https://my.w.tt/9J8gWVc 🕯️*ƘARFEN ƘAFA* 🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmanir Raheem. (1) Ta faka motarta ƙirar Peugeot 406 , kalar sararin samaniya. Ta kai duba ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta na dama. Ganin akwai sauran mintuna ya sa ta zare wayarta daga chaji ta shiga dannawa. Hankalinta ya kai ga saƙon da ya faɗo wayarta kai tsaye maimakon daya cikin kafafen soshiyal midiya da take amfani da su. Murmushi ta yi wanda har siririn wushiryarta ta bayyana a fili ganin sunan wacce ta turo saƙon. "Muhibbat." Ta furta a fili. Saƙo ne kamar koyaushe na gaisuwar juma'a. Ta aikamata da reply sannan ta ajiye wayar a gaggauce ganin har sha biyu ta gota. Fitowa ta yi bayan ta gyara zaman mayafin abayarta. Ba ka ganin komai a jikinta face fuskarta da tafukan hannunta sai kuwa ƙafafunta da suka sha jan lalle. Bayan security man ya tsayar da motocin dake shige da fice don bada dama ga iyaye da yara su tsallaka, ta shige kanta tsaye cikin makarantar. Tun kafin ta karasa garesu suka taho a guje suka rungume ta. Ta rungumesu sosai, gami da saka yatsa saman goshin babbar ta tura ta baya kadan. "Ji, ke ko kunya ba kya girma? Har da ke a waɗanda za'a runguma?" Yarinyar ta turo baki tana gyara zaman jakarta gami da hararar kannennata dake faman yi mata dariya. "Mommy ki musu magana, kuma ai kin ce ni ce mai sunan Hajiyarki kin fi sona." Nan da nan yaran suka yi mata ca kowanne da kalar korafinsa, idan da sabo ya ci ace ta saba da hakan, ba ranar da za ta zo ɗaukarsu daga makaranta basu chajamata kai ba. Su uku amma hayaniyarsu ta fi ta wasu biyar din. Dakyar ta haɗa kansu, wannan yana bai ga jarkar ruwansa ba(water bottle), wannan yana an yagamasa littafi. Bayan ta samu sun zauna a motar ta yi musu tsawar da duk suka nutsu, sannan ta soma tuƙi. Ta madubi ta saci kallon autansu Affan yana yiwa ɗan uwansa raɗa a kunne. Murmushi ta yi gami da girgiza kai daidai lokacin da ta ɗau hanyar da za ta sadata da unguwar Sharaɗa. Tana son yaranta har cikin ranta, zama tare da su ya fiyemata komai. Tana ƙara tabbatarwa su ne mahaɗin rayuwarta, farin cikinta da komai ma, ba don ta rasa mahaifa ba, a'a sam, sai don kasancewar su din kusan basu da kowa da zasu kalla su yi alfahari da samunsa a rayuwarsu sai ita. Ita ce komai nasu a yanzun da rayuwa ta zo musu da tarin sauye-sauye. Bata ankara ba sai ji ta yi ta ci karo da abu. Nan da nan ta ja burki tana salati, shima mai motar bai ko motsa ba, ta kai duba ga ta'adin da ta yiwa motar. A kudi da tsaruwa, ba za'a haɗa motar da nata ba, mota ce red in colour, ƙirar Hyundai Accent. Diyarta wacce tuni ta wangale baki tana girgiza harshe sama da kasa cikin fadin "Lalalala, tab!" Ta ƙarashe ganin yanda Mominsu ta tarwatsawa mai motar fitilar baya (tail light). Ba ta ko kalli ƴar ba don hankalinta ba karamin tashi ya yi, ta bude murfin motar ta fito a gigice. Jama'ar da ke wurin wadanda tare aka tsayar da su a junction duk suka zuba ido suna jira su ga kalar rashin mutuncin da mai motar zai yi mata, tana tsinkayar muryar wani dake goye a baya babur yana fadin. "Ahaf, ai sai macen, dama daga ganin tuƙin kalar ta matan ce. Allah dai Ya kyauta." Ba ta ko kalleshi ba ta ƙarasa ga motar tana mamakin rashin fitowar mai motar wanda daga ɓarnar da aka yi gareshi ya ci ace ya fito, idan ma faɗan ne ko marin ayi a wuce wajen. Cike da fargaba ta kwankwasa gilashin zaman direba. Ba ta yi na biyu ba, aka zuge gilashin, ta ji faduwar gaba nan take. Da alama ba ma a hayyacinsa yake ba. "Yes?" Ta shanye razanar da ta yi a farko ta amsa tana mai nuni da inda ta ɓarnatar. "Wallahi bansan na yi ba, don Allah ka yi hakuri." Ta ƙarashe ba don tana da tabbacin ya karɓi tubannata ba, itama a jikinta ta ji cewar ta rainamishi hankali. Ta yi ɓarnar dubunnai kuma ta tsaya bada hakuri. Ta gaji da kallonta da yake ta janye nata kwayar idanun cikin fidda tsammanin zai yafe ganin har an bada hannu motoci na shan gabansu suna ficewa. Ya kauda kai gami da fadin. "Kar ki damu, ba komai." Bai bata damar godiya ba ya zuge gilashinsa ya ja mota. Ta koma nata motar bayan kallon gilasan da suka tarwatse a ƙasa, a sanyaye ta tashi motar ta bar wurin. 'Kamar a buge yake fa.' Sai kuma ta yi saurin jan istigfari da saƙe-saƙen zuciyar da take kan abinda ba ta da hujja. "Momi ba kowa a motar?" Tambayar ɗanta na biyu ya katseta. Ta basu umarnin su yi shiru kafin ta cigaba da tuƙi jiki a sanyaye, har ga Allah ta gama tsorata da ɓarnar da ta yi, ba ta son rikici ko tashin hankali. Sai kuma lamarin ya zo mata ba yanda ta zata ba. Ta share zancen sa'ilin da ta iso gidannasu. Maigadi ya bude babban kyauren suka shige yaran na ɗagamishi hannu yana maida martani cikin dariya. Sai da suka fita sannan ta saita mazaunin motar can ƙasan ƙaramin rumfar ajiye motocin gidan. Da gudu yaran suka faɗa jikin wata dattijuwar mace dake zaune a falo tare da baƙuwarta. Tana dariya ta rungumesu. "Oyoyo yaran Hajiya, maza aje a cire kaya. Ke kuma ƙawata wa ya taɓa min ke?" Hajiyar ta furta tana miƙawa yarinyar hannu. Ta kuwa karasa ta zauna cike da shagwaɓa ta ce. "Ba Momi ce ba, wai nayi girma ba za ta rungumeni ba." Ta ba Hajiya da baƙuwarta dariya, ya yi daidai da sallamarta. Ganinta ne yasa yarinyar miƙewa da gudu ta yi ciki. Ba ta ce uffan ba ta ƙaraso ta zauna tana gaida baƙuwar Hajiya. Da fara'a ta amsa kafin ta maida kai ga Hajiya. "Yanzu wannan Ramlatu ce ta girma? Kar ki cemin duka wannan bataliyar ƴaƴanta ne?" Jin matar ta ambaci sunanta ya sanya ta kallonta dakyau duk a kokarin ta ga ta tuna fuskarta, sai dai Allah bai sa ta tuna ɗin ba. "Ita ce Hajiya Karama, ai shekarun ba kaɗan ba. Ba ki ganeta ba ko? Kin tuna makwaftanmu na tsohon gida na Yakasai? Duk da dai lokacin ba ki fi ƴar shekara goma ba, da wuya ki ganeta." Ramla ta yi shiru tana dan murmushi, tabbas sai yanzu ta dau fuskar. Tambayar a inda take aure da matar ta yi ya sanya ta daukar jakarta ta mike bayan ta dubi Hajiya. "Bari na ga yarannan." Daga haka ta yi gaba zuwa ɗan corridor da zai sadata da dakunan baccinsu. Wacce aka kira da Hajiya Karama ta bi ta da kallo cike da mamakin daukewar murmushinta alokaci guda, Hajiya wacce kunya duk ta kamata na watsawa Ƙawarta ƙasa a ido da Ramla ta yi, ta yi kokarin sauya akalar hirar, itama ba shiri ta saki don ta yi dana sanin tambayar. Sai da ta tabbatar yaran sun kimtsa, kowanne ya sha kwalliyar juma'a sannan ta koma ɗakinta bayan ta gargaɗesu da shigowa. Daga nan ta kama hanyar fita, idanunta ya kai ga Affan da ya sha jalla iya fara ƙal, ya turo baki kamar zai yi kuka. Danne dariyarta ta yi sannan ta wuce, ta san hukuncin ne bai mishi ba, yaro ne mai maƙon uwa, ba ya kaunar abinda zai sa shi nisa da mahaifiyartasa. Ita kuma a yanda take jinta ba ta kaunar hayaniya ko kusa, so take ta samu kaɗaici ko za ta ji sassaucin abinda ke shirin dawomata. Takan tsinci kanta cikin wannan yanayin duk sadda aka yi mata batun aure ko abu makamancin hakan. Kwanciya ta yi saman gadon bayan ta cire doguwar abayar dake jikinta ya kasance daga ita sai shimi da dogon wando tight. Shiru ta yi tana kallon akwatin dake saman sif dinta, abubuwa da yawa ne acikinsa, kusan za ta iya cewa kaf tarihinta yana ƙunshe cikin wannan tsohuwar adakar. A gaggauce ta juyawa sif din baya gudun kada ta aikata abin dana sani. Lumshe idanunta ta yi a hankali bacci ya dauketa. Ba ita ta farka ba sai wuraren karfe uku da mintuna, shi dinma sanadiyyar tokaremata ciki da ta ji anyi ne, ta ƙurawa yaron ido tana kallonsa, babu ta inda ya baro mahaifinsa. Ko kaɗan bai dauki komai daga halittarta ba. Gyara kwanciyarsa ta yi, ita ta sani, Affan ba ya hakurin rashinta a kusa matukar ba makaranta ya tafi ba ko kuwa ita din tana wurin aiki. A hankali ta dafa kansa ta mishi addu'a sannan ta sauko ta faɗa wanka. Babu sallah a kanta kasancewar tana fashi don haka tana zura doguwar rigar atamfarta falon ta nufa. Wannan karon Hajiya ba ta nan sai yaran dake zaune tare da Kanwarta wacce ake dab da bikinta, A'isha, suna kallon Frozen 2 a tashar mbcmax. Ba ta ce da su uffan ba ta faɗa kicin. Talatu mai aikinsu ta iske tana hada-hadar ɗora girkin dare. Suka gaisa sannan ta fito rike da robar ruwa sai lemun, saman dining ta nufa ta ɗibi shinkafa da miyar da aka dafa sannan ta dawo wurin yaran ta zauna. "Ina Hajiya?" Fadin Ramla bayan ta soma kokarin kai lomar abinci baki tana duban A'isha. "Yaya Munir ne ya zo, su na ciki suna magana." Ta gyada kai kafin ta maida kan yaran da suka ƙurawa farantinta idanu kamar ba su ci ba. Kallo daya ta yi musu duk suka juya kai basu kara marmarin kallonta ba. Ba kaɗan suke shakkar uwartasu a lokuta da dama ba. Sai da ta kammala tsaf ta sha ruwa gami da gyatsa da hamdala kafin ta mike ta kai komai kicin ta nufi hanyar ɗakin Hajiya. Da sallama ta shiga, kallo daya Yaya Munir ya yi mata ya ja kai gefe. Ta yi kokarin shanye wannan ɓacin ran da ya assasawa zuciyarta wanda har ta ji kamar ta juya ta fasa gaidashi. Sai dai kuma ba yanda ta iya ganin Hajiyar ta ganta, ta karasa shiga ta gaida Yayannata. Bai ko kalleta ba ya amsa da "Lafiya." Ya maida hankali ga Hajiya da ke lissafa mishi duk wani abu da suke bukata a gidan dangin cefanen kayan masarufi. "In sha Allah zan sallameki Hajjaju nan zuwa anjima komai da kika bukata zai iso. Allah Ya kara rufamana asiri dai." Da murmushi ta amsa da Amin kafin ta daga murya ta kira Ramla wacce tuni ta kai ƙofa. Shi Munir mutum ne marar dadin sha'ani a wasu lokuta, ga riƙo da fushi. Sau da yawa sai tunaninta ya dinga faɗamata cewar ai don ya yi abin duniya ne sama da kowa a gidan shiyasa yake gorantamata game da lamuran da babu wani da ya isa ya goge faruwarsa cikin kaddarar rayuwarta tunda dai haka Allah Ya tsara. "Na'am." Ta amsa tana duban Hajiya, ya yi daidai da mikewar Yayannata zai fice, Hajiyar ta dakatar da shi ya koma ya zauna ransa a hade don yasan tatsuniyar gizo bai wuce na ƙoƙi. Itama ta zauna ta russunar da kai, har yau tambayar da ta kasa ba yaranta cikakkiyar amsa shi ne. 'Meyasa Uncle Munir ba ya son mu?' Ta hadiyi miyau dakyar, maƙogwaronta har ɗaci yake. "Meyasa haka? Wace irin rayuwa ce? Wane irin halayya ku ke son nunawa? Muniru ba ka jin magana, ba ka ji. Muniru komai lalacewarka naka, naka ne. Hakanan za ka yi hakuri ka shanye dukkan wani abu da zai aikata mai muni ko akasinsa. Ba zai yiwu a sauya abinda ya riga ya faru ba, wanda aka yi a baya ya isa! Ya isa don Allah, ban taɓa sanya maku baki kan wannan lamari ba sai dai hakan ba wai yana nufin abin ba ya damuna ba. A manta da komai ko don albarkacin yaran da basu ji ba kuma basu gani ba. Kai ne babba, yau ba ran Alhaji, kai da ya kamata ka janyo ƴan uwanka a jiki ku hada kai a lokacin da nima ƙiris ya rage ƙasa ta rufen nawa idon, sai ya zamana ba haka ba. Wannan riƙo naka ba inda zai kai ka, inace ko Hilal a yanzu wasa da dariya yake da Ramlatu? Sai kai mai daukarwa kanka dala ba gammo? Da alama kai ne Bilkisun." Hajiya ta jefamishi baƙa sannan ta ci gaba da fada, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, daga uban gayyar har ita suka hau bata hakuri, Ramla banda kuka ba abinda take yi. Sai da Hajiya ta tsagaita sannan ta magantu. "Ya zan yi mishi Hajiya? Ya zan ɓullowa mutumin da ko arzikin gaisuwata idan ya amsa bai wuce don ganin idanun jama'a ba? Shikenan na fita a sahun Dan Adam? Ashe ba zan yi laifi da zan roki Dan Adam irina gafara ya yafemin ba? Kar fa a manta nima ajiza ce, idan hakan bata kasance ba ina ƙaddara za ta jefani? A titi zan haifi yarannan uku?" Kuka ya ci karfinta, Munir ya yi shiru kansa a ƙasa, maganganun Ramla sun shige shi sai dai bai ko kalleta ba ya kara maida hankali ga Hajiya murya a raunane. "Ina mai neman gafararki Hajiya, In sha Allah ba za ki ƙara kuka akan matsalata da ita ba. Daga yau na yafemata. Zan kuma ci gaba da kula da ku gaba daya. Allah Ya yafemu baki daya." Hajiya ta murmusa tana mai amsawa da amin, sai lokacin Ramla ta sassauta kukan ta rarrafa ga Yayannata ta soma magana. "Ka yafemin Yaya Munir, nasan na yi maka laifi. Ka yafemin don Allah." Ance jini jini ne, ya ji tausayinta sai dai bai ji cewar zai iya mance abinda ta yi ba. Kallon da yake mata ya sanya ta jin kunya da nauyi, ta ya za ta mance munanan kalaman da bakinta ya taɓa furtawa gareshi? Ta ina? Sam a'a, sai ta ji kamar a yau ne take fadi, kamar a lokacin take kallonsa tsakar ido tana fadin abinda ke ranta babu ko shakka. Ta sadda kanta kasa tana sharar hawaye. "Shikenan, ya wuce. Allah Ya yafemu baki daya." Daga nan ya mike ya musu sallama ya tafi, ta karasa jikin mahaifiyarta gami da kwantar da kai bisa cinyarta, Hajiya ta dafa kanta tana murmushi. "Ai an gama Ramlatu, da yardar Allah tunanin Muniru ba zai ƙara jefa zuciyarki cikin kunci ba. Allah Ya yi maku albarka, Ya jikan mahaifinku." Ta ƙarashe cikin rawar murya, ta amsa itama tana mai jin saukar hawaye. Sai dai can ƙasan ranta, zuciyarta na fadi mata akwai saura! Kada ta yi saurin yarda da zantukan Yaya Munir. Suka dan taɓa hira da Hajiya sannan ta fito falon, nan ta hangi Affan tsaye yana kuka yayyun na mishi waƙar Amalala. Duba ta kai ga A'isha wacce ke latsa waya tana dariyarsu, dama ba ta sa a rai za ta taimaka mata da wanke jikin yaron ba. A zamanin da ake ciki zai yi wuya a samu kanne masu wannan biyayyar ga ƴan uwansu. Kowacce son jiki da kwuiya ya mata katutu. Sai da ta tsawatar ta kimtsa yaron yana kai ƙararsu cikin jagwalgwalon maganarsa, ta lallaɓashi suka fito falon bayan ta danna inda ya yi fitsarin. Abinci ta zubamishi tana sanyamishi a baki, a hankali ta kai duba ga katon frame din su na family photo dake manne a can bangon wurin dining ɗinnasu. Sau da dama sai ta ga kamar mahaifinnasu bai mutu ba. Kamar ka kira sunansa ya amsa. "Wai nikam Anti Ramla, ba ki da labarin Yaya Munir shima zai yi aure?" Muryar Aisha ta maidota daga duniyar tunani. Ta ji maganar banbarakwai wai namiji da suna Hajara. "Kai A'isha." Cikin sanyin jiki A'isha ta mike zaune gami da taɓe baki. "Wallahi kuwa. Za ki gane wata ƙawata Hunainah? Wacce muka hadu a chat? Duka-duka zuwanta gidannan bai fi uku ba suka hadu. Ashe soyayya suke, ai yanzu ko magana ba na yi da ita. Ban kuma nunawa Anti Bilki sanadiyyata Yaya Munir ya ga Hunainah ba. Bana fatan ma ta sani." Ta ƙasashe tana yanƙwane fuska, ga dukkan alamu auren na Munir bai mata ba. Ita kuwa Ramla kai ta shiga jinjinawa, ikon Allah kenan. Har aure Yayan zai yi ba ta da labari? Ta kasa cewa komai sai ta yi yaƙe. "Na ganeta kam, wata ƴar Gombe da ziyara ya kawota Kano. Allah Ya sanya alheri, Ya hadamishi kan iyalinsa." A'isha ta amsa da Amin kafin ta shiga labartamata irin rashin mutuncin da Uwargidansa Anti Bilki ke tata mishi. Murmushi ta yi, duk da a yanzu ko magana Bilkin ba ta mata, amman ta tayata kishi. Ta kuma san yanda suke da A'isha, kusan duk gidan ma jininsu ya fi haduwa da ita. "Banda abin Anti Bilki, ta kai zuciyarta nesa mana. Komai idan ya faru mai wucewa ne, wuyarta a yi." A'isha ta taɓe baki ba ta kara maganar ba ganin kamar wacce take yiwa, ba za ta bata damar aibata lamarin ba. Karshe ta kira yaran su zo ayi Ludo Game a waya. Aikuwa har da Affan a ƴan kallo. Ta tattara wurin da ya abincin ya ɗan zube kafin ta mika kicin. Da sauri-sauri ta koma ɗakinta ta kulle da muƙulli. Zama ta yi gami da fashewa da kuka. Anya watarana hawayenta ba zasu ƙare ba? Anya ba za'a wayi gari sun ƙafe ba? Rasuwar miji kan zama tonon silili dama? Ko kuwa dai abinda ta shuka ne take girba? Har ɗan uwanta na shirin ƙara aure ba ta da masaniya? Ta kai duba ga hotonsu dake cikin frame saman bedside drawer dinta, su biyar cif da iyayensu suka haifa. Kowannensu fuska cike da fara'a, a sadda suka yi hoton duka-duka shekarunta tara a duniya. Ta kai hannu ta dauka tana duba. Mahaifinsu Alhaji Khalid Mu'azzam dattijon arziki mai kamala. Ya taso a maraya, ya rayu gidan ɗan uwan mahaifinsa Malam Abdullahi har zuwa girmansa a hannun Uwargida Hajja Zulai. Asalinsu garin Daura dake jihar Katsina, neman kudi ya kawo iyayensu nan Kano aka yada zango har suka zama ƴan gari. Alhaji Khalid bai da ilimin boko sai na Arabi, sai dai kasancewar arzikin na Allah ne, sai ya zamana duk wata sana'a da Alhaji Khalid zai yi ta yi albarka. Ya gwada sana'o'i da dama don har sana'ar siyar da taki ya yi, a hankali kuma ya koma siyar da kayan masarufi a kasuwa. Da kadan-kadan sai ga Alhaji Khalid da katon shago a kasuwar Singa inda yake da yara dake ci a ƙasansa. Sai da ya tsaya da ƙafafunsa ya gina karamin gida a unguwar Yakasai. Sannan ne Malam Abdullahi ya taso mishi da batun aure. A rashin saninsa, soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Alhaji Khalid da Autar Hajja Zulai, Rabi'atu. Sosai iyayen sun yi murna da wannan hadin na Ubangiji. Ba a dau dogon lokaci ba aka yi aure. Bayan aurensu da shekara daya Rabi'atu ta haifi ɗanta na fari, Muniru. A wannan shekarar mahaifinta ya rasu. Sun ji mutuwar Malam matuka. Bayan haihuwar Muniru da shekaru biyu ta kuma haihuwar diyarta mace, Zulaihat wacce ta ci sunan Hajja Zulai sai dai ta hana a ɓoyemata sunan sam. Wannan ya sa Hajiya kadai da Alhajin ke kiranta Uwani. Shima tun Hajja Zulai na mitar bata so har ta daina. Kusan za'a ce haihuwar Zulaihat ya zo wa mahaifinta da karin buɗi daga arziƙinsa. Ya gina tamfatsetsan shagon siye da siyarwar kayan maƙulashe da sauransu a unguwarsa ta Yakasai. Shagon ya ci sunan Alheri Store. Nan da nan ya zamo wurin zuwan kowane mai ji da ƙaryar kudi da gayu a wancan lokacin. Sosai ya ja yan uwansa a jiki bai taɓa nuna bambancin komai tsakani. Duk da cewar shi ɗaya ne tal wurin iyayensa, ya kasance mutum mai son zumunci da son ganin nashi sun haɗa kai. Bai samu matsala sosai ba sai dai wasu cikinsu ta ciki na ciki ne daman. Ba kowa zai nunamaka don da za ka nunamasa ba. Sai da Rabi'atu ta yaye Zulaihat kafin ta samu wani cikin, haka Allah Ya yi ta, ba ta samun ciki sai ta gama shayarwa. Wannan karon ma mace ta haifa, Rafee'ah. Bayan haihuwarta da shekaru uku aka haifi Ramlat. A sannan Munir ya kammala firamare yana shirin zuwa sakandire yayinda Zulaihat ke aji na uku a firamare. Sai Rafee'ah ƴar Nursery. Sai da Ramlat ta shekara biyar don har Rabi'atu ta fidda rai da ƙara haihuwa ganin har sannan Allah bai nufa ba, sai ga cikin A'isha. *** Ramlat ta sauke kanta ganin wuyanta na neman riƙewa tsabar kallon hoton, shakka babu ba za ta taɓa mance kalar rayuwar jin dadi da kulawar da suka samu daga iyayen ba. Kusan ba wanda ta fi rashin jituwa da shi irin Yayanta Munir kasancewarsa mugu a wasu lokutan. Haka kawai ba ya barin su sakata su wala. Murmushi tayi ta kara dubanshi a hoton. Akwai shi da zafi da kuma daurewa hakan yasa yake da wuyar sha'ani, idan kuwa ya maka laifi ka kai ƙara, sai ya ɗaura gaba da kai. A kanta da sauki, don shi da Zulaihat basu fiye zama a inuwa daya ba. Kuruciyarsu abin burgewa ce, ta tuna sai da ta shekara tara a duniya sannan suka yi ƙaura daga Yakasai zuwa unguwar Sharaɗa kwanar gandu. Ta daga kai tana ƙarewa ɗakinta kallo wanda a baya tare suke kwana da A'isha, a yanzun kuwa kowa da nashi. Zuciyarta ta yi rauni. "Allah Ya jiƙanka Abbana." Ta furta a fili gami da amsawa da amin. Ƙarar wayarta dake nufowa ɗakin ya katse tunaninta, Ummi ce a guje rike da wayar sai Ansar a bayanta da alama so yake ya kwace wayar. "Mommy an kiraki! Ansar ne ya dau wayar." Ta karɓa tana bugamishi harara ya shiga ƙaryata Ummin. "Kul! Kar ka ƙara. Duk ku fice daga dakin toh." Sum sun suka fita, har wayar ta katse, kafin ta kai ga duba sunan mai kiran an ƙara kira. Ƙurawa fuskar wayar ido ta yi, Hilal? Ta dauka da s🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 02) "Haba Ƙanwata, sai an ga dama za'a amsamin kenan? Sarautar ta motsa." Ya yi maganar cikin shaƙiyanci, ta yi dariya. "Wane mutum. Kawai dai bana kusa kafin na ƙaraso ta katse. Ina wuni Yaya Hilal." Ya amsa cike da fara'a kafin ya ce. "Zan amsa amma fa har yanzu ke mai laifi ce a wurina, kaf gidanku an zo ganin Babyna banda ke, ga shi har gobe suna. Anya kin kyauta Ramla?" Ta rufe fuska da hannu daya tana murmushi kamar a gabansa. "Ban kyauta ba, amma In Sha Allah zan wanke laifina, zan zo washegarin suna." Da dariya ya amsa. "Toh Alhamdulillah, haka nake son ji. Ya su Hajiya?" "Sunanan lafiya." "Ki gaidamin su sosai." Ta amsa da toh sannan suka yi sallama. Ba ta zurfafa tunani ba ta mike ta fita dakin gudun matsawa kwakwalwar da tunani. *** Ranar Lahadi, misalin ƙarfe biyar na yamma, ita kadai ce a gidan, Hajiya ta je babban gida, gidan iyayenta ita kuwa A'isha ta wuce da yara gidan Anti Zulaihat za'ayi birthday din ƴan biyunta, daga can za ta biya ɗaukarsu. Ta fito tsaf cikin atamfarta V.I.P Holland kalar coffee da ratsin ja, an mishi ɗigo ɗigon milk. Dinkin riga three-quarter akai mata sai straight skirt. Ta yafa jan mayafinta madaidaici, ba wani kwalliya ta yi ba, gida kadai ta shafa da man leɓe marar kala. Takalminta mai ja da baƙi, flat. Daga haka ta dau jakarta mai kalar takalmin sai kuwa mukullin mota ta fito. Motarta sai sheƙi take an wanke mata tas. Murmushi ta yi sa'ilin da ta shiga ta ga hatta da komai an na ciki an goge. "Wani aikin sai Nasiru." Ta furta cike da jin wani dadi. Hakanan ta tashi da wani irin farin ciki a yau, bai wuce nasaba da zuwan Yayanta Munir da kuma irin rahar da suka yi wanda an dade rabon da ayi din har take ce mishi za ta sunan Hilal ya yi murmushi. Wannan ya sanya a hanya ta kunna waƙar Hamisu Breaker mai taken So dangin mutuwa. Kalamansa suna ratsata, ga sanyin Ac na shiga dukkan wata ƙofa ta ilahirin fatar jikinta. Gaba daya waƙar na shigarta har tana jin kamar ta zubar da hawaye. Abubuwa da dama sun tsayamata a rai, ta kasa ciresu. Har dai ta tsaya a katafaren shagon Yayansu Munir a yanzu, Alheri Store, ba ta bar tunani ba. Shiga ta yi ta siya kayan jarirai komai pink bayan sun gaisa da mutan shagon sannan ta ja motarta. Har ta iso unguwar Lamiɗo Crescent waƙar take ji, daga ta ƙare sai ta tariyota. Ba ta ji faduwar gaba ba sai da ta ganta a ƙofar gidan Hilal Maigadi ya budemata ƙaton ƙyauren ta shiga. Duk wani sauye-sauye da gidan ya samu, hakan ba zai sa ya ɓacemata ba. Ta ya za ta mance ranar da komai ya samo asali? Dakyar ta samu nutsuwar saita tunaninta, ta faka motar a inda ya dace, ba ta san tarbar da za ta samu daga matar gidan ba. Abu daya ta sani, saboda Hilal ta zo. Ba kuma za ta fasa shiga ba koda hakan na nufin rusa farin cikinta. Falon farko ba ta tarar da kowa ba sa'ilin da ta yi sallama, sai kuma mai aikinta ta fito daga kicin tana amsawa. Bayan sun gaisa da fara'a take sanarmata ta ƙarasa falo na biyu, suna ciki. Ta yi godiya ta sanya kai. Tana tafe tana karewa gidan kallo, abubuwa da dama suna dawowa kwanyarta. Tashin muryoyin da ta ji ya bata tabbacin ba matar gidan kadai bace. Sallamarta ta dauki hankulansu. Wadanda ta gani zaune ya sa ta daukewar wucin gadi. Meyasa da ta fito daga gidansu da nishadinta, ba ta zarce kai tsaye gidan Yayarta Zulaihat ba? Meyasa ba ta ji shawarar A'isha ta ƙi zuwa ba? Sai dai kuma ta faru ta ƙare, an yiwa mai dami ɗaya sata. "Toh fa, wata sabuwa inji ƴan caca. Ramlah, dama ana ganinki? Duniya mai yayi." Maganar ta fito daga bakin wata kakkaurar mace dake zaune kusa da Anti Bilkisu Matar Munir. Ta daure ta ƙaraso ciki tana yaƙe, sai da ta zauna ta gaishesu. Suka amsa ciki-ciki. Ta maida kai ga mai jego da tun ganinta ta sauya fuska. "Sannu Fa'iza, Barka mun samu ƙaruwa, Allah Ya rayamana Amal." Ba wanda ya amsa sai Anti Fareeda wacce ta soma magana, itama tana wata ƴar dariyar shaƙiyanci. "Amma dai Munir bai san za ki zo ba?" Tambayar da Bilkisu ta jefomata kenan. Ta yi mata duban rashin fahimta. Sai kuma ta fasa magana. "Ramla, ya hakuri? Ashe kuma kin samu kanki dakyar. Naji ance har dukanki yake. Allah dai Ya gafartamasa." Wannan karon Anti Murja ce. Su hudu ne a falon, da Fareeda sai Murja da Bilkisu sai kuwa Fa'iza mai jego. Maganar Murja ta daki zuciyarta. Ta kasa hakuri, kafin ta tanka Anti Fareeda ta cafe. "Kee Murja, idan dukan ne ma ai da sauki. Kedai kawai abar kaza cikin gashinta. Dama shi alhaki ai kwuiwuiyo ne, kadan kenan. Da sauran rina a kaba, yanzu ba gashinan ana girbar abinda aka shuka ba." Dukkan zantukan suna shigarta, ta kuma san baƙar suke jefamata, dama ba mai hakurin bace, sai dai yanzun dole ta koyar da ita hakurin da kauda kai. Don haka a gaggauce ta miƙawa Fa'iza ledar. "Gashinan ba yawa Fa'iza. Allah Ya rayamana ita. Ni zan tafi." Ba wanda ya amsa wannan karon, tana dab da ficewa ta ji Bilkisu na fadin. "Ki bi dai a hankali Fa'iza, don wallahi wannan karon daga ke har mijin za ta iya rabaku da numfashinku, don ga dukkan alama zawarcinsa take." Ta tsaya cak gami da juyowa, idanunta kadai idan ka kalla za ka fahimci ranta a mugun ɓace yake. Kamar ta tanka sai kuma ta haɗiye ta yi musu jam'in kallon su din banza da ido kafin ta fice ta bar Bilkisu na daga murya da fadin ta zo ta shaƙeta tunda ba ƙaramin aikinta bane. A miliyan ta bar gidan, sai da ta ɗan yi tafiya mai nisa kafin ta faka a ƙasa wata bishiya kusa da wani mai katin waya, ta kusan awa a wurin tana jinyar kirjinta dake zafi, dakyar ta shiga ambaton Allah sannan ta samu karfin gwuiwar soma tafiya, har da taimakon Allah ta koma gida lafiya. Kai tsaye ɗakinta ta shige ta rufe gam da muƙulli. Zubewa ta yi saman gado ta shiga rera kuka. Sai da ta jiƙa rigar filonta jagaf sannan ta ɗago tana mai dafe kai da goshi. Kukan dai ba ta fasa ba. _'Wace irin ƴa na haifa? Rabi'atu wace irin ƴa kika haifamin?! Anya ba'a yimin musanye a asibiti ba?! Don ina mamakin kasancewar Ramlatu jinina!'_ Ta kara fashewa da kuka tunano kalaman mahaifinta ranar da ta koma gida bayan iyaye da yan uwan da suka miƙata gidan miji basu jima da watsewa daga gidannasu ba. Kiran da ya shigo wayarta ne ya dauki hankalinta. Ta kai duba, Hilal ne. Ta yiwa sunansa ƙuri kamar yau ta soma gani. Lambar ba baƙuwa ce a wurinta ba don kusan tun sadda suke tare ta sanshi da ita. Ina za ta mance soyayyar da suka yi wanda a karshe lamura suka sauya? Ba ta kai ga amsa wayar ba har ta katse zuciyarta ta tafi ga tunanin farkon haɗuwarta da shi. *** Katafaren hall din na Aseem Event Centre ya cika da mata da maza har ma da yara tsiraru kasancewar ranar ake dinner party na Munir Khalid Mu'azzam da Bilkisu Tijjani Dutse. Anko kam an yi shi na wani French lace kalar blue mai kyau. Kannen Ango su huɗu cif sun fito a nasu ankon na daban. A lokacin Zulaihat kadai ce ta yi aure a cikinsu sai Rafee'ah dake da sanya rana a kanta. Kwalliyar wani arnen lace peach suka yi, karshen kyau ƴaƴan Hajiya kam sun yi shi. Duka-duka A'isha ba ta wuce shekaru goma sha biyu ba sannan sai dai ƴar lukuta suke kiranta tsabar ƙiba tubarakAllah. Duk cikinsu Ramla ce baƙa, ita ta dauko kamannin mahaifiyarsu sak, don kaf dinsu mahaifinsu suka biyo. Baƙar fata ce ita, tana da matsakaicin tsawo. Surarta abin a kalla hakanan kyakkyawar halittar fuskarta. Duk da kasancewarta baƙa, sai a ɗauketa da gudu ba'a ɗauki ɗayansu ba. Fuskarta kadai ka kalla za ka tabbatar tana cike da farin cikin wannan rana. Ta dage sai rawa take tana zubawa Amarya da Ango kari, ta yi baya da zummar fita daga gurin za ta kaiwa Rafee'ah gulmar hararar da Munir ya jefamata sanin da ya yi murnar auren da biyu take, ba zato ta ji ta yi karo da mutum har yana kiran wayyo. Ta yi saurin juyawa ganin kansa a ƙasa ya riƙe yatsansa na hagu da ya sha taku a wurinta. Tsinin takalminta ya ji mishi ciwo a ƙafa. A gigice ta durkusa itama tana ganin yanda fatar wurin ta ɗan ɗago. Idanunta suka yi rau, ta dubeshi. "Don Allah ka yi hakuri." Da rawar murya ta ƙarasa zancen sakamakon faɗuwar gaban da ta ji lokaci guda ganin irin kallon da yake mata kamar zai cinyeta. Ya mike tsaye itama ta mike, fita ta ga ya yi daga tsakiyar filin zuwa kujera, kafar ya daga yana duba. Ta karasa sadda wani a gefensa ke mishi magana don ba ta san me yace ba dalilin ƙarar kiɗa da ta cika wurin. "Don Allah ka yi hakuri wallahi ban lura ba." Jin muryar a saitin kunnensa ya sa shi ɗago kai ya dubeta, ganin kusancin ya yi yawa sai ta ɗaga kai, ta yi da niyyar ya ji abinda ta ce saboda kiɗan kan iya hanawa ya ji din. Murmushi ya sakarmata wanda ya kara fiddomata da kyawunsa. Fari ƙal, ga dukkan alamu dai bai saba da wata aba wahala ba. "Kar ki damu, amma sai kin biyani." Ta zaro ido sai kuma ta karyar da wuya gami da marairaicewa. "Ta yaya? Don Allah ka yi hakuri." Wayarsa ƙirar Motorolla ya zaro ya miƙamata. "Sanyamin lambarki." Ta saci kallonsa tana murmushi ƙasa-ƙasa. Shima tuni ya mance da zafin da yake ji a ƙafar ya shagala da kallonta. "Sai dai ta Landline din gidanmu." "Ba matsala a sakamin." Murmushi bai bar saman fuskarta ba ta karɓa ta sanyamishi. Ya karɓi wayarsa fuska a sake. "Ya yi kyau, wane suna zan sanya?" "Ramlat." Ta furta kai tsaye, ya maimaita yana murmushi za ta bar wurin ya dakatar da ita. "Ba ki tambayi sunana ba." Ta waigo tana dubansa. Ya ƙuramata ido kamar ya cinyeta. "Hilal, Hilal Aminu Dutse, amma zan so ki raɗamin My Future Husband." Tana murmushi ta bar wurin da saurinta har tana tuntuɓe sakamakon kunyar da ta kamata. Haka ta koma mazauninsu. Duka ta ji an kai mata a baya, ta kalli mai shi, aminiyarta wacce suka taso tun firamare tare har zuwa yanzu da suke Sakandire aji na hudu, Amrah Abdullahi. Ɗaga gira ta yi tana dariya. "Na fa ganki da wani haɗaɗɗen guy. Wato dai su Kb kika rainawa wayo da kike hanasu lambar waya." Ta harareta da murmushi dauke saman fuskar, Kb wani yayan wata ƴar ajinsu ce, a makaranta ya ganta yake so, sai dai ta ce sam bai yi mata ba. "Ke kam wa ya fadamaki soyayya muke? Shikenan ba dama ku gaisa da mutum sai cibi ya zama ƙari?" Harararta Amrah ta yi. "Aikin ɓurr, faɗawa wanda bai sanki ba. Matar da gaisuwar ma ba ki damu ki yi da wani namijin ba. Lallai ma, an gaisheki toh. Idan ta yi wari na ji." Ganin yanda take neman yin fushi ne ya sanyata riko hannunta tana dariya. "Haba tawan, ai kema kinsan ya wuce ace sai ta yi wari kya ji. Ba fa wani abu bane." Nan ta bata labarin Hilal, suka dinga dariya ta ɗora da fadin. "Amma wallahi ya kwantamin, ko ba komai yana da kyau kuma da alama dangin Amarya yake. Nidai ina sonsa." "Saboda shi son ba shi da wuya ko Ramsy?" Ta kirata da sunan da suke fadamata a makaranta. Ta zubamata dara-daran idanunta, kafin ta kara satar kallon Hilal wanda ga mamakinta wajen da take ya ke kallo. Murmushi ya sakarmata ta yi saurin juyar da kai numfashinta na harbawa da sauri. Amrah na lura da su, banda murmushin itama ba abinda take zabgawa. "Na yarda Ramsy kin harbu. Allah Yasa ya zamemaki alheri. Farin cikinki, shi ne nawa." Ta ɗago ta dubeta duba na kaunar ƴan uwantaka da amincin dake tsakaninsu. "Ameen tawan. Kina son abinda nake so, shiyasa nima nake ji da ke." Suka murmusa sannan suka ci gaba da shagalinsu. A daren bayan komawarsu gida ta shiga wanka. "Ramsy! Tun dazu fa wani wai shi Hilal ya kira yana nemanki, yanzun ma ina tunanin shi ne." Ai da sauri ta watsa ruwa ta ja zani ta fito gudun kada wani a sashin Hajiyarta ya dauka. Suka dubeta suna dariya ganin kumfa a kafaɗarta ta dama da kuma ƙeyarta. Ta fisge kan waya a hannun ƴar uwarta da suka zo daga Daura, Naja'atu. Sai dai ganin fisgewar ta janyo kan wayar gaba daya daga saman tebur. Ta ja guntun tsaki. "Ke Ramla, wai hala sabon kamu kika yi?". Fadin Najaatu. Harara ta bugamata. "Yo ke Naja sai an hwaɗi maki? Ai gahi kina gani." Cewar Sa'adah. Itama dai daga Daura ta zo. Ita dai Ramla gaba ta yi zuwa banɗaki ta bar su suna mata shaƙiyanci, ba ta kai ga abinda ta yi niyya ba, wayar ta ƙara ringing, da sauri ta fito suna mata dariya ta ɗaga. "Assalamu alaikum." Ta furta har muryar na ɗan rawa. Ya amsa mata sannan ya ce. "Haba don Allah, wallahi ba ki ji yanda gabana ya shiga faɗuwa ba duk a zatona halinku na mata ki ka yimin. Wato dai na dauka wrong number kika ban." Ta dan lumshe idanu sannan ta bude tana murmushi, su Najaatu sun tsuramata ido kuwa, ganin haka ta juyamusu baya. "Kiyi magana ko hankalina zai kwanta don Allah." "Ka yi hakuri, bana kusa ne." Ta ji ya sauke numfashi. "Alhamdulillah. Na kasa samun nutsuwa Ramlat, yanda nake jinki a raina tun daga haɗuwarmu zuwa yanzu, jikina yana bani kece mahaɗin rayuwata. Don Allah a amshi Hilal da hannu bibbiyu. Kinji?" Ba karamin dadi kalamansa suka yi mata ba. Tana murmushi ta amsa. "In Sha Allah." "Hakan na nufin?" Ya nemi sani. Ta gyada kai kamar yana kallonta. "Na karɓa." Hamdala ta ji ya yi yana zuba godiya har ya bata dariya. Sai kuma hira ta ɓarke. Nan yake fadamata shi din cousin din Bilkisu ne. Mahaifinsa Alhaji Aminu, yaya ne ga Alhaji Tijjani mahaifin Bilkisu. Su mazaunan unguwar Goron Dutse ne. Ya hada Degree dinsa a fannin Accounting, yanzu haka kuma yana shirin zuwa Malaysia haɗo Masters. Ta nutsu tana jin jawabinsa, a karshe ya dora da fadin. "Tsakani da Allah nake sonki, kuma da aure. Ba don karatun ya zama dole ba, da sai ince a dauran auren kawai na wuce da ke Malaysia. Toh na tabbatar kema ɗalibar ce kamar ni, ko kuwa?" Suka dan dara, har cikin ranta take jin ya kwanta mata dari bisa dari. "Toh yanzu dai nima sai ki biyani bashin labari. Fadamin tarihinki." Ya buƙata. Ta fayyace mishi asalinsu da kuma matakin karatunta a yanzu. "Nayi murna da samunki My Future, kuma ina ji a jikina kece matata da yardar Allah. Muyi fatan Allah Ya cikamana burinmu. Kafin na tafi zan iya kawomaki ziyara?" Ta kasa cewa komai din farin ciki, sai dai kuma tana shakkar Yaya Munir ya ji labarin ta soma tsayawa hira da wani namiji yanzun. Don haka ta girgiza kai. "Ka bari da kaina zan gayyaceka gidanmu. Ka ji?" Yanda ta ƙarashe zancen a shagwaɓe ya haddasar mishi da wani yanayi mai wuyar fassarawa. Ya yi gyaran murya kafin ya samu kwarin gwuiwar amsawa. "Shikenan My Future, ni naki ne. A koyaushe kuma a kowane mataki na rayuwa da yardar Allah. Zan jiraki, ba kuma zan gaji da nayi ta jira har sadda Allah Ya so ba." Murmushi take dagaske. Son Hilal na kara kewaya dukkan ilahirin jikinta. Sun shafe awanni suna hira sannan suka yi sallama. Ta kai duba ga masu yi mata ɗan baki, wasu sun yi bacci yayinda wasu ke waya. Miƙewa ta yi ta maida kan wayar ta ajiye sannan ta faɗa banɗaki don ci gaba da uzurinta. *** Kamar da wasa, sabo mai tsanani ya shiga tsakaninta da Hilal, tun tana takatsantsan kada Hajiyarsu ta gane har dai wataran ta kama ta tana waya, Hilal ya kira lokacin Hajiya na kusa da wayar ta ɗaga. Kafin ta kai ga magana ta ji muryarta, ta yi mamakin jin kalaman soyayyar da ɗiyarta ke zabgawa. Karshe ta ajiye kan wayar ta leƙa ɗakin, tana tabbatar da ita ce din, kawai ta ja mata kofar. Idanun Ramla ya raina fata. Washegari da safe ta shiga kicin ta iske Rafee'ah na aiki. Tana ganinta ta yi kwafa gami da dariya. "Kin ɓallowa kanki ruwa yarinya, Hajiya ta ji ki kina waya da Hilal. Za ki yi bayani dallah-dallah." Ta ƙaraso gami da daga kafaɗarta idanu a waje. Rafee'ah ta ture hannun tana dariya. "Wallahi kar ki cinyeni kina kallona da wannan manyan idanunnaki kamar mujiya." Tsukke fuska Ramla ta yi, ba fada take nema ba, so take ta ji abinda Hajiya ta ce. "Don Allah Sister ki bari, me Hajiya ta ce? Za ta fadawa Abba?" Taɓe baki Rafee'ah ta yi tana tsamo dankali a cikin mai da cokalin girki. "Oho, kya dai yi bayani, dama na lura ko karatun da kika saba duk karshen sati kin wani rage saboda soyayya, ke ga Laila ko? Toh ai idan ta fadawa Yaya Muniru ya lakaɗamaki duka kin huta." Haushin Rafee'ah ne ya soma kamata, kawai ta juya bayan ta harareta ta fice daga kicin din. A falo suka yi kiciɓus da Hajiya tana taimakawa A'isha da tsifar kai tana mitar dama ita ba ta son kitso ya cika ƙanƙanta. Ganin Ramla sai ta daure fuska. Tun daga nan ta sha jinin jikinta. Ta karasa a sanyaye ta gaidata, maimakon ta amsa ta jefamata tambaya. "Da wa kike waya haka karfe taran dare?" Kirjinta na dukan tara-tara dakyar ta samu abin fada. "Wani ne." "Shi wanin bai da suna?" Ta girgiza kai, kafin ta amsa mata, Abba ya yi sallama ya shigo, cikin Ramla ya bada wani sauti ƙululu. Ta san Hajiya ta fi Abba rashin fahimta sosai sai dai tana da saukin kai lokuta da dama, shi kuwa Abba akwai tsauri akan hukunci wasu lokutan. Idan ya ce a'a, zai yi wuya ya dawo ya ce eh. Wannan tasa ta tsoraci ya kwace wayarta ya kuma rabata da Hilal har abada. Bayan an gaidashi, ya shiga yiwa Hajiya faɗan tsifa da safiyar Allah ko karyawa ba'ayi ba. Ta ba da hakuri sannan A'isha ta mike ta rufe kan ita kuwa ta fice wanko hannu. "Zo nan Ramla, meke faruwa ne ke da Uwartaki?" Ta mike ta ƙaraso ta zaune gefe sai dai ta kasa magana. "Jiya ta sanarmin ta kama ki kina waya wuraren tara na dare. Fadamin, wanene shi? Kuma a ina yake?" Da mamakin sauƙin kan da Abba ya nunamata ta sunkuyar da kai. Tiryan-tiryan ta shiga labartawa Abba wanene Hilal da kuma da niyyar da yake sonta. Ɗan hade gira Abba ya yi. "To shi haka ake neman aure? Meyasa ba zai soma yimin zancen ba? Sannan duka-duka a Ss1 kike yanzu Ramla. Kina zaton zan iya aurar dake yanzu? Ko kuwa kina ganin ya dace a cireki a makaranta ki yi aure yanzu ba tare da kin kammala ba? Inada burin naga kun yi karatu koda a gidajen mazajenku ne. Amma ban ce lallai ba, kuma a sanin da nayi maki kema kina da wannan ra'ayin. Me zai sa ki sauya?" Ta ɗago kai sai a sannan ta kalli Abba idanunta rau rau kamar wacce aka ce kar ta ƙara shiga harkar Hilal. "Abba dama ya ce yana son zuwa wajenka, ni ce ke tsoro. Kuma na fadamasa ni ba yanzu zan yi aure ba sai na kammala Sakandire." Murmushin manya Abban ya yi, ya lura dai diyartasa da alama soyayya ta sauyata. "Kin tabbata kina sonsa Ramlatu?" Daga yanda ya kira sunan ta tabbatar ba wasa. Ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya kara maimaita wa, ta gyada kai. Ya kara maimaitawa a karo na uku, sai kuma ta tsinci kirjinta da bugu da sauri-sauri. Ta ji wani gumi da ba ta san dalilinsa ba ya ketomata a goshi. Wani yanayi na sanyin jiki ya mamayeta. Ta daure ta yakice nauyin da bakinta ya yi a lokacin ta amsa da "Eh Abba." Sai ta ga ya yi murmushi har haƙoransa suka bayyana. "Shikenan, ki ce ina son ganinsa gobe." Da toh ta amsa sannan ta mike ta yi daki tana jin muryar Rafee'ah dake jera kwanuka saman ledar cin abinci na mata dariya. Jikin kofar dakinnasu ta jingina, wasu hawaye ta shiga fitarwa da ba ta san asalinsu ba. Damuwa ce ko akasinsa? Murna ce ko bakin ciki? Babu daya da kwakwalwarta ta buɗamata. Wayar ta nufa ta kirashi, ya kuwa dauka ta sanar mishi abinda Abba ya ce sannan ta ajiye wayar ta koma falon. Ana cin abincin amma jikinta a sanyaye yake, abin mamaki sai sannan ta ga sakin fuskar Hajiyar, ba ta san dalilin fushinta a farko ba. Amma ta san dalilin sakin fuskar yanzu na murnar hukuncin Abban ne don har Rafee'ah na tsokanarta bayan fitar Abba akan za ta yi kewarmu. Tana fadin Autarhttps://my.w.tt/ub8deMQ0g9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 03) "A farko nayi tsammanin irin samarin zamanin nan ne masu hurewa ƴanmata kunne da zantukan banza da dare. Sai kuma da naji ko waye, naga ashe na gida ne. Toh Allah Ya tabbatarmana da alheri." Hajiya ke koro wannan bayanin sa'ilin da Ramla ke gyaramata gado ita kuwa tana gaban madubi tana goge jiki ta fito daga wanka. Murmushi Ramla ta yi ta kara maida kai ga aikinta. "Allah kuwa Hajiya ba ruwansa. Kuma fa yace zan karasa karatuna." Abin ya sanya Hajiya dariya. "Ai shikenan ƴar nema, Allah Ya sanya alheri." Ta amsa a zuci tana dariyar itama. Hilal ya zo suka yi magana da Abba, sosai yaron ya shiga ransa. Karshe ya ba shi iznin zuwa hira sai dai ya ce ya kasance jifa-jifa saboda ɗaliba ce. Ya kara da mishi iznin turo magabata a tsaida ranar biki. Wannan magana ta fi kowacce yiwa Hilal dadi. Ya dinga godiya. Karshe suka dan taɓa hira da Abba cikin barkwanci, koda zai wuce Abba ya hanashi akan lallai ya tsaya ya ci abinci. A kunyace ya ƙaraso cikin falon. Tana zaune tare da Rafee'ah a falo, sai ganinsa suka yi. A guje ta mike ta nufi daki don sanya hijabi, ita kuwa Rafee'ah me za ta yi banda dariya. Ya zauna suka gaisa tana fadin. "Masha Allah Angon ƙanwata. Allah Ya sanya alheri." Cike da jin dadin wannan maganar ta Rafee'ah ya amsa yana shafa keyarsa. Abba ya shigo tare da Hajiya sanye da mayafi. Cikin girmamawa Hilal ya kwashi gaisuwa sannan suka dunguma saman ledar da tuni Rafee'ah ta haɗa komai na abincin dare. Abba ya shiga wulga idanu. "Ina ita Ramlar? Auta kiramin ita maza." A'isha ta mike da sauri ta nufi hanyar dakinsu. Daidai nan Yaya Munir ya yi sallama, a bayansa Amaryarsa Bilkisu. Hangame baki Yaya Munir ya yi ganin Hilal, shi kuwa sunkuyar da kai ya kara yana dariya ƙasa-ƙasa. Bai mancewa gidansa ya soma zuwa suna ƙusƙus da yar uwarsa Bilkisu game da zuwa ganin Abba. Koda ya tambayi wane Abban, sai ya bagarar yana fadin idan ta yi wari zai sanarmishi. Wannan ta sanya Munir kallon Bilkisu, ta yi mishi dariya cike da kunya ganin idon surukan a kansu. Ya dauke kai bai ce komai ba suka ƙarasa. A wurin cin abincin yake jin abinda ke wakana tsakanin kannennasa. Murmushi kawai ya yi gami da fatan alheri. Ajiyar zuciya Ramlat ta yi don ba haka ta zata ba. "Kin ci sa'ar Yaya Munir, da alama dai giyar soyayya ke kwasarsa. Ba ki ga yanda yake nan nan da Anti Bilkin ba. Amarya ba ta laifi." Zantukan Rafee'ah ya sanyata dariya. Hararar da Yaya Munir ya watsomusu tamkar ya ji abinda suke tattaunawa shi ya sanyasu nutsuwar dole. Bayan tashin iyayen, Yaya Munir ya dubi Hilal. "Kai wato abin ƴar rufa-rufa ce ko? To gashinan ai ya fito fili. Allah Ya sanya alkhairi." Hilal ya murmusa yana satar kallon masoyiyartasa. "Ameen Yayanmu." Dariya Anti Bilkisu ta yi gami da riƙe haɓa. "Oh ni, yau Mami ta zo ta ga autanta a gidan surukai." Ya ɗan harareta don koda ta girmeshi da kaɗan, shi har yau bai ma yarda ta girmeshi din ba. "Toh ke wa ya sanyamaki ido wai? Kuma ai ta san da zancen. Ni yanzu dai gaskiya a bani aron my wife to-be mu ɗan yi hira." Ai Ramla ji ta yi kamar ta nutse. Ta kasa cewa komai, bayan sun keɓe da Hilal ya zubamata idanu kamar ya hadiyeta. Kunya ta kamata ta sanya tafukan hannunta ta rufe fuskar. "Wai me? Kunya ko? Na ci alwashin kawar da shi wataran. Ko ince nan ba da jimawa ba da yardar Allah. Yau fa ina cikin farin ciki." Ta sauke hannun tana murmushi. Ya nuna ta da yatsa. "Ko ba ki faɗa ba nasan kema hakan ne." "Yaushe ne tafiyarka?" Ta sauya akalar zancen. "Nan da sati biyu in Sha Allah. Zan fa yi kewa. Kinga da kin kammala zan iya tafiya da ke kawai." "Gwara da ban kammala ba kenan." Ya ɗan fiddo ido. "Au bakya kaunar ki bi ni? Kin fi so muyi nesa da juna kenan." Girgiza kai ta yi. Sun ɗan jima suna hira sannan suka yi sallama ya wuce don dama ya yi sallama da mutan gidan. *** "Kin tsaida Hilal matsayin mijin aurenki. Kar na ji ko kuma na ga kin tsaya da wani saurayin koda wasa. Duk wanda ya nuna yana sonki, ki ce an miki miji. Sannan banda yawan waya, muddin naga kin rage maida hankali a karatu da kaina ba saƙo ba zan amshe wayar har sai kin zana SSCE. Kin ji ko?" Kirjinta ke wani irin bugu, ta ɗago ta dubi Yaya Munir, fuskarnan tamkar bai taɓa dariya ba. Daga ita sai shi a hanyar barandar fita daga cikin gidan, kiciɓus suka yi yayinda yake shirin fita. Ta gyaɗa kai. "Magana za ki yi da bakinki." "Naji Yaya, zan kiyaye in Sha Allah." Sai sannan ta ga murmushinsa har abin ya bata mamaki. "Shikenan." Abinda ya furta kenan ya yi gaba, ta bi bayansa da kallo kafin ta soma tafiya zuwa falon jikinta a sanyaye. Tana shiga nan ma Bilkisu da Rafee'ah suka yi mata ca da tsokana, nan take Rafee'ah ta kira Zulaihat ta fesa mata. Abin ya mata dadi itama sosai ta kuma yi musu fatan alheri. *** Sati daya da wannan zancen, aka kawo kudin sa rana da karamin akwati daga gidan su Hilal. An sanya shekaru biyu da wata uku wanda ya yi daidai da sadda za ta kammala sakandire. Amrah a gidansu ta wuni ranar suna murna. Sai dai jikin wacce ake tayawar a sanyaye. "Wai ke mene duk kin yi wani sanyi kamar ba ke ba?" Fadin Amrah. Ta yi saurin riƙo hannun Amrah din ta ɗora saman kirjinta. "Kin ji yanda yake bugu, bansan dalili ba. Tun soma maganar aurena da Hilal gabana ke faɗuwa, ki tayani addu'a Amrah." Murmushi Amrah ta yi. "Kar ki wani damu wallahi, kawai dai baƙon al'amari ne kike ji saboda zancen auren. Kinsan kowace mace dole ta ji sauyi idan aurenta ya taho, ko kin manta Anti Zulaihat da kika ce ita har kuka tayi ranar sanya ranarta?" Ta gyaɗa kai tana jin wani sanyin dadi, hakane fa. Ta yi murmushin samun nutsuwa kaɗan. Misalin hudu da mintuna na yamma ta sanya mayafin abayarta, fitowa ta yi da zummar takawa Amrah ta hau tasi. Ba tare da sanin kaddarar da ke bibiye da fitowar ta a daidai wannan lokacin ba. Suka miƙa suka fito daga lungun gidan zuwa babban titi, hirarsu suke sha har da dariya. Wannan fitar ita ce Mafarin komai. Ita ce silar soma shigarta cikin dukkan matsalolin da take fuskanta a yanzu. *** Buga ƙofar ɗakin da ake yi ba kakkautawa ya katse dogon tunanin da ta faɗa. Ta ajiye wayar hannunta wanda Hilal har ya gaji da kira ya hakura ya yi text, nan ma ba ta samu damar budewa ba. "Wai Ramlatu bakya ji ne? Me kike yi haka?" Jin muryar Hajiya ya sanya ta saurin miƙewa jiri na kwasarta. Murya a dusashe ta amsa. "Ganinan Hajiya." Ta karasa ta budemata ƙofar. Hajiya ta yi mata ƙuri da ido tana kallonta. Kafin ta yi kwafa. "Duk wanda bai ji bari ba, ai zai ji hoho. Haba Ramla, na ce miki karki je gidannan amman taurin kai irin naki da har yau kika kasa yaƙarsa ya sanya ki takawa gidan Hilal. Taurin kan da ya kamata a yanzu kin hankalta cewar halaka ce ga dukkan wani dan adam. Koda dai, ke za ki bada labari. Gashinan ai kin je kin jiyowa kunnuwanki. Ai tunda Muniru ya ce Balki ma za ta ni nasan ba za'a ƙi gasamaki mai zafi ba. To madallah, sai ki gama kukannaki ki fito ki damamin koko na sha magani. Ya yi kyau." Da haka Hajiya ta fice ranta a ɓace. Ramla ta yi shiru, shakka babu kam ko me aka yi ita jazawa kanta. Sai dai kuma ya za ta yi ta watsawa mutumin da d Ta koma ciki ta faɗa banɗaki bayan ta rage kayan jikinta. Wanka ta yi sannan ta fito ta sanya kaya. Sai da ta kwashe mayafi da jakarta da ta cillar a tsakar ɗakin sannan ta ɓalli Paracetamol ta fito. Hajiya na zaune a falo tana kunce garin magani, tana ji tana yiwa Talatu bayanin maganin, wai na ciwon ƙafa ne ta samo wurin Hajja. Kicin ta shiga ta sha maganin kafin ta hau kiciniyar dama kokon. Sai da ta kammala ta fito ta ajiyewa Hajiya, itama ta ɗiba ta sanya sugar ta soma sha. "Yarannan basu dawo ba." Harara ta samu daga uwartata, kafin ta amsa. "Waye zai je daukosu?" Sai sannan ta tuna cewar ashe ta ce za ta biya daga gidan Hilal su taho gida. "Sai ki kokarin zuwa daukosu, na riga da na sallami Haladu sai gobe zai zo." Ta amsa da to gami da duban agogon dake manne jikin bangon falon. Karfe shida da mintuna, magriba tana kan hanya. Tana jin Hajiya na yiwa A'isha waya akan kar su sake su taho a ɗan sahu, gatanan zuwa ɗaukarsu. Ba ta yi mamaki ba sanin da ta yi ko da can Hajiya ba ta fiye son shigarsu abin haya ba idan magriba ta wuce. A gaggauce ta shanye kokon ta nufi daki. After dress blue mai kauri ta dora saman doguwar rigarta ta dau wayoyi da mukullin mota ta fice. Hajiya ta bi bayanta da kallo, a kullu yaumin tana tausayawa rayuwar Ramla, matsalolinta sun girmewa shekarunta a nata tunanin. Sai dai kuma Allah Ya fi ta sonta. Ta yi nisa don har ta hau titin unguwar Zulaihat, ƙarar wayarta ta dauki hankalinta. Ganin ta ƙi yankewa ne ya sanya ta dauka. Murmushi wanda ya fi kuka ciwo ta yi. Shi wata irin halitta ne na daban mai halayyar ƴan aljannah. Da ace kirki na yawa, za ta iya auna irinnasa a wannan mizanin. "Assalamu alaikum." Ta furta a tausashe a lokaci guda tana hankalta da yanda take sarrafa sitiyari. Ajiyar zuciya ya soma saki kafin ya amsa. Bai ko bari ta gaidashi ba ya dakatar da ita a ƙagauce. "Shi kuma wannan aljanin ya sunansa ne Ramlat? Na fa gaji da yaƙarsu. Kimin rai ki daina zafafawa wurin yanke hukunci mana." Ta yi murmushi mai sauti. "Kar fa ka dauki hakkin bayin Allahn da basu da laifi. Ka yi hakuri na amsa laifina." "Shikenan na hakura, kuma kema ina mai ba ki hakurin. Na ji hayaniyar ababen hawa, ko.." "Ina hanyar gidan Anti Zulaihat, zan dauko yara." Ta katseshi da hanzari kusan hankalinta ya tafi gurin cunkoson da ta hanga dab da ita. Ta ja burki ta tsaya sa'ilin da Hilal ke mata fatan sauka lafiya da kuma sallama. "Nagode." Ta furta tana ajiye wayar gami da kara kallon mutumin da fitilun mota da mashin suka taimakamata da ganin fuskarsa. Dogo ne kuma mai madaidaicin jiki. Idanunsa rufe da bakin gilashi yayinda ya zuba hannuwa cikin aljihun cotton din wandonsa da aka rubuta Adidas a gefe. Rigarsa mai hula sai dai bai rufe sumar kansa da ita ba, fararen kafafun cikin bakin silifas, ya fita daban da ruwan tokar shigarsa. Ta kai duba ga inda hannunsa ya taɓa a jikin motar, ba kalar ta rannan ba ce, wannan wata ce maroon in colour, tana da tudu ba kamar waccan ba. Shakka babu an yi mata wawan karta. Matsakaicin bakinsa yake motsawa yana magana, ba alamun wasa a fuskarsa. Kunnuwanta suna iya tsinkayar kaɗan daga abinda wani ke fadi cikin mutanen gurin don kuwa shi ba ta samu damar jin nashi sautin ba. "Tunda har ya ba ka hakuri don Allah ka yi hakuri Yallaɓai, nayi amannar ba shi da abin biyanka wannan ta'asa. Don Allah ka yi hakuri." Buga bayan motarta da wani ɗan Karota ya yi gami da fadin. "Hajiya muje mana!" Ya yi sanadin da mutumin kallo inda take, ko da ace akwai gilashi a idanunsa, tabbas ita din ta ga alama yake kallo, da azama ta dauke kai ta ja motarta tana mai jin faɗuwar gaba. *** Jin sallamar Maminsu ya sa duk suka rugo a guje suka rungumeta har twins din Anti Zulaihat. Tana dariya ta turesu ta zauna a kujera mafi kusa da kofar falon. "To nikam a kyaleni kar a faɗar da ni don Allah." "Kuma fa tsaf zasu iya faɗar da ke din, don yanzu ba wani nauyi za kiyi ba." Cewar Anti Zulaihat, Ramlat na dariya ta dubeta. "Kai Anti. Happy Birthday my twins." Ta fadi tana ture Affan wanda ke kokarin hawa cinyarta ta kamo hannun Hassana da Hussaina. "Kai Sis kamar ba za ki zo ba? Kada dai a gidan Hilal kika wuni." A'isha ta ƙarashe cike da zolaya don ta ji ƙishin-ƙishin an gumamata a gidan daga bakin Hajiya. Harararta ta yi ta kauda kai. "Kema kinsan za'a rina ai wai an saci zanin mahaukaciya. Gobe ma kya kara." Itama Anti Zulaihat ta ƙara iza wutar ɓacin ran a zuciyarta. "Allah Shaida na je domin Hilal, kuma duk abinda mutum ya yi don kansa. Can ta matse musu." Taɓe baki Anti Zulaihat tayi tana murmushi sai dai ba ta ƙara magana ba ganin mijinta ya shigo. Ramla ta gaidashi. Dr Shareef ya amsa yana kokarin zama. "Ramlatu manyan ƙasa masu kuɗin gwamnati, ke dai ganinki wuya yake. Yanzun ma nasan yaranki kika biyo." Ta yi dariya kafin ta amsa Zulaihat ta cafe. "Aa toh, ashe Abban Khalifa ka gane. Ai karfi da yaji ta maida kanta wata kifin rijiya, yanzu daga Ofis sai gida. Allah dai Ya kyauta." Murmushi ya yi. "Aure zamu yi mata mu huta ai. Allah Yasa ma wanda za ta aurar ya hana aikin gaba daya mu ga yanda za ta yi." Ya ƙarashe cike da barkwanci. An zo gaɓar da ba ta so, wannan ya tilasta mata miƙewa tana duba agogon dake manne a bangon falon. "Nidai bari mu wuce, Hajiya ba ta kaunar tuƙin dare." "Ahaf, ai daga an dauko batun aure sai ta sauya akalar, toh ma ga iya gudun ruwanki. Ba inda za ki je." Fadin Zulaihat. Ita dai ba ta tanka ba sai kallon da ta watsawa A'isha dake dariya sannan ta yi gaba tana yi musu sai da safe. Har bakin motar Zulaihat da yaranta biyar suka musu rakiya. Ta rankwafo saitin Ramlat. "Malama akwai muhimmiyar maganar da zamu yi. Idan ma ba ki samu shigowa ba Ni zan shigo gidan." Ta dan dubeta fuska a yamutse. "Allah Yasa zancen gizo wannan karon ta bambanta da ta ƙoƙi." Harararta ta yi. "Idan ma ta zama daya ya zama dole ki bi, ba ki da zaɓi. Ko ma mene idan muka tashi yinta za ki ji. Sai da safe ku gaidamin tsohuwata." Daga haka ta kama hannun yaranta suka koma ciki, twins na kuka akan a bar musu su yaran su kwana. Su kansu ba da son ransu ba sai dai makaranta ta share dukkan son ransu.https://my.w.tt/ub8deMQ0g9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 04) *** *ADAMAWA* _*ALHASSAN AMINU*_ Ya kai tsawon mintuna uku tsaye a falon sai dai nisan da ta yi a tunani bai sa ta hankalta ba. Dattijuwa ce da za ta yi kimanin shekaru sittin a duniya. Ya daure ya kara maimaita sallamar, sai a sannan ta ɗan yi firgigit ta dubeshi da amsa tana kokari kauda kai da share fuska. "A'a, Biyu? Yaushe ka shigo? Sannu." Ta furta duk a lokaci guda, ya karasa bayan ya cire bakaken silifas din ƙafarsa ya durkusa gabanta gami da riko hannunta. "Ya isa, ya isa haka don Allah Dada. Har yaushe za ki ci gaba da damuwa akan abinda ba'a hannunnu yake ba? Addu'armu ita ya fi buƙata. Kiyi hakuri, akwai ciwo, sai dai mun yi imanin komai yana da lokaci." Ta dubeshi, ta girgiza kwarai ganin yanda ruwan hawaye suka ɓata ɗan farin gilashinsa har suka biyo saman fuskarsa. Hannunta ta zare ta cire mishi gilashin gami da dauke hawayen da tafin hannunta. "Sau da yawa wasu abubuwan fin ƙarfin zuciyoyinmu suke. Rauninmu ya sa bamu da karfin aiwatar da abubuwa da dama. Nauyinmu yakan rataya a wuyanku. Na daina, na daina Biyu, kar ka kara. Ganin kukanka damuwa zai ƙaramin. Allah Ya magance mana, Ya karkato da hankalin ɗan uwanka gida a duk inda yake rayuwa." Da murmushi ya amsa da Amin a hankali. Shi yana ji a jikinsa kamar da wuya ace dan uwannasa na raye duk tsawon wannan lokacin. Idan ma yana raye to ya manta da wanzuwarsu a doron ƙasa. "Ya su Fatima?" Ta tambaya cikin harshen fulatanci, ya maida mata amsa fuska sake, cikin son kawar da duk wannan damuwar. "Tana nan, gobe zan kawomaki ita ta yi miki sati ma." Nan da nan kuwa ta washe haƙora. "Allah Ya kaimu." Ya amsa da Amin sadda yake kokarin maida gilashinsa. "Ina waccan ƴar ƙauyen?" Murmushi Dada ta yi. "Ba ta jima da ficewa ba, ta raka Addarku gidan ƙunshi." Gyada kai ya yi, ya kawar da zancen da batun tafiyar da ta zo mishi zuwa Kano, ya kara da fadin. "Darakta ya ce na wakilceshi a wani meeting da za'a gudanar." Ta fadada fara'arta. "Sai ka karasa ka gaisarmin da Modibbo." Jin ta ambaci Modibbo ya sanya annurin fuskarsa raguwa. "Me hakan ke nufi?" Ya dubeta, shi take duba da son jin abinda zai fito daga bakinsa. Gane hakan ya sanyashi murmushin yaƙe. "Zan je in Sha Allah Dada." Ta yi murmushin itama "Allah Ya yi maku albarka. Ya yayemana damuwarmu." Ya amsa da Amin cike da tausayinta. Ta sanya rai a abinda har abada ba ya zaton za su ƙara ji ko gani daga gareshi. Fatansa Allah Ya ƙarawa Dadarsu hakuri da dangana. Washegari kuwa sai da ya biyo ya saukemata Fatima sannan suka kara sallama ta kara jaddada mishi ziyartar Modibbo ya amsa da toh kawai sannan ya kama hanyar Kano. *** *KANO*     _*Lamiɗo Crescent*_   Wata hamshaƙiyar mace ce mai kimanin shekaru arba'in da ɗoriya zaune saman ɗaya daga cikin kujerar dinning, an jera kayan maƙulashe kala-kala a gabanta. Waya take tana zabga murmushi ga dukkan alamu tana jin dadin tattaunawar. Hajiya Zeenatu kenan.   Hankalinta ya kai ga mijinnata wanda ke saukowa daga matattakala sannu-sannu kamar mai ciwo a tafin ƙafa. Kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai. Daidai sadda ya ƙaraso ta cire wayar a kunne bayan sun yi sallama da abokiyar wayarta ta.   Ta dubeshi kamar ta haɗiye sa'ilin da yake zama saman kujerar dake fuskantarta. Kallo take ƙarewa matashin mijinnata wanda da ace ta yi aure da wuri da kuma ƙuruciya, da ta haifi sa'ansa ko wanda da kaɗan ya rage ya kai shi a girma. Hannunta ta ɗora saman haɓa ta zubamishi idanu shi kuwa banda danna waya ba abinda yake. Yana sanye da wata shadda da aka fi kira da Commisioner fara ƙal, an mishi dinki ba mai hayaniya ba kuma na zamani irin na matasan da ke ji da gayu da kuma kudi. Baƙin agogon fatar da ya ɗora a tsintsiyar hannunsa na hagu shi ya ƙara taimakawa wurin haskaka fatarsa mai cike da gargasa a idanunta. Ta kara kallon halittar ƙira da kuma fuskarsa wanda ke ƙara sanyawa ta ji shi ɗin nata ne ita kaɗai a duniya, don ita aka halittoshi. Har abada babu wata da za ta raɓarmata wannan inuwa da ta ke ganin don ita kaɗai aka ƙagi ni'imarsa. A yanzun da ya zauna nesa da ita, gani take kamar an jonamata mayen ƙarfen da ba zai rayu ba tare da ya kusanci ƙarfen da ke hakilonsa ba. Wannan ya sa ta miƙewa gami da nufar kujerar dake gefensa ta zauna bayan ta ja shi sosai zuwa jikinsa. Wayar hannunsa ta karɓa, wannan yasa shi ɗago kai gami da dubanta, duk da irin saƙon da ta karɓa bai sa ta girgiza ba. A ganinta wannan ba komai bane idan har ita din mace ce mai jarin juyawa, to ko birnin Sin ne za ta iya takawa ta je don cimma kowace manufa.   "Lafiya?" Ya furta yana ɗan lumshe idanu wanda hakan halittarsa ce, halittar da ta bambanta shi da halittu irinsa. Wanda da kallo ɗaya za ka bambancesu. Hajiya Zeenatu ta sauke wani ajiyar zuciya don jin so da kaunar matashin mijinnata na ƙara yin amai a cikin zuciyarta.   "Komai ma anyi Ranka Ya Daɗe, ni wannan fushin ba zai wuce bane? Daga radda aka yi ai ya ci a ce ya wuce kuma an rufe babinsa. Na ba ka hakuri tun a ranar, me zan maka bayan wannan don Allah, uhum?" Ta ƙarashe cikin sigar jan hankali irin na gogaggun matan boko kuma ƴan shagwaɓa. Nan da nan ya ji tsikar jikinsa ta tashi, kwanakin nan kawai dannewa yake sai dai zuciyarsa na tsananin kaunar su shirya, yanda yake kwana da wuni da tunaninta haka ita kuma ta ɗaure fuska ta sauya mishi akan laifin da ba shi ya gayyato ba.   "Ya wuce." Ya furta dakyar bayan ya tattaro nutsuwarsa. Ta ɗago hannunta wanda ya sha adon awarwaro da zobuna na gwal ta ɗora gefen fuskarsa da saje ya zagaye.   "Ka tabbata?" Murmushi ya yi ya kalleta gami da dauke kai, bai c komai ba. Dama ta san ba lallai ya ce din ba, mafi yawan lokuta shirun ne amsarsa. Da rawar jiki ta shiga serving dinsa tana jan sa da hira, nan da nan ya sake suka ci abincin suka haura sama sai turaka. Tana gefen gado zaune tana waya ya fito daga wanka. Ganin yanda take tsuma ya sanyashi maida hankali gareta.    "Su a banza a wofi!! Ko sun manta mu ne gwamnatin?! Bar ni da su!" Kiit! Ta kashe wayar.   "Ofishin haraji zamu je." Abinda kawai ta iya ce mishi kenan itama ta faɗa banɗaki. *🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem 05) Safiyar talata da misalin karfe tara da mintuna, ta shiga ma'aikatar Revenue wurin aikinsu. Kai tsaye ofis dinsu ta  wuce bayan ta gaisa da idon sani. Nan da nan ta haɗe fuska ganin wanda ke zaune tare da abokan aikinta suna hira. Mutumin nema yake ya takuramata, sallamarta ya sa duk aka amsa, ya kuwa zubamata ido kamar ya haɗiyeta. "Kai kam Oga Ahmad ka taki sa'a ga dukkan alamu. Ga wata ga zara." Ba ta san sadda ta watsawa Halima mai wannan furucin kallo ba, itama Halimar ta yi don zolaya, hakan yasa ta basar da hararar gami da dariya ciki-ciki.   "Ai kuwa dai Halima. Gwara da Allah Yasa na yi sammako. Ganin na Ramla wuya yake."   Ba ta tankawa kowa ba ta zauna saman kujerarta ta maida hankali ga Rabi suna gaisawa. Jin maganar mutum ta yi a gefenta yana fadin. "Haba Gimbiya Ramla, wannan ɗaurewar fa? Ina fatan dai ba daga ni bane?" Ko kallo bai isheta ba, to girman ne ya zube warwas!  Ya riga ya tureshi tun radda ya bayyana fitsararsa ƙarara. Ya gama bambamin surutunsa ya fice. "Ba ki da wayo Ramla, da ni ce da damarki, za ki yi mamaki." Ta maida duba sosai ga Halima, "Idan wannan shi ake kira da rashin wayo Halima, to ki jera Ramla a sahun farko. Kema ina roƙamaki shiriya." Daga haka ta maida kai ga aikinta ba ta saka baki cikin caa da abokan aikin maza da mata suka yi ga Halima ba wacce ranta ke susa da maganganun Ramla. Ta kuma ci alwashin sai ta rama ko ba jima ko ba daɗe.     *** Suka yi parking ɓangaren da aka ware don ajiye ababen hawa. Kusan a tare suka fito. Kai tsaye  Hajiya Zeenatu ta fiddo waya ta dannawa Chairman kira. Suka ɗan yi magana sannan suka kashe. Da kwatancensa suka nufi ofishin, ba tare da wani jinkiri ba aka yi musu iso zuwa ciki.     Aliyu Dikko matashin da zai shekara arba'in da ɗoriya ya dubeta fuska a washe. "Manya gatan wasa, ganinki sai da dalili." Ta yi dariya tana mai zama sa'ilin da suka zauna. "Ai ku ne gwamnati, shiyasa dole ku za'a bi ko an ƙi. Ba don wankin hula na neman kai ni dare ba ai ba ka ganni ba." Ya ƙyaƙyace da dariya gami da maida hankali da matashin da tun gaisuwar da suka yi bai ɗago ba balle ya shiga maganarsu, asalima waya yake sarrafawa.   "Ah lallai kam. Wannan ƙaninmu ne?" Tambayar ta sa ya ɗago kai ya watsamasa wani irin kallo kafin ya dubeta fuska a murtuƙe. "Please mu yi abinda ya kawomu." Ganin haka ta shiga nutsuwarta ba shiri.   "Chairman jama'arka sun min laifi duk da dai da nawa laifin. An ƙullemin shago saboda kuɗin haraji. Wannan abu ba ƙaramin tozarci ne a gareni ba don haka na zo nayi clearing komai." Ya jinjina kai, zai so ya san wane saurayin da har ya iya jan Hajiya Zeenatu kamar raƙumi da akala sai dai kuma ba fuska. Waya ya ɗauka ya danna kira kai tsaye ga department ɗin da ke kula da wannan ɓangare. Mintuna kaɗan shugaban department din ya hallara. Cike da girmamawa ya gaida Chairman. Ya saurari dukkan jawabinsu kafin su mike su bi bayansa don aiwatar da abinda ya dace.   "Bismillah ku zauna." Oga Ɗalhatu ya umarcesu bayan sun isa ofishinsa. Ya kira abokiyar aikinsa da ya ke da tabbacin takardun Hajiya Zeenatu a hannunta suke.   Ramla na zaune ta dukufa shigar da wasu bayanai kwamfuta, tana yi tana hamma da duban lokaci. Sa'arta ɗaya ba ita ke da alhakin ɗauko yara ba a'a ranakun Litinin zuwa Alhamis bisa yanayin aikinta wanda sau da dama sai huɗu suke tashi. Sai dai a yau ɗin gani take ta gaji ba kaɗan ba, kamar ba za ta iya kai wannan lokacin ba, haka kawai ba ta jin dadin jikinta. Kiran da Oga Ɗalhatu ya yi mata ne ya katse komai da take yunƙurin yi, ta miƙe ɗauke da file din Hajiya Zeenatu har wani abokin aikinta Salihu na faɗin Hajiya ta ji wuta ta kawo kanta suna dariya. Da sallama ta shiga ciki bayan an amsa mata. Gaba ɗaya sun bata baya, sai Oga Ɗalhatu dake fuskantar ta. "Yauwa ƙaraso Ramlatu." Ta shigo sosai, ido hudu ta yi da Hajiya Zeenatu, hakan yasa ta gaisheta da ɗan murmushi. Ita kuwa ta amsa ciki-ciki tana kauda kai. Ba ta ga dalilin da za ta sakarwa kowace ɗiya mace fuska ba muddin tana tare da Mijinnata. Tana kishinsa, kishi mai tsanani. Ramla ta kauda kai da mamakin hali irin nata, sam ba ta ko kalli mutumin da suke tare ba balle ta maida hankali gurin gaidashi.   Bayanin Oganta take sauraro kafin ta karkata ga Hajiya Zeenatu ta fara yi mata bayanin duk abinda ya dace ta yi kuma ta biya cikin kwarewa da sanin makamar aiki.   Ya ɗago kadan ya kalleta, aka ci sa'a itama idonta ya sauka a kansa sadda ta ɗan rausaya ido duk cikin bayani. Kirjinta ya harba, ina za ta mance fuskar da tun kallon farko ya kasa ɓacemata? Shi ne, shi dai da ta yiwa ɓarnar dubunnai ya yi mata afuwa. Ya haɗe cikin maroon voyel sai hula da ta hau da kayan. Ɓata lokaci ne ka tsaya siffanta tsatsar kyan da Allah Ya mishi. Gareshi kuwa, kallo ɗaya kwaƙƙwara ya mata sai ya ɗauke kai. "Aikinki za ki yi ko kuwa kallon mazan wasu?!" Ta ji kalaman Hajiya Zeenatu tsakar kanta, sai sannan ta ankara da tafiyar tsutsar da kalamanta suka soma yayin furtawa sakamakon kallon sanin da ƙurillar da take yiwa abinda bai shafeta ba. Sai dai zafin kalaman Hajiyar ya sa ta ɗaure fuska. Har aka kammala komai suka tafi ba ta ko ƙara kallonsa ba, balle shi kuma da ba ta gabansa. "Kinsan Allah mijinta ne, makwaftan wata ƴar uwata ce. Wallahi a ranar farko da na gansu tare sun fito daga gidansu ban yarda ba don har ina cewa ta samarmin lambarsa, ƙarshe na yarda don akan na gaidashi a bakin ƙofa, matarnan har ɗaga hannu ta yi da zummar marina ya riƙe hannun sannan ya ja hannunta suka koma ciki. Tun daga ranar ban ƙara wannan gangancin ba." Hirar Najaatu da Halima ta tsinkayo daga nasu mazaunin, tsalam ta ji Salihu ya sa baki. "Ke Hali dubu! Yanzu wannan mijinta ne?" Tana ji Halima ta hau rantsuwa da fadin kwarai kuwa. Nan da nan aka hau yin caftarsu, daga mai cewa kuɗi ya gani ya yi wuf da ita sai mai fadin bai yarda ba saboda sam saurayin bai yi kalar babu ba. Uffan ba ta ce musu ba har lokacin tashi ya yi, ta haɗa tarkacenta ta yiwa kowa sallama ta fice. Tuƙi take sai dai hirar da akai akan matashin da Hajiyar da aka kira da matarsa ya tsayamata a ƙahon zuciya. 'Me ya kai shi? Da ƙuruciyarsa da komai? Kyakkyawa kuma ɗan gayu irin wanda babu macen da za ta ganshi ba ta ji sonsa ba? Me ya kai shi auren wacce ko ba ta yi sa'ar mahaifiyarsa ba, za ta zo a babbar yayarsa?' Nan da nan zuciyar ta warwaremata zaren da ta ƙulla ba tare da shan wahala ba. 'So! So ne! Ba abinda ba ya sa wa, kamar yanda ya sa na aikata abinda bansan zan iya ba.' Ta haɗiyi miyau tunanowa da ranar da ko daga bacci ta farka za ta bada labarinsa. ***   _*SANADI*_ Bini-bini sai ta kalleta ta ci gaba da tafiya tana murmushi. Ƙarshe Ramla ta gaji ta kai mata duka a baya tana dariya. "Wai ko ke aka sanyawa ranarnan sai haka!" Dariyar suka yi gaba ɗaya. "Wallahi ba ki ji yanda nake murna ba. Ba don na gama tsallena cikin gida ba da yanzun ƙarawa zan yi." Tsaki da dariya ta yi kawai ba ta ce uffan ba. Sai da suka ƙarasa har titi Ramla ta samu ɗan sahu kafin su yi sallama ta soma ƙoƙarin tsallakawa hannun da zai mayarta gida.    "Ƴan mata bamu chanji mana." Ta juya inda maganar ke fitowa, adaidaita ce ta yi parking a gabanta, sai da ta ji ba za ta iya yafewa kanta ba sa'ilin da idanunsu suka haɗu, da ba ta kalleshi ba, abubuwa da dama ba zasu chanja daga zuciya zuwa gangar jikinta ba. Sai dai kuma nan take ta ƙaryata. Shima da yake daga cikin ɗan sahun watsi ya yi da nashi a kwandon shara ya maida kai zuwa cikin abin hawar. "Babu kenan." Ta ji muryar ɗan sahun sa'ilin da yake sauka yana nufar abokin aikinsa da zummar karɓar chanji. Bisa kuskure idanunsu ya ƙara sarƙewa, ta yi saurin janye kwayar idanunta shi kuwa an zo gaɓar da ya yi amannar hakurinsa ya ƙare.    Ta gifta napep din har ta  samu nasarar tsallakawa. Haka kawai take zuba sauri don ta isa gida, ba ta yi aune ba ta ji muryar mutum a bayanta. "To ni kuma da ba ɗan unguwa ba kina wannan saurin idan na ɓata fa? Kar ki kaini gidan ƴan yankan kai." Cak ta tsaya gami da juyowa, bata san sadda ta yi suɓutar baki ba. "Biyoni ka yi?" Duk yanda ta so kar ta ƙarasa faɗi bayan ta ankara da suɓutarsa hakan ya faskara. Murmushi ya yi ya ɗan tako kaɗan. Kusan a gigice take duban layin, fatanta kada koda wasa Yaya Munir ya ganta tsaye anan. Wannan yasa ta juyawa da zummar soma tafiya. "Don Annabin Rahma ki tsaya." "Sallallahu alaihi Wa sallam." Ta furta a hankali sannan ta dubeshi.   "Malam wallahi an sakamin rana yau ɗin nan ma, don Allah ka yi hakuri ka daina bina. Matsala za ka jawomin a gida." Ta furta rai a haɗe sannan ta soma tafiya kirjinta na harbawa. Fatanta Allah Yasa ya dakata. "Ni duk ba wannan ba, nima inada matar aure. Kwatance za ki min." Ba ta fasa tafiyar ba, bai fasa bibiyarta yana magana ba. Dole ta tsaya ganin an kusa shan kwanar layinsu. Ta dubeshi da idanunta masu firgita maza. Ya kuwa lumshe nashi ƙananan idanun masu kama da na mai jin bacci ya bude, shirunta na nufin tana jinsa kenan "Wani gida nake nema, bansan kalarsa ba. Ba zan ce ga girmansa ba, kuma da ace ma da hali naga gidan ban ƙi ya zama mallakina ba na har abada. Amma kinsan me? Matar gidan ta nunan ba ni da wurin zama cikin gidanta. Ni ne da nacin tsiya na kasa haƙura. Idan na kasa mallakar gidannan, bana jin akwai gidan da zai ƙara burgeni koda kuwa ace wanda nake da shi yanzu ne! Ki tausayamin don Allah." Ya ƙasashe cikin karaya, rabin hankalinta na ga kallon hanya rabin wajensa, ko kusa ba ta gane wannan tatsuniyar ba don haka kai tsaye ta ce. "Wallahi ban gane komai ba Malam, ka rufamin asiri ka tambayi wani ko wata sai anjima." "Saƙo na ƙarshe don Allah, nima daga nan zan juya na tafi kar na sha wahala." Dole ta ja tunga ta juyo tana dubansa, shima ƙara narkar da idanunsa ya yi cikin nata gami da jingina kansa jikin bishiyar darbejiyar dake bayansa. Ta kauda kai tana ƙara yiwa kanta tunin wannan ba HILAL bane tsaye. "Bana yiwa mace kallon da ya wuce biyu, amma kin janyomin sauka a unguwar da kusan bani da kowa, ban taɓa bin mace a baya ba, don wannan ba ya cikin sabgar ALIYU, kin sanya na biyoki. Bansan gaskiyar sanyamaki rana ba duk da cewa fuskarki ba ta maƙaryata bace, sai dai ki taya kaina da kuma ke addu'ar kada mu kasa cika alƙawarin waɗanda muka ɗauka matsayin abokan rayuwarmu. Fatan alheri MATAR GIDA." Daga nan ya juya bai ƙara waiwaye ba, duk da dukan da kalaman suka yiwa zuciyarta, bai sa ta fasa ci gaba da tafiyar ba. Sai dai fa tana tafe tana yiwa kalaman filla-filla, sannu-sannu kuma take haddarsu. Ta kasa fahimtar manufar, ba kuma ta marmarin ta fahimta ɗin don a ganinta bai da amfanin komai, wannan ta sa ta yin watsi da shi. Sai dai daga lokacin Aliyu ya yiwa mafarkanta illar da har ta soma tunanin ba mutum bane! Hilal ya zo suka yi sallama sadda zai wuce Malaysia, kowannensu wata irin kewa  yake ji, Ramla kuwa kasa jurewa tayi ta shiga hawaye. "Aa please, za ki yimin illa babba fa. So kike ina tafe ina tuna kuka maimakon murmushinki? Kar muyi haka da ke. Kinji? Idan kin yi kuka ni kuma na yi me?" Ganin duk yana neman hargitsewa sai ya ba ta tausayi. Ya shiga rarrashi. "Ki kwantar da hankalinki kinji? Da kaina zan siyamaki waya na aikomaki don ba zan jure rashin jinki ba. Ramla ba don karatu dole ne ba kuma ina sonmu da shi wallahi Hilal zai iya ajiye karatun ya aureki daga baya ki ƙarasa naki a gidana. To ba zai yiwu ba, komai bisa tsari ya fi. Ki yi hakuri kin ji?" Ta share fuskar tana murmushi. Kukanta biyu ya haɗarmata, kirjinta bugu yake bana wasa ba, tana ganin kamar akwai wani ɓoyayyen lamari da zai fi ƙarfinta, jikinta na bata akwai babbar matsala sai dai wani ɓangare na zuciyarta na ƙarfafarta akan kar ta ba shaiɗan damar wasa da hankalinta. Yanda Hilal ya dage rarrashi ma duk sai ya bata tausayi dole ta nuna mishi ta sauko, suka rabu kamar kar su rabun. Tuni ya yi sallama da su Hajiya da Abba, wannan tasa kawai wucewa ya yi. Hotunanta kala-kala na takarda ta ba shi har yana fadin zai sa a mishi enlargement dinsu ya kafa a ɗakin kwanansa na makaranta. Dariya kawai ta yi. Daf da zai bar gidan ya dakata gami da fiddo wani ɗan akwatin ƙarami na zobe, kai tsaye ya miƙamata yana murmushi. "Karɓi mana." Ta sa hannu ta karɓa tana kallo. "Duk da ba zancen alƙawari yanzu, saboda inada yaƙinin irin kaunar da muke yiwa juna, ina da tabbas a kanki Ramlata. Ki sanya a hannunki, ya kasance har bayan dawowata shi zan tarar a hannunki. Wannan kaɗai zai sa ni farin ciki. Ina miki fatan alheri." Daga nan ya fice a gaggauce don da alama ya soma karyamata zuciya. "Azurfa mai kyau." Shi ne abinda Rafee'ah ke kira yayinda ita kuwa ta mike ta bar falon zuwa ɗaki. Kuka ta ci sosai na abu biyu da ta rasa da wanda za ta ji. Sai da ta yi mai isarta ta share fuska, ta ɗau alwashin rabuwa da tunaninsa balle ya kai ta da mafarki. Ta ƙara gaskata mafarkan  Aliyu duk kissimawar shaidan ce, shi ke mata yawo da hankali a mafarkanta. "Daga rana irin ta yau babu ni ba tuna dukkan wani abu da ya shafeka Aliyu, har abada. Allah ina neman tsarinKa daga sharrin shaidan da kuma na zuciya da saƙe-saƙenta." Sai dai kuma wasu lamuran sun fi gaban yanda dukkan bawa ke ɗaukarsu. Duk a rashin sanin cewar yanzu aka fara! ***    Ƙarar ababen hawa ya cika kunnuwanta, dole ta saita kanta ga ci gaba da tuƙi cikin nutsuwa da kwarewa, a hankali ta sa bayan hannunta ta share fuska. Daidai wani boutique ta yi parking ta fito.  Kai tsaye ta shiga, tunda Ummi da Ansar suka ƙwallafa rai akan halartar Children's Day. Ta shiga ciki kai tsaye ta nufi ɓangaren kayan yara. Tun kan ta ƙarasa ta hango bayan mutumin riƙe da waya a hannunsa yana video call bai ko damu da tsilli-tsillin mutanen dake shagon ba wadanda wasu ke kallonsu suna dariya wasu kuwa su yi gaba. "Wannan kina so?" Ya ɗaga wani takalmin, yarinyar ta turo baki kamar mai shirin kuka ta girgiza kai da mirza idanu. Ya sauke ajiyar zuciya. "Tee ya zan miki uhm? Duk wanda na ɗaga bai miki ba? So kike Mominki ta yi mana dariya ko?" Matar shagon ta ƙara ɗauko mishi wasu tana dariya kaɗan-kaɗan. Ramla kallon yarinyar kawai take tana tasbihi ga Ubangijin da Ya ƙageta. "Daddy ga wata Mami can a baya, ni ta zaɓamin. Dada ta cemin ba ka iya zaɓe ba." Cewar yarinyar har tana riƙe haɓa da turo baki, jin abinda yarinyar ta faɗi yasa ta saurin juyawa ta ɗora hannu saman shelf din da ya fi kusa da ita kamar hankalinta bai kansu. Tana jin dariyar yarinyar, shi kuwa uban koda ya juyo sai ya ji kunya kaɗan cikin yaren fillanci ya yiwa yarinyar sallama ya katse kiran.    "Ki ji fa, idan matar aure ce kuma fa?" Ya yi maganar yana duban Matar dake aikin ciro mishi takalma, ta dubi Ramla da ke sauraron su kadan kadan. Ta yi dariya. "Wannan Customer ɗinmu ce Oga,na san Madam ba ta da aure."   Ya kara duban Ramla kafin ya mike da nufin aiwatar da abinda ɗiyar ta nema, a sannan ita kuwa Ramla har ta ɗauki wata doguwar riga mai hula wanda ta tabbatar zai yiwa ɗiyarta. "Assalamu alaikum." Ta dubeshi, zaro idanu waje ta yi. Ganinsa anan ya yi masifar ba ta mamaki da kuma tsoro. To ina Hajiyar? Yaushe ya sauya kaya daga voyel maroon zuwa shadda ruwan toka? Ta kasa magana, shi kuwa bai maida hankali wurin kula da hakan ba ya shiga neman alfarmar ta zaɓamasa takalmin da zai yiwa ɗiyarsa. Ta kasa magana don gaba daya ta tsorata. "Hello." Ya ƙara faɗi gami da ɗan rankwafar da kai. Ta ɗan yi firgigit sai ta basar cike da dakiya. "Ba damuwa." Suka ƙarasa wurin takalmin, ta shiga dubawa bayan ta tambayi size dinta. Jefi-jefi za ta kalleshi da tsantsar mamaki, sai dai duk abinta ba za ta taɓa yin shishshigin tambayar ko shi ƴan biyu bane. Wani takalmi ja ta ɗauki mai adon fulawa, tana murmushi ta miƙa masa. "Wow, gaskiya Madam kin iya zaɓe." Fadin ma'aikaciyar wurin. "Allah Yasa ya burgeta." Ramla ta fadi da murmushin da ya fi kama da yaƙe don har yanzu kirjinta bai bar bugu ba tsabar kamannin da ta gani ƙarara na wannan mutumin da mijin Hajiya. Shi kuwa Alhassan banda murmushi ba abinda yake dokawa, iyakar burgewa takalmin ya mishi har cewa ya ke. "Idan Tee ba ta so takalminnan ba to ba bulala za ta sha." Suka yi mishi dariya. "In Sha Allah za ta so." Daga fadin haka ta mike yana mata godiya, ta koma ga kayan maza hannunta rike da rigar da ta daukarwa Ummu. Sai da a kammala ta nufi wurin biya. Duk yanda ta nuna ba ta so hakan bai sa Alhassan fasa biyamata kuɗin kayayyakinta ba. A karshe godiya kawai ta yi, kusan tare suka fito kowa ya nufi motarsa suna kara yiwa juna godiya. Kallonsa take har ya bude mota zai shiga, hatta da tafiyarsu ɗaya ce, a yanzu ta yarda su ɗin ƴan biyu ne babu ko tantama. Har za ta tayar da mota ta ji maganarsa a gefenta. "Mami, yi hakuri ki sanyamin number dinki, I promise you ina komawa garinmu zan kira na ba ki albishir takalmi ya burge ɗiyarki. Kuma itama ina son ta miki godiya ko?" Ta yi jim kamar ta ce a'a, ya kuwa narkar da fuska. Sai ta yi murmushi ta karɓi wayar ta shigar da lambarta. Ya karɓa ya yi godiya suka yi sallama. A hanya tunanin biyun masu kama kawai take yi wanda bambancin su fara'a da akasinsa. Banda wannan kamar ta yi yawa. Haka har ta isa gida  tana zancen zuci. https://my.w.tt/ub8deMQ0g9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem 06) *** Tun fakawarsa a gaban ƙaton ƙyauren na gidan Muhammad Modibbo ya ji ɓacin rai ya lullluɓe dukkan wata walwalarsa. Ya kalli gidan, abubuwa da dama suka shiga dawowa kwanyar Alhassan Aminu. _"Tunda ubanku ya bijirewa umarninmu ya auri bare ai ko sata aka ce kun yi zan yarda. Har abada zuri'armu ba za ta karɓi Uwarku ba balle ku da ku ke yaranta."_ Ya runtse idanu tuna kalaman babban wan mahaifinnasu da ya yi. Ba don Dada ba ba zai taɓa shiga gidan ba. Sai dai matsayi da girmanta ya zarta hakan. "Sai yau ku ka tuna da ni?" Dattijon mai shekaru sittin da ɗoriya ke wannan kalaman cikin harshen fulatanci sadda ya dubi Alhassan dake zaune a gabansa ya sunne kai. Murmushin yaƙe ya yi. "Ba haka bane, ayyuka ne suka yi min yawa. Ayi hakuri." Ya maida da harshen fillanci don Modibbo Hausar ba kasafai take fita ba. "Ka koma, duk radda ka yi ritaya wurin aiki sai ka dawo a ci gaba da zumuntar." Daga haka Modibbo ya mike ya shiga ɗakinsa. Idanun Alhassan suka kaɗa, dama yasan a rina! Bai ma tsammaci zai yarda su gaisa ɗin ba. Ya mike gami da zaro hankicif a share goshinsa. Duba ya kai ga ƙaton enlargement din na yaran Mamman Gidado dake manne a falon, yaransa goma sha biyar cif har mahaifinsu wanda ke bi ma Modibbon. Ajiyar zuciya ya saki ya fice daga falon da sauri. Sashin matan gidan ya wuce, su biyu ne kuma duk daga zuri'a guda sai dai ɗaya ɗiyar wa, ɗaya kuma ɗiyar ƙani. Ɗakin Uwargida Hajja Fatuma ya soma shiga. Kadahan-kadahan ta amsa mishi, wurin yaranta ne ya samu tarba sosai, bai yi mamaki ba don dama basu da matsala tsakaninsu su cousins. A ɗakin Hajja Amarya kadai ya samu shimfidar fuska, dama can ita ke mutunta su da ɗan uwansa da mahaifiyarsu. Anan ya shantake har girki ya kwasa suna dariya karshe ya mata sallama ta bada turarukan wuta a kaiwa Dada sai na matarsa. Yara yasa suka shiga da kayan lemuka da ya yo tsaraba, bai ko kara shiga ba ya ja motarsa. Washegari kuwa sammako ya yi ya bar garin Kano. ***   *ADAMAWA*    Tana tsaye jikin madubin ɗakinta tana kokarin gyara zaman ɗaurin ɗankwalinta. Doguwar riga kalar ruwan madara ta sanya wanda aka yiwa aikin paint work.  Sauri-sauri take don tasan mijinnata na dab da shigowa gidan dalilin waya da suka yi ya sanarmata ya shigo gari. Sai dai saurinta ya kusan haifar da nawa sakamakon hon dinsa da ta ji a bakin gate. Ba ta san sadda ta turo baki ba don ita kam a duniya ba abu mai wuya wurinta irin ɗaura ƙaramin ɗankwali. Ta yi jifa da shi gefe ta koma wardrobe ta dauko karamin mayafin da ya dace da kayan ta fita. A falon suka ci karo, ya sakarmata murmushi gami da ajiye ledar saman kujera ya buɗemata dukkan hannuwansa, aikuwa da sassarfa ta ƙarasa ta shige, ya maida hannuwan ruf.   "Sannu da zuwa Abu Fatima." Ta fadi tana mai ɗagowa daga jikinsa. Ya ja karan hancinta. "Kema sannunki. Kin yi kyau sosai." Ta yi godiya, daga nan suka faɗa ɗaki, ta taimaka ya yi wanka ya rama sallolinsa kafin su fito falon. Miƙar da ƙafafunsa ya yi saman kujera haɗi da kiran wash. Ta ɗaga ƙafafuwan ta zauna sannan ta ɗora saman cinyarta. Cike da tausasawa ta dubeshi. "Sannu Abu Fatima, ka kwaso gajiya." Ya lumshe ido da murmushi. "Bari kawai Ummina, na sha tafiya ba kaɗan ba amman Alhamdulillah tunda na cimma nasarar abinda ya kaini. Zuba abincin." Ya fadi yana mai miƙewa zaune bayan ya sauke ƙafafunsa. Yana cin abinci yana mata hirar diramarsa da Fatima. Banda dariya ba abinda ta yi. "Ci gaba da biyewa yarinyarnan dai, watarana sai ta ba ka kunya. Hum, naga kokarin ma Matar da ta biyewa shirmenku." Harara ya watsamata. "Shikenan, kin ja wa kanki na fasa ba ki taki tsarabar." Ta kama kunne tana murmushi. "Na tuba. A yimin afuwa." Ya yi murmushi kawai. *Kausar* kenan, matarsa kuma ƴar uwarsa. Sun gina rayuwa ta fahimta, so da kuma kaunar juna. Ɗiyarsu guda a duniya Fatima, tun daga kanta Allah bai ƙara ba su haihuwa ba.   Sai washegari ya je gidan Dada, bayan sun gaisa ya isar da sakon gaisuwar Modibbo da jama'ar gidansa  gareta, ta ji ba don ta yarda ba. Ya ba ta tsarabar da Hajja Amarya ta ba shi. Murmushi ta yi.   "Wannan kam na yarda."  Shima murmushin ya yi bai ce uffan ba. "Daddy takalmina." Fadin Fatima tana kara mannewa jikinsa gami da turo baki. Ya na dariya ya janyo leda, ya bude kwalin ya soma kokarin sanyamata a ƙafa. "Wowww! Daddy ya yi kyau sosai." Dariya ta basu shi da Dada. "Sai ki zo ki yiwa Mamin Boutique godiya." Ta mike tana tsalle ganin yanda takalmin ya yi kyau a kafarta kamar wata balarabiya. Ƙarshe ta rungume wuyan Uban tana magiyar a kiramata Mamin Boutique. Ba musu ya fiddo waya ya danna kira.   *** KANO Misalin ƙarfe biyar da mintuna ne na yammacin ranar, dawowarta kenan daga wurin aiki ta miƙe ƙafa a falon cikin yayyunnata mata wadanda a ƴan kwanakin suke shigowa dalilin bikin A'isha da ya taho gadan-gadan. Rafee'ah ke riƙe da takarda da biro tana lissafin kayayyakin da ya rage a siyo a kasuwa  yayinda Zulaihat ke nunamusu wasu hotunan sabbin warmers ƴan Dubai a waya.     "Kai Maman twins, sun yi kyau sosai wallahi." Fadin Ramla tana ƙara sanyo kai ta gefe ita da A'isha.   "Kyau ai ba ɗaya ba Ramla. Nidai idan ma ba za'a siya wa Auta ba ina so zan siya."   Fadin Rafee'ah tana ƙara kallon hotunan cikin santi. "Kai Sis. Aa nidai ina so wallahi." Fadin A'isha, ganin Hajiya ta kalleta sai ta ji kunya ta ruga ɗaki. Dariya suka yi gaba ɗayansu. Daidai sadda ta ji ƙarar wayarta, ta koma mazauninta ta ɗauka. Ganin baƙuwar lamba ne ya sanya ta yi mata ƙuri, sai dai tuna ko akan abinda ya shafi wurin aikinta ne ya sanya ta ɗagawa da sallama. "Waalaikumussalam wa rahmatullah Mamin Boutique." Ta ɗan yi shiru sanadin abu biyu, jin muryar namiji da kuma jin sunan da ya ambata. "Sunana Alhassan Aminu, wanda ku ka hadu a Afrah Boutique dake kan..." "Ayya sai yanzu na gane. Fatan kana lafiya?" Ta katseshi da sauri ganin yanda ƴan uwan suka raba hankalinsu, wani a abinda suke wani kuwa a kallonta ana ƴar dariya ƙasa-ƙasa. Suka ƙara gaisawa sannan ya miƙa wayar ga Fatima. "Assalamu alaikum Mamin Boutique. Ina kwana."   Yanda yarinyar ta yi sai da ta murmusa don kuwa ta burgeta. Ta amsa mata, nan yarinyar ta shiga zubamata hirar takalmi ya yi kyau Maminta ba za ta yi mata dariya ba. Ita dai Ramla ta biyemata, karshe Abbannata ya karɓi wayar. "Idan kika biyemata sai ku cinyemin kuɗin wayar ai." Suka yi dariya kusan a tare, ya ƙara yi mata godiya ta bada saƙon gaisuwa ga mutan gidan daga bisani suka yi sallama.        "Mene?" Ta furta tana mai duban Maman twins da Rafee'ah.   "Kin fimu sani ai, har kin samu wani majnun ɗin ba labari ko?" Ta saki baki kawai ta kasa magana. "Bar ta. Ni kai da naga ana shirin kasamin in law." Hajiya ta dubi Maman twins. "Wa kenan?" "Baba Bashir yayan Baban twins mana, wanda matarsa ta rasu. To ai shi ne ya ga Ramlar kwanaki can ya nunan ana so. Maganar kenan da nake son nayi da ita amma ƴar albarkar ba ta kirani ba, ba ta zo gidannawa ba." Ramla ta ja guntun tsaki. "Don Allah ku bar wannan maganar, shi fa da kuke ganin mun yi waya, takalmi ne na tayashi zaɓar ƴarsa shi ne dalilin da ya kira suka yimin godiya don takalmin ya burge ƴar. Maman twins shi kuma Bashir ai kin ba shi lambata, sau ɗaya ya taɓa kirana kuma na ɗaga mun gaisa na ba shi hakuri. Mai kuma zan daga kiransa ya kara cemin?" Daga haka ta kwashi tarkacenta ranta na zafi ta kama hanyar barin falon.    "Ai fa, wannan zafin rai da taurin kan ba zasu taɓa bari ki yi gaba ba Ramla. Ki dai bi sannu tunda yanzu ke mai ba wa wasu labari ce. Kinga dai makomarki." Ba ta san sadda ta juyo gaba dayanta ba tana duban Rafee'ah wacce ta fusata. Ba dai ta ce komai ba ganin Hajiya na tsawatarwa ta juya ta wuce ciki, sai dai kafin ma ta kai ga shiga dakin tuni ta soma fidda hawaye. Tana ƙarasawa ta rufe gam da muƙulli ta faɗa saman gado. Ta yiwa kanta illa, tun ran gini tun ran zane, tana kyautata zaton dalilin ne yasa abu kadan ta aikata sai cibi ya zamo mata ƙari. Miƙewa ta yi ta rage kayan jikinta ta faɗa wanka. Koda ta fito shiryawa ta yi cikin doguwar jallabiya mai ɗankwali. Idanunta ya kai ga ɗan akwatin mai kalar golden da ke ajiye saman mirror dinta. Ƙarasawa ta yi ta buɗe, wani envelope ta fiddo ta zauna gefen gado ta buɗe. Hotunan ta ciro tana ƙaremishi kallo. Wani lokaci ta tuno wanda har abada ba zai gushe daga kwakwalwarta ba. ***    *MATAR MUTUM* Tun tafiyar Hilal ta ƙara jin kewa ta cika zuciyarta. A bangare guda ga tunanin Aliyu da ya zamemata abin yi safe da rana. Wannan ta sanya suna kammala zana jarrabawarsu ta zango na biyu a makaranta, (2nd term), ta tattara Abba ya kaita Yakasai ta yi hutun a can ko ta sami nutsuwa.    Ta ci sa'a kuwa jikokin gidan wadanda suka kasance sa'anninta duk suna nan suma. Aikuwa suna ganinta suka ruƙunƙumeta da murna. "Oh yarannan shikenan kuma za ku hana bakinmu ya huta da bari-bari kamar wasu ƴan shekara hudu. Ai ko su A'isha sun fi ku hankali." Cewar Talatu ƴar kawun Abba wacce ta dawo nan da zama daga Daura. "Bar su su yi son ransu Talatu idan ba so kike yanzu Hajja ta maidaki Daura ba." Fadin Abba yana dariya. Hajja dake taunar goro tana tayashi. "A'a to, rabu da su. Wataran sai labari duk suna gidajen aurensu." Maganar Hajja ta ba su Ramla kunya, duk suka mike su ka yi ɗaki har suna bangazar juna. "Magulmata." Fadin Hajja cikin dariya. Abba ya shantake har da cin kwaɗon zogale kafin daga bisani ya yi musu sallama.   Washegari da misalin karfe uku na yammaci ƴanmatan su biyar, Usaina, Maryam, Jidda, Nafisa sai Ramla. Suka shirya suka fita zuwa gidan babban ɗan Hajja Zulai, Kawu Kabiru don ziyara. Tun kafin su fita titi Ramla ke mitar ita kam ba wacce za ta dauka saman cinyarta sai dai su yi abin hawa biyu. "Kai Mrs Hilal, don ɓarnar kuɗin mota?" Fadin Jidda tana auna abinda zasu kashe daga Yakasai zuwa Zoo road. "Aa fa, da gaskiyar ƙawalli, ba zan yarda nima na ɗora kowaccenku a cinya ba, ke kuma Jidda idan har za ki iya hawa bayan kujera shikenan."Faɗin Usaina. Ta ƙasashe suna dariya don ita kanta ta faɗa ne, a ƙiba kam duk Jidda ta fi su. "Allah Ya kiyaye." Cewar Jidda. Aikuwa dai sai rabawa suka yi, kusan a tare suka samu abin hawa, Ramla da Usaina su biyu kacal a adaidaita sai Jidda, Maryam da Nafisa wuri guda. Sai da suka kusa Zoo road ya samu fasinja. Sallama ya yi ya shigo, kusan da sauri ta dubeshi. Shi ne, shima yana zama ya kai duba gareta. Duk da yanda ta yi saurin kauda kwayar idanunta gefen Usaina wannan bai hanashi ganeta ba. Ta ƙara matsawa jikin Usainar ganin yanda jikinsu ke ɗan gogar juna. Murmushi ya yi ya matsa ta yanda ya san za ta fi sakewa. Bai ce uffan ba banda murmushin da yake faman dokawa, abin mamakin shima Zoo road ya nufa. A hankali ta kai duba gareshi ta cikin karamin gilashin ɗan sahu. Kwayar idanunsu ya sarƙe da juna ta yi azamar janyewa. Ba ta ƙara gangancin kallonsa ba, mutumin da take kwana da tashi da tunaninsa. Kirjinta bai bar bugu ba, ba ta fahimtar zantukan da Usaina ke yi. "Sauka mana." Ta ji muryar Usaina karo na biyu, sai sannan ta dawo nutsuwarta ta dubi gefenta, tsaye ta hangoshi a waje yana sallamar mai adaidaita. Ta kauda ido ta fito, Usaina na bayanta. "Ɗauka har da nasu." Ya furta ga ɗan sahun. Nan suka ce a'a, ya rantse shi zai biya, Ramla na shirin jan musu ta ji Usaina ta ɗan bugi kafaɗarta alamar ta yi shiru. Godiya suka yi mishi, hango su Jidda sun tsaya ya sanya Usaina nufarsu. "Ramlat." Ta tsaya cak gami da juyowa ta dubeshi, ba ta yi mamakin jin ya ambaci sunanta ba don Usaina ta kira sunan ya fi a ƙirga cikin adaidaita. Ya ɗan matso kaɗan. "Karo na biyu Allah Ya yi haɗuwarmu. Tun sadda na sanyaki a idanuna har yau bani da sauran sukuni. Wallahi ina sonki!" Ya furta fuskarsa na nuna alamar gajiyawa da kuma gaskiyar abinda ke ransa. Ta matse yatsun hannunta jin yanda kirjinta ke bugu, ta ɗan kuramasa idanunta da suka cicciko da kwalla. Shima kallonnata yake da nashi mayun idanun wadanda tuni sun dulmiya cikin tafkin kauna da shauki. "Ayya ka yi hakuri Malam, wallahi an sakamata rana. Nan da shekaru uku ba kaɗan bikinta." Kalaman Usaina ya maidota hayyacinta, ta tsinci bakinta da maimaita abinda aka ankarar da ita. "Eh, an sanyamin rana. Ka yi hakuri." Ya yi murmushin yaƙe. Ya dubi Usaina. "Kaicon wanda zai yi wasa da damarsa. Akwai kuskure a jan lokaci har haka. Watakila kuma rabon Aliyu ce. Ina muku fatan alheri." Ya dubi Ramla da fuskarsa wacce ta yi narai-narai. "Matar mutum Ramla, matar mutum.." Daga haka ya juya ya bar wurin. Ramla ta tsaya kamar wata mutum-mutumi. Kafaɗarta aka jijjiga. "Ke dillah can! Mene hakan? Waye shi? Ko kin manta da sanya ranar da ke kanki? Ke Usaina waye shi?" Duk Nafisa ke wannan kalamin daidai sadda suka ƙaraso, zantukan ƙarshe sun sauka saman kunnuwansu. Tuni ta soma tafiya kanta a ƙasa, tana ji Usaina na basu labarin abinda ya faru suna jan tsaki da kiran kwalelansa. Can kuma ta ji suna koɗa iya ɗaukar wanka da kuma kyan da Allah Ya mishi daidai gwargwado. Ta shiga tariyowa. Milk shadda ya sanya da aka yiwa aiki daidai da zamanin, ya dora hula brown da ratsin milk din. Dogo ne don har ya fi ta da kaɗan, yana da hasken fata. Tafiyarsa ma kadai za ta burge mutum. Yana da ɗan duhun lebba, gashin kansa a cike luf-luf wanda ya taho har gefen fuskarsa ya haɗe da ɗan ƙaramin gemunsa. Lafuzzan Aliyu ma kadai abin burgewa ne. Murmushi ta yi wanda ya taho tare da hawaye, ta yi azamar sharewa lokacin da Maryam ta dafa kafaɗarta. Ta kai duba gareta. "Ina za ki?" Sai sannan ta waiga ta gansu tsaye a ƙofar gidan yayinda ita kuwa ta ɗan yi gaba. Tabbas tunanin Aliyu ba zai kasheta ba. Ta yarda matar mutum kabarinsa don haka ta haramtawa rai da gangar jikinta tunaninsa tunda har shima ya fahimci Hilal ne zaɓin Allah a rayuwarta, kamar yanda shima ya samu daidai shi. 'Allah Yasa hakan kake nufi.' Ta furta a ƙasan ranta. Sun wuni cur a gidan Kawu Kabiru tare da iyalinsa, tun Ramla na ƙin magana da faɗawa tunani har dai ta yi watsi da komai sai dai ta kasa yakice kalmar Ina sonki da Aliyu ya furta. Da zarar ta tuno a karon kanta sai ta saki murmushi. Sai yamma suka bar gidan. Haka ta ci gaba da rayuwa gidan kakanninta tare da su Jidda, duk kuwa hakan bai tafiyar da tunanin Aliyu ba. Abinda ke tsorata ta bai wuce yanda so da kaunarsa ke neman rinjayar zuciyarta ba. Har yakan maida tunanin Hilal gefe guda ya ajiye. Sai da ya rage sauran kwanaki uku su koma makaranta sannan duk aka watse kowannensu ya koma gidansu, nan ma ji suke kamar kar a rabu. *** "Wai ke ba za ki buɗe kofar ba? Me kenan hakan? Ba'a isa a faɗamaki ki ji ba?" Muryar Maman twins ta bugi kunnuwanta, ta share hawayenta ta tattara hotunan ta maida mazauninsu sannan ta bude kofar fuska a haɗe. Shigowa ciki Maman Twins ta yi tana fadin "Allah Ya shiryamana ke Ramla, bansan sadda za ki rabu da wannan bakin ran naki ba. Haba jama'a! To sai ki fito Hajiya na nemanki." Ta miƙe ta bi bayanta zuwa falon. Hajiya sosai ta buɗe mata wuta kan ba ta son irin haka, dole ta ba Hajiyar hakuri itama Rafee'ah ta bata. Kafin su bar gidan sai da ya kasance komai ya wuce kamar ba su yi ba. *** Kwanci tashi asarar mai rai, cikin ikon Mai Duka bikin A'isha ya taho gadan gadan, ana saura sati ƴan Daura suka dinga cika gidan. Wasu a can Yakasai wasu kuwa anan wurin Hajiya. Ana saura sati a sanya A'isha a lalle Ramla ta ɗauki katukan daurin aure da na wuni ta kai ofishinsu. Ranar da ta kama Asabar kuwa, takanas ta shirya yara sai gidan Muhibbat wanda daga nan zasu wuce gidan Ramla rabon kati. Mutane biyu masu muhimmanci a 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem 07) Daga ita sai Affan suka fita. Unguwar Gwammaja nan suka soma nufa gidan Muhibbat don ta tabbatar idan ta shiga gidan Amrah za ta ɓata lokaci, ko ba komai an dade ba'a hadu ba dalilin tafiyar da Amrah ta yi zuwa Lagos tare da Maigidanta wanda rabin aikinsa a can ne. "Don Allah ina iya ɗaukar fasinja?" Muryar ɗan sahun ta katse tunaninta, ta kai duba ga wanda ke tsaye shima yana kallonta yana jiran amsa, abubuwa da dama hakan ya tunamata, ta daure ta dubi mai adaidaita fuska a haɗe. "Ba haka muka yi da kai ba. Ko ka mance shata na ɗauka?" Kafin mai adaidaita ya ce wani abu mutumin ya kauce gami da bata hakuri. Wannan tasa ɗan sahun fisgar abin hawar da alama ransa bai mishi dadi ba. Ta ƙara riƙe Affan kar ya tuntsira ba ta ko damu da yanda ɗan sahun ke shirga uban gudu ba. Hankalinta ya tafi ga tunani. Meyasa abubuwa da dama suke ƙin ɓacewa daga kwanyarta? Ba ta jin har ta mutu za ta mance da Aliyu. ***    _*ABIN ƁOYE*_ Tafiya na kara yin nisa, makonni na shuɗewa zuwa watanni, har ta kai lokacin da Ramla suka kammala aji na hudu a Sakandire suka wuce SS2 kai tsaye. A wannan lokacin idan ta ce ta huta daga tunanin Aliyu tasan ƙarya ne. Motsinta da komai ya zama shi, ramarta na tada hankalin Hajiya. "Na tsammaci ko kujiba-kujibar bikin Rafee'ah ne ke ramar da ke yanzu kam na tsorata. Ki fadamin mene damuwarki? Ko ba ki ga yanda kika bi kika lalace bane? Idan ma tunanin aure kike ki tattara ki ajiye a gefe tunda sanin kanki ne Abbanki ba zai aurar da ke ba sai kin kammala Sakandire. Wannan ai shirme ne. Kalli yanda ko abin kirki ba ki yi ba a jarrabawa, ni ban ga amfanin wayar da Abbanki ya siyamaki yanzu ba, na tabbata kuma zai kara dauke hankalinki ne kurum daga karatu!" Duk wannan bambamin da Hajiyar ke yi, Ramla na zaune tana fidda hawaye ga wayar da Abba ya damƙamata Nokia mai tocila rike a hannunta, ƙala Hajiya ba ta ce ba sadda aka yi budurin ba ta wayar sai bayan fitar Abban ta ke fitar da abinda ke ranta. To itama ta gaji! Ta gaji da tunanin mutumin da ba ta san inda za ta ƙara ganinsa ba. Tunaninsa na taɓa walwalarta, ya kasance ba ta murna da kiran Hilal, ba ta murna idan ya yi mata aike ta hannun Yaya Munir. Yakan tambayeta ko lafiya ta ce ba komai. Duk a rashin sanin cewa yanzun ba shi take da muradi ba, soyayyar wani can da ba ta san inda za ta ganshi ba, ya fi komai dagula lissafinta. "Shikenan, kin yi shiru ina magana kin rabu da ni! Tunda haka kika zaɓa ki yi ta zama da kuncinnaki, sai dai wallahi kin ji na rantse muddin wannan shekarar a zangon karatunki na farko (1st term) naga ba ki tsinana abin a zo a gani ba, da kaina ba Muniru ba, zan kwace wayar na kuma hanaki fita. Shashasha kawai!" Ta dawo nutsuwarta sa'ilin da Hajiyar ta miƙe za ta fice daga falon. Da sauri ta ƙarasa ta sha gabanta, kallon da Hajiyar ta mata sai jikinta ya yi sanyi, ta sunkuyar da kai tana ci gaba da kuka a hankali. Tsakanin ɗa da uwa sai Allah, ba ta san sadda ta ja hannunta ba suka zauna saman kujera. "Menene Ramlatu? Kun samu matsala da yaron ne?" Ta na nufin Hilal, ta tsinci kanta da gyaɗa kai. "Amma mun shirya, don Allah kiyi hakuri Hajiya. Na miki alƙawarin chanjawa, wannan karon ba zan ƙara ba ku kunya ba a karatuna." Jikin Hajiya ya yi sanyi, nan ta shiga yi mata nasiha akan kar ta sake ta sabarwa da kanta haka. "Don kin yi faɗa da mutum bai zama dalilin da za ki sauya rayuwarki ba. Kenan ko kun yi aure haka za ki dinga yi? To kul! Shi rashin jituwa idan an yi nan take ake yiwa juna sulhu kuma a nemi gafarar juna. Idan ba mai fahimta bane sai ki bari idan ya huce daga baya ki nemi gafararsa. Wannan damuwar bana so, kar ki ƙara." Ta amsa da to gami da godiya. A ranar ta yi kokarin sauyawa kuwa, ta rage kulle kanta a ɗaka tana tunane-tunane, gidan yanzu daga ita sai Auta A'isha tun bayan bikin Rafee'ah. Hakan da ta yi sai ya kwantar da hankalin Hajiya. Ita kuwa duk abinda take daurewa take gudun matakin da Hajiya za ta dauka a kanta.    Yau wunin gidan Rafee'ah zasu yi tare da Auta A'isha. Tun safe suka shirya Abba ya ragemusu hanya ya basu kudin mota. Sai da direbansa ya taremusu abin hawa drop har gidan Rafee'ah sannan suka rabu. A hanya suna tafe tana yin game na snake a waya, kusan a lokacin kaga budurwa da irin wayarta ba karamar babbar yarinya bace. Wannan ta sa take latsawa cike da jin ta isa. A daidai junction suka tsaya, ba ta ankara ba ta ji an zare wayar daga hannunta. Cikin razana ta juyo har tana shirin fasa ƙara, yana kan mashin yake dubanta  yana dariya. Kirjinta ya buga da ƙarfi, ta kasa gaskata cewa shi ɗin ne. Hakan ya sa ta lumshe ido ta kara budewa. Ya sauya, ya yi wani fresh, wannan karon ƙananan kaya ne cikinsa. Bakin jeans da riga green wanda ya karɓeshi sosai. "Barkanki." Ta yi kasa da kai gami da amsawa murya na rawa. "Yauwa." Ta ɗago ta mika hannu. "Bani wayata." Ta ƙarashe a kasalance, sai dai wani irin annashuwa take ji can ƙasan ranta, ta kasa daina murmushi. Kullum adduarta Allah Yasa ta ƙara ganinsa. "Allah Ya karɓi addu'ata, ba zan bari ki tafi ban da lambarki ba." Maganarsa ta katse tunaninta, ta saci kallonsa ya shiga latsa wayarta. Daidai nan aka basu hannu ya ce ma ɗan sahun su tsallaka sai su yi parking. Ba musu akai hakan. Ya danna kira wayarsa ta dauki ƙara, ta saci kallon wayar, wata ƴar ƙaramar waya ce Lg flip mai murfi ya fiddo. Wayarta ya miƙamata gami da kasheta da kallo. "Nagode, Allah Ya kaiku lafiya." Daga nan ya ja mashin ɗinsa sabo fil ya yi gaba, suma suka wuce. Ranar wuni ta yi cikin annashuwa, ji take kamar an mata albishir da aljanna.   Tun daga wannan ranar suka yi wani irin ɗinkewa da Aliyu. So da kauna mai karfi ya shiga tsakaninsu, duk kuwa a sannan ta ji cewar ya yi aure har tsawon sati hudu. Kishi mai tsanani take yiwa matarsa kuma ƴar uwarsa MUHIBBAT.   Duk yanda ta kai ga ɓoye alaƙarta da Aliyu abin ya ci tura don tuni Abin Ɓoye ya fito fili.   *** "Gwammaja daidai ina?" Muryar ɗan sahun a zafafe ya katsemata tunanin baya da ta faɗa. Ta sauke ajiyar zuciya tana mai gyara Affan da ya fara bacci ta hau yin kwatance har suka isa kofar gidan Muhibbat. Ta sallami ɗan sahun ta tashi Affan, ya kuwa farka suka kama hanya.   Gidan Muhibbat take karewa kallo, gani ta yi kamar koyaushe ƙara ƙawatashi ake da sabbin furanni da kuma abubuwan ɗaukar ido. Da sallama suka sanya kai falon.   Matar gidan ba ta nan sai masu yi mata hidima su biyu sun shantake suna kallon fim na  AfricanMagic Hausa. Sai kuwa yaran Muhibbat su biyu a saman kujera wasa. Babban zai yi sa'ar Ansar yayinda ƙaramin ya girmi Affan da kadan. Fuskarta ba baƙuwa ce garesu ba, aka gaisa, Mujahid da Ammar suka gaidata. Fuska a sake ta amsa kafin ta dubi Affan. "Ba gaisuwa?" Ganin haka ya sunne kai yana wangale baki. "Bari a kirata." Cewar ɗaya cikin masu aikin tana nufar sama, yayinda ɗayar ta mike ta nufi kicin. Toh kawai Ramla ta ce tana mai ƙarewa gidan kallo lokaci guda tana kara jinjina arzikin mijin Muhibbat. 'Kin manta itama daidai gwargwado suna da rufin asiri?' Wani ɓangare na zuciyarta ta tunatar da ita wacece Muhibbat. _*Mahaifinta Justice AbdulRazak Buba, tsohon alƙali ne a wata babbar kotu ta ƙasa. Ƴan asalin garin Kano ne gaba da bayansu, duk a zuriar Marigayi Malam Buba shi ne fitaccen mai arziki wanda sunansa ya shahara har wasu a zuri'ar kan ara su yafa. Babban family house ne wanda kusan duk ana tare wuri guda. Muhibbat ita kadai ce ɗiyarsa mace wacce yake so kuma yake matukar ji da ita. Ita ce kuma wacce kaddarar aure ya faɗa mata wanda a yanzun ya zama tarihi.*_ Ƙamshin turaren da ya mamaye falon ne ya ankarar da ita zuwan Muhibbat. Ta ɗago kai tana dubanta lokaci guda suka sakarwa juna murmushi mai nuni da tsantsar kauna da farin cikin ganin juna. A gefe guda kuwa kamanninta da ALIYU take ƙara gani zahiran wanda har Muhibbat kan rikiɗemata zuwa kamannin Affan wanda ke matukar kama da mahaifinnasa. Fara ce mai matsakaicin tsawo, tana da siririn jiki sai dai ba mai muni ba. Gashinta luf-luf ya kwanta har saman goshinta. Mace ce mai hakuri kuma mai yawan fara'a. Ba ta daukar lamura da zafi. Cikar kamala dai Muhibbat ta kai, jaruma ce har gobe a idanun Ramlat, yayinda bata fasa  yiwa kanta kallon zalamammiya kuma mai laifi a idanun Muhibbat ba. "Kai Madam, kinga yanda kike ƙara mulmulewa kuwa? Anya nan gaba za ki nuna kin san mu?" Muhibbat ke wannan kalamin sa'ilin da take zama da kamo hannun Affan, lokaci guda tana ƙarewa Ramlat kallo cikin dariya. Harararta ta yi da wasa gami da jan guntun tsaki. "Kin ji wata magana, ina hutu a wurina nida koyaushe ina hanyar Ofis? Hutu ai sai ku Hajiyoyi." Suka dara. "Ba ki kyauta ba, shi ne kika bar Ummina da Ansar a gida? Wannan autan na ƙagu ki yi aure a mishi ƙanwa ko ƙani mu ga ta autantaka." Taɓe baki Ramlat ta yi sa'ilin da take kurɓar ruwan da aka ajiyemata. "Ke kika san wannan, ni kam ai na rufe babin aure har abada." Jiki a sanyaye Muhibbat take dubanta. "Kar ma ki fara wannan tunanin, shi aure lokaci ne. Idan ya zo ko bakya so sai mun wanke ki mun kaiki. Kuma da yardar Allah ma kina so za'a yi shi. Duka-duka ashirin da nawa kike?" Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, ta basar da zancen ta hanyar janyo jakarta. "Kar ki dameni da wannan zancen, ni karɓi wannan." Ta miƙa mata envelope da ta ciro, ɗaya na kamu da yini ne da za'a yi a Meena Event Centre yayinda ɗaya na dinner party ne da ango ya shirya a Marhaba. "Allah Sarki mai sunan Mamana za'a fada kwaryar manya, toh Allah Yasa zamu gani. Ya kawo na ƴan baya. Ko Affan?" Ta ƙarashe gami da rungume Affan wanda tuni ya sake yana dariya. Murmushi Ramla ta yi, zuwa yanzu masu neman ta yi aure dariya ma suke ba ta wasu lokutan. "Akwai fa taro da za'a yi na family, har jikoki gaba daya. Ba ki da labari?" Ta girgiza kai. "Ba wanda ya fadamin, to wa zai fada?" Harararta Muhibbat ta yi, "Ai dole a fada ko don yarannan. Ina jin nan da sati biyu zasu gudanar. Zan biyo mu tafi tare da yarana." "Toh." Shine kawai abinda Ramlat ta ce, ba ta wani jima sosai ba ta mike. Duk yanda Muhibbat ta so ta tsaya ta ci abinci ta nuna akwai wuraren da za ta je kan ta koma gida. Dole Muhibbat ta cika Affan da kayan zaƙi kala-kala ta takomata har farfajiyar gidan suka rabu. A hanya tana tafe tana tunaninta. So da kauna tsantsa idan an ajiye na ƴan uwantaka a gefe, Muhibbat ta nunawa Aliyu. A yanzun sai soyayyar ta koma kan yaransa. Har ta tsayar da adaidaita suka yi cinikin unguwar Gaida ba ta bar tuna tarin laifuffukan da ta aikata ga Muhibbat din ba. ***    *Son Zuciya* Zaune take ta zuba uban tagumi ta yi shiru, kai ta ɗaga tana kallon ƙaton enlargement na hotonta da Aliyu. A ƙasa an rubuta sunansu. Aliyu Abdussalam Buba da Muhibbat Abdulrazak Buba. Za ta iya cewa ita ke son shi, son da take mishi ya hanata ganin aibunsa.   Tun suna yara suke shakkar haɗa inuwa da shi, don ko kusa ba ya wasa da su. Mutum ne wanda ya fita zakka a zuri'arsu, don kuwa a iya saninsu Aliyu giya ce da kwaya kawai za'a ce yana sha su ƙaryata. Ya soma shaye-shaye a ɓoye ba tare da sanin mutan gida ba. Hakan ya samo asali ne daga manyan ɓatattun yaran masu kuɗi da yake abota da su a sakandire, Innarsa Amina bafulatanar Gombe, mace mai hakuri wacce ba'a taɓa yin kace nace da ita ba duk kuwa da tarin facaloli da kuma kishiyoyinta biyu da take tare da su. Aliyu ɗa na fari a wurinta hakan yasa koda wasa ba ta sakewa da shi. Kusan rayuwarsa ya yi ta ne a hannun kakarsa Abulle matar Marigayi Malam Buba. Da wuya ka ganshi cikin gidan Mahaifinsa Abdussalam sai dai sashin Abulle wacce ta dauki son duniya ta ɗora akan Aliyu. Wannan tasa a duka yaran Malam Abdussalam,  Aliyu ne kadai ke makarantar manyan masu kuɗi irin na yaran Justice bisa jajircewarsa akan shi ba zai yi makarantar da za'a rainashi ba. A sannan sai da Mahaifinsa ya ji kamar ya mishi duka don shi mutum ne mai zuciyar nema da kuma son kyautata iyalinsa da daidai karfinsa. Yana aiki a ma'aikatar  ilimi ta gwamnati. Mahaifiyar Aliyu ita ce matarsa ta biyu. Yana sonta da kuma tausayamata ganin ita kadai ce ya auro daga nesa.    Abulle ce ta dage Justice ya mayar da Aliyu makarantar yaransa, wannan abu ba ƙaramin bakin jini ya janyo wa Aliyu wurin iyalan Justice ba idan ka cire Muhibbat da ke jin kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don dadi. A hankali bayan sun tasa, ta tattara ta koma gidan Abulle da zama itama kawai don ta dinga sanya Aliyu a idanunta. Ranar farko da ta soma ganinsa a makaranta yana shaye shaye da abokansa, ranar ta gigita. Za ta gudu ya kamata ya fallamata mari dama da hagu akan yanda ta gani ta binne a nan kar ta sake ta fadawa wani ko wata a gida. Wannan ta sa ta kama bakin dole. Abin mamaki soyayyar da take mishi bata ragu ba sai ma tausayi da yake ba ta. Kewarta da yayyunta suka yi har ma da iyayenta ta sa Justice da kansa ya zo ya lallaɓa Abulle dakyar ya tafi da ita. Abulle ta rantse kaf a jikokinta Aliyu da Muhibbat ne ƴan gaban goshinta.   Aliyu na aji na biyu a jami'a kowa ya fahimci mummunan ɗabi'ar da ya faɗa na shaye-shaye, karatun ma ba ya bar maida hankali, kullum yana daki yana bacci. Taro kuwa na family an yi akan Aliyu ya fi a kirga, Innarsa kan shiga daki ta yi kuka son ranta. Shi kadai namiji da Allah Ya bata sai kannensa mata uku, sai dai ya zamemata wani tambari wanda ake faƙewa da shi a ci mutuncinta. Mahaifinsa kuwa ya ce sam ba zai yarda ba sai dai yaronsa ya koma gabansa. Wannan ne silar komawarsa gidansu. Duk wannan bai sa Muhibbat ta fasa so da tausayin Aliyu ba, takan rufe kanta a daki ta ci kuka ta kuma bishi da kyakkyawar addu'a akan Allah Ya shiryeshi. Rayuwa ta yiwa Aliyu zafi yakan ji kamar ya yi hauka duk ranar da Babansa ya kulleshi a ɗaka ya hanashi fita ko nan da can. Makaranta dama ba labarinta don tun ranar da aka rabashi da gidan Abulle ya zuciya ya ce ya fasa karatun gaba daya. Ranar da ya ɓalle ya fice daga gidan, bai koma ba sai da ya yi mankas. A ranar Innarsa ta yanke jiki ta fadi. Tun daga wannan rana ba ta ƙara lafiya ba. Ciwon Innarsa ya sanyaya jikinsa kadan, duk da a ganinsa matar sam ba ta damu da shi ba hakan bai mantar da shi matsayinta wurinsa ba. Bayan farfadowarta ya daukar mata alkawarin ya dainawa, ba ta ce mishi uffan ba har ya fice. A hankali kuma ya dinga ɓoye munanan halayyarsa, ya maida turare abin fesawarsa, ba ya taba yarda ya zauna na awanni da yan uwansa gudun kar a ga sauyawar leɓɓansa adalilin shan taba. Sai dai ya zama masifaffen karfi da yaji, ya daina ragawa duk wata mace da za ta gasawa Innarsa magana. Akwai ranar da ya kusan yiwa Amaryar babansa duka duk don ta zagi Inna a fakaice. Wannan ya fusata Baban ya ce ya bar mishi gidansa. Zuciya irin ta Aliyu ya sanyashi haɗa komai nasa ya koma gidan Abulle. Ba abinda ya boyemata har da karin gishiri, nan kuwa ta tara meeting ta gargadi kowa akan takurawa Aliyu da ake. "Duk wanda ba zai bi shi da Addu'a ba kar ya zageshi ya kara bin duniya. Kai kuma Abdussalamu ba ka isa ka rabashi da gidan ubansa ba. Ko yau yaro ya ga dama zai je. Don kunga an samu ya soma gyaruwa shikenan kuma sai ku kara sanyashi ya bi duniya? Ke kuma Amarya ki ci gaba, idan dai za ki ci gaba da gasawa Amina magana, yaron nan ba zai fasa kirɓarki ba. Shashasha." Nan yaran suka shiga ba ta hakuri gami da nunamata kuskuren Aliyu cikin sanyi. Aliyu ya ba Amarya hakuri aka ce ya ci gaba da zama anan gidan Abulle. Bayan watsewar surukan da jikoki, Abulle ta nemi shawarar ta yanda za'a inganta rayuwar yaron tunda ya ƙi boko. Nan take Justice ya kawo shawarar a dorashi kan kasuwanci. Ba musu kowa ya yi na'am. Justice da kansa ya dauki nauyin budewa Aliyu shago da komai. Nan kuwa Abulle ta yi ta sanyamasa albarka daga nan aka tattauna batun auren yanmatan da suka isa aure a zuri'ar da zarar sun kammala Sakandire don a sannan suna ajin karshe. Budar bakin Abulle ta ce. "Banda Muhibbat, na yi mata miji." Kalamanta sai da yasa kirjin Justice bugawa, tsoransa kar ya zamana abinda yake gudu ne zai afku. Duk yanda suka so jin waye mijin Muhibbat ta ƙi basu fuska. Asalima goronta ta hau tauna ta ce su mike su bata wuri ta sallame su. Jiki ba kwari dai Justice ya tafi. Ita kuwa Abulle tun wani dare da ta kama Muhibbat na kallon hoton Aliyu tana kuka ta ci alwashin sai ta auramata shi. Ba ta bari ta ganta ba ta juya ta ci gaba da baccinta cike da farin ciki da tausayin yarinyar. Cikin luɗufin Allah zaman kasuwa ya karɓi Aliyu, dakyar yake ajiye wasu kudaden don shi da za'a bar shi ya yi facaka zai fi son hakan. Bai fasa shaye-shayensa ba sai dai ya fi yi da dare wanda daga ya sha ya ɗan yi tamɓelansa zai ɓige da bacci. Taba kuwa ko a kasuwa zuƙarta yake don zuwa lokacin bai dauketa abar tashin hankali ba. A wannan lokacin ne kuma Inna ta tashi lafiya kalau, daga baccin rana ta gamu da ajalinta, ta rasu. Mutuwarta ta girgiza jama'ar gidan musamman kishiyoyinta wadanda suka cika da dana sanin zaman gaba da hassadar da suka yi da ita. Batun mijinta kuwa ba'a magana, Abdussalam ya shiga tashin hankali marar misaltawa. A gefen Aliyu da yaran Innar mata suma ba'a magana. "Ka ji tsoron Allah." Shi ne abinda Innar ta fi yawan fadamasa a kalamanta masu tsawo, sai a sannan ya san yana son mahaifiyarsa halinta na banzatar da lamuransa kawai ya tsana. Yan uwanta daga Gombe duk sun zo. Mutuwar Inna ya karawa Abulle da Muhibbat tausayi da son Aliyu. Suna kammala Sakandire magabata suka yiwa Muhibbat caa akan ta fiddo da miji, ita kuwa ta kasa zaɓen ko ɗaya saboda Aliyu. Aka yi sa'a koda Abulle ta tari Aliyu da zancen Muhibbat don jin ta bakinsa sai ta ga ya hau murmushi, nan take ya nuna ya amince don dama ya jima da sanin yarinyar na sonsa. A cewarsa ko ba komai zai ƙara martaba a idon duniya kasancewar mahaifinta wani ne kuma ɗan uwan mahaifinsa. Tashi ɗaya kowa ya ce bai yarda da auren ba, Justice dai ya yi alkunya ya yi shiru, daidai da mahaifin Aliyu bai amince a ba Aliyu auren Muhibbat ba. Ita kuwa Abulle ta rantse ko bayan ranta aka ƙi aurawa Aliyu Muhibbat ba ta yafewa yaranta ba. Kuma bakinta sai ya bi su, wannan ya tashi hankulansu, a dole suka amince. Justice ya yi mamakin murnar da Muhibbat ta nuna. A gefe guda Mamarta Saudatu na cika da batsewa. "Dama kina sonsa?" Ta riga Justice jefamata tambaya, ta kara sunkuyar da kai tana murmushi kafin ta mike a guje ta nufi daki. Saudatu ta dubi Justice dake hamdala da alama abin ya mishi dadi. "Kana nufin ka amince da auren yaron da ya fitini kowa a dangi da ɗiyarka kamila?" Yayi murmushi. "Allah Ke shiryawa, kuma Ya shirya Aliyu sai dai a ci gaba da yi mishi addu'a. Farin cikin Muhibbat ya fiyemin komai, fargabana kar ya kasance ba ta sonsa. Tunda har tana sonsa shikenan, Allah Ya tabbatar da alheri. Ba zan ƙi bin umarnin Mahaifiyata ba." "Tabɗijam!" Abinda Mama ta furta kenan. Rigima sosai ta tayar akan lallai sai dai a fasa auren, karshe Justice ya zuciya ya fita harkarta, har yaji ta yi da ta gaji ta dawo ɗakinta. Abulle ta rantse ba don darajar ta haifomata sanyin idaniyarta Muhibbat da sauran jikoki ba da sai ta saka an saketa. A dole ta dangana aka yi auren Aliyu da Muhibbat wanda alokacin ya yi nisa da son Ramlat. Muhibbat ta sauke ajiyar zuciya, ta kara maimaita sunan Ramlat da mijinta yake yawan  kiranta da shi a shimfiɗa. Hannu ta sanya ta dauke hawayenta. Kauna da son Aliyu abu ne da ta fara tun ba ta mallaki hankalin kanta ba. Ba kuma ta jin za ta daina. Addu'a za ta dage da yi har Allah Ya fidda Ramlat daga ran mijinta. Ba ta santa ba ko a hoto, ta dai santa a bakin mijinta. Takan yi mamakin yanda Ramla ke aminta su yi waya da mijin aure har cikin dare. Ta rasa gane SON ZUCIYA ne ko kuwa a'a? Fatanta Allah Ya karkato hankalinsa gareta su ci gaba da rayuwa kamar yanda suka fara a farko. *** *DAWOWA 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 08)        _*Dawowa Labari*_ A kofar gidan Amrah ɗan sahu ya ajiye Ramlat. Ta biyashi tana mai kama hannun Affan wanda duk ya ɓata kayansa da cakulet suka fara knocking. Aka bude, harararta Amrah ta yi. "Sai yanzu ko? Yinin kenan?" Ramlat na dariya ta juya. "Shikenan, bari mu juya daga nan." Da sauri ta kama hannunta ta maidota baya suna dariya. "Ni ban ce ba, yi hakuri." Suka shiga ciki suka zauna, nan take sanarmata sai da ta biya gidan Muhibbat. "Allah Sarki Muhibbat, matarnan akwai kirki wallahi. Ba ruwanta, kinsan babu ranar da ba za ta turomin gaisuwar juma'a ba." Murmushi Ramlat ta yi. "Ai wannan daban take cikin mutane ma. Allah dai Ya bamu ikon yin zumuncin mu ma." Amrah ta amsa da Amin. Ramlat ta shiga waige-waige. "Ke ina ƴata wai? Tun da kika ce min kun dawo ita nake son ganin yanda ta girma." "Tana wurin Mama na kai mata yaye. Abinda ya ban mamaki ko ciwon nono ban yi ba." Ramlat ta dara. "Kika sani ko wani cikin ya shiga? Tsarabar Lagos?" "Allah Yasa. Ai nikam ina so wallahi." Ba ta yi mamakin kalaman Aminiyarta ba don tun bayan aurenta sai da ta shekara biyar ba ta samu ciki ba sai yanzun. Mijinta Ɗahiru ya ce ba ita babu planning sai ta yi biyu. "Allah Ya kawo mai albarka toh. Nidai yanzu yunwa nake ji." Miƙewa suka yi a tare zuwa kicin Amrah na fadin. "Mutuminki ɗan wake nayi niyyar yi kuwa, na haɗa komai ki dora ruwa idan ya tafasa ki yi sakin bari na yanka mahaɗin." "To da ban zo ba fa?" Amrah ta yi dariya. "Ai kuma tunda kin zo din magana ta kare. Yi hakuri ki taimaka ban jin dadin jikin." Haka ta soma sakin ɗan waken tana yi suna hira. "Ni kuwa ina Hilal?" Tambayar Amrah ta tunasar da ita yanda suka yi a kwanakin baya, text ya yi mata akan ta sanyamishi rana da lokaci ya zo su tattauna abu mai muhimmanci sai dai ba ta yi karambanin ba shi amsa ba, daga ranar kuma bai ƙara nemanta ba. "Kamar ban kyauta masa ba, amma a wurina hakan ne daidai." "Me kika yi mishi?" Jin abinda Amrah ta ce yasa ta fahimci zancen zucin ya fito fili, nan ta bata labarin yanda suka yi.  Ajiye wuƙar hannunta ta yi ta juyo da mamaki ƙarara saman fuskarta tana dubanta. "Meyasa kike yiwa kanki irin wannan gangancin?" Cikin rashin fahimta ta ɗan dubeta. "Wane gangancin kuma?" Haushi da takaici ya kusan  kashe Amrah anan tsaye. "Tambaya kike Ramsy?  Ko kin manta na tunamaki waye Hilal? For all abinda ya faru bai sa ya juyamaki baya ba, bai kuma sa ya bar sonki ba, don me yanzu kin samu damar gyara laifukanki kike kokarin juyamasa baya? Allah Kike son yiwa butulci?" Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, ba ta ce komai ba ta juya ta ci gaba da sakin ɗan wake, sanin hali na idan ta ga dama ba za ta ce uffan ba yasa Amrah itama ta ci gaba da aiki sai dai ta kumbura kiris ya rage ta fashe. Dama sun saba irin haka tun yarinta. Ita kuwa sai da ta kammala ta wanke hannu ta jira ya dahu ta kwashe ba ta ko tsaya tambayar inda filas yake ba ta dauko. Sai da za ta zuba ne Amrah ta dakatar da ita. "Wannan na Daddy ne." Tana nufin mijinta, murmushi Ramlat ta yi don tasan ƙawarta ta shaƙa, ta fice daga kicin rike da plastic din da Amrah ta yanka kayan cin dan waken. Sai da ta soyamusu manja sannan ta fito itama. A falon suna zaune sannan ne Ramlat ta dubeta a nutse. "Tsaya don Allah ki saurareni." Amrah ta dakatar da zuba ɗan waken da take kokarin zubamusu bayan ta ɗibarwa Affan nashi ya ja gefe. Harararta ta yi. "Me kuma za ki cemin bayan kin maidani wata banza don kawai ina nunamaki abinda ya dace." Hannunta ta riko tana dubanta. "Kiyi hakuri, wallahi duk ba haka bane. Amrah yanzu ke a tunaninki da wane ido zan kalli Hilal na ba shi dama a karo na biyu bayan ni ce ummul aba'isin duk wani abu da ya faru a baya? Ko kin manta ba da Hilal kadai zan zauna ba? Akwai matarsa kuma akwai danginsa da babu ranar da zan goge bakin fentin da na yiwa kaina a idanunsu? So kike na bar wa ƴaƴan da zan haifa da shi abin gori? Yanzun ma wadannan din da ya na ƙare? Kin fi kowa sanin abinda ya faru, kuma kin fi kowa sanina Amrah. Da ace zan iya auren Hilal, da tuni yanzun wani labarin ake banda wannan. Amma bakin alƙalami ya bushe, zan iya yin aure ga kowane mutum a doron ƙasa banda Hilal. To balle ma auren babu shi a gabana yanzu, na gwammace na zauna na kula da yarana. Hakan zai fiyemin komai dadi." Tausayinta sosai ya kama Amrah, har ba ta san sadda hawaye ya zubomata ba, ita kanta uwar gayyar sai jin ɗuminsa ta yi saman kuncinta. Ta kuwa shiga yi ba kakkautawa. "Na cuci rayuwata Amrah, na cutar da mutane da dama wanda har gobe ban bar dana saninsa ba. Amrah har gobe ina tunanin bakin cikina ne sanadin mutuwar Abbana duk kuwa da irin rabuwa ta salama da amincin da muka yi. Ƴan uwana ba sa fahimtana, har gobe suna min kallon mai laifi a idanunsu. Ya zan yi ne wai?" Nan fa suka shiga kukan har Affan wanda ganin Mominsa na kuka shima ya shiga yi. Dakyar suka rarrashi kansu sakamakon ƙarar da Affan yake da kuka yana rirriƙe Ramlat. Komai da komai ya shiga dawowa kwanyarta, daga lokacin da ta saki jiki suka soma gudanar da soyayya mai karfi tsakaninta da Aliyu, daga lokacin ne komai ya faro asali wanda har gobe ta kasa goge *BAƘIN FENTIn* a zuƙatan masoyanta. ***    *BAƘIN FENTI* _*Komai yana da sila, komai da mafarinsa. Duk abinda bawa bai ɗora kan turba mai kyau da tsari ba, mafi yawan lokuta ƙarshensa nadama ne! Koda ace a haka kaddarar ta zo masa.*_ "Wai Ramsy me kike ne? Ki fito kina ɓata lokaci." Muryar Amrah kenan sa'ilin da ta ke kokarin shigowa dakin. Zuwa yanzu ta kai matakin da ba ta jin za ta ɓoyewa kowa a duniya sonta ga Aliyu. Wannan tasa ko bayan shigowar Amrah ba ta fasa amsa wayar a nutse ba ba ta ko damu da kallo da murmushin Amrah ba. "Kai wannan Hilal, shi ba ya  jin kudinsa ko? Daga Malaysia mutum ya kira a yi ta wayar fin sa'i biyu? To nidai don Allah ya kyalemin ke ai daya, idan ba haka ba wallahi zamu yi lattin." Ba ta da niyyar ba ta amsa, ta fahimci ba ta gane wanda suke wayar ba, ko ma ta ce ba ta sanshi ba. Daga dayan gefen Aliyu wanda ke zaune a falon Muhibbat yayinda ita kuwa ke kicin tana shiryamusu abincin rana ya ɗan hade fuska kamar tana kallonsa. "Baby waye Hilal? Baby ashe ban Kai darajar da har yanzu za ki iya sanar da mutane ni din kike so ba ba wani banza ba? Watanni goma da soyayyarmu wanda ya fi karfin na wadanda suka kwashe shekaru goma suna yi shine har yanzu ban samu karɓuwa ba? Sai anjima." Ya katse wayar gaba daya yana fitar da huci.  Fitowarta kenan daga kicin, ta ji dukkan abinda yake fadi, sai dai ta yi kamar ba ta ji ba. Ranta na ƙuna kamar koyaushe, ta haɗiye kwallar dake barazanar tona abinda ke ranta. Ganin ya ɗan kalleta ya kauda kai ya ja tsaki ya sanya ta kakalo murmushi ta nufi inda yake zaune a darare. "Yaya na kammala girkin." Ya yi mata kallon sakara. Ta sauke kwayar idanunta, a duniya idan da abinda ta tsana ya biyo bayan kallon wulakancin da Aliyu ke mata a lokuta da dama. "Sai aka ce miki yunwa nake ji? Ga jaki kin ajiye? Mtsww!" Ya ja dogon kafin ya mike tsaye ya sa kafa ya ture Centre Table a zuciye har yana kifewa, ɗan flower vase din dake kanta na ado shine ya fashe. Bai ko waiwaya ba ya sa kai ya fice daga gidan. Ta zubawa ɓarnar da ya yi mata ido, ko ba komai kudi aka sa aka siyamata. Ba abinda ta nema ta rasa na ƙawata gida wanda iyayenta basu yi mata ba, yayyunta maza kuwa ba wanda bai ba ta gudummuwarsa ba duk kuwa da irin tsanar da suka yiwa Aliyu. Kuka sosai ta shiga yi tana tattarawa, Aliyu bai damu da ita ba. Ta hakikance ba ya sonta, ba kuma ya tausayinta. Ita kullum ke kwana da tashi da bakin cikinsa, ga so da tausayinsa wanda ke sanyawa ta ɓoye aibunsa a idon danginsu har a gaban Abulle wacce koyaushe cikin sanyamusu albarka take. Burin Abulle ta ga ɗa ko ƴarsu sai dai har a sannan Allah bai ba ta ciki ba. Ba kuma ta zargin Aliyu da komai. "Allah ga mijina, Allah Kai ke shiryawa, Allah Ka shiryamin shi. Ka karkato da hankalinsa gareni." Ta furta a fili tana mai daga hannu gami da kuka, sannan ta shafe fuskarta ta ci gaba da tsince ɓarnar da ya yi.       A gefen Ramlat hankalinta idan ya yi dubu to ya tashi, hawaye take tana kara dialing lambarsa sai dai amsa daya ce, a kashe. Wannan ya tashi hankalin Amrah. Ta dubeta a gigice gami da dafa kafaɗarta. "Ke, meyafaru da Hilal din? Me yace maki? Mun shiga uku." Ambaton Hilal da ta ƙara ya farkar da Ramlat. Ta buge hannunta a saman kafaɗarta ta hau masifa. "Hilal Hilal! To hell with him! Haba! Sai kiramin Hilal kike, a sanadinsa kin sa Aliyu ya yi fushi da ni! Ya kashe wayarsa bansan kuma me zai aikata ba! Dole ne zuwa walimar?! Ba zan je ba! Nace ba zan je ba ko za ki kaini dole?! Wallahi zuwanki bai min rana ba! Ni ki tafi kawai ki rabu da ni!" Yanda take rufe ido tana zuba masifa iyakar gaskiyarta shi ya fi komai ba Amrah mamaki. "Aliyu kuma? Waye hakan? Yanzu akan wani banza Aliyu kike min masifa?" Ai kiran Aliyu da banza shi ya kara tunzura Ramlat. Ta nuna ta da yatsa. "Kin yi na farko ya zama na karshe Amrah don wallahi ba don ina ganin mutuncinki ba sai na gasamaki abinda zai miki zafi a rai! Aliyu ya fi karfin ki kiramin shi da banza! Kika kara kuma Allah Ya isa! Ba zan je walimar ba ki tafi ki kyaleni! Aliyu shi nake so kuma da iznin Allah shi kadai ne mijina anan duniya!" Daga nan ta juya a fusace ta soma cire kayanta tana tsaki. Amrah ranta ya dinga suya har bata san sadda ta shiga hawaye ba. "Akan wani Aliyu kikemin Allah Ya isa? Idan kin kara ganina a gidanku kimin abinda ya fi haka." Daga haka ta juya ta fice. Allah Ya taimaka Hajiya na wurin Abba, A'isha kuwa kallon cartoon  da take a tashar Spacetoon ya dauke hankalinta. Ita kuwa Ramlat ko a kanta, tashin hankalinta fushin Aliyu. Ta kwanta lamo tana fitar da hawaye, text ta shiga aikamasa kashi kashi. _*Sweet na tuba don Allah Ka yafemin. Sweet fushinka barazana ne ga lafiyata. Wallahi sweet kai kadai nake so, Kar ka manta na san da zaman Hilal din amma nake sonka." _*Wallahi Sweet Aliy zuciyata za ta buga. Wallahi har fada muka yi da Amrah a kanka. Ka yafemin. Wallahi don ba ka yanda na ci mutuncinta ba.*_ _*Sweet Aliy har walimar ban je ba saboda kai. Na kasa samun nutsuwa. Sweet Aliy ka yafemin ka bude wayata. Na maka alkawarin fadawa kowa kai nake so. Ka ji? Kuka fa nake. Kaina ma ciwo yake*_ Haka ta yi ta rubuta malamai kashi-kashi tana aikawa sai dai duk ba ya tafiya adalilin wayarsa a kashe. Ta kuwa ci gaba da rusa kuka, dakyar ta samu ta mike ta yi alwalar la'asar ta shiga sallah. Tun tana cikin sallar ta ji wayarta na kara, sallamewa kawai ta yi ba ta ko ida ba ta nufi wayar a guje. Ganin mai kiran ya sa ta ɗagawa da sauri ba tare da ta jira ya ce ba, ta ce. "Sweet Aliy ka yafemin don Allah, na tuba wallahi ba zan ƙara ba." "Zan yafemaki Baby amma sai kin fito na ganki. Ina nan bayan layinku. Ba zan iya bacci ba idan ban sanyaki a ido ba." Wani dadi ta ji a ranta, "Yanzu zan zo Sweet, ban minti biyar." Sallar da ba ta yi ba kenan ta bar shi a sai ta dawo, nan da nan ta shafa hoda ta sanya lip gloss, kayan zuwa walimar da ta cire su ta mayar. Ta ja mayafinta, sai da ta kama kofa za ta fice daga dakin ta ji faduwar gaba, me Amrah ta ce ga su Hajiya kafin ta fita? 'Ko me ta faɗa ita ta sani, ke dai kar ki ƙara laifi wurin Aliyu.' Wani bangare na zuciyarta ya ba ta shawarar da nan take ta dauka. A hankali ta fito tana ɗaga labulen da ya raba dakunansu da falon, babu kowa sai A'isha da ta gaji da kallonta tana bacci. Hamdala ta yi ta fice da sauri. Tun kafin ta karasa a hangoshi tsaye gaban mashin ɗinsa. Ya haɗe cikin shadda kalar sararin samaniya, babu hula a kansa sai dai ya yi kyau kwarai a idanunta. Kirjinta har wani bugu yake tsabar so da kaunarsa. Shima ya zubamata ido yana ji kamar ya saceta su gudu. "Ba ki kyautamin ba." Ya furta yana dubanta da shanyayyun idanunsa. Ta yi narai-narai da idanunta. "Ka yi hakuri don Allah." "Banda wannan, na hakura ai tun kallon farko da na miki na mance dukkan damuwata. Sai dai ba ki kyautamin da kika yiwa Aminiyarmu wulakancin da kika faɗa ba." Sai a sannan ta tuna da ta yi laifi, ta jinjina kai. "Haushi ta bani, banza fa ta kiraka." Ta fadi cike da wauta. Ya ji ciwon kalmar sai dai ya yi murmushi. Har a ransa ya ji haushin Amrah na kiransa da banza. "Kiyi hakuri, a kanki komai zan dauka zan kuma shanye muddin za ki zama rabona. Idan dai kina don farin cikina ku shirya a yau ba gobe ba." Ta shiga gyada kai. "Zamu shirya, zan je har gidansu na ba ta hakuri amma yau ba ta nan ta tafi walimar da na fadamaka zamu je dazun. Idan muka hadu a makaranta gobe zan bata hakuri ka ji? Ka yi hakuri don Allah Sweet Aliy." Ya dan lumshe idanunsa yana murmushi, murmushin da ke ƙara tafiya da imaninta. "Ya isa, shikenan ya wuce. Allah Ya kaimu goben. Da ban ganki ba, ba zan iya bacci ba." Wani sanyi da dadi suka lulluɓe zuciyarta. Nan da nan kuma suka shantake da hirar soyayya kamar kar su rabu. Sai dab da karfe shida suka rabu, ba ta iya tafiya ba sai da ta ga tafiyarsa sannan ta juya cike da annashuwa ta koma gida. "Sai yanzu ku ka dawo? Kun so ku yi dare." Abinda Hajiya ta fadi kenan, sai ta ji kaunar Amrah a ranta, wato dai ba ta sanarmata rigimarsu ba. "Eh Hajiya, ki yi hakuri." Hajiyar ta gyada kai tana kallon yanda ƴar ke zuba uban fara'a kamar wacce aka yiwa albishir da aljannah. Gudun kada Hajiyar ta watsamata tambayar da za ta kasa amsawa game da walimar, ya sanya ta saurin shigewa daki gami da faɗawa kam gado tana murmushi, Aliyu shi ne komai nata a yanzu, ba kuma ta jin har abada za ta bar shi ko me za'a yi, kuma ko me zai faru. Tunawa ta yi da sallar la'asar, da sauri ta mike ta faɗa banɗaki ta kara dauro alwala sannan ta tayar da sallar kusan ma a sallar banda murmushi da addu'ar Allah Ya sa ta zama matar Aliyu ba abinda take.        *** Muhibbat tun tana zuba idon ganinsa ya dawo gidan har ta gaji, ragowar abinci ranar ta juye ta miƙawa wasu makwaftansu marayu suka yi ta godiya.  Tasan ko ta bar shi Aliyu ba zai taɓa ci ba don a cewarsa ba ya son kwantai. Ba ta gaji ba ta ɗora sanwar dare, tuwon semo ta yi da miyar danyen kuɓewa, a gefe kuma ta yi farfesun kifi sai kunun aya. Komai ta jera inda ya kamata ta faɗa wanka, tana fitowa ta haɗe cikin doguwar riga ƴar kanti mai ɗankwali. Ko ba ado ita din kyakkyawa ce, hakan dai bai hanata daukar kwalliyar ba. Ta fesa turare ta fito falon tana addu'a cike da tsoron yanda zai shigo gidan. Fatanta kar ya shigo a maake kamar yanda ya saba. Jin karar mashin dinsa ya kara kaɗa hanjin cikinta. Ta miƙe da sauri ta bude kofa, a kan idonta ya yi parking ya shigo. Ta yi mamakin ganinsa cike da walwala. Itama sai ta saki fuska. "Sannu da zuwa." Ya riko ƙugunta yana murmushi kafin ya kai mata sumba a kumatu. "Yauwa Matar." Ta rufe kofar suka karasa falon zuciyarta kamar ta fito ta taka rawa tsabar farin ciki duk kuwa da tasan silar farin ciki nasa. Ramlat ce! Ganinta ya je ya yi hakan yasa shi sakarmata fuska sai dai hakan bai dakusar da nata jin dadin ba. Murmushin Aliyu da dariyarsa ma kadai abin so ne a wurinta. Ta taimaka ya yi wanka, ga mamakinta sosai ya ci abinci har suna hirar abinda ya shafi danginsu. Ga duk wanda ya ga Muhibbat ya san tana cike da farin ciki. A karshe ma ya ja hannunta suka shige ɗaka. Tun da ya soma sarrafata yake kiranta da suna Baby, wani sa'in ya ce Ramlat sai kuma ya ce oh i an sorry na manta. Har ya yi ya gama ba ta fasa fitar da hawaye na baƙin ciki, ta waiga ta dubeshi yana baccinsa hankali kwance, miƙewa ta yi ta tsarkake jikinta ta fito zuwa ɗakinta. Nafila ta yi ta zauna tana addu'a tana kuka. Sau da dama takan ji kishin Ramlat, sau da dama kuma takan ji ko ma mene Aliyu ne ya ba da fuskar da komai ke faruwa. Sai ta dinga kallon wasu abubuwan ba laifin ita Ramlat din bace. Ta gaji da kukan ta dau Kur'ani ta karanta sannan ta haye gadon ɗakinta sai bacci. Da asuba koda ta mike ta yi alwala ta shiga tashinsa. Wayar da yake ta tsaida ta. "Baby ki tashi mana ki sallah, ban san wannan baccin fa. Uhum? Ina magana kina min magagin bacci ko?" Kasa ƙarasawa ciki ta yi da sauri ta maida kofar ta rufe ta koma ɗakinta cikin hawaye. Mutumin da sai ya ga dama yake tashi salla idan ta tashe shi, shi ne har ya iya tayar da wata yin ibadar. Abinda bai taɓa yi gareta ba kenan, koda dai lokuta da dama ita keda kokarin tashi salla ta tayar da shi. Wannan karon kasa zubda hawayen ma ta yi ta haɗiye abinta.     *** _*Alhamdulillah, your future husband is back. I can't wait to see you. Love you.*_ Saƙon da ya shigo wayarta misalin bakwai na safe kenan, sa'ilin da take shirin fita makaranta, saƙon da ta tabbatar na Hilal ne. Wani makokon bakin ciki ya turnuƙe zuciyarta har ba ta san sadda ta ja tsaki ba. Sai me idan ya dawo? Ba dai za'a yi mata dole a auren wanda yanzun ta tsana ba. Haka ta kammala saka uniform ranta na suya, ba don Sweet Aliyunta zai kira ba da ta kashe wayar gaba daya ta bar ta a gida. Sai dai duk sadda ta samu dama takan ɓoye a banɗakin makaranta ko cikin aji idan ba malami ta kirashi su gaisa. "Ke kuma lafiya kike cin magani? Hala ba ki da labarin dawowar mutuminki?" Hajiya ke zancen cikin murmushi don tun jiya Munir ke fadamata Hilal ya dawo.  A dole Ramlat ta ƙaƙalo murmushi bayan ta haɗiye dankali da kwai da ta sanya a bakinta. "Yanzu da safe yake fadamin." Ta kai duba ga agogon fatar dake daure a hannunta tana mai miƙewa. "Hajiya zan yi latti muna da test. Sai na dawo.". Daga haka a gurguje ta fice Hajiyar na mata addu'a sai dai tana dan nazarin yarinyar da yanda ta ga kamar ba a walwala da zuwan Hilal din. Fatanta kar abinda take tsoro ya tabbata.https://my.w.tt/ub8deMQ0g9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 09)     Tun shigarta ajin ta hango Amrah ta sauya wurin zama daga kujera mafi kusa da ita zuwa can ɓarin hagunta, ba ta yi mamaki ba don dama duk sadda saɓani ya haɗasu sai an gane a ajin ko don sauya wurin zama. Ba ta yi gigin zuwa inda take ba ganin malaminsu ya taho. Sai dai kusan rabin hankalinta yana gareta, a yanzun ta gane kurenta sosai, Amrah yar uwa kuma Aminiya tun suna yara bai kamata ace ta yi mata hakan ba. Yanzun ta fi koyaushe bukarta kasancewarta abokiyar shawarar da suke haƙowa su binne ba tare da kowa ya ji ba. Sai dai a ranta tana da yaƙinin muddin ba za ta bata goyon baya game da sheƙar da ta sauya ba, komai ma ya biyo baya ba matsalarata bace. At her age, Babu wani ko wata da za ta bari ya tauyemata ƴancinta. Test har biyu suka yi, da na Economics da Commerce, bai bata wuya sosai ba, ko ba komai tana da basira daidai gwargwado sannan ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin karatu bisa shawara sanyin idaniyarta. Ana tashi break ajin duk an fita sai ita sai kuma Amrah da ta maida hankali ga kwafar note. Wurinta ta nufa kai tsaye, ko ba ta ɗago ba ta san ita ce, takaici ya kamata. Nan da nan kalaman da ta jefata da su suka dawomata, wasu hawaye ta ji sun soma wanke mata fuska. "Ko ba amintaka tsakaninmu Ramlat, zan ci darajar kaunar da nake miki kamar ƴar uwata ta ciki ɗaya. Akan namiji kika zageni kika wulakantani tamkar ba ki sanni ba. To ni kuwa me za ki cemin? Tsayuwarki ba ta da amfani don yanzun babu komai tsakanina da ke face gaisuwar musulunci, shima gaisuwar idan naga za ki wulakantani ba lallai ba tilas." Tana maganar tana jijjiga biro tana fidda hawaye, itama kanta uwar gayyar hawayen take. Damuwa biyu suka tarar mata, ga na bakin cikin dawowar Hilal da kuma gaggawar bari a sanyamusu ranar aure da ta yi, ga kuma na zafin abinda ta aikata ga Aminiyarta wanda har sai da Aliyu ya ankarar da ita kuskurenta. Hannunta ta kama wanda dole Amrah ta tsayar da rubutun don dama tuni ta daina fahimtar abinda take kwafa sakamakon hawayen da ke maida idanunta gani dusu-dusu. Littafin kuwa duk ya soma jiƙewa. "Ki yafemin don Allah don Manzon Allah s.a.w, nayi kuskure ba zan ƙara ba. Na fahimci laifina. Idan na kara ki dauki dukkan matakan da kika yi niyya." Jin chanjawar muryarta da kuma kukan ya karya zuciyar Amrah, basu soma ƙawance don wani can ya rabasu ba. Sun saba su yi fadansu kuma su shirya ba tare da sun bari wani third party ya shigo tsakaninsu ba. Dakyar ta yarda suka shirya karshe kuma suka hau hira har da dariya tamkar ba su ba. "Waye Aliyu?" Tambayar da Amrah ta jefomata kenan. Sai da gabanta ya fadi tsabar so da kaunar mai sunan. Ta lumshe idanu ta bude tana murmushi gami da duban agogon tsintsiyar hannunta. "Saura 3mins a dawo class, ki bari idan an tashi i promise to tell you everything about him." Murmushi ta yi. "Shikenan." Ana tashi kuwa suka ci sa'a ba'a zo ɗaukar kowannensu ba, don haka suka samu wuri can ƙasan bishiya saman kujera suka zauna. Babu abinda ta ɓoyemata dangane da Aliyu da karfin dangantakarsu a yanzu. Cikin hawaye ta kara da fadin. "Wallahi wallahi kin ji rantsuwa ta ƴar musulmi, ban taɓa son wani yanda nake son Aliyu ba, ciki kuwa har Hilal! Ba zan iya auren Hilal ba, ba kuma zan yarda a auramin wanin Aliyu ba ko waye shi." Baki sake Amrah ke dubanta. Ko a jiyan da suka yi wannan rikicin, ta san cewa ko wane Aliyu, Ramlat ta yi nisa a begensa. 'Ko asiri ya mata?' Girgiza kai Ramlat ta yi gami da dariya mai ciwo. "Kinsan Allah ba wani asiri, wannan son tsaftatacce ne." Amsar yasa ta fahimtar zancen zucinta ne ya fito muraran. "Wallahi gani nake kamar wata Ramlatun ce zaune anan ba Ramsy Ramlat da na sani ba. Kwanakin nan dama na lura da yanda walwalarki ta sauya, na lura sauyi a yawancin abubuwanki ta yanda hatta da wayarki kina kaffa-kaffa kar a taɓamaki. Ashe wata tsiyar kike shirin tafkawa!" Nan da nan Ramlat ta ɗan sauya fuska. "Ki bar kiran tsiya akan abinda bawa ba shi da iko a kansa, ko daga labarin da na ba ki na haɗuwarmu da Aliyu, ke kanki kin san haɗin Allah ne ba yin kanmu ba. Wallahi na guji Aliyu kamar gudun rai da ajali amma kuma ya zan yi tunda Allah Ya ƙaddara akwai ɓoyayyen lamari tsakaninmu?" Miƙewa Amrah ta yi a fusace. "Na gaji da jin wannan tatsuniyar! Na gaji da jin wanin Hilal a bakinki Ramsy! Me ya shiga kwakwalwarki wai? Ramsy Hilal fa? Mutumin da kika so a ganin farko, ban taɓa zaton irin wannan son mai shiga a yaɗuwar farko yana shafewa ba. Shawarar da zan ba ki shi ne ki nemi zaɓin Allah, kar ki biyewa zuciya ki yi saki na dafe, kar kuma ki biyewa sharrinta ki ƙare a zaɓen tumun dare! Ki sani babu hannun Amrah a cikin shafin Aliyu, har gobe ina sonki da Hilal kuma ina hango maki kyakkyawar rayuwa da mutum kamili irinsa da yardar Allah. Ban san Aliyu ba ban kuma taɓa ganinsa ba, sai dai ina miki rantsuwa bai kwantamin ba. Allah Ya ganar da ke Ramsy. Kin ban mamaki." Daga haka ta juya tana shirin barin wurin ta ji amon muryar ƙawarta wanda ko cikin bacci ta tashi ba zai ɓacemata ba. "Hilal dai! Ke ki aureshi mana muga ƙarshen so!" Ta yi maganar cike da tsawa da nuna jin zafi ta ƙarara, anan Amrah ta gane irin nisan da Ramsy ta yi a lamarin Aliyu. Ta juyo a sanyaye, kuka ta yi zaman yi mai nuni da ranta na suya, tana tare da damuwa. Tausayi ta ba ta sai dai ba ta jin za ta taɓa ba ta goyon baya ta bar nagartaccen mutum mai alƙawari irin Hilal akan wani wanda ba su san halayyarsa ba. Ta koma ta zauna gefenta, sai da ta bari ta yi mai isarta sannan ta soma magana a tausashe. "Kiyi hakuri Ramsy, ki yi hakuri da dukkan kalamaina." "Me za ki cemin tunda kin kasa fahimtana, idan kika kasance ta farkon juyawa lamarina baya, ya kike son na yi?" Ɗan murmushi Amrah ta yi, tausayin Ramlat da kuma Hilal na cin ranta. Shakka babu an mishi kwacenta lamarin zai ba da wuya. "Kiyi hakuri, na yi kuskure. Shawara kika buƙata ko?" Ta gyaɗa kai kamar wata ƴar goye. "Addu'a, ki yi addu'a sosai na neman zaɓin Allah. Ki hakura ki tausasa zuciyarki kar ki biyewa son ranki. Ramlat ga duk namijin da zai kiraki a lokutan da yake tare da matarsa ta sunnah har a ranki ki ji maƙurar so yake maki ina tabbatar maki kin yi babban kuskure. Juma'ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganeta. Wannan cin fuska ne, ina roƙonki ki bar shiga hakkin wata saboda zai iya zuwa kanki ki ji haushi. Ba karfin sonki bane ya sanya, ki lura." Ta ci gaba da ba ta shawarar mika lamura ga Allah da kuma ci gaba da ɓoye batun Aliyu a gida, Ramlat ta dauki shawararta tunda ko ba komai akwai sauran lokaci na kammala karatun da kuma auren. A ranta ta kudurta ganar da Hilal a sannu-sannu yanda zai fahimci ta sauya sheƙa ta kuma bar ra'ayin aurensa. Batun rabuwa da Aliyu bai taso ba! "Amrah Abdullahi! Bala yana magana!' Suka juya ga mai maganar, Zuhra Ishaq ce ƴar ajinsu wacce suka fi kira da Big Mama saboda ƙibarta, tun tana jin haushi har ya zamemata jiki. Tsaki Amrah ta ja tana mai miƙewa da daukar jaka lokaci guda tana aikamata daƙuwa jin ta raina direban gidansu wanda a haife ma zai haife su. Tare suka tako da Ramlat tana ƙara ba ta shawara. "Nagode, zan yi aiki da shi. Ki tayani da addu'a dai." Murmushi Amrah ta yi ta bita da toh, sai dai kuma ta san kafiyar Ramlat, fatanta kar ta jawo abinda zai hargitsa lamura. Tun da yammacin ranar da suka yi waya ya sanarmata zai shigo bayan Isha'i su gaisa take cika take batsewa, duk wanda ya kalleta ya san ba ta cikin walwala. "Ke kuma meke damunki wai?" Fadin Zulaihat da ta wuni a gidan. "Bar ta Uwani, ta yi kuncin ta gama, yanda kika ganta tun sadda ta ji labarin dawowar yaronnan take cika da batsewa. Ban san kuma me hakan ke nufi ba. Ina fatan kar ta ba ku kunya." Hajiya ke maganar ranta a ɓace don dama tun ɗazun ƙuncin da Ramlat ke yi da tsakin da take bugawa akai-akai ke cin ranta, magana ce kawai ba ta yi ba. Maganar Hajiyar yasa Zulaihat kallonta dakyau, ga mamaki ma hawaye ta shiga sharewa. "Meke faruwa ne Ramlat? Kun yi faɗa ne?" Ta girgiza kai, takaicinta yasa Hajiya sungumar Khalifa yaron Zulaihat na farko suka bar falon. Zulaihat ta dawo gefenta ta zauna. "Fadamin damuwarki. Ko Hilal din ne ba ki yi murna da zuwansa ba?" Duk kwarin gwuiwar da take tunanin tana da shi sai ta ji ta kasa kataɓus, ta kasa fadawa Zulaihat abinda ke ranta game da Hilal. "Ko kin daina sonsa?" Ta dubeta da sauri ganin ta harbo jirginta. Girgiza kai Zulaihat ta soma tana murmushi gami da yi mata kallon yarinya karama don duka a sannan ba ta fi sha biyar ba. "Kar ki soma don Allah Ramlat, ina mai tabbatar maki ba wanda zai goyamaki baya. Kar ki sake ki ɓullowa da wanin Hilal matsayin saurayinki. Take-takenki kenan wanda ba zan so ya janyomaki wani tambari kuma abin yayatawa ba a dangi. Ture ma batun dangin da kuma mu, ba ki kyauta ba, za kuma ki amsa sunan mayaudariya. Ina so ki binne kuma ki ci gaba da haɗiye abinda ke ranki, ki tattara wajen miƙa wa Ubangijinki. Shi zai zaɓamaki abinda ya fi alheri. Kar ki yarda kuma kar ki yi gangancin bada kofar da za'a ƙara fahimtar inda kika dosa. Allah Ya kyauta don kuwa akwai matsala." Daga haka ta mike ta bi bayan Hajiyar zuwa ɗaki, itama ganin ba amfanin zamanta sai ta koma ɗakinta, kuka ta yi son ranta sannan ta fito. Ta ga alamar babu wanda zai fahimceta, zuwa yanzu za ta kwantar da hankalinta har ta kammala Sakandire, a wannan lokacin ne za ta san abin yi. Da wannan shawarar ta ɗan saki ranta ta sauya, koda Hilal ya zo hakanan ta danne komai ta hau gyara jikinta babu ko kwalliya. Tana jin muryarsa yana gaisawa da su Hajiya, can kuma ta ji an murda kofar ɗakin an shigo. A'isha ta gani. "Yaya, Hajiyata ta ce ki je waje ga Yaya Hilal." Ta gyada kai tana hararar A'ishar cike da bakin ciki. Mayafin abayar da ta sanya kawai ta ja ta rufe kanta, a falon ta tarar da Hajiya don tuni Zulaihat ta tafi. "Hajiya zan je." Ga mamakinta fuskarta a sake ta amsa. "Toh wuce mana. Kar ki kai dare dai." Ta amsa da toh tana satar kallon ledojin da ke kusa da kafar Hajiyar wanda ba tantama shi ya kawo. Yana tsaye jikin motar ƙirar Honda wacce ta yi daidai da zamanin. Bayansa take hangowa, cikar kamala da ingarman jiki irin na maza ƴan kwalisa kuma abin muradin kowace mace, Hilal ya kai. Tana tafe kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tana karantarsa, zuwa lokacin ya juyo shima ya zubamata idanunsa. Kallon da take mishi da ace a sannan akwai sauran cikakken nutsuwa tattare da shi, zai fahimci ba kallo ne mai nuni da kewa ba, kallo ne na ƙurillah, na ƙeƙe da ƙeƙe. Kallo ne na son gano abinda ya fi Aliyunta da shi wanda har ake zubamata gargadin ɓoye sittin zuciyarta. Shakka babu ya sauya, fatarsa ta kara murjewa, farinsa kuma ya kara fitowa. A gefe guda ya kara kyan da zai burge ƴanmata banda ita. "Assalamu Alaikum." Ta furamta muryarta can ƙasan maƙoshi. Ya amsa yana mai jin kamar ya sanyata a aljihu su tafi tare. "Ina wuni. An dawo lafiya?" Nan ma bai ƙasa a gwuiwa ba ya amsa kafin ya bata umarnin su koma wurin kujeru zai fi. Suna tafe yana kallonta yana murmushi, ita kuwa banda guntun tsakin da take a ƙasa ranta ba komai. Hankalinta ma kacokan ya koma ga wayar da ta baro jone tana chaji, tsoronta kada Aliyu ya kira ba ta kusa ya yi fushi.   "Faɗin yanda nayi kewarki ma ɓata baki ne. Ban ma san da kalmar da zan yi amfani wurin nunamaki kewarki da nayi ba. Ina sonki My Future, ba don akwai sauran rina a kaba ba, ai da aurenmu ko wata ba zai kai ba." Ya ƙarashe zancen a marairaice, ba ta san sadda ta watsamishi wani kallo ba wanda ya ba shi dariya don a zatonsa na wasa ne. "Ok I'm Sorry, I don't meant it. Sai dai har ga Allah ina jinki sosai a raina. Kamar fa karamaki kyau ake." Duk wasu kalamai da yake fadi ba burgeta yake ba, murmushin yaƙe kawai take a wasu lokutan don ba yanzu take son fito da abinda ta binne ba. Duk kokarinta sai da Hilal ya gane kamar da matsala. Ganin haka ya nunamata zai wuce sai an kwana biyu tunda ya dawo kenan. "Kamar ba ki yi murna da ganina ba. Haka kawai jikina ke ba ni kamar akwai matsala. Please ki fadamin kuskurena ni kuma na miki alƙawarin gyarawa." Tsaki ta ja a kasan ranta, a fili kuwa ta yi murmushi. "Na yi murna sosai fa, kawai dai yau na wuni da ciwon kai. Kuma hakanan nake jin jikina ba dadi. Kar ka damu." Ta shiga istigfari a ƙasan ranta, shi kuwa tuni ya rude don dagaske ya yarda. "Shi ne ba ki fadamin ba, ban ji dadi ba. Please yi hanzari ki je ki sha magani ki kwanta kinji? Zan kiraki anjima." Ta gyada kai. "Nagode. A gaida su Umma." Ta juya da sauri don dama jinta take kamar a kan ƙaya. "Hey!" Dole ta dakata gami da juyowa. Yana rike da murfin mota yana bin ta da kallo kamar ya haɗiyeta. "I so much love you!" Maimakon ta amsa, sai ta bishi da murmushi da azama ta juya ta ci gaba da tafiya, a bangarensa ya fassara hakan da kunya. Wanda shi ke karamasa ƙaimi wurin sonta, duk kuwa da wani sashi na zuciyarsa bai gamsu da tarbar da ya samu ba. 'Na yi tunanin fiye da haka, zumuɗi, walwala, ɗoki.' 'Ka manta ba ta da lafiya? Ka yi mata uzuri. Ba ta da abin so idan ba kai ba.' Da wannan tunanin ya ji karfin gwuiwa, hakan ya dawo da walwalarsa, burinsa yanzu ya haɗa dukkan takardun karatunsa ya bautawa ƙasarsa sannan ya kama aiki. Hankali da nutsuwarsa kacokan su dawo kan abar sonsa. ***    Tafiya na ta tafiya, rayuwa na zuwa na sauyi masu tarin yawa. Kama daga siffofin halittu har ya zuwa zuciyoyi da kuma nasarori ko akasinsa. Hakan ce ta faru da Ramlat sadda take cuku-cukun zana jarrabawar WAEC/NECO don hada kwalin Sakandire.  Dukkan wata cika ta ƴa mace ta sameshi idan ka cire rama da ƙashin wuyar da ta yi sakamakon zullumin da ta jefa kanta ciki ganin na taso da shiri gadan-gadan na aurenta da Hilal da zai biyo baya nan da watanni hudu. "Ke za ki soma shiga gidan aure a class din mu. Ina ji daga ke sai G smally." Faɗin Amrah sadda take kokarin gutsirar eggroll da ta ke korawa da lemun Pepsi. Da gayya ta ƙi duban fuskar ƙawarta don tasan cikin dayan biyu ne, ko ta samu harara ko kuma.. "Mtsw, aikin banza!" Murmushi Amrah ta yi ganin ta ƙarasamata tunanin da ba ta san tana yi ba. "Mene abin tsaki? Ai gwara ki yi wani sabon abin, ba abinda zan fahimta. Tunda ke ba kya jin shawara har ta kai matakin da za ki karyar zuwa gidanmu don kawai Aliyu ya zo ku gaisa." Kwarewa Ramlat ta kusan yi da lemun Mirinda da ta ke sha. Murmushi Amrah ta yi ta ci gaba da cin Eggroll dinta hankali kwance. "Allah Ya isa, kina neman kasheni da rai. Toh wa kike faɗawa? Ke bari na fadamaki, yanzu ko kofar gidanmu Aliyu zai taka ba na fargaban komai. Ke dai ban sanki da tone-tone ba. Gwara ki ci gaba da ɓoyen wannan sirrin. Ni wannan yanzu bai fiye damuna ba. Damuwata wai Muhibbat tana da ciki. Kuma cikin Aliyu." Ta ƙarashe tana mai jin kwalla na cika idanunta, baki sake Amrah ke dubanta. Karshe sai ta sanya salati kafin ta ɗora. "Kin hadu da aiki, kin kuma hadu da wahala wallahi Ramlat. Shiga hurumin kuma da ba naki ba za ki fara? Amma dai ina fatan ba ki nuna bakin cikinki a gabansa ba? Tunda ke ba kya aiki da hankalinki yanzu." Guntun tsaki ta ja gami da harararta wanda ya yi daidai da zubowar hawayen. "Mene naki a ciki idan na nuna toh? Waye ba ya kishin abinda ba ya so? Ban gama sanin mene aure ba, amma naji a wurin wadanda suka yi cewar idan mace tana da ciki tana samun kulawa sosai a wurin miji, yana kuma son abinda ke cikinta. Hakanan kuma soyayyar zai koma kan abinda ta haifa, duk kuwa da 100% nasan Aliyuna ba ya son Muhibbat amma kishi halal ne." "Kishi da matar aure? Matarsa ta sunnah? Ramlat kina tsoron Allah kuwa? Kar ki yarda ki zama mai irin wannan kishin na hauka, kar ki yarda ki haramta abinda Allah Ya halarta. Cin amanar Muhibbat da ku ke yi kuna waya har tsakar dare bai isheki ba sai abinda ke cikinta ya tsonemaki idanu? A'a Ramlat, kar ki kusa kuma kar ki yarda ki dora kanki a wannan turbar. Wallahi da ace akwai halin da za'a iya ciro zuciyar mutum a cire son wani a ransa, da tuni na ciro taki na wanketa tas na cire sunan Aliyu na maida gurbinsa da na Hilal. Ke da kanki kin fada da bakinki Hilal yana sonki, ya kuma gane cewar yanzun ba kya sonsa, kin ce ya sha kiranki ya ji call waiting, hakanan bai karaya ba kuma bai fasa batun aurenki ba. Wane so ne zai biyo bayan wannan? Yan uwansa da Mahaifiyarsa suna sonki, suna ganin girmanki, ji yanda Anti Bilki ke miki kamar kanwarta da ku ke ciki ɗaya. Akan wani can da ba ki da tabbacin aurensa kin sanya ƙafa kin ture duka wannan karramawar da Ubangiji Ya yi miki, kina kara cusa kai inda ba lallai ki yi kwarjini ba a idanun ƴan uwa da iyayensa. Kar ki manta, Muhibbat cousin sister ɗinsa Kuma matarsa ce, ina rabaki! Ina rabaki!" Ko ba'a faɗa ba jikinta ya yi sanyi, sanyin da ya zama na fargaba. Ko ba komai kalaman Amrah sun dan taɓa zuciyarta amma hakan bai sa ta ji za ta iya hakura da muradinta ba. Don haka ta dubeta kurr. "Kamar yanda ki ka ce Allah Ya karramani, kar ki manta Shi ke iko da zuciyata. Ba ni na sanya son wannan Bawan a raina ba, haka kawai na wayi gari da so da kaunarsa. Ba kuma zan iya hana kaina ba, batun shiga hakkin Muhibbat naji zan karbi hakan, zan daina. Amma ki sani, ba zan taba ganin kiran Aliyu na ƙi ɗagawa ba koda ace ina tsakiyar Teku ne ina kokarin nitsewa ba. Ba zan yi ba kuma ba zan fara ba. Zan kuma yi kokarin ɓoye kishina a kanta, saboda abu ne da idan aka yimin ba zan ji dadi ba, sai dai so hana ganin laifi. Ki bar sanya auren Hilal cikin ƙaddarata, babu shi, babu shi kwata-kwata a littafin rayuwata, kedai Allah Yasa mu kammala karatu lafiya. Duk wannan shirin da su Abba da Hajiya ke yi kallonsu nake, don zai tafi ne a gidana da Aliyu in Sha Allah." Murmushin da take bugawa ya sa Amrah ƙara gasƙata zurfin soyayyarta ga wannan mutumin. "Allah Ya kyauta, Ya hanemu mugun ji da gani." Abinda ta iya furtawa kenan kuma magana ta karshe tsakaninsu kafin su mike su shiga aji karfe uku don gabatar da lesson duk a cikin shirin zaman jarrabawa. *** Juyi yake yana kara tunanin zantukan da ya yi da Ramlat game da shirin aurenta da aka fara, gaba daya kansa ya kulle don ji yake muddin ya rasata ba shi da sauran nutsuwa balle kwanciyar hankali, ya kai duba ga inda Muhibbat ke kwance tana bacci sannan ya mike ya dauki wayarsa ya fice daga dakin. https://my.w.tt/At99ZcOeF9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 10) Tarr ta bude idanunta jin motsin bude kofar. A hankali ta kai hannu saman dirowa ta dauko wayarta gami da duba lokaci, karfe uku saura mintuna, mayarwa ta yi ta ajiye kirjinta na wani irin zugi tana cin ɗaci a maƙogwaro. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar falon, kunnuwanta ba zasu iya juriyar sauraron hirarsu ba don haka ta dawo dakin. Banɗaki ta shiga ta kama ruwa gami da ɗauro alwala, nafila ta yi raka'a biyu, ta jima cikin sujjada tana zubar hawaye gami da kai wa Allah kukanta kafin ta ɗago ta sallame. Nan ma Alkur'ani ta jawo ta karanta a karshe ta yi addu'a ta shafa. Shi kuwa Aliyu tun da ya kira ya soma zazzaga ruwan kalamai ga Ramlat mai nuni da kewa da kuma damuwar halin da za su shiga idan wani abin ya afku. "Na kasa bacci, na kasa samun nutsuwar yi, kin kuma san ke ce. Ina tsoron na rasaki Baby." Ya ji motsin rufe kofa, ya waiwaya sannan ya kara kishingida ya ci gaba da wayarsa hankali kwance. Daga ɓangaren Ramlat ta kara cusa kai cikin bargo yanda A'isha ba za ta motsa ba. "Na fi ka shiga wannan zulumin, Sweet Aliy babu ta yanda zan rasaka in sha Allahu. Ka kwantar da hankalinka." Murmushi ya yi mai sauti. Nan kuma suka shantake suka shiga hira har da kyakyacewa. Muhibbat zaune saman darduma ta zurfafa cikin tunani, ta ji labarin kaddarorin aure da dama, sai dai irin nata ya bambanta da kowanne. Ta yi sanadin sauyawar lamura da dama. Ta rugurguza farin ciki da dukkan tanadin da ta yi a zamantakewar aurenta. Shigowarsa dakin ya katse tunaninta, ya kai duba ga inda take, sai kuma ya dauke kai ya koma saman gadon ya kwanta gami da juyamata baya. Ta tsayar da idanunta ga kallon bayannasa, a duniya ba namijin da take so irin mijinnata, dama so na rikiɗewa har haka? Da me wannan baiwar Allahn ta fi ta? Meyasa yake ƙuntatamata saboda ita? Meyasa ta kasa samun zaman lafiya a rayuwar aurenta duk a dalilinta? Ta dauka duk mace mace ce! Wasu hawaye masu ɗumi suka zubomata ganin halin ko in kular da yake nunamata aduk sadda irin hakan ta faru. Bacci har da sakin munshari ta tsinceshi yana yi. Ta kai hannu ta shafi cikinta ɗan watanni biyu kacal, a hankali ta lumshe ido tana addu'ar neman sassauci da kalar rayuwar mijinta. *** Hajiya ta yi mata ƙuri da ido. "Kwanakin nan kin fiye yawo, kin je gidan Amrah ya fi a kirga, yau kuma Muniru ki ka tuna? Yaushe sabo mai karfi ya shigeku har haka?" Ta turo baki kadan. "Dan uwana ne fa Hajiya." Abba dake karanta jarida ya ɗago kai yana dariya. "To kinji amsarki ai. Kwana nawa ne za ta tattara ta bar miki gidan ke da autarki? Ki bar ta ta sada zumunci, ta samu lada biyu. Na juma'a da kuma zumuncin." Ramlat ta sauke ajiyar zuciya, dama tana sane ta tambaya a gaban Abban don tasan zai goyi bayanta. Tun safe Hajiyar ke cin magani tana mitar wai ta sauya daga Ramlatun da ta sani akan ta shigo tana waya ta yi shiru har ta fita daga dakin. Wannan ne kuma ya tabbatar da zargin Hajiyar cewa akwai saurayin da ke huremata kunne a yanzu. Koda Hilal bai ce komai ba, ita ta lura ɗiyar ta bar rawar kafa a kansa da komai ma. "Ban wayarki. Idan kin dawo kya karɓa." Maganar Hajiyar ya daskarar da ruwan jikinta, ta bude baki za ta yi magana sai dai tuni miyan bakinta ya daskare jin muryar Abba na magana cikin nuni da goyon baya. "Ba ta idan har za ki tafin. Tunda gidan Yayanki ne ai ba damuwa. Zuwan dai ake kokarin hanaki." Ba haka ta so ba don dama da biyu take son fitar, Aliyu na son ganinta ko ta wane hali don su tattauna su samarwa kansu mafita sai dai kuma da alama karyarsu ta kare muddin wayarta ta shiga hannun Hajiya. Ba ta da zaɓin da ya wuce ta fiddo wayar daga jaka ta miƙa wa Hajiyar. _Idan lokacin bayyana soyayyarmu bai yi ba har yanzu, sai yaushe? Sai yaushe ne za'a san abinda muke ta ɓoyansa? A soyayya ba'a shakka balle tsoro. Idan aka yi hakan ba'a yi mata adalci ba, ba'a fitar da hakkinta ba._ Wadannan kalaman Aliyu ne, nan take ta ji wani kwarin gwuiwa. Ƙarƙari Hajiya ta bincika wayarta ta kuma bibiya shiga da ficen kiranta. To me ta aikata? Ai ba haramtacciyar soyayya ba ce. 'Nema cikin nema?' Ta ture tunanin ta hanyar yi musu sallama ta fita, Abba ya bita da kyakkyawar addu'a yayinda hankalin Hajiya ya koma ga wayar ta yi mishi ƙuri kamar mai jiran amsa daga cikinta. "Menene wai Rabi'atul Adawiyya? Meke damarmin ke da zuciyarki? Kwanakin nan ina lura da tsaurin da kike ƙara yi game da yarinyar nan. Ta yi wani abu ne?" Hajiya ta yi shiru tana dan kallonsa, ta fi kowa sanin halin mijinta, yana da sauki amma idan ranshi ya ɓaci babu kyau. Bai fiye zargi ba kamar yanda bai fiye daukar magana ba idan har ba shi ya ganewa idanunsa ba ko kuma yana da hujja. Tasan idan ta furta wani abin bisa zargin zai iya yiwuwa nata ne zai yi wari don haka ta ɗan murmusa. "Ba komai Abban yara, tunaninka ne kawai ya ba ka hakan. Ramar da take yi ne kawai bana so, a kanta aka fara aure?" Ya riko hannun Hajiya yana murmushi. "Kar ki damu, ko kin manta ban da auren shirin zana jarrabawa ta ke? Na dan lokaci ne In Sha Allah. Ko kin manta kalar naki zullumin dab da aurenmu?" Da sigar wasa ta harareshi suka yi dariya gami da yiwa Ramlat din kyakkyawar addu'a. *** Cike da fara'a Anti Bilkisu ta tarbeta. "Lale marhabin da Amaryarmu. Yau an tuna da ni?" Ramlat ta kama hannun Maama babbar ƴar Yaya Munir suka zauna saman kujera. Tana dariya "Kai Anti, ko wata fa ban yi ba rabona da gidannan." Taɓe baki Anti Bilkisu ta yi tana dan murmushi. "Ai shikenan, nasan da mutuniyata ce har da kayan kwananta zan ganta. Kin dai wanke kanki tunda kin zo. Yau na huta da shiga kicin." Dariya ta yi kawai sanin halinta, wato dai tana nufin A'isha don sun fi ɗasawa, dama murnar da take na zuwannata kusan da biyu ne. Wata irin mace ce mai son jiki da ba ta son aiki, burinta kawai a yi mata, wasu lokutan akwai ta da shan ƙamshi da kuma sakarwa mutum hidima duk sadda ya kai mata ziyara, wannan ta sa ba ta fiye zuwan ba. Da ace ta san ma dalilin zuwannata da sai ta ji kamar ta shaƙeta. "Mutuminki kuwa jiya kusan wuni ya yi a gidannan, kinsan fa ni ya damƙawa haɗa lefe don haka ki min biyayya idan kina son ganin tsala-tsalan kaya." Tsaki ta yi wanda ba ta san ma ya fito fili ba, da mamaki Bilkisu ta dubeta. "Tsaki ki ka yi?" Sai ta ɗan basar. "Wayata na tuna na bari a gida, kuma ina son yin waya. Don Allah ban aron ta ki." "Au, toh ki gama wayar a karshe ki ce ya turon kati don nasan ƙararwa za ku yi." Ta ƙarashe tana mai sanya kai ta fice daga falon zuwa ɗaki. Da sauri Ramlat ta mike ta nufi kicin, lambobin da suka riga suka zama tamkar lazimi a wurinta shi ta shiga rubutawa kafin ta danna kira. Sai safa da marwa take yi a kicin din har kiran ya shiga. "Assalamu alaikum." Ta tsinci muryar mace, muryar da ba ta yi kama da ta Muhibbat ba don akwai sadda ta taɓa kiran Aliyun, ta daga ta ce ba ya kusa. Ranar ta tabbatar sun kusa yin kaca-kaca da Aliyu don har rantsuwa ya yi mata a kan idan tana so ma zai sauwakewa Muhibbat duk a dalilin kishin da ta motsamata. "Hello." Aka kara fada daga can bangaren sai dai ta kasa magana. Tana shirin katse kiran cike da faduwar gaba ta tsinci muryar macen. "Kanwarsa ce Habiba, Yaya Aliyun yana ciki wurin likita su na magana." Da wani irin matsanancin tsoro ta watsamata tambaya kamar a tsawance. "Meya sameshi?! Wane asibitin ne?" Habiba sai da ta ɗan yi shiru kafin ta yi magana cikin rashin wayo. "Anti Muhibbat ce ta yi ɓari, ya bar wayar a dakin ne, idan ya dawo zan fadamasa kin kira." Da sauri ta katse kiran ta kuma goge lambar daga wayar. Tasan ba ta son Muhibbat, ba kuma tsana ba, a'a, kishinta take. Sai dai fitar cikin ya zo mata a bazata, ba ta san sadda ta shiga fitar da hawaye ba, ta ajiye wayar a gefe ta hau fiddo kayan girki jikinta a sanyaye. Ba ta taɓa jin tausayin Muhibbat din ba sai a wannan rana.   Tana cikin gyara kayan miya ta tuna ba ta ma tambayi Antin abinda za'a dora ba, tana niyyar fita ne kuma ta ji wayar ta dauki ƙara, jiki a sanyaye ta karasa ta daga, lambar Aliyun ne. "Ki yi hakuri, waccan ƴar rawar kan ce ta ɗaga. Ta fadamaki muna asibiti ko? Kar ki damu fa zan zo din. A ina za mu hadu?" Ita kuwa wane irin rashin adalci ne wannan da zai sa ta nemi ganinsa a yau duk da tashin hankalin da matarsa ke ciki yanzu? Ko ba komai a yau Muhibbat ta cancanci duk wata alfarma. Don haka ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta shiga girgiza kai kamar yana gabanta. "Ka yi hakuri, nima ce maka zan yi Hajiya ta karɓi wayata har sai na koma gida sannan za ta maidomin. Yanzu haka ina gidan Yaya Munir, wannan wayar Anti Bilkisu ce." "Kenan ba zamu hadu ba?" "Ka yi hakuri don Allah Sweet Aliy, a yau Muhibbat na bukatar kulawarka. Ka ce ina mata sannu. Zuwa gobe zan san yanda za'a yi mu hadu ko bayan tashi daga makaranta ne." "Yau ita ta samu wannan alfarmar a wurin sarauniyar masu kishi?" Ya fadi cike da zolaya yana ƴar dariya. Murmushi kawai ta yi mai sauti. "Ai ina tunanin gida zasu wuce da ita har sai ta samu lafiya. Naga yayyunnata sai wani kallo suke watsamin kamar ni na janyo zubewar cikin. Mtsw, ita kanta In-law ba don darajar Granny ba sai na fadamata maganar da za ta hanata bacci." Ta gane In Law din da yake nufi, wato Mama mahaifiyar Muhibbat, a duniya ya sha fadamata ya tsani matar saboda ko kallo bai isheta ba har gobe. Idan ma ya gaidata amsawar kamar mai taunar maɗaci haka ake yinta.      "Allah Ya bata lafiya." Ta furta cike da tausayi. "Ke na yi wani karambanin. Wayarki na soma kira kafin wannan. Har kuma saƙo na aika da ban ji kin ɗauka ba." Ta fiddo ido waje game da riƙe kirji. "Dagaske?" "Yes, amma ya naji kamar kin razana? Mene a ciki? Mene don Hajiya ta san da zamana? Ko kina tunanin lokaci bai ba da zamu bayyana abinda ke zukatanmu? Saboda Allah na gaji da wannan ɓoyon!" Ta ɗan sauke ajiyar zuciya. "Me ka rubuta a sauƙon toh?" "Idan kin koma gidan kya gani. Sai anjima." Ya katse kiran, nan da nan hankalinta ya tashi har garin saurin ta kirashi, kiran Yaya Munir ya shigo ta katse. Sai da ya kusan katsewa sannan ya daga. "Me za ki cemin kuma?" Ta marairaice. "Ka yi hakuri. Wallahi nima yanzu bana tsoron kwan ya fashe kowa ya ji. Kawai dai na tambaya don na sani, amma ka yi hakuri." Sai da ta kwashi mintuna uku tana bada hakuri, karshe ya hakura ya shiga karfafamata gwuiwa akan kar ta kusa ta ji shakkar komai akan abinda yake ƴancinta. Ya na kara nunamata muddin ta bari ta auri mijin da ba ta so za ta tafka kuskure. Ita kuwa ƙara hawa take gami da hango gaskiyar hakan. Tana ji kira na faman shigowa ta ƙi maida hankali a kai, sai da aka soma warning na karewar kati sannan ta tuna ita ta kira suka yi sallama bayan ya dorata kan hanyar da za ta bi ta fidda abinda ke ranta idan Hajiya ta mata zancensa. Ba tare da ɓata lokaci ba ta goge dukkan shiga da fitar da lambarsa ta yi a wayar. Hamdala ta yi kafin ta fita ta kaiwa Antin wayar. "Me zan dafa?" Ta katse Anti Bilkisun dake kokarin daga wayar mijinta, cikin maida hankali ga wayar a gaggauce ta amsamata. "Duk abinda kike so ki dafa kawai. Hello." Ta ƙarashe da daga wayar Munir. Cikin sauri Ramlat ta yi gaba tana ji Anti Bilkin na ba shi hakuri da cewa ba ita ke amfani da wayar ba, can kuma ta ji tsakinta da masifa. Taɓe baki Ramlat ta yi don ta san kaɗan daga aikinta kenan. Ko a jikinta don tana da tabbacin zai wahala Yaya Munir ya isketa cikin gidan. Ai kuwa ta ci sa'a don tana kammala girka shinkafa da miya, suka ci. Ba ta ko biyewa mitar Anti Bilkin ba na ta karar mata da kudin kira kuma ta hadata faɗa da miji, ta tattara ana la'asar ta yi gaggawar barin gidan cike da kwarin gwuiwa ta doshi gidansu don kuwa tana ji daga zuciya da gangar jikinta, yanzun tana da abin faɗa, tana kuma da abin kare kanta. Ta gaji da ɓuyar. ***    "Gida zan tafi da ita, ba zan bari ta koma gidansa a wannan halin ba. Ba kuma zan bari kakarku ta ci gaba da juyamin yarana ba son ranta. Dole wannan karon a yiwa abin tufka." Fadin Mama tana huci cike da takaicin halin da Muhibbat ke ciki. Duk wannan karfin ikon tana yi ne bayan tafiyar Abule gida don a farko Abule ta kasa ta tsare cewa kafarta kafar Muhibbat din, ita za ta kula da ita, acewarta ta ga jiya kuma ta ga yau, don haka sai dai ta koyar da wankan jego. Dakyar su Justice suka lallaɓata ta bar asibitin.   Ta zubawa mahaifiyarta idanu tana mai jin hawaye na sauka bisa kuncinta. Sosai ta goyi bayan hakan, ta ji ta kuma gani za ta koma gidan iyayenta. Komawar da za ta zama na har abada. Wannan na nufin alaƙarta da Aliyu ta ƙare. Lumshe ido ta yi bayan ta share hawaye ta yi shiru kamar mai bacci tana ci gaba da sauraron yanda yayyunta maza da kuma Mamar suke fadin albarkacin bakinsu. Don babu wanda bai taɓa ganin cin kashin da Aliyu ke mata ba, musamman mazan da suka fi kowa sanin har gobe bai bar shaye-shaye ba.    Ta tuno yanda komai ya faru har ya yi sanadin faduwarta da kuma suma.     _Tana zaune a falo ta zubawa talabijin ido sai dai rabin hankalin ya tafi ga tunani, cikin wannan halin ta ji bugun ƙofa kamar za'a ɓalla. Da hanzari ta mike ta fito tsakar gidan, shakka babu bugun ne. Wannan yasa ta tuna bai fita da mashin dinsa ba, asalima mashin din kwana biyu ta bar ganinsa, ta kuma ji yana waya yana kiran siyarwa zai yi ya siya wani._    _Hijab ta zura gami da daukar mukullin gidan jiki na rawa ta nufi kofar a ranta tana mamakin abinda ya hanashi daukar nasa mukullan. Kai tsaye ta bude gami da kaucewa ganin mutum ya shigo a hargitse kuma yana tangaɗi. Ji ta yi cikinta ya yi wani irin juyawa, tabbas yana sha, amman duk ranar da ya yi niyyar sha zai umarceta da fita daga dakinsa ya kulle, takan sa kunne ta ji yana tamɓelansa har bacci ya kwashe shi. Kusan rabin mayen a kiran sunan Ramlat ko kuma Baby zai ƙare sai kuwa zage-zage._   _"Ki rufe ƙofar kin tsaya kina kallona kamar farin wata."_ _Ya yi furucin da muryar ƴan maye. Jiki na rawa ta rufe suka koma ciki tana ambaton Allah a'a zuciya. Abinda kawai take tunani bai wuce na kasancewar mashayi uban ɗan cikinta ba, ta shafi cikin da tun da ya murda bai saki ba tana kuka sosai. A haka ta iskeshi ta zube a saman dinning table yana bude kulolin abinci gami da watsar da murafan a tsakar falon. Ba don plastic bane da ya fasamata._     _"Ke, ban hanaki yimin tuwo a gidannan ba?"_ _Ta share hawaye, ya za ta yi? Abinda ke cikinta shi yake da muradi, ta kasa cin komai tun safe. Ganin kuma sun jima ba su ci bane ya sanya ta girkawa._ _"Ka yi hakuri."_ _Miƙewa ya yi ya ƙaraso inda ta ke, ba zato ta ji ya ɗauketa da mari, abinda tun da take za ta iya cewa ba'a taɓa marinta ba da girmanta. Wannan ta sanya ta yin baya a gigice, ba kuma zato ta bugu da bangon dake gefen 3 steps na hawa dinning din wanda ya yi sanadin gocewarta ta fadi akan cikin da ko fitowa bai yi ba. Ba shiri ta saki wani mugun ƙara gami da ambaton Allah, a hankali ta daina motsi. Shi kuwa ya nuna ta da yatsa._ _Tsabar raini ya shiga tsakaninmu shi ne za ki kwanta bacci ina magana? To don uwar ubanki ki yi ta baccin mana! Aikin banza!"_ *** Ta ƙara runtse ido, tabbas ta ji wannan kalamin can tsakar kanta kuma kamar a mafarki, koda ta farka a gadon asibiti ta ganta Abulle a gefanta tana sharar hawaye da surutan kada Allah Ya sa ta mutu ba ta ga yaran Aliyu da Muhibbat din ba. Ta kudurta wannan buri na Abulle ba zai samu ba da yardar Allah, ta hakura da Aliyu koda sonsa zai zama ajalinta. Ta ba shi damar auren wacce duk yake so. Ita kam karatunta da yace ba ya so shi za ta koma yanzun. Bangaren iyaye sun dauka a karon kanta ta ce ba za ta koma makaranta ba, ita da Aliyun ne kaɗai suka san sirrin rashin komawarta. Duk don ya kuntata mata ya ce ba za ta koma ba.   Tana ji yayyunnata suka fita a dakin sakamakon sallamar su Amarya da sauran mutanen gidan.   *** Aliyu na tsaye a farfajiyar asibitin, shigowarsa kenan. Ko kallonsa ba su yi ba, shi kuwa ya bisu da banzan kallo da harara, yana tafe yana tunanin me ya yi mata? Daki-daki ya tuno dukkan yanda aka yi. _Yana tangaɗi ya kife saman kujera bacci ya yi awon gaba da shi bayan ya yi magaginsa ya gama. Bai farka ba sai da sanyin asuba ya ratso falon. Cikin mamaki ya tashi gami da dafe kansa dake ɗan sarawa. A hankali ya shiga tariyo abinda ya faru daki-daki, shi dai ya san sun siya kayan maye da abokansa. Anan motar abokinnasa suka sha banda G Baba wanda ke tuƙi yana musu dariyar rashin hakurinsu na ƙarasawa gida. Duk cikinsu shi ɗaya ne ya yi aure banda su da ke kokarin hada takardun Degree. Bai manta sadda suka kawo shi gida ba suka yi gaba, bai kuma yi kasa a gwuiwa ba wajen budurin da suka yi da Muhibbat. Da hanzari ya mike ya nufi hanyar ɗakinta, ba ta nan, banɗaki ma haka. Ya fito da niyyar nufar nashi dakin ya hango mutum kwance a hanyar wurin dinning table. Jiki na rawa ya karasa, ba karamin kaduwa ya yi na ganin jini ba. Kai tsaye ya kira family doctor din su Muhibbat din da ma jama'ar gidan. Ba ɓata lokaci ya mishi bayanin halin da take ciki, sanin tana da ciki ya sanya shi bada umarnin kawo ta asibiti. A gigice ya fita da zummar kwankwasawa makwafcinsa, ya ci sa'a ya fito don zuwa Masallaci. Lurwan ya dubeshi._ _"Lafiya kuwa Aliyu? Meyafaru?"_ _"Muhibbat ba lafiya, taimaka ka kaimu asibiti nan kusa ne don Allah."_ _Ba tare da ɓata lokaci ba suka je asibitin aka karɓeta suka wuce masallacin asibitin suka yi sallah, likita ya tabbatar da fitar cikinta._ "Sai kuma shikenan a dinga yi min kallon mai laifi? Mtsw" Ya ƙarashe da tsaki don shi dai yasan da ace a hayyacinsa ne ba zai yi wannan gangancin ba. To tunda ta faru ta ƙare kuma shikenan. A ranar aka sallameta bayan an tabbatar babu wata matsala, Mama ta tattara diyarta suka koma gida. Ita kanta ta ji dadi da ta ji Muhibbat na batun a raba aurensu da Aliyun. Ranar da take jira kenan. ***    Da sallama ta shiga gidan, ta yiwa Hajiya sannu da zuwa, ko arzikin kallo ba ta samu ba. Cikin sauri ta fice dakinsu, sai dai tana shiga ta ji an rufe kofar, da hanzari ta waiga. Hajiya ce tsaye da wayarta a hannu, ta ƙaraso tana dubanta. "Zauna magana zamu yi." Ba musu ta zauna a ƙasa ta sadda kai.   "Banda Hilal, akwai wani da kike kulawa ne?" Ta kalli uwar sai kuma ta sadda kai. Jin ba za ta yi magana ba yasa Hajiyar kara magana. "Na tambayeki ba don ban riga da na sani ba, a'a, ina so ne da bakinki inji kin fada. Idan akwai ya sunansa? Kuma tun yaushe ku ke tare?" Ta runtse ido tana mai jin ko'ina a jikinta na amsar kuwwar Aliyu, gwara kam a yi ta ta ƙare. "Sunansa Aliyu."I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/RjJi0Rs2J9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! A madadina da ƴan rof. Ina kara mika sakon gaisuwata ga Husna Yarbaiwa bisa rasuwar mijinta. Allah Ya mishi Rahma, Yasa aljanna makomarsa. Allah Ya raya yaransu.😭😭👏🏿 11)   Wani murmushi na bakin ciki da takaici Hajiya ta yi. "Shi dai wanda ke karamaki ƙaimi wurin ganin kin bijiremana? Kin saɓa umarninmu? Kin ci amanar mutumin da ya yi dakon jiranki? Kina cikin hayyacinki kuwa?" Daga kalaman Hajiya ta fahimci cewa r bincike ta mata a wayar. Ta ɗan turɓune fuska yayinda idanunta suka cicciko da kwalla. "Wallahi Hajiya ina son shi. Kuma shi nake son au..." Buge bakin da Hajiyar ta mata ne ya dakatar da ita lokaci guda hawaye suka shiga kwaranyomata. "Kin isa?! Har kin isa kin kai ki bude baki a gabana ki ce wanin Hilal kike so?! Innalillahi wa inna ilaihir ra'ajiun! Na shiga uku ni Rabi'atu! Ashe zan ga wannan rana? Ke Ramlatu, ba ki isa ba! Nace ba ki isa ba don uwarki! Babu wanda zai hana aurennan! Wato kin raina mu? Kin raina mahaifinki! Uban wa ya ce ki ce kina son Hilal ki kuma amince da aurensa?!" Hajiya ta ci gaba da fada, yi take tana ƙarawa ita kuwa Ramlat sai kuka, duk abinda Hajiyar ke fadi ji take ba abinda zai sa ta fasa son Aliyu.  Tashin hankalinta kawai ɓacin ran Hajiyar, banda haka ba wani abu. Hajiya ta gama faɗan sai kuma ta hau nasiha da nunamata kuskuren yin nema cikin nema da kuma hanyar da ta dauko wanda ba zai ɓille ba. Ita kam shiru kawai ta yi ba don tana aminta ba. Ba don kuma za ta sauya ra'ayi ba, asalima ji take kamar ana bude zuciyarta ana ƙaramata soyayyar Aliyunta. "Kiyi hakuri Hajiya." Ta fadi tana riko zaninta ganin ta mike a fusace za ta fice kuma babu niyyar za ta ba ta wayar. Kallonta Hajiyar ta yi, ita ta haifi Ramlat don haka ta san kafiya da taurin kai irinnata zai yi wuya lokaci daya ta saduda. Wannan kaɗai ya tashi hankalinta ganin cewa dagaske yanzun ba ta son Hilal, kuma dole ta aureshi. "Hakuri daya ki cire yaron daga ranki. Don waya zan ba ki amman sai kin kammala jarrabawa. Ba abinda zai sa a fasa aurenki da Hilal, don haka ki bar ma mafarkin hakan." Daga nan ta sanya kai ta fice. Kukan Ramlat abu biyu ne, kwace wayarta da kuma batun auren Hilal da Hajiyar ke jaddadamata duk kuwa da cewa ta san ba ta sonsa. Anan ta gane shirun ba zai mata amfani ba, kawaici da kauda kai ba zasu ƙareta da komai ba face tsananin bakin ciki da kuma nadama. Za ta cutar da kanta kamar yanda Aliyu ya faɗi muddin ba za ta fito fili ta nuna ta sauya ra'ayi ba. Ranar baccinta ya kasance rabi da rabi, duk juyi Aliyu take tunani, sanin da ta yi baccinsa ragagge ne idan bai ji muryarta ba. Sai kusan Asuba sannan bacci ya yi awon gaba da ita. ***   Ranakun da suka biyo bayan su za ta ce ba mai dadi bane sam a wurinta don kuwa Hajiya ta sanyamata takunkumi akan waya. Ba tare da sanin cewa tun a satin da hakan ta faru ta hadu da Aliyu a gidan su Amrah ya kuma cika alƙawarin kawomata karamar waya yanda za su dinga magana a ɓoye ba tare da ta bari a gida an san tana da wayar ba. Nutsuwa da maida hankali ga jarrabawarsu ta Waec da ta yi har suka kammala  ya sanya Hajiya ganin kamar ta fara mancewa da babin Aliyun.    Don ta Hilal suna hira a wayar Hajiyar bai kuma damu da jin cewa an kwace wayarta ba. Haka kawai hankalinsa ya kwanta da hakan. Ganin lokacin suna cikin shirin jarrabawar Neco ya sanyashi dauke kafa daga gidansu sai dai ta wayar, shi ɗin ma ba koyaushe ba dalilin yana dan jin nauyin Hajiyar.    ***    A gefen Aliyu har sannan Muhibbat ba ta dawo ba don kuwa sosai ta tayar da bore akan ta gama zama da Aliyun. Iyayenta ba wanda bai ba ta goyon baya ba, Abulle ce ta yi tsalle ta dire akan babu mai raba auren. Sai da Muhibbat ta yi wata biyu cif a gida sannan Abulle ta taka har bangaren Justice da zummar maidata. Ta kuwa ce sai dai takardarta. "Ke Hibbatu, kar fa kiga ina lallaɓaki don ina sonki, ba ki isa ki kashe sunnar ma'aiki ba. Aure abin wasa ne? Ko kin manta yanda kike kwana kina kuka akan son Zakina?" Hawaye ta share tana kallon Abulle. "Bana sonsa, yanzu bana kaunarsa, ba zan koma gidansa ba. Ki yi hakuri nidai kawai ya ban takardata." Nan fa Abulle ta sanya kuka wai Maryama ta zuge ɗiyarta. A karshe ta tara meeting don ganawa da kowa. Anan ma Muhibbat ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta ce ita kam ba za ta koma ba. Da yake Allah bai ƙaddara nisan zama tsakani ba, duk son Abulle da auren hakanan ta hakura aka rabasu. Kowa ya budi baki shaidar Muhibbat yake da hakuri, kunya da kawaici. A ganin iyayen tunda har ta iya karya bille ta furta kalmar saki, akwai dalili babba wanda kuma aka bar shi a sirrinsu tunda ba ta ce uffan ba.   Sakin ya fiye mata duk da irin son da zuciyarta ke yiwa Aliyu, so wanda ta girma da shi kuma ta raineshi. Sai dai an zo gaɓar da ta hakura, ba kuma za ta iya ci gaba da tafiyar ba.  A bangaren Aliyu sai da jikinsa ya yi sanyi amman kuma bai wani damu ba ko ba komai zai auri zaɓinsa kuma abar sonsa.    *** Jarrabawar NECO kadai ya ragewa su Ramlat wanda tuni aka soma. Ta rame koyaushe ba ta da aiki sai kuka da tunani. Hankalinta ya gaza kwanciya, matsowar auren da irin shirin da ake yi ya fi komai ɗagamata hankali. Zuwa lokacin Hajiya ta gama fahimtar har sannan ba son Hilal take ba, ba kuma ta ɓoyewa Anti Zulaihat da Rafee'ah ba. Aikuwa ranar da suka zo gidan suka tararmata.   "Kar ma ki fara wannan iskancin! Wallahi kika bari ya je kunnen Abba sai kin gane shayi ruwa ne. Ke ba abin kunya bane ba ma ace kin yaudari Hilal? Ya yi rayuwa a ƙasar waje, ya ga wacce ta fi ki komai da komai bai sa ya ji zai sauya sheƙa ba, sai ke da amana ta miki ƙaranci ko?" Ta turo baki gami da tsuke gira, kalaman Rafee'ah ba karamin zafi da suka suke yiwa zuciyarta ba. Kai tsaye ta ba ta amsa babu shakkar komai. "Ai ba ni na sanyawa zuciyata son Aliyu ba, Allah ne Ya haɗamu. Kuma da yardarSa, shi zan aura. Hilal ni na kawoshi na ce ina so yanzu kuma nace bana so bana ra'ayinsa, yanda ba'a yiwa wani cikinku dole ba nima..." Marin da Anti Zulaihat ta watsamata ya sanya ta yin shiru da dafe kuncinta. Ta mance rabon da fuskarta ta ji mari, jin zafin zuciya da na marin na neman haɗemata ya sa a haukace tana kuka ta ci gaba da magana murya a sama. "Eh! Eh! Ba zan daina son Aliyu ba! Zan iya kashe kaina muddin ku ka aurar da ni ga Hilal! Bana sonsa! Bana sonsa ko za'a yimin dole?" Tana gama magana ta fice a guje daga dakin Hajiyar zuwa ɗakinta ta rufe kofar gami da sanya muƙulli ta zube kasa tana kuka. Sa'arta guda Hajiyar na sashin Abba. Zulaihat da Rafee'ah suka shiga kallon kallo tsakaninsu da tsananin mamaki da kuma sanyin jiki. "Cabɗi! Akwai aiki!" Fadin Rafee'ah bayan ta farfaɗo daga suman zaunen da ta yi. Ita kuwa Zulaihat salati ta yi ta shiga safa da marwa a tsakar ɗakin kafin ta tsaya ta dubi Rafee'ah mai fama da karamin ciki. "Wallahi aikin asiri ne. Maza-maza Hajiya ta zo a san abin yi."    "Kamar kin shiga zuciyata wallahi. Ko waye shi kin san bai barta a banza. "    "Meke faruwa? Hayaniyar me ku ke yi?" Kusan a razane suka juya, Abba ne a gaba sai Hajiya a gefensa. Shakka babu muryar Ramlat ce ta fiddosu. "Bakomai Abba." Fadin Zulaihat cikin son kwantar da hankalin Uban nasu. Itama Hajiya shiru ta yi sanin abinda ke gudana, ranta na ɓaci don har wani huci take fitarwa, tuni ta gane hayaniyar Ramlat ce, kuma ba akan komai ba sai akan Aliyu. Tana jin Abba na fada akan kar su ƙara. "Ku mata ne, bai dace a dinga jin muryarku a ɗage haka ba, bana so kar a kara." Suka amsa da toh kafin ya fice Hajiya ta dubesu kamar ta yi magana sai ta fasa ta bi bayansa.   Ita kuwa Ramlat sai da ta ci kuka mai isarta kafin ta fito, kusan hakan ya zamemata jiki, duk sadda abu ya ɓata ranta, ta fi kaunar ta kulle ɗaki ta yi kuka har ta huce a karon kanta kafin ta fito. A falon ta iskesu gaba daya har Abba, a gefe ga Yaya Munir shima ya zo. Kusan ma a kanta suke tattaunawa, ta ɗan ja burki ganin ba su ganta ba ta dan koma baya. Batun furnitures ake yi sai kayan kicin da za'a damƙa ragamarsu a hannun Zulaihat.   "Komai na Ramlatu ina so ya zama na musamman, kamun kan yarinyar ya fi komai burgeni, ba ta biyewa samarin zamanin nan ba, ba kuma ta tarasu ba barkatai. Hakan ya fi komai kyau, kuma shi ya fi dacewa da dukkan wata ɗiya mace da ta san ciwon kanta. Allah Ya yi mata albarka da ku gaba daya." Idan ka cire Yaya Munir da ya amsa fuska a sake, su Hajiya kam sun amsa cike da tausayin Abban wanda bai da masaniyar abinda ɗiyarsa ke shukawa. "Ni kaina Ramlat ta burgeni ta kuma shayar da ni mamaki Abba. Allah Yasa ayi komai lafiya a gama. Ya basu zaman lafiya."    Aka amsa addu'ar Munir da Amin. Ta juya a hankali ta koma dakin, wani sabon kukan ta shiga yi. Ji take inama za ta iya ture dukkan komai ta mika zuciyarta ga Hilal, inama za ta iya wannan kawaicin ta auri Hilal ko don wannan kyakkyawar shaidar Abba da Munir gareta ya bibiyi rayuwarta. Sai dai kuma daga sadda dare ya raba, duniya ta dauki shiru sai kukan karnuka, kunnuwanta suka shiga sauraron kalaman Aliyu masu tsumata da ƙaramata dukkanin kwarin gwuiwa, daga sannan ta sanya ƙafa ta shure tunanin kalaman mahaifinnata da Yaya Munir.  Ta ƙara rudewa susucewa akan Aliyu. Ta kuma kudurce da kara daukar mishi alkawarin yanda ya rabu da Muhibbat dominta, haka za ta rabu da Hilal ta aureshi.     Ta shagala iyakar shagala wurin fayyace mishi abinda ya wakana a yau da kuma irin tijarar da ta yi duk a kanss, ba zato ta ji an yaye bargon rufarta gaba daya. A gigice ta mike duk a zatonta A'isha ce, sai dai ganin Hajiya tsaye a kanta ya sanya cikinta ɗurar ruwa. Kafin Hajiya ta ce komai sai da ta ɗaga wayar ta haɗa da jikin bango ai kuwa ya fadi anan ya tarwatse,Ramlat jiki na rawa ta bude baki da zummar magana ta dauketa da mari hagu da dama.   "Waya?! Wayar dare?!! Har wuyanki ya kai wannan kaurin? Ramlatu wace irin jaraba ce wai! Wane irin jahilin so kike yiwa Aliyu? Anya ba asiri ya yi miki ba? Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" "Waye shi? Meke faruwa?" Ba Ramlat ba, hatta da Hajiyar sai da ta ji hantar cikinta ta kaɗa. Abba ne ke tambayar tsaye bakin ƙofa sanye da doguwar jallabiya, basu san adadin lokacin da yake a tsayen ba, sai dai ya ji komai. Ba wani abu da bai shiga kunnensa ba. Jikinsa har rawa, kallo ɗaya za ka ga tsananin ɓacin rai da mamaki shimfiɗe saman fuskarsa, yake ya ƙaraso cikin dakin. Ya ji sunan Aliyu a bakin Hajiya sai dai ya fi kaunar ya gasƙata don tsoro yake ya zamana kunnuwansa ne suka sami matsala. Ya dubi Hajiya ya kuma kai duba ga Ramlat kafin ya dubi wayar dake a tarwatse a ƙasa.   "Dare ya yi, ko mene a bari zuwa safe." Abinda ya iya kokarin furtawa kenan kafin ya fice. Hajiya ta kwashi wayar da ta tarwatse ta dubi diyarta. Ramlat ta kaɗu da ganin hawaye a fuskar Mahaifiyarta, har ta fice ta ja kofar ba ta iya cewa uffan ba. Ta hada kai da gwuiwa ta shiga kuka, kuka iyakar ƙarfinta. Ba za su gane ba, ba kuma zasu fahimta ba, son Aliyu kawai take. So marar algus. Wannan daren ta rasa inda za ta sanya kanta, ta rasa kwanciyar hankali da nutsuwarta, a hankali wani bangare na zuciyar ya shiga yi mata tuni da addu'a ko ta samu mafita. Ko za ta samu Abba ya tausayamata ya bar ta da auren zaɓin ranta.   Shi kuwa Abba kasa bacci ya yi ya zauna gefen gado ya yi shiru. Koda Hajiya ta shigo, ya zaunar da ita a gefensa. "Rabi'atu kar ki ɓoyen komai, fadamin dukkan halin da diyarki ke ciki." Ta sunkuyar da kai cike da tsabar tausayinsa, duka-duka yaushe ne ya gama yabonta? Yau kunnuwansa zasu jiyemishi abinda ta san zai wahala idan bai yi mishi shamaki da bacci ba a wannan daren. Duk abinda ta sani game da Aliyu ba abinda ba ta sanarmishi ba.   "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Shi ne abinda Abban ya furta. ***    Ranar ta Asabar ce misalin ƙarfe tara da mintoci na safe, sai dai sakamakon hadarin da ya soma haduwa a sararin samaniya ya sanya garin yin luf-luf. Iska mai dadi na hurawa mai sanya annashuwa da walwala a zukatan bayin Allah idan ka cire zuƙatan iyalin Alhaji Khalid Mu'azzam da suke jin kamar sun yi rashin wani babban giɓi nasu.  A haka Yaya Munir ya shigo gidan ya tarar da su, ya zo adalilin daurin auren da zasu je na ɗan abokin kasuwancin Abban. Ya yi mamakin ganin rayukan iyayen nasa a ɓace, ya kuma yi mamakin ganin taron nasu akan Ramlat ne wacce ta ƙunshe can gefe guda kanta a ƙasa tana kuka, wannan ta sa ya yi shiru yana son jin daga inda matsalar take.   "Ki fadamin waye Aliyu? Tun yaushe ku ka soma mu'amala? A ina kuma ku ke haduwa?" Ta ɗago kai ta kalli Abban cike da firgici da kuma rashin abin fada don kwata kwata ba ta fahimci inda maganar ta dosa ba. Wace irin haduwa Abban ke nufi? Wace kuma irin mu'amala? "Aliyu?" Fadin Yaya Munir da mamaki. Abba ya ɗaga mishi hannu sannan ya dakamata tsawan da ya sa ta kara karfin kuka gami da soma magana.   "Ina rantsuwa da Ubangijin da Ya busa numfashina Abba, babu wani abu da ke tsakanina da Aliyu face soyayya mai tsafta. Wallahi Abba ina sonsa. Don Allah ka yi hakuri." Abba kusan kasa motsi ya yi a wurin, ya kuma rasa bakin magana don ganin komai yake kamar a mafarki. Hajiya kuwa ta yi shiru don ita lamarin ma ya fara bata tsoro, ta kuma kasa yarda da cewa asiri ne Aliyun ya yi mata kamar yanda su Zulaihat suka ce, ta riga ta san kafiyar diyarta. "Me kenan? Ke za ki fadamin waye Aliyu ko sai na tattaki yanzu?" Yaya Munir ke zancen cike da mamakin jin sabon lamarin da bai da masaniya a kai. A jiyan ne yake ji daga bakin Bilkisu batun hirar da ta yi da Hilal wanda yake tsoron sauyin da ya soma gani a wurin Ramlat din har yana goyon bayanta da ganin kawai yanayin karatu ne. Sai ga wata sabuwa inji ƴan caca.   Sanin halin Yaya Munir dagaske zai iya tattakatan yasa ba shiri ta basu labarin Aliyun a taƙaice da kuma tarihinsa. Don tsabar bakin ciki bai san sadda ya mike ya shiga kai mata duka ba ta duk inda ya samu, sai da  Abba ya dakatar da shi sannan ya koma mazauninsa yana huci. "Rabu da ita Muniru, kyale ta. Abinda kika manta Ramlatu, Khalid ba ya magana biyu. Ina miki rantsuwa da Allah ko za ki mutu sai dai ki mutu a dakin Hilal, ba kuma zan fasa daura aurenki a lokacin da muka sanya da magabatansa ba. Idan ke din ɗiya ce ta halal, ba za ki watsamin ƙasa a ido ba. Na miki uzuri a wannan karon, na kuma dauki hakan da kika yi a wauta. Daga yau, yanzu a daidai wannan lokacin, kar ki kusa na kara jin wani tashin tashina game da Ali.." "Ka yi hakuri Abbana, don Allah ka yafemin. Wallahi ina sonsa, bana son Hilal, na tsaneshi! Abba kar ka yimin auren dole." Wannan karon Hajiya ce ta mike tana kuka tana mai rufeta da duka. "Kaicon ɗiya irinki! Haihuwarki ba ta ƙareni da komai ba! Wallahi gwara naga mutuwarki da ganin wannan rana." Babu wanda ya yi yunkurin kwatarta a hannun Hajiyar, ita kanta Ramlat ta gwammace ta mutu a hannunta. Ta gwammace koma mene ta tarar muddin za'a yarda da zaɓinta. Kuka da dukan Hajiyar bai kashe bakinta daga magana ba. "Ku yimin rai ku bar ni na auri Aliyu, wallahi shi kadai nake so. Ku yafemin don Allah. Yaya Munir ba'a yi maka dole ba! Kar ka bari a tauyemin rayuwa." Anan ne Abban ya dakatar da Hajiya, ya dubi Munir wanda idanunsa suka kaɗa, ji yake kamar ya shaƙe Ramlat ta mutu ko iyayensa zasu huta da bakin cikinnan. Mamakinsa bai wuce na yanda akai ta shaƙu da soyayyar gayen ba, yaushe aka fara da har ya zurfafa? "Idan wannan shi ake kira da so, na yi tirr da irin naki. Ina miki kallon yarinya mai biyayya ashe ba haka kike ba! Ke kuma Rabi'atu har yaushe ki ka bari yarinyarnan ta yi nisa da soyayya haka ba tare da kin sanarmin ba? Wane irin zama kike yi da ita? Ina tsoron ace mu ne ba mu kula da kiwon da Allah Ya bamu ba! Muniru yau ba gobe ba, duk inda Aliyu yake a gidan Justice Abdulrahman Buba, ka nemomin shi." Daga haka Abban ya bar falon a fusace har walkiyar da ake zubawa tana hasko falon ga kuma ruwa da ke zuba kamar da bakin kwarya. Yaya Munir ya shiga rarrashin Hajiya kafin ya nemi ta ba shi dukkan wayoyin na Ramla ya gani, hakan tasa suka mike zuwa dakin Hajiyar ba wanda ya kalleta fuskokin a haɗe. Ganin haka Ramlat ta mike da saurinta ta faɗa ɗaki ta kulle gudun kada ma Yaya Munirun ya fito ya hau ta da duka a karo na uku. Jikinta ko'ina tsami yake yi, fuskarta kuwa shatin hannun Hajiyar ce kwance a kai. Tausayin kanta da na Aliyu ya kamata, ta sani ko giyar wake Abban ya sha ba zai yarda da aurensu ba. Ba kuma zai kira Aliyun bane don magana ta nuna rarrashi ko tausayawa, tana da tabbacin gargadi ne zai yi mishi da kuma datse alaƙarsu. *** Komai sai ya sauya, tun daga ranar da Abba ya yiwa Aliyu cin mutuncin da ba ta taɓa zaton ya iya ba akan ya bar masa ɗiyarsa, komai sai ya sauya. Daga Aliyu, zuciya ya yi ba kuma da kowa ba sai Abban, ya kuma ci alwashin ko guduwa ne zai iya yi da Ramlat, son da yake mata ba zai tafi a banza ba. Hatta ita kanta Ramlat ji ta yi idanunta sun rufe ta bar ganin kowa da gashi akan abinda take so, kullum ganin da take auren dole zasu yi mata. Amrah yanzu ta bar bata goyon baya, hatta Umma mahaifiyar Amrah ta ji koken Hajiya ta kuma rantse kan bata da masaniyar fitar da Ramlat ke yi zance a gidanta. "Amma kuma ta ƙare! Ba za ta kara faruwa ba Hajiya Rabi, wallahi yarda da tarbiyyar yaran ce ta sanya duk muka saki jikinmu da su, ashe ba haka ba. Allah Ya kyauta." Cewar Hajiya Balki kenan uwa ga Amrah.   Abba ya tara yaransa kaf meeting, ya Kuma rantse akan duk wanda ya bar Ramlat yin zance a gidansa bai yafe ba. Ba kuma ga Aliyun ba, hatta da Hilal. "Mutuncin hira a zo gidanku a sameki, don haka ban yarda ba. Ba kuma zan lamunta. Kar ki kuskura na ganki da yaronnan Ramlat, ko labari ya riskeni sai kin gayawa aya zaƙinta. Tunda ba ki da mutunci a yanzun ba kya ganinmu a mutanen da suka isa su fadamaki ki ji." Ta ɗago kai ta dubi Abban wanda tsakanin lokacin da aka soma maganar har ya rame. Ta dubi ƴan uwanta, sakon hararar da kowanne ke aikamata ya sanya ta sadda kai ƙasa. "Nikam Abba da za ka yimin iznin tafiya da ita gidana ina ganin kamar zai fi. Da kaina na kaita makaranta kuma na je na dawo da ita gidan. A ganina wannan hanya ce kawai zamu bi mu toshe duk wata kofar da zai sadata da wannan gayen." Rafee'ah ce ta cafe zancen Yaya Munir. "Wallahi nima hakan naga zai fi." Murmushi mai ciwo Abban ya yi. "Kayya, ku bar wannan maganar. Ko kun manta alaƙar ita Bilkin da Hilal? Bana son su fahimci komai. Hakan zai janyomata tsana daga dangin shi Hilal din. Ku barmin ita anan, amanarta a karkashinmu take, za kuma mu yi iyakar kokarinmu." Kukan da ta fasa ne ya sanya suka maida hankali gareta. Miƙewa ta yi ta zube saman gwuiwoyinta, duk a zatonsu kukan na nadama ne da kuma sauya ra'ayi, sai dai tun kan aje ko'ina ta basu haushi. "Ku yi hakuri don Allah Abba, ku yafemin. Da ace akwai yanda zan yi na cire Aliyu daga zuciyata da na yi. Abba idan aka yimin auren dole zan iya mutuwa!" Wannan karon Abban ne ya kai mata duka, bai fasa dukan ba yana fidda hawayen ganin wannan rana na bakin ciki, babu kuma wanda ya hanashi. "Ka yi hakuri Abba! Ka tausayamin ka auramin wanda nake so! Zan iya mutuwa wallahi!" Kalamanta suka kara harzuka zuciyarsa, yana cikin dukan sai gani akai ya zube. Da wani irin gigicewa iyalinsa suka yi kanshi. "Abba! Abba!!" Fadin Zulaihat, Rafee'ah har ma da A'isha wacce ke jin tsanar Yayarta har cikin ranta. Hajiya kuwa salati take tana karawa daidai sadda Yaya Munir ya daukeshi ya yi hanyar waje babu ko takalmi a kafafunsu. Babu wanda ya kara bin ta  Ramlat suka dunguma zuwa motar Munir dake shirin fita. A'isha ce ta dawo a guje ta dauki Hijabin Hajiya ta koma, ta dai ga Ramlat ko motsi haka ta fice. Bayan tafiyarsu ta dawo ciki, Indo sabuwar mai taya Hajiya aiki ta fito daga ɗakinta. "Auta meke faruwa?" Kuka kawai A'isha ke yi ta kasa amsawa. Ganin Ramlat shimfiɗe a ƙasa ya sanya Indo da matukar razana ta yo kanta. "Innalillahi! Ramlatu! Ramlatu!!" Sai dai ko kusa babu alamar za ta motsa. Ta miƙe da jiki na rawa ta shiga kicin ta dauko ruwa ta hau yayyafamata. Cikin sa'a kuwa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta bude idanu gami da fadin. "Na shiga uku Abba kar ka mutu, kar ka auramin shi." Indo ta san inda zancen ya dosa, ko ba komai ta tsinkayi abinda ke faruwa a gidan kwanakinnan, ta taimaka mata ta kai ta daki. Sai sannan ta dawo hayyacinta sosai. A gigice ta mike tsaye har tana jiri.   "Abba, Abba, ina Abba?" Ganin ba amsa kwakkwara wurin Indo ya sanya ta maida akalar tambayar ga A'isha dake faman kuka. "Ai ke kika kashe mana shi idan ma ya mutu. Sun tafi asibiti." Kasa nutsuwa ta yi ta fito bayan ta zura hijabi, asibitinsu daya ne a duniya, ma'ana inda ya kasance na family dinsu. Zuwansa gidan kenan adalilin son ganinsa da Abban ke yi, da kansa ya kirashi a jiyan cewa ya zo yau din zasu yi wata magana. Hakan yasa shi zuwa cike da faduwar gaba don ko motarsa bai shigo da ita ciki ba. Kiciɓus ya yi da sanyin idaniyartasa, sai dai ruɗun da ya gani saman fuskarta ya sanya shi tareta a hargitse. "Meke faruwa Ramlat? Ina za ki je?" Ta tureshi kusan a gigice ta dakamasa tsawa. "Dalla Malam ka kyaleni! Nace bana sonka! Bana sonka! Ka rabani da farin cikina, ka rabani da iyaye da yan uwana! Yanzu kuma sanadinka Abba na can asibiti kwance! Ka fita a hanyata!" Ta yi maganar tana kuka kafin ta ja tsaki ta giftashi ta fice a gidan ta mika hanya. Hilal wanda ya kasa kwakkwarar motsi, idanunsa suka kaɗa. Sai kuma ya lura da hatsarin da ke cikin tafiyarta ita daya a wannan halin, komai zai iya faruwa. Da zafin nama ya shiga motar ya tayar, wani wawan ribas ya yi ya kuma sha gabanta gami da bude murfin motar. Ta dubeshi, ta san muddin ba ta hau ba babu yanda za ta yi, kusan ma titin ba ababen hawa sosai, cikin sauri ta shiga. Magana daya da ta shiga tsakaninsu bai wuce sunan asibiti ba, daga haka kowanne ya yi shiru zuciyar na tafasa. Hilal kam ya kasa gaskata abinda ya ji daga bakinta, mutuniyar da ya ke ji kamar ana kara mishi sonta a kowace daƙiƙa. Har suka isa asibitin, ba ta ko bari ya saita parking ba ta ɓalle murfin ta fice da gaggawa. Shima fitowar ya yi ya bi bayanta cikin sanyin gwuiwa.    I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/JS1CQzbtN9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem Ina mika gaisuwa ga duk wadanda aka yi wa rashi. Allah Ya musu rahama. Ya kyautata namu zuwan. Ameeen 12) Su Hajiya ta soma hangowa a tsaye a ƙofar wani daki wanda nan take jikinta ya bata Abba ne ciki. Kai tsaye ta doshi dakin, kafin ta kai ga murɗa kofar ta ji an fisgota har tana faduwa, dama jikinta ba wani kwari ba, ko'ina kuma ya mata tsami sai dai hakan bai sa ta yunkura ta mike ba tana kallon Yaya Munir dake tsaye yana mata banzan kallon da ba ta taɓa gani daga gareshi ba. "Kin zo ki karasamana shi? Kin ji labarin bai mutu ba shi ne kika biyoshi asibitin?" Ganin bai lura da Hilal dake tahowa ba ya sanya Rafee'ah saurin yin magana murya a dan bude kadan. "Hilal sannu da zuwa, tare kuke?" Hakan da ta yi sai ya ankarar da Yaya Munir, ya dubeshi, shima karasowa ya yi yana dubansa kafin kuma jiki a sanyaye ya dauke kai ya durkusa ya gaida Hajiya da tambayar mai jiki. Ramlat ta ja gefe ta zauna saman kujera a ɗarare, kanta a cikin cinya tana kuka. Bayan ya gaisa da Munir ne yake jin abinda likita suka ce. "Ba wani abu bane, kawai ƴar damuwa ce ta sanya hawan jininsa tashi, amma da sauki. Likitan na ciki shiyasa muka fito." "Ya Salam, dama yana da hawan jini? Allah Ya ba shi lafiya kuma Yasa kaffara ne." Suka amsa da Amin. Yaya Munir ya kasa bada amsa ta farko ga Hilal, su kansu basu san Abban da hawan jini ba sai dai sun yi amannar koma mene adalilin damuwar da ya saka a rai game da Ramlat ne. Basu jima sosai anan ba likita ya fito, ya dubesu. "Kun yiwa Abbanmu yawa fa, a yanzu bama son wata damuwa da za ta tashi hankalinsa. Ina rokonku idan ba damuwa a kyaleshi da mutum daya zuwa gobe idan ya samu ya ɗan huta sai ku dawo." Zancen likita ya yi matukar tasiri a zuƙatansu. Aka ba Hajiya damar ganinsa, ta shiga, yana kwance idanunsa a rufe. Ba ta so ta mishi zancen da zai tayar da hankalinsa karo na biyu hakan yasa ta fita. Yaya Munir ya ce zai zauna abinda zasu bukata a ba direba ya kawo don haka duk suka dunguma zuwa motar Hilal don tafiya gida, yayyun banda harara ba abinda suke watsawa Ramlat a fakaice. Tana ji tana gani ta ƙara hawa motar mutumin da ta kira a maƙiyinta karo na biyu. Har suka isa gida ba wanda ke magana. Godiya sosai su Hajiya suka yi mishi kafin su fita, har sun soma tafiya ya kira Ramlat. Kaifafan idanun Hajiyar ce kawai ya dakatar da ita, ta juya ta isa wurinsa yayinda suka shige cikin gida. "Kiyi hakuri, a karo na ba adadi ina kara ba ki hakuri. Ban san irin son da kike yiwa shi wanda kika samu har kike ganin ya fi ni ba Ramlat, sai dai kowane irin so kike mishi, bai yi zaton za ki mance da ni haka da sauri ba. Na dauka soyayyarmu soyayya ce mai tsafta da muka soma a karon farko da muka fara sanya juna a idanu. Bansan me na miki ba kika tsaneni har haka, sai dai inada yaƙinin muddin muka yi aure ni Hilal sai na mantar dake batun kowane namiji da yardar Allah. Ina kara jaddadamaki ina sonki, ina miki kaunar da ban san adadinsa ba. Ba irinki ake samu a kyale ba Ramlat. In Sha Allah komai zai wuce, zan jure." Bai tsaya jin amsarta ba don yasan masu zafi ne, bai tsaye kallon fuskarta ba (dama tun soma maganar bai kalla ba), yasan ba zai ci karo da murmushinta mai tafiyar da damuwarsa ba. Motarsa ya shiga sai dai ya kasa tashinta, kallonta yake tana tsaye a inda ya bar ta, bayanta yake iya hange ba fuskar ba. A hankali kuma ya ga ta soma takawa ta shiga gidan. "Me na yiwa Ramlat? Ina da wani aibun ne?" Ya samu kansa da yin tambayar da ta tafi a iska don babu mai amsawa, kifa kansa ya yi saman sitiyari. Tun babu wanda ya san damuwarsa, tun yana kokarin dannewa har ta soma fitowa fili. Kullum kamar ana ƙaramasa sonta, har yau bai yarda ba ta sonsa ba. Asiri ko tsafi ba abu ne da ya yi amannar su na tasiri ba a koyaushe, sai dai haka kawai yake zargin sauyawarta da cewa asiri ne. Yana sonta, ba ya jin kuma zai iya rabuwa da ita. Zai jure dukkan kunci da tsananin da zai fuskanta daga gareta. Yasan muddin ya tunkaro gidansu a haka, babu ɓata lokaci Mahaifiyarsa za ta gano damuwar dake kwance saman fuskarsa, don haka ya yanke shawarar zuwa ga Yayarsa wacce ko ba komai za ta sanyashi dariya, mace mai raha da kirki. Idan kuwa aka ɓatamata rai, mutum sai ya toshe kunnensa daga habaici da bakaken maganarta. Gyaɗi-gyaɗi, anan gidan Anti Fareeda yake. Yayarsa ta farko a wurin iyayensu. Daga ita sai Murja kafin kuma shi. Da yaranta ya soma cin karo, hangame baki ya yi ganin ƴaƴan Murja, Hanan da Ammar suma a gidan. Wannan ya ba shi tabbacin itama Murja na gidan. Duk yanda ya so kaucewa kar su gane damuwarsa hakan ya faskara, akwai shakuwa tsakaninsu, kamar yanda kuma suka saba magancewa juna su yi su binne ba tare da kowa ya ji ko ya gani ba. Basu da dadi su duka idan an taɓosu. Don haka ya zaɓi ya ɓoye abinda ke tsakaninsa da Ramlat. "Yanzu kai Hilal ka kyauta? Kasan ina kasuwanci shi ne ka tsallakeni ka damƙa ragamar lefe ga Bilki? Abinda ka yimin a wurinka shi ne daidai?" Murja wacce ba ta fiye barin magana a cikinta ba ta kasa hakuri sai da ta fesar duk kuwa da idon da Fareeda ke mata akan ta yi shiru. Ya ɗago ya dubeta. "Nayi zaton duk daya muke. Amma ki yi hakuri wallahi ban kawo komai ba, na yi amfani da cewa Billy tana tare da su, za ta fimu sanin ra'ayin Ramlat. Na tuba kaina bisa wuya don Allah." Harararsa kawai Murja ke yi, Fareeda ta cafe zancen tana murmushi. "Ai sai ki yi hakuri, ya fiki gaskiya. Bilkisu da mu duk abu daya ne. Wannan ba karya, kuskuren da kike ganin ya yi miki Allah Ya ba ki hakuri Yaya Babba." Suka yi dariya, anan ne yake musu batun service dinsa tunda result ya fito. "Ai kai auren gata za'a yi maka, ga gida ga mata ga kuma kudi shaƙe a account dinka. Banda kai, wa Baba zai yiwa haka?" Fadin Murja cike da zolaya, suka yi dariya gaba daya. "Shi fa kadai ne namiji, ke kuwa mene ba zai gani ba? Allah dai Yasa ka kammala service cike da sa'a kaima ka tsaya da kafafunka." Murmushi ya yi, zamansa da yayyunnasa ya mishi amfani kwarai, ko ba komai kaso tamanin cikin damuwar da ya ƙunso sun ragu. "Naga Amaryartaka ma ta sauya, ɗan kiran da take mu gaisa ta bari. Idan na kira wayarta kuma a kashe. Naji Umma ma ta ce ta jima rabon da su yi waya." Maganar Murja kenan karo na biyu wanda ya katse tunaninsa. Nan da nan ya basar. "Af na manta ma, yanzu haka daga asibiti nake an kwantar da Abba ba lafiya amma da sauki. Ita kuwa Ramlat jarrabawa ce ta sa Hajiya karɓar wayarta." Duk suka sanya salati cike da jimami kafin su yi fatan Allah Ya ba shi lafiya. Ya jima sosai suna tattaunawa game da biki tare da ƴan uwansa kafin ya fice. *** Washegari da karfe hudu na yamma aka sallami Abba ya dawo gida, hakan bai hana wasu cikin abokan kasuwancinsa zuwa dubiya ba. Hajja ma ba'a bar ta a baya ba, ta dinga fadan meyasa ba'a sanarmata da wuri ba. Dakyar aka lallaɓata. "Jiya fa aka kai shi Hajja. Kiyi hakuri don Allah." Cewar Yaya Munir da ya gaji da mitarta. Ya mike tsaye, ya dubi Bilkisu da ta zo dubiya, sai raba ido take cike da burin sanin meke faruwa har haka, sai dai babu wanda ta ga alamar zai fadamata. "Mu wuce." Maganar Yaya Munir ya katse mata tunani, ta mike ta kara yiwa su Hajiya sallama sannan ta bi bayansa suka tafi. Ta saka a ranta sai ta san meke faruwa a gidan. Bayan da kowa ya watse ne Hajiya ke labartawa Hajja halin da ake ciki, Hajja ta hau salati ta sa aka kira mata Ramlat. "Yanzu ke Ramlatu wa zai ɓata ran iyayensa saboda son zuciya? Anya kina da hankali? Yaron da koyaushe yabonsa muke, yana zuwa har gida ya gaishemu? Inace kwanaki har Daura kika cemin ya je an gaisa?" Ta maida akalar zancen ga Hajiya dake ji kamar ta murɗe wuyan Ramlat din kowa ya huta. "Hakane ya je." "Ahaf, irin wannan yaron kike so mu watsawa ƙasa a ido? To ba ki isa ba! Don ƙaniyarki a farko wani ya ce ki kawomana shi ki ce kina so?" Maimakon ta samu goyon baya irin wadanda kakanni ke yiwa jikokinsu, sai ta ga saɓanin hakan. A barta ma ta ji da abinda ke damunta, a barta ta ji da rashin ji da ganin Aliyu. Gobe ne take da jarrabawa wanda daga shi takarda biyu ta yi musu saura su kammala duka, ko ta halin ƙaƙa a goben sai ta yi yanda za ta yi ta haɗu da shi. Rankwashin da ta ji a ka yasa ta farfadowar ba shiri. "Don ƙaniyarki shine ina magana kika yimin shiru?" Ta ɗago rinannun idanunta da suka faɗa ta dubeta hakan ya yi daidai da zubar ruwan hawayenta, to me za ta ce? A yanzun wa ya ke ta ita a gidan? Wa ke damuwa da ci ko shanta? Hakanan Indo za ta kawo abinci ta maida ba ta ko kalla ba, da ta gaji da horar yunwar don kanta ta yiwa kanta fada take ci duk kuwa da cewa ba wani dandanonsa a bakinta. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ke Ramlatu, ashe zan ga rana irin haka? Wane zamani muke ciki ne da yara kana musu magana amma hankalinsu na can wani wuri? Ina rabaki, ina rabaki da namiji! Matukar kika bari ki ka shiga hannunsa sai kin manta hanyar garinku." Hajja dai har ta yi ta ƙare ba abinda Ramlat ta ce sai kuka, Hajiya don takaici ma tashi ta yi ta koma wurin mijinta wanda ya samu bacci. Sai a sannan Ramlat ta mike tana share hawaye rai a ɓace. "Ni dai don Allah ki kyaleni Hajja, wannan fa rayuwar aurena ce, idan kuwa kun matsa na auri Hilal, za ku tarar da gawata a gidansa." Daga haka ta sa kai ta bar falon inda Hajja ta yi sokoko tana bin ta da ido don ita lamarin ma tsoro ya ba ta. A haka Hajiya ta risketa, ganin ba Ramlat a wurin yasa ta sanin inda zancen ya dosa, ba ta kai ga zama ba Hajja ta dubeta. "Wai ni Rabi'atu, kina yiwa yarannan addu'ar neman tsari kuwa?" Wani murmushi Hajiyar ta yi. "Hajja kenan, idan dai lamarin wannan yarinyar ne toh ki kwantar da hankalinki. Ta yi nisan da ba ta jin kira, ba kuma ta jin maganar kowannenmu. Don haka mun zubamata ido, idan an yi auren ma je mu yi mata sutura a miƙata gidanta na gaskiya. Kinga ai sai ta girbi abinda ta shuka sannan." Hajja ta san halin diyarta idan ranta ya ɓaci don haka sai ita ba ta ja zancen ba, banda Allah Ya kyauta ba abinda ta ce. *** Cikin sauri-sauri ta shirya cikin uniform ta fito, Hajiya na falon ta gaidata. Ko kallo ba ta samu ba balle kuma ta amsa. "Na tafi." Nan ma ba amsa, idanun Ramlat suka cicciko da kwalla, ta mike ta kama hanyar fita. "Idan bamu isa da ke ba, idan ciwon da kika jazawa mahaifinki bai isheki darasi ba. Ki je ki hadu da Aliyu a yau, sai dai ki sani idan magana ta shiga tsakaninku ban yafemaki ba." Ji ta yi kamar an zaremata dukkan lakar dake jikinta, an kashe duk wata gaɓa na jikinta. A hankali ta juyo ta dubi Hajiyar. Itama Hajiyar kallonta ta yi. "Kin raina karfin alaƙar da ke tsakanin uwa da abinda ta haifa ko? Ko kina dauka shekarun da muka yi a duniya mun yi su ne a wofi? Ki gyara lamuran rayuwarki, lokaci bai ƙuremaki ba Ramlat, kar duniya da abinda ke cikinta su ruɗeki, kar ki wannan kuskuren." Ta tsinci kanta da furta toh kafin ta juya ta soma tafiya tana bitar maganganun Hajiyar, masu sauki a baka sai dai kuma nauyinsu wane dutsen dala. Hawaye take har dakyar take ganin gabanta, a karshe ta share, ta kuma daukarwa rai da gangar jikinta alƙawarin za ta kiyaye haduwarta da shi, za ta daure. Amrah ta tareta sadda suka fito daga jarrabawa. Ɗago kai ta yi tana kallonta. Tausayin Ramlat ya sanya hawayen da take riƙewa tun ganinta da ita a safiyar ranar, ya soma tsiyaya. "Haba Ramsy, ki tausayawa kanki ki tausayawa rayuwarki da tamu don Allah. Kin sauya kin koma wata daban da bamu sani ba. Kin illata walwala da farin cikinmu da kuma naki, akan me? Allah da Ya halicci soyayya bai halicci hakuri da dangana ba? Ko kuwa kin fi karfin ki rungumi ƙaddara kamar kowane bawa? Ballantana ina da tabbacin muddin kika zauna da mutum irin Hilal ba za ki taɓa dana sani ba." Wani murmushi mai ciwo Ramlat ta yi gami da ɗan kauda kai kafin ta kara dubanta. "Ita soyayyar ba ƙaddara ba ce? Ko kin manta cewa bawa bai isa ya ɗorawa kansa abinda Allah bai ɗora mishi ba? Hakuri ana yinsa idan bakin alƙalami ya riga ya bushe, sai dai nawa alkalamin har yanzu a jiƙe yake. Na dauka idan duk duniya za'a haɗa kai a ƙi goyon bayana, banda ke Amrah. Sai ki ka shayar da ni mamaki, ki ka kara fahimtar da ni nisan alaƙarmu, kin bada tazara ba kaɗan ba. To ki sani, yanzu na soma son Aliyu, kuma in sha Allah zan zama mallakinsa ko ba jima ko ba daɗe." Daga haka ta gifta ta wuce itama tana nata sharar hawayen. Amrah ta bi ta da kallo cike da kara jin tsanar Aliyu har cikin ranta, babu irin haka da ta taɓa faruwa garesu sai a kansa. "Da yardar Allah ba za ki taɓa auran Aliyu ba Ramlat, wannan Aliyun ba alheri ne ga rayuwarki ba." Ta furta a fili. *** Ga Ramlar kuwa, tana fita ta yi turus, ta kasa koda motsi don gani take kamar mafarki, Aliyu a makarantarsu? 'Kema kinsan zai iya faruwa, mutumin da ba ya ji kuma ba ya ganinki?' Fadin wani sashi na zuciyarta tana mai ci gaba da kallon Aliyun dake tsaye ƙasan wata itaciya a kofar makarantarsu. Shima ita ya zubawa idanun, kamar yanda ta rame shima haka ya rame. Ta shiga kalle-kalle, sai da tabbatar babu alamar an taho daukarta kafin ta soma yunkurin tsallakawa. A gaggauce ta isa wurinsa ta tsaya suna kallon juna, abubuwa biyu suka faɗomata a rai lokaci guda. Na farko dokar makarantar da ta hana tsayuwar taɗi, muddin aka lura da hakan to fa za'a ɗau mataki. Na biyu zantukan Hajiyarta da suka fi komai tsayawa a ranta. Sai ta soma ja baya, ga samu ga rashi. Ya yi nasarar riko gefen hijabinta, a dole ta tsaya ta kuma juyo sadda ya saki. "Ba zan iya hakura da ke ba, ke din nake so Baby. Zan iya jure komai saboda na aureki. Rashinki kwanakinnan yana wahalar da zuciya da gangar jikina. Me zan yiwa Abba ya so ni? Kamar yanzu ba kya tausayina kema, kar ki manta na sadaukar da komai saboda ke. A dalilinki na rabu da Muhibbat, bana kula kowace mace. Kar ki sakamin da auren wani ba ni ba, ba zan jure ba." Duk zantukan tana jinsu har ƙwaƙwalwa, ji take inama za ta iya cewa wani abu, sai dai ba za ta saɓawa Hajiya ba. Dabara ta faɗomata, a gaggauce hannu na rawa ta sauko da jakarta a baya sannan ta durkusa ta ciro takarda da biro. Shima bai yi ƙasa a gwuiwa ba wurin durkuson, maimakon abinda ta maida hankali wurin yi (wato rubutu), sai ya maida hankali wurin kallo da karantar yanda ta rame idanunta suka zurmuƙa ciki. Siririn karan hancinta ya ƙara fitowa, ji ya yi inama yana da damar da zai iya daukemata hawayen da suke bin karan hancin zuwa baka. Ta kammala rubutun ta miƙa mishi takardar, ya karba yana dubanta har suka mike a tare. Dakyar ta iya juyawa da sauri yana kiranta ba ta ko waigo ba. Tasan a hakan ma ta saɓa umarnin Hajiyarta, dole kuma ta nemi gafara. Ta taki sa'a har za ta koma cikin makaranta wata ta kirata wai an zo daukarta. Ta juyo da azama za ta nufi mota, Amrah ta hango tsaye a wurin Aliyu tana mishi magana shi kuwa yanzu ya bada baya maimakon a farko da yake kallon gaba. Hankalinta ya tashi, sai sannan ta kula da wanda ma ya zo daukarnata, Abbanta ne. Ba damar ta je garesu, ganin kaifafan idanun Abban a kanta ya sa dole ta bude motar ta shiga. Ita kuwa Amrah sosai ta ja wa Aliyu kunne akan ya rabu da kawarta. "Ka raba ta da iyayenta, ka raba ta da mutumin da zuciyarta ta soma so a duniya. Me kake nema haka? Ance ba za'a ba ka ita ba, meyasa ba za ka hakura ba? Ka daina bibiyarta, ba don na zo na zama katanga tsakanin fuskarka da na mahaifinta ba, da yau ban san halin da ganinka zai jefashi ba." Sai a sannan ya fahimci dalilin zuwan yarinyar da kuma dawowarta ɓarin da dole zai juyo. Manufarta ta burgeshi sai dai kalamanta sun ba shi dariya hakan yasa shi murmusawa. "Ban taɓa ganin Amrah ba sai yau, duk kuwa da cewa kafata ta taka kofar gidansu ya fi a kirga a dalilin Baby. To ba zan yi mamakin kalamanki ba, amma ina so ki sani. Daga ni har Ramlat, Allah ne Ya haɗa soyayyarmu. Ina mai ba ki hakuri sai dai ki yiwa yar uwarki uzuri, shi so ba ruwansa da komai, ki mata uzurin halin da take ciki yanzu. Ba yin kanmu bane. Addu'arki ita ce abin bukatarta da ni dinma a yanzu, abu daya kawai nake so ki rike a ranki. Wannan dai banzan Aliyun, idan Allah Ya ƙaddara shi ne mijin Ramlat, babu mahalukin da ya isa ya tsayar. Na bar ki lafiya." Ya wuce ta bishi da kallo, takaici biyu. Wato dai ba zai saduda ba, a gefe kuma ta tuna sadda ta ambaceshi da banza. Amman ai ba ta furta a gabansa ba, hakan na nufin Ramlat na ba shi labarin duk wani abu da aka ce game da shi. Wani wawan tsaki ta ja tana mai jin kamar ta samu Ramlat din ta yi mata dukan kawo wuƙa. *** _*Ba zan iya ce maka uffan ba bisa alkawarin da na dauka sanadin Hajiya ta, ina kaunarka Sweet Aliy, har gobe kai ne zaɓina. Ka sa a ranka babu mai yimin dole, babu shi. Ko an yi ba zan zauna ba. Zan fito kawai domin na aureka. Na maka wannan alƙawarin. Abba bai da lafiya, an kai shi asibiti yana da hawan jini, a yanzu dole za mu ɗan yi hakuri mu rage haɗuwa. Don Allah ka dinga cin abinci. I love You._* Ya ninke takardar ya zura a aljihu, son wannan yarinya ba zai kashe shi ba. Kai tsaye gida ya nufa wurin Abulle. "Kai Zakina, kana kuwa cin abinci? Wannan uban ƙashin wuya? Kodai so kake a maido maka da matarka yanzun nan na kira Babanta na tursasashi?" Ya ja guntun tsaki gami da shafar suma. Kwantar da kai ya yi jikin kujera ya lumshe ido. Nan da nan Abulle ta sa aka kawo mishi abinci. "Maza ci wannan daga gidan Babanka Alƙali ne, irin wanda kake so." Abincin gidan Justice kusan ya fi kowanne dadi wannan ta sanha jikokin ke rububi idan an aikowa Abulle. Ita kuwa ɗan gaban goshinnata take ajiyewa. A dole ta sanyashi a gaba ya dinga ci kamar mai tauna magani. Karshe ma ya ture kwanon. "Ni fa aure zan yi." Nan da nan Abulle ta washe haƙora. "Kai Alhamdulillah, ko kai fa. Wa ka samu?" Ya runtse ido. "Wacce nake so iyayenta ba sa sona. Sun mata miji, kuma itama nan duniya ni take so." Nan da nan ta daure fuska. "Kar dai wacce Babanka Abdussalam ya ce iyayenta sun aiko nemanka akan ka fita hanyarta?" Ya dubeta sosai, sai kuma ya daure fuska. "Na meye za'a dinga yawo da zancen kuma? Wannan kuma ya zama terere. " Abulle ta yi mishi daƙuwa. "Nace karbi nan, don an fadamin shi ne terere? Kai yanzu ba abin kunya bane ma a ji wai kana son yarinya an turo a yi maka kashedi don ka rabu da ita? To ahir dinka! Ka rabu da ita tun wuri kafin ka jawomin ƙananun magana cikin gidannan." Ya taɓe baki, shi kam ba wanda zai iya rabashi da Ramlat, ba zai yi dakon so a banza ba. Duk ma macen da ya hango sai ya ga ba ta kaita ba, idan kuwa ya rasata ya yiwa kansa. *** *A KWANA A TI think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/Dbu9FChHQ9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 13) *A KWANA A TASHI..* Su Ramlat sun kammala karatunsu sun yi bankwana da makarantar Sakandire.    Ranar da za'a yayesu kuwa, duk wani farin ciki da ƴan ajinsu ke yi, banda ita a ciki don a ganinta babu wani abin ƙayatarwa musamman ganin yanda gadan-gadan mutan gida ke shirin biki. Bikin da aka matso da shi aka rage lokacinsa, duk sanadin kar ta ƙara tadamusu batun Aliyu. Yanzu da kowa ke murna ana hotunan bankwana, ita din tana zaune a gefe saman kujeru sanye da gown ja wanda wuyar rigar da kuma hannun aka mishi kwalliya da yellow. Gashinta a tufke babu kitso, ta ɗora hular gown din a kanta ya zauna ɗas. Duk irin kyan da ta yi, ganin muninta take, ace rana irin ta yau babu wani nata da ya zo tayata murna, sai iyayen Amrah da yayyunta da suke kokarin jawota jiki duk domin kar ta ƙuntata. Ramar da  ta yi ba karamin tada hankalin Umman Amrah ya yi ba har ta ja ta gefe ta yi mata fada sosai akan ɗorawa rai abinda ba shi ba. Yanzun da ta ja gefe ta zauna, suna daukar hotuna ne, a ganinta hakan zai fiyemata don ba wani kyau za ta yi ba, a ganinta ramar kadai ma ta dusasar da ita. To ma idan ba ta rame ba me ake so ta yi? Ba ta iya bacci balle cin abincin kirki, Hajiya ba ta yaɓamata magana sai dai magana ta kwakkwaran mintuna biyar ta bar haɗasu. Abba kuwa jan ta ya shiga yi a jiki ganin yanda uwar ke mata duk don ta sake, ta hakura kuma ta fawwalawa Allah lamuranta. Shi kam ta tabbatar banda yau zai je Daura tare da Yaya Munir, to zai zo mata a wannan rana. Su Zulaihat dama ba ta sanya rai ba.   "Ramsy!" Ta daga kai ta ga mai kiran, JJ ce. Itama dai ajinsu take. Inda ta mata nuni da yatsa ta bi da kallo kafin ta ce   "Ki zo!" Daga nan ta juya ta tafi, ita kuwa Ramlat tunda ta ɗora idanu ga wanda aka nunamata, ta ji kamar kwai ya fashemata a ciki. Sanye cikin shadda sky blue, ya kafa hula zanna bukar. Sajensa a kwance luf-luf. Yanda take karantar ramar da ya yi a satittikan da suka yi basu ga juna ba, don kuwa batun waya takan ari wayar Indo a ɓoye ta kira ba tare da ko Hajiya ta sani ba. Rokon Allah da Annabi s.a.w take yi mata akan ta ɓoye sirrinta.   Ta yi zurfi cikin tunani da kuma kallonsa babu ko kyaftawa, ya gaji ya biyo sahunta ya ja kujera ya zauna kusa da ita a cikin hall din mai jama'a maƙil. "Kin wahalar da ni fa, dakyar aka ganomin inda kike. Baby kin yi kyau. Bari na miki hoto." Ya fiddo wayarsa Blackberry  wacce ake kan yaayi a lokacin, ya shiga daukarta bai ko damu da  murmushin yaƙen dake a fuskarta ba. Jiki a sanyaye kuma ya maida kai ga kallonta. "Baby ki yi magana ko na samu nutsuwa, gaba daya kin yi wani sanyi kamar ba Babyna ba wacce daga ta yi tozali da ni take manta komai da kowa." Ji ta yi ya kara karyar da zuciyarta, sai ta soma kuka bayan ta saka tafukan hannunta ta rufe fuskar. Duk yawan danginsu a rasa mai zuwa tayata murna ranar da ta fi buƙatar hakan? Kukan ya tashi hankalin Aliyu. Bai san ma sadda ya kama hannuwan ba ya saukesu daga saman fuskar. Ya yi daidai da shigowar Abba da Yaya Munir cikin hall din. Har zasu kama hanya Abban ya ga rashin kyautuwar a rana irin ta yau bai je wa diyartasa ba hakan yasa shi umartar Yaya Munir akan su soma biyawa kafin su wuce. Ba don Yaya Munir na so ba ya bi umarnin. Tun shigowarsu suke rarraba idanun inda zasu hangota. Amrah ce ta soma hango Abban, da sauri ta taho ta gaidashi. Mahaifinta ma ya ƙaraso suka yi musabaha cike da fara'a.   "Ai da ace ba ka zo ba, har gida zamu je mu sameka mu ji dalili." Fadin Dr Abdullahi mahaifin Amrah cike da zolaya. "Ban isa ba, sai dai kuma da nasan za ka zo din da ban zo ba, zuwanka ma ai ya wadatar. Yaranmu ne." Suka yi dariya sannan Yaya Munir dake ta kalle-kallen ko zai hangota ya gaisheshi. Abba cikin murmushi ya dubi Amrah.   "Na tayaki murna ƴata, Allah Ya sanyamaku albarka a abinda ku ka karanta yanzu da ma wanda za ku yi nan gaba." Itama da fara'a ta amsa da Amin. "Ina ƙawartaki?" Fadin Abban a karo na biyu, shi kuwa Munir karaf idanunsa suka faɗa kan Ramlat, bai ga wanda suke tare ba, sai dai tabbas kuka take hannunta kuwa idan ba idanunsa ke mishi gizo ba, yana cikin tafukan hannun namijin. Da sassarfa ya soma tafiya da nufin zuwa wurin, ji ya yi an riko kafadunsa, juyawa ya yi. Hilal ne, ba shi kadai ba har da kannensa biyu, Jidda da Zahra. Jidda ta fi sa'ar Ramlat ba ita kuwa Zahra za su yi kai ɗaya da Auta A'isha. Musamman ya taho da su don su taya sahibarsa murna, har iyayen na mishi dariyar yanda yake rawar ƙafa babu kunya. Sun cakare cikin wasu rantsastsun abaya kalar ruwan toka da kwalliyar baƙin fulawoyi a jiki. Farare tas kamar shi Hilal din, don za'a iya cewa sun ma fi shi kyau. Suka gaida Yaya Munir. Ya amsa, kafin ya mikawa Hilal hannu su yi musabaha. A wannan lokacin idanun Ramlat suka kai garesu, a gigice ta dubi Aliyu kafin ta zare hannunta ta mike tsaye. Ya dubeta sannan ya dubi inda ta kura idanun, wasu gayu biyu da kuma mata ƴan kwalisa ne. Yasan Yaya Munir don a gabansa Abba ya mishi kashedi. Ɗayan kuwa ne bai san ko waye ba.     "Me ya kawo Yaya Munir da Hilal? Abba ya zo kenan?" Jin ta ambaci Hilal ya sanya Aliyu kara dubansa dakyau, da ka kalli idanun za ka hango tsananin kishi balle kuma fuskar da ta sauya nan take har wani ja ja take yi. Bai san lokacin da ya ja tsaki ba, ya mike yana dubanta. "Saboda wannan ne dama aka ƙi ni a gidanku? Don bani da kudi? Don Aliyu talaka ne ba shi da komai sai rufin asirin Allah? Shikenan Ramlat, bari naje don ba zan tsaya a wulakantani ba. Ga wannan, ya fiddo karamin akwati daga aljihu ya ajiye a kujerar da ya tashi, daga haka ya sa kai da sassarfa ya tafi. Da sauri ta dauki akwatin tana kokarin bin bayansa, caraf aka rike hannunta. Yaya Munir ne. "Yau sai kin raina kanki da wayonki! Don ubanki wato har taɓa jikinki yake? Sa'a daya kika ci, Hilal ya zo wurin nan wallahi da yau sai na miki cin mutuncin da ba za ki manta ba. Ƴar iskar banza da wofi!" Sai ta ɗauke wuta, hawaye kawai ke zuba babu amon kukan. Ƴar iska yau ta zama a wurin Yaya Munir. Zafi goma da ashirin ya haɗarmata. A hankali ta bude jaka ta zura ƴar akwatin da Aliyu ya ba ta ciki daidai sadda Munir din ya saki hannunta. "Ki zauna nan ki gyara fuskarki tun ban saɓamaki ba!" Tana kumburin da komai ta share fuska. Koda ta ciro saboda kaifafan idanun Yayannata dake a kanta, a dole ta ɗan murza, ta maida jaka. Sai dai kafin a je ko'ina wasu hawayen sun taho ba shiri ta ɗaukesu da hannu sakamakon hararar da Yaya Munir ya watsamata. Daga haka suka nufi wurin da suke tsaye har su Abba. "My sweet Aunty." Faɗin Jidda sa'ilin da ta rungumeta a jiki, ji ta yi kamar ta watsamata garwashin wuta sai dai idanun su Abba ne ya hanata daukar matakin da zuciyarta ta rayamata, wato ta tureta ta faɗi.  Dole ta kakalo murmushi suka kara gaisawa. Itama Zahra haka ta yi mata, Hilal dai na gefe yana kallonta yana kara wassafa yanda so ya koma ƙi.    Abba ya yi mata murmushi, a kallo daya ya karanci abubuwa da dama  a cikin kwayar idanunta, ya kauda kai sadda ta karasa ta gaidashi. "Allah Ya muku albarka." Aka amsa da Amin. Nan kuma aka ɗauki hotuna, bayan wucewar Abba da su Yaya Munir har iyayen Amrah. Jidda dake rike da karamar Camera na Hilal ta ce. "Yayana matso na muku hoto da Aunty." Ya saci kallon Ramlat dake tsaye gefen Zahra, ba musu ya matso yayinda Zahra ta ja baya. "Ina wuni." Ya gaidata, gaisuwar da ya ankarar da ita ashe fa ko kallon inda yake ma ba ta yi ba balle ta gaidashi. Ciki ciki ta amsa. "Lafiya kalau." "Oh, don Allah ku daina magana, ku kallo nan." Maganar Jidda ya sanya su dubanta lokaci guda, aikuwa ta shiga hotuna ba kakkautawa. Don kanta Ramlat din ta ja baya. Hakan yasa Hilal kallon Jidda. "Ya ishemu haka, ke idan kin soma ba ki san ki daina ba." Ta yi dariya, jiki a sanyaye ta ke duban gefen Ramlat din, tuni ta soma tafiya da nufin barin wajen. "Lah, Aunty ina za ki? Dawo ku yi hirarku bari mu ɗan zagaya. Dama akwai wata old schoolmate dita a nan, bari naga ko zan ganta." Da wayo ta ja hannun Zahra suka tafi suka bar su, abinda tunaninta ya bata da sauyin Ramlat shine sun samu saɓani da yayannasu ne shiyasa ta sauya, barinsu su kadai zai sa ta sauko daga dokin fushin. "Idan ba damuwa mu ɗan fita daga hayaniyarnan please." Ta kalleshi, idanunsa sun kaɗa, ko menene yau Hilal ta kai shi bango. Yanayinsa ya sanya ta kasa yin musu, suka soma tafiyar kamar ba sa so har suka fice daga Hall din. Can parking space suka isa kasan wata itaciya saman kujeru suka zauna.    Duk kalaman da Hilal ke zubamata na ban hakuri da rokon ta dawo da soyayyarshi a ranta, ba ta san ya na yi ba, hankalinta na ga ta hanyar da zasu tattauna da Aliyu. Wannan ta sanya ta dubansa. "Za ka yimin wata alfarma?" Ya ƙuramata idanu, sai ya murmusa "Ba abinda za ki nema wurina ban miki ba." Ajiyar zuciya ta saki, ba kuma ta ji a ranta ya burgeta ba, duk kuwa da cewa tana danne wani tausayi  dake tasomata yana son mamaye zuciyar, ganinta hakan ne daidai. "Ka sanya Yaya Munir ya ban wayata, ka nunamusu yanzu komai ya wuce. Don Allah ka yimin wannan alfarmar." Kamar ya ce mata sadda aka kwace bai san dalili ba, bai kuma kamata ya shiga tsakani ba, sai dai ya share. "Zan san dabarar da zan yi a ba ki wayarki." Ga mamakinsa sai lokacin ya ga murmushinta. "Nagode sosai." Wata ajiyar zuciya ya sauke gami da miƙewa tsaye tun kan kishi ya ci gaba da nuƙurƙusarsa. "Ki jirani ina zuwa." Bai jira amsa ba ya wuce. Ta bishi da kallo. Handsome da shi, zai burge kowace mace, amma banda ita. Tana son tuna wani mugun abu da Hilal ya taɓa yi mata sai dai babu ko daya banda tarin alkhairai. "To ya zan yi? Banda iko da zuciyata." Ta furta a fili sa'ilin da idanun suka cika da kwalla. Ba ta ji takunsa ba sai wani kwali mai kyalli da ta gani, ta dubeshi. Murmushi yake mai kama da yaƙe. "Karɓa, kyauta ne gareki. Ina kara tayaki murna." Ta murmusa itama gami da karɓa. "Nagode sosai." "Muje ko? Ina son zuwa wani wuri ne." Ta amsa da toh, daga nan suka koma ciki ya hada kan su Jidda suka tafi. Jidda ta ji dadi ganin sauyi a saman fuskar Ramlat, wannan yasa ta fahimci abinda take zargi a farko hakanne. Wato dai saɓani suka samu. ***   "Wai nikam Rabi'atu, ina yiwa yarannan daidai? Hukuncin da na yanke akan auren Ramlatu da yaronnan ban mata gata ba?" Yanda yake maganar murya a karye ya ɗarsa tausayinsa ba kaɗan ba a zuciyar Hajiya. "Babu wani hukunci mai tsauri da ka taɓa yankewa Abban Yara. Kowane uba burinsa ɗiyarsa ta auri kamilallan yaro mai kyakkyawar nasaba. Kuma Alhamdulillah, Yaronnan ya kai yanda ake so. Don Allah ka bar sanyawa ranka tunani na daban har ya taɓa lafiyarka." Ya yi murmushi gami da kara rungume matarsa. "Aliyu da Ramlatu ke so, yaro ne mai kyakkyawar nasaba sai dai a iyaka bincikena yana shaye-shaye. An sanar da ni goyon kaka ne, ba wanda ya isa ya fadamasa ya ji. Uwa uba bai yi wani zurfi a karatun boko ba balle kuma na addininsa, koda ace na yi niyyar bai wa Ramlatu zaɓinta, ba zan iya daukarta na kai inda za ta yi baƙin jini ba. Ina son yarana. Ina son su samu wanda zai kularmin da su ko bayan ranmu. Meyasa Ramlatu ba za ta yiwa kanta faɗa ba?"   Tashin hankalin Hajiya dai ganin Abba ta yi yana hawaye, itama ba ta san sadda ta fara ba. "Yaran ne muke haifarsu bamu isa mu haifo da halinsu ba. Addu'a kawai ya kamata mu ci gaba da yi musu. Allah Ya shiryamana su, Ya bamu ikon kula da amanarsu da Ya damƙamana. Sai dai hakkinsu ne su bi mu, hakkinsu ne su so abinda muke so. Mun tayasu son abinda suke so, meyasa su ba zasu hakura da son ransu su yi mana biyayya ba? Gani suke muna yin wani abin ba don muna sonsu ba. To ya zamu yi? Addu'ar ce dai. Ina tabbatar maka sai ta fi mu alfahari da wannan zaɓin in sha Allah." Ta ƙarashe tana ci gaba da daukemishi hawayen, ba tare da ta damu da natan dake kwarara ba. Shima ya sharemata yana murmushi gami da sumbatar goshinta. "Allah Ya yi maki albarka. Ina alfahari da dukkan yaran da muka haifa. Ramlatu ma tausayi take ban, sau tari ne idan ta aikata wani abun sai na cika da mamaki, kamar ba jininmu ba." "Kar mu yi saɓo, addu'ar ta fi duk wannan." Suka ƙara murmusawa cike da jin wani ɗaci a kasan ransu kafin kuma su hau tuna yanda a lokacin iyayensu ake auren ɗiya ba ta ko samu damar ganin mijin ba kuma ta yi biyayya ta zauna. Karshe suka tattara komai suka ajiye gefe suka fuskanci rayuwarsu. ***    A satin biki aka kawo lefe da komai da ya kamata.   Gyaran jiki sosai aka shiga yiwa Ramlat, mutanen Daura sun soma zuwa gidan. Yau ma tana zaune wata gwaggonta, ƴar dan uwan mahaifinta daga Daura, ta tasata a gaba da wani hadin magani ta shanye. Dole ta kwankwaɗe ta mike ta bar wurin suna zolayarta. Kai tsaye wayarta ta ciro wanda tuni Hilal ya sanya an damƙamata. Aliyu ta hau kokarin nema a waya, ba zato ta ji an zare wayar a hannunta. Amrah ce tsaye fuska ba fara'a. "Kar ki cemin har yanzu kina kiransa? Kwana uku ya yi sauran a sanyaki a lalle Ramlat, ki ji tsoron Allah. Kar ya kasance har bayan aurenki za ki ci gaba da kula wannan mutumin." Tun soma maganar take watsamata banzan kallo kafin ta ja tsaki ta kwace wayarta. "Ai an so hakan ta faru shiyasa aka yi gangancin haɗani aure da Hilal. Ba zan fasa ba, nace yanzu na fara Amrah. Idan kin ga dama ki yi shiru idan ma ba ki ga dama ba ki yimin terere a dangi. Mtsw." Ta gifta ta wuce cikin banɗaki ta rufe.  Ta san nan ne kaɗai wurin da za ta yi wayar sirrin da Aliyu. Amrah ta saba da wannan cin fuska na Ramlat akan Aliyu, wannan ta sanya ta girgiza kai da fadin Allah Ya kyauta. Daga nan kuma ta dauki kyallen anko don abinda ya maidota dakin kenan, zasu fita kasuwa siyowa wasu mutan Daura anko. Su Naja'atu ne zasu yi mata rakiya. Saboda biki nan gidan duk suke kwana.   *** Tana fitowa daga banɗakin ta ga Bilkisu zaune a gefen gado tana shayar da ɗiyarta. Fuskar Bilkin a daure take dubanta, ta kauda kai itama. Maganar duniya ba ta ɓuya, tuni Bilkisu ta gane komai ta sanar da su Fareeda, har ma can dangin Hilal sun soma ƙananan magana. Babansa ne ya tsawatar da abin ya kuma ce kar ya ƙara ji. Mamar Hilal da kannensa kuwa sun soma jin tsanar Ramlat, banda Hilal na gyara wasu lamuran da kalamai, da wutar da Bilkisu ta kunnamishi a gidan ta janyo mishi fasa aure da Ramlat. Sai dai mahaifinsa mutum ne mai magana ɗaya, yanda ya dage akan ba wanda ya isa ya hanashi aurawa Hilal abinda yake so, hakan ya kashe bakin kowa sai ƙananun magana da ba'a rasawa wurin mata. "Ina wuni Anti Bilki." Ta gaisheta ciki-ciki don yanzu ba wani mutunci suke ba. "Lafiya kalau Laila ta Majnun." Sanin cewa magana ta yaɓamata ne yasa ba ta ce komai ba.   "Ni na rasa abinda Hilal ya gani ya maƙale maki alhalin yanzu ba kya ta ta shi. Wallahi mata hudu ya so zai iya aura a lokaci guda. Amma da yardar Allah ko ya aureki sai mun mishi aure." Cewar Anti Bilki tana mai kwantar da Yasmin a saman  tana jijjigata don ta yi bacci. Ramlat dake shirin tayar da sallah ta dubeta rai a ɓace. "To ko hakan za'a yi? Ki tambayeshi wanda ya nacewa wani tsakanin ni da shi. Nace bana so, bana yi, wai dole ne?" Ta ja tsaki ta fice daga dakin zuwa can bayan gidan wurin ciyayi ta zauna tana aikin kuka. Ita kuwa Bilkisu ranar wuni ma ba ta yi ba a gidan yanda ta yi niyya, ta goye diyarta ta fice ba da sanin mijin ba. Duk borin da ta je ta tayar a gidan su Hilal game da kalaman Ramlat din, iyakar su matan kawai ta tsaya don su Jidda har da kukan takaici da tausayin yayansu. Ji suke kamar a fasa gaba daya  sai dai ba su da ta cewa tunda iyaye maza sun tsawatar. *** Duk wani hidima da za'a yi Abba ya ce ayi kafin a daure aure, don a cewarsa ana daura auren to fa dakinta za'a miƙa ta.   Shagulgulan koda sun yi armashi, basu yiwa Ramlat ba. Baƙin komai take gani. Dinnerparty Hilal yace ya fasa ganin irin shirin da ƴan uwansa ke yi na gasawa Ramlat magana a ranar.   "Shirun Ramlat na nufin abubuwa da dama." Fadin Hajiya bayan daurin aure, a sadda Zulaihat ta bi ta sashin Abba don amsar laffayar da Ramlat din za ta sanya. "Nima nayi mamakin yanda ta kwantar da kai ake bikin lafiya ba kamar yanda na zata ba. Amma ko ma mene ita ta sani. Mijinta ne yanzu, idan ma ta wulakantashi ita za ta kai kanta wuta." Cewar Zulaihat cikin halin ko in kula. "Uwani kenan, ku dai dinga zagayawa kuna yi mata faɗa. Ta dauki duniya da zafi, ta sauke." Ba ta son ma zancen, don haka ta sungumi karamin akwatin da aka zuba kayan da duk Ramlat din za ta yi amfani da shi a ranar farko bayan kai ta gidan kafin a kawomata sauran akwatin, ta fice daga falon. Hajiya sai ta tsinci kanta da kasa fita wurin yan uwanta, ta zauna ta yi shiru cikin tunanin meke tafiya a zuciyar yarinyarnata. "Allah Yasa dagaske kike Ramlatu." Ta furta cikin faduwar gaba kafin ta yunkura ta mike ta fita. ***   Dogon hijabi ta sanya a saman leshin da ke jikinta. Ga kunshi da kitso an mata. Kwalliyar fuskar ta kara fiddo kyawunta sosai. "Ina zuwa?" Cewar wata Hannatu ƴar Gwaggonsu Sa'adu ta Daura. Murmushi ta ɗan yi. "Yanzu zan dawo." "Ki sauri don Allah, yanzu za'a zo nemanki tunda an yi magriba." Ta ja guntun tsaki ta fice. Allah Ya taimaketa har ta fice ba ta hadu da su Zulaihat ba. "Malam Hassan. Malam Hassan." Ya fito daga dakin gugar. (Daki karami a gidan inda Malam Hassan ke musu gugan kaya) "Na'am." Ta ɗan waiga sai kuma ta yi shiru sanadin wasu da suka zo wucewa. Ta kauda fuska har suka fita. Cikin sauri ta dubeshi. "Ya ake ciki?" Cikin rashin gaskiya ya kalli jama'a kafin ya ba ta amsa. "Bayan gidan na ajiye, na tabbatarmaki ba wanda zai kawo komai don kusa da inji ne." Ta yi murmushi. "Nagode." Daga nan ta daga zani ta fiddo kudi masu yawa kulle a leda ta mikamasa. "Abinda kake zargi ba shi zai faru ba kamar yanda na rantsemaka. Barazana ce kawai." Ya yi murmushi ya gyada kai. Shi ko mene ba damuwarsa ba ce tunda ya ji dumus. Hankali kwance ta koma ciki, suka yi kiciɓus da Zulaihat. "Ina kika je?" Ta yi murmushi. "Shikenan kuma ba damar na yawata a cikin gidanmu?" "Nan da awa kadan za ki bar gidan zuwa gidanki kema." Fadin wata abokiyar wasansu Asabe. Aka yi dariya, ita kuwa ta shige don kaucewa kaifafan idanun Zulaihat din dake kanta, kallon rashin yarda tsantsa take mata. *** Aka kammala shirin kai ta gidan miji, Abba ya ce aje zai je har gidan washegari ya yi nashi fadan. Hajiya kuwa ta ce wanda yayyunta da gwaggonni suka yi ya wadatar. "Saura ku yafemata." Cewar Dije abokiyar zaman Hajja. Daga Abba har Hajiya suka ce sun yafemata duniya da lahira. Tana kuka aka tafi da ita gidan Hilal. Gidan da ta ke mishi kallon wuta.   Aka watse aka bar ta, jikin Amrah a sanyaye, ta kara juyowa ta dubeta da lulluɓin har lokacin. Dawowa baya ta yi tana hawaye ta lalubo hannunta ta rike.   "Na sanki Ramlat, ba ki fiye cire abu a ranki da wuri ba. Na sanki kamar yunwar cikina. Kiji tsoron Allah. Ki ji tsoron Allah." A hankali ta ji Ramlat ta zare  hannunta daga nata. "Amrah muje, suna jiranmu." Fadin Maryam da ta leƙo. Amrah ta mike tana kallon Ramlat, kafin kuma a sanyaye ta juya ta fita bisa gargadin Abba da ya ce ba ya son abar mutum ko daya da zummar wani siyan baki. Kamar jira ta ke sahu ya dauke, kamar jira ta ke ta bar jin motsin kowa a gidan. Ta bude lulluɓin laffaya gaba daya ta fito. Babu kowa kamar yanda ta zata, ba ta damu da dukiyar da aka zuba a gidan ba, bai isheta kallo ba hakan yasa a gaggauce ta fita. Komai da sauri take yi tana kara waigen kofa har ta zagaya bayan gidan. Nan ta iske baƙar ledar da ta tabbatar shi ne saƙonta. Ta dauka ta jijjiga sannan ta murmusa. Ledar ta cire ta dauki sakon zuwa ciki. Ta adana a karkashin gadon ta zauna.   "Komai zai zo karshe a yau, daga yanzun ba wanda zai kara tadamin hankali akan Hilal. Babu shi!" Ta furta a fili, ƙarar bude gate da ta ji ne ya sanya ta warware ɗankwali da yin wurgi da ribbons dinta a gefe. Idanunta kuwa dama kallo ɗaya za ka yi mata ka gane irin kukan da ta ci. "Yau ko ni! Ko kai Hilal!" Ta ƙara fadi.I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/iRW2CA35T9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 14)    Kallo ɗaya za ka yi mishi ka hango annashuwa a zuciyarsa. A jikinsa yake ji komai ya zo karshe, a jikinsa yake jin ya samu soyayyar Ramlat da yardar Allah. Sai dai bai san meyasa kirjinsa ya hau bugu bayan daka motarsa da fitowarsa ba. Ya ɗan yi shiru yana kallon kofar gidan, bai jima da rabuwa da babban amininsa Ma'aruf ba. Sosai ya ba shi shawarwarin da suka dace game da zamansa da Ramlat. Ya dauka dari bisa dari. Ya kalli sama, walkiya ake yi sosai ga hadari. A hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan ya yi kari cikin gidan. Ya rufe kofar falon sannan ya ƙaraso ciki da sallama, falon ya tsaya ƙarewa kallo. Ɗakin Amarya kam ya yi kyau iyakar kyau, abu daya idan ya tuno yakan dakushe farin cikinsa sai dai kuma karfin gwuiwar da ya samu daga Amininnasa shi ya rinjayi komai har ya sa shi nufar hanyar ɗakinta da sallama. Bai son gayyar abokai da sunan rakiyar Ango.    Ya cika da mamakin rashin ganinta zaune  a saman gadon kamar yanda ya zama al'adar aure.      "Ramlat."  Ya kira da tattausan murya yana karasa shigowa dakin. "Tooh." Ya kara ambata ganin farin laffaya da ɗankwalinta yashe saman gadon, hanyar banɗaki ya kalla, kai tsaye ya shiga bayan ya ajiye babbar riga da hula saman gadon.  Nan ma wayam, sai tashin kamshin turaren wutan da aka sanya da kyallin fararen tiles da ya kashemishi ido.   "Gani nan!" Sautin muryarta a sama, wannan ne ya sa shi juyowa da sauri yana kallonta baki sake. Ya kai duba ga jarkar da ke hannunta na hagu da kuma ashanar da ta rike a dayan hannun.  Tana tsaye a tsakiyar dakin, kallo ɗaya za ka yiwa idanun ka san ta ci kuka ba kaɗan ba. Tana tsayen amma jan majina take yi, ga wasu hawayen da ke ƙara sauka saman fuskarta. "Ramlat? Me ya haka?" Ya furta cikin nuna dakiya sai dai zuciyarsa tamkar ta fasa kirjin ta fito tsabar tashin hankali. Duban tsana take mishi. "Ka fini sanin mene haka Hilal tunda ka nace akan lallai sai ka zauna da ni! Nace bana sonka! Na fasa aurenka! Amma ka tursasa lallai sai da aka auramaka ni! Dole ne? A farko wa ya yimin dole? Ba ni na kawoka gidanmu na nuna ina sonka ba? To na fasa! Na fasa! Bana sonka amma ka nunan kai maye ne! Kafin ka cinyeni ni zan soma kashe ka! Dama ni rayuwata ta kare tunda har aka daura aurena da mutumin da na fi tsana! Muddin ba ka sake ni ba wallahi ina maka rantsuwa da Maƙagin dare da rana, yanzu ba anjima ba, zan watsa fetur dinnan kuma na kyafta ashana mu mutu gaba daya! Kar ka yi tunanin guduwa domin na rufe ko'ina a gidannan! Na rufe ɗakunan!" Tunda ta soma maganar ya ƙuramata ido, mamaki da baƙin ciki suka cika zuciyarsa. Bai taɓa kaiwa ƙoluluwa a ɓacin rai bisa yanda take mishi ba irin yau. Bai kuma taɓa zaton za ta aikata makamancin hakan ba. "Ramlat? Yau soyayya ce ta koma ƙiyayya? Dama ƙiyayyar ta yi zafin haka? Kin manta Hilal? Kin man..." Bai kai ga ƙarasawa ba ya ga ta ɓalle murfin jarkar ta hau watsa kalanzir a tsakar dakin har da bangwaye, ba ta ko damu da yanda ya ke jiƙa riga da hannunta ba. Cak ta ji ya riƙe hannuwan wanda ya yi sanadin faduwar jarkar a ƙasa. Idanunsa sun kaɗa saboda tsananin tashin hankali da ɓacin rai. Ganin yanda take kici-kicin kwatar kanta ya sanyashi watsi da hannun har hakan ya yi sanadin faɗuwarta a ƙasa, har lokacin ba ta bar kuka ba, ganin ta na kokarin kyafta ashanar ya sa ƙafa ya buge hannun, ashanar ta faɗi a ƙasa. Durkusawa ya yi saitinta. "Ba sai kin kai ga kashemu ba! Ki je ki auri wanda kike so, ni Hilal na sake ki. Sai dai ki sani, idan har da hakkina, Allah zai min sakayya. Shakka babu kin yimin butulci, kin tarwatsa dukkan farin cikina. Kaicon wannan ranar." Daga haka ya mike yana kallon yanda take dariya tana share hawayen fuskarta. Ya juya saboda kallonta ma kuma ɓata ransa yake. Shakka babu mai hakuri bai iya fushi ba.  "Ina za ka? Ai da saura!" Bai yi niyyar tsayuwa ba sai dai dole ya tsaya din jin ya murɗa kofar amman ko gezau. Jakar hannunta ta nufa ta fiddo karamin littafi (Memo) da aka raba na bikinsu, a take ta yage bangon ta yar a ƙasa, ya bi bangon da kallo, hotonsu ne, bai mance ko ranar da za'a yi hotunan sai da ta gasamishi maganganu masu zafi, sai dai hakanan ya danne ya shanye. Kallonta kawai yake yana ƙara mamakin yanda so ya koma ƙi. Ramlat  da a baya zai iya bugun kirji ya ce ta fi sonsa kan yanda yake sonta. Yau ita ce ta juyamasa baya lokaci guda. Bai dauka abin zai biyo har cikin aurensu ba. Ba kyawunta ne ko diri ya ruɗeshi ba, kaunarta yake da zuciya ɗaya. Da ace ɗayan biyun da ya lissafa ne, ba zai rabu da ita ba tare da ya gogamata tabon da har ta mutu ba za ta mance ba. Bai kuma mance yanda Ummansa ta ɓatamasa rai ba duk akan ya nace sai ya aureta. "Tunanin me kake? Karɓa ka rubutamin a rubuce." Daddaɗar muryarta da a yanzun ta zama kamar ta zakanya a kunnensa ta katse shi. Ya karɓa yana kallon kwayar idanunta, ta yi amfani da wannan damar ta harareshi ta tsuke baki gami da kauda kai. Ya maida kai ga takardar yana kammalawa ta karɓa. Bakinsa na rawa ya ce. "Ban mukullin." Ba ta ko kalleshi ba ta ciro mukulli cikin riga ta miƙamasa. Ya karba da sauri ya bude kofar ya fice zuwa falo.   A gaggauce ta mike ta zura hijabinta dogo na sallah da aka daukomata. Ta dauki jakarta ta fito. Yana zaune a falo ya dafe da hannuwansa biyu yana fidda hawaye kirjinsa na suya. Ba ta ko kalleshi ba ta fita, burinta ya cika. "Duk abinda ya faru, ka so faruwarsa!" Ta furta a fili kuma a hankali sa'ilin da take share hawayen fuskarta.    Tana tafe tana sharar hawaye, ga wata irin iska da ake yi da walkiya. Allah Ya taimaketa ta samu abin hawa kai tsaye gidansu ta nufa. Ta yarda idan ma kasheta za'a yi, su kashe. Ko mene su yi mata. Amman ita kam ba za ta iya zama gidan Hilal ba da sunan mijinta kuma a waje tana cin amanar mijin aurenta na sunnah ba. Ba za ta iya wannan munafuncin ba don ta san karshen abinda soyayyar Aliyu da auren Hilal zai jawomata kenan. ***   Abba ya dubi Hajiya da murmushi a saman fuskarsa. "Yau ina cike da farin ciki. Na kashe matsalar Ramlatu, fatana yanzu Allah Yasa ta zauna lafiya da mijinta." Hajiya dake kakkaɓe shimfiɗa ta yi murmushin yaƙe. Har lokacin hankalinta bai kwanta ba. Sam ba ta da wata nutsuwa. "Amin." Ba tare da ta kalli Abban ba, ta ci gaba da aikinta. Ya sa hannu ya riko hannunta, hakan ya dakatar da ita ta dubeshi. Tsoro,  fargaba su ya hango cikin kwayar idanunta. "Ya aka yi? Ashe ba za ki fawwalawa Allah komai ba? Ki bar tunanin wani abu akasin alheri." Ta gyada kai kawai tana jin saukar ruwan hawaye. Hayaniyar da suka jiyo na mutanen gidan ya sanya su kallon juna cike da rashin fahimta. "Meyafaru?" Fadin Abban  hankali a dan tashe, Hajiya kuwa kirjinta ne ta shiga bugu fiye da baya. Da hanzari suka fito suka nufi babban falon gidan na Hajiya.    Tana tsaye jikinta sharkaf sakamakon ruwan da ya yi mata duka cikin adaidaita sahu, kuka take yi yayinda taron dangin uwa da uba suke neman ba'asi hankali tashe. Hajiya ji ta yi jiri na shirin kayar da ita hakan yasa ta samu ta zauna saman kujera tana salati. "Ya isa haka!" Tsawar da Abba ya daka cike da karfin hali don jikinsa ma rawa yake yi, shi ya katse su duka. Kai tsaye ya karasa ga Ramlat ya kama hannunta suka shiga bangarensa. Irin su Zulaihat da Amrah da suka san komai dangane da auren, kuka kawai suke yi sanin cewa koma mene Ramlat ta shuka wata tsiyar ne. *** "Daina kuka Ramlatu, ya isa, ya isa. Ki fadamin meke faruwa?" A hankali ta ciro takardar a jakarta, babu inda ba ya rawa a jikinta ta mikawa Abban. "Don sonka da Annabin rahma s.a.w, Abba ka yafemin. Ba zan iya zama da Hilal ba." Ta furta tana sheshsheka sosai. Abban ya fita shiga tashin hankali,ya fita shiga ruɗu. Hannunsa rawa yake, kirjinsa zafi yake. Yana ji inama mutuwa ta taddashi tun kafin ya haifi ɗiya kamar Ramlat?  Daidai lokacin da Hajiya ta turo kofar ta shigo. "Wace irin ƴa na haifa? Rabi'atu wace irin ƴa kika haifamin?! Anya ba'a yimin musanye a asibiti ba?! Don ina mamakin kasancewar Ramlatu jinina!"   Ta riga ta gane, ba'a hayyacinsa yake ba, ta san ɓacin rai ne. Ta ƙaraso sosai gwuiwa a sanyaye ta kai karbi takardar da Hilal ya rubuta sakin. Na saki Ramlatu saki daya bisa tursasawarta. Allah Ya zaɓamin wacce ta fiyemin ita alheri. Itama Ya bata abinda take so. Abban ya mike zuwa dakinsa. Waya ya ɗauka ya kira Yaya Munir ya fadamishi dukkan abinda ya faru. Ya kara da fadin. "Gobe da safe ka zo muje gidan su yaronnan. Ina rantsuwa da Allah, muddin ina numfashi Ramlatu sai ta auri zaɓinta. Sai ta auri wanda ta ke so." Daga haka ya katse kiran, ya zauna ɗabas gefen gado. Bai san ya akai ya soma gani bibbiyu ba, sai ji ya yi ya kife zuwa ƙasa. *** Hajiya tana kuka ta ke magana a falon. "Kaicon mai taurin kai da bauɗaɗɗen hali irin naki. Kaicon ƴa da ba za ta yi biyayya da iyayenta ba. Ina jiyemaki makomar rayuwarki Ramlatu." Kowannensu kuka yake, Hajiya ta mike har hakan ya zaburar da Ramlat don a zatonta duka za ta sha, sai dai ta ga ta shige daki ta bar ta nan zaune. Ita kuwa Hajiya ba ta ga dalilin dukan ba, wanda ke jin magana kuma ya ke da gatan a fada ya ji ko a tursasa ya bi, shi ne suke da ikon idan bai ba su daga hannu su daka. Banda Ramlatu, ta nuna musu iyakarsu. Mijinta ta hango kwance a ƙasa rub da ciki. Hannu ta sanya a kai cike da matukar gigicewa ta buga salati iyaka ƙarfinta. A zabure Ramlat ta shigo, Hajiya tana jijjiga Abban tana kiran sunansa. "Kar ka mutu Khalid! Ba ita kadai ka haifa ba! Kar ta kashemana kai!" A can falo kuwa jin salatin Hajiya ya shigo da mata da ƴan samari (baƙin Daura) ƴan biki cikin falon Alhajin. Sai dai ba wanda ke da ikon ƙarasawa dakin Abban sai Zulaihat da ta nufi ciki da sauri. Idanun Rafee'ah ya wacce ta zauna dalilin jin wani murɗi da cikinta ke yi ya kai saman takardar da ke kan kujera, ta dauka tana karantawa, sai ta ji kamar an karawa tsohon cikinnata ƙaimi wurin murɗawar. Ta matse takardar da karfi tana rike cikin da salati. Daidai sadda aka fito da Abba, samarin suka tari Hajiya da Zulaihat suka rikeshi aka fita. "Ku dube ni!" Cewar Rafee'ah da ke murkususu  riƙe cikinta ɗan wata bakwai, ga hawaye caɓe-caɓe saman fuskarta. Ai tuni wasu cikin iyaye aka yi kanta aka taimaka ta mike, ga ciwo a jikinta, ga tunanin Abbansu da kuma wannan tashin hankali da bakin ciki da Ramlat ta jawomusu a wannan rana. Motar Abba har ta yi gaba, har lokacin ruwa ake ba ƙaƙƙautawa. Itama Rafee'ah motar kai yara makaranta aka ciro, daya daga cikin baƙin Daura ne, Dauda, direban tasi. Shi ya tuƙasu cike a Bus zuwa asibitin. Tana gefe tana kuka kamar ranta zai fita, ba wanda ya kara kallonta, duk wanda ma ya kalla ya tambayeta meke faruwa ba ta ko kallonsa balle ta amsa. Amrah ce ta nufi inda take ta ja hannunta suka shiga daki ta kulle kofar. Ta dubeta a gigice, idanun sun yi ja. Kasancewar Amrah farar fata ya sanya hatta da fuskar ta dauki ja na wacce ta ci kuka. "Me kika aikata?" Ramlat ga ɗago ta dubeta cikin sheshsheƙa. "Me ake zaton zan aikata don Allah Amrah? Me ake zaton zai faru da aure irin nawa? Ya sakeni. Ya sakeni saki ..." Bata kai ga ƙarasawa ba Amrah ta fidda hannu ta dauketa da lafiyayyan mari. Marin da ya hargitsata ya kuma sa ta cika da dumbin mamaki. Amrah ƙawa kuma Aminiya ita ta fidda hannu ta mareta? Abinda koda wasa ba ta zata ba, ya zo mata a hagunce. Kafin ta farfaɗo daga tunanin da ta faɗa na tuna ƙarfin alaƙarsu da Amrah din. Ta ji kaifafan kalamai na fitowa daga bakinta. "Wallahi ba ki da hali! Ba ki da hali! Na tsaneki! Haka kika zaɓarwa kanki? Haka kike da son kanki? To ki sani, tun kafin wani ya wulakantaki! Ke kika soma wulakanta kanki! Tun kafin wani ya ci zarafinki! Ke kika soma nuna ke din ba kowa bace ba ki da daraja da mutunci ko ƙanƙani! Ki yi kuka da kanki Ramla! Ki kuka da kanki bisa duk abinda zai biyo baya! Sai dai ki saka a ranki! Allah Madaukakin Sarki Shi ne Ya ce mu bi iyayenmu! Sun mana komai, sun kyautata mana. Ke kuma kin zaɓi ki saɓamusu saboda wani banzan Aliyu! Saboda wani shashasha da bai san ciwonki ba! Wallahi Aliyu ba ya sonki! Kema kuma ba sonsa kike ba! Hauka kike! Ni Amrah Abdullahi ki sani, a yau a wannan rana kuma, babu ni babu ke! Ba zan iya ƙawance da mai hali irinnaki ba. Ban yi sa'ar ƙawa ta gari ba mai daukar shawara. Yau idan Abba ya mutu saboda banzan son rai irinnaki, ki sani kina cikin masifa. Bani babu ke! Na tsaneki." Tana kaiwa nan ta bude kofar ta fice daga dakin a guje tana kuka. Ramlat ta zube a wurin tana kuka sosai har da sheshsheka. Sosai maganganun Amrah sun shigeta, kuka take kamar ranta zai fita. Mutuwar Abba da ta ambata shi ya fi komai tsayawa a ranta don haka ta mike a gigice ta fito. Matan da ke falo suna jimami suka dubeta. "Ke Ramla ina za ki?! Ke!" Fadin Yakumbo yar uwar Abba. Masu kwari suka bi bayanta dakyar ta yarda ta zauna ta jira su dawo gidan. Idan Abba ya mutu ba za ta yafewa kanta ba! Da gaskiyar Amrah, tana da son kanta da yawa. ***   Da gaggawa aka shigar da Abba ciki, itama Rafee'ah an miƙata Labour room don an tabbatar haihuwa ce ta tahomata kuma bakwaini.   Hajiya na zaune tana kuka har lokacin ba ta cewa kowa komai ba, Hajja ta zauna gefenta. Cikin fada take magana. "Wai menene ke faruwa Rabi? Bamu kai mu ji bane? Haba! Tun a mota nake tambaya an min shiru!" Baba Hajara diyar Hajja ta biyu ta caɓe. "Nima dai Hajja abinda ban gane ba kenan. Sai kuka ta ƙi magana. Ga Rafee'ah ma na naƙuda. Ki fadi meke faruwa ko hankulanmu zai kwanta." Zulaihat ta ƙaraso wurin rike da takardar sakin Ramlat da Rafee'ah ta damƙamata kafin a shige da ita daki. Ta dubesu tana kuka. "Sakin Ramlat fa aka yi. Ita ta sanya Hilal ya saketa. Wannan ne dalilin faduwar Abba, da kuma naƙudar Rafee'ah." "Wace Ramlatun aka saka?" Cewar Hajja, tambayar dake zuƙatan maza da matan gurin kenan saboda rudewa ma sun kasa gasƙata batun Zulaihat. To mene abin ɓoyon? Abinda komai ya riga ya bayyana, zubewar girma da bada kunyar da ake tsoro ya afku. Irin ABINDA AKE GUDU (Batool Mamman) ya riga ya faru. Don haka sai ta musu filla-filla yanda zasu gane. Sai ga mata na kuka da salati. "Ni dama na san ba inda dolen nan zai kaimu. Kamar na sani Rabi'atu na ce ki fadawa Khalid a fasa. Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Wannan wane irin zamani muke ciki? Lokacin da aka mana auren bamu san mazajen ba ma, mu ce me?" Hajja ke wannan batun tana kuka. "Amm, don Allah Mama ku yi hakuri. Kun yi yawa a asibitin nan, ga marar lafiyarmu ba ya son hayaniya. Don Allah ku ragu, ko kuma ku yi shiru. Kuna damun sauran marasa lafiya su ma." Likita ke wannan jawabi a tausashe. Ya dubi Zulaihat don fuskarta kadaiya shaida sai ta Hajiyar. "Kina iya biyoni ofis." Ta amsa da toh tana share hawaye ta bishi a baya. Can kuwa Nos ta fito ta na fadan ba wanda ya tsaya wurin Rafee'ah gashinan ta haihu kuma ana bukatar kayan amfani. "Me ta haifa?" Har suna hada baki wurin tambaya. "An samu namiji. Itama kuma da sauki jikinnata." Suka sauke ajiyar zuciya, nan aka yiwa mijin Rafee'ah waya akan ya zo kuma ya taho da kaya da gaggawa, ta haihu. Abinda ya jefashi cikin ruɗu da mamaki kenan, an haifar masa bakwaini. *** Likita ya yi faɗa kwarai akan yanda aka bari jinin Abba ya hau sosai, ya kuma ce anan zai riƙe shi har sai ya warware. Zulaihat kuka kawai take. Ya kammala rubutun ya miƙa mata takarda. Har ta mike ta dawo. "Dr don Allah ko za ka kiramin Munir a waya." Likitansu ne, hakan yasa suka saba sosai da mutan gidan. Ya fiddo wayarsa ya dannawa Munir kira. Shi kuwa Munir dama tun sadda ya dinga kiran wayar Abban ya ji ba'a dauka, ya fito ya taho bai ko damu da ruwa ba. Kwanciyar hankalinsa daya, uayi tozali da Abban.   Ya na hanyar nufar gidan ne, kiran Dr Sunusi ya shigo. Da mamaki ya ɗaga, maimakon ya ji muryar Dr Sunusi sai ya ji ta Zulaihat. Ba shiri ya gangara gefen titi kirjinsa na bugu ya ɗaga. "Hello Baban Yasmin, Zulaihat ce." "Meke faruwa Zulaihat? Ina Abba? Ya kirani ya yimin wasu zantuka marasa dadin sauraro." Cikin kuka ta soma zayyane mishi dukkan abinda ke faruwa bayan fitar Dr daga dakin. Salati kawai ya ke, jiki na rawa ya katseta. "Ganinan zuwa Zulaihat, don Allah a ragu a asibitin. Ki ban Dr, kar ya bar kowa ya shiga wurin Abba yanzu." Ta amsa da to ta leka ta mikawa Dr Sunusi sannan ta yi gaba. Shi kuwa Munir ya jaddada wa Dr Sunusi cewa kar ya bar kowa ya shiga wurin Abba daga nan suka yi sallama ya sauya location zuwa asibitin. ***  _*Bayan Cudewar Awanni*_ Safiya ce, garin ya yi sanyi kuma ya yi luf-luf kamar a lokacin wani hadarin ne zai hadu ruwa ya ƙara sauka kamar yanda aka kwana ana yinsa. Kamar wacce laka ya fashewa a ciki, haka ta shiga taka barandar asibitin. Idan yaro zai yi mata kallo ɗaya, nan take zai ayyana a ransa cewa mahaukaciya ce. Ga duk mai hankali kuwa zai ga tsantsar tashin hankali da damuwa cike fal shimfide a saman fuskarta. "Mutuwa akai mata da alama." Ta tsinci muryar wasu mata a gefe, ba ta kallesu ba balle ta tofa. Ba kowa ta ke ganewa ba,ba kuma kowa take gani ba. Abbanta kawai take son sanyawa a idanu. Da shi ta kwana kuma ta tashi. Hijabin jikinta duk ya cukurkuɗe ya yi jirwaye na ruwan hawayen da ta dinga gogewa da shi. Silifas ne a kafarta na baƙin gidansu, ba ta san inda nata yake ba. Ta dai tuna da shi Hajja ta yi amfani wurin dukanta. Fuskarta yatsun Amrah ne kwance a samansu wadanda har yanzu basu baje ba.  Tana fashin sallah, wannan yasa ba ta kalli gabas ba balle fuskar ta ci darajar wanki. Ta dai tsarkake inda ya zamemata dole saboda kyankyami irin nata, ko ba komai kula da lafiyar jikinta ne. Ta shanye komai a awannin da suka biyo baya. Zagi, tsinuwa da ma duka, duk ta dauka daga dukkan wadanda acewarta sun kai su yi mata su. Ta ji ta dau komai idan har za'a bar ta ta ji da abinda ke cin ranta. Har ta iso dakin da Abba ke kwance tana tunani mai zurfi, ta gane dakin a dalilin hango Mijin Rafee'ah, Isma'il da ta yi zaune a saman kujera, gefensa Yaya Munir ne su na magana. Yaya Munir na kallonta tana kallonsa. _"Ban yarda ɗayanku ya taɓa lafiyarta ba, kar wanda ya tuhumeta akan abinda ta yi, ni da kaina zan auramata wanda take so. Na dauki laifina na yi mata auren dole kamar yanda ta ce."_ Ya tuna kalaman Abbannasu a jiya ga Hajiya, Zulaihat da kuma shi Yaya Munir din. Sai dai ya yiwa kansa alkawarin babu shi babu Ramlat. Don haka ya kauda kai kamar bai ganta ba. Isma'il ne ya tsayar da ita suka gaisa yana mata fadan ba ta kyauta ba, tsam Yaya Munir ya mike. "Muje ga Rafee'ah ko?" Ya katse Isma'il. Hakan yasa shima ya mike suka tafi. Ta bisu da kallo idanun taf da kwalla sannan ta murda kofa ta shiga dakin Abban da sallama. Babu kowa a ciki sai Abban dake kwance ya yi shiru idanunsa biyu. Ya juyo ya dubeta, ga mamakinta murmushi ya yi mata. Ta sunkuyar da kai ta ji saukar hawayen da take riƙewa a saman kuncinta. Hannu ya miko. "Zo nan Ramlatu." Tana tafiya kamar a iska tsabar ramar da ta yi ta zauna saman kujerar gefensa ta rike hannun sai kuka. "Abba don Allah ka yafemin. Abba na tsani kaina, na kasa rankwafar da zuciyata na yi maku biyayya. Abba ka yafemin na tuba. Na shirya zama da Hilal kamar yanda ku ke so. Ku ce ya maidani. Wallahi zan zauna." Murmushi Abba ya yi, ya shiga girgiza kai. "Kin ji nace ba zan ba ki Aliyu ba? Ko wani ne ya ce hakan? Ki yi shiru ki daina kuka, ni na yi laifi da na dage wurin yi miki aure da wanda bakya so. Ki yi hakuri ki yafemin kinji? Zan aura maki Aliyu cikin satinnan in sha Allahu. Yau zan koma gida ba zan ƙara kwana a asibitin nan ba. Idan har Khalid na raye, sai kin auri zaɓinki. Ki daina kukan. Na yafemaki duniya da lahira. Allah Ya yi maki albarka." Ya ƙarashe da rarrashi, ta kasa gane zantukan Abban suka dosa. Ta kasa gane dagaske yake maganar ko kuwa mai harshen damo ne? Don haka ta bi umarninsa ta share hawayen. Ya dinga jan ta da hira har ta yi dariya. Hankalinta ya ɗan kwanta. Amman maganar Abban ta shiga yawo a kwanyarta cike da rashin gamsuwa. Maimakon ma ta yi murna, sai ta shiga firgici da kuma faduwar gaba. Daga nan ta karasa dakin Rafee'ah, ba ta shiga ba, ta hango baby mai kyau dai, ta yi murmushi sannan ta koma ga Abban. *** Kwana biyu da sallamar Abba, ya sallami dukkan baƙi ƴan Daura, ya basu hakuri akan abinda Ramlatu ta yi. Daga nan ya tara iyalinsa ya tsawatar akan bai yarda ko maganar banza wani ya yiwa Ramlat ba. Abba da mahaifin Amrah, da ma wasu a ƴan uwa, suka dunguma har gidan su Hilal. Suka ba iyalinsa hakuri cike da nadamar abinda Ramlatun ta aikata don tuni sun ji abinda ta yi har ya saketa. Bai ɓoye wannan ba. Wannan ya ɗan sassauta ran iyayen Hilal, ko ba komai iyayen Ramlat sun nuna ba hannunsu. Basu nemi sulhun kome ba, koda sun nema iyayen Hilal sun yanke wannan alaƙar. Hatta Alhaji Aminu mahaifin Hilal wannan karon ya yi Allah wadai da irin Ramlatu. Toh Abban ma bai da ra'ayin komawarta. Washegari kuwa kamar yanda suka nemi iyayen Aliyu, sai gasunan sun zo. Ba ɓata lokaci Abba ya karbi sadakin ƴarsa. Nan aka daura auren Aliyu da Ramlat don duk wani bincike an yi ta hanyar Yaya Munir an kuma tabbatar daga Hilal har ita Ramlatun babu idda a kanta. "Ga sadakin aurenki Ramlatu, na auramaki Aliyu. Ina fatan wannan zai faranta ranki. Zai sa ki dawo da walwalarki. Ki kuma maido soyayyarmu a zuciyarki?" Ta ɗago ta dubi Abba tana hawaye. Abban murmushi yake har hakoransa tana hangowa. Ita ya kamata ta yi irin wannan kalar fara'ar, sai ya kasance ita ce mai kuka, Abban da mutan gidan na dariya. Hajiya ma sosai ta sakarmata fuska. "Ramlatu matar Aliyu. Allah Ya baku zaman lafiya." Wannan ne kalaman Hajiyar kafin ta fita zuwa asibiti wurin Rafee'ah duba lafiyarta. Ramlat ta shiga daki ta zauna, ta yiwa kudin da Abba ya damƙamata kuri da idanu, abin mamaki su dinma jiƙasu ta soma da hawayenta. Ranar da ya kyautu ta yi rawa da juyi, ranar da ya kyautu ta fi kowa farin ciki. Abin mamaki kuma ya sanyata, kukan ta shiga yi kuwa iyakar ƙarfinta, koda za'a shaƙeta ba za ta ce ga dalili ba. Ba ta da masaniyar cewa Mafarin kenan!!! ***   https://my.w.tt/iRW2CA35T9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 15) Kallo ɗaya za ka yi mishi ka hango farin ciki tsantsa da walwala marar misaltuwa a saman fuskarsa. Sigari ya sanya a bakinsa yana zuƙa lokaci daya yana fesarwa. Ihu da kurantawa shi kawai ke tashi daga bakin maza da matan wurin. "Cau cau Aliyu Angon Ramlat!" Fadin G Baba. Hakan sai ya kara tunzura Aliyu har sai da ya zuƙe kara biyu cikin ƙanƙanin lokaci kafin ya kwantar da kai yana kallonsu ƙasa-ƙasa yana doka murmushi. Ko ba komai yau burinsa ya cika. Ko ba komai ya mallaki abinda ya jima yana dakonsa. Ya na a jingine da kujera cikin club ɗin, yana kallon yanda ake rawa da rausaya mata da maza. Duk ana yi don tayashi farin cikin  samun cikar burinsa. Hannu ya zura a aljihu ya ciro bandir din dubu daya ya bude ya watsamusu. Aka hau kwasa ana ihu da kara korantashi. Abin na mishi dadi. Wayarsa dake saman tebur ya duba, kira ke shigowa ba kuma na kowa ba sai na Granny. Ya mike tsaye ya yi musu bankwana ya fice. Yau bai sha abin maye ba don ya fi son a yi komai cikin hayyacinsa ya gani. Bai daga kiran ba har sai da ya bude sabuwar karamar motarsa Honda wanda Abulle ta sanya aka siyamishi ya shiga. Ya soma tuki a nutse kafin ya dauki waya ya kira Granny. "Ina ka shiga wai? Ka zo mu tattauna game da lefen." Ya yi murmushi gami da kara  lumshe lumsassun idanunsa. "Ina hanya Kakus, gani nan tafe." Ya kashe kiran bayan ta mishi addu'ar zuwa lafiya. Ya kai duba ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Karfe tara da mintoci na dare. Buga sitayari ya yi gami da sakin ƴar ƙara da furta. "Yes!!" Cike da nishadi ya kara gudun motar gami da ware kiɗa. Har ya isa gidan bai kashe  kidan ba duk kuwa da hango iyayensa maza da ya yi zaune a saman tabarma ƙasan ƴar rumfa a farfajiyar gidan. Duk sadda irin hakan ta kasance, tattaunawa suke game da wani abun mai muhimmanci. Kallonsa suke har ya kashe motar ya fito zai nufi cikin gida ba tare da tunanin gaishesu ba. Idan da sabo ya ci ma su saba. Malam Abdussalam cike da takaicin halin ɗannasa ya sunkuyar da kai. "Kai! Aliyu?!" Fadin Kawu AbdulRashid wanda ke bi wa Malam Abdussalam a haihuwa. Aliyu ya maido akalar tafiyar garesu. "Gani. Sannunku." Yanda ya gaishesu kerere ya fi komai baƙanta ransu. Daƙuwa Justice ya wurga mishi. "Ungo wannan! Yanzu kai tsabar iskanci da rashin kunya mu kake yiwa gaisuwa irin na ƴan iska?" Nan ya gane kurensa, sai ya durkusa yana shafar suma. Dama ya riga yasan har gobe dattijon haushin sakin da ya yiwa ɗiyarsa yake. Yana cikin farin ciki yau, don haka bai shirya wani abun ya ɓata ransa ba. "Ku yi hakuri." Ya ce kai tsaye cikin tausasa murya. Banda warin taba ba abinda ke tashi a jikinsa. Sun gaji da magana daya akansa. "Allah Ya shiryeka Aliyu, Yasa wataran ka sauya." Cewar Kawu AbdulRashid ransa na zafi. Nan Justice ya shiga magana. "Yarinyar nan mun ji labarin abinda ta aikata, kuma ta yi a bakin duniya duk don ta aureka. Ta yi laifi, ta yi kuskure. Mahaifinta ya damƙa amanarta gareka, da kunnenka ka ji kalamansa." Aliyu ya gyada kai cikin son tuna abinda Abban ya furta gareshi ranar da ya karbi sadakin Ramlat a hannun magabatansa. *"Ramlatu amana ce Allah Ya ba ni, yanzu kuma amanar za ta koma kanka. Ban ce lallai sai ka kyautata mata ba, ban kuma ce lallai sai ka yi mata adalci a rayuwa ba, duk wannan hakki ne da ya rataya a wuyanka ko ban faɗa ba. Ka ji tsoron Allah a lamuranka, kar ka manta zai tambayeka duk wani abu da ka aikata a rayuwa."* Bai mantawa a lokacin murmushi ya yi kawai. *'Ba dai haka ka so ba Abbanmu. Sai dai ba za ka hana abinda Allah Ya yi ba.'* Nan take ya ce a cikin ransa. "Don ubanka ina magana kake dariya? Wane raini kenan?" Kalaman Justice suka katse tunaninsa, ya ankara da murmushin da yake zabgawa har haƙoransa na bayyana. "Ayi hakuri." Ya kara fadi. Kowanne ya tofa albarkacin bakinsa kan ya riƙe amanar yarinya, daga nan ya yi musu godiya ya mike da uzurin Abulle na nemansa. Mahaifinsa ya bishi da kallo gami da addu'ar shiriya. Yaran ka haifa ba ka isa ka saita halayyarsu ba. Kiciɓus suka yi, ba haka ta so ba. So ta yi da sauri ta bar dakin Abulle kafin ya cimmata. Shigarta dakin Abulle don kai mata goron da ta dauko a dakin Daddynta. Jin Abulle na mitar Aliyun ya zaunar da ita zaman jiransa ya sa ta katse hirartasu ta yi mata sallama ta fito tana sauri ta bar bangarennata. Sai dai kuma ba yanda ta iya tunda gashinan gabanta. Ta daure ta haɗiye komai dake tasomata. "Ina wuni Yaya Aliyu." Bai san yana da kunya ba sai a yanzun, ya kauda kai daga kallonta. "Lafiya. Ya kike?" Ba tare da ta amsa ba ta wuce da sauri ta yi hanyar kofar sashinsu. Bayanta ya bi da kallo, Muhibbat kenan. Ya sa kai dakin Abulle. Salati ta shiga yi kafin ta hau yi mishi fadan sigari da ya sha. Taɓe baki ya yi, ya mance da hakan shaf bai jefa alawa bakinsa ba, bai kuma fesa turare ya tsaye a waje na mintoci ba kafin ya hau mota ya tuƙo. Ya mance rabon da ya shigo gidan yana warin taba. "Wai ni don Allah ki bar kunnena ya huta. Shikenan don kin ji warin abu a jikina sai ya kasance sha na yi? Ko a addini an hana irin wannan yanke hukuncin. Idan ina sha tsawon lokacin nan ba za ki sani ba sai yanzu? Mtsw, Abokina ne ya sha, shi na ziyarta shi ne ƙamshin ya biyoni." Hakan da ya faɗa sai kuma ta gyara zama ta hau jijjiga kai. "Kuma fa hakane. To ka kara kiyayewa dai. Raɓar abokai ɓata gari ba naka bane. Na soke abotar. Yanzu dai ya batun lefe? Mahaifinka cewa ya yi na farko an maka, na biyu kai za ka yi. Duk da haka Alƙali da sauran kawunnanka sun ɗan ba ka wani abin ka haɗa ka yi." Murmushi ya yi. "Lefen Baby ina son ya fi na kowa. Ina son a bude a kirashi da lefe. Masu yi mata habaici da zagi a kan aurena su daina. Don haka da kaina naji zan hada abina koda ace hakan na nufin karyewar jarina." Baki sakaka Abulle ta saki tana kallonsa kafin ta magantu. "Um um dai Zakina, ba za'a yi haka ba. Ƴar dangi ma ba ka ce hakan ba sai akan bare? Ina rabaka fa." Ya yi dariya. "Abulle tawa ni kadai,  Baby ai ta isa na yi mata komai. Koda kuwa komai nawan zai ƙare a kanta." Ta taɓe baki. "Fadi dai sunanta na zahiri, shi zan fi fahimta. Ramlatu ko? To naji, ungo nan." Ta daga filo ta fiddo damin kudi ta mikamasa. Ya karba ya zura a aljihu. "Wai nikam me zai hana ka mayar da yarinyarnan ɗakinta ne? Naga dai tsiraicinka yafi rigar aro ta mutane." Miƙewa ya yi tsam! "Sai da safe Kakus. Kwanta ki yi bacci abinki. Nima na tafi nawa lissafin." "Ai fa, ba dama a dauko magana sai ka kauce. Toh har gobe ban ga wata ɗiya da za ka kawo na ji ina sonta a raina ba irin Muhibba." Daga kafada ya yi alamar ke ta shafa ba kuma tare da ya komai ba ya fice daga dakin. Ko a ransa bai ƙara tada zancen Muhibbat din ba. ***   "Kai Allah Ya rayamana mai sunan Abba." Fadin Zulaihat kenan cikin waya tana murmushi ranta fari ƙal. Ramlat na daga kicin tana dahuwar indomie ta ji wannan kalamin. Anan ta fahimci sunan Abba ɗan Rafee'ah ya ci. Kwalla suka tarar mata, a yanzu ba ta rabo da hakan. Tunda aka daura aurenta da Aliyu, komai ya daina yi mata dadi. Ba kuma don ba ta sonsa ba, har gobe tana jinsa a ranta. Wuyarta ya kira wayarta ko kuma ta kirashi, za ka ganta cikin farin ciki da annashuwa. Kalamansa masu taushi da dadi, wanda ke nuni da nutsuwa da kuma cikar hankali, sun fi komai yi mata dadi a ranta. Sai dai ba ta nufin ta rabu da yan uwanta a dalilinsa, duk suna amsamata idan ta yi magana, sai dai irin amsawar da gwamma kar su yi. Babu fara'a babu sakin fuska. Sama-sama suke amsawa kamar ba sa so.  An kwaso kayanta kaf a gidan Hilal, a daren jiya ya zo har gidan ya riski Abba a falonsa. Sun jima suna magana sannan ya tafi. A hirar Zulaihat din da Hajiya ta ke jin cewa hakuri ya ba shi. Hakuri bisa sakin ƴarsa da ya yi. "Ke wane rashin hankali ne za ki kunna gas har abu ya ƙone haka? Gobara kike son jazamana? Ko mu dinma kashemu za ki yi?" Ta waiga ta dubi Zulaihat s'ilin da ta sanya hannu ta kashe gas din. "Hajiya ta ce ki yiwa Mijinki magana za'a je a yi jere don Abba ya ce a satinnan za ki tare. Ya kawo muƙulli." Tana kaiwa karshe ta fice a kicin din, kawai sai Ramlat ta fashe da kuka. Haka to za su ci gaba da yi mata? Indo ta risketa tana kuka, ganin ta dage wurin rarrashinta duk kuwa da haushinta itama ta ke, ya sa ta daukar wayarta ta bar kicin din. Abincin da ba ta ci ba kenan. ***   Akwati takwas cif Aliyu ya shaƙe da kaya na gani na faɗa. Yakasai gidan su Hajja aka kai lefen kamar yanda Abba ya bada umarnin a yi.   "Anya Rabi'atu wannan yaron ba ya cin haram a aikinsa? Wannan wane irin kaya ne ya shaƙowa yarinyarnan?" Hajja da mamaki ya kasheta a zaune  ke wannan furucin cikin waya ga Hajiya. Hajiya ta yi murmushi mai ciwo. "Ko ya ya dai Hajja ai ita yarinyar ta fi kowa sanin yanda aka haihu a ragaya. Tunda ya kawo lefe an karɓarmata shikenan. Ta je ta yi ta sakamishi." "Kai Rabi, na rabaku da irin wannan fushin fa. Meyasa Khalid ya biyewa yarinyarnan bai yi bincike ba? Har da gwal a sarkokin." "Hajja ina zuwa zan kiraki." Hajiya na fadin hakan ta katse kiran. Ba wai don abin bai tayarmata da hankali ba, sosai hankalinta ya tashi. Yaron da aka ce a kasuwar ma ba wani mayar da hankalin a zo a gani yake ba. Ba ta son tunkarar mijinta da wannan batun, don ta lura yana cikin damuwar auren Ramlatun har lokacin. Wannan ta sa ta kira Munir. Kafin ma ta yi nisa ya katse zancen. "Hajiya ke mahaifiyata ce. Don girman Allah kiyi hakuri ki bar min zancen Ramlat. Hajiya ki zubamata ido tunda kun mata abinda take so. Ku yi hakuri ku bi ta da addu'a idan da bukatar hakan. Ba ita kadai ku ka haifa ba, muna raye zamu share kukanku. Ki yi hakuri, ki sanya a ranki hakan ya zama alheri ba sharri ba." Da wannan ya samu ya zame kansa daga abinda Hajiyar ta kawomishi, na bincike akan harkar Aliyu. 'Wane bincike bayan mai afkuwa ta afku? Komai ta fanjama fanjam!' Ya fadi a kasan ransa. ***   "Ai yanzu kin girma, kin mallaki hankalin kanki, ba kya bukatar nasiha daga gareni. Duk abinda kika aikata ga rayuwarki daidai ne." Kalaman Hajiya suka shigeta sosai, ta cikin laffayar da Zulaihat ta naɗeta a ciki, kuka take. Ba ta san sadda ta bude lulluɓin ba ta karasa ta dafa cinyar Hajiyarta. "Don  son Annabin Rahma s.a.w Hajiya ki yafemin. Ki yafemin ko zan ga haske a rayuwata. Na yi miki laifi, ki yafemin don Allah." Zuciyar uwa mai rauni, ta cika da tausayinta. Tausayi na abinda take hangomata wanda ita ba ta hanga ba. Shaye-shayen da Abba ya ce Aliyu na yi ya tsayamata a ƙahon zuciya. Ta daure ta mike bayan ta zame jikinta. "Ku wuce Uwani, dare  yana yi. Allah Ya bada zaman lafiya." Ba tare da ta ƙara magana ba ta shige banɗaki, Zulaihat wacce ko a jikinta ta amsa da Amin kafin ta ɗago Ramlat. "Mrs Aliyu mu karasa ga Abba ko?" Ta riga ta ɗan kusan da biyu Zulaihat ke kiranta da hakan, suka shiga Abban na zaune saman darduma yana karanta Alkur'ani mai girma. Ya ɗago ya dubesu, tunda ya dora idanu akan Ramlat bai kifta ba. "Ramlatu an fito?" Yanda ya furta cikin taushi ya sanya zuciyarta kara narkewa. Ya yi ƴar dariya. "To mene abin kuka? Yanzu kin zama matar aure. Komai ki ka yi, ko za ki yi ki sani cewa Allah Yana kallonki. Ki ji tsoronSa wajen gudanar da lamuranki. Ramlatu duniya da kike gani tana da faɗi, sai dai zuƙatanmu sun fi ta faɗin. Idan mun yarda da hakan, mun  cikata da alhairai masu yawa, mun yi irin aikin da Allah Zai farin ciki da mu. Mu zama cikin ceto AnnabinSa s.a.w. Duk isa da taƙamar mace, ba komai ba ce a wurin mijinta. Ki rike wannan, ki bi mijinki sau da kafa. Kar ki sake ki zama mai tona asirinsa." Abba ya ci gaba da koro jawabai, ba Ramlat kadai ke kukan ba, hatta da Zulaihat kukan take. Kukan tausayin wannan uba mai matukar don ɗiyarsa da alheri, mai mafarkin ya ga ta yi aure a inda ba za ta taɓa wulakanta ba. Sai dai kash, burinsa bai cika ba. "Nagode Abba, Abba kaima ka yafemin. Hajiya ta ƙi yafemin. Abba ka tayani roƙonta." Nan take ya umarci Zulaihat ta kira Hajiya. Ta bi umarninsa sai gasunan tare. "Na yafemata idan don haka ka kirani." Ta tari hanzarinsa don tasan kafiya irin ta Ramlat da naci. Murmushi ya yi. "Mun gode Hajiyarmu. Ban riƙe ki ba a rai kinji Ramlatu? Tashi ki tafi dakin mijinki. Allah Ya yi muku albarka. Ya dauwamar da ku a dakunan da'iman." Daga nan suka mike zasu fita, dakatar da su ya yi. Da kansa ya taso ya lalubo hannun Ramlat wacce lallenta na tun bikinta da Hilal shi ne a hannun, har baƙin ya soma gogewa. Alkur'ani mai girma ya sanyamata a ciki. "Babu wani hasken da ya wuce haskenSa. Babu magani da kuma waraka face ta hanyar karantashi da kuma addu'a. Kar ki yi wasa da tilawarsa." Wani kukan ta kara kecewa da shi, maimakon Abban ya koma mazauninsa, sai ya kama kafaɗarta ya yi mata rakiya har cikin motar da Aliyu ya turo. Iyayen Aliyu su na kallo, sannan ya koma cikin gidan zuciyarsa a karye. *** _*MRS ALIYU*_   Ya kara jawota jikinsa ya rungume, kuka take sosai. Duk kuwa da cewar ta tsarkake jikinta ba ta bar jin radadi-radadi ba. "Haba Baby, damuwa kike son na shiga ne? Sai kuka kike, ya zan yi miki ki daina?" Ta soma ƙoƙarin tureshi daga  jikinta. "Ni ka rabu da ni." Ya yi murmushi gami da kara kankameta. "Ni ba zan iya rabuwa da ke ba Baby. Ki yimin duk abinda kika san zai sa ki huce. Kinji?" Ta turo baki, ya sa hannu ya shiga sharemata hawaye. "Fadamin me kike son na yi miki a rayuwa kwatankwacin wannan farin cikin da kika ban, kinsan an ce yaba kyauta tukuici." Ta tsinci zuciyarta da jin dadin kalamansa. Ba ta san sadda ta yi murmushi ba. Damarta kenan, ya kuma kamata ta yi amfani da shi kar ya wuce. "Karatu nake son ka bar ni na ci gaba." Ya rungumeta yana ƴar dariya. "Wannan mai sauki ne Baby. Ki ajiye a ranki kin yi karatu kin gama, wannan ya zamemin kamar farilla, fadi wata bukatar." Ta yi shiru, jin saukar dumin hawaye saman fatar kirjinsa ya sanya shi ɗago haɓarta yana dubanta. "Baby, meyasa?" Ya yi maganar kamar mai raɗa. Ta sauke kwayar idanunta daga kallonsa. "Sanadinka na shiga tarin matsaloli. Na jure dukkan wuya, na karya dukkan alƙawura, don Allah ka rikeni amana, ka bani kulawar da iyayena da dangina zasu aminta da zaɓina. Ina  son mu ba marar ɗa kunya." Ya yi murmushi. "Kina shakku a kaina ne? Ko kina kokwanto akan son da nake miki? To ki daina, har mai ɗa sai mun ba kunya a zamantakewarmu. Ki kwantar da hankalinki." Ta yi murmushi, so da kaunarsa na ninkuwa cikin ranta. Nan kuma labarin ya sauya. ***   Soyayya ce tsantsa ke gudana a gidan masoyan, Aliyu dakyar yake iya fita kasuwa ya ga yanda yaransa ke tafiyar da lamura. Iya soyayya da shagwaɓar Ramlat har mamaki yake ba shi. Hakan ke kara susutar da shi. A wannan lokacin yana takatsantsan da shan dukkan wani abun maye a gaban Ramlat.     Sai da suka cika sati biyu da aure sannan suka shirya zuwa gaida iyayensa. Ta haɗe cikin leshinta maroon ta yafa farin mayafi sai takalmi da jakarta suma farare. Ta yi ado daidai gwargwado, ta ciko kadan, ramarta ta ragu sosai. Hakan ya ƙaramata kyau.   "Babyna kin yi kyau kamar mu fasa fitar." Ya fadi yana rungumo ƙugunta. Ta watsamishi kallon soyayya ya kama saitin kirjin gami da lumshe idanu yana murmushi. "Ahh, kasheni za ki yi ko?" Dariya sosai ta shiga yi ta kwace jikinta. "Muje don Allah." Ya kamma hannunta suka nufi motarsa. Tafiya suke suna jinsu kamar a gajimare. Wakar Nazifi Asnanic mai taken Jamila da Jamilu shi ke tashi a motar, hannunsa na dama cikin tafin hannunta. Ji take kamar ba ta da wata matsala da ta yi saura a duniya, kamar wata sarauniya haka take ji musamman yanda Aliyun ke rera wakar yana dubanta jefi-jefi. Har suka iso wakokin soyayya daga Asnanic da Nagudu kawai suke ji. "Mun iso Madam." Ta ɗan harareshi da wasa sannan ta yunkura da zummar maida takalminta da ta cire a zaman motar. Kafafunta suka taka wani dunkulallen abu kamar takarda. Ta sa hannu ta dauka sa'ilin da ta zura takalmin. Daidai sadda Aliyu ya bude mata murfi ta fito. Kirjinta ne ya buga, ko ba ta shan sigari, ta san wannan dai karan sigari ne. "Mene wannan?" Ta tsinci kanta da watsa tambayar duk don ta samu tabbaci. Yatsuntsa ta ji ya sa ya karba gami da yin cilli da shi yana tsaki. "Wannan banzan ne, G Baba ya sha min a mota." Ta ji hankalinta ya kwanta, ta sauke ajiyar zuciya. "Muje Baby, yau Kakus za ta ganki." Ya karasa zancen da riko hannunta su soma tafiya cikin son basarwa. Har ga Allah ta yarda da zancensa. ***   "Masha Allah, ashe kishiyartawa itama ba baya ba kamar wata balarabiyar Sudan." Dariya Aliyu ya yi, itama Ramlat murmushi ta yi gami da ƙara sunne kai. Abulle kuwa har ranta ta ji tana son Ramlatun, ta dage akan sai ta ci abinci, a dole ta tsakuri tuwo miyar agushin da ta diremata. Daga nan suka fice sashin mutan gidan. Jikin Ramlat ya yi sanyi matuka da irin tarbar da ta samu a gurinsu, ta dauka zasu kaunaceta kamar yanda Abulle ta nuna, sai dai abin ba haka ba. Bangaren karshe da suka shiga, bangaren Justice. Aliyu ya nufi falon Justice yayinda ya ce ta shiga ciki. Shi kam banda ma dole da Abulle ta yi mishi da ba zai shiga ba. Hajiya Maryam ta kalleta ta watsar, tun kan su shigo labari ya zo mata daga bakin Autar Kawu AbdulRashid, Hannatu.  Sanye cikin hijabi ta fito daga dakinsu don amsa kiran Mamarta. Ta ci karo da Ramlat zaune ƙasan kujera ga Mamar ta kurawa talabijin idanu abinta. "Muhibbat, ga matar Aliyu ta zo a gaisa." Kusan lokaci guda suka kalli juna, kowannensu kallon ƙurillah yake yiwa ɗan uwansa. Kowacce so ta ke ta gano abinda ta fi ƴar uwarta. Bangaren Ramlat, kammanin Aliyu  take gani a fuskar Muhibbat. Shakka babu ba ta hango abinda za ta gwada mata ba. Hakanan Muhibbat, sai dai ta ce da Ramlat din baƙar fata a kanta, banda wannan ba za ta ce ga abinda za ta gwada mata ba itama.   Murmushi suka saki a tare, murmushin da ya fi zama na yaƙe. Kowanne na kokarin danne abinda ya ke ji game da ɗan uwannasa. Suka gaisa a mutunce sannan Muhibbat ta koma ɗakinta. Rufe kofa ta yi ta sauke ajiyar zuciya. Ya dace ta shafe komi a yanzu itama ta ci gaba da gudanar da rayuwarta. A bangaren Ramlat, sai ta hango wani sanyi da taushin zuciya a wurin Muhibbat din, ba ta taɓa zaton ma za ta jure ganinta koda da sakan daya bane. Sai ta kasance mutan gidan ga dukkan alamu su ke tayata kishin.  Tana nan zaune har Aliyu ya turo a kirata, ya dubi kwayar idanunta yanda ya sauya. Cikin sauri ya tallafi fuskarta. "Baby meke faruwa? An fadamaki wata maganar ne?" Ganin hanyar baranda ce ta shiga falon Justice, sannan hanya ce ta jama'a yasa ta kauda fuskarta tana murmushi. "Ba komai. Mu tafi." Sauke ajiyar zuciya ya yi. "Na dauka wani abin suka fadamaki yanzun na shiga na nunamusu ainahina." Mamakin kalaman ya sanya ta dubansa, sai dai tuni ya soma tafiya yana bata umarnin ta biyoshi. 'Kin manta sunansa Aliyu? Gadanga ƙusar yaƙi. Ba dai zuciya ba.' Faɗin wani bangare na zuciyarta. Ta samu tarba mai kyau kamar yanda ta zata, don dukkan dattawan sun karɓeta hannu bibbiyu da salama. Banda mata da sauran yan uwan Aliyu, wasu ƴan mata ma tana jin sadda suka saki wata shewa da guɗa, ta kuma san da ita ake. A mota shi ke ta zuba hira banda ita, ta karanci abubuwa da dama a gidansu Aliyu. Amman kuma suna isa gida ta bar zancen a gefe guda a ƙasan ranta saboda soyayyar da Aliyu ya shiga nunamata mai kashe duka lakan jiki. ***   Tsakaninta da iyayenta sai waya, za ta kira su dauka a gaisa. Yaya Munir kuwa ta tabbatar blocking dinta ya I daga kiransa don a farko sai ta jira ya yi ta ringing ba zai ɗaga ba, yanzun kuwa gaba daya ma ta bar samunsa. Amrah kuwa ƙarara ta fito ta yi mata kaca-kaca akan ba ta son kiranta. Itama karshe ta nunamata tana da zuciya, ta tattara ta watsata a kwandon shara. Sakamakon jarrabawarsu ta fito, Aliyu da kansa ya shiga fafutukar nemarmata Admission a B.U.K.   _"Kai Baaba, kar ka yarda matarka ta fi ka Degree idan kuwa ba haka ba kana cikin kwale-kwale."_ Sa'ad ke ba shi wannan shawarar sadda ya shiga jami'ar Bayero wurinsu. Shi kam bai jin wannan a dalilin da zai tauye farin cikin Ramlat. Ko ba komai shi ma DAN ADAM ne, yana da zuciya, ya kuma yarda da cewar ta mishi halacci.   _"Bar ɗan iska! Wato kai za ka yi jidalin kudin karatun ma?"_ G Baba ya furta hakan. Aliyu ya toshe kunnensa ya kuma zagesu tas. Karshe suka zuba ido su ga gudun ruwansa. *** *WASA FARIN GIRKI* Tsalle ta shiga yi har da juyi kafin ta kara wani tsallen ta faɗa jikin Aliyu, ya kuwa yi mata kyakkyawar runguma suna dariya. Murnar ba ta komai ba ce illa ta samun Admission a jami'ar Bayero. "Wash! Baby karyamin wuya za ki yi wai?" Ta sakeshi suka yi dariya. "Ban isa ba Sweet Aliy. Nagode sosai sosai. I love You so much." Ya ja hannunta ta faɗa jikinsa. "Muje ki nunamin a zahiri." Daga nan ya shiga yi mata raɗa a kunne. Ta kauce suna dariya. Sai da komai ya kammala sannan ta yi mishi rakiya har wurin motarsa, kamar kar su rabu haka ya ja ya fice Kasuwa. Wayarta ta dauka da zummar kiran Hajiyarta su gaisa, sai dai abin takaici ba kudi a ciki. Nan take ta tuna katin da Aliyun ya siyamata a darenjiya da suka fita shan ice cream, yana tsokanarta akan ba zai bata ba sai ta ce tana sonsa sau cikin carbi, ita kuwa dariya kawai ta yi. Daga nan ya zura a aljihu ta mance ba ta karɓa ba. "Alhamdulillah." Ta furta a bayyane cike da nishadi, ta nufi dakinsa. Kai tsaye wandon da ya cire jiya ta fiddo a kwandon zuba kayan wanki. Zura hannunta keda wuya, ta ji kwali da wani abu. Ba ɓata lokaci ta ciro duka. Kirjinta ya bata dam! "Kwalin taba da lighter?" Ta faɗi a mamakince, zama ta yi gefen gado jiki ba ƙwari, ta kasa yarda Aliyu mashayin taba ne. Ganin komai ta ke kamar a mafarki. 'Ba ki ganin yanda leɓɓansa keda duhu?' Faɗin wani sashi na zuciyarta. To ta ya za ta yanke hukunci da hakan bayan cewa akwai masu irin halittar? (Baƙin leɓe) "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Allah Yasa tunanina ba gaskiya bane." Ta fadi a fili. Kamar ta maida inda ta ganshi, sai ta barshi a saman gadon don kawai ta ji me zai ce. Jiki ba kwari ta shiga laluba daya bangaren, anan ta ci karo da katin wayar ta ciro, ta maida wandon kayan wanki ta fita. Murnar da take duk ta dusashe don haka koda ta gama shigar da katin a waya, sai ta ɓige da rubutawa Abba text tana mai sanarmishi da cewa ta samu Admission a B.u.k. *** Abba na zaune sun karyawa a falo, da iyalinsa. Wayarsa ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ya kai duba sa'ilin da yake kokarin kurɓar shayin citta da kanumfarin Hajiya. Ganin sunan Ramlatu na yawo a saman wayar yasa shi ajiye kofin a gaggauce ya bude sakon. Murmushi ya ɗan yi. "Madallah." Ya furta cike da dakiya. Hajiya ta dubeshi tana murmushin itama. Suka hada ido. "Ƴarki ta samu gurbin karatu a jami'ar Bayero. Sai ki bita da addu'a." Idan ya ce ƴarki, ta gane wacce yake nufi, don haka ta kauda kai ciki-ciki ta ce. "Allah Ya bada saa." Abba ya amsa da Amin gami da godiya. Ita mamakin Abban ma take yanda yake nuna halin ko'inkula da abinda Ramlat ta yi musu. Mutum mai tsauri idan aka taɓosbi, shi ne ya sauko har haka. Tana mamaki kam. A wajenta abu ne da bai da saukin wucewa, ba kuma ta jin kafafunta za ta taka gidan Ramlat har abada. *** Ɗaure fuska ya yi. "Binciken kuma na menene kike yimin?" Ta bude baki gami da tattara fatar gira tana kallonsa. "Bincike? Ni ba bincike na je ba, katin da ka siyamin na je ɗauka. Sweet Aliy don Allah ka fadamin gaskiya. Hankalina ya kasa kwanciya wallahi, sigari ka ke sha?" "Idan ina sha sai me? Please Baby Ina roƙonki ki kyaleni. Haba, na shigo gida ba ki kai ga ban abinci ba za ki ƙara min yunwa? Tunda nake da MUHIBBAT ba ta taɓa yimin irin haka ba. Bana so please ki bari idan kina so a zauna lafiya." Yana kaiwa nan ya shige bandaki gami da rufo ƙofar. Da ace tasan asarorin da suka hau kansa a Kasuwa, da ba za ta tareshi da batun wani banzan sigari ba. A dalilin ya burgeta, ya yi amfani da maƙudan kudadensa na saro kaya ya haɗa lefe, bai tsaya anan ba sai da ya haɗa da cin bashi. Yanzun kwanciyar hankalinsa daya, ya samu Abulle ta shigemasa gaba wurin Justice ko zai ga haske. Ta kasa kwakkwarar motsi, kamar dai kunnuwanta ne basu ji daidai ba. Ta fi tunanin mafarki ne, za kuma ta farka. *Wannan zahiri ne, mai dogon zango!*      I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/Cxvlk7xM09 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. _Littafin Ƙarfen ƙafa dungurugum sadaukarwa ce gareki yar uwa kuma mai bani kyawawan shawarwari a dukkan tafiyata. Barr Firdausi Kabir. 🤩🤩🤩👏🏿Allah Ya bar zumunci. Baki ba zai iya misalta godiyata gareki ba. Allah Ya bar kauna fisabilillah. Ameeen. 💞💞Madallah da yar uwa kuma ƙawa ta gari._🤲🏿💃🏿💃🏿 16) Juyi kawai take amman baccin ya ƙi zuwa. Tunanin Aliyu na shan sigari ya fi komai dagula lissafinta. Kishin yabon Muhibbat da ya yi a gabanta ya fi komai ci mata tuwo a kwarya. Ga kewarsa da take ji, tun zuwanta gidan basu taɓa raba makwanci ba. Wannan na daga dalilan da ta kasa bacci ba tare da shi a kusa ba. Kamar yanda ba ta yi bacci ba, haka shima. Karfe kusan ukun dare ta fito falon da zummar daukar ruwa. Ji ta yi an rungumeta ta baya, za ta yi ihu ya rufe bakin. "Baby ni ne fa." Sauke ajiyar zuciya ta yi, sai kuma ta shiga kokarin tureshi. "Ka rabu da ni." Ba ta yi aune ba ta ji ya ɗauketa cak zuwa dakinsa, duk yanda ta so ta kwace abin ya ci tura, sai da ya ajiyeta saman gado kafin ya yi saurin ƙarasawa ya datse kofar yana nishi. "Baby kin soma nauyi wallahi. Wai! Kin ji hannuna?" Ta kara murtuƙe fuska sai hawaye. "Ni ka budemin na fita, ƙishin ruwa nake ji." Ruwan ya miƙomata na roba, ta karɓa ta sha. Zama ya yi gefenta gami da narkar da murya. Gaba daya ya koma kalar tausayi. "Baby na tuba. Ba zan ƙara ba. Zan yi kokari na daina idan hakan zai sa ki farin ciki." Ta ɗan soma jin sanyi, ya sa hannu ya shiga sharemata ruwan hawayen. Yana kara kashe jikinta da kalamai masu dadi, duk inda ta ɓullo sai ya toshe. Har dai ya ci nasarar shawo kanta. ***   "Kai Zakina, kana da hankali kuwa? Duka-duka yaushe Alƙali ya ba ka gudunmuwar biki? Yanzu don rashin ta ido ka ke so ya karamaka jari? Kar fa ka manta ba haifarka ya yi ba." Kalaman Abulle sun matukar ɓatamasa rai. "Eh ki gorantamin! Dama kema nasan ba sona kike ba, kowa ma a gidannan ya tsaneni ya tsani ci gabana. Toh ai shikenan, duk abinda zai faru ya faru. Idan aka soma bi da ni ofishin ƴan sanda kwa fidda kudi wurin belina." Yana kaiwa nan ya sa kai zai fita, Abulle tuni ta yunkura ta rike gefen rigarsa. "Haba Zakina, Gadanga ƙusar yaƙi. Me ya yi zafi shi ba wuta ba da za ka dinga batun ƴan sanda, da yardar Allah ba za ka taɓa tozarta haka ba har abada. Jari ko? Ka kwantar da hankalinka ai ni na haifi Alƙali ba shi ya haifeni ba, don haka dolensa ya yi yanda nake so. Sha kuruminka anyi an gama. Haba ɗan marayana? Yi dariyar mana." Yanda ta yi din sai ya sanya shi murmusawa. "Yauwa ko kefa Kakus, ke fa kika haifesu, ba wanda ya isa ya ketare umarninki. Idan ma sun gwada ki yi musu kuka da barazanar tsinuwa ki ga idan za su ƙi." Ya ƙarashe murya ƙasa-ƙasa, bai damu da duk ma abinda za ta ce ko ta aikata ba, shi dai ya tsira a wajen Alhaji Yusha'u, ya biyashi kudadensa ya kuma farfaɗo da kayan shagonsa. "A'a, bai kai ga nan ba. Ai idan an tafi ga hakan ban ma isa ba, shi a wa? Kai dai ka kwantar da hankalinka kawai. Da kaina zan kiraka na damƙa maka." Sai sannan ya saki dariyar farin ciki, wannan ya kwantar da hankalin Abulle. Kauna da tausayin Aliyu na kara ratsa ta. Kusan dagaske babu mai sonsa a gidan, ta kuma sani halinsa aka tsana, toh hannunka kuma ai ba zai ruɓe ka yanke ka yarr ba. "Yanzu ka sa ranka a inuwa dai. Wannan bushewar taka ne ban san ta menene ba Zakina. Kodai kishiyartawa ce ba ta kiwatamin Kai yanda ya dace?" Ya sanya harshe ya lashi busassun leɓ ɓansa yana murmushi. "Babyna tana kiwata fiye da zatonki. Har ta fi diyarku kula da ni." Taɓe baki Abulle ta yi. "Mu gani a ƙasa, wai an ce da kare ana biki a gidansu. To Allah na tuba ko sadda kake auren Muhibbat ka fi haka kyau da sheki." Miƙewa ya yi gami da jan tsaki. "Kinga Kakus na tafi, ba zai yiwu na tsaya sauraronki kina zagarmin mata ba. Sai anjima." Bai bari ta kara tankawa ba  ya yi wuf ya fice a ɗakin ya bar ta ta dogon salati.   Shi kansa ya sani yanzun sigari da kayan maye na kara hudashi yana shiga cikin jikinsa. Ƴan dabarun da yake yi ma a baya don kar gano komai zuwa lokacin ya gani ya daina. Shikenan kuma ba zai huta da rayuwarsa ba? Zai ɓata lokaci da tsoron mutan duniya. A'a. Ya gaji. Ba ruwan Ramlat a ciki, shaye-shayensa ne.   Ya ayyana hakan a ransa. *** "Saboda bishiyar kudi ce da ni?" Ya furta ransa na wani zafi, zafin ba na komai bane sai irin yadda Mahaifiyartasu ke biyewa son ran Aliyun kamar shi kadai ne jikanta. "Kai AbdulRazaƙi, ni kake faɗawa haka? Na shiga uku ni Abulle, dama akwai ranar da zan yi magana ka nunamin iyakata? Oh duniya ina za ki da mu? Allah Ya jiƙan Malam, Allah Ya kawo nawa ajalin na mutu ku huta." Justice ransa ƙara ɓaci, ya yi maimakon ya lallaɓata kamar yanda suke yi idan ta soma irin wadannan zantukan, sai ya hau faɗa, ta inda yake shiga ba ta nan ya ke fita ba. "Nan kika ɗaurewa yaronnan gindi ya je ya haɗa lefen burga, ba yanda ba muyi don a tsawatar ba kika hau yi mana barazana da tsinuwa muka kama bakunanmu. Shi yaron bai an muna da details na dukkan abinda yake shukawa ba a gari? Ko an fadamasa don mun ba shi jari ba ma sanya idanu? Sai ki yi ta zama kina biyewa yaro yana ƙara lalacewa? Sisina ba zai ƙara shiga hannun Aliyu ba da sunan wai jari." Yanda ya dage yana surfa ruwan faɗa sai Abulle ta yi lakwas ta kuma kasa kataɓus. Ko irin rikon da Aliyu ya yi ga ƴarsa bai sa ya ɗauki zafi irin na yau ba. Duk cikin yarannata ta fi su sanya da  kuma yanke hukunci cikin sanyin zuciya ba da hargagi ba, ta san Alƙali magana daya yake, idan kuwa ya yi to fa shikenan ta zauna. Yana da wahala ya yi ja in ka da ita, yau kam ko daga yanayin fuskarsa za ka fuskanci ransa dagaske a ɓacen yake don har wani ja-ja yake yi. "To ai shikenan, zan aika kauye wurin Shehu,(mijin mai tayata aiki Ladidi da ta damƙa mishi amanar kiwo) ko bijimina ne sai a siyar na ba shi. Amma ka yi hakuri ka tambayeshi wanda ke binsa bashi ka biyamishi. Ka yimin wannan alfarmar domin Allah da Annabi s.a.w. Yaronnan maraya ne, babansa bai da karfi. Ni ce komai nashi, hannunka ai ba zai ruɓe ka yanke ka yar ba." Ta yi maganar cikin karaya har da sharar kwalla, yasan har yanzu dai ana jika. Abulle ba za ta taɓa bari Aliyu ya san zafin nema ba da kansa, kowane gata burinta ta yi mishi. Ganin hawayenta ya sa shi saurin magana. "Shikenan, bashi ko? Zan biyamishi, zan tura da kaina wurin Alhaji Yusha'un da ya ce yana binsa. Na san mutumin a yanzu shi ne shugaban ƴan kasuwar kwarin, da kaina zan biya. Wannan ya miki?" Sai ta hau dariya da sanya albarka. Haka ya fita yana kara jinjina kaunar jika da kaka dake tsakanin bayin Allahn. *** *Bayan Watanni Biyu* Allah Madaukakin Sarki Mai sauya dukkan lamura, Shi ke da ikon mayar da talaka Sarki, ya kuma maida Sarki talaka. Kamar haka, Ya kawo sauyuka masu dama a rayuwar auren masoyan. *** Handout ne a hannunta tana haskawa da fitilar waya. Ta bararraje a kan gado daga ita sai karamin vest da gajeran wando. Mace ce mai gashin jiki, ga zufa. Duk da kasancewar ta bude winduna ta daga labulayen dakin, hakan bai hanata jin zafi ba, karatun ma ba shiga yake ba. Aliyu kuwa tunda ya sa ƙafa ya fita da maraice, har yanzun karfe takwas na dare ba shi da niyyar dawowa. Ta miƙe tana jan tsaki ta hau rage kaya ta faɗa wanka. Wankanta na biyu kenan daga Magriba zuwa lokacin. Ta goge jiki, wannan karon bata bi ta kan undies ba, ta zura karamar rigar bacci mai jikin cotton, duka-duka tsawonsa iyaka guiwarta ne. Ta tufke gashinta wanda rabonsa da relaxer tun na aure. Hakan yasa ya kakkarye, kitso kawai take buƙata yanzun. "Haka za'a rayu babu wuta? Nepa ma ba samu ake ba? Tab." Ta furta a fili, za ta iya cewa tun tasowarta ba ta san matsalar wuta sosai ba a gidansu. Koda zasu rasa wuta, na ƴan kwanaki ne. Yanzun kuwa a gidan Aliyu ta haura wata bata ga kyallin wuta ba. Ƴan Nepa sun musu zagaye ya fi kirga akan su biya kudi sai dai Aliyu ya ce bai da halin biya, suka gaji suka yanke jonin direct din da suka yi. Banda wannan ma lamura da dama sun sauya, idan ta ga Aliyu ya yi cefanen kaza toh fa wata ribar mai tsoka ya ci a kasuwa. Naman miya na neman kakare musu. Duk wata cima ta jin dadi ya ja baya. Ta miƙe a hankali ta fito zuwa falo ta na kallon farfajiyar gidan. Motar Aliyu na nan kamar yanda ta zata don a yanzu sai ya shafe kwanaki biyu na bai fita da mota ba sai mashin da ya siya, duk a dalilin jarinsa ya karye. Jingina ta yi jikin window ta kurawa hasken farin wata idanu tana tunani. Tunanin gidansu take, tunanin yanda aka yi watsi da lamuranta. Abba ya hanata taka gidansa, duk sadda ta ce za ta je sai ya ce mata duka-duka yaushe ma aka yi auren. Karshe ya rantse idan ya ga kafarta a gidan yanzu zai saɓamata. *"Kewarku nake Abba, kewa sosai, babu wanda ke zuwa gidana, daga dangin Aliyu har ku, ya kuke so nayi da rayuwata? Har yanzu ba ku bar fushi da ni ba?"* *Tana jin sadda ya yi murmushi mai sauti.* *"Kiyi hakuri Ramlatu, muna sonki ne, da ba ma sonki ba zamu tayaki son abinda kike so ba kinji ko? Ki shekara tukunna, ki shekara. In sha Allah a sannan ko ba ki fadamin ba, ki taki da iznin mijinki ki zo mu gaisa. Hakan ya miki?"* *Ba haka ta so ba, sai dai kuma babu yanda ta iya, ta amsa da toh yayinda kwalla suka cikamata idanu. Ba za ta iya fadawa Abba cewa Aliyu na shan taba ba har a gidan kuma a gabanta, tasan dariya zai yi mata. Don haka suka yi sallama bayan ta bada saƙon ya gaida Hajiya domin ba ta daukar wayarta.* Ramlat ta sauke ajiyar zuciya, ɗumin da ta ji a saman fuskarta ya tabbatarmata da zubar hawayenta, ta sa hannu ta share. A yau ta tsinci zuciyarta da kewar ƙawa kuma aminiyarta Amrah. Gashinan dai makarantarsu ɗaya, abinda suke karanta ma ɗaya, sai dai koda wasa Amrah ba ta taɓa bata fuskar da za su gaisa ba balle magana ta haɗasu. Ranar da ta taɓa kuskuren yi mata magana, nan take Amrah ta yi mata Allah Ya isa idan ta kara nunawa ta santa. Wannan ne ya bata haushi har ta kasa ɓoyewa ta sanar da Aliyu, sai da ta yi danasanin fadamasa da ta yi don zagin Amrah ya yi, irin ashar din da idan wani zai ce mata Aliyun ya iya, za ta musanta. *"Babu ke babu ita! Babu ke ba ita! Kika kara ma kulata nima ban yafe ba!"* Kalamansa sun mata tsauri, ta yi danasanin furtawar da ta yi, kusan ma ba ya ganin mutuncin kowa nata yanzu, daga ta soma batun kewar gida zai ce ai basu damu da ita ba. Tunaninta ya katse sadda ta ji ana ƙoƙarin bude ƙyauren gidan. Ta sa hannu ta share hawayenta gami da goge gumin da ya tsastsafo a goshinta. Maimakon ta ganshi da mashin, sai ta ganshi shi ɗaya, abinda ya daure mata kai bai tsaya rufe kofar ba ya soma kokarin nufo cikin gidan. Tabbas dai Aliyun ne kamar yanda farin wata ya haskamata fuskarsa da kuma t-shirt fa jeans din jikinsa. A gaggauce ta koma daki ta sanya dogon hijabin sallarta kuma na zuwa makaranta har ƙasa ta fito rike da fitilar wayarta. A barandar kofar falon suka yi kiciɓus. "Oops! Baby sorry. Ina mangareki ko?" Ta hau murza idanunta, kirjinta ya shiga bugun tara-tara. Ga abu dai a gabanta amma ta kasa gaskatawa, hakan yasa hannu na rawa ta dago ta haske fuskarsa ido a waje. "Aliyu?" Ta furta cikin tabbatarwa da kuma alamar tambaya lokaci guda, kafafunta ta ji sun hau wani irin mazari, kwakwalwarta ta kasa daukar abinda ta gani a fuska da yanayin gangar jikin Aliyun. "Bani hanya Malama." Ya kara fadi cikin muryar ƴan maye. Ba ta da niyyar kaucewa ya kuwa bangajeta ta fadi ƙasa ya shige yana kundumar ashar. Ta kama leɓɓanta biyu da hannunta na hagu kamar mai karɓar punishment a makaranta, kukan take yi amma gani take kamar idan ta bude bakin ihu ne zai fito madadinsa. Tunawa da ta yi kofar gidan a bude yake ya sanya ta miƙewa ta je ta rufe. A hanzarce ta koma ciki, a falon ta sameshi ya zube anan kasan tiles yana maganganu barkatai marasa ma'ana da tsari. "Aliyu? Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Aliyu me zan gani? Me..me...me?" Ta kasa ƙarasawa tana sheshshekar kuka, ta zube a gabansa. "Aliyu ka ce mafarki nake, don Allah ka daina yimin irin wannan wasan. Na yarda na sani taba kawai kake sha, ka bar yimin wasan maye, wallahi ba zan iya dauka ba. Na shiga uku ni Ramlat." Ta ƙarashe tana mai riko hannunsa. Cikin wani irin dariya na shaƙiyanci ya kamo tufkar da ta yiwa gashinta da iyakar karfinsa har ta saki ƙarar azaba. "Keee, au baby...don uwarki da kika aureni ba ki...san...ina..hawa...sama...ba? Baby...kin cinyemin kuɗina...na talauce...amma na tsira da hawa gajimare..." Ta yi nasarar ƙwatar gashinta, da wani karfin zuciya don kuwa yanzun ba ta jin kowane karfi a jikinta ta mike za ta gudu daki, ba zato ta ji ya riƙe kafar sai ga ta yiff! Ta fadi saman tiles, baki da goshinta suka ƙumu a ƙasa. Kan ka ce me sun yi suntum! Kuka sosai ta soma. "Ka kyaleni Aliyu! Don Allah ka rabu da ni karka kasheni!" Ta firta jikinta na mugun rawa, za ta iya rantsewa ba ta taɓa yin ido hudu da mutum yana maye ba sai a ranar. Ta fi gani a akwatin talabijin. Jikinta na rawa bai fasa rabata da hijabi ba kuma ya ketamata t-shirt din dake jikinnata ba, ya shiga sarrafata ya dora dukkan karfinsa a kanta. Fadi yake. "Shege G-Baba...ya ce na yi son raina dake na huce....Baby farar ƙafa gareki...ubanki bai ban komai ba....Hahaha..uban Muhibbat har gida ya ba..." Bai karasa ba sakamakon hankaɗashi da ta yi ya bugu jikin kujera, ta mike a guje ta shige ɗaki ta rufe da muƙulli. Anan cikin duhun ta zube ta shiga rera uban kuka, innalillahi wa inna ilaihir raajiun kuwa, ta ambata ya fi dubu. Aliyu mashayi? Wani irin dunkulewa ta yi a wurin ta shiga risgar kuka. KEWA, yau kewar iyayenta da ƴan uwanta take ji. A yau ta yi dakacen biyewa zaɓin ranta. Tausayin kanta ne ya lulluɓeta. Ta yi kukan mai isarta, tana jin yanda yake surfamata ashariya ta uwa da uba mara kyawun sauraro, ya gaji da bugu ya kife anan, tana jin fita da saukar munsharinsa. Miƙewa ta yi kanta na wani irin bala'in sarawa ta zura doguwar riga, ta tattare takardun ta kwanta saman gado,yanda ta runtse idanu haka ta budesu. Baccin ya tafi, damuwa da bakin ciki sun tararmata sun tsaya a ƙahon zuciyarta. Nan da nan zazzaɓi ya sauka a jikinta, haka ta kwana tana rawar ɗari. *** Sanyin asuba da kuma iskar dake kaɗawa ce, ta tasheshi daga baccin da ya shimfiɗe yana yi, ya bude ido gami da tallafe kansa da ya yi mishi wani gingirigim. A hankali hasken wayar Ramlat ta taimaka mishi wurin gane inda yake kwancen. Zumbur ya mike tsaye, komai ya dawo mishi tiryan-tiryan. Bai mance yanda ya sha magungunan mura na saka maye a tare da su Sa'ad ba a club. Ya je musu da ɓacin ran yanda a yanzun kasuwancinsa ya ja baya babu wani albarka, har ta kai ya rage facaka yanda ya dace, suka duramasa abin maye, ya yi ta sha babu kakkautawa duk domin ya ji sanyi. Bai kuma mance yanda suka kawoshi gidan ba, yana da tabbacin mashin dinsa ma can ya bari. Wani wawan tsaki ya ja, ya gaji da wani ɓoye-ɓoyen banza. Shi da gidansa? Ai dole ma wataran ta san halinsa. Maimakon ya kwankwasamata, sai ya wuce dakinsa ya kara shimfidewa saman gado, babu tunanin tashi sallar Asuba. A gefen Ramlat kuwa, dakyar ta iya lallaɓawa ta yi alwala ta yi sallah, jiri sosai ke kwasarta, ta mike ta koma saman gado, kwanciyarta ba jimawa ta ji amai na yunkurin tasomata. A guje ta faɗa banɗaki ta shiga yunkurin sai dai banda ruwa ba abinda ke fita. Ta gaji da yunkurawar ta wanke baki ta fito. Kifewa saman gadon ta yi ta shiga rera sabon kuka, tunaninta kawai mutuwa za ta yi. Babu wani mai sanyaya zuciyarta a yanzun, Aliyu tana fushi da shi, fushi mai tsanani. Gani take ta tsaneshi, ba kuma za ta iya ci gaba da zama da mutum mashayi ba. *** Motsin bude ƙyauren gidan ne ya farkar da ita daga azababben baccin da ya kwasheta ba tare da ta shirya ba. Rana tarr a saman kanta, Allah Ya taimaketa ma babu makaranta, Asabar ce. Ba laifi jikin da sauki sai dai ciwon kan bai sauka ba, bakinta babu ɗanɗanon komai. Wanka ta faɗa. Doguwar riga jallabiya kawai ta zura ta daure kanta da ɗankwalinsa. Cikin faduwar gaba ta bude kofar falon, don bata da tabbacin fita ya yi ko shigowa. Ganin ba kowa sai wayarta da kaya a yashe saman kujera ya bata tabbacin shi ne ya maido su wurin. A hankali ta taka ta dauka ta kai daki, gaban madubi ta kara tsayawa tana kallon yanda goshi da bakinta suka kumbura suntum. Hawaye ta shiga fitarwa, ba ta isa ta je wa Abbanta da wani zancen ba akan Aliyu. Sai dai kuma shi kadai ne ke sauraron ta, banda shi ko waya ta kira su Zulaihat sama-sama suke amsawa. Kicin ta koma ta dafa ruwan shayi da kayan kamshi kamar yanda Hajiyarta ke yi, ta zauna tana sha. Ba ta jin cin komai don haka ko kulolin tuwon da ta yi ba ta kalla ba balle ta iya ɗumamawa. Babu abinda ta iya gyarawa a gidan, nan falon ta naɗe tana rawar sanyi, ciwon kai ya fi na baya. Ruwan shayin da ta sha shima haka ta amayar da shi. Bacci wahalalle ya kara daukarta, ba ta ji ƙarar shigowar mashin dinsa ba, sai jin hannunsa ta yi saman goshinta. A firgice ta farka, ganinsa ya sanya ta zabura za ta ruga ɗaki. Ya riketa gam a jikinsa, kawai sai ta fashe da kuka jiki na rawa. "Don Allah ka yi hakuri ka rabu da ni, na tsaneka Aliyu, meyasa ka ɓoyemin munanan halinka? Wallahi ba zan iya ci gaba da rayuwa da kai ba." Ya ɗago fuskarta yana mai riko haɓar. "Baby wannan shi ne so? Don kin ganni a halin da ƙaddara ta jefani shi ne za ki gujeni? Baby maimakon ki ji tausayina ki tayani addu'a? Meyasa kika zo kusa da ni? Kalli yanda na ji miki ciwo? Baby baki da lafiya, jikinki zafi, muje ki sanya hijabi na kaiki asibiti. Kinji?" Cikin karfin hali ta fincike jikinta ta faɗa saman kujera tana sheshsheka. "Kar ka kara kirana da Baby. Wannan kuma ba ƙaddara ba ce, son zuciyarka ne! Kana saɓawa Allah kana kiran hakan kuma da suna ƙaddara? Wallahi sam ban yarda ba!" Kalamanta sun soma yi mishi zafi sai kuma ya danne, lallaɓata kawai yake don ba ta jin dadi, don kuma wani abu da ya ƙudurta a ransa game da itan. Wannan tasa ya gane faɗa da zafi ba nashi bane. Ɗakinta kawai ya shiga ya fito da dogon hijabi ya taho da wayarta. "Haba, ashe wayarki ba chaji shiyasa na yi ta kira bana samunki. Muje idan mun fita na bada chaji. Ki tayani addu'a, akwai wani ciniki da zan yi yau, idan ya faɗa har kaza zan siyomana, na kunna mana inji. Rashin wutar ya isheni." Maimakon ta ji sanyin kalamansa, sai ta kasa jin hakan. Asalima baƙaƙen maganganun da ya jefeta da su a daren jiya har da zagin iyayenta sun fi komai tsayuwa a ƙahon zuciyarta. Ta haɗiye komai ta danne, ita kanta yanzun tana bukatar a duba lafiyarta, tana jin jikinta kamar babu jini balle ruwa, kamar ma a yau ɗin za ta mutu. *** "Congratulations, kina da ciki wata biyu." Kalaman da ke fitowa daga bakin likitiyar suka sanyata jin hanjin cikinta kamar zasu tarwatse. "Ciki kuma? Dama haka ake cikin?" Abinda ta fadi ya sanya daga Aliyun har Likitar dubanta, shi Aliyu ko fuskarsa kadai ka kalla za ka san yana murna da hakan duk da cewa yana auna yanda nauyi zai ƙara hawa kansa. "Yes ciki, haka report ya nuna. Yaushe rabon da ki ga al'adarki?" Tsabar rudewa ma ta mance da wani batun al'ada, ita tun zuwanta gidan Aliyu ba ta taɓa ganin jini ba. Shima Aliyun sai a sannan ya ankara da hakan. Maimakon ta yi murna, maimakon a ga tana dariya sai ta rike cikin tana kuka kamar wacce aka fadawa ranar da za ta mutu. "Bana so, wallahi bana so! Dr ki zubar da shi." Wani wawan mari Aliyu ya dauketa da shi. Ta rike ƙuncin a zabure ta mike tana dubansa cike da dumbin mamaki. "Haba Malam, matarka ta sunnah? Ita za ka mara? Wane rashin hankali kenan? Koda ta yi kuskure ba ka ganin yarinya ce, bai kyautu ka lallaɓata ba? A ina aka taɓa marin mace, matar ma ta sunnah?" Bai ko kalli Likitar ba wacce haushi da takaicinsa ya kamata. Ta zagayo ta kama hannun Ramlat da gaba daya ta gigice kukan ma ya tsaya cak. Ashe dai akwai marin da ya fi karfin kuka. "Please get out. Ka bamu wuri." Yana huci ya yi kwafa gami da hadata ita da Ramlat din ya watsamusu wani banzan kallo, har ya kai ƙofar ya juyo ya hau magana. "Kika kuskura kika yi gangancin zubarmata da ciki, daga ke har ita sai na yi shari'a da ku!" Daga haka ya fice gami da banko ƙofar da ƙarfi har iskar na bugunsu. Dr Sadiya ta zauna kujerar da Aliyu ya mike, sannan ta maida Ramlat din mazauninta suna fuskantar juna. 'Ga ta a haka yarinya mai hankali da nutsuwa, sai dai da alama ba ta yi dacen miji ba.' Cewar Dr Sadiya a ƙasan ranta. Tausayin Ramlat ya kamata,ta danne ta soma yi mata nasiha. "Ramlat ke fa musulma ce, cikinki koda shege ne ya haramta ki zubar balle kuma cikin sunnah. Ba ki yi kama da mutuniyar banza ba, ba kuma ki yi kama da mata ballagazazzu ba wadanda basu je makaranta ba. Ko mene ya yi zafi a rayuwarki, ki dinga tunawa da Allah. Shi ne Mai yaye dukkan wani azaba. Ki kwantar da hankalinki, idan ma haihuwa kike tsoro ki miƙa lamuranki ga Ubangiji, In sha Allah sai kiga kin haihu lafiya. Mutum nawa ne za ki ga su na neman haihuwar ba su samu ba? Wata ma da kudi za ki ga ta zo nan tana neman maganin da za ta sha ta samu ciki. Wata kuwa har kuka take yi tana faɗin yanda miji da danginsa ke wulaƙanta ta duk akan ba ta haihu ba. Ke kuma da Allah Ya ba wa cikin ma na sunnah ki ce bakya so? Kenan kina nunawa Ubangiji ba ki yi murna da kyautarSa ba?" Ta girgiza kai tana share hawayen da sai a sannan suka zubo, so ta ke ta ce ba haka bane, so ta ke ta ce yaron ko yarinyar da ke cikinta, ba ta so su dauki ɗabi'un mahaifinsu, sai dai kuma ba za ta iyaba. Ko ba komai wannan sirrinsu ne. Dr Sadiya ga ci gaba da lallaɓata da ba ta shawarwari har sai da Aliyu ya gaji ya dawo ofishin. "Wai me ake yi? Ni fa zan iya barinki ki kwana anan idan ba ku kammala ba." Ya yi maganar a fusace, Ramlat ta mike ta yiwa Dr Sadiya godiya, ita kuwa ta miƙa wa Aliyu file din suka fita. Tun a asibitin tana jinsa yana jan tsaki har dai suka siya magani suka fito yana mitar kudinsa sun kare. "Wallahi injin ma na fasa kunnawa, kudin sun ƙare. Zan dai siyamaki kazar tunda na sakamaki rai." Gyada kai ta yi kamar kadangaruwa, fuskarta duk ta kumbura saboda kuka. Bini bini sai ta shafi cikinta. Iskar mashin na neman yi mata yawa don haka sai ta dukunkule ta kwantar da kai kadan a gadon bayansa. Hakan da ta yi dukkansu sai suka ji wani sanyi da kaunar junansu yana kara ɗarsuwa a zuƙatansu. "Ina sonka Sweet Aliyu, ba zan iya rabuwa da kai ba." Ta furta a hankali, kalaman sun ratsashi. Ya yi murmushi gami da ɗan rage gudu. "Baby wa ya ce miki zan iya rabuwa da ke? Ai mai rabamu sai mutuwa Baby. Don ina shaye-shaye addu'a za ki yimin har na daina, kin ji?" Ya ji sadda ta gyada kai a jikinsa, kusan a tare suka yi murmushi. Murmushin tana yi hawaye na zuba, zuciyarta ta kasa tsanar Aliyun. Soyayyarsa da na abinda ke cikinta suka haɗarmata. Ta kuma daura ɗamarar faɗa wa Allah matsalarta akan Ya shiryamata mijinta. Sai gashinan Gen din da yake cewa ba zai tayar ba, sai da ya siya mai rabin galan ya kunna suka ga haske. Ranar tattalinta ya dinga yi gami da fadamata karya da gaskiya duk don ta ji tausayinsa ta kuma yarda ba'a son ransa ya soma shaye-shaye ba. Ya kuwa ci galabar hakan. ***🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. _Assalamu alsikum ƴan uwana. Na gode sosai da addu'oinku. Allah Ya bar zumunci. Ameeen ameeen._ 17) Tun fitowarsu take bin bayanta, har suka bar wurin jama'a sosai. Tsayawa ta yi cak gami da juyowa a fusace. "Wai Malama bibiyar ta menene? Me kike nufi? Kin san ni ne?" Maganar ko kadan ba ta fusata Ramlat ba. Asalima hawaye ta soma ƙoƙarin zubarwa. Amrah da sauri ta kauda kai gefe, ba ta son ko kusa ta karya zuciyarta, ita kanta ta yi kewar aminiyarta sai dai kuma tunda har hakan ta zaɓamusu zai fi. "Kiyi hakuri, don Allah ki yi hakuri ki yafemin Amrah. Kowa yan guduna, idan kema kin gujeni wa nake da shi? Da ke kadai na saba shawara, ki yi hakuri ki yafemin kuskuren da na maki." A ɗan sace Amrah ta kalleta. 'Ta rame.' Ta ayyana a ranta. A fili kuwa ƙara tamke fuska ta yi gudun kada ta nuna rauninta a fili. "Ai ba ki yimin laifin da na riƙe ki da komai ba. Mutum duk abinda ya zaɓarwa kansa, sai a zuba ido a bar shi da zaɓinsa. Ba ma miki mummunan fata ko kadan." Ta juyo don ta san idan ta ci gaba da tsayuwar tsaf Ramlat za ta kalamance ta. Yanzun sai ta sauya dukkan ra'ayinta. "I am pregnant." Ta furta a hankali bayan ta kara matsawa gaba kadan. Cak kuwa Amrah ta tsaya, ta juyo tana dubanta. Gyada kai ta shiga yi tana share fuska. "Eh Amrah." Har ga Allah jin cewa tana da ciki ya sanyayawa Amrah jiki. 'To ko wannan shi ake kira rabo? Wannan auren kaddarar Ramlat ce.' Ta yi maganar a zuciya, ganin jama'a na kallonsu ya sanya Amrah magana. "Allah Ya raba lafiya. Na miki murna sosai. Kinga ana kallonmu, ki wuce gida kawai, gobe ma hadu a makaranta. Na yafemaki." Ta ƙarashe da dan murmushi. Ramlat ta ɗan rungume kafaɗarta tana ƴar dariya. Ko ba komai za ta maido amintarsu. Tare suka jera suka fita waje, abin hawa ne ya rabasu. Hatta Amrah sai sannan zuciyarta ta yi sanyi. ***   Kofar falon a bude, wannan ya kara tabbatar mata da zargin maigidan na nan, tun a bakin ƙyauren ta ga motar da a yanzun ta shaida na abokinsa G Baba ne. A gajiye take lis amman murnar shirinta da Amrah ya mantar da ita hakan.   Tun kafin ta saka ƙafa a falon, ƙaurin sigari da kuma hayaƙinsa ya baƙunci hanci da idanunta. Hira suke suna haɗawa da ashariya. Ji ta yi zuciyarta na tashi. Ta daure ta karasa shigowa falon da sallama. Suka dubeta. Aliyu ya saki murmushi. "Baby, kin dawo?" Gyada kai ta yi, don takaici ko kallon G Baba ba ta tsaya yi ba balle su gaisa ta yi ɗakinta. Zama ta yi bakin gado ranta na wani irin zafi. Kallon agogon bangon ta yi, shida na dab da yi. Kwafa ta yi ta rage kayan jikinta fa faɗa wanka.   A falon kuwa, G Baba ya zuƙi sigari ya fesar. "Madam dinka fa ba ta yi murnar ganina ba. Hala ba ta son wannan hayaƙe-hayaƙen?" Wani tsaki Aliyu ya ja, ɓacin rai sosai Ramlat ta jazamishi.   "Don uwarta an fadamata ni ban isa da gidana bane? Ko an fadamata shashashan miji ne? Zan je na sameta ai! Sa'arta ɗaya tana dauke da Baby." Wani mugun kwarewa G Baba ya yi, Aliyu ya tsaya cak yana kallonsa. "Lafiya? Ka zuƙa over Malam." Sai da G Baba ya kora ruwa sannan ya samu nutsuwa. Ya ɗan dubi kofar dakin sannan ya juyo ya kalleshi. "Ciki? Kai murna kake Madam dinka ta haihu yanzu? Kasan irin nauyin da zai ƙara hawa kanka kuwa? Wani fita eh yane, wani hawa gajimare duk raino zai sa ka daina. Kai Zaki! Yawane wallahi! Nawa kake ma yanzu? Gaskiya ku san abin yi game da cikin." Aliyu ya daure fuska kamar bai taɓa dariya ba. "Malam kar ka kara yimin zancen banza! Shege ne da za ka ce kar na bari ya fito duniya? Kai ka fi kowa sanin duk iskancina bai wuce zuƙe-zuƙe da ƴar romance ba, amma bana babbar harka balle a samu akasi. Toh don me za'a haifarmin ɗan sunnah ka nemi ka kashen gwuiwa. Ba dan iskan da zai sa na zubar da cikin Baby." Ya ƙarashe gami da watsawa G Baba harara. Shi kuwa G Baba ya kara yarda da irin son da Aliyu ke yiwa Ramlat. Ya tabbata shi ya shafi abinda ke cikinta. Aliyu kaifi daya ne idan ya ga dama, idan har ya yi irin tsaurinnan to ba mai juyamishi ra'ayi wannan ta sanya ya ja bakinsa ya wayance da yi mishi kirari hadi da fadin. "Ko ba komai ai ma zo mu ƙarawa sama ado." Suka cafke gami da wata irin dariya. ***   Ramlat zamanta ta yi a dakin bayan ta idar da sallar La'asar da ba ta yi kam lokaci ba. Tana jin yunwa, sai dai ba ta kaunar ganinsu. Kwantar da kai ta yi a saman hannunta jikin gado tana daga zaune saman darduma, tunani mai zurfi ta faɗa gami da riƙe cikinta. Har sannan tana kara jinjina lamarin, wai ciki ne da ita.  'Cikin mashayi.' Wani bangare na zuciyarta ya ayyana mata, ta jima anan zaune har wahalallen baccin da ba ta samu yinsa da safe ba ya soma fisgarta sai dai cikinta na ta ƙara saboda yunwa. A hankali ta ji hannu saman fatar cikinta. Firgigit ta bude idanu, Aliyu ne durkushe ya daga rigar yana shafa cikin. Suka hada ido, murmushi ya sakarmata. Ita kuwa warin sigari ke tayarmata da zuciya don haka ta mike da sauri ya riko hannunta gami da miƙewar shima. "Baby lafiya?" Ta rufe baki da hancinta da hannu ta shiga tureshi tana girgiza kai. "Don Allah ka fita, warin taba, zan yi amai wal..." Yunkurin aman ya katseta, da sauri ta faɗa banɗaki shi kuwa ya fita daga dakin. Ba wani abin kirki ta amayar ba, ta wanke baki ta fito, ganin baya dakin yasa ta daukar turare mai sanyin kamshi a bakin madubi ta ɗan fesa a jikin wani dan handkerchief ta toshe hancin sannan ta bude winduna  dakin. Kiraye kirayen sallar Magriba ne ya sa ta mike ta zura hijabinta. Sai da ta yi sallah sannan ta mike ta nufi falon don Aliyun ya shigo har sau biyu kafin ta idar. Maimakon ƙamshin sigari, sai ta ji ƙamshin turaren wuta. Ba kowa a falon hakan ya bata tabbacin Aliyun ne ya kunna. Ta saba duk sadda ya gama busa hayaƙinsa za ta yi azamar daukar kaskonta ta kunna gawayi ta saka turare. Sai ta ji hakan da ya yi ya burgeta, kaso hamsin na damuwarta ya yaye. Sai a sannan ta ci dora abinci mai saukin dahuwa ta ci, ta shiga karatu. *** Washegari da ɗokinta ta fita daga gidan. Aliyu ne ya kai ta saman mashin dinsa.    Koda ta shiga Malami ya shigo basu sami damar gaisawa da Amrah ba sai dai wannan karon sun samu zama wuri guda. Ana tashi, kowa ya fice daga ajin suka yi zamansu. "Mai ciki ba za ki ci komai ba? Rana fa ta yi." Fadin Amrah cikin murmushi. Harararta ta yi sannan ta ja guntun tsaki.   "Ni har tsoron haihuwar ma nake." "A gidan Aliyun ko kuwa me?" Tasan Amrah da biyu ta yi tambayar, ba kuma ta so ta bada kofa yanzu Amrah ta san sirrin gidanta. Ta fi kaunar Amrah ta dawo da tausayi da kaunarta a zuciya kamar dai a baya. "A'a, kada na mutu wurin haihuwa." Dariya Amrah ta yi. "Sai kuma aka fadamaki haihuwar ƙarar kwana ce? Addu'a za ki yi, In sha Allah za ki haihu lafiya. Af, ga saƙon Umma ma. Ta cemin ki dinga shan kayan marmari da abinci lafiyayye. Kar kuma ki yawaita daukar abu mai nauyi. Kuma wai ko nan gaba za ta aikomaki mene? Oho na manta. Ta ce dai na miki albishir tana nan zuwa." Dadi, farin ciki da annashuwa suka cika zuciya da fuskar Ramlat. Daga washe haƙora tana dariya sai ga hawaye na fita. Hawayen tana da wata uwa da ba ita ta haifeta ba, amman ta tuna da ita. Tana kokarin ba ta kulawa irin ta uwa. "Meye abin kukan?" Fadin Amrah da ke jin zuciyarta itama na neman karyewa. Ta daure ta tattaro dauriyar wuri guda, ta shiga zolayarta. "Oh, wa ya ga Ramsy da ɗa? Naga yanda za ki yi raino. Wai har ki shayar." Ta ƙarashe gami da sanya dariya, itama ba ta san sadda ta dara ba ta hau share fuskarta.   "Kema ai kamar yau ne." Taɓe baki Ramlat ta yi. "Ni da aure sai na kammala karatu in Sha Allah." Murmushi Ramlat ta yi kafin su taɓa hira, so take Amrah ta jefomata tambayar da ta shafi gidanta ko dangin mijinta, sai dai ta lura kokarin kaucewa hakan ma Amrah ke yi. Don haka itama sai ta kara rufe cikinta ba ta kaunar su sami wata matsalar. ***    Bayan sati biyu hankalin Ramlat a kwance, za ta yi waya da Abbanta da kuma Hajiya wacce a sannan ta ɗan sassauta kadan. Umman Amrah kuwa kiranta take sosai su yi hira ta yi ta kwantar mata da hankali. Ta dauketa kamar ƴar da ta haifa a cikinta. Bangaren Aliyu, ya rage zuwa ya yi mata shaye-shaye a gida kamar yanda ya daina shigomata a buge. Hakan ya kara kwantar da hankalinta ba kaɗan ba. Abinda ke yawan bata mamaki ya daure mata kai, banda Abulle babu wani ko wata a dangin Aliyu dake zuwa gidanta, zargin ba sa kaunarta ya kara tabbata a kansu. Don haka ta ja jikinta ta kama kanta. Hakan bai hana ta kira mahaifin Aliyun ta gaidashi, shi kam lafiya sumul yake amsamata.      A yammacin juma'a ta fito falon bayan ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando Pakistan. Tashinta daga bacci kenan bayan ta dawo daga makaranta. Kicin ta shiga ta hau kiciniyar yin tuwon semo da miyar kuka kasancewar hakanan ta ji tana sha'awarsa. Sai dai me? Babu gas. "Ya Salam." Ta furta a fili. Jiki a sanyaye ta fito falon tana jan tsaki, waya ta dauka ta lalubo lambar Aliyu ta kira.   "Kamar ya babu gas? Har gas din gidan ya ƙare?" Shi ne tambayar da ya jefomata bayan ya saurari bayaninta. Ta ciji leɓɓanta ta kasa cewa komai. Sai kuma ta ji ya ja tsaki kafin ya ce. "Nidai wallahi banda kudi, kema kin sani kuma. Yanzu haka ganinan wani banza dan gin..." Kiit, ta katse kiran, a duniya ta tsani ta ji yana ashariya. Abin na ƙona ranta. "Allah Ka shirya." Ta firta a fili, ita kam yunwa ta ke ji don haka ta mike. Ta tuna da lemun da ta gani Aliyu ya ajiye a fridge da safiyarnan, sadda aka kawo wuta. Ta soma shiga kicin ta dauko ragowar bireda ta fiddo lemun. Tun kafin ta ƙaraso ta bude ta shiga kwankwada. Sosai ya yi mata dadi. Tana zama ta hau tauna biredin, idanunta na kan wayarta dake ƙara kuma sanin Aliyun ne ta ƙi ɗagawa. A hankali kuma ganinta ya soma zama dishi-dishi. A kokarinta na  ajiye robar lemun saman Centretable sai ya zube a ƙasa. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Mene haka?" Ta fadi cike da karfin hali. Ita ta san me take ji. Jirin na kwasarta, yana kokarin fitar da ita daga hayyacinta. A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ta danna. Cikin muryar ƴan maye ta soma magana. "Aaaaaliiii." Ba ta ji me yake cewa ba ta wurgar da wayar, ta mike ta na tafe tana rangaji da zagaye falon, ba ta yi aune ba ta ci uban tuntuɓe da takalminta ta bugi gefen mararta da tv stand ta zube anan. Duk da ba'a hayyacinta take ba sai da ta saki ƙara. *** A hargitse ya banko kofar falon ya shigo. Kallo ɗaya ya yiwa robar lemun ya san abinda ke faruwa. Jijjigata ya soma. "Baby! Baby! Ramlat!" Ya rasa na kira, cak ya ɗagata ya fita. Ba kuma zai yiwu ya sanyata a mashin ba, dole ya dawo da ita ya fita ya taro ɗan sahu suka bar gidan zuwa asibiti. *** "Ka yi hakuri, cikinta ya riga da ya zube." Bayanin Dr Lamin kenan bayan ya gama faɗawa Aliyu cewa a jininta da aka auna an samu tabbacin ta sha kwaya mai ƙarfi, ya kuma yi faɗan meyasa ya bar ta yin shaye-shaye duk kuwa da sanin da ya yi tana da ciki. Ga mamakin shi kansa Aliyu ya kasa cewa komai, har Likitan ya yi faɗa ya kammala. Batun zubewar cikin ya fi komai ɗagamishi hankali. Idanunsa suka kaɗa. 'Ko mene laifinka ne ai! Da ba ka ajiye a gidan ba, ta ina za ta gani ta dauka tunda ba halinta ba ne!' Faɗin wani sashi na zuciyarsa. *** Awanni kaɗan bayan farfaɗowarta ya shiga. Ta ɗago idanu ta dubeshi sai ta soma hawaye.   "Kaga abinda halinka ya jazamana ko?" Ya zaune gami da riko hannunta. "Laifinki ne, meyasa ba ki ɗaga wayata ba ina ta kira? Tunawa nayi na ajiye a fridge shiyasa na so na gargaɗeki." Ta kauda kanta kawai, cike da bakin ciki. Abin kunya sanadin shaye-shayen mijinta, cikinta ya zube.     "Kaicona." Ta furta a fili, sai kuka. Kewa, kewar iyayenta take. Don haka ta juyo ya dubeshi. "Bani wayarka." "Ki yi me?" "Abbana zan kira." Ya daure fuska. "Ki ce mishi kin sha abin maye cikinki ya zube? Asirinmu za ki tona? Dama ya lafiyar giwa ballantana an jefeshi da kashi? Toh ki je ki gwada tona asirin namu. Naki ne zai fi wari, ni dama ba ganina suke da gashi ba." Daga haka ya mike ya sa kai ya fice a zuciye. Ta bishi da kallo, wani malolon abu ta ji ya tsayamata a maƙogwaro. Tana jin haushin irin kalaman da Aliyu ke yi akan iyayenta. Ko ba komai iyayenta kuma su suka haifeta. Dole ta takawa abin burki. 'Kin manta ke kika bada ƙofa.' Cewar wani bangare na zuciyarta, hakan sai ya karyarmata da gwuiwa. Ta yi shiru ta soma hawaye. Tana jin haushi da tsanar kanta akan duk abinda ya faru tsakaninta da yan uwanta, a gefe guda kuma don Aliyu ya zama kamar bugun numfashinta wanda ba ta jin za ta iya rayuwa babu shi. Sai dai kuma hakan ba zai hana ta janyo ƴan uwanta jiki ba, ta dinga ziyartarsu koda ba su zo mata ba. Ta kudurta sauya takunta tun kan abu ya yi nisa. ***   Sai da ta yi kwanaki uku aka sallameta daga asibiti. Shi ne lokaci na farko da ta ga matan mahaifin Aliyu a gidanta da sunan dubiya. Ba su kadai ba, har su Abulle da Mamar Muhibbat sun zo. Kana ganin fuskokin za ka san dole akai musu. "Ikon Allah, kema dai ina ce ba shi ya jawomaki ɓarewar cikin ba?" Cewar matar Malam (mahaifin Aliyu) ta farko, Atine. "Wane zancen banza ne haka ke Atine? Wa kike nufi da ɓarar da ciki? Au dama sharrin da za ku yiwa Zakina kenan?" Fadin Abulle cikin masifa. Wannan yasa Atine fadin "Allah Ya ba ki hakuri Baba." Abulle ta yi kwafa. Ramlat dai tana zaune ta dukar da kai a saman kujera don Abulle ta hanata zama ƙasa.    Sun jima a gidan don har sai da Abulle ta saka yanmatan jikokinta su yiwa Ramlat girki a risho. Haka suka shiga suna kunkuni. Har gobe ba sa kallonta da gashi, Muhibbat ce tasu. A karshe kowa ya watse aka bar ta ita daya ta yi ta godiya kuwa. Komawa ciki ta yi ta ga yanda suka yi kaca-kaca da kicin din, ta kuma sani da biyu suka yi hakan. Haka ta daure ta kimtsa ko'ina. Tana jin sadda Abulle ke cewa Zalihat diyar Atine ta zauna ta kwana biyu yarinyar ta yi kememe uwarta na turata ta fice ta shige mota. Murmushi ta yi mai ciwo. Ta dauki waya cike da so da kewar iyayenta ta dannawa Hajiya kira. Ringing uku ta ɗaga da sallama. "Hajiya." Ta fadi a raunane zuciyarta a karye. Daga dayan bangaren Hajiya ta ji gabanta ya fadi, ta daure. Kwanakinnan da tunanin Ramlat take kwana da tashi. Tun sadda aka ce ta yi ɓari ta kira Zulaihat da Rafee'ah akan su shirya su je. Yanzu kam sun amince zasu je bisa umarninta. "Ramlatu, ya gida? Ya jikinnaki?" Wani sanyin dadi ya saukarmata a zuciya. Yau ne karon farko da Hajiyar ta kira sunanta ta kuma bata kulawar da ta dace. "Jikina da sauki Hajiya. Hajiya yaushe za ki zo? Ki yafemin don Allah Hajiyata." Kukan da take riƙewa ta shiga yi. "Hajiya kin yi shiru. Hajiya ki yafemin." "Na yafemaki Ramlatu, na yafemaki duniya da lahira. Ki kwantar da hankalinki. Ki bi mijinki, Allah Ya yi maki albarka. Gobe yayyanki zasu zo." Rasa kalar farin cikin da za ta yi ma ta yi. Sai ga ta nan tana dariya. Suka yi sallama da Hajiyar ranta fari sol. Ta ɗago kai kenan ta hada ido da Aliyu. Yana jingina kansa cikin bangon falon yana zuƙar taba da fesarwa. Ganin ta kammala wayar ya tako ya zauna gefenta. "Su waye zasu zo?" Ta mance da batun wani sigari ko warinsa, rungumeshi ta yi sosai cike da farin ciki ta amsa. "Tayani murna, Hajiya ta yafemin, ga Anti Zulaihat da Anti Rafee'ah zasu kawomin ziyara gobe." Ga mamakinta sai ta ji ya ja tsaki. Ta ɗago tana kallonsa. "Da yake ba ki da zuciya ko? Duk irin rashin kaunar da suka nunamana akan wani banzan Hilal bai ishemu ba? Wane irin kalamai ne ita Zulai din ba ta ce a kaina ba? Ita kuwa Rafee'ah wato tsabar tsana har.." "Ya isheka! Ya isheka!!" Ta tsinci muryarta da fada, bakinta da kakkarwa, jikinta da rawa. Ta miƙe tsaye kyam da ƙafafunta. Idanunta a rufe cike da masifa!  