[8/7, 7:35 AM] Aisha Galadima: *_typing_*📲 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA.........!!._* _{🔪wuk'a bata hudashi!🗡}_ *_Bilyn Abdul Ce_*🤙🏻 *_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*😜 ( بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ ) _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *SADAUKARWA* _Wannan littafi sadaukarwane ga mahaifina *Malam Ibraheem Musa (Na-Ali),* ya Rabbi kakai Rahma, Ni'ima, gafara a kabarinsa, ya ALLAH ka ni'imta ruhinsa zuwa aljannarka, da dukkan sauran musulmai, mudaya bari ALLAH ka rayamu cikin ni'imominka da rahmarka._😭👏🏻 _Ya ALLAH ka hana mak'iya da shaid'anu samun nasarar raba kayinmu, ALLAH kabamu ikon aikata khairan akowanne lokaci😭._ *I love you so much baba* _(Muna kewarka wlhy)_😭😭 *Na gaisheku, nagartattun dangi* Nafisat Ibraheem Musa Hauwa'u Ibraheem Musa Musa Ibraheem Musa (Abba) Fateema Ibraheem Musa (ummi) Muh'd Atteku Ibraheem Musa Libabatu Ibraheem Musa Shu'aibu Ibraheem Musa Jameela Ibraheem Musa Muh'd shamsuddeen Ibraheem Musa Aisha Ibraheem Musa. *_bilkeesa Ibraheem Musa_*😉 Namik'o gaisuwar bangirma marayun ALLAH, ALLAH ka k'aramana soyayyar juna👏🏻😁 *_'yan uwana ababen alfaharina_* Yaya Abdullah (city phone's) Aunty Ruk'ayyat (Maman khausar & Raudah). _Ina k'aunarku sosai, fiye da tunanin mai hasashe, ALLAH ka k'ara had'e kayinmu har Abadan, ALLAH ka k'arama mahaifiyarmu lafiya da tsawon kwana._😭👏🏻 *_inamai farincikin sake had'uwa daku fan's, a buk na 12 dana rubuta, ALLAH yasa mu amfana da abinda zaizo._* _ya ALLAH ina Neman tsari daga cecekucen social media_👏🏻 *idan kasan bazaka/bazaki iya jurewaba, karki/karka karantamin littafi, Dan sak'ona zan Isar, duk Wanda bashida hangen fahimtar sak'on, kada ya wahalar dakansa wajen bibiya, Dan banason gutsiri tsoma👉🏻🤫.* _kuma duk Wanda yacanjamin wani Abu ban yafeba_🤐 *_part 1 loading_* _(littafi Na d'aya📕)_ 0⃣1⃣ *Sautin* kukane ketashi acikin gidan, wasuma harda kururuwa da ambaton sun shiga uku, wasu nafad'uwa k'asa ana kamosu, duk Wanda kagani acikin gidan kasan yana cikin matuk'ar tashin hankalin rasa wani abu muhimmi. Nikaina dai kukan nasu yatada hankalina. Nakoma dagacan gefen wata matashiyar budurwa dabazata wuce shekaru 13 ba aduniya, dukda k'arancin shekarunta sainaga Nisan hankalinta, domin kuwa ita kukan NATA yana fita cikin salamane, babu kururuwa balle fad'uwa k'asa, kamar yanda sauran 'yan uwanta keyi. Kafin na samu damar tanbayarta dalilin kukan nasu? naji ta furta *ALLAH sarki babanmu, ALLAH ya gafarta maka*, yau katafi kabarmu, ALLAH daya bamukai babu shawararmu, yau yakar6eka babu shawararmu, (ALLAH kenan, buwayi gagara misali), jiya iyanzu yana taredamu, yaukuma mun wayi gari and'aukesa. Takuma fashewa da kukanta mai tsuma rai, Wanda inba kusada ita kakeba, bazaka ta6ajin sautinsaba. (Humm wannan rasuwa ta tadamin mikin nawa tabon Na rasa mahaifina, a ranar 1 ga watan Rajab, wata uku kenan😭, ALLAH yagafarta musu baki d'aya, ameen). Wani dattijone datun d'azu suke shigi da fici daga wani d'aki zuwa tsakar gidan yace, "ya salam! Habadai Dan ALLAH, wannan kuka bashine zaidawo mana da Malam Abubakar duniyaba, amatsayinku Na musulmai wannan kururuwar da ihun bai kamacekuba, addu'a Malam yake buk'ata agareku amatsayinku Na iyalansa, kukanmu bazai dawo mana dashiba, amma hak'urinmu da nutsuwarmu zaisa murok'a masa gafarar UBANGIJIN Al'arshi. Dan ALLAH muyi hak'uri hakanan, ALLAH ya gafarta masa, yabamu hak'urin rashinsa. Tunda dattijo yafara magana gidan yay tsit, wannan nasiha tashi tayi tasirin saka kowa yin shiru, saidai shashshekar kukan wasu da ajiyar zuciya. Cikin 2hours aka gama had'a gawar marigayi Malam Abubakar, nagartaccen malami, masani akan ilimin addini, mai kishin musulinci da musulmai, mafad'in gsky komai d'acinta, mai hak'uri da kawaici, mai uzuri ga komai Na rayuwa da halayen bil-adam. ALLAH ya gafarta masa, Dan bak'aramin rashi akayiba kam yau, ALLAH yad'auki Malam Abubakar bayan gajeriyar jinyar dayasha ta kwana 18 kacal, wadda tazama sanadin ajalinsa, yabar duniya bayan sallar asubahi, mintuna 3 da idar da sallar da ALLAH yabashi ikon sallata, wadda tazama ibadarsa tak'arshe adoron k'asa. Yarasu akan abin sallarsa, dan ko gusawa baiyiba saida aka zare ransane d'ansa da k'anwarsa dake d'akin sukaga ya tuntsure kasa yaraf. To saimuce ALLAH ya gafarta masa, da dukkan 'yan uwa musulmai dasuka rigamu gidan gsky. *_marayu inayinku wlhy🙋🏻‍♀, ALLAH yak'ara mana hak'uri😭_* Bayan kammala had'ashi, aka kira matansa biyu Barirah & Fad'ima domin yin bankwana, sunmasa addu'a da Neman gafararsa, sannan suka fito cikin kuka. Daga nan aka buk'aci ganin 'ya'yansa, wad'anda suka kasance adadin su 9. d'akin barirah uwar gida nada 6, sai amarya Fad'ima nada 3. Suma sunma mahaifinsu addu'a da fatan alkairi, duk suka fito cikin kuka. Mintuna kamar 17 da haka aka fito da gawar Malam Abubakar zuwa gidansa na gsky, sosai sautin kuka yafara tashi, haka akafitadashi sunaji suna gani, basuda damar hanawa.😭 *_mutuwa kenan, maimaida mata zawarawa, mai mayar da yaro maraya, mai yanke jin dad'in duniya, mai yanke abota da 'yan uwantaka._*😭 Yakai bawa ka aikata alkairi kodan tsoron wannan ranar👈🏻, yau babana yarasu, gobe abokina, jibi matata, gata d'ana, wlhy watarana Kaine zaka tafi👈🏻😫. An sallaci gawar Malam Abubakar a k'ofar gidansa, sannan yasamu rakkiyar d'umbin mutane zuwa makwancinsa. Zuwa yanzun kam gidan yagama cika da mutane, anata gaisuwa ga wad'anda abin ashafa. To dama akance idan kaje gidan mutuwa kakan shaida Wanda akaimawa, wannan maganar haka take, dankuwa zuwa k'arfe 2na rana wasu harsun fara sakewa, harma suna lodama cikinsu abinci, saidai ga 'ya'yansa bahaka bane, Dan kallo d'aya zaka musu ka tabbatar har sannan suna tartare da damuwa sosai. Wannan kenan👌🏼. *7days ago* Ayau akayi addu'ar bakwai d'in Malam Abubakar, bayan lafawar komai kuma shak'ik'ansa suka had'a taro Na family. Ba'a samu nutsuwar kowaba sai 1:43pm zuwa sannan mutane duksun baje, 'yan uwa Na nesa Dana kusa kowa Yakama gabansa, sai shak'ik'ai, irinsu k'annensa da yayunsa. Dattijo m. Bilyamin shiya fara gabatar da sallama agaresu, yayi doguwar addu'a ga mamaci Malam Abubakar, harmada sauran al'ummar musulmi dasuka rigamu. Daga nan yaja dogon bayani akan gado da kuma biyama mamaci bashi da kar6o abinda yakebi, yaymusu nasiha da nusar dasu muhimmancin rik'e zuminci, da kuma addu'oi ga mahaifinsu, yanda zasu rik'e maraicinsu harya amfanesu. Ya tausasa murya tareda binsu da kallo d'aya bayan d'aya, ya ce, "kuyi hak'uri da abinda zan fad'a, musammanma iyayenku mata, nasan duk uwa tana buk'atar tarayune da 'ya'yanta, saidai k'addara tarabasu, badan ansoba, kamar dai yanda nake gani kuma yau zata nisantaku da naku, Dan hakan shine babban gata dazamuyi gareku, kuma shine abinda zamuyi mu kwatanta k'yaunarmu ga d'an uwanmu, bayan k'asa tarufe idonsa mukula da zuriar daya bari. Sosai naga tashin hankali a fuskar iyayensu dasu Kansu 'ya'yan. M Bilyamin yacigaba da fad'in, bazamu kwashe mukusu dukaba, amma ZAMU d'auke k'ananun cikinsu, saboda sunfi buk'atar kulawarmu. Kamar yanda kuka sani, Jafar da Murtala sun mallaki hankalinsu, kuma yakamata abarsu domin kula daku iyayensu mata, basukai k'arfin daza'a bar musu nauyin k'annensuba tukunna, dukda kuwa sunada shekaru 24&26 aduniya. Saikuma Fadeela & Hafsat suma zasu k'arasa zamansu da iyayensu mata tunda aurensu saura wata 1 da sati 1. To amma Sadiya da Rufaida da Aysha zasu dawo hannuna, Sadiq(Abba) zai koma wajen Asma'u, Ummulkhairi zata koma wajen Ahmad, ALLAH yasa hakan danayi yayi daidai kuma zaku goyamin baya. Gaba d'aya suka amsa da gamsuwa. M bilyamin yaji dad'in hakan dasukai masa. Kukan Gwaggo bintu ne yakatsesu, cikin kuka mai tsanani tace, "yaya bilya ni mizaisa awareni ak'i bani d'a ko d'aya acikin tsatson Yaya babba, shin har yanzu baku yarda da tubanaba kenan? Kuna k'yamata kamar kamar baya?, aganina nafi kowa buk'atar yarannan, kodan rashin haihuwa daban samuba, amma babu komai namuku uzuri. Tamik'e tana sharar kwallah dafad'in zan koma, ALLAH ya gafartama yaya babba... Harta fara tafiya Malam bilyamin ya tsayar da ita dafad'in bintu!. Cak tatsaya, tana cigaba da matse kwallah. Yace, " dawo ki zauna". Babu musu tadawo wajen zamanta. Cikin tausasa harshe yace, "kiyi hak'uri bintu, banhanaki d'aukar yaro kod'ayaba, saidai ina dubi da cewar bakina zaune bane a gidan mijinki, kema akare kike, wlhy bintu muna tausayinki akan rashin haihuwa, amma munsan ALLAH shine mai badawa, k'ila rashin haihuwar taki shine alkairi agareki. Kanta ta jinjina tana share kwalla, tace nayarda dakai yaya, kuma nagamsu da hujjarka, amma batun akare nake bai tasoba, agidan *Alhaji Abdallah Jigawa* ban rasa komaiba, kuma inada k'yak'yk'yawan muhali kamar namai aure, gidan sunada tarbiyar danasan konaje da wani acikin yarannan baza'ayi nadama ba. Kuma Alhaji Abdallah zai rik'esu tamkar 'ya'yansa, tunda shima yana rik'on marayun, Dan ALLAH kuji tausayina kubani 1, nima zan kalla naji dad'i, tunda ALLAH ya k'addara nikad'aice ware acikinku. Sosai maganganunta suka ta6a musu zuciya. Kuma sunsan tabbas suka hana bintu d'iyansu duniya zata zagesu da kallon danbasu fito CIKI d'aya baneba (Dan ita gwaggo bintu baba suka had'a dasu malam bilyamin, itakad'ai babarta tahaifa agidansu, kuma ita kad'aice 'yar uba). Dogon numfashi Malam bilyamin yasauke, yace shikenan, saiki d'auki d'aya, wakika za6a?. Caraf gwaggo bintu tace, ''Ai'sha yaya. Gaban Ai'sha da mamanta ya yanke yafad'i, sosai tsoro ya bayyana agaresu. Shikamsa Malam bilyamin saida mamakinsa ya bayyana, Dan kuwa kowa yasan gwaggo bintu basa shiru da Maman Aysha, tuni basa shiri. Jin sunyi shiru gwaggo bintu takatsesu da fad'in yaya kodai akwai matsalane?. Da Sauri Malam bilyamin yace, "a'a bintu, anbaki, ALLAH yatayaki rik'o. Duk aka amsa da ameen. Amma banda Aysha da mamanta, wad'anda suka shiga tsananin tashin hankali.........🖊 _hummm komiyasa ba'a son bama gwaggo bintu Aysha?, Wayema Alhaji Abdallah Jigawa? Miyekuma alak'ar zamanta da gidan?, idanma tatafi da Aysha wane irin zama zatayi a can d'in?, shin yama tarbiyar gidan take? Tanada inganci kamar yanda gwaggo bintu tafad'a?._ Dukma abar wannan batun, Aysha zata amince tabi gwaggo bintu gidan Alhaji Abdallah Jigawa kuwa? Mikuma yasa gwaggo bintu ta za6i Ayshar ma to?. Taku har kullum, Bilkeesa Ibraheem musa (bilyn Abdul). Kukasance dani😉👌🏼, awannan labari mai matuk'ar rikita-rikita.🤐 Yanzufa aka fara Fan's, kumuje zuwa oooh *_I love you all my fan's_*😍 [8/7, 7:35 AM] Aisha Galadima: *_Typing_*📲 🤰 *_CIKI DA GASKIYA.......!!_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*😜 *Sadaukarwa* _My sweet dady_ (ALLAH ya gafarta maka)🤲🏻 *_part 1_* (littafi na d'aya) 0⃣2⃣ Bak'aramin kuka Aysha tasha ba, hakama mamanta tayi kukan a 6oye, fadeelama tasha kuka Dan za'a rabata da 'yan k'annenta masu d'ebe kewarta, amma babu yanda zatayi, Dan dolene kowa yabi umarnin k'anin mahaifin nasu, Wanda ayanzu ya maye musu gurbin mahaifi agaresu, tunda basuda kamarsa. Tunda safe gwaggo Asma'u tawuce da Abba katsina, (a can take aure). Hakama uncle Ahmad yawuce da Ummulkhairi Jigawa wajen aikinsa (shima iyalinsa nacan). Itakam Aysha sai zuwa gobe idan ALLAH yakaimu da safe zasu wuce da gwaggo bintu zuwa Abuja. _______________________ *Washe gari* *(Sabuwar rayuwa)* Haka Ai'sha tatashi sukuku kasancewar kuka datasha itada fadeelah yayarta a daren jiya, haka sukaita kuka har saida mama ta tsawatar musu, daga baya kuma tayi musu nasiha da nuna musu muhimmancin hak'uri da yarda da k'addara, tak'arashe dayima Aysha nasiha akan takare mutuncinta a bak'on muhallin dazata tsinci kanta. Kada ta kasance mai kwad'ayi da shiga sabgar da babu ruwanta, banda rashin kunya ganagaba da ita, takuma ringa yima gwaggo bintu biyayya amatsayinta na k'anwar mahaifinta, kada tasake wani yarud'eta ya lalata mata tarbiyyar dasuka gina tsawon shekara 13, koda kuwa a yaran gidanne, tarik'e addininta kada tazama mai sakaci dashi, takula sosai. Nasihar mama tashigi Aysha, kuma ta kar6a cikin kuka da alhinin rabuwa da mahaifiyar tasu, wadda tunda tayi wayau basu ta6a rabuwaba koda na kwana d'aya, Dan marigayi baya barinsu zuwa ko ina Hutu, indai ziyara tawuce ta wuni d'aya basa zuwanta. Haka suka kwana Aysha na kwakume da mama har asubahi, bayan sunyi sallar Asuba gwaggo bintu tashigo tace Aysha tashirya dan sotake su Isa da wuri. Itadai mama batace uffanba, tana zaune tana lazimi, Aysha tamik'e tana shiri tana kuka, gwaggo bintu kam tafita tanamai ta6e bakinta. *6:30am* Aysha tashiga d'akin Umma (abokiyar zaman mama), Umma nazaune afalo tana waya Aysha tashigo ta zauna ak'asa tana sharar kwallah. Ganin haka Umma takatse wayar tata, takamo hannun Aysha tamik'e, kusada ita ta zaunar da'ita tareda rungumeta, ALLAH Sarki shatu d'iyar albarka, kiyi hak'uri kinji, yazamuyi, haka ALLAH ya tsaramana rabuwa daku badan mun shiryaba, inamiki fatan Alkhairi kinji, kibar kuka tunda kinga nanda wata 1 ma zaku zo bikinsu Hafsat, insha ALLAH zamu kasance masu muku Addu'a aduk inda kuka tsinci kanku, amma kirik'e addininki, kada kiyarda kiyi sakaci dashi, banda biyema shed'anun mutane, kitsare mutuncinki kikula da kanki kinji, ALLAH yabamu hak'urin rashin juna, ALLAH yajik'an Malam. Sosai Aysha taji dad'in nasihar Umma, Dan tana kallontane tamkar mama, tanajin dad'in yanda Umma da mama ke zaman lfy, tunda take bata ta6ajin sunyi fad'aba, ko kuma habaici irinna kishiyoyi. Gwaggo bintu ce shigo tana fad'in yaya barirah barta mutafi hakanan, nikam ina mamakin son 'ya'ya irin naku, yakamata dai kusama zukatanku salama. Umma batace komaiba, Dan tasan bak'ar magana gwaggo bintu tafad'a mata, kuma idan dasabo sun sabaji, Dan kokad'an gwaggo bintu batada kirki, (irin dangin mijinnanne masu d'aukar matan 'yan uwansu da zafi). Sudukansu ba k'aunarsu takeba, saidai tafi nuna k'iyayyarta ga Maman Aysha, kasancewar Maman Aysha tanada zafi, bata barin saita kwana, Dan bata ragama gwaggo bintu kokad'an. sunaji suna gani gwaggo bintu tad'auke Aysha suka tafi. Kukakam sunshashi, barema sa'adiyya da Rufaida, wad'anda suka kasance kusan sa'anni, amma yazasuyi an rabasu da 'yar uwarsu. Mama kam k'in fitowama tayi daga d'akinta harsu Aysha suka tafi. *_ABUJA_* K'arfe 12:30 a garin Abuja tayi musu, tunda sukataho Aysha tanata barcinta, bayan tagama shan uban kuka, kokad'an gwaggo bintu batace mata uffanba barema ta lalasheta, sun tsaya awata tasha wadda Aysha batasan inaneba, daganan suka shiga wata taxi wadda tatsinkayi maganar gwaggo bintu tana fad'in akaisu mai-tama. Tafiyar dabata wuce 47mnts ba takawosu wata katafariyar anguwa, mai k'yawun gaske, wadda aka k'awata da manyan gidaje na alfarma, tun ahanya Aysha taketa yaba k'yawun birnin na Abuja, aganintama yanda ake fad'arsa yaci uban haka k'yau, Dan wlhy kamar ba 9ja ba. Tunanin Aysha baikuma tainkewaba saida suka kutsa kai cikin gida mai k'aton bak'in gate, Wanda ba'a bud'e musuba saida mai gadi yatabbatar dasu waye, ganin gwaggo bintu yasashi washe baki tareda bud'e musu k'ofar. Mai gadi yace, "Maman yara kece yanzu da rana tsaka?. Wlhy kuwa d'an gwari nice, nasameku lfy?. Lfy lau, yak'arin hak'urinku?. To sai godiyar ALLAH, d'an gwari, bara muk'arasa ciki, namaji gidan tsit ko lfy?. A lfy lau, kinsan yara suna makaranta, samarin gidanma duk sunfice wajen aiki, wasu kuma makaranta. Hajiya babba ma tana wajen aiki. Sanin shegen surutun d'an gwari yasa Gwaggo bintu katseshi dafad'in to ALLAH yadawo dasu lfy bara muk'arasa muhuta. Har sun fara tafiya d'an gwari yace, "Maman yara! Ina kuma kika samo mana wannan mai k'yau d'in haka?. Cikin k'osawa da surutunsa tace, " d'iya tace. Batajira amsarsaba tacigaba da tafiya, ganin haka yasa Aysha tacigaba da binta abaya. Masha ALLAH!, Aysha tafirta ahankali Dan ganin wani katafaren falo mai kamada gari guda, iya had'uwa falon yahad'u, ank'awatashi da kujeru sets uku akowace kusurwa, set d'aya jajaye, d'anyan farare, d'ayan bak'ak'e, kowanne 6angare kuma akwai kayan kallo, sai can gefe ankafa dogon tebir mai d'aukeda kujeru rututu, aranta tace kaji wani dinning saikace tebirin taro. Babu kowa afalon, sai sassanyan k'amshi dake tashi acikinsa, Dan ko'ina tsaf yake, kuma k'al-k'al, babu wutar lantarki, wannan yasa akad'an d'aga wasu daga cikin labulolin falon hasken rana yashigo, dukda kuwa a gefen danning akwai wani dogon gilas fari tas da'aka k'awata wajen dashi, hakanne yak'arama falon k'awataccen haske mai cika idanu..... Jin an mangareta yasata dawowa hayyacinta daga dogon tunanin, gwaggo bintu ce ta watsa mata harara amma batace komaiba, sai yanzu Aysha tafarga da matar dake tsaye cikin shiga ta alfarma, bazata wuce shekaru 53 ba aduniya, saidai yanayin jikin k'iba datake dashi yak'ara mata yawan shekaru da girma, durk'ushewa Aysha tayi awajen tana gaisheta. A d'an yatsine ta amsa, saidai bata d'aure musu fuskaba, amma dukda haka Aysha taji babu dad'i. Maganar gwaggo bintu taja hankalin Aysha, cikin muryar ladabi gwaggo bintu ke fad'in hajiya ga d'iyatanan nazo da ita danta d'an ringa taimakona dawasu ayyukan saboda girma dake k'ara saukamin. Yayi. kaiwai hajiya tafad'a, sannan tagyara zaman Jakarta tana fad'in nawuce aiki saina dawo. Kai gwaggo bintu ta jinjina tana mata addu'ar dawowa lfy. Jikin Aysha yayi sanyi sosai, Dan yau taga wulak'anci irinna masu kud'i da'ake fad'a, ko kad'an batason dizgi arayuwarta, saima abinda yafi firgitata shine furicin gwaggo bintu datace wai tataho daita danta tayata aiki. Kenan aikatau aka taho da'ita tayi?, gabantane yayi mummunar fad'uwa, da sauri tace kai ALLAH ya kiyaye, nida gatana nazama 'yar aiki? Ina bahaka baneba, banji zance daidaibane. Jan hannunta gwaggo bintu tayi suka nufi wajen dining table, wata k'ofa daked'an gefe ta Gila's suka nufa, gwaggo bintu ta danna wani green d'in Abu k'ofar tabud'e, wani k'amshi mai kwantar da hankalin mai shak'a yadoki hancinansu, mutanene ak'alla sunkai hud'u a kichin d'in. Kusan atare sukace lale marhabin da Maman yara, baki sosai gwaggo bintu ta washe tareda musu sannu da aiki, tak'arasa gaban wata k'yak'yk'yawar mace, fara tas da'ita, itama tanada d'an jiki, amma matar d'azu tafita k'iba, ita kuma wannan kamar zatafi ta d'azun shekaru, Dan zatakai ak'alla 48year's aduniya, saidai k'yawunta da kwarjininta sun 6oye yawan shekarunta, (aganina harda jin dad'ima) tana sanye da doguwar riga bak'a wadda tak'awatu da adon fararen duwatsu, tayi rolling d'ankwalin rigar a kanta, bak'aramin k'yau tayiba kuwa, kaikace tafito daga jinsin larabawane. Durk'usawa gwaggo bintu tayi yanzuma, cikin nuna girmamawa tace hajiya ina yini? Munsameku lfy?. Fuskarta d'aukeda murmushi tace lfy lau Alhmdllh Maman yara, yak'arin hak'uri kuma? ALLAH yagafarta masa. Ameen yarabbi hajiya, ya yaran?. Duk suna lfy. Kowa yana makaranta. Aysha dake durk'ushe itama tace inayini?. Kallonta sosai hajiya tayi, haka kawai taji girarta tadama ta harba, hakama k'irjinta saida yad'an buga, ahankali tafirta "innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un". Sannan ta amsama Aysha gaisuwarta, har yanzu idonta nakan Ayshar, tace Maman yara wannanfa?. d'iya tace Aunty Amarya, tawajen mai rasuwarce nataho da ita. ALLAH sarki 'yanmata ya sunanki?. Kan Aysha ak'asa tace, "A'ISHA!". Masha ALLAH Ayshatu humairah, yahak'urin rashin mahaifi?. Idon Aysha taf da kwallah tace, " Alhamdllh mama. Aunty Amarya taji dad'in sunan da Aysha takirata dashi, tace ALLAH yagafarta masa, yabaku hak'urin rashinsa kinji. Kowa a kichin d'in ya amsa da amin. Bayan gwaggo bintu tagama gaisawa da sauran mutanen sukaimata gaisuwa, Aysha dai kuka yahanata gaidasu. Kulada kukan datakeyi hajiya tace, "Maman yara kushiga cikin Ku huta kafin muk'arasa girki, yau mun makarane wlhy. Da girmamawa gwaggo bintu ta amsa tareda Jan hannun Aysha suka fita. Binsu da kallo hajiya tayi, wani tausayin Aysha da k'aunarta suka tsarga zuciyarta lokaci d'aya, haka kawai yarinyar tashiga ranta, (amma saita alak'anta hakan da tausayinta na maraici). Nace humm anya kuwa Hajiya?.🤔 Daga nana fita suka kumayi daga falon gaba d'aya zuwa wani gini madaidaici dake can baya, shima yanada k'yansa, amma k'aramine sosai, suntadda matsakaicin falo mai d'aukeda kujeru set 1, sai d'akuna ak'allah hud'u, gwaggo bintu tabud'e d'aya da makulli suka Shiga, d'akine madaidaici mai k'atuwar katifa, sai wardrop d'in bango da abinda ba'a rasaba. Kaya kawai suka ajiye gwaggo bintu tashige wata k'ofa, inaga band'akine awajen. Wannan yatabbatarma Aysha shine 6angaren dazasu zauna kenan. Ba'a wani d'au lokaciba gwaggo bintu tafito, da'alama alwala tayi, tace Aysha taje itama tayi. Bayan sun gabatar da sallah cikin wad'anda suka Tarar a kicin takawo musu abinci, zama tayi suka k'ara gaisawa da gwaggo bintu. Daganan surutu ya 6alle a tsakaninsu Wanda yawanci duk gulmar 'yan gidance da labarin abinda yafaru bayan tafiyar gwaggo bintu wajen rasuwar abbasu Aysha. Itadai Aysha taci abincinta, tana kuma saurarensu daki-daki. Zuwa can iya Hama ta mik'e, tana fad'in bara naje Na huta kafin uwar saka aikincan takiramu, kinsan duk ranar aikin Hajiya Bilkeesu babu mai Hutu agidannan, itabata hutaba batabar wani yahutaba, barema yau Alhaji Na gari. Ha6a gwaggo bintu tarik'e tana fad'in ke Dan ALLAH?. wlhy kuwa yana nan, yau kwanansa uku da zuwa, jiya hajiya babba ta ajiye aiki, yau hajiya Bilkeesu takar6a. Cikin magana irinta gulma gwaggo bintu tace, haba nifa ko ince, nayi mamakin tadda hajiya Saudah agida irin lokacinnan. Ina hama ta ta6e baki tana fad'in hummm, kemadai k'yafad'a aii. Daganan tafice abinta. Aysha tace, "ALLAH ya k'yauta azuciyarta, dankuwa su gwaggo bintu sun bata mamaki sosai, suna k'ark'ashin arzik'in mutane amma suna gulmarsu da saka musu ido alamarin gidamsu...............🖊 *I love you all my fan's*😍 [8/7, 7:36 AM] Aisha Galadima: *_Typing_*📲 🤰 *_CIKI DA GASKIYA.......!!_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*😜 *Sadaukarwa* _My sweet dady_ (ALLAH ya gafarta maka)🤲🏻 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _Godiya gareki billy s fari, luv you so much_ . ,´¯`, ,´¯`:,..../ /¯/.../..../ ••••••••••••••••• /../.../..../..,----, /../.../....//´...........`. Happy /../.../..../......../´¯\....\ •••••••••• ('.('..('....('.........|. 💙🍁💙 \.....................`\.../´...) \.......💙...../ New book \.... 💙.../ •••••••••••••• \......................./ |......................|Billyn abdul 💙█⚀⚃⚄⚅⚃⚀█💙 .🇯🇵.¸ ¸.🇯🇵   (✺`“•.\\ . // ¸. •"´✺)   “•¸.. 💙🍁💙 .•“   (✺¸.•“// \\`“•.¸✺)   💙ciki da gaskiya💙 💙█⚀⚄⚅⚃⚄⚀█ 💙 0⃣3⃣ Gwaggo bintu ta kalli Aysha dake zaune a gefen katifa ta rabga uban tagumi, gaba d'aya kewar iyayenta da 'yan uwanta sun addabeta, jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta a Kano.... Ta6atan da gwaggo bintu tayine yakatse mata tunaninta, tajuyo tana kallonta, harara gwaggo bintu tasakar mata tareda fad'in waike wannan dogon tunanin namiyene? Kosukike mutanen gidan sud'auka satoki nayine?. Aysha tagoge kwallan dasuka cika mata idanu, kanta tashiga girgizawa alamar a'a, Dan tana magana zata iya 6arkewa da kuka. Baki gwaggo bintu ta ta6e, murya adak'ile tace saiki mik'e mushiga gaida mutan gidan. Aysha tamik'e jiki a sanyaye, afalo suka iske su iya hama suna kallon film d'in kalan dangi, sai k'yalk'yala dariya suke zubawa, gwaggo bintu tace musu bara mugaida Ammah da Alhaji da hajiya babba. To afito lfy cewar karime tana dariya, ammafa AMMAH bata dawoba. Gwaggo bintu tace, "to bara mugaida uwargidan. Dariya su iya hama suka farayi, itama gwaggo bintu dariyar takeyi. Tsakar gidan kwanyar yake da haske tamkar rana, ko'ina kwayayen wutane masu k'yau, da sallama suka Shiga k'aton falon d'azun. Bakajin komai sai hayaniyar yaran gidan Dana TV's, dan duk tvn uku akunne take, kuma kowanne rukunin kujeru akwai yaran. Aysha tuni tsoro yakamata, Dan haka take bata cikason Shiga jama'aba. Yaran suna ganin gwaggo bintu suka fara fad'in oyoyo Maman Yara, k'ananunma zuwa sukayi suka rungumeta,, wannan ya tabbatarma Aysha da kowa yasan gwaggo bintu agidan. Aysha takai dubanta ga set d'in fararen kujerun inda matasan samarin gidan suke zazzaune, wasu a kujeru wasu ak'asan center rug, su kusan 7 ne awajen, sai surutu suke zubawa suna dariya, kallonta yatsaya akan Wanda ke a tsaye yanata zabga surutu, fira sukeyi akan Ball, wannan yasa suka rud'e da gaddama, kowa Na k'ok'arin kare Team d'insa. Sun birge Aysha sosai, Dan duk suna kama da juna, d'ayan gefen kuma 'yammatane su hud'u, Wanda zasu iya zama sa'annin juna, saikuma biyu dasuma Kansu d'aya, amma basukai Girman Na farkoba, sai kuma k'ananun yara biyar suma bidabi. Cikin ladabi Aysha tagaida matasan samarin kamar yanda gwaggo bintu ta umarceta. Duk suka amsa idonsu akanta, ganin bak'uwar fuska, Na tsaye mai surutu yace uhhm INA Maman yara tasamo mana pretty girl d'innan?. Wanda ke kusadashine ya shuri k'afafunsa, cikin wasa yace kai Musleem kaga takanka, anya kuwa bakai za'a farama aure agidannanba?. Da sauri musleem yadafe inda Ramadan ya shureshi, yace, " kutt kai ya Ramadan rufamin asiri mana, ga ya khaleel can mai shekaru 32 baya maganar aure saini daban wuce 25 ba, gasu ya Sultan & ya mujaheed nanma. Hararsa ya Sultan tayi, yace, " mukad'ai ka raina ko? Kafad'a agaban ya khaleel mana in ba tsoroba. Dariya suka kece da'ita gaba d'aya, cikin dariya Muhseen yace, "wlhy yafad'a inbaici k'aniyarsaba, kwanaki naje falon Baffah gaidashi lokacin ya khaleel nagida, saina tadda ana MASA fad'a, bammajifa akan abinda ake MASA fad'an ba, saidai nafahimci akan aurene amma wlhy tun agabam Baffah yake antayamin harara har muka fito...... Ananma dariya suka kumayi, yanzu harda 'yanmatanma, dan sunajiyo hirar yayun Nasu. Aysha dai da firar tatashi domin ita kanta Na 'ak'asa, saida gwaggo bintu tace tatashi suje sannan tamik'e da k'yar saboda kunyar matasan samarin, masu matuk'ar birgeta, ganin kansu ahad'e family's abin sha'awa, ga zallar k'aunar junansu dasukeyi daga gani. Harsun fara tafiya Hafeez yace, "Maman yara 'yarkice?. Dariya Maman yara tayi, tace, " 'yatace Hafeez, d'iyar yayanace daya rasu naje gida. Kusan atare sukace Maman yara rasuwa akayimiki? ALLAH bamu saniba, munzata kinje gidane ziyara. Nan suka shiga mata gaisuwa, dayawansu tausayin Aysha yashigesu, Zunnurain sarkin tausayi har idonsa yacika da kwallah. Godiya gwaggo bintu tamusu takama hannun Aysha suka nufi 6angaren hajiya babba. Tana zaune hakimce a falonta, tana karatun jarida, babbar macece hamshak'iya, kallo d'aya zaka mata Kasan tagama jik'uwa da 'yan canji, gawata tak'ama da Isa irinta manyan mata 'yan boko, itamadai tanada k'ibarta babu laifi, saidai bak'ace, amma akwai k'yawu sosai, sanye take cikin doguwar Riga mai sul6i, zamu iya dangantata da rigar barci, Tamata k'au, dukda fuskarta babu alamun annuri, sai tsabagen mulki da tink'aho, gefenta 'yammatane su uku, biyu Kansu d'aya, d'aya kuma dagani tagirme musu, da kyar 'yan matan suka amsa sallamar tasu. Gwaggo bintu tazube ak'asa tana gaida hajiya babba, saida taja wasu mintuna sannan ta ajiye jaridar hannunta tana amsawa da lfy cikin isa. Cikin rawar murya Aysha ma ta gaisheta, ita saima yanzu takula da ayshar, tsuramata idanu tayi kurr batareda ta amsaba. Aysha tayi k'asa da kanta, Dan ganin kallon kurillar da hajiya babba kemata, ita kanta gwaggo bintu talura, Dan haka gabanta yashiga fad'uwa, Dan batasan manufar kallonba, takuma kwana da Sanin rashin mutunci da k'yamar talaka irinna hajiya babba, wannan yasa Sam 'yan aikin gidan basuda kwarjini agareta da 'ya'yanta. Hajiya babba tayi gyaran murya, cikin isarta tace bintu! Wannan yarinyarfa?. Muryar gwaggo bintu narawa tace am... Am.... Hajiya d'iyar yayanace mai rasuwa aka bani. d'an yatsine fuska hajiya babba tayi tareda gyara zaman siririn farin spece d'inta, batareda tace uffanba tad'auki jaridarta tacigaba da karatu. Sukam 'yan matannan sai kallon wulak'anci sukema Aysha da gwaggo bintu kanta. Wajen mintuna 3 babu Wanda yakuma cewa komai, yaran kowacce tana latsa waya, babbarce taketa latse-latse a laptop. Wayar hajiya babba dake gefenta tahau wringing, d'aya daga cikin 'yanmatan tayi saurin d'auka, cikin ihun murna tace, "lahh ya khaleel ne. Atare sauran sukace haba dai?. Kafin tabasu amsa hajiya babba ta kwace wayarta tanata zuba murmushi, akunne takara tareda fad'in my lovelyson kana lfy........ Harara Husnah tamakama su gwaggo bintu, tace Malam kibamu waje haka ko. Gwaggo bintu tace yihak'uri 2. Tsaki Hasnah tayi itama, gwaggo bintu taja hannun Aysha suka fita. Yanzuma ran Aysha ya sosu sosai, Dan takula wad'annan basuda kirki. Har yanzun samarinnan nata hirarsu, 'yan matanma sunkoma inda suke, Dan haka surutu yak'aru sosai a falon. Harsun Aysha suka nufi d'ayan 6angaren basu saniba, sunkusa shigewane suka tsinkayi muryar 'yar k'aramar yarinyar tana fad'in maman yara Ammah bata nan, taje Jigawa tun jiya, yanzu daddy da Aunty suka tafi d'akkota a airport. Ayya Noor d'in Aunty ngd, ALLAH yadawo dasu lfy. Daga nan gwaggo bintu suka fice, 6angarensu Na 'yan aiki suka koma, suka tarar Har yanzu su iya hama Na kallon film abinsu. Sulalewa Aysha tayi takoma d'akinsu. Babu dad'ewa gwaggo bintu tashigo itama, takalli Aysha tace idan barci kikeji tashi naraki wajen kwananki, Dan tare zaku ringa kwana da Bishirah. To gwaggo, Aysha tafad'a a sanyaye. Bayan gwaggo bintu taraka Aysha d'akin Bishirah tabarosu. Cikeda fara'a Bishirah takalli Aysha, tace zoki kwanta mana, ko bak'yajin barcine?. Guntun murmushi Aysha tayi, tazo bakin katifar ta zauna a d'arare. Bishirah tace yasunanki?. Aysha!. Aysha tafad'a atak'aice. Sunanki mai dad'i cewar Bishirah tana dariya, tace nikuma sunana Bishirah, iya hama ce Mamana. Kema aiki aka kawoki ko?. Kallonta Aysha tayi, ahankali ta girgiza mata kai alamar a'a, saidai k'asan ranta tana mamakin shegen surutun bishirah. Bishirah tayi murmushi, tashi tayi daga kwanciyar datayi, tadafa kafad'ar Aysha, cikin murya kasa-kasa tace nasan son kud'imsu iya bazai bari abarkiba, kema cikinmu zaki koma. Gaban Aysha yafad'a, tayi shiru tanabin Bishirah da kallo. Bishirah tayi 'yar dariya takoma ta kwanta, tana fad'in ki kwanta, saboda tunda asuba zamu tashi. Aysha da mamakin surutun Bishirah yacikata, tazame ahankali ta kwanta, harta lumshe idonta saikuma tabud'esu akan Bishirah, muryarta a sanyaye tace Dan ALLAH kibani labarin gidannan da abinda yak'usa. Nakasa fahimtar komai, musamman yawan Matan gidan da yaransu, harma da mabanbantan halayensu. Dariya sosai Bishirah tayi, cikin dariya tace aii bazaki gane komaiba Aysha agidanan saida bayani, wannan shine zaisa kizauna dakowa lfy, kisan halin kowa da yanda zaki zauna dashi. Tagyara kwanciyarta zuwa rigingine. Bayan takalli Aysha tace, "kibini bashi wata rana zan fad'amiki, kamar yanda Nima iya tafad'amin. Cikin rashin jin dad'i Aysha tace, " miyasa ba yanzuba?. Saboda bamuda lokaci isashshe, gobe yaran gidan sunada makaranta, Dan haka k'arfe 4 Na asuba za'a tashemu, mukwanta Dan musami isashshen barci, namiki alk'awarin ranar weekend zanbaki tarihin gidan *_Alhaji ABDALLAH JIGAWA._* Gyad'a kai kawai Aysha tayi, amma taso tasan komai tun ayaud'in, tayi addu'ar barci tagyara kwanciyarta, sadai ganin bishirah batayi addu'arba abin yabata mamaki, bata mata maganaba talumshe idonta, saboda gajiyar hanya darashin isashshen barci nafargabar baringida akwan biyun baya, yasaka barcin saurin d'aukarta yanzun..........🖊 Fan's kubini bashi a page 4. Yasin nagaji😒, kamarma nadaina buk d'in, dannaga kamar baya muku dad'i🤨??. Comments d'inku shine alamun nuna jin dad'inkufa🤥. zan tsaya anan harsai naga comments naku ehe😏. *I love you my sweet fan's*😍 [8/7, 7:36 AM] Aisha Galadima: *_Typing_*📲 🤰 *_CIKI DA GASKIYA.......!!_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*😜 *Sadaukarwa* _My sweet dady_ (ALLAH ya gafarta maka)🤲🏻 *_part 1_* (littafi na d'aya)📕 0⃣4⃣ Kamar yanda Bishirah tafad'a kuwa hakance ta kasance, k'arfe 4am iya tazo ta tada bishirah, amma banda Aysha daketa barcinta. Aysha bata farkaba saida wasu masallatan suka fara kabbara sallahma, ahanzarce ta tashi tana ambatar addu'ar tashi daga barci, kallonta takai gefenta inda bishirah take kwance, amma saitaga wayam, tunowa da firarsu ta daren jiya tayi, tagirgiza kai cikin takaicin rashin 'yanci da talaka ke fuskanta ak'asarnan, barcinma bazakayi isashsheba, saida tsayayyen lokacin tashi domin hidimtawa wasu, ganin tunani zaisata makara sallah yasata mik'ewa, bata 6ata lokaciba tafad'a toilet d'in dake d'akin ta d'auro alwala. Bayan tagabar da sallarta tayi azkar a gaggauce tatashi. 6angaren tsit yake, alamun duk suntafi bautar data zaunar dasu agidan, ran Aysha babu dad'i tafice itama, cikeda fargaba tanufi 6angaren mutanen gidan, k'ofar arufe take, kuma bazata iya bud'ewaba, harta juya zata koma inda tafito saiga matasan gidan suduka, sunsako k'yak'yk'yawan dattijo a tsakkiya, kafin tabar gurin harsun k'araso gareta, dole tazube guywoyinta ak'asa tana kwasar gaisuwa, duk suka amsa mata, dattijo Alhaji Abdallah yakafama Aysha ido, haka kawai yaji gabansa yafad'i, girarsa ta dama ta harba, (in bilynku nace komiyasa?) yad'an lumshe idanunsa tareda maidasu kan yaransa yana tambayarsu da ido wacece?. Mujaheed yace Baffah d'iyar Maman yarace. d'an murmushinsu Na manya yayi batareda yace komaiba yacigaba da tafiya, matasan yaransa suka take masa baya. Muslim ne yadawo baya yacema Aysha mikike nemane?. Har yanzu tana a durk'ushe kanta ak'asa tace zanje wajensu Gwaggona natayasu aiki, shiru yayi yana nazarin waye gwaggonta?, saican yace, "kina nufin Maman yara?. Kanta tagyad'a masa batareda tayi maganaba, yace, " OK tashi Na nunu miki. K'ofar baya ta kichin Muslim ya nunama Aysha yace kishiga suna aciki. Baijira cewartaba yajuya abinsa. Bayansa tabi dakallo harya 6ace mata sannan tashiga Inda ya nuna mata. Aikam duk suna ciki, Rabi ce kawai babu, tanacan tana gyaran babban falon gidan, Aysha tagaida kowa, sai sannan talura da hajiyar jiya dasuka tadda akichind'in lokacin dasukazo, matsawa tayi tadurk'usa har k'asa ta gaisheta. Yanzuma cikeda fara'a hajiya ta amsa mata, tad'ora dafad'in Aysha nazata kinacan kina barcin gajiya?. d'an murmushi Aysha tayi tace, "a'a mama natashi nayi sallah. OK tojeki kwanta abinki kinji. A'a mama banajin barci, zan tayaku aikin. Kai Aysha bazaki iya da wannan aikinba yamiki girma. Lah mama inayi aii, kullum mune mukeyi agidanmu nidasu yaya fadeelah, kubani komiye zan iya insha ALLAH. Aysha tayi matuk'ar birge hajiya bilkeesu, harcikin ranta taji k'aunar yarinyar... ___________________________ Gaba d'aya yaran gidan sun hallara ak'aton dinning table d'in suna breakfast, wasu sanye da Uniform, wasukuma sunsha kwalliyarsu ta mayan guys, bakajin komai sai k'arar filets da cokula, sai surutun wasunsu k'asa-k'asa, Aysha da Bishirah suna daga kichin suna wanke-waken kwanikan da'aka 6ata. Kwas-kwas Hameedah tafito daga 6angarensu, ko Inda sauran 'yan uwanta suke bata kallaba, haka suma babu Wanda yadamu da'ita, Dan kowa yasan k'arancin tarbiyyar 'ya'yan hajiya babba agidan. Mintina4 tsakani dafitarta saigata tadawo tana k'unk'uni, dinning table d'in tanufa, babuko tausa harshe tace, "ya Ramadan kazo kacire motarka zan fita, dankayi blocking d'ina. Yawancinsu duksaida suka kalleta. Cikin 6acin rai Ramadan yace, " ank'id'in fitsararriya, kebaki iya gaida kowaba? Nangurin dukba yayyanki baneba, yaymaganar yana nuna sauran 'yan uwansa. Baki Hameedah tamurgud'a tana k'unk'uni. ran Ramadan yakuma 6aci, yace Dan Uwarki mikike fad'a?. Baki takuma murgud'awa. Yatashi afusace zai fallamata mari....... Karka kuskura kata6amin yarinya.... Maganar hajiya babba tariski kunnuwansu, kowa yamaida Kallonsa gareta. Tacigaba dafad'in Dan Uwarka Bilkeesu ita tahaifamin 'yarne? dazaka ware kwanji kadakarmin ita?, wlhy koda wasa karwani shege yak'ara wannan kuskuren, inba hakaba rayuka zasu 6aci, kajimin shegen yaro. Ramadan ya kalleta, amma momy kinaganinfa abinda takema mutane? Mu sa'annintane? Tazo tawuce bata gaida kowaba, kosu ya Mujaheed fa bata gayarba...... Tobazata gayar d'inba, kokuwa dolene saita gaishesu? Sud'in ubantane? Bare ace yawajaba agareta saita gaidasu?..... Har Ramadan yabud'e baki zaiyi magana......hajiya Bilkeesu takatseshi da daka MASA tsawa. Ramadan!!! Karna sakejin maganarka anan, kaje kacire motarka tafita. Idonsa jajur yace, "amma Aunty...... Dakatamin, nace karka sake magana ko, wuce kajanye motarka. Saida ya watsama Hameedah harara sannan Yakoma wajen zamansa yafigi key d'in motarsa a dinning yafita. Hajiya babba da Hameeda suka take masa baya, hajia babba nak'ara zazzaga masifa da zagin Aunty. Girgiza kai kawai Aunty tayi, tak'arasa dinning d'in Tanama sauran fad'a. cikin ladabi Sultan yace, " kiyi hak'uri Aunty, wlhy laifin yarinyarne, kinsansudai basuda kunya.. Komadai miye kukama girmanku, banason fitina kunsani. Hak'uri sukaita bata suduka. Hayaniyarmi nakejine?..... Ammah dake fitowa 6angarenta tafad'a. dattijuwar kwarai kenan mai lafiya da tsawon kwana. Aunty tarissina tagaisheta, cikeda kulawa ta amsa, tad'ora dafad'in Bilkeesu mike faruwa?. Murmushi Aunty tayi, babu komai Ammah. Wane babu komai, bayan naji muryar fitinanniyarnan tana shegantamin jikoki, wlhyfa aka k'ureni zand'au mataki agidannan, amma nasan maganin 'yar banza. Hak'uri Aunty tabata, hakama yaran, sannan suka gaidata cikin ladabi, itakuma ta amsa tanamai farinciki da d'unbin k'aunar jikokin nata, masu matuk'ar sonta da tattalinta. Su Aysha dake la6e suna kallon komai suka saki murmushi, Dan tsohuwar taburge Aysha. Ramadan Na shigowa falon Baffah yafito cikin shigarsa ta kamala, wato farar shadda mai d'inkin 'yar ciki da malun-malun, tasha aiki sai maik'o takeyi. Duk abinda ke faruwa yana jiyosu daga 6angarensa, wanka yakeyi shiyyasa bai fitoba. Kallon Ramadan yayi, yace INA Hameedan?. Baffah tafita, cewar Ramadan a ladabce. Jinjina kai yayi, amma baice komaiba, yak'arasa Inda Ammah take yagaidata, yaransa mata suka gaisheshi, ya gaisa da mazan tun bayan dawowarsu masallaci. Yakai dubansa ga Aunty, da ido yaymata magana, tareda ban hak'uri. Tayi murmushi da nuna jin kunyarta gareshi. Dayawan yaran sunga soyayyar iyayen nasu, wannan yasakasu murmushi, sunajin sanyi dak'ara k'aunar babansu harma da mamansu dukda ba dukansu Aunty tahaifaba. Baffah yak'araso yazauna a dining d'in shima aunty tahad'a MASA break d'in. (Haka yakeyi, inhar yana gidan cikin iyalinsa yakecin abinci, wannan ak'idarsace). Aysha sai juya lamarin gidan takeyi azuciyarta, itadai agidansu tatashi taga mahaifiyarta da kishiya, amma Bahaka taga anayiba, kuma suma yaran Kansu a had'e yake, babukuma Wanda ya Isa ya raina wani acikinsu, akwai Respect d'in nagaba tsakaninsu, idankace kuma zaka kuskure kaci uwaka, Dan Umma da mama kowanne tanada ikon hukunta d'an kowa, shiyyasa bakowa yake banbance yaran gidanbama. Itakam tanason k'arin bayani gameda wannan family. Haka taita tunani harsuka kammala aikinsu. Basu samu gidan yayi hankaliba saida kowa yafice, yaran wasu suntafi aiki, wasu schools, hakama hajiya babba da hajiya saudah duksun fita. Daga hajiya Bilkeesu sai Ammah, saikuma su 'yan aiki mazansu da matansu. Shima mai gidan yafice tuni.............🖊 *I love you all my Fan's*😍 [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing_*📲 🤰 *_CIKI DA GASKIYA.......!!_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO......._*😜 *Sadaukarwa* _My sweet dady_ (ALLAH ya gafarta maka)🤲🏻 *_part 1_* (littafi na d'aya)📕 0⃣5⃣ A kwana atashi babu wuya wajen ALLAH, yau kwanan Aysha 10 cif agidan Alhaji Abdallah Jigawa. A tsawon kwanakinnan ta fiskanci k'alubale da dama, dakuma wasu abubuwa dasuka danganci mutanen gidan, taga abubuwan ban haushi, taga naban mamaki, taga naban dariya, taga Na birgewa, taga Na al'ajabi. a6angaren dangantakarta da gidan kuwa tazama cikakkiyar 'yar aiki, Dan kowacce hidima da'ita aciki, saidai abinda batada sani akansa shine, kotanadaga cikin jerin masu albashi? Kokuwa itad'in 'yar tayice kamar yanda gwaggo bintu ta ambata aranar dasuka shigo gidan. Babban kuma abinda kecin zuciyarta shine rashin tantance al'ummar gidan da matsayinsu, sunayen k'alilanne aciki tarik'e, suma dantaji ana ambatane. Yauma kamar kullum sungama tik'ar aikin gyaran gidan, ko'ina yayi fes sai d'aukar ido yakeyi, ga k'amshin tiraren wuta natashi. Bishirah data gama dai-daita gudun AC falon takai dubanta ga Aysha, to muje na gama, kinga muma ZAMU huta kafin sudawo su 6ata. Murmushin yak'e Aysha tayi da tausayin Kansu, tanamai jin zafin katsewar karatunta da zama haidimar wasu adalilin maraici, dayanzu tana cikin jerin masu Shiga ss1, amma k'addara tadad'e da guntule wannan burin nata, tana rok'on ALLAH daya k'yautata rayuwar sauran 'yan uwanta karsu tsinci Kansu cikin hali irin nata. ALLAH yasa iyayen ruk'onsu sucigaba dajan akalar tarbiyyarsu da iliminsu kamar da. Dukda tana k'yautatamusu zato, dantasan gwaggo Asma'u da uncle Ahmad bazasu kasance irin gwaggo bintuba, to barema kawu bilyamin dake amsa suna tamkar mahaifinsu. Damadai itace batayi dacen uwar rik'oba kafd'insu, shiyyasa kuwa yafi nuna tausayi akanta....... Firgigit tadawo hankalinta saboda zingurar da bishirah Tamata. Aysha tunanin mikikeyine haka?, yakamata kisaki jikinkifa, ai yanzu kinzama 'yar gida, gakida kwana har goma acikin garin Abuja. Ajiyar zuciya Aysha tayi. Bishirah tace, "jekiyi wankan saikizo nabaki labarin 'yan gidannan. Cikeda d'oki Aysha Tace, " Dan ALLAH da gaske kikeyi?. Wlhy kuwa da gaske. Da Sauri Aysha tatashi tafad'a wanka, Dan yanzu komai NATA yadawo d'akin bishirah, tsakaninta da gwaggo bintu gaisuwace kawai, Dan bawani janta takeyi ajikiba. _____________________________ *_Alhaji Abdallah Jigawa family's_* Alhaji Abdallah Rufa'ee jigawa shine cikakken sunan maigidan, d'an asalin jihar jigawane a garin ringim, ALLAH yayima mahaifinsa Malam Rufa'ee rasuwa dadad'ewa. Alhaji Abdallah yana sana'ar saida carpets ne a babbar kasuwar wuse dake Abuja, ahankali ubangiji yacigaba da bud'a masa harkokinsa harya bud'e kamfaninsa na kansa, Wanda yasami had'in guywa da k'asar Turkey, Alhamdullah kasuwancinsa yabunk'asa matuk'a ak'asar, yanzu haka sunada reshen kamfanin a Kano, Lagos, sokoto, Jigawa. Matansa uku da 'ya'ya 21. Hajiya Laurah itace uwar gida, wadda sukan kira da hajiya babba, yaran kuma suna cemata (momy). cikakkiyar 'Yar bokoce dantayi karatu mai zurfi, ko kad'an hajiya laurah batason talaka, macece mai tunk'aho da tak'ama, shikansa Alhaji Abdallah nuna masa isarta takeyi, tad'auki aikinta sosai da muhimmanci, kokad'an babu maijin dad'in zama da'ita agidan, saboda halayyarta, musamman hajia Bilkeesu. Yaranta 6, Zuwairah, Shukurah, Ibraheem khaleel, Hameedah, Hasna, Husnah. Sai Hajiya Bilkeesu, tanada yara 11, Rufa'ee, ALLAH yamasa rasuwa wata uku dasuka shige sakamakon had'arin mota zaije jigawa. Yanzu akwai 10 Sultan, Mujahedeen, Amatullah, Ramadan, Zunnurain, Muslim, Muhseen, Amal, Tasleem, UmmuNoor. Itakam tanada hak'uri, ga kawaici da sauk'inkai, kowa natane, batada k'yamar talaka, saima tazauna tayita hira da 'yan aikin gidan, gatada taimako, batayi karatu mai zurfiba, iyakarta Secondary aka aurama Alhaji Abdallah ita, tana yarinya d'anya, kobayan aurensu batacigaba da karatuntaba, danhaka bata aikin komai saina kula da mijinta da 'ya'yanta, wannan yasa suka taso cikin tarbiyya. Alhaji Abdallah nasonta sosai saboda k'yautatawarta agareshi da mahaifiyarsa. Yaran gidan nakiranta (Aunty Mamie). Sai amarya hajia saudah, itamadai balaifi akwai girman kai, amma batakai hajiya babba ba, itamadai ma'aikaciyar Ce, Lauya ce maizaman kanta, ita wata irin mutumce dabata damu da damuwar kowaba, cikikam harda 'ya'yanta, (shiyyasa yaranta duk sunfi shak'uwa da Aunty Mamie) takan bama aikinta muhimmanci fiye da komai, kakan dad'ema baka ganta cikin lamuran gidanba, hajiya babba taso suhad'ema hajiya bikeesu kai itada hajia saudah, amma hajia saudah tace ita ba wannane agabantaba. Yaranta 4 Hafeez, Shuhudah, Maleekah, Nurudden. Itakuma suna cemata Ummee Amarya. Mahaifiyar Alhaji Abdallah tana nan gidan taredashi, itace tsohuwar dakika gani, anabata kulawa sosai agidannan, babu maison abinda zai ta6ata, idan kika cire hajiya babba da 'ya'yan tokowa jiyake da'ita, ya khaleel ne kawai halinsa ya banbanta ayaran hajiya babba, danshi babu ruwansa. Wannan shine tak'aitaccen tarihin gidannan. Kinada tambayane??. Ajiyar zuciya Aysha tasauke, cikin kafe bishirah da kallo tace, tambayata biyuce zuwa uku. Tafarko suwaye sauran yara uku danagani dakuma 'yanmata biyu?. Dariya Bisheerah tad'anyi, cikin tsokana tace Ashe kinfahimci labarin sosai?, 'yan mata biyu dakika gani, Hamdiyya da Naseeba yaran k'anin Alhaji Abdallah ne, uncle Ma'aruff, suma suna nan zaune awajen Aunty Mamie, karatu sukeyi anan sudasu Amal. K'anan su uku kam yaran aunty Amatullah ne, 'yan uku, suna k'asar Japan itada mijinta, shine aka kawosu nan gidan saboda school. Jinjina kai Aysha tayi alamun gamsuwa, tacigaba da fad'in yaran hajiya babba fa? Dan uku nagani yanzu agida?. Eh, biyu sunyi aure, Anty zuwairah tana Lego's itada mijinta, sai Anty Shukurah tananan abuja, amma yanzu suna kasar Jordan shekara uku kenan, wai mijin natane yake karo karatu, yaya khaleel kuma bansan takamaimai k'asar dayakeba, Dan shi yanzu zai iya cemikima yana Najeria, anjima kuma kiji yabar k'asar, haka yake yawo k'asashen duniya saboda yanayin aikinsa. "Aikin mi yakeyi?." Wlhy ban saniba Aysha, amma naji sunacewa ko d'an sandane, kamardai haka naji su iya hama nafad'a kwanaki. Amma kwanannanma zakiji yazo k'asar saboda hutun k'arshen shekara dakuma meeting na family dasukeyi. Shiru Aysha tayi, Dan haka kawai tasamu kanta da fad'uwar gaba, Bishirah ta ta6ata tareda fad'in shikenan kin gama tanbayar taki?. Jiki amace Aysha tad'aga mata kanta, kafin Bishirah tace wani Abu kiran da Rabi kemusu yakatseta. Atare suka amsamata, sannan suka fito inda take. Kichin suka shiga domin tanadar abincin rana, yaran gidan sunkusa fara dawowa, yaukuma aikin hajia saudah ne. Itakam tanama wajen aikinta. Duk ranakun aikinsu itada hajiya babba 'yan aikine keyin komai, sa6abanin Anty Mamie dakan tsaya ayi komai da ita, shiyyasa yaran kanyi farincikin aikinta, Dan koba komai zasuci mai dad'i da tsafta...............🖊 nagaji bara nahuta😏😢, kuma inajin yunwa😋, muhad'u a page 6 guys😉 *I love you all my lovely fans*😍 [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) *_Dolene namik'o sak'on jinjina da godiya agareku 'yan group d'ina, ALLAH yabar zuminci, inajinku sosai aruhina, inayinku irin tamau-tamau d'innan, I love you so much_*😘😉 0⃣6⃣ Gaban Aysha sai fad'uwa yakeyi sakamakon kiran da hajia babba ta aiko karime Tamata. harsuka shiga falon tana addu'ar daduk ta iso bakinta. Hajiya babba nazaune tareda wata hamshak'iyar mace, daganinta kasan naira ta zauna. Karime tarissina tana fad'in hajia ga Ayshar nan. Kai kawai hajia babba ta gyad'ama karime alamar taji. Karime nafita daga falo Aysha ta durk'ushe tana gaishesu, babu Wanda ya amsa acikinsu, saidai suna binta da kallon k'urullah, musammanma bak'uwar ta hajia babba. bayan kamar 4mnt hajia babba tace, ''aminiya kingantafa, ai zata iya nake gani?. Wani murmushin k'asaita hajia khaltum tasaki, tagyara zamanta tana k'arema Aysha kallo lungu da sak'o, Aminiya ai zancenma zata iya labarine, zan iya cemiki tunda muke business d'innan baki ta6a samun hajaba irin ta wannan lokacin, ai young girls irin wad'annan su ake so dama, ALLAH kad'ai yasan irin ribar daza'a samu anan 👉🏻🙎🏻‍♀tayi maganar tana nuna Aysha datayi k'asa dakai tamkar munafuka. Amma jikinta sai tsuma yakeyi saboda tsoro da firgicin zaurencen Nasu hajia babba, ko kad'an Aysha bata fahimtar komai a zancensu, saidai tanaji ajikinta ba alkairi baneba, addu'oin Neman tsari tafara a can k'asan zuciyarta...... Hajia khaltume takatseta da fad'in yarinya yasunanki?. Muryarta Na rawa tace Aysha. Nice name!. Cewar hajia khaltume. Daga nan suka sallami Aysha tatafi. Tana tafiya 6angarensu tana sharar kwalla, haka kawai taji tana tausayin kanta, gashi su hajia babba sun gargad'eta kada tasanarma kowa kiran dasukai mata, inba hakaba komi yabiyo baya ita tajama kanta. Gaff taci karo da Abu, dasauri tad'ago kanta, amma kafin tasan wata bige ansauke mata Marika har biyu. Dafe kuncinta tayi saboda azaba, ke Dan ubanki bak'ya ganine?.... Maganar matashiyar Husnah ta katseta. Dan ALLAH kiyi hak'uri Anty Husnah wlhy bankula baneba, Aysha tayi maganar tana durk'usawa ak'asa, haryanzu hannunta Na dafe a kuncinta. Muhseen yak'araso inda suke da sauri, yace k Husnah lfy kuwa?. Cikin huci tace wai 'Yar iskar yarinyarnan hartakai ta bangajeni, Muhseen. kiyi hak'uri to, tayi kuskure amma bazata sakeba, ke Aysha bata hak'uri. Hak'uri Aysha takuma bata cikin kuka. Hasnah taja tsaki sannan tara6a gefen Aysha tashige, harda takama Aysha yatsun kafa. Aysha tafashe da sabon kuka dantaji zafin takawar. shikansa Muhseen yaga takawar da Husnah tama Aysha, danhaka ya rintse idanunsa yayinda Aysha tafashe da sabon kukan, tabashi tausayi sosai, yace kiyi hak'uri kinji, watarana sai labari, idan kina tafiya kiringa kula. Aysha ta jinjina kanta tana share hawaye, sannan tamik'e. Lafiya kuwa ya Muhseen?. Kallonsa yayi yace babu komai Hafeez, Husnah Ce tamari Aisha wai ta bangajeta, shine nake lallashin ayshar. Itadai kawai zalincinta yamotsa, Dan nasan babu yanda za'ayi Yarinyar ta bangajeta tana sane, ALLAH ya sakamata. Ameen dai Hafeez. Yinin yau zumbur Aysha ad'aki tayisa, kowa ya tambayeta saitace batada lafiyane, itakam sokawai take tasamu hanyar guduwa daga gidan, Dan bazata zauna acutar da'itaba. Babban tashin hankalintama shine gwaggo bintu, kokad'an bata cika damuwa da lamarintaba yanzu, yau d'innanma kowa yazo yaji damuwarta amma banda ita, takuma fashewa da kuka mai ban tausayi, lallai tayarda maraici daban yake, Inda mahaifinsu Nada rai waya Isa yamusu koda kallon kaskanci, tatuna gidansu da rayuwa irinta family nata.... Haka taita kuka mai tsuma rai, hardai zazza6in gaskiya yasaukar mata. Bishirah ce taita kula da'ita har zazza6in yasauka, koda tatashi da safe taji sauk'i sosai, saidai damuwa da fargabar abindasu hajia babba suke kullama rayuwarta gashikuma takasa sanarma koda bishirah ne saboda tsoron gargad'in dasukai mata. *_Bayan sati d'aya_* Zuwa yanzun Aysha tahak'ura da yunk'urin guduwa, dantabi dukkanin hanyoyin daya dace amma babu nasara, yawan kula da ita da bishirah keyi kuma yasata sakin jikinta sosai, Dan bishirah tagirmi Aysha dakusan 2years. Yau tunda suka tashi suketa bautar girke-girke saboda zuwan ya khaleel k'asar, harma da Aunty zuwairah daga Lagos. Su Aunty Amatullah kuma sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Zuwa k'arfe 2pm suka kammala komai, gidan yad'auki k'amshin girki dana turare, mafi yawan yaran gidan basu dawoba, wasu nawajen aiki, wasukuma basu dawo school ba. Suma su Aysha 6angarensu suka dawo sukai wanka. Wajen k'arfe uku Aunty zuwairah ta iso daga Lagos, yaran gidan basuwani damu da zuwantaba, saboda itama masifaffiyace kamar hajia babba, indai tazo gidan saita addabi kowa, k'annentane kawai suketa farinciki saikuma hajia babba. Sudai su Aysha tunda suka gama shigarmata da kayanta ciki sukadawo harabar gidan suka zauna, karatun littafin *magana jarice* Aysha ke karanta musu itada bishirah, Dan bishirah batayi karatun bokoba ita. lokacin sallar la'asar nayi suka shiga ciki, bayan sun idar suka kuma dawowa wajen suka zauna, zamansu baifi da 10minutes ba d'an gwari ya wangale k'aton bak'in gate d'in gidan. Jibga jibgan motocine bak'ak'e wulik keshigowa ajere harsu biyar. Da sauri Bishirah tamik'e tana fad'in ya khaleel ya iso. Haka kawai Aysha tasamu kanta da fad'uwar gaba, innalillahi... Tashiga ambata, mutan gidan duksun fito harda aunty Mamie. Saidai mutanen sauran motocin hud'u suka gama fitowa wad'anda ke sanye cikin bak'ak'en suit wulik sannan d'aya daga ciki yabud'e motar tsakkiya wadda tafi kowacce mota k'yau da tsari. Bak'ak'en takalma sau ciki masu matuk'ar k'yaune suka fara bayyana, saikuma farar k'afar wandonsa. Fitowarsa gaba d'aya tasaka Aysha ambatar masha ALLAH!! batareda tashirya fad'an hakanba. Dogone sosai kuma k'ak'k'arfa, dukda yanacikin suit farare hakan baihana cikar haibarsa bayyanaba, yanada haske sosai amma baza'a kirasa fariba kuma ba bak'i baneba, yana matuk'ar kama da mahaifinsu Alhaji Abdallah, saidai kawai yafishi fari, kamar yanda dukkan sauran yaran suka fishi haske, shida Tasleem ne kawai kalarsu d'aya, sunmmafi kama da juna. A 6angaren k'yawun fuska kam dolene kakirashi kamilalle, komai nashi masha ALLAH, a kwai hanci kam daidai da tsarin faffad'ar fuskarsa, gawani saje daya k'awata taswurar kamilalliyar fuskar tasa, bai tara sumaba kuma kansa ba kwal-kwal yakeba, yabar 'Yar kad'an data kwanta luf akan nasa tamkar mai sabon aski. Agaskiya guy d'in yahad'u masu karatu, tako ina ubangiji yayimasa k'yak'yk'yawar hallitta Dan bashida makusa, idanunsa kawai abin sone ga kowacce mace, Dan gsky ba maza dukaba keda girman ido da haske irinna *Ibraheem Abdallah Rufa'ee (J!)