayi sanadin tashin shi daga daddaɗan baccin daya ɗauke shi tun bayan da yayi sallar asubahi, hannu ya miƙa tare da jawo wayar dake akan bedsite drawer, tsaki yayi mai sauti bayan yaga sunan wanda yake kiran nashi tare da kara wayar a kunne. "Dama nasan babu wanda zai dinga yimin irin wannan kiran idan ba kai ba, sarkin naci mai zan maka kake damuna." Daga ɗaya ɓangaren Abdallah ne yayi dariya kana yace. "Haba mana M. J kiran arziki na maka fa bana tsiya ba." "Naji faɗi dalilin kiran." "Yaushe zaka dawo Naija ne mu fara shirye shirye, kasan bamu da wani isasshen lokaci fa." "Shirye shiryen me kenan." "Banasan wulaƙanci fa M. J, kana nufin auren naka guda ba zamu gwangwaje ba.?" "Dalilin kiran naka kenan.?" "Ehh shi ne dalilin kiran najj yaushe zaka shigo." "Toh sai anjima, bana da lokacin tattauna magana mara amfani yanzu." "Zancen auren naka ne babu amfani." "Sai anjima please." ya faɗa yana mai katse kiran. Tsaki ya kuma yi a karo na ba adadi cike da takaicin wannan auren da za'a yi mishi, duk wasu tsari nashi an rusa mai, babu yadda ya iya dole yayiwa mahaifinsa biyayya amma tabbas yana da shiri sosai akan matar da aka ce za'a haɗa shi ta ita. ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ Ƙishin ruwa ne ya damu Zarah wacce ke kwance akan tamfatsetsen gadonta, agogo ta kalla ƙarfe 2:15nd, a hankali ta saukk daga kan gadon tare da zura silifas a ƙafarta ta nufi ƙofar fita daga ɗakin zuwa kitchen domin ɗauko ruwan da yau ta manta bata shigo dashi ba yau, saboda yawan shan ruwan da takeyi duk sanda zata farka da dare. Gora biyu ta ɗauka bayan ta isa kitchen ɗin tare da apple ɗaya kana ta rufe ƙofar kitchen. Kamar ance ta waiwaya, haske ta hango a babban falon da Abbansu ke saukar baƙi lokacin da yake raye, cike da mamaki ta nufi hanyar falon domin dai ta tabba ta kashe wutan falon kafin su kwanta bacci. Abinda ta gani ne ya matuƙar bata mamaki tare da tabbatar mata da duk wani zarginta, Raliya ce....... ✍🏼 _Ku yimin uzuri please, ina shirin rubuta jarabawa ne shiyasa bana samun damar yin long pages. Ur prayers also needed._ By Jasmine *ASP ZARAH* _PAID BOOK_. _Domin samun damar cigaba da karantawa biya N300 kacal ko kuma N500 na VIP. Tuntuɓi 07048961623 domin biya a saka ki a group._ *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* *M*. *W*. *A* *Free page* ____Raliya ta gani riƙe da wani abu da take da tabbacin camera ne tana ƙoƙarin mannawa a gefen inda wani babban family photo ɗin su yake, take ta samu duk wasu amsoshin da take buƙata akanta domin tun kallon farko da tayi mata ta hango alamun rashin gaskiya a tattare da ita. Rakuɓewa tayi a jikin window bayan ta hangota ta nufi ƙofar fita daga cikin falon, tana tsaye harta wuce ta shiga ɗakin da aka bata a matsayinta na ƴar aiki, shiga tayi cikin falon batare da ta kunna wutan da ta kashe ba ta nufi inda taga ta ajiye abun, kamar yadda tayi tsammani camera ce da zata iya ɗaukan duk wani shige da fice a falon sannan idan ba mutum ya sani ba babu wanda zaiyi tunanin akwai camera a gun. Ɗauka tayi tare da nufar ɗakin Raliyan, ta wani ɗan rami dake jikin ƙofar ta leƙa ga mamakinta sai ganinta tayi zaune akan katifar ɗakin da ƙaramar laptop a gaban wanda tana iya hangar abinda ke wakana a cikin laptop ɗin, ido ta waro gani hoton ɗakin ta ya bayyana a ciki tare da duk wani abu da ta gabatar tun daga dawowarta har zuwa yanzu. Kunnenta ta kara a jikin ƙofar ganin Raliya ta ɗauki wayarta ta kara a kunne. Batasan me aka faɗa ba daga ɗaya bangaren sai amsar da ta bayar. "A'a ranka ya daɗe, ina tunanin sun chanja tsarin gidan ne domin gabaɗaya an canja tiles ɗin da muka sani an saka wasu shiyasa bangane wanda zai kaini underground din ba." "Alpha." Zarah ta furta a hankali. Tabbas yanzu zarginta ya tabbata Alpha ne wanda ya turo Raliya tayi basaja a matsayin ƴar aiki, bayan sun tabbatar da bata gida a lokacin domin tabbas da tana gida baza a ɗauki Raliya aiki ba. Rufe na'urar taga tayi tare da kwanciya akan katifar, wani murmushi ne ya suɓuce mata bayan ta gama haɗa wasu abubuwa a cikin kwaƙwalwarta, hanyar ɗakinta ta nufa cikin sassarfa. Tsayawa tayi a tsakiyar dakin tana tunanin ta ina zata fara bincikar cameera din, wardrobe, haka taji tamkar anyi mata raɗa a kunne da sauri ta nufi wajen ta tsaya tare da karema wajen kallo sosai har lokacin da idonta ya hasko mata karamar camera acan saman wardrobe din, murmushi tayi tare da jawo stool ta hau sannan ta ciro camera ɗin. Jujjuyashi tayi a hannunta kafin ta ciro wani ƙaramin box ta saka a ciki, ruwan da ta ɗauko ta zauna tasha kana ta koma ta kwanta. Washegari bayan tayi sallar asubahi da kanta ta shiga kicin ta haɗa musu abin karyawa saboda tafiyar safe su Jidda zasuyi zuwa Bauchi, ƙarfe bakwai na safiya ta gama shirya komai a dinning kana ta nufi ɗakinta domin yin wanka kasancewar itama zata fita aiki. Cikin shirinta ta fito ta samesu a falo harda Baaba suna zaune, gaishe da Baaba tayi kana suka gaisa da Sa.Jid. "Ina kwana Anti." Raliya ta faɗa lokacin da take goge TV stand, sai a lokacin Zarah ta lura da ita, cikin wani ƙayataccen murmushi ta amsa wanda ya saka Raliyan shiga kogin tunani na dalilin yin murmushin nata. Dinning suka nufa duka harda Baaba da bata cika cin abincin acan ba, Jidda ce tayi serving ɗinsu duka sannan suka fara cin abincin. "Yauwa Zara'u, munyi waya da mahaifinku ɗazu yake gayamin Muhammadu zai iso anjima sannan zuwa jibi zai ƙaraso nan ku zanta akan shirye shiryen da zaku gabatar." cewar Baaba. "Uhmm." shine abinda kawai ta furta bayan ta saka tissue ta goge bakinta. "Kinyiwa Ubanki badani kikeyi ba, mutum sai shegen miskilanci na tsiya." ta kuma faɗa. Idonta ne ya kawo ruwa ta kalli Baaban da nufin yin magana sai ta rigata. "Sulaimanu nake nufi." ta kuma faɗa tana harararta. Dariya Jidda tayi kana tace. "Gaskiya Baaba zanyi missing ɗin dramar ku da Sahibaty." "Mene ne kuma meizu.?" Baaba ta faɗa cikin gyatsina. Wannan karon har Zarah da Saleem saida suka dara sosai. "Rabo da su Baaba kwanan nan zan kaiki London a koya miki turanci kema." cewar Saleem. "A'a ɗan nan meye haɗina da turanci kuma, ku dai da suka asirce ku sai kuyi ta fama." "Kunga idan kuka biyewa Baaba to tabbas yau zaku rasa flight, ku hanzarta na sauke ku a airport ɗin nima aiyuka gareni sosai a office." cewar Zarah tana miƙewa. Suma miƙewa sukayi inda Jidda ta shiga ta fito musu da trolleys ɗinsu. "Mu zamu wuce Baaba sai munzo biki." Inji Saleem. "Ɗan albarka mungode Allah yabar zumunci, ai bikin ma a can Gombe za'ayi muma duk zamu tattara mu biyo bayanku acan za'ayi komai." "Toh Allah ya kawo ku lafiya." "Ameen yaron kirki, a ƙara hakuri dai da juna." "Idan ma da ni kikeyi ba kulaki zanyi ba kinga tafiyata." cewar Jidda. Har gurin mota ta rakasu tana musu addu'ar sauka lafiya har saida taga sun fice a gidan kana ta juya ta koma falo. Basu daɗe da isa airport ɗin ba jirginsu ya tashi bayan sunyi sallama cike da kewar juna da zasuyi, zuciyarta gabaɗaya babu daɗi ta nufi office ɗinta. Bata ko yi minti biyu da zama a kujerarta ba Bala ya shigo bayan ya nemi izini, ganin yanayin da take ciki yasa ya ajiye takardun daya shigo dasu ya fice, takardun da ya ajiye ta jawo tare da fara nazartarsu, bayanai ne kan wani da suke zargin yana safarar miyagun kwayoyi wanda zai shigo garin Bauchi nan da kwana biyu, inda ta wannan hanyar suke fatan tabbar da zarginsu tare da kamashi muddin zarginsu ya tabbata. Tsaki taja mai sauti bayan tayj tunanin hanyar da ita kaɗai ce mafita a garesu batare da sunsha wahala ba, da kanta take so tayi wannan aikin gudun kada a samu matsala musamman yadda yawancin jami'ai yanzu zuciyarsu ta gurɓace da son kuɗi, saidai kuma batason aikin dazai dinga kaita hotel ko kaɗan amma babu yadda ta iya dole wannan karon tayi wannan aikin da kanta. Gabaɗaya wuninta na yau a office tayi shi ne cikin tsara yadda aikin zai kasance cikin sauƙi batare da sunsha wahala ba, sai ƙarfe shida tabar office ɗin bayan ta zaɓi team ɗin da zasuyi aikin tare. Bata tsaya doguwar hira da Baaba ba yau saboda a gajiye take, hakan yasa bayan sunci abincin dare ta wuce ɗakinta ta kwanta. ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ "Momi zamu wuce." cewar Abdallah da suka fito a sashin M.J cikin shirinsu na tafiya garin Bauchi ganin amarya Zarah, sunyi kyau cikin dakakkiyar farar shadda da suka saka iri ɗaya sai zuba ƙamshi sukeyi musamman M.J da ya fito a asalin ango mai shirin amarcewa da sabuwar amarya. "Yauwa ƴaƴan kirki ga wannan ku kaiwa ƴar tawa, ku gaishemin da Mamana kuma." cewar Momi dake zaune tana miƙawa Abdallah wata ƙaramar jaka. "Me amaryar mu ta samu ne haka Momi." ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe jakar. Hannunshi ta buge kana tace. "Ban yarda a buɗe ba, ku bata shi yadda na baku." "Toh Momi mun wuce." "Allah ya kiyaye hanya ku gaishesu." M.J ke jan motar yayinda Abdallah ke gefenshi yana zuba surutu, tun yana kulashi har ya gaji ya daina wanda hakan yasa shima Abdallah ya maida hankalinashi kan wayarsa saboda sanin halin miskilanci irin na M. J. ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ Cikin shirinta na ƴan sanda ta sauko ƙasa hannunta riƙe da agogo tana ƙoƙarin ɗaurawa, yayinda take ɗauke da wata jakar baya madaidaiciya mai matuƙar kyau da sheƙi. "Zan wuce office Baaba." ta faɗa bayan ta zauna a hannun kujera tana ƙarasa ɗaura agogon. "Yanzu Zara'u mijin da zaki aura zaizo ganinki amma bazaki haƙura da zuwa aikin nan ba yau." "Aiki mai mahimmanci zan gabatar Baaba sannan bazai wani ɗaukeni dogon lokaci ba idan ya iso ki kirani sai na dawo, sannan Raliya ta shirya musu abinda ya dace." "Shikenan Allah ya bada sa'a ya kuma kare." "Ameen Baabata nagode sosai." ta faɗa tana ficewa a falon. Kai tsaye office ta nufa, bata wani ɓata lokaci sosai ba suka wuce hotel ɗin da zasuyi aikin acan bayan ta canja kaya zuwa doguwar rigar abaya sannan tayi rolling da gyalen rigar. Mintuna kaɗan suka isa, can nesa da gate ɗin sukayi parking, mintuna kaɗan sai ga wata tsadaddiyar mota ta shiga hotel ɗin. "Jeka Bala ka tabbatar kayi kyadda ya dace." Zarah ta faɗa. "Toh ranki ya daɗe." Ya faɗa yana mai fita a motar, tabbas idan bakasan shi ba baza kayi tunanin jami'in tsaro bane saboda kalar shigar da yayi ta ƴan iska, kai tsaye farfajiyar hotel ɗin ya shiga tare da nufar inda motar tayi parking. Glass ɗin motar ya ƙwanƙwansa, sauke gilashin baya akayi inda wani hamshaƙin mutum ke zaune. "Lafiya kuwa ɗan saurayi." cewar Alhajin. Waige-waige Bala tayi kamar mara gaskiya kafin ya fara magana irinta ƴan shaye-shaye yace "Alhaji naga kamar kazo hutawa ne shiyasa nace bari nayi maka tayin zafafa ko zasu tayaka hutawa." "Shigo daga ciki." ya faɗa bayan ya buɗewa Bala ƙofar. "Banason idanun mutane shiyasa nace ka shigo daga ciki, yimin bayani sosai." "Ya Alhaj akwaisu dayawa fa amma yanzu ɗayace ta rage, sunanta end of discussion saboda zazzafa ce sosai." cewar Bala tamkar me maye. "Kada kasani asarar kuɗi fa ka kawomin ƙazama kamar ka." ya faɗa yana gyatsina saboda kayan jikin Bala sun matuƙar yagalgale. "Ina fada maka ya Alhaj, zafafa nake dasu bari na nuna maka hotonta." ya ciro wayarsa a aljihun wandon jikinshi, hoton da Zarah ta ɗauka ɗazu ya nuna mishi wanda take sanye da doguwar riga. Laɓɓansa ya lasa bayan yaga hoton kasancewar sa manemin mata yasa babu ɓata lokaci ya fito da rafar kuɗi na dubu-dubu ya ajiye guda biyu a cinyar Bala tare da faɗin. "Kirata yanzu tazo." Sowa Bala yayi tare da danna kiran wayar Zarah yana faɗin. "End of discussion harka ta tashi maza kizo yau kakarmu ta yanke saka." Katse wayar yayi yace. "Yanzu zaka ganta yanzu ya Alhaj." Buɗe kofar motar akayi inda direban Alhajin ya shigo tare da faɗin. "Na gama komai yallaɓai ga key ɗin ɗakin nan room 234 a sama." "Ohk" kawai yace tare da karɓan key ɗin. A daidai wannan lokacin kuma M. J da Abdallah suka shigo garin Bauchi sannan kai tsaye suka nufi hotel ɗin domin kama masauki, Abdallah ne ya fita a motar domin zuwa kama musu ɗaki, bai ɗauki lokaci ba ya dawo imda aka basu room 233 buɗe ƙofar yayi tare da faɗin. "Mr. President sai ka fito mu shiga." Fitowa yayi suka nufi cikin hotel ɗin, a wannan lokacin ma Zarah da Alhaji Mati sun fito a motarsa suma da nufin zuwa ɗakin da aka kama mishi. Abdallah da M. J ne a gaba yayinda suku ma suke baya a lokacin da suke haura matattakalar dazata sada su da inda jerin ɗakunan suke. Tamkar ance ya waiga.......... _Insha Allah daga next page bazan ƙara free page ba, nagode sosai da ƙaunar da kuka nunawa littafina. ASP ZARAH VIP GROUP, ASP ZARAH FANS 1 DA ASP ZARAH FANS TWO INAYINKU SOSAI DA SOSAI NAGODE MATUƘA._ _BY_ _JASMINE._🌸🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ _Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba biya N300 kacal ko kuma N500 na VIP, tuntuɓi 07048961623._ *🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️ *M*. *W*. *A* __Kallo ɗaya yayimata ya gane ta saboda yawan ganinta da yake yi a cikin mafarkinshi tun bayan haɗuwarsu da ita a Abuja, take yaji wutar tsanarta ta ƙara ruruwa a zuciyarshi, tsaki yaja mara sauti bayan ganin irin kallon da Alhaji Mati yake yiwa Zarah na tsantsar maitar buƙata, tamkar zuciyarsa zata fito waje haka yake ji lokacin dayaga sun shige ɗakin bayan an buɗe mata ƙofar. Kwafa yayi shima yabi bayan Abdallah suka shige nasu ɗakin. "Duk sanda nayi magana sai ka dinga ƙaryatani bayan sai na tabbar nake faɗa, gashi yau dai ka tabbatarwa idanunka." cewar M.J Kallonshi Abdallah yayi cikin rashin fahimta yace. "Kai da waye kake magana haka." "Ina tare da wani bayan kai ne anan.?" cike da jin haushin tambayar ya amsamai. "Sorry ranka ya daɗe bangane akan me kake magana ba." "Kwanakin baya ba tare da kai mukayi maganar wata ƴar sanda a Abuja." "Oh wannan yarinyar da har yau nake fatan sake ganinta , gaskiya duk da bansanta sosai ba ta burgeni matuƙa." "Mtswww" M.J yaja tsaki tare da kuma faɗin "Sai kayi kuma ai, itace wacce muka hauro tare suka shiga next room ɗin nan." Miƙewa Abdallah yayi daga kwancen da yake tare da cewa. "M. J banason wasa fa wai da gaske kake police ɗin nan ce muka hauro tare dasu." "Dama ina wasa da irin wannan maganar ne." "Allah ya kyauta" shine kawai abinda Abdallah ya faɗa tare da miƙewa ya shige toilet, bai jima ba ya fito bayan yayi wanka. Shima M.J toilet ɗin ya shiga yayi wanka ya fito, basu wani jima ba suka fita domin isa inda zasuje. A ɓangaren Zarah kuwa bayan shigarsu ɗakin, hannunta Alhaji Mati ya riƙo da nufin janyota jikinsa ya rungumeta saidai kafin yayi hakan cikin dabara ta zame hannayenta tare da zama a gefen gadon tana faɗin. "Alhaji bazaka watsa ruwa ba tukun, kayi dogowar tafiya kayi wanka zaka fi jindaɗin aiwatar da komai cikin nutsuwa." "Tabbas wannan shawarace mai kyau, bari nayi wankan na fito, ko zaki taimakamin ne." ya ƙarasa faɗa yana mai kashe mata ido. "A'a shiga kafito dai, yanzu nayi wankan kafin na fito." Bai ce komai ba ya cire babbar rigarsa tare da shigewa banɗakin, ganin shigarsa yasa tayi saurin nufar inda akwatin kayansa yake, bata wani sha wuyar buɗewa ba saboda ta rigada tasan komai, kamar yadda suke zargi, kaya ne sosai a saman jakar saidai acan ƙasa rafar kuɗi ne sosai sai hodar ibilis. "Zaku iya shigowa Bala zarginmu ya tabbata ku shigo cikin shiri." ta faɗa a hankali. A buɗe ƙofar take dan haka jami'an suka shigo tare da yiwa ɗakin ƙawanya cikin shirin ko ta kwana. Zigir! haihuwar mahaifiya , haka ya fito daga banɗakin yana faɗin. "Gaskiya baby ina...." maganarshi ce ta katse take tashin hankali yayiwa fuskarshi tambari, juyawa yayi da nufin komawa cikin banɗakin saidai hakan bai yiwu ba sakamakon damƙarshi da wani jami'i yayi, zagaye shi sukayi sa'an nan wani a cikinsu ya taimakamai da kayansa, shidai ya kasa cewa komai illa rawar ɗari da yakeyi, ankwa aka ɗaura mishi hannu tare da tisa ƙeyarsa aka wuce dashi batare da an bashi damar magana ba duk da irin kallon da yakewa Zarah na zargi tare dason yi mata maganan. Bincike suka cigaba da gudanarwa tarw da sauran jami'ai biyu dake tare da ita, sun jima kafin suka tattara zuwa ofishin nasu. Sai da Abdallah ya tirsasa M.J kafin ya yadda suka tsaya a wani mall suka yiwa Zarah siyayyar abubuwan da sukasan mace zata buƙata musamman mai shirin yin aure. Cike da murna Baaba ta tarbesu bayan isarsu gidan, nan suka gaisa tare da hirar yaushe gamu wanda yawanci tsokanace kawai take yimusu, sun daɗe suna hira kafin daga bisani Abdallah yayi ƙarfin halin tambayar Zarah ganin har zuwa wannan lokacin batazo ba sai Raliya dake ta hidima dasu. "Zara'u dai sai shiriyar ubangiji, saida nace karta fita aikin nan yau saboda zuwanku amma tayi biris dani wai akan idan kunzo akirata aiki zatayi mai mahimmanci a can ofishin nasu." cewar Baaba cikin kwafa. "Allah sarki dama tana aiki ne.?" Abdallah ya kuma tambaya. "Ehh tana aiki kuma itama shugaba ce a wajen, ko bataje ba bazata samu matsala ba amma dan naci saida ta tafi, bari na kirata ta dawo yanzu ungo dubamin numbarta anan zakaga ansaka Zara'u." takarasa faɗa tana miƙa mishi ƙaramar wayarta. Shidai M. J yanajinsu amma bai tanka ba, saidai ranshi yayi mugun ɓaci da lamarin wannan yarinyar da akeson ya aura, wato an faɗa mata zaizo shine ta saka ƙafa ta fita. Kiran wayar ake tayi amma bata ɗagawa, hakan yasa M.J ya umurci su kuma falon Abba su zauna, nan suka bar Baaba tana ta mitar Zarah taƙi ɗaga mata waya da gangan saboda bata da gaskiya. 🥶🥶🥶🥶🥶🥶🥶🥶 A hankali ta kulle ƙofar tare da murɗa key ɗin jiki kana ta isa kan gadonta ta zauna tare da fiddo da wata ƙaramar waya da ke ta kawo wuta alamun ana kiranta, karawa tayi a kunne tare da faɗin "Barka da safiya ranka ya daɗe." "Baki da hankali ne Raliya, shin ban tsara miki yadda nakeson ki gabatar da komai ba, wato saboda kinga bakya kusa dani kike tunanin zakiyi abinda kikaga dama ko? Toh wallahi duk wani motsinki kinsan a tafin hannuna yake, saboda bakisan mahimmancin abinda ya kaiki ba har zakiyi saken da za'a cire camera daga inda kika aji. Mtssww! Baki san darajar wannan abun da muke nema koh, wallahi ki kiyayeni Raliya kiyi abinda nagaya miki cikin tsari, yanzu tayaya zamu samu masaniyar inda abun yake bayan ancire cameras ɗin, kiyi gaggawar nemowa kanki mafita tun kafin raina ya kai ga ɓaci, Nonesense!." Batare da jiran abinda zatace ba ya kashe wayar. Kuka mai ciwo ne ya kwace mata, kifa kanta tayi akan pillow tare da fara rera kukan cike da takaicin maganganun mutumin da take matuƙar so da ƙauna a gareta, a gefe guda kuma takaicin cire cameras ɗin ne ya dameta wanda ta tabbar wannan aikin Zarah, ta rasa gane alƙiblarta, tamkar mai aljanun da suke faɗa mata sirrin mutum haka take, a ɗan zaman da sukayi ne ta fahimci haka. Tabbas a da taso ta rangwanta mata kodan albarkacin Baaba, amma a yanzu batajin ko iyayenta dake kabari ne zasu dawo rayuwa suce ta haƙura da satar Diamond ɗin nan ba zataji maganarsu, dole ta sake shiri domin tasan ta wannan hanyar ne kaɗai zata iya cimma burinta na rayuwa da Alpha a matsayin masoyi. Miƙewa tayi tare da share hawayen da ya ɓata mata fuska ta nufi ƙofar fita daga ɗakin saboda jin kiranta da Baaba keyi. "Gani Baaba". Ta faɗa bayan ta iso falon. "Yauwa Raliya kiramin direba na aikashi ya tahomin da Zara'u tunda naga batada da niyar dawowa." "A'a Baaba kinsan yanayin aikinsu fa, ki barta zata dawo yanzu idan yaje ma ba lallai su barshi ya ganta ba." "Shikenan amma tabbas zata gamu da fushina idan ta dawo, yanzu da ba ƴan gida bane ai kunyata mu zatayi kenan." "Ayi haƙuri Baaba, kina buƙatar wani abu ne." Raliyan ta faɗa tana mai sunkuyar dakai ƙasa. "A'a bakomai jeki kema ki huta kinyi aiki sosai." "Nagode" ta faɗa tare da nufar ɗakinta. ✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️ *SINGAPORE* Daddy ne zaune da wani kyakkyawan matashin saurayi a wanj keɓaɓɓen lambu mai cike da shukoki kaloli daban-daban, kallo ɗaya zaka yiwa saurayin kaga tsantsar kama da sukeyi da Zarah da kuma Rahama saidai ƙarin hasken fata da Zarah tafiso duka, hannun Daddyn na akan kafaɗar saurayin da idanuwanshi sukayi jazir saboda kukan daya sha, hankacif ya saka tare da ƙara goge mishi idanunshi yana faɗin. "Kayi haƙuri Son muma har yanzu haka mukeji a zuƙatan mu bayyanawa ne kawai bama yi, amma kayi hakuri ka biyoni mu koma gida." cewar Daddy "Daddy bazan iya zama a Nigeria ba alhalin babu waɗanda zan iya gani na samu farin ciki." "Kada kace haka As-Siddiq zaman ka anan bashine zai iya dawo da waɗanda suka rasu ba, idan kace baka da kowa toh mufa ko baka ɗaukemu a matsayin iyaye bane dama, ƴan uwanka mata fa, bawai ina nufin bazan iya riƙesu bane tamkar ƴaƴan da na haifa amma suna buƙatarka a kusa dasu