Kallonta kawai yake yana zuƙa da fesarwa, maimakon ɓacin rai, murmushi yake, murmushi sosai har da dora ƙafa daga saman Centre Table. "Ƙarya nayi?" Shi ne abinda ya furta.  I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/xcmnTANK99 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 18) "Nace ƙarya na yi?" Ya kara maimaita tambayarsa ganin ga tsaya cak tana kallonsa. Sai sannan ta kauda idanunta daga kansa. "Ya isheka! Aliyu ya isheka! Ban raina iyayenka ba, ban taɓa faɗar kalma marar dadi a kansu ba, kar ka fara da nawa. Kar ka koyamin. Ba zan dauka ba. Ko ba komai sun haifamaka ni." Wata dariya ya yi kafin ya kashe sigarin a karamin farantin tasar Ramlat din da ya mayar na kashe taba. Miƙewa ya rungumeta tana kaucewa. "Sorry Baby, Allah Ya ba ki hakuri. Ba zan ƙara ba." Ta zame jikinta kawai ta nufi daki. Dakyar ta sauko ta bar fushin ganin yanda ya ke lallaɓata kuma ta san kwanan zancen sai dai dole ya hakura don ba dama. *** WASHEGARI Tun zamansu a falon suke kallon ko'ina gami da taɓe baki.  Can kuma Zulaihat ta dubeta. "Matar Aliyu, ya jikin?" Ba ta son suna kiranta da wannan sunan, ta fi kaunar Ramlat din da aka yankamata rago da shi, sai dai furta hakan tasan wata baƙar maganar za ta ƙara tofamata, don haka ta haɗiye ɓacin ran ta yi yaƙe tana ɓarewa Khalifa ledar alewa. "Jiki da sauki. Na warware. Yau dai Allah Ya yi kun zo min." "Yanzun ma don kin haɗamu da uwarmu ne, gudun ɓacin ranta ne ya kawomu gidanki. Kinsan ba duka aka taru aka zama ɗaya ba." Fadin Rafee'ah kenan wacce dama tun ɗazun take ba Daddy nono tana wani jijjiga ƙafa. Murmushi Ramlat ta yi. "Kowa dai da irin kaddararsa." Tsaki Rafee'ah ta ja, ita kuwa Zulaihat ta yi dariyar rainin wayon Ramlat. "Allah Ya kyauta, Ramlat baki abin magana." Ta yi murmushin da bai kai ko'ina ba. Duk a zatonta zuwan yini suka yi mata, ashe ba haka ba. Duka-duka basu fi mintuna talatin ba suka miƙe. Baki sake ta ke dubansu. "Wai ba dai tafiya ba?" "Ah, me zamu zauna mu yi? Ko an fadamaki namu mazan ba sa sonmu suka bari muka zo?" Zulaihat ke fadi sa'ilin da take gyara zaman mayafinta. Idanunta suka cicciko da kwalla. "Don Allah ku tsaya ku ci abinci, wallahi na yi girki kuma idan ba ku ci ba zai iya lalacewa." Tausayinta ya ɗan tsirga Zulaihat, ko ba komai kanwa ce garesu, ta lura babu wani ƙiba na amarci da Ramlat ta yi face rama. Hasken fatar ma ta tabbatar ma cuta ne. "Ke kika san wannan, nikam muje Sis. Baban Khalid bai ce na jima ba, kuma kinsan zai dawo daga Gusau." Zulaihat ta koma ta zauna. "Mintinan kadan zamu ƙara Rafee'ah, yi hakuri mu ci abincin. Yunwa nake ji dama." Ta fadi ne kawai don Ramlat din ta ɗan ji sanyi ganin har ta soma hawaye. Guntun tsaki Rafee'ah ta ja don ita ba ta son ma tuna cewar a gidan Aliyu da Ramlat take. Ganin haka da sauri Ramlat ta faɗa kicin ta shiryo musu lafiyayyan jellof din shinkafa da taliya da ta girka musamman domin su, ya ji alayyahu da kifi. Cima ce da ta san suna masifar so musamman idan Hajiyarsu ce ta girka da busasshen kifi. Tun kafin ta ƙaraso ƙamshin ya bugesu. Rafee'ah na zaune tana buga game  wayarta, Zulaihat kuwa ta kwashi gara suna hira. Ana cikin haka, sai ga Amrah ta kira. Daga makaranta takanas ta taho dubiya. Cike da farin ciki ta yi kwatance, ta leka ta tarbota a gate. Ita kanta ta yi mamakin ganin su Rafee'ah a gidan. Wannan shine taimakon da Ramlat ta samu, abincin ya ƙare tas sai wanda zasu ci ita da Aliyunta. Zuwan Amrah ya daukemusu hankali aka shiga hira sosai, sai dai Rafee'ah na kaucewa hirar da za ta haɗata da Ramlat din. *** Shaf ya mance da batun wasu baƙi, abu ne da ba'a saba ba. Ya saba ya wuni kasuwa ya dawo ya riski matarsa ita daya. Kusan ma a fusace yake, mashin dinsa a waje ya bar shi, wayar da abokin kasuwancinsa Nabil ya mishi ita ta ƙara fusatashi. Shikenan ba dama ka ranci kuɗaɗen mutane sai su takura maka a waya. Ya ci alwashin cika abinda ya yi niyya yau, ya tabbatar hakan zai ba shi ribar da zai maida bashin ya kuma kashe wata matsalar. "Dalla malam nace maka gobe zan ba ka kudinka! Dan ....uwarka ka rabu da ni!" Jin abinda ya ce, Nabil ya fusata shima ya shiga surfa mishi ashar. Shima bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya hau ramuwa har ga shigo cikin falon. Idanunsa sun rufe bai ko lura da mutanen da ke zaune ba. Gaba daya idanunsu yana kansa, Ramlat kirjinta ne ya shiga bugu da sauri.  Wani irin ashar yake ƙundumawa kamar tsohon ɗan tasha. Zulaihat ta dubi Rafee'ah kafin ta maida dubanta ga Ramlat wacce ke jin kamar ƙasa ta buɗe ta nutse a wurin. Ta saci kallonsa, ya gama wayar ya zaro lighter daga aljihunsa, sanin me hakan ke nufi ya sa Ramlat saurin miƙewa gami da ƙarasawa inda yake. "Sannu da zuwa. Muna da baƙi fa." Ta furta murya na ƴar rawa. Sai a lokacin ya san da ita a falon, ba ma ita din ba, ya ankara da mutanen da ke zaune. Mutanen da ya kira da maƙiyansa. Kallon da ya watsamusu kallo ne na raini, kafin ya maida duba ga Ramlat cikin halin ko'in kula. "Sai me? Inace ke suka zo dubawa? Me zan musu? Ai wanda ke yi da ni, da shi nake yi. Mtsw." Ya ƙarashe da tsaki ya yi ciki, ta daskare a tsaye, ta kasa koda juyowa ta dubesu. Rafee'ah a fusace ta mike tsaye ta ja zanin goyon Daddy ta saɓeshi. "Sai ku tashi mu bar gidan. Gobe idan an ƙara ganin ƙafarmu a yi mana fin haka. Dama wane mutunci ko karramawa za'a samu wurin wannan mutumin?" Rafee'ah ke maganar a fusace, ba ta jira komai ba ta fisgi gyalenta daga saman kujera ta ɗauki jakarta ta yi gaba. Ita kuwa Zulaihat jiki a sanyaye ta mike tana ƙara maimaita Allah Ya kyauta kamar wani karatu. Ita abin dauremata kai ya yi da kuma mamaki. Bangaren Amrah kuwa, itama miƙewa ta yi ta hau gyara zaman ɗankwalinta da ya sunce. Sannan suka kama hanya. Ramlat ta juyo tana dubansu, sai a sannan ta yi yunkurin magana ta karasa da sauri ta tsayar da su. "Don Allah ku yi hakuri. Wallahi ransa ne a ɓace. Ba haka yake ba, ku yi hakuri don Allah." Wani murmushi Zulaihat ta yi. "Ai ba ke kika yi mana ba, mijinki ne. Kuma ko ba komai gidansa muka zo, kinga ko shari'a ta kayar da mu. Koma ciki kawai, ma yi waya." Tana kuka kuma tana ji tana gani suka kama hanya. Ta riko hannun Amrah. "Sakarni don Allah Ramlat, ma haɗu a makaranta. Ko me ya faru ke kika ja. Ke ce silar komai. Ke kika bada ƙofa aka daina ganin naki da mutunci." "Abu ba zai wuce ba Amrah?" Maimakon ta samu amsarta, sai Amrah ta kwace mayafinta ta ja hannun Khalifa suka bi bayan su. Rafee'ah tuni ta yi waje, tana tsaye tana jijjiga Daddy dake kuka, ita kanta hawayen take fitarwa, hawayen takaicin Ramlat. Tana ganin Zulaihat ta dubeta. "Me aka gujemata tun farko? Dama ai wanda bai ji bari ba zai ji hoho. Me dama za ta samu a wurin mashayi idan ba irin hakan ba?" Zulaihat ta mata ido ganin Amrah ta taho, sun dauki sirrin shan sigai da kayan mayen Aliyu matsayin sirri da ba kowa ne ya sani ba. Suna jin kunyar Amrah ta ji sai dai kuma basu da masaniya itama tana da labarin waye shi. Haka suka dunguma gwuiwa a sake su ka bar unguwar Rafee'ah ma faman mita. Zulaihat itama tana kiran sai ta faɗa wa Hajiya. "A'a Anti don Allah kar ku yi haka. Ko don Abba, kar fa ku manta har yau Abba na kan shan maganin hawan jini. Don Allah kar ku jefasu cikin damuwa. Ramlat ai ba ta je ta faɗa ba, kuma da alama mu din ne bai son gani a gidansa saboda ta riga ta nunamasa bama ganinsa da ƙima da mutunci. Shirun zai fi zama alheri ga su Hajiya." Amrah ke maganar a tausashe. Sun fahimci manufarta, don haka suka yi na'am da hakan. Sai dai kowa zuciyarsa ba dadi. ***   Kai tsaye ɗakin ta shiga da hawaye caɓe-caɓe saman fuskarta. Abinda idanunta ya gane mata ne ya sanya ta sakin baki ta haɗiye kalamanta. Sif din kayanta ya bude ya fiddo karamin akwatin sarƙoƙinta yana bincikawa. Wani dan gida wanda ta sanya auduga ta saka gwal dinta na wurin Abba a ciki shi ya fiddo. Sai wani set na gwal din da ya siyamata. Da sauri ta karasa ta fisgesu. "Mene haka? Me kake nufi?" Kallonta ya yi  fusace. "Me nake nufi kike tambaya? Siyarwa zan yi! Kudi nake so! Bashi ya min yawa, shagona kaya sun tasar ma ƙarewa, ko so kike ku rasa komai ne?" Zuciyarta na wani irin tuƙuƙi ta shiga girgiza kai. "Wallahi ba za ka siyarmin da zinaren da Abbana ya siyamin ba. Ko wanda ka siya  ai ya tashi daga naka, nawa ne. Don haka ba ka isa na ba ka ka siyar ba. Anya Aliyu kana cikin hayyacinka kuwa?" Hannu ya fidda ya ɗauke ta da mari Wanda ya yi sanadin zubewar gidan sarƙar, suka tarwatse a ƙasa. "Bayan laifin da kika yimin na kawomin tumakai cikin gida, hakan bai isheki ba sai kin kirani da mahaukaci?! Sarƙa kuma naga shegen da zai hana na siyar, idan kuma ubanki ne ya bani kudin na siyamaki sai ki faɗa!" Tana kuka ta shiga tattarawa ta dunkule a hannunta, ya shiga kokarin kwacewa. "Ba za ki saki ba? Wallahi zan miki dukan kawo wuƙa yanzu!" Ya ƙarashe gami da kai mata naushi a ciki. Ƙara ta saki, kafin ta ce. "Shikenan! Zan ba ka naka ka siyar amma wallahi banda na wajen Abba." Bai ko saurareta ba sai da ya kwace duka, zai fita ta rike ƙafarsa, wani harbin ya kai mata da ya samu bakinta, nan da nan ya kumbura ya soma fitar da jini. "Kar ka yimin haka! Ai Abbana ya siyamin shima! Ka bani na wajen Abba!" Ta miƙe a guje ta bi bayansa har harabar gidan, zai fice ta rike rigar gam tana kuka. Ya tureta, ganin ta ƙi sakinsa ya sanya a aljihun gaban rigarsa ya hau kai mata duka yana ashariya. Kira yake ita ce silar karyewar arziƙinsa. "Banza mai farar ƙafa! Ba abinda ubanki ya ban da na aureki ai. Shi waye da ba za'a ci arziƙinsa ba!" Wani karfi ne ya zo mata, ta kama hannunsa ta ciza iyakar ƙarfinta. Jin zafin ya ratsashi ya finciketa ya kai mata mari ga ci gaba da narka tana ihu. Yana ji ana kwankwasa gidan ya ƙi budewa. Sai da ya mata lis sannan ya bude ya dubi makwafcinsa dake tsaye. "Aliyu lafiya? Hayaniyar me nake ji?" Wani banzan kallo ya watsamishi kafin ya fito gaba daya ya rufe kofar gam! "Malam ba matsalarka ba ce, wannan hurumina ne da iyalina." Daga haka ya hau mashin ya tayar ya fice. Ramlat jikinta ya yi mugun tsami, ta kudurta a yau ba za ta kwana gidan Aliyu ba. Haka ta daure ta mike tana ɗingishi ga fuska a kumbure ta nufi ciki. Dogon hijabinta ta zura sannan ta dauki wayarta da purse dinta wanda ta tabbatar akwai kudi a ciki ta fita. Sa mukullinta ta yi amfani ta bude gidan, kai tsaye gidansu ta nufa. Ɗan sahu na kallonta ta madubi tana kuka, ya tausayamata don daga gani an san duka ta ci. Har kofar gidan ya sauketa. Ta fito ta karasa, cak kuma ta tsaya tana kallon kofar gidan. Tunani take ta shiga ko kar ta shiga, yanzun ne ta tuna da komai, yanzun ta tuna da irin rabuwar da aka yi. To amma ya za ta yi? Su kadai ne tilas dinta, don haka ta shiga kwankwasawa. Malam Musa ya leƙo, ganinta sai ya hau mamaki. Ga fuska duk a kumbure. "Hajiya Ramlatu, kece a tafe? To .." Ya bata hanya da sauri, ba ta tsaya ko gaidashi ba ta tambaya ko Abba na gida. Ya tabbatarmata yana ciki. "Kwana biyun nan bai fiye fita ba saboda yanayin jikinsa da ya motsa." Ta dubi Malam Musa da hawaye saman fuskarta. "Meke samunsa?" Cike da tausayi ya amsa. "Kamar dai naji Babban Yaya na cewa hawan jininsa ne ya motsa. Amma da sauki ai." Ta yi shiru, ba za ta iya tunkarar Abbanta da abinda zai kara dagula lissafinsa ba, ta dubi gidan nasu. Wasu hawaye masu ɗumi suka zubomata. Shikenan ba ta da cikakken ƴancin zuwa gidansu kamar sauran ƴan uwanta? Ba za ta zo ana murna da ɗokin ganinta ba? A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ta juya ta fita. "Ya za ki tafi? Ya kamata ki shiga ciki Ramlatu, dubi yanayin da kike." Tasan yanayin bai wuce na dukan da ta ci ba, har wani dan jiri take ji. Ko a islamiyya ba'a taɓa yi mata irinsa ba. Ta yi murmushin yaƙe ta girgiza kai. Dakyar ma take iya ganin fuskar Malam Musa saboda ruwan hawayen da suka taru a kwarmin idanunta, jan majina ta yi. "A'a ba zan iya shiga na tayar da hankalin Abbana ba. Zan dawo wataran." Daga haka ta yi gaba, ba ta kara waiwayowa ba. Kallon gidan ma karyar da zuciyarta zai yi. Tana tafe tana ɗingishi ga hawaye. Duk wanda ya ganta sai ya kalleta, hakan ya sa ta rufe fuskar kasan da hijabi. Haka ta ƙarasa ta wuce gidan Umman Amrah.    *** "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Oh ni jikar Mamman, yanzu shi Aliyun ne ya miki wannan dukan kamar an aikoshi?" Fadin hakan da Umma ta yi sai ya kara karyar da zuciyar Ramlat. Ba ta ce komai ba banda kuka. Jiki na rawa Umma ta ɗauki waya ta dannawa Dr Abdullahi kira. Nan ta sanar da shi komai, ya bada umarnin ta taho da ita asibitinsa. Ba shiri Umman ta taimakawa Ramlat suka wuce asibiti. Har sannan Amrah ba ta dawo ba, a bakin Umman ta ke jin, za ta biya gidan kakanninta. Dr Abdullahi bayan ya sanya an wankewa Ramlat ciwukan da ta ji, ya kirasu ciki ofishinsa. "Me ya yi zafin da zai miki wannan dukan? Ba shi da hankali ne?! Da wani asibitin ne ba za'a karɓeki ba sai da sa hannun ƴan sanda. Wane irin hauka ne wannan? Ko yana shaye-shaye ne?" Dr Abdullahi ke fadi cikin tsananin ɓacin rai kai ka ce Amrah aka taɓa. Koda dai dama ba ya bambantasu. "Dama..dama..ya kwashemin gwala-gwalai ya tafi siyarwa. Shi ne na yi kokarin hanawa, ya hau dukana." Salati Umma da Dakta suka sanya. Miƙewa tsaye Dakta ya yi yana huci. "Wannan dole a dauki mataki don ba jaka aka auramishi ba. Jahili ke dukan matarsa, don an auramaki zaɓinki ba yana nufin za'a kyaleki muna ji muna gani a zalunceki ba. Kin fadawa shi Khalid din?" Ta girgiza kai a tsorace. "A'a don Allah kar ka fadamishi Baba Dakta saboda hawan jininsa." Ta basu tausayi, ya ce Umma ta maidata gida sai ya nemi Aliyun sun yi magana. Hakan ya yiwa Ramlat dadi, Baba Dakta ya karɓi lambar Aliyu. Daga nan suka wuce gidan suka bar shi a ofis. *** Amrah ta sha mamakin ganinta a gidansu, sai dai ta tsorata da yanayinta. Ba ta son yin kuka a gabanta don haka sai ta shige banɗaki da zummar yin wanka ta ɓige da kuka. Kukan tausayin aminiyarta. Ta fito ta sameta kwance tana kallon wayarta kamar mai jiran wani abu. "Allah Yasa ba kiran Aliyu kike jira ba." Ta ajiye wayar ta dubeta gami da gyara kwanciyarta. Murmushi kawai ta yi ba tare da ta tanka ba. "Dakta ya ce ya kira Aliyun ya ce ya zo yana son ganinsa ya kuma fadamasa kina gidanshi, ya ce toh amma kinga har tara bai zo ba. Ina da tabbacin ba zai zo ba yaron nan." Umma ke maganar cikin takaici tana duban Ramlatun. Ta kasa cewa uffan banda taunar abinci da take yi kamar mai cin magani. Amrah ce ta taya Umma takaicin har ta bata labarin abinda ya yi musu a gidan, ita dai ba ta sa baki ba. Karshe Umma ta musu sai da safe ta fita. Ramlat ta ɓallo magani ta kora da ruwa. Cikin son daukemata hankali daga tunani, Amrah ta yi ta jan ta da hirar abinda aka yi a makaranta yau, har ta fiddo handouts tana yi mata bayanin da za ta gamsu. *** "Ranka ya dade." Cewar Malam Musa bayan ya rufe ƙyauren gidan. Abba wanda shigowarsa kenan daga masallaci ya dakata gami da dubansa fuska a sake. "Ya aka yi Malam Musa." Malam Musa ya ƙaraso ya ɗan russuna kadan. "A gafarceni Alhaji, farko na so na yi shiru saboda yanayin jikinka, toh kuma kaga bansan halin da shirun nawa zai jawo ba." Abba ya gyara tsayuwarsa. "Faɗi kawai Malam Musa. Meyafaru?" Malam Musa ya sauke ajiyar zuciya. "Ɗazun da rana ne Ramlatu ta zo fuskarta duk a kumbure, bakinta da goshi na fitar da jini. Yanayin dai babu kyau don naga har ɗingisawa take yi kuma..." "Ramlatu? Ta zo gidannan? Hatsari ta yi ko me? Meyasa ba ta shigo ba?" Yanda Abban ya rude sai da ya tsorata Malam Musa, ya yi danasanin furtawa. Wannan yasa cikin rawar murya ya karasa. "Ta tambayeni kana gida na ce eh sai dai ba ka jin dadi. Hakan yasa ta fasa shiga ciki." Abba ya dage goshi yana salati. "Haba Malam Musa, meyasa tun ɗazun ba ka sanar da ni ba?" Bai saurari kalamansa ba ya koma cikin gidan da sauri. Ganinsa a hargitse yana kwalawa Hajiya kira, ya kaɗa hanjin cikinta, miƙewa tsaye ta yi ta tarbe shi. "Abban yara lafiya?" "Mukullin mota za ki ban, dauko da sauri. Ramlatu ba lafiya. Ta zo gidannan dazu." Yanda ya rikice itama sai ya ruɗa ta. Ta kama shi ta zaunar "Don Allah ka samu nutsuwa Abban Yara, In Sha Allah ba abinda zai samu Ramlatu, ka nutsu bari na kawomaka mukullin." Ya zauna yana ajiyar zuciya akai-akai kamar wanda ya yi gudu. "Daukomin, yi sauri. Yaron nan kashemin ita zai yi." Cikin sauri ta shiga ciki bayan ta ba A'isha umarnin kawomishi ruwa. Maimakon ta dauki mukullin, sai ta dau wayarsa ta shiga kokarin kiran Munir. Sai dai kiran Dakta da ya shigo ya katse mata yunkuri. Gani ta yi hakan ma faduwa ce ta zo daidai da zama, ta daga gami da sallama. Bayan sun gaisa ya ce ta ba shi Abba. "Don Allah Dakta ka lallaɓashi, ya rikice an ce mishi Ramlatu ta zo dazu, so yake ya yi tuƙi..." "A'a ki ce mishi tana gidana. Bani shi mu yi magana." Jin haka sai ta mutu da mamaki. "Kina ina ne Rabi? Ba ki gani bane wai?" Ganin Abban ya shigo har sannan a rikice, ta sanyamishi wayar a kunne hadi da fadin. "Dakta ne, ku yi magana." Nan Dakta ka sanarmishi Ramlat na gidansa, ya fadamishi ya kwantar da hankalinsa ba wani abun tashin hankali bane. "Dare ya yi, ka zauna don Allah. Gobe da kaina zan kawomaka ita a yi magana." Abba ya shiga jinjina kai kamar yana ganinsa. "Shikenan Dakta. Amma fadamin, sakinta ya yi?" Abban ya ƙarashe zuciyarsa a karye, koda ace bai son Aliyu, a rayuwa ba ya fatan ɗiyarsa ta yi aure ta fito har a dinga ƙirgamata aure. Tausayinsa ya ratsa Dakta. "Bai saketa ba Alhaji, kar ka damu don Allah, in Sha Allah gobe da safe zamu shigo." Abba ya yi ta godiya har sai da Dakta ya katse wayar don bai ga bambanci tsakanin Amrah da Ramlat ba. Ya ɗago ya dubi Hajiya sannan ya zauna saman kujera. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!Nasan dukanta ya yi, nasan za'a rina. Ramlatu kaddararki kenan, Allah Ya shiryeshi. Ya kawomaki lamarin da sauki." Hajiya ta amsa da Amin. ***I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/SsZqCOwIcab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 19) Dakin ya yi shiru, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan Ramlat. Abba jikinsa ya yi sanyi jin abinda Aliyun ya aikata ga ɗiyarsa. Ga duka ga kuma kwatar dukiyar da ta ke mallakinta a yanzu.   "Wannan yaron anya zai zo?" Fadin Dakta wanda ransa ya soma ɓaci da shirgasu da Aliyu ya yi. Abba shima nashi ran a ɓace yake. "Ka rabu da shi Dakta, idan ma bai zo ba, za ta koma. Kawai dama so nake ya zo din don na gargadeshi akan duka, ba jaka ba ce." Hajiya dai banda uhm ba abinda ta ce. Ita kuwa uwar gayyar yanzun ma kukan ya kasa fita, ta yi shiru kawai tana kallon kafet da kumburarrun idanunta. Har aka kwashe awa daya, Dakta ya mike ya yi musu sallama zuwa wurin aikinsa. Shima Abba ya mike ya shirya ya fita. "Duk abinda ke faruwa ke kika jazawa kanki Ramlatu! Gashinan tun ba'a je ko'ina ba kin fara girbar abinda kika shuka. Kin bude baki kin nunawa namiji ƴan uwanki ba sa sonsa, kin jawowa kanki da kuma iyayenki raini. Kin kafe akan ke lallai sai yaronnan, yanzu ai gashinan auren da ba'a shekara ba an soma jibgar Amarya. Ban kuma san me zan ce ba." Hajiya ke maganar a zafafe, sai kuma ta miƙa ta bar falon ranta na ƙuna. Ramlat ta yi shiru tana tauna maganar Hajiyar. Tabbas ko me ya faru ita ce silarsa. Wani duka, zagi, cin mutunci da akai mata kafin aure, ba wanda ba ta faɗa wa Aliyu ba. Asalima shawararsa ta ke bi ta aikata duk abinda ta aikata. 'Shi yana zagin nasa ƴan uwan a gabanki banda iyayen Muhibbat da suka ɓata ransa?' Faɗin wani bangare na zuciyarta, tabbas ta sani, ko batun ƴan uwansa za ta yi, zai ce ba ya so. Ta sharesu tunda shi za ta aura. Ba su damu da shi ba, amman shi kam bai yarda an wulakantasu ba. Sai ita ce wawuya ta saki baki har ya rainamata ƴan uwa? Sai a sannan ta ji hawayenta sun zubo. "Na yiwa kaina illa da kaina." Ta furta a fili, dakyar ta mike ta shige tsohon dakinsu wanda yake mallakin A'isha a yanzu. Kwanciya ta yi tana tunane-tunanenta kafin wahalallen baccin ya kwasheta. ***   "Tana gidansu!" Ya fadi cike da tsawa ganin Abulle na neman takura mishi da tambaya. Ita kuwa gani ta yi daren jiya da kuma safiyar ranar duk a gurinta ya ci abinci. "Idan ma abincin naki ne ba kya son na dinga zuwa ina ci ai shikenan, sai na zauna na mutu kowa ma ya huta. Komai Aliyu! Komai Aliyu! Ƴan uwannawa ma ba sona suke ba, da Ni mai arziki ne bibiyar da za'a dinga yimin ba kaɗan ba." Abulle dai ta kama bakinta ta yi shiru jiki a sanyaye. Ta gane yau ran Zakinnata a ɓace yake. Sai da don kansa ya ci gaba da shan shayin da biredi da kwai sannan ta soma magana a nutse cike da rarrashi. "Allah Ya huci zuciyar Gadanga ƙusar yaƙi. Haba Zakina, mene abin fushi don nayi tambaya? Abin bai kai nan ba ka ji, ba wanda ba ya sonka, halinka suke cewa sun tsana wannan ma nasan don ba su baka damar kun zauna tare ba ne. Ita kuwa Ramlatu me ya yi mata zafin da har ta tafi gidansu?" Ransa ya ɗan sosu, idan yace bai yi kewar matarsa ba toh wannan karya ne. Yana son Ramlat, irin son da bai yiwa wata mace ba. Haushin da ta ba shi akan me ba za ta taimaka mishi lokacin babu ba. Yana sane ya ƙi zuwa gurin iyayenta, tsoro yake kar ace ya saketa, shi kuma ko sama da ƙasa za ta haɗe  bai ga wani dan adam din da zai sa ya saki matarsa ba. "Hutu na ba ta, za ta dawo." Abinda ya cewa Abulle kenan, ganin za ta matsa ya mike ya mata sallama ya wuce. A kofar gidan suka yi kiciɓus da Malam mahaifinsa. "Kai zo nan." Ya karasa ya ɗan russuna yana cin magani. "Meke faruwa ne kai da iyalinka? Mahaifinta ya kirani akan yana son ganinka." Ya kara tamke fuska. "Ba abinda ya faru, anjima zan je." Malam ya yi shiru yana dubansa, yana son yaron, halinsa ya tsana. Girgiza kai ya yi. Da alama shima da nashi kuskuren, ko kusa ya watsar da lamarin Aliyun ba ya ta tashi sam. Ya fi bada kulawarsa ga ƙannensa. "Aliyu ka ji tsoron Allah a lamuranka. Wannan yarinya amana ce ta Allah a hannunka. Duk abinda ka yi mata ka sani Allah sai Ya tambayeka. Har sai yaushe za ka gyara halayyarnan taka ka zamo abin so da kauna ga kowa a dangi? Aliyu ba fa kai muka tsana ba, halayyarka ce ba ma so." "Toh Malam don ba kwa so ai hannunka dai ba zai ruɓe ka yar ba. Addu'a za ku ci gaba da yi mini." Takaicinsa ya kama Malam, haka yake. Ba dai a yi magana bai maida martani ba. "Shikenan addu'a ko? Za mu ci gaba da yi, za kuma mu ɗora akan wanda muke yi. Yanzu dai don Allah ina rokonka, don yanzu ka fi karfin na umarceka, ka je ka taho da matarka. Ka dawo da ita ɗakinta. Duka-duka yaushe aka yi auren? Shikenan za'a soma ƙirgamaka aure?" Ya shafi ƙeya, ko ba komai yau Malam din ya fadi kalamai masu nuni da sassauci da kuma kwantar da hankali a gareshi. Ba kamar yanda ya saba haduwa da ƴan uwansa su yi mishi caa ba. Sai ya tsinci zuciyarsa da yin sanyi kadan. "Zan je anjima idan na tashi daga kasuwa." Murmushi Malam ya yi. "Ko kaifa, Allah Ya shiryeka. Ya yi maka albarka." Ya amsa da amin, ya mike ya tafi. Ya manta rabon da maganar arziki ya shiga tsakaninsa da Malam din. *** Tana daki ta yi jugum tana tunanin yanda ta yi fashin makaranta. A gefe guda Aliyu ne a ran, tunaninsa da kuma so da kauna su ke addabar zuciyarta. Ta yi kewarsa ba kaɗan ba. Don Aliyu wata jarrabawa ce daga Allah wanda ba za ta iya tsallakewa ba. Mutan gidan ba laifi sun sakarmata musamman Abba. A ranar misalin biyar na yamma ta ji Abba na fadin Aliyu ya zo. Gabanta ya fadi. Ta koma cikin daki ta zauna bakin gado, can kuma sai ga A'isha ta shigo tana kallonta a fisge. "Ki zo inji Abba." Ta mike ta zura hijabinta ta fita. A falon saukar baƙi suka ta iskesu. Kallon juna suka yi da Aliyu, kowannensu da abinda yake saƙawa a zuciya. Ta kauda idanunta ganin Abba na hankalce da su.   Abba ya bata dama ta fadi duk abinda ya faru, Aliyu nan take ya amsa duka laifinsa. Ya kuma ba da hakuri da daukar alkawarin ba zai kara dukanta ba. Ya kuma ce muddin ya samu kasuwa ta koma daidai zai mayarmata da zinarenta. Abba ya tambayeta ko  ta yarda da hakan, nan take ga mamakinsa ta yi na'am. Ya jinjina lamarin, sai kuma ya yi dan murmushi. "Ai shikenan, Allah Ya kara kauda fitina, Ya kiyaye gaba. Ki je ki shiryo ku wuce." Ta mike ta koma ciki. Ba jimawa ta fito ta dubi Hajiya dake zaune a falo. "Hajiya Abba ya ce na bi shi." Murmushi Hajiya ta yi. A ranta dama tasan Ramlat fushinta na ƙalilan ne. "Toh, Allah Ya kiyaye gaba." Ta amsa. Har ta yi gaba Hajiya ta yi magana. "Ko kina son jar miya sai na bayar a yi miki, gobe a kawo kinga zai taimaka maki saboda karatunki." Ta rasa kalar farin cikin da za ta yi, ta hau washe hakora. "Ina so Hajiya. Nagode sosai." Hajiyar ta murmusa kawai. Ta bi ƴarta ta da kallo a raunane. 'Allah Ka zama gatanta. Ka shaida, na yafewa Ramlatu.' Ta furta a ƙasan ranta. Falon Abba ta shiga yana zaune shima. "Abba zan wuce." Ɗago kai ya yi ya dubeta. Shiru na ƴan mintuna kafin ya nisa. "Shikenan Ramlatu, Allah Ya tsare gaba. Don Allah ki dinga kiyaye harshenki, miji ya fi gaban wasa. Ya wuce dukkan wani matsayin da kika sani. Aljannarki na gareshi. Ki yi mishi biyayya, ki kuma kasance mai hakuri a rayuwarki. Ramlatu addu'a, karatun Alkur'ani, su ne babban makaman kowane bawa da kike gani. Ki rike su ba da wasa ba. Wannan rayuwar ta sauya, ku dinga nemawa kanku tsari daga sharrin masu sharri ta ko'ina. Musamman matan aure yanzu, wata Alkur'anin ma ba daukarsa take ba balle har ta karanta. Sai ki ga abin kunya mace na cewa ita rabonta da tilawa ma ta mance. Karatun sai na Sallah, wata ma sai a sallar ta kakare idan ta idar ta bude ta duba inda ya kufcemata shikenan ta mayar ta ajiye. Me ya yi zafi? Me muke nema a duniyar? Ramlatu kar ki wasa da Alkur'ani, kar kuma ki yi wasa da ibadarki. Idan na ce ibada har bin mijinki. Kinji?" Ta gyada kai gami da furta Toh. Da gaskiyar Abba, ita kam tunda ya bata Alkur'ani sai dai ta dauka ta goge ƙurar ta mayar ta ajiye amma ba za ta ce ta bude ta karanta ba. Addu'a ma tana yi amma ba ta dagewa yanda ya kamata. "Nagode Abba, zan kula In sha Allah. Abba ba zan gaji da neman gafararku ba..." "Sau nawa zan ce na yafemaki Ramlatu? Toh idan ba ki gaskata ba yau ki gaskata. Wallahi ni Khalid na yafemaki duniya da lahira. Allah Ya miki albarka, Ya baki ikon cinye wannan jarrabawar. Sai hakuri Ramlatu, ko yaya bawa ya yi ba daidai ba, ko ya ya zai ga sakamakon hakan. Ki yi hakuri, ki ƙara hakuri a kowace tafiya. Maza idan suka shiga halin babu ba abinda ba zasu yi ba, zuciyarsu kan tunzura ne nan da nan. Komai mace ta yi sai zuciyar ta ayyanamusu cewa saboda yanzun basu da shi ne. Shima ki dinga tayashi da addu'a, addu'ar mace ga mijinta babu hijabi." Kuka take, kukan da ta kasa riƙewa. Abba kuwa ban baki yake ba ta gami da nasiha har sai da ya sanyata dariya. A ranta kaunar Abbannasu na kara shiga zuciyarta. Abba mutum ne mai riko da fushi, sai dai tana mamakin sauyawarsa. Dama mutum kan sauya har haka? Shi kuwa Abba ji yake kamar ya tambayeta Aliyun ya daina shaye-shaye amma sai ya bar wa cikinsa. Addu'ar da ya ce ta shafe komai. ***   A hanya suna tafe cikin ɗan sahu, don Aliyu bai je da mashin ba. Kowannensu ya yi shiru babu mai kula dan uwansa, asalima kowanne wuri daban ya zauna. Shi yana karshen kofa, itama haka. Tsakiyar suka bari fili ba kowa. Har suka isa gidan ta shige shi kuma ya tsaya sallamar ɗan sahu. Kallon ko'ina ta hau yi, ya yi kaca-kaca, dama tasan hakan ce za ta faru. Yana daga cikin mazan da basu iya koda tattara kaya ba, balle akai kan shara. Kai tsaye ɗakinta ta faɗa ta shiga banɗaki ta dauro alwalar Magriba jin an soma kiraye-kirayen. Sai da ta idar kafin ta faɗa wanka, garin ba laifi sanyi ya soma shigowa kadan-kadan. Doguwar rigar bacci ta sanya ta ɗora zani a saman. Yanda ta bar dakin haka ta iskeshi, ta rufe kit ta mayar mazauninsa, ta tattara ko'ina. Tana kokarin fita falon suka ci karo a bakin ƙofa. Dauke kai ta yi daga cikin nashi shanyayyun idanun masu kashe dukkan wata gaɓa ta jikinta. "Zan wuce." Ta fadi ganin duk inda ta bi sai ya bi ya kare. Ba zato ya rungumeta tsam a jikinsa. Ba ta da kuzarin kwace jikinta. Ita kanta hakan ta fi buƙata. Wasu hawayen ta shiga fitarwa, ya dinga shafa gadon bayanta yana bata hakuri. "Ki yi hakuri, nayi laifi ba zan kara ba,  ke ce kin kasa fahimtar cewa babu ce ta ke cina. Idan ba ki rufamin asiri ba wa zai rufamin? Duk fa kudin da nake samu akanki yake ƙarewa. Bashi na ci wanda ake barazanar kai ni ƙara kotu, Baby idan ba ta hanyar dukiyarki ba, wurin wa zan je? Wa zai rufamin asiri?" Hakan da ya fadi sai ya kashe jikinta. Ta ɗago kai tana kallonsa. "Shi ne za ka kwata da ƙarfi, meyasa ba ka yimin bayani yanda zan fahimta ba? Dukana fa ka yi Sweet Aliy, duka fa? Ina soyayyar da..." Bai ba ta damar ƙarasawa ba  ya haɗe bakunansu wuri guda. Karshe ma suka koma cikin dakin zance ya sauya. ***   Tun daga wannan ranar sai komai ya wuce, zamansu ya dawo lafiya kalau. Hajiya ta mata aiken jar miya kaya guda. Taimako daya da Allah Ya mata, Aliyu yasa an gyaramusu wutar nepa kuma ko yaya zai wuya rana ta fito ta faɗi ba'a kawo ba, wanna ya bata damar saka miyar a fridge. Idan ta dawo makaranta sai dai ta dumama. Wataran kuwa ba ta amfani da shi, sai dai ta yi tuwo da miya ko kuma jellof. Rayuwar sai sam barka, samun Aliyu yana ƙara ja baya. Har ta rage damuwar shaye-shayensa. Yanzun ta fi maida hankali ga tilawar Alkur'ani da kuma addu'a kamar yanda Abba ya tunasar da ita, sai take jin ta wata daban.   Satinta uku bayan sun kammala gwajin aji ta soma amai da ciwon kai. Tashin farko da likita ya aunata ya tabbatar tana dauke da juna biyu. Wannan karon Aliyu bai yi wani ɗoki ba, a hanya ma jimamin yanda rayuwar za ta yi mishi tsada yake. "Ga kudin makarantarki, ga cefanen gida kuma yanzu ga ciki." "Allah zai rufa asiri." Abinda ta iya cewa kenan, tana jin sadda ya ja tsaki, ita kuwa tunani ne ya ɗarsu a ranta. Ko dai sana'a za ta soma gwadawa ne tunda akwai kudin sadakinta yana nan ba ta taɓa ba,ta ba Abba ajiya, dakyar ya karɓa a lokacin don cewa ya yi babu abin hannun Aliyu da zai riƙe. 'To wace ma sana'a tunda ba wuta ake samu ba?' Wani bangare na zuciyarta ya tunasar da ita. Ta kudurta za ta yi shawara da Amrah ta ji. *** "Kuɗinki suna nan ina juyamaki Ramlatu, fadamin me kike don ki yi da su?" Kalaman Abban suka yi mata dadi a zuciya, iyaye ta yarda iyayen ne. Ba su da buri sai na ci gaban ƴaƴansu. Cike da murna ta sanarmishi sana'a dama take tunanin yi, don ragewa Aliyu wani nauyin." Abba daga bangarensa ya yi murmushi, ya ji labarin tana da juna biyu daga bakin Hajiya. "Hakan nada kyau Ramlatu, kar ki zama mai yawan roƙon miji hakan na zubda girma kuma ya jawo raini. Sai dai a yanzun wace sana'a kike ganin za ki yi?" Ta kara gyara riƙon wayar, kai tsaye ta yi amfani da shawarar Amrah tace "So nake koda kayan kamshi na girki da kuma yaji na dinga yi ina sanyawa a robobi." "Kina ganin makwaftanki zasu siya?" Ta yi shiru, tun zuwanta unguwar ba ta shiga gida kowa ba adalilin Aliyun da ya hana, kuma bai bada fuskar da wani a makwaftan zai shiga gidansa ba. Sau daya wata Maman Nawal gida mai kallonsu, ta gwada shigowa bayan tafiyarta ya nuna baya son gulma, ba ta kara gigin barin wata ta shigo ba. Suma kuwa suka shareta. "Kin yi shiru." Fadin Abba. Ta sauke ajiyar zuciya. "Abba ban taɓa shiga makwaftana ba, ba ya so." Abba daga can ya yi shiru, sai kuma ya amsa. "Kinga Ramlatu, ki maida hankali ga karatunki, In Sha Allah zan daukemishi nauyin biyan kudin makarantarki. Sana'a ba zai yiwu ki yi ba saboda ba kya shiga makwafta kuma ba ki ɗaukesu ƴan uwa ba, don haka ba zasu siya kayanki ba. Sannan hakan ba rayuwa ba ce, ko hakan kika  gani muna yi da makwaftanmu?" Ta girgiza kai ta ce. "A'a Abba." "To ki daina, ki nusar da shi hakkin makwafta da ya rataya a wuyanku. Zan ci gaba da juyamaki kudinki Ramlatu, na budemaki  acc. Allah Ya yi musu albarka." So da kaunar Abbanta suka ƙara ratsata. Kunya sosai ta ji, ita ta kasa bin abinda yake so, gahinan yana tayata son abinda take so da ganin ta zauna a gidan aurenta. Godiya da addu'a ta shiga jerowa har sai da Abba ya katse kiran. Ta jima tana tunanin rashin kyautatawar da ta yi ga iyayenta, a hankali ta shafi cikinta. 'Shima zai iya zuwa duniya ya bijirewa umarninki, ya za ki ji?' Ta sunkuyar da kai ta yi shiru, ranta duk babu dadi.   "Allah Ka yafemin." A furta a fili. Hawaye kam sun zamemata kamar abin ado a fuska. ***   Ta dauka zai yi faɗa ko kuma ransa ya ɓaci, sai ta ga akasin hakan, murna sosai ya hau yi har da rungumeta. "Allah Ya karawa Abbanmu arziki. Kai naji dadi." Murmushi ta yi, Aliyu kenan mai abin mamaki. Wato dai ji ya yi dagaske an taimaka mishi an daukemishi nauyi. Ita da ya bari ma ta yi karatun hakan ma ya yi mata dadi. "Amin." Ta amsa a fili. "Af ke Muhibbat da aure zata yi." Ya fadi cikin nuna halin ko'in kula. Jikinta ya ɗan yi sanyi. "Dagaske? Yaushe ne bikin?" Taɓe baki ya yi. "Gashinan dai ki karanta, ita ta ban ta ce na kawomaki don Allah. Wai ta so zuwa amma ba lokaci, za dai ta zo kawomaki anko." Ta karba ta bude ta karanta. Engineer Kabir Ishaq Sodangi, sunan mahaifinsa ba ɓoyayye bane don ya rike mukamai da dama a gwamnati. "Allah Ya nunamana. Na tayata murna." Cike da zolaya ya kashemata ido daya. "Ko? Kina murna ta rabu da Aliyunki. Ya zama naki ke kaɗai." Hararar zolaya ga watsamishi, ya yi dariya. "Yauwa ta karbi lambarki ma, za ta kira. Ai kuma kinsan me? Wallahi har gobe yarinyarnan tana mutuwar sona. Da na bata fuska sai ta ce na maidota ɗakinta." Maimakon maganar da ba ta haushi sai ta hau dariya, idan mace irin Muhibbat ta rabu da Aliyu, me za ta dawo ta yi mishi? Ya ɗan hade gira. "Ke wallahi Baby ban da aika-aikar da kika yi, zan fa iya rantsemaki Muhibbat ta fi ki sona. Kawai dai ita din ba ƴar daba ba ce. Ba ta iya barazana da kisa ba." Dariyarta ta dauke dif, sai lokacin ya shiga yin tasa yana kara jan ta. "Kai Baby kema fa shu'umar kanki ce. Na dai fada ne kawai, amma ban taɓa zaton za ki iya aikatawa ba. Taɓ! Har na hango idon wannan Hilal din a lokacin? Ni da mujiya." Ya kara bushewa da dariya. Ita kuwa sai sannan ma ta tuna da wani Hilal a duniya, ko wane hali yake ciki a yanzu? Oho. Ta daure fuska. "Please bana son irin haka. Bana so." Ya taɓe baki. "Nayi shiru toh kada ina bacci ki hau ruwan cikina da wuƙa." Haushi da bakin ciki ya sa ta miƙewa za ta bar mishi falon, ya kuwa fisgota ta dawo jikinsa. Nan da nan kuma ya san yanda ya yi aka bar zancen gaba daya. *** "Haba Hajiya! Meyasa za ku dinga kula lamuran yarinyarnan yanzu?! Har yaushe? Har yaushe ne? Kuna tsammanin hakan da ku ke yi shi zai ankarar da ita ta ce kuskurenta? Don Allah Hajiya ku cire hannunku a kanta. A gabana fa kika bada miya aka kai mata, yanzu kuma tunanin yi mata snacks kike? Ina mijinnata? Har soyayyar ta gushe? Har soyayyar ta tafi?!" Munir ke wannan faɗan kamar zai ari baki, wancan karon ma dannewa kawai ya yi. Hajiya a sanyaye take dubansa. "Muniru?" Jin maganar Abba duk suka juya, sam basu ankara da shigowarsa falon ba. Ya ƙaraso ya zauna.       I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/ptlD4eEPhab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 20) "Idan ba mu ja ta a jiki ba wa zai ja ta? So kake mu bar yarinya ciwon zuciya ko hawan jini ya kama ta? Ai hannunka bai taɓa ruɓewa ka yanke ka yarr ba, duk lalacewar Ramlatu, dole mu amsa sunan mahaifanta. Hakazalika duk yanda ka kai da tureta daga dukkan abinda ya shafi rayuwarka, ƴar uwarka ce. Yau ko babu ranmu kai ne uba kuma uwa garesu. A sanadin sharewar da kake cewa mu yi mata, kasan illar da hakan kan iya jawowa? Kasan illar kaɗaici da zama da damuwa a ƙwaƙwalwa kuwa? A'a Muniru, kar ka soma. Fushi da riƙo ba zai kaimu ko'ina ba, ba ka kaini fushi ba, amman gashinan a inda nake ganin zan iya na kasa. Ramlatu tamu ce, kamar yanda muka haifeku, haka muka haifeta. Ban maka lallai ka yi zumunci da ita ba kai da iyalinka, sai dai ka sani, ba ka isa ka cire jininta daga naka ba. Allah Ya riga ya haɗaku matsayin ƴan uwa." Abba ya ci gaba da kora bayanai da nasiha har sai da Munir ya ji dama bai shigo gidan ba, da ba zai ji batun kai ma Ramlat snacks ba har ya yi magana. Hakanan ya ba Abban hakuri aka bar zancen ba don kuma ya ji a ransa zai iya yafewa Ramlatun ba. ***   Kanta ya dauki chaji sakamakon jarrabawar da zasu fara na zangon farko a aji daya na jami'a. Tattara litattafan ta yi ta watsar gefe gami da kwanciya saman three-sitter har da lumshe ido. Garin an tashi da hazo da sanyi hakan yasa ta rufe ko'ina ta kuma sanya jibgegiyar rigar sanyi da safa. Lokacin karfe uku da mintuna na rana sai ka rantse biyar din yamma ne. Aliyu bai dawo ba hakan ya bata damar ƙin yin abinci, indomie kawai ta dafa ta ci abinta da zummar sai yamma ta girkamusu tuwo. Wayarta ce ta dauki ƙara, ta ja guntun tsaki don ba kaɗan baccin ya soma yi mata dadi ba. Ganin baƙuwar lamba kamar ba za ta ɗaga ba, sai kuma ta ɗaga. "Assalamu alaikum." Muryar ba za ta taɓa gushemata ba, ta santa tun mamallakiyarta na matsayin da take a yanzun, wato matar Aliyu. (Muhibbat ce) "Waalaikumussalam." "Amarya gani a ƙofar gidanki." Haka kawai Ramlat ta ji gabanta ya faɗi. Tunawar da ta yi da batun kawomata iv da Aliyu yace za ta yi sai ta ɗan sami nutsuwa. "Toh ganinan zuwa." Daga haka ta ɗauki ɗankwalinta da ya ɗan zame ta ɗaura ta fita. Tsaye ta ganta, suka yiwa juna murmushi. Hanya ta bata ta shigo.     A falo suka yada zango. Bayan an gaisa ne ta mike ta kawomata ruwa da lemu mai sanyi. Muhibbat kam gidan take bi da kallo tana jin zuciyarta na son karyewa. Idan ta ce babu burbushin son Aliyu a ranta, ta yaudari kanta. Soyayya ta mishi da zuciya daya tun yarintarta har girma, sai dai kuma ta samu wanda ya fiyemata shi alheri. "Ga ruwa." Maganar Ramlat ya katse tunaninta, ta basar da murmushi ta dauka, pure water ne marar sanyi sai dai sanyin gari da ya shafeshi. Ga Ramlat, duk ta kasa sakewa, laifukan da ta yi mata kawai ke yawo a kwakwalwarta. Muhibbat din ce ma ta daure ta shiga jan ta da hirar karatu, a hankali kuma suka soma sakin jiki da juna. Abin mamaki hira sosai har da tuntsira dariya. Kiran sallar La'asar ce ta katse hirar. Suka mike gaba daya suka yi alwala. Bayan sun idar ne Muhibbat ta soma haramar tafiya don bata kaunar haɗuwa da Maigidan. Ba yanda Ramlat ba ta yi ba akan ta jira ta yi girki amma ina! Har bakin gate ta rakota, tana son ta ce mata ta yi hakuri ta yafemata dukkan laifukan da ta yi mata a baya, sai dai kunya da jin nauyi yasa ba ta san ta inda za ta fara ba. Zaman yini kawai da suka yi ta fahimci kyawawan halayen Muhibbat din. Tun ma ran gini dai tun ran zane, da wata ce ko kofar gidanta ba za ta tsaya ba balle har ta shigo. Gaisuwar mutunci ba zai haɗa su ba har abada. "Nagode sosai, In sha Allah zan zo. A gaidamin su Mama don Allah." Haka ta iya furtawa, murmushi Muhibbat ta yi. "Zasu ji sosai. Nima a gaidamin Yayannawa." Daga haka ta fice, ita kuma ta rufe ƙofar ta koma ciki. Katin auren ta dauko ta ƙara karantawa, duka-duka ma sati uku kaɗai ya yi saura bikin. "Allah Yasa zamu gani." Ta furta a fili. ***   Ƙarfe tara ta wuce, goma ta buga ta tsere ta bar sha daya, babu alamun shigowar Aliyu. Tsoro ya soma kamata, wayarta ta duba akwai ƴan chanji. A gaggauce ta danna mishi kira. Maimakon muryarsa, sai ta ji muryar mace a gefe guda kuwa ƙarar ƙiɗa ne da hargowar matasa. Kasa gasƙata abinda kunnuwanta suka jiyemata ta yi, ta fi kyautata zaton hayaniyar mata da mazan wurin ne ke shiga kunnuwanta. Don haka a gaggauce ta kara fadin. "Aliyu? Kana ina ne?" Shiru ya ɗan biyo baya sai ta ji hayaniyar ta ɗan ragu. Muryar dai ta ɗazun ce ta ƙara amsa kuwwa cikin kunnuwa da kwakwalwarta. "Baby ko? Babynki na nan karkashin kulawata, kar ki damu yau girkina ne. Zuwa gobe i promise you zan maidomaki abinki. Goodnight." Ta bude baki da zummar surfawa matar bala'i ta ji an katse. Hannunta har rawa yake wurin ƙara dialing. Wannan karon gaba ɗaya ma kashe wayar aka yi. Rasa meke mata daɗi ta yi, ta kasa tantance a duniya take, duniya irin na mutanen da ta saba rayuwa da su, ko kuwa dai wata duniyar ce daban. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Aliyu? Kuma da mace?" Ta furta gami da dafe cikinta wanda ya ɗan murɗa, ta tabbatar banda Allah ne kaɗai Mai iko akan uwa da abinda ke cikinta, babu abinda zai hana cikinta zubewa a lokacin jin irin yanda yake murɗi. "Aliyu?" Dagaske ta kasa gaskatawa, zumbur kuma sai ta mike ta zura hijabi saman rigar da wandon baccinta, har ta murɗa ƙofar ta fito zuwa barandar gidan, ta tsaya cak. Iska da sanyin da ke busowa ya ci ace ɗan Adam ya nemi mafaka cikin bargo, banda Ramlat wacce bai sa ta daina zufa ba. Hawaye take fitarwa mai zafi, a hankali kuma ta juya ta rufe ƙofar falon. Nan bakin ƙofar ta zauna ta dunƙule wuri ɗaya ba ta ko damu da sanyin tiles ba dake ratsa dukkan wata gaɓa ta jikinta. Kuka sosai take yi. Duk a zatonta iyakarsa shaye-shayen, ashe a munanan aikin da yake yi har da neman mata?   *"Ramlatu addu'a, karatun Alkur'ani, su ne babban makaman kowane bawa da kike gani. Ki rike su ba da wasa ba."* Ta tuna kalaman Abbanta. Zumbur ta mike ta shiga ɗakinta, alwala ta ɗora ta fito ta yi nafila. Ta jima cikin Sujjuda tana kaiwa Allah kukanta kafin ta yi sallama ta shiga karatun Alkur'ani.  Tana yi tana hawaye. Komai na dawomata daki-daki, tun daga batun aurenta da Hilal har yanda ta bijirewa iyayenta akan zaɓinta. *"Ke yarinya ce Ramla, ba ki san abinda ubanki ya hangomaki ba. Na taɓa ganin shaiɗaniyar zuciya irin taki da ba ta san Annabi ya faku ba? Wannan taurin kai irin naki Allah Ya miki magani."* Kalaman Tsohuwa Hajja ya dawomata tiryan-tiryan. Wani sabon kukan ta kece da shi, shakka babu gaskiya Hajja ta faɗa. Yanzu tun ba a je ko'ina ba ta na ta fuskantar matsaloli da dama. *"Kina shiga haƙƙin aurena, kar ki manta kema mace ce."* Ta runtse idanu tana jin kamar a sannan take karanta saƙon da Muhibbat ta taɓa rubutomata a baya. Wanda ba ta mancewa har ƙararta ta kai ga Aliyu, ranar ta tabbatar sai da ya ci mutuncinta duk a dalilinta. "Zunubaina masu yawa ne, Allah ina neman gafararKa." Ta furta a hankali, a daddafe ta ci gaba da karatun sannan ta sallame ta yi addu'a mai yawa. Neman gafara ne da kuma roƙawa mijinta shiriya da kuma tsari daga dukkan munanan ayyuka. Ranar yanda ta ga dare haka ta ga rana, waya ta dauka ta dannawa Amrah kira sai kuma ta katse kiran. Me za ta ce? Bayan koma mene ita ce sila. A hankali ta shiga tuna dukkan rikicin da aka yi akan aurenta, wani rashin kunya, taurin kai, kafiya, babu irin wanda ba ta tuna ba. 'Ba zan taɓa ganin laifinku ba.' Ta fadi a ƙasan ranta. *"Ba ina alfahari ba My Future, sai dai wallahi wallahi, na fi dukkan wani namiji da ba muharraminki ba sonki. Ki dawo Ramlatun da na sani a baya, please and please ki maido Hilal cikin zuciyarki."* Ta runtse ido gami da yin istigfari, wannan tunanin ba amfanin da zai mata, dukkan inda dai Hilal yake tana mishi fatan alheri a rayuwa.  Aliyu wani bangare ne na jiki da zuciyarta, sonsa halitta ne da ba ta isa ta yayewa kanta ba. ***   WASHEGARI Kishi mai tsanani cike taf zuciyarta sa'ilin da ta yi ido hudu da shi a falon, har lokacin shaiɗaniyar muryar matar bai bar amsa kuwwa a kanta ba. Ta kauda kai kamar ba ta ganshi ba ta nufi hanyar fita zuwa makaranta ba tare da tunanin cin wani abu ba matsayinta na mai juna biyu. Hannu ya sanya ya tare ƙofar. Ta ɗago idanunta da suka rine tsabar ɓacin rai. Ba kuma za ta ce tsana ba, don ba ta tunanin akwai ɓurɓushinsa. Kokari take ma ta ɗorawa zuciyar amma abin ya ci tura. Bata da ikon hakan. "Malam matsa na wuce." Ya ƙi motsi illa dai ya ƙafeta da mayatattun idanunsa dake kashemata dukkan wata gaɓa a jikinta. "Ki yi hakuri, ina mai haɗaki da Allah. Wallahi ba'a hayyacina nake ba. Kafin na taho sai da na yiwa Zee dukan da ba za ta kara marmarin kallona ba balle .." "Ban tambayeka komai ba, nidai kawai ka matsamin na wuce ina da jarrabawa. Don Allah ka matsa." Ta ƙarashe wani takaici na tahomata, kuka take son yi dakyar ta iya danneshi. Ganin dagaske ba za ta saurareshi ba sai kawai ya matsa a sanyaye, ta fice daga gidan ta kyaleshi. Ita kanta ta yi mamakin yanda ya kwantar da kai har yake kokarin kare kansa, Aliyun da bai fiye damuwa da kafa hujjar da mutum zai yarda da shi ba. Shi dai idan ya aiwatar to ya aiwatar. Amma a lamuranta, ba haka abin yake ba. *** "Wai ke meke damunki ne? Ina fa lura da ke kamar ba'a hayyacinki kike ba. Anya kuwa kin rubuta abinda ya dace?" Tambayar Amrah ta katse tunaninta. Ta yi murmushin yaƙe. "Ba komai,kawai yanayin jikina ne, jiri nake ji idan ban nemi abu na sanyawa cikina ba akwai matsala." Jin haka Amrah ta mike da sauri. "Zama bai ganmu ba Maman Baby, tashi muje." Ba musu ta mike suka nufi wurin siyar da abinci. Amrah na son ƙara tambayarta dalilin damuwarta sai dai ba ta san ta ya za ta fara ba. *"Ƴar uwarki ce, ki yi hakuri da dukkan abinda ya faru tsakaninku. Yanda ta mana laifi, kema ta yi maki. Ki dinga kokarin bata shawara a dukkanin tafiyarku. Allah Ya maki albarka keda iyayenki, Ya fiddomaki miji da zai riƙe ki bisa amana."* Ta tuno alfarmar da Abba ya nemi ta yi mishi akan Ramlat satin da ya wuce. Ita kuwa koda Abban bai nema ba, ta yi amannar ba ta da Aminiyar da ta fi kauna sama da Ramlat din, komai za ta ɗaukeshi ba komai ba. Kuma koyaushe za ta kasance tare da ita koda ace Aliyu zai mata zagin uwa uba. Bai isa ya rabata da Ramsy ba. "Amrah ina cikin damuwar Aliyu." Muryar Ramlat din ta katsemata dogon tunanin da ta faɗa, a gaggauce ta dubeta. "Fadamin damuwarki Ramlat. Me ya yi maki wannan karon?" Shiru ya biyo baya har suka karasa suka nemi mazauni, Amrah ta yiwa waiter magana ta fadi abinda zai kawomusu sannan ta kara dubanta dakyau. Kafin ma ta kai ga magana Ramlat ta soma, kaf ta bata labarin abinda ya faru gami da fadin. "Rabuwa da Aliyu shi ya fiyemin alheri Amrah. Sai yanzu na hango abinda ku ke hangomin. Ba zan iya rayuwa da shi haka ba. Amrah na yi kuskure, na yi nadamar abinda na aikata. Ya zan yi? Ya zan yi da jinin Aliyu dake tattare da ni? Yan uwan Aliyu babu mai sona, abin mamaki wacce na zaci za ta fi kowa ƙina da guduna, ita ce har da zuwa ta kawomin katin gayyatar aurenta har ta zauna mu yi hira da dariya. Ina alhakin Muhibbat zai bar ni? Ina hakkin iyayena zai bar ni na ji dadin zaman aure? Na gaji, zan roƙi Aliyu ya sakeni na yi biyayya ga iyayena." Wani murmushi Amrah ta yi, a ranta tasan karya ne Ramlat ta iya rabuwa da Aliyun. Ta danne tausayin da ya ke tasomata. "Tun ran gini tun ran zane Ramsy." Ramlat ta gyada kai tana sharce majina. "Na yarda, hakane na yarda. Ko mene ni na jazawa kaina. Amma bansan Aliyu mashayi bane, bansan kuma yana zina.." "Astagfirullah, kin tabbatar ya aikata zinar? Kina da shaida? A'a Ramsy, kar ki bari shaidan ya yi wasa da hankalinki. Ba'a yankewa mutum hukunci haka, hukuncin ma na zina kai tsaye. Ke ba ki san tuggun mata ba? Ki dai kwantar da hankali ki ji me zai ce. Sannan sakin da kike kirawa kanki, kinsan wanda za ki ƙara aura? Kin manta da cikin jikinki? Ai wannan kadai ma ya isa duk wani mai miki kallon kin bijirewa iyaye ya yi maki uzuri. Yanzu da ace..." Ta yi shiru har sai da aka ajiye musu plate din fried rice da chicken da kuma lemu da ruwa aka bar wurin sannan ta ci gaba. "Ba wanda zai so ki haifi shege. Komai lalacewar abu gwara kin haihu ƙarƙashin inuwar aure. Ya fiyemaki sutura. Nasan ba ki ci komai ba daga yanayinki, mu ci abincin ma yi maganar daga baya." Ba musu suka yi bismillah, Amrah na satar kallonta cike da tausayi ganin yanda take kai loma, sai da ta cinye tas kafin ta dauki ruwa ta kora. Daga bisani ta soma shan lemun. "Ko za ki ƙara?" Fadin Amrah tana dubanta. Girgiza kai ta yi ta harareta da wasa. "Haba dai, kamar wata jaka?" Taɓe baki Amrah ta yi. "Har kin tunamin da Smally, ci ba ƙiba." Suka yi dariya, nan kuma aka shiga tuna rayuwar sakandire. Wasu sun yi aure wasu kuwa suna dan ganin gilmawarsu a B.U.K musamman mazan. Wasu kuwa basu samu sun shiga ba. Bayan sun kammala suka nufi aji, anan ne Amrah ta bata shawarwari gami da kara nunamata illar yanke hukunci cikin fushi. A hankali kuma ta ji zuciyarta ta yi fes, ta kara godewa Allah da samun Aminiya irin Amrah. ***   Sun kai wurin sati suna fushi da juna don tun yana ba ta hakuri yana lallaɓata har ya watsar. Karshe kuma suka shirya don har ankon Muhibbat ya siyamata. Allah Ya taimaketa lokacin sun kammala jarrabawa, wannan ya bata damar shirin biki a nutse. Rana daya kawai za ta je, ranar yini. Amman hakan bai hanata fargaba ba, gani take yi kamar idan ta je habaici da zagi kawai za ta kwasa ta dawo.   Ranar yinin tun karfe daya ta shirya. Anko ta sanya an mata ɗinkin doguwar riga yanda ba za ta takura ɗan cikinta ba. Ta yi kwalliya sosai abinta. "Wannan kwalliya haka, duk murnar ce?" Fadin Aliyu cike da zolaya, ta harareshi ya yi dariya. "Ai ni na dauketa matsayin ƴar uwa, wallahi ko yau ta so dawowa ɗakinta, ina marhaba." Dariya sosai ya yi sa'ilin da ya ke kokarin rufe ƙyauren ita kuma tana tsaye jikin mashin tana jiransa. Mota dama tuni ya siyar da abarsa. "Dakyau Mrs Aliyu, amma dai ban yarda ya kai zuci ba. Irinku ai ba'a yi maku kishiya, wataran ƙurmus za'a wayi gari kun ƙone mijin da kishiyar." Turus ta yi tana dubansa idanunta nan da nan suka cika da kwalla. "Bana so Aliyu, bana son irin wannan wasan. Dadin abin ma kai ne babban shaiɗanin da ka yi sanadin mutuwar aure." Ya daure fuska tamau. "Ni kike gayawa magana?" Kamar ta ce an fada din, sai kuma ta haɗiye ta kara daure fuskarta ta kauda kai. "Wallahi sai dai ki taho ke ɗaya, na fasa kai kin. Aikin banza kawai! Har wuyanki ya kai ki yi kirana da shaiɗani? Duk shaiɗancina na kai ki? Mai saɓawa iyaye kawai." Cikin jin masifa da takaici ta kara magana. "Oho dai, dadin abin dai na shirya da iyayena, kuma idan fitsari abin banza ne kaza ma..." Wani bahagon mari ya ɗauketa da shi wanda ya yi sanadin raguwar gudun numfashinta. "Kai! Haba Ranka Ya dade, wa ke dukan matarsa haka?" Faɗin wani dattijo yana mai jan kekensa ya tsaya ganin abinda ya faru. Wani banzan kallo Aliyu ya watsamasa. "Ina ruwanka? Matarka ko tawa? Dallah can wuce!" Ya fadi cike da tsawa, kafin ya haye mashin dinsa har yana tunkuɗeta ya soma kokarin tashinsa yana fadin baƙa. "Ni akwai macen da ta isa ta zageni na kyaleta? Wallahi babu don uwarta." "Aliyu ba uwata kake zagi ba wallahi sai dai uwar.." A zuciye ya sauko daga saman mashin din ya kara kai mata naushi a baki. Wani ihu ta kwarara wanda ya janyo hankalin matasan dake can gefe  suna kallonsu. Da sauri suka taho, yana kokarin kai mata bugu aka rirriƙeshi. Ashar yake musu yana kiran su sakeshi tunda ba matarsu bace. "Kai dallah ba ma san hauka! Matarka jakarka ce da za ka kamata da irin wannan duka? Wallahi yanzu sai mu miƙa ka hukuma!" Fadin wani matashi cikin muryar dabanci. Aliyu ya ɗan sha jinin jikinsa, ita kuwa jiki na rawa ta bi shawarar wani matashi da ya ce ta shige makwafta. Da gudu-gudu ta faɗa makwaftan kuwa. Matar na zaune tana tsifar kai sai ganin mace ta yi a kanta. "Innalillahi, baiwar Allah daga ina?" Ramlat ta durkusa tana kuka ga wani kunya da ya addabeta. Wannan ne karon farko da ta shigo gidan. "Makwafciyarki ce, matar Aliyu. Don Allah kimin rai ki bari na zauna kafin ya tafi, wallahi kasheni zai yi, yana waje maza sun rikeshi." Matar ta yi shiru da mamaki, ashe dai dagaske ne da mijinta kwanaki ya ce ya ji ihunta har ya kwankwasa Aliyu ya nemi zaginsa. "Toh, shigo." Ta fadi tana jan ɗankwali ta rufe gashinta, Ramlat ta bi bayanta zuwa falon. Ba laifi falon mai kyau, sai dai daga gani ba wani karfi garesu can ba. Ruwa ta daukomata ta ajiye. Ba ta iya sha ba, sam ba ta cikin hayyacinta. Jikinta har lokacin rawa yake. Kallo ɗaya matar ta gane ciki ne da ita. Tausayinta ya kamata. "Kiyi hakuri." Ramlat dai kuka take ta kasa cewa komai. *** A waje kuwa dakyar aka raba Aliyu fada wannan matashin da ya nemi zaginsa, ya buga mashin ya kara gaba. Yaron matar da bai fi shekaru goma sha uku ba, ya shiga gidan da sallama. Matar ta amsa. "Ya wuce?" Fadin Ramlat. Yaron ya gyada kai. "Eh, yanzu ya tafi." Zumbur ta mike ta dubi matar. "Nagode sosai, nima tafiya zan yi." Gyada kai kawai ta yi don ita ta kasa magana, ko sunan Ramlat din ba ta sani ba. Har Ramlat ta kai ƙofa ta biyota. "Baiwar Allah." Ta juyo ta kalleta. Jakarta da ta bari ta miƙa mata gami da fadin . "Sunana Jamila amma ana kirana Maman Anas. Ya sunanki?" Ta karbi jakar. "Ramlat." Gyada kai Maman Anas ta yi. "Don Allah Ramlat kar ki yanke hukunci cikin fushi, komai ya yi zafi maganinsa Allah, kinji?" Murmushin yaƙe ta yi ta amsa da toh gami da godiya. Tana fita ta sauya hanya saboda kunya,mutanen wurin sai nunota ake yi. Hawaye take dakyar take ganin gabanta, kai tsaye ta tari abin hawa zuwa unguwar Yakasai gidan Hajja.  I just published "BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/K6spRvSBkab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 21) "Yanzu na dai yaji kika yi?" Hajja ta fadi tana jin kamar ta tashi ta kara rufeta da sabon duka. Ramlat ta kalleta. "Haba Hajja, duka fa? Duka a waje har sai da aka kwaceni. Kiyi hakuri amma nidai ba zan koma ba." "Ku ne yaran yanzu! Babu yanda ba'a yi da ku akan ku yi hakuri ku bi zaɓin iyayenku amma sai ku tiƙe lallai sai abinda ranku ke zo. Ku lallai sai kun nunamana kun yi boko, koda dai wasunku ma ba bokon hakanan suke wannan tsiyar. Gashinan auren bai je ko'ina ba kin fara yawon dakan yaji. Ba bakin magana dai Ramlat, miƙewa ta yi ta shige ƙuryar ɗakin Hajja din ta yi kwanciyarta zuciyar na raɗaɗi. Har lokacin zafin marin da Aliyu ya yi mata ba ta bar jinsa ba.  Shikenan kowace mace na zaune gidan aure da daraja da ƙimarta, ita nata ya zube a idanun Aliyu? Da ace yana gani ai ba zai ɗaga hannu ya bugeta ba. Biki kam ta fasa zuwa ko za'a mutu. Tun tana jin sababin da Hajja ke yi har ta bar jiyowa, baccin wahala ya yi awon gaba da ita. ***   YAMMACI   Munir da iyalinsa ne suka yada zango wurin Hajja, daga gidan su Bilkisun suke shi ne suka ga dacewar su leƙo. Hira ta yi hira har Hajja ta gangaro kan Ramlat. "Ramlat kuma?" Fadin Munir cike da mamaki, Bilkisu ta ƙara buɗe kunnuwanta da son jin abinda ke faruwa. Hajja idanu sun rufe balle Munir din, sun mance matsayin  Bilkisu wurin Hilal balle kuma a wurinsu. Komai da ya faru ta kwararo mishi, miƙewa ya yi zumbur ya faɗa ɗakin. Bacci take tsakaninta da Allah, ba ta yi aune ba ta ji an kai mata wawan bugu a ƙafa. A firgice ta farka gami da salati.   Kallonsa take kirjinta na wani irin lugude, babu wannan ƙauna da tausayin na ƴan uwantaka a kwayar idanunnasa. "Tashi ki bar gidannan tun ban ɓaɓɓallaki ba!" Abinda ya ce kenan. Idanunta suka cicciko da kwalla tuni hawayen suka soma zuba. "Yaya Munir.." "Yimin shiru! Ni ba Yayanki bane, You have no right to call me Yaya! Kin maida mutane shashashai wadanda basu san me suke yi ba! Kin zaɓi Aliyu akan uban kowa yanzu kuma kin koma yawo bin gidajen dangi kina ɓatawa zuri'armu suna. Ba ki isa ba! Wallahi Ramlatu kin yi mugun kaɗan! Wato kin ga kin kasa kashe iyayenmu da baƙin cikinki, shi ne kika taho wurin tsoffinmu ki hallakamana su. Ai ke Ramla da ƴar halal ce ta gasken, ko kasheki Aliyu zai yi ba za ki kallemu ba balle ki kawomana kokenki. Daga yau na miki iyaka da mu, idan su iyayennamu sun kasa fadamaki cewa ke Annoba ce a garemu, toh yau ni Muniru na fada. Ki fita hanyarmu da zuri'armu. Wallahi bama sonki mun tsaneki! Ko mayya kike ya ci ace zuwa yanzu kurwar da kika ci a danginnan ya isheki." Ta kasa kwakkwaran motsi, daga yanda numfashinta ke bugu ta tabbatar ba mafarki bane. Wane irin tsana Munir ya yi gareta? Bude baki ta yi amma ta kasa furta komai, a hankali ta zame ta sauko daga gadon ƙarfen Hajja ta lalubi ɗankwalinta da mayafi da kuma jaka, jikinta har rawa yake tsabar wani irin ɓacin rai. Ita kuwa dagaske ko Aliyu zai dinga yanka namanta gunduwa-gunduwa ba za ta kara zuwa ta kai ƙararsa ba. Ba ta son koda kallon Munir don ganinsa take kamar wani bare a wurinta yanda yake dubanta a yanzun. A gaggauce ba ta ko tsaya sallah ba ta fito falon ya biyo bayanta. "Ke ina za ki je? Muniru korarmin ita ka yi? Ina kuma kake son ta faɗa?" Fadin Hajja tana miƙewa tsaye a rikice, Bilkisu ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya wani azababben dadi yana yawo daga kai har kafafunta tana ji kamar ta yi tsalle ta rungume mijinta. Burinta ta ga Ramlat a wulaƙance fiye da yanda ta yiwa ɗan uwanta. 'Kaɗan ma kenan!' Ta faɗi a ƙasan ranta, Ramlat kuwa ba ta ko lura da ita ba, ba ta tsaya amsa kiran da Hajja ke faman kwalamata ba, ta zura takalminta ta bar gidan. A hanya har tuntuɓe take yi tsabar sauri da tunani har ba ta kula da abinda ke gabanta. Haka har ta iso titi tunanin kalaman Munir ke mata yawo a kwanya. Wani wawan burki da aka ci, gami da salatin da jama'a suka ɗauka ya ankarar da ita dalilinta ne. Ta hau titi ba ta sani ba, ta hau ba'a hayyaci ba har mota na shirin ɗauke ta. Ta tsaya cak, mai motar wani dattijo, ya fito ya dinga surfamata ruwan masifa. Abu daya ta dauka a ciki, kalmar da ya yi amfani da ita. "Ba ki da hankali!" Wannan kaɗai ya tsaya a kwakwalwarta. Tana hawaye ta gyada kai. "Eh ban da hankali. Ka yi hakuri, ka yi hakuri." Abinda ta iya faɗi kenan kafin kuma ta tsinci kanta da ƙarasawa wurinsa ta durkusa. "Don Allah Baba ka yi hakuri. Wallahi banda hankali ka taimaka ka kaini asibiti." Kowa kuma sai ya tsaya kallonta, kallon taɓaɓɓiya, ita kuwa kuka take, kukan da take jin har ta mutu ba za ta daina ba. Kukan dana sani, kukan nadama. 'Bijirewa iyayenki ne ya jawomaki.' Wani bangare na zuciyarta ke mata tuni. "Ke mene haka? Tashi ki tafi na yafemaki. Allah Ya kiyaye gaba." Dattijon ya samu kansa da faɗa don abin kuma mamaki ya koma ba shi. Ta miƙe cikin bin umarninsa har da godiya ta ja gefen titi ta tsaya. So take ta tari abin hawa da zai maidata inda ta fito, gidan Aliyu. Gidan da a yanzu Muniru ya tabbatar mata nan kaɗai ne gatanta. Dakyar ta iya ɗaga yatsa ta tsaida napep har sannan idanun wadanda aka yi abin gabansu suna kanta. Ta fadi sunan unguwa ta hau ba ta ko tsaya ciniki ba. Ɗan sahun har da saita madubi yana kallonta, kuka take yi babu makari (hannu ko gefen mayafi), ba ta damu a ganta ba. Ba ta da zaɓi akan ko ɗaya. Nadama ce tsantsa da dana sani. "Bansan zai jawomin baƙin jini har haka ba, a lokacin giyar soyayya ce ta kwasheni. Ban san haka zan koma ba. Ramlat nada gata ta kowane bangare, iyayena ba su rageni da komai ba. Amma na kasa yi musu biyayya akan abinda bai taka kara ya karya ba, wannan wane irin sakamako ne? Ni na dawo haka?" A fili take zancen, ko kuma zantuka. Mai adaidaita sahu tun yana tsoro da yi mata kallon taɓaɓɓiya har ya gane kamar damuwa ce da ɓacin rai ya jawomata komai. Tausayinta ya kamashi, kamar ya ce dama duk wanda bai bi iyayensa ba, rayuwa za ta zo mishi a baibai, sai kuma ya ja bakinsa ya yi shiru. Dakyar ya samu ta mishi kwatancen inda za ta sauka, ta ciro dari biyar ta mikamasa babu batun karɓar chanji. A farko ta yi niyyar shiga gidan Maman Anas, sai kuma kalaman Munir suka tunzurata ta bude gidan Aliyu ta shiga. Mashin dinsa yana nan kuma inji a kunne shaidar ya dawo, tana shiga falon hayakin sigari da ƙamshin shisha ya karaɗe hancinta, ko mutum dakyar kake iya hangowa a falon. Ba ta yi mishi magana ba, shima bai mata ba sai ido da ya bi ta da shi har ta shige ɗaki. Bai taɓa zaton dawowarta a ranar ba, wannan ya ɗan kashemasa jiki. Yana son Ramlatu, abinda ya sanyawa ransa shine ba ta iya magana ba. Shi kuma ba ya son raini, idan shi ya fadamata, ya isa ne. Ita kuwa ba ta isa ta fadamasa ya kyale ba. *** Sallolin da suke kanta ta biya, zama ta yi tana lazimi har aka kira Magriba ta ɗora da shi. A hankali yunwa ta addabeta, ta fito falon. Hayaƙin ya tafi sosai, sai ta kula da labulayen da ya ɗaga, gami da ware fanka. Kai tsaye kicin ta shiga, Allah Ya taimaka tana da miya don haka taliya fara kawai ta dafa ta dumama miyar. Nan ma koda ta fito ba ya falon, ɗakinta ta wuce, ta dawo ta dauki ruwa ta koma ta kulle da muƙulli.   Tana cika cikinta ta jawo wayarta da zummar kashewa. Karo ta ci da sunan Muhibbat na yawo saman screen din da alamar message. Budewa ta yi ta soma karantawa.   *Assalamu alaikum matar yayana. Naji shiru ba ki zo ba, Yaya ya cemin ba ki jin dadi. Ba haka na so ba dai, amman ba komai. Allah Ya saukeki lafiya. Nagode sosai."* Wasu hawaye suka zubomata saman ƙuncinta, Muhibbat su ne irin matan da ake kira ƴan aljanna. Mace ce da ba ta da riƙo, ba ta da fushi. Idan ma ta yi, ba ta da wuyar sauka. Ta sani, laifukan da ta yi mata ba zasu ƙirgu ba. Ta tsinci kanta da rubutamata saƙo kamar haka.   *Kyawawan halaye su ne linzami a kowane tafiya. Su ne nagartar kowane ɗan adam da cikar kamala. Ki godewa Allah, kin dace da samun haka. Ina mai jin kunyarki a koyaushe. Ki yafemin, ni mai tarin laifuka ce gareki. Ki yafemin domin Allah.* Tana kaiwa nan ta aikamata, wayar ta ajiye ta mike ta soma kokarin rage kayan jikinta. Ruwa ma dakyar ta ke taɓawa ta yi alwala tsabar sanyin gari. Wayarta ce ta dauki ƙara, ta yi azamar dubawa. Hajiya ce. "Salamun alaikum, Ramlatu kina lafiya?" Wani rauni ta ji da na zuciya da gangar jiki. "Waalaikumussalam. Hajiya ina wuni?" Ta amsa kafin ta kara tambayar tana ina? "Ina gidana." Shiru ya dan biyo baya kafin Hajiya ta ce. "Toh Alhamdulillah. Bari na bar ki haka dare ya yi. Da safe ma yi magana." Daga haka Hajiya ta katse kiran ta bar Ramlat da bin waya da kallo. Sai kuma jikinta ya bata watakila sun yi magana da Hajja. Hakan bai mata dadi ba, kenan zargin Munir na jefa iyayensu cikin damuwa ya tabbata a kanta. ***   Ita kuwa Hajiya tun bayan Magriba Hajja ta kirata ta fadamata komai. A farko ma ta dauka Ramlatun gidan ta je.   Hajiya ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba,  ta kira Munir ta yi mishi tas ta kara da fadin. "Don ka wulaƙanta ƴar uwarka a gaban Bilki me yake yi? Idanunka sun rufe ka mance wacece Bilki a wurin Hilal! Ko bayan ranmu kai ba mai rufe sirrin Ramlatu bane? Wato ka gwammace Ramlatu ta shiga duniya a bayan babu mu, akan ta zauna cikin sutura a gidanka? Wallahi Muniru koda wasa na ji ka ƙara sanya baki cikin lamarin Ramlatu sai na saɓamaka tunda ba alheri ne ke kai ka ba!" Daga haka ta katse kiran tana hucin ɓacin rai. "Me ya yi?" Muryar Abba ya sanya kirjinta dokawa tara-tara. A falonsa take wayar duk a zatonta wanka ya shiga. Ya ƙaraso yana dubanta. "Me ya faru ga Ramlatun?" Ta rasa me za ta ce, dole ta fadamasa. Ransa ya ɓaci, shima wayar ya cira ya kira Muniru. Ranar dai Munir sai da ya yi dana sanin zuwa gidan Hajja har ta kai shi da ganin abinda zai jawomasa ɓacin ran iyaye.    Bayan kammala wayar, Abba da kansa ya umarci Hajiya ta kira Ramlatun ta ji inda take. Hankalinsu bai kwanta ba sai da suka tabbatar tana gida. "Goben ba kiranta za ki yi ba, da kanki za ki taka ki je gidanta." Abinda Abban ya fadi kenan bayan kammala wayar Hajiya da Ramlatun. Hajiya ta jinjina kai, Abban har ya mance da alwashin da ya ci na cewa ba dai su taka gidan Ramlatun ba idan  ta auri Aliyu. Murmushi kawai ta ɗan yi. Ɗa da mahaifi kam sai Allah. ***   "Sau nawa zan ce ka rabu da ni? Na gaji da tuban muzurunka!" Ta fadi a fusace bayan ta yarfe hannunta daga nashi. Aliyu ya kara marairaicewa. "Ki yi hakuri Baby, kema kin sani ina sonki. Ban san meyasa kika kasa gane cewa raini kawai na tsana ba. Wannan kaɗai ne dalilina na kai maki hannu. Amma wallahi matukar kin kiyaye ba zan ƙara ba. Ki yi hakuri don Allah." Ta yi shiru kawai ta kyaleshi ta ci gaba da ninke kayan wankinta. Kwanaki biyunnan kayanta na wanki sun taru, ba ta iya wankin saboda kasala da kuma zirga-zirgar makaranta. "Yauwa ki haɗa kayan wankinki wuri guda, yau zan kai maki wurin mai wanki da guga. Naga ma zannuwan gadonki suma sun yi dauɗa." Ranta ya ɗan yi sanyi amma ta waske ba ta nuna ba. Duk daurewarta da rashin sakin fuska sai da Aliyu ya rinjayeta suka shirya. Karshe ma har ya ja ta dakinsa ya biya bukatarsa. Sai gasunan suna hira da dariya abinsu. Shi ya taimaka mata da komai na gidan suna dariya. Wayarta ta yi kara suna falo a zaune suna hira. Ganin sunan Hajiya ta dauka da sauri, wannan karon muryarta a sake ba kamar jiyan ba. "Gamunan a kofar gidan naki. Allah Yasa dai shi dinne, nan dai Rafee'ah ta kwatantawa Malam Tanko." Ta dauka mafarki take don haka ta kaiwa cinyarta duka, aikuwa sai ta mike har da doka tsallen murna, Aliyu na kallonta kawai. "Toh Hajiya bari na leƙo na gani." Ta katse kiran a gaggauce ta dauki ɗankwalinta ta daura. "Ya dai?" "Hajiyata ce ta zo Sweet Aliy, ka tayani murna." Ba ta ma saurareshi ba ta fita da sauri. Aliyu ya bita da kallo yana tunanin anya kare bai lashewa Ramlatu zuciya ba. Tsohuwarnan ba ta taɓa takowa gidansu ba sai yau. Amma ya zama dole ya danne ɓacin ransa, ko ba komai yana saka ran ba hannu Rabbana za ta zo gidan ba. Ya mike ya shige dakinsa don sanya sutura ta kamala madadin singelet da gajeran wando dake jikinsa. Hajiya ta shigo bisa jagorancin Ramlat ta zauna. Jikin Ramlatu har rawa yake don ta ma rasa irin tarbar da za ta yi mata. "Hajiya ki ƙaraso dakina." "A'a bar ni anan dai." Fadin Hajiya tana ƙarewa falon kallo, ba laifi ya yi kyau. Aliyu ya fito da sallamarsa. Nutsuwar da ya yi da kuma kalar gaisuwar da ya yi ga Hajiya ba karamin burge Ramlat ya yi ba har mamaki ya kusan kasheta a zaune. Hajiya ta amsa fuska a ɗan sake, kafin kuma ya mike yana amsa gaisuwar A'isha ya fice daga gidan. Ba wani jimawa Hajiyar ta yi ba amman Ramlat ta ji dadi ba kaɗan ba. Ta so Hajiyar ta ci abinci ta ce sam. Dakyar ta samu Hajiyar ta karasa ɗakinta ta gani da kuma kicin. "Gida ya yi kyau, Allah Ya yi albarka." Ta furta sadda take karewa kicin din kallo. Da zumuɗi Ramlat ta amsa. Har kofa ta yi musu rakiya tana jin kamar kada su tafi, farin cikinta ma har da saƙon da Abbanta ya aikomata na kudi. So yake ta rage tambayar Aliyu komai musamman na dawainiyar makaranta, burinsa ta zauna lafiya ba tare da ta miƙa hannu da yawan bani-bani ga miji ba. ***   BAYAN WATANNI TAKWAS Dubansa ta ke ranta a ɓace, shi kuwa tsayawa ya yi yana karemata kallo. "Ba don tulelen cikinnan ba Baby, wallahi da sai na kifar da ke na bi ta kan gadon bayanki na fice." Ta gyada kai. "Za ka iya ai! Wannan kadan ne daga aikinka. Aliyu ina aka taɓa haka? Tun yaushe nake maka batun kayan Baby kana yimin kwana-kwana. So kake na je asibiti a zageni? Kai kullum zancenka ba zai gagara ba! Kullum zancenka kenan! Ni na fadamaka lallai i lalla sai ka yimin abin kece raini? Naji na yarda ko nawa ka kashe ka siyi irin wanda kake da muradi wannan kai ta shafa, amma wannan na amfani urgent bai kamata ka yi wasa da shi ba." Ta fadi kamar ta yi kuka. Ta gaji da gafara Sa ba ta ga ƙaho ba. Haihuwa ta matso kullum cikin ɓoye laifin Aliyu take tana cewa ya siya kayan haihuwa don ta gaji da abin maganarsa. Auren da duka-duka ko shekara biyu ba su rufa ba ta kai ƙararsa ya fi a ƙirga, ciki ne kadai ke sanyawa ba ya kai mata bugu yanzun, amma fa bai fasa dukkan wani rashin mutunci ba, sai abinda ya ƙaru. Ga sauyin rayuwa da ta ƙara lulluɓesu, komai sai a hankali. Ta lura ba shi da niyyar yin ko yaya ne. "Kin gama?" Ya fadi yana hade gira. Ta kalleshi a kaikace, duk shan sigari da shaye-shaye ya ƙara motsar da shi, koyaushe ci yake amma a bushe. Leɓɓansa kuwa baƙin da suka yi ko sha'awa basu ba ta. "Nace kin gama?" Shiru ta kara yi mishi. "Ke bari ki ji, ya dace ace kin gama sanina amma kamar bokon kike zuwa  kawai ba don ki amfana da iliminki ba Baby. Ni Aliyu ba ki isa ki sauya ra'ayina ba, abinda nayi niyya shi zan aikata. Ko yau kika haihu washegari zan siyo duk abinda ya kamata, na fadamaki akwai kudadena a wurin Shamsu Case, wannan satin zai ban, a kanki da Babynmu zai ƙare. Ke wai ba daga gidanmu za'a kawo kayan ba ma? To ki samamin lafiya." Zai gifta ta kara tare hanyar, shi dariya ma ta ba shi. Gaba daya hancin ya bude ga uban rama da ta yi. Wuyanta wani baƙi da ya ƙara ba'a magana, hakanan fuskarta. "Naji, naji za'a kai daga gidanku, amma don Allah ka yimin wannan alfarmar ka fidda kanka da kuma ni kunya a asibiti, haba Aliyu, ta yaya zan je banda ko zanin rufe yaro? Na gama cika baki a ko'ina ka yimin dukkan siyayyar da ta dace, haihuwa fa ba'a saka mata rana, ko yaushe za ta iya kama mutum." Tsaki ya ja. "Shikenan, ba dai rigar jariri ba ce da famfas? Zan tahomaki da su." "Ba su kadai ba ne, ko ka manta da list din da na ba ka na asibiti?" Ya taɓe baki gami da sanya hannu ya kauda nata hannun jikin ƙofa. "Ki turomin ta text." Daga haka ta kauce din ya fice, ranta fatan ya kasance gaskiya take. Alokacin kuwa ta fiddo takardar ta shiga rubuta dukkan muhimman abubuwan ta aikamasa. Fatanta Allah Yasa ya siyo din, zuwa yanzu ta gama sanin Aliyun ba shi da tabbas ko kadan. Zai yi wuya ya daukarmata alkawari ya cika. Rayuwa yanzun ta kara juyamusu baya, kasuwa ta ja wa Aliyu baya sosai, hakan kuma har da rashin maida hankalinsa ga abinda ya dace. Babban bakin cikinta yanda ba damar ya ganta da ƴan chanji sai ya san yanda ya yi ya dauke. Ta sha zuwa ta ganshi cikin sif dinta yana mata bincike. Wannan abu ya fi komai ci mata tuwo a kwarya. Idan ma ya dauka ta riga ta san a mashaya yake ƙarar da su. Akan hakan har yaji ta yi zuwa gidansu, ta share dukkan gargadin Munir ta watsar. Sai da ta yi kwanaki goma cif sannan Aliyu ya kasheta da dadin baki ta shirya ya zo suka tafi. Iyayen kawai kallonta suka yi. Kusan a yanzun ma basu kaunar shiga faɗanta da Aliyu don a karshe kunya take ba su. *** "Please kar ki dameni, sata kike so nayi na kawomaki wai? Ban samu kudi ba, iyakar abinda zan iya yi kenan. Mtsw." Ta bishi da idanu kafin ta maido duba ga kayan da ya siyomata. Gwanjo ne, gwanjon ma ba masu kyau ba. Rigunan jarirai ne, biri da wando kala uku sai karama ta ciki shima kala uku sai wani tsohon showel fari wanda ya tashi daga farin ya koma ruwan madara. Sai kuwa famfas leda guda. A gefe kuwa Pad din mata ce karamar leda guda sai man goya da reza. "Shi kadai za ka iya siya Aliyu? Wannan su ya dace da haihuwarka ta farko? Ɗan farko fa Ali..." "Dillah Malama ki yimin shiru mana!" Abinda ya ce kenan a tsawance wanda bai ko girgizata ba, idan da sabo ai ya ci ace ta sabI think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/HMV9ZSdNmab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 22) "Ba zan yi shiru ba saboda wannan wulaƙanci ne! Ka wulaƙantani da abinda ke cikina. Haba Aliyu! Sai ka ce ba kai ka min cikin ba? Wai dama soyayyar da kake yimin a baki ne? Wane zaƙin kalamanka ne ban ji ba akan ɗanmu na fari kafin na shigo gidanka? Wannan shi ne tukuicin son?" Ta ƙarashe kamar za ta fashe da kuka, idanun sun kaɗa tsabar baƙin ciki da ɓacin rai. "Mtsw. Soyayyar ta ci uwarta! Soyayya ta wuce wanda na nunamaki a shimfiɗa? Inace yanzu tukuicin son ne a cikinki? Da ace bana haihuwa ni bansan ma irin gorin da za ki yimin ba. Ramla abinda zan iya siya kenan, banda arzikin da ya fi hakan, idan kuma sata kike so na yi ni Aliyu ba ɓarawo bane, na zan fara a kanki ba. Ko yau kasuwa ta tashi ai ɗan koli ya ci riba. Har mamakin ma yanda kike kokarin sauyamin tunani nake wallahi, bani da tabbas ko kin soma bin malaman tsubbu. Ina mamakin yanda wataran nake bin ra'ayinki na aikata abinda ban yi niyya ba. Dadin abin Babana Malami ne, zan bazama neman tsari." "Yau kuma shirka kake zargina da aikatawa? Kodayake ba ka da laifi, ko me ka aikata laifina ne da na nace akan aurenka. Dama kyakkyawar damina daga bazara akan gane ta! Aliyu wannan bakin cikin ya isheni, na gaji da shaƙarsa. Aliyu kai da abinda ya shafeka bana sonsu, ka sauwakemin na koma na yiwa iyayena biyayya ko zan ga haske a rayuwata. Na jima ina nadamar aurenka, yau kam na gaji. Na hakura da kai ko kai kadai ne ɗa namiji a duniya." Wata dariya ya yi mai ban haushi da ya sanya hawayen da Ramlat ke dannewa suɓucewa ya zubo. Ya shafi fuskarta ta buge hannun ta ja baya tana sheshsheƙa. "Baby, wallahi kinji rantsuwar ɗan musulmi ba wanda ya isa ya rabani da ke. Aurena da ke mutu ka raba. Kar ki ji ina batun wai bana sonki, ba zan iya rabuwa da ke ba har abada. Kiyi hakuri dai mu ci gaba da lallaɓawa a haka. Maman Baby kuma Baby." Daga haka ya soma tafiya zai bar ɗakin, ta yi wani irin zabura ta bi bayansa ta rike rigarsa ƙam ta baya idanunta har rufewa suke yi. "Sake ni Aliyu. Domin Allah ka sakeni!" Ta zame ta durkusa a ƙasa mararta na tsunkulinta. Ya dubeta ya ja tsaki. "Wai Baby kin san tsinuwar Allah da Mala'ikun da kike jawowa kanki bisa wannan furucin? Baby na fadamaki ba zan sakeki ba. Ban aureki don na sakeki ba har abada." Ta ci gaba da kuka sosai, ya fisgi rigarsa ya yi gaba ya kyaleta anan. Sai da ta yi mai isarta kafin ta mike jikinta duk ya yi mata nauyi ta zauna gefen gado tana faman tunani. Kayan ta kara kallo ta kauda kai. Ba ta da ko sisi a hannunta balle ta fitar ta siya abinda ya dace, idan kuma ta bar kayan da Aliyu ya kawo ita ce da jin kunya a asibiti. Don haka ta mike ta tafasa ruwan zafi ta kawo ta jiƙasu. Tunani sosai ke daukarta ranta na suya, tana kokarin yin takatsantsan adalilin kulawar da aka ce ta yi saboda muddin ba ta yi wasa ba za ta kamu da hawan jini. Mararta na kara murɗamata. Ta yi kokarin tashi ta wanke kayan sai dai ta kasa. Abu kamar wasa tun yana yi yana lafawa har ya soma yin tsanani. Aka yi Magriba, Isha'i ta zo ta gifta, ba labarin Aliyu, cikin kuma bai bar ciwo ba. Juyi kawai take tana salati, cikin taimako na Ubangiji wayarta ta dauki suwwa. Ta kai hannu ta daga ba ta tsaya duba sunana ba ta sanya a kunne. "Assalamu alaikum." Daga jin muryar Abbanta zuciyarta ta karye, shi kuwa ya kira ne ya yi batun bude account na banki da ya ce ta yi, ta soma kuka ba ta ko iya amsa sallamar ba. "Ya Salam, Ramlatu? Lafiya kuwa?" "Abba cikina, ciwo yake min." "Ina shi Aliyun?" "Ya fita." Ta amsa murya na rawa. "Kwantar da hankalinki, yanzu zan turo Rabi." Bai tsaya sauraron komai ba ya katse kiran. Ta yi jifa da wayar. Awa daya na ta rufa ba ta ji ana kwankwasa kofar gidan. Kuka kawai ta sanyawa ji take kamar ba za ta iya takawa ta je ta bude ba. Hajiya ce ta kara kiranta a waya. "Lallaɓa ki zo ki bude Ramlatu, daure don Allah " Ta amsa dakyar sannan ta mike, dakyar ta iya ganin inda ta ajiye mukullin, tana tafe idan ya murɗo sai ta tsaya cak tana salati, koda ta je kofar kasa zura mukullin ta yi ballantana ta bude. "Ranki ya dade zuro mukullin ta ƙasa kawai, sai na bude." Ta ji muryar direban Hajiya. Dakyar ta iya daga hannun ta tura mukullin, ya bude Hajiya ta shigo hankalinta a tashe ga Indo mai aikinsu a bayanta. Suka kamata zuwa cikin mota. "Kayan haihuwa fa?" Hajiya ta tambaya. Nuni kawai ta yi da cikin gidan, tana so ta kai karar Aliyun ba dama. Abinda take gudu ne zai afku. Hajiya ta koma ciki, a saman gadon ta hango ledar kaya da taimakon hasken nepa da suka kawo wuta. Ɗagawa ta yi ba ta ko tsaya dubawa ba ta fito. A mota suna tafe ta tambayeta. "Su ne kayan haihuwar?" Kai kawai ta gyada tana kuka. "Eh su ne Hajiya. Wash Allahna." Suka shiga jeramata sannu, Hajiya ta kira Abba a waya ranta a ɓace amma ta danne. "Alhaji na ce a kirashi a fadamasa mun yi asibiti da ita, naƙuda ce." Abba ya amsa da toh. Tana son sanarmasa cewa basu wani siya kayan haihuwa ba amma ta yi shiru. Sai da suka karasa asibitin da Ramlatun ke awo kamar yanda ta fadamusu sunan, aka karɓeta aka shige Labour room da ita. Nurse ta nemi a bada kayan haihuwa ta miƙamata. Koda ta bude ta dubesu, kafin ta yi magana Hajiya ta amsa. "Yi hakuri yanzu za'a kawo sauran, rudewa ne." Taɓe baki kawai Nurse din ta yi tana murza ido don bacci ma ya soma daukarta. Hajiya ta dubi Indo. "Indo ki tsaya ina zuwa.," Ta amsa da toh. Kai tsaye Hajiya gidan Ramlat suka koma, har sannan Aliyu bai shigo ba, kayan Ramlat din ta dauka kala biyu da kuma undies ta sanya a leda ta fita don ba ta kaunar ma ta haɗu da surukinnata. Sai dai me? A farfajiyar gidan suka yi kiciɓus ya shigo yana busa karan sigarinsa. Yana ganinta ya ɗan russuna ya gaidata ba tare da ya jefar da sigarin ba, ya dai cire a bakinsa ya riƙe a hannu. Hajiya ta ji kunya da takaici sun rufeta, sai da ta ji inama wata can cikin dangi ta kira ta tsaya a lamarin Ramlatun ba ita ba. Duk cewar da ake yana shaye-shaye ba ta zaci rashin kunyarsa akai ya kai wannan gejin ba. "Yauwa lafiya kalau. An fadamaka tana asibiti ko?" "Eh yanzu zan taho." "Allah Ya taimaka." Abinda ta ce kenan ta yi gaba. Ya bi bayanta da harara cike da ɓacin rai, wato Ramlat har ta san ta kira gida ta ce tana naƙuda amma ta ƙi sanarmishi? Don ba shi da kudi ya talauce shi ne za ta mishi tonon silili a duniya. "Idan naje asibitin Allah Ya tsinen." Abinda ya furta kenan bayan ficewar Hajiyar gami da jan tsaki da nufar ciki. Wanka kawai ya yi ya sauya kaya gami da nufar club. Hajiya ba ta nufi asibiti ba sai da ta soma biyawa wani  Nassarawa ta yi amfani da kudin da Abba ya bata ta rike ko za'a buƙaci wani abu ta siya duk abinda ya kamata na jariri bisa umarnin Abban wanda daga baya ta ga dacewar ta fadamasa. Ya jinjina lamarin ba kaɗan ba. ***   "Alhamdulillah." Abinda Hajiya da Indo suke fadi kenan sadda suka tsinkayi muryar jariri na tsala kuka. Nurse ta fito da fara'arta kamar ɗazun ba ita ke yatsina ba. "Hajjaju ga fa kishiyartaki ta fito duniya." Murmushi Hajiya ta yi ba ta amsa ba sai Indo ce ta amsa da Barka Barka. ***   Abba ya yi farin ciki sosai da jin batun haihuwar Ramlat, idar da sallar nafilarsa kenan yana mai roƙamata sauƙi da rangwamen naƙuda a wurin Allah. Ya yiwa kaf yan uwanta har Munir text ya sanarmusu da haihuwarta. Babu wanda bai kira ya tayashi murna ba, Munir bar wa cikinsa komai ya yi ya kira Abban ga mishi murna da tayashi farin ciki. Abba ji yake kamar ba'a taɓa haifamasa jika ba. "Allah Ka shiga lamarin Ramlatu, Ka yafemata kura-kuranta. Allah Ka dubeta da dukkan rahmarKa. Ka rayamata abinda ta haifa." Ya furta a fili yana kara jinjina lamarin Aliyu da aka ce bai taka ƙafa ya je asibitin ba. *** Ta bude idanunta tar bayan ta fito daga wanka inda ta kimtsa jikinta da taimakon Indo. Dinki ciki da waje aka yi mata, azaba kam ta sha ta godewa Allah. Idanu ta ƙurawa jaririyar tana kallo, so da kaunarta na ratsa dukkan sassan jikinta. Ta kauda kai ganin Hajiya na kallonta, murmushi kawai Hajiya ta yi ta cigaba da murje dukkan dauɗar jikin yarinyar. Yanzun ne ta siyo bahon wanka har da gado mai net na jarirai. Aliyu bai zo ba, kuma bai kira ba, wannan ya fi komai taɓa zuciyar Ramlat. Ta fakaici idanunsu ta zubda hawaye. Wuraren karfe biyu Hajiya ta yi niyyar tafiya gida, Abba ya ce ta zauna ta kwana babu damuwa. Idan ma wani abu ne ita Indo ta dawo gidan saboda A'isha. Ta yi zamanta tana jinjina irin kaunar da Abba ke yiwa Ramlatun, ko Uwani (Zulaihat) mai sunan Hajja uwar riƙonsa ba ya yi mata hakan. ***   "Wai ke mijinki ba zai zo ba? Ki kirashi ki ce an sallameki." Hajiya ce ta gaji da jiran gafara Sa ba ta ga ƙaho ba ta karya bille ta yi magana. Ramlat abin ya jima yana ci mata tuwo a kwarya, daidai da Abulle da wasu a dangin Aliyun sun zo ganin jaririyarta amma banda uban gayyar. Idan ta kira har ta gama ringing ba zai ɗaga ba, a karshe ma saƙo ya turomata ta waya cewar wallahi ƙafarsa ba za ta taka asibiti ba tunda ba shi ya kai ta ba. Wadanda suka kai ta su zamemata gatan su biya duk abinda aka kashe. Idan ma ta ga dama daga asibitin ta wuce gidannasu ba shi da kudin ciyar da ita da abinda ta haifa. Talaka ne Aliyu. Wannan shi ne saƙonsa. Ta ƙara kallon Hajiyarta, tasan abin ya yi mata ciwo ne kuma ta gaji ne ta yi magana. Zulaihat da Rafee'ah suna gefe suna cin abinci ba wanda ya ce uffan. "Hajiya ya ce ba zai zo ba." "Ba zai zo ba kamar ya? Me yake nufi da hakan?" Ta sunkuyar da kai tana fidda hawaye don ita wulakancin Aliyu har mamaki yake bata, kamar wanda aka shiga tsakaninsu. "Uhum, Allah Ya kyauta." Fadin Zulaihat kenan, Rafee'ah ta amsa da amin. Yau ne zuwanta na farko asibitin ita kam, hakan ma don Hajiyar ta kira ta mata tas a waya ne. "Kenan suna ma bai shirya ya yi maki komai ba?" Ba ta ko iya amsawa Zulaihat tambayarta ba, bakin ciki da kunya sun rufeta. "Wannan abun ya yi yawa, wannan wane irin jahilci ne ke dawainiya da shi?" Hajiya ke wannan sababin, har ta yi ta gama ba wanda ya amsa a yarannata don su kam gani suke ai dama wanda bai ji bari ba zai ji hoho. *** Da yammaci bayan an yi sallama, Ramlat ta yi mamakin yanda Hajiya ba ta kara ce mata uffan akan Aliyu ba. Ba ta kuma san yanda aka yi aka biya kudin asibitin ba, ta san dai ba Aliyun ba ne. Ta tattara suka wuce gidansu da ita. Hakan ya fi komai yi mata dadi, idan ta juya ta dubi jaririyarta a hannun Rafee'ah, sai ta ji wani sanyin dadi ya rufeta. Ta lura ko ba komai yan uwanta na son yaranta kawai ita din da Aliyun ne basa kauna. Duk kauce kaucen Rafee'ah ta yi ta kyale ta hakura ta karbi yarinyar. Har suka je gida ba wanda ya tayar da zancen Aliyun. Daki guda aka bata da ɗiyarta. Hajiya da kanta ta dauki jaririyar ta kai wa Abba. "Masha Allah." Ya furta yana murmushi. "Kamar Ramlatu tana karama." Ya fadi gami da duban Hajiya. Murmushi ta yi maganar Aliyu na cinta sai dai ta bar wa cikinta tunda Abban ya ce a rabu da shi a zubamasa na mujiya. "Wane suna suka zaɓamata?" Fadin Abban yana kallon Hajiya ganin bai fi saura kwanaki biyu ya rage sunan ba. "Ina ya ɗaga wayarta balle ya faɗa? Sai dai a tambayota." Abba ya murmusa, Hajiya dai ko yaya abu ya ɓata ranta sai ta san yanda ta fitar ko yaya ne. "Tambayota." Ya fadi kai tsaye. *** Ramlat ta dubi Hajiyarta. Ita kuwa wa take da shi sama da Hajiyar yanzu? Iyayenta sun mata komai duk da irin tokar da ta baɗamusu a idanu. "Kin kuramin ido, ko shima sunan sai kin tambayeshi?" Hajiya ta furta a zafafe. "A sanyamata Rabi'atu." Hajiya ta ɗan yi shiru sai kuma ta fita. Kamar ta ce ba ta son jinin Aliyu da sunanta sai kuma ta share. Tana fadawa Abba ta yi daki ta kyaleshi yana dariya. Kai tsaye ya yiwa yarinyar huɗuba. *** Ranar suna komai da aka yi Abban ne karfinsa. Daga gidan Aliyun an kawo kayan barka, kamar yanda Abban ya ce, ba su nuna komai ba suka karba duk kuwa ba kayan a zo a gani bane. Yarinya ta ci sunan Hajiya su na kiranta da Ummi. Hajiya tun tana kawaicin har ta saki ranta dalilin kaunar yarinyar da Allah Ya doramata. Balle kuma Abba wanda koyaushe tana hannunsa idan yana gida. Wannan gatan kadai ya ɗan rage damuwar Aliyu a ran Ramlat, ta dai yi rama ta kuma yi duhu. Amrah na zuwa lokaci zuwa lokaci musamman daga makaranta, tana koyawa Ramlat abinda aka yi a ajin. Yaya Munir bai leƙo gidan ba koda wasa sanin da ya yi Ramlat din tana nan. Bilkisu kam zuwanta biyu gulma na kawota, duk irin habaici da za ta yi ko bakar magana, Ramlat ba ta kallonta balle ta amsa. A nan ma ta ke jin batun auren da Hilal zai yi, kai tsaye ta ce Allah Ya sanya alheri ta share batun wanda ba haka Bilkisun ta so ba. *** Aliyu ba waya kuma bai zo ba har suka cika kwanaki arba'in cif a duniya. Kamar daga sama kuma suna cikin kwanaki sittin a gidan Hajiya, sai ga Aliyun. "A kyaleshi, ban yarda a nunamasa wani abin ba. Wanda ya yi nagari, kansa. Ba yanda kika iya ke kuma, sai hakuri." Abban ya fadi bayan ya je ya yi magana da Aliyu, hakuri kamar koyaushe shi Aliyun ya bada ya kuma ce ba zai kara irin kuskuren ba kamar dai alkawarin da yake yi a baya idan magana ta zo kunnen magabata. Tuban muzuru kenan tunda ba ya fasawa. "Toh Abba." Cewar Ramlatu idanunta cike taf da kwalla. Ta mike tana gyara zaman mayafinta, bisa umarnin Abban ta je su gaisa da Aliyun kafin a sanya ranar komawarta. *** Yana falon saukar baƙi ya yiwa jaririyar ƙuri da idanu, sallamarta ya sa shi ɗagowa ya kalleta. Gaba dayansu sun yi kewar juna. Ta kauda idanunta tana jin tsanar kanta da irin son da take yiwa wannan halitta. Bayan ta gaidashi ya matso jikinta sosai. "Baby dubi yanda rashinki ya ramar da ni. Baby ina miki Laifuka, wallahi ki sani, bansan ya zan yi na yaƙi wannan fushi da zuciyartawa. Kin fi kowa sanin ina sonki, ina son abinda kika haifarmin. Takaici da bakin cikina, kiran da kika yi waya a gidanku a kaiki asibiti amma kika kasa kirana. Haba Baby, kinsan ba ki kyauta ba." Ta kalleshi da niyyar gasamishi bakar magana, sai dai hawayen da ta gani a fuskarsa ya kashemata jiki. Ya kwantar da kansa a kafaɗarta. Ta runtse idanu, wutar so da kaunar Aliyu na kara dagula lissafinta, yana don cin galaba a kanta kamar koyaushe. Ta ɗan ja jiki za ta matsa, ganin haka ya ɗago yana kallonta. "Baby, wayo kika yimin. Ummi kamar ki ta dauka sak. Amma ta fi ki dimple mai kyau." Ya ƙarashe yana sanya yatsansa dai dai inda ke lotsawa a kumatunta. Itama ta kurawa yarinyar ido, kaunarta na ratsata. Suka kasa kauda idanu daga kan diyartasu har sai da aka ɗauki lokaci. "Aliyu kana wahalar da ni, kana cutar da zuciyata. Aliyu don girman Allah ka sassautamin." Ta fadi a raunane don ba ta ma san wane irin sassauci ba, ai ba shi ta sanya sonsa a kirjinta ba. Kuma bai da ikon cirewa, balle ya yaye din. "Fadamin, me da me kike so na bari, zan daina har abada. A kanki yau Malam har kuka ya yimin ya kuma rantse idan ban je na nemi gafararki da ta iyayenki ba sai ya kwashemin albarka." Murmushi mai ciwo ta yi. Tasan a zuciya da zafi irin na Aliyu ba dai ya tako kofar gidansu a karan kansa ba. Dama dai da walakin goro a miya don Malam din shima har rago ya kawo na suna, ya zamana raguna biyu aka yankawa Ummi da na Abban. Ta kuma fahimci Aliyun da Malam yanzu ba laifi sun sami jituwa. Ban baki, rarrashi, alƙawari daban-daban, ba irin wanda bai daukarmata ba kafin ya yi mata sallama da zummar zai kira waya. *** Hajiya ta yi mata ƙuri da idanu yanda take ta shirin komawarta gidan Aliyu. Magungunan duk da ta kawomata na gyaran jiki ta shanye tas. Ta sallama lamarin Aliyu da Ramlatun, ta san kuma muddin wani ya shiga tsakani shi zai sha kunya. Tana da tabbacin abinda Abba ya hango kenan shi ne dalilin kama bakinsa da kuma rashin saurin yankewa lamarin nasu hukunci. "Hajiya na shirya." Maganar Ramlat din ya katse mata tunani, ta kara dubanta. Ta sha daya daga cikin atamfarta Holland wanda Abba ya siyamata na fitar suna, ta yi kwalliya daidai gwargwado abinta. Ummi an mata kwalliya itama sai kamshi take abinta. Ta kauda kai ta share ƴar kwallar da ta cika idanunta. "Shikenan Ramlatu, Allah Ya kiyaye hanya. A ci gaba da hakuri dai. Kowa da kaddarar rayuwarsa. Tashi ki je Abbanki na falo." Ta amsa da toh gami da nufar ciki. Hajiya ta bita da ido, duka-duka yarinyar ko shekaru ashirin ba ta kai ba amma jarrabawar rayuwa sun mata dabaibayi. "Allah Ya kawomaki sauki cikin lamuranki." Ta furta a fili. *** A can ma Abba nasiha ya yi mata sosai kafin ya ba ta kudi sosai ya kuma ce ta yi kokarin bude bank account ko don ma makaranta. Ta yi ta godiya har da hawayenta sannan ta mike ta tafi ya bi bayanta da ido. Ji yake da yana da halin sauyamata wannan kaddarar da tuni ya yi, sai dai komai na hannun Madaukakin Sarki wanda zaɓi da kuma ikonSa ya fi na kowa da komai. *** IDAN KIƊA YA I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/5VwehILsqab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 23) IDAN KIƊA YA CHANJA... Watanta biyu da dawowa gidan, komai ya sauya. Shaye-shayen Aliyu ya ta'azzara duk kuwa da yanda yake kara ramar da shi, yake kara motsewa. Akwai sadda ta bar Ummi a falo tana kicin, sai fitowa ta yi ta ga hayakin shisha na tashi a falon yarinya na jan numfashi dakyar. Ranar har dukanta ya yi saboda cecekucen da suka yi. Ta gaji iyakar gajiya, wannan ne yasa gaba daya rabin hankalinta kacokan ya koma ga kula da Ummi. Idan ka ga dariyar Ramlatu toh tana tare da ɗiyarta ne. Tana yawan shiga wurin Maman Anas duk kuwa da gargadin Aliyu, har ya yi ya bari. Maman Anas itama takan shigo su yi hira ta kara bata shawara da adduo'i. Don halin Aliyu ba ɓoyayye bane. ***   Wataranar Talata ta dawo daga makaranta a gigice, Ummi ke kuka ta rasa meke damunta. Ta yi rarrashin ta shayar da ita amma shiru, kuka ya ƙi ci ya ƙi ƙarewa. Waya ta dauka ta kira Aliyu bayan ta yiwa yarinyar wanka ta sauyamata sutura. "Ki kai ta asibiti mana." "Da ace da kudi a hannuna kaima kasan daga makarantar zan kiraka na wuce. Wallahi kudin mota kadai..." "Naji kar ki isheni. Nima dai kinsan ba wani kudin a jikina. Kuma dama sai yau kika san amfanina har kika kirani, kwanakinnan ai na dauka kin koma ƴar kanki mai cikakken iko. Tunda ko ba komai na bar ki kin koma jami.." Ta katse kiran, ba ta son hayaniya, kukan Ummi kadai ma ya isheta. Ta dauketa bayan ta zura hijabi ta fice gidan Maman Anas. "Kukan me take haka?" Fadin Maman Anas sadda ta sa hannu tana karɓarta. Itama Ramlat kamar ta yi kukan ta ce. "Wallahi ban sani ba, tun a makaranta take kukannan kinga ba mu tashi ba ma na taho kawai." Nan Maman Anas ta taɓa cikin ta bubbuga. "Ga abinda ke damun yarinya, cikinta ne a kumbure." Daga haka ta yi mata dabarar su ta manya, gishiri kaɗan ta sa a ruwan ɗumi ta ba ta, aka samu cikin ya lafa ta yi shiru. Ganin haka ta miƙamata ita. "Sa mata nono a baki." Ba musu Ramlat ta karɓe ta, sai lokacin hankalinta ya ɗan kwanta. Ta shiga ba yarinya, karshe ma yarinyar ta daina karɓa ta yi shiru, can ta soma nishin kashi. Ganin haka Ramlat ta yi dariya. Harara Maman Anas ta watsamata cike da wasa. "Kinji ki, sai yanzu kika samu nutsuwa kenan? Ramlatu kenan." Dariya ta kara yi. Nan kuma ta mike hadi da yi mata godiya ta bar gidan. A bakin kofa ta tarar da mashin din Aliyun, wannan ya bata tabbacin ya dawo gidan. Babu fargaba ko shakkar komai ta shiga ciki, a falon ta tarar da shi yana safa da marwa, tana shigowa ya yi kanta kamar zai kai mata duka, ba ta ko kalleshi ba ta gifta ta wuce. Ya bi bayanta zuwa dakin. "Don tsabar iskanci ina magana kin katse waya kuma kika fita ba da iznina ba? Ita Maman Anas dinnan ko uwarki ba kya jin maganarta yanda kike jin nata a yanzu! Toh wallahi Ramlat kika kara shiga gidan matarnan ban yafemaki ba!" Kamar da dutse ya ke magana, haka ta yi shiru ta cirewa Ummi wando ta dauketa zuwa banɗaki don yi mata tsarki. "Kee! Ni kika maida ɗan iska ina magana kin kyaleni?" Tana jinsa ta yi banza har sai da ta gama uzurinta ta fito ta sakawa yarinyar wando ta shimfiɗe. Tana jinsa ya yi ƙwafa ya fice daga dakin a fusace. Sai a sannan ta bi hanyar da ya bi da kallo, kwanakinnan iskancin ƙaruwa yake. Tunda ya soma wani sabon chatting a waya wai shi Whatsapp shikenan ya zama shagalalle. Sai ya kai biyun dare yana hira a waya, abin yana mata ciwo matuƙa. A gefe daya kuma babban tashin hankalinta na ganin tun dawowarta gidan ba ta ga al'adarta ba, ga yanayin sauyi da ta ke ji na tashin zuwa da yawan ciwon kai da kuma baya. Faɗan da ta yiwa kanta, shi ne ɗaure ɗamarar zama da Aliyu a kowane hali na rayuwa. Barin sirrin zamanta da shi a cikinta, ta gaji da yin abin kunyar daka yaji kuma ta dawo. Ga Abba da kwana biyunnan bai jin dadin jikinsa. Wannan ma babban tashin hankalinta ne. Ta sauke ajiyar zuciya sadda ta ga dagasken dai Ummi ta yi nisa a bacci sannan ta mike ta kimtsa jikinta da neman abinda za ta sawa bakinta na salati. *** Maimakon karfe sha biyun da ya saba shigowa a ƴan kwanakinnan, karfe takwas da mintuna ne daren ba zato sai gashinan ya faɗo gidan. Tana falon tana duba takardun makaranta, Ummi na gefenta kwance idanunta biyu ta ƙura idanunta ga takardun da fitila ta haskesu. Jefi-jefi takan kalli yarinyar ta yi murmushi ko kuma ta yi mata wasa. Ko kallonta bai yi ba kamar yanda itama ba ta kalleshi ba har ya shiga ɗakinsa ya fito. Ƙamshin turaren da ta ji ya sanya ta kallonsa, ya sauya ƙananun kayan dake jikinsa zuwa shadda ruwan madara har da hula abinsa. Sai ya koma mata Aliyunsa sak wanda ta sani tun farkon haduwarsu, bambancin, wannan Aliyun a rame yake ga leɓɓansa da suka ciza suka ƙara yin duhu fiye da baya. Ance ko yaya mijinka ya kai ga lalacewa, kana kishin abinka musamman ma auren da aka yi akan tafarkin so da kauna. Hakan ce ta faru ga Ramlat, ji ta yi gaba daya ta rasa nutsuwarta, shi kuwa yana tsaye da taimakon fitilar karamar wayarsa da ya sanya a baki yake haska hannunsa yana gyara zaman links. Miƙewa ta yi ta je har gabansa ta tsaya. Ya dubeta gami da haske fuskar da fitilar bayan ya riƙe a hannu. "Lafiya?" Ta matsa kadan. "Kalau, ina kake nufin zuwa?" Wani murmushi ya yi. "Au fita ma a bokon naku akwai ƙa'idarta ko? Toh zance zan je. Akwai magana?" Ta daure fuska. "Babu, amma ka sani duk abinda kake yimin a gidannan, Allah Zai min sakayya. Ka auro dubu ma Aliyu, sai dai ka sani, duk radda ka yi aure toh babu Ramlat a gidannan." Ya yi dariya sai kuma ya ja tsaki. "Ke kika san wannan. Idan kuma sakin a hannunki yake sai mu gani. Kin dai zabi boko yanzu akan kowane hidima na gidanki ko? Sai ki ci gaba." Daga haka ya gifta ya wuceta yana mai ɗaga wayarsa da ta addabeshi da ƙara. "Hey Zee, ganinan tafe yi hakuri." Zee din da ya ambata sai da ta ji kirjinta ya buga, wani zafi zuciyarta ke mata. Zee dai shaiɗaniyar da ta taɓa kwana da mijinta? Ramlat ta kasa nutsuwa, sai kuma ta ga da gaskiyar Aliyun, ita ce ta sauya a tafiyar zamansu, wato dai sauyin maimakon ya jawomata martaba da kyautatawa daga Aliyun, sai abinda yake mata ya ƙaru. 'Yanzu ke Aliyu ma ya yi aure wannan ba abin kunya ne gareki ba? Abin a yi maki dariya?' Wani ɓangare na zuciyarta ta ankarar da ita. Karatun da ba ta iya ƙarasawa ba kenan, tattare takardun ta shiga yi ta maida jaka, ta dauki Ummi suka nufi daki. Bacci ya gagareta kamar yanda nutsuwa ta kauracemata. Ta rasa ina za ta sa ranta ta ji dadi, waya ta ciro ta shiga kokarin kiran Aliyun, ya yi ringing har ya katse bai ɗaga ba. *** A lokacin shi kuwa yana tare da su G Baba da su Zee ana banke-banken hayaƙi da shafa jikin ƴan mata. Zee na kusa da shi kamar ta koma jikinsa. A duniya tana son Aliyu, ta kuma lura ba ta samun damarsa sai idan yana cikin ɓacin rai da ta gida, abinda ta karanta kenan. Don haka yanda ya dinga biyemata suna faranta ran juna da soyayya irin ta shan minti abin ba karamin dadi ya yi mata ba. _*"Duk sadda kika samu dama, ki yi yanda ki ka yi ya kusanceki. Koda ciki bai shiga ba, ki mishi karyar kina dauke da cikinsa, duk yanda zai yi akan ki zubar, ki nuna ba ki shirya hakan ba sai dai ya aureki"*_ Kalaman ƙawarta Nancy suka faɗomata a rai. Ta tabbatar yau din ce damarta. Tana kallon sadda wayarsa ke faman hasken kira, da kanta ta dinga katse kiran. A karshe ma ta kashe wayar gaba daya. 'Sorry Babyn Aliy, yau ma nawa ne. Wancan karon koda ban yi nasara ba, wannan karon zan yi.' Fadin Zee wacce take faman ɗurawa Aliyu lemu wanda ta sanya kwayoyin da shi kansa sun fi karfinsa. G Baba ya kalleta suka kashewa juna ido gami da ƴar dariya. Wannan shi ne burinsa, zai fi so ma Aliyun ya kusanceta, ko ba komai yana tare da bakin cikin Aliyun yanda bai taɓa kwanciya da wata mace ba a harkar Bariki. Kusan ma ba wannan a gabansa, bar shi da abinda ba za'a rasa ba. So yake ya kashe bakin fariya da jin kai a wannan fagen irin na Aliyu. *** Sanyin Asuba da na gari ne ya farkar da Ramlat, ta bude idanunta ganin hasken fitila tar a kansu shaidar an kawo wuta ma cikin daren amma bacci ɓarawo bai sa ta ankara ba. Fanka kam tun shigowar sanyi ta daina kunnawa. Ta miƙe ta sauko bayan ta gyarawa Ummi lulluɓin da ta yi mata da bargo. Alwala ta soma t gabatar da sallar Asuba. Cike da fatan ya kasance Aliyu ya dawo gidan ta fita zuwa dakinsa, gwuiwa a sake ta ja ƙofar ganin bai dawo gidan ba. Kasa komawa dakin ta yi ta zauna a falon. Wuraren bakwai kukan Ummi ya fargar da ita daga tunanin da ta afka, ta mike ta daukota. Abin mamaki da tashin hankalin, har sha biyu na rana babu Aliyu ba labarinsa. Ta kasa nutsuwa, ta kira wayar kuma ya fi sau talatin ba ta shiga. Jikinta kuma sai ya yi bala'in sanyi. Tsoro da fargaba suka shige ta. Ta goye Ummi tana jijjigata ba don ta yi bacci ba. Bugun da ta ji a bakin ƙaton kyaurensu shi ya maidota hayyacinta. Da sauri ta shige daki ta fiddo muƙulli ta yafa gyale ta nufi kofar. "Waye?" Ta tambaya da tsoron amsar da za'a bata. "Ni ne Idi direban Alƙali." Ta san waye Idi don sadda ta je yawon arba'in na Ummi, Justice da kansa ya sanya Idin ya maidota gida. Kamar yanda ta san Alƙalin mahaifin Muhibbat, amma tsabar rudewa ma ta manta ko waye. "Banganeba." Ta fadi kamar ta yi kuka. Ya hau dogon bayani ta bude kofar a karshe. "Cewa aka yi na zo na kaiki asibitin Malam, maigidanki ne suka yi hatsari daren jiya. Amma jikin da sauki." "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Toh, to ganinan." Ta fadi tana jin kuka na tahomata, ta juya kamar za ta koma gidan sai kuma ta ce. "Ai zan iya zuwa a haka ko?" Tsabar rudewa ma ta rasa da wanda ya cancanta ta yi shawara. Idi ya kauda kai cike da tausayawa. 'Allah wadarannaka ya lalace, banda ma aure aure ne, me mace kamila irin wannan za ta yi da yaron da ya kusa mutuwa a hanyar dawowa daga saɓon Allah?' Fadin Idi kenan a ƙasan ransa don ya ɗan tsinkayi fadan da iyayen maza ke yi game da abinda suka tsinta daga bakin yan sandan da suka kawosu asibitin. "Kiyi hakuri." Shi ne abinda ya iya fada. Ta koma ciki don kanta ta sanya hijabi ta fito ba ta ko dauki waya ba, silifas din amfaninta na gida ne a kafarta. *** A Emergency ta iske mutan gidan su Aliyu ciki har da Abulle a gefe tana ta kuka da salati. Ta karasa kawai ta durkusa gaban iyaye mazan wadanda su ne mafi kusa da inda take. "Lafiya kalau Ramlatu, sai hakuri kin ji? Kar ki damu jikin ba wani rauni ya samu sosai ba." Wannan shi ne jawabin Malam gareta. Ta gyada kai tana dauke hawayen fuskarta. Sai da ta je wurin Abulle sannan take jin abinda ya faru cikin ɓarin zance irin na Abullen. "Yanzu yaronnan sai da ya jawomin abin kunya abin magana a gidannan? Fisabilillah wannan wane irin bakin ciki ne ace wai a motar mace ka yi hatsari kuma likitoci sun auna sun tabbatar ma ba a hayyacinka kake ba, ka sha kwayoyin da suka fitar da kai hayyaci? Ke yanzu haka kike zaune da shi ba ya kwana a gida shi ne ban isa ki fadamin ba? Yanzu da ko rubutu ne da rokon Allah ba sai na saka a shiga yi mishi ba? Wani kallo take yiwa Abulle wanda kai tsaye za ka kirashi da harara, ita kanta ba ta san sadda ta yi din ba, ga mamakin Amaryar Malam dake kallon wannan dirama, Abulle ta kauda kai gami da fadin Allah Ya kyauta ba tare da ta nemi maida baƙa da hayayyakowa Ramlatun ba yanda ta saba yiwa duk wanda ya yi mata ba daidai ba. Ramlat ta kauda kai, jikinta har wani tsuma yake, bakin ciki da takaici ne suka tararmata. Da ta san abinda akai kenan da ba ta zo asibitin ba. Likita ya tabbatar za'a iya sallamarsa da dare don ba wata buguwa ya yi ba Banda buguwar kai da ya jawomasa nannauyan baccin fita hayyaci. Fatansu kawai ya farfaɗo cikin hayyacinsa. "Ita yarinyar fa?" Tambayar da Justice ya yi ya maido Ramlat hayyacinta, kunya ta dabaibaiyeta, hawaye take kanta a ƙasa, jiri take ji tana daga zaune wanda ta tabbatar da a tsaye take zubewa itama za ta yi. "Af, an samu an kira wani nata kuwa?" Fadin Likitan. "Tukunna dai, bamu santa ba. Sai dai ko idan ta farfaɗo a tambayeta." Likita ya jinjina kai. "Da sauki jikinta, karaya ce kafa da hannu sai rauni a goshi, mun yi mata dressing, ba dai ta dawo hayyacinta ba tukunna amma muna da ran itama lafiya don ba ta sha abinda yaronku ya sha ba." Kowannensu kunya ta kamashi, Malam har hawaye ya share cike da bakin cikin kasancewar Aliyu ɓatacce. Addu'a yake mishi ba dare ba rana akan Allah Ya shiryamasa shi. Gaba daya mazan suka tafi, duk yanda Abulle ta so a kyaleta har ya farfaɗo suka ƙi, haka suka tasa uwarsu a gaba da zummar da yamma zasu dawo, Amarya da Ramlat kadai aka bari. Kuka take bayan ta kwance goyon Ummi ta mikawa Amarya yanda ta bukata, ta janyo hijabin ta rufe fuskarta, Aliyun ma ba bukatar ganinsa take ba, takaicinta ya tafi ga abin kunyar da ya jazamusu. Idan ta tuna da mace aka ganshi wacce ba ma muharramarsa ba ya fi komai baƙanta zuciyarta. Ta ƙara gane ba ta yi sa'ar aure ba, miƙewa ta yi ta nufi hanyar fita. "Ina za ki je?" Fadin Amarya wacce ita kanta zaman ya isheta. Ta dubeta da jajayen idanunta tana jan majina. "Waje zan ɗan fita yanzu zan dawo." Amarya ta gyada kai, yau kam ta ji tausayin yarinyar a ranta. Ramlat ta fita tana jan ƙafa har waje, tafiya kawai take cikin tafkeken asibitin na Malam tana zagaye, kuka take, kuka kamar wata taɓaɓɓiya tana ambaton Allah. Ba ta ko damu da idanun jama'a ba, ƙasan wata bishiya da aka saka kujeru ta samu ta zauna, hawaye take fitarwa tana jin wani kaɗaici a ranta. Kamar ta yi wani babban rashi alhalin ita din tana da gata, tana da iyaye da kuma yan uwa. "Abinda kuke jiyemin kenan?" Ta fadi a fili tana sheshsheka. Jikinta har rawa yake, so da kaunar yan uwanta ke ratsa dukkan gaɓɓanta. Idanunta ya kai ga wasu ma'aurata kuma inyamurai zaune a can gefe guda. Meatpie da lemu suke sha, mijin na rike da yarinyar a cinyarsa, matar kuwa ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe. Har suka kammala suka mike, yana rike da jakarta da kuma hannun ɗiyarsu da bata wuce shekaru biyar ba. Kallon ƙurillah take musu har sai da suka kalleta ta ankara ta sauke idanunta. Tana ji suna cewa watakila mutuwa aka yi mata ba ta ko ɗago ba. Ta jima a wurin kanta na sarawa zuciyarta na tashi, ba ta samu sauƙin kirjinta ba sai da ta matsa can gefe ta yi amai, wata baiwar Allah na mata sannu har da siyo ruwa ta bata ta sha. Godiya ta yi sannan ta kama hanya ta koma da tunanin Ummi kada ta farka. Ai kuwa Amarya ta gani a waje sai jijjiga Ummi take tana kalle-kallen inda za ta hangota. Tana hangota ta hau fadan inda ta tafi ta bar yarinya na kuka. Karɓarta kawai ta yi ta bata hakuri, wuri suka samu suka zauna ta sanyata a hijabi ta hau bata mama. "Ai bai farka ba har yanzu, nima gajiya nayi da ganin tashin hankali na fito. Wani aka kawo kamar ma ƙafarsa ta ruɓe don kamar an daddatsata abin tausayi. Gyada kai Ramlat ta yi ta kauda kai. "Sai fa hakuri Ramlatu, zama da irin Aliyu sai hakuri. Kinga da yanzu kina can gidanki hankalinki kwance amma to, tunda mai afkuwa ta riga ta afku ba yanda aka iya sai hakuri." Murmushi mai ciwo Ramlat ta yi, tasan dama suna da labarin aurenta da Hilal da kuma abinda ta aikata, sun jima suna yadamata habaicin da ta san iyakar gaskiyarsu ce. Nadama da dana sani suka ƙara tararmata. "Ramlatu?" Ta ɗago kai jin murya kamar ta Dakta. Shi ɗin ne kuwa ga dalibai a bayansa, dama yakan zo asibitin sai dai ba koyaushe ba. Ta miƙe da mamakin yanda aka yi ya ganeta, durkusawa ta yi ta gaidashi ya amsa. "Me kike yi anan?" Za ta yi magana kuka ya ci ƙarfinta, Amarya ce ta fadamasa Aliyu ne ya yi hatsari yana ciki. "Ya Salam, bari na karasa. Ki yi hakuri, ki bar kukan." Ta gyada kai sannan ya wuce. Tsoron kada ya ji abinda ke damun Aliyu ya fadawa Abbanta mai fama da kansa ya sa ta miƙewa zumbur har Ummi na kokarin suɓucewa daga hannunta sakamakon gefen hijabinta da ta take ba ta ko lura ba. "Miƙota." Fadin Amarya. Ba musu ta miƙa ta ta bishi ciki, ta iskeshi tsaye wurin likitan da ta gane shi ya karɓi Aliyu. "Baba Dakta." Ta kira sunan, ya dubeta. "Ina zuwa Ramlatu." Ta gyada kai ta ja baya kadan. Jikinta rawa yake ga wani dumi da ya dauka. Ta haɗiyi miyau har ya kammala ya nufota. "Na ji duk abinda ke faruwa, Allah Ya ba shi lafiya." Ta amsa da wani matsanancin kunya, kanta ta sadda kasa hawaye na ɗiga jikin hijabin nata. "Abba, don Allah kar ka fadamasa, bai da lafiya. Kar ya ƙara tada hankalinsa, ni ce silar duk abinda ya faru gareni, don Allah a bar ni na yi kukana ni kadai. Baba Dakta ka rufamin asiri kar ka bari su sani. Abinda na shuka nake girba." A raunane ta ƙarashe, tausayinta ya kamashi. Ya ja numfashi. "Ba zan fadamasa ba Ramlatu kinji? Kema muna miki fatan komai ya zo karshe. Kema ba ki da lafiya ko?" Ya fadi ganin yanda take rawar sanyi, ta dubeshi. "Bansan me nake ji ba." Ya kama hannunta suka nufi wurin likitocin. "Dr Amina." Ya kira sunan daya ciki, ta mike cik da girmamawa ta ƙaraso, umarni ya bata akan ta dubamasa jikinta. Ba musu ta kama hannun Ramlatun cike da kulawa suka shiga wani dan daki. Duk abinda ya kamata a biya na Ramlatu, Baba Dakta da kansa ya biya. Hutu take buƙata sakamakon juna biyun dake jikinta. Baba Dakta ya jinjina lamarin, hatta Amarya ta yi mamaki ta kuma yi addu'ar Allah Ya raba lafiya. Cikin ikon Allah bacci wahalalle ya yi awon gaba da ita bayan an bata lafiyayyan abinci ta ci. Daki ne a wadace, ga Ac a kunne. Amarya itama abincin ta ci ta kwantar da Ummu gefen Ramlatun ganin ta yi bacci. A waya ta sanar da Malam ya kirata idan sun shigo don tana wurin Ramlatu wacce ake yiwa ƙarin ruwa. Tana so ta ce juna biyu ne da ita amma ta bar wa cikinta sai sun zo din. ***I just published "BABI NA ASHIRIN DA HUDU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/TmTSyIbktab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 24) "Ka ji tsoron Allah, da ace kai din mai hankali ne da dogon tsinkaye, wannan lamari da ya afku kadai zai sa ka gane son da Allah ke maka da bai ɗauki ranka a hanyar saɓonSa ba. Me kake nema a duniya haka Ali? Meyasa ka fita zakkah cikin iyalina? Idan wannan bai isheka ishara ba ban ga kuma abinda zai sa ka nutsu ka yi hankali da lamarin rayuwa ba." Malam na kaiwa nan ya ja jiki ya bar dakin gami da bin bayan ƴan uwansa, Abulle ba ta ce uffan ba don jikinta wannan karon itama ya yi sanyi, har kuka ta yi tana ƙaƙaba laifin ɓatancin Aliyu a kanta.    Aliyu ya lumshe idanunsa ya bude yana duban mutan ɗakin, Abulle ce sai Atine uwargidan Malam sai kuwa kannensa mata sannan ƙalilan daga samarin gidansu.  Kalaman Malam sun taɓa zuciyarsa, jikinsa ya yi sanyi. Bai taɓa dauka zai rayu ba, kusan ma duk abinda ya afku ba'a hayyacinsa yake ba. Ya ji dai sadda Zee ta ja hannunsa akan ya zo ya mayar da shi gida tunda ba zai iya jan mashin dinsa ba. Yana gani bibbiyu ya bi bayanta zuwa motarta. "Tana ina?" Ya yi maganar a fili. "Wa? Ramlatu? Tana can itama ta samu bacci, tana dauke da juna biyu amma abincin kirki ba ta iya maida hankali wurin ci ba?" Abulle ke wannan dogon jawabin da ba shi ya nema ba. Gabansa ya fadi, yanzun ne ya tuna da Ramlat. Da wace fuska za ta kalli abinda ya aikata? Me za ta ce? Kuma ciki ne da ita? A zuciyarsa yake wannan tattaunawar kafin hankalinsa ya ɗauku kan hirar da ta ji Amarya da Abulle nayi bayan ficewar kannensa. "Ai yarinyar ƴar mace ce, uban ma ba'a san inda yake ba wai haka naji su Alhaji na fada. Ba kiga uwa ba, an sha kwalliyar gwala-gwalai da alama dai akwai arziki. Maimakon a ga ta yiwa yarinyar fada ko ta nuna jin kunyar abinda ɗiyar ta aikata, sai kawai ta nemi ma yin faɗa akan dalilin ita yarinyar na yin tuƙin dare. Har da cewa meyasa ba ta kira Direba ya tuƙa ta ba. Sai da ta sa aka sallami diyarta ta biya komai da aka bukata ta fice da ita wai sauya asibiti zasu yi." Salati sosai Abulle ta shiga yi jin wannan bayani, Aliyu kam yana daga kwance kansa ke sarawa da wani irin sarawa wanda yasan dalilinsa. Kwanakin da ya yi bai sha sigari bane ke son tambayarsa. *** "Girma kake ƙarawa Zakina, ga matarka yanzu wani cikin ne gareta, don Allah don sonka da Annabi s.a.w ka daina wannan shaye-shayen. Ba amfanin da yake maka. Don Allah Zakina idan ma kana aikata zina itama ka daina kar fushin Allah Ya sa.." Riko hannun Abulle ya yi dake faman kuka. "Zan daina, zan daina My granny." "Yaushe za ka daina? Da ace Allah Ya dauki ranka yanzu, me za ka je ka ce? Ta wane hanya ka mutu?" Gabansa ya fadi, ya haɗiyi miyau maƙwat. Jikinsa ya kara yin sanyi kwatankwacin yanda nasihar iyayensa maza ya jefasa. Jinjina kai ya yi. "Zan daina." Ya fadi a can ƙasan maƙoshi karo na biyu. "Na fi so naji ka ce ka daina akan za ka daina. Za ka daina na nufin ba lallai ba, kuma akwai sauran lokaci, amma ka daina shi ne ka aiwatar kuma ba za ka ƙara ba." Ya lumshe idanu ya bude. Abulle na kara kallonsa hawayenta na zuba. Kyakkyawan yaro ne a baya, fari ƙal wanda a yanzu ya yi duhu kamar ba shi ba. Aliyu mai fararen haƙora kamar tangaran lokacin da ya fara zama saurayi, yanzun ya rine ya koma kalar ruwan goro. Hura mata iskar bakinsa ya yi, duk da cewa ya yi brush hakan bai sa iskar wari ba, kadan kenan daga illar shan sigari. Abulle ta kauda kai ta share hawayen. "Ina Babyna? Naji kun ce ciki gareta, Granny Banda jari yanzu, bana so kuma na kara baƙanta ran Baby irin wanda na mata a farko." Harararsa ta yi. "Me  kake son cewa?" Murmushi ya yi, yasan ta dauka jari zai nema amma madadin hakan ce ta faru. "Bashin banki zan ci, ko kuma na siyar da gidannan na siya wanda bai kai shi girma ba, sauran kudin na ƙara a kasuwa muga abinda Allah zai yi." Ta yi shiru. "Ma dai yi maganar idan ka fito kawai." Bai ja ba shima ya bar zancen kafin ya mike da zummar zuwa wurin matarsa. *** Bisa jagorancin Abulle suka karasa dakin Ramlat, tana zaune saman darduma ta idar da sallar Magriba yayinda Amarya ke gefe tana yiwa Ummi wasa. Ya sa hannu ya karbi Ummi ya rungume. Kallo ɗaya ta yiwa Aliyu ta sunkuyar da kai, kallon ba ta son yi balle ta tuna silar komai. A yau ta gane amsar tambayarta ta baya. A lokacin da aka daura aurenta da Aliyu ita ke kuka iyaye da ƴan uwanta na dariya. Ashe kukan ma a sannan ta soma, shi ne farko kuma ba shi ne karshe ba. Ba ta san hawaye take ba sai da ta ji tafin hannunsa saman fuskarta ta yi saurin rikewa gami da ɗago kai. Sai lokacin ta kula su biyu ne a dakin. Kallon na tsaneka ta ke jefamishi. Shi kuwa kallonta yake idanunsa cike da nadama da dana sani. "Kar ka kara gigin taɓani, Ramlat b mazinaciya bace wallahi. Ka je can ka.." Ya yi saurin toshe bakinta da hannu, duk kokarinta na ganin ta cire hannunsa ta kasa,  kawai sai ta fashe da kuka ranta na zafi. "Baby kiyi hakuri. Baby wallahi wallahi ban taɓa kusantar kowace mace idan ba matar aurena ba. Baby yaudarata suka yi, kwaya mai ƙarfi irin wanda ban taɓa sha ba suka ba ni na sha. Ban kuma san inda kaina yake ba har muka shiga mota mai afkuwa ta afku." A sannan ne ta fincike hannunsa ta watsa mishi banzan kallo, gaba daya ya ji wani nadama ta mamayeshi. Idan ance akwai ranar da zai ji kunyar mace zai rantse ƙarya ne. "Wannan ba damuwata ba ce. Damuwata haihuwar da nake yi da kai. Aliyu ba don ina tsoron halakar da zan faɗa ba wallahi ina maka rantsuwa da Allah sai na zubda abinda ke cikina. Sai dai na sani laifi ne zan kara akan kuskuren da nayi tun farko na auren mutum irinka wanda bai san darajar kowa ba sai kansa! Kai har kaima ba ka san darajarka ba! Ba ka san darajar da Allah Ya yi maka ba. Ba ka taɓa godemaSa ba ta hanyar aikata nagari wanda kowa zai gani ya sakamaka albarka. Mun haihu da kai kuma ga wani rabon Aliyu, idan a baya ba ka da wani da ka ke jin kunyarsa ai a yanzu ko don darajar yaranka wani abin za ka kiyaye. Wane ɗa ne zai farin cikin kasancewarsa ɗanka? Ummi idan ta isa aure kana tunanin manemanta ba zasu gano tarihin ubanta ba su fasa? Shikenan kai babu wani abu naka nagari, shikenan duk inda za'a je a tambayi tarihinka kai mutumin banza ne? Aliyu meyasa ka rufemin kai waye, meyasa ka ɓoyemin munanan halinka ka nunan kai nagari ne? Kaicon abinda ka sani na aikata, kaicona da na zaɓi na saɓawa iyayena akan mutum irinka. Ba duniya ba, daidai da ni kaina tsanar kaina nake idan na tuna irin tijara da fito na fiton da nayi da ƴan uwana akanka. Yanzu gashinan ina girbar abinda na shuka. Wallahi ban kyautawa kaina ba." Ta cure wuri guda gami da saka kanta cikin cinyoyinta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, idanunsa suka kaɗa suka yi ja, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi, a gefe guda kalaman Ramlatun suna mishi zagaye cikin ƙwaƙwalwa da zuciyarsa. Ummi kuka take yi ganin yanda uwarta ke kuka, Ramlat ta kasa ɗago kai balle ta karɓe ta. Cak ya mike ya fita kafin ya dawo ya yi zaman dirshan a gabanta, har sannan kansa ciwo yake kamar ya kife a wurin. "Kiyi hakuri Baby, kiyi hakuri." Ɗago kai ta yi tana kallonsa da ɗan murmushi. Majina ta ja. "Um um Aliyu, ai kamata ya yi muyi yanda muka saba, ka kamani ka jibga, ka kamani ka zagi iyayen da suka kawoni duniya. Iyayen da na bijirewa umarninsu a kanka, na guji zaɓinsu duk domin na faranta maka. Idan yau ka zagesu waye ya bada ƙofar? Gani kake ni na baka ƙofar ka yi musu duk abinda ka so, ka fadi dukkan wasu bakaken kalamai a kansu. Toh Aliyu naji ni ce, amma na dauka idan so da kauna na gaskiya ne, karen gidanmu ma sai ka girmamashi balle kuma wadanda suka yi silar zuwana duniya? Na gaji, Aliyu na gaji. Aliyu idan kana sona dagaske, kana kaunar Allah da ManzonKa s..a.w, kana kuma kaunar iyayenka ka sauwakemin na je na yiwa iyayena biyayya. Ka sakeni na je nayi auren da martaba da darajata za ta..." "Ramlatu!" Gaba daya suka kai duba ga bakin ƙofar, Baba Dakta ne a bayansa Amrah da Umma. Ya ƙaraso ciki da sallama suka amsa. Aliyu ya mike ya gaidashi, Amrah sakin baki ta yi tana duban hawayen da Aliyu ke fitarwa. Baba Dakta ya amsa gami da yi mishi sannu da jiki. Daga nan ya gaida Umman Amrah cikin girmamawa. Itama ta amsa ta mishi sannu. Bayan sun zauna ya dubi Ramlat. "Kina cikin hayyacinki kuwa? Mijinki kike cewa ya sakeki? Kinsan zunubin da kika kwasa sanadin wannan furucin? Kar na ƙara ji, duk tsanani yana tare da sauki musamman idan bawa ya miƙa lamarinsa ga Allah. Kar fa ki manta kina dauke da juna biyu, wannan damuwar sai kin daina sakawa ranki. Kinji ko?" Ta gyada kai tana share hawaye wasu na zubowa. Amrah mai saurin kuka har ta soma tayata. Baba Dakta ya mike suka fita tare da Aliyu. A waje ya yi mishi dukkan nasiha ya kuma kara da cewar ya riƙe amanar ƴarsu da suka damƙamishi. Aliyu ya yi godiya don ko ba komai ya taimaka masa daga daurin dabaibayin da Ramlatu ta yi mishi, yasan ba don shi ba haka zasu yi ta ja in ja akan ita sai ya saketa. ***   Ranar da aka sallami Aliyu ya dawo gidan, tuni dama Ramlat ta rigashi dawowa. Sosai kuma likita ya gargadeshi akan shaye-shaye da illolinta.   Kwanakin da suka biyo baya suna faruwa ne sama-sama ga mutanen gidan.  Duk kokarinsa na shawo ka Ramlat abin ya ci tura, ya kasance ba ya fita yawon dare, idan ya shigo gida da yamma shikenan sai dai ko masallaci da yanzun ya soma zuwa sallah. A baya zuwan bai dameshi ba, ya gwammace ya yi sallarsa a daki. Ta yi faɗan har ta gaji ta bari. Wataranar Asabar ta tashi tana son ziyartar yayyunta, gidan Munir ne ba ta jin za ta iya takawa  tunda ya nuna ba zai iya yafemata ba. Ta tabbatar idan ta je duk abinda ya yi mata ita ta kai kanta. Tun safe ta lura ba shi da niyyar fita, wuraren karfe goma ta cimmasa a daki. Kwance yake yana juyi, kwanakinnan tana lura da shi a fisge. Yana cikin damuwa, girki ma idan ta yi bai fiye ci ba. Ga yawan shan Panadol da ya shiga yi kusan kullum ciwon kai. Kallonta yake tun shigowarta dakin sai kuma ya ja guntun tsaki ya kauda kai. "Ina kwana." Bai amsa ba, bai kuma kalleta ba. Ta haɗiye ta kara gaidashi. "Ba zan amsa ba! Ki rabu da ni idan ma mutuwar ce na mutu Baby! Ya ku ke so mutum ya yi? Me kuke so ya zama?! Ance Aliyu dan iska ne kuma mashayi! Yanzun kuma da Allah Ya taimaka ya soma kokarin gyara rayuwarsa, nan ma bai burge ba! Kin juyamin baya ba kya shigowa inda nake sai dai ki yi girki ki dankwafarmin ki shige daki saboda mayunwaci ne ni! Ke haka Allah Ya ce ki yimin? Haka Ya ce ki yiwa Mijinki?!" Ya na kaiwa nan ya mike zaune gami da jan tsaki kafin ya riƙe kansa da bai bar sarawa ba.   Ta yi mishi ƙurr da idanu tana kallonsa kafin ta nisa. "Ka saka a ranka ba don mu kawai za ka gyara ba, saboda karan kanka da kuma Ubangijinka. Ba mu da wuta ba mu da aljanna. Nayi kuskure, ka yi hakuri." Ganin ta sauko yasa shima ya sauko ya lallaɓa don dama neman shirin yake, ya gaji da zaman gabar. Sai da ya biya bukatarsa kafin ya bata umarnin ta shirya da kansa ma zai sauketa gidan Zulaihat din. Wannan ya kara tabbatarmata dagaske Aliyun ya soma kimtsuwa. Ta shirya cikin wata atamfarta da ta ware cikin sabbin da za ta dinga fita unguwa, ta shirya Ummi cikin riga da wando ƴan kanti ɗaya daga cikin kayan da Abba ya siyamata. Ta yiwa gashinta ado da ribbons kala-kala ya yi mata kyau. Duk wanda ya gansu yasan suna cikin farin ciki. Har kofar gidan Zulaihat ya kai ta, suka yi da shi za ta je gidan Rafee'ah a can zai isketa ya ɗauketa. Hakan ya sa ya bata ɗari uku ya riƙe dari biyunsa, a cewarsa ita kenan a aljihun, dari biyar. *** Kallonta Zulaihat take har Ramlat ta gaji ta yi magana. "Wai Maman Khalifa lafiya?" "Kin rame ne, kuma kamar dai kina da ciki." Ta kauda kai a kunyace ta dai daure ta amsa da eh. "Ciki dai Ramlat? Yanzu ba ki ji shawararmu kin yi family planning ba?" Zulaihat ta furta don takaici bai sa ta iya ja bakin ta yi shiru ba. Ramlat ta kasa magana ta yi shiru kawai sai hawaye. "Tab, Allah Ya kyauta to. Ya raba lafiya." Nan ma kasa maganar ta yi. Ganin kamar Ramlat din batun cikin na tada hankalinta yasa Zulaihat ta barshi suka shiga hirar bikin da ya taso na su Naja'atu da su Maryam jikokin Hajja. Su biyar cif za'a aurar nan da wata biyu. "Ki dai samu ya yi maki koda anko ne koda bai bada ma gudunmuwa ba, ke sai ki duba idan kina da hali ki yi. Sannan don Allah ki dinga cin abinci sosai ko za ki ɗan maido jikinki kar a yi ta yawo da ke a cikin taro." Ta gyada kai. Sai wuraren karfe hudu ta nufi gidan Rafee'ah. Ita kanta ta yi mamakin ganin Ramlat da ciki sai dai banda Allah Ya raba lafiya ba abinda ta ce don ba ta son shiga sabgarta da Aliyu. Aliyu bai zo daukarta ba sai wuraren takwas na dare. Sun gaisa da Rafee'ah da mijinta sannan suka bar gidan. *** BAYAN WATA DAYA.. Tsumma ne a ƙasan ƙafarta tana goge inda mai ruwa ya ɓatamata a falon tana tsaki. Sati biyu kenan da dawowarsu sabuwar unguwa kuma sabon gidan da ko ruwan famfo babu sai dai a siya. Aliyu ya fadamata ƙudurinsa na siyar da gidan don ya samu na jari, ba tare da ta san inda zasu koma ba ta amince. A cewar ta da ta zo ta ga yanda ginin yake da ba ta amince ba sannan ga dukkan alamu idan damina ta zo dakunan zasu yi warin ruma da kuma alamun danshi a jikin bangon. Ciki da falo ne a gidan sai fyallen daki guda daya, sai kicin hade da store. Ba daki daya a tsakar gida. Babban damuwarta bai wuce ganewar da ta yi yanzun Aliyu tuban muzuru ya yi, ta kamashi ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba yana shan sigari a ɓoye. Ta yi kukan ta yi faɗan amma a banza, wannan ta sa ta zubamasa ido ta maida hankali ga kaiwa Allah kukanta. Shigowarsa falon ne ya bata damar dauke tsummar ta amsa sallamarsa a ciki. "Baby wani wari kamar na gardi nake ji." A kufule ta amsa. "Mai ruwan da ka turo ne." Ya ja tsaki. "Kai rashin ruwan nan ya soma damuna. Ga cacar kashe kudi. Mtsw." A ranta ta ce kai ka sani, ta shige kicin abinta. *** "Biki ko na dangina fa bana anko ke kin sani. Yanzu ma da muke ta kai, wa ke ta kaya?" Wannan na daga cikin dalilin da ba ta son tambayarsa wata bukata. Kusan ma yana daga abinda Abbansu ya gargadesu, tambayar miji wata buƙata kar ya kawo maka raini. Wani abin ne ba za ka iya shiru ba. "Aliyu ban taɓa neman ka yimin wata sutura ba sai yanzun, abu ne na fita kunya. Cikin dangi da yan uwana zan shiga. Don Allah ka taimaka dai ka yimin." Ya ɗan yi shiru yana wani cin magani, can kuma ya ce. "Shikenan kiyi addu'a a samu kudi. Sannan batun sutura har yau ai kina morar suturorin da na miki, ko ba komai na kashe sama da miliyan daya a lefenki." "Ba sai ka gorantamin ba." Ta fadi ranta a ɓace. Bai ce uffan ba don yanzun bai fiye bari su yi dogon sa'insa ba, a cewarsa juna biyu ne da ita. Hakanan yana kokarin ganin ya kiyaye kai hannu jikinta da sunan bugu. Ta shige daki a fusace ta kyaleshi anan tare da ƴarsa. *** Allah Ya taimaketa dai ta samu ya kawomata atamfar ankon amma ba kudin ɗinki. Hakanan ta yi godiya ta ƙuƙuta ta bada ɗinkin, zuwa yanzu takan leƙa makwafta saboda halin rayuwa da son kiyaye shari'ah. Ta ciko ba laifi sai dai ga duk wanda ya ganta da ciki sai ya tanka. Har ta gaji ta fice daga cikin masu auren ta koma bangaren Amaren cikin ƴan mata ta zauna. Kallon kowaccensu take cike da burgewa. Amrah ta saje a cikinsu ta ci ado har ta gaji sai hira da shewa ake. Ta tuno da nata ƴanmatancin, kauda kai ta yi gami da mirza idanunta gudun saukar ruwan hawayen da ya tahomata. Ita da ƴan uwanta amma a karan kanta kunyar kanta take ji na abubuwan da suka afku wanda har abada tarihinta ba zai goge a zuƙatansu ba. Ko ba komai ta bar baya da ƙura. Amrah na hankalce da ita hakan yasa ta miƙewa ta karɓi Ummi a hannunta ta zauna ta shiga jan ta da hira har ta saki jiki. *** Aka kammala biki lafiya aka kai yan matan dakunansu, ba ta samu zuwa kai su ba don ta gaji da habaice-habaicen da wasu a dangi ke mata game da aurenta. Zamanta ta yi a gida abinta. Kamar koyaushe bayan kammala girkin dare ta yiwa ɗiyarta wanka ta shafe jikinta da hoda yanda za ta ji sauƙin zafin da ake a gari, ga ba wuta a unguwa don sai a fi sati biyu ma ko wata babu kyallinta kamar yanda ta soma shaidawa kuma ta ji daga bakin makwafciyarta. Shigowar Aliyu gidan ya bata mamaki, koda dai yanzun bai kaiwa dare sosai a waje, amma ta yi mamakin ganinsa wuraren bakwai da mintuna. Zama ya yi gefen gadonta yana dan yamutse-yamutsen fuska. "Lafiya?" Ta nemi ba'asi. Dan guntun tsaki ya ja yana mai ɗan sosa kirjinsa. "Kamar dai banda lafiyar Baby, zuciyata sai ta dinga tashi ga gudawa da nake tun safe haka nake zaryar banɗaki a kasuwa." "Allah Ya sauwake, Ya baka lafiya. Ya kamata ko chemist ka leka." Ya jinjina kai yana mai sa hannu ya dauki Ummi dake faman mikomasa hannu tana ɓangala dariya. *** ABU KAMARI just published "BABI NA ASHIRIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ZRLvPBGxyab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Rahmanir Raheem. 25) Abu kamar wasa, ƙaramar magana ta zama babba. Cutar amai da gudawa ta yiwa Aliyu kamun kazar kurkuku. Chemist ya je aka haɗa mishi magunguna. Koyaushe yana gida, hankalin Ramlat ya tashi. Abu ya wuce kwanaki ya koma sati, Aliyu ya bi ya ƙara ramewa ya yi duhu. Abin ya zamewa Ramlat goma da ashirin, ga ciki ga raino kuma ga kula da miji. Ganin abin ya ci tura ta tursasa mishi da taimakon Baban Nusaiba makwafcinsu, aka kaishi asibiti da motar Baban Nusaibar. Ta bar Ummi a makwafta. "Madam, ba ka ji bane?" Ta ɗan dawo hayyacinta ta kara duban inyamurin Likitan. "Ka dauka ka je ka biya a yi." Gyada kai kawai ta yi ta mike ta fito zuciyarta cike da tunani ga faduwar gaba. Tsoronta kar ta je Aliyu wani cutar ya shafo mai rikitarwa. Likita ya tabbatar gudawarsa bai da alaƙa da abinda yake tunani ke damun Aliyun, wannan ta sa har scanning sai da ya ce a yi. "Ya ake ciki Maman Ummi?" Fadin Baban Nusaiba. Ta dubeshi idanunta duk sun faɗa sun yi ciki, ita kanta ta rame sai ƙaton ciki wanda  sai ka rantse ya kai watanni takwas. "Ba komai, bari na karasa na biya." Ya gyada kai gami da amsawa da toh. Allah Ya taimaka ta taho da Atmcard dinta, ganin kudin hannunta ba zai isa bane ya sa ta fita ta zaro kuɗin. Komai ta biya aka yiwa Aliyu duk abinda ya dace. A nan ne Baban Nusaiba ya yi mata sallama kan zai koma. Godiya sosai ta yi mishi har ya fita sannan ta maido dubanta ga Aliyu wanda ya samu bacci.   Hawaye ta ji sun zubomata sakamakon tunanin da ya yi mata tsinke. Yanzu idan ya mutu me zai koma ya cewa UbangijinSa da Ya ba shi aron rai da kuma lafiya a rayuwa ya kasa tsayuwa ya kyautata rayuwarsa kuma ya godewa wannan ni'ima? Ba wannan ba ma, wace cuta ce da Aliyu? Idan wannan tambayar ta faɗomata a rai, numfashinta har tsayuwa yake cak tsabar firgici.   Tana wannan tunanin ta soma hamma kafin itama ta soma gyangyaɗi saman kujera don ɗakin ba su kaɗai bane, akwai majinyata har uku a bayansu. Ƙarar wayarta ce ta katsemata baccin, ta yi firgigit ta ɗauka. Amrah ce. Miƙewa ta yi ta fita daga waje. "Na ji shiru ba ki shigo makaranta ba, kuma nayi niyyar zuwa gidannaki ban san kwatance ba." Ta haɗiyi miyau mai zafi. "Muna asibiti, an kwantar da Baban Ummi bai da lafiya." "Ya Rabb, meke damunsa?" Ta gano rudewar da Amrah ta yi, ta kuma fahimci dalilin. Hakan ya ƙaramata rashin nutsuwa da tsoro. "Wallahi ban dai sani ba Amrah, an mishi test." "Toh Allah Ya sauwaƙe, Ya ba shi lafiya. Zan shigo ko zuwa gobe ne tunda yanzu kam na kama hanyar gida akwai tazara." Nan suka yi sallama ta mata godiya. Ganin dacewar ta kira ta sanar a gidan su Aliyu yasa ta dannawa Malam kira. Bayan sun gaisa ta fadamishi Aliyu ba lafiya suna Akth. Nan da nan ya ce gashinan zuwa suka yi sallama. ***   Bayan awanni biyu, tana zaune gefen Aliyu wanda ke shan kunun gyaɗa da Abulle ta kawomishi sai dai hankalinta ba ya tare da su, yana ga Malam da ƙanin Aliyu, Mudan. Suna wurin likita kai sakamakon Aliyun. Kirjinta dukan tara-tara yake yi. Fargaba kan ba'a magana. "Ya kamata ki je gida ki huta." Ta kalli Aliyu mai wannan batun cikin karfin hali. Girgiza kai ta yi. "Um um." "Nima abinda zan ce kenan, ki tafi gida tunda shi Mudan ne zai kwana, gobe kya shigo. Ai da gajiya, ke dai sannu Allah Ya saukeki lafiya." Fadin Abulle cike da kulawa, kaunar Ramlatu sosai ke ratsata, tana lura da yanda take ba Zakinnata kulawa. Shigowar Malam ne ya sanya hankalinsu komawa garesu, fuskar Malam ba za ka iya tantance yanayinta ba. "Kun dawo? Me likitan ya ce?" Abulle ta nemi sani. Malam ya samu wuri ya zauna. "Babu komai, sai dai likita ya tabbatar ciwon zuciya na barazanar kama yaron, ya kuma ce lallai ya bar shan duk abinda zai gusar da hankalinsa ko ya shaƙi iska marar dadi, idan kuwa ya ƙi komai ma zai iya faruwa. Shi gudawar sanadin me ma..?" Ya maida akalar tambayar ga Mudan don shi ya mance ma tsabar damuwa. Mudan ya dora. "Bacterial infection ne wanda shan sigari ya haddasa masa, shi ya kawomasa gudawa.  Amma ya ce in Sha Allah wannan mai sauki ne. Ya dai ce dole ya kula ya bar shaye-shaye saboda cutar dake masa barazana." Salati kawai Abulle ke yi ta shiga yiwa Aliyu faɗan ya taimaka mata ya bari, tun tana yi har ta shiga kuka. Aliyu idanunsa suka kaɗa, ya kasa kallon kowa musamman ganin jama'ar ɗakin sun zubamusu idanu gami da baza kunne. Cak ta mike tsaye. "Zan wuce gida." Abinda ta ce kenan. Suka dubeta. "Toh Ramlatu, ki je da Mudan ya taho da kayan shi Alin. Ba sai kin yo girki ba, daga can gida sai a kawo. Allah Ya baki lafiya kema. Sai hakuri kin ji?" Malam ke wannan jawabin cikin nutsuwa. Ta gyada kai, har lokacin danne hawayenta take yi, ba ta ko kara kallon Aliyun ba suka fice tare da Mudan. A hanya ma ba ta ce uffan ba duk kuwa da irin korafin da Mudan ke yi akan Aliyun da takaicin abin, suna isa ta haɗamasa abinda za'a buƙata, tare suka fito. Ita ta nufi makwafta ta dauko Ummi shi kuma ya miƙa titi. Sai da ta zauna a falon tana duban Ummi dake wasanta, ta kara kai duba ga cikinta, kafin wasu zafafan hawaye su soma wanke mata fuska. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ita ce kalmar da ta shiga ambata tana kara nanata wa. Daga wannan sai wannan, komai na zuwarmata a daki-daki. Rayuwa kenan, kalar rayuwar da ta ke hangowa zasu yi da Aliyu a baya, ba irinta ta samu ba. Ta shanye dukkanin komai ta hakura, yanzu kuma ga wata sabuwa. Kukan ta shiga yi sosai, wayarta ta dauki ƙara ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin ɗauka ba tare da ta duba ko waye ba. "Assalamu alaikum." Ta fadi cikin muryar kuka. "Waalaikumussalam. Ramlatu? Meke faruwa ne? Kukan me kike?" Ta yi firgigit ta dawo nutsuwa da hayyacinta, ABBA ne. Da sauri ta saita kanta ta shiga ƴar dariyar yaƙe. "Lah Abba ina wuni? Ba kuka nake ba, mura ce ta ke neman yimin kamu." Shiru ya dan biyo baya can kuma Abba ya yi magana "Kin tabbata Ramlatu?" Ta gyada kai tana jin sabon kuka na tahomata. "Eh Abba." "Shikenan. Ya karatu? Ina fatan dai komai lafiya? Kar ki ga ina ta tambaya, mafarkinki nayi cikin wani irin yanayi shiyasa na damu." So da kaunar Abbannata ya kara mamayeta. Ta shiga murmushi har cikin zuciyarta. "Abba lafiyata kalau. Abba na gode na gode. Abba ka yafemin don Allah. Na yi maku laifuka masu tarin yawa, na so kaina.." "Zancennan ba ya wucewa ne Ramlatu? Ban hanaki tayarwa ba? Sau nawa za'a ce maki ya wuce?" "To na daina. Ya jikinka?" Ya yi murmushi mai sauti. "Jiki da sauki Ramlatu, ba abinda ke damuna yanzun." Ta tsinci zuciyarta da yin sanyi, dadi ya rufeta. "Allah Ya karamaka lafiya Abbana." Ya amsa da amin, ya tambayi Ummi. Nan ta hadashi da ita tana mishi jagwalgwalon hausarta ya yi ta dariya. A karshe Ramlat ta maida wayar kunne. "Wai ita ƴar nan ba za'a bani aronta ba?" Ta kasa gaskata kunnuwanta, ba ta taɓa zaton Abban zai nemi Ummin a gidansa ba. Da wani irin farin ciki da ya mantar da ita bakin cikin Aliyu ta amsa. "Abba ko yau ka aiko a daukarmaka ita." Dariya Abba ya yi. "Yanzu yamma ta yi Ramlatu, gobe zan turo Autar Hajiya ta daukarmin ita amma ki nemi iznin mahaifinta." Sai sannan ta tuna Aliyu, ta ji kamar ta  fadawa Abban rashin lafiyarsa amma ta ɓoye gudun kar Abban ya shiga damuwa. Suka yi sallama, shigowar saƙo ya sa ta dauka. Aliyu ne. Ta bude ta shiga karantawa. _*"Na cuci kaina Baby, na cutar da mu. Kaicon rayuwar da na zaɓarwa kaina. Ki yi hakuri ki yafemin. Ki tayani addu'a, da yardar Allah zan daina. Na daina din ma Baby. Abin ne ya ke zamemin kamar karamin hauka idan ban yi. Ciwon kai da damuwa su tararmin."*_ Ta ɗan yamutse fuska kawai ta share batun. Dakyar ta iya miƙewa ta shiga wanka ƙofa a bude saboda Ummi. Babu komai a kicin din sai wani guntun Doya da Aliyu ya siyo. Kusan kwana uku kenan da ƙarewar abincinsu sai maneji. Dafa doyar ta yi, Allah Ya taimaka tana da sauran yaji ta ci da shi.  A daren ta yiwa Aliyu text na zuwan Ummi gidansu, bai hana ba sai fatan alheri. ***   Washegari kuwa tun safe Mudan ya kirata akan kar ta zo za'a basu sallama zuwa anjima, hakan na yi fiyemata don bata kaunar shiga asibitin a yi mata kallon matar mashayi. Abin da kunya. Wuraren karfe sha daya na safe sai ga Amrah, ba jimawa sai ga A'isha ta zo ɗaukar Ummi. A tsaitsaye ko zama ba ta yi ba har Ramlat ta mike ta shiga dakin dauko jakar Ummi da ta haɗa kayanta.   "Ke kam Auta ko zama fa ba ki yi ba." Fadin Amrah tana kallon A'isha dake tsaye tana dan yiwa Ummin wasa. Ko ba komai yarinyar ta shiga ransu sosai. Taɓe baki ta yi. "Wallahi Anti Amrah sauri nake, kinsan yau za'a soma bikin Yaya Hilal. Zamu je tare da Anti Bilkisu, tana can tana jirana." Daidai sadda Ramlat ta fito, karaf maganar ya shiga kunnenta. Ji ta yi gabanta ya fadi, Hilal zai yi aure? Ko ya ya dama tasan sai ta ji wani iri. Hilal mutumin da ya yi mata so da kaunar da wani ɗa namiji bai mata makamancinsa ba. Ya mata so a sadda ya kamata ace ya fi kowa gudunta adalilin wulaƙanci da cin mutuncin da take mishi, sai dai madadin hakan cewa yake "Bana miki son da zan iya barinsa a lokaci guda." Ta sauke ajiyar zuciya gami da share fuskarta da gyarawa gudun kada su gane. Karasowa ta yi sadda A'isha ke koɗa matar Hilal. "Ba ki ganta ba wallahi kyakkyawa da ita ga kirki. Har waya suna yi da Hajiya." Jakar ta miƙamata. "Gashinan." A'isha ta karɓa tana kallonta kadan don so take ta ƙular da ita. Amrah da bata gane ba ta yi murmushi. "Aikuwa na yi mishi murna wallahi. Allah Ya basu zaman lafiya." "Amin. Na wuce." Suka yi mata fatan alheri ta fita. Shiru ya biyo baya kafin Amrah ta dubeta. "Wai meke samun Aliyun?" Ta haɗiyi miyau mai daci, nan ta kwashe dukkan abinda ke faruwa ta fadamata.  Salati kawai Amrah ke yi, hakan ya kara raunana zuciyar Ramlat ta fashe da kuka. "Kinga sakamakon abinda na aikata ko? Duk abinda kika ce ya faru a kaina. Na wulakanta kaina kafin kowa ya wulakantani. Na fita zakka a cikin ƴan uwana. Amrah rayuwata ta ƙare, na kashe kaina da hannuna. Ban taɓa riskar farin ciki mai daurewa a aurena da Aliyu ba banda bakin ciki da takaici. Me zan ce ga yarana a sadda suka dubeni suka tuhumeni da zaɓamusu mahaifi irin .." Hannun Amrah ta ji a saman bakinta, ta shiga girgiza mata kai tana fidda hawaye. "Ya isa, ya isa don Allah Ramlat. Ki gaggauta istigfari, kin fita hayyacinki har kin soma kalaman saɓawa mahaliccinki. Kar ki manta, Allah Ya riga Ya rubuta zuwan yaranki duniya ta jikin Aliyu. Ki yi hakuri ki yi ta istigfari da nemawa mijinki shiriya. Addu'ar mace ga mijinta ba ya faɗuwa. Komai ta roƙamasa, Allah zai amsa." Gyada kai Ramlat ta shiga yi tana sauke numfashi. Haka suka wuni da Amrah, tana cike da jin kunya ganin Amrar ce ta fita ta yi musu cefane da kudinta ta dawo suka girka dafadukan taliya suka ci. "Kina da labarin yajin aikin da aka soma kuwa?" Fadin Amrah, ta zaro ido. "A'a, ki ce sun tafi?" Taɓe baki Amrah ta yi. "Asuu ai basu yi ba, ina ta so na fadamaki na manta. Zaman gidan ya ganmu. Karatu a ƙasarnan ya zama abinda ya zama." Ramlat ta numfasa. "Allah Ya kyauta." Suka amsa da amin. Amrah na nan Aliyu ya dawo, gaisawa kawai suka yi sannan ta wuce. ***   BAYAN SATI DAYA. Jikin Aliyu sosai ya yi sauki don har ya ci gaba da fita kasuwa. Sabon yaron shagonsa Sama'ila, ya je ya tarar ya tafiyar da komai duk kuwa da irin ɓarnar da ya mishi na karya wasu cikin farashin kayayyakinsa. Shi a nasa tunanin ya yi dabarar da kayan zasu siyu.   Kayan abinci ya soma kaiwa gidansa, duk abinda yasan za'a buƙata. Hakan da ya yi ya yiwa Ramlat dadi, ba ta fita ko'ina iyakacinta makwaftansu sai fita awo asibiti.  Zaman gida sosai ya kamata musamman sanadin yajin aikin da ake wanda ba ta ga ranar kammalawa ba. ***   Ummi ta zama ƴar Hajiya, koyaushe idan Abba na gida suna tare. Wannan ne silar da yasa Munir dauke ƙafa daga gidan. Ba ya kaunar ganin yarinyar tare da su.  Akwai sadda ya gaji ya yi magana "Yanzu Hajiya ba za ku maida yarinyar nan ba?" Ta daure fuska. "Ai dama ina kula da kai, na lura da take-takenka Muniru. Ka fita idona, ko ba komai ai hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yarr. Duk lalacewar Ramlatu kanwarka.." "Shikenan, shikenan Hajiya. Allah Ya huci zuciyarki. Da yardar Allah ba zan ƙara magana a kai ba." Ta yi kwafa. "Ka ma ƙara mana Muniru. Ka ma ƙara tunda kai zuciyarka ba ta san afuwa da mantuwa ba. Mu da muka haifeta mun yi hakuri sai kai ko? To ka ci gaba." Shi dai ya yi shiru ya lallaɓa ya bar gidan. ***   "Yaron nan da yake auren Ramlatu fa naji kamar jama'a na raɗe-raɗin yana da cutar ƙanjamau, shiyasa nace gwara na faɗa maka." Abba ya ji gabansa ya fadi, ya tsurawa manajansa Audu ido. "Wa ya fadamaka wannan zancen? A ina ka ji?" Audu ya gyara zama don dama maganar na cinsa, kwana hudu kenan da ya ji daga bakin ƙaninsa Lamin wanda yake abokin kasuwancin Aliyun a kasuwa. "Laminu ƙanina, ai kasan kasuwarsu daya. Kwanakin baya a asibiti ma ya kwanta, yanzu haka dai ya koma kasuwa kowa na takatsantsan da shi." "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ka tabbatar da wannan zancen Audu?" Audu ya gyada kai cike da karfin gwuiwa. "Kwarai kuwa Alhaji, wannan magana haka take." Abba ya mike tsaye da sauri. "Alhaji." Abba ya daga mishi hannunsa wanda har rawa yake. "Tafiya zan yi Audu, ka kula da komai." Cike da ladabi Audu ya gyada kai da kara russunawa har Abban ya fita. Wani a shagon da suke kira Garzali ya ƙaraso wurinsa. "Amma ba ka kyauta ba Maigida, sai da nace kar ka fadawa Alhaji wannan zancen amman ka ƙi." Audu ya harareshi. "Kai waye da za ka fadamin abinda ya dace da wanda bai dace ba Garzali? Kar ka manta a ƙasana kake, idan na ga dama sai na yi maka sanadin barin shagonnan." Garzali ya daga hannu alamun saranda ya wuce ya na mai ba shi hakuri. *** Shi kuwa Abba yana fita, Idi na ganinsa ya taso da sauri, wasu a gefe na gaida Abba bai ma tsaya amsawa ba. "Muje." Ya fadi hana kama hannun ƙofar motar, da sauri Idi ya bude da muƙulli ya budemasa ya shiga. Shima ya shiga ya ja suka wuce.   Idi na lura da yanda Abban ya yi shiru yana fidda numfashi, ya kasa hakuri ya cez "Ranka ya dade ko asibiti zamu wuce?" Abba ya yi murmushin takaici ya girgiza kai yana ci gaba da jin wani zafi a kirjinsa. "Aa idi, kai ni cikin iyalina. Ba komai." Idi ya amsa ba don ya so ba suka nufi gidan. Abba kuwa tunanin da ya soma zuwa kansa shi ne Ramlatu ta kamu da cutar ƙanjamau. 'Shikenan ya cuci ɗiyata,ya kashemin rayuwarta. Innalillahi wa inna ilaihir raajiun.' Abba ke nanata wa a ransa. Ya zama dole ya je ya dauko ɗiyarsa. ***   "Please Zaki ka bar bibiyata. Haba! Wai dole ne na kulaka?" Aliyu baki sake yake duban G Baba wanda ke kokarin shigewa wata haɗaɗɗiyar Jeep sabuwa dal. Koda dai dama, mahaifinsa mai kudi ne, yanzun kuma ya samu aiki ya bar yawon shashanci aure ma zai yi. "G Baba, ni kake cewa na daina binka? Don ubanka ka manta waye ni a wurinka ko?" Aliyu ya ƙarashe da ƴar zolaya, so yake ya samu ko rance ne yana son yin odar abayoyin mata daga Dubai. G Baba ya kalleshi kallon raini kafin ya ja guntun tsaki. "And so? Wai don Allah ka yi zaton ban san cutar da ke damunka bane? Kana yawo da HIV shi ne kake so na ci gaba da yawo da kai sunana ya ɓaci a hanani auren Teemah? Haba Zaki, kai kanka kana iya tunawa iyakarmu bariki, ko gidanmu ka ga na taɓa kuskuren kai dayanku? No! So please ka fita daga rayuwata ka bar bibiyata. Ni wallahi daga  yau abotar tamu ma na datseta da ƙaton almakashi. Ban sanka ba, kai ma ka saka a rai ba ka sanni ba. Ka je can ka ji da lafiyarka. Mtsw." Daga haka ya shige motarsa ya bar filin parking din na kwari. Dama kasuwar ya shigo ganin wani abokin Dad dinsa wanda zai hadomishi lefe daga Dubai. Aliyu ya bishi da kallo har ya fice. Ranar iyakar wuya ya kai, wato kowa ma kallon mai cutar ƙanjamau yake mishi shiyasa kowa ya juyamasa baya a kasuwar.  Dawowarsa kenan daga wani gidan abinci ya hango G Baba zai tsallaka ya biyo bayanshi don dama yana ta kiransa a waya bai daga ba, shi ne ya mishi wannan cin kashin. Haka ya koma kasuwar ransa na suya, karshe ma kasa zama ya yi ya mike ya tafi gida don dama lokacin tashi ta kusa. Ramlat na zaune tana karatun Alkur'ani bayan ta gama girki sai ganinsa ta yi, ya zube saman kujera ransa a ɓace. Ta kauda kai ta karasa aya ta yi addu'a ta maida Alkur'anin sannan ta dubeshi. "Kowace irin damuwa gareka, don Allah ka dinga yimin sallama." Ya gyada kai kawai, ta mishi sannu da zuwa ta shiga ciki ta kawomishi ruwa da zoɓon da ta dafa. "Bismillah." Ya karɓi kofin da ta miƙomishi ya ɗan sha ya ajiye. Idanunsa a kaɗe ya dubeta. "Meyafaru?" Ta tambaya bada shiri ba. "Kallon mai cutar Ƙanjamau ake yimin a kasuwa Baby. Kowa guduna yake. Bansan wa ya yaɗa wannan jita-jitar ba, an ɓatamin suna Baby. Shikenan. Yau har G Baba ke guduna?" Ta sunkuyar da kai tana mai jin ciwo a ranta. "Ka yi hakuri." Abinda ta iya cewa kenan. Ya yi ƙwafa "Wato ga Aliyu banza shashasha ko? G Baba ya ci mutuncina ya nunamin daman can Bariki ce ta haɗamu, wato su masu wayo. Usman ma da na kira text ya yimin wai na rabu da shi, duk wanda na kira a cikinsu kauracemin yake. Ashe dama ni ke musu kaunar tsakani da Allah? Wai har G Baba ke iƙrarin na rabu da shi kar na ɓatamasa suna a fasa aura mishi budurwarsa?" Ramlat ta dubeshi tana murmushin takaici. "Wannan bai isheka ishara ba? Bai isheka dalilin da za ka gane rayuwa ba ka watsar da munanan halayya ba kaima? Wadanda ka rikesu ƴan uwa kuma kake jin maganarsu sama da ta kowa, su ne suka juyamaka baya. Koda ace cutar gareka na tabbata ba za ka taɓa zaton za su juyamaka baya haka ba. Idan yanzu duka wadannan jarabtar da Ubangiji ya yi maka bai sa ka shiryu ba, me zai sa ka nutsu Aliyu?"   Ya tsuramata idanu tana fidda hawaye, za ta miƙe ya riko hannunta ya maidota ta zauna. Rungumeta ya yi a jikinsa. "Kiyi hakuri, wallahi ban kara shan komai ba tun da na dawo sha asibiti. Na ce miki ba zan ƙara ba, ki ta yimin addu'a." "Allah Mai amsawa ne, amma kaima sai ka tsarkake zuciyarka da kyakkyawar tuba. Duk abinda zai sa ka ji kana sha'awar aikatawa sai ka ƙaurace mishi. Ka maida hankali wurin bautar Ubangijinka, sai kaga Ya taimakemu." Ya gyada kai yana mai amsawa da toh. A karshe ya mike ya nufi daki ya kwanta, ba ta bishi ba don ita kanta tana bukatar jinyar nata zuciyar. Wayarta ta dauki ƙara, ta mike ta dauka. Hajiya ce. "Ramlatu, maza-maza ki zo Abbanki ba lafiya."   "Innalillahi! Hajiya meke faruwa?" Ba amsa, a firgice kuma a rude ta nufi daki, tun kan ta isa take kiran sunan Aliyu.   Yana naɗe saman gado, shi kadai yasan kwanakinnan da bai sha abin maye ba ya yake ji. Ga damuwar abinda abokansa suka yi mishi na cinsa, ya kasa samun nutsuwa, zuciyarsa na tursasashi akan ya je ya sha ko zai ji sanyi amma yana yiwa kansa faɗa da tunasarwa kansa har abada ya daina.  Jin yanda Ramlat ke kiransa ne yasa shi miƙewa a razane ya tarbeta har tana kokarin faduwa. Hanya kawai take nunawa tana kuka. "Baby nutsu please, fadamin meke faruwa?" "Abba, Abba ba lafiya Aliyu. Ya ce na je, don Allah ka kaini Aliyu." "Kiyi shiru, yanzu zamu je ki ganshi. Kiyi hakuri." Daga haka ya fito rike da hannunta, hijabinta da ta cire ya dauka ya mayarmata. Bai yi karambanin daukarta a mashin ba gudun kar ta kifemasa a hanya. Titi suka nufa suka sami abin hawa. ***   Kusan a guje ta shiga dakin da Abba yake kwance a asibitin. Gaba daya iyalin Abban ne a dakin sai Baba Dakta wanda bai jima da shigowa asibitin ba.   Kai tsaye ta yi kan Abban. "Abba! Abba!!" A hankali ya bude ido lokacin da Zulaihat ta janyeta. Munir na gefe yana ji kamar ya je ya shaƙe Ramlatun. Ko ma mene ai ita ce ta ja. Hannu Abba ya mika, ba musu Ramlatun ta saka hannunta cikin nashi tana wani irin kuka. "Ya cuceni, ya cutar min da ke Ramlatu." Aliyu wanda har ya murɗa kofar dakin zai shigo ya tsaya cak ya fasa. Ya juya ya koma da baya ya zauna saman kujera cike da jin kunyar kansa da kansa. Abba ya ci gaba da magana dakyar. "Meyasa tun farko kika dage akan sai shi? Ba ki hango abinda na hangomaki ba ko? Ba ki hango aibunsa ba Ramlatu. Yanzu shikenan ya cutar min da ke ya sanyamaki ciwon da ba'a warkewa." Ji ta yi numfashinta ya tsaya cak, ta shiga jawoshi da ƙarfinta. "Abb..Abba...me..kake nufi?" Abba ya runtse idanu yana jin saukar hawaye. Ba shi kadai ba, hatta da mutanen dakin abinda suka kawo shi ne, Ramlatu ba ta san komai game da ciwon mijinnata ba. "Abar zancen haka Alhaji Khalid, ba'a son yawan maganarnan naka. Don Allah ku ragu a dakin." Abba ya girgiza kai. "A'a Dakta, bana jin ciwonnan nawa na tashi ne. Ka bar ni na yi sallama da iyalina. Ni kadai nasan me nake ji." Ya fadi gami da runtse ido sai hawaye. Hakan ya kara ruɗa mutanen dakin. A'isha kuka har da sheshsheka hakanan su Rafee'ah. Shi kuwa Munir idanunsa ne suka kaɗa sai sauke ajiyar zuciya yake. "Abba an ce maka Aliyu nada ƙanjamau ko? Abba wallahi karya ne, ko wa ya fadamaka karya yake!" Abinda Ramlat ta fadi kenan sakamakon tunanin da ya zo mata. Yan uwan da ma iyayen kallonta suke cike da takaici, wannan wane irin so ne da har ciwon Aliyun ma ɓoyonsa take? "Ramlatu kinsan Aliyu na dauke da ciwo kika yi shiru? Tun yaushe?" Hajiya da ta kasa hakuri ke wannan tambayar tana duban diyarta a kidime.   I just published "BABI NA ASHIRIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/f5qPHpmrzab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 26) Cikin kuka ta dubi Hajiyar. "Wallahi Hajiya ba ƙanjamau ce da shi ba. Jita-jita ce kawai. Ciwon zuciya ce ke barazanar kama shi sakamakon shaye-shaye, sai Infection da ya jawomasa gudawa shine har ya kwanta asibiti na kwana ɗaya. Abba ka tashi don Allah, Abbana kar ka mutu saboda damuwata. Abba ka yafemin. Kaicona " Kukanta ya ƙi tsayawa, Abba ya kara damƙe hannunta. "Rabi ki yi shiru. Ki yi shiru. Haka Allah Ya tsara wa Ramlatu. Dakta." Ya maida dubansa ga Baba Dakta. "Ka taimakamin a yiwa Ramlatu gwajin jini, idan har tana dauke da cutarnan don Allah a gaggauta dora ta kan magani." "Abba, wallahi lafiya kalau. Abba dagaske nake maka, ina rantsuwa da ..." "Kina da tabbas? Mene hujjarki?!" Munir ya katse a zafafe. Ta dubeshi sai kuma ta kasa magana. Baba Dakta ya bada umarnin duk a fita a bar Abban. Suka fita dukkansu, likitan Abban ya shigo ya kara dubashi sannan ya fito. "Muje Ramlatu." Fadin Baba Dakta. Ramlat ta dubeshi kamar wata wawiya, yau ita za'a yiwa test akan cutar da ko a mafarki ba ta taɓa ganinta da shi ba? Me ya jawomata wannan tozarci da wulakancin? 'Auren Aliyu.' Cewar wani ɓangare na zuciyarta. Sai a sannan kuma ta tuno tare ta zo da Aliyu, ta waiga baya wurin hakan yasa ta maida dubanta ga Baba Dakta. "Baba Dakta wallahi wallahi..." "Yi hakuri, yi hakuri Ramlatu. Kwantar da hankalinki, ki bari ayi din ko don samun nutsuwa da kwanciyar hankalin Abbanki. Kina so ya samu lafiya ko?" Ta gyada kai gami da jan majina. "Yauwa ko kefa, muje." Ta bi bayansa bayan ta bi yan uwanta da kallo. Munir harara ya watsamata, ta kauda kai tana kuka. Test aka yi mata na jini sannan ta dawo wurinsu ta zauna. "Ya ake ciki? Me sakamakon ya bayar?" Fadin Hajiya tana dubanta. Ta bude baki za ta amsa sai ta kasa, kuka ya ci ƙarfinta ga wani bakin ciki da ya tsayamata a ƙahon zuci. Auren Aliyu ya jawomata wulaƙanci, yau ita ake yiwa kallon mai cutar ƙanjamau? 'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!' Ta fadi a karo na barkatai. "Hajiya nifa banda komai, bana dauke da kowace cuta. Hajiya don Allah ki yarda da ni. Wallahi ba ƙanjamau ne da Baban Ummi ba." "Allah Ya tsinewa kalar so irin naki Ramlatu! Son da har za ki ɓoye cutar mijinki ki rufamasa asiri ki cuci kanki! Wallahi Hajiya ya ci ace kun fidda hannunku a lamarin yarinyarnan, wanda fa ya yi nisa ba ya jin kira! Sanadinta Abba ya fada cikin wannan halin, ai ba ita kadai ku k haifa ba! Tunda ita ba ta bi ku ba, kuma bai kamata ku damu da lamuranta ba. Ta je idan ma mutuwa za ta yi ta mutun mana idan har Abba zai rayu! Mtsww!" "Kai kuma mene sunanka?! Me za mu kiraka da shi? Ka tsaya kana fada alhalin Abba ba lafiya? Wannan shi ne girman?!" Zulaihat ke maganar a fusace, tun ɗazun ya kai ta wuya dannewa kawai ta yi. "Ke! Ni kike faɗawa magana?" "An fadamaka din! Don kawai kana babba..." "Ya isa! Haba mana!" Hajiya ta katsesu a tsawance, faɗan Muniru da Zulaihat sakamakonsa bai fiye kyau ba. Muniru ya juya a zuciye ya bar wurin, Hajiya ta dubi Zulaihat. "So ku ke ku nunan halinnaku a asibiti? Shikenan ai." Ta ƙarashe a fusace. Rafee'ah dai banda hawaye ba abinda take yi, magana ma ta kasa saboda tunanin Abban yayinda A'isha ta kwantar da kai a cinyar Rafee'ah ta yi shiru tana kallon kowa. Ramlatu kuwa kukanta ma har ya yi yawa. Suna nan zaune Baba Dakta ya nufosu fuskarsa dauke da murmushi. Suka zubamishi idanu. "Alhamdulillah, koda Aliyu na dauke da wannan kwayar cutar, bai kai ga shafamaki ba Ramlatu. Komai naki lafiya kalau yake. Ki kwantar da hankalinki." Gaba daya suka sauke ajiyar zuciya. Murnar da suke bai wuce yanzun Abban zai farfaɗo ba idan ya ji sakamakon gwajin da aka yiwa Ramlatun. Baba Dakta ya shiga dakin ya karasa har gadon Abban yana murmushi, sai dai me? Cak murmushin ya dauke da sauri cikin rawar jiki kuma ya kai hannu bisa tsintsiyar hannun Abban. Ya kara kaiwa saman kirjinsa don bai gasƙata abinda ke faruwa ba. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Baba Dakta ya furta kafin ya dubi fuskar Abban, kamar za ka kira sunansa ya amsa ga wani dan murmushi. Hannu ya sa ya ja zanin rumfar ya rufemishi fuska. Ya jima a tsaye yana tunanin t hanyar da zai sanarwa iyalin rasuwar Abban. A karshe dai ya daure ya fita ya fadamusu. Kowannensu ya saka salati. Dif! Kukanta ya dauke sai kallo. Ta kalli wannan ta kalli wancan. "Kuka ku ke yi? Abba ai bai mutu ba. Ku daina kuka." Abinda ta fadi ne ya tabbatarwa Baba Dakta ba'a hayyacinta ta ke ba, ya karasa ya riko hannunta. Ta dubeshi tana murmushi har dimples dinta na lotsawa. "Abbana bai mutu ba, bai mutu ba fa Baba Dakta. Muje na ganshi, zan fadamasa lafiyata kalau. Zan fadamasa bana dauke da ƙanjamau. Yanzu za ka ga ya tashi, baccin wasa yake." Ta ja hannun Baba Dakta zuwa dakin Abban. Gaba daya suma suka shiga ciki banda Muniru da har lokacin bai dawo ba. Mayafin ta yaye ta riko hannun Abba. "Abba bacci ko? Ka tashi don Allah. Na warke, Baba Dakta ina result din?" Ta juya a firgice ga Baba Dakta, sai kuma hankalinta ya kai saman tebur ta hango takardar maganin Abba wanda a zatonta shi ne na test din. Ta ɗago ta na nunawa Abban kamar mahaukaciya. "Abb..Abba, ka ga, negative. Banda komai wallahi. Aliyu ma na fadamaka lafiyarsa kalau. Abba ka yi magana." Hajiya ta ja hannunta suka fita bisa umarnin Baba Dakta, ya maida marufin ya rufewa Abban fuska. *** Suna tafe zuwa mota tana sambatu, Hajiya na damƙe da hannunta. "Hajiya bai mutu ba, wallahi Abbana bai mutu ba. Haba! Haka ake mutuwar?! Ai ba haka bane! Mutuwa ba haka take ba! Abba bai mana sallama ba! Um um Hajiya, Abba fa bai mutu ba. Wayyo Allahna!" Hak rike kai da karfi kafin ta yi baya, Allah Ya taimaka Zulaihat na bayansu, ta riketa da karfi. Tuni ta suma. Ba shiri da taimakon wasu mata a wurin aka rirriƙeta zuwa ciki. Dawowarsa kenan daga masallaci ya hango taron mata, har ya kauda idanunsa, hankalinsa ya kai ga Rafee'ah da ke kuka. Cikin sauri har yana tuntuɓe ya karasa. "Ke lafiya?" Ta dubi Muniru kafin ta faɗa jikinsa tana kuka. Ya ɗan tureta. "Abba?" Abinda ya fadi kenan ya yi saurin nufar cikin asibitin. Hawaye kawai ya shiga fitarwa sadda ya ci karo da gawar Abban. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ya fadi a fili. *** Kafin ka ce me, mutuwar shahararren dan kasuwan Alhaji Khalid ya karade garin Kano. Mutum ne mai jama'a kuma mai girmama mutane. Yana da saukin kai da tausayi ga gaskiya da amana. Mutum ne mai son zumunci kwarai. Shakka babu an ji mutuwarsa ba kadan ba. Jama'a da dama sun halacci jana'izarsa, mutanen Daura an zo sosai. Aliyu ya girgiza matuƙa da mutuwar surukinnasa. Abban da ya ke yiwa kallon maƙiyinsa a baya kafin ya fahimceshi da kuma irin kaunar da ya ke yiwa Ramlatu. Bai mance nasihar da ya sha yi mishi ba a duk sadda zasu hadu ko kuma ya je gida. Adalilin faɗa da Ramlatu. Shakka babu ya tausayawa iyalinsa musamman Ramlatu dake kwance gadon asibiti har aka yi jana'izarsa ba ta san ina kanta yake ba. *** Hasken rana ne ya tasheta daga nannauyan suman da ta yi, ta yi cak tana nazarin dakin da take. Tabbas gadon asibiti ne, ta dubi hannunta, ruwa ne ake ƙaramata. A hankali ta motsa. "Sannu kin tashi?" Ta tsinci muryar Indo a gefenta. A hankali kuma ta gyada kai. Indo ta fita da zummar kiran likita kamar yanda ya ba da umarni. Firgigit ta mike. 'Abba! Ina Abba?' Ta yi tambayar da babu mai amsamata, ta fisge ruwan da ake ƙaramata ba tare da jin nauyin cikinta ba ta nemi hanyar fita. Karo suka ci da likita, duk yanda Dr Sunusi ya so ta tsaya hakan ya faskara, a dole ya kyaleta suka wuce gida da Indo. Kuka take yi sosai don tuni ta gano abinda ke faruwa, ta yarda kuma yanzun cewa Abban ba ya duniyar nan da take ciki. "Ya bar min duniyar, ya tafi ya bar ni da abinda na zaɓa sama da su. Ya bar ni nayi yanda na so. Shikenan babu sauran mai sona..." "Haba Ramlatu, ki yi hakuri, ki dauki dangana. Kar ki manta kina da Allah, don ya karɓi abinda ya ba ki aro sai ki ce don me?" Ta girgiza kai kawai. Indo ta ci gaba da ba ta baki. A nan take fadamata anan Aliyu ya kwana, ya je don kawo abin kari ne daga gida. Ba ta ce komai ba har Indon ta kira lambar da Aliyu ya sanyamata ta fadamishi sun wuce gidan. A falon ta iske mata maƙil, ta karasa ciki har wurin Hajiyarta ta zauna. Nan kuma aka shiga yi mata sannu da gaisuwa, kawai ta rungume Hajiyar ta shiga kuka mai tsuma zuciya. Wannan ya kara yiwa Hajiya fami, ta shiga sharar hawaye. Su Zulaihat kam ba'a magana dama, idanun sun yi ja. "Ba'a bar ni na ga Abba ba." Ta fadi cikin sheshsheka. "Sai hakuri Ramlatu, haka Allah Ya tsara. Allah Ya ba ki lafiya." Ta kasa amsawa Hajja, dakyar aka lallaba ta yi wanka ta sha ruwan shayi. *** BAYAN KWANA ARBA'IN Har sannan Ramlatu na gidansu, su Zulaihat ma dakyar suka koma nasu gidajen sai da Yayan Hajiya, Kawu Dauda ya yi musu fada ba shiri suka tattara a kwana ashirin suka tafi. Ita kuwa Ramlatu ta kasa lekawa ko waje ballantana ta fita. Aliyu kusan kullum sai ya zo, har abin ya soma isar Hajiya. Ta kira Bana Dakta ta mishi maganar. Da kansa ya nemi Aliyu suka je yin gwaji bayan ya ba shi hakuri ya fadamasa dalili. Koda sakamako ya fito ya yi mamaki ganin Aliyun shima lafiya kalau yake, ya kara jinjina lamarin Allah. Ya tabbatar ajali ne kawai ya riski Abban ta wannan hanyar. Washegari Baba Dakta da kansa ya zo ya tisa Ramlatu a gaba suka wuce ya kai ta gidanta. Ranar ta yi kuka kamar ranta zai fita sakamakon famin da hakan ya yi mata game da mutuwar Abbanta. Murmushi da dariyar Abban sun kasa gushewa a zuciyarta. Kalamansa na nasiha gareta daki-daki su ke faɗomata a rai, wannan kadai ma yana kara sanyata zubda hawaye. Komai na duniyar ya fice a ranta. *** Zamansu da Aliyu ya sauya, ta koma wata shiru-shiru. Aliyu na shaye-shaye ko ba ya yi, ya zama ba damuwarta ba. Ta daina shiga hayaniya, ta daina shiga lamarin kowa da komai. Ummi har sannan ba ta dawo ba, tana wurin Hajiya. Tana lura da yanda Aliyun ya chanja, yakan wuni a gida idan ya so, wataran kuma ya fita kasuwa. Duk yanda ya so ta saki jiki ya kasa. Koyaushe cikin kuka. "Dana sani ban aureka ba, da na sani na bi zaɓin Abbana." Abinda takan yawaita fada kenan wanda take sosa zuciyar Aliyun da shi. Shi kansa yasan ya mata rashin kyautatawar da ya ci ace ta yi nadamar aurensa, sai dai ko mene ne ai shima ya zalunci wata a dalilinta. *** BAYAN WATANNI BIYAR Cikin Ramlatu ya cika watanni tara. Abin da ya bata mamaki tun a wata na takwas Aliyu ya haɗomata komai da ta bukata na haihuwa, abu ne da ba ta zata ba. Zuwa sannan ta ɗan saki zuciyarta, addu'a babu ranar da ba ta saka Abbanta ciki duk sallah. Kulawa sosai suke ba wa Hajiya daga ita har ƴan uwanta. Kowannensu gudun ɓacin ran Hajiyar yake yi. Ɓangaren Aliyu kuwa, ta ga sauyi sosai don ga dukkan alamu ya bar shaye-shaye. Koda ya na yi ba ta taɓa kamashi a gidanta ba. Ba ta dai gajiyawa da yi mishi nasiha da tsoratar da shi game da rayuwa da mutuwa. Tana dai godiya ga Allah yanda ya soma chanjamata shi, ya soma shiga cikin ƴan uwansa, har Alkur'ani yakan dauka ya yi tilawar inda ya iya. Har a sannan ba su koma makaranta ba. Ranar wata juma'a da rana Allah Ya taimaka Aliyu na gida, naƙuda ya kama ta. Suna zuwa asibiti ba tare da daukar tsawon lokaci ba ta haifo ɗanta namiji. Sai da aka gyarasu ita da jaririn sannan Aliyu ya sanarwa jama'a. Hatta su Zulaihat sai da suka zo ganin jariri banda Hajiya. "Wannan dai kamanninki ya dauka Ramlat." Cewar Rafee'ah tana dan murmushi, dukkansu har sannan ba su gama maido kumarinsu ba. Abba ne ya faɗomata a rai sadda aka haifi Ummi. Wani irin kuka ya kwacemata, tun suna cewa mene hakan? Har su ɗin ma suka shiga sharar hawaye. Kowannensu ya fahimci tunanin dan uwansa. Ganin yan uwan Aliyu sun soma zuwa ya sanya suka danne abinda ke zuƙatansu cike da jimami. A ranar aka sallameta ta koma gidanta. Abulle ce ta turomata wata dattijuwa da za ta taimaka mata da wanka na sati biyu. *** "Mu sanya masa sunan Abba?" Ya fadi yana dubanta, ta kurawa yaron idanu kafin ta girgiza kai. "Meyasa?" Ya fadi cike da mamaki. "Saboda abubuwa da dama, ka yi hakuri ka yi mishi huduba da duk sunan da ya dace. Amma banda sunan Abba." Ya ƙuramata idanu kafin ya jinjina kai kawai. Bayan ya kammala ya dubeta. "Sunansa Ansar. Allah Ya rayamana." Murmushi ta yi ta dauke kwallar idanunta na tunawa da Abban. Haka suka ci gaba da rainon Ansar, ba'a yi taron suna ba. Suna cika sati biyu, dattijuwa Yaha ta tattara da goma ta arziki da Ramlatu da Aliyu suka hadamata ta bar gidan tana ta godiya. Sai da suka yi wata goma cif suna yajin aikin makaranta tukunna aka koma. *** BAYAN SHEKARA DAYA.. *Allah Mai iko akan kowane bawa, Shi kadai buwayi gagari misali. Mai shiryawa kuma Mai Rahma.