* Cikin takun k'asaitarsa yake nufo family nasa, saidai fuskarnan tasafa babu fara'a, amma kamala da dattako sun lullu6eta. Ammah ce tak'araso ta rungumeshi dafad'in oyoyo maigidana. Yafita tsawo sosai, yarik'eta da k'yau yanamai farincikin ganin kakar tasu, suma yaran suka k'araso gareshi sunamai farinciki damasa sannu dazuwa. Zame jikinsa yayi yak'arasa inda momy take itama ya rungumeta, my lovely son Sannu dazuwa. Yauwa momyna I miss you, yafad'a yana d'agowa daga jikinta, hannunsa takama tana dariya, nima haka yarona ina kewarka kusadani. Lallausan murmushinsa yasaki, sannan yanufi aunty Mamie dake tsaye itama tana murmushi. Hark'asa ya duk'a yace Aunty barka da gida, munsameku lfy?. Hannunta takai tashafa kansa, idanunta cikeda hawaye saboda tuni Rufa'ee ta datayi, tace lfy lau babana, kunzo lfy?. Jinjina kansa yayi kawai, danta Sosa masa inda kemasa k'aik'ayi, tatuna masa d'an uwansa Wanda suka tashi tamkar tagwaye, komai nasu tare sukeyi, aikine kawai ya banbantasu, yamik'e jiki asanyaye suka k'arasa ainahin falon gidan.........🖊 *ina yinkufa🙋🏻‍♀*😘🤧 [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 0⃣7⃣ Harsuka shige Aysha dasu bishirah nabinsa da kallonsun sha'awa, bak'aramar damuwa hakan yasaka Aysha ba, harda d'an kukanta sakamakon tuna nata ahalin itama, harga ALLAH tana kewar gida da 'yan uwanta, dama bikinsu Yaya Fhadeela take kwad'ayin zuwa kuma and'aga sainanda watanni uku. Basu sake jin d'uriyar mutanen gidanba har dare, sai bayan isha'i ne aka aiko Nureedeen yakira Aysha da bishirah. Da sallama suka shiga katafaren falon, dukda sunsan bama lallaine wani yajisuba, 'yan matan gidanne kawai ke kallon film. Su Aysha sukamusu sannu. Duk suka amsa musu cikin k'yak'yk'yawar alak'a, dansu ba'a musu tarbiyyar wulak'anta 'yan aikiba. Bishirah tace Anty Amal gamu. Kai bishirah wayace ina kiranku?. A'a dama Nuriddeen ne yace muzo, tonazata kokune ke kiran. Bamu baneba inagato Aunty ce ko Ummee, amma kuzauna ina zuwa. Amal namik'ewa saiga Aunty Mamie tafito daga 6angarenta, Amal tace yauwa Aunty kece kika aika Nurri kiransu Aysha?. Eh nice, suna inane?. Aysha da bishirah sukataso suna fad'in gamu Aunty Mamie. Yauwa kuzo muje nad'an sakaku wani aiki nan. Aunty Mamie nagaba su Aysha nabinta abaya harzuwa 6angaren samarin gidan, Wanda yau shine farkon zuwan Aysha, Ya Zunnurain da ya Mujahedeen da Hafeez ne kawai afalon suna kallon kwallo, sai Musleem dakecan gefe yana duba books, da alama wani bincike yakeyi ko aiki. Duk suka gaida Aunty Mamie, sannan ya mujahedeen yace Aunty Mamie baki aikomin maganinbafa. O namanta wlhy Mujaheed, amma miyasa baka tunaminba? Haryanzu wajan namaka ciwone?. Eh wlhy yanayi, d'azufa har zazza6i yakusa yasakarmin. To ALLAH ya sawak'e, Hafeez jeka d'akina saman madubi kad'akko box d'inan kakawo masa yaduba. To aunty, Hafeez yafad'a yana mik'ewa. Su Aysha sukaima ya mujahedeen sannu, kansa kawai ya jinjina musu, danshima akwai d'ankaren miskilanci. Aunty tace babanafa?. Yana d'akinsa, cewar ya Zunnurain. A'a ahakan kuma yazauna? Bayan yace, ''d'akin duk datti. 'Yar dariya mujahedeen yayi, to aunty aikinsan halin kayanki dai, amma baima dad'e dashigaba tunda yanzun muka dawo masallaci. Ok, bara baduba, inasu Muhseen?. Sunje wani waje shida ya Ramadan. Sultan fa?. baffah ya aikesa inaga. Ok. Anty tanufi d'akin khaleel, harta fara tafiya tagasu Aysha BASA binta, tace kutaho mana. Saida tamasa Knocking sannan yabud'e k'ofar, sanye yake cikin wando da Riga ash colour, rigan mai bud'ad'd'en k'irjice, amma yasaka vest ak'asa, wandonma iyakarsa guywarsa, sai silifas bak'i ak'afarsa, wani ni'imtaccen turare yabigi hancin su Aysha, suduka saida suka lumshe idanunsu. Yana ganin aunty Mamie yasaki murmushi, cikin girmamawa yace Aunty Mamie kece?. Eh babana, d'akin za'a k'ara gyara maka nasan kana iya cewa kakasa barcima aciki. Wlhy kamar kinsani aunty, yanzun Yakama shirin tafiya d'akin sultan nakeyi Dan nikam k'yank'yamin d'akinnan nakeyi, kokad'an ba'amasa wani gyaraba. A'a babana, aiko nagasu Hasnah sungyara d'azun da safe. 'Dan tsaki yaja, yace Aunty miwad'an Nan yaran suka iya banda rashin mutunci yay maganar tareda komawa cikin d'akin, Aysha da bishirah sukabi bayansa shida aunty. Mamakine yakashe Aysha, Dan itakam bataga wani dattiba awannan d'akin, gashinan Fe's, saidai 'Yar k'ura, wadda hakan yana nufin Wanda yay gyaran d'akin yanada gandar tsayawa k'alk'ale Abu, amma babu wani dattifa. Aunty tace to babana gasunan zasu sake gyara maka, saika nuna musu ko. To Aunty sufara da toilet. Tsaf Aysha tagyara toilet d'in sai shek'i yakeyi, daidai da bokiti da butoci saida tawanke masa k'al, har tayils d'in jikin bangon bayin kanshi yad'auki haske, turarirrika tagani kala-kala masu saka bayi k'amshi, suma tad'auka duk tasaka. Koda tafito d'akin babu bishirah, abin yabata mamaki, shikad'aine zaune akujerar d'akin yana danna wayarsa, dukji tayi tatakura, hakadai tafara cire zanin gadon, kunfar data had'a abokiti tatsoma k'aramin tawul aciki tafara goge fuskar gadon dashi, saida ta goge tsaf yanata k'yalli sannan tad'akko zanin gadon zata mayar. Daddad'ar muryarsace tadaki kunnenta, yace, "karki mayarmin deity bedsheet d'in nan a bed. d'agowa tayi tana kallonsa, saidai amamakinta haryanzun kansa ak'asa yake, yana danna wayarsa. wajen mintina uku baisake cewa komaiba, itakuma Aysha tana kallonsa kamar tasami TV. K! Karfa ki cinyeni, kinwani k'uramin kwala-kwalan idanuwan kinnan. Aysha tayi k'asa da kanta cikeda kunyar kamatan dayay tana kallonsa. Cikin k'asaitarsa yamik'e zuwa Waldrop d'insa, yad'ako bedsheet Fari tas, saman gadon ya ajiye yakoma inda yataso yakuma zama. Aysha tad'auka ta shinfid'a, bata sake kallon inda yakeba harta kammala komai, yarage mata shara da mopping, tanaso tamasa magana tanajin tsoro, kusan mintuna 5 suna ahaka, saiga bishirah tashigo da tire, inda yake taje ta ajiye masa, cikin girmamawa tace ya khaleel gashi. Shiru bai amsaba har wad'ansu seconds kuma haryau waya yake dannawa, sannan zuwa can yace waye yadafamin?. Murya narawa tace Aunty Amal ce. Kansa kawai ya jinjina mata, yay mata nuni da hannu alamar tatafi. Aysha kamar tayi kuka, tanason yima bishirah magana amma tanajin tsoro. Waike tsayuwan yana miki dad'ine?.... Muryarsa tadaki kunnen Aysha. Cikin in ina tace um....um ....dama shara ne yarage da mopping zanyi, shine saikuma naga.....um.... 'Dago dara-daran idanunsa yayi yasauke akanta, bak'aramar figigita Aysha tayiba, dan yamata kwarjini sosai, ga fuskarnan a d'inke babu alamar sauk'i. Yaja gajeren tsak'i tareda janye idanunsa daga gareta, yace kinga idan zakiyi kiyi, inkuma bara kiyiba kiyita zama awajen useless kawai. Cikin taushi muryar tasa ke fita, amma shi adole fad'a yakeyi. Ran Aysha yasosu, harga ALLAH batason dizgi, amma takula wannan mutumin bashida kirki, yandama taji yaran gidan suna hirarsa yawuce nan. Shararta tafarayi, saida tazo inda yake sannan yakwashe k'afafunsa yamaida saman kujerar. Daganan babu Wanda yasake kula d'an uwansa, harta kammala komai. Yanzuma saida tabaje ko ina da k'amshi sannan tacemasa tagama, baice mata k'alaba, itakuma tagaji da tsayuwa takama hanya zata tafi, harta kama handle d'in k'ofar yace, "k! Zonan.. Gaban Aysha Na dukan uku-uku tadawo inda yake, durk'usawa tayi agabansa cikin sanyinta tace gani. Tashi ki had'amin shayinnan. Mik'ewa tayi daga durk'uson taje inda k'aramin table d'in glass d'in yake tafara had'a masa shayi. Knocking d'in k'ofar akayi, dak'yar ya iya bud'e baki yace kowaye yashigo. Hameeda Ce tashigo ko sallama babu. Ya Khaleel kazo inji momy. Wata uwar harara ya maka mata da wad'annan fararen idanun nasa, tayi k'asa dakai tanad'an zun6uro baki. K! 'Yar iska baki iya sallamaba ne ko!. fitarmin ad'aki kona 6allaki stupid girl kawai. Saida ta ballama Aysha harara sannan tafita tana k'unk'uni k'asa-k'asa, dantasan inhar yaji kashinta yagama bushewa. Shikam tana fita yaja wani wawan tsak'i Wanda yatsorata Aysha, ALLAH yasotama tagama had'a shayin, yanzukam koneman izininsa batayiba tafice da saurinta. Shima baice da ita komaiba yad'auki shayinsa yahausha, ko zafima bayaji. Saida yagama tsaf sannan yacanja kayansa zuwa jallabiya fara tas yatashi yafice. Wajen baffansu yafara zuwa, saidai bayanan yafita, saikuma yashiga 6angaren Ummee Amarya. Tana zaune afalonta hakimce, sai Nureedeen da Ummunoor da Asharaff dake wasa agefe, da 'Yar fara'arta tace a'a khaleel ne ak'asar tamu?. Shima guntun murmushi yayi yana fad'in eh wlhy Umme, munsameku lafiya?. Lfy lau muke, ya aikinku?. Alhmdllh Ummee. Daganan sukai shiru, Dan babu wani sabo tsakaninsu da ita, Su UmmuNoor dasuka hangoshi yanzun suka taso da gudu sukayo kansa. Yanason k'annen nasa, yataresu da murna, duk gaidashi sukayi, Asharaff yace Uncle! Muma yaushene dadynmu zasuzo shida Maah-Maah d'inmu?. d'an murmushi yamasa tareda Jan kumatumsa yace my son zasuzo suma soon insha ALLAH tuni Asharaff yamik'e yana tsallen murna, shidai Khaleel sai murmushi yakeyi. Yamik'e yanama Umme saida safe, cikin kulawa ta amsa masa. Daga nan sai 6angaren Ammah tsohuwa............🖊 *_Muje zuwa guys_*😉 _luv you all_ [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 0⃣8⃣ Tana zaune tana dama fura yay sallama, daga ita sai Tasleem da maleeka, tana ganinsa ta washe hak'ora da fad'in a'a lale da mai gidana. Zama yay kujerar gefenta shima yana murmuahi, Ammah tsohuwa mikikema jagwalgwalo haka da hannu?. Furace nake damawa, zakawanice jagwalgwalo kajimin d'an kwal uba kai. Dariya su Tasleen sukayi sannan suka gaidashi, Ammah datagama kammala dama furarta tace ke maleeka d'akko kofi nasama yayanku fura, kuma kud'iba dannasan wannan hirar badan ALLAH akazominba. Kai Ammah hakama zakice?. Eh mana ai gsky ce. dan gidanku da hakananne daba yanzu kuntafi gun iyayenkuba kuna k'aryar saboda kada Ku makara makaranta. Shikenan Ammah zamu dena zuwa miki hira aii ko. Yo kada kuzo mana, aii Bilkeesu tazo itada babanku. Ya khaleel dai yana saurarensu amma yay shiru. Bayan maleeka takawo kofuna Ammah ta zuba musu suka d'auka suka fita, Dan sunsan halin ya khaleel ba'a had'a inuwa dashi. Ammah takalli Khaleel tace kaifa saraki nazuba?. no Ammah, ni nasha shayi yanzun, kinsan bancika ammafani da Abu mai sanyiba aii. Baki tata6e tana fad'in aikaikam matarka tabani da iyayinka billahillazi, daga kace Baka cin wannan, saikace baka son wannan, mutum saikace goyon junnu. Lallaima Ammah, idanma nid'in goyon junnu ne ai hardake ciki, tunda taredake aka raineni. A'a A'a saidai iyayenka, badai ka gado Bilkeesu ba itada kasha nononta, Dan ita batada wannan fad'in ran naka, mutum kullum fuska ahad'e, shiyyasama sukayi saurin d'aukarka aikin d'an sanda alokaci, sukazo kuma suka had'aka da wannan aikin namarasa kirki. Dariya yayi awannan karon, kai AMMAH aikin nawane namarasa kirki?. Eh mana, bagashinan yahanaka aureba, kullum shekaru kesake zuwa maka amma kak'i kagane, ga hallidu nan da aka haifeku lokaci d'aya yanada yara 5, yanzu haka babbar 'yarsa nanda kaka za'a iya mata aure wlhy. Bakinsa yad'an ta6e yace Ammah aure lokacine, idan nawa yazo aizanyi, nifa har yanzu banga yarinyar dataminba, kumani nafison auren k'aramar yarinya ma, irin 'yar 17-18-20 d'in nan. Ahakan ne zaka auri yarinya, anya kuwa kana kallon kanka amadubi iro?, wane sakaren ubane zai d'auki 'yarsa k'arama ya aurama k'aton gardi kamarka. Dariya tabashi sosai datace k'aton gardi, saida yadara son ransa sannan yace kai ammah, ammafa kinmin wulak'anci, yanzunan nine k'aton gardin?, bakomai zan rama aii. Yo iro, nifa gasky make fad'a maka, yakamata kanemo matar aure hakanan, idanfa bakayiba su Sultan bazasuyi tunanin yiba, dama marigayine ked'an nuna alamar kamar zaiyi, tokuma sai mutuwa tad'auka manashi. Cije le6e Khaleel yayi, muryarsa a sark'e yace ALLAH ya gafarta masa. Amma tace amin. Mik'ewa yayi yana fad'in Ammah bara naje mugaisa da momy itama, saida safe. To ALLAH ya tashemu lfy maigida, ALLAH ya kawo kishiya tagari. Fitayay yana guntun murmushi. Ammah tabishi da kallon tausayi, tasan maganar marigayi Rufa'ee datayice ta Sosa MASA zuciya, to amma yazasuyi da hukuncin ALLAH, saidai hak'uri aii. Da sallama yashiga falon momy. Aunty Zuwairah dasu mufeela duk suna falon, momyce kawai babu. Fuskarsa ahad'e yace Aunty zuwairah bakiyi barciba?. Banyiba khaleel, amma kaikam ina kamak'ale hakane? tundazunfa momy ta aika Mufeeda kiranka. Um naje gaida jama'ar gidanne, Dan bamu gaisa dakowaba. Aunty Zuwairah ta ta6e bakinta, humm aini babu macen data isa nabita har d'akinta gaisheta wlhy. Banza yamata bai tankaba, Hasnah tace, ''yo ALLAH natuba aunty bama keba koni k'arama basu isaba wl..... Hararar da ya khaleel ya balla mata tasakata yin shiru, k'ofar d'akinsu yanuna musu da hannu, alamar sutashi subar falon. Sanin halinsa yasakasu tashi sunata zum6ura baki. Adaidai nankuma momy tafito daga d'akinta itada gwaggo bintu wadda tayo sharkaf da zufa, kaikace k'arya tayi aka turketa acan. Wani kallon tuhuma khaleel kebinsu dashi, daga momy har gwaggo bintu. Ganin kallon dayake musu yasaka momy had'e fuskarta, tace saiyanzu kagadamar zuwa Ibrahim?. Batareda yabata amsaba yazamo daga kujerar yana gaisheta. Saida tazauna sannan ta amsa masa, takumacewa ko sak'ona bai iso makabane sai yanzu?. Ya iso momy. Uyum rainine yahanaka zuwa tun d'azun?. Nanma shiru yayi. Tasan halin muskilancinsa, danhaka tad'akko wata maganar. Mi yarinyarnan keyi ad'akinka?. Ayanzunkam kansa yad'ago yakalli mahaifiyar tasa, momy yarinya kuma? wace kenan?. Saida tayi kwafa sannan tace yanzuma rainamin hankalin zakayi kenan? Ko mufeeda bata tadda yarinyar nan Aysha a d'akinkaba? wlhy Ibraheem inad'aga maka k'afa fa akan lamarin gidannan, amma wlhy kakusa kakaini bango, kaiwai bakasan ciwon kanka baneba? baka kishina amatsayina Na mahaifiyarka?. Please mom, nikam kidaina sakani awannan aikin naku, shiyyasafa wlhy banason zaman gidannan sai dole, nibanga laifin matan gidannanba, iya gwargwadon iko suna gimamaki amatsayin matar Baffa babba, why not kema kikwantar da hankalinki azauna lfy, yanzu kodansu Mujahedeen ba'a ragama Aunty Mamie ba? hakama umme, itabama sabgar gidannan take shigabafa, wlhy ko kad'an banason k'ananun magana arayuwana, Dan ALLAH Momy kiyi hak'uri adaina sakani ciki nidai, kuma ku dinga hak'ur....... To Ubana cigaba Damin fad'an to. No mom niban Isa miki fad'aba, kawai inaso agyarane. To bazan gyaraba, nace bazan gyaraba, nitashi kafitamin, wlhy Ibraheem ka kiyayi randa zanmaka bankad'a agidannan, shashashan yaro kawai lusari, ainasan tuni Bilkeesu tagama shanyeminkai tun kana yaro, aini k'addara tajamin wlhy, kuma babu Wanda yajamin masifar nan sai Ammah, Dan dabata k'arrafa Bilkeesu tashayarmin dakaiba da bantsinci kaina awannan jarabarba, inaji INA gani d'ana yafison kishiyata akaina, abin bak'incikinma kai kad'ai tillo gareni namiji, amma ka KASA sharemin hawayena, saisu zuwairah dasuke mata. ALLAH ya huci zuciyarki momy, nidai gaskiya nake fad'a miki, masu iya magana sukance *CIKI DA GASKIYA... WUK'A BATA HUDASHI* Inzaka fad'i fad'i gaskiya, komai taka jamaka kabiy..... Kai tashi kafita!!. girgiza kai khaleel yayi kawai sannan yamik'e. Aunty Zuwairah tace kai amma kaji haushin kanka Khaleel. ta gefenta yara6a yafice abinsa batareda yakalli ko inda takeba. Aunty Zuwairah tarik'e ha6a tanabinsa da kallon mamaki, 6acewarsa tasata dawo da kallonta kan momy, anya momy ba aimiki musayar khaleel a asibitiba kuwa? yaronnan yana Abu saikace ba jininkine ke yawo ajikinsaba?. Momy tace, "K! Bansan shirme" kada kik'ara 6atan rai kuma, wannan wace iriyar maganace. A'a momy yihak'uri...........🖊 _awannan ga6ar yakamata masu karatu suyi wata tambaya, ko tattaunawa akai, shin ya akayi khaleel yasha nonon Aunty Mamie?, bayan kuma momyce mahaifiyarsa?.🤔_ *masu karatu har yanzufa a shimfid'a Muke, bamu kamo zaren labarinba tukunna* *kumuje zuwa guy's😉😹😘👌🏼* [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 0⃣9⃣ Zuwa yaukam gidan yagama cika, kowa ya hallara, Anty Amatullah ma sun iso, hakama Anty shukurah. Aikam su Aysha suna cin uwar aiki, aduk lokacin data ke6e kanta gefe takanyi kuka Na tausayin kanta, haka kawai takoma boyi-boyi agidan wasu, dagatanta dakomai, ya ALLAH ka kawomin iyakar wannan bauta, takuma fashewa da dakuka, ada idan wani yace zata tsinci kanta awannan yanayin wlhy saita k'aryatashi, amma gashi silar maraici komai datama rayuwarta tanadi yagama wargajewa, k'addara ta guntule mata karatunta, maraici ya rabata da iyayenta da 'yan uwanta, duk wani gatanta ya ku6ce mata..... Aysha! Aysha!! Waimikike tunanine? 'Yar karamarki dake harkin fara saka rayuwarki a garari?, haba Aysha, ki k'ar6i k'addararki da hannu biyu mana, akwai yara irinki dasuka fad'a fiye da halin dakike ciki, kodan ni har yanzu bakisan nawa tarihin baneba?. yanzu kitashi kije Maman yara nakiranki. Share hawayenta tayi, jiki a sanyaye tamik'e tafita. Gwaggo bintu nazaune bakin katifarta tana k'idaya kud'i masu uban yawa, shigowar Aysha baisata dainawaba, saidai ta nunama ayshar gefen katifa alamar tazauna. Saida tagama tsaf sannan tadubi Ayshar tana washe baki, shatun gwaggo kenan, yanaga fuskar taki haka? Kuka kikayine?. A'a gwaggo, abune yafad'amin a idona, amma bishirah taciremin. To madallah. Yanzudai Albishirinki.. Cikin mamaki Aysha tace, "goro", Dan yau itace rana tafarko da gwaggo bintu tasakar mata fuska tunda tazo gidan. Yauwa shatuna, dama wani alkairine yazo miki, burinki yacika yau, hajia babbace ke tambayata kinyi karatu? Shine nace eh, amma iyakarki aji uku ko?. gyad'a mata kai Aysha tayi kawai. Yauwa, to shine tacemin akwai d'iyar k'anwarta kaltume a k'asar waje, tanada ciki, kuma cikin nabata wahala, shine akeso ajedake kizauna da ita harta haihu, daga nan kuma saikici gaba da karatunki a can k'asar wajen, tak'are maganar da washe baki. Dukda Aysha k'aramar yarinyace batakai girman hangen nesaba, amma saitaji maganar bata kwanta mata araiba. Amma gwaggo kekuma kin yarda damaganar tasune?. Eh mana nayarda Aysha, ni aii karatun nake miki kwad'ayi, yanzu hakama nakira Yaya bilya nasanar MASA komai, kuma sunyi magana da hajia babba, mamankima ansanar mata, kuma duksun amince, yanzu zakuje anjima ayimiki hoto Dan nanda sati d'aya zaku bar k'asarma. Gwaggo! Sati d'ayafa kikace?. Eh sati d'aya nace, kenifa banason iyayi, inama laifi data za6eki, baga bishirah nanba amma tace ketakeso saboda kinada hankali da ilimi, amma shine zaki kawomin shirme. Kwallar data cikama Aysha ido tasamu damar zirarowa akumatunta, batadamu da sharewaba, muryarta narawa tace, "to gwaggo Na amince, amma yaushe zanje Kano? namusu sallama, gakuma bikinsu Yaya Fadeela ma yakusa, koza'a bari sai bayan bikin?. A'a Yaya yace basaikinzoba, tunda zakuzo Idan Zata haihu, bikinsu Fadeela kuma aibadole saikina nan za'ayiba. Amma zantanbayi hajia babba idan lokacin yayi saisu sakoki a jirgi kizo kiyi kwana hud'u ko?. Shiru Aysha tayi saboda k'unar da zuciyarta kemata, kokad'an zuciyarta bata amshi wannan zancenba, amma tamik'a lamarin ga ubangijin talikai. Su Aysha anje anyo hoto, hajia kaltume Ce tazo sukaje, daganan sukaje har airport nanma sund'an dad'e sannan aka dawo da'ita gida. 'Yan gidan basusan hidimar da'akeyiba, Dan gwaggo bintu tagargad'i Aysha akan kada tasanarma ko bishirah. Sosai Aysha tarame, saita k'ara tsawo da fari, tak'ara zama silent sosai, kuka kam hartayi ya isheta, taduk'ufa tana sanarma ALLAH kukanta, Dan kokad'an tafiyar bata kwanta mata Araiba, haka kawai takeji akwai lauje cikin nad'i akan tafiyar, saidai batada madafar dafawa barema tasami hangar ku6uta daga tarkonsu hajia babba, gawani abinda kebata mamaki, ayanzu sosai gwaggo bintu kebata kulawa, gawasu magunguna datake bata Wanda tarasa namiye?, ita kanta hajia babba yanzu tarage mata kallon wulak'anci, takuma hana yaranta hantararta, yanzu ko aikin gidanma gwaggo bintu bata barinta tayishi, lamarin nadamunta gaskya. ______________________ Wajen k'arfe biyar Na yamma su Aysha suna harabar gidan zaune itada bishirah, hira sukeyi, amma bishirace k'arfin firar tayau, Dan kokad'an yanzu Aysha batason yawan magana, yanzu hakama batawani fahimtar firar da bishiran kemusu, takasa hankalinta waje ukune, firartasu, dakuma tunanin gida, saikuma ya khaleel dayafito daga k'ofar babban falon gidan, sanye yake cikin jajayen kaya masu ratsin bak'i, ko ina ajikinsa arufe yake, kayan suna kama Dana training, yarik'e hular kamar tamashin ahannunsa, taku yake cikeda isa irinta zaratan maza k'arfafa masuji da tashen samartaka, yayinda yagittasu sai k'amshinsa yagauraye hancinansu, Aysha Na mamakin yanda kulum dakalar k'amshin dazakaji ataredashi, baka isa cewa ga ainahin turaren dayake sakawaba, kullum da kalar kamshin dazakaji ataredashi. Gani sukai yak'arasa wajen wani k'aton mashin mai masifar k'yau, shima jane da ratsin bak'i, dakayan da mashin d'in iri d'ayane, bawani mashin baneba illah (Power bike🏍). Hular kwanon yad'ora ahannun mashin d'in sannan yaymasu Aysha nuni da hannu alamar suzo. Suduka saida gabansu yafad'i, Aysha uwar tsoro tace bishirah munshiga uku, kodai yagane muna kallonsane?.nifa harga ALLAH tsoron bawan ALLAHn nan nakeyi?. Aysha muje kada musake laifi. Atsorace suka k'araso wajen, yajingina da mashin d'in k'afafunsa sark'e da juna, hannunsa d'aya acikin aljihun wandonsa, d'ayan kuma yana wayane. Cikin dadd'an sauti muryarsa ke fita, yana maganane acikin harshen turanci, turanci kuma maik'yau Wanda kosu masu yaren bazasu nuna masa iyawaba, no sir karka damu, insha ALLAH zan kamasa, yanzu haka akwai plan dana had'a domin cafkesa. ''Ok thanks you sir!" Bayan ya yanke wayar baikulasu Aysha ba, yakuma kiran wani. Babu dad'ewa aka d'aga, yanzukam da Hausa yake maganar. Adams inafata Kun shirya? OK kakira Emanuel & Taheer, ga Joseph nan shida Youseef taredani. Ok, nabaku nanda 5minutes, kasan banason jira. Baijira cewarsaba ya yakashe wayar. Dagacan Adams yace kai *j!* ko matsala. Dubansa yamaida Kansu Aysha dake durk'ushe, cikinku waye yamin gyaran d'aki ranar?. Bishirah tace Aysha ce Ya khaleel. Key ya jefamusu yana hawa bashin d'in, gashinan aje amin gyara yanzu, idan kingama ki ajiye key d'in ahannunki idan nadawo zan kar6a, idan kuma aunty Mamie tadawo kafin nadawo kibata kawai. Kafi su Aysha subashi amsama harya saka hular yaja mashin d'in yafita. Bishirah Dan ALLAH tunda baya nan yau muje kitayani, kinga saimu gama dawuri kafin 'yan gidan sudawo, wlhy inagudun matsala, bakiga Harar da Anty Hameeda taminba ranar, nasanma daba a gabansa bane saita dakeni. Tabama bishirah tausayi danhaka tace mujeto. Aikam dandanan suka gyara ko ina yad'auki k'amshi mai dad'i, cikin minti 30 suka kammala komai, d'akin suka kulle masa suka dawo tsakar gidan suka zauna, dagashi har 'yan gidan babu Wanda yadawo har gab da magriba, sannan ya Zunnurain yadawo daga aiki, saikuma ga Muslim shida hafez amashin, da'alama su daga makaranta suke. Su Aysha Na niyyar tashi, d'an gwari yabud'e gate, mashinan ajere harasu 6 suka shigo gidan, ya khaleel ne agaba, bayan yakashe nasa mashin d'in yasauka tareda zare hular kansa yajuya yana kallon sauran. Kutabbatar kunshirya mana komai atsare gobe idan ALLAH yakaimu, kundaiga miya faru yau, so kowa yasan irin shirin dazayi. OK sir suka fad'a atareda Saluting nashi. Shima yamayar musu da murtani sannan yabasu izinin tafiya. Hafiz ne yak'ar6i hular yana fad'in wellcom Yaya. Thanks you hafez. Da sauri Aysha tak'arso kafin yashige, tacemasa sannu sannan tamik'a masa key d'in. Kar6a yayi batareda ya amsa mataba yayciki abinsa.............🖊. *_kumuje zuwa lovely fan's_*😹😘 [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 1⃣0⃣ Alhaji Abdallah Jigawa zaune gaban mahaifiyarsa Ammah yazo gaisheta kamar yanda yasaba akowace Safiya. Sund'an ta6a hira sannan yace to Ammah bara nayima Musleem d'in magana yazo yakaiki asibitin kafin rana tayi ko. Eto babu laifi yazo d'in, waini ina iro? Tun jiya da yamma bansake sakashi a idonaba, koya komane?. Haba Ammah, yaza'ayi mu'azzam yatafi baki saniba, kinsan aikin nasu, jiya bayan isha'i yake sanarmin zaije wani aiki, to inagama a can yakwana Dan badashi mukaje masallaciba da asuba. To ALLAH ya taimaka, amma dai yakamata yarannan amusu magana sufito da matayen aure, baikamata kahad'a gurguzun samari agidaba harsu wajen 7, idan wani ya iya tsare kansa wanifa acikinsu bazaiyiba, kanaganin yanda aketa magana awajen taronnan. Kiyi hak'uri Ammah zanmusu magana, nima zaman nasu haka ya isheni, musammanma mu'azzam da sultan da mujahedeen. A to kadai k'ok'arta, ayanzu ko hafizu aka bama mata zama zasuyi bare su iro masu shekaru 30. To Ammah zasuyi insha ALLAH kwanannan. *_Hotel_* Tsaye yake a tsakkiyar d'akin cikin d'an hanzarinsa namasu kuzari yake shiryawa, sanye yake da kaya bak'ak'e irinna police d'in 9ja, saidai akwai abubuwa dasuka banbanta Dana sauran police d'in, bak'aramin k'yau kayan suka masaba, k'yawun haibarsa da cikar kamala irinta nagartaccen ma'aikaci ta bayyana gareshi, abinka da dogon mutum kuma k'ak'k'arfa, gakayan sund'an kamasa, anutse yake d'aura bak'in agogo a tsintsiyar hannunsa, yad'anja gajeren tsaki tareda gyara zaman belt d'in k'ugunsa daya zauna d'am kamar dashi aka haliccesa. 'Yar jakar dake gefen gadon yabud'e, wata 'Yar k'aramar bindiga yafiddo tareda mata serves da bullet sannan yasak'alata agefen k'ugunsa, yad'auki bak'in space ya mannama idonsa, dubansa yakai ga agogon hannunsa yad'an ta6e baki tareda shafa kwantaccen sajensa, Wanda baicika yawaba saboda yanayin aikinsa. Wata bak'ar riga naga yad'auka akan gadon yasaka, abayanta an rubuta *_(POLICE INTERPOL)_* 😨tofa masu karatu, 'yan sandan duniyafa kenan?👨🏼‍✈🤔, Ashe ya khaleel babban gwaskane?.🤥. Wayarsa k'irar Nokia dake wringing yad'auka, akunnensa yakara, bansan mi'akacemasa daga canba, nadaiji yace, "no kacigaba dabinsa abaya, amma kada kayarda yagane kana binsa, akwai Joseph da youseef suna binka abaya kaima, gamunan tahowa nida Adams da Emanuel da taheer, kakula sosai banason Marsala kaima kasani......kitt ya yanke wayar yana murmushin mugunta dafad'in Devid kazo hannu. Ak'ofarsa tafita yahad'uda zaratan bodyguard d'insa su hud'u, saluting nasa sukayi, shima kad'an yak'ame jikinsa tareda nuna musu hanya, matsawa sukayi yawuce gaba sannan suka take masa baya. Agaban wad'ansu bak'ak'en jibga jibgan motoci sukaja birki. Matasan samari 3 dake jingine jikin mota d'aya suka iso gareshi da hanzari, suma k'amewa sukayi tareda Sara masa, shima yayi kamar yanda sukayi. Kallon fuskar abokin nasu sukayi, sukaga babu alamar wasa ataredashi, yau a ogansu yafito ba abokiba, Dan har aka bud'e masa mota yashiga bai sake kallon Inda sukeba, dama gashi yatoshe idanu dabak'in Google😎. Suma Shiga tasu mortar sukayi, motarsace agaba tasu Na binsu. Shikad'aine zaune a sit d'in baya, masu tsaronsa d'aya Na driving d'aya nagefen mai zaman banza, laptop Ce acinyarsa yana aiki, fuskarnan acinkushe, babu alamar sauk'i ko sassauci. Suraj! Kayi amfani da number Adams kaganarmin Inda yake Karon farko danaji daddad'ar muryarsa ayau, muryar khaleel batada sanyi sosai, kuma batada hargagi, tana tsakatsaki. Cikeda girmamawa Wanda yakira suraj dake gefen driver yace OK sir. Ganinayi suraj ya manna wani Jan abu🔴k'arami dabai wuce girman ma6alliba ajikin glass d'in motar, saiga rubutu yawatsu akai. Mamakine yasakani zaro ido waje😨, araina nace cigaba. Ahaka Suraj yagano inda suke, yajuyo yana fad'in sir! Suna Jesse Jackson street, gidana 47. OK. Ahaka Suraj yayta nunama driver hanya, (nidai yau nazama 'Yar k'yauye gaskiya🤕) Gogan nakukam har yanzu idonsa nakan laptop harkokin gabansa kawai yakeyi hankalinsa kwance. Ajikin wata church suka tsaya, d'ago manyan idanunsa yayi yanason sanin dalilin tsayawar tasu, hango Adams yayi yana nufo inda suke yasakashi had'iye maganarsa tareda maida kansa ga laptop d'insa. Adams daya k'araso yabud'e motar yashigo. Da sallama Adams yashigo, ya amsa masa cikeda k'asaitarsa, har yanzu kuma bai d'agoba. Adams yace, "Weldon sir!". Yauwa kaima sannu yafad'a batareda yad'ago d'imba har yanzu. Adams yasan halin kayansa, Dan haka yafara koro bayaninsa kawai, sir naga inda suka shiga, suna gidan Na 116 gefen haggu, saidai nakula gidan yanada fasifar tsaro, Dan Devid yanada matasan yara 'yan daba masu had'arin gask......... Hannu yad'aga masa........ Aiko Adams yay tsit tareda had'iye maganarsa, jikake mukuttt, harda wata 'Yar munafukar zufa data tarumasa agoshi, dukda AC dake aiki amotar kuwa. Ahankali yad'ago yana kallon Adams, yasaki wani k'ayataccen murmushi, *Wanda nasan yakashe 'yanmatan group d'ina😆😜* lol. Duba nan yafad'a tareda turama Adams laptop d'in agabansa. Sosai Adams yazaro ido waje, tabbas yagama yadda ogansu kwarone, shita hidimarma saka farar Court yakeyi ajikinsa, bayan yazare rigarsa ta sama, yazaro bindigarsa dake k'ugu yatura cikin takalminsa, sannan yasake gyara zaman wandonsa, duba yakai kan agogonsa tareda furzar da huci yajuya yana kallon motarsu Taheer dake gefensa, dasauri driver yafita yabud'e masa motar sannan suma sauran suka fito. Adams daketa binsa da kallon kamar yasamu magiji,🖥, ahankali yafurta ALLAH yak'ara lafiya sir Ibraheem Abdallah j, tabbas kai jarumine acikin jarumai, ga gaskiya da rik'on amana, Kasan aikinka sosai, kuma ka yarda da kanka, kamar yanda muma muka yarda da aikinka 100%. J! ALLAH yakare manakai aduk inda katsinci kanka aduniya baki d'aya👍🏻...... Hhhhhh to amin Adams, irin wannan kirari haka😅, mudai saimun gani ak'asa zamu yaba nida masu karatu😉. Koya kukace Fan's??🤷🏽‍♀. Yanzuma saida su youseef sukayi salute nasa sannan Taheer yamik'a masa wata madidaiciyar jaka da key d'in mota. Yace, ''kuzama ready fa, Dan banyi zaton komai zaitafi cikin sauk'iba. Atare suka had'a baki wajen fad'in OK sir!!. d'an harar yamusu sannan yabar wajen. Atare suka murmusa dansunsan dalilin hararar tasu. Wata k'aramar mota fara mai masifar k'yau dake gefensu yabud'e yashiga, yalumshe idanunsa ahankali yafurta ya ALLAH!. ya sauke sassanyar ajiyar zuciya, adu'oin samun nasara sannan yayma motar key. Ahankali yake tafiya yana kallon gine-ginen da nazarin numbers d'in gidajen anguwar, harya Isa gida mai number 116, yacije le6ensa nak'asa tareda zare glass d'in idonsa, kallon tsaf yayma gidan har tsawon 2minutes, guntun murmushi yayi yamaida glass d'in sa. hankalinsa kwance yake danna horn, kaikace gidansa yazo. Ba'a bud'e gidanba, amma wani matashin saurayi Fari yafito yana k'arema motar kallo.. Da hannu j yamasa inkiya dayazo, babu musu saurayin ya iso ga motar J yasauke glass d'in fuskarsa cikin salon nuna shima tantirine yace, "hii my guy yane?. Oga Devid ko yana nan?. Saida saurayin yak'arema j kallo ya tabbatar shima d'an tashane. (Dan j yasaka wata hular gashi, kaikace kansane, bashida maraba da 'yan isakan guys). Saurayin yayma j alamar yana zuwa. Wani lallausa murmushin samun nasara Ibraheem Abdallah j yayi, ya hango nasara amatakin farko. Babu dad'ewa dashigar saurayin gidan, aka bud'e masa gate. Still saida yasaki murmushin gefen baki sannan yaharba motar zuwa cikin gidan.............🖊 _karfa Ku rud'e, ya khaleel shine *J*_😂 *_muje zuwa my Guy's, luv you so much😻😻😘_*🤙🏻 [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 1⃣1⃣ Aminiya anya kuwa wannan shawaran naku yayi? Yakamata kubarta taje taga iyayrnta, tunda ansanar dasu karatu zataje. Humm Amihiya bazaki ganebane, yarinyar tanada wayo, idan muka bata damar zuwa gida, tofa zata 6allo mana aikine, ninaga kamar tausayi nason canjakifa. Bahaka baneba, shikenan nagamsu, yanzu jirginmu zai d'aga nanda 3days. daga nan magana hajia babba da hajia kaltum sukeyi k'asa-k'asa wadda banajin komai nikam. _______________________ Sosai gidan yake da matakan tsaro, da ido yaringa k'irga zaratan k'artan da aka baza a tsakar gidan kawai, cikin 30seconds yagama nazarinsu, kowanne rik'e yake da makami mai had'arin gaske, jirasuke ace kulle suce Ca's. Gyara zaman space d'in idonsa yayi, yad'auki jakarsa yafita amotar. Gaba d'aya idon k'attan nan nakansa, cikin takunsa Na bajinta tareda samun cikakken training yak'arasa inda yake k'yautata zaton nanne k'ofar Shiga gidan, ananma akwai k'artai hud'u dasuke sanye cikin bak'ak'en kaya, babu alamar Rahma a fuskokinsu ko kad'an, kowanne kuma yatoshe da bak'in space. Kafin ya khaleel yakai ga k'arasawa garesu aka dakatar dashi. Wata basarwa yayi tareda huro iska daga bakinsa, yay wata tsayuwar giginya awajen cikeda isarsa. Mutum biyune suka k'araso inda yake, bincikensa sukayi sosai, harcikin jakar dake hannunsa, sun tabbatar baya tareda komai sannan suka barshi yashiga. d'aya acikinsu yaymasa jagora.. Babban falone Wanda yak'awatu da kayan alatu masu birgewa, basu tsaya ananba, saida suka wuce falo uku kuma ko'ina da 'yandaba, sannan suka k'arasa ga k'afar wani dogon bene, ananma sunwuce faluka biyu sannan suka Isa fadar Oga David. Bak'aramin mamaki abin yabama ya khaleel ba, to wai tayayama d'an iska kamar David yatara yarannan majiya k'arfi haka?.... Da wannan tunanin aransa suka k'arasa, da wani k'aton mutum suka fara karo, saikuma sauran masu tsaronsa. Yana zaune bisa kujera ta alfarma, yayi crossing k'afarsa, agabansa teble ne dake shak'e da kayan giya kala-kala masu tsadar gaske, zamu iya kiransa matashi Dan ashekaru bazai wuce 40-42 ba, daka gansa kaga cikakken inyamuri, farine tas, amma daga gani Na kantine. Wani kallo yakebin Khaleel dashi maikama Dana son Sanin kai waye!?, shima dai khaleel kallonsa yake cikeda nazari. Cikin muryarsa Mara dad'inji (kunsan dai ibo akwai k'atuwar murya😹)lol, yace young man waye kai?. Murmushin gefen baki khaleel yayi, datakumsa Na Isa da k'asaita yak'araso Inda Oga David yake. Batareda anbashi izinin zamaba ya juya kujera yazauna. Sosai salon ya khaleel yabirge Oga David. Ya khaleel daya zauna shima saiyayi crossing k'afarsa kamar yanda Oga David yayi. Wata tsawa masu tsaron Oga David sukaima khaleel. Amma amamakinsu ko gezau, saima wani k'asaitaccen murmushi daya sakar musu. Hannu Oga David yad'agamusu alamar subarshi, yakalli khaleel dake kad'a k'afa yace, "young man waye kai!?". Khaleel ya shafa sajensa tareda zare space d'in idonsa, k'afarsa yasauk'e k'asa, saida yaja 1minute sannan yace, " young tiger!!." Wata mahaukaciyar dariya Oga David yakece da ita, saida yayi mai isarsa su khaleel Na kallonsa sannan ya tsagaita, cikin rainin wayo yace really?. Ya khaleel yay guntun murmushi, k'afarsa yamaida ya hard'e yana fad'in yes! of course!!. Da Sauri masu tsaron Oga David suka nuna khaleel da bindugunsu, sai huci suke ko. Oga David Yakuma d'aga musu hannu yana fad'in cool down my boys. Duksaida sukai kwafa sannan suka janye bindugunsu. Khaleel kam bakinsa yata6e yana k'ara gyara zamansa, sai kara tamke fuska yakeyi. Barasa Oga David yad'auka, yazuba haif cup yamik'ama ya khaleel. Gira d'aya ya khaleel yad'age sama tareda yimasa alamar thanks. Oga David ya k'ank'ance idanu yace miyasa?. Murmushi ya khaleel yayi, cikin salonsa yace banashan barasa. 'Yar dariyar bakada wayo Oga David yayi, sannan yafara shan kayansa, murya a kausashe yace mike tafe dakai wajena?.. Business!. Business nami? Kasanni kasuwancina dayawa. Ayya namaka murna David d'an kasuwa, ni nazomaka da business d'in hodar iblis. Cikin mamaki Oga David yake kallon ya khaleel, young man waya nuna makani. J ya wulk'ita idanunsa yana huro iskar bakinsa, cikin salon yarda dakai _yace, "sunanka David, wasu nakiranka Davido, wasu kuma D-bay, sunanka Na yare Chubuzor, cikakken sunanka chubuzor Obiner, anhaifeka a jihar Enugu state, ak'aramar hukumar Ezeagu local government, awani k'auye Ugwuakulu, dadynka manomin rogo da kwara ne, mom naka tana sana'ar yin manja, Ku uku iyayenku suka Haifa, sauran matane, kayi primary & secondary naka a k'auyenku, daga nan kazo cikin Enugu state a University Ensuka, kana karatunka fannin medicine, bakada k'ok'ari kokad'an, saima k'ungiyar 'yan coltezing daka bud'e, kuna fashi kuma, rashin k'ok'arinka yasa aka koreka a school._ _Wannan ya6atama babanka rai yakoreka shima daga gidansa, tundaga wannan lokacin kabar Enugu state kakoma Lagos state kazama rik'ak'k'en d'an fashi da makami, har kwangilar kashe wasu ake Baka, kahad'a gawurtacciyar Daba mai had'arin gaske, kasamu kud'i sosai, kasamu d'aurin gidin wasu k'usoshin gwamnati kafara safarar miyagun kwayoyi da safarar yara zuwa wasu k'asashe ana bautar dasu, wasukuma suna karuwanci_ Bak'aramin daskarewa Oga David yayiba azaune, gabad'aya yagama raina Kansas. Ya khaleel yay murmushin mugunta yad'age girarsa yana fad'in kagamsu da sanin dana maka yanzun?, 🤨. Nibana business sainasan dawa zanyi, saboda tsaro ba tsoroba. Cikin gadara da isa khaleel yace kokana buk'atar k'arin bayanine?. Ayanda yaymaganar saiya fusata Oga David, yawani huro hanci, tareda k'ara kumbura fuska, shima cikin nasa salon namasu ido atsakarka ya bushe da dariya yajuya jajayen idanunsa. Tuni j yagano Oga David yanabama yaransa umarnine da idanu, kafin yayi wani yunk'uri sunyi attack nasa da bindugu. d'an murmushi khaleel yayi, yaduk'e k'asa tamkar zai gyara takalminsa saiya zaro bindugu har 2, da sauri yad'ago yanuna Oga David da d'aya tareda d'ana kunamar bindigarsa🔫, d'ayar kuma yana nuna yaran, cikin tsawa yace, " wlhy koku sauke bindigunku kokuma Na tarwatsa kansa yanzunnan. Cikin Oga David yabada wani k'ululu saboda tsoro, yatabbata khaleel zai iya tarwatsa kannasa,, idanumsa duksun firfito waje, nuni yakema yaransa akan subi ubarnin khaleel. Ransu duk a6ace suka sauke bindugun k'asa. K'arar harbi naji Wanda yasakani razana, Dan ban lura dawaye yayiba, saida nakai dubana kan khaleel sainaga shine ya harbi wani yaron Oga David dayay yunk'urin harbinsa a kaikaice. Wannan harbin shine yajawo hankalinsu taheer dake a waje sunajiran kota kwana, gidan suma suka danno kai. Dagananfa akafara musayar wuta, ga isakar hadarin dagarin yahad'a yafara tasowa. Al'amura sun tsananta, bakajin komai sai k'arar harbi, Dana wuk'ak'e. A cikikam khaleel yana cikin Risky, shikad'ai cikinsu, sauk'insa d'ayama yadamk'e Oga David yayi attack d'insa, suna tsoron Harbin khaleel su sami ogansu, dawannan damar yataso k'eyar Oga David suka fito, ya kulle sauran yaran ad'akin, falonma dai wani yak'inne, karokam iya karo akeyi, nidai inadaga waje cikin tsoro masu karatu🤧😳. Kimanin 2hours ana Abu d'aya, sannan saigasu khaleel sun fito, dayawansu sunsami raunuka, youseef ma harbi yasamu akafad'a, shikansa khaleel anyankeshi da wuk'a ahannu. Ansaka yaran Oga David amota, yawancinsu dukda mugun raunuka, Oga David harbi biyu yasamu, k'afarsa da cinya, sai zabga ihu yakeyi kuwa. Anguwar tayi tsit, kowa yana cikin matuk'ar tsoro saboda harbe-harbe daya karad'e anguwar, harsuka kwashesu sukabar anguwar babu Wanda yalek'o waje...........🖊 Nace matsorata kawai😂. *_love you all_*😻😻 [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 1⃣2⃣ Dr Abraham ne yay treatment nasu suduka, ancirema youseef bullet shida Oga David, babu Wanda yasakebi takansu Oga David, ansakasu amak'argama, yaransa daban shima daban. Ya khaleel yakallisu Taheer dakowa yake zaune agalabaice, guys bara nad'anje gida, nanda 4hour's zan dawo, Adams zaikawo muku abinci bye. Kawunansu kawai suka iya d'aga masa, shima baijira cewarsuba yayo waje. Yau takasance weekend, duk ahalin gidan suna nan, bakajin komai sai hayaniyar su Arfat dake wasa a falo, sunbaje kayan wasansu sai tsalle-tsalle sukeyi. Aysha nagefe tana goge-gogen dining. Cikin fushi Hasnah tafito daga 6angarensu, wata uwar ashar data zundumama su Ashraff yasaka Aysha tsaida aikin nata tajuyo tana kallonsu, Hasnah tace Ku Dan ubanku bazakubar mutane suyi barciba? Kunbi kuncikamana gida da ihu tamkar goyon maguzawa! ko haka uwarku da uban naku suka koyar dakune? 'Yan iska gadon ta6ara........ Tassss!!! Kakejin saukar mari akumatunta, agigice tadafe kuncinta, Dan marin yazo mata abazata, Aysha kanta daba ita aka maraba saida rintse idanunta. Kafin Hasnah tagama ganin mai Marin nata yacigaba da dukanta, ball yake da ita kamar afilin kwallo, tuni kururuwarta tacika gidan, sai kwala kiran sunan momy take cikin kuka da neman ceto. Babu shiri ahalin gidan sukayo waje, kowa yafito yay arba damai dukan hasnah saiyaja tunga gefe yana zaro ido, Ammah da Baffah ne k'arshen fitowa, sai momy abayansu, cikin tsabagen masifarta tace ubanwaye yake dukarmin yarinya? ta ture Hameedah dake kan hanya takutso kai tsakkiyar falon.. itama kanta idanu tazaro waje da mamakin yaushema yawo gidan?, ganin duk garatan samarin gidan babu mai yunk'urin kwatar mata yarinya ahannunsa yasata kiran sunansa cikin tsawa!. Ibraheem!!!!!. Cak yatsaya daga dukan nata, kansa na kallon k'asa, sai huci yakeyi dan 6acin rai. kowa yayi cirko-cirko, kaf k'annen nasa babu mai jarumtar matsawa kusa dashi. Baffah yatako ahankali har inda yake tsaye, jawosa yayi jikinsa ya rungume, ahankali yasauke wata nannauyar ajiyar zuciya, sun sami kusan minti 3 ahaka sannan yad'agoshi, fuskarnan tayi jajur, abinka da mutum mai haske, girgiza kai baffah yayi, sannan yace, "Mu'azzam! Miya farune? Yaushema kadawo gidan? Yay maganar yana kamo hannun sa da'aka nad'e da bandeji. Haryanzu ransa a6ace yake, Dan haka ya girgizama baffah kai kawai saboda bazai iya maganaba. ganin haka yasa Ammah k'arasowa inda suke, hannunsa takama tana fad'in zoka zauna kahuta kaji Iro!. cije le6ensa nak'asa yayi, idonsa nakan momy dake rungume da Hasnah tana 6arzar kuka haryanzun. harya farabin Ammah saikuma yatsaya, cikin k'ara hasala yadakama Hasnah tsawa!, k!! Wlhy idan bakima mutane shiruba saina ida 6allaki 'yar iska kawai mara mutunci!!. Da sauri Hasnah tasaka hannunta ta toshe bakinta tana k'ara k'ank'ame momy. Momy takallesa itama cikin 6acinrai, dukda takasa cemasa komai amma idanunta sun nuna alamun gargad'i da tsana agaresa, tayi kwafa tareda kuma rungumo Hasnah jikinta. Shima iska yahuro daga bakinsa, yacigaba dabin bayan Ammah dake rike dashi har yanzun. Haka kawai Aunty Amatullah taji zafin kallon da momy taima Khaleel, cikin sanyin jiki tanufi hanyar kichin. Duk bidirinnan da akeyi Ummee amarya batako lek'oba, tana d'akinta, kuma tanajin duk hidimar da akeyi. Aunty Mamie kam tana wanka, tak'agara tagama tafito dantaga mike faruwane?. Ruwa mai sanyi Aunty Amatullah tamik'ama Khaleel boda zufar dayaketayi, hannu yasa yakar6a tareda sakar mata sassanyan murmushi, muryarsa a raunane yace, "ngd lil Ama.. Itama murmushin tamasa. Wannan lamari bak'aramin kule zuciyar momy yayiba, wato saboda tsabagen munafinci ga yarinyarta yadoka dukya fasa mata jiki da sassafen nan, amma babu Wanda yace da ita koda sannu, saishi dayayi ta'asar suke bama kulawa. Ture kan Hasnah tayi daga jikinta, azafafe tamik'e tak'arasa inda suke, harya kai kofin ruwan bakinsa ta ka6eshi yafad'i ajikinsa, gabad'aya ruwan yazube MASA, dasauri yarintse idonsa saboda sanyin ruwan dake ratsa masa jiki. Tanuna aunty Amatullah da d'anyatsa tana fad'in k! Dan uwarki Bilkeesu ahir d'inki dashigarmin rayuwar 'ya'ya, tsafin na Uwarki haryakai kishayarmin dad'ana agabana? Wlhy ko Bilkeesu bata isaba, ALLAH yafiku, dama nasan uwarkuce ke saka Ibraheem yana tsanar 'yan uwansa ciki d'aya, annamimai, insha ALLAHU aniyarku saidai tabiku kuda Uwarku marasa tarbiyya...... Da Sauri Baffah yakatseta.... K! Laurah! Wai miye matsalarkine?, yamzunan saboda ALLAH bazakiyi bincike akan hukuncin da mu'azzam yayiba? Dan Nasan yanada dalilinsa, haka kawai bazai kama dukan hassana ba aii. Kuma naga aii yanda hassanah take d'iyarki hakama Mu'azzam d'ankine bare kidasama mutane kambun masifa, kokunyar yarannan bak'yaji? Kiringa cin mutunci mahaifiyarsu agabansu? Yanzu miye laifin Bilkeesu danta nuna kulawarta ga Mu'azzam?..... Eh aibazaka ganiba tunda kaima sunanka yana wajen bokan saman tsauni, wlhy kuma afitamin hanyar yaro, kokuma ran uban kowa ya6aci agidan, munafincin banza dawofi. Kaikuma sallamamme kasameni inajiranka.....fuuuu takama hannun Hasnah dake d'ingishi suka shige 6angarenta, Husnah da Hameedah Na take musu baya. Babu Wanda yakuma cewa komai. Ammah ta dafa kafad'ar khaleel dayay k'asa da kansa, tace tashikaje kacanja kayanka kaji iro, kacigaba dama mahaifiyarka Addu'a ALLAH ya shiryeta. Baice komaiba yatashi yanufi 6angaren samarin gidan. Suma baya suka take masa, ya Sultan ne kawai babu, yaje bauchi. Suma 'yan matan kowa zame jikinsa yayi suka koma d'akinsu, ammah ma 6angarenta tatafi, ganin haka su Aysha suma suka sulale sudasu gwaggo bintu sukai kichin. Amal tace wlhy ya khaleel yana bani tausayi, aikin nan nasu yanada had'ari sosai, bansan miyasa yaza6eshiba?. Wlhy bake kad'aiba cewar Hamdiyya, ya khaleel yanada kirki, kwata-kwata ba halinsa d'aya da momyba, duk d'akinsu yafi kowa mutunci, shidai barshi darashin son raini, bayason arainashi. Shuhuda tace, "kumsan ALLAH ya khaleel yafisu ya Muhseen kirki, gashida son 'yan uwansa, indai ka iya zama dashi zakaci riba, dukda kasancewarsa murd'ad'd'en mutum mai tsatstsauran ra'ayi. Naseeba tace gaskiya kuka fad'a wlhy, shi ya khaleel kaifi d'ayane, kuma yanason had'inkan gidannan dukda mahaifiyarsa batason haka, bazan 6oye mukuba nadad'e inason ya khaleel amma tsoron Momy yasa nasama zuciyata salama. Tab wlhy kin taimaki kanki, aii ya khaleel inba matar dazataci uwarsu Aunty Hameeda dasu aunty zuwairah ya auroba tofa akwai matsala, bazata ta6ajin dad'in zama da momyba agidannan. Wlhy hakane Amal. Hakadai sukaita hirarsu. Tasleem kam tuni tatafi kaima Aunty zancen abinda yafaru. Fitowarta kenan daga wanka Tasleem tashigo d'akin, fad'awa tayi jikin aunty tafashe da kuka. K! Miye hakane wai? bana hanaki halinnanbane wai Tasleem? minene yafaru kika shigomin da kuka?. Aunty ya khaleel ne yaji k'aton ciwo a hannunsa, kuma yadaki aunty Hasnah, Momy sai fad'a takeyi Dan Aunty Ama... tabashi ruwa yasha. Da sauri Aunty tace, "ciwofa Tasleem? yana ina yanzu?. Yana 6angarensu cewar Tasleem tanacigaba da sharar kwallah. A gurguje Aunty tazura doguwar riga tafito, afalo tawuce su Hamdiyya dasuka fito yanzu, Naseeba tayi dariya, tosu auta sunkaima aunty gulma, dama nalek'ata tana wanka. Shuhuda tace ALLAH Sarki aunty, yanzu dukzata rud'a kanta, dukda wulak'ancin da Momy take mata agidannan baya hanata kulawa ga ya khaleel. Amal tataso daga kujerarta tadawo tsakkiyarsu Shukurah, sotake tayi gulma, amma bataso su maleeka da Tasleem suji, cikin k'asa-k'asa da murya tace kunsan wani Abu?, kai suka girgiza mata, tacigaba da fad'in wlhy ina mamakin yanda aunty take matuk'ar damuwa da al'amuran ya khaleel, nifa sainaga kamar tafi Momy sonsa. Wlhy gaskiyarki Amal, nifa nadad'e inaso namuku gulmarnan amma inajin tsoro, sainake gani kawai had'uwar jinice, kugafa yanda Momy take nunwa batason aunty acikin agidannan k'uru-k'uru, amma yanda aunty take nuna kulawarta akan ya khaleel kosu ya Sultan batama haka. Shuru sukayi suna nazarin maganar amal, shuhuda tace kumafa gaskiyarku amal. Naseeba zatayi magana Ammah tashigo falon, cikin rakad'inta tace to magulmata halan annamimancina kukeyi?. Gaba d'aya sukayi dariya, Hamdiyya tace mumun Isa gulma da uwar masu gida. Amma tad'ingiso 'Yar k'afarta tana fad'in yonasani. Nanma dariya sukayimata. Shuhuda tace yauwa Ammah Dan ALLAH munada tambaya?. ALLAH yasa nasani to. Kinma Sani insha ALLAH. Ammah kid'an bamu tarihin agidannan mana kafin haihuwarmu. Dariya Ammah tayi, kai kujimin magulmatan yara, mikuma yakawo wannan zancen?. Bakomai wlhy Ammah, munasonjine kawai. Shikenan zan Baku, amma kubari sai ALLAH yakaimu dare. Murna sukaitayi harda tsallensu, Ammah namusu dariya.......