a matsayinka na wanda zasu dinga gani tamkar ɗan'uwana da ya rasu, kaine kaɗai zaka iya rarrashinsu musamman Zarah da ita bata kukan fili saina zuciya wanda yafi ƙuna, kayi haƙuri ka shirya mukoma gida tare dan Allah ina neman wannan alfarmar." "Daddy kai ubane a wajena baka da buƙatar neman alfarma a wajena, umarni kawai zaka bani na aiwatar, insha Allahu zuwa ƙarshen shekara zan tattaro na dawo gida." "Me zaka tsayayi anan har ƙarshen shekara? Bayan haka ma bikin ƴan uwanka za'ayi nan da wata ɗaya da sati biyu ka shirya kawai mu tafi tare." Idanunshi da suka fara washewa ya waro wanda hakan yayi mishi kyau matuƙa, kafin yace. "Wasu ƴan uwan nawa kuma Daddy." "Ehh ƴan uwanka Zarah da Jawwad, insha Allah nan da wani lokaci za'a ɗaura aurensu." "Amma ita Zarah ce ta amince da auren Bro Jawwad ɗin? Ko dama suna soyayya ne ban taɓa sani.? Amma yarinyar nan batada hankali duk ana maganar nan shine bata taɓa faɗamin ba ɗazu ma fa munyi waya da ita amma take cemin babu komai, yanzu ina ita ina miskilancin M.J mut..." lura da yayi da wanda suke maganar ne ya sashi yin shiru batare da ya gama maganar ba tare da sunkuyar da kanshi ƙasa cike da kunyar maganganun daya yiwa Daddyn. "Kada kaji kunyata Son, ko nine a matsayinka tambayar da zanyi kenan yanzu tamkar uba kake a garesu kanada damar yin bincike a duk wani lamari daya shafesu." "Kayi haƙuri Daddy, zan shirya mu wuce tare." "Toh nagode Son, Allah yayi albarka". "Ameen" yace kana ya tsiyayi ruwan dake ajiye akan teburin wajen yasha, nan suka zauna suna hira kafin daga bisani suka miƙe tare da barin wajen. 👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️ Saida ta kammala duk wasu mahimman abubuwa da duka dace game da case ɗin kafin ta nufi gida cikin hanzari saboda jiran da ake mata . Da sallama ta shiga falon, ganin Baaba a zaune ta sha kunu ne yasata faɗin "Dan Allah ayimin afuwa Baabata aikine mai matuƙar mahimmanci ya tsayar dani." "Zaki wuce kije ki samesu ko yaya." "Haba ko wanka bazaki bari nayi ba, da kayan aikin zanje ne wai" "Wallahi idan baki wuce ba zan saɓa miki, yo menene ai gwara suka ganki da kayan aikin su san ba ƙarya na musu ba, ki wuce kafin raina ya ɓaci" Babu yadda ta iya haka ta nufi ƙofar falon Abban saboda batason tayi abin da zai ɓata ran Baaba tunda yanzu ita kaɗai ta rage musu. Abbdallah na kishingiɗe a doguwar kujera yayinda M.J ke zaune yana danna waya, sallamar da akayine tasa ya miƙe daga kwancen yana amsawa shikuwa M.J. ko ɗago kanshi baiyi. "Amaryar..." maganar Abdallah ce ta katse lokacin daya kalli Zarah lokaci ɗaya kuma ya waro ido, kallonta ya ƙarayi sosai tana sanye da abaya amma hakan bazai hana mutum ganin kayan Ƴan sanda dake jikinta, dariyarshi ya ƙunshe tare da amsa gaisuwar da take mishi. "Amaryarmu kin shanya mu har mun bushe." "Ayi haƙuri dan Allah aiki ne ya tsayar dani shiyasa ." ta faɗa tana zama a kujera. "Toh gaki ga angon dai domin yayi fushi kinga ko kallonki yaƙi." Kallon shi tayi kana tace "Barka da zuwa ayimin hakuri na barku kuna ta jira." Kusan second goma dayin maganar kafin ya ɗago da nufin kallonta, ido ya waro sosai domin tabbatar da abinda ya gani, miƙewa yayi tare da nufu inda take zaune yana tafa hannayenshi......✍️ _Tammat Bi hamdulillah! Nan na kawo ƙarshen free pages, ga maison cigaba da karantawa sai a tuntuɓeni. Nagode sosai da addu'o'in ku da soyayyarku a gareni, sakallahu khairan._ *By* *Jasmine*🌸🌸 07048961623 *ASP ZARAH* Tsayuwa yayi a gabanta na wasu sakonni kafin ya durƙusa a gabanta yace. "Naji mamaki matuƙa sannan nayi farin ciki da wannan zaɓin na mahaifina, a ɓangare guda kuma ina takaicin haɗani aure da karuwa da za'ayi, sannan mace mai fuska biyu. Albishir da shawara zan miki a yanzu.." Maganar shi ta katse saboda dafashi da Abdallah yayi yana cewa "Haba M.J wane irin magana kakeyi ne haka.?" "Kayimin shiru Abdallah bana buƙatar jin komai daga gareka, ka zuba ido kawai." Baice komai ba ya kuma ya zauna cike da takaicin abinda M.J din yakeyi. Sunkuyawa ya kuma yi tare da dafa kujerar ta take kai da hannunshi biyu ta yadda suna iya jiyo numfashin juna. "Ina baki shawarar ki shirya tarban kowani ƙalubale da zaki fuskanta a zaman da zakiyi a cikin gidana domin zai kasance tamkar maƙabartarki domin zakiso ki tsince kanki cikin kabarinki fiye da gidana, sannan ina miki albishir cewa bazan dakatar dake daga aikin naki ba wanda kike rufarufa dashi kina aikata saɓon Allah amma ki sani bazan lamunta ba ace kina aurena kina yawon karuwanci. Banza, ballagaza, karuwa kawai mazinaciya." Ba iya Zarah ba hatta Abdallah saida yaji zafin kalaman M.J akan Zarah, sunkuyar da kanshi yayi cike da jin kunyarta amma uban gayyar ko a jikinshi illa ma zama da yayi ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tare da tsiyaya ruwa a kofi yana sha. Tun bayan rasuwar iyayenta bata sake tsintar kanta cikin baƙin ciki da ɓaci rai irin na yau ba, zuciyarta takeji tamkar xata tsago ƙirjinta ta faɗo, a yau tanaji duk wanda zai kirata da kalmar _Marainiya_ bazata ƙi amsawa ba, kamar ko da yaushe idan ranta ya ɓaci bata taɓa iya yin kuka na hawaye saidai na zuciya. Abdallah ne yayi ƙarfin halin magana ta hanyar faɗin "Dan Allah Zarah kiyi haƙu...." "Karka ƙarasa Abdallah mutane masu daraja ake baiwa haƙuri idan anyi musu ba daidai amma ba marasa tarbiyya irinta ba, tashu mu tafi." Bai kuma tankawa ba saboda tsananin ɓacin rai illa bayanshi da yabi bayan shi suka fice a falon. Tafi mintuna talatin a zaune ta kasa ko da motsawa, bakin ciki tamkar zai kashe ta, murmushin yake tayi ƙoƙarin yi saboda muryar Baaba da taji a bakin ƙofar falon. "Me kikeyi anan kuma Zara'u bayan sun tafi." cewar Baaba daga bakin ƙofar. Miƙewa tayi cikin fara'ar da ta aro tace "Tunanin masoyina nakeyi, inajin tamkar na kai kaina gidanshi mu cigaba da rayuwa." Kaucewa tayi daga dukan da Baaba ta kawo mata tana dariya. "Allahu ya shiryaki Zara'u, muje kici abinci nasan wunin yau duka bakisa komai a cikinki ba." Nan suka fice a falon tana ta ƙoƙarin biyewa zolayar Baaba cikin dauriya gudun kada ta fahimci wani abu, sai da ɗan tsakuri abincin kafin ta barta ta wuce ɗakinta. Gaban hoton iyayenta ta isa tare da ɗauka ta rungume a ƙirjinta, sai a wannan lokacin kukan yayi nasarar zuwa mata, batayi jayayya ba domin itama tanason yin kukan ko zai rage mata raɗaɗin da takeji a zuciyarta, nan ta shiga rera shi mai taɓa zuciya. Ƙarar da wayarta keyi ne yasa ta tsagaita da kukan tare da miƙa hannu ta ɗauki wayar , ganin mai kiran nata ne murmushin da batasan dashi ba ya kwace mata, da sallama a bakinta ta kara wayar a kunne, sai da ya amsa sallamar kafin ya fara jero mata tambayoyi. "Meyasa kika amince da auren Bro Jawwad.? Dama kuna soyayya? Meya hanaki sanar dani halin da ake ciki har kina shirin yin aure amma kin kasa sanar dani? Meke damunki ne?" "Duk wannan tambayoyin Bro wacce kakeso nafara amsa maka ne.?" Ta faɗa cikin marairaicewa "Duka nakeso ki amsamin, haba mana little wannan zurfin cikin naki yayi yawa." "Toh ya kakeso nayi Yaya, me kakeso nace maka." "Gaskiya nakeso ki faɗamin tsakaninki da Allah, kada ki ɓoyemin komai dan girman Allah baki da wanda ya fini a halin yanzu kinji." Cikin sanyin jiki ta amsa mishi da "Toh". "Kuna soyayya da M.J ne.'' Tambayar tazo mata wani irin amma ba yadda ta iya tunda tayi alƙawarin faɗar gaskiya duk da bataso wani yasan halin da take ciki. "A'a Yaya" Numfashi yaja mai ƙarfi kafin yace. "Ya akayi kuma kuke shirin yin aure?" Shiru tayi batare da tayi magana ba. "Ki amsamin banason nadawo nayi abinda bai kamata bane." "Dear zakazo ne." cikin ɗoki tayi tambayar. "Ehh" ya faɗa a takaice sannan ta cigaba da cewa. "Ki amsamin tambayata, kun haɗu da juna ne." "Ehh basu daɗe da tafiya ba ma yazo Bauchi" "Ya kukayi dashi." "Yaya..." "Shikenan tunda bakyason magana idan nazo zan nemi mafita da kaina ko da kuwa dakatar da auren ne.'' ''Haba Bro...." Bai jira ta ƙarasa ba ya kashe wayar gabaɗaya, zama tayi ta dafe kanta da hannuwa biyu, lallai ya kamata tasan yadda zatayi ta rarrashi ɗan uwan nata akan maganar auren nan duk da itama a yanzu tana dana sanin amincewa amma ƙaddara ta rigayi fata. 🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢🪢 Babu wanda ke magana a cikinsu har suka isa masaukin nasu, sun daɗe a zaune kafin Abdallah yace "Yanzu M.J abinda kayi kana ganin ka kyauta kenan.?" "Mene abin rashin kyautawa anan." "Oh kai kana gani kayi daidai kenan, ya za'ayi kaje kana zagin baiwar Allah batare da ka tabbatar da abinda kake zargi ba, ina faɗa maka aikin ƴan sanda babu inda baya iya kai mutum daga inda ya dace har inda bai dace ba, amma kaje kana cin zarafin yarinyar nan, baya ga haka ma fa ƴar uwarka ce, why M.J?" "Idan ka gama saika faɗamin, look Abdallah wannan rayuwata ce and yarinyar nan ni zan zauna da ita ba wani ba, banason ka kuma yin magana akai babu ruwanka da lamarin dake tsakanina da yarinyar nan." "Kamar yadda kace zan fita a lamuranka da yarinyar nan amma inaso ka saka a ranka cewa ranar da zakazo kana neman alfarmata na shiga lamuran bazan shiga ba." "Bazan buƙace ka bama" yana gama faɗin haka ya shige bandaki, shikuwa Abdallah miƙewa yayi yaje reception da nufin binciken tun yaushe Zarah suka kama ɗakin, saidai hirar da wasu matasa sukeyi ta ɗauke mai hankali, nan ya zauna can gefe yana sauraron su, mata biyu ne da namiji ɗaya. Ɗaya daga cikin matan ne tace. "Wallahi bantaɓa jin ƴan sanda sun matuƙar burgeni kamar yau ba, kiga yadda yarinyar nan ta kama munafikin mutumin nan cikin sauƙin da babu wanda zaiyi tunanin." "Ai baku ga komai ba indai ASP Zarah ce, idan ta zaƙolo muku wani mai laifin sai mamaki ya kusa kar ku, wanda kake tunanin bazai taɓa aika wani mummunan laifi ba idan kaji laifin shi sai kayi ta mamakin yadda yake aikatasu." cewar saurayin. Hirar Zarah suka cigaba dayi wanda yawanci yabonta ne sukeyi tare da jinjina ma yanayin yadda take aiki da gaskiya da riƙon amana, gabansu Abdallah ya ƙarasa tare da baiwa saurayin hannu suka gaisa sannan yace.....