* "Zan bi ka Abba." Ummi ke fadi har da kukanta, Ramlat dake zaune tana shayar da Ansar ta dubeshi. "Don Allah Baban Ummi ka taimaka ka tafi da ita. Ba sai ka sauketa wurin Hajiyar ba? Magiyar ta isa." Aliyu na gyara zaman hular kansa ya harari Ramlat kadan. "Kin ji? Yarinyarnan dai nema take ta koma gidan Hajiya din din din, wato shikenan mu sai dai ta kawo mana ziyara ko? To na ƙi wayon, nima ina sonta kusa da ni." "Anya ba ka fi son Ansar ba?" Ta fadi tana mai kanne mishi idonta guda. Ya ɗan daure fuska. "Na hanaki tada abinda ya wuce ba kya ji Baby." Ta yi dariya. "Afuwan." Abinda ta ce kenan sadda ta cire nonon a bakin Ansar da bacci ya yi awon gaba da shi. Kwantar da shi ta yi sannan ta mike ta karasa ga Aliyun ta taimaka mishi da sanya links na hannu. Kallon juna suke yi cike da so da kauna, abubuwa da dama suka shiga dawo musu a kai. "Idan ban godewa Allah da Ya ban mace ta gari kamar ki ba Baby, me zan yi?" Ta yi murmushi wanda ke karamata kyau. "Allah Ya yi miki albarka. Wallahi idan har ni Aliyu, aljannarki a ƙarƙashina take, na ɗagamaki na ƙara ɗagawa ki shigeta." Ta yi dariya. "Dagaske nake." "Toh na gode sosai." Ya ja karan hancinta. "Ni zan fadi haka Baby." Murmushi ta yi shi kuma ya daga Ummi cak ya ba ta sumba a kumatu. "Daukomata takalmi." Jin haka Ummi ta kara wangale baki, Ramlat na dariya ta karasa ɗakin ta dauko. Yana rike da ita ta sanyamata, rakiya ta musu har bakin kofa sannan ta dawo. Kwanciya ta yi tana tunanin abubuwa da dama. Sauyawar Aliyu ya fi komai yi mata dadi a zuciya. Tun mutuwar Abba, sai kuma abin ya zama kamar yayewar matsalarta. Tun tana ganin Aliyu kamar karya yake bai bar shaye-shaye ba, tun tana ganin kamar komai yana yi ne don ganin idonta har ta zo ta fahimci dagasken ya bari. Maimakon shan sigari sai ya koma ma'abocin shan ruwan shayi mai citta da kanumfari wanda hakan ya kara taimakawa wurin danne mishi kwadayin sigari balle kwaya. Duk abinda zai tunamishi da bariki ya yi watsi da shi, ya dinga cusa kansa wurin mutane nagari, y kasance maimakon idan ya dawo daga kasuwa ya je matattarar yan iska, sai ya sauya da zama a masallaci tsakanin Magriba da Isha'i yana jin tafsirin Malamai. Wasu lokutan Ramlat takan farka ta ganshi durkufe cikin Sujjada yana kuka da addu'a. Ita kanta takan ji hawayen ya cika idanunta ta kasa komawa ta mike ta yi alwala ta yi zaman tayashi. Abu kamar wasa, lamarin ya ci gaba da tafiya a haka. Malam har hawaye ya yi don dadi ganin sauyawar dansa, ya kuma kara yarda cewa bawa bai isa ya shirya dan uwansa ba idan Allah bai shirya ba. Anan ne Aliyu ya gane cewar ashe ba shi ne ba'a so ba, halinsa aka tsana. Abulle ma ta yi kuka don murna. Akwai da yawa da suka kasa gaskata Aliyun, har lokacin basu shiga harkarsa. Dama haka rayuwa take, ba lallai ne kowa ya so ka ba, hakanan ba ka isa ka ce ba ka da maƙiya ba. A bangaren Aliyu da yan uwan Ramlat din ma sai godiyar Allah, ya zamana zai je har su ɗan yi hira da Baba Dakta. Hajiya ma sannan ta sakar mishi sai dai akwai ƴar kunya tsakaninsu. Tsakaninsa da Munir kuwa ko gaisuwa bai haɗasu. Koda ya gaidashi ba amsawa yake ba. Ƙarƙari idan ya yi sallama zai amsa yana cin magani. Wannan tasa shima ya watsar da lamarinsa. Har Gombe ya kwashesu suka je ya sada zumunci da yan uwan Innarsa, sun yi mamaki sosai don ganin abin suka yi kamar mafarki. Kusan Aliyu tun Innarsa na raye rabonsa da su. Wannan ta sa sosai suka tarbesu suna tattalinsa da iyalinsa har suka dawo. *** Ta shiga binsa daga daki zuwa falo, da ya gaji sai ya tsaya yana kallonta. Ta turo baki kadan. "Baby, meye wai?" Ramlat cike da shagwaɓa ta amsa. "Muhibbat ce fa Baban Ummi. Ta tako gidannan ya fi a ƙirga. Har ta haihu a yi suna ban je ba? Gaskiya ban kyauta ba wallahi." Ya taɓe baki, ta kuramishi idanu tana murmushi cike da so da kaunarsa da yanzun ta ke ji ba kaɗan ba. Ya ɗan murmure hakanan ya yi haske kadan ba kamar a baya ba. Kasuwa ta dan dawomishi daidai don yanzun yana maida hankali sosai. "Nayi zaton ma asibiti za ki cemin za ki, ashe ba haka ba ke yawo kike son fita." Ta daure fuska. "Ni lafiyata kalau, na fadamaka ba ba ciki bane. Ko ka manta na yi planning?" "Planning wane iri ne wannan da za ki dinga amai da kwadayi? Yaushe rabonki ma da al'ada?" Ta numfasa ba don ta wani dauki abin da muhimmanci ba don dama idan ba ta mance ba Nos ta fadamata cikin side effect din maganin har alamomin masu ciki ko daukewar jini zai iya jazamata. "Shikenan zan je, amma daga nan zan wuce gidan Muhibbat. Don Allah!" Ta fadi da sauri ganin yana kokarin cewa a'a, ya yi dariya. "Shikenan, a gaishesu. Ki dai tabbatar kin je asibitin." Ta rungumeshi gami da yin godiya. Ya bata sumba a kunci gami da bata kudin mota da na ganin likita. Yana fita itama ta shirya tsaf ta goya Ansar ta fice. *** RUBUTACCEN I just published "BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/pcYjI4bZBab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 27)   "Ke kam sai ayi magana ki yi shiru." Maganar Muhibbat ya katsemata tunani a karo na barkatai, ta kakalo murmushi ta dubeta. "Kai ban ji ba." "Cewa nayi ina Ummina?" Cike da kaunar yanda Muhibbat ke sonta da abinda ta haifa ta amsa. "Tana can gidan Hajiya." "Kai jamaa, da alama dai Hajiya ta kwacemana Ummi." Dariya suka yi lokaci guda. Hira dai ta yi hira har hakan ya mantar da Ramlat damuwarta na cikin da ke jikinta. Duk da amsar da Likita ya ba ta sadda ta mishi tambaya hakan bai gamsar da ita ba sai da ta ƙara tambayar Muhibbat. "Wai nikam Sis, dama ana iya samun ciki ko anyi family planning?" Muhibbat ta dubeta, me za ta yi ba dariya ba. Yi ta ke ba kakkautawa har sai da Ramlat itama ta dara. "Mene wai na dariya toh?" "Ah ba komai fa. Sai dai na harbo jirginnaki. Ai idan Allah Ya so ikonSa, ba planning ba, ko mahaifar aka juya sai ki ga an samu ciki. Meyafaru?" Jiki a sanyaye ta ce. "Implant na saka, abin mamaki wai ana yimin test aka ga ina da ciki. Wai gocewa ya yi." Jinjina kai Muhibbat ta yi. "Ana haka, na sha ji ana fadin haka. Wata har allura ta yi amma bai karɓeta ba sai ga ciki. To ke me zai dameki? Ai ko ba komai Ansar ya shekara." Ajiyar zuciya ta saki, kuma fa hakane. Idan a baya munanan ɗabi'un mijinta ne ta ke gudu, yanzun komai ya kau, ya zama labari da yardar Allah. Muhibbat ta ci gaba da ba ta shawara akan kar ta damu ba komai. A karshe ta ji zuciyarta ta yi sanyi. Sai wuraren yamma ta yi mata sallama ta bar gidan bayan ta diremata turmin atamfa cikin wadanda ta samu na barkar Ansar. Godiya sosai Muhibbat ta yi kuma ko kadan ba ta raina ba duk kuwa da cewar ta fi karfinsa. Har kofar falon ta yi mata rakiya suka yi sallama. ***   Juyi ya shiga yi da ita yana karawa, ita kuwa banda dariya ba abinda ta ke, hakan da ya yi ya zo mata a hagunce don ta yi mamaki. Ba ta zaci ganin irin wannan farin cikin a fuskarsa ba. Farin ciki ne da ya taho tun daga ƙahon zuciyarsa. Ya shiga sumbatar duk inda bakinsa ya kai a fuskarsa.  Ta kauce gami da faɗawa kan kujera tana dariya lokaci guda tana mai watsa mishi harara. "Kai don Allah Abban Ummi. Duk rawar ƙafar don cikin ne? Ciki na uku?" Zama ya yi a gefenta gami da riko hannunta. "Bar ni na yi murna kinji ko? Kyaleni Baby. Allah Yasa ki haifarmin mace na sanyamata sunanki. Kin cancanci komai daga gareni." Ita dai murmushi take tana kara godiya ga Allah da tarin ni'imominSa wanda ba ya yankewa. Yau Aliyu ke ɗoki da zumuɗi mai yawa haka saboda ance tana dauke da juna biyu? Kumatunta ya ja wanda ya maidota hayyacinta. Suka yiwa juna murmushi kafin ya jawota jikinsa ya soma aika-aika😜. Kukan Ansar ne da ya fado daga saman kujera cikin bacci ya katsemusu komai, kusan a tare suka isa wurinsa ya rigata daukarsa. Safa da marwa ya shiga yi yana jijjiga yaron, hakan ya bata damar tsayawa ta kurawa Aliyun idanu cikin duniyar tunani. Kwallar farin ciki suka cikamata idanu ta sharesu. Abbanta ya faɗomata a rai, ta tabbatar da yana raye zai fi kowa farin cikin shiryuwar Aliyunta. Ta so ace Abba da Aliyunta sun yi rayuwa kamar na ɗa da uba tun a baya, ta so ganinsu tare a zaune suna hira da dariya. Sai dai kuma Allah bai nufi hakan da faruwa ba. ***   Labarin cikinta har gidansu, ta sha dariya wajen su Zulaihat da suka hadu a gida. "Dama za ki ka da yin Ubangiji ne? Kallonku kawai nake." Hajiya ke wannan zancen tana gutsirar goronta wanda ya zamemata jiki. Ramlat ta yi dariya. "Yanzu dole ki yaye Ansar fa ko?" Rafee'ah ke zancen tana dubanta. "Anya kuwa? Ni gani nake kamar ba matsala tunda ta ce likita bai hana ba." Fadin Zulaihat. "A'a ba zai yiwu ba, dole ma a yayeshi. Idan ya rame itama ta rame fa? Ai dukkansu abin ba zai zo musu dakyau ba." Hajiya ta furta cike da kulawa. Kulawar da idan Ramlat ta dubi ƴan uwannata ta ga dukkansu a cikin lamuranta suka tsoma baki sai ta ji dadi da farin ciki sun lulluɓeta. A ranar dai haka ta koma gida ba Ansar don Hajiya ta ce ba zai yiwu ya ci gaba da shan mama ba. Har da ƴar kwallarta na tausayin yaron, don ma dai yana da kumarinsa. Ganinta ita daya Aliyu ya ci dariyar da ta ishe shi. "Ai koda ba ki yayeshi ba, da hannuna zan daukeshi na miƙa wa Hajiya ko na kaiwa Amarya shi. Ta ya za ki zauna kina ci gaba da shayarwa ga ciki? Ba zan yarda ba." Ta turo baki ta shige wanka ta kyaleshi zaune gefen katifa. Allah Ya taimaketa ba ta yi ciwon yaye ba sai dai sun kara ciccikowa. Hankalinta ya kwanta ta koma rainon cikinta da zuwa makaranta abinta. ***   BAYAN WATANNI TAKWAS.. Binsa kawai take da kwando yayinda yake aikin lodar kayan jarirai kala-kala unisex. "Don Allah ya isa haka Sweet Aliy." Bai ko kalleta ba balle ya saurareta. "A ina ka samu kudi haka?" Ta ƙara jefamasa tambaya don ita kam abin ma tsoro ya shiga bata duk kuwa da ta san yanzun Aliyun na samu fiye da baya. Ganin ta ƙi ɗaga ƙafa ta bi bayansa, ya janye kwandon ya yi gaba ya kyaleta yana duba wasu turaruka na jarirai.    "Wannan ba Ramlatu bace?" Jin an ambaci sunanta ne yasa ta juyawa bangaren da ta ji muryar. Kallon kallo suke da juna. Kamannin Hilal sak a fuskokinsu. Tuni ta gane su waye, Anti Fareeda da sai Murja da ƙaton ciki wanda haihuwa yau ko gobe. Ta saki murmushi sadda suka ƙaraso gareta, Murja ko gaisuwarta ba ta amsa ba ta jefomata tambaya.   "Kema wani cikin ne da ke? Bilki ta ce haihuwarki biyu yanzu ta uku. Kin ji labarin auren Hilal ko? Kinga Allah ba azzalumin bayinSa ba ne." "Dadina da ke Murja wataran kamar yarinya kankanuwa, ke har sai an ce miki ciki gareta? Saukinta daya ma na sunnah ne. Uhum, gwara ma da aka yi yunwa halin kowa ya fito. Da yanzun da auren Hilal za ta haifi shegu." Kallonsu take, kamar wacce aka ƙullewa baki ta kasa magana, kirjinta wani tafarfasa yake yi. Ta juya kawai ganin idanunta ya ciki da kwalla. Fareeda ta kara magana. "Kinsan ma naji ance mijin ƙanjamau ne da shi. Ga duka na safe daban na rana daban." Ta ƙara daga kafarta daidai sadda Murja ta kara magana. "Ai dama Allah ba azzalumin bayinSa bane, tun ka aje ko'ina yarinya ta soma ganin sakayya. Ni dama kishiya ya ƙaromata muga ta karshen soyayya." Tuni ta yi gaba ta bi bayan mijinta kamar ba ta ji ba. Karo suka kusan yi, da sauri ya riƙe kafarta. Kallon kallo suke da juna, ya sa hannu ya gogemata hawayen. "Meyafaru? Keda wa? Ina can ina kokarin biyan kudi na waiga ban ganki ba. Lafiya?" Ya ƙarashe yana daga wuya kamar zai hango abinda ya ɓata rannata, bai ga kowa ba sai wasu mata biyu dake kallonsu. "Ba komai fa, abu ne ya shiga idona." Ya daure fuska, zai kara magana ta yi saurin giftawa ta gefensa ta soma tafiya gami da fadin. "Don Allah mu je." Bai bi ta kanta ba ya wuce zuwa bangaren matan yana dan dube-dubensa, so yake ya ga ko zai ga fuskar da ya sani cikin ƴan uwansa ko na Ramlat din amma babu ɗaya. Zai wuce ne ya ji wata a gefensa kamar da rada tana fadin. "Ko shi ne mijinnata?" Ya waiga ya kara kallonsu, shi ɗin suke kallo dai, hakan ya ba shi tabbacin su ne silar hawayen Ramlatu. Ganin dai zargi ne ba shi da tabbas ya sanya shi watsamusu banzan kallo ya wuce, duk suka sha jinin jikinsu suka kauda kai.   "Kinsan fa mashayi ne, kar ya kawomana duka." Fadin Murja a tsorace bayan tafiyarsa. "Atoh, gwara ni banda komai, ke kam naƙudar dole zai sanyaki ko ya kaiki lahira." Suka tuntsire da dariya sai dai fa ba haka suka so ganin Ramlat din ba. Alamun jin dadi sun bayyana a fatarta da kuma jikinta, sun so ganinta a yamushe yanda za su fi jin dadin kai labari, amma hakan ma da suka yi mata sun dandana mata wani bakin ciki. Wannan yasa hankali kwance suka ci gaba da siyayyar abinda ya rage ga Murja. ***   Tun a hanya yake masifarsa jin diramar da ta yi a shagon da ya uwan Hilal,  har suka dawo gida, ita dai ba ta iya tankawa ba banda hakuri da take ba shi. Koda suka shiga  ita ya bari da baza kayan tana kallo, kallon take amma zafin kalaman su Murja ya tsayamata a ƙahon zuci. "Mtsw. Sai ki zauna ki yi ta kuka akan abinda ba wanda ya isa ya sauyamaki. Ko mene ya riga da ya faru, akwai dan iskan da zai hana. Don ubansu me suka ce? Da shege za ki haifa a gidan Hilal din ko? Dama hakan ce ta faru naga uban da zai hanani dauko ƴaƴana!" Ta dubeshi a razane, sai kuma ya shiga istigfari. Ransa sosai ya ɓaci don shi a duniya ya tsani a yi mishi abu bai rama ba. Ya so ace a gabansa suka yi yanda zai zazzagamusu bala'i ya nunamusu haukartasa. A karshe kuma ya koma lallaɓata, ya shiga jan ta da hirar Baby gami da nunamata kayayyakin su ka shiga dariya zuciyarsu ta yi sak. *** Rayuwarsu abin sha'awa, zama na so da kauna da aminci irin wanda Ramlat ta jima tana mafarki, Allah Ya tabbatarmata da shi. Tana zuwa makaranta abinta, Amrah na nan ta ƙi kula kowane saurayi don ta rantse sai ta kammala karatunta.   Babu laifi suna zumunci da yan uwan Aliyu yanzun musamman wadanda suka hada uwa. Sukan zo itama ta jajjemusu tare da Aliyun. A yanzun ba abinda ya fi burgeta sai zaman karatun da Aliyu ke dauka duk karshen sati wurin wani Limamin unguwarsu. Haihuwar Ramlat ya kama a watan azumin Ramadana, alokacin bai fi sati uku ya yi saura a kama azumin ba. A sannan karatu ya dau zafi don su na aji na biyu zango na farko sakamakon yajin aikin da aka dinga tafiya wanda hakan ya ɗan kawomusu cikas a karatun. Wataranar Asabar tana zaune a tsakar gida ta dage tana research a Google na wani project da aka bata. Aliyu na daga gefenta ya kwanta saman filo ya zubawa sararin samaniya ido yana kallo. Shirunsa da ta ji ya yi yawa ne yasa ta dubansa. Ganin hankalinsa ma ba ya kanta ne ya sa ta mika hannu ta ɗan matsa yatsun ƙafarsa suka yi ƙara. Ya juyo ya dubeta gami da ɗan lumshe idanunsa ya bude. "Lafiya? Me kake tunani?" Murmushi ya ɗan yi. "Rayuwa nake tunani Baby. Duniyar tsoronta nake kara ji, tuna watarana zan mutu fargaba hakan ke sanyani. Idan na zauna ina lissafi sai na ga kamar ban taɓa aikata abin kirki ba. Tun ina saurayi iyayena ke shaƙar bakin cikina, na tsoma kaina a harkar shaye-shaye. Na dauki rayuwar da ba tawa ba, yawo da ƴaƴan masu hannu da shuni, na ɗorawa kaina. Na baƙanta ran jama'a da dama, a karshe ko ban aikata zina ba, na shafa jikin matan da ba nawa ba. Idan na tuna akwai ranar da zan koma ga Allah, a binne ni cikin raminnan, a doramin itace a kara bina da kwali sannan a rufamin ƙasa a fuska, ina shiga matsanancin tashin hankali Baby.  Daidai da ɓangarenki na cutar da ke, na kasa daukar nauyinki, na kasa kula da lafiyarki, na kasa ciyar da ke a lokuta da dama kamar yanda sutura da shanki bai cikin damuwata a wasu lokutan. Ban tsaya anan ba na jawomaki abin gori, na kashe aurenki don na rayu da ke. A sanadina iyayenki sun zubar da hawaye a kanki, nayi amfani da karfin son da kike yimin na yaudareki. Anya duk wannan tarin saɓon da nayi, Allah zai dubeni Ya sanyani sahun muminan bayinSa?" Kallonsa take tun soma maganarsa, kamar yanda take fitar da hawaye, haka shima yake fitarwa. Girgiza mishi kai ta shiga yi. Ta ture litattafan ta karasa gareshi gami da damƙe tafin hannunsa cikin nata.    "Kar ka kara irin wannan kalaman, Ubangiji Mai Rahma ne. Wanda ma bai tuba ba, kira Ya ke yi akan ya zo ya nemi gafararSa zai yafemishi, ballantana wanda Ya kusantoShi da neman gafara ba? Ai shi At-Tawwabu ne Mai yawan karɓar tuban bayinSa. Koda wasa kar ka sake zuciyarka ta jefaka cikin kokwanto Allah Ba zai gafartamaka ba. Ka yi irin tuban da Ya ke so, ka kuma nemi gafarar wadanda  ka aikatawa ba daidai ba. Me ya fi wannan dadi? Abinda ya riga ya faru ba mu isa mu sauyashi ba." Gyada kai Aliyu ya shiga yi sai kuma ya yi shiru, Hilal, shi ya faɗomasa a rai. "Na nemi wata alfarma?" Ta tsinci muryarsa karo na biyu. Ta kara dubansa ta gyada kai. "Hilal, ki nemar mini gafararsa, ki ce ya yafemin koda ace Allah bai ban ikon saduwa da shi ba a rayuwa." Ji ta yi gabanta ya fadi, ta daure fuska gami da harararsa. "Bana son irin wadannan kalaman naka. Kana magana kamar wanda ya ga mutuwa." Ta ba shi dariya sai ya murmusa gami da shafa fuskarta ya sumbaci hannunta dake sarƙe da nashi. "Ke kuma ba kya so ko me? Malam ya cemin hakan na karawa Bawa imani. Kinga yanzu ko ba komai mun samu lada. Ke tsaya ma, sai fa ki ce za ki yi aure idan na mutu ko? Duk wannan tarairayar wani za ki yiwa? Caɓ!" Maganar ta ba ta haushi, fisge hannunta ta yi ta dauki littafi ta dauka ta shiga  makamishi a kirji. "Bana so! Bana so! Ka daina yimin wannan zancen." Ya riƙe hannuwanta gami da jawota jikinsa yana dariya.   "Allah Ya huci zuciyarki toh. Na tuba, ai mutuwar ma sai dai ta daukemu tare In sha Allah. Sha kuruminki." Sati uku da wannan maganar.... ***    DUK MAI RAI... Ranar juma'a wanda ya kama acikin goman farko na azumin Ramadana, tun tashinsu take jin wani irin nauyin jiki, haka kawai ta ke jin babu dadi daga yanayin kallon da Aliyu ke bibiyarta da shi. Daɗin daɗawa, duk inda ta sanya ƙafa yana biye da ita, idan ta yi magana sai ya koma wurin yaransa wanda tuni ya cire kunya ya je gidan Hajiya ya kwaso su. "Abban Ummi, lokacin sallah ya yi, ka tashi ka je tunda yau dai ka ƙi kasuwar." Ya sauke Ansar daga saman cikinsa ya mike zaune. Daga shi sai jallabiya doguwa. Dan guntun tsaki ya ja yana murmushi. "Yau din ne ganinan dai Baby. Jikin babu dadi kamar dai mai fama da zazzaɓi." Ya ba ta tausayi. "Toh ko za ka karya azumin ne?" Girgiza kai ya yi lokacin da ya mike. "Haba dai? A'a. Kedai ƙatuwar gandiya ki yi ta shan abinki, daga baya na sha dariyar ramuwar da za ki yi." Ta ɗan harareshi kafin ta dubi su Ummi. "Oya ku zauna nan ina zuwa." Daga nan ta mara mishi baya zuwa dakin, wanka ya shiga don haka ta fiddo mishi farar shadda da hula. Yana fitowa ya shiga shiri. "Ya kamata muje Daura idan kin haihu." "Toh." Ta ba shi amsa gami da ƙarasawa ta shiga taimaka masa wurin shiri. Kallonta kawai yake bayan ya sanya kaya tana sharce mishi gashi da comb. Jikinta ya yi sanyi da kallon, ta hura mishi idanu. "Wai lafiya Abban Ummi?" Ya sauke ajiyar zuciya. "Ba komai. Bari na gaggauta tafiya ko ya ya na samu huɗuba." Ta amsa da toh, ta dauki darduma ta feshe da turare ta miƙa mishi, har kofar falon suka yi mishi rakiya. Ya dawo da baya ya dubeta. "Kinsan me za ki dafamin yau?" Kai ta girgiza. "Ɗanwaken nan mai ɗan karan daɗi." Ta yi dariya. "Mutum ya yi azumi ya nemi ɗan wake? An shiga uku da wannan dan waken." "Kema kinsan ina sonsa." Ta gyada kai tana dariya, ita kuwa ta san yana son dan wake, har tayata sakin ɗanwaken yakan yi. "Sai na dawo." Ta amsa gami da yi mishi addu'a kafin ta koma ciki. ***    Tun tana kallon ƙofa har karfe uku, kwakwalwarta ta bata ya biya wani wurin daga masallaci hakan ne yasa ta kwantar da hankalinta ta ci gaba da shirin kayan shan ruwa. Ba ta jin dadin jikinta dauriya kawai ta ke, da ace ta cika watanni tara cif, da sai ta ce naƙuda ne duk da cewar yanzun ma za ta iya haihuwa don sati kawai ya rage ta shiga watanni tara. Kofar gidan da ake kwankwasa ne yasa ta saurin baro kicin din da murnarta ta fito, jikinta ke bata Aliyun ne sai dai ta yi mamakin dalilin da yasa bai tafi da nashi mukullin ba. Maimakon Aliyun, sai ta ji muryar makwafcinsu Baban Maryam. "Baban Maryam ina zuwa." Ya amsa da toh, ta koma ciki ta dauko katon hijabi ta rufa, kirjinta na bugu, dakyar take jan ƙafa har ta karasa ta bude.  "Amm, dama lambar wayar Malam nake so." Ta gane Malam, mahaifin Aliyu. Ba ta yi mamaki don yasan waye Malam ba saboda kusancinsa da Aliyu a unguwar ya fi na sauran makwabtan. Dafe kirji ta yi. "Lafiya?" Murmushi ya kakalo. "Lafiya kalau Alhamdulillah. Wata ƴar magana zamu yi." Ta ɗan yi shiru, kamar ta tambayi mijinta sai ta ga rashin kyautuwar hakan. Komawa ciki ta yi ta dawo da wayarta ta bude lambar hannunta har rawa yake yi ta miƙa mishi ya kwafe. Godiya ya mata sannan ya wuce, dakyar ta iya rufe kofar. Shi kuwa Baban Maryam gidan ya shiga a gaggauce ya nemi matarsa Hajara ta je ta zauna tare da Ramlat don Aliyu ya rasu a masallaci. Allah Ya taimaka tare suka tafi kuma sun samu zama cikin masallacin. Kuka Hajara ta sanya gami da salati. Ya yi saurin dakatar da ita. "Ya isa don Allah kar ta ji ta razana, yanzu yana can mun kai shi asibiti don a tabbatar ko mutuwar ce. Ta gyada kai sannan ta rarumi Maryam ta goya a baya ta fice gidan Ramlat. *** Ramlat na ganinta sai ta kara rudewa, dakyar Maman Maryam ta iya danne kuka da damuwarta ta shiga jan ta da hira da dariya kamar gaske. A karshe ta samu ta ɗan sake sai dai bini-bini za ta dubi wayarta, a karshe da ta gaji  ma duban Maman Maryam ta yi. "Wai ke kam ba ki da aiki yau ne? An fa yi la'asar. Ki tashi." Tausayinta ya kama Maman Maryam, tun zuwanta ta hangi damuwa tsantsa a saman fuskarta. Tasan ko ba komai jikinta ne ya bata. Maman Maryam ta daure ta harareta, za ta bada amsa kenan aka shiga kwankwasa kofar gidan. Kusan ma sakin ludayin miyar ta yi don yanzu a ɗan karamar cylinder na gas take girki, Maman Maryam ce ta karasa ta kwashe mata sauran ɗan waken ta kashe wutar. Ta bi bayanta tana salati don tasan yau kam mai faruwa ta afku, rabuwa ta har abada ce ta samu Ramlat da Aliyunta. *** "Hajiya? " Abinda ta ce kenan da mamaki ƙarara, idanunta suka cicciko da kwalla, ko'ina na jikinta ya fara rawa. Hajiya ta shigo gidan sosai sai Umman Amrah. Ta ja hannunta suka shiga ciki ba ta ko tsaya amsa tambayoyin da Ramlat ke jifansu da shi ba. "Meyafaru Hajiya? Kin yi shiru. Ki fadamin. Umma menene?" Babu mai amsawa. Sai da suka shiga ciki suka zaunar da ita suka yi mata doguwar nasiha da ya sanyata  kuka, Abba kawai ta shiga tunowa. A karshe suka sanarmata labarin mutuwar Aliyu. Abin mamaki sai kukan ya tafi, ta shiga murmushi, murmushi sosai.   "Ramlatu, kinji abinda na ce?" Hajiya ta fadi a ɗan tsorace don a zatonta ko taɓuwar hankali ce. Ramlat ta girgiza kai ta a murmushi gami da jan majina. "Ya yi mutuwar da bai kyautu na zubar mishi da kwalla ba ai, ya yi irin mutuwar da kowane DAN ADAM zai so ya samu irinsa. Da azumin Ramadan a bakinsa, cikin dubban jama'a, a hanyar bautar UbangijinSa. Idan ba godewa Allah ba, na yiwa Aliyu addu'a, me ya kamata na yi?" Wannan tawakkalin nata ya raunana zukatansu, ta kuma burgesu ainun. Suka wuce da ita zuwa gidan iyayen Aliyu inda anan aka kai gawar Aliyun. Abulle tun da aka yi mutuwar tana kwance ba ta san inda kanta yake ba. Maza da mata kuka ake yi akan rashin Aliyu. Aliyun da dama a cikinsu suka tsana.    Tuni an mishi sutura, kowa kallonta yake da mamakin yanda ta daure. Da katon cikinta ta durkusa gaban gawar Aliyu ta yi mishi addu'a sannan aka ɗaukeshi a makara aka fita da shi. Wannan fitar ce ta daga hankalinta, ta sani idan aka tafi an tafi kenan. Ba za ta ƙara ganinsa ba, ya bar gidan kenan bari na har abada. Tun tana ganinsu daidai har ta soma ganin bibbiyu kafin ta zube a wurin.    Koda ta farka bayan an yayyafamata ruwa, sai ta farka da wani irin azababben naƙuda. Tuni aka rarumeta zuwa asibiti.   A wannan yanayin Ramlatu ta haifi ɗanta namiji. ***   Rashin Aliyu babban rashi ne da ba za ta taɓa mancewa ba. Ta yi rashin Abba, ta zo ta rasa Aliyunta. Mutane biyu mafi girma da daraja a gareta. Cikinsu ba wanda bai taka rawa a rayuwarta ba. Sai a sannan ta yi kuka iyakar yinta, ta rungume jaririnta a jiki tana jin kamar ta hadiyeshi don so da kauna. Kamanninsa da Aliyu kamar an tsaga kara an karya, hatta da hasken fatar Aliyu ba abinda ya bari. Hirarrakin da ya dinga yi mata a kwanakin ne ya shiga dawomata, ta kuma fahimci ba na komai bane face bankwana. Irin ba kwanan da idan an tafi ba za'a ƙara waiwaye ba. Ba za'a kara dawowa ba sai dai a je a tarar. "Sunansa Affan." Abinda ta ce kenan tana duban Umman Amrah. Umman ta yi mamaki don ta dauka sunan mahaifinsa zai ci, sai dai ta gyada kai ta karɓi yaron ta kaiwa Malam don ayi mishi huduba. Ita kuwa sunan da Aliyun ya zaɓarwa ɗan kenan tun kafin ya zo duniya, ba ta ga dalilin da zai sa ta sauya ba.   Tun daga lokacin rayuwarta ta dawo sabuwa, tun daga nan komai ya sauya. Ta koma mai yawan daure fuska a maimakon sakinsa, ta zama wata shiru-shiru irin shirun da sai ta so take sakin jikinta ta yi magana da dariya. Har ta kammala takaba ta koma makaranta ba ta sauya zani ba. Hajiya ta rungumi jikokinta kamar ita ta haifesu, nasiha da ban baki shi ne abinda take yiwa Ramlat koyaushe. Dakyar ta soma sakin jiki har ta kammala karatunta ta hadu takardunta, a sannan ne kuma aka yi bikin Amrah suka bar ƙasar da mijinta. Baba Dakta da kansa ya yi cuku-cuku ya samarmata aiki a ma'aikatar kula da haraji ta ƙasa na branch dinsu dake Kano. (KIRS)   A duniyar Ramlat, babu aure, babu kula kowane namiji da sunan soyayya. Ta hakura da kowane jin dadin rayuwa, ta gwammace ta kula da yaranta har su girma su zama wani abu a rayuwa. Wannan tasa ba ta taɓa bada fuska ga kowane namiji ba. Ta kame kanta, ta kuma rike mutuncinta. Duk nacin mai naci sai dai ya hakura. Haduwarsu ta farko da Hilal bayan shekarun da suka biyo baya, abinda ta soma roƙonsa shi ne gafara. Ta nemi gafararsa akan laifinta kafin ta nemawa mijinta gafararsa. Ranta ya yi haske ta kuma yi godiya da jin cewar ya yafe tuntuni. Daga lokacin ne kuma ya dawo da zumunci a tsakaninsu. Tun tana kaucewa tana dauke kai, har dai ta hakura ta ɗaukeshi matsayin Yaya Munir a wurinta kamar yanda ta ke yiwa Muhibbat kallon yar uwa kuma ƙawa a wajenta. ***    CI GABAN LABARI....      I just published "BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/z1qmOMpjFab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 28) Ana saura kwanaki uku kacal bikin A'isha, Ramlat ta yi kitsonta yiri-yiri da ƙunshi. Da kanta ta ɗaurawa Ummi ƙunshi na gam bisa tilastawar Hajiya don ta rantse Ummi sai an mata ƙunshi. "Kema dai Hajiya, wannan yarinyar za ki dinga biyewa. Ai gashinan ta ɓatan lokaci." Fadin Ramlat sadda ta ke goge ƙafar Ummi da ƙaramin tawul, lallen duk ya caɓa ya haura ba ta zauna ba. "Ko ma mene dai ai ta yi din, ke wane irin caɓar da lalle ne ba ki yimin ba kina ƙarama?" Dariya Ramlat ta yi ganin abin ya juyo kanta.   Ana gobe za'a sanya A'isha a lalle suka shiga kasuwa tare da Rafee'ah, siyayya sosai suka yi na abinda ya rage na kayan daki, maimakon su yi gida, sai suka wuce kai tsaye gidan A'isha dake unguwar Badawa layout suka kai. Anan suka iske masu aikin wuta na ta fama. Sai da suka tabbatar komai sun saka yanda ya dace sannan suka baro gidan. A kan titin Rafee'ah ta saki baki ganin yanda Ramlat ke tuƙi kamar mace. "Ke Ramlat, ki yi hankali da ni wallahi kar ki kashe Baban Daddy ni." Dariya Ramlat ta yi sadda ta sha gaban wata Crv-Honda ta yi gaba. "Kin cika tsoro wallahi, ina nake gudu?" "Kinga ko? Kin gani ki daina wannan over-taking din, ki rufan asiri nidai. Shiyasa na tsani zama gaban mota ko a tafiya ne, haka kawai ki ƙashe ni lokacina bai yi ba." Dariya sosai Ramlat ta yi daidai sadda mai Honda dinnan ya taho da mugun gudu ya sha gabansu. "Wancan dai ya dauka tsere muke da alama, toh ba.." Ai Rafee'ah ba ta iya ta ƙarasa ba ganin yanda itama Ramlat ta fisgi motarta ta kara shan gabansa tana mai duban motar ta gilashinta tana dariya. Ina wuta Rafee'ah ta jefata, nan ta shiga fada kamar ta ari baki. Wai tana mace tana wasa da rayuwarta. "Shikenan naji na daina." Abinda ta ce kenan har sannan dariyar mugunta take. Junction din state road ne ya tsayar da su, anan ne suka tsaya dab da motar. Kamar ance su waiwaya, gaba daya suka dubeshi baki sake, an ci sa'a kuwa ya sauke gilashin.  Mamaki suke da murmushi gaba dayansu, shi kuwa dariya yake musu. "Hilal?" Fadin Rafee'ah wanda ta fi kusa da inda yake. Suka yi dariya a tare. Ita kanta Ramlat ta sha mamakin ganin shi ne. Ba su san shi da wannan motar ba. "Kai Maman Affan, wannan gudun naki gaskiya zai sa mu rabaki da motarnan." Ya fadi yana duban Ramlat bayan sun gaisa da Rafee'ah. "Bar ta, ai ba ka ji yanda ƴan hanjina suka kaɗa ba wallahi. Sai da na gwammace bamu fita a motar ba, dama sai da ta ce mu hau ɗan sahu ni kuma na gwammace na zuba mai mu tafi a motarta." Ita dai Ramlat kauda idanunta ta yi tana murmushi da kuma gujewa kallon da Hilal ke watsamata. "Yanzu ina ku ka yi?" Ya fadi sadda aka soma yi musu horn ta baya, shaidar an bada hannu. A gaggauce Rafee'ah ta ce. "Gida muka nufa." Kai kawai ya gyada ya fisgi motarsa, itama ganin haka ta ɗan bada wuta kadan. "Allah Sarki, wannan bawan Allahn har yanzu fa sonki yake." Ta yi kamar ba ta ji me Rafee'ah ke fadi ba, karshe ma ta ɓige da kunna muryar Umar M Shareef cikin waƙarsa na Zan rayu da ke. Ji ta yi Rafee'ah ta kashe hakan yasa ta dubanta sannan ta kauda kai ta maida titi. "Wato ba kya son maganar ko? Ke abu baya wucewa ne Ramlat? Idan shi ya manta abinda kika yi mishi ya dawo yana bibiyarki, ke kuma a wa da ba za ki mance Aliyu ba ki..." "Don girman Allah mu bar maganar. Ina haɗaki da Allah ki yi shiru." Ta yi ta roƙon Rafee'ah har abin ya dauremata kai, karshe Rafee'ah ta sauke ajiyar zuciya. "Ai shikenan, rayuwarki ce." Ba ta tanka ba illa dai har suka isa gidan ba wanda ya kara magana. Ta lura kowa ya tashi burinsa ta koma gidan Hilal alhalin ita tasan ba mai yiwuwa bane. Ba ma Hilal ba, auren gaba daya ta hakura da yinsa. Ai idan mace za ta iya rike kanta da mutuncinta shikenan. Wannan shi ne tunanin Ramlat. *** Suna shiga kai tsaye wanka kawai ta yi ta sauya kaya sannan ta fita tsakar gidan inda mata ke aiki, wasu aikin sinasir wasu kuwa suna yayyanka albasa. Kowa dai da aikin da ya ke yi, ta wuce kai tsaye cikin sa'anninta su Naja'atu su Maryam. Ana yi ana hira da shewa. Wannan ya fi komai yi mata dadi, ta ji wata irin nutsuwa. Yaran duk suna falon Hajiya su na wasa. Hira suke na abinda ya danganci magungunan mata. Kowacce da kalar wanda take koɗawa a cewar ta ta ga aikinsa sosai. "Ke Maryam, bari na fadamaki wani abu, wallahi kinji rantsuwa ta Allah, wanda na samu wajen Ƴar Maraɗi ba karuwai ba, daidai da masu kishiya, miji bai isa ya haɗa matsayinsu ba. Abin nufi komai naki zai zama daban, za ki bambanta da kowace mace a wurin miji." "Kuma shiga hakki fa?" Ramlat ta tsinci kanta da jefawa Sa'adah ƴar Daura wacce yanzun aure ya maido Kano, tambaya. Sa'adah ta taɓe baki. "Amma dai ai banda kishiya ko?" "Ke Sa'adah, duk da haka fa ba daidai bane. Wasu magungunan ma duk haram ne amma mata son zuciya ya rufemana idanu." Fadin Naja'atu kenan. Nan dai suka ci gaba da tattaunawa game da magungunan da mata ke amfani da shi duk don su samu gurbi a zuƙatan mazansu. "Maman Affan, tun dazu wayarki ke ta ringing." Ramlat dake hawaye saboda  albasan da ta ke yankawa, ta bude idanun dakyar tana kallon wata ƴar uwarsu Dije da ta damƙa amanar wayarta a hannunta. Karɓa ta yi tana sharce fuska gami da dubawa. Lambar baƙonta ne na Mall, ta yi mamakin dalilin kiran kuma a karo na biyu. Me kuma zai ce da ita? Take tambayar kanta, ta share kawai ta koma bakin aikinta, ba jimawa wayar ta ƙara daukar ƙara. Ganin shi ne dai yasa ta miƙewa ta bar wurin tana ji suna mata tsiyar wai ta gaji da nuƙu-nuƙun ta faɗa tarkon wani. "Assalamu alaikum." Shi ne abinda ta ce, maimakon ta ji muryarsa sai ta ji muryar yarinyar ya doki kunnuwanta. "Waalaikumussalam wa rahmatullah wa barakatuhu. Mami." Dan murmushi ta yi, madadin takaicin da ta ji a farko na shiga rayuwarta da mutumin zai soma, sai ta ji sanyi jin muryar yarinyar da ba ta wuce tsarar ɗanta ba.   "Fatima, kina lafiya?" "Lafiya kalau Mami. Ga Dada." Kafin Ramlat ta ce wani abu, tuni ta damƙawa Dada wayar. Sai murya ta ji. A ladabce suka gaisa ta kara da fadin. "Ki yi hakuri fa kin hadu da rigimar Fatima, tun dazu ta matsawa ubannata sai ya kiramata ke kun gaisa wai ita dai tana sonki wataran ya kaita ta ganki." Dariya Ramlat ta yi. "Ba komai Dada." Ta fadi kamar yanda ta ji suna kiranta. Suka ƙara gaisawa sannan suka yi sallama ta katse wayar. Kallon screen din ta tsaya jiki a sanyaye. Tunaninta ya tafi ga mahaifin Fatima wanda kamanninsa tamkar an tsaga kara an karya da Mijin Hajiyar da suka zo ma'aikatarsu. Kodayake, ba nan ne haduwarsu ta farko ba sai dai ya tsayamata a rai. Tsayuwar da kawai so take ta san alaƙarsu da Baban Fatima. Ta kuma sani, ba ta da wani dalilin da za ta fake da shi ta yi tambayar. To wa ma za ta tunkara cikinsu. Ajiyar zuciya ta saki ta koma cikin ƴan uwanta ba ta ko kula jan da suke yi mata ba. Murmushi kawai ta yi don tasan ba wannan ne a gabanta ba. ***   Ranar juma'a aka sanya Amarya a lalle, sai da ta je wurin aiki ta dawo ta iske farfajiyar gidannasu da aka ƙawata da kayan kyale-kyale, ya yi kyau sosai. Babu batun anko, kowa kayansa ya sanya. Ta hade abinta tsaf cikin atamfa Batik kalar orange mai surkin ja. Ba ta yi wani kwalliyar a zo a gani ba, yanda dinkin ya zauna ɗas a jikinta ba karamin kyau ta yi ba. Kai ba ka ce ta haifi yara uku ba. Anyi lalle lafiya, an ci an sha. Amrah da Muhibbat sun zo dukkansu, anyi hira da dariya abinsu tsaf. Sai da Magriba ta doso kafin a soma tafiya yin Sallah, tuni Muhibbat ta wuce.  Ramlat kuwa kasancewar ba ta da Sallah yasa ta miƙewa ta zauna, dole ta tashi ba don ta so ba don Amrah ta rantse sai sun je ta taimaka mata da cirewa Zaituna famfas don tunda ta zo bikin, yarinyar sai ta ƙi zama wurin Ummanta, ta naniƙe mata. "Kedai wallahi kin shiga uku da kwuiyar masifa, ace famfas dinma ba za ki iya fiddawa yarinya ba?" "Naji ko me za ki ce, ki yi ta faɗa. Nidai ki cire din." Fadin Amrah, murmushi kawai Ramlat din ta yi. Suna shiga dakin, ta ji kamar ta juya. Bilkisu ce zaune sai kanwarta Salma, sai wata budurwa da ba ta sani ba. Suna daga gefe zaune yayinda Zulaihat ke dakin tana sallah. Sanin da ta yi ta gaisheta ne yasa ta yi gaba zuwa banɗaki ta bar Amrah suna gaisawa. Ta cirewa Zaituna famfas ta fito daidai sadda Bilkisu ke tambayar Amrah. "Ni kuwa don Allah ba Muhibbat ce tsohuwar matar Aliyu na ganku tare ba?" Amrah ta saci kallon Ramlat da ta dauke kai tana maidawa Zaituna wando kamar ba ta san me suke ba, ta kara duban Bilkisu da murmushin yaƙe. "Eh ita ce." Taɓe baki Bilkisu ta yi. "Shi ne har da zuwa gayyar soɗi? Kai wasu ma akwai karfin hali, wato har gayyatar ta aka yi?" "Gwara da kika gyara Anti, kin yi kiɗanki kuma kin yi rawarki. Ba gayyar soɗi ta zo ba, Ramlat da kanta ta kai mata katin gayyatar." Amrah ke maganar tana murmushin tura haushi. Maimakon haka sai Bilkisu da Salma suka tuntsira dariya. "Wai, Sis? Dan adam ma bai da kunya wallahi." Salma ke fadi tana duban Bilkisu. Ramlat ta dubi Amrah. "Malama kin fasa alwalar ne? Zan koma can kya iskeni." Daga haka ta sa kai za ta fita, maganar Bilkisun ta dakatar da ita. "Yanzu ke Ramlat tsabar rashin ta ido, matar da kika yiwa kwace ita ce yanzun kika dawo kina wani zumuncin neman suna da ita? Ta dai bi a hankali kar a maimaita ƴar gidan jiya." Cak ta kasa koda motsi, juyowa ta yi ta dawo da baya. Ta san take-taken Bilkisun. Tun safe take jefa habaici, ta zagi dangin miji ta zagi kishiya, duk don Yaya Munir zai ƙara aure ne. Zuwanta gidan bikin kusan da biyu ta yi. "Ramlat, fita daga dakin nan." Ta dubi Zulaihat wacce idar da sallarta kenan, ta kara da roƙarta. "Don sonki da Allah da ManzonSa s.a.w nace ki fita." "Ki kyaleta mana, au karya aka fada? Da ta tsayamin kerere tana da bakin magana ne?" Bilkisu ta fadi har tana fidda huci da girgiza ƙafa, dama kiris take jira ta yi musu tas don yanzun cikinsu ta tsani kowa, kallonsu kawai take yi. Mijinta zai ƙara aure tasan har da amincewarsu da na uwarsu. Maimakon Ramlat ta yi magana sai ta  fasa gami da kara rike Zaituna a jikinta su bar dakin. Koda ta koma farfajiyar gidan, kurawa ƴanmatan dake rawa kawai ta yi amma ta kasa cewa uffan. Tunani ta fada, ba Bilkisu ce farkon fadin hakan ba game da alaƙarta da Muhibbat, akwai sadda mahaifiyar Muhibbat din ta isketa a gidan ƴarta, tana jin sadda ta ke yiwa ƴar faɗa akan don me za ta dinga jawota gidanta. Wannan abu ya yi mata ciwo, yana daga dalilan da yasa ta janye jiki daga Muhibbat din, sai dai matar na mata kauna ta don Allah, wannan tasa ba ta rabo da taɓota ta whatsapp ko ta aikomata saƙon gaisuwar juma'a ta text. Dalilin kenan da yasa itama ke ganin kirkinta. Ji da ta yi an taɓa kafaɗarta ne yasa ta kallon mai shi, Amrah ce. Zama ta yi. "Kar fa maganar waccan banzar ya dameki, ai bayan fitarki kamar su doki juna ita da Maman Twins. Wallahi tas ta yi mata har da cewa aure kamar Munir ya yi ya gama. Matarnan ta yi jijjiga da zuba ruwan bala'i, ke da tana da iskokai a ta tayar. Ashe itama Maman Twins ciki take da ita, da safe wai ta mata magana ta dauke kai kamar ba ta ji ba. Sau kusan uku suna hakan, kuma ta ji ƙananun maganganun da take game da auren Yaya Munir tana zagin dangin miji." Murmushi Ramlat ta yi. "Ya ci ace na daina damuwa da lamarinta, na lura ba na ƙare bane." "Atoh, ashe dai kin gane. Ya kamata ki yiwa kanki fada. Damuwa ba ta maganin komai." Gyada kai kawai ta yi, zuwan su Naja'atu ne yasa su sakin zancen a ci gaba da raha. ***   Washegari tun safe suka tashi aka shiga aikace-aikace, sauƙinta ɗaya, wasu ayyukan na abinci, Hajiya bayarwa ta yi order. Kamu da yini ne wanda za'a fita a yi a wani katafaren event centre na masu faɗa a ji. Ango da kansa ya kama wurin.   Karfe uku aka sanya, sai dai halin mutanenmu, ba'a soma tafiya ba sai bayan la'asar. Ƴan matan Amarya ankonsu daban, wata Atamfa ce kalar fari da blue. Fadin irin kyan da suka yi ma ɓata baki ne. Hakanan a ɓangaren ankon sisters, maimakon su uku, (Ramlat, Zulaihat da Rafee'ah), sai ya kasance su duka suka yi har su Naja'atu su Amrah da ma wasu cikin ƴan uwansu na cikin gari. Atamfa ce su ma blue zallah mai adon fari kaɗan kaɗan ba kamar na ƴanmatan ba. Wannan karon sosai Ramlat ta yi kwalliya domin mai kwalliyar aka dauko ta musamman har gida ta yiwa jama'a da dama. Amarya da ƙawayenta kuwa fita suka yi. Wurin ya cika taf, Amarya da Angonta Hisham sun yi kyau har sun gaji. Maza da mata ne a wurin kowanne da nashi ɓangaren. Shiga take tana fita ita da Rafee'ah da su Naja. Amrah karamin cikinta mai ɗan karen laulayi yasa ta samun gefe ta yi zamanta tare da Affan da Zaituna ba tare da ta biyemusu ba. Takan kalli Ramlat akai-akai ta yi murmushi. Ita kanta aminiyarta ta yi mata kyau. Ta jima rabon da ta ganta cikin walwala da farin ciki irin haka, sai ta dawomata Ramlat dinta sak da suna ƴanmata kafin komai ya sauya. Ita kuwa Ramlat, waje ta nufa ta tarbo matan ofis dinsu da suka zo mata takanas bikin A'isha. Halima, Naja'atu Azare, Fa'iza da Zuhra. Halima sai cin magani take don tun a motar Zuhra da ta nemi ayi gulmar Ramlat din, suka ƙi bada fuska ta cika ta yi fam. Yanzun kuwa ganin irin masu hannu da shuni da aka tara a wurin sai jikinta ya yi sanyi, ko ba komai wutsiya raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Ramlat suna da kudi daidai gwargwado, kamar yanda ta lura, dangin Angon su ma ba baya ba. Har suka karasa suka nemi wurin zama ba ta bar mamakin yanda wurin ya haɗu ba. "Malama rufe bakin." Muryar Samira ta katse tunaninta, ta harareta. "Bana son iskanci." Suka yi dariya, ita kuwa Ramlat bayan sun gaisa gaba ta yi ta kyalesu don samar musu abinci. "Hali Dubu!" Halima ta juya tana neman mai kiranta, ido hudu suka yi da Salma ƙanwar Bilkisu, kuma abokiyar karatunta. Nan da nan ta saki fuska ta mike ta nufi wurinta, itama Salma ta nufota suka rungume juna kafin a saki ana shewa da murnar ganin juna. "Kai Salma, dama kina duniya?" Salma ta yi dariya, kiɗan da aka kunna ne yasa ta jan hannun Halima suka ɗan fita daga hall din. "Halima Halee Baby! Kin kama ƙasa kin yi bakam ba'a ji da ganinki kwana biyunnan har a whatsapp." "Wane kama ƙasa aikin da bai taka kara ya karya ba Salma? Kedai muna fatan nan gaba mu kama ɗin, mu samu wani mai hannu da shunin." Suka yi gami da kara cafkewa. "Family din Ango kike ne?" Salma ta tambaya tana dubanta. Taɓe baki ta yi. "Ko ɗaya, yayar Amaryar ce ta gayyacemu. Abokiyar aiki na ce. Ofis din mu ɗaya." "Ramlat?" Fadin Salma cike da mamaki. Itama Halimar kallonta take gami da ba ta dukkan hankalinta. "Kwarai ita fa." Yamutse fuska Salma ta yi. "Amma dai ba ƙawarki ba ce?" "Meyasa ki ka yi wannan tambayar?" Cewar Halima cikin zaƙuwa. "Tab, kin tuna auren wani Cousin brother dina da na ba ku labari a WhatsApp? Wanda nace maku matarsa ta kusa kashe shi ranar da aka kai ta gidansa?" Da sauri Halima ta shiga gyada kai kamar ƙadangaruwa. "Yes yes, na tuna!" "Toh ai ita ce. Sanadin da ya saketa kenan, ta dage da auren wani Aliyu. Na fadamaki sai ya yi shaye-shaye ya zo ya yi mata tsinanan duka ya kyaleta ba ci ba sha. Dakyar dai ta samu salama bayan mutuwa ta rabasu. Ni naji ma Anti Bilki na cewa wai Ƙanjamau ta kasheshi." Halima ta saki baki da hanci kafin ta yi wata dariya. "Ke Salma! Ki rantsemin da Allah." Salma ta ja tsaki. "Na taba yi maki irin wannan wasan? Lallai ma, ai yanzu ta ƙi auruwa kowa tsoronta yake ji. Ku dai bi a hankali da ita ko a ofis kar ta shafamaku mugun abu." Halima wani dadi da farin ciki ya mamayeta, wannan labarin ya fi komai yi mata dadi. Ko ba komai anan za ta huce haushin tsanar da ta yiwa Ramlat da cin mutuncin da ta ja mata a ofis. Suka yi sallama da Salma suka dawo wurin bikin, a hanyar ma sai ƙaramata gishiri da siga ta ke yi. Abinda aka yi da wanda ma ba'a yi ba duk ta haɗa ta faɗawa Halimar. Burinta itama ta ɓatawa Ramlat suna a ko'ina. Koda Salma ta koma mazauninta, gaba daya ta kwashe yanda suka yi da Halima ta fadawa Bilkisu. Dadi kamar ya kasheta. Har kyauta ta ce za ta yi mata. Suka yi ta dariya ransu fari ƙal. A ɓangaren Ramlat kuwa, haka ta yi ta hidima da ƴan ofis dinsu har suka tafi, ta yi mamakin yanda Halima ta sakarmata kamar ba ita ba. A karshe ta yi musu rakiya har wurin mota bayan ta kaisu sun gaisa da Hajiyarta sun mata fatan alheri. "Amma zaku zo dinner goben ko?" Ta fadi sadda ta kama murfin motar tana dubansu. "Me zai hana? Za mu zo." Halima ta fadi cikin sauri. Duk suka dubeta. Ba wanda ya yi magana suka amsawa Ramlat da cewa zasu zo. Ta kuwa ji dadi ta yi godiya. Daga nan suka ja suka bar wurin ta koma ciki. *** WASHEGARI... LAMIƊO CI just published "BABI NA ASHIRIN DA TARA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/FLZKsoqJJab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 29) LAMIƊO CRESCENT A hankali ya ɗago kai daga kallon jaridar da ya ke ya maida saman fuskar wayarsa dake faman ruri a saman tebur. Murmushi ya yi, irin murmushin da idan har ka gani saman fuskarsa to bai ɗauki mutum nan kusa ba. Ko sallama bai kai ga yi ba ya soma yi mishi mita. "Kai dai wallahi anyi ɗan iska, wato dagasken dai ba za ka zo ɗaurin aurena ba ko? Ni za ka yiwa wannan tsiyar!" Dafa goshinsa ya yi gami da ɗan runtse ido. "Oh no, dagasken gaske na mance fa. Yi hakuri." "Hakuri kake bani? Ba zan hakura ba wallahi muddin ban ga ƙeyarka a dinnerparty ɗina ba! Ka kyauta sosai!" Hisham bai jira cewarsa ya katse wayar, sakaka ya bi wayar da kallo kafin ya ajiye yana murmushi. Tunda ta soma taka matattakalar benen idanunta gaba daya a kansa, yanda yake murmushi ya sanya ta jin wani abu mai kama da kishi ya soki ƙahon zuciyarta. Kaf duniya ba ta jin akwai wanda ya isa shiga rayuwar mijinnata har ya sanyashi ya murmusa idan ba ita ba. Tunaninta gaba daya ya tafi ga zargi kamar yanda ta saba, wato da mace yake waya. Wannan ya ƙaramata saurinta ta shiga haɗa step bibbiyu tana saukowa, ikon Allah ne ya kawo Hajiya Zeenatu cikin falon ta yi mishi kerere a ka.   Ya ɗago ya dubeta gami da lumshe idanu ya bude. "Me akai?" Ya nemi sani cikin halin ko'inkula. Hannu ta kai ta ɗauki wayarsa ta shiga sarrafawa don tunda suke bai taɓa sanya password lock a wayarsa ba, koda zai sanya, Hajiya Zeenatu ta san mabuɗan, abin da ke ba shi mamaki, ba shi da hurumin da zai ɗauki wayarta ya sarrafa yanda ta ke sarrafa nasa.   Bai katseta ba har ta gama shiga da ficenta, asalima maida hankali ya yi ga jaridarsa, zuciyarsa na jin ciwon abinda ta ke aikatawar, bakinsa ya kasa motsawa balle ya tsawatarmata, bai ji yana da jarumtar da zai ce ba ya so ba.   Zama ta yi gefensa  gami da riƙo hannunsa tana murmushi, ya dubeta ya maida martani wanda ya fi kama da yaƙe. "Ashe fa Hisham an yi aure? Gaskiya bai kamata ace ba ka je daurin aurensa ba." Ya jinjina kai yana dan yaƙe. "Hakane, yanzun ma ya ce lallai fa sai naje mishi Dinner." Ta yamutse fuska. "Wane irin dinner kuma? Salon ka je wata ƴar iska ta ganka ta nuna tana sonka? Abinda ba zai yiwu kenan ba, ya yi hakuri daga baya idan sun tare sai muje har gida mu ga Amarya." Ya dubeta ya ɗan ɗaure fuska, yana jin kamar ta ragemishi wani farin ciki  a rayuwa, sai dai ita din ba ta laifi koda ace uwa da ubansa ta zaga. "Shikenan, duk yanda kika ce, hakan daidai ne."   Hajiya Zeenatu ta yi murmushi mai kyau har ruwan ɗorawar hakoranta suka bayyana. Ya kauda kai, ta shafi gefen fuskarsa. "Shiyasa nake ƙara sonka mijina ni kaɗai! Zan fita sai na dawo." Gyada kai kawai ya yi sannan ta mike, doguwar rigar shadda ce a jikinta sai wani karamin mayafi da ta yafe kanta da shi, san shigar bai mishi tsarin da matar aure za ta fita da shi ba. Ya kauda kai gami da sauke ajiyar zuciya. Inda za ta je ma bai sani ba, ba jimawa dai ya ji tashin motarta. A hankali ya kwantar da kai jikin kujera gami da lumshe idanu. Yana bukatar tunani, sai dai tunanin ya jima da gushewa. Duk kokarinsa, duk irin yaƙin da yake da zuciya da kwakwalwarsa, sun kasa ba shi haɗin kai. Kamar yana aka saba ne ya afku, matsanancin ciwon kai wanda ya sanyashi hakurin dole ya miƙe ya haye sama. ***   Tun ƙarfe takwas na dare farfajiyar ƙawataccen Event Centre din na Marhaba, ya cika ya batse da yan mata da samari matasa sai tsirarun iyaye. Kwalliya iri-iri kawai ka ke gani. Wasu tuni suka shige dakin taron yayinda wasu suka tsaya ƙyam jiran saukar Amarya da Ango. Tana daga can gefe tsaye cikin wani arnen baƙin lace, ta ɗora silver head. Ummi kadai ce ta biyota wurin taron, zaman ɗankwalinta take gyaramata tana faɗan muddin ta ƙara cirewa sai dai ta nemi mai ɗauramata don ita ba baiwa ba ce. "Ni kuma bawa ne, na yarda na amince idan har ƙarƙashinki zan yi aiki zan yi din koda ba biya." Tun soma maganar ta juya tana kallonsa. Ya haɗe cikin wata gogaggiyar shaddarsa ruwan ƙasa, murmushi kawai ya ke yana dubanta babu ko kyaftawa. "Uncle Hilal!" Faɗin Ummi kafin ta fisge jikinta daga na uwar ta yi gaba a guje ta rungumeshi. Ya durkusa yana mai ɗago fuskarta yana dariya, dariyar ba ta komai ba ce sai na ganin yanda Ramlat ta haɗe fuska don Ummi ta tafi ta bar ta da ɗankwali a hannu wanda ya warware gaba daya sai jerin ƙananun kalbar da aka yi mata ke yawo a iska. "Kin ƙara yiwa Mami laifi. Kinga." Ya yi mata nuni da Ramlat, ganin haka Ramlat ta kauda kai bayan ta watsawa Ummin harara, ta rufe motarta ta jefa muƙulli jaka ta nufosu. Ganin hakan yarinyar ta tsorata ta yi bayan Hilal da sauri gami da fadin. "Mami please ki yi hakuri, sunan Hajiya fa ne da ni." Kusan da hakan ta saba cin galabarta, Ummi akwai wayo da saurin ba da hakuri bisa laifi. Kusan dariya ta basu daga ita har Hilal din. Ya mike tsaye bayan ya yakice Ummi dakyar a jikinsa. "Ba za'a yi mata afuwa ba?" Ta ɗan harareshi tana murmushi, ya lumshe idanu ya budesu a kanta, sai kuma sannan ta farga da katoɓarar da ta yi, ko meye na yi mishi murmushin? Da saurinta ta kauda kai ta soma tafiya da nufin barin wurin.  Riƙon da ya yiwa ɗankwalin Ummin ne yasa ta kallonsa, kasancewar ya tarkata dukkan nutsuwarsa a kanta yasa kai tsaye idanunsu suka sarƙe cikin juna, ta yi saurin janye nata idanun.     "Ana kallonmu fa." Ta furta a ƙagauce, zuciyarta har zafi ta soma. Takaici da haushin kanta ne ke mamayeta. Wani sashi na zuciyarta ihu yake mata, yana mata tunin bai kyautu ace har ta mance baya ba. Bai kyautu ta saurari kowane namiji ba, ko ba komai ta yiwa kanta alƙawarin gudanar da rayuwarta babu aure, ta raini yaranta har su zamo abin alfaharinta duniya da lahira. "Lah, Yaya Hilal?" Kusan a kidime ta kai duba ga mai maganar, Salma ce tare da Halima. Zuwan su Halimar kenan ta ha hannunta don ta yi mata hotuna. "Ramlat?" Fadin ita Halimar. Lokaci guda Hilal da Ramlat suka dubi juna kafin ta kauda kai da sauri ta sakarmasa ɗankwalin Ummin ta yi gaba wurin Halima. Murya na rawa ta ce. "Ha..lima., yaushe ku ka zo?" Halima wacce a farko bakin cikin hadadden gayen da ta gani tare da Ramlat ke tafarfasa zuciyarta, ta ji wani sanyi jin da ta yi  Salma ta ambaceshi da Hilal, wato shi ne dai wanda Ramlat ta gujewa aurensa. 'Marar rabo.' Ta fadi a ƙasan ranta, a fili kuwa murmushi ta yi tana wani ƙwarkwasa a sonta ta burge Hilal. "Bamu jima da zuwa ba, ashe kina nan kina tsinkar fure.  Ki ce shiyasa ki ka ƙi sauraron Oga. Kina da zazzafa a hannu." Kalaman Halima wanda da biyu ta yi, ya kara baƙantawa Salma rai, ta karasa ga Hilal a zafafe. Ita kuwa Ramlat kallon ba ki kyautamin ba ta watsawa Halima ta yi gaba, Ummi ta rarumi dankwalin ta bi uwarta a guje tana kiran ta ɗauramata.   Salma kuwa ta dubi Hilal cike da bakin ciki. "Yaya kar dai ka cemin ka dawo a karo na biyu zawarcin Ramlat? Duk abinda ta aikata gareka ka mance?" Daure fuska ya yi yana kallon yarinyar da duka-duka ba ta dade da daina yoyon majina ba, a cewarsa. "Ke, yaushe muka soma ƴar haka da ke? Sa'anki ne ni?" Ta ƙara turɓune fuska, zarginta dai ya tabbata. Tasan idan ta kara magana to zai iya yi mata duk abinda ya so, wannan ne dalilinta na juyawa fuu ta ja hannun Halima su bar wurin a fusace. Ta kuma rantse babu mai dakatar da ita daga faɗawa su Anti Fa'iza da Murja, ko ba komai ta hanyarsu saƙon zai fi saurin isa kunnen iyayen Hilal waɗanda suka rantse ko bayan ransu basu yarda da aurensa da Ramlat ba koda hakan akwai yiwuwarsa. Wannan rantsuwa ce da umarni da suka faru tun Ramlat na gidan Aliyu, tun sadda ta fusata zuƙatan iyayensa.   A ɓangaren Ramlat dakyar ta samu ta maido walwalarta sai dai ko yaya ta waiga ta hangi Halima manne da Salma sai ta ji wata irin faɗuwar gaba, a bakin Naja'atu Azare take jin ashe sun san juna tun suna B.U.K.  Jin hakan bai ƙare ta da komai ba sai ƙarin fargaba. Ana kammala dinner, Ango Hisham ya wuce da Amaryarsa gida don dama sai da aka kai ta sannan aka taho Dinner. Daren ranar baccin Ramlat rabi da rabi ne, tunaninta me zai biyo baya don ta tabbatar dole Salma ta sanarwa Halima wani abin da ya danganci rayuwarta ta baya, tana ganin kiran Hilal da text dinsa akan yana so su yi magana koda ta mintuna ne amman ta ƙi ɗagawa, a ƙarshe ma ta kashe wayar gaba daya.   "I am sorry Hilal." Ta furta a fili yayinda wasu zafafan hawaye suka zubomata ta ɗaukesu da tafin hannu. *** Ta shiga ofis dinsu da sallama tana mai duban abokan aikinta. "Yau dai Hajiya Ramlat kin so makara." Ta yi murmushi tana duban Salihu mai wannan furucin, ko kusa ba ta son jaye-jayen wasa hakan yasa ta wucewa bayan ta gaida kowa ta zauna a mazauninta. Matan ta duba da mazan da suka halarci daurin aure ta yi musu godiya da fatan Allah Ya kara dankon zumunci daga nan ta maida hankali ga wani aiki da Oga Ɗalhatu ya ba ta tun wancan satin. Ta dukufa wurin aiki, Ofis ya cika irin cikar da ta tsana, wato ƴan wasu ofishin su shigo nasu domin hira, wannan yasa tunda ta sunkuyar da kanta ta wasu rubuce-rubucenta a computer ba ta ɗago ba, kamar yanda ta daure fuska kamar ba ta taɓa dariya ba musamman ganin har da Oga Ahmad wanda ke kokarin sanyata a hirar tana ƙi. Babban abinda ke ba ta mamaki wasu cikin matan ma da aurensu amma yanda suka zage kamar ba auren a kansu. Kamar da wasa ta ji Halima ta zage tana bada labarin da nan take ya sanyata gumi duk kuwa da irin sanyin Ac da ke kaɗawa a ɗakin. "Toh ai yanzu zamanin ne ya sauya. Soyayyar da ƙarfi da yaji ma kwatarta ake yi Oga. Sai na tuno da labarin wata da aka bani, ranar da aka kai ta ta nemi kashe Angon saboda ba ta sonsa, aikuwa ya saketa ta auri zaɓinta amma fa ta ci gidansu. Duka, zagi ba wanda ba ta sha ba. A karshe dai yanzu sun rabu, ta na nan kuma ta dawo tana bin shi saurayinnata na farko kamar jela, kai ka ce karyar da ta hango ƙashi, nema take ƙarfi da yaji sai ya aureta." Buɗar bakin Oga Ahmad ya ce. "Ai wallahi ta yi kaɗan don ubanta! Wannan ma an yi ƴar iskar gaske. Au sai da ta ga rayuwa za ta dawomin?" "Ni kuma da ni ne, zan aureta ko don na koyamata hankali. Sai na sa ta raina kanta fiye da yanda wancan na farkon ya rainata." Fadin Salihu kenan har da cire hula hira ta yi dadi. Abin sai ya koma kamar muhawara, wannan ya kawo nashi, waccan ta kawo. Halima ta saci kallon Ramlat yanda nan take ta fice hayyacinta, ta kauda kai tana wani irin murmushi, ji take kamar nan duniya ba ta taɓa samun farin ciki da walwala kamar ta ranar ba. Zaman ofis din ya gagareta, ta tabbatar idan ta ci gaba da zaman to fa ruɗun da ta shiga zai bayyana kowa ya gane. Tsalam ta mike gami da daukar jakarta, hannunta har rawa yake ta zura takalminta da ta cire don kafafun su huta kai tsaye ta nufi hanyar fita. "Ah, Ramlat ina za ki je kuma? Da sauran lokaci fa a tashi." Fadin Halima kamar ta daka tsallen murna, Ramlat ta juya ta watsamata wani banzan kallo ita kuwa ta murmusa gami da kashemata ido ɗaya. Wannan ya kara ba Ramlat tabbacin da gayya ta yi. Tana sane ta yi mata abinda ta yi din.   "Ba ta ko saurari kiran da wasu cikin ofishin ke mata ba, ta bude kofa ta fice. A hanyar baranda suka ci karo da Ogansu Ɗalhatu. Ya dubi agogo, sauran bai fi mintuna talatin ba a tashi. "Ramlat, tafiya? Lafiya kuwa?" Ta dubeshi dakyar, ba don ya zamto shugaba ba a gareta, za ta iya giftashi kawai ta wuce don yanda ta ke jin kanta. Yaƙe ta yi. "A yimin afuwa Oga don Allah, ban jin dadi dauriya nake." Cike da tausayawa ya ce. "Assha, sannu. Allah Ya ba ki lafiya. Ko dai na sanya a kaiki?" Ta girgiza kai. "A'a zan iya tafiya ba komai. Nagode." Zai kara magana tuni ta giftashi ta wuce da sassarfa. Sai dai tun kafin ta karasa ga motarta, hawaye sun wankemata fuska, hannu na rawa dakyar ta iya bude ƙofar motar ta shiga. Kuka sosai ta ci fuskarta cikin mayafi, dakyar ta iya dauriyar share fuska ta yi ribas ta fita.   Rabin tuƙin yinsa take yi ba'a nutse ba. Abinda ta ke gudu ya faru, a hankali abinda ta shuka ya soma fitar da tsirrai, tana tsoron ya fidda ƴaƴan da zasu nuuna har nata ƴaƴan su samu rabonsu. Tun ba'a je ko'ina ba, komai ya soma bayyana. A yanzun da tsoro ya shigeta, tana ji a ranta za ta iya barin aikinta idan har hakan zai tseratar da mutuncinta da na yaranta a idon duniya. Za ta killace kanta a gida. 'Kin manta cewa watan watarana dama sai rana makamancin wannan ya zo? A gidan a tunaninki kin tsira?' Ta hau gyada kai kamar ƙadangaruwa  kamar mai ganin zuciyarta a fili. "Zan tsira, yarana ba zai shafesu ba tunda ba su da laifi! Ni mai laifin a yimin kowane irin zagi zan jure!" Tana maganar a fusace ita daya a mota, ba ta yi aune ba ta kai dab da dab da wata mota, duk kokarin ganin ta ci burki hakan ya faskara har sai da ta daki bayan motarsa. Masu salati na yi hakanan masu fadin kai! Kai! Suma suna nasu. Luguden da zuciyarta ke yi ya ƙaru, ɓacin ranta ya ninka na farko. Ta kasa koda motsi, ta kasa fitowa balle ta je ta ba mai shi hakuri ta nemi gafararsa. 'Da ka san damuwar da ke cikin zuciyata, da ka yimin uzuri kamar irin wanda na taɓa samu a wajen wani...' Ta kasa ƙarasa zancen zucinta ganin wacce ta fito daga mazaunin kusa da direba. Shakka babu fuskar ba ranar ne farkon ganinta da ita ba. Fuskar da ta zo har ofishinsu.   "Isa da taƙama za ki nunamana?! Kin yiwa motata illa kin zauna kin hakimce ko gezau? Ke ƴar gidan uba wace ce?!" Sanin da ta yi ita din mai laifi ce yasa ta fitowa daga nata motar, har lokacin akwai hawaye a fuskarta. Wannan hargagin na Hajiya Zeenatu bai dameta ba kamar yanda sanyo ubanta ciki ya yi mata zafi, ko ba komai shirunta ya jazamata.   "Kiyi hakuri don Allah." Ta fadi tana haɗiyar yawu, damuwar da ke ranta ma ya isheta. Kowa ya yi mata caa akan ba ta kyauta ba yayinda Hajiya Zeenatu ta dage akan lallai sai ta raina kanta, sai ta biya ɓarnar da ta yi mata.   Ramlat kallonta kawai ta ke sakaka, ita ta ma rasa me za ta ce da ita. Hakuri kawai ta ke bata don ba ta jin yin faɗan musamman a yanzun da ta ke jin tsanar kanta har cikin ranta. Basu yi aune ba sai jin ƙarar murfin mota suka yi, hankalinsu ya kai gun. Kowa kallonsa yake har ya ƙaraso yayinda Ramlat ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru, ba ta taɓa zaton wani abu zai ƙara sa ta ganshi ba. Yanzun kan ta yi amannar ba zai kyaleta ba sai ta biya ɓarnar da ta yi musu, ko ba komai yanzun zai ce da gayya take mishi ta'adi. Shi kuwa koda ya ƙaraso kallonta ya yi na ƴan sakanni, kallon sani ya yi mata, kallon na ganeki. Ta kauda kai shima ya kawar, kallon da ya kai Hajiya wuya, ta daga hannu da nufin marin Ramlat, caraf ya riƙe hannun. Jama'a aka saki baki don diramar ma tafiya yanda ya kamata, an baza baki da hanci, go slow kam sun haɗa, masu zagi na yi, masu tsayuwa kallo suna nasu aikin. Hajiya ta dubeshi a fusace. "Ita yar iskar ina ce za ta tsaya tana ƙaremaka kallo?! Dama nasan ai da biyu ta bugi motar! Na ganeta! Ba ita ce wannan marar kunyar ba ta Revenue? Za ki san ki taɓoni!" Daga haka ta fisge hannunta ta yi gaba, Ramlat na hawaye ta ke kallonsa. Bakinta ya yi nauyi, dakyar ta motsa. "Ka yi hakuri. Wallahi ba da gangan na aikata ba." "Ba komai." Ya fadi ƙasa-ƙasa, daga nan bai ce uffan ba ya wuce ya shiga mota ya ja suka bar wurin. Itama motarta ta shiga tana ji wasu na fadin. "Ke kam Allah Ya so ki da rahmarSa. Tab!" Wasu kuwa cewa suke. "Ina rahmar? Ba ku ji me Hajiyar ke fadi ba? Da alama ta san ma'aikatar yarinyar, za kuwa ta yi mata sanadin barin aiki." Ita dai Ramlat wacce kanta ke bala'in sarawa, ta ja motarta dakyar ta bar wurin. Koda ta isa gida, Hajiya ta tambayeta abinda ya faru ganin yanda ta yi kaca-kaca, idanunta jage-jage da hawaye. Ba ta ɓoyewa Hajiyar komai ba. Ranta ya ɓaci. "Ai ga irinta nan! Ga irin ABINDA AKE GUDU nan Ramlat! Shekara nawa da wucewar abu, yanzu gashinan yana bibiyarki. Ita kuwa wannan Hajiyar a zatonki za ta kyaleki ki ƙara taka ma'aikatarku? Uhm, Allah Ya kyauta." Daga nan Hajiya ta yi shiru tana huci, ta tausayawa Ramlat amma fa haushinta ba ta da matakin dauka, ba ta da abin yi don kuwa Ramlatun ce ta fara ɓatawa kanta suna. Har Ramlat ta yi ɗaki ba ta ce mata uffan ba. Ta kudurce a ranta za ta bar aiki, sai dai kuma ta ya za ta dinga wasu cikin hidindimunta har ta taimakawa gida da yaranta? Ta mirgina saman gadon gami da lumshe ido. Can kuma ta buɗe su cikin zurfin tunani. Ya yi daidai da dawowar yara daga islamiyya, gaba daya suka shigo ɗakinta suna mata sannu da zuwa. Tana murmushi ta mike zaune. "Kun dawo?" "Eh, yau Affan bacci ya yi ta yi a aji." Cewar Ansar, Affan kuwa ya yi lamo jikinta, ta shafi kan yaron tana murmushi. "Wai haka?" Ya gyada kai, bai iya ƙarya ba ko don tsoro. Suka cikata da surutu, dakyar ta korasu su wuce chanja kaya. Aliyu ya faɗomata a rai, mutumin da ya bar duniya bayan ya yi kyakkyawar shahada, shi ne ake jefamata bakar magana ake yayata abinda ta aikata dominsa? 'Ko me ya faru, laifinki ne.' Ta shiga gyada kai tana gaskata sashi na zuciyarta dake tunasar da ita hakan. Shakka babu laifinta ne. Dakyar ta samu ta shafe babin a kwakwalwarta ta mike ta shiga wanka. Ta san ƙaryarta ta iya barin aiki saboda Hajiya Zeenatu. Addu'a ya fiyemata komai. Shi ne makamin kowane mumini. *** "Aikin banza! Kaima ai kallonta ka tsaya yi! Akan wane dalili?" Hajiya Zeenatu ke wannan kalamin, tun dawowarsu gida duk inda ya saka ƙafa sai ta bishi da zafafan kalamanta na zargi. Idanunsa suka kaɗa, zai shiga wanka ta nufi kofar banɗakin. "Wankan me za ka yi? Wato ba ka ga girman laifin da ka aikata ba ko? Shi ne har za ka shiga wanka?! Wallahi ka jawowa yarinyarnan! Sai nayi mata sanadin aiki! Sai na wulakanta ta!" "Daga ranar da kika sanya aka koreta aiki, ki kwana da sanin da kaina zan dauketa aiki a Office dina!" Cak! Ta tsaya,ta kasa kwakkwaran motsi, dakyar ta iya haɗiye yawun da ya tararmata a baki. Cikin tsananin mamakin kalamansa ta ke dubansa. Wannan ba Hussein din da ta saba juyawa ba ne, bai yi mata kama da wanda zai ɗauki wargi ba. Kalamanta ba su ƙara kashemata jiki sun jefata ruɗu ba sai da ta ƙara tsintar muryarsa. "Yes Zeenat! Ina miki rantsuwa da Allah daga ranar da kika yi kuskuren raba yarinyarnan da aikinta sai ta dawo aiki a ƙarƙashina! Idan kishi na kisa, ya kashe ki! Haba! Wannan wane irin masifa ne! Wane irin takunkumi ne? Kin hana mace ko ɗaya aiki a gidanki, kin hana na yi aiki da mace a ofis! Babu dama ki ga mace ta kirani ko ta yimin magana ta media sai ki ɗau zargin duniya ki aza a kaina! I'm fed up! Nifa ba yaro bane!" Daga nan ya gifta ya shige banɗaki gami da banko ƙofar har sai da ta tsorata. Gumi ke tsiyaya daga saman fuskarta duk da Ac dake gudu a dakin. Safa da marwa ta shiga yi gami da kwance ɗankwalinta, akwai babbar matsala! Akwai abinda ke shirin faruwa. 'Ko ita ce yarinyar da Gora ya gargadeni a kai?' Ta fadi a kasan ranta, shekarun baya da suka gabata, Gora ya gargaɗeta akan abinda zai iya afkuwa muddin ba ta kula da lamarinta da Hussein ba. Ya tabbatarmata ita ce za ta zamo silar rushewar kowane aiki. Wannan ne dalilin da har gobe ta ƙi jinin kowa ya raɓarmata Hussein. Namiji daya tamkar da dubu a rayuwarta. A kansa ta aikata abinda acewarta shaiɗan ba zai iya ba. "Dole na dauki mataki!" Ta furta a fili kafin ta fice daga dakinsa zuwa nata a gigice.I just published "BABI NA TALATIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/5Py5Xl04Mab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 30) Wannan abu da ya faru, sai ya ƙara ragewa Ramlat walwalarta a Ofis. Tambayar duniya ƴan ofis din sun yi amma ta nunamusu ba komai. Tsakaninta da Halima gaisuwa kawai, daga nan ba ta kara bari wani abin ya shiga tsakaninsu. Ga Halimar hakan ba karamin dadi ya yi mata ba, ko ba komai ta samu wani makami wanda yake ganin a koyaushe za ta iya rushe Ramlat din da shi. Wannan girma da ƙimarta da ake gani a daina. ***   Bayan sati daya da auren A'isha, ranar Lahadi misalin karfe uku na rana, Ramlat ta shirya cikin riga da skirt na leshinta ja, ya yi mata kyau sosai, fuskarnan banda hoda ba abinda ta shafamata, sai gidan A'isha. Nan ma sai da A'ishar ta yi ta roƙonta akan ta zo. Abin ita har mamaki ya ba ta, yarinyar da basu fiye ɗasawa ba, raini ya shiga tsakaninsu, yau ita ke nemanta? Murmushi ta yi, aure ba karamin gyarawa mutum zama yake ba. Kodayake me akai da maza ma? Ɗan sahu ta hau zuwa gidan A'isha,   su Ummi tun safe Muhibbat ta zo ta ɗaukesu don halartar taronsu na Zuri'a. ***    Kai tsaye ta shiga cikin falon da sallamarta, A'isha ta amsa tana mai fitowa daga kicin cike da zumuɗi da jin dadi. "Kai Maman Affan, wai sai yanzu? Wallahi kamata ya yi ki zo tun safe ki wuni." Harara ta ɗan watsamata tana murmushi. "Ko? Ga babbar kobo, to ban iya wannan katoɓarar ba." Dariya A'isha ta yi, ita kuwa Ramlat sai bibiyarta take da kallo yanda ta yi fresh ta yi ɓulɓul abinta tsaf. "Toh don Allah ku din ne ba wanda na ƙara gani a gidannan, nasan shirye-shiryen auren Yaya ma zai iya ɓoyeku amma ai ba hujja ba ce." Taɓe baki Ramlat ta yi tana mai ajiye jakarta. "Ke ni rabani, ba wani shiri da nake yiwa bikinnan. Inace dai mijinki ba ya nan?" Ta tambaya sadda ta dakata da yaye mayafinta da take shirin yi. Girgiza kai A'isha ta yi. "Ya fita amma ba jimawa zai dawo, abokinsa ne zai zo  shi ne ya fita yin cefane. Ni wallahi naji dadin zuwanki, ko ba komai za ki taimaka mu shirya daddaɗan abinci." Ramlat ta ji inama ba ta zo ba. Ba taya girkin ne matsalarta ba, ba ta so Hisham din yana gida ba ne. Dakyar A'isha ta samu ta lallaɓata ta zauna. Ba jimawa kuwa sai ga Hisham. Shi kansa ya ji dadin ganin Ramlat, mutum ne mai barkwanci don ko kadan bai tsaya wani kunya ko ƙumbiya-ƙumbiya ba. Itama ganin haka ta ɗan saki jikinta, daki ya shige su kuwa suka nufi kicin suka shiga aiki, Ramlat na mitar inama ba ta zo ba. Ita dai A'isha ba ta iya magana ba don tasan yanzun sai ta fadi abinda zai sa ta bar gidan ba shiri. Sai da suka yi la'asar suka faɗa kicin. Fried rice suka yi wanda ya sha hanta. Suka yi chicken pepper sai hadin salad da lemun Mango. Komai suka jera saman tebur, A'isha ta shige don yin wanka. Ita kuwa dakin da ke falon ta shige ta hau shirin tafiya gida. "Gaskiya Antinmu ba inda za ki je, ki yi hakuri mu ci abincin gaba daya. Na rantse har gida zan kaiki." Hisham ke maganar cikin alamun roƙo. Duk yanda ta so ta ƙi hakan ya gagara, magiya irin na Hisham sai da ya ci galaba a kanta, ta kara duban su da zummar magana, wayar Hisham ta yi ƙara. Ya dubesu kafin ya ce "Inaga ma ya ƙaraso. Bari na fita." Daga nan ya fice, dole Ramlat ta koma ta zauna A'isha na mata dariya. ***   Hussein ke tuƙin, Hajiya Zeenatu tun washegarin rikicinsu ta yi tafiya zuwa Abuja wurin Aminiyarta a yanda ta sanarmishi sai dai a zahirin gaskiyar  Nijar suka wuce. Wannan karon wajen wani buzu za ta je don samarwa kanta mafita. Dama an dade ana ba ta labarinsa.    Waya yake cikin nutsuwa, sai ka nutsu za ka san me yake fadi. Magana yake fitarwa kamar ba ya so, a zahiri haka muryarsa ta ke. Motsa bakin yake kamar ba ya motsawa. Ya yi parking a wani madaidaicin gida, ya sa hannu ya bude murfi ya fito. Hisham dake tsaye ya ƙaraso suka cafke suna dariya. Ya haɗe cikin shaddarsa blue. Ya dora hula mai adon fari da ruwan blue. Sai yatsunsa biyu na dama da basu rabo da zoben azurfa guda biyu, sai agogo ruwan silver da ya ɗora.  A Gym suka soma haɗuwa da Hisham, har yawan haduwartasu ya sanya shakuwa mai ƙarfi ya shiga tsakaninsu. Hatta da Hussein ya yi mamaki don bai zaci zai sakarwa kowane mutum fuska ba har su zama abokan juna. To sai ya kasance Hisham mutum ne wanda nan da nan za'a iya sabo da shi, yana da barkwanci sosai. Duk da irin abotarsu, sai ya kasance a waje. Koda wasa bai taɓa gayyatarsa gidansa ba balle ya fadamishi wani abu da ya dangance shi. Shi ɗin dai ya gayyaceshi sun gaisa da iyayensa ba sau daya ba kuma ba biyu ba. "Kamar ni a yi bikina a ƙare shi ne ko ƙeyarka ban gani ba ko? Daidai kenan?" Taɓe baki Hussein ya yi. "Kana da mita. Hakurin ne ba za ka iya ba? Ba abin tada jijiyar wuya a abinda ya wuce." Hisham ya yi ƙwafa, shi kuwa murmushi kawai ya yi, har suka karasa ciki suna ɗan hirarsu. ***   A'isha ta mike ta fito daga ɗakin ta bar Ramlat kwance saman katifa. Sun gaisa da Hussein kafin Hisham ya dubeta. "Ki cewa Yayarmu ta fito don Allah." Ta amsa da toh tana murmushi sanin halin ƴar uwarta, ba lallai din ta yarda ta fito ba. Aikuwa kamar yanda ta zata hakan ne, cewa ta yi ba ta ga dalilin fitar ba tunda ba ita ce matar gidan ba.   Yanda ta faɗa haka A'isha ta kai saƙon ba surki, abin sai ya Hisham dariya shi kuwa gogan kamar bai san ana yi ba. Wayarsa yake amsawa da Hajiya Zeenatu wacce ta tafi kamar ba ta tafi ba, bini-bini za ta kira ta ji a inda ya ke. A karshe ma cewa ta yi za ta gaisa da Hisham din. Ya cire wayar a kunne ya miƙa wa Hisham. "Madam." Hakan da ya faɗa ya ankarar da Hisham ko wace, suka gaisa sai dai ya ɗan yi turus jin muryar kamar ta babbar mace amma bai nunamishi ba. A karshe ya mikawa A'isha wayar kamar yanda ta buƙata. Ita kanta ta yi mamakin jin muryar mace kamar Hajiyarta. Abinda ta kawo, matar ƙatuwar murya gareta ne kawai, banda wannan ba wani abu. Sai da ta kawowa Hussein ruwa da lemu kafin ta koma wurin Ramlat. ***   "Kai kin ganshi? Wallahi kamar wani buzu." "Astagfirullah, ke fa matar aure ce." Ramlat ta katseta da sauri. Anan itama ta ankara da katoɓarar da ta yi, ta ja istigfari kafin ta yi dariya. "Allah kuwa ban faɗa don wani abu ba, kawai dai na ganshi ɗan gayu. Da ace ba ki taɓa aure ba kuma ke fara ce, ba karamin matching za ku yi ba." Daure fuska ta yi, ta ɗan ji takaicin kalaman A'isha, sai ya ɗan yi mata fami da irin cin zarafin da Halima ta yi mata a ofis. Ganin yanda fuskarta ta sauya ne yasa A'isha gyara zancenta. "Kiyi hakuri, wallahi ba wai ina nufin wani abu ba, kawai ganin irin yanda ya haɗu ne sai nake ga kamar bai dace ma ya auri wacce ta taɓa aure ba ball.." "A'isha! Ya isa haka don Allah ki rabu da ni. Wai ni sa'arki ce?" Ɗan taɓe baki A'isha ta yi tana murmushi. "Allah Ya ba ki hakuri babbar Yaya, na yi shiru." Ramlat ba ta ƙara magana ba don tasan ban hakurin ma irin na ƙannen zamani ne. Karshe ma miƙewa ta yi ta soma gyara mayafinta. "Tafiya zan yi, tunda har na miki mai wuyar ai shikenan." Anan ne kuma A'isha ta marairaice. "Wallahi ba zan iya cin abinci da baƙon nan a wurin ba. Don girman Allah ki yi hakuri ki zauna. Ya ce fa har gida zai kaiki." Gaba daya ta koma kalar tausayi tana roƙonta. Wayar Ramlat ta yi ringing, ganin Hajiya ce yasa ta nunawa A'isha "Kin gani dai da idonki ko? Uwata nemana ta ke yi." Daga haka ta ɗaga wayar, aikuwa tambayar da ta soma jefomata shi ne me ya tsayar da ita? Da sauri A'isha ta karɓi wayar ta yiwa Hajiyar bayani gami da roƙon alfarmar Ramlat ta jira har baƙon ya tafi sannan Hisham ya maidota. Dakyar Hajiya ta amince don ta ce ba hannunta idan Munir ya tambaya. Suka kammala wayar ta mikawa Ramlat, bayan gama jin bayanin Hajiya ta amsa da toh kawai kafin ta wurgamata harara. Dariya A'isha ta yi tana kara nema afuwa. *** Sai da suka idar da Magriba sannan suka hau saman dining table. Sai a sannan ne da Hisham ya matsa, Ramlat ta fito.   Bayansa kawai take hangowa don ya ba ƙofar ɗakin baya, ko kadan ba ta gane ko waye ba har ta ƙaraso da sallama. "Haba ko kefa Antinmu, amma ace tun ɗazu sai kiranki ake kina togewa." Murmushi kawai ta yi jin kalaman Hisham, shi kuwa Hussein jin an ce Anti yasa ya tsammaci wata babba ce don haka ya ɗago ya dubeta da zummar gaisuwa. Yanda bakinta ya tsaya a bude haka na shi ya dakata, mamaki ne a saman fuskar kowannensu. 'Wannan matar ko dagasken dai mayya ce?' Fadin Hussein a zuciyarsa cikin son gasƙata abinda matarsa ta hasaso a kan Ramlat. Mamakin yawan haɗuwartasu yake. Ta kai har ya ganeta, kamanninta sun yi zaman dirshan a ƙwaƙwalwarsa. Toh haka itama Ramlat, haduwarsu na ba ta mamaki. Da kuma ace ta san shi ne baƙon, da har ya fita ba za ta yarda ta fito ba. "Kun sa juna ne?" Tambayar Hisham ya katse kallon ƙurillar da suka tafi yiwa juna, kusan a tare suka kauda kai, ta ƙaraso ta maze ta zauna kujerar dake kallonsa. A'isha da Hisham dai abin mamaki ya basu, yanayin sauyawar kowannensu. "Ina wuni, an zo lafiya?" Ta gaisheshi cikin dakiya da kuma son kauda zargi daga zuƙatan ma'auratan da suka zubamusu ido. Shima ya amsa a tausashe.   "Lafiya." "Wai ba za ku amsamin ba, kun san juna ne dama?" Hisham mai naci, ya ƙara neman ba'asi. Hussein ya dubeshi da dara-daran idanunsa yana dan murmushi. "No, yau ne ma farkon ganin da na yi mata." Ta dubeshi da sauri, itama ita din ya kalla har lokacin murmushinsa bai gushe ba. Me yake nufi da yau ya soma ganinta? Ta dubi Hisham ta yi murmushin yaƙe kawai. "Uhm, idan ma ta yi wari ai ma ji, ko ya kika ce Princess?" Ya fadi yana duban A'isha mai kokarin zubawa Hussein abinci. Dariya kawai ta yi don ita kam kanta ya daure, ta kuma sani Hussein ya fi ƙarfin Yayarta. Da kamar wuya abinda Hisham ke nufi ya tabbata. Ramlat ji ta yi kamar ta ɗaga farantin tangaran din ta kwaɗawa Hisham a kai tsabar haushin da ya ba ta, shi kuwa Hussein shanyewa ya yi kamar bai gane inda zantukan Hisham din ya dosa ba. Tunda ta ɗora kai saman farantin da A'isha ta yi serving dinta, ba ta kara ɗagowa ba balle idanunsu su yi katarin haɗuwa. 'Dan uwansa ya fi shi kirki, sam bai da kirki wannan.' Ta fadi hakan a ƙasan ranta, a fili kuwa guntun tsaki ta ja wanda karaf ya shiga kunnensa. Ya ɗago a hankali ya dubeta, ƙaramin bakin ya kalla da mamakin ma yanda tsaki ya fito daga cikinsa. Koma mene ya san da shi ta ke. Murmushi kawai ya yi ya ci gaba da cin abincinsa a nutse.   Ita kuwa Ramlat gyara ƙafafunta da za ta yi, ta ji ta taka wata lallausar ƙafa kamar carpet. Alokaci guda ta yi aiki biyu, ta janye ƙafar a razane gami da dubanshi idanu a waje, kallon da ya jefamata ne ya yi sanadin ƙwarewarta. Ta shiga tari ba ƙaƙƙautawa su A'isha na mata sannu gami da zubamata ruwa a kofi. Shi kuwa ci gaba ya yi da kai lomarsa irin ko a jikinsa. Sai da ta sha ta samu nutsuwa kafin ta mike tsaye. "Ina za ki kuma?" Ta dubi A'ishar. "Na ƙoshi, gida ma nake son tafiya yanzu." "A'a ki jira, kinga ma Allah Ya so ni da rahmarSa. Tunda ga Hussein sai ya kaiki har gida tun da Madam dinsa ba ta nan, kuma ni sai na zauna na kula da tawa Madam din." Da wani irin sauri ta juyo ta kalli Hisham. Shi kuwa ransa fari ƙal, ya shinshino wani abin tsakaninsu. Koda ba soyayya ba, toh shakka babu akwai wata a ƙasa, bai yarda da cewar basu san juna ba.   "A'a, zan tafi kar ka damu." Daga haka ta faɗa ɗaki ta dauki jakarta da mayafi, jikinta har wani rawa yake tsabar kaɗuwa ta fito. "Ai fa na rantse sai dai ki jira abokina ya saukeki." Ji take inama Hisham din ba sa'anta bane yanda za ta ji dadin gasamishi baƙar magana. Dole ba yanda ta iya ganin A'isha na nanata mata ba haka suka yi da Hajiya ba, zama ta yi ta daure fuska kamar kunun tsamiya. Har ya kammala cin abincinsa bai ce musu uffan ba, sarai ya ji shirin Hisham din, ya kuma san da biyu ya yi. Shi dariya ma ya ba shi amma bai yi ta a fili ba, wato dai dagasken Hisham gani yake kamar wata alaƙar ce ta soyayya tsakaninsa da wannan baiwar Allahn.   "Alhamdulillah. Abinci ya yi dadi. Nagode." Abinda ya ce kenan yana goge baki da tissue, ya zura hannu ya ciro kudin da bai san adadinsu ba, ya ajiye saman tebur. "Ga tukuici ka ba Amarya." Hisham ya yi dariya sosai yana kallon falon inda A'isha ke zaune tare da Ramlat.   "Ai ba ita daya ta girka ba, kusan ma ƙarfin aikin Antinmu ce ko ince Yayarmu." Hussein ya ɗan ɗaga kafaɗa da sunan ko a jikinsa gami da miƙewa. "Nidai na bayar, girki kuma ya yi dadi." Murmushi Hisham ya yi sanin hali. Kudin ya dauka ya je ya dire saman cinyar A'isha. "Ga tukuicinku na girki, Abokina ya yaba." Ramlat ba ta ce uffan ba, A'isha ta shiga godiya bai ko amsa ba sai murmushi da ya yi mata. "Toh Madam, ni zan wuce. Allah Ya bar zumunci." A'isha ta mike tana ƙara yin godiya. Ya yi waje. Hisham ya dubi Ramlat. "Antinmu don Allah ki yi hakuri ki taso ku tafi." "Wai shi ya ce maka zai kai ni? Ni da ka bar ni na hau adaidaita." "A'a. Wallahi na san Hussein daidai gwargwado, yana da kirki. Ina tabbatarmaki har ƙofar gida zai kaiki." Ta sauke ajiyar zuciya, dolenta ta taso suka fito, Hisham da kansa ya budemata mazaunin kusa da direba ta shiga. A'isha na gefe tsaye tana kallonsu. Wanna dacewar da ta ke kira ba zasu yi ba, sai ta ga sun yi fiye da dukkanin zatonta. Murmushi take, wani irin murmushi mai haɗe da zumuɗi da kuma fatan alheri. Har Hisham ya zagaya suka yi sallama da Hussein da ke tsaye jikin motar ya riƙe murfin motar, ba ta daina kallonsu ba. Suka yi sallama ya kara yi mishi godiya sannan ya shiga motar. A nutse ya soma tafiya har ya bar layin, wani shiru ne kawai ke gudana tsakaninsu. Kowanne da abinda yake saƙawa a ransa. A ɓangaren Hussein murmushi ya yi, tunaninsa kawai Hajiyartasa, da za ta ga yarinyar a gaban motarsa yau kam hauka ne kawai ba za ta yi ba. "Kin hau motata ba ki sanar da ni inda zan kaiki ba." Wani kululun baƙin ciki ya tokaremata ƙahon zuci. Yana magana kamar ma ita ce ta ce za ta hau ya manta cewa bisa tilas take zaune a ciki. "Wace unguwa?" Ya tambaya kai tsaye ba tare da ya dubeta ba, kuma bai tsaida motar ba. "Sharaɗa." Ta furta a ciki-ciki, sai a sannan ya juya ya kalleta, fuskarta na kallon waje. Ya maida kai ga tuƙinsa, gudu kawai yake ita kam ko a jikinta.   "Alaƙarku fa?" Ta ji muryarsa cikin kunnuwanta, sai a lokacin ta dubeshi. Cikin rashin fahimta ta ce. "Me ka ce?" Fuskarsa a sake ya dubeta kaɗan, ta kauda kai shima ya kawar. "Alaƙarki da Hisham." Kamar ta ce ba matsalarta ba ce, sai ta ji ta kasa. Ta ɗan ja sakanni kaɗan kafin ta amsa. "Mijin ƙanwata ne." Ya gyada kai daidai sadda ya sha kwanar da za ta sadashi da titin sharaɗa.   "Sai ina?" Ta dubeshi, ita wannan magana guntu-guntun takaici yake ba ta, ganin ba ta gane ba ya ce. "Ina zamu yi?" Ta yi mishi kwatance har lokacin muryarta ba daidai ba, ta rasa dalili. Gyada kai kawai yake yana sauraronta da dukkan hankalinsa, har ta gama ya rasa dalilin da yasa bai so ta tsaya din ba. Ya numfasa ya shiga bin kwatancen har suka iso layin da take fadi. "Ya isa, zan sauka a nan." Ya dubi wurin, akwai jama'a ba laifi, gidajen unguwar ya kalla, ba laifi suna da kyan gani. "Kofar gidanku fa?" Girgiza kai ta yi. "A'a ba sai mun ƙarasa ba. Nagode." Gyada kai ya yi. Ta murɗa kofar ta ji ta gam! "Kiyi hakuri. Ina mai ba ki hakuri on behalf of my wife na abinda ta yi maki kwanaki." Ta ɗan tsuke fuska. "Wa kenan? Ai ban sanka ba balle har wani abu ya haɗani da matarka. Ni dai Ramlat kake nufi?" Wani murmushi ya yi da har haƙoransa suka bayyana, irin murmushin da Hajiya Zeenatu kadai ke da ikon gani. Ta ɗan kauda kai daga kallon da ya ke jifanta da shi, murmushin ya kara kashemata gangar jiki da ruhi. "Ramuwar gayya kenan fa?" Ta yi shiru ba ta amsa ba amma ta ɗan murmusa itama ganin ya ɗagota. "Shikenan. A gaida su Mama." Daga haka ta ji ƙarar cire lock. Ta dubeshi kafin ta fita ta leƙo ta window. "Nagode, zasu ji. Nima a gaidamin Hajiya." Kusan ta faɗa da biyu hakan yasa shi dubanta, lokaci guda suka yiwa juna murmushi, daga nan ta soma tafiya babu ko waige. Har ta isa ƙofar gidansu ta bude murfin kyaure, sai a sannan ta waiga, yana tsaye ga mamakinta bai tafi ba, cikin sauri ta shige gidan tana mai dafe kirji da wurgawa kanta tambayar abinda ta aikata. Shi kuwa ji ya yi kamar ana jan sa, kwakkwaran motsi kasawa ya yi sai aikin kallon tafiyar nutsuwarta har ta shige gidan. Wayarsa ce ta katsemishi tunanin da ya dulmiya wanda ko za'a kasheshi ba zai ce ga dalili ba, sai sannan ya tuna da cewar murmushi yake, murmushin da ya ƙi ɗaukewa daga saman fuskarsa. Hajiya Zeenatu ke kiransa, ji ya yi gabansa ya faɗi. Ya kasa daukar wayar, haka ta yi ta ƙara har ta katse. Gumi ya shiga tsastsafowa daga goshinsa, ya yi ribas ya bar layin. Gani yake kamar ya aikata wani ƙaton zunubi ga Hajiya Zeenatu. Ji ya yi ya tsani kansa, har lokacin gabansa faduwa yake don tsoro da fargabar inda zai ce mata ya ke. Bai samu nutsuwar kiranta ba sai da ya ganshi a ƙofar gidansa. "Ina ka shiga wai? Me kake yi? Wannan wane irin ziyara ce da bai isa a kammala a awa uku a koma gida ba?" Ya kasa tsawatarwa, ya ji ba shi da wannan kuzarin. Ƙarshe ma ya ɓige da bata hakuri da rarrashi. "Allah Ya huci zuciyarki, yanzu ganinan a gida. Wanka ma zan yi na kwanta na ci abinci a gidan Hisham." "Wanka? Wane irin wanka?" Ya ɗan yi shiru yana jin zuciyarsa na tuƙuƙi, tuhumar ta yi mishi kama da na zargi. "Me kike son ki ce?" Daga can Hajiya Zeenatu ta yi saurin gyara zancenta. "A'a ba komai, gani nayi garin da ɗan sanyi." Ya yi murmushi mai sauti. "Eh haka fa. Amma kin manta mijinnaki ba ƙazami bane ba ko?" Ta yi dariya, daga bisani suka yi sallama. *** HAJIYA ZEENATU...        I just published "BABI NA TALATIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/hTaZiBjDOab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 31) HAJIYA ZEENATU..   Niamey, Nijar. Tun ajiye wayartasu zuciyarta ta kasa sukuni, ta yi shiru kawai ta zubawa talabijin idanu ba don yana fahimtar yaren ba.   "Ba za ki daina shirmen tunanin ba ko? Na fadamaki ba sau ɗaya ba kuma ba sau biyu ba, mun zo inda za'a share kukanmu." Hajiya Batool Aminiyar Hajiya Zeenatu ke wannan zantukan. Ajiyar zuciya ta yi ta ci gaba da kallonta, dama tun soma maganar hankalin ya koma kanta. "Nasan da haka, amma ina jin tsoron tabbatuwar wancan lamarin Batool, kema kin sani kamar yanda na sani, kwaɓewarsa ba za ta yi kyau ba." Wani dan bazawarin murmushi Hajiya Batool ta saki. Ga ta dai siririya da ita amma naira sun zauna. Yatsunta ta jera zobunan gwal har ya yi yawan da bai yi kyan gani ba. "Ai sai ki yi, gobe da safe wanda zai mana rakiya zai zo mu tafi. Idan ba ganin wannan saurayin mijinnaki a kwalba kika yi kina juyashi ba, ba za ki kwantar da hankalinki yanda ya kamata." Sai a sannan ta yi dariya sosai, ranta kuma ya koma ƙal kamar takarda. "Na ci wuya kafin na cimma dukkan buri a kan Hussein, kema kin san da haka ai. Huum, sai yanzu rana tsaka bayan na gama sanin wa nake tare da shi, wata banza ta zo ta tadamin hankali. Anya kuwa ma dagaske Gora yake? Ni dama tun sadda naga ya hau canki-canka da matsalar da ta kawo wata budurwa, na shiga shakku a kansa." "Toh ba na fadamaki ba, yanzu haka kawai kudinmu ya ci. Akwai irinsa da yawa ai, ba tsoron Allah su zalunci mutane su damfaresu." Fadin Hajiya Batool har da yamutse fuskarta mai kama da kashi. Ta mance su kansu ba tsoron Allahn suka sa gaba ba. *** Washegari kuwa da sassafe sai ga wani tsamurmurin buzu mai jin Hausa raɗau ya zo Hotel din da suka sauka. Shi ya yi musu jagora har wurin Isuhu Bakka Tsoron Allah. Layi sosai suka tarar amma kasancewar ɗan rakiyar ba baƙonsa ne mutumin ba, yasa ya basu umarnin su jira sannan ya shiga ciki. Can ya fito ya musu umarnin su taso. A bakin kofa suka tsaya suna ji mazauna wurin wadanda mafi yawansu mata me, su na zaginsu da yaren kala-kala, Hajiya Zeenatu da Hajiya Batool suka kalli juna don abin ma dariya ya basu. "Wai fa harara a duhu." Fadin Hajiya Batool. Wacce ke ciki na fitowa suka faɗa ɗakin bisa jagorancin ɗan rakiyarsu. Wani ƙaton mutum ne fatarsa har wani ja ta ke yi, yana zaune saman wata ƙaton carpet gefensa kayan tsubbu ne kala-kala, ya naɗe fuskarsa da farin naɗi sai kayan jikinsa baƙaƙe. Kallo ɗaya za ka yi mishi ka san buzun ne na gasken gaske. Suka gaidashi sai dai yarensu ma ba ji yake ba, ɗan rakiyar ya juya harshe ya shiga nanata abinda suke faɗa. Tun da ya soma bai katseshi ba kansa kawai yake gyaɗawa gami da yi musu kallon ƙurillah. Can ya watsa tambayar wacece a cikinsu. Saurayin ya nuna Hajiya Zeenatu ganin ita ke koro jawabin. Ya yi mata kallon tsaf sannan ya maida kai ga ƙasar dake shimfiɗe gabansa. Tambayar sunan mijinnata ya yi da kuma ita kanta. Bayan an faɗamasa ya ci gaba da zanensa a kan ƙasa can ya ɗago ya dubi saurayin yana murmushi yana jawabi, sai da ya gama tsaf sannan saurayin ya dubesu, dama duk sun matsu su ji abinda ke faruwa. "Cewa ya yi, ya ga ma mijinnaki saurayi ne, kuma ƴan biyu ne.  Shi kansa ƴan uwansa basu zauna ba, suna ci gaba da nemansa sannan sun tashi tsaye da addu'a irin wanda sai an yi dagaske. Ya kuma ce akwai mace ɗaya da babu makawa sai ya aureta koda za'a shekara goma ne, rubutacce ne. Ita ce za ta rushe dukkan wani gini da kika yi. Ai ya ce ya gani, ba wurinsa kika soma zuwa ba, kafin zuwanki nan, akwai wanda  ya yi maki aiki." Hanjin cikin Hajiya Zeenatu suka ƙulle, iskar fankar dake kaɗawa bai hana gumi ya tsastsafomata daga goshinta ba. Ta haɗiyi miyau, ta dubi Isuhu don bilhakki fargaba da tsananin kishi ya mantar da ita ba ya jin yarensu. "Ya kammanin yarinyar yake?" Saurayin ya faɗamasa. Girgiza kai ya yi gami da yin yare. Duk suka zubawa saurayin idanu suna jiran jawabi. "Ya ce ba zai ce ga kamannin ba, amma yanzun haka sun haɗu da juna." Ta haɗiyi miyau hankalinta a matukar tashe, idanunta har hangomata Yarinyar kwance jikin Hussein yake. Dagaske dai Gora ba ƙarya ya faɗamusu ba. Nan da nan idanunta suka kaɗa har da ƴar kwallarta. "Don Allah Malam ka taimakamin, wallahi ba zan iya haɗa Hussein da kowace ɗiya ba. Idan har Hussein ya rayu da wata mace koda ta hanyar fasiƙanci ne zan iya mutuwa wallahi. Nidai ko kasheta ne a yi kawai na huta. Idan har mutuwarta zai sauyamin kaddarata shikenan. Ko nawa ne zan biyaka wallahi." Tana kaiwa nan, saurayin ya faɗamishi. Ya yi shiru yana ci gaba da bugun ƙasarsa kafin ya ɗago ya yi jawabi. "Abu ɗaya ya ce za'a iya, shima yana da matuƙar wahala, bai kuma yi miki alƙawarin lallai ne ya yiwu ba.  Idan har za ki iya ku bar garin da ku ke yanzu zuwa wani. Ya kasance komai naku ya sauya daga wannan garin don yana da tabbacin koma wace ce a garin ta ke. Amma kuma ya ce zai wahala shi mijinnaki ya amince da hakan. Sannan yana mai ba ki shawara da kar ki yi wasa da abinda zai ba ki na mallaka, muddin kika yi sake ƴan uwansa na dab da sanin inda yake. Bayyanuwarsa garesu kuwa daidai yake da rushewar duk wani tubalin da ki ka gina." Hajiya Zeenatu ba baka sai kunni, gyada kai kawai ta ke. Ai ko bangon duniya ne za ta iya zuwa muddin mijinnata ba zai suɓucemata ba. Sai dai dagasken itama ta sani, abu mawuyaci ne ya amince da barin garin Kano. "Naji, zan kiyaye ko menene. Zan bi dukkan tsarinsa." Isuhu ya gyada kai cike da gamsuwa bayan ya ji bayanin daga bakin saurayin. Miƙewa ya yi ya shige ƙuryar ɗaki. "Hajiya Zeenatu, ki ce gwara da muka zo?" "Uhum, bari Hajiya Batool, gaba daya cikina ma ya kaɗa wallahi kamar na saki a wando. Jikina yana bani cewa wannan tsinanniyar yarinyar ce da ke bibiyarmu kamar mayya. Ai ko birnin Sin ya ce na koma zan koma balle kuma na bar garin. Naji na yarda zan damƙa amanar dukiyata ga Manaja, idan ya so ko mene ni din sai na dinga zuwa Kanon. Ba zan zauna a yimin sakiyar da ba ruwa ba. Shekara nawa ina yawon kashe kuɗi da fashi a maƙabartu akan Hussein? Ko wacece ta yi kaɗan." Ta ƙarashe a kausashe. Hajiya Batool ta shiga jinjina kai. "Nima ban yarda da ki zauna ki zuba ido komai ya lalace ba. Bari ya fito na shigar da nawa ƙoƙon barar akan wannan shegiyar surukartawa da ke neman mallakemin ɗa. Haba, komai yanzu nashi ƙarewa yake yi a wajenta?" Hajiya Zeenatu dai ba amsa, kowa ya ji da nashi matsalar. Ba jimawa ya dawo dauke da wasu jarkoki biyu na ruwan magani sai wata leda. Tiryan-tiryan ya yi bayani. Ɗan rakiyarsu ya kallesu. "Wannan jarkar ya ce tsakar dare za ki tashi daidai sadda hasken farin wata ya fito, za ki fita tsakar gida tsirara ki yi wanka da shi har na kwana uku. Shi kuwa wannan ɗayan, tsarki za ki yi da shi ki yiwa Mijinki girki da shi har na tsawon sati daya ya ci. Sai wannan ƙullin maganin, ki tabbata kin sanya cikin turare irin mai maiƙonnan, ki dinga shafawa duk sadda mu'amala da ta haɗaki da shi. Shi kuwa wannan layar, a tsakiyar bola za ki binneta ba tare da kowa ya ganki ba, wannan layar shi zai sa ki mallaki mijinki yanda ko uwarsa ba ta isa ta ganshi ta ce ya biyota ya je ba. Shi kuwa abincin da za ki girka masa, shi zai mantar da shi yarinyar muddin ku ka bar garin, ba kuma zai ƙara tunawa da ita ba balle har ya ji yana son zuwa ya ganta. Kinga kenan babu damar da zai ƙara sanyata a ido, idan ya sanyata a ido toh komai zai rushe." Tunda Hajiya Zeenatu ta ke, ba'a taɓa yi mata bayani kan aikinta ba ta ji ɗigon farin ciki ba sai a wannan karon. Gaba daya jinta take kamar wacce aka ɗaure da jijiyoyin jikinta, ta kasa kwakkwaran motsi banda kai da ta gyaɗa, shima sai da Hajiya Batool ta taɓota. Hawa saman bola ta binne ba matsalarta ba ce, ta shiga makabarta ma ta kwaƙule ido akan abin duniya wannan ba ta ɗaukeshi wani abu mai wuya ba. Tsakar dare ne ta tabbatar ba wanda zai iya ganinta kan bola, za ta iya wannan. Abu mafi ciwo mai sanyamata ta ji ta tsani kowace ɗiya mace, bai wuce na zuciyar Hussein da wata za ta mallaka ba. Wannan ya fi komai yi mata zafi. Gani take kamar ta hakura da sauya garin ta zauna ta bibiyeshi har ta yi tozali da yarinyar ta cakamata wuƙa a maƙoshi. Murmushi ta yi, sai lokacin ta samu sukuni, sai a sannan ta samu mafitar da a ganinta ya fi na wannan Malamin. Koda ba ita ba, za ta sanya a kashemata ita yanda wata ma ba za ta ƙara sha'awar shiga rayuwar Hussein ba. Har Hajiya Batool ta gama shigar da nata koken aka ba ta magunguna, Hajiya Zeenatu ba ta san anyi ba don ta tafi tunanin yanda za ta kashe baƙar dagar da ke shirin ruguza gininta. Isuhu kallon Hajiya Zeenatu kawai yake yana nazari, a ido ma karantar mutum yake balle kuma ga ya buga ƙasa. A jikinsa yake jin ba za ta aikata yanda ya ce ba sai abinda zuciyarta ta saƙa mata. Murmushi kawai ya yi don ya ga irinsu da yawa. Ya kuma tabbatar za ta yi kukan nadama, da ƙafarta za ta dawo wajensa ta nemi wani taimakon, a lokacin ne zai nunamata iyakarta. Suka kammala suka biya maƙudan kuɗi kafin su mike su fito, saurayin shi ya kai musu har mota sannan ya wuce da su gidan ƙawar Hajiya Batool, Hajja Mari (Maryam). Kasuwanci ne ya soma ƙulla ƙawancensu, saurayin yaronta ne yardajje mai mata ire-iren aikinnan. Ita ta haɗasu da shi don su je ayi musu komai. Hajja Mari ta shiryamusu lafiyayyen abinci iri-iri, a karshe ta kara jaddadamusu kada su yi wasa da aikin Isuhu Bakka Tsoron Allah (Ba ka tsoron Allah) don shi ɗin aikinsa kamar yankan wuƙa ne. Duk wannan bai sa Hajiya Zeenatu ta sauya ƙudurinta ba. Sun sha hira sosai a gidan Hajja Mari kafin su yi mata sallama saurayin ya maida su masaukinsu da zummar washegari zai zo ya kai su tasha su hau mota zuwa Maraɗi, anan ne kuma direban Hajiya Batool zai zo ya iskesu su wuce Kano. ***   ADAMAWA Kusan a hargitse ya shigo gidan, Dada ya soma cin karo da ita zaune saman kujera tana faman haɗa zufa. Ya karasa da sauri ya zauna daga shi sai doguwar jallabiya. "Dada lafiya? Meyafaru?" Ya yi tambayar yana dubanta da kulawa. Girgiza kai ta soma tana sharar hawaye. "Mafarki nayi marar dadi akan ɗan uwanka. Jikin yana ƙara bani yana raye kuma a duk inda yake yana bukatar addu'armu." Al-Hassan ya sauke ajiyar zuciya gami da ɗan runtse idanu ya bude cike da damuwa, ba ya son ya sanar da ita nashi kalar mafarkin kar hankalinta ya tashi, kusan shima kwanakinnan yana yawan mafarkinsa cikin wani irin yanayi. "Kiyi hakuri Dada, addu'armu ya fi buƙata a duk inda yake. Idan ma yana rayen Allah zai amsamana roƙonmu, Zai sadamu da shi in sha Allah." Dada ta share hawayenta ya fi a ƙirga amma kara tsiyaya suke. "Kana ganin ina raye zan sake ganinsa?" Da murmushi ya amsa. "In Sha Allah Dada. Za ki ganshi." Ta hau gyada kai. Can kuma ta ce. "Kawunka Modibbo ya kira, ya gasamin maganganu masu zafi duk akan iyayenku, na dauka tunda basu duniyar komai ya wuce, ashe ba haka ba?" Ya kara kallon Dada, twin sister din mahaifinsu, Aminu Gidado. Ubansu daya da Modibbo sai dai ba uwa daya ba.  A dakinsu su biyu kacal uwarsu ta haifa kafin ta rasu.   A rashin Aminu da matarsa, ta riƙe Alhassan da Hussein tamkar yaranta na cikinta ko ma fiye da hakan. Don irin son da ta nunamusu ko iyayensu sai hakan. Yanda ta damu da rashin Hussein kai ka rantse ita ta durkusa ta haifeshi ba Aminu ba. "Tunanin me ka ke yi?" Ta faɗi tana mai hankaltarsa. Ya yi murmushin yaƙe. "Babu komai Dada." Kafin Dada ta kara magana, wata kyakkyawar budurwa wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka san bafulatanar ce ta gaske, siririya kuma fara tas. Hafsat kenan, Autar Dada.  Hannunta dauke da Flask na ruwan zafi, ta saki baki tana kallon AlHassan, ya harareta, hararar da ta bata dariya. "A'a me ya yi zafi? Ka zo ka rarrashi tsohuwar tamu ko? Yau tun safe ta rikicemin da koke-koke kamar wacce aka yiwa mutuwa. Ashe sai da ta kiraka ta samu sukuni." Fadin Hafsat sadda take shigowa falon sosai. "Dada wataran sai na ɓalla ƙashin yarinyarnan kuma na dauketa na miƙa asibiti an gyara tas! Ta rainamin ke da yawa da sunan Auta, to kuwa maganinta zan yi, aure zamu yi mata." Tuni Hafsat ta nemi dariyar da take ta rasa, nan da nan ta marairaice. "Allah Ya huci zuciyarka Abu Fatima, don Allah ka yi hakuri." Murmushi ya yi ganin ta yi mishi wayo, wato amfani da sunan da Kausar kadai ke kiransa da shi. Dada dai ba ta sanya baki ba sai murmushi. A karshe dakyar Hafsat ta shawo kansa ya janye ƙudurinsa. Ita a duniya ba ta da buri sai na zurfafa karatu. Wannan ne dalilin da yasa ba ta kula kowa, samarin zuri'arsu masu kawomata hari su ne suka tilastamata zaman gida ta daina shiga sabgar yan uwa gudun kar a ƙaƙabamata auren zumuncin da bai taɓa bata sha'awa ba. Duk yanda Dada ta so AlHassan ya karya a gidan hakan ya faskara, ya lallaɓa bayan ya ga ta maido walwalarta ya yi gaba zuwa gidansa cike da damuwar rashin ɗan uwansa wanda a yanzu sosai yake ji a ransa cewa yana raye. Ba kamar a baya da yake tunanin ya mutu ba. Idan kuwa hakane, zai kara zage damtse wurin cigiyarsa. ***   KANO. Ramlat da ƴan uwanta sun haɗu suna kallon lefen Hunainah Amaryar Muniru. Zulaihat tun soma kallo take murmushi can dai ta ɗago ta dubeshi. "Wato dai wannan auren ko aurenka na fari ba ka saki bakin aljihu irinsa ba. Nidai ina ƙara faɗa, ka rabamusu gida wallahi don Bilkisu ba kanwar lasa ba ce." Ya harareta. "An fadamaki akwai macen da za ta firgitani har na kasa daukar mataki a kanta? Gida dole na haɗa su, ai idan ita Bilkisun ta ga kyautatawar da Hunainah za ta yimin shi ne da ta hankalta ta gyara." Rafee'ah ta cafe zancen. "Um um dai Yaya, wallahi naga irinku da yawa kuma daga karshe sai ku zo ku lashe aman da ku ka yi. Duk yanda kake tunanin mata ya wuce nan. Zama gida daya ba kwanciyar hankali." Ya taɓe baki, ko ba komai yana cikin farin ciki ba ya neman rigima da kannennasa. "Aikin banza kai, haka itama Hunainah ta dagemin akan lallai ba ta son zamanta da Bilkisu don kawai ta mata irin abinnan na mata, ta kirata a waya ta firgita ta da yi mata gargadin aurena. Ni kuwa a ranar hannu ne kaɗai ban ɗaga akan Bilki ba. Albarkacin su Yasmeen ta ke ci, ai na faɗamata. Ni akwai macen da za ta kawomin wargi ban yi kasa-ƙasa da ita ba?" Ramlat ta ɗago kai ta dubeshi wani dan murmushi ya suɓucemata kafin ta maida kai ta ci gaba da jera kayan shafar da ta ciro. Yaya Munir kenan, ga dukkan alamu zai iya dukan mace idan ya so. Tana jiyemishi tsoron wani abu, sai dai ba ta furta ba don ba fata take mishi ba, ta bar wa cikinta. Amma kuma buɗar bakin Zulaihat ta ce. "Af, wannan dai alamu sun nuna za ka iya dukan matarka. Kar dai ka zama Ali.." Sai ta yi saurin yin shiru, har a ranta ba ta ji dadin sunan Aliyu da ya tahomata ba, ta dubi Ramlat da ko kallonta ba ta yi ba kanta a ƙasa. Rafee'ah ta yi mata ido akan ta yi shiru. Koda ma Rafee'ah ba ta fadi ba, ita mai kama bakinta ce, a kasan ranta ta roƙamasa gafarar UbangijinSa. "Ki fita idona wallahi Zulaihat! Kar kiga kin haifi wadannan yaran masu kama da kulɓa har yanzu ba ki fi karfin na mareki ba." Maganar Yaya Munir duk sai ya basu dariya har Ramlat din da ta haɗiye zancen Zulaihat, ko ba komai ta ga nadama a fuskar Yayarta. Zulaihat ba kanwar lasa ba, haka suka yi ta cacar baki da Munir a karshe dai fitowar Hajiya daga ɗaki suka yi shiru bayan ta tsawatar. Bai bar gidan ba sai da ya rantse Zulaihat ba za ta je kai lefe ba don cewa ya yi da ace banda Hajiyarsu, Abban yana da wata mata zai ce Zulaihat ba ɗiyar Hajiyarsu ba ce. Haka ya gama bambamin faɗan ta rainashi ya zura takalmansa ya bar gidan. *** Washegari aka kai lefen Hunainah, Umman Amrah ce ta jagoranci tafiyar, aka tsaida nan da sati biyu biki. Ramlat ba ta samu zuwa ba saboda aiki. Sai da ta taso kafin ta tsaya a wani katafaren wurin siyar da kayan maƙulashe na A&Z. Ba ta taɓa zuwa ba sai dai talalr wurin har a gidajen rediyo tana ji. A duniya tana son ta ga ta faranta ran Hajiyarta da yaranta idan har tana da kuɗi a jikinta. Albarka sosai Hajiya ke sanyamata duk radda ta samu kuɗin da ta yo musu siyayyar kayan dadi suka ci. Kamar yanda ta saba, waya ta yi ta ce kar su ɗora tukunya, wannan abu ya fi komai yiwa mutan gidan daɗi. Ranta fari sol ta rufe motarta ta nufi ciki. Da ace Ramlat na da masaniyar wurin ko mallakin wanene ko wacece, har abada ba za ta tako ƙafarta ciki ba. Ko sakanni uku ba ta yi da shiga ba, wani al'amarin da ya kusan tarwatsamata kwanya ya afku.  I just published "BABI NA TALATIN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/gSzBjkXxTab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 32) Katafaren wurin hawa biyu ne, na farkon kayan snacks ne kala-kala, saman kuwa wurin siyar da ice-cream ne kowane irin ɗanɗano. A farfajiyar wurin kuwa kaji ne manya gashin inji ake siyarwa.  Kai tsaye saman ta haye ta nufi wurin masu kula da wurin, ƴanmata da samari ne ƴan ƙarya a wajen, basu ko tsonemata ido ba, burinta ta yi abinda ya kawo ta ta bar wurin, sai dai tsayuwarta ba jimawa kamar ance ta waiga,  ido huɗu suka yi da juna, daidai sadda ta fito daga wata ƙofa. Kallon mamaki da tsana ta ke yiwa Ramlat har ta ƙaraso inda take a matuƙar fusace. "Ke! Wai ke wace irin mayya ce?! Duk yanda na kai ga nesantaki da mijina hakan bai isheki ba? Wannan wane irin bibiya kike mishi?!" Ba Ramlat ba, gaba daya mutanen wurin suka maida hankali ga Hajiya Zeenat dake tsaye tana cika da batsewa. Ramlat ta kai maƙura da irin wannan cin mutuncin da Hajiya ke mata. A yau ta ji shirun ya gagareta don haka ta watsamata banzan kallo sama da ƙasa. "Daga ke har mijinnaki ba ku isheni kallo ba. Kuma ma banda abinki Mama, ai matar da ta yarda da kanta a zuciyar mijinta, ta kuma yarda da mijinnata, babu wata ɗiya mace da za ta razanata balle har ta damu kanta. Sa'arki ɗaya, ba zan iya haɗa miji da sa'ar uwata ba, da babu abinda zai hana ni auren mijinki ko don na nunamaki bambancin aya da tsakuwa!" Hannu Hajiya ta ɗaga da zummar marinta, caraf ta riƙe hannun tana murmushi kafin ta yarfar. "Kin yi kaɗan Mama. Mari wata dai ba Ramlat ba." Tana kaiwa nan ta juya a fusace ta kama hanyar barin wurin, tana jin Hajiya na kwalawa Maigadin wurin kira, har suka kusan cin karo da Ramlat, tana sauka yana hawa, ta kuma ji sadda ta ke bada umarnin koda wasa ya ƙara bari ta shigo wurin ya tabbata ranar barin aikinsa kenan. Ranta a tsananin ɓace  ba ta ko kallon gabanta sosai, ba ta yi aune ba ta yi karo da mutum, tsantsin tiles da ya kusan kifar da ita yasa ta saurin riƙe kafaɗarsa da dukkan hannuwanta. Ƙamshin tsadadden turarensa ne ya kashe dukkan wata lakar da ke jikinsa. Ko sakan ba ta yi ba ta saita kanta gami da kauda hannunta a jikinsa, kallon kallo suka yi. So yake ya tambayeta dalilin ɓacin ranta, amma ganin wacce ke saukowa tana haɗa matattakala bibbiyu zuwa uku yasa shi yin shiru. "Dama na faɗa! Yarinyarnan karuwa ce! Karuwa ce! Kun gani ko? Kun ga kalar iskancin da ta ke yi a jikin mijina ko?!" Samari da ƴanmatan da aka bari a sama tuni suka garzayo ta jikin gilasai suna kallon ƙasan. Wadanda basu taɓa ganin mijin Hajiyar ba sai a sannan suka ganshi, ƴanmata ido ya soma wani kakkarwa, basu taɓa zaton haka mijin Hajiyar yake ba. Wasu kuwa suna ganinsa a wurin don mafi akasari don shi suke takowa su zo, amma basu taɓa kawowa a ransu mijin wannan uwar matar ba ce. Ramlat ta dubeshi da idanunta wadanda ɓacin rai ya sauya, gani take ya kamata ta rama abinda Hajiya ke mata. Babu ruwanta da abinda zai biyo baya, idan har hakan zai baƙantawa Hajiyar to a wurinta daidai kenan. Murmushinta da ba kowa ke ganin irinsa ba ta jefamasa gami da yi mishi kallon da sai ka rantse wani masoyinta ne take tare da shi. Shi kuma har sannan ɓacin ran abinda Hajiya Zeenatu ta yi bai sakeshi ba, fuskarsa a ɗaure. Sai dai ganin irin murmushin da Ramlat ke mishi, bai san ya akai ba sai ya tsinci kansa da maidawa kura aniyarta. "Ka yi hakuri Heart, ko ma mene zan jure a kanka. Kar fa ka yi tunanin zan bar ka a kowane yanayi, wallahi ta yi kaɗan ta firgitani. Soyayya kuma yanzu muka fara. Ina jiran kiranka." Tana kaiwa nan ta ɗaga yatsunta biyu tana murmushi ta bar wurin, Hajiya Zeenatu ta kunduma ashar gami da ɗaga ƙafa da zummar bin bayanta, caraf ya riƙe damtsen hannunta. "Ba girmanki bane!" Abinda ya fadi kenan cikin sanyin muryarsa kuma ƙasa-ƙasa yanda ita ɗaya ce za ta ji, samari da ƴanmata  wurin da abinda Ramlat ta yi ya burgesu suka hau tafi da ihu har da masu fiito. Baƙin ciki da takaici ya sa Hajiya watsawa mijinta kallon banza da jajayen idanunta, ta yi rantsuwa akan sai ta kashe Ramlat da hannunta. Hussein sai ya raina kansa a hannunta. Ga mamakinta kamar karamar yarinya ya shiga jan hannunta suka fita daga wurin ya cusata a motarsa, fitowa ta yi ya dubeta. "Ina za ki?" Wani banzan harara ta watsamasa da ya sanya shi rudewa. Ya kasa magana sai faduwar gaba. "Ki yi hakuri." Bakin ciki bai bar ta ta yi magana ba, ta rasa wannan wane irin aiki ne, wani sa'in ya yi tasiri a kansa, ya dinga shakkarta, wani sa'in kuwa sai ka rantse babu ko ɗigon asiri a kansa. "Ai ba kai ka kawoni ba! Ka motarka ka bar wurinnan tun kan na yi maka abinda za ka yi nadamarsa!" Kamar wanda mahaifiyarsa ke ba shi umarni, ya bude gidan gaba ya shiga. Gilasan duk a sauke. Kallonsa Hajiya Zeenatu ke yi har ya tashi motar, fuskarnan ba'a sake ba kuma ba'a ɗaure ba, duk iyakar nacinta ta kasa gano kalar rikiɗewar da maganganun Ramlat ya jefashi ciki. Idan ta tuna ranta baƙi yake, komai dangane da Ramlat take da buƙatar sani. Wannan kuma ba zai mata wuya ba, ta ci alwashin rusa dukkan farin cikinta koda za ta rasa dukkan abinda ta mallaka. Jikinta ke ƙara ba ta ita ce yarinyar da Isuhu da Gora suka yi mata gargaɗi a kai. Har ya bar wurin ba ta fasa kallonsa ba kafin a rikice ta shige nata motar ta bar wurin. Kai tsaye gidan Hajiya Batool ta nufa. *** "Me na faɗamaki?! Ke kin tsaya kan lallai ba za ki bar garinnan ba da hannunki za ki ɗauki mataki a kan yarinyar! Ai wallahi Zeenatu ji nake kamar na ɗaukeki na jefa a wuta tsabar haushin da kika bani!" Hajiya Batool ke zuba wannan ruwan masifar kamar ta ari baki. Dama cike take da ɓacin ran yanda tana wankan magani a tsakar gida Maigadinta ya ganta, takaicin ya ɓatamata aiki ne yasa ta sallameshi ta kuma yi mishi gargadi mai girma akan yunƙurin tona asirinta. Hajiya Zeenatu ta share hawaye. "Wannan bala'i da me ya yi kama, yarinya ta zamemin ƘARFEN ƘAFA? Yarinyar da a haife a haifi wanda ma ya girmeta balle ita? Wallahi ina kara fadamaki kowane gari zan je tunda har aka tabbatarmana sai ya aureta toh za ta biyoshi tunda mayya ce. Abu ɗayan dai shi ne mafita, na kasheta da hannuna ko kuma na gallabi rayuwarta ta yanda na lahira ma sai ya fi ta jin dadi. Batool ina son Hussein fiye da yanda nake son rayuwata, ba irin mazan da ake dandanawa bane a kyale, kuma wallahi wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na ga bayan Ramlatu." "Au kin ma san sunanta ashe?" Ta gyada kai. "Har inda take aiki na sani, zan kuma ci ubanta." Hajiya Batool ta jinjina kai cike goyon  bayan aminiyarta. "Duk abinda ya dace ki aikata ki yi idan har zai nesanta ta daga Hussein. Amma kafin komai, ki soma yi mata kyakkyawan gargadi, idan ta ji shikenan, idan kuwa bai samu shiga ba sai ki aikata yanda kika so." Da haka suka ci gaba da saƙe-saƙensu akan Ramlat. ***   Ramlat kuwa, wani wurin ta nufa ta yi musu siyayya, ko kusa ba ta ji ko ɗarr da abinda ta aikata ba asalima wani irin murmushi da dariya take ita kadai a mota cike da nishadi. Ko ba komai yau ta rama abinda Hajiya Zeenat ke mata akan zargi da baƙin kishi irinnata. Da wannan nishaɗin ta isa gida, Hajiya sai da ta kasa hakuri ta tambayeta. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta sanarmata duk yanda lamuran suka faru. Baki sake Hajiya ke dubanta. "A'a Ramlatu, kar fa ki jajiɓomana abinda ya fi ƙarfinmu. Ke ko tsoro ba kya ji." Taɓe baki ta yi haɗe da murmushi tana kokarin kai tsokar nama bakinta. "Hajiya kar wannan ya dameki, daidai nake da ita tunda ita ba ta da hankali. Ni wallahi ban yarda da ita  ba ma." Jinjina kai Hajiya ta yi. "Ba dai ruwanki da ita, idan ta yi miki sanadin aiki ai ta gama da ke tunda ta san  inda kike aiki." "Da yardar Allah ba ta isa ba." "Ai shikenan." Faɗin Hajiya ta ƙara da addu'ar neman tsari, Ramlat ta amsa da amin gami da lumshe ido kadan tana tuno da irin kallon da Hussein ya ke jifanta da shi, kallon da ya nemi rikitata ta kasa abinda ta ci burin aikatawa, taimakon Allah ne kaɗai yasa ta ƙarasa jawabinta ta bar wurin. A gefe guda tausayinsa ne ya mamaye zuciyarta, ta kuma ƙudurta taimaka mishi da addu'a don hankalinta bai kwanta da Hajiyarsa ba. Misalin karfe sha daya na dare, tana kwance Affan a gefenta ya yi bacci, ita kuwa tana kan whatsapp suna hira da Amrah tana bata labarin abinda ya faru yau suna dariya har Amrah ke gargaɗinta akan irin wannan gangancin acewarta irin su Hajiya ba haka suka tsaya ba. Dawowar mijin Amrah ne yasa suka yi sallama ta ɓige da kallon status. Da sauri ta mike zaune tana ƙara kallon sunan Mutumin Mall kamar yanda ta yi saving lambarsa. Status ya dora na wata yarinya kyakkyawa da ba ranar ta soma ganinta ba. "Dama yana whatsapp ban taɓa lura ba?" Ta fadi a fili kamar mai jiran amsa daga wani ko wata. Kallon hoton yarinyar ta shiga yi tana murmushi. "Fatima." Ta furta a fili sannan  ta yi screenshot. Hoto na gaba ne ya kusan zautar da tunaninta, ji ta yi cikinta ya murɗa, ta ajiye wayar ta faɗa banɗaki sannan ta fito. Gumi na tsastsafomata ta ƙara ɗaukar wayar tana dawo da hoton baya ta kalla. Su biyu ne cikin shigar ƙananun kaya iri ɗaya sai bambancin kala. Ɗaya yana sanye da farin t-shirt, ɗayan kuwa sky blue ce. Banda hakan da kuma farin gilas din da ya ɗaya ya sanya a idanunsa, za ta iya rantsewa ta ƙara duk na hoton mutum ɗaya ne. Kuma nan take za ta ce HUSSEIN ne. Rubutun da ya yi a ƙasan hoton ne yasa ta yin salatin da ba ta shirya ba. "Idan kana raye Hussein, ina riƙon Allah Ya bayyana mana kai. Ƙwaƙwalwa da zuciya ba zasu taɓa yarda cewar ba ka tare da mu ba." Cikin sauri ta yi screenshot na hoton sannan ta yi cropping ta yanke wurin rubutun mai kama da cigiya kafin ta yi saving, hannunta har rawa yake yi. Tana so ta ce mishi ta san inda dan uwansa yake amma ta fi son ta tabbatar da zarginta. Tana son Hussein ya yi ido hudu da hoton ta ga yanayin da zai faɗa. Anan ne za ta san yanda za ta ɓullo ta faɗawa mutumin mall inda ɗan uwansa yake. Dama ita sam ba ta yarda da Hajiya Zeenatu ba, yanzun kuma ta ƙara tabbatar da zarginta. Ta kara komawa kan Status din, ga mamakinta ya cireshi. Sauke ajiyar zuciya ta yi, tunda dai ta yi screenshot ai shikenan. A daren dai baccinta ragagge ne, ita kanta ba ta san inda za ta ƙara haɗuwa da Hussein ba balle har magana ta haɗasu na dogon lokaci sai dai hakan bai karyamata gwuiwa ba. Ba za ta fasa abinda ta yi niyya ba. *** Tuƙi yake amma murmushi yake yi akai-akai, daki-daki yake tuna kalamanta da irin kallon da ta jefeshi da shi, koda ace bai kai zuciyarta ba, ba ta da masaniya akan tasirin da ya yi mishi. Ya ɗan kalli garin yanda ya yi luf luf, yammaci ne kuma babu rana dalilin damina da ke kokarin shigowa, wurare da dama a garin Kano ya samu labarin an yi ruwa. Bai tsaya ko'ina ba sai a wurin  Gym dinsu. Ya fito sanye da wandonsa three quarter sai rigarta marar hannu sai baƙar jaka da ya rataya a kafaɗarsa. Da wannan ya nufi ciki inda nan ya tarar da Hisham ya dage sai ɗaga ƙarfe ya ke. Suka yiwa juna dariya gami da cafkewa. "Shegen sama! Ban tsammaci ganinka nan kusa ba ai. Ka biyewa aure ka soma ajiye tumbin." Dariya Hisham ya yi yana tsane gumi da ɗan ƙaramin towel. "Ba'a magana kai kam, aure ƙarshe ne. Wallahi ba don kai ba bazan fito ba don bani da niyya, sai gashinan ka shanyani sai yanzu." Zama Hussein ya yi yana gyara ɗaurin igiyar fararen canvas ɗinsa. "Yi hakuri. Ban kyauta ba kam." "Ina jinka, ya akai?" Hussein ya ɗan yi shiru don bai san ta inda zai fara ba, can dai ya numfasa. "Za ka tuna yayar Madam dinka da na kai gida?" 'Anzo wajen.' Hisham ya ayyana aransa, murmushi ya yi. "Yes, Antinmu Ramlat." Ya gyada kai yana shafa suma, "Ita, sun samu matsala da Madam ɗita. Ina kuma tsoron kar ta yi mata sanadin aiki da ma abubuwa da dama. Nasan halinta da baƙin kishi." Cikin rashin fahimta Hisham ya ce. "Yimin dalla-dalla." Tun farkon ganinsu da Ramlat har zuwa abinda ya faru a A&Z bai ɓoyemishi ba. Hisham dai ya cika da mamaki, diramar ƙarshe ta ba shi dariya sosai ya kuma yi mamaki don bai zaci Ramlat din za ta aikata ba. Ɗaukar ta ya ke matsoraciya kuma shiru-shiru marar son hayaniya. "Mamaki nake." Hisham ya fadi yana ci gaba da dariya gami da riko hannun Hussein da ke binsa da kallo kamar ranar ya soma ganinsa.   "Wai meye hakan?" "Um um, amma fa duk da bansan wannan Madam din taka ba, gaskiyar magana ta ɗauki hanyar da ba zai ɓullar da ita ba. Kishi ko hauka? Ba ta san yanzu kai ya waye ba? Nikam Ramlat ta burgeni wallahi, wannan ma.." "Nima ban ce ba ta kyauta ba, amma na fi ta sanin matata. Idan a kan kishi ne komai ma za ta aikata. So nake ka ja mata kunne don Allah, ta nesanta kanta daga inda zasu haɗu balle har wani saɓanin ya ƙara shiga tsakaninsu." "Abinda ban gane ba, tausayinta kake har kake son ba ta kariya ko kuwa tsoron Madam dinka kake?" Hussein ya yi shiru bai amsa ba can kuma ya dubeshi. "Alaƙar da ke tsakaninta da  matarka na duba, amma fa zahirin gaskiya ba ta kyauta ba. Ko ba komai dakyar na shawo kan Madam ta fahimci dagasken ba komai tsakanina da ita. Kar ka ƙara cewa ina tsoron matata." Ya ƙarashe cike da rashin gaskiya, shi kansa ya sani yana shakkar Hajiya Zeenatu. "Kuma dagasken ba komai tsakaninka da Ramlat?" Gabansa ya fadi, ya kauda kai daga duban Hisham gami da ɗan murmusawa. "Yarinyar kallonta nake kamar irin Boss ɗin nan, komai ta yi dariya yake ban, tana burgeni. Amma ban taɓa son wata irin son da na yiwa Hajiya ba,har gobe bana jin akwai wacce za ta kai Hajiya a zuciyata." Ya ƙarashe da wani irin rauni na zuciya da gangar jiki, a karon kansa yake ji kamar ba hakan bane, amma a wani ɓangaren na zuciyarsa ji yake kamar ana ƙara tabbatar mishi da cewa eh! Ba shi da kamar Hajiya Zeenatu. "Owk!" Abinda Hisham ya ce kenan, ya ji kuma ba don ya yarda ba. Ya hango abubuwa da dama a saman fuskar abokinnasa. Can ya ƙara karambanin watsamasa tambayar da ya taɓa kwatanta yinsa bai ji da dadi ba. "Kai wai yaushe za ka kaini na gaida Mummynmu ne?" Kamar walkiya, ya nemi annurin fuskar Hussein ya rasa, kamar wanda ya haɗiyi garwashin wuta, haka fuskarsa ta soma wani ja-ja ga gumi da ya soma tsirfowa saman goshinsa. Miƙewa ya yi kamar wanda aka mintsila ya dauki jakarsa. A ruɗe Hisham ya miƙe tsaye ya riƙe mishi kafaɗa ya fisge har hannunsa na bugun wani ƙarfen motsa jiki, koda da zafi, bai ji ba. Yatsa ya shiga nunawa Hisham. Ya soma magana da muryar da ta ɗauki hankulan jama'ar wurin. "Kar ka ƙara! Wannan ne gargaɗi na ƙarshe da zan maka! Bana so! Har abada banda kowa a duniyata sai Hajiya Zeenatu! She meant everything to me! Ita kadai ce dangina. Ka rike wannan ka ji?" Ya ƙarashe a sanyaye, abin mamaki hawaye ya shiga fitarwa, a hankali ya juya ya soma taku ya bar Hisham tsaye a wurin baki a bude. Ga mamakin Hisham da mutanen wurin, faduwa ya yi. A guje suka yi kansa, Hisham ya tallafoshi, idanunsa a rufe sai numfashi yake fitarwa sama-sama "Hussein, me ya yi zafi haka? Ka yi hakuri don Allah." "Maida ni gida." Abinda ya iya fada kenan cike da wata iriyar kasala. Jama'ar na ta yi mishi sannu, wani ya riƙe jakar yayinda Hisham ya saƙalo hannun Hussein a wuyansa suka nufi motar Hussein din. Sai da ya zaunar da shi kafin ya koma da sauri shima ya dauko tarkacensa ya zuwa a aljihu suka bar wurin. Yau ne zuwansa gidan Hussein karo na farko, dakyar yake mishi kwatance wannan karon muryarsa ta bude ba kamar ɗazun ba kamar yanda idanunsa suka bude sosai. A gaggauce Maigadin ya bude ƙyaure ganin motar maigidan, Hisham ya tura hancin motar ya faka. Hajiya Zeenatu na zaune a falo tana amsa waya ta ji sallamar da ba muryar mijinta ba. Turus ya yi kamar yanda itama ta yi tsaye tana dubansu. Ganin yanayin Hussein ya sa ta ƙarasawa da sauri. "Habeebee meke samunka? Kai kuma waye?" Hussein ya zauna ya amsa. "Hisham ne." Ta dubi yanayin Hussein din sannan ta dubi Hisham wanda ke gaidata. Ta amsa fuska na yabo ba fallasa ganin irin duban mamakin da ke saman fuskarsa. Ya riga ya gane matsayinta wurin Amininsa don tun shigowarsu idonsa ya kai ga makekan enlargement din da ke dauke da fuskokinsu. Daga irin rikon da ta yiwa Hussein kadai ya ci ace duk mai hankali ya gane alaƙarsu. 'Taɓ!'  Abinda ya ce kenan a ƙasan ransa. A ƙarshe ya daure ya ɓoye mamakinsa ya saki fuska. Zai ba ta bayanin abinda ya faru ne ya ji Hussein ya tareshi cikin rawar murya. "Amm..dama kaina ne ke ciwo da jiri, ganin ba zan iya tuƙi ba yasa nace ya kawoni. Kiyi hakuri idan ganinsa ya ɓatamaki rai." Sai lokacin ta wayance gami da sakin fuska "Haba kai kuwa, mene abin ɓacin rai don abokinka ya kawoka? Wani zubin kamar yaron goye idan ka fadi wani zancen. Sannu, zauna mana bari na kawomaka ruwa." Hisham ya girgiza kai yana dariyar yaƙe. "A'a ba komai tafiya zan yi, nima yawa Amaryar na jirana." Suka yi dariya, ya yi mata sallama sannan ya fice cike da tsantsar mamakin wacce ya gani matsayin matar abokinsa. "Akwai wata a ƙasa." Abinda ya ce kenan bayan fitarsa daga gidan. Jikinsa ya ba shi akwai wata a ƙasa. Har ya koma wurin Gym ya dauki motarsa ya yi gida, bai bar tunanin lamarin Hussein da matarsa ba. Da ma duk abinda ya faru tsakaninsu. *** "Wai mene ne?" A'isha ke tambayar Hisham cike da damuwa ganin yanda yake mata Safa da marwa a tsakar falon, idan kuma an ɗan jima ya ce "Taɓ!" Ya dubeta sai ya kama hannunta suka zauna. "Ba komai Princess, kar ki damu. Amm..please kiramin Antinmu a waya ki ban." Cikin rashin fahimta ta ce. "Wacce a ciki?" "Ramlat." Nan da nan tunanin A'isha ya tafi wani bigiren, murmushi ta yi don gani take fatanta ne zai tabbata tsakanin abokin mijinnata da Yayarta. Ta mike ta nufi ɗakinta ta dauko wayar kai tsaye ta dannawa Ramlat kira. Bayan ta ɗaga sun gaisa ta sanarmata saƙon Hisham sannan ta miƙa masa. "Ranki ya dade Antinmu." Daga daya bangaren Ramlat ta ɗan yi murmushi mai sauti. "Angon ƙanwata fatan kuna lafiya?" "Lafiyarmu kalau, don Allah alfarma nake nema a wurinki." "Toh wace iri?" "Ina son idan kin samu lokaci ki zo gidana ko kuma na sameki wurin aiki wata ƴar magana zamu yi mai muhimmanci." Shiru ya ɗan biyo baya, ba wanda ya ce uffan tsakaninsu. Ga Hisham, dama ya bata ta nutsu ta bashi amsa, ga Ramlat kuwa jinin jikinta ta sha da kuma fargabar dalilin Hisham na nemanta.  Can dai ta nisa. "Shikenan, gobe In sha Allah daga wurin aiki zan biyo." "Yauwa Antinmu, Nagode sosai. A gaidamin ƴaƴana." Daga nan ya miƙa wa A'isha kan wayar ya shige daki cike da damuwar abokinsa. "Auta, lafiya dai ko? Ba wani laifin kika yi ba?" Dariya A'isha ta yi jin tambayar da Ramlat ta watsomata ta cikin wayar. "Wallahi lafiya sumul, bansan menene ba amma ina fatan alheri ne." Ajiyar zuciya mai karfi Ramlat ta sauke. "Shikenan Auta, sai Allah Ya kaimu goben." Daga nan suka ajiye wayar. ***   Ramlat ta kasa sukuni tun bayan wayar, har ta kasa hakuri sai da ta faɗawa Hajiya. Shiru Hajiya ta yi na ƴan daƙiƙa kafin ta ce. "Toh ko wani laifin Auta ta yi ne yake ɓoyewa?" Girgiza kai Ramlat ta yi. "Na tambayeta ta tabbatarmin lafiya kalau. Ko mene dai idan naje goben in sha Allah zan ji." "Ya za ki yi da kiran da Dakta ke miki?" Gabanta ya fadi, ɗazun da yamma a hanyarta ta dawowa daga wurin aiki ne ta amsa wayar Baba Dakta akan yana nemanta a gidansa. Tun sadda ta ji hakan ta rasa sukuni, tasan tatsuniyar gizo bai wuce na ƙoƙi. "Kin yi shiru." Hajiya ta furta tana kallon yanda ta ke dama fura cikin nono ba  tare da ta san me take ba don inda ludayin ya ke kallo daban da abinda ta ke. Maganar Hajiyar ya maidota  cikin nutsuwarta. Sauke ajiyar zuciya ta yi. "Nasan ba wani jimawa zan yi a gidan A'isha ba, da zarar mun kammala zan wuce gidan Baba Dakta kafin na shigo." Girgiza kai Hajiya ta yi tana murmushi. "Ramlatu kenan, ba haka za'a yi ba. Ina gidannan ina gidan Baba Dakta? Ki tashi dai ki je yanzu kinga goben kin huta. Miƙomin furar na dame abata." Ta kalli Hajiya a raunane, babu damar ta ce a'a, ta mike jiki a sanyaye ta miƙamata. "Mami zan bi ki!" Ummi ta furta tana ɗago kai daga zanen da take na makaranta. Daƙuwa Hajiya ta mata. "Gidanku, wato ma ba karatun kike ba kunnenki yana nan ko? To babu inda za ki je, idan kuma kika bi ta babu ke ba shan fura." Ai da sauri ta ce ta fasa. Murmushi kawai Ramlat ta yi ta nufi daki, hijabinta kawai ta zura ta dauki wayarta ta fito. A sannan ko sallar Isha'i ba'a yi ba, an dai kusa kira. Ta yi musu sallama ta fita. ***   Zuciyarta kamar ta yi tsalle ta fito sadda ta gama jin dogon jawabin da Baba Dakta ya ɗauko game da batun aure. Sai da ya gama nunamata muhimmancinsa ga rayuwar ƴa mace kafin ya bita da nasiha mai ratsa jiki, daga karshe ya tafi kai tsaye ga inda ya sa gaba. "Lokaci ya yi da ya dace ke da kanki ki yiwa kanki faɗa ki fiddo mijin aure Ramlatu, na kyaleki don a ganina kina da ƴancin da za ki zaɓawa kanki abokin rayuwa wannan karon ba tare da waninmu ya tilasta maki ba. Ki tsaida hankalinki ki yi tunani mai kyau. Akwai da dama waɗanda suka zo wurina neman aurenki kamar yanda shima kawunki Bashir ya sameni da batun maneman aurenki sun sameshi. Toh koda a baya bamu ba su damar neman yardarki ba, wannan karon ba zamu hanasu ba Ramlatu. Babban burinmu shi ne mu ga kema kin yi aure. Aiki ba ya hana aure idan har mijinki ya amince, idan kuwa bai amince ba sai ki zamanki a daki ki nemi wata sana'ar kamar yanda ƴar uwarki ta yi." Yana nufin Amrah. Wato ma dai ana zuwa har can Yakasai neman aurenta? Wannan abu ya dauremata kai, kodayake yana daga dalilinta na dauke ƙafa a gidan Hajja, a gidan ma akwai ɗan Kawunta da ke sonta sai dai mahaifiyarsa ta ce sam ba da ita ba. Wannan shine rikici ma na karshe da akai har zuwa gidan ya fice a ranta. Basu da masaniyar babu Kamalu a ƙoƙon ranta, ba ma shi kadai ba, kowane namiji ma ba ya gabanta. Aliyu ta so, kuma har gobe akwai kaunarsa a zuciyarta. Rana bai taɓa fitowa ya faɗi ba tare da ta yi mishi addu'a ba. "Kinji ko?" Maganar Baba Dakta ya katsemata tunani. Gyada kai ta yi tana share kwallar da ta cikamata idanu. Cikin sallamawa ta amsa. "Eh Baba Dakta, da yardar Allah zan yi yanda ku ke so." Murmushi ya yi gami da gyara zaman gilashinsa. "Allah Ya yi maki albarka. Ya zaɓamaki abokin rayuwa wanda za ku rayu har abada cikin aminci, so da yarda." Kunya ta sanya ta kasa amsawa sai murmushi. "Sai abu na gaba, meyasa bakya tura yarannan su gaisa da dangin mahaifinsu?" Ta ƙara russunar da kai. "Kwanaki ma fa sun je family meeting dinsu." "Aa, wannan ba hujja ba ce, ai inada labarin shima ba da son ranki ba wannan yarinyar ta wurin Justice ce ta zo ta tafi da su kina cika da batsewa kamar alkubus ko?" Dariya ta yi shima ya tayata don dama ya fadi ne don ta maido walwalarta. Mamaki take yi na inda ya samu labarinnan amma ta fi zaton a bakin Amrah ne. "Ba'a haka Ramlatu, yanda kike da iko a kansu, su ma suna da iko. Wannan karon idan aka yi hutu idan ma ba ki sanya an kai su ba, da kaina zan kwashesu na kai. Dolensu ne fa, idan kika hanasu zumunci da su, wataran da ƙafarsu zasu taka su je, lokacin ne kuma za ki sha kunya." Har sannan murmushi take, kaunar Baba Dakta na ƙara ratsamata zuciya da gangar jiki, tana jinsa kamar Abbanta. Irin kulawa da kaunar da yake nunamusu, ko Abba yana raye abinda zai yi kenan. Daidai gwargwado yana kokari wurin kula da gidansu, abinci duk wata sai Nana Dakta ya ajiyemusu, samun mutum kuma amini irinsa abu ne mai matukar wahala a wannan ƙarnin. Ba ita ta bar gidan ba sai da suka ci abinci ta yi sallah. Hajiya ta ji dadin dalilin kiran Baba Dakta, ta kara da fadin. "Ai gwara dai ya tunasar da ke, idan kuwa kin fi kaunar mu zauna muna haɗa ƙugu a gidannan sai ki yi kiga idan zai ɓullar da ke. Gwara ni na tsufa na ci ƙuruciyata yanda ya kamata." Dariya ma maganar ta ba Ramlat, furarta da aka bar mata ta sanya a fridge, ta tashi yaran da suka sheme a ƙasa suna bacci ta kai kowannensu makwancinsa. Affan kuwa sai da ta tabbatar ta kai shi ya yi fitsari kafin ta kwantar da shi saman gadonta bayan ta kakkaɓe. Ta yi mishi addu'a sannan ta faɗa wanka. ***   WASHEGARI just published "BABI NA TALATIN DA UKU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/JH0s4CH5Wab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 33) Tunda ta ji kira daga sama wai kuma daga Chairman Aliyu Dikko ta ji kanta ya yi ringingin, ma'aikata dai sun fi dubu a ƙasan bawan Allahnan, ta ina har ya ganeta da har zai turo Oganta ya kirata? Sai kuma da ta tuna Oga ya nema kafin ita ne yasa ta gane bakin zaren. Kai tsaye tare da Oga suka shiga wurin Chairman. Matar da ta gani zaune yasa ta shan jinin jikinta. Sanadin aikinta dai Hajiya Zeenatu za ta yi mata. Sai cika take tana batsewa, kallon da take watsamata tun shigarta ofis din ya sanya Ramlat daga kallo ɗaya ba ta ƙara duban inda take ba har suka karasa. Chairman ya na juyi saman kujerarsa yake duban wacce aka kira da Ramlat duba irin na ƙurillah. Ya haɗiyi miyau maƙwat. Koda ya taɓa ganinta ya manta saboda dubunnan matan da ke zirga-zirga a Revenue. "Yallaɓai gatanan." Oga Ɗalhatu ya ƙara magana a karo na biyu ganin kamar Chairman ba ya tare da shi, Chairman ya yi gyaran murya kafin ya maido nutsuwarsa ya saita kansa. "Yauwa Ɗalhatu, kana iya tafiya." Cike da girmamawa Oga Ɗalhatu ya amsa gami da barin wurin. "Wannan ita ce?" Chairman ya fadi gami da ɗauke kallonsa kamar ba ya so daga kan Ramlat zuwa na Hajiya. "Ita ce! Karuwa la'ananninyar Allah! Ita ce ke bibiyar mijina.!" Zuciya ya zo wa Ramlat wuya, wannan suna da Hajiya ke laƙabamata ya isheta. "Ni ba karuwa ba ce, kuma da kike fadin wai ina bibiyar mijinki, ki tambayeshi ki ji sau nawa shi ya tako zuwa gidanmu da sunan zance." Ba zato Hajiya ta shammaceta ta kifamata mafi, itama ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta ɗaga hannu da zummar ramawa, tsawar Chairman ta dakatar da ita ta sauke hannun tana kara zura dara-daran idanunta cikin na Hajiya. Itama Hajiya Zeenatun kallonta take kafin cike da zafin rai ta dubi Chairman. "Me na faɗamaka?! Me nace game da yarinyar nan?! Wallahi Dikko idan ba ka sallami wannan yarinyar a ma'aikatarka ba ka sani abinda ka binne a hannuna yake, da kaina zan tona asirinka a ..." "Haba Hajiya Zeenatu, ya isa mana! Haba!" "Ke wuce ki bar nan!" Ramlat ta haɗasu duka ta watsamusu banzan kallo kafin a fusace ta bar ofis din, ba ta jin ko ɗarr, ta shirya abinda ya fi kora daga aiki ma a yi mata idan har akan Hajiya ne. Matar da ba ta san darajar dan adam ba, ba ta kaicon a koreta daga aiki.    "Me kake nufi da hakan Dikko?!" Hajiya Zeenatu ta furta rai a ɓace. Shima daure fuska ya yi yana saita tunaninsa. "Na ce ki bar komai a hannuna zan dauki mataki a kanta ko?" "Dikko na sanka kamar yunwar cikina, kar ka yi wasa da hankalina." Wani murmushi ya yi. "Haba Hajjaju, na fadamaki da kaina zan dauki mataki don wallahi nikam na ga abinda ba zan kyale ba." Ta yamutse fuska. "Me kake nufi?" Ya gyara zama ya kora ruwa a cikin ƙaton tumbinsa sannan ya yi mata bayani daki-daki, wani murmushi ta yi kafin kuma ta kwashe da dariya yana tayata. Da yatsa ta nuna saitin kwanyarta. "Kai dinnan na yarda akwai ƙwaƙwalwa!" Ya shafi sanƙonsa. "Haba Hajjaju! Ai mun ci dubu sai ceto. Ke dai ki kwantar da hankalinki." Da wannan ta mike ta fice. *** Da wani irin fushi take tuƙi, yanda Hisham ya matsu ta je su yi magana haka itama ta matsu ta je ta ba shi saƙo ya faɗawa Hussein akan matarsa. Har ta isa ƙofar gidan A'isha ba ta ji wani sassauci a zuciyarta ba. Maigadin zai budemata ƙyaure ta dakatar da shi, ko'ina ta rufe ta faɗa gidan.   Falon babu kowa shiru, sallama ta yi ba amsa don haka ta yi zamanta tana jijjiga ƙafa, tunawa da ta yi ba ta yi sallar La'asar ba ne yasa ta miƙewa ta faɗa ƙaramin ɗakin saukar baƙi na A'isha. *** A'isha ta fito daga daki ta yi turus ganin jaka da mayafi, can kuma ta fahimci ko na wace, da wani ɗoki ta faɗa ɗakin da ta san za ta iya ganinta ciki, ai kuwa ta ji motsin ruwa a banɗaki, ba jimawa Ramlat ta fito. A'isha ta tsaya wani sakaka tana kallonta. "Ke kuma ina kika shiga na zo ina ta sallama shiru?" Maimakon ta ba ta amsa, sai ta jefamata tambayar da ke cinta. "Lafiya kuwa? Kinga yanda idanunki suka kumbure suka yi ja?" Guntun tsaki ta ja, tana jan skirt din atamfarta don ya sauka sosai. "Bani hijabi." Abinda ta ce kenan ba ta ko damu da ba ta amsa ba, A'isha ta juya ta fita can kuma ta dawo dauke da Hijab. Warware hijabin ta yi ta shiga kokarin zurawa. "Ki kira mijinki idan ba ya gida ki ce na zo, sauri nake ba zama zan yi ba A'isha." Daga haka ta shiga kokarin tayar da sallah hawaye na ciccikowa daga idanunta. A'isha dai ta lura akwai matsala don haka ta fita ta ja mata ƙofar.  Wayarta ta fitar ta kira Hisham kamar yanda ta nema ta sanar da shi zuwan Ramlat din. Ya yi mamaki don a zatonsa sai zuwa yamma. "Ki ce ta ɗan ƙara hakuri, nan da awa In Sha Allah zan iso." Daga haka A'isha ta katse wayar. Kicin ta faɗa ta haɗomata abinci a faranti da lemu da ruwa. Komai ta haɗa ta kai mata ɗakin, a sannan ta idar da sallah  ta zauna kawai ta yi shiru.  Ƙarasawa ta yi ta ajiyemata a gefenta kafin ta ce. "Mun yi waya ya ce nan da awa zai iso  in Sha Allah." Gyada kai kawai Ramlat ta yi. "Wai don Allah meke faruwa haka ne? Duk kin tayarmin da hankali na rasa nutsuwa." Sai a sannan ta ɗan yi murmushin yaƙe. "Ba komai." Haushi ya sa A'isha miƙewa ta fice. Sai duk kuma ta ji ba ta kyauta ba, ai laifin wani ba ya shafar wani. Don haka ta janyo plate din ta tsakuri abincin gami da korawa da lemu.  A falon ta tarar da A'isha ta ƙura wa talabijin idanu tashar Zee World. Babu tabbacin ma hankalinta na wurin. Zama ta yi. "Ke Auta sarkin fushi, ba wani abu bane ba fa. A wurin aiki ne aka ɓatan rai." Ganin haka itama A'isha ta sauko. "Kai amma kin faɗarmin da gaba, dama nayi tunanin hakan. Allah Yasa dai ba wannan Halimar ba ce." Murmushi Ramlat ta yi. Ta tuna irin walwalar da Halima ke yi na ganinta cikin wannan yanayi, wanda dai ba ya sonka zai wuya ya so ka.  Share batun suka yi suka koma hirar abinda ya shafi bikin Munir. A hankali kuma zuciyarta ta ɗan yi sanyi. Karfe biyar da wasu mintocin, Hisham ya shigo gidan. Gaisawa kawai suka yi yana jan ta da zolaya sannan ya faɗa ciki don kimtsawa, A'isha ta mara mishi baya. Ba jimawa ya fito da alama wanka ya yi, ya sauya daga manyan kaya zuwa jallabiya.   "Antinmu ina wuni." Ta ɗan harareshi. "Na gaji da wannan doguwar gaisuwar, na ƙagu ka faɗamin  dalilin wannan neman don nima inada magana." Ya yi dariya. "Allah Ya ba ki hakuri toh." Daga nan ya bata labarin komai har zuwa kan kauracewa Hajiya Zeenatu da Hussein ke buƙatar ta yi. Wani huci take yi har hancinta na buɗuwa da rufewa. "Ka gama?" Cikin haɗiye dariyarsa ya gyaɗa kai. "Zan so ace shi wanda ya turo ka da wannan saƙon yana zaune tare da mu..." "Sai na kirashi." Ya katse ta da hanzari, ta ja guntun tsaki. "Banda wannan lokacin, sai dai ka fadamasa ta cikin gida ake fara komai kan a duba waje. Ya isa da matarsa ne za ta dinga bibiyata har wurin aiki tana ɓatan suna? Waye mijinnata da har ya ishi mutum kallo? Wallahi nikam na fi karfin zama inuwa daya da wannan banzar matar tasa ko nace uwar mata don a haife ma ta haifeshi." Ta shiga basu labarin abinda  Hajiya Zeenatu ta yi yau a ofishinsu. Hisham kansa shima ransa ya ɓaci. "Amma wannan dai ba ta da hankali ko?" A'isha ta furta cike da ɓacin rai. Ba tare da Ramlat ta kula ba ta ci gaba da magana tana duban Hisham "Don haka ka yi mishi magana, matarsa ta fita hanyata! Wallahi darajar zumuntarku da shi nake dubawa, amma idan har bai dau mataki a kanta ba, ni kuma ba zan fasa gasamata magana a ko'ina muka hadu ba idan ta taɓoni. Abin nata ya wuce hankali har wurin aikina? Me ma tsaremata wai? Ni ba son Mijinta nake ba, shima ba sona yake ba! Ya kamata ta san wannan!" Gyada kai Hisham ya yi. "Hakane, gaskiya kuma abin na neman wuce gona da iri. Kiyi hakuri don Allah, ni da kaina daren yau ba gobe ba da yardar Allah zan sameshi mu yi maganar. Sai dai fa Ramlat, akwai abinda ya ban mamaki da kuma ɗaurewar kai game da Hussein." Za ta so su yi maganar sai dai a yanda yau ranta ke a ɓace sunansa ma ba dadin faɗi yake mata ba, don haka ta mike tsaye tana yamutsa fuska. "Nikam mun gama magana ai inaga, gida zan wuce kafin Hajiya ta neme ni." A'isha da Hisham suka dubi juna, murmushi Hisham ya yi, ya mata uzurin halin da take ciki na ɓacin rai. Har mota suka yi mata rakiya sannan suka koma ciki. Kai tsaye ya dau waya ya kira Hussein ya sanarmasa yana son su yi magana, suka ajiye wajen da zasu haɗu. ***   Hajiya Zeenatu ta dubi mijinta da ya ajiye waya. "Fita za ka yi kenan?" Ta fadi zuciyarta na wani irin sanyi na farin ciki, ko ba komai za ta samu ta fita nata aikin. Fuskarsa cike da mamakin yanda yau ba ta mishi ƙorafin fitar dare ba ya dubeta. Dariya ta ɗan yi ta kama hannunsa ta ɗan murza. "Naga kamar da Hisham ka yi waya. Ai ba zan hanaka zumunci da shi ba. Ko ba komai ya so ka da alheri bai bar min kai cikin mawuyacin hali ba rannan. Amma naga kamar da ɗan hadari a garin." Murmushi ya ɗan yi. "Kar ki damu Hajjaju, ba nisa zamu yi ba ai, dayake shima nan Lamiɗo Crescent ya ke." Ba haka ta so ba don haka da azama ta tari numfashinsa. "Toh amma fa gaskiya ina son ka tahomin da Balangunnan na rijiyar zaki mai dadi. Na kasa cin abincin John." "Yanda kike so hakan za'a yi." Suka yiwa juna murmushi kafin ya mike ya dauki wayoyinsa da mukullin mota. "Sai na dawo ko?" Ta gyada kai tana wani lumshe masa idanu a son ta burgeshi karshe. Tana jin fitarsa ta mike da azama ta hau sama tana nishi da gyara ɗaurin zaninta da ke neman faɗuwa. Sai da ta soma fiddo ruwan maganinnan ta faɗa banɗaki ta yi tsarki da shi tas ta maida cikin jarkar sannan ta maidashi maɓoyarsa. Daga nan ta sanya layar a jaka ta dauki mukullin motarta ta fita.   Maigadin dai ba abinda ya shallesa, tashi ya yi ya bude ta fice ya maida ƙyauren gida. Tuƙinta take tana mai jin wani ƙarfin gwuiwa na zuwarmata wanda ke ƙara sanyata jin ba za ta fasa abinda ta yi niyya ba. A farko ta dauka lamarin Ramlat mai sauƙi ne da za ta iya maganceshi da hannunta, gari ne ba za ta bari ba, asalima ba za ta taɓa aikata yin wanka a tsakar dare ba kuma ba don ba za ta iya bane, sai don a ganinta asarar lokaci ne don babu abinda zai sa ta bar garin saboda Ramlat. A cewar ta Ramlatu ta yi kaɗan, gwara dai ta yi wanda za ta mallake Hussein yanda fita ma sai da izninta zai yi. Kallon sararin samaniya ta yi yanda ake zuba walƙiya. Ta ƙara maida hankali ga tuƙinta tana sharara gudu kamar wata namiji. Ba ta tsaya ko'ina ba sai a wani filin Allah da ba gida gaba babu a baya. Gari sai walƙiya ake yi da iska mai daɗi. Wani rami ne ƙato wanda a ƴan unguwar basu komai da shi sai aiken almajirai su zubarmusu da shara sai kuwa ƴan shaye-shaye da kan zo su maida wurin matattara. Babu tsoron jinnu balle shaiɗanu ta nufi bolar gadan-gadan. Tsammaninta babu kowa a wurin saboda yanayin iskar da ake da kuma walkiya, a zatonta za ta yi aikinta ta kammala kamar yanda Isuhu ya ce kar wanda ya ganta, sai dai tana hawa saman bolar gami da kokarin zura layar, wata fitila ta hasketa ga kuma hasken walƙiya. "Kaii...wa..ye anan?" Daga yanayin maganar za ka san ɗan maye ne. Cikin Hajiya ya ɗuri ruwa, ba ta yi aune ba wani ruwan hawaye ya tahomata, ba wai tsoron ɗan mayen ne ya shigeta ba illa ɓatamata aikin dubunnan da aka yi. "Allah Ya isa Batool!" Abinda ta ce kenan a fili don da shawararta ta zo wannan bolar, sam ba nan ta so zuwa ba. Hankali a tashe ta sauko duk da hakan sai da ta soke layar. Daidai nan ɗan mayen hannunsa riƙe da wuƙa ya zagayo yana ƙara kallonta sosai. Zobunan gwal ne a hannunta duk da ta saka mayafi bai hana a gani ba. Da sauri ta ce. "Kana so? Gwal ne?" Wata dariya ya yi yana rangaji. Ta saba karawa da irinsu. Kafin ya kai ga magana ta ciro ta damƙa masa. "Kai Hajjaju! Kin san homular! (Formular)" Ita dai haushinsa take ji kamar ta shaƙeshi,  ta fice a wajen yana ta mata kirarin da ba ta ma fahimta don a hargitse ta ke. *** Ga Ramlat kuwa, kasa sanarwa Hajiyarta ta yi akan abinda ya faru a wurin aikinsu ta yi, ta dai sanarmata dalilin kiran da Hisham ke mata. "Toh kinga wannan ma kadai ya isa ki yiwa kanki faɗa ba ruwanki da shiga harkarta ballantana har ta kaiku da samun matsala. Àllah Ya rufa asiri dai." Daga haka suka rufe zancen. *** Hussein ya yi shiru ya kuma baza kunne yana sauraron Hisham har ya kai aya, fuskarsa kadai ka kalla za ka ga damuwa da ɓacin rai kwance. "Kenan duk abinda nace ba ta ji ba?" Fadin Hussein a kausashe. "Ramlat ko wa?" Hisham ya nemi sani. Girgiza kai kawai Hussein ya yi kafin yace. "Ka bata hakuri, ka kuma..." "A'a Malam, wallahi na gaji. Nima fa ina da aikina ba masinja ba ne. Haka kawai sai a takuran da kaiwa da kawowa wurin faɗar saƙo. Toh na gaji fa, ana cin lokacinmu nisa Princess. Haba, aure ko wata ba'a yi ba an ban sabon aiki?" Harɗe hannu Hussein ya yi a kirji yana dubansa fuska dauke da murmushi, ya maida idanunsa sararin samaniya yana ganin yanda ake zuba walkiya da kuma iska. Ba ta "Give me her digits." Ba Hisham ba da mamaki ya kusan kaiwa ƙasan gwuiwa, hatta shi ɗin da ya nemi lambar sai da ya ji faɗuwar gaba, ya nemi tsoro da fargabar abinda hakan zai haifar ya rasa, ji yake kamar akwai abinda ke danneshi. "What did you say?" Hisham ya faɗi kusan a birkice. Maimakon ya amsa sai ya fiddo wayar ya ajiye saman mota ya bude murfin zaman direba ya shiga ya soma kokarin tayarwa. Ganin haka Hisham ya dauki wayar bayan ya fiddo tasa wayar, hannunsa har rawa yake yana mai jin wani farin ciki, fatansa yake so ya tabbata. Lambar Ramlat na Mtn da Airtel duka sai da ya ɗuramasa, kowanne ya ɗan danna kira amma sai ya kashe bai bari ya shiga ba, so yake dai lambobin su fada cikin Log. Ta cikin gilas ya miƙa masa wayar. "Shegen sama, gashinan ba ruwana kuma idan Hajiya ta gani, wallahi kar ma ka ambaci sunana. Ban yi saving ba, idan ka ga dama ka sanya Rabe a kan sunan ko Talle Mai Wanki." Dariya sosai Hisham ya ba shi, suka hau yi can kuma ya ɗan lumshe ido ya bude. "Zan rama ɗaya bayan ɗaya wallahi, ka yimin duk abinda ka ga dama yanzu. Sannan ni ba da wata manufa ma nemi lambar ba kar ka yi zaton akwai wata bayan Zeenat, wai don na ragemaka zirga-zirgar ce. That's it." Hisham dai dariya ya yi bai ce uffan ba. Suka yi sallama ya ja motar ya nufi Rijiyar Zaki. *** Washegari direba ta sanya ya kai yara makaranta, ko bakomai tana son yin baccin safe kadan sannan ta yi shirin Ofis. Ga garin ya yi luf sakamakon ruwan da aka samu a daren jiya. Wannan ne ya bata damar komawa bacci mai dadi bayan tafiyarsu. Ba ita ta farka ba sai da wayarta ta Soma ringing. Duk yanda ta kai ta share hakan ya gagara don mai kiran bai yi ɗaya ya haƙura ba. Da wani irin takaici ta mike ta ja tsaki kafin ta duba sunan dake yawo sama screen. Hilal. Ɗagawa ta yi da sallama. "Ayya na tasheki a bacci kenan. Shikenan ma yi magana anjima. A yi bacci lafiya." Bai jira cewarta ba ya katse kiran, murmushi ta ɗan yi ta kara maida kanta cike da kasala. Wayar dai ta ƙara ringing, a dolenta ta miƙe zaune. Lambar Salisu na ofishinsu ke yawo saman screen. Ta ɗaga da sauri. "Ramlat, kina ina ne?" "Haba Yallaɓai, ba sallama ba komai?" Ƴar dariya ya yi sannan ya yi sallamar suka gaisa, ya ɗora. "Kiyi hakuri, abin ne naga gwara na sanar da ke shiyasa shaf na mance da wannan batun." Cikin rashin nutsuwa ta zuro kafafunta ƙasa. "Lafiya Salisu?" "Ji nayi Oga Ɗalhatu na maganar an miki sauyin wurin aiki, za ki koma ɓangaren Chairman, a matsayin secretary ɗinsa." Kirjinta ya bada dam! Koda ace ranta a ɓace yake jiya, ba ta mance irin shu'umin kallon da Chairman Aliyu Dikko ke watsamata ba. Ba ta son ta munana zato game da abinda ba ta da tabbacinsa kamar yanda take ganin baƙin jama'ar ma'aikatar da ke gulmar Chairman din da cewa ɗan iska ne. Don haka sai ta kyautata zato. "Ko kina da masaniya ne Ramlat? Naji ba ki ce komai ba?" Dan murmushi mai sauti ta yi. "Banda ka faɗi bani da labari Salisu. Yanzu ai zan shigo ofishin In sha Allah. Sai na ƙaraso." Daga haka suka yi sallama, shiru ta yi na ɗan lokaci, so take ta gani ko za ta iya fahimtar manufar yin hakan, sai dai duk iyakar tunaninta ba ta gane komai ba. Tasan dai ko mene ba alheri ba ne tunda mutumin Hajiya ne. Miƙewa ta yi ta shiga wanka, a gaggauce ta shirya cikin doguwar rigarta na Atamfa, mai kawai ta shafa kafin ta zura hijabinta dogo ta dauki duk abinda take ɓukata ta fito. Sai a sannan ta tarar da missedcalls har uku duk daga mutanen Department dinsu ne. Ba wanda ta bi, ta karasa ta gaida Hajiya dake zaune suna hira da Ladidi. "Yau dai babu niyya. Daga jin sanyin gari kin shantake." Dariya ta ɗan yi. "Wane sanyi? Ai da saura ruwan Hajiyarmu. Bai kankama ba tukunna!" "Allah Ya bamu damina mai albarka dai." Fadin Hajiya, suka amsa. Ta gaidata karo na biyu kafin ta dubi Ladidi su gaisa sannan ta karya a gaggauce ta fita. Ba ta iya ta sanarwa Hajiya sauyin da aka yi mata ba, bar wa cikinta ta yi har sai ta je ta ji asalin abinda ke wakana. *** AKWAI WATA AI just published "BABI NA TALATIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/WcD6L9EP0ab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 34)    AKWAI WATA A ƘASA... Gaban Notice Board ta soma tsayawa, shakka babu dagaske Salisu yake, ajiyar zuciya ta sauke bayan kammala karanta bayanin sauyin da ta samu.  Sati mai zuwa za ta fara sabon duty dinta.   "Allah Yasa hakan ya fi alheri." Ta fadi a fili sannan ta karasa cikin ofis dinsu wanda kiris ya rage ta bar shi. Bayan sun gaisa ta zauna. "Za dai mu yi kewarki anan Ramlat, ko ba komai kin fi wasu a nan." Fadin Oga Ɗalhatu, aka ɗan dara idan ka cire Halima da hassada da bakin ciki ya cikamata zuciya, yanda ta ke jin tsanar Ramlat a yanzun har ya fi na baya. Ta jima tana burin kasancewar mai aiki a ƙarƙashin Chairman duk kuwa da cewa hakan bai rage ko ƙara albashinta ba, amma dai tasan alhairan da ita za ta kwantar da kai ta samu wurin Chairman, ba lallai ne ita Ramlat ta yi ba. "Ki dai bi sannu don kinsan ko waye shi." Cewar Halima tana yamutse fuska. "Kedai ba ruwanki, zato zunubi. Kuma kin fi kowa sanin Ramlat da halayyarta." Fadin Zuhra kenan. Ramlat kallonta kawai ta yi ba tare da ta tanka ba, tsaf ta gama gane wacece Halima da kuma irin takun saƙar da take yi da ita wanda ita kam ba ta ga dalilinsa ba. Da wannan damuwar ta dawo gida ta sanar da Hajiya halin da ake ciki. "Toh ke meye naki na damuwa? Sauyi ne fa kawai, idan batun kamun kai ne ai na yarda da ke bana jinki a wannan ɓangaren. Allah Yasa hakan ya zamemaki alheri." Ta amsa da amin.   Bayan Magriba suna zaune tana koyawa yaranta Homework, Maigadi ya yi sallama a bakin ƙofar suka amsa. Jin saƙon wai ana sallama da Ramlat ya ba ta mamaki, ta dubi Hajiya, itama kallonta take tana murmushi. "Ka ce tana zuwa." Bayan tafiyarsa ta dubi Hajiya. "Haba Hajiya, mutum da bansan ko waye ba, yanzun ai ba'a irin haka, da ace ya san ni toh ba zai rasa lambar wayata ba. Ta nan zai neme ni." Harararta Hajiya ta yi. "Kuma ya zama dole ki fita ba, naga alamar kin fi kaunar zama a haka babu aure, toh ya isa. Nima kamar Babanki Dakta, ba zan ƙara biyemaki ki kori masu zuwa wajenki ba. Idan ma a baya an yi bai wuce na tausayawa marayunnan ba. Tashi maza ki je." Kamar ta yi kuka ta ce. "To wa zai ƙarasa koyamusu?" "Jeki, nasan duk daɗewa ba za ki wuce awa ɗaya ba. In Sha Allahu ma ba su kai ga yin bacci ba. Tunda kin sallami Affan ai da sauƙi." Miƙewa ta yi ranta duk ba dadi, hijabi kawai ta zura ta kama hanya su Ummi na kiran a dawo lafiya, a tahomusu da alawa. Harara kawai ta watsamusu ta yi gaba ta bar Hajiya da dariya. Sai dai me? Wanda ta gani ya matuƙar shayar da ita mamaki, sakin baki ta yi kafin kuma su yi dariya a tare.  "Kai Yaya Hilal, yaushe ka zama baƙo a gidannan? Kuma fa ko Malam Bala bai fadamana wanda ke sallamar ba." Dariya ya yi. Sanye yake cikin shaddarsa ruwan toka, ya karya hularnan ta zannah Bukar ta zauna caras a kansa. Yana daga cikin mota zaune a inda ya fiddo ƙafarsa ɗaya waje. "Ke din ce sai da hakan, farko na so kiran wayarki sai kuma na fasa tunda nasan dai zai wahala ace a wannan lokacin ba kya gida. Malam Bala kuma ni na roƙeshi akan kar ya ce ni ne saboda yau zuwan naki ne ke ɗaya." Ta ɗan sadda kai ta yi shiru, ta san tatsuniyar gizo ba ta wuce na ƙoƙi. Abu ne da ba ta jin har abada za ta iya aminta da shi. "Ɗan zagayo mana ki zauna." Ba tare da musu ba ta zagaya ta bude motar ta shiga, kamar yanda ya bar ƙofa a buɗe, itama hakan ta yi. Gaidashi ta soma tare da tambayar iyali da wajen iyayensa. Ya amsa mata cike da annashuwa. "Kin ɓuya da yawa, ta ko'ina gujemin kike kamar rai da ajali. Na rasa hanyar ɓullomaki. Sai na kiraki ki share ki ƙi ɗauka, daga baya na samu text dinki wai ba kya kusa ne nayi hakuri. Anya kuwa?" Kunya ta kamata, ashe dai ya gane. Ita kuwa dalilinta na yin hakan a ganinta mai ƙarfi ne. Kokarin nesanta kanta da shi ta ke yi ta kowace hanya don ba ta son jawowa kanta magana. "Ka yi hakuri." "Na yi, amma ba duka ba. Ramlat, Maman Ummi, Ansar da Affan. A karo na biyu ga Hilal nan, bai kuma zo da niyyar yaudara ba. Aure ne ya kawoshi idan har kin amince." Ajiyar zuciya ta saki don dama ta san maganar kenan, jikinta ya yi sanyi da irin wannan soyayyar ta Hilal gareta. Ta dubeshi, shi dinma ita yake kallo babu ƙaƙƙautawa. Ɗan kauda idanunta ta yi. "Ko da can ma ba ka zo min da niyyar yaudara ba balle kuma yanzu. Asalima ni ce na yaudareka. Ka yi hakuri Yaya Hilal. Don Allah ka yi hakuri." Ta ƙarashe a raunane, ita sam ba ta san ta "Ka yi hakuri." "Ba hakuri za ki bani ba, dalilinki na guduna za ki faɗamin. Idan da wajen da na kuskuro na gyara." Girgiza kai ta shiga yi, kwalla ta soma ciccikomata idanu. Hilal wane irin mutum ne mai matukar sanyi da hakuri? Wace irin soyayya yake mata da ya kasa ganin laifinta? "Akwai abubuwa da dama da ya kyautu na gujeka dominsu. Ba ka taɓa yimin laifi ba, ba zan iya kallon danginka a karo na biyu ba a matsayin matarka. Bayan abinda ya faru wa kake tunanin zai ƙara kallon Ramlat matsayin matar kirki? Wallahi da kaina na faɗa, bani da kirki, ban yi halin hakuri da dattako na iyayenmu ba. Ka yi hakuri Hilal, mu ƙaddara ba'a rubuto aure tsaka.." Ta kasa ƙarasawa saboda kunya da kuma irin hararar da ya watsamata. Can kuma ya numfasa ya runtse ido. Da ace ta san yanda yake jinta a rai da ba ta ce haka ba, a gefe guda kuma bai mance irin kalaman da iyayensa suka yi gareshi ba muddin ya ce zai aureta ko bayan ransu ne. Kansa ya yi zafi da yawa. "Ka yi hakuri." Ta kara nanatawa, a wannan lokacin tuni hawayen sun zubo. Ya bude idanunsa da suka kaɗa ya dubeta. "Bana jin har abada zan manta da ke Ramlat, you are my first love. Ki daina bani hakuri, da ace zan iya da tuni na rarrashi zuciyata. Aurenki da Aliyu na dauki hakan matsayin rubutaccen al'amari wanda ba makawa sai ya faru. Albarkar auren gashinan mun gani (yana nufin yaranta), don haka ni wallahi tuni na yafe abinda kika yi gareni. Idan da naki a sannan, nima ai akwai nawa tunda ni na naace akan sai na aurekin ko ba so. Kar ki saurin yanke hukunci a kanmu, na baki nan zuwa sati kiyi tunani mai kyau, koda ba ki kirani ba, da zarar lokaci ya cika zan kawo kaina." 'Allah Sarki.' Ta furta a ƙasan ranta. Da wannan suka rabu ya bata kayan maƙulashe na alawa da biskit da ya siyowa yara. Ta karɓa gami da godiya suka yi sallama ta shige ciki.   Hajiya zaune a falo ta a gyangyaɗi kaɗan-kaɗan, yaran sun ƙurawa talabijin idanu su na kallon Angrybird. "Waye ne ya zo?" "Yaya Hilal ne." Hajiya ta mike zaune. "Yaronnan dai dagaske ya ke yi." Ramlat ta zauna jikinta a sanyaye. "Na rasa ya zan yi Hajiya, ya dage aurena ya ke son yi. Na rasa hanyar ɓullomasa ya fahimci illolin da hakan zasu haifarmin a danginsa da wurin matarsa." "Nima bana goyon bayan aurenki da shi, sai dai bamu san abinda Allah Ya ɓoye ba tunda har ya kasa hakuri ya dawo karo na biyu. Shawara ki dage da addu'ar neman zaɓin Allah, duk abinda Ya yi mai kyau ne." Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa. *** A kwana a tashi ba wuya a wurin Mai Rahma, bikin Munir ya taho. Ana gobe za'a yi ɗaurin aure ƙalilan daga mutanen Daura suka iso don Hajiya ba ta yi gayyata ba duba da cewar ba'a jima da bikin A'isha ba.   An daura aure lafiya, a daren aka yi shirin tafiya dinnerparty. Ramlat da yayyunta mata har A'isha da Amrah wacce basu daukarta bare cikinsu,  ankonsu iri daya na wani leshi peach colour. Kowannensu riga da skirt ya zauna ɗas a jikinsa. Motarta daga ita sai Amrah don Yaya Munir ya ce babu yara. Suna tafe suna hira, anan take ba ta labarin sauyin da aka yi mata wurin aiki, ta kara da fadin. "Tsorona daya, rashin sanin taƙamaiman manufar wannan Chairman ɗin. Ina tsoron ya kasance wani mugun abin ne." Amrah tana taunar cingam din da ya zamemata ciki tun tana laulayi har a yanzun da cikinta ya shiga watansa uku. "Kar wannan ya dameki, ai kinsan kanki. Daidai gwargwado kin san mutuncin kanki kina kuma karewa. Addu'a za ki yi ta yi akan Allah Ya kareki daga sharrinsa. Ba abinda zai faru amma shakka babu dai akwai wata a ƙasa!" Jinjina kai Ramlat ta yi. "Wallahi ko ba ki faɗa ba Amrah, ni ban taɓa ganin mace mai irin kishin na wannan matar ba." Amrah ta ɗan muskuta. "Af, kin ce za ki nunamin hotonsa." Ta yi murmushi. "Mu ƙarasa tukunna." Daga nan suka faɗa wata hirar ta daban har ta ke sanarmata da kiran da Baba Dakta ya yi mata. Amrah banda dariya da hamdala ba abinda ta ke yi. Wurin ya cika sosai, mafi yawa dangin Amarya Hunainah ne. "Ke me ya kawo waccan wurin nan?" Cewar Amrah tana kallon Salma kanwar Bilkisu. Idanun Ramlat ya kai gare ta. Taɓe baki ta yi. "Au ke duk hirar da su Maman Twins suke yi ba ki ji ba? Cewa fa aka yi itama Bilkin za ta zo. Ita gwanar kissa." Suka yi dariya suka karasa ciki basu kara kallonta ba. Salma ta bisu da harara ta ja dogon tsaki gami da fadin "Munafukan banza!" Koda sun ji basu tanka ba. Sai da suka samu wuri suka zauna kafin Ramlat ta fiddo wayarta ta lalubo hoton ƴan biyun da ta dauka ta miƙa wa Amrah. Sakin baki da hanci ta yi tana kallonsu. "Wow! Ke wai Twins ne? Toh ai banda gilashin da ke idanun daya, ba za ka ganesu ba. Lallai wallahi ban ga laifinta ba, dole ta yi kishi. Amma kika ce babba ce?" Amrah ta ƙarashe fuskarta ɗauke da tsantsar mamaki. Dariya ta ba Ramlat. "Dattijuwa ma kuwa don idan ma ba ta yi sa'ar Hajiyarmu ba, kadan ya yi mata saura ta yi. Ke kin gani kinsan wuff ta yi da shi." Suka yi dariya can kuma Amrah cike da tausayawa ta ce. "Wallahi nidai sai naga kamar ba banza ta bar shi ba. Wannan kyakkyawa ya tsaya a auren sa'ar uwarsa? Gaskiya jikina na bani akwai wata a ƙasa Ramlat." Ramlat ta gyara zama don ta sosamata inda ke mata ƙaiƙaiyi. "Ke kenan da ba ki ma ga matar ba. Ni banda duka wannan kinsan cikin biyunnan na hoto ba wanda ban hadu da shi ba?" "Me kike nufi?" Amrah ta tambaya da rashin fahimta.   Ramlat ta bata labarin kaf haɗuwarta da Mutumin Mall (AlHassan) da kuma Hussein da ma yanda aka yi ta ga hotonnan. "Tun ganin bayanin da ya rubuta kasan hoton na kara tabbatar da zargina. A farko da na ganshi a shago na gane ƴan biyu ne, tunanina sai ya ba ni ko su na tare ne da ya zo  Kanon  jin daga baya ya ce shi Adamawa su  ke. Wannan ne ya kara sanyawa na dasa alamar tambaya ga lamarinnan. Mai yiwuwa su na nemansa ne basu san ma inda ya ke ba, mai yiwuwa kuwa mallakeshi Hajiyarnan ta yi sun san inda ya ke amma ya ƙi sauraronsu." . "A'a haba dai, me kika ce ya rubuta? Allah Ya bayyanamusu shi, kinga kuwa basu da masaniyar a inda yake rayuwa ma kenan. Gaskiya Ramlat babban jihadi za ki yi idan har kika zama silar saduwarsa da ƴan uwansa." Jinjina kai Ramlat ta yi zuciyarta cike da tsantsar tausayin Hussein da AlHassan. "Ina fatan na yi hakan Amrah, sai dai abu ɗaya, ina tsoron na ɗauki matakin da zai sa ya bar gari a rasa inda ya shiga. Ma'ana, idan kai tsaye na cewa shi Abban Fatima cewa nasan inda ɗan uwansa ya ke, idan ya zo ya ganshi shi kuma ya ƙara sauya garin da za'a rasa ina ya ke, kinga anan an yi ba'a yi ba, wannan ne dalilin da yasa zan fi kaunar na soma sanin meke faruwa ko ya ya ne daga shi na Kanon kafin a san abin yi. Wallahi tun sadda na ga wannan hoton, Hussein ya shiga cikin jerin mutanen da nake tayawa da addu'a. Tausayi ya ke ban, na kuma rasa dalilin da yasa nake yawan tunanin lamarinsa." Wani murmushi Amrah ta yi gami da dafa hannunta. "Tunda kika ga haka, babban alheri ne haɗuwarki da wadannan bayin Allahn. Ɗari bisa ɗari na goyi bayanki, ko yaya ki samu ki soma tunkarar Hussein, sai dai ki sani, idan har bai saba da ke ba, ba lallai ne ya ba ki damar da za ki san wani abu dangane da shi ba. Ki nemi yardarsa kafin ki nemi ko menene. Abu na biyu ki yi takatsantsan da duk abinda zai sa matarsa ta ƙara ganinki tare da mijinta. Na uku kuma wanda shi ne ma ya kasance na farkon fari, ki haɗa da addu'a sosai, nima zan tayaki. Allah Yasa ta dalilinki wannan bawa ya sadu da ɗan uwansa." Murmushi sosai Ramlat ke yi har dimple dinta na fitowa raɗau. "Amin amin." Ta amsa cike da jin dadi da kuma farin cikin samun Aminiya kuma ƴar uwa ta gari.   Washegari aka kai Hunainah ɗakinta, Ramlat ba ta je ba don ta san za ta hadu da dangin Hilal sosai a bangaren Bilkisu. Ta dai ji irin salon Bilkisu wacce ba ta nuna komai ba asalima nunawa ta yi ta karɓi Hunainah da hannu bibbiyu za kuma su zauna da juna bisa amana. Da wannan dangin Hunainah suka miƙata ɗakinta wasu na yabon hakurin da Bilkisu ta yi yayinda wasu ke fadin ai ta ciki na ciki. ***   Ranar Litinin ta soma aiki a matsayin sakatariyar Chairman. Tana zaune a inda aka tanadar mata ya shigo bayansa daya daga cikin ma'aikatansa ne rike da jakarsa. Kallonta ya yi sannan ya shige ciki bayan a ladabce ta mishi barka da zuwa. Jimawa kaɗan ya kira wayar dake saman teburinta, ta mike ta shiga ciki tana kara gyara zaman ƙaton hijabinta don ta yiwa kanta alkawarin ba za ta ƙara sanya mayafi ta zo aiki ba ko don tseratar da kanta daga sharrin Chairman. Idan ma wancan karon wani abin ya hango, wannan karon sai dai ya gama baza idanun ya haƙure. Abinda ba ta sani ba shi ne, tafiyarta kaɗai ma abin ɗaukar hankali ne.   Yana zaune ya na waya, ta shiga da sallama bayan ta kwankwasa ya mata iznin shigowa. Tana tsaye har ya kammala wayar wannan mayun idanunnasa yana kan fuskarta kamar ya cinyeta. Ta yi tsaki ya fi a ƙirga a ƙasan ranta. "Malama Ramlatu, have a seat." Abin ya mata banbarakwai namiji da suna Hajara, ta zauna a ɗarare. Bayani ya shiga koromata akan abinda ya shafi aikinta, ita dai kai take gyaɗawa a ladabce tana amsa da kuma fadin za ta kiyaye. Abu ne da Staff Officer ya gama shaidamata, ba ta ga dalilin da a karo na biyu zai maimaita ba, a ganinta don hira ne kawai. Bayan ya kammala ya ce. "Ba ki yi mamakin dalilin da yasa kika dawo ƙarƙashina ba?" Sai lokacin ta dubeshi, ta yi saurin kauda kanta don ba ta kaunar wannan shegen kallon ƙurillar da yake jifanta da shi. Kallo na ƴan duniya. "Aiki ba inda ba ya kai mutum." Abinda ta ce kenan kawai. Ya yi baya ya kwantar da kai jikin kujera yana ƴar dariya. "Hakane kuma. Har kin kara burgeni, da alama kina da kyautata zato. Nayi tsammanin za ki firgita ganin kusancina da Hajiya Zeenatu." Fadin hakan yasa gabanta ya fadi, ta dubeshi cikin dakiya. "Ko kusa, ai mutum bai isa yi maka abinda Allah bai yi ba." Maimakon ta ba shi haushi matsayinsa na shugabanta, sai ta burgeshi ainun, ya kara jin kamar wani magnet na fisgarsa zuwa gareta. Ba ya so ya yaɗa manufarsa da wuri, don haka cikin dakiya ya sallameta bayan ya ba ta umarnin duk wanda ya zo idan har staff ne ba ya buƙatar ganinsa. Da wannan ta amsa sannan ta fice daga ofis din don dama abinda ta ke jira kenan. Bayan fitarta Chairman Aliyu Dikko ya runtse idanu ya ɗan bugi tebur yana murmushi. "Wannan ita ce daidai da ni, ita ce kalata." Ya fadi a fili cike da jin wani nishadi. Abu na farko da zai soma siye zuciyarta da shi, shi ne kyauta. Zai yi komai da zai sa ta saki jikinta da shi ta kuma daina yi mishi kallon banza. Idan har hakan ta faru shi zai san yanda zai yi ya shawo kanta. Da wannan ƙudurin ya ji wani sauki daga abinda ke cinsa duk akan Ramlat. ***   Ruwa ake tamkar da bakin ƙwarya, tana tsaye gefen titin da babu yawaitar ababen hawa sai tsilli-tsilli, kamar ta yi kuka haka take ji don tsabar baƙin ciki. Ace motarka ba ta tashi ɓaci ba sai a wannan lokacin? Ta dauki duk abinda yake da muhimmanci ta fito bayan tsagaitawar ruwan hannunta rike da lema. Sai da ta buɗeshi kafin ta rufa jikinta. Ta dauki jakarta ta rufe dukkan gilasai da kuma motar. Nan kuma ɗan sahu ya yi mata wuyar samu. Tsaki ta ja ya fi a ƙirga, ranar Asabar din ƙarshe wata ne, daga gidan Rafee'ah ta ke nan kan titin Rijiyar Zaki. Ba don ta riga ta yi mata sallama ba ta fito, kuma daga titi zuwa lungun gida Rafee'ah akwai tazara sosai, da babu abinda zai hanata juyawa ta koma.   Daidai sadda wata baƙar Ford ta wuce ta a guje, a hankali kuma mai motar ya yo baya har zuwa gabanta. Ta kalli motar ta kauda kai, za ta yi gaba ne ya sauke gilas. "Assalamu alaiki." Juyowa ta yi ta dubeshi, sanye cikin baƙar rigar sanyi marar nauyi, hular rigar mai igiya biyu kwance a baya wuyansa, duka duka tsawon hannun rigar iyakar damtsensa ne wannan ne ya bada damar bayyanar murɗaɗɗun hannuwansa masu zubin ƙarfin, tsintsiyar hannunsa daure da agogon fata baƙi sai zobunan azurfarsa da ba ya rabo da su. Ta tsinci kanta da maida mishi martanin murmushin tana mai amsa sallamar. Ba ta taɓa tsammanin ganinsa a wannan lokacin ba. "Motar ce ta samu matsala?" Maimakon ta yi magana sai ta ji kamar an ɗaure bakinta, hakan ya sa ta gyaɗa kai. Ya ɗan dubi sararin samaniya har ruwa na ɗigarmasa a saman karan hanci. "Gashinan kuma ina tsoron ruwa balle na fara gwada aikin kanikanci a kan motarki. Shigo na kai ki." Turus ta yi, kamar ta ce a'a, maganganun da suka yi da Amrah ya faɗomata a rai, ta zagaya ta shiga sannan ta zuge lemarta, za ta ajiye a ƙasa wurin kafarta ya karɓa ya cilla baya. Ta rufe ƙofar ta dubeshi. "Nagode." Ya ja motar yana murmushi. "Rike godiyarki ki fatan Allah Ya kaimu lafiya tukunna." Murmushin itama ta yi. 'Matsoraci mijin hajiya.' Duk a zatonta a zuciya ta fadi, sai ji ta yi ya yi wata dariya kafin ya ce. "Hajiyar da na yi wuff da ita ko?" Da sauri ta dubeshi duk sai ta ji kunya ya kamata ta hau kame-kame. "Lah ni wallahi ban ce ba. Me ma nace?  Me wai ka ji na fada? Don Allah I'm sorry." Ya kannemata ido ɗaya yana murmushi kafin ya maida idanunsa saman titi. "Alright, naji ba ki ce komai ba. Ni dama ban ce kin fadi ba duk kika wani tsargu kanki. Kin dai kirani da Your Heart ko?" Wannan karon ji ta yi inama yana da halin buɗe motar ta yi ficewarta.   