🖊 Kuyi manage da wanga. *_inayinku irin sosai-sosai, tamau-tamau d'in nan wlhy🙋🏻‍♀😉_* [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: [8/1, 2:31 PM] Mai gadon Zeenari👈🏻😉: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 1⃣3⃣ Ransa duk a6ace yake, yarasa miyasa momynsa ke irin wannan halin? gashinan tazama malamar yaranta, sukad'aine baud'ad'd'u agidan, tsomwwww yakuma jan tsaki yana cije le6ensa nak'asa. Wlhy dayasan abinda zai tarar kenan, dabazai shigo gidannanba, dama aikine Nanne yatsayar dashi a k'asar, ganin yanada d'an time shine yazauna agidan, Dan rabonsa da gidan tun rasuwar k'aninsa Rufa'ee, yadafe kansa danjin yana sara masa, shi mutumne mai matuk'ar zuciya, Abu kad'an yake hassalashi yayi sama. Kwanciyarsa yayi bisa doguwar kujerar falon nasu, sudai k'annen nasa duksuna zaune suna kallonsa cikeda tausayi, babu Wanda yace masa k'ala. Saida yakwantane cikin k'arfin hali Mujahedeen yace, "ya khaleel daka koma d'aki aii. d'ago manyan idanunsa dasukai jajur yayi yana kallon mujahedeen d'in, yasakar masa guntun murmushin 6acinrai kawai, saikuma yalumshe idanunsa yagyara kwanciya. Zunnurain yace ya khaleel please mana. Mik'ewa yayi dak'yar, yace, " is OK, kowa yaje yayi kwanciyarsa, nima bara nawatsa ruwa. Kawuna suka d'aga MASA kamar k'adan garu. Saida yaga kowa yashige d'akinsa sannan shima yashiga. Arud'e aunty tak'araso falon 'yan samarin, babu kowa aciki, saidai ko'ina yayi need, dukdama ba akai gayin sharar safeba, k'ofar d'akin ya khaleel tak'arasa tayi Knocking. Fitowarsa kenan daga wanka, wajen k'ofar ya matso yana tsane ruwan jikinsa da k'aramin tawul, yace, ''wanene?". Aunty Mamie taisaurin cewa nice babana bud'e. Cikin hanzari yaja jallabiya blue mai gajeren hannu yasaka, aladabce yabud'e k'ofar yafito, a falo ya hangota, k'arasowa falon yayi har k'asa yadurk'usa ya gaisheta (harga ALLAH yana matuk'ar ganin kimarta, idan yana tareda ita yakanji wani iri saboda kwarjinin datake masa, shima baisan miyasa hakanba, kodan tana nuna kulawarta agareshi? oho. gashi ance nononta yasha yana k'arami). Aunty ta amsa kamar yanda tasaba, cikin kulawa tace babana miya sameka? Tasleem tacemin kaji ciwo ahannu, ina wankane lokacin. Murmuahi ya khaleel yayi danganin yanda aunty Mamie tarud'e, ko Momy batayi irin rikicewar nanba, ya yarda da aunty Mamie, danhaka yakan iya fad'a mata sirrin aikinsa kai tsaye ya 6oyema Momy, haka kawai yakejinta daban da kowa agidan, (dukda Momy tana cusa musu k'iyayyar aunty fiye data kowa agidan kuwa).... Aunty ta katse masa tunani dafad'in yadai babana?. Ajiyar zuciya yasauke, aladabce yace karki damu aunty, dama bawani Abu baneba yankane kuma nasamu dukkan kulawa. Arazane aunty tace babana yankafa? garin Yaya haka tafaru dakai? Kai nidai wannan aiki naku nabani tsoro wlhy, haka kawai naji gabana nata fad'uwa tun jiya Ashe Kaine...... Shine me uwar tsurku, wlhy Bilkeesu kifita sabgata banason shishshigin dakikemin akan Ibraheem!, tundani banta6a damuwa dashiga sabgar 'ya'yankiba. Kaikuma sakarai kazauna kana kwance mata yanda akayine? Wlhy Ibraheem kazama sallamammedai, kaico da wannan zuciyar taka, gakadai kamar jarumi awaje, amma shiryayyen sakarai akayi, koda yake ba laifinka baneba, anrigaya an rubuce sunanka a allon bak'in k'arfene, kai nidai ALLAH ya tsinema malamin dayaymiki wannan aikin Bilkeesu akan Ibraheem. Khaleel yakatse Momy cikin 6acin rai, haba Momy Dan ALLAH, wai wane maganganu kikeyi hakane?, haba Momy, nibansan mi aunty Mamie takemiki acikin gidannanba kike k'inta haka, tanada kirki wlhy m....... Dakk'uwa Momy tamasa, cikin masifa tace, "kaida kirkin nata kunci uwarku, wlhy idan Baka rufemin bakiba anan sainaci Ubanka sallamamme kawai. Shiru khaleel yayi, amma ransa yakai k'ololuwar 6aci, shiyyasa kokad'an bayason zaman gidannan, idan yabar k'asar ko kewar gidan bayayi. Can ya tsinkayo muryar Momy tana cigaba dacima aunty mutunci, wadda tuni tabata hak'uri tafice daga 6angaren, idan dasabo tasaba aii, tun suna zamanin k'uruciya ake Abu d'aya, tarasa wane irin kishi mai zafi hajia babba keyi da'ita? Amma bata nuna kishinnan mai zafi akan hajia saudah, (amma itada hajia Fad'ima sunsha wahalarta tun abaya, saida tayi k'ula-k'ullar datayi Alhaji Abdallah yasaki hajia Fad'ima, mace mai kirki dasanin yakamata). Tofa masu karatu, wacce hajia Fad'ima??, itama matar Alhaji Abdallah ce kenan? Kamar yanda aunty Mamie tafad'a. Toko tana ina yanzun🤔🤕 ?. Bara mucigaba dabin labari dai😢. Ganin Ammah afalon yasa aunty k'ara gyara nutsuwarta, Dan kokad'an batason surukar tasu tasan abinda yafaru, barema har zancen yakai kunnen mijinsu. Rissinawa tayi tagaida Ammah, cikin fara'a Ammah ta amsa mata, tana k'aunar Bilkeesu saboda k'yawawan halayenta. Aunty tace masu Amal kutashi muje kichin kuhad'a abincin yayyenku, yau har 11 ba'a karyaba. To suka fad'a suna mik'ewa. Suna shiga kichin d'in saiga Momy tafito daga 6angarensu khaleel tana hura hanci, saud'aya ta kalli Ammah tace barka da gida Ammah, tayi shigewarta 6angarenta. Kwafa Ammah tayi tana fad'in lalatacciya kawai, saiyanzu kika ganni? d'azun bakina ganinaba amma kika wuce mai bak'in halin tsiya, ai wannan yaron bai dace damacen farkoba alkur'an, ALLAH dai wadaran zuri'ar jummai, ya halinki ya halin uwarki dukda tana k'anwata kuwa. Haka taita mita da zagin Momy, hardasu gori kuwa, dama anfad'ama ammah masifane. Duk abinda yafaru tsakanin momy da aunty Mamie da ya khaleel su musleem najin komai, suna zaune jigum-jugum, abin nadamunsu, suna d'agama Momy k'afane kawai saboda tana matar mahaifinsu, kuma tanacin darajar ya khaleel, akullum kuma aunty Na nuna musu kadasu sake Susaka Baki akan abinda ke faruwa tsakaninta da Momy, babu ruwansu, mahaifiya Momy take agurinsu, inhar suna d'aga mata murya, to itama data haifesu zasu iya yimata fiye dahaka, wad'annan abubuwan ke taka rawar gani wajen sakasu kauda kai akan lamarin gidan gaba d'aya, amma abubuwan naci musu zuciya ainun. Musanman ma ya mujahedeen da aunty Amatullah dasuka kasance masu zuciyar tsiya kamar ya khaleel. Shikam khaleel yanacan cikin 6acin ran da Momy tabarsa, sai tsaki yakeyi yana shafa mai, ALLAH da Momy ba mahaifiyarsa baceba datuni yagyarata agidannan, kwata-kwata bayason halayenta, duk gidan tafi kowa fitina, wani lokacin jiyake inama ba'itace ta haifeshiba (idan yay irin tunanin yakanyi saurin yin istigifari, daneman tsari daga sharrin shaid'an maisaka waswasi a zukatan bayin ALLAH). Amma gaskiya halayen Momy basa birgesa itada 'yan uwansa, ahaka yagama shirinsa yahaye gado danyad'an huta, babu dad'ewa barci yay awon gaba dashi, dama yagaji over. Yau har 11 babu Wanda yafito breakfast, su Aysha sun kammala komai tuni, sungyara ko ina yad'auki k'amshi. Suna d'aki itada Bishirah, Aysha nagyara kayanta, itakuma Bishirah Na tsifar kanta. cikin sauke ajiyar zuciya Aysha tace kai bishirah wlhy nikam d'azun ya khaleel yabani tsoro, saidai kuma abinda yabani mamaki dukda dukan Hasnah dayayi babu Wanda yace masa baiyi dai-daiba, garama hajia babba naga kamar taji haushinsa. Komiyasa?. Saboda batason gaskiyane kawai Aysha. Haka yake jibgarsu idan suna kai hak'urinsa mak'ura, shiyyasa idan yana gidan duk wani iskancinsu basayinsa, itama natabbata batayi tunanin zaidawo gidanba yanzun. dabazama tafara aikata abinda tayiba. Bak'aramar firgita Aysha tayiba, har taune le6enta takeyi wajen fad'in kina nufin zai iya hukunta kowa akan lamarin cikin gidannan?. Bishirah tagyad'a kai alamar tabbatarwa. Shiru Aysha tayi, jikinta duk yayi sanyi, harga ALLAH tana tsoron masifaffen mutum, ballatana wannan murd'ed'en k'aton mutumin, gashi dogo masha ALLAH...... Bishirah tace, "yadai Aysha?". K'utt Aysha tahad'iye yawu sannan tace babu komai, amma wlhy har gidan yama fita raina nikam. Maganar Aysha taba bishirah dariya, kinga karki damu kanki, indai ya Khaleel nema zai iya barin k'asar gobe idan ALLAH yakaimu, tunda kika gansa yanzuma wani aikinne yazaunardashi. Itama Hasnahr ita tajama kanta dukan, dukda nasan batayi zaton ganinsa yanzuba........... Shiru kawai Aysha tayi, amma harga ALLAH atsorace take, jitayima gara tabar k'asar kamar yandasu hajia babba sukace, amma tana fargaba wlhy, gashi ance k'asashen waje turanci akeyi, itakuma bata iyaba sosai, anya karatun nata zaiyi tasiri? dukda kwad'ayinsa datakeyi, gashima har yanzu zuciyarta bata amince dawai karatun za'a turataba, dukda basu 6oye mataba sunce harda hidimar wasu zataje a can. Bakomai tadogara ga ALLAH, shizai tsareta akowanne yanayi. Damuwarta d'ayace su mamanta, tanason ganinsu kafin tawuce, shiyyasa tadage da sallar dare akan ALLAH yad'orata akansu hajia babba subarta taje tama iyayenta bankwana, kodan tasamo albarkacinsu........🖊 *ALLAH yana tare dake Ayshar mu kinji😭* *I love you all😻😻😻* [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) *_kai kuji d'an Adam butulu bai godema ALLAH ba, halayyarmu 'yan Najeria har yau bamu canjaba, zagin shugaba damuke bazai zama alkairiba, buhari ba ALLAH bane, ba kumfayakunneba, buhari mutum kamar kowa bashi zaya canjaba, mutashi mugyara halinmu, mubar hassada, dayin gaba._* *_kuka muke tsaro ak'asa, abaya bamu samuba, ayanzu munsamu tsaron bamu godema ALLAH ba, sai zagi da 6atanci wannan ba kimaba, muyi addu'a ga dattijo, ALLAH yamasa jagora!!._* _'yan arewa wlhy mufarka daga nannauyan barcin damukeyi, su koyaya nasu yake sonshi sukeyi, amma mu kud'ine kawai agabanmu ba mutuncinmuba, so KUKAN KURCIYA JAWABINE.........👈🏻_. 1⃣4⃣ Shiru kakeji kowa yanatsu afalon Ammah yana jiran labari, Aysha & bishirama suna ala6e tacan baya, dansunji lokacin da Ammah tace da daddare zata fad'amasu Naseeba tarihin ya khaleel, sukam suna buk'atar ji. Saida Ammah tagama dama fura kowa yad'iba sannan tafara bada bayani kamar haka. 👇🏻 to dafarkodai kunsan mahaifinku da sana'arsa, Laure dai itace matarsa ta lalle ta farko kenan, da mahaifiyar Laure dani uwarmu d'aya ubanmu d'aya, ninasha nono nabata. alokacinda mahaifinku Abdullahi yafara samun kud'i sai kakanku Malam Rufa'ee yamatsa masa akan yayi aure, nayi biris dasu kasancewar shine d'ana nafari, bansaka musu bakiba har tsawon shekara 1, nima rashin aurensa Na damuna. Ninakawo shawarar ahad'a Abdullahi aure da Laure d'iyar k'anwata, kasancewar nasan tana sonsa amma yak'i bata fuska. Badan Abdullahi yasoba akayi aurensa da Laure, watanta Tara da kwanaki 17 agidansa tahaifi d'iyarta mace wadda taci suna Zuwairah, bayan haihuwar Zuwairah da shekara d'aya Abdullahi yace zai k'ara aure, yasamu wadda yakeso anan cikin garin Kano. Naso nahanashi amma kakanku yahana, yace nabarsa tunda ALLAH ya halatta masa. Ansha bikin Abdullahi da Fad'ima, yarinyar kirki, saidai bak'aramin tashin hankali Abdullahi yafuskanta awajen Laureba, sosai tatada hankalin kowa. Kokad'an Fad'ima batajin dad'in zama da Laure, ana haka ALLAH yayima kakanku rasuwa, Rasuwar tata6a Abdullahi sosai shida d'an uwansa Ma'aruff dukda alokacin yana makaranta. Bayan Rasuwar kakanku Abdullahi yadawo damu Abuja da zama, saboda kasuwancinsa yadawo nan. Dawowarmu da shekara 2 Laura takuma haihuwar mace aka sakamata Shukrah, alokacin kuma Fad'ima tayi 6ari itama. Alokacinne Babanku yak'ara aure ya auro Bilkeesu, tashin hanakali yakuma k'aruwa agidan, sosai Laure Tahana kowa zaman lafiya. Bawani Abu ne kuma Kecin zuciyartaba illah haihuwar mata datakeyi, ita a haukanta kishiyoyinta zasuzo su haifi maza su kwace gida, bayan tun Abdullahi Na talakansa ta aura. Batasan ba'ayima ALLAH wayauba. Tsakanin Fad'ima da Bilkeesu babu wata Matsala kam, zamansu lafiya kamarma ba kishiyoyiba, hakane kuma ke k'ara hasala zuciyar Laurah Bayan shekaru uku suka kuma samun cikin suduka uku, saida cikkunansu suna kai watanni 5 Fad'ima tayi 6ari Wanda yabama kowa mamaki, amma saboda hak'urinta tace haka ALLAH ya k'addara. Bayan wata biyu da 6arin Fad'ima itama Bilkeesu tayita zubar da jini, da'akaje asibiti sai akace maganin zubda cikin akabata tasha aruwa, amma cikin ikon ALLAH cikin bai fad'iba. Alokacin hankalin babanku yatashi. yatsare Matan NASA yana bincikarsu, kowacce tashiga kare kanta, ganin abin zai kawomusu 6acin rai nace yabarsu nizan bimko komai dakaina. Rana d'aya ALLAH yakawoma Bilkeesu da Laure haihuwa, amma laurece tafara nak'uda. Laure tahaihu amma k'awarta kaltume tak'i sanar damu abinda ta Haifa, sai yawo da hankali suke mana. saboda Bilkeesu tana cikin tsaka mai wuya har ana shirin yimata theater, shiyyasa bamu damuba, tunda dai Lauren tahaihu lfy. Dr yajanye mahaifinku danya saka hannu a yima bilkeesu aiiki, nikad'ai aka bari ak'ofar d'akin da Bilkeesu take nak'uda, Fad'ima kuma taje siyo ruwa za'a sakamata. Ina nan tsaye saiga Nurse d'in dake kula da Bilkeesu tafito tace tahaihu mace, amma yarinyar batazo da raiba. Munji babu dad'i nida mahaifinku, amma Bilkeesu nata tausarmu akan muyi hak'uri. Alokacinne kuma mukaji Laure tahaifi d'a namiji, babanku yayi murna dahakan. Saidai wata sabuwa kuma, tunda muka dawo yaron Laure yak'ishan nononta, daga baya da'aka bincika sai akaga nonon nafita yellow ne, anbashi madara yak'isha, gashi yanata tsanyara kuka, yatada hankalin kowa, ganin halinda jariri yake aciki nace akawosa Bilkeesu tagwada bashi nono, Laure tayi tsalle tadire tace bata aminceba, saida namata biji-biji sannan tabari Bilkeesu tabama jariri nono, abin mamaki anabasa yakar6a kuwa, abin yabama kowa mamaki da al'ajabi, amma bamu kawo komai aranmuba. Hummm wata badak'ala kuma babanku yayma jariri hud'uba da sunan mahaifin Bilkeesu, wato Ibraheem khaleel, babu Wanda yasani sai ranar suna. Bak'aramin rikici akayi da Laure ba, amma mahaifinku yace bata isaba, haka yakeson sunan d'ansa kuma babu mai canja masa. Daga nan Bilkeesu tacigaba da shayar da Ibraheem, watan Ibraheem uku babanku yasaki Fad'ima saboda maganin zubar da ciki daya gani ad'akinta, wai shitakesha tana zubar da cikinta, itacema tabama Bilkeesu alokacin data zubar dajini. Harga ALLAH banyardaba alokacin, dayayi shawara danikuma bazai saki Fad'ima ba. Bilkeesu ma tasha kuka sosai dantanason Fad'ima, hakadai Fad'ima tatafi muna kewarta saboda mutuniyar kirkice. Shekarar Ibraheem 1 Bilkeesu tasamu ciki, itama ALLAH ya azurtata da haihuwar namiji shine marigayi rufa'ee K'iyayyar Bilkeesu takuma k'aruwa ga laurah, tatsaneta sosai, wani abumma tana tsoron aikatashine sabodani agidan. Tundaga haihuwar Ibraheem kuma Laure bata sake haihuwaba har Bilkeesu tayi haihuwa biyar. *Rufa'ee, Sultan, mujahedeen, Amatullah, Ramadan, Zunnurain*. Saikuma suka haifi Hameeda da Musleem atare, daganan Bilkeesu takuma haihuwar Muhseen, itakuma 'yan biyu, Hasnah & Husnah. Alokacinne kuma babanku ya auro Saude, itamadai tanada nata mugun halin, amma tafi Laure, Laure taso suhad'ema Bilkeesu kai itada saude amma sauden tak'i amincewa. Saude tahaihu tahaifi Hafeez, Daganan suka haihu tare itada Bilkeesu kuma, Bilkeesu Amaliyya, saude Shuhuda, suka k'ara Tasleem da Maleekah, suka k'ara Ummunoor da Nureeden, daganan kuma haihuwar taimusu adabo. Ibraheem yatashi yaro marason hayaniya, yanason 'yan uwansa, akwai hak'uri da zuciya idan kakai hak'urinsa k'arshe, tun yana primary yarone me shegen naci dabin kwankwanto akan Abu, yana son kallon film na bincike, lokacin daya shiga secondary dole aka sakamasa TV ad'akinsa, saboda son kallon film Na bincike-bincike, akwai wata basira da ALLAH yayma yaron. Inhar za'ayi laifi agidannan arasakuma Wanda ya aikata, inhar yaji kuma, tofa saiya gano mai laifin acikin bincikensa, wannan tunanin yasaka mahaifinku barinsa shiga d'an sanda, Dan acewarsa irinsu Ibraheem ake buk'ata a police saboda iya bincike da naci. Ibraheem yasamu nasarar shiga d'ansanda cikin sauk'i saboda yanayin k'irarsa, dogon mutumne tsayayye, ALLAH yabashi suffar k'arfi irinta masu d'amara, gashida kwakwalwa da jajircewar aiki, daganan yasamu k'arin daraja zuwa hukumar 'yan sanda ta duniya, kukuka San sunanta da turancinku😑. Dariya su Hamdiyya suka kwashe dashi saboda furicin Ammah Na k'arshe. Sukace Ammah sunanta Police Interpol (NIS). Oho kudai kukasani nidai nagama nawa. _______________________ *_Ibraheem Abdallah Rufa'ee jigawa shine sunan jarumin namu, mahaifinsa nakiransa da suna mu'azzam saboda sunan mahaifin aunty Mamie gareshi, aunty Mamie tana kiransa babanta, hajia babba tana kiransa Ibraheem saboda tabak'anta zuciyar aunty Mamie, (Dan sunan mahaifi bawasaba). Awajen aiki suna kiransa J! Saboda tak'aitawa. J kyakykyawan Namijime dogo, wankan tarwad'ane, yanada cikar zati irinta zaratan maza, a6angaren k'yau kam masha ALLAH, komai najikinsa yadace da halittarsa, kokad'an bayason raini, kuma mutumne ma'abocin tsare gida, bazaka ta6a ganinsa cikin dariyaba, murmushima saiya gadama yayinsa, wannan yasa mutane suke ganin yadace da aikinsa Na d'ansanda._* *_idan tsautsayi yasa kafad'a tarkon j kagama shiga uku, zaiyi amfani da basirarsa ya cafkoka, wannan yasa yasamu d'aukaka fiye da sauran 'yan uwansa awajen aiki, j baya shaye-shaye, baya Neman mata, bazaka ta6a ganimsa awajen wani ashararanciba, mutumne kamilalle ma'abocin bin dokokin ubangiji, yanada ilimin addini dana zamani Alhmdllh._* _yadad'e yana bibiyar Oga David, kusan wata uku, awannan lokacinma tundaga k'asar Japan, yabiyo sahunsa, yasamu damar kamashine kuma tadalilin tatsar bayanai ga wani yaron Oga David dasuka kama, khaleel yanashan shiga aiki mai had'arin gaske ALLAH ne kawai ke ku6utar dashi, yana samun taimako daga abokansa taheer, Yousuf, Joseph, saidai shi ogansune awajen aiki._ *tuntuni aketa fama dashi yayi aure amma yak'i, saiyace akwai lokacin, koya la6e akan aiki yamasa yawa, bakuma 'yanmatan yarasaba, a'a bashida ra'ayin aurenne kawai, Dan ya khaleel akwai farinjini, turawan da bak'ar fatar ko ina 'yanmata binsa suke da Nuna masa tsantsar soyaya, amma kokad'an baya basu fuska, yafison auren yarinyar d'anya, saidai bansan dalilinsaba nikam, to komadai miye baffa dai yana d'aga masa k'afane kafin yamasa sambad'e-bad'e. Yanzu yanada shekaru 32 yanacikin ta 33 da haihuwa. gakuma k'anne cikeda gida.* Wannan shine j 👌🏼...........🖊 *inayinkufa, kumuje zuwa page 15😻😻* [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 1⃣5⃣ Ubangiji ya kar6a addu'ar Aysha hajia babba ta amince suje Kano suwuni Dan da driver ma aka had'asu yakaisu, bak'aramin gargad'i Aysha tasha barazana. Haka sukatafi itada gwaggo bintu da yakubu direba. Kasancewar tafiyar asuba sukayi k'arfe 11:24am acikin birnin Kano tamusu, amotama gwaggo bintu nata kwakwkwafar Aysha. Ita Aysha ma dariya suke bata wlhy, kokad'anma batadamu da fargabarsuba, damuwarta tafi karkatane da d'okin san ganin mamanta da ummah, saikuma yayunta tunda tasan k'annenta duk basa cikin Kano yanzun. Motar natsayawa kojiran yakubu yagama parking batayiba tafice da gudunta tana kwala kiran sunan ummah da mama. Ummah Ce kawai a tsakar gida tana tace kullun awara dasuke sonci yau, mama kuma tana bayi, Aysha tadaka tsale tad'ane ummah tana fad'in wayyo ummanah nayi kewarku wllhy. Tuni Ummah tasaki abin Tatar tarungume Aysha itama, suduka kukan farinciki sukeyi, mama jin karad'in Aysha yasata fitowa da hanzari. Aysha tasaki ummah taje tamak'alk'ale mama, adaidai nan gwaggo bintu tashigo, ganin yanda Aysha tad'ane mama yasaka gwaggo bintu ta6e baki. Da k'yar Aysha ta iya sakin mama, su saima yanzu suka lura da gwaggo bintu daketa wani 'yan yatsine-yatsine, sunsaba da halinta shiyyasa suka watsar da lamarinta suka mata tarbar mutunci su. Dukda Aysha tana fuskantar wahalhalu agidan Alhaji Abdallah, hakan baihana jikinta murjewaba, tak'ara girma da k'iba, ga hasken fatarta yak'uru sosai Dan Aysha farace tas dama, yanayin canjin abinci darashin yawo arana saiya k'ara hasken NATA, Aysha doguwace gaskiya dukda dai ba irin shantaleliyarnanba, idan zata tsaya kusadasu ya khaleel dogaye sosaima baza'aga tsawontaba, farace tas kuma k'yak'yk'yawa, tana masifar kama da mama, Aysha batada k'iba, amma k'ila zuwa nangaba idan hankalinta yakwanta tak'ara girma zatad'an k'ara k'iba fiye da yanzun, a6angaren k'yawun fuska kam ba'a magana komai yaji masha ALLAH, tanada manyan idanu da dogon hanci, ga zara-zaran gashin ido masu d'aukar hankali, idan Baka saniba saika rantse tak'arane, kuma natane, idan Aysha tak'ara girma zuwa nangaba dolene akirata sarauniyar mata gaskiya. Mama taji dad'in ganin yanda Aysha tayi k'yau, wannan yasaka hankalinta k'ara kwanciya dazaman Aysha gidan Alhaji Abdallah, tasan yanzu hankalin d'iyar tata akwance yake tunda gashi har za'akaita makaranta k'asar waje itada yarangidan. (Nace hummmm kedai mama abar kaza cikin gashinta kawai, su gwaggo bintu sundai tsarakune). Sai wani dama-dama gwaggo bintu takeyi da Aysha saboda gudun karta fad'i wani Abu, su mama basu kawo komai aransuba, gwarama Fadeela da Hafsat sukam saisukaga kamar Aysha nacikin damuwa, amma gaba d'aya gwaggo bintu tahana Aysha sakewa barema tafad'a, dak'yar gwaggo bintu tayarda Aysha tashiga makwafta ta gaidasu, Duk ida taje sai sha'awar kyawun data k'ara akeyi, itadai batacewa komai saidai dariya, damacan asali Aysha bamai yawan surutu baceba, idan kaga tafiya magana akan Abu tofa takai makurar cutuwa dashi, bayan sallar azuhur suka ajiye uwar tsaraba da hajia babba tayimusu sukai sallama Aysha nakuka suka taho, jitayi kamar kada tadawo Abuja ma, amma tanason tacigaba da ganin ya khaleel koda daga nesane, tunda tafara ganinsa yake bala'in birgeta. (Hummm Aysha miye sirrin🤔?.) Sunbiya tagidan kawu bilyamin, suntarar yaran gidan duksun tafi islamiya tahfiz, suma su Aysha sunayi sanda mahaifinsu Nada rai, amma yanzu rashin gata dukya ruguzawa rayuwarta wannan tanajin. Aysha bataji dad'in rashin ganin su sadiyaba, tayi kewarsu sosai, amma yazatayi. Tunda suka kamo hanyar Abuja takifa kanta da guywa, ahankali taketa rera kuma maiban tausayi da tsuma zuciya. 5:pm suka iso abuja. Hummm abinda yabama Aysha mamaki bai wuce ganin sunnufi wata anguwar dabanba sa6anin maitama. Abinda Aysha bata saniba shine bayan tafiyarsu Kano hajia babba tasanar da 'yan gidan cewar Aysha bazata dawoba, wai k'anin mahaifinta yace makaranta zai sakata. Lamarin ya Sosa zuciyar aunty Mamie, takumaji haushin gwaggo bintu sosai tunda bata sanar da itama Aysha zataje gidaba, dama tanada k'udirin saka Aysha amakaranta, jiratake hankalin ya khaleel yakwanta tasakashi yasamoma Aysha school mai k'yau, to gakuma abinda yafaru. Tunda Aysha tagansu a gidan hajia kaltum jikinta yayi sanyi, lallai tasan yau tafaru ta k'are kam, kukadai tashashi awannan daran, tayi mai isarta tahak'urema ranta. ____________________ Ahanzarce yafito daga 6angarensu, kansa ak'asa yana k'ok'arin d'aura agogonsa, sanye yake cikin Uniform d'in aiki, kayan sunmasa matuk'ar k'yau da fito da kwarjini dacikar haibarsa, duk bin kwankwantonka baka Isa banbance turaren da ya khaleel ke amfani dashiba, akowane lokaci dasabon k'amshin turare zakajishi, hakan yana cikin dabarun aikinsa. A'a babana saurin mikakeyi hakane?. Wlhy aunty IG ne yamin kiran gaggawa, shinefa nake hanzarin fita, security na jirana awaje. Amma duk saurinka yakamata ka karya koda kad'anne, yanzu hakama bakasha maganinka ba, wannan ciwon dakake rainawa idan baya samun kulawar magani saiya girmama. Hular hannunsa ya matse a hammta tareda had'e hannayrnsa biyu alamar rok'on tabarsa yatafi🙏🏻, please Mamie. Aidama bahanaka tafiyar zanyiba agogo sarkin aiiki, bara nahad'a maka katafi dashi office d'in, katabbatar kuma kacishi. Kai Anty Mamie, saikace wani d'an Nursery school?. Dariya aunty tayi batareda tabashi amsaba tafara had'a masa break fast acikin lunch box, shikuma yanufi gaida sauran masu gidan. Momy ma tafita aiiki, su Anty zuwairah kuma basu tashiba, da Hameedah kawai yagaisa itama tana shirin fita aikine, Umme ma tafita aiki, baidad'eba a 6angaren Ammah, yashiga wajen Baffah. Yana zaune afalonsa yanajin labarai a redio ya khaleel yashigo, cikin girmamawa suka gaisa. Baffa yace, "har za'a fitane mu'azzam?. Eh wlhy baffa yay maganar yana kallon agogon hannunsa. To ALLAH ya tsare manaku, nagama wannan karon kadad'e ak'asar?. Eh wlhy inada ayyukan cikin gida 9ja sosaine, amma dukda haka zanje Indonesia nextweek, daganan nabiyo ta france, zandad'e sosai a Najeria wannan karon. To masha ALLAH, kaga kenan ad'an lokacinnan saikayi aure tunda zaka dad'e. Shafa kai ya khaleel yayi, fargaba dukta cika masa zuciya, bai iya cewa komaiba. OK idan tsoron matan kakeji saina duba maka, dama ance police akwai tsoron mata, Ya hannun naka?. Hannu da sauk'i baffah, ya amsa maganar k'arshe Dan gusar data farko. Dariya baffa yayi, tashi kaje kada ka makara, zamuyi maganar a tsanaki.... Kafinma baffa yarufe bakinsa har ya khaleel yamik'e kamar Wanda yake zaune acikin wuta.😂 Baffah madai abin yabashi dariya, amma saiya murmusa yanabin khaleel d'in dakallo harya fice. Yauwa Anty bara nawuce, asaka yariyarnan tagyarmin d'akina yayi datti sosai, musammanma bathroom d'ina. Wai Aysha kake nufi?. Ni banma san sunantaba Anty Mamie, amma farar dai. eh ayshace. Bata nan, takoma Kano wajen iyayenta, saidai bishirah tagyara kokuma cikinsu Amal. To Mamie, amma yaushe takoma? yana tafiya. Jiya-jiya, takoma makarantane wai. Yaje daidai fita falon yace shikenan su Amal su gyaramin idan basuda school saina dawo. Motocine guda uku ak'ofar gidan, yana fitowa sauran security suka shiga Sara masa, hannu kawai yad'aga musu yana gyara zaman hularsa akansa, bak'aramar kamala da kwarjini hular tak'ara masaba, aka bud'e masa motar tsakkiya dasauri yashiga ya zauna. Aguje sukabar anguwar, jiniyarsu dukta karad'e kunnuwan jama'a. A office d'in IG yak'ame tareda yimasa salutes, IG yakar6a ma ya khaleel shima tareda nuna kujerar gabansa yana fad'in J! bismillah. Zama ya khaleel yayi, IG yamik'a masa hannu suka kumayin musabaha.🤝🏻, ya hannu?. Alhmdllh sir. Yauwa J! Koka tatsi bayanai daga David kuwa? Dan nasan yanada iyayen gida. Yes sir, nima nayi nazari akan hakan, amma ban binciki komai agareshiba dama sai yau. kamar yanda yaransa yafad'a akwai manyan k'usoshin gwamnati da 'yan kasuwa dake tareda David, amma ya tabbatarmin baisan kowaba acikinsu, Dan aikin sirri sukeyi da David, kuma baya barinsu su yaransa Susan komai akan hakan. Saidai nad'an samu wani solution, amma kamar yanada rauni. OK nami kenan? Miyasa kuma Baka yarda da ingacinsaba?. Saboda ban tabbatarba, dama Akan wani Alhaji ne, Dan ana gobe zamu kama David naje club d'in dashi David yake zuwa inhar yana 9ja.. Dayake Amashin naje wajen, lokacin danake k'ok'arin shiga ciki shikuma motar Alhajin nafita, nakuma ga fuskarsa. Abinda yasa nazargi Alhajin nacikinsu, nayi hira dawata yarinya a cikin club d'in ta tabbatarmin da cewar club d'in na David ne, duk kuma Wanda nagani awajen yanada alak'a dashi. Anawa kuma tunani babu yanda za'ayi mutum mai daraja kamar alhajin Dana gani, inhar bashida alak'a da David yace zaizo wajen, tunda yanada kud'in daza'a kaimasa mata har gida ko hotel, babu kuma alama data nuna yasha wani Abu alokacin, balle muce shaye-shaye yakaisa wajen. Jinjina kai IG yayi, cikin gamsuwa da bayanan ya khaleel yace, "yes kanada tunani maik'yau j!, so yakamata asakama Alhajinnan idanu, nasanka zaka gano inma yana taredashi, Dan nayarda dakai 100%, kasan aikinka. Thanks you sir! Ya khaleel yafad'a cikin nuna alamun jin dad'i dayabon ogan nasa. Jin jina kai IG yayi tareda mik'ama ya khaleel wani file, ga wannan file d'in, Case d'in yaron nanne Mansur Lawan, Wanda aka kama da coken a airport d'in Nijer, so inaga zasu bamushi nanda 2weeks k'ila, saikayi k'ok'arin bincike akansa shima, amma zaka samu had'in guywar hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyi ta k'asarnan, ya mik'o masa guntun pepper, ga number shugaban hukumar nan, kayi k'ok'arin Ku had'u, kokuma ka wakilta Wanda kayarda dashi, dannasan aiki yamaka yawa. OK sir, zanyi k'ok'ari insha ALLAH. ALLAH ya taimaka Ibraheem Abdallah jigawa, I'am proud of yau akowane lokaci, ina yabawa da aikinka danka cancanta. Musabaha sukayi sannan ya khaleel yafita zuwa office d'insa..................🖊 *Rashinyin comments nawasu groups zaisa narage yawan typing , nasan kuna karantawa amma babu comment, sai k'alilan acikinku sukeyi, agaskiya bazai yuwu na ajiye ayukana nazauna INA typing wani lokacin har 2times yazama babu wani nuna alamun jin dad'inkuba.* *sannan inhar buk d'innan yay nisa bazan kuma turama wani ta PC ba, bazan iya had'a typing da posting ba sannan kuma ana bina PC ana rok'on naturo, ina jin kunyarku amatsayin masoyana, amma gsky zuwa nagaba zansaka bak'in Google😎.* ALLAH yasa mudagyara. 😻😻😻😻😻😻😻😻 [8/7, 7:37 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) *_Nagaisheku dayawa-dayawa_*🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀😻 1⃣6⃣ *_Sanadin maraici_*😭 Dolene Aysha takira wannan tafiya datazo acikin k'addarar maraicinta, sanadin maraicine yasata zuwa Abuja har hajia babba taganta, awannan ranar da'ana kuka hawaye suk'are dana Aysha sunk'are tas, tayi kuka hartaji babu dad'i. Amma Abu mafi cin zuciya da ruhi shine rashin ko inkula da gwaggo bintu tanuna agareta, aganinta kobabu komai tasamu sassauci ga gwaggo bintun koda kuwa Na lallashine. Amma Sam bahaka baneba ga gwaggo bintun. Har lokacin da Suka rakosu airport gwaggo bintu batace da Aysha ko yi hak'uriba, wannan ne yak'ara rura wutar bak'inciki da tsananin kishinkai ga ayshar. Tak'udiri aniyar inhar yakasance da gaske karatun aka turata tofa zata tsaida hankalinta waje d'aya tayishi kodan takar6ama kanta 'yanci alokacinda hakan zaizama nadamarsu gwaggo bintun. Tafiyace data kasance harsu kimanin bakwai, akwai hajia kaltume, sai wata matashiyar budurwa Dabaza ta wuce shekaru 28 ba, mai suna kubra, saikuma 'yanmata hud'u wad'anda dukkansu zasukai shekaru 18-19-20, Aysha ce kawai mai shekaru 14. Tun'a airport tafiyar tasu tarabu, hajia kaltume tad'auki 'yammata uku ita cikon ta hud'u, mukuma matashiyar budurwannance tad'aukemu nida budurwa d'aya mai amsa suna Besi, suma sauran 'yan matan nakula duk yarene. Gefe hajia kaltume taja Anty kubra suna magana, ak'allah sunkai 18minute's suna tare, saida aka fara kiran masu tafiya, da sauri sukayi sallama tace mutaso jirginmu zaitashi. Wasu hawayene masu zafi suke zarya akumatun Aysha, wai yaune zatabar k'asarta akan zalincin wad'ansu mutane, tunda take bata ta6a zuwa kudancin 9ja bama bare tabar k'asar, ko a arewacinma bako ina tasaniba, tafiya takeyi tamkar wadda kwai yafashema acikin ciki, jitake wata k'aunar k'asarta Na ratsata, tanason k'asarta amma za'a fiddata tak'arfin tsiya akaita bauta wata k'asa dabatasan kowaba. Anya kuwa hukumomin k'asarta suna aikinsu da k'yau?, shikenan yanda talaka bashida 'yanci cikin k'asarmu hakama bazai ta6a samun 'yanciba awata k'asar, talauci abune mai ciwo, tasanadin talauci ake hajijiya da al'ummar k'asarta Nijeria. Shin sai yaushene talaka zai samu 'yancine a Africa ma baki d'aya?........ Rankwashin daya sauka tsakkiyar kan Ayshane yafarkar da ita daga nannauyan tunanin data tafi. K! Dallah kidawo cikin hankalinki, wlhy kikayi abinda yakawo mana Matsala saimun k'arar dadukkan danginku, kajimin wawuyar yarinya, 'Yar k'arama dake sai tsaurin ido. Aysha Na share hawaye tace kiyi hak'uri Anty bazan sakeba. Kima sake kiga abinda zai biyo baya mana. Ankira sunayen su Aysha, bayan kammala dukkan wani bincike da ainan-ainan suka samu Shiga jirgi. Addu'oi Aysha taitayi azuciyarta, Ashe duk yanda muke hasashe da tunanin jirgi a sararin Saminiya yawuce gaban haka, lallai dukkan wani bawa mai imani yashiga jirgi dolene ya tsarkake sunan ALLAH da k'ara yalwatar imani acikin ruhinsa, yo inba hikimar ALLAH ba, yama za'ayi duk girman jirgi yatashi sama, haryayi gudu batareda ya fad'o cikin k'asaba, lallai akwai ni'imomin ubaginji ga bayinsa akan jirgi. Hakadai taita tunaninta har aka kammala Kiran sunan masu tafiyar. Alokacin da jirgi zai tashi Aysha ta rintse idanu kam, tareda rirrik'e hannun besi dake kusada ita dukda kuwa tana d'aure da belt ne. Koda akazo tambayarsu mizasuci acikin jirgi Aysha KASA magana tayi, saboda batajin turanci, (kowadai yasan lalacewar makarantunmu Na arewa, inhar kanaso yaronka yaji turanci tofa saidai kasakashi private school, amma gaskiyar magana Government schools namu sunada k'arancin kulada ilimin 'ya'yan talakawa, shiyyasa kullum mune ak'asa😎). Da taimakon besi aka kawoma Aysha abincin, kad'an ta tsakura Dan baimata wani dad'ibama. Tafiyar awoyi 8 takaisu wata k'asa da Aysha batasan sunantaba, sunyi hutun awoyi 2 sannan suka samu canjin jirgi. Ayanzuma tafiyar awani 11 takaisu wata k'asar, anankam sun isa da daddare, Dan haka suka nemi masauki, Aysha Na mamakin k'yawun k'asashen azuciyarta, komai Nasu acikin tsari da tsafta yake tafiya bakamar k'asashenmu Na Africa ba, wanda son mulki Dana dukiya yagama kashewa, mukuma talakawan zuciyarmu tagama mutuwa saboda jiran abamu, (da wannan damar 'yan siyasar k'asarmu sukeyin amfani suna hajijiya da mu). Ba'a hotel suka saukaba, kubra ce takira wani yazo har airport yad'aukesu. Tundaga yanayin guy d'in Aysha tasha jinin jikinta, kokad'an bashida k'yakyk'yawar alak'ar dazai amsa suna mutumin kirki, tunda yakafama Aysha ido yakasa d'aukewa, tun abin nabama Aysha mamaki harya fara bata haushi tashiga Neman tsarin ALLAH daga sharrinsa. K'yakyk'yawan gida sukaje Wanda Aysha talura dukan gidajen sassan masu k'yaune kamarsa, (to dama turai ai ba'a cika banbance talaka damai arzik'iba, sabodasu sun tsare martabar k'asashensu). Komai agidan atsare yake, babu tarkacen hauka ko kad'an, saidai akwai abinda bai birge Ayshaba agidan, sune manyan hotunan 'yammata Na turawa tsirara, Aysha takauda kanta tana Jan tsaki azuciyarta. Bayan sunyi wanka aka kawo musu wani kalar abinci, kokad'an Aysha da besi sunkasa cinsa, gwarama besi tadaure tad'an tsakura, amma Aysha lemo taita bankama cikinta Dan bazata iyacin wannan jagwalgwalonba. Amma kubra hankalinta kwance takeci, wannan yatabbatarma su Aysha ita ba bak'uwar cin irin abincin baceba, suna gamawa su Aysha suka koma d'akin da aka basu itada besi. Aysha tayi addu'ointa nabarci ta kwanta cikeda kewar k'asarta da iyayenta, besi nashirin rage musu hasken d'akin akashigo burum, mai gidanne yashigo, yayinda kubra tabiyoshi abaya da sauri tana masa magana cikin harshen France, dagashi sai gajeren wando, gashi atsaye babu wata k'ibar arzik'i ko k'irar cikakkun maza, daka gansa cocaine tagama ragad'eshi..... Tunanin Aysha yatsaya lokacin da kubra ke fad'in please mana my man........sauran maganganun su Aysha basaji, Dan itama besi batajin France d'in, daga turanci sai yarenta saikuma Hausa d'ai-d'ai, to aysharma dai daga Hausa babu dad'i babu k'ari, aturancin dai takan tsinci k'ananun kalmomi. Da k'yar kubra tasakashi yafita, sannan tacema su Aysha su sakama d'akin key. Aysha takalli besi ido tab da hawaye, anty misuke nufi?. Shiru besi tayi Dan bata fahimci maganar ayshaba. Saidai Aysha tad'an jagula turancinta, shima awajensu Ummunoor take d'an tsinta. Sannan besi tagane, (indai mutum najin turanci, ko ayaya aka jagula masa zai d'an fahimta). Cikin gur6a tacciyar hausar besi tace sholy baki gane ba?, aii tunda muka sauka a airport yake fad'ama Anty kubra waimu kayanashine Dan kinmasa, yanason young irinki. Shine tace masa a'a banshiba. Todaganan suka koma magana da France, nikum banajin language d'in France. Shiru Aysha tayi tana had'a maganganun besi amizani, amma kokad'an takasa musu fashin bak'i saboda k'arancin shekarunta, dakuma kokad'an tunaninta baita6a karkata ga hakanba dukda kasancewarta yarinya mai basira da k'yakyk'yawan tunani. Haka sukai barci badan Aysha tanajin dad'in barcinba, sai juye-juye takeyi da tunani kala-kala. Amma bahaka baneba ga besi, hankalinta kwance take barcinta, tayi wani rashe-rashe agadon, dagani kasan batasaba samun irinsaba ko kwatankwancinsa. Tashi Aysha tayi tashiga toilet d'in dake cikin d'akin, ta d'auro alwala tazo tacire hijjabi a handbag d'inta, tasaka d'ankwalinta ta kabbara sallah batareda tasan inane gabasba, acewarta ko ina aii ALLAH yana nan kuma yana kallon bayinsa. Dama d'azun ahaka tayi sallalolin da ake binta. Saida dare yay nisa Aysha tasamu barci awajen datayi sallahr, zuwa sannan kam tasamu sauk'in damuwarta. Tunda safe suka koma airport, ayanzukam taxi suka hau yakaisu, Dan Wanda yad'akkosu jiya yanajin haushin anhanashi hutawa shiyyasa basu samu rakkiyaba agareshi. Ayanzu kam tafiya awanni 6 ce takaisu inda Aysha take addu'ar ALLAH yasa sunzo kenan, Dan itakama tagaji matuk'a da hawan jirginnan, saboda rashin sabo jikinta sai masifar ciwo yake mata, ga ciwonkai Wanda take k'yautata zaton yunwce, Dan tunda suka baro 9ja bata sake cin wani muhimmin abuba, kai tunma randa sukaje Kano da gwaggo bintu... __________________________ *_Nigeria_* Koda yashiga Office saiyayi k'ok'arin bin umarnin aunty Mamie, lunch box d'in data had'oshi da ita yabud'e, shiryayyen breakfast ne aciki mai nagarta da d'and'ano, koba'a fad'aba yansan wannan girkin aunty mamien sane, yana k'aunar matarnan, Dan komai nata daban yake Dana matan gidan, subasuda damuwa saina aikin gwamnatinsu, basu kula da 'ya'yansuba barema mijinsu, wannan halayyar tasu momy yasakashi sha'awar auren k'aramar yarinya wadda batada zurfi da ak'idar yin aikin gwamnati, halayen Anty Mamie nak'ara masa k'aimi wajen sha'awar hakan. Dukda azagayensa Na k'asashen duniya yaga mata dayawa dasuke aikin gwamnati kuma suna bama 'ya'yansu da mazajensu kulawa, to amma masu iya magana kance ruwan daya dakeka shine shine ruwa...... Kai mutumina duk dad'in abincinne?. Firgigit yadawo hayyacinsa, k'aramin tsaki yaja tareda danna laumar dankalinsa abaki, amma idonsa nakan mai maganar. Taheer yazauna yana dariya, J! wai dad'in abincine haka?. Saida ya had'iye nabakinsa sannan yabashi amsa da kaid'inne d'an iska aii, yanzu zaka katsemin jin dad'ina, kuma ma aii aikawa nayi akiraminkai amatsayin oganka ba abokiba. Wata dariya Taheer ya tuntsure da ita, yace to sorry sir, bara mugama cin abincin saika koma serious, Dan yanzun kana komawa amatsayin Oga abincinnan da k'amshinsa yacikan hanci haramiyata, dama nafito gida ban karyaba. Harararsa Ya khaleel yayi tareda fad'in tuzurum banza kawai, ALLAH yakamata Ummi Tanaka aure kodan iskancin daka koya. Oh nawa tuzurancinne ya to she maka idanu kawai? kai baka duba yawan shekarunka? ALLAH ka k'ara wasu shekaru anan gaba matarka tsoho zata aura, taheer yay maganar yana danna laumar dankali abakinsa. Duka ya khaleel yakai masa, amma saiya kauce. Yace, "kai mara mutunci barmin office". Hhhh ALLAH babu inda zanje sai tumbina yacika Malam. Kwafa ya khaleel yayi, yad'auki cup d'in tea yana sha da Harar taheer. Oho kayita hararata har abusa k'aho Dan ALLAH, abincinedai babu fashi sainacishi, tunda ba matarka ta girkaba momyce. Dariya ya khaleel yayi yace aiba momyn baceba yaro. To waye?. Aunty Mamie ce. Kai ammafa ta iya girki, wannan weekend d'in dolene nashigo gidannan gaisuwa. Shege gaisuwar kwad'ayiba. Dariya kawai taheer yayi yana fad'in komadai tamiye lada zan samu aii. Bayan yakammala cin abincin yagyara wajen, daga nan ya khaleel yaci serious, fuska a tamke Yakoma yima taheer magana. Shima taheer d'in ya zama seriously saboda afagen aiki suke yanzu, ya khaleel amatsayin Oga yake ba abokiba a halin yanzun. Bayan sungama tattaunawa suka mik'e domin zuwa Inda aka rufe Oga David..............🖊 Kuyi manage da wannan yau naje anguwa nagaji. *_kujamuje Fan's, comment naku shine k'arin k'aimina wajen k'ayatar wannan littafin, Dan haka yawan comment's yawan dad'in novel😻😻😻😻😂_* [8/7, 7:38 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) *_kuna raina masoyana, ina kuma alfahari daku, especially 'yan group d'in pharty Zarah, & Manshat group, comments naku Na k'ayatar dani ainun, dolene idan bikin ya J! Yatashi ajedaku😉😂😍._* 1⃣7⃣ Wasu matasan 'yan matane sukazo tarbar su Aysha, sun rungume juna suda anty kubra cikin nuna alamun sunyi murna da ganinta, suduka biyun bak'ak'en fatane, amma jindad'i da sauyin rayuwa yasakasu komawa fresh, haske kawai turawan zasu iya nuna musu. d'aya ta kalli Aysha cikin fara'a tace, "woow Beautifull babie!! Tayi maganar tana shafa kumatun Aysha, tana tambayarta yatake? cikin harshen turanci. Murmushin yak'e Aysha tayi, amma takasa amsata. Anty kubra Ce tasanar dasu Aysha batajin turanci. Abin yabasu mamaki, amma saisuka basar, itama besi sukayi welcoming nata, itakam ta amsa musu yanda yakamata. d'aya acikinsu take tuk'a motar, sai surutu suke zubawa da Anty kubra, itadai Aysha batajin komai, besi kam tana sairarensu. Had'ad'd'en gida suka sauka, tundaga waje komai yabirge Aysha Dan babu abin kushewa. Cikin gidanma komai yagamaji 100%, saidai kowane Bango yasha lik'e-lik'en abubuwa kala-kala, wani Na birgewa, wani naban haushi, (rayuwar turai sai ahankali) suntarar dawasu 'yan matan ak'alla hud'u agidan, duk suna zaune afalo, d'aya ta tadakai da cinyar hamshak'iyar matar dake zaune cikin wando da riga, dukda tanada 'Yar k'iba kayan sun matuk'ar mata k'yau. 'Yanmata biyu suna gefe suna game d'in lido, yayinda d'aya ke karatun English novel. Gaba d'aya suka taso suka rungume Anty kubra harda matarnan. Sai murna sukeyi, matarce takama hannun Aysha tana fad'in kubra kincika alk'awari gaskiya, dama John yanata damuna bebynsa-bebynsa. Dukda harshen English suke magana, shiyyasa Aysha bata fahimtar komai. Ita gabad'ayama hankalinta nakan kallon 'yan matan, kaf d'insu babu mai shigar arzik'i, watama daga ita sai pant & bra, saiwata shegiyar Riga shara-shara data d'ora asama, wadda sakatama bashida amfani tunda bai rude mata komaiba. Besi kam ko'a kwalar rigarta, saima birgeta da 'yanmatan sukayi. Sudukansu bak'ak'en fatane, kuma Aysha Na k'yautata zaton duk 'yan Nigeria ne. Bayan su Aysha sun huta sunci abincin da Aysha tacishi akan dole, danjin yunwa zata hallakata, sauk'intama akwai snacks aciki. Wanka sukayi kowanne aka bashi kayan dazai saka Dan dagasu sai handbags dama sukazo, hajia kaltum tace ba'a buk'atar suje dakomai. Aysha takalli kayan idonta cike da kwallah, yama za'ayi tasaka wad'annan kayan amatsayin sutura? Kai bazai yiwuba gaskiya, zaune tayi abakin gadon d'aure da towel tazabga tagumi. Jin anta6ata yasaka d'ago manyan idanunta dake cike da gashi gazar-gazar tana kallonta. Cikin maganar kurame budurwar ketambayar Aysha lfy?. Itama tamayar mata Cewar babu komai, batason kayannan. Shuru budurwar tayi tana kallon Aysha, zuwa can tace to wad'anne kikeso?, cikin harshen Hausa tayi maganar. Wannan yasaka Aysha kallonta a kid'ime, dak'yar ta iya d'aga baki tace Dama kinajin hausa?. Murmushi mai ciwo budurwar tayi, cikin halin ko in kula da tambayar ta aysha tace karki damu akanjin Sanin wannan, gawad'an nan wando da rigar kisaka, nasan rigar zata kai miki har guywa, saiki d'ora wannan rigar sanyin Asama Dan akwai sanyi ak'asar gaKi bak'uwar shigowa. Jinjina kai Aysha tayi, jikinta a sanyaye tad'auki kayan zata koma toilet tasaka. No dawo kisaka anan mana, ni fitama zanyi, batajira cewar ayshaba tafice abinta. Binta Aysha tayi da kallo harta fice, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana girgiza kanta, kai bata yarda wannan matar bahaushiya baceba, jibifa shigarta, gajeren wandone iya cinya Na jins, yayi masifar matseta, sai 'Yar Riga dabatakai ko cibiyartaba, tashare hawayen dasuka gangaro akan kumatunta, oh ni Aysha, wace irin rayuwa kuma aka kawoni nayi anan? Nida akace zanje nakula da matar aure mai ciki, amma ankayoni gidan gardawan 'yanmata, wlhy gara gidansu hajia babba sau dubu, koba komai addininmu d'aya yarenmu d'aya k'asarmu d'aya, ya ALLAH kayi dubi ga marainiyar ALLAH, karka basu damar cutar dani ubangijina. Tana kuka tana shiryawa, tagama tsaf tasaka hijjab d'inta, sallah tagabatar batareda tasan ya lokacin yakeba, Bakuma tadamu da sanin inane gabas. Zaune suke suduka afalon, kowa yana introduced d'in kansa. Babbar hajiya tace sunanta Anty Glory, amma anakiranta Anty Glo... Suma suka fara nuna Kansu kowa nafad'ar sunanta, tafarko tace Happy, 2 oyilola, ana kirana lola, 3 Serah, 4 Queen, 5 Shelyn, ana kirana Lyn, 6 meerah. Aysha takafeta da edo tana maimaita meerah a la66anta, wadda tamata hausace d'azu, wannan yakuma tabbata 'Yar uwartace bahaushiya kenan?. Ta6ata Anty Glo.... Tayi alamar tafad'a itama. Ahankali tace Aysha. Anty kubra tace zaku iya kiranta sholy. Kallonta Aysha tayi dasauri, Anty kubra ta maka mata harara. K'asa Aysha tayi dakanta. Daga nana fira suka cigaba dayi, itadai Aysha batajinsu bakuma tasaka baki. Da daddare maimakon Aysha taga kowa Na Neman makwanci saitaga su Lyn sunata wanka da kwalliyar kece raini. Kowaccensu cikin shigar rashin mutunci tafito, sukazo suna sumbatar kumatun Anty Glory tareda mata bey. Inakuma zasu wad'annan??. cewar Aysha azuciyarta, saidai babu mai bata amsa. Ganin tafara barci Anty Kubra tace taje takwanta a d'akin meerah inda tayi wanka d'azun. Tashi tayi tatafi tabarsu sunama besi magana. Koda taje d'akin bata kwantaba, saitayi alwala taita nafilfili abinta daneman agaji wajen ubangijin talikai, dukda ita bata fahimci komaibama har hanzun. ____________________________ Tunda yafito k'ananun security suketa k'ame masa, hannu kawai yake d'aga musu, Taheer nabinsa abaya shida Emanuel. d'akinda Oga David yake aka bud'e suka shiga, did'im da duhu tamkar dare, saida Ema yakunna wasu fitulu masu hasken tsiya (irin wanda inhar aka haska idonka dasu saika daina gani nawucin gadi). Da sauri Emanuel yagarama ya khaleel kujera guda d'aya tal dake acikin k'aton d'akin, Oga David yanacikin wani keji, (dolene mukirashi keji kasancewar k'arfunane irinna cel kamar baca azageye tsakkiyar d'akin), Oga David yana zaune rashe-rashe a galabaice, kansa aduk'e alamar yana gyangyad'in wahala. K'aramin fito ya khaleel yayi tareda d'an buga k'arfen da key. Da sauri David yad'ago, ganin ya khaleel ne yasashi aro jarumta ya yafama kansa, murmushi maikama dayak'e yayi, murya agalabaice yace, "halan kasamu TV ne? Kazo katasani gaba, waimiyasama kakawoni nan wajen? Ko salon naka business d'in kenan?. Wani murmushin k'asaita ya khaleel yasaki tareda shafa kwantaccen gashin sajensa dabai cika yawaba saboda askewa dayakeyi, baice komaiba sai ID cat d'in aikinsa daya nunama Oga David. Cikin d'age gira yajanye abinsa yana fad'in why not idan kanason mud'ora daga inda muka tsaya a business d'in namu. David yay dariya, yaro kana wasa da Lion fa. Ya khaleel yata6e bakinsa cikin salon ko inkula yace ayya had'in yayi daidai kenan, ga Lion, ga kuma young tiger🐅. David zai sake magana Taheer yadaka masa razananniyar tsawar datasa bakinsa rufewa 6am. Murmushi kawai ya khaleel yayi, cikin muryar data k'ara razana David yace Chubuzor Obinar! Suwaye abokan kasuwancinka?. Babu. Abinda David yafad'a kenan yay shiru. Ya khaleel yatsura masa manyan idanunsa masu shegen kwarjini, acikin razananniyar murya yace waye Alhaji Alasan kwangila!!?. Wata zabura David yayi, yanayinsa kad'ai ya isa yanuna maka yarazana dajin sunan, amma dayake ance d'an iska d'an iskane bakinsa Na rawa yakuma cewa bansanshiba. Ran ya khaleel yafara 6aci, yakula sai an d'umama jikin David zai basu had'inkai. Ganin yanayinsa yasaka taheer fad'in kafad'a masa David kafin yanzun kayi nadamar turjiyarka. Wata dariyar rashin mutunci David ya kece da ita, cikin dariyar yanuna Taheer, kai d'an k'arami!. da oganka nake magana bakaiba, bar manya suyi zancensu wannan ba shigarka baceba. Tsawa ya khaleel yadaka masa Short up!!!!!!!!!. Yanda yay maganar cikin k'araji saida ya girgiza hantar securitys d'in dake waje. Taheer yace azuciyarsa David kashiga uku, tunda harkayi gangancin saka ran j! 6aci haka........ Kwala kiran Samuel da ya khaleel yakeyi shine yakatse tunanin Taheer. Cikin tsawa ya khaleel yace Sam..... Kaida Mahfouz ku koyama shegennan ladabi!!, dayasan yanda zai ringamin magana!!!!. Jikin Samuel narawa yace, "OK sir, sorry sir! Tareda Salute. Bai tankaba yafita a harzuk'e. Taheer kam kujerar da ya khaleel yatashi yaja yazauna danson ganin yanda za'aci uban Oga David......... ___________________________ Akusan tsaye Aysha takwana tana fad'ama ALLAH damuwarta da rok'on yakareta. Su meerah kam basu dawo gidanba sai k'arfe 5 Na asuba, Aysha Na sallar asubahi tashigo d'akin. Kallo d'aya zaka mata kagane abuge take. Bin Aysha tayi da kallo cikin mamaki da kad'uwa, itafa tamanta anamayin sallah, takaudakai cikin k'unar rai tafad'a kan gado ko takalmi bata cireba. Aysha ta idar da sallah tajuyo tana kallon meerah dake kwance rubda ciki, tausayinta Yakama Aysha, dantakula kamar tanacikin damuwa tun ajiya. Addu'a tayi tacigaba dayin azkar d'inta. Darana Aysha da besi sai Anty kubra da Anty Glory ne kawai ke warkajaminsu agidan, amma duk sauran 'yanmatan gidan wuni sukayi barci, (dare yazame musu rana, rana tazama darensu). *_Bayan sati biyu_*...........✍🏿 *hannuna zafi🙌🏻 aradu😿* *_I love you so much all my lovely Fan's_*😻😻😻😻😻 *~Team👉🏻 ya J! & Sholy!~*😂👌🏼 [8/7, 7:38 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) *_gaisuwa da fatan alkairi agareku dears_*😻 Miss Xoxo (tawan)😘 Ayusha muh'd Feedo 'yar ficika. Pharty Zarah. Sadeeya smart. Reefat yahaya. Aysha Umar Abubakar. Aysha Manshat. Bily s Fari. Mrs hameesu taura. *_bilyn Abdul namuku fatan alkairi, I love you so much my lovely friend's_* _inayinku, inasonku, ALLAH yabar mana zuminci_😍😍😍😘😻 1⃣8⃣ Ido kawai baffa yatsare ya khaleel dashi, yayinda shikuma yayi k'asa dakai k'irjimsa na dukan 100-100 saboda k'aryar daya sambad'ama baffan. Shimutumne kaifi d'aya, Wanda baisan 6oye-6oyeba amagana, kaitsaye yakeyinta kuma cikin tsantsar gaskiya. Amma yarasa miya shiga kansa awannan lokacin daya za6i yin k'aryar dankawai yasamu ku6ta da zancen auren da iyayen sanasa sukeson tasashi gaba akansa?, shifa harga ALLAH har yanzu baiga matar dazai kira kalarsabama, ballantana tadace da ra'ayinsa, shikuma bayason auren dabana soyayyaba, gudun sa6awa ubangijinsa wajen k'untata rayuwar yarinyar data Shiga tarkon aurensa........ Ta6ashin da baffah yayi yasakashi sauke ajiyar zuciya, amma har yanzu yakasa d'ago kai yadubi baffan saboda nauyin maganar data shiga a tsakaninsu, dukda bada fatar Baki yafad'aba arubuce yabama baffan. Canai katashi kaje mu'azzam. Jinjina kai yayi tareda mik'ewa, har yanzu kansa sinne, gudun karsu had'a ido da baffah. Harya fice daga falon baffah nabinsa dakallo, saida ya6acema ganinsa sannan yamaida Kansa ga takardar hannunsa da ya khaleel yabashi, shiru yay yana sake nazarin rubutun. Akuma lokacin aunty Mamie tashigo falon da sallama, kasancewar yau aikintane. Kuma tahad'u da ya khaleel d'in ahanyarta tashigowa 6angaren baffah. Baffansu miya farune wai?. Kansa yad'ago yana kallonta, yad'an muskuta domin bata gurin zama akusadashi kasancewar asaman 2setae yake zaune. Kofin dake hannunta tafara ajiyewa akan table d'in dake tsakkiyar falon, sannan tazauna kusada mijin nata. Ina saurarenka, abinda tafad'a kenan tana dubansa. d'anyatsansa d'aya yasa yana Sosa gefen bakinsa, ya ce, "humm wai maganar aure nasake yima mu'azzam, kasancewar naga Sultan & Mujahedeen sun tsaida Matan aure, to amma shine yabani wannan takardar. "Yay maganar yana bata takardar hannunsa". A'a baffansu fad'amin kawai abinda takardar tak'unsa, Dan mawuyacine nafahimci abinda aka rubuta, kasancewar ilimin nawa bamai zurfi baneba. Baice komaiba yafara mata bayani. _takardar tana k'unshene da bayanan likita akan wai mu'azzam d'in bashi da lafiyar dazai ajiye mata yanzu, Yakuma kai tsawon shekaru biyu da Sanin matsalar, kuma sun d'orashi akan magani dazaisha natsawon shekara biyar._ Kasa magana aunty tayi, shiru yaratsa falon, kowanne da irin tunanin dayakeyi tsakanin baffah da aunty Mamie. Zuwa can aunty Mamie tanisa, muryarta a sanyaye tace, "ALLAH to yabashi lafiya. Amma azumin mi yake yawanyi? Kuma basai alhamis da litininba?. Kallonta baffah yakeyi cike da nazarin maganarta, yace, " Bilkeesu Kodai Mu'azzam hanyar gujema aure yakeyi? Saboda wani Abu dayake aikatawa bamu saniba?. Lamarinsa yafara damuna, anya kuwa yaronnan baya Neman mata?, tsawonfa shekara 2 kenan INA fama dashi akan aure amma yana kawomin k'auli da ba'adi, ada tunani nake saboda aikinsane, amma yanzu nafara zarginsa da aikata wani Abu, shekarunsa sunkai yaso ajiye iyali dakansa, amma yaronnan sai yawo da hankali yakemin. Kullum Ammah nad'oramin laifin saka MASA idanu. Nayima mahaifiyarsa magana tanuna halin ko inkula dabatun. Kayi hak'uri baffansu, badamuwa yakamata kayiba ko fushi, mucigaba damasa addu'a koma wane hali yake Ciki, kuma Dan ALLAH kadaina zarginsa da aikata Neman mata, kawai nidai abinda nafahimta ga babana yakasa tsaida hankalinsa waje d'ayane yasamu matar aure. Kasandai miskilancinsa aii. Shiru baffah yayi yana nazarin maganar ta aunty Mamie da gaskatata. Yasauke ajiyar zuciya dafad'in to ALLAH ya k'yauta. Yacemin gobe idan ALLAH yakaimu zaije Indonesia. Eh Nima yafad'amin jiya, ALLAH yatsare dai yakaremanashi da sauran 'yan uwansa daga Sharrin rud'in zamani aduk Inda suka tsinci Kansu. To amin baffansu, zo6on tazuba MASA tabashi. Yakar6a yana murmushi da kashe mata idanu. Murmushinsu Na manya tayi tace, "kai baffansu kafa girma". Siririyar dariya yasaki yana rungumota dafad'in aini bana tsufa wajen my bilyna, kokin manta sunan namune? *(Bilyn Abdull)*🤣 Dariya tayi tana sinne kanta ajikinshi, hakane kuma mijina uban 'ya'yana, saidaifa naga wata harta kwaykwayemu🤕. Kai haba da gaske?. ALLAH kuwa, writer ce wai ita Bilyn Abdull. Barta dear na, aidai tasamu gwanjon mune ko?😉. Hakane kuma tafad'a tana k'ank'ame dattijon mijinta, Wanda har yanzu kwarjini da kamalarsa natare dashi, uwa uba k'yawu d'an asali, da dukkan yaransa suka gado agareshi. A6an garen ya khaleel kam yana cikin farincikin tsarinsa ya tsaru, danhaka yayta komansa cikin nishad'i awannan ranar. (Ni dariyama yaba ni masu karatu,😂 da girmansa yana gudun aure🤧). __________________________ Su Aysha 'yan turai, acikin sati biyunnan abubuwa dayawa sun faru, ciki kuwa harda fara fahimtar turanci da Aysha tayi, ga wani k'yawun data k'ara da haske, k'ibacedai kam tana nan yanda take, kasancewar batacin wani abincin kirki, Dan abincin k'asar baimataba. Meerah cema ked'an tausaya mata tasaya mata snacks, shine yazamo mata abincikam ayanzun. Kad'an-kad'an meerah ke shiga lamarin ayshar, dukda bawani zaman fira sukeyiba. Itama Aysha bata damu dayin hira da kowaba agidan, garama besi datakejinta kamar 'Yar uwa saboda zuwa dasukayi tare. Tunda Aysha tazo sau d'aya suka ta6a fita itada Anty glory da lola zuwa wani had'ad'd'en super market akaima Aysha siyayyar kayan sawa masu k'yau da tsada, dayake sunce taza6ane da kanta saitad'an za6i Na mutunci, wad'anda kodai yayane zasu suturta jikinta. Anty glo..... Kuma tak'ara za6ar mata wasu, wasukam Aysha tak'udiri aniyar bazata sakaba wlhy. 6angaren takalma ma da sauran tarkace duk anza6a ma Aysha, hardasu bra🤣, kasancewar irgar ayshar tatasa sosai, sunkuma Isa asaka musu bra, amma Aysha bata sakawa saidai best. Alokacin dasuke gwada sease d'in ayshar duksai kunya takamata, aiko Lola tadingama Aysha dariya........ Kasancewar Aysha Ce k'aramar cikinsu sai suketa bata kulawa, kowa k'aunar Aysha yakeyi dabata gata, babu maison ganinta acikin damuwa, musammanma Anty glo da meerah. Anty glo.... Jin Aysha take kamar 'yarda tahaifa, dan takai haihuwar kamarta d'in, saidai shashancin data saka Agaba yahanata nutsuwa tayi auren bare tahaifa. Itakam meerah tanajin Aysha awata tsokar jikinta, kasancewar yarensu d'aya addini d'aya, dukda ayshar batasan hakaba har yanzu, Dan wani lokacin d'abi'un meerh sukasha banban Dana cikakken bahaushe ko musulmi. Tanason sanin wani Abu dangane da meerah, amma tana tsoron Shiga hurumin Daba nataba, dukda Aysha takasance k'aramar yarinya tanada Nisan hankali da k'yak'yk'yawan tunani akan Abu. Yauma duk suna baje afalon gidan, Wanda sukaima kaca-kaca da abubuwa Na ciye-ciye Dana game. K'id'ane ketashi Wanda ya addabi kunnen Aysha. Queen da Lyn da happy nata tik'ar rawa abinsu hankali kwance, babu mai shigar arzik'i kuwa aciki, meerah da Serah nadaga gefe suna kallon wani Abu a waya, Lola kam bama agidan takwanaba yau itada besi, Dan tuni besi tafara zaman 'Yar gari, tanabinsu Lyn yawon darensu, shigar fidda tsiraici tagama kwarewa, wannan yasaka Aysha fara jada baya da ita. Knocking k'ofar akayi, k'ararrawa tayi k'ara, tajikin computer dake gefe Anty glory taga wanene. Woow! John agari yau tafad'a tana mik'ewa da dakatar da serah dake shirin zuwa tabud'e masa. Saurayine fari, zamu iya kiransa kai tsaye bature, badogo baneba, bakuma gajere baneba, hakama bashida k'iba, sanye yake da suit jajaye wad'anda suka fidda ainahin kalar fatarsa, gawani shegen aski irinna tantiran bariki, gefen idonsa Na haggu akwai zanen Tartu anyi hoton kada🐊awajen. Kasancewar suit d'insa mai gajeren hannune Tartu d'inma ya bayyana akan hannayensa, sai taunar cingom yakeyi, idonsa toshe da bak'in glass. Kallo d'aya Aysha tamasa takauda kanta, yayinda dukkan 'yanmatan suke zuwa d'ai-d'ai suna rungumeshi da gaidashi. Shikuma saiwani yatsine-yatsine yakeyi da shan k'amshi. Amma idanunsa nakafe akan Aysha dake sanye cikin wandon jins blue da farar riga mai layi layin bak'i, kanta dayasha wanki yana d'aure da siririn bak'in gyale. Ganin kallon kurullar dayake mata yasaka Aysha warware gyalen tayafoshi gaba yarufe mata matsashin k'irjinta dayake d'as ariga. Cikin tak'amarsa yatako har kujerar da Aysha take yazauna, zumbur Aysha tamik'e tana fad'i *_Allahu Akbar, ALLAHU a'azzu min khalk'ihi jami'a, ALLAHU a'azzu mimmaa akhaafu wa ahzaru, a'uzu bil laahil Lazii laa ala ardhi illaa bi 'iznihi, min abdika fulaanin, wa junuudihi wa atbaa'ihi wa ashyaa'ihi minal jinni wal insi. Allahumma kun lii jaaran min sharrihim, jalla sanaa'uka wa jallah jaaruka, wa tabaaraksmuka, walaa ilaaha gairuka’’._* _(ALLAH shine mafi girma. ALLAH shine mafi buwaya daga dukkanin halittarsa. ALLAH shine mafi buwaya daga abinda nakejin tsoronsa kuma nake shayinsa. Ina neman tsarin ALLAH, Wanda babu abin bautawa da gaskiya saishi, mai rik'e sammai daga su ruguzo a kan k'asa saida izininsa, daga sharrin wannan bawa naka, da rundunarsa, da mabiyansa, da k'ungiyoyinsa Na aljanu da mutane, ya ALLAH kazama mai tsari agareni daga sharrinsu. Yabonka ya girma, kuma kariyarka ta buwaya, kuma alherin sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba kai ba)._ Kowa afalon binta yayi da kallo, harda shi kansa John, dayaji wani irin fad'uwar gaba da kwarjinin da Aysha tamasa, dukda kasancewarta k'aramar yarinya wadda ayak'ini zaima iya haihuwar kamarta d'in. Meerah kam kauda kanta tayi gefe tana share hawaye da tausayin ayshar, dantasan yau babu makawa mugunnan john saiya maida Aysha cikinsu. Anty glory kanta jitai tsoron Aysha yashigeta da tausayinta, itace cikin basarwa takauda abinda yafaru dayima john magana cikin harshen Turanci tana dariya. Sorry john, karka damu batasan nufinkabane. Wani kallo yabi aunty glory dashi yana wani mar-mar da idanunsa k'anana, amma glory banbaku dama kuyi training d'intaba kafin inzo?. Shima cikin harshen nasara yake maganar. Takatseshi da fad'in bansan zakazo akusabane, tunda baka sanarminba, amma kak'ara mana lokaci kad'an. Iska yahuro daga bakinsa tareda crossing k'afarsa yace well saidai nayi abinda yakawoni koda ta k'arfine, Dan yarinyar tahad'a dukkan abinda nakeso ga mace. Kuma dollars nawa nasauke muku danna samu yanda nakeso. Kinsan banida d'aga k'afa akan abinda yamin, yaymaganar yana maida allonsa ga Aysha. Wadda tuni tashin hankali ya bayyana afuskarta saboda kamo zaren zancen datayi cikin basirar da ALLAH yabata. Da sauri tanifi d'akin meerah, shima yamik'e da Sauri yatake matabaya. Cusa kai meerah tayi afilo tareda sakin wani irin kuka..............🖊 *_munga ta kanmu🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀😭_* [8/7, 7:38 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) *_wanga page nakune 'yan group d'in Abba gana Na House of novels, inayinku kamar yanda kuke ataredani koda yaushe, masoyan asali kenan tun zamanin bilyn Abdull afarkon rubutu.😍😍😍😍😻_* 1⃣9⃣ Jikin Aysha har rawa yakeyi wajen dannama k'ofar key tana kuka dakiran sunan ALLAH, wata tsanar hajia babba da hajia kaltume da Na ratsata, cikin kuka tace, "gwaggo bintu kinci amanar zuminci, kinci amar ALLAH, kinci amanar maraici, ya ALLAH karka basu damar ketamin haddi, ya ubangijina badan niba badan halina katsareni daga sharrinsu, wayyo ALLAH na, ALLAH katsareni daga k'addarar zina, ina tawassali da sunayenka k'yawawa, dan alfarmar manzon nan namu mafi soyuwa agareka aduk cikin bayinaka, ya rabbi indai har dominka nakeson tsare kaina kakareni, bazayiba ya ALLAH.............. Duk maganganun da Aysha keyi akunnen John dasu Anty glory ne, babu maijinta Dan dukansu basajin hausar, garama aunty glory najin kad'an, itama zaman turai yasata mata abubuwa dayawa a hausar. Jin yanda take fidda kuka duksai tausayinta yakamasu. Harshi kansa john d'in, haka kawai yaji bazai iya mata doleba. Ahanakali yashiga Knocking k'ofar yana fad'in babie please bud'e k'ofar, bazan ta6a ta6akiba saida izininki, kibud'e zanyi magana dakene, bazan cutar dakeba. Duk cikin harshen turanci yake maganar, bakowane kalma ayshan ke fahimtaba, amma tafuskanci Inda zancensa yadosa, saidai zuciyarta bazata ta6a aminta dashiba, domin hakan bai cancanta dashiba. Tazame jikin k'ofar tazauna jagwaf tana kuma sakin kuka mai tsuma zuciya dakiran sunan mama da Umma, tak'arashe dafad'in ALLAH ka k'u6tar dani daga zalincinsu. Shiru duk sukayi suna saurarenta dukda basajinta. Meerah kuma tamaki tamotsa daga inda take zaune, tanacan sai zabga kuka takeyi da tausayin halin da Aysha Zata tsinci kanta ayau. Amma jin abinda yake faruwa saita d'ago kai tana kallonsu tsaye cirko-cirko ak'ofar d'akinta, wannan yatabbatar mata cewa Aysha tasamu damar kulle kanta. Batasan sanda tasaki sassanyar ajiyar zuciyaba, ahankali tace, ''Alhmdllh ya ubangijin talikai. Suduka suka bar jikin k'ofar, su happy sukadawo falon suka zauna, Anty glory da john kuma suka nufi d'akin Anty glory d'in, da'alama magana zasuyi. Bayan kamar mintuna talatin Anty glory tafito daga d'akinta, 'yanmatan takebi da kallo d'aya bayan d'aya, wannan ya tabbatar musu da john ya hak'ura da Aysha yana buk'atar d'aya acikinsune, kallon Anty glory yatsaya akan meerah, wannan yasa meerah tayi kivin-kicin da fuska, Dan damacan tatsani John, shine mutum nafarko daya fara keta mata haddi, kai gadukkan 'yanmatan ma, har wad'anda suka bar gidan ayanzun. Kamar Anty glory zatayi magana saikuma tayi shiru tamaida kallonta kan besi dasuka shigo ana rikicin Aysha. Besi oya tashi muje. Babu musu besi tatshi suka doshi d'akin Anty glory. Aysha kam k'in bud'e kanta tayi har kusan bayan awoyi 6, saida meerah Tamata magana da kanta, takuma tabbatar mata da john yabar gidanma tareda rantse mata sannan tabud'e d'akin.............. __________________________ Tun Bishirah nazuba idon ganin dawowar Aysha kusa harta fidda rai, Dan babu Aysha babu gwaggo bintu. Lamarin yafara damun bishirah hartama iya hama magana akan hakane. Itakamta iya hama lamarin yad'aure matakai, Dan gwaggo bintu bata ta6a tafiya Kano tadad'e hakaba. Randa su Aysha suka cika sati biyu da Barin k'asar gwaggo bintu tadawo gidan Alhaji Abdallah, saidai babu Aysha, tambayakam tashata harta fitar hakali, daidai da musleem kasa hak'uri yayi saida yatambayi gwaggo bintu, danshifa tun randa yaga Aysha yakamu Da son yarinyar, yakuma yima Kansa tanaji da kamu, Wanda baisan yayi (abanzaba), gabad'aya gwaggo bintu sotayi tarud'e lokacin dataji musleem yace tabasa address d'in gidansu Aysha a Kano, zaije dakansa yadawo da'ita, shida kud'insama zai sakata makarantar. Cikin in'ina da had'iyar mugun yawu tace um...um alhaji k'arami kabarmusu 'yarsu kawai, Nima saida sukaci muntuncina suka kwace abarsu, to...to aganina barar musu ita yafi komai alfanu da zaman lfy.... Yanda take zufa babu gaira babu dalili yasaka musleem tsura mata idanu. Shikansa ya khaleel dake kan dining yana lunch saida yad'ago ido yana kallonta, (kunsandai ma'aikaci, kuma irinsu ya khaleel da bincike yazamemusu jiki, koyaya rashin gaskiya yake tattare dakai saisun haskoka). Baiyi niyyar saka baki amaganar tasuba, amma yanda yaga gwaggo bintu nazufa dukda sanyin AC dake falon saiya kafeta da manyan idanunsa masu rikita Mara gaskiya. Cikin muryarnan tasa mai karsashi yace Maman yara kibasa mana, idanke sunmiki shibazasu masaba aii, idanma damatsala sai Anty mamie taje dakanta, dannaji itama tanada burin maida yarinyar school. Bak'aramin tsorone yabayyana ga gwaggo bintu ba, Dan hard'an guntun fitsari tasaki azanenta, tunda take da khaleel agidan basu ta6a magana mai tsawo kamar hakaba, saboda shi ba mutum bane maison yawan magana ballema hartayi tsawo atsakaninku, kumama bayashiga harkar kowa agidan, baya saka 'yan aikin gidan wani aiki, kome yakeso amasa saidai yafad'ama Anty Mamie ko momy susakasu su masa. Idonsa yakauda akanta, yamaida kan filet d'in albus d'insa, kusan mintuna 2 bai d'agoba, su gwaggo bintu ma duksunyi shiru daga ita har musleem dake murnar shigar ya khaleel azancen. Yakuma kafe gwaggo bintu da idanunsa, haka kawai yad'ora alamomin tambaya (??)akan matar, kauda idonsa yakumayi akanta yamaida kan musleem dashima yakafeta da idanu. Kai! Kabarta tunda tagaya maka reason nata, why not kahak'ura tunda bakasan sirrin families nataba. Kamar musleem zaifasa ihu yagyad'a kai, Dan tarbiyyarsuce bin maganar magana dasu. Ya khaleel baikuma cewa komaiba yacigaba dacin abincinsa hankali kwance. Kowa afalon yayi mamakin saka bakinsa dayayi amaganar, Dan sunsansa baya shiga abinda baidameshiba, haka yake tun yana yaro. Ammah dakecan gefe zaune tace dadai tabayard'in sai a kar6ota, Dan yarinyar tanada hankali, ni wlhy kamama takemin da fad'ima tunda nafara ganinta. Aunty Mamie tace, "Amman ashe bani kad'aiba Na hango kamarnan, wlhy tunranda Maman yara tazo da yarinyar naga kamarsu da Yaya fad'ima. Gwaggo bintu dai bata fahimci maganar tasuba, ita tama k'agara tabar falon. Muhseen yace, "wace fad'imar?". Matar babankuce, amma sun rabu tun bayan haihuwar iro da wata uku. Shiru kowa yayi Afalon, Amal dake kiyama su nuri aikin islamiyya tace nikam ina kwad'ayin ganinta wlhy. Ya khaleel daya kammala cin abincinsa yamik'e yabar falon batareda yasake tankawaba. Kowa da kallo kawai yabisa. _________________________ Rayuwa tanata shurawa, kowace rana akwai abinda zai faru, wani farinciki wani abin kuka, wani Na al'ajabi, wani Na mamaki. To zamu iyacewa zuwa yanzu Aysha tana cikin Na farincikin, saboda samun k'yak'yk'yawan labari datayi ga Anty glo....., kowa ya kalleta agidan yasan tana tareda farinciki. Ameerah dake kwance agadonta tana charts takai dubanta ga Aysha dake addu'a bayan ta idar da sallar dare data zame mata jiki akowacce rana. Jitai idonta yacika da kwallah, tashare da sauri saboda juyowar da Aysha tayi tana kallonta. Anty meerah wai yaudai babu inda zakuje kenan?. Murmushin yak'e meerah tayi, tatashi zaune tana tufk'e gashin dokin data k'arama kanta, my lil Sholy nicedai ban fitanba, amma su Queen aii tuni sun tsufa a club, yau hardama Anty glo.... Ido Aysha tad'an zaro, Anty meerah da gaske? Dama Anty glo..... Tana zuwa club itama?. Wata 'Yar dariya meerah tasaki, kai lil sholy kinda abin dariya, aii tafiyar tamu duk d'ayace da ita, nima abinda yahanani fita saboda kene, banason abarki ke d'aya agidan. Waima mi aunty glo.....tafad'a miki jiya danaga takiraki d'akinta?. Mik'ewa Aysha tayi daga inda tayi sallan, tacire hijjabinta, doguwar rigace ajikinta pink har k'asa, tayi masifar mata k'au da haska farar fatarta, gashi tad'an k'ara girma da murjewa saboda yanayin k'asar ya kar6eta. Prigh tanufa tad'akko robar ice-cream, Zama tayi abakin gadon, tareda bud'ewa tafara shan kayanta, itadai meerah tana binta da kallo. Anty meerah waikinsan mita fad'amin?. Saikin fad'a lilyna. Humm catayi wai mutumin ranar yace, "tamaidani school, yanzu haka sunkammala komai akan makarantar, zanfara zuwa, wai yanaso na iya turamci sosai. Waini Anty meerah waye shi agidannan?. Girgiza kai kawai meerah tayi cikin k'unar rai, tace, "Aysha bani Aron hankalinki nan nafad'a miki mikikazoyi *Cayman islands (UK)*. Aciki zakiji tarihina da k'addarar data kawoni nan, dukda dai dagabaya muka dawo wannan k'asar, da a India muke zaune. Idon Aysha kam akan meerah dake sharar kwallah, itama duksai ranta ya jagule. amma tana saurarenta. Meerah race........... Amin afuwa muhad'u page 20 danjin mi meerah zata sanarma ayshar ne🤔?????. ************************* Ya khaleel kam yaje k'asar Indonesia, inda yay kwanaki 9, dama aikine yakaishi, yabaro k'asar yanufi France inda Headquarter d'insu take, a birnin *Lyon*, nan d'inma yasamu kwanaki 12 yabaro yataho k'asar haihuwarsa Nigeria............🖊 *_Dan girman ALLAH kudaina cewa ina wuta d'innan kuna bina da fetur🙏🏻, karku fad'a abakin mala'iku surubuta🤕, gara kuma mahaifina addu'ar neman gafara, zaifi sakani cikin farinciki da yadda da k'aunarku gareni😭, shine zai nunamin jin dad'inku._* inayinku my Fan's👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻. _idan nasamu dama k'ila nak'ara anjima😂_ 😍😍😍😍😍😍😍😻 [8/7, 7:39 AM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) KUKAN KURCIYA.....👇🏻🤕 *_Shugaban kasa Buhari yayi jawabi mai ban tausayi da kuma sanyaya jikin duk mai hankali, jiya Al-hamis a Bauchi._* *_A ziyaran da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai birnin Bauchin Yakubu, shugaba Buhari yayi jawabai masu sosa rai dangane da makomar Kasar mu Nigeria da tsarin siyasar miyagun shugabanni 'yan jari hujja_*Shugaba Buhari yace: "Allah Ya sani bisa kokarin tunani na shine in tabbatar na dora Nigeria kan mizanin da zaku yi alfahari da ita nan gaba.* *_Akwai wahala cikin kawo sauyi a Kasa , amma muna jure shi iyakar iyawar mu, ko makiya sun tabbatar mun dauki saiti kan makomar Kasar mu Nigeria, amma 'yan jari-hujja munyi musu laifin da bazasu yafe_*mana ba, laifin shine rufe musu kofofin sata, su ba damuwar su bane Nigeria ta kone ta babbake su sayar da tokan ta su gudu*, *Sun sako mu a gaba yanzu da dukkan karfin su suna bukatar a kyale su su wargaza 'dan abinda muka fara gyarawa.* *_Basa fatan alheri ko miskala-zarratin wa Nigeria da al'ummar ta_* *_Babu wani zabi gare mu, zabi yana gare ku al'ummar Nigeria, idan kun gaskata kokarin mu ku sake zaban mu mu dora daga inda muka tsaya, hakan zai zama alheri gare ku, idan kuma kun karyata mu ku_* *koma gare su ('Yan jari hujja) su lalata makomar ku da Kasar ku.* *_Amma tabbas wata rana zaku tuna na fada muku gaskiya, kuma na dora ku akan gaskiya, kuma na rike ku da gaskiya, zabi naku ne, kan makomar Kasar ku ba batun siyasa ce a raina ba wallahi face makomar ku nan gaba.."_* Jawabin shugaban Kasa MuhammaduBuhari Hafizahullah kenan. Alherin Allah Ya kai ga shugaba Buhari Allah Ka tsare manashi daga dukkan sharri Allah Ka daukaka darajar sa duniya da lahira Allah Ka bashi dukkan nasarar da yake nema Allah Ka zama jagoran sa. Bilyn Abdull *_idan kagane ba buhari zakaimawaba, kanka zaka taimaka da yankinka, harma da addininka, Idan har mai hankali zai nutsu to zaigane 'yan arewane keta wannan haukan , saboda son mulki da hanyar Neman yin wawaso akan dukiyarmu kamar yanda suka saba abaya_* _Wlhy 'yan arewa mu farka, domin kauda mak'iyanmu, wad'anda shekaru aru-aru basu kawo mana sauyi a arewarmuba, kuma wlhy yanzuma yaudararmu sukeyi bazasu gyaraba, shiyyasa suka KASA had'a hannu damai kishinmu sudawo da martabar Yankin mu, burunsu kawai kud'unmu, da mulkarmu_. _mubar siyasar shirme, mukoma ta cancanta kamar yanda kudancin k'asarmu keyi😭👈🏻_ 2⃣0⃣ Sunana na yanka Halematussa'adiyya, kasancewar sunan kakata naci iyayena ke kirana Ameerah. Ni 'Yar asalin garin sokoto ce, amma yanzu muna zaune da iyayena a Kaduna, nima a Kaduna aka haifeni, mahaifina mutumin kirkine, yanada k'ok'ari wajen kare mana mutunci dukda bamai kud'i baneba. Ga mahaifiyata kam Sam bahaka baneba, macece mai son birga da son mu'a mullah da hajiyoyin birni. Mu 5 iyayenmu suka haifa, nice d'iya ta uku acikinmu, yayyena biyu Suwaiba da 'Daheera duk halin mama suka biyo, kuma suna bin hud'ubarta daki-daki, wannan yasa suka tashi a fand'are, abin nadamun mahaifinmu, amma bashida damar tankawa. Awajena kawai yake samun sauk'i da sassauci, Dan bana k'etare zancensa, ahaka muka kammala secondary, yayinda nikad'aice nayi sauka acikinsu. Mahaifinmu yakiramu tareda sanar damu mu fido mijin aure, yabamu watanni uku rak. Nad'an shiga damuwa, saboda bana kula kowa, amma inada samari masu sona, ahaka nafidda Aminullah acikinsu, yayindasu Anty 'Daheera baba nata fama dasu, saida ya tsoratar dasu akan zai saki mama sannan suka kawo mazajen aure. Ansaka mana biki wata 11 saboda baba yasamu kammala yimana kayan d'aki. Bikinmu yarage saura wattani hud'u ALLAH yayma baba rasuwa, sakamakon had'arin mota daga Kano zuwa Kaduna. Mutuwar baba tata6ani matuk'a kuma najigatu nida sauran k'annena biyu baza. Amma gasu mama da su Anty Suwaiba bahaka bane, domin sufa duniya sabuwa fill, ko arba'in d'in rasuwar baba ba'ayiba mama ta aika gidan samarinmu cewar tafasa aurar damu. Dan acewarta bamu gama morar kanmuba bazamuje muyita bautawa k'artan banzaba, nashiga tashin hankali Aysha, Dan alokacin auren kawai nake buk'ata kasancewata mace mai yawan sha'awa. Rashin mafita yasakani dagewa dayawan azumi domin kame kaina daga halaka. Humm awata ranar laraba nadawo daga islamiyya agajiye saboda inazuwa hadda alokacin, saina tararda su mama sunbaje kud'i afalo suna irga, kud'ine masu shegen yawa, tsoron kud'in yasakani zaro ido waje da tambayar ina suka samu?. Mamace cikin hasala tace satowa mukayi Dan ubanki. Shiru nayi, jiki a sanyaye nashige d'aki domin cire uniform d'ina. Damuwar ganin kud'innan tahaifarmin dayawan kuka, na tabbata bata k'yak'yk'yawar hanya su mama suka samu kud'inba, to amma tambayata itace a ina suka samun?. Bansaniba, wannan yasaka nasama zuciyata salama, sati biyu da kawo kud'inan akafara gyaran gidanmu, gyara kuma namasu kud'i ahannu, aikam kamar jira 'yan anguwa keyi akafara surutu mahaifiyarmu tasakamu karuwanci, dama shiyyasa ta lalata aurenmu. Maganarnan tana k'onamin rai, amma banida amsar gamsar da jama'a, Dan nima bansan tushen kud'inba. Hummm inafad'a miki Aysha ranar saiga wata hamshak'iyar hajiya tazo gidanmu, dakaga matar nan kasan kud'i sungama zaunawa agareta, sunyi maganganunsu da mama, daga k'arshe aka kirani, wai matar nan tad'auki nauyin karatuna zuwa turai, tunda takarduna sunyi k'yau. ALLAH sairki rashin Sani, sainaita tsallen murna, Dan aganina zanbar gidanmu da abubuwan bak'inciki suka tare aciki. Cikin k'ank'anin lokaci aka gama mana komai, muka cane k'asar India. Wannan tafiya itace tazamarmin tushen nadama da Dana Sani. Itace ta wargatsa rayuwata daduk wani tanadina, itace ta zama hajijiya dake wajiga zaren rayuwata ayanzu, tayi maganar tana kuka maicin zuciya. Aysha ma natayata. Tacigaba dafad'in munsauka k'asar india, hajia Fanta Ce takawo mu, intak'aicemiki dai bantashi nadama ba, saida john yaketa haddina adaren Dana kwana 2 dashigowata k'asar India, saida suka shayar dani kayan maye a drink sannan yayi yanda yaso dani, nayi kuka nakuma yi bak'inciki. Ashe ba makaranta zanyiba, kawoni akayi nayi karuwanci kawai, ankawonine domin cin amanar ubangijina. Abubuwa sun kwa6emin Aysha babu mai lallashina ko tausaya min, tun ina d'ari-d'ari da harkar har zuciyata takarye saboda bak'incikin mahaifiyata nafad'a tsundum, na tabbata tasan komai amma tabadani aka taho dani wata k'asar, Aysha mahaifiyata fa, wadda duk duniya tafi kowa sanin zafina, kaico da hali irin nami Mamana. Meerah tafashe da kula. Aysha bata hanataba, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru. Meerah tace, ayshan shed'anci da shagala yasakani daina sallah, nadaina azumi, na daina karatun alkur ani, dukna maye gurbin wad'annan da shaye-shaye, kwana a club, wlhy Aysha har blue film anta6ayi dani. Bak'aramar zabura Aysha tayi da jin furucin meerah ba. Cikin tsoro tace, ''Anty meerah da gaske?. Murmushi mai ciwo meerah tayi, tacije le6enta nakasa, tareda fad'in humm Aysha kedai abar kaza cikin gashinta kawai, ni k'arancin tunanina nayi hakane dundan aita d'orama mahaifiyata zunubi, tunda itace silar komai. Girgiza kai Aysha tashigayi, cikin kula tace, "Anty meerah kinyi kuskure, ba'a gyara 6arna da 6arna, kinyi sakaci dakika bar ALLAH, Barin sallah shine mak'asudin ruguza dukkan rayuwarki, barin azumi da karatun alkur'ani sune dalilin haddasuwa k'unci ya yawaita aduniyarki. Dakinsani kin kar6i k'addararki tafarko saboda fyad'e aka miki, bacikin hankalinki kika aikataba, kifa Sani yanzu ba mama kad'ai ake rubutama zunubiba hardake kanki, tawani fanninma kinfita wlhy. Anty meerah kituba tunda lokaci bai k'ure mikiba, ki gyara mu'amullarki da ALLAH tunkan yakamaki da azabarsa, kiyi gaggawar farkawa daga nannauyan barcinki tunkan mutuwa tazo ta d'aukeki, wlhy kikabar duniya ahaka wuta zakije, saboda kindaina sallah, kindaina azumi, kindaina karatun alkur'ani zancen ALLAH, Anty meerah banbancin kafiri da musulmifa sallah, duk Wanda yabar sallah yayi asarar daza'a shekara dubu anamasa jaje. Please Anty meerah😭😭😭😭😭 kicanja, kinada sauran lokaci, karki bari yawuce abanza agareki Dan Alfarmar mazonmu. Itakanta meerah kuka takeyi kamar zata shid'e, suka rungume juna itada Aysha suna kuka mai cin rai da zuciya, saida sukayi mai isarsu sannan Aysha tafara bana meerah NATA labarin..... Sosai meerah ta girgiza da labarin Aysha, cikin raunin murya tace, "Aysha sun yaudareki keda iyayenki, babu wani karatu dasuka kawoki ko kula damai ciki, sunkawokine kiyi karuwanci, danki samamusu kud'i. Nasan hajia kaltume sosai, itama dila ce ta safarar yara, hajia babba cedai gasky ban saniba, inaga sune dillalan zaune masu samo yara subayar, wad'an nan sunfi kowa samun kud'i, Dan inhar suka samo yarinyar za'a d'auki hotonta aturama su hajia fanta, sai sukuma suturama wad'anda ake kaima yaran k'asa-k'asa irinsu Anty Glory kenan, sumafa zasu saka hoton yaranne akasuwa, idan ansamu Wanda yataya to zai biya mak'udan kud'i, hardana jirgi da duk wani cuku-cuku daza'ayi kafin kisamu nasarar baro k'asarki, kinsandai Yanda yankinmu na Africa yagama lalacewa da cin hanci da rashawa, su sunsan hanyar dazasubi abaro k'asar dake, ak'asashen turai kuwa kowaccenmu da abinda yakawota ake sakawa, wasu karatu, wasukuma abubuwane daban-daban, amma mafi yawanmu karatune. Wannan millions kud'in dasuka tura shine za'aita rabawa tundaga kan iyayenki, dillaliyar data samoki, dakuma wadda zata fiddoki k'asar. So wani yabiyane kizauna dashi natsawon shekaru biyu ko d'aya, harma uku, wasu kuma sau ma 1 kacal, karki d'auka wai 'yan Nigeria kawai ake kawowa, a'a 'yan k'asashen Africa ne daban-daban. Wannan shegen john d'in dakike gani, duk yarinyar da'aka kawo shike fara amfani da ita, inhar wajen Anty glory aka kawota, idan yay amfani dake saiya had'aki dawani kuma, dagananfa ke harka tabud'e miki, zakije kiyi harkokinkima kisamu kud'inki kisa ajaka. Aysha nayadda babu abinda yakai addu'a daraja da kariya, lallai addu'a da maida lamarinki ga ALLAH ya d'oraki akan azzauman nan har suka yanke shawarar kaiki makaranta, Queen tacemin tanada shekaru 13 aka kawota amma wannan baihana john kaca-kaca da itaba, dukdama su yawancinsu dasaninsu sukazo. Amma kinga ke aranar saiya hak'ura yabarki, wlhy john tantirine dakike ganinsa, kariyar ALLAH ce kawai tahana ya6alle k'ofar yayi yanda yaso dake. Kicigaba da godema ALLAH. Sannan kada kisa wasa akaratun dazasu sakani kiyi, kitsaya kiyi domin zai amfanemu. Insha ALLAH zan ku6tar dake dakud'in Dana tara, kedai kisaka himma, kicigaba da kare mutuncinki, karki biyema k'awaye dansuma suna taka rawar gani wajen wargaza tarbiyya, ballan tanama anan turai da 'ya'yamsu suke 'ya'yan ido, tunda komai kayi su awajensu 'yancine. Godiya sosai Aysha taitayima meerah, suka rungume juna sunajinsu tamkar jini d'aya, uwa d'aya uba d'aya. Aysha tace Anty meerah to kema Dan ALLAH ki canja, kituba ki daidaita rayuwarki, kibar shaye-shaye daduk wani Abu mara k'yau, kikoma tamkar yanda kike adad'inki, Ameerah maison Addini da tsoron ALLAH. cikin murmushi ameerah tace namiki alk'awari zan canja Aysha, zan koma yanda kike buk'ata, zan koma Ameerah ta tagari, dagayau namiki alk'awari bazan sake shan wani abin mayeba, bazan sake aikata zinah ba, da duk wani abinda yasa6ama ubangina, zancigaba dayin istigifari domin ubangiji mai yawan gafarane, zanyi tuba irin Wanda ALLAH keso. Tsalle Aysha tadoka tad'are meerah tana murna. Oh my lili I Love you, kinzamemin alkairi aduniyata, inaji ajikina ALLAH ya turokine domin ki canjani, ALLAH yakareminke, ya ALLAH kada kabasu damar cin galabar wannan marainiyar yarinyar dabatasan komaiba gameda rayuwa har yanzun. Daga nan meerah takuma sabuwar kalmar shahadah, acewarta (da karta tazama cikin kokwanto gamma tayi komai yanda hankalinta zai kwanta), harda wankan shiga musulinci tayi, tad'auro alwala tafito, dukwani abinda yasa6ama shari'a dake ajikinta tacireshi, kama daga gashi farce da sauransu. Jinta takeyi sakayau, takoma wata halitta daban, saida Aysha takuma tunamata wasu abubuwa dayawan sannan sukayi sallar asubahi tare, Dan yaukam kwanan zaune sukayi.😃 Bayan sunyi karatun alkur'ani Wanda kowaccensu ALLAH yabata baiwar ajiyarsa a kwakwalwarta, sukayi azkar suka kwanta, Dan har sannan su Serah basu dawo gidanba, hakan yana nuna ansha shagali jiya a club............ ___________________________ Gaba d'aya hankalin gwaggo bintu atashe yake, tasan wanene khaleel, tasan aikinsa da bin kwankwanto akan Abu, bak'aramar razanata kallonsa yayiba, tana tsoron abinda zaije yadawo. Ganin batada mafita tanufi 6angaren hajia babba, dawowarta kenan daga aiki. Dafarko hajia babba tayi nufin korar gwaggo bintu, amma ganinta abirkice yasa ta saurareta. Itama hankalinta yatashi, tasan halin d'an nata sarai. Cikin matuk'ar damuwa tace, bintu dolene kibar gidannan awannan ga6ar. Idanu gwaggo bintu tazaro waje, hajia babba ki tausayamin, banida inda yafi nan wlhy. No, kwantar da hankalinki, bawai zaki koma Kano baneba, Lagos zaki tafi gidan zuwairah, kizauna nawani lokaci kafin abubuwa su daidaita, wannan shine kawai kwanciyar hankalinki. Tana gama fad'ar haka tanuna mata k'ofa alamar tatafi. Tamkar gwaggo bintu zata fasa kuka haka tabar 6angaren...........🖊 *_nace hum gwaggo bintu!, dukfa d'an daya hana uwarsa barci, wlhy shima bazaiyiba👈🏻☹_* Masoyan gwaggo bintu amin afuwa🤣 *_Barka da dare my Fan's😍😍😍😍😍😘😘😘😘_* [8/7, 9:24 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) *_Nagode sosai da addu'arku ga mahaifina, ALLAH ya gafarta dukkun musulmai baki d'aya, kuna sakani farinciki wlhy masoyana, ngd, inayinku sosai-sosai._* I love you k'atin-k'atin😍😍😍😻😻😻😘😂 2⃣1⃣ *_Kano_* Alhmadulillh su mama sun fita takaba tuni, suna zamansu lafiya da k'yautatama juna kamar yanda suka saba. Matar uncle Ahmad tahaihu suketa shirin zuwa Jigawa suna. Kawu bilyamin dakansa yabada mota akaisu harda iyalansa. Sun isa Jigawa lafiya ansha suna kuma lfy, da yamma mama tashirya danufin zuwa wani gida gaida abokan arzik'i data sani. Itadasu Rufaida suka tafi da sadiya. Tun'a k'ofar gidan sukaci karo da zuk'ek'iyar mota bak'a wulik, su Rufaida sunata santin motar, mamadai batace dasu komaiba, sai murmushi datakeyi. Gidane madaidaici mai d'akuna uku, babu kowa a tsakar gidan, amma a share yake tas, saida sukayi sallama sau kusan uku sannan aka amsa, wata dattijuwar tsohuwa tafito tana kuyi hak'uri inata amsawa, karar TV tahana kuji...... Maganarta takatse saboda ganin su mama, kai wanake gani kamar fad'ima haka?. 'Yar dariya mama tayi, tace, "wlhy kuwa inna mune mukazo garin, shine nace bara Nazo Na gaidaku andad'e ba'a had'uba. Aikuwadai wlhy, 'yanmata kushigo kunji. Rufaida da Safiya suka shiga gaba, mama nabinsu abaya. Falone irinna tsoffi, amma komai atsare, sai 'yanmata biyu dake zaune, kowa da 'abinda takeyi. Bayan sun gaisa inna tace haba fad'ima shikenan kuma anyanke zuminci shekara kusan ashirin?. Kuyi hak'uri inna, nayi laifikam amma amin afuwa, insha ALLAHU za'a canja. To ALLAH yayi albarka, wad'annan jikokinane ko?. Dariya mama tad'anyi, kanta ak'asa tace eh inna amma nawajen abokiyar zamatane. ALLAH sarki, masha ALLAH, amma fad'ima kardai had yanzu Baki haihuba?. A'a inna akwai uku. ALLAH Sarki, ALLAH ya albarkacesu. Ta kalli 'yanmatan nan biyu datum d'azu suke satar kallon mama Dan tamusu kama dawata dasukanta6a Sani. Tasleem tashi kuhad'o abinci mana ga mamanku wadda Baku saniba. To inna, tasleem da maleeka suka fad'a suna mik'ewa. Mama tabisu da kallo tana murmushi, inna wad'annanfa nawajen waye?. Fad'ima 'ya'yankine aii, 'Yar farar tawajen bilki Ce, d'ayar kuma d'iyar amaryarsuce, tare suke da Ibraheem da babansu. Ikon ALLAH, yanzu yaran Bilkeesu nawa?. Wai aii bilki anzama kaza uwar 'ya'ya, aibayan bariwarki gidannan haihuwarta 12, saidai d'aya yarasu kusan wattani goma kenan. Lallai Bilkeesu ALLAH yaraya manasu to... Ameen dai fad'ima, yanzu kuwa kuna inane dazama?. Inna INA nan cikin Kano, amma ALLAH yayima maigidanma rasuwa kusan wattani Biyar kenan. Sallallami inna tafara dafad'in oh ni Dije ALLAH yajik'an musulmai........ Shigowar mutanen biyu yasaka su Rufaida gaishesu. Muryar Wanda mama taji yasakata kid'ima tad'ago ido da sauri. Kallon ido cikin ido sukaima juna, ita tafara janye nata ido tayi k'asa dakai. Inna tace Abdillahi kundawo?. Jikinsa a sanyaye yace, ''eh inna mundawo. Matashin saurayi yace, "lallaima tsohuwarnan, nibazakice nadawoba ko?. Dariya inna tamasa yo Ibraheem kakoma mana, aidai bakaine Malam irona Na gaskiyaba ko? Aini tunda k'akiyin aure munraba jaha. Aikam saidai muraba harma k'asa kuwa. Dariya akad'anyi. Mama tagaida dattijon mutumin, ya amsa mata cikin kafeta da idanu, itakuma tak'i kallonsa. Shi ya khaleel ma sai yanzu yalura dasu mama, gaisheda mama yayi yanason tuno ina yasan wannan fuskar?. Su maleeka suka shigo da kulolin abinci. Mama tayi k'arfin halin fad'in wai Babane yagirma haka?. Kwarai kuwa fad'ima shine, Ashe zaki ganeshi?, gashinan d'an kwal uban yak'i aure. Kai Dan gidanku mamarkace wannan. Ya khaleel yashafa kansa, cikin murmushi yace, " inna aiban santaba kuma." Katanbayi Abdillahi aishi yasan kowacece. Juyawa yayi yana kallon Baffah datuni tsohon tsumi yamotsa masa, sai satar kallon mama yakeyi. Baffah fad'amin to. Dak'k'uwa Baffa yawatsa masa, yana fad'in ungo wannan Dan k'aniyarka. Dariya sukad'anyi. Su Rufaida kam dukda kasancewarsu yara tuni ya khaleel yatafi da imaninsu. Yau sanye yake cikin shadda marun, wando dariga d'inkin zamani, rigar iyakarta cinyarsa, ya d'ora hulla zanna Bukar datai mugun fito da ainahin suffarsa ta Hausawa, sai k'amshi yake tashi ajikinsa mai sanyin dad'i. And'an ta6a hira wadda mama da baffa suka kasa sakewa, kowa da abinda yake sak'ama ransa. Ya khaleel madai baya cikin hirar, Dan tuni Yakoma can gefe saman wata kujera yazauna yanata danne-danne awayarsa, lokaci-lokaci yakan amsa calls da ake masa. Su mama sukamik'e domin tafiya. Inna tace, 'Dan ALLAH fad'ima kidinga waygowa yanzun, kuma insha ALLAH zamuzo bikin Fadeelah, Agaida yaran Dan da abokiyar zaman, ALLAH yak'ara hak'uri kinji. Amin inna mungode, ALLAH yak'ara lafiya. Su maleeka suka mik'e danyin rakiyarsu, Dan tuni har sabo yashiga tsakaninsu dasu Sadiya. Baffa yakira Tasleem yabata Rafa's d'in kud'i yace tabasu suhau mota, shima ya khaleel yakira yay dad'i akai. Inna dama fad'ima nazuwa gidannan?. A'a wlhy, rabona da ita tunda kuka rabu, nima nayi mamakin ganinta, Ashe k'anin mijintane yake anan, matarsa ta haihu shine sukazo suna, 'Yar albarka bata mantamuba tazo gaishemu. Jinjina kai kawai baffa yayi, batareda yace komaiba. Ya khaleel daya dawo falon yace, "wai Dan ALLAH inna wacece ita?". Matar babankuce dasuka rabu bayan haihuwarka da wattani uku, yarinya mai hankali dasanin darajar mutane, kagadai ni amatsayin uwar kishiya nake gunta, amma wlhy tamkar mahaifiyarta tad'aukeni, (inna mahaifiyar aunty Mamie Ce masu karatu). Shiru ya khaleel yayi, danshikam k'yaunar matar tashigeshi sosai. Inna tace, ''kajima mijin nata yarasu wattanni 5 dasuka wuce. Da Sauri baffa ya kalli inna, suna had'a ido yay k'asa da kansa. Murmushinsu Na manya inna tayi, danta gano wani Abu ga Baffan....... To komiye masu karatu?.😂 _____________________________ Waini meerah kindaina zuwa club ne? naga 2days saikice kinajin barci, kodai kinyi fad'a da babyn kine?. Murmushi meerah dakema Aysha kitson makaranta tayi kawai, amma batace komaiba. Lyn ta ta6e baki tana hararar meerar, o miskilancin yamotsane? Kokuma kinsha abinda yafi k'arfin kankine?. Eh, meerah tafad'a batareda takalli inda Lyn takeba. Itama saitaja bakinta tayi shiru, dantasan sarai meerah tafita buyagin rashin mutunci. Aysha najinsu, saidai tanata danne danne awayar meerah abinta. Washe gari akakai Aysha wata had'ad'd'iyar makaranta dake nan bayansu, komai nad'an gata aka matashi, saita saje da 'ya'yan turawan kasancewarta fara tas, kuma k'yak'yk'yawa, kawai dai duk inda bak'i yashiga acikin turawa dolene ka shaidashi saboda yanayin halittarmu datasu akwai banbance-banbance. Amma badan hakaba saika rantse cikin tsatsonsu tafito. Taji nasihar meerah sosai, wannan yasakata maida hankali akan abinda yakaita, dukda haka tayi k'awa maisuna *Arena* itama baturiyace 'Yar asalin k'asar, amma tanada yanayin sanyi kamar Na Aysha, tasu tazo d'aya kam da Aysha sosai, kuma itace ke k'ok'arin k'ara fahimtar da Aysha abinda bata saniba, kasancewar har yanzu tanada sauran rashin gane turancin. ____________________________ Gwaggo bintu tuni tahad'a inata inata tacane Lagos, tatafine akan zata zauna da aunty zuwairah saboda cikin datake dashi, sudai su aunty Mamie sunyi matuk'ar mamaki, danba yau Anty zuwairah tafara cikiba, kuma wani baita6a zuwa ya zauna mataba sai awanan Karon, alhalin wannanma itace haihuwa ta hud'u dazatayi. Tunda gwaggo bintu tasauka gidan Anty zuwairah bataga wata fiskar rahamaba agareta, babu wata tarbar mutunci data samu, ballatana kallon arzik'i. d'akin masu aikin gidan aka kaita. Aikam bak'in ciki tamkar yakarta🤣. ______________________________ Tunda baffa sukadawo daga Jigawa yakasa sukuni, duk-yar zama wani kala dashi, har yanzu yana k'aunar fad'ima, Dan itace first love nasa, auren had'i akamasa da hajia babba, amma fad'ima za6inshice, akanta yafarason wata 'ya mace aduniya, shiyyasa yakan jita daban acikin mata, tundaga randa yafara ganin Aysha tatuno masa da Fad'imarsa, saboda wata muguwar kama dayaga yarinyar nayi da ita, baikawo komai aransaba alokacin, amma tabbas tundaga lokacin yaji yana begen son ganin fad'ima, saidai basan ina zai dosaba wajen sansanin indama take, gashi iyayenta duksun rasu tuni. Yaduk'ufa da addu'a tun'a lokacin, saigashi ALLAH ya kar6a masa, harda albishir mafisaka farinciki, shine fad'ima batada auren kowa akanta yanzu, harma ta kammala ida, Abu mafi damunsa kuma, halin ko'in kula da fad'ima tanuna akanshi dasuka had'u a Jigawa, 'ya'yansa kawai tasakarma fuska, saikuma matarsa bilkisu dataita tanbayar labarinta, amma shi yitayi kamarma bata sanshiba, yacije le6ensa tareda juya kwanciyarsa, gaba d'aya yarasa walwalarsa. Umme amarya dake gefensa kwance duktana lura dashi, kasa hak'uri tayi, tace, "waini alhaji lfy kuwa?". Murmushin k'arfin hali kawai yasakar mata, muryarsa a sanyaye yace, ''babu komai Saudah, kawai kainane yake ciwo". Ayya todakasha magani. A'a barshi kawai, kedai yi barcinki, kinga gobe idan ALLAH yakaimu kinada aiki. Shiru tamasa, kasancewarta mace mai halin ko inkula akan abinda bai shafetaba, amma amatsayinta Na lauya ta tabbatar yanada damuwa, bayason fad'a matane kawai. To itama batadamu dasonjiba. Kowa yaji da matsalarsa kawai. Shikam yak'i sanarmatane saboda gudun rigima, yatabbata kaf matan NASA Bilkeesu Ce kawai zai Tara da zancen azauna lfya, danhaka zaiyi hak'uri har ranar aikinta tazo, Dan gobema hajia babba Ce dashi. Anty Mamie kam tun randa sukadawo daga Jigawa su Tasleem sukabata labarin komai, kuma mahaifiyartama tasanar da ita komai awaya, tayi farinciki matuk'a, kuma tana addu'ar ALLAH ya tabbatar baffah yace zai dawo da Yaya Fad'ima gidansa, zatafi kowa farinciki, dantana k'aunar matar, bata ta6a mata kallon kishiyaba saidai 'Yar uwarta. Tayi gum dabakintane Dan taga iya gudun ruwan baffan, tafiso yafad'a mata da kansa kamar yanda inna tace taja bakinta ta tsuke............🖊 *_tofa masu karatu, wannan cakwakiya dayawa take, daga wannan sai wannan, kucigaba dabin d'iyar Malam danjin yanda abubuwa zasuyita warwarar zare._*😉😅✌🏻 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😁 [8/8, 8:05 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _Wannan page nakune 'yan Group d'in *FIDDAUSI SODANGI* & *NICE & CUL HAUSA NOVELS* I love you so much my Darlings Fan's, inayinku, ina sonku, kamar yanda kuke sona._ 😍😍😍😍😍😻😘😂 2⃣2⃣ Nikam momy miyasa zaki turomin matarnan?, nifa bancemiki ina buk'atar 'yan aikiba, nawa sun isheni. to naji, amma kimin alfarmar barinta tazauna anan zuwa wani d'an lokaci, nima bacanayi tazauna ananba aii. Shikenan momy, ammafa wlhy aikin zanke sata, danbazata zauna min saidai taci ta kwantaba. Bakida matsalar wanan, kisakata komiyema, itama aii 'Yar aikince, shikuma d'an aiki babu wani banbanci tsakanin babba da k'arami, duk'a mizani d'aya suke. To waini momy miyasama kikace tabar nan Abuja?. Wannan sirrinane kam zuwairah. Hummm momy kenan, kekomai da anta6aki saikice sirrinkine, ninarasa wanne sirrine haka?. Ina khaleel? Koyabar k'asar?. Yana nan, bakwa wayane?. Gaskiya kwana biyu bamu gaisaba, kinsandai halinsa da shegen shariyar tsiya, saidai kai kagaji kakirashi, amma hakanan dai bazaka ta6a ganin kiransaba. Saikuta hak'uri dashi, idan yay aure k'ila matar ta canjashi, sai anjima, agaida yaran. Yauwa kayan dakika turo hajia maryama tad'auki Na 2million's, sai hajia Fanta ma tad'auki Na 1.5million. OK momy, Dan ALLAH kimatsa musu wannan karon suhad'amin kud'ina dawuri, Dan dadyn Najwa yace, "nanda sati biyu zaije Germany, inaso nabashi yamin Oder d'in wasu kaya. To babu damuwa, kikira Khursum kuyi maganafa. Zankirata momy, agaidamin 2wins da mufeeda, shima khaleel ace ina fushi wlhy. Dariya momy tayi ta yanke wayar tana fad'in dukzan fad'a to. Ajiye wayar babu dad'ewa ya khaleel yashigo falon da sallama, sanye yake da wando ja iya guywa, sai bak'ar riga mai gajeren hannu, hannunsa d'aukeda system da wayoyinsa. Harya zauna momy nabinsa da kallo, yace, " wash ALLAH nagaji momy". Baki momy tata6e, Ibraheem ainazata kamanta danima agidan?. 😳ido yazaro waje, momy mantawafa?, ni khaleelu jikan Rufa'ee da Mujeetafa, na Isa manta uwata duniyata. Yay maganar yana tasowa daga inda yake, yadawo kusada momy yazauna. A shagwa6e yakamo hannunta tareda kwantar da Kansa saman kafad'arta, haba momy dabakinki kike fad'ar Na manta dake?, to ashema Ibraheem zai manta da kansa kawai sanyin idaniyata?. Da irin wad'annan kalaman yakan tausasa zafin momy aduk lokacin datau hayak'i akansa, tuni kuwa yayi tasirin sanyaya zucyarta, cikin mirmushi takai hannu tashafa fuskarsa. To yarona kaid'inne wani lokacin saina rasa kanka, dama nasan wasu abubuwan bayinkanka baneba, anjuyarmin dakaine kawai. Murmushi ya khaleel yayi kawai, yasan momy bazata ta6a canjawaba kam, yad'ago hannunta nadama dake rik'e a hannunsa Wanda yasha Jan lalle da manyan zobuna Na zeenari har uku ya sumbata, cikin shagwa6a yace, "karki damu my first love d'ina, bazasu ta6a rabani dakeba, Dan kekad'aice mai Ibraheem khaleel duk duniya, ko baffah saidai yabiyo sahu.😅 Bak'aramin farinciki kalam d'an NATA suka sakataba, Dan haka tace, " ALLAH yamaka albarka Ibraheem, kai d'ane ain alfaharin kowacce uwa, ALLAH yacigaba da tsareminkai kaji. Amin mamyna. Yanzudai yunwa nakeji, mizaki bani naci?. Mikakeson ci to?. Komike akwai zanci momy, sonake nad'anyi wani aiki. OK tom bara Nagano mike a kichin d'in?. To momyna, amma naji shiru, inasu Mufeeda?. Mufeeda taje Raka k'awarta biki tunda yamma, basu dawoba. 'Yan biyu kuma sunje wajen baffanku kar6o kud'i, sunason zuwa shopping gobe. Kai momy! Kai momy! ALLAH yarannan basajin magana, yanzu bana hanasu fitar dareba kota yamma gefin magriba?, amma harkika bar mufeedah zuwa biki?. To kayi hak'uri, wlhy magiya taita yimin harda kukanta, wai k'awarsuce, bara nazo nakirata tadawo gida. Baice komaiba yajingina da kujerar yana k'aramin tsaki. Su hasnah suka shigo da murnar samo abinda sukaje nema, amma ganin ya khaleel sai kowacce ta kama kanta, suka aro nitsuwa suka yafama kansu. Ya khaleel barka da dare. Idonsa yabud'e akansu, ya amsa babu yabo babu fallasa. Ganin fuskarsa da d'an sauk'in d'aurewa suka zauna a falon, amma kowacce a d'arare. Yana kula dasu amma yashare. Saima yad'auki wayarsa yahau kiran mufeeda. Harta tsinke bata d'aukaba, saida yay kira Na uku sannan ta d'auka gabda zata tsinke. Wlhy nabaki nanda 15minutes, inhar baki bayyana agidaba sainaci ubanki adarenan, danhar wajen iskancin naku zanzo Na 6a66allaki 'Yar iska kawai. Abinda yafad'a kenan ya yanke wayar. gaba d'aya Mufeeda takid'ime, fad'itake nashiga uku ya khaleel yana gida, cikin hanzari take had'a inata-inata. K'awayenta suka shiga tambayar lfy kuwa mufeey?.. Kai kubarni tafiya zanyi wlhy, ya khaleel yana gida shine yakirani yanzu, dayawansu sunsan khaleel d'in, harma damasu dakon soyayyarsa acikinsu. Harbakin mota sukamata rakiya, dama birthday d'in wani boyfriend nata sukazo, babu wani biki........... Anty Mamie zaune gefen baffah tana had'a masa dinner cikin nutsuwarta. Tagama tahad'a komai agabansa tareda fad'in bismillah. Murmushi yamata, cikin tsokana yace, "saidai kibani abaki". 'Yar dariya tayi, lallai baffansu, yakamatafa kasan ka girma, ga 'ya'ya ga jikoki, ko Najwa d'in Zuwairah aka aurar yanzu zama zatayifa. girarsa yad'age yana fad'in ummyim shikenan kuma Dan inada jika data kusa isa aure bazanyi soyayyaba?. Kanta ta girgiza masa tana murmushi, tace, " wane mutum, ai soyayya bata cancanci kasuwa daga gwarzo irin Abdallah naba. Wata dariyar jin dad'i yayi, yagyara zama yafara cin abincinsa, sunayi suna hira har ya gangaro inda yakeson zuwa. Yauwa nikam Bilkeesu su maleeka sun fad'a miki munhad'u da fad'ima a Jigawa?. Kanta ta girgiza alamar a'a, tad'ora dafad'in kasan basusan wacece itaba shiyyasa bazasu kawo komai. ALLAH Sarki Yaya fad'ima baiwar ALLAH, yanzu kotana inane da aure? Wlhy ina k'aunar baiwar ALLAHrnan baffansu. Murmushi yayi, yad'auki ruwa yasha sannan yagoge bakinsa da tissue, idonsa akan aunty Mamie yace, "ai yanzu batada aure, mijinta yarasu wata biyar kenan, harma tagama iddah. Wani zumud'in farinciki Anty Mamie tayi, cikin matuk'ar murnarta tace, " wayyo baffansu dama kadawo da ita d'akinta, wlhy danayi farinciki. Shiru yayi yatsuramata idanu, yarasa Bilkeesu wace irin macece mai dattako da hangen nesa, (baya raba d'ayan biyu tasan sirrinsa) shine tabiyo masa ta wannan hanyar danta k'arfafashi, ( haka take, inhar talura da yadamu da Abu tokobai fad'a mataba zataita karantarshi harta fahimta, koda abinnan baimata dad'iba to insha ALLAH zatayishi danta faranta masa rai. Rungumota yayi jikinsa yana fad'in Bilkeesu ALLAH yayi miki albarka, ketadabance acikin mata, amma kina ganin dawo da fad'ima gidanan bazai zama matsalaba?, kuma itama sainaga kamar bazata amincebafa? Dan wlhy ajigawa yitai tamkar bata sanniba. Karka damu muyita addu'a insha ALLAH babu abinda zai faru sai alkairi, batun Yaya fad'ima kuma kabari zanje gareta dakaina, tunda kace zata aurar da yariya ko?. Kansa ya d'aga mata. Tace, "amma kasanarma Ammah?. A'a dama kunakeji, amma nasan Ammah zatayi farinciki, dan tanason fad'ima. Hakane, ALLAH yashige mana gaba. Daga nan suka cigaba da tattaunawa, ak'asan ran baffah kam yana tunanin yanda zai tunkari sauran matan nasa, dukda yana ganin Na Umme Amarya mai sauk'ine, hajia babba Ce matsalar, tunda dama bason Fad'ima takeba, harta bar gidan basu ta6a zama lfy ba, kasancewar fad'ima Nada zafi, bata d'aukar raini gakowa. Yanacin abinci tashigo, sai la6e-la6e takeyi, momy ce tace, " waike Mufeeda la6e-la6en mikikema mutanene?. Da baki tama momy nuni da ya khaleel. Momy tamaida kallonta ga ya khaleel daketa cin abincinsa hankali kwance, duk kuma abinda ke faruwa yana kallonsu ta gefen ido, amma yayi kamar baisan abinda akeyiba. Ibraheem!. Momy tafad'a tana ta6ashi a kafad'a. d'agowa yayi yace, ''na'am momy". Kayi hak'uri. Momy hak'urinmi? Mikikamin?. Baniba mufeedah. Maida kansa yayi yacigaba dacin abincinsa, momy bar 'Yar iskarcan, tacemiki biki taje, amma k'arya takeyi. Inataje to?. Tafad'amiki da bakinta. Momy tamaida kallonta ga mufeeda, inakikaje? bacakikaimin ana kamun seematu ba yau?. Shiru mufeedah tayi tana tura baki gaba. Ya khaleel yadaka mata tsawa, Dan ubanki badake ake maganaba?. Zabura tayi gefe, cikin rawar baki race, momy wlhy fa....um....um. Um...um...mi? Mufeeda wai mikikeson maida kankine? Nifa wlhy halayenki sunfara bani tsoro, lfy lau narabu da zuwairah da Shukrah, ammake naga baki biyo hanyar hakanba, to wlhy bazan d'aukaba, babanku zanma magana yahad'a aurenki danasu Sultan wlhy, bazan iyaba, banyi iskanciba, bazan haifi 'Yar iskaba. (Nace, hummm momy kenan, kin salwantar da 'ya'yan mutane, amma kike tunanin naki zasu sami tsaro, a'a momy, ba'a shuka shinkafa agirbi alkama.🤣🤣). Ya khaleel daya gama cin abinci yature gefe, k'afafunsa yakwashe yamaida saman table d'in bayan Hasnah takwashe kwanikan. Yace, ''momy harda laifinki, yarannan babu maifad'a musu basuyi daidaiba agidannan saidai Idan inanan, yanzu ace kamarsu Sultan bazasuga yaranana Na Abu mara k'yauba su tsawata musu? haba momy mana, to wlhy yanzu wani abokinane Hasheem yake sanar dani yaganta a wani Hotel suna rawa suda samari, wai na birthday d'in boyfriend nasu. Amma dayake ita batada mutunci saitace dake biki suka tafi, ALLAH yau saina kusa 6allaki agidanan mara hankali kawai, saboda kingama degree kinfara aiki shine kanji ke hayak'in iskanci ko? To zan sauke mikishi yanzunnan yay maganar yana mik'ewa kanta Kafin tayi yunk'urin guduwa kam ya cafkota, damaruka yafara mata, tad'an daku kam tasamu tagudu d'aki, momy batace komaiba, Dan itakam gwara yayma mufeedan haka kartaje takwaso mata abin kunya, kishiyoyi susami abin yimata gori agida, wannan yasa ta kauda kanta bata hana ya khaleel dukan mufeedar ba..........