Compiled By Umar Dalha Funtua. 🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕 Na Afrah bhai Page 1 Wattpad @afreey101 'bismillahil'rahmanil'rahim **************** "A Shekara ta alif sha tara da sittin da tara 1969 a masarautar 'daura' dake cikin jihar katsina. 'A lokacin ne Sarki 'MUHAMMADU ABDUL-JABBAR UMAR' ya amshi mulki daga wajen mahaifinsa wato SARKI UMAR NA BIYU bayan wata sarka'kiya da fadace fadacen da suka wakana a cikin wannan yan shekarun' bayan rasuwar tsohon sarki Abdul-samadu kenan,a inda jama'a da yawa ne suka rasa rayukansu acikin masarautar da ma garuruwan dake kusa dasu' A cikin wannan karni ne na sarki Abdul-Jabbar ya saka dokiki masu tsauri da yawan gaske ga alummar sa dan samun cikakken kwanciyar hankali a cikin kasar ta sa. "Babu wani mahaluki dake zaune a kasar ta daura ko ince a cikin masarautar ta daura" da bai san da zaman RUMFAR BAYI ba ,waje ne da zan iya cewa DUNIYAR BAYI ,wato a nan ne gaba daya bayin dake masarautar daura suke Rayuwarsu a ciki. 'RUMFAR BAYI na tattare da tahiri da kuma labarai na bayin da suka gabata.. RUMFAR BAYI wajene inda bayi suka maida a matsayin tasu duniyar' dan ko wacce baiwa nada nata irin rawar da ta taka.. ******wannan kenan****** "Gudu takeyi kamar ranta zai fita' bata ko sanin in'da take saka kafarta,macece mai kimanin shekaru goma sha takwas da haihuwa. 'Wani dogon lumfashin taja....sannan naga ta Dafe katoton cikinta, tana zubar da hawaye masu ciwo'kafafunta gaba daya rubar da jini sukeyi duk sun fashe sun kumbura tsabar gudun da take sha..ina zataje?ya zatayi da dan dake cikin cikin ta?dole ne ko bata rayu ba ta haifar da shi...wannan tunanin ne kawai yake yawo cikin kwakwal'warta.. 'Dare ne ya tsala sosai dan babu wani bil adama dake yawo a cikin garin data sami kanta.. ' juye'juye take tayi dan samun wajen da zata boya..can ta jiyo muryoyin kattin mazan dake binta suna neman raba ta da rayuwarta.. 'Wata tsohowar kofa ce ta hango tayi saurin karasawa ta boye a bayan kofar tana jin dan cikinta na masifar juya mata tamkar zai fito dan kansa. 'Tana jinsu suna ta zagaye zagaye a wajen suna faman nemanta' tayi saurin saka hannunta dake rawa ta dafe bakinta ta kulle shi gam jikinta na ba'ri,sbd azabar nishin da takeyi tanajin wata masifaffiyar gajiya na fita a gaba daya jikinta... 'kusan Shudewar minti goma taji shiru hakan ne yake nuna mata sun wuce kenan,ta saki wata irin ajiyar zuciya.. 'Tana kokarin mikewa ne daga durkushen da take taji an fada mata kafadarta.. "Zaro jajayen idanuwanta tayi bugun kirjinta kamar zai fito sbd tsabar tsorata da tayi.. Lafiya baiwar Allah... Taji wata murya mai cike da nutsuwa ta furta daga bayanta.. Da sauri ta juyo suka hada ido da wata mata mai kimanin shekaru 29,sauke ajiyar zuciya tayi.. Lafiya me kike yi anan haka? Matar ta sake tambayar ta..ganin tayi shiru.. 'Tana kokarin bude bakinta ne tayi magana taji marar ta na wani azababben ciwo a take kuma taji wani sanyi a ya ratsa tsakiyar cinyoyinta,ihuu ta saki da bakinta dake a bushi da kyar ta kalli matar tace ki.... ki ki taimaka min......dan darajar ....Allah.... Cikin rawar jiki da tausayawa matar ta juya da gudu tana kwala kiran laure......! Laure....! Cikin sakanni da basu wuce uku ba sai gata tare da wasu mata su biyu sun karaso wajen'ba bata lokaci suka kamata suna mata sannu gaba daya ta gama galabaita ko lumfashinta ma da kyar yake fita.. wani daki suka kaita suna ta yan leke leke...kamar wasu marasa gaskiya.. Laure ta kalli wannan matar tace, JAKADIYA kina ganin abunda muke shirinyi daidai ne kuwa? Jakadiya Taja lumfashi,laure kina tunanin mu barta ne ta mutu ita da dan dake cikinta sbd kawai wata doka ta sarki? (dokar sarki Abdul-Jabbar ta farko itace-kada wanda ya taimaki wani bakuwar fuska a cikin kasar sa) 'Da'yar dake ri'ke da wannan yarinyar me ciki ta girgiza kai,nidai a nawa ganin mu taimaka mata ko ba komi babu wanda zamu bari yasan wannan abun da muka aikata bare har a hukuntamu..ko ya kuka ce? Gyada kai sukayi du'ka sannan jakadiya ta kalli laure,ki fita kisa mana ido a waje sbd tsaro,bana son kowa yasan halin da muke ciki,laure tace hakane sannan ta fita da saurinta.. Shiru ba'ka jin komai sai nishin wahalar da wannan yarinyar takeyi tamkar ranta ze fita.. Cikin min'ti da baifi ashirin da bakwai ba sai ga kukan jariri laure dake waje ta sauke ajiyar zuciya sannan ta leko dakin cikin zumu'din ta.. 'Ganin jakadiya da HANSAI sunyi jugudum jugudum dasu yasa ta fadawa cikin dakin hankalinta a tashe,lafiya ? Ta tambayesu.. " Jakadiya ta kalli yarinyar jiririya dake hannunta sannan ta kalli uwar dake kwance bata lumfashi tace ALLAH YA JIKANKI DA RAHAMA baiwar Allah.. laure ta dafe kirji ban fahimce ku ba?,hansai na goge kwalla tace, Allah yayi wa uwar rasuwa,zaman yan bori laure tayi take jikinta ya hau ba'ri,cikin tashin hankali tace yau mun shiga uku mun lalace shi kenan mu kam Allah yayi kwanan mu ya kare a wannan daren.... "Jakadiya ta watsa mata harara,sannan ta kalli hansai ta mika mata yarinyar dake ta wutsir wutsir a hannunta.. 'tace ungo karbi diyarnan bari nayi wa sarkin kofa magana yazo sai muyi wa uwar abunda ya kamata a kaita makwancinta..dan shine kawai na aminta dashi.. Da sauri laure ta mike tace,me kike nufi jakadiya yanzu fi sabilillahi ya zamuyi da wannan diyar?bamu san daga wacce duniyar yarinyar nan ta fito ba shine zamu rike diyarta?ni dai a nawa tunanin kawai mu kai diyar nan can wajen gari mu barta acan sbd dai ajiyeta a nan wani tonan asirin mu ne.. " Hansai ta girgiza kai,haba laure me yasa ne baki da ko digon tausayi acikin zuciyarki ,yanzu kawai sai mukai jaririyar nan wajen gari mu ajiye ta? 'Jakadiya ta kallesu duka tace,yarda aka haifi wannan jaririyar a cikin RUMFAR BAYI to tabbas ne a cikin RUMFAR BAYI zatayi rayuwa kuma tabbas dolene mu zamu rike ta....tana gama fadar haka ta fice cikin saurinta... 'Sunyi mata wanka sannan jakadiya ta kira su sarkin kofa suka kaita makwancinta cike da addu'o'i da kuma tausayi suka dawo cikin masarautar bakin su alekum... 'Washe gari tunda sassafe kamar ko da yaushe a al'adun su na Rumfar bayi dukkan baiwar dake karkashin Rumfar dole ne zasu tashi duk su hallara a gaban dakin UWAR BAYI DUBU (head maid)' 'Itace mai kula da dukkan harkokin bayi mata da kuma kuyangin dake karkashin inuwar rumfar bayi.. 'Cikin kamala da kuma daurewar fuska DU'BU (uwar bayi ) ta fito daga cikin dakin nata,jakadiya na kusa da ita.. Gaba daya a tare suka gaishe da ita cike da girmamawa kamar yarda suka saba. 'Ta kallesu tana shirin magana ne sukaji kukan jiriri ya karade wajen gaba daya.. Cikin tashin hankali du'bu ta shiga tambayar su,a ina aka samo jiriri a cikin wanann Rumfar bayin da masaniyar ku akai? Jakadiya gaban ta ya fadi hakama laure dake da gefenta.. Shiru kakeji kowannen su ya kasa magana kamar ruwa ya cinye su.. Du'bu tace,ba da ku nake magana ba! Jamila ce tayi karfin hali tace,ina tunanin hansai ce ta haihu a daren jiya tunda ita kadai ce me ciki a duk fadin wannan rumfar.. du'bu cike da mamaki tace hansai dai? Jakadiya tayi saurin cewa,eh! Dan a jiya ni da kaina na amshi haihuwar tata kinsan tunda ta dawo daga rakiyar GIMBIYA KILISHI kasar Rano ta dawo da laulayin haihuwa.. du'bu tace in ko hakane ina taya malam kamilu murna kwarai da gaske (shima bawa ne kuma mijin hansai) Gaba daya wajen suka hau murna,du'bu ta saka laure tayi mata kiran hansai.. " ita kuwa Hansai dama tana fama da wani ciwo ne cikin yan watannin, cikinta se ya kumbura sun'tum tamkar wata me juna biyu,toh a daren jiya ne mijinta kamilu ya samo mata magani daga kasar zazzau tana sha kuma se Allah yasa ta warke..'wannan kenan' 'Laure ce tayi kiran ta bayan ta sanar da ita duk shirin da sukayi wa du'bu a waje. Tana fitowa dauke da jaririyar a hannunta ba'yi suka dau shewa dan kuwa yaune kawai aka taba haihuwa acikin RUMFAR BAYI... "Wannan kenan" "Wattpadians ya kuka ji shi? A ci gaba ko kuwa? It depends on ur comments ooh..😉 [9/18, 3:01 PM] Aysha Galadima:   🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕 Na Afrah bhai Page 2 Wattpad @afreey101                ****************            "Du'bu da kan'ta ta sa'wa jaririyar suna JUWAIRIYA a take rumfar bayi ta hau shewa da murna, dan'yen dabino suka kwaso daga rumbu suka hau rabawa junan su cike da tsantsar farin ciki dan a ganin su tamkar wata babbar kyauta ce Allah ya kawo musu..               "A haka Rayuwa taci gaba da tafiya a inda jakadiya da hansai har ma da du'bu da laure suka ci gaba da kula da JUWAIRIYA dukkanin baiwar dake cikin rumfar bayi tana mutukar son'ta,a haka  labari dai har yaje kunnen GIMBIYA KILISHI wato uwar gidan mai martaba kenan. 'Macece mai shegen son milki da kuma son a girgirmama ta,gata shu'unar mace dan kuwa gaba daya masarautar ta daura babu mahalukin da ake bawa girma kamar ta idan aka cire sarki Abdul-Jabbaru, yaran'su biyu kacal da mai martaba' akwai dan ta yarima JALALLUDEEN shine me jiran kujerar mulki  wato heir apparent to the throne kenan, sai HAMZA kaninsa,ganin gimbiya kilishi ita kadai ce Allah ya bawa kyautar ya'ya maza a kaf duka matayen sarki idan ma an hada har da kwarkwarorinsa (concubines )'gimbiyata kilishi kawai ce bata da diya mace' shiyasa rashin mutumcin nata ya kara girma sannan tsanar sabowar amaryar mai martaba ya shigeta sosai' dan kuwa itama FULANI DIYYA  wato amaryar mai martabar kenan daya auro daga masarautar bauchi tana di'ra ta santalo dan yaron ta namiji daya dilo wato TURAKI (ABDULLAH )sai diyarta ZAINABA. ita kam macece mai son jama'ar ta,indai har kina cikin rumfar ta toh fa lallai ne dole ki so ta dan tana mutukar kyautatawa na kasa da ita balle ga bayin ta,shiyasa kaf masarautar tafi dukkanin matar sarki farin jini da kuma karbowa a wajen Bayi..     ****wannan kenan ***** "Shekaru nata tafiya a inda yanzu JUWAIRIYA na da shekara goma da haihuwa.    'Yarinya ce mai karanbani sosai bata ji,sai dai tasan iyakarta,dan kuwa kullum zaka ganta tana guje gujenta a cikin rumfar bayi wanda hakan yake saka  bayin dake ciki annashuwa. ummanta wato hansai tana kokarin bata tarbiyya irin tasu ta bayi marassa ga'lihu,haka kuma kamilu na mutakar son JUWAIRIYA dan dama ya dade yana neman haihuwa Allah bai basa ba. (kamilu da hansai bayin Allah ne da kaddara ta fado musu aka siyar dasu a matsayin bayi ga masarautar ta daura)      "Tunda juwairiya ta ta'so bata taba ko da lekawa ne cikin masarautar ba dan kullum tana cikin rumfar bayi' gashi bata da abokin wasa dan duk bayin dake ciki da safiya tayi suke ficewa zuwa wajajen uwayen gidansu. .    Kamar kullum yau ma hansai ta gama shiryawarta dan tafiya wajen uwar dakinta wato GIMBIYA KILISHI,ta kalli juwairiya dake zaune ta kura mata idanuwanta masu haske,kamo hannun ta hansai tayi tace kici gaba da hakuri juwairiya kinji abbanki zai zo miki da halawa anjima,juwairiya ta saki dan murmushi sannan tace,umma muje na miki rakiya,hansai ta murmusa sannan ta kamo hannunta, suna kaiwa bakin kofa ta sake hannun juwairiya sannan ta shafa kanta kafin ta fice.      Hansai na tafiya juwairiya tayi saurin karasawa gaban babban kofar ta leka abunda bata taba yi ba kenan sbd gargadin da ummanta tayi mata..     Ware ido tayi ganin jama'a da yawa nata zurga zurgar su ga wani haske da har kashe mata ido yakeyi ga kuma iska me dadi dake kadawa.. Da sauri ta karasa cikin dakinsu ta dauko mayafin ummanta,ta boye shi a cikin doguwar rigar dake jikinta .     A hankali ta karasa madafa waton inda ake shirya wa sarki abincinsa, ta leka nan ta tarar da bayin dake dahuwa suna ta aikinsu,ta juya da sauri ta lulluba mayafin a kanta sannan da gudu ta saka kafa ta fice daga rumfar bayi.. **********      "Tafiya kawai takeyi tana kalle kalle sai washe baki takeyi dan bata taba ganin mutane masu yawa haka ba balle jinsin maza dan kuwa a rumfar bayi babu namiji a ciki. "wani dan zomo ne ta hango fari dashi tas,ba karamin burgeta yayi ba,ta shiga binsa da gudu batayi aune ba taji tayi karo da mutum bum! Da sauri taja da baya...   "Baki da hankali ne?ina kika bar idanuwanki da har zaki taremin hanya ta!! Taji an fada da wata murya me cike da isa da iko..    Dagowa tayi da sauri dan son ganin waye wannan me muryar..yake magana kamar yana kirga lafuzan sa.   Caraf idanunsu suka sarke dana juna.. Wani dan saurayi ne da kalla zai kai shekara sha biyar..    Juwairiya ta kafe shi da ido dan tunda take bata taba ganin me kyau irin nasa ba,ahankali ta fara fahimtar irin kallon kyama da kaskancin da yakeyi mata.. hakan yasa ta shiga bin shigar shi da kallo.. Sanye yake da kayan alfarma kayane masu tsada ga zinari ta ko ina sai kyalli yake..   Ta kalli yaron dake kusa dashi at least shi ze kai 11 years,shima din cikin kayan alfarma yake..     Bakya jina? Tayi saurin ja da baya kadan sannan tace,a tunani na mu biyune da laifin.. 'tunda idan ni bani da ido ai kai kana dashi ba sai ka kauce min ba?    Cike da tsantsar mamaki suke kallonta.. Wacece ita da har zata ringa maida masa magana haka?    Juyawa yayi cike da fusata..cikin daga murya yace,wai ina sarkin Lumbu ne! Sallama kana ina! wayace musu su ringa barin ya'yan bayi masara galihu suna shigowa nan! Cikin sauri wani mutune yazo ya zube a gaban sa,Allah ya huci zuciyar YARIMA ayi min afuwa ayi min gafara!nayi laifi ka yafewa wannan bawan naka...     Wanda aka kira da Yarima ya yamutse fuska sannan ya kalli na gefensa,HAMZA me kake ganin zamuyi dasu?    Hamzan ya tabe baki,kawai mu kaita ga GIMBIYA  tunda dai kowa ya sani BAYI basu da ikon shigowa cikin lumbun TAKAWA (wato sarki)..     RANKA SHI dade ayi musu afuwa.. Sukaji an fada daga bayan su.. 'A tare duk suka juyo suna kallon shi.. Saurayi ne dan shekara 12 kyakkyawa ne sosai rike da hannun yar budurwa da bazata wuci sa'ar juwairiya ba..   Yarima ya daure fuska, saboda me zaka neman musu gafara TURAKI? Turaki yai murmushi sbd a tare muke da ita kulangar ZAINABA ce..      Hamza da yarima suka ja tsaki sannan suka zo zasu wuce ta gefen juwairiya ta dago suka hada ido da yarima ya banka mata harara, ta bi shi da kallon mamaki har ya fice yana jin zafin halayen ta a garesa .... "Da sauri juwairiya ta karasa wajensu turaki ta dukar da kai tace,na gode ranka shi dade..   Da kallo yabi fuskarta,daga ina kike?dan ban taba ganinki a cikin masarautar nan ba..   RUMFAR BAYI ta bashi amsa,ya jinjina kai,zainaba ta  kalli yayanta,yaya turaki ina sonta! Da sauri suka kalli zainaba cike da mamakin furucinta .. Turaki yace,zainaba ke da kika ki amincewa da kowacce baiwa?zainaba tayi murmushi sannan ta juya da gudu tayi tafiyarta..   Turaki ya juya ga juwairiya data bi bayan zainaba da kallo.. Kiyi gaggawar komawa inda kika fito dan na lura ba ki gama fahimtar wasu dokokin masarautar nan ba,yana gama fadar haka yayi ficewarsa... A sanyaye juwairiya ta koma cikin rumfar bayi gaba daya taji bata ma kwadayin sake fita dan kuwa duk mutanen da ke waje basu da mutumci ita kam zaman ta a Rumfar bayi yafi mata dadi inda kowa yake da same rights dinsa....... Wannan kenan! 🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕 Na Afrah bhai Page 3 ******************** "DAN SARKI JIKAN SARKI !! "DAN SARKIN DA BASHI BA SARAUTA!! "AAH LAFIYA TORON GIYA... UWAR SORO"taci gaba da da yiwa yarima jalal kirari..wanda ke kokarin shigewa falon mahaifiyar sa..ko kallon inda take bayyi ba bata .. "Sai Hannu kawai da ya da'ga mata fuskar nan a tamke.. "Gimbiya kilishi na zaune akan kilisarta tasha gayu cikin kayan alfarma zinari ne ba'a mgnr sa.. ga bayi nan sai yi mata hidima suke,hansai na gefe rike da tiren fruits kala'kala..     Kilishi na kallon dan nata ta fahimci cewa ransa a bace yake... Hansai ta kalla tayi mata alama da su fice daga falon.. 'Hansai ta mike sannan tayi wa bayin dake cikin falon mgn akan su fice..    "Kilishi ta kalle sa,yarima lafiya? Yarima jalal ya dauke kansa gefe.. Tasan bazai yi mata mgn ba dan haka sai ta kalli hamza..   Hamza me ya samu yayan naka?   Hamza yaja tsaki,wai fa umma dan..........nan ya fada mata komai.. A fusace ta mike tana huci,wacce baiwa ce da har take da wannan ikon na maida wa yarima mgn!dole ne na hukunta ta dole ne tasan matsayin ta.!!!..   Yarima ya mike da sauri... Kada ki damu umma na lura gidahuma ce dan bata gama sanin matsayinta ba.. Kilishi taja tsaki,dolene ta fuskanci hukuncin abunda tayi!.. Yarima ta riko hannun umman nasa,kada ki damu umma ya sakar mata murmushi.. Da kyal da so'din goshi yarima ya samu ya lallaba kilishi ta hakura.. ********** "Da gudu zainaba ta shiga makeken falon FULANI diyya dake tsare tsab cikin kwaliya ta gargajiya..    'Fulani diyya na zaune a kilisarta ga bayin ta nan duk sun zagaye ta sai hidima suke mata.. "Ganin zainaba ta shigo da gudu cike da murna yasa ta fadada murmushin ta..    Laure dake gefen fulani ta shiga fadin,yar sarki diyar FULANI wannan murna taki dole ta farantawa dukkanin wanda ya kalli wannan kyakkyawar fuskarki rai.. Zainaba tace Allah ko laure? Laure tace kwarai kuwa ranki shi dade.. Fulani ta murmusa,me ya sakaki wannan farin cikin zainaba?   'Ta zauna tana lankwashe kafafunta,fulani na canja ra'ayina ina so a yau din nan nima a bani baiwata..   Fulani ta kalli laure cike da murna,laure tace Yanda kike so ai haka za'ayi gimbiyata.. Laure ta mike da sauri tayi waje.. Cikin minti goma sai gata da wasu yan matan bayi su biyar..     Ta kalli zainaba dake kishingedi tana cin tufa (apple )   Gasu nan ki zaba wacce ta mike gimbiyata..     Zainaba ta kwabe fuska sannan ta kalli fulani,umma duk bani son su.. Fulani ta kalli laure tayi mata nuni da ta koma ta canzo wasu.. Laure ta sake fita ta shigo da wasu yan matan har su shidda.. Still zainaba a shagwabe tace suma haka.. Laure cike da gajiya da wulakancin zainaba ta fice ta sake dauko wasu dan saida ma ta zabo su sannan ta zo dasu.. Zainaba ta girgiza kai tana turo baki.. Fulani ta sauke ajiyar zuciya dan ba yau bane zainaba ta fara wannan fitinar..     Toh wai zainaba wacce irin baiwa ce kike so ne haka?ina tunanin sai dai a kai ki can kasuwar bayi ki siyo da kanki..   Zainaba tayi saurin cewa ah ah RUMFAR BAYI  zaku kaini umma.. Cike da mamaki bayin dake wajen suke kallonta dan kuwa babban kaskanci ne ace jinin sarauta ya shiga rumfar bayi..    Kina da hankali kuwa! Fulani ta fada cike da daga murya..    Zainaba ta turo baki,umma ni wacce nake so tana can a RUMFAR BAYI..   Laure ta hadiye yawu kut amma sanin kuma juwairiya bata fita ko ina.. da wuyane a san da ita a cikin masarautar ma,sai ta sauke ajiyar zuciya tace,ranki shi dade wacece ita yanzun nan na kawo miki ita?    Zainaba ta langwabar da kai.. Sannan tace..   Wata yarinya ce kamar ni haka..    Laure taji kafafunta sunyi sanyi.. Fulani tace,me kike fada haka,kin taba jin a Rumfar bayi akwai yara ne? Zainaba tace wlh umma da bakinta tace mana a Rumfar bayi take..kima tambayi yaya..    Fulani zatayi magana sukaji ana sanar da shigowar turaki..     Sai daya zauna ya gaisar da fulani sannan tace.. Wai turaki wane shirme ne zainaba ke fada,tace min akwai yarinya baiwa dake rumfar bayi kuma ita take so a matsayin baiwar ta ..    Laure ta cije baki...a ina zainaba ta gano juwairiya kuma?   Turaki ya kalli zainaba, ke dama da gaske kike? Zainaba ta gyada kai ni ita nake so ta zama BAIWA ta .. Ya kalli fulani eh mun hadu da wata yarinya dazu tace mana a Rumfar bayi take..   Fulani cike da tsananin mamaki ta kalli laure.. Wai haka? Laure ta kakalo murmushi.. A...eh..eh....kam..anyi haka..akwai diyar hansai ina tunanin itace suka gani din... Fulani ta ce cike da kasaita a kawo min ita nan! Laure ta mike da sauri tace toh ranki ya dade..   Laure na fita ta shiga buga sauri bata zarce ko ina ba se sashen gimbiya kilishi tayi tsaye tana tunanin yarda zata samu mgn da hansai...   Can ta hango wata baiwa ta fito da tire a hannunta,laure ta tare ta da sauri..   ke Yimin mgn da hansai kice mata ina mata neman gaggawa..    Laure na nan jingine da kango sai ga hansai kamar an jeho ta, ta kalli laure ya akayine laure?    Laure tace ina jakadiya? Hansai tace tana can fadar mai martaba ,laure taja lumfashi sannan ta sanar ma hansai yarda ake ciki,hansai ta dafe kirji yau mun shiga uku yaushe juwairiya ta fito daga rumfar bayi? Laure tace ba wannan ba yanzu ya zamuyi?dan fulani ta nemi dana kawo ta..   Hansai tace a gaskiya bana son juwairiya ko kadan tayi irin rayuwar da muke ciki,bamu san asalinta ba bamu san daga wace duniyar ta fito ba amma laure wlh bana son ganin juwairiya cikin damuwa ko kadan,kuma kinsan halinta kwarai bata ji  kada taje tayi wani laifin...... kuka ne yaci karfin ta..   Laure ta dafa ta bari na saka wani bafaden yayi mana kiran jakadiya se mu san nayi. Cikin tashin hankali jakadiya ta karaso wajen su,lafiya naji kira haka,shamaki yake ce sanar min ana nema na bayan kunsan yau ina fa'da ne da kyal na samu waziri yamin alfarmar tahowa..    Hansai na hawaye ta sanar mata da komai,jakadiya taja lumfashi toh miye a ciki?dole ne kun san watarana hakan zata faru,laure tace bari dai na je na kai ta wajen fulani nasan dole ne a gobe zata fara aikinta na BAUTA... Laure ce ta shigo rumfar bayi can ta hango juwairiya tana ta tsalle tsalle tana zolayar du'bu dake zaune tana linkin kaya..    Laure ce ta karasa ta zauna kusa da du'bu tana sanar mata umurnin fulani na son ganin juwairiya.. Du'bu ta gyara zamanta tana murmushin murna dan ita kam ta hannun damar fulani ce sosai sam bata son komai daya danganci gimbiya kilishi.. Tace Allahu akbar ai zainaba ba kadan ta biyo mahaifiyar ta fulani ba,na tabbata juwairiya zataji dadin zama da ita.   Laure tace uhm,sannan taje ta kamo hannun juwairiya, juwairiya tace,goggo laure ina zamuje?laure tace badai ke yawo ba ai gashi nan jin jawo wa kanki aikin BAUTA.. "A kofar sashen fulani akayi musu iso.. Laure taja hannun juwairiya dake ta kalle kalle suka shiga ciki..    Baki sosai juwairiya ta bude ganin kyau da tsarin falon ,can ta hango fulani hakimce akan kilisar ta..   Tayi kasa da kanta,zainaba ce ta mike tana fadin,itace wannan umma kin ga ta nan.. Fulani tayi murmushi tana kallon juwairiya a ranta tace,yarinyar kyakkyawa, ta kalli laure toh kinji laure ita zainaba take so a matsayin kuyangar ta dan haka daga gobe zata fara yiwa zainaba hidima...     Juwairiya tayi saurin kallo zainaba dake kallonta dauke da murmushi, sannan ta kalli turaki dake zaune shiru yana saurarensu.. Laure tace an gama ran fulani ya dade,zainaba ta kalli juwairiya sai mun hadu gobe ko?juwairiya ta gyada kai sannan suka juya suka fice.. "A daren ranar raba dare su jakadiya,laure da hansai sukayi suna fahimtar da juwairiya yanayin rayuwar da zata shiga.. Suka fara da gaya mata matsayin ta,ke ba kowa bace fa'ce BAIWA, yanzu gimbiya zainaba itace uwar dakinki wacce zakiyi wa hidima.. komai takeso shi zakiyi mata babu gardama, ko me tace dole ki amince dashi, duk abunda take so shi zaki so, duk abunda bataso kada kiyi, ki guji bata mata rai, kome zakiyi se kin nemi  izinin ta, ki bauta mata dan a halin yanzu rayuwarki kamar tana hannunta ne..    Juwairiya taji abun banbara kwai,tace amma umma jakadiya rayuwa  tana ga Allah ne ai ko?laure tace hakane amma rayuwarki da zakiyi a wannan masarautar tana hannun gimbiya zainaba ne,dan a kowane lkcn zata iya ba'tar dake...   Juwairiya ta tsorata sosai,jakadiya ta shiga nuna mata yarda duk zata kula da gimbiya zaOneloveuk wata hidima da akeyiwa ya'yan sarauta an koyar da ita,sai cikin dare sosai suka samu rintsawa sbd tambayoyi da juwairiya ta rufe  su dashi.... " Wannan kenan " Share pls n pls vote on wattpad @afreey101 #Onelove [9/18, 3:10 PM] Aysha Galadima: 🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕 (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 4 Wattpad @afreey101       ************************        "Washe gari da sassafe,hansai ce ta shirya juwairiya cikin irin shigar tasu ta bayi, kayane irin na Sa'ki' dinnan riga da zani(blue color kayan fulani dinnan ),laure ta shigo taja hannunta suka fice..    "Tafiya sukeyi juwairiya na ta kalle kalle tana tsallenta cike da nishadi.. ' can ta hango wani yaro dauke da kwando a kansa aciki kuwa su mangoro ne da gwaba gashi tana mugun son mangoro sosai,nan ta kura mai ido tana tafiya tana waiwayen sa,yana dago da kai ya hango ta,ganin yarda take bin kwandon dake kansa da kallone sai ta bashi dariya har sai daya murmusa..     Laure ce ta hadu da wata baiwa suka tsaya gaisawa,juwairiya ta tsaya tana tunanin irin girman masarautar dan sun sha tafiya sosai ga gine gine masu yawa ga shukoki masu kayatarwa..   " Amsa.." Taji ance daga bayanta,tayi saurin juyowa.. Sukayi ido hudu da wannan yaron..yana mika mata mangoro biyu fuskarsa dauke da murmushi.. Ta kalleshi ta saki wani irin murmushin murna,ji tayi laure tace,muje muje juwairiya....   Da sauri ta amshe mangoron ta furta ngd da sauri tayi gaba... Suna isa sashen zainaba ayi musu iso ciki.. Zainaba na hakimce a zaune ana ta mata fifita... Juwairiya ta saki baki ganin kyawun dakin ya burge ta sosai.. Zainaba ta saki fuska sannan tace,wai ya sunan ki ne ma? Sauke kanta tayi kasa tuna mgnr su  yaha ta jiya da sukace banda  hada ido da uwar daki,a sanyaye tace sunana JUWAIRIYA.. Zainaba tace toh muje makewayi (toilet ) dan ina son nayi wankana yanzu.. Juwairiya tayi saurin kallon laure,laure ta gyada kai sannan taje kusa da ita tace,kada ki manta da maganar mu ta jiya,tana gama fadin haka tayi gaba..      Juwairiya kanta a kasa tace ina ne ban dakin ranki shi dade? Zainaba ta dan murmusa sannan ta kalli baiwar dake kusa da ita tana mata fifita tace,kai ta ban dakina sannan ki nuna mata yarda nake son ruwan wanka na.. "toh ranki shi dade ta mike hade da kiran juwairiya suka shiga wata kofa data sada su da wani makeken toilet sai kamshin sabulai yakeyi ga wani bahon wanka na silver a ciki, baiwar ta kalli juwairiya tace,kingani ruwan zafin kadan zaki saka dan zainaba bata son ruwan wankanta yafiya zafi da yayi dumi ya isa' ,ta dauko wasu ganyayya'ki masu fitar da wani sanyin kamshi,tasa hannu ta damka kadan tace kinga haka?juwairiya ta gyada kai,toh haka zaki ringa sakawa duk lkcn da zaki hada mata ruwankan ta,juwairiya duk ta fahimta dan kuwa akwai ta da kaifin basira. 'Se data taimakawa zainaba ta cire kayanta sannan suka shiga ban dakin. 'zainaba ta shige cikin bahon wanka da dan shimin dake jikinta,ta kalli juwairiya,tace.. "cu'da min bayana" juwairiya ta dauko soso mai taushi tazo ta fara cu'ta mata bayan a hankali sbd dai an sanar mata yarda akeyi.    Sai da zainaba ta wanko sosai sannan suka dawo daki,ta kalli juwairiya dauko min wancan akushin,ta dauko tazo gabanta ta ajiye,zainaba ta bude kayan kwalliyarta ne a ciki.   Ta kalli juwairiya...... miko mi'ni jan bakin can,juwairiya tayi sakatoto tana kallonta dan bata ma san minene shi jan bakin ba,zainaba taji shiru tace lah baki san shi ba ne? "Ta gyada kai tana fadin,Allah ya huci zuciyar  ranki ya dade bani da masaniyar me kike bukata idan har ranki ya dade baza ta damu ba ina so ta ganar dani minene shi,zainaba tayi dariya sannan ta dauko jan bakin da kwalli da hoda duk ta nuna mata su'sannan ta tsara yar kwalliyarta da kanta,juwairiya cike da mamaki take kallonta ta saki baki ganin yarda zainaba tayi kyau abunta. sai da ta taimaka mata ta saka kaya sannan suka dawo cikin falo... cikinta ne ya hau rurin yunwa ganin irin delicious din dake jere a gaban zainaba tana ci tana wani yatsina. Tunawa tayi da mangoron ta na dazu data ajiye akan ta'ga (window)lkcn shigowar su. Tadan sadda kai kasa,ranki shi dade zan iya fita yanzu yanzun nan na dawo? Zainaba ta kalleta da mamaki ina zakije? Juwairiya ta dan dafe cikinta sannan tace wata ajiya nayi  a waje zan dauko. Zainaba ta gyada kai zaki iya tafiya.. Da gudu ta fito neman mangoron ta,sai ko ta gansu a inda ta ajiye su din. cikin murna ta dauka ta shiga shansa kamar an aikota duk tayi kaca kaca da bakinta..     "Ashe ke kazama ce? Taji an fada daga gefen ta,da sauri ta kallo wajen,turaki ne ta gani da bawan sa a bayansa.. Ta dan sude hannunta sannan tayi kasa da kai,barka da zuwa ranka ya dade.. Cike da mamaki yake binta da kallo wato yanzu ta fara sanin dokokin gidan kenan? Yauwa kawai ya fada sannan ya shige wajen kanwar sa..    'Yana shiga zainaba ta mike cike da murna,yaya ashe zaka zo? Ya dan daure fuska miye na kirana da sassafen nan haka? Zainaba ta shagwabe fuska,dama fa zan tuna maka ne yau nakeso muje na hau do'ki nima..   Turaki ya lumfasa wato bazaki bar wannan zancen ba ko? Daure fuska tayi,amma ai har fulani na fadawa kuma ta amince naje na da'na dokin nima..   'Turaki ya girgiza kai sanin halin kafiya irin ta zainaba,juwairiya ce ta shigo kamar munafuka se goge bakinta takeyi..     Zainaba ta kalleta ki shirya zamuje hawan doki,juwairiya tace toh ranki ya dade. Tsaye suke a cikin wajen ajiyar dawakan sarki. Zainaba se zumudi takeyi,ta kalli bawan dake tsaye wajen tace,wancan dokin nakeso na hau,ta nuna wani farin doki dayaji kayan ado sosai.. Zubewa kasa bawan yayi yace,kiyi min rai ranki shi dade wannan dokin musamman YARIMA yasa aka shirya masa shi yau din nan..    Zainaba a take ta daure fuska ta kalli turaki dake gefenta,yaya kaji wai na ya jalal ne ta karashe mgnr kamar zatayi kuka.. Turaki yace,kiyi hkr ki zabi wani mana? Zainaba ta zunburo baki,zatayi mgn suka hango yarima yana tahowa cikin kasaitar sa bayi na biye dashi a baya.    Yana karasowa wajen duk suka tsaya kallonsa bayin dake wajen kuwa suka zube suna kwasar gaisuwa..     Bai ko kallon inda su turaki ke tsaye bayyi ba.. idanunsa ne suka sauka akan juwairiya dake tsaye a bayan zainaba bata da ko niyyar dukawa ta gaishe shi..   Ke! Ya fada yana yastine fuska.. Juwairiya ta dago suka hada ido,dauke kansa yayi.. "Na lura har yanzu baki san matsayin ki ba ko?   Sake dukar da kanta tayi tace'barka da fitowa ranka shi dade.. Yarima ya tabe baki sannan ya maida kallonsa kansu turaki.. Zainaba ta daure fuska Allah ya gani bata son girman kai da isa da ikon da ya jalal yake ji dashi.. Lafiya?...yarima ya fada yana musu kallon me kuke a nan?.. Turaki ya murmusa babu komai dama wucewa muka zo yi.. Yarima ya tabe baki ya karasa wajen do'kin sa wani bawa ya taimaka masa ya haye sama abunsa.... Zainaba kuwa ta banka wa turaki harara sannan ta juya a fusace tayi gaba,juwairiya tayi saurin bin bayanta .. "Fulani ce a zaune saman kilisar ta laure na mata tausar kafa suka shigo bayan anyi musu iso.. Zainaba ta fada jikin fulani tana kukan shagwaba,fulani wai me yasa a gidan nan ne akafi girmama su UMMA babba (gimbiya kilishi kenan) da su yaya YARIMA?akan mu? Naga ai mu ma baban mu daya dasu ko?tunda duk mai martaba ne ya haife mu..   Fulani ta sa hannu ta dago fuskarta'da ta fara ji'kewa da ruwan hawaye.. girgiza mata kai tayi,zainaba nasha fada miki ke jinin sarauta ce ba'a san'mu da zubar da hawaye haka ba kaskancine a garemu....    Zainaba ta goge fuskarta.. Toh umma na daina.. Juwairiya dake tsaye fulani ta kalla,sannan ta maida kallonta ga zainaba.. Ya baiwar taki? Zainaba tayi murmushi,tana kula dani sosai umma sannan ta iya aikinta tana da kokari .. Laure dake zaune ta saki lumfashi.. ********* 'Sai da daddare bayan uwar dakin tata ta samu barci sannan a gajiye ta fito daga sashen tana hamma..cike da gajiya dan zainaba akwai shegen son yawo.. Tafiya takeyi cikin duhu sai dan hasken farin wata dake haska mata hanyar kadan..         Maganganu ta fara jiyowa a tsorace ta shiga kalle kalle.. Can ta hango inuwar mutane biyu dake can wani lungu..   Da sauri ta karawa tafiyar tata sauri amma me sai taji kamar muryar TALATU wata sabowar baiwa da'a kawo shekaran jiya..    A hankali ta shiga labewa tana karasawa wajen duk da zuciyarta cike take da tsoro..      Ware ido tayi ta dafe kirjinta ganin wani katon gardi yana neman ya'ge rigar dake jikin talatu dai fisgiwa takeyi amma ina.... yafi karfinta..    Juwairiya ta rasa yadda zatayi gashi mutunen ya juya baya sai dai tufafin dake jikinsa ya nuna mata dan gidan masu dashi ne..    Har ta juya zata wuce sai kuma ta tuna mgnr mahaifiyarta inda take ce mata idan har taga mutum cikin bukatar taimako toh lallai ta taimaka masa ..     Sauke ajiyar zuciyar tayi kafin tayi saurin karasawa wajen wasu fadawa dake tsaron kofar babban zaure..    Dan Allah ku taimaka min wata baiwa na cikin neman taimakon ku, da sauri suka bi bayanta,sai dai suna kawowa wajen suka ja suka tsaya,juwairiya ta kalle su,daya daga cikinsu yace yarinya kiyi hakuri amma nan ba hurumin mu bane ba kema idan har kina son rayuwarki tayi tsawo acikin masarautar nan toh ki kama hanyar gaban ki..    Juwairiya na kallonsu suka fice,ta dafe kanta yau ta shiga uku yanzu ya zatayi kenan?   Dubara ce tazo mata,se data je saitin inda suke har mutumen yayi nasarar kwantar da talatu a kasa ta daga murya sosai tana fadin.. Talatu ! Talatu wai ina kika shigane haka!   Jin an ambaci sunan talatu kuma tabbas wajen da suke ne aka nufo,sai ya mike da saurin sa yabar wajen..     Da sauri juwairiya ta karasa wajen tana kallon talatu dake kuka kamar ranta zai fita..   Tasa hannu ta dago ta tana rarrashin ta.. Suna shiga rumfar bayi hansai da du'bu dake zaune gaban wuta sukayi kansu..   Lafiya juwairiya ina kika tsaya haka?juwairiya ta kalli talatu dake bayanta tana goge kwallar bakin ciki.. Umma dama... Ta sanar musu komai,nan matan bayi sukayi kan talatu cike da tausayawa suka shiga tambayar ta ko yayi sa'ar yi mata fyaden?ta girgiza musu kai nan aka shiga hamdala dan kuwa a wajen su bayi sun dade suna fuskantar  irin wannan kalubalen sosai,ayi musu fyade a banzatar dasu kamar kayan wanki.. Lamarin nan ba karamin tashin hankalin hansai yayi ba,ta jawo juwairiya har daki ta tsaya tana kare wa jikinta kallo daga sama har kasa.. yarinya yar shekara goma amma duk halittun girma sun fara bayyanar mata,bata so kadan a ba'ta rayuwar diyarta dan kuwa a yanzu ji takeyi juwairiya kyauta ce daga Allah a garesu..     Ki zauna ki jirani ga abincin ki can a cikin dan chinan can.. Hansai na fita juwairiya ta jawo dan chinan tana kare ma tuwon dawar dake gabanta kallo,ta tuna da irin abincin da zainaba ta gama ci dazun,dafaffiyar kaza ce,miyar naman shanu ne,dambu dayaji zogaye da kayan lambu,ga juice din inibi ne da aka matse shi aka saka mazarkwaila aciki..    Ta girgiza kanta da sauri dan ganin ta fara hadiyar yawu,oh haka rayuwa take"ta saka hannu ta fara kai wa towun ta loma.. Hansai dakin jakadiya ta shiga suna zaune da laure suna yar firar su.. Hansai ta zauna tana saka tagumi. Jakadiya tace lafiya hansa'u? Hansai ta kallesu,ni fa hankalina a tashe yake wlh,kunfi kowa sanin irin rayuwar da BAYI mata suke fuskanta a wannan masarautar, ina tsoron wani abu ya faru da juwairiya ganin yarda yanzu ko wane dare ake samun matsalar fyaden nan..   Laure tace toh yanzu ya zamuyi?dan wannan yarinyar juwairiya da gani ba karamar mace za'ayi ba.. Jakadiya tace nima wlh ina cikin wannan tunanin amma miye abunyi?   Hansai tace,ga shawara duk suka kalleta.. TABO (scar ) Tabo kuma?duk suka tambayeta cike da rashin fahimtar abunda take nufi..   Hansai ta murmusa TABO zamuyiwa fuskarta dan babu abinda maza suka fi kyamata kamar TABO ajikin mace..duk wani basarake ko mai mulki da dukiya babu abunda ke saka shi kyamatar mace kamar TABO ...   Laure ta kwashe da dariya kuma fa hakane,dan ko kadan idan bayin dake kula dasu ko SA'DAKA ce  suka samu wani dan Tabo ko Konewa a jikinsu toh fa  a ranar ake canza musu su.. Jakadiya tace wannan hakane,hansai ta mike tace kuzo muje.. Juwairiya na faman sude kwano suka shigo,ta gaida su tana fadin,goggo laure ina alkawarina yake? Laure tace  ke fa yar nan baki mantuwa.. Hansai ce ta zauna a kusa da ita tace,juwairiya kina jina..... Wattpad @afreey101 [9/18, 3:10 PM] Aysha Galadima: 🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕 (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 5 Wattpad @afreey101 ************************ "Bayani sosai sukayi mata,a tsorace tace, ummana kada ki damu zanyi kokarin rike mutumcina insha Allahu.. 'Jakadiya ta fita ta dawo da wani tire ta ajiye a gaban juwairiya, laure ta taso dan ita kam gwana ce sosai wajen harkar kwalliya nan duk masarautar ita tayi fice wajen yiwa matan sarki kwalliya ta fitar kunya..    Wasu abubuwa naga ta hada sannan ta riko kyakkyawar fuskar juwairiya ..   Cikin minti goma ta kammala sannan ta kalli hansai tace,ya kuka gani?   Bude baki sukayi duka dan kuwa duk wanda zai kalli fuskar juwairiya  sai yayi tunanin konewa ba'rin fuskarta tayi..     Murmushi sukayi cike da farin ciki,jakadiya ta miko mata wasu kaya ta amsa tana kallonsu,kayane manya manya dan se a saka irin ta biyu a ciki,yanzu wannan sune suturunki kinaji?,juwairiya ta gyada kai. ************** 'Da asuba kuwa sai ga fadawa uku sun shigo Rumfar bayi,du'bu ce tayi saurin tare su.. Lafiya? Fadane daya ne yace,daga gidan GALADIMA muke,yaronsa GARBATI yaga wata baiwa acikin rumfar nan jiya shine ya turo mu mu tafi da ita..     Gaba daya hankalinsu du'bu ya tashi dan sun fahimci garbati ya siya talatune a matsayin SA'DAKAr sa (concubine).. Dakin da talatu ke ciki du'bu ta shiga ta fito da ita tana kuka sosai,fadawa suka fosgota suka gaba da ita.. 'Juwairiya dake rakube duk tana kula da abunda yake faruwa, 'hansai ce ta kamota ta maida ita cikin daki, 'sannan ta sake yi mata nasiha akan kada ta sake a san tabon fuskarta na karyane inba haka ba itama haka za'a zo a tafi da ita kamar yarda aka dauke talatu.. gari  na yin haske haka laure ta shigo ta sake yi mata makeup din tabon ta.    Tana shiga sashen zainaba ta tarar da ita tana ta sharar baccinta. Ruwan wankanta ta shiga ta hado mata sannan ta zauna a gefe ta tsunduma a cikin tunani..   Zainaba ce ta mike taci karo da fuskar juwairiya, da sauri ta dauke kanta tace,ke meya samu fuskarki haka?konewa kikayi? Juwairiya ta mike da sauri tace Allah ya huci zuciyar ki ranki shi dade jiya ne ruwan zafi ya kifar min a fuskata. Zainaba tayi fuskar tausayi Allahu akbar yanzu haka fuskar ki zata zauna kenan?ta yamutsa fuska Juwairiya tayi murmushi kawai sannan ta sanar mata data hada mata ruwan wankanta.. 'Da rana zainaba tace da ita suje gidan waziri.. Fafade daya suka dauka dan yayi musu rakiya.. Duk inda suka bi sai mutane su shiga nuna juwairiya dake bayan zainaba' A haka har suka shiga gidan waziri..     Hajara matarsa ce a zaune tsakar gidan sai diyarta KHADIJA dake gefe tana wasan diyar ka'ra..     'Zainaba na shigowa khadija ta mike da sauri tazo ta rungume ta..   Idonta ne yakai juwairiya dake can baya.. Taja baya kadan tana yastine fuska.. Wannan fa?ta nuna juwairiya.. Zainaba tayi murmushi sabowar baiwata ce.. Khadija tace,au ni tsoro ma ta bani wlh.. Zainaba tace konewa tayi fa,sannan ta karasa wajen hajara ta gaishe ta.     Suna zaune suna wasan su juwairiya na rakube a gefe tayi shiru abunta. Khadija tayi fari da ido tace,wai ina ya jalal ne?kinsan tun ranar dana zo wajen ki rannan ban sake ganinsa ba.. Zainaba ta tabe baki ai ke ya da'ma ni muna gida daya ma se mufi sati bamu hadu dashi ba..   Sunyi fira sai da yamma sannan khadija ta shirya suka taho tare wai ita a dole sai taga yarima yau.. "Suna shiga cikin masarautar can a filin wasa doki ta kyallo shi a tsaye tare da wasu samari sa'annin shi..    Khadija ta kalli zainaba tana washe baki,lah kin ga ma yayan can ashe.. Kafin zainaba ta amsa mata tuni ta ka'ra gaba cikin saurinta,zainaba ta girgiza kai lallai bata san wane irin so khadija kewa ya jalal ba duk da wulakancin da yakeyi mata ita bata ko gani.     'Zainaba na cikin wannan tunanin ne khadija ta dawo da saurinta. Zainaba tace,ah ah ya na ga kin fasa zuwan kuma? Khadija tadan kwabe fuska ai bazan iya zuwa ni kadai ba kada ya gane dan shi naje wajen.. Ta riko hannun zainaba dan Allah muje ki rakani kinga se nace ki nazo yiwa rakiya muka ratsa ta wajen..   Zainaba tace,wa!ni?ah ah wlh ban kije ke kadai abunki.. Juwairiya kuwa dake baya tana jinsu ne kawai,khadija ta hau magiya,dole tasa zainaba amincewa,ta juya tace wa juwairiya mu karasa can juwairiya, kai kawai ta gyada sukayi gaba... ************* "Yarima gaskiya ni kam kayi min wayo gsky,duk yaushe ka kware a kilisa(wasan doki) haka ne? Yarima ya murmusa cike da girman kai..zayyi mgn su zainaba suka iso wajen.. Khadija ta yi saurin gaishe shi ko amsawa bayyi ba ya wani dauke kai. Zainaba ta tabe baki dama tasan haka zai faru ai. Khadija tace,yaya kwana biyu? Yarima ya juyo da shirin dizga ta idanunsa suka kai kan fuskar juwairiya... Ai da sauri ya dauke kai yana fadin.. Menene wancan abun? Wayace kuzo min da wannan abun? Da mamaki duk suke kallonshi.. Ya kalli bawan dake gefensa,fitar min da wancan abun!(kice da kyamata) Ya nuna juwairiya...   Se sannan suka fahimta me yake nufi.. Zainaba ta turo baki,yaya baiwar tawa ce za'a fitar maka?    Ya balla mata harara,bakya ganin fuskarta ne?(in a irritating tune) Khadija ta fisgo juwairiya ta shiga janta daga wajen..    Se da suka sha wata kwana sannan ta jefar da ita kasa tana fadin. Kada ki kuskura ki kara tsayawa a gaban yaya  kinji na fada miki..ta tayi gaba.. Juwairiya taji wani abu ya tsaya mata a makoshi,tsanar yarima ta dasu a zuciyarta, itace wancan abun? Kuka ta shiga yi tana tunanin wacce irin rayuwa ce haka suke fuskanta dan kawai su bayi ne se ake kyamatarsu ana zaluntarsu...   Ta mike hade da kakkabe jikinta sannan ta rakube a gefe tana jiran uwar gidan ta zainaba.... ***********    A gajiye ta dawo rumfar bayi, fuskar nan babu walwala.. Tana shiga ta hango yan matan bayi nata wasan fado'wa wasu na gefe na langa..   Hansai ta karaso wajenta tana fadin,sannu ya'ta se yanzu? Ta gyada kai kafin ta karasa daki a sanyeye. Har taci abinci ta kwanta,taga tunanin wulakancin da yarima yayi mata na neman yi mata yawa a cikin kwakwalwa hakan yasa ta fita waje itama ta shiga wasannin da akeyi abunta... Wattpad @afreey101 [9/18, 3:10 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction ) NA Afrah bhai Page 6 Wattpad @afreey101 ******************* **bayan shudewar shekaru bakwai** 'Gaba daya masarautar a war'gitse take. A sanadiyyar bakin dauren auren YARIMA JALAL da diyar sarkin adamawa wato gimbiya SURAYYA da akeyi a ranar ta yau, wato shidda ga watan sa'tumba.      'Mutane ne tan'kam cikin masarautar ko ina ka kai idonka bayi ne keta hidima ana ta shirye shiryen amsar dan'gin amarya dake tafe daga kasar adamawa...    "Can na hango yan wasan doki suna ta kokarin shirya KILISA(wasan doki),A gefe kuwa yan busan algaita ne ke tayi masu kanguna ma nata bugawa take masarautar ta dau sautin ki'da me kayatarwa,yan wasan wuka da yan farauta ma nata nuna tasu bajintar.. ************* 'Tun asubahi duk baiwar dake cikin Rumfar bayi bata zauna ba,rabinsu duk suna cikin madafa ne ana ta hada'hadar dahuwar abinci na gani na fada. dan shanaye sun fi dari da mai martaba yasa aka yanka su banda kuma kaji da wasu kananan dabbobin. "Hansai ce na hango duk hidima tayi mata yawa. can sai ga wasu kuyangi sun shigo,wajenta naga sun nufa cikin saurinsu daya daga cikinsu tace,hansai wai ina JUWAIRIYA ne gimbiya zainaba na can nata faman nemanta.. tace idan mun ganta mu sanar mata da cewa su hadu da ita a can sashen gimbiya kilishi... 'Hansai ta girgiza kai... lallai wannan yarinyar wato bata tashi ba kenan duk dukan da nayi mata da asubahin nan.. Laure ta kwashe da dariya,ai ni kam gara da Allah yasa zainaba ce uwar dakin juwairiya da ina fada miki tuni yarinyar nan zata jawo mana musiba sbd shegen son jikinta..   Jakadiya tace,haba kun manta aikin data sha ne jiya daddare duk fa itace ta ba're wancan danyen waken. jakadiya ta sake kallon laure dake faman wanke wanke tace,ke laure tashi kije ki sanar mata sakon uwar dakin tata .. 'Lkcn da laure ta shiga dakin juwairiya ta hango kwance akan taburmar ka'ba tayi dai'dai tana ta kwasar barcinta hankali kwance dan shaf ta manta da wani daurin aure da akeyi a cikin masarautar.. Laure ta shiga tashin ta..juwairiya maza ki tashi...! A firgice ta farka tana gogar idanunta dake cike da barci.. Ni kuwa afrah na saki baki ina kallon kyakkyawar fuskarta,laure tace,se ki tashi dan yanzun nan uwar dakin ki tayi aiko a sanar miki daki same ta a sashen gimbiya kilishi... Ai tun kafin laure ta rufe baki juwairiya ta mike da sauri ta zari gyelen ta tayi waje da gudu duk kiran da laure keyi mata bai sa ta tsaya ba ..... Gudu takeyi sosai dan shaf ta manta da maganar da sukayi jiya ita da zainaba.. Yau ta shiga uku! Me ya same ni haka ne? Wane irin bacci ne nayi haka!oh Allah! 'Abun mamaki tana zuwa sashen gimbiya kilishi ta tarar da sashen wayam babu kowa a wajen duk kuwa da  cikar da masarautar tayi a yau.. Ta karasa ciki tana kalle'kalle ko zata ga zainaba tunda tace kayan biki zasu zo amsa a wajen gimbiya kilishin...     'tana faman leke'leke kawai taJi kamar wani ana kokarin shigowa.. Tsoro ne ya kama ta sosai dan kuwa tasan idan har aka kamata a ciki ba tare da zainaba ba kuma babu kowa acikin sashen toh kashin ta ya bushe...    Bayan wani lalube ta boye jikinta na tsananin rawa..se addu'a takeyi Allah yasa ba gimbiya kilishi bace ta shigo ita tsoron matar takeyi..    bata ankara ba sai Jin takon mutum tayi kawai.. Bugun zuciyarta ne ya linku... Ta dafe kirjinta...ganin inuwar mutum a gabanta yasa ta runtse idonta gam dan ta sadakar da an gama kama ta....   Shi kuwa yarima jalal mamaki ne yakeyi ganin inuwar mutum a cikin labule dan kuwa ummansa ta shaida masa data kori kowa daga sashen na ta dan kawai yaje yayi shirin sa tunda nashi sashen cike yake da ya'yan sarakuna abokansa da sukazo dan daurin aure...      Bai bata lkc ba ya yaye labulen cikin zafin nama.... Idanuwansa ne sukaci karo da wata kyakkyawar fuska mai daukar hankali...   Gabansa ne yaji ya fadi..haka kuma yaji gaba daya tunaninsa ya tsaya tsak..jinin dake jikinsa ma ya gaskare waje daya haka gangar jikinsa.. Juwairiya kuwa ganin an yaye labulen sai ta bude idanuwanta da suka fara cikowa da kwalla.. Ganin yarima jalal a gabanta sai ta dafe kirjinta..... Abunda ya bata mamaki shine ganin bashi da niyyar hukunta ta sai ma wani kallonta da yakeyi.. Hakan ne Yasa tayi saurin zubewa a kasa dan ta sadakar yau ta'ta ta ka're.... Yarima kuwa baisan lkcn da yabi ta kasan ba shima,yana mata wani irin kallo data kasa gane na menene shi.. Can tabi kwayar idonsa ta fahimci fuskar ta yake yiwa wannan kallon.. Ai da sauri ta ware idonta tana saka hannayenta ta shafi fuskar ta.. Taji ta fayau,yau na shiga ukuna! A Haka na fito? Banyi tabon ba? Ta mike ba saurinta jiki na rawa ta gudu tayi waje hankalinta a mutukar tashe....    Shi kuwa yarima sai dai kawai yaga bata wajen dan ya lula cikin tasa duniyar..... Da sauri ya mike yabi bayanta,amma ina....bai ga ko keyarta ba a wajen...    Ya dafe kirjinsa dake bugawa.. Me ya faru dashi yanzun nan? Wacece wannan aljanar yarinyar? Ya lumshe ido yana tuna kyakkyawar fuskarta,kafin ya shige kur'yar dakin mahaifiyar sa yana tube kayansa yana murmushin da shi kansa bai san yanayin shi ba.. Juwairiya kam direct rumfar bayi ta koma cikin saurinta,Allah ya taimaketa duk babu jama'a a wajen suna can madafa, ta shige daki ta zube a kasa tana jin kirjinta nata bugawa.. Idan yarima ya gane ta fa?idan ya gano tabon karya takeyi fa? Ta dafe kanta sannan cikin kankanin lkc ta maida tabon fuskarta sannan ta sake ficewa.. **************** "Tana shiga sashen zainaba ta zube a kasa tana neman afuwa.. Zainaba data zama cikakkiyar budurwa mai kyau da aji ta saki murmushi, ina tunanin kin manta da yau din bikin ya jalal ne ko.. Juwairiya tayi kasa da kai.. na sa ni ranki shi dade a gafarce ni... Zainaba ta murmusa babu laifi,tashi muje sashen fulani... 'Koda suka zo shiga lkcn shima Turaki yake karasowa saurayi ne me cike da kamala sam yanayinsa ba kamar na yarima bane dan kuwa kullum shi kam fuskarsa dauke take da fara'a ..       Yana ganinsu ya saki murmushi yace, gimbiya da kawarta,dan haka yake kiransu. A tare sukayi murmushi kafin juwairiya tayi kasa da kanta ta gaisar dashi. Ya amsa a sake sannan suka shige ciki a tare.. "Karfe biyar na yamma dangin amarya suka iso daga adamawa.. Gimbiya kilishi tare da mai martaba da fulani ne suka taro su da tarin bayi da yan ki'da... "Bayan awa daya da aka basu dan hutawa da cin abinci.. Sai aka fito kuma babban fili a inda aka shirya musu babbar liyafa...        Zainaba ta kalli khadija dake ta tabe baki tana yatsina fuska. 'Ke wai har yaushe zakiyi yawo ne,da ajinki ki zauna ana ta miki rashin mutumci.. Khadija ta shagwabe fuska,ai kin san dai ya jalal mijin mace hudu ne ko sannan kowa ma ai ya sani auren hadi ne akayi masa...      Juwairiya ta girgiza kai dan kuwa har ta soma gajiya da surutan khadija kullum bata da abun mgn se ta yarima,ta tabe baki ita kam ko a kafa aka daura mata shi kwancewa zatayi ta yar ta tsani girman kansa da shegen gadara mtsw...... A tare suka mike bayan an aiko musu da sakon cewa za'a fara liyafar. Khadija ta banka wa juwairiya harara. Ke ina zaki? 'A hakan zamu tafi dake  ki sake tsorata ya jalal din? Zainaba ta daure fuska,kinga khadija bana son shishshigi,abunda ya faru da dadewa shikenan kin din ga maimaita shi..    Khadija tace haba zainaba,kalli fa shigar ta ki gani ga fuska kuma a kone.. Zainaba tabi juwairiya da kallo,ita bata damu da tabon dake fuskarta ba amma kayan ne ko irin su jakadiya ma da uwar soro da du'bu ai ba saka irin su sukeyi ba..     Zainaba ta koma daki ta fito da wata jar atamfa... Ta mikawa juwairiya amsa ki canza zuwa wadan nan.. Juwairiya ta ware ido ni?ta nuna kanta.. Khadija tace,da' wa? idan ba ke ba uhm? Juwairiya ta amsa a sanyaye sannan ta shiga ta sanyo kayan.. Tana fitowa sukabi ta da kallo... Duk da dogowar riga ce a jikinta amma sai da shape dinta ya bayyana.. Ita kanta sai datayi mamakin irin dirin ta tunda dai bata taba saka kaya irin wannan ba... ko kadan bataso ta saka kayan ba amma babu yarda zatayi tunda baza ta iya musawa hakan ba.    Khadija ta tabe baki babu laifi... (nan kuwa kishi takeyi.) Zainaba kanta sai data tsorata da ganin canzawar da juwairiya tayi amma ta da'ke tace muje... 'Wuri yayi wuri mutane kamar ba gobe.. Su khadija suka zauna a inda aka tanadar domin su.. Juwairiya kuwa ta koma layin yan uwanta bayi sai kalle kalle takeyi kada su ummanta su ganta da wannan shigar...    Wattpad @afreey101 [9/18, 3:13 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction ) Na Afrah bhai Page 7 Wattpad @afreey101 ****************************** "Ta'ro yayi taro anci an'sha anyi kuma wasanni sosai.. ' sai wuraren karfe goma na dare sannan aka tashi,an kai amarya sashen ta dayaji gyara cikin tsari na gargajiya.      'Surayya an sha wanka cikin turare ga turaren jiki kuyangin nayi mata kamshi kam ba'a mgn.     Wata riga ta saka marar nauyi sannan aka daura mata alkyabba mai kyan gaske..     Tana nan a zaune bayinta na ta kara gyara cikin dakin sai ji sukayi ana sanar da shigowar yarima. Ta kallesu fuskar nan ba a daure tace,ku fita duka! Jiki na rawa duk suka fice da saurin su..   'Da sauri Ta sake gyara fuskarta tana kokarin rufe fuskarta taji shigowar ango.. 'Yarima cikin kasaita ya karasa gaban gadon yana bin'ta da kallo... ya rasa dalilin daya sa mahaifiyar sa ta matsa masa akan ya amince da auren wannan yarinyar.. 'shi dai yasan ko'da ya fara ganinta lkcn da mai martaba ya matsa masa akan yaje zance dan su fahimci junansu kwata kwata batayi masa ba.. Tunawa da wannan kyakkyawar fuskar da ya gani dazu yayi,wacece ita?a ina kuma zai sake ganin ta?   'Surayya dake lullube taji wani irin haushi ya turnike ta, miye haka zai wani shigo ya zauna shiru kamar ya manta da anyi ajiyar ta..mtsw....     Ni kike wa tsaki...? Taji an fada da murya me cike da gadara da kasaita.. Ware ido tayi dan kuwa duk a tunaninta a cikin zuciyarta ne tayi tsakin..    Shiru tayi masa tana runtse idonta.. Yarima ya mike tsaye..yace... 'Naga alamar tun ba'a kai ko ina ba kin fara raina ni ko... 'Surayya tayi shiru tana jin haushin kanta data bari har tsakin ta ya fito fili.. Yarima yaja gundun tsaki,sannan yace bana mgn kana shareni kin gane?.. Surayya tace a sanyeye, kayi hakuri.. Ya sake tabe baki, bude fuskarki... Ta saka hannu a nutse ta yaye lullubinta...    Yarima dake tsaye agabanta ya kura wa fuskarta ido.. Ko kadan baiji kwatankwacin abunda yaji dazu ba..meyasa? Yadan ja tsaki.. Ya sunanki ma? Surayya taji wani irin abu ya tukare mata wuya,mai?miye sunanta?dama bai san sunanta ba kenan?amma ai koda sukaje gidansu ta tabbata yaji sunanta.. 'Tadan daurefuska, baka san sunana ba ashe.. Yarima ya shafa sa'jen dake kwance a fuskarsa..   Tambaya kike?ko mamaki kikeyi? Surayya ta dan murmusa idan nace duka biyun banyi laifi ba..?   Yarima daya so gundura da mgnr yace.. Bana son ana maida min tamabaya ta da wata tamabayar.. Surayya tadan tabe baki,lallai wannan mutumin akwai son mulki.. Sunana SURAYYA...ta fada tana kafe shi da ido.. Yadan gyada kai,toh surayya dan matsa min na kwanta nima yayi mgnr yana karasawa gefen gadon.. 'Surayya haushi ne ya kama ta,wane irin daren farkone haka ta matsa mishi? bashi ma da niyyar yin komai ma kenan?ita dai ba haka taji ana fadin daren farkon ba... tana kallonshi ya rage kayan dake jikinsa yazo ya tsaya yana mata nuni da ido irin ke nake jira dinnan.. 'Surayya taja gefe da sauri yarima ya hau ya kwanta yana runtse idonsa.. Duniyar tunani ya tafi,meyasa yake jin hakane?kodan baya son yarinyar ne?yadan bude idonsa,yasan cewa gobe dole ne gimbiya kilishi ta turo a duba mata ko wani abu ya shiga tsakanin sa da surayya tunda haka al'adar take,ya sake runtse ido,baya jin ze iya kwanciya da yarinyar can a yau, tunani kawai yakeyi har  barci me dadi ya dauke sa cike da mafarkin wannan kyakkyawar  fuskar daya gani..... . ******** 'A wajen juwairiya kuwa,bayan taro ya tashi suka taho tare da zainaba,suna tafiya juwairiya taji kamar takon wani a bayansu,ta kalli zainaba a tsorace itama kanta zainaba haka jikinta ya bata,da sauri juwairiya ta jawo zainaba suka boye bayan wata bishiya,zainaba tayi kasa da murya..   Waye yake bin mu? Juwairiya ta girgiza kai nima ban sani ba ranki ya dade.. Zainaba ta matse hannun juwairiya cikin nata tace.. Yanzu ya zamuyi ? mun shiga uku... Juwairiya ta jawo wani itace ta rike tana jira wanda ke bin nasu ya karaso wajen ta buge shi...        Tafiya yake yi yana waige waige yan matan daya biyo daga wajen taro yake nema ina suka shiga ne?      Baiyi aune ba sai dai yaji saukar itace a bayansa...   Matse bakinsa yayi ya juyo yana musu kallon mamaki.. Gaba daya jikinsu rawa yakeyi.. Zainaba ce tayi saurin cewa.. Waye kai?meyasa kake bin mu? Mustapha ya daga hannunsa irin surrender dinnan yace.. Kuyi hakuri yan mata dama zuciyata ce kuka taho da ita shine nake binku domin an amso ta.. Kallon juna sukayi,juwairiya ta shiga gaban zainaba wai ita nan tana kare tane.. Tace,malam kasan kuwa dawa kake mgn,gimbiya zainaba ce fa DIYAR SARKI kuma uwar dakin juwairiya... Mustapha yace,madalla yanzu zan dan samu nutsuwa tunda na ji sunan masoyiyar tawa ZAINABA....yaja sunan yana lumshe idonsa.. Da kallo suka bishi..balle zainaba dake ta lekowa tana karewa fuskar shi kallo.. Kyakkyawa ne ,chocolate color kuma yana da tsayi sosai se de siririne..     Juwairiya zatayi mgn zainaba ta dafa ta.. Mustapha yace,gimbiyata Allah yasa wani bai min shigar sauri ba ko,ya fada hade da karkace kansa.. Zainaba bata san lkcn da murmushi ya subuce mata ba sannan ta girgiza masa kai cike da kunya ta juya da gudu tayi gaba.. Juwairiya cike da mamaki tabi bayanta.. ************* 'Da safe juwairiya na gani zaune laure na mata kwan'tar(tsifar)kai.. Laure tace,kedai yarinyar nan anyi kazama wlh kitso se ki barshi har kusan wata daya,gashi Allah ya baki gashi amma kwata kwata bakya kula dashi.. wai ni yaushe rabon ma da ki wanke shi ne? Laure jin ita kadai keta zancenta yasa tadan kai mata duka.. Bakya jina ko? Juwairiya ta kai hannu wajen da laure ta duke ta,ta turo baki haba goggo laure ina jinki fa wlh. Laure tace karya kike,wai tunanin menene kikeyi ne haka? Juwairiya tace babu komai,sai kuma ta mike da sauri tana kwace kanta daga hannun laure.. Goggo laure ina zuwa,ta shiga daki tayi shirin ta ta fito da gudu tayi hanyar sashen zainaba... Tana shiga ta tarar da ita a tsaye,da sauri ta karasa wajenta lafiya ranki ya dade?..   Zainaba ta sauke ajiyar zuciya yauwa dama ke nake ta jira,zauna..kiji.... Juwairiya ta zauna tana saurarenta. Zainaba tace,dazu wannan saurayin ya turo min da wasika.. Juwairiya ta saki murmushi me yace ranki shi dade nasan dai da gani sonki yakeyi..ko? Zainaba ta rufe fuska wai haka yace.. Juwairiya tayi dariya kasa'kasa dan ta lura uwar dakin tata ma ta fara zurmawa dayawa.. Zainaba ta gyara zamanta sannan ta buga tagumi,amma kinsan me yace? Juwairiya ta gyara zaman itama ah ah se ranki ya dade ta fada min. Zainaba ta turo baki.. Wai idan na amince masa toh naje da Fure (flower) na same sa a zaure na biyu yana jirana kafin su tafi..    Juwairiya tayi murmushi, kada ki damu ranki ya dade akwai wani fure me kyau dasu yasira ke cirowa zan samo miki shi.. Zainaba tayi murmushi, yauwa juwairiya yi maza kije toh.. Juwairiya na murmushi ta mike ta fita.. "Sashen hamza ta nufa dan anan ne yasira ke aiki,ta jawo ta waje ta tambayeta ina ne take ciro furen? Yasira tadan waro ido,juwairiya yaushe rabon da ki ganni da wannan furen?yanzu fa kinsan an tare sashen.. Juwairiya tace,wai dama sashen waye? Yasira tace,sabon sashen matar yarima jalal ne.. Juwairiya hakanan taji gabanta ya fadi,ta juya kawai tayi gaba.. Tsaye tayi a kofar shiga sashen,tunani takeyi ko ta shiga ko kada ta shiga,bata son ko kadan ta hadu da wannan yariman...    Leke tayi karaf ta hango itaciyar furen kuma akwai dayawa a jiki...   Taja lumfashi sannan kai tsaye tayi wajen tana waiwayen bayanta..    ************* Yarima jalal ne na gani a tsaye gaban surayya dake ta kwasar baccinta a takure. Ya kura mata ido ko tunanin me yakeyi oho.. Haske ya gani yana ratsuwa dakin daga window yana taba fuskarta..   Juyawa yayi yazo gaban window din yana kokarin rufe labulen ya hango ta..   Dauke kai yayi da sauri dan kuwa konannen sashen fuskarta yaci karo dashi ,zuciyarshi yaji ta baci,ya tsani yarinyar can baya son ganin irritating face dinta ko kadan,duk da ze iya kirga ganin ta da yayi a masarautar..    Ya juya kawai ya fito a fusace dan bai ga me ya kawo ta sashen ba..    Yana fitowa bayin dake tsaye bakin kofar suka shiga gaisar dashi.. Bai amsa musu ba kawai yayi waje abunsa.. ****** Juwairiya ta ciro furen daya mai kyau sosai.. takai hancinta tana shakar kamshinsa me sanyi.. Ta tabbata dole ne zainaba ta yaba mata idan taga turen.. Har ta juya zata fice taji ance..     Me ya kawo ki nan! Da sauri ta tsaya tsak.. Cikin kasaita ya karasa gaban ta yana yatsine fuska.. Juwairiya ta zube kasa tana sunne kanta dan tasan babu abunda ya tsana kamar ganin fuskarta.. Dama...dama..uhm..na... Yarima ya daka mata tsawa.. Ki bude baki kiyi min mgn! Bana hane ki da nuna wannan fuskar taki a inda kika san ina nan ba? Juwairiya tace,afuwa zanka shi dade uwar dakina zainaba ce ta umurceni da samo mata wannan furen ta nuna masa furen dake hannunta..    Yarima ya tabe baki,ki ba'ce min daga gani... yana gama fadar haka ya juya yai tafiyar shi.. Juwairiya tabi bayansa da harara sannan ta mike ta kakkabe jikinta tayi gaba....... *********************** Pls share Comments And Vote [9/18, 3:13 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) NA Afrah bhai Page 8 Wattpad @Afreey101 ************************* 'Tana shiga sashen zainaba ta tarar da ita a tsaye sai safa da marwa takeyi. Juwairiya ta mi'ka mata furen dake hannunta, ta amsa tana sakin murmushi me kayatarwa,gaskiya furen nan yayi min kyau sosai,se de akwai wata matsalar kuma juwairiya.. ta karashe mgnr kamar zatayi kuka..      Juwairiya tace,matsalar me kuma ranki ya dade ba dai har sun tafi din ba? 'Zainaba ta girgiza kai,dazun ne fulani ta aiko min da sakon cewa kada na fita ko ina  zata aiko min da wata mai magani ta dubani akan yawan ciwon cikin nan da nake fama  dashi ,kin kuma san halin fulani, har fa wani bawa ta ajiye a kofata wai dan kada na gudu sbd bana son magani..yanzu ya za'ayi na fita kenan?          'Juwairiya tadanyi tunani kadan sannan tace inda ranki ya dade ba zata damu ba ina da shawara.. Zainaba tace da gaske? Juwairiya ta gyada kai .. Zainaba tace fadi muji.. Juwairiya tace ko naje na sanar dashi bazaki iya fitowa se shi din yazo nan.. Zainaba ta ware ido... Ah ah bana so yazo nan juwairiya..ta karashe mgnr a shagwabe tana kallon juwairiyar.. Can kuma tace,yauwa! Tasa hannu taja juwairiya zuwa dakinta... 'Cire.....ta fada kai tsaye.. Ciki da mamaki juwairiya ke kallonta..me zan cire ranki shi dade ? Zainaba ta nuna kayan dake jikin juwairiya..cire kayanki ki bani.. A tsorace juwairiya tace,kiyi hakuri ranki ya dade amma..... Zainaba tayi dariya,ba ina nufin ki tu'be min ba dan naga jikin ki ba.. Ah ah ina so ne muyi canjen kayane kawai kin ga babu wanda zai san ni ce na fita bake ba ko?     