I just published "BABI NA TALATIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ULR1OMRi4ab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 35) "Shiru?" Ta maida kai ga kallon gilas duk ta rude. "Ramlat." Ya Rabb, tamkar wani balarabe haka ta ji sunan ya fito raɗau a bakinsa. Ba ta san sadda ta juyo ta kalleshi ba. Hankalinsa na kan tuƙi, hanyar da ya ɗauka bai mata kama da inda ta nufa ba, asalima miƙa wa cikin rijiyar zaki kawai ya ke. "Ina zamu je?" Ta fadi murya na rawa. Murmushi ya ɗan yi. "Siyar da ke zan yi, ko ba komai hankalin Madam zai kwanta." Abin sai ya bata dariya, ta yi murmushi mai sauti gami da lumshe ido ta budesu. "Nikam ba zan siyu ba." "Really?" Ya furta  gami da ɗan ɗaga gira yana jifanta da wani irin kallo. Cikin dakiya ta amsa. "Kwarai ma kuwa, idan ka siyar da ni ba wanda zai kyaleka." Ya yi ƴar dariya. "Kuma sai ya kasance ba wanda ya ga shigowarki motata." "Amma ba ka daga cikin marasa imani, ba ka yi kama da ɗaya ba. Ina kyautata maka zato." Bai ce komai ba banda murmushi irin wanda har fararen haƙoransa suka bayyana. Hannu ya kai ya kunna music, waƙa ce ta yabon Annabi s.a.w da harshen larabci  na Maher Zain mai taken Ya Nabi Salam Alayka. Shiru ta yi duk da ba jin larabcin ta ke ba amma yabon yana ratsata sosai, muryar Hussein mai bin waƙar ya fiye mata muryar mawaƙin daɗi. Ta  kara yin laƙwas gami da bada dukkan nutsuwarta. Daidai wurin wani tukuba wacce a gefenta kujeru ne wuri-wuri cikin wata ƴar rumfa, ya nemi wuri ya tsaya. Ta kalli wajen tana mamakin yanda ruwa bai sa babu cunkoso a wajen ba, kamar ta ce mishi sai ya bi uban layinnan zasu tafi sai kawai ta fasa ta yi shiru. "Ban mintuna kaɗan." Bai jira amsawarta ba ya ɓalle seat belt ya fita. Sai a sannan ne ta lura da cewa three-quarter ce jikinsa, kunya ta sa ta kauda kai daga kallonsa. Fitarsa ba jimawa wayarsa ta shiga ringing. "Zeenat." Sunan da ta gani kenan saman kafcecan screen din da babu tsaga ko ɗis, gabanta ya faɗi. Har ta kammala ringing ba ta yi karambanin ɗagawa ba, kafin dai ya dawo ta yi ƙara fiye da sau uku. Anan ta ƙara gane naci da rashin hakuri irin na Hajiya Zeenat. Ta tsinci zuciyarta da daukar zafi, har hura hanci take don takaicinta, ita kanta ba ta da dalilin jin hakan. Yana zuwa ya ajiye ledojin a baya hadi da kallonta. "Sorry, na bar ki kina jira." Duk sonta da ta saki fuska ta kasa. "Bakomai." Hannu ya kai ya dauki wayar, nan da nan ya ɗan sauya. "Ɗan yi shiru please." Kallonsa kawai ta yi ganin yanda ya nutsu, waya yake latsawa kafin ya ɗaga. Anan ta ji yana ban hakuri kafin daga bisani ya ce yana hanyar dawowa. Taɓe baki  ta yi ta kauda kai gefe, tasan da za'a ce tsoro yake zai ce ba haka ba. Can kuma ya ajiye wayar ya tashi motar suka tafi.   Jin wannan karon bakinsa ya mutu ne yasa ta kalleshi. Fuskarsa kamar a sake kamar kuma ransa a ɓace, ta kauda kai cike da jin babu dadi don haka ta ja shi da hira. "Yaranka nawa?" Murmushi ya yi ya ɗan dubeta. "Kina son yara ne?" Ta maida dubanta ga titi tana murmushin itama. "Yara ai abin so ne. Wa zai ƙi su?" "Naki ba su isheki ba?" Ta ɗan yi shiru tana tunanin wa ya fadamasa tana da yara ne? Ko dai Hisham ne? Muryarsa ta katse tunaninta. "I saw your WhatsApp profile." Fadin hakan da ya yi shi ya tunasar da ita hoton yaranta ne akan dp dinta sannan a settings dinta kowa yana iya ganin dp idan har yayi saving lambarta. "Hakan na nufin.."  Ta fadi da sauri tana kallonsa. Wani kallo ya jefamata da ta kauda ƙwayar idanunta. "Wajen Hisham na karɓi lambar, ba don komai ba kuma, kar ki fassara please ki yi zaton sabon kamu kika yi." Ta murmusa. "Dama kai kam ai sai Hajiya." Ya yi shiru kaɗan yana murmushi, har ta fidda rai zai yi magana can ta tsinkayeshi. "Amma dai kin san ni mijin mace huɗu ne ko?" Ta dara kadan. "Um um, ban ga alamun hakan ba. Kai da aka kafamaka ƙahon zuƙa ana bi duk inda ka yi?" Ya shiga jinjina kai gami da kaɗan yatsa jikin sitiyari. "Ke ba'a kada ki a magana ko?" Ya ba ta dariya. "I'm sorry." Ta furta kanta tsaye. Ya kai hannu ya dauki gilashinsa baƙi ya manna a idon, ta saci kallonsa, murmushi kawai ya ke dokawa da ya ƙara masa kyau. Wani ajiyar zuciya ta sauke. Ba ta ga baƙin Hajiya na kishin wannan haɗaɗɗen ba. Har suka isa bai ƙara magana ba banda muryar Maher Zain da ya ƙaro  a waƙarsa ta Thank You Allah. Nutsuwa sosai ta yi har da kwantar da kai jikin kujera tana sauraron waƙar. Koda suka iso Sharada, shiru ta yi ta zuba ido tana so ta gani ko zai gane gidansu. Ta sha mamaki ganin ya shiga kan layin. Kamar wancan karon ta juyo ta dubeshi. "Zan sauka anan." "Don me? Kar saurayinki ya ganni?" Ya furta yana tafiya a hankali a dalilin ruwan da ya cika wurin. A raunane ta ce. "Ni wallahi ba wani saurayi, kawai dai.." "Kar ace ni saurayinki ne?" Ya fadi wannan karon idonsa a kanta, daga cikin gilashin yake ƙare mata kallo. Ganin kamar kallon na ƙurillah ne ya sanya shi kauda kai ya maida bisa hanya. Ita ta ma rasa ta cewa. Ganin ya tsaya daidai ƙofar gidansu ne ta fahimci rannan dai ya gane gidan da ta shiga. Dubansa ta yi, ya fidda gilashin ya dubeta. "Shikenan?" Tsuke baki ta yi kafin ta bude motar za ta fita ta ce. "Nagode Allah Ya saka da alheri." Murmushi ya yi ganin tana shirin rufo ƙofar. "Ji mana." Dakatawa ta yi gami da duban ƙyauren gidan a tsorace sannan ta sunkuyo kanta ta dubeshi kamar ta yi kuka. "Mene ne?" "Ban mukullin motarki. Zan sa a kawomaki." Ta ciro ba musu ta miƙa masa har da godiya. Dama burinta su saba yanda za ta tunkareshi da batun ƴan uwansa. Tasan kuma tana bukatar jin ta bakin Hisham ko akwai abinda ya sani shima. Hannu ya kai ya ɗauko lemarta da ƙullin leda ɗaya na nama ya miƙamata yana faɗin. "Idan ba so kike mu dawo gidannan da Madam ba, riƙe ki tafi da su." A tare suka yiwa juna dariya, ta karɓa ta mishi wani irin kallo kwatankwacin wanda ta yi don baƙanta ran Hajiya. "Itama ta san ni din ba kanwar lasa ba ce yanzu." Ya ɗaga gira. "Really? Idan kin yarda za ki maimaitan kallonnan a gabanta, shigo mu tafi." Wani irin kunya ya mamayeta, ta yi saurin ficewa ta rufemishi ƙofar, ya lumshe idanu ya bude yana kallonta, dab da za ta shige gidan ta juyo ta ɗaya mishi hannu tana murmushi, ga mamakinsa shima ɗagamata ya yi, ta juya ta shige ciki shi kuma ya ja ya tafi duk jikinsa a sanyaye. Kamar yanda mamaki bai bar shi ba hakanan itama ta ke ta mamakin kanta. Abin mamaki har ta shiga falon Hajiya murmushin ta ke yi. Ta tarbi yaranta har da ɗaga Affan ta juya da fadin "Oyoyo Babyn Mami." Suna ta dariya ta karasa ta zauna gami da fadin wash. "Sannu, amma kin jima. Mun yi waya da Rafee'ah ta cemin kin bar gidanta da wuri. Ina kika tsaya?" Ta ajiye mayafinta a gefe bayan ta ajiye ledar a saman tebur, lema kuwa Ummi ce ta karɓe ta nufi ɗaki da shi. "Mota ce ta macemin a hanya wallahi." "Ya Salam, to yanzu ya kika yi?" Murmushi Ramlat ta yi, fuskar Hussein ke yawo a kwayar idanunta. "Abokin Hisham ne ya ganni, shi ya kawoni har ƙofar gidannan." "Mijin Hajiyarnan?" Yanda Hajiya ta fadi ido waje sai ya ba ta dariya. "Shi." "Ai shikenan ke kika sani, ki yi ta jajiɓo yaronnan idan ta zo har gidannan ta jibgeki ba abinda zan ce." Dariya ta yi. "Ta jibgeni fa Hajiya? A gabanku?" "Atoh, ai naga alamar kamar alaƙar taku ƙara yin gaba ta ke." Jiki a sanyaye ta girgiza kai. "A'a fa Hajiya, ba komai tsakaninmu wallahi banda mutunci." Hajiya ta murmusa. "Allah Yasa toh." Ramlat ta basar da zancen. "Ga nama nan ma ya siyamin." Daga nan ta mike ta nufi ciki don sauya kaya sai dai maganar Hajiya ta ɗan shigeta. Dagaske sabo ke neman shiga tsakaninta da Hussein. Kamar kuma irin sabonnan da ba shi ta nema ba, irin wanda ba shi suka shirya da Amrah ba. Ta kai hannu ta fiddo wayarta daga jaka, kai tsaye ta shiga whatsapp kan dp dinta. Hoton yaranta ne, Affan da Ansar sanye da shadda iri daya, hular Affan har  goshi, Ansar kuwa ta zauna ɗas a kansa. Ummi daga bayansu ta dafa kafadunsu suna dariya kamar yanda mai hoton ya basu umarni. Murmushi ta yi ta shafi hoton tana tuna kalaman Hussein. Wato dai ya san tana da yara kuma ba ta da aure? Da alama a wurin Hisham ya nemi ƙarin bayani.   'Har zuciyarki ta soma saƙa wani abu akan wani ɗa namijin?' Wani bangare na zuciyarta ya ankarar da ita, ta yi saurin kashe wayar ta ajiye gefe, rage kayan jikinta ta yi ta faɗa wanka. A ganinta wannan kuskure ne babba. Don haka dole ta yi takatsatsan, kyakkyawan jihadin da ta yi niyya kawai za ta aiwatar akan wadannan ƴan biyun. Daga nan babu komai! ***   Washegari safiyar Lahadi da misalin ƙarfe takwas na yamma, Malam Bala ya yi sallama a kofar falon. Ita kadai ce a falon tana taimakawa Ladidi da tsintar shinkafa, yara na ɗaki wurin Hajiya,ta amsa ta leka suka gaisa. Muƙulli ya miƙomata. "Gashinan wani ne ya kawo ya ce a ba ki inji Yallaɓai, ga motarnan an shigo da ita ma."   Ta karbi mukullin. "Ya tafi?" Malam Bala ya amsa da eh. Ta mishi godiya sannan ta dawo ciki ta ajiye mukullin. Wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta dauka ta duba. "Mota duk ta yi datti ba wanki, gashinan, za ki biya kudin wankinta." Abinda aka rubuta kenan, wannan ya ba ta tabbacin har wankemata ya sa aka yi. Dariya ta yi kafin ta maida mishi martani bayan ta ƙare wa lambar kallo. "Nagode Yallaɓai, Allah Ya bar zumunci." Ta aikamasa kenan ta ga akwai saƙon da ya shigo ba ta ko lura ba. Hilal ne. Kirjinta ya fadi, idan ba ta mance ba yau an zarta sati da maganarsu, damuwa ta sauka saman fuskarta a yayinda ta karanta saƙonsa.   "Ban sani ba ko hidima ce ta miki yawa kamar yanda ta sha kaina har ban samu zuwa akan lokacin da muka tsayar ba. Ina fatan komai lafiya? A sanyamin ranar da zan zo idan ba damuwa." Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta rasa ma amsar da za ta ba shi. Ita ta sani, babu soyayyar bawan Allahn nan (Hilal) a ranta face tausayi da kuma ganin daraja da ƙimarsa. Ta yi addu'ar istihara sosai amma ba ta jinsa ko kaɗan. Ta rasa amsar bayarwa don haka ta ajiye wayar kawai ta ci gaba da aikinta.    Ita da kanta ta yi musu girki, shinkafa da miya. Tana kammalawa ta fito falon inda suke zaune ya yi daidai da shigowar Munir gidan dauke da yaransa. Daga ganin yanayin fuskarsa da irin daurewar da ya yi ka san cewa akwai matsala. Ya zauna yana gaida Hajiya a daure, ta amsa gami da jefamasa tambayar dake zuciyar Ramlat. "Lafiya kuwa? Meyafaru na ganka da su Yasmeen?" Ya shafi kai yana amsa gaisuwar Ramlat kamar ba ya so. Ya ba Yasmeen umarnin su shige ciki da su Ummi. Yasmeen ta ja  ƙannenta uku suka ɗunguma gaba daya zuwa ciki. Da yake yarinya ce mai wayo, gaba daya itama fuskarta ta koma kalar tausayi. "Wata ƴar hatsaniya aka yi da Bilkisu da Hunainah akan kawai yarannan su na shiga bangaren Hunainah. Ita yarinyar tana sonsu tana kuma jansu a jiki, toh ashe ita Bilkisu ranta na baci. Dama ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba ta ke nuna ba ta kaunar zuwan yaranta wurin Hunainah. Yau da na gaji don Yasmeen ta kwana sashin Hunainah shi ne ta kama yarinyar ta buga, ni kuma na yanke hukuncin zamansu a wurin Hunainah tunda abin haka ne, toh wai shi ne Bilkisu ta dauko wuka har da kai wa Hunainah yanka a kafaɗa ta yankamata hannun riga, wai ita ta rantse idan har na rabata da su za ta kashe Hunainah. Wannan ne dalilin da yasa ni kuma na korata gidansu na kwashi yaran na ce bari na kawosu nan idan ya so zuwa anjima sai na tafi da su. Haba! Wannan masifar ta ishe ni, Hajiya kusan kullum sai Bilkisu ta ɓullo da sabon rikici. Daga wancan sai wannan! Nikam gaskiya ta soma isata don zan iya sauwaƙe..." "Kar ka fara! Nace kar ka fara! Idan ka yi ba da yawuna ba wallahi. Wane shashashan namiji ne zai saki matarsa ta farko kuma Uwar ƴaƴa? A'a kar na kara jin batun rabuwarnan a bakinka. Yanzu kai dama anan ba sai da na gujemaka irin hakan ba? Ban maka magana game da haɗa matannan gida ɗaya ba? Ka nunamin kai namiji ne da mace ba ta isa tankwarawa ba. Ai zaman lafiyar ake nemamaka. Toh ga irinta nan, tun ba'a je ko'ina ba ta soma yunkurin kashe baiwar Allah." "Hajiya ɗan rigima fa ɗan rigima ne, koda ba gida ɗaya suke ba, sanin da na yiwa Bilkisu za ta iya takawa har gidanta. Toh Hajiya a hakan ma fa zargina take da rashin adalci ina kuma ace gidansu ba daya ba?"   Ramlat dai ta yi shiru tana kallonsa yanda duk ya fice a hayyacinsa.      Yanda aka banko labulen falon aka shigo yasa duk suka kalli kofar. Bilkisu ce buguzuzum da ita. Kalar mayafin daban da atamfar da ke jikinta. Da ganinta ka san ba'a nutse ta ke ba. Kai tsaye wurin Munir ta tunkaro hannunta a ƙugu.   "Ka bani yarana tunda ba kai ka haifamin ba!" Idanunta jage-jage da ruwan  hawaye. A fusace ya mike Hajiya ta yi saurin riƙe hannunsa. "Kai bana son hauka. Yi shiru abinki Bilki, zauna don Allah ki nutsu. Yaranki suna nan, kuma zan ba ki kayanki ki tafi da su." Wani kwafa ta yi ta zauna tana kuka har da share majina. Ramlat ta mike ta yi ɗaki don ita takaicinsu ma ta ke ji. Mace ta riga da ta raina mijinta ko kadan ma ba ta ganin girmansa. "Allah Ya kyauta." Ta faɗi a fili. Kayan islamiyya ta fiddowa yaranta ta ba kowanne nashi kafin ta shiga shirya Affan. Har ta kammala ta fito ta zubamusu ruwa a robobi ta basu Hajiya na ta shari'a tsakanin miji da matar. Idanunta ya kai ga Bilkisu, wata uwar harara ta watsamata, ita abin ma sai ya ba ta dariya ganin ai ba ita ta kai zoman ba, ratayar ma ba'a ba ta ba. Hijab ta sanya don ta fi kaunar ta bar musu gidan wannan yasa ta dauki wayarta ta yiwa Hajiya sallama da zummar za ta kai su Ummi makaranta daga haka ta fice don hankalin Hajiyar ma ba ya gareta kawai ta amsa da jeki. ***   Koda ta miƙa yaran ta wuce gidan Umman Amrah. Ta saki baki ganin Zaituna. "Wai Umma har yanzu ba su ɗauketa ba?" Umma ta dara. "Sun dauka mana, maidomin abata suka yi. Kusan tun bikin Muniru." Ramlat ta murmusa. "A'a wannan dai ta zama kishiyar ta gaske. A bar maki ita kawai." Kama baki Umma ta yi. "Wannan Babannata ne zai bar ta?Bari kiga nan kusa za ki ganshi ya zo daukarta. Yaran yanzu da shegen son ƴaƴa, wa ya sani ma ko ita ke turoshi." Dariya sosai abin ya ba Ramlat. "Kema dai ɗiyata ina nan ina addu'a Allah Ya zaɓamaki miji nagari mu sha biki. Ba na jin dadin ganinki a gida da kuruciyarki. Ai ina jin ba ki yi talatin ba ko?" Da murmushi ta girgiza kai. "Ban kai ba Umma. Kin manta watanni kawai na ba Amrah." Umma ta yi dariya. "Ke da Amrah ai rigimarku sai ku, ki ce kin girmeta itama ta ce ta girmeki." "Allah na girmi Amrah." Ita dai Umma ta amsa da toh sannan ta mike zuwa daki tana dariya, can ta fito rike da wani littafin adduo'i ta mikawa Ramlat. "Ki dinga karantawa, akwai adduo'i sahihai da kuma nafiloli. Kar ki yi wasa don Allah." Ta amsa da toh, mutanennan suna da burin ta yi aure, ba za ta ce ba ta so ba. Sai dai tana duba yaranta, ba ta kaunar yin nisa da su. Aure kuma ance ba inda ba ya kai mutum. Kwanciya sosai ta yi saman kujera sadda Umma ta mike ta wuce bangaren mijinta da ta ji tsayuwar motarsa. Wannan ya ba Ramlat damar danna waya, lambar Hussein ta bude ta ga dacewar ta yi saving. Cak ta tsaya tana tunanin sunan da za ta ɗora akan lambar, can kuma ta yi murmushi ta rubuta Mr Wuf. Ita kanta abin dariya ya bata.   Daga haka ta faɗa whatsapp ta shiga duba contact har ta faɗa saman lambarsa. Dp dinsa na wani ƙaton ocean ne sai rana da ta ɗauko faɗuwa daga sama. Murmushi ta yi ta je kan Status na profile. Busy kawai aka rubuta da alama kuma ya jima sosai a hakan.   Tana komawa kan whatsapp ta ci karo da sallamar Alhassan. Ganin yana online ta amsa da sauri. Suka gaisa ta tambayi Dada da iyalinsa. Ya amsa har da turo emoji na nuna jin dadinsa da hakan. Ya tambayi mutan gidansu shima.   _*"Ina nan shigowa Kano karshen satin da zamu shiga in sha Allah. Zan kawomaki Fatina ku gaisa idan ba damuwa. Address?"*_ Ganin abinda ya rubuta ne yasa ta saurin miƙewa zaune. Alhassan zai shiga Kano? Kodai yana da ƴan uwa a Kano? Wannan tambaya ce da ba ta da amsarta. Ga haɗiyi wani yawu kafin ta amsa mishi.   _*"Kano na marhabin da ku, Allah Ya kawoku lafiya. Ashe muna da ƴan uwa a Kano kenan._* Ta tambaya cike da ƙaguwa . Dariya ya aikomata kafin ta ga yana recording. Ta bude ta saurara. "Eh toh, muna da yan uwa. Akwai yayan Babanmu a Kano. Yanzun ma biki za'a yi na samarin yaransa har biyu,  shi ne zan kawo su Dada da Maman Fatima. Ina fatan za ku hadu ku gaisa?" Abinda ya ce kenan, ta yi shiru, gaba daya ya dulmiyar da ita cikin tunani. Kenan Alhassan suna da dangi a Kano? Toh ta yaya zai yiwu ace ba su taɓa cin karo da Hussein ba? Anya zai yiwu? Ace kuna gari  daya ba ku taɓa sanin juna ba. Kodai Hussein din ne bai da zumunci? Abinda ta yi ta rayawa kenan,can ta tuno ba ta ba shi amsa ba, gudun kar ya yi tunanin wani abin ne yasa ta ba da amsa. _*Wow, Allah Ya kaimu toh. Zan so na ga Fatima.*_ Suka ɗan taɓa hira kafin su yiwa juna sallama. Ita dai ta ajiye wayar kawai amma hankalinta gaba daya ya tafi ga tunanin wannan lamarin mai ban mamaki da ɗaure kai. Ba ita ta bar gidan ba sai da lokacin tashin yaranta ya yi, ta so ta ƙi shiga wurin Baba Dakta saboda kar ya yi mata batun aure, a karshe dai ta daure ta shiga kuma har suka gaisa ta fito suka taɓa barkwanci, bai mata zancen ba. Tana shiga da yaran falon Hajiya, ta ga babu su Munir balle yaransu sai Hajiya da Ladidi da ke tattaunawa. Hajiya na ganinta ta yi dariya. "Ja'ira, wata kika gudu kika bar ni da su ko?" Tana dariya ta zauna. "Me zan ce? Na saka baki Yaya Munir ya ce na mishi rashin kunya? Ya suka ƙare?" Taɓe baki Hajiya ta yi. "Na yi musu dai nasiha daidai gwargwadona. A karshe sun ba juna hakuri suka kwashi yaransu suka yi gaba." "Allah Ya daidaita lamarin." Suka amsa addu'ar Ramlat da Amin. ***   LAMIƊO CRESCENT. Kallon abincin ta ke kamar ta fasa ihun kuka tsabar takaici da bakin ciki. Ta dage ta yi girki da ruwan maganin tarkinta amma Hussein ya tahomusu da wasu manyan kifaye har uku gasassu da aka sanya chips a gefe da kayan tumatir albasa sai ɗan yaji a wata ƙaramar roba. Ci ya ke yana jin dadinsa ya dubeta.   "Madam tunanin me kike ne? Wannan fa don ke na siyo. Please come and join me." Ita a dole shagwaɓa irin ta masoya, ta yamutse fuska. "Ni a'a gaskiya, na dage na maka girki da kaina da hannuna yanzun kuma ka cemin ka ƙoshi?" Ya yi murmushi. "Shikenan, ki sanyamin a fridge I promise you, da shi zan yi breakfast. Hankalinki ya kwanta?" Ta ji sanyi a ranta, murmushi ta kasheshi da shi, ya maida kai ga abinda ya ke ci. John ta kwalawa kira ya shigo sanye da rigar kuku, umarnin ya juye ya sanya a fridge ta ba shi sannan ta matso ta soma tayashi cin kifin. Sanin da ta yi Hussein ba ya magana biyu, zai wuya ya ƙi yin abinda ya furta yasa hankalinta kwance ba ta ko damu ba. Sai dai kuma ga mamakinta da safe tashi ta yi sai filin gado ita kadai babu shi ba dalilinsa. Takardar da ta gani ta dauka ta karanta, sanarmata ya yi ya samu kiran gaggawa zai wuce Abuja meeting, abu ne da suka sanya rai har sun fidda za'a samu sai gashinan ya yiwu, ta yi hakuri idan ya yi rashin kyautawa. Hawaye ne kawai Hajiya Zeenatu ba ta yi ba. Ta kirashi a waya sai dai a kashe, ta ja tsaki ya fi a ƙirga. ***   Kuɗin take ƙarewa kallo ba tare da ta iya kataɓus ba. Ta kasa bin umarnin Chairman ɗin nata ta dauka balle har ya je jakarta. Kuɗin da ya ninka albashinta sau biyu. Da mamaki ta dubeshi, kallonta yake ƙasa-ƙasa. "Me zan yi da su?" Dariya ya yi, duk a zatonsa ta ruɗe ne saboda yawan kuɗin, bandir na dubu har guda uku ai ba wasa ba. Ya kara turo kuɗin. "Dauka dai ki riƙe tukunna Madam Ramlat." Girgiza kai ta yi. "Ka yi hakuri Yallaɓai ka faɗamin kudin na menene tukunna." "Kyauta ce daga gareni, wannan ba komai bane daga irin kyautar da nayi maki tanadinsu. Don Allah kar ki ce ba za ki karɓa ba. Ke musulma ce,k kuma kin san ba kyau maida hannun kyauta baya." Har wani gumi ta ji ya tsastsafo saman goshinta duk da sanyin nu'arar Ac dake kaɗawa. "A'a, a'a, ka yi hakuri. Nagode wallahi amma ba zan iya karɓa ba." Daga haka ta kama hanya har tana tuntuɓe ta shiga kokarin ficewa daga ofishin, kiranta ya yi ta tsaya cak jin muryarsa ta koma irin ta  ubangida da bawansa. Sai da ta juyo ya ɗan saki fuska ya koma magana a tausashe. "Ga duk wanda ya sanki a wannan ma'aikatar, yabon kyawawan dabi'unki ke fitowa daga bakinsa, ban ci karo da wanda har yau ya kusheki ba. Don Allah kar ki sa na ga baƙinki, ki karɓi kyautarnan domin girman Allah da Annabi s.a.w" Kallonsa ta ke kawai, ya koma kamar ba Chairman ba, ya maida kansa mutum mai rauni. Banda ma rainin wayo, su waye suka santa a wannan ma'aikatar har haka da yake cewa wai an shaideta. Bandir daya kawai ta dauka shima sai da ta ji wani faduwar gaba, ta kudurta a ranta ba za ta kashe ko sisi daga kudin Chairman ba. Za ta adana ko don gaba. Zai kara magana ta ce. "A'a, ka yi hakuri don Allah, wannan ma ya isa. Kar ka yimin dole. Nagode Allah Ya kara girma." Ya yi murmushi, ko ba komai ya ji dadi. Ta sanya kudin a jaka ta fice ta barshi da shafa sanƙo. Gani yake kamar yanzun ba son jikinta kadai ya ke yi ba, har da ma halayyarta da ɗabi'unta. A hankali ya shafi sanƙonsa yana jin kamar ya samu mata ta uku. ***      I just published "BABI NA TALATIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/GuBmViwNabb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 36) A hanya tana tafe tana juyayin wannan lamarin, ta kasa gane inda Chairman ya dosa. Tana tsaka da wannan tunanin ne wayarta ta yi ƙara. Ganin sunan Hilal na yawo yasa ta kasa ɗagawa, can dai ta ga bai kamata ba don haka ta ɗaga. Maimakon muryar Hilal ya doki kunnuwanta, muryar matarsa Fa'iza ce. Sallamar da ta yi ma ba ta samu amsarta ba. "Ai shaiɗanu irinku basu bukatar a amsa sallamarsu. Ke ba ki ji kunya da kike bibiyar mijin aure ba? Mijin da kika so cutarwa har kika yi ikirarin kashe shi? Koda dai, ba ke ya kamata na fadiwa hakan ba, shi marar zuciyar da kika lashewa kurwa shi ya dace na tunkara da batun! Ina miki gargadi tun wuri ki fita daga rayuwar mijina! Ki fita! Mijina ba sa'an aurenki ba ne! Ya fi karfinki! Ke ba ma shi ba, duk wani kamilin miji da yasan me yake ba zai tunkareki da sunan aure ba sai da karuwanci! Ko ba komai ba wanda bai san kina da ƙanjamau ba, kowa yasan tsohon mijinki!" Tun soma maganarta, Ramlat ta gangara gefen titi ta faka motar. Shiru ta yi mata har ta kai aya.  A zantukan ba wanda ya yi mata zafi kamar na sanya Aliyu da ta yi a zancen. Ta sa hannu ta share hawayen da ke sauka daga kwarmin idanu har suna kokarin shigewa bakinta. Ta bude baki da zummar magana ta ji muryar Hilal a ɗage yana yiwa matarsa masifa. "Wane rashin hankali kenan?! Da iznin wa kika ɗauki wayata?... Ba ta jira ta ƙarasa jin hayaniyarsu ba ta kashe wayar gaba daya don ba ta bukatar ji daga kowa. Kwantar da kai a saman sitayari ta yi zuciyarnan na tafarfasa. Ko mene ita ta aikata abinda dole a zageta don shi, sai dai babu dalilin da za'a sanyo Aliyu cikin sabgarnan. Aliyu ya yi kyakkyawar mutuwa irin wanda ko mutumin kirki  ne ya samu ya dace. Da ace Fa'iza ta kwantar da hankalinta, babu Hilal a zuciyarta, ba ta yi mishi so irin na aure. So take mishi na ƴan uwantaka, tana mishi kallon yayanta da suke ciki ɗaya. Ajiyar zuciya ta saki kafin ta maida hankali ga kallon yanda hadari ya yiwa garin luf. Wani murmushi ta saki mai ciwo tana share hawaye, addu'a ta yiwa Aliyunta sannan ta kunna karatun Alkur'ani, ta ja motarta.   Ba ta faɗa wa Hajiya abinda ya faru ba sai dai har dare wayarta a kashe. Kamar daga sai ga Hilal, lokacin suna falo zaune saƙon zuwansa ya isketa daga bakin Malam Bala. Ta yi shiru, Hajiya ta dubeta don dama ta lura gaba daya ba ta da walwala. Sanin da ta yi koda ta tambaya babu amsa yasa ta yin shiru kawai ta zubamata idanu.  Yanzun da saƙon zuwan Hilal ya risketa, ta lura da yanda ta ƙara ɗaure fuska. "Meke faruwa ne da ke? Tun shigowarki kin wani cukune, yanzu an ce ana kiranki kuma kin ji wanda ke tafe amma ba ki da niyyar zuwa." Ramlat ta dubeta kamar ta yi kuka. "Hajiya ba komai, kawai..." "Tashi ki je." Ganin umarni ne kai tsaye ta ba ta yasa ta miƙewa ta shige daki, can ta fito yafe da gyale akan doguwar rigar atamfarta ta fice. Yana tsaye kamar koyaushe jikin motarsa, ta karasa ba tare da ta bari sun hada idanu ba. Sallama ta mishi kafin su gaisa sannan ta ja bakinta ta yi shiru. "Ramlat na miki laifi, kiyi hakuri." Murmushin yaƙe ta yi. "Ba abinda ka yimin, asalima ko me Fa'iza ta fadi gaskiya ce ta faɗa. Sai dai don Allah ina roƙonka akan muyi hakuri hakanan. Kaunar da ka nunamin Allah Ya saka da alheri. Har abada nasan banda masoyi kamar ka." Ta ƙarashe da wani irin rauni, kuka ke son kwacemata, tunaninta ya tafi a shekarun baya na irin cin kashin da ta yi mishi. Hawaye ta shiga fitarwa ba tare da ta sani ba.   Ta ɗago ta kalli farin hankicif da ya miƙomata kafin ta dubeshi, murmushi ya ke mata wanda ya fi kuka ciwo yayinda idanunsa suka kaɗa. Zuwa yanzun shima ya saduda kuma ya ji zai hakura ko don kar ya faɗa fushin iyayensa. Akan Ramlat, yau Fa'iza ta kai ƙararsa gurin iyayensa. Sosai aka buɗemishi wuta kuma sun kara rantsuwa akan tsinuwa gareshi idan ya dage akan aurenta. Ta sa hannu ta karɓa ya soma magana. "Ramlat kar ki damu, nima na ji a raina yanzun zan iya hakura da ke ba kuma don ina so ba. Ina miki kyakkyawan fata a koyaushe. Ina roƙon Allah Ya kawomaki sauyi a rayuwa, Ya zaɓamaki mijin da ya fi ni, mijin da zai kularmin da ke ya kuma nunamaki dukkan kauna da soyayya. Allah shaida ne, na so na aureki, sai dai a matakin da nake kai yanzu zan iya faɗawa fushin iyaye da na Mahaliccina. Ya zamemin dole na hakura kar biyewa son zuciyata ya jazamini." Ya ci gaba da kalaman da ke nuni da irin alhininsa na rabuwarsu. Haka ta yi ta fidda hawaye a karshe suka rabu ran kowannensu babu dadi. Allah Ya taimaketa Hajiya ba ta falon sai yara da suka sheme duk sun yi bacci, jiki a saluɓe ta kai kowannensu makwancinsa ta yi musu addu'a sannan ta koma falon da zummar kashe kayan kallo. "Yaushe kika shigo?" Ɗagowa ta yi bayan ta kashe socket din talabijin ta dubi Hajiya. "Ban jima da shigowa ba." "Lafiya?" Ta watsomata tambayar ganin yanda take fidda hawaye, ta kasa danne kukanta, kawai sai ta fashe da kuka. Umarni ta bata akan ta zauna su yi magana. Nan ta zayyanemata yanda suka yi da Hilal. Jinjina kai Hajiya ta yi. "Allah Sarki, yaron kirki. Dole ki yi kuka Ramlatu, rashin mutum mai hakuri da nagarta kamar Hilal abu ne mai ciwo. Da ace ba mai hakuri bane, hanyar ma da kika bi ba zai kalla ba ballantana har ya bi ɗin. Allah Ya sasanta shi da mai ɗakinsa, ke kuma Allah Ya yi maku zaɓi." Ta amsa sannan suka yi sallama kowannensu ya shige ɗaki. Wanka ta soma yi ta sauya kaya gami da kwanciya saman gado. Tausayin Hilal kawai ta ke ji yana nukurkusarta, a karshe ta yi addu'a ta kwanta. ***   Washegari tun safe ta shirya ta fita da yara makaranta. Caa suka yi mata kowanne da nashi kalar ƙorafin, daga ba'a ga fensir ba sai mai kawo ƙarar Antinsu ta bugeshi. Ita dai ban da murmushi ba abinda ta ke yi, idan da sabo ta saba, kowanne da nashi ƙorafin musamman Ummi da Ansar wadanda har sun soma koyawa Affan.    Ƙarar wayarta ne yasa ta dauka, ganin sunan Mr Wuff ya ba ta mamaki. Ta dakatar da hayaniyar su Ummi kafin ta ɗaga da sallama daidai sadda aka tsayar da su a junction. "Yaranmu ne suka sanyaki murmushi ko tunanin bazawarinki?" Abinda ya ce kenan bayan amsa sallamar, hakan ne yasa ta saurin kallon titi. Gaban wata Jeep ta hangeshi zaune a kujerar kusa da direba. Da alama wani abin ya tsayar da su, kallonta ya yi kafin a hankali ya rufe gilashin motar. "Hey, kar ki cinyeni da kallo. Kamar ma kin manta cewar tuƙi kike ko?" Harara ta bankamasa don ta san koda ita din ba ta kallonsa, shi idanunsa yana kanta. "Meye abin kallo a fuskarka? Nikam ban ganshi ba. Na kalleka ne don na tabbatar kai dinne da sassafe haka ba wani ba." Murmushi ya yi tamkar tana kallonsa. "Allah Ya tsare hanya, drive carefully." Daga haka bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta ajiye wayar ba ta kara kallon inda motarsu take ba amma ya sanyata dariya. A bangarensa kuwa, ƙara jingina ya yi yana ƙaremata kallo daga ita har yarannata, ya lura babbar ta fi ɗiban kama da ita akan na tsakiyan da ƙaramin. Yanda suke ta hira suna karkatowa da zummar kallon  fuskarta ba karamin burgeshi ya yi ba. Direba dai ya yi bakam, ga labari na sukarsa amma ba wani da zai faɗawa.  Burinsa kawai su kai gida ya samu Joseph mai gadinsu, inyamuri kuma mai jin yaren Hausa sosai su tsegunta. Da alama dai Yallaɓai aure zai yi, sun tabbata ba karamin bomb ne zai fashe ba. Har aka ba su hannu yana  satar kallon Ogannasu, hankalinsa duka yana ga Ramlat da yaranta. Kusan tunda ya daukoshi daga Airport bai yi mishi wani kwakkwaran magana ba sai yanzun da ya ga budurwarsa. Farin ciki sosai direban ke yi, ko ba komai Yallaɓai zai samu sa'ida daga wurin Hajiya Zeenatu. Su kansu suna mamakin yanda akai ya ƙare da auren mace kamarta. ***   Har ta sauke yaranta a makaranta ta kama hanyar ofis ba ta bar tunanin wayar da suka yi da Hussein ba. Sosai ta ke mamakinsa, idan da a farkon ganinta da shi wani zai ce mata yana da sauƙin kai har haka toh fa za ta musanta, za kuma ta ƙaryata nan take. Da alama wannan yana daga cikin nasarar jihadinta. Ta shaƙu da shi sannan a ƙarshe ta shiryashi da ƴan uwansa. Wannan kaɗai ne burinta. Tana faka motarta ba ta kai ga barin parking space din ba, suka ci karo da Halima. Wani irin kallo Halima ke bin ta da shi tana murmushi. Bayan sun gaisa ta ce. "Sakatariyar Chairman, wato ko nemanmu ma kin daina." "Ko rannan na shiga ke kuma ba ki zo ba." Fadin Ramlat cikin dakiya don yanzun ba ta kaunar  shiga duk wani lamari da ya shafeta. Ta riga ta gane ba masoyiyarta ba ce. Halima ta ɗan taɓe baki. "Oh, haka fa. Ai mancewa na yi, an faɗamin. Ina fatan dai za ki saki jikinki ki ajiye kauyanci gefe ki ci arziki inda kika ganshi." Ɗan haɗe gira Ramlat ta yi tana mata duban ido cikin ido. "Bangane hausarki ba, me kike nufi?" Dariyar ƴan duniya ta yi. "Dama ba lallai ki gane ba, amma nidai ina mai ba ki shawarar kar ki yi wasa da damarki." Daga nan ta ficewarta ta bar Ramlat tsaye. Wani murmushi ta yi gami da girgiza kai itama ta soma tafiya nutse. Ta rasa ranar da Halima za ta nutsu ta yi hankali, kullum tunaninta iri guda ne. 'Allah Ya shirya.' Ta furta a ƙasan ranta. ***   "Wannan asarar kuɗi har ina wai?!! Duk aikin da na ɗauko sai ya lalace! Abu ne da bai taɓa faruwa da ni ba duk tsawon wannan shekarun! Ina tsoro kuma." Hajiya Zeenat ke wannan ƙorafin kamar ta zubda hawaye a tsakar falon Hajiya Batool da misalin ƙarfe uku da mintoci na rana. "Ni na rasa ma me zan ce. Kusan duk  yanda aka kurantamana wannan mutumin ba haka muka riska ba. Kinga yanzu wai yaronnan Dubai zasu wuce da shegiyar yarinyarnan siyayyar kayan haihuwa? Ban isa na faɗi aibunta ba zai hau ni da  faɗa kamar shi ya haifen." Tsaki Hajiya Zeenatu ta ja. "Ke naki ai da sauƙi tunda ba mijin bane, ni ina miki maganar duk aikin da nayi sai ya lalace. Duk abinda na ɗauki niyyar na yi sai kiga an yi rashin sa'a a kai. Jikina ne ke yin sanyi, amma ba zan karaya ba. Har abada kuwa." Ta ƙarashe tana mai goge zufa sa'ilin da kwakwalwarta ta tafi ga tunanin wani abu da ya kasance a can baya wanda nan da nan ya jefamata tsoron da ta ke gujewa a zuciya. "Toh wai me zai hana mu koma wajen Gora? Kamar dai aikinsa ya fi na wannan buzun. Duk buge ce." Jinjina kai Hajiya Zeenatu ta yi. "Kuma hakane, kin fadi gaskiya." Cewar Hajiya Zeenatu cikin karaya, yanzun dai ta saduda, banda ma asarar kuɗi, aikin ma da ta yi nema ya ke ya rushe, nema yake ya zama tamkar ba ta taɓa yi ba. Ita da kanta ta soma ganin sauyi acikin rayuwar Hussein. Ya rage shakkarta. Suka yi ta tattauna yanda zasu ɓullo wa matsalolinsu kafin su yi sallama su rabu zuƙatan duk babu dadi. *** BAYAN SATI ƊAYA. Tun shigowarsu garin na Dabo tumbin giwa Fatima ke ji kamar tayi fiffike ta yi ta zagaye gari tsabar farin ciki da jin dadin yau ga ta a Kano. Da wayonta haka dai ba ta taɓa zuwa ba. Don haka bakinnan nata a wangale ga hannunta riƙe da cakulet tana sha. Uban ya dubeta yanda ta hakimce gaban mota, duk son uwar da haka, hakura ta yi don ba ta iyawa rigimar Fatima wani sa'in, zamanta ta yi kusa da Hafsat da Dada. "Wai nikam Fatima kodai a Kanon zamu bar ki ne?" Fadin Kausar tana dariyar yanda yarinyar ta kifa goshi a kan gilashi tana ƙarewa waje kallo. Da wani ɗoki ta dubi Mamarta ta gyaɗa kai, yanda ta yi duk sai ta ba su dariya. "Allah Ya rayaki dai Fatin Biyu" Dada ta furta da dariya. AlHassan wanda walwalarsa ta ɗan ja baya tun shigowarsu garin sai a sannan ya ɗan saki fuska. Autar Dada ta ɗan dunguro kanta. "Ke da ace za'a bar ta kinga alamar ba za ta zauna ba?" Aka dara. Haka suka yi ta hirarrakinsu har suka kai gidan Kawunsu Modibbo. Yana parking ya budemusu ƙofa kafin ya zagaya ya sa yara su fiddo akwatunan. Ya ɗaure fuska ya sauya kamar ba AlHassan ba mutum mai yawan fara'a. "Zan je na dawo." Abinda ya ce kenan, Dada ba ta yi mishi dole ba ganin sauyinsa, ta kauda kai don tasan ba da son ransa suka zaɓi kwana a gidan Modibbo ba madadin ɗaki a Hotel da ya yi niyyar kama musu. Suna shigewa ciki shima ya ja motarsa ya fice. ***   Kausar ce tsaye bayan ta dawo daga ɗakin Amarya tana duban yanda Dada ta zage tana faman aiki tuƙuru a sashin Hajja Fatuma. Tana kallon yanda jikokin Hajja Fatuma suke yin yanda suka so babu mai kwaɓa balle magana, yaranta mata na hakimce saman kujera suna hira da sha'aninsu ita kuwa ta shiga cikin ƴan aiki ana gyaran kaji. Juyawa ta yi ta koma sashin Amarya dakin da suka sauka. Nan ta tarar da Hafsat tana sauyawa Fatima sutura zuwa na bacci, a gefenta Rasheeda ce, ɗiyar Amarya da zasu yi sa'anni da Hafsat. Su dai kam dama jininsu ya hadu don har chatting suna yi. Ganin yanda Kausar ta shigo fuska a ɓace yasa Hafsat gane inda zancen ya dosa.   "Anti kin ce ta zo ta ci abinci?" Sai a sannan ne ma ta tuna abinda ya kai ta wurin Dadar, ta ja guntun tsaki. "Kinga halin mantuwa ko?" Miƙewa Hafsat ta yi a fusace, ita kam yau sai ta taho da uwarta don ba bauta ta zo ba. Za ta fice Kausar ta riko hannunta. Ta dubi Rasheeda. "Don Allah kirawo Dada." Rasheeda ta mike ta fita. Ta riga ta san komai dangane da irin tsangwamar da Dada ke sha a wurin Hajja da Modibbo mahaifinsu har ma da wasu cikin ƴan uwansa.  Ta kuma rasa dalilin wannan ƙiyayya, a ganinta abinda ya wuce ya riga da ya wuce. "Kai Adda, nidai wallahi da kin bar ni na je, na gaji da wannan abu. Tun zuwanmu awa nawa yanzu ace Dada ko abincin kirki ba ta ci ba? Daga zuwa gaishesu ta dawo sun haɗata da aiki don rashin tausayi, kuma shi ne ita ta karɓar? Nidai sai na gayawa Hamma.." "Kul! Kar ki soma. Kinsan dama ba da son ransa aka yi wannan tafiyar ba, abin ya zo mishi ne a ba yanda ya iya. Yanzu kika kirashi tayar da hankalinsa kawai za ki yi kuma ranmu ya ɓaci. Ke dai ki bi gargadin da Dada ta yi maki a rabu lafiya. Gasunan dai kinga su Hanifah duk suna zaune, nima ban ishesu kallo ba tunda a cewarsu ina auren AlHassan." Yamutse fuska Hafsat ta yi. "Wallahi Adda, Adda Hanifah ƙarya take. Son Hamma take yi kamar yanda ɗan adam ke son rayuwarsa. Ai inada labarin komai, kuma ma.." Sai ta yi ɗif, sai yanzun ta ke tuna katoɓarar da ta yi, ta ɗan datse harshe da haƙori ta yi shiru. Dada da ke tsaye bakin ƙofa ta ƙaraso ta bata rankwashi a kai, ita kuwa Kausar dariya ma ta yi. A saninta ko giyar wake AlHassan ya sha ba zai auri Hanifah ba. Har abada ya tsani zuri'ar  Modibbo. A wani ɓangaren kuma itama ta san da wannan soyayyar ta Hanifah ga mijinta, takan ga kiranta sau tari a wayarsa, bai yi saving lambar ba, amma ita tana da lambar a wayarta. Allah Ya hana bincike, shiyasa ba ta zurfafa ba. Sai kuma sanin da ta yiwa Modibbo na bala'in son kansa da kuma ƴaƴansa, wannan ne waekness dinsa. Duk abinda yaransa ke so koda ba ya son abin, zai yi yanda zai yi ya nemamusu farin ciki. Wannan ya yi sanadin lalacewar wasu a yarannasa. "Ke za ki biyewa wannan shashasha har ki wani tsaya zurfafa tunani? Kin yarda da abinda ta ce kenan?" Dariya Kausar ta yi tana girgiza kai. "Ko kadan." Suka ɗan dara, Hafsat ta turo baki.  "Toh nidai gaskiya Dada ba zamu yarda da wannan aikin da kike fita ba, idan kika ci gaba zan kira Hamma." Dada ta yi murmushi cikin harshen fulatanci ta amsa. "Dayake shi ya haifeni ko? Banda abinki Hafsatu, ni da gida ɗan uwana? Wa ya fadamaki abinda na yi faɗuwa ce? Babu, zumunci na sadar kuma Allah zai duba."   Ita dai Hafsat ta ja hannun Fatima suka fice zuwa falon Amarya. Banda Dada ta tilastamata kuma tana son zuwa gurin Rasheeda, ba abinda zai sa ta tako ƙafarta Kanon, a yanzun ma ji take da ace akwai wasu ƴan uwannasu can za ta yi tafiyarta.      Da yammacin ranar AlHassan ya iso ƙofar gidan Modibbo, waya kawai ya yi ya ba Hafsat umarni fitowa tare da Fatima su yawata. Da wani irin ɗoki Hafsat ta mike ta shirya Fati suka fice ba su ko tsaya sallama da kowa ba banda Adda Kausar da suka faɗawa ta sanar Dada.    Fuska ta daure ganin yanda Taheer ɗa ga Hajja Fatuma ya tsuramata idanu yana kallo. Bafulatanin usuli wanda daga ka ganshi ka ga jinin Mamman Gidado. Dagasken gaske tana lura da yanda yake wani safa da marwa a sashin Amarya wanda hatta da Rasheeda sai da ta nuna mamakinta a fili, acewarta abu ne mai wahala ka ganshi a sashin nasu. Har ta isa ta buɗewa Fatima gaban mota ta shiga itama ta bude gidan baya ta faɗa babu walwala. Alhassan ya dubeta yana murmushi sadda ya ja motar. "Ke kuma ke da wa?" Turo baki ta yi. "Bakomai." Ya taɓe baki. Ko me ya faru ai su suka sani, shi dai kam dama bai nunamusu yana son zuwan ba. "Daddy ina zamu je?" Cewar Fatima a ɗokance. Ya ja kumatunta da murmushi. "Surprise ne." Ya yi ta biyemata su na surutu har suka iso tafkeken shagon na A&Z.    Hafsat sai a lokacin ta saki ranta, suka fito suka jera ciki. Da ka gansu ka san jini ɗaya ne. Kai tsaye suka hau sama, ma'aikatan sai kallon AlHassan suke yi kusan a mamakance. Duk a zatonsu Mijin Madam ne, ganinsa da budurwa ya ba kowa mamaki, har da samari da ƴanmatan da suka mayar da wurin wajen zuwansu. Shi kuwa Alhassan wayar da aka kirashi ce ta sanya shi ba Hafsat kudade tare da ba ta umarnin ta suyamusu duk abinda ya dace, yana jiranta a waje. Sauri yake sosai yana son barin hayaniyar cool music da ke tashi a wurin ganin Director ɗinsa na wurin aiki ke kiran. Magana ce za su yi mai muhimmanci. Karo ya ci da ita sadda ta sanyo kai nan take wayarsa ta faɗi, ya ɗago ita kuwa ta matsa baya gami da fadin. "Yi hakuri fa." Ɗagowar da zai yi sai da ta ji hantar cikinta ya kaɗa. Ba don ace tare suke tafe da mijinta Hussein ba, kuma yana cikin  mota sanye da kananan kaya, madadin wannan da ke sanye da shadda blue, za ta rantse shi ne tsaye. Murmushi ya yi mata da nunamata ba komai kafin ya yi gaba. Har tana tuntuɓe haka ta juya ga mararta da ta cika taf da fitsari, haka ta karasa ga Hussein wanda ya juyamusu baya yana kokarin rufe motar. Ganinta a gigice yasa shi dubanta da mamaki. "Lafiya?" Dafashi ta yi gami da riƙe kai. "Lafiya, a'a ba lafiya, muje don Allah. Jiri nake ji shiga mu tafi." Hussein dai abin ya dauremishi kai, zai yi musu abin mamaki Hajiya ke roƙonsa ya bar kowace magana a gefe su wuce su koma gida. Ba ta da lafiya. Dole ya shiga motar bisa umarninta itama ta shige. Ba ta samu nutsuwa ba sai da ya doshi gate, sai dai kafin ya kai ga fita jikinsa kawai ya yi wani irin la'asar yayinda ya ji kirjinsa na dukan uku-uku, ya kalli bayansa ta mirror. Bai ga kowa ba face wani matashin da ba zai fi shi a shekaru ba, tsaye jikin mota ya juyamusu baya yana amsa waya. "Ya kake tafiya kamar ba ka so? Ka yi sauri don Allah." Maganar Hajiya ta dawo da shi nutsuwarsa, ya ɗan ƙara ƙarfin gudun. "Wai meke faruwa? Naga lafiya muka shigo wajennan." Girgiza kai ta yi tana share gumi. "Nima dai ban sani ba. Watakila plantain da kwai da na ci ne ya ɗan juyamin ciki." "Kuma kika ce jiri?" Ta ja guntun tsaki ganin zai ƙureta, ita dai yanzu ta fi kaunar a kyaleta tayi tunani mai kyau. Wannan ya nuna twin brother din Hussein ya zo Kano kenan? Lallai dole ne ta hana Hussein zirga-zirga. A farin farko dai za ta bincika ta ji dalilin zuwansa, idan har zama ne na dindindin, barin Kano na har abada ya gansu ita da mijinta koda ba ya so. Haka ta yi ta tufka da warwara, Allah-Allah take su isa yanda za ta samu damar yin tunani mai kyau.   Shi kuwa AlHassan koda ya gaji da gaisuwar da wasu daidaikun ma'aikatan masu wucewa suke mishi sai kawai ya shige cikin motarsa ya zauna ya ci gaba da wayar. Har su Hafsat suka fito ɗauke da ledoji yana waya. Hayaniya kwakkwara hanasu ya yi, kusan har ya soma tuƙi suka yi tafiyar mintoci yana waya. Can dai ya katse ya ajiye, da murmushi ya dubesu. "Sorry, ban kyauta muku ba ko?" Fatima ta turo baki ta gyaɗa kai. Dariya ta basu. ***   "Hajiya Ramlatu, ina son ganinki." Shi ne abinda ya ce kenan bayan ta saka wayar a kunne. Ramlat ta ajiye kan wayar ranta na zafi, tsabar raunin hankalin Chairman ya soma isarta, tana kallon abin kamar da biyu yake yi.    Ta mike ta gyara zaman naɗin laffayarta ta tabbatar ko'ina na jikinta ya ƙara rufuwa ruf sannan ta ƙarasa ciki. Kallon haramun dai bai fasa ba don haka ta daure fuska. "Gani Yallaɓai." Ta faɗi a ladabce cikin basarwa don yanzu ta bar ganin ƙima da mutuncinsa. "Amm..yanzu a kan aiki muke don haka ba zan ce komai ba. Sai dai idan ba damuwa ko za'a yimin iznin zuwa gida?" 'Anzo wurin.' Ta fadi a ƙasan ranta. Girgiza kai ta yi. "Ka yi hakuri Yallaɓai..." "A'a kinga Ramlat, ba batun nayi hakuri bane. Tsakani da Allah ba zan iya ba. Na fadamaki yanzun muna bakin aiki ne, magana ce kuma zan zo muyi ta fahimta." Shiru kawai ta yi, ganin ta ƙi ce mishi uffan ne ya sa shi magana. "Zan ba ki daga nan zuwa Monday, please ki yi tunani mai kyau. Ki sani, koda ace a baya sharri ne a zuciyata, yanzun babu ɗigon wannan Ramlatu. Wallahi babu." Yanda yake magana kamar wani yaro sai ma ya so ba to dariya, ita dai ba ta ce komai ba. "Shikenan kina iya tafiya." Ta juya ta fice ba ta ce mishi uffan ba, Chairman ya bita da kallo kafin ya lumshe idanunsa ya sauke ajiyar zuciya. Sanin gidansu Ramlat abu ne mai sauƙi a wurinsa, sai dai ya fi kaunar bi ta hanyarta ko don ya goge wannan kallon girma ya faɗin da ta ke yawan jifansa da shi. Ko ba komai dai da gaskiyarta. Da niyyar cuta ya zo sai soyayyarta na gasken ya sauya komai. ***  I just published "BABI NA TALATIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/4aFXFyDdjbb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 37) LAMIƊO CRESCENT "Ki soma faɗamin wannan ƙullen da kike yimin na mene wai? Ina da aikin yi, kin hana ni fita." Hussein ke maganar a tausashe da ɓacin rai saman fuskarsa. Zeenatu dubansa take yi don ta rasa ma hanyar ɓullo mishi. Ba ta son fitarsa, jinta take kamar wata zararriya, gaba daya babu aikinta ɗaya da ya tafi daidai. A baya ta rantse ba za ta bar garin Kano ba amma kam a yanzun a shirya ta ke da yin nesa da duk abinda zai sa Hussein ya suɓucemata. "Tafiya zamu yi, Kano nake son mu bari." Kallonta kawai yake yi cike da tunanin meke damunta har haka. Dariya ta so kwacemasa don shi kansa yana mamakin irin ƙwarin gwuiwar da ya ke samu na yi mata jayayya akan duk abinda ya zartar a yanzun. "Kinsan me kika ce kuwa?" Ya fadi kansa tsaye yana kallonta har sai da ta ji ƙirjinta ya bada dam! Dakyar ta haɗiyi yawu. "Me kake son ka ce? Jayayya za ka yi da ni? Ba za ki bi ra'ayina ba?" Ya yi shiru kawai yana kallonta da wani mamaki, wani tsana yake ji kamar yana son tasomishi sai wata soyayya da bai san mafarinta ba ta zo ta danne wannan tsanar. Kauda kai ya yi gami da miƙewa daga saman gadon. "Kiyi hakuri, abu ne da ba zan iyaba." Daga haka ya faɗa banɗaki. A gigice Hajiya Zeenat ta miƙe ta fice zuwa ɗakinta. Wanka ta yi a gurguje ta shirya. Kamar yanda ta zata hakan ce, ya shirya da zummar zuwa ofis. Bai yi mamakin shirin da ta yi ba illa murmushi da ya yi, abin kam ya ba shi dariya. Wannan bibiyar bai san kuma ta mece ce ba duk da a bayan ma tana yi mishi don wani sa'in kamar daga sama haka yake ganinta a  ma'aikatarsu.   Ya shirya suka fita tare, ita ke tuƙi don a cewarta za ta fita daga nan duba Hajiya Batool ba lafiya, bai damu da gasken take ko a'a ba. Ya dai amsa zuciyarsa a ɓace. *** Tuƙinta cikin nutsuwa take yi, yau gaba daya ta makara a dalilin zazzaɓin da ya kama Ansar sai da ta kai shi asibiti tukunna ta maida shi gida. Ta so ta ƙi zuwa sai dai hakanan ta daure tunawa da aikin duba wasu files na Tax.    A harabar wurin parking ta ajiye motar ta ƙarasa ciki. Ko zama ba ta kai ga yi ba wayar dake saman tebur ta ɗau ƙara, tsuke fuska ta yi gami da jan tsaki ciki-ciki. Tun sadda suka yi haka da Chairman ta ƙi jinin abinda zai sa ta haɗu da shi sai dai ba yana ta iya. Wayar ta ɗaga da sallama, ya amsa gami da ba ta umarnin ta je. Dire wayar ta yi ta ajiye jakarta ta fita bayan ta gyara zaman hijabinta. Yana zaune da manyan kaya har da babbar riga, idanunsa sanye da gilashi yana danna laptop. Shigowarta yasa shi kallonta. 'Ban yafe ba.' Ta furta a ƙasan ranta. A fili kuwa gaidashi ta yi a ladabce, ya amsa yana wani washe haƙora. Bayan gama jin dalilin da yasa ba ta shigo da wuri ba ya gangara kan abinda ke cin ransa. Chairman ke kiran yana sonta, dama tuni ta riga ta gane. "Ke ba yarinya ce karama ba, nasan kinsan me nake nufi kike kaucemin. Wallahi na gaji, bani da burin da ya wuce na aurenki a yanzu Ramlat. Don Allah kar ki ce za ki ƙi. Na miki alƙawarin gidanki daban, ba zan haɗaki da matana ba." Ya kammala surutansa tana sauraro, ƙarshe ta soma da ba shi hakuri. "Inada wanda zan aura don har anyi magana." Wata dariya ya kece da ita, hatta ita Ramlat sai ta ji maganar nata banbarakwai, ta kara hade fuska. "Haba Hajiya Ramlatu, yanzu fa na gama fadamaki ke ba yarinya ba ce. Wane sokon ne zai yi gangancin tsallake sati biyu ba'a ɗauka muku aure ba? A'a ban yarda ba gaskiya. Nidai ki karɓi ƙoƙon barata ki ba address da kanki a ganina zai fi mana mutunci." Ta yi shiru, ya ci gaba da magiya kamar ba Chairman mai cin magani a gaban staffs ba, haka ba don ranta ya so ba ta mishi kwatance. Ranar kowa ya kalleshi yasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa. Koda aka tashi, kai tsaye tsohon department din da take ta ziyarta. Ta kuwa ci sa'a duk suna ciki, aka gaisa ba ta ko bi ta kan Halima mai amsa gaisuwar ciki-ciki ba. "Yanzun nake shirin shiga wurinki. Ƴar halak kin ƙi ambato." Ta kai duba ga Naja'atu Azare mai wannan batu, suka yi dariya. Takardar gayyatar biki ta fiddo daga jakarta ta miƙa mata. Murmushi sosai Ramlat ke yi har fararen haƙoranta na bayyana. "Kai na ji dadi sosai wallahi, ki ce abun ya zo. Allah Ya nunamana, Yasa muna raye." Aka amsa da Amin. Hira ta tsaya yi a karshe suka dunguma gaba daya matan suka fita, Halima har lokacin fuskarnan ba fara'a. "Wai ke me akai miki kike ta cin magani?" Saudat ke tambayar tana dubanta. "Ba komai, sai Allah Ya kaimu." Daga nan ta yi gaba ta bar su. "Wai nikam Ramlat kamar dai akwai wata a ƙasa tsakaninku da Halima, na lura duk sadda kike wuri ba ta fiye kaunar hakan ba." Samira ke wannan maganar tana duban Ramlat. Ita kam murmushi kawai ta yi, tana ji suna faɗin rashin kyautatawar Halima a lokuta da dama ita dai ta musu sallama ta nufi inda ta yi parking. Idan da sabo ya ci ace dama ta saba da halinta. Murmushi ta yi da wani bahagon tunanin da saƙe-saƙen zuciya ke jefawa ɗan adam ya ziyarceta, wato ace ta yarda da auren Chairman, Allah Kadai Yasan irin kiyayyar da za ta fuskanta daga Halima. Ba ma daga gareta kawai ba, har da yawa cikin matan wajen. ***   Zaune gaban Boka Gora, Hajiya Zeenatu ce da Hajiya Batool kowannensu rai a ɓace. "Shekaru sama da goma muna tare da kai, kar ka yi mana haka. Ka taimakemu ka kula da damuwarmu. Bamu da wanda muke da shi da zai share hawayenmu face kai." (Wa'i'yazubillah) Gora ya yi wata dariya ta shaiɗanun da suka riƙa kafin ya ɗaure fuska tamau. Ya kwalalo musu manyan idanuwansa da suka sha kwalli. "Kar ku rainamin hankali! Wa ya fadamaku zan kasa sanin kun yi doguwar tafiya har wata ƙasa don a yi muku asiri? Cin amanar da zai biyo bayan dukkan taimakon da na yi muku a baya kenan! Yanzun da ku ka zo me kuke so nayi bayan komai ya warware! Komai ya lalace! Ke Zeenatu! Ki fara tattara kayanki ki bar ƙasarnan don asirinki ba zai je ko'ina ba sai tonu! Ita dai yarinyar da na gargaɗeki a kanta, ita ce silar rushewar dukkan ayyukanki! Ke kuma Batulu! Nan ba da jimawa ba, ɗanki zai zo da batun ƙarin aure! Auren da zai rushe duk wani asiri da kika yi tsakaninsa da matarsa! Anan ne duk abinda kika binne zai fito fili muraran!" "Ƙarya kake! Wallahi ƙarya kake! Dama na faɗamaki kar mu zo wurinsa!" Hajiya Batool ke maganar jikinta har yana ɓari, fuskarnan wacce man bleaching ya maida jawur, sai ƙara kyalli take. Ita kuwa Hajiya Zeenatu idanun kamar an watsa barkono. Ba ta san hawaye ke fita daga idanunta ba sai da ta ji suna kokarin shigewa bakinta. Shi kuwa Gora banda wata shegiyar dariya ba abinda yake yi don ko kaɗan kalaman bai ɓatamasa ba, ya saba ganin irin wannan hauka da jahilcin na mata.   Tsawa Hajiya Zeenatu ta dakawa aminiyarta ganin gaba ɗaya ma ta ƙi maida hankali ta nutsu su nemi mafita. Ita da take da tashin hankalin rasa miji irin Hussein ba ta yi gigitar da Hajiya Batool ta yi ba. Ta sa mayafi ta sharce gumi idanunta a kansa. "Mun tuba, wallahi mun tuba ba zamu ƙara saɓawa umarninka ba. Ka taimakemu Gora, a wannan gaɓar idan ka ce za ka bar mu, ba wanda zai tsira." Ya ci gaba da kallon ƙasar da ke shimfiɗe gabansa yana ƴar dariya gami da gyara hannun babbar rigarsa. "Akwai tsada..." Bai ma kai ga ƙarasawa ba duk suka tari numfashinsa. "Zamu biya ko nawa ne, wallahi ko duka abinda muka mallaka ne." Ya jinjina kai, kaf ba wacce bai san halinta ba a cikinsu. Yana da karatun kowaccensu don tun ana damawa da su a siyasa da bariki yake tare da su. Maida hankali kan ƙasa ya yi can kuma ya ɗago ya dubi Hajiya Zeenatu. Yanzu da ace zai faɗi ainahin abinda ya gani, toh ya tabbatar kuɗaɗen da suka Kaɗaita masa ba zai samu ba, gwara ma Hajiya Zeenatu akwai sakin hannu, anan ne suka sha bamban da aminiyarta da ta kasance marowaciya. "Aikinku zai yiwu, sai dai dama ai na riga da na faɗamaku akwai kashe kuɗi. Batun kuma shi mijinnaki ina tabbatar maki ba zai haɗu da ɗaya cikin ƴan uwansa ba. Sai dai kuma ki kara kiyayewa ga barin kowace mace shiga rayuwarsa. Idan na ce kowacce, ina nufin hakan!" Ya fadi kai tsaye, kusan bayanai biyun ƙarshe da ya yi sun kasance abinda ya hanga ɗin. Jinjina kai Hajiya Zeenatu ta yi, nan kuma Gora ya shiga lissafomata abinda za'a siya. Da ta gaji ta bude jaka ta fiddo bandirin ɗari biyar sabbi har biyu ta ajiye a gaban buzunsa. "Gashinan, na bar maka wuƙa da nama, duk abinda ya kamata nidai a yimin don Allah. Sannan idan da hali a yiwa ita yarinyar turen aljanu su zama silar ajalinta. Nidai ko haukatamin ita ne don Allah a yi Gora." Wani murmushi Gora ya yi ya sa hannu ya dauki kudin gami da faɗin. "An gama! Kedai kawai ki sha kuruminki." Daga haka ya juya ga Hajiya Batool wacce ganin irin yanda ya  kwantar da hankalin Hajiya Zeenatu da bayanan gamsuwa da kuma karfafa gwuiwa, itama sai ta ji nata ya kwanta. Nan ya shiga kora mata karya da gaskiya itama ta hau ta zauna ta cikashi da kudin. Kafin dai a bar gidan Gora an shirya, dariya ake yi har yana neman su ba shi haɗin kai yanda suka saba. "Alƙawari ne mun yi maka, zamu cika mu ziyarceka da zarar aiki ya kammalu." Cewar Hajiya Zeenatu da take ji kamar an mata albishir da mutuwar ɗan uwan Hussein. Wata dariya suka yi tare kafin su fice. Sai a sannan hankulansu ya kwanta. ***    BAYAN KWANA UKU.   Tun wuraren biyu na rana ta samu kira daga Alhassan (wanda tuni ta sauya mishi suna daga mutumin mall zuwa Alhassan kamar yanda ta ga username ɗinsa a WhatsApp). Sanarmata da batun zuwansu da iyalinsa ya yi, wannan tasa bata zauna ba, ita da Hajiya da Ladidi suka shiga kicin don yin kayan maƙulashen tarbar baƙi. Suna tsaka da aikin sai ga Zulaihat da Rafee'ah, mamakin irin wannan garar da ake shiryawa ta kamasu. "Baƙi za ku yi ne Hajiya?" Cewar Zulaihat tana duban kajin da Ramlat ke soyawa. "Au, ashe mu ba zamu ci daɗi ba kenan sai zamu yi baƙi?" Dariya ta basu. "A'a, amma dagaske naga kayan ne da yawa har da su zoɓo da ginger. Duk na waye?" Murmushi Hajiya ta yi. "Ku tambayi ƙanwarku." Ramlat ta sanarmusu batun zuwan Alhassan wanda suka taɓa jin ta yi waya da su. Rafee'ah ta kama baki tana dariya. "Ah lallai, ki ce surukinmu ne zai iso. Kai abu ya yi kyau." Yamutse fuska kawai ta yi kafin ta murmusa, ita dariya ma suke ba ta idan suna haɗa ta da AlHassan. Ko za ta kwana ta na faɗamusu zumunci ne kawai tsakaninsu ba yarda zasu yi ba don haka ta ja bakinta kawai. Hajiya da su Zulaihat suka koma falo, itama tana kammala suyar ta haɗa chicken pepper dinta ta zuba yanda ya kamata, da taimakon Ladidi suka kwashi kayan zuwa saman tebur. Lemukan suka sanya a firij. Tana zama a falon ba jimawa, wani tunani ya faɗomata a rai, cikin sauri ta mike zuwa ɗaki. Wayarta dake hannun Ansar wanda ke kwance yana buga game ta karɓa haɗi da faɗin. "Kaima Monday ta zo ba zama za ka yi ba sai ka je makaranta tunda ka warke." Ya hau tura baki. "Tashi ka je ga su Maman Twins da Anti Rafee.." Ba ta kai aya ba, da murnarsa ya dira ƙasa ya fice. Murmushi ta yi kawai. Abinda ya shigo da ita ta tuna hakan yasa ta saurin kiran Hisham. Bayan sun gaisa ya gama jan ta da tsokana yanda ya saba sannan ta samu damar magana. "Idan ba damuwa don Allah ka shigo gidanmu kamar wuraren biyar haka." "Toh Antinmu, ina fatan dai ba ƙarata Princess ta kawo ba? Dagaske sharri take min." Murmushi Ramlat ta yi, Hisham ba ya rabo da zolaya. "Ni ba haka nace ba, abu ne mai muhimmanci akan abokinka, sai dai duk abinda za ka gani kar ka yi magana. Please." "Shikenan, kar ki damu, In sha Allah zan shigo." Daga nan suka yi sallama ta faɗa wanka. Koda ta fito, ba kwalliya ta yi ba sai dai ta gyara fuskarta ta shafa hoda da man leɓe. Ko ba komai baƙinta ne. Ta shirya ta fito falon daidai sadda su Ummi suka dawo daga makaranta. Dakyar Ramlat ta korasu islamiyya har Ansar don a farko ganin iyayennasu sun so su ƙi zuwa. Sai a sannan su Rafee'ah masu kwasar  garar abinci suka yi wa Ramlat kallon tsaf ganin yanda ta sh sutura mai kyau. Ramlat ta yamutse fuska kadan. "Ku faɗa kawai, abinda ku ke nufi ba shi bane." Dariya suka yi. "Kin ji yarinya da tsarguwa." Fadin Zulaihat tana duban Rafee'ah. Taɓe baki Rafee'ah ta yi, ita me za ta ce? Ta dai lura Ramlat ba ta kaunar maganar aure don haka a yanzu nata mujiya. Aka bar zancen aka faɗa labarin gidan Yaya Munir wanda a yanzu don kansa ya zo ya samu Hajiya ya rantse rabawa matansa gida zai yi. Wannan kalami ya sa su dariya musamman Zulaihat abokiyar takun saƙarsa. "Maganinsa! Tun farko nan ba na nunamasa hakan zai fiyemishi ba amma ya nunan shi din gwani ne. Kuma adali." "Toh dai yanzu ko mene ai shikenan tunda ya riga da ya faru." Faɗin Hajiya kenan. Haka suka yi ta hira kafin a kira la'asar duk su mike don ɗauro alwala. Wurare karfe hudu da rabi sai ga wayar Alhassan, nan ta ƙara yi mishi kwatance, a ƙarshe ma ta fita don tarbarsu. Har suka ƙaraso idanunta na wani gefen, ya fito daga motar sanye da dark blue din shaddarsa sai gilashin da ke ƙaramasa kyau. Ya karya hula kamar Bakano. Yarinya karama ta fito ta sha ƙananun kitso shuku a kanta, an sanyamata ribbons masu kyau da ya ƙaramata kyau. Ganin har da dattijuwar da nan take jikinta ya bata cewar ita ce Dada, yasa ta ƙarasawa tana ƙara yi musu barka da zuwa. Kausar da Hafsat sosai Ramlat ta burgesu, ta jagorancesu har cikin falon Hajiya wanda aka ƙara kimtsawa, Alhassan ne dai ya toge a farfajiyar gidan ya ƙi shiga. Bayan sun zauna aka gaggaisa, can kuma ta shiga daki ta kira Hajiya. Su Zulaihat ma suka biyo bayanta. Dada ba ta jin hausa sosai, a haka dai aka gaggaisa, wani abin Hafsat ce ke cin gyaranta. "Kinga abin Allah mai haɗa zumunta." Fadin Hajiya tana murmushi ganin yanda Fatima ta maƙalewa Ramlat kamar dama can sun taɓa haɗuwa. "A bar ki a nan za ki zauna?" Fadin Hafsat tana duban Fatima wacce ke ƙara shigewa jikin Ramlat. Da sauri ta wangale baki gami da gyaɗa kai, duk sai ta sanyasu dariya. Anan ne Ramlat ke ji dagasken dai su na da ƴan uwa a garin, kwatancen da ta yi yasa nan take suka gane gidan musamman Hajiya da Yakasai ya zama unguwar da ta ci ƙuruciyarta a ciki. Sai dai basu taɓa shiga gidan ba don ba wani fita suke yi ba sosai a unguwa, hakanan su ma mutan gidan ba kowa suke shiga sabgarsa ba sai wanda ya isa. *** Hisham gwanin cika alƙawari sai gashinan ya zo tun ma biyar saura. Babban abinda ya ƙara kwadaita masa zuwan bai wuce na cewa da ta yi lamarin ya shafi Hussein ba. Ya faka motarsa a waje, Maigadi na shirin bude gate ya dakatar da shi gami da nuna yanzun shima zai fito. Bayan sun kammala gaisuwar ya ƙaraso ciki, ji ya yi kansa ya sara yayinda kirjinsa ya shiga dukan tara-tara. Ba don a yau ɗin ya ziyarci Hussein a ofishinsa ba, ya kuma san kalar kayan da ya sanya da ma kalolin motocin gidan Hussein din, zai iya rantsewa ya ƙara wannan na tsayen Hussein ne. 'Kenan Hussein ƴan biyu ne?' Ya jefawa kansa tambayar da nan take ta amsamishi da eh. Tambayoyi kala-kala ke ɗawainiya da shi. Ya ƙaraso ganin da ya yi Alhassan ya zubamasa idanu fuska a sake, wayar da yake dannawa ya mayar cikin aljihu gami da miƙamishi hannu. Musabaha suka yi, hatta da muryarsu sai ya ji tana mishi kamanceceniya. Ja ya yi ya tsaya cikin danne mamakinsa, damuwa sosai ya mamayeshi. Ya tuna gargadin Ramlat akan kar ya yi wata katoɓarar don haka ya daure yana jan Alhassan da hira da zolaya kamar ya sanshi. Anan ya kara tabbatarwa ba Hussein bane, wannan wani ne daga Adamawa kuma sunansa Alhassan. Yana so ya tambaya ko yana da wani dan uwan haihuwar amma ya danne. Kafin dai Ramlat ta fito ta yiwa Alhassan iso don ya shiga gidan, Hisham da AlHassan hira suke yi sosai, ya fahimci kusan halayyarsu ta daya don har Alhassan ma ya fi Hussein sakin fuska. Ramlat na ganinsu tare ta karasa, suka hada ido da Hisham wanda ke kallonta bakinsa cike da tarin tambayoyi, ta gaidashi. Ta yi musu jagora zuwa falon Hajiya. Nan aka ƙara gaggaisawa sannan AlHassan suka koma sitting room. Abinci da komai ta kai musu. Bayan kammala ci, suka yi shirin tafiya. Ya yi daidai da dawowar su Ummi daga makaranta. "Yaranki ne?" Dada ta fadi tana kallon Fatima, murmushi ta yi kawai ta sunkuyar da kai. "Ai Dada daga gani ma ba tambaya, wannan yarinyar tana kama da ita sosai." Kausar ta fadi tana mai jawo hannun Ummi da nutsuwarta ya burgeta. "A'a, wallahi ta fi ta kyau." Fadin Hafsat, tana nufin Ummi ta fi Ramlatun kyau. Nan Kausar da Hafsat aka shiga musu, su Zulaihat me zasu yi ba dariya ba. A karshe suka yi musu sallama suka kama hanyar tafiya zuciyoyin kowannensu cike da farin ciki. Babu ma kamar Hafsat wacce kafin fitowarsu daga gidan Modibbo ranta ya ɓaci da yanda Modibbo ya amsa gaisuwarsu a wulaƙance. A hanya har rantsuwa ta dinga yi ba za ta ƙara zuwa wata sabgarsu ba. Ba wanda ya kulata don kowa ransa ba dadi. A yanzun tana jin za ta iya zuwa ta yi fiye da sati ma a Kano saboda karamci irin na Ramlat da ƴan gidansu. Ko ba komai ta samu wasu ƴan uwa a garin. A ɓangaren Dada ji take inama haka Modibbo da sauran ƴan uwanta ke sonsu, da ta tabbatar ba ta da sauran damuwa. *** Bayan tafiyarsu Ramlat ta takowa Hisham har wurin motarsa. Cike da damuwa ta tari numfashinsa, kaf yanda ta haɗu da AlHassan ba ta ɓoyemishi ba. Ya jinjina kai ya ƙara sakin ajiyar zuciya karo na ba adadi. "Wallahi kaina ya ƙulle Ramlat, wannan lamari da ban mamaki yake. Zargina ya tabbata na cewa Hussein rabashi aka yi da ƴan uwansa. Koda ba rabasun aka yi ba, toh lallai akwai wani laifi da aka aikata gareshi har ya yi sanadin da ya fidda kowa a babin rayuwarsa. Mutane masu mutunci da kamala, sun bani tausayi sosai na rashin sanin inda yake." Ranta ya sosu, sosai ta ji tausayin Hussein ya ƙara mamayeta. Ta karyar da wuya. "Bari kawai, ni kaina abin yana dauremin kai. Amma fa bana son sanar da su komai, ba kuma na son su haɗu da juna har sai mun gano bakin zaren." Jinjina kai Hisham ya yi. "Gaskiya ne Ramlat, don Allah ki dage, ki ƙara shawo kan Hussein yanda za ku shaƙu. Watakila ta hanyarki mu samu wani information din tunda na lura wallahi ya soma damuwa da ke." Gabanta ya fadi. Ta dubi Hisham sosai. "Bangane ba." Murmushi ya yi don ba ya jin dariyar dalilin damuwa da tausayin abokinsa da ya mishi ƙatutu. Tayar da motarsa ya yi. "Ke dai ki yi aikinki. In Sha Allah nasarar ma da kike tunani zamu samu fiye da ita." Ta amsa da toh kawai ba tare da ta tanka ba, dakyar ta iya ba shi sallahun gaida A'isha. Har ya ja motar tana juya maganarsa ta ƙarshe, to wace irin damuwa da ita kuma? Ta kasa fassara wannan kalamin. *** 'Addu'a, shi ne abinda ban fiye maida hankali wurin yi ba." Ya furta a fili cikin ba kansa amsa, shi kadai ne a mota yana ja bayan dakyar ya samu fitowa daga takunkumin Hajiya Zeenatu na yi mishi rakiya duk inda zai je. Ya yi wannan maganar a sanadin wa'azin Mufti Menk da ya gama saurara a motar, malamin na tunadar da Bawa akan ya dinga zama yana yiwa kansa hisabi, mene ne abinda ya san yana aikatawa kafin lokaci ya ƙuremasa. Damuwa da ƙunci suka cika zuciyarsa, ko sallah ya yi a gaggauce yake yinta, bai damu da zuwa Masallaci ba ya bi jam'i ko lokutan azumi balle kuma sallar Asuba wacce wani zubin sai rana ta fito take gabatar da ita. Idanunsa suka kaɗa, shakka babu shi laifukansa nada yawa a wurin Allah. Ruwa ake yi tamkar da bakin kwarya bai fasa tuƙi ba sai dai yana tafiyar ne kamar wanda kwai ya fashewa a ciki. Wannan ma kadai ya isa ya jawowa bawa munanan abubuwa, yana da matsala babba ta wannan fannin. Da wannan tunanin ya isa gida cike da tsantsar damuwa. Hajiya Zeenat ba ta nan wannan yasa shi kai tsaye nufar ɗakinsa, sai da ya rage kaya ya yi wanka kafin ya sauko ƙasa. Nan ya iske John ya jera kwanukan abinci saman tebur. Budewa ya shiga yi kafin ya ja tsaki ya maida ya rufe, babu ɗaya da ya burgeshi balle ya ji zai iya ci. Wayarsa ya jawo ya shiga dannawa, kai tsaye whatsapp ya shiga. Shi ɗin ba ma'abocin bude Status bane, sai dai yakan bude na mutane masu muhimmanci a wurinsa. Sunan HEART da ya hango a jerin wadanda suka dora Status ne yasa kansa tsaye ya bude. Hotonta ne zaune saman kujera a falo, ta rungume wata kyakkyawar yarinya suna dariya. Kirjinsa ya bada dam! Ya kara zooming ya kurawa yarinyar idanu. Da ace ya taɓa haihuwa, ba abinda zai hana ya kira yarinyar da ɗiyarsa. Can kuma ya tuna kamanni ne kawai, murmushi sosai yake yana kallon yarinyar da ita kanta RAMLATUN. Sun burgeshi sosai, yarinyar ta shiga ransa ainun. Ya yi niyyar screenshot sai ya fasa, wannan ba halayyarsa ba ce don haka suka ya zaɓi turamata saƙo kamar haka. "Mutane sama da dari biyu sun ga Status dinki. Hakan daidai ne?" Yana aikawa ya saki murmushi gami da sauka daga whatsapp din. Wayar ya ajiye, hakanan sai ya ji wani kwarin gwuiwar ya ci abincin. Ya kuma rasa ta ina.  I just published "BABI NA TALATIN DA TAKWAS" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/IcdWtyGJpbb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 38) Shigowarta dakin kenan bayan sun yi sallama da Hajiya. Wani hamma ta saki tana mai rufe baki, a gajiye liƙis take jin ta. Kakkaɓe gefen da za ta kwanta ta yi, hankalinta ya kai ga wayarta, shaf ta mance da ita a chaji, ta cika tun awanni biyu ma da suka wuce.   Zareta ta yi ta shiga cikin whatsapp ganin saƙonnin da suka faɗo daga kunna Data. Saƙon Hussein ya sanyata dariya ba kaɗan ba, ta maidamishi amsa.   "Ba fa celebrity ba ce." Daga haka ta yi zaman jiran amsa har gyangyaɗi ya soma fisgarta, can dai ta hakura ganin ba ya kusa ta kashe wayar ta yi addu'a ta kwanta. ***   Ruwan da ake kamar da bakin ƙwarya ya sa ta barin yara a gida don sun kammala jarrabawa kusan wasa kawai ake a makarantar yanzun, itama ba don fitar ta zama dole ba da babu inda za ta je. Amrah ce ba lafiya, abin tsoron kuma lokacin haihuwarta da saura don duka-duka cikin bai kai wata shida ba. "Ki je zuwa anjima ma leƙa. Kar dai ki manta da kiran Kawunnaki. Ki karasa Yakasan idan ruwan ya tsagaita." Wani ɗaci Ramlat ta ji da bayanin karshe na Hajiyarta, tasan kiran da Kawun ke mata bai wuce akan aure ba. Ita shikenan yanzu kowa idanunsa a kanta, an takura akan sai ta yi aure.  Dama tun da Hajiyar ta soma batun kai yara dangin Babansu don su ci hutunsu a can, ta soma jin ba dadi. Babban takaicinta yanda tun rasuwar Abulle babu wanda ya kara nemansu banda Malam da ke kira lokaci zuwa lokaci su gaisa ko kuma ita ta kira. Hakanan Justice duk sadda zai yiwa yaran ƴan uwansa kayan sallah toh zai haɗa da su. Kannen Aliyu ta yi musu uzurin aure, amma a ganinta hakan bai kai dalilin da zasu dauke ƙafa da hankalinsu daga kan yaransa ba. Ko ƙafarsu ba ta tako ba ai akwai waya. "Kin yimin shiru kina wani ƙunƙuni, idan ba za ki je ba sai ki kira ki faɗamasa." Hajiya na kaiwa nan ta mike a fusace ta yi ɗakinta. Sauke ajiyar zuciya Ramlat ta yi, ranta har sannan babu dadi haka ta gyara zaman mayafin abayarta maroon ta fita rike da kwandon abinci. Idan ka ganta ba za ka ce ta haifi yara har uku ba, Allah Ya yi mata baiwar jiki mai kyau kuma wanda ya samu kulawar da ta dace.   Har ta iso asibitin da Amrah suke ba ta cikin walwalarta. Ɗahiru ta soma kiciɓus da shi a barandar emergency, suka gaisa ya fadamata lambar dakin sannan ya fita. Ta karasa, Amrah na kwance tana bacci sai Umma a gefe. Ta karasa suka gaisa da Umma. "Wai, gaskiya kin yi kokari, ana wannan ruwan kika fito?" Murmushi ta yi. "Umma ai dole ne, ƴar uwata guda ba lafiya fa." Ƴar dariya Umma ta yi. "Kinga da sauki ma, likitan ya ce wai Malaria ce kuma kinsan ba'a son Mai ciki da ita, amma yanzu Alhamdulillah. Ba ta jima da samun baccin ba ma." Jinjina kai Ramlat ta yi tana maida dubanta saman fuskar Amrah, duk ta ajiye wani kumatu. "Allah Ya bata lafiya." Daga nan ta ajiyewa Umma kwandon suka shiga hira kadan-kadan. Sun kai kusan mintuna sha biyar kafin Amrah ta farka. "Ya jikin?" Umma ta furta tana dubanta. Gyada kai ta yi tana kokarin miƙewa zaune. "Alhamdulillah, kan ya sauka ma." Yanda ta furta ma ka san ba lafiyar. Suka yi mata sannu. Da taimakon Ramlat, ta shiga banɗaki ta yi alwala ta wanko baki. Suka dawo ta zauna, Ramlat da kanta ta zubamata farfesun  naman ragon da ta kawo wanda ya ji karas da ɗankali. Ta haɗamata shayi sannan ta haɗa na Umma, itama ta zubamata farfesun. Suna ci su na taɓa hira. Ruwa na tsagaitawa Umma ta wuce gida da zummar za ta turo kanwarta (ita Ummar),  Magajiya ta zo ta zauna da ita. "Ya na ganki wani iri?" Amrah ta watsowa Ramlat tambaya tana dubanta. Murmushin yaƙe ta yi. "Ba komai." Girgiza kai Amrah ta yi. "Karya ne wallahi. Dama shiru nayi don Umma na wurin amma tun da na dora idanu a kanki na gane akwai matsala." Shiru Ramlat ta yi kafin kuma ta soma fitar hawaye, a yau dai zuciyarta ta motsa da kewa mai yawa na Aliyunta. Da ace za ta rasa duk abinda ta mallaka don kawai Allah Ya ba ta damar ganinsa su yi magana ko sau daya ne, da tuni ta aikata hakan.  Sai dai kuma ita mutuwar gaskiya ce, barin duniya ce ta har abada da babu dawowa sai dai ka je ka tarar. "Lafiya kuwa?" Cewar Amrah kusan hankali a tashe, ganin tana neman jefa mai juna biyu cikin matsala ta yi saurin dauke hawayenta ta hau murmushin yaƙe. "Ke ba fa wani abun tada hankali bane." Nan ta kromata dukkan abinda ke faruwa, murmushi Amrah ta yi. Ta lura ba maganar kai yaran gidan kakanninsu ne tashin hankalin ƙawarta ba sai maganar auren da ake budemata wuta a kai. "Yanzu don Allah Ramlat kin fi kaunar ki yi ta zama haka ba aure? Kina zaton hatta Abba idan ace yau yana doron ƙasa zai yi murna da zamanki haka? Ko a tunaninki Aliyu zai yi farin ciki da zamanki haka babu aure? Wallahi kin ji na rantsemaki cikinsu babu wanda zai so ki ƙare rayuwarki a haka. Kema fa mace ce, a karon kanki sai dai ki ɓoye, kinsan cewa kina bukatar auren. Kina son wanda zai kula da ke da rayuwarki." Amrah ta ci gaba da kwantarwa Ramlat hankali ta hanyar nasiha da rarrashi. Tun Ramlat na jin haushin maganganun har ta soma gane dagaske duk abinda ta fadi babu ƙarya ko sharri a ciki. "Batun yara kuwa kema kinsan ba ki isa hanasu zumunci da dangin mahaifinsu ba koda su din ba sa ta su." Murmushi kawai Ramlat ta yi a nan. "Ke ni ina Muhibbat ne? Kwana biyu na ji ta shiru a WhatsApp." "Tana nan, ko juma'ar da ta wuce mun gaisa. Ta yi rashin lafiya kwana biyunnan wai." "Allah Ya bata lafiya." Cewar Amrah. Zuwan Baba Magajiya kanwar Umma ne ya ba Ramlat damar yi musu sallama ta tafi. Yayyafi-yayyafi ake yi garin ya yi luf-luf da sanyi mai sanya nutsuwar zuci. Tana tafe tana tauna zantukan Amrah har ta isa ga motarta. ***       YAKASAI.. Kanta kamar ya tsage biyu, bakinta ya yi mata nauyi yayinda ta ƙurawa Kawu Bello idanu don ji take kamar babu sauran laka a jikinta. Ta rasa ma me za ta ce, ta kasa fahimtar idan bayanan suka dosa. Batun dai zai bayar da ita ga CHAIRMAN ALIYU DIKKO ya fi komai ba ta mamaki da kuma dariya. "Kin yi shiru kin tsuramin idanu kamar wani sa'anki?! Sarai kin ji ai abinda na ce! Mun gaji da zubamaki idanu, ke ba ki kawo wani kin ce kina sonsa ba, kuma ke ba ki ba masu sonki dama ba! Toh na bayar da ke ga Chairman, zai soma zuwa hira wurinki ku fahimci juna. Nan da sati uku ma zan dauramaku aure." Ya ƙarashe yana fitar da wani huci har da muzurai, bakin ciki ya sa hawayen ma kasa zubowa. Wato Chairman shigo-shigo ba zurfi ya yi mata kenan? Ta ya akai ma ya san gidan kakanninta? "Ki je ki saurari zuwansa cikin satinnan, saura kuma wannan karon kamar yanda kika nunamana a baya, yanzun ma ki nuna ba mu isa da ke ba. Dama ai mai hali ba ya fasa halinsa. To mu zuba da ke." Wasu zafafan hawaye suka zubomata, ta kasa duban Kawun har ya mike ya bar mata dakin. Jiki a sanyaye ta share hawayenta, ta mike ta koma sashen Dada. Nan ne ta samu Dada ta shiga kwantar da hankalinta da hanyar nasiha da nunamata muhimmancin auren a gareta. Ita dai ji ta yi gidan duk ya isheta, sallar la'asar kawai ta gabatar kafin ta yiwa Dada sallama ta yi ficewarta.   A zauren suka yi kiciɓus da Kamal. "Ashe Ramlat arzikina kika raina ban sani ba, kin nunamin ba za ki iya aurena ba saboda a gidanmu ba'a sonki, yanzu ai gashinan da wannan maigidannaki ya fito kin kawoshi har ya ga Kawu. Ki dai bi a hankali duniya ce, ta fi bagaruwa iya jima!" Yana kaiwa nan ya gifta ta ya wuce, ta bishi da kallo sannan ta fice, a hanyar tana tafe tana hawaye sosai.  Komai ba ya mata dadi, wannan ne yasa ta zaɓi kaɗaicewa ita ɗaya ba tare da kowa a kusa da ita ba. Wani Rainbow Park ta je, wuri ne mai karancin hayaniya, mutanen da ke a wurin tsilli-tsilli, ba ruwansu da harkar kowa. Wannan ne yasa ta zaɓi can wurin da za ta je ta samu nutsuwar zuciya.    Cikin wata rumfar kara ta nufa inda aka jera kujeru, iska mai dadi wurin ke bayarwa. Akwai ƙarancin jama'a a Park din adalilin ruwan da aka yi.   Tunani kawai take tana fitar da hawaye masu ɗumi. Duniyar da abinda ke cikinta take ji sun ishe ta, an ce bazawara nada ƴancin zaɓin wanda ta ke so, amma tana ji kamar ba ta da wannan damar. ***   Tafe yake a hanyarsa ta zuwa wurin Gym. Tafiyarsa yake cikin nutsuwa yana sauraron yabon Ya Habibal Qolbi na Sabyan Gambus. Waƙar sosai yake jin dadinta, murmushi yake. Hankalinsa ya kai ga motar da ko a mafarki, lambarta ba za ta ɓacemasa ba. Ɗan tattara gira ya yi don son tabbatar da abinda idanunsa suka gani, ya nemi wuri ya yi parking. "Me ta ke yi anan?" Ya samu kansa da furtawa a fili alhalin ya san babu mai amsawar.   Fitowa ya yi ya kara kallon lambar don tabbatarwa. Can kuma ya fito ya shiga Park din don son tabbatarwa kansa. Sanye yake da wando da riga na kamfanin Adidas, farare da layi-layin navy blue a gefen hannu da wandon. Ƙafafun cikin farin canvas.    Gashin kansa ya kwanta luf-luf har a ƙeya, baza dara-daran idanunsa ya shiga yi wanda gashin ido ke kokarin rufewa duk sadda ya kyafta. Har ya juya cikin fidda ran ganinta a wurin, idanunsa ya kai gareta cikin rumfa. Tana zaune ta ɗora gwuiwar hannunta saman kujera ta kama dage kanta da tafin hannu. Kamar tunani take yi mai zurfi, kamar kuma hawaye ne saman fuskarta. Don so ya tantance, sai ya ƙarasa. Sallama ya yi amma ga mamakinsa ba'a san ya yi ba. Jan kujera ya yi da ke fuskantarta ya zauna. Wannan ƙarar ce ta maidota hayyacinta, ta dubeshi da idanunta da suka ƙanƙance suka yi ja. Shima zubamata nasa kwayar idanun ya yi fuskarsa da wata kwantacciyar damuwa. Ta yi saurin share fuskarta, sosai ta kaɗu da ganinsa a wurin, ta kuma yi mamaki.    "Assalamu alaikum." Ya kara maimaitawa, ta amsa a ciki-ciki. Miƙewa ta yi da niyyar barin wajen, ya yi saurin riƙe gefen dankwalin abayarta wanda ba shiri ta koma ta zauna. "Lafiya?" Ta fadi murya a ƙasan maƙoshi. Murmushi ya yi. "Ke zan tambaya, daga ganina sai ki gudu. Zauna ki ci gaba da hawayen ni tayaki kawai na zo yi." Ta kauda kai daga barin kallonsa, ba ta ce uffan ba, zuciyarta ba ta cikin nutsuwar da za ta yi wani murmushi har ta kai ga darawa. Yau an motsa mata dukkan damuwarta. Yau ta tuna da mutane biyu masu ƙima da daraja a wurinta kuma mafi soyuwa a zuciyarta da ta rasa.   "Kiyi hakuri, komai na duniya mai ƙarewa ne. Wannan hawayen faɗuwa ce a wurinki ba nasara ba. Babu abinda zai yayemaki. Kema fa kin sani. Wani abin muna ji muna gani amma yake gagararmu tankwarawa saboda ba mu isa ba, sai yanda aka ce da mu, sai yanda akai da mu." Ya fadi hankalinsa na kanta. Ta dubeshi, lokacin da ta ji saukar wasu sabbin hawayen, ba kanta kawai ta tausayawa ba, kalamansa na karshe kamar dan tsakure ne daga tasa matsalar a iyakar fahintarta domin kuwa ba shi da masaniya akan nata. "Ka san damuwata ne? Ya akai ka san ina nan?" Ta furta kanta tsaye a sadda ta ke kokarin share hawayenta. Ya yi murmushi. "Gashinan rubuce saman fuskarki." Ta kara tsuke fuska ganin ya share tambayarta ta biyu. "Kinsan me?" Ta dubeshi gami da girgiza kai. Ya maida hankali kan wayarsa dake ringing, ganin sunan Hisham na yawo saman screen ya ɗaga. "Ba zan samu shigowa ba." Abinda ya ce kenan bayan sun gaisa. Ramlat ta saci kallonsa, ba shiri ta kauda nata idanun ganin irin duban da yakemata. Tana jin muryar Hisham na tambayar dalili. Murmushi ya yi mai sauti. "Ina tare da Heart." Daga nan ya katse kiran. Kalmar Heart da ya furta ta sanya gabanta faɗuwa, ta dubeshi, ganin ya ɗagamata kira ta kauda kai. Ya ajiye wayar saman teburin. "Tambayarki ta biyu ce ni kaina amsarta nake nema. Nasan dai a wautana motarki na gani, na haddace lambarta fiye da zatonki. Sai dai na rasa ya akai jikina ya bani ke ɗin ce ke jan ta, kuma har na zaɓi shigowa nan na ga wanda kika zo gani. Sai kuma na ganki ke ɗaya kina hawaye. Nan take tunanina ya bani cewar watakila faɗa ku ka yi ya tashi ya bar ki ko kuma bai zo ba. Ma'ana, ya yi disappointing dinki." Murmushin takaici ta yi. "Babu ko daya cikin hasashenka, asalima a karon kaina na zaɓi nan matsayin wajen da zan samarwa zuciya da kwakwalwata nutsuwa." "Kina zuwa kenan?" Ta ɗan taɓe ƙaramin bakinta gami da girgiza kai. Ya bi bakin da kallo ya kauda fuska yana murmushi. "Heart." Ya furta a hankali, sai dai ta ji shi sarai. Miƙewa ta ƙara niyyar yi ya hanata ta hanyar rike mayafin karo na biyu. Dole ta zauna. "Tafiya zan yi." Yanda ta furta kusan a fusace sai ta ba shi dariya. "Ba ki isa ba ai, uzuri ne fa da ni kika dakatar da ni." Ta saki baki da mamaki. "Yaushe?" "Yanzu mana." "Ni na faɗa?" Ya girgiza kai. "Abar maganar, kawai dai shawara zan ba ki. No matter what, ko meke damunki kar ki bari hakan ya sa ki zo irin wuraren nan. Ki yi hakuri, babu matsalar da wani ko wata zai magancemaki. Ki miƙa wa Allah lamuranki. Ki dage da kai kukanki gareShi. Wannan shi ne babban kuskurena a baya wanda a yanzun ya ke farautana." Ya ƙarashe cike da tsantsar damuwa, ta dubeshi da kulawa. "Ban yi zaton kana da damuwa ba, Allah Ya maka dukkan ni'ima. Kuma.." "Ke Allah bai miki dukkan ni'ima ba?" Ta kauda fuskarta daga kallonta. "Ni kuwa Allah Ya yiwa ni'ima. Ya bani lafiya, Ya ban iyaye da ƴan uwa masu sona, Ya ban ƴaƴa. Alhamdulillah." Tana kaiwa nan ta saci kallonsa. Kamar ta so karantar damuwarsa da yanda ya sauya lokaci guda. Can kuma ta ga ya ɓige da jinjina kai. "Yes, you are right. Alhamdulillah." Yanda ya yi maganar a sanyaye sai ya bata tausayi. "Gwara ki tafi, yamma ta yi." "Kana da ƴan uwa a garinnan?" Abinda ta ce kenan. Wani banzan kallo ya watsamata da ya razanata. "Ba ki damar shiga rayuwata hakan ba yana nufin har da lasisin da za ki tambayi abinda ya shafi rayuwata bane. Ya kamata ki san wannan." Yana kaiwa nan ya mike a fusace ya yi gaba. Ta bishi da kallo duk sai ta ji hankalinta ya tashi, bata taɓa ganinsa a yanayi makamancin wannan ba. Labarin da Hisham ya ba ta sadda magana makamanciyar haka ta haɗa su shi ya fado ranta. Da sauri ta mike ta dauki jakarta da zummar mara mishi baya. Wayarsa ta gani ajiye, ta dauka ta bi bayansa. Sai dai har ya kai ƙarar fita. Kafin ta karasa har ya shige mota ya tayar. Zagayawa ta yi da sauri ta bude mazaunin gefe ta shiga. Ya buga sitayari murya a kausashe ya ce "Fita!" Girgiza kai ta yi hawaye na zuba. "Ka yi hakuri don Allah, wal..." "I said get out!!" Ya faɗi cikin tsawa hadi da buga sitayari iyakar karfinsa har sai da ta razana. Idanunsa kamar an watsa barkono. Yanda jikinsa ke rawa itama haka nata jikin ke yi. Ta bude murfin motar ba shiri ta fita. Bai bari ta karasa rufewa ba ya fisgi motar har yana kokarin buge wani mota. Mai motar ya dakata da sauri yana duramasa ashar. Hussein bai ma san yana yi ba. Ita dai Ramlat kirjinta je dukan tara-tara da irin gudun gangancin da ta hangoshi yana yi, hawaye kamar famfo take fitarwa ba ta ko damu da kallon da jama'ar wurin ke bin ta da shi ba. Ta shiga motarta ta bar wurin cike da jin haushi kanta, me ya kai ta wannan gangancin? *** MAFARIN KENAN.....     I just published "BABI NA TALATIN DA TARA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/dCw5vESQqbb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 39) Jikin Hajiya ya yi sanyi bayan gama sauraron Ramlat. Sam ba ta tsammaci hakan ce za ta faru ba. Ta dauka dai faɗa akan fiddo mijin kawai za'a yi mata. Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon yanda Ramlat ke kuka kamar ranta zai fita. "Ke fa na yarinya ba ce, kin kuma sani dama can ba'a yi miki dole ballantana a kwata wannan karon. Da ace wani ne ba shi Maigidannaki ba, toh ba lallai ya dameni ba. Amma sam bana son wannan haɗi na Yaya Bello. Duk ke kika jaza wa kanki ai Ramlatu, tun yaushe ake biyamaki karatun fidda miji kin ƙi haddacewa balle ki yi aiki da shi? Yanzu gashinan an miki shigo-shigo ba zurfi." Ramlat ta dubeta tana sharce hawaye. "Nima Hajiya ba wai ba zan bi umarninsa ba ne, sai dai nasan waye Chairman tunda ni ke aiki karkashinsa. Ya sha nunamin zai zo gidanmu ina ƙin ba shi dama don na riga na san waye shi. Ban ɓoyemaki komai dangane da alaƙarmu ba. Yanzu kam an zo gaɓar da zan bar ma'aikatar Revenue, ba zan iya ci gaba da zamansa ba. Ya kamata ace dama tun a baya na yanke wannan hukuncin. Amma yanzun ma lokaci bai ƙuremin ba." Kai Hajiya ta jinjina. "Ina bayanki, ya dace yanzu kuma ki bar masa ma'aikatar duk da ba tasa bace ta gwamnati ce, kinga kenan ba shi da wata ƙafar da zai yi amfani da ita wajen cin zarafinki ko yi miki bita da kulli. Ni ai tunda ki ka ce ya san waccan matar hankalina bai kwanta ba." Nan da nan Hussein ya fado ranta, ta dubi Hajiya. Ta ji tana son zayyanemata komai.   "Hajiya kin tuna baƙinmu na Adamawa?" "Ta ya zan mance su, mutane masu karamci haka Ramlatu? Meyafaru?" Hajiya ta tambaya cike da ƙaguwa. A zatonta, abinda ƴan uwan Ramlat din ke zargi ne zai tabbata, wato soyayya tsakanin Alhassan da ita. Abinda ba za ta yarda ba kenan ko don mutunci da girmamawar da Kausar ke mata. "Kinsan kuwa suna da alaƙa da Hussein da nake ba ki labari mijin Hajiya Zeenatu?" Ido waje Hajiya ke dubanta. "Alaƙa wace iri?" Tiryan-tiryan ta ba ta labarin duk abinda ta sani. Sai ga Hajiya na salati har da hawayen tausayi.   "Kai duniya! Mata me muka dauketa ne? Matattarar da za'a dauwama ko me? Zunuban kanmu kaɗai bai isa ba sai mun zalunci wasunmu? Kaico da wannan rayuwa. Allah Ya sakawa wannan yaro, Allah Ya karya ƙadarin wannan mata." Hawayen Ramlat suka ci gaba da ambaliya, sam ba ta faɗa wa Hajiya abinda ya faru tsakaninsu a yau ba, hankalinta ya yi kansa sosai, tana son ta ji muryarsa ko don tabbatar da lafiyarsa. "Amma wannan fa ba karamin aiki ba ne na wasa, addu'a ce sosai zamu dukufa ga yi masa. Zuwa anjima zan kira Kawunki Malam Yakubu. Na tabbatar shima zai taimaka. Ba a banza matarnan ta bar shi ba." Zantukan Hajiya masu dadin sauraro suka katsemata tunani. Wani sanyin dadi ta ji, har ta mance kaso mai yawa na damuwarta, ta yi murmushi gami da godiya. Daga wannan ta mike ta bar mata dakin zuwanata. Nan ta iske yaran sun yi baja-baja saman gadonta ana game a waya. Dubansu ta yi gami da murmushi, haka kawai ta ji har ta soma kewarsu. Maimakon ta korasu kamar yanda ta saba, kawai sai ta zauna ta biyemusu tare da alƙalanci.    Sai da wani tunani ya faɗomata sannan ta karɓi wayarta ta basu umarnin zuwa falo. Agogo ta duba, ƙarfe shida da rabi na dare, so ta ke ta kirashi amma ba ta kaunar abinda zai je ya dawo don haka ta zaɓi aikamasa saƙo. ***   LAMIƊO CRESCENT... Yana zaune kamar kurma yana sauraron Hajiya Zeenatu da ke buɗewa John wuta akan ya yi girkin da mijinta ya kasa ci. Ɗora laifi kacokan ta yi akansa, shi dai ƙara russunar da kai ya yi yana ambaton "Sorry Ma." Hussein da abin ya ishe shi, miƙewa tsaye ya yi gami da daukar wayarsa. "Please ya isa haka, na fadamaki yunwar ce kawai ba na ji, ba wai girkin ba ne." Yana kaiwa nan ya nufi matattakala. Ta bishi da kallo kafin ta maido dubanta ga John, harara ta watsamasa gami da ba shi umarnin tafiya. Hankalinta ya koma ga tunanin abinda ta shirya yi. Wato shan maganin da Gora ya ba ta wanda ya tabbatar da zarar Hussein ya kusanceta za ta samu ciki. Samun cikinta ne zai mantar da Hussein tunanin kowa da komai face tattalin da zai koma ba ta.   Wannan ta sa da sauri ta jawo kofin ruwa ta daga riga ta ciro ƙullin maganin ta zuba gami da gaurayawa ta kafa baki, ba ta ɗago ba sai da ta shanye tas tana wani murmushi.   Shi kuwa Hussein, zube wayoyin saman gado ya yi ya shiga rage kayan jikinsa, wanda ya ke da niyyar shiga, ƙarar shigowar saƙo ya ɗauki hankalinsa. Duban wayar ya yi, kamar kada ya buɗe sai kuma ya tuna da saƙon da za'a aikomasa na abinda ya shafi aikinsa. Madadin hakan ya ci karo da sunan da hannunsa ya rubuta saman lambar da ya ɗauketa da wani irin muhimmancin da bai san dalili ba.   _*Heart*_ Ya furta tamkar baya so kafin ya kai ga buɗewa. *_"Dukkanmu ajizai ne, mukan yi kuskure da saninmu ko kuma akasinsa. Bana fatan na yi abinda zai jefaka cikin ɓacin rai da damuwa. Shakka babu, Ramlat mai laifi ce, na yarda na shiga personal life dinka, na zaƙe da yawa. Ka yi hakuri, ka yi hakuri. Hakan ba za ta ƙara faruwa ba. Ka ji?"*_   Murmushi ya yi, ya kara karantawa ya fi sau uku, ya so ya gogeshi daga wayar amma ya ji ba zai iyaba. Wani nauyi hakan ya yi mishi don haka sai ya fasa, ya sanyawa wayar muƙulli ya jefa saman gado. Har ya shiga banɗaki bai bar murmushi ba. Fitowarsa ba jimawa ya sanya kayan bacci, shigowar Hajiya Zeenatu ne ya sa shi dubanta. Saura kaɗan wata dariya ta kufcemasa. Rigar bacci ce a jikinta shara-shara kuma marar tsawo don duka tsawon iyakarsa gwuiwa. Ƙaton tumbinta da  ruguza-ruguzan mamanta wadanda suka zube sun kwanta luf sun bayyana cikin rigar. Damtsenta kuwa a cike sosai sai dai ba ka misalta shi da na karfafan maza ba. Akwai bambanci. Duba sosai ya ke mata, riga dai gatanan mai ɗan karen kyau da daukar ido. Lumshe idanunsa ya yi yayinda wani tunani ya bijiromasa.   'Za ta yi kyau sosai.' Ya furta ƙasa ransa, ankara da kuskuren kalaminsa ne yasa shi jan istigfari. Sai kuma lokacin ya tuna da bai yi sallar Isha'i ba ya ke shirin kwanciya. Abin yana damunsa, ya rasa me ke shagaltar da shi daga bautar UbangijinSa, ma'ana gabatar da sallah akan lokaci. Abin yana mishi ciwo, sai dai mafi yawan lokaci ji yake kamar wanda aka mantar. Sau tari ma wani bacci ke zuwa ya rufe idanunsa da zarar an soma kiraye-kirayen sallah. Ganin ya mike yasa Hajiya Zeenatu tunkaroshi, hannayenta biyu ta sanya saman kugunsa. Ya yi mata murmushi mai kama da yaƙe. Duk yanda ya so nunamata tsana ko wani abun, sai ya ji ya kasa. "My Zeenat, kin yi kyau sosai." Wani sanyin dadi ya mamayeta, ta sumbaci leɓɓansa. "Nagode Sweetheart." Ganin tana kokarin wuce gona da iri yasa shi janye jiki. "Bari nayi sallah." "Sallah, wace sallar?" Yanda ta fadi a mamakince shima sai ta jefashi cikin mamakin kalamanta. Ya zubamata idanunsa mai adon fari ƙal da baƙin kwayar idanu siɗik. "Me kike nufi? Wace Sallah muke yi matsayinmu na musulmai?" Gaban Hajiya Zeenatu ya bada dam! _*"Kiyi duk yanda za ki yi, ki dinga shagaltar da shi daga ibada, zamu turamasa arnen aljan wanda zai tayaki yaƙi. Ina kara gargadinki! Kar ki kusa ki bari ya dinga sallah akan lokutanta!!!"*_ Wannan yana daga cikin farkon abinda Gora ya fadi mata sadda suka soma zuwa wurinsa a karon farko game da lamuran Hussein. Ganin ta tsaya tana kallonsa yasa shi giftawa ya fice zuwa banɗaki. Ta bi ƙofar da kallo. 'Ke me zai dameki? Ba yanzu za ki yi aikin da za ki samu ciki ba? Idan kika samu komai zai zo karshe!' Wani ɓangare na zuciyarta ya tunatar da ita. Ta sauke ajiyar zuciya tana wani irin murmushi kafin ta zauna gefen gadon. Tana kallonsa ya yi sallah a tsanake, ya yi addu'a kafin ya naɗe dardumar ya mike. Mintuna talatin da suka biyo baya, komai ya kammalu kamar yanda ta ke so, murmushi kawai take kamar koyaushe cike da gamsuwa idan ka ɗauke Hussein wanda ransa sam ba dadi. Kusan hakan ce ta saba faruwa da su, zai iya cewa wahalar da shi kawai ta ke yi a kowace tafiya don ba wani gamsuwa yake ba. Ganin ta soma jan munshari yasa shi miƙewa ya faɗa banɗaki. Can ya fito ya sauya kaya, yunwar ɗazun ce ta dawo mishi. Matsawa ya yi ya tasheta. Cikin magagin bacci ta dubeshi. "Lafiya?" "Muje ki ɗan ɗumaman abinci, nasan yanzu John ya sanya a fridge." Yamutse fuska ta yi. "Wallahi na gaji, ko nan da can ba zan iya motsawa ba. Ka je kawai ka tasheshi ya yi maka." Daga haka ta juya ta cigaba da bacci, girgiza kai ya yi gami da gyaramata abun rufa. Wayoyinsa ya dauka ya fita daga dakin cike da damuwa. Kamar akwai abinda ya rasa, kamar yana da wata damuwa amma ya kasa gane kan zaren. Maimakon ya kira John da ya wuce Boysquarters, sai ya ɓige da dafa ruwan shayi, ya zaɓi shan tea da bread kawai. Sai da ya kammala ya dawo falon, wayarsa ya fiddo ya kunna Data. Kwanaki biyu kenan rabonsa da hawa online, wannan tasa saƙonni suka shiga faɗowa, da na mutanen da ya sani da baƙin lamba kamar koyaushe. Ya kuma riga da yasan baƙin lambobin bai wuce na mata, idan da sabo ya ci ace ya saba.   Saƙonta ya ɗauki hankalinsa, ya kuma yi mamakin ganinta online, ya kara duban lokaci. Ƙarfe goma daidai na dare. Murmushi ya yi ganin amsar da ta ba shi a wancan lokacin, maimakon mayar da martaninsa sai ya ɓige da wata tsokanar. "Ba ki yi bacci ba? Da wa kike hira toh?" Yana aika hakan sai ya maida kai ya ci gaba da shan shayinsa. Tausayinta ya ji ya mamaye zuciyarsa, shakka babu sam bai kyauta ba. *** A ɓangaren Ramlat, tana kwance ne tana kallon Status, duk duniyarta ba dadi. Ga lamarin Chairman ga kuma Hussein da ya yi fushi da ita. Tana shirin sauka ganin uban hamman da ta ke dokawa, sai ta nemi baccin ta fasa ganin saƙon da ya shigo. Da wani irin ɗoki ta buɗe ta karanta. Murmushi sosai take yi haɗe da dariya ciki-ciki. Ko ba komai hankalinta ya kwanta. "Kai nake jira, hakuri nake so na ƙara ba ka." Abinda ta aikamasa kenan. ***   Yana kammala shan shayin, ya dauki wayar, ganin abinda ta ce yasa shi jin wani daam, lumshe idanu ya yi kafin ya buɗesu. Sai kawai ya zaɓi kiranta. Kai tsaye ya dokamata kira, sai da ya kusan katsewa sannan ta ɗaga. ***   "Kira war haka? Ina Madam dinka? Ka rufan asiri." Abinda ta ce kenan bayan ɗaga wayar. "Ni kenan na tonawa kaina asiri ko? So kike yi a gane damuwar da ke kwance saman fuskata na jefaki a damuwa?" Maganarsa sai ta yi mata nauyi, ta rasa amsar bayarwa, can ta daure. "A'a, ni ce mai laifi, ni na zaƙe da yawa. Ka.." "Kika ƙara bani hakuri ina miki rantsuwa da Allah za ki ganni a gidanku yanzu." Yanda ya yi maganar daga ji ka san ba wai faɗa ya yi ne kawai ba. Kirjinta ya soma bugu da ƙarfi, ta ji kanta na neman tarwatsewa. Ta kasa gane a maudu'in da za ta jefa kalamansa. Ta rasa abinda ya haɗa kalmar hakuri da batun ziyartarta a wannan lokaci don haka sai ta kasa cewa uffan.  Shiru ya biyo baya na ƴan sakanni sai numfashin junansu da kowanne ke jin fitarsa. "Ɗazun na ce kinsan me? Ba ki bari na ƙarasa ba, yanzun ki bani damar na ƙarasa maganata." Ta kasa ce mishi uffan. Har ya kara magana. "Na baka." Ta furta a hankali. "Ke ce mace ta farko bayan Zeenat, da lambarta ya shiga cikin wayata har nayi saving. Ke ce mace ta farko da ƙafata ya taka har gidansu, ke ce mace ta farko da na zauna muka yi hira da ita har na tsawon mintoci ba tare da naji hirar ta ishe ni ba. Kawai dai idan so ki sani, kina da babban matsayi a rayuwata da ba zan ce gashinan ba. I want you to keep staying in my life, ina jinki kamar wata ƴar uwata mai bani ƙwarin gwuiwa. Kamar dai kina ban ƙarfin ci gaba da rayuwa, na daina tunanin inama Allah Ya dauki raina, na bar tunanin bani da kowa a duniya. Please Ramlat, kar ki gujeni ko me zai faru, ko me zan miki. Kiyi hakuri, nayi maki laifi a ɗazun da ni kaina ba haka na so ba. I just can't do otherwise idan aka zo irin wannan lamarin. Ban kuma san dalili ba." Wani sabon yanayi ke shigarta game da HUSSEIN, wani abu take ji na yawo tun daga tsakar kanta har yatsun ƙafafu. Zuciyarta gaba daya ta cika da tausayinsa. Ganin kamar tana neman wuce gona da iri yasa ta saurin magana. "In sha Allah hakan ba za ta faru ba. Allah ne Ya haɗa mu, ban isa na kawo karshen zumuntarmu ba. Ina rokon Allah Ya yayemaka dukkan damuwarka. Sai dai don Allah ina roƙonka akan ka dage da kai kukanka gareSa. Kamar yanda ka bani shawara a ɗazun, kaima yanzu ina so ka yi amfani da hakan." Murmushi ya yi mai sauti yana ƙara gyara mazaunin wayar, ƙafafunsa a saman kujera. "Kina shiga haƙƙin Madam ɗita fa." Harara ta bugamishi kamar yana kallonta, wani abu ta ji kamar ya soke ta a ƙahon zuci mai kama da KISHI. "Ai ba ni na kiraka ba, sai da safe." Tana ji yana dariya sadda ta datse kiran. Ita kuwa kwanciya ta yi ta shiga duniyar tunani. Murmushi sosai ta ke yi, wani sabon yanayi take ji game da Hussein wanda a yanzu ta kasa ƙaryatawa. Tunaninta ya tsaya cak! A gefe guda kuma tausayin kanta ya mamayeta. Wato dai ta gama fahimtar ta faɗa SON MASO WANI. Miƙewa ta yi ta faɗa banɗaki ta dauro alwala, nafila ta shiga yi kafin ta yiwa Hussein addu'a ta musamman. ***   Washegari ta tashi ranta fari ƙal, kaso mai yawa na damuwarta ya yaye. Ta yarda ta kuma aminta, ta rasa dabara ko wani makami da za ta kare kanta na cewar ta faɗa tarkon SO. Tana kai yara makaranta ta wuce kai tsaye Head of service inda ta kai takardar neman transfer da ta rubuta. Kusan sun yi waya da Zulaihat da Rafee'ah, duk sun goyi bayanta don a cewarsu mutunci ya fi komai.    Kai tsaye ofishinsa ta nufa ganin da ta yi ya iso. Kwankwasawa ta yi gami da sallama, jin muryarta da gaggawa ya bata umarnin shigowa. Ta shiga fuska a haɗe. Kallonta yake har da ɗan miƙewa duk ya rikice. Ya san da cewa ya mata laifi amma ba yanda ya iya, gani ya yi idan ya biyemata to fa za ta kai shi ta baro ne. Ba tare da ta damu ta gaidashi ba ta fiddo ƙaramar envelope waanda ta sanya dukkan kuɗaɗen da ya bata. "Idan har wannan ce damar da ka samu na zuwa tambayar aurena a gidan iyayena, to ka sani daga yau na rusata. Kuma kar ka manta, ni ba yarinya ba ce ballantana ka yi tunanin za'a tursasani ko a yimin dole akan aurenka." Ta zazzage kudin saman tebur. "Ka ƙirga ka gani, idan da su kake taƙama har ka yimin wannan aika-aikar, ko sisi ban taɓa a cikinsu ba. Ina fatan daga yau komai zai wuce. Kar kuma ka kara tunanin cewa zuwa wurin Kawu Bello zai ba ka dukkan wata dama a kaina." Daga haka ta juya da zummar tafiya ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Ta juyo tana dubansa fuska a daure. Gaba daya ya sauya fuska. "Haba Ramlat, saboda na bi hanyar da addini ya tsara na neman iznin aurenki gurin magabata shi ne za ki watsan ƙasa a ido? Wannan wace irin kiyayya kike nunamin? Ina da kudi, ina da gidaje da dukkan matsayin da na cancanci ki so ni dominsu, amma ke wannan duk bai sa kin saduda ba. Idan don matana ne, wallahi wallahi ba zan haɗaki gida ɗaya da su ba. Kin ji rantsuwar ɗan musulmi. Ya kike nema ki yimin wannan kwalelan?" Ta dubeshi duba na raini, ita dariya ma ya soma bata. "Ni kudi bai isa ya siyeni ba, hakanan ba kuɗi ake nema a zamantakewar aure ba. Yarda, biyayya, kauna, so, mutunci, daraja da ƙima dama sauransu, su ake neman a aure. Babu ko daya da ka samu a idona. Ina kara neman alfarma akan ka rabu da ni ka fita daga rayuwata. Ba zan iya aurenka ba." "Idan kudi na siyan soyayya! Wallahi Ramlatu sai kin aureni koda ba kya so! Mu zuba ni da ke!!" Ya fadi a tsawance, kalaman sun faɗarmata da gaba, ta dake ta yi murmushi. "Allah Zai tsayamin." Daga haka ta sa kai ta fice dama ba da niyyar zama ta zo ba. Maimakon ta yi gida sai ta nufi gidan Amrah da aka sallama, ƙara duba jikinta. Ta sameta kamar ba ita ba don Magajiya har ta koma gida. Tun a asibitin suka sauya shawara, da ace ta dawo gida gwara Magajiyar ta biyota gidanta su kwana tare. "Ya na ganki wata iri? Ke kullum dai da damuwa kike zuwarmin." Amrah ta ƙarashe cike da zolaya. Harara ta samu daga Ramlat. Sai kuma ta ja tsaki. "Ke kinsan dalilin wai da yasa Kawu ke nemana?" Amrah ta girgiza kai. Nan ta labartamata komai da komai har haduwarta da Hussein da yanda ta kaya tsakaninta da Chairman yanzun a Ofis. "Kai jama'a! Wai shi wannan mutumin da me yake taƙama ne? Ai sai ki yiwa kanki kiyamullaili, ba zama za ki yi ki zuba ido ba. Wallahi ki yi kokarin fito da miji ki yi aure abinki ya fiyemaki alheri, ke kanki kinsan tunda ya furta ba kyaleki zai yi ba." Ramlat idanunta suka cicciko, batun fito da miji sai ya yi mata famin rashin Aliyu. Banda kaddarar mutuwa da ke kan kowa, yanzun da ba tana cikin inuwar aure  ba? Waye zai ganta har ya ce yana sonta ko kuma ita ta ji son mutumin da ya yi mata nisa? "Ni wallahi da ace wannan Hussein din ba shi da mata, wallahi zan so ki aureshi. Mutum ne iya mutum. Ke ko shi ko dan uwansa Hassan." Kalaman Amrah suka sa ta fiddo idanu tana dubanta, Amrah ta yi dariya. "Meye toh? Allah kuwa ni na fi so ma ki yi auren nesa. Kinsan mutane magulmata ne. Abinda ya riga ya wuce ma sai su ɗagoshi. Kuma fa ni sai naga kamar Hussein dinnan sonki yake." Guntun tsaki Ramlat ta ja. Gabanta na faduwa, yanzun ko sunansa aka ambata sai ta ji sauyi a zuciya da kwanjinta😜 "Malama mu bar maganarnan, ba ta da fa'ida." Dariya sosai Amrah ta yi, ta fuskanci inda Ramlatun ta sa gaba kawai dai ta yi shiru ta ga gudun ruwanta. Matar da ko labarin Hussein ta ke bada wa sai yanayinta ya sauya. "Uhum, a juri zuwa rafi." Fadin Amrah kafin ta kai mangwaron da ta kammala yankamusu bakinta. Harara ta kuma samu daga Ramlat. *** ADAMAWA..    I just published "BABI NA ARBA'IN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/dlZmI7H2Cbb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 40) *Assalamu alaikum. Masu karanta Karfen Kafa ku yi hakuri. Na fadamaku exams zan soma gobe In Sha Allah. Daga wannan post din kuma sai sadda ku ka ji ni. Nagode sosai sosai.* ADAMAWA.. Ɗaure fuska ya yi kamar bai taɓa dariya ba yana duban Dada, cikin harshen fulatanci ya yi magana. "Akan me zai sauka a gidannan? Me hakan ke nufi?" Dada ta harareshi. "Taheer ɗan uwanku ne, don ya zaɓi gidannan matsayin wurin kwanansa ba laifi bane. Kar ka manta ɗan ɗan uwana ne." AlHassan ya ɗan dafe goshi, sam bai ji dadin wannan hukunci ba. Sallamar direba rike da ƙaton akwati yasa AlHassan miƙewa. "Ni zan wuce Dada, akwai inda zan je." Ta bishi da a dawo lafiya, a kofar suka yi kiciɓus da Taheer. Dauke kai ya yi kamar bai ganshi ba zai wuce, da sauri Taheer ya karasa ya mika masa hannu da sallama. Akan dole ya bude nashi hannun suka gaisa daga nan bai ƙara cewa uffan ba ya yi gaba. Taheer ya bishi da harara, dama ca ya tsaneshi saboda girman kai. Shi kuwa ya zo kuma sai ya cimma manufarsa, idan ana so dole sai Hafsat ta so shi ta kaunceshi. Sai ya aureta. Dada ta tarbeshi a mutunce, aka mika kayansa dakin su AlHassan na baya. Hafsat dake makaranta tana dawowa ta yi kiciɓus da shi a falo yana cin abinci suna hira da Dada kamar dama can sun wani saba. Turus ta yi tana kallonsa ranta na wani irin zafi, Dada ce ta lura da ita. "Mene na tsayawa haka kamar kin ga Dodo?" Dada ta furta cikin harshen Fulatanci sanin da ta yi Taheer din kusan ba abinda aka koyamusu, manyan yara Modibbon ne kaɗai masu jin fulatanci. Su kam saura sai Hausa da turanci. Maganar Dada ya kai hankalin Taheer ɗin ga Hafsat, ƙuramata idanu ya yi, ta watsamasa harara ta kauda kai gami da karasowa ciki. Maimakon ta ba shi haushi sai ta ba shi dariya. Ya yi murmushi. "Welcome my dearest." Ya faɗi sanin da ya yi shi ɗin ma Dada ba ji ta ke ba. Ciki-ciki ta gaidashi saboda hararar da Dada ke watsamata. Ya amsa a sake. Ta mike ta faɗa ɗakinta har wani kwalla ta ji sun cikamata idanu tsabar ɓacin ran ganinsa. Ta rantse ba za ta ƙara kwana a gidannan ba, gidan AlHassan za ta wuce. Tana soma haɗa kaya kenan sai ga Dada. Nan ta yi mata kaca-kaca ta kuma rantse muddin ta ce za ta bar gidan sai ta saɓamata. "Ku kenan haka ku ke son na mutu da bakin cikin ban shirya da ƴan uwana ba? Yayana ya mutu ya bar ni zuciyarsa cike da burin ganin watarana su Hamma Modibbo sun riƙemu matsayin jininsu kuma ƴan uwa, bai samu ya ga hakan ba, sai yanzun da Allah Ya soma amsa addu'a ta har gashinan wani a gidan Modibbo ya yi sha'awar zuwa gidannan ku ke neman ku sanyamin ciwon kai? Toh sa ƙafa ki fita daga gidannan mu zuba ni da ku!" Dada na kaiwa nan ta fice ranta na suya. Hafsat ta yi cilli da atamfar da ke hannunta ta fashe da kuka. Dada ba ta san manufar Taheer na shigowa gidannan ba. Ita kuwa ta rantse nan duniya ba wanda zai sa ta aurensa. Sai dai ko me zai faru ya faru. ***.     _*So ne baƙin duhu zallah, a faƙaice zai yi ma illah, ciwon so ba ya biɗar sassaƙe...*_           *Hamisu Breaker.*   KANO. Karfe biyar da mintuna na yammacin Asabar, tsaye yake jan abin motsa jikin na (Treadmill), daga shi sai riga da  gajeran wando. Ya sanya tawul a saman wuyansa, a hankali yake tafiya ba kamar Hisham dake gefe yana zabga uban gudu ba. Kacokan kusan hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, Hisham  ya kalleshi ya fi a ƙirga, karshe ya tsayar ya sauka yana maida numfashi, kai tsaye water bottle ya dauka dake gefen jakunkunansu ya shiga kurɓa can ya ƙaraso ya tsaya gami da dafe ƙarfen da Hussain ke kai, ya ƙuramasa ido. "Lafiya?" Ya fadi yana maida numfashin gajiya. Hussein ya dubeshi. Sai a sannan ya yi amfani da ƙaramin tawul din ya goge gumin da ke zirarowa daga goshinsa har yana ɗiga daga karan hancinsa zuwa baki. "Me ka gani?" Gira Hisham ya ɗaga yana murmushi. "Sai wani tunani kake kamar wanda ya faɗa tarkon so." Kallonsa Hussein ya yi a karo na biyu kafin ya sauka ya zauna saman kujera. Hisham bai hakura ba ya ƙaraso ya zauna gefensa. "Kai mutumin, na fa gama gane bakin zaren. Ka dai yi gamo." Guntun tsaki Hussein ya ja. "Kai maganar ma da ba ta kamata ba yinta ka ke yi. So kuma? Ban da lokacin shirmennan." Murmushi kawai Hisham ya yi. Kamar ya ce wani abu sai dai bai ce ba. Wayar Hisham din ce ta dauki ƙara, ganin sunan da ke jiki ya sanya shi satar kallon Hussein yana murmushi. Shi kam bai ma san yana yi ba, wai harara a duhu. "Ranki ya daɗe Antinmu." Fadin hakan yasa Hussein satar kallonsa, ya basar kamar bai gani ba, can ya ce. "Af,  wayarta ba chaji ne toh inaga don ba ta saba kashewar ba." Can ya ƙara faɗin. "Toh Allah Ya kaimu goben, amma dai a tahomin da yaranmu." Hussein ya gaji da satar kallon ya juyo gaba dayansa yana mai tsuramasa idanu. Dariya Hisham ya yi, ba don bayanin Ramlat din ya ba shi dariya ba sai dai yanayin amininnasa. "Ayya toh Allah Ya maidomana su lafiya. Allah Ya kaimu goben. In Sha Allah idan na koma zan sanarmata." Daga haka ya kashe wayar. Yana dariya ciki-ciki ya ce. "Kai kuma wannan mayun idanun da ka tsuramin fa? Toh wallahi kurwata kurrr!" Duka Hussein ya kai mishi a kafaɗa, ya yi dariya. Shi kuwa ya mike ya dauki jakarsa ya yi gaba zuwa hanyar banɗaki. Yana jin Hisham na fadin. "Oho dai, na gane komai!" Har ya kammala shiri yana maimaita kalmar na gane komai din da Hisham ya furta. Sai da ya kimtsa sosai ya fito, wannan karon dogon wando ja ne ya sa da t-shirt bodyhug fara ƙal. "Sai ka taho." Hisham ya bude baki. "Au haka za ka yimin? Toh ai shikenan. Nidai gobe kam ba zan zo ba, inada baƙuwa ta musamman a gidana." Taɓe baki Hussein ya yi. "Matsalarka." Daga haka ya yi gaba bayan ya yi sallama da ƙalilan da suke a dakin motsa jikin. Hisham ya bishi da kallo yana dariya. ***   WASHEGARI... Cikin shirinta tsaf na riga doguwa ta shadda kalar sea green ya sha adon stones. Mayafi ƙarami ta ɗora samansa. Tuƙi take hankalinta kwance, kaso na damuwarta Sati daya kenan da ta nemi sauyin wurin aiki, ta samu takardar sauyi daga ma'aikatarta zuwa ma'aikatar ilimi. Wani farin ciki na musamman take ji, ko ba komai za ta rabu da alaƙaƙai. A gefe guda kuma ta gama fahimtar yanda ta yi nisa a son HUSSEIN. Soyayyar da idan ta tuna shi ma dadi take ji, murmushi take yi Ta bude hirarsu ya fi a ƙirga, ta tuna zantukansu ya fi sau dari a satinnan. Ji take inama yanda take jinsa shima haka take a wajensa. Har ta ƙaraso gidan A'isha ba ta bar tunaninsa ba. "Assalamu alaikum." Ta furta sadda ta isa ƙofar falon, ƴar aikin A'isha mai suna Bingel, ta amsamata sallamar. Laulayi da ta soma ne yasa dole Hajiya nemarmata ƴar aiki wata dattijuwa. Suka gaisa ta karasa cikin falon daidai da fitowar A'ishar daga ɗaki. Baki Ramlat ta saki tana kallon yanda duk ta zabge ta rame. Ta ƙaraso ta zauna. "Kai Auta, duk laulayin ne?" Yamutse fuska A'isha ta yi kamar ta yi kuka. Cike da shagwaɓa ta amsa. "Wallahi Maman Affan ni duk cikin ma ya isheni. Allah kuwa ji nake kamar a .." "Astagfirullah! Kar ki karasa Princess. Ina rabaki." Suka dubeshi, Hisham ne wanda ya fito daga dakin sanye da jallabiya. Dariya ma suka ba Ramlat. Ta dara kadan, ya ƙaraso yana hararar A'isha. Daga bisani suka gaisa da Ramlat. "Kin ganta nan, girki ma yanzu ba ta fiye yi ba yayi dadi. Wataran gishiri ya yi yawa, ko maggi ya yi yawa. Wai dama haka ake laulayin da shegen tsawo da kuma wuya?" Murmushi sosai Ramlat ta yi. "Irin naku kenan sai hakuri." Nan dai ya yi ta caccakar A'isha ita kuwa sai cika take da batsewa. Dariya kawai Ramlat ke yi, ganin dagasken fita yake son yi siyo abinci ta mike tsaye. "Haba dai, wallahi ka barshi bari na girka tunda na zo." Ya kuwa shiga godiya, ya ja hannun A'isha wai ta zo ta kwanta ta huta ya mata tausa. Kunya ya kama Ramlat, ta yi saurin faɗa wa kicin tana murmushi. A can ƙasan ranta ƙara godewa Allah ta yi da baiwar da ya yiwa ƴan uwanta na mazaje nagartattu masu sonsu. Tunanin Aliyu ya faɗomata da yanda aka sha fama akan aurenta da shi da kuma Hilal. Idanunta suka ciko da kwalla. Ta haɗiyesu sakamakon Bingel da take tare da ita a kicin din.       Shinkafa da miya kawai ta girka, ganin suna da kayan ganye sai ta yanka kabeji da su karas ta haɗa coleslow.   Ta shirya komai saman tebur kafin ta dawo falon ta zauna tana danna waya. Muhibbat ta kira suka gaisa ganin kwana biyu ba su yi magana ba. A karshe ta nemi Amrah a waya suka hau hira. Har zuwa sadda A'isha  ta fito.   Zama ta yi tana hamma, dagasken dai bacci ta yi don idanunta da fuska sun nuna. "Ya kike ji yanzun?" Gyada kai ta yi. "Da sauki sosai. Sai dai yunwa." Murmushi Ramlat ta yi. "Daukomin hijab sai ki je ga abincin can saman tebur." Miƙewa Aishah ta yi ta koma daki, ca ta fito rike da Hijab da darduma. Ramlat ta shimfida ta tayar da sallah, tana cikin sallar Hisham ya fito yana amsa waya. "Dagaske kake ko wasa?" Can kuma ya ce. "Ok ganinan zuwa." A'isha ta dubeshi tana kokarin zuba abinci a plate. Kafin ma ta tambaya ya amsa da dariya yana satar kallon Ramlat. "Wai kinsan kuwa Hussein ne ya zo yana waje? Bari na shigo da shi." Daga haka ya fita, har suka shigo tare ba ta idar ba. Jin sallamarsa sai da gabanta ya fadi kafin ta yi istigfari a zuciya ta maida hankali ga sallarta. Sai da ta idar ta shiga addu'a hannun har yana rawa. Ya na zaune kujerar da ke fuskantarta. Gaisawa suke da A'isha  amma kusan hankalin yana kanta. A'isha ta saci kallon Hisham ya kashemata ido daya. Ta girgiza kai, ta san dama shi ya haɗa hakan. Ramlat ta kasa cire hijabin, ta mike ta ninke dardumar. "Ina wuni." Ta gaidashi, ya amsa a hankali. Rabonsu da juna tun wayar a suka yi kwanaki, ko a WhatsApp bai ƙara kulata ba. "Ku muje mu ci abinci, don wallahi Princess yunwa take ji." Fadin Hisham yana mai miƙewa. "Na ƙoshi." Daga Hussein har Ramlat kusan a tare suka furta, abin sai ya ba Hisham da A'isha dariya. Suka saci kallon juna, kunya ta kama Ramlat ta kauda kai. Shi kuwa Hussein murmushi ya yi. "Toh duk sai kun ci wallahi." Fadin Hisham. A dole suka bi bayansa, Ramlat ta dage a falon za ta ci. "Kai Sis." Fadin A'isha kamar ta yi kuka. Hussein ya ja kujera ya zauna bai ce musu uffan ba. Wayarsa ta yi ƙara ya mike cak ya fita gami da fadin. "Ina zuwa." Hajiya Zeenat ce, tambayar inda yake ta hau yi, ya dafe goshi. "Ina gidan Hisham, wani abu?" "Shi ne ba za ka fadamin ba? Na dawo gida ban ganka ba." Ransa ya ɗan sosu. "Da za ki fita yawon biki kin fadamin?" "Ni kake faɗawa haka?" Fadin Hajiya Zeenatu cike da wani irin firgici. Ya lumshe idanu ya bude. "Sai na dawo." Daga haka ya katse kiran. Ya koma ciki. Madadin ya ganta a tsakar falon, sai ya ganta zaune kujerar gefen da ya tashi, ya karasa ya zauna. "Hala Madam din ce ko sabuwar kamun da muka yi?" Fadin Hisham yana ƴar dariya da satar kallon Ramlat. Kirjin Ramlat ya buga, wani irin kishi ya turniƙeta. Ba ta san Hisham na da zancen da hankali ba zai dauka ba, zance marar kan gado ba, sai yanzun. Wani haushi ya bata, abincin ma ya daina yi mata dadi, dama tun zaman Hussein ƙamshin turarensa ya mamaye ilahirin jikinta ya haifarmata da kasala. Yanzun jikinta ya idasa mutuwa. "An fadamaka kowa irinka ne kenan." Abinda Hussein ya ce kenan bai ƙara uffan ba ya bar Hisham da dariya. Tunda ya soma cin abincin wani dadi ke ratsa kunnuwansa. Ya kasa ɗagowa har sai da ya yi nisa da soma ci, can dai ya dubi Hisham. "Nikam Princess dinka hala ta yi makarantar koyon girki ne." Haba! Ai daga Hisham din har A'isha da uwar gayyar Ramlat, dariya suka ya basu. Ya dubesu yana dan yarfa hannu, ya tsaida kallon kan Ramlat. "Mene abin dariyar?" Ta sunkuyar da kai tana murmushi. "Antinmu kinga karo na biyu wannan bawan Allahn na buga santi akan girkinki. Gaskiya yau goron da zai ba da kamata ya yi ya fi na rannan." Ita dai ba ta ce komai ba, ta kasa ci gaba da kai lomar, karshe ma miƙewa ta yi. "Na ƙoshi." Daga nan ta yi gaba da sauri ta koma cikin falon ta zauna ta basu baya tana sauke ajiyar zuciya. Shima gogan bai ƙara magana ba har ya kammala ci ya mike ya bar Hisham da A'isha ma ƙusƙus. Wuri ya samu ya zauna yana danne waya, sai dai rabin hankalinsa a kanta yake. Tun yana satar kallo har ya koma kallon sosai. Karshe ya maida hankali saman wayar, whatsapp ya shiga. Ganinta online ya taɓota. "Thank you." Ta bude saƙon kafin ta saci kallonsa, murmushi yake amma idanunsa na saman waya. "Kallon fa? Kar ki mata kwace." Jin bing na shigowar saƙo ta maida hankali ga wayar. Abinda ta gani kenan, ta turo baki kadan ta kashe data gami da jefa wayar cikin jaka. Miƙewa ta yi ta dauki mayafinta ta nufi dakin baƙi. Hijab din jikinta ta cire ga gyara zaman mayafin ta fito. Lokacin su Hisham sun dawo falon. "Ba dai tafiya ba?" Fadin A'isha. "Tafiya zan yi, Hajiya ta ce kar nayi dare." "Kai kamar wata karamar yarinya. Ko hira fa bamu yi ba. Prince ka yi mata magana." Fadin A'isha a shagwaɓance. Sakin baki Ramlat ta yi don ita abin ma na A'isha da Hisham mamaki yake bata. Soyayyar dai kamar ana ƙaramata zuma. "Ji, toh banda uzurin gabana da zan ƙare a gidanku?" "A'a amma don Allah ki zauna, kinga fa yanzu shida, ga hadari a gari..." "Shiyasa ai zan tafi, kinsan ban fiye tuƙi idan ana ruwa ba." A'isha kuma ta rasa abin faɗi. Hisham dama bai ce ba, so yake abokinsa ya ce! Jakarta ta dauka cikin lallashi ta ce. "Haba Autar Hajiya, In sha Allah za ki ganni kwanannan, ai yanzun sai ana leƙowa ana dubaki. Yauwa Maman Twins ma sun ce na fadamaki suna nan zuwa." Jin haka yasa A'isha sakin ranta kaɗan. "Toh ai shikenan. Allah Ya kaimu." Ramlat ta amsa da amin tana murmushi. Hussein ya mike yana duba agogo. "Nima zan gudu." "Kamar hadin baki?" Fadin Hisham. Girgiza kai Hussein ya yi. "Yamma ta yi ga hadari." Gyada kai Hisham ya yi. "Ai shikenan, don ma dai kai din baki da hanci ne. Ba nisa sosai." Hussein bai amsa ba ya bi bayan Ramlat da tuni ta fice. Hisham na dariyar mugunta ya yiwa A'isha raɗa a kunne ya bi bayansu. "Innalillahi, garin yaya?" Fadin Ramlat a hankali tana jin kamar ta yi kuka. Hussein ya juyo yana dubanta, iska na faman ɗaga mayafin nata da ja mata rigar. Tayarta ya gani a sace. "Ya Salam, Antinmu garin yaya hakan ta faru?" Fadin Hisham sadda ya karasa yana kyafkyafta idanu ganin iska na neman yi mishi lahani. Kamar ta yi kuka ta dubi Hisham. "Wallahi nima bansani ba." Ta furta cike da takaici. A'isha ta danne dariyarta, game din dadi yake mata sosai. Tuni Hussein ya bude motarsa ya shige ya ba ta wuta. "Shigo na kaiki." Abinda ya ce kenan. Ta dubeshi ta maida duba ga su Hisham. "Je ki don wallahi hadarinnan yanda ya haɗe ba zan iya fita ba. Sai dai ko ki kwana zuwa safe." Ta haɗa daga shi har A'ishar ta watsawa harara. "Gobe na ƙara zuwa gidanku." Nan kuma suka hau aikin ban hakuri, ta karasa ta bude gidan gaba ta zauna. Hussein ya dubi abokinsa. "Sai mun yi waya." Daga haka ya fice bayan Maigadi ya budemusu ƙyaure. *** Tunda suka kama hanya yake murmushi, ya san ko mene aikin Hisham ne. Amma hakan ba karamin dadi ya yi mishi ba, ya juya ya kalleta. Ta takure kanta wuri guda, ta wani rungumi jaka. Basu yi mintuna biyar da soma tafiya ba aka soma ruwa dagasken gaske. Ganin irin karfin ruwan yasa dole ya taka burki ya sauka ya gangara gefe. Wayarta ta yi ringing ta duba, Hajiya ce. Hakuri ta bayar gami da bata tabbacin ta taho. Hajiya na faɗa akan ba ta ji dadin hakan ba suka yi sallama. Tasan a zatonta ita ke jan motar, ba zata fadamata ga abinda akai ba. "A dalilinki na zo gidan Hisham." Ya fadi kansa tsaye yana kallon yanda ake zuba walkiya da ruwa kamar da bakin ƙwarya. Ta dubeshi da mamaki, maimakon murmushi, wani kwantaccen damuwa ta gani shimfide saman fuskarsa. Ya karkato yana dubanta, ta kauda kai saboda nauyin da kwayar idanunsa suka yi cikinnata. I just published "BABI NA ARBA'IN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/GhWrzYe49bb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 41) *Assalamu Alaikum yan uwana. Fatan Alheri ga dukkanku. Ina matukar farin ciki da irin addu'o'inku gareni. Allah Ya bar zumunci. Ameen.* *Ban kammala Exams ba, amma aski ya zo gaban goshi. Nagode sosai.* "Kar fa ki fassara kalamaina." Ta yamutse fuska kadan. "Fassara ta me?" Ya yi murmushi yana dubanta sannan ya maida kai ga tuƙinsa. "Akwai hoton da nake da buƙata a wurinki." Ta saci kallonsa. Ba ta tanka ba ya ɗora. "Wata little angel da na gani kwanakin baya kin ɗora hotonku tare. Ita ba ƙatuwa ba kuma ba siririya ba. Fara ƙal." Da gaskiyar Bature da yace Blood is thicker than water.  Fati yake nufi. Murmushin da ba ta san ta iya shi ba ta shiga yi kafin ta saita kanta da tunaninta. "Ka santa ne?" Taɓe baki ya yi gami da girgiza kai. "Ko daya, kawai dai yarinyar ta burgeni sannan ina jinta kamar ƴar da ta fito daga jikina." "Alhamdulillah." Tsabar ruɗu yasa ta furtawa a fili har ya kai dubansa gareta. "For?" Ya nemi ba'asi. Murmushi kawai ta ke yi. "Murmushin fa? "Ba murmushi nake ba." Ya dubeta sai kuma ya yi dariya. "Toh kuka kike yi." Ta shafi bakinta sai kuma ta sunkuyar da kai tsabar kunya.  Ya sanya hannu ya kunna music. Wannan karon ma dai muryar Nancy Ajram ke tashi. Abinda Ramlat ta fahimta, Hussein ma'abocin jin waƙoƙin larabawa ne. Shiru ya biyo baya har suka kai ƙofar gidan su Ramlat. Kirjinta ne ya bada dam ganin Yayanta Munir tsaye a jikin motarsa yana amsa waya. Tunda motar ta tsaya ya ƙuramata idanu yana son ya shaida waye.   Hussein ya dubeshi sadda ya ke ƙoƙarin cire Seat Belt din da ya sanya.  Kamanninsa da Ramlat kawai ya gani da kuma irin firgicin da ke saman fuakar Ramlat din, ya fahimci ko waye. Bai cewa Ramlat komai ba ya fita, itama ganin haka ta fito kirjinta na lugude. Yaya Munir da ganin Ramlat ya ba shi mamaki, dakyar ya iya miƙawa Hussein hannu suka gaisa. Ita kuwa Ramlat tana gaidashi wuf ta faɗa cikin gida.   "Ke kuma lafiyarki?" Tambayar da Hajiya ta watsomata kenan ganin shigowar da ta yi a hargitse. Girgiza kai ta yi ta zauna kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki. "Ba komai." "Hala kin haɗu da yayannaki a waje?" Ta gyaɗa kai, ba ta kai ga bata amsa ba sai ga Munir din. Abinda ta ke gudu ne ya kasance, faɗa sosai ya shiga yi akan don me za ta shiga motar abokin Hisham. Hajiya dai mamaki ƙarara don ba ta da  labarin hakan. "Ku yi hakuri, wallahi tayar ce ta sace. Ga Auta ba lafiya shiyasa dole Hussein din ne zai kawoni. Kunsan yanayin unguwarsu ba'a samun abin hawa cikin sauƙi." Ta faɗi jiki a sanyaye. Harara Yaya Munir ya danƙara mata. Hajiya kuwa jin Hussein ne yasa ba ta ƙara uffan ba. Dakyar dai ta lallaɓashi ya tafi. Bayan fitarsa ta miƙe ta yi ɗaki, sai bayan sallar isha'i sannan ta fito, ta ƙara wanka ta sanya doguwar rigar bacci da ƴar hula. "Gidan gaba ɗaya sai ya yi ba daɗi wallahi." "Uhm, ni zan faɗi haka ba ke ba Ramlatu, nayi kewar yarannan kamar na kira waya a maidomin su." Murmushi Ramlat ta yi ta zauna. "Hajiya kinsan wani ikon Allah? Yau da kansa ya tambayeni hotin Fatima. Wai haka kawai yarinyar ta burgeshi, na aikomasa hotunanta." Hajiya ta ɗan yi shiru alamar nazari. "Fatima wacce?" "Ɗiyar baƙonmu na Adamawa." "Ikon Allah, jini ba wasa ba. Allah Sarki." "Ni kaina nayi mamaki." "Allah Ya ci gaba da taimakonmu, in sha Allah za'a dace. Wataran komai zai zama labari." Cikin gamsuwa Ramlat ta jinjina kai tana murmushi, fuskar Hussein na yawo cikin ƙwayoyin idanunta. "In sha Allah." Ta maimaita. ***   Ranar litinin da tana kammala shiri ta fito, a gaggauce ta karya ganin tana dab da makara. Haka ta fito titi don har sannan Hisham bai ga damar maidomata motarta ba, ba kuma ta ƙara kiransa ba tunda ta ji yana kiran shi ba shi da kuɗin gyaran taya toh ta san da biyu ya ke yi.       Ta yi tafiya kaɗan kafin ta fito bakin titi ta samu abin hawa. Zamanta keda wuya cikin Napep, wayarta ta ɗauki ƙara. Halima ce. Kamar ba za ta ɗaga ba sai kuma ta ɗauka. "Ke kuwa Ramlat ba faɗa me ya kawo gaba? Shikenan don kin bar Revenue  an rabu?" Yaƙe ta ɗan yi kamar a gabanta. "Ayya Halima ba haka bane. Allah Ya huci zuciyarki. Fatan kuna lafiya, Ya sauran mutanenmu?" "Uhm, lafiya kalau, sai dai kin tafi kin bar baya da ƙura." Da mamaki ta ce. "Ban fahimta ba. Wani abu aka yi?" "Eh, yanzu ba wanda bai san cewa Chairman yana sonki ba. Idan ma kina tunanin bamu sani ba gwara ki san cewa ƙwai ya fashe." Wani ɓacin rai ya zo wa Ramlat wuya, ta danne komai. "Shi ne me? Don yana sona mene a ciki Halima?" "Aa ba komai bane, Allah Ya ba ki hakuri. Yanzun sai na faɗi zancen da zai yimin sanadin wurin neman halal ɗina. Dama shawara zan ba ki kawai don matar Chairman ba kanwar lasa ba ce." Don tsananin ɓacin rai ba ta san sadda wani wawan tsaki ya suɓucemata ba. "Daga ita har mijinta basu ɗaɗani da ƙasa ba, ke kinsan ni kuma kin san halina. Bana kallon mutum irin Chairman matsayin nagartaccen namiji da ya isheni kallo ballantana har na ƙulla alaƙa ta dindindin da shi, wato aure. Ke dai da ya tsolemaki ido har ki ka kasa haƙurin bar wa cikinki gulmar sai ki je can ki ƙarata." Daga haka ta katse wayar ta kasheta gaba ɗaya ma tsabar takaici da ɓacin rai. Har suka isa ta sauka ba ta ji sassauci a ranta ba. Ita ta soma zargin ma Halimar ce ta kwatantawa Chairman din gidansu na Yakasai. Can kuma ta ja istigfari a ƙasan ranta. *** * ADAMAWA* AlHassan ke ta zuba sauri a hanyarsa ta komawa cikin babban shagon siyar da kayayyaki na Alkhairat Mall adalilin mantuwar da ya yi na wallet ɗinsa saman teburin Cashier. Karo suka ci da wani matashi da kallo ɗaya za ka yi mishi ka san ruwa biyu ne, kamar dai ɗan Sudan kamar kuma ɗan Nijeriya. "Sorry please." Faɗin AlHassan kenan yana dubansa a fisge, Matashin ya zaro ido kafin ya saki ƴar dariya yana nunashi da yatsa. "Hussein!" Daga haka ya rungumeshi yana dariyar farin ciki, AlHassan ya tsaya cak! Ya kasa magana kwakkwara, can dai ya ɗago ya dubeshi da kyau, kamar ya so sanin fuskar sai dai Allah bai ba shi ikon tunawa ba. Rasheed da ya lura da irin kallon da yake binsa da shi, sai jikinsa ya ɗan yi sanyi. Daidai sadda wani ma'aikacin wurin ya nufosu, duban AlHassan ya yi. "Yallaɓai ai na fita ban iskeka ba mun yi saɓani, ga wallet ɗinka ka manta." Ya karɓa da godiya, Rasheed dai kallo yake sai kuma a sannan tunaninsa ya ba shi anya kuwa wannan Hussein ɗin da ya tako takanas daga ƙasarsa don ya gani ne? Nan da nan jikinsa ya ba shi Twin brother ɗinsa ne wato AlHassan Aminu. "My name is Alhassan Aminu, Hussein's Twin Brother." Rasheed ya shiga murmushi da gyaɗa kai, bai lura da yanayin sauyawar fuskar Alhassan din ba, daga yanayin farko zuwa wani yanayi na daban mai nuni da alhini da kuma sosuwar rai.   Alhassan ya nemi su ɗan fito farfajiyar wurin. Ba musu Rasheed ya bi bayansa. Ji yake kamar ya yi tsuntsuwa ya je ga Abokinnasa, shekarun da suka gabata ya yi masifar kewarsa. A hanyar ma su na tafe ƙorafi ya ke zubawa AlHassan na yanda Hussein ya kasa cika alƙawarin kawo mishi ziyara sai shi ne ya cika a karshe. "Kusan satina ɗaya a garinnan na kasa gane gidanku, har na fidda rai don har na yi komai na komawa garinmu sai yau cikin ikon Allah muka haɗu da kai." Duk yana maganar ne cikin harshen turanci, Alhassan ya ba shi address din gidansu kafin su yi musanyen lambar waya suka rabu. Rasheed dai ya yi mamakin dalilin da yasa bai ba shi lambar Hussein ba, ya so tambaya kawai sai ha bar wa cikinsa. Da wannan ɗokin ya nemi adaidaita ya koma masaukinsa, siyayyar da bai yi ba kenan tsabar murnar cimma abindanya kawoshi. Tun a hanya ya kira mahaifiyarsa yake labarta mata haɗuwarsa da AlHassan da yanda ya rungumeshi a zatonsa Hussein ne. Ta tayashi murna sosai sannan suka yi sallama. ***   *KANO* Tana zaune bayan kammala wasu aikace-aikace, ta tuna da cewa wayarta a kashe ta bar ta gaba ɗaya yinin ranar, da sauri ta jawota ta kunna. Mintuna ƙalilan da kunne Data, saƙonni suka shiga faɗowa daga Whatsapp. Wanda ta ke burin ta ga ya aikomata saƙo babu shi a ciki, har tana shirin ajiye wayar sai ga text message ya faɗo, ta duba. Ba ta kai ga buɗewa ba sai ga kira, duk daga mutum ɗaya wanda ta daukeshi SPECIAL.   "Kashe mutum kike kokarin yi." Ta ɗan dafe ƙirji kafin ta saita kanta tuna a inda ta ke, lumshe ido ta ɗan yi tana murmushi. A baya zabta ƙaryata idan wani ya ce za ta ko kalli wani ɗa namiji ta ji ya burgeta balle ta kaunaceshi, a yanzun kuwa tana jin Hussein a ranta. Da wani irin ƙauna mai sanyi, da wani irin so mai cakuɗe da sinadarai masu ban mamaki. "Tuba nake yi, me na yi?" Ya sauke ajiyar zuciya wanda ya ratsa kunnuwanta. "Kin kashe wayarki bayan kinsan na kamu da son Beautiful Angel dinnan da kika ɗora a status."   Runtse idanu ta yi cikin son haɗiye abinda kunnuwanta su ka yaudareta da son ji. Maimakon hakan sai ta ji abu daban, cikin sarewa da sanyin jiki ta amsa. "Ka yi hakuri, na ma manta cewa na kashe wayar. In sha Allah yanzu zan turamaka." "Ok! Na gode, ina jira." "Toh." "Naji muryarki ta sauya, hope komai lafiya?" Ta ciji leɓbanta na ƙasa tsabar haushin kanta da ya kama ta, toh mene dalilin da za ta ba shi damar fahimtar wani abu? "Lafiya kalau, ina wurin aiki ne." Shiru ya biyo baya can kuma sai ya amsa. "Ok ba damuwa. Idan kin koma gida kya turomin. Thanks." Daga nan ya katse kiran. "Ke kam dai naga alamar da wani gwanin naki kike waya." Ta kai duba ga Hajiya Salma, darakta din department din da ta ke. Kasancewarta mace mai raha da haba-haba yasa ake sonta. Ga ba ta da wuyar sabo. Murmushi kawai ta yi ba ta ce uffan ba. Ta faɗa whatsapp, Hussein din ma ba ya online, haka ta turamasa duk hotunan Fatima da ke kan wayarta har wanda Fatiman ke tare da Hafsat. Babu dai nata ko ɗaya a ciki. Karfe biyar da kusan rabi ta bar Ofis zuwa gida. Gaba daya jikinta a sanyaye yake sakamakon soyayyar da ta ke yiwa kanta shamaki da ita, amma kamar zuciyar ba ta jin kashedinta. Ƙara cusa kanta take yi cikin lamuran Hussein dumu-dumu. Idanunta ga cicciko da kwalla, ta sharesu. Ya dace ta yi baya-baya da shiga shirginsa tun kafin ta yi nisan da ba ta jin kira a sha'aninsa. Ko babu Hajiya Zeenatu, Hussein ya fi ƙarfin ajinta. A ganinta, wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa.    Haka ta wuni cike da kasala, sai dab da Magriba sannan ta fito ta faɗa kicin, kunu ta dama, ta zubawa Hajiya  wacce ke azumi cikin flask mai riƙe zafi. Dama ta iske tuni an yi Ƙosai. Wannan tasa ta haɗamata da lemun zoɓo da ya sha kayan ƙamshi. Sai da ta tabbatar ta haɗa komai saman darduma kafin ta koma ɗaki, alwala ta ɗauro. Wayarta na kyallin shigowar saƙo don haka ta duba.   *"Thank You."* Abinda ya turomata kenan. Murmushi kawai ta ɗan yi ta shimfiɗa darduma.   Misalin ƙarfe takwas da rabi suna zaune a falo tare da Hajiya, kallon Tarkon Ƙauna suke a tashar Arewa24. Gaba ɗaya hankalin kacokan yana kan talabijin, sallamar Baba Maigadi ta ɗauki hankulansu. Suka amsa. Saƙon Ramlat ta yi baƙo yake tafe da shi. Nan da nan ta ɗaure fuska, tana da tabbacin Chairman ne don dama Kawu yace ta zuba idanun ganinsa a satinnan. Umarnin Hajiya ta bi kawai ta miƙe ta shiga ɗaki, Hijabin sallarta ta zura ta fita. Kamar dai yanda ta tsammata hakan ce kuwa, yana tsaye ya sha wata narkakkiyar shadda da aka yi mishi aiki a jiki. Ƙaton tumbinsa shi za ka soma haskowa kafin ma ka kai ga ganin komai. "Mtsw." Ta ja guntun tsaki tana jin kamar ta juya, dolenta ta daure ta ƙarasa. Ganinta ke da wuya, ya ƙara daidaita tsayuwarsa yana mai ƙuramata idanu ga wani haƙoransa da suka bayyana shi a dole murmushin ƙauna ya ke. "Ranki ya daɗe Ramlatu." "Ina wuni." Ta gaidashi ciki-ciki. "Lafiya kalau Hajjaju. Wato sai kika ganni kwatsam. Wallahi kasa hakurin na soma kiranki nayi saboda jina nake kamar na shiɗe jiya tsabar tunaninki da ya.." "Ina mai neman alfarmar ka tafi kai tsaye ga abinda ya kawoka, komai nawa nakan ba lokaci muhimmanci. Da ace dai ka sanar da ni zuwannaka tun wuri zan fi samun sukunin tsakurar maka mintoci kaɗan daga lokutan da nake sa shi. Yanzu dai akwai abinda nake yi ka katsemin hanzari. Amma bari na ƙara faɗamaka haƙiƙanin abinda ke zuciyata dangane da kai. Inaga hakan zai taimaka wajen ganin ba mu shiga haƙƙin juna ba." Chairman Dikko wanda ya zubamata idanu kamar ya haɗiyeta tsabar so, ya jinjina kai gami da gyara tsayuwa. "Na ji abinda kika ce, ko daga yanda kika tarbeni nasan me kike nufi, kar ki manta kin faɗamin ai tun kafin na tako nan. Amma Hajiya Ramlatu, duk wasu bayananki ba zai sa ni Dikko na haƙura da ke ba, ina sonki, wani irin so da rabona da shi tun a kan Mairo uwargidata. Don haka zan jure dukkan ƙiyayya, na rantsemaki da Allah kika shigo gidana ba za ki ƙara marmarin fita ba saboda daɗin da zan jiyar da ke. Ga kuma madarar ƙauna." Ya ƙarashe da wata shaƙiyiyar dariya. Ta bishi da kallon tsana, ta sauke idanunta kirjinta na ƙara zafi. Kasa cewa komai ta yi har ya kammala sumbatunsa, karshe ta dubeshi. "Dare ya fara, na kuma gaji da tsayuwar." Ya sauke ajiyar zuciya gami da duban agogo. "Wallahi ban san lokaci ya ja har haka ba, amma nidai don Allah ki ƙara dubawa tunda dai su Kawu sun riga da sun ba ni ke. Kinga kuwa babu abinda zai hana aurenmu, ki sanyawa ranki salama ki yi tunanin alherikan da ke jiranki a gidana." Ta ƙara ɗaure fuska, ba ta bari sun yi doguwar sallama ba ta juya ta nufi ciki. Ba jimawa da shigarta sai ga Baba Mai gadi da ledoji har uku shaƙe da kaya, da sauri ta karɓa da zummar maida mishi, babu shi babu motarsa. "Ai ina ce miki ya wuce, ba ki ji ba." Faɗin Baba Maigadi, cike da takaici ta dubeshi.   "Don Allah Baba kar ka kara amsar saƙon wannan mutumin." Baba ya ɗan yi shiru, ita kanta Ramlat din sai ta ga rashin kyautatawa tunda dai Baba Maigadi ba ruwansa da alaƙarsu. Juyawa ta yi ta koma ciki. "Wai ke wannan kumburin da kike yi, ba fa wanda ya matsa akan sai kim aureshi." Hajiya ta furta tana dubanta. Ramlat da tuni idanunta sun cicciko da kwalla ta amsa. "Ni Hajiya abinda ke tayarmin da hankali, bai wuce yanda Kawu ya yi saurin aminta da shi ba. Fisabilillah babu bincike babu komai? Ni nasan waye Chairman, ba abinda suka sani a kansa." "Ke wa ya faɗamaki ana dogon bincike akan mai muƙami ko dukiya? Hum, Ramlatu a zamaninnan ba'a wannan. Bar ganin Yayyuna ne, amma na fi ki sanin halinsu. Ke dai ki dage da addu'a, muddin kuma kina son ki shafe maganarsa toh wallahi ki watsar da komai ki fiddo mijin aure. Shi ne kwanciyar hankalinki da namu baki ɗaya. Ai kin dai ji abinda Uwani ta faɗamaki. Yanzu da ace kin tsaida hankali wurin ɗan uwan mijinnata ai da yanzun sai dai wata maganar ba wannan ba." Ramlat kirjinta ya yi nauyi, ta share hawayen da ya soma sauka saman fuskarta. Miƙewa ta yi ba ta ko yi marmarin ganin abinda ke cikin ledojin ba ta faɗa ɗakinta. Gefen gado ta zauna gami da zabga tagumi. Tana cikin tsaka mai wuya, ita ta sani. Wanda ta ke masifar so kuma ta ke jin za ta iya aura bai san ma tana yi ba. Runtse idanunta ta yi tana mai sa hannu ta dafe kanta.   "Ya Allah!" Ta furta a fili, fuskar Hussein kawai ta ke gani cikin ƙwayar idanunta. Ta buɗe idanun, tuni sun kaɗa sun yi jazur. A hankali ta kai duba ga hotonsu na Family, Abbanta ta ƙurawa idanu. Take dukkan wani faɗi-tashi da aka yi akan zancen aurenta da Aliyu ya faɗomata. Murmushi ta yi da ya fi kuka ciwo, soyayyar Abbanta ya mamaye zuciyarta, yanzun komai ya zama tarihi. Abba ya bar ta da kewa ta har abada, hakanan Aliyu. Ta tsinci kanta a sabuwar rayuwar da ba ta san abinda zai haifarmata a gaba ba. *** ADAMAWA Misalin ƙarfe biyu da mintuna na ranar Talata, Rasheed ne zaune yana faman haɗa gumi ga idanunsa da suka kaɗa suka yi ja tsabar tashin hankali. Labarin ɓatan amininnasa ya matuƙar girgiza shi. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ya furta a fili, Dada dai hawaye ta ke yi hakanan Hafsat da ke raƙuɓe a gefe ta dora hannu saman cinyar Dada. Rasheed ya dubi AlHassan cikin harshen turanci. "Ban ji dadin wannan labarin ba sam! Sai dai ina ji a jikina duk inda Hussein ya ke yana raye, bai mutu ba. Sannan meyasa ba ku yi cigiyarsa ta gidajen rediyo  da talabijin ba? Na dauka wannan ce hanya mai sauki da za ku yi saurin ganoshi." AlHassan ya jinjina kai. "A farko duka mun yi wannan amma a karshe sai muka watsar mu ka fawwalawa Ubangiji. Ni kaina ban yarda cewa Hussein ya mutu ba. Amma ya zamu yi? Babu inda ba mu nemeshi ba, sai dai ba wani labari." Rasheed ya runtse idanu cike da ɓacin rai, ransa na suya. "Kuma babu wani abokin gaba da ya ke da shi? Wanda ku ke zargi?" "Babu." Rasheed ya yi shiru, so ya ke ya tuna ko akwai abinda ya manta game da Hussein. Duk iyakar kokarinsa ya kasa, a ƙarshe dai AlHassan ya shiga roƙonsa akan ko labari ya ji na abinda ya danganci Hussein don Allah ya sanarmusu.  Bai bar gidan ba sai da ya ci abinci, nan ma kawai cusawa yake, ba zai ce cimarsu ta bambanta ba don shi kam ruwa biyu ne, mahaifiyarsa ƴar jahar Katsina ce. Jimami da alhinin ɓatan Amininnasa ne ke sukarsa. Da wannan ya musu sallama ya bar gidan. Ranar dai ya tayarmusu da alhinin Hussein, wunin ranar sun yi shi sukuku ba daɗi idan ka cire Taheer da bai san me ake ba. Burinsa kawai ya shaƙu da Hafsat kuma ta kaunaceshi, sai dai abin ya faskara. ***   KANO Wata wawuyar dariya Hajiya Zeenat ke yi tana ƙara rungume wayarta a kunne, ƙafafunta kamar za su rabu da cinyarta tsabar girgizasu da take. Kallo ɗaya za ka yiwa yanayinta ka fahimci ko ma wane kalar labari ake ba ta ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba. "Kai Dikko! A ganka nan a bar ka inda kake! Da ace za ka san daɗin da wannan labari ya min za ka sha mamaki. Kai ma kwallon shege ne!" Can kuma ta ƙara nutsuwa ta ce. "Kana ji na? Kar ka sake ka yi wasa! Kar ka ɗaga ƙafa, wani ganin ba ta sonka ko ta tsaneka wannan duk a banza ce muddin ta faɗo hannunka. Ka dai ƙara ƙaimi wajen sakarwa makwaɗaitan iyayennata aljihu, na tabbatar maka ƙarfin dukiya ya fi komai tasiri a duniyarnan. Don ubanta dole ma ta sarara ta aureka. Ni kuma na maka alƙawarin wata kyauta mai tsoka muddin ka mallaketa matsayin matarka." Jin haka daga can ɗaya ɓangaren, Chairman ya shiga zuba godiya da kirari, wannan ya ƙara fasa kan Hajiya Zeenatu, har wani lumshe ido take tana murmushi, koda ta ji motsin saukowar mutum daga bene ta yi sallama ta ajiye kan wayar. Duban mijinta ta shiga yi tana murmushi sosai, ranta na wani irin sanyi kamar ƙanƙara. Shi kuwa bai san ma tana yi ba, kacokan hankalinsa yana kan wayar da yake amsawa na Hisham game da kasuwanci na haɗin gwuiwa da suke son yi. Har ya sauko ya ƙaraso bai kammala ba, ganin irin kallon da ga ke jifansa da shi yasa shi fadin. "I will call you back." Daga nan ya katse wayar. "Lafiya?" Abinda ya ce kenan. Ta yi farr da ido, ya kauda kai. "Ba komai, kawai dai kyau ka yimin Yallaɓaina." Ɗan murmushi ya yi bai ce uffan ba. "Amm, dama ina son zuwa asibiti." Ya dubeta. "Meke faruwa?" Cike da ƴar damuwa ta ce. "Kwanakinnan komai na ci sai na ji kamar zan yi amai, ga yawan kasala." Kirjinsa ya bada dam! Haka kawai zaton da ya yi sai bai mishi wani dadi sosai ba. Ya daure ya gyada kai da murmushin da ya fi kama da yaƙe. "Ya kamata ki je, ba'a wasa da lafiya." Ta ƙara rausaya ƙwayar idanunta. "An gama Baby, da safe za shirya na je. Fatana Allah Yasa mu ji alheri." Ta ƙarashe tana shafa cikinta, ya yi murmushi kawai ya maida hankali kan wayarsa. Hotom Fatima ya buɗe yana kallo, gani yake idan har Hajiya Zeenatu za ta haifamasa irinta, toh yana marhaba. Kaunar yarinyar ya ke ji sosai. Abu daya ya tuno da ya ji ba dadi, wato dai rabon da ya ga Ramlat ma a online tun ranar da ta turo mishi hoto. "Wannan kuma wacece?" Tambayar Hajiya Zeenatu da ya yi saurin maidoshi tunaninsa. Ya sauka daga whatsapp din ya rufe wayarsa, cikin faɗuwar gaba ya ƙirkiro ƙarya ya shirgamata. "Ƴar sister din Hisham ce. Ta miki kyau ko?" Nan da nan annashuwar saman fuskar Hajiya Zeenatu ya dawo, ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi. "Sosai yarinyar ta yi kyau. Zamu haifi fiye da hakan ma." Ya gyaɗa kai kawai. *** "Wai wa ya faɗamaki ina sonsa? Ni wallahi ban taɓa sauraronsa ba." Ramlat ke faɗi a gundure, gaba ɗaya zancen Chairman ya isheta. Ta kuma lura mitar Rafee'ah ba mai ƙarewa ba ce. "Ai shikenan, idan dai kina son a tabbatar da hakan sai ki daure ki fiddo miji. Ko kuma shawara, ki samu Baba Dakta kawai ki faɗamasa." Cewar Rafee'ah. Ramlat ta yi shiru, da sun san damuwar da take ciki na son maso wani da basu takuramata da zancen Chairman ba. "An faɗamaki Baba Daktan shima zai saurareta ne idan ba wani ta kawo ta ce shi za ta aura ba? Malama ki yiwa kanki faɗa tun wuri wallahi idan ba haka ba za'a ji kunya. Baban Twins yana da labarin Chairman Dikko, ba abinda ban sani ba na tarihinsa." Wannan karon ma shiru ta yi, Ramlat ta yi dana sanin dawowarta gidan da wuri, da ace ta san da zuwansu ba abinda zai kawo ta. Ta dawo ta iske Hisham ya gaji da zolayar ya aikomata motarta. Yinin ranar da tunanin Hussein ta cinyeshi, don dakyar ta dinga fuskantar aikin da ke gabanta, yanzun kuma ta zo ta iske yayyunnata, sun sanyata tsakiya kowanne da kalar nashi zancen. Tsam! Ta mike tsaye ta kwashi tarkacenta na ofis da zummar wucewa. "Au, mu za ki yiwa rashin ta ido? Don ana faɗamaki gaskiya?" Ta kasa ba Anti Zulaihat amsa, cike da damuwa ta dubeta kawai. "Wuce abinki, ke kika sani. Rayuwarki ce." Ta furta a zafafe, Ramlat ta ciji lebbanta tsabar takaici, karshe ta yi gaba zuwa daki tana ji Hajiya na fadin su bita a sannu. Ruwan ma kasa watsawa ta yi don haka ta bi lafiyar gado ta kwanta, a hankali ta shiga fitar sa hawayen baƙin ciki. Kewarsa ta ke ji kamar ta yi me, ga wani irin sonsa da ke nuƙurƙusarta, kwana biyu ba su yi magana ba, bai ganta online ba kuma bai nemeta ta waya ba. Wannan yasa ta ƙara tabbatarwa ita kaɗai ke haukan sonsa. Ta kai minti goma sha biyar a haka ba ta iya ko motsawa ba, tausayin kanta take ji, da ace su Ummi na gidan, ko ya ya zasu ɗebemata kewa, kiran sallar Magriba ce ta tasheta. Ta faɗa banɗaki ta kama ruwa ta yi alwala. Sai da ta idar da sallah kafin ta ninke Hijab ta fice zuwa falon. Wannan karon ta yi ƙoƙarin saita zuciyarta ta ƙaƙalo walwala, suka ci gaba da hira da ƴan uwanta kamar wani abu bai faru ba. Tattaunawa ce game da bikin da ya taso a Daura, wanda zasu tafi dukkansu don karshen sati ne. Su ma basu ƙara tayar da batun Chairman ba. Sai bayan sun bar gidan, Hajiya ta shige daki don watsa ruwa, itama ta faɗa nata ɗakin da niyyar hakan. Ganin hasken shigowar saƙo bai sa ta yi wani rawar ƙafa ba, hakan ya faru ba adadi a yini biyunnan, sai dai daga ta duba, saƙon Muhibbat ne ta ke gani, wani lokacin Hilal, wani lokaci kuwa saƙon kamfanin layukanta. Tunanin hakan yasa ta ƙin daukar wayar har sai da ta fito daga wanka ta gama shafe-shafenta ta shirya cikin riga da wando na bacci. Ta dora rigarta na sallah ta shimfida darduma. Sai da ya idar da sallar Isha'i ta yi duk abinda ya dace sannan ta ƙara samun nutsuwa. Kai tsaye ta nufi wurin wayar, sunan da ta gani a saƙon ya sa ta jin nauyi a ƙafafunta, kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, haka ta buɗe bayan ta zaune gefen gado. *Na lura kina da kishi, wato don ban nemi ki turomin hotonki ba ne yasa ki ke shan ƙamshi ko? Oya, a turomin yanzu. Happy?* Lumshe idanu ta yi tana murmushi.   I just published "BABI NA ARBA'IN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ysuMTT3Orcb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 42) Dukkan godiya tabbata ga Sarki Allah. Tsira da aminci su kara tabbata ga Ubangijin Talikai. Ina kara amfani da wannan damar wurin godiya gareku gaba daya. Alhamdulillah na kammala exams lafiya sai fatan sa'a in sha Allah. Ina godiya da hakuri da uzurinku gareni. Allah Yabar zumunci. Ameeen. Sai dai kar ku manta dama ba kullum nake posting ba, ina tsallake kwana daya. Allah Yasa mu ga karshen Ƙarfen Ƙafa lafiya. Ameen. ****** *Ya ya zan yi in misalta soyayya..? Ya ya zan yi in fasalta soyayyaa..? Ita ce ba'a siye da kudi duk dukiyaa..Ita ce mai gida na mulki shi ne zuciyaaa..Ta sanya mai ƙarfi ya sunkuyaa..ya zubda hawayen idaniyaaa..!* Umar M Shareef Hoton ɗan aljan mai murmushi kawai ta tura mishi. Aka yi sa'a ya hau online. Ganin ya buɗe ta yi saurin kife wayar ta runtse idanu kamar yana gabanta, kirjinta na wani dukan tara-tara. Jin ƙarar shigowar saƙo yasa ta karkata wayar a hankali kamar marar gaskiya ta duba. *"Please."* Don ƙara tabbatarwa ta ƙara murza idanu ta duba, roƙonta fa ya yi? Anya? Kuma akan hotonta? Ina Hajiyarsa? Duk wannan tambaya ce da babu mai amsamata sai shi, har abada kuma ba za ta tambaya ba. Ta jingina kanta jikin gado tare da miƙar da ƙafafunta. *"Angel ɗina ya hana ni aikawa kowa hotona."* Ta ba shi amsa duk kuwa da cewa ba ta ji dadin amsar ba, sai dai ta lura idan ta biyewa kanta, za ta iya tona asirin zuciyarta har ya gane inda ta dosa. Ya buɗe, kusan mintuna biyar shiru, goma, sha biyar, duk shirun ne, shi bai sauka online ba kuma bai ce uffan ba. Ramlat dai har bacci ya soma fisgarta babu amsa daga Hussein. Don haka ta ajiye wayar ta mike ta kakkaɓe shimfidarta ta kwanta. Ta soma addu'oin kwanciya bacci kenan wayarta ta yi ringing. Da sauri ta kai idanunta, lambar da ta gani ya hargitsa kwanyarta, miƙewa zaune ta yi b shiri. Sai da ta kusan yankewa kafin ta samu nutsuwar ɗagawa. Leɓɓan ke rawa, zuciyar na ƙara ƙaimi wurin bugu sai dai lanƙwasa harshen har ta iya haɗa kalma kwakkwara ta gagara. 'Haka so yake?' Ta jefawa zuciyar tambaya. Ta san ba wannan ne farkon soyayyarta ba, wanda ta shimfiɗa a baya ya girmi wannan. Sai dai wannan shigarsa da tasirinsa mai sauri ne kuma mai sanyaya zuciya da ruhin ma'abocinsa. "Kin yi shiru." Ta dawo daga duniyar tunanin abinda ya yi mata nisa, TAZARAR DA KE TSAKANINSU kamar tazara ƙasa da sararin samaniya ne. Ɗumi ta ji a kumatunta, wani ɗanɗano na gishiri ya sauka a  leɓɓanta ta cije leɓɓan. Kitt! Ta katse kiran, ba ta tsaya anan ba sai kawai ta kashe wayar gaba daya ta jefa gefen gado. Kwanciya ta yi ta runtse idanu, me ya rinjayeta har haka? Hussein fa? Kamanninsa suka yi dirar mikiya cikin idanunta, tunaninta ya ɗauketa ya cillar tun daga ranar da ta soma ganinsa har zuwa yanzu da suke tare. "Ka fi ƙarfina Hussein, Allah Yayemin wannan jarrabawar." Ta furta a fili, ta yi addu'a ta kunna Mp3 Suratul Baƙara na tashi a hankali tana bi. Tun tana tunani har bacci ya yi awon gaba da ita. ***   "Baƙo?" Ta furta a mamakince tana mai tsurawa Baba Maigadi idanu, tana kyautata  zaton kunnuwanta ne basu ji daidai ba. Daga ita sai hijab saman rigar baccinta wanda ta dora zani a samansa. "Nima kaina nayi mamaki Ranki ya daɗe, sai dai kuma kallo ɗaya na yi mishi uzuri." Daga haka ya juya bai ƙara dogon jawabi ko ƙarin bayani ba. Ta bi bayansa baki galala sannan ta ɗago idanunta ta dubi agogo dakyau. Bakwai da rabi da safe. 'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!' Ta furta a zuciya, Hajiya ba ta kai ga tashi ba. Itama baccin ta kasa, ta rasa ya za ta yi da ranta, babu jimawa da fitowarta falo ta ji kwankwasar Baba Maigadi, ya kuma isar da saƙo ya bar ta tsaye da mamaki da fargaba. Ta dai daure ta yi shahada ta zura silifas ta fito. Fuskarta fayau sai dai albarkacin ruwan alwala da ta yi yasa ya yi kyan gani. Ido da ido suka dubi juna, daga shi sai riga da wando na sport. Ya zura hannu cikin aljihun wando, idanun sun yi luhu-luhu hakanan sun kanƙance, gashinnan a birkice kamar yanda fuskarsa ta nuna. Ta kasa kauda idanunta kamar yanda shima ya kasa kauda nasa, kirjinta lugude yake kamar ana surfa gero. Ya tako har gabanta ya tsaya. "Me na miki? Ki fadamin laifina, kiyi hakuri." Ta lumshe ido ta bude don mamaki, sai a sannan ta samu damar magana. "Me ka yimin Hussein? Ba abinda ka yimin ni." Ya girgiza kai, ta kalleshi sau daya ta kauda idanunta da sauri. "Kin kashe waya ba ki yimin magana ba, don nace ki turon hoto? Wasa nake maki. Ki yi hakuri, na shiga rayuwarki da yawa." Ta girgiza kai, kamar yanda idanunsa ya kaɗa, haka nata ya cicciko da kwalla. "Ni wallahi ba abinda ka yimin, kuma maganar da nayi wasa ce kawai nayi ba wai da wata niyya ba. Shi ne dama ka doko sammako? Ka yi hakuri." Ya yi shiru bai daina kallonta ba. Ganin shirun ya yi yawa ta kara kallonsa. Hussein tambayar kansa yake abinda ya ruɗashi, ya hargitsa tunaninsa. Mene abin ɗaga hankali don Ramlat ta kashemasa waya? Me ya birkita kwanyarsa har bacci ya kauracewa idanunsa kamar yanda ya kasa bambance daidai ko akasinsa? Hajiya Zeenat baccinta take sharɓa ya fito, meyasa tunanin ta farka ta nemi ba'asi bai faɗomasa a rai ba sai yanzun da ganin Ramlat ya haifarmasa da sukuni da kwanciyar hankali? Sai dai kuma akwai wani duhu da ya kasa nemo haske a cikinsa, watakila sai nan gaba! Ya ayyana a ransa. "Shikenan, zan tafi. Ki gaida su Mama." Daga nan ya juya ya shige motarsa, iska da sanyin safiyar na busata, ba ta fasa kallonsa ba har ya shiga motar. Gilashin ya sauke yana kallonta, sakanni biyu zuwa uku kafin ta farga, ta juya da sauri ta faɗa gida. Ya ja motar kamar wanda kwai ya fashewa a ciki. Allah Ya taimaka Hajiya ba ta falo, da sauri ta shige dakinta ta rufe, a bakin ƙofar ta zame ta cure wuri guda, kuka ko dariya za ta yi? Ba ta sani ba, ba ta da tabbacin abinda kwakwalwarta ke kokarin hasasowa sai dai ta jera Hussein a sahun mutanen da suka san ƙima da darajar *ƊAN ADAM*. Ta sauke ajiyar numfashi tare da neman tsari daga Ubangijinta akan sharrin zuciya da saƙe-saƙenta. ***   "Daga ina kake?" Ta yi tambayar ba tare da ta bari ya ƙarasa fitowa daga cikin motar ba, ya kalleta kallon tsaf. Gabansa na faɗuwa sai dai akwai wani ƙwarin gwuiwa da yake ji na iya kallon cikin idanun Hajiyar da ɗan ƙaramin kuzari. "Bai kamata ki fito haka ba." Ya fadi a sanyaye ganin daga ita sai doguwar rigar bacci, damtsen hannun duk a waje ga tumbi da ya ɗaga rigar. Hajiya Zeenat idanunta a kaɗe, ji take kamar ta shaƙe wuyan Hussein saboda wani irin kishi da ya mamayeta. Tasan ƙarya ne a kowane yanayi mace ta ga Hussein ba ta ƙyasa ba, ta kuma sani ba zai taɓa zuwa wajen kowace mace ba musamman da safiyar fari. Amma tana son tabbatar da inda ya je don ta samarwa zuciyarta hujjar da za ta nutsu sosai. Gaba ya yi zuwa cikin gidan, ta mara mishi baya. Yana niyyar taka matattakala ta riƙe hannunsa. Ya runtse ido da sauke ajiyar zuciya alamar gajiya, bai bari ta ƙara tambaya ba ya tari numfashinta. "Wasu takardu na kaiwa Hisham. Shikenan?" Ta bishi da kallo tana mai sakin hannun, ya haye sama. Ƙarya abu ne mafi muni cikin munanan ɗabi'u, ya shiga istigfari a ƙasan zuciyarsa. A ɓangaren Hajiya Zeenat, tasan waye Hussein, ƙarya ba ta daga cikin shirginsa, don haka sai ta gasƙata amma ta soma jin tsanar Hisham a ƙoƙon ranta. Yana neman shigemata hanci da ƙudundune. Ta yi ƙwafa kawai ta bishi saman. Kwanciya ya yi ya rufe har kansa da bargo saboda bai shirya amsa wasu tambayoyin daga Hajiya Zeenat ba bayan wancan. Murmushi ya tsinci kansa da yi, murmushi sosai, Ramlat da firgicin dake kwance samam fuskarta shi ya ƙayatar da shi a yanzun. *** "Jimin ja'irar yarinya! To ba kya sonsa wa kika kawomana za ki aura? Ko an faɗamaki akwai wani cikin iyayennaki da za ki je wa da wannan magana su ɗauka?" Dada ke wadannan kalaman sadda Ramlat ta kai mata ziyara da kuma roƙonta akan a janye batun Chairman. Jin abinda ta ce Ramlat ta ɓata fuska. "Da ace kinsan waye shi da ke za ki zama farkon wacce za ta ce aa." Ta zayyanemata kaf labarin Chairman, tun Dada na faɗin toh meye a ciki? Har ta yi shiru tana gyaɗa kai. Ramlat na kaiwa aya ta dubeta. "Toh yanzu ya dace ace kun bayar da jininku ga wannan mutumin? A ma ɗauke duk wannan, bana sonsa. Ba shi da kyawawan ɗabi'un da zan kaunaceshi dominsa. Bana son na maimaita gidan jiya, abin nufi, ina gudun na saɓa umarninku a karo na biyu naga ba daidai ba." Murmushi Dada ta yi ba tare da ta furzar ba. Ta jinjina kai. "Ai shikenan, zan yi magana da shi Bellon, ya dace su yi bincike mai kyau a kansa, idan da hali ma gwara a tattara a ajiye zancensa gefe. Sai dai kuma da sharaɗin ki fiddo miji nan kusa. Da ƙananun shekarunki ba zamu zubamaki ido ki yi ta zama haka ba aure ba kuma kina yawon wurin aiki, babu ƙima da mutunci a hakan Ramlatu." Ramlat ta gyaɗa kai cikin tausayawa kanta. "Ki tayani addu'a Dada, Allah Ya zaɓamin nagari." Dada ta amsa da amin. Ta ɗora da faɗin. "Yaushe angwayen nawa zasu dawo ne?" Murmushi Ramlat ta yi, tana gyara zaman mayafinta, takanas ta biyo daga wurin aiki don ta roƙi alfarma wurin Dadar. "Ni kaina ina kewarsu, amma mun yi waya da Muhibbat ta cemin za ta je ta ɗaukosu zuwa gidanta su yi kwana biyu tukunna ta maidosu. " "Allah Ya nunamana. Za ku je Daurar?" Dada ta ƙarashe tana ɓallar goronta daidai sadda Ramlat ta dauki jakarta. "In sha Allah zamu je. Inace su Nusaiba ma duka za su je?" "In sha Allahu. Ai bikin na gida ne." Fadin Dada, a karshe suka yi sallama ta fice ba ta ko yi sallama da sauran jama'ar ba don tana jin haushinsu ganin mafi yawa na goyon bayan Chairman. Ita mamakin ma irin karɓuwar da Chairman ya yi a gidan ta yi don ko a gidansu bai samu hakan ba. ***   Tsakaninta da Hussein sai gaisuwa, ta rasa dalilin sauyawar alaƙarsu. Wani jzolaya da wasa duk ya daina. Kamar wani kalma na sabo bai taɓa ratsawa tsakaninsu ba. Wannan ya jefata damuwa, ga matsin lamba daga Chairman wanda ba dare ba rana sai ya kira. sai dai har ya kammala ringing ba ta ɗauka, idan ya dameta kuwa ta latse wayar gaba ɗayanta. Tafiyarsu Daura ta gabato har Hajiya zaa je wannan karon sai Amarya Hunainah wacce ta saki jiki da su sosai ake zumunci ba kamar Bilkisu ba wacce tun hayan auren Munir ta haɗe danginsa kaf ta jerasu layin munafukai. Wannan ne ya siyawa Hunainah daraja da ƙima ba kaɗan ba a idanun su Ramlat. Gidanta ne dai har sannan  Ramlat ɗin ba ta taka ba, ba kuma don wani abin ba. Ana gobe zasu wuce gaba daya su Rafee'ah har Hunainah mai karamin ciki sun zo cikin gidan kwana, Aisha ma ta na nan ta zo ayi sallama. Hira suke yi cike da nishaɗi ana dariya, sallamar Munir ce ta katsesu. Suka amsa ya dubi Ramlat. "Ke wancan na wajen ne Chairman din naki?" Nan da nan annashuwar Ramlat ta dauke. "Zuwa ya yi?" Ta fadi ranta a ɓace, tasan ya kira ta ƙi ɗagawa ya yi mata text akan zai zo su gaisa ta maida masa martanin ba ta buƙatar hakan. "Nikam dai bari na leƙa naga waye wannan Chairman din." Rafee'ah ke faɗi tana ƙoƙarin miƙewa. "Shi auren a igiya kika ratayeshi? Ba ki da kai fa Rafee'ah naga alama." Munir ya fadi gami da harararta. "Goɗai-goɗai da ke kina abinda ko Auta ba za ta yi ba. To ki je ki ce masa me? Ki leƙa wuta ma ko?" Dariya suka sa mata idan ka cire Ramlat da ta yi daki ranta na ƙuna. Kamar ba za ta fita ba, sai kuma ta yanke ta je kawai ta tunkare shi komai zai faru ya faru. Mayafin rigar jikinta ta yafa. Koda ta fito lokacin Hajiya na zaune. "Ke dama haka kike zuwa hirar fuska kamar baƙin tukunya?" Munir ya faɗi yana duban Ramlat da ta nufi Hajiya don sanarmata.  "Yaya Munir nidai da ka roƙarmin alfarmar mutuminnan ya bar zuwa gidannan. Na faɗamasa ya kyaleni bana sonsa wallahi." Taɓe baki Munir ya yi. "Au, wato dai gidan jiya kike neman a maimaita? Ai yanzu babu mai miki dole Ramlat, a baya ma ba'a iya anyi maki ba sai yanzu? Ta inda aka hau ai ta nan ake sauka, ki samu wadanda suka karɓi kuɗinsa." Yanda gaban Ramlat ya buga da ƙarfi, haka fuskokin Hajiya da su Zulaihat ya nuna razani da mamaki. "Me kake nufi? Kuɗin auren Ramlatun su Yaya Bello suka karɓa?" Munir ya dubi Hajiya yana mai murmushin tambayarta. "Haba Hajjaju, a karɓi kuɗin auren Ramlatu ba ki sani ba? Kawai dai yana sakarmusu bakin aljihu ana bushasha." Wani wahalallan ajiyar zuciya Ramlat ta sauke, cike da bakin ciki ta kama hanyar ficewq daga falon. Maganar su dinma sai suka bar ta anan adalilin Hunainah dake wurin, ko ba komai suna buƙatar sirri. ***   "Girman kujerarki ce tasa na jure dukkan wata shanya da kika yimin, sai dai koda na bushe ganinki ya maidani ruwa tsundum."   Murmushi yake yana ci gaba da dubanta, jinsa yake kamar wani saurayi mai shekaru talatin idan yana gabanta. Ramlat ta dubeshi a ɗaure. "Ina haɗaka da girman Allah da ManzonSa s.a.w ka fita hanyata. Kaga mu ba yara bane da za mu tsaya muna magana da maimaici. Ina za ka ji daɗin zaman aure da wacce ba ta jinka a ranta? Wane kyautatawa ka ke tunanin za ta yi gareka?" Chairman ya yi wata ƴar dariya. "Kina tunanin barazanar kisa a daren amarcinmu zai sa na sake ki? Aa Hajjaju, wannan namiji ne ba muna maza ba. Ba ki da abinda za ki faɗarmin da gaba har ya yi sanadin rushewar alaƙarmu." 'Innalillahi..' Ta kai har ƙarshensa yayinda jiri ke neman kwasarta. Dakyar ta samu ta daidaita tsayuwarta bayan ta dafe Black Camry din Chairman. Wani yawu ta haɗiya. "Me kake nufi?" Ta fadi cikin sarƙewar harshe. Chairman ya yi dariya karo na biyu. "Abun dariya, kunkuru ya yiwa busjiya ƙafa, banda abinki Ramlatu ai maganar duniya ba ta ɓuya, kin ɗauka haka kike zaune ana ganin ina neman aurenki ba'a kawomin sukarki ba? Ai ba zai yiwu ba. Kedai ayi sha'ani kawai." Shiru ya biyo baya ga idanunta sun cicciko da kwalla. "Idan ka gama zancen zan koma ciki." Chairman ya marairaice. "Haba Ramlatu, me kike gujewa a auren mutum irina mai muƙami da kuma rufin asiri? Kinsan adadin matan da ke neman irina kuwa? Da za ki ga matan da ke bina za ki cika da mamaki. Ramlatu sonki nake dagaske amma kin ƙi fahimta. Da ace na biyewa Kawunnanki da tuni an daura auren, yanzu ma abinda ya kawoni batun turowa ne suka bn iznin nayi, shi ne na zo mu kara daidaitawa kafin lokacin." Kamar wacce aka harbawa mashi, haka ta ji wani radadi a kirjinta. Daidai sadda ta ke share hawayen da ya zuba saman kuncinta ta kalleshi. "Me ka ce? Iznin ka turo fa suka yi maka?" " Kwarai kuwa, kuma kinsan dama ce da ba zan taɓa bari ta suɓucemin ba. Na zo ne don kawai na kwantar da hankalinki, ki ƙara samun nutsuwa da ni don idan har ina numfashi kina yi, babu wanda ya isa ya rabani da ke." Ranta ya ɓaci ainun. "Sai mu gani inda ake dole! Aure ne bana yi, ba zan aureka ba. Ina mai tabbatarmaka ko ka turo babu inda zancen zai ɗara." Daga nan ba ta juya ba ta ko waigo ta ji dalilin kiran da ya shiga kwalamata ba. *** "Lafiya?" Kusan lokaci guda suka jehomata tambayar ganin yanda ya faɗomusu ɗakin. Ta kasa magana sai kallo, karshe ta wuce ɗaki. Ganin haka Munir ya mike ya fita waje, Chairman ya shige abin hawa har ya fice. Ya dawo ciki ya sanar da su ya tafi. Gaba daya suka bita dakin idan ka ɗauke Hajiya da Munir da suka faɗa tattaunawa game da lamarin Ramlatun. "Ai mafita fa a wajen su Kawu shi ne kawai ta nemo wani ta kai musu. Yanzun bata da abinda zai kwace ta a hannunsu. Su gani suke sun kama dami a akala. Rannan ma na shiga gidan na tarar Malam (Kawu Rabe) yana ta rubutu, wai mai neman auren Ramlatun yake rubutawa na tsarin jiki. Kinga kuwa ba karamin kamu suka yi mishi ba, fahimtar da su barin aurennan sai da taimakon Allah." Hajiya ta yi salati. Tana mamakin ƴan uwannata, idan kuma ta tuna wasu abubuwan da suka wanzu a baya na irin rashin jituwarsu a wasu lokutan matsayinsu na ƴan uba, sai ta ga fiye da hakan ma zai iya afkuwa. Haɗin kan ma da yanzun ake yi da iyalinta tasan bai je koina ba. Yaransu dai gashinan sun fi su hankali. "Biri ya yi kama da mutum, Allah Ya kyauta." Ta furta a fili ranta na zafi. Munir ya amsa da amin. ***   A bangaren Ramlat kuwa, daga Zulaihat har Rafee'ah zagin Chairman suke su na ƙarawa. Hunainah dai tausayin Ramlat ta ke ji sosai. "Kema kin so hakan ta faru, ai kinsan babu yanda za'ayi a zubamaki ido. Ruwan ido ne ko me? Don ba za ki ce ba ki da manema ba. Korarsu kike kin ƙi ba kowa fuskar fitowa, daga samarin har masu auren da dattijai. Ai gashinan ana neman yi miki bita da ƙulli." Fadin Rafee'ah dake jin kamar ta shaƙe Ramlat tsabar takaici. Ta furzar da bacin ran ta hanyar dakawa ɗiyarta Daddy  tsawa ganin kokawar da suke da kanwarsa Afrah. "Uhum, kema dai Rafee'ah kya faɗa. Ai tunda haka ta zaɓa sai ta zauna a cuceta. Koda dai watakila za ta iya tunda ba yau farau ba." "Ba yau farau ba? Meyasa abinda ya wuce ba za ku bar tayarwa ba? Meyasa ku ka riƙi abinda na aikata ku ka kasa yimin uzurin kasancewata cikin ajizai kamar ku?" Ramlat ta furta da duban Zulaihat. Su kansu ba wai da wata niyyar abin ke tasomusu ba, sai dai a lokuta irin haka idan ta ƙona ransu, takan motsa musu da abinda ya wuce ɗin. "Anti Hunainah ki zo inji Uncle." Daddy wanda ya fita ya shigo yana faɗi iyakar ƙarfinsa. Hunainah ta miƙe ta fita don yin sallama da mijinta. "Har maganar ta kai ku kasa dannewa a gaban Hunainah?" Cikin karyewar zuciya Ramlat ta furta. "Hum ai shikenan. Allah Ya kyauta." Rafee'ah ta faɗi tana mai miƙewa ta fice daga ɗakin. Sosai Zulaihat ta fuskanci ƙanwarta. "Ya kamata ki nutsu ki yiwa kanki faɗa Ramlat. Ke ba yarinya ba ce, kin taɓa aure kin kuma hayayyafa, ba girmanki bane a soma ƙirgamaki aure wannan ne yasa gwara ki watsar da komai ki fuskanci rayuwa tun lokaci ya ƙuremaki. Da ki yi auren jeka na yi ka, gwara ki dau dogon lokaci ki auri wanda za ki zauna da shi har mutuwa ku rayu. Idan har ba ki tsaida wani kin kawo matsayin miji ba, kina ji kina gani za'a ɗaura aurenki da wanda ki ke gujewa. Na fadamaki ki nutsu ki san me kike. Ki kuma haɗa da addu'a, za mu tayaki." Ramlat ta gyada kai tana jin wani sassauci na ratsa zuciyarta. Zulaihat ta fita ta bar ta anan zaune. Shiru ta yi tana mai ƙurawa hannunta da ya sha lalle idanu, mutuwa mai tonon silili. Hakan ta ayyana yayinda hawaye nta suka soma ɗiga. *** Tafe yake cikin shiga ta alfarma, a gefensa Hajiya Zeenatu ce tana zabga uban murmushi. Hannuwansu sarƙe cikin juna. "Husseini!" Ya ji wata murya ta kwalamasa kira, kusan lokaci guda suka juya shi da Hajiya Zeenat. A fuskar Hajiya Zeenatu, tashin hankali ne tsagwaronsa, idan ka ɗauke Hussein wanda idanunsa suka kaɗa suka yi jazur. Damƙe hannunsa da Hajiya Zeenatu ta ƙara ya sanyashi dubanta a hargitse. "Husseini kai ne?!" Ya juya ga matar da ke tsaye tana dubansa dakyau.       I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/i7Akdw4Ovcb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 43) _*Tafe yake cikin shiga ta alfarma, a gefensa Hajiya Zeenatu ce tana zabga uban murmushi. Hannuwansu sarƙe cikin juna.*_ _*"Husseini!" Ya ji wata murya ta kwalamasa kira, kusan lokaci guda suka juya shi da Hajiya Zeenat. A fuskar Hajiya Zeenatu, tashin hankali ne tsagwaronsa, idan ka ɗauke  Hussein wanda idanunsa suka kaɗa suka yi jazur. Damƙe hannunsa da Hajiya Zeenatu ta ƙara ya sanyashi dubanta a hargitse.*_ _*"Husseini kai ne?!" Ya juya ga matar da ke tsaye tana dubansa dakyau.*_ _*"Kar ka je gareta! Zo mu tafi!"*_ _*Hajiya Zeenatu ta furta iyakar karfinta. Matar na jin haka ta taho gadan-gadan da zummar nufar Hussein kai tsaye tana fadin.*_ _*"Ni ce Husseini! Dadarka ce! Ka manta ni?"*_ _*Ba ta kai ga ƙarasawa ba ta ci uban tuntuɓe za ta faɗi. Sai dai caraf aka riƙeta. Hussein ya dubi mai shi, mace ce cikin fararen kaya. Daidai sadda Hajiya Zeenatu ta soma jan hannunsa, hawaye yake fitarwa yana dubansu da wacce bai san ko wacece ba. Caraf aka riƙe hannunsa, dole suka tsaya cak.  Fuskar Ramlat ya gani na wani haske da kyalli, murmushi ta ke yi madadin kukan da Dada da kuma shi suke yi, ta ɗago hannunsa ta sanya a cikin na Dada ta matse su.*_ _*"Har abada babu wani ko wata da zai ƙara shiga tsakaninku."*_ _*"Ƙarya kike!" Hajiya Zeenatu ta furta tana ihu.*_   *** "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Ya furta a fili yana maida numfashi kamar wanda ya yi tsere, jikinsa gumi yake fitarwa duk kuwa da sanyin da ke a ɗakin. Kirjinsa bugu yake da sauri-sauri. Ya kai duba ga makwancin Hajiya Zeenatu. Bacci take ta lulluɓe har kai da bargo. A hankali ya dauki wayarsa a gefen gado ya kalli agogo, biyar saura mintuna, tabbacin Asuba ce. Don haka ya mike yana juyayin mafarkinsa. 'Dada?' Ya maimaita a zuciyarsa yana juya sunan, yana da wata mai suna Dada? Kuma a ina? Tunani ya yi mishi yawa har ya ɗaura alwala ya fito, kansa wani irin sarawa ya ke. Me mafarkinsa ke nufi? Ramlat ya gani, ihun kuma da Zeenatu ta yi na menene? Babu mai amsa masa, wannan tasa ya  fice daga dakin zuwa falo gami da shimfida darduma ya yi nafila. Bayan idarwa ya yi addu'a. Masallaci zai fita, don haka sai ya koma dakin ya tashi Hajiya Zeenat sannan ya fita. Ta bishi da kallo har ya fice sannan ta ja tsaki tana miƙa, ta lura da wani ustazanci da ya soma. Sallah a masallaci ya daina wuce shi, ita dai tana jin tsoron ibadar da ya soma maida hankali a kai. Ko ba komai ai ta sani wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Ƙarfin ikon Allah da addu'a ya shallake dukkan ƙarfin mai ƙarfi.   