🖊 *_Bara mulek'a mutanen UK su Aysha sholy_*🤪 *_gaisuwa🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀_* [8/10, 4:28 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 2⃣3⃣ *_yaukam tafiyar tawa akawai 'Yar rakiya, Dan miss xoxo tahad'o kaya itafa sai UK👜._* *_Tagaji so take tagano muku Aysharku🤣_* Idan munrasa kud'in jirgin dawowa saimu mak'ale a can kawai, dama kullum da ji6in goshi nake had'a natafiyar😂. *_Islands (UK)_* _Da acefa zan aureka, zan biyayya abayanka._ _ina sonka, nayaba da halinka, k'yanjiki da surarka, sahibi da hannunka kaban ruwa._ _ninai sa'a kan masoyi mai fara'a, kaikafara sa shadda duk garinmu an shaida d'an uwa._ K! Wai lafiyarki kuwa?. Meerah tafad'a tana zungurin Aysha dake kwance akan gado idonta arufe tanata rero wak'ok'i, tayi wannan tasaki takama waccan. Firgigit Aysha tatshi zaune, ganin Anty meerah sai kunya takamata tayi k'asa dakai tana murmushi da fad'in Anty meerah yaushe kikazo?. Ya za'ayi kisan nashigo sholy? Kinfad'a soyayya, dama nadad'e ina zargin hakan wlhy, meerah tayi maganar cikin damuwa da fargabar kodai Aysha tafad'a tarkon wani cikin yaran turawannan?, karfa ayi gudun gara, afad'a gidan zago kuma. Meerah tace, "sholy please kifad'amin gaskiya waye zai wargazamin tanadina danakeyi akanki?". Yanda meerah tayi maganar cikin damuwa yasaka Aysha d'ago manyan idanunta dake cike da gashi ta saukesu kan Anty meerah, kaitashiga girgiza mata cikin sanyinta tace, " wlhy Anty meerah babu kowa". To amma Aysha wannan wak'ok'in hausar dakikeyi koda yaushe suna nunamin akwai soyayyar wani aranki, kada ki 6oyemin, bazan hanaki sonshiba, zanduba cancantarsane kawai. Dan ALLAH kada ki 6oyemin, inhar kind'aukeni yanda na d'aukeki. Ajiyar zuciya Aysha tasauke tareda had'iye yawu, muryarta Na rawa alamar shirin yin kuka tace wlhy Anty ba anan yakebafa, tun a gida Nijeria ne, kumafa nima banyarda sonshi nakeyiba, Arena ce tacemin sonshi nakeyi. Meerah ta girgiza kai tana kallon ainahin k'uruciyar ayshar, matsowa tayi kusada ita takama hannunta, to nayarda ba sonshi kikeyiba, amma fad'amin wanene?. Aysha tad'ago ido tad'an kalli meerah saikuma tayi murmushi, ALLAH Anty ba sonshi nakeyiba, haka kawaidai nakejin nadamu dashi, kofa nature tunaninsa saiya dawo, ninamasan yafi k'arfina. Hhh aini sunansa nace fad'amin my lil. Kai Anty ya khaleel nefa. Bak'aramar dariya meerah tayiba, wai Aysha tasan soyayya, takatse dariyar tana kallon aysha, karki damu, Indai ya khaleel ne baifi k'arfinkiba, kedai kitsaya kiyi karatu, duk sanda yaganki dakansa zai soki, kuma zakice ninafad'a miki. Aidama tuni nafahimci wani Abu, tunda kika bani labarin gidansu, yanda kike Shiga shauk'i inkinzo Kansa da kurantashi dakikeyi nagane yayi kamun zuciyar sholyna😂. 6oye fuskarta Aysha tayi tana dariya. Meerah kuma taita tsokanarta. A6angaren karatun Aysha kam saidai muce Alhamdullahi, komai yana tafiya yanda yakamata kam, tana k'ok'ari dak'ara fahimtar abubuwa yanda yakamata, Arena kuma nak'ara bata taimako wajen zaburar da ita abinda bata saniba. Wad'annan abubuwan suka had'u wajan bunk'asa ilimin Aysha da k'arin kwazonta, ayanzu haka suna shirin yin exams, wannan yasaka ayshar sake maida hankali sosai, meerah ma Na taimakonta wajen k'yautata mata da d'auke hankalinta ga damuwa ko tunanin gida da ayshar kanyi akoda yaushe, inhar ta tuno gida takan zauna tasha kuka harsai taji tagaji, meerah bata hanata, Dan aganinta kukan zai rage mata nauyin zuciya da damuwarta. Alhmdllh itama meerah a 6angarenta komai natafiya yanda yakamata, tayi tuba Na gaskiya, duk abinda tasan zai ta6a imaninta tana guje masa, kullum da k'aryar dazata sambad'a saboda kartaje club, bata shaye-shaye yanzun, Anty glory tatsareta ranar da tambaya akan canjawa datayi. Sai kawai meerah tafashe mata da kuka. Hankalin Anty glo yatashi sosai, tashiga tambayarta miya farune?. Meerah kan ta karkace ta sambad'o k'arya wai sunyi fad'a da saurayinta, Dan takamashi yana muna furtarta da wata budurwa. Anty glo....tayi tsaki, yo saime? Shine zakiyi kuka akansa? Kema kiwatsar dashi, gari dayawa wai mutuwa tashiga birni. Karin maganar Anty glo.... Tasaka Aysha dake gefe tana duba books d'in school NATA gumtse dariya. Anty glo....tacigaba dafad'in kibarsa nasan wani zaizo aii, kinada k'yanki da k'uruciya, shine banza Dan dama nagaji da ganinku tare. Dama madam Joy ta turomin kaya daga Nijeria suna zuwa Zamfara had'aku keda Aysha da besi, yanzu kihuta kawai abinki harsai kinsha gyaran kece raini. Gaban Aysha yafad'i, itakam haryanzu fargabar kaidinsu Anty glo.... Nabata tsoro, kuzo Ku ajiye yara kawai Dan biyan buk'atarku, aranta tace, "ALLAH yamana tsari daga sharrinku". A can kuwa meerah cewa tayi inayinki Anty glo..... d'inmu, aikinki Na kyau tayi maganar tana rungumeta, aranta kuwa fad'i take tsinanniya aniyarki tabiki, awanan karon tuba nayi Na gaskiya, insha ALLAH kun kusa nemanmu kurasama, baradai Aysha takammala karatunta. Anty glo....taji dad'in furucin meerah kam, sai washe hakwara takeyi. Ahaka happy tashigo ta samesu, daga ita sai bes iyakar cinya, ko bra babu ajikinta, 🎁abinda ke hannunta tamik'ama Anty glo....., waigashi wani yakawo abaiwa sholy. Ido Aysha tazaro waje, Anty happy nifa?. Eh ked'in, cewar happy. Kar6a Anty glo.... Tayi tabud'e, 💐filawa ce mai k'amshin tsiya aciki, saikuma d'an kwalba mai kyau anzuba k'ananun kifin roba aciki da ruwa, sunata yawo acikin ruwan, wata 'Yar takarda Anty glo.... ta zaro anrubuta. *_for you! my Hayatee._* Cikin mamaki duk suke kallon Aysha, Anty glo.... tamik'ama Aysha kayan. Itamadai juyasu take tayi, amma tagaza gane wanene zai iya tura mata wannan sak'on?, tad'an shinshina fulawar, kamshi mai dad'i yadaki hancinta, harsaida ta shak'a ta lumshe idanunta, kamar tata6a jin k'amshinan, to amma a ina?, wannan itace tambayar. Sholy waye ya aiko miki?. Wlhy Anty glo....ban saniba nima?. Anty glo.... Tamaida kallonta ga happy, happy waye yakawo?. Wata 'Yar budurwace Anty glo.... Aysha tayi saurin fad'in ALLAH Arena cemato. Kai amma ta rud'ar dani. Suma su Anty glo.... Duksun amince hakad'inne. (Nikamdai nace ALLAH yasa to)🤭 Washe gari koda suka had'u a makaranta Aysha batayima Arena maganarba, tace, "inhar batayi mataba, itama bazata yimataba ko". Har suka kammala exams d'in kuwa arena batayi maganarba, itama Aysha ta share batayimataba. Haka rayuwa tacigaba da tafiya, su Aysha sunkammala exam d'imsu, Alhmdllh tayi kwazo kam, dantasamu nasarar shiga grade 2, (kunsan sufa ba jss ko ss suke cewaba) kuma kwakwalwarka ke kwatarka sukam. Sosai Aysha tak'ara maida hankali akaratunta, Dan Arena Na taimakonta sosai, turancikam anwuce wajen tuni, idan tana zuba yaren turanci saika d'auka haihuwa da girman cance, abincinsuma tafara kwarewa daci😂. Yau takama weekend basuda school, Dan haka meerah tace, ''tashirya suzaga gari". Dama haka take mata, inhar batada school ko wani uzuri sai Anty meerah tad'auketa takaita wajaje daban-daban, dukdan ta d'ebe mata kewar gida dana 'yan uwa. Baramu lek'a Nijeria kuma. Amma zanbar xoxo a UK kawai😜 *_Nigeria_* Baffah ya sanarma Ammah zancen fad'ima, bak'armin farinciki Ammah tayiba kam, Dan shikansa baffan yayi mamakin yanda Ammah ta nuna murnarta sosai. Takumace karyaji komai ita zata sanarma matansa. Bikinsu fadeelah ma da ita za'ayishi. Yaji dad'in kalamanta kam, dan haka yafara shirye-shirye abinsa. Baffah shiri babu amincewar amarya😂. *_Kano_* Tunda mama suka dawo daga Jigawa abubuwa dayawa suke caccakar mata rai, amma saita d'ebesu tawatsar baya saboda shirin bikinsu Fadeelah dayaketa kawo jiki. Shiri akeyi sosai, Dan kawu bilyamin da kawu Ahmad suna k'ok'ari, tamkar Malam Abubakar mahaifin su Aysha nadarai. Amare Hafsat & fadeela kam aii ba'a magana. Sunata shan gyara wajen gwaggo Asma'u, Dan kusan sati biyu kenan tad'aukesu suna wajenta a katsina. _____________________________ Zaune suke awajen shak'atawar, wajene had'ad'd'e Wanda akayishi Dan hutawa kawai, yaran turawa da iyayensu kowa nata uzurinsa awajen, bak'ak'en fata d'ai-d'ai sukan gitta. Meerah sanye take da wandon jins bak'i tad'ora wata farar Riga mai santsi, sai jibgegiyar rigar sanyi ja data saka a sama, takawo siririn gyale tarufe kanta dashi, tayi k'yau sosai masha ALLAH. Aysha kam Na sanye da wando da Riga itama, Jan wando da yellow d'in Riga, tasaka pink d'in rigar sanyi Asama, bata saka d'ankwaliba, saidai taja hular rigar sanyin har saman kanta, takalminta mai igiya yellow yayima k'afarta k'yau ainun, zagaye wajen sukeyi anutse suna 'Yar hirarsu cikin harshen Hausa. Aysha tsaya tareda rik'e k'ugunta tana dad'in wash Anty meerah, ALLAH nagaji over. Matashin saurayi bak'in fata dake zaune bisa kujera yana karatun wani story book yad'ago da sauri danjin yarensa a inda baiyi zatoba. Kallon Aysha da meerah yakeyi cikeda mamaki. Meerah tayi dariya, to raguwa zomu k'arasa can muzauna kihuta. Binsu yayi da kallo harsuka zauna, yasauke ajiyar zuciya yana maida kansa ga karatunsa, amma saidai yakasa hakan. Tsam yamik'e yanufi indasu Aysha kezaune sunacin popcorn🍿...........🖊 *_tofa masu karatu, kowaye wanan?._*🤔 Kubiyo mata agidan Abdus'salam kawai💋💋💋🌹 *_inayinku yasin🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀😍😘_*✌🏻 [8/11, 4:23 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _su tawan anji dad'in UK anmak'ale acan, waibazata dawoba sai Aysha tagama karatu🤣🤣_ *_Miss Xoxo a UK_* Maisak'o yakawo nakai mata.😂✌🏻 2⃣4⃣ Assalamu alaikum 'yan mata. Atare suka d'ago kai, cikin tsantsar mamaki suke kallonsa, Dan basu ta6a tunanin jin yarensu abakinsaba. Ya d'age gira sama tareda fad'in Ku amsa mana. Aysha Ce tayi k'arfin halin amsashi. Amma meerah har yanzu baki bud'e take kallonsa. Shimad'in hankalinsa Na kanta, yace zan iya zama?. Yanzuma Aysha Ce tabashi amsa cikin gyad'a kanta. Zama yayi bisa kujerar dake kallonsu, kuyi hak'uri idan natakura mukufa. Sai sanan meerah tasami bakin magana, a'a babu takura, sai daifa......... Kinyi mamakin jin nayi Hausa ko?. Yak'arasa mata maganar cikin murmushi. Kanta tagyad'a masa. Yayi 'Yar dariyar basarwa tareda mik'a hannu yad'ebi popcorn d'in cinyar Aysha, yakai bakinsa yana fad'in dukda ba'amin tayiba kam. Sorry uncle, Aysha tafad'a tana langa6e kai. Murmushi yamata, thanks my lil sister. Yamaida kallonsa wajen meerah. Anty meerah koba'ayi maraba dani baneba?. A'a, kayi hak'uri, mamakine kawai dai nakeyi. Karkiyi mamaki akaina, sunan Naufal yahaya Zubair, d'an asalin k'asar Nigeria, amma haihuwar Canada, babana d'an Nigeria, Mamana 'Yar Canada, so nayi rayuwar Nigeria sosai shiyyasa na'iya Hausa, yanzu haka mom & dad, brothers-Sisters d'ina duk suna Canada, aikine Na wattani 6 yakawoni nan Georgetown. Yak'are maganar da d'age gira sama. Murmushi sukayi suduka. Yace, "friends nawafa?". Meerah tad'an murmusa, mukam labarin namu bashida tushen dazakayi sha'awar jinsa. Ko? To shikenan, nabada uzuri, afad'amin suna. Ameerah & Aysha. Nice names drillings. Hira sosai yake musu, harsuka saki jiki dashi, Dan Naufal yanada saurin sabo kam. Shine yakaisu har gida, bayan uwar sayayya daya narka musu. Anty glo...... Sai Murna take meerah tayo babban kamu. Nace hummm. ____________________________ Biki kam ya kankama, bak'i suncika gidansu Aysha, sai hidimomi akeyi. Gida yagama d'inkewa kasancewar gobene d'aurin aure. Washe gari wajen 10am babu zato saigasu Anty Mamie akano, hardasu inna 'yan jigawa. Mama rasa wane irin farinciki zatayi tayi, saikawai tarungume Anty Mamie suka saka kuka atare. Nanfa akaita lallashinsu daban magana. Duk wani ainan ainan da aunty Mamie akaita yinsa. Hakama Amal, Hamdiyya, Naseeba, Shuhuda sunshige cikinsu Fadeela amare anata abubuwan arzik'i dasu. Gabda d'aurin aure gayyar matasan gidan suka iso, ya khaleel ne kawai babu, danyana kasar Algeria tun jiya. Bayan an d'aura aure, Anty Mamie tace mama taje falon Abbansu Aysha ana kiranta. Bata kawo komai arantaba tatashi tafita. Sanye take da jar atanfa mai ratsin brown d'in zane, tamata matuk'ar kyau, kasancewar mama batada k'iba kuma batawani haihu da yawaba sai shekarunta suka 6uya sosai, tana nan k'yak'yk'yawarta fara tas. Da sallama tashiga falon, k'amshin turarensa yafara mata sallama, cikin dakiya tashiga, amma ganinsa saiya sakata fad'uwar gaba, (waimi Alhaji Abdallah keso da'itane?) Idonsa akanta yace, "kiyi hak'uri fad'ima ki k'araso ciki". Kamar zata juya saikuma tadawo tashiga, kobabu komai hidimarta yahalarta shida iyalansa. Baikamata ta wulak'antasaba. Zama tayi kujerar dake nesa dashi, kanta ak'asa tace ina yini, anzo lfy. Murmushi yayi, haryanzu Fad'imarsa Na nan bata sauyaba, mace mai zafi da sauk'inkai. Ya amsa mata gaisuwa tareda murnar aurensu fadeelah, yad'ora damata gaisuwar mijinsu. Daganan shiru yabiyo baya. Ganin haka mama tamik'e tana fad'in mungodefa, ALLAH ya maidaku gida lfy. Da sauri yakatseta, sorry inaso muyi magana. Komawa tayi tazauna, saidai yanayinta yacanja kam. Ganin haka shima saiyaci serious. Fad'ima nasan haryanzu abinda yafaru abaya yanasaki jin haushina, amma ina so kigane cewa k'addarace da rabon haihuwar wad'annan 'ya'yan, wani baya haihuwar d'an wani, ALLAH ya rubuto saikinzo kin haifesu anan, amma inaso kisan haryanzu kina cikin ruhin Abdallah Rufa'ee. Muba yara baneba, baikamata muzauna zancen yaraba, ina rok'onki arzik'i kidawo d'akinki, amatsayin matata, kenafaso aduniya, kuma har yanzu inasonki. Bak'aramar razana maganarshi tasaka mamaba, muryarta narawa tace anya kasan mikake fad'a kuwa?. Nasani fad'ima, yardarki kawai nake buk'ata, wlhy inhar kin amince ayau d'inan za'a maida aurenmu. Zumbur mama tamik'e, cikin fusata tace, ban aminceba, bakuma zanta6a amincewarba, wanan maganar tatsaya iya ni da kai, Dan banaso takawo 6acinran mutane dayawa. Tana gama fad'a tafice daga falon. Baffah yadafe kansa dake sara masa, ahankali yafurta fad'ima ki canja mana, wlhy dolene ki amince da buk'atata koda yardarki ko babu. Nikam nace baffah Ashe kai ya khaleel yabiyo jarumta😂. Magani to kaida hajia mama wakeda nasara🤣. _____________________________ Sabo sosai yashiga tsakanin Naufal dasu Aysha, yanzukam Aysha tasamu Uncle, sosai takejinsa matsayin d'an uwa, shima hakan take agareshi, yarik'e Aysha da meerah tamkar 'yan uwansa dukda haryanzu baisan komai akansuba. Sosai Aysha take maida ahankali akan karatunta, k'awance itada Ariana kam kullum k'ara dank'o yakeyi, ga uncle d'inta da Anty meerah suna bata kulawa sosai, tazama 'Yar gata, jinta yakeyi kamar tana tareda su mama, agefe d'aya kuma son ya khaleel nata kuma sakin jijiya da rassa azuciyarta, ita kanta har mamaki lamarin ke bata, idan kuma tatuna shid'in jinin hajia babba ne sai tsoro yakamata. Saidai tanata gayama ALLAH, Dan sosai bata wasa da ibada, har azumin litinin da alhamis yitake abinta. Wanan yake k'arama meerah k'arfin guywa itama, akoda yaushe take kara tubarma ALLAH 6arnar data aikata, tanakuma nemawa mahaifiyarta shiriya itama, shiyyasa take kara k'aunar Aysha aranta, domin itace silar komai. Dawowarta kenan daga school taci karo da motar ya Naufal, k'arasawa tayi wajen motar tana washe baki. Shima tundaga nesa yake hangota, Dan haka yabud'e motar yafito. Ya Naufal lfy naganka kai 1? Ina aunty d'in?. Murmushi yayi tareda fad'in no lil sholy yanzu tashiga gida zata d'akko Abu. Ya school?. Alhmdllh ya Naufal. Kinadai k'ok'ari ko?. Eh wlhy inayi Yaya, insha ALLAH Sonake wanan karonma aje dani grade 3. Eye kaga big girl, kinga daga nan sai high school kenan?. Cikin dariya tace insha ALLAH Yaya. Ana haka saiga meerah tafito, Aysha tarungumeta tana fad'in I miss you my sweet Anty. Me 2 my lil sholy. Ya Naufal yay dariya, dansuna birgeshi, kaikace ciki d'aya suka fito. Aysha tashige gida yayinda sukuma suke binta da kallo suna murmushi, suna k'aunar yarinyar harcikin zuciyarsu, Dan ta cancanta asota akuma k'aunaceta. Naufal yadawo da kallonsa kan meerah cikin sauke ajiyar zuciya. Meerah nidai haryanzu ina barar jin labarinku kam, munzama d'aya amma har yanzu bansan komai akankuba. Hum karka damu lokaci nazuwa dazaka San komai, bamu 6oye makaba Dan rashin yarda, a'a lokacine kawai baiyiba. Naufal mutumne mai sauk'in kai, Dan haka yace o right babu damuwa, ALLAH yakaimu lokacin. Amen meerah ta fad'a. Daga nan fira sukacigaba dayi har Aysha tafito sanye da doguwar Riga brown ta d'ora farar rigar sanyi asama, hannunta d'aukeda robar ice-cream. (Nace kaga 'Yar hutu😄). La ban hanaki shan kayan sanyinnanba sholy? wai bak'ya ganin yanda mura tatasoki gabane?. Langa6e kai Aysha tayi gefe, cikin shagwa6a tace, "sorry ya Naufal, ALLAH katanbayi Anty meerah sau d'aya kawai nakesha arana. Kallonsa yamaida kan meerah, kekike biye mata kenan? banace kidaina saya mataba. Hannu biyu meerah tahad'e alamar ban hak'uri, kayi hak'uri ya Naufal, ALLAH Lola Ce tasaya mata baniba, nima ganinsa kawai nayi ahannunta bayan tabata, danma kada nakwace shine takaima Lyn ajiya. Girgiza kai Naufal yayi, yace, " zand'au mataki aii". Ganin kamar ransa ya6aci Aysha tamik'a masa robar ice-cream d'in gabad'aya. Kayi hak'uri Yaya bazan sakeba, tayi maganar tana kama kunnuwamta. Murmushi yayi yana fad'in promise?. Yes my sweet Yaya promise. Shikenan kisha wanan, amma yazama first & least, duk randa nakeson kisha zan sayo miki dakaina kinji. Murna taitayi, tana kar6a takoma cikin gida dagudu. Dariya Naufal da meerah sukayi, Dan sunsan haryanzu k'uruciya Na d'awauniya da ayshar, haryanzu tana 14years ne, amma gab take dashiga 15. Sallama shima yayma meerah yatafi gida, dama daga wajen aiki yabiyo danyaga lafiyarsu. Daga Aysha sai Serah da Queen a gidan, saikuma meerah data shigo yanzun, saurankam suna wajen shek'e ayarsu. Besi ma anzama 'yan gari tuni, harka take da manyan guys kam. ______________________________ Ansha biki an shashshare, yanzu dagasu saisu, kowa Na mamakin rashin zuwan gwaggo bintu kuwa, gashi wayartama bata shiga gabad'aya. Basusan tanacan tanashan wahalaba wajen Anty zuwairah ba, kokad'an yaran Anty zuwairah basuda kunya, karma Najwa da Huzaifa suji labari, sunyi mugun raina gwaggo bintu, duk wata k'urar aikinsu saisu d'auka sukai mata. Bata isa kuma tayi maganaba su had'ata da mamarsu, Anty zuwairah kam ta balbaleta damasifa ga gori da cin mutunci. Haka gwaggo bintu zataita sharar kwallah, gaba d'aya zaman gidan ya isheta, jitake kamarma tagudu Kano. To amma idan taje wace amsa zata basma mama idan ta tambayi d'iyarta?. Wanan shike tad'a mata hankali, ranar da lissafinta Yakama bikinsu Hafsat jitayi kamar tayi tsuntsuwa taganta a Kano, amma babu dama. A 6angaren zancen mama da baffah kam Anty Mamie tayi iya bakin k'ok'arinta Dan mama ta fahimta amma Sam tace babu wanan maganar a tsakaninsu. Hardai suka tafi babu wani canji daga mamar akan ra'ayin rik'au d'inta. Wanan yasa bayan biki da kwanaki 6 baffah yazo yasami kawu bilyamin da zancen, sun tattauna sosai harda yanda zasu 6ulloma lamarin. Wanan yasaka zuciyar baffah d'an samun sauk'i, harya Tara manyan 'ya'yansa maza yafad'a musu zai dawo da matarsa fad'ima. Duk sunmasa addu'ar fatan alkairi, Dan ba'a musu tarbiyyar rashin fahimtar abuba, dama kuma Anty Mamie tasanar dasu komai tunkafimma suje d'aurin aure su Fadeelah. Saidai har yanzu Uwargida sarautar mata hajia babba da Umme amarya basusan waynar da'ake toyawaba, Dan baffah ya kwakwkwafi yaran akan suyi gum dabakinsu da zancen harsai ya tabbata. Saidai kuma kash baffah ya makaro, Dan hajia babba ta tunkaro d'akinsa aranar dayake sanarma ya khaleel daya dawo jiya zancen yashiga kunnenta. Hummm airanar saida ta tada hankalin kowa agidankam. Dole baffah yabar mata gidan dankarsu tafka abin kunya agaban yara. Umme amarya kam koda tadawo taji zancen batace komaiba, Dan ita wanan baya d'aya daga cikin matsalolimta kam. Washe gari babu Wanda yasani hajia babba da hajia khaltum suka nufi Kano Dan sun sami address d'in gidansu mama ahannun Tasleem dasuka tsare da kurari. Tana kuka tabasu, amma tayi gum dabakinta bata sanarma Anty Mamie ba gudum kartasha fad'a, kilama harda duka Anty Mamie zata mata..............🖊 Hummmm masu karatu koya zata kaya? Idan su hajia babba sun Isa Kano?.🤔 Bara mubisu muma domin ganema idonmu🤥. Duk mai buk'atar ciki da gaskiya.... Daga farko Yaje wajen mai wannan number zai samu😂. 08100955951 I love you all my Fan's🤗🤗😍😍😍😍😘😘😘😘. [8/12, 4:08 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _Deexerh, my sweet Dee.....wanga page nakine ke kad'ai, yau sai islands uk😍😍._ 2⃣5⃣ Indai Dan Maman Hafsat kika dage dak'in yarda da aurenan yakamata ki amince yanzu Maman Aysha, tunda kindaiji itama d'in tagoyi bayan kiyi aurenki. Itama kuma inhar ta amince nid'in M. Basher yanada burin aurenta, kuma tasan zancen tunda anfad'a mata, sabodake kuma tace bata aminceba, tunda yanzu kema gashi zakiyi saikuyi hak'uri kawai kiyi. Auren shine mutuncinku, Dan Yaya Abubakar bazai ta6a dawowaba, dolene kuma yaranku saida tsawatawar namiji. Mama ta share kwallar data cika mata idanu, nifa kawunsu aurensane bazanyiba kam, dacanma damuke da kuruciya ban zauna da uwargidansa lfy ba bare yanzu, banason yawan fitina gsky.. Kafin kawu bilyamin yace wani Abu sunji ana kwala sallama a tsakar gida. Fitowa sukayi suduka, saidai ganin manyan hajiyoyin yasakasu tsayawa suna kallonsu da mama ki. Itakam mama tunda taga hajia khaltum da hajia Laura ta shaidasu, wanan yasa tamaida kallonta ga kawu bilyamin tana fad'in kagani ko, wanan shine abinda nakeso kugane kaidashi kawunsu. Wacece ita?. Matarsace mana, kanagani tundaga Abuja tawanko k'afa harzuwa Kano sabodani. Aii na'isa kenan, hajia babba tafad'a cikin kakkausar murya tana k'arasowa wajen mama, tanunata da yatsa tana fad'in Fad'ima! Kamar yanda gidan mijina yafi k'arfin zamanki abaya, ayanzuma wlhy yafi k'arfinki, duk aure auren Abdullah babu Wanda bataiminba sama dake, saiko waccan bak'ar dagar Bilkeesu, itama kuma gaf nake dayin maganinta, kunhad'a plan keda ita akan ki koma, hhhhhh kunyi kuskure wlhy, Dan baki Isa komawa wanan gidanba kisaka aranki!!!. Ke kam wacce irin macece haka?. Kawu bilyamin yay maganar wa hajia babba. Harara ta ballamasa amma bata tankaba. Mama tace, "kawunsu yi shirunka, aii baki yafad'a kuma dolene abashi amsa daidai dashi". Hajia Laurah kinyi kuskuren tunanin kin Isa hana fad'ima komawa gidan Abdullahi, kema kinsan wacece fad'ima, kuma haryanzu ina nan yanda kika sanni ban canjaba, adakam kinyi nasanar raboni da gidan Abdullahi, wanan kuma k'addarace darabon haihuwar 'ya'yan da ALLAH bai k'addaro zasu zama nasaba. amma kinsan wani Abu kuwa? adakam babu tunanin komawa gidansa ataredani kodaya buk'aci hakan, amma a yanzu kodan Na nunamiki ked'in banza a banzace zankoma. Kishirya tarbar fad'ima amatsayin kishiya nanda sati d'aya rak Laurah. Kuma kiyi hanzarin barinmmin gida kafin nasaka afiddaki awani yanayi..... Hajia khaltum ta hayayyak'o cikin masifa, itakam hajia babba saidai antayama mama kallon banza takeyi. Da sauri mama tadakatar da hajia khaltum. A'a 'Yar kore! Tsaya matsayinki, kinsanni ba hak'urine daniba yanzu saina sassa6a miki kamanni. Kama kanki tunkafin asamu matsala, kuma karku bari Na aikata abinda nafad'a muku. Mama tai shigewarta d'akinta, su Umma da kawu bilyamin suna take mata baya. Aifa su hajia babba sai zabga jaraba akeyi, dacin mutunci wasu mama. Babu Wanda yasake kulasu, harsuka kai aya sukabar gidan, hajia baba arikice take da kalaman mama dantasan zata iya aikatawa, wanan kad'anne daga aikin fad'ima, adad'inma bata raga mataba Dan ita bata d'aukar raini. Dama ajirgi sukazo, kuma ajirgin suka koma. Mama kam kaitsaye tasanarma kawu bilyamin ta amince. Koda yakira baffah yafad'a masa duk yanda komai yafaru sai baffah yayta farinciki. Shikam zuwan hajia Laurah yamasa rana, badan karya takalo tsiyaba dahar k'yautar kud'i zai mata, ya tabbata badan hakan tafaruba fad'ima bazata ta6a amincewaba, tunda har Ammah da inna sukai mata magana amma tabasu hak'uri. Sun tsaida komai, ranar sati kuma za'a d'aura auren😂. Yeee baffah yaci nasara, is a gold! 💃🏻 is a goooooal!!!, shaku shaku is a goal! One corner is a goal!!💃🏻💃🏻💃🏻, zamusha bidiri yasin. Team, baffah & mama😂😂💪🏻. *_Bayan sati 1_* Masha ALLAH an d'aura auren baffah da mama, m. Bashir da Ummah, wanan aure kam yabama mutane dayawa mama ki, amma ansaka albarka sosai aciki. Sunce babu wani biki dazasuyi, Umma ma zatayi zamanta ne agidan, mama kuwa sai Abuja. Agurguje please🤧 Hajia babba tatada hankalin kowa agidan, wanan yasaka ya khaleel 6acin rai, suna dawowa daga d'aurin auren baffah yad'iba kaya kala uku yay tafiyarsa gidan Taheer. Kwana uku kuma da d'aura auren mama tatare, sunsha kuka itada Umma, Dan Umma da matan kawu bilyamin ne sukad'ai sukamata rakkiya, sai gwaggo Asma'u da gwaggo Asubi k'anwar mama. Sun sami tarbar arzik'i daga wajen Anty Mamie da Ammah, amma hajia babba kam lamarin sai addu'a, umme amarya kam koma ganinta basuyiba. To mama dai tatare agidan baffah. Saimuce ALLAH yabada zaman lfy. Keda hajia babba kam masu karatu sunci karki raga mata😂🤐. Masoyan hajia babba amin afuwa🤣🙌🏻. __________________________ *_Bayan wani lokaci mai nisan zango_*😬 Abubuwa dayawa sunfaru awanan lokuta dasuka shud'e, masu dad'i damarasa dad'i, Na dariya dana kuka. Aciki harda kammala karatun Aysha, tasamu sakamako mai k'yau, yanzunkam inhar tasamu dama zata wuce da karatuntane zuwa high school, (college University) saidai bamuda tabbacin hakan zai iya faruwa kam, Dan bamusan misu Anty glory ke shirya ma rayuwar ayshar ba. Har yanzu tana nan da dagiya akan addu'a, tak'ara girma da k'yau, saboda yanayin abinci mai inganta jiki, dakuma canjin muhallin zama. Meerah ma dai alhmdllh, matsaloli sunmata sauk'i saboda su Anty glory suna zaton soyayya takeyi da Naufal. Itadai batacewa komai, Dan baita6a cewa yana sontaba. Amma suna samun kulawa awajensa itada Aysha, dukda kuma har yanzun baisan komai dangane dasuba. Shi azatonsama tare suke dawani nasu anan k'asar. Tashin hankalinsu yanzukam bai wuce kwanakin aikinsa dasuka taho gangarar k'arewaba, yana shirin komawa Canada. Abin nadamun Aysha kam, idan ta tuna ya Naufal zai barsu har kuka takeyi. Ita kanta meerah dauriya kawai takeyi amma tana cikin damuwa, gashi takula su Anty glory sunata k'ule-k'ulle akan Aysha, amma tagaza gane namiye?. Sosai yanzu Anty glory tamaida hankalinta wajen kula da ayshar da koya mata abubuwa kala-kala, gyaran jiki bata abubuwa Wanda meerah tasan basu dace da ayshar bama gaba d'aya. Tarasa ina zata saka kanta danta samu hanyar ku6tar da Aysha, danta d'auki alk'awari bazata ta6a bari su Anty glory su ruguza rayuwar ayshaba kam. Yau duk suna gida, babu Wanda yakwana a waje, kid'ane ketashi acikin gidan, kowa da harkokin dayakeyi, Aysha dai hankalinta nakan game acikin IPad d'in da Ya Naufal ya saya mata, gaba d'aya Attention d'inta yatafi ga game d'in, sai sakin murmushi takeyi saboda yanda take enjoying d'in game d'in. Meerah sai kallonta takeyi cikin tausayawa, kokad'an bata damu da tata rayuwarba, Dan tuni tasan tazama tarihi wajen rugujewa, ta Aysha ce agabanta ayanzu. Amma takula kuruciya tasaka Aysha shagala da mance abinda aka kawota yi, kodan saboda kulawar datake samune awajensu?. oho. K'arar doorbell yadawo da meerah hankalinta, hakama su Lyn, Happy taje tabud'e, ganin Anty kubra yasakata sakin ihu da rungumeta. Suma sauran duk fitowa sukayi Dan ganema idonsu. Babu Wanda baiyi murna da ganin Anty kubra ba, sai Aysha da meerah, Dan Aysha tana ganin wadda akema ihun takoma wajen zamanta tacigaba da game d'in ta. Garama meerah tayima Anty kubra dariyar hak'ori. Yanzuma Anty kubra tare take da 'yanmata biyu wad'anda zasukai 17-18, saikuma k'aramar yarinya dabata wuce 15 ba, zasuyi kai d'aya da Aysha. Bak'aramin mama ki Anty kubra tayiba da ganin yanda Aysha takoma, sai ta6ata takeyi tana yabawa. Itadai Aysha batace da ita k'alaba Dan tagama tsanar Anty kubra daduk wani mai irin halayenta, wlhy daza'a bata dama zata iya salwantar da rayuwar Anty kubran. Kwana biyu dazuwan Anty kubra saiga john yazo, bak'aramin tashin hankali Aysha da meerah suka shigaba awanna karon, Dan basuda tabbacin Aysha zata tsira, tunda dama cayayi bayan ta mammala karatu, kuma tagama kusan 4weeks ma kenan. tunda ya iso gidan idonsa nakan Aysha, sai had'iyar yawu da lashe la66a yakeyi saikace tsohon maye, tarema sukazo da abokansa biyu, suma duk turawane. Aysha dai tashige d'aki ta 6uya, hankalinta yatashi, sai yau tadawo daga shagalar datatafi Na manta abinda aka kawotayi, gatanda Anty meerah ke bata da ya Naufal ya dulmiyata a mantuwar ko ita wacece?.😭 Shigowar dataji anyi yasakata k'ara sautin kukanta, azatonta anty meerah ce. Saidai ta6a kafad'arta dajin muryar john yana fad'in hii baby, miye matsalarkine??. Yasakata d'agowa abirkice, ta watsa masa manyan danunta dake a rikice. Jiyayi gaba d'aya tsigar jikinsa yatashi, Aysha ta takaloshi gaba d'aya, yay saurin kai hannu danufin rungumota. Zabura tayi zata gudu ya damk'ota tafad'o cinyarsa. A'uzubillahi minashshaid'anirrajimm!!!! Aysha tafad'a da k'arfin. Yayinda shikuma john yamatseta yana wata dariyar rashin mutunci, danshi baisan mi ayshar ke fad'aba.........✍🏿 Hummm yaukam dai to🤐😶, amma bara nayi shiru kawai😭. Ayi manage yau inada bak'i😍✌🏻 *_Dan ALLAH mai buk d'ina SANADIN BIKIN SALLAH, ya taimakamin dashi_* Sonake nayi Documenting nashi please🙌🏻, ataimaka. *_yau bana cikin walwala🕴, my lil sholy._*😰 [8/14, 7:12 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _My dota Aneeluv & Raheenat mammoudou. Gaisuwa agareku da fatan alkairi my dears_ 😍😍😍😘✌🏻 2⃣6⃣ *Sosai* suke kiciniya, amma da alama John yabar ayshar ne kawai, Dan k'arfinta danashidai ba d'ayaba. Aikam saida tagaji Dan kanta tahak'ura saboda galabaitar datayi, sai nishi takeyi da hura hanci. John yatsira mata idanu yana murmushi, cikin harshen turanci yaja hancinta yana fad'in o baby!, kingafa kin wahalarmin da kanki, ina mamakin yanda zuciyata ke tausayinki da sonki, alhalin banta6a hakan gawata bak'ar fataba, amfaninku agareni naji dad'i daku, Ku nemomin kud'i, kumin bauta. Amma ke tadabance acikinsu, wani lokacin har nakan fad'a tunaninki, anya ked'in mutum Ce?. Harara Aysha ta dallah masa da manyan idanunta, sannan tamurgud'a bakinta, da Hausa tace, "a'a aljanace, kuma wata rana bak'ak'en fatar saisun zamemaka dodonni, saika zama bawansu, kud'in dasuka tara maka saisun koma nasu, jindad'in dasuke sakaka saiya zame maka masifa, mugu azzalumi haihuwar asara. Shiru yayi yana kallon yanda bakinta ke motsawa, burinsa kawai ya d'and'anesa, bajin kalamanta yakeyiba, amma tabbas yanayinta yanuna rashin kunya take masa, amma bai damesaba, jin Aysha yakeyi daban acikin halittu, komai nata na burgeshi sosai, haryakanji kamarma nangaba zai iya aurenta, koyanzu dayakeson d'an d'anar zumarta amatsayin masoyiya zai aikata hakan ba wai Dan kwad'ayiba. Yamatse Aysha tsam ajikinsa, yayinda itakuma jikinta ke rawa, tana karanto duk addu'ar datazo bakinta. Abubuwan daya fara mata yasakata dagewa ta gallah masa cizo a damtsen hannunsa. Uhchhhh! Yafad'a sabodajin azabar zafi, abinka dajikin bature harta hudamasa wajen da mayun hakwaranta. Amma john yakasa sakinta, kam yarik'eta da d'ayan hannunsa, yayinda yake yarfe Wanda tacijeshi d'in. Aysha kam sai dariya kecinta ganin yanda yake yatsina fuska dafad'in oooh baby, shiii!!. Ganin tana masa dariya shima saiyayi dariyan, yad'auketa cak yana fad'in aii saina rama. Ganin yanufi gado da ita yasakata sakin kuka dabashi hak'uri, amma ko'a jikinsa.... _______________________________ Yaya Fad'ima lfy kuwa?. Anty Mamie tayi maganar tana kallon mama data dafe k'irjinta tayi shiru ajikin Fright. Dan suna kichinne suna girkin rana, kasancewar girkin mamane sai Anty Mamie ke tayata. Wlhy Bilkeesu jinayi gabana yayi wata mummunar fad'uwa, ga girata ta haggu NATA harbawa da Sauri tun d'azun, dama da safe nayi wani mummunan mafarki akan AI'sha. To muyita addu'a Yaya fad'ima, ALLAH yajishemu alkairi, amma ita ayshan tana inane wai nikam?. Tana karatu. To mucigaba damata addu'a ALLAH yakare manager ita ako inane. Jin jina kai mama tayi, ak'asan zuciyarta kuma tanata addu'oi ga d'iyar tata dabatada takamaiman indama take ahalin yanzu, tunda gwaggo bintu bafad'a musu k'asar da ayshar zata tafiba. Harsuka gama girkin sukuku mama take, haka tanufi d'akinta tayi alwala kasancewar lokacim azhur yayima. Saida tayi nafila Raka'a biyu, tamik'ama ALLAH kukanta akan yakare mata marainiyar d'iyarta ako INA ta tsinci kanta, tayi kuka sosai a sujuda d'inta, hakama a sallar azhur taita mik'ama ALLAH kukanta... _____________________________ John NATA bidirinsa da Aysha, wadda har shid'ewa takeyi saboda azabar kuka dakiran sunan ALLAH yakawo mata agaji, saida yakai inda yake kwad'ayin zuwan saikuma yadakata yatsaya yana kallon ayshar ransa a6ace, yaja wani wawan tsaki tareda tureta gefe yasauka a gadon. Ganin haka yasaka Aysha sauka da gudu tashige bathroom tasaka key. Dubawa tayi danson ganin miya dakatar da john daga yunk'urin keta mata haddi? Bata ta6a tunanin zata tsiraba kam a yau. Jini tagani sosai ajikinta, tasauke ajiyar zuciya mai k'arfi da mik'a godiyarta ga ubangijin talikai, lallai ubangijine yayi belin ta tunda ya k'addaro zuwan period d'inta alokacin dabatayima tunaniba, a lissafin tama sai next week yakamata yazo mata. Takuma k'an k'ame jikinta da john yagama rabata da suturarta, kukan farinciki tak'ara fashewa dashi, saida tayi mai isarta sanan tashige cikin 🛀🏻 tana wanka, yayinda hawaye kecigaba da zirara akumatunta har yanzu. Duk inda hannunta yakai tatuna john yata6a saitace ALLAH ya Isa tsinanne haihuwar asara, ALLAH ya wargaza rayuwarka fiye da yanda kake wargaza ta 'ya'yan jama'a, ya ALLAH kahana wannan kafirin farinciki arayuwarsa😭, dagashi harsu hajia babba. Sama sama take jiyo kuka, wannan yasakata tsayawa tsam tana saurare, jitaifa da gaske kuka akeyi acikin d'akin, saita fito daga cikin kwamin wankan tazo jikin k'ofa tana lek'awa tajikin 'Yar k'ofar da'aka tanada domin hakan. Zaro manyan idanunta tayi waje tana fad'in innalillahi Ngozi!. Amma john d'innan mugune. Tarintse idanunta tausayin yarinyar nasake shigarta, jitake sautin kukan Ngozi tamkar ana watsa mata garwashin wuta a sassan jikintane. Yarinyar sai kiran Jesus takeyi da dadynta harda momy da brother d'inta, saboda azabar datakesha a wajen john. Ganin tadamasa da Sha'awar da Aysha tayi, gashi kuma tana period, shikam yanada k'yank'yami, wannan yasaka yabar ayshar, to amma bazai iya hak'uraba, saiyasa aka kawo masa yarinyar da Anty kubra tazo da ita shekaran jiya, wadda zasuyi kaid'aya da aysha, dafarko yarinya tayi muk'uy tana jin dad'in wasanni da john keyi da ita, shiyyasa Aysha batasan wainar da'ake toyawaba sai ihunta taji kawai. Haka Aysha takasance, ita kuka a bayi Ngozi kuka a hannun john, har saida taji shiru sai shashshekar kukan Ngozi kawai. Cikin sand'a takuma lek'awa kamar muna fuka, saitaga babu john ad'akin sai Ngozi dake kwance share-share kamar sabuwar gawa. Ahankali tabud'e tafita bayan tasaka farar rigar wanka, tanad'e kanta da k'aramin towel. Koda taga halin da Ngozi take ciki saita durk'ushe takuma sakin kuka mai tsuma zuciya, dayanzu ita john yayma wannan cin mutunci, dayanzu ita ya kacaccala haka kamar saniyar watanda. Ngozi sai d'aga ma Aysha hannu take alamar ta taimaketa, muryarta ko fita batayi sosai saboda ihun datasha. Aysha tamatsa kusada ita tana cigaba da zubarda kwallah, ahankali takamata Ngozi tayunk'ura zata tashi, azaba tasakata kiran Jesus!!!!!!!!!. Itama Aysha saita kwalla k'ara kawai, danta tsorata. Adaidai lokacin Anty glory da Lola da Anty kubra suka shigo d'akin dagudu, yayinda meerah datasha uban kuka take binsu abaya, Dan ita azatonta angama wargaza tanadinta akan Aysha. Gaba d'aya su Lola suka kwashe da dariya ganin abinda ke faruwa. Amma banda meerah data nufi Aysha tana fad'in my lil miya faru dake? Miya faru? fad'amin. Jikin meerah Aysha tafad'a tasaki kuka, cikin kuka tace, "babu komai Anty meerah, amma jibi yanda yakusa kashe Ngozi, k'aramar yarinya saboda z...... Da sauri meerah ta toshe bakin Aysha gudun kada tamusu bankad'a, Dan furucinta daidai yake da Dana Sani. Anty glo.....tadafa bayan Aysha tana dariya, sholy kardai ki rud'a kanki, nasan kema gab kike dakar6ar irin wannan sak'on, dakin hak'urama yamiki yau dayanzu kin wuce wajen, nakula tsorone dake. Shimadai mamakin d'aga miki k'afar dayakeyi nake wlhy. Babu Wanda ya tanka tsakanin Aysha da meerah. Lola tad'auki Ngozi zuwa d'akinta, danta taimaka mata wajen kimtsa jikinta, su Anty glo...kuma suka fita suna dariyar shak'iyanci. Aysha tarakasu da harara da tsinuwa azuciya. Zanin gadon dayay kaca-kaca da jini meerah tafara nad'ewa zuciyarta Na k'una. Aysha tace, ''gsky Anty meerah bazan kuma kwana a bedsheet d'innanba, kawai asakashi abola. Shiru meerah Tamata, Dan ita hankalinta yatafine ganema musu mafita domin ku6tar da ayshar. Ganin Anty meerah bata tankaba itama Aysha saitayi shiru... ____________________________ Wlhy band'auki kud'innanba, kuji tsoron ALLAH yarannan, dagirmana kudinga muzantani, har abin yakai yau da d'oramin sata? Gwaggo bintu tak'ara maganar da fashewa da kuka. Baki Najwa tamurgud'a mata, yo inbake kika d'aukaba wanene? Momy dai tasan bamu ta6a mata sataba ehe😏. Hakamasu Ebera basu ta6amana sataba saida kikazo gidannan akayi yau, Dan haka wlhy kifiddama momy kud'inta kafin muyi miki 'Yar zazzage. Gwaggo bintu tafashe da kuka tanata rantse-rantse, su Huzaifa kam sai k'yalk'yata dariya sukeyi sunga gwaggo bintu Na kuka. Anty zuwairah tace jeki, anjima zan nemeki. Kamar munafuka haka gwaggo bintu tafita tana kuka, wai yau yaranda tayi jikoki dasune suke cimata mutunci, itadai wlhy zanman gidannan ya isheta, gara tasan abinyi, wlhy barin gidannan zatayi bazata zaunaba, anya kuwa ba hak'k'in marainiya baneba yafara kamata?. Can gefe tasamu tanata kuka, da dana sanin kuskurenta, gashinan tanaji tana gani zaman gidan datakejin dad'i ya gagareta, shiyyasa akace *_CIKI DA GASKIYA WUK'A BATA HUDASHI!_* lallai wannan zance gaskiyane, inhar kanada gaskiya komai rintsi hankalinka a kwance yake. Ita gata rashin gaskiyar yahanata kwanciyar hankali.😰 Yanzu miye mafita? Kodai taje Kano tafad'ama mama gaskiya? Asirinsu hajia babba ya tonu kawai. Kai wannan gangancine kuma, su hajia babba sunfita k'arfin aiko a k'asarnan, Dan sunada d'aurin gidi sosai, gasu masu arzik'i, kada taje reshe ya juye da mujiya kuma. Kai yanzu miye mafita?. Wata zucia ta ce addu'a. Hakane kuma tafad'a tana kad'a kai. _____________________________ John kam yak'i tafiya yana nan, jira yakeyi Aysha tagama period danya d'auki alk'awarin cika burinsa awannan karon, ganin Surar Aysha yasa bazai iya d'aga mata k'afaba. Akwana biyunnan Aysha dukta tsangwami kanta, harwata ramar wahala tayi kuwa, Saboda tunani dayawan kuka. Ita kanta meerah tana cikin wani yanayi da rikitaccen tashin hankali. Yau gidan shiru kowa yafita harkokinsa, dama john ba a gidan yake kwanaba. Aysha ce kawai sai Serah da meerah, itama serah batada lfy ne shiyyasa bataje ko inaba. Kallon film d'in *SARAFINA* yad'auke hankalin Aysha da Serah, cikin sand'a meerah tashiga d'akin Anty glory gudun karsu ganta. Bincike takeyi cikin hanzari, nikaina bansan mitake nemaba. Takusan gama dube d'akin bataga komaiba, hawaye yacika mata idanu, akuma wannan lokacin ne su Anty glory suka dawo gidan, shigowar Anty kubra yasaka meerah shigewa bayan wata k'atuwar flower dake kusada bathroom d'in Anty glory. Jikinta sai rawa takeyi, Anty kubra tafara dube-dube danjin kamar numfashin mutum. ganin haka meerah tasaka hannu da sauri ta toshe bakinta. Bayan kamar 6-second Anty kubra tadainajin motsin saita shiga bathroom, dama fitsari yashigo da ita d'akin. Saida tafito tazokuma saitin flower d'in tad'auki wani story buk acikin kantar dake wajen tafice. Meerah jitai tamkar tasaki fitsari a wando awannan lokacin. Kubra tad'auki nvl d'in tayi fitarta tana 'yar wak'arta. Da Sauri meerah tasake fitowa tacigaba da dube-dubenta, harta fara fidda rai dasamun abun takama hanyar fita saikuma tadawo baya, katifar gadon tad'aga, tafara dubawama anan, cikin ikon ALLAH tahangi wani akwati k'arami a k'ark'ashin gadon, da hanzari tad'akko shi. Tagabato fitowa daga d'akin tajiyo muryar Anty glory nacewa waini ina meerah?. Aysha tace, ''tana d'aki, inaga wani abun takeyine ko barci. Ok, bara nawatsa ruwa. Anty glory tafad'a tana nufowa d'akin nata. Da Sauri meerah takoma bayan filawar d'azun tamak'ale, Anty glory tashigo. Tofa waya yima gadon haka?. Gaban meerah yafad'i. Tacigaba dafad'in ko kubra ne itafa dama aii mayyar gadoce, kayanta tacire tashiga wanka abinta. Meerah tayi wuf tafita, dasauri tanufi hanyar d'akinsu saboda hankalinsu Anty kubra yatafi kan TV. Harta kama handle d'in k'ofar Anty kubra ta hangota, a'a meerah dama ba barci kikeyiba..............✍🏿 *_wayyo baba ina kewarka wlhy, ALLAH yagafarta maka, yasadaka da rahamarsa._*😭😭🤚🏻✋🏻. Bazaku ringa samun posting ba kullum k'ila, saboda wasu 'yan dalilai.✋🏻😒, idankuma andace naringayi.🏃‍♀ *_Team Sholy_*😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😘✌🏻 [8/15, 1:05 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _Sak'on gaisuwar nakune yau 'yan group d'in miss xoxo *HOME OF NOVELS & HAMAGEE AND FAN'S*, gaisuwar ku babbace ina godiya da k'auna._ _inayinku wlhy, irin sosai d'innan😍😍😍😘✌🏻_ 2⃣7⃣ Cikin rawar baki data jiki meerah tace, umm...um Anty kubra ina kichin ne, sanyi nakeji shine nadafa shayi nad'ansha a can. Bata jira cewar Anty kubra ba tafad'a d'aki wuff. Haka kawai kubra taji bata yarda da meerah ba, dasauri tamik'e tanufi d'akin nasu. Saidai tana shiga ta iske meerah kwance agado tana hawaye. Kuka kuma? Waike mike damunkine? Naga wannan karon tunda Nazo duk kinwani canja? Kodai wani yafara tsara miki wani abune?. Zaune meerah tatashi, a'a Anty zauna kiji abinda yasakani kuka, wlhy Naufal ne ko! Wai mukai fad'a jiya, shinefa yace wai murabu kawai, nikuma wasu kud'i nakeson tatsa ajikinsa, idanma zamu rabunne saimu rabu, tunda dama kinsan mu rayuwarmu babu doguwar soyayya. Dariya Anty kubra tayi, tace, akan wannan kike 6ata ranki, kwantar min da hankalinki, bayau saura kwana 6 birthday d'in John ba? Kuma yace anan k'asar zaiyi celebration?. Eh Anty. To aranar zan koya miki wani salon dazakiyi maganin iskancinsa, ki gayyatoshi kedai. Cikin murna meerah ta rungume kubra, kekyace murnar gaskiya takeyi, amma a can cikin ranta fad'i takeyi nima aranar zanbaku mamaki aii. Dan nasan dukkan shirin dakukeyi akan Aysha ranar. Bayan fitar kubra ad'akin meerah tad'aga filo tazaro box d'innan, dama tanajin tafiyar Anty kubra tacusashi awajen. K'ark'ashin gadomsu tasakashi itama tafad'a wanka cikin farincikin tasamu nasara. Bayan tafito tad'auki wayarta tayima ya Naufal text message, tana turawa tatshi tahau d'aukar abubuwansu masu muhimmanci tana shiryawa a k'aramar bag. Saida tagama tsince komai tas sanan tad'aukar musu kayan dabasufi seat 5-5 ba suma tasaka awata bag d'in. Kafin Aysha tashigo tagama komai tasaka bag d'in cikin wardrobe nasu. Koda Aysha tashigo bata Sanar mata komaiba, fira sukad'an ta6a Aysha tayi barci, itakuma tatashi tafita fallo kar a d'auka wani abun suke kullawa. Da daddare meerah tashirya tafita club kamar yanda suka saba, Aysha kam barcima tayi kwanciyarta. Bayan kowa yagama kwalliyarsa tarashin mutunci yafita, meerah tadawo gidan, dama tunkan tafita saida tad'auki mataki akan CCTV d'in dake falonsu data k'ofar dazaka fita zuwa titi. Bag's d'inan tad'auka tafita dasu, ya Naufal dake mota takaimawa, yauwa ya Naufal kaje dasu, sauran bayani kuma saimun zauna, insha ALLAH zakaji komai daya angancemu a wannan karon. ALLAH Sarki Naufal sarkin sauk'in kai, murmushi yamata tareda fad'in karki damu, bara nawuce kada wani yadawo cikin 'yanmatan gidan naku. OK. Bayan tafiyar ya Naufal meerah tadawo tad'auki box d'in data d'akko ad'akin Anty glory tamaidashi, danta d'auki abinda takeso aciki. Kuma ficewa tayi bayan tamaida CCTV cemara d'in gidan yanda suke cikin dabara batareda samun wani kuskureba. Fitarta babu jimawa Anty glory da anty kubra suka dawo sukam, Dan meerah ma taga sanda aka ajiyesu amma tad'an 6uya dankarsu ganta. Dukda haka saida Anty glory tace nikam sainaga kamar meerah ta gitta yanzunnan. Kai a'a gaskiya glory, kodai kinsha abinda yafi k'arfin kankine? Cewar kubra. ALLAH sainaga tamkar itane. To ba itabace kuwa, idonkine kemiki gizo kawai. Shiru Anty glory tayi tunda batada hujja. Duk firar dasukeyi meerah namak'ale tana jinsu, saida taga sunshiga gidan sanan tafita daga Inda take 6oye. Kusan atare suka dawo dasauran 'yan gidan, daganan suka Shiga ramuwar barci kuma. _____________________________ Tafiya yakeyi cikin Nutsuwa da k'asaitarsa, kaida kagansa kasan kaga jarumin ma'aikaci, su Samuel na take masa baya. Inda Oga David yake rufe suka nufa, yaud'inma d'akin dund'um yake da duhu, saida aka kunna fitulu masu hasken tsiya. Bak'aramin girgiza nayiba daganin yanda aka maida Oga David, gaba d'aya yafita hayyacinsa, Wanda yasansa ada bazai ta6a shaidashiba ayanzun kam. Khaleel ya zauna idonsa akan Oga David d'in, fuskarnan d'am-d'am babu alamar sauk'i, iska ya furzar daga bakinsa, yad'age gira sama, tareda crossing kafafunsa, cikin muryarsa mairazana marajin magana yace, "David Obiner! haryanzu kana kan bakanka ne?". Dak'yar David ya iya d'ago kansa, idanunsa suna lumshewa da bud'ewa cikin matuk'ar nuna wahaltuwa, maganarma bafita takeyi dak'yauba, yace young man kona fad'a maka babu abinda zaka iya musu, munada d'aurin gidin manya-manyan jami'an tsaro takowanne fanni, harma acikinku, karkaga kasamu nasara akaina kacigaba da walar da kanka dason kama sauran friend's nawa, nima kuskure aka samu, kuma zanfita, kasaka aranka nakusa fita anan gurin, daga wannan lokacin kuma zan nuna maka k'arfin ikona. Murmushi ya khaleel yayi, haryanzu kuma idonsa nakan David, yasauke k'afarsa k'asa yanacigaba da kallonsa, kaikace television yasamu, bindigarsa yaciro a k'ugunsa yana gogata a gemunsa, haryanzu baice komaiba, kallon dai David d'in yakeyi. Su Samuel da youseef ma suna tsaye suna kallon ikon ALLAH, sunsan shirunnan Na J bakomai bane face hasala da zuciyarsa keyi, kuma tabbas yau sai David ya d'an d'anama aya zak'inta.......... Basuko kai k'arshen tunaninsuba sukaji k'arar bindiga da ihun Oga David alokaci d'aya. Babu Wanda hantar cikinsa bata motsaba, amma gogan naku tamkaa bashine yayi harbinba, yawani d'age gira sama yanacigaba da wasa da bindigarsa hankali kwance. Saida David yagama ihunsa da murgina-mirginar azabar shigar bullet ajikinsa yakoma fidda numfashi dak'yar ga uwar zufa daketa kwarara tako ina ajikinsa, kaikace wanka yayo, ga k'afarsa da ya khaleel yaharba sai zubda jini takeyi. My Sweet Friend! Kashirya fad'ane?. Ya khaleel yay maganar yana latsa wayarsa. David da azaba ta Isa yace, "bazan fad'aba, amma tunda kace kai jarumin ma'aikacine mai kwazo akan binciken mai laifi mizai hana naga kwazon naka, kana kiran kanka young tiger amma kakoma kare mai dogara ga uban gidansa, mizaisa ka la6e a bayana wajen nuna jarumtarka, inhar kacika tiger kaje daji domin farauto abincinka, hakan shine zai tabbatarmin kaid'in jarumine, amma cigaba daneman bayanai awajena yanasani kallonka amatsayin kare Wanda kullum sai uban gidansa yanemomasa abincin dazaici". Saida yama David kallon mintuna 4 sannan yamik'e yana wurwura bindigarsa, baicema kowa k'alaba yabar d'akin. David kuma yakece da dariyar mugunta, dukda muryar tasa agalabaice take. Bai waigoba, kuma baice kalaba harya fice, cikin hanzari su youseef suka take masa baya. Koda yashiga office saiya kulle kansa, baya buk'atar kowa yabiyoshi abaya. Zama yayi yakifa kansa saman decks, maganganun David ne ke k'ona zuciyarsa, musammam dayace sunada d'aurin gindi wajen jami'an tsaro daban-daban, lallai biri yayi kama da mutum, (kullum aiki sukeyi dare da rana amma babu wani sauk'i Na raguwar 'yan ta'adda) wasuma koda ankamasu daga baya sai kotu ta ku6tar dasu, kenan manyansune kefiddasu?. Ya furzar da huci abakinsa, tareda mik'ewa yashiga zagayen office d'in, tabbas dolene yacanja taku, domin tsuntsu mai wayo tabaki ake kamasa, baikamata bincikensa yatsaya iya nanba, zai fad'ad'ashi domin samun nasarar burinsa, *CIKI DA GASKIYA....