Juwairiya ta gyada kai,wato wayo zakiyi wa fulani ko?amma idan aka kama mu fa?ni gsky tsoro nakeji.. Zainaba ta murmusa kada ki damu bazan jima ba zan dawo,kedai kawai cire kayan ki bani.. Juwairiya a sanyaye ta cire kayanta,zainaba ma ta cire nata ta bata.. Juwairiya tabi kayan da kallo,ina zata iya saka wadan nan kayan? Ta girgiza kanta,ranki shi dade bani da matsayin da san saka wadan nan kayan.. Zainaba ta harare ta,amsa! Kuma umurni nake baki daki saka su yanzun nan! Juwairiya ta amsa a tsorace.. Tana kallon zainaba bata nuna wani kyama ba ta saka nata kayan tana dariya tace,lallai ke kam wannan kayan naki ashe walawa kike yi sosai..(ta fada tana jujjuyawa cikin katoton rigar juwairiya ) Juwairiya dai da kallo kawai take bin ta,a sanyeye ta saka kayan itama atamfa ce riga da zani sai wata alkyabba ja da ruwan madara,ita kanta tayi mamakin yarda kayan suka amshe ta.... Zainaba tabi ta da kallo,lallai juwairiya Allah yayi mata baiwa dayawa,se de kawai yanayin data tsinci rayuwarta ne...      Zainaba tace,toh ni na tafi,ta dauki furen ta tana sake fadin,babu wanda zai gane ni ce,ta saki murmushi tayi gaba.. juwairiya ta zauna a takure tana tunanin idan wani ya shigo fa yanzu tasan tabbas kashin seya bushe..     Motsin dataji ne a waje ana sanar da shigowar turaki yasa ta saurin komawa shinfidar zainaba ta kwanta hade da juya bayanta ta rufe rabin fuskarta..    A tsanake ya shigo falon cike da takonsa yana mamakin rashin ganin juwairiya da bayyi ba..     Yan matan fulani naji mun kusa hutawa da jinyar ciki ko?dazu fulani ke sanar min an kawo me magani daga cikin katsina..      Juwairiya tayi wiki wiki da ido,bata so ko kwakwaran motsi tayi turaki ya gano ita ce.. Turaki ya zauna yana mamakin shirun da zainaba tayi masa.. To wai ko barci take ne ? Yana wannan tunanin ya mike har ya kai bakin kofa yace, ko ina kawarta ta tayi yau oho..    Juwairiya najin fitar sa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike zaune,se a lkcn ta nuna da inda take zaune(wato akan kilisar zainaba ),ta mike da sauri tana sake kallon shigarta,tabbas bata taba saka kaya irin wannan ba,ta dan murmusa zataso ummanta dasu jakadiya su ganta a cikin irin wannan shigar.. Wani tunani ne yazo mata.. Da sauri naga ta shige dakin zainaba ta dauko mirror tana kallon kanta..     Ita kanta wani lkcn idan taga fuskar ta a haka tsoro take bata.. Hannu tasa a hankali ta fara goge tabon har kyakkyawar fuskarta ta bayyana..     Ta kurawa fuskarta ido.. Motsi taji daga falon.. Da sauri ta mike jiki na ba'ri ta fito zuwa falon tana leke... Sai ji tayi bawan dake waje yana daukar izinin zainaba  dan zagawa bayan gida..   TOh! Kawai ta fada a da'ke sannan tace,wai ina zainaba ta tsaya ne?(tayi mgnr kamar ta fashe da kuka) Gani nayi Tadan jawo hular alkyabbar ta rufe rabin fuskarta tana fadin,dole ne naje na dawo da ita tun kafin asirin mu ya tonu,ba tare da wani tunani ba tayi waje da saurinta.. ************** 'Surayya na tashi daga barci taga wayam babu yarima a dakin. tsaki taja cike da takaici,wai yau itace gimbiya surayya ake wulakantawa har haka,wulakancin ma wai daga namiji.. Ta juyar da kwayar idonta tana tuna irin  samarin dake tururuwa a wajen neman aurenta,amma gashi sbd wata tsohuwar abokantaka dake tsakanin mahaifinta da mahaifin yarima jalal an kawo ta nan se wulakanta ta akeyi..       Ta kalli shinfidar gadonsu cike da takaici,ta tabbata duk bayin da zasu shigo da kuma yan uwanta da zasu zo mata bankwana toh gulma ce zata kawo su dan  ganin  yarda daren farkon ta da yarima ya kasance... Abu daya data tsana a rayuwarta shine a ga kamar bata isa ba (she hates pple downgrading ha),bata son ko kadan a raina ta,sbd ta mallaki komai a rayuwarta, tana da kyau,gata diyar sarki,yanzu kuma matar yarima me jiran kujerar mulki... Wani tunani ne yazo mata.. Ai da sauri Ta mike da ta tube duka kayan dake jikinta tas.. Sannan tasa hannu ta hargitsa shinfidar gadon,ta dauko yar karamar wuka dake cikin tiren fruits ta hawo kan gadon tasa wukar a finger dinta tana runtse ido ta tsakawa kanta wukar kadan'sannan ta samu jinin ta dake ta di'qa ta shiga shafawa a wani bangaren gadon....        Yamutsa gashin kanta tayi dayasha gyara sannan ta ja bargo ta rufe kanta tana kuka kasa kasa..(yarima yayi kadan ya jawo mata raini,dolene ta nuna masa wacece SURAYYA)    'Bayi ne tare da yakumbon ta suka shigo dakin da jakadiya a bayansu..    Ganin halin da take ciki yasa duk suka saki murmushin murya suna gyada kai cike da gamsuwa.. Yakumbo ta karasa wajenta tana dago da ita zuwa jikinta.. Sannu surayya,sannu UWAR GIDAN YARIMA JALALLUDEEN... ai duk mace idan tayi aure dolene ta fuskanci wannan  daren farin cikin,amma daurewa zakiyi kinji? Surayya dake sunne kai ta gyada kai,yakumbo ta ciro zanin shinfidar  ta mikawa jakadiya dake ta gyada kai cike da farin ciki,lallai yarima an  girma...      Jakadiya na amsar zanin da saurinta ta karasa sashen gimbiya  kilishi dan aiwatar da umurninta..     Uwar soro na ganin jakadiya ta karaso sai washe baki takeyi.. yasa tayi sauri wajen fadin isowarta cikin kirarinta masu tsada...     'Gimbiya kilishi na a kishin'gi'de jakadiya ta shigo tana bayyana mata zanin dake hannunta.. Wani irin murmushi ta saki.. Jakadiya tace, gimbiya uwar gidan mai martaba, ina miki albishir da a daren jiya yarima ya zama cikakken namiji....    Kilishi ta gyada kai cike da gamsuwa tace,wannan albishir naki jakadiya ba karamin farin ciki ya saka ni ba,dan haka ina so ki samu shamaki a baki azurfa goma a matsayin Tu'kwicin ki.......    Gu'da jakadiya ta saki hansai dake zaune kusa da kilishi na tayata sai murna sukeyi..ni kuwa afrah nace 'Oh" *********** "Mustapha ya dade tsaye a babban zaure yana jiran zuwan zainaba.. Shiru har sai da abokinsa yazo ya sake sanar dashi  cewa shi kadai ake jira su tafi rana keyi...   Ya cire rai kwarai da zuwanta har ya juya zai fito ya hango wata ta tunkaro wajen..se de shigarta kawai ya nuna masa ba ita bace ba..      Yana fitowa tana karasowa wajen.. Ta yaye lullubin dake kanta tana sauke lumfashi sosai sbd tsabar gudun data sha.. Mustapha cike da mamaki yana bin ta da kallo,wai dama kice haka? Zainaba ta gyada masa kai sannan ta fito da furen data boye cikin riga ta mika masa..    Wani irin farin cikine ya lullube sa.. Yasa hannu ya amsa sannan yace.. Nagode kwarai da kika amshi tayin soyayyata,ina miki alkawari akan bazakiyi dana sani ba gimbiyata.. "Zainaba ta rufe fuskarta cike da kunya tana murmushi.. Mustapha yace,duk da baki damu da sanin sunana ba bari ni nayi karanbanin fada miki.. Zainaba ta bude fuskarta tana kallonsa kafin tace,kawai ka riga ni fada ne amma nima yanzu nake shirin tambayarka.. Mustapha ya gyara tsayuwarsa, kice ma har tunanin mu iri daya ne kenan ko? Zainaba ta murmusa kawai.. Yace,toh sunana Mustapha dan gidan WAMBAN kano..ina fata matsayina yakai da yin soyyaya da diyar sarkin daura...    Zainaba tace,kwarai kuwa.. Yace toh nagode.... A nan suka hau yar firar su sama sama... ********* 'A wajen juwairiya kuwa sauri kawai take bugawa,har tazo hanyar da zata kaita inda su zainaban suke amma sai ganin jama'a tayi sunyi yawa a wajen sosai.. Ta cije yatsan ta,yanzu ta ina zata bi kenan? Hanya da'yace kawai zata iya kaita kuma sai ta bi ta sashen samarin gidan,wato sashen su turaki kenan.. Kafada ta daga lkcn data karasa sashen taga babu kowa a wajen,ta saki lumfashi tace, ina tunanin duk suna fa'da ne...    Tafiya take cikin sauri kanta a kasa.. Batayi au'ne ne kawai taji taci karo da mutum..   A tsorace ta dago da kanta..... 'HAMZA.... ta furta a cikin zuciyarta.... A take tsoro ya mamaye ta. dan ba sau daya ba,ba sau biyu ba tana jin bayin dake aiki a sashen sa suna yawan fadar halayensa na mugunta idan har akayi masa ba daidai ba toh lalle a ranar kashin ka ya bushe ne..     Fitsari ne kawai bai fito mata ba.. Amma mai? Gani tayi hamza ya tsaya kamar an shuka shi a wajen... Kallonta kawai yakeyi baya ko kyafta idonsa..   Ta'ke tabi inda kwayar idonsa dan gano inda yake kallo ajikinta dan ita a tunaninta ko kayan dake jikinta ya gane na zainaba ne su.. Amma se gani tayi fuskarta kawai ya kura wa ido.. 'A Take ta fahimci ta sake tafka kuskuren fitowa ba tare da tabon fuskarta ba..    Hamza yaja lumfashi...yace, Baiwar Allah kin samu batar hanya ne...? Yarda yayi zancen cikin wata kaukausar murya ne yasa ta sake jin hanjin cikinta sun motsa..    Da kyal ta iya furta..... Eh..ka.. kayi hakuri...tayi kasa da kai tana shirin wucesa ne taji murya a bayansu.. Hamza me ya tsayar dakai haka?bana fada maka sauri nakeyi ba... Yarima ne......( ta fada ba tare data kalleshi ba,dan ta gane muryarsa ce )... 'Yarima kuwa dake fitowa daga cikin falo ya tsaya yana kallon hamza kafin yakai dubansa kan budurwar dake kusa dashi...   Ware ido yayi a take yaji kirjinsa ya buga..bum! Itace.....ya furta a zuciyarsa. ..    Juwairiya kuwa najin fitowarsa tayi saurin guduwa daga wajen tana dafe kirjinta....      Da sauri yarima ya karasa gaban hamza dake ta sakin murmushi. . Hamza dama kasan ta ne? Hamza ya kalle sa' wa fa? Yarima yace yarinyar data bar wajen nan yanzu.. Hamza ya sosa keyarsa.. Ah ah yaya kawai dai yanzu na kanta nima,ina tunanin ko tayi batar hanya ne.. Dan daga gani ma tana cikin yan uwan surayya ne da suka zo jiya,sbd ni dai ban ma taba ganin irin fuskarta a wannan masarautar ba..   Yarima yaja lumfashi tabbas hakane yar uwar matarsa ce ita, toh amma kuma jiya ai idan bazai manta ba daya ganta lkcn ma su surayya basu iso garin ba?ya juya zuciyarsa cike da damuwa da tunane tunane kala'kala....lallai yana kyautata zaton GA'MO ne yayi..... ********* Vote n comments N pls share too      [9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 9 Wattpad @afreey101 ******************* "Juwairiya na komawa sashen zainaba tayi saurin dauko kayan kwalliyarta ta maida makeup din tabon ta duk da beyi daidai ba amma da wuya ne mutum yayi ssurin gane hakan. Tana kammalawa zainaba na shigowa sai faman tsalle takeyi tana murna abu ga sabon shiga. *************   Juwairiya na shiga rumfar bayi taji labari da dumi duminsa.. A Lkcn ma tana zaune ne a dakin du'bu suna cin dan wake jakadiya suka shigo da hansai da laure..     'Nan jakadiya ke kwashe musu lavarin duk abunda ya faro tsakanin yarima da amaryarsa,kunya ce ta lullube juwairiya, ta mike zata fice dan lbrn nasu yafi karfin kunnenta.. ' can tajiyo jakadiya na fada musu irin kyautar da gimbiya kilishi tayi mata sai murna sukeyi.. ********** Bayan sati.....   'Surayya ce zaune a gaban gimbiya kilishi..      Hansai tayi sallama ta shigo dauke da tire dake cike da kayan kwalama.. Ta ajiye musu a gefe sannan ta koma wajen zamanta ta zauna..    'Gimbiya kilishi tadan lumfasa..tace, Ina fata babu wata matsala? ko akwai wani abu dake kike bukata ne? Surayya tayi kasa da kanta..ita kuwa ke da matsala,kullum sai dai miji ya shigo mata daki yayi kwanciyarsa ko kallon arziki baya yi mata mtsw...   a fili kuwa cewa tayi,Babu komai umma..ta fada a kunyace.. Kilishi ta murmusa.. Nasan zaman kadaici ya fara gundurar ki,saboda tun zuwanki kina sashen ki ba wani dan fita,amma kada ki damu za nsa yarima da kansa ya fita dake  cikin masarautar tamu dan ki bude ido.. Murmushi surayya tayi tace,godiya nake umma..     Kilishi ta dauko alawar madara daga cikin tiren da hansai ta ajiye.. Kinga wannan alawar?itace mafi soyowa a wajen yarima...dan haka idan kinason faranta masa rai wata rana ki yi kokari ki gabatar masa da ita ina tabbatar miki da zai ji dadi sosai.. Surayya tace,Allah umma?ai kuwa zan gwada inshaAllah..     Suna cikin yar firar su sukaji ana sanar da shigowar da yarima da hamza...      'cike da kasaita suka shigo.. Sunsha gayun su cikin tufafi mai tsadan gaske.. Surayya tabi yarima da kallo.. Har cikin zuciyarta tasan sbd kyawu da tsari irin nasa ne yasa ta amince da mgnr auren su ...dan yarima jalal yayi ne babu karya... 'Zama sukayi sannan a tare suka gaisar da mahaifiyar su.. Kilishi cike da murnar ganin yaran nata tace,har kun dawo daga rakiyar mai martabar ne?. Hamza ya amsa da eh umma ai tun dazu ma muka dawo a gidan waziri muka tsaya...   Yarima yayi shiru sai sauraren su da yakeyi...    Surayya ce ta mike duk suka bi ta da kallo.. Tiren kayan kwayam din ne ta dauka ta ajiye a gaban yarima... Da kallo ya bita kawai yana mamakin karfin hali irin na yarinyar,dan kuwa lbrn karyar da tayi na daren farkon su yazo har kunnen sa lallai ya jinjina mata. Alawan madarar ta dauko ta mika masa tana murmushi. . Yanzu umma ta gama sanar min da cewa kana sha'awar alawar nan sosai..   Yarima ya dauke kai gefe.. Sannan yayi kasa da murya yarda itace kawai zataji yace.. Ba'a fada miki idan har ya fito daga hannu irin naki ba bazai taba burge ni ba? 'Surayya tayi murmushin ya'ke,sannan dan da'ga murya tace ai ban san cewa azumi kakeyi yau din ba...watarana zan samu damar gabatar maka dashi,ta mike ta maida tiren inda yake.. Kilishi da mamaki tace,azumi kakeyi a yau din? Na dauka ai se litinin kakeyi ai? Yarima yadai jinjinar dakai kawai,lallai wannan yarinyar muguwar yar rainin wayo ce.. Kilishi ta kalli surayya,ki tashi ki koma sashen ki gobe da yamma yarima zai zagaya dake cikin masarautar, surayya ta mike cike da yanga tayi sallama da kilishi tayi waje a kufule da irin hali na yarima. ******** 'Washe gari  juwairiya ta nemi izinin tafiya da yamma dan tana da wankin ta take so tayi musu ita da ummanta.. Zainaba ba wani bata lkc ta amince mata,cikin jin dadi ta taho zuwa rumfar bayi... 'Koda ta kusa isowa sai hango su yarima tayi da amaryarsa surayya tare da bayi a bayansu suna tafiya cikin nutsuwa sai dai ba wani mgn sukeyi ba,amma ko waye ya kalle su sai sun burge sa dan dukkanin su ba baya ba wajen tsara ga'yu..     Surayya ta kalli yarima dake tafiya cike da kasaita sai shan kamshi yakeyi,tunda suka fito ko A bai ce mata ba.. Yarima can fa inane?ta nuna saitin Rumfar bayi.. Yarima yabi inda hannunta ya nuna da kallo.. Karaf idonsa yakai juwairiya dake kokarin shigewa cikin saurinta...     Da sauri ya kauda kansa tsikar jikinsa na tashi..yaars.. "Surayya jin yayi mata shiru kuma a gaban bayin ta ne wanda ita hakan raini take gani zai jawo mata,sai ce mai tayi kace me?banji ka ba,(wato dai ta maida abun kamar yayi mgn ne itace bata ji shi ba)     Yarima yadan matse baki kafin yace RUMFAR BAYI  kenan... Ta sake maimata sunan,tana jin lbrn wajen daga wasu bayi a can masarautar su amma bata taba tsanmanin haka wajen yake ba...     Tabi wajen da kallo... Yarima ya juyo yana fadin, a nan zamu tsaya? Surayya ta saki murmushi, ah ah yarima bazamu je kogin mai martaba bane?na ji lbrn cewa kogin mai martaba ya kayatu sosai.. Yarima yadan ja tsaki kafin yace,muje.... ******** "Juwairiya na shiga rumfar bayi taga wayam kamar anyi shara,taja lumfashi su kenan kullum basu da lkcn kansu.. Dakin jakadiya ta shiga ta kwaso wankin su ita da laure,sannan ta shiga nasu dakin ta kwaso nasu suma wankin,can daga bayan rumfar bayi akwai wani ruwa mai gudana daga can kogin mai martaba ruwan ke fitowa,toh a nan ne suke wankin kayansu.. 'Juwairiya ta samu dutse ta zauna a kai sannan ta zube kayan wankin a kasa tana kallon dajin dake gabanta... Lumfashi taja,ko yaushe zatayi rayuwa kamar kowane dan Adam me daraja? Ta girgiza kai, ki daina irin wannan tunanin juwairiya, haka rayuwar ki zata kare a bautawa uwar dakin ki zainaba...ta gyada kai sannan ta hau yin wankinta... Ba karamin wanki tasha ba,ganin garin da sauran haske ga iska na ta kadawa hadari ya taso.. sai tsinci kanta cikin wani irin nishadi...     Hadari ne sosai har an fara yayyafi,murmushi tayi tunawa da tayi babu kowa a cikin RUMFAR BAYI sai ita.. 'Ta karasa gaban ruwan tana kallon reflection din fuskarta a ciki,hannu tasa ta dinga  dibar ruwa kadan kadan tana watsa wa fuskarta har ta wanke tabon dake jiki..   Ta mike tana tsalle tana jin dadin yarda ruwan saman ke sauka akan fuskar ta data daga sama cike da nishadi......... Pls Comments Share Vote [9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Page 10 Wattpad @afeey101 _Notice-thanks for all the love *TEAM RUMFAR BAYI*,ur comments always gives me straight,pls keep on supporting me n add rumfar on wattpad my what'sApp fans,i need ur votes too pls...much love_ **************** "Surayya ta bude baki tana kallon irin tsarin kogin na mai martaba, ta juya bangaren da yarima yake a tsaye yana shan kamshi,gaskiya wajen nan ya hadu sosai,watarana nima zan zo nayi wanka a nan,dan ina masifar son shiga ruwa balle mai dumi haka,kasan ko a gi.....kallon da ya watsa mata ne yasa taja bakin ta tayi shiru..      Yayyafi ne aka farayi.. Yarima yace muje ko? Surayya ta make kafada sannan ta karasa cikin kogin tana wasa da ruwan cike da nishadi.. "Takaici ne yasa yarima karasawa wajen a fusace ya daka mata tsawa.. Baki ji ni bane! A tsorace tayi losing balance dinta ta fada cikin kogin.. Ihu ta saka tana kallon yarima..(irin ka taimaka min dinnan) Tsaki yaja ya shiga ruwan shima yana kokarin jawota.. Tazo fita ne hannunsu na sarke dana juna,ta jawo dan yatsansa da karfi... ai kuwa zoben azurfan dake hannun yarima ya sullube cikin kogin ruwa yayi gaba dashi.. Cikin tsananin tashin hankali yace.. "Zobena..."baki da hankali ne!? Surayya tace,toh miye ? Ba zobe bane kawai... Ko fa a yau dinnan kace a yi maka wani sabo a cikin daren nan za'a kawo maka shi,toh miye na wani tashin hankalinka,ta karashe mgnr tana kallonsa (giving him i dnt care look)... Yarima ya banka mata harara kafin cikin sauri yabi inda zoben ya tafi...surayya se kwala masa kira takeyi yayi banza da ita.. 'Tafiya kawai yakeyi ga ruwa ya fara yawa a lkcn...   Bai taba zaton kogin yana tsawo haka ba...    Wata murya ce yaji ana ta rera waka cike da nishadi.. Ya dago kansa cike da mamaki...   caraf sai Hango ta yayi tana ta tsalle tsallen ta tana rera wakarta hankalinta akwance.... Har zai dauke kansa'kawai idonsa ya sauka akan fuskar ta...    Wani irin ware ido yayi yana mamakin ganinta a wajen... Wai wacece wannan yarinyar? Gabansa nata faduwa kallonta kawai yakeyi ya kasa dauke idonsa.. Ita kuwa juwairiya bata ma lura dashi ba a wajen,tana gama tsalle tsallen ta ta kwashe wankinta dan dama batayi shanya ba ganin hadari,ta dauki kwal'lar ta tayi gaba...       Yarima yaja lumfashi, ina ne can din data shiga?me yasa wai ya damu da sanin wacece ita?me yasa bazai mance fuskarta ba?meke damunsa haka?       Ganin tunani na neman yi masa yawa ne ya dauke kansa da sauri yaci gaba da neman roben sa,da kyal ya ganshi wani dutse ya tare shi ya dauka yayi gaba yana waiwayen hanyar da ta bi... ********* "Bayan kwana biyu yarima ne yayi kiran magaji zuwa sashen sa_(magaji yaron waziri ne kuma babban aminin jalal ne)_   Magaji daya gaji da jiran yarima yayi masa mgn'yayi gyaran murya yace.. Yadai ranka shi ya dade?ka kirani kuma naji kayi shiru..da fatan dai lafiya ko?   Yarima yaja lumfashi kafin gyara zaman sa yace,magaji ko kasan iya inda ruwan kogin mai martaba yake kaiwa? Magaji yadan yi tunani sannan yace idan bazan manta ba naji ance ruwan har fa RUMFAR BAYI  yake kai wa..da wani abun ne? Yarima yadan girgiza kai "rumfar bayi fa kace? Magaji yace kwarai kuwa.. Yarima yadan yi shiru,amma shi fuskar da yake gani batayi kama da wata baiwa ba sannan ma ranar ai da kayan alfarma sosai ya ganta..       Magaji ne ya katse masa tunanin sa.. Wai yarima meke damun ka ne? Ka sanar dani mana ko zan iya taimaka maka.. Yarima ya kalleshi,babu komai magaji tashi ka tafi.. Magaji ya jinjina kai sannan ya mike ya fice.. Yarima ya mike shima,bawansa ya kira ya fada masa yaje ya sanarwa surayya a dakinta zai kwana yau... Bawan na fita kuyangi suka shigo dan hada mishi ruwan wanka.. Suna hadawa yace dasu zasu iya tafiya..   Kayan jikinsa ya rage sannan ya shige cikin bahon wankan yana lumshe idanuwansa.. ***************   "Surayya na cikin cin abinci ne bawan yazo ya isar da sakon yarima.. Zo kuga Murna a wajen surayya tu're abincin dake gaban ta tayi dan a take taji ta koshi,bayinta ta kalla sannan tace dasu su shiga su sake gyara mata dakinta...    "Ba karamin gyara suka sha ba,surayya jiki na rawa ta shiga ban daki da wasu bayin aka wanke ta tas sannan ta fito ta turare jikin ta ta saka rigarta mai santsi ta barci sannan ta zauna jiran yarima.. Shiru shiru babu yarima ,surayya taja tsaki,wannan kuma wane irin salon wulakancin ne? Har sha dayan dare babu shi.. surayya na nan zaman jiran sa sai gyangyadi takeyi..can taji ana sanar da zuwansa..   Ta mike da sauri ta zauna tana daure fuskarta..    Yarima na shigowa dakin kamshi ya daki hancinsa.. Ya lumshe ido hade da saukesu akan surayya data harde hannayenta ta juya masa keya..     Tabe baki yayi kafin yace.. Badai ni ake jira ba har aka kai wannan lkcn ba'a kwanta ba? Ta juyo tana kallonsa shima ita din yake kallo..    Cike da masifa tace,wai me yasa kake jin dadin wulakanta ni ne uhm? Yarima ya cire alkyabbar jikinsa..yace, Menene wulakanci a ciki? "Sanar dake na yi zuwana?ko kuwa zuwan nawa sashen ki bayan shudewar kwanaki biyar.. "Surayya ta turo baki,sannan tazo ta haye saman gado tana tunanin yarda zata aiwatar da shawarar yakambo data aiko mata da wasika jiya..     Gadon shima ya hau sannan a natse ya jawo bargo ya rufe jikinsa..   Surayya ta runtse ido sannan ta shige cikin bargon itama ta matsa daf dashi ta sa hannu ta rungume sa ta baya..   Yarima najinta a jikinsa yaji wani abu ya tsarga masa a gaba daya jikinsa... Surayya ta na fitar da lumfashi ta kai bakinta saitin wuyan sa ta sumbata,cak yarima yaji wutar sa ta dauke,a take ya juyo suna kallon junansu dan akwai dan hasken fitila a dakin..    Me kikeyi hakan....ya fada da muryarsa da ta canza amo (sauti) Surayya ta kura masa ido batace kome ba.. Yace ko bakya jina ne eyeh?.. Ta sake motsawa kusa dashi,wai yarima ni ba matarka bace ba?meyasa ne kake min haka...ta karashe mgnr a shagwabe.. Yarima ya kamo hannunta...me nake miki? Surayya ta zunburo baki,kaima ka sani ai wulakan.....bai bari ta karasa ba ya hade bakinsa da nata yana sumbatarta cikin salon sa..    A wannan daren ne yarima da surayya suka san minene aure... *********** "Juwairiya ta kalli khadija da zainaba dake ta muhawara akan zuwansu sashen matar yarima..     Zainaba ta rike kugu tace,kedai kawai khadija ki ce kishi ne ke damun ki kuma duk tsiyar ki se naje ganin matar yayana ehe.. Khadija ta banka mata harara, ai dama nasan duk abotar karya kike dani.. Zainaba tayi dariya tana rungume ta,haba kawalli kema miye naki dan Allah ba gwara kije ma ki ga yarda take ba ma dan kisan inda kika dosa.. Khadija tace kuma fa haka ne,duk da dai naji ana ta wani fifita kyawun ta.. Zainaba tace yanzu dai muje mu ganewa idonmu ko?...   Shiryawa sukayi juwairiya dai jinsu kawai takeyi....    Suna kai wa sashen juwairiya taja ta tsaya a waje,zainaba ta juya tana kallonta muje mana? Juwairiya ta girgiza kai ku shiga kawai ranki ya dade zan jiraki anan.. Khadija ta harare ta ai gwara ki tsaya a nan din kam tun kafin ganin ki ya jawo mana wani rainin.. Ko tanka ta juwairiya batayi ba ta samu wani dan dutse ta zauna a kai... ********* Bayan anyi musu iso ciki ne suka shiga suka zauna a falonta suna jiran fitowarta.. Khadija tabi kwalliyar falon da kallo tana yatsina fuska lallai kam an kashe kudi a nan ... 'A wajen Surayya kuwa kwana biyun nan cikin wani irin farin ciki take,ganin yarda yarima yake dan kula ta ba karamin dadi hakan ke saka taba..    Cikin tafiyarta ta yanga ta shigo falon.. Sannunku kawai tace musu ta zauna.. Zainaba tace,nayi fushi dake matar yaya.. Surayya ta danyi murmushi dan ta fahimci kanwar yarima ce zainaba diyar fulani diyya..    Haba kanwar mu ni ce ai ya kamata nayi fushin,tunda nazo baki ko leko ni ba.. Zainaba tayi murmushi hakane kuma gsky,kinsan halin mijin naki ne sai muna bi a hankali.. Surayya tayi dariya jin ance mijinta.. Khadija kuwa se kare wa surayya kallo takeyi.. Can dai tace,matar yaya nidai nasan baki sanni ba,sunana khadija kawar zainaba ce sannan diyar waziri.. Surayya tace,kanwar magaji kenan ko? Khadija tadan murmusa kawai.. Surayya ta kalli baiwarta,ya baki kawo musu abun tabawa bane? Baiwar tayi kasa kai sannan ta mike ta fita.. ************ "A can wa'je kuwa juwairiya na nan a zaune tana wasa da kananun duwatsu kanta a sunkuye,tana rera yar wakarta dan debe mata kewa..               Magaji ya kalli yarima 'lkcn suna tafiya ne dan zuwa sashen surayya'    Lallai ango ka ganka kuwa?wannan hasken da kake ta yi lallai gimbiya surayya ta iya ki'yo.. Yarima ya tabe baki,ta iya ki'yo fa kace?wa'to ni din wani dabba ne ma kenan da har ake ki'yona ko? Magaji ya kwashe da dariya..maida wukar abokina.. Yarima yace,ba wannan ba,ya kake gani zamu bul'lowa mgnr da mai martaba ya fada mana dazu? Magaji ya lumfasa gsky al'amarin kamar da girma kaga fa se munje har can chadin mun hadu da wannan mutumin.. Yarima ya jinjina kai yana shirin mgn ne kawai yaji wannan muryar da ko a mafarki yaji ta sai gabansa ya fadi...(muryar juwairiya dake dawainiya da zuciyar yarima)     'Da sauri yabi inda sautin muryar ke fitowa da kallo.. Hango ta yayi can gefe a zaune tana wasa da duwatsu kanta a sunkuye..    Cikin saurinsa ya karasa gabanta...    Bai tsaya wani tunani ba yasa hannu a ha'bar ta(chin) ya dago da fuskarta....idanuwansa kamar zasu zazzago kasa.. ********* Juwairiya a tsorace take kallonsa dan kuwa ji kawai tayi an dago da fuskarta..    Yarima na ganin fuskarta ya ture ta gefe da karfi cikin zafin rai.. "Ba ita bace" Ya fada a zuciyarsa, ya runtse ido cike da takaicin ganin fuskar juwairiya dake saka tsikar jikinsa tashi.. ya juya bai ce komai ba yayi gaba..fuuuu   Juwairiya tabi bayansa da kallo cikin mamaki tace,miye kuma hakan? ********   "Ko gama sanar da isowarsa bai bari anyi ba ya shige ciki abunsa,magaji dake biye dashi yana tambayar sa miye hadin sa waccan baiwar ya tsaya yana bin bayan sa da kallon mamaki ...    cike da tunanin abunda yarima yayi yanzun nan magaji yace,a ina kuwa nasan waccan fuskar? Girgiza kai yayi,kai ba ita bace gsky,dan waccan fuskarta ba haka take ba.. Yana cikin wannan tunanin shima ya shige ciki.. *********** Surayya na ganin yarima ya shigo ta mike tsaye itama cikin zumudi dan baya zuwa sashen ta da rana haka..   Ko kallon inda suke bayyi ba ya shige cikin daki abunsa..    Zainaba ta tabe baki ko ma ya tsaya su dan gaishe shi.. Magaji ne ya shigo yana fadin , ah ah ashe yan matan suna nan suma.. Surayya tayi murmushi,ai kuwa dai sunzo ganin yayarsu ba.. Magaji yace ai sun kyauta,nima bari na karasa wajen umma babba,ya fice..    Surayya duk ta kagu su khadija su tashi su tafi dan ta shiga wajen mijin nata,tayi tsaye ita taba bi yarima dakin ba ita kuma  bata zauna ba..   Zainaba ce ta fahimci kamar su take jira su wa're..,dan haka ta zunguri khadija dake ta tabe baki,tashi muje khadija nasan fulani na can na jiran mu tunda fada mata zamuje sashen ta ko? Khadija tadan harareta kasa'kasa,sannan ta mike,surayya kuwa ba karamin dadin hakan taji ba,murmushi tayi ta kalli zainaba tace,nagode sosai da ziyara kanwar mu,ko amsar su bata jira ba ta shige cikin daki da saurin ta.... Wattpadians/what'sApp fans lets know our status... Who r d.. Team yarima's? Team juwairiya? Team surayya? #rumfar bayi... [9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 11 Wattpad @afreey101 ****************** 'juyi kawai yakeyi a gadon barci ya'ki daukarsa,ya kalli gefen da surayya take a kwance tana ta sharar barcinta hankali kwance.. "gobe ne zam'to tafiyar su kasar chadi,ga tunanin wannan yarinyar gaba daya yaki barin kwakwal'warsa,ya mike ya zauna yana dafe kansa,ya za'ayi ya nemo ta a cikin dubban bayin dake cikin rumfar bayi,wata zuciyar kuma tana gasgata masa cewa wannan yarinyar ba baiwa bace.. Ya koma ya kwanta yana sauke lumfashi bayan ya yanke wata shawara wacce kila ta amfane shi(ni ko afrah nace ko wacce shawarar ce? )... **************** "Da safe juwairiya ta gama shirinta tsaf,tana fitowa daga dakinsu taga an jera bayi layi layi kamar ana asambili.. "Mamaki ne ya kamata sosai ta karasa wajen ummanta dake ta kokarin jera wasu fuskar nan a daure kam..    Lafiya umma?ya naga duk sun ja layi?haka   Hansai ta dan girgiza kanta cike da jimami tace, kema shiga layi ki bi mu.. Juwairiya a tsorace tace harda nima umma?ina zamuje ne haka? Laure dake karasowa wajensu tace, sashen gimbiya kilishi zamuje,dan haka inaso ki nutsu da kyau nasan dai ko hauka sukeyi bazasu dauke ki cikin yan tafiyarsu ba..   "Hansai ma kallon diyar tata kawai takeyi,a tsorace take sosai dan kuwa idan har za'ayi tafiya irin wannan kuma aka bukaci daukar bayi mata dan a tafi dasu,toh duk akasari dawowa sukeyi da ciki wasu kuma ace an sayar dasu ga mutanen can garin,wasu a lalatasu,wasu kuwa a maida su SA'DAKA..    "Juwairiya ta dafa ummanta,kada ki damu umma na fahimci duk tsoron da kikaji sbd ni ne ko... Hansai ta dan kamo hannunta, idan mukaje kada ki kuskura ki dago da kanki kina jina?duk da ma nasan da wuya ne a zabe ki,juwairiya tayi dariya tana nuna mata tabon fuskarta,tunda inada wannan umma ba inda zani je.. A sanyaye hansai ta gyada kai,hakane .. Yanzu shiga layin mu tafi.. ***************** "A sashen gimbiya kilishi kuwa,yarima ne tare da magaji da hamza a zaune gabanta.. Kilishi tace,na saka duk a kawo muku bayin dake masarautar nan,ku zabi wacce tayi muku dan bana so kuje can ana yi muku kallon baku isa ba..dan ni burina a kullum shine ku samu girgimawa a wajen mutane..      Magaji yayi murmushi, godiya muke umma.. Hamza yace,abun mamaki wai yau yayane da kansa yake son tafiya da bayi mata... ba'cin kullum fada yakeyi min idan na dauke su.. Yarima ya banka masa harara. . Kilishi tace ina ruwanka toh?ka manta jiya ba yau bace?duk suka saka dariya.. Suna cikin mgn sai ga jakadiya da du'bu sun shigo suna sanar dasu an tara bayin suna waje..     Yarima gaban shi ne ya fadi,idan ya ganta a cikin bayin can ya zayyi?addu'a kawai yakeyi Allah yasa bata cikinsu wata zuciyar kuma na addu'ar Allah yasa ya kanta.. Cikin wannan tunanin ne ya karasa waje shima yana baza idanuwansa ta ko ina... Kilishi ta kallesu cikin kasaita tace,yarima....je ka duba wadan da sukayi maka,ta mika masa wata sanda kamar yadda al'adar su take idan yaga wacce tayi masa zai sa sandar ne ya nuna ta dashi...     Cikin tafiyarsa me daukar hankali ya karasa gaban bayin dake jere kowacce ta sunkuyar dakanta cike da ladabi...    ************ "A wajen juwairiya kuwa tana jin ance yarima...gabanta ya fadi..ras! Ta sake sunne kanta kasa tana matse hannayenta duk da tasan ita dai ba daukarta ma zayyi ba amma hakanan bata son ya sake wulakanta ta kamar yadda ya saba..   Yarima na tafe har ya kusa kai wa karshen layin kawai ya hango side view dinta, bai gama tantance ko wacce yake tunani bace kawai kai tsaye ya saka sandar cikin saurinsa ya dauke mayafin data lulluba akan ta..     Jikin juwairiya ne ya hau rawa,miye hakan? Ita ya zaba? Kodai bai gane ta bane? Yau ta shiga uku...runtse ido tayi kawai.....tana ji kilishi na cewa KE!! Fito...! ********** Shi kam yarima wani irin yamutse fuska yakeyi ganin wacce ya canko,me yasa wannan me konannar fuskar ta cika bibiyar rayuwar shine? Tsaki yaja ya koma gefen su kilishi ya tsaya dan gaba daya ranshi ya baci..    A sanyaye juwairiya ta fito ta tsaya kamar ta rusa ihu takeji.. Kilishi ta yamutse fuska tana mamakin duk a cikin bayin nan wannan ce yarima zai dauka?ko da yake tasan dan nata,komai nashi na daban ne..      Kilishi tayi gyaran murya tace,toh sai kije ki shirya kayanki dan tafiyar tasu cikin nan da minti talatin ce... Ta juya wajen magaji,kai ka koma ka zabar muku sauran dan naga ra'ayin abokin naka sai a hankali...tana gama fadar haka ta shige ciki abunta..   Du'bu da jakadiya duk ransu bai so aka zabi juwairiya ba ko kadan,toh balle hansai da laure dake gefe suna hawayen bakin ciki...      Yarima ya banka wa juwairiya harara kafin ya wuce magaji da hamza suka bi bayan sa..     Ai suna watsewa bayin duk sukayi kan juwairiya dake kuka,hansai ta kamo hannunta suka karasa rumfar bayi..    Suna kuka suna hada mata yan kayan ta..   Laure tace,kada ki damu juwairiya babu abunda zai faru dake se alkairi.. Hansai ma sauke lumfashi tayi,ta riko hannun ta.. Hankalina yadan kwanta jin tafiyar tasu yarima da magaji ne,na tabbata babu wani abunda zai faru dake dan kuwa yarana ne da suka san abunda sukeyi,ki kwantar da hankalinki kinji?duka kwana uku zakuyi zuwa biyar,kada ki manta da tabon fuskar ki shine kariya a gareki kinji? Juwairiya ta gyada kai kafin ta dau kullin kayanta ta fice.. ********** Tana fitowa ta hango zainaba can gefe a tsaye tana jiran shigowar ta.. Da sauri ta goge hawayen ta tayi wajen ta.. Zainaba na ganinta ta fara hawayen itama a shagwabe tace.. Yanzu fi sabilillahi dauke min ke yaya jalal zayyi.. Juwairiya tayi murmushi, kada ki damu zanki ya dade babu me dauke miki ni,tafiya kawai zamuyi mu dawo kinji.. Zainaba ta gyada kai,muje kiyi sallama dasu fulani... Suna shiga sashen fulani diyya,juwairiya ta zube kasa tana kwasar gaisuwa.. Fulani a sake ta amsa mata tana fadin,ashe dake zasuyi tafiyar? Juwairiya tace uhm,fulani tace,toh Allah ya dawo daku lfy,gaba daya falon suka amsa da amin..     Suna fitowa waje suka ci da turaki.. Yana ganinsu ya sauke idonsa kan juwairiya,a take ya fahimci hankalinta a tashe yake..    Gaida shi sukayi,yayi murmushi yace,ah ah yan matah ana ta bankwanar ne? Zainaba ta shagwabe fuska,yaya harda kai zolayar ko? Turaki yayi dariya,naga ai kwana uku ne kawai miye abun damuwa?ya karashe mgnr yana kallon gefen juwairiya..     Juwairiya tadan murmusa kawai.. Turaki yace,addu'a kawai zakuyi abunda akaje nema a samo shi lafiya,yana gama fadar haka ya shige ciki cikin takunsa...   Zainaba ta ja juwairiya zuwa sashen ta.. Wani kulli ta miko mata.. Gashi ki ringa ci ahankali a hanya kinji.. Juwairiya cike da murna tace nagode ranki ya dade... Wani bawa ne yazo yana sanar dasu ana neman juwairiya... ************* Motace irin ta da dinnan,sai wata bus.. Juwairiya da gudunta ta karasa wajen.. Yarima da magaji na tsaye da sauran bayin duka an gama saka kayansu a cikin motocin..     Tana zuwa duk suka maida kallonsu gareta.. Yarima yaja tsaki...lallai ya gama kufsawa kansa yanzu haka zai tafi da waccan yarinyar yana kallon konannar fuskar sa,mtsw .. Surayya ce ta karaso wajen tare da baiwa a bayanta..      Wajen yarima taje ta mika masa kullin dake hannunta.. Se daya kalle ta sannan ya maida kallonsa kan kullin yace,menene? Tadan karkace kai, Ka amsa mana kaga fa akwai mutane a wajen,yadan yi yake sannan ya amsa ya shige mota,surayya tabi bayin dake wajen da kallon wulakanci balle ma juwairiya data gani duk a tsorace... Suna shiga mota shamaki da galadima sukayi musu addu'ar suka lafiya sannan suka hau hanya... "Toh ya kuke ganin wannan tafiyar zata kasance?" Keep following rumfar bayi [9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima:          *RUMFAR BAYI*       (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 12 Wattpad @afreey101 ***************** "Sunyi tafiya mai nesan gaske kafin suka iso Daular borno..    "Yarima dake zaune a bayan mota yace wa bawan dake tu'ka su,idan muka shiga  borno sai mu a tsaya a  masarautar su mu kwana zuwa gobe sai mu karasa chadin.. 'Magaji ne ya gyara zamansa yace,ai mun shigo Daular borno tun dazu yarima tunanin me kake ne haka?ba dai har ka fara kewar surayyar taka ba..yayi mgnr cike da zolaya.. Yarima yaja tsaki kawai yana kallon window.. 'A can cikin bus kuwa su juwairiya ne,tunda aka shigo kasar borno ta maida hankalinta akan kallon window tana karewa tsarin garin kallo...har taga sun shiga wata katowar kofa sai gasu acikin masarautar ta borno.. 'Ido ta ware tana kallon mutane dake ta zurga'zurgar su duk da dare ne amma harkar gabansu kawai sukeyi.. Rabi ce ta dan tabo ta ganin motar su ta tsaya,muje juwairiya.... 'A sanyaye ta fito daga motar jikinta duk a gajiye tana rungume da kullin kayanta.. Daidai lkcn ne shima yarima ya fito yana wani shan kamshin sa.    Har fadar mai martaba aka kai su suka kwashi gaisuwa sannan aka saka wasu matah su kaisu masaukin da zasu kwana zuwa goben.. Masaukinsu ya hadu sosai dan komai an wadata su,tunda Takawa (mahaifin jalal)ya riga ya turawa sarkin borkon sakon zuwan su. daki daya aka ware wa su juwairiya ,sai daki daya na yarima, daya kuma na mazan bayi sai dakin magaji... Suna shiga kowaccen su ta kwanta cike da gajiya,basu dade da shigowa ba sai ga sakon magaji ya iso musu daga wajen wani bawa,wai a cikin su ukun wata taje ta hadawa yarima ruwan wankan sa..     'Rabi ta marairaice ta kalli juwairiya,waye zai je a cikin ku dan ni kam wlh bazan iya zuwa ba jikina ciwo yakeyi sosai.. "Zabba'u itace karama a cikinsu,dan haka tace,ni wlh tsoro nakeji kuma ni ban ma iya hada ruwan wankan ba  tunda ni a madafa nake dama..   "Juwairiya tadan hararesu,kawai ku fito fili kuce ni naje mana.. Dariya sukayi sannan a tare sukace.. Dan Allah juwairiya ke kije.. "Juwairiya zatayi mgn bawan dake waje ya sake cewa, baku ji bane? !ba a barin yarima yana jira,juwairiya ta zunboru baki sannan ta mike tana sake gyara kayan dake jikinta kafin ta fito..    Bawan na gaba tana binsa a baya har suka shiga bangaren su yarima..   Magaji ne kawai a falon zaune.. Yabi juwairiya da kallo, shiga ga dakin can ya nuna mata wata kofa.. Toh tace kawai jiki a sanyaye ta shiga kofar..    Yarima ta hango a zaune kan dago ya jingina bayansa a kan gadon ya lumshe idonsa.. Ta rasa me zatace masa, wace irin gaisuwa zatayi masa.. Dan haka se ta lallaba zata shige kofar data ke tunanin ta ban dakin ce..      'Haka aka koyar dake!!!? Muryar yarima ta da'ki dodon kunnenta.. Da sauri ta juyo ta hango shi yana kallonta fuska a daure.. Dawowa tayi baya tace,afuwa zanka shi dade na dauka barci kake ne... Ya yamutse fuska yayi sannan ya maida idonsa ya lumshe..   Juwairiya ta shiga toilet din ta hada ruwan wankan sannan ta fito ta tarar dashi a tsaye..tace.. Na gama...ta sunkuyar dakai.. Tsaki ya danyi haushin kansa kawai yakeji daya za'bi ta a tafiyar....ya kasa gane meyasa wannan yarinyar take shiga rayuwar sa..     tsaki ya dan'yi kafin yace,Zaki iya tafiya,ya mike a natse yana cire alkyabbar dake jikinsa.. Toh tace kawai ta fice.. Tana fitowa falon ta sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi.. Magaji ne yayi dariya... Tayi saurin kallonsa dan ta manta ma akwai mutum a falon.. Yace duk tsoron yariman ne? Juwairiya tayi dan murmushi sannan ta fice tana jin kunya sosai.. Da asuba suka hau shiri,wannan lkcn rabi ce taje ta hada masa ruwan wankan dan juwairiya kekeme tace itama ta gaji..     Da sassafe  kuwa sai ga kayan karin kumallo an kawo musu me rai da lafiya,suka ci sosai kafin suka hau hanya.. ************* "Sun sake shan wata tafiyar mai nisan gaske kafin suka shigo kasar chadi...    Ba karamin mamakin nisan garin juwairiya tayi ba... A wani wajen saukar da baki ne suka yi masaukin su..   Su juwairiya na tsaye gaban kofar dakin da aka basu suna jira a bude musu magaji ya karaso wajen...     Ya kalli juwairiya yace, yarima yace kije ki hada masa ruwan wankan sa.. Juwairiya ta gyada kai kawai amma can cikin zuciyarta haushi ne kawai takeji,ko ya dan bari ma su dan huta,koda yake su bayinsa ne bai damu da samun hutun su ba,shi kullum se shegen son wanka kamar wani kifi mtsww... 'Kullin kayanta ta mikawa rabi sannan ta juya tabi bayan magaji tana mamakin wai ita yarima da kansa ya kira bayan kullum se ya mata gargadin zuwa inda yake mtsww... ************** 'Ta same sa ne a cikin wani makeken falo.. Da sallama ta shiga ya amsa mata ciki ciki idonsa na kan wata takarda..    Barka da hutawa ranka shi dade.. Yayi banza da ita,se hannu daya sa ya nuna mata kofar toilet kawai..   Tadan ja lumfashi kafin ta shiga ban dakin...   Da kallo ta bi toilet din ganin irin nasa tsarin.. Toh fa ina zan samu ruwan a nan?ta fadi tana rike kugu...    Ganin bata da masaniyar hakan ne yasa ta leko tana kallon yarima amma ta kasa magana.. Yarima naji a jikinsa kallon sa akeyi amma ya da'ke ya share ta...   Juwairiya tadan ja tsaki kadan,sannan ta koma cikin toilet din tayi tsaye...   Yarima ya mike tunawa da yayi famfo ne a cikin toilet din  kuma tabbas da wuyane ta san shi tunda can masarautar su, mai martaba da matan sa ne kawai ke dashi a ban dakin su..     Toilet din nufa cikin tafiyar sa a sanyaye.. Ita kuwa juwairiya tabe tabe ta shiga yi dan gano inda zata samu ruwan..    Sai ji tayi an bude kofar toilet din.. Ta juyo da sauri tana kallonshi..   Yarima bai  ko kalleta ba ya shiga tafiya yana kusanto inda take a tsaye.. A tunanin juwairiya kashin ta ne ya gama bushewa tunda ta bata masa lkc har haka tasan bazai barta ba tsoro ne ya dirar mata..     Yarima kuwa wajen fanfom dake kusa da ita yake son zuwa ya kunna... Tana jin yazo kusa da ita sosai sai ta zube a kasa tana shirin mgn kawai taji saukar ruwa  a jikinta dan dama fanfom  bayanta yake a karkashin sa ta du'ka ..     Yarima ya harde hannayensa yana kallon yarda ruwa yake wanke juwairiya tas...     Ita kuwa a tsorace take sosai daga ina zuwan nan ya fitowa haka? Ta dago fuskar ta da ruwa ke sauka a kai... Yarima yaji gabansa ya buga,bum! Bum! Minene haka? Ya fada cikin tsananin mamakin ganin tabon dake jikin fuskar juwairiya yana wankewa a hankali ahankali .. Kura mata ido yayi kawai yana kallon ikon Allah..    Ita kuwa juwairiya jin ruwa ya cika mata ido yasa ta mike da sauri tasa hannunta tana goge ruwan daga idonta..     "Sauke hannunta daga fuskarta yayi daidai da bugawar zuciyar yarima cikin tashin hankali... Me zai gani haka? I...TA...CE !!!!! Ya furta da karfi.... Juwairiya ta tsorata sosai jin yarda yake ta furta itace itace kuma yana nuna ta..   Yarima ya karasa gabanta.... kawai ji tayi yasa hannunsa me taushi yana shafa fuskarta... Idanuwanta kawai ta zazzaro tana kallonsa.. Lafiyarsa kalau? Taja baya da sauri a firgice ... Hakan yasa hankalin yarima ya dawo jikinsa..   "Haushin kansa yadan ji.. Ya daure fuska kamar ba shi ba yace kiyi sauri ki hada min ruwan..ya juya da saurin sa ya fito daga toilet din.. Daki ya shiga yana dafe kirjin sa.. Mamaki tsantsa a cikin zuciyarsa.. Dama itace? Amma me yasa take boye fuskarta ne  da wannan tabon? Lallai kuwa itace me wannan fuskar da ya dade yana son gani,ya shiga tuna duk haduwar da sukayi a baya.. Murmushi yayi kawai cike da farin ciki.. Wata zuciyar tace masa,yanzu tunda ka ganta se  kuma me? Sonta kake ne? Ah ah ya girgiza kai  da sauri ni nayi soyayya da wata baiwa?Allah ya tsare ni.. Dolene ya saita kansa kada yaja wo wa kansa raini a wajenta.. Haka nan yayi ta murmushi shi kansa ya rasa dalilin hakan... *********** Juwairiya kuwa shaf ta manta da wani tabo a fuskata ,tana gama hada ruwan ta fito ta tarar da baya cikin falon.. Ta kalli kofar dakin.. Ko ta shiga ta sanar dashi ne? Tadan girgiza kai,kada kije ya kuma ci mutumcin ki a banza.. Ta samu wuri ta rakube a gefe dan jiransa.. Sai jin fitowar shi tayi.. Yana ta wani kallonta bai ce mata komai ba ya shige toilet din.. Tadan ja tsaki,ko yace min zan iya tafiya ma mtsw.. Haka tayi ta zama har ya fito daga shi se dan wani yadi daya daura a kugunsa..   Juwairiya tayi saurin dauke ido tana jin gabanta na faduwa...... Please Vote [9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima:           *RUMFAR BAYI*        (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 13 Wattpad @afreey101 ********************    'kallon ta yayi Ya dan saki murmushi, kafin nan ya daure fuska yace,ke!... Ta dago da kanta a tsorace amma bata kalli in da yake ba.. 'Yarima ya shafi sumar kansa Yace,ki biyoni.....sannan yayi cikin dakinsa.. A sanyeye jikinta na rawa ta bi bayansa a tsorace...   Tana shiga dakin ta iske shi a tsaye yana goge jikinsa cike da nutsuwa.. Tayi kasa da kanta da sauri.. Yarima yace,har yanzu baki san aikin ki ba ne? A cikin sarkewar murya tace na sani? Ya karasa gabanta ya mika mata dan karamin kyallen dake hannunsa.. Jiki na rawa ta amsa.. Ya koma ya zauna yana juya mata bayansa,kawai be ce da ita komi ba.. 'Juwairiya ta karasa ta tsaya a bayansa da kyallen a hannunta.. Se data ja lumfashi sannan ta runtse ido ta shiga goge masa jikinsa.. Tana gamawa taja gefe da saurinta..ta runtse idonta kirjinta na bugawa.. 'Yarima ya saki murmushi sannan ya mike ya karasa wajen kayansa ya dauki man shafawar sa . yana shafa man yana kallon juwairiya dake rakube a gefe idanuwanta a kulle gam! haka kawai sai ya tsinci kansa a cikin wani irin nishadi.. "Zo ki taimaka min ya fada kai tsaye yana mika mata alkyabbar dake hannunsa.. Ta bude ido taga ya gama shirin sa tsaf cikin wani farin yadi mai sauki ,ta karasa ta amsa alkyabbar sannan ta taimaka masa ya saka..        Maganar wani bawa sukaji daga can cikin falon... Yarima ya fito tana biye a bayansa.. Abincine kala kala aka kawo masa..    Bawan ya du'ka har kasa yace,ranka shi dade sun ce na baka hakuri akan kayi hakuri da wannan ya nuna abincin daya shigo dashi,saboda dare yayi ne basu samu damar gaba tar maka da abinci masu yawa ba..     Yarima yace banu komi zaka iya tafiya.. Juwairiya ta dan tabe baki duk wannan kayan dadin shine harda wani bashi hakuri..tab lallai ta yarda yarima babban mutum ne.. 'Yarima ya kalleta yaga idanuwanta kyam akan abincin.. Zama yayi kawai yana lankwashe kafafunsa.. Juwairiya ta dan hada karfin da gareta tace.. Ranka shi dade zan iya tafiya? Yarima ya girgiza kai... Juwairiya tace na shiga uku wai meke damun mutumin nan ne?(a cikin zuciyarta).. Yarima ya lumshe ido ya bude,kafin yace,zo ki bani abincin.. Juwairiya a sanyaye ta duka ta zuba masa abincin a cikin plate sannan ta ajiye a gabansa tana kokarin mikewa yace.. A ba'ki zaki bani...dan na gaji dayawa.. Juwairiya gabanta ya fadi,... 'A baki'?ta fada a tunaninta cikin zuciyarta tayi mgnr se ji tayi yace.. Da a hanci zaki bani? Ta girgiza kai,ai ko zainaba bata zama a bata abinci a baki.. Tsokali ta dauka ta debo abincin kadan a ciki sannan ta mika masa.. Yarima na kallon fuskarta ya bude baki ta saka masa abincin aciki.. Cike da takura take basa abincin har yayi mata nuni da ya koshi.. Dadi taji sosai dan ta san yanzu dolene ya sallameta tunda dai ba ita zatayi masa barcin ba..    Ji tayi kawai yace.. 'Saura ke ki ci' Ta dago da mamaki tace,Ni? Yarima fuska ya daure yace ban sani ba.. Juwairiya ta rasa yarda zatayi wai "saura ke ki ci"kodai kunnenta ne yaji mata badai dai ba..? Yarima ya mike kawai yace,idan kin gama zaki iya tafiya... Yana shiga daki juwairiya ta sake kallon delicacies din dake wajen ko kwatan abincin yarima bai ci ba..      Gyara zamanta tayi a wajen tana fadin.. 'Gwara naci dan kada ma ayi asarar abincin nan da mutane dayawa basu da halin kamar shi...     Cin'yar kaza ta dauka tana yashe lebenta,se yau Allah yayi zata dandana irin wadan nan abincin oh"dama su ummanta na nan suci tare..     Yarima dake labe a bakin kofa ya saki murmushi yana ta kallon yarda take cin abincin da gani ta kwaso yunwa sosai, tausayinta ne yaji ya kamasa..   Juwairiya taci tasha sosai sannan ta kwashe sauran tayi gaba dashi dan ta kai wa su rabi suma su sa wa bakin salati. Tana shiga dakin ta tarar basu a ciki ko ina sukaje oho,sallolinta tayi sannan ta zauna ta sake maida tabon fuskarta shaf bata kawo ya wanke bane a toilet din yarima duk a tunaninta a wajen alwala ne ta wanke sa. "A daren yarima yayi barcin farin ciki sosai dan har mamakin kansa yakeyi,duk da baisan matsayin yarinyar a cikin zuciyarsa ba amma zayyi kokarin kyautata mata tunda dai ko ganin ta ma kawai a kusa dashi ya na saka shi farin ciki. *************** "Da sassafe kuwa itace ta fara tashi taje tayi wanka sannan a cikin toilet din ta zauna ta maida tabon fuskarta.    Suna zaune rabi nata lin ke musu kayan shinfidar su akazo yin kiran su,duk suka mike suka fito waje.. Sashen yarima suka shiga hade da sallamarsu.. Yana zaune tare da magaji suka shigo.. Idanuwansa gaba daya akan juwairiya suka sauka. A take yaji kwanciyar hankali na ratsa sa duk da kuwa tabon dake fuskarta a yanzu bayajin kyamarsa ko kadan... Shi dai kawai ya kasa gane dalilin ta na boye fuskarta da takeyi da wannan tabon na karya. "Magaji ne ya kallesu..sannan ya amsa musu gaisuwar su.. Ga wannan ya mika musu wasu kaya dake ajiye a gefen sa.. Zaku saka su ne yanzu dan zamu fita daku.. Rabi ce taje ta dauki kayan sannan tayi godiya suka juya dan ficewa..se jin muryar yarima sukayi yace.. Ke!!!! Su duka duk suka juyo a tare dan basu gane wacce 'ke' din bace yake nufi..    'Shiga ki hada min ruwan wankana...' Tsuru'tsuru sukayi dan basu gane wacece acikinsu yake bawa umurnin ba.. Magaji ne yadan fahimci rashin ganewarsu akan furucin da yarima yayi, dan haka sai ya nuna rabi dake tsakiyarsu,ke shiga ki had... Bai kai ga gama maganar ba kawai sai ganin yarima yayi ya nuna juwairiya, waccan nake nufi... "Juwairiya gabanta ya fadi,ta gyada kai a sanyaye sannan tayi hanyar ban dakin.. Magaji ne ya kalle shi,a zuciyarsa kuwa mamaki yakeyi,meye ke damun yarima da waccan yarinyarne,da zasu taho duk yawan bayin da aka kawo musu ita kawai ya zaba,Allah yasa ba abunda yake tunani bane,dan kuwa indai hakan ya faru,ya tabbata abokin nasa zai sha wahala ba karama ba...   Ya dai da kallon? Yarima ya fadi yana kallon magaji daya tsura masa ido.. Magaji ya mike..ah ah babu komai idan tayi tsami ai zan ji ..yana gama fadar haka ya fice.. Yarima yayi murmushi, tsami? Ya maimaita yana girgiza kansa..kafin ya mike ya shige daki..    Juwairiya na gama hada masa ruwan wankan ta fito. Bata iske shi falon ba dan haka dakinsa tayi sallama ta shiga.. Yana zaune wasu takardu ne a gabansa yana gyara wa,juwairiya tayi kasa da kai.. Na gama ranka shi dade.. Ya dago yana kallonta.. Kije ki shirya ki dawo... Da mamaki tace,na dawo? Yarima ya danyi tsaki bai amsa mata ba.. Juwairiya a sanyeye ta fita tana mamakin halayen yarima sam ta kasa gane me yasa ya canza mata haka.. "Bayan sun shirya cikin wasu riga da zani na hadin atamfa da shadda, rabi ta kalli juwairiya cike da sha'awa tace,lallai juwairiya kin ganki kuwa? Juwairiya ta dan kalli jikinta me nayi?ko ba haka ake saka kayan ba ne? Su rabi suka kwashe da dariya, ah ah kyau kikayi acikinsu wlh ,ko dan bamu saka kaya irin wannan ne? Juwairiya tayi murmushi, gaskiya ne amma ni kam kayan nan sun takura ni dayawa,rabi tayi dariya dan bakya yawan daura zani ne shiyasa amma ni kam sun min wlh Allah yasa su bar mana kyauta ma.. Juwairiya na dariya ta fito dan komawa wajen yarima.. Da sallama ta shiga falon,yana zaune ga kalaci nan an kawo masa amma bai taba ba.. Barka da hutawa ranka shi dade.. Yarima ya dago yana bin ta da kallo daga kasa har sama.. Ba karamin canzawa tayi ba da kayan,a zuciyarsa yace,sai ma idan babu wancan tabon a fuskarta...    Zo ki bani abinci... Toh... Tana a tsugunne ta hada masa abincin,ta dawo gefen daman'sa ta zauna a nutse sannan ta fara basa abincin yana ci kamar baya so.. Ya isa haka...ya daga mata hannu.. Gyada kai tayi ta mike tace,ranka ranka shi dade zan iya tafiya? Ya girgiza kai.. Zauna ki ci' Ta dan kalli fuskarsa babu alamun zata iya yi masa gardama.. Ta koma ta zauna amma ta kasa cin abincin.. Kina bata min lkc' Ya fada a da'ke yana kallonta.. Afuwa nake ranka shi dade amma akwai abincin mu a can dakinmu.. Yarima ya tabe baki... Na lura har yau dai baki gama sanin dokokin dake cikin bauta wa uban gidan ki ba, ba'a yiwa yarima gardama kin gane? Ta gyada kai sannan ta jawo apple ta dauka ta kai baki hannunta na jawa.. Gani tayi yarima ya dauki plate ya shiga zuba abincin a ciki sannan ga mamakin ta a gabanta ya ajiye plate din.. Gabanta na faduwa ta kalleshi.. Ya harare ta,ki cinye shi tas! Ta zaro ido' Yace ni kike zarowa ido? Tayi saurin sa'dda kanta kasa,afuwan ranka shi dade.. Yadan murmusa kafin yace,toh fara ci.. Ta saka hannu ta fara ci a kunyace,wai meke damun yarima ne?kodai duk so yakeyi ya siye ta da dan abincin da yake bata dan kawai ya kwanta da ita?    A tsorace ta dago tana kallonsa.. Taga hankalinsa na wajen takardun da yake dubawa.. Anya? Ai bata tabajin ance yayiwa bayi fyade ba,ta girgiza kai kila dan sunzo wani gari ne bayaso ace basa kula da bayin su,amma me yasa ita kawai yake kyautatawa haka?koma dai miye ita ba zata taba bari a lalata rayuwar ta ba ehe...    Tunanin me kike?hala bakiji me nace bane ko? Juwairiya ta dauke hannunta daga cikin plate din tace,na koshi ne ranka ya dade.. Yarima ya daga kafada, toh tashi mu je.. . Juwairiya ta mike tayi gaba harda su tuntube.. yarima yabi bayanta da murmushi s "matsoraciya " Yau kunji ni shiru,tun safe na fita schl ne daz y.. Pls Vote [9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 14 Wattpad *************** "Gidan wani babban dan kasuwa sukaje wanda yana cikin manyan yan kasuwa na duniya gaba daya.. gidane na zamani mai kyan gaske gashi makeke sosai har yaso ya tsorata su juwairiya...   ' Zo kuga kallo kuwa wajen su, rabi har dasu sakin baki,tana zungoro juwairiya da zabba'u..     A waje suka zauna kan wasu fararen kujeru masu kyau su kuwa su yarima suka shige ciki dan an aiko wani ya shigar dasu... "Sun dade a zaune wajen, juwairiya gaba daya zaman ya gundure ta,dan tun suna firar kyaun gidan har kowa ya gaji yayi shiru.. mikewa tayi tana dan shawagi a wajen..can ta hango wasu fure masu kyan gaske dan bata taba ma ganin irin su ba a can kasar tasu (rose flower) Da sauri tayi wajen tasa hannu ta tsi'go daya tana murmushin ta mai kayatarwa.. *************** Yarima tare da magaji na tare da wannan babban dan kasuwan dan isar da sakon mai martaba na son fara fafada kasuwancin sa a nan kasar ta chadi.   Yarima ya gama bayani ya dauki cup din tea da a gabatar musu yayi dan sipping kadan... Ya gyara zamansa... Open glass din dake gefen su ya kalla... Can ta hango ta rike da furen a hannu ta na dama tana murmushinta... Hakanan yaji ta burge sa sosai ga view din wajen se ya kara mata kyau a idon yarima,ya murmusa kawai yana kokarin dauke kansa ne kawai yaga wani saurayi na karasawa wajen ta... ******** "Yan mata ya kike? Taji an fadi da hausar da bata goge sosai ba.. Ta dago ta kalleshi da rashin sani... Lafiya ta fada tana rusunawa kasa.. Yace No ah ah basai kin rusuna min ba,kema din da mutanen nigeriyar kika zo? Juwairiya tace eh tana dukar dakai.. Ya saki wani irin shu'umin murmushi yana karewa jikinta kallo...dan ya fahimce baiwa ce ita... Furen hannun ta ne ya fadi kasa sbd tsabar a tsorace take sosai,jikinta har rawa yakeyi ganin irin kallon da mutumin yakeyi mata har da yashi leben sa..   Da sauri ta du'ka dan daukar furenta tayi gaba..   Kawai sai jin hannunsa tayi a kugunta yana shafata... A firgice ta dago tana kallonsa cike da tsoro.. Miye....ha...ka?muryarta na rawa ta fada.. Yayi mata murmushin yaudara.. Yan mata ina son irin ki sosai,zaki zauna dani?zan siye ki da kudi masu yawa na baki ga'ta da yan'ci....    Mamakin kalamansa tayi sosai...kuka ne yazo mata ba shiri dama abunda ake fada kenan?yau ta shiga ukun ta.. Shi kuwa ganin haka sai yasa hannu ya jawo ta jikinsa wai ze lallashe ta.. ************** "Yarima gaba daya wutar sa daukewa tayi,fushi da takaici ya mamaye zuciyarsa ,cup din dake hannunsa ne yayi wurgi dashi da karfi... Duk su magaji suka kalleshi da sauri cike da mamaki. Ya mike kawai cikin bacin ran da baisan me yasa yake jinsa ba yayi waje...      """"Juwairiya nata kokarin ture mutumin daga jikinta cike da tsoro,kuka takeyi sosai ganin wani irin sabon al'amarin da bata taba fuskantar irin shi ba,duk da tabon dake fuskarta amma wannan mayen mutumin sai da ya tunkare ta haka,ko su nan basa kyamatar masu tabon ne...   Bata ankara ba sai ji tayi an fisgo mutumin cikin karfin gaske.. Tayi sauri ja da baya tana kallon yadda yarima ke saukar wa mutumin nan tagwayen marika..   Mamaki sosai ne ya rufe ta,meyasa yarima ke taimake ta,wacece ita?ita ba kowan kowa ba banza baiwa marar galihu...    Da kyal magaji ya amshi mutumin daga hannun yarima yana mamakin karfin halin sa..gashi kuma wannan deal din da sukazo dashi da kyal ne ya zama successful tunda yarima ya gama kufsa musu...    Dan kasuwan kuwa ba karamin fushi yayi ba dan kuwa kanin sane yarima ya gama jubga,su tafi kawai yace musu zasu ji daga gare sa idan yayi shawara.... Yarima ko a jininsa suka tattara sukayi gaba. Juwairiya kuwa hawaye basu dauke mata ba su rabi ne ke ta lallashinta... ****************** Koda su ka dawo masaukin su yarima kwanciya kawai yayi akan gado yana jin wani abu a cikin zuciyarsa.. tambayar kansa yayi miye dalilinsa na ka're mutumcin wannan yarinyar? Duk yarda yaso ya gano dalilinsa kasa wa yayi... Magaji ne ya shigo yana kallonsa kawai ya girgiza kai.. Zama yayi kusa da shi yace.. Gobe da sassafe zamu koma tunda dai mun zo munyi abunda ya kawo mu sai dai a tunani na kai ma kasan abunda ka aikata ba zai.... Yarima ya tsayar dashi.. Na sani magaji,ba zai amince da deal dinmu ba...amma inaso dan Allah kada wannan lbrn yakai wa su mai martaba ko umma... Magaji ya gyada kai kada ka damu zan gargadi dukka bayin da mukaje dasu.. Yarima yace yauwa sannan ya koma ya sake kwanciyarsa.. Magaji ya mike ya fita kice da tambayoyi a cikin zuciyarsa... "Har dare ya tsala sosai juwairiya na takure a gefe tana fitar da kwalla, se yanzu ne ta fuskanci duk abubuwan da su ummanta ke fada mata.. Ita dai Tsoro takeji sosai,addu'ar ta daya Allah yasa gobene komawarsu, ta koma rumfar bayin ta wajen su ummanta masu sonta,Allah kadai yasan halin da zasu shiga idan sukaji abunda ya faru da ita yau.... Yarima ma dai bai samu barcin ba ko kadan,duk yarda yaso ya samu runtsawa kasawa yayi,yana nan kwance shiru.. Can ya mike yana fadin,ko ta bar kukan yanzu? Ya ja lumfashi hade da mikewa ya saka riga ya fito waje..    A gaban kofar su ya tsaya yana rike da kugunsa,kodai har tayi barcin ta ? Yana kokarin juyawa yaji shashshekar kukanta daga cikin dakin... Tsayawa yayi kawai ya rasa me ya kawo sa wajen ma?zuwa zayyi ya lallashe ta ko me?shi yarima jalal ya lallashi mace!!!! inaa... ai hakan ze zubar masa ki'ma da girman sa ne...yadanyi tsaki yana jin kukanta na ratsa shi a sanyeye ya juya ya koma dakinsa.. *************** "Da safe idanun juwairiya duk sun kunbura dan bata samu runtsawa ba a wannan daren.. Har suka gama shirin su Rabi se faman sake lallashinta takeyi..   Suna gama shirin ne magaji yazo ya sanar Musu da su fito za'a tafi yanzu,juwairiya tayi mamaki da yarima bai kirasu hada masa ruwan wanka ba da safen..   " A tsaye gaban mota suka tarar da shi ya jingina, fuskarsa kawai zaka kalla ka fahimci baya jin dadi sosai.. Juwairiya ta kura masa ido,ya taimaka mata jiya taimakon da ba zata taba san yarda zata gode masa ba... Ji tayi magaji na fadin,yarima ya jikin naka?kodai mu kara kwana ne sai ka kara jin sauki tukun? Gabanta taji ya fadi,bashi da lafiya me ya same shi?kodai ta jawo masa wani babban matsalar ne jiya?    Rabi taji tadan taba ta,suka shiga cikin motar su hankalinta na kan yarima... ************** "Tafiya kawai sukeyi amma juwairiya tunanin yarima takeyi,ta rasa me yasa takejin tausayinsa dan bashi da lfy,tasan ita ba kowa bace a wajen sa,kodan ya taimaka mata ne jiya oho.. Lokacin da suka iso kasar daura dare ya tsala sosai..   Suna fitowa daga cikin mota juwairiya ta hango yarima yayi sashen sa yana tafiya kamar bayaso...     Lumfashi ta sauke,ko ya jikin nasa yanzu? Wai meke damunta ne,yarima ne fa,yarima jalal,me jiran kujerar mulkin kasar daura,yana da wadan da zasu damu dashi da suka fi ta mahimmanci da daraja a rayuwarsa..   Gyada kai tayi,dan kawai ya taimake ni shiyasa na damu da lafiyarsa,ta saki lumfashi tana murmushin jin dadin dowawar ta,kullin kayanta ta dauka tayi rumfar bayi da gudun ta.. Tana shiga duk suka zo suna rungume  ta cike da murnar dawowar ta,hansai ba karamin dadi taji ba ganin diyar ta dawo lafiya... ******************    Washe gari.. Yarima ne zaune a gaban mai martaba.. Sannunku da dawowa jalal ina fatan kun dawo mana da labari mai dadi.. Yarima ya gyada kai,amma munyi dashi akan zai neme mu idan ya yanke shawara.. Mai martaba yace,babu damuwa sai mu jira shi muji ai... Yarima ya mike daidai lkcn da aka sanar da shigowar su Turaki tare da zainaba..        Zainaba ce ta fara gaida shi,a sanyaye ya amsa mata,suka gaisa da turaki kafin ya fito daga bangaren... "Hango ta yayi a tsaye tana wasa da yatsun hannunta da gani jiran zainaba takeyi a wajen.   Haka nan yaji wani sanyi ya ratsa sa hatta ciwon kan da ya tashi dashi se yaji ya tafi bat!..      Ita kam juwairiya tana tsaye ne amma sai taji kamar ana kallonta.. Ta dago a hankali.... Sai Hango shi tayi cikin kayan alfarma kamar kullum,amma mai?sai kawai taji zuciyarta na ayyana mata cewa "yayi kyau" Ta girgiza kanta da sauri ta sake yin kasa da kanta tunda tasan ya tsani ganin fuskarta... Shi kuwa yarima tana yin da kasa da kai sai yaji wani iri,ya tuna yarda yake kyamatar ta a baya..       