✍️ *By* *Jasmine*🌸🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ "Dan Allah naji kuna magana akan wata ƴar sanda shine nace bari nazo naji gaskiyar batun." Dake saurayin irin masu surutun nan ne bai tsaya wani dogon nazari ba ya fara labarta mishi abinda ya faru awanni uku da suka wuce, na yadda Zarah ta jagoranci jami'i sukayi basaja suka kama mutumin da babu wanda zaiyi zaton mai laifi ne, ya daɗe yana zayyano mishi kyawawan halinta tun daga kan shiga har fannin aiki, ganin saurayin bashi sa niyar dakatawa ne yasa Abdallah miƙewa tare da ajiye musu rafar kuɗi akan teburin da suke zaune ya wuce sama. Murmushi yayi mai cike da ma'anoni, tabbas bazai gayawa M.J wani abu da ya sani akan Zarah ba, zai barshi har zuwa lokacin da zai gano da kanshi, a wannan lokacin zai taya Zarah ramuwar abinda ya mata amma duk da haka yana fatan ya saduda da wuri kafin dare yamai nisa. Ko da ya kuma ɗakin bai nuna mishi wata alama dazai gane yana cikin wani yanayi akan abinda ya faru ba, hirarsu suka cigaba dayi har zuwa lokacin da aka kira sallar magrib suka fito masallacin dake farfajiyar hotel ɗin domin sauke farali. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Duk yadda taso taƙi saka abin a ranta ta kasa, kusan kwana tayi a zaune tana tunanin mafita babu shawarar da zuciyarta bata raya mata ba daga mai kyau har wanda bai dace ba, daga ƙarshe dai ta yanke shawarar ɗaukar lamarin a duk yadda yazo mata, zata karɓi tayin kowane irin zama da yakeso suyi, damuwarta ɗaya ce kuma ya magance mata wato cigaba da aikinta, bata da wani sauran abinda zata damu dashi matuƙar zai yarje mata cigaba da aiki. Washe gari idonta yayi luhu-luhu saboda rashin baccin da bata samu ba ga kuma kuka da tayi sosai, hakan ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani har taji bazata iya fita gurin aiki ba, tana kwance akan sallayar da tayi sallar asuba ta kasa miƙewa ta koma kan gadon. Ganin har ƙarfe takwas Zarah bata sauko ba yasa Baaba miƙewa da kanta ta haura saman domin duba lafiyarta, da sallama ta shigo saidai duhun dake ɗakin bai barta ta hangi komai ba, lalubawa tayi har Allah ya bata sa'ar samun switch ɗin ta kunna haske ya gauraye ɗakin, kalle-kalle ta farayi ganin bata ganta kan gadon ba har Allah yasa ta hangota acan kusurwar da take sallah. Da hanzari ta ƙarasa inda take tare da tattaɓa jikinta ganinta a duƙunƙune. "Subhanallahi Zara'u baki da lafiya shine baki faɗa ba tuntuni a kaiki asibiti, saiko zauna da ciwo a jikinki haba sai kace ƙaramar yarinya." Cike da juriya da ƙarfin hali tayi ƙoƙarin miƙewa zaune tare da jingina bayanta a jikin gado tace. "Ba wani abu ke damuna ba fa Baaba, kawai ɗan ciwon kai ne daya haddasa min zazzaɓi amma yanzu zanyi wanka nasha magani." "A'a Zara'u ban yarda da wannan ba ki lallaɓa kiyi wankan sai a rakaki asibiti, ko kuma zaki jira su Muhammadu suzo ne saisu kaiki naga kamar zaifi." "Baaba nace miki karki damu ba wani abu bane fa zansha PCM yanxu zai sauka." "Tunda haka kikace ai shikenan Allah ya baki lafiya, dama naga baki sauko bane nazo faɗamiki cewa ɗazu Babanku ya kirani wai sun fasa bari sai wani sati saboda Sadiku ya matsa sai sun dawo shine yau zasu biyo jirgin yamma su dawo." Wanj irin zabura tayi kamar ba mai jinya ba tace. "Da gaske Baaba.?" "Mtsww! Iskancin banza, ni ina nan na ɗaga hankali na baki da lafiya ashe ƙarya kike yi tunda har zaki iya wannan zaburar." "A'a fa Baaba, kinsan daɗewar da nayi banga ɗanuwana ba dole nayi ɗoki yanzu da naji zai dawo." "Shikenan ai kiyi wanka kizo ki karya saiki sha maganin." "Toh yanzu zan sauko." "Karma ki sauko yanzu inkin so." Ta faɗa tana mai ficewa daga ɗakin. Miƙewa tayi dakyar saboda sarawa da kanta keyi ta shige banɗaki, ruwa mai ɗumi ta tara ta shiga ciki, ta daɗe a kwance cikin ruwan kafin ta canja shi ta tare wani kana ta ɗauki sponge ta fara murzawa jikinta a hankali har ta gama ta ɗaureye jikinta kana ta fito a ruwan ta ɗaura towel tare da ficewa a banɗakin. Zama tayi gaban dressing mirro tana ƙarewa kanta kallo ganin yadda damuwar dare ɗaya ke neman ramar da ita, ya zama dole tayiwa kanta alƙawarin cire duk wani damuwa dake ranta akan wannan auren ta maida hankalinta wajen binciken inda zata nemo _Alpha_ domin zuwa yanzu tanajin wani irin kwarin gwiwa akan binciken da take a kanshi, tana iya gudanar da komai batare da tsoro ko shakkar wani abu zai faru da ita, hakan na ƙara bata tabbacin cewa lallai ta kusa tozarta Alpha a idon duniya. Abu ɗaya yanzu takeson sani shine haƙiƙanin inda yake rayuwa, zata iya riskar kowani haɗari matuƙar zata gano inda yake, hanya ɗaya gareta yanzu, hanya ɗaya tak! Wato Raliya. Ta hanyar Raliya ne kawai zata iya gano inda Alpha yake, dole tasan yadda zatayi ta samu duk wasu bayanai a gurin Raliyar. Tunanin damuwar Alpha da tayi ne ya mantar da ita badakalar auren dake gabanta, mayukanta ta shafa tare da wadata duk wata gaɓa na jikinta da turare, gaban wardrobe taje ta tsaya tare da kallon tulin kayanta dake ciki, idonta ne yakai kan kayan sports ɗinta dake can gefe a ninke, zaro su tayi tare da ƙura musu ido tana tuna lokacin baya da kowace ranar lahadi sai sunyi wasanni kala-kala da yayarta Rahama saboda haka ma Abba ya saka aka ƙawata musu wani sashi na cikin garden dinsu da kayan wasanni, wasu lokutan ma hatta Abban yakan kasance tare dasu domin shima yana matuƙar son wasan Table Tennis. Wasu marayun hawaye ne suka zubu daga idonta, hannu tasa ta share tare da yiwa iyayen nata addu'ar samun Rahamar ubangiji, kayan ta mayar ma'ajiyarsu kana ta ciro wata material kalar blue da golden, ɗinkin riga da skirt ne wanda ya matuƙar karɓan jikinta. Wayarta kawai ta ɗaukan sannan ta fice a ɗakin. "Ya jikin dai" Baaba ta tambaya bayan saukowarta cikin falon. "Da sauƙi." ta faɗa a hankali. "Allah ya ƙara afuwa, ga kalaci akan dinning idan kin gama saiki sha magani." "Toh" ta faɗa tare da miƙewa ta nufi dinning ɗin da Raliya ke gurin tana ƙara ƴan goge-goge, kujera ta jamata ta zauna tare da cewa. "Ina kwan Anty." "Lafiya" ta amsa a taƙaice kana ta kuma cewa. "Jeki kawai." ganin Raliyan na ƙoƙarin zuba mata abincin. Tea kawai tasha sha sai dankali da ta ɗan tsakura, sannan ta miƙe ta koma cikin falon ta kwanta a doguwar kujera, tana daga kwance take ƙarewa Raliya dake zirga-zirga kallo, tabbas akwai abinda take ɓoyewa domin tun zuwanta gidan bata taɓa ganinta babu hijabi ba kullum cikin saka hijabai take kowani irin aiki da takeyi ko yanayi da ake ciki. Toh mene ne Raliyan bataso a gani??? Ta tambayi kanta, shiru tayu na wasu mintuna kafin ta saki wani murmushi mai sauti wanda har saida ya jawo hankalin Raliyan dake moping, tabbas ta samu amsa. Lallai akwai tatto ɗin Alpha a wuyanta wanda batason a gani shiyasa ko da yaushe take cikin hijabai. Wayarta da tayi ringing ne ya katse mata tunanin da takeyi, da murmushi a fuskarta ta ɗaga tare da karawa a kunnenta. "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida." Jidda ta faɗa daga ɗaya ɓangaren. "Dama nasan idan bake ba babu mai kirana da sanyin safiyar nan." "Saboda baki da aurene yasa kike ganin yanzu yayi safiya, toh yakike ya angon namu? Kun gana dai koh?" "Yanzu wace tambaya zan fara amsa miki maganaɗisu." "Duka nake buƙatar sani." "Alright to duka lafiya lau." "Hmm to ya angon kun sasanta dai koh." Shiru tayi batare da tace komai ba, hakan yasa Jidda cewa. "Wato ɗan iskan maganganu yazo ya faɗa miki koh? Kuma shine kika zuba mishi ido batare da kin ɗau mataki ba, wai ke wace irin mace ce habibaty." Batayi mamakin jin abinda ya fito a bakin Jiddan ba domin idan da sabo ta saba da wannan halin nata, sau da dama ko bata faɗa mata abu Jidda na iya fahimtar hakan a yanayinta, da fari tayi tunanin ko Jidda nada aljanu akanta ne masu gayamata sai daga baya ta gano nature ɗinta ne hakan da kuma tsantsar ƙaunar da takeyi mata shiyasa take iya karantar ko wani yanayi nata, ƙwafa tayi kana tace. "Toh madam mai gani har hanji ya kikeso nayi idan ba shirun ba." "Wato abinda ya faru kenan dai, ke kuma saboda gaki mai biyayya kika zura ido kina kallonshi yana gasa miki maganganu, toh wallahi ki kiyayeni tun kafin nakai maƙura na shiga lamarin da bai shafeni ba." "Kiyi hakuri Mama" Zarah ta faɗa cike da zolaya. "Toh na haƙura ƴar nan, yanzu ya ake ciki wasu event zamu shirya ne naga alaman idan aka biyewa ra'ayinki bazamu gwangwaje." Dariya tayi sosai kana tace. "Kinsan nifa ustaziya ce." "Matar uztazu koh, shikenan ma bazan kuma yi miki magana ba zanjira Ammi su shigo next week sai mu tsara komai da Sis Rahama." Miƙewa tayi zaune daga kwancen da take tace "Wace Ammi." "Ammi nawa muke dasu dama.?" "Wato saboda anjireni a cikin dangi yasa duk wanda zaizo kasar ba'a faɗamin koh". "Ke kika sani nikam na tafi gurin habibi na." Kafin ta kuma magana kashe wayar, miƙewa tayi da nufin zuwa ɗaki sai....✍️ *VIP ayimin haƙuri dan Allah jiya banji daɗi ba shiyasa banyi typing ɗin ba. Sorry dan Allah*👏 *ASP ZARAH*👩‍✈️ Shigowarsu ce ta dakatar da ita daga ƙoƙarin miƙewa da take domin zuwa ɗakinta, sallamar da Abdallah keyi ta amsa ɗauke da murmushi a fuskarta. Bakj M.J ya kyaɓe lokacin daya zauna a kujera tare da faɗin "Mutum a fuska kamar na Allah saidai a baɗini ɓarnar da ake aikatawa ko kare bazai shinshina ba, Allah dai ya shirya wanda ya mayar da kanshi kwarkwar." "Ameen kuma gani kuturwar uwa zama dani dole." ta faɗa cike da basarwa kamar ba ita tayi zancen ba. "Amaryarmu ni dai yunwa nakeji ki rabu da wannan angon naki ki ceto rayuwata." Taƙaitacciyar dariya tayi har kyawawan haƙoranta suka bayyana sannan dimple ɗinta ya lotsa, ta gefen ido ya kalleta cikin rashin sanin dalilin dazai saka yaji haushin fara'ar da takeyi ma Abdallah. Kallo ya bita dashi lokacin data miƙe har ta shige kicin, tsaki ya kuma ja sannan ya kalli Abdallah yace "Akan wani dalili zaka dinga sake mata fuska haka.?" Dariya yayi harda buga ƙafa kana yace. "Ikon Allah! Tunda baza kayi mata fara'a ba ai saika bar masu yimata koh bawai ka dinga jin haushin mu ba." Bai kulashi ba sai miƙewa da yayi ya nufi ɗakin Baaba, shima miƙewa yayi tare da bin bayan shi domin zuwa gaida Baabar. Ganin basa cikin falon yasa ta shirya musu komai a dinning, ɗakinta ta kuma ta ɗau mayafi da makullin mota ta fita domin zuwa kasuwa tayi cefanen abubuwan da zata buƙata na girkin tarbar ɗan uwanta da kuma mahaifinta. Yayanta nason masa sosai shiyasa zata fita da kanta ta siyo sauran abubuwan buƙata na miya da basu dashi. Tare suka fito falon da Baaba inda suka nufi dinning table yin breakfast. "Bari na kirata ta zuba muku, Zara'u" cewar Baaba, Raliya ce ta taho da sauri ta iso gabansu tare da cewa "Hajiya Baaba bari