* aii wuk'a bata hudashi, yasan zaitsinci kansa a k'alubale iri-iri, amma tabbas ranar biyan buk'ata aii rai ba'a bakin komai yakeba inji k'uda. Wani malalacin murmushi yasaki, saboda wata mafita da zuciyarsa takawo masa. Ya lumshe idanunsa tareda rumtse hannayensa biyu✊🏻. Yace yeeess!!.. Tundaga nan yafara canja taku, yakoma aikin *Sirri* iya kansa kawai, saikuma amintattunsa youseef, taheer, Joseph, Adams, sukansu bakomai suka saniba. __________________________ Tunda abinnan yafaru da Ngozi da Aysha ta kalleta saitaji kuka yazo mata, tausayi sosai yarinyar kebata, ga matuk'ar tsorata da abin kebata aduk lokacin data tuno yanda john yayma Ngozi kaca-kaca, gaba d'aya tarasa sukuninta, had mafarkin abin takeyi. Idankuwa john yazo gidan aii yanzu zakiga tsoro ya bayyana a idonta, duksai ta rikice tarasa kwanciyar hankali. Wasunsu sukan mata dariya, Damata kallon shirme, ciki kam harda Anty kubra. Idan john yazo gidan haka zaita binta da kallo saikace tsohon maye, itakam daya zoma take shigewa d'akinsu tasaka key, baya binta, Dan acewarsa takusa zuwa hannu, haka kawai kuma bayason takurama yarinyar, saboda jinta yakeyi ajikinsa. Yau takama birthday d'in john, tunda safe su Aysha basu hutaba, suyi wannan suyi wannan dukda bama agidan za'ayiba, awani hotel za'ayi.. Mai kwalliya ta musamman aka d'akko Dan yima Aysha ita kad'ai, abin yabama Aysha mamaki, dama tunjiya Anty glory tabata wata arniyar riga mai k'yau da fidda tsiraici wai tasaka, Aysha zatayi magana meerah ta zungureta Tahana. Yaukuma saiga mai kwalliya tazo, yanzuma Aysha tayi yink'urin yin gaddama amma meerah tahanata, tana kuka ana kwalliyar, harsaida mai kwalliya yagaji yamata magana sannan tadaina kukan, kwalliya tafitar hankali akama Aysha, bama kowane zai iya shaidataba idan yaganta, tayi k'yau saikace aljana, hakama datasaka rigar pink, tayi masifar mata k'yau, saidaifa tafidda mata jiki sosai. Idonta taf da hawaye ta kalli meerah, Anty meerah yanzunan Dan ALLAH ahaka zan fita saikace kafira?. To Aysha yazakiyi? Tunda haka suka za6i kije wajen aii dole kiyi hak'uri kije, kinsan dai banida wani k'arfin hanaki fita haka, amma ga rigar sanyi kisaka asama, idan sunyi magana kisanar musu sanyi kikeji. Tunda lalla6aki akeyi zasu barki da ita. Meerah tak'ara k'asa damurya tace akwai wani Abu mai muhimmanci dazaki d'auka agidannan?. Aysha tace, "Anty kamarya?". Kamar yanda kikaji nafad'a, aii Hausa nayi miki. Shiru Aysha tayi tana kallomta, tarasa wace masifa Anty meerah takoya kwana biyun nan?, amma afili saitace bara naduba. Aysha tagama bincikenta bataga wani Abu muhimmi dazata d'aukaba, hasalima duk taga ankwashe komai, har takardunta Na makaranta daduk wani Abu nata important. Sai around 9pm agogon k'asar suka fito, kowa yashiga motar saurayinta, meerah batada saurayi yanzu kam, kuma tace kada ya Naufal yazo wajen saboda gudun zargi, Anty kubra tace meerah tashigo motarsu. Aysha kam awata had'ad'd'iyar mota aka kaita, Ashe john yana ciki, addu'oi taketa zubawa ga gabanta sai fad'uwa yakeyi. Yayi k'yau shima cikin Suit bak'ak'e, ainahin suffarsa ta bature cikakke tafito, baice ma Aysha komaiba, saidai yakamo hannunta yarik'e, jitai tamkar anjinginata ajikin wuta, sai addu'a takeyi itadai damik'a lamuranta ga ALLAH. Aysha tanada jiki mai k'yau, Wanda bakowane zai ganta yace shekarunta 15 ba, musamman data kasance doguwa babu laifi, komai nata cif yake saboda tana ganiyar girmane. Sun isa had'ad'd'en hotel d'in, wajen daza'ayi komai atsare yake, saida kowa yagama shiga sannan john da Aysha suka shigo, wajen dund'um ankashe fitila, har Aysha tafara tsorata saikuma taga haske ya gauraye wajen tareda ihun mutane, flower's akaita watsa musu masu k'amshi, harsuka isa wajen zamansu, Aysha jitake tamkar tayi kuka. Duk abinda ke faruwa idon meerah nakan Aysha. Biki yacigaba da gudana, yayinda aketa shaye-shayen giya damasu shak'ar cocaine da sigari, john saifama da Aysha yakeyi tasha wani Abu tak'i, daya d'auki kofin giya zaika bakin Aysha sai meerah ta dallama Aysha harara, da sauri Aysha take kauda fuskarta tak'i sha, k'yaleta yayi tareda kiran abokinsa gefe. Su sukasan misuka k'ulla, meerah kuma duktana kallonsu, dama tabama Aysha waya, tatura mata message da hausa. Aysha naganin haka tagyad'a ma meerah kai, idonta tab da hawaye. Wajen around 12 waje yakacame anata rawa, wasu duk sungama buguwama, hannun Aysha narik'e Dana john kaikace tare aka haliccesu, itadai Aysha binsa kawai takeyi tamkar rak'umi da akala, duk gift d'in da akabama john saiya mik'ama Aysha ta ajiye, ana haka sai akaga waje yayi dud'um ankashe wuta. Tsorone Yakama Aysha yayinda taji andamk'i hannunta Na dama, Na haggu kuma john yana rik'e dashi, karki damu nice, kiyi dabarar dazaki kwato hannunki wajen john. To Anty, Aysha tafad'a jikinta narawa, Aysha tad'an matsa jikin john, murya k'asa-k'asa tace baby bara nacire takalmina nagaji dashi. OK yafad'a yana sakin hannunta. Aii yana saki meerah taja Aysha suka fito da hanzari, sai k'utsawa sukeyi cikin jama'a. John kuma tuni ya damk'e hannun wata yarinya atunaninsa Aysha Ce, (dama shine yasaka akashe wutar, Dan soyake yad'auke Aysha yakaita wani d'aki, bayan ya shak'a mata cocaine). Da sauri yashak'ama yarinyar cocaine, atunaninsa Aysha Ce, cak yad'auketa yafice. Su Aysha kam ALLAH ya tsaya musu sunfito daga wajen, saidai kuma security suka taresu, saboda ganin yanayin dasuka fito arikice. Sai magiya sukeyi ank'i barinsu, ga ya Naufal sai kiran meerah yakeyi akan suyi sauri time yakusa cika. Hazbinallahu wani imal'wakil, kawai Aysha ke ambata, cikin kuka meerah take rok'onsu akan ayshace takeda wani ciwo zai tashi, shine zasuje asibiti, su taimakesu please. Ganin Aysha Na kuka, kunsan bature da tausayi, saisuka barsu suka fito. Motar da ya Naufal yazo suka k'arasa wajen da Sauri, amma cikin ilimi sukayi abin, dankar aganesu, saboda lamarine Na CCTV camera ako ina su'acan turai. Suna shiga motar suka fara hango mutane ana fitowa, da'alama su ake nema, saboda sunga Anty glory da john sunama Security bayani. Da sauri Ya Naufal yaja motar yabar wajen. A can kuwa john nad'aukar yarinya wadda yakema zaton Aysha yafita, sai aka kunna fitila, saida yashiga d'akin daya tanada domin keta haddin Aysha sai yayi tozali dawata tsohuwar budurwarsa, wadda tun zuwansu wajen ya ganta, dama itama tana Neman hanyar dazusu had'une da john, amma yanata shareta, saboda aganinta yasamu Aysha, ganin fitilar wajen tamutu shine tasamu damar matsowa gareshi, shikuma baimasan itad'in baceba. Jefata yayi saman gado kawai yadawo hall d'in da hanzarinsa, Neman Aysha yafarayi, Anty kubra tagansa ta tambayesa, yasanar mata halin da'ake ciki. Daga nan suka fara Neman Aysha, saidaga Bayama suka farga babu meerah, Anty glory tace suje waje, dama taga tun d'azun Aysha da meerah namaganar kurame, wannan dalilin ne yasakasu fitowa har wajen security. Sukuma suka tabbatar musu sunga su Aysha, kuma sunfita yanzunnan za'akai d'aya aciki asibiti batada lfy. Duk sun d'auka gaskiyane asibitin su meerah suka tafi, Dan basu ta6a tunanin meerah zata iya guduwaba. Mota suka shiga suka nufi asibitin dasukanga likita idan matsala tafaru da d'ayansu. Su meerah suna hango motarsu alokacin, saboda ya Naufal yatsaya saya musu wani Abu. Yana dawowa motar meerah take sanar masa taga su john sun biyosu. Murmushi yayi yace, 'karki damu bazasu ganemuba, tunda basusan motarba, ammafa gaskiya dolene kamar yanda muka tsara gobe kuwuce Canada, abokinama yagama muku komai, Dan haka gobe dawuri zaku tafi insha ALLAH. nima nanda 2days zan biyo bayanku. John yanada kud'i sosai, Dan haka zaibi duk hanyar data dace wajen nemanku, kuma zuwa nanda kwana biyu kacal zasu fahimci kun gudu. Hakane ya Naufal mungode sosai da taimakonka akanmu. Sai alokacin Aysha tafahimci halin da'ake ciki. Kuka kawai ta6arke musu dashi saboda tsabar farincikin wannan taimako Na bayin ALLAH, ta tabbata domin ita suketa wannan k'ok'arin. Harsukaje gidan ya Naufal tana kuka, sukuma suna aikin lallashi. Bayan sun huta Naufal yakira dadynsa yamasa bayani akansu Aysha kamar yanda yasani, mahaifinsa mutumin kirki yace babu damuwa, aii d'a nakowane, yadaiyi k'ok'ari subaro k'asar kam gobe idan ALLAH yakaimu saboda gudun matsala Naufal yace to Dady. Duk yanda sukayi da dadynsa saida yasanar musu, sunyi murna sosai damasa godiya. Yace karku damu, ayanzu baikamata kukoma Nigeria ba, Dan acan sunada d'aurin gindin yin duk wani 6arna, abune maisauk'i suganoku. Kuyi hak'uri kuzauna a Canada zuwa wani d'an lokaci saiku koma gida. Sun yarda da maganarsa, Dan haka suka masa godiya kuwa. Aranar daga Naufal har meerah da Aysha kwana sukayi akan sallaya suna mik'ama ALLAH kukansu da godiya agaresa. Washe gari tunda wuri suka fito zuwa airport, dama kayansu ya Naufal yaturasu tun kwana biyu dasuka wuce, tunda shima yana shirin barin k'asarne. *_airport_* A airport bayan kammala komai su Aysha suka samu shiga jirgin farko dazai sauka Canada. Shigarsu babu dad'ewa Naufal ya hango john, da'alama wani abunne yakawoshi airport d'in. Cikin sauri ya Naufal ya6uya. Amma yana kallon duk wani shigi da ficinda john yakeyi a airport d'in. Hankalinsa yakai k'ololuwar tashi alokacinda ya hango john da Security d'in airport d'in biyu sun nufi cikin jirgin dasu Aysha ke aciki.........✍🏿 😬 *_Nima ya Naufal atsorace muke nida masu karatu._*😰 I love you all😘😘😘😘✌🏻 [8/16, 6:32 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 2⃣8⃣ A k'ofar jirgin yatsaya domin yazone wajen wani abokinsa Captain ne, shinema zai tuk'asu Aisha zuwa Canada. Gaban meerah ne yafad'i alokacin data hangi john, mayafinta takuma ja tarufe fuskarta sosai, dama Aysha barcima takeyi. Abokinsa yak'araso suka gaisa cikin rungume juna. John yatambayesa ko akwai jirgin dazaije Africa a yau?. Kai a'a gaskiya, inagama gaba d'aya week d'inan babu wani jirgi dazaije Africa, amma next week akwai mai zuwa Africa, zai sauka Nigeria babban birnin k'asar Abuja. Murmushi yayi yace OK, inason sanin list d'in masu tafiya aranar, zanshigo kafin jirgin yatashi. OK babu damuwa. Ya Naufal na'a wajen 6uyansa yahango fitowar John, ajiyar zuciya mai k'arfi yasauke, tareda fad'in *_Alhamdullahi alah kulli'halin!_*. Saida ya tabbatar john yabar airport d'in sannan shima yatafi. Kaitsaye gidansu Anty glory yanufa. A k'ofar gidan ya iske motar john. bayan yayi Knocking d'in k'ofar besi tabud'e masa, cikin mamaki take kallon Naufal d'in, shikuma yafuske abinsa yana tambayar ko meerah na nan?. Besi tace aimuma nemansu akeyi, harma ana shirin zuwa gidanka ko sunacan. A tsorace ya Naufal yace banganeba? Inasu meerah sukedashi bayan nan?. Anty glory datakejin zancensu sama-sama talek'o dantaga wanene?, ganin Naufal ne tace Kaine? Dama su meerah basa tare dakai?. Wai wane zance kukemin hakane? nifa kuna wani juyamin tunani, Ku warwaremin abinda ke faruwa mana. OK kashigo to, Anty glory tafad'a dan hango gaskiya k'arara atareda Naufal. Sunmasa bayanin duk abinda yafaru, yayinda Naufal yanuna matuk'ar shiga tashin hankali, yace shin yanzu duk inda suke zuwa anje basa nan?. Duk anje, mu munma fara zargin kodai sun gudune? yanzu haka daga airport nake, amma an tabbatarmin babu wani jirgin daya tashi zuwa Africa a yau. John ne dake zaune yanata kora giya yayma ya Naufal wannan bayanin, daka gansa kasan yana cikin damuwane. Dan john bak'aramin so yakema Aysha ba, baima San yana sonta da gaskiyaba sai ajiya data ku6ce masa, babban tashin hanaklinsa karsu tona masa asiri, tabbas kashinsa yagama bushewa kawai. Ya d'aga kwalbar giya gaba d'aya saida ya shanyeta tas sannan ya ajiye. Ya Naufal ma duk yanuna matuk'ar tashin hankalinsa, su Anty kubra sai lallashinsu sukeyi daban hak'uri, suna karfafa musu guywar za'a gansu, dansu meerah basuda Samar Baron k'asar su kad'ai. A can k'asan zuciyar ya Naufal kam dariya kawai take cinsa, dannewa kawai yakeyi. *_Canada_* Jirgimsu Aysha yasauka a Canada, Dady Momy da k'annen ya Naufal uku sukazo tarbar su meerah. Basuwani sha wahalar ganeauba, saboda matuk'ar kama da ya Naufal keyi da dadynsa, suma su Dady ya Naufal yatura musu hotunansu Aysha, danhaka suka ganesu dawuri. Tarba ta mutunci suka samu awajen iyayensu Naufal, mahaifiyarsa baturiya k'yak'yk'yawa, hakama k'annensa duk kama suke da ita, shikad'aine yake kama da babansa. Komai cikin tsari yake agidansu Naufal, sosai tsarin familie nasa yabirsu Aysha, al'amuransu akwai fahimtar juna kam, ga komai cikin ilimi, saidai sunkula akwai k'arancin kula da addini ga mutanen gidan, dukda mahaifiyarsu Ya Naufal ma ta musulunta. Ifteehal k'anwar ya Naufal ta uku, itace sa'ar Aysha, shekarunsu d'aya, saidai banbancin launin fata da yanayin rayuwa, Dan ifteehal tanada girman jiki babu laifi 'Yar lutiyace, amma bawai sosaiba. Baradai namuku gwari gwari, gidansu ya Naufal su 7 ne, dadynsu momynsu sai ya Naufal shine babba, sai Maheer, Ifteehal, Safwan, Iklaas. Akwai k'aunar juna kam tareda jama'ar gidan, komai nasu abin birgewa daban sha'awa. Mahaifiyasu ya Naufal (Momy) akwai kirki, tajawo su Aysha jikinta sosai yanda zasuyi sabo dasu. Bak'aramin tashin hankali su Anty glory suka shigaba alokacin dasuka gama bincike d'akin su Aysha kaf, sunkwashe dukkan wani Abu Nasu mai muhimmanci, wannan yana nuna alamar tabbas sungudu. Wata takarda Anty kubra taci karo da ita k'ark'ashin filo, da hanzari ta d'auka ta warwareta. Kowa yay shiru ana sauraren abinda ke ciki. _Kar ku nememu. domin bazaku ta6a Ku samemuba, munbarku har Abadan, mun muku nisa, abinda kuma kuka aikata akanmu, munbarma ALLAH ikonsa, yafimu sanin yanda zaiyi daku._ _Ku sanarma Naufal ma ALLAH yaymasa sakamako da abinda yamana, Dan ubangijinmu yafimu sanin abinda ya cancanta ga mutane irinsa._ Wannan shine kad'ai abinda ke'a rubuce. Jikin kubra da glory sai rawa yakeyi, john kam aii ya daskare a zaune, ayanzu kam yadaina zargin Naufal d'in, danshi da gabad'aya zarginsa yanaga Naufal, harma yasaka wasu mutane sufara bibiyar Naufal. Ashe bashine yataimaki su meerah ba, to wanene ya taimaka musu? tabbas da taimakon wani suka gudu, kuma yanada tabbacin basubar k'asar nanba, suna aciki tabbas, lallai yad'auki alk'awarin nemosu, yana samunsu kuma kashesu zaiyi kawai. Mutanen dayasa suringa bibiyar Naufal yakira, yace subarsa yajanye aikinsa akan Naufal d'in. Glory kam da hanzari tanufi d'akinta tafara binciken box d'in datake Tara dukkan bisar yaran da'aka kawo, jikinta rawa yafarayi alokacin datayi tozali babu ta Aysha da meerah, jitayi jiri kawai naneman kwasarta k'asa, tayi saurin dafe gado tazauna k'asa ragwaf. A wannan halin kubra tazo tasameta, dasauri ta'iso gareta tana tambayar ba'asi. glory bata iya bata amsaba, sai tura mata box d'in tayi gabanta. Itama bak'aramar razana tayiba, lallai kam lik'insu Na gab da 6ulewa, dolene ad'auki matakin gaggawa kafin komai ya lalace. Waya ta d'auka tashiga kiran duk wani mai fad'a aji a k'ungiyarsu, ta tabbatarma kowa da guduwar su Aysha daga hannunsu. Dayawansu hankulansu yatashi, kuma sun fara haramar d'aukar mataki. Nace to ALLAH Na nan aii.😰 ______________________________ Dan ALLAH Alhaji kafahimceni mana, ai wannan abin kunyane, kana haihuwa 'ya'ya Na haihuwa. Nifa ALLAH inajin kunya. Murmushi baffah yayi, idonsa kam akan mama, yace fad'ima kenan, nikam azatona murna zakiyi da cikinnan, amma sainaga sa6anin haka daga gareki. Nikuwa kinga yanzu babu wani abinda yake sakani farinciki kamar natuna kinada ciki, zaki haifamin yara, koba komai zanga k'ananun yara nima agidana, nad'auka nayi farinciki. Humm duk yarannan har 22 da ALLAH yabaka baka godeba kenan, kuma duka shekararsu Nurridden nawama? Basufi 5-6 bafa, aibasukai girman daza'ace anfara kwad'ayin k'ananun yaraba. Haka kike gani dai, Dan ALLAH mubar zancennan, kinsandai da hankalina da girmana bazan amince kizubarmin da cikiba, inason kayana, dukda inada yara 22 bawai nagaji da haihuwar baneba, matannan duk tsaida haihuwarsu sukayi saboda rad'in Kansu, bada kuma yawunaba, Bilkeesu Ce kawai naga yakamata tahuta saboda wahalar datasha a haihuwar Tasleem da Ummunoor, nace a tsaida haihuwar alokacinda ta haifi Ummunoor, daga bayama kuka taitamin akan tanaso itadai tacigaba da haihuwarta, da k'yar nasamu tahak'ura, shima saida likitan yamata bayanin illar da rashin hutawar zai haifar mata sannan. Amma kinga laura dakanta tatsaida haihuwarta tun aihuwar 2wins, hakama Saudah. To kekuma ALLAH yabanike maimakon kicigaba da haifamin saikice a'a, ina son cikina, kuma banason kik'ara min wata magana akansa wadda zata iya kawomana 6acin rai. Shikenan bazan sakeba, amma gaskiya nikam inajin kunyar rainon ciki acikin manyan 'ya'yanmu. Abin yaso bama baffa dariya amma saiya dake, 'yace OK babu damuwa, saiki shirya mutafi Turkey kawai bayan bikinsu Sultan, idan kika haihu saimu dawo. Shiru mama tayi tana nazarin maganar, ganin haka baffah yace nabaki dama kije kiyi tunani akan hakan...................✍🏿 Mama Ashe zamusha suna, ALLAH yaraba lafiya😂😂😂😂, su Aysha za'asha k'anne🤣. *_l love you all_*😍😍😍😍😍✌🏻. [8/16, 6:32 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 2⃣9⃣ Gaba d'aya su john sungama tada hankalinsu wajen Neman su Aysha, harda ya Naufal amasu Neman, duk inda ake tunanin zasuje anje, amma babu koda labarinsu, hargisansu Ariana k'awar su Aysha, itama saida taji babu dad'i, dantana k'aunar Aysha sosai, amma tabbas tasan wata rana zasu had'u. Ranarda aka sanarmai jirgi zaije Nigeria tunda wuri yaje yatare a filin jirgin, duk wani shigi da ficin fasinjoji a idonsa akayi, har aka gama komai jirgin yatashi baiga komai kama dasu Aysha ba. Wannanma yak'ara tada hankalinsu sosai. +++++++ Su Aysha kam suna Canada hankalinsu kwance, komai suka buk'ata suna samunshi, babu tsangwama bare k'yara, basu 6oye komaiba kuma alabarinsu, sun fad'ama Dady komai, yakumayi alk'awarin taimaka musu. Sannan yace, "zai madasu makaranta, Dan iliminsu shine zaizama makamin daxasu kar6o 'yancinsu harma da sauran yaran dasuke cikin irin halin da aka sakasu. Su Aysha sunyi matuk'ar farinci da hakan, sun d'auki Dady tamkar mahaifinsu, kuma suna k'ok'arin gyara tafiyar addinin yaran gidan, dansuga sunada k'arancin kulawa anan 6angaren. Sosai Dady yaji dad'i, Dan dama Naufal ne mai k'ok'arin hakan, tokuma aiiki yamasa yawa ayanzu. _____________________________ Bikinsu Sultan da Mujahedeen nata gaba towa, yayinda cikin mama keta k'ara girma, amma tanata k'umshe kayanta bataso asani. Batasan tuni Ammah tafargaba, Dan haka taketa bata kulawa, sosai lamarin yarink'a bama mama kunya, danta lurama kamar kowa yasan tanada cikin agidan. Dan sosai hajia babba ke nuna mata k'arin k'iyayya da tsana. Ko kad'an bata kulata, ita kanta hajia babba tsoron mama takeyi sosai tundacan barema yanzun, duk dai sanda suka had'u sai hajia babba tayima mama habaici, wai abin kunya tsofai-tsofai mama tayi ciki. Tun abin nadamun mama harya koma bata dariyama. Koda aka shiga hifimar bikinsu ya Sultan mama itace akan komai, babu laifima umme Amarya nad'an saka baki awasu al'amuran. Komai anyishi Na girma da arzik'i, ansha bidiri sosai da bired'e. Tundaga randa aka d'aura auren ya khaleel yabar gidan, Dan bayason adameshi da surutun k'annensa sun rigasa aure, duk da dama shican bai bama dangi fuskar wasa dashiba. To bikidai yatashi lfy, ankawo amare anan cikin gidan, dagacan baya baffah yasayi k'aton fili da dad'ewa ya ajiye domin 'ya'yansa, duk Wanda yatashi aure saidai yad'iba nasa yagina, Dan anraba musu tuni, akwai katanga tsakaninsu dasu ainahin cikin gidan, sai akayi k'ofar dazata sadaka danan cikin gidan baffah, yayinda gate d'in gidan yake a can baya, saiya kasance layinsu daban-daban. Bayan biki babu dad'ewa baffah yad'auke mama suka lula k'asar Turkia. Bazasu dawoba saita haihu. +++++++++++++ A UK kam su john harsun fara sanyi daneman su Aysha, wannan yasaka ya Naufal tattara inasa-inasa yamusu sallama yadawo Canada. Alokacin su Aysha harsun fara University hankalinsu kwance, kasancewar Dady lecturer ne a makarantar. Sosai su Aysha suka dage, Dan Canada suna amfani da yare biyu ne, English & French. Sosai sukayi murna da dawowar ya Naufal kusafasu, yakwashe komai yabasu labari bayan barinsu islands UK, sunsha dariya sosai, wani gurin kuma su John sukansha tsinuwa. ____________________________ Rayuwa tashud'a sosai, abubuwa nata gudun fanfalak'e, tuni mama ta haihuwa 'yan uku duk maza, bak'aramin farinciki wannan familie suka shigaba, idan kacire hajia babba datakeji kamar ta 6atar da mama da 'yayanta, wad'anda sukaci sunan baffa, da Baban mama da Baban baffan. *_Rufa'ee (khalefa), Dawud (Affan), Abdallah (Adeel)_*. Yara harsun fara wayo abinsu, kowa sansu yakeyi agidan, kasancewar sune k'anan. Amma banda 'yan 6angaren hajia babba. Ya khaleel ne kawai babu ruwansa, shidama baya raba d'ayan biyu. Kowa nasane agidan, yana bama su mama girmansu, yana k'yautatama k'annensa da iyayensa, yana nan har yanzu baya d'aukar raini. #### Suma dai su Aysha karatu natafiya musu yanda yakamata Alhamllah kam, Aysha ank'ara girma sosai, tazama big girl abinta, yanzu tana shekara ta 16, takusa shiga 17. Amma idan kaganta saika d'aukama takai 18 saboda jindad'i da kwanciyar hankalinsu data samu, takanyi tunanin gida, wani lokacin takansha kukanta saboda kewar su mama da 'yan uwanta, meerah da ifteehal sukan lallasheta danuna mata ladan mai hak'uri, aganinsu aii komai yazo k'arshe, tunda Dady yace dasun kammala karatunsu nanda shekara 1½ dakansa zai maidasu Nigeria, wannan yasama Aysha tak'ara maida hankalinta sosai ga karatun. Bata kula kowa, Dan it's ko aboki namiji batashi a school, inhar baka ganta tareda ifteehal ba to zaka ganta tana karatu ko latsa waya, Maheer ne kawai Aysha take sakewa dashi bayan Naufal data d'auka amatsayin babban wa. Son ya khaleel kam yana nan mak'ale a zuciyarta, kullum k'ara girma yakeyi dasakin rassa, amma ta danne kayanta bats amince kowa yasaniba. Meerah da ya Naufal kam soyayya mai k'arfi tashiga, 100% iyayensa sun amince masa ya auri meerah. Acewar Dady aii zaiyi jihadi ne, kuma meerah ba it's tasaka kanta a wannan halinba. Kiwa yayi farinciki da wannan had'i, karfa Sholy da ifteee da maheer suji labari, sosai suke arinciki. *_bayan shekara 1_* Aysha sanye cikin bak'in dogon wando, ta d'ora jar riga wadda takai mata har guywa, hakama rigar sanyinta ja mai k'yalli, tayane siririn bak'in gyale akanta, sosai tayi k'yau, danta k'ara girma da cikar hallita, komai nata Na babbar mace yagama bayyana. Ya Naufal daya fito daga d'akinsa yace oya lil sholy ina iftee kuzo Na saukeku inada wajen zuwa. Kai ya Naufal, nikam tunda bikinku yamatso kaida Anty meerah duk kunwani rud'ar da kanku, idan sauri kakeyi kabamu key d'in kawai mutafi. No kumuje Na ajiyeku kawai, idan kuma zaku jira maheer ne to nawuce abina, dadyma yau bazaije aikiba. Tab broth munada exams fa yau, inamu inajiran sarkin barcin can. Iftee dake fitowa saga d'aki tafad'a. Gaba ya Naufal yayi abinsa, tofa zanwuce abina. Da Saudi sukabi bayansa. Tunda suka shigo makarantar yau gaban Aysha keta fad'uwa, ga girarta ta dama sai harbawa takeyi, addu'oi taitayi azuciyarta. Kasanceaar itada ifteehal kiwa da abinda yake karanta yasa basa tare ayanzu. Gama exams d'insu kenan Aysha tafito amatuk'ar gajiye, tafiya take kamar zata fad'i, ga yunwa, class d'in su ifteehal tanufa Dan bata iya cin abinci saida ita, tunda tazo school d'in batada k'awa sai ifteehal, sauran duk k'awayen hello hii ne, garama wata 'Yar Nigeria mai suna Khursum, itama bawani sakin jiki ayshan tayi da itaba, saboda tsaro, Dan haka kawai halayen Khursum d'in basa birge Aysha, kullum kuma Anty meerah tana nuna mata tayi taka tsantsan da mutane, saboda tasan su John bawai sun daina Neman su baneba. Kan Aysha ak'asa tana danna waya domin kiran ifteehal saitaji kawai tayi karo da Abu. Da sauri tad'ago tana kallonsa, fad'uwar gaba, tsinkewar zuciya, daskarewar jini duk suka riski Aysha alokaci d'aya. Cikin mamaki take kallonsa, ko'a mafarki bata ta6a tunanin ganin mai kama dashibama awannan lokacin........... ✍🏿 *_kowaye Ayshar tagani?.🤔_* *_I love you all_*🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻😘😘😘. [8/17, 10:10 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _Alkairin ALLAH ya iso agareku 'yan group d'in *MAMAN SHUEIM NOVELS & MAMAN SHAHEED FAN'S & UMMU NOOR NOVELS WORlD* ina godiya sosai da k'auna._. _bilyn Abdul tana yinku_😄🙌🏻 😍😍😘😘 3⃣0⃣ Sanye yake cikin suit blue, sunyi masifar yimasa k'yau, k'yawun haibarsa da nagartaccen annuri yana nan, babu abinda ya canja agareshi. Saima k'yawu da kwarjini dataga yak'ara mata, fuskarnan ad'aure tamau kamar yanda tasanta ashekarun baya. Kallon ido cikin ido sukaima juna, kowannensu saida tsigar jikinsa ta tashi, Aysha tayi azamar janye dara-daran idanunta daga kallon rikitattun nasa. Bakinta yamata nauyi, tama rasa mizata furata, farin cikin ganin ya khaleel zatayi kokuma kuka? wanne yadace agareta arin wannan ranar?, gata ga abin sonta Wanda baimasan tanayiba..... Maganarsace takatse mata tunaninsa, muryarnan tasa maisaka marajin magana nutsuwa tadaki dodon kunnenta, cikin harshen turanci yake maganar, dan baimayi zaton yarinyar tasan wani yare hausaba a duniya. K! hankalinki yana a tsakkiyar kaine dabakisan abinda ke a gabankiba?. Ba halin Aysha ne rashin kunya gana gaba da itaba, amma a yau saita samu kanta da murgud'ama ya khaleel d'in baki, tana magana k'asa-k'asa cikin k'unk'uni. Da Hausa takeyin maganar, amma bayajin mitake fad'a, saibakinta daketa motsawa ya tsirama mayun idanunsa. Bata ankaraba taji anbige mata baki, hannu tasaka da sauri tadafe bakin nata saboda zafin dataji ya ratsata, kafin kacemi hawayen sunfara gudun zirnaniya a kumatunta. Yaja siririn tsaki yana hararta, saida yara6a ta gefenta zai wuce sannan yace, ''gobema kisake ma wani rashin kunya". Wlhy ALLAH ya isana, Aysha tafad'a cikin harshen Hausa. Tsayawa yayi cak daga tafiyar dayakeyi, baiji mitaceba, amma saiyaji tamkar Hausa tayi, kai kodai kunnenane yajiyemin k'arya?. Ya khaleel yafad'a yana waigowa inda Aysha take. Saidai tuni tayima nisa dawajen, amma kamar ance tajuyo, saigata ta waigo, suna had'a ido tamasa gwalo dasaka hannayenta a kunne kamar yanda yara keyi idan Suna tsokanar 'yan junansu😂. Da d'an gudunta tashige bayan wasu samarin d'alibai ta 6uya. (Ho Sholyn Anty meerah🤣🤣🤣) Samun kansa yayi dasakin murmushi, tunda yake baita6a had'uwa da shashashar yarinya irin wanga d'iyaba, yakuma Jan k'aramin tsaki tareda juyawa yacigaba da tafiya, har sannan murmushin yakeyi Wanda shikansa baima San namiyeba. Aysha naganin yatafi tafito daga gun 6uyanta, wani nishad'i nadaban takeji ayau d'innan, tadad'e batayi farincikiba a rayuwarta, wai yau itace tareda ya khaleel, tabbas tasanma bai ganetaba, to yama za'ayi yaganeta, tunda ko'a wancen lokacin bawai ta Isa yawani tsaya kallonta baneba, ita tundama take dashi basu ta6a kallon ido cikin idoba sai yau, ta lumshe idanunta tanamai tuna kwayar idon ya khaleel d'in maicikeda kwarjini da abubuwa masu wuyar fassara ga ma'abocin kallonsa. Tasanma yanzu yadad'e dayin aure, k'ilama harda 'ya ko d'a, jitai wani bak'in cikin ya soki k'irjinta, taja tsaki tana fad'in yoni INA ruwanama da aurensa mtsowww. Kekam wakikema tsuk'a?. Cewar ifteehal data iso wajen Aysha da idanunta ke a lumshe har yanzu. Da Sauri Aysha tabud'e idonta, tab yaushe kikazo?. Yaza'ayi kisani, nifa sometimes kina bani mamaki, kina Acting like mai soyayya wlhy, shin kodai kinfad'a tarkon wanine a k'asar tamu?. Harara Aysha tazabgama iftee, a'a Auren wani nakeyi k'arewar soyayya, ni muje muci abinci yunwa nakeji parrot kawai. Tsaki iftee tayi, tayi gaba tana fad'in ai gwamma dani parrot ce, kekuma dutsi ko?. Aysha tayi murmushi, Dan tasan ifteehal tashaki haushine, bataso ayshar nace mata parrot. Gaba d'aya yau duk Wanda yaga yanayin Aysha yasan tana cikin farinciki, harma mom takasa hak'uri ta tambayeta. Aysha tace lah babu komaifa mom exams d'in yaucedai tayi dad'i sosai. Meerah dake zaune gefen mom dama suna list d'in abinda zasu Sayo Na shirin bikin ya Naufal d'in da meerah sukeyi. Ta kalli Aysha tana nazarinta, ko kad'an bata yarda da zancen Na Aysha ba, zuwa yanzun kam saidai tabama wani labarin Aysha amma badai abataba. Itama ayshar ganin kallon da Anty meerah kemata yasakata mik'ewa tashige d'akinsu itada ifteehal. Mirmushi kawai meerah tayi, tacigaba da abinda takeyi. ______________________________ Taheer gobe idan ALLAH ya kaimu zamubar k'asarnan, Dan bincike ya tabbatarmin yarinyar ba d'iyarsa baceba, amma akwai yarinyarsa wadda matarsa tarasu tabari tana nan America Tana karatu, kuma daga nan Canada yawucene Domin dubata itama. Ayanda ita wannan yarinyar take nunamin kamar d'iyar tasa batajin magana, so babbar hanyar dazamu sami bayanai akansa sosai shine d'ayanmu yayi soyayya da yarinyar ta kwana goma kacal. OK Na fahim ceka, amma ina ganin awannan fagen kaiyakamata kataka rawar gani, Dan babu macen dazakace kanaso bata sokaba, saboda yanayin k'arancin lokacin damuke dashi. Harara ya khaleel yasakarma youseef, amma bakada hankali alhaji, kaima kasan wannan ganganne wlhy. Dariya suka yi suduka, Taheer yace, "boss ALLAH kuwa gaskiyar youseef, kaine kawai zaka samu damar samun zuciyarta cikin k'ank'anim lokaci, Dan nasan wlhy tun a zuwan farko zata amince maka. Indai sainine zanyi soyayya da yarinyar nan to Ku tabbata bazamu kama Alhaji Alasan kwangila a nanba kuwa, kuma wannan itace damarmu ta k'arshe akansa. Taheer kaine zakayi soyayya da ita. Yana gama fad'a yatashi yashige d'aki. Binsa kawai sukayi da kallo suduka, Taheer ya sauke ajiyar zuciya yana maida kallonsa ga youseef, anya kuwa j yanada lfy youseef?. Miyasa kace haka kaikuwa Taheer?. Gani nayi ko kad'an mata basa agaban j, tunda nake dashi banta6ajin yayi hirar maceba wlhy, kaduba yanda mata ke mutuwa akansa ammashi ko kallon arzik'i basu isheshiba, yakai lokacin dazai buk'aci mace kusa dashi amma banta6a ganin j yarik'e hannun wata yarinyaba ALLAH kuwa. nida kai duk muna Neman mata, amma koda wasa wannan harkar bata ta6a birge j ba, saima fad'a dayake mana akullum akan muji tsoron ALLAH. Humm hakane gaskiyarka Taheer, ALLAH bazan 6oye makaba abin nadamuna, Dan sosai ina k'aunar j, inajinsa tamkar d'an uwana najini bawai aboki ko oga a wajen aikiba kawai. d'azu damuke jiransa amota cikin makaranta, sainaga kamar yatsaya da wata yarinya. Ashe ka kula, nima nagansu, nadaiyi shirune kawai, amma nasan koda zamu tambayesa yanzu zaice babu komaine kawai. Mugwada tambayar tasadai to, idan mun samu amsa to, kasansa maganarma ta kud'ice awajensa. Dariya Taheer yayi yace Oga J kenan, shidai komai nasa yanada banbancin tsari dana sauran jama'a. Ya khaleel kam wanka yakeyi hankalinsa a kwance, saidai tunanin yarinyar data masa gwalo yakasa barin zuciyarsa, murmushi yaketa saki aduk lokacin da zuciyarsa ta tariyo masa murgud'a bakin data masa da gwalo, ahankali ya furta mara kunyar banza kenan, ya ture tunaninta da k'arfin tsiya ya maye gurbinsa dana Alhaji Alasan kwangila, wanda sukebi tundaga Nigeria domin son kamashi, yaja wani dogon tsaki, a zuciyarsa ya furta kazo hannu aii insha ALLAH, duk Wanda yafad'a tarkon Ibraheem Abdallah dama yad'auka yagama shiga uku kawai. Yasaki lallausan murmushinsa dasai yagadama yakeyi yana saka rigar wanka pink. Haka kawai yakejin nishad'i tun lokacin dasuka had'u da yarinyar nan, shirmenta yayi tasiri a zuciyarsa, batareda yasan daliliba. ____________________________ Momy nifa maganar gaskiya zantaho da matarnan idan zamuzo meeting na k'arshen shekara. Babu damuwa Zuwairah, kitaho da itad'in, aii yanzu komai ya wuce. Alhmdllh, wlhy nikam dama ta isheni. Kai zuwairah, nibansan lokacin dazaki fara son mutaneba? Daga ke har mijin naki halinku d'aya, gashinan kun koyama yaranku kuma. Hhhh kai Momy ALLAH kinbani dariya nikam, ammafa kemad'in haka kike. Yauwa wai kuwa Momy bazakima khaleel magana yayi aurebane? Kidubafa har matan su Sultan sun haihu, gashi ana shirin yima Mufeedah aure itadasu Amal, shi koniyyar auren ma baida ita. Kinsandai halin Ibraheem sarai, amma idan kukazo wajen meeting sai ataru amasa magana, damage hajia Salma NATA damuna akan d'iyarta Abeeda, kinga saimuji idan yanada ra'ayinta, Dan Nima namasa sha'awar yarinyar k'yak'yk'yawace. To shikenan, ALLAH ya kaimu lokacin, yasa kuma ya amince, kinsandai mird'ad'd'en halin d'an naki aii. Shukurah tacemin dayaje k'asar yaje har gidanta, nace taci gari. Gaskiya kam, aidama ki lura shida Shukurah suna d'asawa, saboda halinsu Na kamancece niya da juna, 'yar banzar yarinyar nan dana fad'a mata auren babanku cewafa tayi ALLAH yasanya alkairi. Hhh kema dai Momy miye nama fad'a matan, kinsan dai Shukurah banza ce walhy. Barta aizatazo ta iskeni, harda wani turo kayan jarirai wa makirar matarnan Fad'ima. Dan ALLAH Momy da gaske?. Wlhy kuwa, Ashe ban fad'a mikiba alokacin. Kin manta baki fad'aminba, lallai Shukurah, amma yarinyarnan batada hankali, wai yaushema tasanta dahar tayimata aike?. Yo saita Santa, ai zanma tufk'ar hancine, baradai tazo k'asar. Shike nan Momy, bara nabarki kigaida autocinki. To zasuji sai anjima. Momy ta sauke waya tana cigaba da mitar cima mama mutunci, su Mufeedah sai k'ara tunzurata sukeyi. (Nace ALLAH ya k'yauta dai). Falo nafito inda mafi yawancin yaran gidan suke, su Amal da Shuhuda sai matan su ya Sultan, Abashiyya da Ummu-Ayman, Hamdiyya da Naseeba suna Jigawa sunje gidansu. Sai Tasleem da maleeka, hira suketayi abinsu hankali kwance, sai dariya sukeyi, daka gansu kasan suna cikin nishad'i. Musleem yafito daga d'akin mama d'aukeda Affan daketa tsula kuka, sai cillashi sama yakeyi yana ca6ewa danyayi shiru. Aymana matar Mujahedeen tace, "wlhy Musleem kada ka kado yaron nan k'asa, Anty Mamie tacika tara ka kayar mata da auta". Tsayawa yayi daga cilla Affan ya kalli Aymana d'in, lallaima Anty Aymana mikika maidanine?, kalleni da k'yau nakusa yin aure, shiyyasa nake koyon raino kafin matata tazo. Dariya suka sanya masa, shikam yawani tsare gida alamar babu wasa amaganar tasa, Anty Mamie dake tsaye a dining tana shirya abinci tace, " sannu musleem kaji. Idanu yazaro, kokad'an baiyi zaton Mamie Na a falonba. Cikin sauri yashige 6angarensu, mama tayi dariya, dan itama daga kichin tana jiyosu, tace ai gaskiya yafad'a, kinga k'anne duk sai suriga babban Yaya aure, idan yaga sunayi shima yayi zuciya yayi aii. Hum Yaya Fad'ima aini lamarin babanama tsoro yake bani, inaga saiya tsufa zaiyi Auren?. Aniyarku tabiku annamimai, anzo antasamin yaro gaba za'a cinyeshi da baki, nibansan mi rashin auren Ibraheem yatsare muku ba agidannan, wlhy mugun bakinku saidai Yakoma akan 'ya'yanku. Hajia babba ce kezuba masifa alokacin datake fitowa daga 6angarenta, su hasnah Na take mata baya, cikin gayu suke nafitar hankali, da'alama wani gurin zasuje. Kowa kallonsa yamaido akansu, amma daga mama har Anty Mamie babu Wanda yakallima inda take. Anty Amarya tashigo falon da sallama, da'alama dawowarta kenan daga aiki, Dan rik'e take da jibgegiyar rigar lauyeyi da handbag d'inta. Itama tsayawa tayi tana kallon ikon ALLAH, dukda mutumce mara son shiga abinda bai shafetaba lamarin hajia babba nabata mamaki, ita kokad'an bata d'agama kowa hulaba agidan. Yanda take zazzaga masifa kaikace 'ya'yanta takema fad'a. Gashi falon yayi tsit kowa yana saurarenta. Mama tad'ago cikin matuk'ar fusata tace, ''k! Hajia Laurah ya isheki haka mana, shin wai mud'in 'ya'yankine kokuwa kina mulkar wanine acikinmu? dazaki zauna agaban 'ya'yanmu kinacin zarafinmu?. Baba dai matsayin d'a yake awajenmu, babu kuma yanda za'ayi ahanamu sakashi cikin hirar 'ya'yan gidannan. Wai ko har yanzu bakisan kin girma baneba?. Har hajia babba tabud'e baki zatayi magana baffah yadakatar da ita tahanyar fad'in, kar wanda tasake magana acikinku, yamaida dubansa akan yaransa da surukansa, kowanne yayi k'asa dakai, Amal harda kukanta, Dan abinda ke faruwa agidansu yana damunta. Tsaki baffah yaja, yajuya zuwa 6angarensa yana fad'in kuduka hud'un kuzo Ku sameni. Baijira cewarsuba yay shige warsa. Tsaki hajia babba taja takama hanyar fita abinta tareda fad'in babu abinda ya'isa dakatar dani daga fitata, saidai adakatar dazaman harsai nadawo. Babu Wanda yakulata taja 'ya'yanta daketa hararsu Anty Mamie saikace sa'anninsu suka fice. Babu Wanda yasake fad'in komai, mama da Umme amarya da Anty Mamie suka nufi 6angaren baffah..........✍🏿 *_Love you all😘😘_* [8/18, 8:08 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _bara namik'o gaisuwar ban girma my kakus, (maimuna) & Maman Khaleed & Dan mom, ALLAH yabar zuminci._ _bilyn Abdull namik'o gaisuwar ban girma agareku_ 😍😍😘✌🏻 3⃣1⃣ Tab lallai yarinyar nan tantiriyace J, kallafa kaga shigar dake jikinta?. In banda abinka youseef ba 'yar gata baceba, kowafa yasamu rana yay shanya, aii duk Wanda yasayi rariya yasan zata zubda ruwa. Mafi yawancin yaranmu idan anturosu karatu k'asashen k'etare abinda sukeyi kenan, kadubafa ko agida Nigeria yanda jami'oin mu suke, saikayi babbar sa'a zakasamu Na kirki acikinsu, haka zakaga weekend anata kwasar 'yan matan jami'a zuwa d'akunan maza, kaikace gidan karuwaine, iyaye kuma sunacan sun saki baki 'ya'yansu Na karatu a jami'a, wani har k'afafa zakaga yanayi. Inhar ak'asarka ana irin wannan 6arnar kuwa, yakake gani lokacin da 'ya'yanmu suka gama samun damar zuwa karatu k'asashen k'etare?. Shiyyasa Baffah baita6a yarda yakai d'ansa karatu wata k'asaba, kaf d'inmu agida Nigeria mukayi karatu, saidai wani coast yafiddaka amma bashi yakaikaba. Ai wlhy haka yanada k'yau, nifa tsoronma aure nakeyi, aje a haifamaka d'anda zai kaika lahira baka shiryaba. Youseef kenan, zakaima ALLAH wayone?, aii ka tabbata yanda kata6a 'ya'yan wasu sai anta6a naka, dama masu iya magana nacewa (wanzami baya son jarfa). Youseef zaiyi magana saikuma yayi shiru. Saboda isowar Taheer wajen. Ya zauna yana sauke numfashi. Suduka idanunsu akansa, wai miya farune kaketa wani hura hanci kamar kayi noma?. Mtsoww kabari kawai j, ALLAH yarinyar can bala'ice, inaga kawai muyi amfani da hanya tabiyu, ita ayanda nalurama bata harka saida turawa. Murmushin k'asaita ya khaleel yayi, yagyara tsayuwarsa tareda cin serious, ganin haka ya tabbatarma su Taheer amatsayin ogansu zaiyi magana ba abokiba. Mik'ewa sukayi tsaye suma, suka k'ame dama salutes. Cikin sanin darajar kai shima yamayar musu murtani, ya kalli agogon dake manne a tsintsiyar hannunsa, sannan yamaida kallonsa ga Taheer, inason magana da headquarter d'inmu nan America. OK sir. Taheer yafad'a da girmamawa. A cikin mintuna dabaifi 5 ba Taheer yagama komai, daga nan kai tsaye babban Office d'in shugaban Interpol Na America suka nufa. Sungama dukkan shigi da ficinsu, tareda samun had'in guywar 'yan uwansu police interpol na k'asar, insha ALLAH a Daren ranar suka had'a tarkon kama Alhaji Alasan Atiku kwangila.. ___________________________ Baffa ya kalli matan nasa, ransa duk a6ace yake, yace ina Laurah?. Kowa tayi shiru batareda sun bashi amsaba, Dan basusan mizasuce dashiba. Shima baidamu dajin amsar tasuba, yaciro wayarsa daga aljihu yakira hajia babba, harta yanke bata d'agaba, Yakuma kiranta a karo Na biyu, nanma saida takusan tsinkewa tad'aga tana Jan tsaki. Kina INA? Baffah yayi maganar cikin serious. Nafita, itama tafad'a adake. OK, yamiki k'yau sosai, kuma INA mai tabbatar miki inhar Baki dawoba wlhy saikinyi Dana Sanin fitarki, idan kinji wasa kuma kada kidawo d'in, ya yanke wayarsa kawai. Ran hajia babba ya6aci, amma tasan sarai wanene Baffah, baya d'aukar raini koda wasa, duk iskancinta tasan kalar datake masa, amma tanajin shakkarsa sosai. Tsawa tadakama driver, wadda tasakashi taka birki cikin hanzari, balbaleshi tayi damasifa akan Yakoma gida. Su Kansu su hasnah Lamarin yabasu tsoro. Afusace tashigo 6angaren baffa, babu Wanda yace da ita k'ala acikinsu umme amarya, baffa kam dama tun d'azu yashige bedroom d'insa. Sai surutai hajia babba takeyi, wai anyi munafurcinta, babu Wanda yakulata har baffa yadawo falon. Cikin tsare gida yafara musu fad'a, yace, ''kukam wai sai ayaushene? zakusan kun girma, gida cikeda 'ya'yanku da surikai amma bakubar raba abin kunyaba, wlhy inamai gargad'inku akan wannan yazama shine first and last dazaku k'aramin haniya agida, nagaji da iskancinnan hakanan, da girmana kuringa zubarmin da mutunci wajen Matan 'ya'yana da 'yan aikin gida, awannan karon gargad'i namuku, next time idan aka sake mataki zan d'auka akai. Daga nan kuma saiya kwantar da murya cikin hikima da dattako irin Na dattijan kwarai yafara musu nasiha, duk kuma sai jikinsu yayi sanyi, har ita hajia babba d'in, suduka hak'uri suka bashi da alk'awarin insha ALLAH baza'a sakeba. Yayi farinciki, da fahimtarsa dasukayi, sund'an ta6a hira daga nan ya sallamesu. Fitarda hajia babba batayiba kenan aranar. Suna fitowa daga ang6aren baffa suka Tatar Zunnurain yadawo da Ammah daga asibiti, dama yakaita taga likitane saboda ciwon k'afarta. Duk rissinawa sukayi suka gaisheta, tareda mata sannu. ______________________________ A Canada kam su Aysha sunata shirin bikin ya Naufal da Anty meerah, shirin biki akeyi Na 'yan gata, dukda bawasu dangine a can d'inba saidai 'yan uwan momy, kuma duk Christen ne, saikuma abokan arzik'i Na dady da ya Naufal, Maheer ma danasa gayyar, hakama Aysha da Ifteehal. Amarya meerah tasha k'yau, dukda takan ke6e tasha kukan bak'incikin halin rayuwa data Shiva abaya, wai yanzu amatsayin budurwa zatayi aure ko bazawara? Shikenan bazata kai abinnan mafi daraja ga kowacce 'ya macen kwarai ke zuwa gidan mijinta dashiba?. Sauk'in tama ya Naufal yasan komai dangane da rayuwar datayi abaya shida iyayensa, amma ya amince zai aureta ahaka, Dan acewarsa aii ita yakeso ba jikintaba. Takanji a zuciyarta kamar ta cutar da Naufal d'in, Dan bai dace da Auren mace irintaba, dukda yasanar da ita gaskiya yana Neman mata, amma insha ALLAH ya bari, Dan tundaga lokacin dayaje Islands UK bai k'ara tarayya dawata maceba. Amma dukda haka tad'aukama kanta alk'awarin ko a nangaba Naufal yace zaiyi aure bazata ta6a hanashiba, wannan shine tukuycin dazatama Naufal saboda sadaukarwar dayayi akansu a rayuwa, bakomai yasakata amincewa da aurensaba sai k'yautatawar da yayi musu shida iyayensa, amma dukda haka saida akasha gumurzu da ita kafin tayarda da soyayyarsa, Dan tadad'e dacire kanta alayin wad'anda zasuyi aure aduniya. Amma shi ubangiji gafurunne kuma rahimun, saiya shiryeta alokacinda batayi zatoba, yakar6i tubanta batareda dubi da munanan ayyukan data aikataba, harma yadarajata ya k'addara yin aure acikin kundun tarihin rayuwarta, itakam mizatace wa Ubangiji? Banda tayita bautamasa da godiya agaresa, tak'ara tsoronsa da taka tsantsan wajen gujewa sa6a masa. Hawaye suka cigaba da zirara a kumatunta. Ahankali taji ana share mata, tasan Aysha ce, danhaka tarik'e hannunta tareda jawota jikinta suka kuma fashewa da kuka. Anty meerah ki godema ALLAH, yakamata kidaina kukannan, komai yayi farko zaiyi k'arshe, ALLAH yamana sutura irin wadda ba kowa yake baiwaba, banta6a tunani rayuwa zatayi mana k'yawun ganiba, amma dayake bamuda hak'in kowa akanmu sai ALLAH ya katangemu saboda adalcinsa. Bamuda abinda zamu sakama ya Naufal da iyayensa dashi, saidai muyita rok'a musu gafarar ubangiji har randa zamu amsa kiransa. Dan ALLAH kibar kukannan haka, kinga karkije gidan ya Naufal arame. Murmushi meerah tayi, tasharema Aysha hawaye, itama ta share mata. Ya Naufal dake tsaye a bayansu shida mom suma duk sai tausayinsu yakamasu, harga ALLAH suna k'aunar Aysha da meerah, saboda yaran komai nasu abin koyine, kawaidai k'addarace tayi haijiya da rayuwarsu, gashi kuma sun kar6eta da hannu biyu, basu zama masu butulci ga ALLAH ba. Ahaka aka shiga shagalin biki, dukda bawani armashi yayiba kamar anan gida Nigeria daza'ayi cikin dangi, amma komai yatafi cikin tsari, meerah tazama amaryar Naufal babu uwa babu uba alamarin aurenta, wannan shinefa maraicin dole, amma tagodema ALLAH, kobabu komai mahaifiyarta ta turota tayi karuwanci saboda kwad'ayi abin duniya, gashi zata koma gareta da aure, wannan kad'ai ayace ga mahaifiyar tata, hardama masu hali irin NATA nason zuciya. (To halimatus-sa'adiyya & Naufal, ALLAH ya sanya alkairi, yasa musha suna kafin aje Nigeria😂). _____________________________ Cikin nasara su ya khaleel sun sami damar cafke Alhaji Alasan kwangila. Dan danan gidajen TV da redio suka d'auka, k'asashen waje dana gida Nigeria, kasancewarsa babban mutum a k'asar ta Nigeria. Hankalin mutanensa yatashi sosai, ciki harda manyan k'asarnan, Dan sunsan tunda aka fara dashi wataranafa Kansu za'a zo. Aciki harda manyan ma'aikata na jami'an tsaro a fannoni da dama, cikin ma'aikatar su Ya khaleel ma akwai. Washe gari suka iso dashi Nigeria, duk k'ok'arin 'yan jarida nasonjin ba'asi akan kamashin ya khaleel yak'i basu had'in kai, daga bayama kashe wayoyinsa yayi yatafiyarsa gida. Kasancewar weekend ne kuma safiyace yashigo gidan babu kowa afalo, duk yawancinsu sunata barci, sai 'yan aiki kawai dake had'a abinci a kichin, Dan yau aikin hajia babba ne. d'akin NASA fes yake, Dan kullum sai Anty Mamie tasaka an gyarashi dukda baya k'asar. Wanka yashiga first, bayan yafito yazura kaya marasa nauyi yay kwanciyarsa. Har around 12 yanata barci bai tashiba, zuwa sannan mutanem gidan sun tashi, ganin motocinsa da Securitys nasa ya tabbatarma da mutan gidan yadawo, amma babu Wanda yayi yunk'urin zuwa d'akinsa. Sai d'aya saura yatashi, yakuma yin wanka yay shiri cikin k'ananun kaya yafito, Baffah yafara zuwa ya gaida, sukad'an ta6a hira har zuwa kan aikinsa da kama alhaji Alasan dasukayi, anan yay break fast, daga nan yaje suka gaisa da Ammah, wadda tatasashi gaba da fad'a akan rashinyin aure, hak'uri yabata da tabbatar mata insha ALLAH yakusa auren. Amma ta ta6e baki tana fad'in ALLAH yasa, kullum ma bahaka kake fad'iba, Iro aurofa shine cikar kamalar kowanne d'a namiji, harma da macen, bakasan yanda rashin aurennan naka ke damunaba, amma nakula ita mahaifiyarka abin ko damunta bayayima. Kiyi hak'uri to Ammah, insha ALLAH saikin goya yarona. To ALLAH yasa, yakuma tabbatar dahakan. Yashiga yagaida mama da Anty Mamie, harda umme amarya, fitowarsa falo k'annensa duk suka gaidashi damasa sannu da zuwa, daga nan yatafi gun tsohuwarsa, kusanma a can ya wuni. ___________________________________ Akwana atashi babu wuya wajen ALLAH, su Aysha an kammala karatu, zuwa yanzu kam tazama cikakkiyar 'Yar jarida, tasamu result mai k'yau, itada ifteehal, kowa yayi farinciki agidan, Dan har party aka shirya musu. Sunata shan hutunsu agida, alokacin kuma dady yace, sufara shiri zasuje Nigeria, jira kawai akeyi Anty meerah ta haihu, Dan cikinta yatsufa sosai, haihuwa ko yau ko gobe. Murna dai anar Aysha harta rasa wace iri zatayi, wai itace zata koma k'asarta ta haihuwa, k'asar da'aka rabota da it'a tak'arfin tsiya, k'asarda zalincin wasu mutane yasakata nisa da ita, k'asar datafi k'auna fiyeda kowace k'asa a duniyarnan, k'asar data share tsawon shekaru hud'u bata cikinta, zataje taga mama da Umma, su Anty fadeelah, hafsat, ya Qaseem dasu Rufaida, wayyo dad'i zataje Nigeria. Dariya su ifteehal suketa mata, itakam ko'a jikinta, murnarta taketa zubawa. Ana cikin wannan haline sukaji doorbell Na k'ara. Safwan ne yaje yabud'e, matashin yaro dabazai wuce sa'an Safwan d'inba yamik'ama safwan bag🛍 mai k'yau, wai abama sholy. Safwan yakar6a cikin mamaki tareda maida k'ofar yarufe. Aysha yamik'ama sak'on ta amsa tana tafad'in namiye Safwan?. Bayani yayi mata. Harzata bud'e mom tahanata, tace, ''taje d'aki tabud'e". Batayi musuba tatshi itada Ifteehal sukaje d'aki. 🎁bud'ewa sukayi, flower🌹ce tanata k'amshi, saikuma kwalba mai k'yau wadda ruwa ke'a ciki da tsuntsaye biyu,🕊 d'aya da fire a bakinsa yana mik'ama d'aya, sai zobuna biyu a can k'an tsuntsayen d'aya kan d'aya💍, k'ananun kifaye nata yawo aruwan. Aysha tasauke ajiyar zuciya tareda tunanin sak'o makamancin wannan da aka ta6a bata a UK 2years dasuka shud'e, hartayi tunanin Ariana Ce takawo mata. Da sauri tatashi zuwa gurin ajiye muhimman abubuwanta, kwalbar ruwa maid'aukeda kifaye da'aka kawo mata awancan karon tad'ako, iri d'ayace data yau, banbancinsu kawai tayau akwai tsuntsaye da zobuna acikin ruwan bayan kifaye, ifteehal ma kallonta takeyi cikin mamaki, da sauri ta y kwalaben takoma kan sak'on, yauma akwai k'aramar takarda, tazarota da sauri tabud'e. *_Ranar aurena yazama gaske mafarkina, nacika burina innasameki miradina!._* Wannan shine kawai arubuce, Aysha ta maimaita baitikan yafi sau goma, to wanenen wannan?, abinda ya d'aure mata kai shine wak'ar Hausa, to, wanene? Kodai ya Naufal ne? Kai anya kuwa?. To amma idan bashi baneba itakam wanene, hartayi rayuwar islands tabarota bata ta6a had'uwa da kowaba bahaushe sai ya Naufal. Kuma tabbas mai wannan sak'on yasantane, yanakuma tareda ita tun'a UK d'in. Tadafe kanta datakejin yana Sara mata, wani k'aramin akwati takuma fiddawa ja, yayi k'yau sasai, tabud'eshi, had'ad'd'en zobene Na diamond💎. Yahad'u sai d'aukar ido yakeyi, acikinsa anyi wani rubutu da salo. Su Aysha sungaza gane me aka rubuta acikin zoben. Saikuma turare mai masifar k'amshi, Aysha ta shinshina turaren talumshr idonta. Jitake tabbas tata6ajin wannan k'amshin, amma a ina?. Shine abin tambayar. Koda takaima Anty meerah kayan tagani tayi matuk'ar mamaki itama, sunyi hasashensu harsun gaji amma sungaza gane wanene mai sak'on. Ita kanta meerah tafara zargin kodai Naufal ne?. Dan shekara 2½ dasuka wuce lokacin da'aka kawoma Aysha sak'on farko basu dad'e da had'uwa da Naufal ba. Anya kuwa bashine mai basajar nanba??. Zata gwadashi danta tabbatar.........✍🏿 Nidai bilyn ku nace, "ALLAH kad'ai yasan karatun kurma🤣". *_kumuje zuwa fan's, anzofa wajen😍😍😍😍😍😘_* *nima nabaku diamond💎💎💎💎💎🤣* [8/23, 9:23 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 3⃣2⃣ Cikin sand'a take fitowa daga 6angaren nasu, kaikace sata zatajeyi, ahaka tafito babban falo, ananma shuru kowa yashige d'akinsa, ya Ramadan ne kawai zaune yanata danne-danne a lap-top, da alama wani akin yakeyi, kuma aikin yayi matuk'ar d'aukar hankalinsa. Ahankali tabi bayansa tashiga ta kicin, ta k'ofar baya tafice, tsakar gidan ko'ina k'wanyar yake da hasken lantarki, ta tsakanin motocin dake barbaje a harabar gidan tarink'abi, kasancewar yaran gidan kowa yana gida, ya khaleel ne kawai bama ya k'asar (amma suna saran dawowarsa a yau). Koda ta'isa k'ofar gate d'an gwari nakan benci sai zabga gyangyad'insa Na k'addara yakeyi, tazabga tsaki tareda shurin k'afarsa, firgigit yafarka yana niyyar saka ihu, da sauri tace, "ALLAH kamin ihu sainasa baffa yakoreka, kajimin wawan mutum. Tuni d'an gwari yanutsu danjin muryar mufeedah, amma jikinsa haryanzu k'yarma yakeyi, ta balla masa harara tana fad'in dallah bud'emin k'ofa. Kamar d'an gwari zai fasa kuka yace, " madam duk randa Alhaji yagane kina fitan dare zai punishing d'ina, ki tausayamin". Yama kasheka ina ruwana, munafiki idanhar bakaine zaka fad'aba waye yasan ina fita, wlhy duk randa hakan tafaru sainasa ankashemin kai, kai har uwarka saina saka ankashe, kadai San banida kirki, bud'emin k'ofa jio, shashasha mara lissafi, kadamu mutane da wannan banzan hausar naka Mara dad'in ji. Jikin d'an gwari narawa yabud'e mata k'aramin gate tafita. Tana fitowa tacire k'aton hijjabin jikinta, daga ita sai guntun siket iya cinya, tasaka riga maikama da best ko cibiyarta bata rufeba, shigar tata saikace 'Yar basketball. Kad'an tabar jikin gidan nasu ta tadda wata farar mota 'Yar k'arama, bud'ewa kawai tayi tashige abinta. Hi! babe. Tafad'a tana wani far da idanu. Woow!! zumata kinyi k'yau, yau wankannan Na musammanne, nima zanyi biya Na musamman kam. Still tayi far da idanunta, cikin salon tantiranci tace ka cancanci fiye da hakama, wlhy kodagani sai 👙kace nazo maka zanzo, kai ko tsirarane. Wata dariyar jin dad'i yayi, yace, ''kina cikin aikina wlhy, my Mufeey, zumata kenan". Ya akayi yau? Naga kinfito da wuri. Kabari kawai, aii boss ya khaleel baya nan, kuma bansan miya saka 'yan gidan barci da wuri hakaba, Momy kuma itace da baffah shiyyasa duk nasami fitowa akan lokaci. Dariya yaytayi tajin dad'i, tun'a mota suka fara masha'arsu. (Nace, "ALLAH ka shiryemu, Momy gafa abinda kike gudun, dama masu iya magana kance, *Ciki da gaskiya* wuk'a bata hudashi🤷🏽‍♀). _______________________________ Har yanzu kan yana ciwo my Noor?. A'a ya daina ma tun d'azun wlhy, yanzukam saidai baya, shima kad'an-kad'an, zuwa anjima ma zakaji shima ya daina. To ALLAH yak'ara afuwa, babyna dai yana baki wahala. 