Juyawa yayi a sanyaye ya fice... ******************** "Surayya na gani a tsaye a gaban sashen yarima,gaba daya hankalinta a tashe yake tunda taji ance ya dawo da zazzabi jiya bata runtsa ba..      Tana hango shi ya tunkaro sashen tayi saurin zuwa wajen sa.. Yarima ya jikin ka? Ya kalleta kawai yayi gaba ya shige ciki..   Surayya ta kalli baiwar dake bayanta,ki jira ni a nan,itama ta shige ciki da saurinta...      Yarima ta iske a kwance yana kallon sama... Ta shigo ta zauna a kusa dashi tana kai hannunta saman goshin sa,zafi taji rau,da sauri ta dauke hannun tana kallonshi cike da tausayawa, a shagwabe tace,zazzabi ne fa a jikin ka.. Yarima ya lumshe ido,shi kansa ya rasa dalilinsa na kin shan magani tun jiya,duk runtse idon da zayyi se ya hango abunda ya faru tsakanin wannan yarinyar da mutumin nan,me ke damun sa ne haka?    Surayya tadan turo baki,ka tashi muje sashen umma kasha magani,kasan dai idan taji baka da lfy kuma baka sha magani ba hankalin ta ne zai tashi... Yarima ya bude ido ya sauke su akan surayya,me yasa bazai so ta bane? Hannu yasa a sanyaye ya shafa gefen fuskarta.. Surayya taji wani irin yaar a gaba daya jikinta..se kallonsa kawai takeyi..ko me ya same shi haka kuma oho?    Ka tashi...ta sake fada a sanyaye. . Yarima ya mike zaune yana fadin.. Kije ki turo min da me maganin kawai.. Surayya cike da murna tace,da gaske? Yarima yayi banza da ita yana juya mata lulu eyes dinsa.. Ta mike da sauri tayi waje.. Shi kuwa yabi bayan ta da kallo.... " _Kuyi hakuri baku ji ni ba jiya,data na ne ya kare,idan nayi subscription zaku ringa jina akan lkc"_ Please Vote [9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 15 Wattpad @afreey101 ************ ".....Bayan sati biyu...."     "Juwairiya na zaune a cikin RUMFAR BAYI, lkcn karfe goma na dare ne amma a cikin rumfar se ka rantse da Allah ko shidda ta yamma batayi ba. dan kuwa sai a lkcn ne suke samun yin duk wata hidimar kan su,irin su wanki,kitso da sauran su...     " Rabi ce ta kalleta tana jefa gyadar dake hannunta cikin bakinta.. Ya dai juwairiya kinyi shiru sai mgn nakeyi kin wani share ni... Juwairiya tayi dan firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data tafi.. Kai Ina fa kinji rabi,kikace mai ma? Rabi takai mata dukan wasa,ai dama nasan uwar shegu kikayi dani.. Laure ce ta karaso wajensu da yan kayanta a hannu..    Juwairiya ta kalla tana narke murya,diyata ga ka'ron wankina.. Juwairiya ta zunboro baki,goggo laure duka duka fa sati biyu kenan danayi miki wanki.. Laure tace,ke yar gari yo ni wanki har nawa nayi miki da kina yar jaririyarki uhm! Juwairiya ta juyar da kai,laure takai mata duka tace,ni kike juyawa ke'ya?yar fama kawai.. Hansai ce ta karaso wajen nasu, ta kamo hannun juwairiya, sannan ta kalli laure,babu ruwanki da diyarta ,wanki kuma bazatai ba,ai ba ajiyeta kikayi ba,muje ya'ta,laure ta rike baki,ni hansai?ni hansai?lallai ina nan zamana zaku dawo ai,kici gaba da shagwaba ta kema sai tace baki isa ba... ta ja tsaki ta juya tayi gaba.. Juwairiya da hansai suka shige daki suna mata dariya.. ************** "Da sassafe ranar alhamis juwairiya tayi shirin ta tsab sannan ta wuce wajen uwar dakin ta.. Tana shiga sashen zainaba ta same ta a zaune.. Ta gaishe ta tana kokarin shigewa ban dakine zainaba tayi saurin kiranta.. Juwairiya zo kiji.. Tazo ta duka har kasa tace gani.. Zainaba tace so nake kije min gidan waziri ki amso min wasikar da Mustapha ya aiko min da ita jiya,juwairiya tayi murmushi wato baki manta da ranar ta yau ba kenan? Zainaba ta murmusa tana gyara zaman ta,ni kaina mamaki nakeyi wlh,kullum cikin addu'ar Allah ya kawo min wannan ranar nake,tunda yace min ze aiko min da lambar wayar su ta landline gaba daya na zaku dana kira naji muryar sa.. Juwairiya ta saki baki cike da mamakin kalaman zainaba.. Zainaba ta taso ta rufe mata bakin tana dariya.. Juwairiya tayi murmushi sannan ta mike tace toh bara naje na dawo, da sauri ta juya ta fice..... ************** "A nutse take tafiyar ta har ta fito babbar kofar masarautar,can ta hango su a tsaye tare da wani bawa (wato yarima da magaji kenan) Da sauri ta dauke kanta sannan ta karawa tafiyar tata sauri...    Magaji ne ya fara hango ta,ya kalli yarima yana sosa kashin kansa yace,ni fa wancan yarinyar se na riga gani kamar na santa a wani waje..   Yarima ya kalli gefen da magaji ke nuna masa... Can ya hango ta sai buga sauri takeyi kamar zata tashi sama.. "Ina zataje?" Ya fada acikin zuciyasa... Magaji ne ya dafa sa ganin hankalin sa baya tare dashi.. Muje mana kasan fa yau inna ta hada abinci damu kuma tace dole na taho dakai,rannan haka kayi min wayo naje nasha fada na.. Yarima yayi murmushi dan kuwa yana jin dadin abincin innar sosai,kai fa ka cika korafi dayawa,ko ranar ma ai umma ce ta tsare ni a sashen ta,magaji yace,naji din muje dai kada muyi rana....    "Juwairiya har tayi musu nisa sai ji tayi kawai ta taka wani abu a kafarta.. da sauri ta dage kafar tana sakin ihun azabar da taji.. Waje ta samu ta zauna tana dago da kafar ta duba me ya tsake ta haka..     Wata kwalba ce kuma ba kadan ba ta fasa mata kafar se jini ke fita.. Kuka sosai juwairiya keyi tana rike da kafarta ta... ************* Yarima da magaji na tafe suna yar firar su sai jin shashshekar kuka zasuyi acan gefen hanyar.. Magaji ya girgiza kai,yanzu haka yaran nan ne masu guje guje a hanya.. Yarima yakai dubansa inda sautin kukan ke fitowa..     Caraf ya hango ta a zaune rike da kafarta se jini ke fita...    Gabansa ne ya fadi.. Me ya same ta? Da gudunsa ya karasa wajenta magaji na kiran shi amma inaa...bai ma san yana yi ba.. Juwairiya kuwa ji kawai tayi ya fisgo kafarta.. A tsorace ta dago tana kallonsa cike da  mamaki.. 'Yarima?'...ta fada a ranta... Ai da sauri ta kwace kafar ta zube kasa a mutukar tsorace... Kayi hakuri ranka shi dade,amma kama kafar baiwa iri na kaskanci ne a wajen ka... Yarima ya tsaya yana kallonta,tun daga kan kafafunta da babu ko takalmi,zuwa kayan jikinta kodaddo har kan fuskar ta... Lallai ko mahaukaci ya kalleshi ya kuma kalli juwairiya sai ya fahimci level dinsu ba daya bane ko kusa,yarima yafi karfin yarinya irin juwairiya, ko ma a matsayin SA'DAKARsa bata kai ba.. Amma meyasa ya damu da ita ne haka? Ya mike tsaye yana daure fuska,sannan yana jin haushin abunda ya aikata yanzu.. Juwairiya taji yayi shiru hakan yasa ta dago tana kallonshi.. Ita yake kallon shima,da sauri ta maida kanta kasa tana jin azabar zafi a kafarta... Magaji ne ya karaso wajen shima.. Lafiya yarima wai baka ji ne ina ta kiran ka? Turus yayi ganin yarima tare da wannan half burned face din...     Juwairiya ta sake fadin,ka gafarceni ranka ya dade nayi sanadiyyar tsayar daku daga uzurinku,tana gama fadin haka ta shiga kokarin mikewa tana matse baki...      Ji tayi kawai an kamo hannunta... Ba ita ba har magaji se daya kalli yarima da mamaki..   Yarima ya maida ita inda take a zaune... Wani kyalle ya fito daga cikin alhujin wandon sa ya mika mata.. Juwairiya duk a tsorace take,wai meke damun yarima ne?me yasa yake yi mata haka?bai san cewa yafi karfin ya kyautata mata bane? Me yasa yanzu yake nuna kulawa a gareta?ita dai tsoro takeji idan aka gansu a nan fa?wayyo Allah idan gimbiya kilishi taji wannan lbrn kashin ta ya bushe...     Yarima kallonta kawai yakeyi jikinta har rawa yake sbd tsoro,idanunta cike da kwalla. Ya ajiye mata kyallen a jikinta sannan ya mike tsaye baice komai ba yayi gaba... Magaji ma yabi bayansa... Kallon kyallen tayi se fitar da kamshi yakeyi,me yasa ya ajiye mata shi? Ta shaki kamshin dake jiki... Yarimaaaa me ke damunka kwanan nan ne? Har ta mike taji kafarta na mata zugi,ta kalli kyallen yarima se lkcn ta fahimci me yasa ya bata kyallen,dan ta daure kafar ta ne.. Ina zata iya saka wannan kyallen me kyau da tsafta ta daure kafarta me datti.. Wani ganye ta dauka ta yagi rigarta kadan ta daure kafar dashi...sannan ta fara tafiya da kyal da kyal tana rike da farin kyallen a hannunta... ************** Inna na zaune a tsakar gida tana dibar ruwa a cikin kofi su magaji sukayi sallama suka shigo.. Da fara'ar ta sosai ta amsa musu tana zolayar yarima.. Ango shikenan sai aka yarda mu ko? Yarima na murmushi ya zauna akan taburmar dake shinfide a tsakar gidan..    Magaji ne ya amsa innar da cewa.. Inna baki ga har wani haske ya kara bane? Inna tayi dariya,sannan ta kwalawa khadija kira..     Khadija kuwa dama tana jin muryarsu ta jawo kayan kwalliyarta ta shiga shafe shafenta.. Inna na kiranta ta gyara kayan jikinta ta fito... Idanunta kyam akan yarima...tace.. Ya jalal ina wuni? Ya dago a hankali yace lafiya kawai yana tunanin ko wannan sukuwar yarinyar ta gane manufarsa na bata kyallen oho..   Inna tace maza khadija shiga madafa ki dauko musu abincin su.. Khadija ta juya cike da yanga zata shige madafar kenan taji muryar juwairiya tana rangwada sallama... Da sauri ta juyo tana kallonta..   Yarima da magaji ma sunyi mamakin ganinta a gidan... Idanun yarima a kafarta suka sauka.. Ganin babu kyallen se wani ganye a kafarta yasa yaji wani iri a zuciyarsa,yasan tsoro ne ze hanaka daure kafar dashi... Amma hakanan se yaji babu dadi.. Har zai dauke kansa ya hango kyallen a hannunta ta rike shi gam cike da daraja.. Murmushi kawai ya saki ba tare da ya sani ba..    Juwairiya ta karasa ciki tana gaisar da inna.. Inna ta amsa mata a sake tana tambayar ta me yasame ta a kafar.. Kwalba ce na taka.. Ta fadawa inna a sanyeye.. Yarima kuwa gaba daya hankalinsa na kansu..    Khadija ta shige kicin ta dauko musu abincin ta ajiye a gabansu,sannan ta karasa wajen juwairiya tana fadin,ayyah JUWAIRIYA sannu... Yarima yaji gabansa ya buga JUWAIRIYA ya maimaita sunan,dama sunan ta kenan?ashe tana suna?wani irin dadi sunan yayi masa....JUWAIRIYA maimaita sunan babu adadi a cikin zuciyarsa...... "Khadija kuwa sbd ta burge yarima yaga ita me tausayin bayi ce,sai ta ce,zo ki zauna na saka miki magani.. Ta jawo hannun juwairiya.. Juwairiya ta shiga girgiza kai ah ah ki barshi kawai babu komai,sakon zainaba ne nazo na amsa nasan tana jirana sauri nakeyi...   Khadija zatayi mgn se ji sukayi ance... "Me yasa kika fiye gardama?! Da mamaki duk suke kallonsa.. Ya dauke kai yana bude kwanon dake gabansa...kamar bashi ne yayi mgnr ba. Khadija mamakine ya kashe ta,wai yau yarima jalal ne da kansa ke tsoma baki acikin mgnr da bata shafe shi ba,mai?"me yasa kika fiye gardama" yau she yasan juwairiya da har yasan ta fiye gardama din?oh!tafiyar su ko?toh amma a yan kwanakin ne har yasan ta haka?kishi ne ya cika zuciyarta..   tunani kala kala khadija keyi har bata lura da inna harta bawa juwairiya wasikar ba ta mike zata fice.. Da sauri ta sha gabanta,haba juwairiya baki ga yarda kafarki ta fara kunbura bane?ta fadi da yanayin tausayi tana kallon yarima da gefen idonta.. Juwairiya ta dan kallo inda su yarima suke zaune har sun fara cin abincinsu.. Hada ido sukayi dashi,tana kokarin dauke idonta taga ya mata wani irin kallo,hakanan taji gangar jikinta ta fahimtar da ita me kallon nasa ke nufi.. (na amince da taimakon khadija) Khadija tace muje mana... Nagode juwairiya ta fada ta dawo ta zauna..    Khadija ta juya gunsu yarima tana matse muryarta tace.. Ya magaji ina wannan maganin naka? Magaji yace ki duba cikin dakina.. Khadija ta mike ta nufi dakin.. Magaji kuwa mikewa yayi shima dan karo musu miyar fankasun da suke ci..    Aka bar yarima da juwairiya a wajen su kadai........ _"Team RUMFAR BAYI ina gaisuwa,nagode da addu'o'in da kuke yimin,sannan ina ganin comments dinku i rlly appreciate alot,thanks alot,Allah yabar zumunci.._ *Team juwairiya*90% *Team yarima*70% Keep Sharing Voting And Commenting [9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima:           *RUMFAR BAYI*       (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 16 Wattpad  @afreey101 ***************** "Me yasa bakiyi amfani da kyallen dana baki ba?"    Juwairiya taji muryar sa me dadin saurare a bayanta yana mgnr kamar bayaso dan itama zuciyarta na wajensa da bazataji me yace ba..   Juyowa tayi kanta a kasa kafin tace a sanyeye.. Kayi hakuri ranka shi dade amma bazan iya daure kafata da abunda ya fito daga hannunka ba,dan ko kadan ban kai wannan matsayin ba..   Yarima ya jinjina kai..sannan yace da ita, Daga yau duk umurnin dana baki ina so ki bi shi inda har kin dauke ni a matsayin da nake din.. juwairiya ta gyada kai da sauri.. Kinci abinci? Tambayar tazo mata a ba zata.. Juwairiya taji kamar ta nutse,miye na sa wai idan taci abinci ko bata ci ba..   Girgiza kai tayi.. Yadan ja lumfashi idan kin koma cikin masarauta ki same ni a sashena... Zatayi mgn taji karasowar khadija... Khadija ta mika mata maganin tace ta shafa,ta amsa da hannu biyu ta shafa ,sannan khadija da kanta ta daure mata kafar.. Godiya sosai juwairiya tayi mata sannan ta fice.... *********** "Har ta kai wa zainaba wasikar amma ta rasa taya zata je sashen yarima,me yasa yace mata taje?tunani ne ya cika ta sosai har bataji firar da zainaba ke mata ba..   Zainaba na lura da ita tace,lafiya juwairiya ko kafar ce?.. Kije kawai ki huta zuwa anjima. zansa fulani ta aiko min da wata baiwar.. Juwairiya ta samu kanta da jin dadin hakan.. Ta mike tayi mata godiya kafin nan ta fice.. *************** "Tana fitowa daga sashen sukaci karo da turaki zai wuce ..   Tayi saurin gaishe sa.. Ya amsa yana kallon kafarta.. Ciwo kikaji ne haka?ya fada cike da kulawa.. Juwairiya tace eh dazune wlh.. Turaki yace ayyah,muje na baki magani kiyi amfani dashi.. Juwairiya zata fara mu'sa masa sai kawai yayi gaba,dole tasa ne tabi bayanshi.. 'Tafiya kawai takeyi,amma hankalinta na kan umurnin da yarima ya bata na zuwa sashen sa...       Suna shiga sashen a bakin kofa taja ta tsaya,turaki ya shiga ya fito mata da maganin,amsa tayi tana masa godiya... Turaki ya saki murmushi yace, ki rin ga kula da lafiyar ki.. Juwairiya ma murmushin tayi tace nagode sosai yaya turaki.. Juyowar da zatayi ta hango yarima da hamza a tsaye zasu wuce..   Idanuwansa a kanta.. Gaba daya taji wani irin faduwar gaba.. Yarima ya dauke kai kamar bai gansu ba yayi gaba abunsa... ******** "RUMFAR BAYI ta nufa kai tsaye babu wadu bayi dayawa a ciki,dakin du'bu ta shiga,ta tarar itama bata nan.. Komawa tayi dakinsu ta canza kayan jikinta sannan ta zube akan taburma.     Da sauri ta mike ta dauko kyallen da yarima ya bata dazu tana kare masa kallo,wata zuciyar na tunashe ta  umurnin sa na zuwanta sashen sa.. Ta mike da sauri ta fito kai tsaye tayi sashen nasa..    Ta dade a waje tana tunanin ko kada ta shiga..     Can dai ta tayi shahada ta shiga tana addu'a Allah yasa ba wani laifin tayi masa ba. bawan dake waje ne ya sanar da shigowar ta...     A sanyaye cike da tsoro ta shiga falon da sallama..    Zaune yake ya lumshe idonsa.. Ta samu waje ta takure sannan tace.. Ranka shi dade gani nazo.. Har cikin ransa yaji sautin muryar ta.. A hankali ya bude ido ya sauke su akanta..   Juwairiya tayi saurin dukar da kai.. Yarima yace,zauna yana nuna mata waje a nan kusa dashi kadan.. Juwairiya ta kalleshi taga yarda ya tsare gida dole yasa taje ta zauna wajen a takure.. Yarima bai bata lkc ba ya kwalawa bawansa kira.. Se gashi ya shigo cikin saurinsa.. Yarima ya fada masa dayaje ya sanar da du'bu a can rumfar bayi a kawo masa abincinsa yanzu.. Bawan ya amsa da toh kafin nan ya fice.. Juwairiya dai ta rasa me zatace masa,yace  mata tazo sashen sa amma ya ajiye ta a nan yayi shiru,ga ciwon dake kafar ta yana dan damunta kadan kadan... A wajen Yarimakuwa  ya rasa meke damunsa,me yasa yake son ganin wannan yarinyar a kullum ne kusa dashi?me yasa ta dame sa har haka?     Yadan kallo ta, tsoronsa ma takeyi daga gani,yaja lumfashi me dumi,kafi karfin baiwa kamarta yarima...ya fadawa kansa..       Haka yayi ta tunani a zuciyarsa har bayi suka shigo da abincin jere a cikin tiren silver. sai faman kallon juwairiya sukeyi cike da mamakin ganinta a sashen. balle kuma a inda take zaune dan kuwa basu da hurumin zamaa  wajen,balle kuma wai tare da yarima cab...!     Suna gama shirya abincin suka fice bakin su kunshe da gulma iri iri..     Juwairiya ta lura da hakan dan kuwa tasan a Rumfar bayi gulma kala kala ake kawo musu.. Ta tabbata sai lbrn zuwanta sashen yarima  ya kai wa ummanta..    Ta kalli yarima shi kam ko a jikinsa ma.. Mikewa tayi da sauri tace,uhm ranka shi dade bari na zuba maka abincin.. Jiki na rawa ta kai hannun ta dan daukar plate dake ajiye gabansa..    Sai jin saukar lausassan hannun yarima tayi akan nata..   Tsikar jikinta ce ta tashi.. Gabanta na faduwa ta kalleshi ido a bude... Yarima ya motsa bakinsa,duk da shima baisan dalilinsa na taba jikinta ba kawai dai bayajin yin mgn ne kuma yana so ya tsayar da ita daga daukar plate din. Ki barshi...ya fada yana dauke hannunsa daga nata.. Juwairiya tace toh! Zan iya tafiya? Yarima ya girgiza kai ,zauna kici...ya nuna abincin dake gabansu. juwairiya ta waro ido ta dafa kirji Ni? Yarima yace me kika dauke ni?Giwa?baki ga naci abinci bane dazun? Juwairiya tayi wiki wiki da ido,nima zanci anjima...ta fadi kamar zatayi kuka.. Yarima ya daure fuska,umurni ne nake baki ba zabi ba... A sanyaye ta zauna.. Yarima ya basar abunsa... Juwairiya ta kalli delicacies din dake gabanta, miyau ta hadiye dan rabonta da abinci tunda safe da suka karya..   Ta kalli gefen yarima taga ya dauke kai gefe.. Abincin ta diba ta hau ci da saurinta dan ta samu ta tafi da wuri..    Yarima yayi murmushin gefen baki. Tana kammalawa ta mike,nagode zanka shi dade Allah ya baka kujerar mulkin daura..   Ya saki murmushin da bai san lkcn daya subuce masa ba.. Juwairiya mutuwar tsaye tayi...dan bata tunanin ta taba ganinsa yana murmushi haka,kyau da kwarjini yayi mata har bata san ta kafe shi da ido ba.. Yarima ya kalli kafarta... Na lura kin samu masu baki magani dayawa ko? ba sai na baki wani ba...   Juwairiya ta dauke idonta tana kallon kafar,murmushi ta saki tunawa da kyallen daya bata dazu..sai ta kwanto shi daga zaninta ta mika masa.. Ga wannan Allah ya baka yawan rai,nagode kwarai da gaske...   Yarima yabi kyallen da kallo.. Sannan ya mike yazo kusa da ita ya tsaya..      Bana amsar abunda na bada a matsayin kyauta.. Juwairiya ta dago da sauri,kyauta ya bata?ita juwairiya har ta kai yarima ya bata kyauta?       Yarima ya lura da mamakin furucin sa takeyi,yace zaki iya tafiya.. Juwairiya ta juya da sauri tayi waje... ************* "Tana shiga tafe tana tunane tunane,har ta kawo wajen ajiyar dawakai,hango mahaifinta tayi yana bawa dabbobin abinci... Ai da sauri da gudunta ta karasa wajensa... Lah baba! Ta fadi da karfi.. Ya juyo cike da farin cikin ganin ta,juwairiya kece haka? juwairiya ta saki dariya baba yaushe ka dawo?shine umma bata sanar min da dawowarka yau ba?ta karashe mgnr cike da shagwaba..   Baba ya kamo hannunta,jiya da daddare na samu dawowa,juwairiya tace nayi kewarka baba sosai,ka tafi ka barmu... Baba yayi murmushi kiyi hakuri juwairiya kinsan fa cewa sarki da kansa ya bani umurnin tsayawa a can kasar kanon ta dabon,sannan shima mai martaba na can yaki barina na dawo kasata akan lkc, yanzu ma haka sati daya kacal zanyi na koma.. Juwairiya ta jinjina kai,su kenan basu da yan'ci sai yarda akayi dasu,gsky BAUTA batayi ba... Zama tayi a wajen babanta suka sha fira har yamman dare sannan ta koma rumfar bayi... "Tana shiga laure tazo ta fisgo ta cikin karfi,da mamaki take ta kallon yarda take ta janta  har suka shige daki... hansai na a zaune ta buga uban tagumi...    Miye haka goggo laure?juwairiya ta tambayeta... Laure ta kai mata dankwashi akai,ubanki ne !wato ke juwairiya duk yarda muke jan kunnenki ba zaki san matsayin ki ba ko?   Juwairiya tace,na sani mana...me akace nayi kuma?tayi mgnr a sanyaye..dan tasan ruwa baya tsami banza.. Hansai tace,me ya kaiki sashen yarima? Baki san waye shi bane? Acikin wannan watan fa zai zama sarkin daura !!!yafi karfin yarinya irin ki!bakya tausayin rayuwar ki ko!??? Juwairiya ta kalli hansai da mamaki,tace sarki? Laure tace,kwarai kuwa,mai martaba zayyi murabus ya basa mulki kwanan nan!... Hansai ta kamo hannunta, juwairiya a kullum ina fada miki,ke Baiwa ce!ki kare mutumcin kanki... Juwairiya tayi murmushin yake,na fada miki umma ki yarda dani,kawai fa sako naje amsa a wajensa,kuma shi ya umurceni dana je wlh.. Laure tace,ki kula dai kinsan haukan kishin matarsa atooh.. Juwairiya ta gyada kai zan kula goggo... ************** "Gimbiya kilishi ta kalli fulani diyya suna zaune a fadar mai martaba. ina ganin tunda lkc ya matso kusa ya kamata mu fara shirye shirye a kan lkc.. Fulani tayi murmushi, hakane zan saka turaki ya hadu da hamza se suyi duk abunda ya dace.. Mai martaba ya murmusa, sai dai nima akwai alkawarin da nake so na cikashi a wannan babbar ranar.. Kilishi tace,muna jinka.. Mai martaba yace,akan auren yarima ne da diyar waziri nasan kun san da wannan mgnr amma ina ganin kamar lkc yayi dana cika alkawarin dana dauka shekaru dayawa da suka wuce,tunda dai anyi auren sa na farko .. Kilishi tadan tabe baki,hakane tunda ya zama dole mu cika wannan alkawarin.. Fulani tayi murna sosai tace,lallai yarima ya cika dan gata,mai martaba yace,ai da mun gama dashi zamu zo kan sauran suma,sbd dai akwai diyar galadima da nake so a hada da shi hamza,shi kuma turaki nayi masa mgnr jikar sarkin zazzau... Kilishi murmushin yake tayi dan ita kam tana wa hamza tanadin diyar sarkin katsina,mai zanyi da wata diyar galadima lallai kam.... "har an gama mgnr su kenan suma?fulani ta tambaya cikin tsantsar farin ciki .. Mai martaba yace kwarai kuwa lkc kawai nake jira.. Fulani tace toh Allah ya kaimu lfy.. ************** Surayya ce ta karaso cikin lambun cike da fara'ar ta,yanzun nan ta samu labarin na'din yarima da za'ayi a karshen satin nan...    Hango sa tayi a tsaye yana karewa wasu tsuntsaye kallo...   Ta karasa da saurinta ta rungume sa ta baya tana murna sosai..   Yarima yana jin kamshin ta ya gane itace.. Surayya tace,ina taya ka murna sosai sarkina... Yarima yadan murmusa,kodai kina taya kanki murnar zama gimbiyar daura?... Surayya ta dawo gabansa,duka biyun daidai ne... yarima ya gyada kai.. Surayya ta kamo hannunsa,sai yaushe zaka bani damar shiga zuciyarka? Yarima ya kura mata ido,surayya ta karkace kai,naji lbrn aurenka da diyar waziri,hawaye suka taro a cikin idanuwanta.... Yarima yace, na zata duk wannan bazai dame ki ba... Surayya tace,inji wa?ai duk mulkin mace bazaso ayi mata kishiya ba.. Yarima ya jinjina kai.... ************ Juwairiya tare da zainaba suna tafe sai lbrn wasikar da Mustapha ya aiko mata take bata... Suna kawowa kofar lambu zainaba tace,mu dan shiga naji kukan tsuntsayena,ta janyo hannun juwairiya suka shige ciki....   "Turus sukayi ganin yarima da surayya rungume da juna... "Juwairiya taji gabanta yayi wani irin muguwar faduwa har se da ta saka hannu ta dafe shi..   Zainaba kuwa sakin baki tayi..ganin basu ma ji shigowar su ba yasa tace, sannunku masoya...!   Da sauri duk suka juyo suna kallonsu.. Yarima idanuwansa akan juwairiya dake tsaye ta dauke kanta gefe,haka nan takeji zuciyarta wani iri,meye nata aciki dan kawai miji da mata na more rayuwar su..tasan dai ita harta mutu bazata samu wannan ba..    Zainaba tace,lallai yaya ashe haka kake kaima? Yarima ya banka mata harara,sannan yace me ya kawo ki nan? Zainaba ta kamo juwairiya dake tsaye kamar an shuka ta,laah toh kuyi hakuri idan dan mu ne yanzu ma zamuyi tafiyar mu.. Surayya sai wani murmushi takeyi,tazo zata kamo hannun yarima,ya kauce yana sake kallon su juwairiya dake shirin barin wajen..    Zainaba! Ya kira sunan kamar me koyon mgn,zainaba cike da mamaki ta juyo dan kuwa ta dade bataji yayan nata ya kira ta da sunanta ba..   Ta dawo gabansa tace na'am yaya.. Yace inaso ne kiyi min wata alfarma, zainaba tace ina jinka yaya... Ki bani waccan....! Ya nuna saitin da juwairiya take a tsaye..     Ba zainaba ba har surayya da juwairiya se da gabansu ya fadi.. Sai a lkcn ne surayya ta shiga scanning din juwairiya tana jin wani irin tsanarta ta dasu a zuciyarta, wacce baiwa ce har ta isa ta saka yarima ya bukace ta... Ruwan harara ta shiga zubawa juwairiya, ita kuwa baiwar Allah ma bata san tana yi ba..     Zainaba da mamaki tace,wa kake nufi yaya,dan a iya sanina baka ma son ko ganin fuskar juwairiya... Yarima ya kasa amsa mata dan kuwa sai a lkcn ne ya fara jin haushin kansa,me yasa ya bari mgnr ta fito daga bakin sa... Gani sukayi kawai ya wuce abunsa kamar bashi bane yayi zancen.. Surayya ma tazo wucewa zuciyarta kamar ta fashe..ta tsaya daidai saitin juwairiya sannan taja dogon tsaki tayi gaba.. Zainaba tace oh iko sai Allah... ************************ WATTPADIANS _"Announcement- its a RUMFAR BAYI GIVE AWAY..._ _Get 5 people to add n vote for RUMFAR BAYI on wattpad"_ _"Your reward- you will always be the first reader of every page i write till the end of the story inshaAllah "_ _Am waiting fans,all the best to the 2 winner's_ [9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:          *RUMFAR BAYI*       (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 17 Wattpad @afreey101 *************** "Gidan waziri suka shiga,mutane har sun fara tarowa kasancewar yau ne sa lallen khadija.. A dakinta suka tarar da ita tasha gyaran jiki se fitar da kamshi takeyi...    Tana ganin zainaba ta fada jikinta tana murna sosai.. Zainaba tace,kai duk murnar auren ya yariman ne haka? Khadija ta dago tana murmush sosai, kema ai kin sani,mafarkin da na dade inayi gashi har ya kusa zamowa gsky. na kusa mallakar rabin raina,ta kamo hannun zainaba, zainaba gobe yarima  zai zama mijina,ina tunani a duk duniyar nan babu wanda tafi ni farin ciki...     Surutai kawai khadija ke sakar musu cike da tsantsar murnar ta. juwairiya kam gaba daya taji jikinta yayi sanyi,ta rasa dalilin da yasa duk lkcn da khadija zata ambaci sunan yarima toh sai zuciyarta ta buga..     Ganin zaman na neman gagararta ne sai ta mike kawai ta fito waje.. Mata ta iske cike da tsakar gidan ana ta faman girke girke..    Ji tayi kamar lumfashin ta baya fita sosai.. Da gudu ta bar cikin gidan ta karasa can bayan gidan kusa da ra'fi mai gudana da ruwa...     Sauke ajiyar zuciya takeyi sosai,wai meke faruwa da ita ne,me yasa take mafarkin yarima? Meye hadinta dashi?yafi karfin ta me yasa zuciyarta bazata bar tunaninsa ba..!     Zama tayi a wajen saman grass, jin iska na kadata sai lumshe ido takeyi... *************** "Ango kasha kamshi! Magaji ya fada yana washe baki.. Hamza yace,ai yaya kai kam dan gata ne wlh mata biyu cikin wata biyu kacal.. Turaki yayi dariya,yarima ya banka musu harara,sannan ya amshe alkyabbar sa dake hannun magaji yana tayashi shiryawa..      Hamza yace,gsky wannan sa lallen ya kamata mai martaba ya bari mu dan cashe ko ya kuka gani?.. Turaki ya kai masa duka,kai fa hamza dan duniya ne wlh,a ina ka taba ganin maza sunyi rawa a sa lallen? Hamza ya mike yana fadin,ba sai a fara a kan mu ba,ni dai Allah ya gani gobe  A na'din sarautar ya yarima se na cashe abuna,kasan fa har wannan mawakin na dauko dake can kasar nijar.. Magaji yace,kai hamza akwai son bidi'a,duk suka saka dariya..    Daga waje ne aka shiga sanar da shigowar da surayya.. Duk suka kalli juna suna murmushi, kafin nan suka mike,magaji yace,a lallaba mata ita don Allah... Yarima ya tabe baki yana basarwa.. Suna fita ta shigo cikin adonta sai baza kamshi takeyi...     Kallon juna sukayi,yarima ne ya fara dauke idonsa yana kokarin saka hular sa.. Da sauri taje ta amshe hular sannan tayi murmushin yake tace.. Wannan aikina ne ... Yarima yace,sai yau kika sani kenan? Surayya ta turo baki,toh kana kiran na ne na saka maka? Ya wani basar yana fadin,naga kinsha shiri sai ina? Surayya ta dan harara shi,ina fa?gidan amaryar zamuje dasu umma.. Yarima ya jinjinawa makircin surayya,sannan yayi murmushi ya fice abunsa ya bar nan cike da takaici..   Surayya ta jefar da yar jakar dake hannunta, cike da fusata tace, dole ne nasan abunyi,ya za'ayi ace kamar ni yarima yake wulakantawa son ransa,sannan hakan bai isa ba ma ko shekara banyi da aurensa ba zasu sake aura masa wata?   Ta tuna zancensu da yakumbo,lkcn data fada mata mgnr juwairiya..  _ ''Miye abun tashin hankalinki akan wata banzar baiwa can ke da za'ayiwa kishiya cikin kwanan nan,idan har kinaso ki siye zuciyar yarima toh ki tabbatar kece kika fara haifa masa Da wanda ze ga'je shi a mulki"_   "Surayya ta ciji lebenta na kasa,taya zata samu damar wani haihuwa bacin sai yarima yaga dama yake kwana da ita,dole ne ta san abunyi,dan ta lura gimbiya kilishi ma zata iya juya mata baya indai har wannan yarinyar ta shigo kuma ta rika ta haihuwar... ************** "An gama dukkan shirye shirye na sa lallen khadija.. Surayya , Fulani diyya ,gimbiya kilishi tare da sauran matar sarki ne suka zo gidan, tare da su jakadiya,du'bu da kuma sauran bayi dayawa dan kawo musu lallen amarya.. "Bayan an zauna ne sai ga tawagar su yarima tare da abokansa da kuma yan uwa.. Nan aka tanadar wa amarya da ango wajen zamansu kamar yadda al'adar tasu take,sannan aka fara gudanar da event din,su jakadiya ansha gu'da,hansai sai raba idanu take ko zata dan hango diyarta amma bata ganta ba. ko ina ta shige oho?.          Zainaba dake rike da hannun khadija ta shiga neman juwairiya dan ta dauko mata wani sako a dakin khadija data manta. "A tsakiyar su khadija da yarima dake zaune taje tace a hankali, khadija kinga bari naje na dan duba juwairiya tun fa dazun ban sa ta a idona ba ko gida ta koma oho?amma nasan ma da kyal ne ta koma can bata nemi izini na ba.. Khadija tadan tabe baki,toh shikenan amma kada ki dade dan Allah,zainaba tayi murmushi kada ki damu yanzu zan dubo ta na dawo... Duk wannan zancen nasu yarima yanaji..    Ina take?ya tambaya a cikin zuciyarsa sai lkcn ne ya lura da bata a wajen,hakanan yaji yana son yasan ko tana lafiya,zuciyarsa ke ta azazzalar sa...    Kallon turaki yayi dake kusa dashi.. "ina zuwa" bai bari ya amsa masa ba kawai yayi gaba abunsa... Gimbiya kilishi na lura da tashin da yayi daga wajen,ina zai je?ta tamabayi hansai dake gefenta,hansai tace,gimbiyata wata kila ban daki zai shiga,kilishi ta jinjina kai cike da gamsuwa.. Shi kam yarima fita yayi yana ta dube dube,lkcn har duhun yamma ya farayi...    ************** Juwairiya kuwa barci ne ya dauke ta a wajen dan dama bata samu barcin kirki ba a daren jiya...     Yarima na zagayawa bayan gidan ya karasa gaban rafin yana sauke lumfashi.... me yasa zai damu kansa sabida wata baiwa can? Yaja tsaki yana shirin juyawa sai kawai can ya hango ta...ta jingina a jikin wani bishiya tana ta sharar barci a takure..      Karasawa yayi wajen ya kura mata ido,zuciyarshi yaji wasai ganin tana lfy,amma wannan barcin fa?   Bakinta yaga yana motsi... Ya duko sosai ahankali kusa da fuskarta dan son jin me take fada... Ya..ri...ma.....! Yaji ta furta.... Ware ido yayi cike da mamakin jin sunansa a bakinta.. Murmushi ya saki yana kare mata kallo,tabon fuskarta ya kalla yana son yaji dalilin da yasa take yin sa?       Bai ankara ba sai gani yayi ta bude idonta tangaram a kansa..     A tsorace take kallon sa... Shi din ma yadan tsorata da ganin ta bude idonta,yana kokarin gyara tsayuwarsa kawai yayi loosing balance dinsa sai tim! Ya fadowa juwairiya ajiki suka zube a kasa su duka..    Wani irin kamshi ne ya mamaye hancin ta,taja lumfashi mai karfi,nauyin yarima ne yasa tayi saurin dago da idonta. Hada ido sukayi,ta hada duka karfinta ta sa hannu ta ture shi gefe...   Yarima ya lumshe ido yana jin wani irin yanayi yana ratsa shi..    Juwairiya tayi saurin mikewa tana kallonsa.. Sai kuma Da sauri koma ta zube a kasa tunawa da tayi waye ta ture yanzun nan,yarima jalal ne fa....    Allah ya huci zuciyar ka,kayi min afuwa...    Yarima ya mike yana kakkabe kayan dake jikinsa...      "Ni kika ture a kasa? Juwairiya a tsorace tace,kayi hakuri ranka shi dade, kayi min rai... Yarima yadan murmusa, me kikeyi a nan? Juwairiya a zuciyarta tace,kai ya kamata na tambaya ai,me kakeyi a nan bayan ana can ana sa lallen amaryar ka....!       kallon da yake yi mata ne yasa ta fuskanci katobarar da tayi,wato mgnr zucin da takeyi ta fito fili kenan?wayyo Allah ta shiga uku.. Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta,gani tayi ya tako zuwa gabanta,kirjinta na ta bugawa ...jitai yace,    "Kina son sanin meyasa na baro amarya ta nazo nan? Juwairiya ta waro ido tana girgiza kai.. Murmushi yayi,juwairiya ta kura masa ido kyaun sa na kashe ta.. Bai sake cewa komai ba yabi ta gefen ta ya wuce abunsa...... "Thanks fans,i can see that some of you r doing well with the GIVE AWAY" Please Vote And Share [9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:         *RUMFAR BAYI*      (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 20 _"Congratulations to my 2 winners @530_khadeejat and @haliemahtou_ _Thanks alot for ur effort i really appreciate muah😘_" ************* "Rabi na fitowa jakadiya ta tare ta,har kin dauko sakon ne? rabi da jikinta ke rawa tana tsoron kada layar dake jikinta ta fado a gani tace,uhm na dauko,jakadiya tace,sai kuyi haramar komawa ina ita juwairiyar? Rabi kam sauri kawai takeyi tabar wajen dan haka tace ai ta dade da tafiyar ta,bata jira me jakadiya zata sake ce mata ba kawai tayi gaba abunta..    Tana fitane,jalal ya shigo dasu shamaki a bayansa,TAKAWARKA LAFIYA TORON GIWA...! Jakadiya ta shiga wa'sa jalal itama, sabon sarki mai mulkin zamani,an shigo lafiya? Jalal ya daga mata hannu kawai yayi shigewar sa ciki..    Direct kofar wajen shakatawar sa ya nufa dan anan ne kawai yake iya samun privacy dinsa. yana bude kofar ya lumshe idonsa hade da jingina bayansa a jikin kofar daya kulle...     Juwairiya dake tsugunne a gaban flowers sai ji tayi kawai an rufo kofa gam!. A tsorace ta juyo.... Sai ganin jalal tayi a tsaye ya lumshe idonsa,ya kuma daura hannunsa daya akan goshinsa.. sanye yake cikin manyan kaya na alfarma ga sajen fuskarsa daya karawa fuskar tasa kyau,daga inda take a tsugunne ta kura mishi ido zuciyarta na kyasa kyau irin na jalal...       Jikinsa ne kawai ya bashi kamar ana kallonsa.. Ya bude ido ahankali yana mamakin yanda akayi bayi suka samu shigo masa garden bada izinin sa ba...    Caraf ya ganta a tsugunne kamar daga sama.. Ba karamin mamaki yayi ba,dan asalima gani yake kamar mafarki ne yakeyi.. Irin kallon da take bin'shi dashi ne yasa shima ya kura mata nasa idanuwan.. Sai da suka shafe minti daya a haka..kafin kafafun juwairiya sukayi mata tsami,sai alokacin kuma ta tuna da halin da take ciki,tayi saurin mikewa jiki na rawa tace...   Allah ya huci zuciyar ka,kayi min afuwa dama batar hanya ne nayi...ku...ma..sai...na..ga..waj... Jalal ne ya tsaida ita..da daga mata hannunsa dayayi..    Shiiish ya daura yatsan sa akan leben sa..sannan ya shiga takowa har ya kawo gabanta ya tsaya..   Kirjinta ne ya shiga bugawa....tayi saurin sauke idonta kasa..      Jalal da muryarsa mai dadin amo yace, me ya kawo ki sashen na?ko baki san hukuncin shigowarki nan din ba ne? Juwairiya ido ya kawo kwalla,na..na..sani..amma...ka..kayi hakuri dan..darajar Allah...    Jalal ya murmusa yana jin wani irin nishadi na dibar sa..   Dago ki kalleni...ya bata order.. Juwairiya ta sake kasa dakai,mai martaba yin hakan a gareni kamar raini ne.. Jalal ya sake murmusawa,sannan ya kama hannunta... a tsorace ta dago da kanta suka hada ido dashi,ji tayi gaba daya jikinta yayi lakwas...    Jalal ya janyo ta sannan naga ya bude wata secret door sun shige daga ciki...       Bude baki tayi ganin su a cikin kogin mai martaba...    Jalal ya kura mata ido ganin yarda ta saki baki tana kallon wajen.. Juwairiya ta juyo tana kallonsa.. Wani irin murmushi ta sakar masa da ita kanta bata san miye dalilin ta na yi masa shi ba..      Jalal yaji bugun kirjinsa ya linku,bai taba ganin ta tayi murmushi haka ba..   Juwairiya ta zare hannunta daga nasa tana sake juyawa tana kare wa wajen kallo.. "Jalal ya kura mata ido kamar ya samu TV..   Wani tunani ne yazo mata acikin zuciyarta ,sake juyawa tayi ta dawo kusa dashi ta dukar dakai.. Cikin sanyin murya tace.. "Ranka shi dade idan bazaka damu ba ina so nasan dalilinka na kyautatamin da kakeyi a cikin yan kwanankin nan,nasan bani da hurumin yi maka wannan tambayar ,amma zuciyata na mutukar son taji amsar ka..   Jalal ya lumshe ido ya bude.. Me zai iya fada mata,shi kansa bai gama sanin dalilin sa ba..   Tambayar dake cin zuciyarsa ce ta fado masa shima ,meya sa take boye fuskarta da wannan tabon...?     Juwairiya taji shirun yayi yawa.. Ta dago suka hada ido... Gani tayi jalal yasa hannu ya fisgo ta da karfi.. A tsorace ta shiga bashi hakuri..amma inaaa bai tsaya ko ina da ita ba sai gaban kogin...     Jikin juwairiya ya hau rawa..kayi hakuri ranka shi dade na tuba!bazan kara ba..kayi min rai!   Jalal bai saurare ta ba.. kawai sai ji  tayi yasa hannu a wuyanta  ya tura kanta cikin ruwan..    Wani irin ihu ta saki tana jan lumfashi kamar zata mutu,me yasa jalal yake shirin kashe ta?me tayi masa?tunani iri iri ke yawo acikin zuciyarta,ta sadakar da sake yin wata rayuwar sai ji tayi ya dago da ita ya fito da kanta acikin ruwan..     Idanuwanta ne da sukayi ja ta kura masa ido cike da tsantsar tsoro da kuma mamakin abun da ya aikata mata a yanzu.. Jalal kansa kallon fuskarta yakeyi kafin nan ya juya ya koma kofar da suka fito... bai dade ba ya sake dawowa gabanta dauke da mirror a hannunsa.. Duk abunda yakeyi kallonsa kawai takeyi,ta rasa me yake tunani haka,kashe ta yake sonyi??? Jitai yace...    "Kalla nan"   Madubin dake rike a hannunsa ta kalla... Fuskarta ta gani tangaren babu ko di'gon tabo a jiki..    Ware ido tayi sannan ta kallesa da sauri.. Jalal ya gyara tsayuwarsa.. Zaki iya fada min dalilinki na boye fuskarki da wannan tabon na karya? Gabanta ne ya shiga faduwa jikinta ya hau rawa,tun yaushe yarima yasan wannan sirrin nata?yau ta banu!   Jalal ya sake fadin.. Idan har zaki iya fadamin dalili toh nima zanyi kokari na samu amsar tambayar ki na kyautata miki da nakeyi...   "Juwairiya taji kuka yazo mata,me zata iya fada masa?taya zata iya fada masa ma sbd ta tsare mutumcin kanta ne yasa take boye fuskarta da tabon karya...   Zubewa tayi a kasa tana kuka sosai.. Jalal ya dan dafe kansa.. Kafin ya duka kasan kusa da ita yace.. Ba kuka na tambaye ki ba! Juwairiya ta dago da jajayen idonta tace. Ranka shi dade  idan na fadi maka nayi hakan dan kawai na tsare mutumcin kaina ne zaka yarda dani? Jalal cike da rashin fahimta yake kallonta.. Juwairiya ta shiga goge hawayen ta tana sake fadin.. A wajenku ku masu mulki da iko mu bayi ba komai bane ba,kun dauke mu tamkar kayan kazanta ko kayan da zaku iya sakawa ku yar ba tare da kun damu da feelings din mu ba.. bamu da wani galihu ko girma a idon ku.. ta nuna kanta tace,ni yarinya ce dana taso cikin tarbiyyar iyayena wadanda suke bayi a karkashin ikon ku,na taso ne acikin RUMFAR BAYI kuma tabbas naga yarda mata yan uwana suke fuskantar musgunawa da cin mutumci a wajen wadan da suka fisu karfi da mulki.. Taja lumfashi... A lalata rayuwar su ko kuma a siye su a matsayin SA'DAKA ba'a damu da nasu ra'ayin ba. mahaifiyata a kullum cikin tunanin yarda zata tsare min mutumcina takeyi,sbd haka ne sukayi min wannan tabon a fuskata dan ya  taimaka wajen tsare ni daga maza masu lalata rayuwar bayi mata irina.. Jalal tunda ta fara mgn yake saurarenta har ta kai Aya bai tsayar da ita ba.. Kukan ta taci gaba dayi cike da takaicin yarda asirin da suka dade suna boyewa ya tonu.. kuma wai Sarki jalal da kansa ne ya gano su shikenan kokarin su ya zama a banza...       Ji tayi kawai an fisgo ta.. sai saukar kanta taji a fadadden kirjin jalal me fitar da wani irin kamshi me sanyi...    Gaba daya wutar ce ta dauke... Meke damun yarima? Jalal ya rasa me yasa ya kasa controlling kansa,juwairiya ta fara kiciniyar kwace kanta.. Jalal ya sake ta yana maida lumfashi, sannan ya mike tsaye ya juya ya fice daga wajen cikin saurinsa.. Juwairiya ta bi bayansa da kallo,ta kasa yarda da zuciyarta, tasan jalal yafi karfinta nesa ba kusa ba amma me yasa tajiki ajikinta kamar ya fara having feelings akan ta,ta girgiza kai da sauri... kai inaaa tausayi kawai take basa..     Mikewa tayi da sauri tunawa da tayi dadewar da tayi a wajen,ta tabbata zainaba zata neme ta.. Da gudu ta fito falon tana yan leke leke ga mamakin ta babu kowa a wajen,ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito waje tana sake rufe rabin fuskarta ta da mayafin dake kanta...      "Juwairiya " Taji an kira sunan ta a lkcn da take kokarin barin sashen .. A dan tsorace ta juyo sai ganin umayma tayi tana mata wani irin kallo.. Murmushin dole tayi mata tace,umayma ashe kece? Umayma tace uhm ni ce,juwairiya tace,bari na karasa toh tayi saurin barinta a wajen tayi gaba .. Umayma ta jinjina kai,mai ya kawo juwairiya turakar sarki jalal?lallai akwai wani abu kasa... dole ne tasa ido akan ta.. "Umayma na shiga ta samu jakadiya ta fada mata sakon surayya na son ganin jalal.. Jakadiya ta shiga ta sanar masa yace shi bazai ga kowa a yanzu ba,dan yana hutawa ne.. Jakadiya ta fito ta fadawa umayma, ba haka suka so,umayma jiki a sanyaye ta koma sashen surayya..    Murmushin mugunta surayya tayi,ta kalli umaymah tace, babu komai zanci gaba da jiransa,tunda dai mun samu wannan yarinyar tasha maganin hana daukar cikin ai bani da wata matsala dan yanzu ni kam.. Umayma ta murmusa kada ki damu ranki shi dade,na samu wata baiwa mai amana sosai a can madafar kuma na fada mata sakon ki,ta amince zata rinka saka maganin acikin abinci gimbiya khadija. surayya ta jinjina kai cike da gamsuwa tace,aikin ki yana kyau umayma... ************* "Khadija ta kalli rabi bayan fitar zainaba tace daga dakin,yadai kin ganta kuwa? rabi ta fito da layar data kunshe acikin zaninta ta mika mata,khadija tayi saurin amsa tana fadin, ki kiyaye bakin ki!bana son jin sirrina yana yawo acikin wannan masarautar  kin gane? Rabi ta gyada kai,khadija tace yauwa muje na koma sashena... ******************** Bayan sati daya...    "A cikin yan kwanakin da suka wuce gaba daya jalal bai zauna ba, kullum suna cikin fa'da aiki yayi masa yawa sosai,duk irin nemansa da matan sa keyi bai sa ya  kula kowaccen su ba.    A yau ma dai sun samu dan hutu ne shine ya zo dan gaida mahaifiyar sa.. Gimbiya kilishi na hakimce akan kilisarsa.. Cike da kulawa tace, jalal kaga yarda ka koma kuwa? Ina tunanin lkc yayi da zaka canza bayin dake kula dakai kamar yarda al'adar masarautar  take..    Jalal yace,ummana kenan,aikine fa kawai yakeyi min yawa,yadan langwabar da kansa ya sake fadin,kin san kuma ban saba da irin wannan aikin ba.. Kilishi ta girgiza kai ,gobe ka shirya dan dama mahaifinka yayi min mgnr da dadewa.. nace masa mu dan baka lkc ka kara hutawa,toh tunda dai na lura kai kullum acikin aikin kake sai nayi tunanin dole ne kawai na fitar da rana da kaina. Jalal ya gyara zaman sa yana fadin,toh umma zan shirya idan har hakan kike so,kilishi tayi murmushi yauwa dan albarka ..   Hansai ce ta shigo falon tana fadin,Allah ya kara maka yawan rai yanzun nan baiwar gimbiya khadija  tazo da sako a fada maka..    Jalal yadan tabe baki,kilishi tace kai wannan yarinya da jaraba take.. Hansai tace, tace a sanar  maka tana son ganinka idan babu damuwa.. Jalal baice komai ba ya mike yana kallon kilishi,umma bari na tafi.. Kilishi taji gaban ta ya fadi,cike da bakin ciki tace,ban gane bari ka tafi ba duka duka yaushe kazo? Kodan kaji kiran matar ka ne? Jalal ya murmusa,haba umma ke kinsan danki ai.. Magaji ne na saka a kira min shi tun dazu kuma na tabbata yana jan yana jirana acikin Fa'da.. Kilishi tayi murmushi,toh yi maza kaje ai na dauka rawar jiki kakeyi wa wannan figaggiyar yarinyar. Jalal na murmushi yayi ficewarsa.. "Khadija ta kalli rabi tace,kin tabbata sakona yakai gareshi? Rabi tace,wlh a kan kunnena hansai ta fada masa.. Khadija taja tsaki,yanzu a kalla anyi  kusan 5hr amma shiru babu yarima.. Ta kalli rabi,jeki ki dubo min sashen surayya ko yana can.. Rabi tace toh ranki ya dade..   "Rabi na isa sashen surayya ta shiga tambayar bayin dake waje ko mai martaba yana ciki? Duk suka tabbatar mata da cewa baya nan kuma ya ma dade bai zo ba.. Ta dawo ta sanar wa khadija duk irin ruhoton data kwaso.. Dariyar farin ciki khadija ta saki dan a yanzu ne ahankalin ta zai samu kwanciya tunda dai ba ita kawai yarima yake sharewa ba... _"Gaskiya readers ina jin dadin ganin comments dinku ba kadan ba.._ _@RALLYN SAMEENA_ _@MEELANCY #team_ _jalaljuwai_ _Duk naji dadin_ _comments dinku wlh Allah yabar zumunci_ *GODIYA NAKE PHERTY* Muje zuwa...👇🏽 Team RUMFAR BAYI...     [9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:             *RUMFAR BAYI*        (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 18 Wattpad @afreey101 *************     "A can cikin gida kuwa, gimbiya kilishi taji shiru shiru babu yarima bai dawo ba gashi har an kusan gama sa lallen.. Fulani diyya ce ta kalli laure tace, jeki ki saka turaki ya fita ya nemo jalal,laure tace toh ranki ya dade sannan ta mike ta tafi.   Surayya kam tana can gefe da wasu matan cousins dinsu yarima,sai wani murmushin farin ciki takeyi ganin yarda yarima ya tashi yayi tafiyarsa gashi kuma har yanzu bai dawo ba..    Asiya ce ta kalleta,lallai kuwa surayya na yarda kin gama sace zuciyar yarima.. Karima ta saka dariya,gaskiya ne wannan,tun fa dazu daya fita har yanzu shiru bai dawo ba. baiwar surayya ce tazo tayi mata rada a kunne,surayya ta kallesu kafin nan tace,ni zan tafi yanzu tunda dai dare ya soma yi kuma banga amfanin zaman mu a nan ba tunda har shima angon ya sallame kanshi ,gaba daya suka saka dariya.. "Turaki ne ya fito waje dan neman sa,sai hango sa yayi ya tunkaro gidan yana ta sakar da wani irin murmushi mai kayatarwa.. Mamaki ne ya kashe shi dan ya dade bai ga yarima yana irin wannan murmushin haka ba..   Bai gama mamakinsa ba ya hango juwairiya ta bullo daga wajen itama,kuma ga babban mamakinsa itama din silent smile take fitarwa..     Girgiza kai kawai yayi,dan yasan waye yarima yasan kuma halinsa dan haka  bazai zarge komai ba. Karasawa yayi ya taro sa,yarima na ganinsa ya hade rai,ya akayi? Turaki yace,haba yaya tun fa dazu kayi ficewarka gashi har an gama taron ma kai kawai ake jira a tashi. Yarima yadan ja tsaki,kafin yayi gaba.. *********** Washe gari........ "A yau ne ake bikin daurin auren yarima jalal da kuma khadija,sannan kuma a yau din ne  jama'ar dake kasar daura zasu halarci na'din sarautar sabon sarkin su wato JALALLUDEEN... "Tun safe masarautar take a cike tab da mutane daga kowane yanki na nigeria dama tsallake, makida sun zo daga kasar nijar sannan mahauta ma sun zo ana ta yankar shanu ana ban'karesu ana ta gashe su..     RUMFAR BAYI  kanta a cike take,dan kamar yarda al'adar take,duk lkcn da ake wani na'din sarautar sabon sarki toh sarakuna da masu kudi da shuni suna bada kyautar bayi ga masarautar dake bikin, kamar wata kyauta ce ko wani abun bajinta ne hakan. ****************** "UMAYMA" Surayya ta fada cike da murnar ganin baiwar ta dake mata hidima tun a can gidansu. budurwa ce yar kimanin shekaru ashirin da haihuwa,bakace sosai amma fa akwai kyawu babu laifi.. Umayma tayi murmushin murnar ganin uwar dakinta bayan rabuwarsu tun lkcn aurenta.. Ranki shi dade nayi farin cikin sake ganin ki.. Surayya tayi dariya nayi kewar ki a kusa dani umayma,dole ne nayi wa yakumbo godiya sosai data turo min dake nan . Umayma tayi wani irin shu'umin murmushi, sannan ta kalli sauran bayin dake wajen tace,ku bamu waje! Duk suka fice suna mamakin iko irin umayma sai kace itama din ba baiwar bace kamar su..    Surayya ta gyara zaman ta tace,da magana a bakin nan naki umaymah,kwararo min su naji... Umayma ta  matso sosai gaban surayya, ta fito da wani kulli acikin rigarta,ta kwance shi ta fito da wani garin magani.. Ungo wannan gimbiyata ,surayya ta amsa tana juya kullin maganin,menene shi din? Umayma ta gyara zama tace,yakumbo ta aike ni wajen malam jatau dake can yobe,ya bani wannan maganin na daukar cikine da wuri.. Surayya dadi ya mamaye zuciyarta,tace,da kyau umayma..amma kinsan fa shi yarima ba kullum yake son yin abun ba,gashi har ma yau amaryar sa zata tare kinga idan har ya kwana da ita tana iya samun ciki a daren farkonta..    Umayma ta gyada kai cikin gansuwa sannan ta mike taje tayiwa surayya ra'da a kunnenta.. Take naga surayya tayi wani shewa tana kyalkyata dariya, gsky naji dadin zuwanki umayma dan aikin ki na kyau!!!... ************* "Karfe biyu na rana aka daura auren. sannan karfe hudu na yamma mai martaba yayi murabus daka mulki, a take kuma aka na'da YARIMA JALALLUDEEN  a matsayin SABON SARKIN daura ...   Shewa da murna mutane suka shiga yi cikin tsananin farin cikin su... Masu kirari suka soma kwararo shi kamar haka... "LAFIYA DARZAZA AMALEN SARAKUNA "LAFIYA BA HAU DA WANI BA SAUKA WANI "LAFIYA BANGO MADAFAR BAYI.. "LAFIYA TORON GIWA... "AN GAISHE KA SABON SARKI MAI SABON ZAMANI" Yarima dake cikin shiga irinta sarakuna yasha nadin sa ga alkyabba ta alfarma yasha,sai kyalli yakeyi yana daukar ido... Duk wanda ke wajen sai da kyasa sa,magaji na gefensa hakama hamza da turaki sai washe baki sukeyi....       Karfe shidda na yamma aka fara shirye shiryen tafiya liyafa... ************* "An kawo amarya khadija sashen gimbiya kilishi,hansai ce ke ta musu hidima dan zainaba na can sashenta tana shiryawa yau rabin ranta Mustapha zai zo shima tare da abbansa wato wamban kano.. Juwairiya ta kalli zainaba data sha gayu kamar a sace ta.. Cike da sha'awa tace,gaskiya yau gimbiyata sai kin rikita Mustapha wannan kyau haka..?ta karashe mgnr tana cike bakinta.. Zainaba ta murmusa cikin tsananin murna tace,Allah ko juwairiya nagode da yabawa sosai.. Juwairiya ta dauko turare daga cikin akwatin karfen zainaba tace,kada ki manta da wannan...   Zainaba tayi dariya yauwa aminiyar nagode,juwairiya na dariya ta shiga fesa mata turaren a take kamshi ya gauraye dakin..     Zainaba ta kalli juwairiya,kayan jikinta na nan jiya e yau,tace,haba juwairiya yau fa ya kamata ace kema kin dan canza ko?,kin manta yau fa babbar ranar farin ciki biyu ce a wajen mu, auren ya jalal da khadija da kuma murnar nadin sabon sarkin mu "AMALE" (wato SARKI JALALLUDEEN)    Juwairiya tayi murmushi,  har ranta take taya shi farin ciki,amma tasan a yanzu yayi mata nisa sosai, ko samun lokacin yi masa wannan murnar ma baza ta samu ba...   Zainaba ta dauko wasu kaya ta mika mata,amsa nan.. Juwairiya ta kalli kayan,kafin ta amsa,zainaba tace,fulani ce ta saka ayi miki su..bana son gardama kije kema ki shirya yanzu dan ina so muje sashen umma babba wajen khadija..   Juwairiya tayi godiya sosai,sannan ta fice.. Sashen fulani ta fara zuwa,ta same ta sai hidima takeyi da mutane,da kyal ta samu laure tayi mata iso wajenta tayi mata godiya sosai,kafin ta tafi se data nuna wa laure kayan ta gani itama.. """Rumfar bayi ta wuce kai tsaye.. Bayi ta iske suna ta hidimar su,wajen du'bu ta fara zuwa ta nuna mata kayanta cike da murna,du'bu ta yaba sosai sannan ta shige dakinsu ta hau shiri...    Kayane na zamani riga da zani,sai dai rigar ba irin tasu bace mai kai wa har gwiwa,ita wannan karamace sannan tadan kama jikinta kadan. Madubi ta dauko tana karewa fuskarta kallo... Ina ma ace zata iya fita a haka ba tare da tabon fuskarta ba... Ta shafa fuskar tana lumshe ido,fuskar yarima kawai take hangowa acikin zuciyarta ,ta girgiza kanta da sauri,meke damun ki juwairiya? Kin manta waye me wannan fuskar, sarki ne fa!A'kul dinki!    Tadan ja lumfashi kafin ta maida tabonta, ta mike tsaye ta sake gyara zaman mayafinta sannan ta fito.. A kofar Rumfar bayi zata fita kenan taci karo da mutum.. Taja da baya tana dago da kanta...   Ido hudu sukayi da umayma... Ba'kin ta ne yaso tsorata juwairiya.. Ita kuwa umayma dama ba mai fara'a bace dunkum da ita. da kallo tabi juwairiya tana kyasa kyaun dirinta,amma konewar fuskarta ne yasa tadan ja tsaki,ai da ace itace me wannan dirin babu abunda zai hanata jan hankalin mazan masarautar nan,hasken fatar juwairiya ya sake daukar hankalinta..       Juwairiya kuwa ganin yarda umayma ke binta da kallo yasa tace,yi hakuri ban lura bane.. Umayma tadan yi murmushi babu matsala kema baiwa ce a nan din? Juwairiya tace kwarai kuwa, amma ban taba ganinki ba ko yau kikazo ne kema? Umayma tace ,eh yau aka kawo ni,ina sashen surayya uwar gidan sarki...   Juwairiya ta tabe baki a zuciyarta, amma a fili tayi murmushi, ni ina sashen zainaba kanwar sarki kuma diyar sarki.. Murmushi sukayiwa juna kafin juwairiya ta fice abunta.. Umayma kuwa ta daure fuska, wacece wannan?shine tambayar dake cikin zuciyarta.. ***************** "Gimbiya kilishi ta kalli hansai tace,an kai wa khadijan kayan da zata saka? Hansai tace na kai mata ranki ya dade, jakadiya ce ta shigo tana sanarwa kilishi sakon tsohon sarki Abdul-Jabbar yana neman ta a sashensa. kilishi tace,gani nan zuwan ina fata shi jalal din ya gama shirin sa ko?jakadiya tace,ai tun dazu Ya kammala shirin sa,kilishi ta murmusa cikin tsantsar farin ciki sannan ta mike ta fice dan amsa kiran mijin ta.. *************** "Taro yayi taro an ware wa amarya da ango (sabon sarki jalal)wajen zamansu,sannan aka tadanarwa iyaye da manyan baki wajen su suma,bayi kam na can daga baya suna leke.. Zainaba tare da juwairiya suka shigo filin,Mustapha ne ya taso yayi saurin taro su yana washe baki.. Juwairiya ta gaishe shi ya amsa a sake yana karewa zainaba kallo..      Sai da suka karasa wajen zamansu sannan juwairiya ta juya dan komawa wajen bayi yan uwanta ta tsaya itama.. Caraf ta hango shi a zaune cikin kayan alfarma yayi kyau har ya gaji.. Kirjinta ne ya buga ganin surayya da khadija sun saka shi tsakiya..    Ji tayi kamar kafafunta na rawa,tayi kokarin tafiya taji ta harde da zanin jikinta..... ta tafi zata fadi sai ji tayi an riko hannunta...    A tsorace ta dago suka hada ido da Turaki.. Murmushi ya sakar mata... "Kamar ance ya dago da idanunsa.. Aikuwa can ya hango su hannayensu a sarke da juna,ji yayi zuciyarsa ta fara zafi..    A take annurin fuskarsa ya dauke.. Surayya ta kallesa tana narke murya,haba sarkina kadan saki rai mana,kai fa a yau kafi kowa murna a duniyar nan. khadija dake gefe ta tabe baki,lallai dole sai ta san irin zaman da zatayi da waccan matar dan ta lura munafuka ce ta karshe.. Da gefen ido take kallon jalal,fuskar nan a tamke,tadan sauke ajiyar zuciya, ita dai tana son shi a haka...    "Kwace hannunta juwairiya tayi tana kasa da kai,nagode ranka shi dade, Turaki yace,babu damuwa sannan ya wuce itama tayi gaba.. Can kusa da rabi ta tsaya,sai ga umayma tazo taja layi kusa da ita,kallonta kawai juwairiya tayi batace komai ba,umayma kuwa murmushi tayi tace,zanso mu zama kawaye idan bazaki damu ba? Juwairiya tadan yi murmushi tace,ai duk baiwar dake cikin Rumfar bayi yar uwa na dauke ta,umayma ta danyi yake tana ki'tsa wani abu acikin zuciyarta.. Na Afrah bhai [9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:         *RUMFAR BAYI*     (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 19 Wattpad  @afreey101 *wannan naki ne didi @Fertyma Zarah* ********** "An sha shagali sosai har kusan tara na dare kafin taron ya watse..     Sarki jalal ne ya shiga babban turakar sa (sashen sa) inda aka canzawa tsari daga tsarin na mahaifinsa wato tsohon sarki kenan..     " Jakadiya ce ta shigo da kuyangi har cikin makeken dakinsa,ta fada musu yarda zasu hada mishi ruwan wanka da sauran hidimarsa,kuyangi biyu ne suka shige cikin dakin suka gyara shi tsab dan kwanar amarya.. A can wajen khadija amarya kuwa,bayan ta dawo daga taro a gajiyenta, gimbiya kilishi ce ta aika mata da hansai da kuma sabowar baiwarta wato rabi, nan hansai ta shiga nunawa rabi yarda zata kula da uwar dakin nata,rabi sai washe baki akeyi tana murnar samun karin girman da tayi..   An gama shirya khadija tsab cikin kaya na gani na fada. suna shirin fitane dan zuwa kai ta can turakar sarki jalal sai ga surayya tare da umayma sun shigo cikin sashen..    Wajen zama rabi ta nuna musu,sannan ta dawo kusa da khadija dake ta jin haushin tsaida su da akayi ta zauna..    Surayya ce tace, su amarya an sha kamshi,dama nazo ne dan nima na bada tawa gudunmawar tunda dai ban samu lokacin bayar wa ba ko..   Umayma ce ta ajiye tiren dake hannunta wanda dashi ne suka shigo. surayya tadan yi murmushi kafin nan ta sake cewa, wani tsumi ne dama da aka kawo min shi daga kasar Cameroon, nayi amfani dashi kuma na yaba sosai,tunda dai ba karamin rikita sarkina yayi ba a lkcn,ta karashe mgnr cike da kissa..    Khadija taji wani abu ya tsaya mata a wuya,sarkinta?ya rikice?lallai ma wannan matar..   Tadan dago kai tana murmushin yake kafin nan tace a takaice ,toh nagode..ta shiga kokarin mikewa.. Umayma ce tayi saurin fadin,ah ah gimbiya khadija ai  kamata yayi ki dan nuna karamci,ta shiga zuba tsumin a kofi.. Surayya ta amsa kofin ta mikawa khadija,kidan sha ko kadan ne na tabbatar miki gobe se kin gode mini..     Khadija tadan kalli rabi,rabi tayi mana alama da kada tasha,khadija tadan tabe baki..   Jakadiya ce ta rangwada sallama tana sake nanata musu sarki jalal na jiran amaryar sa.. Khadija data ka'gu sosai data tafi wajen rabin ranta... cikin sauri da jawar jiki ta amsa kofin ta kafa kai ta shanye shi tass tana nunawa su surayya cikin kofin (irin am done zaku iya tafiya). Surayya tayi murmushin murna,yauwa ko kefa kinga nima se naji dadi ai,rabi ce ta kamo hannun khadija sukayi gaba abunsu.. Umayma da surayya suka kalli juna suna murmushin mugunta  cike da gamsuwa.. ************** "A wajen Jalal kuwa yayi wankansa ya saka kaya masu saukin gaske,se kamshi yakeyi ..   Yana zaune a saman darduma ta alfarma yaji sallamar khadija daga can falo..   Bai motsa daga inda yake  ba har ta shigo dakin cike da yangarta ta sauke idanunta akan sa.. Wani irin kyau da kwarjini yayi mata har bata san lkcn da ta saki murmushi ba tana wani kafe shi da ido..   'Idan kin gama karemin kallon se kije ki kwanta"   Khadija tadan waro ido kunya duk ta lullube ta.   Jalal ya mike cike da kasaitarsa ya juya mata baya..sai ji kawai yayi an rungumo shi ta bayan.. Khadija ta kwantar da kanta a bayansa tana fadin.. "Haba ya jalal meyasa kake bawa zuciyata wahala ne?kasan fa yarda na damu dakai tun muna yara...amma se ka ringa wani share ni..ta karashe mgnr a shagwabe.. Yarima yaji jikinsa yayi sanyi,idan har yace bai san khadija ta mutu a kansa ba toh karya yakeyi wa kansa..     Lumfashi yaja sannan ya kamo  hannunta ya maido da ita gabansa yana kallon fuskarta har kwalla sun fara cikowa a cikin idanunta..    "Meyasa kike Sona? Khadija tayi saurin kallonsa,dama ya san tana sonsa kenan? Meyasa? Ya sake maimaita tambayar.. Khadija ta shagwabe fuska,nima ban sani ba ai,kawai dai komai naka wlh burgeni yakeyi tun bansan cewa sonka nake ba har na girma na fahimci hakan.. Yarima yaja lumfashi,sannan a cikin zuciyarsa yake ganin wautar tambayar da yayi mata,juwairiya ce ta fado masa a rai,meyasa ya damu ita sosai?shima dai kamar yarda khadija ta fada,bai sani ba..     Jin khadija a jikinsa ne yasa ya dawo daga duniyar tunaninsa.. Rungume sa tayi tsam... A take yaji wani irin yanayi a gaba daya jikinsa.. Ya lumshe ido ya bude su ahankali ,kafin ya dauke ta cak ya ajiye a kan gadon dake gabansa.. ************** "Juye juye kawai takeyi a kan taburma,ta rasa meke damunta, duk yarda taso tunanin jalal ya fita daga cikin kwakwal'warta kasawa tayi.. Mikewa tayi zaune tana kallon gefen da ummanta take a kwance,sai sharar barcinta takeyi..    Fita tayi daga cikin dakin dan zuwa ta dauro alwala...tayi nafila ko zata samu nutsuwa.    Motsi taji daga can cikin madafa,mamaki ne ya kamata dan kuwa duk mutanen dake cikin rumfar bayi a wannan lkcn sunyi barci..    A dan tsorace ta karasa kofar madafar tana leke..    Ba'kin ta kawai yasa ta gane wacece a wajen ,duk da kuwa babu wani isasshen haske a wajen.. Umayma ta furta a hankali me takeyi a wannan lkcn? Gani tayi umaymar ta juye wani abu daga cikin jug,tasa ruwa da yawan gaske ta wanke jug din tas,sannan tayi murmushi me ma'anoni dayawa...     Tana kokarin juyowa juwairiya tayi saurin barin wajen,tana tunanin wat is umayma up to? *********** "Da safe jakadiya ce ta shigo dakin jalal bayan fitarsa. Can ta hango khadija a kwance jikinta duk yayi tsami ga zazzabi me zafi ya rufe ta..   Subhanallahi ranki ya dade! Nan jakadiya ta shiga kiran kuyangi dan su taimaka mata.. Sai da aka kimtsa ta sannan jakadiya tace ko a kai ki sashen gimbiya kilishi ne dan ki dan samu shan magani? Khadija ta girgiza kai,ah ah sashen fulani zani.. Jakadiya ta kalli rabi tace,taimaka mata kuje.. "Fulani diyya ce da kanta ta shiga kula da khadija,labari kuwa yaje har kunne kilishi, haushin khadija ne ya kamata sosai,wai tana so ta jawo mata raini. "Juwairiya tare da zainaba ne suka shiga sashen fulani dan ganin jikin khadija kamar yarda lbrn ke ta yawo acikin masarautar.    