Jiki a sanyaye ta miƙe tana tunanin mafita. 'Ku bar ƙasar zuwa wata ƙasar kawai!' Wani ɓangare na zuciyarta ya shawarceta. Sai dai tana tunanin ta yanda za ta sa Hussein ya amince da wannan shawarar da tun ba yau ba ta ke ƙoƙari a kai. ***   Misalin shida na safe, iyalan gidan Alhaji Khalid Mu'azzam sun fito fess sun sha wanka har da yaransu idan ka dauke Ramlat da nata yaran ke gidan Muhibbat. Dalilin yaran ne Ramlat ta yi ƴan soye-soye na snacks da zasu ci a hanya. Ta sha adon doguwar rigar atamfa kalar ruwan toka da sirkin ja da yellow an mata dinkin Bubu. Ta ɗora ƙaramin mayafi kalar ja a samansa. Murmushi ta ke sai dai iyakarsa leɓɓanta bai kai ga shiga zuciyar ba. Tunani goma da ashirin take duk ita daya, rayuwar yaranta, auren Chairman, soyayyar Hussein da ta ke ji kamar Son Maso Wani ta ke yi kawai. Wannan ne yasa da safe ta tashi idanun ƙozai-ƙozai shaidar bacci bai wadaceta ba. Bayan sun ɗuru a motar da Munir yasa aka hayo musu ta kasuwa, tana daga can baya tare da yara sai Hunainah a ɗayan gefen. Ta bude whatsapp, ta gwada yiwa Hussein sallama sannan ta sanarmasa da tafiyar da za ta yi zuwa Daura. Daga nan ta sauka online ta kira Amrah suka ƙara sallama. Ba ta son yi mishi text gudun kada ya faɗa hannun Hajiya Zeenat. 'Koda shi ne abu na ƙarshe da zan maka, in sha Allah zan yi Hussein. Zan sulhuntaka da ƴan uwanka.' Abu na farko da ya faɗo ranta bayan wannan tunani, shi ne Kawunsa da aka ce yana zama a Kano. Da dabara za ta nemi cikakken sunansa a wurin Hafsat, sauƙinta ma unguwarsu ɗaya da kakanninta (Hajja). Ta toshe kunnuwanta da earpiece tana sauraron Suratul Maryam tana bi a hankali idanunta a lumshe. Wakokin soyayya ba ta da muradinsu a lokacin kasancewar ba karamin ingiza zuciyarta suke yi ba akan Hussein. Tafiya ta yi nisa, shiru na ƴan sakanni, karatun ya tsaya, ta duba. Kira ne daga Hussein. Kirjinta ya bada dam! Ta ɗaga ta yi sallama a hankali tana mai satar kallon su Hajiya, hirarsu suke yi na dangi yayinda Hunainah ta rufe kanta da mayafi alamun bacci ya ɗauketa ko zai ɗauka, ba ta da tabbaci. "Tafiya ba sallama? Ba ki faɗamin ba sai yau?" Daga yanda ya yi furucin za ka fahimci ɓacin ransa. Daƙyar ta iya motsa leɓɓan. "Ka yi hakuri." Shiru ya biyo bayan can kuma ya sauke ajiyar zuciya. "Naso yau na ganki." Ta yi luum da idanu, ta kasa yarda da abinda kunnuwanta suka jiyemata. "Uhm?" Ta nemi ba'asi. "Hoton zan karɓa ta ƙarfi tunda an hana ni." Ya faɗi a shagwaɓance, ya sanyata murmushi tana mai sunkuyar da kai kamar yana gabanta. "Zan turomaka." "Promise?" "Yes." "Kinsan hoto ɗaya rowa ce ko?" Ta ƙara faɗaɗa murmushinta. "Uku fa?" Tana jin sautin murmushinsa. Can ya amsa. "Thanks. Allah Ya kaiku lafiya." Bai jira amsarta ba ya katse kiran, karatun ya ci gaba. Kaso saba'in na damuwarta ya ragu, ta ji wani kwarin gwuiwa. Nan da nan ta shiga Gallery dinta ta hau kallon hotuna. Duk wanda ta ga shi ya dace ta aika sai ta ga kamar bai kai ba. Ruwan ido, abinda ta tsana ta ke jin haushi a wurin Amrah, ita ce yau ta ke yinsa. Dakyar ta haƙura ta zaɓi wasu guda uku ta aika kasancewar da network a wurin da suke nan da nan ya je, ba ta jira godiyar ba ta sanya wayar a Airplanemode tana murmushi.   Koda suka isa yan uwan sun sha mamakin sauyawarta. Ƙofar Baaru kusa da gidan Sarkin Daura, nan ne ainahin gidan iyaye da kakannin su Abba da Hajiya yake. Gida ne babba na gandu, zaman iyaye da ƴaƴa. Sun tarar da su Nusaiba mutan Kano duk an hallara. Hajja da abokiyar zamanta ma suna nan. Gida ya cika da ƴan uwa gwanin dadi. Sashen Ƙanin Malam Abdullahi kakanta nan ta yada zango wurin su Nusaiba sa'anninta, don ba ta kaunar zama da su Rafee'ah, zancen dai daya ne, na Chairman. Ta fiddo miji ta gujewa aurensa. Karshe ta watsar da duk wani tunani ta rage sutura ta shiga wanka. Bayan ta fito ta tarar su Nusaiba gaba daya na zaune ana kari da doya da kwai da shayi wanda ya ji citta da kanumfari. "Ke kuwa Ramlatu yaushe za mu sha naki bikin?" Ta yi kamar ba ta ji maganar Gwaggo Hansai ba, ta ci gaba da goge ruwan jikinta.  Ba ta ce uffan ba. Duka Dije kanwar Gwaggo Hansai din ta kai mata bakinta cunkushe da burodi. "Ja'ira, ai tana jinki. Ta fi kaunar muje ana daurin aure ta dawomana. Maimaita tarihi ko? Toh dagaske banni ƙara zuwa bikinta." Aka yi dariya don an san zolaya ce ta Dije, ita dai Ramlat ta kara tamkewa ta mike ta kwashi kayanta, ta fasa shirin a falo, ta koma uwar ɗaka. *** Kamar wanda aka daskarar da jinin jikinsa haka ya yi ɗif, a hankali ya sauke ƙarfen da  ke hannunsa yana maida numfashi, gumi kam kamar ruwa haka yake ɗiga daga cikin gashinsa, saman fuska har zuwa jikinsa. Kallon Hisham ya ke yi da wani irin faɗuwar gaba. Hisham ya toshe kunnuwansa da earpiece yana gyada kai alamun waƙar da yake ji na tsumashi sai dai kacokam hankalin yana ga Hussein. Yana sane ya fesamasa batun auren Chairman da Ramlat duk kuwa da cewar yasan maganar rawa take yi ba ta tabbata ba. Amma ɗan hakin da ka raina ai shi ke tsonemaka ido. Gwara tun wuri ya yiwa abin tufka, ko ba komai zai ƙara karantar inda Amininnasa ya dosa. Tasowar ta Hussein, da kuma fisge Earpiece din daga kunnensa duka-duka abin ya zamewa Hisham kamar kiftawar idanu. Ya haɗiye dariyarsa ya kara daure fuska. "Lafiya Malam? Me ya yi zafi? Daga cewa Chairman Aliyu Dikko zai au.." "Kar ka ƙarasa." Ya fadi a kausashe yana nunashi da yatsa idanun sun kaɗa cike da wani irin matsanancin kishin da bai san mafarinsa ba. Hisham ya cika da mamaki don bai zaci abin zai kai haka ba. A hankali Hussein ya zauna a gefensa ya yi shiru, can kuma ya dubeshi a sanyaye. "Wasa ka ke yi, sai dai irin wannan ba maganar wasa ba ce. Please kar ka ƙara." Hisham ya karkace yana dubansa. "Don me? Toh kai mene naka ciki? Me zai dameka? Menene haɗin biri da gada?" Ran Hussein ya yi tsananin ɓaci. "Ni ka ke kira biri? Hisham har wuyanka ya kai tsaikon da za ka haɗani da biri?" Dariyar Hisham ta kasa ɓoyuwa, lallai ya ƙara yarda Hussein bai iya Hausar ba. Dariyar ta kara fusata Hussein wanda dagaske ya ji zafin birin da Hisham ya ambata. Abin ya haɗemishi biyu don haka ya mike ya dauki jakarsa don suturta jiki. Hisham ya bishi da kallo yana mai ba shi tausayi. A yanzu ba shi da abar kauna sai Ramlat, sai dai ya rasa dalilin abokinnasa na ƙin ba wa zuciyarsa abincinta. Ko a ɗazun, kasancewar Hussein ya  rigashi zuwa wurin motsa jikin, kama shi ya yi dumu-dumu da hoton Ramlat din yana kallo yana murmushi. Ganinsa ya wartsake ya sanya wa wayar muƙulli. Yana nan zaune ya fito, madadin gajeran wando, ya sanya dogo mai santsi fari ƙal mai haɗe da riga. Ya sanya baƙin gilashi yanda idanun suka ɓuya. "Sai Allah Ya kaimu." Ya furta can ƙasan maƙogwaro yana duban Hisham din a fisge. Hisham ya rike hannunsa. "Haba abokina, ka yi hakuri idan ɓacin ran da na jefaka ya kai girman haka. Karin magana na yi maka, haka Bahaushe ke karin maganarsa. Ba wai da gayya na haɗaka da dabba mafi muni ba." Hussein ya sa hannu ya dan ja karan hancinsa kaɗan yana duban gefe. "Wani abu na ƙara faɗi?" Hisham ya dubeshi dakyau. "Ba ka faɗa ba, amma ba haka muka saba sallama ba. Mafi yawan lokuta tare muke fita. Yau kuma ba alamar za ka jirani." Guntun tsaki Hussein ya ja. "Sauri nake." Ya furta kai tsaye har da duban agogonsa kalar silver. "Karin maganar ce ko damuwar Ramlatu ce?" Ya ji tambayar Hisham kamar daga sama, shiru ma mintuna kafin ya dubi Hisham ta cikin gilashin. "Abinda ka fadi gaskiya ne?" Yanda ya yi maganar a sanyaye, sai hakan ya sanyaya jikin Hisham. Shirun da ya yi, Hussein ya samu amsarsa. "Sai da safe." Daga fadin haka  ya yi gaba. Murmushi Hisham ya dan yi. Shakka babu da Ramlatu za ta samu Hussein ba karamin farin ciki zai mata ba. Yana matukar son ganinsu tare sai dai kuma sanin tarihin Ramlatun kan sanyaya masa jiki. Anya Hussein zai gan ta da gashi? ***  _*Nan kusa za'a yi bikin Ramlat da Chairman Aliyu Dikko don na ji labarin zai kai kuɗi.*_ Wannan kalaman ke yawo a kwanyarsa har ya hanashi maida hankali ga tuƙin da ya ke yi. Dole ya gangara gefen titi ya kashe wayar ya kwantar da kai bayan kujera. Runtse idanu ya yi na ƴan mintoci kafin daga bisani ya ƙara fiddo waya ya buɗe hotunan Ramlat yana ƙaremusu kallo. Saura ƙiris ta zama mallakin Chairman yana nufin abubuwa da dama. Shugabanta wurin aiki, wanda ya fi shi kudi da muƙami, wannan na nuna kwaɗayi ƙarara. Hira da ita da ma kallon hotunan har da ganinta a zahiri zai zama haram a gareshi, wannan ma wata damuwar ce mai zaman kanta. Ransa idan ya yi dubu to ya ɓaci, kirjinsa zafi yake. Mafarkinsa na ƙara yawo a kwanyarsa, gaba daya ya hargitse lokaci guda. Ya tuna abu daya kwakkwara da ya danganci rayuwarsa ya kasa. Neman haske cikin duhu yake amma abin ya gagara. Koda ya tsananta tunani, kansa ya ci gaba da sarawa da ƙarfi, cikin dauriya ya kai hannu ya kunna CD na karatun  Al-kur'ani da ke kan rediyon. A hankali ya soma samun nutsuwar zuci da na gangar jiki, ɗif, sai ya nemi yanayin ya rasa. Wannan kadai ya tabbatar da zargin da ya sha yiwa kansa a baya, wato ba shi da lafiya, kuma ya zamar mishi dole ya ga likita. Ya kwashe mintuna biyar a wajen yana kallon motocin da ke safa da marwa kafin daga bisani ya ci gaba da tuƙinsa. ***   BAYAN KWANAKI UKU..   ADAMAWA Tun fitowarta daga ɗakin ta ke ƙunƙuni tana zuba abincin zuciyarta na tuƙuƙi ga wani ƙololon abu dabya tokaremata ƙahon zuciya. Tahir kallonta yake kamar ya haɗiye, nan duniya ba ya jin akwai wacce zai so sama da Hafsat. Aure ne yana ji a jikinsa tamkar an yi an gama. "Kin yi kyau." Ya faɗi kamar mai raɗa bayan ya ƙaremata kallo cikin  riga da siket din jikinta na Atamfa. Harara ta watsamasa, ba don ta so ba ta dawo gidan don a farko tattarawa ta yi ta koma gidam AlHassan da zama. Ya yi murmushi madadin hararar ta ƙona ransa, wannan ya ƙara ba Hafsat haushi, ta ja tsaki. Ita kuwa Dada ta ci gaba da hirarta da Tahir ranta na mata wani irin dadi. Kusan yanzun ta saba da shi sosai don kamar ba yaron da a baya ya ke wucesu kerere babu ko gaisuwa ba. Ta kuma ƙara fahimtar ɗabi'un yaron, jikinta na ba ta cewar duk wani mugayen halayensa akan waɗanda ba ya so ya ƙare. Kuma zuga ce kawai. "Dada anya ba nan zan dawo da zama na dindindin ba?" Ya fadi yana mai kallon Hafsat, ta dubeshi da sauri, ya kashemata ido ɗaya, ta mike sadda Dada ke ba shi goyon bayan maganarsa fuskarta a sake. Ya yi daidai da sallamar AlHassan. Suka amsa, Tahir ya gaisheshi, ya amsa a ɗan sake don yaron ya soma ɗan sakin jiki da shi, ya fahimci koda yana da matsalar, a yanzun ta kau. "Ke kuma zo dama ina nemanki." Muryar AlHassan ya katse Hafsat daga tafiyar da ta soma. Ta ji kamar ta sa ihu, Tahir kam ransa ya ƙara fari ƙal sadda ya soma kai lomar abincin da ta girka da hannunta. Ta dawo ta zauna ta gaidashi kamar ta yi kuka. AlHassan ya murmusa don yasan kanun zancen. "Jiya ina kika je? Na zo ance kin fita." Ta ɗan tura baki. "Gidan su Iklima na je." Ya ɗan ɗaure fuska. "Kuma ai na hanaki zumuncin da yarinyar ko kin manta?" "Ka yi hakuri." Ta faɗi a ƙagauce don Allah-Allah ta ke yi ta shiga ciki don tserewa kallon da Tahir ke mata. "Shikenan, je ki." Ya ba ta umarni lura da ya yi har sannan babu wata shaƙuwa tsakaninta da yaron. Shima ya fi kaunar hakan ko don gudun abinda zai je ya zo. Wayarsa ta yi ƙara, ya duba, Rasheed ne daga Saudia. Ya ɗaga suka gaisa a mutunce. "Ina ta so na kiraka sai dai Allah bai ban iko ba sai yanzu. Ya su Dada?" Alhassan ya murmusa. "Alhamdulillah, gamunan duka lafiya. Nima rashin lambarka ne ya sa na hakura. Fatan ka iske mutan gidan lafiya?" "Duka kowa lafiya. Akan Hussein ne nayi kiranka. Na tuna wani abu." Jin haka AlHassan ya miƙe da sauri har Dada da Tahir na binsa da kallo. "Lafiya?" Dada ta tambaya. Ya ɗan dubesu. "Babu komai Dada, bari na amsa waya ina zuwa." Daga nan ya fita waje da sauri-saurinsa. Hannunsa har rawa ya ke yi. "Ina jinka Rasheed, me ka tuna?" Rasheed ya ba shi labarin kaf abinda ya faru a ranar da suka yi bikin kammala makarantarsu a DUBAI shi da Hussein. Bai ɓoyemishi wani labari da Hussein ya ba shi ba a ranar har suke dariya. Safa da marwa AlHassan ya fara gami da dafe goshi. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!Meyasa ban tuna da hakan ba? Meyasa muka kasa tunawa da cewar itama za ta aikata?!" Rasheed ya amsa. "Nima ban tuna da lamarinta ba sai yanzun da Mamina ta ankarar da ni!" Cikim gigicewa AlHassan ya ƙara jefamasa tambaya. "Maminka? Ta santa?" "Eh ta san ta, farin sani ma! Zan tambayi dukkan wani bayani game da ita zuwa safiyarku zan kiraka, ina ji a jikina ɓatan Hussein nada alaƙa da ita. Mu binciki inda take don mu tabbatar." Gumi sosai AlHassan ke yi, kirjinsa na bugu da ƙarfi. Ya dafe goshi karo na biyu. "Please kar ka ɓata lokaci Rasheed." Ya fadi kamar zai yi kuka. "Na damu da Hussein, na daukeshi dan uwa ba aboki ba. In sha Allahu komai zai zo karshe. " Jinjina kai AlHassan ya yi cikin son gasƙata hakan. Daga bisani suka yi sallama. "Meyasa ban tuna da ita ba?!" Ya fadi a fili zuciyarsa na wani zafi. Kamar faifan bidiyo haka komai ya shiga dawomasa filla-filla. Ya runtse idanu yana addu'ar neman dacewa. ***   DAURA.. Idan Ramlat ta ce bikin ya yi mata dadi toh fa ƙarya ce kawai saboda kusan faɗa iyayen aka yi game da aurenta da Chairman wanda ba su da labarin zuwansa har Daura gaida tsoffin sai a sannan. Hankalinta da na yayyun ya tashi. "Wato dai Chairman makircinnasa ya kai inda ya kai!" Cewar Sauda bayan sun gama sauraron labarin Chairman daga bakin Ramlat. "Mtsw, iyayenmu ne abin duniya yanzu sai ya rufemusu ido wallahi, daga ƙin gaskiya sai  ɓata fa. Yanzu idan aka bari kika aureshi mene makomarki? Nikam gaskiya ke na fi jin haushi ma wallahi Ramlat, kiyi hakuri kinsan ban iya ɓoye abinda ke raina ba. Amma kefa bazawara ce, ta ya ya kuma ta ina za ki zauna a tauye hakkinki? Kamar ba ke ce kika jajirce a baya har kika auri wanda ranki ke so ba?" Naja ta fadi ranta na ƙuna, Ramlat dai dubansu take kowa da irin kalar ƙorafinsa. Zagi kam Chairman ya sha. Tsam! Ta miƙe ta fita dama hijab ne a jikinta, tana ji suna kiranta da tambayar ko haushinsu ta ji amma ba ta ko iya waigowa ba. Kai tsaye ɗakin Malam Yahaya tsoho mai ran ƙarfe, cikin maza shi ɗaya tilo ya yi saura a ɓangare iyayen su Abba, wato Malam Abdullahi, Mu'azzam da ma sauransu. da suka rasu. Yana zaune yana shan fura ga rediyonsa a kusa, sallamarta ya dauki hankalinsa, ya amsa ta karasa ta zauna. "Wace ce ne? Ko Uwani ce?" Ya tambaya yana kakkanne idanu don ba kasafai ya ke gane mutane ba. Bakin har rawa yake ta amsa   "Malam ni ce, Ramlatu." Ya yi ƴar dariya. "Ki ce Amaryar Dikko ce. Ince dai lafiya?" Kiranta Amaryar Dikko ya ɓata ranta ainun, ta haɗiyi miyau mai ɗaci. Idanunta sula cicciko da kwalla. "Malam don Allah ka taimakamin, kai kadai za ka yiwa su Kawu Bello magana su ji. Wallahi bana son Dikko, don Allah ku ban lokaci na muku alƙawarin kawomaku wanda zan aura nan kusa da yardar Allah." "Wane magana kike yi haka Ramlatu? Abinda ki ka aikata a baya ne kike kokarin maimaita shi a yanzun? Ki fita idona wallahi! Ni ba ubanki ba ne da kika raina." Zuciyarta ta yi wani irin nauyi, ta kasa daurewa sai da hawayen suka zubo. Wannan baƙin fentin da ta gogawa kanta ba ta san sadda zai gogu har yan uwa su yi mata kallon mutum mai ƙima ba. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta zayyanemishi duk wasu munanan ɗabi'un Chairman da ta sani. Ya yi shiru yana saurare har ta kai aya. Shiru ya biyo baya kafin ya jinjina kai. "Shikenan, zan wakilta Iro  (babban ɗansa) ya bincikamin a can Kanon. Idan har babu ɓurɓushin gaskiya game da abinda kika faɗa lallai ki sani, ni da kaina  zan ɗaura aurenki da mutuminnan." Ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin dama-dama. Kusan tun zuwanta banda Gwaggo Hansai da ta fahimceta da ɗaiɗaiku cikin gwaggonnin nata, sai yanzu ta samu nutsuwar da ba ta ji ba. Ga zafin Hussein ba ta ƙara magana da Hussein ba yau kwana huɗu kenan da zuwanta garin. A sanyaye ta mike ta fita, kiciɓus suka yi da Harira ɗiyar Amaryar Kawu Bello ta biyu, dagaske laɓe ta yi a zauren. Sai dai ta wayance. "Af, ke ce a ciki? Dama abincin Malam ne Gwaggo ta ce na miƙa." Ta gyadamata kai kawai ta yi gaba. Ta rantse dai ba ta auren Chairman. Don haka za ta bi ta salama ta san yanda akai ta rabu da shi. A baya ta yi tunanin za ta iya hakurin zama da shi ko ba so, sai dai yanzun da so da kaunar Hussein ke ƙara ruruwa a zuciyarta, ba ta jin ko kusa za ta iya. Allah-Allah ta ke yi su koma Kano don tuni ta samu cikakken sunan Kawun su Hussein dake Kano a wurin Hafsat. Dabara ta yi mata da cewar ta shiga Yakasan ta ga wata mai kama da ita. A haka har ta gangaro inda Hafsat ta yi mata bayanin cikakken sunan Kawunnasu. Babban burinta ta koma Kano ta je ta sameshi. Ta fi kaunar bin komai daki-daki.   Maimakon ta koma ɗakin, sai ta wuce sashin surukar Malam, matar Iro, Hajara, anan ta yi zamanta tana danna waya. Muhibbat ta kira suka gaisa sannan ta haɗata da su Ansar da Ummi aka gaisa. Ba karamin kewar yarannata ta yi ba, ta yi musu albishir na dawowarsu a gobe. Saƙo ta ga ya shigo, saƙon daga AlHassan, ta mike zaune da azama ta shiga whatsapp. *"Ƙanwata, kinsan wata Hajiya Zeenatu Bashir a Kano? Ta taɓa zaman Saudiyya, kuma tana taɓa siyasa a baya. Yanzu dai ban da masaniyar komai a kanta."* Dafe kirji ta yi. Shikenan duk yanda aka yi NESA CE TA MATSO KUSA!      I just published "BABI NA ARBA'IN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/LUjPZHlQycb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 44) _*"Eh na san ta."*_ Har ta rubuta hakan, sai ta goge da sauri. Toh idan ta ce ta san ta kai tsaye me ta yi kenan? Girgiza kai ta yi. Shiru ta yi na  ƴan sakanni ba zato wayarta ta shiga ringing. Ta duba, AlHassan ne. Ta danna gami da karawa a kunne. Dakyar ya samu nutsuwar amsa sallamarta. "Kin buɗe saƙona ba ki ce komai ba. Kin san ta?" Ramlat ta sauke numfashi. "Ka yu hakuri sai dai magana ce mai tsawo da ba za ta yiwu ta waya ba, yaushe za ka samu shigowa Kano?" "Ko gobe ne zan iya tahowa Ramlat. Ki amsamin da kin san ta ko aa." Ganin irin ruɗanin da muryarsa ta nuna, yasa ta saurin amsa mishi. "Na san ta. Har abinda ba ka zato duk na sani, idan da dama gobe.." "Kar ki damu, gobe in sha Allah zan zo Kano." Ya katse hanzarinta da gaggawa. Ta amsa da toh, godiya ya yi mata ya katse kiran. Abu na farko da ya daurewa Ramlat kai, ta yaya Hussein ya gane zai iya samun wani bayani ta hanyarta? Sannan a ina ya san sunan Hajiya Zeenatu? Wannan tambayar babu mai amsamata sai shi da kansa don haka ya haɗiye abinta. Ta shiga zullumi ba kaɗan ba, ganin ta kasa danne abin, kawai sai ta kira Hisham. "Ran Amarya ya daɗe." Ta ja guntun tsaki, Hisham tun sadda ya ji labarin Chairman ya ke zolayarta. "Ba wannan ba please, magana ce da ta shafi Hussein." Jin haka sai ya maida hankali. Ta ba shi labarin yanda suka yi da AlHassan har da ƙudurinta na zuwa ganin Kawun Hussein dake zaune a Kano "Da mamaki ace mutumin dake zaune cikin ƙwaryar Kano ya kasa sanin akwai wani jininsa a Kanon. Sai dai ban san irin raunin alaƙar dake tsakaninsu ba. Ina goyon bayan ki gwada zuwa ki sameshi. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ta ya ya Hussein zai soma fuskantar lamarin? Anya ba kuskure ba ne kai tsaye AlHassan ya tunkareshi ba?" Ramlat ta jinjina kai. "Shiyasa nake son zuwa na faɗawa Kawunnasu. Idan ma ya sani ka ga za mu sani, amma ba na jin zai sani. Haba, ɗan uwansu fa." "Hum, shikenan Ramlat. Allah Ya maidoku lafiya. Ya ɗora mu a kansu." Ta amsa da amin kafin ya ba Aisha wayar suka gaisa da taɓa hirar Daura daga bisani suka yi sallama. *** WASHEGARI... *LAMIƊO CRESCENT* "Na yarda, wace ƙasar ki ka zaɓa mana?" Mamakin amsar Hussein ya daskarar da Hajiya Zeenatu lokaci guda, ta ƙara matse layar hannunta domin ta yi imanin shi ne dalilin da yasa ya yi amanna da zancenta. 'Allah Ya yi maki albarka Hajiya Batool aminiyar kwarai.' Ta fadi a ƙasan ranta bayan ta tuno shawararta ta bi ta je wurin Bokansu ta karɓo layar. Farr ta yi da ido baki yaƙi rufuwa tana duban Hussein da rabin hankalinsa ke kan Laptop ɗinsa yana shigar da wasu takardu don son kauda damuwar da ke sukarsa a ƙirji. "London nake son mu je, ka ga daga nan sai a binciki lafiyata sosai akan matsalar haihuwa. Kana iya ɗaukar annual leave." Ta fadi cikin dabara tana mai kissimawa a ranta shikenan Hussein ya yi bankwana da Nijeriya har abada. Ba tare da ya kalleta ba ya amsa a gaggauce. "Ki yi duk yanda ki ka so." Yana kaiwa nan ya miƙe ya nufi sama. Ba ta dakatar da shi ba don ita fa ya gama biyanta. Da wani irin farin ciki ta kira Hajiya Batool ta fesamata. Dariya suka yi lokaci guda. "Habawa! Wa ya faɗamasa Borno gabas ta ke? Ai wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa." Cikin nishaɗi Hajiya Zeenatu ta gyara zama. "Allah Ya barmin aminiyar kwarai. Yanzu ki yiwa ɗanmu magana ina so ya yimin duk wani shiri na tafiya." Suka yi dariya sannan suka ci gaba da ƙulla-ƙullarsu. *** Kasa zama ya yi sai kwanciya, kwanciyar ma bai fi minti uku ba ya miƙe zaune gami da dafe kai. A hayyacinsa ya amincewa Hajiya Zeenatu, gani yake nisan da zai yi daga gareta shi zai sa ya mance da dukkan lamuranta. Hisham ba zai yi ƙarya ba don ya baƙanta ransa hakanan kawai, a farko yana mata kallon wata halitta ɗaya tallin tal da ta dakatar da shi daga biyewa Hajiya Zeenatu tun farko akan su bar garin, yau kam har Ƙasar ya amince su bari idan hakan zai ba shi farin ciki. Zai nisantashi da ita kuma ya yaye damuwarsa. To wa ya ke da shi da zai damu? Ba shi da uwa bare uba, ba danginsa babu na Hajiya Zeenatu. Wannan abu sau da dama kan ɗauremasa kai matuƙa kuma ya jefashi cikin tafkin tunani iri-iri. Nan da nan farar fuskarsa ta yi ja kamar yanda idanun suka kaɗa. Ya riƙe kansa da ke sarawa da ƙarfi yana salati. Tun yana gani daidai har ya dawo gani dishi-dishi. Ya yi kokarin mikewa tsaye sai ji kake tim! Ya fadi. Ta turo ƙofar ta shigo ranta fari sol bayan kammala wayarta da Hajiya Batool. Turus ta yi ganin Hussein a ƙasa. Wani ƙara ta saki kafin da sauri ta nufeshi. "Hussein! Hussein?!" Babu alamar zai motsa, don haka ta dauko ruwa ta yayyafa, nan ma shiru. Ganin haka ta yi wurgi da robar ruwan ya malale a kafet ta fita daga dakin. "John! John! Ola!" Kusan lokaci guda ma'aikatan dake kicin har wajen su uku suka fito. "Yes Ma!" Umarni ta ba su akan su hayo su taimakamata. Da gudu suka nufi saman, suka cicciɓi Hussein. Mayafi kawai ta dauka sai mukullin mota da ta damkawa John ta bi bayansu tana kuka. Kai tsaye suka wuce asibiti. *** Sun sauka lafiya a Kano. Bayan kimtsawa suka hadu suka ci abincin rana. Fuskar Ramlat cike da fara'a don  tun safe bayan dawowarsu Muhibbat ta kawo su Ummi. Affan ya maƙale mata duk inda ta sa ƙafa yana biye. Labarin gidan su Aliyu da na Muhibbat kuwa ta sha har ta gode Allah. Ta lura dai ba su fuskanci kowace matsala daga dangin Aliyu ba don a yanda bakin Ummi ba ya shiru sai ta fesamata. Da yammacin ranar gidan ya rage daga ita sai Hajiya da su Ansar don tuni masu auren duk sun tafi gidajensu. Ta shirya tsaf da niyyar zuwa ganin Kawu Modibbo kafin zuwan AlHassan wanda tun safe ya shaidamata cewar yana hanya. Ba ta ɓoyewa Hajiya komai ba na halin da ake ciki. Hajiya ta jinjina lamarin. "Ramlatu Allah Yasa a dace. Allah Yasa karshen wahalar yaron nan ce ta zo." Cike da tausayawa Ramlat ta amsa da amin. Suka yi sallama ta fita, ba ta ɗauki mota ba don haka kawai ta fice. Har za ta wuce ta ga kyautuwar leƙawa gidansu Amrah su gaisa da Baba Dakta. Wannan yasa ta karya kwana ta shiga gidan da sallama. Umma ta amsa fuska a sake. "Mutanen Daura, saukar yaushe?" Dariya ta yi tana mai kama hannun Zaituna da ta maƙalƙaleta tana oyoyo. "Tun safe muka iso, Hajiya ma ta kira ba kya kusa." Umman Amrah ta bude baki. "Af, an yi haka. Na ga kiranta toh da alama dai wannan ɗiyartaki ce garin son a kunna mata kallo ta kashemin ƙarar." Murmushi sosai Ramlat ta yi gami da shafa kan Zaituna tana mitar yanda amosali ke cinyemata gashin.  Can kuma ta ɗago. "Baba Dakta ya na nan kuwa?" "Ba ki taki sa'a ba Ramlatu, yana asibiti." Ta mike tsaye. "Toh Umma zan dawo anjima in sha Allah. Zan ɗan fita ne." Umma ta amsa da toh, suka yi sallama  ta fice. ***   Gidan ta tsaya tana ƙarewa kallo. Gida ne da ta sha zuwa ta wuceshi, ba ta mancewa akwai sadda suka taɓa shiga tun suna yara ita da su Amrah tsinko mangwaro aka koro su. Murmushi ta ɗan yi tunawa da cewar gidan ƴan uwan mutum mafi soyuwa a zuciyarta ne ashe. Ta ƙarasa ta yi sallama ga mazauna ƙofar gidan sannan ta sa kai ciki. Ɓangare biyu ta gani sai kawai ta faɗa na biyun. Wata baiwar Allah dattijuwa ta soma cin karo da ita zaune a tsakar gida, a gefenta wata budurwa tana gyaran alayyahu, wanda nan take ta gane fuskarta dalilin hotunanta da ta ke gani a status din Hafsat, sunan ne dai ba ta jin za ta iya tunawa. Suka amsa sallamarta suna dubanta, duba na rashin sani. "Sannu da zuwa, bismillah. Rasheeda kai ta falo ina zuwa. " Faɗin Amarya fuska a ɗan sake, sosai Ramlat ta ji dadin tarbar da ta samu. Ta bi bayan budurwar da aka kira Rasheeda zuwa falo. Falo ne mai girma ya sha ado. Ta zauna a saman ɗaya daga cikin hadaddun kujerun da aka zuba. Rasheeda ta gaidata ta amsa fuska a sake sannan ta je ta kawomata ruwa da lemun zoɓo. "Na gode." Cewar Ramlat sadda ta dauki ledar ruwan ta sha kaɗan ta ajiye ragowa. Amarya ta shigo ta zauna. A ladabce Ramlat ta gaidata ta amsa fuska a sake. "Sai dai kamar ban shaida fuskar ba." Murmushi Ramlat ta yi. "Eh gaskiya ba ki san ni ba Anti. Sunana Ramlat Khalid Mu'azzam. Kusan sanadin AlHassan Aminu Mamman dake Adamawa na san gidannan. Kwanakin baya ma sun zo biki nan suka biya ta gidanmu." Kawai sai ta ga Rasheeda ta sa dariya haka Amarya. "Ke ce Mamin Fatima ko? Mai zaɓamata takalmi? Ya bamu labari." Da wani irin salama na jin dadin kalaman Rasheeda itama ta yi dariyar kadan. "Ni ce, ai kema ina ganinki na shaidaki don ina yawan ganin hotonki a status din Hafsat." Jin haka Amarya sai ta samu nutsuwa sosai da Ramlat, dama tun farko ba ta yi mata kalar mace marar kamun kai ba. Nan aka kara gaisawa da tambayar su Hajiya wanda ba karamin mamaki ya ba Ramlat ba. A karshe Ramlat ta gangaro kan abinda ya kawo ta. "Ina neman izni ne, ina son ganin Kawu Modibbo." Jin haka Anti Amarya ta amsa cikin kwarin gwuiwa. "Wannan ba matsala ba ce Ramlat. Bari na yi miki iso, ina zuwa." Hakan ya faranta ran Ramlat, ta dauka ganinnasa zai mata wuya ko kuma wani ko wata zai nemi sanin dalilinta na son ganinsa, sai dai akasin hakan ce ta faru. Ko ba komai ta gaskata kirki na Amarya, wanda ya sha bamban da na Hajja Fatuma kamar yanda ta ɗan ji kaɗan cikin labarin matannasa a bakin Hafsat. Yarinyar akwai hira idan ta so. Jim kaɗan sai ga Amarya ta dawo, yanayin sanyin jikinta sai ya sa Ramlat shan jinin jikinta itama. Amarya ta daure tana murmushi mai kama da yaƙe. "Za ki iya jira har bayan Magriba kuwa? Ina gudun kar ki dare." Nan ta gano matsalar, don haka ta saki fuska. "Lah ba komai Anti, Allah Ya kaimu." Amarya ta yi murna da hakan, ta kunnamata kallo ta ba ta remote koda za ta sauya tasha daga nan ita kuma ta koma bakin aiki kasancewar girkinta ne. Ba jimawa da kunna kallon aka dauke wuta, nan take jin Amarya na ba Rasheeda labarin wai Hajja Fatuma ce ta ce tunda ba lokacinta ba ne sai ta yi hakuri da duk wani baƙonta da ke son ganin Modibbo, idan na ta lokacin ya shigo ta yi duk irin damun da ta so yiwa furarta. Murmushi Ramlat ta yi na yaƙe, ta dai lura akwai takun saƙa tsakanin matan gida. Waya ta fiddo ta kira Hajiya ta fadamata. "Anya kya zaunar musu har Magriba? Ba kya dawo ba ki hakura zuwa gobe?" Girgiza kai Ramlat ta yi. "Hajiya lokaci zai ƙuremin idan ya kai gobe, mu dai yi hakuri tunda kinga biyar da rabi ma ta wuce, kamar yanzu ne za'a kira sallar in sha Allah." "Ai shikenan, Allah Ya kaimu anjima. Sai kin dawo." Ta amsa da amin suka yi sallama. Ba ta kai ga ajiye wayar ba, kiran AlHassan ya shigo. Suka gaisa. "Dole ta tsayar da ni a Gombe sakamakon lalacewar abin hawa. Na so kwarai na shigo yau, amma gobe da sassafe in sha Allahu zan taso." Hakan ya dan yiwa Ramlat dadi, ko ba komai lamuran zasu tafi yanda ta so. "Ayya ba komai, Allah Yasa hakan ya zama alheri." "Amin, sai dai kin ƙi sanar da ni komai game da abinda na nema." Sauke ajiyar zuciya ta yi. "Ka yi hakuri, idan ka shigo har wanda zai ba ka mamaki duk zan faɗamaka kuma zan kaika ka ganewa idonka in sha Allahu." Ya dan yi shiru, shirun da yasa Hussein faɗomata a rai, shi ya saba yi mata hakan. Kewar Hussein sosai ta ke ji ta kuma kudurce ko bai mata magana ba ita kam yau za ta taɓoshi ta whatsapp. "Shikenan. Allah Ya jisshemu alheri." Ta amsa da amin cike da tausayinsa. Dan uwan da Allah kadai yasan tun sadda ya ke bulayin neman ɗan uwansa. Ta ji idanunta sun cika da kwalla daidai sadda suka yi sallama. Ta shiga whatsapp ta aikawa Hussein saƙo, ta jima tana kallon profile dinsa wanda bai dora komai ba a idanunta tana wassafo hotonsa, karshe ta sauka. Ba jimawa aka shiga kiraye-kirayen sallah, Rasheedat ta jagorance ta zuwa ɗakinta. Alwala ta ɗaura ta tayar da sallah saman dardumar da ta iske an shimfidamata. Ta jima tana addu'ar nasara akan lamarin Hussein, shi kansa ta yi mishi addu'a kwarai kafin ta shafa ta miƙe. Abinci aka zubomata, dolenta ta ci tana kallon tsarin yaran Amarya gwanin sha'awa. An idar da sallah ana kuma neman haddar karatun da aka biya na Islamiyya. Can kuma sai ga Amaryar ta fito sharr kamar sabuwa, ta shirya cikin riga da siket na leshi ta cakare abinta tsaf. Da fara'arta ta dubi Ramlat. "Yi hakuri fa Ramlatu, bari idan na shiga zan miki magana sai ki zo." "Toh Anti. Kin yi kyau tubarakAllah." Hakan da ta fada ya ba su dariya har yaran. Amarya ta yi godiya ta wuce ɓangaren Mijinta. Sosai abin ya ƙayatar da Ramlat. ***   Taimakon gaggawa likitocin suka shiga ba Hussein har Allah Yasa ya dawo hayyacinsa. Hajiya Zeenatu ta rasa sukuni, banda safa da marwa babu abinda ta ke yi a harabar bakin kofar dakin da Hussein ke kwance. Can ɗaya daga cikin likitocin ya fito, da hanzari har mayafin na sulalewa ta ƙarasa. "Dakta ya farfado?" Daktan ya yi murmushi gami da gyara zaman gilashinsa. "Alhamdulillah Hajiya, ɗanki ya farfaɗo, ki kwantar da hankalinki." Ta tamke fuska. "Mijina ne." Mamaki karara a fuskar likitan kafin kuma ya haɗiye don ba abinda ya shafeshi ba ne. "Ok, idan ba damuwa ki biyo ni zuwa ofis." Daga haka ya yi gaba. "Matsalar Hussein damuwa ce da ta haddasa masa ciwon kai mai tsanani. Sai jininsa da ya hau, sai kin kula sosai da cimarsa har ma da walwalarsa domin irin ciwonsa na bukatar kulawa kuma ba ya son yawan tunani." Hajiya Zeenat ta yi shiru a ranta tana jin takaicin Hussein da zai  sa damuwar wani abu bayan ita ce duniyarsa. "Kin ji abinda na ce?" Tambayar ta katse tunaninta. Ajiyar zuciya ta saki. "Naji kuma zan kiyaye. Yanzu ina iya ganinsa?" Likita na ƙaremata kallo ya gyada kai. "Eh Hajjaju." Ta mike tana watsa masa kallo mai kama da harara, ba shiri ya janye idanunsa tunda ya san shi ya jaza wa kansa da ya bita da kallon kurilla. Ba kuma don sha'awa ba, sai don ya ga abinda ya kwaɗaitar da mara lafiyarsu da ta kira da Hussein har ya ji ita ya ke da muradin zama abokiyar rayuwarsa. "Su ta shafa." Ya ƙarƙare tunanin ta hanyar furta hakan a fili. Hajiya Zeenatu ta shiga ɗakin da Hussein yake, wannan karon babu kowa sai shi ɗaya. Idanunsa a lumshe, a farko ta yi zaton bacci ya ke, sai dai rufe ƙofar da ta yi yasa shi kallonta. Ta sakarmasa murmushi tana mai ƙarasowa ta zauna gefen gadon ta kama hannunsa. "Sannu Hussein, ya jikin?" Gyadamata kai kawai ya yi ya kara kauda kansa. "Ba zan kwana a nan ba, su sallame mu." Yanda ya yi zancen ka san iyakar gaskiyar kenan ba wasa. Cikin rarrashi ta shigo kokarin fahimtar da shi kuskuren hakan, sai dai yanda ta kafe haka ya kafe har abin ya tsorata ta. Aikuwa dai karshe sai sallamar aka ba su da lodin mgunguna bayan an ƙara jaddada masa akan ya kula sosai da jikinsa. Su na komawa gida ma'aikatan suka tarbeshi tare da yi mishi sannu. "Dalla Malamai ku matsa! Ba kwa ganin yanayin jikinsa ne?" Hussein ya dubi Hajiya Zeenat, a fuskarsa ta gane bai ji dadin abinda ta yi ba. Ya tsaya ya amsa gaisuwarsu ita kuwa ta yi gaba tana tsaki. Godiya ya yi musu san nan ya shige ya bar su da gulmarta. Sallar Magriba ya soma yi san nan ya shiga wanka. Yana fitowa ya kimtsa, Hajiya Zeenatu kuwa tana ƙasa ta na bada umarnin abinda za'a girkawa mijinnata. Ya dauki wayarsa, ya ga missedcalls din Hisham sai kuma na wani abokin aikinsa. Data ya kunna ya leƙa whatsapp. Shiru ya yi ya ƙurawa sunanta idanu yana kallon saƙon da ta aiko ba tare da ya buɗe ba, ya hangi dai sallama da gaisuwa, sauran ne bai da masaniya. A hankali aka zare wayar daga hannunsa. Hajiya Zeenatu ce, gabansa ya faɗi. "Haba Yallaɓai, yaushe ma ka farfaɗo da za ka ɗauki waya? Ba dai ka manta sharuɗɗan Dakta ba?" Ta ƙarashe tana duban wayar, tuni ta shiga key, shima yanda ta ke kallo haka ya ke kalla, ganin ta rufe ya sanya shi sauke ajiyar zuciya. Gaba daya ta kashe wayar tana mai duban soyayy duk a kokarinta na gudun kar ya sauya shawarar da ta kawomasa a ɗazun. "Wayar a hakura a bar ta zuwa gobe. Yanzu mu je ƙasa ka jira abinci sai ka sha magani." Ta faɗi gami da riƙe hannunsa. Ya ciji leɓɓansa, haka nan ya ji bai kyauta ba bisa rashin ba da amsa ga Ramlat sai dai maganganun Hisham na faɗomasa a rai sai ya yi gaggawar fidda tunanin. *** Mintuna kusan goma sha biyar sai ga kiran Amarya a wayar Rasheedat. "Muje na yi miki rakiya." Haka kawai Ramlat ta ji faɗuwar gaba, ta amsa da toh tana mai haɗiyar yawu mai ɗaci. Da sallamarta ta sa ƙafa a falon. Dattijo cikin shigar kamala, kana ganinsa ka ga cikakken bafulatani. Tundata shigo yake yiwa fuskarta kallon tsanaki don son tantance ko akwai inda ya santa ko kuwa yau ne farkon ganinsa da ita. Ta karasa ta gaishe shi, Amarya tuni ta mike zuwa ɗaki. Hakan kan faru, idan har Modibbo nada baƙo, sukan ba shi wuri ya gana da ita. "Baiwar Allah daga ina?" Ya tambaya cikin hausarsa da har sannan ba ta ginu kamar ta Bahaushe ba. Ta hadiyi miyau gami da ambaton Allah. Ta gabatar da kanta sannan ta ɗora bayan ya shaidamata eh ya san Malam Abdullahi kakanta kuma ɗan unguwar da yake, Yakasai. "Kawu dama magana ce da ta danganci Hussein, dan uwan AlHassan da ake nema." Shiru-shiru, ba ta ji ya ce uffan ba don haka ta ɗago kai. Yanayin dake shimfiɗe a fuskarsa ya tsorata ta, ya kuma kaɗa hanjin cikinta. "Kina da labarinsa? Ke wace ce?" Wannan ne tambayoyin da ta samu da suka ƙara cilla ta a kogin tunani da mamaki.   I just published "BABI NA ARBA'IN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/gqyFr6qwCcb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 45) ALLURA TA TONO GARMA... "Kurma ki ka koma?" Ta  dawo hayyacinta ta kalle shi gami da girgiza kai. To me za ta ce bayan ta gabatarmasa da kanta? "Ina gargaɗinki da ki cire kanki a abinda bai shafeki ba. Idan kina son tsira da lafiyar kwakwalwa da na gangar jikinki ki fita hanyar Hussein da Zeenatu." Da wani irin razana ta dubeshi, wannan ƴar fara'ar dama tun soma labarin ya kauda ita a saman fuskarsa sai ya zama kamar wani Mugyambo a idanunta. Kwallar da ta cika kurmin idanun suka soma sharara. "Ka...ka..san Hussein yana nan? Ban ambaci Zeenatu ba, ka san..." "Ke Bingel! (Yarinya). Ke wacece da za ki tuhume ni? Ina gargadinki karo na biyu kuma na ƙarshe ki tashi ki binne maganarnan a nan wurin da kike zaune. Idan ba ki ƙi ji ba, ba kya ƙi gani ba. Duk abinda ya faru gareki sanadin fasa wannan zancen, ki yi kuka da kanki!" Ramlat kirjinta na bugu, hawayenta na kwaranya, kwakwalwar ta tsaya cak ta bar aiki. Ta kasa haɗa kowane lissafi, jin ta take yi kamar ba'a duniyar mutane ba. Kamar wata duniyar ta daban ta ke ciki mai tsananin ruɗani da azaba. Kallonsa ta ƙara yi, girman tuni ya zube ƙasa warwas! Kallo ne kamar wacce ke zaune gaban sa'anta. "Ka na da hannu a komai? Ka na a ɓatar da Hussein daga zuri'arku? Me ya yi maka haka da zafi?" "Kina ƙara dulmiyar da kanki cikin tafkin nadama da da na sani, kalaman da kike yi za su rushe duk wani farin ciki na rayuwarki. Ki kama kanki! Ki tashi ki bar min gida tun kina da sauran lafiyar aikata hakan!" Miƙewa ta yi a sanyaye, har za ta fice ta juyo ta dubeshi yana faman muzurai. Dattijon da bai kama daraja da girmansa ba, babu amfanin ganin ƙimarsa. "Kawu ka sani, Allah na bayan masu gaskiya. Ƙarya fure ta ke ba ta ƴaƴa." Daga nan ta bankaɗa labule ta fice, ba  ta jin za ta iya jiran yin sallama da Amarya. Babu inda ta ƙara shiga a gidan haka ta fice tana hawaye.   Tafiya ta ke ƙafafun na harharɗewa, kalaman Kawu daki-daki ta ke tunawa tana ƙarin fahimtar dagaske dai akwai hannunsa a cikin ɓatan Hussein. "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Ta ambata a fili, tausayi sosai da wata irin ƙauna ta Hussein ya ƙara mamaye zuciyarta. Ji ta ke komai za ta iya aikatawa muddin hakan zai dawo da Hussein cikin ƴan uwansa. Wayarta ta yi ƙara, Hajiya ce. Yanda ta ke kuka ba ta jin za ta iya amsawa, don haka ta mayar da wayar jaka. Kafin ta bar lungun sai da ta tsaya ta saita kanta ta share fuska. Abin hawa ta tsayar ta faɗa. "Malama ba ki faɗi inda zan kai ki ba." Ta haɗiyi miyau. Dakyar ta faɗi sunan unguwar ta yi shiru, kanta ke sarawa ga wani zazzaɓi-zazzaɓi. *** Tsam! Modibbo ya miƙe ya shiga ɗaki, Amarya na zaune na kallon wani ƙaramin bidiyo na Ibro tana dariya, ganin mutum ya faɗo ba sallama ya sa ta ɗan razana kafin ta sauke ajiyar zuciya. Tun kafin ta nemi ba'asi ya katsemata hanzari.  "Fita zan yi, ki je kawai idan na dawo zan kiraki. Akwai uzurin da zan gabatar." Ya faɗi a kausashe, ta miƙe jikinta a sanyaye ta fita fuskar cike taf da tarin tambayoyin da babu mai amsa mata sai Ramlatu. Sai dai sama ko ƙasa babu ita, hatta su Rasheeda sun yi mamakin da ba ta biyo ta musu sallama ba. Fitar Amarya ya ba Kawu Modibbo damar buɗe sif ɗinsa ta kaya, can ƙasan ya zura hannu ya ɗauko wani ɗan akwati mai girma da duk faɗin gidan babu wanda ya isa ya taɓa. Hankalin ma bai kai gareshi ba. Cikin rigarsa ya zaro mukullin da ba ya rabo da shi a jikinsa, ya buɗe, kwakwalwa ce! Kwakwalwa ta ƊAN ADAM! Ta yi baƙiƙirin a madadin jan da ta ke da shi har da jini-jini a shekaru masu yawa. Idanun Kawu Modibbo suka kaɗa. "Ita ce! Ita ce yarinyar!" Abinda ya faɗi kenan a fili kafin hannu na rawa ya maida ya rufe. Gumi ya shiga tsastsafowa daga fatar jikinsa. Ya sa hannu ya share. Tun komai bai ƙarasa lalacewa ba zai yiwa  abin tufka. Ya ayyana hakan a ransa yana jin tsanar Hussein tsagwaronsa a fili da ɓoye. Miƙewa ya yi ya dauki waya ya danna kira direbansa. "Kana ina?" Daga can aka ba shi amsa kafin ya dora. "Ka fiddo mota, fita zamu yi." Daga nan a gaggauce ya dauki hula ya rufe kansa ya fita yana zuba sauri. ***   Ramlat bakinta ya yi mata nauyi, ta kasa ba Hajiya labarin abinda ya faru. Damuwar da ke kwance samam fuskarta yasa Hajiya ta fahimci ba lafiya. Ganin ta shige daki sai ta mara mata baya. "Ke mene ne wai? Shi Kawun ne ba ki samu gani ba ko wani abin ne ya faru da Husseinin?" Girgiza kai ta yi. Tunanin ta faɗa ɗin ya rinjayi komai, ko ba komai Hussein na bukatar addu'a, don haka ta karya bille ta labartamata duk yanda suka yi da Kawun. Hajiya ta saki salati. "Ni Rabi wannan rayuwa da ban mamaki. Ban taɓa jin labari makamancin haka ba tunda uwata ta haifeni. Kai.." Hajiya sai ta soma hawaye, ita kanta tausayin Hussein ke ɗawainiya da ita. Hatta da abokin haihuwartasa ma tausayinsa take ji. Miƙewa ta yi tana jan hanci. "Addu'a zamu dage da yi, ke kanki yanzu ki dage da addu'a don mutum idan aka ce mugu ne komai ma zai aikata. Bari na kira Malam na faɗamasa, shima ya tayamu da addu'a." Daga nan Hajiya ta fita ta bar Ramlat da tarin damuwa. Dakyar ta iya mikewa ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar isha'i, zaman dirshan ta yi saman dardumar jefi-jefi tana sharar hawaye. Addu'a sosai ta yi kafin ta miƙe ta nufi gefen gado ta zauna. Hayaniyar su Affan ta ishe ta don haka ta kora su waje. Waya ta ɗauka ta hau kan whatsapp, babu alamar Hussein ya hau. Yau ɗaya ta ɗaura ɗamarar kiransa. Don haka ta sauka ta danna masa kira. Wayar a kashe. Damuwarta madadin ta ragu sai ta ƙaru, ganin dukan na nema ya yi mata yawa, sai ta miƙe ta koma falo ta yi jugum. Ba jimawa Hisham ya kirata. Ta ɗaga. "Antinmu shiru, ina jira na ji yanda ku ka yi." Ta haɗiye hawayenta da ɓacin rai. Komai ba ta ɓoyewa Hisham ba, ya dinga salati da salallami karshe dai ya kwantar mata da hankali. "Kar ki sanya damuwa a ranki Ramlat, in sha Allah kamar yanda kika ce toh hakan ne, Allah Ya fi su. Mu dage da addu'a." Ta amsa da toh. Kamar ta tambayeshi ko sun yi waya da Hussein sai ta share. *** Washegari haka ta shirya ta fita wurin aiki ranta a jagule. Ga wayar Hussein da ke a kashe. Ta gwada kira har cikin dare don tsautsayi amma ba ta shiga. Tuƙi ta ke kusan ba za ta ce a cikin hayyaci ba. Don haka ba ta kawo da cewar an basu hannu ba sai da ta ji wani ruɗaɗɗen Hon daga bayanta. Hakan ya fusata ta, ta madubi ta ke duban mai shi. Ido da ido suka kalli juna, yana cin magani. Wannan karon ba Tinted glass din  a motar da yake. Yanda ya ɗaure fuska ba alamun fara'a ya fi komai ruguza lissafinta. Asalima ba wani wawan overtaking da ya yi ya kaɗa hancin motarsa sai da ya daskarar da ita ya jazamata ɗaukewar numfashi na ƴan dakiku. "Me nayi masa?" Ta ambata a fili, da rawar jiki ta ja motar bayan ta gaji da tsinuwa da zagin mutanen da hankalinta ba'a kansu yake ba. Koda ta gangara sai ta nemi wuri ta tsayar da motar. Hankalinta ya gushe na ɗan lokaci. Tunaninta abinda ta yiwa Hussein, shi dai ta gani kamar yanda ya gan ta amma ya kauda kai. Wannan abu ne da bai taɓa afkuwa ba tsakaninsu. Ta ɗauki wayarta da karar shigowar saƙo ya katsemata tunani, kuɗi ne har dubu ɗari aka aikomata. Ta kai duba ga lambar mai account din. Aliyu Dikkl. Hakan ta gani a rubuce. Ranta ya ƙara ɓaci, ga babu lambar acc balle ta mayarmasa. Ta ja tsaki. Kai tsaye ta ƙara kiran wayar Hussein, wannan karon ringing ta ke yi sai dai har ta katse bai ɗaga ba. Ta kuma kira nan ma shiru, a karo na uku ma babu alamar za'a ɗaga. A na huɗu sai ji ta yi an kashe wayar gaba ɗaya. "Meke faruwa?" Ta ambata a fili. Kawai sai ta ji zuwa wurin aikin ma ya fita a ranta, don haka ta ba kanta mintuna kusan biyar a tsaye tana jin karatun Alkur'ani tana hawaye kafin daga bisani ta samu ƙwarin gwuiwar da za ta tashi motar. Gidan Amrah ta nufa, a hanya ta kira ɗaya cikin abokan aikinta, Hindu. Uzurin rashin lafiya ta bayar domin dagasken ba ta jin dadin zuciya da gangar jikin. *** Amrah ta yi mata duban tsanaki bayan gama sauraron dukkan bayanin Ramlat. Ita kanta kwallar ce ta cicciko mata. "Yanzu AlHassan ɗin bai shigo ba?" Ramlat da kanta ke jikin kujera sakamakon zazzaɓi-zazzaɓin da ta ke ji. Ta girgiza kai murya a dusashe. "Mun yi waya da shi yanzu da zan fito, abin hawa ne ba'a kammala gyara mishi ba, yana tunanin ma bar musu zai yi ya biyo motar kasuwa."   "Kai! Wannan lamari akwai wata sarƙaƙiya a cikinsa Ramlat. Sai dai kuma ki zauna don Allah ki yi tunani ko dai akwai abinda ki ka aikata ga Hussein har ya ɗauke maki wuta haka? Ni fa gani nake da walakin goro a miya." Cike da damuwa ta ɗago ta zauna sosai tana duban Amrah da ciki ke ƙara girma. "Da ace akwai abinda nake jin zan ba dukkam girma da kulawa bayan iyaye, ƴaƴa da ƴan uwa, wallahi ya biyo bayan Hussein. Kin san ni, kin kuma san halina Amrah. Ina son Hussein, son shi nake yi da ban san iyakarsa ba. Akan me zan ƙuntata masa? Ni duka-duka ma yaushe rabon da ko chatting nayi da shi balle haɗuwa face to face? Ban sani ba, ban san me na yi ba. Ni dai babban burina koda zai zama abu na ƙarshe da zan mishi, shi ne na sada shi da ƴan uwansa da taimakon Allah." Amrah ta jinjina kai, shakka babu Ramlatu na son Hussein, so mai yawa. Tana tsoron tarihi ya maimaita kansa idan har dangin uwa da uba suka dage mata akan auren Chairman. Sauƙinta ma wannan karon su Hajiya na goyon bayanta. "Ko Hisham zan tambaya?" Maganar Ramlat din ta maido ta hayyacinta. Gyada kai ta yi. "Ki tambayeshi tunda amininsa ne. Ba zai rasa abinda ya sani ba." Da haka ta danna wa Hisham kira. Yana ɗagawa suka gaisa. "AlHassan din ya iso kenan?" Ya nemi sani. "Aa, wannan tsakanina da Hussein ne." "Ina jinki Ramlat." Ta ba shi labarin irin sauyin da ya ke mata. "Ko akwai wani abu da ya ce maka na yi mishi don Allah?" Shiru ya biyo baya kafin Hisham ya ce. "Ya Salam!" Jin haka ta gyara zama tana kallon Amrah don dama a speaker ta sanya. Suka nutsu. "Meyafaru?" Ta tambaya kirjinta na dukan uku-uku. "Ki yi hakuri, ina ga wannan laifina ne, yanda na ɓata kuma ni zan gyara. Kar ki damu don Allah. Zan kira ki anjima ko kuma ince zai yi kiranki da kansa. In sha Allahu." Daga haka ya katse kiran. Suka dinga mamaki. Tunanin Ramlat me Hisham ya faɗawa Hussein? "Hisham ya san batun aurenki da Chairman?" Amrah ta nemi sani. Maganar Ramlat ji ta yi kamar an sokamata mashi a ƙahon zuci don haka maimakon amsa sai ta harareta ta ja guntun tsakin da ya ba Amrah dariya. "Allah Ya ba ki hakuri. Mancewa nayi fa." Ta cije lebɓa gami da girgiza kai ba ta ce komai ba. *** MISALIN ƘARFE SHA ƊAYA.. Rubutu yake kamar wani Mango Park ba ya ko kallonsa, Hisham ya ƙuramasa idanu da mamaki. Ya sauya kamar ba Hussein din da ya sani ba. "Malam ya ina magana ka kyale ni? Ba ka ji me nace ba?" Ya ɗago ya dubeshi, ya ji, dukkan wani labari da ya ba shi, ya ji ba wai bai ji ba. Sai dai duk da hakan shi bai ga ta inda zai fara rage KISHIN Ramlat da ya ke ji ba. Ya soma yarda da abinda ya ƙaryata da gangan, ba kuma ya son sanya ta a matsala. Wannan ne dalili sauyawar sai dai ya ji wani sanyi kaɗan a maimakon tsananin zafin da ya ɗauka a farko duk akan lamarin aurenta da Chairman. "Kunne ke ji, kuma na saurareka. Ka yi kokari." Harara Hisham ya watsamasa yana danne tausayinsa. "Shi ne za ka share ni? Nima fa takanas na taso don wanke laifin Ramlat amma ina da abin yi ai. Aikina na baro na zo." Wannan ne karon farko da ya yi murmushi daga jiya zuwa yanzun, Hisham yana da raha. Ko ya ya ka zauna da shi sai ya sanyaya ranka. "I'm travelling to London." "For what?!" Yanda Hisham ya nemi sani a hargitse, hakan ya ba Hussein mamaki har ya kalleshi, ganin ya zaro ido sai ya buɗe tafukan hannu gami da ɗaga gira cikin dakiya. "Me akai na razanar? Tafiya ce kawai ta 3months." "Gwara da Allah Yasa na zo." Hisham ya faɗi a fili kuma a hankali. Da ace ba su haɗu ba ba zai sani ba kenan. Lallai dole su yi komai cikin gaggawa. "Me ka ce?" Hussein ya tambaya. Girgiza kai ya yi. "Ba komai. Yaushe za ku wuce?" Damuwa ƙarara a fuskar Hussein sai dai ba ƙaramin ƙoƙorin dannewa ya ke ba. "Ba na jin za mu wuce satinnan. Ya dai danganta da samun Visa." Ya faɗi a sanyaye. 'Innalillahi wa inna ilaihir raajiu'un!' Hisham ya ambata a zuciya gami da mikewa. "Ok ok, Allah Ya nunamana. Bari na wuce sai mun haɗu anjima." Hussein ya bishi da kallo har ya fita. Abinda ya kawo a rai shi ne damuwa ce tsantsa na ganin za su yi nesa da juna. Ya dafe kai da hannu. Shi kansa damuwar ce ke cinsa, tunanin tafiya ya bar Ramlat da Chairman kan ci masa tuwo a kwarya. Sai dai ya tabbatar furta wata kalma a kanta zai zama kamar barazana ga rayuwarta. Hajiya Zeenat ta sha faɗamasa gami da cin alwashin kashe duk wata mace da za ta shiga rayuwarsa. Ba a bayan idanunsa ba, a gabansa ta ke faɗi ya na kuma ji a jikinsa fiye da hakan ma za ta aikata. A hankali ya ɗauki waya ya kunna Data wacce rabonsa da whatsapp tun ranar da Hajiya ta kwace wayar. Saƙonni suka shigo har da nata. Ya shiga ya karanta. Gaisuwar safe ce ta mishi gami da tambayar ko lafiya. Ya dinga binyana karanta hirarsu da bai fi a ƙirga ba. Murmushi sosai ya ke yi san nan ya bude hotonta yana kallo. Ya kai kusan minti biyar ba'a hayyaci ba, tashin hankalinsa ya ƙaru. A hankali ya rufe hoton ya aikamata saƙo. -*"Ki sa ranki Hussein ɗan uwanki ne. Ya na buƙatar addu'arki a duk inda zai je. Akwai wani duhu da na kasa fita, ke na gani kin fitar da ni kin sadar da ni da haske. Ina fatan mafarkina wataran ya tabbata. Ban ce ina sonki ba, ban kuma ce ina tsananin kishinki ba, amma ina roƙonƙi akan kar ki yi garajen aure. Nemi zaɓin Allah. Ke ba yarinya ba ce. Ina miki fatan alheri koyaushe."*_ Ya aikamata ya kashe datar, dakyar ya ci gaba da abinda ya ke ransa a jagule. *** Kawu Modibbo tsaye a tsakar falonsa. Safa da marwa ya ke yi yana ƙarawa. Babu wani cikin iyalinsa da ya yi ƙoƙarin dosar inda ya ke, Amarya kanta haƙura ta yi da kwanan ta koma sashinta ta kwana. *_"Kamar wuta da ruwa, haka ta ke barazana ga ayyukanka. Na sha faɗanaka, ba kai ɗaya ke aikin ba, akwai masu yi. Naka kan rinjayesu ne wani lokacin, kamar yanda nasu kan rinjayi naka aikin. Ina tsoron shaida maka muddin ba'a kawar da yarinyarnnan ba, aikin shekara da shekaru zai lalace. Za'a rasa dukkan wata nasara a kansa. Abubuwan da ka ke gudun afkuwarsu a rayuwarka, za su afku!"_* Waɗannan jawabi na Tsoho, shi ke yawo a kwanyar Kawu Modibbo suka kuma hanashi sukuni daidai da sakan. Daren jiya kasa runtsawa ya yi balle har ya samu damar baccin. Idan komai ya lalace, hakan na nufin bayyanuwar komai. "Lokaci ya yi da za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe da ke ZEENATU." Ya furta a fili kafin ya samu wuri ya zauna kamar kayan wanki. *** ƘARFE BIYU... Ta karanta saƙon Hussein sau ba adadi, sai dai ba ta fahimci komai ba. Cewar ba ya sonta ba kuma ya kishinta wannan ya haifar mata da matsananciyar damuwa. Kukan da ta yi ya jazamata tsananin ciwon kai. Hajiya na ganin haka ta tsorata, abinda ya faɗo a ranta kada ace wani mummunan abin ya sami Ramlatu sanadin wannan yaro, bayan ta taimaka mata ta sha magani ta shiga tofe ta da addu'a. Ummi kam su na Islamiyya ba su da labarin wainar da ake toyawa. Wuraren ƙarfe huɗu da mintuna ne. Wayarta ta yi ƙara, dakyar ta iya ɗagawa. AlHassan ne. "Na shigo Kano, ina hanyar gidanku." Ta amsa da toh, a daddafe ta miƙe, babu laifi kan ya daina sarawa. Ta shiga ta yi brush ta kama ruwa ta yi alwalar jiran la'asar. Fitowa falon ta yi bakinta duk jikinta ya yi mata nauyi. Hajiya na zaune tana amsa waya. "Ita Ramlatun?!" Hakan da Hajiyar ta faɗi ya ɗau hankalinta, ba ta katse ta ba har ta kammala wayar. "Ke da kanki ki ka ba shi Dikko damar turo kuɗi? Yaya Bello ya shaidamin ai sun ma gama magana ya turomaki kudin aurenki ta akawun dinki da ki ka aikamasa." Dafe kanta ta yi tana salati, kirjinta na bugu da sauri-sauri. "Ni kuma Hajiya? Wallahi ban.." Ɗif ta yi, sai lokacin ta tuno da kuɗin da ya turomata account. Ranta idan ya yi dubi ya ɓaci. Ta faɗawa Hajiya gami da nunamata sannan ta ƙara da faɗin. "Amma wallahi ban san inda ya samu lambar account ɗina ba. Ban sani ba. Me ake nufi da ni wai?" Ta karashe hawaye na son zubomata. A fusace Hajiya ta mike tana faɗa. "Bari na je gidan! Ba su suka haifarmin ke ba don haka ba zan zauna rayuwarki ta ƙare haka ba Ramlatu! Idan shi Munirun ya kasa ni zan je na same su." Daga haka Hajiya ta faɗa ɗaki ta bar Ramlatu da ruɗewa da kuma hawaye. Waya ta ɗauka ta kura Zulaihat ta sanarmata komai, itama hankali a tashe ta ce za ta je can gidan su Dada kar abin ya ɓaci. Hajiya ta fito ta kama hanya ta fita. Mintuna talatin bayan fitar ta sai ga kiran AlHassan yana shaidamata zuwansa ƙofar gidan. Ta mike ta shiga ciki ta gyara fuskarta da ta kumbura. Dole haka ta haƙuranta fita hakan. Tuni an gyaramasa ɗakin Muniru na baya, ta yi mishi iso ya shiga yana bin ta da kallo. "Lafiya dai ko?" Ta yi murmushin yaƙe. "Lafiya kalau. Sannu da zuwa." Ya amsa karo na biyu, shi ba wannan ya ke da muradi ba. Labarin Hajiya Zeenatu da adireshinta ya ke da buƙata. Abinci ta kawomishi ta kuma ce ya yi hakuri har su yi sallah tukunna. Daurewa ya yi ya amsa da toh sannan ta fice. *** "Rai kan ga rai?" Hajiya Zeenatu ta faɗi tana murmushi da wani irin mamaki shimfiɗe a fuskarta tana duban Kawu Modibbo da ke zaune a ofishinta na A&Z. Ya share goshi. I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/rSOQW4y2Gcb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 46) "Kin san dai ruwa ba ya tsami banza. Kamar yanda kin sani, na sani, komai nisan jifa ƙasa zai faɗo. Toh idan ba mu yi dagaske ba, asirinmu na dab da tonuwa." Nan da nan ta haɗe rai. "Me kake nufi?" Kawu Modibbo ya gyara zama yana mata kallon ƙyar. "Wata yarinya ta zo min da zancen da ya rushe dukkan walwalata. Tana ƙoƙarin shaidamin cewar ta san inda Husseini yake, duk da ba ta fito fili ta yi bayanin komai ba, amma daga yanda ta ambaci shi Hassan ta alaƙantashi da Husseini shakka babu akwai babban al'amarin da ta sani." "Ya sunanta?" Hajiya Zeenatu ta nemi sani a hanzarce yayinda kirjinta ke bugu, tana tsoron kar hasashenta ya zama gaskiya. Sai dai abinda ta guda shi ya faru, sunan da ta ke fatan kar ta ji, shi dai ta ƙara tsinkaya daga bakin Kawu Modibbo. "Ramlatu ta ce sunanta." Wani miƙewa da Hajiya Zeenatu ta yi sai da shi kansa Kawu ya ƙara tsorata. Jikinta ya shiga rawa nan da nan idanunta suka kaɗa. "Baƙa ce, ba ta da jiki sosai kuma.." "Abinda ya tunkaro mu, ya fi ƙarfin mu tsaya ɓata lokaci a kan suffantawa ba. Ki faɗi kai tsaye idan kin santa." Ya faɗi cike da ƙagara. Ta haɗiyi miyau tana goge gumin goshi. "Tsinanniyar yarinyar da aka sha yimin gargaɗi a kanta kenan! An tabbatarmin muddin ban nisanta Hussein daga duniyarta ba, to shakka babu komai zai lalace. Kenan yanzu ta gano dangin Hussein? Wannan mayyar ina ce?!" "Mafita za mu nema. Kin sani, baragurbin kwai idan ya fashe, yakan shafi kowa ba mutum guda ba. Za ki fi ni shiga matsala. Kin san komai don haka a bar kaza cikin gashinta. Tun lokaci bai ƙure ba ya kamata a ɗau mataki." "Kasheta zan sa a yi." Kai tsaye ta furta tana fidda hucin ɓacin rai. Kawu ya dubeta sosai, duk da cewar yana shuka abubuwa a doron ƙasa, bai taɓa tunanin ya kashe rai ba.  "Kina ganin hakan zai haifar da ɗa mai ido?  Kisa na nufin abubuwa da dama ciki kuwa har da rabuwarki da shi Hussein don za ki ƙare a kur..." "Dakata, ai ba ni zan kashe ba. Zan saka a kashe ne. Mace ƴar uwarta zan saka, ita kanta ba za ta fahimci komai ba. Na santa a bakin Dikko, mayyar kuɗi ce da za ta iya aikata komai saboda shi. Don haka ka bar min wuƙa da nama yanda ka ce, za ka sha mamaki nan da awannin da suka rage kafin safiya." Kawu ya jinjina kai, suka ƙara shawarwarinsu sannan ya fice. A gaggauce Hajiya Zeenat ta kira Hajiya Batool ta ba ta labarin komai har shawarar da suka yanke. "Wannan ya yi kuma ina goyon baya dari bisa dari. Gwara tun wuri a yi ta kuma ta ƙare." Da wannan suka yi sallama ta kira Chairman a waya. Cikin gaggawa ta ce "Ka turomin lambar yarinyarnan." "Wa?" Ya nemi sani. "HALIMA." Dariya ya ɗan yi mai sauti, sanadin Halima ya san duk wani tarihi na Ramlatu, duk da cewa ya san da biyu ta faɗamasa, amma ya zamar masa tamkar ƙarin makaman yaƙi a wurin iyayen Ramlatun har ya same ta. Sanadin wannan ne ya sanya har holewa ya yi da ita na sati kafin ya biya ta da maƙudan kuɗaɗen da suka kusa zautar da ita. "Wani abu ne ya taso?" Ya nemi sani. A ɓangaren Hajiya Zeenat ta ja tsaki. "Wankim hula ke neman kai ni dare, turomin yanzu-yanzu." Daga haka ta katse kiran ta kwashi tarkacenta ta fita. Ba zai yiwu su tattauna da Halima a wurin ba. Hussein zai iya shigowa kowane lokaci. Tun kan ta kai motarta lambar Halima ya shigo. Kai tsaye ta ɗauka ta kira bayan ta daidaita zama cikin mota ta rufe. "Hello." Halima ta furta. "Kina magana da Hajiya Zeenatu mamallakiyar A&Z." Hajiya Zeenatu ta yi shiru don ba ta san ta ya za ta soma bayani ba. Ga mamakinta sai ji ta yi Halima ta ce. "Lah, na san wurin ai ina zuwa lokaci -lokaci. Ai kin taɓa zuwa inda nake aiki kwanaki can kika biya kudin haraji. Na sanki sosai. Ranki ya dade, Allah Ya ƙara girma." Murmushi Hajiya Zeenatu ta yi, dagaske ba za ta samu matsala da wannan ba. Don haka ta muskuta. "Halima ina son ganinki, idan ba damuwa a yau kuma a yanzu." "Aa babu wata damuwa Hajiya, ki fadi inda zan zo na sameki kawai." Nan Hajiya ta yi mata kwatancen gidan Hajiya Batool. Ta dinga amsawa daga bisani suka yi sallama bayan Halima ta tabbatar mata yanzun za ta taho. ***   Hajiya ta isa unguwar Yakasai ranta a tsananin ɓace, ko sashin Hajja ba ta shiga don tasan tsaf za ta hanata tada kowace magana. Kai tsaye ta wuce rumfar Malam Bello inda anan ne yawanci Kawunnan ke zama a sha hira kuma a tattauna matsaloli. Da yake rana ce, aikuwa ta ci sa'a ganinsu a rumfar. Su biyar zaune, Kawu Bello, Kawu Sunusi, Kawu Jamilu, Haruna sai Usman. Kawu Bello na ganinta ya haɗe gira, ta ƙarasa ta zauna aka gaisa. "Sai kuma kika ji an turo kuɗin Ramlatu ko?" Kawu Usman ya furta yana washe haƙora da duk goro ya ɓata. Ta haɗe gira. "Na ji Yaya, sai dai sam ba'a kyauta ba. Ba ku yiwa yarinya daidai ba. Kada ku manta Ramlatu ba yarinya ba ce yanzu, addininta ya ba ta damar zaɓen miji a karon kanta. Idan ma ku ka dauke batun ta, na tabbatar ku kanku ba ku tsaya wani dogon bincike a kan mutuminnan ba saboda.." "Saboda yana da kudi ko? Haka kike so ki ce! Wato mu gamunan mayun kudi? Rabi yaushe kika sauya haka? Kina son ki nunamana ke da Khalid ku ka haifi Ramlatu?" Kawu Bello wanda tun zuwanta ya ke a fusace shi ne ya hau wannan kumfar bakin. Hajiya ta ɗago ta dubeshi don tuni ta soma hawayen idanun sun ƙanƙance. "Ba iko nake nunamaku da Ramlatu ba, amma fisabilillah duk irin munin ɗabi'u  mutuminnan da na lissafamaku a baya bai hana kun murzawa idanunku toka ba kun ba shi damar ya turo kuɗi. Wannan auren ba zai taɓa yiwuwa ba idan har ina raye, ku gafarce ni amma Ramlatu ba za ta auri Chairman ba." "Yanzu na fahimci inda Ramlatu ta ɗauko kafiya da taurin kai. Ashe ba a ƙasa ta kwasa ba, a nono ta tsotsa. Wato yanzu da babu ran Malam shi ne ki ka samu kwarin gwuiwar cin karenki babu babbaka Rabi. A baya ke yarinya ce mai takatsantsan da ɓacin ran ƴan uwanki, amma saboda kin haifa, kina kuma taƙama da dukiyar marayun yaranki da ubansu ya bari, shi ne za ki wulaƙantamu. To gwara da aka yi tusa ai halin kowa ya fito." Sosai kalaman Kawu Haruna sun soki zuciyar Hajiya kamar mashi, ta kalleshi ta kasa magana. Sai Kawu Usman ya sa baki "Ni abinda ban gane ba Yaya Bello, kai da bakinka ka tabbatarmin da yardar Ramlatu a auren wannan mutumin, yanzu kuma sai na ke jin sabon labarin da ya sha bamban da wanda na sani. Wato dai dole ne za ku yiwa yarinya? Wannan ai ba girmanmu ba ne." Ya fadi a sanyaye amma ransa a ɓace, haka yake mutum mai hakuri da gudun duniya. Sai a lokacin Kawu Sunusi ya tanka ta hanyar zubawa Usman daƙuwa. "Ka ci ƙaniyarka Usmanu, mu sa'anninka ne da za ka yi fito na fito da mu? Ai ko Murja ba za ta yi mana haka ba." Kawu Usman jin Kawu Haruna yana sanya Yayarsa ciki ya sa shi jan baki ya yi shiru sai dai ya rantse ba zai ƙara sa hannu a cuci yarinya ba. "Aa Haruna, zancen Usmanu gaskiya ne, ni kaina ai shi Bello cemin ya yi da amincewar yarinya aka yi komai. To ba za ta saɓu ba, ke Rabi ki je. Ni da kaina zan yi kiran shi Dikkon na ba shi hakuri. Ita Ramlatu ta je ta ciro kudin ta turomin da hannuna zan ba shi." Kawu Jamilu ke maganar a daure, kasancewar shi ne babbansu  a wurin don daga Kawu Yakubu sai shi, kuma bai fiye magana ba sai ta ɓaci wannan yasa suke ɗan shakka-shakkarsa. Kawu Bello ya soma share gumi, babu abinda ke ba shi tsoro sai yanda zai yi ya biya kuɗaɗen da ya ci na Chairman. Ƙananun filaye har biyu ya siya ba tare da sanin ƴan uwannasa ba. Wannan tashin hankalin ya sa ya kara magantuwa. "Haba Yaya, ka mance da auren Ramlatu na baya? Ka mance irin tijarar da ta yi mana? Yanzu Rabi ke har kin mance kina ɗauremata gindi?" Hajiya wacce ta ke jin ya zamemata dole ta koma wajen Malam Mu'azzam ƙanin babansu na Daura ta yi shiru ba ta ce masa uffan ba. Suka ci gaba da ja in ja, daga ita har Kawu Usman ba wanda ya ƙara tankawa. Kawu Jamilu ya kafe lallai a mayar da kudi yayinda Bello da Haruna suka ce sam ba zai yiwu ba. Wannan ne karon farko da suka yi mishi musu a rayuwa. Ko ba komai shima Haruna ya ci rabonsa. A karshe dai Hajiya ta mike ta wuce sashin Hajja ina ta tarar da Zulaihat zaune su na tattauna maganar. "Aa, kenan dagaske dai Uwani ta ke za ki zo?" Hajiya ta harari Zulaihat wacce ita kuma yanda idanun Hajiyar ya yi ja ya ɗaga hankalinta. Ta koramusu duk yanda aka yi. Hajja ta yi salati. "Ke Rabi! Ban ce ki bari zan je na same su da kaina ba?" Hajiya ta girgiza kai. "Ki bar ni kawai Hajja, ni yanzu gobe ma Daura na nufa zan je na sami Baba Mu'azzam da kaina mu tattauna." "Hakan ya kamata ki yi tun farko ba yanzu da muka dawo ba. Meyasa tun acan shi ba ki mishi bayani ba sai yanzu da ki ka je kike kokarin rushe zumuntarku da ƴan uwanki." Hajiya ta kalli Mahaifiyarta da mamakin furucinta, ga dai Hajja girma ya ja amma kyawun jikinta yasa ta ke nan ƙyam da ita tubarakAllah. "Ƙarya na yi kike kallona Rabi? Meyasa za ki tunkare su, ni ban isa ki zo ki fara shawarta ta ba shi ne za ki yi gaban kanki. Yanzu idan wannan ya haɗaku rikici fa? Mun cika alƙawarin da muka ɗaukarwa Babanku kafin rasuwarsa na ganin zumuncinku ya kara ɗanko?" Hajja ta karashe gami da fashewa da kuka. Hankalin Hajiya da Zulaihatnya tashi, suka shiga ba ta hakuri da neman gafara, dakyar ta sauko ta kuma yi mata fada sosai. "Idan irin haka ta faru ba'a yanke hukunci cikin fushi. Hakuri ake yi da kuma kai zuciya nesa." Ta amsa da toh tana sharar kwalla. *** Zufa sosai ya shiga ketowa Halima, kirjinta na dukan tara-tara. Da gaskiyar ƴar uwarta da ta taɓa gargaɗinta akan son abin duniya. _*"Watarana idan ba ki yi hankali ba Halima, son kudinki zai kai ki ya baro. Kuɗi sheggun abu ne da idan har ka sa a ranka za ka aikata komai don ka same su, toh ina mai tabbatar maki cewa wataran za su yi sanadin rushe rayuwarka."*_ "Kin yi shiru Halima." Hajiya Batool ta faɗi tana murmushi yayinda Hajiya Zeenatu ke kallonta cike da nazari tana shakkun ko za ta yi musu abinda suke so. "Ba fa a kyauta za ki yi wannan aika-aikar ba. Hajiya Zeenatu za ta dauki nauyinki ki je duk ƙasar da kike so ki rayu cikin aminci da walwala. Za kuma ta ba ki gida da mota mallakinki. Ke ba wannan ba, duk abinda kike so za ta yi maki. Kawai ke dai ki aikata abinda muke sonki da shi." Halima da jikinta ke kakkarwa ta sharce gumin da sanyin Ac bai sa sun fasa zuba ba. Duban Hajiya Zeenatu da Batool take kamar wasu zakuna wanda kwakkwarar numfashi idan ta fitar bai musu ba za su tashe ta daga aiki yanzun. Ta yi shiru tana nazarin kudaden da kuma sauyin rayuwar da za ta samu. _*"Abu ne da kika jima kina nema, kullum kina cikin kallon hotunan ƴan film da yaran masu hannu da shuni kina kwaɗayin ki samu fiye da haka. Lokaci ne ya yi Halima, mene don ki kashe rai ɗaya tilo kin gudu? Nawa aka yi?"*_ Nan da nan ta samu wani irin sukuni a ranta. Da murmushi ta ɗago ta dube su wannan karon. Wannan ya sa suka dubi juna su ma suka murmusa. "Hakan na nufin kin amince?" Cewar Zeenatu. Ta gyada kai tana dariya. "Ɗari bisa ɗari na amince Hajiya, na tsani Ramlatu sai dai ban zaci zan iya kasheta ba, amma yanzu yanda nake ji zan mata duk abinda ya kama idan har hakan na nufin samun ɗaukaka ta a duniya. Na dai so ace tana raye za ta ga yanda Halima za ta zama, amma ba komai, yaranta za su gane mata." Ta ba su dariya sosai har da cafkewa. Sai kuma aka shiga tattauna yanda za'a yi komai kuma a darennan. Ta yi shiru tama sauraronsu tana gyada kai. A karshe ta ce. "Na amince. Duk yanda ku ka ce zan bi na yi." Murmushi Hajiya Zeenatu ta yi. "Yauwa ƴar gari, yanzu bani lambar ita Ramlat din. Ki tabbata kin isa wurin kafin ta je." "An gama ranki ya daɗe." Tana kai wa aya ta ciro waya ta ba ta duka lambobin Ramlatu guda biyu sannan suka Hajiya Zeenatu ta ba ta kudi har dubu ɗari wai ta ɗan taɓa. Wannan ma ya ƙara zuzuta Halima. Ta fice da murnarta da kuma ɗaukar ALWASHI. *** Hajiya da Zulaihat suka zauna saman kujera, Ramlat ta fito daga ɗaki da sauri. A farko ta yi zatom shiriritar Ansar ne da ya ke batun dawowarsu. Lokacin ƙarfe shida na yamma, don haka ba su yi wani dogon zance ba sai da aka idar da Magriba. Zama suka yi Hajiya ta ba Ramlat labarin duk yanda aka yi. "Ai yau ba gobe ba, ki je ki fiddo kuɗaɗen nan ki kawo su kwana a hannuna. Da kaina zan koma na kai wa Yaya Jamilu." Ramlat kamar ta rungume Hajiyarta don dadi, ta dinga godiya da addu'a. Murmushi kawai Hajiya ta yi. "Shikenan ma kinga sai ki ragemin hanya." "Kai Maman Twins, nan da nan ba mota zan ɗauka ba." "Haba ƴar Hajiya ƴar gatanta, daure don Allah muje da mota kinga ko yaya kika ɗan ragemin zai min sauƙi." Ramlat ta yi murmushi. "Baƙonmu ya zo?" Hajiya ta tambaya. "Eh tun ɗazu, yanzu ma nake shirin zuwa na kirashi mu yi magana. Wallahi duk ya matsu." "Wa kenan?" Zulaihat ta nemi ba'asi. Nan Hajiya ta labarta mata, sosai ta ji ya ba ta tausayi. Ramlat ta mike ta yiwa AlHassan iso, suka gaisa da Hajiya da kuma Zulaihat, a karshe suka yi mishi addu'ar Allah Yasa a dace da abinda ake nema ya yi ta jin dadi da godiya. Bayan fitarsa Ramlat ta bi bayansa gami da ba Zulaihat hakuri kan yanzun za ta dawo. A harabar gidan suka zauna saman kujera. Ya gyara zaman gilashinsa yana dubanta. "Nema ne da muka jima mu na yiwa Hussein, yanzu sai abin kusan muke tunanin ya zo ƙarshe idan har yana raye kuma yana hannun matarnan." Ya ba ta labarin duk yanda suka yi da Rasheed abokin Hussein, ya ƙara da fadin. "Don Allah my sis idan har da wani abu sa kika sani game da matarnan kar ki ɓoyemin. Jikina yana bani ɗan uwana yana raye." Tausayi sosai ya bata don har idanunta suka cicciko da kwalla. Ta sharesu. "Ka kwantar da hankalinka, labari ne mai tsawo kamar yanda na faɗamaka. Shakka babu nasan inda Hajiya Zeenatu ta ke kamar yanda na sani cewa Hussein yana tare da ita tsawon shekarun da ku ke nemansa." Ai wata irin zabura da Alhassan ya yi ya mike tsaye sai da ya razanata. "Dagaske kike?! Hussein na hannunta?! Ya akai kika san Hussein din?! Tashi muje ki kai ni wurinsa don Allah." Jikinsa har rawa yake yi, ga mamakinta ma hawaye ya soma. Dakyar ta kwantar da hankalinsa. "Don Allah ka zauna mu yi magana. Idan har daga jin wannan ka shiga ruɗani, ta ya za ka iya amsar dukkan labarin da zan ba ka?" Hakan da ta faɗi sai ya koma mazauninsa yana jero hamdala ga UbangijinSa. Lallai kukansu ya zo ƙarshe. Hawayen Dada zai daina zuba. "Mami! Mami!!" Suka dubi yaran, AlHassan na ji kamar ya zanesu don sun katsemishi hanzari. Wayarta ce su ke kokarin miƙo mata. Ta karɓa tana fadin mene. "Kira aka yi kuma an miki saƙo." Fadin Ummi, ta karba ta basu umarnin su koma ciki. Har za ta ajiye wayar saman cinyarta, ta hangi suna kamar ma Hussein a karshen saƙon da aka turo wacce lamba ce. "Yi hakuri don Allah." Ta faɗi a gaggauce, hannu na rawa ta buɗe. _*"Za su kashe ni. Ramlat ke kaɗai za ki iya taimakamin. Ki zo ki cece ni. Hussein."*_ Ta karanta ya fi sau uku, hannunta na rawa, wani saƙon ya ƙara faɗowa. Adireshin wurin da yake ne kawai. "Wai meye haka? Innalillahi." Ta furta tana mai mikewa da fashewa da kuka. Da sauri AlHassan ya karɓi wayar don dama ba a nutse ya ke ba. Yana karantawa ya dubeta. "Hussein ɗina zaa kashe?! Su waye? Taho mu je!!" Duk a hargitse ya yi wannan kalamin, ya nufi motarsa amma mukullin na ɗaki, don haka a guje ya koma ciki har yana mance ɓangarensa a gidan yana faɗawa falon Hajiya, ganinsa a rude yasa Hajiya miƙewa tare da Zulaihat. "Lafiya?" Suka nemi sani. Maimakon ya amsa sai ya kasa don haka ya fice, Allah Ya taimaka ya gane dakin, ya shige ya dauki mukullinsa a aljihun kayan da ya fidda. Su Hajiya tuni sun fito harabar gidan inda Ramlat ke safa da marwa cike da tashin hankali tana kuka kamar ranta zai fice. "Meke faruwa?" Tuni AlHassan ya tayar da mota yana mata horn. Ta dubi su Hajiya. "Za su kashe Hussein." "Ki taho mu je ko?!" Tsawarsa ta sa duk suka dubeshi, su Hajiya na ta salati gami da fadin. "Kai Hassan kar ka yi tuƙi a wannan yanayi! Ka tsaya!" Amma ina! Ramlat ba ta ƙarasa rude ƙofar ba ya ja, Baba Maigadi tunda ya ga an tayar da mota ya tsaya bakin gate, ganin ya taho kawai sai ya buɗe masa. Ita ce ta dinga yi mishi kwatance, sai dai kafin su kai wurin saƙo ya ƙara faɗowa. "Dakata!" Ta faɗi da babbar murya. Ya ci wawan burki yana jin wani irin mutuwar jiki, idanunsa da yake gani dishi-dishi a dalilin faɗuwar gilashinsa a ƙasan ƙafafunsa, ya ƙuramata su. "Sun kashe shi?" Yanda ya yi maganar a sanyaye yasa ta dubansa da nata idanun da suka yi kaca-kaca da hawaye.  I just published "BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ffa2oRRGKcb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 47) "Aa, ba kisa ba ne." Ta miƙa masa ya shiga karanta saƙon. "_*Muddin ki ka sake ki ka zo da wani ki tabbatar babu abinda zai hana mu katse numfashin Hussein a doron ƙasa."*_ "Ka bar ni na je ni kaɗai kar su kashe shi." Ta faɗi da gaggawa, da sauri ya ja motar ya gangara gefe. "Kinsan me za'a yi? Sauka ki shiga adaidaita sai na bi bayanki." Ta gyada kai sai kuma ta dube shi. "Toh kuɗin.." Ba ta karasa ba ya hau laluben aljihu, ya zaro kudin da bai san nawa ba ne ya miƙamata. Har ta sa kai ta fita, ta leƙo. "Ka kira Hisham ka sanarmasa, ka kuma ba shi kwatance." Daga haka ta wuce da sauri, Allah Ya taimaka ta samu abin hawa da wuri. Tana shiga yana biye da ita, lokaci guda kuma ya kira Hisham ya sanarmasa komai. Hisham wanda dama hankalinsu ke a tashe sanadiyyar kiran da Hajiya ta yi mishi kan Ramlatun da Hassan. Da gaggawa ya amsa da cewar yana nan tafe da hukuma. Daga haka AlHassan ya kashe kiran. *** Hisham ya gwada kiran wayar Hussein sai dai duk wayoyinsa a kashe. Wannan ne ya sanya shi ruɗewa, ya kuma gasƙata maganar Ramlat haka yake. Da sauri ya mike ya zari mukulli. Aisha ta tare shi tana kuka. "Don Allah kada ka je kai kaɗai" Ya kama gefen fuskarta. "Please ki kwantar da hankalinki, in sha Allah ba abinda zai faru. Ba ni kadai zan je ba, zan biya wurin ƴan sanda." Daga haka ya samu ta gyada kai gami da yi mishi fatan nasara. Hisham koda ya fito bai tsaya ko'ina ba sai babban hedikwatar ƴan sanda na Bompai. Shiga ya yi kai tsaye ya yi report. Kallonsa sosai Sajan ya yi. "Me ce ce shaidarka?" Ya riƙe goshi. "Saƙo suka yi mata, kuma ƙanwata ce." "Ina saƙon?" Hisham kamar ya shaƙe shi ya amsa. "Na faɗamaka ba ni suka aikawa ba, ita da aka aika wa tana can ta kama hanyar zuwa ita kadai ba tare da wani ba. Don Allah ku taimakamin." Har Sajan zai magana sai ga D.P.O ya shigo. "Meke faruwa ne?" Hisham ya dubeshi, baki sake D.P.O ke dubansa. "Aa, Hisham Muhammad, me ka ke yi anan? Lafiya kuwa?" Hisham wanda mamakin ganin yayan marigayin abokinsa, Safwan ya kamashi, a gefe guda wani farin ciki marar misaltuwa ya shige shi. Nan ya ba shi labari a gaggauce. D.P.O Musa ya yi salati. "In sha Allahu za ta kuɓuta, amma na fi tunanin it is just a trap. Gwada kiranta ka ce ta dakata kar ta ƙarasa." Jin haka Hisham ya shiga kiran Ramlat amma ina! Ba ta ɗaga ba. Wannan yasa D.P.O ya ba sajan umarnin maza a ɗauki mota a je. Ba shiri suka dunguma suka fita Hisham na mishi godiya. *** Fili ne sosai na makarantar Gwamnati, unguwa ce mai masifar shiru, sai a kwashi tsawon mintuna talatin ba ka ga abin hawa ko ɗaya a wurin ba. Mai Adaidaita na ƙorafi da tambayarta abinda ya kawo ta irin wannan wuri sai dai ba ta tanka masa ba. Kiran Hajiya har da su Hisham da Yaya Munir yana ta shigowa sai dai ba wanda ta amsawa. Text ya faɗo ta yi saurin dubawa hannunta har rawa yake sai dai ba ta fasa addu'a ba,ba ta fasa maimaita addu'a a zuciyarta ba. 'ALLAHUMMA ANTA 'ADHUDEE WA ANTA NAASIREE, WA BIKA UƘAATILU' (Ma'ana: Ya Allah Kai ne Majinginata, kuma Kai ne mai taimakona, kuma da Ƙarfinka ne zan yaƙesu). _*"Mun hangoki, ki tabbatar da tafiyar mai napep ɗinnan, ki tako ki shigo makarantar ke kaɗai. Ki tabbata kin kashe wayarki."*_ "Tsaya! Ya isa. Anan zan sauka." Yanda ta faɗa sai da ya tsorata mai napep din har ya juyo ya dubeta, hasken fitilar motar bai sa ha ga fuskar sosai ba. Ya ja ya tsaya ta sauka ta miƙamasa kuɗin. "Chanji fa?" "Na bar maka." Ta faɗi ka tsaye, ya yi godiya ya kaɗa abin hawa ya juya ya tafi yana waigenta da mamaki. Ta ci gaba da addu'a tana dosar cikin makarantar bayan ta kashe wayar gaba ɗaya. Mamaki da tsoro ta ke yi, me zai sa a kama Hussein a kuma kwo shi irin wannan wuri? Tafiya sosai ta yi har ta soma shiga wuraren ajujuwa. *** AlHassan ya fito daga motarsa a hankali ya shiga takowa zuwa cikin filin da duhu ya mamaye sai kadan daga haskenfarin wata. A hankali ya ke tafe, madadin ya bi inda Ramlat ta bi sai ya zagaya. Wayarsa a mota ya bar ta gudun kada haskenta ya ankarar da su wanzuwarsa a wajen. *** Halima wacce ta ci riga da wando baƙaƙe ta kuma sanya mask a gaba ɗaya fuskarta tana hango Ramlat. Yanda Ramlat ke ƙara takowa haka kirjinta ke bugu fat! fat! Ta kai duba ga mutumin da ta sanyawa baƙin kyalle ta rufewa fuska gaba ɗaya. Cikin raɗa-raɗa ta ce. "Ta taho, ka soma acting." Ya amsa da "An gama!" Halima ta ƙara lalubo aljihunta ta fiddo bindiga. Ta nufi Ramlat. *** Ramlatu dake cikin tafiya sai ji ta yi an rufe mata baki da ƙarfi, ta shiga kokarin kwatar kai sai jin bakin bindiga ta yi a saitin kanta. "Ina Hussein yake? Na ji idan zai tsira ni ku kashe ni don Allah amma kar ku kashe Hussein." Daga haka aka soma tafiya da ita har inda wani mutum da ta ga inuwarsa kadan sakamakon hasken farin wata, yana ta walainiya da kai alamar ya jigata sosai a hannunsu. "Ramlat." Ya faɗi da wani irin sanyi kusan kalar muryar Hussein da ya yi haddarsa. Kuka sosai Ramlat ta shiga yi. Za ta nufeshi Halima ta ƙara yo baya da ita. Juyo da Ramlatun ta yi, Ramlat ba damar gudu. Hankalinta na kan Hussein yayinda idanun ke kallon masheƙin da ke tsaye a gabanta. "Mene ribarku idan kun kashe Hussein? Me ku ke da buƙata?" Wata dariya Halima ta yi kamar ta yara ƙanana, ta sauya murya. "Ubanki za mu yi! Ai ke muke nema! Ke kuma aka ce mu kashe ba Hussein ba. Kai Gwaska!" Tana fadin haka wanda ke zaune da ta yi zaton Hussein ne ya miƙe ya yakice kyallen. Nan ta ga wata sura marar kyan kallo don kamar babu ɗigon imani cikinsa. Ya ƙaraso, yanzun ne tunanin Ramlat ya ba ta cewar tarko ne aka yi mata kuma ya faɗa. Da wani irin sauri ta ja gefe ta yunkura za ta gudu, tuni Gwaska ya damƙe ta tana kokarin ihu ya rufemata baki. "Ki kashe ta! Me kike jira?!" Ya yi maganar a tsawance ganin Halima ta kasa sarrafa bindigar kamar yanda ya koyamata. Ta runtse idanu ta harba ba tare da saiti ba. Wata ƙara Gwaska ya saki sakamakon samunshi da ta yi a cinya. Ramlat ganin hakan ta ture shi za ta gudu, Halima ta damƙota. "Ki kashe ta nace!" Gwaska ya fadi iyakar karfinsa yana dafe da cinyarsa. Jin haka AlHassan ya fito daga maɓoyarsa sai dai kafin ya karasa tuni Halima ta ƙara sakin bindigar wanda cikin sa'a ta samu Ramlat a kafaɗa. "You are under arrest!" Muryar mutum suka ji. Gaba daya suka juya, fitilun motocin da ke shigowa gurin ya haskewa Halima fuskar AlHassan. Ta zaro ido ta cikin mask din fuskarta. Hussein ne?! Hajiya dama karya ta yi da ta ce ta saka shi bacci? Ganin haka ta yunkura za ta gudu sai dai da wani irin zafin nama na ɗaya daga cikin ƴan sandan, ya cafketa tana kiran wayyo Allah. Ramlat dake zube anan tana gani dishi-dishi hannunta na dafe da kafaɗarta da Gwaska ya samu. Ba shiri ta zube a ƙasa. Wani irin sunguma da AlHassan ya yi mata a gigice yana ambaton sunanta, amma ko motsi. "Kai ta mota mu je asibiti!" Hisham daga bayansa ya faɗi a gaggauce. Kafin ka ce me, sun isa mota tuni rigar AlHassan ta ɓaci da jini. Hisham ya bada umarnin tafiya da su Gwaska da nufin zai je station din daga baya. Suka tafi da ɗan sanda saboda ba da shaida. Munir wanda ya taho, suka yi waya ya ke sanarmasa halin da ake ciki, hankali a tashe ya juya kan abin hawa ya nufi asibitin da Hisham ya kwatantamasa. Kafin su je ya riga su isa, don haka suna zuwa ya tarbesu. Shi ya karɓi Ramlat ya ƙarasa ciki da ita. Sai dai aka kammala dukkan wani sa hannu aka hau ceton rai da gaggawa. Munir ya kira gida ya faɗawa Zulaihat wacce ke faman kiransa a waya. Jin abinda ya faru daga ita har Hajiya suka kasa zama gidan suka nufo asibitin. "Laifina ne, meyasa na bar ta ta je ita kaɗai ban maramata baya ba?" "Ka daina faɗin haka Hassan, rai da ajali duk a hannun Ubangijin al'arshi su ke, kaddararmu ce haka. Mu yi fatan samun saukinta." Hajiya ta faɗi tana mai sharce hawayen saman kuncinta. AlHassan hankalinsa sam bai kwanta ba, ga tsananin son ganin Hussein da ya ke yi. Yanzun da ya san inda yake sai ya ke jin kewarsa ta ƙaru. Fitowar Likita ne yasa suka dubeshi. "Alhamdulillah an cire harsashin, ba dai ta farfaɗo ba. Amma muna sa ran komai zai zo da sauƙi. Dafin bai shiga jikinta sosai ba." "Alhamdulillah." Suka furta kusan a tare. Hajiya ta dubi Zulaihat bayan sun gama addu'a da godiya ga Allah. "Uwani maza ki wuce Muniru ya sauke ki gida, dare ya yi. Ni zan tsaya anan da ita." "Aa Hajiya, ba za'a yi haka ba. Su Ummi da aka bari a gida fa?" Cewar Zulaihat. "Ina ce Ladidi na nan? Zan ƙarasa na nemi alfarma ta kwana yau dai ɗaya. Daga nan zan haɗaku a waya idan da abinda ki ke buƙata sai na dawo na kawomaki. " Faɗin Munir yana mai ƙarashewa da mayar da akalar zancen ga Hajiya. Suka yi na'am, Hajiya ta ƙara duban AlHassan. "Hassan sai hakuri ka ji? A kara godewa Allah tunda a baya ma ba'a san inda yake ba. Yanzun kuma da Allah Ya nuna in sha Allahu komai zai zo karshe. Kar wannan ya dameka. Ya kamata ka wuce gida duk ka ɓata jikinka da jini." AlHassan ya jinjina kai yana gyara zaman gilashinsa, suka yi sallama aka tafi aka bar Hajiya ita kaɗai ta na jiran likitoci su kammala su ba ta umarnin shiga. A harabar asibitin bayan tafiyar Munir da Zulaihat, Hisham ya dubi AlHassan. "Dama nayi mamakin ta yanda za'a ce wani abin zai sami Hussein. Ba wai ba za ya taɓa faruwa ba ne, sam aa, sai dai idan har zargina ya tabbata da hannun Hajiya Zeenatu a abinda ya faru ga Ramlat to ba zai taɓa zamtowa an riski Hussein a wurin ba. A irin son da Zeenatu ke yiwa Hussein ba za ta bari a haɗa baki a cutar da shi ko ya ya ba." "Kai ma kana da labarin Hussein kenan?" AlHassan ya tambaye shi da gaggawa. Ya gyaɗa kai yana duban agogo. "Ina da labarin komai, na taƙaice maka Hussein aminina ne, bani da aboki sama da shi a faɗin duniya. Sai dai kuma ya dace ko me zamu yi kada ya wuce gobe, idan ba haka ba za mu rasa damar mu." "Me kake nufi?" Tiryan-tiryan Hisham ya ba shi labarin duk abinda ya sani dangane da Hussein. Ya ɗora da faɗin. "Babu damar a yiwa Hussein zancen ƴan uwansa, ba ya so. Da zarar ka tambaye shi game da asalinsa, kansa zai ɗau zafi ya sauya gaba ɗaya. Ransa kuma idan ya yi dubu toh zai ɓaci. A ranar idan mutum bai yi dagaske ba girmansa zai iya faɗuwa a idanun Hussein." "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Mace ce? Ita ta rabamu da Hussein? " "Hum, sai addu'a." Hisham ya furta, a ƙasan ransa yana jimamin yanda AlHassan zai ji idan ya gane da sa hannun Kawunsa ciki. Hakan yasa bai faɗamasa ba har sai gaskiya ta yi halinta. "Ya za'a yi na gan shi yanzu? Bana so su kai ga barin ƙasar." "Kada ka damu, a gobe da safe in sha Allah zan haɗaka da ɗan uwanka. Za ku ga juna." Murmushi AlHassan ya yi mai haɗe da dariyar farin ciki, kasa hakuri ya yi sai da ya rungume Hisham yana murna. "Na gode, Na gode sosai. Allah Ya bar zumunci." Hisham ya yi dariya gami da dukan kafaɗarsa. "Ameen. Kar ka samu damuwa. Ka kara godewa Allah, sannan Ramlat. Ba karamin namijin ƙoƙari ta yi akan ɗan uwanka ba." Murmushi sosai AlHassan ya yi tare da fatan Allah Ya ba ta lafiya. Hisham ya amsa kafin su yi sallama, shi ya nufi gida, Hisham kuwa ya zarce Police Station don jin abinda ake ciki. *** _*LAMIƊO CRESCENT*_ Safa da marwa ta ke faman yi a tsakar falon, ta ɗauki waya ya fi a ƙirga. Kiran Halima ta ke jira kamar yanda suka yi alƙawari.Ta kira Hajiya Batool ya fi sau goma don ta ji ko sun yi waya amma shiru ka ke ji, Malam ya ci shirwa. Ta kara kai idanunta kan wayoyin Hussein da ke ajiye saman kujera. Baƙin kishin Ramlat ya ƙara ƙarfi a zuciyarta. Ta gwada amfani da yatsarsa ta buɗe wayar, hakanan ta gwada shiga lambobin Ramlat, HEART da ta gani a rubuce ya sanha ta saki ƙarar da har sai da John suka fito daga kicin zuwa falo. Ta dakamusu tsawar da dole suka koma. Hajiya Zeenatu ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani malolon abu ya tokaremata maƙoshi. Awanni biyu kenan da ta ba Hussein lemo ya sha wanda ya yi sanadiyyar baccinsa, a wannan lokacin ba abinda ta ke burin ji sai saƙon mutuwar Ramlat. Wayarta ta yi ƙara da wani irin zumuɗi ta duba. Tsaki ta ja ganin lambar Kawu Modibbo, sai da ta kalli ƙafar benen ta tabbatar babu mai saukowa sannan ta amsa a fusace. "Ina jinka." "Ya ake ciki?" Ta safe goshi gami da runtse ido cikin soma gundira da  tunani. "Ni kaina na gaji da tambayar kaina. Abinda ya fi shi ne zan nemi Halima har gidansu na bincika." "Ga dukkan alamu lamura sun ɓaci." "Ina tsoron hakan ta kasance." Ba ta jira cewar Kawu ba ta kashe kiran. "Zeenat." Da wani irin ruɗewa ta juyo tana dubansa, yana dafe da goshi a hankali kuma ya shiga saukowa daga matattakalar. Ta yi kokarin saita kanta ta karasa gareshi da murmushin yaƙe. "Sannu, ka sha bacci." Hussein ya gifta ya karasa ya zauna saman kujera kansa na ci gaba da sarawa. "Me ki ka ban na sha?" Ya tambaya ba tafe da ya kalleta ba. Ta zauna gefensa. "Ba ka samun bacci yanda ya kamata, ga gargadin likita da ya ce ka dinga samun hutu, shiyasa na sanyamaka maganin bacci a lemu na kashe wayoyinka." Ya dubeta da idanunsa da har sannan ba ya jin baccin ya sakeshi. "Haba Zeenat, shi ne dalilin sanyamin  maganin bacci? Meyasa haka? Wane irin hutu ne ba na samu? Cuta ba ta Allah ba ce?" "Hakane, to ka yi hakuri." Ya mike rai a ɓace ya ɗauki wayoyinsa ya haye sama. Ta bishi da kallon munafuki karon farko a rayuwarta. "Ka ci darajar son da nake maka Husseini, da yau sai ka gane shayi ruwa ne." Ta furta a hankali yanda ta san ba zai ji ba. Har hango hotonsa da Ramlat ta ke yi a kwayar idanunta. Takaicinta, meyasa ba ta nemi kwararrun ƴan daba sun aiwatar mata da komai ba? Meyasa sai Halima? Ta ja tsaki tana sharce gumin da fargabar ko Hussein ya ji wayar da ta yi ya haifarmata. *** "Ita kuma wace ce wannan?" Hisham ya tambaya yana karewa Halima da ke faman sharɓar kuka a bayan cell  kallo. "Sharrin shaiɗan ne wallahi, don Allah don Annabi s.a.w ku yafemin wallahi nayi alƙawari ba zan ƙara ba. Nima san..." _*"Halima, ki tabbata koda wasa aka samu matsala, kar bakinki ya yi kuskuren ambaton sunan ɗaya daga cikinmu. Ki ce kawai dai kina kishin Ramlatun za ta auri Chairman dinku ne. Ki ka kuskura ki ka yi gangancin tonamana asiri, ki sani rayuwarki ce za ta ƙare a doron ƙasa saboda za mu bar ki ki rayu kuma ki mutu a gidan yari ba tare da mun ɗauki matakin fiddoki ba. Idan kuwa ki ka bar komai a cikinki ki ka faɗi yanda na ce, toh shakka babu ina mai tabbatarmaki ko kwana uku ba za ki yi a hannun ƴan sanda ba za mu sanya a fiddo ki kuma ki bar garin. Idan kunne ya ji....jiki ya tsira."*_ "Kin yi shiru? Me ki ke son ki ce?!" Tana kuka sosai ta dubi Sajan da ke mata tsawa, a gefensa Hisham ke tsaye yana jiran ji daga bakinta. Girgiza kai ta yi. "Nima sharrin shaidan ne." "Ƙarya ki ke! Ba haka ki ka so ki ce ba!Ki fito ki faɗi wanda ya sanya ki!" Cewar Hisham a ruɗe. Ya ja, itama ta ja. Gwaska tuni an yi asibiti da shi. Dole haka Hisham ya hakura ya bar case hannunsu sannan ya wuce gida, lokacin sha biyu ta wuce. *** WASHEGARI... Da sassafe Hajiya Zeenat ta shirya. Motsinta ne ya tashi Hussein dake bacci. Ya dube ta sadda ta ke kokarin ficewa daga ɗakin. "Lafiya? Ina zuwa haka da sassafe?" A firgice ta juyo tana dubansa,ta wayance da yaƙe. "Am..am..dama Hajiya Batool ta kirani ba lafiya har an kai ta asibiti ma. Shi ne zan je dubiya." Ya gyada kai kawai ya juya ya kara jan bargo, ta sauke ajiyar zuciya ta fice. Ta bar Hussein da tunanin irin nasu auren, wannan wane irin aure ne da mace ke da ikon fita ba tare da iznin miji ba? Anya kuwa hakan zai haifarmusu da ɗa mai ido?  Ya sauke ajiyar zuciya gami da lumshe idanu cikin tunanin laifinsa ne tunda tun farko haka su ke yi. Bai kuma san ya hakan ta faru ba.   Wayarsa ce ta yi ƙara, sunan Hisham ya gani yana murmushi ya ɗaga. "Kira da safiyar Allah, bashin me na ci?" "Haba Malam, ina ka shiga ne wai? Jiya na kira duka wayoyinka amma a kashe, lafiya dai ko?" Hussein ya lumshe ido ya ja guntun tsaki tuno da shirmen Zeenatu. "Share kawai, lafiya lau ne. Ya aka yi?" "Ba ka da labarin an kai wa Ramlatu hari?" Wani irin miƙewa Hussein ya yi gaba ɗayansa har santsin bargon na ƙoƙarin kifar da shi ƙas. "What?" Labarin komai Hisham ya ba shi. "Tana wane asibitin?" Ya sanarmasa. "Yanzu zan zo." Daga nan ya katse kiran bai jira komai ba. ***    MISALIN ƘARFE TAKWAS NA SAFE...   Hawaye ta ke fitarwa yayinda ta ke tariyo komai a kwanyarta. A yanzun da Hajja ke salati da tambayar wa zai aikatamata hakan? Itama a sannan kwakwalwarta ta shiga aikin tunani. Kasancewar ta juyamusu baya ya sa ba wanda ya lura da tashinta. Cikin dare dai ta farka sannan ta ƙara komawa bacci. "Abin dai da ɗaure kai." Hajiya ta furta tana ƙara riƙe carbin hannunta da ta ke ja. "Nifa ina zargin matar Hussein wallahi. Tunda..." "Yi shiru kawai Rafee'ah, zato dai zunubi. Irin haka ne sai ki ga ana zaton wuta a maƙera sai aka same ta a masaƙa." Rafee'ah ta yi shiru amma dai kam zuciyarta cike take da zarginta. Kwankwasa ƙofar da aka yi ne suka bada iznin shigowa. Hisham ne da AlHassan, suka karasa aka gaisa. "Kada dai ace har yanzu ba ta farfaɗo ba?" Cewar Hisham. "Aa, ta farfaɗo cikin dare, har na taimaka ta ɗan zagaya. Sannan ta yi salla da Asuba ma. Baccin ne dai ya ƙara kwasarta." Ramlat da ke jin bayanin Hajiya sai ta runtse idanu, wani radadi kafaɗarta ke mata, sai dai idan har za ta iya jure wannan adalilin Hussein, idan har zaa iya yaudararta a kafamata tarko a kansa, toh ba karamin so ta ke yi mishi ba. Ta ƙara aminta da hakan. "Au dama idanunki biyu?" Cewar Rafee'ah wacce ta zagayo domin gyaramata ɗankwalin kanta da ya zame. Ta dube ta, ganin tana hawaye ta sa hannu ta shiga sharemata. "Haba Ramlat, meye kuma na kukan tunda Allah Ya riga da ya tsare? Yi shiru don Allah. Ko za ki tashi zaune?" Ta gyada kai. Da taimakon Rafee'ah ta miƙe zaune ta jingina da filo. Ta gaida Hajja da su Alhassan. Wayar Hisham ta yi ƙara ya duba, shi kansa AlHassan tunda ya ji batun zuwan ɗan uwansa ya rasa sukuni. Burinsa kawai ya gan shi don ya tabbatar da komai. Aikuwa shi ɗin ne. "Kana waje? Ok gani nan zuwa." Yanda Hisham ya miƙe hakanan shima AlHassan ya mara mishi baya. Rike hannunsa ya yi. "Ka yi hakuri, nan zai shigo, ka jira ya karaso ciki ka ganshi." Ramlat da kirjinta ya tsananta bugu ta dubi Hisham a hargitse. Nan da nan wasu hawayen suka kwaranyo. Baki na rawa ta ce. "Hussein..Hussein ne?" Hisham ya dubeta. "Shi ne, ku kwantar da hankalinku yanzu zan kawo shi." AlHassan a dole ya dakata sai dai ya kasa tsayuwa wuri guda, safa da marwa ya shiga yi yana kallon ƙofa. Koda aka tura ƙofar aka shigo. Hisham din ne a gaba, a bayansa kuma Hussein. Kamar wani gunki haka AlHassan ya ja burki yana kallonsa ƙurr. "Hussein...?" Ya furta, furucin da ya ja hankalin Hussein dake sanye da Maroon shadda da hula, ya dubeshi. I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/IRx4QB4kMcb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 48) Kallonsa yake yi sosai kirjinsa na bugawa da sauri. Ramlat ta runtse idanu tana mai addu'ar komai ya tafi daidai. Da wani irin sassarfa AlHassan ya tako ya rungume Hussein kawai sai ya soma kuka. "Hussein." Ya ƙara kiran sunansa karo na biyu, Hussein ya yi ɗif sai hawaye da ke zuba saman fuskarsa. Ji ya yi kamar ana saramasa guduma a tsakiyar kansa, a hankali ya soma ganin dishi-dishi, lokaci guda idanunsa suka juye yayinda baƙin kwayar idanun ta ɓace ɓat. Hisham da ke tsaye a baya shi ya lura da sauri ya karasa ya rike Hussein. Jikinsa wani irin kakkarwa ya ke yi. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Cewa Hisham yana rike hannun Hussein, jin haka AlHassan ya ɗago wanda saura kiris Hussein din ya zube don kuwa da jikinsa ya samu madafa. "Riƙe shi sosai." Cewar Hisham, suka taimaka suka fitar da shi sai wurin likita. Ramlat tuni ta miƙe tsaye. Su kansu su Hajiya sun rude. Ganin tana kokarin ficewa yasa Rafee'ah riƙo ta. "Ina za ki je? Ba ki ganin halin da ki ke ciki? Idan kin je lafiya za ki ba shi?" Ta girgiza kai tana hawaye, ta bude baki sai dai ta rasa me za ta ce don haka ta koma ta zauna. Hajiya ce ya fidda waya don ta kira Malam ta sanarmasa halin da ake ciki. Nan take ya ce maza ta aiko a karɓi ruwan da ya haɗa da ganyen magarya ya yi addu'o'in karyewar sihiri. Ba shiri ta yiwa direbanta waya ta ce ya biya Yakasai ya karɓo mata saƙo. ***   Duk iyakar awon da likitocin su ka yi ba su gano komai game da ciwon Hussein ba. Don haka koda suka samu ya bar jijjigar, idanun suka dawo daidai sai Likitan da ya karɓi Hussein ya fito wurin su AlHassan. Suka tarbe shi da gaggawa. "Ku yi hakuri.." "Mutuwa ya yi?" Faɗin AlHassan a gigice, girgiza kai Likitan ya yi yana mai riƙe hannunsa. "Ko kusa ba haka ba ne, asalima yanzu mun samu komai ya daidaita. Sai dai hakikanin gaskiya ba za mu ce ga abinda ya jawomasa hakan ba, yanzu dai halin da ake ciki, dole zamu yi mishi tests don mu gano ainahin inda matsalar take." Suka jinjina kai. "Ba damuwa Dakta. Allah Ya ba shi lafiya." Cewar Hisham da hankalinsa ya ɗan kwanta. Bayan wucewar Dakta ya dafa kafaɗar AlHassan wanda ya cire hular kansa tsabar gumin da fargaba ta haifarmasa. "Kada ka damu ɗan uwa, na fadamaka dama duk sadda maganar dangi ko ƴan uwa ta haɗa mu da Hussein ya kan shiga wani irin hali, ina kuma ga yau ya yi ido huɗu da ɗan uwansa?" "Hakane, sai nake ganin kamar ba na asibiti ba ne." AlHassan ya faɗi bayan kai karshen nazarinsa. "Hisham, ya jikinnasa?" Suka juya, Rafee'ah ce. Ta karaso suka yi mata bayani. "Allah Ya ba shi lafiya. Kada ku damu, Hajiya ta aika a karɓo ruwan ganyen magarya mai addu'o'in karya sihiri, da yardar Allah komai zai daidaita." AlHassan ya sauke ajiyar zuciya yana ɗan murmushin jin dadi da wani irin kaunar zuri'ar da ke kara mamaye zuciyarsa. "Na gode kwarai, Allah Ya sakamaku da alheri. Allah Ya bar zumunci." Ta yi dariya kadan. "Ameen. Ai yiwa kai ne. Bari na koma, dama Hajiya ce ta ce na sanarmaku sannan na gano halin da yake ciki don marar lafiyarmu ta tashi hankalinta sai kuka ta ke yi." Murmushi AlHassan ya yi yana mai hasashen wani abu da tun a jiya ya yi zaman dirshan a kwakwalwarsa. *** TA FARU TA ƘARE... "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Halimar aka kama?!" Hajiya Zeenatu ta faɗi tana tsaye a bakin ƙofar gidan Kakar Halima wacce ke rike da ita. Ƙanin Halima uwa daya uba ɗaya wanda daga ita sai  shi, su uku iyayensu suka haifa kafin rasuwarsu, dayayar Halima, Halima sai Yusufa. Kakarsu ta karɓi riƙo. Yusufan ya share hawaye yana duban Hajiya Zeenatu. "Wallahi ranki ya daɗe, ɗazu aka yi mana waya, naje har ofishin ƴan sandan na sami Aunty Halima, wai dumu-dumu aka kama ta da bindiga za ta yi kisa. Wannan abu ne da ko a mafarki ba mu zaci faruwarsa ba. Su biyu aka kama, shi ɗayan ko Gwaska ko wa? Yana asibiti. Yanzu Kaka na kwance ba lafiya tun da ta ji halin da ake ciki." Hajiya Zeenatu wacce ta yi mutuwar tsaye, ta yi sauri ta dawo hayyacinta. Baki na rawa ta ce. "Ta..ta..faɗi wadanda suka sanya ta?" Kallon da Yusufa ya yi mata na nazari sai da ya sa ta sakin ƙaramar tusa mai haɗe da fitsari ba shiri. Ya girgiza kai. "Abin kunya ne ace saboda ɗa namiji za ta aikata hakan. Kishi ne kawai don uban gidansu na aiki zai auri abokiyar aikinta Ramlat. Haka ta sanarmin." Ya karashe da wani irin jin kunya. Ajiyar zuciya Hajiya Zeenatu ta sauke ta juya za ta shige mota. "Amm..Hajiya, na ce sai dai ban sanki ba. Kema wurin aikinta ki ke ne?" Ta juyo. "Eh, tare muke aiki." Tana kaiwa nan ta juya da sauri ta faɗa mota, ta ja. Kiyayewar Ubangiji ce kawai ta isar da ita gidan Hajiya Batool. Itama nan ta iske ta su na dambe da surukarta. Dakyar ta raba su. Ɗan Hajiya Batool ba ya nan ya yi tafiya Dubai, shi ne surikar ta zo gidan kwana. "Haba Hajiya, me ya yi maki zafi za ki tsaya dambe da suruka? Ke kuma don ba ki da kunya wannan ba uwar mijinki ba ce?" Fareeda wacce ke tsaye tana huci ta narkawa Hajiya Zeenatu uwar harara kafin ta saki dariya gami da tafa hannu. "Ahayye! Ai fa da yake daga ke har ita jirgi ɗaya ya kwaso ku dole ne ki ga laifina! Tsoffin banza da ba su riƙe girmansu ba ai ba zan ji kunyar taka su son rai ba. Kin tauye hakkin yaro kin danne kina zaune da shi! Ko an fadamaki bani da labarin mijinki? Kina kai min uwar miji yawon bin bokaye don mijina ya ƙara aure ko? To wallahi karyar ku domin tun kan a haifi uwar mai sabulu balbela ke da farin kai. Don haka idan ku na son na lulluɓe dukkan sirrikanku to ku tabbatar an fasa batun auren Mijina da kowace shegiyar kucaka. Idan kunne ya ji..." Ta ƙarashe da rike kunne kafin ta wuce tana dariya ta bar su baki galala. Bayan shigewarta ɗaki Batool ta yi gaba ta haye sama, Hajiya Zeenatu ta bi ta a baya. Su na shiga ɗaki suka sa mukulli. "Batool akwai matsala!" Hajiya Batool da ta zauna rike da ƙugu tana ambaton wash sakamakon cizon da ta sha a wurin Fareeda. Ta amsa wa Hajiya Zeenatu kamar za ta yi kuka. "Matsala nima cikinsa kika tarar da ni Zeenatu. Kamar Gora yaudararmu ya ke yi yana cin dukiya a ɓagas. Ni na rasa kan wadannan lamuran." Hajiya Zeenatu ta yarfar da jaka da mayafi, da sauri ta faɗa banɗaki. Can kuma ta fito ta zauna tana sharce gumi. Ta kora dukkan bayani ga Hajiya Batool gaba dayanta a rude. "Ya zan yi ne Batool? Ga Visa ta yi wuya an ce mu kara hakuri zuwa sati na sama, ga wannan lamari na neman kwaɓemin? Ba mu ga ta zama ba Batool, ta inda aka hau dai ta nan ake sauka idan ba haka ba mai afkuwa za ta afku. Ba ni da tabbacin Halima ba za ta tonamana asiri ba. Ban san iyakar lokacin da za ta riƙe sirrinmu matsayin sirri ba. Wannan fa barazana ce garemu. Tashi za ki yi mu kama ƙafa muje mu ga Gora tun kafin komai ya lalace." Hajiya Batool ta share hawayen takaici, yau ita suruka ke dambe da ita,  ta rantse sai ta ga bayanta tunda dama ba ta haifarmata ko ƴartsana ba sai afkin ci da kasayarwa. "Muje. Bari na lallaɓa." Ta miƙe dakyar ta dauki gyalenta. Suka fice. Fareeda na leƙensu ta window ta yi dariya ta saki labule. A fili ta ce. "Munafukan banza, da alama an tafi yawon abinda aka saba. Zama daram ni Fareeda!" Ta furta tana mai zama kan gado tana dariya. ***   Tunda Hajiya Zeenatu ta sanarmasa da batun kama Halima ya gaza samun nutsuwa. Don haka ya kira Dada a waya karon farko. Hakan ba karamin mamaki ya ba ta ba don har sai da ta ce. "Yaya lafiya dai ko?" "Ah lafiya kalau mana Amina, ba damar na kira ki kenan sai idan babu ita? Mtsw. Ina yaran nan kuwa? Husseini? Yana gari?" Dada ta amsa a sanyaye. "Aa, ya shigo nan Kano wani uzuri na ma'aikatarsu, bai ƙaraso nan ba?" Wani zufa ya karyowa Kawu a goshi, ya samu wuri ya zauna ɗabas! Sai ya ɓige da faɗan borin kunya. "Ina na isa dama ya zo wurina? Ai ban isa ba! Kin koyawa yara tsanata da tsanar iyalina. Sai ki yi idan hakan zai haifarmaki da ɗa mai ido! Mu din dai mu ne nasu." Daga haka ya katse wayar bai saurari ban haƙurin Dada ba. Miƙewa tsaye ya yi yana sunturi, ba zai yiwu ba. Babu abinda zai ruguza dukkan sirrinsa. Idan ya tabbata lamarin Hussein ne ya kawo AlHassan garin Kano kamar yanda Bokansa ya buga ƙasa ya bincikamasa, toh shakka babu komai ya rushe. Tonuwar asirinsa kamar jin kunyarsa ne a cikin dangi, ya san duk tsanar da sauran yan uwansa suka yiwa jinin Aminu da Amina (Dada), bai kai tsanar da ya yiwa HUSSEIN ba. Ya dau waya ya dannawa Hajiya Zeenatu kira, haka ya yi ta ringing ba'a ɗaga ba, wannan yasa shi kasa zama ya fice daga gidan don ƙara tuntuɓar Bokansa karo na ba adadi. *** Ya mike zaune dakyar daga saman gadon da yake kwance. A hankali ya dafe kai yana salati. "Sannu Hussein, ka tashi?" Ya dubi mai maganar da sauri, shi dai wanda ya gani a ɗazun ne mai kama da shi. Ɗan uwansa da ya daina sanyawa a idanu shekara da shekaru. Ƙuri ya yi mishi da idanu, daidai nan Hisham ya miƙamasa kofin ruwan tofi. "Shanye duka please." Ba musu ya karɓa ya shanye tas. Kamar yanda jini ke zagaye a cikin jiki, haka ya dinga jin ruwan na zaga dukkan wata gaɓɓa ta jikinsa, a hankali hawayen da suka sauya kalar kwayoyin idanunsa suka samu damar kwaranyowa saman kuncinsa. AlHassan ya taso ya zauna a gefe gami da sanya hannu cikin nasa. "Hussein, ka gane ni?" Gyada kai kawai yake yi bakin na rawa amma kalmar A ta kasa fita daga bakinsa. Kawai sai ya ɗora hannunsa haɗe da na AlHassan saman goshi ya shiga kuka kamar ransa zai fita. Hisham a hankali ya juya ya fita daga ɗakin yana share kwallar dake kokarin zubowa a kokarinsa na katse ta yana mai hamdala ga Mahaliccin Sammai da kuma Ƙassai. "Na gane ka. AlHassan Aminu Gidado." Hussein ya furta da kakkarwar murya, jin haka AlHassan ya ƙara jan sa a jiki shima yana kukan. Zai so ace Dada na zaune a dakinnan, matar da idanunta ba su taɓa kafewa da zubar hawayen rashin Hussein ba. Kullum kiranta, amanar Allah ne su din a hannunta, koyaushe ɗorawa kanta laifin ɓatan Hussein ta ke yi. "Ina Daa...da, Baba Naziru.?" Hussein ya tambaya, AlHassan ya ɗago fuskarsa da wani irin murmushi mai haɗe da dariya-dariya. "Dada tana nan, tana nan kullum cikin kuka da addu'ar Allah Ya nunamata kai. Babban burinta ta samu wani ko wata da zai kawomata kai koda labarin mutuwarka ne, ita dai ta san cewa ka mutu cikin musulunci kuma an maka kyakkyawan sutura. Da yawa ya faru bayan gushewarka Hussein, abubuda da dama sun faru garemu da baki bai isa ya buɗamaka su ba." Hussein ya jinjina kai yana jan hanci. "Eh, da yawa ya faru. Irin yawan da ban taɓa kawo wa kaina a rayuwa ba. Ban sani ba ko ni na jazawa kaina ko kuwa dai.." Rufemasa baki AlHassan ya yi yana girgiza kai. "Kar ka ce komai ɗan uwana, ka yi shiru mu ƙara godewa Allah da ganin wannan ranar da muka kwashe shekaru muna jira. Haɗuwa da Ramlatu alheri ne garemu baki ɗaya. Ina zan manta da ita da zuri'arta?" Hussein ya ci gaba da dubansa da idanunsa da suka kaɗa. A idanun AlHassan ya gano karin bayani ɗan uwannasa ke nema. Murmushi ya yi. "Mai hali ba ya fasa halinsa, ashe ba ka sauya ba?" Suka yi dariya gami da ƙara rungume hannun juna gam! Kamar ance ga wani abu zai ƙara raba su. Tirya -tiryan ya ba shi labari tun daga haɗuwarsa da Ramlat har zuwa yanzu da aka harbe ta sanadinsa. Hussein ya yi shiru, ya rasa me zai ce. Ya kuma rasa wane yanayi ya ke ciki, tunani sosai ke neman shigarsa don haka ya gaggauta yanke tunanin. "Mu je na ganta don Allah." Ba musu suka mike, ya zura takalmansa, bini-bini za su kalli juna shi da ɗan uwansa su yi murmushi, haka suka jera idanun jama'a a kansu don ba karamin burge su suka yi ba musamman masu juna biyu, nan suka fara addu'ar su ma Allah Ya basu ƴan biyu masu bala'in kama irinsu, su gan su sun girma haka tare. ***   Gora ya duba, ya ƙara buga ƙasa ya duba, ya ɗago kai ya kalli Hajiya Zeenatu da Hajiya Batool da ke zaune gabansa cike da wani fargaba da tsoro. "Lafiya dai?" Zeenatu ta nemi sani. Ya girgiza kai ya ƙara maida hankali ya yi buge-buge da rubuce-rubucensa. Can ya ɗago ya dubesu yana sharce gumi. "Bana jin akwai sauran duhu da yanzu haske bai mamayeshi ba a rayuwar mijinki. Yanzu haka maganar da nake maki yana tare da ɗan uwansa. Gaskiyar magana babu sauran asiri a jikin yaronnan. Da alama akwai wanda ya tsayamasa." (Allah Ya raba mu da aikin jahilci da jahilai. Ya kiyayemana imaninmu. Ameen). "Na shiga uku na lalace ni Zeenatu!" Ta dora hannu a kai ta kurma ihu da kuka. "Na fadamaki ai! Duk ranar da ya yi tozali da abokin haihuwarsa aikinki ya rushe. Ko kin manta wannan gargadin? Toh bari ki ji, akwai wani babban bala'i da ke tunkaroki daga ke har Batulu, ina mai gargaɗinku akan ku gaggauta barin garinnan kafin komai ya ida lalacewa. Wallahi kun ji na rantsemaku, taku ta kare domim ruwa ya ƙarewa ɗan kada!" Gora ya na kaiwa nan ya mike ya gyara zaman malun-malun hadi da ɓantalar goro ya hau tauna. Da wani irin tsalle Hajiya Zeenatu ta miƙe ta shaƙe wuyansa ya hau kakari. "Karya ka ke wallahi! Karya ka ke! Nawa na kashe?! Har kabari na tona! Hatta da jariri nayi amfani da shi duk akan Husseini! Karya kake ka ce duka wannan aikin ya tashi a banza Gora! Dole ne ka nemomin mafita idan kuwa ba haka ba wallahi sai na kashe ka!" Gora wanda ya ji shaƙa dakyar ya iya ɓanɓare hannun Hajiya Zeenatu daga wuyansa. Bai yi wata-wata ba ya kwaɗamata lafiyayyen mari da rawar hannu ya hau nunata da yatsa. "Ni ki ke kokarin kashewa? Yau sakamakon da za ki yimin kenan? Shegiya ƴar zina! To ki sani kin taɓowa kanki tsuliyar dodo, yanzu kika soma ganin bala'i da masifa! Babu ke ba jin dadi a rayuwa wallahi. Ni na miki wannan alƙawarin." Jin haka ta ƙara daka tsalle ta shaƙe wuyansa ta hau bori, ga hawaye caɓe-caɓe ga zani na neman kuncewa sanadin jijjigar da ta ke yi. Tana faman ikrarin ko mutuwa ta yi kaɗan ta raba ta da Hussein.  Hajiya Batool ta yi iyakar yinta amma ta kasa kwatar Gora don haka ta bazama rumfar da matan aure da karuwai har ma da ƴanmatan ke bin layin ganin Gora, ta nemi ɗoki. Nan da nan suka bazama aka shigo dakyar suka kwaci Gora wanda tuni ya galabaita har ya suma. Ruwa aka watsamasa ya farfaɗo. Idanun na kyarma ya shiga nuna Hajiya Zeenatu. "Za ki yi dana sanin wannan yunƙuri da ki ka yi na kashe ni Zeenatu. Sai na nunamaki waye ni! Na fi karfin wulakancinki!" "Hoo! Shege tsinanne wanda ba ya kallon gabas! Ni Zeenatu baƙar ashana ce! Ka san tarihina ka kuma san asalina! Babu uwar da ban gani ba don haka ka shirya! Sai na ga bayanka da karyar bokancinka. Ba wanda ya isa ya raba ni da Hussein! Wallahi sai na kashe ko waye!!" Da haka Hajiya Batool ta janye ta suka bar wurin zuwa mota. Hankali a tashe   Hajiya Batool ke tuƙi, Allah Ya taimakesu gilashin mai duhu ne sosai ba'a ganin haukar da Hajiya Zeenatu ke yi. Ita Hajiya Batool ma ta fi ta kwanciyar hankali. Ita dai Hajiya Zeenatu kira ta ke sai ta kashe AlHassan da ma Ramlatu idan hakan ne kadai hanyar da za ta rayu da Husseininta! *** Tana zaune daga ita sai Rafee'ah da Amrah, Hunainah da Zulaihat sai Muniru.  Hajiya ta wuce gida wanka da ɗan runtsawa. Hira suke yi amma ita kam tana zaune ko abincin da aka zubamata ta kasa ci, hankalinta na kan Hussein. Kwankwasa ƙofar da aka yi ce ta sa da sauri ta dubi ƙofar. Amrah ce ta mike tana gyara lulluɓi ta buɗe. Basu damar shigowa ta yi baki sake tana ƙara kallon tagwayen masu tsananin kama. Bambancin kaya da gilashin AlHassan ne kawai ya raba su. Hisham ke bayansu. Idanun Ramlat ya kasa ɗaukewa a kansu, ta kuma kasa tsaida hawayen farin ciki. Kawai sai ta shiga murmushi ga hawaye na zuba. I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/97Mzs8D3Qcb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 49) Gaisawa suka yi da Munir yana ƙara taya su murnar daidaituwa. "Allah Ya kara kiyayewa, Ya yi sakayya" Cewar Munir. Da murmushi ƴan biyun suka amsa da amin. A hankali ya kai duba ga Ramlat, ganin haka ta yi saurin sunkuyar da kanta. Ya maida idanunsa ga ƴan ɗakin, kafin waninsu ya kai ga cewa wani abu, an ƙwanƙwasa ƙofar. Hisham wanda ya fi kusa da ƙofar ya buɗe. Chairman Aliyu Dikko ne tsaye daga bayan masu kula da lafiyarsa biyu, yana aikin gyara zaman malun-malun dinsa. "Assalamu alaikum. Don Allah nan ne ɗakin da aka kwantar da Ramlatu Khalid?" Faɗin ɗaya cikin security din da suke tare. Hisham ya dubesu, yanzun ya gane ko wane. Kofar gaba daya ya buɗe. Suka dubeshi, Ramlat nan da nan ta haɗe fuska gami da gyara zaman mayafin da ya ɗan rufe jikinta. Hussein ya harɗe hannu a kirji yana kallonsa kamar yanda shima Chairman ya yi musu ƙuri da idanu. Ya kalli AlHassan kuma ya kalli Hussein ɗin wanda bambancin sutura da kuma gilashi kadai ya sa ba zai iya rantsuwar mutum guda ba ne. Ya daure ya dake yana mai miƙa hannu a yi musabaha, Munir da AlHassan duk suka miƙa banda Hussein wanda ya kauda kai, fuska a ɗaure ya dubi ɗan uwansa. "Muje ko?" Yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin, ganin haka da yawa cikinsu ma suka fita, ya yi saura daga Ramlat sai Chairman. Ya zauna saman kujera gami da ba ƴan rakiyarsa umarnin tsayawa daga waje. "Sannu Baby, ashe kuma harbinki aka yi? Su waye wadannan?" Tun Baby da ya kira ta da shi, ta ji gabanta ya yanke ya yi wani irin faɗuwa, ba wanda ya faɗomata a rai sai Aliyunta. Ta yi mishi addu'a a ƙasan ranta kafin ta ƙara yin ƙasa da kanta, har dai ya kammala ɓaɓatunsa ya mike ba ta ce mishi uffan ba sai da ta ga ajiye bandir na ƴa dubu har biyu a gefenta. "Bana so, ka ɗauke abinka." Ta furta a kausashe. Ya yi murmushi. "Haba Baby..." "Kar ka ƙara kirana da wannan sunan!" Ya jinjina kai. "Na ji, lokacinki ne yanzu, ki yimin duk abinda ki ka yi niyya. Nan ba da jimawa ba za ki koma ƙarƙashin ikona." Ta ja guntun tsaki, ya gyara zamam rigarsa ya fice. Ba jimawa da fitarsa su Amrah suka dawo ɗakin. "Yau naga ikon Allah, wannan shi ne ƙarfin hali wai ɓarawo da sallama. Mutumin nan ba zai gaji ya kyaleki ba?" Faɗin Rafee'ah tana ɗaga kuɗaɗen da Chairman ya ajiye. Kafin Amrahbta ce wani abu aka ƙara ƙwankwasa, da sauri Rafee'ah ta ajiye kuɗin. Ɗaya daga cikin abokan tafiyar Chairman ne, manyan ledoji ne har uku ya shigo da su. Ya ajiye. "Ranki ya daɗe, Alhaji ya ce a miƙo. Allah Ya ƙara lafiya." Har zai juya Ramlat ta dakatar da shi. "Maida." Ya yi murmushi. "Ki yi hakuri Ranki Ya Daɗe, ban isa na ketare umarninsa ba. A dai yi hakuri a karɓa." Daga haka ya kama ƙofa. Za ta ƙara magana Amrah ta girgizamata kai, dole ta haɗiye gami da yin ƙwafa. "Ki rabu da shi, ba laifinsa ba ne tunda dai shi ɗan aike ne. Allah Ya kyauta. Amma dai babu alamar mutuminnan zai saduda." Amrah ta fadi bayan ya fice. "Wai nikam Aunties, anya Hussein ba ya son Antinmu? Kun ga yanda fuskarsa ta sauya da ganin Chairman?" Hunainah ta furta tana duban dariya ƙasa-ƙasa na zolaya. "Ke Hunainah! Kin riga ni a fili amma nikam na rigaki a zuci. Ni wani kallo ma na gani kamar a duniyar romeo da juliet wallahi." Abinda Rafee'ah ta ce ta basu dariya sosai idan ka cire Ramlat wacce ta san ba haka tsakaninta da Hussein, asalima ita ke kiɗa da rawarta. A fakaice ta share kwallar da ta cika idanunta. Shigowar Munir ya sa suka bar maganar, hakan ya fi komai yi mata dadi. Anan ya ke sanarmusu Hussein sun wuce tare da AlHassan da Hisham daga can za su biya wurin police station. "Af, nikam Yaya su waye suka yi wannan aika-aikar? Sun yi magana?" Ya taɓe baki jin tambayar Rafee'ah. "Eh toh, su na ta dai walagigi da hankulan jama'a, amma ko mene idan an shiga kotu gaskiya za ta yi halinta. Mace ce, sunanta Halima. Ta dai yi ikrarin kishin Ramlatun ne yasa ta aikata hakan. Ganin za ta auri Chairman. Wannan shi ne rashin sani wanda ya fi dare duhu. Idan ma da gaske take, toh ta yi a banza." "Ya sunanta?" Ramlat ta tambaya a hanzarce. Ya ɗan yi shiru don shi kam ya mance ma da sunan. "Nan fa ɗaya, na mance." "Halima?" Ta tambaya gabanta na faɗuwa. "Yes! Sunan kenan. Amma ya aka yi ki ka sani?" Girgiza kai ta yi, ta ba su labarin takun saƙar da suke yi tun zuwanta ma'aikatar Revenue kafin ta bar shi. "Amma ba na tunanin ta san akwai wata alaƙa tsakanina da Hussein." "Ki kwantar da hankalinki ke dai, ko ma mene yanzu kam ai zai fito fili tunda an cafke ta." Ramlat ta girgiza kai karo na biyu tana duban Yaya Munir. "Hakane, amma ban taɓa zaton tsanar da Halima ta yimin ya yi ƙarfin da ko bindiga aka ba ta za ta kasheni ba, na yi mamaki matuƙa." "ƊAN ADAM aka ce maki, mai wuyar gane hali. Allah Ya kyauta." Cewar Amrah. Suka amsa da Amin. Ita dai Ramlat har sannan mamaki bai sake ta ba, ta ƙara jin tsanar auren Chairman. *** Chairman Aliyu Dikko, wanda ganin mijin Hajiya Zeenat da wani photocopy dinsa ya ɗaurewa kwanya, ya kasa haƙuri sai da ya fiddo waya ya dannamata kira. Har ya katse ba ta ɗaga ba sai a karo na biyu sannan ta ɗaga. *** Lokacin tana gida ta hargitse tana jiran shigowar Hussein don su bar garin zuwa wata Jahar kafin lamura su kwaɓe. Ga dai tana ta kiransa ya ƙi ɗagawa. Lokacin ne kuma kiran Chairman ya shigo, kamar ba za ta ɗaga ba a farko, sai dai ta ɗaga. "Nikam Zeenat, mijinki Hassan da Husseini ne?" Ta saki rigar Hussein da ta ke shirin sanya wa a akwati. Gaskiyar Gora kenan da yace su na tare? "Lafiya? Kin yi shiru?" "A ina ka gan su?" Daga amsar ya fahimci ruɗewarta. Kai tsaye ya ce. "A asibiti na je duba Amaryata Ramlatu, kinsan harbinta aka yi. Shi ne na tadda su a ɗakin. Sai wani hararata yake yi kamar na kashemasa wani. Na yarda da zarginki, son yarinyarnan yake kuma kwalalensa." Tusa Hajiya Zeenatu ta saki wanda ya tahomata da guntun kashi. Ta sharce gumi ta hau safa da marwa. "Yanzu a can ka baro su? Wane asibitin?" "Zan miki ƙarya ne? Nawa za ki ban idan na miki ƙaryar? Idan kina son ganewa idanunki ki taka ki je." Ya sanarmata asibitin, ba ta jira komai ba ta katse wayar. Banɗaki ta shiga ta sauke nauyin cikinta, ta kimtsa jiki sannan ta fito. Sun rabu da Hajiya Batool akan zasu haɗu su je wani ƙauye domin a yi musu aiki maikyau. Sai dai ba ta jin za ta jure wanzuwar Ramlat a doron ƙasa, za ta sa a karo na biyu a kashemata ita. Duk abinda zai faru sai dai ya faru. Ta fice daga gidan gaba ɗaya. *** Chairman da tun bayan kammala wayarsu da Zeenatu ya yi shiru yana tunani. "Ina maka rantsuwa da Allah zan sa a kashe Ramlatu idan ni ban kashe ta da hannuna ba muddin ta yi kuskuren shiga rayuwata da mijina." "Dakata!" Ya ba direba umarni, ganin haka direban ya ja ya yi parking a gefe. Chairman ya fidda waya ya ƙara kiran Hajiya Zeenatu, yana ta ringing ba ta ɗaga ba. Haka ya yi ta dialing shiru, don haka ya yi saurin cewa direban ya mishi magana da daya daga cikin abokan tafiyarsa. Da sauri direban ya fita zuwa ɗayar motarya kira. "Sir." Chairman ya dube shi. "Ku juya ku koma asibitinnan, ku tabbatar kun kula da marar lafiyarnan. Ina zuwa." Ya hau lalube cikin hotunansa har ya fiddo hoton Hajiya Zeenatu a wajen wani taron biki da suka hadu. Koda wasa ban yarda ku bar wannan matar ta shiga dakin ba." Ya jinjina kai cike da girmamawa ya karbi odar ya koma motarsa. Motar Chairman ya wuce su kuma suka juya zuwa asibitin. *** Hussein ya yi shiru kawai yana kallon Halima wacce har sannan ta ƙi faɗar gaskiya. Sai ka rantse hankalin a kanta yake, amma ina! Zuciyarsa na wani ɓangaren, sai hura hanci ya ke yana ƙara cin magani. Garin Kanon ta fita ransa, so yake su juya tare da ɗan uwansa kawai. Sai dai kafin nan yana son nunawa Hajiya Zeenatu kurenta. Yana son maka ta a kotu yanda za ta fuskanci fushin hukuma, duniya kuma ta san da abinda ta aikata. Wayar AlHassan ta yi ringing, gani Dada sai ya yi murmushi ya fita daga station din. Hisham ya ɗan daki kafaɗar Hussein kaɗan, dubansa ya yi kawai ya watsamasa harara ya kauda kai. Dariya sosai Hisham ya yi. "Ikon Allah, to ni kuma me na yi? Nasan fa me ke cin ranka" Hussein ya gyara tsayuwa gami da ɗan lumshe idanu bai ce uffan ba. "Kar ka yiwa kanka saki na dafe, tun kafin lokaci ya ƙuremaka gwara ka faɗamata abinda ke ranka." Ya dubi Hisham. "Me kake nufi? Kuma wa kake nufi?" Hisham ya bude baki zai magana ya ɗaga mishi hannu. "Malam bana son shirme, yimin shiru. Kai a komai sai ka sanya wasa da zolaya. To ka fita idona." Dariya sosai ya ba Hisham. Daidai sadda AlHassan ya dawo ya dubesu yana dariya. "Lafiya dai? Tom and Jerry?" Murmushi kawai Hussein ya yi. "Dada ce?" Ya tambaya. Gyada kai AlHassan ya yi yana murmushin shima. "Yes, ita ce. Sai dai ban fadamata komai ba, na dai ce ina tafe da wani babban albishir." Jinjina kai Hussein ya yi. "When? Nima na ƙagu na gan ta." "Very soon in sha Allah." "Maiduguri fa?" Cewar Hussein kamar zai yi kuka. Dariya AlHassan ya yi. "Duk za mu je da yardar Allah. Saboda rashinka na ɗauke ƙafa, ganina yana sa Hajjo kukan tunawa da kai. Wannan ta sa tsakaninmu sai waya." "Ina son hukunta ta." Hussein ya fadi zuciyarsa na zafi, fuskar Hajiya Zeenatu ya ke haskowa da kuma cuɗanya iri-iri da ya yi tare da ita. "Muje daga waje please. Nan ba wurin tattauna wannan zancen ba ne." Suka dubi Hisham mai magana, su ka maida hankali ga Halima da ta yi musu ƙuri da kumburarrun idanunta. Duk hirar da ake yi tana ji, kalaman Hussein na ƙarshe ya sa tsoro ya ƙara kamata. Kada dai ita yake nufin a hukunta? Ita kam ta shiga uku. Ba ta mance shawarar da kaninta ya ba ta ba da ya zo. "Idan kinsan ba da gaske kike ba Yaya Halima, ki fito ki fadi gaskiya kafin lokaci ya ƙuremaki. Nidai gaskiya ban yarda da abinda kika faɗamin ba." Ta share hawaye tana ci gaba da kokwanto a ƙasan ranta. Ta faɗa ko kuma ta yi shiru? Ita kanta ta rasa wanne za ta zaɓa. Har suka fice tana kallonsu. Ta bi wurin kwananta da kallo, ta ja majina. Anya Hajiya Zeenatu dagaske ta ke za ta cire ta a wannan taskun? Shiru ta yi, karshe ta yanke shawara ta aika ƙaninta wurin Hajiya Zeenatu ya yi mata bayanin halin da take ciki. *** Ramlat ta yi shiru, ita kadai a dakin, su Rafee'ah sun wuce, sai Hajiya dake bandaki ɗauro alwalar sallar Azahar. Nos Khadija ta kwankwasa ta shigo tana jan kayan dressing din ciwo a ɗan keke. Suka yiwa juna murmushi. Ɗan zaman da ta yi a asibitin sun saba, mace ce mai kirki. "Su kuma waɗannan ƴan sandan da aka zubamana a bakin ƙofa fa? Da alama dai Angonnaki na baki kulawar da ta dace." Wannan ne karon farko da ta ji haushin Nos Khadija, sam ba ta son abinda za'a haɗa ta da Chairman. Tun kafin su Munir su tafi, suka zoda zummar tsareta bisa umarnin ubangidansu. Har ta soma faɗa Munir ya ce ta rabu da shi kawai. Shi ya sani. Taɓe baki ta yi ba ta ce komai ba. Daidai sadda Hajiya ta fito, suka gaisa da Nos Khadija gami da yin ƴar raha don mace ce mai tsokana da kuma ja da wasa. Tana cire Bandage din kafadar suna ta hira abinsu, bayan ta goge ta ƙara rufewa sannan ya dubi Ramlat jin Hajiya na faɗan ba ta son cin abinci. "Ki dinga cin abinci don Allah Ramlat, haba yar uwa, ina yabonki? Ki ci yanda idan na ba ki magani ba zai sanyaki jiri ba. Yanzu zan dawo." Ta gyada kai ba don ta so ba, ita kawai komai ma ba dadi ya ke mata. *** Hajiya Zeenatu tunda ta doshi barandar ɗakin da Ramlatu ta ke ta hangi wasu masu kayan ma'aikata tsaye a bakin ƙofar ta yi turus. Wuƙar da ke cikin jakarta yasa ta kasa ƙarasawa, juyawa ta yi tana tunanin ina mafita? Ta ya za ta cimma burinta? Yanzun ta tabbatar Hussein ba zai kara yi mata kallon mace mai daraja da ƙima ba a idanunsa, amma tabbas idan ta bar Ramlat na yawo a doron ƙasa tofa shakka babu, wataran za ta ji batun aurensu. Abinda ba za ta taɓa ɗauka ba har abada. A kan idanunta, Nos Khadija ta shiga, hakanan a kan idanunta ta fito. Wata dabara ta faɗomata don haka koda Nos Khadija ta zo wucewa ta wurinta ta saki fuska sosai suka gaisa. "Nace don Allah idan babu damuwa, ina son ganinki." Nos Khadija ta bita da kallo, a shekaru ta girme mata sosai hakanan kuma ba ta yi mata kama da wacce ta fito daga ƙaramin gida ba. "Shikenan, ba ni minti biyu." Hajiya Zeenatu na murmushi ta gyada kai. Ba jimawa Khadija ta dawo suka ɗan fita waje. Shiru Khadija ta yi tana jin bayanan Hajiya Zeenatu. Kirjinta ya shiga dukan uku-uku. "Ki sani, wallahi-wallahi duk wani jin dadi na rayuwa kin sameshi kin gama matukar kika yimin aikin da na sanyaki. Zan ba ki duniya iyakar ƙarfina. Za ki taka duk ƙasar da kike so, za kuma ki shiga duk inda kike so a faɗin garinnan ba wanda ya isa ya ce maki don me?" Jikin Khadija ya ɗauki wani irin rawa. Tunda take a duniya, tunda ta ke, ba ta taɓa jin lamari irin haka ba. Wani irin tsoron da ba za ta iya misaltawa ba ya shige ta. Daga yanayinta Hajiya Zeenatu ta gane babu nasara don haka ta bude jaka ta fiddo bandiran kudi ƴan dari biyar guda biyu ta miƙamata, Allah Ya taimaka babu jama'a a wurin, ta ɗago mata lafiyayyar wuƙa sabuwa fil ta nunamata. "Ki zaɓi ɗaya Hajiya Khadija, idan ba haka ba ni da kike gani don na kasheki ba komai ba ne a wurina. Sai na ɓatar da ke da ma ƴan gidanku. Don haka zaɓi ya rage naki, na baki nan da awanni biyu, duk abinda kika yanke ki kira ki sanarmin. Kar ki manta rayuwarki a tafin hannuna yake." 'Ƙarya kike, Allah ne Mai iko da rayuwakanmu.' Nos Khadija ta fadi a fili don ba ta jin tana da kwarin gwuiwar faɗa a zahiri. Ta gyada kai kawai a fili, ta karɓi kudin ba don ta so ba ta zura a aljihun wandonta. "Ina tsumayenki. Ga lambar wayata." Hajiya Zeenatu ta fadi karo na biyu tana miƙamata karamin complimentary card mai dauke da numbobin wayoyinta a jiki. Nan ma Khadija gyada kai ta yi. "Je ki." Ta ba ta umarni, ta juya da sauri ta shige ciki har tana cin karo da wata mai tsohon ciki. "Yi hakuri don Allah." Matar ta bita da kallo kawai gami da jan tsaki irin na masifaffun masu ciki. Haka ta wuce ta a mita. Koda ta karasa dakin Nurses, ba ta tarar da kowa ba don haka da sauri ta ciro kudaden hannu na rawa ta cusa a jaka ta zuge zif. Bandaki ta shige ta soma watsawa fuskarta ruwa tana salati a ƙasan ranta. Yau da wane rashin sa'a ta fito daga gida? Kawai sai ta shiga hawaye, nutsastsiyar fuskar Ramlatu da kuma na Hajiya mai cike da dattako da kamala take tunawa. Ta ya ya? Ta wace hanyar za ta iya kashe wannan baiwar Allahn? Duk da dai idan ta so abu ne mafi sauki a aikinta, za ta iya kasheta irin kisar da zai yi wuya kafin a gane ita ce silarsa. Amma ina! Ba'a ba ta wannan tarbiyyar ba kuma ita ba haɗamammiya ba ce akan abin duniya. Kaɗan ma da ta ke samu ya wadatar da ita. Sai da aka kwankwasa ƙofar sannan ta fito. Karo suka yi da Nos Jamila. Ta bita da kallo. "Dije, lafiya?" Murmushin yaƙe ta yi ta hau murza idanu. "Ba komai, abu ne ya faɗa idanuna." "Aa Dije, faɗamin gaskiya." Girgiza kai ta yi, ba za ta iya ba, tana tsoron abinda zai sanadin rayuwarta. "Ko haihuwar ki ka karɓa, don nasan halinki na tausayi." Dariya ta ba ta. "Oh na tuna, ashe fa ba duty naki bane yau." Cewar Nos Jamila karo na biyu. Ita dai Khadija ta sulale ta fice daga ɗakin. Maganin ma kasa komawa ta ba Ramlat ta yi sai wata ta aika. *** Hussein da AlHassan zaune a falon gidan Hisham suna cin lafiyayyen girkin Aisha. Gogan ci yake kamar an mishi dole. "Wai Hussein lafiya? Ko kaima jinyar kake taya Ramlat?" AlHassan ya fadi yana murmushi don tuni ya ɗago shi. "Mene haɗina da ita? Kawai dai na damu da harbin ne, na kuma rasa waye zai yi ƙarya da ni ya harbe ta. Shiyasa na kasa fahimtar mai laifin, me ya sani tsakanina da ita da ya zaɓi hanyar kasheta ta amfani da ni." "Da mamaki kam, amma ko ma mene in sha Allah nan ba da jimawa ba zai bayyana. Har wanda ake ɓoyemana." Hisham ya furta yana kashe mishi io ɗaya, AlHassan ya yi kamar bai gansu ba ya ci gaba da kai loma yana murmushi. A yau jinsa yake kamar a duniyar gajimare tsabar murnar ganinsa zaune tare da ɗan uwansa. Hussein din ma banda harara bai cewa Hisham uffan ba, saboda gudun zargin sai ya saki jiki ya ci abinci. Bayan sun kammala ya mike. "Ina zuwa?" Fadin AlHassan don ba ya son ya ji Hussein din ya matsa daga gareshi. Murmushi Hussein ya yi. "Gidan Hajiya Zeenatu." "Aa, bai kamata ka je kai kaɗai ba. Muje tare." Jinjina kai Hussein ya yi cikin amincewa da zancen dan uwannasa. Suka ɗunguma suka fita, Hisham ya takamusu har ƙofa kafin ya dawo ciki. Kusan shima yau dai jinsa yake sak. Babu sauran damuwa. *** RAMIN ƘARYA.... I just published "BABI NA HAMSIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/S2N0l9OdWcb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 50) Tun daga farfajiyar gidan ma'aikata suka dinga al'ajabin ganin ƴan biyunnan. Har dai Malam Bala mai guga ya ka sa hakuri. "Yallaɓai ashe ku ƴan biyu ne." Hussein suka dubi juna da AlHassan, kauna ta jini na ƴan uwantaka na ƙara ratsa zuƙatansu, banda kaddara me zai raba su? Su da suka rayu tare a mahaifa guda. "Eh Malam Bala, we are twins." Fadin Hussein wanda ya ƙarashe da kallon su John. Nan suka shiga washe hakora suna gaida AlHassan da fadin abinda ya bambantasu, hakan ya ba ƴan biyun matasan dariya. Hussein ya yi ciki yana murmushi, ya bar su da AlHassan. Yasan matar gidan ba ta nan kamar yanda ya ji daga masu gadin, don haka ya shiga bin ko'ina na falon da kallo. Tafkeken hotonsu shi da ita ya ƙurawa idanu kamar wani fulanin daji da bai san hoto ba. "Ita ce. Makira." AlHassan ya fadi a hankali, sai sannan Hussein ya juyo da rinannun idanunsa ya dubeshi. "Idan na ce maka ban san ta ya ya na aureta na za ka yarda? Idan na ce maka ba da son raina..." "Ba fa sai ka faɗi komai ba ɗan uwa, na maka farin sani na kuma san kalar macen da ka ke so. Ko ka mance cewa ka ban labarin haɗuwarku da tayin kaunar da ta yi maka? Ban san dalilin da yasa na kasa tunawa da hakan ba, ban kuma san dalilin da yasa na amince ka bar mu ne saboda ka auri wacce ka ke so. Amma ban taɓa kawo wa ita ce ba nasan dai babbar mace ce kamar yanda ka faɗi." Sauke ajiyar zuciya Hussein ya yi gami da jinjina kai. Falon suka koma suka zauna. Nan kuma AlHassan ya shiga ba shi labarin abubuwan da suka faru a bayansa. Rasuwar Baba Naziru mijin Dada da kuma rasuwar ƴar uwar kakarsu da ta riƙe su kamar jikokinta da yaran cikinta suka haifamata ba su Dada ba. "Allah Yay musu rahma. Yasa aljanna makoma. Baba Naziru ya rasu da bakin cikina." Girgiza kai AlHassan ya yi. "Kar ka ce haka. Wallahi har ya rasu kewar ka ya ke, ya kuma faɗa ya ƙara, ba halinka ba ne." Hussein ya jinjina kai. "Yaushe za ku tafi?" AlHassan ya tambaya. "A satinnan. Ina neman alfarma a wurinka, koda kun haɗu da ita kar ka nuna mata komai kamar yanda nima ba zan nuna ba." Hussein ya faɗi idanunsa cikin na ɗan uwan. Da mamaki AlHassannya tambaya. "Dalili?" Hussein ya yi mishi bayanin duk abinda ya ke buƙatar yi, a farko AlHassan ya ji abin kamar babu amfani, a karshe kuma sai ya hau murmushi sosai. "Good, hakan shi ne daidai." Abinda ya ce kenan bayan gama sauraro. Hussein ya ɗan ciji leɓɓansa gami da shafa sumar kai. Daga farfajiyar gidan kuwa, Hajiya  Zeenatu ce ta shigo ta yi parking ta fito. Ta sauke ajiyar zuciya ganin motar Hussein. Ta shirya tunkurarsa, ta shirya fuskantar kowane irin ƙalubale. Ita din mace ce, kissa ba komai bane. Murmushi ta dan yi tana mai jin ƙwarin gwuiwa da haka ta shiga gidan. *** Yusufa ya zaro ido yana duban Halima da ke faman zuba zance. "Yaya Halima anya kina da imani? Yanzu saboda kudi ki ka yarda ki aikata duka wannan? Yaya Halima ba ki yi tunanin rana irin wannan za ta zo ba? Ke fa talaka ce, ba ki da makaman yaƙi, su kuwa masu kuɗi ne, kinsan ba za su kamu ba. Meyasa kullum shi talaka kwadayi ke kai shi ya baro? Anya kuwa kin yiwa kanki adalci? Kin mana adalci? Ɗan abinda kike samu na albashi bai wadace ki ba?" Yanda Yusufa ke hawaye haka itama ta ke sheshshekar kuka. "Na cuci kaina, ban san cewa ni din mahaukaciya ce ba dai yanzu Yusuf. Nidai don Allah ka taimaka ka je ka sami Hajiya ka yi mata bayanin komai, nasan ba za ta rasa hanyar da za ta fitar da ni ba musamman idan ta ji ina  barazanar tonamusu asiri." Ya share fuskarsa, shiru ya yi don babu alamar zai je din. Halima ta dinga yi mishi magiya da roƙo har tana durƙusawa. Ɗan uwa daban ya ke, nan da nan ya ji zuciyarsa ta karye, ya daukar mata alƙawarin a yau zai je ya sami Hajiya Zeenatu tunda washegari ne shiga kotu. Ta ba shi kwatancen gidanta har ma da na A&Z, daga bisani suka rabu akan duk yanda ake ciki zai dawo ya sanarmata. *** Ramlat ta yi shiru tana tunani bayan tafiyar abokan aikinta wadanda takanas suka zo dubiya. Can dai ta kasa hakuri ya dubu Hajiya dake zaune saman darduma tana shan kankana. "Nikam Hajiya ya ake ciki batun mayar da kudi? Su Kawu sun ƙara magana?" Hajiya ta yi murmushi. "Ina fa Ramlatu, Hajja ta ce na bar komai a hannunta. Yanzu dama abinda ake ciki, ina so ke ki bada katin ATM dinki na damƙawa Yayanki ya je ya ciro ya kawomin. Da kaina zan je na same su na damƙamusu kuɗaɗen idan ya so ko a yaransu ne su nemi ɗaya su aurawa Dikkon. Ke dai ki kwantar da hankalinki kawai. Kuma kada jin hakan yasa ki dauka na goyi bayan ki yi ta zama a gabana ne babu aure, sam, ba zai yiwu ba. Shima wannan din halayyarsa ce ba ta yimin ba kema kin sani. Don haka ki yi kokarin fitar da mijin aure. Ko Baba Dakta ai kin ji me ya ce." Murmushi ta yi mai kama da yaƙe gami da gyaɗa kai. Hajiya ba ta san me ke damunta ba, ba kuma auren ne ba ta so ba. Kawai dai ba wanda ta ke jin kaunarsa a ranta irin Hussein. Bayan Aliyunta, shi ne namijin da ta yi amannar za ta iya rayuwa da shi a kowane yanayi. Sosai yanzun tana jin saukin hannun don ita kam da ace za'a ba ta sallama a ranar za ta so hakan. Sallamar da aka yi yasa duk suka dubi ƙofar gami da amsawa. Nos Khadija ce, ta ƙaraso ciki. "Ke kuwa ɗiyata daga cewa bari ki ke ki dawo na ji shiru sai wata na gani a madadinki." Murmushin yaƙe Khadija ta yi. Ta rasa ma me za ta ce, tuno zantukan Hajiya Zeenatu kaɗai yakan kaɗa hanjin cikinta balle idan ta ci karo da salihan bayin Allahn nan da ba su yi kama da mugaye ba. Ita kuwa in za ta iya aikata wannan ɗanyen aikin? Ai koda babu ƴan sanda tsaye a bakin ƙofar ba za ta iya ba. "Ayi hakuri Hajiyarmu, ɗazun sallah na tsaya yi bayan na idar kuma wani aikin ya ɗaukemin hankali. Sannu Ramlat, ya jikin?" Da murmushi itama Ramlat ta amsa. "Alhamdulillah. Jiki ya yi sauki." Ta jinjina kai. "Dama zuwa na yi na muku sallama sai kuma Allah Ya kaimu. Zan wuce gida." Suka yi mata godiya sosai sannan ta juya ta fice idanunta cike taf da kwalla. Ba ta tunanin har a ba su sallama za su ƙara ganinta. ***   Sallamarta ta sanya su maida hankula gareta musamman AlHassan wanda ke zuci-zucin ya haɗa ido da matar da ta yi sanadiyyar rushewar dukkan farin cikinsu na tsawon shekarunnan. Tun daga  bakin ƙofar shigowa ta saki jaka gami da ƙarasowa tana kallonsu kamar wasu sabbin halittu. "Hussein! Kar ka cemin wannan ɗan uwanka ne. Ku ƴan biyu ne dama?" Ta shiga nuni da Alhassan da yatsa da wani rawar baki ta karasa zancen. Kawai a karshe ma sai ta karasa da sauri. "Innalillahi, wallahi kuna kama. Wa ye wannan din? Huss.." Bai bari ya ci gaba da sauraron rainin hankalinta ba ya yi saurin katse ta. "Yes yes, shi ne. AlHassan Aminu Modibbo, ɗan uwana ne. Daga Adamawa." Ya fadi yana kallonta da burin ya ga yanayin da za ta shiga, sai ta maze ta hau sharar hawayen munafurci. "Alhamdulillah. Allah Ma ji roƙon bayinSa. Allah yanda Ka nunamin dan uwan mijina ina roƙonka da Ka sadar da ni da nawa dangin." Kawai sai ta fashe da kuka sosai. Hussein ya ɗora kafa ɗaya saman kujera gami da rike baki da hannu ɗaya yana wani murmushi, AlHassan shi kansa abin nata dariya ya ba shi. Ido Hussein din ya mishi don haka ya shiga acting. "Haba Hajjaju, ki kwantar da hankalinki. Komai ai na Allah ne. Ai ko shekaru miliyan za'a yi ana shuka rashin alkhairi, akwai ranar ƙin dillacin. Kinsan hausawa sun ce ramin ƙarya ƙurarre ne. Ina nufin da sannu kema Allah zai sada ki da naki ƴan uwan. Mun jima muna nemansa, a zatonmu ma ya mutu, sai dai kwatsam labari ya iso mana can Adamawa cewa an ga mai kama da ni a Kano, kamar da wasa ina zuwa na haɗu da shi. Ai ba abinda za mu ce ga Ubangiji sai godiya. Ya ban labarin irin kulawa da soyayyar da ki ke nuna mishi, muna godiya sosai sosai fa." Mamaki, tsoro ko farin ciki? Oho, Hajiya Zeenatu ba ta san wanne ta ke ji ba. Dagaske ne Hussein bai zarginta da komai haka ma dan uwansa ko kuwa dai su na mata shigo-shigo ba zurfi ne? _*"Kin manta waye Hussein? Mutumin da bai iya ɓoye ɓacin rai ba? Ga dukkan alamu son da ya ke yi miki ya hana ya zarge ki. Wannan ne zai sa ɗan uwansa ma ba zai zargeki ba. Ko ba komai daular kadai da suka tarar da dan uwansu a ciki, zai hana su zargi komai a kanki."*_ Wani sashi na zuciyar Hajiya Zeenatu ke mata wannan tunin, nan da nan ta gaskata hakan, wani farin ciki ya dabaibaye ta. Ta shiga rawar ƙafa gami da yin nan nan da AlHassan. "Me ka fi so dan uwanmu, me za a girka maka?" Ya yi murmushin da bai kai zuci ba. "Ko me kika sa aka girka zan ci Hajjaju." Ta yi dariya tana duban Hussein wanda ya dauke kai ya maida hankali ga wayarsa. "Shikenan an gama! Kai fa Mijin? Me ka ke da muradin ci?" Ba tare da ya dube ta ba ya amsa. "Duk abinda ki ka sanya a girka." "Shikenan. Ai yau da kaina zan shiga kicin, da hannuna zan muku girki don yau ranar farin ciki ce gare mu. Rana ce da ba za mu mance ba." Anan ne Hussein ya ɗan kalleta ya yamutsa fuska. Ta wuce sama da sauri da niyyar sauya kaya. Bayan tafiyarta ya yi jifa da wayar ya riƙe kai zuciyarsa na zafi. Dakyar ya iya kai zuciya nesa bai shaƙe wuyanta ba. "Akwai wuya fa, dakyar na iya jure kallon fuskar matarnan taka." AlHassan ke maganar yana dubansa, ya dago ya ja guntun tsaki. "Ka daina haɗa ni da ita please." Murmushi kawai AlHassan ya yi ya dubi agogo. "Ya kamata mu yi haramar tafiya masallaci, daga nan ina son wucewa asibiti na ga jikin Ƙanwata." Shiru ya samu maimakon amsa daga bakin Hussein kawai dai ya mike ya nufi bandakin dake falon, can ya fito. Ganin alwalar ya yi  shima ɗan uwan ya mike ya shiga toilet. Daidai sadda Hajiya Zeenatu ta sauko cikin wata doguwar riga ƴar kanti da ta matse ta, albarkatun tumbinta duk sun fito sun yi layi-layi. Ya kauda kai yana ji kamar ya yi amai da ya tuna tsawon lokacin da ya ɗauka yana haɗa jiki da ita. "A'a, ya na ga kun miƙe? Ina shi AlHassan din?" Hussein ya ci gaba da ɗora agogonsa bai ce komai ba. Don kanta ta ba kanta amsa. "Oh, yana toilet kenan. Lallai kam don Magriba ta kusa. Bari na leka kicin sai na koma na yi alwalar nima." Murmushin gefen kumatu ya yi jin wani sabon salo, kiran sallah da wutsir. Hajiya Zeenatu da batun ɗora alwala? Jinjina kai kawai ya yi ta sauke ajiyar zuciya ta yi hanyar kicin tana kwala wa John kira. AlHassan na fitowa suka kama hanya. Daga masallaci, suka dawo suka shiga motar Hussein din, a waya ya ke sanarwa Hajiya Zeenatu fitarsu. "Haba haba don Allah, girki fa zan muku yanzu." Sai da ya daki sitayari gami da jan tsaki don wani irin ɓacin rai da shagwaɓar Hajiya Zeenatu ta jawomasa. Yana gani AlHassan na mishi hannu alamar ya nutsu. Ya daure ya amsa. "Kiyi hakuri Madam, yanzu za mu dawo, ba wani jimawa za mu yi ba. Kayansa zan kai shi ya kwaso daga Hotel." Bai bari ta karashe amsawar ba ya kashe wayar. *** Yusufa wanda a kan idonsa mota ta fice daga gidan da Halima ta mishi kwatance, ya bi motar da kallo, ganin ba'a ganin na ciki ne yasa shi maido hankali ga Maigadin. Da sauri ya karasa tun kafin ya karasa rufe ƙyauren. "Sannu Baba." Maigadin ya dube shi. "Yauwa ɗan samari, lafiya dai?" "Lafiya kalau. Don Allah nan ne gidan Hajiya Zeenatu?" Gyada kai Baba Maigadin ya yi. "Eh kwarai, nan ne." Sauke ajiyar zuciya Yusufa ya yi. "Alhamdulillah, don Allah wurinta na zo. Idan ba damuwa ka yimin iso Baba. Ka ce mata Halima ce ta turo ni.  Sunana Yusufa." "Toh banda abinka ɗan samari, Halima kawai babu wata inkiya ko wani abun? Idan ta ce ba ta gane ba fa?" Yusufa ya yi shiru, ya san ko sunan ubansu zai faɗa a banza don ba lallai Hajiyar ta san ta da wannan sunan ba. Don haka dabara ta faɗomasa. "Yauwa, ka ce ƙanin Halima ne ma'aikaciyar Revenue. Aikoni ta yi." Kasancewar Baba Maigadi ba baya ba, daidai gwargwado yana da ilimin boko yasa fadin sunan bai ba shi wuya ba. Ya ce ya shigo ya tsaya daga bakin ƙyauren, Yusufa ya yi godiya ya shigo. Ya dinga bin tamfatsetsan gidan da kallo cike da jinjina irin dukiyar da ala narkar. Sai ya gan shi wani ƙaramin alhaki kuma wani almajiri a gaban gidan. Koda Baba Maigadi ya isar da saƙon ga Hajiya Zeenatu, nan da nan ta daure fuska. "Na ba ka damar barin ko wane kare da biri  shigowa gidana?!" Baba Maigadi ya dan russuna a ladabce. "Ki yi hakuri ranki ya daɗe, na dauka kinsan Halimar ne. Amma.." "Kai dalla yimim shiru hakanan! Ka koma ka ce mishi babu wata Halima da na sani don haka ya gaggauta bar min gida tun kafin ya yi maka sanadin aikinka." Jin haka ai da sauri Baba Maigadi ya kara bada hakuri tukunna ya kama hanya da sauri-sauri. Idan aka yi mishi sanadin aiki kuma ina ya kama? Yusufa na hango shi ya ƙuramishi idanu. Maimakon ya ji ta ba shi damar ganawa da ita, sai ya ji akasin hakan. A ƙarshe ma Baba Maigadi bude mishi kyaure ya yi yana mai ba shi hakuri da roƙon ya tafi tun bai jazamishi ba. Haka Yusufa ya fita jiki a matukar sanyaye. Ta tabbata dai karshen Halima ne ya zo. Komai yanzun zai iya faruwa gareta tunda har ta bari zuciyarta ta rinjaye ta wurin aikata abin dana sani da kuma nadama. *** A farfajiyar asibitin ya faka motar. "Muje ko?" Cewar AlHassan ganin Hussein din ba shi da niyyar fitowa. "Ka fara shiga, ina nan zuwa. Akwai wayar da zan amsa ne." Bai takura mishi ba ya yi gaba zuwa ciki, Hussein ya kwantar da kai saman kujera gami da lumshe idanu. Hoton fuskar Chairman Aliyu Dikko ya kasa fice mishi. Ya kasa mance ganin da ya yi mishi a wajen Ramlat. Kwankwasa gilashin motar da aka yi ne ya maido shi hayyacinsa, ya ɗago kai ya sauke gilashin. Ganin Hisham ya ja guntun tsaki. Hisham ya dora hannu saman windon. "Yanzu na ga Twin brother dinmu, ya cemin kana mota shi ne nace bari na zo na ji abinda ha dakatar da kai daga shiga." Hussein bai ce uffan ba, hannu kawai ya sa ya ƙaro volume na waƙar da ya ke ji. Hisham ya zagayo ya bude mazaunin gaba ya shiga gami da kashe waƙar gaba daya. "Kana da tabbacin abinda ka ke yi zai haifarmaka da ɗa mai ido? Kana da tabbacin wacce ka ke so za ta so ka a wannan halin? Meyasa ka ke kokarin hana zuciyarka abincinta a koyaushe?   Meyasa ka ke hana idanuwanka ganin irin sadaukarwar da Ramlat ta yi maka da gangan?" Hussein bai ce uffan ba, bai kuma katse shi ba don haka ya ci gaba. "Anya Hussein ka san wace ce Ramlatu?" "Mutum." Ya amsa kai tsaye yana murmushi gami da kallonsa.  Hisham ya harareshi. "Eh mutum ce, amma ta bambanta da irin mutanen da ka ke mu'amala da su." "Rabinta aljana ce?" Ya ƙara watsamasa tambayar da ta ƙara kai Hisham bango. "Kana ƙin gaskiya da gangan, amma magana ta gaskiya, Ramlat ba irin macen da namiji zai kyale ba ce." "Ya aka yi ta rabu da uban ƴaƴanta?" "Wai ban taɓa faɗamaka baban yaranta rasuwa ya yi ba?" Hisham ya tambaya da mamaki. Hussein ya girgiza kai. "Bana jin mun taɓa hirar, idan ma mun taɓa to na manta kam. Allah Ya yi mishi rahma." "Amin."Hisham sai ya karkace ya hau ba shi labarin rayuwar Ramlat tun daga farko har zuwa rasuwar mijinta a tsakiyar filin sallar juma'a kuma cikin watan azumi. Hussein ya yi shiru bai katse shi ba har ya kammala. "To meyasa yanzu ba za ta auri Yallaɓai ba? Ko ba komai zai jiyar da ita farin cikin da za ta mance dukkan ƙuncin rayuwa." Hisham ya ji kamar ya shaƙe shi. "Ba wannan nake nufi ba, kai nake so ka auri Ramlat ko don irin son da ka ke mata. Wallahi ba ta dace da kowane namiji ba sai kai." "Na taɓa ce maka ina sonta?" Hussein ya fadi kansa tsaye yana murmushi, wani irin murmushi tun daga ƙasan zuciya. Hisham ya kara jin haushi da takaicinsa. "Dan iska kawai, sai ka zauna kar ka aure ta din!" Yana kai wa nan ya bude motar ya fice. Hussein ya tashi motarsa ya yi ribas har ya kusa yin sama-sama da Hisham banda Allah Ya sa ya matsa gefe. Murmushi ya ke yi ganin yanda Hisham din ya fusata ya na surfa bala'i. Ya juya kan motar ya fice daga asibiti zuciyarsa kamar an narkar da ƙanƙara. Awanni biyu zuwa uku, sai ga shi nan ya dawo niƙi-niƙi da kayan dubiya ya bar su a cikin motar, sai da ya shiga masallaci ya gabatar da sallar isha'i sannan ya karasa ciki. Aka yi sa'a masu gadin Ramlat sun yi gaba bisa umarnin da Chairman din ya bayar. Sai kuma goben za su ƙara dawowa. Kwankwasawa ya yi ya shiga da sallama,  gaba daya mutanen da ke dakin suka amsa. Ya karasa shiga bai ko kalleta ba ya durkusa suka gaisa da Hajiya. Ta amsa da fara'arta tana kara taya shi murnar haduwa da ɗan uwansa. AlHassan na zaune yana cin abinci kai ka rantse dama can wani irin mugun sabo aka yi da juna. A'isha ce abokiyar hirar, ana ta dariya. Hisham wanda ya kauda fuska bai ko kalleshi ba. Hussein ya mike ya nufi gefen Ramlatu, tun shigowarsa kirjinta ke harbawa da sauri-sauri. "Sannu, ya jikin?" Ya fadi ƙasa-ƙasa, hirar da su AlHassan ke yi ya hana Hisham mai kasa kunne jin gulma. A hankali ta dube shi., fuskarta ta yi fayau. "Alhamdulillah da sauki." "Allah Ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin ta kuma yi mishi godiya. Har zai juya ta yi magana. "Na tayaka murna, Allah Ya kara kiyayewa." Ya juyo kansa ya dube ta. Ta kasa gane ma'anar kallon don haka ta kauda kai. "Na gode sosai." Daga haka ya koma wurin su Hajiya. Nan Hajiya ta ba Aisha umarnin ga zuba  mishi abincin. Bai yi musu ba don dama yana jin yunwar kadan kuma ba ya son ko loma daya na abina Zeenatu ta girka ya shiga cikinsu shi da ɗan uwansa. Kusa da Hisham ya zauna saman kujera maimakon gefen AlHassan wanda ke zaune saman darduma. "Ka gama fushin?" Ya fadi daidai saitin kunnen Hisham yana murmushi. Murmushin shima Hisham ya yi. Ko ba komai zuciyarsa ta yi tas ganin bai ba shi kunya ba ya shigo. Aka zuba mishi abinci ya soma ci. Ramlat gaba daya fa an kasa sakewa, ita ce ta ja mayafi ta gyara sai kuma ta ja zani. Har dai garin juye-juyenta ta fama ciwon aikuwa ta saki ƙaramin salati. Ya ɗago idanu ya dube ta, ita din ma shi ta kalla. Sai ta janye da sauri tana amsa tambayar Hajiya. "Lafiya lau Hajiya, fami nayi kaɗan." "Sannu, ki dinga bi a hankali." Cewar AlHassan. Ita kuwa Aisha ta mike ta nufi wurinta tana gyaramata zaman mayafin da ta ke ta fama da shi. "Sis, wannan irin rashin sukuni? Ko duk a dalilin Hussein ne?" Ta fadi murya ƙasa-ƙasa yanda Aisha din ce kadai za ta ji. Harara ta bi ta da shi ita kuwa Aisha ta yi ƴar dariya.     I just published "BABI NA HAMSIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1009630651?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=ynI1KGJjd7sQQHwi7y8Hy%2FURSw8ZoDbiFN7aldIK5sou8xXacVQ1hbP5MNPCrtXe3NJxi6hvqSx39DOvHzE2aH8gSWFQR%2FiXs3hPnnEYhollJSFusGkC3Jmu6jUkimqk 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 51) Shi kuwa gogan abincinsa kawai yake ciki fuskarsa cike da wani irin nishaɗi. Ya kammala ya dire farantin. "Hajiya muna godiya." Murmushi Hajiya ta yi don tagwayen ba karamin burge ta suke ba. "Yaushe ne tafiyar taku Adamawa?" AlHassan ya amsamata. "Gobe da zarar an shiga kotu an fito za mu wuce." "Allah Sarki, toh Allah Ya nunamana. Sai dai zan so na ji taƙaimaiman tarihin abinda ya faru gareku a baya." AlHassan ya murmusa. "Kar ki samu damuwa Hajiyarmu, in sha Allah komai za ku ji gaba dayansa." Ta jinjina kai. "Allah Ya nunamana lokacin." Aka amsa da amin. Ramlat ta yi shiru, itama abinda ta ke son ji kenan, tana son sanin yanda har Hajiya Zeenatu ta yi nasara akan su. Kwankwasa kofar da aka yi gami da sallama yasa duk suka mayar da hankali. Nos Farida ce. Suka gaisa sannan ta miƙawa Ramlat takarda. Cikin raɗa-raɗa ta ce. "Gashinan, Khadija ta nemi da na ba ki." Ta karɓa da mamaki ta kuma yi godiya. Daga nan Farida ta juya ta fice. Ta ɗago ta dubi mutan dakin wadanda ita suke kallo. Ta maida hankali ga takardar ta warware ta shiga karantawa. _*Assalamu alaikum,*_ _*Ramlat ina miki fatan alheri da kuma samun lafiya. Akwai wani lamari da nake son sanarmaki. Wata mata ta yi barazanar hallaka ni matukar ban aiwatar da aikin da ta sanya ni ba, wato na kashe ki. Laifi ne da har abada bana fatan na aikata koda a kan maƙiyina ne. Ina mai ba ki shawara akan ki nar asibitin nan da gaggawa domin idan ma ni na kasa aiwatarwa za ta iya siye wani da kudi ya cikamata burinta. Taku mai kaunarku, Khadija Ashir.*_ Bakin Ramlat ya shiga rawa yayinda idanunta suka cicciko da kwalla. Tsam! Ya miƙe ya ƙaraso wurinta ba zato ta ji an zare takardar daga hannunta. Ta dubeshi, shima ita ya ke kallo cike da zargi kafin ya maida hankali ga takardar. "Meyafaru ne?" Hajiya ta nemi sani. Ya miƙawa Hisham, Hisham ya karanta a fili. Hussein ya sa kai ya fice daga ɗakin. Su Hajiya suka sanya salati. "Wai wace ce wannan matar mai neman ganin bayan Ramlatu? Oh duniya ina za ki da mu? Nikam ko maganin asibitin nan ban yarda a ƙara kawowa ki sha ba Ramlatu." Maganar karshe na Hajiyar sai ya ba AlHassan dariya. "Kar ki damu Hajiyarmu, ba abinda zai sami Ramlatu da yardar Allah. Sai dai ya kamata a bi shawarar Khadija, a ɗauke ta daga asibitin." "Dama ai Likitan ya fadi, yanda take samun sauki zai iya ba mu sallama gobe ko jibi. To ai kuwa gwara a yi komai." Can wayar Hisham ta yi ringing, Hussein ne. Hisham ya saurari bayaninsa sai ya yi murmushi ya katse kiran. "Ga wanda ya fi mu can ma ya tafi nema maku sallama a darennan." Da mamaki Aisha da AlHassan har su na haɗa baki wurin tambayar waye? "Hussein." Aisha ta saci kallon Ramlat tana murmushi, itama Hajiya murmushin ta yi kawai ba ta ce komai ba. Kamar dai da wasa, haka Hussein a daren ya yiduk cuku-cukun da zai yi har aka ba su Ramlat sallama a daren.  Suka haɗa komatsansu, Hajiya da Ramlat a motar Hussein, shi kuwa Hisham da madam dinsa suna tare. Amrah wacce har ta kamo hanya, sai waya suka yi mata suka sanarmata da batun sallama. Ita kanta ta yi mamaki. A hankali ta ɗago kai don tun shigar ta motar kan yana a ƙasa. Caraf suka haɗa idanu ta cikin gilashin kasancewar AlHassan ke tuƙin wannan karon. Ta sauke kanta, shi kuwa ya samu damar ƙarewa fuskar kallo yanda duk ta faɗa kamar wacce ta yi cutar wata guda. A hankali ya kauda kai, suka yi ido hudu da AlHassan da ke satar kallonsa, murmushi AlHassan ya yi mishi shi kuwa ya gyara zama gami da ɗan ɗaure fuska kadan yana shan ƙamshi. Har gida suka kai su, Ummi da su Ansar duk suka fito a guje suna mata oyoyo, za su fada jikinta Hussein ya yi saurin riƙo Affan wanda ya fi kowa kusantarta, ita kuwa ta dafe hannu tana kiran wash! "Ba kwa ganin ciwonta?" Ya faɗi a hankali, suka fasa rungumeta su na dariya. Ya kama hannunsu zuwa wurin mota. "Ku zo muje" Ramlat ta bisu da idanu kafin ta juya ta bi sahun su Hajiya zuwa ciki. Shi kuwa Hussein ledojin dubiyar da ya loda a boot, shi ya ciromusu ya damƙa musu. "Oya, maza ku je a kaiwa Mami sai ta ba ku." Affan ya hau washe baki ganin Hussein ya fiddo alewa daga aljihu ha bude ya sanya mishi a baki. Murmushi sosai shima ya yi mishi ya bishi da kallo har ya ɓacewa ganinsa. Bayan Hussein sun koma gida, Hajiya Zeenat ta tarbe su da fara'a tana mai danne takaicin da suka ɗuramata. Hussein ya dan sakarmata. "Ki yi hakuri, gidan Hisham muka ci abinci ba haka na so ba." Ganin yanda ya fadi cike da kulawa yasa nan da nan ta ji zuciyarta ta sake. Ko ba komai hanyar lafiya a bita da shekara. Yanzun dai kaffa-kaffa ta ke yi kar kwaɓarta ta yi ruwa. Da haka ya nunawa AlHassan dakinsa kafin shima ya shige nashi dakin. Hajiya Zeenatu ta yi mamakin da ya bari ta kwana tare da shi duk da bai yi mata kama ko hannunta ba, asalima baya ya juya da nufin bacci yake ji.Ta so su yi batun tafiyarsu London ammata share, har lokacin jikinta a sanyaye yake, burinta yanzu gari ya waye ta shiga asibitin da Ramlatun take ta ga ko ta aiwatar da aikinta. "Gobe in sha Allah zan yi ƴar tafiya." Hajiya Zeenatu ta tsinci maganar Hussein wanda ta yi zaton bacci ya ke kamar daga sama, ta mike zaune gami da kunna fitila. Har sannan ya bata baya. Ya yi crossinh hannaye  a kirji. "Ina za ka je kuma?" "Adamawa." Ya furta kai tsaye gami da juyowa ya kalli tsaka idanunta. Duk sai ta ji ta rikice, hanjin cikinta sun kaɗa. Ta haɗiyi miyau, Hussein zai je Adamawa? Hannunta ya ɗan riƙe ba don ya so ba. "Ya naga duk kin sauya? Ba kya son na je na ga ƴan uwana?" Ta yi murmushin yaƙe. "Ko kusa aa, amma na ji haushi da ba ka shirya tafiya da ni ba, da ace ka yi niyyar muje tare za ka sanar da ni akan lokaci." Ya yi ɗan murmushi. 'Makira.' Ya furta can ƙasan ransa. A fili kuwa ya shafi gefen fuskarta. "Ki yi hakuri, bansan yanda za su kalli lamarin aurenmu ba. Gwara naje na yi musu bayanin komai a tsanake cewa auren soyayya muka yi. Kinga hakan zai fi armashi." Ta ji wani sanyi kamar kankara, tana so ta yi shakku akan zancensa sai dai kuma ta kasa. Ta shiga gasƙata dukkan kalamansa. Hussein ya ci gaba da yi mata daɗin baki har sai da ta gasƙata da kanta cewar dagasken Hussein sonta ya ke yi ba wasa a ciki. Da wannan ta ji salama amma duk da haka tana tsoron a hana shi dawowa. "Za ka dawo garinnan kuwa?" Ya yi murmushi ya lumshe idanu. "Wa zan bar wa ke?" Ya fadi ba da manufa biyu, ta ji wani sanyi har sai da ta dara cike da shauƙi. Da wannan suka kwanta bacci. *** ƘARSHEN ALEWA..! A ranar Talata sha biyu ga watan Maris, kotu ta yankewa Halima da Gwaska hukuncin shekaru goma zuwa sha biyar a gidan yari a dalilin yunkurin kisan kai. Halima ta yi kukan nadama sosai, karshe ta nemi alfarma wurin ƙaninta akan ya je ya nemar mata gafarar Ramlatu. Yusufa na hawaye haka suka rabu da Yayarsa aka tsitsa ƙeyarta suka bar kotun. A can gida, Ramlat ta ji labarin komai a waya daga Hisham, kuka sosai ta yi na tausayin Halima. Haka ta dinga samun kira daga tsofaffin abokan aikinta na ma'aikatar Revenue, da yawansu sai yanzu suka san dalilin kamen da aka yiwa Halima. Sun jajantawa Ramlat gami da yin Allah wadai da son abin duniya irin na Halima wanda ya kai ta ya baro. "Ai godiya za ki yiwa Allah don yau kam duka ranarki ce. Ga shi dai an yankewa wadanda suka zalunceki hukunci, ga Kawunki Jamuli ya karɓi kuɗi, ya kuma tabbatarmin da kansa yau ba gobe ba, zai damƙawa Chairman kayansa. A yi ta ta ƙare. Ke kuma ya ce idan kima kara warwarewa ki je yana son ganinki. Maimakon farin ciki sai ya ci gaba da hawaye jin kalaman Hajiya, dama tun safe ta karbi Atm card din kuma ta fice tare da Munir. Uwa daban ta ke, ita ta tsaya tsayin daka tare da Hajja wurin karɓar mata ƴanci. Sallamarsu ce ta katse dukkan tunaninta. Suka dube su. Shaddar ba iri guda ba ce, sai dai kowannensu fari ƙal ya sanya. AlHassan da hula a kansa, yayinda gogan ya fidda nashi a mota, sai sumarsa kwance. Hajiya tun shigowarsu take murmushi da yi musu adduar neman tsari da kariya a ƙasan ranta. Ita kuwa tun da ta kalle su ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki. Suka karaso suka durkusa suka gaida Hajiya ta amsa fuska a sake. Suka yi mata murnar shari'ar da ta gudana, ta ta yi ta musu addu'a sosai. Ana haka sai ga Zulaihat da Rafee'ah  suma, sun ji labarin sallama. Suka karaso daidai sadda AlHassan ya dubi Ramlat. "Kanwata ya jiki?" Ta yi murmushi. Ta gaishesu. Ya amsa shi kuwa Hussein ya yi kamar bai ji ba yana kallon twins din Zulaihat. Bayan zamansu aka kara gaisawa su na muu godiya. "Zamu wuce Adamawa Hajiyarmu." "To ƴaƴana, sai kuma yaushe?" Hussein ya amsa wannan karon. "Nan ba da jimawa ba za mu dawo in sha Allah." Ta jinjina kai ta yi musu fatan isa lafiya. Hakanan suka kama hanya. Rafee'ah ta yiwa Ramlat ido, ba musu ta mike ta takamusu, ba laifi yanzu hannun da sauki sosai. A daidai barandar shiga dakin ta ci burki. "Allah Ya tsare, Ya kaiku lafiya. Na gode sosai." "Ke za mu yiwa godiya sosai. Allah Ya bar zumunci." Ta yi murmushi. "A gaidamin Fatina." Ya yi murmushi. "Za ta ji in sha Allahu." Daga haka ya yi gaba, Hussein ya dube ta. "Yarinyar da kika aikomin hotonta?" Ta gyada kai tana murmushi. Sai a sannan ta ga ya yi mata murmushin shima. "Ina kara godiya gareki. Allah Ya ba ki miji nagari. Oh, ashe kin samu. Allah Ya nunamana aurenku." Ya karashe yana taɓe baki. Ta rasa ma me za ta ce, ya bita da wani irin kallon da ta kasa fassarawa. "Ki kula da shan magungunanki, kada ki tsorata, likita da kansa ya rubuta da kaina na karɓomaki. Ba za ki mutu ba." Ta dan yi murmushin yaƙe, ya juya ya  tafi. Jiki a saluɓe itama ta koma ciki. *** HUSSEIN AMINU MAMMAN MODIBBO... Alhaji Aminu Mamman Gidado, haifaffan garin Adamawa ne gaba da baya. Su goma sha biyar cif mahaifinsu ya haifa. Mamman Gidado yana da mata uku, uwargidansa wacce suke kira da Inna, ta haifamasa yara tara cif a duniya, sai mai bi mata Yakumbo wacce ta haifi yara biyu. Hassan da Hussaina wanda a karshe suka koma hannun Inna da zama. Hajara (Hajjo) kuwa tana da yaranta  huɗu cif a duniya.   Wani irin rayuwa ake gudanarwa a gidan Mamman Gidado, rayuwar da hatta da maigidan shakkar Inna yake yi balle a kai ga mata da yara. Inna wata irin mace ce murɗaɗɗa mai baƙar zuciya, a duniya ba ta kaunar ace wani ne sama da ita koda a matsayi ko wani abin. Auren gida na zumunci aka yi musu da Mamman Gidado. Sai kuma cikin ikon Allah ya zamana Yakumbo ta fito daga gida na sarauta a garin Mubi. Mahaifinta shi ne wazirin Sarki. Wannan girma da nasaba ta Yakumbo sai ya jazamata baƙin jini fiye da na kowa a wurin Inna. Ita ta soma yiwa Yakumbo gorin zama bare a gidan don Hajjo ma ƴar aminin kakansa ce aka aura. Yakumbo tana shakkar Inna sosai, tana kuma bin ta sau da ƙafa. Mijinsu ba karamin so yake yiwa Yakumbo ba, tana matsayi babba a zuciyarsa da bai jin ko Inna ta samu. Wannan ta sanya mutuwarta ba jimawa  shima ya soma jinyar ajali. A gaban idanunsa Inna ta sha hana Amina da Aminu abinci, wataran Hajjo a sace take basu. Dangi kuwa ba'a taɓa ganin laifin Inna don a waje nunawa take nan duniya tana sonsu kuma tana riƙe da su da amana. Wannan tasa hatta ga yaranta maza da mata sun tsani su buɗe idanu su ga Amina da Aminu musamman ganin irin kyauta da gatan da ake nunamusu duk sadda suka kai ziyara Mubi suka dawo. Kayan da Inna ba ta sanyamusu kenan, duk zuwansu dama gargadi ne sosai da jan kunne ta ke musu akan kar su sake su yi yunkurin tonamata asiri. Modibbo wanda ya kasance ɗa na bakwai a wurin Inna, kusan shi ne babban mugun da ya fi kowa tsanar yaran Yakumbo. Ya sha kama su a makaranta ya jibga ya kuma kwace abincin da Hajjo ta girkamusu. Gori na uwa da uba bai fasa yi musu ba. "Wai meye amfanin riƙon da ake musu anan? Tunda suna tutiyar dangin uwarsu masu arziki ne, ki tattara ki maida su mana!" Modibbo ya fadi a zafafe. Yar uwarsa kuma Yayarsa Adda Salma ta karɓe. "Ashe ka gane, ni wallahi haushinsu nake ji,wannan Aminar ma kyanta ya yi yawa, ko makaranta muka je sai a yi ta wani zuwa ana daukarta. Ji nake kamar na shaƙeta na huta. Da zan samu reza na tsaga fuskar ma zai fi." Sauran suka yi dariya har Inna Idan ka cire Karime da Adamu wadanda su kadai suka fita zarra akan sauran, basu taɓa nuna kiyayya ga Amina da Aminu ba.  "Allah ne Ya ba ta kyan, kuma ai..." Buge bakinta Modibbo ya yi da ƙarfi. "Dama ke da Adamu ina kula da yanda ku ke shishshigewa yarannan! Marasa zuciya da kishin uwa!" *** Da wannan irin kiyayyar Amina da Aminu suka taso, boko dai basu isa su je ba sai yaran Inna, islamiyya kadai suke zuwa. A wannan rayuwar, Waziri ya fadi ya mutu, kasancewar mahaifiyar Yakumbo ta jima da rasuwa ne yasa babu wanda ya kara waiwayarsu balle ya maida hankali wurin kula da su daga Mubi. Yar uwar Yakumbo tilo, Zahida, ita kuwa tana aure a Saudiyya. Kafin ta shigo gari akan jima sosai. Shekaru suka ja a wannan halin, Aminu ya yi saukar littatafai da dama na addini. Mutum ne mai matukar kokari da saurin daukar karatu. Lokaci ɗaya kuma ya bazama neman ilimi a garuruwa daban-daban. Inna ko a jikinta, don a ganinta ba wani ci gaba da zai samu face ya ƙare a almajiranci. A sannan babbar ɗiyarta Hansatu, ta kammala karatunta a fannin shari'a a jami'ar Adamawa. Yayinda Salma ta karancifannin Kasuwanci. Duk an musu aure a sannan.    Modibbo yana ajin karshe inda shima dai yake karantar fannin Kasuwanci. Adamu da Karime su ne a babbar Sakandire sai Hadiza, Safiya, Tahir a karamar Sakandire,  Maimuna Autar Inna a firamare. A islamiyya ba su taɓuka abin a zo a gani, gwara ma Karime, tana da kokari sosai don ta yi sauka.   Yaran Amarya Hajjo hudu, suma duka suna karatu. Bayan tafiyar Aminu almajiranci da watanni biyar sai ga Hajiya Zahida da yaranta daga Saudiyya. Sun dawo kenan sakamakon sauyin wurin  aiki da mijinta ya samu zuwa Adamawa. An saukeshi daga Ambasada. Kai tsaye wurin ƴaƴan yar uwata ta soma zuwa. Ranar da ta je ta tarar da Inna na jibgar Amina da sunan wai ta tsaya sauraron bare wanda kwata kwata ma ba jinin Fulani ba ne. Da biyu Innar ta yi hakan ganin yaron mahaifinsa mai kudi ne, sunan zuri'arsu ba ɓoyayye ba nema ƙasar. Ya ganta ne a hanyar dawowarta daga islamiyya. Wannan tashin hankalin da Hajiya Zahida ta tarar yasa ta rantse ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ta tafi da Amina. Kaca-kaca suka rabu da Inna, a karshe ta ci nasarar dauke Amina tana kukan rashin sanin inda Aminu ya tafi. Da wannan suka wuce Mubi, sosai ta nunamusu ɓacin ranta akan yanda suka yi halin ko in kula da yaran Yakumbo, hatta aiken da takan yo a kai musu ba ya riskarsu. Da wannan bakin cikin ta zauna, sati na cika ta tattara yaranta har Amina suka wuce sabon gidansu a cikin Yola. Wannan ne dalilin ingantuwar rayuwar Amina wacce gaba daya yaran ke kiranta Dada. Babban ɗan mijin Hajiya Zahida  (ɗan Uwargidansa da ta rasu, riƙonsa ya koma hannun Zahida) Naziru, tunda ya dora ido a kan Amina ya ji nan duniya ita yake so da aure.   Sosai abin ya yiwa Hajiya Zahida dadi, hakanan shima mijinta bai ƙi ba. A yan uwan mahaifiyarsa ba wanda ya nuna kiyayyar abin ko don irin rikon da Hajiya Zahida ta mishi, ba jimawa kuwa aka sha bikinsu. Amina ta yi kukan rashin dan uwanta a kusa, haka ta hakura ta fawwalawa Allah suka tare a gidan Naziru wanda babu nisa sosai da gidan Hajiya Zahida. ***   Bayan shekaru masu dama, Dada ta haifi yaranta uku duk mata, tana da cikin na hudu ne ba zato ba tsammani Naziru mijinta ya ɗaukesu sai gidan Hajiya Zahida. Wanda ta gani ne ya sanya ta zuwa a guje ta rungumeshi sai kuka, tana yi shima yi yake. Ta ɗago ta dubi wata mace fara ƙal da ita kyakkyawa, a gefenta wasu kyawawan yara ne su biyu da zasu girmi yaranta, komai nasu iri daya. Haka kawai jikinta ya bata wannan iyalin Aminu ne. Ta rungume matar kafin ta rungumi yaran tana cike da farin ciki. Sai bayan an zauna an nutsu ne ya ke basu labarin inda ya je. Ashe bayan tafiyarsa da tawagar almajirai ba inda suka yada zango sai Maiduguri, ya fada hannun wani Malami kuma barebari cikakke, Malam Banakura. Mutum mai sanin daraja da ƙimar almajiransa. Aminu bai ɓoyemishi komai dangane da Asalinsa ba. Tausayi da kaunar Aminu suka shiga Malam. Ya rikeshi tamkar ɗan cikinsa, duk da tarin Almajiran Malam, Allah bai ba shi haihuwa ba. Kuma matsalar daga gareshi ne. Uwargidansa Yakura, mace ce mai halin Dattako, ta rike yaran yan uwa da dama ta kuma aurar da su. Yara biyu kadai suka rage a hannunta sannan, Zahra da Yusha'u.   Zuwan Aminu sai ta haɗa da shi ta rikesu duk kuwa da cewar ya girmi Zahra nesa ba kusa ba. Sai dai zai iya sa'an Yusha'u. Haka suka rayu har suka kara girma, noma da kiwo shi ne sana'ar Malam bayan koyarwa, Aminu ya tsunduma wurin taimakawa Malam.  A hankali kuma Allah Ya sanyawa abin albarka. Koda shekarun aure suka kai, Malam ya fahimci irin soyayyar dake tsakanin Zahra da Aminu, bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya auramasa ita da iznin iyayenta. Mahaifinta buzu ne kuma Maigadi, mahaifiyarta ce ƙanwa ga Yakura matar Malam. Kyakkyawar mace mai gashi har ƙugu, yarinya mai yawan ibada da kunya.   