'Yar dariya meerah tayi tareda kallonsa, tace, "karka damu, ai zan ramane". Shima dariyar yamata, yana fad'in kokuma kirame ba, wlhy nifa da Dady zaima yarda dakawai muntafi ki haihu a Nigeria, naga lil sholy tak'agara ayi tafiyarnan, tunifa tagama had'a kayanta. Dolene taso zuwa gida, nikaina hak'uri kawai nakeyi, shekara 9 ba kwana tara baneba, amma nafison saina haihu, sai dai kawai naje musu da d'a ko 'ya. Cikin murmushi ya Naufal ya sumbaci goshinta, yana fad'in ALLAH ya saukeki lfy to, aii duk yanda kikeso haka za'ayi, kece mai mulkin Naufal zuciya da rayuwa. Meerah tayi murmushin jin dad'i, d'an box d'in zoben Aysha Na diamond tad'akko, tace nikam Ring d'innan zaiyi nawa a kud'in Nigeria dana nan k'asar?. Kar6ar box d'in Naufal yayi, itakuma meerah ta tsura masa idanu dansan fahimtar wani Abu. Bud'e box d'in yayi, yafiddo Ring d'in sai k'yalli yakeyi, d'an murmushi yayi, batareda yace komaiba yamaida Ring d'in a box d'in yarufe. Meerah tace, " ya haka kuma?". Kamar ya?. Tanbayarkafa nayi kud'insa, amma babu amsa kamayar ka ajiye. Eh, namayarne saboda bansan kud'inba, ke inama kika samu zoben?. Meerah tad'anyi shiru, sai zuwa can tace, ''wanine yata6a banishi, shine kawai yau naganshi akaya na d'auko. Shiru yayi bai tankaba, saima kanta daya d'auke daga cinyarsa yamik'e abinsa, kinga bara naje wajen Dady muyi magana, Dan inason mufara tura kayanmu kafin lokacin tafiyar mu, inasaran zuwa next week k'ilan ki haihu insha ALLAH Dan EDD d'inki yakusa cika. bai jira cewartaba yafice abinsa. Binsa meerah tayi da kallon mamaki, kenan da gaske shine yabada Ring d'in wa Aysha?. Tayi murmushin takaici, tareda share guntun hawayenta, ALLAH ya tabbatar da alkairi tafad'a tana mik'ewa da k'yar, insha ALLAH bazata zama shashashar maceba wajen hana mijinta abinda yakeso, Dan batasan mi ALLAH ya shiryaba akan hakan. Tundaga ranar bata kuma yimasa maganar ba, tamaida ma Aysha zoben kuma, sati uku tsakani meerah tatashi da nak'uda. Tasha wahala kam hardai ALLAH yabata ikon haihuwar d'iyarta mace, mai matuk'ar kamada kakarta mom, meerah bak'a Naufal bak'i, amma ALLAH ya azurtasu da haihuwar baturiyar yarinya mai kamada mahaifiyar Naufal, shi bai d'akko kamannintaba d'iyarsa ta d'akko. Fad'amuku farin cikin da familie d'innan sukayi 6ata lokacine, kamarma Aysha taji labari, jitake tamkar yayarta uwa d'aya uba d'aya ta haihu. Yarinya taci suna Zainab sunan mom, zasuna cemata (Raudah) to ALLAH ya raya Raudah, bawani taron suna akayiba, amma sund'anyi party acikin gida, dangin Momy kuma da abokan arzik'in ya Naufal duk sunzo, hakama gayyarsu Aysha da Maheer, hardasu iklas da Safwan. Watannin Raudat biyu a duniya suka fara shirin tahowa k'asarsu ta haihuwa Nigeria. Fad'a muku zumud'in da Aysha keyi a lokacinma 6ata lokacine, amma nabaku dama Ku k'iyastama zuciyarku.😄 ________________________________ Yau kam mama da Anty Mamie da Abashiyya da Aymana da gayyar 'yan matan gidan, Shuhuda, Amal, Hamdiyya, Naseeba, maleeka, Tasleem, UmmuNoor, Nuriddin, suka shirya zuwa Kano sunan Fadeela data haihu, Dan ita bata haihu ba sai yanzun, Hafsat kam tanada yaro d'aya harda ciki yanzu. Har 6angaren hajia babba Anty Mamie taje, tace, su Hasnah sushirya suma aje dasu, amma sukace bazasujeba, wai sunada lectures a ranar, hajia babba Na zaune tanajinsu amma batace komaiba. Mamie ma bata maida kaiba barema abin ya6ata ranta, dama dankar ace sunware sukad'ai sun tafi shiyyasa tafad'a. Hafez da Musleem ne suka d'aukesu suka tafi, ita Ammah dama tana can, tun haihuwar da kwana d'aya tayi gaba. Sosai baffah yahad'a shatara ta arzik'i akaima fadeela, harma dasu Ummah, akwati biyar yacika da kayan arzik'i, banda kayan haihuwa da Anty Mamie tahad'a Ammah tayi gaba dasu. Gidan duk sai yayi shiru babu dad'i, Umme Amarya ma tabada turmin zani uku da kayan jarirai 5 sai 'yan tarkace tace akaima fadeela. Amma hajia babba ko yajinta babu, hakan ko kad'an bai damu mama ba, Dan dama bata sa akaba. Sun isa kano lfy, d'akin mama Nada suka sauka, Wanda Umma tasaka aka gyarashi fes, gidan ya canja sosai, saboda gyaran da mama tasaka akai masa tuni. Dama tabama Ummah jari tanata juyawa, ga mijinta itama mutumin kirki, yarik'e Umma da yaransu da daraja, ko'a haihuwarnan ta fadeela dukkan abinda uba keyi saida yayi. Bayan Wanda kawu bilyamin yayi shima, hakama Umma duk abinda uwa yakeyi tayishi. Dan haka koda sukazo sun tararda komai ready. Su Amal ma basu dad'e ananba suka kwashi kayansu sai gidan fadeelah mai jego, a can suka taradda Ammah, Dan itace ke zaune da Fadeelah. Hafsat ma tana gidan. Aikam nan sukaita shan shargallensu, duk wani aiki da dangin mai jego kanyi a daren suna su sukayishi, babu ruwansu da k'yamar talaka, sunshige cikimsu Ruk'ayya k'annen mijin fadeelah anata harkar arzik'i, Ammah taji dad'i sosai, Dan ita tsohuwace tagari. Maison k'arfafa zuminci dakuma girmama mutane. Wannan yasaka take alfahari da Anty mamie, saboda k'yak'yk'yawar tarbiyyar da yaran suka samu daga gareta, kowa yabonsu yakeyi awajen taron. Washe gari jaririya taci suna Ummu-hanee, saimuce ALLAH yaraya fadeelah. Wajen Ummah aka dawo da'ita wankan jego. Kwanansu mama hud'u akano suka tafi Jigawa, Dan duba inna, tayi murnar ganinsu itama sosai, kwanansu biyu suka koma Abuja, Ummulkhairi tanata zabga kuka saitabi mama, dama tun a Kano taketa dama-dama da ita, 'yan uku kam kamar ta cinyesu, itama tayi k'anne, ta tashi daga autar mama😀tunda gasu Khaleefa, (yarinyar tayi girma sosai itama). ___________________________ Akwana atashi babu wuya wajen mai duka, dagari ya waye saikaga rana tayi, babu dad'ewa kaga dare yarufa, sati kam yazama tamkar kwana, yayinda wata yazama sati, shekara batada wahalar zuwa saidai muce ALLAH yasa mucika da imani. Ayaune jirginsu Aysha yasauka k'asarsu ta haihuwa, wato Nigeria. Yanda kasan bak'auya haka Aysha takoma, gaba d'aya gani tayi k'asar ta sauya mata, sun sauka a Abuja, amma ko kusa Aysha bata ganeba, tabar k'asar tanada shekaru 14, tadawo cikinta tanada shekaru 17 dawasu watanni, cikin hikima tayita share hawayen farinciki, babban burinta shine taganta a Kano kawai, to amma Dady yace, "anan Abuja zasu sauka agidansu, sai bayan sun huta zasu rakasu itada meerah, kowacce taga iyayenta. Meerah kam sosai takeyin kuka tun'a jirgi, saida ya Naufal yayta lallashinta, da nuna mata muhimmancin yarda da k'addara, k'yak'yk'yawa ko mara k'yau. Sun sauka agidansu Naufal d'in dake a Garki Area 7, gidane mai matuk'ar kyawu da girma, yayi k'ura sosai kasancewar ba zama sukeyi acikinsaba, dama ya Naufal ne yafi zama a Nigeria, shima kusan shekaru uku kenan rabonsa da k'asar, garama Dady yazo shekara 1½ kenan, gidan dake makwaftaka dasu suka shiga, sosai akaita murnar zuwan nasu, Annan sukayi salloli dacin abinci. 'Yan aikin gidan kuma sukaje sunata tik'ar gyaran agidansu Naufal d'in. Bayan sun gama suka koma can. Aysha sai gimtse fuska takeyi saboda yaron gidan daya dasamata ido da kallo tamkar yasamu television, sai balla masa harara takeyi da murgud'a baki. Amma ko'a jikin Shakur, danshikam Aysha tagama tafiya da imaninsa. Har gidan yarakosu dazasu taho, sai wani dama-dama takeyi da Aysha yanama Raudat dake hannunta wasa. Daga k'arshe da Aysha taga yatasa rayuwarta agaba saita mik'a masa Raudat d'in. Ifteehal kam mizatayi banda dariya, Dan komai dake faruwa akan idonta itada meerah, shikam Maheer dariyar mugunta yay tayima Shakur d'in, Dan shima yadad'e yana nuna alamomin so ga Aysha amma tana shareshi danuna masa bama ta fahimceshiba. _____________________________ Agidam baffama yau gwaggo bintu da Anty zuwairah da yaran ta sukazo daga Lagos. Gwaggo bintu dukta fita hayyacinta, gawani uban bak'i datayi, daka ganta kasan tanashan bak'ar wahala a hannun Anty zuwairah. Ita kanta hajia babba kasa hak'uri tayi, saida tacema Anty zuwairah shin bintu ciwo tayi agidankine zuwairah?. A'a Momy mikika ganine?. Naga dukta fita hayyacintane cikin shekaru 2½. Baki Anty zuwairah ta ta6e, wlhy mamy tak'idai kwantar da hankalintane, amma ban rageta da komaiba, kullum hankalinta yana gidannan, shiyyasama nakasa hak'uri zuwa lokacin meeting d'in Na tattata muka taho tunda dadyn Najwa ba yanan, kartaje ta mutumin agida. Momy bata sake cewa komaiba. Itama gwaggo bintu tuni ta lalla6a zuwa 6angarensu Na 'yan aiki, Dan batada cikakkiyar lafiyama, ko mutamen gidan bata shiga gaida kowaba. Yaranma duk basa nan, masu aiki sun tafi, masu zuwa makaranta sun tafi, Ammah kuma tana Jigawa ma ita, mama da Anty Mamie kam kowacce tana'a 6angarenta, umme amarya Na wajen aiki itama. Matansu ya Sultan ma suna nasu 6angare, dan ba kullum suke shigowa cikin gidanba dama. Su iya hama duk sunyi mamakin ganin yamda gwaggo bintu tafita hayyacinta, amma basuda ikon tanbaya, Dan damacan tsoronta sukeji, bishirah ce taita bama gwaggo bintun kulawa, (itama tazama budurwa sosai) harma ansaka mata ranar aure, zata auri wani d'an uwansu a can Kaduna. Amma zai zauna da'ita a Suleja, anan yake 'yan kasuwan cinsa...................✍🏿 *_Fatan alkairi agareku, inafata ansha bikin sallah lafiya?, ALLAH ya maimaita mana ta bad'in bad'ad'ad'a, Yakuma gafarta mana ayyukanmu Marasa k'yau dasuka wanzu a cikin wannan shekarar, ALLAH ka gafartama mahaifanmu, ka yace musu, kabama marasa lafiyarmu lafiya, muda Muke da ita ka k'ara mana, ALLAH ka yaye ma kowa damuwarsa, ka kawo mana sauk'i cikin al'amuranmu Na yau da kullum, ALLAH ka d'ora musulinci akan kafirci, ka karya kafirci da kafirai, ka d'aukaka musulinci da musulmai, katsare mu muda addininmu daga hannun azzaluman duniya, ALLAH kaza6a mana shuwagabanni nagari, ka k'arama shugaban k'asarmu lafiya, ka kareshi ga dukkan Sharrin masu burin cutar mana dashi, ya ALLAH ka zaunar da k'asarmu lfy, ka shirya al'ummar musulmai Baki d'aya, kabamu damina mai albarka, ka tsarkake mana zukatanmu duniya da lahira._* Ameen ya rabbi🤚🏻✋🏻😭 Barkanmu da dawowa, acigaba da gashi my Guy's😚😉. 😘😘😘 [8/24, 8:20 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _wannan gaisuwa takuce ku kad'ai 'yan group d'in *CIKI DA GASKIYA FAN'S* sak'onninku na isowa agareni, ina yinku 100%, ina sonku wallah, alkairin ALLAH yakai gareku._ 😘😘😘❤❤ 3⃣3⃣ Kwanan sa kusan uku kenan da dawowa k'asar amma baije gidaba, saboda wani aiki daya rik'eshi, wani mutumi sukesan kamawa, kuma yanada had'arin gaske, kasancewar sa tsohon d'an ta'adda. Sun d'ana masa tarko sosai tun wajen wata 5 daya wuce, har yanzu ALLAH baisa ya fad'a a tarkonba. Mutumin a Rivers state yake, cikin port-harcourt. Cikin shirin Uniform d'in police interpol yake, yaukam da bindugu biyu yafito, kokad'an fuskarnan babu alamar sassauci, duk lokacin da ya khaleel yad'ora hular aikinsa yakan k'ara kwarjini da cikar haiba👮🏼‍♂. Sosai Uniform kemasa k'yau, gashi dogo mai suffar k'arfi masha ALLAH, cikakken training daya yasamu yakansaka suffarsa tsorata mazanma ba mataba kawai, ga tsare gida irinnan jaruman ma'aikata nagartattu. Cikin Nutsuwa yake tafiya, wadda hakan tamkar halittarsace, komai ya khaleel zai maka anutsuwarsa yake, komai zafin daya d'auka awajen aiki ko rikiCewar abubuwa kuwa. Bayansa Joseph ne da Youseef, Samuel, Adams, Taheer, saikuma mutum uku wad'anda bansansuba kam, da alama dai cikin k'ananun ma'aikatan suke. Da sauri d'aya aciki yabud'e masa motar, harya taka zai shiga saikuma yajuyo yana kallonsu, in serious tone yace, ''komai zakuyi kuyi da kula, saboda anguwar tanada jama'a, banason aikinmu yashafi wani mara laifi, so Ku kula. Kowa zaiyi tafiyarsa shi kad'aine, Adams shiga muje. OK sir!!! Suka fad'a tareda Salutes nasa. Batareda maida murtaniba yashige motar ya zauna abaya, yayinda Adams & Emanuel ke a gaba. Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanu, addu'oin Neman nasara ga ubangiji kawai yakeyi, yayinda gefen zuciyarsa take masa hasashen idan ta kwa6e ko ansami nasara. Daka gansa kaga tibiran mahaukaci, kokad'an babu wata hujja dakakeda ita wadda zaka nuna rauninsa da amsa sunan mahaukacin, zaune yake kusada wani mai shayi Wanda yakasance ba haushe d'an balaguro, gefe d'aya kuma mai gasa naman tsirene da balangu, dandazon matasane awajen anata hirar duniya, wasu ta siyasa wasukuma ta yanayin rayuwa, harma da masu ta ball. Wani matashin saurayi dayaci indome yarage yamik'e zuwa gaban mahaukaci daketa zane-zane ak'asa, kaikace lissafin kud'i yakeyi kona shekarunsa. Mik'a masa filet d'in yayi, babu musu ya kar6a, saidai maimakon yaci, saiya juye cikin bak'ar ledan buhu datake hannunsa akowanne lokaci, yamik'ama matashin saurayi filet d'in yana tuntsura dariya. Girgiza kai kawai matashin saurayi yayi yakoma rumfar mai shayi ya zauna. Wani yace nifa kunsan wani Abu?. Akace a'a. Tunda mahaukacin can yazo wajennan, kimanin watanni uku kenan, banta6a ganin yaci abinciba, komi zaka bashi saidai yazuba abuhun ledar can, kuma kullum anan yake kwana. Wlhy gaskiyanka ne, amma k'ila yanaci mune bama maida hankali shiyyasa bama ganewa. Wani yace, nifa tausayi yake bani, ruwan shekaran jiya duk akansa yak'are. Wlhy haka yakeyi, ammafa ni a kwanakin baya sonayi nad'an rud'e, sainaga mahaukacin daya fara zama awajennan tamkar yafi wancan d'in suffar k'arfi dad'an tsawo? Danni farkonma zuwansa ban yarda mahaukaci baneba. Ashe bani kad'ai nakula da hakanba, kasan ALLAH nima sainake ganin tamkar ba wannan baneba Wanda yafara zuwa, ni wannanma baifi sati 2 ba nafara ganinsa anand'in, saikuma na daina ganin wancan. Kudai kuna masa kallon tsorone, k'iladai aljanunsa ke canjashi, wani matashin saurayi ne mai wannan maganar, tun d'azu kuma baisaka baki a hirarba sai yanzu, yanata danna waya abinsa. Jin shigowar sak'o yasaka ya khaleel bud'e shanyayyun idanunsa, wayar yad'auka yaduba, cikin d'an rikita yace, "Adams akwai matsala kenan?". Da sauri Adams yace sir! Matsalarmi kuma? Naga komai yana tafiya yanda muka tsarashi. Hakane, amma wai mutanen wajen sun fara tantama akan Mahfouz, yanzu katura masa sak'o yabar wajen, yaje inda muke had'uwa zanzo na samesa. OK sir!, Adams yafad'a yana k'ok'arin tura sak'o da wayarsa. Sunata hirar mahaukaci, Wanda ko alamar yasan misuke fad'a baiyiba, kamar an tsikaresa sukaga yatashi yana lalube-lalube abuhunsa, barin wajen yayi yanata surutai kamar yanda yasaba, babu Wanda yadamu dabarinsa wajen, harya 6acema ganinsu. Mintuna kamar 20 dabarinsa wajen saigashi yadawo, yanata 'yan surutansa, yakoma inda yasaba zama ya zauna. Mai Nama yace kai jama'a, ALLAH kuwa nafara gaskata maganar guy d'incan daya tashi, kugafa mahaukacin nan yanzu. Suduka kallonsu suka maida kansa, yanata zane-zane ak'asa, mai shayi yace kakula yanzu kuma yad'an k'ara tsaho da k'iba, kai aljanima shaid'anine, babu abinda baya iyawa, kai Malam wannan bawan ALLAH da k'alau yake aii wlhy bak'aramin namiji za'ayiba. Gsky kam, irin wad'annan suka damk'eka aii saidai lahira Dan babu mai kwatarka kuwa. Suna cikin hirar mahaukaci saiga wasu ratsa-ratsan motoci sunshigo anguwar. Wannan bawani sabon Abu baneba ga 'yan anguwar, akwai wani gida kad'an da rumfar mai shayin, kullum haka suke ganin manyan motoci nashigi da fici agidan, kowa yasan wani gawurtaccen tantirine agidan, amma kasancewar baita6a cutar da 'yan anguwarba shiyyasa ba'a damu dashiba, ko police shakkar zuwa anguwar sukeyi, Dan sosai ake tsoron anguwar a garin na port. Kallone yakoma sama lokacinda mahaukacin nan yaje gaban motar farko yakwanta a akan titin, sunyi horn d'in duniya yak'i tashi, ganin haka boss d'in yafito a fusace. Hakama dukkan yaransa da bodyguard d'insa. Har d'aya ya saita bindiga zai harbeshi boss ya dakatar dashi tahanyar d'aga masa hannu. K'arasawa yayi gaban mahaukacin yana lek'en fuskarsa. Wata wawura mahaukaci yayma boss. Kunsan abin mamaki da al'ajab😨😨kuwa??. Bindigace a hannun mahaukaci ya saita kan boss d'in dashi, yayinda yake fad'in kuna motsawa saina alburushe kansa wlhy, kowa ya ajiye bindigarsa. Shiru sukayi basu ajiyeba, kowa sai huci yakeyi, 'yan anguwa kam anyi irko-cirko ana kallon ikon ALLAH, masu tsoro kuwa tuni sunsha agida.🏃‍♀ Boss d'in ya jinjinama yaransa kai alamar su sauke bindugunsu, wasu sun ajiye, amma wasu basu ajiyeba. Alokacine matashin saurayi mai cewa aljanu suke canja mahaukaci yak'arso wajen, yagaggun kayan yafara yagewa daga jikin mahaukacin. 🤥Bakowa baneba face ya khaleel, k'asan kayan haukarsa kam Uniform d'in aikinsane, sai alokacin su taheer da police masu yawan gaske suka fara fitowa daga ma6oyarsu, nanfa aka fara musayar wuta, tsakanin 'yan ta'adda dasu ya khaleel. Kowa Yakama gabansa yana Neman ma6oya, bakajin komai a anguwar sai k'arar harbe-harbe ketashi. Wai idan bakayi bani waje, inji masu iya magana. 🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀. Misalin awanni biyu aka d'auka anguwar a hargitse, ansamu nasarar kwamushe wasu yaransa, wasunsu kam an iza k'eyarsu barzahu, wasu kuma sun sami harbi da raunuka, acikin 'yan sandama wasu sun sami harbi, wad'an da aka kama duk aka zubasu amotoci, Ambulance 🚑kuma takwashe police d'in dasuka samu rauni, Dan dama da guzurunsu sukazo. Saida ya khaleel ya tabbatar an kammala iza k'eyar kowa sannan, shida sauran jiga-jigansa irinsu Adams kawaine awajen, Samuel yasamo masa ruwa yafara wanke fuskarsa daya shafe da bak'in Abu, hakama Mahfouz. Sai asannan 'yan anguwar sukad'an fara fitowa, suma masu k'arfin halin kenan. Sun shiga cikin gidan, bincike sosai sukayi, dukkuwa abinda suke buk'ata sun samu, suka fito kowa yanufi mota. Sai kallonsu akeyi, wani yace, "wlhy ko rantsuwa zanyi babu kaffara aciki, wancan (ya khaleel) shine Wanda yafara zuwa wajennan a matsayin mahaukaci, sati biyune dasuka wuce aka canja da wancan (Mahfouz). Gaskiyar ka wlhy, hakane. Ya khaleel dake jinsu yayi murmushin k'asaita, sannan yataka yashige motar da'aka bud'e masa. Tabbas ya khaleel ne yafara zuwa a matsayin mahaukacin, sati biyu dasuka wuce wani aiki yataso masa zuwa Saudia shine Mahfouz ya maye gurbinsa. Tunda suka tafi kwance yake kawai ajikin kujera, duk abinda yafaru sai dawo masa yakeyi azuciya tiryan-tiryan, lamarin tamkar shirin film ko novel, baita6a tunanin zasu samu sauk'i hakaba wajen kama tantirinnanba saboda had'arinsa, amma Alhmdllh ALLAH ya sauk'ak'a komai, dukda and'an sha gimurzu dai. Ahaka suka isa hotel d'in dasuka kwana, kafin da yamma jirginsu ya tashi zuwa Abuja. ____________________________ Komai cikin fargaba da yanayin kasala take yinsa, tanajin Raudat na kuka tun d'azun amma takasa lallashin yarinyar, kukama ita kanta takesonyi amma takasa saboda soyewar da zuciyarta tayi. Ahaka ya Naufal yashigo d'akin ya sameta, kai tsaye wajen d'iyarsa daketa tsanyara kuka yanufa, ya d'auketa da sauri yana ra6ata da jikinsa tareda fad'in oh my dear mah-mah, waye yata6amin ke?. Duk abinda ke faruwa idon meerah na akansu, amma azahirin gaskiya zuciyarta bata atare dasu, girgiza kai kawai ya Naufal yayi shi Kansa meerah tausayi take bashi, tun jiya batada wani sukuni, bare safiyar yau, kamata yayi yaud'in tazama ranar farin cikinta da zumud'in ganin mahaifiyarta da 'yan uwanta, amma ko kad'an babu d'igon hakan daga gareta, sa6anin Aysha daketa murna. Shinfid'ar da Raudat yayi akan sofa, yamatsa kusada meerah data zuba tagumi har yanzu kuma idonta akansu. Rigarta yad'auka data ajiye asaman cinyarta yafara k'ok'arin saka mata, bata hanashiba, Dan batada wani k'arfin shirya kan nata, tsaf yagama kimtsata, ya d'akko gyale ya lullu6a mata, sannan yad'auki Raudat da handbag d'inta irinta masu goyo, yakama hannun meerah batareda yace uffan ba suka fice. Tuni su Aysha duksun fito, dad & mom, safwan, Iklas, duksun shiga mota. Sai ifteehal da Aysha dake a tsaye jikin motar Maheer. Da ido ya Naufal yamasu Aysha magana akan sushiga mota, yabud'ema meerah tashiga itama, sannan yashiga gaba kusada Maheer, ifteehal na tsakkiya, Aysha na gefe kusada Maheer. Suna fita daga gidan wasu zafafan hawaye suka zubo a kumatun meerah, bata bari kowa yaganiba taja gyalenta tarufe, ya Naufal ne kawai yalura da ita, saboda dukkan hankalinsa na akanta. Dama Raudat tana hannunsa. Tun Aysha na d'agowa suna had'a ido da Maheer dake binta dawani mayen kallo harta bari, Dan duk jikinta itama yayi sanyi k'alau, musaman dataga yanayin da anty meerah take aciki, wadda yakamata tafita murnar ganin family NATA, kasancewar shekaru 9 bata k'asarta, gakuma alkairin haihuwa data samu tasanadin aure, amma duk wannan bai k'arfafa guywar Anty meerah ba tayita zumud'i. To barema ita da iyayenta basusan mi'aka turata tayo a turaiba, tunda yaudararsu akayi. Tafiyar 3hours ce takaisu Kaduna, dayake ba gudu sukeyiba, saboda yin driving irinna turai, tundasu komai nasu yana tafiyane da doka, bakamar nan Nigeria ba da ba'a binta. Meerah tafad'a musu anguwar dazasuje, kasancewar dad'ewa bata k'asarma gaba d'aya bare garin yasakata manta hanyoyi, gashi kuma ansamu cigaba nawasu al'amuran, koda sukaje anguwarma saida sukayi tambaya, kasancewar gidansu meerah sanannene saboda mamansu tanayin markad'e da, shiyyasa akece mata mama mai markad'e. Sun tanbayi wani d'an dattijo dake facin tayoyin keke a k'ofar wani shagon provision. Dattijo yay shiru alamar tunanin gidan, zuwa can yace, "kai ban ganeba, amma bara muji komai shagonnan yasani. Ak'ilu! Dattijo ya kwad'ama mai shago kira. Ak'ilu ya amsa yanamai lek'o kansa ta window n shagon, yace, "m. labaran miya farune?". A'a dama mutanen nan ne, suke tanbayar gidan mama mai markad'e, koka santane?. Ak'ilu yace kai dallah k'aba kawai, gidansu 'Daheera 'yar maye fa, wadda aka guntule k'afar babarsu sati hud'u dasuka wuce. Wata fad'uwar gaba meerah taji, har ganinta yakau Na wucin gadi. Ta tsinkayo muryar labaran nafad'in okey ai namantama wlhy, kuje ga yarona yarakaku, kai auwalu tashi karakasu gidan, aika sani ko?. Eh, Awwalu yafad'a cikin zumud'in murnar zai hau babbar mota. Motarsu mom yashiga, saboda tasu ya Naufal d'in acike take babu waje. Har k'ofar wani tsohon gida yakaisu, Wanda gefen katangar hannun haggu tazube, anyi katangar da ledar buhu, meerah tarintse idonta tana ambatar innalillahi'wa inna ilairraji'un. Tabbas wannan gidansune, koda tahad'a shekaru tara bata cikinsa koda yaushe zuciyarta Na ciki, gidan dukya fita hayyacinsa, kamar bashi baneba tabari yana sabo, Sai d'aukar ido da burgewa yakeyi alokacin, amma yanzu kaikace almajiraine ke'a ciki, saboda tsabar fita kukkurjewa da bangon yayi. Jiki a sanyaye duk suka fito, amma banda meerah, wadda saida ya Naufal yafito da'ita dakansa, Raudat tana hannun Maheer. Ya Naufal da meerah ne Agaba, kama hannunta dayayine ya tilasta mata binsa badan tasoba. Su Aysha Na take musu baya, yayinda mom & dad ke'a k'arshe. Da sallama suka tura tsohon milk d'in gate d'in suka shiga, tsabar daud'ar dayayi yakoma brown kuwa. Mama daketa faman Jan d'uwawu, saboda babu k'afa 1, an yanke, tafito daga toilet tad'ago tana amsa sallamar tasu. Cak numfashinta yad'auke alokacin datayi tozali da'abar begenta, ko shekara 100 Ameerah tayi basa tare saita gane abarta, barema shekara 9..................✍🏿 Nace humm🤕 *_Kutttt sosaifa nakeyinku my sweet Guy's, kudai kawai ALLAH ya kaimu ranar bikin babyna, duksai kunyi rawar one corner_*🤣🤣🤣😍😍😍😍😍😘😉 [8/25, 9:17 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _Kuna raina *HAUSA NOVEL FARIN CIKI* kuma, bilyn Abdul bata manta dakuba._ _ina yinku aradu_😍😍😘 3⃣4⃣ To masu iya magana nacewa d'a da mahaifa sai ALLAH, hakance tafaru da meerah, dukkan wani 6acin ranta da tsanar mahaifiyar tata datayi, hakan bai hanata kwace hannuntaba dagana ya Naufal tanufi mama da gudu tana kuka, kanta tafad'a tana rubzar kuka mai matuk'ar tada hankalin mai saurarenta. Ya Naufal dasu Aysha duk sunyi tsaye suna kallonsu, wasunsuma kuka sukeyi suma. Kusan mintuna 4 meerah da mama nata kuka, kuma suna'a rik'e da junansu. Ganin kukan zaiyi yawane yasaka mom matsawa ta janye meerah daga jikin mamar saboda ganin halin ciwo da mama take aciki. Rasa inda mama zata ajiye wad'annan 'yan gayu tayi, sukam su mom babu ruwansu, tabarmar dake a falon suka zazzauna, Raudat cedai keta kuka saboda zafi bata sababa, gashi dama yaud'in da akwai rana. Maheer daketa faman jijjigata akan tayi shiru yace waimike damun Raudat ne? Dukta rud'e wlhy. Mom tamik'a hannu ta kar6eta, cikin hausarta dabatama iyaba sosai tace maybi zafine, tafara k'ok'arin cirema yarinyar Riga, mafici mama tamik'o Dan ama Raudat fifita. Dad yakar6a yana fifita Raudat data fara rage kukan tana sauke ajiyar zuciya ajikin mom, kai kace wata babbace. Saida ta tsagaita da kukan sannan mom tamik'ama ya Naufal dake kusada ita, Naufal mik'ama Meerah tabata abincinta. Kar6arta yayi tareda sumbatar goshinta, my dear mah-mah sorry kinji, zafine kawai yamiki yawa nasani, yamik'ata wajen Meerah da gaba d'aya hankalinta na'akan mamanta. Saidama ya zungureta sannan tajuyo tana kallonsu shida d'iyar tasa, da ido yamata nuni yunwa. Batace komaiba takar6eta tad'ora a cinya, mama dai tana kallon ikon ALLAH, da al'ajabin abinda ke shirin faruwa, wai Meerah da d'iya. Bata k'ara gaskatawaba saida taga tafara shayar da yarinyar sannan. Dad datun d'azun yake kallon mama a sace, yadai daure yace nikam baiwar ALLAH Na tambayeki mana?. Mama tace ina saurarenka Alhaji. Dad yagyara zamansa, yayinda duk idon yaran ke'a kansa Dan mamakin furucinsa ga maman meerah. Yanisa sannan yace, kama kikemin dawata a sokoto mai suna Zainabu 'yar Dije. Mama da idonta yacika da hawaye, tace tabbas itace, kuma tunda kashigo nake maka kallon Sani, saidai banida tabbas akan ko yahaya ne k'anin malam Abdul'majedu?. 'Yar zabura dad yayi, bakinsa har rawa yakeyi yace tabbas shine, Abu kina nufin da gske kece?, ina d'an uwana Abu? Kardai kice Ameerah jini nace? Karki cemin haryanzu baki canjaba Zainabu?. Inna lillahiwa'inna ilairraji'un, dad yashiga ambata yana hawaye. Tofa falo yayi tsit ana kallon ikon ALLAH, mama da dad duk kuka sukeyi, Wanda babu Wanda yasan ma'anarsa cikinsu ya Naufal.. ____________________________ Tunda suka zo gidan gwaggo bintu batada lfy, wannan yasaka matan gidan babu Wanda yasan da zuwanta gidan. Sun sandai zuwairah tazo, itakam dama babu matar datake gaidawa agidan, saima tazo tagama zamanta baifi tahad'u dasu Anty Mamie sau uku ba, shima sai idan tata ta fiddota daga 6angarensu, amma bada nufin gaida matan gidanba, to yanzuma girma yak'aru ga daraja, saboda dawowar mama tayi alk'awarin tadaina shiga 6angaren ko waccensu. Iya hama ce takaima mama gulmar dawowar Gwaggo bintu gidan, harda halin datake ciki. Anty Mamie akwai tausayi. Wannan yasaka hankalinta tashi tanufi gefin masu aikin taduba gwaggo bintu, ganin halin datake ciki yasakata kiran Hafiz yayi driving nasu zuwa asibiti itama tana nan tahowa zata gama wani aiki. Hafiz yad'auki iya hama da gwaggo bintu dake kashir6an cikin halin rashin lfy yatafi. Komai shiyayita k'ok'ari aka mata, har aka basu gado, sai a sannan Anty Mamie ta k'araso itada ya Zunnurain daya kawota. Da taimakonsu aka kammala komai, gwaggo bintu tafara samun kulawa. ___________________________ Saida sukayi kuka mai isarsu sannan falon yay tsit, dad yace Abu miya dawo daku Kaduna? Nidai nasan harna bar k'asarnan kuna sokoto?. Hawaye mama tashare, cikin nadamar abinda ta aikata tace yahaya ka gafarceni, tabbas ni azzalumace, kuma na cutar dakai kaida d'an uwanka. Tabi su ya Naufal da kallo tana hawaye, tace bara nabaku labarin wacece zainabu 'Yar dije. *Tuna baya* Kamar yanda kuka sani mu 'yan asalin sokoto ne, amma a k'aramar hukumar Gwadabawa, Ni bama cikin gwadabawa nakeba, ina awani k'auyene Bamana, tallar kayan koli ke kawoni cikin gwadabawa, a k'auyenmu na Bamana babu Wanda baisan Zainabu 'Yar dije ba, tun ina k'aramata banajin magana, Dan ko'a gidanmu babu Wanda ya isa yasani nayi, babata dije bata yarda ko hararata ayiba agidan, kasancewar nikad'ai tahaifa aduniya. Tallan kayan koli danake zagawa k'auyika da cikin gwadabawa yasaka idanuna suka k'ara bud'ewa, kokad'an bansan bariba. Ayawon tallata nahad'u da Abdul'majedu, soyayya kuma tak'ullu a tsakaninmu, har akayi aurena da Abdul'majidu danginsa basason auren, musammanma yahaya, Dan yasanni sosai, idan nakawo talla har majalissarsu nake zuwa. Wannan k'iyayya da yahaya ya nunamin yasakani tsanarsa, kokad'an bana raga masa bayan na auri yayansa, kullum babu abinda nakeyi sai had'asu fad'a, saidai abdul'majidu baya kulawa. Hakan yana k'onamin rai, dan aganina Abdul'majidu yafison k'aninsa dani. Saida mukayi shekaru goma bansami haihuwaba, zuwa sannan yahaya yayi aure. Harma matarsa tayi 6ari, 6arin datayi yatada hankalina, gashi tafini samun jin dad'i ajaken mijinta, hasalima arzik'insu mikeci. Wata ranar talata muka tashi da alhinin rasuwar mahaifiyarsu yahaya, sosai yahaya yayi rawar gani akan hidimar rasuwarnan ta mahaifiyarsu, yabon da akaitama yahaya awajen rasuwar ya6ata raina Dan haka na kullaceshi a zuciyata. Shiryawa nayi naje k'auyenmu, na fad'ama tsohuwata komai, ita tabani shawarar abinda yakamata nayi yahaya yabar gidan, shawararta kam tayi tasiri, Dan ina dawowa washe gari nakira yahaya d'akina akan zamuyi magana, lokacin Abdul'majidu baya gida. Saida yashigo d'akina da sallama, ina la6e abayan labule nikam, yayta sallama nak'i na amsa mishi, saiya nemi guri ya zauna Dan azatonsa ina band'akine. Ina nan ala6e ban fitoba saida naji motsin dawowar Abdul'majid, wuf nafito natsala ihu ina kiran kwarti-kwarto. Kankace mi gida yacika da jama'a, yahaya dukya rud'e, mutane kuma sai tsinarsa sukeyi, babansu harda kuka da matarsa, awannan karonkam Abdul'majidu ya yarda yahaya yazo kwartanci d'akina. Sannan ya haddasa fad'a sosai a tsakaninsu, ko kad'an Abdul'majidu yak'i sauraren yahaya, gashi ina k'ara kunna musu wuta daga gefe. Matar yahaya kuwa takoma gida, tace bazata iya kallon wannan abin kunyaba, daga Bayama sai iyayenta suka nemi yasaketa. Gwadabawa tayima yahaya zafi, babansu da yayansu suna fishi dashi, ga matarsa anrabasu, wannan yasa yashirya batareda sanin kowaba yabar Gwadabawa. Wayyo hakan yamin dad'i, daga nan duniya tazama sabuwa agareni. Shekarun yahaya kusan uku dabarin gida mukaji labarin wai wani Alhaji yatafi dashi k'asar waje, sai da naji babu dad'i, Dan banason naga yahaya yacigaba arayuwarsa. Alokacin kuma gaskiya tafito. Mahaifinsu yahaya yasan gaskiyar magana akan tuggu nashiryama yahayan, abin ya6ata ransa, harya kwanta ciwon dayazama ajalinsa. Tundaga rasuwar baba muka fara fuskantar matsaloli a k'auyenmu, sai zagina akeyi, shima kansa Abdul'majidu bai tsiraba, ahaka ALLAH yabamu ciki alokacin, munyi murna sosai kuwa, nahaihu da kwanaki 9 babata dije tarasu, nashiga tashin hanakali sosai, dama itace me k'arfafamu, aikam rasuwarta garin gwadabawa yagagaremu zama, dole muka d'akko d'iyarmu Suwaiba muka gudo sainan Kaduna........... Kaf takwashe labarin zamansu na Kaduna tabamasu dad labari, harda barin Ameerah k'asar. Da bala'in data shiga bayan tafiyar Ameerah, yanzuma basusan inda Suwaiba takeba, 'Daheera kuwa tazama 'Yar shaye-shaye, k'annen Ameerah biyu kam tuni suka koma sokoto, itakuma taita ciwo, dak'yar tasamu makwafcinsu ya taimaka mata zuwa asibiti, shine akace tanada ciwon sugar (diabetes), anasakamin dokoki akan abinda zan ringaci, amma nak'i bin doka, saboda lokacin duniya nakaimin, akwai kud'i a hannuna, shekara ta 2 kenan wani maruru yafitomin, yayi ruwa anmatse, amma saiya k'ara wani ruwan aka matse, yak'arayi, hakadai yayta girma harya zamemin gyanbo ak'afa, ganin k'afata zata ru6e nahad'a dukkan kaddarar dana siya dakud'in tafiyar amirah nasaida, shine makwafcin nan nawa mutumin kirki yasake kaini asibiti aka guntule k'afar, Dan since zata harbi dukkan jikina... Tak'arshe maganar da rushewa da kuka. Labarin ya girgiza su Naufal, mom kanta dabawani jin hausar takeba sosai saida tayi kuka, da mamakin wannan murd'ad'd'ar rayuwa. Shima dad yabata labarin cigaban daya samu tundaga barinsa gida, har zuwansa turai, da karatu dayayi, yanuna mata matarsa daduk 'ya'yansa, harda had'uwar Naufal da Meerah a islands UK, Dama auren dake tskaninsu, harda k'yautar Raudat da ALLAH yabasu. Mama tak'ara fashewa da kuka, da jinjina Girman mulkin ALLAH, tana Neman gafarar ameerah tana kuka, da nadamar abinda ta aikatama gudan jininta da kanta. Ya Naufal yace nifa nayi mamakin irin wannan k'auna dake tsakaninmu da meerah, ashedai jininace ban saniba, ALLAH mai alkairi kenan, maji6incin al'amuran dake 6oye. Mama kamar zata cinye Raudat danso, itace jikarta data fara gani aduniya, to cikin 'ya'yan natama wakeda niyyar aure, suwaiba ma Takai shekaru uku rabonta da gidan, 'Daheera kan saidai addu'a. Hotel suka koma suka kwana, akabar meerah nan susha hirar yaushe gamo da mahaifiyarta. Amma ina Raudat kuka takwanayi, zafi ya isheta, ga sauro, abinda bata Sababah. Dole washe gari ya Naufal yanemo Generator da AC aka sakamusu, a daddafe sukayi kwana uku, washe gari kuma suka rankaya Kano da nufin idan sun dawo daga Raka Aysha Susan yanda zasuyi da mama, Dan baikamata abarta ananba. *kano* .................✍ Kumuje zuwa Guy's😄, Sholyn Ku a kn😉. 😍😍😍😍😍😍😘 [8/25, 9:58 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 3⃣5⃣ Kano tadabo tunbin giwa, kofa dami kazo dagaske munfika😜, amma banda tsiya🤕. Tunda akace sunshigo Kano farincikin Aysha ya bayyana, babu abinda kake gani tareda ita sai farin ciki tsantsa, itakam tsaf tagane gidansu, dukda canje-canje da'aka samu kuwa, gidanma gaba d'aya ya canja mata, danyasha sabon fenti sai d'aukar ido yakeyi, 'yan anguwa kam sai kalon zuk'a-zuk'an motocin sukeyi, hardasu Kansu masu motocin, ko kad'an babu wanda yagane Aysha, to yama za'ayi kad'auka Aysha bahaushiyace, balle tak'ara girma da k'yau, kaikace irin bak'ak'en Amurakawan nanne, itakam dayawansu ta shaidasu, saidai dukta mance sunansu, murmushi taketa zubawa abinta, dakanta tamusu jagora zuwa cikin gidan, tunda sukayi sallama tafara kwala kiran mama da Ummah. Fadeela daketa faman jijjigar Ummu-hanee tana kuka talek'o Dan mamakin kiran da ake kwalama iyayen nata. Tsam tatsaya tana tantama akan shin Aysha ce? Kokuma watace mai kama da Aysha?, gadai kamannina na Aysha ajikin matashiyar budurwar, amma ko dawasa ba'a fara kiranta Aysha ba. Da gudu Aysha tak'arasa wajen Anty fadeelah, ta mamuk'eta tana ihun murnar ganinta, ihunne yatada Ummah dake barci saboda kanta dakeyin ciwo. Ai Aysha naganin Umma tasaki Fadeelah taje ta d'are Ummah, wayyo ummanah nayi kewarki wlhy. Ummah tarungume Aysha, hawaye nazuba a kumatunta tace Aysha dagaske kece? Dama zaki dawo garemu? Shikenan babuke babu bintu?. Meerah mom ifteehal natsaye suna kallonsu cikin burgewa. Dad da Naufal maheer suna k'ofar gida suna jiran amusu iso. Fadeelah Ce taimasu mom marhabun, aka shiga dasu falon Ummah, haryanzu Aysha na nane da Ummah, sai tanbayar mama takeyi, babudai Wanda yabata amsa. Bayan zamansu ne fadeelah takawo musu ruwa, Ummah kuma takira number mijinta da kawu bilyamin, hardasu Qasim yayunta wad'anda aketa shirin bikinsu. Aysha tak'ara fad'in Umma wai ina mama?. 'Yar dariya Ummah tayi. Tace Aysha mama na Abuja abinta. Abuja kuma Ummah? to wajen wa?. Aure takeyi, Ummah tafad'a tak'aice. Nan take fuskar Aysha ta canja, idonta tab da kwallah tace aurefa Ummah?. Kishin sosai a idanun Aysha tana taya mahaifinsu kishi. Babu Wanda hace komai saboda shigowar Mijin mama da kawu bilyamin, saisu dad dake binsu abaya. Gaishe gaishe aka fara, kowa sai d'okin ganin Aysha yakeyi, ita kuma tana jikin Ummah rik'eda Ummu-hanee. Su dad sunyima su kawu bilya bayani akan Aysha, amma sun 6oye komai kamar yanda Aysha tabuk'ata, Dan so take da kanta tad'au mataki akan su gwaggo bintu. Sunce Aysha karatu taje, kuma tun farko a hannunsu take, kowa yaji dad'i kuwa, sunsha godiya sosai. Kafin kacemi anhad'a musu cima mai k'yau da gamsarwa. Dukda bawani sabawa da cimar sukayiba sunci babu laifi, ita kanta Aysha ta fara manta cimar k'asarta, (kowa yabar gida, aii dolene gida yabarsa).. Aranar aka kira mama aka sanar da'ita dawowar Aysha, tayi farinciki, jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta a Kano, lokacin suna shirin zuwa asibiti duba gwaggo bintu. Tace zata taho Kano gobe idan ALLAH ya kaimu. Kawu bilyamin yace a'a tayi hak'uri, insha ALLAH nanda kwana uku za'a kawo mata Aysha har gida. Wannanne yasakata hak'ura da zuwan. Aranar su dad suka baro Kano, Aysha harda kuka dazasu taho, sunyi sallama akan saita zo Abuja, suma daga nan Kaduna zasu tsaya, sai zuwa jibi zasu shiga Abuja, daga nan zasuje sokoto ma. Zuwa yamma saiga Hafsat, su Rufaida da sadiya ma saigasu, gida yagama had'uwa, Aysha tana tsakkiyar danginta, jitake kamar ta shekara dubu basa tare, sukam sai sha'awarta sukeyi, danta canja musu gaba d'aya, saikace wata baturiya, anyi-anyi takira mama tak'i, dukda d'okin ganinta datakeyi wai fushi takeyi da ita akan tayi aure, hakama Ummah duk haushi suke bata ita adole kishin babansu takeyi. Makwafta sai shugowa akeyi ganin Aysha 'Yar turai, kai kace wani abin kallo aka kawo gidan. Koda yake Aysharfa ta cancanci azo kallonta, Dan komai nata ya canja, dolene kaganta ta burgeka harka lalace wajen kallonta. Har washe gari bata canja zaniba, 'yan uwa sai tururuwar zuwa ganin Aysha akeyi, itakam kowa yazo kar6ar mutumci take masa, dama can ba halin Aysha bane wulak'anta jama'a. _____________________________ Su mama sun isa asibiti itada Anty Mamie domin duba bintu. Saida doctor d'in dake dubata yafito sannan suka shiga, gwaggo bintu na zaune akan gado, ta jingina da filo, bishirah nabata abinci, sallama dasu mama sukayice tasakata d'ago ido tana kallonsu da amsa sallamar ahankali. Ganin mama yasaka gwaggo bintu wata zabura, har taune harshe takeyi wajen fad'in fad'ima! Kece?. Mama ma tace, "bintu! Dama kece mara lafiyar?". Hawayene suka shiga zarya a kumatun gwaggo bintu alokacin data tsinkayi muryar Anty Mamie na fad'a mata aii itace Baffansu ya aura kwanaki ko, kuma matarsace tunkan ya aureta, jikinta sai rawa yakeyi, tabbas tasan mama tata6a aure kafin ta auri yayansu, kenan Alhaji Abdallah jigawane dama tsohon mijin nata?, nan take zufa tafara ambaliya akowane sashe najikin gwaggo bintu, fad'i take a zuciyarta nashiga uku ni binta, yanzu yazanyi da wannan kulli? Ina zan samoma matarnan 'yarta? Nasan dolene ta tambayi ina Aysha, ni bintu nashiga Tara, nikuma k'arshena yazo kenan, hajia babba kin cuceni keda shaid'anin daya bani k'arfin guywar yarda daku. Babu Wanda yazargi wani Abu tsakanin Anty Mamie da mama, duk zatonsu ciwon ne yake damunta, dukda mama tana ganin kamar mamaki gwaggo bintu tayi dakasancewarta matar mai gidanta. Sunkai mintuna 30 a d'akina sannan sukai musu sallama suka fito, amota mama take sanarma Anty Mamie dangan takar dake tsakaninta da gwaggo bintu (wadda suke kira Maman yara), Mamie tayi dariya, tace haba shiyyasa naga ta nuna mamakinta da ganinki, lallai ALLAH kenen mai hikima. Mama tace aikuwa dai, (bata fad'ama Mamie komaiba dangane da rashin k'aunar da gwaggo bintu take nuna mata, lokacinda tana matar yayanta). Harda sukazo gida abin na'a zuciyar mama, amma bata damuba, tunda alhamdulillah 'yarta tadawo gareta. Gobe idan ALLAH ya kaimuma, zatazo Abuja itada fadeelah. _____________________________ Washe gari Aysha da fadelah sukayi shirin zuwa Abuja, da mortar haya zasu hawo, amma sai kawu bilyamin yabada motarsa akaisu. Hakan yayma Aysha dad'i, dan dama batason hawa motar hayar. Kasancewar tafiyar yamma sukayi sai around 6:30 suka iso anguwar ta mai-tama. Gaban Aysha ne yaketa luguden fad'uwa tunda suka shigo anguwar, danta gane anguwar data zaunace kafin barinta k'asar, mamakine ya isheta akan miya kawo mama nan?, batama tsinkeba saida taga mortar tatsaya k'ofar gidan alhaji Abdallah Jigawa tana horn, kallon fadeelah tayi, tace Yaya fadeelah anan mama take aure?. Eh, nanne Aysha, fadelah tafad'a kanta tsaye. Shiru Aysha tayi tana had'iyar yawu, aranta tace *Cakwakiya kenan*, lallai nabar *baya da k'ura*, wannanfa shine *Kwai cikin k'aya*.🤥 Abubuwa dayawa sun canjama Aysha, bakamar zuwanta da gwaggo bintu ba, taga ancanja gate d'in gidan, hakama ansamu wasu sauye-sauye, fentin gidanma bawanda tasani baneba.dukda sun isa ana shirin magriba ne hakan bai hana anguwar kasancewa cikin hasken wutar lantarkiba, ko ina farr da haske. 'Dan gwari mai gadi dai haryanzu shine gateman d'in gidan, amma yad'an kara manyanta, bakamar sanda Aysha ta sanshiba. Aharabar gidan baba bala yayi fakin, kamar ankwashema Aysha jini haka tafito daga motar, handbags nasu kawai suka d'auka, sauran kayan baba bala yace suje za'a shigo dasu, fadeela sai zumud'in Shiga takeyi dantayi kewar mama, amma ga Aysha Sam abin Bahaka baneba, tafiya takeyi kwakwalwarta na tariyo mata baya, jitakeyi kamar yauma tazo gidanne amatsayin boyi-boyi Mara 'yanci. Rungumetan da akayine yasakata sakin ajiyar zuciya da d'ago kanta, Ashe harsun shigo falon batama saniba, mamace tarungume Aysha cikin matuk'ar kewar 'Yar d'iyar tata, itama Aysha ganin haka saita k'ank'ame Maman tareda sakin wani irin kuka dabasan dalilinsaba. Fadeelah dai 'Yar kallo takoma. Babu kowa a falon, Duk sun shige d'akuna Dan gabatar da sallah, 'yan uku ne kawai ke k'iriniyarsu. 6angaren mama suka yanda zango, saboda tsabar farinciki mama tama kasama Aysha magana, sai kallonta takeyi tana zuba murmushi. Ayshar Ce tagaji tace Mamana nayi kewarki, ina sonki, amma shine kikayi aure bansaniba ko? Tak'are maganar da turo Baki gaba. Daga fadeelah har mama abin yabasu dariya, Dan haka suka dara abinsu. Mama tace to Aysha ayima mama afuwa, nasan kina kishin babankune, amma inaso kiyarda da k'addara, haka ALLAH ya hukunta mana, nima bawai da son raina baneba kinji. Aysha ta jinjina kanta, saitaji tama daina jin haushin mamar, wanka sukayi sukai salloli, mama tayima umma-hanee itama, 'yan uku na nane zasu Aysha, Aysha sai dad'i takeji suma yanzu mama ta haifesu dayawa, gata da k'anne maza, abinda tadad'e tana sha'awa kenan. Bayan sunci abincin da mama ta shirya musu suka mik'e danzuwa gaida mutan gidan, harsun fara shirin Fita saiga Anty Mamie tashigo, a'a inakuma zakuje?. Fadeelah tace zamuzo gaishekune Mamie. A'a fadeelah kuzauna Ku huta, wanan wahalar tafiya aii tayi yawa, da safe sai'a gaisa aii, nima sallah natsaya yi shiyyasa ban lek'oba tunda kuka shigo, Dan 'yan uku sunkaimin labari. Mama tayi dariya, aii wad'annan 'ya'yan naki bilkesu sune redio mai jini. Mamie ma dariya tayi, tace a'a a'a, ai abunda suka gani suke fad'a. Aysha sai kallon Mamie takeyi tanajin k'aunar matar aranta, amma talura bata ganetaba, taji dad'in hakan, Dan dama bata fata kowa yaganeta agidan, hakanne zai bata damar aiwatar da aikinta akan su hajia babba hankali kwance. Mamie tace d'iyata 'yan turai, ya turai da karatu?. Murmuahi Aysha tayi, cikin rissinar dakai tace alhmdllh Mamie, munsameku lafiya?. Lfy lay muke, yagajiyar hanya?. Alhmdllh. To masha ALLAH, mamie tafad'a tanama ummu-hanee dake hannunta wasa. Mamie ce tahanasu zuwa gaida kowa agidan tace su huta, dama baffah bayama k'asar, Ammah kuma tana Jigawa. Daman takanje tayi dogon Hutu a can idan tajuyo mata..............✍🏿 *_I love you all😍😍😍😍😘😘😘😘_* [8/26, 8:48 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 3⃣6⃣ Washe gari su Aysha basu tashiba sai around 9, wanka sukayi sannan mama takawo musu breakfast sukayi, bayan sun kammala suka fita gaida mutanen gidan. Da Anty Mamie da umme Amaraya kawai suka gaisa, itama bata fita da wuri baneba, hajia babba kam tafita aiki, samarin gidan kowa yatafi uzurinsa, hakama su Amal, shiru gidan, 'yan ukuma sunfara makaranta shiyyasa gidan yayi tsit. Sun d'an dad'e a 6angaren Anty Mamie sannan suka dawo d'akin mama. Mama takallesu cikin soda k'aunar y'ay'an nata, tace, "kutashi Ku shirya baba bala yakaiku shoprite kuyo tsaraba. To suka fad'a suna mik'ewa, Aysha tasaka wando da Riga sunmata k'yau. Amma sai mama ta harareta, nifa matsalata da shiga al'adun wasu kenan, duk taka tsantsan d'inka sai yaro yakoyo abinda va tarbiyyarsaba, Aysha cire kayannan kisaka wannan less d'in, mama tayi maganar tana mik'ama Aysha farin less mai k'ananun jajayen fulawoyi. Kamar Aysha zatayi kuka haka takar6a, itafa kayannan nauyi suke mata yanzu wlhy, amma bazata iya yima mama musuba, itama dai tasan masifar mama darashin d'aukar raini. ALLAH yasotama siket ne ba zaniba, kayan sunyi masifar mata k'yau, gashi basu kama mata jikiba, bata d'aura d'an kwalinba, Dan bazata iya da wannan kayan nauyinba, siririn Jan gyale tayane katta dashi, gashinta datayi parking a tsakkiya yanata kyalli da k'amshi saiya zauna d'am a gyalen, har ana hango jelar gashin data kwanta a dokin wuyanta kad'an, saboda gyalen shara-shara ne, kasancewar yanda tayi acuci da gashin nata ya zauna sosai sai gyalen yad'an zama kad'an daga gaba, kwantaccen gashin gaban goshinta yayi luf-luf kamar atsaya kaita kallonta dan kyawun datayi. Ita kanta mama saida tafurta masha ALLAH a zuciyarta, Dan tasan d'iyar tata abar kalloce. Aysha tad'auki Ummu'hanee akafad'a tafita tana zun6ura baki, ita adole fushi takeyi ansakata saka kaya masu nauyi. Fadeelah tabiyo bayanta rik'eda 🏧 d'in mama tana dariya. Tunda suka Isa shoprite d'in k'irjin Aysha ke bugu da sauri-sauri, addu'a tafara karantowa ahankali, basuwani 6ata lokaciba suka fara duba abinda suke buk'ata, Aysha ce rik'eda keken🛒tana za6a tana sakawa bayan tad'an duba bayan, Anty fadelah Na rik'eda Ummu'hanee tana taya ayshar da shawara. Har sund'an gota shoprite d'in yadakatar da Emmanuel, Ema yataka burki ahankali yana fad'in yes sir. Kamar bayason magana yace Ku koma baya mushiga shopping zan d'anyi. OK sir EMA yafad'a a giramame. Saida Ema yanuna ID cart d'insa aka bud'e musu gate d'in da sauri, motocin uku suka Shiga ajere. Adams ne yabud'e masa k'ofa yafito, cikin takun Nutsuwarsa kamar kullum yake tafiya, yayinda su Ema ke take masa baya. Sanye yake cikin Uniform d'in aiiki, amma babu hula a hannunsa, ko gun d'insama a mota yabarta, kallon yaransa yayi yace kowa yad'auki abinda yake buk'ata, baijira amsarsuba yay gaba. Adams ne kawai yay saurin jawo keken yabi bayansa. Sukuma sauran sunata Murna, da yabon adalin ogan Nasu, Wanda yasan darajar Na k'asa dashi, bashida bak'inciki ko kad'an, ga k'yautar ban girma, komai nasa abin sone, haka kowa yafara d'aukar za6insa suna zuba masa addu'a azuciyarsu. Bugun zuciyarta ne yatsananta, waige-waige tafara, Dan lamarin yafara tsoratata, babu wani alamar abinda yashafi rayuwarta awajen, Dan haka ta dake tacigaba da duba abinda take buk'ata. K'un k'unan kuka da Ummu Hanee tafarane yasaka fadeelah komawa gefe tana jijjigata, Aysha kuma tak'arasa d'aukar abinda zasu d'auka. Taku yakeyi cikin nuna shinfa jarumine mai wadataccen jini, kasaitarsa da kwarjini sun taka rawar gani wajen bayyana kwarjininsa, musamman kayan aikinsa dasuka k'ara haska chocolate colour d'insa mai matuk'ar taushi da d'aukar idanu, k'asumba tad'an taru masa afuska, hakama kansa akwai Y'ar kwantacciyar suma, hakan yanada nasaba darashin lokacin kai, Dan aiki ya cakud'e masa sosai a d'an tsakaninnan. Yana tafiyane kunnensa manne da waya, magana yakeyi ahankali kuma cikin nutsuwa, Wanda baisaniba saiya d'auka da matarsa ko budurwarsa yakeyin wayar, fuskarsa babu walwala, yanayi yana duba abinda yad'auka, saiya d'an karanta kafin yajuyo yasaka a keken da Adams yake turawa. Wannan salo nasa yayi masifar tafiya da y'an Matan wajen, kai hardama samari ma'abota son burga. Dukda zuciyarta Na masifar harbawa hakan baisa tadamu da kallon wad'anda ke bayanta da gabantaba, anutse takai hannu zata d'auki wani kwalin biscuit, shima yakai hannu. Akan nata hannun yad'ora nashi, da sauri kowa yajanye danjin wani masifaffen shock daya jasu atare, lokaci d'aya suka zubama juna idanu, burkitattun idanunsa masu girma da haske suka shige cikin Na Aysha manya masu yalwataccen gazar-gazard'in gashi. Da sauri Aysha ta janye idonta cikin tsinkewar zuciya tace ya khaleel!, amma a hankali batareda yaji mitaceba, sai dai motsin la66anta dasukasha pink d'in janbaki. Shikuma saiya d'an zaro idanunsa waje da mamaki yanunata yana fad'i you!!. Itama saita dake tajuya idanunta dake matuk'ar d'aukar hankalin duk wani mai kallonta, ta murgud'a masa baki. Ya salam! Yafad'a ahankali yana janye wayarsa daga kunnensa, yadafe kansa. Ra6awa Aysha tayi tagefensa tawuce bayan tad'auki biscuit d'inta. Ahankali yasaki siririn tsaki, aransa yace Aljana, mikuma tazoyi 9ja? Bayan a Canada yata6a ganinta?. Murmushi Adams yayi, Dan ganin yanayin ogan nasa, addu'a yakeyi aransa ALLAH yakai damo ga harawa, kobai ciba zaiyi sukuwa akanta. Ahankali ya sauke ajiyar zuciya tareda jan tsaki afili, yacigaba da d'aukar abinda yakeso. Awajen biyan kud'i suka iske Aysha, Adams ne yabi layi dan biyan kud'insa Dana Oga hardasu Ema dakowa yad'akko abinda yakeso. d'aukar Ice-cream da Aysha tatsayayi yasaka su ya khaleel suka zama sune abayansu wajen biyan kud'i, dayake Adams shiyyasa bata damuba. Ya khaleel nacan tsaye gefe tareda wani abokinsa dasuka had'u yanzunnan. Bayan anduba kayan tamik'a musu ATM d'in suka cire. Dukda zuciyarta Na farinciki da ganinsa hakan bai hanata k'in kallon indama yakeba, kad'an yarage tafita wasu garadan samari suka fad'o wajen suna ihu, hannunsu rik'eda bindugu. Gaban Aysha yafad'i, aranta tace 'yan fashi?. Harbin da macen cikinsu tayine yasaka illahirin mutanen wajen zubewa a k'asa, saidai banda ya khaleel dako gezau baiyiba, ita kanta ayshar ALLAH bai saka mata tsoroba, Dan kunnenta kawai tatoshe saboda k'arar bindigar, bayan tasaki ledojin hannunta. Ya khaleel yafara ta6a aljihumsa, amma saiyaji babu gun ko d'aya, hankalinsane yad'an tashi, gashi babu yaronsa ko d'aya akusadashi, abokinsa kam tuni yabi layin masu kwanciya ak'asa, sai ta6a k'afar ya khaleel d'in yakeyi waiya kwanta. Ya khaleel bai kulashiba, hankalinsa Na wajen ta'ina zai samu bindiga?. Aysha talura sarai da nufinsa, wannan yasakata kallon garjejen k'aton kusada ita, Wanda shi kansa tsaye ya khaleel yayi attack. Hankalintane yatashi lokacin dataga yafara saita kunamar bindigarsa. Cikin wani salon jarumta Wanda batasan tanadashiba ta wulla handbag d'inta tadaki hannun guy d'in, bindigar da bullet d'in daya harba sukayi wani tsalle. A cikin salon samun cikakken training ya khaleel ya ca6e gun d'in. Budurwar tayo kan Aysha da bindiga, yayinda saurayi d'aya Yakuma sakin kunamarsa akan ya khaleel, hankalin Aysha yayi masifar tashi lokacinda taga bullet d'in gadan-gadan a tsakkiyar kan ya khaleel daya juya baya zai sauka. Wani wawan tsalle tayi, saigata gabansa, tayi masifar hankad'ashi iya k'arfinta, kad'an yamatsa saboda batakai matsayin iya turashiba, hakanma tayi jarunma, dan dukkan k'arfin datake tak'ama dashi tasaka. Turashin datayi saiya zama bullet yadawo saitinta zai sauka bisa k'irjinta. Adai-dai lokacin kuma ya khaleel d'in yajuyo dansan ganin Wanda ya hankad'ashi haka?. Cikin zare idanu yakai mata wawura, jikinsa har rawa yakeyi yaymata runfa da faffad'an k'irjinsa, bullet d'in yasauka a gadon bayansa, kasancewar akwai Riga, makarin bullet ajikinsa sai bai shigaba yafad'i. Tana rungume a k'irjinsa, yayinda yake aduk'e da ita, cikin salon iya aiki ya harbi k'afar d'an fashi d'aya, yakuma juyawa cikin zafin nama yaharbi k'afar d'ayan, macen kuma sai harfi takeyi babu ka'k'k'autawa, amma babu Wanda yasamu ya khaleel ko Aysha acikinsu, Dan sosai Aysha ta mamuk'e ya khaleel saboda a tsorace take yanzu. Su Ema dake shigowa tabaya suka hankad'a macen tadaki keken baskets d'in dake jere agefe suka tafi suuuu itadasu. Sai asannan ya khaleel yad'ago, amma haryanzu yana rungume da Aysha datayi lamo ajinkinsa. Kowama awajen yamik'e tsaye ana kallon ikon ALLAH, wasukam har yanzu a tsorace suke da lamarin. Sunkama 'yan fashin su hud'u, ya khaleel sai alokacin yasamu damar janye Aysha daga jikinsa, itama lokacinne tadawo hayyacinta, hannunta yarik'e GAM anasa, batareda wani tunaniba. Cikin 'yan fashin guda d'aya dake hannun Adams yak'arasa, haryanzu hannunsa rik'eda nata, baiyi wata wataba ya harbi k'afarsa d'aya kamar yanda yayma sauran, wata razananniyar k'ara kuwa yasaki, da sauri Aysha ta fisge hannunta daga cikin Na ya khaleel ta toshe kunnenta. Saima yanzu yatuna da hannunta Na cikin nasa, sakin hannun yayi da sauri, Dan baya buk'atar azargi wani Abu daban, amma tabashi mamaki over, wai ita wacece?, yarinya kamar aljana, ga rashin kunya ga jarumta, wani gefen zuciyarsa yace gakuma taimako, dam badan itaba da dolene cikin harbi biyu da'aka masa bai saniba dolene d'aya yasamesa . Amma duk itace tabashi kariya, gata 'Yar ficit, yay maganar yana k'aremata kallo sama da k'asa. Itakam Aysha har lokacin hannunta Na acikin kunne takuma lumshe idanunta. Maganar Adams ce tasakashi janye rikitattun idanunsa daga kanta, yamaido kan Adams, Adams yay salute nashi, yana fad'in sir! Mukira police mubasu su?. No, yafad'a atak'aice. Nufar inda gyalen Aysha yake a yashe da handbag d'inta yana fad'in Adams inason binciken kwana biyu akansu, Dan da'alama ba fashine yakawosuba, wani suka biyo. K'arewar maganarsa tayi dai-dai da dawarsa kusada Aysha data fara bud'e idonta yanzu a hankali. Batareda yace mata uffanba ya yafa mata gyalen akanta kamar yanda yaga tayi d'azun, yamik'a mata handbag d'inta fuskarnan ahad'e babu walwala. Kar6a tayi fuskarta akwa6e, kokad'an yagaza fassara yanayinta, ya kauda kansa daga kallonta, ahankali yafurta *_Thanks_*, yacigaba da takunsa cikin nutsuwa harya fice batareda yakuma ko waiwayotaba. Adams ne yadawo yad'auki kayansu, yamatso kusada Aysha datake tattara nasu wad'anda suka zube, cikin ma'aikatan wajen wani Na tayata. Mungode sosai 'Yar uwa, Adams yafad'a yana murmushi. Itama murmushim tayi ta jinjina masa kai dafad'in babu komai yiwa Kaine. Godiya yakuma yimata sannan yafice da sauri. Itama takar6i ledojinta tana waige-waigen Neman Yaya fadeela. Can ta hangota tafito daga wani lungu rik'eda Ummu'hanee. Ajiyar zuciya tasauke, tace Yaya Fadeela kina lfy keda my dota?. Lfy lau muke Aysha, keza'a tambaya wannan, sannu da k'ok'ari, irin wannan jarumta haka?. Murmuahi kawai ayshan tayi tace muje to. Sai kallonsu mutane keyi, ma'aikatan wajen kam godiya suketaima Aysha, itadai tafita tana mamakinsu, azuciyarta kuma tana farincikin tabama abin sonta kariya da k'arfin ikon ALLAH, Dan ba wayonta baneba. Koda suka fito tuni motocin ya khaleel sun fice daga wajen, baba bala yataresu arikice da tambayarsu suna lfy?. Lafiya lau baba bala suka bashi amsa da gamsuwa. Mota suka shiga Yaya Fadeela naba baba bala labarin yanda abun yafaru. Aysha kam tayi shiru, hankalinta nakan ya khaleel, tana tunanin randa zasu had'u yakuma ganata acikin gidansu, Dan taga yayi mamakin ganinta a 9ja, bayan kuma a Canada yasanta. Wayarta tazaro tanemo layin Anty meerah, dantayi kewarta, wayar akashe, tamaida akalar kiran kan Ifteehal, itama Switch up, d'an tsaki tayi, Dan batason kiran maheer ya takura mata. Tamaida wayar bag danufin zuwa anjima zata sake gwadawa. Ahaka suka k'arasa gida, suna shiga harabar gidan taci karo da motocin ya khaleel Na niyyar fita daga gidan, da'alama sun kawoshine yace suma suje su huta, dama haka yake musu, saboda sanin hakkin d'an Adam, yasan yanda yake da uzuri, suma sunadashi, wasunsuma harda masu iyali, kuma aii suma suna buk'atar hutu, kamar yanda duk lokacin dazaizo gida danufin ya huta yake zuwa. Saida suka fara sauke 'yan fashin a inda yadace, sanan suka kawoshi gidan. Gaban Aysha Na lugude suka fito daga motar, cikin gidan suka shiga kai tsaye.............