A daki suka tarar  da ita kwaryar magani a hannunta sai yatsine fuska take rabi na ta lallashinta tasha.. Zainaba ta zauna a kusa da ita.. Matar sarki jalal na zata ai ke jaruma ce .. Khadija ta banka mata harara.. Juwairiya kuwa sai faman kallon khadija take tana jin wani abu yana tsirga mata acikin zuciyarta.. Khadija ta ware ido tana dafe kirjinta tace,wayyo Allah na yau na shiga uku? ,zainaba tace me ya faru kuma yanzu sarkin ra'ki?khadija ta matso kadan tayi mata a kunne (akan she forgot her underwears a dakin jalal) Zainaba tayi kasa da murya,kada ki damu,ai su jakadiya zasu dauke miki komai,khadija ta girgiza kai nidai bana son ne wannan matar tasa taje ta gani na jawa kaina wani sabon rainin a banza.. Khadija ta jawo rabi tana mata rada akunne cikin mgn kasa kasa tace,ki koma sashen ya jalal a dakinsa ki dauko min wata bakar laya dana manta acan,kada ki kuskura wani ya gani!gyada kai rabi tayi sannan ta mike zata fita..    "Zainaba ce ta kalli gefen da juwairiya take tace,juwairiya kuje tare da rabi sashen ya jalal din.... Khadija ta dan harare ta ki bari rabin taje ita kadai mana? Zainaba tace,ah ah ai juwairiya tafi ta sanin jakadiya ,khadija ta tabe baki..sannan da ido tayi wa rabi gargadi... juwairiya kam bama son zuwan take ba dan wani abu take ji yana mata yawo a makoshinta, Ta kalli rabi tace muje,rabi tace toh sannan tabi bayanta suka fice. khadija ta dafe kirjinta tana addu'ar Allah yasa jalal bai ga wannan layar data fadi daga jikinta ba jiya ,goggonta ce ta bata ita akan idan ta kwana dashi da wannan layar ajikinta toh tabbas zata samu waje acikin zuciyar jalal,ko innarta ma bata san sunyi wannan sirrin ba.. *********** ""Suna shiga makeken sashen na sarki jalal suka tarar da jakadiya tare da wasu kuyangi suna ta hidimar su. Juwairiya ta karasa wajen jakadiya ta gaishe da ita,jakadiya tace,meya kawo ku nan juwairiya,da fatan dai komai lfy ? kunsan fa baku da ikon shigowa turakar sarki ba tare da wani babban dalili ba.. Rabi ce tace, uwar dakina ce gimbiya khadija ta aiko mu daukar wani sako aciki data manta.. Jakadiya ta jinjina kai,sannan ta kira wata kuyanga tace takai su dakin jalal su duba amma kada su dade..     "Tunda suka saka kafa a cikin falon juwairiya ke kallon ikon Allah,lallai an kashe duniya me tarin yawa a wajen nan,wani ado ne na zinari ta hango daya mutukar burke ta sosai..      Rabi kam da sauri ta shige dakin tana waiwayen juwairiya, can ta hango ta kamar an dasa ta a gaban wannan frame din,ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shige da saurinta ta shiga neman inda zataga layar..   Ita kam juwairiya tana nan a tsaye babu kowa a cikin falon sai ita kadai dan kuyangar data shigo dasu ma ta fice..   Wata kofa ta hango a bude iska nata kadata..    Hakanan take son ganin ina ne wajen shi kuma,tasan dai daga yau bazata taba sake samun damar shigowa nan din ba..    A hankali ta karasa wajen kofar tana leke.....       Bude baki tayi da idanu gaba daya cikin tsananin burge ta da wajen yayi tace,mashaAllah....     "Dan karamin wajen shakatawa ne da aka gyara shi da flowers da fruits iri iri sannan aka saka mishi kujerar lilo,yayi mutukar kayatuwa..       Sbd yarda ya tafi da zuciyar juwairiya bata ma san lkcn da ta saka kafa ciki ba tana karewa wajen kallo cike da ban sha'awa.. ********** "Sarki jalal ne ya fito daga fada tare da magaji da turaki a gefensa.. Kallon su yayi a gajiyensa yace,ku karasa da sauran cases din kaina ke ciwo zan dan shiga na huta..    Shamaki da sallama ne suka rufa masa baya suna masa kirari hade da gyara masa babbar rigar jikinsa.. "Rabi ba karamin nema tasha a dakin ba,a can karkashin gado ta hango layar da saurinta ta dauketa ta tura a cikin zani sannan ta fito..    Ganin babu juwairiya a falon sai tayi tunanin ko har ta tafi ne.. _"'Kuyi hakuri da wannan zuwa anjima inshaAllah_ _RUMFAR BAYI give away,thanks for all d readers that participate in my next post i will ANNOUNCE the 2 winners"_ TEAM RUMFAR BAYI [9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima:            *RUMFAR BAYI*        (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 21 Wattpad @afreey101 _juma'at mubarak all may Allah forgive us our sins amin_ **************** "Washe gari"    "Juwairiya na gani a zaune ta buga uban tagumi,yanzu menene mafita a gareta? Ta shiga kallon yarda bayi ke ta wani rawar jiki  suna gyara jikinsu dan kawai su samu yarima ya zabe su a cikin sababbin masu mishi hidima asashen sa..     Ita kuwa ya zatayi yanzu?tasan da cewa indai har tana ganin shi a kullum toh zuciyarta bazata taba samun sukuni ba,gashi kuma abun haushin ma yasan konewar fuskarta duk karya ce..    Laure ce ta dafa kafadarta,a sanyaye ta dago ta kalleta,laure tace taso muje,juwairiya ta mike suka shige cikin dakin jakadiya..    Hansai ta kalle ta tace, haba yar umma wannan hade rai har haka? Juwairiya ta turo baki.. Jakadiya tace,ki kwantar da hankalinki juwairiya,na tabbata mai martaba bazai dauke ki ba ma,hansai tace,ni fa mamakin ma wadancan yaran nake da suke ta rawar jiki.. Laure tace ki kyele su duk so suke me martaba ya dauke su ko sunje su samu waje a can kinsan wasu da shegen kwadayin abun duniya suke...    Jakadiya ta girgiza kai,matsalar dai itace,duk lkcn da sarki ya ga wata baiwa daga cikin su kuma ya kyasa ta har ya kuma kwana da ita toh daga ranar zata zama SA'DAKARSA,wasu ma a haka suke karatar rayuwar su bai sake waiwayen su ba,masu rabon haihuwa kawai ne ba'a mantawa dasu a tarihi,toh wannan rayuwar har wani abun kwadayi ce? Juwairiya dake sauraren jakadiya taji jikinta duk yayi sanyi ,wato dai ita baiwa ba zata taba samun damar zama mata kamar kowacce mace ba?sai dai amatsayin kwakwara?       Hayaniyar da sukaji ne daga waje yasa su duk mike duka,laure ta kalli juwairiya, ki kwantar da hankalinki diyata,wannan tabon na fuskar ki kawai ya isa me martaba yaki zabar ki.. Juwairiya ta jinjina kai tana tausayin iyayen nata, Wato su a nasu tunanin wannan tabon ne ze taimake ta?lallai da sun san da cewa jalal yasan komai da basu saka rai a kan shi ba.. "Suna fitowa suka tarar da bayi duk an ja layi, kowaccen su na ta addu'ar samun nasara dan aiki a sashen sarki kamar wani garin girma ne suka samu..    Du'bu ce tazo taja hannun juwairiya ta kai ta cikin layin itama..    **************** "A waje kuwa... Sarki jalal ne tare dasu shamaki dakuma wasu fadawan ana ta kwararo masa kirari.. "Zaune yake a wata kujerar alfarma ga kuma lema (umbrella) an rike masa yana shan iskan inuwa abunsa.. Fuskarshi a daure tamau sai shan kamshi yakeyi abu ga jinin sarakai... A haka bayin suka ringa fitowa set by set. duk wacce tayi masa kalar tsabta sai yayi wa shamaki kwatancen ta a kunne shi kuma shamakin yaje ya sanar wa uwar soro itake zuwa ta dauko su ta kai gefe... Set dinsu juwairiya ne zasu fita yanzu,gabanta nata faduwa,zuciyarta ta kasu kashi biyu. Kallo daya zakayi mata ka fahimci a tsorace take sosai ..    Fitowar ta yayi daidai da saukar da idanuwanta  akan fuskar yarima..   Ji tayi duk karfin ta yana so ya kare.. Ta dauke kai da sauri taja kafarta taje ta tsaya akan layin.    Shamaki ne ya dan duka wajen kunnen yarima yace.. Allah ya kara maka yawan rai ga wasu nan sun sake fitowa suma..    Jalal kamar bayaso ya dago da kansa.. Caraf ya kyallo ta a cikin su..    Ya lumshe ido ya bude su ahankali,se yanzu ne yake jin dadin wannan selection din. bai wani bata lkc ba ya sanar ma shamaki wacce yake so acikinsu.. Shamaki ba karamin mamaki yayi ba dan kuwa sai yarima ya dauki kusan minti sha biyar bai zaba ko daya ba, amma ji yanzu ko minti daya bai dauka  ba ya zabo wancan.. Shamaki ya fadawa uwar soro.. Juwairiya kuwa kanta na kasa ta damke hannayenta.. Ji tayi kawai an dafa ta.. Ta dago a tsorace tana kallon uwar soro.. Uwar soron ta gyada mata kai,kware  kuwa yarinya mai martaba ke ya zaba a duk cikin wannan layin! Dum dum dum kake ji kirjin juwairiya nata bugawa.. Tadan kallo sa kasa'kasa... taga yarda ya wani hade rai,tadan ja tsaki a cikin zuciyarta toh me yasa zai zabe ta? ji yarda ya wani dauke fuskarsa...wata zuciyar kuma dadi takeji dan zata ringa samun ganin sa a kullum..    Cikin rumfar bayi ta koma,ta tarar da lbr har yaje kunnensu hansai,rungume ta kawai sukayi suka fada cikin daki.. **************** "Umayma ce na gani  a zaune tana lillasafo wa surayya bayin da yarima duk ya zaba jiyan.. Tana kaiwa kan juwairiya surayya tayi saurin mikewa daga kwancen da take.. "Kina nufin harda wannan yarinyar me konannar fuskar? Umayma tace kin san tane ranki ya dade? Surayya taja tsaki,dole ne kuwa mu saka ido a cikin sashen sarki.. umayma kin gane,inaso ki samo min baiwa da zamu aminta da ita kina jina? Umayma tace an gama ranki shi dade.. ****************** "Da safe jakadiya da kanta ta kawo wa juwairiya kayan da ringa kasawa (kamar matsayin uniform kenan)   Sai da ta gama shiryawa sannan suka fito dan tafiya..   Juwairiya ta kalli jakadiya,kiyi gaba inna bari na dan shiga wajen zainaba ,jakadiya tace,toh amma kiyi sauri dai,juwairiya tayi murmushi sannan da gudu tayi gaba.. "Tun kafin ta idasa shiga sashen take jin ihun zainaba, hankalinta a tashe ta shige  da saurinta...    "Laure ta iske a tsaye tare da zabba'u a gefenta ,zainaba sai zazzaga masifa takeyi.. Ni wlh babu wata baiwa da za'a canza min,ni juwairiya nake so! Laure kamar ta fashe da kuka tace,Allah ya huci zuciyar ki,jiya fa mai martaba da kansa ya zabe ta a matsayin sabowar baiwarsa,dole ne kiyi hakuri a canza miki da wata.. Zainaba zatayi mgn juwairiya tayi saurin karasa wajenta.. Dan Allah ranki shi dade kiyi hakuri.. Zainaba ta damko hannunta muje wajen fulani dolene ya jalal ya barmin ke... "Haka zainaba tayi ta jan juwairiya har sashen fulani diyya.. Turaki da fulani na zaune suna gaisawa sai ganin su kawai sukeyi kamar daga sama. Zainaba ta fashe da kuka tana fadin.. Ni dai wlh fulani kije ki fadawa abba ya jalal ya barmin baiwa ta bazan bawa kowa ita ba! Fulani ta mike tana fadin,haba zainaba kinsan fa a yanzu jalal shine mai wuka da nama acikin masarautar nan.. Zainaba ta kalli turaki dake ta kallonsu yana jin abun wani banbara kwai,me yasa ya jalal zai dauke juwairiya? Haka nan yaji wani irin abu a cikin zuciyarsa...    Ya turaki dan Allah muje ka tayani rokonsa? Turaki ya mike a sanyaye,ki yi hakuri zainaba kinji? Zainaba ta kalli juwairiya dake gefenta tana yan hawayen rabuwa da uwar dakin tata. Allah ya gani ba karamin shakuwa tayi da ita ba..    Naji zan bar masa ita...amma da sharadi idan har ita ce ta amince zata zauna acan din.. Juwairiya taji gabanta ya fadi.. Fulani tace wane irin sakarci ne haka? Zainaba bata tanka ta ba ta sake jan juwairiya suka fice turaki na bayansu yana faman kwalawa zainaba kira.. "A sashen sarki jalal taja burki,jakadiya ta fito da sauri ta tare su,zainaba tace,jakadiya ina ya jalal?inason ganinsa dan Allah.. Jakadiya zatayi mgn sai ga yarima ya fito cikin shigar alfarma se baza kamshi yakeyi..khadija ce a gefensa tana wani yanga sai faman gyara masa alkyabbar jikinsa takeyi..      Zainaba ce ta karasa gabansa tana kuka..   Jalal ya tsaya yana kallonta da mamaki.. Cikin muryar tausayi tace,dan Allah ya jalal kabar min baiwata ta nuna gefen da juwairiya take.. Sai a lkcn ya lura da juwairiya dake gefen zainaba tana goge hawayen ta..    Ji yayi zuciyarsa ta buga,ya sake kallon zainaba yace cike da kasaita,sarki baya mgn biyu kanwata.. Zainaba tace,nidai yaya bazan iya bar maka ita ba sai dai idan itace tace min zata iya zama a nan din.. Khadija dake faman hararar juwairiya tace,ya jalal kawai ka bar mata ita mana me zakayi da wannan me konannar fuskar.. Har cikin ransa yaji kalamanta..     Zainaba ta kalli juwairiya, ki fada min gsky na barki a nan kinaso?zaki iya rayuwa a inda ake kyamatarki?    Juwairiya gabanta ya hau faduwa zuciyarta ta kasu kashi biyu...   ga Idanu duk a kanta... bakinta ne ya soma rawa tana shirin mgn ne.. sai ganin turaki sukayi ya karaso wajen.. Bai tsaya wata'wata ba ya fisgo hannun zainaba sannan ya kalli jalal yace..kayi hakuri yaya......ya shiga jan zainaba sukayi waje...    Khadija taja dogon tsaki itama kafin tabi bayansa tana wurgawa juwairiya harara... Yarima dake tsaye ya maida kallonsa kan juwairiya dake ta sharar kwalla..    Karasawa yayi gabanta yana rungume hannayensa a kirjinsa kafin nan taji yace a takaice..   "Ki saka a zuciyarki bazan taba bari ki subuce min ba......" Yana gama fadar haka yayi tafiyarsa...   "Juwairiya tabi bayansa da kallon mamaki.. Bazai bari ta subuce masa ba? Me hakan yake nufi? Ta dafe kanta, lallai idan batayi a hankali ba yarima yana gab da rikita mata lissafinta... ************* "Jakadiya ce da kanta ta shiga da juwairiya wajen shakatawar yarima,tace nan ne wajen aikin ki juwairiya,nan ne kawai nake ganin zai nisantaki daga duk wani rikicin gidan sarauta..   Juwairiya ta murmusa tace,nagode da kulawarki inna jakadiya.. "Da daddare duk sun gama aikinsu suna tsaye suna jiran jakadiya ta fito ta sallame su,sai ga surayya ta shigo tare da umayma a bayanta.. Taci gayu kamar zata kasar sarauniyar kyau (yau ne kwananta)   Ko kallon inda su juwairiya suke batayi ba.. Umayma kam harda zuwa ta gaisa dasu tana karewa juwairiya kallo.. ************ "A daki surayya ta iske shi ya kwanta ya lumshe idanuwansa.. A tunaninta ko barci yakeyi,dan haka tadan ja tsaki,ba haka taso ba ko kadan...amma ya ta iya..   Kayan jikinta ta dan rage sannan ta haye kan gadon tana matsawa kusa da shi..   Duk abunda takeyi yarima yana jinta amma yayi mata shiru..    Rungume sa tayi tana daura kanta a kan kirjinsa me fadi.. Taja lumfashi kafin nan ta runtse idanunta.. "Yarima gaba daya yaji kamar ya ture ta daga jikinsa.. Ga tunani duk ya gama cika zuciyarsa, dazu da zainaba tayi wa juwairiya wannan tambayar yaso yaji amsar ta kwarai da gaske..amma bai san irin halin da zai shiga ba idan har ta fadi abunda zuciyarsa bazata so taji ba.. _zakuji update anjima inshaAllah_ Team RUMFAR BAYI       [9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima:           *RUMFAR BAYI*        (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 22 Wattpad @afreey101 _gaskiya ina godiya sosai,my wattpad fans are rlly d best,hakama fans din rumfar bayi na whatsapp duk ina jin comments dinku wlh Allah bar zumunci amin_ "Ahankali ya bude idanuwansa... ya kalli fuskar surayya da barci me nauyi ya dauke ta, sannan ya saka hannu ahankali ya janyeta daga jikinsa ya sauko da kafafun sa kasa ya zauna a gefen gadon yana dafe kansa da duka hannayensa...    Muryar jakadiya ce yaji yana sallamar bayin dake waje....     Haka nan ya samu kansa da mikewa ya zura kaya a jikinsa..sannan ya saka takalmansa ya fito daga dakin.. Jakadiya da tsananin mamaki take kalle sa dan a duk tunaninta ya dade da yin barci. tace,da fatan dai lafiya ko ranka ya dade? Jalal yadan murmusa mata sannan yace, lafiya kalau jakadiya zan dan fita ne na dawo ba da dadewa ba. Ya sake yin kasa da muryarsa yace.. fitar sirri ce wannan dan haka ki rufa min asiri kinji?dan yasan jakadiya na iya sanar wa kilishi.. Jakadiya tayi murmushi, toh amma bari na saka a kira maka shamaki se yayi maka rakiyar ko? Jalal ya girgiza kai,ah ah ki barshi kawai ni kadai zan fita,bana son ma kowa ya san fitar kin gane? jakadiya ta jinjina kai kafin ta karasa ta bude masa kofa ya fice.. ************ "Tunda suka ba'ro sashen sarki suke ta buga sauri... kasancewar dare ne babu wani isasshen haske a hanyar..   Juwairiya da aka baro can baya ta daga murya tace.. Wai baza ku jirani bane..? Wata baiwa dake cikinsu tace,kema ki daga kafa dan Allah kina tafiya kamar wata me tausayin kasar kinsan dai dare ne atooh..   Juwairiya kamar zatayi kuka ta karawa tafiyar ta ta sauri,dan ita kam tana tsoron duhun nan sosai..      Sun sha kwana kenan kawai taji an damko hannunta da karfi.... A mutukar tsorace ta kware baki zata saka ihu..sai ji tayi wani abu me shegen taushi ya rufe mata baki,sannan aka shiga janta da karfi...     Fitsari ne kawai batayi ba sbd tsananin tsoron da fargabar data shuga...    Can bayan wani kango aka sake ta duhu ne sosai a wajen dan haka tayi yunkurin guduwa tana laluben hanya... Sai ji tayi kawai taci taro da mutum bum! Lumfashi me tsayi taja dan ko ba'a fada mata ba tasan waye... Kamshin sa kawai data ji yasa ta gane YARIMA NE.... Jalal ya sake kama hannunta suka dawo saitin da kawai dan haske a wajen..   Yana sakin hannunta ta dago da sauri suka hada ido dashi..   Jalal ya harde hannayensa yana kara matsawa gabanta..   Tadan ja baya kadan..tana fadin.. Ka ka kayi hakuri ranka shi dade..   Yarima yaja burki yana fadin,hakurin me zanyi? Juwairiya ta girgirza masa kai.. Jalal yace,"nazo ne dan ki fada min amsar ki ta dazun?   Ta dan ware ido,amsata wace kenan?ranka shi dade..? Yarima ya gyada kai yana matse lebensa na kasa.. Dariya yaso ya bata,wato dan kawai yaji amsatar ta ne.. shine ya fito da a cikin daren nan?sannan kuma har ya baro matarsa a daki?ya biyo ta ita baiwa?.   Ina jinki?ya fada yana gyara tsayuwarsa... Juwairiya ta rasa me zata ce masa,bakinta ya shiga rawa.... Ni ni ai babu wani zabi a gare ni,duk inda kuka kaini ai dolene naje nayi aikina..     Mgnr da tayi ne yasa jalal yaji wani iri har cikin zuciyarsa,wato ita baiwar su ce duk inda suka ajiyeta a nan zata zauna..   Juwairiya jin yayi shiru... sai ta dan sace kallon sa da gefen idonta..    Wai me yasa yarima ya fiya kyau ne haka?taji zuciyarta na tambayar ta..   Jitai yace.. "Ki shiga dakina gobe ki gyara min shi"(hakanan ya tsinci kansa da fadin hakan,dan zuciyarsa na mutukar kwadayin ganinta a kullum) Kafin ta bashi amsa ya juya ya fara tafiya.. Da sauri tabi shi tasha gabansa tana fadin..   Ranka shi dade ba nan bane wajen aikina..,bazan iya samun shiga na gyara maka dakin ba..kayi hakuri..   Yarima ya daure fuska.. Umarni ne nake baki a matsayina na sarkin ki.. dan haka bana son wani dogon zance.. Juwairiya ta samu kanta da langwabe masa kai gefe,sannan tayi kasa da kanta tace toh ranka shi dade..    Jalal yayi murmushi kafin yace "wuce muje.. Ta kalleshi da mamaki,ina zamuje?   Yace ina zaki je da? Tace rumfar bayi zan koma ai.. Yace toh muje... Tace,A tare zamu?ta waro ido.. Ka bari kawai zan tafi da kaina.. Jalal bai tanka ma ta ba ya shige gaba ya fara tafiya..    Juwairiya da sauri tabi bayansa dan kuwa tasan bazata iya komawa ita kadai din ba a wanannan dare ga kuma duhu.. "Yana gaba tana biye da shi a baya.. Gani nayi juwairiya sai faman sakin murmushi takeyi tana kallon  yarda yarima ke tafiyarsa cikin kasaita da yanga kamar ba namiji ba..duk takun da zayyi cikin nutsuwa yakeyin sa..   Ta shafa gefen fuskarta cike da nishadi.. ooh Allah me nasa ikon..wai yau kamar ta baiwa diyar bayi. SARKI da kansa yakeyi wa rakiya a cikin dare..     Dadi ne fal a cikin zuciyarta, sai shakar kamshin da yake bazawa a hanyar takeyi. "Shima din jalal murmushi yakeyi yana mamakin kansa,wani irin nishadi ke dawainiya dashi,ya rasa dalilin da zuciyarsa ke mutukar son kadaicewa wannan yarinyar.. Tafiya yakeyi kamar baya so.. Dan dama ba wani son suyi saurin yakeyi ba. baya kaunar su iso rumfar bayi da wuri..     Tsayawa yayi ya juyo dan ganin ko yayi mata nisa...(cike da kulawa kamar yarda ko wane gentleman zayyi." kun de gane😉) "Juwairiya kam tayi nisa sosai a cikin nata duniyar.. dan ko kadan bata ma lura da tsayawar da yayi ba...sai ji tayi taci karo da wani mutum..bum!   A tsorace ta dawo hankalinta.. sannan taja baya da karfinta..zanin jikinta ne ya ta'diye ta..ta tafi zata fadi..    Yarima yayi saurin saka hannayensa ya taro ta.. Sauke lumfashi kawai takeyi dan ya shammace ta... "Kurawa juna ido sukayi na wani lkcn me tsawo.. kafin ya gyara mata tsayuwarta yace..    Tunanin me kikeyi haka? Juwairiya ta samu kanta da fadin.. "Tunanin ka"! Waro ido tayi da sauri jin abunda bakinta ya furta..ta zube kasa a mutukar kunyace..    Jalal kuwa samun kansa yayi da jin dadin furucin ta"tunanin ka"ya lumshe ido...     Juwairiya ta shiga bugun bakinta.. Kafin tace,kayi hkr ranka shi dade subutar baki ne nayi tunanin kaina nakeyi..me yasa ma zanyi tunanin mai martaba ai ban kai wannan matsayin ba..   Yarima ya bude ido yana kunshe dariyar sa..dan ya fahimci kunya taji.. Mike! Ya fada a daken sa.. Ta mike tsaye ta kasa ko kallonsa.. Muje.... Ya fada yana ci gaba da tafiya.. Har suka kawo kusa da rumfar bayi juwairiya bata daina jin haushin kanta ba..   Ya tsaya yana juyowa gabanta.. Ki shiga.. Ta gyada kai.. Har ta fara tafiya ta sake dawowa da saurinta..   Nagode kwarai da gaske ranka shi dade.. Ya jinjina kai kawai bai ce komai ba. sannan ya juya ya fice...   Juwairiya ta dafe kirjinta sannan ta juya dan shigewa cikin rumfar bayi sai murmushi takeyi..   caraf sai hango umayma tayi a tsaye bakin kofar tana kare mata kallo..    Gabanta ne ya fadi.. Kada dai umayma taga mai martaba yanzun nan? Umayma ta kura mata ido cike da tuhuma. fitowar ta kenan jin su hansai na jajen rashin dawowar juwairiya da wuri.. Waye wancan daya rako ta?umaymata tambayi kanta dan bayansa kawai ta iya hangowa sbd duhun wajen...,lallai kuwa akwai abunda wannan yarinyar ke boyewa..dole sai ta shiga jikinta sosai dan ta gano miye sirrinta..     Da sauri ta kamo hannun juwairiya,kin dawo?dama neman ki zan fita yanzu wlh.. naji ne su laure nata cigiyarki ganin abokan aikin ki sun dade da dawowa babu ke..   Juwairiya tayi murmushin yake,ai a baya suka baro ni ne.. Umayma tace Allah sarki muje ciki toh.. Juwairiya ta gyada kai suka shige ciki a tare.. ************ Washe gari...   Gimbiya kilishi ce tayi kiran surukan nata..   Ta kallesu duka daya bayan daya kafin tace..   Ina fatan ku duka kun samu labarin yarda al'adar masarautar mu take... Idan har aka na'da sabon sarki toh dole ne idan ya cika sati na biyu a mulkinsa matansa ne da kansu zasu shiga madafa suyi masa girki...      Khadija tadan murmusa dan dama ita jiran wannan ranar kawai takeyi,dan ta burge jalal ta samu yabawar sa.. surayya kuwa uwar son jiki cewa tai... Umma amma dai na yau din kadai ne ko? Kilishi ta gyada kai,yau da gobe ne tunda matansa biyu.. dan haka dolene ku raba rana kun yarda yayi muku. wacece zatayi yau sannan wacece zatayi gobe..?   Khadija tayi saurin fadin,ai umma tunda surayya ce babba ita ya kamata tayi yau din ni sai nayi gobe ko?   Kilishi tace hakan ma yayi,ta maida kallonta kan surayya, kije ki shirya zan hadaki da du'bu dake Rumfar bayi.. Surayya tayi saurin yatsine fuska,umma a cikin RUMFAR BAYI zamuje yin girkin? Kilishi girgirza kai tace,ai jinin sarauta baya shiga rumfar bayi..kanskanci a garemu hada jiki da bayin mu.. akwai madafa a can sabon bangare.. dan haka a can ne zakuyi girkin naku,sai ki zaba bayin da zasu taimaka miki.. Surayya ta gyada kai sannan ta mike cike da haushin wannan banzar al'adar ta fita.. *************** "Da safe" "Koda juwairiya ta shigo sashen sarki,sai ta samu kanta da rasa taya zata shiga dakin na jalal. taji dai ance tun asubahi surayya tabar sashen..   Jakadiya ce tayi kiranta,da sauri ta karasa wajenta.. Kallonta tayi tana wani nazari kafin tace,ki shiga dakin mai martaba ki gyara masa.. Juwairiya tace ni? Jakadiya tace kwarai ke juwairiya . Ta gyada kai kafin tace,toh inna.. "Sannan ta nufi hanyar dakin.. jakadiya kuwa tabi ta da kallo tana mamakin yarda jalal yasan har sunan juwairiya kuma ya bukaci data tura masa ita gyaran dakinsa,Allah dai yasa ba abunda take zargi bane.. ************* Tana shiga dakin ta ware ido ganin irin girmansa ga furnitures masu shegen kyau da tsada,dakin ya tsaru iya tsaruwa..      Motsin dataji ne a cikin toilet ya tabbatar mata da cewa yarima yana ciki..   gyara daurin zanin ta tayi sannan ta sa'bi tsintsiyar dake hannunta ta shiga gyaran dakin cikin kwarewa.. Ba karamin mamakin dadewar yarima acikin toilet tayi ba,sai kace wani mace?     Tana goge goge ne taji fitowar shi daga cikin ban dakin..    Kamshin sabulun wankansa ne ya daki hancinta.. Ta juyo dan gaisar dashi.. Sai ganin sa tayi daga shi se wani dan towel ya daura a kugunsa..   Tayi kasa da kai da saurinta.. Tace barka da safiya mai martaba.. Ya kura mata ido.. Sannan ya shiga tafiya wajen da kayansa suke yana fadin.. "Na lura baki dauki mgn ta da mahimmanci ba ko? juwairiya tace,kayi hkr ranka shi dade.. Yayi shiru ya shiga shirinsa.. juwairiya ta juya dan ficewa ta basa waje.. Jitai yace... "Ki zauna ki jirani" Batayi gardama ba Ta samu waje ta zauna kasa.. Da gefen ido take kallon yarda yake shiryawar sa cikin nutsuwa da kasaita,ya shafa turare sun kai shidda (tadan matse baki,shiyasa yake kamshi abunsa)..    Sai daya gama shirinsa tsaf sannan ya dawo ya zauna a gefen gado yace..   Ina son anjima da daddare ki same ni a can wajen da muka hadu jiya.. Juwairiya ta gyada kai..   Jakadiya ce ta rangwada sallama.. Juwairiya jiki na rawa ta mike ta koma bakin kofa ta tsaya. Jakadiya ta shigo tadan kalleta tace, idan kin gama kije umayma na neman ki a waje.. Juwairiya ta gyada kai ta fita.. Jakadiya ta karasa wajen jalal tana fadin..      AMALE bango madafar bayi,dama yanzu ne gimbiya kilishi ta aiko da sako a fada maka.. Jalal ya jinjina kai irin inajin ki.. Jakadiya tace,idan ranka shi dade bai manta ba a al'adar masarautar nan duk cikon sati biyu na sabon sarki matansa ne da kansu zasu fito suyi masa girki.. Dan haka ne yau sarauniya surayya zata shiga madafa da kanta ta girka maka abinci na gani na fada. gimbiya kilishi tace a sanar dakai kada kaci komai har lkcn da za'a gabatar maka da abincin.. Jalal ya gyada kai yace,naji jakadiya, magajin ya iso ne? Jakadiya tace,ya iso ranka shi dade yana can a falo yana jiran fitowarka.. ************ "Juwairiya na fitowa daga cikin dakin yarima ta tarar da magaji zaune a falon..   Ta duka har kasa ta gaishe dashi.. Magaji a sake ya amsa mata,harta mike zata fita yace.. Bakiji ba.. Ta dawo tace na'am.. Ya kurawa fuskarta ido.. Kafin yace,Ina tunanin kamar na san fuskar nan taki shekaru da suka wuce..   Juwairiya se a lkcn itama ta dago tana kallonsa sosai..   Kallon juna sukayi kafin a tare suka nuna junansu suna fadin.. MANGORO ko??????... Murmushi sukayi wa juna.. Magaji yace,haba ko da ince ni na san nasan wannan fuskar ashe ke din ce.. Juwairiya tace,ai kuwa dai ni ce kaga ko ranar ban samu damar yi maka godiya ba.. Magaji yayi dariya ah ah ai ya wuce shekaru dayawa,kinsan kuwa tunda ga ranar ban sake ganinki acikin masarautar nan ba ,har nemanki nayi. Juwairiya tace,Allah sarki ai lkcn ne na fara aiki a sashen zainaba shi ya sa. Yana shirin mgn sai ga jakadiya tare da yarima sun fito..   Jalal idonsa akan juwairiya,ganin murmushi akan fuskar ta yasa shi kallon magaji... Shima din yaga murmushi akan leben sa...   Daure fuska yayi yace.. Magaji muje ko? Magaji yace mai martaba sai yanzu aka samu fitowar? Yarima yayi banza da shi..dan yasan halin magaji da zolaya.. Jakadiya ta kalli juwairiya, ke baki je neman da ake mikin bane? Juwairiya tayi saurin guduwa tabar wajen.. Jalal yayi gaba shima.. Magaji yayi saurin binsa a baya yana fadin.. Takawarka lafiya darzaza amalen sarakuna.... ************ "Har suka shiga fada jalal bai kalli inda magaji yake ba.. Magaji kuwa zancen nata cinsa a rai.. Kasa hakuri yayi Yace,wai ka san kuwa mai martaba yarinyar nan itace dai wacce na taba gani shekarun baya.. Se lkcn jalal ya kallo shi.. Wace yarinyar? Magaji ya washe baki.. Wannan me konannar fuskar mana da mukaje da ita chadi.. Nayi mamaki sosai ma da ta gane ni itama wlh.. Yarima ya tabe baki..yaci gaba da aikin gabansa. *************** "Zainaba ta kalli zabba'u,tashi muje sashen khadija.. Zabba'u tace toh ranki ya dade.. "Sun shiga sashen suka tarar da goggon khadija tazo.. Zainaba ta gaishe ta sannan ta dawo falo ta zauna tana jiran khadija ta sallame goggon nata.. "Goggo ta kalli khadija,ina fata kin gane bayanin da nayi miki ko? Khadija ta murmusa na fahimci duk bayanin ki goggo,kada ki damu zan samu wacce na yarda da ita ta shiga cikin bayin da zasu tayata girkin sai tayi yarda kika fada din.. Goggo tace yauwa nizan koma.. "Sun fito falo zainaba ta kalli khadija dake ta washe baki.. Yadai ko goggo tazo miki da wani albishir din ne? muje zuwa👇 TEAM RUMFAR BAYI   [9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction ) Na Afrah bhai Page 23 Wattpad @afreey101 _"@ Ayshat maghili,Admin TEAM RUMFAR BAYI group thanks for the effort love😚"_ ***************** "Khadija ta saki murmushi, ai abunda ma yafi albishir tazo min dashi..   Zainaba ta gyara zamanta,Allah ko?sannu yar lelen goggonta.. Khadija ta kwashe da dariya.. Kafin tace,wai ina Mustapha ne?kinsan dai da an gama mgnr bikin su ya turaki da hamza kanki za'a dawo ko?    Zainaba ta lumfasa,nima damuwata kenan wlh,kuma gashi kinsan halin abba da shegen son auren hadin nan daya burgeni ko kadan.. Khadija ta dan zungureta,ni ai auren hadin ba karamin taimaka min yayi ba,ke kinsan in ba dan shi ba ai bazan taba samun ya jalal dina ba.. Zainaba tace ke kenan,ni kin ganni nan ma kadaici duk ya ishe ni a cikin yan kwanankin nan, tun dauke min juwairiya da mijin ki yayi..    Khadija ta tabe baki.. Kema dai zainaba da rigima kike, kawai ki bari sai lkcn auren ki yayi sai ki zabe ta a matsayin kyautar ki daga wajen mai martaba.. Zainaba ta sa dariya,wlh kin kawo shawara kawata.. Suka saka dariya a tare.. *************** "Umayma da kanta takai juwairiya har wajen surayya. . Surayya ta kalle ta cike da kyamata tace.. Ki shirya zamu shiga madafa dake yanzu.. Juwairiya tadanyi mamaki amma ta share tace toh ranki ya dade .. "Tunda suka shiga madafar suka soma aiki ba kama hannu yaro.. Surayya kam na hakimce akan kujera tana basu orders cike da isa..   Har sun kusa kammala aikin juwairiya dake gefe ta jinjina kai ganin irin delicacies din da aka shiryawa yarima.. tana mamakin yarda mutum daya zai iya cinye duk wadannan abincin.. Abinci har kusan kala goma sha biyar?ina zai kaisu? Aiko duk tsokali daya yayi a duka se cikinsa ya koshi.. Tadan tabe baki,ko dayake duk bajinta ce ake son a yi masa..   Juyowar da zatayi kawai ta hango wata baiwa na barbada wani gari acikin tukunyar miya..    Da sauri ta karasa wajenta.. Baiwar tayi saurin kakkabe hannunta tana kallon juwairiya da kananun idanunta tace,lafiya? Juwairiya tace,me kika zuba acikin tukunyar nan yanzun nan? Baiwar ta watsa mata harara tace,zargi kikeyi?toh babu abunda na zuba sai gishiri..tana gama fadin haka tayi gaba da sauri.. Juwairiya taji gabanta ya fadi.. Meye ta zuba a abincin yarima?ta tambayi kanta.. Hankalinta ne yadan tashi dan ita kam bazata so a cuci yarima ba...   Umayma ce tazo tayi kiranta akan surayya tace su fara kai abincin can babban falon jalal.. **************** Rabi ce ta shigo sashen khadija da gudun ta.. A daki ta tarar da khadija a zaune gefen gado.. Ta samu waje a kasa ta zauna tana lankwashe kafafunta tace.. Albishirinki ranki ya dade? Khadija ta saki murmushi bani in sha.. Rabi tace yanzun nan muka gama da mgn da wannan baiwar da muka saka aiki acikin bayin gimbiya surayya.. Kuma Ta tabbatar da min cewa tayi yarda muka bukaci tayi... Khadija ta kwashe da dariya cike da murna sosai.. Tace naji dadin albishir din nan sosai.. Dan Babu wacce zata samu yabawar jalal sai ni ni kadai kuma... Su uwar gida manya,dole ne asha kunya da wulakanci ayau.. Ta kalli rabi,Allah yasa dai ta zuba dan'tsamin nan dayawa acikin abincin dan bana so ko kadan girkin wannan matar yakai cikin cikin ya jalal dina.. Rabi tace kada ki damu ranki ya dade na tabbata tayi komai kamar yarda muka tsara.. *************** "Su juwairiya sun gama jidar abincin zuwa sashen jalal.. An gana gyara falon tsab kamar za'ayi wata uwar liyafa..   Kuyangi biyu akabari sai surayya data sha wata uwar kwalliya tana zaune gefe tana jiran fitowar yarima..    Kallon su juwairiya tayi,tace duk zaku iya tafiya.. A sanyaye juwairiya ta fito tunani duk ya cika zuciyarta.. Ta kasa yarda gishiri ne wannan baiwar ta saka a cikin abincin yarima,kodai wanine ke son halakar da shi?toh amma waye zai so cutar da sarki? Da wadan nan tunane tunane ta isa rumfar bayi..     ******** Sai da jalal ya gama shirin sa tsab acikin kayansa masu tsada sannan ya fito falon.. Surayya ta mike cike da kissa tace.. Sannu da fitowa sarkina.. Yarima ya jinjina kai yana shirin zama .. Surayya tace,na tabbata zaka yabawa kokarina.. Yarima ya kalli jerin abincinan dake gabansa.. Lallai kinsa aiki,duk wannan abincin ina zan kai su? Surayya tace,haka zakace ma kenan ki? Jalal ya murmusa bai ce komai ba.. Surayya ta banka wa kuyangin harara,ku zuba masa mana kuka tsaya kallon mu..    jiki na rawa sukayi serving din yarima first dish,wanda ya kun'shi (farar shinkafa me kayan lambu da miyar tsokar shanu,sai dafaffen kwai a gefe), Jalal ya dauki tsokali cike da yanga ya tsakuri abincin yakai bakinsa..     yamutse fuska yayi yana Matse baki jin wani irin mugun tsami ya gauraye masa baki.. Da sauri Ya kalli surayya a fusace.. Miye wannan?harshena kike shirin cirewa..!ko kashe ni kike son yi? Surayya taji gabanta ya fadi tace a rikice me kike nufi jalal? Yasa hannu ya ture plate din daga gabansa... ya tura mata shi yace.. Dandana kiji ma kanki mana!wannan ai muguntar banza ce.. Surayya hannu na rawa ta dauki tsokali ta soma dandana abincin..    Da sauri ta zubar dana bakinta..tace..na shiga uku! Meye haka?wallahi ba haka abincina yake ba..ta fadi kamar zata rusa kuka..   Jalal yaja tsaki hade da mikewa cike da haushi ya fice daga sashen abunsa.. ************ "Juwairiya gaba daya ta kasa tsaye ta kasa tzaune,tunanin halin da yarima yake ciki kawai takeyi,ta kagu duhu ya fara taje ta same sa a inda yace su hadu.. laure ce ta kawo mata kwanon abincinta da bataci ba. kewai ban gane miki ba?tunda kika dawo kike a nan zaune kin buga uban tagumi sai kace wacce ta ka'yar da uwar miji..lafiya ? Juwairiya ta girgirza kai tace,babu komai goggo laure amma ni na koshi da wannan abincin ki koma dashi.. Laure ta ajiye kwanon hannunta,nasan dai bakici komai ba dan haka ki ajiye zuwa anjima idan kin gama muraja'ar,tana gama fadar haka ta fice.. Juwairiya ta mike itama tana kallon jikinta,a haka zataje wajen yariman?taji zuciyarta ta fada .. Wasu kayanta masu dan haske ta canza sannan ta lallaba tayi waje da gudu.. ************** "Tunda ta fito Gaba daya tunani takeyi,Allah dai yasa babu wani abunda ya faru da shi..     Tana isa wajen ta samu wani dutse ta zaune akai tana buga uban tagumi.. Daga kai tayi ta kalli sama,garin yayi duhu amma hasken taurari ya kayatar da daren..    Ta dade a wajen zaune,zuciyarta na gargadinta ko dai yarima bazai samu zuwa bane?wata kilan ma ya manta da haduwar tasu a nan..     Ta mike a sanyaye, dama mai take tunani wacece ita da yarima zai zo ya same ta,wata zuciyar tace mata,toh ai shine ya bukaci ku hadun? Mtsww....(whatever ) *************** "Koda ya fito daga sashen sa da hamza sukaci karo a hanya.. Hamza ya bishi da kallon tuhuma yace.. Yaya sai ina ne haka da daren nan?gashi babu wani bafade a tare dakai.. Jalal yadan dafa kafadarsa,hamza kenan kasan fa ko sarki yana son sirri..shiyasa ban gayyaci kowa a fitar tawa ba..   hamza ya mishi kallon rashin fahimta.. Jalal ya murmusa.. Hamza..ya kwashe da dariya yana cewa ooooh sai yanzu na gane ai yaya,amma kasan dai duk inda zaka wuce a masarautar nan indai a haka kake... (ya nuna shigar alfarmar dake jikin yarima) to dole ne mutane su shaida ka.. kaga ba wani batun sirri kenan... Jalal ya jinjina kai ganin lkcn da dan sauran haske ko ina zai wuce sai an lura dashi.. Hamza yace,kana son taimako na? Jalal yace,wane irin taimako zakayi min kanina? Hamza yace duk da bansan ina ne wajen sirrin naka ba amma ina tunanin da ka batar da kama zai fi.. Jalal yadan kwabe fuska,ni da masarauta ta ina matsayin sarki sai na batar kamanni na dan na samu sirri.. Hamza yayi dariya,ka yarda dani yaya.. Jalal ya danyi shiru,baya son kowa yasan inda zayaje,kuma da gskyr hamza, idan ya fita a haka akwai yan gulma da kai rohoto.. Na amince... Hamza yace toh muje.. Sashen hamza suka shiga.. Hamza ya saka wani bawansa da ya kawo masa kaya irin na low class dinnan,ya mikawa jalal gashi ka saka.. Jalal ya yatsine fuska ni zan saka wannan?(ya yastine fuska yana kallon kayan dake hannun hamza) Hamza ya zauna a gefensa,haba yaya ai a hakane kawai zaka iya fita cikin masarautar nan babu wanda zai gane ka.. Jalal ya jinjina kai kafin yadan ja tsaki ya amsa yaje ya saka.. Yana fitowa hamza ya kwashe da dariya.. Jalal ya harare shi..kafin ya fice abunsa cikin sauri yana jin haushin tsaida shi da hamza yayi.. ******************* "Juwairiya kuwa har ta fara tafiya abunta dan komawa rumfar bayi sbd dai ta cire rai da zuwan nasa...    Jalal kuwa na can sai buga sauri yakeyi..(duk inda wuce se yaga kamar za'a gane shi,amma ga mamakinsa ko kallo bai ishe kowa ba). Yana karasowa wajen ya hango ta tana tafiya zata bar wajen.. Karasawa yayi zuwa bayanta yace.. "Ji mana yan mata...."     Juwairiya ta juyo da sauri tana kare masa kallo daga sama har kasansa..      Waro ido tayi cikin mamaki tace.. Mai martaba kai ne haka? Jalal ya samu kansa da murmusawa..   Juwairiya tayi kasake tana kallonsa.. Yace mu karasa can.. da ina zaki tafi? Juwairiya tayi kasa da kai tace.. na zata ai ka fasa zuwa ne..    Jalal ya samu waje ya zauna.. juwairiya ta kura masa ido tana godewa Allah da babu abunda ya same sa..    "se Ki zauna idan kin gama tunanin.." juwairiya tayi dan firgigit..ta nemi waje itama ta zauna,gaba daya dadi ya lullube ta,wai ita juwairiya ce zaune da sarki guda a waje daya kuma a kadaice...    Jalal kallonta kawai yakeyi.. Shiru har kusan minti talati bai ce komai ba.. juwairiya ta dago ta kallesa,gani tayi ita yake kallo,tace,mai martaba kace na same a nan..? Jalal ya gyada kai...jitai yace.. Ina so na sake baki wani umarnin ne... Juwairiya tace ina jinka..ranka shi dade.. Jalal ya gyara zamansa..kafin yace.. Akan tambayar da kikayi min ne jiya na son sanin dalilina na kyautata miki da nakeyi.. Juwairiya taji gabanta ya hau faduwa.. Yaci gaba.. A gaskiya ni kaina ban san dalili ba.. Amma inaso kiyi min wata alfarma..ko nace umarni nake baki,ki zauna tare dani (stay by mu side) har sai na samo amsar tambayar,dan ni kaina tana ci min tuwo a kwarya..     Juwairiya taja lumfashi ,na zauna tare da shi?kamar ya kenan? Jalal kamar yasan me take tunani.. Yace,ki zauna a sashena kiyi min hidima har lkcn da zan samu amsar..nake nufi.. Juwairiya ta gyada kai,ai ni dama bani da wani ikon barin sashenka mai martaba dan haka kada mai martaba ya damu..   Jalal ya saki murmushi me kayatarwa sannan ya kalli jikinsa..yace.. Ban taba saka kaya irin wannan ba.. Juwairiya ta kalleshi itama tana dariya kasa kasa sai kace ba yarima dan gwalisa ba..yasha wasu tazarce..    Jalal ya kura mata ido, "ni kikeyi wa dariya? Baki san duk sbd ke bane... ! Juwairiya ta waro ido...sbd ni?ta nuna kanta.. Jalal yaji haushin furucin da yayi.. Ya dauke kai kawai yana kallon taurarin dake sama.. Juwairiya ta mike tace.. Ni zan taf... Mgnr ce ta yanke mata jin kukan da cikin yarima yayi..kululululu...    Da sauri ta kallo shi.. tace ranka shi dade yunwa kake ji ne? Jalal ya runtse ido, dan rabonshi da abinci tun da safe.. wai duk dan sbd wata al'adar masarauta..mtsww.. juwairiya da mamki tace a zuciyarta ,na zata ai se yafi kowa cika cikinsa a yau?,duk wadannan kayan dadi?ko bai ma ci bane?saboda yazo wajenta?inaaa ah ah ! Ai bata da wannan mahimmanci a wajen sa.. Jalal ne ya mike bai ce mata komai ba sai kawai ya shiga jan hannunta..   Juwairiya a tsorace tace ina zamuje?ranka shi dade? Yarima yaja burki kafin ya sakar mata hannun yace.. Rakiya zakiyi min, kuma umarni ne nake baki.. Juwairiya tayi kasa da kai kafin tace,toh muje..   Jalal ya juya cikin kasaita suka fara tafiya.... Muje zuwa...👇 TEAM RUMFAR BAYI    [9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 24 Wattpad @afreey101 I Pherty dedicate dis chapter to Zauren Biebie Isa Group, Sameena Aliyu Novel Group and Pherty Novel Group, Afrah na godiya❤ ********************* "Tafiya kawai sukeyi amma juwairiya sai ta tsinci kanta a cikin farin ciki sosai..     Yarima ne zata yiwa rakiya? Uhmm lallai ta samu wuri kam.. Tuntube ne tayi hakan yasa ta dawo hankalinta.. Sai Can ta hango sa yayi mata dan nisa.. kuma sai ta taga ya nufi hanyar fita daga masarautar ..   Ai da gudun ta ta karasa gefensa tana fadin.. Allah ya kara maka yawan rai,dama wajen masarautar zamuje ne?naga dare yayi ne?    Jalal ya tsaya tsak yana kallonta,kafin yace da ita kai tsaye.. tsoro kike ji? Ta dago ta kalleshi itama.. Ta girgirza masa kai.. Yace,baki yarda dani bane? Ta kafe shi da ido,kafin ta sake girgiza masa kanta.. Ya jinjinar da kai kawai yayi gaba.. Itama tabi shi a baya da saurinta... "Sun sha uwar tafiya me nisa kafin suka kawo babban gate din fita.... Fadawa ne sun kai biyar dake gadin wajen.. "Tsayar dasu akayi.. "Kai sai ina!! Jalal da juwairiya suka ja suka tsaya.. Fadawan suka sha gabansu.. Baku ji me akace muku bane? sai ina? Jalal har ya dago a fusace dan yayi musu rashin mutumci sai kuma ya tuna da shifa a yanzu ba sarkin su bane.... Sunne kai ya shiga yi dan baya so su gano shi.. Juwairiya ta lura dashi dan haka tayi saurin dawowa gabansa dan ta kare shi... kafin nan ta hada duk karfinta tace..   'Umarni ne aka bamu daga wajen fulani, masu fataucin kayane suka shigo kasar shine aka tura mu dan amso sakon ta sbd juyawa zasuyi da asuba..    "Fadawan suka shiga gyada kai cike da gamsuwa kafin nan suka bude musu gate din sukace,kuyi hanzarin dawowa... Juwairiya tayi musu godiya kafin nan suka fice.. "Cikin gari suka shiga, juwairiya dai bin sa kawai takeyi tana mamakin abunda ya kawo su har cikin gari da daddaren nan..   A gaban wani me gasasshen kifi da dankalin hausa ya ja ya tsaya.. Juwairiya ta kalleshi,uhm yunwar dai yaji kenan.. Gani tayi yayi tsaye kawai bai ce komai ba sai faman kallon kifin yakeyi..   Kusa dashi ta dan matsa tace,ranka shi dade ba siya zakayi bane?   Ya gyada mata kai.. Murmushi tayi dan ta fahimci cinikin ne bai ma san yarda akeyi yinshi ba. (She don't blame him tunda dai komai yake so yana dashi a ajiye ba sai ya fita ya nema ba)    "Me siyar da kifin ta kalla,malam a bamu kifi biyu da dankalin biyu shima.. Jalal dai kallonta kawai yakeyi,gani ma yayi ta shiga zabar musu manya mayan kifin tana fadawa me siyar da kifin su take so.. Me kifi ya saka musu acikin takarda.. juwairiya ta amsa ta mikawa jalal.. Ya amsa yana kallonta.. Tace mai martaba kudin sa fa?. Ya saka hannu cikin aljihun sa yaji wayam.. Runtse ido yayi dan sai yanzu ya tuna da cewa ba kayan sa bane a jikinsa.. Juwairiya ta waro ido tana kasa da murya tace.. Badai baka fito da kudin ba? Jalal ya gyada mata kai yana cije lebensa.. Juwairiya ta dafe goshi tace, yanzu ya zamuyi kenan? Jalal ya kalli zobunan dake hannunsa a jere ya ciro daya daga ciki ya mika mata.. Ki biya shi da wannan dan na tabbata kudinsa kawai ze iya siyen daya wajen nan sau biyar..   Juwairiya ta saki baki tana kallonsa.. Jalal Ya juya da kansa ya mikawa mutumin zoben sannan ya karasa wajen wani kututturen itace ya zauna.. Juwairiya ta juya wajen me siyar da kifin tace masa.. Malam Ka ajiye min zoben can gobe zan kawo maka kudinka na amshe shi.. Me kifi ya daure fuska a take.. dan shi kam har ya hau murna yayi kudi a dare daya.. Cikin haushi yace..Toh dai idan baki zo da wuri ba ki sani siyar dashi zanyi.. Juwairiya tace zan ma zo din ka ajiye min... "Tsayawa tayi tana kallon yarda yarima ke cin kifin...cike da yanga yake tsakurar shi.. Baki ta tabe,ji abunda aka fito siya tunda masarauta amma kalla yarda yake cin sa..   Jalal ya dago yace,magana kike? A take ta daburce dan a tunanin ta acikin zuciyarta ne tayi mgnr..ni ni bance komai ba ranka shi dade.. Jalal ya nuna mata kusa dashi yace zauna.. Ta zauna babu gardama.. Takardar kifin ya ajiye a kan cinyar ta yace..    Ciyar dani... Ta waro ido.. Shima din yayi yarda tayi.. Wato ya waro idon shima yace.. Na ga ai kin fi ni sanin yarda ake cin sa ko? Juwairiya tayi wiki wiki da ido.. Baki ya bude yana mata nuni da ido akan ta fara aikinta.. Juwairiya ta sauke lumfashi kafin ta saka hannu ta ciro tsokar kifi ta cire kayoyin sannan ta hada da dankalin ta kai bakinsa ta tura.. Ware ido yayi ganin ta cika masa bakinsa tab.. juwairiya tace,ka cinye ranka shi dade yafi dadi a haka,ta dage masa girar ta daya.. Jalal ya fara ci yana lumshe ido.. A haka tayi ta basa har ya daga hannu yace ya koshi.. Tana shirin cire hannunta daga cikin kifin yace.. Kema kici.. Ta girgirza kai,duk da itama din tana dan jin yunwar.. Jalal ya daure fuska.. Umarni ne..! Ta gyada kai sannan ta fara ci itama,ya tsare ta da ido.. "Sai cikin dare sosai suka dawo cikin masarautar..    Juwairiya taga yayi hanyar rumfar bayi.. Da sauri tasha gabansa tace.. Ranka shi dade ai dare yayi sosai kawai ka koma sashen ka.. Jalal ya kura mata ido..kafin yace.. Yaushe kika zama bai bani shawara ? Juwairiya ta matse bakinta.. Yace wuce muje.. Ta gyada kai suka hau tafiya... "Suna kawowa kusa da rumfar bayi yaja burki.. Juwairiya ta kallesa..nagode ranka shi dade.. Jalal ya jinjina kai,har ta fara tafiya sai jitai yace.. "Kada kije kina mamakin me yasa sarki guda zai jaki kuje kifi a waje..   Juwairiya tayi saurin juyowa tana kallonsa... Ya dauke kai yana ci gaba da cewa.. "Tun ina karami nake kwadayin naci kifin wajen nan watarana,amma ban samu damar hakan ba sai yau.. Juwairiya ta saki murmushi tana shirin mgn ne sukaji muryoyin bayi suna shirin fitowa..   Ai da sauri juwairiya ta janyo sa suka boye bayan wani kango... Jalal ya kura mata ido ganin yarda ta matse shi ajikin bango tana lekawa taga ko bayin sun wuce..    Wani irin shock ne yakeji a gaba daya jikinsa.. Ya kurawa gefen fuskarta ido.. Juwairiya kuwa ganin bayin lekowa sukayi kawai suka koma ciki sai ta sauke ajiyar zuciya me nauyi.. Ina zata iya bari wani ya ganta da sarki jalal!?tab bazata taba bari asirin su ya tonu ba.. Ta dago da kanta.. Sai gani tayi fuskokinsu sunyi dab da juna har tsinin hancinsu na gogar na juna..    Gabanta ne ya shiga faduwa.. Dama haka ta matse shi?wayyo... Ai da sauri taja baya tana kasa da kanta.. Jalal ya murmusa kafin yabi ta gefen ta ya fice...... ****************** "Surayya ta kalli umaymah tana damke hannayenta cike da tsananin bakin ciki da fusata.    Na tabbata wani ne ya saka a batamin girkina!kuma wlh wlh bazan yafewa ko wanene wannan ba,ni surayya bana barin bashi! Umayma ta dafa kafadarta,ranki shi dade kema ai kin san wacece zata iya yi maki irin wannan katobarar.. ina kyautata zaton gimbiya khadija ce.... Surayya ta gyada kai,lallai dole ne na koyawa wannan yarinyar hankali!!dan ta gane ni ba abokiyar yin ta bace!!! ************** Washe gari... "Juwairiya gaba daya tunda ta tashi daga barci take cikin farin ciki .. Hansai ta lura da hakan dan haka tace,lallai diyata wannan murna haka meya farune ? juwairiya ta murmusa,bata taba yin barcin me dadi irin na jiya ba.. Girgirza kai kawai tayi tace,umma babu komai wlh,kinsan haka Allah ke ikon sa watarana se kawai kaji ka tashi da farin ciki.. Hansai ta rungume ta,Allah ya baki duk farin cikin dake cikin duniyar nan diyata..juwairiya tayi dariya kema haka ummana.. *************** "Tana fitowa daga cikin rumfar bayi tayi hanyar sashen zainaba dan ta gaishe ta kafin tayi reporting wajen aikinta.. Tafiya kawai takeyi cike da murnarta har bata lura da turaki da hamza dake tsaye a gefen hanyar ba..    Turaki ya kura mata ido tun kafin ta karaso wajen da suke.. Ga mamakin sa ko kallon inda suke batayi ba bare ma ya saka ran ta gaishe su..       Hamza ya kalla yace,kayi gaba kawai ina zuwa... Bayan juwairiya yabi yana mamakin me ya dauke mata hankali har haka... Sai da suka kawo kofar shiga sashen zainaba sannan ya jira sunanta.. "juwairiya. ... Ta juyo tana kallonsa da mamaki..kafin tace ranka ya dade ina kwana? Ya murmusa lafiya lau,yau kin kawo wa kawar taki ziyara kenan? Juwairiya ta gyada kai.. Yace toh yayi kyau,sannan ya juya ya fice yana sakin murmushi.. Juwairiya ta shige ciki da murnar ta..    Zainaba ta tarar ta tule kaya a gabanta zabba'u na gyara mata linkinsu .. Tana ganin juwairiya da murna ta tare ta.. Sun gaisa sosai kafin juwairiya tayi mata sallama ta fice... ****************** "Koda ta shiga sashen sarki jakadiya ce ta tsayar da ita akan surayya na nan cikin dakin jalal.. ta jira sai ta fita sai ta shiga ta gyara..     Wani abune ya tokare mata makoshi,ta fito waje ta zauna a waje gaba daya duk farin cikin data fito dashi ya gushe... *************   "Sarkina ba zaka tashi haka nan bane? Surayya dake zaune akan gadon jalal tana shafa kirjinsa ta fada cike da kissa..    Yarima ya gyara kwanciyarsa barci ne sosai a idonsa kasancewar  bai kwanta da wuri ba jiya.. Cikin kasalalliyar murya yace.. Surayya ki fita ki bani waje mana,nace miki barci nakeji ko?   Surayya ta tabe baki...tana tunanin a ina umayma ta tsaya? ********** "Juwairiya na waje umayma ta shigo sashen dauke da tire ta rufe shi da wani dan kyalle..    Juwairiya ta kalleta, su umayma manya.. Umayma ta washe baki,lah juwairiya ai ban lura dake bane ma,wai ni jiya ina kika shige ne da daddare ? ta karashe mgnr cike da son jin gulma, dan ta nemi juwairiya jiya a Rumfar bayi bata ganta ba.. juwairiya taji gabanta ya fadi.. Ina fa zanje?dare yayi sosai ina dakin du'bu tare dasu goggo laure.. Umayma tayi murmushi a zuciyarta, lallai wannan yarinyar ita zatayi wa karya?har fa dakin du'bun ta shiga bata ganta ba,amma a fili sai cewa tayi..   Allah sarki bari na shiga uwar dakina na jira.. *********** Jakadiya ce ta shiga dakin jalal ta sanar ma surayya zuwan umayma.. Murmushi tayi a zuciyarta.. Sannan ta mike ta falon.. Umayma ta cire kyallen data rufe tiren data shigo dashi.. Glass cup ne cike da fresh milk.. Surayya ta amsa tana kallonta.. Kinyi yarda nace..? Umayma ta gyada kai.. Surayya tayi murmushi sannan ta koma cikin dakin da tiren a hannunta ..    Ajiye tiren tayi a kan wani dan karamin table sannan ta koma kan gadon jalal ta kai bakinta saitin kunnensa tace.. Sarkina ga madara can na ajiye maka ,idan ka tashi dan Allah kasha kaji?    Jalal cike da zakuwar tafiyar ta daga dakin yace.. Naji... Ta murmusa hade da kai masa sumba a goshinsa sannan ta mike ta fita tana addu'ar Allah yasa yasha madarar.. Dan dolene itama ta zama wulakancin da khadija tayi mata.. **************** _"Ni kuwa nace kome surayya ta shirya oho...."_ Muje zuwa 👇 TEAM RUMFAR BAYI [9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 25 Wattpad @afreey101 *Pls do visit n vote Me* _This page is for you TEAM RUMFAR BAYI groups..😍_ ****************** "Surayya na fitowa daga cikin dakin ta jawo umayma gefe tace da ita.... ki samu waje ki tsaya a nan har sai kin tabbatar min da jalal yasha wannan madarar kina ji?... Umayma ta gyada kai kada ki damu ranki shi dade(ur wish is my commad) ... Surayya tace yauwa, sannan ta nufi hanyar fita.. A nan ta hango juwairiya a zaune ta takure.. Ta watsa mata harara tayi gaba.. Juwairiya ta girgiza kai kawai tabi bayanta da kallo..      sai ga Jakadiya tazo tayi kiran ta bayan fitar surayya da minti kusan talatin..     ************** A hankali ta shiga dakin tana kare masa kallo.. Idonta ne yakar kan gadon.. A can ta hango sa ya takure waje daya yana ta barcinsa.. Me yasa jakadiya tace ta shigo bayan jalal din ma bai tashi ba.. Har ta juya zata fita sai kuma ta dawo da sauri ta je gaban gadon ta tsaya..     Kirjinta na bugawa ta kurawa fuskarsa ido tana tunanin me yasa zuciyarta take son ta kai ta inda aka fi karfin ta ne...juwairiya jalal yafi karfin baiwa kamar ki...    Taja lumfashi....zata juya ta fita kenan.. Sai Ganin wani kwaro tayi yana shirin hawa kan jikin jalal..dan har ya haye kan abun rufar sa.. Da sauri ta kai hannunta wajen ta kore masa shi.. Tana shirin gyara tsayuwarta ne kawai taji tayi losing balance dinta ta fado a kansa tim! "Jalal ya farka a fusace yana fadin.. Surayya wai me nace miki ne huh! Ga mamakin sa sai ganin juwairiya ce saman jikinsa tana mutsu mutsun tashi..gabanta nata faduwa..     Har sa samu tayi kokarin dafawa da hannunta zata mike sai kawai taji ya sake fisgo ta ta koma fadawa a kansa..    Waro ido tayi tana kallonsa cike da tsoro... Jalal ya tsare ta da ido..jitai yace.. "Kinsan kuwa miye hukuncin abunda kikayi yanzun? Bakin ta na rawa ta girgiza masa kai.. In a naughty tune yace.... Baki san da cewa duk baiwar da ta hada jikinta dana sarki ba ta zama mallakinsa.... (wato concubine dinsa)   ta Sa'ke ware idonta dan ta tsorata sosai.. Jalal yayi murmushin mugunta..kafin yaja hancinta yace.. Haka kike so ai... Shiyasa kika kawo kanki kan shinfida ta ko? Juwairiya kamar ta nutse ta shiga kokarin tashi tana girgiza kanta.. Jalal ya sake ta yana kunshe dariyar sa..ta mike tana jin kamar lumfashin ta ya dauke.. se jan iska takeyi tana dafe da kirjinta..   Shi kansa yarima ji yakeyi kamar gangar jikinsa kamar ba tasa ba dan duk jikinsa ya daskare waje daya.. "Juwairiya ta karasa wajen window tana jan lumfashi tana lumshe idonta,kafin ta dawo ta fara kimtsa dakin..   Jalal ya sauko daga kan gadon idonshi yakai kan cup din fresh milk din da surayya tace ta ajiye masa.. Karasawa yayi ya dauka yashanye duka dan ji yake makoshinsa duk ya bushe..    Ke...! Ya kira juwairiya dake kokarin kakkabe kujera.. Zo ki fitar da wannan..ya nuna tiren gabansa.. Ta gyada kai tazo ta dauka ta fita.. Yabi ta da kallo kafin ya saki murmushi.. "Tana fita ta mikawa wata baiwa tace ta tayata fitar mata dashi..   Umayma dake lebe tana kallonsu ta saki murmushin murna ganin kofin madarar babu komai a ciki.. Ai da gudu ta karasa sashen surayya.. Surayya ta mike da sauri ganinta.. Umayma tace, ranki shi dade sarki jalal yashanye madarar nan duka.. Surayya ta kwashe da dariya.. Haka nake so...! Ai wannan shegiyar yarinyar sai ta raina kanta yau itama.. Umayma tace,kwarai kuwa ranki shi dade shiyasa na samo mana wannan maganin me fitar da dandanon harshe (lack of taste) kinga komai zata girka ma sarki jalal bazai taba jin dan danon sa ba..ko kokarinta zai zama a banza Surayya ta gyada kai,shi yasa nake alfahari dake umaymah duk suka saka dariyar samun nasara.. ************* "Juwairiya na gyaran dakin jalal na zaune akan kujera yana kallonta.. Har dai ta fara tsarguwa da irin kallon nashi,duk dagowar da zatayi se sun hada ido dashi,.. Wai yau bashi da aikin yi ne ko me? Ko wanka bata ga yana niyyar shiga yayi ba ma..    "Tana kammala gyaran ta kalleshi.. Na kammala ranka shi dade ka huta lafiya.. Jalal yayi saurin mikewa yasa hannu ya fisgo ta baya.. Ta kalleshi da tsantsar mamaki.. Langwabar da kai yayi yace.. Ke nake jira ki shiga ki hado min ruwan wankana.. Juwairiya tadan yi kasa da kai.. Amma mai martaba ai akwai kuyangin da suke hada maka.. Jalal ya samu kansa da fadin.. "Ke nake so kiyi min...." juwairiya taji mgnr har cikin kokon zuciyarta wani dadi ne ya ziyarce ta.. Ta samu kanta da kallonsa cikin ido.. Sai dayaji gabansa ya fadi.. Can cikin kun'nansu suka jiyo jakadiya na sanar da shigowar kilishi sashen.. Ai Gaba dayansu sai da suka tsure. Juwairiya ta rasa ina zata saka kanta.. Jalal kansa sai da ya dan rikice.. Tsintsiyar dake kasa ya dauka ya mika mata da sauri.. Sannan ya koma ya kwanta kan gado shi kuma.. Kilishi ta shigo dakin cike da takama.. juwairiya tayi saurin zubewa ta gaisar da ita.. kallon kyama tabi ta dashi sannan tace.. Bamu waje... Da rawar jiki juwairiya tabar dakin.. "Kilishi ta kalli yarima.. Wane irin barci ne kayi yau jalal? Baki na can a fada ka shanya su.. Jalal cike da rashin fahimta yace baki kuma? Kilishi ta yatsine fuska.. Wai Galadima ne tare da mutanen sa suka zo wajen mahaifinku ajan mgnr auren hamza da diyarsa.. Jalal ya jinjina kai,ai ban san da zuwan su bane umma..ina jin magaji ya shafa'a ne bai fada min ba jiya... Kilishi ta tabe baki,ni wlh bama son wannan hadin nake ba.. Jalal yace sbd me umma? Kilishi tace,kai kana ganin dacewar jinin sarauta  kamar hamza ya hada zuri'a da wata diyar galadima can? ai yafi karfinta nesa ma ba kusa ba... Ta gyara zamanta,shiyasa nake masa sha'awar diyar sarkin kano amma kasan halin mahaifin naku.. Jalal dai da kallo kawai yake bin ummar tasa,tun ba yau ba yasan ta da shegen son mulki,kwata kwata bata kaunar wanda bashi da mulki ko abunda duniya..    Ya jinjina kai yace,umma ai hamza mijin mace hudu ne...ko ya aure ta ai zaki iya hadasa da yarinyar da kike so ko... Kilishi tayi murmushi hakane kam ka kawo shawara..yanzu dai tashi ka shiga wanka ka shirya.. Yarima ya gyada kai sannan cikin subutar baki yace , "gashi kuma har ta tafi bata hada min ruwan wankan ba"(in a disappointing tune)   Kilishi da mamaki tace.. Wacece? Jalal yadan daburce.. Ah eh ina nufin baiwar data fita yanzun.. Kilishi tadanyi jim,kafin ta mike tace,ni zan tafi amma kayi da jiki dan Allah kada mahaifinku yayi fushi dakai.. *************        "An saka bikin diyar galadima da hamza nan da wata biyu kacal,sannan tsohon sarki Abdul-Jabbar ya bawa jalal umarnin tafiya kasar zazzau a gobe kan maganar auren turaki da jikar sarkin..     "Su khadija manya kuwa ana can madafa an dukufa hadawa yarima delicacies kala'kala..   Har gidansu ta aika rabi dan ta tambayo mata recipes din mamanta,sbd ta san jalal najin dadin abincin innarta sosai.. "Bayan sun dauki lkc me tsayi suka kammala komai sannan ta shige sashenta ta sake kimtsawa taci gayu kamar a sace ta..sannan ta nufi sashen jalal.. ************ A gajiye sosai jalal ya dawo daga fa'da,dan haka jakadiya ta saka kuyangi suka hada masa ruwan wankan sa..   Sai daya yi wanka ya  dan wuta sannan jakadiya ta shigo ta sanar masa da zuwan khadija..   Jalal yadan ja tsaki.. Sannan ya mike yana tunanin ita kuma wane irin shirmen zata basa yau.. "Khadija na ganin ya fito ta mike da sauri ta taro sa.. Ya jalal sannu da fitowa.. Jalal ya amsa da yauwa ya zauna.. Khadija ta kalli rabi tace,zuba masa mana.. Rabi tace toh ranki ya dade.. Khadija sai sakin murmushi takeyi tasan dole ne abincin da tayi ya tafi da tunani yarima..    Jalal ya kalli plate din sannan ya kalleta..   Ina fatan kema baki zo da niyyar bata min lkc ba,dan na lura ba wani abun arziki kuka iya ba.. Khadija ta turo baki,nidai ba haka nake ba yaya,dan Allah kaci kaji...   Jalal ya tabe baki kafin ya fara cin abincin... 3 spoon kawai yayi amma ya kasa dai daurewa ya ajiye cukayin hannunsa.. Khadija ta shagwabe fuska, ya naga ka ajiye cukalin? Jalal ya girgiza kai dan bai taba cin abinci da bashi da dandano ba kamar wannan.. Khadija tayi fuskar tausayi.. Jalal ya dago ya kalle ta.. "Khadija bazan iya ci gaba da cin wannan abincin naki ba dan bashi da dandano ko kadan..   Gabanta ne ya fadi,tace ban fahimce ka ba ya jalal.. Jalal yaja tsaki ya dauki cup din ruwa yasha sannan ya mike ya koma dakinsa..     Khadija cikin sauri ta shiga dandana abincin, babu abunda ya rasa komai yaji zam zam,toh me yasa ya jalal zai ce mata abincin ta babu dandano? Kuka ta farayi sannan a fusace ta bar sashen cike da bakin ciki.. **************** Washe gari ..       "Jakadiya ta samu juwairiya a dakinsu da asubahi.. Tace,juwairiya inaso kije sashen mai martaba yanzu.. Juwairiya dake linke kayan shinfidar su tace.. Inna tun yanzun kuma? Jakadiya tace,kinsan fa yau ne tafiyarsa kasar zazzau dan haka ya bukaji dana tura ki dan shirya masa kayansa.. Juwairiya ta gyada kai sannan ta shiga shiryawa.. ********* "Koda ta shiga sasheen fadawa ne kawai a waje babu kowa a ciki..    "A hankali ta shiga dakin..   Ta hango sa yana ta sharar barcinsa.. Taja lumfashi sannan ta karasa wajen kayansa ta shiga hada mishi...   "Jalal ya bude ido ahankali jin motsi a cikin dakinsa..   Ware ido yayi ganin haske gari har ya waye..   Mikewa yayi zaune yana dafe kansa.. Sai hango ta yayi ta juya baya tana linke masa babbar rigar sa.. Kura wa bayanta ido... Juwairiya taji ajikinta kamar ana kallonta.. A hankali ta juyo suka hada ido dashi.. Tayi saurin dukawa kasa ta gaishe da shi.. Ya shafa fuskarsa yana amsa mata..kafin ya sauko daga kan gadon.... Muje zuwa 👇 TEAM RUMFAR BAYI [9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 28 Wattpad @afreey101 ******************** "Bayan wata daya... 'A cikin wannan watan daya gabata, ba karamin shakuwa ce ta shiga a tsakanin jalal da juwairiya ba.. Duk lkcn zata shigo kyara masa daki toh sai sun samu lkc sun sha yar firar su duk da dai ba wani mgnr kirki bace amma hakan yana saka zuciyoyin su cikin tsantsar farin ciki... "Kamar yau ma ta shigo sashen nasa danta gyara masa dakin ta tarar da baya ciki,tayi mamaki sosai da haka har ta kammala gyaran bata ganshi ba... Ta fito falo kenan taji kuyangi nata kananan maganganu kasa kasa..    Shiga tayi cikinsu dan taji me suke fada..jitai sunce.. "Gsky Allah yayi wa sarki jalal kyawu"kin ganshi kuwa?kamar wani balarabe.. A take duk Suka shiga leken kofar wajen shakatawar sa.. Juwairiya tabi su itama sai hango shi tayi kwance akan kujerar lilo barci ya dauke sa..fuskar sa kamar me murmushi ga cute lips dinsa da dogayen eye lashes dinsa..      