Zamansu ya yi albarka sosai, sai da suka shekara kafin ta samu cikin ƴan biyu. Ta sha wuya sosai kafin ta haifesu. Sai da ƴan biyu suka shekara goma cif a duniya, Malam ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Sosai ya gargadi Aminu kamar koyaushe akan ya je ya nuna iyalinsa a gida. Wanna tasa ana yin arba'in na Malam, shima hankalinsa ya yi gidan. Shi ne zuwan da ya yi a yanzun, Dada ta ci kuka ta kuma yi korafin nisanta kansa da ya yi da ita har ba ya tunanin halin da ta shiga. Hakuri sosai ya ba ta, ɗan uwa rabin jiki, nan da nan kuma ta mance da komai. Ya nemi labarin abubuwan da suka faru bayansa, anan yake jin labarin mutuwar Inna bayan ta yi fama da jinya. Addu'a kawai ya yi mata tsoron Allah na ƙara shigarsa. Nan yake jin auren da Modibbo ya yi da kuma zaman da ya koma yi a Kano inda yake kasuwanci, sai Adda Salma da mijinta ya koma Gombe. Sauran yan uwa kuwa suna nan a Yola, Karime ma ta yi aure hakanan Adamu.  A yaran Amarya Hajjo ma, autanta ne kaɗai bai kai ga yin aure ba sannan.  Washegari suka dunguma zuwa dangin mahaifinsu. Sun samu tarba ta ban mamaki a wurin yan uwan mahaifinsu wannan ya kara tabbatar musu cewa dama can shakkar Inna ce ta sanya ake baya-baya da su, ko dai kuma don yanzun Dada na auren mai kudi ne shima kuma Aminu ya samu rufin asiri daidai gwargwado ne don har gidajen gona da dabbobi yana da su? Oho, ba su da masaniya. Aminu bai yi ƙasa a gwuiwa ba sai da ya je gida yayyunsa mata duka idan ka cire Adda Salma da ke Gombe. Ya yi mamakin ganin yanda har sannan babu ɗigon kaunarsu a cikin idanuwansu, asalima sai da suka goranta masa na auren Bare a cikinsu don dukkansu auren gida akai musu. "Kai da Amina kun fita zakkah! Gwara ita, ta auri Fulani kai kuwa bayinmu ka je ka kwaso mana. Har abada ba zamu taɓa daukarki daya a cikinmu ba. Tsana yanzu aka fara." Wannan shi ne munanan kalaman da Gwaggo Hansatu ta watsawa Zahra da har ya sanyata hawaye. Karime ce dai ta rasa inda za ta sanyasu don farin ciki. Ta rungume HASSAN DA HUSSEIN cike da murna da jin dadi har da kukanta. Haka aka rabu cikin aminci, suka dunguma zuwa Mubi. Nana ba laifi an musu tarba. Aminu bai ƙasa a gwuiwa ba sai da ya shirya zuwa Kano sada zumunci da Modibbo. Ya tarar da matansa biyu, Hajja Fatuma da Amarya. Tun shigowarsu ya dinga watsamusu banzan kallo yana gyara zaman malun-malun. Ba haka ya so ganin Aminu ba, so ya yi rayuwarsa ta lalace yanda rigar jikinsa ma zai gagareshi. Ya mishi tsanar da ko a inuwa ba ya son ganinsa sai rana. Da harshen fulatanci Aminu ya gaida shi. "Gaisuwar ta mece ce? Ni waye a wurinka? Shekaru nawa ka tafi yawan maula, sai yanzun ne za ka je ka dawomana da SADAKAR YALLAH?" Cikin dakiya Aminu ya amsa. "Ba sadakar Yalla ba ce, sunanta Zahra. Matata ce." Harara Aminu ya watsamata, ƴan biyu suka ƙara nanewa a jikinta suna bin wanda aka kira Yayan Babansu da kallon tsoro da tsana.   "Bare ce! Yanda uwarka ta shigo gidanmu tana matsayin bare, kaima haka ka je ka kwasomana abin fadi da gori! Har abada wannan matar ba za ta zauna cikin zuri'armu ba. Sai yanzun ka tuna da mu ka kwaso jiki ka taho zumunci ko? Toh ni Muhammadu, ban sanka ba! Bani da wata alaƙa da kai, ƙafarka na ƙara gani a gidana Allah Ya isa. Duk abinda na yi maka kuma kai ka ja wa kanka. Ku kuma kuma kallona kamar Mayu!" Ya maida akalar zancen kan Hassan da Hussein da suke kallonsa, duk da karancin shekarunsu, haka bai sa sun gaza fahimtar wasu abubuwan da yake faɗi ba don Hausa sak ya yi ko don ya baƙantawa Zahra. Da wannan cin kashin da rashin mutuncin na Modibbo, Aminu ya tattara iyalinsa suka juya ko kwana ba su yi ba. A mota ya yi ta rarrashin Zahra da ban hakuri. Ita kuwa murmushin yaƙe ta yi kawai ta nuna ba komai tunda dai bai ɓoyemata alaƙarsu da su ba tun farko. Labarin komai na irin riƙon da ya samu a hannun uwarsu ta sani.   Watansu daya suka yi shirin komawa, nan fa Dada ta rikice da kuka da rantsuwar ba ta yarda ba, a karshe ta dage ma sai dai a bar mata ƴan biyu ta riƙe, dabararta na yin hakan, don kawai su dawo da wuri a dinga ganinsu. Aminu ya rasa ya zai yi da yar uwarsa, ga mamakinsa Zahra da kanta ta riƙe hannun Hassan da Hussein ta damƙawa Dada tana murmushi. "Yarana mallakinki ne Dada. Gasunan na bar miki su duniya da lahira." Wannan abu har gobe Dada ba za ta mance shi ba, kuka sai ya koma dariya. Har tasha suka yi musu rakiya suka dawo. Abin mamaki Hassan da Hussein ko a jikinsu don sosai sun saba da Dada da iyalinta a ɗan zaman da suka yi tare. *** Mummunan labarin hatsarin mota da rasuwar Aminu da Zahra ya riskesu. Wannan ya yi sanadin fitar cikin Dada, ta sume.     I just published "BABI NA HAMSIN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1010093134?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=azuNeDf8BzRGeUbQ5hUohOGx2aTzO5EgG0sslypZUWd87KXOqPMoNqGJcWUIJ7lkGQPCJLaZwnIqw7s7g8N0NU%2BMfRV98U0i0%2BriYhHA5YJps5E19e%2B0H%2FQy%2Br8BBzme 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 52) Sosai mutuwar ta girgizasu, anan suka ƙara jinjina kudurar Ubangiji. Wato dai da yanzun har yan biyun za'a rasa shikenan babu tarihin Aminu da Zahra a doron ƙasa. Allah Ya taimaka, Aminu ya bada kwatancen inda suke zaune a Maiduguri, da haka suka karasa bayan an sallaci gawar Aminu da Zahra an binnesu a nan cikin Yola. Yakura ta ji mutuwarnan ba kaɗan ba, dama tana cikin takabar Malam. Hakanan iyayen Zahra su kansu mutuwar ta dake su. Sai da aka yi arba'in aka raba gadon ƴan biyu. Ba wanda ya hana Dada tahowa da Hassan  da Hussein. ***   RAYUWAR ƳAN BIYUN Rayuwa mai dadi suke yi a wurin Dada da mijinta, basu san matsalar rashin uwa ko uba ba. Kaunar da Dada ke yi musu har kusan matsala ta so ba ta da Naziru don gani yake kamar ba ta kula da yaransa irin yanda take rike da yan biyu. Wannan ne dalilinta na ɓoye son a zuciyarta. Makaranta mai kyau na masu gata suke zuwa don dama sun soma firamare, ci gaba kawai suka yi.   Tafiya ta ci gaba da tafiya har ƴan biyu suka kammala firamare suka soma kokarin tafiya Sakandire. A sannan ne Dada ta danne zuciyarta ta shirya da yaranta kaf suka halarci bikin ƴar Modibbo a Kano. Yaran babu mai murna haka Dada ta yi ta lallaɓasu gami da nunamusu muhimmanci da ladan dake cikin sada zumunta. Koda zuwansu suka sauka a gidan wani abokin Baba Naziru don yaran sun rantse baza su je kwana gidan Modibbo ba har da kukansu, anan ne Dada ta goyi bayansu, ita kadai ce ta karasa gidan dan uwannata  ta sauka dakin Amarya don duk ta fi mutan gidan kirki da dadin mu'amala. Ita ke yawan ba Dada hakuri akan yanda rayuwa ke tafiya. Hajja Fatuma ta yi bakin ciki da saukar Dada dakin Amarya ganin ita ce ke aurar da ɗiyarta.   Ranar wuni direba ya kawo yaran Dada kaf. Basu samu matsala sosai ba don hidimar biki ta sanya ma ba wanda ya hadu da Modibbo sai dai a wurin yaran su Adda Salma da sauran yan uwa, sun sha hantara. Sai da aka kammala bikin sannan Dada a karo na biyu ta kwashi yaran suka shiga bangaren Modibbo don su gaidashi su yi mishi sallama, wancan karon ya ganta sarai amma ko amsa gaisuwarta bai ba. Modibbo zaune shi kadai a falonsa, ta samu damar shiga dalilin ranar girkin Amarya ne. Yana ganinsu ya daure fuska tamkar bai taɓa dariya ba. "Ke har yanzu ba ki tafi ba?" Dariya ta ɗan yi. "Eh, amma gobe zan wuce. An yi biki, Allah Ya..." "Dakata, ke har wani bakin alheri ne da ke? Ai ni kaf zuri'ata ba za ta ga rashin alheri ba. Tashi ki ficemin daga gida! Zaman ya isa hakanan, biki ya ƙare tunda kin zo gayyar soɗi ai sai ki tattara ku koma." "Dada tashi mu tafi! Ba zamu kara dawowa ba! Na tsaneshi!" Da sauri Dada ta kalli Hussein ta rufemasa baki, shi kuwa Modibbo ya mike ya zo ya fisgoshi. "Kai! Dan iskan yaro, ni sa'anka ne? Haka aka koyamaka ka zageni?" Ya bubbuge bakinsa kafin ya murɗe kunnensa, Hussein sai huci kawai amma kukan ma ya ƙi yi. Dada na hawaye yaran na tayata ta mike ta ja hannunsu ta fito ba ta kara magana ba. Sosai ta gargadi yaran akan kar wanda ya fadawa Baba Naziru abinda ya faru, suna cike da ɓacin rai da jin haushin Modibbo wannan ta sa ba su amsamata ba. Ba ma kamar Hussein da ya ji duniya ya tsani mutumin. ***   Tafiya na ci gaba da tafiya, yan biyu suka kammala Sakandire, a sannan sun zama matasa, Hassan na sanya farin  gilashi a sannan a dalilin matsalar ido da yake fama da shi. Wannan ne ya taimaka wurin bambance su. Baba Naziru bai yi ƙasa a gwuiwa ba wurin nema wa kowannensu gurbin karatu a fannin da yake so, AlHassan ya samu fannin Accounting  a jami'ar Oxford, London. Yayinda Hussein ya tafi AUD a Dubai. *** Tsakaninsu da Nijeriya sai an musu hutu.  A wani zuwan ƙarshe da Hussein yi hutu, don wani lokacin hutunsu kan bambanta da na Hassan. Hutu wanda daga shi kuma sai kammala karatunsu. Bisa tursasawar Dada ya ziyarci ƴan uwan Babansu. Sosai ya samu tarba a hannun Adamu da Karime kamar koyaushe, zuwa Kanon da Dada ta ƙaƙaba ya fi komai dagula lissafinsa. "Nikam ba zan je ba." Cewar Hussein ransa a tsananin ɓace. Daƙuwa Dada ta mishi gami da harara, ya kauda kai. "Duk rashin ƙaunar da zai nunamaka ai hannunka bai taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ba. Mu mun san muhimmancin zumunci don haka dole ne ka je idan har na isa da kai." Ganin yanda ta dage har da ɓata rai yasa shi lallaɓa ta ya kuma shirya tsaf ya bi motar kasuwa ya tafi har da tsaraba Dada ta shirya ya kai. Tun a ƙofar gidan Kawun ya soma cin karo da samarin gidan, haɗe girar sama da ƙasa ya yi kamar bai taɓa dariya ba ya ƙarasa. Ciki-ciki ya yi musu sallama sai dai ba wanda ya yi yunkurin amsawa, wannan ya fi komai ƙular da shi. Wato don ubansu har sannan ba su ɗauke su wata tsiya ba. Ya yi kwafa ya karasa ciki. Ba laifi ya samu tarba daga Amarya sosai, ganin haka ya ƙi shiga ɓangaren Hajja Fatuma ya shantake har dai ta sanarmishi da shigowar Kawun daga kasuwa. Tsam ya miƙe ya nufi sashinsa. Yana zaune saman kujera ya shiga da sallama. Dubansa ya yi yana mai amsawa sai dai ganin ko waye ya karasa amsawar ciki-ciki. Hussein ya taɓe baki don dama ya shirya ganin fiye da hakan. "Barka da yamma." Ya gaida shi a ladabce. "Kai, me ya kawo ka gidana?" Kallonsa ya yi kyam. "Zumunci." Kawu ya ji wutar tsanar Hussein ta ƙara ruruwa a ƙoƙon ransa, shekaru kusan bakwai rabon da ya tako gidansa, Alhassan kan shigo koda ba ya so. "Na lura ba ka da kunya! To ko Aminu ubanka bai isa ba balle kai! Ni na fi ƙarfin tsagerancinku! Illar auren bare kenan... "Ubana Aminu ya rasu, gidan da ya je ba wani da zai dawwama a duniya bai je ba. Gidan biyu ne, wuta da aljan. Don Allah Kawu ka yimin dukkan zagi, banda ambatar iyayena." Miƙewa Kawu ya yi ma matukar fusata. Jikinsa har rawa ya ke yana kumfar baki. "Ni ka ke faɗawa baƙar magana?! Ni? Na maka kama da sa'an Uwarka?!" Hussein caraf ya mike a fusace, bai san sadda ya soma ɗaga murya a magana ba. "Kawu! Tsanar ta isa haka! Haba! Wadannan mutanen da ka ke zagi babu ranar da ba sa yi mana nasiha akan mu bi ku mu yi biyayya! Mene laifinsu ma zuwa a bare?! Waye bare? Ina ku ka samo wannan al'adar marar tushe?! Wallahi wallahi! Ina girmamaka ne domin Dada, darajar su ka ke ci nake ragamaka a dukkan wulakanci da cin kashin da ka ke yi! Amma... (Ya nuna shi da yatsa) Daga yau na zubar da girman a idona na take shi! (Ya yi amfani da ƙafarsa wurin murje ƙafet ɗin ɗakin) Daga kai har zuri'arka duk wanda ya ƙara gangancin cin zarafin iyayenmu sai na nunamaku cikakken ɗan halak ne Hussein! Mu zuba da ku!" Yana kaiwa nan ya juya yayinda kalaman Kawu ke shiga kunnuwansa. "Ni ka ke gayawa magana haka? Lallai zan nunamaka ƙarshenka!!" Wannan kalaman tsaf sun shiga kunnensa sai dai ko kaɗan bai ji ko ɗar ba, bai tsaya sallama da kowa ba ya kama hanyar fita. A zaure suka hadu da daya cikin samarin gidan ɗa ga Hajja Fatuma, Bashir. Fiito ya soma yi yana waƙe wanda hakan ya ƙular da Hussein ya kuwa haɗa kansa da bango ya bishi da lafiyayyen mari. "Ubanka ma ya yi kaɗan balle kai!" Daga haka ya fice ya bar shi da ihu da kururuwa. Ranar dai gidan abokin Baba Naziru ya kwana washegari da sassafe ya juya gida Adamawa. Kwanansu uku, ya yi mamakin yanda Kawu bai kira Dada ya sanarmata ba, shima ya haɗiye bai faɗa ba. Har hutunsa ya ƙare bai ji wani bayani ba don haka da dariyar mugunta ya bar ƙasar. Ya dai gane a baya ma Kawunnasu wuri ya samu! *** Daga AlHassan har Hussein, kowanne ya na iyakar kokari wajen yin karatu yanda ya dace. Basu da wani buri face su fito first class ko don su farantawa  uwa da uban da suka rikesu tamkar su suka haifesu rai. Hussein saurayi ne mai daure fuska da tsauri a wasu lokutan, zai yi wuya ka ga dariyar Hussein. Ya killace kansa ya kasa yin abokai sai abokinsa daya haifaffen garin Saudiyya kuma mazaunin can, Rasheed. Sun shaƙu sosai da Rasheed wanda ya kasance ruwa biyu. Mahaifiyarsa irin Takarunnan ne dake zuwa daga ƙasashe daban-daban, sai dai ita din ƴar Katsina ce a Nijeriya. Mahaifinsa kuwa haifaffen garin Makkah ne a Saudiyya. Zama ne ya haɗasu har aka kai ga yin aure, Allah Yasa Rasheed ta hanyar aure suka haifeshi. Wasu ƴanmata basu a gaban Hussein, akwai da yawa da suka yi suka gaji bai ko kallesu ba. Don ya wulakanta duk macen da ta tunkareshi ba kunya ta nuna tana sonsa, ba komai ne a wurinsa ba lokacin. Hakan yasa wasu da yawa suke komawa tsanarsa shi kuwa ya dau hakan wai harara a duhu don bai ɗaukesu da wata ƙima ba. Ɓangaren karatu, kusan yana daga cikin ƙwarin ajinsu wadanda za'a iya kira da gifted. Allah Ya ba shi fasaha da saurin daukar karatu hakanan Rasheed. Da taimakon Allah lokacin yayesu daga makaranta ya yi. Murna a wurinsu ba'a magana idan ka cire Rasheed da Hussein wadanda basu kaunar rabuwarsu. Sun tabbata sai ziyara ce za ta ƙara haɗa fuskokinsu, kafin ma a ziyarci junan zai iya daukar lokaci. ***   Hajiya Zeenatu Bashir wacce ta kasance marainiya, ta tashi a hannun kakarta mai son abin duniya. Sanadin hakan ne ta hadata da wata Agent mai safarar yara zuwa Saudiyya aikatau da Bara. Ta yi wannan aikin na shekaru goma kafin a karshe kanta ya waye ta samu ta tara kudi sosai ta dawo gida Nijeriya.  Haifaffiyar garin Katsina ce, sai dai kasuwancinta da kuma rasuwar Kakarta a shekarun baya, ya maidota Kano da zama. Ta zama mace mai zaman kanta, sun haɗu da Ƙawarta Hajiya Batool  wacce itama ta ke kasuwanci, a jirgi sadda za ta dawo daga Saudiyya. Nan suka ƙulla aminta sosai, don haka koda ta dawo Kano sai suka hada jari suka ci gaba da harkallar kasuwanci. Tana da zaurawa da dama waɗanda ta k rage dare da su,wannan a wajenta bakomai ba ne, a irin wannan harkar ne ta san da zaman Aliyu Dikko  wanda a baya sun zuba lokacinsu tare duk kuwa da tazarar shekaru biyu da ta ba shi. Haduwarta da wani ƙusa a gwamnati yasa jarinta daɗa faɗaɗuwa, ta soma fita sarin kaya Dubai tana kawowa katon shagon da ta buɗe a nan Sabon gari, kuma takan taɓa siyasa musamman wurin kamfen. A wani zuwan karshe  da ta yi ne a wani shagon kayan kwalam ta haɗu da wata ƙawarta da suka hadu a aikin Hajji, Hajiya Basira ƴar asalin garin Katsina da aure ya kai ta Saudiyya. Da mamaki ta kira sunanta, Hajiya Basira na ganinta suka cafke suna dariya. Kowannensu bakinsa cike da hira, karshe dai tare suka fito zuwa masaukin  Hajiya Basirar. Anan ne ta ke jin cewa ɗanta Rasheed ne ya kammala karatu ta zo bikin yayeshi.  "Ke dai Hajiya Zeenatu kin ƙi yin aure kin zauna kina cin karenki ba babbaka, nima fa nayi irin rayuwarnan a baya kafin Allah Ya tseratar da ni, kin fi kowa sanin yanda rayuwa irin haka ke ƙarewa." Wani fari da murmushi Hajiya Zeenatu ta yi. "Me kike ci na baka zuba ne? Tunda na tara abinda na tara dagaske yanzun nima aure zan yi. Kwantar da hankalinki." Suka yi dariya gami da cafkewa. "Yauwa, yanzu naji batu." Da wannan suka shiga hirarsu kafin a karshe Hajiya Zeenatu ta yi mata sallama da alƙawarin goben za ta zo su je taron yaye ɗanta a makaranta. *** Washegari kuwa ta cika alƙawari, a gidan Rasheed da Hussein suka kwana sai dai da sassafe suka koma cikin makaranta. Hajiya Zeenatu suka ɗunguma zuwa makarantar. Wuri ya cika ya batse, dalibai sun sha kyau sun gaji. Baba Naziru ne kaɗai ya zo wa Hussein, hakan ma ya mishi dadi sosai. "Yauwa ga ɗannaki." Muryar Hajiya Basira ya katse Hajiya Zeenatu daga kan wayarta, tunda ta ɗora idanu akan wani matashi da bai fi shekaru ashirin da biyar ba, mai cikar kamala da zati ta ji kamar an shanyemata  jinin jikinta. So da kauna da sha'awa wanda ya fi komai rinjaye, ya tafi kacokan kan HUSSEIN. Tafe suke tare da Rasheed yana murmushinnan mai kashe zuƙatan ƴan mata. Har suka ƙaraso suka ɗan russuna suka gaishesu, Hajiya Zeenatu ba ta iya amsawa ba. Kallo ɗaya Hussein ya yi mata bai ƙara ba tuni kuma ya ɗan daure fuska, kallo ne irin wanda ya san ƴanmata da ke bibiyarsa na yi gareshi, wannan ma kusan ya fi nasu muni a wajensa don kallo ne har da na haram. "Ana gaisheki." Sai a nan ne Zeenatu ta dawo hayyacinta ta amsa gami da taya musu murna. Hussein dai rarraba idanu ya ke, can ya hango Babansa, da sassarfa ya karasa ya rungumeshi. Shima Baba Naziru shi yake nema, suna murmushi suka saki juna ya mishi fatan alheri. Har suka bar wurin Hajiya Zeenatu tunanin Hussein ta ke yi, so da kaunarsa take ji na ratsata. Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta nemi lambarsa wurin Rasheed. Ta kuma nuna ta na son ganinsa. Rasheed bai kawo komai ba ya gayyaci Hussein gidansu, haka ya bar Baba Naziru a Hotel ya zo. Suka kebe da Hajiya Zeenatu "Lafiya Mama?" Abinda ya soma cewa kenan da ya soki Hajiya Zeenatu a ƙahon zuci. Murmushi ta yi da yin fari cikin jan sa. "Lafiya dai dan samari, oh, Hussein na Hassan." Ya ɗan daure fuska. "Sauri nake yi." Ta gyara zama. "Ka yi hakuri na sa an kiraka na kashemaka dukkan uzuri ko? Ba komai bane Hussein, wallahi sonka nake tun ganin da .." Dariya da ya shiga yi ne ya dakatar da ita kafin ya gimtse. Kallon raini ya watsamata ya mike tsaye "Dube ki don Allah! A haihuwar kauye wallahi kin haifen amma hakan bai sa kin ji kunyar ki kalleni ki ce wai kina sona ba! Ƴanmata ma basu isheni kallo ba ballantana kuma ke ƙatuwar da an girma ba'a san an girma ba. Don Allah ki kama girmanki , zai fi miki akan wannan budurwar zuciyar." Daga nan kama hanya zai fita. Muryarta ya tsaida shi. "Za ka yi dana sanin wadannan kalaman da ka furta gareni Hussein." Ya juyo yana murmushi ya dubeta don dagaske abin dariya ya bashi musamman na ganin hasashensa ya zama gaskiya, girgiza kai ya yi. "Naji daga bakin ƴanmata bila adadin. Ki yi duk abinda kika yi niyya, ni din dai har abada na fi karfinki." Daga haka ya banko labule ya fice ya bar Hajiya Zeenatu na cika da batsewa. "Alwashi na ci! Wallahi wallahi Hussein sai na aureka, sai na juyaka kamar waina a tanda." Ta furta a fili. Bata rabu da Rasheed ba sai da ta yi mishi dabarar da ta karbi har address din Hussein na Adamawa kamar yanda ya fadamasa. Da wannan ta koma Kano cike da shaukin Hussein da bege. ***   Ƴan biyun Dada suka dawo Adamawa da sakamako mai kyau, kowa a dangi murna yake. A sannan aka yi bikin ƴan matan Dada su uku, aka bar ta daga ita sai Auta Hafsat wacce a sannan take ajin farko a Sakandire.   Da shekara daya suka kammala bautar ƙasa aka shiga neman aiki, a sannan ne  alaƙa ta soyayya ta ƙullu tsakani Alhassan da Kausar. Shi kuwa Hussein ya rantse ba zai auri kowa a dangi ba don auren dangi ba ya burgeshi musamman kasancewar a sanadinsa aka tsani iyayensa. "Duk da haka ka fito da matar aure. Ba zamu zubamaka idanu ba." Abinda  kakansu kuma mahaifin Baba Naziru ya ce kenan. Taɓe baki Hussein ya yi. "Ga matarka nan Hajiya Zahida mai naira, nikam ta isheni." Aka sa dariya. Hajiya Zahida ta gyada kai. "Eh na isheka, amma ina bukatar abokiyar zama." Miƙewa ya yi. "Bari naje, ina da aiki dagaske." Ya fadi da harshen fulatanci. ***   MAFARIN KOMAI... Yammacin Laraba ce a garin Adamawa,  fitowarsa kenan daga katafaren shagon Ikhlas, hannunsa rike da leda ya siyo Ice-cream. Tana tsaye jikin motarta, tun fitowarsa daga gida ta ke biye da shi, koda shigarsa shagon, ta ja kwallin da Gora ya bata, da tabbacin duk inda ta yi ido hudu da Hussein, komai zai kasance yanda ta so. Da wannan ta yanke tunaninta ta ƙarasa inda yake. "Hussein." Fuska a daure ya ɗago ya dubi mai maganar, ido cikin ido suka kalli juna. Wannan ɓacin ran da ya tasomasa da wannan daure fuskar, sai ya nemesu ya rasa, wata soyayya ce ke shigarsa da kauna. Kansa ya yi wani nauyi, ga mamakinsa, murmushi ya shiga yi mata. "Nasan ba ka gane ni ba, Hajiya Zeenatu ce da ku ka haɗu a Dubai." Maimakon baƙar magana sai ya yi ƴar dariya da lumshe ido. "Na ganeki mana, Zeenatu ai kyanki kadai ma ba zai sa na manceki ba." Wani dadi da farin ciki ya kusan zautar da Hajiya Zeenatu. Gora da Hajiya Batool ta shiga sanyawa albarka. Sanadin Hajiya Batool ta san Gora, yau gashinan ya ba ta abinda bata taba tsammanin zuwansa da sauƙi ba. *** Tun daga wannan ranar magana da tunanin Hussein ya koma kan Hajiya Zeenatu, kamar yanda ta kwaɓeshi da faɗar alaƙarsu a gida, haka ya bi. Idan bai ji muryarta ba har hawaye yake fitarwa ya bazama hotel din da ta sauka. Hussein ya sauya a gidan, Dada ta zaunar da shi ta mishi tambayar duniya ya nunamata ba komai. Hakanan Hassan ya kasa gane kan ɗan uwansa. Haduwar Hajiya Zeenatu da Hussein na karshe ta fashe da kuka ta nunamasa idan har yana sonta ya amince ya biyota su wuce Kano a dauramusu aure don kuwa ta tabbatar ba wanda zai amince da aurensu a danginsa tunda ta girmeshi. Hussein ya ji maganar babbarakwai, hankalinsa ya tashi. Yana so ya ce mata a'a amma abin ya faskara, ganin bai ce komai ba ta ƙulla gaba da shi ta ce ya rabu da ita har abada ba ta sonsa. Kowa ya kama gabansa. Ta fadi hakan ne don ta san ba mai yiwuwa bane, tuni ta juyamasa ƙwaƙwalwa ta hanyar zubamishi siddbaru a abinci da abin sha. Wani irin soyayyarta ke addabarsa da wani irin tsoro. Sai dai batun ya bar ƴan uwansa dominta ne ya ji kamar ya mishi nauyi. Da wannan suka rabu ta koma Kano kamar yanda Hajiya Batool ta bata shawara, sun riga sun san zai biyo bayanta don aikin da aka yi mishi mai karfi ne. Layu ne aka sanya a gaban gawar mace. Hakanan an kwaƙule idanun jariri sabon haihuwa an haɗa da maganin. *** Kwanaki uku ya biyo baya Hussein ya rame ba walwala. Wannan ya tashi hankalin kowa. Aka haɗa meeting aka zaunar da shi don jin bayani. "Aure nake so a yimin. Na samu matar aure amma ta girmeni don za ta yi shekaru arba'in. Wallahi ita nake so, don Allah kar ku hanani aurenta."   Ran kowa ya ɓaci, nan Baba Naziru ya rantse ya kara ba zai aureta ba. Kowa kuma ya goyawa hakan baya ba tare da sanin abinda hakan zai haifar ba. Ga mamakin kowa Hussein ya mike a fusace. "Eh dama ai kun fi son Hassan! Shi da ya kawo wacce ya ke so wane ne ya hanashi? Sai don zan auri bare? To ai nima uwata bare ce a cikinku don haka ba wanda ya isa hanani auren wacce nake so!" Daga nan ya fice daga dakin ya bar kowa baki a sake. Dada kuka ta sanya saboda kunyar da Hussein ya bata. A karshe Baba Naziru ya fusata ya ce da kansa zai zaɓamasa matar aure. *** Washegari cikin dare Hussein ya shirya kayansa da takardunsa masu muhimmanci, ya kalli Hassan dake bacci na ƴan dakiku. Kirjinsa na faduwa hakan bai sa ya sauya ƙudurinsa ba. Hannu ya kai ga wani hotonsu da suka yi a tsaye da ƙananun kaya, asalin hoton a waya suka yi amma saboda kyansa suka wankeshi suka sanya a frame. Ya dauka ya cusa a jakarsa. Ji yake kamar muryar Hajiya Zeenatu na amsa kuwwa a kunnensa. Gani yake idan har ya kara kwana bai je inda take ba haukacewa zai yi. Daga wannan tunanin ya sa ƙafa ya bar gidan. Maigadi na can yana sharar bacci ya fice gaba daya. Wannan tafiyar da Hussein ya yi, shi ne tafiyar da bai ƙara takowa gidansu ba har wannan lokacin. *** Koda ya isa Kano ya nemi Hajiya Zeenatu, ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Da kanta ta daukoshi daga tasha zuwa gidanta. "Nasan dama ba za ka iya rayuwa babu ni ba." Da jajayen idanunsa ya dubeta ya bi ta da murmushin yaƙe. Ta mike zuwa dakinta ta faɗa bandaki, zirr ta yi ta wanke jikinta da ruwan magani kafin ta dawo ta shirya ta rambaɗa kwalli. Wani  gari ta ɗebo a hannunta ta dawo falon. Yana kallonta har ta zauna, a hankali ta bude tafin hannun ta huramasa a fuska. Tun yana ganinta daidai har ya yi luuum ya soma lumshe ido. Wani magana ta shiga yi mishi a dodon kunne yana nanatawa. "Ni kadai ce a wajenka, ni kadai ce a zuciyarka, ba ka da dangin da ya wuce ni. Ba ka da kowa a duniya sai ni." Ya nanata, tun yana yi har a hankali ya kwanta kamar mai bacci. Wani mahaukacin dariya ta sanya. *** Malami har gida ta kirawo ya daura aurenta da Hussein. Rabon goro da aka yi a makwafta ne ya sa suka san ta yi aure. Daga wannan lokacin  Hussein ya zama mallakin Hajiya Zeenatu ita kadai, jallin jal! Ya samu aiki a wani babban kamfani ta hanyarta, tun yana matsayin ma'aikacin  har a karshe saboda jajircewa da amanarsa da kuma sanin makamar aiki, ya zama Manajan kamfanin. Hajiya Zeenatu likkafa ta ci gaba, ta gina shaguna da dama, auren Hussein sai ya zama kamar wani buɗi a kasuwancinta. Ta dinga samun albarka a ciki kamar me. Har ya kasance ta bude shagon siyar da gwala-gwalai a sabon gari, tana kuma da na abayoyi, takalma da jaka a sabon gari. Suka hadu ita da mijinta suka bude katafaren shagon kayan maƙulashe mai suna A&Z Snacks and more. ***   CI GABAN LABARI...   I just published "BABI NA HAMSIN DA UKU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1012068713?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=j0FhiwXlITINd2s%2FHQAEEJr6H0gN34Yx%2FYGs482Ps7p3eJzBM%2FSmZhkqmfmpfxwFqACqKgF4HYZBiBOLOGtFCjGLt%2FaBpqaFBTls4fQJ%2Fq25n%2BYh6%2FU6TYbmPJBSRTTM 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 53)    ADAMAWA Hafsat ce tsaye a farfajiyar gidan suna hira da Tahir, murmushi sosai ne saman fuskarta, ko ba'a faɗa ba duniyar ta mata daɗi. Tahir kuwa jin komai yake yi kamar a mafarki, dama an ce mai hakuri kan dafa dutse har ya sha romonsa, yanzun gashinan ya gani. A hankali soyayyarsa ta kama zuciyar Hafsat. "Dariya na ba ki?" Ya fadi yana murmushin shima. Hafsat ba ta kai ga ba shi amsa ba, suka ji hon. Nan da nan ta rude, ta san AlHassan ne don ya kira Dada ya sanarmata cewar yana hanya, ba wanda zai zo gidan da darennan idan ba shi b, hakan yasa ta dubeshi. "Mu yi magana ta waya. Bari na shiga ciki." Ba ta bari ya kai ga amsawa ba ta yi gaba da sauri. Tahir ya shafi ƙeya yana murmushi. Daidai sadda motar AlHassan ta faka, ya nufi wurin. Sai dai ya tsaya cak yana kallon wanda ya soma fitowa daga mazaunin gefe. Kamar AlHassan kamar ba shi ba, kafin ya kai ga tantancewa sai ga AlHassan ya buɗe murfin ƙofar ya fito Wani tsalle da Tahir ya yi ya rungume Hussein yana ihun murna sai da ya ba AlHassan mamaki, sai kuma ya yi dariya. Duk wanda ya zauna da Dada ko na minti talatin ne, sai ya san yanda take kewar Hussein. Balle kuma Tahir wanda dama shi a baya ya san Hussein din, duk da ba su wani saba ba. Sanadin zamansa a garin kuma a gidan yasa shi damuwa da damuwar Dadan har yakan taya ta addu'a. Suka dunguma ciki zuwa falon, Hussein jikinsa har rawa yake, burinsa kawai ya sanya Dadarsu a ido. Tana falon zaune, a gefenta Fatima ce ke cin Popcorn duk ta ɓata hannunta da madara. Hafsat kuwa ɗaki ta shige gudun kar AlHassan ya gan ta. Sallamarsa ta yi yanayi da ta AlHassan, hakan yasa Fatima wurgi da ledar Popcorn a guje ta nufeshi idanunsa akan Dada, ya durkusa ya ɗaga ta cak kafin ya rungumeta. Dada tsam ta miƙe jiki na rawa tana mai ƙuramasa idanu, a hankali idanunta suka ciko da kwalla. Nan da nan ta shiga zubar da hawaye, ta kalli AlHassan ta dubeshi, da sauri ya ajiye Fatima wacce ta yi turus tana kallon wanda ya ɗaga ta alhalin ga babanta a baya ya shigo. Da sassarfa ya isa ga Dada ya rungumeta kawai sai hawaye masu ɗumi suka zubomishi. "Dadata." Dada ta lumshe idanu ta bude, shakka babu ba mafarki ta ke yi ba. Da sauri ta ɗago kan Hussein ta na shafa fuskarsa da duka hannuwanta biyu. Kukanta bai tsaya ba hakan ya jawo mata rawar murya. "Husseini, kai ne? Dagaske kai ne tsaye a gabana? Allahu Akbar." Kawai ta kara ƙarfin kukanta. Ya ja hannunta suka zauna saman kujera, ya zame hannunsa guda cikin nata. Ya shiga sharemata hawaye. "Ni ne Dada, Hussein dinki ne. Na dawo gareki Dada. In sha Allah ba zan ƙara nesanta kaina da ke ba. Ki yafemin, wallahi ba ni da laifi." Ta shiga girgiza masa kai amma ina! Ta kasa magana don kuka sai kuma ta shiga dariya da hamdala. "Yaya Hussein?" Hafsat ta fadi a hankali bayan fitowarta daga ɗakin hayaniya ta ƙi ƙarewa. Ta ƙarasa itama ta rike hannunsa, kallonta ya ke yi da mamaki kafin ya yi ƴar dariya ya dubi Dada. "Auta kenan?" Ta yi murmushi kawai, ba ƙaramin mamaki ya yi ba. "Shekaru bakwai fa Husseini, jiya ba yau ba. Tun kana da shekaru ashirin da takwas muka rabu da ganinka." Hawaye Dada ta share tuna irin jinyar da ta yi adalilin rashinsa. "Ya isa kukan please Dada. Mu godewa Allah tunda yanzun ya cika buri." AlHassan ya furta don har ga Allah ba ya son ganin ana kuka, musamman ma kukan Dada. Nan fa aka shiga nan nan da Hussein, abinda ya fi so a baya, wato fura da kuma dambun shinkafa, shi Dada ta sa Hafsat ta yi. Dakyar Hussein ya rarrasheta akan a bar Dambun dare ya yi sai zuwa gobe. Bayan sun gabatar da sallar isha'i suka zauna zaman hira. Shiru ya yi yana jin AlHassan na waya da su Hajiya yana sanarmata cewa sun sauka lafiya. Bayan ya kammala ne aka shiga hira. Tiryan-tiryan AlHassan ya ba Dada labarin komai tun daga farko har ƙarshe. Dada kuka ya dawo sabo. Takaicinta yanda matar ta ɓatawa ɗanta ƙuruciyarsa. "Me ka ke jira ba za ka saketa ba Husseini?" Murmushi Hussein ya yi gami da ɗan matsa ƙafar Dada kaɗan. "Komai yana da lokaci My Dada, ki kwantar da hankalinki." Ba haka Dada ta so ba, sai dai kuma ba ta tsoron komai tunda ta san ki mene yanzun da asiri a ciki. Da yardar Allah kuma hakan ba zai ƙara faruwa gareshi ba. Tahir dai kallonsu yake kawai, ya lura da ɗan sauyin da Hussein ya soma gwadamishi tun da ya ji alaƙarsa da Kawu. Bai yi mamakin komai ba don ya san dama za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Shi kam yana tunanin fasa tafiya Kano da zai yi a goben sai zuwa jibi duk kuwa da irin wayar da Kawun ke dokamishi akan ya dawo. Washegari da safe dangi suka cika ganin Hussein, Gwoggo Karime har da kukanta, takanas ta tahowa da Hussein lafiyayyen farfesun da ta girka da hannunta. Hakanan shima Kawu Adamu, hatta da sauran yaran Inna da ke a Adamawa da yaran Hajjo sun zo ganin Hussein. Gida ya cika ana murna, ya yi mamakin yanda suka sauya. An sha hira kamar ba gobe. Fatima tunda ta gane dan uwan mahaifinta ne ta maƙale masa, wannan kaunar nata da ya soma yi tun bai san dangantakarsu ba yana nan daram a ransa sai ma ƙaruwa da ya yi. Kowa ya yi Allah wadai da Hajiya Zeenatu, har da masu kuka. Ranar dai har dare bai samu kansa ba sai dakyar. Hajiya Zeenatu ta kira sai hakuri ya ba ta ya nunamata ana ta tambayarta da son ganinta. "Ko na biyo hanya gobe na zo?" Ya yi murmushin mugunta jin irin wannan wauta daga matar da ta kusa dosar shekara hamsin. "Aa Hajjaju, ki yi zamanki, idan zan ƙara zuwa sai mu dawo tare. Dawowar dindindin." Wannan amsar ya ba ta sai ta ɗan yi turus, a karshe dai ya yi mata dabara ta sake kafin su yi sallama. Ƴan Maiduguri labari ya riskesu su ma sai murna. Hussein ya san zama bai gan shi ba, zaga dangi ya zamar masa dole. ***    BAYAN SATI BIYU.. KANO Ta fito daga motarta a farfajiyar asibitin Baba Dakta. Amrah aka yiwa aiki sakamakon faɗuwar da ta yi a bandaki da ya jazamata naƙudar dole, cikinta bai jima da shiga wata na takwas ba, an ciromata Baby Boy. Yaron sai ka rantse ya shiga watansa tara cif sannan ya fito duniya. Ta zagaya ɗayan gefen ta ɗauki kwandon abincin da ta kawomusu Da ka ganta za ka fahimci tana cike da farin ciki. Tun da ta ji labarin auren da Chairman zai yi na huce haushi take jin ta kamar an mata albishir da gidan aljanna. Yanzun ta kara tabbatarwa babu abinda zai ƙara haɗa ta da shi. Ta sha adonta cikin laffaya dark brown mai adon milk flowers a ƙarshensa. Fuskarta babu wani heavy make up, hoda kawai ta shafa sai man leɓe mai danƙo. Ga duk wanda ya ganta sai ya ƙara kalla, Allah Ya ba Ramlat ƙira mai kyau, sai ka rantse ba ta taɓa haihuwar ko ƙwai ba ballantana ɗan mutum. Da wannan takun ta ƙarasa cikin asibitin zuwa dakin da aka kwantar da Amrah. Ta murda kofar da sallama ta shiga. Umman Amrah na zaune gefe tana kurɓar ruwan shayi, ta karasa suka gaisa. Amrah na bacci. Ajiye kwandon ta yi ta ƙarasa ga gadon Babyn, murmushi kawai ta ke yi tana ƙaremishi kallo, duka-duka yau kwanansa hudu a duniya. "Ki ciro shi mana Ramlat, ke da ɗanki." Ta juyo tana dariya kadan. "Um um, gwara ya yi baccinsa Umma. Ni gani ya yi yana juyewa zuwa kamannin Zaituna." Umma ta yi murmushi. "Gashinan dai, sai sauya kamanni ya ke." Ta jinjina kai. "Naga kin warware sosai yanzu, ko don kin ji labarin auren Chairman ne?" Umman ta karashe da dariya, itama dayake abinda ke ranta kenan sai ta sa dariyar. "Umma bari kawai, sosai fa na ji dadin rabuwa da alaƙaƙai." Dariya sosai ta ba Umma. "Kai Ramlatu ba ki da dama, wato alaƙaƙai? Ko ya suka ƙare da Kawunnaki?" Ta ɗan taɓe baki. Chairman a farko cewa ya yi dole Kawu Bello ya biyashi kudaden da ya kashemusu, daga karshe dai ya yafemasa ya ce komai ya wuce. "Yanzu ki ka zo?" Muryar Amrah ta katse su. Suka dube ta. "Yanzu na zo, sannu ya jiki" Amrah ta amsa tana kokarin mikewa zaune, cikin sauri Ramlat ta karasa ta taimaka mata. Ita ta yi mata rakiya bandaki ta yi fitsari da kuma brush sannan suka dawo. Umma kuwa ta gyara shimfidar ta kwantar da ita. Ramlat ba ta wani jima ba ta yi musu sallama ta fice zuwa wurin aikinta. Tana tafe tana tunani, idan har Hussein zai iya mance ta ko a whatsapp bai neme ta ba, ita kuwa meyasa ba za ta dangana ta hakura da shi ba? Ta gama saddaƙarwa babu ita a ransa, ba ya ta tata. Don haka tana ji har zuciyarta ta hakura da soyayyarsa. Da gaskiyar Auta A'isha da ta taɓa ce mata gani take kamar Hussein ya fi ƙarfinta, yanzun kuwa ta yarda kuma ta gasƙata. A hankali ta sa bayan hannu ta share kwallar da ta cika idanunta. Muddin zai faɗomata a rai to fa sai ta ji kwalla. Wayarta ta ɗauki ƙara, ta kai duba. Baban Hanif, kamar yanda ta sanya sunansa, wani ne da ba su yi ko sati da haɗuwa ba, ta kai yara shopping, a farko ya dauka tana da aure don haka ya hakura, sai dai haduwarsu ta biyu a kofar gidan Hisham kasancewar shi gidansa a Badawa Layout yake, ya ganta. Ya san Hisham don haka bai ƙasa a gwuiwa ba ya faka motarsa ya sauko suka gaisa da Hisham, ta gaidashi ta shige cikin motarta. A bakin  Hisham ya ke jin cewar ba ta da aure, anan ya nunawa Hisham yana so. Hisham ya yi shiru a sannan, a karshe ya nunamasa ba ruwansa ya nemi soyayyarta. Da kansa ya yiwa Ramlat magana ta fito daga motarta, ta tsaya ta dan saurareshi. Ita kuwa ganin tunda har Hisham bai hana ta kulashi ba, kuma aminin Hussein ne, to tana da tabbacin babu alamar Hussein na sonta. Wannan yasa ta dangana ta hakura ta ba Baban Hanif dama. Sauke ajiyar zuciya ta yi ganinhar wayar ta katse ba ta ɗaga ba. Ya ƙara kira ta ɗaga. Bayan amsa sallama ta ba shi uzurin tuƙi dole ya hakura. *** "Shi kika tsayar kenan matsayin miji?" Tambayar Baba Dakta ya sa gabanta ya faɗi, kanta a ƙasa yayinda yake zaune saman darduma idanunsa sanye da gilashi yana duba wani littafi na addini. Ta haɗiyi miyau, ta hakura yanzun za ta auri Baban Hanif. Ko ba komai ta yaba da hankali da nutsuwarsa. Hatta da Hajiya wannan karon da ma yan uwanta kansu, hankalin ya kwanta da shi. "Eh Baba." "Ramlat, kamar yanda ki ka amince da aurensa, bana son jin wata magana ta ɓullo daga baya." A hankali hawayenta ya zubo, ba wanda ya fadomata a rai sai Aliyu da kuma yanda aka yi gumurzu a lokacin bikinsu. Abbanta ta tuna wanda a yanzun ta ke kallon Baba Dakta kamar shi. Basu da hadi sai zumunci tun shekara da shekaru da ya kasance Baba Dakta har yana da karfin ikon yanke hukunci a kan iyalin Abbansu, kuma ta zauna.   "Na ba ki nan da kwanaki uku, ki yi tunani dakyau, idan har kin amince ki zo ki sanar da ni. Zan ba shi damar ya turo magabatansa. Allah Ya zaɓamaki abinda ya fi alheri." Ta kasa amsawa a fili sai a zuci, jiki a sanyaye ta mike ta mishi sai da safe ta kama hanyar gida. Kiran kenan daman, koda ta isa gida ba ta ɓoyewa Hajiya komai ba. Hajiya ta yi murmushi. "Yaron ya san abinda ya ke yi da alama, kuma ko ba komai ɗan babban gida ne tunda Kakansa ma abokin Kakanki ne, wato Mahaifina. Zuri'ar Imam Shu'aibu Lawwali bani da shakku a kansu da yardar Allah. Kuma ke a dadinki ma tunda ba gida daya zai haɗaku ba da matarsa." Ramlat ta yi shiru jikinta a sanyaye kawai tana sauraron Hajiya. Ta daure ta yi murmushin da bai kai zuci ba. Tana ji a ranta ko mutuwa za ta yi, wannan karon ba za ta ba iyayenta kunya ba. An yi ta kuma an ƙare. A wannan yanayin Munir ya shigo gidan a fusace, suka dube shi. Oyoyon da su Affan ke mishi bai amsa ba. Bayan zamansa Hajiya ta dubeshi bayan amsa gaisuwarsa. "Lafiya kake kuwa?" Ya yi kwafa. "Hajiya, wallahi Bilkisu ta haukace. Ba ta da hankali. Akan zama a gaban mota ta kama Hunainah da duka." "Da cikin?!" Fadin Hajiya da Ramlat har suna hada baki. "Na gaji! Wallahi na gaji da wannan rigimar ta Bilkisu. Haka kwanaki ta kawo wannan ƴar iskar ƙanwarta Salma, yan iskan samarinta na zuwa tafiya da ita night club ni kuwa na kora ta gidansu ba zan iya ba." "Kai ba wannan ba, ka ce ta daki yarinya, yanzu ya ake ciki?" Munir da har lokacin bai huce ba yana aikin karkaɗa mukullin hannunsa, ya dubi Hajiya. "Ba ta yi mata rauni ba, ni ne dai na raunata Bilkisun, kuma na kora ta gidansu na sake ta." "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Kana da hankali kuwa? Yanzu kai ba za ka iya hakurin zama da mace ba? Haba Muniru! Ai idan rai ya ɓaci, hankali ke dawo da shi." Ya saki baki don mamaki, duk irin cin kashin da Bilkisu ke yi amma ana kiran meyasa ya sake ta? Hajiya sosai ta yi faɗa ta ce ta ba shi nan da gobe ya maida aurensa da Bilkisu kafin ransa ya ɓaci. Ganin bai samu goyon baya ba haka ya tattara ya fice sai gidan Baba Dakta. Nan ma dai duk kanwar ja ce, sai dai ɗan saukin da ya samu jin cewar Baba Daktan zai kira Kawu Jamilu su je gidan tare a washegari. *** Kwanaki ukun da Baba Dakta ya ba Ramlat na cika, bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ƙara kiranta don jin ta bakinta. Kai tsaye cikin fawwalawa Ubangiji lamarinta ta ba shi damar yi mata zaɓi a wannan karon. "Idan har shi ka zaɓarmin Baba, na amince zan zauna da shi kuma ba zan ba ku kunya ba." Baba Dakta sosai ya ji dadin batunta, ya sa mata albarka karshe ya ce duk abinda ya yanke daga baya za ta ji. Da wannan suka ajiye maganar. "Kar ki yi gaggawar amincewa da Baban Hanif." Amrah ta furta bayan Ramlat fitar Umma daga dakin kasancewar ta dawo gida an sallame su. Ramlat da ta ƙurawa Zayyan idanu, yaron Amrah, ta yi murmushi. "Ba zan yi ba in sha Allah. Watakila shi ne alherina, na dai bar wa Allah zaɓi, duk abinda Baba ya yanke kaina shi ne daidai. Idan ya amince da aurena da Baban Hanif shikenan." "Ba ki tunanin Hussein kan iya dawowa watarana?" Ta hadiyi miyau a kokarinta na danne damuwarta. "Koda ya dawo mene ne haɗina da shi? An faɗamaki kalmar so ta taɓa shiga tsakaninmu?" Amrah ta sauke ajiyar zuciya, ta sani da gaskiyar Ramlat. Hussein bai furta yana sonta ba, kuma ko a waya ba ya nemanta. "Amma sai naga kamar yana sonki." Ta girgiza kai. "Tunaninki kenan, yanzu dai a bar zancen ba shi da wani amfani." "Ai shikenan. Allah Ya yi maki zaɓi na alheri." Daga haka Amrah ba ta kara tada zancen ba. ***   BAYAN KWANAKI UKU... BAZATA..... Tana kwance a saman doguwar kujera tana karatun wani littafin hausa mai suna KE ALHERI CE a wattpad, dariyar Nene ta ke yi sosai har ɗankwalinta na zamewa. Tana sanye cikin riga da siket ƴan kanti da ya yi mata kyau. Ummi da su Ansar suna farfajiyar gidan su na wasa, sai ji ta yi su na ihun oyoyo Uncle. Ta yi ƙasaƙe tana sauraro can kuma ta yi murmushi don jikinta ya ba ta idam ba Hisham ba toh Hilal. Mikewa zaune ta yi ta gyara zaman ɗan kwalin kanta, ta mike gaba daya da zummar ɗauko mayafi, sai dai sallamar wanda ta ji ya katse dukkan yunƙurinta. "Wane ne ya zo ne nake jin...Au, Husseini?" Hajiya dake fitowa daga daki bayan idar da sallah ta ke tambayar, ganin wanda ke tsaye bakin ƙofar suna kallon kallo da Ramlat yasa ta katae tambayar. Ramlat da sauri ta fada daki don ɗauko hijabi, shi kuaa ajiyar zuciya ya sauke ya ƙaraso ya durkusa yana gaida Hajiya da bakinta ya ƙi rufuwa. Gaba daya ya sauya sai ka ce wanda ya fita ƙasar waje, ya ƙara kyau da ƙiba abinsa. "Dama za ka dawo ɗannan? Ni na ɗauka kuma sai dai mu bi bayanka da kayanka. Nan abokinnaka shima ya zo ya gama jajensa." Dariya ta ba shi. "Ayi hakuri Hajiya, na yi laifi ko a waya  ban sanar maku batun zuwana ba." "Ba komai ai." Nan kuma aka shiga hirar yaushe gamo, Hajiya ta aiki Ummi kiran Maminta don kawo ruwa. Ta fito cikin dakin  ba ta ko kalli inda yake ba ta shige kicin. Hussein yana nazarinta a hankali. Har ta kawo ruwa ta ajiye da murya ƙasa-ƙasa ya ce. "Kin fi koyaushe kyau." Ta ɗan dubeshi, ya watsamata lumsassun idanunsa yana murmushi. Ta kauda kai kirjinta na bugu da sauri-sauri. Zubamishi ta shiga yi a kofi hannu na rawa. Koda ta miƙa maimakon ya karɓa sai ya ɓige da tambayar Hajiya. "Na yi zaton zan tarar an yi bikin Ramlat." Ta dube shi ranta na zafi, wato dai yana kara tabbatar mata babu ita a shafin rayuwarsa. Ta mike ta nufi daki sadda Hajiya ta soma ba shi labarin yanda ta kaya da Chairman. Bai katse ta ba har ta kammala. "Allah Ya kyauta." Shi ne kadai abinda ya furta. Daga bisani ya sanyo wata hirar daban inda a karshe ya kira Dada a waya video call ya haɗa su suka gaisa, Dada godiya ta shiga yi sosai da sanyawa Ramlat albarka. A karshe ta nemi gaisawa da Ramlatun, Ummi ta karɓi wayar ta shige dakin a guje ta kai wa Ramlat da ke kwance saman gado. "Mami, ga Dada." Tana shirin magana sai ganin fuskar Dada ta yi saurin mikewa zaune ta maudo fara'arta. Suka gaisa har ta ba Hafsat ma suka gaisa. Godiya kam ta sha shi, tuni Ummi ta fice daga dakin. Daga bisani suka yi sallama ta katse kiran, dama a wayar Hafsat ne. Hankalinta ya kai ga hotonsa dake saman screen din, ya rungume throw pillow guda a kirjinsa yana kwantar da kai yana murmushi. Sai take ganin kamar ita ya ke yiwa murmushin hakan yasa ta yi saurin jan guntun tsaki gami da hararar wayar kadan kafin ta cillar da zummar sai Ummi ta shigo ta maida mishi. Kwanciya ta yi har sai da ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayarta. Ta jawo ta duba, lambar da ba ta sani ba. Ta bude. _*"Wayartawa itama raba ni da ita kike son yi yanda ki ka yimin iyaka da HEART?"*_ I just published "BABI NA HAMSIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1013598891?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=1t7u8q%2B2i2CmVekKWI5wFx%2BLsRJJivM5TtUSxqfucEgX0H3IsSDvgfmbOaj%2FRM2R1oO3SAwAvV7%2FIJ95dbqOXcbxCoIbZ9MIciCSdP0fW4VijXfBR0gyHI42Cn5Za4Rc 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 54) Ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci, takaici ya sa ta wurgi da wayar gami da hararar wayarsa da ke ajiye ta ja tsaki. Ta rasa gane me Hussein ya ke nufi da ita, ba ta san wane matsayi ya ajiye ta ba. Ta cije lebbanta tana karkaɗa ƙafa daidai sadda Ummi ta faɗo ɗakin a guje. "Mami, wai inji Uncle.." Ba ta bari ta ƙarasa ba ta yi saurin yi mata nuni da wayar. "Maza dauka ga ta can ki miƙa masa." Ummi wacce ba shi ya aiko ta ba, ta girgiza kai sai dai ba ta fasa ɗaukar wayar ba kazalika ta ci gaba da zancenta. "Wai ki zo zai tafi." Harara ta watsawa Ummin. "Ki ce ba ki ganni ba." Ummi ta bude baki. "Mami kin fa hana mu.." "Kika karasa sai na buge bakinki. Naji ba zan zo ba wuce ki ban wuri." Rai ba dadi Ummin ta fice, Ramlat ta sauke ajiyar zuciya. Kwanciya ta yi sai dai karatun littafin da ta ke yi ma ya fice a ranta. Ba zato ta ji muryar Hajiya. "Ramlatu yaushe ki ka sauya? Baƙo ya zo domin ya gaishemu shi ne za ki aikamasa mugun kalamai? Me kike nufi da ba za ki je ba? Wani abun ya haɗa ku ban sani ba?" Jikinta sai ya yi sanyi, Hajiya ta ba ta umarmin fita, a dole ta mike tana ba ta hakuri sannan ta gyara zaman hijabin ta fice ranta na tururi. Ba kowa falon sai wata ƙatywar leda a gefe, don haka ta tsaya gami da juyowa da zummar komawa ciki, suka yi kiciɓus da Hajiya. Harararta ta yi. "Ki je yana waje tare da yara. Tsaraba ya kawomusu. Ki mishi godiya don Dadarsa ta aikomin fura da nono." "Toh." Ta amsa a ciki-ciki tamkar ba ta so sannan ta fice, ita dai Hajiya bin bayanta da kallo ta yi da mamakin wannan sauyi a fuska da gangar jikinta. *** Yana zaune a mazaunin direba ƙafarsa ɗaya a waje, alewa ce a hannunsa yana kokarin ɓarewa Affan.  Ta kauda kai daga kallonsa ganin ya ɗago nashi kan, kallonta yake da murmushi a saman fuskarsa. Sai kuma ya miƙawa Affan alawar ya dube su. "Oya ku shiga ciki." Dama haka suke jira musamman Ummi da ke rike da ƙatuwar ledar kayan kwalam da ya damƙa mata su je su sha. Ba ta son hararar da uwar ke watsomata wannan ta sa ita ce farkon sheƙawa a guje sauran ma suka mara mata baya. Ta rasa dalilinsa na korar yaran don haka ta ja numfashi ta furzar. Cikin dakiya ta dubeshi kirjinta na bugu da sauri-sauri. "Hajiya ta ce na kara miƙa mata godiya. Allah Ya saka da alheri. Mun gode sosai da ɗawainiya." Ya murmusa yana shafa sumar kai. A hankali ya kai hannu ya bude dayan murfin na motarsa. Dubanta ya yi. "Dan zagayo ki zauna ki ban aron koda mintuna biyar ne, magana zamu yi." Ta yi shiru ba ta tanka ba, karshe ma ta daure fuska don ta san wani sabon rainin hankalin ne. "Please." Ya furta a sanyaye, sai ta ji ba za ta iya jan musu ba don haka ta zagaya ya bita da kallo har ta shigo ta zauna. Shiru ya biyo baya har dai ta ƙosa amma ba ta ce komai ba, shi kuwa yanda ta ke hura hanci ke ba shi mamaki da dariya. Ya ɗan murza karan hancinsa kafin ya soma magana cikin nutsuwa. "Satina sama da biyu a Adamawa, ba ki samu damar yimin ko gaisuwar juma'a ba, why?" Ranta ya sosu ainun. "Ina tunawa  da wadanda suka tuna da ni. Bana sanya ka layin wadanda suka zamemin wajibi na nema balle na gaida." Ɗif ya yi kamar mutuwa ta ratsa, ta daurewa zuciyarta ba ta kalleshi ba sai dai ta ji wani irin sanyi a zuciyarta ko ba komai ta ɗan huce daga maganar da ya gasamata. Sai ta tsinci kanta da murmusawa. A hankali ta saci kallonsa don ganin yanayinsa, ga mamakinta murmushi sosai yake haƙoransa a waje, ya juyo rabin jikinsa ya tallafi haɓarsa da hannunsa ɗaya yana kallonta. Ta kauda kai. "Hakan ma na gode sosai. Kin burgeni. Rashin wancan mutumin ne yasa ki ka sauya har ki ke gasan magana ko? Hum, za ki huce." Ba ta ce uffan ba hakan yasa ya gama shan ƙamshinsa ya ɗora. "Alhamdulillah, na sadu da iyaye da yan uwana lafiya. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin Talikai. Wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da har abada Hussein ba zai mance da Ramlat ba. Na je Mubi kuma na je Maiduguri. Ban taɓa zaton  zuwan rana makamancin hakan ba, komai ya faru bisa jajircewarki akan dukkan lamurana. Na gode. Ina kara godiya da fatan alheri gareki. Har abada ba zan mance da halaccin da ki ka yi gareni ba. Allah Ya ba ki abinda kike so kuma ya ke sonki." Ta dubeshi, idanunsa a lumshe har lokacin murmushin ya ke, ganin zai bude yasa ta janye nata idanun kirjinta na bugu. Ta rasa wane irin so ne na Hussein a zuciyarta. Son da ba ta jin ya kai irin wanda ta yiwa ALIYUNTA. Idan Aliyu da dadin kalamai ya rinjayi zuciyarta, ta rasa da me Hussein ya rinjayi nata zuciyar. "Zan tafi." Abinda ya ce kenan. Ta sa ƙafa kawai ta fice ta rufe mishi ƙofar ba ta ce uffan ba kamar yanda bai tanka mata ba har ta yi gaba abinta. Murmushin ya ƙara yi gami da lasar lebbansa. Allah kadai Yasan sirrin da ke cikin zuciyarsa. Ya sauke ajiyar zuciya ya tashi motar ya fice. *** Hajiya Zeenatu ta rausayar da kai ta ƙara duban Hajiya Batool da ta saki baki tana kallonta,  murmushi ta saki ta ce. "Kina mamaki ne?" Hajiya Batool ta furzar. "Kema ai kin san dole akwai mamaki Zeenatu, shi Hussein din ne ya sauyamaki mota? Har ya ke tambayarki abinda kike da buri a yanzu? Kuma ya amince da ku bar ƙasar babu wata gardama? Anya kuwa Zeenatu ba wani tarkon ya ke shiryamaki ba? Ƴan uwansa kuma sun yarda da zamanku tare? Anya babu lauje cikin naɗi?" Ɗaure fuska kaɗan Hajiya Zeenatu ta yi. "Me kike son ki ce? Na fiki sanin Hussein, bai iya yaudara ba. Ko a baya balle kuma a yanzu. Duk isar mutum bai isa ya kawo mishi wargi ba balle ya yi ƙarya dominsa." Hajiya Batool ta tsaya kawai tana yi mata kallon sakarya. "Ke ba wannan ne damuwata ba, wasu shegun ƙuraje ne suka fesomin a cinyoyina. Ba ƙaiƙayi balle zafi, su dai gasunan ne kuma suna ɗurar ruwa." Hajiya Zeenatu ta katse tunanin Batool, kusan ma katse zancen ta yi don ba ta son ji. "Ya kamata dai ki je asibiti. Tunda dai ko ba komai za ku ci duniyarku da tsinke yanzun." Suka sa dariya gami da cafkewa duk kuwa da cewar jikin  Hajiya Batool bai gama gasƙata sauyawar Hussein ba. *** Tsaye suke a farfajiyar katafaren shagon na A&Z, Hisham sai faman shan ice cream yake a roba yayinda Hussein ya maida hankali ga danna waya. Tattaunawa suke yi game da abinda ya ke son shiryawa akan Hajiya Zeenatu. Shi Hisham ma duk haushi ya ke ba shi don haka ya ja guntun tsaki. "Kai nifa wallahi haushi ka ke ban idan kana zancen matarnan. Ban taɓa zaton ko second ɗaya za ka iya ƙarawa da ita a gida ɗaya ba. Ban zaci za ka ƙara wayar gari ka gan ta kuma ka bar ta a gidanka ba. Da kunnenka ka ji ita Halima na yimin rantsuwar cewa akwai sa hannun matarnan a abinda ta aikata. Na ji, babu kwakkwarar hujja mai ƙarfi da kotu za ta kama Hajiya Zeenatu da shi akan hakan, amma kai kana da hujjojin da za ka iya ɗaukar kowane mataki a kanta ba dole sai hukuma ba. Kafin na furtamaka cewa Zeenatu ce ta sa Nos Khadija aikata kisa, kai ka soma furtawa kuma ka sa na nemi gidan yarinyarnan da kaina na nunamata hoton Zeenatu ta tabbatarmin cewa ita ce. Me ya yi saura? Me kake jira bayan komai ya fito fili." Hussein ya yi murmushi gami da zaro hankicif a aljihu ya miƙamasa. "Goge bakinka, ya ɓaci." Hisham ya harareshi kafin ya warce ya goge ice cream din da ya ɓatamasa gefen baki tsabar masifa. "Ba na abu kai tsaye, na fi kaunar komai da cikakken hujja Hisham. Sannan ma tsaya, me kake nufi game da Matata? Ina sonta fiye da yanda ta ke sona. Har abada ba na jin akwai wani ko wata da ya isa ya raba ni da Zeenatu. Zan iya yin komai don ganin na sanya ta farin ciki. Kar ka damu da komai, komai da na fada ko kuma ya faru, ba komai bane. Abinda zai faru a gaba shi ne abin kallo. Shi ne abinda zai fi burgeka a lamarin soyayya." Hisham ya bishi da kallon taɓaɓɓe, sai dai wacce ya gani tsaye bayansa ta jikin gilashin motar Hussein, yasa ya gano dalilin sauya maganar Hussein din. Shigowarta wurin kenan daga gidan Hajiya Batool, a waje ta yi parking ta ajiye motarta don ba jimawa za ta yi ba tana sauri ta koma gida ta girkawa mijinta abinci, wani abun ta mance a ɗazun dole ta dawo ɗauka. Hussein wanda ya yi kamar bai ganta ba, ya ci gaba da magana. "Kar ka yarda da maganar mutane, Zeenatu ba za ta taɓa kisa ba balle har ta sanya wani ko wata ya yi yunkurin yi. Na fika saninta. Don haka duk wanda ya faɗamaka Zeenatu ita ce silar shigar Ramlat wannan yanayi, karya ce." Wani gumi ta ji ya yankomata, ta yi saurin juyamusu baya ta sharce. A hankali ta saita nutsuwarta kafin ta juyo ta tako inda suke tana murmushi. "Ah, ku na nan?" Sai a sannan suka yi kamar lokacin suka ganta. "Sannunki, yaushe ki ka zo?" Ta maida duba ga Hisham tana jifansa da wani irin kallo kafin ta maida ga Hussein. "Yanzu na shigo, mantuwa nayi zan dauka. Sannu abokinmu, ya gida?" Hisham ya sauke ajiyar zuciya, dakyar ya ƙaƙalo murmushi ya jefamata. "Lafiya kalau Uwargidan Hussein." Ta gyada kai. "A gaida mutan gida." "Za su ji." Daga haka ta yi gaba, Hisham ya bi bayanta da harara. Murmushi Hussein ya yi. "Hararar fa?" Tsaki Hisham ya ja. "Kai dai ban san sadda ka koyi makirci ba." Dariya kawai Hussein ya yi, shi kadai ya bar wa cikinsa abinda ya ke shiryawa. *** "Resigning?" Darakta ya maimaita da mamaki da kuma jin wani irin karyewar zuciya. Cike da ladabi Hussein ya jinjina kai. "Yes Sir." Kwata-kwata abin bai mishi dadi ba, samun mutum irin Hussein da ya iya gudanar da kasuwanci da amana da kuma ƙwarewa abu ne mai matuƙar wahala. Kwandala idan ba ta Hussein ba ce ba zai taɓa ci ba kamar yanda duk wani marar gaskiya da ha'inci, nan da nan ya ke ganoshi kuma a take ya yanke masa hukunci kafin ya sanarmasa. Hussein bai katse tunanin Darakta ba don dama ya san za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, Darakta Sa'ad mutum ne da ya ke kaunarsa kamar ɗan da ya haifa. Don ma Hussein din bai fiye son shigewa mutane ba, da ya tabbata zumuncinsa da Daraktansa sai ya fi haka. "Meye uzurinka amma?" Darakta ya tambaya ransa ba dadi. Murmushi sosai Hussein ya yi yana jinjina wannan kaunar. "Adamawa zan koma da zama, cikin dangina." Da mamaki ya ce. "Dama kai din ɗan Adamawa ne?" "Eh." "Ikon Allah." A karshe dai suka yi magana mai tsawo kafin Darakta ya dakatar da shi zuwa lokacin da zai samu wanda zai maye gurbinsa. Da wannan suka ajiye magana. *** "Wai nikam Alhaji na rasa gane kanka. Ban san me zai sa zuciyarka ta sauka daga dokin fushin da ka hau ba." Kawu Modibbo ya daure fuska sosai yana kallon Anti Amarya. "Me kike son ki ce?" Anti Amarya ta sauke ajiyar zuciya. "Ya dace ace zuwa yanzu ka watsar da makaman yaƙinka kamar yanda ƴan uwanka suka watsar. Ya dace ace yanzu gabar da ke tsakaninka da su Dada ya wuce. Ko maƙiyin Dada ya kira ya tayata murnar ganin Hussein amma kai kam na..." "Ni kike faɗawa maganar banza da wofi?! Ke kinsan waye ni kuwa? Idan har kina so ki tsira da mutuncinki da kuma aurenki, ki yi gaggawar fita a idona! Wannan ne gargadi na karshe da zan maki game da lamarin Amina da iyalinta. A wurinki ki ke ganin komai ya wuce, amma ni har abada ba zan taɓa bari wata alaƙata shiga tsakanin ni da yara da ba'a san asalinsu ba! Aminu dai ya zo ya kawomana karuwarsa ya kuma tafi ya bar munda bara gurmi a cikin zuri'armu. Na ji! Amma ba wanda ya isa ya yi min dole kan na karɓe su. Shi kuwa Tahir yau ko ni ko shi tunda ya zaɓi zama da su a kaina! Zan nunamasa ni ne nan ubansa!" Kawu Modibbo na kai wa nan ya mike ya nufi ɗaki, ransa idan ya yi dubu ya ɓaci, ga Bokansa ya tabbatar masa babu sauran ƙofar da wani asiri zai shiga jikin Hussein da sauri sai dai a sannu. Yanzun ya gama gane ba iyakar tsana kawai ya yiwa zuri'arnan ba, har da bakin ciki da kuma jin tsantsar hassadar yanda ba su rayu a wulakance kamar yanda shi da Innarsa a baya suke fata ba. Sai ya kasance koyaushe sai dai ya yi ta jin labarin nasarorinsu. Ga dai yaransa nan amma kowanne da kalar shashancin da ya sa gaba, kalilan ne a yaran suka kama dahir. Wato dai suka yi karatu kuma su ke aiki, aikin da bai kai darajar na AlHassan ba. Ko iyaka nan aka tsaya ya san za su yi mishi dariya, abinda ba zai jure ba kenan. *** "Ya akai ɗan uwa?" AlHassan ya fadi kai tsaye daga ɗayan ɓarin. Hussein ya kara gyara zaman wayarsa duk kuwa da cewar tuƙi ya ke yi. "Lafiya, batun maganar da muka yi, yaushe za ka zo?" Murmushi mai sauti AlHassan ya yi. "Ai ka ji, dama sai da na ce maka ka yi hakuri mu taho tare komai zai fi bada ma'ana, yanzu gashinan tun ba ka tafasa ba za ka ƙone." Hussein ya ɗan cire hannunsa saman sitiyari ya shafi sumar kai yana murmushi kafin ya mayar. "I'm sorry, ka san.." "Ko ba ka faɗa ba na sani. Na san kuma dalilinka. Hakan ma ya yi daidai. Fadamin, me ka zo ka tarar?" Tiryan-tiryan ya ba shi labari, AlHassan ya yi dariya. "Alhamdulillah. Wannan ma nasara ce. Zeenatu get ready." Suka ɗan taɓa hira abinsu suka yi sallama. *** Da yammacin ranar juma'a, tana zaune saman kujera suna hira da Baban Hanif, damuwa karara ta bayyana saman fuskarsa. "Mamin Affan, ban san dalili ba, amma gabana faduwa ya ke, sai na ga kamar zan rasaki, sai naga kamar duk wannan rawar ƙafartawa zai zama mafarki." Ta ɗago kai da zummar ba shi amsa da ɗan murmushi saman fuskarta, ya yi daidai da bude ƙaton kyauren gidan, motar Hisham ce ta shigo sai dai a gefensa mai zaman banza, Hussein ne. Kauda idanu ta yi gami da danne bugun da kirjinta yake ba tare da fuskarta ta nuna ba. "Me zai sa ka fargaba? Akwai wani lamarin da ya fi karfin addu'a? Komai na Allah ne." Ya jinjina kai, har sannan bai ji zuciyarsa ta sake ba. Yana son faɗamata sakamakon da binciken tarihinta ya ba iyayensa amma ya danne a ransa har zuwa sadda zai kammala nashi binciken ya gane gaskiyar lamari. Daga cikin motar kuwa, Hisham ji ya yi wani murmushi ya suɓuce masa, abinda ya fi dadi, ya ji na zuwan da ya yi da Hussein gidannan. A farko Hussein bai yi niyyar zuwa ba, sai dai kwadayin ladan da ke cikin ziyartar iyaye da ma yan uwa da asibitoci a ranar juma'a yasa shi cewa su je din. Sai da suka soma zuwa gidan iyayen Hisham din suka ci abinci kafin su zo gaisuwar surukai kuma yan uwa a wajensu yanzun. A farko Hussein gardama ya ke mishi kan zuwa ziyartar Kawu Modibbo da Hisham ya ke so su yi a ranar, sai dai shigowarsu gidan da mummunan tozalin da ya yi ya sa shi yin ɗif har hakan ya ankarar da Hisham shima ya kai idanunsa garesu. "Muje ko?" Hisham ya katse tunaninsa yana kara nazartar yanayin sauyawar fuskarsa. Babu annuri. "No, shiga ka fito." Dariya mai karfi ta kama Hisham sai dai dakyar ya haɗiye, idanun Hussein din akan Baban Hanif yana son tuna inda ya taɓa ganinsa. "Ah, wai Hajiya Ramlatu kake kallo? Kai wai dama Haris ne? Bari na je mu gaisa." Hussein a sannan ne ya watsawa Hisham banzan kallo kafin ya ja tsaki, kusan a tare suka fito daga motar. Baban Hanif na ganinsu ya taso da fara'a ya karaso. Maimakon Hussein ya tsaya kawai sai ya yi gaba yana shan murr ko inda suke bai kalla ba. Baban Hanif ya bishi da ido sadda hannunsa ke cikin na Hisham su na musabaha. Ramlat ta dora kafa daya kan daya tana fitar da wani irin murmushi mai kama da yaƙe. Sauyawar Hussein ya mugun kasheta da ba ta mamaki. "Ranki ya dade, girman kujerarki." Sai a sannan ta sauke ƙafar ta gaida Hisham fuska a sake. Daga bisani shima ya yi ciki. Kusan mintuna sha biyar suka kwashe a cikin gidan kafin Ramlat ta shigo. Kiciɓus suka yi a bakin ƙofar. Kallon da ya watsamata ne yasa ta hadiye gaisuwar a fatar bakinta. Ganin shi bai ba ta hanya ba kuma bai ce uffan ba yasa cikin dakiya bayan ta saukar da kanta ta gaishe shi. "Ba girin-girin ba dai, ta yi mai." Ya fadi a sanyaye amma zafin maganar ya fi komai buga zuciyarta. Ta dubeshi, ya kauda kai ya bi gefenta ya wuce. Ta bi bayansa da kallo cikin rashin gane inda zancensa ya dosa. "Ah Hajajju, har kin gama taɗin?" Ta juyo ta dubi Hisham tana murmushin hadiye damuwa. "Har za ku wuce?" "Eh kinsan da yake ba iyakar nan muka tsaya ba. Yau dai ladan juma'ar muke kwadayi." Ta jinjina kai. "Allah Ya saka da alheri." Ya amsa da amin. Wani wawan hon da Hussein ya yi sai ya ba Hisham dariya. "Kinga bari na tafi kafin na ba shi haushi ya koma Adamawa a ƙasa." Ta yi dariyar da ta tsaya a fatar baki. Hanya ta ba shi ya wuce. *** BANKWANA DA MASOYI.... I just published "BABI NA HAMSIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1015298066?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=APuHCxKNugEN8dtZunyL4O%2FJKBns%2FO08vTjSCIlxF7AhR%2BRuxyUYJF8vGaw9PlhcYs%2Fd5Guq41cilqJPUF4w8sQuGhQdsC6bSLWR4oVKhbuxPFsqscrPZn1s%2BR6QxkUd 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 55) "Na kasa gane kanka. Wai me ya sauyaka haka?" Hussein wanda ke jin kirjinsa har wani zafi yake ya kasa magana sai guntun tsaki da ya ja. "Allah Ya kyauta. Amma idan har dagaske kana son Ramlat toh ya kamata ace zuwa yanzu ka bada kai bori ya hau. Bana son wannan zurfin cikinnaka alhalin ni na sani wallahi ko mijinta na farko sai an yi dagaske zai kamo ka a son da ka ke mata." Nan ma dai shirun ya kara samu maimakon amsa, Hisham dole ya ja baki ya yi shiru don ya soma jin haushi. "Zamu je Yakasan?" Ya tambaya bayan ya yi tuƙi mai ɗan tazara daga gidan su Ramlat. Ajiyar zuciya ya saki ya dubeshi da jajayen idanun da ɓacin rai ya rinar. "Ba zan iyaba. Mu yi hakuri ko zuwa gobe ne, ba ta ɓaci ba." "Ok!" Yanda Hisham din ya amsa sai ya tabbatar da fushi ne don haka ya yi ɗan murmushi. "Ka yi hakuri." Shima Hisham don ya rama sai ya shareshi, a karshe ma ɗaya daga cikin waƙoƙin Breaker ya kunna mai suna So. A hankali Hussein ya lumshe idanu yana sauraron waƙar, wani abu ke ratsa zuciya da gangar jikinsa sai dai kuma yana ji a jikinsa ba mai yiwuwa bane. Daga yau zai mishi iyaka da zuciyar da gangar jikinsa har sai ya ga abinda hali ya yi. *** Hajiya Zeenatu ta ƙara buɗe zanin jikinta, fitowarta daga banɗaki kenan. Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi, maimakon da ta soma shafa cream na ƙuraje da likita ya ba ta, kurajen su mutu sai abin ya kara yin gaba. Don a farko iyakar cinyarta ne kadai, yanzun kuwa har su na kokarin dabaibaye dukkan wata gaɓa daga ƙugunta zuwa ƙasa. Ta kuma lura da wani abu guda, ko yaya ruwan ya taɓa jikin fatarta sai wani kurjin ya fito. "Na shiga uku ni Zeena! Me zan gani?!" Ta dora hannu a kai nan da nan idanunta suka fito ƙululu kamar za ta yi kuka. Wato dai don bakin ciki cuta bai tashi yi mata kamun kazar kurkuku ba sai da ta ke dab da more rayuwarta da miji? Sai da komai ha daidaita babu tsafi balle asiri? Wani irin miƙewa da ta yi sai da zanin ya faɗi, ba ta bi ta kai ba ta karasa sif na kayanta, doguwar riga ta sauya hannunta har wani irin rawa ya ke yi, ta gwammace yau ta je babban asibitin Malam ta ga likitan fata. Tana ji a jikinta abin daga fatarta ne. Ba ta yi tunanin ciro waya ta kira Hussein da zummar neman izni ba, sai da ta shiga mota, koda ta fadamasa a dawo lafiya kawai ya ce daga nan bai ƙara uffan ba, itama ba ta son ya kara don yanzu ta lafiyarta ake. Babban tunaninta yanzu komai na tafiyarsu London ya zama ready, ga samu ga rashi. Haka ta ke ji a ranta. *** Yau kwanaki biyu kenan da Yusufa ke zaryar gidan su Ramlat sai dai ba ya samunta. A karshe dai ya nemi lambar wayarta ya kira. Bayan sun gaisa ya yi kata kwatancen ko waye shi. Jin ya ce shi ɗin ƙanin Halima ne yasa ta maida hankali ga sauraronsa. "Aunty maganar ba ta waya ba ce, saƙo ne daga Yaya Halima, tun ba yau ba ta ban ta ce na isar gareki. Na so ajiyewa wurin Maigadin gidanku amma kuma bana so ya kasance bai isa hannunki ba." Da mamaki Ramlat ta gyara zama saman kujerar Office din. "Kana ji? Ko zan maka kwatancen ofishin da nake aiki sai ka kawomin." Cikin zumudin hakan ya amsa da toh ya kuma yi mata godiya. Wuraren karfe biyar da  mintoci na yamma sai ga Yusufa. Da kanta ta fita suka gaisa, sau ɗaya ta taɓa ganinsa, rashin lafiyar Kakar Halimar da ya tashi suka je dubiya asibiti daga tsohuwar ma'aikatarta. Suka gaisa kafin ya ciro takarda a ninke ya miƙa mata. "Ki yi hakuri wallahi saƙonnan ya fi sati a hannuna, rasuwar Kakarmu ce ta sanya ban kawomaki ba sai yanzun.  " Cike da jimami ta ce. "Kaka ta rasu? Allahu Akbar, Allah Ya yi mata rahma. Yasa aljanna makoma. " Yusufa ya amsa da amin. Daga haka suka yi sallama bayan ta mishi ihsani. Kasancewar an kusan tashinsu daga aiki yasa kawai ta jefa a jakarta. Ba ita ta samu damar warware takardar ta karanta ba sai bayan Magriba. Lokacin ta samu nutsuwar wanka har ma da na cin abinci. Ga abinda ta kuntsa. _*Assalamu alaikum Ramlat.*_          _*Da farko zan soma da ba ki hakuri, haƙiƙa na sani ni Halima ban cancanci komai daga gareki ba ballantana har ki yafemin. Sai dai duk da haka ina mai nadama da dana sanin abinda na aikata gareki. Ni mai laifi ce, ina neman gafararki Ramlat. Hassada da son abin duniya irin nawa ya kai ni ya baro. Yau ganinan a gidan da ko a mafarki ban taɓa zaton zuwansa ba.*_ _*Na aikata bisa tursasawar Hajiya Zeenatu da kawarta Hajiya Batulu. Duk irin tsanar da na yi maki ba zai sa na yi yunkurin kashe ki ba. Duniya aka kwaɗaitamin, ni kuma na karɓa da gaggawa ba tare da tunanin abinda zai je ya dawo ba. Ina neman gafararki. Ki yafemin domin Allah Ramlat. Wallahi a yanzu haka na tsani kaina. Ba ni da kwanciyar hankali daidai da kwayar zarra. Ki yafemin ko zan samu ganin haske a rayuwata da kuma mafarkaina. Na gode.*_ _*Halima Shehu.*_ Ajiyar zuciya ta saki sannan ta ninke takardar, a hankali ta sanya bayan hannu ta share hawayen saman fuskarta. Ba ta taɓa kawowa Hajiya Zeenatu ce ta sa Halima kasheta ba. Sai dai tayar da zancen ta san ba shi da amfani, ta bar wa Allah komai. Ta ƙurawa takardar idanu sai kuma ta yi murmushin yaƙe ganin cewar Halima ba ta da masaniyar ita ta jima da yafemata ma. Gefen dirowar gadon ta buɗe ta cilla. "Mami! Mami!" Ansar ne ya shigo hannunsa riƙe da wayar Hajiya yana game. "Wai Hajiya ta ce ki zo, ga Baba Dakta ya zo." Ta ji kirjinta ya buga. Ta amsa da toh sannan ta mike ta yafa mayafin doguwar rigar da ke jikinta. Hajiya na zaune ta sha lulluɓi su na ɗan taɓa hira. Ta karasa ta durkusa ta gaidashi. Ya kalleta da fara'arsa. Ta mike ta koma kicin ta kawomishi ruwa da lemu. Sannan bisa umarnin Hajiya, ta ja yaran zuwa ciki don su yi magana. Hankalinta ya kasa kwanciya a dakin, zirga-zirga kawai ta shiga yi, ganin an kwashi mintuna yasa ta kasa hakuri sai da ta ɗan kasa kunne. Ta ji Hajiya da na fadin. "Ai wannan ba a bukatar jin ta bakina ko ita Ramlatun. Ramlatu da Amrah duk daya ne. Dukkan hukuncin da ku ka yanke a kanta nasan ba za ta taɓa yin da na sanin zaɓinku ba in sha Allahu. Balle kuma dama akwai fahimtar juna tsakanin yaran. Ni dama hankalina ya fi kwanciya da shi tunda ko ba komai ba wannan ne aurensa na farko ba. Allah Ya sanya alheri. Ya sa ayi muna raye." Ramlat tuni ta ji wani gumi na tsastsafo mata, kirjinta ya tsananta bugu, ta ji Baba Dakta na kara godiya da yiwa Hajiyar addu'a. A karshe ma yake batun zai je takanas can Yakasai ya ga su Kawu su yi magana. Gwuiwa a sake ta juya ta koma saman gadon, Affan ya damu da kai ƙarar Ummi ta ɗauki wayar Mamin, ba ta san sadda ta dakamasa tsawar da dukkan yaran sai da suka tsorata ba. Ta ja guntun tsaki ta riƙe kai, salati kawai ta ke yi da addu'ar Allah Yasa hakan ya zamemata alheri. Ta dafe saitin kirjinta, ba ta taɓa zaton lamarin aurenta da Baban Hanif zai zo mata da yanayin ɓacin rai kwatankwacin na Hilal ba sai yanzu. Sai dai wannan karon alƙawari ta yiwa kanta, ko me zai je ya zo, za ta rungumi zaɓin iyayenta da hannu bibbiyu. "Ki godewa Allah da zaɓinSa. In sha Allah jikina yana bani wannan aurennaki shi zai zama na dindindin duk kuwa da cewar sai an yi hakuri kuma an kai zuciya nesa saboda kananun maganganun da kan iya tasowa." Wannan shi ne kadai abinda ta ji a bakin Hajiya, nan ta tuna wayarta a safiyar yau da Baban Hanif, inda cike da damuwa yake sanarmata irin tashin hankalin da yake fuskanta daga iyayensa game da aurenta da ya yi niyyar yi. Labari ya zo musu cewar ta taɓa yunkurin kisa a aurenta na farko. Wannan ne dalilin da yasa gaba ɗaya a kwanakin ta kasa gane inda ya nufa. Ramlat ta dubi Hajiya karo na ba adadi tun zamanta a falon, waya Hajiya ta shiga yi da Munir, ta kasa kunne amma a karshe ma sai Hajiyar ta miƙe ta nufi ɗaki. Ranta sai ya soma ɗan baci. Ko ba komai ba wannan ne aurenta na farko ba, ya kamata ta san wa za ta aura ai. Hakan kuma bai nufin jayayya za ta yi da su. Ko kadan, ta rantse koma waye ta yarda kuma ta amince da aurenta da shi, kawai dai tana son sanin waye. A gefe guda kuma jikinta yana ba ta cewar ta yi BANKWANA DA HUSSEIN. Bankwana na har abada. "Mami! Wayarki." Ta sa hannu ta karɓa a hannun Ummi. Baban Hanif din ne kuwa ya kira don haka ba ta jira ya kara ba ta bi bayansa. Sai da ta shiga daki ta rufe kafin ta amsa sallamarsa. Bayan sun gaisa a gaggauce ta ce. "Kun yi magana da Baba Dakta ne?" "Eh ya kirani dazunnan da yamma, mun yi magana sosai da shi. Labari ya zo maki kenan?" Ta kasa magana kawai sai ta kashe wayar gaba daya, kai ta dora saman gwuiwar ƙafafunta ta shiga rera kuka. Kukan jin zafin Hussein da ya kasa kallonta matsayin masoyiyarsa. Ta gasƙata cewa yanzun babu wani abu da zai ƙara shiga tsakaninta yanzun. Ta ji kuma ta hakura da zaɓin Allah. Dakyar ta iya miƙewa ta faɗa ɗakin yaranta, kowannensu ta gyarawa gado don yanzun ta sauyamusu da gado kanana na yara kowanne da na shi. Ta kakkaɓe, ta ba su umarnin kwanciya. Kasancewar sun saba da baccin wurin hakan yasa su na kwanciyar bayan ta sa sun yi addua, bacci ya ɗauke su. Ta yi shiru tana kallonsu bayan ta gama kwashe shirgin kayan da suka zubar a ƙasa ta ninke kayan sif din da ya lalace. Aliyunta ne ya faɗomata, zuciyarta ta ƙara karyewa, nan ta shiga rera wani sabon kukan. A karshe don kanta ta rarrashi zuciyarta ta share sannan ta fita ta ja musu ƙofar. "Ashe AlHassan ya zo garinnan?" Ta dubi Hajiyar da le tambayarta, robb ta ke faman shafawa a ƙofofin hancinta. "Ban sani ba wallahi. Yaushe?" Murmushi Hajiya ta yi. "Ai da Husseini muke waya, sai ya ba shi muka gaisa. Wai jiya-jiyan nan. Amma ya cemin zuwa gobe zai shigo in sha Allahu." "Allah Ya nunamana." Ta fadi a ɗan gaggauce don ji ta ke yi kamar ta fashe da wani kukan. Hajiya na lura da ita kuma abin na ba ta mamaki amma ba ta ce uffan ba. Ta san dai idan ma da wani abu na daban a zuciyar Ramlatun, dole yanzu ta yi kokarin kawar da shi tunda dai bakin alƙalami ya riga da ya bushe. *** Tun sadda Hajiya ta shaidamata cewar ana nemanta a Yakasai, Kawunnanta, kirjinta ke bugu da sauri. Affan wannan karon maƙalewa ya yi zai bi ta, dole ta shirya shi suka fita tare. Adaidata Sahu suka hau kasancewar motarta ta samu matsala. A hanyar ma babu cikakkiyar nutsuwa tattare da ita sakamakon tunanin abinda zai biyo baya da ta sa a rai. Kiran ko kusa bai ba ta mamaki ba, ta san dama tunda har aka ce an mata miji to komai ma za ta gani. Har dai suka iso ba ta jin ta ba Affan kwakkwarar amsar tambayoyinsa na shirme da ya ke mata. Karshe ma da ya dameta cewa ta yi za ta bar shi a cikin Napep din dole ya ja baki ya yi shiru. Ɓangaren Baba Dije ta soma shiga. Bayan sun gaisa ta ce. "Ina tayaki murna ƴarnan, kin yi goshi wannan karon ba shakka. Allah Ya sanya alheri ya nunamana lokacin." Ta rasa yanayin da ta shiga. Ta kasa amsawa hakanan ta kasa cewa komai don haka kawai sai ta mike ta fita tana murmushin yaƙe. "Ayiririri!" Guɗar da ta ji yasa ta waiga, Baba Hajara ce yayar Hajiyarsu. Su uku ne kadai mata a wurin Hajjar, Baba Hindu, Baba Hajara sai Hajiya. Mazan kuwa su uku, Kawu Jamilu, Kawu Bello da Kawu Sunusi, su ne manyan maza a ɗakin. Jiki a sanyaye ta gaida ta kafin ta karasa ɗakin Hajja itama Baba Hajara na daga bayanta. Hajja ce zaune tana shan fura, tana ganin Ramlatun itama ta saki fuska. "Kishiyar ce a tafe kenan? Sannu da zuwa." Ita dai ba ta ce uffan ba, Affan ya karasa a guje ga Hajja. Zama ta yi gwuiwa a sake kafin ta maida hankali ga Baba Hajara. "Wai Baba lafiya?" Baba Hajara ta zauna tana dariya, ba ta kai ga magana ba Hajja ta katse ta. "Na rabaki, idan ba so kike tarihi ya maimaita kansa ba. Ki bari ta ji komai daga bakin Ubanninnata. Ai ba abinda zamu ce ga Dakta (Baba Dakta) sai godiya da fatan alheri. Allah Ya biyashi da aljanna. Yanda yake nunamaku kulawa kamar ƴaƴan da ya haifa a cikinsa, Allah Yasa aljanna makoma. Na ji ma ance ya kawomaku kayayyakin abincin azumi, to nan ma haka ya aikomin. Wannan bawan Allah sai fatan alheri da fatan Allah Ya jiƙan iyaye." Baba Hajara ta amsa da amin, itama Ramlat ta amsa ta hanyar motsa lebbanta amma dukkan wata gaɓɓa ta jikinta ta yi sanyi. Can kuma sau ga shigowar saƙo. Hussein ne. Ta bude hannunta har rawa ya ke don yanzu ta kasa fahimtar komai. _*"Ban yarda da dukkan wani so da za'a yi shi kafin aure ba. Ban kuma yarda akwai kulawar da namiji zai yiwa mace ba da za ta kere kulawar miji ga matarsa. So da kauna na gaskiya ya fi ma'ana idan aka zama mallakin juna. Ina taya junanmu murna."*_ "To wai me yake nufi?" Ta tambaya a fili bayan ta karanta ya fi sau biyar amma ba ta gane komai ba. "Wa kenan?" Hajja da Baba Hajara har suna haɗa baki wajen tambaya. Ta ma kasa cewa uffan sai kai da ta girgiza tana sharar gumi ga kwalla cike a idanunta. "Idan ma za ki saka ranki a inuwa tun wuri gwara ki sanya don wannan karon na tabbatar wanda za ki aura ba fetur ba, Allah Yasa tankin mai gaba daya za ki zazzaga maku, zai yarda ku mutu ƙurmus! Sawun giwa ya take na raƙumi!" Hajja ke wannan sababin ta karashe da kurɓar furarta ta bar Baba Hajara da dariya. Ita dai Ramlat ba ta ce komai ba sai hawayen da ta shiga sharewa, gaba daya gaɓoɓin jikinta sun yi sanyi, yanzun kuma abin haushi ya ke bata. "Yaya Ramlatu ki zo inji Kawun Zaure." Wato Kawu Jamilu kenan wanda shi hanyar shiga sashinsa na daga wurin zauren gidan, ai ba ta ma jira Hauwa diyar Kawu Sunusi ta karasa faɗin saƙon ba ta yin zumbur ta miƙe tsaye har wayarta na faɗuwa amma ba ta ko damu da ɗauka ba. Tana ji Hajja na fadin. "Kuma yarinya ta dawomin daki da baki kamar gonar auduga sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Maza Affan bani wayarnan idan mijinnamu ya zo sai ya siyamata wani." Tana jin dariyarsu amma babu wanda ta tanka asalima baki ta turo ta ɗan ja guntun tsaki tsabar ɓacin rai. Haka ta dinga tafiya har sashin Kawu Jamilu, duk a zatonta shi kadai ne, sai ganin sauran Kawunnan da ta yi zaune ƙasan bishiya suna taɓa hira. Ta karasa gami da durkusawa ta kwashi gaisa. Suka amsa fuska a sake duk da cewar kanta a ƙasa yake amma sautinsu ya nuna hakan. Sai da aka gama gaisuwar da ɗan barkwanci kafin Kawu Jamilu ya yi gyaran murya ya soma magana. "Toh Ramlatu, abu na farko shi ne mu miƙa godiyarmu ga Ubangiji domin Shi ya yi mana dukkan ni'ima. Ya kuma so ki da dukkan rahma da mu ɗin gaba ɗaya. Alhamdulillah." Ya ɗan ja numfashi gami da gyaran murya sannan ya ci gaba. "Kamar yanda ki ka ji daga bakin mutanen gida, abin alheri ne ya sameki. Babanki Dakta ya yi maki zaɓi bisa damar hakan da kika damƙa maki. Kar kuma hakan yasa ki yi zaton cewa shi da kansa ya haɗa auren, aa, shi yaron ma asali tun ana zancen aurenki da Dikko ya tunkari Baba Daktan da batun aurenki sai dai Baba Daktan ya ba shi hakuri ya kuma sanarmasa da batun Dikko, a karshe ya yi mishi kwatancen gidannan ya ba shi lambar wayar Kawunki Bello cewar yana iya zuwa nan wurinsa ya faɗamasa ko Allah Zai sa a dace. Da yake shima yaron nada hankali ya ce aa babu komai, ya yarda Allah bai kaddara ke din rabonsa ba ce. Ba ya son ya yi nema cikin nema. Wannan ne dalilinsa na janyewa bayan ya nemi alfarmar su bar maganar tsakaninsu. Yanzun ma da kika ji, magana ce ta kawo magana shiyasa ya faɗamana shi Babannaki. Sai kuma cikin ikon Allah lamarin aurenki da shi Dikko ya lalace, anan ne kuma bayan kin bar wuƙa da nama a hannun Daktan, ya ba wancan yaron iznin turo nashi magabatan bayan shawarar da ya yi da mu kuma muka amince. Alhamdulillah, Ramlatu ke ba yarinya ba ce, mun kuma sani, yanzun kin fi baya hankali. Kin kuma ƙara hankaltar rayuwa. Mun sani, wannan karon ba za ki ba mu kunya ba in sha Allahu." Zufa sosai ta ke fitarwa, ta hadiyi miyau mai ɗaci, ba ta bar ambaton Innalillahi a ƙasan ranta ba har zuwa sadda Kawu Jamilu ya miƙomata damin kudi ƴan ɗari biya-biyar a baƙar leda bayan ya warware ledar ya turo kudin gabanta. "Wannan ne kudin aurenki, dubu ɗari gashinan. Juma'a mai zuwa cikin yardar Allah za'a ɗaura aurenki da HUSSEINI MODIBBO. Ina ce haka sunan yake ko?" Ya karashe yana duban yan uwansa da dariya, suka dara lokaci guda. "Hakayake Yaya." Kawu Sunusi ya bada amsa. Ta rasa me za ta ce, ta kuma rasa me za ta yi, a zaune ta ke amma jiri ta ke ji. Kanta ya yi wani irin sarawa, lokaci guda ya shiga ciwo. Hawayen da ta tsayar a ɗazun, suka ci gabada kwaranya su na ɗiga saman k rafar ɗari biyar biyar din da Kawu ya ajiyemata. Wa ya faɗamusu sonta yake? I just published "BABI NA HAMSIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1017117739?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=NPwmUPq5q%2BNDXCvudnu9VtPx9xZ93DXS%2BXNO4Gp8IGMT8cs%2FH9GyIFlv%2Fhb%2BKgVVkXrnM1fZVi41cUdjwyw1cEK3IG5H1c7vZKRmCwE0POba10BIvSct65MXWSFYf6%2Fz 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 56) 'Me yake nufi da ni?' Ta jefawa zuciyarta tambayar da nan da nan ta samo amsar da ta ji wani mugun ɗacinsa. Hussein na nufin ra'ayinta ba komai ba ne, yana nufin koda ba ta sonsa ta rayu da shi. Ko kuma dai daga saƙon da ya turomata yana son ta fahimci ya gane tana sonsa amma ya dinga basarwa. Nan da nan ta ji wani haushinsa ya mamaye zuciyarta. Ta ci alwashin sai ta rama abinda ya aikata gareta, ba za ta taɓa yin musu a aurensa ba, amma ta rantse sai ya gane shayi ruwa ne. "Allah Yasa hakan ya zamemin alheri." Ta ba Kawu amsa a hankali, gaba daya suka amsa da amin cike da jin dadi. Suka sanya mata albarka a karshe suka sallameta. Mikewa ta yi bayan ta share hawayen yanda ba za su gani ba, ba tare da ta ɗau kuɗin ba ta bar wajen. Kawu Sunusi zai magana Kawu Jamilu ya katseshi da zummar za su damƙawa Hajiya. Ba ta wani jima cikin gidan ba ta yi musu sallama sai dai ba su fahimci komai ba don ta ɗan saki fuska kamar ba ita ba. Koda ta koma gidan, ba abinda ta nunawa Hajiyarta. Wannan ya kwantar da hankalin Hajiyar don dama tun fitar Ramlatun ta ke cikin zullumin ta yanda za ta karɓi lamarin. "Idan kin sauya kayan sai ki fito mu shiga kicin, na fadamaki yau Hassan zai shigo a gaisa." Maganar Hajiya ta katse yunkurinta na shigewa ɗaki da ta yi niyya, ta juyo ta amsa da toh bayan ta haɗiyi miyau mai ɗaci. *** Hajiya Zeenatu ta shigo falonta gaba daya jiki a sanyaye, likita ya duba ta amma ya ce bai gane komai ba, karshe aka haɗata da tests kala-kala akan ta yi ta kawo sakamako a gani. Ranta gaba daya a jagule ga wani jiri-jiri da ke ɗibanta. Turus ta yi ganin mutum zaune a falon. Ta daure ta shigo da fara'ar da bai kai zuci ba. Suka dubeta gami da amsa sallamarta. Hussein ne fuskarsa cike da wani farin ciki sai AlHassan dake zaune yana amsa waya Madam dinsa Kausar, ganinta yasa shi yin sallama da ita. "Ah, ɗan uwanmu zuwa babu sanarwa?" Ya yi murmushi, sai yanzun dai ya zo gidan dan uwannasa don haka ba su hadu da Hajiya Zeenatun ba sai a yau, amma a Hotel ya sauka tare da Kawunsu Adamu wanda shi a yau da safe ya juya ya kama hanyar Adamawa. "Hajjaju, Allah Ya huci zuciyarki. Nima zuwan ne ya tasomin babu shiri. Aiki na zo yi daga kamfaninmu na can. Ko shi Ogannaki haka ya gan ni babu zato ba tsammani." Ta yi dariyar yaƙe gami da satar kallon Hussein da ya ɗora ƙafa ɗaya saman kujera hankalinsa ya koma kan waya yana zabga murmushi. "Hakan ma ai daidai ne. Dama kuwa ina da saƙon da zan bayar a kaiwa Ɗiyata. Gwara da Allah Ya kawoka." Ya yi dariya yana gyara zaman gilashinsa. "Ba ki da matsala. Tana godiya." Daga haka ta maida duba ga mijinta. "Yallaɓai barka da hutawa." Ta fadi da wani irin shagwaɓa wanda ya ba AlHassan dariya, sai dai ya haɗiye kawai ya miƙe. "Bari na ɗan amsa waya." Yana kaiwa nan ya fice zuwa farfajiyar gidan, wannan ya ba Hajiya Zeenatu damar ƙarasowa ta zauna gefen Hussein. Ya ɗan dubeta da kulawa. "Ya jikin naki?" Cike da damuwa ta karya wuya. "Likita ya duba ni, ya ce  ba zai gane taƙamaiman matsalar ba sai an yimin gwaje-gwaje.  Yanzu dai haka ya ban gwaji zuwa gobe zan koma mu gani. Amma na fi kaunar na hakura idan mun je London sai a yimin magani sosai." Ya gyaɗa kai yana murmushin da ke ƙara tafiyar da imanin Hajiya Zeenatu a kansa.    "Saurin me ki ke? Ita lafiya ta fi komai ai. Ki kwantar da hankalinki. Tunda har kika ga na dakatar da aiki toh hakan na nufin na shirya koyaushe ne ma mu bar ƙasar. Abinda ya fi yanzu ki je goben ki yi gwaje-gwajen har a gano matsalar a shawo kanta. Gwara ki ɗan samu sauki sai mu wuce.  Amma fa sai mun fara biyawa Adamawa kinga su Dada kun gaisa." Ko ɗarr ba ta ji ba, a wautarta gani ta ke har a sannan babu wanda ya gane da hannunta a ɓatan Hussein. "Yanda ka tsara hakan za'a yi Ranka ya daɗe." Kauda kai kawai ya yi bai ce uffan ba, ta mike ta haye sama. Ya bi bayanta da kallo, sai kuma ya yi murmushin mugunta. Shi kadai ya san me ya bar wa zuciyarsa. Tabbas sai Hajiya Zeenatu ta kusa haukacewa idan ta gano taƙamaiman shirin da ya ke yi. Wayarsa dake ringing  ya duba. Hisham ne. Murmushi ya yi don ya san labari ya isa kunnensa. "Kai dan iska ne fa! Wai me nake ji daga bakin My Princess? Dagaske kai ne ka kai kuɗin auren Ramlatu?" Lumshe idanu ya yi, sunanta kaɗai idan ya ji sai tsigar jikinsa ya tashi. A hankali ya shafi sumar kansa. "Mamaki ka ke yi? Ba haka ka ke so ba?" Dariya Hisham ya yi. "Haka nake so, sai dai ka rainamin hankali fa. Zan rama amma. Kar ka yi tunanin zan tayaka campaign." Taɓe baki Hussein ya yi kamar yana kallonsa. "Campaign after marriage? Ni zan yi abina dama." Hisham ya ɗan dara don shi abin kam dadi ya yi mishi ba kadan ba. Addu'a ya yi da fatan alheri. Hussein ya amsa da amin kafin su yi sallama. Agogo ya kara dubawa, da sauran mintuna a kira sallar Magriba. Ya ƙagu ya ganshi a gidan su Ramlat. So ya ke ya sanyata a idanunsa. Bai zaci za ta ga saƙonsa ta shareshi ba, abin ya ba shi mamaki. Hakan yasa ya ke son zuwa ganinta da kansa. *** Kawu Modibbo rai a ɓace ya ke amsa wayar ƙaninsa Adamu. "Me ya kawoka Kano? Wato Adamu har wuyanka ya yi kaurin da za ka shigo inda nake ka kasa nemana? Idan kuma aka yi magana sai ka nuna ka fi uban kowa riƙon zumunci ko?" Kawu Adamu da mamakin yanda Modibbo ya san da zuwansa garin Kano ya ba da amsa ta wayar. "Wa ya fadamaka na je Kano?" "Ɗanka Yahaya muka yi waya ya cemin ka shigo Kano tare da Hassan. Ko karya ya ke yi?" Ganin yanaamsawa a zafafe ne yasa dole Kawu Adamu ya sauko ya shiga bada hakuri da fadin. "Wani ɗan uzuri ne ya shigo da ni, kuma shigowar ta gaggawa ce shiyasa ban samu na karaso ba. Amma ayi hakuri don Allah." Kawu Modibbo ya yi shiru, can kuma ya ce. "Wane uzuri ne haka?" Har Kawu Adamu zai ba shi bayani sai ya tuna roƙon alfarmar da Hussein ya yi mishi akan cewar ba ya son Kawun ya san da batun aurensa. Bai faɗamasa dalili ba ko ba komai dai ya sani Kawun bai kaunarsu, amma shi kuma ya ce ba komai zai mishi wannan alfarmar. "Daurin auren wani ɗan abokina ne ya kawo ni." Kawu Modibbo ya ji sai dai bai yarda ba, maimakon ma ya ci gaba da sauraronsa kawai sai ya yanke wayar. Shiru ya yi yana tunani, ɓacin ransa na ƙara ninkuwa. Yanzun ya lura yan uwansa da wadanda ma suka tsani Amina da Aminu a baya da kuma wadanda dama ke sonsu, duk sun hada kai, shi aka ware. Wani bakin ciki ya ji a ransa, karshen satinnan zai tattara ya je Adamawar tunda akwai bikin yar gidan ƴar uwarsu, Gwaggo Karime. Tunda gaba daya za'a hadu, zai kara zaman meeting da yan dakinsu ya ji dalilin wannan sabon sauyin. *** Bakwai da mintuna, Ramlat ta hada lafiyayyen friedrice da gashin kifi wanda a gefensa ta soya dankali ta saka sai sauce. Ta yi zoɓon da ya ji kayan kamshi ta sanya a firij. Sosai ta saki jikinta musamman wayar da suka yi da Amrah ta kara ba ta shawarar yanda za ta tafiyar da Hussein har ya fahimci shayi ruwa ne. "Sannunki, sai a je a kimtsa jiki. Allah Ya yi albarka." Ta juya bayan ta dora komai saman tebur, ta dubi Hajiya da ke fitowa daga ɗaki. Murmushi ta yi kawai ta kauda kanta. Ita kadai ta san me ta ke kissimawa a zuciyarta. Kwafa ta yi don gani ta ke komai ma za ta iya kawai don Hussein ya fahimci ya ƙuntata mata. Maimakon kimtsawar, sai ta zube saman gado, wayarta ta jawo. Missedcalls har uku duk daga Baban Hanif. Kafin ta gama shanye mamakinta sai wani kiran ya kara shigowa. Ta ɗaga da sallama, ya amsa. "Allah Ya huci zuciyarki Maman Affan, ina ta kira an ƙi a saurare ni ballantana kuma a yimin uzuri." Ta mike zaune. "Ka yi hakuri, ba haka bane. Ba na kusa. Ina wuni ya gida?" "Lafiya kalau. Babu damuwa, na yi." Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ɗora maganar. "Na so maganar da zan maki ya kasance gani ga ki, amma ba na tunanin yanzu ina da wannan ikon na zuwa kofar gidanku. Da farko ina mai ba ki hakuri bisa dukkan wani abu da ya faru a dalilin aurenmu. Na yarda haka Ubangiji Ya tsaramana. A gaskiya Ramlatu, tun fara zancen aurena da ke, iyayena suka dakatar da ni bayan bincikensu yasa sun binciko tarihinki. Sun kuma gane cewar aurenki biyu ba kamar yanda ki ka fadamin cewa aure daya ki ka taɓa yi ba. Duk da labarin aurenki na farko da aka ban, hakan bai sa na gwuiwata ta sare ba. Na ci gaba da zuwa wurinki, idan ba ki manta ba, kin sha tambayata meke damuna, na ce maki ba komai. Wallahi wannan shi ne dalili." Ya ɗan tsahirta, itama ba ta ce komai ba don dama ta san hakan kan iya faruwa, sai dai ba ta zaci za ta ji zafin abin har haka ba. "Kina ji na?" Ya tambaya, ta amsa da Uhm. Sannan ya ɗora. "A takaice dai, wancan dalilin shi ne yasa iyayena suka ce sam ba da yawunsu ba muddin na aureki. Ina kokarin shawo kansu ne sai ga kira daga Kawunki (Baba Dakta), ya yimin maganar turo magabata, na ba shi bayanin halin da ake ciki. A karshe ya nuna ya kamata na hakura tunda har iyaye ba su so. Koda an yi ba dadinsa za'a ji ba. Amma wallahi Ramlat ina sonki. Ba yanda..." "Karka damu, komai ai nufin Allah ne. Allah Bai kaddara zan zama iyalinka ba. Mu bar shi a haka. Allah Yasa ya zamemana alheri." Ajiyar zuciya ya saki har tana jin hucinsa kafin ya amsa da amin. Daga nan suka yi sallama tare da yiwa juna fatan alheri. Ta kurawa wayar idanu cike da tunani, kenan wai wannan abu da ta kusan aikatawa har ake fasa aurenta dominsa, da ace ta aikata yaya kenan? Nan da nan ta ji kwalla ta cicciko a idanunta. Da yanzun tana cikin yanayi irin wanda Halima ta tsinci kanta, da yanzu ita an ma kashe ta. Tausayin Hilal da ya fadomata a rai ta ji, rabonsa da Kano yanzun wata kusan biyu kenan. Tun sadda ya zo ya yi musu sallama akan ya samu sauyin wurin aiki zuwa Benue ba su ƙara jinsa ba sai jefi-jefi idan ya samu hawa online a whatsapp sukan gaisa. "Uncle oyoyo!" Muryar Ansar da Affan ta ji daga falon, wannan ya nunamata cewa Hussein sun shigo din kenan. Ta mike ta shinshina jikinta, gaba daya kamshin girki ta ke yi, dolenta dama ta yi wankan ko ba don shi ba don haka sai ta rage kaya ta ja zanin wankanta ta fada bandakin. Bayan ta fito ta shirya tsaf cikin doguwar rigarta na material, ba ta shafa komai a fuskarta ba, shimfida darduma ta yi ta zura hijabi ta hau sallar isha'i. Hajiya ta shigo har sau biyu tana magana. Na farko ta shigo tana wanka, na biyun kuwa yanzun tana sallah. Koda ta idar a gaggauce ta ninke dardumar ta fita. Ba ta son Hajiyar ta ƙara dawowa a karo na uku ta san rai ne zai ɓaci. Ba tare da ta cire hijabin ba ta fita. Su biyu ne da shiga iri ɗaya, shadda ce ruwan blue, hatta da karamin aikin da aka yi musu iri guda ne. Hular kansu ma hakan ta ke, sun yi kyau har sun gaji. Su biyun ne kadai a falon, Hussein na zaune a ƙasa yayinda AlHassan ke saman kujera yana danna waya su Ummi zagaye da shi. Sallamarta ya sanya shi ɗago kai ya dubeta. Ta wani ɗaure fuska babu wani zumudi balle har ta kalleshi. Sai kawai shi din ya ci gaba da kallonta ƙasa-ƙasa yana kokari ya ga sun hada idanu. So ya ke ya karanci idanun ko zai gane manufar sauyawar fuskarta. Ta karaso gami da zama a hannun kujera ta gaishesu. "Ranki ya dade Mrs Hussein, girman kujerarki ne ai. Idan laifi muka yi a yafemana, irin wannan shan ƙamshi, fitowar sai an ga dama?" Kalaman AlHassan suka sa ta murmusawa, tana jin nauyinsa hakanan kawai. "Ba haka bane, sallah na tsaya yi ne." "To dafatan an samu a addu'a? Allah Ya amsa." "Amin. Ina zuwa." Daga haka ta mike ta nufi kicin, sarai ta na kallon Hussein ta gefen idanu, kallonta yake sosai, ta yi mamaki kwarai ganin ba ya daga cikin ɗabi'unsa. Kayan abincin ta hada komai a tebur har ruwa da lemu ta ajiye kafin ta dawo falon ta yi musu iso zuwa saman teburin. "Nikam da dai za ki sa a ƙasa ya fi min dadi. Kai fa?" AlHassan ya fadi gami da duban Hussein. Ya gyada kai alamar hakan ma ya yi. Ta amsa da toh sannan ta koma kicin ta dauko katuwar ledar abinci wacce da wuya su yi amfani da ita idan ba azumi ne ya taho ba. Yanzun kam gashinan a kusa-kusa. Falon ta dawo ta matsar da centertable sannan ta shimfida. Bisa kuskure idanunta ya kai kansa, ta kauda kai lokaci guda tana kara hade fuska. Juyawa ta yi bayan ta ba Ummi umarnin bin bayanta. Marasa nauyin ta dinga ba ta ta kawo falon, ita kuma ta ji da masu nauyin. Komai ta jera, tuni AlHassan ya sauko, tana ji yana jan Hussein da hira amma yana amsawa tamkar ba ya so, a karshe sai shima ya kama girmansa ya watsar da shi ya maida hirar ga Ramlatu don tuni ta kora yaran ɗaki da kallo kawai. Sun san halinta, muddin aka yi baƙi zasu ci abinci to fa basu isa su zauna ba musamman ma tunda sun ci. "Wai nikam Ramlat a ina kika koyi girki haka? Kamshin kadai ya mamaye hancina har yawuna ya tsinke tun kafin na kai baki." Ba ta san sadda ta yi dariya har fararen haƙoranta na fitowa ba. "Wurin Hajiyata mana. Amma dai ka bari ka ci kafin ka yanke hukunci." Ta karashe gami da turamasa plate din da ta shaƙe da shinkafa ta kuma ɗoramasa kifin a gefe, ga zoɓo har turiri yake a kofi. AlHassan ya jinjina. "Gaskiya ne. Amma ko a ido ai an san mai dadi." Ba ta ce komai ba banda murmushin, ta ja plate ta shiga zuba wa Gogannata wanda ya hau danna waya amma kacokan hankalin a kan hirarsu yake, shi kansa ƙamshin abincin dukan kofofin hancinsa yake yi, ya haɗiyi miyau ya fi a ƙirga. Ƙamshin zoɓon da ya ji citta da abarba da su flavour, yana kara kwaɗaitamasa son sha. "Bismillah." Ta fadi da wani salon kashe murya kamar ba ita ba. Ya ɗago kai ya dube ta. Hankalinta na ga zoɓon da take tsiyayawa a kofi ammafa kirjinta wani bugu yake don ta san idanunsa a kanta su ke kamar yanda jikinta ya ba ta. "Na gode." Ya fadi a ciki-ciki, ta ajiyemishi zoɓon, ta mike ta bar falon. Koda ta kai ƙofa, ta dan saci kallonsa, har sannan ita ya ke bi da ido duk kuwa da cewar ya kafa kofin zoɓon a baka. Mamaki ya sa ta saurin kauda ki ta shige daki. Wani dadi ranta ya yi tana jin kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Wato dai haka Hussein ke ji idan ya na mata wannan shan ƙamshin. Ta yi dariya ita ɗaya a ɗaki kafin ta kife saman gadon cikin annashuwa. Sai da aka kwashe mintuna talatin sannan Ummi ta shigo kiranta. Ta maida hijabin ta fito, sun kammala har ma Hajiya ta fito, kayan kuwa ta tabbatar Ladidi ce ta kwashe tunda ba ta kai ga tafiya ba. Hussein ya miƙe ya fita tare da Ansar, zuwa can sai ga Ansar din ya dawo. "Mami, ki zo inji Uncle." Ta dan saci kallon Hajiya da AlHassan, hira suke abinsu kamar uwa da ɗa, ganin ba su damu da kallonta ba yasa ta miƙewa ta shiga daki. Sai da ta ɓata mintuna fiye da biyar ba don kuma wani abun ta ke shafawa ko gyarawa ba, can kuma ta fito ta fice. Yana tsaye a jikin motarsa ya harde kafafu hakanan hannunsa a harɗe a kirji. Tun tahowarta ya ke kallonta. So da kaunarta na ratsa dukkan wani ɓangare na zuciy da gangar jikinsa sai dai shafe mintocin da ta yi ba ta fito ba ya yi masifar sosa ransa. Don haka koda ta tsaya sai shima ya ja baki ya yi shiru. Ramlat ta soma gajiya da tsayuwar don haka ta dubeshi babu fara'ar a zo a gani. "Shikenan ina iya tafiya?" Kallon da ya watsamata yasa ta kallon gefe guda. "Idan har ba ki daukeni a bakin komai ba, kina iya tafiyar." Shiru ya biyo baya, jin ba ta ce komai ba sai ya sauke ajiyar zuciya. "Akwai abinda na yi maki? Ko kuwa duk baƙin cikin na rabaki da masoyinki karo na biyu ne?" "Komai nufin Allah ne. Haka ya tsaramin a rayuwa. Na kuma karɓa da hannu bibbiyu." "Hakane, sai dai kina nufin ba da son ranki ba?" Yanda ya yi maganar da wani irin sanyi, yasa ta yin murmushi kadan. "Kamar yanda kaima ba da son ranka ba, haka nima yake a wurina. Ina ganin dai mun yi anko." "Yaushe kika fara duba? Me kike nufi da mun yi anko?" Daga muryarsa ta gane ɓacin ransa, ta kara gyara tsayuwa gami da ɗan dubansa. "Daga ni har kai, mun yarda da kaddara mai kyau da marar kyau saboda mu din musulmai ne. Kamar yanda na ji batun aurenmu da kai daga sama, haka Allah Ya bani ikon karɓar lamarin matsayin kaddarata kuma mai kyau. Ko ba komai na shaida kana da ɗabi'u masu kyau daidai gwargwado. Hakanan iyayena da suka haɗa ni da kai, na tabbatar ba za su cutar da ni ba har abada. Bana so na ƙara yin gangancin saɓa umarninsu." Tana kaiwa nan ta sunkuyar da kai don ba ta kaunar kallon da yake jifanta da shi da ta kasa ganewa. "Ba wannan na tambayeki ba. Tambayar da na maki, kenan ba...Shikenan dai. Hakan ma is good." Ya fasa nanata tambayar, sai ya share. Can kuma ya kara magana. "Ku mata kun fi kaunar wadanda za su tsaya su na furtamaku kalaman so a baki alhalin idan aka yi auren ba lallai su iya tafiyar da lamuranku yanda ake so ba. Ina da tabbacin har da wannan a bahagon tunaninki." "Me ya kawo batun so? Ai bana jin akwai shi a tsakaninmu. Ba ka san cewa ko ba aure ana yin so ba?" Ya ji zafin kalamanta don haka shima ya shirya ramuwa. "Shiyasa ki ka kasa hakuri da auren da babu so?" Ta dubeshi, wani murmushi ya ke ganin ya ci galaba ta fusata. Ta kasa haɗiye maganar da ke cinta, ta maida mishi martani nan take. "Yanzu ai gashinan zan yi. Ko ba komai a rayuwa ana koyon darasi, da auren so da wanda ma babu soyayyar, duk darasi ne a gareni. Na kuma gani. Idan a baya na yi na soyayyar, yanzu na hakura zan jarraba wanda babu soyayyar na ji yanda ake ji. Ko itama tana dauwama ko aa." Tana kaiwa nan ta soma tafiya da zummar barin wurin, ya riƙo hannunta ta dawo baya. Ta juya da sauri gami da kokarin janyewa amma ina karfin ba ɗaya ba. "Ka cikani tunda dai ka riga ka san cewa haramun ne." Idanunsa tuni sun kaɗa. Shi Ramlat ke nufi da ba ta so ko me? "Idan wasa ki ke yi, bai miki kyau ba. Ina miki rantsuwa da Allah, ko yankar naman jikin Hussein za ki dinga yi kullum kina gasawa tsabar ƙiyayya, sai kin zauna da ni muddin aka ɗaura aurenmu. Idan kika ga kin fita daga gidana, to ki sa a ranki, ƙasa ce za ta zama makwancinki a ranar. Babu fitar yaji ko kuma saki. Kar ki shigo gidana da makami, zan miki tanadin kala-kala sai wanda kika zaɓa. Zan iya mutuwa, amma har abada kar ki ji a ranki za ki shigo gidana kuma na rabu da ke. Har abada Ramlat." Ta dubeshi da idanunta da suka cicciko, ba karamin fusata ya yi da zantukanta ba. Jikinta ya yi sanyi, ya saki hannunta ya faɗa motar gami da rufewa da karfi. Ta ci gaba da tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta bar harabar wurin zuwa ciki. I just published "BABI NA HAMSIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1018053716?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=H1vXb7%2FW6A2U5P8fFwbtuiA8loSGt%2B%2BNft8tDKy3EJM810crtMGUnxqUIIutxZI04rTU84moV3sLlZ4ErYDW%2BHsUJ6yuYaxKr9kgvrgaa2%2BsQQrAwLvUCmdmO42m8ACV 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 57) Kiciɓus ta yi da Alhassan dake fitowa, ta yi saurin sunne kai kamar mai jin kunya. Shi kuwa a fisge da suka hada ido ya gane kamar ranta a ɓace yake. "Har ka fito?" Ta furta cikin dakiya, ya dan yi dariya. "Na fito Amarsu, zan wuce. Gobe dai zan koma Adamawa sai ranar daurin aure in sha Allah." "Allah Ya tsare hanya. A gaidamin su Aunty Kausar da Fatima." "Zasu ji in sha Allahu." Daga nan suka yi sallama ta shige ciki shi kuma ya nufi wurin motar yana ta tunani. Koda ya shiga, ya dubi Hussein da ya ɗago kai daga saman sitiyari. "Lafiya? Na ganka wani iri kamar yanda itama Ramlatun na lura da damuwa a fuskarta. Meyafaru?" "Nothing." Ya amsa a gajarce sadda ya tayar da motar suka bar harabar gidan. AlHassan bai kara magana ba banda baki da ya taɓe. Sai da suka yi nisa ne kafin ya ji ya kamata ya ce wani abu ko da shawara ce sanin halin mutumin. "Idan mutum yana son mace, kwantar da kai ya ke yi ya nemi soyayyarta. Mace ba ta son gadara ko taƙama, mace kulawa ta ke so da kuma a nunamata soyayya a fili kuma a gaban kowa. Ban san me ya haɗaku da Ramlatu ba, amma na kalli abin a mahangar ba ka taɓa soyayya ba, asalima matan ke binka a baya kana yanƙwana su. Idan har ka ce ta wannan hanyar za ka siye zuciyar Ramlatu, abun zai ba ka wuya daga kai har ita. Kar ka yi wasa da damarka." Hussein tun soma maganar ɗan uwansa, bai katse shi ba, kamar yanda kunnuwansa ba su bar sauraronsa ba. Sai da ya kai karshe ne ya ɗan yamutse fuska. "Su matan ba za su iya hakuri da kowace kulawa ta biyo bayan aure ba? Dole burinsu tun su na waje a nunamusu?" Abin ya ba AlHassan dariya. "Ka taɓa ganin inda aka yi cinikin biri a sama? Ko kuwa su matan kana tunanin sun san gaibu da nan take za su karanci halayyar mutane irinku? Su ba wannan a gabansu, su dai su gani a ƙas. Kuma dama ai amfanin taɗin kenan, a fahimci juna a kuma ga ko za'a iya zama a jure halayyar juna. Na tabbatarmaka idan ka ci gaba da tafiya a wannan shan ƙamshin naka da rashin maida hankali, za ka sha wuya a hannun Ramlatu bayan aurenku." Murmushi Hussein ya yi don shi mamaki ma maganar ya ba shi. "Wai zan sha wuya hannun Ramlat? Anya? Don Allah na yi kama da mazan da za su sha wuya hannun mace?" Murmushin shima AlHassan ya yi gami da gyara zaman gilashinsa. "Da sauranka ɗan uwa. Bari na kyaleka, gani ya kori ji. Nidai idan ta fara gasa maka aya a hannu, kar na ganka a ƙofar gidana." Suka yi yar dariya a tare. Shi Hussein dariya yake don ganin hakan yake kamar wani almara ko tatsuniya. Bai ce Ramlatun ba ta da kyau ko tsarin da namiji zai rikito a kanta ba, tunda shi shaida ne, ganinsa da ita tun farko ya ji kawai ta burgeshi kafin ya tantance abinda ya ke ji taƙamaiman a kanta, sai dai ya na da ja akan cewa akwai macen da za ta iya juyashi ba tare da asiri ba kamar dai Hajiya Zeenatu a baya. Amma zai jira ya ga irin juyawar ta Ramlatu. Kulawar ba zai nuna ba kamar yanda dan uwansa ya buƙata har sai bayan aurensu. ***   Tana tuƙi a hanyarta na zuwa Ofis bayan ta sauke yara a makaranta, tana tunanin zantukan Hajiyarta. _*"Magidannaki fa ya bukaci ki bar aiki hakanan tunda can Adamawa za ki zauna. Ko ba don haka ba dama na fadamaki duk radda kika tashi aure idan mijin da za ki aura bai amince ba, to za ki bar aiki."*_ Sauke ajiyar zuciya ta yi. Kenan dai rabuwarta da yaranta ya zo, wani kewarsu ta ji ya kamata. Dama tasan aiki ko ba dade ko ba jima za ta bar shi kamar yanda suka yi da Hajiya a farko. Hon da aka cikamata kunne da shi yasa ta kara nutsuwa a tuƙinta, ganin ma ba wani tare hanya ta yi ba sai abin ya yi mata zafi, ta cikin gilashi ta ke duban motar, sam ba ta ganeta ba. Don haka ta yi gefe ta ba mai motar hanya. Ido suka hada ya yi mata murmushi ita kuwa dubansa ta shiga yi baki a sake sai kuma ta dara. "Hilal?" Ta furta a bayyane, a hankali ta ga ya ja gefe ya yi parking, itama dolenta ta tsaya don su gaisa. Ba ta kai ga fitowa ba ya rigata isa wajenta. "Ranki ya daɗe." "Yaya Hilal?  Saukar yaushe a garin?" Ya yi ƴar dariya. "Ko kwanaki uku ban yi ba da zuwa, shima daurin auren abokina ne ya kawoni, amma nan da jibi zan koma in sha Allah." Ta yi murmushi. "Allah Ya nunamana. Ya Fa'iza da Ɗiyarmu?" "Suna nan kalau. Ai nake gidan Sis Bilki jiya, na ji kuma abin alheri. Allah Ya sanya albarka. Yasa zamu gani." Ba ta yi mamakin yanda aka yi Bilkisun ta sani ba, tana da tabbacin daga bakin Mijinta ne. Amma faɗawa Hilal sai ta gani kamar da biyu ne. Cike da jin nauyinsa ta amsa. "Amin. Ina godiya. Wato dai da ace ba mu haɗu ba anan sai dai mu ji labarin ka tafi ko?" Dariya ya yi. "Ni na isa na shigo garin nan ban je na ga Hajiyarmu ba? Aa sam. Wallahi yau nake cewa zan shiga zuwa yamma haka." Ta jinjina kai. "Allah Ya nunamana." "Amin amin. Bari na bar ki kada na sa ki makara. Sai na shigo din." Ta amsa da toh gami da yi mishi fatan alheri, ya rufemata murfin motar sannan ya wuce zuwa tashi motar. Ta ja numfashi ta furzar, Hilal kenan, mutumin da ya kaunaceta don Allah. Gaba daya ya sauya ya ajiye kumatu. Ga duk wanda ya gan shi zai fahimci yana cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Wayarta ce ta yi ringing daidai sadda ta ke kokarin hawa titi. Ba tare da ta duba ba ta daga gami da karawa a kunnen da sallama. "Ke da waye tsaye a titi?" Tambayar da aka watsomata ba tare da an amsa sallama ba yasa ta gane ko waye. A hankali ta ɗaga kai ta dubi mirror, motarsa na nesa kaɗan da nata. Ta fi kyautata zaton daga wurin motsa jiki ya ke. Murmushi ta yi daidai sadda ta hau titi ta harba motarta. "Ba ka da hurumin sanin da wanda nake magana. Kar ka manta ban kai ga zama matarka ba." "Hakane, ba ki kai ga zama ba. Amma kin manta cewa haramun ne nema cikin nema? Ke musulma ce." Dariya ya ba ta jin yanda ya zaƙalƙale.  Yanda ta ke tafiya a sannu, haka yake biye da ita da motarsa a sannun. Ta kauda kai kamar ba ta san da shi din ba. "Babu wanda ba ya kuskure." "Haka kika ce? To naga kin ƙara tsayuwa da wani ɗan iskan! Duk abinda na yi mishi, ke kika ja. Sannan lokacin da za ki ajiye yawon gantalin aikinnan ya yi! Ba zan lamunta ba." "Wannan kuma ba ka da hurumi a ciki, ajiye aiki sai lokacin da naga dama. Ka bar tada jijiyoyin wuya tunda har yanzu aure bai tabbata ba tsakaninmu. Akwai sauran lokaci." Tana kaiwa nan ta katse wayar ta taka motarta, sai dai ba ta je ko'ina ba ya zo ya gifta ta har yana kokarin buge wani ɗan sahu. Bai ko tsaya ba ya yi gaba. Ta bi shi da kallo tana dariyar farin ciki, ko ba komai ta san ta ba shi aiki. Wannan nishadin yasa ta ware waƙar Breaker na Jarumar Mata tana saurara har ta karasa wurin aiki. Hussein bai kara kiranta ba kwata-kwata a wannan ranar. *** Bisa umarnin Yayanta Munir, ta rubuta takardar barin aiki. A wannan satin Rafee'ah ke zuwa ta kai ta gidan mai gyaran jiki. Ya kasance Ramlat ba ta da lokacin kanta balle na yara, ɗawainiyarsu ta koma hannun Hajiya da direba mai safa da marwar kai su makaranta da daukowa. Waya ba ta kara shiga tsakaninta da Hussein ba sai dai kokari kawai ta ke yi itama don tana kewarsa. Ya aiko da wani leshi mai tsadar gaske da kuma atamfofi har kala uku suma masu tsada sai mayafai da jaka da takalma, sai kuwa tsarka kala biyu da abin hannu duk na fitar biki. Ba ɓata lokaci aka kai wurin dinki tare da wanda Munir ya siyamata.   "Wai ke angonnaki yana zuwa hira kuwa? " Ta dakatar da shafa man da take yi a jiki ta dubi Amrah wacce ke zaune saman gado tana shayarwa. Taɓe baki ta yi. "Mutumin da ko waya ba ya kirana." Da mamaki Amrah ta ce. "Bana son sharri Ramlat." Harararta ta yi. "Kawai sai na zauna na kantara maki karya saboda ina tsoronki ko?" Murmushi Amrah ta yi. Nan ta kwashe duk yanda ake ciki ta faɗamata har maganarsu ta karshe. "Kai amma kin fadi mai zafi da yawa Ramlat, to ko za ki rama ai kya bari ya zo hannu tukunna. Shima dai da alama yana da zafin kishi tunda ya kasa nemanki har yau. Amma kar ki kara tunanin wai ba ya sonki, wallahi Hussein na miki son da ba ki san adadinsa ba. Da kansa fa ya je ya fadawa Baba Dakta yana sonki da aure tun ma a lokacin Chairman. Abinda kawai na kula, kamar yanda ya faɗamaki, shi mutum ne da bai yarda da wata soyayya kafin aure ba. Ya fi imanin cewa soyayya ta gaske tana zuwa ne bayan an yi aure. Kuma kar ki yi mamaki, irin su Hussein sun iya tattali da nuna kauna ga mace. Ina goyon bayanki, idan ku ka yi aure ki nunamasa kefa mace ce, amma ba wai ina nufin kar ki masa biyayya ba, aa, ki dai ja ajinki yanda zai gane shayi ruwa ne. Ke ba yarinya ba ce, na tabbatar kin gane me nake nufi." Suka yi dariya gami da cafkewa don tuni Ramlat ta taso ta dawo gefenta. "Ai ko yanzu ya ganki ya san kin sauya. Kin kara kyau gyaran jikin ya karɓeki. Duk inda kika gifta kamshi kawai kike kamar mai wanka da turare. Nidai akwai tsarabar da zan maki na kananun kaya, saura ki ƙi sanyawa." Murmushi Ramlat ta yi, sai kuma ta ji zuciyarta na neman karyewa. "Allah Ya jaddada rahma ga Aliyu." Ta furta a fili, Amrah ta amsa da amin.  Nan kuma suka shiga tuna baya, sai da Amrah ta ga dagasken Ramlat kukan take son yi don idanun sun cicciko da kwalla, sai ta share gami da sanyo wata hirar. "Zan so naga yanda waccan bakar munafukar za ta yi idan ta ji labarin aurennan." "Ni kuma kinga tsoron ranar da za ta sani nake yi. Sai kuma mamakin dalilin Hussein na ƙin ɗaukar mataki a kanta. Idan na yi tunanin ko yana sonta dagaske, ba ki san ya nake ji ba." "Gaskiya da mamaki ace yana sonta, nidai jikina sai ya bani kamar so yake sai ya nunamata ita din ba komai ba ce kafin ya dauki mataki. Ai ko don yanda ta dinga kai maki hari, ya cancanta dama Hussein ya aureki mu ga ta tsiya." Ramlat dai dariya kawai ta yi. "Kin sanar da Muhibbat?" "Eh na fadamata, ta ce za ta shigo ranar daurin auren tunda dai wunin ma duk rana daya ce." "Allah Ya nunamana." Ramlat ta amsa da amin gami da lumshe ido.   A daren bayan ta yo wa Amrah rakiya kofar gida don Dahiru ya zo daukarta, sai ganin Hussein ta yi. Suka dubi juna da Amrah da mamaki. Amrah ta murmusa. "Kinga ɗan halak, ashe dai yana tafe." Ita dai Ramlat mamaki ma ya hanata cewa uffan. Suka karasa daidai sadda ya fito daga mota suna gaisawa da Dahiru, daga nan ya amsa gaisuwar Amrah har da karɓar Baby ya yi mata wasa sannan ya yi musu sallama ya shige ciki ko inda Mutuniyartasa ta ke bai kalla ba. Ita ma ta dauke kai ba ta damu ta gaidashi ba. "Wai ke ba Angonnamu kenan ba? Shi ne ko gaisuwa." Dahiru ya fadi cike da zolaya. Ta harareshi don dama sun saba. "Ban ga damar gaidashi din ba." Ya daga kafada. "Ai shikenan. Mu dai maza ba'a ja mana aji." "Ko?" Cewar Amrah cikin son a tuna baya. Ya yi dariya kawai ya bude motarsa ya shiga. "Allah Ya bamu alheri Amarsu. Sai da safe kafin wannan Madam din ta ɓallomin ruwa." Dariyar suka yi kawai, ta bude gidan baya ta ajiyewa Amrah ledarta. Ba ta juya ba har sai da ta ga sun ja mota, ta koma ciki tana son ganin yanda za su kwashe da Gogannata. A hankali ta ke takawa tamkar mai tafiya akan ƙaya, murmushi kawai ta ke zabgawa tana duban sararin samaniya wanda taurari da kuma watan na Rajab da bai fi kwanaki shida da bayyana ba. Hakan na nunk da kusantowar da wata azumin Ramadan ke ƙara yi. A hankali kuma ta maida kanta ƙasa ta ci gaba da tafiya har ta kusa barandar da za ta sada ta da falonnasu. Yanda ta ganshi a tsaye hakan ya dauremata kai, ta yi zaton yana ciki su na gaisawa da Hajiya, ko kuwa dai ya shiga ne ya fito? Oho. Ba ta da tabbaci, ganin kallonta kawai ya ke yi sai ta sunkui wa kai, koda ta karasa har za ta gifta sai kuma ta ga rashin kyautuwar hakan, don haka sai ta tsaya ta gaishe shi. Maimakon ya amsa kawai sai ya kuramata idanu, idan ya ce ba ta sauyamasa ba, to ya yi karya. Ta wani cicciko ta yi haske, kamshi ke tashi kawai a jikinta. Ramlat ta ji shirun ya yi yawa don haka ta ɗan ɗago kai. Nan da nan ya daure fuska ya hadiye murmushin da ya yi niyyar suɓucemasa. Ya wayance da ɗan jan karan hancinsa da jan hancin kamar mai mura. "Am...Meyasa ki ke giftawa cikin maza da uban ƙamshinnan? Koda ace babu maganar auren wani a kanki, kina sane da cewa haramun ne ko?" Kanta a kasa ta yi murmushi a kasan ranta ta ce. 'Ka ji da masifaffen kishinka.' "Ni ko fita ba na yi yanzu." "Ko? Meyasa na ganki a waje? Idan mijin Amrah ne, mijinki ne?" Ta ɗago ta dubeshi sai ma ya ba ta ƴar dariya. Maimakon ta ba shi haushi sai ta burgeshi, kawai sai ya jingina kai jikin gini yana kallonta. Ganin haka ta  hadiye dariyar. "Allah Ya huci zuciyarka." Lumshe ido kawai ya yi ya bude. "Matso, magana za mu yi." Ba musu ta dawo ta tsaya daga gefensa. Kamar ta ce masa su nemi wurin zama amma kawai sai ta share. "Kamar yanda na san cewa kin sani, yana da kyau na kara faɗamaki da bakina. Bayan aurenmu Adamawa zan kaiki. Kano sai dai mu zo ziyara. Abu na biyu babu batun aiki, ko a Kanon ko a Adamawa. Ba zan jure ganin ina fita nema, matata na fita ba.  Kar ki ce za ki haɗa kanki da Zeenatu, wannan daban take hakanan tsarin rayuwarta daban da taki. Ina fatan kin fahimta?" Ramlat da ta kasa haɗiye kishin Hajiya Zeenatu, ta gyada kai, ciki-ciki ta amsa. "Na ji." Jin yanayin sauyawar muryarta ya sanya shi ɗan matso da kai kaɗan yana murmushi, cikin rada-rada ya ce. "Mece ce damuwarki? Hajiya Zeenatu ko kuma maganar aiki?" Ta juyo da zummar harararsa, sai dai ganin irin kusancin ya kai har fuskarsu na dab da haɗewa yasa ta saurin ja baya tana maida numfashi. Shi kansa sai da ya ji wani yarr tun daga yatsar ƙafafunsa zuwa kwakwalwa. Ya sauke ajiyar zuciya. "Ina iya tafiya?" Ta nemi sani a gaggauce. "Kin gaji da ganina? Sati nawa ba ki ganni ba?" Baki sake ta dubeshi. To ma duka-duka yaushe suka hadu a titi ya cashe mata? Sai kuma ta juya kanta kawai tana duban yatsun kafafunta. "Shikenan, zan kiraki a waya. Kina iya tafiya." Ta amsa da toh sannan ta nufi ciki. "Ba ki ji ba." Ya katse ta, ta ciji lebban bakinta don ita kam ba ta son kallonnasa, ta daure ta juya. Murmushi kawai ya yi mata. Sai aikin kallo, ta gaji da rashin maganar ta juya abinta zuwa ciki.    Yau kam duk juyinta tunanin Mijinnata ne, ta yi mamakin sauyinsa amma ta fi kyautata zaton kawai kewarta da ya yi ne ya chanja shi. Koda ta kammala shirin kwanciya, ta ji bai kira ba sai ta yi zaton ya yi bacci. Da Asuba bayan ta idar da sallah, ta zare wayar a chaji. Ga mamakinta missedcalls har biyar duk na Hussein sai saƙon da ya turo. Ta bude. _*Kin kyauta kenan?*_ Ta yi murmushi, Hussein rigima kenan. Ita shaf ba ta tsammaci zai kira ba tunda har goma ta wuce ga kuma bacci na cin idanunta don kwanakinnan ba ta fiye samun yi sakamakon sammakon zuwa wurin gyaran jiki da ta ke yi. Madadin ta ba shi amsa sai kawai ta share ta jefa wayar gefen gado sannan ta fita gaida Hajiya. Koda ta dawo, biyawa ta yi ta tashi Ummi da Ansar su yi sallah. Ba ta ci wuya ba suka tashi domin sun riga sun saba. Kamar yanda ta yiwa Hajiyar, hakanan su ma suka shiga suka gaisheta. Ƙarfe takwas a gidan Hajiya Bingel Sudan ta yi mata, ta yarda sosai da gyaran matar don ta san ta kan gyara. Duka-duka ba a sani jima da farawa ba amma gaba daya ta sauya, sai dai ba laifi Yayyunnata mata sun kashe kudi. Koda ta koma gida ta iske kaya jibgi a falo, ashe kasuwa su Maman twins suka je. Tarkacen kayan kicin ne kala-kala da Munir ya bada a siya. Babu laifi kullum kudinsa daɗa albarka ya ke yi. A bakin Rafee'ah ta ke jin zancen furnitures, wai Baba Dakta ya ce komai da ya danganci wannan a barshi a hannunsa. Ta kara jinjina riƙon zumunci da kuma abota na Baba Dakta wanda bai taɓa bari sun koka da rashin Abba ba. "Kai wannan Jug din ya yi kyau. Ga azumi ya taho, har na hango bakin Hussein yana kwankwaɗar lemu." Rafee'ah ke maganar tana dariya, gaba daya suka sa dariyar har Ramlatu. "Ke dai Rafee'ah ban san sadda za ki girma ba. Yara uku amma har yanzu da sauranki." Rafee'ah na dariyar furucin Hajiya, Maman Twins ta ce. "Ai da alama sai Baban Abba ya rangaɗomata kishiya." "Shi ya isa? Taɓdi! Ai shiyasa ko magana ya dauko nake katseshi da cewa ko gidanmu daya tal na tashi na gani. Soyayya tun na yarinta har girma don haka kada ma ya fara." Daƙuwa Hajiya ta mata. "Ungo nan! Kin isa ki ja da ikon Allah? Yau Isma'il ya so aure ai kuwa baki isa ki hana ba. Ba gwara kishiyar ciki ba da a yi maki ta waje ba?" Nan fa aka shiga hirar kishiya, Maman Twins na fadin ita kam tana ma ji a jikinta Baban Twins aure yake son yi tunda ginin da ya fara na bangare biyu ne. Ita dai Ramlatu ta yi shiru kawai tana duba kaya, idan abin ya ba ta dariya ta dara. Can kuma maganar ta dawo kanta. "Kedai me kishiya irin Zeenaru take ko wa? Wallahi sai kin tashi tsaye da addu'a. Azkar safe da yamma kar ki bari ya wuceki. Ni na ji dadi ma tunda ba wuri daya zai haɗaku ba." Ta dubi Maman Twins. "A ina kika ji?" "Ni ya fadawa. Na fi zaton akwai dai abinda ya ke nufi a kan matar, amma bari mu zubawa sarautar Allah ido. Ke dai kamar yanda Uwanin ta fada, ki zage damtse da addu'a. Ya sanar da ni ma zuwan matar Hassan da wasu cikin yan uwansu, amma ba gidansa za su sauka, masauki zai kama musu. Ba yanda ban yi ba da shi akan ya bari su zo nan yace babu komai." Hajiya ke zancen ita dai ba ta da labari ma sai lokacin. Sai kuma suka koma batun rakiyar Adamawa, su na tantance wadanda ya kamata su je. "Bilkisu fa? Ke an fadamaki Bilkisu za ta shiga sabgar Ramlat?" Rafee'ah ta tambaya da mamaki jin Maman twins na batun Bilkisu. "Toh aikuwa za ki sha mamaki tunda Munirun da kansa ya sanarmin cewa za ta je. Kuma ita ta amsa da hakan." Hajiya ta fadi. Nan dai Maman twins aka hau rantsuwar gulma ce kawai za ta kai ta. Haka suka yi ta tattaunawarsu abin gwanin sha'awa. Aisha ciki ya soma nauyi ba kasafai ta ke fitowa ba. *** WASHEGARI... "Ki soma shirya kayanki. Tafiya ta zo." Hajiya Zeenatu ta dubi mijinnata gabanta ya fadi. "London ko ina?" Ba tare da ya dubeta ba ya ce. "Adamawa kafin London. Ai na faɗamaki zamu je yan uwana su ganki ko?" Ta dan yi shiru tana tuna wayar da suka yi jiya da daddare da Kawu Modibbo. Gargadi ya yi mata a kan zuwa Adamawa don a cewarsa ya zo garin, bai kuma ga wata alama da ke nuni da cewar ta samu karɓuwa ba, asalima labarin da ake shi ne, asiri ta yi ta rabashi da mahaifarsa. "Kin yi shiru." Hussein ya furta gami da ɗan riƙo yatsun hannunta yana murmushin yaudara. Ta bishi da na yaƙe. "Hum, kana ganin ba ni da matsala da su? Za su karɓe ni da hannu bibbiyu?" Hussein ya ci gaba da bin ta da kallo, abinda ya ke zargi ya kara tabbata. Jiya ya ji tana waya kuma tsaf ya ji me tace. Sai dai bai gama fahintar waye ke tare da ita a danginsa ba, ko ma waye dai ya lura sun jima su na tare. Zai bi ta sannu har wayarta ta fado hannunsa ya dauki lamba. "Kamar kowane dangi, akwai masu murna da ci gaban mutum da ma wadanda ba su yin farin ciki. Ba zan rantse maki cewa duka dangina su na sonki ba Zeenat, musamman abinda ya faru tsakaninmu wasu su na daukar alhakin ki cewa ke ce silar komai. Amma bangaren yan uwana kuma shaƙiƙaina, ba ki da wata matsala. Don haka ki kwantar da hankalinki. Ban taɓa fadamaki ba saboda bana son sanyaki cikin wani hali. Amma yanzu ya zama dolena na faɗa don kar ki ga wani abu a wajen wasu ki ji ba dadi. Ba zaman kowa kike ba face ni." Wani dadi ya lulluɓeta, ta ji a duniyar nan ta kara son Mijinnata. Ba ta sadda ta rungumeshi, ya runtse ido yana ji kamar wuta ta ɗosana a fatar jikinsa. "I love you." Ta furta a hankali. Ramlat ce ta fado a ransa kafin ya ce. "I love you too." Da wannan ya shawo kanta ta mike har da batun za ta shiga kasuwa ta soma siyan tsaraba. Ya fiddo kudi zai karamata ta girgiza kai da binsa da hararar wasa. "Ah haba, yan uwanmu ne fa. Rike abinka, da kudina zan musu tsaraba." Ya yi murmushi kawai. Yana binta da kallo, ya lura kwana biyunnan kurajen nata da sauki sun fara mutuwa, ta dai ce na gargajiya ta soma karɓa ta gaji da zirga-zirgar asibiti. Shi dai ba abinda ya shafeshi. Kusantarta ne tuni ya bari. *** *RANA BA TA ƘARYA!*    I just published "BABI NA HAMSIN DA TAKWAS" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1019046229?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=4ocpUEJVa%2B0bXSp4wxbK3lhNgthMCA7nB5QC2dclyyGJkYlECeIGKhiQUzgNGFlkVbskOsJU12vwNQbJIqJ2Pbn6%2F7TbXN1B%2BYmSMvxcC1P2DtDikL9OR4lEi83T5hqO 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 58) Ana gobe ɗaurin aure tun da safe, suka bi jirgi zuwa Yola. Awa biyu da mintoci ta kaisu. Kamar yanda Hussein ya shirya, Kausar da AlHassan ne masu zuwa tarba. Kausar tun da ta ga Hajiya Zeenatu ranta ke zafi dakyar ta iya tankwara zuciyarta. 'Allah Ya isa.' Ta fadi a kasan ranta, Hajiya Zeenatu kuwa wani dadi ta ji ganin irin tarbar da ta samu a wurin Kausar duk da shekarun da ta ba ta. Suka dunguma a motar AlHassan zuwa gida. Bai yi gangancin sauketa a gidan Dada ba don ya tabbata Dada za ta iya kasa hakuri don ba ta iya ɓoye abinda ke ranta ba wasu lokutan sai dai ya san akwai ta da hakuri. "Anan za ki zauna sai zuwa gobe idan an huta sai a leka dangi. Hakan ma ina ce ya yi miki?" Hajiya Zeenatu dake karewa dakin da aka ba su kallo ta juyo tana dubansa fuskarta cike da damuwa. "Yanzu dagasken a yau za ka juya? Gaskiya idan hakane zan jira a gidannan zuwa sadda za ka shigo garin sai mu leka dangin tare. Wallahi haka kawai na ke jin fargaba." 'Me akai da maza Zeenatu?' Ya furta a ƙasan zuciyarsa a fili kuwa murmushi ya yi kamar gaske ya shafi gefen fuskarta. "Shikenan, yanda ki ka ce hakan za'a yi. Nima kin riga da kinsan dalilin komawar, ban larasa handling komai a wurin aikinmu ba ne, gobe juma'a in sha Allah da zarar na kammala, Asabar da safe zan taho." Ta gyada kai. "Babu wata damuwa. Allah Ya kaimu." "Amin. Amma toh ko bikin ba za ki leƙa ba? Na fadamaki Cousin Sister ce a wurina." Ta tuno da hakan don Kawu Modibbo ya fadamata zancen bikin don shi ne silar zuwansa garin shima. Sai dai ya gargadeta da shiga dangin gudun samun matsala don haka ta girgiza kai. Shima Hussein kawai fada ya yi don ya gwadata, amma tuni ya ji tana batun ba bikin da za ta leka da wanda suka yi waya kwanaki. "Ka yi hakuri dai, ka ga ba'a san ni ba. Zan jira har ka dawo ka gabatar da ni a wurinsu." Ya jinjina kai. "Ba damuwa." Daga haka ya rage kayan jikinsa ya shiga bandaki, can ya fito, wanka ya yi. Ya sauya kaya ya feshe jikinsa da turare. Hajiya Zeenatu ta ƙuramasa idanu, kananun kaya ya sanya. Rigar da ya sanya milk mai gajeran hannu sai blue jeans. Tsayawa suffanta kyawun da ya yi mata ta sani ɓata baki ne, mijinta kara kyau ya ke koyaushe da kuma ƙuruciya musamman gashinsa baƙi siɗik da ya kwanta a sumar kansa irin na Bafulatanin Yola wanda ke kara fiddo da zahirin waye Hussein. Ta shagala a kallonsa da jin wani irin tashin hankali da kishin zuwan da za su dinga yi Yolan yanzu, tana da tabbacin idan matan Kano ba su yi nasarar raba ta da shi ba, to wadannan kyawawan matan na fulanin Yola za su iya rinjayar zuciyarsa. Hakan tunaninta ke ba ta. Har ya kammala ya ɗaura agogo ta shagala a tunani. "Muje mu ci abinci, su na jiranmu." Ya fadi ba tare da ya kalleta ba, jin shirun sai ya ɗaga kai yana dubanta. Ta shagala a tunani, sai da ya ɗan yi tafi kusa da ita sannan ta yi firgigit. "Um, am..me ka ce?" "Tunanin me kike? Nace mu je mu ci abinci daga can zan biya wurin Dada sai na wuce Airport." Ta yamutse fuska. "Sai zuwa anjima zan ci, yanzu bacci nake ji." Ya ɗan ɗaga kafaɗa. "Ok. Bari naje, idan kin yi nisa a baccin ba sai na tasheki ba. Zan wuce." "Allah Ya kiyaye hanya." Ya fice yana mai amsawa da wani irin nishadi a ƙasan ransa. A falon ya yada zango, yana cin abinci su na hira da AlHassan da Kausar duk akan tsarin bikin. "Yanzu kenan ita kadai za ta zauna a gidan? Yaushe Amaryar za ta zo nan? Don naji ana cewa tare duka za su shiga dakunansu." Kausar ke neman sani. "Asabar za su zo. Ke dama ai yanzu ba zancen zuwanki Kano saboda matarnan. Su Hafsat dai da saura sai su je." AlHassan ke maganar. Kausar ta jinjina kai. "Allah Ya kaimu." Shi dai Hussein loma kawai ya ke, yana kammalawa ya mike ya gyara bakinsa. Koda ya shiga munshari Hajiya Zeenatu kawai ke yi. Ya ja mata kofar bayan ya dauki abinda zai dauka yana tsakin takaicin aurenta. Tare da AlHassan suka shiga gidan Dada. Kullum ta gansu sai ta ji kamar an yayyafawa zuciyarta ruwan sanyi. Tana tare da su Baba Yakura yan Maiduguri da ma sauran yan uwan mahaiyarsu. Aka gaggaisa kafin ya yi musu sallama da zummar wucewa Kano. "Allah Ya kaika lafiya Ango. Mu dinma ai yanzu zamu wuce. Kai dai tunda a jirgi ne za ka riga mu sauka." Ya yi murmushi jin abinda Gwaggo Lubabatu ƴar abokiyar zaman kakarsu ta bangaren Uba da ke Mubi ke fadi, ya yi addu'a akan Allah Ya kawo su lafiya sannan aka kara yin sallama ya tafi. ***   CIKAR BURI.. Gidan cike yake da yan uwa da aboka arziki, tun safe ake shige da fice na dora sanwa. Dangi an cika a madafi ana aiki ana kwasar hira. Fuskar kowa ka gani cike da farin ciki musamman Hajiya da har kwalla sai da ta yi don kuwa sun debemata kewar Abba. Cikar da suka yi ya motsa zuƙatan mutan gidan da tunanin Abba, bikin ganinsa suke yi tamkar na wata budurwa ba bazawara ba. Ƴan Daura da yawansu sun zo hakanan kafatanin mutan gidan Hajja su na nan. A bangaren Baba Dakta ma, hatta Kanwarsa Hajiya Nabila da yan uwan Umman Amrah duk sun hallara. Wannan shi ne kadai karar da zaa yiwa Hajiya mace mai son mutane da kuma zumunci. Don sun shaida, Hajiya ko ba ta je sabgarka ba, to hannunta zai je. Ba ta gajiya da kyautatawa hakanan marigayin Mijinnata. A ganinsu wannan ce karar da zaa yi. Kowa ya bude baki ya ga cikar gidan cewa ake, har ma da auren Ramlatun, shima ya yi albarka kwarai. Duk wannan shagalin da ake, Ramlat na can tare da Amrah da kuma Rafeeah a gidan kwalliya. Dama tun ana gobe daurin aure suka je aka tsaramata lalle a ƙafa da hannu na gani na fada. Hakanan duk a ranar aka yi mata kitso sirara. Maryam Cutie ce gwanar kwalliyar, tsayawa faɗin irin kyawun da ta yi ba'a cewa komai. Kasancewar Maryam kawar Rafee'ah kuma ba ta da matsala ne yasa ba su wani jima su na roƙo ba ta amince za ta bisu har Adamawa don yiwa Amarya kwalliya ta musamman. Ba ta samu matsalar hakan daga mijinta sosai ba don shi mutum ne mai fahimta hakanan sanin da ya yiwa Rafee'ah da mijinta ne yasa bai yi ja in ja ba. "TubarakAllah Masha Allah." Amrah ta fadi tana kallon Ramlat baki ya ƙi rufuwa tsabar kyawun da ta yi mata. Ko aurenta na farko ba ta tsaya ta nutsu an mata kwalliya kamar hakan ba. Murmushi Ramlat ta yi jin yanda su ke koɗa ta. Farin leshin wurin Muniru ta sanya an mata dinkin gown. Maryam Cutie ta yi mata dauri na gani na fada a karshe ta yafamata gyalen kamar yanda ya dace . "Ke Ramlatu, kinga yanda kika sauya?" Rafee'ah da ke tsaye gaban madubi tana dauri ke fadi, ita da Amrah suma duka Maryam ta fito da fuskokinsu ba laifi. "Ya isa kar ku cinyeta." Fadin Maryam tana dariya. Hotuna ta shiga yi mata tana mai yin alfahari da baiwar  iya kwalliya da Allah Ya ba ta. Ta tabbata fuskar Ramlat ko kasar waje za ta a haka, to fa za ta ciri tuta. Sai wuraren sha biyu suka kama hanya zuwa gidan, ita dai Ramlat jikinta duk ya yi sanyi, fatanta Allah Yasa wannan ya zama aure na karshe a gareta wanda mutuwa ce kawai za ta raba. Allah kuma Ya ba su zaman lafiya. Koda suka shiga gidan nan ma haka yan uwa suka yi caa ana ta koɗa kyawun da Amarya ta yi, kunya ta kamata ganin Hafsat diyar Dada, sai a sannan ta kula da zuwan yan Adamawan. Hafsat ta ja hannunta zuwa can falon Abba na baya da aka kai su, suka karasa ta durkusa ta kwashi gaisuwa. "TubarakAllah, Amaryar Hussein kyakkyawa da ita." Matar ta fadi da hausarta da ba ta fita sosai. Ita dai Ramlat kanta a kasa tana murmushin jin kunya. Sai da Hafsat ta sanya ta zauna ta dinga daukarsu hotuna kafin a karshe ta yi musu sallama ta fito tare da Hafsat. Nan fa Hafsat ta shiga cikinsu aka dinga raha kamar dama can an shaku sosai. Su Nusaiba duk sun zo, daga mai goyo sai mai ciki. Suna zaune a daki sai ga Salma da Bilkisu, dama Hunainah ita kam tun safe tana gidan, ko sadda suka shigi tana kwance ta yi rashe-rashe a saman gadon suna kwasar hira da kanwar miji kuma aminiyarta A'isha. "Amarya Ramlat. " Bilkisu ta fadi tana yamutse fuska musamman jin bakin cikin ganin Hunainah ta riga ta zuwa. A ranta ta ce 'Cusa kai.' Ramlat ta gaidata da murmushi saman fuskarta. Ta mance rabon da ta sanya Bilkisun a idanu, gaba daya ta kara wani fari fat sabida shafe-shafe ga wani uban ƙiba da ta ke narkawa, ita kuwa Salma har tambarin baƙi-baƙi ya yi mata a fuska. Ramlat ta ja hannun Yasmeen  suna gaisawa, yarinyar yanzu ta bar sakewa sosai kamar a baya don dif haka uwar ta raba ta da gidan. Yanzun ma da biyu ne zuwannata, ba ta san mijin Ramlatun ba. Ko a hanya suna ta gulmar abin suna dariya don har Salma na fadin Allah Yasa wani Alhajin ne mai mata uku da katon tumbi. A jikinsu ba su taɓa kawo wai matashi mai jini a jika zai aureta ba musamman idan an san wacece ita. "Murja da Fareeda ma suna tafe, Hilal ya fadamusu tunda ke ba ki iya gayyata ba." Ramlat ta dubi Amrah, Amrah ta kanne mata ido don ta san gulma ce. "Ayya, ban yi zaton za su zo bane. Allah Ya kawosu lafiya kuwa. Ina murna." Bilkisu ta taɓe baki ita kuwa Salma murmushi ta yi ta dora kafa daya kan daya tana girgizawa. Sai dai kyakkyawar budurwar da suka gani da aka kirata da yar uwar mijin Ramlatun duk sai suka soma shan jinin jikinsu. A hankali Salma ta yi magana saitin kunnen Bilkisun.   "Anya wadannan mutanen su na da labarin wace ce Ramlat a baya?" Bilkisu ta ce "Oho musu, nikam daga suturar jikin yarinyar kamar dai ba karamin mutum shegiyar ta kwaso ba. Ai kuwa ƙafata ƙafarsu har Adamawan naje na ƙarewa danginnasu kallo sosai." Salma da takaici da bakin ciki ya cika zuciyarta, ita kasa magana ma ta yi. Shekararta sama da ashirin da biyar yanzu amma ko auren fari ba ta yi ba, ga Ramlat har ta kara samun wani ɗanɗasheshan. Don jikinta ya fara ba ta hakan. Burinta yanzu a daura auren ya shigo ta karemasa kallo. *** Yana kishingide saman kujera a gidan Hisham wanda ya shiga wanka, hotunan da Hafsat ta hankaɗomasa ta whatsapp ya ke aikin kallo, sosai ya yi zooming hoton Madam din tasa ya kasa kauda ido. Murmushi ya ke yana jin soyayya mai tsafta na kara mamaye ko'ina na zuciya da kwakwalwarsa. Ba zato ya ji an fisge wayar, ya dan dago a ɗan razane don sam bai ji tahowar Hisham din ba. Hisham wanda ke daure da tawul ya ja tsaki. "Aikin banza, sai afkin karewa mace kallo amma ba a iya tattali ba. To ka tashi, yanzu Yayanmu ya kira ya ce sun iso, ka tarbo su suna waje." Hussein ya mike zaune gami da dan dafe kai kafin ya mike ya ja guntun tsaki yana gyara zaman rigarsa ta shadda fara ƙal sai dai babbar rigar na ajiye bai sanya ba. "Ka ci gaba da shiga rayuwata. Kuma ma meyasa ya kiraka bai kira ni ba?" "Ganin dama." Daga haka Hisham ya yi ciki da wayar Hussein din a hannunsa don ya shirya, Hussein ya bishi da harara don sosai ya ragemasa nishadi, a bakin gate ya ci karo da su. Ganin wanda bai zata ba sai kawai ya tsaya kamar wani gunki baki a bude. "RASHEED?!" Ya furta kai tsaye kafin da azama su yiwa juna wata wawuyar runguma da bubbuga gadon baya ana dariya. Can ya sakeshi suka kara cafkewa su na dariya. Nan da nan idanunsu suka kada kuma kamar wadanda ke shirin kuka. Tabbas sun yi masifar kewar juna. Bai ma ga sauran yan uwansa uku da ke tare da su ba sai da ya gama gaisuwar da Rasheed. Najib, Faruk da kuma Khalil duka Yola idan ka cire Faruk da ya zo daga Mubi. "Allah Ya isa, ban yafewa  matarnan." Rasheed ya fadi sadda suka nutsu suka zauna a falo. Murmushi Hussein ya yi. "Ka bar damuwa da ita, ta kusa zama tarihi. Momi ta zo?" Rasheed ya jinjina kai. Yana nufin mahaifiyarsa, Hajiya Binta. "Yes tare muke, tana can Yola wurin Dada." Haka suka yi ta hirarsu cike da nishadi, shi dai Hussein bini-bini zai duba agogo. Ganin lokacin sallah na ƙaratowa ya dubesu. "Ya kamata mu hanzarta wuce masallaci ko?" Lokacin sallah ya gabato." Me zasu yi ba dariya ba. "Lokacin sallah ko lokacin daura aurenka? Kai Malam ba ka da kunya wallahi." Faruk ya fadi yana dariya. "Bar shi kawai, ai idan bai yi hakan ba bai cika sabon shiga ba." Hussein dai har ga Allah sun soma ba shi haushi, dagaske so yakeya ga an hanzarta an tashi an tafi. "Na rantse zan muku ƙofi yanzun nan ku ga maciji." Ya fadi yana mai mikewa tsaye suka yi dariya sosai shi kuwa ya shiga zura babbar riga yana mai tafiya gaban madubin dake falon yana gyara zamanta. Karshe ma hular ya dauka ya shiga gyaramata zama yana ji AlHassan na cewa su tashi don da alama Angon  zai iya ficewa ya bar su.  Nan kuma wadanda ba su da alwala duk suka dora sannan aka kama hanya bayan Hussein ya feshe dukkan jiki da turaruka masu tsada da kamshi har kala uku. Bababn burinsa Ramlat ta zama mallakinsa kafin kowane irintsautsayi ya gifta da ba ma ya fatansa. *** Misalin karfe biyu da mintuna, dubban jama'a suka shaida daurin auren HUSSEIN AMINU GIDADO da RAMLAT KHALID MU'AZZAM akan sadaki har dubu ɗari wanda nan take aka damƙawa Babanta Dakta matsayinsa na waliyyinta. Bakin Hussein ya ƙi rufuwa, sosai daurin auren ya tara mutane. Hilal kansa sai da ya halarta, duk da Hussein ya san shi, haka suka gaisa faran-faran suka yi hotuna. A karshe aka dunguma gaida iyaye. *** Babu damar sallah a wurinta sakamakon tana fashinsa, sai dai ta yi sujjadar godiya ga Allah kuma ta yi addu'a sosai. Bayan ta mike ne Amrah ta ba ta tissue. "Don Allah kar ki ɓata kwalliyar mana." Ta karba tana goge hawayen. "Kukan munafunci ne kawai, mace sai ka ce yau aka taɓa dauramata aure. Aure na uku?" Bilkisu ta fadi da dariyar kissa, Hafsat jin ta ce aure na uku yasa ranta ya ɓaci, dadinta Hussein bai ɓoyemusu komai na labarin Ramlat ba. Dama tun zaman Bilkisun da irin kallon da suke jefamata ita da abokiyar rakiyarta ta ji sun ba ta haushi. "Ko aure na nawa ne ai aure ne. Duk wacce ta san me ta ke yi dole zuciyarta ta karye a wannan rana, ko bakomai ta san nauyin da Allah Ya ɗoramata." Maganar Hafsat ta zo wa su Bilkisu a bazata, wato dama sun san komai? Nan da nan ransu ya kara yin baƙiƙirin musamman Murja da Fareeda da basu jima da shigowa ba, suma dai ganin kwakwaf dinne. "Muje falo ga Angon ya zo." Fadin Muhibbat da ta shigo, ta ja hannun Ramlat suka fice, Aisha kam ji ta yi kamar ta goya Hafsat don dadi, balle kuma Rafee'ah da ke dariyar shaƙiyanci. Sosai Hafsat ta burgesu don kanta a waye yake ba karya. Ai su Bilkisu na jin haka suka bi bayansu rii duk domin su ganewa idonsu Angon Ramlatu. Ai kuwa sun yi kyakkyawan gani da ya birkita tunaninsu. Yana durkushe gaban yan uwan Ramlatun ana kwasar gaisuwa, sai ga Amaryar. Nan da nan tsofaffi aka sjiga guɗa da kirari. Ya kasa kauda idanunsa a kanta, ita kuwa ganin irin kallon da yake mata babu kunyar ido yasa ta yi ƙasa da idanunta. Tsakiya aka zaunar da ita shima ya zauna, yan uwa aka baibayesu mai hoto ya shiga aikin dauka. Kirjin Hussein banda bugu da sauri babu abinda ya ke yi, ji yake kamar ya ja ta ya sanya a babbar riga ya gudu da ita. Sai da aka kammala hotunan har da mutan Adamawa sannan Ango da tawagarsa suka fice. Murja da Fareeda dai fasa yinin aka yi aka dunguma aka tafi yayinda Bilkisu ta daure suka zauna. Amma Salma rantsuwa take yi da ƙarawa cewa asiri ne kawai aka yiwa Hussein domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, ko makaho ya shafa Hussein ya san ya wuce aurar Ramlat duk da dai itama ba baya ba. *** Sai wuraren bakwai na dare sannan jama'a suka soma tafiya, wadanda suka rage da zasu je Adamawa ba su da yawa. Ramlat ta yi ɗai-ɗai saman gado tana hutawa duk ta gaji don yau ba karamin zirga-zirga ta sha ba a cikin gidan kawai. Kowa ya zo sai an kirata an ɗauki hoto, wannan zamani na hoto har haushi ya ke ba ta. "Ke kinga mutuniyarki ko? Ta kasa ɓoye abinda ke cikinta? Kai Allah Ya rabamu da hassada mugun ciwo." Amrah ke zancen ganin duka na dakin babu bare, daga su sai Nusaiba sai Aisha sai kuwa Hunainah dake sallah. Murmushi Ramlat ta yi. "Ni mamaki ma abin ya dinga ban, ta madubi fa ina kallon yanda suke hararata amma da mun hada ido sai su basar." "Ke wa ya taɓa samun daukaka idan bai hadu da yan hassada ba? An fadamaki tsakani da Allah za ta je Adamawarnan? Ni wallahi ban san sadda Bilkisu za ta sauya ba. Gaba daya a farko kamar ba za ta yi ba." Fadin Rafee'ah wacce ke shan wani youghurt da ƴan Yola suka kawo. "Dama DAN ADAM ance mai wuyar gane hali." Aisha ta furta. Haka aka yi ta hira, har zuwa sadda Hafsat ta shigo da sauri ta hau kan gadon gami da sanyawa Ramlat waya a kunne. Ta kalleta kafin ta tambayi waye cikin rada-rada ta ce. "Angonki." "Assalamu alaikum." Ta ji muryarsa sadda ta rike wayar sosai a kunnen, amsa sallamar ta yi. "Shi ne kika kashe wayarki ko? Gaba daya kin sa na rasa nutsuwa." Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuna ashe fa tun a wurin kwalliya ta kashe wayar ba ta ƙara bi ta kai ba. "Ina neman afuwa." "Naji, amma yanzu ki fito ina mota. Gaisawa kawai zamu yi." "Ka..." Bai bari ta kai aya ba ya katse wayar, dole ta cire ta miƙawa Hafsat da hankalinsu gaba daya ba ya kanta. Ta matsa kusa da Amrah ta mata raɗa. Amrah ta murmusa. "Kar ki manta dai, yanzu miji ne a wurinki ba manemin aure ba. Umarninsa za ki bi kawai. Ki je ba komai" Ta mike ta gyara zaman dankwalinta ta yafa gyale sannan ta fice. Tana jin yanda matan dakin suka dauki sowa murmushi kawai ta yi ba ta ko juya ba. A farfajiyar gidan ta ga mota sabuwa dal sai sheƙi ta ke, ba ta yi zaton shi ne a ciki ba sai da ta zo giftawa ta ji ya mata hon, hakan ya ba ta damar bude kofar don ba'a ganin na ciki. Shi din ne zaune kuwa, ta shiga ta rufe sakamakon AC da ke a kunne. Kamshin motar da kamshinsa sun hadu da sanyi sun saukarmata da ni'ima a zuciya. Ta dubeshi, ya cire babbar riga hakanan hular na ajiye saman gaban motar. "Ina wuni." "Lafiya." Ya furta tamkar ba ya so. Can ya ce. "Ya gajiyar biki? Anya kin ci abinci? Sai naga kamar kin faɗa." Ita mamaki ma ya ba ta don haka ta kasa amsawa. "Kin yi shiru." "Uhm, na ci." "Kin fa zama matata, amma na lura da ke tun dazu kamar murmushin dole ki ke yi." Yanda ya yi maganar kamar zai yi kuka yasa ta dubansa, gaba daya ya juyo ya matsa dab da ita, ta ji nauyinsa, shi kuwa hakan yake so dama, tun shigowarta ya ke kokarin su hada ido amma hakan ya gagara. Za ta juya kai ya yi saurin riƙo haɓarta ya karkato da kan. Ta dora hannunta a saman nasa da zummar kautarwa. Sai dai ya rike hannun tamau. "Please ka sakarmin hannu." Ta ci gaba da kokarin kwacewa don ba ta shiryawa hakan ba. A hankali ya saki hannun. "Na saki. Shikenan?" Ba ta ce uffan ba. "Ki je kawai, sai mun yi waya ko?" Ta saci kallonsa, kamar dai fushi ya yi. To ita kuwa me za ta ce? Ina sabon da za ta sake don ya rikemata hannu? "Kin tsareni da ido, ba na kyaleki ba?" Yanda ya yi furucin sai ma ya ba ta dariya, ta kauda kai tana murmushi. "Ni kike wa dariya?" "Aa." "Kin ma iya ki ci abinci, ni da ban ji ki ba kasa daurewa nayi da komai har sai yanzu da na zo na ganki. Idan na tsaya wassafa kalar farin cikin da nake ciki, zamu kwana mu wuni a nan." A hankali ya jawo hannunta mafi kusa da shi ya damƙe cikinnasa. Wani yarr ta ji kamar yanda shi kansa sai da ya ji wani shock. Ya ƙurawa lallen idanu. "Allah Ya bani ikon riƙe ki amana Ramlat. Ya ba ni ikon yi maki adalci a zamantakewarmu. Na san na ɓatamaki rai da yawa, amma ki yi hakuri. Haka nake, ban yarda da soyayya kafin aure ba, bayan aure ke kanki yanzu son zai fi maki armashi a kowace tafiya. Abubuwa da yawa ba ma sai na fada ba tunda ke ba yarinya ba ce ko?" Ta saci kallonsa don gaba daya sautinsa ya sauya, gira ya ɗaga mata yana jifanta da tattausan murmushi. Ta kauda kai ta shiga kokarin zame hannunta. "Na dauka zaman hakuri da biyayya kawai zamu yi ai tunda cikinmu ba wani mai kaunar ɗan uwansa." Ba zato ya fisgota kafadarsu na gogar juna kamar yanda fuskokinsu tuni ya hadu wuri guda sai hucin numfashinsu da ke gaurayewa. "Kina da tabbacin bana sonki? If yes, prove it." Ta lumshe idanu tana shaƙar kamshin lemon mint da bakinsa ke yi. A hankali kuma ta yi nufin yin baya ya rike kanta kafin ba zato ta ji bakinsa a nata. Shirun kusan mintuna biyu kafin ta tureshi ya yi baya, babu kwari a jikinsa, don haka ya jinginar da kai yana kallonta da soyayyun idanunsa. Ita kuwa sai afkin goge baki da ta ke yi bayan ta zari tissue dake saman gaban motar. Ya kauda kai kadan yana dariyarnan irin na wanda aka rainawa wayau. "Kai, ni kike gogewa baki don na taɓashi?" Ta daure fuska ta harareshi. "Saboda ban shiryawa hakan ba. Ai ba haka tsarin zamantakewar tamu ya ke ba." Daga nan ta wurga tissue din a jikin motar duk dacewar hatta da kujerun baa ciremusu ledojinsu ba. Tana kokarin bude kofar ta fita ya kara yi mata wata wawuyar fisga, duk kokarinta ta kwace abin ya gagara. Haka ya taramata miyansa a baki kamar yanda bai kauda bakin ba sai da ya ji ƙarar tafiyarsa, loko da saƙo sai da ya tabbatar ya gauraye a bakin kafin ya saketa. Iyakar shaƙa ta shaƙa, ta bankamasa wata hararar. Ya ɗaga mata yatsu. "Good night Love." Ta bude kofar kawai ta fice, ya bita da kallo yana jin kamar kar ta tafi saboda wani tsananin kewa da ya kamashi nan take, har sai da ta shige gidan kafin ya lumshe ido da murmushi can kuma ya buga sitayari. "Ya Rabb!" Ya fadi cike da nishadi, soyayyar Ramlat na kara ƙaimi a ransa. Dakyar ya samu kuzarin jan motarsa, kafin ya fice daga gidan ma sai da ya kira wayar Hafsat ya jaddada mata akan ta shaidawa Ramlat ta kunna wayarta. I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://www.wattpad.com/story/229538078?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=3RG5g2a5w6izCuKU8HhNqobuQjDF3XsdSGdqdVtdShDrSoD84AKgTAv38ifr8A0P6JNqIoYXqVCm072j3Kj010bX%2FXCFmaovF0BtpPRfTxUwRF7KoTA35HGU0Qpfh9Zn 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 59) Kusan gaba daya mutan dakin bacci suke yi idan ka cire Amrah da ke zaune tare da amniyarta tana tayata wajen shirya kaya a ƙatuwar akwati. Wasu kayayyakin kuwa su na fitarwa domin bayarwa. Amrah na lura da yanda gaba daya ba ta da sukuni, jefi-jefi takan sa hannu ta share bakinta. "Wai ke kam lafiyarki kuwa?" Ta dawo hayyacinta. "Me kika gani?" Harara ta watsamata. "Kamar ya me na gani? Alhalin ina lura da yanda tun dazu kike wani shagala da shafa baki, saurin me kike?" Ranta ya kara baci ta ja tsaki. "Me kike nufi? Idan ma wani abin kike nufi gwara ki watsar tun a nan don kinsan irin zaman da na shirya za yi da Hussein." Amrah ta jinjina kai. "Ko wane irin zama ne ba zan hanaki ba tunda ke ba yarinya karama ba ce da zan tsaya ɓata bakina, abu daya da zan tunasar da ke, yanzu Hussein ya tashi a kowane matsayi ya hau matsayin mijinki. Idan kin gyara kanki, idan kin ɓata ma ke za ta shafa." Shiru kawai Ramlat ta yi ba ta kara tankawa ba. Can kuma aka kwankwasa kofar dakin da sallama aka shigo. Hafsat ce sanye da riga da wando na bacci kasancewar ita ta kafe ta ƙi bin yan uwansu Hotel, hakan yasa Hajiya ta mata wuri a makeken gadonta. Hamma ta ke zabgawa duk suka dubeta. "Adda wannan Yayannamu ya hana ni bacci wallahi, don Allah ki tausayamin ki kunna wayarki ku yi magana. Ni ga wayata ma na bar maki a nan don wallahi da zarar na soma nisa a baccin yake tashi na." Dariya ta ba su, aikuwa ba wanda ya kai ga cewa komai sai ga wani kiran. Da sauri Hafsat ta miƙamata. "Yauwa gashinan. Sai da safe." Ta fice Amrah na addu'ar Allah Ya tashemu lafiya. Ita kuwa Ramlat wayar ta ɗaga ta ɗora bisa kunne yayinda Amrah ta juyamata baya ta ci gaba da aikin da tuni ma sun ƙarƙare sai tattarawa. Sallama ta yi, jin muryarta sai ya sauke ajiyar zuciya. Shiru ya dan biyo baya kafin ya tanka. "Kin hana ni bacci Heart." Ta ɗan saci kallon Amrah wacce hankalinta na can wurin harhaɗe kaya ba ta ce masa komai ba. "Meyasa ba ki kunna wayarki ba? Kinsan zan nemeki, zan so na ji muryarki. Bacci ya kauracemin, ba ni da burin da ya wuce na ganki a gidana. Heart, kin yi shiru." Ta ɗan daure ta yi magana. "Me zan ce?" "Ko mene ne ki fada daidai ne. Amma kar ki kara kuskuren da ki ka yi dazu, idan kuwa hakan za ki ci gaba a zamantakewarmu, za ki sha wahala a wurina." Murmushi ta yi mai sauti. "Dariya ma na ba ki?" "Ko kusa, bacci fa nake ji." "Ni kuma ban shiryamasa ba, hira na ke son mu yi. Koda dai tambayar da nake son yi maki ba ta waya ba ce, sai mun haɗu ga ni ga ki." Nan ma ba amsa sai shirun daga wajenta, har Amrah ta mike ta fada bandaki ta dauro alwala, yana ta magana Ramlat sai uhm ko uhm uhm. Tana kallo Amrah ta kashe fitilar dakin ta bi lafiyar gado kusa da Babynta ta kwanta. Cikin takaici Ramlat ta ce. "Malam kowa fa ya kwanta, nima gyangyaɗi nake, ina son..." "Be serious Heart, ko kadan ba ki tunanina?" Ta lumshe ido ba tare da ta tanka ba. "Talk." Ya fadi a hankali. Ita har mamaki ma ya ke ba ta. "Shiru ma fa magana ce ko? Inji Hausawa." Ya kara fadi yana yar dariya, ta cije lebba don takaici, wato ma ya riga da ya fassarata. "Kai ka san wannan, ni abinda ya tsayar da ni daban ne. Sai da safe bacci nake ji." Ba ta jira komai ba ta kashe wayar gaba daya. Mikewa ta yi tana murmushi har ta na tuntube da ƙafar Dijen Daura da ke bacci a saman katifa. Hakuri ta ba ta sannan ta fada toilet. Alwalar itama ta yi ta nemi wurin kwanciya. *** Tun da Asuba masu tafiya Adamawa suka tashi ba'a koma ba. Daga mai wanka sai mai sanya kaya, wasu kuwa da ba za su sami zuwan ba, sai suka fada kicin don yin abin kari. Ramlat dake bacci sakamkon tana fashin sallah, dolenta ta wartsake don ba karamin takuramata su Rafee'ah suka yi ba akan ta mike ta yi wanka. Bayan ta fito ta shirya cikin atamfar Holland kalar light blue da fari, ta yafa farin mayafi sannan ta fita wurin yaranta. Ta dauka za ta gansu cikin damuwar tafiyarta sai dai da sauki musamman ga Ummi da Ansar wadanda suka shaku sosai da Hajiya. Affan ne ma ya dan yi wuri-wuri da idanu da ya tabbatar dagasken tafiyar Maminsa za ta yi. Itama dannewa kawai ta ke amma tsananin kewarsu ta ke ji tun kan a je ko'ina. Kiran da Hajiya ta mata ne yasa ta lallaɓa Affan da ya kanainaye a jikinta ta fita. Can ƙuryar daki ta isketa. Ba ita kadai ba ce har da Umman Amrah da ta shigo tun sassafe da kuma su Baba Hajara da sauransu. Nasiha sosai suka yi mata, Hajiya a karshe ta tofa da cewar sun gama magana. Ta yiwa Ramlat addu'a kawai. Ita kuwa banda afkin kuka ba abinda ta ke fitarwa. Iyayenta masu sonta da komai, a baya ta bijirewa saboda son zuciyarta. Nan ta bude baki ta na mai kara neman gafararsu akan abinda ta aikata a baya. Murmushi suka yi. "Banda abin Ramlatu, ai kowa ya fahimci kaddara. Ba komai kedai komai ya wuce sai da kawai yanzu ki maida hankali wurin biyayya ga mijinki." Wata Gwaggonta daga Daura ta fadi. *** ADAMAWA... Hajiya Zeenatu hakanan ta ji faduwar gaba, shigar da Hussein ya yi da irin fara'arsa sai ta soma wani tunani daban. Ganinsa ta ke yi kamar wani Ango. Ya kammala ɗora agogon hannunsa bayan ya idar da sallah, murmushi ya ke tun sadda suka yi magana da Hafsat ta tabbatarmasa da isowarsu garin su ma. Dama habyar da ya biyo daban da tasu. "Hussein." Jin ta kira sunansa kai tsaye yasa shi dubanta. "Duk wannan fara'ar ta mecece? Wani kyau ka yi kamar wani Ango. Gabana faduwa ya ke yi. Yaushe za mu je ka kaini mu gaisa da danginka?" Ya yi wani banzan murmushi ya  rike kafadunta. "Kar ki damu, kin ga yau daurin auren yar uwata ake yi, ke kuma na sanki ba kya son cunkuso da wani hayaniya, ki yi hakuri gobe zamu shiga ku gaisa da kowa. Kallon banza aka yi maki Hussein ba zai rabu da mai shi ba. Sannan kina batun wai Ango, na dauka kodayaushe ni Ango nake a wurinki? Toh ki kwantar da hankalinki, babu macen da ta ishe ni kallo har naji ina sonta. Ke kinsan yanda nake." Yanayin da ya furta kalmar karshen kawai sai ta kara shan jinin jikinta, ga wayarta ta rasa ya aka yi ta fada ruwa balle ta tambayi Kawu Modibbo ko akwai wani labari, yanzun dai ta ƙi tashi Hussein kuma ya karɓe ya ce zai siyomata wata da kansa. Abinda ba ta sani ba, da gayya ya tankwaɓar da ƙaton jug na ruwan dake saman centre table, burinsa dama ta rasa hanyar jin kowane labari. Bai bar gidan ba sai da ya tabbatar ya kwantar mata da hankali, har cewa ya yi ta dauko mayafi su fita tunda hankalinta bai kwanta ba, soyayyar Hussein da ganin tsantsar gaskiyarsa a yanzu ta rufemata ido ta yanda ba ta tuna komai da kowa, hakan yasa ta kasa hasaso wani abin musamman ma da ta ga ta fito falon Kausar na mishi batun bikin da ake yi. Hankalinta ya kara kwanciya bayan fitar Hussein din da Kausar ta shiga budomata hotunan auren da ake yi tana kallo tana ƙara jin sanyi a ranta. Ta na kuma kara tabbatarwa zuri'arsu Hussein kyawawa ne tsantsa. *** Bangaren Marigayi Baba Naziru wanda ya sha gyara da fenti daga AlHassan, nan aka kai Ramlat kafin lokacin da Hussein zai yi gininsa. A sannan yan uwanta suka hau aikin jere da ma sauran abinda duk ya kamata. A ranar daga su sai su, an kawomusu abinci da abubuwan sha. Da daddare suna zaune ana hira, wayarta ta yi kara, Mr.Wuff. Murmushi ta yi ta dan mike ta bar wurin zuwa can wani dakin da ta tabbatar babu kowa ciki. "Assalamu alaikum." Ta furta a hankali. "Waalaikumussalam. Fatan an iso lafiya?" Ta dan lumshe ido kafin ta bude tana bin dakin da kallo, shima gado ne aka shimfida a dakin, don wannan karon gatan da ta samu har gado biyu aka yi mata. "Alhamdulillah." Shiru kamar ba wanda zai tanka can kuma ya ce. "Kin shiryawa abinda zai biyo bayan aurenmu?" Ta ji maganar banbarakwai. "Kamar ya?" Murmushi ya yi mai sauti. "Za ki haɗu da Uwargidana mana." Ranta ya sosu matuka, kishi mai zafi na Zeenatu ya mamaye koina na zuciyarta. "Ina ruwana da ita? Zamana da nata ba iri guda ba ne. Ko ba komai ita ai auren soyayya aka yi kamar a cinye juna." "Sai aka fadamaki kema ba zan iya cinyekin ba? Wai meyasa kike son koyaushe ki nunan babu soyayya tsakaninmu? Dama akwai soyayyar da ta girmi aure?" Ta kasa ba shi amsa don har lokacin kiran Zeenatu da uwargidansa da ya yi yana mata zafi, ta rasa rashin zuciya irinta Hussein da ya iya rayuwa da matar da ta rushe dukkan wani tubalin ginin rayuwarsa saboda son zuciyarta. "Shiru ki ka yi?" Ya tambaya. Ta dan turo baki kamar yana ganinta. "Bani da abin cewa." "Saboda kin san ba ki da gaskiya ne kawai. Na dai fadamaki, ki shiryawa hakan. Tsoro ba naki ba ne, dama na riga da nasan ke jaruma ce. Amma ban sani ba ko har a fannin kishiya." "Wanda aka damu da shi ne ake kishinsa, tunda ba na kishinka me zai dameni da matarka? Don haka kar ka samu damuwa, ita dai za ka yiwa wannan kashedin. Zan kwanta sai da safe." Ta katse kiran ranta a tsananin ɓace. Me Hussein ya gani a tattare da Zeenatu har yake mata son da ba zai iya rabuwa da ita ba wai? Ita ta rasa dalilin da yasa duk laifin da ta yi masa ba ya ganin ko ɗaya. Wato har shaidamata yake ta shiryawa haɗuwarta da ita saboda ya san ba zai yi kyau ba. Ramlat ta yi kwafa, ta mike da zummar barin dakin sai ga saƙonsa ya shigo. "Kashe waya ba shi zai sauya zancena ba, ba kuma zai hana na faɗi ba. Ki shiryawa haɗuwarki da Uwargidana. Anan za ki gane so da kuma ƙiyayya." Ta harari wayar tana jin kamar shi din ta harara, sai kuma takaici yasa idanunta cikowa da kwalla ta yi azamar daukesu ba ta bari sun zuba ba. Daga nan ta ja tsaki ta fice daga ɗakin. *** Washegari da safe suka gudanar da  shagali irin na al'adarsu da suke kira Fansa, inda dangin Ango ke kawo kayan abin ci da sha ga dangin Amarya ba tare da sun ga Amarya ba. Da yammaci aka hau shirye-shiryen buɗar kai. Maryam Sambo (Cutie) ta fente fuskar Amarya da kwalliya wanda ya fi na ranar daurin aure. Maganar kyau ma na Ramlat ba sai an tsaya ana ɓata baki wurin faɗa ba. Ta yi kyau iyakar kyau, ga ta nan dai ba farar mace ba, amma Allah Ya mata baiwarSa a halittarta. Wannan karon ma Leshi ne golden cikin kayan da Hussein ya bata ta sanya an mata dinkin gown. Bilkisu dai gaba daya sai ta kara raina kanta, bakin ciki kuwa kamar ya kasheta. Ba ta taba zaton family din da Ramlat za ta shiga su na da wannan kuɗin ba. Hatta da muhallin Ramlatun, ya ci a kalla a ƙara kalla duk kuwa da cewar tsohon gini ne sai dai ya yi tsari sosai. Gaba daya suka fita katon rumfar da aka tanada a babban filin tsakar gidan gadon na Marigayi Alhaji Gidado. An lulluɓe jikinta gaba daya da turmin zanin atamfa yanda ko fuskarta ba'a gani. Nan kuma dangin su Hussein aka shiga fansar fuskar Amarya, Dada nan take da ba da Dubu ɗari na fansa, haka nan ma yan uwansu na Mubi da Maiduguri kowa ya shiga kawo nasa. Amrah ce gwanar faɗin nawa Amarya ta samu. Ita dai Ramlat na ƙunshe tana murmushi a ƙasan zanin don al'adar tasu ta burgeta matuka sai dai  da zarar ta tuno batun haɗuwarta da Hajiya Zeenatu da Hussein ya yi sai jikinta ya yi sanyi sai dai kuma ta tabbatar addu'a ne maganin komai. Hafsat a matsayinta na ƙanwar Ango ita ta mike don zaɓawa Amarya suna, a karshe ta radamata suna Amal. Sunan da kafatanin dangin za su dinga kiranta da shi kenan.   Bayan an kammala aka kwashesu zuwa gida. Da daddare ana zaune gaba daya ana hirar bankwana.    "Amal." Suka yi dariya gaba daya jin sunan da Amrah ke kiran Ramlatun. Ita kam tasan kafin ta saba da sunan za'a jima. Anan wata ma ke tambayar Kishiyar Ramlat. "An cemin tana nan amma ban ganta ba." "Anya ta zo Adamawa? Ina ji fa a Kano za ta zauna ita." Cewar Rafee'ah. "Ta huta. Zama da dangin miji gari daya ai sai tsautsayi." Babu wanda bai kalli Bilkisu ba, ita kuwa sai karkade kafa ta ke don dama da biyu ta yi maganar tana jira a tanka. Umman Amrah ce ta hana kowa magana karshe ma aka maida hankali ga hirar bikin yanda ya yi kyau. Koda za ta kwanta tana ganin kiran Hussein ta ƙi ɗagawa don ba ƙaramin haushi ya ba ta ba. Karshe ma ta katse wayar. *** A bangaren Hussein sam bai samu ya fita ko'ina da Hajiya Zeenatu ba sai a washegarin bikin bayan dangin Ramlatu sun kama hanyar Kano, ya zo tare da su AlHassan, Kausar da ɗiyarsa. Har yanzu akwai yan Maiduguri da Mubi wadanda ba su kai ga tafiya ba sakamakon dakatar da su daga yin hakan a Hussein ya yi, kowannensu na da labarin Hajiya Zeenatu, sai dai ba su ji cikakken ba sai yanzun da suke burin ji. Falon a cike yake, tun da ta ji suna juya harshe, wasu fulatanci wasu kuma yaren barbanci. Bayan an gaisa Hussein ya gabatar musu da ita sai kuma kai tsaye suka nufi ɗaya falon na Dada, babu cunkoson mutane kamar na farkon. Dada ta ƙuramata idanu, kusan koda ta girmemata ba da shekaru masu dumbin yawa ba. Suka gaisa da mutanen dakin, ita dai Hajiya Zeenatu an gaisa amma ba ta gamsu da kallon da kowanne ke bibiyarta da shi ba. Anti Amarya matar Kawu Modibbo itama gidan ta sauka, wannan karon dai Modibbo bai hanata ba, da biyu ya bar ta ta je don ya gama shan jinin jikinsa, yakan kirata akai-akai ya ji ko ana wani abin. Ita har mamakinsa ma ta dinga ji, ta kuma soma wani tunanin. 'Yanzu wannan ce azzalumar matar da ta raba ni da ɗana?' Dada ta faɗi a ƙasan ranta, nan da nan tsanar Hajiya Zeenatu ya kara cika zuciyarta. "Amm..Dada. Hafsat ba ta nan ne?" Dada ta dubi Hussein, alama ya yi mata da ido akan kar ta nuna wani abu. Ta yi dan murmushin yaƙe. "Ta shiga wurin Amarya saboda kowa ya watse, kar a bar ta ta yi zaman kaɗaici." Hajiya Zeenatu dai ba ta ce uffan ba amma a ranta tana ta tunanin dama Dadar ba ita kadai ce wurin mijinta ba? "Zeenatu." Muryar wata mata ta ji, daidai sadda ta juya ta dubeta. Zumbur ta mike ido waje ta ke dubanta. "Hajiya Binta?" Hajiya Binta mahaifiya ga Rasheed ya karaso tana murmushi. Hajiya Zeenatu ta dan saki jiki ta karasa suka rungume juna amma gaba ɗaya jikinta ya yi wata irin mutuwa. Ta dago ta dubeta. "Yaushe kika zo ƙasarnan? Me kike yi a nan?" Yanda ta yi tambayar a mamakince yasa Hajiya Binta murmushi tana kara hadiye mamakinta, don koda ta ji labarin duk abinda ke faruwa har kuka ta yi don tausayawa Hussein. Ita ta ba Hussein dukkan shawara akan ya ɓoye dukkan batun aurensa da Ramlatu gareta don ta san komai na daga shaiɗancin Hajiya Zeenatu. "Ina nan tun sadda Allah Ya bayyanamana Husseini. Ko kin manta amintarsu da Rasheed?" Ta gyada kai tana yaƙe. "Ban mance ba. Rasheed din yana nan shima?" "Eh yana nan, ya dan fita ne ma, yanzu za ki gan shi ya dawo." "Ok." Shi ne kawai abinda Hajiya Zeenatu ta iya faɗa kenan jikin a matuƙar sanyaye. "Dama kun san juna?" Dada ta jefo tambayar ga Hajiya Zeenatu. "Eh, Ƙawata ce." Ta amsa a dake, saura kaɗan dariya ta suɓucewa Kausar, AlHassan ya sa ƙafa ya ɗan taka ta don ta gimtse. "Bayan an zauna sai Hussein ya fidda waya. Hafsat ya kira ya ce ta taho sashin Dada tare da Amal. Hakan da ya fadi yasa ta fahimtar komai, don haka da toh kawai ta amsa. *** Ramlat da tun soma wayar Hafsat ta kafeta da ido. "Hamma Hussein ya ce mu je." Ta gyada kai, ta yi wankanta ta ci ado da wata shadda da aka yi mata dinkin doguwar riga ya sha aiki. Ta cakare ɗaurin ɗankwali don Ramlat ba baya ba. Ta ɗora mayafi a saman kayan ta zura takalmi suka fita tare. Hakanan ta ji gabanta na bugu da sauri-sauri, ta kara kallon Hafsat wacce ke wani zumudin suna tafiya sai janta da hira take amma ba ta fadi dalilin wannan rawar ƙafar ba. A ƙofar falon farko suka yi sallama, kunya sosai ya kama Ramlat don ba ta zaci ganin sauran jama'a ba. Ta durkusa a kunyace ta gaishesu. Cike da fara'a aka amsa, nan kuma wata tsohuwa ta ɗauki guɗa da biyu. Jin haka daga cikin dakin, sai ga Kausar ta leƙo, Hafsat na ganinta ta tsallaka. "Adda, dagaske ta zo?" Hafsat ta tambaya da raɗa-raɗa, Kausar ta yi dariya ta nuna ƙofar falon. "Tana ciki." Hafsat ta harari ƙofar. "Makira, yau ƙarshenta ai ya zo." Suka yu dariya sabida duk da harshen fillanci suke maganar, Ramlat ta karaso. "Muje ko?" Sai kuma ganin Kausar suka shiga gaisawa, wasu mutan falon duk sun mike sun biyo baya don ba su kaunar abinda za'a yi ya kasance babu su. Gaba ɗaya ana zazzaune har Hajiya Zeenatu da ta soma sakewa ganin Hajiya Binta har su na hira. Tana so ta tambayeta yanda su Dada suka ɗauketa amma babu dama tunda ba su keɓe ba. Ba su kadai ne a falon ba. Sallamar da aka yi duk ta dawo da hankulansu bakin ƙofar musamman ganin yanda wuri ya ɗauki guɗa. Hafsat ce ta soma shigowa sai Kausar, bayansu kuwa Ramlatu. Wani irin miƙewa tsaye Hajiya Zeenatu ta yi a matukar gigice. Babu chanjawar da za ta yi ta kasa ganeta tsabar tsantsar tsanar da ta yi mata. Ido waje ta ke duban Ramlatu, daga kan kafafunta har zuwa dukkan gaɓoɓinta babu inda ba ya rawa. Ba ta ƙara razana ba sai da ta ji muryar wata na fadin. "Ƙaraso ciki ki zauna, Amaryar Husseini. Lale lale da kyakkyawar halittarnan." Wani ihu Hajiya Zeenatu ta kurma kafin ta yi tsalle da nufin isa ga Ramlatu. I just published "BABI NA SITTIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1021339453?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=4X2TU9EgqK9sZlhD1RiJLYSmRa3JHzKonALRYeMQgs42rcaB4hSZEFfZEuyDyjNLmgxQTxRGGIYovRiJIB7fWJjhHoMqPgV6u1FPxMnKYkUE%2FDXuKH3NHflk4iDkMg3R 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 60) Caraf aka damƙe hannunta, ta dubeshi tsakar ido ya yi mata wani kallon banza, kallo na tsana da ya jima yana dannewa. Idanun Hajiya Zeenatu ya yi wani mugun kaɗawa. Ganin komai ta ke kamar a mafarki. Wani irin uban zufa ya haɗemata duk da iskar da fankokin ke bayarwa. Yarfar da hannunta ya yi. Bai kuma yi wata-wata ba ya dauketa da mari hagu da dama. Kallo daya idan ka yiwa fuskar Hussein za ka fahimci tsantsar ɓacin ransa. Abu ne da ya jima yana dannewa. Hannunsa har rawa yake sadda ya ke nunata da yatsa yana magana. "Ko a mafarki! Kar ki ƙara tunanin cutar da matata!" "Hussssseiin.." Ta furta da rawar murya ga hanjin cikinta da ta ke jin sun dunkule wuri guda. Idan ba ta yi ƙarya ba ma, ta ji fitar tagwayen tusa daga jikinta. "Yes, Hussein ne. Wanda kika kashewa rayuwar shekaru biyar! Kika raba shi da asalinsa! Ki ka tauye kuruciyarsa don kafirin zuciya da zalunci irin naki! Idan ke mahaukaciya ce da ba ki gano kuskurenki ba, kika daukemu shashashai ki ka ci gaba da yin yanda ki ka so da tunanin kin ci galaba ko kuma tunanin ni Hussein ina sonki, kin yi ƙarya. Kin manta yanda muka hadu kuma muka rabu a farkon haɗuwarmu? Har tunaninki ya ba ki damar hango ni matsayin masoyinki? A'a, kin yi kuskure! Dama wannan ranar nake jira. Na auri mafi soyuwa a wurina da iyayena, mafi ƙi a wurinki sannan na yar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda! Ko ba komai yanda kika tako garinmu kika daukeni cikin dangina, hakanan na dawo." "Hussein! Karya ka ke! Karya ka ke wallahi! Ni za ka ci wa mutunci?! Ka san irin son da nake maka?! Ka rasa wa za ka auro sai wannan baƙar ashanar?" Nan fa ta tubure ta dinga maka ashariya, wani marin ta ji, wannan karon ba Hussein ba ne. Dada ce da fuskarta ta gama jiƙewa da ruwan hawaye. "Rufemana baki! Makira azzaluma kawai! Kina zaton wawaye ne mu! Allah Ya isa tsakaninmu da ke! Alhakinmu da kika ɗauka na tsawon wannan lokacin sai Allah Ya sakamana walla.." Kuka ya ci karfin Dada har muryarta na shaƙewa, kusan ma da yawa hawayen suke yi musamman don tausayin Dadar wacce ta yi uban jinya da Hussein ya ɓace kafin ta samu waraka amma fa koyaushe cikin kuka ta ke da addu'a. Ramlat ita kanta kukan ta ke yi sosai, daidai sadda Hussein ya zura hannu a aljihu ya fiddo takarda ya kama hannun Zeenatu ya damƙamata. "Meye wannan?! Me kake nufi? Dama ka kawo ni cikin danginka don ka ci mutuncina? Me ka ke son ka cemin?" Tana maganar tana jijjiga takardar yayinda take kuka har da majina.  