✍🏿 Kuyi manage da wannan, yau ina busy.✋🏻 I love yau all😍😍😍😘😘😘😘😘😘❤❤❤❤❤. [8/27, 1:35 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 3⃣7⃣ Tunda sukayi sallama su Amal dake falon suka taso da gudu suka rungume fadeela, kowa Na k'ok'arin d'aukar ummuhanee dake hannunta. Aysha gefe takoma tana kallonsu cikeda birgewa, saida suka gama murnarsu sannan suka lura da Aysha, itama sunmata tarar mutunci, amma abinda talura dashi shine babu Wanda yaganeta, hakan yamata dad'i kuwa. Haka sukaita kaya-kaya agidan har yamma, amma Aysha bataga koda gilmin ya khaleel ba. Duk suna zaune afalo, amma banda samarin, Dan duk basu dawoba, hajia babba tadawo daga aiki, sannu da zuwa suka hau yimata, ciki-ciki ta amsa tayi shigewarta 6angarenta. Idan da sabo sun saba da hakan, harma yazame musu jiki, Aysha kam afakaice tarakata da harara, sannan batayi gaisuwarba koda yaran sukayi. Kwala kiran sallar magriba yasakasu mik'ewa suduka, su Shahuda sukaja Amal d'akinsu, Su Tasleem kuma Aysha, ita bama sallar takeba tana fashin sallah. Su Tasleem duk sukayi alwala, Aysha Na kwance a gadonsu tana latse-latse a awayarta, kukan Adeel tajiyo a falo, har Maleeka zata fita Aysha tace zokiyi sallarki, bara Na dubasu. Maleeka tace to, Aysha kuma tafita. Miya faru kake kuka Adeel?. Cikin kukan ya nuna Haleefa, ta maida kallonta kan Haleefa dayay kwal-kwal shima yana niyyar kukan. Mekamasa?. Cikin tsamin bakinsa Na yara yace Anty bacineba icimin biscuit d'ina. Shine kadakeshi? Haleefa kaji tsoron ALLAH, yayan kanefashi?. Affan yarik'e hannun Aysha yana fad'in Anty nimafa sai ya dukeni a school tazun, kuma cena fad'ama ya khaleel. O kai haleefa ALLAH ya shiryeka dubeka....... Bata k'arasaba taji affan ya fusge hannunsa anata yakwasa aguje. Juyowa tayi da sauri Dan ganin shima Adeel yagudu sai Haleefa dayaja baya zai 6uya abayanta. Kasa ya duk'e suka shige jikinsa, bataga fuskarsaba saboda yaran sun kare, amma jin yanda kirjinta keta harbawa taji ajikinta shine, dak'yar tacira k'afa danufin barin falon ta tsinkayi Golden voice d'in nan nasa na kiran ke maleeka zonan. Bak'aramar fad'uwa gabanta yayiba, dan bataso had'uwarsu yau ba, ganin tamak'i juyowa ransa yafara 6aci, k! Banason iskancifa, bakiji minacebane?. Jiki a sanyaye Aysha tajuyo gareshi, wata 'Yar zabura ta mamaki yayi, yanunata da d'anyatsa zaiyi magana kenan saigasu Maleeka sun fito, 6oyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya wayance dafad'in k! Kikawomin tea. Yana gama fad'a yakama hannun Adeel da Affan zuwa 6angarensu, Haleefa nabinsu abaya a6oye. Itama Aysha ajiyar zuciyar ta sauke ahankali, su maleeka kam sai dariya suke saukewa, Tasleem tace kije kicika aikin oga, Dan wlhy ya khaleel babu ruwansa da bakuwa, kuma tunda ke yace babu Wanda zaikai shayin baikusa cinyeshi da jarabar masifarsaba, kema daga nan kun k'ullah kenan. Miya farune? Mama dake fitowa ta tambaya. Tasleem tafad'a mata ya khaleel ne yace Aysha takai masa tea. Mama tace to shine take tsaye kuma? Kiwuce yana nan nama dafa masa tun d'azun, dan naga zaije masallacine shiyyasa ba'a kaiba. Kamar Aysha zata fasa kuka haka takeji, kicin d'in taje ta d'akko k'aramin tire mai d'aukeda falas d'in tea, sai mug da cokali k'arami. Falon tadawo tana tura baki gaba, tace, maleeka rakani, nibansan d'akinsaba. Hararta mama tayi, tace kishiga nan aibazaki rasa d'akinba, anty Mamie data fito tace a'a Yaya fad'ema, kibari ta nuna mata, in bandama abin babana yazakasaka bak'uwa aiki, ai saiya bari tad'an k'ara kwana biyu ko. Mama tace ko zuwanta kenan gidan yasakata aiki badole ta ajiye jakka tayiba, tayi shigewarta kichin. Maleeka taraka Aysha 6angarensu samarin gidan, bin komai Aysha takeyi da kallo, komai Na falon bawanda tasani baneba, ancanja komai, saidai fes yake tamkar yamda tasani abaya, ak'ofar d'akin ya khaleel maleeka tatsaya, tace gashinan. Aysha ta langa6e kanta tamkar zatayi kuka, kai maleeka please kirakani mana. Idanu maleeka tazaro, kai Aysha rufamin asiri, tunda ke yasaka aikin walhy naje yanzu saiyaci k'aniyata, kedai jeki zan jiraki afalo, aii babu abinda zai miki, shifa sai an ta6ashi yake fad'a, kuma ma su Adeel suna wajensa aii. Babu Wanda Aysha zatayi haka taja k'afa tamkar wadda kwai yafashema aciki, ciki-ciki tayi sallamar, yana zaune akan sofa, dagashi sai wando 3quarter da vest fara k'al, duk su Adeel suna jikinsa, ya ajiye musu lap-top d'insa suna kallon cartoon, shikuma idonsa a wayarsa yana danne-danne. Rumtse ido Aysha tayi gabanta Na fad'uwa, bak'aramar firgita tayiba daganinsa haka, Dan damtsen hannunsa yamugun tsoratata, tai saurin kauda kanta daga kallonsa. Har yanzu idonsa nakan waya, su Affan ko bama susan tashigoba, kallon cartoon yad'auke hankalinsu. K! Idan bazaki ajiyeba ki koma dashi. Haushi yaso kama Aysha, amma saita dake, tajawo k'aramin glass table dake gefensa tad'ora, saida tafara tafiya takusa k'ofar fita yace dawo. murgud'a bakinta tayi sannan tajuyo, alokacin kuma yad'ago suka had'a ido, Aysha tayi saurin janye nata, tunba yanzuba wlhy tsoron mayun idanun nan nasa takeyi, gashi yanzu sund'an shanye alamar haryanzu akwai sauran gajiya taredashi. Kafeta tayayi da idon nasa, wannan yasakata gaza koda satar kallonsa, tambayar daya jeho matace tasakata d'agowar dole. K wacece!? Batasan sanda bakinta yasu6ce tace kamarya? Ni wacece?, ni mutumce mana, tak'arashe maganar da murgud'a baki. Aransa yace akwaifa rashin kunya buhu-buhu awajen yarinyarnan.. Afili kuma saiya gallah mata harara, k banason tsiwa, mikikazo yi gidanmu?. Baki Aysha taturo gaba, cikin shagwa6a tace nima kuma gidanmune, ahankali tace bare amin gori. Su Halefa dake jikinsane yahanasa tashi, dasai ya saita bakin yarinyarnan wlhy, amma cikin tsawa yace anturokine lek'en asirina ko? Shiyyasa kike bibiyata?. Aysha batasan sanda tasaki wani mugun murmushiba, harta samu kwarin guywar kallon cikin idonsa, amma kwarjinin dake taredashi yasakata saurin janye idon nata, da gudu tabar d'akin batareda ta bashi amsaba. Kuttt! Yafad'a yana binta da kallo, yana rasa mizaice, saikawai yaja ajiyar zuciya, dolenema yayi bincike akan yarinyarnan, danyasan wacece ita?, shifa mamaki take basa, saikace aljana, tunda yake babu macen data ta6a kallon tsakkiyar idonsa sai yarinyarnan, duk girman mace kwarjini yake mata takasa masa kallon minti2 ma, bare cikin idonsa, duk jidakan yarinya da isarta, inhar zatazo wajensa tace tana sonsa, kotazo suyi wata magana, wlhy inhar yadasa mata idonsannan na 1minute kawai saikaga jikinta narawa, tashiga hankalinta daganin bakin Rijiya bawajen wasan makaho baneba. Amma yau ga yarinya k'arama, wadda k'annensa nawajen 15 sun girmeta, ta kalli tsakkiyar idonsa. Ya furzar da huci daga bakinsa, Wanda yasaka su Affan kallonsa. Aysha kam koda suka koma babban falon wajen sauran yaran, batawani dad'e Na firaba tatashi takoma d'akin mama, firarce ta'isheta, dama can Aysha bamai son hayaniya baceba, Anty meerah takira sukasha hirarsu, wai gobe idan ALLAH ya kaimu zasu dawo daga Kd, harda mama Dan dad yabiya za'a kaita india asaka mata k'afar roba. Aysha tayi farinciki sosai, Dan mama tabata tausayi, rashin k'afa bala'ine. Fadeela zuwa tayi tad'auki kayan barcinta Dana Ummuhanee, d'akinsu Amal zata kwana, Aysha tace aii ina gadon uwata, saida safenki. Bayan tafiyar fadeela mama tashigo ta kimtsa, baffah yadawo yanzu babu dad'ewa, kuma girkin mamane. Ganin haka Aysha tace aikam bara Na shirya Nima d'akinsu Tasleem zanje Na kwana, bazan kwana nikad'aiba. Mama tace a'a kiyi kwanciyarki, inasu Affan? Basai Ku kwana tareba. Mama suna d'akin wannanfa mutumin, kuma k'ila a can zasu kwana. Waye mutumi? Mama ta tambaya tana fesa turare. Wanda yace nakai masa tea d'azun. Zai dawo dasu indai babana ne, idan yana gida dama canne wajen hirarsu tunma basukai hakaba, dayaga sunyi barci zakiga ya kawosu. Mama bata jira amsar aysharba tafice abinta zuwa 6angaren baffa. Mama nafita Aysha tamik'e tashiga wanka, bayan tafito tashirya cikin wando dogo da Riga Na cartoon kalar popul, sunmata kyau, tana gaban mudubi tana tufk'e gashinta Dan bataso tayi barci dashi ahaka, yaturo k'ofar yashigo, da sauri Aysha tajuya tana kallonsa. 'Dauke yake da haleefa da Adeel a kafad'a, sa6anin d'azun yanzu yasaka doguwar jallabiya, Affan nabiye dashi abaya, da'ala shi baiyi barcinba. Ko kallonta baiyiba yad'orasu a gadon mama, saida yagyara musu kwanciya sannan yanufi Waldrop d'insu ya d'akkomusu kayan barci. Mamaki dukya cika Aysha, aranta tace irin wannan samun waje haka. Tana jingine da madubi tana satar kallonsu ya canjama yaran kayan barci su duka, sannan yamusu addu'ar barci ya shafa musu, Affan yace Yaya ni awajenka Jan kana. Murmushi yayi tareda jawo yaron jikinsa, yace haba my lil bro d'ina, kaga zomu kwanta, nima yau a gadon mama zan kwana, amamakin Aysha saitaga ya kwantar da yaron a jikinsa shima yaja filo ya kwanta, ahankali yake bubbuga bayan yaron idonsa a lumshe Aysha samun kanta tayi da sak'a wani Abu a zuciyarta, tasaki sassanyan murmushi, jitake inama tunanin nata yazama gaskiya. Duk abinda takeyi ya khaleel Na kallonta ta k'asan idonsa, bakinsa yata6e ya kauda kansa daga kallon nata. Saida ya tabbatar barcin Affan yayi nisa sannan ya kwantar dashi kusadasu Adeel yakuma yimusu addu'a yarufesu da bargo yafice abinsa, batareda ya nuna yamasan dawata hallita a d'akinba. Da uwar harara Aysha taraka bayansa harya fita. Yana fita tafad'a gadon tareda jawo filon daya d'ora kansa ta rungume tareda lumshe manyan idanunta, jitake kamar ya khaleel ta rungume, ga sassanyan k'amshin turarensa natashi ahankali, shidai baka ta6a cewa wannan shine turarensa Na dindin din. Shima yana fita 6angaren mom yanufa. Babu kowa afalon sai Mufeeda dake barci, itama nakula bawai barcin takeyiba, takune kawai naneman hanyar dazata fita anjima wajen saurayinta atafi shek'e ayar da'aka saba, Dan batama San ya khaleel yadawoba. Ganinsa yasaka gabanta fad'uwa, amma saitayi lamo kamar tana barci. Tashinta yayi yace tashiga d'aki, tatashi tana wani Mirza ido, kaikace gaske barcin takeyi, lah ya khaleel yaushe kadawo?. d'azun. Yafad'a a tak'aice. Yace Momy fa?. Takwanta tun d'azun saboda tagaji tace, su Hasnama sun kwanta. Yace kema shige ki kwanta. Ranta A6ace tashige d'akinta, amma tana addu'ar ALLAH yasa fita zaiyi. Samun kansa yayi dason zama afalon, saboda American film d'in dasuke nunawa a Fation yamasa k'yau, yad'auki remote d'in yakoma saman 3seter ya kwanta. Kamar mufeeda zata fasa ihu haka taji, gabanta yaywata muguwar fad'uwa lokacim datajiyo wringing d'in wayarta dake gefen ya khaleel..................✍🏿 😍😍😍😍😍✋🏻 [8/28, 8:09 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) 3⃣8⃣ Biris yayi da wayar yacigaba da kallonsa, harta yanke aka kuma kira Na 2, kiran daya kuma shigowane yahasala zuciyarsa, wani uban tsaki yasaki, tareda kwala kiran mufeedah!!. Dama tana la6e, jin kiran daya kwala mata yasaka 'yan hanjinta wuntsilawa, afili tace shikenan namutu yau, wlhy ya khaleel kasheni zaiyi kawai. Wai dan ubanki bakiranki nakeyibane. Jikinta narawa tafito, sai mutstsuka ido takeyi alamar abarci tataso, yawatsa mata wata harara da mayun idanun nan nasa, jitayi tamkar tasaki fitsari awajen. 'Dauka wayarki kibarnan kafin namiki dukan mutuwa. Aibama tabari yak'arsa fad'a tafisgi wayar dasauri ta runtuma da gudu tana mai godema ALLAH daya tserar da ita. Tana shiga d'aki aka sake kira, d'agawa tayi dasauri, har taune le6enta nak'asa takeyi wajen saurin yin magana, haba babie tunda kaga kayi kiran farko ban d'agaba aikasan akwai matsala, yanzu dakaja ya khaleel yad'auki wayar yaduba wlhy da daga ni har kai mungama yawo. Wai kina nufin wayar tana hannunsa?. A'a tana kusadashine.........tabashi labari.. Ajiyar zuciya yasauke, kai my mufeey ALLAH ya taimakemu, wlhy karkiji wasa tsoron yayan nan naki nakeji, bashida mutunci idan kafad'a tarkonsa, ga wani abokina nan agidan yari zai k'are rayuwarsa ta dalilin yayanki. Kai kajimin, ainasan laifi yayi yakamashi, Dan ya khaleel akan aikinsane kawai hakan kefaruwa tsakaninsa da mutane, saikuma mu k'annensa dayakeyi Dan kulada tarbiyyarmu. Hakane, yanzu yaza'ayi kenan?. Tab ai wlhy yau saidai mud'auki Na Annabawa, Dan yana falonmu zaunema yana kallo, nibanma San yadawo k'asarba. To shikenan saida safe. Baijira cewartaba ya yanke wayar yana mitar saidai ke, amma wlhy nikam sainaje Na more, ga 'yan mata nan buhu-buhu a birnin Abuja. Bai bar falonba saida film d'in yak'are, sanda yafitama mufeedah tagaji da la6e-la6enta tayi barci. *_Washe gari_* Har 8:30am Aysha bata tashiba, tuni su Affan sunbar d'akin, ita kad'ai taketa juye-juyenta a gado. Kowa ya hallara a dining har baffah kasancewar weekend ne, Ammah ce kawai babu tana Jigawa abinta. Anty Mamie takalli dukkan yaran babu Aysha da ya khaleel, har mufeedah dasu hasnah suna nan, Dan dolene suzo tunda harda baffah, gakuma zakin gidan yana nan, Momy dama saita gadama take cin abinci dasu, babu kuma ya Sultan da ya mujahedeen, sunacan 6angarensu da matansu. Muslim tashi kakira babana, kekuma maleeka kira Aysha. Da to suka amsa. Babu dad'ewa saiga ya khaleel sunfito shida musleem, har k'asa ya durk'usa ya gaida iyayen nasa, k'annensa suka gaisheshi. Yaja kujerar ya zauna, saida mama takuma aika tasleem sannan su Aysha suka fito, da alama saida maleeka tasha dagama wajen tashin Aysha, dan kayan barcinema ajikinta sai hijjab data d'ora iya kugu a saman kayan barcin, daka kalli idonta kasan yanzu tatashi a barci, saboda akwai ja acikinsu, gasukama sun k'ara zama manya, durk'usawa tayi tagaida baffah, ya amsa cikin fara'a, harda dafa kanta yana mata lale marhabun dadawowarta kasarta, (dan mama tayi masa bayanin komai dangane da dawowar Aysha kasar dakuma zuwansu itada fadeelah, shikam yace Aysha tazo kenan, dan bazata koma kanoba, tunda yaso adawo da Ummulkhairi nan amma kawu bilyamin yabashi hak'uri saboda tana hannun uncle Ahmad ne, to yanzu kam shima tashi d'iyar tadawo gareshi acewarsa, mama dai dariya kawai tayi, amma ak'asan ranta tafiso Aysha tayi aure, dan tasan mijin nata akwai son karatu, harma tambayarta matakin karatun ayshar yayi, tace, "wlhy bata saniba, saidai ya tambayrta".) Ta gaida Anty Mamie da umme Amarya, sannan tagaida sauran samarin gidan da 'yan mata, babu Wanda yaganeta, amma dai musleem ya kafeta da idanu. Baffah yace tashi kizauna d'iyata yanuna mata kujera d'aya data rage wadda take kusada ya khaleel. Jitayi tamkar tafasa ihu, amma babu damar hakan, dan baffah kallon mahaifi take masa ba mijin uwa ba. Haka ta zauna duk atakure, bayan mama tagama had'ama baffah abincinsa ta zubama Anty Mamie da umme Amarya, tazubama kanta, Aysha dake kusada ya khaleel tace tatashi ta had'a masa shima, bak'aramar kid'ima zancen Maman yasakataba, dukda wani sashe Na zuciyarta yana farinciki. Babu yanda zatayi tahad'a masa komai, yanata danna waya abinsa tamkar baisan mi'akeyi a dining d'inba, tana gamawa tazagaya tazubama ya Zunnurain da ya Ramadan, ta iso kan Musleem daketa kallonta tun d'azun, magana yay mata k'asa-k'asa batareda kowa yajishiba, _Ammafa kin had'u wlhy_, Aysha tayi murmushi, itama tace kaima haka ya musleem. Tsayawa yayi cak daga danna wayarsa, yad'ago fararen idanunsa yakafe Aysha da musleem da idanu, Muhsen ne yalura da kallon da ya khaleel yakeyi, ya zunguri musleem, kai Malam ka kulafa, babban Yaya yana harararka. Da sauri musleem yad'ago suka kuwa had'a ido da shi, ya watsa masa uwar harara, kasa dakai musleem yayi damamakin hararar, babu yanda za'ayi yace yaji maganar dayakeyi da yarinyar. Amma irin sannan uwar harara haka. Ita Aysha ma tuni tayi gaba, harta zubama Hafiz, tana kaiwa kan mufeedah ta ajiye bowl d'in hannunta tadawo wajen zamanta. Wani tuk'in bak'in ciki yatokare makoshin mufeedah, wai agola tazo tana nuna musu Isa, wadda in auren wuri tayi saita kusa haihuwar kamarta. Aysha kam ko'a kwalar rigarta, dan ita duk abinda yashafi hajia babba ta tsaneshi, ya khaleel ne kawai yafita zakka acikinsu. Kowa yagama zuba abincin baffah yay bismillah, kowa yayi aka fara break, Aysha dukata takura, sai juya cokalin takeyi, shikam wandama takeyi da shi ko'a kwalar rigarsa, abincinsa yakeci hankali kwance, duk sanda zata d'ago saisun had'a ido da Musleem da Zunnurain, saita kuma zama atakure, tarasa wannan kallon kurullah dasuke jifanta da shi, hakadai aka kammala cin abincin kowa yafara kama gabansa Aysha bata wani ci abin kirkiba. Itace ta biyard'in mik'ewa. Hartaja kujerarta baya tamike tajiyo muryarsa yana fad'in dawo ki zaune. Kowa saida yad'ago ya kalleshi, Aysha datasan da ita yake tayi kamar bata ganeba tafara tafiya, da d'an k'arfi yace Aee'sha dake nake. Yanda yakira sunan saida tsigar jikin Aysha yatashi, kowa kuma kallonsu kawai yakeyi, babu Wanda yasaka baki. Dawowa ayshar tayi ta zauna, yad'ago suka had'a ido, tayi saurin janye nata, filet d'in abincinta da cup d'in shayi yanuna mata, wakika barma wanna🍵🍝?. Kwal-kwal tayi da idanu, cikin turo baki tace nifa Na k'oshi. Shiru yayi yacigaba dashan tea d'insa. Mama ta dakama Aysha harara, wakike turama wannan shegen bakin? Koshi sa'ankine?. No barni da'ita mama, tabari harna gama shan tea d'inan batayi abinda naceba taga yanda zanyi da'ita. Anty Mamie tace a'a babana ba'ayi hakaba, Aysha zauna kici kinji, zama da yunwa bashida dad'i, INA kallonki bakici wani abincin kirkiba kam, kobak'yasonsa?. Da sauri Aysha tace a'a Anty Mamie, to maza kici kinji. Kai tad'aga, idonta tab da hawaye, bawai ta k'oshi baneba, har yanzu takasa sabawa da d'and'anon abincin 9ja, tafison taci snacks kawai tad'ansha Ice-cream d'inta. Baffah dai baice komaiba sai murmushi, yatashi yabar wajen, daga haka kowa yafara zare jikinsa kafin ta shafesa shima. Dagashi sai ita aka bari, tura abincin kawai takeyi badan dad'iba. Saida taci mai yawa sannan ta saci kallonsa, harta fara hawaye tace ni wlhy nak'oshi, cikina zai fashe. Banza yay mata, saida takuma maimaitawa sannan ya harareta, daga yau kikuma min rashin kunya, ALLAH saina saita wannan bakin naki, faratun banza, tashimin anan....... Baikai karsheba tamik'e, d'an tsaki taja Wanda yasakashi d'agowa da sauri ya kalleta, ta murgud'a bakinta ahankali tace ALLAH ya isana kuma. Da gudu tabar wajen. Shiba gunkiba shiba butun butumiba haka Yakoma awajen, hanyar databi kawai yabi da kallon, dolensane ya saita wannan matsiwaciyar yarinyar, shi baima ta6a ganin wadda ta rainashi kamar yarinyarnanba, wai yama akayi hakan tafaru?, tunda suka fara had'uwa a Canada yarinyar nan tafara masa rashin kunya, dolene ya gyara mata zama kafin lamarin ya wuce haka, tashi yayi zuwa 6angarensu, zuciyarsa cikeda tunani matakin daya kamata yad'auka akan yarinyar. _______________________________ Bayan su Aysha sunyi wanka mama tamusu iso zuwa wajen baffah, yana zaune afalo shida Nuredin, Noor da y'an uku. Su Aysha sukayi sallama. Cikin fara'a ya amsa musu, suka zauna ak'asa suna k'ara gaidashi, nanma cikeda kulawa ya amsa, ya kar6i ummuhanee yamata addu'a, to fadeelah da ankoma yakamata kuma ki koma gidan mijinki kinji, wankan yayi haka. Kan fadeela ak'asa tace to baffah insha ALLAH. Ya maida kallonsa kan Aysha da itama kan nata na ak'asa tana wasada zoben hannunta, Aysha ya karatun? Anyo nasara dai ko?. Kanta tad'ago fuskarta d'aukeda murmushi, eh baffah, komai Alhmdllh, nasamu result mai k'yau, yanzu hakama bautar k'asa zanyi. Yayi k'yau, ALLAH yayi jagora. Mama datun d'azun bata saka bakiba tace, ''dama kin cire wannan batun aranki, babu wata bautar k'asa dazakije, kawu bilyamin yace aure zai muku, domin k ma ya jinkirta saka ranar su Rufaida, gwarama kinutsu ki fidda mijin aure. Hawaye suka zubo a kumatun Aysha, baffah ya kalli mama ransa ad'an 6ace, haba fad'ima, miyasa zaku hanata cikar burinta?, Aysha dai d'iya tace nima, kuma ina bata goyon baya, zankira m. Bilyamin d'in muyi magana. Muryar mama a sanyaye tace kayi hak'uri to. Baice komaiba yamaida hankalinsa akansu Aysha, nasiha yamusu sosai dakuma nuna musu shima mahaifinsune, Duk sanda suke buk'atar Abu babu wani shamaki su sanar masa, ashirye yake damusu komiye inhar baifi k'arfinsaba. Godiya su Aysha sukayi masa, dajin k'aunar tsohon mai mutunci dasanin darajar d'an Adam, suma suna kallon sane tamkar mahaifi, zakuma sucigaba da hakan har karshen rayuwarsu, Haka yayta jansu da hira, har suka saki jiki dashi, sund'an dad'e awajensa sannan suka fito. Mama tace suje su gaida hajiya babba. Saida gaban Aysha yafad'i. Tunda suka doshi 6angaren suke jiyo dariyarsu Husnah, da alama rayuwar tamusu dad'i, koda su Aysha sukayi sallama babu Wanda ya amsa musu sallama, saboda dariya taci k'arfinsu, har itama hajia babba dariyar takeyi, kowannensu da dawani kati a hannu saikace hotuna, kuma tabbas abinda sukema dariyar kenan. Sallamar suka k'arayi dad'an k'arfi, sai sannan Mufeeda dake kujerar kusada k'ofa taji, waygowa tayi zata amsa......amma ganin fadeelah yasakata fasawa, ta gimtse fuska. Suma su momyn daina dariyar sukayi, kowa yaci magani, Aysha da fadeela suka durk'usa k'asa momy ina kwana? Munsameku lfy?. Wata yatsina hajia babba tayi, cikin ko inkula tace lau. Daga nan babu Wanda yasake tankawa, durk'uson ne ya ishi Aysha da kallon banzar da'ake musu, tad'anja tsaki tareda yunk'urin mik'ewa tsaye. Da sauri suka kalleta suduka, gaban hajia babbane ya fad'i, sai yanzu talura da Aysha, gani take kamar ta ta6a ganinta. Ganin yanda tadasa mata idanu yasaka Aysha kauda kai tana Neman tsarin ALLAH daga sharrinta, tareda k'arajin tsanarta azuciya. Hasnah tace k! Ubanwa kikema tsaki?. Kalon banza Aysha tamata ta ta6e baki, kinga Yaya fadeelah tashi muwuce kinji, Aysha tayi maganar cikeda salon tura haushi. Da sauri hasnah tamik'e tayo kan Aysha, kam balastin, aikam yau saina sauke miki abinda ke kanki. Murmushi Aysha tayi, Wanda ya k'ona ran Hasnar, tace ni mai saukemin kayan kaina saiya shirya y'an mata, Dan nafi k'arfin manyankima balle ke, Aysha ruwan daminace, kona wuce saina dawo, kumani k'adan garen bakin tuluce, akarni akar tulu, abarci Na 6ata ruwa. Sak'o Na Isar ba shawaraba🙅‍♀. 🤣magana cikin magana Aysha tafad'a. Amma babu Wanda yafuskanci zancen nata, tara6a hasnah dake tsaye tamkar gunki tafice abinta, fadeelah ma ta take mata baya, itama zuciyarta cikeda nazarin maganar k'anwar tata, Dan bata fuskanci inda zancen yadosaba..................✍ 😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘😘😘. [8/29, 6:44 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1_* (littafi na d'aya📕) _my dear Ayusher Muh'd, gaisuwa agareki da fatan alkairi, ALLAH yabarmu tare,, alkairin ALLAH ya iso agareki k'awar arzik'i_ Bilyn Abdul na yinki wlhy 100%. ❤😍😘 Masoyan buks d'inta kuyi shiri Na musamman, Dan tana nan tafe da buk d'in mai suna *_YUSRAH!!_* kada kubari ayi babuku, karkuma kumanta da sunan. *_YUSRAH!_* Coming soon👈🏻😍 3⃣9⃣ Wai nikam mikike nufi da maganarki Aysha?. Lah babu komaifa Yaya fadelah, ganinai zasu raina mana wayo, nifa bana d'aukar raini wlhy. Shiru fadeelah tayi bata tankaba, Dan bata aminta da kallon da hajia babba kema Aysha ba. Haka kawai takejin aranta akwai lauje cikin nad'i. _____________________________ Tunda abin yafaru yakasa barin zuciyarsa, gani yakeyi ya aikata babban lefi, tunda yasan kansa baita6a rungumar d'iyar kowaba sai yarinyarnan, ALLAH kuma shine shaidarsa baiyi hakan dawata manufaba, sai danya bata kariya, amma kokad'an zuciyarsa takasa sukuni, jiya kwana yayi akan abin sallah yana Neman gafarar ubangiji akan hakan, ya lumshe idanunsa ahankali yana mai cije le6ensa Na k'asa, shiru nad'an wani lokaci baisake koda motsawaba. Wayarsace tafara wringing, yabud'e idonsa da k'yar tareda jawo wayar, ganin mai kiran yasakashi mik'ewa zaune, cikin girmamawa yace momy barka da rana. Bansan mitace masaba dagacan, nagadai yamik'e yanacewa OK inazuwa. Da sallama yashiga falon, k'annen nasa suka shiga gaidashi, ya amsa fuska babu walwala. Zama yayi kusada momynsa ya d'ora kansa gefen kafad'arta, my momy I miss you wlhy. Murmushi tayi, tashafo kansa, nima haka yarona, inafatan komai normal. Alhmdllh momyna. Nazo d'azun kinata barci abinki. Wlhy kuwa nagajine shiyyasa. Momyna ki ajiye aikinnan haka ki huta mana, basai kifara kasuwanciba, ni zan baki jari da kainama. Karka damu Ibraheem, insha ALLAH ina gab da ajiyewar, nima nagaji. Yauwa momyna kokefa. Takardar dake gefenta ta mik'a masa yatashi daga kafad'arta yana kallon takardar, momy miye aciki haka?. Kar6i kaduba mana. Amsa yayi yabud'e, hotunane wajen 8 aciki, cikin rashin fahimta yakalli momyn tasa, momy pictures d'in waye?. Dad'ina dakai kenan, kaduba mana. Zamansa yagyara sosai yafara kallon hotunan, k'yak'yk'yawar yarinyace ajiki kuma fara tas, komai da mace ke buk'ata Na burga ALLAH yabata kam, ya khaleel yad'an ta6e bakinsa tareda maida pictures d'in a takardar, yace momy nagani to. Bakace tayi k'yauba to?. Ah momy miye had'ina da'ita dazan yaba k'yanta?, amma tunda sokike nafad'a to tayi k'yau, saidai shigar tata batadace data y'ay'an musulmai hausa fulaniba. Y'ar dariya momy tayi, tace wannan tayine dominka, sunanta Aleeya, d'iya ga tsohon minister kud'i, ayanzu kuma jakada a k'asar England, su biyu iyayensu suka haifa, itace auta, cikakkiyar likitace kuma kwararriya acan England, naza6a maka ita amatsayin matar aure, ALLAH yasa zaka yabama k'ok'arina. Y'ar zabura yayi saboda maganar tayi mugun shigarsa, yace, ''momy matar aurefa? ahakan?. d'aure fuska momy tayi, tareda kallonsa, Aleeya ta cancanci zama matarka, d'iyace mai nasaba, tanada ilimi, ga uwa uba k'yawu, nasan duk iya lalubenka baka samo koda wadda takama k'afarta, abaya nace ka auri Abida, amma ganin Aleeya saina canja shawara, yanzu itace za6ina. Bai iya cewa komaiba sai kallon momyn dayakeyi. Husnah tace ALLAH ya khaleel Anty Aleeya tahad'u, kuma zata dace da ra'ayinka, kasanf........... Hararar daya balla matace tasakata jan bakinta ta tsuke, yace kutashi anan. Suduka suka mik'e da sauri kowa tanufi d'akinta. Shikuma yadawo da kallonsa kan momy daketa hucin 6acin rai. Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru yacije le6ensa, shiru nawasu mintuna babu Wanda yasake magana. Zuwacan Yace shikenan momy zanyi bincike akanta, insha ALLAH inhar tacika yanda nake buk'ata zaki sameni mai biyayya agareki, dukda banji sontaba ko kad'an araina. Washe baki momy tayi tana kamo hannunsa, karka damu yarona, insha ALLAH Ma zaka sota wata rana, kwanan nanma zatazo Nigeria, ALLAH yatabbatar da alkairi, nagaji da zamanka haka babu aurene, ga baffanku NATA damuna akan aurnka, shiyyasa namaka za6in girma, Wanda su Bilkeesu zasu tabbatar har Abadan namusu rata, tabar k'afafa y'ay'anta sun rigaka yin aure. Baice komaiba sai d'aga kansa dayayi kawai tareda cije le6ensa, shikad'ai yasan k'unar da zuciyarsa ke masa. Daga nan shiru sukayi, hakan yasa momy ta shafa kansa cikin murmushi tace jeka ka kwanta ka huta kaji, idan ka nutsu mayi maganar. Kansa ya jinjina, batareda yace uffanba yafice daga falon. Afalo ya iskesu Aysha itada Zunnurain, jiyayi zuciyarsa takuma hasala, harya wuce saikuma yadawo baya. Karaf suka had'a idanu da Aysha, ya watsa mata harara, murgud'a masa baki tayi ta kauda kanta gefe. Ransane yakuma 6aci, cikin kaushin murya ya kwala kiran Zunnurain!!. Zunnurain dabaisan da shigowarsa falonba yajuyo da sauri, na'am Yaya, yafad'a yana tasowa. CiGaba yayi da tafiya, wannan yasaka Zunnurain bin bayansa yana cema Aysha ina zuwa. OK tafad'a. Koda suka shiga sai kawai yacema Zunnurain ya zauna wani aiki zai masa. Zunnurain yad'anso yayi zargin wani abu, amma saiya kauda hakan aransa, Dan baisan wane aiki zai masaba, kuma yasan wanene yayan nasu. System d'insa ya d'akko ya kawo masa, tareda nuna masa aikin dazai masa, shikansa baisan dalilinsa nayin hakanba, kawaidai bayason ganinsa da yarinyarne kawai. Aysha data gaji da jira saita tashi takoma d'aki, dama suna maganane akan bautar k'asarta datakeson zuwa. ______________________________ Da yamma meerah takira Aysha akan sun dawo, zuwa anjima zasuzoma nan gidan su gaida su mama. Sosai Aysha take farinciki, dantayi missing d'insu sosai, da murnarta ta sanarma mama da yaya fadeelah. Suma sunyi farinciki, dandanan aka shirya abincin tararsu. Bayan sallar magriba kuwa saigasu, Aysha da Ifteehal da anty meerah suka rungume juna, sunacike da murnar sake had'uwa, tasakesu takoma kan mom, itama tayi kewar ayshar, su Safwan ma suka rungumeta, ya Naufal yanata murmushi dabin Aysha da kallo. Saida tagama murnar ganinsu sannan tace ya Naufal I miss you. Oh sai yanzu kika san dani?, kofa kirana awaya bak'yayi?. Hannu tasaka tarufe fuskarta🙈, sorry yayana, amin afuwa, wlhy murnar ganin su mamane ya mantar dani. Maheer dake gefe shida shakur yace habawa yarinya, ALLAH saina rama nima. Wayyo ya Maheer d'ina, inata kewarka, inata kewarka kamar nayi tsuntsuwa nazo Kd. Bakinsa yata6e yana mata hararar wasa, to sarkin tsari, nibama wajenki nazoba dama, mama nazo gaidawa. Aff nasan saikamafi kowa kewata ALLAH, dojewa kawai kakeyi. kafin yabata amsa Shakur yace beauty kin k'ara k'yau da girma. Ita saima yanzu tagansa, gidan su yazo, shiyyasa bazata masa wulak'anciba, tayi y'ar dariya tana kallonsa, da gaske ya Shakur?. ALLAH kuwa beautyna. Baki tad'an ta6e taigaba tana kar6ar Raudat dake hannun ya Naufal. Dad da baffah suka k'araso, daka gansu kasan sunsan juna dama. Mazan 6angaren baffah suka shiga, matan kuma 6angaren Anty Mamie, dan tace itace uwar y'ar. Ansha hirar yaushe gamo, yayinda su mom suka saki jiki dasu mama saboda tarbar mutunci dasuka samu. Aysha taja anty meerah d'aki ta zayyane mata komai gameda Auren mama da baffah. Sosai meerah tayi murna, tace yauwa Aysha wannan shine matakin farko nacikar burinmu, amma ina gwaggonki?. Nima Tunda nazo gidan bangantaba, bankuma tambayaba, kinsan abin saida taka tsantsan, yanzudai sonake nafara ganin Bishrah, awajentane kawai zansamu dukkan bayanan danakeso. Gaskiyane, ammafa nayi farinciki da kowa yakasa ganeki agidanan. Wlhy nima haka Anty meerah, hakan yana cikin nasarar aikinmu shima. Aikamdai, ya khaleel fa?. Baki Aysha ta ta6e, yana nan shima, Aysha takwashe yanda sukai dashi a shoprite dakuma had'uwarsu agidan. Dariya sosai Anty meerah tayi, lallai Aysha kinyi jarumta sosai, ammafa karki yarda yasan kina sonsa, ki kama kanki sosai. Tab yo Anty meerah hauka nakeyi, rashin kunyarma dakiga ina masa ganinai yana Neman shiga hancina, amma karki damu zan sake takune, saidai damuwata mama da kawu bilyamin. Wai bazanje bautar k'asaba aure za'amin, ni basusan inada buruka agabanabane. Dariya meerah tayi, cikin tsokana tace, kawai kice ya khaleel yafito musha shagali abinmu💃🏻. Kai Anty meerah, kema hadake ko?, nifa koda nake sonsa bawai inason aure baneba yanzu. Hhhhh to shikenan maida bakin, yanzu dai kawo kunnenki kiji wani Abu. Matsawa Aysha tayi, cikin rad'a meerah takema Aysha magana, wannan yasa banji misuke magana akaiba🤕. Fitowata nayi nabarsu awajen. A 6angaren su baffah kuwa sunata hirarsu da dad, sunsan juna tuni, baffah yakira ya khaleel awaya yazo suka gaisa, dad sai mamaki yanda khaleel d'in yakoma yakeyi, Dan rabonsa dashi tun bai wuce 18years ba. Dad yace andai ajiye iyali ko?. K'asa ya khaleel yayi dakai yana murmushi. Baffah yace baiyiba, inata fama, amma kuma insha ALLAH Ana gab dayi. Da sauri ya khaleel yad'ago yana kallon baffah, cikin tsinkewar zuciya ya maimaita maganar ta baffah a zuciyarsa, _ana gab dayi!_, to gabda yin me?. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa, baffah yana lura da halin dayake ciki, aransa yayi dariya yana fad'in d'an jakar uba aii maganinka zanyi wannan karon. Tundaga nan ya khaleel yadaina saka baki a hirar, dama can eh, a'a Ce maganar tasa. Sai around 11 suka bar gidan, tuni sabo yashiga tsakaninsu da mutan gidan, kowa yayi aboki kuma. Aysha harda 'yan kwallanta, taso ace tafiyar dazasuyi Sokoto gobe harda ita aciki wlhy. Bayan tafiyarsu suka dawo d'aki, mama sai yaba kirkin bayin ALLAHN takeyi, suna d'an hirar zuwan bak'in wayar mama tayi wringing. Ummah ce, Dan haka tad'auka da murmushi, Yaya ina yini? Kune da daddare haka?. Wlhy kuwa fad'ima, ya yarana?. Lfy lau suke, duk gasunan muna tare dasu, bak'i akayi yanzu suka tafi, mama tabama Ummah labarin zuwansu mom. Sosai Ummah taji dad'in hakan. Ummah tace munfara maganar bintu dake d'azu wayata tamutu, shiyyasa nakasa hak'uri nak'ara kiranki yanzu. Au wlhy kuwa Yaya, tana nan babu lfy, abinda yasa kenan banmata maganar Aysha ba, sonake ta warke, Dan inason jin wasu bayanai daga gareta, Dan tareda Bilkeesu mukaje dubata ranar, shiyyasama nakuma k'yaleta. Hummm abin mamaki, yakamata kam ki bincikar mana ita, kidubafa tunda tatafi da yarinyar nan bata kuma zuwa kano ba, kuma kince tunda kikaje gidan baki ta6a ganintaba. Wlhy kuwa yaya, shiyyasa kawai naji yakamata nasan wani Abu, sainake ganin kamar kawai lauje cikin nad'i bamu saniba, tunda tace mai gidanne yabiya kud'in karatun, harma da y'ay'ansa ciki, kuma banga wannan alamarba, hasalima babu Wanda ya nuna yasan Aysha agidan. Lallai maganarki gaskiya akwai lauje cikin nad'i, yanzudai bara nabarki saida safen. Ki gaishe da jama'ar gidan. To zasuji yaya, nima agaidamin yarana. Bayan sunyi sallama fadeelah tace mama wai miya farune?. Babu komai fadeelah. Ina ayshar kuma?. Tashiga wanka. OK, kijeto ki kwanta, nasan k'awayen naki nacan nazuba ido. Jin jina kai fadeelah tayi, tamik'e, dama ummuhanee nawajensu Hamdiyya, tafita zuciyarta na waswasi akan abubuwa dayawa, saidai batasan yazata kama lamarinba harya zama hujja agareta.................✍ ❤❤❤❤😘😘😘😘😍 [8/29, 6:44 PM] Aisha Galadima: *_Typing📲_* 🤰🏻 *_CIKI DA GASKIYA........_* _{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_NIKA'DAI WRITER ASSO........_*😜 *_Sadaukarwa_* _My sweet dady_ ~(ALLAH ya gafarta maka)~ 🤲🏻😭 *_part 1 🔚_* (K'arshen littafi na d'aya📕) *_Alhmdllh masoyan ciki da gaskiya, wannan shafin nakune aduk inda kuke, ngd sosai da k'aunar dakuke nunama buk d'in, ALLAH yabar zuminci, nima ina sonku da k'aunarku over wlhy._* ❤❤❤❤😍😍😍😍😍😍😍😘😘😘😘. 4⃣0⃣ Duk zungurar da mama tayima Aysha adaren jiya saboda gwaggo bintu, Aysha tak'i cewa uffan, kuma tadage akan ba nan gidan suka zaunaba sanda ta d'akkota. K'yaleta mama tayi, Dan batason Aysha ta fahimci wani Abu, saidai batasan ayshar tagane komaiba. Saidai tunaninta ina gwaggo bintun?. Washe gari bayan sun kammala break fast Aysha tazare jikinta zuwa 6angaren masu aikin gidan, shiga tayi tamkar mai neman wani Abu, Rabi da iya hama kawai ta taras a falo suna kallo, aranta tace ana nandai da hali. Suna ganinta suka hau washe baki, Rabi tace ko ana kiranmu ne?. Murmushi Aysha tayi, cikin basarwa tace, "a'a, kawai zan wuce garden ne najiyo dariyarku, shine nace bara Nagano miya baku dariya haka?. Iya hama tagyara zama tana fad'in wlhy babu komai. film ne muke kallo. Aysha takalli TV n, Indian hausane suke kallo, batace komaiba tafito, can cikin garden tashige, takira wayar Anty meerah, bayan sun gaisa ta shaida mata bataga alamun gwaggo bintu na gidanba, Dan d'akinta arufe yake, kuma bataga bishirah ba. To Aysha wakike ganin zaki tambaya batareda ya zargi komaiba?. Tab aikam hakan zai zama Matsala, danni bansan mi mama keson ganowaba, jiyafa titsiyeni tayi damuka kwanta. Tofa, saifa munlura sosai, Dan inhar suka gano dakansu za'a wargaza mana aiki. Kiyi k'ok'ari Sanin Inda gwaggo bintu take ko bishirah, sune kawai murfin rife sirrinmu, Dan su hajia babba hatsibi baine. Karki damu zan k'ara himma insha ALLAH, k'arfe NAWA zaku wuce birnin Shehu?. Saida yamma ma, zamubi jirgin 5pm ne. OK zankiraki, ammafa dole musake secret numbers, wasu zasu iyamana bincike a wayoyi su wargaza mana aikinmu Anty meerah. Nima nayi tunanin haka Aysha, amma kibari mudawo daga soskot....... Motsin dataji abayantane yasakata saurin kashe wayar, tajuyo da sauri, gabantane yafad'i Dan ganinsa tsaye abayanta, hannayensa zube cikin aljihun wandonsa Na bak'in jins, yanda yakafeta da mayun idon nan nasane yasakata aro sabuwar nutsuwa ta yafama kanta, sannan ta had'e fuska tareda kauda kai daga kallonsa. Mamaki tabasa, yarinyar abubuwanta sunfara bashi tsoro, kullum da Sabon salo zaka ganta, yaukuma a sahun munafunci yaganta, yo idanba munafinciba mizai kawota k'arshen garden yin waya? Duk yawan d'akunan gidan. Ra6awa tayi tagefensa zata wuce yace, "k!. Shiru tamasa tacigaba da tafiyarta. Tsawar daya Daka matace tasakata tsayawa cak, bak'aramin wakitawa y'an hanjinta sukayiba, damacan dauriya takeyi, Dan atsorace take da tunanin koya ji mitake fad'ane, dama akuma kamar yana mata zargin wani Abu daban, tunda ranarma ya tambayeta ko an turota lek'en asirinsane?, hawaye suka cika mata idanu, amma tayi jarumtar tsaidasu. Batasan yak'araso Inda takeba, saida alamun tsayuwarsa taji kusada ita, wannan yasakata d'an d'agowa tasaci kallonsa, idanunsa k'yam akanta, ahankali ta janye NATA tareda lumshesu. Shima saiya kauda Kansa daga kallonta yana furzar da huci abakinsa. Baki yabud'e zaiyi magana wayarsa data fara wringing takatsesa. Cirota yayi daga aljihun wandonsa yakara akunne. Hello Youseef miya farune?. J! Kana inane?. Ina gida mana, miya faru kake magana akid'ime haka?. J! Kayi sauri, ina k'auyen Dutsen Alhaji, nabiyo bayan Barau modibbo ne, please kayi Sauri. What!!, barau modibbo fa?. Kasan mikake fad'ama? da gaske kakeyi kuwa?. Wlhy da gaske nakeyi j!, tundaga airport nake binsa, naje raka Abbah zai tafi Egypt ne, naga Barau modibbo ya sauka a jirgin dayazo daga Spain. OK OK ina zuwa, kakira su Ema.... Kace muhad'u acan, basai sunzo d'aukataba zanje dakaina. Da sauri ya kalli Aysha dake tsaye har yanzu tana sauraren wayar tasa, please maza d'akina cikin drowan gefen gado ki d'akkomin bindiga da key d'in mota, maza da sauri. Yama manta waya aika, saboda akid'ime yake. Hajia babba dake k'ok'arin shigowa garden d'in tatsaya cak, jin wayar da ya khaleel keyi tayi mugun kid'imata, ta maimaita sunan cikin matuk'ar razana, *BARAU MODIBBO!!* lallai yau k'arya zata k'are musu, umarnin dataji yana bama Aysha ne yasakata juyawa da sauri 6angarenta, akid'ime tad'auki waya tashige bedroom d'inta, harda kullewa, wayar hajia Khaltum takira, number busy. Tasaki wani irin tsaki, jikinta har rawa yakeyi. A hanzarce Aysha tadawo d'aukeda guns guda biyu, ta lullu6esu dawani hanky d'insa gudun kada wani yaganta. A harabar gidan ta isakeshi yana yaye tamfol da aka lullu6e dawata azababbiyar mota mai k'yau da tsari. Ya kar6a cikin hanzari, yashige motar, aguje yafigeta, ganin haka d'an gwari yabud'e gate da sauri. Bak'aramar kid'ima hajia babba tayiba, saboda tana hangen fitar figa da ya khaleel yayi saga gidan ta window d'in d'akinta, gumine yashiga karyo mata. Hannunta Na rawa takuma kiran number hajia khaltum. Yanzun kan ta sameta, tana d'agawa tace aminiya k'aryarmu ta k'are. Kamarya aminiya? Miya kawo maganarnan?. Ibraheem sun d'anama Barau modibbo tarko, kuma kinsan kamashi tamkar muma an kamamune, Dan bamuda wani sirri Wanda yawuce Barau modibbo. Bak'aramin wuntsilawa y'an hanjin cikin hajia khaltum sukayiba, tunda taji bayanin Aminiyar tata. Itama kanta zufar ke keto mata, muryarta Na rawa tace Aminiya mun d'ebo ruwan dafa kanmu, lallai yau naga sharrin d'an kunama.🦂 Bata jira amsar hajia babba ba tayanke wayar, tareda fara Neman layin Barau modibbo. ___________ Aysha Na tsaye inda ya khaleel yabarta tamkar gunki taji wayarta Na wringing, dubawa tayi saitaga mama. Batareda tad'agaba ta nufi cikin gidan. A d'aki ta iske mama da yaya fadeelah, mama tana sakama ummuhanee kaya, fadeela kuma Na d'aura d'an kwalinta. Mama tad'ago tana kallon Aysha data shigo sukuku, ke lfyarki kuwa?. Babu komai mama, Aysha tafad'a da sauri. Ido mamar ta tsura mata, kimsan banason k'arya dai. Kamar Aysha zatayi kuka tace, "mama ya khaleel ne". Khaleel kuma? Miya faru dashi?. Babu komaifa, naga ankirashi awayane, ya d'auki bindugu yafita akid'ime, wlhy tausayi yabani, inajin tsoro, tak'arashe maganar da matso kwalla. Murmushi mama tayi, danta gano wani Abu tartare fa ayshar, tacigaba da sakama ummuhanee kayan tana fad'in to kimasa addu'a, ALLAH ya tsaresa, insha ALLAH babu abinda zai samesa, aikinsane yazo da hakan. Kai Aysha tad'aga kamar zata rushe da Kuka. Mama tace jeki shirya zakuje dubiya asibiti. Da to Aysha ta amsa, tashiga bayi tad'an wanko fuskarta tafito, bak'ar doguwar Riga mama tabata. Badan taso sakawarba tasaka, Dan Rabin hankalinta yana kan ya khaleel, jitake kamar tayi tsuntsuwa tabisa, komai yafaru a gaban idonta. Fadeelah takar6i d'an kwalin rigar ta nad'a mata, kaikace wata balarabiya ce, dukda batayi kwalliyaba, farar fauda kawai tashafa kad'an sai kwalli. Mama tabasu kud'i tace su sayi kayan marmari a hanya, suje ga Ramadan can yana jiransu a waje. Har zasu fita, Aysha tace mama wai wama zamuje dubawa?. Kuje mana, aii zaku gani, Ramadan yana jirankufa, zaitafi aikine narok'esa ya ajiyeku tunda asibitin yake, kukuma bakusan asibitinba. To mama saimun dawo. Adawo lfy mama tafad'a tana mik'ewa, jikinaba, a cikeda tunanin yanayin Ayshar, afili tace Aysha dama kin fidda khaleel aranki, babu yanda za'ayi gudan jinina yahad'u da gudan jinin hajia laurah, abindama bazai ta6a yuwuwaba kenan, dama cikin y'ay'an Bilkeesu ne tabbas Dana amince miki, amma d'an hajia laurah bazai ta6a Auren y'arda tafito daga tsokar jikinaba🤕 wannan ALWASHI ne👉🏻. Afalo suka iske ya Ramadan yana jiransu, ganin sun fito yamik'e, yauwa kumuje karna makara ko, yay maganar yana kallon agogon hannunsa. Fita sukayi har bakin motarsa, fadeelah tashiga baya, dole Aysha tashiga gaba, shima ya zauna a mazauninsa yaja motar suka fice. Saida yatsaya wajen saida kayan fruits kamar yanda fadeelah tarok'a, dakansa yafita yasayo komai da'ake buk'ata da kud'insa, sannan yadawo suka cigaba da tafiya. ________________ Neman duniya hajia khaltum takasa samun Barau modibbo, takira wani makusancin yaronsama yak'i d'auka, bak'aramin tashin hankali takuma shigaba, sai kai kawo takeyi tsakanin falonta da bedroom, ga zufa dake ketowa adukkan sassan jikinta, tasan wanene Ibraheem Abdallah, takuma San mizai iyayi, wlhy kasancewar mahaifiyarsa a wannan lamarin bazai ta6a d'aga musu k'afaba, tabbas bayyanarsu a wannan harkar itada mahaifiyarsa tamkar bayyanar wani tone-tone ne agaresu, dolene Ayi *Walk'iya* kowama yagansu, wata gudawace taji tazo mata babu shiri, dagudu tanufi bayi. Tana gudawa tana turama Barau modibbo massage a wayarsa. ______________ Duk yanda youseef kemasa kwatance haka yabi, har ya isa cikin dutsen Alhaji, a can k'arshen gari gidan Na Barau modibbo yake, shikad'ai, tamkar gidan mayu, dagani kasan wannan gidansane Na sirri, babu Wanda yasan dashi. Rigar makarin bullet Adams yabashi yasaka, yakuma d'urama bindigarsa bullet, saida yacikasu fam sannan suka zagaye gidan, kuwa tafiya yakeyi cikin sand'a, idan and'an tafi sai a tsaya ana sauraren ko akwai Wanda yafito, dahaka har wasunsu suka sami damar shigewa ainahin cikin gidan. Cikin sand'a ya khaleel yabi tabayan wani mazgegen k'ato dake tsaye da bindiga AK 47 ahannu, bakimsa yay saurin toshewa da hannunsa ya murd'e wuyansa, jikake k'ak'assss!!!!! Ya karya Wuyan, yajefar dashi awajen tim, sannan yakuma rik'e bindigarsa cikeda kula, yana tafiya cikin sand'a. Wani yakuma hangowa agabansa, yay saurin janyo buhun ledar dake kan wani dirom a tsakar gidan, tafiya yake cikin sand'a yana bin bango, harya kai inda yake, da sauri ya kunshe kamsa acikin buhun ya kulle, buge buge yafara saboda rashin fitar numfashi, ya khaleel yakuma murd'a bakin bukun, bai sakiba saida yaga jikin mutumin yasaki alamar ya mutu sannan ya hankad'ashi ya daki bango. Wani icce yad'auka ya mazgama Wanda ke tsaye bakin k'ofar a kai, da sauri yazube awajen tareda sakin razananniyar k'ara, wannan ne yasaka su Barau modibbo farga da abinda ke faruwa.... _______________ Su Aysha sun isa asibitin, har d'akin da gwaggo bintu take kwance, da bishirah Aysha tafara cin karo, wata iriyar zabura tayi da zare ido waje, tayi saurin kai dubanta ga gwaggo bintu dake kwance bisa gadon. Cikin muguwar fad'uwar gaba gwaggo bintu take kallon Aysha, dukda batada tabbacin itad'ince ko ba ita bace, Dan Aysha ta canja sosai...............✍ _to masu karatu, idanfa kere🏑 Na yawo zamo🐇na yawo wataran za'a had'u._ *yau dai ga Aysha ga kuma gwaggo bintu, shin mikuke tunanin zai farune?.* *ga ya khaleel can zai damk'i ogan su hajia babba, mikuke tsammanin zai biyo baya?.* *mama Na zargin gwaggo bintu, kuma tanada burin bincikenta akan wanda yafidda Aysha k'asar waje karatu, kunga koda Aysha tayi yunk'urin 6oyewa mamafa zata tono, yakuke ganin za'a kwashe?.* *ya maganar auren Aleeya da ya khaleel? Kunsan dai ya khaleel ya d'aukama mama alk'awarin amincewa, aganinku babu lauje cikin nad'i akan had'in auren Aleeya da ya khaleel?, kuyi nazari, gakuma baffah yayi wani furuci akan auren ya khaleel d'in, shin shikuma wacece za6insa? Dan nasan ba shirinsu d'aya da hajia babba ba, kuna ganin hajia babba zata yadda?, kokuwa baffah zaiyi hak'uri danasa za6in?, ko za'a had'a masa sune suduka?, towama baffan zai za6ama ya khaleel?.* *mi Aysha da meerah suke shiryawa su gwaggo bintu?, tabbas akwai 6oyayyen tarko dasuke shirya musu, to amma nami? Kuma zasu sami nasara?.* *ya maganar soyayyar da Aysha kema ya khaleel?, ga mama ta d'auki alwashi akan hakan, shin burin Aysha zai cika kuwa?.* _kutttt cakwakiya nacikin *CIKI DA GASKIYA* part 2, karku bari abaku labari, zaizo muku da abubuwan mamaki, soyayya mai k'ayatarwa, k'aryar wasu zata k'are, gad'an Karen tone-tone, za'ayi WALK'IYA fa, kuma zamuga kowa, hardama wad'anda bakuyi tunaniba, akwai abubuwan al'ajabi, mamaki, tsoro, k'ayatarwa, kai hardama naban haushi._ Kudai kawai Ku kasance da Bilkeesa Ibraheem Musa, (bilyn Andull) danjin yanda zata kaya. Marubuciyar... _Rashin Sani!!._ _Auren k'addara ko biyyaya?._ _k'anwar uwace ko kishiyar uwa?._ _Ni da aminayata!!_ _Nawaff!!._ _Sabon al'amaree!!_ _Kukan kurciya....!!_ _Ban saketa ba!!_ _Abdul-maleek bobo!!_ _Karayar arzeek'i!!_ _Sanadin bikin sallah!!_ _Ciki da gaskiya...!!_ Wanda bai karantaba yanema akasuwar online🤣😘😜 K'ak'ak'ak'a, wata rikita rikita sai a CIKI DA GASKIYA part 2, yana nan tafe nan kusa kad'an. *_CIKI DA GAAKIYA!!.... (wuk'a bats hudashi), kashi Na biyu._* *COMING SOON!!!!!.* Ngd sosai masoya, ina alfahari daku, ina k'aunarku, inayinku 100%, karku gaji, kukasance dani a part 2❤❤❤❤❤😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘. K'aunarku dabance a zuciyar bilyn Abdul😍😍😍😍😍😍😍😍🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀🙋🏻‍♀saikun jini.👍🏻👍🏻.