Ta kura masa ido tanajin yarda bayi keta kyasa sa,a ranta kuwa cewa tayi,duk son da nake maka nasan bazan taba samun ka ba... Jakadiya ce tazo ta kore su daga wajen.. Sannan ta kalli juwairiya tace, kije waje magaji ya turo ayi masa kiran ki.. Mamaki ne ya kamata,me kuma zatayi wa magaji?      Fita tayi tabi bayan bawan da aka aiko kiran nata..   A gaban wata bishiyar mangoro taga bawan ya tsaya.... Sai hango magaji tayi a tsaye yana sakar mata murmushi ya jin gina jikinsa da bishiyar... Tayi saurin gaishe shi.. Ya amsa mata a sake yana fadin..     Kinyi mamakin kiran da nayi miki ko? juwairiya ta gyada kai.. Yace dama ina so ne na baki wata yar kyauta.. Juwairiya ta dago ta kallesa.. Ya nuna mata bishiyar yace na baki wannan bishiyar mangoron... Juwairiya ta kwashe da dariya. Magaji yabi ta da kallo yana jin sa a wani a irin nishadi... Kafin yace,ba wasa nakeyi ba fa? Kinga wannan bishiyar duk lkcn(season) din mangoro toh sai kin samu wanda yafi na ko ina zaki a jikinta..kuma a yarda na lura ke mayyar mangoro ce ko? Juwairiya tayi murmushi tace toh nagode ranka ya dade.. Magaji ya samu waje ya zauna.. Sannan ya nuna mata waje itama ta zauna a can nesa dashi.. Magaji yaja lumfashi kafin yace, na san rayuwar bauta acikin wannan masarautar ba karamin wahala ne da ita ba,amma zuciyata na son taji dan tarihin ki ko kadan ne.. Duk da nasan a tarihin bayin dake cikin masarautar nan kece kadai aka taba haifa a cikin RUMFAR BAYI...   Juwairiya taja lumfashi, hakane ranka shi dade, amma ni rayuwata babu wani labarin da zan iya bada shi.. wanda baka sani ba.. Tun ina shekara goma na fara bauta..    Magaji yaji tausayinta har cikin zuciyarsa.. Ya jinjina kai...(yana tunani a zuciyarsa,kodai ya fada mata sirrin dake zuciyarsa ne?sai kuma wata zuciyar ta hane sa) Ya kalle ta yace.. zaki iya tafiya nagode da lkcn da kika banu.. juwairiya ta mike kawai tayi masa godiya kafin ta fice.. ******************* "Washe gari.. "Umayma ce ta kalli surayya,Allah ya kara miki yawan rai.. ina tunanin kawai yakumbo ta bamu damar zuwa wajen bokan ta, tunda dai har wata daya ya shude babu wani alamun ciki a tattare dake.. kuma kar na fara jin kusun kusun daga bayin dake sashen gimbiya kilishi,wai ta fara mgn a rashin haihuwar ku har wannan lkcn.. Surayya cike da takaici tace,nima ina wannan tunanin umayma..kema kin sani bazan taba bari wata ta haifawa jalal yaron da zaya gaje shi ba sai ni!ta nuna kanta!ni surayya! Shiyasa har gobe bazan bar ciyar da khadija wannan maganin ba har sai na samu MAGAJIN'SARKI.. Taja lumfashi tace ya mgnr wannan yarinyar? Ina fata kin dasa mana wacce zata saka musu ido dan ni wlh zuciyata bata kwanta da aikin da takeyi a sashen sarkina ba.. Umayma tace kada ki damu...koma miye sirrin da take boyewa muna daf da sanin sa.. Surayya zatayi mgn kenan sai ji sukayi ana sanar da shigowar khadija.. Umayma tace, ko wane gulmar ta kawo ta kuma? "Cikin takon girma khadija ta shigo cikin falo tare da rabi a bayanta.. Surayya tayi murmushin yake,ah ah amarya da kanta da sassafe haka.?   Khadija tayi murmushi,gani nayi kamar zumuncin dake tsakanin mu ya fara rauni.. Surayya ta tabe baki,zumunci?ta maimaita.. Khadija tace,daga sashen umma nake yanzu,tace nazo wajenki dan mu tautauna akan shirye shiryen auren su ya hamza da ya turaki.. Surayya ta gyara zaman ta,na dauka ai su umman ne zasuyi komai.. Khadija ta girgiza kai,mu a nan masarautar matan sarkine ke gudunar da duk shirye shiryen daya danganci gidan sarauta.. Surayya ta jinjina kai.. *************** "Ina jinki.... ina kika je jiya da safe? juwairiya ta kalli jalal daya tsare ta da tambayoyi akan jiya daya tashi bai ganta ba..   Ta dan sauke kai kasa tace... Magaji ne yayi kirana.. Jalal ya daure fuska sannan bai ce mata komai ba kawai ya gama shirinsa yayi gaba.. Juwairiya ta saki murmushi,lallai yarima akwai shegen miskilanci.. Har ta mike dan ci gaba da gyaranta taga ya sake dawowa ya dauki hular sa ya sake ficewa.. ***************** "Biki ya matso ana ta faman shirye shirye masarautar ta cika tam da mutane sosaidaga kowane yanki na arewa.. "A yau ranar juma'a ne kuma Aka daura auren HAMZA DA NAFISA sai kuma TURAKI DA SAMIRA..   "Yarima gaba daya ranar bai samu zauna ba ko kadan ba,dan Fada ma ba karamin cika tayi tba ab..bashi da ikon fita ko nan da  can,sai magaji dake ta kokarin ganin ya taimakawa amininsa nasa.. "A can cikin gida kuwa,matan sarki ne ke ta hidima da jama'a sai ka rantse da Allah kansu a hade yake,amma kowacce tana yi ne kawai dan burge sarki jalal da kuma gimbiya kilishi mahaifiyar sa.. "Amaryar hamza aka fara kawowa nafisa direct sashen gimbiya kilishi akayi da ita.. SAMIRA kuwa matar turaki sai yamma likis suka iso kasancewar daga kasar zazzau suka taho.. Ita kam a sasheen fulani diyya aka ajiye ta... "Da daddare mai martaba sarki jalal ya shirya musu liyafa ta gani ta fada.. Gimbiya kilishi ta bukaci surayya da khadija dasu zaunaa wajen shirya nafisa..      Surayya ta kalli kayan dake hannun khadija tana yatsine fuska,kina nufin wannan kayan zata saka? Khadija tace eh mana.. Surayya taja tsaki sannan ta fito da wasu kayan tace,wannan na tanadar mata dan haka su zata saka bana son wani feleke.. Nan fada ya kaure a tsakanin su.. Nafisa kuwa sai kallon su takeyi cike da mamakin kishi irin nasu.. *************** "Jalal daga fa'da sashen baki suka nufa shi dasu magaji.. A nan ya tarar da yan uwan SAMIRA samari da manyansu daga kasar zazzau.. Khaleed ne kawai ya sani a cikin su.. Dan haka dashi ya fara gaisawa..haka nan kuma ya samu kansa da tambayar khaleed din ko ina AMMI? Khaleed yayi dan murmushi,ai ka san yan mata kusan biyar aka daurawa aure a yau din,toh AMMI na can kasar bauchi sunje kai diyar wajen ya ladan.. Jalal ya gyada kai sannan ya karasa ciki ya shiga gaisawa da sauran.... """A gajiye sosai ya shiga sashensa dan shiryawa kafin lkcn liyafar yayi.. Dakinsa ya shige Yayi wanka ya shirya cikin kayan sa da sukaji ado sosai,ga rawani na alfarma yasha.. Har sun fito tare da angona ya kalle su yace ina zuwa... Komawa yayi cikin sashen nasa ya dauko wata sarka ta zinari irin chain dinnan,ya zura a cikin aljihunsa sannan ya fice.. "Zainaba ce ta saka ayi mata kiran juwairiya dan su shirya samira.. Juwairiya cike da murna ta shiga dakin na fulani.. Samira na zaune a gefen gado ta lullube kanta da babban mayafi.. Zainaba na ganin juwairiya tace,wai ina kika shige ne juwairiya ? kinsan kuma dolene na bukace ki a kusa dani yau.. Juwairiya tayi murmushi tace.. kiyi hkr ranki ya dade ina can RUMFAR BAYI ne muna taimakawa a cikin madafa.. Zainaba ta jinjina kai,sanann ta kalli samira..tace.. Amaryar yaya bude fuskar taki mana mu gani? Ko mu kike jiwa kunyar? Samira a kunyace ta yaye mayafin.. Sai cin karo tayi da fuskar juwairiya.. Ware ido tayi tana kallonta kafin tace ,tana kama da AMMI wlh,ta fada tana nuna juwairiya, kallon rashin fahimta sukayi mata.. Samira ta shiga kallon tufafin dake jikin juwairiya, a take ta fahimci baiwa ce.. Mamaki ne ya kamata dan haka ta ja bakin ta tayi shiru... "Cikin dan kankanin lkc zainaba, juwairiya da kuma laure suka shirya samira cikin kayan alfarma tayi kyau mutuka.. "Zainaba komawa tayi sashen ta ta shirya sannan ta bawa juwairiya kaya itama tace taje ta canza hakama zabba'u..         Juwairiya komawa tayi rumfar bayi dan shiryowa..   Lkcn da zata fito sai ta tarar kamar anyi shara a masarautar babu kowa duk an hallara acan wajen liyafar..       Cikin sauri itama ta karasa wajen.. Angwaye da matansu ba karamin kyau suka kayi ba..   Idanuwanta ne suka shiga neman inda zaga yarima.. Can ta hango sa tare da magaji suna mgn ta kura masa ido.. Kamar ance ya juyo sai hada ido sukayi da ita.. Murmushi ya sakar mata a fakaice..sanan da idanuwansa yayi mata signal akan ta bi bayanshi..kafin ya fara tafiya cikin takon kasaitarsa.. juwairiya ta kalli su umayma da rabi dake gefen ta tace dasu ina zuwa kafin tayi gaba... Khaleed dake gaisawa dasu khadija ya hango ta kamar daga sama.. Kallo ya bita dashi,gefen fuskar ta kawai ya iya hangowa amma yaga dan kaminta da Ammi,da saurinsa ya sake binta da kallon tana kokarin wuce su sai hango dayan gefen fuskarta ta yayi a kone,nazari ya shiga yi,wacece ita???????? **** Juwairiya na tafiya... Umayma ta bi bayanta da kallon zargi wata zuciyar tace mata ta bi ta kawai,ai da saurinta ta shiga bin bayan juwairiya.. Can nesa da inda ake liyafar jalal yaja ya tsaya yana juyowa dan ganin ko ta taho.... Juwairiya ta karaso wajensa da sauri tana mamakin irin kyaun da yayi yau se kace shine angon..   Jalal yace wannan kallonfa? Ko nayi miki kyau ne? Juwairiya tayi saurin dukar da kai.. Jalal ya mika mata sarkar daya fito da ita daga cikin aljihunsa.. Amsa.. Ta bi sarkar da kallo sannan ta kalleshi..tace.. Ranka shi dade me yasa zaka bawa baiwa kamar ni irin wannan kyautar.. Ai bayi basu da ikon saka duk abunda ya danganci kwalliya... Jalal yaji wani iri har cikin zuciyarsa. ..... Yana son ya sanar da ita sirrin dake cikin zuciyarsa amma yana ganin kamar lkc bayyi ba.... Sai ya tuna lkcn da ya fahimci cewa SONTA YAKEYI.... "_Suna zaune ne tare da magaji a cikin lambu da wani yammaci.._   _Ya kalli magaji yana fadin.. Abokina dan Allah na tambaye ka mana?_ _Magaji ya ajiye tufar(apple)da yake ci ya maida hankalinsa wajensa..yace Ina jinka AMALE fadi naji.._ _Jalal yaja lumfashi kafin yace.. Idan kamar haka mutum ya damu da wata sosai kuma a kullum zuciyarsa na muradin yaganta yana begen ta a kowane lkc...yana jin dadin mgn da ita,yana kaunar kasancewa da ita,yana tunaninta,amma ya kasa gane matsayin da zaya ajiyeta a ciki zu..... Magaji ne ya kwashe da dariya sosai.. Jalal ya kallo shi yace meye haka? Magaji yace,meyasa kawai ba zai gene cewa SON TA yake ba?.._ _Ko wanene shi dai bako ne a cikin soyayya nake gani, dan duk abubuwan da ka fada yanzu soyayya kawai ce ke kawo su..ya dai sake tunani,..._ _Dan ba karamin SON TA yakeyi ba,kuma ya kamata yayi gaggawar sanar da itama.._ _Jalal yabi shi da kallo kafin yace, idan kuma yafi karfin ta fa?ina nufin(level)dinsu ba daya bane.._   _Magaji ya gyara zamansa,ni a ganina indai yana sonta har haka duk wani matsayi ba wani abun damuwa bane ,idan ya aureta ai duk sun zama daya ko? Jalal ya jinjina kai yana nazarin kalaman magaji..."_ TEAM RUMFAR BAYI [9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima:             *RUMFAR BAYI*          (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 26 Wattpad @afreey101 ******************      "Juwairiya na kallonshi har ya karaso zuwa gabanta ya tsaya.. "Kin hada min kayan? Juwairiya tace, yanzu na gama ranka shi dade.. Ya lumshe ido, toh shiga ki hada min ruwa nayi wanka.. Juwairiya tace toh sannan tayi hanyar toilet da saurinta..     "Ta fito ta sanar masa ta gama,bai ce mata komai ba ya shige toilet din.. Yana shigane ta samu damar gyara masa dakin tsab..    Ta kalli kofar toilet din,ta kammala komai na aikinta amma sai ta samu kanta da rashin fita son daga cikin dakin..yau zayyi tafiya ko ba komai tana so suyi sallama.. Matse baki tayi sannan ta fita ta dawo falon ta zauna akasa dan jiransa.. Jalal na fitowa ya tarar babu ita a dakin,bai ji dadi ba kodan dan yaso ace yayi sallama da ita... Sai daya dauki awa daya yana shiri kafin ya fito cikin shiga ta alfarma..    Caraf ya ganta a zaune ta rakube a waje daya.. Murmushi ya saki ya karasa wajen yana fadin.. "Ya baki tafi ba? Juwairiya tayi saurin mikewa.. Uhm dama dama uhm yauwa jakadiya ce tace na jira ta a nan.. Ya jinjina kai dan zuciyarsa ta gama basa shi take jira...   Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya nufi wajen shakatawar sa da ita.. Ya sake hannun nata sannan ya rufo kofar wajen. Juwairiya gabanta ne ya shiga faduwa.. Jalal yace.. Yau zanyi tafiya...ya karashe mgnr cike da wani irin yanayi.. juwairiya ita kanta se dataji wani iri.. da murya me cike da sanyi ta samu kanta da fadin.. 'Yaushe zaka dawo? Ya kurawa kwayar idonta kallo.. Kwana biyune.. Juwairiya tayi murmushin yake tace.. Allah ya dawo dakai lfy ranka shi dade.. Jalal ya gyada kai.. Nagode.. Hayaniyar su shamaki ya jiyo daga waje.. Yaja lumfashi ni zan tafi.. Ta jinjina kai ta kasa furta komai.. Ya juya har ya kai bakin kofa ya sake juyowa..   Bai bata wani lkc ba ya janyo ta jikinsa..dan gaba daya kasa controlling zuciyarsa yayi..   Juwairiya taji gaba daya duniyar ta tsaya mata tsak... Sai da suka shafe seconds talatin kafin yayi karfin halin sakinta ya juya da sauri ya fice........ ************* "Yana fitowa waje ya tarar da fadawa sun cika wajen gasu magaji da turaki suna ta jiransa suma.. Ya karasa wajen su cikin takon girma kafin suka nufi sashen gimbiya kilishi ga baki dayansu..   A nan suka tarar dasu surayya da khadija kowacce najin da kanta..   Sallama sukayi musu...sannan suka sake zuwa sashen mahaifinsu anan suka iske fulani sukayi musu sallamar suma kafin suka dau hanya.. "Sun isa kasar zazzau da yamma sosai.. Sarki ya saka aka kaisu masaukin su.. Abinci kala kala aka kawo musu suka ci sosai kafin duk suka bi lafiyar gado sbd sauke gajiya.. ***************   Yau kwanan jalal daya da tafiya amma juwairiya duk ta rasa me ke mata dadi, har fada take wa zuciyarta,ke wacece a wajensa da zaki damu dashi haka uhm? Ta girgiza kai,yarima ka barni na huta! Ta kalli zobensa data amso dazun wajen me siyar da kifi..ya zanyi da kai yarima? Zabba'u ce ta shigo dakin ta sanar mata da sakon zainaba na son ganinta a sashen ta..    Tana fitowa daga rumfar bayi suka hade da umayma.. Umayma tace,sai ina haka juwairiya, ko saurayin naki zakije gani ne? Gaban juwairiya ya fadi,ta ware ido tana dafe kirjinta.. Saurayi kuma?ta fada cike da faduwar gaba.. Umayma tayi dariya ke wasa fa nakeyi miki.. Juwairiya ta sauke ajiyar zuciya,kee kuwa kin cika uwar zolaya.. Umayma ta jinjina kai sukayi sallama kowaccen su ta kama gabanta.. "A can kasar zazzau kuwa,sarki da kansa ne ya bukaci ganinsu da safe,suka shirya suka same sa a palace dinsa..      Sun fara mgnr yarda auren zai kasance sarki ya saka a kirawo masa dansa na fari wato mahaifin yarinyar da ake son hadawa da turaki..     yana shigowa fa'da ya kwashi gaisuwa wajen mahaifinsa sannan aka saka ranar biki.. Turaki dai kallonsu kawai yakeyi dan shikam dan dole ne zai yi wannan auren. jalal ne ya sanar dashi sakon mai martaba  dayaje yaga yarinyar can a gidansu aka hada shi da wani bawa..ba da son ranshi ba ya tafi.. "Jalal tare da magaji kuwa autan sarki khaleed ne ya shiga yawo dasu a cikin masarautar..    Sun kawo sashen amaryar sarki khaleed ya hango ta tana kokarin fita da bayinta a zagaye da ita..    AMMI...! Ya kira sunanta yana karasawa wajenta.. Jalal da mgaji ma suka bi bayansa..    Ammi ga surukan SAMIRA sunzo harda ma yayan mijin nata sarki JALALLUDEEN.. Wacce aka kira da Ammi jalal ya kura wa ido.. A ina yasan irin wannan fuskar? Noo haba inaa...juwairiya?zuciyarsa ta raya masa..tabbas akwai kamanni a fuskokinsu.. Ya girgiza kai,amma basu da wani alaka da juna ai,mayb kawai kama ce daga Allah.. AMMI ta kallesu da kulawa suka gaisa,jalal kuwa ya kasa dauke idonsa daga kallonta yana mamakin yarda akayi matar take kama da juwairiya baiwar Rumfar bayi.. ************* "Badai kina nufin akwai wani da wannan me konannar fuskar take gani ba cikin masarautar nan? Umayma ta gyada kai,na tabbata akwai ranki shi dade, dan danayi mata tambayar dazu wlh idanuwanta sun nuna tsoro tda fargaba.. Surayya ta jinjina kai,toh amma wane irin dolo ne banza da zai so wannan abun?fuska duk a kone.. Kuma tasan da cewa baiwa ce ita bazata taba iya aure ba,ba tare da an yanta ta ba. Umayma ta gyada kai dole ne kuwa mu gano wanene take gani. Surayya tace,ki saka mata ido dan akwai zargin da nakeyi... *************    "Yau kwana biyu da tafiyar su yarima kuma a yau ne ake saka ran dawowar su..   Gimbiya kilishi da kanta ta saka ayi mata kiran du'bu dan ta sanar da ita duk shirye shiryen da za'ayi musu.     "A wajen juwairiya kuwa haka nan ta tsinci zuciyarta a cikin farin ciki sosai tun da ta lbrn.. Sai dai duk farin cikin ta bata kai ga na matan sarki ba.. Dan ba karamin shiri sukeyiwa dawowar mijin nasu ba.. Kowacce da irin kissar da take kullawa... ************** Sai da yamma kilis su jalal suka shigo cikin masarautar, sai da suka fara zuwa wajen sarki Abdul-Jabbar sukayi masa bayani akan amincewar sarkin zazzau acikin alliance din hada auren,kuma a take aka saka ranar biki rana daya dana hamza kamar yarda suka bukata.. Murna sosai fulani da mai martaba sukayi,sai dai shi gogan wato turaki,ko digon son yarinyar babu a cikin zuciyarsa... "A gajiye jalal ya shigo sashen nasa,yana shiga dakinsa ya sauke ajiyar zuciya yana sakin murmushi kafin nan ya furta.. "Yau zan ganta...ya lumshe idonsa.. Kayan jikinsa ya cire sannan ya shige cikin toilet dan watsa ruwa.. "Yana fitowa ne kawai ya tarar da surayya a zaune tana jiransa..    Mikewa tayi da saurinta tazo gabansa tana amsar dan karamin towel din dake hannunsa..   Shidai da kallo kawai yake binta.. Surayya ta shiga goge masa ruwan dake jikinsa tana masa wani irin salo... "Kirjinsa take goge masa tana yawo da hannunta a kai cikin kissa.. Yarima yayi saurin rike hannunta zayyi magana kenan kawai yaji ta fara kai masa sumbata a gaba daya jikinsa.. "Jikinsa ne yayi lakwas, surayya na ganin haka tayi murmushin samun nasara.... Dan dama tasha alwashin a yau sai yarima ya kwana da ita tun kafin khadija tama saka shi a ido.. Gashi kuma tasha maganin da yakumbo ta aiko mata  dashi na daukar ciki da wuri...addu'ar kawai Allah yasa ciki ya shiga... *************** "Juwairiya ce zaune a cikin RUMFAR BAYI tana jin haushin hanata zuwa sashen jalal da jakadiya tayi.. Gashi kuma Zuciyarta na mutukar son ganin fuskarsa..    "Rabi ce ta zauna a gefenta tana dafa kafadarta..tace.. Wai ni lafiyarki kuwa juwairiya? Kwana biyun nan kin cika  zama ke kadai wlh.. Juwairiya zatayi mgn sai ga umayma ta karaso wajensu tana washe baki kamar gonar auduga.. Rabi taja tsaki..ke kuma fa? Umayma ta dalla mata harara..da akayi me? Rabi tace,naga se wani washe baki kikeyi sai kace baiwar da aka yan'ta ta..   Umayma ta rangwadar da kai.. Ba dole nayi murna ba tunda dai a wannan lkcn ina kyautata tsanmanin uwar dakina na can akan shinfidar sarki JALALLUDEEN.... "Ba rabi ba har juwairiya dake sauraren su sai da zuciyarta ta buga.. Tayi saurim dafe kirjinta.. Me ke shirin faruwa da ita..."kishi" Ah ah me yasa zatayi kishin sarki da matarsa... Ta dafe kirjinta.. Rabi taja dogon tsaki sannan ta mike da gudu tabar wajen dan zuwa sanarwa khadija.. Umayma tahau gu'da...sai can ta hango yarda juwairiya dafe  kirji.. Yanayinta ta karanta kawai kafin tace.. Yadai juwairiya lafiya? Juwairiya ta kakaro murmushi sannan ta mike da sauri ta shige dakinsu...   Kwanciya tayi tana sauke lumfashi me dumi..    Ya kamata kisan abunda ya dace dake juwairiya ta fadawa kanta..       "Take taji jikinta ya dau rawa dan dama tana jin signs din zazzabi ajikinta tun satin daya wuce.. "Hansai ce ta shigo da fitilar kwai a hannunta cikin dakin.. Har ta fara mitar kwanciyar wuri da juwairiya ta tsira.. Sai hango ta tayi tana rawar sanyi.. Ai da sauri tayi kanta.. Juwairiya ke miye ke damunki haka? juwairiya ta kasa mgn dan harcenta yayi mata nauyi.. Hansai ta fita da gudu tayi kiran du'bu da laure.. Laure na taba jikin juwairiya tace,zazzabi ne mai zafi ya rufe ta.. Du'bu tace subhanallahi.. Hansai ta girgiza kai,ai dama dole ne zazzabi ya kama juwairiya tunda ta maida gaban kogi wajen zamanta duk iskar duniya ya kare akanta.. Du'bu tace bari naje na hado mata magani.... ****************** "Da safe jakadiya ta shiga dakinsu juwairiya, ta ganta a kwance jiki kam sai a hankali.. Hansai ta kalla tace,Allah ya bata lfy ni bari na karasa wajen aikina,zan saka wasu bayin suyi mata (covering)aikinta.. Hansai ta jinjina kai dan itama in ba dan dole ba bazata iya fita tabar diyar ta acikin wannan halin ba.. *************** Tunda sassafe jalal ya farka yayi wa surayya kora da hali.. Ya zauna yana ta jiran shigowar juwairiya.. Amma shiru shiru har ya gaji da jiran ta bata shigo ba.. Jakadiya ce ta rangwada sallama ta shigo dakin.. Jalal dake zaune ya amsa ta ciki ciki..   Allah ya kara maka yawan rai ayi min afuwa na shigo ne dan nunawa wannan baiwar aikinta.. Sai lkcn jalal ya hango baiwar dake bayan jakadiya.. Jiyai tace,ki shiga ki hada masa ruwan wankan sa sannan ki dawo dakin ki gyara shi..   Jalal gaba daya wutarsa ta dauke,me yasa jakadiya zata kawo masa wata baiwar ba juwairiya ba ta gyara masa daki?ina ita juwairiyar take?me yasa aka canza masa ita?     "Wasa wasa dai har ranar ta ka're jalal bai sa juwairiya a ido ba.. Koda ya shiga fa'da ma ba wani abun kirki yayi ba magaji ne ya taimaka masa yayi masa rabin aikinsa..    "a Kwana na biyu yarima ya rasa mafita,kullum a falonsa yake wuni dan ganin ko zai hadu da ita amma shiru. gashi baya son ya tambayi jakadiya dan bai san wane irin kallo zatayi masa ba..    "Dan haka ne ya shirya dan zuwa sashen kanwarsa zainaba yasan koma miyene zata sani tunda tana kaunar juwairiya sosai.. "Koda zainaba taji sallama na sanar da isowar jalal sashen ta ba karamin mamaki tayi ba.. Ta mike tsaye har ya shigo ya zauna kafin itama ta samu wuri ta zauna fuskarta dauke ta da tsantsar mamakin ganinsa..   "Jalal ya sakar mata murmushi.. Yadai?wannan kallon fa? Zainaba tace,wlh mamaki nakeyi wai ya jalal da kansa ne a sashena.. Jalal ya murmusa,nazo bada hkr ne nasan kanwata tayi fushi da yayanta ko? Zainaba ta shagwabe fuska, ni na isa nayi fushi da Sarki? Jalal ya shafa sa'jen sa,gashi har umma ma fushin da ake dani ya shafe ta,tunda ta fada min kin daina zuwa gaishe ta ko? Zainaba ta turo baki.. Jalal yayi dariya..toh ya ake ciki ne menene lbr..? Zainaba a take yanayin ta ya canza,damuwar dake ta cinta a rai ta rasa kuma dawa zatayi sharing yasa kwalla sulalowa akan kumatun ta..    Jalal yaji hankalinsa yadan tashi,kodai wani abu ne ya samu juwairiya?dan a ganinsa zainaba bata tare da wani damuwa..    Cikin kulawa yace,haba zainaba menene kuma na zubar da kwalla.. Zainaba ta kallesa tana nazari,maybe Allah ya turo mata ya jalal ne dan ya taimake ta..   Gyara zama tayi sannan ta fada masa komai a tsakanin ta da Mustapha.. Jalal ya kura mata ido kawai yana fadi a zuciyarsa TIRKASHI..   Zainaba ta katse shi da cewa,wlh yaya bana son ayimin wani auren hadi kamar yarda akeyi muku,ni Mustapha nake so kuma shi nake son na aura..    Jalal a take zufa ta shiga ke'to masa.. Lallai akwai chakwakiya nan gaba... Dan kuwa ya samu lbr a wajen gimbiya kilishi.... Tun ZAINABA  na yar jaririyar ta mai martaba ya bawa MAGAJI  ita,duk da shima magajin bashi da wani masaniya akan hakan................... Toh fa........ Muje zuwa 👇 TEAM RUMFAR BAYI [9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima:             *RUMFAR BAYI*          ( A historical fiction) Na Afrah bhai Page 27 Wattpad @afreey101 **********************         "Jalal ya gyara zamansa yana kallon zainaba cike da tausayin irin tata kaddarar .. "Ki kwantar da hankalinki kanwata kawai kici gaba da addu'a Allah ya zaba miki abunda yafi alheri kinji,ke da ma ko fara mgnr auren ki abba bayyi ba.. Zainaba tace,ah ah yaya dan Allah nidai ka taimake ni,nasan idan kayi wa abba bayani bazai ki amincewa ba.. Jalal ya rasa me zai ce mata,sbd dai magajin nan amininsa ne kuma yasan waziri ma bazai taba aminta ba ace an bawa dansa zainaba kuma taje ta auri wani can daban..       "Zabba'u  ce ta shigo falon da sallama.. Zainaba tace,yadai zabba'u ya na ganki ke kadai?ina juwairiyar? Zabba'u tayi fuskar tausayi.. Ranki ya dade juwairiya fa bata jin dadi tun kwana biyu da suka wuce.. Hankalin zainaba e ya tashi mutuka,a take ta mike tsaye tana fadin,shine baki sanar min ba? Zabba'u tace,kiyi hakuri ranki ya dade amma itace tace min kada na fada miki dan tasan hankalinki ne zai tashi.. Zainaba jiki na rawa tace,muje na ganta.. Da sauri zabba'u ta shiga gabanta, ranki shi dade kin manta bazaki iya shiga rumfar bayi ba..   Zainaba taja tsaki ta koma ta zauna cikin takaici..   Jalal kuwa duk yana saurarensu,hankalinsa ba karamin tashi yayi ba shima.. Dama bata da lafiya ne? Toh Meya same ta? A wane hali take ciki yanzu?     Mikewa yayi kawai ba shiri yayi sallama da zainaba sama sama ya fice.. "Gaba daya a ranar jalal tunanin yarda zai saka juwairiya a idonsa yakeyi..yana son yaji ko ya jikinta da sauki ko yayi tsanani?amma bashi da me bashi wannan amsar.. Da yamma magaji ne yazo yaja shi da kyal suka je yin wasan doki..(Polo ) Lkcn daya dawo sashen sa sai ya tarar da khadija a dakinsa tana zaman jiransa...    Tsaki yadan ja yana mamakin nacin wadan nan matan nasa..kullum sai sun kawo kansu wajen miji..mtsw.. "Khadija kuwa tana ganinsa ta saki murmushi, ya jalal sannu da shigowa.. Jalal yace,yauwa a takaice.. Khadija taje ta kamo hannunsa  ya jalal wai nayi maka laifi ne? Jalal ya kalleta,laifin me zakiyi min khadija..? Ta shagwabe fuskarta.. toh ba naga ne daga ganina da kayi ba sai ka wani daure fusaka,kamar bakayi wani farin cikin ganina ba.. Jalal yayi murmushi ya shafa gefen fuskarta yace.. ba haka bane..kawai dai abubuwa ne sukayi min yawa.. Khadija ta rungume sa,kada ka damu komai zaizo maka da sauki idan akayi sabon na'din (palace counsel)... ********* "Wasa wasa juwairiya jiki sai daya kai ta har kusan kwanaki biyar bata fita daga cikin rumfar bayi ba tana ta jinya... Sai dai tana samun sako daga wajen zainaba dan har fulani kanta ta saka aka kawo me magani ta shiga har cikin rumfar bayi ta duba ta.. "Yau kam ta tashi jikinta da sauki sosai tana zaune ne kwanon abinci a gabanta tana ta faman tsakurar sa kamar bataso.. Tunani kawai takeyi yarda take jin zuciyarta kamar tayi tsuntsuwa ne taje sashen yarima ta dan gan sa.. hansai ce ta kalleta duk ta rame tace,juwairiya kodai sai na nemo miki maganin cin abincin ne? Juwairiya tayi murmushi kada ki damu umma,kawai bakina din ne babu wani dadi shiyasa..hansai ta jinjina kai kawai.. "Mai martaba ina tunanin kawai a kai mutanen nan gidan yari.. "Magaji dake zaune gefen jalal suna cikin fada ya fada..   Ji yayi jalal bai ce masa komai ba,dan haka ya dago yana kallonsa.. Ya rasa meke damun abokin na sa kwana biyu haka bashi da wani nutsuwar kirki kullum se dai ya zauna shiru..     A hankali ya karasa gaban throne din jalal ya dafa shi.. Jalal ya kalleshi da sauri lafiya? Magaji yace,dan Allah ka fada min abunda yake damun ka.. Jalal yasa hannunsa ya janye hannun magaji daga kafadar shi..yace Na sha fada maka babu komai dake damuna wai meyasa ka cika naci ne?..   Magaji ya jinjina kai yana bin shi da kallo.. ko yaushe jalal ya daina fada masa sirrin sa?oho... Kodai ya daina daukarsa amininsa ne? ********************* "Da yamma juwairiya ta fito can bayan rumfar bayi gaban kogi inda suke wankin kayansu ta tsaya..    Iskan dake kadawa ta shaka... Murmushi ta saki tana murnar samun lafiyarta,gobe dai inshaAllah zata saka jalal a idonta.. ********************* "Washe gari tun da asuba take ta shirinta.. Jakadiya na lekowa tayi saurin mikewa tace,inna muje na shirya.. Jakadiya tabi ta da kallo kin tabbata jikin naki ya warware? Juwairiya tace kwarai kuwa inna.. Jakadiya tace toh muje dama nayi kewar ki... "Suna shiga sashen juwairiya taji zuciyarta tayi wasai..    Da saurinta ta fada cikin dakin..dan jakadiya ta sanar mata ta shiga kawai matan sarki basa ciki.. "Can kan gado ta hangosa a kwance..   Tayi saurin karasawa tana kurawa fuskarsa ido...kamar yadan rame shima.. Gani tayi yana motsa bakinsa.. Bata ankara ba kawai taji yana kokarin furta sunanta.. Juwai.... Tayi saurin kai kunnenta kusa dashi dan ta tabbatar ko sunan ta din yake son furtawa.. Aikuwa dai juwairiya yake ta furtawa.. Washe baki tayi kafin tace a hankali.. Na'am ranka shi dade... Ga babban mamkinta sai ta ga ya bude idanunsa tangaren ya sauke su akanta.. Ai a tsorace taja baya tana jin kirjinta na bugawa.. Shi kuwa jalal da sauri ya mike ya sauko daga kan gadon ya tsaya a gabanta..yana mamakin ganinta.. Murna sosai ya ziyarci zuciyarsa har baisan sanda yasa hannu ya fisgo ta zuwa jikinsa ba..   A tare duk suka sauke ajiyar zuciya mai nauyi...    Acikin kunnenta taji yace.. Ina kika shige uhm? Juwairiya tayi murmushi tana shakar kamshin sa.. Bani da lfy ne.. Jalal ya dago ta daga jikinsa yana kare mata kallo duk ta rame tayi wani irin haske.. _"A Take ya tuna da amaryar sarkin zazzau AMMI,tabbas suna mutukar kama da juwairiya, amma taya hakan ya faru?wata zuciyar tace masa kana mamakin da ikon Allah ne?jalal ya girgiza kai da sauri,tabbas kamanni ne kawai daga da Allah..tunda dai bai ga wata alakar da zata hada matar sarki da kuma baiwar Rumfar bayi ba"_ Lumfashi yaja kamin yace.. Ya jikin naki yanzu? Zatayi mgn ya sake cewa, ah ah ina zuwa ma dai... Fita yayi bai dade ba sai gashi ya sake dawowa..    Juwairiya zatayi mgn sai ji tayi jakadiya na sanar da shigowar me magani.. Da sauri ta kalle shi.. Kafin tace.. Mai martaba naji sauki fa.. Jalal ya zauna a gefen gado yana fadin.. Ina so ne kawai na tabbatar....   Me magani ya shigo jalal ya nuna masa juwairiya yace.. ka duba min ita.   Me magani yace.. Na duba ta?ya nuna juwairiya cikin mamakinsa.. Jalal bai tanka masa ba.. Me maganin ya bukaci data zo ta zauna.. A sanyaye taje ta zauna ya duba tan.. Sannan ya tabbatar wa jalal ta samu lafiya...ya amshi kudinsa ya fice.. Jalal ya dawo kusa da ita yace.. Kinga Yanzu na yarda.. Juwairiya ta gyada masa kai sannan ta nufi hanyar toilet.. "Jalal na tsaye yana sakin murmushi sai ji yayi ana sanarwa surayya zata shigo ciki.. Daure fuska yayi a take.. Surayya kuwa na shigowa ta rungume sa cike da murnar ta..tana fadin.. Sarkina kasan kasan yanzun nan na samu wasika daga masarautar mu matar yayana ZAID ta haihu..    Jalal ya tabe baki yace,toh shine zaki fado min daki da sassafe haka? Surayya ta sake matse shi ajikinta.. Wa nake dashi a duk fadin masarautar nan da zan(sharing)farin cikina dashi idan ba kai ba..     Jalal na shirin mgn sai ga juwairiya ta fito daga cikin toilet idanuwanta a kansu..    Ji tayi gabanta ya fadi.. Jalal da saitin kansa ke fuskantar hanyar toilet din ya hango ta a tsaye amma ga mamakinsa.. "Kishin sa sosai ya hango a cikin idanuwanta... murmushi yayi a zuciyarsa dan kuwa yasan ta fara son sa ne.. shi kuma haka nan yaji zuciyarsa taji dadin hakan sosai...      Surayya ce tadan sake shi jin yayi mata shiru sai kallon juwairiya yakeyi data dauke kai gefe..    Surayya tadan kalli inda yake ta faman kallon har bai lura ta sake shi ba.. Ganin juwairiya ce wajen sai wani abu ya tsaya mata a wuya.. Ta daka mata tsawa.. "Ke! Juwairiya tayi saurin karasawa wajenta.. Fita! Ko baki san abunda ya dace bane?kika zo kika wani yiwa mata da miji tsaye a kai..kidahuma kawai mtsww... juwairiya ta juya da sauri tabar dakin.. Jalal ya kalli surayya cike da takaici.. Surayya na kokarin kamo hannunsa tace,wlh na tsani wancan yarinyar sarkina.. gara ma dai da Allah yasa ta kone wannan fuskar mtsw.. Jalal ya kwace hannunsa bai ce mata komai ba ya shige toilet abunsa..    Surayya ta bi shi da kallo tana wani tunani kafin ta juya ta fice itama... **************** "Turaki ni fa ban fahimci abunda kake nufi ba... (fulani ta fada tana kallon turaki dake zaune a gabanta ya dukar dakai kasa)   Fulani ta sausauta murya,Turaki inaso ka fahimci haka kaddarar GIDAN SARAUTA ta ga'da',kuma na tabbata mahaifinku bazai zaba maka abunda zai cutar dakai ba.. kayi hakuri kamar yarda saura sukayi ka rungumi auren nan ka fahimce ni? Turaki kamar ya fasa ihu ya gyada kai.. Fulani tace yauwa,bana son wata dogon mgn nan gaba tashi ka tafi Allah yayi maka albarka. A sanyaye ya mike ya fice jikinsa duk yayi sanyi... ****** From afrah...👇 _"Salam readers,pls ga masu complaining akan ina jefa English words a writing dina suyi hakuri. Dan ina sakawa ne if i lost d word in hausa,i knw its a historical story,bt ina kokarine kawai dan na samu nayi muku update da wuri basai na tsaya tambayar mutane me kaza ke nufi da hausa ba,no body is perfect manage d way i write pls am sorry_.. And yes _Naga wasu comments dinku kuma naji dadin su sosai da sosai,NIMA INA YINKU IRIN SOSAI DIN NAN😘_ _Keep them coming..dan suna kara sakawa naji dadin yi muku typing da wuri..._ TEAM RUMFAR BAYI all d way..... *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 28 Wattpad @afreey101 ******************** "Bayan wata daya... 'A cikin wannan watan daya gabata, ba karamin shakuwa ce ta shiga a tsakanin jalal da juwairiya ba.. Duk lkcn zata shigo kyara masa daki toh sai sun samu lkc sun sha yar firar su duk da dai ba wani mgnr kirki bace amma hakan yana saka zuciyoyin su cikin tsantsar farin ciki... "Kamar yau ma ta shigo sashen nasa danta gyara masa dakin ta tarar da baya ciki,tayi mamaki sosai da haka har ta kammala gyaran bata ganshi ba... Ta fito falo kenan taji kuyangi nata kananan maganganu kasa kasa..    Shiga tayi cikinsu dan taji me suke fada..jitai sunce.. "Gsky Allah yayi wa sarki jalal kyawu"kin ganshi kuwa?kamar wani balarabe.. A take duk Suka shiga leken kofar wajen shakatawar sa.. Juwairiya tabi su itama sai hango shi tayi kwance akan kujerar lilo barci ya dauke sa..fuskar sa kamar me murmushi ga cute lips dinsa da dogayen eye lashes dinsa..      Ta kura masa ido tanajin yarda bayi keta kyasa sa,a ranta kuwa cewa tayi,duk son da nake maka nasan bazan taba samun ka ba... Jakadiya ce tazo ta kore su daga wajen.. Sannan ta kalli juwairiya tace, kije waje magaji ya turo ayi masa kiran ki.. Mamaki ne ya kamata,me kuma zatayi wa magaji?      Fita tayi tabi bayan bawan da aka aiko kiran nata..   A gaban wata bishiyar mangoro taga bawan ya tsaya.... Sai hango magaji tayi a tsaye yana sakar mata murmushi ya jin gina jikinsa da bishiyar... Tayi saurin gaishe shi.. Ya amsa mata a sake yana fadin..     Kinyi mamakin kiran da nayi miki ko? juwairiya ta gyada kai.. Yace dama ina so ne na baki wata yar kyauta.. Juwairiya ta dago ta kallesa.. Ya nuna mata bishiyar yace na baki wannan bishiyar mangoron... Juwairiya ta kwashe da dariya. Magaji yabi ta da kallo yana jin sa a wani a irin nishadi... Kafin yace,ba wasa nakeyi ba fa? Kinga wannan bishiyar duk lkcn(season) din mangoro toh sai kin samu wanda yafi na ko ina zaki a jikinta..kuma a yarda na lura ke mayyar mangoro ce ko? Juwairiya tayi murmushi tace toh nagode ranka ya dade.. Magaji ya samu waje ya zauna.. Sannan ya nuna mata waje itama ta zauna a can nesa dashi.. Magaji yaja lumfashi kafin yace, na san rayuwar bauta acikin wannan masarautar ba karamin wahala ne da ita ba,amma zuciyata na son taji dan tarihin ki ko kadan ne.. Duk da nasan a tarihin bayin dake cikin masarautar nan kece kadai aka taba haifa a cikin RUMFAR BAYI...   Juwairiya taja lumfashi, hakane ranka shi dade, amma ni rayuwata babu wani labarin da zan iya bada shi.. wanda baka sani ba.. Tun ina shekara goma na fara bauta..    Magaji yaji tausayinta har cikin zuciyarsa.. Ya jinjina kai...(yana tunani a zuciyarsa,kodai ya fada mata sirrin dake zuciyarsa ne?sai kuma wata zuciyar ta hane sa) Ya kalle ta yace.. zaki iya tafiya nagode da lkcn da kika banu.. juwairiya ta mike kawai tayi masa godiya kafin ta fice.. ******************* "Washe gari.. "Umayma ce ta kalli surayya,Allah ya kara miki yawan rai.. ina tunanin kawai yakumbo ta bamu damar zuwa wajen bokan ta, tunda dai har wata daya ya shude babu wani alamun ciki a tattare dake.. kuma kar na fara jin kusun kusun daga bayin dake sashen gimbiya kilishi,wai ta fara mgn a rashin haihuwar ku har wannan lkcn.. Surayya cike da takaici tace,nima ina wannan tunanin umayma..kema kin sani bazan taba bari wata ta haifawa jalal yaron da zaya gaje shi ba sai ni!ta nuna kanta!ni surayya! Shiyasa har gobe bazan bar ciyar da khadija wannan maganin ba har sai na samu MAGAJIN'SARKI.. Taja lumfashi tace ya mgnr wannan yarinyar? Ina fata kin dasa mana wacce zata saka musu ido dan ni wlh zuciyata bata kwanta da aikin da takeyi a sashen sarkina ba.. Umayma tace kada ki damu...koma miye sirrin da take boyewa muna daf da sanin sa.. Surayya zatayi mgn kenan sai ji sukayi ana sanar da shigowar khadija.. Umayma tace, ko wane gulmar ta kawo ta kuma? "Cikin takon girma khadija ta shigo cikin falo tare da rabi a bayanta.. Surayya tayi murmushin yake,ah ah amarya da kanta da sassafe haka.?   Khadija tayi murmushi,gani nayi kamar zumuncin dake tsakanin mu ya fara rauni.. Surayya ta tabe baki,zumunci?ta maimaita.. Khadija tace,daga sashen umma nake yanzu,tace nazo wajenki dan mu tautauna akan shirye shiryen auren su ya hamza da ya turaki.. Surayya ta gyara zaman ta,na dauka ai su umman ne zasuyi komai.. Khadija ta girgiza kai,mu a nan masarautar matan sarkine ke gudunar da duk shirye shiryen daya danganci gidan sarauta.. Surayya ta jinjina kai.. *************** "Ina jinki.... ina kika je jiya da safe? juwairiya ta kalli jalal daya tsare ta da tambayoyi akan jiya daya tashi bai ganta ba..   Ta dan sauke kai kasa tace... Magaji ne yayi kirana.. Jalal ya daure fuska sannan bai ce mata komai ba kawai ya gama shirinsa yayi gaba.. Juwairiya ta saki murmushi,lallai yarima akwai shegen miskilanci.. Har ta mike dan ci gaba da gyaranta taga ya sake dawowa ya dauki hular sa ya sake ficewa.. ***************** "Biki ya matso ana ta faman shirye shirye masarautar ta cika tam da mutane sosaidaga kowane yanki na arewa.. "A yau ranar juma'a ne kuma Aka daura auren HAMZA DA NAFISA sai kuma TURAKI DA SAMIRA..   "Yarima gaba daya ranar bai samu zauna ba ko kadan ba,dan Fada ma ba karamin cika tayi tba ab..bashi da ikon fita ko nan da  can,sai magaji dake ta kokarin ganin ya taimakawa amininsa nasa.. "A can cikin gida kuwa,matan sarki ne ke ta hidima da jama'a sai ka rantse da Allah kansu a hade yake,amma kowacce tana yi ne kawai dan burge sarki jalal da kuma gimbiya kilishi mahaifiyar sa.. "Amaryar hamza aka fara kawowa nafisa direct sashen gimbiya kilishi akayi da ita.. SAMIRA kuwa matar turaki sai yamma likis suka iso kasancewar daga kasar zazzau suka taho.. Ita kam a sasheen fulani diyya aka ajiye ta... "Da daddare mai martaba sarki jalal ya shirya musu liyafa ta gani ta fada.. Gimbiya kilishi ta bukaci surayya da khadija dasu zaunaa wajen shirya nafisa..      Surayya ta kalli kayan dake hannun khadija tana yatsine fuska,kina nufin wannan kayan zata saka? Khadija tace eh mana.. Surayya taja tsaki sannan ta fito da wasu kayan tace,wannan na tanadar mata dan haka su zata saka bana son wani feleke.. Nan fada ya kaure a tsakanin su.. Nafisa kuwa sai kallon su takeyi cike da mamakin kishi irin nasu.. *************** "Jalal daga fa'da sashen baki suka nufa shi dasu magaji.. A nan ya tarar da yan uwan SAMIRA samari da manyansu daga kasar zazzau.. Khaleed ne kawai ya sani a cikin su.. Dan haka dashi ya fara gaisawa..haka nan kuma ya samu kansa da tambayar khaleed din ko ina AMMI? Khaleed yayi dan murmushi,ai ka san yan mata kusan biyar aka daurawa aure a yau din,toh AMMI na can kasar bauchi sunje kai diyar wajen ya ladan.. Jalal ya gyada kai sannan ya karasa ciki ya shiga gaisawa da sauran.... """A gajiye sosai ya shiga sashensa dan shiryawa kafin lkcn liyafar yayi.. Dakinsa ya shige Yayi wanka ya shirya cikin kayan sa da sukaji ado sosai,ga rawani na alfarma yasha.. Har sun fito tare da angona ya kalle su yace ina zuwa... Komawa yayi cikin sashen nasa ya dauko wata sarka ta zinari irin chain dinnan,ya zura a cikin aljihunsa sannan ya fice.. "Zainaba ce ta saka ayi mata kiran juwairiya dan su shirya samira.. Juwairiya cike da murna ta shiga dakin na fulani.. Samira na zaune a gefen gado ta lullube kanta da babban mayafi.. Zainaba na ganin juwairiya tace,wai ina kika shige ne juwairiya ? kinsan kuma dolene na bukace ki a kusa dani yau.. Juwairiya tayi murmushi tace.. kiyi hkr ranki ya dade ina can RUMFAR BAYI ne muna taimakawa a cikin madafa.. Zainaba ta jinjina kai,sanann ta kalli samira..tace.. Amaryar yaya bude fuskar taki mana mu gani? Ko mu kike jiwa kunyar? Samira a kunyace ta yaye mayafin.. Sai cin karo tayi da fuskar juwairiya.. Ware ido tayi tana kallonta kafin tace ,tana kama da AMMI wlh,ta fada tana nuna juwairiya, kallon rashin fahimta sukayi mata.. Samira ta shiga kallon tufafin dake jikin juwairiya, a take ta fahimci baiwa ce.. Mamaki ne ya kamata dan haka ta ja bakin ta tayi shiru... "Cikin dan kankanin lkc zainaba, juwairiya da kuma laure suka shirya samira cikin kayan alfarma tayi kyau mutuka.. "Zainaba komawa tayi sashen ta ta shirya sannan ta bawa juwairiya kaya itama tace taje ta canza hakama zabba'u..         Juwairiya komawa tayi rumfar bayi dan shiryowa..   Lkcn da zata fito sai ta tarar kamar anyi shara a masarautar babu kowa duk an hallara acan wajen liyafar..       Cikin sauri itama ta karasa wajen.. Angwaye da matansu ba karamin kyau suka kayi ba..   Idanuwanta ne suka shiga neman inda zaga yarima.. Can ta hango sa tare da magaji suna mgn ta kura masa ido.. Kamar ance ya juyo sai hada ido sukayi da ita.. Murmushi ya sakar mata a fakaice..sanan da idanuwansa yayi mata signal akan ta bi bayanshi..kafin ya fara tafiya cikin takon kasaitarsa.. juwairiya ta kalli su umayma da rabi dake gefen ta tace dasu ina zuwa kafin tayi gaba... Khaleed dake gaisawa dasu khadija ya hango ta kamar daga sama.. Kallo ya bita dashi,gefen fuskar ta kawai ya iya hangowa amma yaga dan kaminta da Ammi,da saurinsa ya sake binta da kallon tana kokarin wuce su sai hango dayan gefen fuskarta ta yayi a kone,nazari ya shiga yi,wacece ita???????? **** Juwairiya na tafiya... Umayma ta bi bayanta da kallon zargi wata zuciyar tace mata ta bi ta kawai,ai da saurinta ta shiga bin bayan juwairiya.. Can nesa da inda ake liyafar jalal yaja ya tsaya yana juyowa dan ganin ko ta taho.... Juwairiya ta karaso wajensa da sauri tana mamakin irin kyaun da yayi yau se kace shine angon..   Jalal yace wannan kallonfa? Ko nayi miki kyau ne? Juwairiya tayi saurin dukar da kai.. Jalal ya mika mata sarkar daya fito da ita daga cikin aljihunsa.. Amsa.. Ta bi sarkar da kallo sannan ta kalleshi..tace.. Ranka shi dade me yasa zaka bawa baiwa kamar ni irin wannan kyautar.. Ai bayi basu da ikon saka duk abunda ya danganci kwalliya... Jalal yaji wani iri har cikin zuciyarsa. ..... Yana son ya sanar da ita sirrin dake cikin zuciyarsa amma yana ganin kamar lkc bayyi ba.... Sai ya tuna lkcn da ya fahimci cewa SONTA YAKEYI.... "_Suna zaune ne tare da magaji a cikin lambu da wani yammaci.._   _Ya kalli magaji yana fadin.. Abokina dan Allah na tambaye ka mana?_ _Magaji ya ajiye tufar(apple)da yake ci ya maida hankalinsa wajensa..yace Ina jinka AMALE fadi naji.._ _Jalal yaja lumfashi kafin yace.. Idan kamar haka mutum ya damu da wata sosai kuma a kullum zuciyarsa na muradin yaganta yana begen ta a kowane lkc...yana jin dadin mgn da ita,yana kaunar kasancewa da ita,yana tunaninta,amma ya kasa gane matsayin da zaya ajiyeta a ciki zu..... Magaji ne ya kwashe da dariya sosai.. Jalal ya kallo shi yace meye haka? Magaji yace,meyasa kawai ba zai gene cewa SON TA yake ba?.._ _Ko wanene shi dai bako ne a cikin soyayya nake gani, dan duk abubuwan da ka fada yanzu soyayya kawai ce ke kawo su..ya dai sake tunani,..._ _Dan ba karamin SON TA yakeyi ba,kuma ya kamata yayi gaggawar sanar da itama.._ _Jalal yabi shi da kallo kafin yace, idan kuma yafi karfin ta fa?ina nufin(level)dinsu ba daya bane.._   _Magaji ya gyara zamansa,ni a ganina indai yana sonta har haka duk wani matsayi ba wani abun damuwa bane ,idan ya aureta ai duk sun zama daya ko? Jalal ya jinjina kai yana nazarin kalaman magaji..."_ TEAM RUMFAR BAYI            *RUMFAR BAYI*         (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 29 Wattpad @afreey101 _SORRY-am sorry fans jiya ban samu nayi muku update ba sbd school,kuyi hakuri da wannan..#teamjuwairiya #teamyarima #teamRumfarbayi_       ****************     "Juwairiya ce ta saka hannu ta amsa sarkar daga hannunsa ganin yayi shiru na tsawon wani lkc. a tunanin ta ko fushi ne yayi dan taki amsar kyautar tasa..    Jalal yayi firgigit yana kallonta cikin kwayar idonta.. Juwairiya ta sakar masa murmushi itama tace.. nagode sosai ranka shi dade Allah shi kara budi da tsawon rai.. Jalal ya rausayar da kai bai ce komai ba.. Sai hannu daya saka ya sake karbar sarkar daga wajenta sannan ya dawo zuwa bayanta ya tsaya..   Yana kokarin saka mata sarkar ne yake fadin.. "Kici gaba da hakuri juwairiya ki bani wani lkc zan sanar dake amsar tambayar ki nan ba da dadewa ba... "Umayma dake labe can bayansu tana leke dan ganin da wanda juwairiya take tsaye..taja tsaki..mtsw Dan Duhu ne a wajen sosai sai inuwar su kawai take iya gani..gashi kuma mutumin ne a bayan juwairiya ta dan kare shi..   Tsaki taja tana shirin juyawa ne kawai ta hango rawanin sa.. Gabanta ne ya shiga fadowa.. Dan kuwa babu wani mai dau'ra rawani haka face SARKI JALALLUDEEN,duk wanda yake kan mulki kawai ake yiwa wannan na'din rawanin... Ta shiga girgiza kanta ,inaaa ai ko kallo ma juwairiya bata ishe sa,namiji kamar jalal yana kuma matsayin sarki bazai kula mace kamar juwairiya ba.. Tabi inuwar da kallo tabbas sarki jalal dogon namiji ne kamar haka.. Cike da tunani kala kala ta juya da sauri tabar wajen...har tana hadawa da tuntube... * * * * An tashi taro lafiya kowa yayi hanyar sa dan zuwa sauke gajiya..    Ni kuwa afrah nace bari na dan leko muku dakin sababbin ma'auratan. """""Lkcn da turaki ya karaso sashensa.. bayi jar sun gama shirya samira cikin kayan barcinta masu saukin gaske.. Ga kamshi tanayi sbd gyaran data sha.. an rufe mata fuska da mayafi dayaji ado sosai..       Yana shigowa dakin ya hangota a zaune kan gado mai rumfa irin na da din nan..    Zuciyarsa ce yaji tayi masa wani iri,idan yana tuna irin mafarkin da yakeyi na son kasancewa da wacce zuciyarsa ke muradi.. Amma gashi sbd kawai suna jinin sarauta an tauye musu wannan hakkin.. Tsaki yaja kawai ya samu waje akan kujera ya zauna abunsa .. Samira taji shiru na wani dan lkc.. Ahankali ta bude mayafinta sai hango shi tayi a zaune ya dafa kai..   Lumfashi taja tana tuna kalaman kakarta.. "Samira Kada kice dan mijin da aka hada ki dashi baya sonki ki zauna hakan ya riga damunki har ki jawowa kanki wani ciwo,yarda akayi miki dole shima fa haka aka yi masa,dan haka inaso ki zauna ku fahimci junanku kin gane?" Samira ta sauko daga kan gadon ahankali ta dawo wajensa ta zauna.. Turaki yayi saurin dagowa ya kalleta.. Babu laifi samira kyakkyawa ce gata kuma da fara'a sosai dan murmushi yaga tana yi masa..   Jiyai tace.. Ka kwantar da hankalinka,nasan baka sona ko? Turaki ya kura mata ido,ita kuma wannan ya take?kai tsaye tana fadin tasan baya sonta? Katse mishi tunani tayi da cewa.. Nima kuma bana sonka..! Se dayaji kalamanta har zuci.. Samira ta murmusa taci gaba da cewa dan haka kada wani abu ya dame ka,ai zamu iya kasancewa kawaye ko? Turaki ya samu kansa da gyada mata kai.. Samira ta mika masa karamin yatsan ta toh yimin alkawari.. Turaki ya samu kansa da sakin murmushi yana mamakin yarinta irin ta samira.. Samira ta daure fuska.. Bani mana.. Ganin bashi da niyyar yin abunda tace, yasa ta fisgo hannunsa da kanta ta kulla alkawarin kawancen nasu..    Turaki yabi ta da kallo.. Gani yayi ta haye kan dayan karamin gadon tana fadin.. Ka kwana a kan wancan dan nikam bani da wani isasshen tsawon hawan sa.. Turaki ikon Allah kawai yake kallo.. Yana nan a zaune se munsharinta kawai ya jiyo.. Ya mike yana fadin.. Lallai wannan bata da wani damuwa abunta.. "Can dakin su HAMZA kuwa..    Yana shiga ya tarar da Nafisa a gefen gado zaune.. Ya karasa wajenta kanta a kasa ya zauna a kusa da ita sosai har jikinsu na gogar na juna. Nafisa taji iri dan kuwa bata taba zama da namiji haka ba.. Tana kokarin dan matsawa ne hamza yayi saurin kai hannunsa kan kugunta ya janyota gaba daya jikinsa..yace.. Haba matas ai ba haka akeyi ba..tsoro na kike ne? Nafisa ta girgiza kai.. Yace yauwa ko ke fa yanzu bari na tayani rage duk wadannan ya nuna kayan jikinta da kuma sarka da yan kunnenta.. Nafisa dai tayi masa shiru.. Hamza kuwa ya shiga cire mata yan kunnen yana kare mata kallo.. Cike da salonsa ya shiga shinshinar wuyanta.. Ni kuwa afrah nace,oh su hamza abun nema ya samu.... ****************** "Washe gari kuwa da sanyin safiya umayma ta isa sashen surayya gulma na cin ta..   Ta samu tashin ta kenan daga barci .. Surayya ta kalli umaymah dake tsaye lost in her thoughts..dan se da tazo take tunanin ko kada ta sanar ma surayya? Yadai umayma kika shigo kikayi min tsaye? Umayma ta samu waje kasa ta zauna tana lankwashe kafafunta .. Tace.. Ranki ya dade wani lbr ne na kawo miki amma ni kaina ban kai ga tabbatar dashi ba.. Surayya tace ina jinki.. Umayma ta kwashe duka zarginta ta fadawa surayya... "Kan uban nan!!!!! Surayya ta fada a mugun fusace.. Umayma jiki na rawa tace,amma fa ranki ya dade ba wai na tabbatar dashi bane ni a ganina ma bashi bane,dan sarki jalal yafi karfin baiwa kamar juwairiya .. Surayya taja tsaki tana tuna lkcn da yarima ya fadawa zainaba ta basa ita(lkcn a cikin lambu). tabbas ko ba shi bane dole ne ta koyawa wannan yarinyar hankali!!!harma ta isa ta hada miji da ita?ai ko a matsayin SA'DAKA baza ta taba bari yarinyar ta shigo rayuwar jalal dinta ba..dole ne tasan abunyi, dan zuciyarta ta dade da zargin yarima da wannan yarinyar, abu dayane kawai zai iya raba su idan ita yarinyar ce ta tona masa asiri a cikin al'ummar sa ta fadi meke tsakaninsu... ta tabbata jalal bazai taba yafe mata ba, ace kamar shi sarki yana kebewa da baiwarsa a lungu cikin dare,ai girma sa ya gama zubewa a ikon mutane.. Umayma ta kalla tace, kije ki kiramin da ita.. Umayma tace,kin samu wani mafita ne? Surayya tayi murmushin mugunta,dole ne itama ta dan rama dizgata da jalal yakeyi... **************** "Juwairiya kam ta gama shirin ta tsab ta dauko sarkar da yarima ya bata jiya data cire ta boyeta.. Murmushi ta sakar kamin ta mike ta fito.. Karo sukaci da umaymah.. Umayma ta kalleta fuska a daure.. Kije uwar dakina na kiran ki.. Juwairiya taji gabanta ya fadi.. Tana kirana? Umayma tace,kwarai sannan tayi gaba.. "Lkcn da juwairiya ta isa sashen surayya a waje ta tarar da ita zaune akan kujera tana shan kamshi tana ka'da kafarta.     Juwairiya na shirin gaishe da ita taga wasu bayi su biyu sun finciko ta ta fadi a gaban surayya.. Surayya ta banka mata harara kafin tace.. 'Na lura baki gama sanin matsayin ki a wannan masarautar ba ko? Juwairiya ta duka da kai.. Surayya tace,dake nake mgn ! Juwairiya tace na sani ranki ya dade. Surayya a fusace ta damko gashin kan juwairiya dake lullube cikin mayafi,tana kallon fuskarta tace, da wa aka kama ki jiya daddare?waye shi!!!!!! Juwairiya gabanta nata faduwa,ta rasa wace amsa zata bata dan kuwa ko kashe ta zatayi zataba taba fadin sunan jalal ba.. Surayya ta kara kolewa.. tasa kafa ta hankade ta gefe.. Tunda bazaki fada min a lallama ba ina tunanin zaki fi son fadawa SARKIN DORINA !ko!!!! Da sauri juwairiya ta dago ta kalleta idanuwanta kamar zasu zazzago sbd tsabagen tsoron daya shige ta. Jiki na rawa ta rarrafo gaban surayya ta shiga bata hkr tana zubar da hawaye masu ciwo. Surayya tayi murmushin takaici kafin ta kalli baiwar dake bayanta tace,ku dauke min ita daga gabana sannan ku Kaita can RUMFAR HUKUNTA BAYI inaso sarkin dorina ya tabbatar da ta fadi sunan wannan mutumin kafin yamma... Bayin sukazo suka dauke juwairiya sai kuka take gwanin tausayi..    Umayma tabi bayan surayya da sauri tana fadin.. Lallai ranki shi dade na yaba da hankalinki.. Kinga yanzu koma waye juwairiya take boyewa dolen ta ta fada mana,sannan idan tayi kuskuren furta sunan sarki jalal ko gimbiya kilishi kadai ta isa ta hallakar mana da ita.. Surayya tayi murmushin mugunta tabbas hakane umayma... **************     "Tunda aka taho da juwairiya daga sashen surayya bayin dake kan layin suka hau rike baki suna tauyawa kaddararta...    An shiga da ita RUMFAR HUKUNTA BAYI sarkin dorina ya saka aka kwantar masa da ita flat.. Ya dawo wajen da kanta yake.. jikinta sai rawa yakeyi sbd tsoro..ta dago ta kalli jajayen idanunsa.. Cikin kakkausar murya yace.. Ki fada min sunan wanda aka kama ki dashi jiya daddare!!!!! Juwairiya ta cije harshe ga mugun tsoron da takeji amma bazata iya taba fadin sunan shi ba.. Sarkin dorina yace,toh shikenan tunda girman kai ne dake ina tunanin wannan itace maganin ki...ya nuna katuwar dorinar dake hannunsa.. Ya dawo daidai saitin tafin kafarta ya shauda mata ita cikin kwarewarsa.. ***************** A hankali ahankali dai lbr ya fara yawo acikin masarautar.. Wannan bawan ya fadawa wancan baiwar gulma ta ko ina.... "Rabi Ce ta fito daga sashen khadija dan zuwa aiken ta.. Gani tayi bayi sai jinjina kai suke suna kusun'kusun.. Ta karasa wajen su ta shiga tambayar su dan tasan akwai lbr da dumin dumin sa..     Ware ido tayi ta dafe kirjinta... Juwairiya aka kai RUMFAR HUKUNTA BAYI? Ai da saurinta ta koma sashen khadija ta zube a kasa tana maida lumfashi.. Khadija ta kalleta da mamaki.. Ke kuma ya haka? Ina aiken da nayi miki yake? Rabi ta kalle ta.. Ranki shi dade lbr ne naji yanzun nan.. Wai gimbiya surayya ta saka akai juwairiya can RUMFAR HUKUNTA BAYI  wajen sarkin dorina..   Khadija ta ware ido.. Wajen sarkin dorina fa kika ce?bama wajen du'bu a cikin RUMFAR BAYI ba? Rabi tace wlh haka akace.. Khadija tace,lallai surayya bata da imani ko kadan.. Toh me tayi mata ne haka? Koma zainaba taji lbrn abunda ke faruwa? Rabi ta kwantar da murya tace,dan Allah ranki ya dade ki taimakawa juwairiya.. Khadija ta tabe baki,lallai wato so kike naje na zubda girmana a wajen surayya sbd wata baiwa can ko!lallai kuwa kinyi kadan!!! Rabi tabi ta da kallon takaici,su dai mutanen nan basu da ko digin taisayi a cikin zuciyarsu,wato dan kawai kaga ta zubda girma da ajinta a gaban kishiyarta shine bazata iya taimakawa baiwar Allah ba..mtsww wata sa'in mulkin ma jaraba ne.. "Lbr ya gama circulating acikin masarautar daura har ya kai ga kunnen gimbiya kilishi...(wai surayya ta saka akai wata baiwa can RUMFAR HUKUNTA BAYI)     Kilishi ta kalli hansai dake mata fifita.. Lallai ya kamata na san irin takun da zanyi da wannan yarinyar surayya, dan a yarda nake gani tazo ne da shirin shafe tarihina a cikin wannan masarautar.. Hansai(da bata da masaniyar diyarta ce wannan baiwar) ta jinjina kai tace.. ai Allah ya kara miki yawan rai,lbr ma har ya fara yawo akan,gimbiya surayya na kokari wajen siye zuciyar sarki jalal..dan ta samu dukkan (authority)a cikin masarautar nan..      Gimbiya kilishi cike da bakin ciki tace aikuwa tayi kadan ... (dan kuwa a duk fadin masarautar daura gimbiya kilishi ce kadai mace da ake tsoro kuma ake jin maganarta fiye data sarki... amma a yarda take ganin taken taken surayya yanzu tana dab ne da dauke mata wannan matsayin da ta dade tana gina shi..) ******** Turaki na hango yana kokarin karasawa gaban fa'da dan amsa kiran sarki jalal.. Caraf kunnensa ya jiyo masa firar da wasu bayi sukeyi..   "Eh wlh wannan yarinyar me konannar fuskar nan ce,ai na tausaya mata wlh"    Ribas yayi ya dawo wajensu..yace.. Me naji kuna fada yanzu? A tsorace duk suka zube kasa.. Allah ya kara maka yawan rai ayi mana afuwa.. Turaki yace,mgnr da kuke fada yanzu ita nake so naji...dan haka kuyi gaggawar sanar dani.. Daya daga cikinsu yace.. Dama ranka shi dade gimbiya surayya ce ta saka aka kai wata baiwa can RUMFAR HUKUNTA BAYI...    Gaban turaki ya fadi..a zuciyarsa yace.. Juwairiya ce... Ai da sauri ya juya ya fice ko shiga cikin fa'dar ma fasawa yayi... "Zabba'u ta shigo falon zainaba a rikicenta.. Uwar dakina kinji lbrn da naji yanzu.. Zainaba dake hakimce akan kilisar ta tace.. Wane lbr ne haka daya rikita ki.. Zabba'u ta zube akasa.. Juwairiya ce juwairiya ce ranki ya dade gimbiya surayya ta saka aka kai can RUMFAR HUKUNTA BAYI...    Mai!!!!! Zainaba ta mike da sauri,surayya!! Me juwairiya tayi mata haka?   Jiki na rawa ta mike tace wa zabba'u muje... Can sashen surayya ta shiga kai tsaye,ta tarar da ita hakimce tana cin kayan marmari ga bayi nan nata mata hidima.. Zainaba rai a bace tace.. Matar yaya,inaso kije ki saka a saki juwairiya yanzu.. Surayya tayi murmushi,tace.. Zainaba ina tunanin kin manta da wacce kike mgn ko? Ta nuna kanta,gimbiya surayya ce fa uwar gidan sarki jalal.. Kuma akan mgnr wannan yarinyar bazan taba bari ta tafi ba tare da an hukunta min ita ba,dan haka zaki iya tafiya.. Zainaba a fusace ta fita.. Ta koma sashen fulani,nan ma babu sa'a, 'samira kawai ce tabi bayanta tana dan bata baki akan tayi hakuri sannan tayi tunani idan akwai wanda take ganin ze iya taimaka mata taje wajensa.. Zainaba ta jinjina kai kafin ta mike da gudu ta fice... ******* Jalal kuwa baya da masaniya a kan komai ke faruwa. Dan tunda ya shigo fada bai samu fita ba.. Ga zuciyarsa dake ta azazzalar sa da son ganin juwairiya, kome ya hanata zuwa yau da safe oho?ko rashin lafiyar ne ya dawo?    Magaji ne ya dafa sa.. AMELE ina ganin ya kamata kaje ka huta hakanan.. Jalal yayi mika cike da gajiya yace.. Yanzun nan kuwa dan ba karamin aiki nasha yau din nan ba.. Magaji yayi dariya ai na lura hanklinka ma ya fara barin wajen nan.. Jalal ya mike fadawa suka zo suka zagaye shi suna masa kirari..   Har ya fito daga fa'da sai ga zainaba ta karaso wajen hankalinta a tashe...    Jalal ya kalleta yace,lafiya zainaba? Zainaba ta karasa kusa dashi tace ya jalal ina son mgn dakai a sirri..   Jalal cike da mamaki ya sallami fadawan wajen sannan ya maida hankalinsa wajenta.. Zainaba ta fashe da kuka... Ya jalal bani da wanda zai taimake ni sai kai.. Jalal yace taimakon me kike so kanwata?   Zainaba tace,dan Allah ya jalal kaje ka umarci surayya da ta dauke hukuncin da ta saka ayi wa Juwairiya a RUMFAR HUKUNTA BAYI...     Dum dum dum kakaji zuciyar jalal na bugawa.. Mai!!!!!kike nufi da surayya na hukunta juwairiya? ???? ya fada cikin mugun tashin hankali...!!!! Zainaba tace,nima ban san dalili ba amma wlh yaya juwairiya na cikin halin taimakon mu.. A rikice sosai jalal yace muje... Zainaba ta sauke ajiyar zuciya dama ta sani ya jalal ne kawai zai iya ceton juwairiya daga wajen surayya tunda taje har wajen fulani amma tace bazata saka baki a cikin harkar surukan kilishi ba dan bata son wani tashin hankali ya shiga tsakani.... (Haka gidan sarauta yake,kowa na kokarin minding business dinsa) ******** "Juwairiya ba karamin jigata tayi ba dan har tafin kafarta sai da duk ya fashe jini nata fita..   Surayya ce ta shigo wajen tare da umayma a bayanta.. Sarkin dorina ta kalla.. Ina fata ka samo min amsar tambayata..waye wannan mutumin da aka kama ta da shi jiya!!!!     "NI NE NAN" taji an fada daga bayansu... Gaba dayansu suka juya cikin tsantsar mamaki suke kallonsa.... surayya da umayma idanuwansu kamar zasu fado kasa...    Bakinta na rawa tace.... Dama kaine...? Ya karaso har gabanta yace.. NI NE na kirata jiya daddare.. Surayya ta kura masa ido.. TURAKI ya daure fuska sosai... Ni banga wata hujjarki na hukunta ta ba dan kawai tabi umarnina... Dan haka inaso kiyi gaggawar dauke hukuncin ki a kanta...   Surayya cike da bakin ciki take kallon shi.. Toh miye alakar ka da ita? Me kake yi da ita acikin dare kuma a lungu?   TURAKI ya fusgar da iskan bakinsa.. Cikin kakkausar murya yace.... SONTA NAKEYI... Gaba daya wajen aka kura masa ido ciki tsananin mamakin furucinsa.. Surayya ta runtse wata zuciyar na mata dadi wata kuwa bakin ciki takeyi,taso sosai juwairiya ta fadi sunan jalal dan ya tsane ta har abada.. Amma wannan turakin yazo ya bata mata shiri mtsw... Turaki ko a jikinsa ya karasa gaban juwairiya da har ta suma sbd tsananin azabar data sha..    Yana kokarin daura hannunsa a jikinta..sukaji shamaki na sanar da shigowar SARKI JALAL (wanda yaji furucin Turaki har cikin kwarewarsa )............... Not edited TEAM RUMFAR BAYI  *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 30 Wattpad @afreey101 ***************** "A mutukar fusace sosai Jalaal ya shigo wajen cikin tsananin bakin ciki da konar rai.. zainaba na biye dashi a bayansa.. Ai gaba daya jikin surayya ya shiga rawa.. Batayi tsanmanin lbrn nan zai je ga kunnen sarki ba dan kuwa ba karamin laifi bane ace matar sarki ta yanke hukunci a kan bayinsa ba tare da izinin sa ko masaniyar sa ba akai ...        Jalal bai yi wani tunani ba ya wanke ta da mari mai rai da lafiya...   