Ɗigon tausayinta ba wanda ya ji don dama kowa da tabon shekarun da ya yi cikin zulumi da kewar Hussein a zuciya. Wani irin tsalle ta daka da zummar shaƙo wuyan Ramlat sai dai tuni matan suka damƙe ta, Hussein shi kallon mamaki ma ya tsaya yi mata na irin wannan ƙarfin halin wai ɓarawo da sallama. Zagi take ƙudundumawa tana kiran sai ta hallaka duk wanda ke shirin rabata da farin cikinta. "Modibbo ya yi gaskiya! Dama ya ce kar na zo! Kar na zo! Ba sona ku ke yi ba! Ashe da gaskiyarsa! Wallahi Hussein ka yi kaɗan! Zamanmu har abada ba na ƙare ba ne! Yanzu aka fara!" Gaba daya Hajiya Zeenatu ta birkice, fuskarta kace-kace da hawaye ga majina tana aikin jansa. Idanunta yanda ya rufe har ba ta san me ke fita daga bakinta ba. Kowa a dakin ya shiga salati jin sunan da ta ambata. Hussein ya ma kasa magana sai murmushi, ga duk wanda ya gani kuma zai fahimci na zallar takaici ne kawai. Dama shi kadai ya zarga, duk kuwa da bai gama tabbatar da hakikanin lambar wayar da ya ɗauka a wayarta ba tunda ba shi da lambarsa, amma daga kiran da ya yi sau daya da kuma muryar da ya ji, jikinsa ya ba shi tare suke komai. Hannu kawai ya harɗe a kirji bayan ya ja baya ya ci gaba da kallon diramar da kowa ya ke jin  sunan wanda ta ambata, babu wanda ya zata. Dada kuka sosai ta ke yi don har numfashinta na sama, wannan ne yasa AlHassan janyeta zuwa ɗaki don kwantarmata da hankali. A hankali Hussein ya juya zai fice, wannan yasa Hajiya Zeenatu bin bayansa fuuu bayan ta ture duk wanda ke gabanta. Koda ta kalli Ramlatu, wani banzan kallo kawai ta watsamata na za mu haɗu sannan ta yi gaba don tasan ba damar taɓa ta yanzun. Hafsat ta yi caraf ta dauki jakar Hajiya Zeenatun ta buɗe ta cusamata takardar da Hussein ya bata wanda ta yi wurgi da shi a tsakar ɗakin sannan ta bi bayanta da sauri. AlHassan dake ɗakin tare da Dada  jin ƙugin tashin mota ya mike da sauri ya fito. Ganin babu Hussein a falon yasa da sauri ya fita. "Kar ka sake ka budemishi gate!" Ya fadi da ɗan ƙarfi yanda Maigadin zai ji kuma da harshen fulatanci. Nan da nan Maigadin ya fasa. Hussein ya ci burki, ita kuwa Hajiya Zeenatu dake bubbuga gilashin mota tana bin motar don ya saurareta, itama ta tsaya cak. Hafsat wacce tuni ta jefamata jakarta tana tsaye kallon dirama da ƙarfin hali irin na Zeenatu. Daidai sadda Hussein din ya fito daga motar. Hajiya Zeenatu ta cakumi wuyan rigarsa bai yi wata-wata ba ya hankaɗata. Sai yanzun ya tuna da akwatin kayanta da ke boot din motar, tun a can gidan ya nunamata za su kwana biyu gidan Dada, don haka ta haɗo komai na kayanta. Ya buɗe ya fiddo akwatin kafin ya ja hannunta tana binsa ta na magana kamar zautacciya. "Hussein ina sonka! Ban taɓa son wani namiji dagaske ba sai kai! Ka yimin rai kar ka rabu da ni! Kar ka manta da dukiyarmu, na tuba ka yafemin don Allah." Wannan karon da alamun karaya sosai a muryarta, shi kuwa shareta ya yi bai ce uffan ba har sai da ya fidda ita daga ƙofar gidan gaba ɗaya. Daidai sadda Rasheed ya dawo gidan don ya ɗan fita. Ganinta ya gane abinda ke faruwa don yana sane da shirin Amininnasa. Akwatin ya diremata ya dubeta a wulaƙance. "Sai ki kama hanya ki bar garinnan idan kinga dama, idan ba ki gani ba ki zauna ki ƙara gwada kashe Ramlat ki gani ko zan bar ki da rai." Daga haka ya juya ya dubi Buzun maigadinsu mai jin fulatanci, cikin fulatancinsa wanda ya ɗan farfaɗo ya ba shi umarnin koda wasa kar ya bari ta shigo gidan. Daga nan ya komai ciki tare da Rasheed. "Na dauka wurin Kawu za ka je. Shiyasa na fito don tsayar da kai." Alhassan ya furta yana dubansa. Ya shafi suma gami da runtse idanu, radadi  ya ke ji idan an ambaci sunan Kawunnasu azzalumi kuma maƙiyinsu da har yau sun rasa gane kan ƙiyayyarsa. "Nan na so zuwa amma na fasa. Zan jira hukuncin Dada." Daga nan ya shiga motar,  AlHassan ya yiwa Rasheed ido alamar ya bi bayansa. Ba musu ya zagaya gefensa ya bude ya shiga. Kallonsa kawai ya yi bai ce uffan ba, bisa umarnin AlHassan din ya bude masa ƙyauren ya fice. A hanya suka ga Hajiya Zeenatu jaye da akwati tana tafe tana waige. Ganin motarsa har hannu ta sanya da nufin tsayar da shi, ya ƙarawa motar wuta gami da jan tsaki. *** Tun faruwar wannan lamari, tsoron Allah ya ƙara shiga zuciyar Ramlatu. Ta ƙara tsoron ƊAN ADAM tunda har nasa bai kyale ba. Wane irin zamani ne wannan? Haka ta yi ta tunani bayan ta koma sashinta. Waya suka yi da Hajiya ta labartamata dukkan abinda ya faru. Salati Hajiya ta sanya gami da ƙarawa, ba abinda ya girgizata sai na jin sunan Kawun Hussein din da ya fito a maganar. Addu'a ta yi gami da ƙara jan kunnen Ramlat akan addu'a da kuma kiyaye Azkar safe da yamma. Daga bisani ta kira wayar Amrah wadanda basu jima sosai da isa Kano ba. Nan ma dai duk hirar suka yi. "Wannan kaɗai zai nunamaki ba karamin matsayi kike da shi a wurin Mijinki ba. Sai ki zage damtse ki kwantar da hankalinsa a wannan gaɓa, kinsan ba karamin damuwa zai shiga a kwanakinnan ba." Wannan shi ne zancen Amrah, nan fa daga Rafee'ah ta kirata, sai Maman twins can kuma A'isha. Kowa mamakin jin abinda Hussein ya yiwa Hajiya Zeenatu ya ke yi, a gefe guda kuma ana tayata farin ciki don zama da Hajiya Zeenatu masifa ne. Don kanta ta gaji da wayar ta ce musu chajinta ya ƙare ta kashe. Miƙewa ta yi ta shiga daki, wanka ta ƙara yi, ta fito ta zauna gaban madubi ta na kallon fuskarta da ta mulmule ta kara kyau adalilin gyaran da ta sha. _*Ki shiryawa haɗuwarki da Uwargidana. Anan za ki gane so da kuma ƙiyayya.*_ Ta tuna kalaman Hussein, a hankali ta ci gaba da murza man a wuri guda na fatar hannunta. Kenan yana nufin ita ɗin ya ke so? Ita ce abar sonsa? A abinda ya faru, zallar ƙiyayya ta gani ya nunawa Zeenatu yayinda ita duk wani a wurin zai shaidi yana sonta. Wannan tunanin ya janyo ta sunne kai tana murmushi, murmushin da ya fito tun daga ƙasan ranta. A hankali ta ɗago kai ta dubi madubi, ba zato ta hangeshi tsaye jikin ƙofar ɗakin. Ta yi sauri ta kauda kai. Kasa motsi ta yi gaba ɗaya don ba halin ta miƙe sakamakon guntun tawul dake jikinta.   Tunaninta ma tun yaushe ya ke tsaye a kanta. A hankali kuma ta ga ya juya ya fita bai ce uffan ba. Ta dafe kirji gami da sauke ajiyar zuciya sannan a gaggauce ta mike bayan ta fesa abinda za ta fesa. Ko ba'a faɗa ba, mijinnata yana tattare da damuwar da ya ke buƙatar kulawarta. Ta gama gane irin ɗaukar da Hussein ya yi mata kamar yanda ta soma amanna da zancen soyayyar da ya ke magana bayan aure.  Riga da siket ta sanya na atamfa, ta yi ɗaurinta tsaf sannan ta fesa turare ta fita gabanta na faɗuwa. Fatanta Allah Yasa ya huce. Koda ta fito ana kiraye-kirayen sallah, har a sannan ba ta samu tsarki ba. Ba ya falon amma ya ajiye wayoyinsa da agogo, wannan ya sa ta fahimci alwala ya shiga don haka itama sai ta koma ɗaki don kunya ta ke ji ya fahimci halin da ta ke ciki. Tana ji sadda ya fice daga falon sannan ta fito. Mintuna kaɗan bayan idar da sallah sai ga Hafsat tare da Kausar. Fatima ta ruga a guje ta rungumeta yayinda Hafsat ta karasa ta ajiye kwandon abincin hannunta saman tebur. Zama suka yi aka gaisa. Nan kuma aka shiga maida zance. "Nifa Adda Amal ba wanda ya bani mamaki sama da Kawu. Wallahi ban san rashin kaunar da yake yiwa iyayenmu da mu ya kai girman hakan ba. Ai shiyasa yau nima na rama a kan ɗansa, ya kirani har ya gaji ban ɗaga ba, karshe ma na aikamasa da zazzafan saƙo. Rasheeda fa ki ga ta kasa zama ma a gidannan ta tafi gida Adda Fati saboda kunya da kuma bakin cikin abinda Babansu ya aikata. Anti Amarya ma wai mijin ya kira ta je can yana nemanta." "Toh ke Hafsat ai dole, amma bana goyon bayan ki wulakanta Tahir tunda ba shi ya yi maki ba. Asalima ke da bakinki kin faɗi irin zafin da ya ke ji na yanda Uban yake hana su zumunci da mu." Kausar ke maganar kafin ta maida hankali ga Ramlat. "Kinga shawarar da zan ba ki,wallahi ki tashi sosai ki riƙe mijinki hannu bibbiyu. Kar ki ga kin rabu da Hajiya Zeenatu ki ɗauka shikenan, ba ita kaɗai ce mayya me kwacen miji ba musamman ma a garinnan. Mijina gashinan har yau ban gama fidda ran watarana ba zai ƙaromin abokiyar zama ba don yanda ƴanmata da zaurawa ke farautarsa tamkar nama." Suka yi dariya. Kausar ta girgiza kai ta nuna Hafsat da yatsa. "Ba abin dariya ba ne, ke ai kin san komai. Ke za ki ba da labari, ko ƙawayenki na makaranta ba sai da na takamusu burki da zuwa gidana ba?" Dariyar dai Hafsat ta ƙara, ita kuwa Ramlat sai ta ɗan tsunduma tunani, wato dai bayan wani yaƙin akwai wani, amma bai kai wancan ba. Motsin bude kofarsa ce ta sanya su jan baki su yi shiru don ɗazun dama sun baro shi ya shiga bangaren Dada, tare  yake da AlHassan. Zama suka yi Hussein na mai kama hannun Fatima da ta yi tsalle ta faɗa jikinsa. Da wani murmushin samun nutsuwar zuci da gangar jiki adalilin nasiha da ban bakin da Gwaggonninsa suka yi mishi. Ramlat ta gaida AlHassan ya amsa fuska a sake. "Lafiya lau Amarsu, ya kwanan baƙunci?" Ta yi murmushi ba ta ce komai ba. Bai wani jima ba AlHassan din, bayan fitar su Kausar don ta je ta harhada kaya su tafi gida, ya ɗan yiwa Ramlat har ma da Gogan yar nasiha akan zamantakewa sannan ya yi musu sallama ya miƙe ya yi gaba.  Shima Hussein ya miƙe ya dubeta, duban shauki da kauna. "Ban mintuna kaɗan, zan je na dawo." Ta gyaɗa kai. "Allah Ya dawomin da kai lafiya." Ya ɗan tsaya ya dubeta na sakanni, kamar ya yi tsokana kawai kuma ya murmusa cike da jin dadin addu'ar ya fice. *** Kawu Modibbo gumi kawai ya ke sharcewa, labarin komai ya riskeshi daga bakin jama'a, hakan yasa don ya tabbatar ya umarci Anti Amarya da dawowa. A bakinta tana kuka cike da takaicinsa ta sanarmasa duk yanda aka yi ta kara da fadin. "Mece ce ribarka idan ka cutar da ɗan  ɗan uwanka? Abu ɗaya da wannan zuri'a ta yi maka da sunan laifi, ba za ka iya tunawa ba saboda babu shi. Babu dalilinsa. Ka ji tsoron Allah tun lokaci bai ƙuremaka ba, ka tuba ka je ka nemi gafararsu." Tana kaiwa nan ta bar shi da shi da Uwargidansa Hajiya Fatuma wacce ita kanta jikinta ya yi mugun sanyi. Ta san ba su kaunarsu saboda bakin cikin daukakar da suka samu, amma ba ta taɓa tsammanin mijinnata zai aikata wani abu makamancin wannan ba. Tambayoyi ne birjik a kwakwalwata na yanda akai ma ya san matar Hussein, har ta soma tunanin ko shi ne ya haɗa auren amma babu mai ba ta amsa, mai amsawar ba ya a hayyacinsa. Ta kara dubansa yanda ya ke faman sharce gumi sai ta kula har wani hawaye ya ke fitarwa, na nadama ne ko akasinsa, ba ta da masaniya.    "Ku harhaɗa kayanku, gobe za mu koma Kano." Ta bishi da kallo har ya shige ɗaki, ranta ya ɓaci, wato dai ba shi da niyyar aikata abinda Anti Amarya ta ce? Ta girgiza kai don ba ta jin zata ɗara ko nan da can ba tare da ta nemi gafarar Dada da yaranta ba na irin kiyayyar da ta musu kuma ta tara yaranta su nema su ma. ***   Misalin karfe goma na dare ya shigo gidan, a lokacin Ramlat har ta gaji da zaman jiransa ga yunwa. Ƴan Maiduguri sun shigo sun mata sallama kasancewar da Asuba za su tafi. Ta sha nasiha sosai sannan suka bar sashinta. Ta ƙarasa ta nufeshi da zummar karɓar ledojin hannunsa, hannunsu ya haɗu wuri guda, ta ji wani yarr, da sauri ta janye ta yi gaba zuwa cikin falon ta ajiye saman tebur. Shi kuwa dakinsa ya shige, har ta kammala jera kayan abincin da ruwa bai fito ba. Can kuma ba jimawa sai gashinan, daga shi sai jallabiyar maroon. Ko ba'a faɗa ba wanka ya yi don ƙamshi kawai ke tashi a jikinsa. Kauda kanta ta yi tana mamakin ma kunyarsa da ta ke ji, ta yarda dai mazan ma suna suka tara don Hussein wani kwarjini yake mata. Tana zuba abincin amma a jikinta ta ke jin ya cika ta da ido yana kallonta, gaba ɗaya sai ta rasa sukuni. Ta saci kallonsa, ita ɗin kuwa ya ke kallon babu ƙakƙautawa. Ta gama zubamishi ta ajiye a gabansa, tana shirin zuba nata ya damke hannunta. Kallonsa ta yi. Murmushi ya sakarmata. "Wannan ya yimin yawa. Zo mu ci tare." Ya fadi yana matso da kujera daf da shi. "Seat." Ya fadi a hankali yana dubanta ƙasa-ƙasa. Ba musu ta zagayo ta zauna, ganin jikinsu na gogar juna ne yasa ta yunkurin ja da baya, hannu ya sa da sauri ya saƙalo ƙugun. "Why?" Ya furta kamar mai raɗa a saitin kunnen. Ta yi ƙasa da kai ba ta ce uffan ba. Ganin haka ya saketa ya soma cin abincin yana haɗawa da sanyamata a baki. Ramlat dai ta ga ta kanta, duk wannan yunƙurin da alwashin da ta ci sai ta neme su ta rasa. Ita har wani shakka-shakkarsa ma ta ji tana yi. Bayan sun ci ya ba ta umarnin ɗauko ledojin da ya shigo da su, ta bude, kaza ce sai lemuka. Ya ja plate ya ajiye, nan ta bude kazar ta zuba, lemukan  kuwa ta kai firij don akwai wani a ajiye. Koda ta dawo nan ma ya dage sai dai ya ba ta, ta gaji da wannan abin don haka ta ɗan yi kicin-kicin da fuska. Murmushi ya yi.   "Oh, ashe fa kin ce ba zaman da ki ka shirya yi da ni ba kenan ko? Sorry." Ta ɗan harareshi da wasa, ya shafi fuskar. "Ko me kika yi, kyau ya ke min." Haka suka ƙarasa ci yana ta jan ta da hira. Falon ya koma ya zauna bayan ya wanke hannu ya kuma rage hasken fitilu. Ta kammala gyara wurin, sauran abincin ta sanya a firij. Niyyarta ta shige ɗaki ta kwanta amma kaifin idanunsa ya hana ta aikata hakan, dole ta dawo ta zauna. Hankalinta ya rabu biyu, tana kallon talabijin, yayinda Hussein ke afkin kallonta. Ta gaji ta juyo fuskarta na nuna alamun gajiya.  "Me nayi don Allah?" Yanda ta marairaice sai ta sanya shi ƴar dariya. Hannu ya miƙamata. Ɗan harararsa ta yi. "Gulma ce fa ba na so Heart." Ta basar. "Wace gulma kuma?" Hannunta ya kamo ya murza cikinnasa. "Har yanzu ba ki tabbatar da babu ƙiyayya tsakanina da ke ba? To a tunaninki tun ma farko, don me na aureki?" Ta rasa amsar ba shi, ita dai gani ta ke kawai rainin hankali ne yasa shi aurenta. Yanzu kuwa ya gama wanke kansa. "Tunanin me kike ne? Na shayar da ke mamaki ko?  Ni yanzu damuwata kamar ma ke ce ba kya sona." Ta kalleshi, ya wani yamutse fuska shi a dole damuwa. Hannunta ya kai saman fuskarsa. Ta lumshe idanu sadda ya shafa tun daga sumarsa har ya gangaro saman karan hancinsa, yana tafiyar da hannun tana jin wani zuum a gangar jikinta. Hannunta ta ke kokarin ɗaukewa amma ba ta da wannan kuzarin. Tana ji ya maida yatsunta bakinsa, ya bi su ɗaya bayan ɗaya ya sumbata. "Faɗamin meyasa ba kya sona? Tsakani da Allah nasan muna da kyau. Haka Allah Ya haliccemu kuma mun godemasa. Ba fa yabon kai ba." Ta maze ta yi gyaran murya kafin ta amsa. "Ka ɗauka kyau shi ke sanyawa a so mutum?" Ya shafi sumar kai yana murmushi da dubanta idanun a lumshe kamar mai gyangyaɗi. "Kin ɗauka bansan rashin ra'ayin hakan ne ya bambanta ki da sauran matan da ke sona ba?" Baki buɗe ta ke kallonsa don ita mamaki ma ya ba ta. Ya yi ƴar dariya ya gyara zama sosai ya fuskanci talabijin ya matso gareta sosai. Daga yanayin nutsuwarsa ta fahimci ko me yake shirin cewa mai ma'ana ne. I just published "BABI NA SITTIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1023106863?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=bdvKCKOC3LLp5bowO1ooPkj4NyQWwtoNnAonSsHZp24WzPeGm2lKyYgVyvV%2Bh9gt6e1Oc%2BZqkJMVkFlQ2xAQQ3P60IL2qqoNgqvumrfhTuosHta7gVySLHczdgg1%2Fq97 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 61) "A rayuwata, kar ki yi mamakin cewa ban taɓa soyayya ba. Ban yi ba tun ma kafin zuwan Zeenat, balle a bayanta." Ta dubeshi, dama idanunsa na kanta, sai ya yi murmushi ya riƙo hannunta ya damƙe cikin nasa yana murzawa a hankali kafin ya ɗora. "Sadda Allah Ya soma haɗa ni da ke, mun haɗu ne lokacin bana cikin nutsuwata sakamakon ɓacin ran wata hatsaniya da muka yi da Zeenat, ban ji komai a kanki ba sai sadda na ƙara cin karo da ke a ma'aikatar Revenue da muka je tax payment. A hankali a hankali haɗuwarmu kan zo akai - akai, tun bana daukarki da wani muhimmanci har ban san yanda aka yi na soma kula da lamuranki ba. Na soma jinki kamar wata ƴar uwata. Ba ki ƙara burgeni ba sai haɗuwarmu a A&Z da kika nunawa duniya da ma Zeenat, akwai soyayya tsakaninmu. Duk a matan da suke bibiyata da sunan so, babu wacce ta taɓa rainawa Zeenat hankali kamar ke." Suka yi murmushin tuna ranar kafin ya ɗora. "Tun daga wannan ranar na ji ina son kusancinnamu ya fi haka, na dinga hasashen da ace gaskiya ne muna soyayyar ya kenan? Wane yunƙuri Zeenat za ta yi? Duk fa da cewar a sannan ina ɗan shakkarta, hakan bai hana ni tunaninki ba. Dangantakarku da Hisham ya ƙara ƙarfin shaƙuwarmu. Da tafiya ta yi tafiya, na fahimci ba wai kawai burgeni kike ba, kaunarki nake dagaske. Akwai ranar  da na ji Zeenat na waya da  Chairman  tana kyakyata dariyar mugunta. Maganarki suke yi akan ya ci gaba da yin duk yanda zai yi ya aureki, za ta ba shi kyauta ta musamman idan hakan ta kasance. A lokacin har jaddada masa ta dinga yi kan ya yi amfani da masu gidan rana, sai kuma ga Hisham ya zo min da batun aurenki da Chairman. Bayan tsananin kishin da naji yana neman zautar da ni, sai na dinga ayyanawa a zuciyata ashe dagaske ƙarfin dukiya na saurin rinjayar zuƙata. Ban yi zaton kina daga cikin kwaɗayayyun mata ba, sai gashinan lokaci guda kin ban mamaki. Daga lokacin kuma tunanina ya sauya a kanki." Ramlat jin haka ta bude baki za ta yi magana ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗora yatsansa ba bakin. Murya a tausashe ya ce. "Yi shiru please, labari ne fa nake ba ki, ki bari na kai ƙarshe." Ta gyaɗa kai sai dai tuni idanunta sun cicciko, ta kasa kunne tana sauraronsa. "Baki ba zai iya misalta maki ɗumbin damuwar da zancen aurenki da mutuminnan ya jefa ni ba. Na rasa walwalata, ke kaɗai nake ganin za ki mayemin gurbin ƴan uwana da ban san su ba, ina da su ko bani da su, ba zan tuna ba. Sai gashinan lokaci guda wani can zai rushemin hakan. A sannan har kwanciya nayi a asibiti, aka tabbatar da cewa damuwa ce. Na rage tunani. Bayan na farfaɗo na kasa samun sukuni da walwala, ban yi ƙasa a gwuiwa ba sai da na nemi gidan Baba Dakta, naje a matsayin manemin aurenki." Da mamaki ta tsuramasa idanu baki a sake, hawayen da ta ke dannewa tun ɗazun suka zubo. Ya yi murmushi gami da sa yatsa ya sharemata. "Kar ki yi mamakin ta yanda aka yi na san Baba Dakta. A hirarrakin da mukan yi da Hisham, yakan sanyamin  shi a ciki don ya cemin ma a wurinsa ya soma neman auren Aisha kafin ya sada shi da Kawunnanku. Yanda na fahimta, banda ma makwafci kuma  amini ga mahaifinku, kun daukeshi tamkar mahaifin. Kuna girmamashi sosai kamar yanda ya ke kula da ku. Sau ɗaya na taɓa yiwa Hisham rakiya gidansa, a wata ziyarar gaisuwar Juma'a da ya yi. Yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa nake ganin girman Hisham, mutum ne mai son sada zumunci musamman ranakun juma'a, wataran yakan ɗauke ni muje tare, wataran kuwa shi da matarsa suke zuwa. Wasu lokutan kuma uzuri kan hana ni zuwa. Ko Hisham bai san na je gidan Baba Dakta ba, ya sa aka kai ni falon saukar baƙi, daga bisani ya fito muka gaisa. Na yi mamaki sosai da ya shaida ni alhalin sau ɗaya muka ga juna. Bayan mun gaisa sai na rasa ta inda zan fara, karshe ya dube ni da kyau ya ce na saki jiki da shi, na daukeshi kamar Uba, kar nayi shakkar komai na fadamasa meke tafe da ni. Wannan yasa nan take na ji kaunar mutumin nan. Zuciyata ta samu nutsuwa na fayyacemasa cewa na zo neman iznin aurenki ne. Ya gama saurarona, a karshe har ya yimin tambayar ko dama muna soyayya da sauransu. Duka na ba shi labarin gaskiyar yanayin alaƙata da ke. A karshe ya yimin yar nasiha game da hakuri da kuma fawwalawa Ubangiji komai, ya sanarmin cewa an riga da an yi maki miji don magana yanzu ma ta je ga Kawunnanki kuma sun karɓi mijinnaki da hannu bibbiyu. Ya bani hakuri ya kuma ce na ci gaba da addu'a duk abinda Allah Ya yi na sa a raina shi ne mafi alheri. Ba haka na so ba, amma na ji sauƙi daga radadin da naji akan batun an miki miji da farko saboda Baba Dakta mutum ne wanda ya iya kalamai masu nutsar da zuciya da kwakwalwa. Anan ne na nemi alfarma a wajensa kan yanda muka yi maganar ya zama tsakanin ni da shi. Murmushi ya yi ya nunamin kar na sami damuwa." Ramlat kallon Hussein kawai ta ke yi, so da kaunarsa na ƙara samun matsuguni a kwakwalwarta da ma dukkan wasu sassa na jikinta. Shima idanun ya ƙuramata na sakanni kafin a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ɗan murza hannunta ya ɗora. "Ramlat, na ci wuya a ƴan tsakaninnan, daga lokacin da na gane ina matuƙar sonki har zuwa sadda ake rikice-rikicen aurenki da Chairman. Ban ƙara samun walwalwa ba. Komai kika ga ina yi maki wala da farin ciki ko akasinsa, kawai yi nake. Idan na yi tunanin zan rasa ki sai na ji hatta da ke din ma haushinki nake ji. Babban dalilin da ya hana na kasa faɗamaki a lokacin, ban gama haƙiƙancewa kina sona din ba ne ko kuwa kawai tausayina kike. Sannan ni mutum ne mai burin duk matar da nake so, na nunamata son a aikace. Ya fi armashi akan mu tsaya muna ta maida martanin kalamai ta waya da zahiri. Ke yanzu abin ma bai fi burgeki ba?" Ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya ɗora zancen. "Kinsan wani abu? Nayi mamaki iyaka da na ji labarin ke ce silar haɗuwata da ɗan uwana, mamaki bai ƙara kashe ni ba sai da na ji labarin a sanadiyyata aka harbe ki. Sosai abin fa ya taɓa ni ya dakarmin zuciya. Wannan ne yasa na ƙara ƙullatar Zeenat. A lokacin kuma na kara ji a jikina babu wani abu da zan iya sakamaki duk wata sadaukarwa da ki ka yi gareni face na maidaki karshen ikona kuma mallakina. A bakin Hisham na soma jin labarin duk wani faɗi tashi da ki ka yi kafin aurenki da Hilal, har ma bayan aurenki da Aliyu. Kinsan me? Sai na tsinci kaina da wani mugun farin ciki, tausayi da ma soyayyarki a zuciyata, amma ban nunawa Hisham ba asalima haushi na dinga ba shi har ya yi fushi ni kuwa na haye mota na wuce na yi maki siyayya na dawo. Bana duba Ramlat, amma a lokacin haka kawai na dinga ji a raina da yardar Allah za ki zama mallakina. Musamman da Hisham ya ba ni tabbacin ba kya son Chairman kuma su Hajiya ma ba sonsa su ke yi ba. Abin dai daga Kawunnanki ne. Wannan ne ya sanya ni cikin annashuwa. Kinga wancan aurennaki, ke ki ka yi kiɗa da rawarki, wannan karon kuwa tunda har yan uwanki ma ba sa ta Chairman, to fa abun zai zo da sauki. Na ci gaba da addu'a da miƙawa Ubangiji kukana har zuwa lokacin da na ji labarin fasa aurenki da Chairman. Sai kuma ga wanj Baban Hanif na neman yimin shigar sauri. Sai dai ban sha wahala da shi ba saboda takanas Baba Dakta ya neme ni ta waya lokacin muna Adamawa ya ce idan har dagaske nake to shi kam hankalinsa ya fi nutsuwa da ni, bai kuma tunkareni ba sai da ya ji ta bakin Hajiyarmu. Bai fadamin dalilin da yasa aka bar maganar Baban Hanif ba, ya dai bani damar na turo magabatana tunda har kin bar masa wuƙa da nama, to shi kuma ya zaɓamaki ni a matsayin mijin aure. Na ji dadin lamarin sosai. Anan ne muka yi shawara da iyayena, ba ɓata lokaci muka taho Kano tare da ɗan uwana da Kawu Adamu. Aka shige gaba aka yi duk abinda ya dace. Kin ji dukkan abinda ya faru." Ta gyada kai tana murmushi, ya saki hannunta ya miƙe, kayan kallo ya shiga kashewa kafin ta ga ya soma rage fitilun falon bayan ya tabbatar kofar falon a rufe ta ke gam! Ganin haka sai ta mike ta tayashi da rufe kofar fita na kicin da kuma kashe fitilun da rufe kofar kicin din gaba ɗaya. Koda ta juyo sai suka ci karo, ya yi saurin riƙota. Goshinsu haɗe wuri guda kowannensu na maida numfashi, za ta zame ya yi saurin riƙeta da kyau. A hankali kuma ya ja baya. "Ban gama ba ki labari ba, ki yi shirin kwanciya ki zo, ina jiranki." Daga haka ya yi gaba tana kallo ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya shiga. Ta sauke ajiyar zuciya, ba ta daina murmushi ba kamar yanda ba ta gaji da jin wannan daddaɗan labarin da ya ke ba ta ba. Ta tuna Kawu Bello da ya ce dama Hussein din ya taɓa neman aurenta wurin Baba Dakta bai samu ba sai a wannan karon. Da wannan tunanin cike da wata iriyar kasala ta ƙarasa ɗakinta. Sai da ta ƙara wanka don ƙamshin da ta ji Hussein yana yi sai ta ke ji kamar ita banda wari ba abinda ke fita daga jikinta. Loko da saƙo duka sai da ta bi ta wanke kafin kuma ta fito ta goge jiki ta shiga mulka turaruka masu kamshi kala-kala. A ƙarshe ta fiddo wata doguwar riga mai hawa farare ƙal ta sanya, ta ɗora hula da ya rufemata gashinta. Duban kanta ta ke yi a madubi, rigar ta ciki da kaɗan ta wuce gwuiwarta sai top din da ta ketare zuwa ƙaurinta. Girgiza kai ta yi, a haka ma kwarjini Hussein ke mata ina ga kuma ta isa gabansa a haka? Da saurinta ta karasa wardrobe ta fiddo zani. Ido ta fiddo waje kirjinta ya harba jin hannuwansa zagaye a ƙugunta. "Kin yi kyau, shi ne ki ke kokarin rufemin abinda Allah Ya halarta min gani?" Ta lumshe idanu, kunya sosai ta ke ji, ta kasa kataɓus. Juyo da ita ya yi suka fuskanci juna. Har lokacin ta kasa buɗe idanun. Kallon fuskarta kawai ya ke yi yana jin sanyi a zuciyarsa. A ƙasan ransa banda hamdala babu abinda ya ke yiwa Ubangijinsa. Jin shirun ya yi yawa ne ta bude idanunta ta dubeshi. Ganin idanunsa har sannan a kanta suke sai ta yi azamar ja baya ta cire jikinta daga nashi.   "Ki yi alwala." Ya juya ya koma ɗakinsa, ta sauke ajiyar zuciya. Hussein zai kasheta da kala-kalan soyayyarsa. Jikinta ya yi sanyi da ta tuna ba ta da sallah, daga yanayin Hussein ba sauki. Sai kawai ta ji ya ba ta tausayi. Ta kashe fitilu ta rufe kofar, tana tafe tana tuna aurenta da Aliyu, ranar da aka kawota sam ba ta da walwala ko misƙala zarra, wannan karon kam Allah kadai Yasan yanda ta ke jin zuciyarta musamman idan ta tuna yan uwanta da ma abokan arziki duk suna son aurenta da Hussein. Wannan ma abin ta ƙara godewa Allah ne. Fatanta Allah Ya basu zaman lafiya da iyali nagari. Yana saman darduma, ga dukkan alamu sallah ya idar, ba ta shiga dakin ba tun da aka kawo ta sai lokacin. Sosai ya burgeta. Dardumar da ta ga ya shimfida sai ma ya ba ta dariya ta danne. Ganin ta koma gefen gado ta zauna ya sanya bayan kammala addu'arsa ya dubeta. "Sallah fa?" Ta kalleshi ta sunkuyar da kai, daga yanayinta ya gane cewa ba maganarsa. Don haka ya mike kawai ya yi nafilarsa ya yi addua, tare suka shafa ya miƙe. "Taho mu kwanta na ƙarasa ba ki labari." Yana fadin hakan ne yana nufar makunnin fitilun dakin, kashesu ya yi gami da kai hannu ya kunna na gefen gadon. Hasken ba yawa, kwanciya ya wuce zai yi kai tsaye. "Ɗan tsaya."  Ta dakatar da shi, ya ja ya tsaya kawai yana kallonta. Abin rufar ta ja ta kakkaɓe gadon ta gyara zaman filon kafin ta dube shi da murmushi. "Bismillah." Ya kwanta itama ta kwanta, fitilar ya kashe. Ɗakin ya yi shiru na wani lokaci, numfashinsu na gauraya wuri guda kowanne na shaƙar daddaɗan ƙamshin jikin ɗan uwansa. Ya kai hannu ya zame hular kanta, yana shafa kitsonta, ta lumshe idanu. Ya soma magana. "Heart, kin yi zaton ba sonki nake ba, kamar ma dai kawai zan aureki ne. Ba ki san cewa Hussein ya soma sonki tun kan ki soma sonsa ba." Duk da cewa babu haske sai da ta zaro ido. Kunya ta sanya ta runtse idanunta. Dama ya san tana sonsa? Shi kuwa jin ta yi shiru sai ya kai hannu saman fuskarta, murmushi ya yi mai sauti. "Kar fa ki yi mamaki, na sani. Sai dai ba karamin nishaɗantuwa na dinga yi idan naga kin yi narai-narai kina son yin kuka duk a tunaninki na bana sonki. Sai Hisham wanda yake sanya ni nishaɗi idan ya sauya fuska yana tayaki yaƙi. Kuma yasan sarai ina sonki amma na nunamasa nifa a'a." Hannunta ya kai saman kirjinsa. Ta nutsu tana jin yanda ya ke bugu da ƙarfi. "Kamar yanda kike jin zuciyata na bugawa a kowane daƙiƙa, wallahi Ramlat haka nake jin sonki a kowane dakika. Kwakwalwata ba ta taɓa samun hutu daga tunaninki ba, kar ki ƙara ji a ranki cewa zaman doya da manja zamu yi. Kar ki ƙara sanya wa a ranki wannan bawan Allahn ba ya sonki. Kinji?" "Uhm." Ta faɗi a hankali, hakan yasa shi janyota ba shiri ya shiga aikamata saƙonnin da suka birkita tunaninta har ta shagala itama wurin maida martani. Nan fa ta ruɗa Hussein, ita kuwa shawarwarin yayyunta da su Amrah ke yawo a  kwakwalwarta. _*"Kar ki wasa da kowacce dama, kar fa ki manta Hussein bai san soyayya ba sai a kanki. Don haka ki saki jikinki ki rike mijinki da hannu bibbiyu."*_ Ta tuno kalaman Maman Twins. ***   WASHEGARI.... Tana jin sadda ya maida kanta saman filo madadin a farko da yake a saman kirjinsa, ya gyaramata ya ƙara rufe ta da tattausan bargon sannan ya miƙe. Murmushi ta yi ta buɗe idanu, banɗaki ya buɗe ya shiga, nan ya fahimci Asuba ce. Ta kai hannu a hankali ta shafi makwancinsa, so da kaunarsa marar adadi na kara ninkuwa a zuciya da gangar jikinta. Idan ta tuna manyan kalamai da kuma yanayin ruɗewar da ya yi duk a kanta, Hussein kuka na hawaye ne kawai bai mata ba, ya yi wani furucin da dole ya ba ta tausayi a sannan wato inama a kanta ya soma aure. Jin motsin fitowarsa bai sa ta rufe idanunta ba saboda fitilun ɗakin a kashe suke. Ganin yana laluben makunni yasa ta saurin rufe idon. Kimtsawa ya yi ya fice masallaci a gaggauce don ya so ya makara. Tana jin fitarsa ta kunne bedside lamp ta mike zaune rungume da bargo, murmushi take kamar wata sabuwar kamu, ta gaji da murmusawar ta koma ta kwanta bayan ta kashe fitilar.  Har Hussein ya dawo ya hau gadon ya jawota jiki, idanunta ƙirr. A hankali kuma wani sabon daddaɗan bacci ya soma fisgarta. Ita ta riga shi farkawa wuraren karfe bakwai da rabi na safe, miƙewa ta yi ta nufi dakinta. Kai tsaye brush ta soma sannan ta faɗa wanka tana ji kamar an mata albishir da gidan Aljanna. Ba ta da wani sauran buri mai yawa a yanzu face na ta kyautatawa mijinta hakanan da addu'ar Allah Ya rayamata yaranta, Ya ja kwanan Hajiyarta mai sonta. Koda ta fito shiryawa ta yi cikin doguwar rigar atamfar da ta matse daga sama, ƙasan kuwa ya buɗe amma ba sosai ba. Ta yi kyau musamman ma kwalliyar da ta yiwa fuskarta. Sai da ta shafa turare a gaggauce kafin ta fito da zummar shiga kicin. Sai dai ƙarar wayarta ya katse hanzarinta, ganin sunan Hafsat ta ɗaga. Suka gaisa. "Dama kira nayi na ji ko kun tashi. Ganinan zan kawomaku abin kari." "Toh Hafsat, sai kin karaso." Daga haka ta ajiye wayar, ba jimawa aka kwankwasa ƙofar. Buɗewa kawai ta yi don ta san Hafsat ce. Suka yiwa juna murmushi. Ta karaso ta ajiye kayan hannunta saman tebur. Duk yanda ta so akan ta tsaya su yi ƴar hira amma ina ta ƙi. "Rufamin asiri Adda Amal, zan dawo anjima dai in sha Allahu. Ban shiryawa faɗan Hamma Hussein ba." Dariya ma ta ba Ramlat, suka yi sallama ta tafi. Ciki ta koma don ta ga ko ya farka. Tsaye ta iske shi daga shi sai gajeran wando sai kuwa tawul yana faman goge sumar kansa. Sunkuyar da kai ta yi gami da kokarin fita. Caraf ya damƙo hannunta. "Dodo na zama?" Ta girgiza kai tana murmushi ba tare data juyo ba. Dawo da ita baya ya yi, ta kasa kallonsa. Karshe ta wayance da gaidashi. Maimakon ya amsa sai ya sumbaci kuncinta. "Kin yi kyau sosai." "Na gode." Ta furta a hankali. "Tunda ba za'a taya ni ba, a zauna a jira na kammala." Ba musu ta karasa gefen gadon ta zauna, ganin ya juyamata baya yana kallon madubi yasa ta ɗago kai tana ƙarewa mijinta kallo da irin baiwa da ni'imar da Allah Ya mishi na kyawun sura. A fakaice yana kallonta, dariya ma ta dinga ba shi, satar kallon na mene alhalin shi ɗin nata ne halak malak? Har ya kammala da gaban madubin ya juyo bai bar murmushi ba, ganin ya juyo kuwa ta yi saurin kauda kai. Ƙananun kaya ya fiddo ya sanya. Ya koma gaban madubin ya fesa turare, a ranta ayyanawa take son ƙamshi irin na Hussein ko mace sai haka. Kafin ma ya tunkarota ta mike, suka dubi juna kowanne da abinda ya ke saƙawa a ransa. Ta sunkuyar da kai. "Barka da Asuba, fatan ka tashi lafiya?" Ya kama hannunta ya jawota ya sa a jikinsa sosai. "Lafiya na tashi, ina fatan kema haka?" Suka kwashi ƴan sakanni kafin ya hau yi mata raɗa a kunne, kunya ta sa ta tureshi tana murmushi. "Mene hakan wai?" Ta faɗi kamar za ta yi kuka. Ya taɓe baki. "Gulma ce bana so." Hararar wasa ta mishi ta juya da sauri ya kuwa bi bayanta yana fadin. "Ni kike wa wannan kallon?" Ganin dai kokarin cafketa ya ke yasa ta juyo tana dariya. "Don Allah ka yi hakuri, na tuba." Ya shafi sumar kansa kawai ya yi gaba zuwa tsakiyar falon. "Nan za ki kawomin mu ci, bana son can." Ta amsa da toh kafin ta yi gaba yana binta da kallo kamar za ta gudu ta bar shi. Sai da suka kammala karyawa tsaf sannan ya bata umarnin saka mayafi su je gaida Dada. Ɗakinta ta koma, dama ba nisa mayafin ya yi ba, ta gyara zamansa sosai ta zura flatshoe. Koda suka kama hanya, hannunta ya lalubo ya kama ya murza har sai da ta lumshe ido ba ta yarda ta kalleshi ba. Ɗan matsowa ya yi har kafaɗunsu na gogan juna. "Wai ni bakin tsiwar naki mutuwa ya yi? Ko na lalubo amsar a daren jiya?" Ta tsaya cak ta shiga kokarin zame hannunta a nashi, ya kara damƙewa yana dariya. "Wallahi sai na ɗaga ki cak mu shiga har wajen Dada. Kin san zan iya ko?" Dole ta hakura ganin akwai ma'aikata a farfajiyar gidan ta kuma tsorata don ta san halinsa dagasken yake. Dada ta yi farin ciki matuƙa da ganinsu, ita kuwa Ramlat wacce ta samu dakyar ya saki hannunta, kunya sosai ta ke ji don ma Allah Ya taimaka baƙi duk sun watse, wasu yau da Asuba suka wuce. Anan wurin Dadar ya bar ta ya fice wurin AlHassan. *** KANO... *DA SAURAN RINA A KABA..!* I just published "BABI NA SITTIN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1024183736?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=kerlmbTD11RJIZ1OU3cjRAuaKiLriOJD0fY0ly4CVNRLiEciXy1qh%2BgcHslN3fAHkmM%2BuxbSZlMyLFyekdT2BAKcap35wfLbDInDLU%2Bf6jBwfeAcG9qlXUARTAIfqHS%2B 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 62) *Assalamu alaikum masoya Karfen Kafa. Ina mai ba ku hakurin jinkirin da ake samu kafin posting. Ku yi hakuri pls. In sha Allah aski ya zo dab gaban goshi.* 🥰 Hajiya Batool ta zabga uban tagumi tana kallon Aminiyarta, ba ta san ta inda za ta fara magance mata matsalarta ba alhalin ita kanta yanzu cikinsa ta ke. Gaba daya ɗanta ya kwashi matarsa sun bar garin sun koma Abuja da zama. Waya ta kira sai ya ga dama yake ɗagawa balle a kai ga aike. Komai na rayuwa ya sauyamata, kasuwancin ya ja baya babu albarka ciki. Hajiya Zeenatu wacce ta gama kai wa bango da shirun Batool, ta kundumar ashar da faɗin. "Wannan wane irin wulakanci ne Batool, na kawomaki kukana ina neman mafita shi ne tsabar wulaƙanci ki ka shareni ki ka maida ni wata banza?! Hussein ne fa, kin fi kowa sanin yanda nake son Hussein amma har na gama ba ki labarin cin kashin da ya yimin gaban yan uwansa ki kasa  jajantamin?!" Tana maganar tana faɗa rai a ɓace. Hajiya Batool ta sauke ajiyar zuciya. "Me zan maki? Wane irin nusarwa ce ban maki ba don Allah? Amma ke makahon son yaron nan ya sanya ba kya ji ba kya gani, ai gashinan ya nunamaki shi na zamani ne!" Hajiya Zeenatu ta yi kwafa, ba abinda ya faɗomata a rai sai cin mutuncin da ya yi mata a farkon haɗuwarsu, da gaskiyar Batool da ta ce makahon so ya rufe idanunta. Ta sauke ajiyar zuciya. "Naji, koma me ya faru, ina da hannu a ciki. Amma kuma kin san ba zan zauna haka ba ko? Kin san sai na rama? Ki tashi mu shirya mu leka wurin Gora. Mene a ciki? Zan durkusa na ba shi hakurin laifin da na yi mishi idan ya so ya samarmana mafita." Hajiya Batool ta yi shiru, itama fa yanzun tana da bukatar hanyar da za ta bi a karkato da hankalin ɗanta gareta, ta kuma amince idan ya dawo ko wacece ya aura idan har hakan zai yiwa Fa'iza ciwo. Abinda ma ta lura da shi, itama kanta Fa'iza tama tsubbace-tsubbacenta shi ne dalilin da yasa ta fi karfinta. Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta tuna kowacece Fa'iza, dama tun can ƴan  gidansu ba wata cikakkiyar tarbiyya ce da su ba, ganin irin arzikin da ubanta ke da shi matsayinsa na tsohon minista ya sanya tun ɗanta bai wani ba soyayyar da Fa'izar ke mishi muhimmanci ba, har sai da ta yi yanda ta yi ta tursasashi. Yanzun gashinan tana girbar abinda ta shuka. "Na yarda muje. Idan ma bai sauraremu ba, za yiwa Mariama waya mu wuce Nijar kawai. Na fi yarda da aikin buzayennan ma." Da wannan suka shirya suka fice wurin Gora. *** ADAMAWA.. Dada ta dubi Ramlat cikin nutsuwa ta ce. "Kinga abin Allah ko? Ba ya kyale azzalumi, shiyasa duk abinda aka dage da kai kuka gareShi, watarana zai shuɗe ya zama tarihi. Ba wanda ya fi ban mamaki a lamarin sai ɗan uwana Modibbo, ban yi tsammanin ƙiyayyar ta kai har haka ba, amma ina nan inda nake, shiru ma magana ce. Allah ne zai maganinsa don nikam ban isa nayi ba. Ba na jin wannan karon zan iya yafemishi wannan zaluncin da ya yimin ni da yarana. Duk yanda zan so na ji alaƙarsa da matarnan, zan jira har zuwa lokacin da zai kawo kansa garemu." Hafsat da ke zaune itama sai ta ji jikinta ya kara sanyi, wayarta ta kara kalla, wani saƙon ne na Taheer ya kara faɗowa, duka dai ban hakuri ne da nuni da yake mata cewar laifin wani ba ya shafar wani. Kalaman soyayya zafafa ya ke jifanta da su, ta yarda so ba karya ba ne, tana son Taheer sosai, duk da son ta ke mishi bai kai wanda shi ya ke mata ba, amma dole za ta sanyawa zuciyarta dangana. Ta san babu ta yanda aurensu zai yiwu. A hankali ta mike ta zame daga falon ta shige ɗaki, hawaye ne ya tahomata sai dai dole ta haɗiyeshi. A yanda ta ke da zafi, ba ta yi zaton soyayyar Taheer zai russunar da ita har haka ba har ma ta ji inama ɗan wani gidan ne daban ba gidan Kawun ba. Ɓangaren Ramlat itama haka ta koma sashinta cike da tunane-tunane, ta kara ganin girma da ƙimar uwar mijinnata. Tabbas mahakurci mawadaci. Kai tsaye ta shiga gyaran duk inda bai ba ta ba, sai da ta tabbatar gidan ya kimtsu babu sauran dauɗa da kayan datti a kicin sannan ta kara gyara jikinta ta shirya cikin doguwar riga ƴar kanti milk mai adon duwatsu. Sam ba shi da nauyi. Ta feshe ko'ina na jikinta da turare. Saman doguwar kujera ta shimfide ta zurawa ƙaton enlargement na hoton mijinta idanu. Murmushi sosai ta shiga yi tana tuna kalamansa da ma saƙonni da dama waɗanda ya isarmata a daren jiya. A hankali ta lumshe idanunta wani farin ciki na mamayeta, wani lokacin ta kan ji kamar mafarki, wai yau ita ce a garin masoyinta kuma matsayin matarsa. Ta jima cikin tunani kafin wani bacci mai dadi ya kwasheta. Ya jima da shigowa gidan, sai dai yana sashen Dada su na tattauna. Koda ya karaso gidan, ya isketa tana bacci murmushi kawai ya yi, ciki ya karasa ya rage suturar jikinsa ya ɗan watsa ruwa don ba laifi garin ana ɗan zafi. Gajeran wando three-quarter ya sanya da yar shirt marar hannu, gaba daya ƙirarsa ta bayyana muraran.  Koda ya fito ya ci karo da Hafsat da ke faman sallama amma gwanartasa ba ta ji ba. Kofar ya bude ya sanya yatsa a bakinsa yana mata alamar ta yi shiru, murmushi kawai Hafsat ta yi hango dalilin, Adda Amal ke bacci. Hanya ya ba ta ta karasa kan tebur ta ajiye kwandon abincin ta juya ta fice ya rufe ƙofar a hankali. Cikin falon ya dawo ya zauna saman kujerar da ke fuskantarta, waya ya ke amsawa da Hisham sai dai rabin hankalinnasa yana ga Ramlatun yayinda ya ke kallon sauka da hawan numfashinta. Harma da yanda rigar ta fiddo surarta fa yi mata kyau.  Wani lokacin kuma ya maida kai ga ƙawatacciyar fuskarta da kallon ke sanya shi nishaɗi. A jikinta ta ji ana kallonta, a hankali ta soma kikkifta idanu kafin ta budesu kaɗan, ganinsa zaune yana kallonta ya sa ta ware duka dara-daran idanun kafin ta mike zaune ba shiri. Kunya ta sa ta mikewa sum-sum don ta shiga ɗaki ta ƙara wanko bakinta, sai dai tana zuwa gefensa ya yi azamar riƙota ta faɗo cinyarsa ta zaune ɗabas. Ta sunkuyar da kai yayinda shi kuwa wayar yake amsawa amma hannunsa guda ya kasa tsayuwa wuri guda, karshe ma zancen kasa fita ya yi yanda ya dace sakamakon fuskarsa da ya tura a ƙasan wuyanta yana shaƙar ƙamshin jikinta. Hisham ko fahimta ya yi ko mene? Kawai sai ji ya yi wayar ta ɗauke don haka ya kalli wayar sai kuma ya ajiye a gefe yana murmushi, ita kuwa Ramlat da gaba ɗaya ta rufe idanunta numfashinta na hawa da sauka da sauri, ta kara yunkurin miƙewa. Ya riketa sosai. "Wai ina za ki je? Ba ki yi missing ɗina ba." Kai ta girgiza ta kasa magana. Ya bi bakin da kallo kafin ya dubi idanu da ta bude a yanzun. "Kin daina magana ko me? Wani abu ki ke ci?" Ya maida dubansa ga bakin da take ƙara damtsewa. Girgiza kai ta yi alamar aa, tana kokarin tashi sai ya ƙara riketa ya yi murmushi. "Oh na fahimta, wato daga bacci kika tashi ba kya son ki yi magana naji wari ko?" Kunya da takaicinsa ta ji har ba ta san sadda ta watsamasa harara ba. Ya kara murmusawa. "Na nawa kuma?" Ta waro ido. "Me kake nufi?" Ba ta san sadda ta yi furucin ba sai kuma ta yi saurin rufe bakin ta mike a guje ta yi daki ta bar Hussein da yi mata dariya. Koda ta wanke baki da fuskar sai kunya ta hanata fitowa falon, ta samu gefen gado ta zauna ta na mai jin haushin kanta. Yanzu dariyar ma da ya yi watakila don ya shaƙi warin bakinta ne. Tana nan zaune ya shigo, fuska ta ɗan haɗe ita a dole kar ya yi mata dariya. Hannu ya miƙamata yana murmushi. Ta kasa miƙamasa nata, sai shi ne ya gaji ya ja kamo hannunta ya miƙar da ita ta faɗo jikinsa har tana take masa kafafu da lausassun tafukan kafafunta. Goshinsu haɗe wuri guda, ta kankame rigarsa don ji ta ke kamar za su zube. "Ko ba ki wanke ba ni ban ji komai ba." "Uhmm."Abinda ta ce kenan, amma ita dai ta san ko yaya mutum ya yi bacci to fa sai a hankali. "Wai idan na riƙe ki me kike ji? Sai naga kina kanne idanu." Wayyo kunya, ta buɗe idanun tarr ta dubeshi da harara, murmushi ya yi don dama kwayoyin idanun yake son gani. "Kai ka ga haka." Daga nan ta zame jikinta ta yi falon ya bi ta a baya. Haushin kanta ma ta ji. Tana zama ya zauna a gefenta, ta matsa, ya matso. Ta dubeshi, ya sakarmata murmushi. Kafin ta yi yunkurin mikewa ya kamata sosai, ya shiga aikamata da sakonni daban-daban wanda dolenta ta russuna. Sai da ya gaji don kansa ya matseta a jikinsa yana maida numfashi. Lalubo kunnenta ya yi bayan ya zagayeshi da harshensa ya shiga yi mata magana a tausashe. "Na fi ki mance kaina idan muna tare. Na fi ki rawar jiki da mazari. Kar ki damu da duk abinda Hussein ya fadi ko kuma zai fada, haka nake, ina son tsokana ko don na yi dariya. Ina sonki sosai, ina kaunarki." Murmushi tayi kafin ta kara shigewa jikinsa, ya kuwa ba ta kyakkyawan mazauni. Sun ɗan jima a haka kafin su mike zaune. "Yunwa fa nake ji." Ya fadi, ta mike, ita kanta yunwar ta ke ji don tuni abincin safe ya narke. Sai da ta soma zuba mishi, tana kokarin zuba wani ya hanata. "Ba fa na son muna raba plate. Ki fahimta please." Ta gyada kai. "Zan kiyaye." Daga nan ta dauki cokali ta matsa suka soma ci. Bayan sun kammala ta tattare komai ta kai inda ya dace. Koda ta dawo shi tuni ya yi daki, alwalar sallar la'asar ya yi. Ya dube ta. "Bari na wuce masallaci." Ta amsa da toh da yi mishi kyakkyawan addu'a sannan ya fice ita kuma ta kara miƙe ƙafa don har sannan ba ta samu tsarki ba. Ta sani sai a gobe za ta samu don ita mutum ce mai ƙidaya kwanakin al'adarta. Hakan na taimakawa kwarai wajen sanin lokacin farawa da kammalawa na kowane wata. Wannan yasa a wayarta ta ke da App mai suna FLO, tana lissafe da kwanakin farawa da kammalawar period dinta. Tana nan zaune ya shigo amma fuskarsa ba kamar yanda ya fita ba, gaba daya a ɗaure. Ya karaso ya zauna  bai ko kalleta ba. Ta ji gabanta ya fadi. "Sannu da dawowa." Kai kawai ya gyadamata, hakan ya ba ta tabbacin ba lafiya ba. Shi kuwa a hanyar dawowarsa ce ya biya wurin Dada, Hafsat ya tarar kadai a falon tana amsa wayar Taheer har tana ba shi shawarar ya gwada zuwa neman aurenta hannun yayyunnata. Wannan ne ya fusatashi, ya kuma kirata da marar zuciya da ba ta tausayin Dadarsu. Ya kammala fatattakarta ya kwace wayar sannan ya shigo. Ramlat gaba daya ta ji damuwa da sauyawarsa don haka ta yi shahadar miƙewa ta karasa kusa da shi ta zauna. Ta daure ta kamo hannunsa ba tare da ta yarda ta kalleshi ba ta ce. "Ka yi hakuri, ko me aka yi maka, ka zama mai hakuri don Allah." Shi kuwa kallonta ya ke kawai. A hankali yanayinsa ya soma sauyawa, ɓacin ransa ya ragu sosai, ba abinda ya ke ji sai matukar kaunar kasancewa da matarsa kuma halaliyarsa. Ita kuwa dagaske bacin ransa ne ya taɓa ta, ba ta kaunar ganinsa a yanayi irin hakan. "Toh ya isa, ko su kike ki jefani yanayin da ba za ki iya magancemin ba?" Sai ta ji gaba daya ya ba ta kunya, ta dan harareshi da wasa tana mai zame hannunta cikinnasa, ya yi murmushi ya zauna sosai yana fuskantarta. "Yarinyar ce naga alamun ba ta ji, ta yi zurfi a soyayya da wancan yaron." Ramlat duka ba ta fahimci me ya ke son cewa ba, ta tsuramasa idanu cike da neman ƙarin bayani. "Hafsat." Ya fadi kai tsaye, nan ta fahimci komai, ta san da soyayyar Taheer ɗan Modibbo da ita  Hafsat din, tausayinsu ya kamata, ta tabbatar laifin Babansa ya shafi soyayyartasu. "Ka yi hakuri." Haka kawai ta iya cewa don ta tabbata idan ta fadi wata kalmar bayan hakan, zai iya hucewa a kanta. Da wannan ta samu suka share  zancen inda ya shiga yi mata bayanin ya soma neman aiki. Ta bishi da addua da fatan alheri. *** KANO Taheer a fusace ya shiga sashin Hajja Fatouma mahaifiyarsa. Tana kallon yanayin fuskarsa ta ji zuciyarta ta taɓu, tun sadda ta fahimci irin son da ya ke yiwa ɗiyar Dada ta san akwai matsala. Kaf cikin yaranta ta fi sonsa, ko don kasancewarsa namiji na farko a ɗakinta? Ba ta da masaniya, to haka ma daga bangaren Modibbo, duk wani tsaurinsa yakan sassauta akan lamarin Taheer. A yanzun da shi kansa Modibbo kunyar kansa da kansa ya ke ji, ya kuma kasa samun sukuni ko ƙanƙani game da lamuran su Hussein, ta tabbatar ba zai iya komai ba don su ba mahaukata ba me da za su ɗauki ƴarsu su ba Taheer duk da irin abinda ubansa ya shukamusu. Maimakon Taheer ya zauna, sai ya durkusa ya kama ƙafarta, ga mamakinta hawaye ya ke. "Hajjata zan iya mutuwa wallahi, kirjina zafi kawai ya ke yi. Ina son Hafsat, bana jin zan iya rayuwa idan babu ita. A yau Hamma Hussein ya kira wayata ya yimin gargadi kan na rabu da ita. Ba zan iya ba Hajjata, ba zan iya ba mutuwa zan yi. Na kasa sukuni tun da muka yi waya da shi, ji nake kamar na shirya gobe na wuce Adamawa." Ta girgiza kai tana sharemasa hawaye da hannunta, ita kanta nata idanun ne suka cicciko da kwalla. "Karatun naka fa wanda saura kiris ka kammala? Kar ka kara cewa za ka wuce Adamawa a yanayin nan a muke ciki, ba za su taɓa kallonka ba. Ba za ka yi wata ƙima ko daraja a wajensu ba saboda tun ran gini tun ran zane. Mahaifinka ne silar komai, a yanzun da girmanmu ya gama faɗuwa a gabansu gaba ɗaya, ba na jin ko karen gidansu zai ragamaka idan ku ka ci karo." Ya numfasa yana jin ciwon gaskiyar da Hajjarsa ke fadi, don ɗacinsa har a maƙwagoro ya ke ji. Ya haɗiyi zazzafan miyau ya dubeta da jajayen idanunsa. "Idan har dagaske Abban ya yi nadama, meyasa ba zai taka da kansa ya je ya samu Dada da su Hamma ya ba su hakuri ba? Idan mutuwa ta daukeshi a wannan yanayin fa? Shi ne silar lalacewar komai, don haka ya je ya gyara. Na fadamaku, idan na rasa Hafsat ba zan rayu ba. Ita ce numfashina." Daga haka ya mike ya fice yana tangaɗi sakamakon jirin da ke kwasarsa, bai kai ga ficewa daga ɗakin ba ya zube warwas a bakin ƙofa. Wani ihu da salati Hajja Fatouma ta yi a lokaci guda wanda ya jawo hankalin mutan gidan har shi kansa Modibbo da ya samu zazzaɓi ya lafamasa ya ɗan fara gyangyadi. Ba karamin gigicewa ya yi da ganin shalelan nasa a yanayinnan ba, tuni ya nemi zazzabin ya rasa balle ciwon kai, nan da nan aka kwashi Taheer sai asibiti. *** Tun zamansu a gabansa, ya haɗe fuska kamar bai taɓa dariya ba. Ba abinda ke mishi yawo a idanu sai irin cakumar da Hajiya Zeenatun ta yi mishi a haɗuwarsu ta ƙarshe kafin wannan. Yanzun tsabar makirci ita ce gabansa har tana kuka da neman gafararsa. Ya yi wani shu'umin murmushi mai nuni da cewa sai ya rama. Kwanaki can ya yi mata aikin da bai yi tsammanin za ta warke da wuri har haka ba, don haka zai mata wanda kaf dukiyar da ta ke taƙama da shi sai ya tarwatse. "Shikenan, na ji ya wuce. Sai dai ina mai gargadinki akan kar ki kara yin gangancin da ki ka yi gareni a baya." Hajiya Zeenatu ta kalli Hajiya Batool suka sauke ajiyar zuciya kusan a tare kafin su dubeshi da fara'a. "Ranka ya dade Gora, ba zan kara ba ko giyar wake na sha saboda na ga abinda na gani bayan na kaurace maka." 'Kaɗan kika gani, yanzun za ki ga fiye da hakan. Gora ba ya yafiya, ba ya mance sharri.' Abinda ya fadi kenan a ƙasan ransa daga nan ya ɗan bubbuga ƙasa kamar gaske, can ya dago ya dubi yanda duk suka kwalalo idanuwansa da fatar duk ta tattare saboda girma ya ja, a ransa ya ce tsoffin banza kawai. A fili kuwa ya yi wata arniyar dariya wanda gaba daya hankalinsu ya kwanta. "Ai wannan auren ba inda zai je, zan miki aikin da shi yaron da kansa zai tattaro ya dawo wajenki, ita kuma yarinyar zan mata aikin da za ta shiga bariki ya daina ganinta da daraja. Hakan ya yi?" Wata dariya Hajiya Zeenat suka sanya har da tafawa ita da Hajiya Batool. "Gora mai gayya mai aiki! Shiyasa duk inda naje sai na dawo gareka nake ganin daidai a lamuran rayuwata (Allah Ya ganar da masu hali irin naki). Hakan ya yimin daidai, dama nafi tunanin kamun kan yarinyar ne ya rinjayi Hussein ban da haka ban ga wani kyau a tattare da ita ba. Na ba ka wuƙa da nama." Ya yi dariya. "Hajjaju kenan, sai dai wani hanzari ba gudu ba, aiki ne mai tsauri domin sai na haɗa da tattaunawa da Sarkin bakaƙen aljanu, kinga kenan sai an yi zubar jini na dabba da jaririn mutum kafin a cimma yiwuwar aiki. Don haka aikin zai kama miliyan biyar." Hajiya Batool ta kalleshi a hargitse kafin ta dubi Hajiya Zeenatu, ta ga alamar ko a jikinta. Asalima ba ta sani ba, yanda Hajiya Zeenatu ke ji a yanzu ko don ta dauki fansa, za ta iya kashe ko nawa ne domin hankalin Hussein ya karkato gareta karo na biyu kuma wanda ta ke fatan ya zama na mutu ka raba. "Na shirya, na shirya ba da koda duk abinda na mallaka ne muddin Hussein zai dawo gareni." Gora ya ji kamar ya daka tsalle, shakka babu ya samu kudaden nan zai gudu ne ya bar garin a nemeshi a rasa, dama har yau shi kansa bai san asalinsa ba, daga almajiranci ne ya zama gawurtaccen Bokan Mata. Zai sauya ƙasar gaba ɗaya ya je ya kama wata sana'ar mai kauri. A fili kuwa cikin dakiya ba tare da ya nunamata komai ba ya amsa. "Shikenan, sai na jiki." Daga nan ya karkata ga Hajiya Batool, itama dai Miliyan Biyu ya nema, nan da nan ta hau zufa sai dai shaiɗan wanda ya kaɗamata ganga da kuma taimakon zigar Hajiya Zeenatu ta yarda ta kuma amince za ya san abin yi. Da wannan suka rabu akan nan da kwanaki uku za su dawo su damƙa masa kudaden da ya bukata. A ɓangaren Hajiya Zeenatu, ta yanke siyar da A&Z ga wani hamshaƙin matashin ɗan kasuwa wanda ya jima yana muradin wajen yana son ya ƙara ƙawatashi ya haɗa da filinsa da ke a gefen wajen ya gina Park na wasan manya da yara ma. Amma fir a lokacin ta ƙi yarda bisa shawarar Hussein da ya ce ba hannunsa idan ta yi hakan. Yanzu kuwa ta shiryawa hakan. Dama a yanzun shagonta na siyar da gwala-gwalai da manyan fashion ya ja baya don ta jima ba ta fita Dubai siyayya ba hakanan ba wani balance na kirki Manajan wurin ke kawomata ba. A ranta ta kudurta siyar da shagon ta bude babban boutique na kayan jarirai da na yara. *** "Damuwa ce ta ke neman illata tunanin yaron, sai kuma yunwa da ke dawainiya da shi wanda ya haddasa masa jiri. Muna tsoron kamuwarsa da hawan jini, don haka don Allah Baba a yiwa yaronnan abinda ya ke so." Wannan bayanin na Likita ya kara ɗaga hankalin Modibbo. Gumi ya shiga tsastsafowa daga goshinsa. Yan da labarin komai daga bakin Uwargidansa, yana da labarin cewa soyayyar Hafsatun Dada ke dawainiya da kwakwalwar Taheer. Bai san kuma ta inda zai soma magancewa ɗansa matsala ba don shi da kansa kunyar zuri'ar Dada ya ke ji. Ga yan uwansa sun juyamasa baya, kowa ya yi tirr da baƙar zuciya irinnasa da ba ta iya yafiya ba alhalin ma tun asali ba abinda Amina da Aminu suka aikata garesu, bisa tunzurawar Innarsu ce ta sa suka tsangwamesu. Haka ya amsawa Likita da cewar zai bincika damuwar Taheer sannan ya mike ya fita. Su Anti Amarya da ke tsaye suka zubamasa idanu har ya shiga ɗakin da aka kwantar da Taheer. Bacci ya ke sosai, ya zauna gefen gadon ya tsuramasa ido. "Ta ina zan soma yi maka maganin matsalarka alhalin nima ina da tarin laifuka a wurin bayin Allahnnan? Ka yafemin, ka bar ni na soma zuwa na gyara nawa ɓarnar kafin a yi maganarka." Ya furta cikin harshen fulatanci, shi kadai ya ke zancensa don Taheer bai ma san yana yi ba, a karshe ya mike babu kuzari ya fice daga asibitin gaba daya ba tare da ya cewa matansa da yaransa dake wurin komai ba. *** ADAMAWA... Wankan da ta yi na musamman ne a daren ranar talata, ba don komai ba sai don sanin da ta yi Hussein babu alamar sassauci a ƙwayar idanunsa. Ya lura da sallolin da ta yi a ranar, wannan ya sanya ya ke faman rawar ƙafa. Koda ya fita, zuma ta dauka ta sha sosai bayan ta wuni a ranar tana kama ruwa da ruwan ɗumi. Idan da sabo har ta saba don zai wuya ka ga Ramlatu na amfani da ruwan sanyi a wannan wuri. Kayan baccin ma da ta sa na musamman ne, riga da dogon wanda marasa nauyi. Rigar mai hannun vest sai top dinta mai dogon hannu. Babu wani underwear da ta sanya a ciki. Ta tabbatar daga kallo ɗaya Hussein ɗinta ba zai iya dauke kansa ba. Duk da Top din rigar da ta ɗora hakan bai hana komai bayyana ba. Ta ƙara mulke jikinta da turare, sai da ta kammala ta tabbatar babu inda ba ya tashin ƙamshi a jikinta sannan ta fito falon inda ya ke zaune ya maida hankali ga danna Laptop, AlHassan yake aikawa credentials dinsa ta email kamar yanda ya buƙata. Koda rashin haske a falon, hakan bai sa hasken tv gaza haskakamasa ita ba. Ya nemi nutsuwarsa na ƴan sakanni amma ina! Sun yi hannun riga, kawai sai ya tsinci hannunsa da rawa, ba don Allah Yasa ya kammala aikawa ba to shakka babu zai haɗa da shirme. Har ta karaso ta zauna a nesa da shi kaɗan bai iya ɗauke kai ba, ba tare da ya tunanin saƙon ya je ko bai je ba, ya kashe Laptop din kawai ya rufe. Mikewa ya yi ya kashe tv, sannan ya karaso, lalubo inda ta ke kawai ya yi ya ja ta jikinsa. A haka ya karasa dakin da ita. *** WASHEGARI.. I just published "BABI NA SITTIN DA UKU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1026513798?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=zZAfOdew2I80pQK%2B2VbvDQ7XLS4cczmz2oO62oVfO8o7sJbUSeKCeiRU7BICDOiu5Jd2MMKmIVdOPNPwwdQQ7sH8y4fVopayPcwrbHPyKEry%2FHqkikgjsm5msqZ9wmV%2B 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 63) A hankali ta ji ana masa susa a cikin kunne. Ta buɗe idanun tarr tana dubansa, ga dukkan alamu alwala ya yi. "A tashi a yi sallah." Ta gyaɗa kai tana sakar mishi murmushi, miƙar da ta yi ya sanya shi kaucewa da ɗan sauri-sauri  ya fice daga ɗakin gudun maimaici. Ta mike tsaye ta shiga bandaki, can kuma ta fito bayan ta wanke baki ta kuma  ɗora alwala. Dolenta ta koma ɗakinta ta ɗauki zani da hijab, anan ta shimfida darduma ta yi sallar, sai da ta yi addu'a mai tsawo tana roƙarwa mijinta dukkan wata rahma da alheri kafin ta gangara ga iyayenta da kuma yaranta. A karshe ta kara nemawa Aliyu da Kakarsa gafarar Ubangiji da ma dukkan musulmai, wannan ya zamemata kamar farillah duk bayan kowace sallah. Tana ninke hijabin tana murmushin tuna daren jiya, a karon kanta ta gama saddaƙarwa son da Hussein ke mata ya ninka ya kara ninka wanda ta ke mishi. Wasu kalaman ma da ya dinga furtawa, ita da kanta idan ta tuno jin kunya ta ke, amma ta san da yake shi din namiji ne, ko a yanzun zai iya maimaitawa. Sai kuma ta yi ƴar dariya kaɗan, ita kaɗai ta san me ta tuna. A ƙasan zuciyarta ta furta kalmar hamdala. Ta shagala cikin tunani don tuni ta kammala ninke hijabin ta koma kan zanin da ta ɗora. Ba ta ji shigowarsa ba, sai jinsa da ta yi ya jawota jikinsa ta baya, ya ɗora wuya saman kafaɗarta. "Good morning." Ya faɗi da muryarsa da ke hargitsata. Ta lumshe idanu tana tuna irin laushin da sumar kansa ke da shi sadda ta yi mishi riƙo son ranta. "Ina kwana, fatan an tashi lafiya?" "Idan na ce ban tashi lafiya ba, na yi karya. Na samu farin cikin da ban taɓa tsintar kaina cikinsa ba, na kuma  yi baccin da ɓata lokaci ne tsayawa misalta daɗinsa. Kece rayuwata Ramlat, na yarda ba zan iya rayuwa da kowace mace a bayanki ba. Ba alƙawari nake daukar maki ba, kamar yanda ba da alfahari nake faɗin haka ba, abu ne da nake ji a jinin jikina. Yanayi ne da na tabbatar ke za ki fahimta. Ina miki son da babu rabuwa. A shirye nake da yi maki dukkan abinda zai faranta ranki. A yau ni Hussein na ba ki wuƙa da nama, ki yanka iyakar yanda ki ka ya yi maki, ki faɗamin burinki a duniya, da yardar Allah koda ya fi ƙarfina zan ƙoƙarta yi maki shi. Ban san farin cikin da ke cikin auren budurwa ba, amma ina da yaƙinin ba za su kai min ke ba." Ya na maganar yana kai hannunsa duk inda ya so. Ta gama shagaltuwa da wani irin sonsa, tana ji a yanzu haka numfashinta na shige da fita ne da so da kaunar Hussein, ba ta san sadda ta juyo ta zubamishi dara-daran idanunta ba wanda ke ƙara tsumashi, kamar yanda duban nasa lumsassun idanun ke tarwatsa tunaninta har ta rasa kalar wanda za ta yi. Sai dai a wannan karon, a yanzun, a kuma wannan rana, ji ta ke ta samu kwarin gwuiwar kallon abin kaunarta tsakar ido, ba kuma don jin raini ba, aa, babu wannan tsakaninsu har abada sai wani irin kauna da ta ke jinsa daga ƙasan zuciyarta. Ba ta san lokacin da hannuwanta ya sauka saman fuskarsa ba kamar yanda ba za ta tuna sadda ta ɗora leɓɓanta bisa nashi ba. Hussein ya ji kalar soyayyar da bai tsammaceta nan kusa ba, bai ɗauka za ta miƙa masa wuya har haka ba, sai da tsayuwa ta nemi gagararsu duk kuwa da irin riƙon da ya yi mata ba na wasa ba kafin ta samu ta daidaita kanta ta rungumeshi. Daidai saitin kunnensa ta shiga magana tamkar mai raɗa. "Kai ne burina, bani da sauran burin da ya wuce kai. Ka zame min wani jigo babba a rayuwata. Soyayyarka da kulawarka su kaɗai ne abin buƙatata. Koda nayi soyayya a baya, ban ji abinda nake ji a kanka ba, ban kuma samu farin ciki kwatankwacin wanda nake ciki a kwanaki ƙalilan da nayi tare da kai ba. Idan har za ka riƙe ni da amana, ni Ramlat zan zame maka tamkar raƙumi da akala. Dama ni ce a ƙasanka, muddin rai, zan maka biyayya. Ba zan ketare ɗaya cikin umarninka ba, wannan shi ne burina. Ka tayani addu'a akan Allah Ya bani ikon cikawa." Bai ce mata uffan ba sai janta da ya yi suka ƙara faɗuwa duniyar masoya. ***    BAYAN KWANAKI UKU..   KANO. A hankali ta shiga fiddo bandir-bandir na dubu ɗaya daga cikin ƙatuwar ledar da ta zo da shi, Gora banda satar kallon ledar da haɗiyar yawu ba abinda ya ke yi, jikinsa har rawa ya ke dakyar ya yi kokarin tankwasa kansa. Har ta kammala ya tabbatar sun cika yanda ya ce, sannan ta mayar ledar ta miƙamasa bai ce uffan ba. Haka itama Hajiya Batool da ta tattara gwala-gwalanta ta siyar ta haɗa da siyar da motarta har ta samu suka kai milayan biyu, ragowar kudin ta adana su a banki. Gora ya gama haɗa miliyan bakwai cif a hannunsa kafin ya kyakyace da muguwar dariya duk suka dubeshi fuskarsu a sake don sun san sun cika sharuɗɗa kuma za su ga aiki nan ba da jimawa ba. Ko ba komai su na tuna aikin da ya yi musu tun farko da suka ji dadi. "Lallai dagaske kun shiryawa buƙatunku, toh ku sa a ranku kamar dama duk wani bala'i da ku ke gani a yanzu mafarki ne don kuwa ina mai ba ku tabbacin cewa burinku na dab da cika. Hussein zai dawo wurinki kamar yanda ita kuma matarsa za ta faɗa duniya ta lalace. Ke kuma! Ɗanki zai dawo gareki koda ace bangon duniya matarsa ta kai shi. Idan ya dawo ko a ranar ki ka ba shi umarnin ya saki matarsa, ba za ki rufe baki ba zai aikata." Don farin ciki sai ga Hajiya Zeenatu da Batool na sakin shewa har da cafkewa. Gora ya dinga washe hakora ya kalli wannan ya kalli waccan. Can kuma ya turɓune fuska kamar gaske  ya hau magana. "A daren yau, ni da kaina zan shiga cikin dajin Falgore, anan baƙaƙen aljanun suka yi umarnin na zartar da dukkan yankan da za'ayi na mutum da na dabba. Gobe kamar war haka, ku dawo na ba ku maganin da za ku yi amfani da shi idan suka shigo hannunku." Ba yau suka saba jin Gora na kiran sunayen dazuka ba da sunan wurin da zai yi aiki, don Gora har Sambisa ya ce musu ya shiga yin wani aiki kuma sun yi imanin hakan. Da wannan irin farin cikin Hajiya Zeenatu ta ce. "Ina mai maka albishir da kyautar sabon gida muddin kwalliya ta biya kuɗin sabulu." 'Makira, me zan yi da gidanki? An fadamaki ni talaka ne? A banza nake aikinnan ban mallaki kadarori ba?' Abinda ya ce kenan a ƙasan ransa yayinda a fili kuma ya kyakyace da dariya shi a lallai ya yi farin ciki da jin wannan kyauta. Haka itama Hajiya Batool ta mishi alƙawarin mota. "Ai kun ƙara ƙarfafa gwuiwana wajen yi maku aikin da ya dace! Ku tashi kawai ku je! Gobe ku dawo ku ji sakamako!" Da haka suka yi mishi sallama suka tafi ransu wasai, su na fita ya mike ya cire babbar rigarsa ya kwashi jakar kudaden ya yi ciki. Nan ya ba yaronsa umarnin duk wanda ya zo kawai a sallameshi a ce ba ya nan. Yaron kasancewar ya san komai kuma tare ma za su yi tafiyar ya sa bayan ya tabbatar da ɓacewar su Zeenatu a layin ya rufe ƙofar sosai yanda ba wanda zai ce Gora na nan. Shi kuwa Gora da shigarsa ya hau shiri don dama ya haɗa kayansa kaf a ƙatuwar jaka. Ya shige wanka ya gyara jikinsa don jinsa ya ke ya zama Alhaji, ya sauya kaya. Sai a sannan yaron ya shigo, shima gyara jikinnasa ya yi, suka ajiye maganar barin garin cikin daren yau ba gobe ba ransu fari ƙal kamar takarda. *** "Taheer mutuwa ka ke so na yi? Da wanne zan ji? Da ciwon da ke cin raina ko kuwa da yanda ka ƙi kwantar da hankalinka ka samu lafiya?" Taheer a wahalce cikin jin zafin kirji ya waigo a hankali ya zubawa mahaifinnasa idanu. Duk da ramar da ya yi  ba ya jin zai fahimci halin da ya ke ciki adalilin soyayyar Hafsat. Ya lumshe idanu bayan ya kauda kai daga duban Modibbo, babban damuwarsa halin da Hafsat ke ciki, wayarta ba ya shiga, ya tabbatar tana can duk abinda ta ke yi hankalinta na kansa, balle kuma shi. "Ku bani abinda nake so, Abba kai ne ka lalata komai, kai ke da alhakin gyarawa. Ka sani, ba za su taɓa ba ni Hafsat ba, ba zan taɓa samunta ba muddin ba ka nemi gafararsu ba. Abba ka yi kuskure, ka biyewa son zuciyarka wurin nuna ƙiyayya ga ƴan uwanka da kuma abinda suka haifa. Yanzu mene ne ribarka? Kowa a dangi na maka kallo da wannan abin. Abba ka nemi gafararsu tun lokaci bai ƙuremaka ba. Tun kana da sauran numfashinka a doron ƙasa." Kawu Modibbo da ya yi shiru kai a ƙasa yana sauraronsa jiki a sanyaye ya rasa me zai ce, ba wai nadamar ce bai yi ba, sai dai tunanin ko da wane idon zai dubi bayin Allahn nan har ya ce su yafemasa ya ke. Tun ma kafin wannan ranar ya san kalar rashin mutuncin Hussein idan aka taɓo iyayensa, balle kuma yanzu da Hajiya Zeenatu ta gama kunce masa zani a kasuwa. Kowa ya san da sa hannunsa a lamarin Hussein din. Sai dai kuma kunyar duniya ba ta kai ta lahira ba ranar da Ubangiji zai tsayar da shi da hisabi. Gwara ya tattara ya koam Adamawa gaba daya da iyalinsa ya nemi gafararsu kuma ya faɗi komai a  gabansu. Da wannan kudurin ya rarrashi ɗan nasa tare da nunamasa komai zai zo karshe don za su je Adamawa. Jin dadin wannan kadai sai da yasa Taheer zama maimakon a farko da ba ya iya tashi sai an taimaka masa. Har abinci ya ci sosai, wannan ya faranta ran iyayen. *** ADAMAWA. A kwanaki ukun nan, kowa ya ga Hussein da Ramlat ya san ba karamin walwala su ke ciki ba ga wata iriyar shaƙuwa da soyayyar junansu. A kuma ranar ne, Hajiya Binta da Rasheed suka dawo daga Katsina inda ta ziyarci yan uwanta. A washegari kuma za ta juya ta koma Saudiya tare da ɗannata. Rasheed ba Hausar kirki sai kame-kame yayinda ita kuma Ramlat ba larabci don haka sai kawai suka juye harshe zuwa English suka ci gaba da hira. Abinci lafiyayye ta yi musu shi da abokinnasa, sai da ta ajiye komai kafin ta ba su wuri tana kauda kai daga kallon da Hussein ke jifanta da shi yana ji kamar ya haɗiyeta don kauna. Ta kwanta rigingine saman gadon, kewar yaranta ta ke ji wannan ta sa ta kiran Hajiya. Bayan gaisuwa Hajiya ta haɗa ta da su. Hira sosai ta dinga yi da yaran, wannan na warce waya, wannan na sako baki yana magana kamar yanda ta fahimta. Dariya sosai suka dinga sanyata jin dagaske su dai so su ke ta dawo Kano ta dinga kai su makaranta a mota. Sai ma a lokacin ta tuna da motarta, yanzun ta san sai dai Hajiya ta ajiye su dinga amfani da shi koda wata matsalar za ta taso da waccan. "Kinga gajen hakurin Yayanku ko? Sai da ya sauwakewa Bilkisu ya ji dadi." Gabanta ya fadi jin abinda Hajiya ta ce. "Kamar ya Hajiya? Me ya kuma haɗasu?" "Uhm, wai gidan Amaryar ta je ta ja ta da fada har da kokarin dukanta, wannan ya fusata shi. Yanzu dai Kawunnanku sun ce tunda ya dauki zafi a kyaleshi kar a tursasa mishi sai ya maido ta, nan gaba itama watakila ta yi hankali. Yarannasa su na hannun Amarya." Ramlat sam ba ta ji dadi ba, ko ya ya halin mutum ya ke, saki wani abu ne mai zafi. Cike da jimami ta ce. "Allah Ya kyauta, Allah Ya daidaita lamuransu idan da alheri." "Ameen." Hajiya ta amsa, kamar koyaushe, nasiha mai ratsa jiki ta ƙara yi mata akan riƙe amanar miji da kuma kyautatamasa. Ta kara nusar da ita game da ibada musamman a watan Ramadan da ke ƙara kusantowa don bai fi saura wata guda da ƴan kwanaki ba. "Allah Yay maku albarka, Ya ji ƙan Abbanku." Ramlat ta amsa zuciyarta a raunane musamman tunanowa da Abbanta da ta yi, har suka yi sallama ba ta dawo daidai ba. A hankali kuma ta kwanta sosai ta juyawa ƙofa baya. Kewar Abbanta ta ke ji, ta tabbatar da ace yau yana raye zai yi matuƙar alfahari da aurenta na biyu, zai kuma ji dadi. Burinsa da kuma farin cikinsa bai wuce nata ba, ya ci alwashi a kanta a bayan aurenta da Aliyu wanda ya zamemata ƘARFEN ƘAFA, da kansa kuma ya janye sakamakon tsantsar kauna da tausayin da yake mata. Mutuwa ba ta barin wani don wani ya ji dadi. A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ba ta san hawaye ta ke ba sai da ta ji tattausan tafin hannun Hussein yana sharemata su. Da sauri ta juyo sai dai babu damar matsawa sakamakon hannunsa ɗaya da ke tokare a gefenta a saman gadon. Ido ya ƙuramata fuskarsa na nuna alamun ba dadi. "Habibty, meke damunki har ki ke hawaye?" Ta girgiza kai ta sunkuyar tana murmushi. "Ba komai, waya muka yi da Hajiya, addu'ar da ta yimin ta sa na tuno Abbana. Shi ne kewarsa ta kama ni." Ya kamo haɓarta ya ɗago suka kalli juna. "Kiyi hakuri, dukkanmu muna da wannan tabon na rashin iyaye duk da cewa kaso kusan ɗari, mun samu kulawar da ta dace a wurin Dada wanda ko su ne sai haka. Haka Allah ke tsarinSa a rayuwa, dukkan mai rai mamaci. Allah Ya gafartamusu." Ta amsa da amin tana mai jin karfin gwuiwa. Ya bita da wani irin kallo yana murmushi, ta yi azamar jan rigarta tana harararsa. Mikewa ya yi ya taɓe baki. "Wane dare ne jemage bai gani ba?" "Daren mutuwarsa." Ta amsa, ya yi dariya, har ya dawo da baya sai kuma ya jinjina kai ya kama hanya yana fadin. "Ki fito ku yi sallama zai wuce." Jin haka ta mike ta maida hijab din da ta cire, fitowa ta yi har Rasheed din ya miƙe tsaye don haka suka yi sallama don ta san ba lallai su kara haɗuwa ba tunda a yau sha biyun dare zasu wuce Airport. *** Bayan sallar isha'i ta shiga suka yi sallama da Hajiya Binta. Mata mai kirki, haka ta sanya ta a ɗaka ta ba ta shawarwarin da za su amfaneta a zamantakewa. Kafin ta yi mata kyautar miski mai kyau marar sirki. Ta yi godiya sosai. Koda ta fito ɗakin Hafsat ta faɗa jin yanda kwanaki biyu ba ta jin ɗuriyarta. A kwance ta isketa yatsarta na dama rike da Counter tana dannawa a hankali. Shigowar Ramlat bai sa ta ɗago ba balle ta san da wanzuwarta a ɗakin. Zama ta yi gefen gadon, hakan ya ankarar da ita, tausayinta ya kamata. Yanzun Dada ta gama faɗan sauyawarta, ta kuma san dalilin tunda Hussein ya faɗamata. Hafsat ta mike zaune da sauri tana goge hawayen saman fuskarta. "Adda Amal, sannu da zuwa. Yanzu ki ka zo?" Ramlat ta gyara zama sosai ta dubeta. "Hafsat kar ki zama marar hakuri da juriya a lamarin soyayya. Ki zama mai hakuri. Kin san illar saɓawa iyaye kuwa?  Na taɓa shiga makamancin halin da ki ka tsinci kanki ciki a baya. Na kuma san yanda ki ke ji, kina jin kamar ba za ki iya rayuwa babu Taheer ba, kina jin numfashinki zai iya ɗaukewa muddin ki ka rasa Taheer matsayin miji ko? Kamar su Dada da Yayyanki ba su yi maki adalci ba." Hafsat ta kwantar da kai saman cinyar Ramlat, sai kawai ta fashe da kuka ta soma magana. "Adda Amal wallahi hakane, na sani Mahaifinsa mai laifi ne a wurin su, amma shi me ya yi musu da za su yanke alaƙata da shi? Dada da bakinta ta yabeshi a ɗan  zaman da ya  yi tare da mu, ta fada ta ƙara, bai ɗauki halin mahaifinsa ba balle na mamansa, Hamma AlHassan ma haka. Hamma Hussein bai zauna da shi sosai ba da na tabbatar zai gamsu da kyawawan ɗabi'un Taheer. Adda Amal sanadin aurena da Taheer zai iya sanyawa su shirya. Babban damuwata Hamma Hussein ya kwace wayata, Rasheeda ta kirani ta wayar Dada tana kuka ta shaidamin yana asibiti kwance ba lafiya." Hafsat na kaiwa nan ta mike zaune, ita Ramlat kallonta kawai ta ke tana fidda hawayen tuna baya, itama dama haka ta kafe? Amma ba za ta taɓa bari Hafsat ta yi irin nata ba. "Adda Amal kimin alfarma ki ban wayarki, sau daya kawai zan kirashi, daga haka ba zan kara ba. Wallahi kawai gaisawa zamu yi na kuma roƙeshi mu ci gaba da addu'a. Har abada ba na fatan na bijirewa iyayena da yan uwana." Ramlat ta yi jim, tana tunanin anya kuwa idan ta yi hakan ba matsala? Sai dai kuma irin magiya da nacin Hafsat ya sa ta miƙamata wayarta. Kasa fita ta yi daga dakin ta jira har Hafsat ta kammala wayar, Ramlat banda kallon ƙofa ba abinda ta ke yi. Tsoronta kar Dada ta faɗo ɗakin don ta san abu ne mai matsanancin wahala Hussein ko AlHassan su shigo ɗakin. Da murmushi ta dubi Ramlat. "Adda Amal." Sai ta rungumeta don farin ciki can kuma ta saketa. "Cemin ya yi za su zo nan da kwanaki kalilan har Babansa, zai zo neman gafarar Dada da su Hamma." Sosai itama Ramlat ta ji dadin hakan. Ta rike hannunta. "Toh kinga ni, don Allah ki saki ranki, kinga Dada kin jefa ta a damuwa. Ta ce ko ganin idon baƙuwarku ba kya yi, ba ki san ki danne zuciyarki da abinda ke cikinta ba. Jefa iyaye cikin damuwa masifa ce a garemu. Kuma ina mai ba ki shawara ki dage da nemawa kanki zaɓin Allah, ki rabu da biyewa son zuciya wurin dagewa akan zaɓinki." Hafsat wacce tuni ranta ya yi fari sumul ta gyada kai. "In sha Allah Addata. Ina godiya sosai. Sai dai Adda ba ki ban labarin da ki ka ce." Ramlat ta murmusa. "Kar ki damu, ai ana tare." "Da'iman kuwa da yardar Allah." Fadin Hafsat, suka dara kafin Ramlat ta fice  ita kuwa bandaki ta shiga ta wanke fuskarta. Ramlat na sallama da Dada sai ga Hafsat din, sosai ta yi mamakin walwalarta, ta karasa ta fda jikin Dadar tana neman gafararta cike da shagwaɓa. Murmushi Dada kawai ta yi gami da jinjinawa Ramlatun. Ta tabbatar aikinta ne. *** A ɓangarenta kuwa, ganin fitilu a kashe ya ba ta mamaki matuƙa, ita dai ta san ba ta kashe ba. Haka ta ci gaba da tafiya a hankali har ta kai ga makunnin, kafin ta kunna ya riga ta. Ta juyo ta dubeshi, kafin ta kai duba ga cikin falon. Baki da hanci kawai ta saki tana dubansa ta kuma maida duba ga abinda idanunta ke gani. I just published "BABI NA SITTIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1028701620?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=0Ip%2BQlXDoaoxyM7eqonDyl6cCNMjLR7b13cfWz0PO6rluIvQeUuu1jHeHigNXBE4IV%2Fm159PS%2BDsIeqGDHiIXMY5fTO3p4OINuf3vYe6Dx12trWJCYsK2knobbhhwa9y 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 64) _*Assalamu alaikum yan uwa Barkanmu da wannan lokaci. Ku yi hakuri kun sha jira, da yardar Allah kiris*_ Wani ƙaton enlargement ne na ɗaya cikin hotunanta da ya ke da su, ta karkace kai tana murmushi har fararen haƙoranta sun fito, sai wani ƙaton kwali da ba za ta iya cewa ga abinda ke ciki ba sai kuwa akwatuna jere reras har guda sha biyu. Ta kai dubansa gareshi, murmushi ya ke sakarmata sosai. A hankali ya matso ya kama hannunta suka karasa cikin falon. Wani ƙaramin kati mai adon heart da fulawoyi ne ya soma daukar hankalinta don haka ta sa hannu ta ɗauka ta bude. _*From the moment I first laid eyes on you, I knew you were a perfect match for me. I love everything about you Heart.*_ Ta juyo ta dubeshi, yana tsaye kawai hannuwansa cikin aljihun wando yana zubamata murmushi. Da ido ya mata nuni akan ta ci gaba da buɗewa. Ba musu ta kai durkusa ta kai hannu ta bude wani karamin gida na zobe, ai kuwa zoben ne mai matukar sheƙi, ya fi mata kama da na azurfa. Ya yi masifar burgeta, idanunta ya ƙara kaiwa saman wani kwalin karami da aka ɗaure bakinsa da igiya mai ƙyalli, ta bude, ganin mukullin mota kawai sai ta ɗago ta dubeshi, idanunta nan da nan suka cicciko da kwalla. Ta ajiye kafin ya taimaka mata da bude akwatinan, kaya ne maƙil, kowanne da set dinsa. Yanda dai ku ka san lefe irin na budurwar yarinya don wannan ma ya fi na budurwar kyau da tsari. Ko iyaka haka aka tsaya a na budurwa sai sam barka. Laces, atamfofi, mayafai, shadda, yadika, abayoyi da dukkan sauran kayayyakin shafa da sarƙoƙi ba abinda ba'a haɗa ba. Wannan ya bata tabbacin ba yau ya soma haɗawar ba. Bayan sun mayar da komai ta dubeshi, tuni hawayen da ta ke dannewa sun zubo. Ya kai hannu da sauri ya ɗaukemata su. Ba ta bar kallonsa ba ta soma magana. "Allah Ya saka da dumbin alheri, na.." Ya kai yatsa saman lebbanta. "Shii...Ba kalar godiyarnan nake so, buƙatar fin haka nake. Kar ki manta kuma haƙƙi ne na maki sutura da ma duk abinda bai fi ƙarfina ba wanda zai farantamaki. Kin cancanci fiye da haka." Ya ƙarashe gami da ɗagamata gira. Kunyar ta nema ta rasa, kawai sai ta juyo gaba ɗaya ta rungumeshi har bayansa na jingina da kujerar. Ya kuwa ba ta kyakkyawan mazauni a kirjinsa, kafin kuma kiɗa ya sauya salo. *** KANO.. Wutar da ta tashi a wani gida dake unguwar ya sa mutane duk suka fito, cikin dare ne da misalin karfe biyu da mintoci. Banda salati da kokarin kashewa ba abinda ake yi. Da yawa suna aikin kashe ta amma fadi suke don kawa kar wutar ta haɗa da nsu gidajen ne amma banda haka dama sun gaji da Maigidan, bokancin da ya ke yi musu a unguwa yana tare matasa abin ya ɓaci. Gora kuwa yana daga ciki banda ihu da neman agaji ba abinda ya ke yi, ya rasa ta inda aka yi wuta ta soma cin gidansa, babban abinda ya ƙara haukata shi neman jakar kudadensa da ya yi ya rasa, ga yaronsa ba ya nan. Wannan ya ɗan ankarar da shi cewa cin amanarsa ya yi. Nan fa ya haukace, tun akwai hanyar ficewa har ya zamana ya rasa ta inda zai bi ya tserar da rayuwarsa daga halaka. Haka dai kafin mutane su yi nasarar tsayar da wutarnan, Gora rai ya yi hali. A ɓangaren yaronsa kuwa har da shi cikin masu kokarin kashe wuta kamar gaske, har ya tafi sai ya yi tunanin gwara ya tsaya ya tabbatar da mutuwar Gora kafin ya gudu, idan kuwa har aka yi rashin sa'a ya tsira, to ya tabbatar duk inda ya shiga a duniya ba zai tsira daga ta'addancin Gora ba. Ganin an fito da Gora a mace ya sanya ya ji wani sanyi a ruhinsa, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya hau mashin dinsa ya wuce can filin makaranta inda abokinsa Jabir da suke kira da Jabson ke jiransa su wuce. Yana zuwa suka cafke su na dariya. Nan ya ba shi labarin komai, ya dubeshi da kyau. "Jakar fa?" Jabson ya yi wani malalacin murmushi gami da mishi nuni da aji. Ya bubbuga kafadarsa suka dara kafin ya shige gaba zuwa ajin, sai dai shigar ya yi daidai da sokamishi wuƙa a baya ta ɓullo ta ciki, Jabson ne. Sai da ya tabbatar ya kashe shi har lahira sannan ya ɗauki jakar ya tsallakeshi. Mashin dinsa ya haye ya bar wurin a miliyan. Shi da garin Kano kuma sai nan da wasu shekaru.   Misalin ƙarfe sha biyu na rana, labarin ƙonewar Gora da tsintar gawar yaronsa ɗan aikensa Salmanu, ya karaɗe unguwar. Ko'ina maganarsu ake yi, ga Jabir abokin Salmanun da aka nema sama ko ƙasa aka rasa. Dama almajirai ne, wannan yasa aka shiga tunanin ko sace Jabir din aka yi bayan kashe Salmanu. Daidai sadda ake wannan hargitsin, motar Hajiya Zeenatu ta tsaya. Tun kafin su fito cikinsu ya ɗuri ruwa ganin yanda gidan Gora ya zama kango lokaci guda. "Ke Zeenatu, anya gidan ne?" Hajiya Zeenatu ta kasa amsawa Hajiya Batool, kokari ta yi kawai ta yi parking suka fito, yaran almajirai na ciki su na ta  ɗage-ɗage ko za su yi tsintuwa. Daga ƙasan bishiya wasu samari suka hangosu. Ɗayan ya ce. "Waɗannan su ne na goma sha takwas kenan, wannan mutumin fa yana wankar mata, yanzu haka ma wani mugun aikin su ka zo ya musu." Wani ya mike. "Bari mu je mu ji, idan ma shi suka zo nema mu ba su labari ko Allah zai sa su tsorata da lamarin rayuwa su shiryu." Ganin haka sauran ma suka mara mishi baya don ba za'a yi babu su ba. "Hajiya wurin Gora ku ka zo?" Hajiya Batool da Zeenatu wadanda sun rasa ta ina za su soma, su ka dubi saurayin kusa a tare suka amsa da eh. "Ayya, ai a daren jiya gobara ta cinye gidansa tas babu abinda ya tsira. Shima ya mutu ɗazunnan aka dawo daga binne abinda aka tsinta na gangar jikinsa. Shima dai yaronsa Salmanu an tsinci gawarsa a filin makarantar Firamare  an kashe shi." Hajiya Zeenatu sai da numfashinta ya bar motsi na wani lokaci kadan, ta kasa magana sai kawai ta ɗora hannu a kai ta fashe da kuka. Jiki na rawa Hajiya Batool ta ce. "Shikenan Gora ya mutu dai ku ke nufi?" Suka bisu da kallo kamar taɓaɓɓu, kusan ma duk kalar ruɗewar da sauran matan da suka zo suka yi, bai kai na wadannan Hajiyoyin ba. Mai magana ɗazu ya matso. "Eh ya mutu. Duk wani mugun aiki da ya ke shukawa ya kare. Ya koma gidan gaskiya inda zai girbi abinda ya shuka din. Kuma ya kamata ku ji tsoron Allah ku tuba daga tafarkin shaidan tun kan lokacinku ya ƙure. Idan har ba so ku ke yi kuma ku zama tarihi ba, ku tafi a wofi." Hajiya Batool ba ta ce uffan ba balle Hajiya Zeenatu da ke faman kuka, ashariya kawai ta ke narkawa Gora kamar ta mance da cewar ya mutu. Har dai dakyar Hajiya Batool ta maidata mazaunin kusa da direba ita kuma ta tuƙa motar suka bar layin, yara duk an cika ana binsu da kallo. Haka suk isa gidan Hajiya Batool hankali a matukar tashe.  Ita kanta Batool din dakiya kawai ta fi Zeenatu, amma ba ta ga laifinta ba don kuwa ta fi ta zazzage bakin aljihu a wannan harkar. Nutsuwa ta gagaresu, Hajiya Zeenatu kawai zama ta yi kamar  kayan wanki a saman kujera tana ci gaba da surfa ruwan bala'i ga Gora da ya jima a gushewa. "Yanzu shikenan Hussein da Ramlatu haka zan zuba ido ku cigaba da cin amanata?! Shikenan wai hakan na nufin sun yi nasara?! Wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na ga bayan Ramlatu da Uwarsa! Sai Hussein ya dawo karkashin ikona. Ba zan dauki wannan dumbin asarar ba! Batool nemomana Maryama a waya! Zuwa Nijar ya kama mu, ya zama dole mu kara gwada aikin Bokansu. Buzaye ne!Za mu yi nasara, za mu yi nasara." Ta na maganar kamar wacce ta samu taɓin kwakwalwa. Itama Batool ta gane zuwannasu Nijar din kawai shi zai zame musu mafita don haka ba musu ta zaro waya ta dannawa Maryama kira lokaci guda kuma tana sharce gumi. Magana sosai suka yi, ba ta ɓoyemata duka asarorin da ya hau kansu ba. Maryama ta jajanta musu sosai karshe ta ce musu za ta yi musu booking na layin ganin Boka Buzu, kawai dai da zarar sun saka ranar zuwa su fadamata. "Gobe ma zamu taso jibi mu iso." Hajiya Batool ta katse ta da gaggawa, ƴar dariya Maryama ta yi kafin ta amsa da toh hadi da musu fatan zuwa lafiya. Washegari kuwa da sassafe suka kama hanyar Nijar, direba ne ya kaisu. Yardaddan direban Hajiya Batool, Audu. Wannan karon ma sun tattara maƙudan kudade don ita Hajiya Zeenatu ba ta bi ta kan Manajanta ba, ta nemi manyan gwala-gwalanta har biyar ta shiha kasuwa ta siyar. Itama dai Hajiya Batool sai da ta haɗa da siyar da kadara, kowaccensu ta taho cike da burin samun abinda aka je nema. Idanunsu ya rufe, gani suke yi tamkar ga su ga burinsu har ya cika tsabar imanin da suka yi da abinda zai kai su. Wuraren karfe sha biyun rana da mintoci suka iso Damagaran, anan suka kwana washegari da sassafe suka kama hanyar Niamey.  Sun sha tafiya sosai kafin su isa Niamey, kai tsaye suka kira Maryama a waya. Da kwatance da tambaya suka iso katafaren gidanta wanda ya sha kayan alatu. Ta musu kyakkyawar tarba, ba kamar wancan lokacin ba, wannan karon gidanta ne na kanta ba na Maigidanta ba. Tun bayan rasuwar Mijinta ta siya gida inda ta ke harkar safarar yara zuwa Ƙasar faransa da ma wasu ƙasashen yawon bariki. A yanzun da su ke zaune a falon suna cin abinci bayan sun yi wanka, ba tare da kowaccensu ta damu da kallon gabas ba, ƴan mata ne ke safa da marwa cikin shiga mai ƙayatar da masu iri  halinsu na bin maza. Babu wacce ba ta fito ta gaida baƙin Madame dinsu ba, a karshe Hajiya Zeenatu ta kora ruwan sanyin da aka ajiyemusu ta dubi Maryama. "Kin tabbatar dai goben babu fashi a zuwanmu wurinsa ko?" Wani murmushi Maryama ta yi ta dauki tuffa ta gutsira. "Haba Hajjaju, zan maki ƙarya ne?" Ganin haka Hajiya Zeenatu ta saki fuska. "Ba haka nake nufi ba, kin dai ji komai ai daga bakin Batool, banda haka nan da kike ganina duk sadda zan runtse idanu ba abinda nake haskowa sai Mijina tare da waccan karamar karuwar. Gani nake duk kwana daya tamkar shekara ce." "Ki sa ranki a inuwa, za ki sha mamakin yanda komai zai lalace. Mijinki ya dawo kamar kwai a hannunki sai yanda ki ka yi da shi." Dariya suka yi har da cafkewa, nan da nan zuciyoyinsu suka ɗan waske sai dai ko ya ya suka tuna asarar da ta hau kansu na miliyoyi sai sun tsinewa Gora. Basu ma batun nemar masa gafara. Kamar yanda Hajja Maryama ta fadi, hakan ce ta kasance. Washegari bisa jagorancin yaronta sai dai ba wancan na farkon da ya taɓa yi musu rakiya ba, suka rankaya gidan Bokansu Buzu. Koda suka tsaya babu layi sosai, kamar wani layin asibiti haka aka basu kati karami mai dauke da numero (number). Wannan dai ba ɗayan bane, wani sabon Boka ne gagarumi da Maryama ta tabbatar musu cewa aikinsa wane wancan! Daga yanda ma ake yi a wurin ba ka ganin kalar talauci a wurin ka san harka ce ta manya don kowacce ta sha shadda mai dandasheshan kyau sai kuwa daidaiku masu leshi. Su da suka yi shigar atamfa ma sai suka raina tasu kwalliyar. Ba don komai ba sai don ba su zo da tsadaddun ba na gani a faɗa. Hankalinsu na kan aikinsu. Sai da layi ya iso kansu suka yi zumbur suka miƙe, ganin su na kokarin shiga tare mai tsaron wurin ya dakatar da su. Cikin Hausarsa da ba ta fita sosai ya dakatar da su. "Ba'a shiga mutum biyu komai kusanci." Jin haka suka dubi juna jin abin banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Ba su taɓa zuwa an musu iyaka da shiga wurin Boka tare ba, karshe dai ganin mutumin na harararsu ya sa Hajiya Batool ta ja baya. "Soma shiga bari na yi jira." Hajiya Zeenatu ta shige ita kuma ta koma ta zauna. Kwarjini iyakar kwarjini mai bada tsoro shi ta gani a fuskar wanda aka kira da Gamsheƙa, fuskarsa babu ɗigon walwalwa. Tana zama babu tambaya ya nemi sanin sunanta kawai kafin ya soma motsa wasu irin ƙaho da duwatsu da ke cikin wani ƙaton abu kamar tire kamar kuma ba shi ba. Sai da ya gama ya dubeta ya shiga kora jawabi. "Mijinki da kika yiwa asiri mai suna Husseini, ya dawo hayyacinsa ya sake ki, ya kuma auri wacce a duniya kika tsana, kuma burinki bai wuce na ganin kin hallakata ba. Sai dai kuma ki sani, tuni kin makara don soyayyarsu babu karfin shaiɗancin da zai iya hallakata. Amma ina mai tabbatarmaki juya tunaninsa abu ne mai sauki idan kin aikata duk abinda za mu sanya ki babu musu." Hajiya Zeenatu wacce idanunta ya rufe nan da nan ta hau gyada kai tamkar ƙadangaruwa. "Wallahi a shirye nake, ko menene zan aikata idan har burina zai samu cika." Ya jinjina kai da yin murmushi mai kama da na mai jin kashi. "Shikenan, a yanzu za sadu da ke ta gaba da kuma baya, daga karshe zan ɗebi abinda ya fita daga jikinki na najasa na haɗamaki wani ƙullin magani wanda za ki tabbatar kin yi yanda ki ka yi, kin fesa a fuskarsa. Sai kuma wani tulu da zan ba ki wanda ke dauke da zucciyar mutum soke da allurai, shi ne mafi hatsari cikin ayyukan da zan maki. Kar ki kusa ki bari ya fashe, muddin ya fashe ki sani komai zai iya faruwa da ke, wannan hukuncin ya rage ga aljanun da suka satomin zucciyar. Don haka kin yarda kin amince za ki iya?" Hajiya Zeenatu wacce tun sadda ya yi batun saduwa ta baya ta yi turus, kirjinta ya shiga dukan tara-tara, abu ne da ba ta taɓa aikatawa ba, bar ta dai da aikata zina shima a baya ne kafin shigowar jarumi kuma namijin duniya Hussein rayuwarta. Daga shi babu waki namiji da ta ƙara yiwa kallon abin marmari. 'Ki tuna fa, wannan namijin kike kwaɗayin maidoshi rayuwarki yanzu Zeenat, kada ki yi sake. Wannan ce kadai mafita.' Wani ɓangare na zuciyarta ta mata tuni, nan da nan ta dubi Gamsheƙa da har ya soma gundira da shirunta. "Na amince. Zan kiyaye dukkan sharuɗa." Ya miƙe tsaye ya ba ta umarnin ta biyoshi. Daga haka ya nufi uwar ɗaga bayan sakin labulen window, hakan ya sa Maitsaron ya fahimci shugabannasa ya shiga aiki. Wannan yasa bai yi gigin lekawa ba. Sun kwashe kusan fiye da awa ana abu ɗaya don Gamsheƙa dai ya samu ya da yake so, a karshe ya fito ya bar Hajiya Zeenatu da ɗibar abinda ya umarceta a kwalba sannan ta mike ta fada bandaki ta dauraye jiki ta fito. Koda ta dawo ta iskeshi har sannan ba walwala kamar ba shi ne ya gama kukan mage ba. Gani ta yi ya haɗamata komai ya miƙamata sannan aka yi bayanin kudade ta biyashi da kudin Ƙasar don tun a Damagaran suka yi chanji. Koda ta fito mai tsaron ya ba Hajiya Batool damar shiga, ita kuma ya ce ta fice don baa kara zama idan an fito, hakan laifi ne babba. A gaggauce ta fita, yaron Maryama zai karbi tulun hannunta dake cikin kwali ta yi saurin dakatar da shi ta ce ya bar shi. Don ji ta ke idan har ba ita ce ta riƙe ba to fa komai zai iya faruwa. Duk fargaba ta cika zuciyarta. Tana nan zaune a motar har kusan shudewar awa guda kafin Hajiya Batool ta karaso, ita har da hawayenta ma don ita kadai ta san me ta ke ji a bayanta tun abinda ya gudana tsakaninta da Gamsheƙa. Hajiya Zeenatu ta kalleta kawai don ta san duk kanwar ja ce. Ita ba tulu sai wani kwalba a cikin kwali, ba su ba junansu labari ba sakamakon ba su daya ne a motar ba, haka suka kama hanyar gidan Maryama kowannensu da abinda ya ke saƙawa. Kamar yanda kowanne ke tunanin bala'in da zai sameshi idan har suka yi gangancin ɓata aikinsu. ***   ADAMAWA Kwanakin da suka biyo baya, banda soyayya ba abinda Hussein da Ramlat ke gurza, gaba dayansu sun sauya sun kara wani fresh da kyau. Hafsat ba ta bar aron wayar  Ramlat a faƙaice ba tana gaisawa da Tahir. Ita dai Ramlat a tsorace take da hakan sai dai ganin Hussein bai taɓa kamata da laifin ba yasa ta ɗan ji nutsuwa kaɗan. Ranar da ta cika sati ɗaya cif a garin Adamawa, tana zaune a falonta, dawowarta kenan daga sashin Dada. Hussein ya shigo fuskarsa kaɗai ka kalla za ka san yana cike da tsantsar farin ciki. Hannu kawai ya waremata ba musu ta ƙarasa ta rungumeshi. Ya kuwa ɗagata cak yana juyi da ita, dariya ta yi bayan ya sauketa ƙasa yana nishi da riƙe ƙugu. "Heart, kin fa ƙara nauyi." Ta turo baki irin na shagwaɓaɓɓun yara, ya yi murmushi da jan karan hancinta kafin ya rungumota ta baya. "Albishirinki." "Goro." "Alhamdulillah, bisa la'akari da workkng experience dina da kuma credentials, Yayanmu ya samarmin aiki a wani Kamfanin gine-gine. Sosai su ka yaba da komai nawa " Ta juyo ta ba shi kyakkyawan sumba a kumatu. Ganin ya jefata da wani kallo ta kauda kai tana murmushi don har sannan wani lokacin Hussein dinta kwarjini ya ke mata. "Congratulation, Allah Yasa a fara a sa'a. Ya kara daukaka." "Ameen dearest one." Daga haka ya jawota ya hau yi mata raɗa a kunne. Daidai sadda wayarta ta yi ringing, kasancewar shi ne a kusa, ya ɗauma, ganin baƙuwar lamba sai ya ɗaga kawai, bai kai da sallama ba muryar namiji ya ratsa dodon kunnuwansa. "Assalamu Alaikum, Adda barka da rana. Taheer ne." Wani irin kallo ya ke bin Ramlat da shi, Ramlat gabanta ya fadi, ta sani dai a dazun Taheer ya kira ya ce yana son magana da Hafsat zai mata wani albishir, ta ce ya bari idan ta shiga gidan sai ta kira. Shaf ta mance, kuma ba ta samu shiga ba sakamakon wankin undies dinta da ta tsaya yi. Jikinta ya bata akwai matsala. Ba ta gama tantancewa ba sai da ta ga Hussein ya miƙamata wayar ya kuma ƙuramata idanu. Ta karɓa da rawar hannu, gaba daya ta ruɗe, tunda suka yi aure ba ta taɓa ganinsa a wannan yanayin ba kuma ma adalilinta sai yau. I just published "BABI NA SITTIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1032619087?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=WqGcOpyrKLCeYJ2pB6S21O2rofM3hfkPhkl8xHn5YliOXRIEhSFgVvGwVllJASGRLQwGf8a%2FEFI9gUseG%2BLsfaQfid671L2Bpg0RFziPc0xIuxqo35SEHCqXV8izbKgB 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 65) _*Assalamu alaikum masoyan karfen kafa. Ina ba ku hakuri mai yawa. Na so kwarai na haɗa post din nan da na karshe na aiko gaba daya, sai dai na sani kun yi hakuri iyaka, makaranta da ma sauran abubuwa ke ɓoyeni da hana ni typing. Saboda damuwar da ku ka yi na hakura zan soma posting wannan, daga shi kuma sai BABIN KARSHE in sha Allah. Ku yi hakuri, na tabbata duk wanda aka ba hakuri baa aikatamasa daidai ba. Amma kuyi hakuri. Ina kaunarku fisabilillah.*_ "Hello. Taheer ba..ta..ba ta kusa." Daga yanayin muryarta ya fahimci akwai matsala, bai kara magana ba ya katse wayar yana mai dana sanin kiranta duk da irin gargadin da ta yi mishi akan muddin ba ita ta nemeshi ba su yi magana da Hafsat, kar ya yi gangancin kiran wayarta. Hussein juyawa kawai ya yi ya wuce ɗakinsa, ta dage goshi tana kiran sunan Allah, shakka babu laifinta ne ko me ya faru. Ta saɓa umarninsa na hana Hafsat waya, tunda yanzun ba amfani, abinda ya ke gudun, tana yi da wayarta. Ramlat ta numfasa, tunani take ta bishi ko ta kyaleshi zuwa anjima kaɗan? Sai dai idan ta rabu da shi, tana tsoron kada ya ƙi cin abinci alhalin daga yanayinsa kadai ma ta fahimci ya kwaso yunwar. Mikewa ta yi tsam ta nufi dakin. Ba ya nan, alamar an kunna ruwa yasa ta fahimci yana banɗakin. Ta nemi wuri gefe gadon ta zauna, ta ɗan jima zaune kafin ya fito ɗaure da tawul a ƙugunsa sai karami a hannun yana share ruwan gashinsa. Bai ko kalleta ba ya yi gaba zuwa gaban madubin, da saurinta ta karasa ta bayansa, ganin abinda ta ke shirin yi, wato rungumoshi, sai kawai ya juyo fuska ba walwala hakan ya dakatar da ita, ta sunkuyar da kai har idanun sun cicciko da kwalla. "Don Allah ka yi hakuri, ba zan ƙara ba. In sha Allahu an yi na farko da karshe." Bai ce mata komai ba ya juya ya bar gaban madubin bayan ya gama abinda ya kai shi. Ramlat jikinta duk ya yi sanyi, ta sa hannu ta dauke hawayen da ya gangaro. Shi kuwa gogan, yana kammala shirinsa cikin kananun kaya ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi, ya fice. Ta bi bayansa da sauri ganin ya dauki mukullin mota, da wani irin gudu da ba ta san ta iya ba ta rigashi isa da ƙofar ta tare. Duban tsakar ido suka yiwa juna, kowannensu sai da yanayinsa ya sauya. Ba tare da ta dauke idanunta ba ta ce. "Don Allah ka saurareni, nayi maka laifi ka yi hakuri ka yafemin." Kamar ba zai tanka ba sai kuma ya kare tamke fuska. "Tun yanzu zan yi hukunci akan abu, ki nunan bai maki ba har ma ki goyawa wannan abun baya, wane irin kallo kike son na yi maki? Ke a yanzu sai dai ki ba wani labarin abinda ya gudana tsakaninmu da uban yaronnan, duk wannan ma bai min ciwo ba kamar yanda har kika iya take umarnina. Ko ban hanaki ba, tunda har kika ga na raba ta da wayarta kin san me nake nufi. Ban wuri na wuce." Maimakon ta matsa sai kawai ta noƙe kafaɗa gami da marairaice fuska, kallonta kawai ya ke yi. Daga yanayinsa ta soma fahimtar ya soma saukowa don haka ta sanya dukkan hannuwanta ta rungumoshi ta kwantar da kai a saman kafaɗarsa. "Ka yi hakuri, na tuba ba zan ƙara aikata laifi irin wannan ba. Please Haskena." Shirun da ta ji har ta fidda ran zai sauko, ta soma kokarin janye jikinta ya riƙo ƙugunta dakyau, fuskarsu ya haɗe wuri guda yana bin karan hancinta da kallo kafin ya maido idanunsa cikinnata. "Kinsan ba na iya fushi da ke ko?" Ta yi murmushi ta lumshe ido gami da gyaɗa kai duk a lokaci guda, a hankali kuma ya shiga aikamata saƙo mai kashe jiki. Karshe dai Hussein fitar da bai yi ba kenan, dama sanadin bacin ran da yake ciki ne ya tilasta masa son fita. Can ta janye jikinta ganin yanda ta matsu da jikin ƙofa. "What?" Ya fadi da dusasshiyar muryarsa. A shagwaɓe ta amsa. "Yunwa." Ya yi murmushi gami da ɗaga rigarta ya shafi cikin. Lumshe idanu ta yi. "Allah Yasa mun samu ƙaruwa." Ta harareshi da wasa kawai ta juya ta bude kofar, ya biyo bayanta don shi kansa yunwar ke cinsa. Sai da suka kammala ba cikinsu hakkinsa kafin kuma ya miƙe ya shiga ɓangaren Dada. Ramlat dai jikinta ya yi sanyi don har tausayin Hafsat ya kama ta, ta tabbatar yau kam Hussein ba zai ɗagamata ƙafa ba. Aikuwa hukuncin da ya dauka a kanta mai tsauri ne don har makaranta ya ce ta zauna sai ya yi magana sannan ta ci gaba da zuwa, amma fita dai ko nan zuwa farfajiyar gidan ce ya hanata. Ya kuma rantse muddin ta kara gangancin yin waya da Taheer sai ya saɓa kamanninta. Da wannan bakin cikin ya bar Hafsat ya fice abinsa. *** NIJAR-KANO Sun ɗau hanya miƙaƙƙa daga Maradi don dawowa Nijeriya, garin Kano. Zuƙatan kowannensu farin ciki ne marar misaltuwa, duk da irin wata azaba da su ke ji a tsakanin mazaunansu, hakan bai sa sun kasa yin murnar samun nasara ba. Kowaccensu ta matse kwalin aikin da ta karɓo a ƙasan ƙafafu, idan kuwa wuri ne mai gargada, sai su yi maza su riƙe dakyau a hannunsu. Har suka isa Kano tulun nan yana matse da su.   Gidan Hajiya Zeenatu aka soma zuwa, suka rabu da Hajiya Batool direba ya yi gaba da ita. Ma'aikatan na ta kallon Madam din tasu riƙe da kwali, abinda suke ta tunani bai wuce ko meye a cikinsa ba. Ita kuwa tana shiga ɗakin ta samu wuri mai kyau ta killaceshi. Yanzu gaba daya tunaninta shi ne na tafiya Adamawa a gobe-gobennan, don ta fi son komai ta yi shi da gaggawa sai dai kuma yanda ta ke jin bayanta naaa azabar da radadi da ciwo, dole sai ta ji sauƙinsa. Don haka ba ta zauna ba, bandaki ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi. Sai dai koda zamanta wani uban ƙara ta saki na azaba. Ranar dai wuni ta yi jiki ba dadi don har da su zazzaɓi. Haka ta samu labari daga Hajiya Batool, ita kam har wani ruwa ta ke fitarwa. Wasa-wasa zazzaɓi ya tsananta ga Hajiya Zeenatu, har washegari da ta ke fatan tafiya Adamawa, abin ya gagara. Dakyar ta iya daukar waya ta kira likitanta. Har gidan ya zo ta kira Emma a waya ta ba shi iznin a shigo da shi. Ya karasa har dakinta,  ya yi mata allura. Koda wasa ba ta bari ya san ɗaya ɓangaren na ciwonta ba, yana kammalawa ya fice abinsa. Aikuwa wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da ita. Ta fi awa hudu tana bacci, kafin ta farka, ba laifi ba kamar sadda ta kwanta ba, kusan ma babu zazzabin sai uban gumi da ta ke yi. Wayarta ta jawo, ta bude rututun missedcalls da ta gani na Manajanta mai kula da shagon gwal-gwalanta. Kafin ta gama shanye mamakin, wani kiran ya ƙara shigowa. Ta ɗaga da saurinta. "Hello! Hajiya, gobara! gobara ta cinye shaguna har da namu! Ga wuta har yanzu an kasa tsayar da ita!" Daga jin yanda ya ke zancen a matukar rikice ya ke don ba laifi shima yakan haɗa da nasa jarin ya juya. Wani irin miƙewa tsaye da Hajiya Zeenatu ta yi, sai ga ta a kan ƙafafunta, jikinta ko'ina ya ɗauki rawa, shi kenan dukiyar da ta ke taƙama da shi yanzun kaɗai a duniya. "Me ka ke cewa Bala? Me kake nufi wai?!" Inaa! babu kwakkwarar amsa, tana ta hello amma kamar babu service ga kuma hayaniyar jama'a ta cika wurin. Ai ko mayafi ba ta tsaya ɗauka ba, mukullin motarta kawai ta ɗauka ta fito hankali tashe. Ma'aikatan na ganinta suka nufota. "Hajiya lafiya?" "Ba za ku gane ba! Yi sauri budemin gate! Gobara a sabon gari!" Hakan da ta fada duk sai suka fahimci inda zancen ya dosa tunda duk sun sani tana da shago a sabon gari, wato dai an samu matsala, da sauri Emma ya karbi mukullin ya ce ta bari ya kai ta ba ta da nutsuwar yin tuƙi. Ba musu ta miƙa masa jiki na rawa ta koma mazaunin kusa da direba. A hanya kamar za ta yi tsuntsuwa, duk irin gudun da Emma ke shararawa ba ta gani. Tuni ta nemi ciwo ta rasa. Cunkoson ababen hawa da na yan sanda har ma da motocin kashe gobara, ya sa dole Emma sai wuri ya samu ya ajiye motar suka karasa da kafa. Hajiya Zeenatu na ganin yanda shagon ya ƙone ƙurmus babu abinda ya bari kawai sai ta faɗi yanke jiki ta faɗi. Nan fa mata da maza aka yi kanta, bakinta tuni ya karkace tana fidda yawu, idanunta kuwa kamar mai harara garke. Emma da ma wasu aka taimaka wurin daukarta zuwa asibiti, Manaja ya yi danasanin kiranta a waya sai dai hakkinta ne ta sani. Kusan ma akwai wadanda sai da suka sume, wasu kuwa banda kuka ba abinda suke yi kama su yi hauka. Asibiti kai tsaye Emma ya wuce da Hajiya Zeenatu cike da tashin hankali, Likitan dai da ya zo mata dazun, Dakta Salisu, wurinsa suka je. Ya yi matukar mamakin ganinta a cikin wannan yanayin, anan Emma ya labartamasa komai. Nan da nan likitoci suka rufu a kanta sai dai kuma  sun makaro, Hajiya Zeenatu an samu ta ɗan dawo daidai amma fa ta hadu da shanyewar ɓarin jiki hakanan tana magana a jagwalgwale miyau na kwaranya ta gefen bakin. Banda hawaye ba abinda ta ke yi, ba abinda ke yawo a ranta sai kudirinta na zuwa Adamawa. A yanda ta ke jinta, ko a wane hali ta ke sai ta je. Sai ta samu Hussein ko ta halin ƙaƙa. Nan kuma Dakta Salisu ya ba Emma umarnin sanarwa mijinta da yan uwanta, Emma nan take ya sanarmasa cewa Ogansu ya rabu da ita. Dama kaf dinsu sai da ya bisu da alheri kuma ya yi musu sallama da zummar ya tafi kenan. Ba su ji dadin hakan ba amma sun mishi murnar rabuwa da muguwar mata irin Hajiya Zeenatu, ko ba komai sun jima da sanin munanan ɗabi'unta da yanda Ogansu ke shakkarta. Ba wacce ta fado a ran Emma sai Hajiya Batool, ya san matar aminiyar Madam ce, don haka ya fice daga asibitin ya nufi gidanta.    Hajiya Batool na zaune tana jin wani mugun farin ciki yanda ɗanta ya kira waya yana sanarmata da cewa a gobe-gobennan zai taso saboda kewarta da ta cikashi, kuma a shirye yake da bin umarninta, dama ita kiranye aka bata, kuma har gshinan kwalliya ta biya kudin sabulu, ta kuma ci burin dole ta sanya ya saki Fa'iza ya auri wacce take so.  Ta kira wayar Hajiya Zeenatu ya fi a ƙirga don ta ba ta labari amma ba ta samunta, karshe ma ta ji wayara kashe. Tana shirin sake gwada kiran, sai ga Mai aikinta ta shigo tana sanarmata da batun zuwan Emma daga gidan Hajiya Zeenatu. Nan ta bada umarnin ya karaso, Emma bayan sun gaisa ya fadamata halin da Hajiya Zeenatu ke ciki. Hankalinta ya tashi ba kadan ba, ta kaɗu sosai. Ba shiri ta ce ya je za ta leka asibitin. A yammacin ta je, ta yi mamakin yanayin da ta riski aminiyarta a ciki. "Zeenatu! Ke ce haka?" Hajiya Zeenatu sai ido da kuma hawaye. Da harshenta wanda maganar ba ta fita sosai ta ce. "Ni..ce. Batool ki kai ni wurin Hussein." Hajiya Batool ta girgiza kai ta riko hannunta. "Ki bari ki warke, ki nutsu kiyi zamanki a asibiti a dinga yi maki magani tukunna. Zan turo Dije ta dinga tayaki zama, za ki warke. Da kafarki za ki je wurin Hussein." Hajiya Zeenatu dai sai hawaye, a ranta kawai bakin cikin abinda  ya faru ta ke ji, da ace ta san hakan za ta faru da tun farko ba ta amsa wayar Manaja ba balle ta je kasuwar. Ji take inama ta kama hanyar Adamawa. Ta kara kallon Hajiya Batool dake ba ta labarin dawowar da ɗanta zai yi, haka kawai maimakon ta tayata farin ciki sai ta ji hassada da kishi sun kama ta, wato aikin Hajiya Batool har ya yiwu ita kuwa babu ɗaya da ta aikata, don aikin tulun ba zai yi tasiri ba sai ta je ta barbaɗawa Hussein hodar da Buzu ya ba ta. Haka tana ji tana gani Hajiya Batool ta fice daga asibitin gami da jadddamata za ta turomata Dije. Ita dai Hajiya Zeenatu gyada kai kawai ta yi, a yau ta ji takaicin rashin ajiye ƴar aiki mace da ta yi. ***   ADAMAWA Baƙin Kano sun sauka lafiya a family house, suka yada zango a ɓangarensu, wannan karon ma an musu tarba sai dai ba kamar yanda aka saba ba. Kawu dai jikinsa duk ya yi sanyi, a ranar da yammaci ya tara manyan dattawan gidan maza da mata yana kuka yana roƙar gafararsu. "Sharrin shaiɗan ne, ku yafemin domin Allah. Itama Aminar da yaran yanzu zan je na nemi afuwarsu." Kowa kam ya yi farin ciki da jin hakan,  ko ba komai har da rashin nadamarsa ne ya ba mutane haushi. Nan dai bisa jagorancin wani ɗan uwan Babansu, Surajo, tsoho mai ran ƙarfe, suka ɗunguma har iyalin Kawun, a yammacin zuwa gidan Dada. *** Kwance yake saman doguwar kujera, yayinda ta ke kwance saman kirjinsa. Sai cuku-cukun miƙewa ta ke yi sakamakon raɗan da ya ke mata a kunne amma hakan ya gagara. Ta ko'ina ya matse ta gam! Ai kuwa bai yi aune ba, yana kai bakinsa saitin nata, ta yi azamar kama leɓensa na ƙasa ta ciza. Bai san sadda ya sake ta ba gami da kama baki. "Aush!" Ramlat na dariya ta mike, daga ita sai riga sky-blue marar nauyi, da kaɗan ta wuce gwuiwarta. Gashinta wanda tuni ta warware kitson yana tufke a baya. "Sorry." Ta fadi tana ɗaga yatsunta bayan ta ja baya sosai tana dariyar mugunta. Hussein ya lashi leɓensa ya manna mata harara. "Zan kama ki, yau ba mai kwatar ki." Ta narkar da fuska. "Haba don Allah Haskena, kai ɗin ne ka ƙi hakuri ka bari na kammala girki. Nikam kana sane ka ce sai wani satin za ka fara zuwa aiki. Don.." Ganin ya yi wani irin miƙewa ya na kokarin cafkota ya sa da wani irin gudu ta shige kicin ta rufe tana dariya. Ya jingina jikin kofar. "Za ki fito ki same ni, na san maganinki." Murmushi kawai Ramlat ta yi mai bayyana haƙora ta ƙarasa wurin tukunyar miyarta, ba don na wutar kaɗan-kaɗan ta ke ci ba, ta tabbatar sai ya ƙone. Shi kuwa gogan yana shirin komawa ya zauna, aka kwankwasa ƙofar falon da sallama. Ya amsa da ba da umarnin shigowa. Hafsat ce, gaba daya jikinta a sanyaye. Ya dube ta fuska a tamke don har lokacin bai gama saukowa daga fushinta ba. Ta gaida shi ya amsa ciki-ciki. "Dada ce ke kira." Ya gyaɗa kai kawai ita kuwa ta miƙe ta fice kirjinta na dukan tara-tara. Tana tsoron abinda zai biyo baya idan ya ga waɗanda suka zo gidan. Sanin halin zuciya irin nasa ne yasa Dada kiran AlHassan a waya akan ya zo gidan bayan ta mishi bayanin komai. Wannan yasa ba ɓata lokaci, AlHassan ya kamo hanya don ba tazara sosai tsakaninsu. "Heart, bari na je Dada na kirana. Kinji ko?" "Toh." Ta amsa ba tare da ta buɗe ƙofar ba. Ya gyara zaman brown tshirt dinsa ya zura silifas dinsa baƙaƙe na maza na yawo a gida ya fice. Tun a farfajiyar gidan ya ci karo da motoci, wannan ya ba shi mamaki ya tabbatarwa kansa baƙi suka yi, amma daga ina? Shi ne tambayar da babu amsarta a yanzun. A ƙofar falon ya ci karo da takalman maza da mata. Haka kawai ya ji gabansa ya fadi da sauri kuwa ya karasa ciki da sallama. Idanunsa bai sauka kan kowa ba sai a kan mutumin da ya fi tsana nan duniya zaune kusa da Dadarsa su na kuka. Ya fahimci komai, ya gane kuma Dada ta sauko ta yarda da dukkan ƙarairayin da ya shiryamata don haka shi ba shi da bukata. Tsigar jikinsa gaba daya ta tashi tsabar ɓacin rai, yayinda idanunsa suka kaɗa, ya ƙaraso ciki da zummar ƙarasawa kai tsaye ga Kawun ya shaƙe wuyansa babu ko tunanin yaransa da ke zaune a falon. Da sauri Baffa Surajo ya mike ya shiga tsakani. Ganin girma da cikar haibar dattijon mai tsananin kwarjini ya sa shi kasa ƙarasawa sai hawaye da suka shiga zubowa kawai daga kwarmin idanunsa. "Me ya kawo shi nan?" Baffa Surajo ya dafa kafaɗar Hussein kafin ya ja hannunsa ya bishi suka zauna saman kujera dakyar. Hussein banda girgiza ƙafa ba abinda ya ke yi yana hararar inda Kawun ya ke, ganin haka Baffa ya riƙe ƙafar. "Ya isa ɗana. Ya isa." Kawu ya taso zai ƙaraso inda Hussein ya ke, da wata irin tsawa ya dakatar da shi. "Kar ka sake ka ƙaraso nan! Kar ka yi wannan gangancin!" Daidai da shigowar AlHassan da sallama, ya kalli mutanen falon ya kuma dubi Hussein mai magana ya sauke ajiyar zuciya. Ya san dama hakan za ta iya faruwa, bai ma yi tsammanin zuwan wannan ranar nan kusa ba, sai dai Allah ne Mai shiryarwa. Ya karasa ya gaisa da Baffa Surajo da matan Kawu har ma Kawun. Ya koma gefe ya zauna gefen Hussein. "Ka yi hakuri mu ji ta bakinsa, ya riga ya zo kuma da iyalinsa baki daya, ka tuna, idan shi ne ya yi mana laifi, iyalinsa ba su da laifi tunda shi ne shugabansu." Da kalamai irin haka Baffa da AlHassan suka taushi zuciyar Hussein. Ya yi shiru bai kara magana ba, wannan ya ba Kawu damar soma magana cike da jin wani tsananin kunya, wato wannan a duniya kenan ma, ina ga na lahira? Allah Ya tsaremu. "Ku yi hakuri, ku yafemin. A ƙiyayyar da na nunamaku har da sharrin zuciya da shaidan. Na sani, Innarmu a baya ita ce kan gaba wurin ƙara rura wutar ƙiyayyarku a zuƙatanmu,  sai ya kasance ni abin ya zame min ciwo domin kuwa ya juye zuwa hassada da tsana. Ban ƙara jin tsanar Amina da Aminu ba, sai bayan auren Amina da mutumin da nake ganin ban kama ƙafar arzikinsa ba. Wato dai Marigayi Naziru, ban kuma gama farfadowa daga wannan bakin cikin na ci gaban da Amina ta samu ba a rayuwa, sai ga Aminun da muke tunanin ma ya mutu, ya dawo. Tun kan ya zo Kano wurina, labari ya riskeni, na yi bakin ciki sosai, Karime kanwarmu ta fadamin da murnarta ni kuwa ban ga abin murna ba a dawowarsa musamman da naji labarin ai rayuwa ta mishi kyau ya dawo har da matarsa da kuma yaransa ƴan biyu. A wannan halin sai ya kawomin ziyara duk kuwa da tarin kiyayyar da nake mishi, sai dai na gasamishi baƙaƙen maganganu wanda har ya mutu a lokacin ban yi dana saninsu ba sai ma dadi da naji a lokacin ganin ya bar min filin duniyar na ci karena babu babbaka." Kawu ya numfasa saboda kukan da ya shaƙe shi, iyalinsa da su Dada kuka suke yi cike da mamakin irin wannan salon ƙiyayyar da bawan Allahn ke yiwa ɗan uwansa na jini. Shi kuwa Hussein ba zai ce ga yanayin da yake ciki ba, sai dai ko kallon Kawun ba ya son yi. Kawu ya ci gaba da magana bayan ya sharce majina. "Bayan shekaru da dama, a wani ziyara da Amina kika sa Husseini ya kawomin, lokacin ya samu hutun karatun da yake yi a Dubai. A wannan zuwan ne yaron ya ban tsoro har nake ganin nan gaba zai iya cin mutuncina a gaban ko su waye. Saboda tunda nake da ke da Aminu, babu wanda wuyansa ya taɓa yin tsaikon da zan faɗa ya faɗa, sai Husseini, ko Hassan bai taɓa yimin cin fuskar da nake ganin  Husseini ya yimin a lokacin ba. Wannan ne dalilina na farko da na ci alwashin sai na tarwatsa rayuwar Husseini. Sai ya rasa dukkan farin cikinsa. Sai dai me? Kafin na kai ga aikata duk wani abu da na yi niyya, na samu labarin ɓacewar Husseini, ya gudu ya bar gida ba'a san inda ya shiga ba. A lokacin idan ka tona zuciyata banda tsananin farin ciki babu abinda na ke ji, har addu'a nayi Allah Ya dauki ransa ma. Bayan watanni uku da ɓacewar Husseini, wataranar lahadi ba ni mancewa, ni da kaina ke tuƙi a mota daga kasuwa zan koma gida, a hanya na hangi wata tsohuwar kwastama ɗita, a baya takan zo ta sararwa Hajiyarta atamfofi a shagona ko kuma yadika na maza ta tafi, a sannan tana budurwa ko kuma nace mace mai zaman kanta amma a karkashin ikon wata Hajiya mai safarar yara zuwa Makkah da sauran ƙasashen waje don aikatau ko akasin haka. Zeenatu kenan, tun a baya Hajiyar ta sha  aiko ta shagona tun ban kai ma ga auren ita Maimuna ba, (Anti Amarya), tun a wancan lokacin muka saba, nakan ba ta shawara akan ta yi aure gudun kar ta ɓata rayuwarta don ni nasan wace ce Hajiya Balki uwar ɗakinta, saboda na sha zuwa gidan muyi cinikin kaya ta siyawa ƴan matan yaran da ke gabanta ko kuma ta siyar, na kuma san irin kalar sana'arta. Daga baya kuma sai na bar ganin Zeenatu, sai wata Raliya ake turowa. Koda na tambayi Raliya, ta bani tabbacin ai Zeenatu ta tafi Makkah, a sannan na ji ba dadi kwarai don ban so ta cuci kanta ba sai dai dama daga yanayin Zeenatu na fahimci maganata ba wani shigarta ya ke ba." Kawu ya numfasa, nan kuma dai dakin tsit ya yi babu mai kuka sai jin wannan labarin mai ban mamaki daga bakin Kawu. Ya ɗora zancensa. "Ganin da na yiwa Zeenatu a haɗaɗɗiyar mota, bai sa na kasa ganeta ba, asalima fuskarta ko kaɗan ba ta sauya ba duk kuwa da ɗumbin shekarun da aka ɗiba. Parking ta yi a gaban wani katafaren shagon siye da siyarwa na maƙulashe, na juya kan mota da sauri na faka a gefenta. Sai dai ban kai ga fitowa ba, idanuna su ka sauka akan Husseini, ba karamin razana nayi ba, sai nake ganin abin kamar a mafarki, fuskokinsu kadai ya nuna suna cikin tsantsar farin ciki. Ban karasa ba, har suka shiga suka fito, mantuwa suka yi ko mene? Ban sani ba, na ga Husseini ya fita ya koma ciki, har zan je wurinta sai naji tsoron kada ya fito ya gan ni, sai kawai na koma cikin mota na jira har ta tashi motarta ta kama hanya ta bar wurin, na bi su a baya har suka isa gidansu. Koda na ga gidan kawai sai na juya da zummar zan dawo na same ta don ba na kaunar Husseini ya gan ni. Bayan kwanaki biyu, a wani yammaci na isa kofar gidan, cikin saa na isketa tana kokarin shiga cikin kyauren, ganin ita kadai ce na yi hon ta juyo, ni kuwa na ja na tsaya na fito. Ta shiga bi na da kallo kamar na neman ƙarin bayani da kuma son tuna inda ta san fuskar, nan take ta tambaye ni. "Kamar na sanka." Na ba ta amsa da eh, kafin na ce kin manta Modibbo na Kwari? Nan da nan ta saki fuska muka kara gaisawa. Na ce "Yaushe kika dawo?" Nan ta ke sanarmin ai ta kai shekara guda da dawowa, daga nan kuma na nemi mu keɓe don mu tattauna wata muhimmiyar magana. Sai dai na tambayeta ko akwai wani saurayinta a ciki? Idan akwai na juya.  Ni kuma na dadi haka don na gane irin zaman da suke yi da Husseini, burina ta cemin ba zaman aure ba ne. Abin ya ba ta dariya. "Aa ai kuma yanzu an girma da wannan kalar rayuwar, aure nayi."  Na jinjina kai ina murmushin da bai kai zuci ba don ba haka na so ba. Sai dai ina bukatar mu zauna na ji bayani sosai. Koda muma shiga ciki, ta sanya aka kawomin lemo da ruwa, abinci kuma na ce aa. Bayan mun nutsu na kara kai duba ga hoton Husseini da ita wanda tun shigowata ya dauken hankali, shakka babu aure ne suka yi. Anan na sanar da ita gaskiyar alaƙarmu da Husseini, a farko ta razana sosai har ma ya ɗaure fuska tamau. Nayi dariya sosai na ce ta kwantar da hankalinta ina bayanta domin ba na shiri da iyayensa, don haka ni ko nan da bangon duniya ma tana iya kai Husseini muddin ba za'a gan shi ba. Faɗin hakan keda wuya ta kwantar da hankalinta saboda na biyomata ta sigar da dole ta samu nutsuwa. A karshe ta ban labarin duk yanda aka yi na dinga dariyar mugunta. Ni kuma na yi mata alƙawarin ko na ji ana raɗe-raɗin an gan shi zan sanarmata, zan kuma yi asirin da zan rufe bakin duk wanda naji yana raɗe-raɗin ya ga ko mai kamarsa ne a kwaryar Kano. Na kuma kara mata da cewa dole tana bukatar asirin da zai kara jin nan duniya ya tsani a tayar da zancen danginsa ko a tambayeshi, amma ta bar komai a hannuna. Wannan ne abinda na san na aikata, ya kasance ana neman Husseini, ni kuma nasan inda ya ke, amma na yi gum. Shiyasa koda Ramlatu ta zo da zancen Husseini, na kore ta na ce ba ruwana. Ban yi ƙasa a gwuiwa ba na sanar da Zeenatu, nan muka ce kawai a kashe ta yanda babu wata hanya da za'a san labarin komai. Sai dai kuma abinda Allah Ya riga ya tsara, ba wanda ya isa dakatar da shi." Kawu Modibbo na kaiwa nan ya dakata ya ci gaba da kuka sosai. Falon banda salatin da Baffa Surajo ke maimaitawa cikin zubar hawaye, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan yaran Kawu Modibbo. "Ku yafemin, ku yafemin don Allah. Na tsaneku akan ba ku aikatamin komai ba, na cutar da rayuwarku. Na hana yarana zumunci da ku duk don bana kaunarku. Ku yafemin. Husseini ka yafemin, Aminatu, Hassa.." Ya kasa ci gaba saboda kuka, Hussein kawai miƙewa ya yi ya bar falon, Baffa ya yi nasiha mai ratsa jiki gami da nuna ladan da ke tattare da wanda ya yi hakuri. Dada nan take ta yafemasa, ta ce komai ya wuce, hakanan shima AlHassan. Wannan abu ya yiwa Kawu da iyalinsa dadi, itama Hajja Fatuma ta nemi gafarar Dada na yanda ta dinga wulakanta ta ita mai miji dadi, Dada na murmushin da ya fi kuka ciwo ta ce babu komai ya wuce. Haka dai aka yi ta neman yafiyar juna.  Taheer sai satan kallon Hafsat ya ke, ita kuwa gaba daya kunyarsa ta ke ji, a gefe guda tausayi da kaunar dan uwanta Hussein ya kara mamayeta, wato dai shi ya san dalilinsa na tsanar Kawu. Ashe mugun abu ya ƙulla masa har haka. *** Ramlat da ba ta san hawa ba ba ta san sauka ba, ta ga mutum ya fado falon, kallo daya ta yi mishi ta gane ba lafiya. Ya zube saman kujera ya runtse idanu, fuskarsa abinka da farar fata ta koma jawur da ita. Ta shiga ambaton Allah a ƙasan ranta, miƙewa ta yi ta zauna gefensa, ba ta ce komai ba amma ta kamo tafin hannunsa ɗaya tana murzawa a hankali, a ranta addu'oi kawai ta ke karantomasa. A hankali kuma ya shiga sauke ajiyar zuciya, ya bude jajayen idanunsa ya dubeta. Sai da ta ji gabanta ya fadi, gaba daya sai ta tsinci kanta cikin damuwa mai tsanani. "Lafiya Haskena?" Gyara zama ya yi, bai ɓoyemata duk abinda ke faruwa ba, kawai sai ta shiga hawaye tana mamaki da tsoron lamarin mutum. Idan naka ya yi maka haka, ina hujjar da za ka ji haushin wani don ya yi maka? Sai kuma ta fahimci kuskurenta, hawayen ba zai ƙarar da Hussein da komai ba face ya kara ganin girman laifin da Kawun ya mishi har ya kasa yafemasa. Don haka ta yi azamar sharesu, ba ta kai ga magana ba sai ga AlHassan ya yi sallama ya shigo, Dada tafe a bayansa. Ta mike da sauri tana musu sannu da zuwa, Allah Ya taimaka ma tun fitarsa ta suturta jikinta sakamakon shanyar da ta kwaso a bayan gidan wurin shukoki. Ta gaida su Dada, Dada ta amsa fuska a ɗan sake. Sai dai itama fuskarta kamar na Husseini, ta yi ja, kuka kam ko ba'a faɗa ba sun yi shi, balle AlHassan. Za ta shige ɗaki, Dada ta hanata, ta bata umarnin zama. Shiru ya ɗan biyo baya. A hankali kuma Dada ta shiga yiwa Hussein nasiha, sosai ta ke yi mai ratsa jiki tana kawomishi misalai na irin hakurin da Annabi s.a.w ya yi da yan uwansa da ma sauran mutane. "Ka yi hakuri ɗana, ka yafemishi, idan ba ka yafe ba, da me zai ƙare ka? Me kake nema a duniya yanzu da Ubangiji bai maka ba? Babu shi, ka saka a ranka ba yanda ka iya, haka Allah Ya so ya jarabceka kuma Ya jarabta. Idan har na isa da kai, kuma har zuciyarka kana jin za ka iya yafewar, domin Allah muje ka fadi ya ji da bakinsa ka yafemasa." Hussein wanda gaba daya jikinsa ya yi la'asar, ba shi da sauran kataɓus, miƙewa kawai ya yi suka fita tare da Dada zuwa sashinta. Ta ba Ramlatu umarnim biyo ta, hijab kawai ta sanya ta bisu a baya. Kawu ya yi murnar sake ganin Husseini, da kansa ya mike jiki na rawa ya kasa gareshi ya rike hannunsa, kawai sai ya soma kokarin durkusawa yana kuka. Da sauri Hussein ya rike hannunsa ya ɗagoshi tsaye. "Ya wuce Kawu, na yafemaka a bar zancen haka." Ba wanda kalaman Hussein bai wa dadi ba, Ramlat ta gaishesu, itama dai gafararta Kawun ya nema, take kuma ta ce ba komai ya wuce. Nan fa gida ya yi dadi amma Hussein bai wani sake sosai ba, sai da aka yi Magriba kafin su Kawu su wuce, Baffa Surajo ya ce lallai gobe duka a hadu a babban gida yana neman kowa da kowa. Ya bada umarnin a sanarwa wanda ba ya nan, na nesa kuwa a rabu da su. Da wannan komai ya wuce. *** Washegari kuwa misalin karfe biyu, Baffa Surajo ya haɗa taron da kowa na zuri'ar Gidado dake a Adamawa ya hallara. Bayan addu'a da doguwar nasiha, ya ba Kawu damar neman afuwan yan uwansa. Nan Kawu ya ba kowa hakuri da kuma daukar alkawarin ba zai kara aikata ko makamancin hakan ba. Kowa ya ji dadin hakan kuwa, karshe kuma ya nemi alfarmar haɗa auren Taheer da Hafsat, nan take Dada ta ce ita ba ta da ja. Hussein zai yi magana ta harareshi, murmushi ya yi. "Cewa zan yi an bayar." Maganar ta ba kowa dariya, Baffa Surajo ya yi mishi daƙuwa. "Ai ba kai ke da alhakin bayarwar ba." Bai ce uffan ba, Hafsat kuwa ai kamaran mata albishir da gidan aljanna. ***    MURFI.... I just published "BABIN ƘARSHE" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1035704431?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=ahGlFX6GFRN4rYLxQybIWR9WrkgGWE36szhMfA7kRFxFwQXwS03Sgp8YSmnHzMO1lgoFTgL30%2Brf0xbkWKei5hlm6ZnndGuZExstbOwboUAs%2BBmTygvZgHsBmhnEg64g 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️ _Rufaida Umar_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. *BABIN ƘARSHE* ADAMAWA BAYAN WATANNI BIYAR.. Amarya Ramlat ta kara kyau da ƙiba sai dai ba irin mai munin nan ba. Sanye take cikin doguwar riga na leshi lemon green an mata dinkin bubu, ta fito daga motar yayinda Hafsat da Rasheeda suka  yi gaba niƙi-niƙi da kaya, ita kuwa tare suka jera da Kausar rike da wasu ledojin. Dawowarsu kenan daga kasuwa, zuwa lokacin sun yi nisa  da shiryen-shiryen bikin Hafsat har ma da Rasheeda wacce za ta auri ɗan Barrister Hansatu (Babbar Yayar su Kawu Modibbo), Mujaheed. Tun da suka rubuta jarrabawar karshe kasancewar tare suke tafiya da Hafsat a karatu, sai Rasheeda ta tubure ta ƙi zaman Kano, ta dawo gidan Adamawa wajen Dada ta yi zamanta. Wannan abu ya yiwa Dada dadi, wai yau ta budi ido ta ga jinin Kawu Modibbo a gidanta, kuma da son ran mahaifin, sai ta ji inama ɗan uwanta baban su Hussein na raye ya ga ranar da ya dinga ce mata za ta zo in sha Allah, ashe kuwan tana tafe. Hamida babbar ƴar Dada wacce aure ya lula da ita har Saudiyya, ta jima rabonta da ƙasar don ko Ramlat tsakaninsu sai dai ta waya ko kuma idan ta kira Hussein videocall suke gaisawa. Ta dube su da kulawa tana ba karamar ɗiyarta Mama. "Sannunku da zuwa. Kun sha wunin kasuwa." Suka yi murmushi lokacin da kowa ke kokarin zama. "Wash!" Fadin Hafsat tana mai kwantar da kai jikin Dada. Ture ta Dada ta yi. "To raguwa, ni matsa ki ban wuri. Gwara ma ki tattara ki bar gidannan ko na huta." "Aa Dada, ina hutu ba kya ganin Auta? Faɗa dai ki ke yi." Cewar Adda Zahra, mai bi wa Hamida, ita a Lagos ta ke da zama. Aka yi dariya. Haka kuma aka shiga bude kaya ana ganin siyayyar da suka yi na abinda ya yi saura na tarkacen kayan girki har ma da sauran kayan kicin da ba'a siya ba. Sosai an yaba da kayan, sai da suka ci abinci kafin Ramlat ta koma sashinta. Wanka kawai ta yi don wani irin zafi ta ke ji, ta sanya kananun kaya riga da siket marasa nauyi kafin ta faɗa kicin. Lissafi ta shiga yi a ƙasan ranta, su Rafee'ah bai fi saura kwanaki shida su zo ba saboda biki. Ta ƙagu ta ga yaranta da kuma Aisha da babynsu. Ta shafi cikinta kaɗan tana murmushi, tana burin Allah Ya ba ta haihuwa ko don ta ga kalar farin cikin Hussein wanda yanzu koyaushe ba shi da zance sai na baby, baby. Haka dai Ramlat tana aiki tana tunane-tunanenta. Sai da ta yi nisa, sai ga Kausar ta shigo, itama kam ciki ne da ita wata uku. Sallama ta yi mata akan za ta tafi, har ƙofa ta yi mata rakiya. "Kai aa ki koma hakanan, ga mijinki can na baro sashin Dada, idan ya ganki haka kin fito ai ni zai ɗorawa laifi." Ramlat ta yi dariya, sai yanzun ta tuna da kalar suturar dake jikinta. Ko ba komai daga rigar mai hannun vest har siket din wanda yake dogo amma kamar roba, duk sun matse ta. "Toh Maman Twins, Allah Ya saukeki lafiya. A gaidamin da Fatina sosai." "Twins dai yana jikinki Madam, amma ba ni ba. Ki bar yimin wannan fatan. Fati kuma za ta ji sosai." Ramlat abin ma ya ba ta dariya, tana mamakin yanda Kausar ke gudun twins. Ita kam da ace za ta samu tana son abinta. Anan dai suka rabu ta koma kan aikinta. Babu jimawa Gogan ya shigo. Ganin tana kicin kawai ya nufi ɓangarensa ya watsa ruwa. Duk tana ji, Allah Ya taimaka dama girkin ƙarashe ne don ta dafa markade ta kuma yi tafashen kazarta kafin su wuce kasuwa. Wannan yasa kawai miyar ta haɗa ta kuma dafa kuskus da ya sha karas da koren wake. Komai ta haɗa a gaggauce ta kawo falon ta jera saman ledar cin abinci. Ƙamshinsa ya soma dukan ƙofofin hancinta, ta ɗaga kai ta kalleshi. Wando ne mai jikin cotton ya sanya sai farar tshirt mai gajeran hannu. Koyaushe Hussein ƙara kyau yake yi a idanunta, kullum ƙuruciyarsa ta ke gani. Har kullum idan zai fita daga gida hakanan sai ta ji wani kishi ya kamata. A kwanakin baya sai da ta kwashi takaici sadda wata Meena ta matsa mishi da kira, hankalinta bai kwanta ba sai da ya tabbatar mata babu komai tsakaninsu karshe ma ya rufe Meenar ta yanda babu damar da za ta ƙara kiransa. Da wannan ya samu hankalinta ya kwanta. Har ya ƙaraso ta shagala ba ta ko lura ba sai da ya kai hannu ya shafi mafi soyuwa a wajensa. Ta dawo hayyacinta ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda ta ɗan harareshi da wasa gami da murguda baki. Ya shafi lebbanta da yatsa hana murmushi. "Ni kike wa haka? Tunanin me kike?" "Ba komai." Ya matso da ita jikinsa ya kwantar da kanta saman kirjinsa. "Ko? Faɗamin gaskiya Malama." Ta lumshe idanu tana shaƙar ƙamshinsa mai sanyamata nutsuwa. "Dagaske fa ba komai. Tunaninka nake yi." Ya sumbaci saman kanta yana murmushi. "Uhum, faɗamin, me kike tunani alhalin ni ɗin naki ne." Ta yi wani tattausan murmushi a hankali ta ɗago kai har hancinta na gogar sajensa. Suka dubi juna. Ya ja karan hancinta. "Ko ba haka ba?" "Hakane." "To kin gani, me zai dameki?" Ta jinjina kai kawai ta murmusa. Nan kuma ta zubamishi abincin, koda ta ce ta ci bai matsamata  kan lallai sai ta ci ba. Haka dai a kwanakin nan kusan kullum sai sun fita siyayya, sai da suka jera kwanaki uku, kafin Hussein ya murtuke ya ce abin ya ishe shi. A gaban Dada aka yi, suna zaune ne sai ga Waleeda cikin shiri ta dubi Ramlat. "Adda Amal, muje ko?" Ya haɗe fuska, ita kuwa Ramlat da ido ta nunamata Hussein alamar bai yarda ba. Waleeda ta dubeshi baki sake sai dai tuni ta haɗiye abinda ta yi niyyar faɗi dalilin kallon da  ya yi mata. Dada ta dara. "To kai Husseini banda abinka, ai fitar ta su ce, ɗinkinsu za su kai. Ka yi hakuri su je a auna su." Ya mike zaune. "Aa bari na aunata sai ita Waleedar ta kaiwa telan. Ba shikenan ba?" Kunya ta kama Dada, ba ta kara uffan ba ta mike ta yi daki, Hussein dama ba yau ya saba ɓaram-ɓaramarsa ba. Ramlat da ta ji kamar ta nutse ta rasa bakin magana. Waleeda dake dariya ciki-ciki ta dubeshi kawai yayinda Hamida ta hau dariyarta sosai a fili don kusan sa'anni suke da ƴan biyu. Sai da ma ta faɗo duniya da watanni biyu aka haifesu. "Me na ce ne?" Ya furta yana neman ba'asi ganin Dada ta mike ta yi daki, su kuwa na falon na dariya. "Au ba ka san me ka ce ba kenan? To ai Dada wuri ta ba ka idan ka auna matartaka sai ta dawo." Ya taɓe baki yana yamutsa fuska. "To meye a ciki? Dada dai ta so jin kunyarta ne. Idan muka haifamata jikoki ta daina. Tashi ita kuma wannan ta ɗauko abin awo." Ramlat ta mishi wani irin kallo kamar ta yi kuka. Ya yi murmushi ya girgiza, kallon ya ji shi a dukkan wata gaɓa ta jikinsa. Miƙewa ya yi ya mata duban zan haɗu da ke kafin ya musu sallama ya fice wurin aiki, lokacin goma da ƴan mintuna. "Dagaske dai mijinki bai bari ba. Ai shikenan, kawai ki ɗauko rigar da za ta yi maki daidai a yi amfani da ita." Waleeda ta faɗi tana murmushi. Kafin Ramlat ta ce wani abu sai ga kiransa. Ta ɗaga da sallama. "Kwalliya ta biya kuɗin sabulu, amma kallon da aka yimin yanzu idan na dawo zan zauna a yimin sau ɗari. Kuna iya tafiya, Allah Ya tsare. Drive carefully." Daga haka ya katse kiran bai jira cewarta ba, ganin yanda ta ke zabga murmushi yasa Hamida kallonta. "Ya bar ki kenan ko?" Ta gyada kai, suka yi dariya. Mikewa ta yi ta koma bangarenta, mayafi kawai ta dauko sai jaka da mukullin mota ta rufe ko'ina. Koda ta dawo, Dada na zaune ta dawo falon. Sallama suka yi mata suka wuce. Wani tsadadden leshi da ya haura dubu ashirin, iyakarsu ne kawai, iyalan Dada, surukai da kuma ƴaƴa, ranar Dinnerparty zasu sanya. Sai atamfar da zaa sanya ranar wuni gaba daya dangi. Sai kuwa wata shadda ta Ramlatun da za ta sanya ranar ɗaurin aure. ***   Ana gobe za'a sanya Amare a lalle ne, ƴan Kano suka iso, dama iyalan Kawu Modibbo tun ana saura kwana uku suma dira. Ramlat ta rasa inda za ta sanya su Rafee'ah don murna. Ga yaranta, Affan ya zama babban mutum, ba kuka sai ma yawan sunkuyar da kai wai shi a dole mai kunya. Yaran sun yi wata irin ƙiba da kyau ga murjewa. Ta dauki Babyn Aisha, kyakkyawa da ita, sunan Mahaifiyar Hisham ta ci su na kiranta da Afnan. Kyau kam wane iyayenta. "Ke kina ta cewa wasu sun yi kyau, kina kallon kanki kuwa a madubi Ramlat? Lallai aurennan ya karɓeki tubarakAllah." Maman Twins ke maganar tana kallonta sosai. Nan fa sauran suka shiga tofa albarkacin bakinsu, ba wacce zuwanta ya ba ta mamaki sai Bilkisu don ita Hunainah ba ta zo ba saboda laulayin ciki na biyu da ta ke yi, ba ta jima da haihuwar ɗanta ba kafin ta kai ga yin wani tsarin iyalin sai ga ciki. Bilkisu kuwa wata uku kenan da dawowarta gidan Muniru, nan ma sai da ta sha baƙar wuyar rayuwa a gidansu, ta duba ta hango babu rayuwar da ta fi ta gidan mijinta dadi wannan yasa dakyar da siɗin goshi ta lallaɓa Muniru har ya sauko ya maidata ɗakinta. Tun komawarta musamman ganin su Yasmeen babu wani alamar wahala tattare da su, sai ta yi sanyi, ta kuma karɓi Hunainah hannu bibbiyu suka zauna lafiya. Hussein sosai ya ke jan yaran a jiki, wani irin so da kaunarsu ya ke ji na musamman a ƙasan ransa har yake ji inama daga jikinsa suka fito. Ya yi amannar son da ya ke musu, ko mahaifinsu sai hakan. Ramlat kuwa banda murmushi ba abinda ta ke yi, ganinsu tare na karamata annashuwa.  A ranar dai da kansa ya ce ta kwanta tare da yaran, ya tabbatar ta yi kewarsu. Washegari aka shiga cikin biki, komai ya tafi cike da tsari. Ranar babu batun anko don kowa kayansa ya sanya, a rana ta biyu ne suka gudanar da yini da rana wanda kowaccensu ta sha ankon atamfa har su Aisha mutan Kano, don tun kafin su zo Ramlat ta aikamusu hoton ankon suka ɗinka. Tun soma sabgar biki ba ta da wani lokacin kanta balle kuma na Hussein, hira ta ragu sosai a tsakaninsu. Sai dai ta kai mishi abinci, zaman da za ta yi wurinsa bai fi na mintoci ba. Wannan abu ya kai Hussein bango, gaba daya ma sai ya daina bari su haɗu. Da daddare idan ta leƙo, ya rufe kofar gam, da safe kuwa duk irin sammakonta ya fice daga gidan, waya kam  ko ta kira bai ɗagawa. Text na duniya ba ya kulata, sam ya kasa yi mata uzurin tana da baƙi kuma su na hidimar biki. Wannan damuwar ta sa a ranta, shiyasa ko ranar da ta kama na dinnerparty, kasa wani kataɓus ta yi. Tana zaune tana kallon kowa na shiryawa, maganar duniya su Zulaihat da su Kausar sun mata akan ta tashi ta shirya amma ta ce sam ta fasa. "Adda Amal kina cewa ba za ki je ba, ga Hamma Hussein can ya ci uban kwalliya ya fita, kuma wallahi idanun ƴanmatan nan kamar su tsiyaye tsabar kallonsa." Jin abinda Falmata yar uwar su Hussein ta Maiduguri ta fadi, ai sai Ramlat ta mike tsaye ranta na susa. Nan aka kwashe da dariya, har itama ta murmusa. "Kishi kumullon mata, ki zauna dai kar ki je. Wallahi sai dai ki ji ana wani labarin." Ita dai Ramlat ba ta biyewa zancen Rafee'ah ba ta shiga bandaki bayan ta rage kayan jikinta, tana ji su na mata dariya. Wanka ta ƙara yi duka rabin hankalin na ga tunanin Hussein, abinka da zuciya, sai nan da nan ta ji itama ai ya mata laifi, ta ji ya bata haushi sosai. Kwafa ta yi tana ƙara cuɗa sabulu a jikinta, aikuwa ta ci alwashin itama ko kallo bai isheta ba a wurin taron. Ta fito ta shirya, da yawansu sun fice har su Rafee'ah da maman Twins.  Aisha da Falmata da kuma Asma'u diyar Hajja Fatuma uwargidan Modibbo sai wata Hannatu itama daga Maiduguri, su ne kadai suka yi zaman jiran Ramlatun don su wuce a motarta.    Leshinta da suka yi anko kalar milk kai adon golden brown ya yi masifar sama a jikinta, ya sha aikin stones shi ta fiddo ta zura. Falmata ta yi mata make-up na fitar hayyaci, kasancewar kwalliyar zamani mai kama da na aljanu bai damu Ramlat ba don ba irinsa ta fi yi ba, sai ta fito ta yi wani azababben kyau. Daman su Rafee'ah  yanda suka ga  ta sauya fatarta ta kara kyau da sulɓi yasa suka dinga yi mata zargin  mai ciki, ita kanta sauyawar na ba ta mamaki. "Wallahi na fadamaki wani abu? Nidai ba ki taɓa kyau irin na yau ba, ko bikinki albarka." Aisha ce ke maganar tana dariya,  harararta Ramlat ta yi ta ja guntun tsaki ba ta ce komai ba, wannan duk abinda ta yi ɗanawa Hussein tarko ta ke son yi yanda zai yi dana sanin wannan fushin da ya ɗauka da ita. Har tunani take ko wa ya sanya a gaban mota suka tafi? Nan fa ranta ya ƙara sosuwa. Ta mike ta yafa mayafinta golden ta dauki purse dinta mai kyalli shima golden, turare mai sanyin ƙamshi ta fesa kafin ta zura takalminta da ya kasance mahaɗin purse din, ta dauki mukullin motarta. Kuɗin liki kam dama tuni sun tsufa a cikin ƴar jakar don tun safe suka bada aka yi masu chanji kowacce ta adana abinta. "Muje." Ta basu umarni, duk suka fito ta rufe ko'ina na gidan. Su Ummi na sashen Dada da yara ana ta wasa don yanzu ba su fiye wani kewar uwartasu sosai ba balle su liƙe mata. Tana tuƙin amma fuskar ba wawalar a zo a gani musamman da ta ga dagasken dai babu motar Hussein a farfajiyar gidan. Aisha ta karanceta tsaf, ta san kishi kawai ke cin ƴar uwarta don haka ta bar janta da hira ta maida akalar hiran ga su Falmata dake zaune a baya haka har suka isa ƙayataccen ɗakin taron na FARHAS Event Centre (Dan Adam). Farfajiyar wurin sai ɗaiɗaikun jama'a, sai da duk suka fita, sannan ta bi bayansu. Aisha ko jiranta bata tsaya yi ba don ba ta son a huce a kanta. Ta na takunnan mai girgiza zuciyar masoyinta kuma mijinta, wanda ya zama normal tafiyarta. Haka ta ƙarasa har ta shiga ciki. Wuri fa ya cika, gaba ɗaya kowa na zaune ana kallon MC wanda ya fiddo Amare da Angwayensu tsakiya yana basu umarnin zama saman wasu kujeru a tsakiyar wurin, wannan yasa hankalin da dama suna kansu ana dariya a nishaɗance. Sun haɗa ido, sai ta dauke kai kamar ba ta ganshi ba, wani irin tururi kanta ke yi ganin wata kyakkyawar budurwa a gefensa zaune, shi kuwa AlHassan Madam dinsa ce a gefensa sun ba MC hankulansu. Takaici ya sanya kawai ta ja kujera ta zauna ba tare da ta ƙarasa wurin su Rafee'ah ba, sai ma bayan ta zauna ta ɗago kai ta ga ashe ƴanmatan gidan kakannin su Hussein ɗin ne. "Kai Adda Amal you look beautiful wallahi." Ta dubi mai maganar Teema ta yi murmushin da bai kai zuci ba. "Thank you. Kuma kun yi kyau." Daga haka ta maida hankali da fiddo wayarta dake faman vibrating, ganin lambar Hussein kawai sai ta maida wayar jaka. Tana ɗaga kai kuwa ta hango su Kausar na ɗaga mata hannu alamar ta ƙaraso. Hannu kawai ta ɗagamata shaidar inda take ya ishe ta.   Sai da aka kira dangin Ango Tahir  don su yi liƙi sannan ta mike suka ɗunguma har su Teema, a hanya suka haɗe da su Rafee'ah aka shige fili, Maman twins na rantsuwar a farko ba ta ganeta ba. Sai dai su na liƙin tuni mazan suma suka taso don zazzage nasu aljihun, ta ɗaga hannu da nufin somawa ya kai hannunsa saman nata. Juyowa ta yi har fuskarsu na haɗuwa numfashinsu na gauraya wuri ɗaya.  A hankali ya zare kudin a hannunta ya shiga liƙawa kaf a kan Amarya da Angon, ta juya za ta wuce ya riƙe hannun gam suka fita tare. Maimakon su koma mazauni sai kawa ya yi waje da ita har wurin motarsa. Ta fincike hannunta, tuni idanunnata sun cicciko da kwalla. "Ka kyale ni." Hussein ya tsaya kawai hannunsa a kirji yana karemata kallo, ta yi mishi irn kyan da baki ba zai iya faɗi ba. Tsananin kewarta da son kasancewa da ita ne ke cin zuciyarsa. "Da iznin wa ki ka zo nan?" Ta tsuke baki, ya kuwa bishi da kallo yana cije lebba. "Ka riga ka san da fitar ai." Ta fadi cike da dakiya. Bai ce uffan ba ya juya ya yi amfani da mukullin motarsa ya bude, hannunta ya kama ya zagaya da ita ya bude gaban motar da nufin sanyata ciki. Ta dubeshi da zummar magana, sai dai yanayin ɗaurewarsa ya kaɗa hanjinta ba shiri ta hadiye abinda take shirin fadi ta shiga a fusace tana huci. Sai da ya zagaya ya zauna sannan ta dubeshi. "Motata fa?" Bai ce mata uffan ba ya yi ribas suka fice. Ranta ya ƙara zafi gashinan ko hoto ba su yi ba da Amaren balle kuma ƴan ankon. "Amma kasan ba kai ka kawoni ba ko?" Idan motar ta bata amsa, toh Hussein ya bata. Wayarta ce ta shiga ringing, ta ciro, kafin ta duba ko ta ɗaga ya karɓe. Ba ta san me aka ce ba  kamsr yanda ba ta san wace ce ba. "Muna tare." Daga haka ya katse kiran ya jefa wayar aljihun gaban riga. Ramlat dai har da hawayen takaici, ba ta bar haskoshi da waccan budurwar ba kamar yanda ta ke jin zafin raba ta da wurin bikin da ya yi. Su na isa gidan ya sa hannu ya zare purse dinta yana kallonta tsakar ido Ta kauda kai tana tura baki. Dariya ma ta ba shi ya murmusa. Mukullin motarta ya zare ya miƙa mata. Yana unlocking kofofin ta bude ta fice zuwa sashinta ranta a jagule. Shi kuwa sai da ya ba direba mukullin da kudin mota akan ya koma idan an tashi ya taho da waɗanda suka je a cikinta. *** Tana shiga ɗakinta ta faɗa saman gado ta shiga rera kuka kamar wata yarinya ƙarama. Ganinta kwnace saman gado tana kuka ya hau doka murmushi, kawai ji yake ya rama shariyar da ta dinga yi mishi a kwanaki biyunnan. A nutse kuma ya soma takawa har ya karasa gadon. Jin ƙamshin turarensa sai ta ɗago ta share fuska, kokarin mikewa  ta ke yi ya riƙo hannunta gami da jawo ta ta faɗa jikinsa. Kanta bisa kirjinsa gaba daya fuskarta ta nutse yayinda hancinta ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa. Lumshe idanu ta yi sadda ya sa hannuwansa gaba daya ya rungumeta tsam. Sai a sannan ta kara tabbatar da cewar ta yi kewar mijinta. A hankali ya zame ɗankwalin kanta ya shiga shafa gashinta. "Duk kawaici da kauda kan da nayi maki don naga gudun ruwanki, ba ki gane ba ko? Kin maida ni kamar wani hoto, kin nunan sabgar gabanki ya fi ni ƙima da muhimmanci. Tun soma bikinnan ba ki da lokacina, ba ki damu da ni ba. Shikenan ni kuma sai na kasa nuna ɓacin raina?" Yanda ya ke magana a tausashe sai jikinta ya yi sanyi, shakka babu kam, ba ta kyauta ba. Ta ɗago a hankali ta dubeshi tana narkar da fuska. "Ka yi hakuri. Na sani ban kyauta ba, amma don Allah ka yimin uzuri tunda dai ka sani biki ne ake yi, ga baƙi ina da su." Ya kama haɓanta suka tsurawa juna ido. "Sai kuma ki ke jin nauyin kwana da mijinki don kina da baƙi? Ki ka kyalewa wasu ƴan matan shi su samu matsugunni a nan?"  Ya nuna kirjinsa yana ɗaga mata gira da murmushi. Nan da nan kishin ya dawo sabo fil ta tureshi za ta mike, ya kara fisgota ya rike gam yana dariya. "Na dauka kishiyar kike ra'ayi." Ba ta san sadda ta harareshi ba, don mamaki sai ya yi dariya. "Shiyasa na ganka da wata busashshiya kana yawo da ita a cikin bainar jama'a don ka zubarmin da ƙima a gane ni Ramlat ban da wata daraja da.." Bai bari ta karasa ba ya tallafi haɓanta ya haɗe bakinsu wuri guda da zafi-zafi. Tun tana yunkurin ƙwatar kanta har dai ta saddaƙar. Can kuma da kansa ya sake ta, ya mike yana dubanta da shanyayyun idanunsa. Da wata irin kasala ya miƙa mata hannu, ba musu ta miƙamasa, suka ɗunguma zuwa nashi ɓangaren. A nan kam alƙalami ba zai iya wassafa yanda masoyan suka kasance ba cike da matsanancin kewar junansu. Ranar dai dinner anan suka ci suka sha abinsu. Koda jama'a aka dawo, ta sha tsokana sai toshe kunnuwanta ta yi kawai. ***   Sati biyu da kammala biki, jama'a kowa ya watse, an miƙa Amarya Hafsat zuwa Kano, tafiyar da ba'a yi tare da Ramlat ba don sam Hussein ya ce ita da Kano ba yanzu ba. Haka ta hakura, Rasheeda kuwa Abuja aka miƙa ta wurin aikin mijinta. Tun bayan bikin ya kasance Ramlat ba ta da kuzari, koyaushe tana kwance, wani lokacin bacci wani lokacin kuwa yanayin jikin ne kawai ba ya mata dadi. Dada kanta ta soma fahimtar sauye-sauyen Ramlatun, abinka da babba, sai ta ce mata lallai ta yi zamanta a ɓangarenta  ta dinga hutawa tunda a sannan Dada ba ita kadai ba ce, wata dattijuwa kuma yar uwarta dake Mubi, Mariya ta dawo nan domin taya Dada zama. Mace ce da ba ta taɓa haihuwa ba ga kuma girma da ya ɗan kama ta babu mijin aure. Ita kanta tana jin dadin zama da Dada. Kamar koyaushe, yau dinma tana kwana a falo, daga ita sai vest fara mara hannu da wando pencil da bai karasa ƙaurinta ba. Tun fitar Hussein take jin tashin zuciya, ta rasa meke mata dadi. Kamshin komai a gidan ma ji ta ke yana hawa kanta, karshe ma miƙewa ta yi kawai ta zura dogon hijabinta ta zagaya ɗan barandarsu da ake hango garden ta shimfida ƙatuwar dardumarta ta zauna. Ba laifi ta ɗan ji sauyi, ahankali kuma bacci ya yi awon gaba da ita. Sallama ya yi har sau uku shiru, da mamaki ya karasa shigowa falon a karshe ya shiga leƙa kicin da dakuna. Bandaki ma wayam, yana shirin leƙawa sashinsa ya hango ƙofar fita ta hanyar kicin a bude don haka ya karasa. Sosai abin ya ba shi mamaki, ba ta taɓa yin haka ba, ga dai iskar fanka da komai a falon amma ta dawo nan ta kwanta, yanzu kam ya yarda ba ta da lafiya. Karasawa ya yi ya sa hannu saman goshinta. Zafin da ya ɗan ji ne ya sa shi shafa gefen fuskar. "Ya Salam." Jin hannunsa ta yi firgigit ta farka da salati. Ya kama hannunta. "Sannu Heart, dama ba ki da lafiya? Tashi muje asibiti." Ta mike zaune tana shafe fuskarta, sosai kam ta yi bacci don har yamma ta kawo kai, ta tuno ko sallah ba ta yi ba. "Ban yi sallah ba." Ya taimaka mata ta mike, yana rike da ƙugunta suka ƙarasa ciki, sai dai su na sanya kai a falon ƙamshin airfreshner da ta fesa ya hautsina mata ƴan hanji. Tana kokarin zama jikinsa daga natata hanyar amfani da hannun damanta ta dora saman kirjinsa za ta tureshi, shi kuwa ƙara riƙo ta yake a rude yana tambayar lafiya. Sai dai ina! Tuni ta soma sheƙa amai har yana ɓata jikin Hussein. Nan da nan ta zaro ido a rikice, ba ta mance sadda ta yiwa Aliyu amai a jiki ba ya ɗauketa da lafiyayyan mari yana ɗura ashariya. "Ka yi haku.." "Shii! Muje ki wanke jikinki." Ya ja ta suka nufi bangarenta, sai da ya cire rigarsa da ta ɓaci har da singilet, kafin itama ya ciremata nata dogon hijabin. Bandaki ya shiga ya hada ruwa. Wankan suka yi tare, duk wani abin ƙamshi da ya ɗauko za ta girgiza kai ta ce ita ba ta so, Hussein dai murmushi ya ke da fatan Allah Yasa abinda yake tunani ya tabbata. Sai da ya daukomata kaya sannan ya wuce sashinsa ɗaure da tawul a ƙugu. Ƙananun kaya ya sa kawai ya fesa turare. Aikuwa tana jin ƙamshin turarensa ta fada bandaki a guje ta shiga sheƙa wani aman, koda zai shigo ya dakatar da shi kamar ta yi kuka. "Ni bana son kamshin turarenka." "Toh fa." Ya tsinci kanshi da faɗi, turaren da a baya take masifar so kenan, Sorry kawai ya furta sannan ya fita daga dakin. Kaya ya je ya sauya sai dai wannan karon bai yi gangancin fesa turaren ba. Suka ɗunguma suka wuce asibiti, ta waya ya shaidawa Dada ya kai Ramlat asbiti. Dada murmushi kawai ta yi da addu'ar Allah Ya bata lafiya. Kyakkyawan albishir din da ya yi fata kuwa shi ya samu, wato dai ciki ne da ita. Yanda ya dinga tarairayarta tun daga asibitin har gida, ita abin ma kunya ya dinga ba ta. Tun daga ranar kuwa kulawar da Hussein ke ba ta na musamman ne, tausayi sosai ta ke ba shi ganin yanda ta ke laulayi mai wahalarwa. Ita kanta abin tsoro ya dinga ba ta, gani take kamar wannan haihuwar farko ne za ta yi don komai sabo ta ke ganinsa. Kafin watannin haihuwar su cika gaba daya ta sauya, ta rame, sai ƙaton ciki wanda scanning ya nuna ɗa ɗaya ne kawai. Kowa kallon mai haihuwar biyu yake mata, duk yanda ta so ya bari ta je Kano ta haihu ya ƙi, itama don kanta ta hakura da batun zuwa don ko nawa za'a ba ta a yanda take ji,  ba za ta iya bin hanyar Kano ba. *** Bacci ya ke sosai, yayinda ita kuwa baiwar Allah ta zubawa silin din ɗakin idanu wanda hasken farin wata ya haska, mararta da bayanta babu inda ba ya ciwo, a hankali ta miƙe zaune tana cije baki, ta rasa ma ina za ta sa ranta, wani irin murɗawa da ya yi ba ta san sadda ta ɗakawa Hussein duka ba. Ya mike kuwa firgigit don a farko bai dauka mutum ne ya dakeshi ba, hannu yasa  ya kunna fitilsr bedside yana kallonta gami da ruƙo ta. Ta matse hannunsa ƙam! "Mutuwa zan yi wallahi!" "No! Naƙudar ce? Bari muje asibiti." Haka ya mike tsaye yana gyara zaman pyjamas dinsa. Dakyar ya samu nutsuwar ganin mukullin motar, ficewa ya soma yi da ita, Buzu Maigadi da  fitowarsa daga bandaki kenan, ya ajiye butar ya karaso da sauri ya taimaka ya karbi mukullin motar ya budemishi yana kwaranyo addu'ar Allah Ya bata lafiya. Lokacin wuraren ukun dare ne. Sai da Hussein ya zaunar da ita kafin ya koma a guje ya dauko akwatin da tun shigar cikin wata tara ta haɗa abinta. Su Dada basu sani ba sai ƙarar buɗe kyaure da rufewa suka ji. Ba shiri ta fito ita da Baba Mariya a ruɗe, nan Buzu ke fadamusu Madam ce ba lafiya. Nan da nan a rude suka kira wayar Hussein, amma ina tana ta ringing bai ɗaga. A dole suka koma ciki don ba direban da zai kai su. Nafiloli suka shiga yi da addu'ar Allah Ya sauketa lafiya don sun sani loda sun je, ba abinda za su iya yi mata sai addu'ar. *** Ramlat suna zuwa ko awa ɗaya cikakka ba ta yi ba ta haifo ɗanta namiji, sai dai kafin Nos ta yi wani yunƙurin, wata naƙudar ta kara zuwar ma Ramlatu, da mamaki Metron da Nos suka ƙara yin kan Ramlat, wannan karon sai da aka haɗamata da ruwan naƙuda, ba karamin galabaita ta yi ba, Hussein kamar kansa zai tarwatse yana daga waje, ga kukan jariri yana ji kuma ana fadin ai ba ta kammala ba. Ga murna ga kuma tashin hankali da tausayin matarsa. Kalmar mutuwar da ta ambata har yanzu ba ta sakeshi ba, fargaba sosai ya ke ciki duk kuwa da ya sani mutuwar ba a baki ta ke ba.   Kukan jaririn da ya kara ji, sai ya rude, ya rasa na farkon ne ko na biyun, kawai sai ya cusa kai ba tare da neman izni ba. Aikuwa wata jaririyar ce aka kara cirowa Ramlat. Ita kuwa ta lumshe ido sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi. Dole ya fita yana murna, kafin a kammala gyarasu ya shiga laluben waya don ya sanarwa Dada da ɗan uwansa sai dai wayam. Hakanan ya hakura ya dinga murna da farin cikinsa shi ɗaya. Gaba daya jariran aka kawomasa, Metron na fadin sai fa ya ba ta goron albishir, dariya ya yi yana ɗaukarsu. "Ki biyoni bashi." Itama dariyar ta yi ta miƙa masa tana fatan Allah Ya rayamasa. Kammanin Dada sak ko kuma yace kamanninsa yake hangowa a fuskar yaran wadanda suma ke cike a kansu a saman fuskarsu. Sumbatar kowannensu ya yi yana mai jin taruwar kwalla a idanunsa, ashe dai wataran mafarkinsa zai tabbata, zai ga gudan jininsa? Ya soma yiwa namijin huɗuba a kunne kafin ya juya ga macen. Daga nan kuma ya yi zamansa yana ƙaremusu kallo, haka har aka soma kiraye-kirayen Assalatu. Aka ba shi umarnin ganin Ramlat, ya shiga ciki. Ta zubamusu do tana kallonsu cike da kauna, yana karasowa ta yi murmushi. "Alhamdulillah." Ta furta, ya ajiye yaran a gefe kusa da ita ya sumbaci goshinta shima ya na hamdalar. Dakyar ya samu ya wuce masallaci. Ana idar da sallah ba jimawa sai ga AlHassan tare da su Dada. Kowa ya ga ƴan biyunnan sai ya hau murna. Dada har da hawayenta tunawa da ta yi da Yayanta kuma ɗan uwanta Aminu. Ranar dai Ramlatu ta sha baƙi dakyar aka fice aka bar ta ita kadai ta samu bacci mai nauyi ya fisgeta. Jariran kuwa su na hannu, wannan ya dauka wannan ya dauka har sai da Hussein ya yi ta maza ya ce ya isa hakanan su ma a bar su su huta. Duk shaƙiyancin da ake mishi ko a jikinsa. Ya shimfidesu a kusa da uwar ya tsaya ya kuramusu idanu yana kallo. Ya kalli Ramlatun ya kallesu. Tausayinta ya kamashi, ba karamar wuya ta ci ba. A karshe dai ya fice ya bar su. Sai da Dada ta lallaɓashi kafin ya koma gida ya yi wanka ya sanya suturar arziki ya kuma biya shago ya siyo kayan jarirai na mace don kusan rabin siyayyar duk na namiji suka yi jin abinda scanning ya bayar. Kwanan Ramlatu biyu aka sallameta, sashin Dada ta koma inda Baba Mariya ke wanketa tas ita kuwa Dada ke wanke jarirai. Hussein ko yana ofis ba ya rabo da waya. Ranar suna aka sanyawa yara suna Amina da Aminu, farin cikin Dada ba ya misaltuwa. Daidai da iyalan Kawu sai da suka zo suna wannan karon har da Umma matar Baba Dakta, Hajiya ma ta so zuwa sai dai makarantar yara ta sanya dole ta hakura amma itama kam zuwa lokacin kewar diyarta take ji. Abinda ya yiwa Ramlatu dadi bai wuce na zuwan Muhibbat ba. Sosai ta yaba da wannan karar da ta yi mata, abin mamaki kuma har saƙo ta samu na kayan jarirai daga iyayen Hilal, matar Hilal ta kira ta mata barka ta kuma yi mata fatan alheri. Koda ta ke ba su Rafee'ah da suka zo suna labarin wayar, dariya suka yi. "Ai ke yanzu wacce da kika sani a baya yanzu ba ita ba ce, ko ma dai mene ai yanzu dole ta sauko tunda aure zai ƙara kuma yanzu ko ba komai ta ga  kin auri wanda ya shanye mijinta a komai da komai na rayuwa. Jinjina kai kawai ta yi tana murmushi a ƙasan ranta tana mai hamdala da Ubangiji. *** Rayuwa sosai ta ke yiwa Ramlat da mijinta dadi, zuwa lokacin gininsa da yake ya kammala sai fenti da ake yi da kuma zuba furnitures da ya yi saura. A wannan lokacin ne kuma ba zato ya yi mata albishir da kai ziyara Kano. Dama tun sadda ta yi kwanaki arba'in ta ke saka rai da hakan, ya nuna ba yanzun ba. Har faɗa suka yi ta gama fushin ta haƙura ta sauko. Haka ta dinga shirya tsaraba, Dada ma ta haɗamata da nata. Hajiya ba karamin farin ciki ta yi ba, abincin da Ramlatun ta fi kauna shi ta girka mata, hakanan Umma itama ta aikomata girki. Su Ummi kamar su haɗiye ƴan biyu wadanda suka dauko hasken mahaifinsu kamar ka latsa jini ya fito. Duk ganin da Ramlat ke yiwa Ummi tana da gashi sadda tana ƙarama ashe ba komai bane idan aka haɗa da na Meena. Kamar yanda suke kiran Amina don Dada sam ta hana a ɓoye suna. Hisham kuwa koda ya ga amininsa sai ya hau dariya da zolayarsa ganin yanda ya ajiye naman wuya ya ƙara zama wani fresh. Har gidan su Hisham din ya je ya gaida mahaifiyarsa kafin ya koma masauki.   Washegari ya juya Adamawa ya bar Ramlat, sati biyu kawai ya ba ta hakanan ta hakura don a son ranta ne ta yi wata guda cif. Ai kuwa a sati biyun ta zage yan uwa da abokan arziki, koda ta je gidan Yaya Munir ta kara shan mamakin zamantakewar matansa wadanda tuni ya haɗe su gida daya. Salma kanwar Bilkisu ita kanta ta sauya ta yi sanyi. Anan suka hadu ta dinga ba ta hakurin abinda ya faru a baya, banda murmushi ba ahinda Ramlatun ta yi don har ga Allah ita kam yanzu dukkan kunci ko bakin cikin da ta shaƙa a baya ta bar sanya damuwarsa a rai sai dai ta tuno ta auna da yanzu ta godewa Allah.   Ana jibi zasu tafi ne ta fita tare da Amrah, daga gidan Muhibbat suke kafin su karasa wani katafaren shago don nemawa Kausar wani man jiki da ta addabeta a kansa. Dama daga Kano ake aikamata, wacce kuma ta ke siya wajenta, nata ya ƙare.   Sai da suka fito Amrah na kara yi mata bayanin wani maganin mata da ta ba ta, ba zato ta ji an kirayi sunanta. Juyawa suka yi a tare ita da Amrah, mamaki ya kama su ganin Chairman da wasu ƴan matan yara da zasu kai shekaru goma sha biyu zuwa goma, bayan yaran sun gaishesu ya basu umarnin shiga shagon kafin ya zo. Ya juyo ga su Ramlat, suka gaidashi fuska ba walwala. Sai da ya soma da neman gafarar Ramlatun kafin ya dora. "Kina da labarin rasuwar Hajiya  Zeenatu ko?" Kusan a firgice ita da Amrah suka ce. "Hajiya Zeenatu?!" Ya jinjina kai da mamakin rashin saninsu. "Ta rasu yau wata hudu kenan, tun dai iftila'in gobara da ya afkawa shagonta ta samu matsalar shanyewar  ɓarin jiki. Haka dai a sanadin jinya komai nata ya ƙare. Sau ɗaya naje duba ta na kuma bada tallafin kuɗi domin a yi mata abinda ya dace. Na isketa cikin mawuyacin halin da har babu wani ko wata da ke tsaye a kanta domin jinya. Nima saƙo ta bayar ta hanyar Ƙawarta Hajiya Batool akan a faɗamin. Ta bar min wasiyya akan duk sadda na haɗu da ke ko Hussein na nemamata gafararku. Ita kanta yanzu Hajiya Batool din kokawa take da tata lafiyar, ciwon Kansar Gaba take fama da shi. Abin dai babu dadi don yanzu haka ɗanta ma ba ya ƙasar, ya juya da iyalinsa ƙasar waje." Chairman na kaiwa nan ya girgiza kai, kansa a ƙasa kafin ya ɗago ya dubi su Ramlat wadanda tsoron Allah ya kuma mamayesu. Wai Hajiya Zeenatu ta mutu. Lallai Allah abin tsoro. "Ki yafemin nima Ramlatu, ko aurenki da na je nema banda soyayya har da sa hannun Hajiya Zeenatu." Ya basu labarin komai, take Ramlat ta ce ta yafemishi, aka rabu suka wuce shi kuma ya shige ciki. "Allah Kenan! Kin ji yanda jikina ya yi sani Ramlat?" Amrah ke zancen tana matsar kwallar tunanin rayuwa, shakka babu DAN ADAM ba a bakin komai yake ba. Ramlat ta sa hannu ta share nata hawayen. "Bari kawai Amrah, duniya abin tsoro. Allah Ya gafartamata. Ni dama ban riƙe ta ba, wadanda ta yiwa su ne abin ji." Amrah ta gyada kai. "Allah Ya basu ikon yafemata." Ramlat ta amsa da amin. Haka suka dinga maganar su na kara roƙon Ubangiji akan cikawa da imani. Washegari kuwa duk yanda ta so Hussein ya amincemata da ziyarta Halima a gidan yari kamar yanda ta ƙudurta, sai dai ina! Hussein ya ce bai lamunta ba. Dakyar da siɗin goshi ta shawo kansa ya amince akan ta nemi Yusufa ƙanin Halima ta isar da saƙo ta hannunsa. Hakan ba yanda ta iya kuwa, ta aikata. Yusufa ya zo har gidansu Ramlatun, bayan sun gaisa ta ke tambayarsa batun Halima. "Yaya Halima tana nan, wallahi wacce kika sani a baya yanzu ba ita bace Anti. Ina nufin sauyi a ɓangaren ɗabi'u da halayya, ta samu sake litattafai da dama na addininta. Koyaushe idan na kai mata ziyara sai ta tambayeni ko ina da labarinki. Amma in sha Allahu yanzu kam ina da labarai kwando-kwando da zan kai mata har da na twins." Ya fadi yana kara sumbayar goshin yaran, Ramlat ta yi dariya. Basu rabu ba sai da ta ba shi kudi da nashi, da kuma na siyayyar abin bukata da ta ce ya yiwa Halima. Ta kara da fadin. "Ka isarmata da saƙon gaisuwata sosai." Yusufa da farin ciki ya sa kwalla taramasa, ya yi ta yiwa Ramlat godiya, ita dai ta karbi yaranta ta yi cikin gida. *** Koda suka koma Adamawa, ba ta ɓoyewa Hussein komai ba, har faɗa ya dinga yi akan don me ta tsaya kula wani ƙaton a waje. Dakyar ta lallaɓashi ta nemi gafara ya hakura ya sauko. A karshe kuma ya ce bai son batun Hajiya Zeenatu. Hakanan ta kyale zancen sai dai ta ci ɗamarar ƙara yinta ko nan gaba ne. Ɓangaren Dada kuwa koda ta ji murmushi ta yi. "Babu sauran tabon matarnan a zuciyata, ni tuni na mance da ita. Na kuma yafemata, Allah Ya gafartamata." Ramlat ta amsa da amin cike da jin dadi. Hakanan bangaren AlHassan shi dama mai sauki ne. Satinsu biyu da dawowa Adamawa suka tattara suka tare a sabon ginin gidansu. Gida ƙerarre flathouse mai shegen kyau. Tsayawa fasaltawa ma ɓata lokaci ne. An ɗan yi liyafa ƙarami wanda yan uwa da abokan arziki suka zo, daman kafin nan sai da aka yi saukar Alkur'ani a gidan. Kowa ya yaba ya kuma sanya albarka. Daga bisani aka watse aka bar Hussein da iyalinsa. *** BAYAN SHEKARA ƊAYA Rayuwa mai tsari da kuma daɗi su ke gudanarwa, ƴan biyu sun yi wayo sun yi ɓulɓul abinsu. Duk inda ka gansu sau sun burgeka, Amina ta fi Aminunta ƙiba sosai, sai dai duk ƙibarta idan rikici ya haɗasu yanzun zai kirɓeta. Ita kuwa ta wangale baki da kuka, idan kuwa ka ce za ka ɗau mataki akan Aminun, yanzun za ta hau taremishi tana dukan wanda ke kokarin dukansa. Shiyasa iyayen basu shiga rikicinsu. Yau ma Ramlatu na zaune jiki duk babu kuzari, gaba daya damuwa ta bayyana karara saman fuskarta, tun safe ta yi test na ciki da pt-strip sakamako ya bata positive, tana jin Aminu na kukan cizon da Amina ta narka mishi a gadon baya, ya kuwa bi ta a guje ya shiga bugu, aikuwa da Ramlat ta fusata ta yi kansu duka biyun ta zane tas. Suka haɗa kai su na kuka ita kuwa ta shige ɗaki don takaicinsu. A haka uban ya shigo ya iskesu. A rikice ya karasa su ma suka faɗa jikinsa, ya rungumesu sosai. "Ya isa my twins, wa ta taɓa ku?" Suka hau nuna ɗaki. "Mamiiii" Amina ta faɗi tana kuka da taɓe pink lips dinta. Ya miƙe ransa a ɓace ya shiga ɗakin. Sai dai ganinta a kwance tana hawaye ya sanyaya jikinsa, duban yaransa ya yi ya kuma dubeta, bai ce komai ba kawai ya kama hannunsu suka bar ɗakin. Sai da ya rarrashe su ya basu kayan cakulet din da ya siyomusu ya ga sai washe baki suke da dariya kafin ya sumbaci kowannensu ya mike zuwa ɗakin. Gadon ya hau ya shafi gefen fuskarta. Ta dubeshi don tuni ta bar hawayen. "Sannu da zuwa." Cike da kulawa ya ce. "Meke damunki? Kukan me kike?" Ta mike zaune ta fada kirjinsa. "Ciki ne da ni." Ya yi murmushi. "Shi ne ki ke kuka saboda ba kya son haihuwa da ni ko me?" Da sauri ta ɗago ta girgiza kai. "Wallahi aa, kawai dai tausayin kaina naji, duka-duka twins ko shekara biyu ba su cika ba." Ya ɗaga rigarta ya sumbaci cikin kafin ya ɗago ya sumbaci lips dinta yana murmushi. "Shi ne me? Tun yaushe nake maki fatan samun cikin? Ina ce har zargin ko kima shan maganin hana ɗaukar ciki nayi maki? Ba halak za ki haifarmin ba? Ramlat ko yara goma za ki haifamin akai-akai, wallahi ina son abina. Ashe dalilin da yasa kika huce akam yarana kenan? To ki shirya dagaske sai na rama musu." Ta harareshi da wasa, ya ɗan ba ta mintsili kuwa a kafaɗa. Ta rike tana kuka shagwaɓa gami da fadin wash. Haka ya dinga lallaɓata kafin ya jawo ta jikinsa. "Akwai goron albishir babba, yana nan tafe nan da wata uku." Ta yi farr da idanunta. "Watan Azumi fa kenan." Ya jinjina kai yana murmushi. *** BAYAN WATANNI UKU.. Kamar yanda ya yi mata alƙawari sai ga shi ta sha mamaki, ashe dama dalilin yi nata Passport kenan? Tafiya ce Umarah za su yi, don murna ranar haka ta rukunkumeshi tana kuka tana sumbatar duk inda bakinta ya kai. Tare da Dada da su AlHassan da matarsa duka za su wuce. A waya suka yi bankwana da mutan Kano da zummar sai sun dawo za ta kai ziyara. Azumi nada kwanaki goma sha biyar suka tafi. Sosai sun yi ibada. Anan ne kuma Ramlat ta ƙara zuwar ma da Hussein roƙo akan ya yafewa Hajiya Zeenatu, da murmushi ya rungume matarsa ya sumbaci goshinta. "Na yafemata, Allah Ya yafemata." Ramlat ta rungumeshi itama da jin dadi. Koda suka koma ɗaki, kasancewar ƴan biyu na tare da Dada, wata ibadar suka shiga yi. Bayan komai ya kammala ya zubamata idanu sadda ta fito wanka tana goge jiki, garin na Makkah ya karɓe ta sosai, ga cikinta ya fito. Ta kara mulmulewa ga kumatu da suka yi mata kyau. Ƙarasawa ta yi ta yi amfani da jelar gashinta ta watsamishi ruwa a fuska, ya kai hannu zai riƙota ta ja baya. Girgiza kai ya yi gami da sauke numfashi. "Wallahi ina sonki." Yanda ya fadi sai da ya ratsa dukkan sassan jikinta, tsikar jikinta ya mike. Ba ta san sadda ta taka zuwa gareshi ba ya kuwa rungumeta sosai suka lumshe idanu. Ji suke kamar su haɗiyi juna. "Ina maka son a baki ba zai misalta ba My Hussein, Abban Twins. Na soma sonka daga sadda na soma ganinka." Ya ɗago ya haɗa fuskokinsu wuri guda, maimakon amsa, sai ya haɗa bakunansu. Can kuma ya ɗago kai ya dubeta. "Sai dai fa a sake sabon.." Ba ta bari ya karasa ba ta rufemishi bakin da nata. Gaba daya ta ruɗa shi. Ta sakeshi tana murmushi da maida numfashi. "Na shirya yin duk abinda zai farantamaka." Daga haka ya sa hannu ya ƙara kashe fitilun ɗakin ta hanyar amfani da makunnin dake gefen gadon. Salo ya sauya. ƘARSHE.. _*Alhamdulillah. Ina godiya ga Allah da Ya nunan kammala littafin Karfen Kafa lafiya. Ina kuma godiya gareku masoya masu karfafan gwuiwa da kuma hakuri da juriyar bibiyar labarina duk da irin tsaikon da akan samu. Ina kara ba ku hakuri bisa duk wani kuskure da ku ka ci karo da shi, dan adam ajizi ne. Ina maraba da kofofin gyara ko shawara amma don Allah ba ta hanyar cin fuska ba. Allah Ya kara haɗamu a wani littafin nawa. Na gode kwarai. Son so fisabilillah mutan Rof, Rof2, Karfen Kafa group, both whatsapp & Wattpad fans duka ina godiya. Allah Ya bar zumunci.*_ _*Godiya Ta Musamman gareki BARR FIRDAUSI KABIR, wallahi ina maki son so fisabilillah. Kaunar da kike yimin ba zan ce komai ba gareki tare da sister dinmu, FADILA KABIR. Allah Ya bar zumunci.*_ _*Ummu Abdoul my editer, chairlady of Fikra. Allah Ya saka da khairan, Sis Batool Mamman, Donutfairy da ma dukkan masu bibiyar Karfen Kafa marubuta. Ina maku son so. Allah Ya bar zumunci. Ameen.*_