na zuba musu, Anty Zarah ta fita." "Ina taje kuma." "Wallahi bata faɗamin ba amma kaman ba nisa tayi ba, naga batayi shiri ba." "Ai shikenan zuba musu, amma zata fita shine bazata sanar da ni ba." Ranshi ne yaji ya ɓaci saboda mummunan zaton da shaiɗan ke kitsima mishi na cewar gurin wani ta tafi domin suyi lalata, baice komai ba ya cigaba da cin abincinsa batare da ya kula Abdallah dake cewa. "Ko dai anyi mata kiran gaggawa ne." "Ina tunanin haka nima, kasan Zara'u da ƙulafucin aiki bataji bata gani idan aka kira ta wannan aikin nasu duk wani abu da takeyi saita ajiye ta tafi." "Yanayin aikin nasu kenan Baaba sunyi rantsuwar kare haƙƙin mutane." "Toh Allah dai ya tsare." "Ameen" Inji Abdallah Ko da suka gama cin abincin falon suka dawo suka zauna, hira suka cigaba dayi da Baaba wanda yawanci akan dawowar da su Daddy zasuyi ne. "Gashi shigowar yamma zasuyi kuma mu yau mukeson tafiya saboda aiki." "A'a ku tsaya mana dai ku gana duk da ma zaku haɗu acan amma ya kamata ace kun tsaya an tarbesu da ku." "Shikenan saidai muma muyi tafiyar jirgin kenan, bari na duba ko za'a samu jirgin dare." "Mezai hana ku ƙara kwana?." "Baaba nace miki fa akwai aiki." "Ku zama na'ura saboda aiki idan kun so." Dariya M.J yayi yace "Duk rashin son magana da nakeyi sai kinsa ni." "Yo me za'ayi da mutum miskili." "Ba zaki gane bane ai Baaba, babu fa'ida ace mutum ya kasance mai yawan surutu." "Shiyasa ma aka haɗa ka da wacce ta dace dakai gurin rashin son magana." Bai kuma magana ba illa cigaba da danna wayar shi da yayi, itama Baaba miƙewa tayi ta nufi kitchen. 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎 "Raliya! Raliya!! Raliya!!! sau nawa na kiraki?" ya faɗa cikin fusata. Cikin shessheƙar kuka ta amsa mai da "Sau uku ranka ya daɗe." "Wai ke wace irin daƙiƙiyar yarinya ce da batasan abinda takeyi ba, duk tsawon lokacin nan da kika ɗauka a cikin wannan gidan aikin me kikeyi da har yanzu kika kasa samo wani gamsasshen bayani .?" "Kayi haƙuri yallaɓai wallahi ina ƙoƙarin ganin na samu masaniyar inda lu'u lu'un suke." "Kullum abinda kike faɗamin kenan, amma sai yaushe ne zaki kawo min wani bayani mai amfani eye.?" "Fashi da makami." "Ke Raliya! Baki da hankali ne, kada ki kuskura ki fara aikata wannan mummunan kuskuren, wannan hanyar ba mai billewa bace. Da mai amfani ce bazamu kai war haka batare da mun mallaki wannan kadarar ba, ko zamu kuma aikata hakan ba nan kusa ba akwai sauran lokaci." "Amma yallaɓai naji kamar batun aurenta akeyi." A kishingiɗe yake amma jin wannan batun yasa shi miƙewa batare da yasani ba, cin hargagi yake faɗin. "Aure! Aure dai? Meyasa baki faɗan hakan tuntuni ba Raliya, sai zuwa yaushe ne ƙwaƙwalwarki zata dinga yin abinda ya kamata ne." "Kayi haƙur..." "Hell with this fucking word Raliya! Hakurin me zanyi, abubuwa na shirin lalacemin kice wai nayi hakuri." "Amma yallaɓai naga wanda zata aura ɗan gida ne shiyasa banyi tunanin komai." "Wanene wanda zata aura ɗin." "M.J ne." Wani murmushi yayi mai sauti kana yace. "Woow! Komai ya kusa zuwar mana da sauƙi, kin tabbata shine wanda zata aura." "Na tabbata ranka ya daɗe yanzu haka ma yana garin Bauchi yazo ganinta." "Ki tsaya ki saurareni dakyau Raliya, wannan ne lokacin mu na samu ko rashi, a yanzu ne muke da damar yin duk wani abu da muka daɗe muna shiryawa, inaso ki lura sosai da duk wani motsinta daga yau, saboda inada tabbacin cewa nan bada jimawa ba za'a nemi sauyawa diamonds ɗin nan wajen zama, ki sanar dani duk wasu bayanai da zaki samu, zan organising team ɗin da zakuyi aiki tare da zarar angano inda suke kiyi ƙoƙarin samu mana bayanai kawai." "Zan kula sosai yallaɓai." "Ohk" kawai ya kuma faɗa tare da kashe wayar. Shiru tayi bayan gama wayar tasu tana tunani, tabbas wannan ita kaɗaice damar da take da ita domin ƙara samun kusanci da Alpha, ya zama dole yanzu ta shirya ɗamarar yin fito na fito da Zarah akan Diamonds ɗin nan, ba damuwarta darajarsu ba ko kuɗin da za'a samu akansu, babban abinda ya dameta shine ta wannan hanyar ne kaɗai Alpha zai dinga ganin ƙimarta har ta samu nasarar cusa soyayyarta a cikin zuciyarsa, saboda sanin yadda yake da babban buri akan Diamonds ɗin. "Lokaci yayi da zanja ragamar wasan nima." ta faɗa cikin wani shu'umin murmushi. 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫 Gefen hanya ta samu tayi parking motarta saboda kiranta da Jidda keyi a waya, hannu tasa ta ɗauki wayar tare da maida kiran daya kuma katsewa. "Ina kika shiga ne nake kiranki bakya ɗagawa." "Toh shugabar masu ƙorafi tuƙi nakeyi." "Kin fita aiki ne?." "Aa cefane naje yi inaso na shiga kitchen da kaina na shiryawa Big Bros abincin." "Nima ai naso zuwa wallahi Sa.Jid ne ya hanani wai saura kwana nawa ne ma da duk zaku dawo Gomben." "Saboda ke gaki mai ƙafar yawo ko.?" "Hmm! Kin cika ni da surutun ku na ƴan sanda baki barni na faɗi dalilin kiran nawa ba." "Wato surutu ma na cika ki dashi ko.?" "Baza dai ki barni na faɗi abinda zan faɗa ba kenan.?" "Ohh sorry ina jinki." "Akwai matsala fa" "Wacce irin matsala kuma." "Jiya naje gidan Momi take gayamin wai a ɗaya part ɗin nan zaki zauna kafin a ƙarasa muku gyaran gidan da zaku zauna." "Yanzu ya za'ayi kenan." "Baki zaki buɗe ki gayawa Daddy kin fiso a gyara muku gidan tukun, idan babu hali ma sai a ɗaga bikin tunda kinga abu ne mahimmaci zamuyi." "Haka za'ayi zamuyi maganar." "Toh shikenan sai anjima ki gaishemin dasu idan sun sauka." "Ok bye." Motar ta kunna bayan ta ajiye wayar sannan ta nufi gida kai tsaye, M.J kaɗai ta tarar a falon bayan shigarta ciki da sallama, bata kulashi ba ta nufi hanyar kitchen, juyuwa tayi tare da aika mishi wani sihirtaccen kallon jin abinda yake faɗa. "Allah yasa dai kin wanke najasar tun a waje baki dawo dashi cikin tsarkakken gidan nan ba." Shigewa tayi batare da tace komai ba, shikuwa tsaki ya furzar mai sauti tare da miƙewa ya bar cikin falon. A zaune ta tadda Baaba a kitchen ɗin tana yankan ɗanyar kuɓewa, ledojin hannunta ta ajiye tare da faɗin "Me zakiyi da kuɓewa kuma Baaba.?" "Babanku ne yace yanaso a mishi shine nafara gyarawa kafin ki dawo, ina kikaje ne.?" "Kasuwa naje na siyo sauran abubuwan da bamu dashi a kitchen ɗin." "Gashi ki ƙarasa wannan bacci ne yaketa ƙoƙarin kamani tun ɗazu zanje na ɗan kwanta, saiki kira Raliya ta kama miki wasu aiyukan." "Toh" tace tare da karɓar rubar da kuɓewar ke ciki, ita kuma Baaba ta fice a kitchen ɗin, saida ta gyara komai tare da fitar da duk wani abu da zata buƙata kafin itama ta wuce ɗakinta tayi wanka da sallah kafin ta fara aikin. Tun ƙarfe biyu ta shiga kitchen ɗin tafara hada-hadar haɗa abincin tarbar baƙin nasu, ita kaɗai takeyin duk wasu aiyuka ba kamar yadda Baaba tace ta nemi taimakon Raliya ba, a dole ne kawai take haƙuri Raliy na kusantar inda take bawai dan tanaso ba, saboda tsanar da takeyiwa Alpha da duk wanda ya dangance shi. Kasancewarta mai saurin aiki yasa kafin la'asar harta gama haɗa komai illa kawai masa ɗin da bata soya ba wanda shima rashin tashin da baiyi ba ne ya hanata soyawa. Baaba ce ta kuma shigowa kitchen ɗin da sallama tana faɗin. "Yanzu Zara'u da nace ki kira Raliya ta kama miki wannan aikin shine kika ƙi koh.?" Sai a lokacin Zarah ta lura da Raliya dake bayan Baaba, kau da kai tayi tare da faɗin. "Naga aikin ba mai yawa bane shiyasa." "Allah ya kyauta wannan halin naki, saka min tuwon nikam idan kin gama." "Toh kije zan kawo miki." "Ban yarda ba sakamin na tafi dashi ko kibawa Raliya ta kawomin." Ba yadda ta iya haka ta saka mata malmalar tuwon guda biyu a plate sannan miya a ƙaramin glass bowl, a wani ƙaramin faranti ta jere mata tare da ɗora mata kwalbar soyayyen man shanu ta miƙawa Raliya farantin suka fice tare. Saida ta wanke abubuwan da tayi amfani dasu kafin ta nufi ɗaki saboda kiran sallar la'asar da akeyi, cikin sauri ta watsa ruwa ta fito bayan shigarta banɗakin sannan ta shimfiɗa darduma tare da tayar da sallah. Ko da ta idar gaban dressing mirro ta nufa domin shiryawa, saboda ƙarfe biyar jirginsu Daddyn zai sauka, simple makeup tayi wanda ya matuƙar yi mata kyau saboda yadda ta tsara shi, wardrobe ta kuma tare da zaro wasu rantsattsun riga da siket na wani dark blue ɗin less mai ratsin fari, cikin hanzari ta saka kayan ganin lokaci na ƙurewa, ba ƙaramin karɓar jikinta kayan sukayi ba musamman data yafa farin gyale mai duwatsu sanna ta saka farin takalmi, wayarta ta ɗauka ganin har ƙarfe 4:40pm yasa ta fita da sauri, bata tarar da Baaba a falo ba hakan yasa tabarwa Raliya dake ƙoƙarin shiga kitchen sallahun soya mata sinasir ɗin tare da faɗama Baaba cewar ta wuce airport. A farfajiyar gidan ta gansu suna ƙoƙarin shiga mota wanda tana da tabbacin suma airport ɗin suka nufa, inda motarta take itama ta nufa batare da ta kuma kallon inda suke ba. "Amaryarmu irin wannan kyau haka kamar wacce ke shirin zuwa gasar kyau na duniya gabaɗaya." cewar Abdallah daya leƙo da kanshi ta window yana magana. "Banda zuga dai." "Da gaske fa, kizo mu wuce tare mana ko ba airport ɗin kika nufa ba kema." "A'a kuje kawai yanzu zan biyo bayanku." "Sai tayi yawon dandin nata kafin nan, kaga bazata haɗa hanya damu mu hanata aikata kudurinta ba." cewar M.J yana taɓe baki kamar yaga wani abin kyama. Hawaye taji......