Surayya ta dafe kuncin ta tana kallonsa cike da tsananin mamaki da takaici.. Jalal fuskar nan a daure ya kalli sarkin dorina da shima jikinsa ya fara rawan...yace, Wato harda kai za'a hada kai a aikata irin wannan (abomination)din a karkashin mulkina!!!!!? Sarkin dorina yayi saurin zubewa a kasa yana neman gafara awajen sarki hakama sauran bayin dake wajen.. Jalal ya kallo gefen da juwairiya take a kwance bata lumfashi runtse ido yayi cike da kunci sosai...duk shine ya jawo mata shiga cikin wannan halin..dolene yayi abunda ya dace.. Har ya yunkura dan zuwa gareta wata zuciyar ta shiga gargaden shi... "(Idan har kayi kuskuren aikata haka a gaban jama'a a yanzun,toh ba karamin bakin jini zaka jawo mata ba,a hakan ma surayya tayi mata wannan danyen hukuncin... toh balle idan ka bayyana sonta a bainar jama'a,ai ko mahaifiyar ka gimbiya kilishi ta isa ta cutar da ita)"    "Surayya ta kalleshi rai a bace.. Sannan ta juya da gudu ta bar wajen cikin bakin ciki da takaici ...umayma tabi bayanta.. Jalal ya kalli zainaba yace,ku dauke ta daga nan a kira me magani a duba ta..yana gama fadar haka ya fice da saurinsa dan bazai iya jure ganinta a cikin wannan halin ba.. "Hansai,laure,jakadiya da lbr yaje musu acan rumfar bayi ba kamarin tashin  hankali suka shiga ba,gaba dayansu damuwa da tausayin halin da juwairiya ta shiga sukeyi.. hansai na kuka sosai tace,dama ashe juwairiya ce ake fada? naji lbrn nan tun dazun a sashen gimbiya kilishi amma zuciyata bata kawo min juwairiya bace ko kadan? 'Dubu tace wlh nima naji lbrn nan yana yana ta yawo a tsakanin bayi acikin rumfar bayi amma ban taba tsanmanin juwairiyar mu bace tunanina tana can wajen aikinta.. Laure tace,ni abunda ban gane ba anan shine.. Me juwairiya tayi wa surayya haka ne? Jakadiya ta jinjinar dakai sannan tace mu karasa can rumfar hukunta bayin na tabbata zainaba zata ceto mana juwairiyar mu.. Suna karasawa suka hango rabi da zabba'u dauke da juwairiya ga kuma zainaba da turaki a bayansu..    Da sauri sukaje suka kama musu ita suna kuka sosai suka nufa rumfar bayi da ita.... ***** "Jalal na shiga sashen sa ya kasa zaune ya kasa tsaye,zuciyarsa yake ji tamkar zata fashe..       Babu abunda ya ke dawo masa a kwakwal'warsa sai furucin Turaki na dazun..INA SONTA? Yaushe turaki ya fara son juwairiya? Yaushe hakan ya faru?itama tana sonshi Yanzu menene mafita a wajensa, yana nan a zaune kaninsa zai dauke masa macen da yakejin sonta kamar ransa? Inaa bazai bari hakan ya faru ba,dan a yarda yake jinta acikin zuciyarsa,bazai taba iya hakura da ita ba... Tunaninsa ne ya katse jin mgnr jakadiya a kusa da shi..   A sanyaye take kallonsa tana tausayawa halin da yake ciki sosai.. "Dan kawai yana a matsayin sarki shine bazai iya samun damar fitowa ya nunawa masoyiyar sa irin son da yakeyi mata ba.. Sbd wani mulki... oh wasu kuma har kwadayin mulkin nan suke....taja lumfashi kafin tace..       Ranka shi dade ka kwantar da hankalinka.. juwairiya na samun kulawa sosai a wannan lkcn.. Jalal ya juyo ya kalleta da idanuwansa da suka canza launi.. Jakadiya tace.. Dama wani bawa ne yazo daga sashen tsohon sarki Abdul-Jabbar,ana neman ka acan.. Jalal jiki a sanyaye ya sake shiryawa ya fita,yana tunanin me yasa mahaifinsa yake faman sa.. ************ "Yana shiga makeken falon ya tarar da family duka a zaune.. Ga kuma surayya acan gefe tana ta kukan bakin ciki,har ita yarima zai daga hannu ya mara a gaban wasu kanskantun bayi? Toh wlh baza ta sa'bo ba....tafi karfin a wulakanta ta haka!... 'Abban ne ya kallesa ya shigo yayi musu tsaye yana mamakin taron me akeyi haka?.. Ka Samu waje ka zauna AMALE... yarima ya zauna a kilisar dake gefe fuskantar tasu hamza da turaki..    Abban yayi gyaran murya yace.. Amale ko zaka iya fada min dalilin da yasa ka marin matarka? Gimbiya kilishi tayi katsalandar fadin.. Dan ya isa da ita mana.. Abban ya daga mata hannu,ba dake nake mgn ba kilishi..kai kuma ina jiran amsar ka.. Jalal ya dauke kai gefe..sannan ya sanar ma abban duk abunda ya faru..   Abban ya kalli surayya..yace, Wai anyi haka? Surayya ta goge hawayen ta,anyi haka abba,amma ni kawai nayi hakan ne dan na san meke tsakanin turaki da wannan baiwar...bawai nayi niyyar na yanke hukunci da kaina bane.. Abba ya kalli turaki.. Meke tsakaninka da wata baiwa?ko ba jiya bane aka daura maka aure ba? Ko so kake ka nuna mana bamu isa dakai ba.. Fulani ta shiga hararar Turaki..cike da takaici.. Turaki ya lumfasa, ba haka bane abba.. Ni sonta kawai nakeyi abba kuma inaso ku bani dama dan na YAN'TAR DA ITA...    Jalal yayi saurin kallon sa.. Zuciyarsa na mutukar harbawa.. Surayya tayi wani irin shu'umin murmushi dan tana lura da irin yanayin jalal ya shiga.     Samira kanta tayi mamakin furucin sa,wai mijinta ne ke son wata baiwa har haka? oh ashe shiyasa yake yawan zaman tunani? ko a jikinta ita kam dan tausayi ma ya ke bata sosai yarda aka saka shi a gaba ana masa tambayoyi..    Abbah yace,kasan me kake fada kuwa? Turaki ya zube kasa... Dan Allah abbah ku taimaka min..na dade ina fama da sonta.. tun tana yar karamar ta Allah ya daura min sonta.. Wata irin tsawa fulani ta daka masa.. "TURAKI! Yayi shiru yana zubar da kwalla.. Jalal mutuwar zaune kawai yayi.. Dama haka turaki ke son juwairiya?    Fulani ce ta mike tazo ta wanke sa da mari.. Baka da hankali ne? Me na fada maka uhm! Gimbiya kilishi ta hau murmushi,ai dama dolene mu ringa fuskantar irin haka...tarbiyyar gidan sarauta bata ishe ka ba turaki..ka yan'ta baiwa ka aure ka a matsayin me...?    Turaki yace,MATATa mana.. Abbah yace duk ku tashi ku fita idan na yanke shawara zuwa anjima zan neme ku.. Gaba daya suka mike suka fita cike da al'ajabi...      Da daddare abban ya sakeyin kiran su..   Ya kalli jalal.. Inaso ka bada izinin ka,turaki ya yanta wannan baiwar a gobe...      Ga baki daya sai da gabansu ya fadi..sunyi mutukar mamakin yarjewar mai martaba Abdul-Jabbar.. Mamaki sosai ne ya rufe su.. Zainaba kuwa murna kawai takeyi,ji take kamar ta tashi tayi rawa dan farin ciki..   Jalal ya rasa meke masa dadi.. Yana nan zaune juwairiya na neman subuce masa.. Kamar me koyan magana a haka ya bada izininsa,ko ba komai ya samu yin abunda ya dade yanaso yayi mata,wato ya yanta ta daga bauta..     Surayya bakin ciki sosai ya rufe ta.. Koda ta koma sashenta... Umayma ce tare da tulin tambayoyin ta. Surayya taja tsaki kafin kawai tace,ki shirya zamu fita yanzu.... ************ "Juwairiya ba karamin jiki ta sha ba dan har se da tayi awa daya bata farfado ba.. Kuka sosai takeyi tana jin azaba da radadi a gaba daya jikinta.. Hansai kanta kukan takeyi tana lallashin ta data sha magani.. Rabi da zabba'u na gefe duk sun buga uban tagumi suna tauyawa kawar tasu.. juwairiya har cikin zuciyarta batayi nadamar rashin fadin sunan jalal da batayi ba.. Oh ! ko yana ina yanzu?a wane hali yake ciki?ta tabbata hankalinsa a tashe yake... Jakadiya ce ta shigo da wata me magani a bayanta da yarima ya sakata taje ta dauko ta.. Me maganin ta hau duba juwairiya..cike tausayawa. ********** "Samira ta kurawa turaki ido ganin yarda yake ta faman sauke ajiyar zuciya.. ba karamin fada yasha a wajen fulani ba wai yana son ya zubar mata da mutumci ya juyawa yan uwansa baya akan mace. ita ba wai yantar da juwairiyar da yayi bane damuwarta,ah ah furta Auren ta da yayi shine bacin ranta,duka duka jiya aka daura masa aure ko yan uwan matarsa basu gama watsewa ba yake so ya ballo musu ruwa...    Samira ta tausaya mishi sosai dama haka So yake?   Ta dawo gabansa ta tsugunna tace.. Turaki inaso na baka wata shawara idan bazaka damu ba.. Turaki ya dago yana binta da kallo.. Tace na tambaye ka? Yayi shiru.. Samira taci gaba.. Ita baiwar da kake so din ka tabbata tana sonka ne? Ko kuwa dai nuna mata iko da mulki zakayi ka aureta a cikin rashin damuwa da(feelings)dinta..    Turaki ya kura mata ido yana wani nazari,tabbas yasan juwairiya bata son sa,dan da tana son sa da zai gane tuni..,yasan dai ta dauke sa a matsayin yayanta ne amma baya tsanmanin tana SON SA...     Samira ta jinjina kai,yanayin ka ya tabbatar min da cewa ba sonka takeyi ba... Ta riko hannunsa.. Idan zan fada maka cewa kaima ba sonta kakeyi ba zaka yarda da ni? Turaki ya girgiza kai..yace.. Sonta nakeyi samira ba zaki taba ganewa ba.. yarinyar nan tun tana yar karamar ta take aikin bauta a rayuwarta,bata san wani jin dadin yarinta ba da kowane yaro yake samu.. bata da wani yanci ko zabi a rayuwarta,haka ta taso a cikin RUMFAR BAYI  babu wani digon farin ciki a rayuwarta.. Dan haka idan auren tane kawai zai sa na fitar da ita daga wannan rayuwar da take ciki toh zan iya sabawa da duk yan uwana dan nayi hakan.. Samira tayi murmushi lallai Allah yayiwa turaki zuciya me kyau..   Tace,TAUSAYINTA kawai kakeyi turaki.. Dan haka a shawara ta indai har kana son kagan ta acikin farin ciki toh lallai ne ka YAN'TAR da ita kawai daga bauta amma kada kayi kuskuren danne mata hakki kace zaka aure ta... Tana gama fadar haka ta mike ta fice... Turaki ya shiga nazarin mgnr samira.. *********     Jalal na kwance a kan gadonsa zazzabi ne sosai ya lullube sa...   Khadija ce ta shigo dakin.. Ganin halin da yake ciki ba karamin tsorata tayi ba.. Da sauri ta fita tayi sashen gimbiya kilishi dan ta sanar da ita.. Hankali a tashe gimbiya kilishi ta shigo sashen nasa..      Tausayi sosai ya bata,dan tasan ko da yana karamin sa baya son ko kadan mahaifinsa yayi masa fada akan gaskiyarsa...lallai dole ta koyawa surayya hankali,dan duk sbd ita ne haka ya faru.. Me magani aka kira ya shiga duba sa.. Khadija na gefe tana masa sannu.. ******* Mutanen ku kuwa su umayma... Wani kauye sukaje can kusa da SANDAMU a nan suka samu wani malamin tsabbu..    Surayya ta fayyace masa komai.. Dariya yayi ya buga kasa yace.. Ni ban ga wani aure a tsakanin wannan baiwar da kanin mijin naki ba... Sai dai kuwa naga wani haske a tattare da yarinyar.. Surayya taja tsaki..ya wuce na yan'cin da take shirin samu gobe.. Malamin yace yanzu me kike so ayi miki?    Surayya tace,so nakeyi kawai gobe idan an gama yan'tar da ita tayi gaba... tabar masarautar mu,dan bana son ta kara waiwayar kasar daura .....   Umayma ta jinjina kai lallai surayya ta cika shu'umar mace.. Malam ya buga kasa ya kallesu.. Kamar anyi an gama ne ranki ya dade.. Surayya tayi murmushin murna sannan ta basa kyauta me tarin yawa suka fice... ************** Washe gari...   Sosai ne juwairiya taji sauki se de kafafunta da kyal take iya tafiya.. Fadawa ne suka shigo har cikin rumfar bayi sukace ana neman ta a can fa'da.. Hansai da laure ne suka shiryata tsab dan lbr har ya gama bazuwa,kan ZA'A YAN'TAR DA JUWAIRIYA... Murna sosai bayi suka shiga yi,lallai Allah yana son juwairiya da alkairi daga ruwa rumfar hukunta bayi sai barin BAUTA daga daya... A fada kam,jalal ne a kan (throne ) dinsa ga sauran royal family duk an hallara kowa ya samu waje ya zauna.. Surayya ma kanta dadi takeji dan tasan abunda ta kulla har wani kagara take ayi ayi a yantar da juwairiyar ta bace daga rayuwar su.. "Juwairiya kuwa na saka kafa acikin Fa'dar idanuwanta suka kai kan jalal dake hakimce fuskarsa babu yabo babu fallasa..dan sosai yake jin dadin yantar da ita da za'ayi.. Ahankali ya dago da kwayar idonsa ya sauke su akan ta yana aika mata da wasu sakwannin masu wuyar fassarawa. Gaba dayansu zuciyoyin su sun dan karaya balle ma shi jalal din da yake ganin kamar(plan)dinsa bazai yi masa wani amfani ba....... Toh readers menene PLAN din JALAL? Not edited Team RUMFAR BAYI *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 31 Wattpad @afreey101 ***************** "A gaban dun'bin jama'a waziri ya Yan'tar da baiwa juwairiya kamar yarda al'adar masarautar tasu take..    "Wani irin lumfashi me nauyi ta sauke.... farin ciki sosai ya ziyarci zuciyarta bata taba jin irin wannan yanayin ba a duk rayuwarta.. Jalal kansa sai da yaji wani irin sanyi acikin zuciyarsa,yau kam zai zama tahiri babba a wajensu,daga inda yake yana kallon yarda juwairiya ke ta sakin murmushi hakan ba karamin dadi yayi masa ba..     Hansai da sauran bayi ne suka shiga congratulating din juwairiya cike da murna su,suna ji dama ace sune aka yantar,dan a wajensu idan aka yantar da baiwa kamar an sake haihuwar ta zata fara sabowar rayuwa me cike da yanci da farin ciki.     Addu'a akayi taro ya watse... "Jalal na fitowa daga fa'da ya koma sashen sa ya saka jakadiya ta turo masa juwairiya can bayan sashensa su hadu yana da mgn mahimmiya da yake yayi mata.. Jakadiya ta jinjinar dakai tana tuna lkcn da suka sanar mata taimakon da turaki yayi mata da kuma furucin da yayi na sonta,ko yanayin fuskarta se da jakadiya ta fahimci juwairiya bata son turaki,jalal ne a zuciyarta..      "Zainaba ba karamin murna tayi ba ta makakkale juwairiya a jikinta,tana jin dadin yarda zata iya hada jikinta da ita a yanzu.. samira ce ta karaso wajensu tare da khaleed dan uwanta, dukkanin su mamakin kamanni ta sukeyi da Ammi har lkcn. samira tace,na taya ki murna sosai.. Juwairiya ta murmusa cike da farin ciki tace nagode kwarai.. Khaleed ya kura mata ido yana tunanin zancen su da sarki jalal yau da asuba Allah yasa yarinyar ta amince.. Wani bawa ne yazo wajen yayi kiran samira,tayi musu sallama ta kama gabanta..    "A daki samira ta tarar da turaki a zaune.. Ta karasa wajensa tace.. Gani ance min kana kirana.. Ya dago ya kalleta..kafin yace.. Nayi tunani akan maganar ki ta jiya.. Surayya tace, kuma me ka yanke hukunci akai..zaka tilasta mata auranka ne,ko kuwa ? Turaki yace bazan taba yiwa juwairiya dole ba..dan haka bashi ne niyya ta ba.. Samira ta saki murmushi tace,naji dadin yarda ka zauna kayi tunani me kyau haka , yantar da ita da kayi ma ya isa ka taimaka mata sosai.. sai dai fa ni wlh wannan juwairiyar tana min kama da AMMI sosai.. Turaki ya gyara zama.. Me kike nufi?wacece kuma Ammi? Samira tadan muskuta.. Ammi amaryar mai martaba ce wato kakana.. Turaki ya girgiza kai,babu alakar da zata hada Juwairiya da ita gsky dan kuwa iyayen juwairiya a cikin masarautar nan suka haife ta kuma naji lbrn yan asalin kasar daura ne.. Samira ta jinjina kai hakane nima nayi wannan tunanin... ******* "Jakadiya ce ta samu juwairiya ta sanar mata da sakon jalal.. Kallon jakadiya tayi a dan tsorace..dan bata zaci tasan me ke tsakanin ta da yarima ba.. Jakadiya tajawo ta zuwa gefe tace.. Kada ki damu juwairiya ina bayanku keda AMALE..yanzu kije yana kiran ki.. Juwairiya na daga kafarta taji wani irin faduwar gaba,muryoyi ta shiga ji a kunnen ta kamar ana kwala mata kira.. Waige waige ta shiga yi.. Fuskokin su laure,hansai,rabi,zabba'u, zainaba kawai take kallo dake wajen tana jin wani irin abu yana tokare mata wuya..   Gaba daya jikinta ya hau rawa.. Jakadiya tace,kije mana kinsan ba'a barin Amale jira.. juwairiya ta gyada kai,tana tafiya ne kawai amma gaba daya zuciyarta a dakule take..ji takeyi gaba daya gangar jikinta bata kaunar zama acikin masarautar.. "Jalal kuwa na zaune akan wani dan dakali yana ta faman zuba ido.. Duk ya rame sbd tunanin da saka a gaba yanayi duk lkcn da yake shi daya.. Yanzu dai addu'ar shi daya ce Allah yasa ta amince da (plan)dinsa...     Hango ta yayi ta taho amma hankalinta kamar baya jikinta... Da sauri ya mike ya karasa wajenta..     Tana ganinsa ta lumshe ido tana dafe kirjinta,wani dan sanyi sanyi a cikin ranta ganin fuskarsa...    Jalal ya kamo hannunta.. Ya jikin ki?ina fatan kin samu lafiya.. Juwairiya ta kura masa ido kawai ta kasa furta komai.. Jalal yace,ki yafe min .... nasan duk nine silar shigan ki cikin wannan halin.. Juwairiya gaba daya ji takeyi lumfashin da take sha'ga yana dauke wa..     Jalal gani yayi ta fada jikinsa babu shiri.. A rikice yace.. Me ya faru? Baki ji dadin yantar dake da a akayi bane?na dauka ai yau ranar farin cikin ki ne.. Juwairiya ta girgiza masa kai.. Idanuwanta na fitar da kwalla ta dago daga jikinsa tana kallon kwayar idonsa tace.. 'Ka taimaka min ranka shi dade..   Jalal cikin murya me sanyi yace.. Bakya son auren turaki ne? juwairiya ta kallesa da mamaki kafin ta girgiza kai.. Jalal ya ce toh taimakon me kike so nayi miki? (A zuciyarsa kuwa yana addu'a yake Allah yasa idan ya bukaci ta gudu daga masarautarsu tabi khaleed kasar zazzau ta yarda...yarda zai samu ya yi shirinsa sosai,dan bazai taba bari ta zauna a nan ba turaki ya aure masa ita,dolene ya samar ma kansa mafita) Ji yai tace..    Ka taimakeni yarima,ina ji a cikin zuciyarta ko sakwon daya nayi a cikin wannan masarautar toh zan iya rasa rayuwata...    Waro ido jalal yayi cikin al'azabi..me hakan yake nufi?me ya same ta dare daya?daga samun yancin ta? Yanayin ta kawai yake kallo,shes not normal..akwai wani abu a kasa dan har kwayar idonta juyawa takeyi tana birkicewa.. Ya sa hannu ya share mata hawayen dake fuskarta..dan tausaya mata sosai,dole akwai abunda akayi mata,dolensa ya kare ta daga sharrikan GIDAN SARAUTA..   kwantar da murya yayi yace.. Naji ki kwantar da hankalinki nima nayi wannan tunanin..(yayi using opportunity din) Zan hadaki da khaleed dan uwan matar turakine ku tafi can kasar zazzau sai ki zauna a wajen kafin na gama shirin da nake na waiwaye ki.. Juwairiya ta damke hannunsa cikin nata.. Kayi min al'kawarin zaka neme ni koman dadewa..ni kuma nayi maka alkawarin jiranka har lkcn da zaka zo min da amsa ta.. Jalal ya janyo ta jikinsa yana cikin wani irin tausayinta a cikin zuciyarsa.. Na miki alkawari JUWAIRIYAR..na miki alkawarin nemo ki a duk inda kike,zan zo miki da sakon zuciyarta.. Taja lumfashi kafin tace nagode sosai AMALE...duk suka sauke ajiyar zuciya.. ******* "Kamar yarda suka tsara da shi da khaleed.. zai saka shamaki ya fitar da ita ta kofar baya sai su hade a can da tawagar du khaleed su wuce zazzau da ita... "Juwairiya ta shiga rumfar bayi da gudu ta shige dakinsu tana rusar kuka.. Hansai na ciki tare da laure suna ta faman murna basu san meke faruwa ba.. Kallonsu tayi.. Kafin ta fada jikinsu ta saka wani kukan... Hankali a tashe suka shiga tambayar ta ko lfy?   Juwairiya ta dafe kirjinta..tace Umma bazan iya ba..bazan iya ba umma,zuciyarta jinta nake kamar zata tsage ya zanyi umma? A rikice laure tace.. Meke damunki haka juwairiya? Juwairiya ta fashe da kuka.. Umma zan bar RUMFAR BAYI zan bar masarautar daura, idan ba haka ba ji nake umma kamar zuciyata zata iya fashewa.. ji nake na tsani duk wani lumfashi da zan shaka a wajen nan.. Hankalin su ba karamin tashi yayi ba.. Kuka suka sosai sukeyi dan a take suka fahimci sihiri ne a jikin juwairiya(kunsan mutanen da' da saurin canfin su) GIDAN SARAUTA  kenan! sunsha ganin ire iren wadannan matsalolin.. Jakadiya ce ta shigo cikin saurinta.. Itama kukan ta saka ganin su a haka ba karamin karaya zuciyarta tayi ba. "ta shiga kwaso kayan juwairiya dan jalal yayi mata bayanin komai,ita kam a ganinta kila wani haske ne yazo musu dan bayyana wa juwairiya ASALINTA ... (dan har kamarsu da Ammi sun fada mata shi da khaleed kuma bata koye wa jalal komai ba ta fada mishi yarda suka sami juwairiya ,jalal ya girgirza sosai amma yasha alwashin indai yana raye sai ya nemo wa juwairiya ASALINTA)        Hansai ta kamo hannun jakadiya suka dan fita waje.. Jakadiya tace,kiyi hakuri hansa'u ni a ganina duk abun nan da ke faruwa alkhairi ne inshaAllahu a wajen juwairiya,kika sani ko wannan tafiyar tayi sanadiyyar saduwarta da yan uwanta na usuli? Hansai na kuka shabe shabe tace,hakane jakadiya, amma ina zata nufa yanzu?wa take dashi? Jakadiya tadan waiga ganin babu kowa a wajen sai ta fayyacewa hansai duk abunda ta sani a tsakanin jalal da juwairiya... Hansai ta ware ido ta saki baki,ta kasa gasgata mgnr jakadiya, amma ko ba komai taji dadin taimakon da jalal zayyi wa juwairiya,gashi kuma Allah ya kawo wa juwairiya ranar da zatayi bankwana da BAUTA.. "Jakadiya,laure da hansai ne suka fito a asirce dan su fitar da juwairiya.. A kofar Rumfar bayi sukaci karo da shamaki yana jiransu.. Juwairiya ta juya tayiwa RUMFAR BAYI kallon bankwana,sannan ta kalli hansai tace.. Umma dan Allah ki bawa zainaba hakuri,kice mata nayi alkawarin aiko mata da wasika idan har na samu masauki me kyau.. Hansai tace,kada ki damu juwairiya zan isar mata da sakonki... 'Ta kofar baya suka fita,a inda suka tarar da motar khaleed tare da wasu maza kuda biyu.. Juwairiya na kuka shabe shabe tayi bankwana da iyayenta sannan tayi bankwana da MASARAUTAR DAURA.... ******** "Gu'da kawai kake ji na tashi daga sashen gimbiya surayya,umayma ta kalleta cike da farin ciki.. Yanzun nan wani bawa yake sanar dani,yaga fitarsu juwairiya ta kofar baya kuma da alama ita akeyiwa rakiya... Lallai aikin malamin nan kamar yankar wuka yake.. Surayya ta gyara zamanta..tana murmushin samun nasara...tace Yanzu dai na kawar da wannan shegiwar yarinyar saura na mallake SARKI JALAL na haifa masa YARIMA me jiran kujerar mulki... Duk suka kwashe da dariya.. ************ "Tunda suka hau kan hanya juwairiya ke ta rusa kuka,sai dai ba karamin wasai takeji a cikin zuciyarta ba,ji take kamar an sauke mata wani katoton dutse daga kanta..    Khaleed ne ya lumfasa ya kalleta.. Ki daina kukan nan haka mana.. Juwairiya ta gyada masa kai ta shiga goge kwallarta..tana jin kewar yan uwanta da kuma AMALEN ta.. Khaleed ya kalli me tuka su yace,idan mun kai malumfashi sai mu tsaya a ci abinci.. Juwairiya ta buga tagumi tana tunanin irin rayuwar da take ciki... Ooh! Yanzu kuma komai rayuwa ta ajiye mata? ...daga aikin BAUTA zuwa samun YANCINTA yanzu kuma tana hanyar yin HAJIRA...... ********** "Ba su iso kasar zazzau ba sai cikin dare sosai... Khaleed na ganin haka ya wuce da ita can bangarensa ya bata wani daki yace ta kwana a ciki zuwa gobe da safe... "Juwairiya tayi masa godiya sannan ta shige cikin dakin da kullin kayanta.. Dakine karami amma ya tsaru sosai dan tunda take ma a rayuwarta bata taba kwana a cikin irin sa ba.. "Ta ajiye kayanta a gefe sannan ta mike ta shige kofar da take tunanin ta ban daki ce.. Alwala ta farayi tana kaiwa wajen wanke fuska ta shafo tabon dake fuskarta, tsaki taja tace,Allah ya kawo min lkcn da zan wanke wannan tabon karyar daga fuskata har abada.. Ta saka ruwa sosai ta wanke shi tas,se taji wani irin wasai a fuskar ta ta,alwalar ta dauro ta fito.. Tana shirin ta'yar da sallah taji an kwankwasa kofar dakin.. Tsoro ne ya dirar mata.. Muryar khaleed taji yana cewa ta bude shine.. Ta karasa ta bude masa kofar... Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci khaleed.. Cikin mamaki ya nuna fuskarta.. Me ya samu fuskarki ina tabon yake? Tayi murmushi tace..lbr ne me tsawo.. Khaleed ya jinjina kai,lallai akwai wani boyayyen al'amari a tattare da yarinyar nan,yaji dadin da jalal yayi wannan tunanin,tabbas akwai (link)a tsananin su da Ammi.. "Takardar dake hannunsa ya mika mata,ga wannan babu yawa dan nasan dare yayi da kyal mu samu abinci daga cikin gidan.. Juwairiya ta bude takardar,balangu me zafi ga kuma yaji a gefe da albasa sai baza kamshi yake.. Miyau ta hadiye tace nagode sosai.. Khaleed yace,babu damuwa se da safe.. juwairiya tace Allah ya kaimu lfy... "Tana shiga dakin,tayi sallolinta sannan ta jawo takardar balangun ta,ta lashi lebenta na kasa,lallai kuwa Allah me iko wai yau itace da cin balangu irin wannan.. "Sai da Taci ta koshi tasha ruwa ta kwanta... ****** Washe gari da safe.. Bayan tayi sallar asuba ta sake komawa barci dan gaba daya jikinta a gajiye take.. Kwankwasa kofar khaleed ne ya farkar da ita daga mafarkin jalal da takeyi.. Ta mike da sauri tana mamakin kanta.. Lallai su juwairiya har an samu wuri,ta fadi tana ma kanta dariya.. Bude masa kofar tayi.. Khaleed yace,ki shirya zan shiga dake can cikin gidan.. juwairiya ta gyada kai sannan ta koma ciki tayi wankan ta ta sake kaya.. Lkcn da khaleed zai dawo har ta kammala komai.. Dan haka tafiya kawai sukayi.... Team RUMFAR BAYI *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 32 Wattpad @afreey101 _"Lovely fans of RUMFAR BAYI i appreciate your love for this story,your comments means alot to me,INA YINKU IRIN SOSAI DIN NAN"_ _#teamyarima #teamjuwairiya #teamJJ #teamJULAL #teamRumfarbayi_ ******************* "Tunda suka fito daga cikin bangaren na khaleed juwairiya ke ta kallon irin tsari da girman masarautar zazzau, tabbas tafi masarautar su nesa ba kusa ba..   "Tafiya sukeyi juwairiya na faman kallon yarda bayi take zurga'zurgar su ,a zuciyarta tace,oh duk dai in da bawa yake dan wahala ne shi.. Gani tayi duk inda suka wuce sai an tsugunna an gaishe da khaleed cike da girmamawa,shi kuma a amsa musu a sake,ta lura ko kadan baya da wani girman kai..    Wani bangare taga sun nufa,me girma da kyaun tsari,yasha sabon fanti..    Suna shiga cikin wani makeken falon ta ware ido tana kallon irin kwalliyar da falon yasha,gasu fan'teka da kwalla duk an yi jere dasu gwanin ban sha'awa.. Khaleed ya kalleta yace,ki zauna mana ya nuna mata waje a kasan darduma.. Wata baiwa ce ta fito daga wata kofa ta zube a gaban khaleed tana kwasar gaisuwa cike da girmamawa.. Ya jinjinar dakai kafin nan yace,marka ina uwar dakin naki take ne?ita na shigo na gani.. Marka dake ta kallon juwairiya tace,ai tana ciki ranka shi dade bari na sanar da ita ka shigo..ta juya ta koma kofar da ta fito da saurin ta.. Juwairiya kam ba karamin tsarguwa tayi da irin kallon da marka ke mata ba.. "Suna nan a zaune shiru kusan minti goma.. Juwairiya taji wani irin kamshi ya daki hancinta.. Tayi saurin dago da kanta... Sai caraf taci karo da fuskar AMMI..dake kokarin karasowa cikin falon cikin shiga ta alfarma..    ita kuwa Ammin gaba daya hankalinta na wajen khaleed ne dan bata ma lura da juwairiyar dake zaune a gefe ta tsare ta da ido ba...    cike da fara'a Ammi tace da khaleed...ah ah mutanen daura ne saukar yaushe? Khaleed yayi murmushi yana gyara zamansa yace,jiya da daddare na dawo Ammi mun same ku lafiya? Ammi tace lafiya kalau... ya kuma ka baro mana samirar? Khaleed yace tana nan kalau ai da bakuwa ma nake tafe Ammi..ya nuna gefen da juwairiya take a daskare tana bin Ammi da kallo..    Ammi ta juya inda taga khaleed na kallo sai cin karo tayi da fuskar data tsorata ta sosai..      Kallon kallo suka shiga yiwa juna ita da juwairiya kamar idanuwansu zasu zazzago.. Khaleed dai gyara zaman sa ya sakeyi yana jira yaga yarda za'a karkare.. *********** *A masarautar daura kuwa* "Jalal hankalinsa a kwance yake sosai dan yasan khaleed zai kula masa da juwairiyar sa.. tunda ya daukar masa alkawarin yin hakan. Yaja lumfashi.. Allah yasa juwairiya ta gano asalinta... shine kawai addu'ar sa a gareta dan kuwa yana so itama ta samu farin ciki a cikin zuciyarta.. A halin yanzu yana zaune ne a cikin wajen shakatawar sa... Ba karamin kewar juwairiya yakeyi ba.. Surayya ce ta shigo da sallamarta... ko kallon inda take bayyi ba.. Zama tayi a kusa dashi ta narkar murya tace.. Sarkina ka yafe min na san kana fushi dani,amma wlh bani da niyyar kai karar ka a wajen abba.. Jalal yaja tsaki yana mamakin halin surayya.. Ta sake kwantowa jikinsa..kaji sarkina kayi hkr.. Jalal a zuciyarsa yace..lallai wannan yarinyar yar rainin hankalin ce,dolene ya ho'ra ta da abunda yasan zai fi yi mata ciwo.. Murmushin mugunta yayi sannan ya kwalawa jakadiya kira.. Sai gata da sauri ta shigo wajen..tace gani ranka shi dade.. Jalal yace,inaso ki aika min sashen khadija a fada mata yau ina gayyatar ta kwana a sashena..   Dam!zuciyar surayya ta buga..lallai ma wato a gabanta yake gayyatar matarsa kwana?babu wani dan kawaici? Jakadiya tayi murmushi sannan tace, An gama Amale..ta fice... Surayya taja tsaki,ta mike rai a bace tabar sa awajen.. Jalal yayi dariya yace kadan ma kika gani Surayya... ************* """Zabba'u ce ta sanar ma zainaba tafiyar juwairiya.. Kuka sosai tayi na kewar ta tana jin haushin rashin zuwanta suyi bankwana.. wasiko kin da Mustapha ke aiko mata ne ta dauka sannan taja zabba'u suka fice zuwa lambu.. Zama tayi akan koren ciyayi dake wajen tana sake karanta wasikokinta dan ta samu damuwar tafiyar juwairiya tayi ta barta ya ragu acikin zuciyarta...         Kallon zabba'u tayi tace,kije ki samo min kayan marmari nasha.. Zabba'u tace toh ranki ya dade.. Zainaba na nan a zaune aka fara iska me karfin gaske ga kuma hadari daya hadu sosai..   Takardun data baje a wajen ne iska ya fara tafiya dasu.. Ta mike da sauri ta shiga kwashe su..     "Magaji ne ya shigo lambun dan samun sukuni a cikin zuciyarsa, bayan yaji tafiyar juwairiya a bakin khadija ba karamin tashin hankali ya shiga ba,dan kuwa yasan har abada bazai sake ganinta ba... Hango zainaba yayi tana ta faman kwasan gudu tana bin takardun da iska ke ta dauka..     Dariya sosai ta bashi..ai kuwa ya shiga kyalkyacewa da dariya.. Zainaba najin sautin dariya ta dago da sauri sai hango magaji tayi.. Ta tsaya tana kallonsa hade da rike kugunta..tace..   Yaya magaji ni kakewa dariya haka ko? Magaji ya karasa wajenta..yana fadin.. Afuwa ranki ya dade... Zainaba ta turo baki kawai taci gaba da abunda takeyi.. Magaji ya duka shima yana taya ta,sai da suka kusa gama kwashewa sai kuma ga ruwa kamar da bakin kwarya...    Zainaba duk ta rikice....gani tayi magaji ya cire babbar rigar sa yazo wajenta.. Da kallo kawai take binsa.. Daga jigar yayi sama yayi musu rumfa da ita.. Zainaba ta ware ido ta juyo tana kallonsa.. Magaji yace,yadai da kallo muje da sauri dan wannan rumfar ba mai dore wa bace.... Tafiya ya farayi tayi saurin binsa itama..   har sai da sukaje sashen ta sannan yaja burki ya tsaya yana dauke rigar daga kansu..   Zainaba ta kalleshi duk sun jike sharkaf.. Gani tayi yana kokarin juyawa ya tafi.. Tayi saurin kiransa.. Yaya magaji!!! Ya tsaya yana kallonta.. Tace mu shiga daga ciki kadan sha ruwan dumi kada sanyi ya kama ka..   Magaji ya jinjinar kai dan kuwa yasan duk lkcn daya sha ruwa haka toh sai yayi mura.. Zainaba ta shige gaba yabi bayanta..    Wajen zama ta nuna masa sannan ta koma daki ta dauko masa bargo me nauyi ta fito..     Mika masa bargon tayi.. Magaji ya girgiza kai,da kin bar shi kanwata.. zainaba ta turo baki sannan da kanta ta jibga masa bargon a jikinsa..   Zayyi mgn ne sukaji shigowar zabba'u. Zainaba ta kalleta,ke kuma a ina kika tsaya ne? Zabba'u ta hau bata hkr.. Tace ya isa haka nan je ki kawo mana shayi mai zafi.. Zabba'u tace toh sannan ta fita.. Magaji ya kalli zainaba,yace.. "Kema baki san da tafiyar ta ba ko? Zainaba tace,wacece? Magaji yace,juwairiya.. Zainaba ta kura masa ido kafin tace,uhm se de tabar min sallahu,duk yarda muke da ita.. Magaji ya jinjina kai,lallai kam ko zainaba bata fadawa ba ashe?toh balle shi kuma... Zabba'u ce ta shigo da tray din ruwan zafin su daya sha kayan kamshi.. Zainaba tace,har ruwan saman ya tsaya ne? Zabba'u tace,eh ranki ya dade yayyafi kawai akeyi.. Zainaba ta dauki kofi daya ta mika wa magaji.... Magaji yasha ruwan zafin kadan sai mikewa yayi ya mata sallama ya tafi... ............... "Nafisa ta kalli gimbiya kilishi dake zaune a kilisarta.. ,umma dama uhm dama inaso ne naje gida a karshen satin nan dan muna da taron bikin yayana da za'ayi..     Kilishi ta kallii gefen da hamza yake zaune yana ta faman shan kankanar abunsa.   "Ta maido hankalin ta kan nafisa dake zaune kanta a kasa..tace..     Ina tunanin baki san a wane irin gida kikayi aure ba ko.. Ai duk macen da zatayi aure acikin gidan sarauta bazata iya fita kwana bakwai da daura auren ta ba..   Nafisa bataji dadi ko kadan ba,ita dai taso ace taje bikin yayanta,gashi kuma mijin nata sai dai yace mata ta nemi izinin mahaifiyar sa... A sanyaye ta mike tace,toh umma ai babu komai bari na koma sashena.. Hamza ya mike shima.. Umma zamu tafi,kilishi ta sakar masa murmushi toh shikenan Allah yayi maka albarka.. Suna fitowa nafisa taja burki ta tsaya tana yiwa hamza kallon bataji dadin hana ta fita da kilishi tayi ba..   Hamzan yayi saurin jawo hannunta yana fadin.. Haba matas kema fa kinsan fitarki yayi wuri dayawa,ki bari kawai ko wata dayane kika cika nayi miki alkawarin kai ki har gidan ku da kaina.. Nafisa ta kwace hannunta,bana so! Tayi gaba tabar shi a wajen.. Hamza yayi kwafa shima ya bi bayanta... **************** *masarautar zazzau* "AMMI ahankali ta shiga tafiya har ta iso gaban juwairiya.. Juwairiya tayi saurin mikewa itama suna karewa juna kallo.. Ammi a take taji kuka yazo mata sosai,ya akai haka ta faru? Ta juya ta kalli khaleed..tace Khaleed!!!babu tantama wannan JININ FATIMA ZARAH (didi😉)CE,babu tantama wannan Diyar ZARAH'U na ce!!! Ta janyo juwairiya jikinta ta kankame ta tsam,Allah na gode maka daka sa'da ni da JININ FATIMA,Allah nagode maka daka bayyanar min dasu!!!..   Juwairiya dai jin abun take banbara kwai,Wacece kuma FATIMA?kuma meye hadin ta da wannan matar da suke mutukar kama da juna?    Ammi ta dago ta tana kallonta cike da tsantsar kauna.. Tace.. Ina fatimar take ita?ina fata a tare kuka zo nan?ina fata fatima ta yafe mana shiyasa ta dawo garemu... dan Allah ki sanar dani ina mahaifiyar ki take? Juwairiya kai tsaye tace tana RUMFAR BAYI.....     Ammi ta tsaya cak tana kallonta.. Rumfar bayi? Ta maimaita sunan.. Khaleed ne yayi saurin mikewa ganin juwairiya ko kadan bata fahimci me ammin take fada ba..    Hannun Ammi yaja suka shige uwar da'ka..   Ammi ta kalleshi,khaleed ka sanar dani meke faruwa ne haka?a ina ka gano mana ZARAH'U? Khaleed yace,ammi ki tsaya ki saurare ni.. Ammi ta girgirza kai tana kamo hannunsa ka fada min.. A ina ka hadu da yarinyar can da babu tantanma diyar fatima na ce,kuma me yasa tace min fatima na rumfar bayi? bacin fatima bata da wani hadi da bauta a rayuwarta! !!... Khaleed yaja lumfashi yana damke hannun Ammi..yace Amim yarinyar can da kika gani,a jiya aka yantar da ita a MASARAUTAR DAURA, baiwa ce...   Ammi ta dafe kirjinta tana fashewa da kuka,yau na shiga uku! Dama halin da fatima ta fa'da kenan? Khaleed yace,ammi ki nutsu kiji labarin da zan fada miki.. Ammi na kuka shabe shabe ta gyada masa kai.. Khaleed ya sanar wa Ammi dan takaitaccen lbrn juwairiya kamar yarda jakadiya da kuma jalal suka sanar masa..   Mutuwar zaune Ammi tayi.. Tabbas Fatima ce,ZARAH'U ce wannan matar data haihu a cikin RUMFAR BAYI, DIYATA wacce ta dade da bacewa kuma YAYARKA ce da muka dade muna nema....   Khaleed ya waro ido yana fadin.. Ina nufin Juwairiya diyar yaya zarah'u ce?zarah'u da nake jin mai martaba yana yawan fa'dar ta?wacce kuka saka yan farauta su nemo muku ita?wacce ta AURI SARKIN KANON DABO?SARKI ABU-TURAB? Ammi tace kwarai kuwa..itace... Khaleed ya jinjina kai cike da al'ajabi.. Ammi tace,da alama yarinyar nan bata san ASALINTA  BA kuma ya kamata ta san ko ita wacece....ya kamata mu sanar da ita mu danginta ne..   Mikewa ammi tayi ta fito falon inda juwairiya take zaune gaba daya tambayoyi ne acikin zuciyarta.. Ammi ta zauna a gabanta tace.. Ya sunanki? Juwairiya tace sunana JUWAIRIYA.. Ammi tayi murmushi ta shafa gefen fuskarta.. Juwairiya kada kiyi mamakin abunda zamu fada miki yanzu kinji?,nasan dai da idonki kin ga irin kamannin da mukeyi ni dake ko? juwairiya ta gyada kai dan shi yafi damunta,menene hadin ta da wannan matar..   AMMI tace toh ke JIKATA ce diyar DIYATA fatima data ba'ce shekaru masu yawa da suka gabata...    Gaban juwairiya ne ya fadi ras!!!! Muryar na rawa tace.. Am am amma ai ni iyayena na can DAURA,kuma mu bayi ne..   Ammi ta girgirza kai.. Ta kalli khaleed tace,yanzun nan khaleed ya sanar dani yarda iyayen naki na can sukayi sanadiyyar samun ki... juwairiya ta waro ido cike da tsantsar mamaki tace,suka same ni!ban gane suka same ni ba,ta shiga girgirza kai,ni ummana ba samu na tayi ba ,haihuwa ta tayi da kanta!!!! Ammi ta kamo hannunta,ki kwantar da hankalinki,ammi tayi kiran Marka.. Se gata ta shigo.. Shiga ki dauko min zanen (painting )din zarah'u a ciki..   Marka tace toh uwar dakina.. Marka ta shiga ta fito da wata takarda ta mikawa ammi ita.. Ammi ta amsa ta bude ta mikawa juwairiya...      Jikin juwairiya ne ya hau rawa.. Ta amshi takardar ta kurawa zanen matar dake jiki ido.. Wani irin abu ne takeji har cikin zuciyarta, tabbas wannan matar tana da alaka da ita,tabbas su hansai samun ta sukayi ba haihuwar ta sukayi ba,me yasa suka boye mata? "sai ta tuna wani lkc da ummanta ta samu wani sabani da laure,taji lauren na cewa.. "Kin manta ba ke kadai bace me iko da ita?idan baki so asirin da muka dade muna boyewa ya tonu toh ki daina nuna min iyaka ta akan juwairiya tunda dai mu duka suka same ta bake kadai ba" Kuka sosai ta shiga yi,tana tuna duk wani lkc da tayi dasu hansai,wayyo Allah ashe basune iyayenta na usuli ba... Ammi ta rungume ta itama tana kukan sosai,tana jin bakin cikin hukuncin da suka yankewa FATIMA gashi yanzu ta tafi ta bar su har abada,diyarta kuma ta ka're a matsayin BAIWA...   Sai da suka sha kuka me isar su kafin Ammi cike da tausayawa rayuwar da juwairiya ta shiga tace,ki zauna a sashena har zuwa gobe kakan ki mai martaba ya dawo daga tafiya,zamu sanar dake labarin iyayenki... Juwairiya ta jinjinar dakai kawai dan ita gani ma takeyi mafarki takeyi... *** Saida ammi ta bata lkc sosai tasha kuka mai isarta sannan ta kamo hannunta suka shige uwar da'ka..   Marka ce tare da wata baiwa.. Ammi tace,ina fata kin hada min ruwan? Marka tace,anyi yarda kika ce ranki ya dade.. Ammi ta kalli juwairiya daga sama har kasanta kafin tace..   Tube kayanki.. Juwairiya tayi saurin kallonta da jajayen idanuwanta.. Ammi tace,tube mu shiga ban daki kiyi wanka.. juwairiya tace a sanyaye,ai nayi wanka dazun.. Ammi tace,ba wannan wankan zakiyi ba yanzu.. wanka ne zan miki dan na goge duk wani dattin bauta dake jikin ki dan a yanzu kin dawo mahaifarki..   Juwairiya tayi kasa'ke tana kallon Ammi.. Marka ce ta murmusa tace.. Ina tunanin kunyar mu takeji ne uwar dakina bari mu baku waje.. Marka ta jawo dayar baiwar sukayi waje.. Ammi da kanta ta shiga cirewa juwairiya kayan jikinta.. Juwairiya ta runtse idonta gam tana mamakin abunda ammi ke aikata mata babu ko kunya ta tube ta tas ta barta da yar shimin dake jikinta.. Ban daki suka shiga,ammi ta umurce ta data shiga cikin bahon wankan dake cike da ruwa me dumi sai kamshi yakeyi..   Juwairiya gaba daya girman/kunyar ammi takeji kuma har zuciyarta tana jin kaunar matar..   Batayi mata musu ba ta shige ciki.. Ammi da kanta da shiga wanke juwairiya tana bata labarai da suka danganci masarautar su..       Juwairiya gaba daya ji takeyi kamar mafarki takeyi...    Tasha mamaki sosai ganin Anyi mata wanka yafi kala biyar.. Data fito daga wannan ruwan ammi ta fita ta kirawo su marka su hada wani.. Ta wanko iya wankowa.. A take kuwa fatar jikinta ta canza.. Tayi wani irin fes da ita.. fatar ta tayi wani irin haske,gashin kanta sai baza kamshi yakeyi.. Tana fitowa daga baton ammi ta nade ta cikin bargo mai kauri ta saka marka ta dauke ta cak dama ita ba wani nauyi ba..     A saman gadon ammi marka ta ajiyeta.. Ammi ta kalli marka.. Kije can MA'DINKA(wajen tailors)ki fada musu inaso suyiwa juwairiya kaya yanzun nan ki kawo min,marka tace toh ranki ya dade sannan ta fice..     Ammi ta zauna a gefen juwairiya tana hada mayuka masu shegen kamshi tace..     Ina so ki daina jin kunyata juwairiya,ni kakar kice babu wata kunya a tsakanin mu kinji?..   Juwairiya ta gyada kai tana murmushi..   Sallamar wasu yan mata guda biyu ne ya katse su..      Ammi na jin muryar su tace.. Ku shigo ciki yan matana har an taso daga makarantar ne?   Yan matan suka shigo ciki...Ammi kin san ko... Mgnr ce ta tsaya musu a makoshi ganin juwairiya da sukayi akan gadon ammin su.. Kallon kallo suka shigayi wa juna.. A tare sukace.. Ammi a ina kika samo me kamar dake haka (her look alike) Ammi tayi dariya, diyarku ce.. Cikin murna suka haye kan gadon suma suna saka juwairiya a tsakiyar su..    juwairiya dai da kallo kawai take bin su.. farare ne kamar ammi amma da ganin su zaka gane yan biyu ne da suna kama da juna..   Ammi na dariya tace.. Juwairiya wadan nan sune Autaye na,ga hassana ga kuma hussaina.. Juwairiya tabi su da kallo.. Hassana ta shafa fuskar juwairiya, diyar mu na kama da Ammi sosai.. Husssaina tace,sosai ma kuwa.. Ammi ta mike tana fadin,toh ku shirya min Jikata na bar muku wuka da nama a hannunku.    Murna sosai suka shiga yi .... Ammi ta fice tana sanar musu marka zaka kawo kayan juwairiya.. "Sun gama shirya juwairiya cikin kaya na alfarma ba karamin kyau tayi ba,zan iya ce muku kamar an canzo mana juwairiya ne dan gaba daya (transforming)tayi..kamar ba juwairiya BAIWAR RUMFAR BAYI ba.. "Jama'ar gidan ne suka shiga shigowa ganin ta,ana ta taya ammi da murna.. Ammi kam baki bar kunne.. Hassana da hussaina kuwa suna makale da ita..   Khaleed ma sai da ya shigo,ya wara ido yana kallon juwairiya yace.. Ammi wacece wannan haka? Ammi tayi dariya,diyarka ce mana..   Hassana tace,ya khaleed kaga yarda juwairiya ke kama da ammin mu ko? Khaleed yayi dariya na gani sarkin surutu.. Juwairiya ta dago tana kallon khaleed, wai dama wannan mutumin kawun tane?   Khaleed ne ya kashe mata ido.. Yadai kina mamaki ko? juwairiya tace ni gani nakeyi ma kamar mafarki nakeyi.. Ammi ta kamo hannunta tace.. ba mafarki kikeyi ba juwairiya duk abunda ke faruwa dake a yanzun GASKE NE.....     Juwairiya ta saki murmushi me cike da farin ciki... Lallai dole ta gode wa Allah daya bayyanar mata da ASALINTA..... Team RUMFAR BAYI  *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 33 Wattpad @afreey101 *************** "Washe gari... "Mai martaba sarkin zazzau ya dawo daga tafiyar sada zumuncin daya tafi..     Labari ne mai dadi ris'ke sa na bayyanar diyar zarah'u... Bai ma san wane irin farin ciki zayyi ba, bai bata wani lkc ba ya saka akayi masa Ammi.. Ammi da kanta ta saka su hassana su shirya juwairiya tsab sannan suka nufi bangaren na mai martaba.. Juwairiya har cikin zuciyarta take jin dadi sosai zata ga kakanta kuma mahaifin ummanta ta gaskiya.. "Sun tarar dashi a zaune saman kujerar sa ta karfe a cikin dakinsa.. Tsoho ne da zaikai shekaru kusan tamanin haka,amma ba zaka taba cewa mijin Ammi bane dan kuwa ta fishi jikin yarinta sosai..tunda dai ya girme mata nesa ba kusa ba..     "Tunda suka cikin shigo dakin sarki ya kurawa juwairiya ido yana kallonta cike da al'ajabi... Tabbas wannan jinin diyar sa ce zarah'u ..   Da hannu yayi mata alama dataje garesa.. Ammi juwairiya ta kalla.. ta gyada mata kai tace kije juwairiya..    Ta taka har zuwa gabansa sannan ta duka kasa ta gaishe sa cike da girmamawa.. Hawaye ne suka cika masa ido.. Sai yanzu yake mugun dana sanin abunda ya aikawa diyar sa..    Ya shiga shafa kanta hannayensa na rawa haka ma lebensa... Yace... Asma'u (AMMI) Ina godewa Allah daya bayyana mana jinin fatima muka ganta tun muna da sauran lumfashi a duniyar nan. ina farin ciki sosai dana samu ganawa da ke... ya fadi yana dago dakan juwairiya, hawaye itama takeyi sosai..   Ammi ta zauna tana fadin.. .. (note an sanarma sarki lbrn juwairiya duka) Ba lkcn zubar da hawaye bane wannan,lkcn farin ciki ne da gode wa Allah... Sannan kuma lkcne da zamu sanar ma juwairiya labarin mahaifiyar ta.. Mai martaba ya gyada kai,cike takaicin rashin zarah'u da sukayi yace,hakane dole ne mu sanar dake Wacece FATIMA wato ZARAH'U mahaifiyar ki.... ******************* *Masarautar zazzau A shekarun baya da suka gabata*.. "Zarah'u itace diya ta farko da Ammi ta fara haifa tun bayan auren su da mai martaba.. yarinya ce mai saukin kai da tausayin gaske gashi bata da wani hayaniya ko kadan,bazaka tabajin tayi fada ko gardama da wani ba..     Ta taso ne cikin so da kaunar mutanen dake cikin masarautar nan.. Dan Ko ina a cikin masarautar nan shiga takeyi tun tana yar karamar ta dan haka babu wanda bai santa ba..     "Zarah'u na da shekara sha bakwai mane ma aurenta sukayi mana caaaa.. Tunda ga yayan yan uwanmu zuwa masu kudin kasar mu.. "hakan kuwa ba karamin tashin hankali ya saka mu ba dan kuwa munyi wa zarah'u alkawarin zamu bata damar zabar mijin da zata aura..    Kuma a wannan lkcn ma a yarda na lura da ita ba auren bane a gabanta karatun da takeyi shi ta saka a gaba.. Ana cikin haka ne kuma sai muka riski ziyara daga sarkin kanon dabo a lkcn daurin auren garba..      Mai martaba ne yayi kiran dukka iyalensa dan gabatar dasu ga sarki ABU-TURAB...     Duk muka hallara a cikin babban falon mai martaba dan gaisawa da babban bakonsa.. Amma banda zabba'u wacce take can bangaren kakarta suna shan firarsu.. Marka ce na aika dan ta sanar da ita neman gaggawar da mahaifinsu keyi mata...    Zabba'u da gudunta ta shigo falon da sallama.. Kallone ya koma kanta.. A lkc guda kuma ta shiga zuciyar sarki ABU-TURAB farat daya....   Bayan mun gama gaisawa ne da sarki duk muka tashi muka fice dan basu waje.. Sarki ya kalli mai martaba yace.. Takawa Duk wadan nan yan matan yaranka ne? Mai martaba ya gyada kai yace,duka yarana na ne ni na haife su.. amma zarah'u ce karama ce a cikinsu duk da tafi su jikin girma... Sarki abu-turab ya jinjinar da kai kafin yayi sallama da mai martaba suka kama hanya.. Sati daya da zuwa ziyarar shi sai ga waziri da wambai sun sake sauka a kasar zazzau... Munyi mutukar mamakin ganinsu dan basu aiko mana da wasikar zuwan nasu ba..     Mai martaba ya saka akayi musu tarba mai kyau suka ci suka sha kafin aka sake zama dan a gaisa.. Waziri bayyi kasa a gwiwa ba ya sanar da mai martaba sakon sarki abu-turah... akan sunga IRI a cikin gidan sa kuma suna so..    Murna sosai mai martaba yayi dan kuwa yayi wa AMINA sha'awar abu-turab din.. Yayi murmushin su na manya yace.. Toh madallah ai babu wata matsala tunda akwai dangantaka mai karfi ta zumunci a tsakanin mu..    Waziri da wambai sukayi farin ciki sosai sannan cike da murna suka koma kasar kano... Bayan sun sanarwa sarki abu-turab amincewar mai martaba ba karamin dadi yaji ba.. A take kuma yaje ya sanar ma mahaifiyar sa HAJJO.. Itama din taji dadi sosai dan kuwa tana mutukar son dan nata ya karo aure sbd irin rikicin da suke samu a wajen matar sa ta faro HINDU... "Bayan wata daya ta shude sai ga sarki ABU-TURAB ya sake kawo mana wata ziyarar amma a wannan karon Zance ne ya kawo sa na Aure..    Mai martaba ya tare shi cikin murnar sa ya kuma saka YAYA BABBA (kishiyar ammi)ta shirya AMINA dan su dan gana da abu-turab din.. A can falon baki inda ya sauka aka shirya musu wajen da zasu kebe dan fahimtar junan su..    "Lkcn da amina ta shiga falon abu-turab ya kyalla ido ya ganta sai ya mike da sauri yana kiran waziri dake waje... Ya nuna amina yace,ba wannan bace nake so.. Waziri mamaki ne ya kamasa..    cikin Fa'da suka koma a nan abu-turab yake sanarma mai martaba shi ba amina ce yake nufi ba wata ce daban.. Mai martaba yayi mamaki dan kuwa a lkcn yan matan gidan duka basu fi guda uku ba.. HAJIYA (kishiyar ammi ce itama )ya sake sanar ma wa akan a shirya BILKISU ta zo fada yana nemanta.. Bilkisu na zuwa abu-turab ya sake cewa ba ita bace..   Sai lokacin ne hankalin mai martaba ya tashi,dan kuwa yasan ba kowa bace abu-turab yake mgn face ZARAH'U ...       Jiki a sanyaye ya saka aka zo aka sanar min dana shirya zarah'u taje fada..    Nayi mutukar mamaki sosai sannan kuma hankalina ya tashi.. A haka na matsa mata ta shirya ta tafi.. Tana shiga Abu-turab yace ai itace yake mgn,shi itaa yake so a basa.. Mai martaba ya rasa yarda zayyi gashi kuma yayi musu alkawari tun da farko akan cewa ya basu.. damuwa sosai ne ya shiga dan ba'asan sarki da mgn biyu ba.. Bayan su abu-turab sun koma kasar su akan zasu dawo dan a saka ranar biki.. mai martaba ya same ni dan neman shawarata..     Rasa abunda zan fada nayi dan kuwa ina son farin cikin ya'ta amma kuma rashin amincewa sarki ABU-TURAB kamar zubar da ki'ma da mutumcin masarautar mu ne..    Cikin rasa wata mafita muka yanke shawarar aurawa abu-turab ZARAH'U... Lkcn dana same ta da mgnr ba karamin tashin hankali ta shiga ba.. Kai tsaye ta fada min ita bata son Shi..    Cikin lalama da dadin baki na samu zarah'u ta amince akan zatayi mana biyayya amma fa ita ba dan tana jin zata iya son abu-turab a zuciyarta ba.. Ba bata lkc Aka saka ranar biki.. Gaba daya jama'ar gidan suka hau jin haushi da kishin mu,har fadi sukeyi asiri naje nayi dan diyata ta auri sarkin kano...    Duk habaicin su bai wani dame ni dan kuwa yarda zarah'u duk ta rame sbd damuwar data saka a ranta nima sai hankalina ya kasa kwanciya da auren dolen da muke shirin yiwa diyar mu.. Ranar asabar da rana aka daura auren zarah'u da abu-turab a ranar kuwa da wani mugun zazzabi zarah'u ta tashi..        Jikinta babu wani sauki a haka muka lallaba aka kaita dakin ta a can babbar masarautar ta kanon dabo... AMMI taja lumfashi tana share kwallar dake fitowa a cikin idanunta..         Tunda zarah'u ta shiga gidan take samun matsala sosai a wajen uwar gidan abu-turab Hindu.. Sai dai saukin abun shine,mahaifiyarsa da shi kansa suna mutukar kula da ita.. Hakuri kawai takeyi a gidan dan kuwa a kowace rana sai ta hadu da tsangwama a wajen HINDU da ma yan uwanta.. Shekarar ta daya a gidan Allah ya bata ciki.... Wayyo zo kiga kishi karara a wajen hindu da tawagar ta...   Lkcn ba karamin kula take samu a wajen abu-turab ba,kyaututtuka sosai yake bata yana nuna mata soyayya..   Hindu ta kasa hakuri da irin bakin ciki da kyashin da takeyiwa zarah'u, dan haka suka hada baki da wani bawa me kula da sashen abu-turab suka kulla wa zabba'u sharri.. Akan tana gayyatar wannan bawan cikin dakinta suna ZINA..      Sarki abu-turab ba karamin girgiza yayi ba da jin wannan zancen ba.. Duk da haka bai yarda ba.. Ya saka aka kirawo masa duka bayin dake aiki a sashen zarah'u dan su bada sheda akan zargin da akeyi mata..      Ga babban mamakin zarah'u gaba daya sukace ai anyi haka,tabbas suna ganin wannan bawan yana shige da fice a dakin zarah'u kullum dare..      Zarah'u ta fashe da kuka mai tsuma rai tana rokon abu-turab daya yarda da ita amma inaaa...yayi fir yaki yace ta kwashe inata inata tabar masa gidan sa...    Cike da tsananin damuwa zarah'u ta dawo masarautar zazzau da karamin cikin ta wata shidda...     Lkcn data same mu da wannan zancen ba karamin fusata mukayi da ita ba dan kuwa mun san zarah'u tasha fadin rashin son da takeyiwa abu-turab.. Daki nakai ta na shiga tuntubar ta ta fada min gsky ko da gaske ne ta aikata abunda ake zargin ta tayi. Tana kuka ta shiga fada min ita shirri ne akeyi mata wannan cikin ma na jikinta na abu-turab din ne...    Mai martaba ba karamin fusata yayi ba,dan lbr ne ya shiga yawo a kasar zazzau akan sarki ya bar diyarsa tayo yaji kuma ya kasa daukar wani hukunci akanta..   Watan zarah'u biyu mai martaba ya hadata da wasu yayyinta suka koma can kasar kano dan yin bi'konta..     Da kyal abu-turab ya amince dasu bar ta su wuce komai ya wuce..     Rayuwa tayi wa zarah'u zafi..dan kuwa abu-turab banzatar da ita yayi acikin masarautar dan babu me kula ta,ko bayin dake tare da ita ma gulmar ta sukeyi.. Cikin ta na wata tara a wani dare hindu ta saka ayi mata (kidnapping)din zarah'u a cire dan dake cikinta a kashe shi ko kuma gaba daya a kashe zarah'un dan bazata taba bari ta haihu acikin masarautar ba. dan dama tayi tayi ta zubar da cikin Allah bai bata iko ba.. Lkcn da aka fita da zarah'u wani bafade ne ya gansu,dan haka yabi bayan kattin har suka kaita wani daki suka ajiye..   Bayan sun ajiyeta ne sai yaji suna mgn akan abunda hindu ta saka su suyi.. Hankalinsa ne ya tashi sosai.. Jiki na rawa yaje ya taimakawa zarah'u suka gudu...     Suna cikin gudun sukaji muryoyin kattin mazan a bayansu.. Bafaden ya kalli zarah'u gaba dayan su sun gama jigatuwa.. Yace,ranki ya dade ki wuce abunki,ki gudu ki ceci rayuwar dan dake cikin cikin ki.. Zarah'u na kuka sosai ta girgiza masa kai.. Bazan iya tafiya na bar ka a wajen wadan nan mugayen mutanen ba.. Bafaden ya runtse ido sannan da kyal ya samu zarah'u tabar shi a wajen taci gaba da gudu dan ceto rayuwar ta dama na dan dake cikinta Ba karamin wahala da jigata tayi ba,gudu kawai takeyi bata san inda zataje ba...       Sai gashi ta shigo kasar daura,ta haife mana JUWAIRIYA sannan  tace ga garin ku nan...... Not edited pls am tire😌 Team RUMFAR *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 34 Wattpad @afreey101 ****************** "Ammi ce da kanta ta saka juwairiya a gaba suka ringa shiga bangare bangare na cikin masarautar dan gaisawa da matan mai martaba da kuma ya'yansa..   Daga karshe Ammi ta kaita wani tsohon sashe na mahaifiyar ta zarah'u ..     Hawaye ne suka shiga zuba daga idanuwanta..ba karamin tausayawa irin rayuwar da sukayi ita da mahaifiyar ta ba takeyi ba... Kallon dakin takeyi cike da tausayin irin rayuwar da mahaifiyar tayi a baya.. Ammi ta dafa kafadarta,ki ci gaba da yi mata addu'a kinji? Juwairiya ta gyada kai sannan tayi wa ammi tambayar dake ta cin ta a rai tun jiya..ta saukar da kai kasa tace..    "Ammi yanzu shi sarki Abu-turab din har yanzu bai gano sharri akayiwa ummar ba? Sannan har yanzu suna tare da matarsa hindu ne? Ammi ta kamo hannunta suka zauna a gefen gadon dake gefen su..   Ta kalli juwairiya tace, kin san indai mutum baya da hakkin wani... Toh Allah sai ya san yarda yayi gaskiya ta fito koma daren dadewa..    Wannan bafaden dai daya taimakawa zarah'u ta tsira daga hannun wadan nan mutane shine ya bayyanar da komai.. Duk da dai ba karamin wahala da azabtuwa yayi ba a wajen wadannan mutanen.. Sai da zarah'u tayi kusan sati daya da bacewa sannan Allah ya kubotar da wannan bawan..   Kai tsaye yan farautan da suka taimake shi sukayi fadar sarki abu-turab dashi..    Shi kuwa ya fayyace wa sarki duk abunda ya faru da zarah'u sannan ya sanar masa da sa hannun HINDU aciki..   Abu-turab a take a rikice susuce.. Ya saka aje a kawo masa hindu da duk mutanen da suke da sa hannun aduk abubuwan da akayi wa zarah'u..    Hindu na jin asirinta ya tuno ba karamin rikice wa tayi ba.. sbd tashin hankali da kuma mugun hali irin nata sai sakawa tayi yayanta ya taimaka mata ta gudu daga masarautar gaba ki daya....    Toh a cikin ikon Allah kwana biyu da guduwar ta ta sai gashi an kawo gawarta har cikin masarautar kano.. wai yan fashi ne suka tare su a hanyar su ta shiga kasar nijar suka kwashe musu duk kudin dake garesu sannan suka kashe su..     Abu-turab bai amsa gawar hindu ba,yace aje can akai wa yan uwanta shi babu ruwan shi da ita tunda ya dade da sakinta..       Abu-turab ya saka mutane dayawa dan neman zarah'u hakama mu ma a nan amma shiru babu wani labari akanta....   Mahaifiyar sa ce ta matsa masa akan sai ya sake wani auren.. Toh a lkcn mijin AMINA ya rasu sai mai martaba ya bashi ita,abu-turab bai wani musa ba aka daura musu aure bayan shekara daya kenan da batan zarah'u... a halin yanzu kuwa har sun hayayyafa sannan kuma ya kara aure bayan ita,ya auri diyar sarkin AZARE JAMILA .... Juwairiya taja lumfashi lallai ta tausayawa iyayen nata.. Ammi tace,kada ki damu idan kika kara kwana biyu zamuje ki gansa kinji? Juwairiya ta gyada kai.. Mikewa sukayi suka bar sashen.. ******** *Masarautar daura...* "Bakin ciki ne da takaici suka taro sukayi wa surayya yawa.. Ace wai a halin yanzu ko kallo bata ishi jalal ba? Sai dai ta ringa samun labarai daga wajen umaymah wai a kullum sai ya gayyaci khadija zuwa sashensa sannan yaje ya dauke ta su riga fita yawon shan iska da yamma... Surayya ta dunkule hannu ta naushi gadon da take a kai..     "Dole ne na san abunyi dolene na tashi tsaye ta nemo wa kanta mafita..... "Jalal ne zaune a kan gadonsa yana tunanin ko a wane hali juwairiya take ciki yanzu?ba karamin kewar ta yayi ba,kodai ya shirya ne yaje zazzau din..?     Sallama akayi ne ya katse masa tunanin sa... Khadija ce ta shigo dakin.. Jalal ya kura mata ido yana wani nazari.. Khadija ta sakar masa murmushi, ya jalal ka tashi muje toh...ina can ina ta jiran ka ashe ko ma niyyar zuwa bakayi ba.. Jalal ya lumshe ido ya bude su ahankali... yau gaba daya baya jin fitar nan gashi kuma ya sabar mata yadan ja tsaki.. Khadija ta karasa wajen sa tashiga jan hannunsa..   Jalal yaki mikewa ko motsi bayyi ba ma.. tana ta faman jansa a dolensa ya mike yana fadin.. Kin cika rigima khadija.. Tayi masa gwalo tace.. naji din nidai muje yaya.. Jalal ya daura alkyabbar sa suka fito.. Suna tafiya a cikin masarautar bayi nata faman gaida su suna yaba dacewar jalal da khadija..    Samira da turaki ne suka hango su fitowar su kenan daga sashen fulani diyya.. Karasawa sukayi wajensu.. Khadija da samira suka gaisa hakama jalal da turaki.. Jalal ya samu kansa da tambayar samira ko ta samu wasika daga can masarautar su? Samira ta girgiza masa kai tace,ah ah ina dai saka rai a cikin satin nan. Jalal ya jinjina kai kawai kafin yayi gaba khadija tayi saurin binsa.. ******** "Rayuwa tayi wa juwairiya dadi.. ba karamin canzawa tayi ba a cikin yan kwanankin nan.. gashi kuma har tana neman kusan wata daya kenan mai martaba bai bada izinin tafiyar ta kasar kanon dabo ba.. Yau dai da kyal ta samu Ammi ta hada ta da wata baiwa suka fito zuwa sashen khaleed.. Suna shiga suka tarar dashi shima ya fito cikinsa.. juwairiya ta gaishe shi tana murmushi,KAWU irin wannan gayun haka? Khaleed yayi dariya,diyata zance zani ..ko zakije ne ki gaisa da matar Kawu.. Juwairiya tayi dariya, khaleed ya kamo hannunta muje zakiji dadin haduwa da ita.. Wani bangare taga sun shiga duk a cikin masarautar.. Ta kalle shi da mamaki.. Kawu matarka acikin masarautar nan take itama? Khaleed yace,kwarai kuwa diyar kanin me martaba ce fa.. juwairiya ta jinjinar dakai,ashe kuma a nan kuna auren hadi.. Khaleed yace,tsoro kikeji? Juwairiya tayi dariya tsoron me? Khaleed yace,a hadaki da wani mana.. Juwairiya taji gabanta ya fadi, a hada ta da wani?AMALEN ta fa?ta cije harshenta,zuciyarta JALAL take so bazata taba iya rayuwa da wani ba,ba zata maimaita irin rayuwar da mahaifiyar tayi ba..... Budurwar khaleed,me suna sumayya tana da kirki sosai,a take shakuwa ta shiga tsakanin su da juwairiya... Washe gari.... da yammacin ranar talata suka fito ita dasu hassana da hussaina..     Juwairiya ta kallesu,wai na tambaye ku mana?   Hassana tace muna jin ki.. Juwairiya tace,idan kamar mutum yana son ya aikawa wani wasika da baya cikin kasar nan taya mutum zayyi hakan? Hussaina ta rike baki..badai diyar tamu har ta samo mana suriki ba?   Juwairiya ta ware ido tana nuna kanta.. Ni ah ah wlh uwar dakina..ah ah zainaba kawata ce nayi wa alkawarin aikawa wasika shine nake son na cika mata alkawarin.. Hassana tace,nidai ban taba aika wasika ba amma muje bangaren hajiya na tabbata ya mas'ud zai sani.. Juwairiya tace toh muje dan Allah..ai kuwa duka dunguma suka tafi.. Suna shiga bangaren hajiya sukaci karo da yasira... Yan biyu suka gaida ita juwairiya ma tayi yarda sukayi..   Yasira ta kurawa juwairiya ido tana tuna kanwarta zarah'u da sukafi shakuwa sosai a baya... Hawaye ne suka ciko mata a ido,ta dauke kai tayi gaba ko mgn kasa yi musu tayi.. Juwairiya taji jikinta yayi sanyi.. Hassana ta dafa ta.. Kada ki damu kanki,bawai dan sun tsane ki bane kawai dai kina tuna musu da yaya zarah'u ne.. Juwairiya ta jinjinar dakai kafin suka shige ciki...    Hajiya uwar gidan mai martaba ce itama ta manyanta sosai.. A cikin falonta suka tarar da ita bayi na ta mata hidima..    Duk suka gaishe ta cikin girmamawa .. Ta amsa a sake tana fadin.. Sai yau kuma yan matan suka tuna dani? Hussaina tace,ah ah wlh hajiya kina ran mu.. Hassana tace,hajiya wai ya mas'ud fa ya na nan kuwa? Hajiya tace,kun bani ajiyarsa ne?yaron da sai nayi sati ban saka shi a idona ba.. Hassana tayi dariya ai dadin autancin kenan.. Hajiya tace,ku duba sa dai can bangaren maza kila ku same shi.. Juwairiya tace,mun gode hajiya.. Hajiya tace,ai duk kin fi iyayen naki hankali.. Suna dariya suka mike suka fice.. Sbd rashin sa'a suna fitowa sashen hajiya wata baiwa ta tare su da sakon Ammi akan suje tana neman su.. "Lkcn da suka shiga bangaren ammin,khaleed suka tarar a falon tare da haruna suna cin abincin rana..    Juwairiya ta gaishe su duk suka amsa a sake... Ammi ce ta fito daga cikin dakin ta tace,wai ku yanzu ace kun fita tun safe baku san ku dawo kuci abinci ba ko? juwairiya tace,kiyi hkr ammi.. Ammi ta kamo hannunta ai baki da wani laifi ke kam yaran can dai dama haka suka gada... Muje ciki na nadanar miki abincin ki.. Yan biyu suka saki baki suna kallon ammin farat daya ta daina kuya dasu sai juwairiya.. Khaleed da haruna ne suka hau musu dariya.. "Washe gari mai martaba yace juwairiya ta shirya zasuje can kasar kano dan ta gana da mahaifinta..    ai kuwa ammi da kanta ta shirya juwairiya tsab,khaleed da haruna ne zasuyi musu rakiya zuwa can din.. *Masarautar kanon dabo...* "Da yamma suka shigo masarautar.. sarki abu-turab na can fada waziri yaje ya sanar masa da zuwan su.. Yayi mamaki mutuka dan a ganin sa mai martaba yayi tsofan da zai ringa damun kansa da zuwa kawo musu ziyara..ko lafiya? "Sashen Gimbiya amina suka yarda zango... Amina tunda taga juwairiya taji gabanta ya fadi.. Ta kalli ammi cike da tsananin mamaki ta nuna juwairiya.. Ammi tayi dariya tace,kwarai diyarki ce amina.. Amina kuka ne ya zo mata,taje ta rungume juwairiya cike da kaunar diyar yar uwarta ta.. Juwairiya tayi kasake tana jin wani iri wai itace yau matar sarki kamar amina take runguma haka,kuma wai yayar mahaifiyar tace... Khaleed ne ya leko dakin yace,ku fito zuwa falo ga sarki abu-turab ya shigo.. Juwairiya taji gabanta ya fadi.. Hannun amina taji acikin nata.. Tayi saurin kallonta..amina ta sakar mata da murmushi kafin tace muje kiga babanki.. "Juwairiya na saka kafa acikin falon ta hango shi a zaune yasha kaya na alfarma sosai ga rawaninsa mai kyau da tsada kyakkyawa ne sosai ga hutu ya zauna masa sosai...