Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen2⃣) ® ✏📖 *FIKRA WRITER'S ASSOCIATION* 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 0⃣1⃣ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI✍🏼 SHIMFID'A 🌍 NIAMEY Niamey shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijar, wanda shi ne birni mafi girma a kasar, dake da girman murabba'in kilo mita (239.30) Tun a karni na 18 ne aka kirkiro Niamey, sai dai a wancan lokacin ba'a dauke shi da wani muhimmanci ba har sai bayan da Faransa ta kafa cibiyarta a wajen a shekarun (1890). A shekarar (1926) ya zamo babbar birnin kasar ta Nijar. Sannu a hankali yawan jama'ar yankin ya yi ta karuwa daga (3,000) a shekarar (1930) zuwa kimanin (30,000) a shekarar (1960). Yawan jama'ar Niamey ya kai (250,000) a (1980), a shekara ta (2000) kuma (800,000). Babban musabbabin karuwar jama'a a Niamey shi ne na yawan kaurar jama'a a lokutan fari. A matsayinsa na babban birnin Jamhuriyar Nijar, akwai wuraren tarihi da suka hada da gidan tarihi na kasa da gidan zoo, akwai kuma cibiyoyin nuna al'adun gargajiya na Amurka da Faransa da Nijar. Hakanan kuma akwai manyan kasuwanni bakwai a birnin. Kashi (90)cikin dari na jama'ar Niamey Musulmai ne, anan ne kuma ake da hedkwatar mabiya darikar kirista ta Roman Katolika. SA'AYRASA MASARAUTAR SA'AYRASA yana bangaren kudu maso gabashin Nijar, kuma yana da girman murabba'in kilo mita (156,906). Masarautar Sa'ayrasa na iyaka da Masarautar Fabarusa, ta Arewaci da Zindar ta Yammaci da Najeriya ta kudanci sai kuma Chadi ta Gabashi. Masarautar Sa'ayrasa ta kasance d'aya daga cikin masarautar da ba su da yawan jama'a, wanda kidayar shekara ta (2001), ta nuna yawan mutanen masarautar ya kusa dubu dari hudu. Jama'ar Masarautar Sa'ayrasa sun hada da Kanuri da Tubawa Hausawa da Fulani da Larabawa. Tattalin arzikin masarautar ya ta'allaka ne kan kiwo da noman rani da kuma na damina. Abubuwan da aka fi nomawa a yankin sun hada da gero da masara da shinkafa da kayan lambu irin timatir da barkono. Sai dai kuma duk da noman da ake yi a masarautar, masarautar ta kasance mafi koma baya ta fuskar noma a Nijar saboda fari. FABARUSA MASARAUTAR FABARUSA shi ne ya fi kowanne yanki girma a masarautar Nijar, wanda girmansa ya kai murabba'in kilo mita (634,209), watau kwatankwacin kashi hamsin da biyu cikin dari na girman Nijar baki daya. Masarautar Fabarusa ta had'a da Hamadar Tenere da Bilma da kuma yankin Air mai cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama'ar Masarautar buzaye ne; akwai kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa. Babbar sana'ar jamaar masarautar ta asali itace cinikin gishiri da dabino, sai dai a shekarun (1990), harkar bude ido ta zama wata babbar sana'ar yankin, hakanan karfen Uranium da ake samu a garin Arlit na samawa Nijar kashi (20)cikin dari na kudin shigar da take samu. NIAMEY 1/01/2000 Tafe su ke cikin mota,tin da suka baro masarautar su wato Sa'ayara ta tsunduma cikin kogin tunani, ba ta gushe ba har su ka shigo Niamey, in da makarantar su wato SOVEREING GIRLS SECONDRY SCHOOL ta ke. Wato ‘ya’yan manya da sarakuna na sassa,masarauta da yankunan jamhuriyyar Nijar waannan makarantar su ke. Ajiyar zuci ta saki ganin sun doshi kofar makarantar, yayin da motoci biyu da ke gaban ta su su faka, ta su wacce ta ke ta uku ita ma ta faka. Waigawa ta yi dan ganin ko d'ayar da ke tafe bayan ta su ta sami isowa,ile kuwa sai gasu sun karaso a hankali su ka faka bayan ta su. Hankalin ta ta mayar kan kofar makarantar ta su. Motoci huɗu ne jere reres su ka taho kawo Gimbya Binta yar sarkin Sa'ayrasa makaranta. Ta fari ɗauke da dogarawa guda biyu da direba, ta biyu bayi ne mata su huɗu, sai kuma wacce Gimbiyar 'yar sarki mai dole ke zaune gidan baya, ta yi ɗai-ɗai ta na shan kamshi, tare da ita baiwar ta ce Bintu zaune gaban mota da kuma direba,sai cikon na hud’un dogarawa ne su huɗu zaune, biyu gaba biyu baya. Tsawar da ta ji an daka mata ya sa ta yi firgit ta dawo cikin hayyacin ta, jin an furta, ‘’idan kin gama rubuta wasikar jakin da ki ka saba sai ki fita’’. Faɗin _(driver)_ matu'kin mota ya na mai muzurai. Hakan ya sa ta saurin fitowa daga motar dan kuwa har sun shigo farfajiyar makarantar ba ta sani ba. Tini sauran bayi yan uwanta sun yi sahu suna jiran fitowar Gimbiya Binta. Cikin su Bintu ta shige ta tsaya kan na ta sahun, yayin da dogarai su ka karaso cikin azama, su ka yi na su sahun ta ɗayan ɓangaran. Daga bayin har dogarawa kalar yadin da ke sanye jikin su ɗaya, ruwan toka ne da shuɗi. Rigar ruwan toka sai zanin shuɗi. Kan su sunkuye babu mai motsi kai kace gumaka aka aje, matu'kin ya buɗewa Gimbiya Binta kofa. K’afafun ta fara fiddowa waje, sanye cikin takalmi fata mai dankaran tsada, sai bayan wasu yan dik’ik’a sannan ta k’arasa fitowa. Tuni suka fara ma ta kirari da faɗin, ‘’taka a hankali Gimbiya yar sarki mai dole, takawan ki lafiya sarauniyar mata’’. Sanye ta ke cikin kayan makaranta, riga da _skert_ buje sai kuma hijabi wanda ke tsayawa iyaka kafaɗa. Alkyabba ce ta alfarma ɗaure bisa kayan makarantar. Cikin sarauta da tak’ama ta ke takawa ɗaya bayan ɗaya ta wuce, su ka rufa mata baya. Haka su ka wuce ciki zuciyar Bintu cike da tunanin halin da akwatin karfen ta zai shiga matukar ba ta dawo da wuri ba dan Ado matu'ki ba mutunci gare shi ba, dan ya koma da kayan Kuka Sheka ba k’aramin aikin sa ba ne. Hantar cikin ta tuni ta kaɗa Motoci sai shiga da fice su ke kasancewar yau rana ce ta dawowar ɗalibai daga hutun zango na uku. Kai tsaye sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka nufa, wanda a k’a'ida kowanne ɗaki dan d’alibai biyu aka yi. A dai-dai katangar da ta raba harabar makaranta da sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka tsaya, dan kuwa babu damar dogarai su shiga ɗakin kwanan kasacencewar dokar makaranta ta hana maza shiga. Nan su ke jiran dogarawa masu ɗauke da akwatina su k’araso su karb’i akwatunan dan karasawa da su ciki. Ita kuwa Gimbiya Binta kai tsaye ta shige,biyu daga cikin bayim biye da ita, ya rage daga Bintu sai bayi guda biyu. Dan sauri jikin ta har ɓari yake, Allah-Allah ta ke su samu su shigar da kayan Gimbiya Binta dan ta samu damar kwaso na ta. Sai da su ka ɗauki kusan minti goma kafin su k’araso ɗauke da kaya niki-niki, wanda kuwa faɗar adadadin su aiki ne ja, wai kuma a hakan ma akwai saura cikin mota. Haka suka shiga jidar kayan su na hawa da su sama,bhar bene na uku tukanna ka isa ɗakin Gimbiya. Ta nan kishingiɗe kan gado, ɗakin yayi fes-fes dama tin ana sauran kwana uku a dawo makaranta a ke gyarawa. Su na hawa su na sauka har sai da su ka yi sahu uku. Bintu na Murna da sun sake komawa za su kwashe sauran kayan. Budan bakin Gimbiya Binta sai cewa ta yi, '’akwati nawa ne su ka rage?’’. ’Daya daga cikin bayin ta amsa mata da, "huɗu ne su ka yi saura ranki shi daɗe'’. Gimbiya ta ce, "to! Za ku iya tafiya kubarwa ɗiyar bayi sauran ta k’arasa hawa da kayan’’. Tuni idanun Bintu ya raina fata, ba wai wuyar hawa da kayan ba ne damuwan ta ba, a'a ita ta dan akwaitin k’arfe ta ta ke. Cikin girmamawa su ka durkusa su na mai faɗin, "an gama ran ki shi daɗe'’, hannu kawai ta ɗan ɗaga musu alamar sa iya tafiya. Cikin hanzari su ka daɗa rusunawa kafin su tashi su ka fice. Ai fa Bintu ba ta san san da ta arta a na kare ba, ta na ji sauran bayin suna dariya suna cewa:- ‘’Ba ke mai yiwa Gimbiya hidima a boko ba, Allah shi k’ara’’, ɗaya ta k’ara da "ai tin da aka zab’e ta wani girman kai ya game jikin ta, ɗiyar bayi a makarantar girma’’. Yi ta yi kamar ba ta ji su ba, ta k’arasa ta ɗauro akwati ɗaya a ka d’aya kuma ta jawo shi a hannu. Ba ta kai ga hawa bene ba ta yi kaciɓus da su, haka su ka wuce ta suna mata dariyar kyeta. Cikin himma ta haye abun ta sama, sai da ta kai ga kofar ɗakin ta tsaya dan ta ɗan sami nutsuwa dan kuwa idan Gimbiya ta gano ta lalle kashin ta ya bushe. A hankali ta tura kofar tare da sallama. Gimbiya ko ta nuna ta san ta shigo bare ma ta amsa sallamar. Cike da nutsuwa ta aje akwatinan sannan ta fito, nan ta sake zurawa a guje, ta kwaso sauran akwatinan kamar dai yanda ta yiwa biyun farko. Aje akwatinan ke da wuya ta juya da niyyar sake fita, Gimbiya ta daka mata tsawa, "ina zaki? Nufin ki ni zan jera mi ki kayan yau kuma ɗiyar bayi?’’. Jiki na rawa Bintu ta zube k’asa ta na mai faɗin, "tuba na ke ranki ya daɗe ni ce zan jera dama sauri na ke dan kwaso nawa kayan kar Ado ya manta ya juya da su’’. Shiru idan Gimbiya Binta ta tanka ko shakka babu dutse ma ya tanka. Da shirun yayi yawa Bintu ta ɗaga kai ta kai kallon ta gare ta, sai gani ma ta yi ta runtse ido kamar mai bacci. Dole jiki ba laka Bintu ta tashi ta shiga jera akwatunan, sai da ta gama tsaf sannan ta durk’usa ta ce, ‘’ran Gimbiya ya daɗe na idda’’. Sai da wasu dak’ikai su ka shuɗe, har Bintu ta na tunanin ko dai bacci ta ke sannan ta ji ta ce, ‘’kya iya kwaso tsummokaran na ki’’. A wulakance ta yi furucin cike da 'kas'kanci. Russunawa ta yi cike da girmamawa ta ce, ‘’godiya na ke ran ki shi daɗe", ta tashi ta fice. Nan fa duk nutsuwar ta ya gushe, ta ranta a na kare, ba ta ji ba ta ba ta gani. Dalibai ma su shiga da fice cikin farfajiyar wajan faɗi su ke, "ta fara, in dai wannan ce dama duk dawowa hutu haka ta ke". A guje ta fito daga harabar ɗakin kwana ta shigo sashen ajijjuwa. Ba ta ga tahowar shi ba sai ji ta yi karo da shi. Ta yi saurin yin baya saura k’iris ta faɗi ya yi saurin sa hannu biyu ya rik’o ta. Sakin baki ta yi ta na kallan sa,ta ma manta da gudun da ta ke. Sanye ya ke cikin bakar _suite_, wankan tarwaɗa be mai dan faffaɗar kafaɗa. Ya na da dogon hanci, yayin da gashin bakin sa da ya zagaye bakin na sa ya k’ara masa kyau da k’warjini. Idanun sa rufe cikin bakin gilashi hakan ya sa ba ta sami damar ganin kwayen idanun na sa ba. Kamar daga sama muryar sa ya dakin dodon kunnan ta,jin ya ce ‘’hankali mana gudun me ki ke haka ke kuwa?’’. Ta yi saurin ja da baya,hakan ya sa shi sakin ta. ’’Yi hakuri dan Allah Ado direba zai tafi da kaya na’’. Bintu ta furta idanun ta na shirin kawo ruwa. Sai a sannan ya dubi kayan jikin ta ya na mai faɗin, ‘’Tabbas wannan shigar ta ki ta bayin Masarautar Sa'ayrasa ne, ina shigowa na ga motocin na su na fita, sun manta da ke ne...?’’, ba ta bari ya karasa maganar ba bare ta bashi amsa ta sa gudu ta na mai faɗin, "shikenan ni Bintu sun tafi da akwati na,shikenan na banu na shiga uku na lalace’’ Cikin rashin fahimta ya bita da kallo har sai da ta kure masa sannan ya d’aga kafad’a ya sauke sannan ya yi ciki abun sa.Isar ta wajan yawan motoci masu kai kawo ya k’aru,sai dai babu motocin Sa'ayrasa babu alamar su. Kwallar da ke idanun ta tuni su ka fara gangarowa bisa kuncin ta. ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 Wannan labari sadaukarwa ne kuma tukwici ne ga FIRDAUSI SODANGI,wacce ta amince da wannan batu na "garin masoya ba ya nisa" har ta kawo ziyarar ta gare ni. Allah ya bar zumunci ya bar kauna Amen. 0⃣2⃣ Bintu na shirin juyawa ta hangi akwatin ta jefe tsakiyar filin, da gudun ta ta k’arasa ta rungumo abin ta ta na maida numfashi. Wani mai mota ne ya ba a mata k’ura sa’annan ya lek’o ya na fa in "shashasha sai kin jawo wani ya taka ki’’ ko aga kai bata yi ba bare ma ta san ya na yi. Ita dai burin ta ya cika ta sami akwatin ta. Offishin shugaban makarantar katan ofishine wande aka kawata shi kai ka ce ofishin shugaban wani yankin ne. Ganin wanda ke zaune gaban sa da kuma abun da ke tafe da shi ya sa shi zufa na ba gaira ba dalili rufe shugaban makarantar. Kana ya nisa tare da fa in "(your excenllency) Ya mai girma....’’ "Aisar,ko ka kira ni Aisar Gaddafi Nur,(his excenllely) ya na gida yallabai’’ ya katse shi hankali kwance. Zufa shugaban makarantar wanda dalibai ke kira Malam Hamisu ya goge,ya na mai gyara murya ya ce "toh Yallbai,yanzu dai nufin za ka yi bad da kama kamar malami cikin wannan makaranta ta mu har tsawan zango aya.....’’ Yana mai murmushi ya ce ‘’ba bad da kama ba Yallabai,gyaran lafazin shi ne ina neman alfarmar koyarwa a makaranta na tsawan zango aya’’ cikin nazari Mallam Hamisu ya ke duban sa "me zai sa dan Shugaban kasa so ya koyar a makarantar nan?na zango aya? Ko shakka babu ya na daga cikin motanen oye wanda ke yiwa kasa bincike da aiki cikin surru, dama ba tun yau ya ke jin maganar ba,kaddai wani sharrin aka kullawa makarantar sa.....’’ Zancen zucin da ya ke yi cikin ran sa kenan dan kuwa ruwa ba ya tsami banza. Can dai ya gyara murya sannan ya ce ‘’Yallabai....’’ ‘’Aisar’’ Saurayin ne ya k’ara katse shi ya k’ara da "tunda zan zauna k’ark’ashin ka ya kamata ka saba da kira na da sunana.’’ Cikin jinjina kai Malam Hamisu ya amsa da "Haka ne Aisar,muna maraba da kai,kuma ina mai tabbatar ma ka mu yan kasa ne masu kishin kasan mu,na gari ma su san ci gaban kasar mu.’’ Ya na mai murmushin nuna gamsuwa Aisar ya tashi tsaye gami da mik’a ma Malam Hamisu hannu ya ce "madallah da kai,kuma na gode kwarai,gobe InshaAllahu zan fara koyarwa sai a bani aji a kuma zaga da ni makarantar sauran Malamai su sanni ko koyar da ni sharad’an makaranta idan akwai, duk abun da ka ke buk’ata in koyar shi zan koyar’’ Mallam Hamisu shi ma in tashi yayi,ya na murmushin yake ya amshi hannun Aisar,fa i ya ke "Madallah Allah ya nuna mana’’ amma a zahirin gaskiya a tsorace ya ke da Aisar. Sai da ya raka shi har kofa ya tabbatar ya tafi sannan ya dawo ofishin sa da sauri dan ha a taron zaman Malamai na gaggawa dan kuwa shi gani ya ke akwai matsala shi ya sa aka mu su shunan Aisar. Shi kuwa Aisar ya na fita shugaban su ya kira ya na mai sheda ma sa yanda su ka yi da Malam Hamisu,Shugaban na su yayi murna kwarai dan kuwa kamfanin da su ke bincike akai kusa da makarantar ne. Ko da ya aje wayar sai ya tsinci kan sa ya na mai waige waige ko zai sake ganin wannan baiwar,amma yawan daliban da ke kai kawo,da wanda su ka sa masa ido ya sa shi kasa gane wacece wace "ba mamaki ma ta sami motar garin na su" abun da ya fa a kenan kafin ya shige motar shi da ya saba basaja da ita ya bar harabar makarantar. Wacece Bintu Bintu Bala Mahuta sunan ta,amma Bintu iyar bayi ake kiranta a masarautar su kasancewa suna aya ta ci da da Gimbiya Binta, wato sunan maihaifiyar ta wacce Allah yayiwa rasuwa wajan haihuwar Gimbiya Binta. Mahaifiyar Bintu wacce ta ke babbar baiwar matar sarki wacce ake kira da uwar bayi,ta haifi Bintu yau,washegari aka haifi Gimbiya Binta kuma mahaifiyar Binta ta ce ga garin ku. Kun ga kenan sunan su aya,banbancin ranar haihuwar su kwana aya,dan haka shekarun su ma aya. Shekarar Bintu goma sha biyar da haihu,mahaifin ta babban bawan wazirin Sa’ayrasa ne,kasancewar haka tare da alfarmar mahaifiyar ta da take babbar baiwar matar sarki mai rasuwa ya sa da za a kai Gimbiya Binta makarantar kwana aka zab’e ta cikin bayi domin kula da ita,dan ko a cikin ‘ya’yan bayi babu wanda ya san fada da al’adun ciki kamar Bintu. Ta wannan hanya aka rab’uka ta cikin makarantar su Gimbiya Binta musammam dan hidimar ta. Amma fa a wahalce ta ke samin ilimi,kai ba ma ilimi ba komai na Bintu cike ya ke da wahala. Wanka ne kawai ba ta yiwa Gimbiya Binta,amma komai na ta ita ce. Wanki da guga da a k’aidar makarantar akwai mai yi musu amma ita Gimbiya Binta sam ba ta yarda sai dai Bintu ta mata,hatta jakar makarantar ta ma Bintu ke gyarawa ta aukar mata. Idan jinga aka ba su sai dai ta yi na ta ta kuma yi na Gimbiya Binta, sai dai idan malamin da ya san rubutun su ne shi ne sai ta jira idan Bintu ta gama ta kwafa. Rubutu kuwa idan an mu su a allo sai dai ta kwafi na Gimbiya Binta,idan sun dawo aki ta kwafi na ta. Batun wajan kwana kuwa aki aya su ke,duk da gadaje biyu ne a akin ba ta isa ta kwanta a gado Gimbiya Binta na gado ba, ah ah sai dai ta sami yar tabarma ta rab’ike daga can gefe a k’asa. Tun masu kula da akin kwanan na magana har sun hakura sun yi shiru dan sun ga tsakanin baiwa da uwar gijiyar ta sai Allah. Bintu ba ta isa ta riga ta bacci ba,kuma dole ta riga ta tashi ta ha a mata ruwan wanka. Wajan cin abunci ba ta isa ta zauna cikin yan uwan ta alibai ta ci abunci ba,sai dai ta jira Gimbiya ta gama,ta raka ta aki ko aji sannan ta dawo ta ci na ta. Kuma a duk in da su ke sai ta tabbatar kowa ya san Bintu iyar bayi ce, shi ya sa ma ta hana ta sa kaya in dai ba shigar bayin Sa’ayyarasa ba idan ranar sa kayan su na gida yayi. Allah ya yiwa Bintu wani abu wai shi tsayi da diri,dan kuwa jikin ta ya girmi shekarun ta. A shekarun ta tana da zubin cikakkiyar budurwa idan ba fuskar ta aka kalla ba ba wanda ba ya b'oye shekarun na ta. Bintu baka ce,irn bakin nan na wayayyun matan nan da ba sa shafa man da zai sake mu su kala. Doguwar fuska gare ta,amma ba mai tsayi sosai ba,ta na da manyan idanu ga hanci har baka,sai wushirya da ke mata kyau duk sanda ta dara ko ta bu e hakora. Ta na da suma matuka,ko ta aure kan ta da kallabi yawan sumar be b’oyuwa. Daga ita har Gimbiya Binta aji uku suke. Ba ta da buri da ya wuce su kai aji shi da su gama makarantar ko ta huta da jarabar Gimbiya,dan kuwa ko k’awaye Bintu ba da shi a makarantar. Aisar Gaddafi Nur Aisar saurayi ne mai kimanin shekara talatin a duniya. Aisar ya da e cikin aikin sa da ya ke matuk’ar so tun kan mahaifin sa ya zama shugaban kasan jamhuriyyar Nijar. Aiki ne wanda ake mu su lakani da mutan b’oye,wato masu bincike da kula da kasa amma ta k’ark’ashin k’asa. Tin hawan mahaifin sa kujerar shugaban k’asa ya na ji ya na gani dole aka dakatar shi saboda yanayin aikin na su na sirri ne hatta sunan da ya ke amfani da shi cikin aikin da ban ya ke da sunan sa na yanka,ba zai yiyu a ha a da siyasa ba dan ba mamaki ma wata rana aiki ya bi ta kan gidan na su. Amma shi ba haka ya so ba. Hakan ya sa sam Aisar ba ya san shiga sabgar gidan gwamnati ko abun da ya shafi harkar siyasar baban shi. Ko zama gidan shugaban k’asan ma be cika yi ba,in ka gan shi ciki toh wajan iyayen sa ya je gaidawa ya tafi,in da Allah ya taimaka ba shi ka ai ba ne ya na da yayye ba laifi, dan ba kowa ba ne ma ya san shi a matsayin an shugaban kasa. Hakan be sa kungiyar Aisar janye dakatar da shi da su ka yi ba,har ma ya fidda rai ya hakura har sai baban shi ya sauka kwatsam ya ji kiran aiki na wani bincike da ya bi ta kan wani kamfani da ke kusa da makarantar su Bintu. Yayi murna kwarai duk da kuwa aikin ba nasa ba ne,shi kawai taimako zai yi shi ya sa sai dai ya rab’uke daga gefe har sai lokacin taimakon yayi. Kungiyar ta su ce ta ba shi izinin neman koyarwa a nan makarantar ta sovereign girls secondry school,su ka kuma ce ya je da sunan sa na ainihi tun da hawan baban sa mulki an fara ya awa cewa ya na kungiyar,kasancewar shi cikin makarantar shi zai ba su damar yin basaja,yanda wancan kamfanin ba za su yi zargin su ake bi ba har su gama binciken su. 2/01/2000 Zaune su ke cikin aji. Kamar yanda ta saba kujerar ta na bayan na Gimbiya Binta. Ta doka uban tagumi in ban da k'ugin yunwa babu abun da cikin ta ya ke dan kuwa raban ta da abunci tin na dare da ke yau sun makara, hakan be sa Gimbiya ta aga mata k’afa ba ta bari ta ci abunci lokacin da ta ke cin abunci,kafin ta gama kuma aka shiga aji. Ta na ji ta na gani sai hakura ta yi. Duka duka ba su kai talatin ba cikin ajin amma gaba aya sun ciki ajin da surutu. Hirar abubuwa masu tsada da k’asashen da su ka tab’a zuwa kowa ya ke. Ita kuwa Bintu da hirar ta su ko hankali ba ya bata sai hamma ta ke,ta kalli agogon bangon ajin,awa aya ya rage a fita gajeran hutu dan cin abunci. Malamin da ya kamata ya shigo kuma ya ki shigowa, sai kawai ta kifa kan ta bisa teburi. Shirun da ta ji anyi ya tabbatar mata da Malam ya shigo aji. Ta yi sauri ta ago kan ta sai gashi kowa ya tashi tsaye ita ka ai ce zaune,baki bu e ganin wanda ya ke tsaye gaban ajin. Kamar yanda ta gan shi jiya yau ma bak’ak’en kaya ne sanye jikin sa,idanun sa rufe da bakin glass. Da kyar ta sa mu ta ja jikin ta ta tashi. Gaishe su yayi cikin harshen turanci nan da nan su ma su gaishe shi. Ya umarce su da su zauna. Da zaman su da jin wani abu ya sauko mata lokaci guda ne,ta yi kasake ta na tunanin wannan wani irin saban lamari ne? Can dai ta yi tunanin dan wannan abun da ya saba zubo mata lokaci lokaci ne. Malam ya gabatar da kan sa a matsayin saban malamin su na fannin zaman lafiya da sulhu [peace and conflict resolution" ta re da fa a ma su sunan sa wato Aisar Gaddafi Nur. Ko da jin sunan aji aka fara kus kus, daga fa in "Gaddafi Nur shugaban kasa?’’ sai mai fa in "haba da ma ni na ga yayi min kama da wanda na sani,ashe dan shugaban kasa ne’’ wata kuma "toh me zai yi da koyarwa kuma?ba mamaki su nan ne ya zo aya dan kuwa an shugaban kasa ya fi karfin koyarwa’’ Ita dai Bintu ta saki baki ta na kallan sa,shi ko lura da ita be yi ba. Gashi ta na fama da wani saban lamari da ke zubo mata har ta na ji ta an fara jikewa. Tun ta na gane abun da ya ke fa a har ta zo ta dena dan kuwa ta fita hayyacin ta. Har fitar sa be lura da ita ba,ita kuwa gaba aya hankalin ta a tashe ya ke ganin abun da ya b’ata ba kayan makarantar ta ba hatta in da ta ke zaune. Aisar na fita jiniya ta yi k’ara,lokacin fita hutun karamin lokaci yayi,dalibai su ka fara fita domin cin abunci da sauran su. Amma tashi ya gagari Bintu. Jaka Gimbiya Binta ta cilla mata yanda ta saba,wato ta auka ta biyo bayan ta. Murya na rawa Bintu ta furta "dan darajar Allah Gimbiya ki yi min rai ki gafarce ni,na tuba’’ cike da mamaki ta juyo ta na duba ta,yan aji tuni kowa ya watse daga ita sai kawayen ta biyu masu masifar girman kai,Ruqayya da Zahira. Zahirar ce ta ce "kun ga shashashar banza,me ki ka yi da za ki hau magiya kamar iyar marok’a?’’ Ruqayya ta amsa da "to menene banbamcin iyar bayi da ta marok’a?’’ Cike da nuna b’acin rai Gimbiya Binta ta ce ‘’jakar tawa ce ba za ki sami damar auka ba ko kuwa tashin ne ya gagare ki?’’ Bintu na kuka ta ce "Allah shi taimake ki,wani abu ne kamar jini ya zubo min.......’’ ‘’JINI!’’ Ruqayya da Zahira su ka ha a baki yayin da su ka ja gefe cikin nuna kyamkya mi. A wulakance Gimbiya ta ce "duk sanda jinin ya dena zubo mi ki kya tashi,dan Allah ku zo mu tafi ko na dai na ganin wannan k’azantar’’ Zahira ce ta auki jakar na ta su ka tafi su ka barni. Tini duk wata yunwa ta dena jin ta,ta aura kan ta bisa taburi ta na hawaye,ta rasa in da za ta sa kan ta. Ba ta jima a haka ba ta ji wani sanyayyen kamshi ya bakonci hancin ta,a hankali ta ago. Hannun sa ruk'e da bakin gilashin sa,fuskar sa auke da alamar tambaya, ya ce ‘’wannan fuskar ina na san ta ne?’’ Bintu ta yi saurin kau da kai gefe ta na mai adduar Allah kar ya tuna. Ai kuwa dai adduar ta ba ta karb’u ba jin ya ce "Sa’ayyarsa,tabbas. Dama ke daliba ce a makarantar nan?me ya same ki ki ke kuka?ko dama ke kullum cikin tashin hankali ki ke? na wucewa na hango ki kai kife kan tebur bayan yan uwan ki dalibai suna can suna cin abunci’’ maimakon ta bashi amsa sai ta yi ka sake ta na kallan sa yayinda hawaye ke zuba daga idanun ta. Ya ce "ba da ke magana ba?ba kya ji ne?’’ rasa abun da za ta ce masa ta yi sai hawaye kawai. Nan fa ya k’ule be sanda ya daka mata tsawa ba ya na mai fa in "tashi tsaye na ce!’’ Ba ta san sanda ta tashi tsaye a gigice ba,nan idanun sa ya sauka bisa kujerar da ta ke zaune,sannan ya dawo da kallan sa ga kayan makarantar ta da ya b’aci. ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 0⃣3⃣ Tausayin ta ne ya lullu6e shi,dan daga ganin yanayin ta ka san fararriya ce. ‘’zauna ina ki jira ina zuwa’’ Ya fad'a a sanyaye,kafin ya juya ya fita ba tare da ya jira ta amsa masa ba,dama ko ya jira in ma ba amsawa za ta yi ba. Cike da da kunya da takaicin yanayin da ya gan ta, ta koma ta zauna, gaba d’aya ji ta yi ta tsani kan ta,kan ta ta kifa bisa teburi. Jim ka d’an ta ji muryar d’aya daga cikin masu kula da d’akin kwanan dalibai,wacce su ke kira iya Dije,ta na fad’in ‘’wacece ne? d’ago kan ki na gan ki’’ Bintu ta d’ago kan ta a hankali ta dube ta. Ganin fuskar Bintu ga idanun nan na ta ya yi jajur dan kuka Iya Dije ta ce ‘’aw Bintu da ke ce?yo menene na kukan har haka? Ai girma ne ya zo,maza ungo wannan zanin ki d'aura mu je ki gyara kan ki’’ Ta mik’a mata zani,hannun Bintu na rawa ta kar6a da saurin ta. Ta tashi a hankali ta d’aura zanin ta na mai bin kujerer da ta 6’ata da kallo. ‘’kar ki wani damu da wannan, Shatu na nan tafe za ta gyara,ke dai mu je ki fara gyarawa tukun’’ Fad’in Iya Mairo yayinda ta d’auki jakar Bintu ta wuce gaba,Bintu na biye da ita. D’akin kwanan d’alibai su ka wuce, d’akin su Bintu ta zauna ta yi jiran ta bayan ta koya mata yanda za ta yi ta gyara kan ta. Sai da ta yi wanka ta shirya sannan ta wanke kayana da zanin da Iya Dije ta bata. Bayan ta gama ne ta je ta sami Iye Dije zaune ta na jiran ta. Kamar wacce ta yi laifi ta d’an ra6e daga gefe,kan ta sunkuye ta ce ‘’Iya Dije na gode da kulawar ki,wallahi ba da sani na ba ne,ban ta6’a ganin irin haka ba’’ Murmushi Iya dije ta yi jin maganar Bintu,kana ta dafa kafad’ar ta tana mai fa’d’in ‘’Yaro dai Yaro ne,dama kowa akwai ranar da ya ke farawa,kuma kowace cikakkiyar budurwa ta na yi,auta ta ma ba ta dad’e da farawa ba’’ Da sauri Bintu ta d’ago kan ta ta ce "Allah? ita ma ta yi kuka?’’ ‘’ah ah’’ Iya Dije ta amsa mata,sannan ta k'ara da ‘’da ke ta tashi cikin mata kuma ta na zuwa islamiya toh ta san komai,kawai dai ta shiga damuwa na rashin sabo,da fatan ki na dai zuwa islamiya a masarautar ku’’ Bintu na mai girgiza kai ta ce ‘’ah ah makarantar allo na ke zuwa,shi ma kuma sai idan babu aiki sosai a fada,da aka sani wannan makarantar ma sai na dena zuwa gaba d’aya’’ Iya Dije ta ce "assha ai makarantar islama na da muhimmanci ga rayuwar d’iya mace, kin ga da kina zuwa da yanzu kin san duka hukunce hukunce da ya hau kan ki, lalle idan an yi huta ki ce da gyatumar ki ta sanya ki cikin islamiya, ba a tsufa da neman ilimi bare ke da kuruciyar ki kin ji ko?’’ Bintu ta gyad’a kai. Kana Iya Dije ta kara da ‘’yanzu hukunci babba ya hau kan ki tunda kin balaga, yanda za a rubuta wa mahaifiyar ki ko ni kai na hukunci haka ke ma za a rubuta mi ki dan kuwa yanzu mu da ke duk d’aya ne har ga Allah, kin tashi daga yarinya. Dan haka ki kula ki kyau ta ta rayuwar ki ta duniya da lahira, ki ruk’e mutunci ki da na iyayen ki. Ba ruwan ki da maza muddin ba da kwakkwaran dalili ba,kin dai san mai wasa da maza karya ce ko?’’ Kai sunkuye Bintu ta jinjina kai alamar ‘’eh’’ Iya Dije ba ta gushe ba ta k’ara da ‘’yauwa, wannan sabon Malamin da ya zo yayi kira akan ki, menene dangantakar ku?’’ Nan fa Bintu ta fara kame kame, ta ce "iye? na’am? Wai wannan d’in nan? wallahi ni ma ban san shi ba Iya Dije,yau ya fara koyar da mu fa" Cikin nazari Iya Dije ta kura mata ido kafin daga bisani ta nisa ta ce ‘’kar ki saki jiki da kowane d’a namiji muddin ba muharramin ki ba ne, wato wadda babu auratayya tsakanin ku, kar ki sakarwa kowa fuska ko hannu kar ki yarda wani ya ta6’a ruk'e mi ki idan ba haka ba mutuwa za ki yi,kin ji ko?’’ A tsorace dan ta ji batun mutuwa ta amsa da ‘’Toh, wallahi dama ni ba ruwa na da maza, ko a masarautar mu ma ba na sakar mu su fuska, yaya Ubaliya ma sheda ta ne’’ Kai Iya Dije ta jinjina alamar gamsuwa. Nan ta cigaba da bawa Bintu shawarwari. Ko da ta zo tafiya har ta kai ga k’ofa ta ce ‘’Bintu ya batun turare ina fatan dai ki na da shi, dan yanayin da ki ke ciki sai fa da turaren’’ Bintu na d’an soshe soshe ta ce "Iye?dama dai Inna ta ta bani garin alimun ta ce ina had’awa da leman tsamin sai na ke gogawa a hammata ta’’ ‘’eh toh wannan ma ba laifi,amma ki na bukatar turare,dama wannan Malamin ya ce na fad’a masa idan ki na da bukatar wani abu,na fad’a masa. Kuma kar ki manta ki na canza wannan audugar da na baki a kankari, ban da k’azanta dan Allah idan ba haka ba kuwa za ki ji ki kina wari na gaske’’ Cike da jin kunya su ka yi sallama, Bintu ta mata godiya sosai. Bayan fitar ta ne ta ji yunwar da take ji ya dawo ma ta, saboda haka sai ta bu6e akwatin k’arfen ta,ta fito da ajiyar garin kwakin ta da kuli ta sha ta k’oshi. Ta na gamawa da saurin ta ta gyara wajan dan kar Gimbiya Binta ta gani ta zubar mata da ragowar. Ko da ta ga ta sami nutsuwa,ta shifid’a tabarmar ta, ta yi kwanciyar ta kafin lokaci ya cika ta koma aji. Gaba d’aya kunyar Malamin nan ne ke damun ta musammam yanzu da Iya Dije ta fed’e mata daga bindi har wutsiya na game da sabon rayuwar da ta shiga,ga shi shi dai kullum ba ya sa’ar ganin ta cikin hayyacin ta. Da wannan tunanin bacci mai dad’in gaske yayi gaba da ita. Saukar marin da ta ji ya sa ta yi firgit ta tashi zaune hannun ta bisa kuncin ta ta na mai murzawa. Ba ta bari ta gama wastsakewa ba ta rufe ta da zagi, fad’i ta ke ‘’dan uban ki wannan bawan har ki zo ki kwanta ki na barcin asara kin manta bauta ya kawo ki makarantar nan? k’azama wawuya!’’ Da sauri Bintu ta d’urk’usa jika na b'ari ta ce ‘’Allah ya huci zuciyar gimbiya, tuba na ke, ban san sa’in da baccin ya sace ni ba, ki min aikin gafara’’ A wulak'ance Gimbiya Binta ke duban Bintu,kafin ta furta ‘’ga wanki can na su diras d’ina,bayan kin gama ki min guga. Kuma ki sani yau bazan iya kwana d’aki d’aya da ke ba cikin wannan k’azantar da ki ke. ki d’au k’azamar tabarmar ki ki aje daga can lungun,kuma ki san abun da za ki ce da su Iya Dije su ka gan ki a nan kwance dan idan ki ka kuskura ki ka kira sunana wallahi sai na lahira ya fi ki jin dad’i’’ Cike da ladabi Bintu ta duk’a ta na mai fad’in ‘’Godiya na ke ran ki shi dad’e’’ Gimbiya Binta ta k’ara da "wallahi na tsane ki,duka cikin bayain fada babu wanda na tsana kamar ke,wai amma a rasa wacce za a had’u ni da ita sai ke!’’ Ta shure Bintu ta wuce ciki,kan gado ta nufa ta zauna d’ai-d’ai abun ta. Kai sun kuye Bintu ta tashi, ta nad’e tabarmar ta sannan ta kwashe wankin Gimbiya. Gaba d’aya a takure ta ke yin komai musammam yanda tafiya ma mai kyau da kyar ta ke gudun kar ta sake b’aci. Sai da la’asar sakaliya ta gama wankin,bayan ta yi shanya ta na shirin fara guga su Zahira su ka shigo d’akin. Nan fa su ka zauna in ban da maganar Aisar babu abun da su ke. ‘’Aisar Gaddafi Nur ai ba k’aramin had’uwa yayi ba’’ fad’in Gimbiya,ta k’ara da ‘’ni abun da ke ban mamaki ganin shi a matsayin malami’’ "ko ni ma na yi mamaki gaskiya’’ Zahira ta taya ta.Ajiyar zuciya Gimbiya Binta ta saki kana ta ce "ni fa k’awaye na wallahi na kamu, gaba d’aya ya shiga rai na’’ Maryam da Zahira su ka sa shewa, Maryam ce ta amsa mata da "ai dama ni tuni na d’ago jirgin ki,kar ki damu ai jinin sarauta ba sa nema su rasa’’ ‘’ko ba dan jinina ba ai na isa a soni,ba ku lura da yanda ya ke kallo na ba ne?’’ Fad’in Gimbiya cike da tak’ama, wanda hakan ya sanya k’awayenta yi mata kirari su na dad’a wasa ma ta kai. Bintu da ke jiyo su daga can gefe ta murmusa cikin ranta fad’i ta ke "Malam Aisar ya cika jarumi tinda har ya shiga ran Gimbiya’’ ajiyar zuciya ta saki ta na mai fatan Allah ya tabbatar da alkhairi. ******* Kamar yanda Gimbiya Binta ta ce,ranar a d’an wani lungu cikin d’akin Bintu ta samu ta ra6’e. Da kyar ta iya samun bacci saboda sauro. Da asubar fari Gimbiya Binta ta tada ita,kuma ba ta bari ta yi amfani da band’akin su ba,sai k’asa ta sauka. Bayan sun shiga aji sun fito hutun cin abunci da azahar, Gimbiya ta hana ta zama cikin d’akin cin abunci,wai ta na sa ta tashin zuciya. Tsaye ta ke bakin d’akin cin abunci, sai had’iyar yawu ta ke dan yunwar yau tafi ta kullum. Rana ko ta take sosai dan kuwa su na sa ran samuwar ruwan sama kwana kusa. Gashi in da ta ke tsaye sam babu inuwa, bini bini sai ta sa tafin hannun ta ta goge zufar da ke faman ketowa bisa kuncin goshin ta. Da ta ga abun ba na k’arau ba ne,ta sanya hannun ta cikin aljihu ta d’auko k'ulin ta da ta d’an k’unso a yar leda. Wata bishiya ta hango,kai tsaye ta nufe shi ta na k’ok’arin kwance ledar k'ulin. Ta gaban d’akin cin abuncin malamai wuce. Ta taga ya hango ta,lokacin guda ya bar cin abuncin da ya ke hannun sa ruk'e da cokali ya bi ta da kallo. Tin da ya ke be tab’a ganin wacce ta iya tafiya tafiya irin na Bintu ba. Tafiya ce a nutse ko wacce k’afa in aka aje sai an tsagaita kafin ta biyu ta biyo ta. Gashi dai babu alamar tak’ama a tattare da tafiyar amma sai ta zama tak’amar ce ma gaba d’aya. Kuma tsayin ta ya sa haka. Be dene kallan ta ba har ta isa ga bishiyar ta zauna. Ganin ta bud’e wata yar leda ta na fitar da wani abu ta na afawa a bakin ta sannan ya tuna fa yanzu lokacin cin abuncin d’alibai ne,me ta ke yi a waje,ya aje cikoli ya tashi kai tsaye ya fito ya nufo in ta ke zaune. Bintu ta ba ta hango shi ba,ba ta kuma ga tahowar shi ba,ta ciko hannun ta da kuli kenan ta afa a bakin ta , sai kawai ganin shi ta yi tsaye kan ta,bakin ta cike da k'uli ta d'ago kai su ka had’a ido nan da nan gaban ta ya fad’i,cikin zuciyar ta kuwa ihu ta kurma ‘’wayyo ni Bintu aradu wagga Malami ya takura ni!’’ 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 0⃣4⃣ Cikin sauri ta tashi tsaye ta gaishe shi da harshen (French) faransanci wanda da dama da shi su ka fi amfani a makaranta. Gaba d’aya ta manta da wani kunyar sa da ta ke ji yanzun da ta gan shi tsaye gaban ta dan kwarjinin da ya mata. Kan ta sunkuye tana wasa da ledar k’wilin ta ya amsa mata a takaice fuskar babu walwala ya ce ‘’me ki ke yi waje lokacin cin abunci?’’ ‘’Gimbiya Binta na ke jira ta gama cin na ta sai ni ma na ci nawa’’ ta amsa zuciyar ta d’aya ba tare da ta d’aga kai ta kalle shi ba. Cike da mamakin amsar ta ta ya ke duban ta, ita sam bata lura da kallan na ta da ya ke ba. Kana ya ce "wacece Gimbiya Binta?’’ jin tambayar na sa Bintu ta bud’e baki,cike da mamaki ta ce "laa ba ka san Gimbiya Binta ba? Yar sarkin Sa'ayrasa fa, wata fara tas kamar d’iyar larabawa, ta na da kwarjini matuk’a’’. Badaban ran sa a 6ace ya ke ba, yanda ta ke kod’a Gimbiyar ta ta sai da ta kusa ba shi dariya. Amma sai dad’a tsuke fuska ya yi kafin ya k’ara da ‘’ban san wakike magana akai ba, amma abunda na ke so na sani shi ne shin dokar makarantar ce sai wata Gimbiya ta gama cin abunci kafin sauran d’aliban su ci ko kuwa?’’ Tuni Bintu ta fara shan jinin jikin ta dan kuwa tabbas idan hukumar makarantar ta ji wannan maganar matsala zai zame mata. Kana ta ce "iye! Na’am? Dama wai,dama ai..........’’. "dama me?” ya katse ta ya na mai duban ta. Nan fa Bintu ta shiga cikwikwiya ledar hannun ta, ta rasa amsar da za ta ba shi. "dokar makarantar ce sai wata Gimbiya ta gama cin abunci kafin sauran d’aliban su ci ko kuwa?’’ ya dad’a maimai ta mata tambayar cikin k’aguwa. Ganin ba ta da niyar amsawa rai 6ace ya furta "menene dangantakar ki da wannan da ki ke kira gimbiya ?ya sunan ki?’’ Cike da tsoro Bintu ta amsa ma sa "sunana Bintu, Bintu Bala Mahuta, ni d’iyar bayi ce, ni ce baiwar da ke kula da Gimbiya Binta ta masarautar Sa’ayrasa.....’’ ‘’wannan ne ya bata damar hana ki abunci? Haka ake gudanar da lamarin wannan makarantar? Saboda zalinci? Toh daga yau ya k’are ni Aisar ba na san zalinci kuma ba zan juri ganin zalinci ba’’ ya na gama magana ya juya a fusace ya fara tafiya, ganin haka Bintu da tun da ya fara magana ta gama firgita, ba ta san sanda ta saki ledar k'wilin ta ba, ta bi shi da sauri tare da shan gaban sa, sai ga ta ta zube gwiwowi biyu a kasa. Da sauri ya ja ya tsaya ya na mai duban ta cike da mamaki ganin duk zafin ranar be hana ta saka tafukan hannayen ta biyu k’asa ba ta mai duk’ar da kai kamar wacce ta ke shirin shigewa k’ark’ashin k’asa. Hankali tashe ta shiga jero masa magiya ta na mai fad’in "tuba na ke, ka gafarce ni, na tuba, ka yiwa Allah da manzon sa kar ka had’a ni da Gimbiya, aradu idan ta ji wannan maganar na kad’e har ganye na,ka min rai, na tuba....’’ ta k’arasa maganar na ta cikin kuka. Aisar kuwa kasa magana yayi ya na mai duban ta cike da tausayawa kana daga bisani ya ce ‘’tashi....." maimakon ta tashi sai ta dad’a kask’antar da kai ta yi kasa ta na kuka, jin kukan na ta ya ke har ran sa. Idanun sa runtse ya ce ‘’ya salam wannan wata irin yarinya ce mai shegen taurin kai! ki-ta-shi-na-ce’’ a hankali yayi maganar kamar mai koyan magana. Sai a sannan ta tashi, amma har lokacin hawayen ta ke. Kallan ta yayi na wasu dan dak’ikai, kafin ya mata nuni da inuwar da ya tadda ta zaune ya ce koma can ki zauna ina zuwa. Baki ta bud’e da niyar yi masa musu, amma ko da su ka had’a ido sai ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’toh’’ ta yi sauri ta koma k’ark’ashin bishiyar in da ta jingina jikin ta, ta na mai mayar da ajiyar zuciya ganin Aisar shi ma ya juya ya tafi. Ta na mai addu’ar Allah ya sa ya hakura kar ya dawo har ta samu ta shiga d’akin cin abunci. Sai a sannan ta lura da ledar k’ulin ta a k’asa ta yi sauri ta d’auko ta ka6e dattin da ya mak'ale jikin ledar kafin ta tura cikin aljihun ta dan kuwa shi ma ya fita ran ta. Jim kad’an Aisar ya dawo d’auke da wata yar bakar leda, ya mik’a mata ledar tare da fad’in "gashi maza ki je ki sami waje ki ci’’ ledar ta bi da kallo, wani irin kamshi ke ziyarta hancin ta daga cikin ledar, tuni ta mayar da mugun yawu, ta na mai girgiza kai ta ce "ah ah na gode ai ba na jin yunwa dama’’ "ba kya jin yunwa?’’ ya maimaita cikin sigar tambaya. Kai ta gyad’a masa alamar eh. Amma mai za su ji? ‘’kulululu’’ sautin da ya fito daga cikin ta kenan wanda ya ke gasgata zargin Aisar na Batun Bintu ba ta jin yunwa yasasshen zance ne. Cike da jin kunya ta sunkuyar da kai k’asa, duk 6acin ran sa sai da ya tsinci kan sa ya na mai murmusawa. ‘’kar6a ki ci maza kafin a koma aji’’ sai da ta d’an yi jim, kafin daga bisani ta sa hannu biyu ta karb’a ta na mai godiya, fad’i ta ke ‘’Godiya na ke, madallah, Allah ya saka ma da alkairi’’ ba ta jira jin amsar shi ba tayi gaba, hannu na rawa ta ke k’ok’arin bud’e ledar dan ganin abun da ya ke, ganin lafiyayya abuncin da ke cikin ledar tuni ta fara k’ok’arin fara kaiwa baki dan ta ma manta da Malam Aysar da ya bi ta da kallo cike da tausayawa har ta k’ure masa. Kai ya jinjina ya na mai shan alwashin maganin wannan zalincin da Gimbiya ta ke yiwa Bintu na hana ta cin abunci cikin d’alibai yan uwan ta. Shin dama har yanzu ana irin wannan zalinci? wannnan wani irin sakaci ne daga hukumar makarantar, da ga alama dai ba banza ta kawo shi makarantar ba, babu mamaki watan rufe makarantar ce ta tashi muddin ana irin wannan zalincin da sanin hukumar makarantar. Da wannan tunanin ya nufi ofishin Malam Hamisu. Yayi rashin sa’a ba ya nan dan haka dole ya hakura ya koma ofishin zaman malamai da k’udirin cikin ran sa. Yanda Bintu ke cin abunci kamar wacce ta shekara ba ta ci ba ya sa ta saurin gamawa kafin su koma aji. Suna komawa kuwa lokacin koyarwar Aisar ne. Da shigowar sa ba tare da 6ata lokaci ba ya fara abunda ya kawo shi, wato koyarwa. Darasin na sa yau akan "Gaba" ne. Aisar ya fara da tambayar misalan yankuna ko masarauta masu tarihin gaba tsakanin su, ba jamhuriyar Nijar kad’ai ba har mok’otan su. D'aya daga cikin d’aliban ce ta d’aga hannu, in da Aysar ya bata damar amsa tambayar, ta ce "kamar gabar da ke tsakanin masarautar Sa’ayrasa da masarautar Fabarusa’’ Aisar na mai jinjina kai ya ce "haka ne ku tafa mata’’ aji aka d’auki tafi "raf raf raf" Bayan haka ya k’ara tambayar "su waye ‘yan masarautar Faburasa cikin ajin nan?’’ wajan mutum uku ne su ka d’aga hannu, bayan wani d'an sakanni ya ce su sauke, masarautar Sa’ayrasa ma su d’aga hannu. D’alibai shida ne su ka d’aga hannu, ciki har da Gimbiya. Bintu kuwa ta na can ta na tunanin duniya, gaba d’aya hankalin ta ba ya ajin. Hannun su d'age be ba su izinin saukewa ba dan shi hankalin sa kan Bintu ya ke, suma kuma ‘yan ajin sun lura da hakan dan su ma d’in Bintu da ta doka uban tagumi su ke kallo. Kamar daga sama ta ji ya ce ‘’Bintu hankalin ki ba ya aji na!’’ ta yi firgit ta dawo cikin hankalin ta ta na mai cire hannun ta daga tagumin da ta yi. Ganin idanun kowa kan ta, ga hannun wasu daga cikin yan ajin har da Gimbiya d’age ya sa Bintu kai duban ta ga Aisar, in da shi kuma ya maimaita mata umarnin da ya ba su. Da saurin ta ta d’aga na ta hannun sama sannan ya ce su aje hannun na su. Wata har da fad’in "wash hanuna" a hankali yanda Aisar ba zai jiyo ta ba. Bintu ba ta tsorata ba sai da ta ga Gimbiya ta juyo ta watsa mata harara. Wani mugun yawu ta had’iya tuni hantar cikin ta ta kad’a. Malam Aisar kuwa be gushe ba ya cigaba da "shin wa zai fad’a min lokacin da gabar ta samo asali?’’ d’aya daga cikin su ta amsa da "gabar ta samo asali ne tun kaka da kakanni amma anfi dangan ta shi da lokacin mulkin sarki Abdulrahaman III na masarautar Faburusa’’ Malam Aisar ya ce a tafa mata sannan ya sake tambayar hanyoyin da ya dace a bi domin kawo karshen gaba tsakanin k’asa da k’asa ko masarauta da masarauta. Dalibai da yawa su ka d’aga hannu, amma ga mamakin kowa sai ji su ka yi ya ambaci sunan "Bintu’’ ‘’Wayyo shi dai sai ya fad’awa kowa ya san sunana ko menene haka?’’ ihun da Bintu ta kurma cikin ran ta kenan. Gaba d’aya ajin idanu su ka zubo mata yayinda ta tashi a hankali murya kamar ba nata ta ba, ta furta abun da ya fara zuwa bakin ta "auratayya tsakanin masarautar’’ nan fa aji aka kwashe da dariya, Zahira ta ce "auratayya tsakanin bayi, d’iyar bayi ta auri dan bayi.....’’ aka dad’a sa dariya. Kunya ta rufe Bintu kamar ta shige k’ark’ashin kujera ta 6uya. "shiru!’’ Aisar ya daka musu tsawa. Aji yayi shiru kamar wanda ruwa ya shanye, ran malam ya 6aci. ‘’wata mara tarbiya ce ta yi wannan maganar?’’ ya tambaya a fusace. Aka rasa mai bashi amsa, har sai da ya sake maimaitawa sannan Zahira ta tashi tsaye gwiwa a sanyaye. Bintu ya duba ya umarce ta da ta zauna kafin ya koma ga Zahira. Ya ce da yan aji kowa ya dube ta, shin ita yar wata yanki ce. Ta na zumb’ure zumb’ure ta amsa da ‘’Niamey’’ kai ya girgiza kan ya ce ‘’Niamey na alawadar da masu hali da kalimi irin na ki, kalamai ne irin na marasa tarbiya wanda su ka tashi a watse, lalle idan har Jamhuriyar Nijar na da yan k’asa irin gaba tsakanin yankuna ba zai tab’a yankewa ba, fitar min daga aji kuma kar ki sake shigowa in har ni ne cikin ajin’’ Zahira ta wuce fuuuu za ta fita ya ce ‘’dube ta k’azama kawai’’ kunya ya rufe ta ta fice da sauri. Jikin kowa yayi sanyi, tin ba ma Bintu ba. Aisar kuwa be sake cikakken minti goma ba ya fice da ga ajin,dan kuwa tabbas d’aliban makarantar na fama da rashin tarbiya na gaske. Surutai kuwa ta sha wajan yan aji, daga mai fad’in "kun ji yanda ya ke kiran sunan ta kuwa?’’ sai mai fad’in ‘’ta yaya ya san sunan ta bayan be ta6a tambayar sunayen mu ba?’’ ita kuwa Bintu kai ta kifa bisa teburi dan Allah kad’ai ya san masifun da ke gudana cikin zuciyar Gimbiya, ta san yau kam sai yanda aka yi da ita wai d'an daudu a kabari. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 0⃣5⃣ Bayan an tashi daga makaranta, ko kallan ta Gimbiya Binta ba ta yi ba ta ta wuce gaba ita da Ruqayya, Bintu na rawar jiki rik’e da jakar Gimbiya ta bi bayan su. Ba su zame koina ba sai d’akin su in da su ka tadda Zahira na jiran su dan gasawa Bintu gurasa danya a hannu. Zagaye Bintu su ka yi tsakiyar d’aki, sai ta fad’a musu yanda aka yi Aisar ya san ta yasan sunanta da har ya ci mutuncin Zahira saboda ita. Bintu na raba idanu ta ce ‘’Dan Allah Gimbiya ki min afuwa, aradu shi da kan sa ya tambayi sunana........’’ Ji ka kake tas! Gimbiya ta kwashe ta da marin da sai da Bintu ta ga wuta a idonta, a gigice ta sa hannu bisa kuncin ta na mai fashewa da kuka. Gimbiya ba ta gushe ba ta ce " Yar iska! A shekarun ki har kin iya karuwanci?!!!’’ Ta sa k'afa ta shure Bintu. "Yo dama ana raba bayi da karuwanci ne Gimbiya?’’ Rukayya ce ta ara ta yafa. Zahira ta k’ara da, "Wallahi tunda ki ka sa mutum kamar Aisar ya ci mutuncina sai kin yabawa aya zak’inta." Ita dai Bintu ta kasa magana, kanta durk’ushe, sautin kuka kad’ai ke iya fita daga bakinta. Gimbiya ta ce ko dai ta fad’a mu su yanda aka yi ya san ta har ya tambayi sunan ta ko ta kira waya fada a zo a mayar da ita Sa’ayrasa. Jin haka haka nan da nan Bintu ta shaida musu komai. Duka da mari babu wanda ba ta sha ba. A fad’ar Gimbiya don tasan tana da k’udirin auren Aisar ya sa ta ke masa shisshigi dan ta 6ata ta wajan shi, toh wallahi ta yi kad’an, duk randa ta yarda wani abu ya k’ara shiga tsakanin su ta tabbatar ranar zaman ta a wannan makarantar ya k’are. "Godiya nake Gimbiya’’ a Abinda ke fita daga bakin Bintu kenan har su ka k’araci masifar su, su ka tafi d’akin Zahira. Bintu na zaune inda suka bar ta, ta had’e kai da gwiwa in ban da ajiyar zuciya babu abun da ta ke, sai ga Iya Dije ta shigo da sallamar ta. Ganinta Bintu ta yi saurin gyara zama ta na mai k’ok’arin goge hawayen da ke fuskar ta gudan kar Iye Dije ta gani. Cike da mamaki Iye Dije ta ce "Bintu lafiya? Me ya sa ki kuka haka? Ya na ga idonki d’aya ya kumbura?’’ "Ba na jin dad’i ne Iya Dije, ciwon kai da ido na ke’’ Bintu ta yiwa Iya Dije k’arya gudun abun da zai je ya dawo. Cikin nuna tausayawa Iya Dije ta ce " Ayya Allah ya sauwake, na ce dai kin je kilinik (clinique, karamin asibitin makarantar) an duba ki ko?’’ Kai Bintu ta girgiza alamar ah ah, sannan ta k’ara da ‘’Ba sai na je ba, ina da magani, idan na sha shikenan." Kallan ta Iya Dije ta ke kamar mai nazarin wani abu, kafin daga bisani ta ce ‘’Toh Allah ya sauke.’’ Ta ja wata yar kujera ta zauna sai a sannan Bintu ta lura da ledar hannunta, a gaban Bintu ta aje ledar kan ta tambaya "Shin al’adar ta ki ta d’auke ne?’’ Cikin nuna jin kunya Bintu ta girgiza kai alamar ah ah. Iya Dije ta ce "Ai bakomai, dama daga kwana d’aya har zuwa kwanaki goma sha biyar yakan iya kai wa. Dama batun turaren ne, Malam Aisar ya ba ni kud’i, sanin ba a bari dalibai su fita daga makaranta yasa na yi karambani na siyo miki’’ Ta sa hannu cikin ledar sai gashi ta fito da kwalaban turare har guda uku, ta aje gaban Bintu ta na fad’in ‘’Kinga wannan Danduwala ne, ga kuma Kafin-kafin, ga Binta Sudan duka na ki ne." Ta k’arasa maganar tana mai washe hak'ora don tasan ba k'aramin gwanin ta ta yiwa Bintu ba, duk da dai rabin kud’in da Aisar ya bata a aljihun ta ya k'are. Bud’ar bakin Bintu sai cewa ta yi "Iye Dije na gode amma dan Allah ki mayar masa, aradu ba zan iya karb'a ba, ba na so’’ ‘’La'ilaha illallahu!" Fad’in Iye Dije ta na mai tafa hannu "Ku ga yarinya za ta watsan k'asa a ido! Ba kya so a na wani dalili? Iyye?!!!’’ Ta yi tambayar ta na mai fidda idanu ganin Bintu na shirin kwance mata zani a kasuwa, don kuwa karya da gaskiya ta had’a ta fad’awa Aisar kan buk’atun Bintu, haka ya bata kud’i CFA na gugan CFA har (10000 CFA), fiye da rabin kud’in ta kashe. Bintu ta rasa amsar da za ta bata, ta tsinci kanta tana mai fad’in ‘’Na ga ba na buk’ata ne Iya Dije.’’ Ba ta ankara ba sai ganin Iya Dije ta yi ta d’aga hannunta tana mai k’ok’arin cusa hancin ta k’ark’ashin hammatar Bintu. Da sauri Bintu ta ja da baya ta na k’ok’arin kwatar kanta, fad’i ta ke ‘’Iye Dije ya haka?” Iya Dije kuwa duk da babu abinda ta shak’a na wari daga jikin Bintu don kuwa Bintu irin mutanen nan ne wanda sam ba su da warin jiki, sai ga ta ta yi baya da sauri ta na mai toshe hanci ‘’Kin ji yanda ki ke bugawa ki na hamami kuwa? Har ki ce ba kya buk’ata? Shi kan shi Malam Aisar d’in wannan hamamin na ki ya ji shi ya sa ya ce na tambaya ko ki na da buk’atar turaren.’’ Jin haka kunya ta rufe Bintu, kamar k’asa ta bud’e ta shige. Ta na mai yin k’asa da ido ta ce ‘’Ai idan Gimbiya ta gani ko ta ji ina kamshin turare ma su k’amshi haka Iya Dije kashi na ya bushe’’ Sai a sannan hankalin Iya Dije ya fara kwanciya, ta ce ‘’Yo ba sai ki 6oye yanda ba za ta gani ba, sai ki na sawa kad’an haka, ni dai ba zan mayar da wanga turare ba’’ Ajiyar zuci Bintu ta saki ganin babu yanda za ta yi dole ta hakura ta kar6a ta na mai godiya. Ita kuwa Iya Dije ko da ta samu ta cusawa Bintu turare sai ta sami kwanciyar hankali, dan da ba ta san yanda za ta yi ta biya da kud’in Aisar da ta ci ba. Aisar kuwa sai da ya tabbatar ya kaiwa Malam Hamisu k’orafinsa kan rashin tarbiyar d’alibai da kuma zaman wata d’aliba a waje lokacin cin abinci ba tare da ya ambaci sunan Bintu ba. Malam Hamisu ya nuna rashin saninshi kan maganar yanayin cin abincin d’aliban, kuma ya yi masa alk’awarin d’aukar mataki. Saidai batun rashin tarbiyar d’aliban ya ce su ma hakuri su ke da su kasancewar kowani tsuntsu kukan gidansu ya ke, amma In sha Allahu za su k’ara tsauri kan lamarin. Washagari da safe wajan taron d’alibai (Assembly), Mallam Hamisu ya ja kunnan d’alibai akan bin duka, musammam wanda ba sa halartar wajan cin abinci idan lokacin yayi, ya kuma tsawatar da hukunci mai tsanani muddin aka ga d’aya daga cikin d’aliban na aikata hakan. Da wannan Bintu ta sami saukin samin cin abinci tare da yan uwan ta d’alibai duk da kuwa sai da ta sha tuhuma gun Gimbiya akan zargin ko ita ta kai k’arar ta. Kwanci tashi haka rayuwa ta kasancewa Bintu cikin makaranta. Gaba d’aya gudun Aisar ta ke, tun shi ma bai gane ba har ya zo ya gane ya daina nemanta. Ita kuwa Zahira hakuri ta je ta bashi tare da sa bakin Malam Hamisu ya hak’ura ya bari ta koma ajin na shi. Gimbiya Binta babu irin cusa kai da ba ta yiwa Aisar, amma sam ba ta gabansa bare ya san ta na yi, manyanta ma yan aji biyar da shida fama su ke bare ita karan kad’a miya acikin jerin ‘yan mata. Da yammacin ranar lahadi, ana saura sati biyu su Bintu su fara jarabawa. Yanda garin yayi wasai, gajimare yayi lub-lub, ciyawa da bishin da ke cikin lambun sun yi kore shar, ga wani ni’imatacciyar iskar da ked’awa wanda sanya rassa da ganyayyakin bishiyun da ke cikin lambun rausayawa suna mai fuzar da feshin ruwa sanadiyar ruwan sama da ya sauka ya kuma tsaya mintina talatin da su ka wuce ne ya sanya Aisar da ke kwance kan kujerar hutun da ke k'ark’ashin d’aya daga cikin rumfunan lambun, in banda kukan tsuntsaye da kuma k’arar saukar sauran ruwan sama da yayi ragowa bisa kwanan rumfar lambun babu abun da ke tashi. Sanye ya ke cikin bakar riga mai k’aramin hannu, da wando wanda ya ke shi ba gajere ba bai kuma kai masa har k’asa ba. Idanunsa lumshe tamkar mai bacci, ko da yake da zai sami bacci da hakan zai fi so dan kuwa tunanin da ya dad’e ya na damun sa yanzun ma shi ya sa shi gaba. Ba kuma tunanin kowa bane, face na Bintu, musammam yanzu da aikin binciken su ya k’are, Bintun ce ta zaunar da shi a makarantar da tuni ma ya dakatar da koyarwa, dan kuwa dai hakin su ya riga ya cimma ruwa a game da aikin su. Abin takaicin shi ne tsakanin sa da Bintu sai dai a aji, duk yanda zai yi ya ganta bayan aji ya gwada amma abu ya faskara, don kuwa dai Bintu gudun sa ta ke k’iri k’iri. Shi kan shi bai san meyasa ya kasa cire yarinyar daga ransa ba, amma dai yau idan har bai sa ta a idanunsa ba zai iya shiga damuwa. Gashi kuma yau lahadi ko makarantar bai shiga ba bare ya ganta a aji. Nan fa wata dabara ta fad’o masa, ya tsinci kansa ya na mai murmusawa. Ajiyar zuci ya saki yayin da ya bud’e idanu a hankali jin d’igar ruwa bisa fuskarsa sanadiyar iska da ta kad’o wani reshe zuwa cikin rumfar. Tashi ya yi zaune ya na mai duba lokaci, k’arfe biyar daidai, ya aje hannu inda ya tashi cikin azama ya na mai k’ok’arin zura takalmi cikin k’afafunsa. Kai tsaye ya fice daga cikin lambun, ya bi ta farfajiyar gidan ya shige falonsa wanda zai sada sa da d’akin baccinsa. Cikin k’ank’anin lokaci ya sauya kaya izuwa farar jamfa da hula tare da farin takalmi. Ya gama fesa turaren sa mai kamshin gaske ya wuce cikin motarsa. Hankali kwance ya fito daga gidansa, sai gashi kan titin francophonie, kai tsaye ya nufi makarantar Soverign. ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 0⃣6⃣ Minti goma kacal ya kai shi makarantar, Allah ya taimake shi ya had’u da Iya Dije a bakin gate ta na shirin fita kenan. Tsaida Ita ya yi, ya nemi alfarmar ganin Bintu. Iya Dije da tun da ta ga Aisar da yamma haka, gashi ranar lahadi ta san banza ba ta kawo zomo kasuwa, ta yi kud’irin samun wani abu daga aljihun sa. Jin buk’atar ta sa sai ta yi hamdala cikin ran ta, ta na mai gyara tsayuwa ta ce ‘’ai kasan yanayin dokar makarantar ne Malam, an hana d’alibai kebewa da Malamai musammam irin wannan lokacin da ba na d’aukar darasi ba’’ Duk da maganar ta Iya Dije ta yiwa Aisar wani iri, jin ta yi amfani da kalmar ‘’ke6ewa’’ amma sai ya basar, ya na mai murmusawa ya ce ‘’ba ki fahimce ni ba Iya Dije, ba wai tsayar da ita zan yi ba, kawai dai sak'o zan bata, na ga fita ma za ki yi ko?’’ nan fa Iya Dije ta samu mafaka, ta amsa da ‘’eh wlh kasuwa zani, zan saro kaya duk da dai ba wani jarin arziki gare ni ba’’ ganin Aisar ya sanya hannu cikin aljihu jikin ta har rawa ya ke. Ilai kuwa sai gashi ya fito da kud’i CFA na gugan CFA, ba tare da ya k'irga ba ya mik’awa Iya dije ya na mai fad’in ‘’gashi ki k’ara kan jarin na ki’’ nan Iya Dije ta cafe kud’i saura kiris ta had’a da hannun Aisar, fad’i ta ke ‘’kai dai ba ka gajiya, madallah, yo ai in da yarda ai na yarda da kai, bara na kira maka Bintu Bala Mahuta, amma dan Allah kar ta dad’e ka ga dai ni fita zan yi’’ Aisar na murmushin nuna jin dad’i ya amsa da ‘’toh, ina nan kusa da ofishin malamai ina jira.’’ da azar6a6in jiki Iya Dije ta koma ciki ta na k'irga kud’in da aka ba ta. Bintu na zaune cikin d’aki, kasancewar Gimbiya Binta ba ta nan ta je karatu, itama ta sami damar yin na ta karatun. Sanye ta ke cikin shigar su na bayin Sa’ayrasa dan ba ta isa ta sa kayan gida ba duk da dai yau d’in kowa ado ya ke yi. Sai ga Iya Dije ta shigo, kallo d’aya za ka mata ka tabbatar da farin cikin da ke tattare da ita. Ta na mai washe baki ta ce ‘’Bintu tashi maza ki biyo ni, Malamin ku ne ya ke neman ki, eh! Malam Aisar’’ jin sunan Aisar Bintu ta fidda Ido tare da fad’in ‘’Iye?’’ Iya Dije ba ta damu da yanayin tsoron da ya bayya na fuskar Bintu ba, ita dai burin ta shi ne ta kai ta ga Aisar ta samu ita ma ta fita, ta ce; ‘’ke tashi mana, ni kasuwa zani kin ga dai yamma ta yi sosai, shida na yi ba lalle na samu shiga ba, kuma kayan abincin ku na sati zan kar6o’’ ‘’Iya Dije dan Allah ki ce ba ki ganni ba’’ ta fad’a ta na yin rau-rau da idanu kamar mai shirin yin kuka. Baki bud’e Iya Dije ta ce ‘’kun ji ni da yarinya, yo me zai mi ki da za ki sa ni yin k’arya da tsufa ta, na k’i na ce ban gan ki ba d’in’’ Bintu ta ce ‘’Iya Dije aradun Allah Gimbiya ta ce idan ta ganni da shi sai na lahira ya fi ni jin dad’i, ki min afuwa ki taimake ni’’ ‘’wannan kuma ke ki ka sani, idan dai ba ke ki fad’a ma ta ba ina za ta san ma kin gan shi? Ko ta na nan ne?’’ Bintu ta girgiza kai alamar aha ah. ‘’toh maza yafa mayafin ki mu je’’ Bintu ta ce ai ba ta da mayafi. ‘’ai kuwa dai ba na tafi da ke ti6i ti6i da ke haka ba, budurwa kamar ki ki ce ba ki da mayafi? A garin na ku haka ki ke yawo?’’ Iya Dije ta tambaya ta na mai duban ta. Kana Bintu ta amsa mata da ‘’ina da su, su na gida ne Gimbiya ta hana ni zuwa da kayan gida’’ Cike da nuna Allah wadai da halin Gimbiya Binta, Iya Dudu ta ce "wannan shi ne zancen 6ir in ji tusa, menene amfanin hana ki ado ko rufe jikin ki ? Ke tashi mu je ko aran zani ne na baki ki yafa ko ma d'auko wannan d’an hijabin nan da ku ke sawa ki yafa, ai yafi babu kaka ta wajan uba’’ . Hakan ko Bintu ta yi, ta na magiya amma Iya Dije ba ta fasa jan ta ba su ka fito daga 6angaran d’akin kwanan d’alibai, tun suna wuce d’alibai wanda ke zaune farfajiyar wajan har ya zama tsilla tsilla kad’ai ake gani, musammam da ka baro sashin kwanan d'alibai su ka shigo farfajiyar makarantar. Ganin sun nufi ofishin malamai gaban Bintu ya fara fad’uwa. *** Wata baranda gaban ofshin malamai su ka hangi Aisar zaune kan kujera, ganin Bintu tuni wani farin ciki ya lullu6e shi har cikin ran sa. Da kyar ya iya jira su ka k’araso in da Iya Dije ta bar shi ta na mai yiwa Aisar kashedin kar fa Bintu ta dad'e. Ba tare da wata damuwa ba tun da ita dai ta cika jakarta da kud’i ta yi gaba ta bar Bintu da Aisar. Ganin yanda Bintu ta bi bayan Iya Dudu da ido, Aisar ya ce Bintu ko bin ta za ki yi ne?” Da sauri ta mayar da hankalin ta gare shi, ta gaishe shi cike da girmamawa. Ya amsa a takaice tare da mata nuni da wata kujera da ke gaban ta sa ya ce ta zauna dan kar ta b’ata k’afar ta cikin ca6in ruwan sama. Ba musu ta ja kujerar can nesa da tashi sannan ta zauna, kan ta sunkuye ta na wasa da yan yatsun hannun ta, ita dai Allah Allah ta ke Aisar ya sallame ta ko ba dan Gimbiya da sauran d’alibai ba, ko dan sanyin iskar damina da ke kad’awa. Jin shiru be tanka ba ya sa ta yanke hukuncin tambayar dalilin kiran na ta, amma ko da ta d’aga kai, sai tsintar idanun ta tayi cikin na sa, ashe duk zaman nan kallo yake k’are mata. Da sauri ta k’ara yin k’asa da ido, ganin haka ya murmusa ya ce "Bintu gudu na ki ke ko?’’ Shiru ba ta amsa masa ba, ya k’ara da ‘’ya karatu? Ki na dai yi sosai ko? Ko da ya ke na ga kin ci gwajin da na mu ku sosai’’ kamar ya na magana da dutse Bintu ta k’i amsa masa. Be gushe ba ya ce ‘’daga wannan zangon zan dena koyarwa a makarantar ku, ban san me ya sa na ke fad’a mi ki ba, amma ina jin ya dace ki sani ne’’ Jin haka Bintu ta tsinci kan ta da fad’uwar gaba, ba ta san sanda ta ce "saboda me? Ba dai laifi mu ka maka ba ko?’’ kai ya girgiza mata sannan ya ce "yanayin aiki ya sa, amma inshaAllahu zan sa a maido da k'anwata makarantar nan kin ga sai ki sami k’awa ko?’’ murmushi Bintu ta yi wanda ke k’ara bayyana kyan ta, hakan ya sa Aisar fad’in "dama haka ki ka iya murmushi?’’ sai kuma Bintu ta tsuke fuska, ta na shirin tambayar dalilin kiran na ta, wayar shi da ta hau k’ararrawa ta tsaida ita. Da ke wayar tafi da gidan ka(handset) be gama cika gari ba, hannun wane da wane kad’ai ake gani, waya ce kirar (Nokia 3310), dan haka baki bud’e ta tsaya ta na kallan wayar har ya d’aga ya kara bisa kunan sa, ji take da zai bata ta d’an kara kunan ta da ba haka ba. Bintu ba ta dad’a shagala ba sai da ta ji ya ambaci sunan Barde, nan da nan ta manta da wani nauyin Aisar da ta ke ji, ta fara Allah Allah ya gama wayar. Ta gani ya kashe ta ce "Malam dama kasan Yaremi Barde na Fabarusa?’’ ‘’ Na san Barde, amma yanzu ba da shi na yi magana ba’’ sai da ya ba ta amsa sannan kuma mamakin yanda aka yi ta san Barde ya kama shi, be san sanda ya ce ‘’Yerima Barde ke? Ina ki ka san Barde ke kuma ki na yar masarautar Sa’ayrasa?’’ ya tambaya cike da mamaki. Nan fa Bintu ta fara jero bayani cike da nuna gwanintar yan ajin su ma ba a barsu baya ba ta ce "ai rannan a aji aka yi hirar shi, ance shi ne mai kyawun duniya kuma k'asar nan kaf babu wanda zai gwada masa k'asaita, rabin yan ajin sun ta6a ganin shi, ni ma ina so na gan shi ko da sau d’aya ne a rayuwa ta’’ Jin kalaman Bintu tuni Aisar ya had’e rai, yayi k’icin k’icin ya fara fad’a "wato a shekarun ku har kun san ku zauna ku yi hirar samari ko? Ba ku san komai ba sai kula samari da karanta littafin soyayya ko?’’ "wallahi malam ba na kula samari ni ba yar iska ba ce’’ furucin Bintu kenan yayinda idanun Bintu su ka fara kawo ruwa, sai a sannan ta ankare da 6aran6aramar da ta yi na tambayar Barde, duk da dai ita ba da wata manufa ta yi. Ganin Bintu na shirin masa kuka har da batun ita ba yar iska bace ya sa hankalin sa kwanciya, wato kenan ba ta kula samarin tun da har ta masa wata fassara na da ban, hakan ya masa daidai har ya na mai murmusawa. Ita ko Bintu ta shi ta yi da sauri ganin wasu d’alibai sun fito daga d’akin karatu, ta ce malam dama karatu na ke Iya Dije ta ce za ka bani sak’o’’ Sai a sannan ya tuna fa ashe ba ranar makaran ta ba ne, gashi shi babu wani sak’o da ya kawo mata dama ganin ta kawai ya ke san yi. Amma gudun kar ta d’auke shi sakarai fakewa yayi da dama ya zo wucewa ne ta makarantar ya ce bara ya tsaya ya ji ta na karatu kuwa, maza ta koma ta cigaba da karatun. Da wannan ta masa sallama, har ta na fad’awa cikin ca6i dan saurin kar wannan d’aliban da ta hango su gan ta tare da Aisar. Shi kuwa gogan na ta ko ganin su be yi da ke su ma d’in lab’ewa su ka yi domin su tabbatar da abun da su ke gani. *** Sai da Bintu ta k'urewa ganin sa sannan ya tashi ya nufi motar sa, ya gifta ta gaban wannan d’alibai da ke leb’e bayan wata yar katanga sam be lura da su ba har ya kai ga motar shi ya shige ya fice daga makarantar. "kut yau kuwa za yi bantan uwa a makarantar’’ fad’in d’aya daga cikin d’aliban kenan wacce su ke Marry yayinda su ke fitowa daga wajan 6uyan su ganin Aisar ya fice. Su uku ne, kuma dukan su yan aji shida ne ma su mik’amin. Marry ita ce mai ruk’e da muk’amin horo, sai shedigyal da kuma mai kula da tsafta da lafiyar d’alibai, wacce su ke kira da Sikanti. Marry ba ta gushe ba jiki na rawa tsabagen masifa ta k’ara da "wai ido na ne ke zagi ko kuwa Malam Aisar na gani da wata kwaila a makarantar nan?’’ Cikin Jimami Shedigyal ta ce ‘’ni ma dai abun nan ya ban mamaki, ki ga yanda mu ke bin sa ya na mana wulakanci amma ya rasa wacce zai bi sai Bintu d’iyar bayi’’ sikanta dan mamaki ta ma kasa magana. Marry ta d’aga k’afa ta doka k’asa cikin ca6ali, nan da nan zanin ta ya 6aci amma ko aji kin ta, idanun ta ya rufe, kana ta ce ‘’ba d’iyar bayi, ko d’iyar saraki ce yau sai ta ci Uban ta, za ta min bayanin dalilin da ya sa ta kyebewa d Malami, kut Malamin ma wanda na ke so dan uban ta? Yau sai ta lashi kashin b’and’akin k’asa dan uban ta Bintu ta ke kowa? Ta yanki tsiya!" ta wuce fuu, dama ga ta jibgegiya tabarakallah. Su shedigyal su ka rufa mata baya, kai tsaye sashin kwanan d’alibai su ka nufa. *** Bintu kuwa komawar ta d’aki ta tadda Gimbiya ta dawo tare da k'awayen ta, ko da ta tambaye ta daga in da ta ke sai ta mata k’aryar Iya Dije ce ta aike ta. Ta ci sa’a yan masifar Gimbiya ba sa kusa, hankalin ta na kan labarin da Zahira ta ke ba su. Can gefe Bintu ta zauna ta na mai mamakin dalilin da Aisar ya fad’a mata na zuwa ganin ta. Zaman ta ke da wuya ta ji ana kwala mata kira "Bintu Bala Mahuta dan uban ki sauko!’’ Ba Bintu ba hatta su Gimbiya sai da su ka kasa kunne su na jiran tsammani. ita kuwa Bintu jikin ta ne ya hau b’ari jin muryar Marry da gaba d’aya ya 6angaran d'akin kwanan d'alibai. Gimbiya ce ta kai kallan ta ga Bintu ta na mai tambayar ‘’yar nema me kuma ki ka yiwa wannan mai fasalin mazan?’’ Bintu ta kasa magana tsabar tsoro, nan fa su ka k’ara jiyo har gowar Marry ta na mai fad’an ‘’dan uban ki na ce ki sauko kimin bayanin wani malami ki ka kyebe a bayan aji!’’ Nan fa Bunti ta kware saboda firgici da tsoran maganar da Marry ta furta, inda Gimbiya, Zahira da Ruqayya su ka tashi tsaye a a tare, Gimbiya na fad’in ‘’ki tabbatar wannan malamin da ake magana akai ba Malam Aisar ba ne!’’ Can waje kuwa tuni d’alibai kowa ya fito jin shela da tonan siririn Marry, wasu ma babu cikakken sitiran arziki jikin su haka su ka fito bawa idanun su abinci dan kuwa sun san koma wacece wannan ta shiga hannun Marry ta kad’e har ganyen ta, musammam jin ance "ta kyebe da Malami." "BINTU BALA MAHUTA! Ko ki sauko ko na zo na sauko da ke ta!’’ fad’in Marry ta na mai kumfar baki. ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 0⃣7⃣ Babu shiri Bintu ta tashi da sauri, jin Mary na maganar sauko da ita ta ka ta san muguntar Mary za ta aika. Hanyar fita ta nufa ta na jera adduoi iri-iri, ta kama wannan ta saki, wani ma ko k’arshen shi ma ba ta iya kai wa. Su  Gimbiya ma ba su yi k’asa a gwiwa ba, biye su ke da ita, ita dai burin Gimbiya ta ji shin da wa Bintu ta ke6e, idan kuwa Aisar ne sai na lahira ya fita jin dad’i, dan kuwa a daren ranar kwanan Sa’ayrasa ne ya kama ta. Ganin Bintu ba ta jira ta k’arasa gabanta ba, ta na haki kamar zakanya ta fizgo ta, ta hard’e kafar ta sai ga Bintu zube gabanta cikin ca6al6alin ruwan sama "Rage tsinannan tsayin naki dan ubanki,  shiyasa ki ke tunanin kin balaga kin isa ke6ewa da malamai." Fad’in Mary ta na mai shararawa Bintu mari. Bintu durkushe bisa gwiwowinta,  hannunta bisa kuncinta inda hawaye ke gangarowa daga idanunta, fad’i ta ke ‘’Ina tuba  Anty Marry, ki gafarce ni, kimin rai’’ Fili ya cika maki’il da d’alibai, kowa na fad’in albarkacin bakinsa, da masu tausayawa Bintu musammam da su ka san ita ba ‘yar kowa ba ce ta shiga hannun Marry, da ma dai ita d’iyar masu mulki ko sarauta ce da duk jarabar Marry sai ta saurara mata gudun abun da zai je ya dawo. Sai  kuma masu mata Allah shi k’ara. Wani wawan mari da Marry ta dad’a kaiwa Bintu, sai ga Bintu a k’asa, sunkuyawa Marry ta yi, hannu bisa kan Bintu ta kama gashinta, ta fisgo ta cikin zafin nama, sai da Bintu ta runtse ido tsabagen azaba. Cikin rad'a ta ce "Ke da wani Malami ki ka ke6e a sashen karatu?’’ Idanun Bintu runtse, da kyar ta iya furta ‘’Ina tuba Anty Marry’’ Cike da mugunta Marry ta fizgi gashin Bintu kamar mai shirin raba gashin da fatar kan Bintu, wani kuka Bintu ta saki, sai ga kallabin ta hannun Marry, inda gashin da dama nad’e shi ta yi cikin kallabi ya warware, sai gashi ya sauka har gadon bayan ta. Ba Marry da su shedigyal ba, hatta sauran d'alibai sai da su ka yi mamakin kyawun gashin Bintu, da ke kullum kanta d’aure ya ke da kallabi, idan ba tsautsayi ba, babu wanda ta ke bari ya gani. Sikanti ba ta san sanda ta ce ‘’Car uban nan, gide akwai mai irin wannan gashin cikin makarantar nanniya?” Shedigyal da wani bakin kishi ya rufe ta ganin gashin Bintu cewa ta yi ‘’Wannan har wani gashin azo a gani ne?’’ Marry kuwa da tuni ta yi mutuwar tsaye, hannun ta rik’e da kallabin Bintu, murmushin mugunta ta saki, ta na mai jinjina kai ta ce ‘’Sikanti ba ni aran almakashina  ki.’’ Gaban Bintu ne yayi mummunar  fad’uwa, ta d’ago idanunta da su ka yi jajur ta na mai duban Marry. Marry na murmushi ta gyad’a mata kai ta ce "Gashinki zan yanke muddin ba ki fad'a min da wanda mu ka ganki ba, bayan kuma kin fad’amin na kai  bayin k’asa ki lashe kashin yan aji d'aya da su ka yi da harshen ki.’’ Wani sabon kuka Bintu ta saki, musamman jin Sikanta ta tura wata yar aji d’aya ta d’auko mu su almakashi. ‘Dalibai ta bi da kallo cikin neman d’auki, amma sam ba ta ga mai niyar taimakon ta ba, kowa na tsoran sa baki kada gobe idan an je wajan matemakiyar shugaban makaranta wacce ta ke mace ce, a ce har da su, suna ji suna gani a had’a da su. Idanunta ya sauka kan Gimbiya, ta watsa mata harara dan ita ko a jikin ta, Ita so ta ke ma a zo a yanke gashin Bintu ko ta samu ta ji wani Malami ne aka gan shi da Bintu, dan kuwa ta san tun da Bintu ba ta musa ba ko shakka babu da gaske an gan ta d’in ne. Hankalin Bintu be dad’a tashi ba sai da ta ga an mik’awa Marry almakashi, yayinda ta tsugunna, ta sa hannu ta tattare gashin Bintu cikin hannun ta, wanda rabi kad’ai ta iya kamawa tsabar cikar gashin Bintu,  tsakiyar gashin ta sai ta almakashin na ta, ta na mai fad’in ‘’Gide da wani Malami mu ka gan ki?’’ Bintu da ta za6i masifar da hukuncin Marry akan na Gimbiya, ta kasa bud'ar baki ta furta sunan Aisar, sai ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’Ki yi hakuri, ina tuba, ba zan k’ara ba.....’’ Jin sautin almakashi ya na ratsawa cikin gashin ta, da kuma sautin mamaki da ya fito daga bakin d’alibai ne ya katse amsar da ta ke bata, idanu runtse yayinda zafafan hawaye su ka zubo daga idanun ta, jin saukar jelar rabin gashin ta k’asa. ‘’Lah'ilaha'illallahu’’ Fad’in Iya Dije wacce dawowar ta kenan ta shigo dan ganin ko Bintu ta koma d’akin ta, ta tadda d’alibai sun yu da'ira, ta na kutsawa ciki Marry na yanke jelar rabin gashin Bintu. Da saurin ta k'arasa in da Bintu ke tsugunne gaban Marry, Shedigyal da Sikanti, ta yi saurin d’ago Bintu ta na mai fad’in ‘’Yo menene zan gani ni Dije?!! Gide wannan wani irin rashin hankali da zalinci ku ke yiwa yarinyar nan?!!! Gide   akan wani dalili?!!! Gide  wa ya ba ku wannan lasisin?!!’’ Ta shiga jera mu su tambayoyi kamar mai shirin taya Bintu kuka ta na mai duban gashin Bintu da su ka yanke. Ba tare da nuna nadamar abun da ta yi ba Marry ta amsa mata da ‘’Kama ta mu ka yi ta ke6e da Malam Aisar....’’ Waje ya kaure da hayaniyar d'alibai, Gimbiya kuwa kukan kura ne kad’ai ba ta yi ba ta je ta shak’o wuyar Bintu. Ran Iya Dije idan yayi dubu ya 6aci, kallabin Bintu ta fizge daga hannun Marry yayinda ta mik’awa Bintu ta na mai fad’in ‘’Gide daura ki koma d’aki, kar ki damu ni Dije sai na bi mi ki hakkin ki, aradu ma kuwa" A sanyaye Bintu ta karbi kallabin, har lokacin kuka ta ke, gaba d’aya kayan ta ya b’aci da ta6on ruwan sama da ta kwaso, kan ta sun kuye ta shige ciki. Bayan tafiyar ta Iya Dije ta mayar da kallan ta ga su Marry kana ta ce ‘’Ni Dije ni na ce Malam Aisar ya bar min sak’o wajan Bintu kasancewar ba zai same ni ba, kuma sak’on ba na kowa ba ne face sak’on Malam Hashim.’’ Wato daga Marry, har shedigyal da Sikanti babu wanda bai tsorata ba cikinsu, dan tabbas sun san matsayin Iya Dije gun Malam Hashim, da sun san da sa hannunta da ba su yiwa Bintu abun da su ka yi mata ba. Tuni idanunsu ya raina fata, cikin kame-kame Shedigyal ta ce ‘’Yetto Allah shi an sheda na hallau daliban nanniya su assheda na, yatsa ban kai ga jikin yarinyar ga ba, idan k’arya na kai aratta kashe ni." Ko da jin haka Sikanti ma ta yi saurin d’age hannu sama ta na mai fa’d’in ‘’Balanta  ni hallau Marry na rako’’ Marry kuwa da ta san k’iri-k’iri Iya Dije ta ganta tana yanke sumar Bintu, jikin ta ne ya hau b’ari, kana ta yi k’ok’arin jan Iya Dije gefe domin bata wani abu dan kuwa kowa ya san Iya Dije da san abun duniya. Amma Iya Dije ta yi kyememe ta k’i sauraronta, sai ma barin ta ta yi awajan ta yi tafiyar ta. Tuni makaranta ta d’auka gobe Marry za ta sha horo, har da masu shagali dan murna. Gimbiya kuwa duk da jin Iya Dije ce ta tura Bintu gun Aisar ba ta fasa mata bambamin wai akan me ya sa ba ta fad’a mata ba ita je a madadin ta tun da ta san ta na san shi, ko damuwa da abun da Marry ta yiwa Bintu ba ta yi ba bare ta saurara mata. Da daddare Iya Dije ta kira Bintu ta na mai jaddada mata kar ta damu, ita za ta tsaya har sai an bi mata hakkin ta, ita dai duk abun da Iya Dije ta ce gaban Malam Hashim ta amsa mata da eh. Da ke Bintu mace ce mai yafiya sai cewa ta yi ‘’Dan Allah Iya Dije ki bar ta kawai ba sai kin wani bi min hakkina ba, Inna ta tace kowa yayi na gari dan kan sa’’ Iya Dije na mai girgiza kai ta ce ‘’Wagga gaskiya d’aita, amma wannan maganar ban barin ta ko dan rufin asirin kai na, aradu ma kuwa!  Yo ki na tunanin idan shi Malam Aisar d’in ya ji bari zai yi? Abun da dai ya fi sauki ki yi yanda na ce kin ji ya?'’ Da wannan su ka yi sallama. Daren ranar Marry kuwa kasa bacci ta yi tsabagen fargaba, gashi ta cire wa d'iyar mutane suna, gashi duk abun nan da ta yi a banza tun da da sanin Iya Dije, babban tashin hankalin ta shi ne matakin da Malam Aisar zai d'auka idan ya ji abin da ta aikata. "Kar dai fa ace ita d’in sai an yanki rabin gashin kan ta!'’ Abin da zuciyar ta ke raya mata kenan, yayinda ta ke kwance bisa gadan ta, kowa yayi bacci ya bar ta. Sai shafa d’an gajeran gashin da be ma kai kamu d'aya ba ta ke, ta san lalle idan da za a cire shi duka ko kwatan wanda ta cirewa Bintu ba zai kai ba. Girman kai ya hana ta iya zuwa ta bawa Bintu hakuri ko ta sami rangwame, "Ni Marry gide tawa ta same ni kishiya tara rana d’aya’’ Ta fad’a a fili yayinda ta tashi zaune ta na mai d'aura han[truncated by WhatsApp] ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 0⃣8⃣ Tin da Iya Dije ta fara jawabi idanun Aisar da ya k’ada yayi jajur ke bisa fuskar Bintu, wacce ke zaune kusa da Iya Dije kan ta sunkuye. Zaune su ke offishin Malam Hashim, dan kuwa gari na wayewa ko taron d’alibai(Asembly) ba a yi ba Iya Dije ta ja Buntu zuwa ofishin, ta na cikin masa jawabi ne Aisar ya shigo sanye da wannan shigar na sa da ya saba, wato (suite) amma wannan karan ruwan k’asa ya saka. Shigowar Aisar babu alamar da Malam Hashim be yiwa Iya Dije na ta yi shiru ba, amma ina ta kasa d’aukan haske. Hankalin sa ba k’aramin tashi yayi ba ganin Asar ya tashi tsaye a fusace ya na mai maimata ‘’ta saka Ciseaux (Almakashi) ta yanke sumar Bintu!’’ shima Malam Hashim d’in tashi yayi, ya na yiwa Iya Dije alama da ido na ta rufa asiri ya ce "Ciseaux kuwa uwa Iya Diya?’’ Ita kuwa Iya Dije amsawa ta yi "kwankwatsi ma kuwa, ba mai bi na bashin rantsuwa, ai ga d’iyar nanniya(ai ga yarinyar nan), gani ya kori ji’’ kan Bintu ta ankara iya dije ta ja dan hijabin jikin ta, sai ga daga hijabin har kallabin na ta hannun Iya Dije, dan kunya kamar k’asa ta tsage ta rufe, musammam yanda rabin gashin na ta ya sauka har gadan baya, rabi ya tsaya iya wuya. Ta so yanke sauran dan ta daidai ta su amma sammakon da Iya Dije ta doka mata ya sa ba ta sami dama ba. Cike da tausayi Aisar ya ke duban ta, ji yake kamar ya ruke ta ya kwashe mata gaba d’aya damuwar ya mayar zuwa kan shi. Gashi saboda shi an wulak’an ta ta, har aka mata cin zarafi ta hanyar yanke mata suma. Malam Hashim kuwa duban sa ga Aisar ya ke, in da zuciyar sa ke jaddada masa lalle watan rufe wannan makaran ta tasu ce ta tsaya... "Bintu....’’ ya kira sunan ta cikin wani yanayi ya na mai sassauta kullin nakatayal (Neck-tie) din wuyar sa, dan ji yake kamar numfashi ba ya isar sa tsabagen 6acin rai. Hatta Iya Dije da Malam Hashim sai da su ka kai kallan su ga Aisar, ita kuwa Bintu kasa d’aga ido ta kalle shi ta yi. Malam Hashim ya gyara murya ganin yanayin 6acin ran da Aisar ya shiga ya ce "Ina Iya Dije, zai fi kyau ku d’an ba mu hili (fili) mu zanta da Malam Aisar’’ ta na mai mik’awa Bintu kallabi da hijabin ta, ta ce ‘’ye to ai sai mu fita rariya (sai mu fita waje), Bintu mu tahi ko?’’ Da saurin ta, ta karb’a ta d’aura kallabin kafin ta sanya hijabin na ta, Iya Dije a gaba ta na biye da ita, idanun Aisar kan Bintu har su ka fita. Shiru ne ya biyo baya na wani d’an mintina, kafin Malam Hashim ya d’aure ya ce ‘’na san abun da ke ran ka, amma ina mai tabbatar ma ka makamancin haka be ta6a faruwa a wanga École ba, wanga da ya faru ma tsautsayi ne Monsieur Aisar (Malam Aisar)’’ ‘’ka na nufin baka san d’aliban ka su na aje makami a tare da su ba Monsieur (Malam)? Ai na zaci k’aida ne hukumar makaranta ta na bibiyan d’akin d’alibai lokaci lokaci dan binciken kayan su domin gudun irin haka? Me ke faruwa a wanga École ? (me ke faruwa a makarantar nan?) Shin me ku ke yi da har irin haka ka iya faru? Ya ilahi da ta kashe d’iyar mutane fa!!!’’ fad’in Aisar wanda tun da ya fara maganar kansa ke kallan silin. Malam Hashim kuwa zufa ne ya lullub’e shi kana ya ce ‘’lillahi warasulihi Monsieur (Malam) abin ga da ya faru tsautsayi nai, na kuma yi maka alkawarin duk matakin da za ka d’auka daidai ta (daidai ne), amma kar ya shafi wanga École(Makaranta) ’’ Sai a sannan Aisar ya mayar da kallan sa ga Malam Hashim, kana ya ce ‘’wannan laifi ne da ba zan iya d’auke ido akai ba, kasan k’asar mu ta Nijar k’asa ce da ke san jama’ar cikin ta, mai daraja dukkan abu mai numfashin da ke cikin ta, a matsayi na na d’an k’asa mai kishin k’asan ga, na ga irin haka na d’auke kai tabbas na ci amanar k’asa ta’’. Jin haka hankalin Malam Hashim ne ya tashi. Sai gashi ya taso ya zo gaban Aisar ya na mai ruk’o hannun sa ya ce "wanga École (makaranta) ta kunshi d’alibai daga kowani sassa da yankunan jamhuriyar Nijar, ruhe (rufe) ta ba k’aramin asara ba ce ga k’asar ga, kai ka sani k’asar mu na buk’atar makarantu ma su inganci irin Sovereign.......’’ "ka na nufin ita kad’ai ta École mai inganci a wanga k’asa ta mu? (ita kad’ai ce makaranta mai inganci a wanga k’asa ta mu?) Kada fa ka nemi ka zagi k’asa ta Monsieur Hashim!’’ Aisar ya katse shi cike da nuna 6acin rai. Cikin sauri Malam Hashim ya girgiza kai ya ce ‘’ba haka na ke nufi ba Monsieur Aisar, yo to na fad’i haka ban yi ma k’asa ta adalci ba, aradu ma kuwa, École (Makaranta) kuwa masu inganci mu ke da su a k’asar mu, amma ruheta kan iya jawo asarar d’aya daga cikin su, sabida Allahu da manzan sa wanga batu ka duba, duk hukunci da za yiwa wannan d’alibar ka mata ita ta jawa kan ta, yo mi zan ce zanin aro ya toye? amma kada laifin wani ya shafi wani’’ Bayan nazari na wani d’an lokaci Aisar ya ce "ko wani hukumci ka ce Monsieur Hashim?’’ Malam Hashim ya jinjina kai kafin ya ce ‘’ko wani hukunci muddin ba zai shafi wanga École ba, ba zai kuma shafi jarabawar gama sakandiri da d’iyar ta ke rubutawa ba....’’ wani irin kallo Aisar ya watsa masa jin maganar ta sa. Da sauri Malam Hashim ya ce ‘’ba dan d’yar ba Monsieur Aisar, dan cigban k’asar mu, ka ga idan ya shafi jarabawar hallau ya shafi cigaban k’asa ta fannin karatu, k’ak’a ka gani?’’ Tashi yayi ya na bai gyara nakatayal(neck-tie) d’in sa, sannan ya ce ‘’na fahimce ka, zan mata hukunci daidai da yanda ta aikatawa yar uwar ta’’ ya na gama magana ya fice in da ya bar Malam Hashim ya na mai zubewa bisa kujera yayinda ya ke goga zufan da shi kan sa be san ya tsefo masa haka da yawan gaske ba. A waje Aisar ya tadda Bintu da Iya Dije tsaye suna jiran tsammani, be iya kallan in da Bintu ta ke ba tsabagen haushin kan sa da ya ke ji akan abun da ya jawo mata. Kana ya dubi Iya Dije ya ce ‘’ko zan iya samin Ciseaux da sabuwar reza gun ki Iya Dije?’’ Cikin fad’uwar gaba Bintu ta d’ago kai ta na mai duban Malam Aisar, sai a sannan ta lura da yanayin shi da ya canza gaba d’aya, ya zama kamar ba shi ba tsabar 6acin rai. Murya a sanyaye ta ce ‘’dan mai sama Monsieur (Malam) ayi hakuri a bar maganar ga, yo to menene dan an aske gashin niya?(menene dan an aske gashi na), in dai dan niya ne arudu na gafarce ta’’ Kallan ta Aisar yayi ba tare da ya tanka mata ba ya sake maimaitawa Iya Dije tambayar, ganin haka Bintu ta sawa bakin ta sakata, in da Iya Dije ta amsa da ta na da su duka, ya ce to ta kawo masa filin taron d’alibai(assembly ground) yanzu ba tare da 6ata lokaci ba. Ya wuce ya bar Bintu da bin bayan sa da ido. Ita kuwa Iya Dije jiki na b’ari ta nufi 6angaran su dan d’auko sak’on Aisar. A wajan taron d’alibai(assembly), d’alibai da malamai babu wanda be hallara wajan ba, filin ya cika mak’il. Bayan sun yi abin da su ka sabayi kullum, wato na daga al’adar makarantar ne aka bawa Aisar filin. Gannin shi gaban su d’alibai su ka yi tsit, ita kuwa Marry zawo ne kad’ai be zubo mata ba, musammam ganin Iya Dije tsaye kusa da Aisar hannun ta ruke da almakashi. Kamar saukar aradu haka ta ji sunan ta bakin Aisar, bayan ya kira Bintu. Nan da nan d’alibai su ka shiga bud’a mata hanya, da kyar ta ke iya d’aga k’afa ta na takawa saboda tsabagen nauyin da k’afar ta yi mata, har ta kai ga Aisar da tun fitowar ta ya ke mata kallan hadarin kaji. Jin umarnin da Aisar ya bata na da ta juya ta tsugunna bisa gwiwowin ta gaban d’alibai ya sa ta matsawa kusa da Aisar ta na magana a hankali dan kar a ji abun da za ta ce tace ‘’dan Allah Monsieur (malam) ka taimaka kada su raina ni’’ wani irin tsawa ya daka mata ya na mai fad’in ‘’matsa min daga nan in ba haka ba ina kishe ki a nanniya!(in ba haka ba ina dukan ki a nan)’’ da saurin ta ta ja baya, ba ta san sanda ta zube k’asa ba jiki na 6ari. Ba tare da wani dogon bayani ba, haka ma d’alibai ba sa buk’ata dan kuwa gaban su aka yi komai dan haka Ciseaux din hannun Iya Dije ya kar6a ya na mai mik’awa Bintu ya ce ‘’kyarbi ki mata abin da ta mi ki jiya!’’ Hannun Bintu na rawa amma ta kasa d’aga su ta kar6a, cikin magiya ba tare da ta iya furta wani abu ba ta ke kallan Aisar ta na mai girgiza masa kai. Ga mamakin kowa sai jin Aisar cikin rarrashi ya ce da Bintu ‘’kar6ar wanga Ciseaux tare da yiwa wanga azzalumar aski shi ne hukunci mahi(mafi) sauki a gare ta, idan ba haka ba barin wanga École nan har abada ba tare da ta gama jarabawar ta ba ya kamata, za6in na ki ne’’ jin haka tuni waje ya kaure da hayaniya d’alibai, masu tausayin Mary da masu Allah shi k’ara wanda su suka fi yawa, in da yan aji shida kuwa idan ran su yayi dubu ya 6aci, dama duk ajin Mary aka fi tsoro, ita ce mai kankaro mu su girman yau ga ta tsugunne gaban kowa kuma a wulk’ance, tsabagen d’ibar albarka ace yar aji uku ce za ta mata aski! Gaskiya sun zube ba nauyi. Sai ga hawaye sha6e sha6e a fuskar Mary. Tuni zufa ya fara kyetowa wa Bintu, musammam da ta kai kallan ta ga Malam Hashim ya gyad’a mata kai dan kuwa dai ba kukan sa ba uwar kishiya ta mutu. Wata malama ce wacce dama ta dad’e da tsanar Mary ta k’araso kusa da su ta na mai fad’in ‘’ Monsieur ba ka san halin wanga d’ya ba ne (wannan yarinyar ba ne), in aka biya ta za mu shekara nanniya ba tare da an samu abun da ake so ba, bari kawai ni na taimaka mata da zab’in’’ ta na magana ne in da ta ke aikawa Marry da sako murmushin yayinda ta sa hannu ta cizge kallabin Mary, Mary ta yi saurin d’aura hannayen ta bisa kan ta domin 6oye cinyayyen gashin ta, ai ganin gashin sai ga d’alibai na darawa. Muryar Mary na rawa ta ‘’in ki na yiwa Allahu ki yi hakuri Madame , kwankwatsi (rantsuwa) na tuba, dan Allah kada ki yanke min suma ta’’ cike da mamaki ta ce ‘’yo ba ki so a yanke na ki shine ki yanke na wata, aradu kwal kwabo zan mi ki ma kuwa, Iya Dije ruk’e min hannun ta’’ ganin Iya Dije ta yo kan ta, ta saurin sauke hannayen ta k’asa, ta na ji ta na gani Malama ta sai ta almakashi bisa d’an gunjin ta, ta daidaici rabin gashin cikin hikimar raba kan gida biyu, ta fara cire na sama sama. Dake Malamar ma ta na fama da mugun ta, sai da ta karb’i sabuwar rezar hannun Iya Dije, ta kwashe rabin gashin Mary tas sannan hankalin ta ya kwanta. Fuskar Mary ba k’aramin muni ta yi ba da kai rabi kwakwaido rabi kwal kabo, ko da yake dama yaya bare sarki ya aiko. Dan kunya da takaici ta kasa ko da motsi bare ta iya d’aga idanun ta ta kalli jama’a, d’alibai ba su fasa ihu da sowa ba, musammam da malamar ta ce ayiwa Marry ihu, su ka d’auka ‘’ihu dube ta kwakwaido da kwal kabo’’ Malam Hashim ne ya matso gaba, in da ya kira Shedigyal da Sikanti, ya had’a har maryam ya kwace kallabin muk’amin su, ya kuma jaddada hukunci mai tsanani ga duk d’alibar da aka k’ara kamawa da makami ba tare da kwakkwaran daliliba, ko da kuwa reza ne. Farin ciki gun d’alibai be musaltuwa, dan kuwa kurace ta mutu, sun huta. Gimbiya kuwa tuni ta sha jinin jikin ta ganin yanda Aisar yayi ruwa yayi tsaki bisa ga lamarin, batun akwai wani abu tsakanin Bintu d’iyar bayi da Malam Aisar tun daga wajan ya fara shawagi tsakanin d’alibai. Har aka sallame su Mary ba ta iya tashi daga tsugunnan da ta yi ba, sai da yan aji shida su tada ita, nan ta saki kukan da dama ya tsaya k’ark’ashin mak’oshin ta, ba ta ta6a jin ta tsani kan ta ba kamar ranar ba. Ko da ya ke ba ita kad’ai ba duka yan aji shidan ma hakan ta ke. Sauran d’aliban kuwa yau ta ke sallah, dan kuwa abin da aka yiwa Bintu gaba ta kai dan sun sami sakewa da wa tayawa, a ranar Bintu ta yi farin jini sai san barka ake yi mata, hatta Gimbiya a ranar sai da ta sarara mata. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ZUWA GA MASOYA "BINTU 'DIYAR BAYI" INA MAI NEMAN AFUWAN KU NA JINKIRIN SHAFI NA GABA DA ZA A SAMU, HAR ZUWA JUMA'A SABODA WANI UZIRI BABBA DA YA SHAFI WANI KARATUN DA NA KE. MADALLAH DA KU. SIDIYA CE KE MU KU FATAN ALKHAIRI🤝 ©Khadija Sidi.....✍🏼 0⃣9⃣ Ranar da su ka gama jarabawa da yammaci, ana gobe za su tafi gida, Gimbiya Binta ta ce da Bintu ta raka ta wajan Aisar, dan ta ga idan su na tare ne kad’ai ya ke d’an sakar mata fuska. Sanye ta ke cikin doguwar riga ta alfarma kalar ja, dake Gimbiyar fara ce ba karamin kar6ar ta kalar ta yi ba, ita kan ta Bintu sai da ta yaba da kyawun Gimbiya cikin ran ta. Bintu kuwa kayan su na bayi ne jikin ta, kan ta tufke da kallabi, jin Gimbiya ta ce za su gun Aisar ya ta ware kallabin dan ya dan rufe mata jiki, amma duk da haka iya ka wuyar ta ya ya tsaya, gashi ita ba mayafi gare ta ba. Gimbiya tafe Bintu na biye da ita ba su zame koina ba sai ofishin malamai. Malaman duka ba sa nan, daga Aisar sai wani malami da su ke kira Malam Sunusi, shi ma d’in su na shiga ya na fita. Malam Aisar da ke zaune bisa kujera ga teburi gaban sa ya na rubuce rubuce, sanye cikin wannan shigar ta sa dai, ko da ya d’aga ido ya ga su Bintu sai ya dakatar da rubutun da ya ke ya na mai aikawa Bintu murmushi. Ita kuwa ta kau da kai karda Gimbiya ta gani ta shiga uku. ‘’assalama’alaikum warahamatullah’’ sallamar Gimbiya kenan gare shi, ya amsa da ‘’wa’alaikum salam’’ Bintu kamar munafuka sai 6uya ta ke bayan Gimbiya ma sallamar ta masa a tak’aice, ya amsa ya na mai k’arawa da ‘’Bintun Sa’ayrasa, ya ki ke 6uya ne, fito sarari mana’’ Gimbiya ta juyo ta watsa mata harara. Jiki a sanyaye, kan ta sunkuye Bintu ta fito sarari. A sannan Malam Aisar ya lura da shigar da ta yi, sai dai duk sanda ya ke ganin ta da irin shigar be tab’a ganin ta sa riga k’arama wacce ta kama ta kamar ta yau ba, gashi zani ne d’aure jikin ta kuma ya fi fitar da surar mace, dad’in dad’awa kuma gashi Bintu ba kad’an ba duk da dai yarinya ce. Nan da nan su ka nemi fara’ar da ke fuskar Aisar su ka rasa, har sai da Bintu ta tsargu ta d’an ja da baya, Aisar na mai d’auke kai da barin kallan ta ya ce ‘’dole ki 6uya mana, tin da kin hito(fito) yawo ba mayafi da irin wanga shigar!’’ Bintu ta sunkuyar da kai ta na mai tunanin ko dai ya manta da tsayuwar Gimbiya a wajan ne ko me? Allah ya sa kar ya ja mata jaraba. Gimbiya na kallan ikon Allah cikin ran ta fad’i ta ke ‘’aikin banza kyaramuwa tsaftar yaye!’’, Aisar be gushe ba ya k’ara da ‘’kul kar ki k’ara hita(fita) haka ko da a masarautar ku ne!’’ Bintu ta amsa da ‘’toh’’ Gimbiya ya ce ta ce "Monsieur Ina wuni’’ ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘’lafiya’’ ganin haka ta ce da Bintu ‘’Gide hita (fita) waje ki yi jira na....’’ be jira amsar Bintu ba yayi saurin katse Gimbiya ta hanyar fad’in ‘’idan kin hita ki wuce d’aki kar ki tsaya waje da wanga shiga ta ki, idan kin gama kya same ta ca’’ Cikin sauri Bintu ta bar wajan ta na mai hamdalar ceton ta da Allah yayi. Bayan fitar Bintu maimakon ya tsaya ya saurari Gimbiya sai ya cigaba da rubuce rubucen sa, kamar be ma san ta na wajan ba. Kamar za ta juya sai dai ta d’aure ta ce ‘’Malam gobe za mu koma gida’’ ba tare da ya d’ago ya kalle ta ba amsa mata ‘’sai aka yi yaya?’’ Gimbiya ta d’an cije le6e kafin ta ce ‘’dama zuwa na yi na maka sallama, na kuma gayyace ka zuwa masarautar mu idan da hali’ ‘’na gode da sallamar, sai dai masarautar ta ku ce ban da lokaci’’ amsar da ya bata kenan. Kana Gimbiya ta dad’a gwada sa’ar ta ta hanyar fad’in ‘’dama wai ina nufin in ka sami lokaci.....’’ ‘’ban da wannan lokacin’’ ya katseta ya na mai kafe ta ido. Ganin haka Gimbiya ta cije le6e ta na mai hamdalar korar Bintu da ta yi da yanzu gaban ta Aisar zai mata wannan cin fuskar. Fuuu ta juya ta fice ba tare da ta sake tankawa ba. Sai da ya ga ta fita ya aja rubutun ya na mai jan tsaki, takaicin sa na ganin ta na masa yawo da Bintu haka babu mayafi, ko wani kare da biri ya kalla! ‘’ba dan karancin shekarun wangad’iya ba, wallahi ba d’iyar bayi, ko d’iyar bola ce sai na aure ta! Amma ba komai lokaci ne ni Aisar mai hakurin jira ne’’ furicin Aisar kenan azahiri ya na mai jadda batun kawo kanwar sa Maryam makarantar ko ba komai ta ke saka Bintu a hanya. Tsaki ya sake ja ya na mai tura rubutun da ya ke gefe dan kuwa lamari in dai akan Bintu ne ya na jagula masa lissafi. Komawar Gimbiya Binta d’aki kan Bintu ta sauke takaicin ta, laifukan na Bintu da yawa ciki har da ta na sane ta bita gun Aisar babu mayafi tsabagen ta na so ta yi masa tallar jikin ta, an fad’a mata shi d’an iska ne? Ta ji dad’in yanda ya yiwa Bintu kurar kare, da kuma ta ce ta jira ta waje shi ne ta bi umarnin uban ta ta koma d’aki. Aiki tuk’uru ta saka ta wanda tun da Bintu ta zo duniya ba ta tab’a yin irin shi ba, hatta kayan ta da ke wanke a goge sai da ta sa Bintu dad’a wankewa da guga, dare yayi kuma ta tura ta lungu cikin sauro, nan Bintu ta kwana ta na mai adduar Allah ya sa iya haka hukuncin Gimbiya ya tsaya, ba za ta aiwatar da alkawarin sakawa a cire ta daga makarantar ba. Washagari da ruwan sama aka tashi, motocin Sa’ayrasa na d’aya daga cikin motocin da su fara isowa. Sai da ruwa ya d’an tsaya sannan bayi da fadawa su ka taimakawa Bintu wajan kwasar kayan Gimbiya, har ya rage akwaitin karfen Bintu kad’ai ya rage a d’akin. Ita kuwa Gimbiya yar sarki mai dole kuma ta na jira a take mata baya zuwa mota, haka Bintu ta na ji ta na gani ta bar akwatin na ta su ka takawa Gimbiya. Ta na shiga mota ta juya da niyar komawa ta d’auk akwaitin na ta, Gimbiya ta tsiyar da ita ta hanyar daka mata tsawa ‘’gide ina kuma za ki?’’ dan a zatan ta wajan Aisar Bintu za ta. Ko da Bintu ta fad’a mata cewar akwatin ta za ta d’auko, minti gama kacal Gimbiya ta bata idan ba haka ba za ta taka zuwa Sa’ayrasa da k’afar ta. Hanyar da za ta kai ta ga d’akin na su Bintu ta kalla, ko zuwa bakin kofar b’angarn sai ya fi minti goma bare kuma ga hawa bene ga nauyin kaya. ‘’ki nan tsaye ne? idan kin fasa ma iya tafiya’’ furucin Gimbiya cike da tak’ama. Cikin hanzari Bintu ta ce ‘ tuba na ke ran Gimbiya shi dad’e’’ kafin ta tafi da sauri, sai da ta tabbata ta wuce ganin su Gimbiya sannan ta arta a na kare. Ta na ji wasu na ‘’fad’in ku kauce ta fara gudun na ta na masifa’’ har dariya ake mata ita kuwa ba ta san suna yi ba. Haurawa ta yi ta d’auki akwaitin ta bisa kan ta. Ta fito daga sashin kwanan na su kenan kamar daga sama ta ji an d’auke ma ta akwatin daga kayin ta. A tsorace ta juya sai ga Aisar sanye dai da shigar nan nasa, amma yau fara ya sa, idanun sa rufe da gilashi, hannun sa ruk’e da wata leda mai d’an girma cikin nuna damuwa ya ce ‘’wanga ya yiwa d’iya mace nauyi’’ cikin kokawa Bintu ta ce ‘’dan Allah ka yi min rai ka bani na tafi, aradun Allah minti goma kacal Gimbiya ta ba ni’’ maimakon ya bata, sai ma dad’a ruk’e akwaitin yayi kafin ya ce ‘’idan kuma ki ka k’ara fa? K’ak’a za ta yi?’ Idanun Bintu na mai kawo ruwa ta ce ‘’aradu tahiyar su za su yi su bar ni a nanniya (wallahi tafiya za su yi su bar ni a nan)’’ Aisar na mai murmushi ya ce ‘’idan su ka tahi shikenan sai na tahi da ke gidan mu hankali kwance’’ ganin za ta sa masa kuka ya ce ‘’shhh..wasa na ke mi ki’’ akwatin ya aje k’asa sannan ya ciro zoben hannun sa ya mik’a mata ya na mai fad’in ‘’kan ki tafi ga ajiya ta Bintu, ina so ki aje min duk sanda mu ka sake had’uwa zan kar6a’’ Cikin saurin ya bar ta tafi, ba tare da ta kawo komai cikin ran ta ba ta sa hannu ta karb’a ta na mai k’ok’arin cusa zuben cikin zanin ta,ya ce ‘’ah ah a yatsar ki na ke so ki saka, nan ya na iya fad’uwa’’ ba musu ta fara k’ok’arin zira zuben, duk da ya so ya mata yawa ta samu ya shiga yatsar tsakiyar hannun ta na dama. Ta yunk’ura za ta d’au akwatin kenan Aisar ya riga ta cikin zafin nama, ya wuce gaba abun sa, da sauri ta bi bayan sa ta na mai fad’in ‘’ Monsieur ka bani akwatin dan Allah’’ shiru ya mata, dake Aisar mutum ne mai kuzari, nan da nan su ka isa ga motocin Sa’ayrasa. Bintu sai karanto adduoin da ta koyo makarantar allo ta ke dan neman tsari daga masifar Gimbiya, dan ba ita kad’ai ba ma kallo da zund’e da ta sha wajan sauran d’alibai ma sai Allah, musammam yan aji shida da dama sun gama tsanar ta, yau ga Aisar Gaddafi Nur yayi dakon akwaitin d’yar bayi. Shi kuwa gogan na ta ko a jikin sa wai an mintsli kakkausa. Suna isa ya sakar mata murmushin da ita kan ta Bintu ba ta san na menene ba, ita dai ta na ganin sabon salo kiran sallah da husir, kana ya ce ‘’wata motar Gimbiya za ta shiga’’ Bintu ta amsa da ‘’ai Gimbiya ta na cikin waccar motar’’ ta masa nuni ga motar da Gimbiya ke ce. Aisar ya kai kallan sa ga motar, ko da yayi ido hud’u da Gimbiya, duk da 6acin ran da ta shiga ganin Aisar d’auke da akwatin Bintu, sai da ta tsinci kan ta ta na mai sakarwa Aisar sakon murmushi. Yayi saurin maido da kallan sa ga Bintu ya na mai fad’in ‘’ba Gimbiyar ki na ke magana akai ba, Gimbiyar Aisar na ke nufi, wata motar za ki shiga?’’ Cike da mamaki Bintu ta amsa masa da ‘’iyye? Na’am? Ni Bintu?’’ kai ya girgiza mata, jiki a sanyaye ta masa nuni dai ga motar da Gimbiya ke ciki, kana ya ce da direba(driver) ya ce ‘’Aboki na bud’e min bayan motar na aje kayan ko’’ jin haka Bintu ta yi saurin fad’in ‘’waccar motar ta baya za a aje kayan’’ Aisar ya ce ‘’toh gidan gaba ko baya ina ki ke zama?’’ ta na hango Gimbiya ta na girgiza kai har da kwafa, ta na mai duban Bintu ta ce ‘’a juri kai zuga gabas, wataran ta zo da ruwa’’ maimakon Bintu ta bashi amsar sai kawai ta kai hannun ta ga murfin motar da niyar bud’ewa, yayi saurin tsaiyar da ita, ya b’ud’e da kan sa, Bintu ta shiga, ita kan ta ta san ta wuce gona da iri. Ledar ya aje bisa cinyar ta, ba tare da ya rufe motar ba ya ce da direban ya fito kai akwaitin Bintu cikin motar da ake ajewa. Direban ya so yi masa musu, amma ko da suka had’a ido da Aisar ya ga waye gaban shi tini ya fito yayi yanda aka saka shi. Aisar ya ce ‘’ki gaida gida ki gaida yan gidan Bintu, sai kin ji daga gare ni’’ kai kawai Bintu ta iya gyad’a masa, yayin da ya mayar da murfin mota ya rufe. Direba ya dawo ya tada mota har su ka fita be dena kallan motar da Bintu ke ciki ba, ji ya ke kamar ya bi bayan su. Da fitar su, ta baya ta ji Gimbiya ta kifa mata mari, ta na mai fad’in ‘’shegiyar kaya!dama wajan shi ki ke san zuwa sai da jiki na ya ban!’’ kuka Bintu ta saka, fad’i ta ke ‘’ki yi min rai Gimbiya, tuba na ke, ba wajen shi na je ba a hanya mu ka had’u, idan karya na kai arratta kashe ni’’ Tas! Ta dad’a kwashe ta da mari ‘’shi ne har da d’aukar d’an akurkin ki ko? Kai direba tsayar motan nan! Direba ya ja ya tsaya, sauran motocin ma tuni suka faka gefe guda ganin na Gimbiya ma ya faka. Ledar hannu Bintu ta fizge ta na bud’e, mayafai ne manya masu kyan gaske har guda goma. Tsaki Gimbiya Binta ta ja yayinda ta sauke gilashin motar ta na ji ta na gani ta wulga mayafan waje, kan idanun Bintu haka su ka sauka cikin ruwan sama da ya kwanta a gefen titi, sannan ta ce ‘’Direba mayar da d’iyar bayin nan cikin bayi sa’annin iyayen ta’’ Direba ya dubi Bintu da ke faman kuka ya ce ‘’yo to ai sai ki hito ko?’’ Bintu na k’ok’arin fitowa ta ji Gimbiya ta ce ‘’ke da wanga ecole har abada! aradu ma kuwa!’’ da ma dai ko ba ta fad’a ba Bintu ta san ta faru ta k’are ramamme ya zagi maye. Haka ta na mai fad’in ‘’ina tuba’’ amma Gimbiya ta mata kunne uwar shegu, yayinda direba ya raka Bintu izuwa motar bayi a wulak’ance. Nan su ka d’auki hanyar masarauta Bintu na mai bakin ciki da fad’uwar gaba. 🐫🐪🐫🐪🐫🐪🐫 Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen2⃣) WHATSAPP NO: +2347039625239 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣1⃣ Bayan Bintu ta ci abinci, ta watsa ruwa, Inna ta shiga ta same ta kwance ta na hutawa. Ganin Inna ya sa ta tashi zaune, Inna na murmushi ta ce "Gide na aza kwana ki ke(na zaci bacci ki ke)’’ Kai Bintu ta girgiza mata, cike da farin cikin yau ga ta da Innarta, ta ce ‘’A falke na ke Inna (ido na biyu Inna)’’ Nan ta zauna kusa da ita in da ta fara mata tambayoyi game da makaranta kamar dai yanda ta saba. Jin Bintu ta ce komai lahiya lau, bai hana Inna fad’in ‘’Ki dai k’ara hakuri da takwarar ta ki, na ce dai lafiya lau ku ke zaune ko?’’ Da har Bintu za ta fad’a mata halin da ake ciki, sai ta fasa don kuwa ta san halin Inna da sa abu a rai, sai cewa ta yi ‘’Lahiya lumi.” "Ngla zauro, Ala barraaz3( da kyau Allah ya yi albarka)" Fadin Inna ta na mai dafa kan Bintu. Bintu ba ta gushe ba ta yiwa Inna tambayar da ya tsaya cikin ranta, ta ce ‘’Inna me ke faruwa ne?’’ Kai Inna ta girgiza sannan ta ce ‘’Wannan annobar ta duk shekara ita ta sake bayyana Bintu.’’ Gaban Bintu ya fad’i ta na mai dafe k'irji ta ce ‘’Fari?’’(Annobar yunwa, sanadiyar k'arancin ruwan sama) ‘’Aradu ma kuwa, wanga ma ai tafi ta kowacce shekara, talakawa mu na cikin wani hali, dussa ma da za a bawwa awaki gagaran mu yake, hatsin da ki ka ga ina tankad’ewa na gidan sarki ne, Allah ya sa ya shigo ta hannuna, na sami dussar ko ba komai ma sami na karin kumallo, na dare kuma ma ci ragowar babban gida.’’ Cewar Inna. ‘’Innalillahi wainna ilaihi rajiun’’ Fad'in Bintu kenan yayinda zufa ya shiga keto mata. Inna na mai girgiza kai ta ce ‘’Abunda mu ke ta fad’a kenan ‘yar nan’’ kana Bintu ta ce ‘’Yo to Inna me zai hana mu nemi taimako wajan sauran masarautar? Ai na ga ba laifi k’asar mu dai akwai abinci ga taimakon juna’’ Inna ta ce ‘’Uhum ina ne ba a nema ba? Su ma ai sun gaji, yau da gobe ya wuce gaban wasa ai, ridda karya kuka tatsa’’ Zuciyar Bintu d’aya ta furta ‘’Fabarusa fa.....’’ Da sauri Inna ta doke bakinta, hannun Bintu bisa bakinta, Inna na mai zare ido ta ce ‘’Kul ashirni zanne(rufa min asiri), shiga uku takabar sarakuwa!(sirika) Kar ki sake ambatan yankin ga dan Allah, kin manta bakar gabar da ke tsakanin mu, ahir ba da ni ba saka lallen kaza!’’ Ajiyar zuci Bintu ta saki tare da fad'in "Yo to Inna ai dalili ne ke sa a kama kaluluwar sarakuwa...(Dalili ke sa a kama kaluluwar sirika)" Inna na girgiza kai ta ce "Na ce ki bar maganar ga Bintu, ba na kwawarniya shiga rumbum k'ore." Ta na mai jinjina kai ta bar maganar, fatanta Allah ya kawo musu d'auki, Inna ta amsa mata da amin. Ranar har Bintu ta kwanta ba ta ga dawowar mahaifinta ba, dama dai idan ana cikin fari har kwana ya kan yi can fada. ***** ****** Washegari da sassafe, Bintu na bacci wata baiwa daga babban gida ta yiwa Inna sallama. Inna da ta yi zatan kiran na ta ne ta ce ‘’Allah sarki, hallau kun ji ni shiru ko?’’ Jin haka baiwa ta ce ‘’Gide kiran ga ba na ki ba Uwar bayi, wannan kira na Bintu ne daga Gimbiya Binta’’ Kafin Inna ta bata amsa, mahaifin Bintu ya fito a fusace, in da ya hau Inna da fad’a ‘’Yanzu ki na nuhin(nufin) wanga d’iya ta na nan ta na kwana(bacci) har k’arfe bakwai na safe ba ki tashe ta ba tsabagen lalacewa! Yagana anya kuwa?’’ Cikin sanyin murya Inna ta furta ‘’Ayi hakuri na ga jiya ta dawo shi ya sa...’’ ‘’Yo to da hakurin ya mutu nawa ki ka biya kud’in sadaka?’’ Jin haka Inna ta ja bakinta ta yi shiru, ba ta ankara ba sai ganin Baba ta yi ya shige d’akin, haka kuma be fasa fad’an da ya ke ba, har ya iske Bintu ta yi d’ai-d’ai ta na baccin ta cikin kwanciyar hankali. Be yi la’akari da rabon da ya sa ta a ido watanni uku kenan ba, ya rufe ta da fad’a da zagi. Ita kuwa Bintu kamar a mafarki ta ke jin muryarsa, a hankali ta bud’e ido, ko da su ka had’a ido cikin magagin bacci ta furta ‘’Baba?’’ A fusace ya yi mata dak’uwa ‘’Baban ubanki! Hegiya kin saki la66a da su k'a66a ki na ta kwanan asara! Tashi maza ki wanke ido ki tahi babban gida!" Nan da nan Bintu ta wartsake, ta na mai raribar hijabinta, ta ce ‘’Yi hakuri Baba, jiya na dawo ban ganka ba.....’ ‘’Yo to ai gashi kin ganni, yar tselan uwa mai kama da kuliya’’ Ko a jikin Bintu haka ta fito Baba na biye da ita, dan kuwa idan da sabo ta saba, dan ba dan Baba shi ya haifeta ba da sai ta ce ya ma tsane ta ne gaba d’aya. Har yanzu mita Baba ya ke, ita dai Inna d’auke kan ta ta yi, ta shiga wasu sabgogin gaban ta. Baba ne ya ce da baiwa mai jiran Bintu ta je ta ce ga Bintun nan ta tafe. Ta na fad’in ‘’Madallah’’ ta kama hanyar ta tafi. Buta Bintu ta d’auka ta kewaya bayi, da ta fito ta sa dakakken gawayi da gishiri ta wanke hakoran ta, sannan ta wanke fuska. Baba da ke tsaye gefe ya na jira ya ce ‘’Maza kama hanya ki yi gaba’’ ‘’Malam na ce a bari ta yi karin kumallo ko?’’ Fad’in Inna cike da nuna damuwa’ ‘’Kayya! Wani kari kuma Gimbiya ta yi kira? Ke rabu da ita, idan kin dawo kya yi karin, wuce ki tafi’’ Cyewar Baba. Silifa ruwan d’orawa ta sanya a k’afar ta, har za ta fita Inna ta ce ta tsaya su tafi tare. Amma Baba ya ce babu wannan maganar, karshen ta ma ya yanke hukuncin raka Bintu da kan sa. Haka ya sa ta ta gaba, ya na biye da ita, duk wanda su ka gani a hanya sai ta tsaya sun gaisa da Baba, a haka har ya kai ta ga filin sukuwa, sanna ya juya ya koma gida. Tafiyar Baba ke da wuya Bintu ta hangi Yerima Nuhu tare da tawagar sa bisa doki, ganin su ya sa Bintu d'aga k’afa ta na mai adduar Allah Ya sa kar su cimma ta, amma ina Allah bai amsa addu'arta ba, domin kuwa ganinta ya sa Yerima dukan bayan dokinsa da dorinar hannun sa a hankali, hakan ya sa dokin k’ara sauri haka tawagar ta shi wanda ya kunshi abokan sa guda hud’u, nan da nan sai ga su gaban Bintu su na mai tada k’ura yayinda su ke jan linzamin dawakan dan su sami su tsaya. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ZUWA GA K'AWATA HYK, SAKON KI NA ARZIKI YA ISO GARE NI, NA KUMA CE AMEN HAR DA KE. NA GODE KWARAI, MADALLAH DA KE, SIDIYA CE KE MIKI FATAN ALKHAIRI🤝 ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣0⃣ *WAIWAYE ADON TAFIYA* Wanene Sarki Sule Inuwa Magaji? Shi ne Sarki na ishirin bisa gadan mulkin Sa’ayrasa. Ya hau kujerar mulki a shekara ta (1984), bayan Sarki Inuwa Magaji mai rasuwa, lokacin ya na da shekara arba’in a duniya. Allah ya azurta shi da ‘ya’ya goma sha takwas, ya birne takwas saura goma a raye, maza takwas, mata biyu. Mata hud’u ya aura, uwargidansa marigayiya Hajja Fatima Abdu, wacce ta rasu bayan shekara d’aya da hawar sa mulki, wajan haihuwar Gimbiya Binta. Haka kuma ita ta haifawa sarki yara takwas, kasancewar auren saurayi da budurwa su ka yi da Mai martaba, ‘ya’yan ta su an manya duk da dai yawanci ba su yi tsahon rai ba dan sai da ta birne hud’u kafin ta samu masu zama guda hud’u. Yerima Inuwa mai shekara talatin, yayi aure har da yara uku, Yerima Nuhu shekara ishirin da biyar, Gimbiya K'amariyya mai shekara ishirin da haihuwa sai kuma Gimbiya Binta . Sai kuma matar shi ta biyu Hajja Salame wacce ake kira Hajja Kilishi, ita Allah be nufe ta da haihuwa ba. Sai ta uku Hajja Maimunatu ana kiran ta Uwar fada, yaran ta biyu, Hassan da Hussain wanda su ke sa'annin Gimbiya K’amariyya sa kuma amaryar wacce ta ke kanwa ce gun Hajja Fatima Abdu, aka d’aura masa bayan rasuwar sa mai suna Masarriya, ana kiran ta da Inna Salti(wacce za ta haihu da yawa), yaran ta hud’u, duka maza. Sun had'a da Yerima Hamza wanda shi ne babba mai shekara goma sha uku, sai mai bin sa Yerima Abdallah dan shekara goma, na ukun Yerima Ahmadu, shekara takwas sai autan ta Yerima Nadir mai shekara biyar a duniya. Kasancewar ‘ya’yan sa mata biyu kacal a duniya da kuma soyayyar da ya ke yiwa uwar su, ya d’auki san duniya ya d’aura ma su, musammam K’amariyya wacce kamar ta d’aya da mahaifiyar ta kamar kabo da kabo. Hakan shi ya zame babban rauni ga Sarki Sule. ***** ****** Sai da su ka shige tsaunika da duwatsu, suna mai ketare yankuna da dama ta sahara, kafin su hau mik'ak'k'iyar hanyar da za ta sada su da Sa’ayrsa. Ta babbar kofar wanda ake yiwa lak’ani da kofar Magaji Babba su ka shiga yanki. Rana ne sosai kwallewa a yankin daga gani ka san ruwa be sauka baw, kamar ma ruwan sama be sauka a yankin ba bana. Jama’ar gari kowa sabgar gaban sa ya ke, daga masu zuwa ko dawowa daga kasuwa, sai masu zuwa gona, mata wasu da goyo wasu da yara a hannu su na ta hidimar su, ya yara su ma ba a bar su a baya ba, su ma da na su sabgar irin ta yara. Babban abun da Bintu ta lura da shi, shine rashin annushuwa da kuzari na jama’ar yankin, ba kamar yanda ta saba ganin jama’ar yankin cikin farin ciki da annashuwa ba. ‘’Shin ko dai akwai wani abu da ke faruwa wanda ba mu da masaniya akai?’’ Tambayar da ta ke yiwa kan ta kenan, amma gudun magana ya sa ta kasa kada baki ta tambayi sauran bayi ‘yan uwan ta, har su ka kai ga kofar fada. Ta k’ofar gabas su ka shiga fada, wanda dama in dai iyalan sarki ne ta nan su ke shiga. Nan da nan jama’ar fada su ka fito tarban Gimbiya, ciki har da k’annan Gimbiyar wato Yerima Hassan da Yerima Husaini, Yerima Abdallah da kuma Yerima Hamza. Murna da farin ciki gun su kuwa ba a cewa komai. Ana cikin wannan yanayin ne Bintu ta fito ta, bayan ta d’au d’an akwatin k'arfen ta, ta ja gefe babu wanda ya lura da ita bare a damu da halin damuwa da ta ke ciki. Ganin Gimbiya ta fito, da sauri ta k’arasa cikin bayi yan uwan ta, in da su ka zube domin kai gaisuwa ga su Yerima, sannan bayi su ka taka mu su baya su ka shege izuwa fada. Bintu na durk’ushe ba ta tashi ba ta ji an tab’a kafad’ar ta, a hankali ta d’aga ido, tuni murmushi ya maye fuskar ta yayin da ta tashi tsaye ta na mai rungume yayan ta Habibu. Cikin farin ciki ya ce ‘’Kauna(kanwa) mu na ta ke kewan ki, tin ba ma Inna ba, yo kawo akwaitin na ki mu tahi ko?’’ Saboda murna Bintu kasa magana ta yi, sai kawai mik’a masa akwaitin ta yi. Akwaitin ya d’auka, ya na ruke da hannun ta su ka wuce sashin su na bayi. A hanya ya ke tambayar ya yaga idanun ta sun yi jajur haka? Ta ce da shi idanun na ta ke ciwo shi ya sa. Ya ce da ita ta dai sha magani dai ko? Ya kara da Allah ya sauwake. 'Bangaran su na bayi b’angare ne mai d’auke da sashi-sashi na gidajen bayi. Gidan su Bintu wanda ya ke na uku cikin jerin gidajen bayi, gida ne ginin k’asa, mai d’auke da d’akuna uku da falo, sai kuma d’akin dafa abinci da kuma 6and'aki guda d’aya. "Dakunan biyu a cikin falo su ke, na ukun kuma tsakar gida ya ke kusa da dak’in girki, in da 6and'aki ke daga can gefe daf da soro. Ba wani girma ne da tsakar gidan ba haka zalika d'akunan, idan ana zafi da kyar su ke iya bacci, musammam yanayi irin wanda su ke ciki a yanzu, ruwa be sauka a yankin ba. Falon na su kuma babu komai ciki daga daga ciminti sai tabarma. A tsakar gida su ka tadda Inna ta na tankad’en hatsi, kasancewar ta bababbariya baka ce wulik, doguwa ta na da dogon hanci, fuskar ta d'auke da zane da fashin goshi irin na al’adar barebari. Duk da Bintu ba ta kama da ita, akan ce tsayi da garin jikin Bintu na Inna ne, haka ma gashin kan ta wanda idan ta ware ya na saukar mata har gadon baya. Da gudun ta Bintu ta je ta rungume ta, Habibu na mai fad’in ‘’Gide ga autar ta ki na kawo mi ki Inna’’ Cike da farin ciki ita ma ta rungume d'iyar ta ta, fad’i ta ke "Usoo am morantiye, wushe k3shero, is3maa?? Nda zawol?"(sannu yan boko, sannu da zuwa, an dawo? Ya hanya?) ‘’Lahiya limi Alhamdulillah, mun same ku k’alau?’’ Cewar Bintu. Inna na mai duban ta cikin nazari ta amsa da ‘’lahiya limi, Gide ya na gan ki da idanu haka jajur?’’ Bintu na fara'a dan gudun kar Inna ta gane halin da ta ke ciki, ta ce idanun ta ke ciwo. Ita ma sai a sannan ta lura da yanda Inna ta rema ta lalace, d’aga idan da za ta yi ta kalli Habibu sai ta ga ashe gwara Inna ma akan shi. Cike da alamar tambaya ta dawo da kallan ta ga Inna, kana ta ce "lafiya kuwa Inna? Ya na gan ku a rame haka? Ina Baba?’’ "Ya na fada.’’ Amsar da Inna ta bata kenan a takaice. Kana Bintu ta ce ‘’Yo to lafiya na ganku haka?’’ Inna ce ta amsa mata da "Yanzu dai ba lokacin tambaya ba ne, Habibu maza k’arasa mata da kayan d’aka, sai ke kuma ki watsa ruwa ki ci abinci ma yi maganar ko?’’ Cike da fargaba Bintu ta gyad’a mata kai kafin ta shige d’akin ta wanda ya ke d’aya daga cikin na falon, Habibu biye da ita. Shigar su ta bi d’akin na ta da kallo, d'an karamin d’aki ne mai d’auke da gado na k’arfe mai (spring)na daidai kwanciyar mutum d’aya, sai kuma wani k’atan buhu gefe in da Bintu ke aje kayan sawa. Ko tabarma babu a d'akin, sai siminti da ya bi ya faffashe rugu rugu. Gefe guda Habibu ya aje akwatin sannan ya fice ya bar Bintu ta na mai zubewa bisa gadan ta a gajiye. Lalle kuwa kowa fa ya bar gida gida ya bar shi. Daga waje ta jiyo Inna na fad’in ‘’Ki hito ki watsa ruwa fa ‘yar nan’’ Bintu ta amsa ‘’Gani nan hitowa(fitowa) Inna’’ 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣2⃣ Ganinsu gabanta nan da nan ta zube k’asa ta na mai fad’in "Rangwame salamun, masu duniya ku na shagalinku, babban bijimi babban Yerima, hadari malafar duniya, barka da siddi!’’ Yerima Nuhu wanda ya ke kyakkyawan saurayi, musammam idan ya sha rawani da shiga irin ta saraki, ya tsinci kan shi ya na mai murmusawa, yayin da abokansa su ka amsawa Bintu da ‘’An gaishe ki yarinya’’ Shi kuwa kallonta ya ke cike da shauki, ya ce ‘’Mu na lahiya Bintu arziki?’’ Dama da sunan da ya ke kiranta kenan. Cike da nuna ladabi ta ce ‘’Lahiya lumi ran Yerima Nuhu ya d’ade." Kai ya gyad’a kafin ya zunguri dokin shi yayi gaba, haka sauran abokan na sa su ka rufa masa baya. Sai da ta tabbatar sun yi nisa sannan ta tashi ta na mai ajiyar zuciya, ita dai har ga Allah ba ta san irin kallan da Yerima ya ke mata ba tun yau ba, shiyasa ma duk inda ya ke ta ke gudun shi, ko da yake k’awarta wacce su ke kira Cangwai ta ce ina ma ita yake yi wa haka da sauran bayi ‘yan uwanta sun shiga uku da tak’ama. Da wannan tunanin Cangwai ta fad’o mata, ta na mai tunanin ko me ya hana ta zo tun jiya ta ganta yanda ta saba oho, bayan kiran Gimbiya za ta je ta duba ko lafiya, idan kuma sun had’u a babban gida shikenan. Cikin wannan tunanin ta k’arasa soran da zai sada ta da cikin gidan sarki, wanda su ke kira babban gida. Ginin k’asa ne wanda aka gina tin tale-tele mai cike da kayan ado na al'ada. Sauro shida ne reras, wanda kowanne d’auke ya ke da shimfid’u da ado, biyu daga cikin su da d'akuna, wasu kuma tsuntsaye ne fal ciki musammam jemagu su ka mamaye saman ginin. Haka Bintu tai ta shiga ta na fita, wani ta tadda dogarai, wasu kuma bayi haka ta na gaishe su har ta fito sarari, sai ga ta farfajiyar gidan sarki. Duk da shi ginin bulo ne, amma komai na gidan tsarin al’ada da kuma tambarin sarauta ke gare shi. Wato tsayawa fasalta irin kyawun gidan sai na cika shafi be k’are, dan kuwa tsari dai na al’ada da sarauta gida ya tsaru. Inna Salti Bintu ta fara cin karo da kasancewar 6angaran ta ne na farko cikin jerin matan gidan. Ta fito daga 6angaran na ta kenan sanye cikin shiga ta alfarma, abin ku da bafulatanar mace Allah ya bata kyau, gashi sam ba ta tsufa. hannun ta rik'e da na Yerima Nadir, sai baiwar ta wacce ta ke biye da ita. Ganinta nan ma Bintu ta zube domin d’ibar gaisuwa ta na mai fad’in ‘’Barka da safiya uwa ma ba da mama, farar aniya alkhairin duniya, jikinki fari, tufar ki fara, zuciyarki fara wane balbela.....’’ Murmushi ta saki ta na mai mamakin yanda karamar yarinya ta iya zaro magana har haka, ko da yake zama da mad’aukin kanwa shi ke kawo farin kai. Shi kuwa Yerima ganin Bintu tuni ya saki hannun Inna Salti ya na mai fad’in ‘’Inna Salti Bintu ce!’’ Har da tsallansa sai gashi jikin Bintu ya na mai rungumota. Ita ma Bintu dariya ta ke saboda farin cikin ganin Yerima Nadir. Inna Salti kuwa kallansu ta ke, ta na mai mamakin wannan soyayya da ke tsakanin Bintu da autan nata, dan kuwa duk cikin bayi babu wacce ya ke sakarwa fuska, amma idan ka ganshi da Bintu ko ciki d’aya su ka fito sai haka. Cikin fara’a Inna Salti ta ce ‘’Brkan ki dai Bintu, an dawo lahiya?” ‘’Lahiya lumi ranki shi dad’e’’ Cewar Bintu. ‘’Toh ja66ama.’’ Yerima Nadir ya dubi Inna Sallati ya ce ‘’Inna Salti zan yi wasa da Bintu’’ Inna Salti na mai murmushi ta ja hannun Yerima Nadir ’’Tunda ka ga ta yi sammako haka, ko shakka babu aiki ke gare ta, ko Bintu?’’ Jin haka Bintu ta san me Inna Salti ta ke nufi, kana ta ce ‘’Dama Gimbiya Binta ce ta yi kira na." ‘’Ka ji ko Nadir? Didi ta yi kiranta’’ Cewar Inna Salti. Ba dai haka ya so ba, amma be fasa tambayar ko anjima Bintu za ta yi wasa da shi ba, in da ta amsa masa da eh, da haka su ka yi sallama, sai da ta tabbatar sun wuce sannan ta tashi daga sunkuyen da ta yi, kai tsaye 6angaran su Gimbiya ta nufa ta na mai fad’uwar gaba. K’atan falo ne mai d’auke da ado irin na gidan sarauta, haka kuma ya na d'auke da d’akuna biyu, kowanne da b’and’aki ciki, wanda na fari shi ne na Gimbiya K’amariyya, sai kuma na Gimbiya Binta daga can 6angaran. Bayi ne guda hud’u ke ta kai kawo. Kai tsaye d’akin Gimbiya Binta ta nufa, ganin babu kowa bakin k’ofar d'akin ya sa Bintu kwankwasawa a hankali. Sai da ta kai wajan minti goma tsaye bakin k’ofa sannan ta ji muryar Gimbiya Binta ta na fad’in ‘’Gide wata maratarbiyar na samu a nan?’ Cikin rawar murya Bintu ta ce ‘’Ran gimbiya ya dad'e Bintu ce....’’ Shiru sai bayan wasu d’an dakik’ai ta sake furta ‘’D’iyar bayi ki ke kowa? Kya iya shigowa’’ A hankali ta murd’a hannun k’ofar, tuni wani ni’imantaccen kamshi ya daki hancin Bintu, sa k’afarta, ta ji ya lume cikin lallausar kafet(carpet), ga wani rab'a mai ratsa jiki da ya kama d'akin. Babu shakka d’akin Gimbiya Binta yana da fasalin d’akin d’iyar turawa. Komai na d’akin fari ne fat. Lullu6e cikin bargo, idanu lumshe ta ce ‘’sai yanzu ki ga damar zuwa?’’ kofar ta mayar ta rufe sannan ta zube k’asa ta na fad’in ‘’Tuba na ke Gimbiya, barka da asuba.’’ Ba tare da ta bud’e idanunta ba ta yi nuni da d’an yatsa zuwa akwatinan da aka jibge gefe guda, sannan ta ja bargo ta rufe fuskar ta. Ko da ba ta yi magana ba, Bintu ta gane umarnin da aka ba ta. Dan haka tashi ta yi ta na mai bin akwatinan da kallo, su goma sha biyu ne cif. Himma ta d'aura, ta bi akwatinan d’aya bayan d'aya ta na fito da kayan ta na jera su cikin durowar Gimbiya. Wasa wasa aikin nan sai gashi ya d'auke ta awa d’aya. Ta na kan akwati na k’arshe ne Gimbiya K'amariya ta shigo cikin shiga na alfarma. Kallo d’aya za ka mata ka tabbatar da farin cikin da ke tattare da ita. Gimbiya K'amariyya fara ce kamar Gimbiya Binta, doguwa ce siririya, dan kuwa sam ba ta garin jiki, ba ba'a ba, irin wannan matan ne da ake yiwa lak'ani da "Muciya da zani" Tsabar rashin jiki. Ta na da kyawun fuska daidai gwargwado dan har ta fi Gimbiya Binta. Da sauri Bintu ta zube ta na mai fad’in ‘’barka da safiya Gimbiya’’ Da fara’ar ta ta masa da ‘’Barka dai, kya iya cigaba da aikinki’’ Bintu ta koma ga aikinta, inda Gimbiya K’amariyya ta zauna gefan gadon Gimbiya Binta. A hankali Gimbiya Binta ta yaye bargon daga fuskarta tana mai murmushi ga yar uwarta, ashe duk lokacin nan idanun ta biyu. ‘’A kwana a hantse sai d’iyar sarakai.’’ Cewar Gimbiya K’amariyya tana mai dafa kafad’ar Gimbiya Binta. Tashi ta yi zaune kana ta ce ‘’Gidai ban fa gane wanga farin ciki na ki ba, hallo ana fama da fari gidai ki na fama da farin ciki? me an surrin?(kin gan ki ban gane wannan farin ciki da ki ke ciki ba, muna fama da fari ke ki na ta farin ciki? Menene sirrin?’)’ Kwanciya Gimbiya K’amariyya ta yi gami da runtse idanu, sannan ta furta ‘’Barde ne’’ Cikin nuna rashin fahimta Gimbiya Binta ta maimata ‘’Barde ne?’’ Idanunta ta bud’e ta na mai duban Gimbiya Binta ta ce ‘’Soyayya na ke da Yerima Barde na Fabarusa!’’ Wato ba Gimbiya Binta ba, hatta Bintu da ke can gefe sai da ta tsaya cak ta na fidda idanu jin batun na Gimbiya K’amariyya cikin ran ta tana mai maimaita ‘’Yerima Barde mai kyawun duniya? Kai ba k’aramin baiwa Allah yayiwa Gimbiya K'amariyya ba’’ Cikin k’aguwa Gimbiya Binta ta ce "Didi ina ku ka had’u? Takawa(sarki) ya sani? Da gaske kyawunshi ya wuce na kowa a duniya?’’ ‘’Wanga tambayoyi haka kauna(kanwa) ta? Kimin d’aya bayan d’aya’’ Kana Gimbiya Binta ta ce ‘’Toh, ina kuka had’u?’’ ‘’A k’asa mai tsarki mu ka had’u, kin san mun je ki na makaranta’’ ‘’Ya san ke wacece kuwa?’’ Gimbiya K’amariyya na mai d’aga mata hannu ta ce ‘’Tsaya dai ki ji komai, bayan had’uwar mu, jinin mu ya had’u, hallo mu ka kulla soyayya mai k’arfi, kullum cikin waya mu ke ta sabuwar wayar tafi da gidanka da ya shigo k’asar ga, mun yi alk’awarin amre(aure) da kuma kawo k’arshen gaba da ke tsakanin masarautar nan ta mu guda biyu, hallo hakan ne ma ya sa Allah ya had’a mu’’ Gaba d’aya Bintu ta manta da aikin da aka saka ta, ta saki baki da hanci ta na jin lamarin ubangiji, ‘’Ashe dai da rabon za ta ga Yerima Barde a rayuwarta’’ Farin cikin da ya mamaye ranta kenan. Kamar daga sama ta ji an daka mata tsawa ‘’Yallah can (dalla can) makira fita ki ba mu wuri! Ki ga yanda ta saki baki da hanci ta na jin mutane, wato ki sami wanda za ki d’auka ki watsa rariya(waje) ko?’’ A firgice Bintu ta dawo cikin hayyacin ta ta na mai raba idanu kamar 6era cikin tarko yayin da ta zube k’asa. Gimbiya Binta bata gushe ba ta k’ara da ‘’Idan na ji wanga magana ta hita rariya(idan na ji wannan maganar ta fita waje) sai dai uwar ki ta haifi wata! Aradu ma kuwa!’’ ‘’Lalle ma kuwa, yo to ai na manta tana nanniya’’ Cewar K’amariyya ta na duban Bintu. Jikin Bintu na rawa ta ce ‘’Tuba na ke! Aradun Allah na tuba, in na kara kada rabbi ya gafirce ni!’’ ‘’Hita yallah(fita dallah) jaka kawai!’’ Gimbiya Binta ta daka mata tsawa. Tuni Bintu ta tashi jiki na rawa ta fita. Bayan fitarta Gimbiya Binta ta ce "Wai har wanga d’iyar bayin ni za ta yiwa alherin maye ramuwa da mugunta? Har ta isa had’a samrayi(saurayi) da ni?’’ Baki bud’e Gimbiya K'amariyya ta ce ‘’Kwarainiya mota a randa! Shi ko wanene wanga samrayi?’’ Gimbya Binta na mai murmushi ta ce ‘’Aisar Gaddafi Nur." Cike da mamaki Gimbiya K'amariyya ta ce ‘’Kai haba dan Allah, Aisar dan shugaban k'asa gide?" Gimbiya Binta ta gyad'a mata kai. "Yo to in ban da abun ki ina tusa zata hure wuta? Ina d’iyar bayi ina dan mulki? Ai komai tsiyar 6arawo ya bar wuta a murhu’’ Cewar Gimbiya K'amariyya. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣3⃣ Kai Gimbiya Binta ta girgiza, tana mai fad’in ‘’Ba ki san makircin wanga d’iya ba ne Didi, bari dai na baki labarin kad’an daga cikin halin ta.’’ Nan fa ta saka Bintu a faifai, k’arya da gaskiya haka ta had’a ta shedawa Gimbiya K’amariyya, ba don komai ba ko don ta samu mai taya ta saka baki a hana Bintu komawa makaranta. Jiki na kyarma Bintu ta fito, Allah ya sa shigowar Inna kenan su ka had’u a rariya. Inna na ganin Bintu ta san akwai abin da ke damunta, tambayar duniyar nan Inna ta yi mata, amma ta k’i fad’a mata, sai k’arya ba ta jin dad’i ta yi mata. Ta na mai mata Allah ya sauwake ta ja ta gefe ta bata fatan dusan da ta taho mata da shi dan karin kumallo kafin ta yi na ta wajan, tabar Bintu ta na zabga loma.               ***      ***      *** Da yammaci, sati guda kenan da dawowa su Bintu. Bintu kwance tare da Inna da Habibu zaune bisa tabarma a tsakar gida su na shan iska dan kuwa zafi ake na gaske ma kuwa. Inna da ya Habibu ke hirar halin da ake ciki na fari a yanki, su na muhawarar yanda za a sami mafita, in da Bintu ta yi kwance can gefe, gaba d’aya tunanin Aisar ne ya addabi rayuwar ta, dan ko yanzu ma tunanin na shi ta ke yayinda ta ke murza zobensa da ke sanye cikin yatsunta. Baba ne ya shigo kamar an jefoshi, fad’i ya ke ‘’An dai wad’i(fad’i) ba nauyi!'’ Tashi su ka yi tsaye a tare, Inna na mai tambayar ‘’Malam lafiya kuwa?’’  Baba ya ce ‘’Yo to tunda aka fara fari ina mu ka ga lafiya? Yau fa kur’ia aka doka a fada, kuma sakamakon shi ne za mu nemi sulhu da kuma taimako daga wajan mak’iya abokan gaba, eh masarautar Fabarusa!’’ Babu wanda bai girgiza ba jin kalamin na Baba. Habibu ne ya ce "Gide a rasa in da za a k’ask’antar da kai sai wajan abokan gaba?’’ Baba na mai d’aga kafad’a ya ce "Ta dai faru ta k’are an yiwa mai damo d’aya sata, don kuwa magatakarda ya tura wasik’a zuwa Fabarusa, idan an amsa gobe da sassahe za a d’auki hanya  tare da Uban Gabasawa(Sarki) da kansa zuwa wajan abokan gaba nema sulhu’’ Ya na gama fad’in haka ya shige ciki Inna na mai bin bayansa. Shi kuwa Habibu silifa d’insa ya ja ya saka sannan ya fice, wato ya fita yad’a zancen kenan. Bintu kuwa komawa ta yi zaune abin ta, duk da dai itama ta yi tunanin neman taimako daga Fabarusa, jin za a je d’in da gaske sai ta tsinci kanta tana mai fad’uwar gaba. ******** Washegari da sassafe Mai Martaba da tawagarsa su ka d’auki hanyar Faburusa. Babban gida sam babu armashi kowa cikin fargaba ya ke. Gimbiya K’amariyya tafi kowa shiga tashin hankali, gashi tun jiya ta ke kiran wayar Yerima Barde amma wayar ba ta shiga. Gani ta ke kamar alakarsu ce ta zo k’arshe. Ita kuwa Gimbiya Binta damuwarta daban ne, tun dawowar su ta ke ta sak’e-sak’e akan abinda za ta ce da Takawa(sarki) ya canza mata baiwa, dan ita aradu ba za ta koma makaranta da Bintu ba. Ranar Allah ya taimaki Bintu ta yi aiki da hidimarta cikin Babban gida ba tare da ta sami matsala daga wajan Gimbiya Binta ba. Da yammacin ranar ta raka Yerima Nadir Lambu, nan su ka ta tad’in su kamar ta sami babban mutum. Labarin makarantar su ya ce ta bashi, nan fa Bintu tai ta bashi, har da labarin Aisar. Bata san ta na kewan sa sosai ba sai da take maganar sa a zahiri ba a zuci ba, wata k’ila ma ya manta da wata Bintu, abun da take fad’awa kan ta kenan. Shi kuwa Yerima Nadir kallon ta kawai ya ke ba tare da ya fahimci in da ta dosa ba, ballantana ya gane halin da ta ke ciki. ****** Bayan magrib ta koma gida, shiru har lokacin sarki be dawo ba. Bayan sun ci abinci suna kwance a falo ita da Inna, sun ci sa’a akwai wutar lantakarki, fanka ke kad’awa ta na mai fitar da k’ara alamar ta fara gazawa.Akwatin radiyon Inna su ke sauraro in da ake labaran duniya. Jin mai karanto labarai ya ce ‘’Jikin shugaban k’asa Gaddafi Nur ya tashi, za'a fitar da shi zuwa k’asar waje domin ba shi taimako’’ Ya sa Bintu tashi zaune da sauri ta na mai tambayar ‘’Inna daman shugaban K’asa be da lafiya?’’ ‘’Eh Allah sarki ai be da lafiya, yo to da k’alau ya ke ai da tuni ya magance wanga fari da mu ke ciki, dan ba kya sauraran labarai ne shi ya sa ba ki ji ba’’ Inna ta amsa mata. Bintu na mai dafe kai ta ce  "innalillahi wa innailaihirrajiun, Allah sarki Monsieur Aisar, suna cikin tashin hankali’’  Inna ta dubeta, ‘’Waye shi kuma Bintu?’’ Nan Bintu ta kwashe labarin Aisar ta fad’awa Innar ta. Fuskarta na nuna rashin jin dad’in labarin, Inna ta had’e fuska. ‘’Ai da walakin goro a miya, shi ya sa mana na ga kin dawo wata wuri wuri da ke, d’an shugaban k’asa Bintu?’’ Bintu na mai tura baki ta ce ‘’Yo to Inna minene ciki? Ba fa wani abu ba ne taimako gareshi kawai........’’ ‘’Wani taimako? Chiim zanne la nya bangin! (rufa min baki ko na buge ki)’’ Inna ta katse ta, ta k’ara da ‘’Taimako ne har da siya miki turare ma su tsada haka Bintu? Binta sudan? Kafin kafin? Danduala? Turaren da sai Saraki kad’ai ke sawa? Kuma ki na dai ganin yanda Gimbiya ta yi mi ki saboda shi? ngoy awo gulgin d3! (ai ga abinda nake fada), yanzu ba za ta bari ko koma maranta (makaranta) da ke ba!" Komawa Bintu ta yi ta kwanta, ta na mai lumshe idanu. Kana ta ce ‘’Allah ya ba shi lafiya’’ "Wa fa?’’ Inna ta tambaya. Bintu na mai bud’e idanunta ta ce ‘’Mahaifin Monsieur’’ Tsaki Inna ta ja, kafin ta amsa da ‘’Yo to amin, amma kanki ya kamata ki yiwa addu’a fero (yarinya) a halin da ki ke ciki, ki ma cire wannan mutumin daga ranki, can ga su gada zomo ya ji kid’an farau ta’’ ‘’Inna Allah na sa a raina." Cewar Bintu. Kamar daga sama su ka jiyo Habibu daga tsakar gida ya ce  "Kin gama komai kauna(kanwa) ta?'' Ashe duk maganar da su ke ya na can zaune tsakar gida ya na jiyo su ba su sani ba. Murmushi Bintu ta saka, ita kuwa Inna cewa ta yi ‘’Ala sakaa (Allah ya kare)" Washegari da asubar fari Bintu na tashi daga barci Baba ne ya fad’o ranta, don kuwa har su ka yi bacci be dawo ba. A tsakar gida ta tadda Inna ta na alwala, ka na ta ce ‘’Inna barka da asuba’’ ‘’Barka dai Bintu, kin tashi k’alau?’’ Inna ta amsa mata. "Lafiya lumi, shin Baba kuwa an dawo?’’ Bintu ta sake tambayarta, inda Inna ta amsa mata da sun dawo lafiya lumi kan ta shige d’akin ta bayan ta gama alwala, ita ma Bintun buta ta d’auka ta shige band’aki. Babban gida kuwa a yau rashin armashin sa ya fi na kullum, babban abin da ya bawa Bintu tsoro da ta shiga gidan da rana shi ne ganin Gimbiya K’amariyya cikin tashin hankali. An hana kowa shiga d’akin ta, Bintu ma dan ita ta takawa Gimbiya Binta baya zuwa wajan Gimbiya K’amariyya ya sa ta d’au haske, duk da dai ita ma iyakacin ta bakin kofa ne. Duk yanda Bintu za ta yi domin binciko abinda ke faruwa ta yi, amma abun ya ci tara, babu wanda ya iya bud’ar baki ya ce komai, dan kuwa kowa tsoran ace shi ya fad’a ya ke. Haka dai Bintu ta koma gida jiki a sanyaye. Ta tadda Inna zaune tsakar gida, kusa da ita ta zauna a gajiye ta na mai fad’in ‘’Inna barka da yammaci, ashe kin taho’’ Bud’ar bakin Inna sai cewa ta yi "Barka dai d’iyarnan, ba dole na taho gida ba, Babban gida yau ba dad’i, fada babu kwanciyar hankali.......’’ ‘’Yo to ina fada ina kwanciyar hankali!’’ Baba ne ya katseta, wanda ya fito daga b’and’aki hannun sa ruk'e da buta, sanye cikin shigar bayin Sa’ayrasa. Kujerar tsakar gida ya ja ya zauna kafin ya k’ara da "ai da ni mai fad’a aji ne a wanga masarauta, da aradu ba a je Fabarusa ba, yo to ina bawa d’an bayi, ina ni ina bada shawara?’’ Cikin k’aguwa ta ji abinda ke faruwa Inna ta ce ‘’Shin ya ta kasance ne Malam? K’ak’a an ka yi ne?’’ Murmushin takaici Baba ya saki kan ya fara ba su labarin yanda ta kasance a masarautar Fabarusa. Wato ba k’aramin fad'uwar gaba Bintu  ta ji ba jin Baba ya ce ‘’Da bud'ar bakin Sarki Abdulrahman sai cewa yayi za mu kawar da gaba, za kuma mu ba ku bashin damun hatsai da dabino yanda aka buk’ata daga gare mu dan ceto rayuwar alumma, amma fa da sharad’i.." "Sharad’in me?’’ Inna da Bintu su ka tambaya a tare. Baba na mai girgiza kai ya ce ‘’Ku dai tsaya ku ji furucin tsohon banza, sharad’in shi ne, Uban Gabasawa(sarki) ya amra(d’aura) masa d’aya daga cikin d’iyoyinsa mata....’’ Gaban Bintu ne ya yanke ya fad’i. ‘’A amra masa d’aya daga cikin d’iyoyin Uban Gabasa?’’ Inna ta maimaita. Kai baba ya gyad’a mata, ya k’ara da ‘’Acewarsa, ba zai ba da zallar dukiya har haka ga tsohon abokin gaba ba, ba tare da ya sami madogara ba, kenan amren d’aya daga cikin Gimbiyoyin Sa’ayrasa shi zai sa dole Uban Gabasawa ba zai yi wasa da dukiyar ta su ba, a fad’ar sarkin Fabarusa fa’’ Hannu bisa ha6a Inna ta ce ‘’Hallo ta nan ya hito?  Ba ya taimako sabida da Allah sai an bashi d’iya? Na ji ance sarkin ga ya bawa shekara tamanin baya, tsufa dai ta yi gardama’’ Gaba d’aya hankalin Bintu a tashe ya ke, musamman da tasan alakar Gimbiya K’amriyya da d’an sarkin Fabarusa, wato Yerima Barde, kuma ta san babu shakka Gimbiya K'amariyya za a za6a ba dai Gimbiya Binta ba. ‘’Shin yanzu ina aka kwan?’’ Muryar Inna ta dawo da Bintu daga kogin tunanin da ta fad’a. Baba ya amsa mata da ‘’Tununna dai, an dai ce za a yi shawara, amma gaskiyar lamarin da kyar za mu kiya , jama’a ana cikin wani hali’’ Ya karkata buta ya fara alwala. Jin haka Bintu ta d’aura kai bisa gwiwa cike da tausayin Gimbiya K’amariyya, duk da dai ba kukan ta ba, mutuwar uwar kishiya. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣4⃣ Bangaren Gimbiya Kamariyya kuwa, tunda jakadiya ta sheda mata halin da ake ciki ta kasa samin nutsuwa, gaba d’aya ta fita daga hayyacinta. Washegari da safe ta na kwance bisa cinyar Gimbiya Binta ta na ta kuka kamar k’aramar yarinya, Gimbiya Binta ce mai rarrashinta. Wayarta ta shiga k’ara, da sauri ta duba, ganin wanda ke kiranta ya sa tayi sauran danna wayar ta kara bisa kunnenta. ‘’Yerima mun shiga uku, Yerima ya zan yi?’’ Muryar Barde kad’ai ta isa rikita mai sauraro, murya ce mai tattare da kwarjini, k’asaita da kuma nutsuwa. Duk da tashin hankalin da take ciki be hana ta runtse idanunta ba yayin da ta ji ya ambaci sunanta "K'amariyya.....’’ Sannan ya fara magana cike da k’asaita ‘’Ki kwantar da hankalinki, babu wanda ya isa ya auri matata, fad’amin shi wannan da ki ke magana akai wanene shi? Waye ubansa? Dan wani masarauta ne?’’ ‘’Fabarusa, amma ba za mu iya jayayya da shi ba Yerima, sawun giwa ya taka na rak’umi....’’ Ta na magana ne cikin shasshek'ar kuka. Hankali kwance Yerima Barde ya ce "Fad’amin sunansa, dan wani gida ne acikin masarautarmu? Shin da me ya ke tak’ama haka ya tsoratar min da Gimbiya?’’ Ta na mai magana a hankali, dakyar ta iya furta ‘’Yerima Mai Mar-ta-ba ne.....’’ ‘’Wanene Mai Martaba?’’ Ya tambaya a takaice. Jin haka ta san be gane in da ta dosa taba, ta ce ‘’Mai Martaba sarkin Fabarusa....’’ 'Dif ta ji Yareima Barde, shiru kamar wanda ruwa ya shanye har sai da ta duba wayar dan azatan ta wayar ce ta yanke. Ganin be yanke ba, a hankali ta furta ‘’Yarima...’’ Dogon numfashi ya ja kafin ya ce "Akwai kuskure, babu wannan maganar, ki saurari wayata zuwa anjima.’’ Ya na gama fad’in haka ya katse wayar. Wani sabon kuka Gimbiya K’amariyya ta saka. Cike da tausayi Gimbiya Binta ta ke dubanta, cikin ranta kuwa ta k’udiri niyyar ceto rayuwar ‘yar uwarta. Ta na mai murmushi ta ce da Gimbya K'amariyya ‘’Didi kar ki damu, aradu sai na share mi ki hawaye, in har na kasa aratta kashe ni.’’ Sannan ta d'auki hanyar fita bayin ta na biye da ita. ******** ********* FABARUSA Yarima Abubakar Abdulrahman wanda aka fi sani da Yarima Barde na Fabarusa, shi ake nufi da wannan kalmar kyau, dan buzu jikan buzu, shi ba sarki ba ya fi sarki iko da mulki. Fari ne sol, dogo mai k’irar nan ada ake danganta su da k’irar zaki. Ya na da faffad’ar kafad’a maji k’arfi da kumari. Sam babu alamar muni a tattare da shi, ya na da dogon hanci da ya zo daf da bakinshi, da manyan idanu mai rikita duk mai kallo. Bak’in gashin da ya sauko tun daga sajenshi ya zagaye fuskarsa, har zuwa saman bakinsa. Abun ku da buzu ya na da suma kamar balarabe, baki wanda yayi lub-lub kwance bisa kansa. Yawan sumar ya sa ba ya damuwa da aski, sai dai ya rage, hakan yasa idan aka gan shi akan yi zaton balarabe ne. Yarima Barde bai da wata sutura da ya wuce farin tufafi, kullum tufafinsa fari ne k'al, haka zalika rawanin ko hularshi. Mutum ne mai tsafta, isa da k’asaita, wanda hakan kan janyo wasu da dama danganta halinsa da mai shegen girman kai. Shi ne na ishirin wajan mahaifinsa, inda ya ke da yayye goma sha tara, goma sha takwas mata duka suna gidajen mazajensu, da namiji d’aya Abdulkarim wanda ake kira Sadauki, tsirar watanni biyar ne tsakaninsu, shekararsu Talatin da biyu da haihuwa. K’annensa goma, mata biyar da maza biyar. Kasancewar hali da ya bambanta tsakanin Barde da Sadauki, inda Barde ya ke da nutsuwa hankali da sanin yakamata, Saudauki shi ne shaye shaye, rashin tarbiya da bin mata. Hakan ya sa Barde ya zama mafi soyuwa wajen mahafinnasu Mai Martaba Sarkin Fabarusa, duk da kuwa da yawa ana lak’anta soyayyar d’an da mahaifin akan soyayyar da Sarki ya ke yiwa mahafiyar Barde ne ya shafi d’an na ta, duk da dai ba ta cikin fada, ko ince k’asar Nijar baki d’aya. Cikin lambu ya ke zaune bisa katuwar darduma, tare da dogarawa uku wanda ke tsaye daga gefe guda. Yanayin da iska ke kad’awa da kuma yanda gayayyaki da furanni su ka yi koreshe shi zai tabbatar maka da daminar bana ta yi kyau a masarautar Fabarusa. Sanye ya ke cikin farar shadda dinkin yar shara, ga farar hular shi da ta sha kari karkace bisa kan sa. Tunda ya aje wayar Gimbiya K’amariyya ya kasa motsawa daga in da ya ke. Dogon numfashi ya saka, ya na mai k'in gasgata abun da ya ji daga Gimbiya K’amariyya, kasancewar ba ya nan sa’in da Sarkin Sa’ayra da tawagarsa su ka ziyarci Fabarusa. Ganin ya yunk’ura da niyar tashi, Dogarai su ka yo kansa da sauri, yayin da d’aya daga cikin su ya matso gaban Yarima ya aje farin takalmi gaban sa, su na mai fad’in "Hattara dai magajin Sarki, hattara salamun Yarima’’ Cikin k’asaita ya zura k’afafunsa cikin takalmin, Dogarai su ka rufa ma sa baya, ba su fasa fad’in "Lafiya salamun Yarima, lafiyarka dama da hauni, dama da hauni lafiya, salamun salamun’’ Isar su bakin kofar lambu, da ke kufar ba ta da tsayi sosai, ga Barde da tsayi mashaAllah. Dogarawa su ka ce "Shafi bisa Yarima, sunkuye salamun’’(ma’ana Badde ya dan sunkuya kada ya bugi hular sa). Da fad’ar haka Barde ya d’an sunkuya, sai gasu sun fito daga cikin lambun. Duk in da su ka gifta sai ka ji ana mik’a gaisuwa. Shi kuwa ko kallo ba su ishe shi ba, Allah Allah ya ke ya isa ga turakar Sarki, sai dogarawan ke amsa masa gaisuwar, haka kuma ba su basa fasu nusar da shi ba ta hanyar kiran lafiya, duk san da su ka yi arba d abin da zai iya tuntu6e da shi, ko wanda zai iya 6ata shi kamar danshi, ko gidan tururuwa ko rami, sai ka ji su na ambaton ‘’Hattara salamun Yerima’’ Haka har su ka kai ga turakar sarki, in da su ka tadda Jakadiya daga bakin kofa. Ganinta Yerima ya tambaya Sarki shi kad’ai ne zai iya ganinsa? Da ke Yerima Barde dan gaban goshin Jakadiya ne nan da nan ta masa iso. Kai tsaye ya shige yayinda sauran dogarawan su ka yi tsaye su na jiran sa daga waje. Da shigarsa ya tadda Mai martaba hakimce, k’ishingid’e bisa wata k'atuwar dadduma da aka yi da fatar rak’umi, yayiwa hannun sa na hagu majingini bisa wani k’aton tintin mai zanen tambarin masarautar fabarusa, hannunsa na dama rik’e da k’aton jarbi ya na ja. Kyakkyawan tsoho ne mai kimanin shekara tamanin a duniya, shi kanshi Barde be k’ara ganin tsufar mahaifin na sa ba sai yanzu da ya gansa sanye cikin farar jallabiya, furfura fal bisa kansa, amma ace ya nemi auren yarinya yar shekara ishirin, wanda ya yi jika da ita, kai har tattaba kunne ma! Gaskiya dai maganar nan da kuskure. Zancen zucin da Barde ke yi kenan yayin da ya zube gaban Mahaifin na sa ya na mai mik’a gaisuwar sa. Amsawa Sarki yayi, tare da fad’in "Barde da wani abu ne?’’ "Barde ya dukar da kai kasa, kana ya ce ‘’Allah ya ja zamanin ka, shin za a taimakawa masarautar S’ayrasa ne?’’ Sarki na mai murmushi ya bashi amsa da ‘’Tabbas za mu taimaka musu, amma fa sai sun ba mu dama’’ Barde bai gushe ba ya k’ara tambayar Sarki ‘’Allah ya taimake ka, tunda su ka zo gare mu, ai sun bada damar kenan, Allah ya taimaki Sabkawa.’’ ‘’Ba su ba mu dama ba, kila dai za su bayar, amsar ta su mu ke jira’’ Sarki ya amsa a tak’aice. Jin haka Barde ya rusunar da kai, kana ya ce "Allah ya d’aukake ka ranka shi dad'e shin wata dama ce wannan?’’ Sai da wasu d’an dak’ikai su ka wuce, kafin Sarki ya bud’i baki ya ce ‘’Ba wata dama ba ce, illa kulla aminci ta hanyar kawar da gaba har abada. Mu na son tabbatar da amincin Sa’ayrasa, kafin mu fidda tsagwaran dukiya wajan taimaka musu, don haka mu ka yanke hukuncin auratayya tsakanin masarautarmu da ta su’’ Gaban Barde ne ya fad’i, cikin ransa ya na mai nanata "Dagaske ne kenan, innalillahi wa innailaihi rajiun!’’ Sarki na mai dubanshi, ganin yanayin da ya shiga ya ce ‘’Mu na sauraran Barde, akwai abun da ya kamata mu sani ne?’’ Nan da nan Barde ya nutsu, ya na mai 6oye halin da ya ke ciki ta hanyar yin nauyin baki ya ce "Babu Allah ya ja da ran Mai martaba, Allah ya tabbatar mana da alkairinsa’’ Cikin nuna jin dad’i Sarki ya ce ‘’D'an mu ya gama magana, mun san a koda yaushe kai mai amincewa da hukuncin mu ne ba tare da ka tsananta bincike ba, shi ya sa ba mu da haufi akanka. Wannan lamari alkhairi ne ga masarautar mu’’ Jikin Barde kamar wanda aka d’aure, zuciya sark’ak’e ya yiwa sarki sallama. Kai tsaye na shi sashen ya nufa, in da ya ji zazza6i na neman rufe shi tsabagen 6acin rai. ******* ******** Sa’ayrasa kuwa, Gimbiya Binta na fita turakar Sarki ta nufa, in da take da tabbacin za ta sami Jakadiya. Ta ko yi sa’a ta same ta ta gama shirya Sarki kenan, ya fita ran gadi. Zaune ta ke farfajiyar turakar sarki, ta na cin goro. Ganin Gimbiya Binta gabanta, ta shiga mata kirarin da ta saba mata ‘’Ture a ga tsiya, a kalla ruwan ido ya tsiyaye, tanka ka lalace, shiga d’aki bakin ciki ya kashe ka, ta Amale(Sarki) kin fi darbejiya d'aci, mai san zama da ke ya tambayi hali.’’ Gimbiya Binta na mai murmushi ta d'agawa bayin da su ka taka mata baya hannu, ma’ana su ba ta waje, nan da nan su ka koma da baya, yayin da Jakadiya ta mata tayin ko za su shiga daga ciki ne? Gimbiya ta ce rariyar ma ba laifi. Sabuwar shifid'a Jakadiya ta mata, In da Gimbiya ta ke tambayar shin ya lafiyar Takawa? Jakadiya na mai girgiza kai ta ce "Bijimin Duniya ana wani hali, damuwarshi ta kai matuk’a, abinci ma ba sosai ya ke iya ci ba, fari da batun tsohon banza na Fabarusa shi ya sako shi gaba Gimbiya’’ Gimbiya Binta na mai duban Jakadiya ta ce ‘’Jakadiya, halin da mai martaba ya ke ciki zai iya illata shi da ma iyalan sa baki d’aya, kuma watsi da lamarin Fabarusa barazanar rasa rayukan talakawa ne, domin za su ga Takawa ya fi san iyalan sa akan talakawan sa, wanda hakan ka iya kawo rabuwar kai a wannan masarauta ta mu, kuma ko shakka babu k’udirin abokan gaba Masarautar Fabarusa kenan’’ Jakadiya na mai jinjina kai ta ce "Sadak’ata Gimbiya, wannan batu na ki na yarda da shi’’ Gimbiya Binta ba ta gushe ba, ta nisa sannan ta k’ara da ‘’Masarautarnan kaf, babu wanda ya kai Jakadiya kusanci da sarki, yanda ya yarda da ke babu na biyunki, ke ki kasan Takawa, ke ki kasan cikin Takawa, shi ya sa ake kama k’afa da ke kan lamarin Takawa, gani na zo da shawara da kuma neman taimako daga gare ki, ban sani ba ko Jakadiya za ta amince da ni’’ Jin haka Jakadiya ta jefa kan ta baya, ta saki wani irin dariya mai k’ara kafin ta fara yiwa kan ta kirari kamar haka ‘’Sai ni Hindu Maryamu, jikar Baba Kilishi, jikar Nana, ban fito ba sai da na shirya ko a lahira rago ake duka dan bantan uba, lokacin iska akan ci 'ya'yan tsuntsu, kuci bayan gaban da k’aya’’ 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪[5/5, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣5⃣ Ko da Jakadiya ta kai ga aya a kirarin ta, ta na mai duban Gimbiya Binta ta ce fad’i in ji, in dai cigaban Babban biji ne sha yanzu magani yanzu. Jin haka Gimbiya Binta ta waiga kudu da arewa, gabas da yamma sannan ta dubi Jakadiya ta ce ‘’bangon gidan ga kunnuwa gare shi Jakadiya’’ Jin haka Jakadiya ta matsawo kusa da Gimbiya Binta, ta amsa da ‘’oh toh toh, bari na matso kusa kar iska ta kwasa ta kai d’akin o o da o o yan bantan uba’’ kunnan ta tafitar daga lullub’in ta, nan Gimbiya Binta ta shiga zayyana mata buk’atun ta, ko da Gimbiya ta gama, Jadiya ta ja da baya ta na mai fad’in ‘’Timirin katauje ba sai da kwandala ba, da kwandalar ne da yafi dama dama, haihuwa babu ciwo sai ka ce fitsari? Gwara ma fitsarin kayi yau da gobe, haihuwar da babu ciwo sai kace ruwan famfo? Gwara ma ruwan famfo ka yi murd’e murd’e’’ Gimbiya da ta gano in da Jakadiya ta dosa, ta na mai kallan gefe da gefe, kusurwa kusurwa gudun kar a jiyo Jakadiya, ta ce ‘’ kar ki ji komai Jakadiya, ina mai tabbatar mi ki idan har ki ka fad’awa Takawa wannan shawara sai ya mi ki babban kyauta, dadin dad’awa kuma ni ma mai mi ki kyautan zannuwa shirin ce, kuma hajjin bana har da ke, aradu ma kuwa’’ Jin haka Jadiya ta ce ‘’yo to menene, dan dai d’an wannan lamarin da be taka kara ya karya ba? An gama ran ki shi dad’e, yau d’in nan ma kuwa’’ Gimbiya na mai jin dad’i, babu shakka tarkon ta ya kama tsuntsuwa ta yiwa Jakadiya sallama, ta bar Jakadiya ta na Allah Allah ta ga dawowar sarki, dan kuwa dai bana kakar ta ta yanke sak’a in dai batun Gimbiya Binta mai yiyuwa ne, ga zannuwa da zuwa hajja, wannan shekara dai ta zo mata da kyau. ****** Bayan an idar da sallar Ishai, kamar kullum Bintu tare da su Innar ta zaune tsakar gida bisa tabarma su na shan iska. Tun da su ka zauna Bintu ta tsurawa zoben hannun ta ido, gaba d’aya ta rasa kwanciyar hankali. Inna ce ta ta6o ta tana fad’in ‘’ba da ke ake magana ba Bintu?’’ Bintu ta yi firgita ta dawo cikin hayyacin ta "eyee? Na’am?’’ cewar Bintu ta na mai duban Inna da Habibu da su ka kafe ta da ido suna kallan ikon Allah. Inna na buga hannu a iska ta ce ‘’yo to ba na fad’a ma ba, ba ta san ka na yi ba Habibu’’ Habibu na duban Bintu da ta sunkuyar da kai, har lokacin hannun ta be bar kan zuben ba, ya ce ‘’Inna kin sa halin ta, akwai damuwa da damuwar wasu, yanzu haka babu mamaki lamarin Babban gida ke damun ta, ko ta ce rashin lafiyar shugaban k’asa. ‘’mtsw wahalar da rai fushi da makwafci’’ cewar Inna ta na mai nuna Bintu da yatsa ‘’ki je ki d'aurawa kan ki ciwo akan wanda ba su san da ke ba bare su san ki na yi’’ Bintu ta dai ba ta ce komai ba, ita kad'ai ta san irin fad’uwar gaban da ta ke fama da shi. Ita dai adduar ta Allah ya sa alkahiri ne yanayin da ta ke ji. ***** **** Babban gida kuwa, Jakadiya ba ta yi k’asa a gwiwa ba, bayan ta gama shirya sarki cikin shirin bacci, Sarki na daga shingid’e, kafin ta raka shi wajan matar da ta za6a ma sarki kwana gurin ta ne ta ke bawa Sarki shawara akan lamarin da Gimbiya Binta ta sheda mata, ta k’are maganar na ta da ‘’watsi da al’amarin Sarki Abdulrahman barazanar rasa rayukan talakawa ne, sake dabara a nemi taimako wata masarautar talakawa za su ga kamar an fi san iyalan sarki akan lamarin rayuwar su, hakan ka iya kawo rabuwar kai cikin wanga masarauta wanda dama k'udirin Masarautar kenan. Tun da Sarki Abdulrahman be ji kunyar yada girman sa ba, da saka rayuwar mu cikin kunci, mu kuwa ba za mu kasa masa bita da kulle ba, dukan kabarin kishiya’’ shiru ta yi dan shan nufashi kafin ta k’ara da ‘’wannan dalili ya sa na yi bincike ta hannnun Gimbiya Binta, ta kuma amince da wannan batu, Allah ya ja da ran sa, idan na yi kuskure a yi min rai, ina tuba’’ Shiru ka je, Sarki na mai juya maganar cikin ran sa, in akwai abun da ya dame shi duk fad’in duniyar nan baya ya ke da farin da alumar shi ke ciki, idan kuma akwai abun da ya fi soyiwa a rayuwar sa, to ya bi bayan iyalin sa, musammam ma yaran sa mata guda biyu, hakan ya sa duk duniya babu wanda ya tsana, ya ke matsayin babban abokin gama kamar Sarki Abdulrahman na Fabarusa. Duk da batun Jakadiya lamari ne mai girma, ya tsinci kan sa ya na mai san yin tuntuntini akai. Ya na duban Jakadiya ya gyara murya ya ce ‘’Jakadiya mun ji wannan batu na ki, duk dai ba mu gamsu ba, za mu yi tunani akai’’ Jin haka Jakadiya ta duk’a ta na mai d’unkule tafin hannun ta na dama yayinda ta d’aga sama ta na mai jinjina ga Sarki, fad’i ta ke ‘’Sukukun bakaka Jatau, mashin da wuta Jatau, idan mai sa6o bai daina ba mai horon ma ba zai fasa ba!lafiya Barden mahadi! Lagiya Sukukun bakaka! Lafiya Darzaza amalen sarakuna’’ ******** 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 [5/5, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣6⃣ Washagari kan Sarki ya zauna fadanci, yayi kiran Waziri da Hadiman sa guda hud’u, dan kuwa tun zantawar sa da Jakadiya, har ta kai shi ga d’akin Inna Salti Sarki be runtsa ba, shawarar Jakadiya ke masa yawo aka. Ai kuwa dai Waziri ma na’am yayi da shawara, a fad’ar sa ‘’karan ban shi an maganin zoman bana’’ Biyu daga cikin Mahadin Sarki su ne su ka banbanta batu, ana su zai fi ga kyau Sarki ya tsaya tsayin daka kan lamarin sa na gaskiya, dan ko da ba su ji ba, wanga magana hallo maganar mata ce. A wannan sanadin ne Sarki ya ce in su na biye da shi za su iya zama fada, in kuwa ba haka ba ya na mai d’aure su har sai hakin masarauta ya cimma ruwa, dan babu damar korar su daga fada su na amintattun Hadiman sarki, surrin fada babu wanda ba su sani. Da wannan su ka ja bakin su su ka yi shiru, su na mai Allah wadar da wanda ya bawa Sarki wanga shawara, dan kuwa Sarki idanu ya rufe madafa kawai ya ke nima, ya kuma sami bahaguwar madafa mai wuyar 6ullewa sai dai fa Allah shi kyauta da aikin dana sani. Bintu na gyaran gadon Gimbiya Binta, ita kuma Gimbiyar na daga kishingid’e bisa tin tin ana mata danna. Sai ga Jakadiya ta shigo jiki na rawa daga gani kasan da magana a bakin ta. Bayi na ta gaishe ta, haka ma Bintu wacce tun shigowar Jakadiya ta ga ta kafe ta ido. Jakadiya na mai duban Bintu ta ce "ko da ban sani ba ke an Bintu’’ Gaban Bintu ne ya fad’i yayinda ta zube k’asa ta na mai fad’in ‘’Allah ya huci zuciyar Jadiya, Bintu na ke ba ki 6ata ba’’ Kallan ta ta ke cikin nazari, kafin ta juya ta dubi Gimbiya Binta, gudun kar sauran bayi su gane sakon da za ta fad'wa Gimbiya, sai cewa ta yi ‘’ta kan kwaba, ta kan kan ta, ta kan akwati mai taya, sai sid’if ta fad’a, sai sid’if na d’auka’’ Jin haka Gimbiya Binta ta saki k'awataccen murmushi, dama abun da ta ke jira kenan, kana ta ce "zannuwa ishirin sun yi kad’an, aradu na k’ara mi ki goma har da kallabi goma’’ Jin haka Jakadiya ta rangwad’a gud'a ta na mai fad’in ‘’yaro wake tab'a mai uwa? Ba zai ci ba kayan kasuwa, sai ni Hindu jikar Baba Kilishi Jikar Nana, godiya na ke Gimbiya’’ Kana ta kai kallan ta ga Bintu ta ce "biyo ni yarinya’’ Gaba Bintu na fad’uwa duk dai ba ta fahimci zancen na Gimbiya da Jakadiya ba, ta bi bayan Jakadiya. Ganin haka wata Baiwa mai kaiwa Yerima Nuhu duk wani labari na game da lamarin Bintu ita ma ta ja kafar ta zuwa neman Yarima Nuhu, dan kuwa dai ita ma ba ta gamsu da wannan lamari ba. Bintu na tafe bayan Jakadiya, ganin in da su ka dosa gaban ta sai faduwa ya ke, musammam da ta ga sun doshi turakar Sarki gadan gadan. Nan su ka tadda Sarki tare da Waziri da Hadimai, bayan su babu wani mahalik’i da ke wajan face amintaccen bawan sarki wanda ake kira Nahana. A bakin kofar turaka Bintu ta kasa d’aga k’afa ta shiga dan tsoro da kwarjini, tun da aka haife ta ko harabar wajan ba ta tab’a shiga ba, bare ace turakar sarki, ga ta ga sarki. Sai da Jakadiya ta d’an jawo ta, na mai mai mata shune da baki ta shiga. Ganin ta gaban Sarki tuni ta zube k'asa ta na mai kwasar gaisuwa. Yau ga Bintu ga Sarki da waziri har da Hadimai, ko shakka babu dole k'awarta Cangwai ta ji wannan labarin. Sarki zaune ya hakimce cikin rawani, ya dubi Jakadiya ya ce ‘’ba mu tarihin wanga d’iya’’ Zama Jakadiya ta gyara, kafin ta ce ‘’Allah ya ja daran Babban bijimi, wanga d’iya sunan marigayiya Baba Kilishi ta ci, hakan tsirar haihuwar ta da Gimbiya k’arama kwana d’ai ta, tare su ka tasa da Gimbiya k’ara, dad'in dad’awa makarantar su d’aya, bambacin su d’aya, wanga dai baiwa ce, kuma d’yar bayi, diya ce gun uwar bayi da kuma wannan bawa da ake kira Bala, eh Mahuta ba ,aradu ma kuwa’’ Waziri ya dubi Jakadiya ce ‘’ai fad'uwa ya zo daidai da zama, uban ta shi an babban bawa nai, ya ta ke da suna?’’ ‘’Fatima, amma Bintu aka ce mata, kamar yanda ake kiran Gimbiya k'arama Binta’’ ta bashi amsa a takaice. Ita dai Bintu ta na nan kai durkushe daga can gefe amma daga tsakiya da ke ba shakka turakar ba dai girma ba, na gaske ma kuwa. Ko kwakkwaran motsi ba ta iyawa, bare ta d’an d’aga ido gudun kar ta had’a ido da Sarki, dan karshen kwarjini ya mata a yau da ta ke ga ta gashi. ‘’Fatima’’ muryar Sarki ta ji ya daki kunnan, tuni ta k’ara nutsuwa ta na mai rusunar da kai kamar wacce za ta shige k’ark’ashin k’asa. Ba mafarki ta ke ba, sarki da kan sa ya kira sunan ta, ina ma Cangwai ta na nan ta gani da idon ta, dan Idan ta ba ta labari sai ta ce k’arya ta yi.....tunanin da ta ke cikin ran ta kenan, jin Sarki ya ce ‘’a matsayin ki na baiwa a gare mu, shin akwai umarnin da za mu ba ki ki bi?’’ Bintu ta yi saurin duk’ar da kai ta ce "tir da bawan da bai bin maganar uban gidan sa, zan bi umarnin Mai martaba, ko da kuwa hakan zai zama sanadin rasa rai na, kwankwatsi ma kuwa’’ Kwalla na kad’ai Hadiman nan biyu ba su zibdawa Bintu ba, shi kuwa Waziri kai ya shiga kad’awa cike da gamsuwa, bare Jakadiya da ta ke ji kamar ta sab’a Bintu a baya tai ta rawa, Allah dai ya kawo mata tsuntsu daga sama gashesshe. Sarki na mai nazarin Bintu na wani d’an lokaci, daga bisani ya ce za ta iya tafiya. Ta na mai godiya ba tare da ta san abun da ake kullawaba ta fita. Bayan tafiyar ta Sarki ya ce ya gamsu da komai na ta, amma ya na so Jakadiya ta sa ido kan ta na wani d'an lokaci kafin su gama zartar da hukunci. Da haka da haka har su ka wuce zaman fada. Da yammacin ranar gaba d’aya walwalar Gimbiya K’amariyya ya dawo. Bintu na zaune gaban ta tana yanke mata farce wayar gida da ke aje d’akin ta ya fara k’ara. Cikin farin ciki ta d’aga, ganin haka Bintu ta tashi da niyar ba ta waje, amma Gimbiya K’amariyya ta d’aga mata hannu alamar ta yi zaman ta. Maganar da Gimbiya ke fad’awa Yarima Barde ne ya bawa Bintu mamaki, ji ta yi ta na fad’in ‘’Takawa dai ya yanke hukumcin aurar da kauna ta Binta ga Mai Martaba Sarki na Fabarusa...’’ Gaba d’aya jikin Bintu yayi sanyi, cikin ran ta tausayin Gimbiya Binta ta ne ya kama ta, har fad’i ta ke "Allah sarki Gimbiya ta ceto rayuwar ‘yar uwar ta, yanzu na gane dalilin maganar da sarki ya min, wato ina d'aya daga cikin bayin da za’a tura tare da Gimbiya Binta, kaiconi Bintu karatun mu kuma shikenan’’ Tausayin Gimbiya da ita kan ta shi ya gajiyar da ita ranar, ta kasa ta6uka komai har dare yayi ta koma gida. Suna cin abinci da Inna, yau sun sami sauran biski daga gidan Sarki. Baba ya shigo babu sallama sai surutai ya ke kamar mahaukaci saban kamu, fad’i ya ke ‘’ta na ina ne wai ma?’’ ganin su a tsakar gida ya ja ya tsaya ya na mai fad’in '’yo to ashe ku nan kusa ma’’ Inna ta yi kasake kafin ta ce ‘’Hallo Malam Lifiya? Yau ko sallamar babu?’’ ‘’sallamar kenan ai uwar matar sarkin Fabarusa’’ cewar Baba ya na mai duban Bintu da sai saka lomar biski ta ke, hannu baka hannu kwarya. Inna na murmushin jin maganar Baba, ta ce ‘’Malam yau kuma raha a ke ji?’’ Cikin jadadawa Baba ya ce ‘’yo to wani raha bayan yanzu waziri ke sheda min, nan da d’an kwanaki za a tura a tsaida ranar bikin Gimbiya Bintu’’ ya k’arasa maganar ya na mai washe baki wanda daga Inna har Bintu sun kasa gane manufar dariyar ta sa. Inna ce ta ce ‘’ayyo, Gimbiya Binta ko? Ai yanzu haka maganar da mu ke kenan, Wallahi yanzu ta ke sheda min’’ Baba na mai duban Bintu ya kai mata dak’uwa ‘’ungo nan yar jakar uba!’’ baki cike da biski Bintu ta tsaya ta na duban Baba. Ganin haka Inna ta ce "Allah sarki, aradu ba munahinci ta yi ba, hira ce ta kawo maganar....’’ Cikin k’ulewa Baba ya ce ‘’yo to na gaji da wannan rashin fahimta ta ki Yagana, gide ina nuna mi ki annabi hallo ki na runtse ido, wannan(ya nuna Bintu da yatsa) ita za a amrar ga Sarki Abdulrahman na Fabarusa a matsayin d’iyar Sarki....’’ tuni Bintu ta kwarai, ta wanke Inna da biskin bakin ta tsabagen tari. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣7⃣ Inna na mai rafka salati gami da dafe k’irji ta ce ‘’lahaila haillallahu mahammada rasulilahi! Bintu kuma Malam? Me ya had’a Bintu da masarautar Fabarusa saboda Allah da manzan sa? Yo to da haka a d’au wuk’a a da6a mana sai mu san kashe mu ake son yi da hujja!’’ Baba na mai nuna Bintu da d’an yatsa wacce ta ke hawaye d’aya na bin d’aya ya ce ‘’ga ta ga ki nan dai shegen biko’’ Kuka Inna ta sa yayinda ta rungumo Bintu ta na fad’in ‘’bar kuka Bintu, bar kuka d’iyar arziki, addua shi ya kamata mu yi, innalillahi wainna ilaihiraji’un’’ Ganin haka Baba ya sa kai ya fice ya na mai fad’in ‘’kwa dai k’araci munahuncin ku, bakin alk’alami ya bushe’’ Ranar sam Bintu ba ta sami bacci ba, kwana ta yi ta na kuka. Shi kan shi yayan ta Habibu ya tausayawa Bintu, zai ji dad’in zama yayan matar sarki, amma kasancewar auren hatsari ne ya sa shi girgiza da juyayin abun. Washagari da ciwan mara Bintu ta tashi, kasancewa al’adar ta ta sake dawowa, ga kuncin zuci da ya addabi rayuwar ta ya sa gaba d’aya ta fita daga hayyacin ta. Ji ta ke dama motar bayi sun tafi sun bar ta a makaranta, in ya so Aisar ya tafi da ita ta huta da wannan rayuwa mara ‘yanci. In kuwa ta tuna shikenan fa ba ita ba komawa makaranta, ita da Aisar sai dai ta hange shi a akwaitin talabijin idan Allah ya sa an nuna shi sai ta k’ara saka wani kukan har da shasshek’a. Ko damar shiga babban gida ba ta samu ba, haka kuma daga Gimbiya K’amariyya har Gimbiya Binta babu wanda ya bi ta kan ta. Musamma Gimbiya da buri ya cika. Ranar sarki ya tara iyalen sa a turaka bayan Jakadiya ta tabbatar ma sa da inganci da ilimin Bintu akan sarauta kasencewar ta tashi gidan sarauta, wanda su ke da yak’inin lamarin da aka k’ulla zai daidaita ba tare da an sami akasi ba. Zaune suke gaban Sarki, Hajja Kilishi ce zaune ta 6arin dama, kusa da ita Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta ne zaune. Sai Uwar fada da kuma Inna Salti, kusa da ita autan ta Yarima Nadir ne zaune daga 6arin hagu. Gaban su kuma ‘ya’yan Sarki ne maza, ciki har da babban d’an sa, dokajin Sa’ayra sa wato Yarima Inuwa, kusa da shi Yarima Nuhu ne. Sai kuma daga can gefe Yarima Hassan da Yarima Hussaini, Yarima Hamza, Yarima Abdallah da kuma Yarima Ahmadu su ka yi na su dairar. Jin batun na Sarki, idan aka d’auke Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta da dama ita ta kulla k’ulalliyar babu wanda be girgiza ba. Yarima Inuwa ne ya duk'ar da kai kana ya ce ‘’Allah shi ja da ran Sarki, shin an zatar da hukunci ne ko kuwa ana buk'atar shawara daga iyalan Mai Martaba?’’ Sarki na mai duban sa ya ce ‘’mun gama yanke hukunci, amma jin ta bakin ku ba laifi ba ne’’ Jin haka sai Yarima ya ce ‘’Allah shi kyautata lamarin Babban biji, komai ku ka zartar daidai ya ke, ina ga zai fi kyau a duba lamarin nan saboda gaba, ran Mai Martaba ya dad’e’’ ‘’Allah ya ja zamanin Takawa, ni ma dai hakan zance, dan kuwa gaban ya fi baya yawa, muddin ba za mu iya yin yanda su ka tambaya ba, zai fi kyau a yi watsi da maganar gaba d’aya in ya so sai mu nemi taimako wani wajan daban ko kuwa a amra masa K’amariyya yanda ya buk’ata’’ Inna Salti ce ta ara ta yafa, dan kuwa kusan ta fi kowa jin d’acin maganar cikin matan Sarki, hakan ya sa ta kasa yin shiru. Tun da ta fara maganar Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta ke hararar ta ta wutsiyar ido. Shi kuwa Yarima Nuhu tun da aka fara maganar ya ke son furta abun da ke ran sa, jin Yarima Inuwa tare da Inna Salti sun share masa fage be yi k’asa a gwuiwa ba ya ce ‘’Ran ka shi dad’e, ka gafarce ni, amma ni a nawa wautar wannan lamari ba shi ne mafita ba, shin ya za mu yi a warware wannan sak’ar idan har aka kulla? Menene makomar wannan baiwa idan Allah ya sa Masarautar Fabarusa su ka gano wannan lamarin? Menene mazaunin wannan Masarauta ta mu? Shin gaba ake san kawarwa ko kuwa wata gabar ake san kullawa? Wannan tunani ya sa na yarda da Inna Salti, mu yi yanda Masarautar Fabarusa ta buk’ata ba tare da wani sark’akk’iya ba, ko kuwa zai fi kawai mu hakura da batun gaba d’aya in ya so mu nemi taimako a wata Masarautar ko ma Gwamnatin tarayya duk da dai shugaban k’asa be da lafiya, da lafiya ya ke na san da ba a kai ga haka ba, kuma ba za a rasa wanda zai duba wanga lamari ba’’ Ko da Yarima Nuhu ya dasa aya, Gimbiya Binta ji ta yi kamar ta kurma ihu, ita kuwa Gimbiya K’amariyya har ta fara kwalla ganin Yarima Nuhu na neman dawo da gaba baya. Shiru ya biyo baya. Har sun fitar da rai da k'ara jin maganar Sarki, daga bisani ya numfasa ya na mai duban Hajja Kilishi ya ce ‘’wani shawara za mu ji daga gare ki? Shin kin amince mu aurar da d’iyar mu ga abokan gaba ko kuwa mu sake neman taimako wanda hakan jinkiri ne wanda ya ke barazana ga rayukan talakawan mu?’’ Hajja Kilishi na mai nusar da kai cike da kissa ta ce ‘’lafiya toya matsafa, lafiya waliyin Allah, lafiya baya goya marayu, lafiya adali! Hukuncin ka daida ta Saka Takura, mun ji mun kuma amince’’ Sarki na mai nuna jin dad’i da batun Hajja Kilishi, haka ya bi sauran iyalan sa kowa na fad’in na shi albarkacin bakin. Duk da Sarki ya san Su Inna Salti, Yarima Inuwa da Yarima Nuhu sun fi gaskiya, sai ya bi san ran sa tare da kafa hujjar an rinjaye su, dan haka maganar ta tsaya. Da wannan su ka watse kowa da abun da ya ke sak’awa cikin ran sa. Musammam Yarima Nuhu wanda ba tun yau ya ke da k’udirin mallakar Bintu ba, ko da kuwa a matsayin sad’aka ce, tin da wata baiwa ta kawo masu tsirkun abun da ta ji Gimbiya Binta da Jakadiya su na kullawa ya kasa sukuni. Ya had’a goma na arziki ya nemi amintacciyar baiwar sa, ya ce ta kaiwa Jakadiya, wato na sharan fage kenan kafin ya je mata da buk'atar sa. Su Gimbiya kuwa ko da su ka koma na su 6angaran mamakin yanda Yarima Inuwa, Nuhu da Inna Salti su ka nuna k’iyayyar su k’iri k’iri ta hanyar k’in amincewa da wannan lamarin, a nasu tun da su ne su ke ciki d’aya su ya fi dacewa ace sun yi na’am da lamarin, amma ga mamakin su waccan da su ke kira yan bakin gida su ne su ka fi nuna kauna gare su. Yarema Nuhu kuwa kai tsaye 6angaran sa ya nufa rai 6ace, babban takaicin sa shi ne a rasa baiwar da za a sa cikin wannan hatsari sai Bintun shi ta arziki, Bintu da ya dad’e ya na saka buri akan ta, gaskiya dole ya san yanda zai yi wannan maganar a rusa ta. Bakin kofa ya ci karo da Baiwar da ya tura gun Jakadiya, hannun ta nik’i nik’i da kayan da ya bata ta kaiwa Jakadiya. Da ganin sa ta zube k’asa ta na mai gaishe shi. Cike da mamaki ya ce ‘’ba ki kai mata sak’on ba ne?’’ Kai duk’e Baiwa ta ce ‘’Allah shi taimaki Yarima, Uwar baka ta sake hali, da na kalle ta sai dak'uwa ta min, kasan Jakadiya gara ce, ga tsiya ga rana, tsiyar ta ya fi ranar ta yawa’’ Jin haka ya gane me ya faru, ma’ana dai Jakadiya ta yi tsiyar ta, ta kuma k'i kar6ar tsarabar sa wanda hakan ya na nufin ba zai sami kowani taimako daga gare ta ba. Cikin zafin rai Yarima ya ce ‘’kya iya tafiya da kayan’’ Sannan ya tsallake ta ya shige ciki ya na mai bugo k’ofar. Yayinda baiwa ta had’e kaya ta yi gaba, Allah ya kashe ya bata. A wuni guda Bintu ta rame ta lalace kamar wacce ta shekara ta na ciwo. Da Baba ya dawo da daddare ya ke sheda mu su an fa aika Fabarusa, zance ya tabbata nan da wata d’aya za a amrawa Sark’i Abdulrahman aure da Binta d’iyar Sarki Sule na Sa’ayrasa. Inna na mai d’aure fuska ta ce ‘’yo to tun da ba da Bintu aka ce ba ai can da su gada, ni dai d’iya ta ba sunan ta Binta ba, Bintu an sunan ta, haka kuma ba d’iyar sarki ba ce d’iya ta ce’’ Baba na mai duban ta ya saki murmushin takaici, kana ya ce ‘’ke kuma d’iyar wacece? Ko in ce ke wacece a Masarautar nan da ga ke har d’iyar ta ki?’’ Inna ta yi shiru, ganin haka Baba ya k'ara '’shirun da ki ka yi ya tabbatar min da kin tuna ashefa ku bayi ne, dan haka ba ku da ‘yanci, ki ma godewa Allah da ya sa amrar da ita ya ce zai yi ba bada ita zai yi sadaka ko sad’aka ba, gide ke dai kin cika butulu. Toh ki saurare ni da kyau gobenan za a zo a tafi da Bintu ga babban gida, hallo dangin ki d’aya ba a yarda kin shedawa ba, yo to ina bayi ina wasu dangi ma in ban da ba'a" Kuka Inna ta saka ta na fad’in ‘’wannan zalinci da ke shirin aikata min da wanga yarinya Allah shi isar mana’’ Ciki Baba ya shige kafin ya lek’o da kan sa ta assabari ya furta ‘’je ki tari Magajin Gabasawa ki sheda masa, yo to ba ni na kar zoman ba, rataya aka bani’’ Ita kuwa Bintu da ke jiyo su daga d'aki zuciya ne kad'ai ba ta had'iya ba, tunani ta ke ina ma Aisar ya na kusa ya kawo ma ta d'oki yanda ya [truncated by WhatsApp]® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣8⃣ Kamar dai yanda Baba ya ce, da sassafe sai ga Jakadiya da amintaccin bayin Hajja Kilishi sun dokowa Inna sammako. Dan takaici Inna d’auke kan ta yi dan kuwa ta kasa bud’e baki ta ce da Bintu ta fito ta bisu. Tun da Bintu ta ji sallamar su ta shige bayan kofa ta yi zaman ta, duk da ta ji buk’atar Jakadiya amma k’yememe ta k’i fitowa. Ana haka Baba ya fito ya rufe Inna da fad’a ‘’Magajin Gabasawan za ki yi wa musu ko kuwa Jakadiya? Iye Yagana? Gide ban san tsaurin idanu fa! Yo to yau ko ke Magajin Gabasawa ya ce zai aura sauki zan yi bare ma wanga d’iya, aikin banza aikin hofi! Ta na ina wai? Gide Bintu hito ki bi su in ba haka ba ina make ke! kwankwatsi ma kuwa!’’ Jakadiya na murmushi ta ce "Mahuta bi su a hankali, ai tsakanin uwa da d’iya sai Allah bare kuma ace za a raba su rana a tsaka, bi su a sannu Mahuta, in ban da ke da abin ki Uwar bayi wanga lamari ai alheri ne aka yiwa d’iyar ki, wanga abu abin san barka?’’ Idan Inna ta tanka ko shakka babu dutse ma ya tanka, ganin haka Baba ya wuce su izuwa d’akin Bintu, ya tadda ita bayan kofa ta had’a zufa da hawaye. Fad’a ya hauta da shi, ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Amma kyememe Bintu ta k’i motsawa bare ta fito. Aikuwa da Baba ya fusata sai ya hauta da zagi, jin haka Inna ta shige d’akin da sauri dan ta san daga nan kuma abun da zai biyu baya. Ilekuwa shigar ta kenan ta ga Baba ya d’aga hannu ya na shirin kaiwa Bintu bugu, nan da nan ta shiga tsakani, ta ce ‘’haba Malam! Ai ka ji tsoran Allah abin ga ai sai yayi yawa maye da hauka!’’ Nan fad’an Baba ya koma kan Inna, ai lalle Inna ke d’aurewa Bintu, dan haka zai fita ya dawo, in dan ya dawo ya ga Bintu gidan nan sai na lahira ya fita jin dad’i. Dan masifa da bambami ko sallama be yiwa su Jakadiya ba ya sa kai ya fice ya na kumfar baki. Bayan fitar sa Inna ta ja hannun Bintu su ka fito tsakar gida. Inna na mai duban ta ta ce ‘’Bintu idan har ni na haife ki, toh na baki umarni ki bi su ku tahi Babban gida’’ Bintu na jin haka ta zube k’asa, hannayen ta biyu ta sa ta ruk’o k’afar Inna ta na fad’in ‘’Inna na tuba, Inna ki gafarce ni, Inna ki min afuwa, Inna kar ki ce na bisu, Inna kar ki yarda a raba ni da ke, kwankwatsi na dena 6ata mi ki rai, idan na k’ara aratta kashe ni’’ Inna na mai janye k’afafun ta daga ruk’on da Bintu ta yi mata ta ce ‘’na yafe ki duk da ba ki ta6a sa6a min ba, ke d’iya ce ta gari, dan haka ki sa Allah a ran ki shi ne kad’ai ka iya mi ki, tashi ki bisu, Allah shi fisshe ki alkairi...’’ Ta na gama fad’ar haka ta shige ciki ta na hawaye. Nan fa Bintu kuka har da birgima. Su Jakadiya su na nan suna gani sarautar Allah duk da dai su ma kukan na Bintu ya so ya d’an ta6a su. Habibu ne ya shigo, ganin abin da ke faruwa ya shiga rarrashin Bintu, har ya samu ta yi shiru. Ya ce da su Jakadiya su yi gaba gasu nan biye da su, bara ya had’o kayan Bintu. Jakadiya ta ce ah ah ba a bukata, ita d’in ta kad’ai ake buk’ata. Gaba su ka yi, hannun Bintu ruk’e da na Habibu, su na tafe ya na bata baki da nasiha har su ka isa kofar Babban gida. Nan ma Bintu ta ce ba ta san zance ba, Habibu be isa ya koma ya bar ta gun su Jakadiya ba. Jakadiya ta fusata ta hau Bintu da fad’a ‘’yau ina ganin walele gi6in takwaru! Gaskiya ne komai girman d’an mara kabo be isa aure ba! 'Yar tusa wacce ba ta san arziki ba! Ki na baiwa d’iyar bayi har kya wa mutane kwawarniya shiga rumbun k’ore, yo to sai ki ma Babban Bijimi musu da kwarnato in ya so a tsire ki ma ga me asara!’’ Bakin Bintu na rawa, ta saki hannun Habibu, wanda d’acin maganar Jadiya ya sa shi juyawa da sauri dan gudun kar ya maida mata ya jawowa Bintu da ma gidan su baki d’aya, ya na jiyo Jakadiya na masife Bintu yayinda ta ke hankad’a kafad’ar ta zuwa ciki, babu yanda zai yi haka ya tafi ba tare da ya sake ko waiwaye ba. 'Dakin Jakadiya aka aje Bintu, nan ta sha kukan ta, ta k’oshi dan kan ta ta yi shiru sai ajiyar zuci kawai. Jakadiya ta shigo kana ta ce ta saka mayafi ki biyo ta, Babban bijimi na jiran zuwan su. Kallabin ta ta ware ta yafa bisa kan ta, babu musu dan kuwa taji tsoran maganar Jakadiya na za a tsire ta, ta bi bayan Jakadiya ba su zame koina ba sai turakar sarki. In da Jakadiya ta tsaya daga waje, Bintu ta shiga daga ciki. Nan ta tadda sauran ilayan Sarki. Gimbiya Binta ba ta fasa watsawa Bintu kallan wuk’anci ba, ita kuwa Inna Salti tsabar tausayin Bintu ne cikin ran ta. Yarima Nuhu kuwa Allah kad'ai ya san tashin hankalin da ya shiga, musammam yanzu da ya ga Bintu gaban Sarki, babu makawa ya na ji yana gani Bintu za ta si6ice ma sa. Tin shigowar ta ya sa saka idanu akan ta, k’irik’iri be damu da ba shi kad’ai ne ba, bare ya damu da fassarar da za a iya masa. Ita kan ta Gimbiya Binta ta lura da irin kallan da ya kewa Bintu, har zunguran K'amariyya ta yi dan ita ma ta ganewa idon ta, bare kuma su Hajja Kilishi har da murmushin mugunta, dan kuwa ta k’i jinin Yarima Nuhu. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. ©Khadija Sidi.....✍🏼 1⃣9⃣ Muryar Bintu a shak’e tsabar kukan da ta yi ta kai gaisuwar ta ga Sarki. Hankali kwance, idan Sarki ya lura da sauyin yanayin da aka samu game da Bintu tsakanin ranar da ta fara zuwa gareshi da kuma zuwanta a yau, bai nuna ba don kuwa ko a jikinsa ya amsa, kafin ya k’ara da ‘’Masarautar mu na godiya ga wanga d’iya ta arziki, kasancewarki baiwa, mun baki ‘yanci, mun ‘yanta ki a yau kin tashi daga baiwa kin zama d’iya mai ‘yanci...’’ A firgice Gimbiya Binta ta kai kallonta ga Sarki ta na mai fiddo ido waje dan kuwa ba ta yi zato ba, kar dai danasani za ta yi, abun da ya fara zuwa zuciyarta kenan yayinda gaban ta ke dukan uku uku. Haka ma kowa na wajan ke kallan Bintu, wacce ta rasa me za ta yi, murna za ta yi na samin ‘yancin rayuwar ta bayan shekara goma sha biyar ta na baiwa, ko kuwa kuka za ta yi ta tashi daga baiwa, amma iyayenta na nan a bayi, tabbas ta tabbata d’iyar bayi. Hawaye ne d’aya bayan d’aya ke gangarowa daga idanun ta, murya na kakkarwa ta ke fad’in ‘’Godiya na ke ranka shi dad’e, godiya na ke Allah shi ja da ran Sarki, Alkhairin Allah ya tabbata a gare Mai Martaba’’ Yarima Nadir da ke jikin Inna Salti ne ya ce " Inna Salti me ya sa Bintu ta ke kuka?" Hannun Inna Salti bisa le6enta ta amsa da "Shhhh" Wato ya yi shiru, shirun ko yayi.Yarima Nuhu wanda shi kansa ya rasa shin wai me ya ke ji a lokacin ji yayi kamar ya isa ga Bintu ya sa hannu ya share mata hawayen idanunta, ji ya ke kamar ya rok’i Sarki a bar ma sa Bintu, ko da kuwa shi ne abu na k’arshe da zai tambaya gun Sarki ya amsa masa. Yau ga Bintun arziki an zama ‘yantacciya, wannan fa shi ake kira ga k’oshi fa ga kuma kwanan yunwa. Sarki bai gushe ba ya k’ara da ‘’Nan da mako hud'u za mu amra miki aure ga Masarautar Fabarusa, da an amra za a ba mu bashin da mu ka buk'ata, hallo tarewar ki can sai nan da mako hud'u kan nan kin sami shiri mai kyau. Ba mu amince ba sai da mu ka tabbatar de ke baiwa ce mai tarbiya, dattako da kuma sirri,kasancewar kin iya zama da d’iyar mu lamun lahiya ba tare da ta ta6a kawo mana kukan ki gare mu ba’’ Gimbiya Binta aka zagayar da kwayan ido ta cikin mayafi, cikin ranta fad’i ta ke ‘’Yo to ba girin girin ba d'iyar bayi, ta mai......’’ Jin Sarki ya ce ‘’Hajja Kilishi ga wanga d’iya za ta dawo gare ki ina fatan ke da Jakadiya za ku sa ta hanya, cikin surri ku koyar da ita dabarun Masarauta duk dai yanda Jakadiya ta sheda mana yarinyar dama mai sani ce, mu na so duk kan nan ku sani ba mu yarda ko da wasa wani ya k’ara kiran wannan d’iyar arziki da baiwa ba, haka kuma ban amince a yi mata yanda ake yiwa bayi ba, ku sani wanga d’iya d’iyar mu ce, dan haka a daraja ta’’ Gimbiya ta cije le6e, ita dai kam wannan lamari ba ya mata dad’i, ya Takawa ya ke san mata sakiyar da ba ruwa ne, ko da yake ma ita ina ruwan ta k’arshen ta ajali ne ke kiran Bintu, dan kuwa girman Masarautar Fabarusa ko jinin saraki sai sun shirya zaman ta bare baiwar da za ta je a matsayin Gimbiya, tun da dai ta ci nasarar sa min Aisar, ga shi Gimbiya K’amariyya ta sami Barde ai hutatai. Abunda ta ke jaddadawa zuciyar ta da ta ke nemen fashewa tsabagen bakin cikin kalaman Sarki kenan, bilhakki danasani ta fara, dan kuwa ba ta yi zato ba. ‘’Za mu mayar da d’iyarmu Binta kasar Nigeria, in da za ta je can ta cigaba da karatu kan mu biya bashi ga Masarautar Fabarusa komai ya warware........’’ Gimbiya Binta ba ta san sanda ta tashi tsaye a zabure ba, ta na mai girgiza kai. Nan kallo ya koma gare ta har sai da Yarima Inuwa ya daka mata tsawa ya na mai fad’in ‘’Gide kin manta gaban wa ki ke ne! ko ma ki zauna kar ki mana sakarci a nan’’ Gimbiya K’amariyya ce ta jawo hannunta, yayinda ta koma ta zauna a gajiye, tuni idanunta su ka kawo ruwa, ba ta san sanda ta furta. ‘’Tuba na ke Takawa, Allah ya ja da ran Sarki a min rangwame tuba na ke kar a bari na yi nisa da Mai Martaba’’ ‘’Ko kuwa dai ba kya so kiya nisa da Aisar Gaddafi Nur ba’’ Fad’in Gimbiya K’amariyya kenan wacce ke rike da hannun kanwarta ta, cike da tausayi ta ke dubanta, dan kuwa ita kad’ai ta san zafin da ta ji jin za a raba ta da masoyinta Barde, yau kuma gashi ‘yar uwarta na shirin rasa na ta masoyinta sakamakon taimakonta da ta yi. Kana ta kada baki ta ce "Allah shi ja da ran Sarki, dan Allah a duba lamarin nan, Binta har yanzu yarinya ce, za ta cutu muddin ta yi nisa da mu.’’ Yarima Nuhu na dubansu, bakinshi kunshe da murmushin mugunta ya ce '’Kar ki fad’awa Takawa wanga yashashen zance haka K’amariyya, idan har wanga d’iya( ya nuna Bintu da yatsa) za ta iya taran aradu da ka ta shiga Masarauta mai girma a cikin badda kama, duk da k’aranci shekarunta, ban ga dalilin da zai sa Binta ba za ta iya zuwa wata k’asar ba domin rufawa masarautar ta asiri ba, yo to menene nan da makwafta Nigeria, ai Nigeria da Nijar d’aita, ko kuwa ki na nufin za a aurar da Bintu matsayin Binta ne kuma jama’a na ganin Binta a k’asar nan, dole sai ta tafi’’ Ya k’arasa magana ya na mai duban Gimbiya Binta da ta ke kuka bilhakki. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. ©Khadija Sidi.....✍🏼 2⃣0⃣ ‘’Nuhu ya yi gaskiya, kamar yanda wanga d’iyar arziki ta mana biyayya, mu na fatan ke ma haka za ki kasance me biyayya a gare mu, saboda haka sai ki zauna da shirin ki na bulaguro nan da mako hud'u, komai za a yi jiyo shi cikin surru, kar ku yarda da kowa sai amintaccun bayin ku. Mun yi magana, Mun sallame ku’’ Cewar Sarki kenan ya na mai kawar da kai daga kallan Gimbiya Binta gudun kar ta karya masa zuciya, dan kuwa shi dai yaransa su an rauninsa. Komawarsu d’aki nan Gimbiya K'amariyya ta ga kuka da daru gun Gimbiya Binta, ba shiri Inna Salti da Hajja Kilishi su ka sallami bayin da ke cikin 6angaran gudun yad’uwar maganar. Wanda kuma su ka riga su ka ga halin da Gimbiya Binta ke ciki, Jakadiya ce ta tara su, cikin hikima ta mu su kashedin ko da wasa kar su yarda a ji halin da Gimbiya Binta ta shiga jin Mai martaba ya ba da amran ta ga Sarkin Fabarusa, duk wanda aka ji a bakin sa sai dai uwar sa ta haifi wani. Ai kuwa dai ba su fasa yad’awa ba, ta yanda Allah ya so ma maganar Jakadiya su ke yad’awa ba asalin zancen gaskiya ba. Dakyar aka samu Gimbiya Binta ta sarara da kukan da ta ke, ita sam ta manta da azanci a maimakon ita za a aurar da Bintu, kasancewar haka ita ma sai an 6oyeta na wani d’an lokaci. Gashi Mai martaba ya ‘yan ta Bintu, wacce ta ke baiwar ta tin tale tale. Bauhaushe dai yayi gaskiya, in za ka gida ramin mugunta, ka gina shi gajere. Da yamma Bintu na zaune d’aki tare da Hajja Kilishi, ilimin zaman fada ta ke ta koya mata, amma ita sam hankalin ta ma ba ya wajan dan haka ba wani ganewa ta ke ba. Zuba ido ta ke ko za ta ga Innar ta, amma babu Inna baba alamar ta. Hajja Kilishi ta ce da Bintu ta lek’a falo ta ce da d'aya daga cikin bayin ta maza su je 6angaransu Gimbiya K’amariyya su k’ar6o ma Bintu sak’o. Ko da Bintu ta fito, ta bayin sai kai kawo su ke cikin hidimansu, sai ta kasa tsaida d’aya ta aika, duk da dai yanzu ba cikin sahun su ta ke ba inji Sarki, ita har yanzu ba ta ji wani canji ba, dan haka yanda su ke haka ta d'auki kanta, sutarar jikinta ma kayan bayin Sa'ayrasa ne wanda dama shi ne a jikinta tun safe da su Jakadiya su ka zo tafiya da ita. Hakan ya sa ta yanke hukuncin zuwa da kanta 6angaren. Ta na sa k’afa cikin falon ta yi ido biyu da Gimbiya Binta, wacce fitowar ta daga d’akin K'amariyya kenan, idanun nan sun yi jajur. Ganinta Bintu ji ta yi kamar ta koma a guje, ile kuwa bud’ar bakin Gimbiya Binta sai cewa ta yi '’Ke har kin isa ki nuna fuskarki gabana dan ubanki! Ya ki nan munafuka!’’ Jikin Bintu na rawa ta k’arasa gaban Gimbiya ta na mai zubewa a k’asa ta ce ‘’Kimin rai, tuba na ke Gimbiya’’ ‘’A gidan ubanwa ki ke tuba! Oho wato Takawa ya ce kin zama daidai da kowa shi ya sa ki ka zo gwada kafad'a da sa’annin ki ko? Shu’uma daina rawar k’afa, kwalla ba amre ba ne! ki na cikin hatsari muddin Masarautar Fabarusa su ka san ke fa baiwa ce kuma d’iyar bayi, zamanki a Masarautar na d’an wani lokaci ne har sai mun cika burinmu, na farko shi ne na gama makaranta na kuma amri masoyi na Aisar, na biyu Didi ta amri burin ranta, wato Barde, na uku Mai Martaba ya biya bashi ba tare da an yi amfani da farin cikin iyalinsa ba, ke kuwa Allah kad’ai ya san ya rayuwar ki za ta kasance, hallo tsire ki Sarki Abdulraman zai sa a yi idan ya gano mak’aryaciya ya ke amre.....’’ ‘’Ku kuwa Masarautar mak’aryata su ka bashi amren ta ba.....’’ Yarima Nuhu ne ya katse ta, da sauri ta juya ta kai kallonta gare shi, ashe ya shigo ba ta sani ba. Ya na jingine jikin bango daga bakin k'ofa, hannunsa sarke bisa k’irjinsa. Sanye ya ke cikin shud’ayan kaya, ya d’aura farar falmaran akai. Bai gushe ba ya k’ara. ‘’Ina tunanin halin da ki ke ciki ya sa ni tattaki dan zuwa na ganki, ba shakka garau ki ke tun da gashi kin sa d’iyar arziki gaba ki na mata yashasshen zance irin na marasa tunani, shin kin manta wanga d’iya ba baiwa ba ce?’’ Yanda ya ga ta cuna baki ya sa shi fad’in ‘’Dakyau, yanzu ina ga kin tuna, dan haka na miki uziri, amma daga yanzu ba na fatan sake tuna miki, hallo za ki kula.'’ Ya mayar da kallonsa ga Bintu, "Bintun arziki tashi ki yi tafiyar ki, gide kar ki sake tsugunnawa haka gaban kowa, tabbas akwai aiki ja gaban Jakadiya muddin za ki kasance mata ga Sarkin Fabarusa dole ki wuce raini, ke ba baiwa bace, kar ki ta6a mantawa da wannan.’’ Da saurin ta ta tashi, ta na mai godiya ga Yarima Nuhu, ta bi ta gaban Gimbiya Binta, ta zo gaban Yarima Nuhu sannan ta fice ba tare da ta damu da ta k’arbo sakon na ta gun Gimbiya K’amariyya ba. Ganin yanda ta ke tafiya ba Yarima Nuhu ba, hatta Gimbiya Binta sai da ta bita da ido, ba ta san sanda ta je tsaki ba ta ce ‘’Mtsw! Ka ga yanda ta ke tafiya d’iyar bayi sai shegen tak’ama da isa.'’ Ciki Yarima Nuhu ya shigo sosai, yayinda ya sami kujera ya zauna ya na mai murmushi ya ke duban k'anwar ta sa sannan ya ce '’Halittarta ce haka’’ Da sauri Gimbiya ta dawo da kallonta gareshi, cikin rashin fahimta ta ce ‘’Na’am?’’ ‘’Ko ba Bintu ba? Tak’ama da isa ba ta gada ba, amma Allah ya mata shi a halittar ta, kin ga baiwar Ubangiji ko? Ba ki ga tsayinta da dirinta ba ne? Su kad’ai sun isa nuna tak’ama, shi yasa na ke mai bakin cikin rasa ta da zan yi ta sanadiyar san rai irin na k’auna ta.’’ Kamar mai shirin yin kuka Gimbiya Binta ta furta ‘’Yarima......Bintu d’iyar bayi ce!’’ Ya na mai had’e rai ya ce ‘’Hakanan k'auna ce ta na ke kuma rainon san ta cikin raina tun kafin na mallaki hankalina, ina jin ta har jinin jiki na duk da kuwa ita d’iyar bayi ce, ni kuma d’an saraki, ki sani na san da duk wani tukgun da ki ka kulla ke da K’amariyya tare da d’aurin gindin Jakadiya! Har ki na da bakin kuka dan ance za ki bar k’asa? Da da ki ke gina ramin muguntar ba ki san za ki iya wad’awa ba?’’ Kuka Gimbiya Binta ta sa, hawaye d'aya na bin d’aya ta ce ‘’Ina soyayya da k’auna ta jini da amintaka? Ni fa ‘yar uwar ka ce jini d'aya, za ka za6i d’iyar bayi akan yar uwarka? Ka ce da ni wasa ka ke, ba ka san wanga d'iyar bayi.’’ Tashi tsaye ya yi, ya na mai danna idanunsa cikin nata ya ce ‘’Ni abinda ya ke ban takaici kenan, jini na ta san ta iya had’a tuggu haka? Kin san abun da ki ke shirin saka babban mutum kamar Takawa ya aikata kuwa? Kin san girman laifin kuwa? Ina mai gargad’inki, muddin ki na so mu shirya ki gaggauta kunce wannan sak’ar da ki ka kulla tun kan ya k’ure miki’’ Ya juya zai fita, har ya kai k’ofa Gimbiya Binta ta k’ara kiran sunan sa ‘’Yarima....’’ A hankali ya juyo ya na dubanta, idanunsa sun kad’a sun yi jajur. Gimbiya Binta na mai hawaye ta sake furta ‘’Bintu d’iyar bayi ce......’’ ‘’Ita na ke kauna kanwata, idan har ki na so na da farin ciki kar ki ja min asarar Bintu ta ta arziki’’ Ya na gama magana ya fice, ya bar Gimbiya Binta ta na mai bin bayansa da kallo. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE 2⃣1⃣ Khadija Sidi......✍🏼 Duniya ta yiwa Gimbiya Binta zafi, ba ta san sanda ta durkushe kasa ta na mai sakin kuka mai tsanani. Gimbiya K’amariyya ce ta fito hannun ta ruk’e da sakon Bintu, gani Gimbiya Binta cikin tashin hankali ya sa ta sakin sak’on na Bintu bisa kujera, ta k'arasa gare ta da sauri ta na mai waige waige cikin fargaban sharrin masu tsirku. d’ago ta yi ta na fad’in ‘’haba ‘yar uwa, ba yanzu mu ka gama rarrashin ki ba, me yayi zafi Binta shi ba wuta ba? Maza tashi mu yi ciki kar bayi su gani su sami abin yad’awa’’ Kanta ta d’aura bisa kafad’ar Gimbiya K’amariyya ta na mai fad’in ‘’na shiga uku Didi, duniya na neman juya min baya, hatta d’an uwa na ya fi kaunar d’iyar bayi akai na ni da na ke cikin umman sa’’ Gimbiya K’amariyya na mai buga bayan Gimbiya Binta a hankali cikin rarrashi, ta ja ta su ka yi ciki. Sai da su ka shiga d’akin Gimbiya K'amariyya, ta sallami baiwar da ke cikin d’akin sannan ta zaunar da Gimbiya Binta bisa gado ta nemi ba'asi akan tsakanin Yarima Nuhu da Bintu. Nan Gimbiya ta fad’a mata yanda ta kasance tsakanin ta da Yarima Nuhu, jin haka ba ta yi mamaki ba, sai ma tsaki da ta ja ta ce ‘’shiga shigila gand’e ma shiga rawar takai! Har kya ma damu da Yarima Nuhu, in dai wajan shiga shirgin da ba na shi ba ne in aka gan shi kowa ya shafa fatiha, ya manta ba kauna ba, ciki d’aya su ka hito da Bintu! kar ki wani damu, zancen komawar ki k'asar Nigeria kuwa InshaAllahu zance ne, kuma in dai Aisar ne ya ma zama na ki an gama’’ Gimbiya Binta na mai kwantar da kan ta bisa gwiwar Gimbiya K’amariyya ta ce ‘’ina godiya Didi, dan Allah kar ki bari Takawa ya raba ni da farin cikin rai na’’ Ta na shafa kan ta ta ce ‘’in dai wannan ne kar ki damu, bayan auren d’iyar bayi na miki alk'awarin shedawa Hajja Kilishi lamarin ki da Aisar, sai a san yanda za a bullowa lamarin, ko?’’ Ta k’arasa maganar ne ta na mai d'ago fuskar yar uwar ta ta, cike da farinciki Gimbiya Binta ta tsinci kan ta ta na mai washe hakora, ashe dai da rabo. Haka dai su ka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali har Gimbiya Binta ta mance da maganar Yarima Nuhu bare ma ya dame ta. Bintu kuwa ko da ta samu ta ganta d'akin Hajja Kilishi, nan ta yi zaune abun ta, da Hajja Kilishi ta tambayi sak’on na ta, sai cewa ta yi ba ta ga Gimbiya K’amariyya ba. Hajja na k'orafin dama ba ta ce Bintu ta je da kan ta ba, ta sake aika wata baiwar ta karb’o sak’on, sannan ta bawa Jakadiya da ta zo tafiya da Bintu. Sak’onni ne na kayan gyra jiki wanda ya had’a da su dilka, halawa, kalta, kurkum dadai duk sauran kayan gyaran jiki wanda musammam Hajja Kilishi ta sa aka mata sautin su daga Agadez. A daren ranar Bintu ta fara shiga hannu, mai gyaran jiki na yi, mai koya mata kissa da dabarun zaman fada na yi, mai mata jawabi yanda sabuwar rayuwar ta za ta kasance na yi. Telar babban gida ma ba a barta a baya ba, haka ta yi tattaki ta zo ta gwada Bintu tare da tafiya da damin siturun da Hajja Kilishi ta zab’arwa Bintu. Hatta gashin Bintu da Marry ta yanke sai da Jakadiya ta saita almakashi ta daidaitasu, ta na mai tambayar ya aka yi gashi rabi dogo rabi gajere. A lalle sai an wayar da Bintu ta fito fes kamar d’iyar saraki. Ita kuwa Bintu ba ta fasa kuka da kewar Innar ta ba. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. ©Khadija Sidi.....✍🏼 2⃣2⃣ Daga ranar zuwa washagari sai ga Bintu an fara wasai. Washagari da safe, Bintu da Jakadiya tare su ka zauna karin kumallo, cin abinci ma sai Jakadiya ta koya mata dan kar ta je ta bada su a masarautar abokan gaba. Abinci ne kala kala na alfarma irin na gidan saraki, kai ka ce ba fari ake a masarautar ba. Bintu na gani Innar ta ce ta fad’o mata a rai, ba makawa ta san yanzu ta na nan ta na fama da hatsi da dusa, amma ita nan ga abinci har da na b’arna a gaban ta. Da kyar ta iya cin kad’an daga abinci, hakan ma sai da Jakadiya ta sab’ar ma ta, ta na mai tuhumar ta da tsabar mugunta ne ya sa Bintu k'in cin abinci, dan a ganta ramammiya ta sa ace tsabar yunwar da ke addabar Masarautar su ne, ko kuwa cutar yunwa ya kama ta. Kan wannan jaraba na Jakadiya ne ya sa ta bi yanda Jakadiya ta ce, ta na mai gwada mata yanda za ta yi haka har dai ta ta6a wanda za ta iya, a dole Jakadiya ta hakura ta rabu da ita. ***** ****** Sai da ya rage saura sati guda auren Bintu sannan Innar ta ta yarda ta zo wajan Jakadiya ganin Bintu, hakan ma sai da Jakadiya ta matsa tukunna. Ganin yanda Bintu ta canza ta yi wasai fatar ta har shek’I ya ke, duk da dai ta yi wani irin rama sai da ta ji dad’i. Sun dad’e suna hira, nan ta ke sheda mata sarki ya ‘yan ta ta. Sam Inna ba ta yi wani murna ba, a fad’an ta da hatsarin da aka jefa d’iyar ta har gwara a bar ta d’iyar bayi har abada. Da Inna ta zo tafiya da kyar Bintu ta sake ta, nan fa taita sana'ar ta ta, wato kuka babu kuma mai rarrashin ta bare ace mata ya isa. Bayin da aka amince da su, wanda su aka yarda su shiga wajan Jakadiya kuwa kishi su ke da Bintu, musammam da su ka ji ashe ita ce za a aurawa sarki ba Binta ba, ga gyara da hidima da ake mata sai kace wata d’iyar saraki. Baiwa ta zama ‘yan tacciya. Da yawan su kan ce kukan munafurci Bintu ta ke, wasu kuwa fad’i suke ina ma su an Bintu, da kakarsu ta yanke sak’a. Babban gida kuwa Gimbiya Binta Hajja Kilishi ta sa a gaba ta na mata gyaran jikin bogi, a lalle ayi basaja gudun ‘yan tsirku na fada. Amma a zahirin gaskiya Sarki ya sa a duba makaranta mai kyau da tsada k’asar Nigeria domin mayar da ita can. Har ila yau daga Gimbiya Binta har K'amariyya ba su fasa k’ulle k’ulle da shige da fice ba dan neman yanda za a yi Takawa ya sauya shawara, amma dai abin ya ci tira. Har kar gaban ta ya sa ko ta kan Bintu ba ta bi, bare ta sa ta a idanun ta. Haka ma Yarima Nuhu, wanda ya rame a ‘yan kwanaki kad’an tsabagen fargaba auren Bintu da ke gabatowa bilhakki. Gashi gaba d’aya an 6oye Bintu cikin fada, raban da ya sa ta a ido tun randa ya zo ya tadda ita da Gimbiya Binta ta na mata cin kashi, duk yanda zai yi ya gan ta yayi amma babu Bintu babu alamar Bintu. Daga bisani ya yanke hukuncin tarar aradu da daka, bayan sun dawo daga shawagi, ko sauka daga dokin sa be yi ba, yayi tattaki zuwa wajan Jakadiya da buk’atar sa na ganin Bintu Kan ya k’arasa ga 6angaran na ta su ka yi kaci6us a hanya, ta fito za ta turakar sarki. Ganin ta yayi saurin jan linzamin dokin domin tsayawa, har sai da dokin ya fara dara da nagarta (tsalle da rawa) cikin yanayin tada kura, Yarima Nuhu na mai damk’e linzamin gudun kar ya ji shi k’asa ya shiga k’ok’arin tsayar da dokin. Jakadiya na mai d’aga hannun ta na dama da ta d’unkule sama ta ce ‘’kiwo sannu Yarima, ba sake ba manko, kamazuru abokin dabara, amincin ka ya fi ga linzaminka’’ (ta na fahimtar da Yarima Nuhu ya nutsu, hankalin sa ya tafi kan linzamin dokin kada ya kada Shie’’ Ko da ta ga dokin ya tsaya, sai ta sa kai za ta yi gaba, Yarima ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar fad’in ‘’ba ki ji ba Jakadiya, wannan zuwan na ki ne’’ Jin haka Jakadiya ta ja ta tsaya, ta na bashi amsa da ‘’anya kuwa ba na ce ah ah ga Yarima ba yayinda na ke kan hanyar da zata sada ni da Babban Bijimi ba?’’ Da sauri Yarima Nuhu ya sauko daga bisa dokin, ya na mai jan linzamin dokin ya dawo daga gefan Jakadiya, wani irin iska mai zafi da k’asa ke busawa duk da dadai la’asar ce sakaliya. ‘’wa ya isa tsayar da Jakadiya a hanyar da zata sada ta da Takawa?’’ Jakadiya na gyad’a kai ta ce ‘’barka da siddi masu duniya’’ ‘’barka dai Jakadiya, gani na zo gare ki da buk’atar ganin Bintun arziki ko da kuwa na ‘yan dak’ikai ne’’ cewar Yarima Nuhu ya na duban Jakadiya. Ko da ta d’aga ido ta kalle shi sai ta ga ya mata kwarjini. Sanye ya ke cikin dokakkiyar shadda koriya d’in ‘yan fakistan. Ya d’aura falmaran ruwan zuma bisa, ga farar hular sa irin ta larabawa wacce ba ta da nauyi bisa kan sa, kafar sa kuwa takalmin fata ne sau ciki, shima kore an yi masa ado da d’igon ruwan zuma. Ganin idan sa ya sa ta kasa yi masa musu kamar yanda ta saba yi masa akan duk abin da ya jib’anci Bintu. Kana ta tsinci kan ta ta na mai fad’in ‘’yo to Yarima ka san abun ga ba haka ake ba, Babban Bijimi ya ce a killace d’iyar bayin nan, amma tin da ka zo da kan ka yi tsimayi cikin lambu, zan sa a rako ta, amma kada ka ruk’e ta, kasan amare ba a san ana ganin su hakan nan sakaka saboda.....’’ ‘’ina godiya Jakadiya, ba zan manta da wannan alfarma da ki ka yi a gare ni ba’’ Yarima Nuhu yayi saurin katse ta dan ba ya san jin maganar da Jakadiya ke masa game da auren Bintu, ya na mai jan linzamin dokin sa yayi hanya da za ta sada shi da lambun ba tare da ya jira amsar Jakadiya ba. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. ©Khadija Sidi.....✍🏼 2⃣3⃣ Kasancewar ruwa be sauka ba, yawanci shuke shuken da ke cikin lambun duk a bushe su ke, sai kukan tsuntsaye da kwari ne ke tashi sama sama. Dokin sa ya saka ya na shawagi cikin lambun, yayin da ya sami wata shifid’a da ke k’ark’ashi bishiyar mangwaro, ya cire takalmin shi, ya zauna sannan ya kuma kishingid’a kan tintin da ke jere bisa shimfid’ar. Be dad’e da zama ba ya hangi wata da ya kasa gane ko wacece ta shigo lambun ta na mai waige waige da alama akwai wanda ta ke dubawa. Daga in da ya ke zaune ya k’ura ma ta ido cikin kokanton abun da kwakwalwar sa ke fad’a masa. Sanye ta ke cikin doguwar riga ruwan zuma, an mata aikin hannu irin na sarauta tun daga sama har izuwa k'asan rigar da jan zare. Kan ta nad’e da jan kallabi, haka ma talkamin da ke sanye k’afar ta ja ne. Ganin ta nufu in da ya ke sai da ya tashi zaune daga kishingid'ar da yayi, ya na mai gyara zama, tafiyar ta ya dad’a gasgata masa abin da ya ke gani, babu shakka ita ce d’in ce. Tin da ta hango shi gaban ta ya shiga fad’uwa, ba a san ran ta ta fito ba, dan ko da Jakadiya ta zo ta tadda tela ta sa ta gaba ta na gwada kayan da aka sa tela ta d’in ka mata, ta na kan na k'arshe Jakadiya ta ce Yarima Nuhu na da buk’atar ganin ta.Ta so cire kayan da ke jikin ta dan ta fi gane shigar su na bayi, amma Jakadiya ta ce ah ah, kada ta 6ata lokaci ta yi maza ta je ta same shi yanzu yanzu cikin Sirri. Gaba d’aya ta kasa sakewa, dan ta kwana biyu ba ta saka k'afar ta waje ba,gashi kayan da ke sanye jikin ta da ma takalmin da ke k’afar ta duk sun saka ta na jin kan ta daban, abun da ba a saba ba, gashi a dole ta na ji ta na gani an sa ta gaba da gyara, lalle sai ta yi kama d’iyar saraki, ita dai wannan masifa ba ta ta6a ganin irin shi ba. Da wanan tunani ta k’arasa gaban sa, amma ko da ta masa sallama ta na mai zubewa a k’asa kamar yanda ta saba duk sanda ya bayyana gaban ta, sai ta ji shiru be amsa ba. Ba ta gusheba kan ta sunkuye ta sake masa sallamar a karo na biyu, shi ma shiru, na ukun da ta sake ne ta d’aga ido da niyar kallan in da ya ke zaune, sai tsintar idanun ta tayi cikin na sa, ya taso izuwa gaban ta ya durk'usa ya na kallan ta kamar zai had'ye ta. Cikin fad’uwar gaba ta yi saurin yin k’asa da nata idanun ta tana mai fad’in tuba ‘’tuba na ke Yarima’’ Niamey ‘Bangaran Aisar kuwa, yau take kwana uku da dawowar su Nijar daga k’asar Ingila, in da aka duba mai girma shugaban k’asa Gaddafi Nur. Zaune Shugaba Gaddafi ya ke a k'awataccin falon sa, tare da babban d’an sa wanda ake kira Junaid da kuma Aisar. Jikin na sa Alhamdulillahi yayi kyau kwaran gaske, wanda hakan ya bashi dama zantawa da 'ya'yan na sa akan abubuwan yau da kullum. Aisar kuwa kamar kullum, yanzun haka ma gangan jikan sa kad’ai ke wajan, amma zuciyar sa na ga Bintu, tunanin Bintu ya hana shi sakat, ya jagula tunanin sa har ya na da yak'inin cewa muddun ba zuwa yayi gare ta ba zai iya shiga wani hali. Cikin wannan hali ne kamar daga sama ya ji Shugaba Gaddafi ya ambato sunan Masarautar ta su Bintu, wato Sa’ayrasa. Wanda haka ya sa yayi saurin dawowa cikin hankalin sa, ya na mai san jin ainihin maganar da shugaba ya ke. Nan ya sami amsar da ya ke buk’ata, takardu guda biyu Shugaba ya mik'awa Junaidu ya na mai fad’in ‘’gashi nan Junaidu wasik’ar gayyata ce daga Masarautar Fabarusa da Sa'ayrasa, wanda za su gudanar da auratayya tsakanin junan su nan da mako guda’’ Cike da farin ciki, kafin ma Junaidu ya kar6a Aisar yayi saurin sa hannu ya kar6e ya na mai fad’in ‘’mashaAllahu, wato Bintu ta yi gaskiya auratayya ce zai kawo silar k'arshen gaba tsakanin wannan Masarautun, wannnan yarinya ba dai kwakwalwa ba’’ Ya na magana ne ya na k’ok’arin bud'e ma'jin waasikar, be san daga Shugabn k’asa har Junaidu kallan sa su ke cike da mamaki ba, musammam Junaidu da be ta6a jin zance wata mace daga bakin Aisar ba, ya ce ‘’Bintu? Wacece Bintu?’’ Sai a sannan Aisar ya tuna ashe fa a zahiri ya yi maganar, ya na mai duban Junaidu hannun sa rike da wasikar da ya bud’e ya ce ‘’wata d’aliba ta ce a makaranta da na koyar mai kwazo da hazak’a, bakin ta na fara jin auratayya na iya kawo k’arshen gaba, yar Masarautar Sa’ayrasa ce’’ ‘’yar wani hakimi ce a Masarautar?’’ Shugaba Gaddafi ya tambaya cike da farin cikin ko dai ya kusa samin sirika ne. Ga mamakin sa sai ji yayi Aisar ya amsa masa da ‘’d’iyar bayi ce.....’’ Shiru ne ya biyo baya, yayinda Aisar ya duk’ufa kan karanta wasik’ar gayyata na musammam da aka aiko daga Masarautar Sa’ayrasa, cike da mamaki ya ce ‘’gide Sarkin Fabarusa da kan sa zai auri d’iyar Sarkin Sa’ayrasa? Na yi zatan tsakanin ‘ya ‘yan su ne? ko da shi ke harkar manya ba a cewa komai’’ ‘’ai auren dama za a yi ne ba hakan nan bak’atatan ba, za su yi ne saboda taimako da Sarki Sule na Sa'ayrasa ya nema daga Sarki Abdulraman na Fabarusa akan fari da ya addabi Masarautar ta su, ka na Ingila shi ya ba ka da labari" Aisar na mai duban sunan Fatima da ya bayyana bisa wasik’ar ya ce ‘’dama ya na da d’iya Fatima ne? Na san dai akwai wata d’iyar sa Binta wacce na koyar a makarantar Sovereign’’ ‘’ni ma dai Gimbiya K’amariyya kawai na sani da ita aka fi fita damawa a masarautar ta su, in dai akwai Fatima sai dai ta kasance kanwa a gare ta, yo to ai Binta Fatima ta ke, ko shakka babu d’alibar ta ka ce ma" Junaidu ne ya amsa masa. Aisar na mai d’aga kafad’a cike da nuna an yi ba daidai ba ya ce '’kai amma yarinya ce sosai, gaskiya auren nan be dace ba bata fi shekara goma shabiyar ba, ina zancen makarantar ta kuma fa? Wannan ai tauye hakki ne, me zai hana a aurar da yayarta ta tunda ita ta kai munzali?'’ Duk abun nan ya na yi ne ba dan kowa ba sai dan Bintu, ta na yawan fad’o masa a rai tun sanda ya ji batun farin da ya addabi k’asar su, rashin lafiya Shugaba Gaddafi shi ya hana shi sakat, yo to ana ta kai wake ta kaya, amma idan ya tuna rayuwar fada ta ke, sai hankalin sa ya kwanta dan ya tabbatar ba za ta6a kwana da yunwa ba. Amma jin za a aurar da Gimbiya Binta ya sa hankalin shi tashi, dan babu mamaki k’arshen karatun Bintu kenan, kila ma ta na cikin bayin da za tura Fabarusa domin kula da Gimbiya Binta. Ya kai duban sa ga Shugaban Gaddafi wanda tun da su ka fara magana be tanka ba, ya ce ‘’Baba na ka duba wannan lamarin saboda Allah, wannan nauyin na Gwamnati ne, ceto rayukan al’umma, ba na Masarautu ba, mun san kana yi, kuma kai me yi ne’’ Maimakon Shugaba Gaddafi ya bashi amsa sai murmushi ya sakarwa d’an na sa. Junaidu ne ya bashi amsa da toh ‘’toh d’an k’asa mai kishin k’asa, kana ina san da Baba ya sa aka hannu za a fitar da damin kud'i dan aika abinci ga Masarautar’’ ‘’to me ake jira ba a aika ba? Me ya kawo jinkirin? In dai rashin lafiyar Baba ne, Baba ya ji sauki, a yi maza a aika dan a taimaki bayain Allah’’ Cewar Aisar cike da damuwa. Shugaba Gaddafi na masa nuni ga takardar hannun sa ya ce ‘’ga amsar nan bisa hannun ka, jin Masautar Fabarusa za ta taimakawa S’ayrasa, da kuma niyar su na auratayya ya sa mu ka dakata, muddin hakan zai kawo k’arshen gaban da ke tsakanin su toh fa babu ruwan Gwamnati da shiga lamarin, sai dai mu bada gudunmawa ta hanyar amsa gayyata da kuma k’ara mu su k’arfin gwiwa, kud’in da mu ka ware dan ciyar da masarautar kuma ya tafi ga wani aiki wanda zai amfane su ta wani fannin’’ Aisar na mai girgiza kai ya ce ‘’na fahimta, Baba na san saboda yanayin jikin ka ba za ka sami halartar d’aurin auren ba, in zan sami dama ina so na zama d’aya daga cikin wanda za su wakilce ka’’ Jin haka Junaidu ya san hakan nan yanda Aisar ba ya san duk wani abu da zai had’a shi da siyasa, ya san banza ba ta kai zomo kasuwa, ya ce ‘’ah ah ka manta ranar za ku koma Ingila domin duba jikin Baba? Ka bari an hutasshe ka ni na je’’ Duk da yayi maganar ne cike da zolaya, sai da Aisar ya tsuke fuska, dan kuwa gani ya ke yanda ya ci burin ganin Bintu, duk wanda zai hana shi ganin Bintu shi an mak’iyin shi, jin za a je Masarautar su ya san tun da d’iyar bayi ce ko shakka babu zai gan ta, ko dan ya sami daman ganin iyayen ta, ya ji ya za su yi da karatun Bintu tun da dai ita Gimbiya Binta aure za a mata, kuma ya rok’e su da kada su cire ta daga makaranta, idan ya kama ne ya d’au nauyin ta, zai yi. Ya na mai tsuke fuska ya ce ‘’zai fi kyau dai kai ka koma Ingila, tun da Baba ya ji sauki, duba shi kawai za a yi ina ga babu amfanin zuwa da ni’’ Shugaba Gaddafi ya ce ‘’to tsakanin ku, idan dukan ku biyun ne ma za su d’aurin auren daidai ne, ina jin sauki sosai, ba na buk’atar rakiyar ku’’ Murmushin jin dad’i Aisar ya saka, cikin ran sa ya na mai fad’in ‘’Bintu na ina nan tafe, ki kwantar da hankalin ki babu mai cire ki daga karatun ki’’ 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪[5/12, 5:04 PM] ‪+234 703 962 5239‬: ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. ©Khadija Sidi.....✍🏼 2⃣3⃣ Kasancewar ruwa be sauka ba, yawanci shuke shuken da ke cikin lambun duk a bushe su ke, sai kukan tsuntsaye da kwari ne ke tashi sama sama. Dokin sa ya saka ya na shawagi cikin lambun, yayin da ya sami wata shifid’a da ke k’ark’ashi bishiyar mangwaro, ya cire takalmin shi, ya zauna sannan ya kuma kishingid’a kan tintin da ke jere bisa shimfid’ar. Be dad’e da zama ba ya hangi wata da ya kasa gane ko wacece ta shigo lambun ta na mai waige waige da alama akwai wanda ta ke dubawa. Daga in da ya ke zaune ya k’ura ma ta ido cikin kokanton abun da kwakwalwar sa ke fad’a masa. Sanye ta ke cikin doguwar riga ruwan zuma, an mata aikin hannu irin na sarauta tun daga sama har izuwa k'asan rigar da jan zare. Kan ta nad’e da jan kallabi, haka ma talkamin da ke sanye k’afar ta ja ne. Ganin ta nufu in da ya ke sai da ya tashi zaune daga kishingid'ar da yayi, ya na mai gyara zama, tafiyar ta ya dad’a gasgata masa abin da ya ke gani, babu shakka ita ce d’in ce. Tin da ta hango shi gaban ta ya shiga fad’uwa, ba a san ran ta ta fito ba, dan ko da Jakadiya ta zo ta tadda tela ta sa ta gaba ta na gwada kayan da aka sa tela ta d’in ka mata, ta na kan na k'arshe Jakadiya ta ce Yarima Nuhu na da buk’atar ganin ta.Ta so cire kayan da ke jikin ta dan ta fi gane shigar su na bayi, amma Jakadiya ta ce ah ah, kada ta 6ata lokaci ta yi maza ta je ta same shi yanzu yanzu cikin Sirri. Gaba d’aya ta kasa sakewa, dan ta kwana biyu ba ta saka k'afar ta waje ba,gashi kayan da ke sanye jikin ta da ma takalmin da ke k’afar ta duk sun saka ta na jin kan ta daban, abun da ba a saba ba, gashi a dole ta na ji ta na gani an sa ta gaba da gyara, lalle sai ta yi kama d’iyar saraki, ita dai wannan masifa ba ta ta6a ganin irin shi ba. Da wanan tunani ta k’arasa gaban sa, amma ko da ta masa sallama ta na mai zubewa a k’asa kamar yanda ta saba duk sanda ya bayyana gaban ta, sai ta ji shiru be amsa ba. Ba ta gusheba kan ta sunkuye ta sake masa sallamar a karo na biyu, shi ma shiru, na ukun da ta sake ne ta d’aga ido da niyar kallan in da ya ke zaune, sai tsintar idanun ta tayi cikin na sa, ya taso izuwa gaban ta ya durk'usa ya na kallan ta kamar zai had'ye ta. Cikin fad’uwar gaba ta yi saurin yin k’asa da nata idanun ta tana mai fad’in tuba ‘’tuba na ke Yarima’’ Niamey ‘Bangaran Aisar kuwa, yau take kwana uku da dawowar su Nijar daga k’asar Ingila, in da aka duba mai girma shugaban k’asa Gaddafi Nur. Zaune Shugaba Gaddafi ya ke a k'awataccin falon sa, tare da babban d’an sa wanda ake kira Junaid da kuma Aisar. Jikin na sa Alhamdulillahi yayi kyau kwaran gaske, wanda hakan ya bashi dama zantawa da 'ya'yan na sa akan abubuwan yau da kullum. Aisar kuwa kamar kullum, yanzun haka ma gangan jikan sa kad’ai ke wajan, amma zuciyar sa na ga Bintu, tunanin Bintu ya hana shi sakat, ya jagula tunanin sa har ya na da yak'inin cewa muddun ba zuwa yayi gare ta ba zai iya shiga wani hali. Cikin wannan hali ne kamar daga sama ya ji Shugaba Gaddafi ya ambato sunan Masarautar ta su Bintu, wato Sa’ayrasa. Wanda haka ya sa yayi saurin dawowa cikin hankalin sa, ya na mai san jin ainihin maganar da shugaba ya ke. Nan ya sami amsar da ya ke buk’ata, takardu guda biyu Shugaba ya mik'awa Junaidu ya na mai fad’in ‘’gashi nan Junaidu wasik’ar gayyata ce daga Masarautar Fabarusa da Sa'ayrasa, wanda za su gudanar da auratayya tsakanin junan su nan da mako guda’’ Cike da farin ciki, kafin ma Junaidu ya kar6a Aisar yayi saurin sa hannu ya kar6e ya na mai fad’in ‘’mashaAllahu, wato Bintu ta yi gaskiya auratayya ce zai kawo silar k'arshen gaba tsakanin wannan Masarautun, wannnan yarinya ba dai kwakwalwa ba’’ Ya na magana ne ya na k’ok’arin bud'e ma'jin waasikar, be san daga Shugabn k’asa har Junaidu kallan sa su ke cike da mamaki ba, musammam Junaidu da be ta6a jin zance wata mace daga bakin Aisar ba, ya ce ‘’Bintu? Wacece Bintu?’’ Sai a sannan Aisar ya tuna ashe fa a zahiri ya yi maganar, ya na mai duban Junaidu hannun sa rike da wasikar da ya bud’e ya ce ‘’wata d’aliba ta ce a makaranta da na koyar mai kwazo da hazak’a, bakin ta na fara jin auratayya na iya kawo k’arshen gaba, yar Masarautar Sa’ayrasa ce’’ ‘’yar wani hakimi ce a Masarautar?’’ Shugaba Gaddafi ya tambaya cike da farin cikin ko dai ya kusa samin sirika ne. Ga mamakin sa sai ji yayi Aisar ya amsa masa da ‘’d’iyar bayi ce.....’’ Shiru ne ya biyo baya, yayinda Aisar ya duk’ufa kan karanta wasik’ar gayyata na musammam da aka aiko daga Masarautar Sa’ayrasa, cike da mamaki ya ce ‘’gide Sarkin Fabarusa da kan sa zai auri d’iyar Sarkin Sa’ayrasa? Na yi zatan tsakanin ‘ya ‘yan su ne? ko da shi ke harkar manya ba a cewa komai’’ ‘’ai auren dama za a yi ne ba hakan nan bak’atatan ba, za su yi ne saboda taimako da Sarki Sule na Sa'ayrasa ya nema daga Sarki Abdulraman na Fabarusa akan fari da ya addabi Masarautar ta su, ka na Ingila shi ya ba ka da labari" Aisar na mai duban sunan Fatima da ya bayyana bisa wasik’ar ya ce ‘’dama ya na da d’iya Fatima ne? Na san dai akwai wata d’iyar sa Binta wacce na koyar a makarantar Sovereign’’ ‘’ni ma dai Gimbiya K’amariyya kawai na sani da ita aka fi fita damawa a masarautar ta su, in dai akwai Fatima sai dai ta kasance kanwa a gare ta, yo to ai Binta Fatima ta ke, ko shakka babu d’alibar ta ka ce ma" Junaidu ne ya amsa masa. Aisar na mai d’aga kafad’a cike da nuna an yi ba daidai ba ya ce '’kai amma yarinya ce sosai, gaskiya auren nan be dace ba bata fi shekara goma shabiyar ba, ina zancen makarantar ta kuma fa? Wannan ai tauye hakki ne, me zai hana a aurar da yayarta ta tunda ita ta kai munzali?'’ Duk abun nan ya na yi ne ba dan kowa ba sai dan Bintu, ta na yawan fad’o masa a rai tun sanda ya ji batun farin da ya addabi k’asar su, rashin lafiya Shugaba Gaddafi shi ya hana shi sakat, yo to ana ta kai wake ta kaya, amma idan ya tuna rayuwar fada ta ke, sai hankalin sa ya kwanta dan ya tabbatar ba za ta6a kwana da yunwa ba. Amma jin za a aurar da Gimbiya Binta ya sa hankalin shi tashi, dan babu mamaki k’arshen karatun Bintu kenan, kila ma ta na cikin bayin da za tura Fabarusa domin kula da Gimbiya Binta. Ya kai duban sa ga Shugaban Gaddafi wanda tun da su ka fara magana be tanka ba, ya ce ‘’Baba na ka duba wannan lamarin saboda Allah, wannan nauyin na Gwamnati ne, ceto rayukan al’umma, ba na Masarautu ba, mun san kana yi, kuma kai me yi ne’’ Maimakon Shugaba Gaddafi ya bashi amsa sai murmushi ya sakarwa d’an na sa. Junaidu ne ya bashi amsa da toh ‘’toh d’an k’asa mai kishin k’asa, kana ina san da Baba ya sa aka hannu za a fitar da damin kud'i dan aika abinci ga Masarautar’’ ‘’to me ake jira ba a aika ba? Me ya kawo jinkirin? In dai rashin lafiyar Baba ne, Baba ya ji sauki, a yi maza a aika dan a taimaki bayain Allah’’ Cewar Aisar cike da damuwa. Shugaba Gaddafi na masa nuni ga takardar hannun sa ya ce ‘’ga amsar nan bisa hannun ka, jin Masautar Fabarusa za ta taimakawa S’ayrasa, da kuma niyar su na auratayya ya sa mu ka dakata, muddin hakan zai kawo k’arshen gaban da ke tsakanin su toh fa babu ruwan Gwamnati da shiga lamarin, sai dai mu bada gudunmawa ta hanyar amsa gayyata da kuma k’ara mu su k’arfin gwiwa, kud’in da mu ka ware dan ciyar da masarautar kuma ya tafi ga wani aiki wanda zai amfane su ta wani fannin’’ Aisar na mai girgiza kai ya ce ‘’na fahimta, Baba na san saboda yanayin jikin ka ba za ka sami halartar d’aurin auren ba, in zan sami dama ina so na zama d’aya daga cikin wanda za su wakilce ka’’ Jin haka Junaidu ya san hakan nan yanda Aisar ba ya san duk wani abu da zai had’a shi da siyasa, ya san banza ba ta kai zomo kasuwa, ya ce ‘’ah ah ka manta ranar za ku koma Ingila domin duba jikin Baba? Ka bari an hutasshe ka ni na je’’ Duk da yayi maganar ne cike da zolaya, sai da Aisar ya tsuke fuska, dan kuwa gani ya ke yanda ya ci burin ganin Bintu, duk wanda zai hana shi ganin Bintu shi an mak’iyin shi, jin za a je Masarautar su ya san tun da d’iyar bayi ce ko shakka babu zai gan ta, ko dan ya sami daman ganin iyayen ta, ya ji ya za su yi da karatun Bintu tun da dai ita Gimbiya Binta aure za a mata, kuma ya rok’e su da kada su cire ta daga makaranta, idan ya kama ne ya d’au nauyin ta, zai yi. Ya na mai tsuke fuska ya ce ‘’zai fi kyau dai kai ka koma Ingila, tun da Baba ya ji sauki, duba shi kawai za a yi ina ga babu amfanin zuwa da ni’’ Shugaba Gaddafi ya ce ‘’to tsakanin ku, idan dukan ku biyun ne ma za su d’aurin auren daidai ne, ina jin sauki sosai, ba na buk’atar rakiyar ku’’ Murmushin jin dad’i Aisar ya saka, cikin ran sa ya na mai fad’in ‘’Bintu na ina nan tafe, ki kwantar da hankalin ki babu mai cire ki daga karatun ki’’ 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 [5/15, 7:22 PM] ‪+234 703 962 5239‬: ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. 