✍️ *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH*👩‍✈️ ...Hawaye taji masu zafi suna ƙoƙarin silalo mata, da sauri ta buɗe motar ta shige domin batason M.J ya gano lagonta. Ta rigasu isa airport ɗin dan haka ta samu guri tayi parking sannan ta fito da jingina da motar ta yadda waɗanda take jira zasu iya hangenta, batayi minti goma da tsayuwa ba jirgin ya fara ƙoƙarin sauka ƙasa daidai lokacin kuma motarsu Abdallah ta iso gurin inda sukayi parking a kusa da tata motar. Matafiya ne suka fara saukowa cikin takon isa na hamshaƙan da suka baro ƙasar turawa, ɗaya bayan ɗaya suka jero akan matattakalar da zata sauko dasu daga jirgin, ido ta baza sosai ta inda zata gano ɗan'uwan nata. Duk da yawan video call da sukeyi amma dakyar idanuwanta suka iya ganeshi saboda kyau daya ƙara, nufowa suke domin ƙarasowa inda suke tsaye ita da su Abdallah, saidai bazata iya jira su ƙaraso ba dan haka ne ta ruga a guje ta ƙarasa inda suke tare da rungume ɗan'uwan nata cikin tsantsar farin ciki, shima hannayensa biyu yasa ka ya maida mata rungumar tare da ɗan bubbuga bayanta jin tana shessheƙar kuka. "Bakyason ganina ne na koma inda na fito ko.?" ya tambaya cikin son yaga ta daina hawayen. Da sauri ta sakeshi tana saka bayan hannunta ta goge hawayen kana tace. "A'a dear murnar ganinka ce kawai ta saka hakan, idan kace zaka koma to nima binka zanyi mu koma tare." Daddy dake tsaye yana kallonsu ne yace. "Wato ni ko sannu fa zuwar ma bazan samu ba duk da ni naje na taho dashi, ai babu damuwa nikam naga warayya ƙarara a fili."Cikin zolaya ya ƙarasa maganar. Ɗan durƙusawa tayi da hanzari tana faɗin "Sorry Daddyna ai nafi kowa murnar son ganinka, barka da dawowa ayimin afuwa." "Babu komai daughter mu hanzarta mu wuce gida naga hadari ya haɗo." Hannushi ta riƙe kamar wata yarinya suka ƙarasa wajen motocin, cikin fara'a suma sukayi musu barka da dawowa, nan aka ɗanyi raha irin wacce ke tsakanin uba da ƴaƴansa kana suka fara ƙoƙarin shigar da kayansu mota domin shigewa gida, Zarah kam hannun Sadiq taja zuwa motarta ta buɗe mishi gidan gaba ya zauna sannan ta dawo domin ɗaukar wasu kayan ta saka a tata motar, daidai lokacin daya sunkuya domin ɗaukar wata jaka itama lokacin da sunkuya zata ɗauka, a hankali yayi magana ta yadda ko Daddy dake tsaye agun bazaiji mai ya faɗa ba yace. "Wato ke a ko ina saikin bayyana salon karuwancin naki ko, saboda asan kin shahara a bariki ne zaki rungume mutum a bainar nasi kuma ki ƙi sakinsa saboda ke ga ƴar bariki ko? Toh Allah yasa dai rungumar iya ta ƴan'uwan taka ta tsaya bata kauce hanya ba." Da sauri ta ɗaga idonta da sukayi jazir saboda ɓacin rai ta kalleshi, wato cin mutuncin nasa har yakai matakin dazai iya zarginta akan ɗan'uwanta da suka fito ciki ɗaya, abubuwan da M.J yake mata idan ta mutu bata rama ba toh tabbas bata yafe mishi ba, batace komai ba ta ɗauki jakar ta nufi motarta. Cikin ƙoƙarin danne ɓacin ran da take ciki ta buɗe mazaunin direba ta shiga motar tana faɗin "Sorry dear na barka kana jira." Kasa amsawa yayi illa idanunshi daya kafeta dasu yanason gano wani abu tattare da ita. "Zarahty kina kallon kanki a madubi kuwa.?" ya tambaya da alamun mamaki a tattare dashi, leƙawa tayi kaɗan ta kalli madubi motar sannan ta ɗan juya ta kalleshi tana cewa. "Nifa Yaya banga inda kwalliyar nan ta ɓaci ba, kawai ka saba da ganin fuskar turawa ne shiyasa komai kake kallonshi sabo." Wanj murmushi yayi da iyaka fuska ya tsaya yace. "Ba batun kwalliya nakeyi ba, ke baki taɓa tsayuwa a gaban mirro kin fahimci how not ok are you ba, baki ga irin ramar da kikayi ba kamar wacce ta fito a prison, wai meke damunki ne haka little." "Ka dawo kenan ai Yaya, toh nidai aikine sukemin yawa bana samun lokacin hutu shiyasa kaga ina ramewa, ni banga ramar danayi ba ma fa." "Ke kam ai bazaki gani ba, amma nasan tabbas bayan aiki akwai wani abu daban a cikin ranki." "Uhmm nidai babu komai fa" "Shikenan I'll figure out myself tunda nadawo ƙasar, ja mota mu tafi gida gashi harsu Daddy sun wuce sun barmu." "Toh" ta faɗa sannan ta tayar da motar suka bar farfajiyar wajen, suna tafe suna hira tamkar wasu sa'anni ko kuma abokai saboda yanayin yadda suke hirar cikin raha da tsokanar juna, wannan na ɗaya daga cikin tarbiyar da iyayansu suka basu a zamanin da suke raye, son juna da kulawa ba tare da la'akarin babba ko yaro ba. Cikin Mintuna ƙalilan suka iso gidan horn tayi aka buɗe ƙofar sannan ta nausa kan motar zuwa ciki, a farfajiyar gidan suka tarar da Baaba tsaye tana jiran ƙarasowarsu. "Sannu da zuwa angona na kaina." tace lokacin data ƙaraso jikin motar, Sadiq ne ya fara buɗewa ya fita ta gefen da take tsayen, baki ta riƙe tare da zaro ido kamar tsohuwar da ta kama kwarto a ɗakin suruka, saboda mamakin yadda jikan nata ya sauya gabaɗaya duk kuwa da yawan ganinshibda takeyi idan suna video call, dariya yayi mai sauti ganin yanayin Baaban da kuma irin tsayuwar da tayi yace. "Haba amaryata irin wannan kallon haka, ko kina tsoron ayi saurin kwace miki ni ne.?" "Kwacewa ta nawa kuma Habu, ai yadda ka rikiɗe ka kuma bature nasan baza'a rasa wata baturiyar data kwace ka ba." "Toh ki kwantar da hankalinki ni ɗin naki ne ke kaɗai kinji my one and only kakaty." "Nifa banason wannan salon iskanci, daga dawowa zaka fara zagina tun daga kan iyaye da kakannina da wannan ɗan iskan yaren." Dariya yayi sosai kafin ya dakata yace "Toh yi haƙuri rabin raina, mu ƙarasa ciki sai muyi magana." Juyawa yayi yana waige-waige yace "Little ta shige ta barmu a tsaye ashe." "Wannan mai baƙin miskilancin ai ba tsayawa zatayi ba." "Ohh tana nan da halin ashe." "Sai abinda ya ƙaru." "Little ba dama Allah ya yaye mata." "Amin idan mai barin ta ne." Nan suka shige falon suka samesu idan Zarah ke zaune a ƙasan kujerar da Daddy yake kai ta ɗaura kanta akan cinyarshi, Abdallah da M.J kuwa suna zaune ne a kujera two seater. Zama sukayi aka shiga gaisuwar yaushe gamo da kuma ƙarin ta'aziyar da aka yiwa juna, sun jima suna hirar kafin Baaba ta umarci duk su miƙe domin zuwa dinning, Zarah ce tayi serving kuwa da abinda yakeso sannan suka fara cin abincin cikin nutsuwa da yadda addini ya koyar. Ko da suka gama ita ta tattare gurin ta kimtsa shi yabkoma kamar ba'aci abinci a gurin ba, falon ta kuma inda ta samu Daddy ya wuce sashin baƙi domin hutawa, zama tayi a gefen Baaba akan doguwar kujera tace. "Dear ba zakaje kayi wanka ka huta ba kaima." "Ke Zara'u kowa saikin ɓata mishi suna ne, mene ne kuma giya ɗin da kike kiranshi dashi." Dariya sukayi gabaɗayan su har M.J da hankalinshi yake akan wayarsa saida ya ɗan murmusa, tsagaitawa Sadiq yayi yace "Gaskiya ba ƙaramin wauta nayi ba na barin Nigeria ko wannan comedy ɗin da kike cirewa ai ya ishi mutum farin ciki na sati guda, Little jeki haɗamin ruwan wanka ganinan zuwa." Miƙewa Zarah tayi cikin dariya tabar falon. "Turanci bai yi muku rana ba tunda kun zubar da al'adun ku." "Kakaty kenan, bari naje nayi wanka na huta sai na dawo mu cigaba." Shima miƙewa yayi tare da bawa Abdallah hannu sukayi musabaha, hannu kawai M.J ya ɗaga mishi lokacin daya miƙa mishi hannu da nufin yin musabahar, baiyi mamaki ba domin tun zuwanshi ya fahimci ɗabi'un M.J ɗin musamman a gareshi da yake ganin tamkar baiyi farin ciki da dawowar tasa bane, kaɗa kai kawai yayi sannan ya nufi hanyar side ɗinshi. A tsaye ya tadda ta tana ƙara kimtsa mishi ɗakin, murmushi yayi mai sauti yace. "Ke dai bakya iya zama bakiyi aikin komai ba." "Tab! Ina hutawa mana, kawai naga baka da wanda zai maka ne shiyasa nakeyi." "Ai kuwa nagode na kusa kawo miki Anty ki huta." "Da gaske Yaya." ta faɗa da ɗoki "A'a bance ba karki kaini gaba." dariya sukayi duka sannan ya shige banɗakin yana faɗin. "Idan kin gama ki ɗaukomin fresh milk." "Toh" Sai da ta kimtsa ɗakin sosai duk da jiya ta shigo ta gyara amma tana ganin abubuwan da yakamata ta gyara musu waje, fita tayi domin zuwa ɗauko fresh milk ɗin. Baaba kaɗai ta tarar a zaune tana kallo sai Raliya dake ƴan goge-goge a gefe. "Yauwa Zara'u yanzu nake shirin aika Raliya ta kiramin ke." "Me zanyi miki kuma." "Bani ke nemanki ba, Abdullahi ke nemanki zakuyi sallama domin daga masallaci zasu wuce." "Ayya bari na haɗo saƙon Momi naje muyi sallama, suna ina ne." "Suna can falon baƙi." "Ina zuwa." Ta faɗa tana haurawa sama da gudu, ɗakinta ta shiga tare da nufar inda ta ajiye jakar tsaraba data tanadar musu da wacce takeso a kaiwa Momi, rufuwar jakunkunan ta gyara sannan ta ɗaukosu ta fito falon, kallon Baaba tayi tace. "Dan Allah Baaba Raliya ta kaiwa Yayana fresh milk karya fito yaga ban kai mishi ba." "Ɗaukomin ni na kai mishi." "Yauwa" ajiye kayan tayi akan kujera sannan ta nufi kitchen ta ɗauko fresh milk ɗin da cup ta miƙa mata, kayan ta ɗauka ta nufi falon baƙin ita kuma Baaba ta miƙe ta nufi ɗakin Sadiq ɗin. "Ahh Baaba da kanki kuma, ita little ɗin me takeyi da bazata iya kawomin ta koma ba.?" cewar Sadiq dake ƙoƙarin fitowa daga bedroom sanye da farar jallabiya. "Bakaji daɗi bane da ni na kawo." "A'a kawai naga kamar ba aikinki bane." "Sai kuma kayi idan bazaka sha bane na maida, ita wacce kake magana tana gurin mijin da zata aura zasuyi sallama domin zai koma inda ya fito." "Yi haƙuri Baaba, dama Bro ɗin yau zasu wuce shine basu faɗan ba." "Gashi ni na faɗa maka ai." "Ehh to nima inaga yakamata naje muyi sallama ko." "Yakamata gaskiya." "Bari naje na dawo sai muyi hirar soyayya." Dariya tayi kawai shi kuma ya fice a ɗakin. Ƙoƙarin riƙe handle ɗin yake domin shiga falon saidai maganganun dake tasowa yasa ya jinkirta domin jin cigaban zancen, muryar M.J ya kuma ji yana faɗin. "Idan kinsan da kuɗin karuwanci kika siyama uwata waɗannan tarkacen ki tattara kayanki ki koma dasu domin rashin arzikina bai kai matakin da zan iya barin uwata tayi amfani da abin haram ba." "M.J wai meke damunka ne akan yarinyar nan, wai ko mantawa kake itace wacce ake ƙoƙarin ɗaura muku aure nan da satikai uku masu zuwa.?"cewar Abdallah. "Abdallah kenan ina sane da duk abinda nakeyi, wannan da kake magana akanta bana mata wanj kallo da ya zarce na mazinaciya, karuwa, sannan kuma fasiƙa mai aikata abinda Allah ya haramtashi, bana mata kallon matar da nake shirin aura domin bata cancanci a alaƙanta ta dani ba bare kuma aje batun aure, ina mata kallo ne na wacce ake ƙoƙarin kawomin domin na horata akan abinda da ta daɗe tana aikatawa." sannan ke kuma, ya waiwaya ga Zarah dake zaune zuciyarta na barazanar faso ƙirjinta ta fito saboda baƙin cikin daya turnuƙeta "Ina ƙara jan kunnenki tare da baki shawara da ki zubar da duk wasu mugun nufinki nason cigaba da bin maza a gidana domin bazan lamunci hakan ba, a cikin gidana dana gina da tsarkakkun kuɗi bana haram ba a dinga aikata saɓon Allah a ciki, mazinaciyar banza mazinaciyar wofi, wa ya sani ma ko a gada kikayi kika tsotso a no..." Tasss!!! Ta katseshi ta hanyar baiwa fuskarshi wadataccen mari zazzafa domin zuwa yanzu bazata iya jure cin mutuncin nasa daya bar kanta ya koma kan iyayanta da basa duniyar ba ma. Baki buɗe suke kallonta, a ɓangaren Abdallah tsantsar farin ciki da mamakin abinda Zarah tayi ne ya hanashi magana, shikuwa M.J baƙin ciki da mamakine suka turnuƙeshi lokaci guda. "Ni kika ɗaga hannu kika mara.?" Ya faɗa yana huci. "Na mare ka kuma in gab da yi maka abinda yafi mari zafi matuƙar zaka taɓa mutuncin iyayena, banza kaw..." Bata ƙarasa ba itama ya wanke mata fuskarta da mari kafin ta kuma ankara ya ƙara wanke mata ɗaya ɓarin da mari mai zafi, saidai ko