(wannan shine mahaifina?) Ji tayi zuciyarta tayi rauni sosai.. Amina tace.. Takawa ga yar taka... Abu-turab ya dago da sauri.. Idanuwansa sauka akan fuskar juwairiya... Mikewa yayi da sauri yana jin zuciyarsa na bugawa a take kuma ya tuna da zarah'un sa.. Hawaye ne suka taro a cikin idonsa.. Amina tajawo juwairiya zuwa gabansa.. Abu-turab ya rungume ta cike da so da kaunar diyar tasa.. Kuka sosai juwairiya takeyi,wai yau itace a jikin sarkin kano kuma wai mahaifinta ne... Abu-turab ya dago da ita yana kare mata kallo yace.. Ya sunanki? Tace sunan juwairiya.. Ya kalli su ammi yana nuna juwairiya, amina ta kama hannunsa,diyar kace ,itace Zarah'u ta haifa maka.. Abu-turab ya zube a kasa.. Ammi taje ta dafa kafadarsa... Sannan suka fayyace masa komai.. Ba karamin tauyawa juwairiya yayi ba,wai jinin sa ce tayi BAUTA...lallai dolene yayi kokari ya bata duk farin cikin dake duniyar nan... A sanyaye Yace ki yafe ni juwairiya ki yafe wa wannan uban naki... Juwairiya ta girgirza masa kai tana zubar da hawaye... "Abu-turab da amina ne suka shiga rokon ammi da mai martaba akan su bar musu juwairiya ta dan zauna a wajensu.. Da kyal suka samu ammi ta amince ta bar musu ita... Muje zuwa TEAM RUMFAR BAYI... 👇 SABOWAR RAYUWAR JUWAIRIYA ko ince sarauniya JUWAIRIYA Sorry for late update Taku AFRAH BHAI....    *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 35 Wattpad @afreey101 *sabowar rayuwa* ******************* "Sarki abu-turab ne da kanshi ya tara dukkan bayin dake cikin masarautar sa..   Gimbiya amina ya saka ta zabarwa juwairiya sababbin bayin da zasuyi mata hidima daga wannan ranar ta yau.. Cike da kwarewa amina ta shiga zabar mata su.. Abu-turab ya jinjina kai yana yabawa zabin matar tasa dan kuwa duk yan matane ta zabo kusam sa'annin juwairiya din..yasan diyarsa zataji dadin zama dasu..      Ya kalli wani dogari yace dashi,ka dauki bayi kuje can sabon sashen dake kusa dana amina a gyarawa juwairiya shi ta zauna a ciki..    Amina ta karaso wajen mijinta tana mai farin cikin ganin sa a cikin wannan yanayin.. Abu-turab ya kamo hannunta suka shige cikin sashen sa.. Ya kalleta yace.. Na gode sosai da taya ni farin cikin da kikeyi inaso ki tayani rikon juwairiya.. Amina ta girgiza kai.. Ka manta diyar zarah'u kamar a matsayin diyata take nima? Gashi kafi kowa sanin yarda yake kwadayin samun diya mace nima ko?   Abu-turab yayi dariya..hakane gimbiyata..gashi kuma kin samu.. Sannan Idan su yarimaADO da Abdullahi sun dawo gobe inaso ki hada su yar uwar su.. Amina tace,ai wannan ya zama dole..mai martaba Abu-turab yace,yauwa inaso kuma ki saka jakadiya ta zauna ta koyar da juwairiya Al'adu da halayen zama a gidan sarauta,tunda dai kin ga a inda tayi rayuwar ta a baya.. Amina ta jinjinar dakai,hakane kada ka damu inshaAllah zakayi mamakin juwairiya,abu-turab yace nagode sosai gimbiyata... "Amina na fita daga sashen abu-turab ta kira jakadiya da hanne (sabowar baiwar juwairiya)ta basu umarni akan su fara koyar da juwairiya da'bi'u da halayen jinin sarauta.. Jakadiya tace,kada ki damu ranki ya dade kamar anyi an gama ne wannan.. Juwairiya na zaune a cikin dakin amina,hanne ta shigo cike da girgimawa tace.. Sannu da hutawa uwar dakina.. Juwairiya taji abun wani banbara kwai.. Hanne ta sake fadin.. Ki fito gimbiya amina nason mgn dake.. Juwairiya ta mike ta filo falon.. Amina ta kalleta cike da kulawa..tace    Juwairiya zo nan kiji..ta nuna mata kusa da kilisar da take zaune.. Juwairiya tayi yarda tace..wato ta zauna a kusa da ita.. Amina tace,inaso yanzu ki bi su jakadiya zuwa sabon sashen ki dan su koyar dake da'bi'u da al'adun mu na gidan sarauta kinji? Juwairiya tayi murmushi ta gyada kai.. Amina tace yauwa diyata tashi kuje.. "Ba karamin haduwa sashen na juwairiya yayi ba,dan a ganin tama yafi sashen zainaba nesa ba kusa ba.. Komai yaji zam zam..   Jakadiya da hanne ne suka shiga koyar da ita duk abunda suka san zai amfane rayuwarta a cikin masarautar dama waje... a matsayinta ta sarauniya juwairiyya kuma diyar sarki abu-turab..    Tunda ga yarda ake zaman kilisa.. Yarda ake tafiya.. Yarda ake cin abinci.. Yarda yake amsa gaisuwar bayi.. Yarda yake bada umarni.. Yarda ake jan aji.. Yarda ake kasaita.. Da dai sauran su......... Juwairiya ta cika da mamaki,wato komai zakayi a gidan sarauta sai an koyardake kenan? Sai ta tuna da halayen YARIMA kau sarki jalal.. A take ta saki murmushi mai kayatarwa.. Hanne ce tace da ita.. Kinfi kyau idan kina murmushi haka uwar dakina.. Juwairiya ta kalleta,itama fa a baya tayi irin wannan rayuwar.. A sanyeye tace da ita Nagode hanne.. "Acikin kwana biyu kacal sai da jakadiya ta tabbatar da juwairiya duk ta koyi abunda suka koyar da ita..   Tabbas kuma an samu canji nesa ba kusa ba,dan kuwa ita kanta juwairiya har mamakin kanta takeyi.. Komai nata ya canza a cikin dan kankanin lkc... Gashi sarki abu-turab na mutukar kula da ita duk da baya samun zuwa wajenta sosai amma yana aiko mata da sakwanni sosai..hakama gimbiya amina duk suna nuna mata soyayya.. A yau ne su yarimaADO suka dawo daga tafiyar su... Sashen ummansu amina suka fara sauka.. Tayi farin ciki sosai da ganinsu.. Cike da zumudi take sanar dasu zuwan  juwairiya... sanan ta fada musu duk lbrn ta tunda tasan basu san ta ba..    Sunyi mamaki sosai wai suna da yaya mace? Amina tace kuje ku dan huta sai ku shiga sashen na ta ku ganta.. "Sai da suka huta sukaci abinci sannan suka nufi sashen nata.. A lkcn juwairiya na zaune a falon ta hanne na gefenta suna yar firar su.. Sai jin sanar da shigowar su YarimaADO sukayi..    Hanne ta kalleta da sauri.. Yan uwanki ne yaran gimbiya amina.. Juwairiya taja lumfashi, ashe itama tana yan uwa?     Cikin takon kasaitarsu suka shigo... Juwairiya ta kura musu ido.. Zama sukayi a gabansu cikin sanyinsu.. Hanne tace,sannunku da shigowa ranku ya dade.. YarimaADO ya jinjina kai kawai yana kallon juwairiya, yace.. Mun same ki lafiya? Juwairiya mamakin irin nutsuwar su takeyi.. Tace lafiya,kun dawo lafiya? Abdullahi yace lafiya kalau yaya,gashi har munzo miki da tsaraba ma.. Juwairiya ta bude baki,ni? YarimaADO ya kalli hanne yayi mata alama akan ta fita ta shigo da sakon.. Juwairiya dai kallon su kawai takeyi,tasan zata girmewa Ado da shekara daya amma ji yarda ya fita girman jiki sai kace shine babba a cikinsu.. Hanne ta ajiye dan akwatin a gaban juwairiya.. Ado yace,ki duba ki gani ko yayi miki.. Juwairiya tasa hannu ta bude.. Ware ido tayi ganin turaruka ne da sarkar lu'ulu'u... Tunda take bata taba mallakar irin wannan kyautar ba.. Hawayene suka shiga fita daga cikin idanunta..   Ado ne ya mike ya dawo kusa da ita.. Ji tayi ya sa hannu ya juyo da fuskarta saitin da yake.. Ta kura masa ido.. Ya girgiza mata kai.. Kada ki damu yaya,munyi miki alkawarin kula dake.. Zamu nuna miki soyayyar da kikayi rashi a baya.. Dan haka kada ki sake zubar da kwallar ki kinji? juwairiya ta yaba da hankalinsa sosai.. Murmushi tayi tace,bazan sake ba.. Ado ya dauki sarkar ya koma bayanta ya saka mata ita.. Juwairiya a take ta tuna da jalal,ta runtse idonta... ina fatan dai bai fara mantawa dani ba?ina fatan bai manta da alkawarin da yayi min ba..   Ji tayi Abdullahi ya rungume ta,ta saki murmushi cike kaunar yan uwan nata... Satin ta daya a masarautar kano.. Yau ta shirya musamman dan zuwa gaida gimbiya jamila a sashenta..     Tafe suke ita da hanne.. Duk inda ta wuce sai bayi sun gaishe da ita.. Juwairiya sanin itama ta taba irin wannan rayuwar.. Duk bawan daya gaida ita sai ta tsaya ta amsa masa cike da sakin fuska..hakan kuwa ba karamin dadi yake yi wa bayin ba. "Gani tayi wani kawai yasha gabansu.. Ta dago suka hada ido dashi.. A tare suka nuna junansu cike da mamaki.. MUSTAPHA  ta fada cikin mamaki.. Mustapha ya kura mata ido.. Lallai ashe dai ke dince JUWAIRIYA.. Juwairiya tayi murmushi nice kuwa.. Mustapha yace,Allah me iko ashe dai ke din yar kasar muce.. Naji ana ta zancen sabowar sarauniyar mu data bayyana ashe kece... Juwairiya ta gyada kai nice kuwa Mustapha..ina kawata zainaba?    Mustapha ya dukar dakai yana fadin ni kaina ban samu rubuta mata wasika ba kwana biyun nan.. Juwairiya tace,yooh me ya faru? Mustapha yace,kinsan abbana har ya kai kudin aurena can gidan sarkin kasuwa toh wlh na rasa da wace kalma zan iya sanar da zainaba.. Dan banyi mata adalci ba ko kadan kin sani.. Juwairiya ta jinjinar dakai.. Kada ka damu Allah zai kawo maka mafita.. Mustapha ya kalleta.. Amma fa kin canza sosai,kin ganki kuwa kamar wata sarauniyar kyau? Juwairiya ta murmusa.. Hanne dake sauraren su tace..ai sarauniyar kyaun ce ranki ya dade. Mustapha yayi dariya yanzu sai ina? Juwairiya tace sashen gimbiya jamila zani je.. Yace toh muje na taka miki... "Ta shiga sun gaisa da jamila,macece me saukin hali sosai,da diyarta firdausi yar kimanin shekara goma.. A take jininsu ya hadu dana juwairiya sai fira suke tayi mata... ************* Masarautar daura... Shekara ta zagayo abubuwa dayawa sun faru a cikin wannan masarautar...      Shirye shiryen bikin BABBAN SALLAH sukeyi dan haka masarautar ta cika tam da mutane... Gimbiya kilishi ce ta saka hansai tayi mata kiran matar sarki dukkansu..    Batayi wani tunani ba kawai ta sanar dasu abunda ke cikin zuciyarta.. Wato na rashin haihuwar su har zuwa wannan lkcn.. Surayya ji tayi kamar ta hau laka'da wa kilishi duka,lallai ma duk kokarin da takeyi? Lallai dan Matar nan bata san cewa dan nata bane baya basu wani hadin kan kirki shiyasa ta tsare su da irin wannan mgnr ta rainin hankali... Kilishi ta sake fadin,idan har baku samu haihuwar nan zuwa karshen shekarar nan ba toh aure zan karawa JALAL sannan na zaba masa kwarkwarori..dan ina son dana ya samu MAGAJINSA tun ina da raina.. Ku tashi ku tafi... Surayya kamar zata tashi sama.. Khadija kam jiki a sanyaye ta fito.. Surayya ce ta tare ta,tace.. ke yanzu ya zakiyi ne?kina dai jin matar nan ko indan bamuyi a hankali ba se ta saka jalal duk ya sallame mu,se kace mune zamu yiwa kanmu cikin... Khadija ta jinjinar dakai kawai dan kuwa ita duk kwanankin nan bata wani jin dadin jikinta ko kadan.. ga amai da kasala da take fama dasu..    Surayya ta shiga binta da kallo,ina mgn kinyi shiru.. Khadija na yunkurin mgn sai ga amai yazo mata...    Rabi ce tayi saurin rikota tana fadin.. Ranki ya dade mu koma sashen ki a kira me magani ta duba ki..    Surayya taji gabanta ya fadi.. Muryar umayma ce taji a bayanta.. Uwar gidana ina kyautata tsanmanin matar nan cikine da ita fa? Surayya taji zuciyarta tayi baki,tace nima ina tunanin hakan..umayma.. Amma Ki shirya yanzu dole ne mu koma wajen malamin nan,dan bazai taba sabuwa ba ace khadija ta rigani haihuwa a cikin masarautar nan... "Magaji ne ya bi jalal da kallon mamaki.. Me kake nufi ne AMALE ?ban gane.. bayan sallah na shirya zamuje kasar zazzau ba? Me zamuyi a can din? Jalal dake zaune a saman kilisar sa ya daure fuska..yace.. Magaji me yasa ka cika shegen gardama ne.. Idan bazaka je din ba ai sai ka fadin min kawai.. Magaji ya girgiza kai,haba WANDARA kasan fa ni mai bin umarnin kane,kawai dai mamaki nakeyi me zai ka kasar zazzau haka cikin kurarren lkc ..? Jalal ya tabe baki.. Magaji ya gyara zama yace... yauwa kama tashi muje ka zabi DOKIN ka na hawa,dan su turaki da hamza kai kawai suke jira ka zaba kafin su zabi nasu suma..   Jalal ya kwabe fuska..yace Bana fa bana jin zanyi wani hawa a wannan shekarar... Magaji ya saki baki yana kallon shi (kwanankin nan gaba daya ya lura jalal ya canza,bai cika yawan fara'a ba ga sai fadan tsiya abu kadan sai ya hau mutum da masifa bacin ba haka ya yake da ba)     Kana nufin a wannan shekarar daura zasuyi hawan sallah babu sarkinsu kenan? Jalal ya daga kafada bai ce komai ba.. Magaji yace,toh bari kaji ma na fada maka abbanka da nawa har sun amshi takardar gayyata daga kasar kanon dabo... Jalal yace gayyatar me.. Magaji yace hawan daushe mana,kasan fa duk shekara ana haduwa kasashe kasashe ana  gasar hawa...   Jalal yaja tsaki ni babu inda zanije,na fada maka dai,bayan sallah da kwana biyu kasar zazzau zamu je kallas... ************ Masarautar kano... Suma a can din shirye shiryen kawai sukeyi,dan sarki abu-turab ba karamin shiryawa wannan bikim sallar yayi ba dan yanaso ya gabatar da diyar sa juwairiya ga al'ummar kasar ta sa.. Ado ne ya shigo sashen juwairiya.. Ya same ta tare dasu firdausi da hanne suna firar su cikin nishadi..    Yaya taso muje ki zabar min dokin da zan hau yau.. Juwairiya tayi dariya..sannan ta mike suka fita zuwa can wajen dawakai..   Wani fari dokin ta zabar masa,yayi murna sosai daga nan sukayi sashen amina.. Anan ta tarar da tulin kayan da abbanta ya saka akayi mata na cin sallah.. Godiya sosai tayi wa amina..sannan ta je har fada ta tayi wa abbanta nata godiya.. *YAU TAKE SALLAH...* Gaba daya masarautar a hargitse take.. Baka jin komai sai Kide kiden ALGAITA DA bugun TAMBARI.. Hanne ta shirya juwairiya cikin kaya na alfarma sosai taci ado har ta gaji kyau kam ba'a mgn.. Sashen amina taje a nan ta tarar da su ADO da Abdullahi sunsha gayun su suma... Abinci me rai da lafiya aka gabatar musu sukaci... Sannan sarki abu-turab ya saka azo ayi masa kiransu..zuwa fadarsa.. Team RUMFAR BAYI Team JULAL...kuci gaba da hkr in the this page JALAL N JUWAIRIYA will surely meet.. .[9/25, 7:53 AM] 0mer Farouk:            *RUMFAR BAYI*        (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 36 Wattpad @afreey101 ***************      "Mutane ne cike a cikin masarautar kano.. Sarakai daban daban daga kasashen nigeria dama na tsallake.. Taro kam ya hadu iya haduwa..        "A can na hango wani kamar sarki JALALLUDEEN akan wani doki yasha gyara na alfarma.. Mamakine ya kamani,nayi saurin karasawa wajen ina kare masa kallo,wannan tabbas shine...jalal ne...       "Magaji dake gefensa saman nashi dokin yace.. AMALE ko kai fa? Yanzu da baka zo wajen nan ba ai da ka ja mana raini..wlh Jalal ya yatsine fuska,yace.. kasan fa in ba dan abbah ya saka baki ba akan sai nazo da bazan zo wajen nan ba kasan bana son hayaniya dayawa... Magaji yayi murmushi yace,gsky sarki abu-turab yayi kokari mutuka,kaga yarda wajen nan ya kayatu kuwa?gashi ina jin ji'te ji'te akan yau zai gabatar wa jama'a  diyarsa data bayyana..   Jalal yaja tsaki,kasan dai bani da wannan lkc da zan  bata.. da mun gama zagayen da ya zaman min dole babu wani abunda zan jira a nan.. Magaji yayi dariya....yace... An gama... "Sun sha zagayen hawan na daushe.. Mutanen kano sun sha kallo,jama'a ne kamar ba gobe.. Lkcn da suka koma cikin masarautar suka tarar da sarki abu-turab da iyalensa yana gabatar dasu ga al'ummar tasa..   Jalal ya juya ya kalli magaji daya ja ya tsaya yana maida hankalinsa wajen da su sarki abu-turab suke..     Tsaki yaja ya juya dogarai na rufa masa baya.. Har yayi taku daya zuwa na biyu ne kawai yaji ana anbaton sunan SARAUNIYA JUWAIRIYA... Ji yayi gabansa yayi muguwar faduwa.....Juwairiya? Yaji gaba daya zuciyarsa na mutukar son ganin fuskar me irin sunan juwairiyar sa..     Da saurin sa ya juya....... Dai dai lkcn da gimbiya amina ke  dauke hular alkyabbar dake rufe da fuskar juwairiya.......   caraf..ya hango fuskar da bayyi tsanmanin ganin ba ko kada.. Ji yayi gaba daya jinin dake jikinsa ya tsaya cak,kwakwal'warsa ta bar aiki a take... Ware ido yayi yana nuna ta daga can cikin dubban mutanen da yake ciki.. Itace......ya furta... Mamaki ne ya rufe sa sosai.. Me takeyi a nan? Meye haka ke faruwa? Me ya kawota kasar kano daga kasar zazzau? Samun kansa yayi da bin ta ido kamar wanda yaga wata fatalwa.. Sai wani haske take tana kashe ido kamar wata taurariya... Ji yayi mutanen dake wajen nata yaba kyawun ta suna susuta tsarin ta..   Lkcn da zai farga sai gani yayi bata a wajen..   A rikice ya kalli dogaran dake wajen yace..ina zuwa kada ku biyo ni.. Da saurinsa yabi hanyar da yake tunanin nan ne ta bi... "Neman ta ya shiga yi kamar wani mahaukaci.. sai can ya hango shigen irin alkyabbar daya hango ta da ita dazun..tafe take tare  da wasu bayi mata a bayanta sai daya dake rike da hannun ta..    Karawa tafiyar sa sauri yayi.. Yasha gaba su da saurin sa yana ssuke ajiyar sa...   Hanne dake rike da hannun juwairiya da fuskarta ke rufe har wannan lkcn.. Ta kalli jalal zata balbale shi... ji tayi mgnr ta tsaya mata a makoshinta sbd irin kyaun da kwarjinin da jalal yayi mata a ido.. Gaba daya bayin suka saki baki  suna kallonshi kamar wani angle.. Jalal da zuciyarsa ke ta bugawa da sauri da sauri.. Ya saka hannu ya dauke hular alkyabbar daga kan juwairiya...    Juwairiya ta dago da saurinta jin kamshin da ba zata taba iya mantawa dashi ba...   Mutuwar tsaye ne sukayi su dukan na wani dan lkc.... suna karewa juna kallo cike da tsantsar mamakin ganin junan su a wannan lkcn..     Jalal ya kamo hannunta da karfi ya shiga janta... Hanne ta yunkura tana sake rike hannun juwairiya gam.. Juwairiya ta girgiza mata kai..kafin tace.. Hanne ina zuwa.. Hanne ta sake ta... jalal yaci gaba da janta har suka karasa bayan wani gini da babu kowa a wajen. "Ya sakar mata hannun yana kare mata kallo daga saman ta har zuwa kasan ta.. Ba karamin kyau tayi masa ba kamar ba ita ba,duk ta canza.. juwairiya kanta kallon shi takeyi.. Jalal kyakkyawan namiji ne ajin farko... irin (guy)din nan ne da kowacce mace take mafarkin samu a matsayin mijinta.. Jitai yace... Kece haka? Ko mafarki nakeyi? Juwairiya bata ce masa komi ba.. sai karasawa da tayi zuwa gabansa ta sa hannu ta muntsine shi a hannunsa... Tace.. Ni ce...kana mamaki ko? Ya gyada mata kai.. Tace toh zan fada maka komai ranka shi dade yanzun nan.. Zauna... Ta nuna masa wani dan dakali.. Jalal ya zauna itama haka..    "Juwairiya taja lumfashi kafin ta shiga bashi dukkan lbrn ta..   Ba karamin tausayawa mahaifiyar ta yayi ba.. shi bai san meyasa mata suka fiye zalunci haka ba sbd son duniya..Allah dai ya kara tsarewa.. Ya sauke ajiyar zyciya.. Abun al'ajabi wai juwairiya jinin sarauta ce itama.. Ya saki wani irin murmushin murna lallai komai yazo masa da sauki.. Yanzu ne lkcn da zai bayyanar mata da irin son da yakeyi mata..      Ya kalleta cikin ido yace.. Na tayaki murnar saduwa da dangin ki.. Juwairiya tayi murmushi tana sadda kai kasa tace nagode ranka shi dade..   Jalal ya murmusa yana fadin... Inaso na kebance dake anjima.. sbd na lura gidan naku yau a cike yake.. Juwairiya tace hakane,sai dai anjiman zaka iya samuna a sashena.. Jalal ya girgiza kai... A sirri nake so mu hadu... Juwairiya ta kura masa ido,tana jin sonsa na ratsa ta.. Tace.. Toh shikenan zan aiko hanne ta sanar dakai a inda zamu hadu..     Ta mike tana kakkabe kayan jikinta..kafin tace.. Toh Sai anjiman kenan ko? Jalal yayi saurin mikewa shima.. Jitai yace.. Wato dan yanzun kinsan umurnina bazai yi tasiri akan ki ba shiyasa kike neman guduwa ba tare da neman izini na ba ko?   Juwairiya tayi murmushi tace haba dai kai fa sarki ne ni kuwa diyar sarkin ce kaga har yanzu umurnin ka dole yayi tasiri a kaina.. Jalal yaja lumfashi...sannan ya samu kansa da furta abunda ke cikin zuciyarsa.. "Nayi kewarki rashin ki a sashena.... Juwairiya tayi mutuwar tsaye... Dan kalaman shi sunyi wa zuciyarta shigar mamaki.. Yadai da kallon kina mamaki ne? juwairiya ta gyada kai cike da kunyarsa.. Yayi dariya yana daga kafadar sa.. Ina jiran sakon ki anjima... yayi gaba cike da tsantsar farin ciki acikin zuciyarsa.. "Taro ya tashi lafiya?baki duk sun wuce masaukinsu...      Jalal da magaji tare da sauran bayin da sukazo daga kasar daura  duk suna sashen bakin inda aka sauke su..     Magaji sai mamakin jalal yakeyi.. Ganin yarda ya wani saki rai sai faman fitar da murmushi yakeyi tun dazun.     Magajin ya dawo kusa dashi yana fadin.. Ni kuwa AMALE dazu kaga diyar sarkin kanon nan? Ni sai nake gani kamar nasan fuskarta a wani wajen amma na kasa tunawa... Jalal yayi saurin kallonsa.. Magaji yace,ko da yake ma me yasa zan tamabayeka kai da kayi tafiyar ka.. Jalal ya mike yana fadin.. Bari na shiga na watsa ruwa... Magaji ya girgiza kai wani abun sai AMALE.. "Juwairiya ta dauko wasu kaya ta saka bayan ta fito daga wanka.. Sai data gama shirinta tsab sannan ta kira hanne... Tace.. Hanne aiken ki zanyi dan Allah.. Hanne tace toh ranki ya dade inaji.. Juwairiya tayi dan jim kafin tace.. Kije sashen da aka sauki bakin mai martaba inaso ki sanar da sarki jalal ya same ni a bayan sashena yanzu.. Hanne ta kura mata ido.. Juwairiya tayi saurin cewa.. Gaisawa kawai zamuyi dashi.. kuma ki fada masa sakon a cikin sirri kinji? Hanne tayi dariya na gane ranki ya dade kada ki damu.. Hanne na fita juwairiya ta fada kan gadonta tana murmushin murna.. Yau dai zata kasance da jalal dinta.. Allah yasa ya sanar da ita amsar da ta dade tana son ji daga bakinsa... "Lkcn da hanne ta shigo sashen bakin wani bawa ta tarar ta fada masa tana son ganin sarki jalal.. Bawan yayi sallama a cikin falo a lkcn jalal da magaji na zaune suna fira.. Bawan yace wata baiwa ce tazo yanzun wai tana son ganin ka ranka shi dade.. Jalal ya mike da saurinsa.. Ya kalli magaji..yace Ina zuwa.. Magaji yabi sa da kallon tuhuma.. Jalal ya fice da saurin sa...yana ji wani irin farin ciki na ratsa sa.. "A tsaye ya tarar da ita ta juya bayanta.. Jalal ya saki murmushi sannan ya karasa wajenta da sallama.. Ta juyo suka hada ido dashi.. A tare suka sakarwa junan su murmushi.. Jalal ya bita da kallo up n down.. Tana sanye ne da doguwa riga kalar ja da baki sai mayafinta kalar fari da digon baki..sai kamshi take bazawa..    Jalal yace.. Kin canza.. Ta kalli jikinta da sauri.. Amma kinfi kyau a haka.. Ta lumshe ido ta bude kafin tace nagode.. Jalal ya gyara tsayuwarsa yace.. kamar yarda nayi miki alkawari zan fada miki amsar tambayar ki duk lkcn da muka sake haduwa.. Ya shafa sajen fuskarsa yana fadin.. Tun a baya ban gama fahimtar abunda yasa nake kyautatamin miki ba,sai bayan wani lkc da zuciyata ta shaku dake... Juwairiya ta kura masa ido.. Jalal ya kalleta cikin ido yace.. Juwairiya.... Yarda ya furta sunan sai da tsikar jikinta ya tashi.. *INA SONKI.........* Wani irin yanayi taji wanda bazata iya fassara shi ba... Zuciyarta nata harbawa..dum!dum!dum! Jalal ya dawo daf da ita ya tsaya.. Kece mace ta farko da zuciyata ta fara kamuwa da sonta.. Bansan dalilin da yasa nake sonki ba.. Amma tunda idanuwana suka ga wannan kyakkyawar fuskar ta ki a wancan lkcn na kasa sukuni... Na rasa meke damuna.. Bani da tunani sai naki.. Ina mutukar jin dadin kasancewa dake.... Juwairiya..... Ina kuma fata kema zuciyar ki ta kamu da son JALAL ko? Wani irin kunya ne ya lullube ta.. Tayi saurin juyawa zata gudu.. Ya cafko ta da karfi yana rungume me a jikinsa... A cikin kunnenta taji yace.. Ko bakya son MIJI me mata biyu ne? juwairiya taji wani iri har cikin zuciyarta a take kuma ta tuna da irin wulakancin da surayya tayi mata.. Sai Ta samu kanta da turo masa baki ta kwace jikinta daga rikon sa.. Jalal yabi ta da kallo.. Ta kalleshi..tace Kasan dai yanzu ba da bane ba ko?dan ina yancina..! Jalal dai kallonta yake..cikin mamakin canzawarta farat daya(but he like ha courage).. Taci gaba.. Toh kada ka kara tuna min da wadan nan matan naka.. Jalal ya rike kugu..yana fadin.. Eyyyeeeeh duk kishin ne haka? Juwairiya  tadan harare shi.. Ba wani kishi so nake kawai ka bari dan bana so.. Jalal yace,toh ina dai jiran amsata zuwa gobe kafin na tafi..   Juwairiya tace wace amsar? Jalal ya rike baki,lallai yarinyar nan  haka kika koma? Juwairiya tayi murmushi  tace eh din.. Jalal yasa hannu ya fisgo ta zuwa jikinsa.. Kallon cikin idonta yayi..yace.. Ina ganin SONA da kishina a cikin wadan nan kwayar idanuwan naki... Dan haka ina jiran amsata sbd bana son wani yayi min shigar sauri kin gane?ya kashe mata ido daya.. Juwairiya ta samu kanta da gyada masa kai.. Yace yauwa ko ke fa.. Muje na maida ke sashen naki.. "Hannayensu sarke dana juna har suka iso kofar sashen nata.. Ya sakar mata hannun sannan ya matso zuwa gabanta.. Ji tayi kawai ya kai wa goshin ta sumba (peck) Ta runtse idonta ta budesu ahankali  tana jin wani irin abu ya na tsirga mata.. Jalal harde hannayensa yayi yana kallonta... ki shiga se da safe.. Ta gyada kai amma ta kasa motsawa ta tafi.. Jalal ya kamo hannunta.. Ko baki gaji da kallona bane.. Juwairiya ta samu kanta da  sake gyada masa kai.. Murmushin murna yayi.. Ya sa hannu a habar ta ya dago da fuskarta.. Suna kallon junan su.. Yace,kada ki damu akwai ranar da zaki gaji da kallon wannan fuskar tawa.. juwairiya tayi murmushi.. Hannunta yakai kan kirjinsa tana jin yarda zuciyarsa ke bugawa..    "Juwairiya kina jin bugun zuciyata? Ta kyafta masa ido.. Idan ban same ki ba.. ban san yarda rayuwata zata kasance ba... juwairiya tayi saurin saka hunnu saman lebensa... Tace.. Shiiiish Jalal yayi dariya.. Toh shiga kije ki kwanta... Tace toh sai da safe... ta juya ta shige ciki cike da farin ciki marar misaltuwa... TEAM RUMFAR BAYI....   [9/25, 7:53 AM] 0mer Farouk:           *RUMFAR BAYI*        (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 37 Wattpad @afreey101 ********************* """"Har jalal ya koma masaukinsa bai bar sakin murmushi me kayatarwa ba.. Magaji kam har ya fara gyangyadi yaji dawowarsa.. Yayi saurin mikewa yana kallonsa..cikin mamakin yace Allah ja zamanka wai ina kaje ne haka..naji shiru tun dazu.. Jalal ya dafa kafadarsa kawai yana sakar masa murmushi.. ya shige cikin daki yana ji inama daya kulle idonsa ya bude yaga har safiya tayi..   "A wajen juwairiya ma tana shiga sashen nata sukaci karo da hanne tana kokarin fita neman ta jin har lkcn shiru bata dawo ba.. Sai gani tayi juwairiya ta wuce ta bata ko lura da ita ba..tana rungume da hannayenta se murmushi takeyi... Tayi saurin bin bayanta tace,uwar dakina! Juwairiya tayi firgigit ta juyo ta kalleta.. Hanne ta kyalkyace da dariya.. Juwairiya ta turo baki tayi ciki da gudun ta har ta kwanta a kan gadonta me laushi murmushi ne ke fita daga bakinta.. Ta jawo filo ta rungume sa tsam tana tunano fuskar jalal da yarda yake lumshe idanuwansa idan yana mgn..    Lallai Allah me yarda yaso,wai ace sarki kamar jalal mai ji da kyau da farin jini a wajen mata shine ya so Baiwar kamar ta?a wancan lkcn.. Idonta ta murza,tabbas tayi dacen masoyi... Wanda ya sota batan mulki ko wani abu data mallaka ba..   Tunani sosai ta zurma har barci mai dadin gasken yayi awon gaba da ita. ********** "Washe gari.. "Da sassafe jalal ya tashi yayi shirinsa tsab.. dan ba karamin kagara yayi garin ya waye ba.. Koda magaji ya farka se ya tarar dashi har ya kammala komai shi kawai yake jira.. Magaji ya mike cikin mamaki yana fadin.. AMALE badai duk zangin komawa iyalin bane haka? Jalal ya harare sa..yace Kayi ka shirya bani lkcn batawa malam. Magaji yace,toh ranka ya dade...an gama.. "A wajen Juwairiya kuwa.. Har makara tayi sallar asuba sbd irin dadin da barcin yayi mata.. har tayi wanka ta shirya amma ta rasa hanyar da zata samu haduwa da jalal dan ta fada masa amsar sa.. Tasan ko tace bata jinsa a ranta toh karya ne takeyi..   Hanne ce ta shigo dakin tace da ita.. Uwar dakina yanzu nan gimbiya amina ta aiko wai kije sashen ta ku karya a can tare.. Juwairiya ta jinjinar da kai sannan ta mike ta saka alkyabba a saman kayan jikinta suka fito daga cikin sashen.. Har sun fara tafiya juwairiya ta kalli hanne..tace.. Wai ni hanne Ta ina ne sashen bakin yake? Wata hanya hanne ta nuna mata.. Juwairiya tace,muje ki rakani toh.. Hanne tayi saurin shan gabanta.. Ah ah ranki ya dade ba girman bane ace kinje har can don neman sa ba..   Juwairiya taji kunya ta kamata,tace toh ya zanyi?hanne Ina so ne na fada wani abu kuma kinga babu yarda zamu hadu dashi yau sbd komawa zayyi kasar su. Hanne taja hannunta zuwa bayan wani gini tace,jirani a nan ranki ya dade ina zuwa...da gudu tabar wajen juwairiya tabi ta da kallo..    """" Juwairiya na nan a tsaye tana jiran dawowar hanne sai ji tayi an kamo hannunta daga baya.. Kamshin sane kawai ya daki hancinta.. Ta saki murmushi babu shiri.. Jalal ya rankwafo da kansa wajen kafadarta yace cikin(husky voice).. Yanzu har kina da ikon sakawa a kira miki sarki kamar ni ko.. Juwairiya ta juyo da sauri suka hada ido dashi.. Jalal se da gabansa ya fadi ganin irin kyan da tayi.... Yace... Fadi inajin ki..da gani bakin nan naki akwai mgn ko..? juwairiya ta rufe fuskarta da tafin hannunta.. tace toh ni me zance?. Jalal yayi dariya.. Kunya ta kikeji ne haka? Juwairiya ta gyada masa kai.. Yasa hannunsa ya cire hannayenta daga kan fuskar ta yace..   Toh bari na taimake ki.. KINA SONA? juwairiya ta kura masa ido kafin tayi kasa da kanta da sauri tana murmushi..   Jalal ya sauke ajiyar zuciya.. Naji dadi sosai..sai ki shirya komawa KASAR DAURA cikin yan kwanankin nan.. juwairiya ta dago da sauri.. Yanzu fa idan ta aure shi dole ta koma masarautar su,masarautar da tayi rayuwa a matsayin BAIWARSU.. Jalal ya kamo hannunta.. Kada ki damu...ina tare dake.. juwairiya tayi shiru...kafin tace.. Ka gaida min da zainaba sannan ka fadawa jakadiya halin da nake ciki a yanzu dan ta sanarwa su umma nasan hankalin su a tashe yake..    Jalal ya gyada kai,toh ranki ya dade.. Dariya sosai ya bata.. Jalal ya kura mata ido yana kallon fararen hakoranta..      Zan tafi yanzu.. Juwairiya taji wani iri har cikin zuciyarta.. Kai ta gyada masa.. Jalal yace,zan shiga fa'dar abbanki muyi sallama dashi.. Ta sake gyada masa kai.. Shi kanshi ji yake kamar kada ya tafi..   Juyawa yayi ya fara tafiya.. Juwairiya tabi bayan da kallo tana ji kamar taje ta rungume sa..     Dauke kanta tayi jin hawaye na niyyar tarowa a cikin idonta..         Bata ankara ba taji dumin mutum a jikinta.. A tsorace ta dago.. Sai ganin jalal tayi rungume da ita.. Ta sauke ajiyar zuciya me nauyi.. Cikin murya me sanyi tace.. Ranka ya dade kada kuyi rana fa? Jalal ya dago daga jikinta..yace Indai dan na kasance dake ne muyi dare ma ba rana ba..    Sakin baki tayi tana kallonshi.. Ta lura yanzu fa bayajin kunyar fada mata wasu kalaman..   Jalal yayi dariya ya saka hannu ya rufe mata bakin kafin yayi gaba da saurinsa.. """"A fa'dar sarki abu-turab....    Sarakuna ne ke bankwana dashi dan komawa kasar su..    Sarkin GWANDU ne ya samu shamaki yayi masa rada a kunne..   Shamaki ya bude baki sosai yace.. Allah ya karawa Sarki lafiya.. Sarkin Gwandu yace a gaya maka.. Sun ga SARAUNIYA JUWAIRIYA a jiya kuma suna son hada zumunci me karfi dakai.. Wato dai ana nemar wa YARIMA FAHAD auren SARAUNIYA JUWAIRIYA... "Caraf kalaman shamaki suka riske Sarki Jalal dake kokarin shigowa cikin FADAR...   Gabansa ne yaji ya fadi..rass,aure!!!!juwairiya! !innalillahi wa'inna ilaihir raji'una"kalmar da yake ta ambato kenan... Ya karaso ciki da saurinsa..   Ji yayi Sarki abu-turab yana fadin..    Bana cikin wadan nan sarakan dake yiwa ya'yansu auren dole.. Dan haka duk YARIMAN dake son DIYATA yazo nan da karshen watan nan zan hada taro na musamman ga masu neman ta dan ta zabi wanda yayi mata..ina tunanin hakane adalcin da zanyi mata..    Wata irin ajiyar zuciya jalal ya sauke,lallai ya jinjinawa sarki abu-turab tabbas yana kaunar diyar sa sosai... Dole ne ya tashi tsaye.. In ba haka ba juwairiya na dab da subuce masa... ****************** "Lkcn dasu jalal suka iso masarautar daura..   Sashen gimbiya kilishi ya zarce dan yasan ita kadai ce zayyi wa dadin baki ta shige masa gaba a wajen auren da yake son yi... Hansai ce ta gabatar masa da abinci kala kala... ya tausaya mata sosai dan ganin yarda duk ta rame sbd tunanin juwairiya..    Sai daya ci abinci ya koshi sannan ya maida hankalinsa kan gimbiya kilishi.. Yace Umma mgn nake so muyi dake.. Kilishi ta gyara zaman ta tace ina jinka jalal... Jalal yaja lumfashi kafin yace.. Umma aure nake so na kara..! Kilishi ta tsare shi da ido.. Jalal yace,umma dan Allah ki shige min gaba wajen abba dan ya amince.. Kilishi tace,ban ki ba jalal dan nima nayi tunanin hakan sai dai har yanzu ban samu wacce nake ganin ta kai zama matar ka ba..   Jalal ya shafa gefen fuskarsa.. Umma jiya na hadu da wata a can kasar kano.. Kilishi ta gyara zamanta.. Diyar wacece ita?yar wacce (family)din ce? Jalal(with full confidence)yace.. DIYAR SARKIN KANO ce umma.. Wani irin dadi ne ya lullube kilishi..tace da kyau AMALE haka nake so.. Nidai indai ta ni ne na amince dari bisa dari kuma zanyi kokari na shawo kan mahaifinka kada ka damu..kaji? Jalal yayi murna sosai sannan ya mike ya fice.. Sai daya shiga sashen khadija ya duba jikinta kafin ya fito zuwa sashen sa.. Umayma dake lebe ta ciji yatsa.. Lallai dole ta sanarwa uwar dakin nan wannan zance.. "Sashen sa ya koma cikin tsantsar farin ciki.. Jakadiya ce ta shigo tare da kuyangi dan hada masa ruwan wankan sa..    Ganin yarda yake cikin farin ciki jakadiya ta kasa hkr tace.. Allah ja zamaninka wannan farin ciki da kake ciki Allah yasa ya dore har karshen rayuwar ka.. Jalal yayi dariya amin jakadiya,kema ina da mgn dake ai jakadiya.. Jakadiya ta kalli kuyangin dake fita daga dakin sun gama aikin su.. Tace ranka shi dade ina jin ka.. Jalal ya dawo kusa da ita yana kasa da muryar sa sannan ya fayyace mata komai kamar yarda juwairiya ta sanar mishi.. Jakadiya zubewa tayi kasa dan kafafunta ma kasa daukar ta sukayi.. Yanzu dama diyar sarki ce juwairiya? Lallai idan kama raye zaka sha mamaki.. Jalal yace,jakadiya inaso mu boye wannan sirrin har sai ranar da ta dawo gidan nan a matsayin matata.. Jakadiya ta sake kallon jalal cike da murnar ta,tace ALLAH ya nuna mana wannan ranar AMALE... ************ Juwairiya na sashen ta suna tare da yarimaADO ne yana koyar da ita karatu.. Hanne ce ta shigo ciki tace da ita wai wani mutum na son ganinta yana waje.. Juwairiya cikin mamaki ta mike ta fito.. Ga mugun mamakin ta BABANTA ne ta gani a tsaye.. Ihun murna ta saka taje wajen sa tana fadin.. Baba ashe ka dawo? Se dana tambayeka aka cemin mai martaba ya aike ka can kasar MALI. Babanta juwairiya yayi murmushi yana kare mata kallo dama zuciyarsa sai data bashi juwairiyar suce ake mgn.. Allah mai iko ashe asalinta na nan kasar kano inda yake rayuwa..    Yayi murna kwarai da ganinta a haka.. Juwairiya a take tayi sashen gimbiya amina dashi ta gabatar mata dashi.. Sannan ta saka sarki abu-turab ya yantar dashi.. Zo kuga murna wajen bawan Allah nan.. Washe gari da sassafe kuma ya shirya sai kasar daura wajen yan uwan sa.. ************* "Karshen wata yazo sarki abu-turab da gimbiya amina suna ta shirye shiryen taron zabar mijin juwairiya da za'ayi. ita kuwa tunda aka sanar da ita sai taji wani iri dan kuwa ita ta riga ta san wanda take so ... "Ranar gabatar da taron gimbiya amina da jamila sune gaba wajen shirya juwairiya.. Kai kace wata amarya ce dan ba karamin kyau tayi ba,ga kaya masu tsada da sarkar gwal data sha..     "Kilishi ta shigewa jalal gaba a  wajen abbansa har ya amince da mgnr.. Ranar tafiya kuwa da kansa yace wa jakadiya ta shirya da ita za'a tafi,sannan ya dauki hamza dan a lkcn magaji yayi tafiya tare da waziri baya gari... Lkcn da suka isa kasar kano,masarautar har ta fara cika da yaran sarakuna daga kasashe daban daban.. Jalal kuwa kallonsu kawai yakeyi dan kuwa yasan yayi musu zarra... ya siye zuciyar wacce suka zo neman soyayyar ta.. Abu-turab da kansa ya saka aka shigo da juwairiya cikin Fadar..bayi na biye da ita a baya .. Wajen zama na musamman aka ware mata,jakadiya da su gimbiya amina na gefenta suma.. Lkcn da aka fara kiran sunayen (princes)din juwairiya addu'a kawai takeyi Allah yasa sarki jalal ya zo yau shima..    Duk wanda ya shigo idan jakadiya ta tambayeta se tace ah ah bai mata ba..    Gimbiya amina tadan rankwafo wajenta tace.. Juwairiya ki kwantar da hankalinki ki zabi wanda kika ji ya kwanta miki. Ta gyada kai tana fidda ran zuwan jalal...   "Kamshinsa kawai taji ya daki hancinta.. Ta kurawa kofar shigowa ido.. Ai kuwa sai ga hamza a gaba jalal na bayansa jakadiya na biye dasu a baya..   Wani irin lumfashi ta saki da karfi.. Jalal kuwa kura mata ido yayi ji yake kamar yaje ya dauke ta daga inda take zaune.. Ganin yarda duk mazan dake wajen sai wani faman kallonta suke..     Shamaki na gabatar da sarki jalal jakadiya ta tambayi juwairiya  (opinion ) dinta akan sa.. juwairiya ta saki murmushi sannan ta gyada kanta cike da tsananin kunya.. Ai a take fada ta hau kida aka hau busa algaita..matan bayi na ta ku'da wajen duk ya karade da kide kide.. Sarki abu-turab ya mike cike da kasaita da murna sosai..ya sanarwa jama'arsa shi Sarki abu-turab ya bawa sarkin daura JALALLUDEEN auran diyarsa sarauniya JUWAIRIYA ... Ihu da shewa aka hau yi..    Gimbiya amina ta rungume juwairiya tana murna sosai.. Jalal baki yaki rufuwa zuciyarshi yaji wasai,sai gaisawa ake dashi ana shi murna.. "Da Yamma mai martaba Abu-turab ya saka aka gyara can sashen da karamin falonsa yake dansu juwairiya su kebence su fahimci junansu(date)    Gimbiya jamila taja juwairiya zuwa sashen ta.. Ta shiga bata shawarwari akan yarda ake fitar da lafazi me dadi da kuma yarda mace zata kama kanta a gaban (suitor)dinta.. Ta shiryata cikin kayan alfarma kafin hanne tazo suka fice.. "Juwairiya na kawowa gaban kofar falon jakadiya tayi saurin tarar ta.. Murna sosai sukayi da ganin junan su,juwairiyata rungume jakadiya tana tambayar ta ko ya su ummanta suke.. Jakadiya tace,kowa na nan kalau,ai babanki ma ya dawo.. Juwairiya tayi murmushi tace,nayi kewar su dayawa.. Jakadiya tace,ai kin kusa komawa garesu,yanzu ki shiga ciki yallabai yana jiran ki.. "Lkcn data shiga falon jalal na zaune a saman kujera cushion... Ya dago ya zuba mata ido har ta samu waje itama ta zauna a kujera me fuskantarsa..         Irin fadin farin cikin dake mamaye a cikin zukatansu bata lkc ne..    Jalal yayi gyaran murya.. Ta dago ta kalleshi.. Jitai yace Nagode....juwairiya Tayi murmushi.. Kafin tace itama... Nima haka...ranka ya dade Jalal yayi murmushi.. Kafin ya sake fadin.. Kinyi kyau.. Ta dukar dakai se yayi tace... Kaima haka... Amma kin fi ni ai tunda kika siye zuciyar mazaje dayawa.. juwairiya ta murmusa..batace masa komai ba.. Shiru ne ya ratsa... Se ji tayi yace... Inaso a karshen watan nan ki tare ni a gidana.. juwairiya ta dan waro ido.. Da wuri haka..? Jalal yadan langwabar da kai.. Nayi kokari ai..kinsan tun yaushe na fara mafarkin kasancewa dake ne? juwairiya ta girgiza kai.. sai ka fada ranka ya dade.. Jalal ya daure fuska.. Bana son wannan "ranka shi dade"din fa..a tunani na mun wuce wurin.. Taja lumfashi.. Toh AMALE...... Ya saki murmushi ko ke fa.. Juwairiya tace,ina jinka toh.. Jalal yace tunda nayi gamo da gatar da fuskar ki nake mafarkin samun ki... juwairiya dadi ya lallube ta.. Jalal ya mike cikin takun kasaita ya dawo kusa da ita zai zauna.. juwairiya tayi saurin matsawa tana kallo kofa.. Baka tsoron wani ya ganmu  a haka? Jalal ya zauna yana fadin.. Sai me? juwairiya ta tabe baki.. Ya kamo hannunta ta bishi da kallo.. Zoben sa ne ya gani a babban dan yatsan ta. Mamaki ya kamashi..yace.. Ina kika samo wannan zoben nawa? Tayi dariya tace ka manta? wajen MAI KIFI..? Jalal ya jinjinar dakai yana dariya.. sannan ya cire zoben ya fito da wani a cikin alhujinsa ya saka mata shi..ya sumbaci hannun nata..    Murmushi kawai takeyi.. Jalal ya kalleta.. Yanzu tunda kina da ikon sakawa shiyasa nazo miki dashi.. Tace.. Nagode Ranka..se kuma tayi shiru..tace auuu nagode AMALE .. Jalal yace ni kuma fa me zaki bani? juwairiya ta amshi zoben daya cire mata (nashi) Ta maida masa a yatsansa.. Jalal ya kai hannunsa saitin bakin ta.. Dariya tayi dan ta gano me yake nufi.. Jalal ya langwabar dakai.. Kinsan abunda nake bukata a wajenki.. Juwairiya ta make kafada.. Kafin ta fakaice shi ta mike da sauri tabar falon tana masa dariya.. Murmushi ya sakar kafin ya mike shima yana fadin... Zamu hadu ne yarinya... *"Invitation"* *Ana gayyatar duk fans din rumfar bayi zuwa daurin auren JALAL DA JUWAIRIYA gobe inshaAllahu...*😅😅 TEAM RUMFAR BAYI *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 38 Wattpad @afreey101 *BIKIN MANYA* ************************** ""Lkcn da su sarki jalal suka sauka a kasar daura.. Labari gaba daya ya gama ya'duwa acikin masarautar... Sarki jalal zai kara aure,kuma diyar sarkin kanon dabo ce amaryar tasa.. Labarin babu inda baije ba,da masu murna da kuma masu bakinci duk yakai garesu.. """Umayma na samun wannan danyen lbrn ta garzaya sashen gimbiya surayya da saurinta ta sanar da ita abunda ke wakana.. Wayyo hauka ne kawai surayya batayi ba....Jalal zai karo aure? Duk ta susuce ta birkice a lkc daya.. "Umayma ta kalla da itama din ke taya ta bakin ciki sosai tace, yau na shiga uku!umayma.. idan itama wannan ta shigo ta samu nata cikin ai na gama yawo...kinsan tuni gimbiya kilishi zata saka jalal sakeni! Umayma tace... ni a ganina ranki ya dade wannan malamin tsabbun gsky aikinsa baya wani Ci.. Toh ace tun kwanakin da muka zubawa gimbiya khadija wannan maganin a kofar sashenta amma shiru kake ji ba wani lbr? Ciki ma sai girma yakeyi..   Surayya tace,gskyr kine umayma tunda ga aikin da yayi mana akan wannan baiwar har yanzu babu wani ci gaba a har wajen yariman ma.. Gashi yakumbo tayi tafiya.. Umayma tace,kada ki damu ranki ya dade mu koma can yanzu mu same shi ya fada mana dalilin da ya saka aikin da yake mana baya CI...duk dukiyar da muke bashi.. Ai kuwa shiryawa sukayi suka koma wajen malam na Sandamu.. Yana ganin su ya kwashe da dariya.. Umayma tace, hattara! Malam yace,nasan ai zaku dawo ne.. Surayya tace,ban gane ba?wato da saninka kenan kake mana aiki baya Ci ? Malam ya buga kasa yace,ai abunda yasa aikin ki baya ci sbd wannan asirin ne da kika yiwa wannan baiwar.. Surayya tace ban fahimce ka ba? Malam yace,aljani daya ne kawai yake min aiki a yanzu bazan boye muku ba.. Toh na riga na tura shi da sunanki akan wannan baiwar,dan haka duk aikin da zan basa da sunanki bazai yi sa ba.. Surayya ta gyara zamanta,toh miye abunyi yanzu?dan ina damuwa sosai wlh.. Malam yace,sai mun warware wancan asirin kafin wani aikin Ya yiwu. Umayma ta kalli surayya.. Surayya tace,toh me muke jira?ai tuni na manta da lbrn wannan baiwar malam,tunda ta bace tabar masarautar mu ai ni a yanzu na gama da shafin ta.. Malam yace toh angama.. A take ya warware asirin da sukayi wa juwairiya... Ya sake kallon surayya.. Yanzu me kike so ayi miki? Umayma ta dawo kusa da surayya tace.. Ranki ya dade me kike so ayi yanzu? Surayya tace cike da tsantsar kishi,a hana auren sarki JALAL..    Umayma ta girgiza mata kai,ranki shi dade yanzu ke kenan haka zaki ta zama ba ciki bare goyo? A tunanina haihuwar da kike nema tafi miki komai mahimmanci a wurinki yanzu? Idan amaryar ta shigo basai mu san abunyi ba a lkcn.. yanzu kawai ya taimaka miki kema ki samu naki cikin ko ba haka ba? Surayya ta jinjina kai cike da gamsuwa da shawarar umayma.. sannan ta kalli malam tace.. So nakeyi nima na samu ciki malam,ka taimaka min..dan ni kadai nake so na haifar wa sarki magajin sa.. Malam yace babu damuwa an gama ranki shi dade .. Ya bata wani garin magani yace,kin ga wannan ki samu kiyi amfani dashi kamar sau biyu..zaki dawo kiyi min godiya.. Surayya da umayma murna ta kashe su.. Suka biya malam da dukiya me yawa suka tafi.. "Samira ta kalli turaki.. Yanzu me kake gani zamu iya yiwa yaya jalal na auren sa.. Turaki ya mike daga kwanciyar da yayi.. Ni a tunanina kawai mu hada masa liyafa ta gani ta fada.. Samira tadan muskuta tace ah ah ba wannan ba..ni nafi son muyi masa abun da zai bashi mamaki ko ya kika ce zainaba? Zainaba data buga tagumi ta dago a sanyaye ta kallesu, ni kam bani da wani abun cewa duk abunda kukayi yayi min.. Nafisa ta dafa ta,kanwar mu kamar fa akwai abunda ke damun ki kwanan nan? Hamza ya jaa hancinta yace,ai nafisa ki bar tambayar ta ma.. indai wannan ce yanzu haka fada tayi da wani.. Zainaba ta turo baki,haba ya hamza ni ka maida uwar fada ko? Magaji ya kai wa hamza duka.. Wai me yasa kake matsa wa yar kanwarmu ne? Turaki yace,wai ni fa wlh mamaki nakeyi,wai ya jalal ne da kansa ya samo wacce yake so.... Zainaba tace ai shine,mutum sai shegen girman kai da kasaita,ko fa matan sa naji ance hakuri sukeyi da shi.. Magaji yace, ai wlh dan baku ga wannan yarinyar nan bane ba,ta hadu karshe ne,amma duk da haka nayi mamaki nima dan Amale bai ma tsaya ganin ta ba ko a ina kuma suka hade oho?.. Samira tace,yanzu dai mu koma kan shawarar mu dan inaso idan su goggo Amina sunzo kawo amarya su sha mamaki..ko ba haka bane? Nafisa tace, hakane kam.. amma ke baki san amaryar tamu bane samira?naji ance goggo ce matar sarkin kanon.. Samira ta girgiza kai,gsky ban san taba nima... A haka dai sukayi ta shan fitar su cike da nishadi... "Jalal kuwa tunda ya dawo yake ta faman shirye shiryen sa,sashen dake kusa da na nasa ya saka ake ta faman gyarawa..dan yana so sosai ya burge juwairiyyar tasa..      ******************** *biki ya matso* "Shirye shirye kawai akeyi babu kama hannu yaro... Masarautun biyu duka basu zauna ba.. Ana ta gayyace gayyacen mutane.. Gimbiya kilishi da fulani sune a kan gaba wajen shirya bikin dan kuwa matan sarki kowacce langwabe wa tayi akan basa jin dadin jikinsu.. Khadija kanta taji saukin laulayin cikin nata,amma kishi ne kawai ya sake kwantar da ita dan har a cikin zuciyarta bata so wannan karin auren da yarima yake shirin yi ba. gashi sai rawar jiki yake yi musu ita abun ma tsoro yake bata kada wannan amaryar ta sa ta shigo ta dauke masa hankali daga gare su.. Lallai suna da aiki jaa a gabansu.. *"Masarautar kanon dabo...*       AMMI da sauran yan uwa daga kasar zazzau har sun sauka.. Yan biyu ne tare da juwairiya a can sashen nata inda gimbiya jamila ta dauko mata wata me gyaran jiki daga can kasar chadi tun ana saura sati uku daurin aure.. Gyara dai kam ba'a mgn dan kuwa fatar juwairiya kamar ta jajirai ta koma.. ga maganguna ana ta dirka mata ita har abun ma ya fara fita kanta.. "Ko yanzu ma Ammi ce ta shigo dakin nata da wani tsumin cikin kofi ta mika mata.. Yatsine fuska tayi,ammi tace amsa mana ki shnaye.. juwairiya ta amshi kofin tana fadin.. Wlh ammi na gaji ne da shan wadan nan magagungunan..ga daci wasu ke garesu.. Ammi tayi murmushi,shanye kedai bana son gardama.. Juwairiya ta daga kofin sama ta shanye shi duka tana yastine fuska.. Ammi tace ko ke fa? Yan biyu ne suka dakin tare da yarimaADO..    Ammi tace toj sarakan yawo se yanzu? Hassana tace,kai ammi yarima ne fa yadan fita damu siyayya a waje.. Ammi ta mike zata fice take fadin.. Nidai kada ku riga jan hankalin juwairiya dan bana son tana yawan yawace yawacen nan.. Ammi na fita yan biyu suka haye kan gadon da juwairiya take a zaune.. YarimaADO yace,yaya kinga.. Ya nuna mata wata wasika.. juwairiya tace menene hakan? hussaina tace,wasika ce daga angonki yarinya.. Hassana tace,lallai wannan sarki da iya soyayya yake.. Juwairiya ta saki murmushi..cikin kunya.. Yarima yace,yanzu ya za'ayi kenan yaya?tunda ba karatun kika gama iyawa ba.. Yan biyu suka kwashe da dariya kawai karanta kowa yaji Ado..ai mu iyayenta ne.. Juwairiya tayi saurin mikewa tayi wajen ado ta fisge wasikar daga hannunsa tana boyewa a bayanta... Dariya sosai suka shigayi mata kafin duk suka fice daga dakin.. Juwairiya ta koma ta zauna a gefen gadon tana ji wani irin dadi na ratsa ta..Amalen ta ya aiko mata da wasika?wasikar soyayya.... Ta bude wasikar da sauri ta kura mata ido.. DAGA SARKI JALALLUDEEN zuwa SARAUNIYA JUWAIRIYYA haka ta gani a saman takardai..   Murmushi ta saki,Allah ya sota ta dage wajen koyan karatun ta.. Kwanciya tayi shame shame kan gadon ta shiga karanta wasikar da kyal kyal tana hada(words)din.... Ta dauki kusan awa hudu...tana krnt wasikar.. Sai ga Hanne ta shigo tace,ki fito ranki ya dade me gyaran jiki na jiran ki.. juwairiya ta turo baki,nifa wlh na gaji da wannan gyaran.. Hanne tayi dariya,amma ai baki ga yarda kika canza bane? Taso muje dan Allah.. Da kyal hanne taja ta suka tafi... """"Sarki abu-turab sashe guda ya gyara dan saukar manyan bakinsa.. (ni kuwa ina yan RUMFAR BAYI grp,ko BQ ne ma a tanadar musu😅) An kira mawaka da masu ki'da daga kowane yanki na nigeria, ga yan busa algaita da masu hawan doki sunzo daga kasashe daban daban..    Masarautar kano ta cika ta batse,gobe kawai suke jira...dan shafa fatiha.. Mai martaba sarkin zazzau ma ya shigo da mutanen sa,su khaleed da sauran yaransa... An shirya babbar kilisa a filin hawa... Sannan a cikin gidan kuma mata na can ta hada'hadar KAMUN amarya... "Tunda ga kasar Sudan gimbiya amina tayi odar kayan da juwairiya zata saka a wannan ranar.. Wayyo Allah zanso kuga irin kyau da kwarjinin da juwairiya tayi,tasha gwalagwalai har ta gaji,ga jan lalle da akayi mata ya fito da ita shar...     Wajen KAMU kansa jakadiya ce da kanta da sauran bayin dake masarautar suka gyara shi...gwanin ban sha'awa..    Abinci kam da kayan kwalam ba'a mgn dan sai anci an ture..ga masu gashin nama a gefe an yanka shanu bila adadin,farfesu dai na kowane dabba a kwashi a nan wajen..   A can na hango muku yan Team rumfar bayi groups anja layi wajen rabon abinci... Yan pherty novels anci anko din lace sai baza ido akeyi.. Yan WATTPADIANS kuwa har da su gayyar Sodi irinsu 😅😅 deejaaat,ceecyblack,haliemahtou 530_khadeejat da sauran su.. ,sai ga kuma jama'ar Taskar marubuta suma sun shigo.. Kai waje dai ya cika ya batse da mutane.. Ammi na hango rike da hannun amarya juwairiya,sai PHERTY a dayan gefen(su babbar kawa manya😉)manya.. Wajen da aka tanadar domin ta suka zaunar da ita.. Juwairiya kanta na kasa dan gani takeyi kamar mafarki ne takeyi,wai yau itace zata auri sarki jalal..? Pherty ce ta kamo hannunta.. Juwairiya ta kalleta tace,anty faty se nake ganin kamar mafarki ne nakeyi wlh? Pherty ta girgirza mata kai,ba mafarki kike ba juwairiya ,me yasa bazaki yarda da CANJIN kaddarar da Allah yayi miki bane? Muna bayanki dari bisa dari kada ki damu kinji? Juwairiya ta saki murmushin murna nagode anty faty,sannan ki tayani mika godiyata a wajen anty Afrah,wadan nan bakin da sukazo domin Ni Allah ya biyasu da gidan aljanna.......    ********* A masarautar daura..... An kammala komai da komai.. Jakadiya ta tara su hansai da laure a cikin daki ta warware musu zari da abawa..    Suma ne kawai basuyi ba sbd tsananin mamaki.. Hansai harda kwallar farin ciki.. Shiyasa naga babanta ya dawo da yancinsa?oh shine ko ya sanar min.. Laure tace,amma naji dadi wlh,kice diyarmu zata dawo garemu.. Jakadiya tace,kwarai kuwa zata dawo amma a matsayin matar Sarki jalal..    Wani sabon farin cikine suka sake shiga.. Allah me iko.... Ai gaba daya wani karfi ne yazo musu suka ci gaba da shirye shiryen da aka saka su na tarbar bakin gobe... """Gimbiya kilishi da fulani ne tsohon sarki Abdul-Jabbar yayi kiran su. Yace,ina son gobe zainaba,turaki da matarsa sannan da magaji suka bi mu zuwa daurin auren  can kanon.. Fulani tace hakan ma yayi.. Gimbiya kilishi tace,nafisa da hamza se su tsaya a nan dan tayamu tarar bakin kenan?. Abba ya jinjina kai.. Eh haka za'ayi... "Umayma ce ta kalli surayya,ranki ya dade ya jikin naki? Surayya ta dake dafe da cikinta tace,anya kuwa wannan maganin na malam bazai kashe ni ba umayma?. Kinji azabar da nake sha kuwa?cikina tun jiya ko barcin kirki ban samu ba.. Umayma ta girgiza kai,kici gaba da daurewa uwar dakina..   Surayya zatayi mgn sai ji sukayi ana sanar da shigowar jalal.... Ai da sauri surayya ta lulluba bargo a kanta tana wani sakin lumfashi kamar wata me shan jiki sosai da sosai din na..   Jalal ya shigo ciki umayma ta gaishe shi ta fice.. Ya zauna a gefen gado yana kurawa surayya ido.. Ya jikin naki? Ta bude ido ta kalleshi cike da kissa tace,da sauki sarkina ya shirin bikin kuma? Jalal ya jinjina kai,muna tayi,yanzu ma nazo ne nayi miki sallama dan gobe da sassafe zamu tafi can kanon.. Surayya kamar ta fasa ihu.. Amma ta daure.. Ai da ace lfy ta kalau da dani za'aje na dauko kanwata.. Jalal ya saki murmushi har cikin zuciyarsa yana tausayawa matansa,tunda aka fara mgnr aurensa duk suka kwanta ciwo.... Ya mike yana ajiye mata wani kulli.. Ga wannan sarka ce ta gwal da na siya muku keda khadija na cin biki.. Surayya ta washe baki,mun gode sarkina Allah ya dawo mana daku lfy.. Ya duka ya sumbaci goshinta,nagode sosai surayya....sannan ya fice tani bayan sa da kallon takaici.. *RANA BATA KARYA*** Masarautar kano ta cika ta batse da mutane daga kowane lungu da sa'ko na nigeria...       Sarki abu-turab ba karamin farin ciki yake ciki ba zai aurar da diyarsa.. Karfe sha daya na safe sai ga yan DAURA..sun dira.. Tsohon sarki Abdul-Jabbar suka hade da mai martaba sarkin zazzau fira ta dinke a tsakanin su.. Su Jalal kuwa sarki abu-turab ya saka yarimaADO da shamaki su kaisu can masaukin su dan hutawa kafin lkcn daurin auren yayi.. Su zainaba kuwa samira ce taja su zuwa cikin gidan nan dan ita kam masarautar ba bakuwar ta bace ba... Suna shiga sashen gimbiya amina samira ta fa'da jikinta cike da murna.. Amina ta dago ta,ashe har kun iso? Samira tace,goggo wai ina su Ammi ne? Amina tace suna can sashen yar uwar taki. Zainaba ta duka ta gaishe da amina.. Amina tace,sannunki da zuwa yan mata ku karasa can din mana bari na saka a kaiku.. Ai kuwa gimbiya amina ta saka wata baiwa ta kaisu can sashen juwairiya..    Suna shiga a falo suka iske yan biyu da firdausi suna ta hidimar su..    Samira na yin sallama yan biyu suka mike cike da murnar ganinta suka rungume ta.. Zainaba kuwa da kallo take binsu,ita addu'ar ta daya Allah yasa ta hadu Mustapha taji dalilin da ya saka ya daina aiko mata da wasikun sa..     Gabanta ne ya yanke ya fadi.. Ganin juwairiya ta fito tare da ammi daga wata kofa... Ware ido tayi tana tsananin mamaki sosai.. Wuce su samira tayi da gudu taje ta rungume juwairiya tana kuka sosai..   Juwairiya kanta sai data tsorata da ganin zainaba.. Amma jin zainaba a jikinta tana kuka sai ta shiga shafa mata baya.. Samira kuwa mutuwar tsaye tayi.. Ammi ce tazo ta riko hannun tana fadin saukar yaushe? .. Juwairiya tasa hannu ta dago zainaba suna kallon junansu.. Tace,haba uwar dakina wannan kuka haka? Zainaba takai mata duka,ai nayi fushi dake.. Ammi ta jawo hannun zainaba din itama ta shige dasu daki ta fayyace musu komai. Murna sosai sukayi. Da saurinsu suka fito falon suka sake rungume juwairiya suna taya ta murna.. Zainaba tace,ni dama na zargi ya jalal wlh,ace farat daya mutum ya canza?ta kalli samira.. sai fa kinga yarda ya tsane ta a baya ,amma lkc guda ya koma me taimakon ta ya dauke min ita daga sashena.. Hassana tayi dariya,ke baki san soyayya ake ta sha ba? Zainaba tace ina kuwa zan sani?dan na lura ita juwairiyar ma bata dauke ni a matsayin kawar taba.. Juwairiya tayi murmushi tana sake rungume ta.. Haba kawalli ta,kinsan fa a duniyar bani da kamar ki.. Duk suka saka dariya... "Magaji ne ya kalli jalal da bayi ke ta faman shiryasa..cikin kayan sa na alfarma.. AMALE ka fada min gsky mana?kasan dai baka da kamar ni ko? Jalal ya juyo yana kallonsa.. Wace gaskiyar kika son ji ne Anaci? Magaji ya zauna a kusa dashi.. Ni na san ranar hawan nan baka tsaya ganin diyar sarki abu-turab ba,toh a ina ka hadu da ita har kuka kulla soyayya haka? Jalal ya kwashe da dariya.. Kai fa ka cika tambayar tsiya kamar wani alkali.. Toh bari kaji in fada maka....... A nan jalal ya kwashe komai ya fadawa magaji.. Magaji ya dafe kirjinsa.. Kai amma kayiwa maza dayawa shigar sauri.. Wato a yarda nake ganin ka saida kaji saida kaji.. Jalal ya amshe..toh saida rakum'ma ne ni...fadi da kyau..! Magaji yace,ahh lallai...wlh ni kaina naso wannan yarinyar a baya.. Jalal ya daure fuska,yace.. hattara dai magaji mallakin  AMALE ce.. Magaji ya daga hannu cikin surrender yace,ai na dade da janyewa ma... Su Turaki ne ya shigo tare da khaleed.. Turaki Ya kallesu.. Wai har yanzu ango bai gama shirin nasa bane?jama'a na waje suna jira.. Magaji yace kasan fa yau AMALE jin sa yake kamar wanda akayi wa albishir da aljanna, gayunsa ma na daban ne Yau!    Khaleed yayi dariya..yace Kuma duk diyata ce sanadi ba.. Turaki yace ban gane ba? Khaleed yace ai bazaka gane bane abokina muje na warware maka kan zaren.. Yaja turaki suka fice... "Karfe biyu da zabi na ranar JUMA'A  ASHIRIN DA TARA GA WATAN DISAMBA.. Aka daura auren SARKI JALALLUDEEN ABDUL-JABBAR,da kuma amaryar sa SARAUNIYA JUWAIRIYYA ABU-TURAB..akan sadaki mai tsokar gaske............ @TEAM RUMFAR BAYI... _Godiya ta musamman ga duk wacce ta samu halartar wannan bikin.. Kada ku damu akwai sauran event idan mun koma can masarautar Daura.. Dan haka ku ci gaba da kasancewa da ni AFRAH bhai.._ XOXO😘😘😘 *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 39 Wattpad @afreey101 ********************** ""Bayan an gama daura aure sai kuma aka fara shirin daukar amarya zuwa can masarautar daura .. Gimbiya amina ce ta kai juwairiya har sashen sarki abu-turab abbanta yayi mata nasiha mai ratsa jiki sosai.. Duk da ba wani shakuwa ce mai karfi ta shiga tsakanin su ba amma sai da juwairiya ta zubar da kwalla sbd tasan sai tayi kewar mahaifin nata sosai.. Daga wajen sarki sai kuma akayi da ita akayi sashen gimbiya jamila itama tayi mata nata fadan sannan ta bata kyautuka masu yawa.. daga nan gimbiya amina ta maida ita sashen ta don shirya ta kafin tafiyarsu.. Su zainaba ne akan gaba wajen zolayar ta.. Sun saka ta a gaba suna ta gulmar sarki jalal wai ance tunda aka daura aure bakinsa yaki rufuwa.. Ita dai amarya tunanin irin rayuwar da zatayi a can masarautar daura kawai takeyi...ya zasu dauke ta?bare surayya data nuna tsanarta karara..kila gara ma khadija,ooh ita dai ta shige su,wata zuciyar tace,kema fa idan kin koma a matsayin matar mijinsu kike ba baiwarsu ba... "An shiryata tsab a cikin leshi me shegen tsada kalar light blue da peach,sannan aka rufa mata alkyabba ta ga'do wacce ake kai duk amaryar data fito daga cikin tsatson masarautar kano..    "Wayyo Zanso kuga gogan naku,wato sarki jalal..kenan.. Gaba daya murna da farin ciki sunyi masa yawa.. Yau dai Allah ya mallaka rabin ransa,ya basa farin cikin rayuwar sa... Baki yaki rufuwa magaji na gefen sa sai zuba masa ruwan zolaya yakeyi amma ko a jikinsa.. Shidai hamdala kawai yakeyi wa Allah..        "An kawo motocin daukar amarya a nan sarki abu-turab ya zabi mutanen da zasu tafi kai ta.. G-amina ce tare da jakadiya,se hanne baiwarta da kuma AMMI,da yan uwa da suka zo daga kasar zazzau.. Dan shi kam Baya son yawan jama'a kada ace can a samu wata matsalar. """""Kuka sosai juwairiya tasha ganin an fito da ita daga cikin masarautar su ga bayi nan a bayansu sai wakar al'ada sukeyi na daukar amarya..(suna mata bankwana kenan)   Hanne kuwa murna kashe ta zata bi uwar dakin ta.. Zainaba dasu samira kuwa sunyi murna juwairiya zata koma garesu.. "Lkcn da suka fito dangin jalal na waje harma da abbansa.. A nan aka shiga motoci liman yayi musu addu'a aka dau hanyar DAURA... ************** Lkcn da suka isa masarautar daura yamma tayi sosai..      Hamza da nafisa tare dasu fulani da gimbiya kilishi ne suka tare su cikin girgimawa.. Juwairiya babu abunda gabanta yakeyi sai faduwa,tana kunshe acikin alkyabba gimbiya amina  da ammi na rike da ita..   Nan aka hau gaishe gaishe gimbiya kilishi ta hada su da jakadiya tace ba sai an kai amarya sashen ta ba,kawai su huce can sashen amaryar dan su samu hutawa sosai kafin anjima.. "Kilishi na barin wajen ta jawo hansai dake ta leken ko zata ga fuskar diyarta.. Sashen khadija sukaje dan kuwa kilishi ta fara jin haushin rainin hankalin da suke son suyi musu..    A hakimce ta tarar da ita tiren kayan kwalam a gabanta.. Rabi na gefe tana ji kamar tayi tsuntsuwa taje wajen tarar su amaryar da akeyi,dan tasan zata kwashi kallo bare ance diyar sarkin kano ce...wai!yanzu se de taji lbr a RUMFAR BAYI kenan?      Kilishi ta kalli khadija rai a bace.. Khadija ta mike da sauri tana fadin.. Umma sannu da shigowa.. Kilishi tace,rike sannunki..haka ake rashin lfyr dama?ni dama na zargi wani abu wlh.. Khadija tayi saurin sadda kai kasa tace,sauki na samu ne yau umma.. Kilishi tace,shine baki fito tarar bakin ba? Ko duk haukan kishin naku ne haka? Kuke son ku jawo mana wani sabon raini daga wajen mutanen nan.. Khadija tace,kiyi hakuri umma zanje yanzu nayi musu sannu.. Kilishi taja tsaki tayi gaba a fusace... Sashen surayya ta sake nufa.. Surayya tasha gayunta ta cancare dan tunda ta tashi yau ciwon cikin da take faman ya ragu.. Ita kam ta riga tayi wa kanta fada.. Sam ba zata taba bari jalal ya gano halinta ba. zata nuna masa har cikin ranta tana son wannan auren nashi da yayi.. tayi murmushin mugunta  (ni kuwa nace manipulator kawai😂)      Umayma ce ta shigo dakin a rikice tace,ki fito ranki ya dade gimbiya kilishi ta shigo.. Surayya taja tsaki,ai nasan sai anyi haka tunda wannan yarinyar  (khadija) tayi irin nata rashin yawon nakin zuwa tarar su.. Ai gashi nan ta jawo mana..    Fitowa tayi kawai da masifa kamar gaske..tana fadin.. Umayma ba sai dana ce miki idan sun iso kizo ki sanar min na fito bane? Kilishi ta kalleta,ke yanzu har kin shirya amma fitowar ta gagare ki? Surayya tayi fuskar tausayi.. Allah umma se da nace a sanar min ba gashi har shiri nayi ba,Ashe ma har sun iso?.. Kilishi taja dogon tsaki ban sani ba... ta juya cike da takaici ta fice hansai ma girgiza kai tayi itama dan sun san duk karya ta shirya indai surayya ce (fake) Suna fita surayya taja tsaki,dan ma rainin wayo ni suke tsanmanin na je na taro kishiya ta mtsww...ai bazai sa'bo bane...! ******************** An gabatar musu abinci me rai da lafiya.. G-amina ta saka hanne ta diba wani a cikin dan kwano sannan ta amsa ta shiga uwar da'ka inda su juwairiya suke.. Gaba daya hankalinta baya wajen,ko firar dasu yan biyu suke tayi ba jinsu takeyi ba.. Ita dai a yanzu abubuwa dayawa ne acikin zuciyarta.. Ya zatayi rayuwa tare da jalal a matsayin matarsa? Ya zatayi rayuwa da matansa..? Ya kuma gimbiya kilishi zata dauke ta? Sannan ga son ganin su ummata da takeyi..   