🕊Special shoutout to all the Atikus🙋🏽🙋🏽 onelove💞😘😘 ©Khadija Sidi.....✍🏼 2⃣4⃣ Kallon Bintu Yarima Nuhu ya ke cike da so da k’auna, murya can k’asa ya kira sunan ta ‘’Bintun arzki, dama haka ki ke da kyau? Anya kuwa Bintu zan juri rashin ki?’’ Kanta a k’asa ta d’an ja da baya, dan kuwa ganin Yarima Nuhu durkushe gabanta ba k’aramin takura ta yi ba, dad’in dad’awa yau kuma ya zo mata da saban salo na magana. Ai kuwa sai ta yi kamar ba ta ji ba. Kana ta ce ‘’Allah shi taimaki Yarima, Barka da yammaci, Jakadiya ce ta ce Yarima na da buk’atar gani na’’ Hannunta da ke rawa ya bi da kallo, in da idanunsa suka sauka bisa zoben hannunta, sai kyalli da shek’i ya ke, ba tare da wani tunani ba ya d'aura hannunsa bisa hannun lta mai d’auke da zoben. Jin sabon salo hannun Yarima Nuhu bisa na ta ya sa Bintu janye hannunta a firgice cikin sauri kamar wacce aka d'aurawa garwashi, nan ta shiga yarce hannun tana ka6ewa kamar wanda wani abu ya mak’ale. Gaba d’aya ta firgice idanunta na shirin kawo ruwa. Cike da mamaki Yarima Nuhu ya ke dubanta, kana ya ce ‘’Haka ki ke k’yank’yamina Bintu? Duk wannan d’aga hankalin da yarfe hannun dan na ta6a ki ne?’’ Sai a sannan ta farga da abun da ta ke, tuni ta zube hannayen nata a k'asa, idanunta na fidda kwallar da dama su ke mak’ale cikin kwayar idanunta, fad’i ta ke. ‘’Na tuba, kamin rai, na tuba, ba na so na mutu Yarima, aradu ba na san na rasa raina.’’ Ya na mai jinjina maganar cikin ransa, cike da mamaki ya ce da Bintu ‘’Wa ya ce za ki mutu?’’ Zuciyarta d’aya, har ila yau ba ta fasa hawaye ba ta ce ‘’Iya Dije ce’’ ‘’Iya Dije?’’ Yarima Nuhu ya maimaita. Bintu na mai gyad’a kai ta ce ‘’Eh Iya Dije, ta ce idan har na sake na bari namiji ya ta6a ni mutuwa zan yi, kwankwatsi ma kuwa.’’ Ga mamakinta sai gani ta yi Yarima Nuhu ya jefa kansa baya ya na mai saka dariya mai sauti. Cikin rashin fahimta Bintu ta duk’ar da kai jiki na rawa. Tashi ya yi, ya koma wajan zamansa na fari, yayinda ya zauna ya na mai kishingid’a bisa tintin cike da mulki da sarauta. Har a lokacin idanunsa kanta ya ke, fuskarsa kunshe da murmushi bayan wasu d’an dakik’ai ya ce ‘’Bintu d’ago ki kalle ni.'’ A hankali ta d’ago kanta, cikin bin umarni ta kai kallonta gareshi, fuskarta cike da hawaye. Gefansa ya mata nuni da shi sannan ya ce ‘’Dawo nan ki zauna.’’ Ta na fidda kwayen idanu ta ce ‘’Iye?’’ Kai ya gyad’a mata cikin jaddadawa, bai kuma fasa mata murmushi wanda ke k'ara masa kyau ba. Cike da shakku Bintu ta tashi a hankali, inda ya mata nuni nan ta je ta zauna, amma can nesa da shi. Ya na mai jin dad’in maganar Bintu, duk da yayi mamaki ace baiwa kamar Bintu batasan komai ba har haka, sakamakon shaidar rashin kamun kai da ake yiwa matasan bayi irinta. Kana ya nisa tare da fad’in ‘’Iya Dije ki ka ce kowa? Ko shakka babu ta yi gaskiya’’ A tsorace Bintu ta d’ago ta kalleshi ta na mai fad’in ‘’Shikenan ni Bintu mutuwa zan yi, na shiga uku na lalace.’’ Dakyar Yarima ya iya kunshe dariyar da ta kusa cin k’arfinsa, ya na mai k'ok’arin d’aure fuska ya ce ‘’Banda yanzu, ba za ki mutu ba tunda ni ba ta6a ki, hallo na yi ba gangan ba, zoben hannunki na ta6a, amma kar ki yarda wani ya ta6a ki muddin ki na so ki yi tsayin rai, musamman idan aka kai ki wannan Masarauta na Fabarusa, ko da kuwa Sarki Abdulrahman ne da kansa.’’ Ta na mai tunani yo dama me zai sa Sarki Abdulrahman ya ta6a ta, ta yi saurin amsawa da ‘’Aeadun Allah ba zan bari ba, hallo ni ma ba na zuwa kusa da maza, Inna ta ta hana’’ Yarima na mai duban zoben hannun ta wanda hakan nan ya ji ya tsole masa ido, ya ce ‘’Wagga zobe na hannunki, wa ya baki?” Zuciyar Bintu d’aya ta amsa masa da ‘’Monsieur Aisar ne ya bani ajiya.’’ Wani bakin kishi ne ya ta so masa jin sunan namiji bakin Bintu, nan da nan ya sha mur ya na mai kausasa murya ya ce ‘’Akan wani dalili zai baki zobe ajiya? Shi waye d’in ki? Ashe dama ki na soyayya?’’ Cikin k’ok’arin kare kai ta ce ‘’Wallahi ba na soyayya, ban ta6a yi ba, idan k’arya na ke aratta kashe ni, Monsieur ne a École ya ce na ajiye masa.’’ ‘’Ciro zoben ki bani’’ Ya ba ta umarni. Har ga Allah ba ta son cire zoben, idanunta na fidda kwalla yayinda ta ciro zoben daga yatsanta, maimakon ta bashi sai ta dunk’ule shi cikin tafin hannunta. Ganin bata da niyar mik’a masa, ya mik’o hannunsa gare ta, a hankali ta d’aga ido ta kalle shi, ya na mai gyad'a mata kai ya mata nuni da hannunshi. Hannunta na rawa, ta aje zoben bisa tafin hannunsa, ba ta ankara ba sai gani ta yi yayi wulgi da shi gefe. Da sauri ta bi inda ya jefa da kallo yayinda ta ji zuciyarta na mata rad’ad’i, sai a sannan tasan ashe zafin da zuciyarta ke mata ba na rabata da iyayen ta kad’ai ba ne, har da na rashin Aisar har abada, gashi idan aka d’auke turarukan da ya bata, zobenshi ne kad’ai ya rage mallakin sa a gunta, ta na ji ta na gani Yarima Nuhu ya raba ta da shi kamar yarda ‘yar uwarsa ta rabata da shi, idan ita dan ta na son Aisar ne, shi kuwa Yarima Nuhu menene na shi azancin? Tambayar da ta yiwa kanta kenan, wanda nan ta ke kuwa ta ji amsarta, Yarima Nuhu na mai duban ta ya kira sunan ta da kakkausar murya ‘’Bintu’’ Hakan yasa Bintu dawowa da kallonta gareshi. Bai gushe ba ya cigaba ‘’Soyayya gaskiya ce, soyayya halal ce muddin ba a tsallake iyakokin Ubangiji ba, ba laifi ba ne don kinyi soyayya, amma ki sani duk duniyar nan da ni ya dace ki yi, Bintu ni mai kaunarki ne, ni Nuhu ni masoyinki ne da ni ya dace ki yi soyayya ba da wani tsoho da ake shirin amra mi ki ba, ko kuwa wancan sokon Monsieur da ya bawa d’alibarsa ajiyar zobe!’’ A tsorace Bintu ta fara ja da baya, ta na mai girgiza masa kai, tsabagen firgici ta kasa magana. Da sauri ya rik’o hannunta, ya na fad’in ‘’Karki guje ni Bintu, ni mai k’aunarki ne, kimin alkawarin za ki aje min kanki amana, ah ah kawai ki shirya mu gudu, duk k’asar da ki ke so aradu zan kai ki Bintu, kar ki yarda a amra mi ki wannan tsohon.’’ Cikin sauri Bintu ta fizge hannunta daga nashi, har lokacin ba ta fasa girgiza kanta ba, yayinda ta ke hawaye d’aya na bin d’aya, tunda ta ke a rayuwarta babu wanda ya ta6a furta kalmar so a gareta, kuma ba ta ta6a zaton zata ji shi daga bakin ko da ‘yantaccan d’an adam ba ne, bare kuma Yarima, Yariman ma na Sa'ayrasa. Hankalin Bintu bai dad’a tashi ba, sai da ta ga kwalla cikin idanun Yarima Nuhu na gangara a hankali bisa kuncinsa, nan ta mik’e tsaye da sauri yayinda kuka ya ci k'arfinta tana mai tattare kasan doguwar rigarta, ta juya da niyyar tafiya, hakan yasa Yarima Nuhu tashi da sauri, ya na mai rik’o kallabinta ya ke fad’in. ‘’Karki tafi ki barni Bintu, aradu zan iya rasa raina, ki tausayamin.’’ Sakar masa kallabin ta yi, gashin kan ta lub lub ya sauko har bisa wuyanta maimakon gadon bayanta da ya saba saukar sakamakon askin da ta sha gun Marry, tana mai tafiya cikin gudu gudu, sauri sauri, ta d’au hanyar fita daga lambun. Yarima Nuhu rik’e da kallabinta ya shiga doka mata kira ‘’Bintu! Bintu!! Bintu!!!’’ Ina ko waige ba ta yi ba bare ta tsaya har ta fice daga cikin lambu, in da ta bar Yarima Nuhu rungume da kallabin na ta bisa k’irjin sa, ya zube gwiwowi biyu k’asa zuciyarsa na bugawa kamar za ta tsage ta fito. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 [5/15, 7:26 PM] ‪+234 703 962 5239‬: ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. DA BAZARKU NI NA KE TAKA RAWA ​FIKRA WRITERS ✌🏽 Ummuabdoul Ummu Hannan Rashida Kardam Sanah Matazu Aysha Kura Batul Maman Bingel Farida Abdullahi Da uwa uba Rufaida Umar, ba zan mance da ke ba. Allah ya bar zumunci. ©Khadija Sidi.....✍🏼 2⃣5⃣ Kai tsaye 6angaran Jakadiya da ya zame mata sabon wajan kwana ta shige, ta tsallake bayi biyu wanda ke ta faman had’e sababbin kayan da aka d’inko mata, ta shige d’akin Jakadiya ta na mai doka k’ofar gudun kar Yarima Nuhu ya biyota. K’uryar d’akin ta shige ta k'udundune ta na mai mayar da numfashi. Ba ta yi minti biyar da shiga ba bayin su ka biyo ta su na mai tambayar lafiya? Ko ta yi gamo ne? Baki na rawa Bintu ta ba su amsa da ‘’Don mai sama ku rabu da ni, ko shakka babu na kusa rasa raina, na shiga uku ni Bintu na lalace, wayyo Allah Inna ta!’’ Kallon junansu su ka yi, su na mai gyad’a kai cikin jaddada zatonsu na Bintu ta yi gamo, har an fara jifanta daga Masarautar Fabarusa tun kan ta shiga Masarautar, su ka juya jiki a sanyaye su ka fito suna mai rufo mata k’ofa. Daga waje baiwa ta dubi ‘yar uwarta ta ce ‘’Gide k'ak'a kenan, kinga har an fara yiwa wagga d’iya ture ko? Babu mamaki wani bakin aljanin aka fara mata ture da shi don ta fita hayyacinta ta ce ta fasa amran ga, wagga sharri sai kishiyoyi, maza je ki shedawa Jakadiya tun kafin abu yayi tsamari.’’ Cike da jimamin abun baiwar ta amsa mata da ‘’Wagga batu gaskiya ta, aradu wagga d’iya gamo ta yi, inda kin lura har launin idanunta ya sauya, bara dai na je ga Jakadiya, mutum hege ne, mutum ba imani.’’ Tana mai ta6a kafad’arta, ta ce ‘’Maza Ladiyo, ni bara na tsaya daga rariya ko da wani abun zai faru.'’ Jikin baiwar na rawa ta fara tafiya, tana fad’in ‘’Eh tsaya Kyallu, bara na ruga na dawo, Allah shi fisshemu daga sharrin mahassada.’’ Ta fice, inda ta bar Ladiyo da tsaron k’ofar Bintu. Ita kuwa Bintu ita kad’ai tasan abinda ke damunta, yau ta ji ta kuma ga abinda ba ta ta6a tsammani ba, ko shakka babu tasan rayuwarta ce ta zo k’arshe, ko kuwa dai Yarima Nuhu ya soma shaye-shaye kamar yanda wasu samari daga cikin bayi su ke yi. Abinda ke d'agawa Bintu hankali shi ne sake rike hannunta da Yarima Nuhu ya yi, ita tasan rayuwarta ce ta zo k'arshe. Jin Bintu ta fara yin gamo tun ba aje ko'ina ba, nan da nan Jakadiya ita ma ta had’o kayan tsubbuce tsubbucenta, haka ma Hajja Kilishi, wacce dama ita aka damk’awa Bintu a hannu. Suna mai jan kunnan bayinnan biyu, Ladiyo da Kyallu, akan kar su sake aji maganar a waje. A gaba Jakadiya da Hajja Kilishi su ka sa Bintu, tambayar duniyarnan sun mata akan gamon da aka ce ta yi, amma shiru Bintu ta kasa ce musu komai don kuwa muddin ta fad’i gaskiya to kashinta ya bushe. Ganin haka su ka yanke hukuncin fara kare ta tun daga yanzu don babu mamakin sammu da aka fara mata har da na d’aure baki. Bintu na ji ta na gani aka fara mata lalas da siracen magunguna, har da na sha da wanka, kan ka ce me tuni ta fita hayyacinta in banda attishawa babu abinda ta ke yi, ko iya haka aka barta ta san ba k’aramin masifa ganin Yarima Nuhu ya jaza mata ba. Bayan siracen da ta sha, sai da Jakadiya ta bi duka ga6o6in jikin Bintu ta na d’aura mata laya, wai gudun kar a zo mata cikin dare, nan ko ba su san in ma akwai aljanin ba zai wuce Yarima Nuhu ba, kai Allah shi fisshe mu aikin jahilci. Saida su ka tabbatar sun gama kafe Bintu kaf, Hajja Kilishi na mai duban Bintu da gaba d’aya ta jigata saboda siracen da ta sha, gashi cikinta har juyawa ya ke tsabagen had’aka na magunguna da Jakadiya ta afka mata duk da sunan makarin sammu da kafiya, Hajja Kilishi ta ce ‘’Ni ko Jakadiya d’iyarnan na shan maganin da’a kuwa(maganin mata)?’’ Jakadiya na mai susa k’eya ta amsa da ‘’Yo to wani maganin da’a za a bawa wagga d’iya za a amran da ita ga tsoho ank’i rami? Ai ni a tunanina tunda dai Sarkin Fabarusa an tsufe ban ji zai damu da abubuwa irin wagga, ko k’ak’a kin ka gani?’’ Hajja Kilishi na mai murmushi ta ce ‘’Tsoho ba mutum ba Jakadiya, yo to maza ma ai ba sa tsufa, kar ki so ki ga yanda Takawa ke ji dani duk farin gemun nan nasa, yauwa tun da magana ta kawo magana, Jakadiya ina mai buk’atar zuwan Takawa gare ni a yau ma, hallo zannuwa da kallabi har guda goma na nan tafe izuwa ga d’akin Jakadiya nan ba da dad’ewa ba’’ Dama dai maganar kenan, ta 6ige da Bintu gudun kar Jakadiya ta ga kamar ta cika naci, don kwana hud’u kenan ita Jakadiya ta ke kai wa Sarki, kasancewar hatta kwanan matan Sarki sai wacce Jakadiya ta za6a tsabagen matsayi irin na Jakadai a fada. Jakadiya kuwa mai idon cin naira, jin zannuwa na tafe tuni ta kada baki ta ce ‘’Yo to menene, in ma sau goma ki ke san zuwan Babban Bijimi aradu gun ki ya ka kwana, an gama ranki shi dad’e, sai kin ga zuwan mu.'' Hajja Kilishi na mai jindad’in yanda Jakadiya ke damawa da ita, duk da dai ta san na d’an k’ank’anin lokaci ne, in dai Jakadiya ce bakin ganga ta ke, arzikinka shagalinka. Ta mata sallama in da ta barta da Bintu ta mai mata jawabin yanda za ta yi ta kare kanta a Masarautar Fabarusa. Ita dai Bintu jinta kawai ta ke, amma ko yaya ta rufe idanunta fuskar Yarima Nuhu ta ke gani yayinda ya ke furta kalmar so a gareta, haka zalik’a maganganunsa ke mata yawo cikin kwakwalwarta. Ko shakka babu Bintu ta yi gamo, amma fa da Yarima Nuhu, mutuwarta kad'ai ta ke jira kamar yanda Iya Dije ta ce muddin namiji ya ta6a ta. Zoben Aisar kuwa d’aya daga cikin bayi ne, wanda saurayi ne, mai kula da lambu ya tsinta yayinda ya ke shara. Ganin zobe mai matuk’ar tsada yayi saurin 6oyewa cikin aljihunshi, don jira ya ji ko mai shi zai nema, idan kuma ba a yi cigiya ba ya kai kasuwa ya siyar ya sami kud’i. ******** Kwanaki uku ya rage auren Bintu. Da hantsi Inna Salti ta kawo ziyararta ga Bintu. Daga ita sai Bintu da ke d'urkushe gabanta ne a d'akin. A sannu cikin lallami Inna Salti ke mata magana, in da ta ce ‘’Bintu ki sani wannan lamari jarabawa ce daga Allah, saboda haka ki kasance mai biyayya sai ki ga kin ci jarabawar. Wagga amre za a yi shi ne cikin surri, duk wanda ki ga ya san wani abu na game da gaskiyar wagga amre to amintaccen fada ne, hallo sai sun rantse ake ba su amanar ga, dan haka kema wagga al'amari ya kasance amana a naki 6angaren, idan ki ka kuskura gaskiyar al’amari ya hito, rayuwarki za ta kasance cikin hatsari Bintu, wanda ba na fata. Daga sanda aka amra miki amre za ki tashi daga Bintu, za ki fara amsa Gimbiya Binta.’’ Numfashi ta ja, sa’annan ta cigaba ‘’Kin dai ga yanda sarauta ta ke, a fada aka haife ki ciki ki tashi har rana ita yau da ake shirin amrar da ke. Hallo sai kin yi takatsantsan da rayuwar da za ki shiga, zaki shiga rayuwar amre hallo a fada, akwai wuyar ganewa. A fada ba kowa ne zai 6ud’i hak’ora ya miki dariya ya kasance masoyi gareki ba, wani sa'in ma mak’iyinki ka iya nunawa kin fi kowa soyuwa a gareshi, haka zalika ba kowani mai 6ata miki ba ne mak’iyi a gareki, ta iya yiyuwa kauna ke kawo 6acin ran, don haka ki nutsu ki gane.’’ Bintu na mai share hawaye sai gyad'a kai kawai ta ke. Inna Salti na mai nisawa ta k’ara da ‘’Ki ji ki k’i ji, ki gani ki k’i gani, ki iya harshenki, hatta bangon fada kunne gareshi, ki kyautata dangantakarki da kowa, ki sa Allah a ranki, ki yawaita addu'a da zikiri, ki kasance mai yawan zama da alwala, shin kin iya azkar?’’ Bintu ta girgiza kai alamar ah ah, Inna Salti na mai gyad’a kai ta ce ‘’Zan yi k’ok’arin sawa a koya miki kan a kai ki ga Fabarusa, ki na yi safe da yamma, ni ma da kika ganni anan addu'a ce da tawassali ga Allah kad’ai ke zaunar da ni a wagga Masarauta bare kuma Masarauta mai girman gaske kamar Fabarusa.’’ Jakadiya ce ta shigo, yayinda ta zube gaban Inna Salti cike da girmamawa duk da dai ba yin Inna Salti ta ke ba, ba ta yi mata kyauta da cin hanci kamar sauran matan Sarki. ‘’Barka da hantsi ranki shi dad’e.’’ ‘’Barka dai Jakadiya, na sameki lahiya?’’ ‘’Lahiya lumi ranki shi dad’e.’’ Kana Inna Salti ta maida dubanta ga Bintu ta ce ‘’Inaso na san adadin bayin da za su bi Bintu Masarautar Fabarusa.’’ Jakadiya na mai gyara zama ta ce ‘’Akwai Ladiyo da Kyallu, wanda Gimbiya Binta ce ta za6esu da kan ta....’’ Jin haka sai da Bintu ta d’ago ta dubi Jakadiya cike da fad’uwar gaba, don kuwa ta san hakannan siddin Gimbiya Binta ba za ta ta6a za6a mata kowani abu ba, muddin ba sharri ba ne. Ita kuwa Jakadiya da ba ta san ma ta na yi ba, ba ta gushe cikin jawabinta ba ‘’Sai kuma Uwanini, amintacciyar baiwar Yarima Nuhu wanda shi da kansa ya buk’aci hakan.....’’ Ihu ne kawai Bintu bata kurma ba jin wannan masifar da ake shirin had’a mata, maganar Inna Salti ne ya d’an kwantar mata da hankali, jin ta ce ‘’Ita fa Bintu? Shin an tambayeta ko ta na da baiwar da ta ke son tafiya da ita?’’ Jin haka Jakadiya ta kai kallanta ga Bintu, ta ce ‘’Bintu shin ko kina da wannan buk'atar gide? Wa ki ka za6a” Bud’ar Bakin Bintu sai cewa ta yi ‘’Innata, dan Allah a tafi da Innata’’ Jakadiya na mai girgiza kai ta ce ‘’Innar ki gobe goben nan za su yi bulaguro zuwa marad’i bisa ga umarnin Babban Bijimi, har sai an sami lafawar al’amura za su dawo, sai dai fa ki za6i wata baiwar.’’ Nan da nan Bintu ta fashe da kuka jin Innarta za su bar gari, Inna Salti ta fara k’ok’arin rarrashinta Jakadiya ta ce ‘’Ai da kin kyaleta ranki shi dad’e, abun ga ne ya zo ga ma su shi, kukan amre da sallallami '’ Inna Salti ba ta fasa rarrashin Bintu ba, har ta samu ta d’an yi shiru kafin ta k’ara bata za6i, inda ta za6i aminiyar Inna kuma mahaifiyar k'awarta Cangwai, wacce aka fi sani da Maman Cangwai. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 [5/15, 7:44 PM] ‪+234 703 962 5239‬: ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. Na gaishe ki aminyar arziki Ummi Aysha, ina alfahari da ke. Allah ya bar zuminci🤝 ©Khadija Sidi.....✍🏼 2⃣6⃣ Da yammaci Inna ta zo mata sallama d’auke da su langar tuwo da miya, da humra da turaren wuta. Tun zuwanta Bintu ta ke kuka, har yanzu da Inna ta ke mata jawabi kamar haka ‘’Bintu kar ki damu, wani hani ga Allah baiwa Bintu. Ki yi addu'a Allah Ya sa hakan da ya zo mana shi an alkahiri, ina so ki sani Allah ne ya za6a miki wagga rayuwa da za ki shiga, ki sa Allah a ranki shi kad’ai zai miki gata.’’ Bintu ta gyad’a kai alamar toh. ‘’Duk da amren ga ba a san ranmu za a yi ba, ki na jinin barebari ba zan bari ki tafi haka ba, wagga(ta nuna kwalaban turarukan da ke aje gaban Bintu da yatsa) tun kina shekara biyar a duniya na had’a mi ki su na binne da niyyar sai amrenki ya tashi na hak’o, wannan kuma langar tuwo da miya da cokali da ludiya wanda na fara miki taro ne, duk da dai na san ba lalle ba ne a bari ki tahi da su ba, gashinan dai na baki a matsayin uwa, na hita hakkinki.’’ Bintu na kuka ta ce ‘’Wallahi ba na so! Ba na so Inna! Inna makaranta na ka so, dan Allah Inna ki taimaka kin ga dai sati uku ya rage mu koma....’’ Rungumeta Inna ta yi cike da tausayawa, Allah kad’ai yasan iya adadin lokacin da su ka d’auka a haka, kafin Bintu ta zame jikinta daga na Inna, kayanta ta nufa ta na mai bincikawa, nan ta fito da turarikan da Aisar ya bata, ta dawo ta durkusa gaban Inna, ta na mai mik’a mata ta ce ‘’Inna ga wagga, dan Allah ki kar6a ko da kuwa ba za ki yi amfani da su ba, wannan kyauta ne tsakanin uwa da d’iyarta, dan Allah Innata, wagga shi ne kad’ai abunda na mallaka nawa na kaina’’ Hannun Inna na rawa ta kar6a ta na mai fad’in ‘’Allah Ya sadamu da alkhairinsa d'iyar arziki, Allah ya sada mu ko da a darussalamu ne, saduwa ta alkahairi......’’ Kuka ne ya su6ucewa Inna, nan su ka yi mai isarsu, har dai Inna ta ga abin ba na k’arau ba ne, dakyar ta janye jikinta ta fice ta na jiwo kukan Bintu. Yarima Nuhu kuwa har da jinya don kuwa babu yanda baiyi ba na ganin an fasa aurennan amma abu sai dad'a kankama ya ke, haka kuma ya so k’ara ganin Bintu amma Jakadiya ta k’i. Ta wannan dalili ya sa ko ganin Gimbiya Binta ba ya san yi, don kuwa ba zai manta da asarar da ta jawo masa da kuma halin da ta sanyashi ciki ba. Haka kuma bai fasa zayyanawa amintacciyar baiwarsa yanda ya ke san ta kula da al’amuran Bintu yanda zai kasance ba zai cutu ba har ya samu ta dawo gare shi. Ana gobe d’aurin aure da daddare aka yiwa Bintu k’unshi irin na amare. Yanda ta ga dare haka ta ga rana, haka ma Yarima Nuhu wanda zazza6i ya rufe har da k’arin ruwa. Aisar kuwa farin cikin zai ga Bintu ne ya hana shi bacci, don da an bi ta tashi da tun aranar zai d’au hanyar Sa’ayrasa, sa idon Junaidu da gudun sharrinshi ya sa ya hakura. Haka ma Yarima Barde wanda farin cikin zai had'u da Gimbiya K'amariyya ya hana shi bacci, da ita kanta Gimbiyar. ******* ****** Washegari tun da sassafe Jakadiya ta sa Bintu wanka da wani ruwan magani gudun kar bak'in da su ka zo daga Fabarusa d’aurin aure su buk'aci ganin amarya, ko kuma Sarki Abdulrahman da kansa ya buk’aci hakan bayan an d’aura masa aure da Bintu ba tare da an shiryawa hakan ba. Leshi fari kyal mai adon koren duwatsu ta ce ta sanya. Farar alkyabba Jakadiya ta d’aura mata bisa, da wani takalmi kore. Kai da ka ga Bintu ka ce d’iyar Sarkin ce, ita kanta Gimbiya Binta da ta shigo ta gan ta sai da ta girgiza, ta kasa zama bare kuma dama tunda Allah ya wayi gari ta ke fama da fad’uwar gaba na ba gaira ba dalili. ‘Bangaran d’aurin aure kuwa, misalin sha biyu na rana tuni babban masallacin fada ya cika mak’il da jama’a, mutan Fabarusa, Mai Martaba Sarki Abdulrahman ya iso tare da tawagarsa, hakimai da dogarai, har da ‘ya’yansa biyu, Sadauki da na shi abokan, haka ma Barde da abokansa biyu, d’aya taubashinsa(cousin) wanda ake kira da Yarima Jafar, sai kuma d’ayan mai suna Khalil wanda ya ke babansa hakimi ne a Masarautar Fabarusa. Haka ma su Aisar tare da Ministocin da su ka taho wakiltar mai girma shugaban k’asa, sun sami isowa, inda aka musu mazauni daga cikin Masallacin. Ba k’aramin kyau Aisar yayi ba, dan kuwa ado ya sha na burgewa musammam saboda Bintu. Dokakkiyar shadda ce jikinsa, ruwan toka, ya sha d’inki da aiki irin na manya, ga hularsa da takalminsa kalar zaran da aka masa aiki da shi, wato ruwan toka mai turuwa, da ka gansa ka ga d’an manya masu ji da mulki. Allah Allah ya ke ayi d’aurin auren a gama ya nemi Bintu don shi ita kad’ai ta kawo shi cikin wannan taro, yak’i jinin taro saboda yanayin aikinsa. Yarima Barde kuwa daga waje yayi zamansa, gudun kar ya shiga ciki taro da turnak’in jama’a su hana shi ya fito da wuri don zuwa ga sahibibar ta shi wato Gimbiya K’amariyya. Sanye ya ke cikin farar shadda d’inkin babbar riga, ga rawani ya sha kai, ka ce za a kira shi Sarki ya amsa. Ango kuwa Sarki Abdulrahman tare da hakiman sa da kuma su Sadauki suna daga cikin masallaci. Dake taro ne na manya da Sarakuna, shaddodi kala-kala tsadaddu ki d'aukar ido da kukama kalar kayan dogarai daga Masarautu iri-iri, abun dai ba a cewa komai, don kuwa wuri ya yi wuri, taro ya yi taro sai kamshi da kid’an algaita, kirari da kiran lafiya na dogarai da marok’a ke tashi. Sarakunan yanki da sassa na cikin jamhuriyyar Nijar babu wanda be sami halarta wajan ba, Sarkin Agadaz ne, Diffa, Marad’i, Zindar da dai sauran su. 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 [5/15, 8:24 PM] ‪+234 703 962 5239‬: ® ✏📖 ​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​ 🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! 🐪🐪🐫🐪 🐪🐫🐪🐫🐪🐫 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪 GARGA'DI KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE. 💌 SAK'ON NA MASOYA NE🤗 Ina godiya da babban murya ga masoyan Bintu d'iyar bayi, na gida Nigeria da kuma mak'ota Nijar. Ina alfahari da ku. Sidiya ce ke mu ku fata na alkhairi🤝 2⃣7⃣ Daga cikin Masallaci aka fara abinda ya had’a jama’a a wannan masarauta, wato d’aurin aure, in da aka umarci waliyin Ango da Amarya su matso kusa. Waziri ne ya fito daga 6angaran Sa’ayrasa, Fabarusa kuma Sarki Abdulrahaman ne ya nuna kan sa a matsayin waliyi. Daga waje Khalil ne ke ta yiwa Yarima Barde hira, amma shi ina hankalinsa na ga Gimbiya K'amariyya, Allah Allah ya ke a shafa fatiha ya tafi garera don jin soyayyar ta ya ke har ransa, bare kuma yau gabar da ke tsakanin Masarautasu za ta kau, za su yi soyayyarsu a zahirance ba tare da wani shakku ba. Jin an shafa fatiha Yarima Barde ya tashi ya na mai fad’in. ‘’Alhamdulillah tunda an amra sai ku tashi mu tafi ko?’’ Har Khalil da Jafar sun tashi, tuni su ka tsaya cak jin marok’a na fad’in ‘’An d’aura auren *Yarima Abubakar BARDE* tare da *Gimbiya Fatima* akan sadaki (50000 CFA)" Yarima Barde da sam bai lura da abinda su ka ji ba tsabagen hankalinsa ba ya wajan, a hasale ya kai kallonsa ga abokannasa ya na mai fad’in ‘’Me ku ke jira ne? Mu tafi, Allah Allah na ke na gana da Gimbiyata.’’ Su kuwa marok’a ba su fasa shela ba. Khalil ne yayi k’arfin hali ya ce ‘’Da ma kai ne Barde?’’ Cikin rashin fahimta Barde ya ce ‘’Ni ne wa?’’ ‘’Angon da aka amrawa amren.’’ Jafar ya bashi amsa a tak’aice. Kai Yarima Barde ya girgiza cike da murmushin irin ban son rainin hankali fa. Khalil ya ce ‘’Saurara ka ji Barde’’ Nan kuwa muryar wani marok’i da ya zo giftawa ta dafda su ya doki kunnan Barde, fad’i ya ke ‘’An amra auren Yarima Abubakar Barde da Gimbiya Fatima....’’ Nan ya ya tsaya cak tamkar wanda aka zarewa rai, su kansu abokannasa sun girgiza kwaran gaske. Daga cikin masallaci, ana gama d'aurin auren, inda kowa ya ke mamakin sauyin al’amura da aka samu, musammam jama’ar Sa'ayrasa, shi kuwa Aisar tunanin hanyar fita daga cikin jama’a yake, domin zuwa neman Bintu ba tare da Junaidu ya ankare ba. Bayin Sa'ayrasa ne d’auke da farantin goro da alawa, su ke bin kusirwa kusirwa in da suke mik’a farin tin jama’a na d'iba san ran su. Bawan da ya zo kusurwar da su Aisar su ke, Aisar ya fara mik’awa, in da ya girgiza masa kai alamar ba ya buk'ata, har bawan zai wuce, nan idanun Aisar su ka sauka bisa yatsun bawan, me zai gani? Zobensa da ya bawa Bintu ne cikin yatsun na shi, bai ankara ba sai ji yayi Aisar ya damk’o hannunshi, a tsorace bawa ya saki farantin hannun sa dan ko shakka babu ya san tawagar shugaban k’asa ne gabansa.Hakan ya dawo da hankalinsu Junaidu da sauran ‘yan tawagar garesu. Aisar na mai duban idanun bawan ya furta ‘’Ina ka sami wagga zo6en? Menene dangantakarka da mai zo6en? Ina Bintu d’iyar bayi?’’ Babban gida kuwa 6angaran Jakadiya, Bintu na zaune tare da su Jakadiya sai ga Gimbiya K’amariyya ta shigo, ta yi kyau kwarai cikin jajayen kaya, ta d’aura alkyabba ruwan zuma bisa kayan, ga bayi nan biye da ita. Ta zo kar6ar mabudin wajan aje baki na musammam domin kar6ar Yarima Barde. Ta na zaune ta na jiran Jakadiya ta shiga ciki dan d’auko mata mabud'in, su ka ji an shigo 6angaren Jakadiya an gud’a. Tuni hanjin cikin Bintu ya kad’a don kuwa ta san ta faru ta k’are an yiwa mai dami d’aya sata, aure dai an aura. Tuni ta fashe da kukan da dama ya tsaya k’asan mak’ogaran ta. Jakadiya ta fito d’auke da mabud’i, yayinda Ladiyo ta shigo jiki na rawa, sai tafa hannu ta ke cikin salati da sallallami. Jakadiya ce ta tambaya ko lafiya, yayin da hankalin kowa ya koma gareta. Cike da ladabi Ladiyo ta durk’usa gaban Jakadiya ta na mai fad’in ‘’Yau na ga lafiyar Allah Maigari gauro talaka da mata hud’u.’’ Cikin k’aguwa Gimbiya K’amariyya ta ce ‘’Me ya faru ne Ladiyo?’’ ‘’Wato Allah shi taimaki Gimbiya, ji da gani dai ba ya k’arewa sai randa kurman bebe ya makance, Sarki Abdulraman na Fabarusa cike ya ke da abin mamaki, wani lamari sai shi.....’’ ‘’Yo to wani abin mamaki? Ya ce ya fasa ne?’’ Jakadiya ta tambaya cikin rashin fahimta. Kana Ladiyo ta ce ‘’Eh to ya fa fasa be kuma fasa ba, da ya tashi yin bazata, sai ya amrawa d'ansa Barde Bintu.....’’ Hakan yayi daidai da ihun da Gimbiya K’amariyya ta kurma ta na mai zubewa k’asa sumammiya. Nan da nan aka yi kanta. Bintu kuwa yanda maganar ya doki kunnenta ta tabbatar ta zama kurma, don kuwa ba ta jin hayaniyar da ake gabanta ‘’Ya amra ma d’an sa Barde Bintu....’’ Maganar da ke ihu jikin kunnenta kenan. Tammat Bihamdillah Nan na kawo k’arshen Bintu d’yar bayi ce kashi na farkon, sai a dakace ni zuwa bayan sallah da rai da lafiya. Ina mai mu ku fatan yin azumi cikin k'oshin lafiya. Dan Allah ku saka kawuna marigayi Alhaji Aliyu Abdullahi Sidi (A.A Sidi) cikin addu’a, Allah ya ji kan sa da rahama. Allah ya sada mu da alkhairin sa. Sidiya ce ke mu ku fatan alkhairi. HASKE Sa'ayrasa S anah Ay aisha Ra shida Saƙlma Fabarusa FA=Fatima/Farida B=Batool R=Rufaida U=Ummuabdoul S=Sidiya A=Asma'u/Bingel. Monsieur Malam École Makaranta Madame Malama Ciseaux Almakashi Gide Ke Hallo Kuma/ haka zalika Rariya Waje Aratta kashe ni Kwankwatsi Aradu Rantsuwa Kwana Bacci Amre. Aure Wagga/wanga Wannan 🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