kaɗan Zarah bataji zafin shi a fuska ba saboda zafin zagin iyayenta da yayi yafi komai ƙuna a gareta. "Kina karuwa har kin isa ki ɗaga wannan hannun naki mai cike da ƙazantar zina ki mare ni, wallahi baki isa ba kuma ƙunci yanzu kika fara shiga cikinsa nonsense." A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shigo duk da halin da yake cike bai hanashi yin sallama ba, kai tsaye inda take a durƙushe ya nufa batare da yayi magana ba, hannu biyu yasa ya miƙar ta ita tsaye tare da riƙe hannuwanta suka nufi ƙofar fita daga falon, ɗan tsayawa yayi sannan yace "Dama sallama nazo yi muku, idan kun tafi Allah ya kiyaye hanya." Yana gama faɗin haka ya ja hannunta suka fice a falon, daga Abdallah har M.J babu wanda ya tanka, shikam Abdallah baƙin ciki yakeji na abinda abokin nasa ya aikata tare da dana sanin wannan rakiya da yayi, a ɓangaren M.J kuwa babu wani abu da yakeji a ranshi face ɓacin ran da Zarah ta sakamai ta hanyar marinshi. Miƙewa Abdallah yayi tare da ɗaukar kayan da Zarah ta ajiye mai ya fita batare daya kula M.J ɗin ba, bayanshi ya bi ganin bai kulashi ba suka fita tare, sun rigada sun sanar da direban dazai kaisu airport ya shirya dan haka bayan motar suka shiga yajasu zuwa airport ɗin. Ko da suka isa basu yima juna magana ba har zuwa lokacin da suka shiga jirgi ya keta hazo dasu. Kuka take me matuƙar ban tausayi da sosa ran duk wani mai sauraro har suka isa ɗakinta, kan gadon ɗakin ta faɗa tana cigaba dayin kukan, shikuwa Sadiq nufar inda hoton mahaifansu dake gefe yayi ya ɗauka tare da rungume hoton a ƙirjinshi, sai a lokacin kukan daya danne ya hanashi fitowa yayi nasarar bayyana kanshi batare dayayi ƙoƙarin dakatarwa ba shima ya fara kukan yana faɗin "Meyasa zai rabamu daku, me muka mishi zai rabamu daku ya barmu cikin gararin rayuwa da rashin gata, Abba! Mami kuna ganin yadda rayuwarmu ta tagayyara da bakwa tare damu, Abba meyasa bakace mutuwar ta ɗaukeni ba ta barka ka kula da ƙannena, Abba inajin kamar na gaza riƙe amanar ƴan'uwana da kullum kake daɗa jaddadamin, Mami kina gani koh? Ki tayani roƙon Allah yayi gaggawar ɗaukan raina bazan iya jure ganin ƴan'uwa cikin halin baƙin ciki da ƙunci ba alhalin ina raye. Kaicona dana kasa riƙe amanarka Abbana yau ga ƴar'uwata tana zubda hawayen baƙin ciki dana maraici sannan ina kusa na kasa aikata komai, Ya Allah kayi gaggawar ɗaukan ra...." Hannu aka saka tare da rufe mishi bakinshi, bashi da ƙarfin dazai iya hana hakan shiyasa ya cigaba da rera kukan shima mai ban tausayi. Zama Baaba tayi a gefen gadon ta ɗora hannun hagunta a bayan Zarah tana bubbugawa alamun rarrashi hannunta na dama kuma na kan Sadiq tana shafawa a hankali. Sun ɗauki tsawon mintuna a haka batare da sun daina kukan ba, ganin haka yasa Baaba tace. "Idan rai ya ɓaci ambaton Allah akeyi ba kuka ba." "Baaba na gaji bazan iya jure wannan baƙin cikin ba, na gaji ta dalilinsu fa muka shiga wannan halin amma abinda zasu saka mana dashi kenan, bazan iya jure wannan cin mutuncin da akeyiwa iyayena ba zan maida musu da Diamonds ɗinsu ko zamu huta da wannan takaicin." Zarah ta faɗa cikin fitar hayyaci, da sauri ta miƙe ta nufi gaban dressing mirro ɗinta tana watsi da duk wasu abubuwa dake kai batare da ta kula da irin ɓarnar da takeyi ba. Sai da zuba komai na kan wajan a ƙasa kafin da fara ƙoƙari tura dressing mirro ɗin gefe. "Me kike ƙoƙarin aikata ne haka Fatimah?" Baaba ta faɗa a fusace. "Bazan iya ba Baaba zan basu Diamonds ɗinsu kawai na huta." ta ƙarasa fada lokacin da tayi nasarar tura dressing mirror ɗin gefe, tsugunnawa tayi a gaban wani tiles a wajen, hannu takai da nufin taɓawa sai dai kamar a danna mata remote ta dakata saboda jin kamar anayi mata raɗa a kunne. "Raliya!!! Batula Raliya na waje." haka taji a kunnenta tamkar wani ke magana, da hanzari da nufi ƙofar fita bata ko ganin gabanta saboda tsananin tashin hankali, da mugun ƙarfi ta buɗe ƙofar. Rasss! Rasss!! Rassss!!! Haka ƙirjin Raliya ya bada sauti wacce ke tsaye a jikin ƙofar riƙe da sound recorder da kuma ƙaramar camera tana ɗauka duk wani abu dake faruwa ta ɗan ramin ƙofar data buɗe kaɗan ganin mutanen ɗakin basa cikin hayyacinsu bare su lura da ita, tsananin tashin hankali da firgici ne ya ziyarceta lokaci guda ta fara ɗika saboda zufar da tayiwa jikinta ƙawanya lokaci ƙanƙani.. Wata irin shaƙa Zarah takai mata........✍️ 😱😱😱😱😱😱😱 *YANZU NE FA ZA'A FARA ASALIN LABARIN _ASP ZARAH_👩‍✈️ MATAR MUHAMMAD JAWWAD KAWAR JIDDAH MATAR SALEEM. LOKACIN DA ZAMUGA ƁOYAYYEN SIRRIN DAKE TATTARE DA JIDDAH YAYI FA🤔* *SHIN ZARAH ZATA MAIDAWA DADDY DIAMONDS ƊINSA KO KUWA ZATA BARSHI A WAJENTA HAR SAI ZUWA LOKACIN DA ZATA KAUDA ALPHA.???* *ME ZAI FARU TSAKANIN ZARAH DA RALIYA NE A WANNAN FITO NA FITO DA SUKAYI.???* *WANI MATAKI DADDY ZAIYI NE IDAN YAJI LABARIN ABINDA ƊANSHI YAKE AIKATAWA GA YARINYAR DATA SADAUKAR DA KOMAI NATA DOMIN KARE DUKIYARSA WACCE TA DALILIN HAKANE TA RASA IYAYANTA SANNAN ƳAR'UWARTA TA FICE A HAYYACINTA.???* *AURAN MUHAMMAD JAWWAD DA FATIMAH ZARAH NA YIWUWA KUWA.???* *SHIN ALPHA YANA SAMUN NASARAR MALLAKAR WAƊANNAN LU'U LU'U MASU MATUƘAR DARAJA.???* *YA BATUN RAHAMA A CAIRO. INA MUSTAPHA KUMA???.* *SHIN TANA SAMUN NASARAR KAMA ALPHA KAMAR YADDA TASHA ALWASHI.???* *MEZAI FARU NE IDAN M.J YA GANE IRIN SADAUKARWAR DA ZARAH TAYI AKAN DUKIYAR MAHAIFINSHI.???* *INA BATUN ALMAJIRAR DA ZARAH TA TAƁA HAƊUWA DA ITA NE.???* _DUK AMSOSHIN TAMBAYOYIN DAMA WASU NA TARE DA JASMINE🌸🌸 A CIKIN LITTAFIN ASP ZARAH👩‍✈️, YANZU AKA FARA_. *BY* *JASMINE*🌸🌸 *ASP ZARAH* Wata irin shaƙa Zarah takai mata saidai cikin zafin nama ta kauce tare da hankaɗa Zarah ta faɗi ƙasa sannan ta nufi hanyar matattakalar da zai sadata ƙasa, ganinta tayi a gabanta tamkar wacce aka jefo kafin ta ankare taji saukar duka ta ko ina a jikinta ta yadda babu ta inda zata iya kare kanta, dukanta takeyi sosai tamkar wacce ta kama ɓarawo a bayan kanta. "Baki da hankali ne Zara'u me tayi miki kike dukanta? Ki sake ta tun kafin raina ya ɓaci." Baaba kenan ke faɗi bayan ta fito taga abinda ke faruwa, shikuwa Sadiq yana gefe a tsaye bai tanka ba domin yasan hakan nan Zarah baza ta yiwa Raliya wannan dukan ba idan ba wani mumminan laifi ta kamata dashi ba. Saida taga ta daina motsi kafin ta sassauta duk kuwa da hargowar da Baaba keyi mata akan ta rabu da ita, hannu ta saka ta fincike hijabin dake jikin Raliyan saidai ga mamakinta ba hijabi ɗaya bane a jikinta, saida ta cire hijabai uku kafin tayi tozali da jikinta kai tsaye hannu ta saka ta juyata daga kwancen da take kamar gawa ta duba gefen wuyanta, kamar yadda tayi tsammani kuwa zanen tatto ne a gefen wuyan nata, bishiyar kwakwa ne da sunan Alpha da aka ƙayata ta hanyar zanen, ɗaki ta shiga ta ɗauko wayarta ta ɗauki hoton gurin kana ta danna kiran waya tana karawa a kunnenta. "Kuzo da mota biyu gidan mu." shine kawai abinda ta faɗa kafin ta juya ga Baaba wacce ke sharar kwalla tana sambatu. Hannunta ta riƙo suka koma cikin ɗakin ta zaunar da ita a gefen gadon itama ta zauna tare da karɓar ruwan da Yayanta ke miƙa mata tasha sannan ta maida kofin yaƙara tsiyayawa ta miƙa ma Baaba itama. "Shikenan kin ja mana zagi a gari Zara'u za'ace mun kasa riƙe waɗanda ke ƙarƙashin mu." "Baaba tun ranar da kika gayamin kin ɗauki yarinyar nan aiki na nunq miki banso ba, haka ne." "Eh sai me dan bakiso ba ai ni inaso, shiyasa kike neman ki mata lahani tana marainiya." "Wai ke waya gaya miki wannan yarinyar marainiya ce Baaba? Spy ce fa aka turo mana a matsayin mai aiki." "Mene ne haka.?" "Ƴar leƙen asiri mana, Alpha ne fa ya turota.? Wani zabura duka su biyun sukayi a tare suka kuma haɗa baki wajen faɗin "Alpha.???" "Kwarai kuwa." "Kin tabbata little.?" "Sosai na daɗe da tabbatar da haka banaso na kamata a bisa zargi ne shiyasa amma da ta daɗe da zama a kurkuku, zo muje ɗakinta ka gani." Miƙewa sukayi duka suka nufi ɗakin Raliyan, sosai Baaba tasha mamakin abubuwan da Zarah ta nuna musu a ɗakin wanda babu ko tantama duk wanda yaga wannan yasan akwai abinda ake ƙullawa. "Tabbas ɗan adam na da wuyar fahimta, ki duba kiga yadda yarinyar nan ta ɓadda kama ta zo min a maraice tana roƙon abata aiki ashe cutar mu tazo tayi, Allah ya toni asirinta. Allah sarki Zara'u shiyasa sam baki yadda ko gurin zama ku haɗa ashe kinsan abinda kika gani, ni kuma duk da haka ban fahimci komai ba." "Gaba saiki kiyaye kisan waɗanda zaki dinga zaɓa kuyi mu'amala tare..." Ringing ɗin wayarta ne ya hanata kai aya a zancen nata. "Ehh ku shigo falo" haka kawai ta faɗa ta kashe wayar. "Jami'ai sun iso muje." "Ina za'a kaita ne little." "Za'a cigaba da tsaronta har zuwa lokacin da za'a kama maigidan nasu a yanke musu hukunci." "Kina ganin hakan bazai janyo wata matsalar ba." "Babu abinda zai faru Yayana da izinin Allah." "Toh Allah yasa." "Amin " suka haɗa baki wajen faɗa ita da Baaba, sannan suka bar ɗakin zuwa falo inda jami'an suke. "Ku tafi da ita Nura a fara kaita asibiti a duba lafiyarta daganan sai a wuce da ita station a rufe ta, ban yarda ko waye yazo a fito da ita ba, sannan duk wanda yazo belinta indai ba jami'i bane to a haɗa dashi a rufe, kuna jin abinda na faɗa koh." "Zamu kiyaye ranki ya daɗe." "Joy da Halima ku ɗauketa ku kaita mota sai ku wuce." Sara mata sukayi duka sannan sukayi kamar yadda tace suka fita a falon. "Allah ya kyauta ya daɗa karemu daga kaidin wannan mutumin." "Amin thumma Amin.'' cewarsu duka. "Yauwa Baaba sai batun auren Little da M.J gaskiya za'a janye ba za'ayi wannan auren ba." "Akan wani dalili za'a janye batun auren? Toh indai akan abinda Muhammadu yakeyi ne wannan auran babu fashi sai anyi shi, watarana ko kuɗi aka bashi yayi wannan abun bazai iya ba." "Amma fa kinajin irin alwashin da yake ɗauka akanta muddin ta amince akayi auran." "Naji tun ba yau ba nasan duk abubuwan da yake faɗa game da ita wanda nasan ba haka bane amma inaso mu tura mishi aniyarsa ayi auran. Duk abubuwan da suke faruwa fa bai sani ba na tabbata ranar dazai san wani abu a game da abinda takeyi zaiyi nadamar komai daya aikata a gare ta, dan haka aure nan da sati biyu babu fashi." "Shikenan Allah yasa haka shine mafi alkhari." "Amin ai addu'ar daya kamata kayi kenan Allah ya zaɓa mata abinda yake shine alkhairi a wannan auren." "Uhmm! Little me kuka shirya game da events ne." "Babu abinda zamuyi Yaya." "Bai kamata ba gaskiya, ko sports daya ai zamuyi." "Hakane fa Bro kuma kamar kasan mun daɗe bama yin sport wallahi." "Eh nasan Sis Rahama zataso hakan sosai." Murmushi kawai tayi mai kama dana ciwo domin duk sanda za'ayi maganar sports sai ta tuna mahaifanta. "Wani wasa kika zaɓa." "Dear inajin volley ball zaifi tunda kaga harda mata a ciki." "Hakane amma gidan Daddy akwai pitch ne." "Ehh mana ai saboda mu yasa akayi sports garden tun waccen lokacin idan mukaje muna playing dasu brother Adil da Nusaiba..." sai kuma hawaye shar ya biyo bayan maganarta ta. "Bana sonki da yawan kukan nan fa little, addu'a kawai zamu cigaba dayi musu, ko kinaso ki haifi yara a rasa gane wacece uwar idan kuna kuka dukanku." Hannayenta ta saka ta rufe fuska tana faɗin. "Kai Yaya." "Ehh mana, tashi muje kitchen mu haɗa dinner kafin Daddy ya dawo." "Ohh kasan na manta da Daddy na gidan nan, ina yaje ne." "Ya fita yun ɗazu zai haɗu da wani abokin kasuwancinsa." "Nagode wa Allah da bayanan wannan abu ya faru." "Muje kitchen ɗin." "Yaya akwai abinci fa." "Ni dai muje muyi ko ma mene ne, da kwaɗayi na dawo ƙasar." Hanyar kitchen ɗin suka nufa suna hira kamar wasu ƙawaye. ''Allah ya shirya ku." "Amin" Zarah ta faɗa daga kitchen ɗin...✍️ *Ayimin uzuri da wannan pls banjin daɗi ne, ayi haƙuri.*👏👏👏👏 *Jasmine*🌸🌸 *ASP ZARAH* _Duk abinda aka sama lokaci..._ Kamar yadda yau ta kasance saura kwanaki biyu kacal a ɗaura auran Zarah da angonta M.J, baƙi na nesa da na kusa duk sun hallara, inda Ammi da Momi suka dage wajen gyara Zarah sosai tamkar wacce zata auri shugaban ƙasa. Babu wasu events da akayi sai sports day da sukayi sai kuma walima da za'ayi bayan ɗaura aure. Suna zaune su uku a wani keɓaɓɓen guri a cikin garden ɗin gidan Daddy, Sadiq ne a tsakiya sai Zarah da Rahama da suke a gefensa kowaccensu ta ɗaura kanta a kafaɗarsa, kallo ɗaya zakayi musu duka ka tabbatar da cewa suna cikin damuwa sosai, idan ko mutum yasa da mutuwar mahaifansu toh tabbas za'ace maraici ne ke damunsu. Sadiq ne yayi gyaran murya yace. "Sis kinji abinda ke shirin faruwa da little fa kuma Baaba ta hana a dakatar da bikin nan, ni banaso taje tana shiga damuwa ne kinsanta da rauni." Rahama wacce tun bayan abinda ya faru ta zama miskila ta wucin gadi, shiru tayi na mintoci kafin tace. "Dakatar da auren bashi ne mafita ba Yaya, mu bari muga idan anyi auren yana cutar da ita sai mu nemi mafita." "Bakomai amma indai ya cutar da ita sai na bi mata haƙƙinta ko da kuwa igiyar zumuncin dake tsakanin mu zata tsinke." "Haka ma bazata faru ba." "Toh Allah yasa, little tashi kije Daddy na nemanki tun ɗazu mantawa nayi ban gaya miki ba." Cikin sanyin jiki Zarah ta miƙe tana faɗin "Ku jira ni fa yanzu zan dawo." "Mu ma yanzu zamu shigo gidan." "Toh sai kunzo". Kai tsaye falon Daddy ta nufa inda yake zaune shi kaɗai da alama ita yake jira, gaishe shi tayi sannan ta zauna a gefe, bansan me suka tattauna ba sai dai daga ƙarshe muryar Daddyn naji yana ta godiya tare da samata albarka. "Daddy ka daina bani kunya ta hanyar gode min, idan kana hakan sai naga kamar baka ɗauke ni a matsayin ƴarka bane." "Har abada zaki cigaba da kasancewa ƴata, amma kinsani cewa godiya wajibi ne ga wanda aka kyautatawa, Allah ya miki albarka ya baki zaman lafiya a ɗakin aurenki." "Amin Daddy." "Babu wani abu da kike buƙata ko." "Babu komai." "Tashi ki kuma cikin ƴan uwa da iyayenki." Cikin rashin kuzari ta miƙe tare da ficewa a falon, wata hanya ƙarama tabi sai gata ta ɓullo a wani babban falo wanda aka wadata da kayan alatu na more rayuwa tamkar ɗakin shugaban ƙasa, Jidda kaɗai ta gani a falon tana duba wasu takardu, zama tayi a gefenta tace. "Ya naga gidan yayi shiru haka." "Ehh duk suna backyard wajen gyaran naman nan, saboda Momi tace kar a barwa ƴan aiki aikin zasu lalata shi." "Ok nima daga falon Daddy nake." Kallonta Jidda tayi na wasu sakanni kafin tace "Ina fata komai ya zama steady." "Ehh babu wata matsala yanzu." "Wa kun haɗu da angon kuwa.?" "Uhmm tun ranar daya bar Bauchi ba mu ƙara haɗuwa ba, Abdallah ne ke jigilar zuwa da kuma kira." "Sai kinyi haƙuri da lamarin angon nan naki idan ba haka ba zai ɓata mana shirin mu." "Dole zan kula domin nima jikina yana bani cewa na kusa kama Alpha da hannuna." "Nima inajin hakan, ya batun Raliya kuwa." "Na saka an ɓoyeta a wani keɓaɓɓan guri sai ranar da burina ya cika zan fito da ita." "Hakan yayi kyau, ya kukayi da oganki ne da kikaje neman transfer." "Ohh Mr. C.P ai saida na tabbatar baya ƙasar kafin naje na processing komai, saidai kawai ya dawo yaji labarin nayi aure a wani gari na barsu da garinsu." Dariya Jidda tayi kafin tace "Kin manta waye CP kenan zai iya miki makircin nasa." Dariya dukayi duka tare da miƙewa suka fice a falon. 💫💫💫💫💫💫💫 A yau ne dai aka ɗaura auren Muhammad Jawwad Sulaiman da Fatimah Zarah AbdulJalal sai fatan samun zaman lafiya a tsakanin ma'auratan biyu duk da ba haka aka tsara ba. Duk da ba'a shirya shagula ba amma mutane sunzo sosai harda waɗanda ma ba'a gayyata ba duk sun nuna bajin ta, da yamma kuma akayi walimar mata a cikin gidan inda malamai sukayi wa'azi sosai wanda duk akan zamantakewar aure ne. An raba kyaututtuka sosai baƙi duk sun tafi suna farin ciki tare da fatan alkhairi. Nasiha sosai Momi da Ammi suka yi wa Zarah wanda ko da mahaifiyar ta ce iyakar abinda zata iya faɗa mata kenan, ita kam in banda kuka babu abinda takeyi saboda tuno mahaifanta da tayi, shikuwa Daddy da aka kai mishi Zarah domin yi mata faɗa kasawa yayi illa kawai yace. "Fatimah yadda kikemin biyayya a matsayina na mahaifinki ina roƙon Allah ya baki masu yi miki fiye da yadda zakimin, nasan ko ba'a faɗa miki ba zakiyi wa mijinki biyayya, Allah ya kareki daga sharrin maƙiya kamar yadda kike ƙoƙarin ganin hakan a kaina, Allah ya dauwamar da farin ciki a zuciya kamar yadda kike ƙoƙarin ganin hakan a kaina, Allah ya albarkaci rayuwarki ya baki nasara akan duk abinda kika sa a gaba." Mutanen dake falon ne suka amsa da Amin, daga haka kuma yabar falon ya shige ɗakinsa domin kwallace ke neman sauko mishi. Ita kam Baaba da aka kai mata Zarah miƙewa kawai tayi ta bar gurin tana kuka kamar ranta zai fita wanda mutane da dama suka fara zargin akwai dalilin da yasa ake ta wannan koke-koken, duk da cewa ansan wannan kukan ya zama kamar na al'ada amma wanda sukeyi ya wuce ƙa'ida. A haka a sakata a mota aka wuce da ita gidanta dake Federal lowcost Gombe, duk wannan budurin da akeyi Jidda bata ciki domin tun yamma Saleem yazo ya ɗauketa a gidan bikin saboda irin kukan da takeyi. Duk yadda Abdallah yaso amma M.J ya tubure akan babu wani wanda zaiyi mishi rakiyar ango, dole suka rabo dashi ya wuce gidansa shi kaɗai. Da haka dai biki ya watse sai fatan zaman lafiya ga amarya da ango. :::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::: Wayarsa dake ta faman ruri ne ya saka dole ya sake baturiyar suke manne da juna akan gado ya miƙa hannu ya ɗauko wayar, ganin mai kiran ne yasa shi firgita tare da sauka a gadon yana kara wayar a kunne. "Barka dai yallaɓai." "Don't dare to yallaɓai me, wato kaje ƙasar waje kana hutawa kabar komai yana lalacewa anan ko, wannan shine amanar da zaka yi min eye? Saboda na wadata ka da kuɗi shiyasa kake duk abinda kaga dama ko.?" Cikin ina ina yace "Ba haka bane yallaɓai ayi min afuwa." Tsawa ya daka mai cikin fusata ya kuma yin magana yace. "Afuwar me za'a maka, wato kai kaje ƙasar waje kana sha'aninka koh, ace ina tare da commisioner of police gabaɗaya amma a kama Raliya kusan fiye da sati uku amma ankasa yin komai akai." "Innalillahi! Yallaɓai Alpha kace an kama Raliya." "Bani da buƙatar maimatawa tunda kaji me nace." "Amma garin yaya waya kamata." "Wa kake tunani.?" Ido C.P ya waro waje kamar wanda yaga wani mummunan abu mai firgitawa yace. "Zarahh.???" "Ka amsa tambayarka." "Ohh shit! Dole zan dawo ƙasar gobe a fito da Raliya." "A fito da Raliya fa kace! kasan ko a wani ofishin ƴan sanda Raliya takr zan iya zuwa na fiddata, amma ba anan take ba bansan a ina yarinyar nan ta ɓoyeta ba. Kayi gaggawar kiranta ka bata umarnin fito da ita a ko ina ta aje ta." "Bari na kira ofishin su yanzu, Raliya bazata kuma kwana a hannunta ba" Umma"Ina jiran sakamako mai kyau." "Toh yallaɓai yanzu zan kira." Cikin rawar jiki ya danna lambar mataimakin shi, ringing biyu ya ɗauka yana gaidashi, bai tsaya amsawa ba ya fara magana. "Ka kira office ɗin ASP Zarah ka bata umarnin sake yarinyar da ta kulle a cell, ka gayamata wannan umarni na ne." "Yallaɓai ai babu wata yarinya a ofishin nan wacce aka kulle." "Ba tambayarka nakeyi ba umarni ne nake baka." "Amma yallaɓai naga Zarah yanzu ba anan take aiki ba, kila bata zda masaniyar abinda ke faruwa ko dai ba ita ɗin bace.?" "Bata aiki kuma ??? ASP Fatimah Zarah Abduljalal nake nufi fa." "Ehh yallaɓai ai ta nemi takardar transfer zuwa Bauchi saboda za'ayi aurenta, jiya ma muka dawo daga ɗaurin auren." "Damn it!! Wane ne ya aiwatar da hakan ba tare da sani na ba." "Yallaɓai ta je Abuja ne daga can ta gama komai, wasu signing ne kawai da akeson kayi ni nayisu a madadinka." "Meyasa ba'a tuntuɓeni ba eyee??" "Ranka ya daɗe kamar naga babu buƙatar hakan." Tsaki ya ja gami da ya kashe wayar batare daya kuma magana ba, kanshi ya dafe cikin taraddadin yadda zai kira Alpha ya gaya mai wannan labarin, gabanshi ne ya faɗi ganin kiranshi na kuma shigowa, cikin fargabar mai zai faru ya ɗaga kiran. "Ya ake ciki??" ya tambaya babu walwala. "Ehmm dama.." "Straight to the point, banason dogon zance." "Yallaɓai wai anyi mata transfer zuwa garin Bauchi saboda zatayi aure acan, jiya ne aka ɗaura auren nata a garin Bauchi." Shiru yayi baiyi magana ba har hakan ya baiwa CP tsoro, sai can yace. "Duk abinda kakeyi kabari a yau ɗin nan ka dawo ƙasar nan, sannan karka kuskura ka kirani matuƙar ba shaidamin zakayi ka kuma Bauchi da aiki ba." daga haka ya yanke kiran. Babu yadda commisioner yayi iya dole ya fara haɗa tarkacensa bayan ya sallami baturiyar da suke tare, cikin lokaci ƙanƙanin lokaci ya gama shirin komawa ƙasarsa Nigeria....✍️✍️✍️ *Tammat bi Hamdulillahi!! Littafi na ɗaya ya ƙare anan, zamu shiga littafi na biyu da izinin Allah kafin sallah. Nima zan ɗanje hutu na kwana biyu kafin mu ɗora.* *Ina yinku sosai Zarah's fans, Mrs. Khaleel from VIP ina yinki sosai ina godiya da ƙaunarki a gareni Allah ya bar xumunci a tsakanin mu. Sai kunjini a kashi na 2*🥰 *By* *Jasmine*🌸🌸