Dafa ta da gimbiya amina tayi ne yasa tayi firgigit ta dago ta kalleta.. Zama tayi a kusa da ita tace.. Ki rage wannan tunanin juwairiya, addu'a da dogaro da Allah shine kawai ya kamata ki saka a gaba.. Zan baki wasu addu’o'i da zaki ringa yi sbd tsari,nasan rayuwa acikin GIDAN SARAUTA ba karamin hadari bane idan baka tashi tsaye wajen rokon Allah ba..balle ke mai kishiyoyi da har suka ki zuwa tarbar ki.. Juwairiya ta gyada kai tace nagode sosai..umma sai dai inaso dan Allah ki saka a kira min su ummana na nan,inaso na gansu... Gimbiya amina tace toh shikenan dama mahaifinki ya bada sako a basu sbd nuna godiya ga rikon da sukayi miki... Gimbiya amina na fita daga dakin ta samu jakadiya ta wajensu knan tace taje ta samu jakadiya ta masarautar daura ta fada mata suna son ganin iyayen juwairiya..     Ba'ayi minti sha biyar ba sai gasu sun shigo sashen...    Juwairiya dake cikin daki ta fito da gudunta.. Sumewa ne kawai hansai,da laure basuyi ba.. Baki bude suke kallonta cike da mamakin canzawarta.. Juwairiya ta fada jikinsu tana kuka sosai.. Hansai ta shiga lallashinta hakama laure.. Ammi da gimbiya amina sukayi musu godiya sosai.. Sannan suka basu dukiya me tarin yawa daga sarki abu-turab.. Da kyal juwairiya ta saka suka amsa.. Gimbiya amina ta sake yi musu albishir akan gobe mai martaba tsohon sarki Abdul-Jabbar yace zai yantar dasu sbd dai mai martaba na zazzau ya fada masa komai akan juwairiya... 'Bayan an gama hutawa ne sai kuma aka shiga shiryawa dan gabatar da babbar liyafa dasu gimbiya kilishi suka hada musu...      Juwairiya ta sha gayu kamar ba gobe,ta haska iya haskuwa.. Kayane Ammi da kanta ta saka ayi mata na musamman..    Samira,zainaba da yan biyu sune a kan gaba wajen shigowa da amarya... Ango jalal yasha gayunsa shima sai daukar ido yakeyi...cikin manyan kala na alfarma ga fuskar nan tayi shar sai sakin murmushi yakeyi,su turaki na zolayarsa.. Ga kuma khadija da surayya a can kusa da gefensa kowacce sai cika take tana batsewa..abun duniya ya taru yayi musu yawa amma babu halin nunawa..     Gimbiya amina ce ta karaso wajen rike da hannun juwairiya fuskarta na rufe acikin babban mayafi me kyan gaske.. A kusa da jalal gimbiya amina ta zaunar da ita tana rada mata wani abu a kunnne.. Kamshinta ne ya daki hancinsa ya lumshe ido yana jin wani farin na mamaye shi.. Juwairiya kam addu'a kawai takeyi acikin ranta..tasan idan har fuskar ta bayyana mutane dayawa zasu girgiza.. Sai jin dumin hannun jalal tayi a cikin nata.. Taja lumfashi.. Yadan kai kansa kusa da ita kadan.. Yace.. Ki kwantar da hankalinki GIWAR AMALE sarki jalal na tare dake.. Ji tayi wani karfi yazo mata.. Ta sauke lumfashi mai nauyi.. A tare duk suka saki murmushi..       Fulani ce ta mike tace,a bude mana fuskar sabowar diyarmu mu kanta..   Zainaba tayi saurin fadin.. Ah ah umma se kun bamu kudin budar kai ko ya kukace?ta kalli nafisa da samira... Samira tace,hakane kam se an biya mu zamu bude fuskar amaryarmu. Yan biyu suka dawo kusa da juwairiya da jalal sukace.. Sarki muna jiran kyauta me tsoka daga gareka..    Surayya ta tabe baki,umayma tayi mata rada a kunne,uwar dakina naji fa ana ta yaba kyawun wannan amaryar.. Surayya taja tsaki,toh sai me?nima ai kyakkyawar ce.. Ta banka mata harara.. Khadija dake gefe ta tabe baki.. Ita dai ta yanke shawarar duk wata kisisina se tayi ta dan samun soyyayar mijinta baza ta zauna wata amarya ta kwace mata shi ba,duk irin shekarun da tayi tana kaunarsa.. "Gimbiya kilishi cikin kasaita ta kalli jakadiya tace,a basu duk iya adadin azurfar da suke so.. Shewa suka hau yi.. Ammi ta karasa ta ya yaye lullubin dake kan juwairiya.... Faduwar gaba ce ya ziyarci gaba daya mutanen dake wajen... Menene haka suke gani? Ya akayi BAIWAR RUMFAR BAYI juwairiya ta koma diyar sarkin kano kuma matar sarkin su JALAL.. Ina TABON nata yake.. Ya akayi fuskarta babu wannan konewar...????????? (So many questions in different minds)    Umayma ta ware ido cikin mugun mamaki tace.. Ranki ya dade ta nuna mata gefen da juwairiya take.. Surayya tayi saurin mikewa tana jin zuciyarta kamar zata tsaga kirjinta ta fito waje..      Meye haka take gani? Dama wannan baiwar ce jalal ya auro.? Ya akayi hakan ta faru..? Ina tabon fuskarta yake?inaaaaaaaa Taji lumfashin ta na niyyar daukewa.. Taya akayi kaskantacciyar baiwar can ta zama diyar wani sarki?     Zufa ta shiga keto mata... Umayma ce tayi saurin zuwa ta kamo hannunta.. ta fakaici idon mutane ta fice da ita da sauri daga wajen dan kada tayi musu(creating scene)a wajen.... Jalal kuwa da juwairiya kallon juna sukayi..suna aikawa junansu sakon soyayya.. Gimbiya kilishi da fulani suka kalli juna cikin al'ajabi sosai.. Ammi na ganin halin da suka shiga sai ta nemi yin mgn dasu.. Gefe suka koma da gimbiya amina.. sannan cikin nutsuwa suka sanar dasu duk abunda ya faru.. Gaba dayansu sunyi mamaki sosai. Wai jinin sarauta ce tayi bauta a karkashinsu.. Gimbiya kilishi ta jinjina mgnr sosai amma tunda dai har juwairiya jinin SARAUTA ce da sauki sosai... "Ansha liyafa an gama lafiya, su magaji an gwangwaje hakama hamza da su zainaba abun dai ba'a magana... Taro ya tashi lafiya kowa ya koma makwancinsa dan sauke gajiya...   ************ Umayma ta dauko ruwa ta bawa surayya da sauri ganin yarda take fitar da lumfashi da kyar kyar uwar dakina ki kwantar da hankalinki..kada mutane su ga'no me muke ciki har asirinmu ya tuno.. Surayya ta zube kasa tana rusa kuka..tana fadin.. Ni jalal zai yiwa haka? Ace ya auro baiwar da nafi tsana a duk rayuwata a matsayin kishiyata? Umayma bazan taba yarda ba ta mike da sauri tayi waje.. Umayma tabi bayanta da gudu tana fadin innalillahi... "Jalal a gajiye yake sosai,yana shiga sashensa yayi wanka ya haye kan gadonsa.. Ba karamin kagara yake yi ba gobe tayi.. ya ganshi tare da amaryarsa juwairiya..ya jawo filo ya rungume.. Ji yayi kawai an banko kofar dakinsa an shigo.. Yayi saurin mikewa yana kallonta da mamaki.. Kamar wata zararriya.. Tayi kansa tana kukan bakin ciki.. Ta rirrike rigar dake jikinsa.. Yanzu ni zaka wulakanta jalal! Ka auro wannan baiwar a matsayin kishiyata bacin kasan yarda na tsane ta.. Kasan BANA SONTA bana son ganinta!!!!.. Jalal ya ture ta daga jikinsa.. Bakya sonta?ya fada cike da takaici.. toh ni INASON TA KUMA INASON kasancewa da ita a tare dani..!!!! Surayya ta mike cikin mugun fusata tace..    Sbd wata baiwar banza ka ture ni haka jalal? Jalal ya dawo inda take zaune a kasa ya nuna ta da yatsansa.. Kada ki kara kiran matata da sunan BAIWA..daga yau sunanta..GIWAR AMALE...gara ma ki koyi fadar hakan daga yau...Gimbiya surayya.. Sannan Ko baki lbrn diyar wacece ita ne? Yayi murmushin gefen lebe.. Diyar sarki take jikanyar sarki.. Ya koma kan gado ya zauna..kuma matar sarki daga yau din nan... Ya daura kafarsa daya kan daya.. Sannan ya fayyace mata asalin juwairiya..dalla dalla.. Surayya taji kamar ta nutsea wajen.. Zuciyarta tayi wani irin zafi... Diyar sarkin kano ce dama wannan yarinyar? Yau ta shiga uku ta lalace,yanzu miye abunyi?ya zatayi? Muryar jalal ce ta katse mata tunanin da takeyi.. Jitai yace da kakkausar murya.. "zaki iya tafiya............ Jiki a sanyaye surayya ta fice daga dakin...tana tafiya kamar zata fadi dan gaba daya bata ganin gabanta.. _Sorry kunji shiru yau. Bana dan jin dadi ne.._ _😘to my big fan data aiko min da credit(katin waya),I LOV U so much.. Afrah na godiya sosai..Allah yabar zumunci da kauna..._ Team RUMFAR BAYI   *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 40 Wattpad @afreey101 ******************* "Washe gari.." "A babban falon tsohon sarki Abdul-Jabbar duk aka hallara dan damka musu amanar amarya juwairiya..    Tsohon sarki yayi godiya sosai sannan ya saka ayi masa kiran hansai da laure ...    Suna shigowa falon a take ya cika alkawarin da ya daukarwa mai martaba sarkin zazzau...wato ya YANTAR dasu kenan.. Zo kuga murna a wajen juwairiya da ma sauran bayi...jakadiya sai taya su murna takeyi...hansai da laure kam ji suke tamkar mafarkine sukeyi...     Fulani da gimbiya kilishi sunyi murna suma sosai saidai ba karamin rashin bayin nasu zasuyi ba sbd dai an dade tare..   Lkcn da akazo rakiyar su Ammi.. Hansai ta tabbatar musu da cewa ba zata bar juwairiya ita kadai a masarautar nan ba,zata zauna tare da ita dan ta kula da diyarta.. Laure ma tace itama bazata bar juwairiya ba zasu kula da diyar su sannan zasu fara kasuwanci dan tallafawa rayuwarsu..   Sosai ammi da gimbiya amina sukaji dadin kalamansu dan dama suma damuwarsu yarda juwairiya zatayi rayuwa acikin masarautar sukeyi Sukayi masu godiya sosai kafin suka hau hanya.. "A sashen sarauniya JUWAIRIYA kuwa,hanne ce da zainaba zaune suna ta shan firarsu.. Hansai da laure suka shigo suna gu'da sosai suna rawa cike da farin ciki.. Juwairiya tayi dariya dan ta san yarda sukeji yau sun samu YAN'CINSU..    Rabi ce shiga lekowa tana komawa.. Tunda taji lbrn juwairiyya ce matar da jalal ya aura take ta son tazo ta ganta.... zabba'u dake zaune a bakin kofar ta hangota ta mike tana fadin.. Ki shigo mana rabi.. Rabi ta shigo ta zube gaban juwairiya tana kwasar gaisuwa..   Juwairiya tayi murmushi tace.. haba rabi nifa ce juwairiyar da kika sani a baya kawarki.. Rabi tace kai amma na tayaki murna sosai ranki ya dade, kingan ki kuwa?kamar ba juwairiyar mu ta RUMFAR BAYI ba.. Gaba dauansu suka kwashe da dariya....... "Da yamma kuwa sai ga jakadiya ta shigo da sakon kilishi akan a shirya juwairiya dan yau kwanan sashen AMALE zatayi.. Jiki na rawa su hansai suka shiga shiryata.. Wanka sukayi mata cikin madara kamar yarda al'adar su take.. Aka turare ta ga mayuka kamsu sanyin kamshi an shafe ta dasu.. Samira da zainaba suka gyare mata gashinta sai santsi da kamshi yake.. laure kuwa murna takeyi sosai yau zata tsantsara wa diyarta kwalliya ba wannan TABOn a fuskata .. "Sosai suka gyara juwairiya ta fito amaryar ta kyau kam ba'a mgn.. Dan har daukar ido takeyi😉.. Zainaba,samira da nafisa tare da jakadiya ne suka kai ta har sashen jalal.. Har cikin makeken dakinsa suka shiga. Mamaki ne ya rufe juwairiya ganin da tayi kamar ba dakin data sani bane,.. Yasha gyara sosai da furenni (flowers) masu kamshi ga fitilu an kunna ko ina ya dau haske..    Zainaba tace yadai Giwar Amale munyi kokari ko kuwa? juwairiya ta juyo tana musu kallon mamaki.. Samira da nafisa suka tafa suna dariya..   Jakadiya ta zaunar da ita kan gadon sannan ta kalli su zainaba tace.. Toh Ku Muje dan nasan duk inda mai martaba yake yana gab da shigowa..    Zainaba ta rungume juwairiya tana rada mata wani abu a kunne.. Juwairiya ta waro ido tana kai mata dukan wasa... Da gudu duk suka fice daga dakin suna mata dariya.. "Ta zauna shiru tana kare wa dakin kallo.. Wai fa nan Dakin da take shigowa gyara ne... yau gata a cikinsa a matsayin matar me dakin.. Taja lumfashi tana shakar kamshi me sanyin dadin dake mamaye da dakin.. Ji tayi kamar ana shirin shigowa dakin.. Tayi saurin hayewa kan gadon ta gyara zamanta tana lullubawa kanta mayafi... "Jalal kuwa dama ya matsu sosai ya dawo sashen sa dan kuwa yasan amaryar tasa na can na jiran sa..    Cikin takun kasaitarsa ya shigo dakin.. Ya hangota can a zaune kanta a duke.. Wani irin murmushi ya saki sannan ya karasa ya zauna a kusa da ita.. juwairiya na jin ya zauna a kusa da ita taji gabanta yadan fadi.. Jalal yace.. Giwar amale ba zaki bude min fuskar taki na gani bane?ko sai na sake biya ne? juwairiya tayi murmushi bata ce masa komai ba.. Jalal yabi hannayenta da kallo sunsha jan lalle ga zoben daya bata yayi das' a yatsanta sai kuma awarwaron azurfa data saka.. Ba karamin burge shi hannun nata yayi ba.. Ji tayi kawai ya kamo hannunta....ya murza dan karamin yatsanta sannan ya saka dayan hannun nasa ya yaye lullubin daga kanta yana karewa kyakkyawa fuskarta kallo..     Juwairiya ta dago suka hada ido dashi.. Wani irin abune sukaji ziyarci gaba daya zuciyoyin su...    Jalal ya lumshe lulu eyes dinsa yace..    Ina gode wa Allah daya bani ikon mallakar ki Giwata.. Juwairiya ta sakar masa murmushi.. Ya saki hannunta ya shafa gefen fuskar ta... juwairiya taji wani irin yaarrr a gaba daya jikinta... jin dumin hannunsa a kan fatar fuskarta.. Jalal yace.. Kinyi shiru ko har an fara mulkin ne? juwairiya ta girgiza kai tana murmushi.. Jalal yace toh tashi muyi nafila ranki ya dade.. Juwairiya ta kalleshi tace a sanyaye.. Ai nayi sallah ni.. Jalal yace,ai na sani,umurni ne nake baki,ki tashi kiyi alwala.. Juwairiya tadan turo baki kafin ta mike ta shige ban dakinsa.. Jalal yabi ta da kallo yana murmushin cike da farin ciki mallakar ta...     "Sai da sukayi nafila raka'a biyu kafin nan jalal ya shiga yi mata tambayoyi akan addini.. Yayi mamaki sosai da iliminta dan kuwa yasan irin rayuwar tayi a baya ta BAUTA...      Gani tayi jalal ya shiga cire kayan dake jikinsa.... Tayi saurin dauke idonta daga gefen da yake zuciyarta na bugawa.. Me kuma yake shirin yi haka? Jalal na lura da ita yayi murmushi kawai ya shige ban daki abunsa.. Lkcn da ya fito har juwairiya ta fara gyangyadi a saman dardumar da sukayi sallar..    Ya dan girgiza kai.. Kafin ya karasa wajenta ya duka yana kare wa fuskarta kallo.. Kai yarinyar nan akwai kyawu yaji zuciyarsa na kyasa masa kyaun matar tasa...    Idanuwansa ne suka sauka akan(dusty pink lips)dinta..yawu ya hade kut.. Ya maida kallonsa kan wuyanta,sarkar dake jikanta ya cire a hankali..ganin zatayi mata nauyi.. Ya ajiye sarkar a gefe sannan ya dawo ya zauna a gabanta yana ta kare mata kallo.. Can dai ya dan mike ya gama shirin kwanciyarsa tsab sannan ya sake dawowa inda take.. A wannan lkcn barci ne me karfi ya fizge ta..    Yasa hannu ya dauke ta tamkar jaririya ya ajiyeta a kan gadonsa.. Ya kalli kayan dake jikinta leshi ne mai nauyin gaske..    A hankali ya shiga zare zanin dake jikinta..yana jin bugun zuciyarsa yana linkuwa..    Yana zare zanin dan siket dinta na ciki ya bayyana fari tas dashi.... Wani juyi tayi..cike da jin dadin barcin da takeyi.. Caraf idanun jalal suka sauka a kan santala santalan cinyoyinta.... Ya dafe kirjinsa yana jan lumfashi.. Bai taba tsanmanin haka yarinyar take ba.. Kodan yana sonta sosai ne? shiyasa surarta ke neman rikitar dashi haka? Ya dawo kan rigar ta..   Yadan dago da ita yana shirin cire rigar sai gani yayi kawai ta farka sun hada ido..    Waro ido tayi tana kallonsa cike da mamaki.. Jalal yaja baya da sauri.. Juwairiya ta shiga neman jawo zaninta.. Jalal ya sake dawowa kusa da ita.. Batayi tsanmanin ba sai ji tayi kawai ya rungume ta tsam ajikinsa.. Yana sauke lumfashi ya shiga mata rada a kunne... Jatai yace...        Na dade ina mafarkin wannan ranar tare dake.. Kada kiyi min gardama dan Allah.. Ki taimaka min Giwar amale.. Ki mallaka wa amalen ki kanki a wannan daren... Juwairiya ta rasa me zata ce dashi dan gaba daya ma kunya ce ta rufe ta.. Ta sunne kanta a kirjinsa.. Jalal ya murmusa kafin ya saka hannu ya dago da fuskarta.. Yana kallon cikin idanunta.. Sai ji tayi ya hade bakinsa da nata... Sumbatar ta kawai yakeyi cikin salonsa... Ni kuwa afrah nace... Su AMALE manya...asha amarci lafiya ni nayi gaba💃 *************** "Lkcn da safiya zatayi gaba daya juwairiya ta gama galabaita.. Dan ko motsi bata iya yi.. Jalal kuwa duk ya rikice ganin halin da take ciki.. Ya rasa me zayyi dan taimake ta.. Fita yayi waje ya samu wata kuyanga dan jakadiya bata ma zo ba lkcn.. Yace taje tayi masa kiran jakadiya a cikin RUMFAR BAYI... Lkcn da jakadiya ta iso sashen ba karamin murna tayi ba..   Ta kalli jalal tace... ka kwantar da hankalinka ranka shi dade,GIWAR ka zata samu lafiya da izinin Allah..   Jakadiya ta fita ta sake dawowa tare da laure.. Sannan ta dauke zanin gadon da suka cire akan shinfidar sarki jalal tayi waje da gudun ta...cike da tsananin murna.. "Lkcn da jakadiya zata shiga sashen gimbiya kilishi.. Umayma ta hango ta tana ta buga sauri kamar zata tashi sama.. Da sauri itama tabi bayanta jiki na rawa...dan kwaso ruhoto.. Jakadiya kam na shiga sashen falon kilishi ta bayyana mata wannan zanin gadon... Kilishi tayi murna sosai tana jinjinar da kai cike da gamsuwa ..sannan ta bawa jakadiya tukwici mai yawa..    Umayma ce ta jawo wata baiwa data fito daga cikin falon kilishi.. Ta tambayeta ko me jakadiya tazo yi wajen gimbiya kilishi..ta ganta tana ta sauri...ko lafiya? Baiwar na murmushin murna ta sanarwa umayma komai.. Gaban umayma ne ya fadi.. Ta dafe kirjinta da sauri.. Yanzu juwairiyar da suke kwana su tashi acikin RUMFAR BAYI a tare itace ta ha'da shinfida da sarki JALAL..?   Kishi da bakin ciki ne sosai ya kamata,ta karasa sashen surayya da saurin ta.. ta fada abunda ya faru.. Surayya dake zaune kamar an dasa ta gun taji wani irin haushi da kishi sun tsaya mata a wuya.. Taja tsaki...kawai batace komai ba... *********** Hansai da laure ne suka kula da juwairiya har dai jikinta yayi dan sauki..ta warware sosai.. Gimbiya kilishi ce ta aiko du'bu da kanta dan a kawo wa juwairiya farfesun naman shanu dayaji kayan yaji sai kamshi yakeyi.. juwairiya batayi mamaki ba dan tasan gimbiya kilishi indai ka cika (expectations)dinta toh zatayi dakai sosai.. Fulani diyya ma ba'a barta a baya ba,dan wasu takalma masu shegen kyau na asalin fata ta aiko mata dasu.. Khadija kuwa zainaba ce taje har sashenta ta kuma bata lbrn juwairiya kamar yarda taji itama.. Al'ajabi ne ya cika ta.. Wai juwairiyar me konannar fuskar nan data raina yau ita ce a matsayin kishiyar ta kuma wai diyar sarki ce ita?..lallai duk wanda ya dauki duniya da zafi zai kuwa ringa shan mamaki a rayuwarsa.. Taja lumfashi dan tasan juwairiya tayi mata nisa sosai a yanzu..ita da take diyar WAZIRI?..tab.   Zainaba ce ta shiga yi mata dan fada akan ta zauna lafiya da juwairiya kada ta biyewa surayya dan kuwa jalal na iya tsanar ta idan ya gano suna ware juwairiya kai...   Khadija ta jinjina mgnr zainaba sosai dan tasan tabbas jalal yana mugun son juwairiya.. Mikewa tayi ta shirya tace wa zainaba ta taso suje sashen juwairiya din.. Zainaba tayi murmushin murna sannan ta mike suka tafi.. Koda sukaje juwairiya ce da hanne a sashen suna yar firar su ,juwairiya na bawa hanne lbrn Rumfarbayi. .   "Tayi mamakin ganin khadija sosai amma ta share.. Khadija kuwa kamar ta sume dan kuwa juwairiya ba karamin rikita ta tayi ba..   Sama sama sukayi fira.. Zainaba ce ma karfin firar tasu.. Hanne ce ta shigo ta sanar ma juwairiya, wai su magaji da turaki sunzo gaishe ta.. Dukkansu suka fito zuwa falon.. zainaba ta kalli magaji tace.. Yaya magaji ina wuni?ya turaki ina wuni? Magaji yadan bita da kallo..sannan yace lfy kanwarmu ashe kuna nan kuma? Zainaba tace muna nan kuwa.. Turaki ya gaida juwairiya cike da zolaya.. Ta amsa a sake tana dariya.. Khadija ma ta gaishe su.. Nan suka shiga fira ana ta dariya.. Sai ga samira itama ta shigo... Ta kallesu tace.. Wato duk kuna nan ashe? Turaki yace,ke ba barci kike ba,uwar son barci se kace wata ka'sa kullum kina kan gado. Samira zatayi mgn kenan se ga jakadiya ta shigo tana sanar da su zuwan jalal..sashen Gaba daya suka shiga kallon kallon .. Jalal na shigowa ciki yayi karo dasu su duka..ya shiga binsu da kallon mamaki.. Magaji ne yayi saurin mikewa..yace.. Tunda dai Amalen ya shigo da kansa mu ai sai mu yashi mu tafi hakan nan ko? Jalal yace,wai tsaya me ya kawo nan din ma ne?naga an cika falo? Ko Baku san bata jin dadi bane zaku zo ku saka ta a gaba da surutu.. Khadija tabi shi da kallo tana jin wani iri... Zainaba tace,afuwa yaya.. Turaki ya kamo hannu samira ya jata sukayi gaba.. Khadija ma mikewa tayi,ganin jalal bai ma lura da ita a wajen ba,sai tayi murmushin yake tace,ya jalal dama gaisawa muka zo muyi da ita.. Jalal ya kalleta,duk ta rame,ko cikin ne? Murmushi ya sakar mata yace.. Ai ita ya kamata taje ta gaishe ki tunda ke yayarta ce yanzu.. Khadija tace babu damuwa ai itace bakuwa.. Jalal ya jinjinar dakai.. Khadija ta rungume juwairiya sannan tayi gaba... Magaji ma kallon zainaba yayi yana mata alama da su tafi... Ta gyada masa kai suma sukayi waje suna dariya.. Jalal yaja tsaki yana maida duban sa kan juwairiya dake zaune shiru tana saurarensu.. TEAM RUMFAR BAYI *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 41 Wattpad @afreey101 ********************** "Sannu da shigowa Amale... Ta fada tana dan rusunawa kasa kanta a sunkuye tana jin kunyarsa na mamaye zuciyarta.. Duk lkcn da zata zauna ita daya sai daren jiya ya fado mata a rai.. Ta gama tabbatar wa kanta cewa jalal na yi mata wani irin so sbd irin kalaman da yayi ta fada mata jiya.. "Jalal dake tsaye tsaye yana ta ka're ma ta kallo ya zauna a kusa da ita sosai yana fadin.. Da gani dai har kin warware daga gajiyar jiya tunda har kika zauna fira dasu magaji ko?ya karashe mgnr a shagwabe cike da kishi.. juwairiya tayi masa murmushi tace.. naji sauki kam ko kallon shi ta kasa yi.. Jalal na lura da ita dan haka ya jawo ta zuwa jikinsa...yana fadin.. ALLAH yayi miki albarka giwar amale.....dan jiya ba karamin faranta kikayi ba.. Ki fada min duk me kike so nayi miki shi.. ko wacce irin kyauta kike so nayi miki alkawarin zan baki ita a yau din nan.. dan kin cancanci kyauta mai girma daga gareni masoyiyata..    Juwairiya ta dan dago suna kallon junansu cike da so.. Tace.. Nagode da kulawarka amalena.. Amma nikam bani da wani abu da nake bukata daga gare ka a yanzu.. Soyayyarka kawai ma ta ishe ni..nayi rayuwa me cike da farin ciki.. Jalal har cikin zuciyarsa yaji dadin kalamanta... Ya shafa gefen fuskarta..yace KE TA DABAN CE juwairiya shiyasa kike kasheni da soyayyar ki.. Juwairiya ta murmusa cike da farin ciki tace.. Sai dai Amale ina so na baka wata shawara idan ba zaka damu ba.. Jalal ya gyara zamansa yace.. Ina jinki tawan.. juwairiya ta kalleshi cikin ido kafin tace.. Ina so ne ka daina share matan ka sbd ni..!sbd na fara jin wasu maganganu suna fitowa daga zuwana.. Kasan dai yin hakan da kake ba karamin jawo min tsana zayyi ba a wajensu.. Ni kuwa nafi son muyi zaman mutumci dasu.. Jalal ya jinjina kai ,tabbas ta fadi gsky amma shi har cikin zuciyarsa yafi son ta dasu,kodan su ba auren soyayya yayi dasu ba?.. Ya jawo hannunta ya shi rike gam..kafin yace.. InshaAllahu zanyi kokari nayi adalci a gareku duka kinji?.. Ta sakar masa murmushi tace.. nagode sosai Amale ALLAH yaja zamanin ka.. ******************* Bayan kwana biyu.. "A cikin kwanakin nan biyu kacal da juwairiya tayi da jalal ba karamin soyayya da shakuwa ba ce ta shiga tsakanin su.. Yana nuna mata soyayya me tsabta,sannan komai take so yana yi mata shi,baya barin ta cikin tunani ko kadan.. Gashi tana samun kulawar su hansai,kullum sashen ta cikin zaman fira sukeyi,samira da nafisa ma suna shigo mata.. Taje har sashen gimbiya kilishi da fulani diyya ta kai musu gaisuwa,ba karamin murna sukayi dan laure da hansai sai da suka fada duk yarda zatayi ta siye(ex)iyayen gidan nasu.. """""""Yau sati su daya kenan da aure A yau ne kuma juwairiya ta gama kwanakin ta na amarci da aka basu ita da jalal.. "sai kuma girkin al'ada da gimbiya kilishi ta sanar mata zatayiwa jalal.. Dan haka suka hau shirye shiryen su.. Hansai da laure ne suka zabar mata duk kalar abincin alfarmar da zatayi wa jalal.. Hanne ce ta shige gaba wajen taimaka mata tare dasu zainaba da samira dan suma cewa sukayi baza'a bar su a baya ba suna tare da ita.. Ko da umayma ta samu wannan lbrn a cikin RUMFAR BAYI ba karamin bakin ciki bane ya lullube ta ba,wai wannan juwairiyar dai da sukayi wa wulakanci suka tozarta suka kore ta daga masarautar nan yanzu itace matar SARKI giwar amale? Ta cije yatsa da saurin ta tayi sashen gimbiya surayya... Tana shiga ta sanar wa surayya lbrn abincin da juwairiya ke yiwa jalal. Ta kara fadin.. Yanzu shi kenan ita kadai ce zata samu ya'bawar sarki kenan? Ba karamin kishi bane ya turnike suryya sai dai babu abunda zata iya yi,ita yanzu ta kanta takeyi,ta samu ciki ta haihu da sarkina.. Ta kalli umaymah cike da rashin mafita tace.. Yanzu wacce hanya ce zamu bi dan mu tarwatsa wannan abincin da take yiwa jalal.. Sai kuma taja tsaki,kai ni duk wannan ma bashi ne gaba na ba,dan maganin malam dai shiru kakeji.. Umayma tayi murmushin mugunta tace.. Ki bar min komai a hannuna ranki ya dade..ni nasan abunda zanyi.. ************* "Sun kammala dukkan abincin da zasuyi ko ina a madafar ya dauki kamshi.. Zainaba ce ta matsa wa juwairiya akan taje tayi wanka ta shirya su zasuje su shirya abincin a sashen jalal.. "Sunje sun shirya komai a sashen na jalal ko ina ya dauki kamshi.. Zainaba ta kalli samira.. Munyi kokari,sukayi murmushin murna kafin dukkannin suka fice da zuwa sashen su... juwairiya na can sashenta tana shiri hanne na tayata..   a lkcn ne Umayma ta lallaba cikin sashen na jalal akan surayya ce ta aiko ta..    Tana shiga falon tayi wajen abincin da sauri ta dauko wani kulli daga cikin zaninta ta bude kwanon miyar tana kokarin barbada maganin a ciki..    "Jakadiya da jalal ne suka shigo sashen... daga can fa'da suke aiken gimbiya kilishi yaje masa akan ya koma sashensa yaci abincin amaryarsa.. Murna sosai yakeyi zai ci girkin Giwarsa.. Sai sauri yake bazawa,magaji ya kalleshi yace,gsky kayi gaba Amale ni kam bazan iya wannan saurin naka ba.. Jalal ya harare shi,toh a gaida su inna dai.. Magaji yayi gaba yana fadin,zasuji.. Jakadiya tayi murmushi tana jin dadin yarda jalal ke son juwairiyar su.. "Caraf suna shiga sashen sai kuwa sukaci karo da mutumiyar ta ku wato umayma tana ta barbada garin maganin ta a cikin lwanon miya..   Kallon juna sukayi cike da Al'ajabi. . Jakadiya ce ta da'ka mata tsawa.. A daburce ta juyo cike da tsananin fargaba... Jikinta na rawa ta zube a kasa.. Jakadiya tace.. Me kike zubawa a cikin Abincin SARKI...! Umayma ta shiga girgirza kai.. Wlh tallahi babu abunda na zuba a ciki jakadiya ,kawai dai naje ne na gyara zaman kwanokan.. Jalal ya cike da mamakin waye yake son kashe shi a cikin masarautar sa?ya rasa abun fadi..     Jakadiya tace karyawata zakiyi?bacin da idanun mu muka ganni ki..kina barbada magani acikin abincin Amale.. Toh Yau taki ta kare!dan kuwa dole ne ki fuskanci hukunci mai tsauri! Jalal ya dagawa jakadiya hannu sannan ya karasa wajen umaymah yace.. Kince baki zuba komai ba a ciki ko? Tace wlh mai martaba ni babu abinda na zuba a ciki.. "Juwairiya da hanne ne suka shigo sashen sai tarar da su sukayi a tsatstsaye.. Jakadiya ta matso kusa da juwairiya ta fada mata duk abunda yake faruwa. A tsorace juwairiya ke kallon umayma.. Ita dama tuni wannan yarinyar batayi mata ba.. Toh menene hujjar ta na saka magani acikin abincin jalal? Kodai surayya ta aiko ta ne? Juwairiya ta girgiza kai babu kyau zargi.. Toh me yasa umayma zata zuba wani abu a cikin abincinta? Jalal ne ya kalli jakadiya yace,kije ki kira min dukka (family)din gidan nan,ni SARKI JALALLUDEEN ina son ganin kowa a nan Yanzu!!!!! Jakadiya ta fice da sauri... Juwairiya dake tsaye mamaki yasa ko koda motsi ta kasa yi.. Jalal ya karasa wajen ta ya kamo hannunta.. Hanne ta karasa wajen umaymah ta rike ta gam wai dan kada ta gudu..     Jalal yaja juwairiya zuwa dakinsa.. Ya kalleta yace.. Ki kwantar da hankalinki zamu gano gsky yanzu inshaAllah.. Juwairiya ta gyada masa kai a sanyaye...kafin tace.. Amale na tambaye ka? Jalal ya gyada mata kai yana jawota jikinsa.. Me ya hana ka cin abincin surayya a wancan lkcn? Jalal yadan yi jim irin tunanin nan kafin yace.. Kasa ci nayi kawai sbd tsamin da yayi dayawa.. Juwairiya tadan murmusa tace.. Ai a lkcn dani akayi wannan girkin kuma tabbas na kama wata baiwa tana zuba wani abu a cikin abincin sai dai dana tunkare ta sai ta karyata kamar umayma take karyawata a yanzu... Jalal yaja lumfashi yace... Ni na rasa meke damun ku mata wlh.. Yanzu sbd son zuciyarku kun kwanmace ku cutar da mijinku dan kawai kada ya yabi kishiyar ku..? Dan a take ya tuna abunda ya faru a lkcn khadija,yaci abincinta babu taste amma da magaji yaci cewa yayi masa lafiya kalau abincin yake..   Juwairiya ta jinjinar da kai.. Jalal ya girgiza kai shima cikin wani irin yanayi.. juwairiya ta yakaci hancin sa.. Ya kalleta.. Ta sakar masa murmushi..tana shagwabe masa fuska.. Ya sumbaci lebenta.. Lkcn ne jakadiya ta shigo ta sanar dasu kowa ya hallara..su kadai ake jira.. juwairiya ta rike hannun jalal,jalal ya lumshe mata ido yace.. Kada ki damu nasan abunda zanyi.. ************ Suna fitowa suka tarar da gaba daya an hallara..a cikin a falon.. Tunda ga kan gimbiya kilishi, fulani, hamza,nafisa,samira,zainaba, turaki,hamza,khadija.. Idanuwa akan juwairiya dake bayan jalal har suka samu waje suma suka zauna.. Gimbiya kilishi ta kalli jalal tace.. Amale ya mukaji kira haka daga sama ne? Fulani tace da fatan dai lafiya dai ko? Jalal ya kalli surayya da gaba daya jikinta yayi sanyi ganin umayma a wajen kuma da alamu bata da gsky dan kuwa jikinta gaba daya rawa yakeyi...    jalal yace.. "Kada ku damu dama so nakeyi ne ku taya ni ganin wani abu.. Jakadiya! Ya kira sunanta.. sannan ya umurce data zuba abincin a cikin plate ta mikawa umayma taci..    Umayma faduwar gabanta ta tsananta sosai.. Jakadiya tayi yarda sarki yace sannan ta ajiye plate din a gaban umayma tace.. Maza ki ci! Su dai sauran mutanen wajen kallonsu kawai sukeyi... dan sun kasa fahimtar abunda ke faruwa a wajen.. Zainaba ce tace.. Haba yaya ya zamu gama wahalar hada maka abincin nan sai ka bawa wata baiwa can taci!    Hamza yace,shine ai na gani nima kuma duk an tara mu a nan sbd mu ga cin abincinta.. Kilishi ta daka musu tsawa.. Sukayi shiru a tsorace ...    Umayma ta kurawa abincin dake gabanta ido tana dana sanin zuwa sashen jalal yau din nan da tayi... Gashi magani ne ta amso daga wajen wani bokanta dan itama Sarki jalal ya kaunaceta ta zama matarsa kamar yarda juwairiya ta zama.. Ta mallake sa ta raba shi da matansa ta zama(apple of his eyes😅) Tsoro ne ya shige ta sosai dan kuwa boka sai da ya tabbatar mata da cewa idan wani yaci wannan maganin ba sarki jalal ba,toh kuwa tabbas sai ya haukace...!! Jalal ya kalli hanne..yace Zauna ki tura mata wannan abincin dan naga bata san menene umarnin sarki ba yanzu..   Hanne kuwa ta sa hannu ta debo abincin nan me uban yawa.. Jakadiya ta saka wasu kuyangi suka kama umayma suka rirrike ta aka shiga tura mata abincin nan tana hadiye shi da kyal kyal...      Sai gani sukayi kawai ta fara dariya kamar zararriya.. Ta kalli jalal tace.. Sarkina....bazaka so ni ba nima? Duk falon hankalinsu ya tashi ciki kuwa harda surayya data gama tsorewa..    Umayma ta sake yin dariya..tace Nima fa ina sonka? Inaso na zama matarka kamar yarda juwairiya tayi kokarin zama itama.. Shiyasa ma naje can wajen boka na amso maganin da zai saka ka ka so ni.. Ka aureni..na zama gimbiyar ka... Abun sonka! Na haifa maka ya'ya Kamar uwar dakina surayya take ta kokarin zuwa wajen malam dan ta samu haihuwa...! Dum dum dum.. Surayya hankalinta ya mugun tashi.. Yau ta gama yawo.. Kowa yaji tana zuwa wajen malam.. Khadija da juwairiya duk suka mike tsaye cike da al'ajabi.. Fulani ta mike itama tana kallon jakadiya tace,fita ki kirawo fadawa  a dauke mana wannan mahaukaciyar daga nan.. Jalal kansa se dayaji abun kamar wani almara... Wai baiwarsa ce ta amso magani dan ya sota.. Sannan uwar gidansa har wajen malamai take zuwa.. Kilishi rai a bace take kallon surayya kafin ta wanka mata mari..masu kyau . Take ta zube kasa tana kuka me ciwo.. Gaba daya falon kallonta sukeyi..   Surayya na dafe da kuncinta tana hawayen bakin ciki.. ko a mafarki bazata taba tunanin wai baiwarta ta hannun damar ta zata ci amanar ta haka ba......kai mutum ba abun yarda bane ba...kwata kwata Kilishi tace,wannan ba baiwarki bace? Tana a karkashin ikon ki shine zaki bari har ta ringa mafarkin kasancewa da Sarki? Surayya na kuka tace.. Wlh umma bani da saniya da wannan danyen aikin da tayi,ni kaina ban san tana da niyyar mallake min miji ba. Kilishi tace,ai duk dake din kuke zuwa wajen bokayen.. Surayya tace.. Umma ni wlh nayi nadamar zuwana wajen wannan malamin,kuma wlh ita ke kaini,ku yafeni dan Allah ta zube kasa tana kukan bakin ciki da nadama... Dama haka umayma take?shiyasa take ta zuga ta akan hallaka juwairiya da khadija?ma kenan? Wayyo Ashe itama nan gaba ita zata hallakar ta mallake musu jalal.. Jalal ne ya zo gaban kilishi yace.. Umma ki kwantar da hankalinki,tunda da dai asirin ta ya tuno yanzu,hukunci ne kawai zamuyi mata.. Turaki yace wannan hakane..dan ya zama ishara a wajen Bayi gaba daya.. Wannan ai (abomination )ne.... Kuma raini sosai ne a wajen SARKI.. **************** An kai umayma can rumfar hukunta bayi,an rufe ta acikin kurkuku (dakin duhu)ga hauka tana fama dashi sai surutai takeyi barka tai... Sarkin dorina ya zane ta tasa tayi lakwas aka jefata cikin dakin aka kulle (oooh ke kuma haka karshen ki yake?) Wannan al'amarin ba karamin ladabtar da surayya yayi ba.. Kullum tana sashenta zaune shiru tana mamakin irin munafuncin umayma.. Yau dai jalal da kansa ya saka a kira masa ita..   Tana shigowa dakin nasa yabi ta da kallo duk ta rame tayi baki.. Zama tayi akan kujera tace.. Gani mai marbata ance min kana nemana.. Jalal ya mike ya dawo kusa da ita ya zauna.. Surayya ta dago ta kallesa.. Jalal yace.. Meyasa zaki ringa saka kanki a cikin damuwa ne haka? Duk fa abunda ya faru ya gama faruwa...se dai Allah ya tsare gaba.. Surayya taji kwalla ta taro mata acikin idonta.. Tace... Jalal bazaka gane bane.. ka yarda da mutum amma ashe munafukin ka ne(backstabber)... Duk irin muguntar da take saka ni inayi ashe tana da wata manufar ta ta a akai..   Jalal ya sauke ajiyar zuciya.. Yanzu dai ai kinyi hankali..ko Se ki nemi gafarar wadan da kika zuluntar.. Tayi saurin kallonsa.. Yace kwarai kuwa.. Surayya tace..ta zube kasa.. Ka yafe ni sarkina... Nasan nayi maka laifuka masu yawa.. Sannan... Ka tayani neman gafarar juwairiya dan Allah.. Jalal yaji dadi har cikin ransa.. Yace.. Zan tayani rukon ta amma inaso kema keje da kanki ki nemi gafarar ta kinji.. Surayya ta gyada kai..zanje.. Jalal ya dagota ya jawo ta jikinsa ya rungume .. Ta saki lumfashi me nauyi tana jin dadin kasancewa a jikin Sarkin nata.. Love you all Sorry kwana biyu i hv nt been updating regularly.. Kunsan yarda abun yake sai a hankali. . Team RUMFAR BAYI     *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 42 Wattpad @afreey101 _"Fans please ina neman addu'ar ku,October dinnan zan fara exams dina inshaAllah,shi yasa zaku ga ina yanke lbrn dan na gama muku shi a cikin lkc na fara karatun jarabawata.._ _Thanks for all your love.._ _Ina Yin'ku sosai😘_ ******************** "Surayya abun duniya ya taro ya fara yi mata yawa.. Girman kai gaba daya ya hana ta zuwa neman gafara a wajen juwairiya.. Gashi kuma yanzu jalal ya dauke mata kafa daga dukkan al'amuran ta ko sashen sa ya daina gayyatar ta.. tun ranar dayayi kiranta tayi masa alkawarin zata je ta nemi gafarar ta har yanzu bai waiwaye ta ba Sai dai taji yaje wajen khadija da amaryarsa..      Yau dai fada tayi wa zuciyarta sosai ganin bata da wata mafita.. ga kuma wannan ciwon cikin daya dawo mata kullum dare sai tayi fama dashi tun lkcn da tasha maganin malamin nan a kwanakin baya ta kasa ganewa jikinta gaba daya.. Ga mafarkai barkatai da takeyi,duniya dai tayi mata zafi sosai,taja lumfashi.. Gara naje na nemi gafarar ta wata kila na samu sausaucin abunda nake ji.. *************** "Abun mamaki juwairiya na zaune a sashenta dasu hansai sai ga surayya ta shigo da sabowar baiwar ta...    Ga babban mamakin su juwairiya sai gani sukayi surayya ta dage sosai wajen neman gafarar ta.. Tayu mamaki sosai amma sai Tace.. babu komai ita ta yafe mata,Allah kansa ma muna masa laifi ya yafe mana balle kuma dan adam?.. Ita dama bata rike ta ba.... Surayya taji dadi sosai,dan gaba daya ma sai ji tayi juwairiyar ta burge ta bata dauki duniyar a bakin komai ba ita kuwa sbd shaidan ya tafi da tunaninta tayi ta wulakanta ta a baya oh?duniya kenan!..       Ai kuwa tun daga ranar sai surayya taji nauyin dake zuciyarta ya ragu sosai,sai dai wannan ciwon ciki da zame mata tilas kullum dare da kyal take samun barci... Ta rasa mafita gashi yakumbo kanta bata kasar balle ta saka ta ta nemo mata magani.. Bayan wata uku.. ****************** A cikin watannin nan da suka gabata ba karami shakuwa da zaman lafiya bane ya shiga a tsakanin  matan sarki jalal ba.. Abun mamaki Yanzu kam surayya sai  shige wa juwairiya takeyi  dan kafin kaganta a sashen khadija toh zaka kanta a sashen juwairiya sau ba adadi duk wani shawara wajenta take zuwa.. sai dai har lkcn ta kasa fadawa kowa abunda take ciki.. duk ta rame ko jalal ya tambaye ta sai tace masa kawai babu komai..kada ya damu.. shi kam ma abun har ya fara basa tsoro dan yanzu ya lura gaba daya surayya bata yarda ta kwana a sashen sa.. Ba kamar da ba da take matsawa sosai sai ya kwana da ita... "Khadija kam ta maida juwairiya tamkar kawarta dan har dakinta inna (mahaifiyarta)tazo tayi mata kaca kaca akan ta samu lbr a gidansu wai goggo na kawo wa diyarta magunguna.... ba karamin tashin hankali ta shiga ba shine tazo da kanta tayi mata fada mai ratsa jiki.. Sannan ta bata shawarwari wadan da zasu amfane ta a zaman auren ta.. Tun daga lkcn khadija ta saduda sosai ta mayar da juwairiya kawarta.. sai su ringa hadewa a can sashen fulani suna shan firar su dasu zainaba... "Kamar kullum magaji ne ya shigo cikin masarautar dan amsa kiran sarki jalal... yana tafe ne yana mamakin neman gaggawar da Amale keyi masa.. Caraf ya hango ta tana tafiya da baiwarta a baya amma da gani hankalin ta gaba daya baya jikin ta.. ganin yarda tazo har ta wuce sa bata ko ma lura dashi ba..     Juyawa yayi yabi bayanta da sauri yasha gabanta.. Duk da haka ko ganinsa ma batayi ba har sai data ci karo da shi..Bum!   A tsorace sosai tayi baya zata fadi kasa.. Yayi saurin taro ta ya rike ta gam yana karewa kwayar idonta kallo.. Wani irin abune yaji yana yawo a cikin cikin sa.. Ita kuwa Ji tayi kawai kirjinta na bugawa da sauri da sauri.. Magaji ya kyara mata tsayuwarta sannan yace.. KANWARMU  lafiya? Zainaba ta danyi kasa da kai tana jin hawaye na sauka akan kuncin ta.. A take hankalin magaji ya tashi yaji gaba daya yana son yaji meke damun ta haka.. Zabba'u ya kalla yace,ki jiramu a can muna zuwa... Zainaba tayi saurin kallonsa.. Sai gani tayi kawai yaja hannunta yayi gaba da ita... Haka nan taji ta kasa yi masa mgn sai bin shi da takeyi kawai har suka kawo cikin lumbu... Ya zaunar da ita akan kujera sannan ya tsare ta da ido yace.. Kanwarmu ki sanar dani damuwarki dan Allah.? Zainaba ta kura masa ido.. Hakanan taji zuciyarta ta aminta da sanar wa magaji damuwarta,dan kuwa ko juwairiya ta kasa fadawa meke damun ta duk da dai tuni juwairiya ta da'go inda damuwar kawar tata tayo asali.. "Lumfashi taja mai tsayi kafin ta fada masa komai dake tsakanin ta da Mustapha.. Magaji yayi shiru yana nazari a kalla har anyi wata hudu kenan zuwa biyar amma babu wasikar Mustapha? Kuma bai neme ta ba? Tabbas akwai abunda Mustapha ke boyewa zainaba.. Magaji ya zauna a gefenta yace,ki kwanta da hankalinki kanwarmu na miki alkawari inshaAllahu zuwa gobe zan nemo miki amsoshin tambayoyinki akan dalilin da ya saka Mustapha na daina aiko miki da wasikun sa.. Zainaba ta saki murmushin murna tace nagode yaya magaji.. Yayi murmushin shima..yace Kada ki damu kanwar mu yanzu dai bari na karasa can fa'da dan Amale ne ma yayi kirana.. Zainaba ta gyada masa kai tace.. nima sashen Giwar amale nayi yanzu.. Suka fito a tare sannan kowannen su yayi hanyarsa... "Lkcn da zainaba ta shiga sashen na juwairiya sai tarar da gaba daya matan gidan tayi a ciki. batayi mamaki ba dan dama duk ranar ta juma'a a nan suke wuni,sai kuma asabari suje sashen khadija,ranar lahadi kuwa sashen gimbiya surayya suke.... Juwairiya ta kalli zainaba tace.. Zauna nan kawata kiji... ta nuna mata waje kusa da ita... dan a Yau juwairiya tayi alkawarin fayyace wa zainaba abunda ake ciki dangane da mgnr Mustapha.. Cike da lallashi ta fara mgn.. "Zainaba inaso na fada miki wani abune dangane da Mustapha..dan na san duk wannan damuwar da kika shiga kwana biyu duk sbd shine.. ko nayi karya? Zainaba taji gabanta ya fadi..ta girgiza mata kai a sanyaye.. Juwairiya taci gaba.. toh mgnr gaskiya na samu wasika daga wajen yarimaADO ne shekaranjiya dan na saka ya nemo min lbrn Mustapha..duk da dai ya taba fadamin zayyi auren biyayya ga iyayensa.. Toh Ado dai ya tabbatar min da cewa a jiya ne aka daura auren Mustapha da diyar sarkin kasuwa na kano.. Zainaba ta runtse ido sai ga hawaye shaaa.. Juwairiya ta rungume ta cike da tausayawa dan tafi kowa sanin yarda zainaba ta mutu akan wannan Mustaphan.. amma ita kam tunda Jalal ya sanar mata da lbrn alkawarin mai martaba na hada auren zainaba da magaji... sai taji ma tafi son ta da magajin sau dubu shiyasa ta dauki alwashin sai ta san yarda tayi ta hada su suka fara soyayya.. kafin auren nasu na tashi.... sbd dai bata son zainaba tayi aure babu ko digon soyayya a cikinsa.. "A sanyaye tace..kada ki damu kawata,na tabbata Allah zai baki mijin da yafi shi.... Zainaba ta share yan kwallan ta.. tace Ni dama naji a jikina akwai babban al'amarin da Mustapha yake boye min.. amma me yasa bazai fadi min gsky ba,menene amfanin soyayyar da yake min?ai bata da wani amfani..ta karashe mgnr cike da jin haushin Mustapha a cikin zuciyarta..ya yaudare ta dayawa..     Samira ce ta dafa ta tace,ai dama shi yasa bin umarnin iyayenmu wata sa'in shi yafi wlh dan sun fi mu sanin abunda duk yafi dacewa da mu.. A baya naso naki auren turaki sbd yarda aka hada auren namu ko sanin irin halittar sa fa banyi ba.. Kakata ce (hajiya ta zazzau)ta taimaka min sosai wajen bani shawarwari gashi a yanzu ina alfahari da mijina dan kuwa bani da kamar sa a duniyar nan.. Nafisa ma ta murmusa tace itama.. Ko ni da baba ya sanarwa inna cewa Hamza ne zan aura ba karamin bakin ciki mukayi ba dan kuwa a gari gaba daya  babu inda lbrn rashin tarbiyyar sa bai je ba.. Mutane dayawa sun sha zuwa har gida su ba'ta sunan hamza a gaban mu,wai yana bin matan bayi wanene wanene...gulma dai iri iri.. Baba kam ya toshe kunnuwansa..dan alkawari ya daukar wa sarki.. Na hakura nima Akayi auren mu.. gashi yanzu muna tare lfy kuma duk sai na gane cewa wasu maganganun ma da akayi a kansa duk karyar banza ce.. "Surayya ta gyara zamanta..(a wannan lkcn idan ku ka ganta se kun rantse da Allah ba ita bace ba duk ta rame sbd ciwo amma har yau babu wanda ta sanarwa abunda ke damunta) Tace.. Nikam da abba da ya sanar min mgnr aurena da sarkin daura.. Da farko a gsky ban amince ba dan ina da manema sosai a lkcn.. har sai da jalal yaje har kasar mu muka hadu dashi.. Sannan ne na amince dashi.. Juwairiya tayi murmushi.... Khadija zatayi mgn.. Zainaba da juwairiya suka kwashe da dariya..    Ta watsa musu harara wato dan kunsan sirrina ko? Juwairiya tace,mun san komai kuwa masoyiyar ya jalal.. Gaba daya suka saka dariya.. **************** Yau juwairiya da kan ta taje har sashen jalal ta same shi ya fito daga wanka kenan..    Kyallen da yake goge jikinsa ta amsa.. Ya sakar mata murmushi yana fadin.. Kamar kin san tunanin ki nakeyi wlh.. Juwairiya na goge masa jikinsa tace.. Ni kaina tunanin ka nakeyi amale amma kasan abunda ya kawo ni yanzu? Jalal ya girgiza kai yana kura mata ido.. Taja hannunsa suka zauna a gefen gado.. Tace amale ni kuwa ko surayya ta samu fada maka meke damun ta? Jalal ya girgiza kai,nayi nayi ta fada min amma taki.. har fa kwana a sashena ma ta daina yi se de tazo ta gaishe ni ta tafi abunda ni kaina al'amarin nata yana daure min kai... ko umma zan sanarwa ta tambayeta oho..mutum sai karewa yakeyi babu wani dalili.. Juwairiya tadan jinjina kai.. Tace... ni kaina ramar da takeyi ta fara bani tsoro har fa baiwarta na kira na tambaye ta ko surayya bata cin abinci ne sosai amma se ta tabbatar da cewa tanacin abinci... Na kasa gane daga ina damuwar take har yanzu? Jalal ya jawo ta jikinsa yana zame dankwalin dake kanta.. Tabbas kin cika me kyakkyawar zuciya juwairiya.. duk abubuwan da surayya tayi miki a baya amma kin damu da ita haka? Juwairiya ta kwantar da kanta a kirjinsa..      Ni ban rike ta da komai ba amale sbd nasan kishi babu abunda baya haddasawa mutum bare mu mata.. Jalal ya sumbaci goshinta,shiyasa nake son ki sosai... juwairiya ta dago itama ta sumbaci goshinsa kafin tace.. nima haka Amalena... Yace kada ki damu dolene mu tuntubi surayya dan ceto rayuwar ta... duk da dai zan iya cewa abunda ta shukane take girbewa yanzu.. Juwairiya tayi saurin rufe masa baki tana girgiza masa kai.. Yayi dariya yana fadin.. to uwar hakuri.. Nidai ba kamar ki bane dole na fadi gsky abuna... ****** "Magaji ne ya kalli juwairiya da tsabar mamaki.. Ta gyada masa kai tana fadin kaji fa abunda daya faru kenan.. ashe wai har yayi aurensa wannan Mustaphan gashi yanzu ni kaina na kasa lallashin zainaba dan ta saka damuwa sosai a cikin ranta kasan yaudara babu dadi ko kadan.. Magaji ya gyada kai cikin jimami.. ni ma a jiya nayi aike can kasar kanon don a gano min meke faruwa dashi ashe shi gayen har yayi auren sa Allah sarki haka kaddarar su take.. Juwairiya ta gyara zamanta..tace Shine nake so dan Allah magaji ka taimaka min wajen saka zainaba ta rage wannan damuwar da ta jefa kan ta a ciki..kaga kaima yayanta baza so ta kamu da wata cutar ba ai ko?   Magaji ya jinjinar da kai dan kuwa shima ya tausayawa zainaba sosai.. Yace babu damuwa zan gwada na gani.. Juwairiya tace nagode sosai magaji.. Ya mike yana fadin.. Ai GIWAR AMALE  duk abunda kika ce nayi miki ya zama dole nayi miki shi ai. Juwairiya tayi dariya.. Ai kuwa godiya nake sosai.. ******* Tunda ga wannan lkcn magaji ya zage sosai wajen farantawa zainaba har mamakinsa takeyi..   kullum Shine duk safiya kafin ya shiga fada sai yayi (branching) a sashen ta sun gaisa.. Da yamma ma haka kafin ya tafi gida sai ya leka wajenta sun yi sallama..   Zainaba tun abun yana isar ta har dai ya zamo itama ta fara jiran zuwan nasa a kullum.. Kamar yau jiya har alkawari yayi mata akan zai zo su fita wajen masarauta tare suyi yawo amma taji shi shiru wannan lkcn abunda bai saba ba..   Ta kalli zabba'u tace.. Kije ki duba min a fada ko magaji yana can.. cike da damuwa tayi mgnr.. Zabba'u tace toh ranki ya dade..sannan ta fita da sauri.. Tana fitane sukaci karo da rabi da khadija su kuma zasu shiga sashen. Zabba'u ta gaishe su tayi gaba abunta.. Su kuwa suka karasa cikin sashen.. Suna shiga zainaba ta mike a tunanin ta ko magajin ne yazo.. Tana Ganin khadija ce sai taja tsaki.. Khadija da cikinta har ya fito sosai tace.. Ai dole ne kiyi min tsaki tunda naji lbrn kin fara mallake min yayana.. Zainaba ta waro ido.. Ni ? yaushe? Khadija ta kalli rabi sukayi dariya.. Ai duk masarautar nan bayi sun gama dauka soyayya kukeyi da yaya magaji wai kullum ashe se yazo sashen ki...hakane?khadija ta kashe mata ido.. Zainaba taja tsaki,ai dama gulma bata yiwa yan masarautar nan kadan.. Khadija ta kalleta da gefen ido kafin tace.. Ai shikenan dama tunda babu abunda ke tsakanin ku dama wani sako ne ya aiko min na fada miki amma.... Ai zainaba bata san lkcn data riko khadija gaba daya ba tace.. Me ya fada miki dan Allah? Dama wlh neman sa nakeyi.. Duk yau bai zo ba.. Khadija ta kwashe da dariya..tace Toh taya kike so marar lafiya yazo nan din ?bacin yana can a kwance.. Zainaba hankalin ta duk ya tashi.. Ta mike babu shiri tace.. Dan Allah khadija kizo muje gidanku mu duba sa.. Khadija tace,lallai ni da wannan cikin? bazan iya wata tafiya ba gsky..kije ke kadai ai masoyinki ne ko? Zainaba taja tsaki ai dama ke ba mutumci bane ya ishe ki,bari naje samira tayi min rakiyar. Khadija tace,yarinya wlh gwara ni.. samirar da laulayin cikin zata miki rakiyar?bari ya turaki ya kamaki.. Zainaba taja tsaki tayi gaba abunta da sauri... "hansai ce ta kalli laure sun saka juwairiya a gaba wai su ala dole dubata sukeyi.. Ace anyi aure har ya kai wata uku kenan amma shiru babu wani lbr?   Juwairiya ta shagwabe fuska tace.. Umma na fada muku ni bani da komai wlh.. Laure tace baki da komai shine duk kika canza cikin yan kwanakin nan.. kece shan mangoro kullum fa sai Amale ya aiko jakadiya da rabin buhu kuma baifi kisha biyar ba.. sai dai mu dau sauran mu kai rumfar cab bayi a shanye shi. Hansai tace, gashi yanzu bakya cin abincin kirki se kin amayar dashi.. Laure tace,ranar ma du'bu cemin tayi kin aika hanne wai danwake kike son ci.. Juwairiya tayi wiki wiki da ido.. Toh umma dan kawai inason danwake shine inada wani ciki?    Sallamar gimbiya kilishi ce sukaji.. Duk suka mike dan gaishe ta.. Ta kallesu tace.. Me naji kuna fadane? Kun tsare min diyata da wasu tambayoyin ku.. Ina ruwanku idan ma cikin ne da ita? (Dan taji komai kafin ta shigo dama jakadiya ce takai mata lbrn kuma tabbas ta gano juwairiya ciki ne da ita,ba karamin murna tayi ba ).. juwairiya ta rufe fuskarta cike da kunyar kilishi.. Hansai da laure sukayi murmushin murna.. Kilishi tace,yanzu dai ina so kulawar ku a gareta ta linku dan yanzu muke bukatar kulawar ko? Ta kalli juwairiya..dake ta sunne kai.. Hansai tace,ai gimbiya kada ma ki damu da wannan dan ya zama dolen mune mu kula da diyarmu. Kilishi tayi murmushi tace toh mun gode sosai.. *********** Labari ne yaje wa SARKI JALAL har fa'da.. Dan dama kowa burinsa yaje yayi masa wannan albishir din ko zai samu wani abu daga wajen sa na tukwici... Wayyo zo kuga murna kamar yayi mai..!dadi sosai ya mamaye zuciyarsa.. Ya kasa ma yarda wai juwairiyar sa ce keda cikin sa a jikinta?.. Ya mike babu shiri yayi waje.. Ko Kafin ya karasa sashenta sai da yayi kyauta har babu adadi duk wanda ya hadu dashi se ya bashi wani daga jikinsa... Yana shiga sashen nata ya tarar da hanne a falon.. Tace masa ai uwar dakin nata na cikin uwar daki.. Ciki ya shige cike da murnarsa.. A lkcn juwairiya na tsaye ne tana daura zaninta.. Sai ji tayi kawai anyi sama da ita.. Jalal na dariya cike da farin ciki marar misaltuwa ya shiga juyawa da ita yana ta shi mata albarka.. Sosai take dariya itama tana rokon sa daya sauke ta kasa.. Jalal ya sauke ta kan gado yana kamo hannayenta duka biyun ya rike gam.. Yace.. Giwata na gode kwarai da gaske.. Juwairiya ta lumshe masa ido tace.. Amale ai Allah ne abun godiya bani ba .. Jalal yaja lumfashi ya daga kansa sama yace.. Ya Allah na gode maka da wannan babbar kyautar da kayi mana,Allah kayi wa dan mu albarka ka kuma sauki matata lafiya.. Juwairiya na murmushi ta amsa da amin.. Jalal yace,wlh bakiji irin farin ciki da nake ciki bane yanzu.. Khadija zata haihu haka ma kema a cikin wannan shekarar zan zama baban yara biyu.... Juwairiya ta dan kamo hannunsa..tace Amale ka kuwa samu lkcn tambayar surayya meke damunta? Jalal ya girgiza mata kai abubuwa ne dayawa a kaina juwairiya.. Amma zan saka hamza ya dauko min me magani zuwa gobe se a duba ta.. Juwairiya taja lumfashi tace hakan ma yayi.. Jalal ya rungume ta yana fadin.. Na kagara naga dan'mu/yarmu ni dake Giwata.. Yadan rike habar sa🤔Ko dawa zayyi kama a cikin mu? juwairiya tayi dariya.. Da ni mana tunda a cikina yake.. Jalal ya dago fuskarta yace.. Ke yarinya SARAKI da babansa zayyi kamanni.. Juwairiya tace amma ai a cikin mamansa yake ko?😛 Jalal yadan turo baki... Wato ma zolaya ta kike ko? juwairiya ta make kafada ni na isa nayi wa baban SARAKI zolaya? Jalal ya mike yana fadin.. Toh bari naje wajen khadija tunda ita har addu'a takeyi danta/yarta yayi kama da ni.. Juwairiya tayi saurin mikewa tana fadin.. Nima ai na yarda.. Jalal ya kwashe da dariya yana sake rungume ta ciki da tsantsar farin ciki da nishadi... Team RUMFAR BAYI *RUMFAR BAYI* (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 42 Wattpad @afreey101 _"Fans please ina neman addu'ar ku,October dinnan zan fara exams dina inshaAllah,shi yasa zaku ga ina yanke lbrn dan na gama muku shi a cikin lkc na fara karatun jarabawata.._ _Thanks for all your love.._ _Ina Yin'ku sosai😘_ ******************** "Surayya abun duniya ya taro ya fara yi mata yawa.. Girman kai gaba daya ya hana ta zuwa neman gafara a wajen juwairiya.. Gashi kuma yanzu jalal ya dauke mata kafa daga dukkan al'amuran ta ko sashen sa ya daina gayyatar ta.. tun ranar dayayi kiranta tayi masa alkawarin zata je ta nemi gafarar ta har yanzu bai waiwaye ta ba Sai dai taji yaje wajen khadija da amaryarsa..      Yau dai fada tayi wa zuciyarta sosai ganin bata da wata mafita.. ga kuma wannan ciwon cikin daya dawo mata kullum dare sai tayi fama dashi tun lkcn da tasha maganin malamin nan a kwanakin baya ta kasa ganewa jikinta gaba daya.. Ga mafarkai barkatai da takeyi,duniya dai tayi mata zafi sosai,taja lumfashi.. Gara naje na nemi gafarar ta wata kila na samu sausaucin abunda nake ji.. *************** "Abun mamaki juwairiya na zaune a sashenta dasu hansai sai ga surayya ta shigo da sabowar baiwar ta...    Ga babban mamakin su juwairiya sai gani sukayi surayya ta dage sosai wajen neman gafarar ta.. Tayu mamaki sosai amma sai Tace.. babu komai ita ta yafe mata,Allah kansa ma muna masa laifi ya yafe mana balle kuma dan adam?.. Ita dama bata rike ta ba.... Surayya taji dadi sosai,dan gaba daya ma sai ji tayi juwairiyar ta burge ta bata dauki duniyar a bakin komai ba ita kuwa sbd shaidan ya tafi da tunaninta tayi ta wulakanta ta a baya oh?duniya kenan!..       Ai kuwa tun daga ranar sai surayya taji nauyin dake zuciyarta ya ragu sosai,sai dai wannan ciwon ciki da zame mata tilas kullum dare da kyal take samun barci... Ta rasa mafita gashi yakumbo kanta bata kasar balle ta saka ta ta nemo mata magani.. Bayan wata uku.. ****************** A cikin watannin nan da suka gabata ba karami shakuwa da zaman lafiya bane ya shiga a tsakanin  matan sarki jalal ba.. Abun mamaki Yanzu kam surayya sai  shige wa juwairiya takeyi  dan kafin kaganta a sashen khadija toh zaka kanta a sashen juwairiya sau ba adadi duk wani shawara wajenta take zuwa.. sai dai har lkcn ta kasa fadawa kowa abunda take ciki.. duk ta rame ko jalal ya tambaye ta sai tace masa kawai babu komai..kada ya damu.. shi kam ma abun har ya fara basa tsoro dan yanzu ya lura gaba daya surayya bata yarda ta kwana a sashen sa.. Ba kamar da ba da take matsawa sosai sai ya kwana da ita... "Khadija kam ta maida juwairiya tamkar kawarta dan har dakinta inna (mahaifiyarta)tazo tayi mata kaca kaca akan ta samu lbr a gidansu wai goggo na kawo wa diyarta magunguna.... ba karamin tashin hankali ta shiga ba shine tazo da kanta tayi mata fada mai ratsa jiki.. Sannan ta bata shawarwari wadan da zasu amfane ta a zaman auren ta.. Tun daga lkcn khadija ta saduda sosai ta mayar da juwairiya kawarta.. sai su ringa hadewa a can sashen fulani suna shan firar su dasu zainaba... "Kamar kullum magaji ne ya shigo cikin masarautar dan amsa kiran sarki jalal... yana tafe ne yana mamakin neman gaggawar da Amale keyi masa.. Caraf ya hango ta tana tafiya da baiwarta a baya amma da gani hankalin ta gaba daya baya jikin ta.. ganin yarda tazo har ta wuce sa bata ko ma lura dashi ba..     Juyawa yayi yabi bayanta da sauri yasha gabanta.. Duk da haka ko ganinsa ma batayi ba har sai data ci karo da shi..Bum!   A tsorace sosai tayi baya zata fadi kasa.. Yayi saurin taro ta ya rike ta gam yana karewa kwayar idonta kallo.. Wani irin abune yaji yana yawo a cikin cikin sa.. Ita kuwa Ji tayi kawai kirjinta na bugawa da sauri da sauri.. Magaji ya kyara mata tsayuwarta sannan yace.. KANWARMU  lafiya? Zainaba ta danyi kasa da kai tana jin hawaye na sauka akan kuncin ta.. A take hankalin magaji ya tashi yaji gaba daya yana son yaji meke damun ta haka.. Zabba'u ya kalla yace,ki jiramu a can muna zuwa... Zainaba tayi saurin kallonsa.. Sai gani tayi kawai yaja hannunta yayi gaba da ita... Haka nan taji ta kasa yi masa mgn sai bin shi da takeyi kawai har suka kawo cikin lumbu... Ya zaunar da ita akan kujera sannan ya tsare ta da ido yace.. Kanwarmu ki sanar dani damuwarki dan Allah.? Zainaba ta kura masa ido.. Hakanan taji zuciyarta ta aminta da sanar wa magaji damuwarta,dan kuwa ko juwairiya ta kasa fadawa meke damun ta duk da dai tuni juwairiya ta da'go inda damuwar kawar tata tayo asali.. "Lumfashi taja mai tsayi kafin ta fada masa komai dake tsakanin ta da Mustapha.. Magaji yayi shiru yana nazari a kalla har anyi wata hudu kenan zuwa biyar amma babu wasikar Mustapha? Kuma bai neme ta ba? Tabbas akwai abunda Mustapha ke boyewa zainaba.. Magaji ya zauna a gefenta yace,ki kwanta da hankalinki kanwarmu na miki alkawari inshaAllahu zuwa gobe zan nemo miki amsoshin tambayoyinki akan dalilin da ya saka Mustapha na daina aiko miki da wasikun sa.. Zainaba ta saki murmushin murna tace nagode yaya magaji.. Yayi murmushin shima..yace Kada ki damu kanwar mu yanzu dai bari na karasa can fa'da dan Amale ne ma yayi kirana.. Zainaba ta gyada masa kai tace.. nima sashen Giwar amale nayi yanzu.. Suka fito a tare sannan kowannen su yayi hanyarsa... "Lkcn da zainaba ta shiga sashen na juwairiya sai tarar da gaba daya matan gidan tayi a ciki. batayi mamaki ba dan dama duk ranar ta juma'a a nan suke wuni,sai kuma asabari suje sashen khadija,ranar lahadi kuwa sashen gimbiya surayya suke.... Juwairiya ta kalli zainaba tace.. Zauna nan kawata kiji... ta nuna mata waje kusa da ita... dan a Yau juwairiya tayi alkawarin fayyace wa zainaba abunda ake ciki dangane da mgnr Mustapha.. Cike da lallashi ta fara mgn.. "Zainaba inaso na fada miki wani abune dangane da Mustapha..dan na san duk wannan damuwar da kika shiga kwana biyu duk sbd shine.. ko nayi karya? Zainaba taji gabanta ya fadi..ta girgiza mata kai a sanyaye.. Juwairiya taci gaba.. toh mgnr gaskiya na samu wasika daga wajen yarimaADO ne shekaranjiya dan na saka ya nemo min lbrn Mustapha..duk da dai ya taba fadamin zayyi auren biyayya ga iyayensa.. Toh Ado dai ya tabbatar min da cewa a jiya ne aka daura auren Mustapha da diyar sarkin kasuwa na kano.. Zainaba ta runtse ido sai ga hawaye shaaa.. Juwairiya ta rungume ta cike da tausayawa dan tafi kowa sanin yarda zainaba ta mutu akan wannan Mustaphan.. amma ita kam tunda Jalal ya sanar mata da lbrn alkawarin mai martaba na hada auren zainaba da magaji... sai taji ma tafi son ta da magajin sau dubu shiyasa ta dauki alwashin sai ta san yarda tayi ta hada su suka fara soyayya.. kafin auren nasu na tashi.... sbd dai bata son zainaba tayi aure babu ko digon soyayya a cikinsa.. "A sanyaye tace..kada ki damu kawata,na tabbata Allah zai baki mijin da yafi shi.... Zainaba ta share yan kwallan ta.. tace Ni dama naji a jikina akwai babban al'amarin da Mustapha yake boye min.. amma me yasa bazai fadi min gsky ba,menene amfanin soyayyar da yake min?ai bata da wani amfani..ta karashe mgnr cike da jin haushin Mustapha a cikin zuciyarta..ya yaudare ta dayawa..     Samira ce ta dafa ta tace,ai dama shi yasa bin umarnin iyayenmu wata sa'in shi yafi wlh dan sun fi mu sanin abunda duk yafi dacewa da mu.. A baya naso naki auren turaki sbd yarda aka hada auren namu ko sanin irin halittar sa fa banyi ba.. Kakata ce (hajiya ta zazzau)ta taimaka min sosai wajen bani shawarwari gashi a yanzu ina alfahari da mijina dan kuwa bani da kamar sa a duniyar nan.. Nafisa ma ta murmusa tace itama.. Ko ni da baba ya sanarwa inna cewa Hamza ne zan aura ba karamin bakin ciki mukayi ba dan kuwa a gari gaba daya  babu inda lbrn rashin tarbiyyar sa bai je ba.. Mutane dayawa sun sha zuwa har gida su ba'ta sunan hamza a gaban mu,wai yana bin matan bayi wanene wanene...gulma dai iri iri.. Baba kam ya toshe kunnuwansa..dan alkawari ya daukar wa sarki.. Na hakura nima Akayi auren mu.. gashi yanzu muna tare lfy kuma duk sai na gane cewa wasu maganganun ma da akayi a kansa duk karyar banza ce.. "Surayya ta gyara zamanta..(a wannan lkcn idan ku ka ganta se kun rantse da Allah ba ita bace ba duk ta rame sbd ciwo amma har yau babu wanda ta sanarwa abunda ke damunta) Tace.. Nikam da abba da ya sanar min mgnr aurena da sarkin daura.. Da farko a gsky ban amince ba dan ina da manema sosai a lkcn.. har sai da jalal yaje har kasar mu muka hadu dashi.. Sannan ne na amince dashi.. Juwairiya tayi murmushi.... Khadija zatayi mgn.. Zainaba da juwairiya suka kwashe da dariya..    Ta watsa musu harara wato dan kunsan sirrina ko? Juwairiya tace,mun san komai kuwa masoyiyar ya jalal.. Gaba daya suka saka dariya.. **************** Yau juwairiya da kan ta taje har sashen jalal ta same shi ya fito daga wanka kenan..    Kyallen da yake goge jikinsa ta amsa.. Ya sakar mata murmushi yana fadin.. Kamar kin san tunanin ki nakeyi wlh.. Juwairiya na goge masa jikinsa tace.. Ni kaina tunanin ka nakeyi amale amma kasan abunda ya kawo ni yanzu? Jalal ya girgiza kai yana kura mata ido.. Taja hannunsa suka zauna a gefen gado.. Tace amale ni kuwa ko surayya ta samu fada maka meke damun ta? Jalal ya girgiza kai,nayi nayi ta fada min amma taki.. har fa kwana a sashena ma ta daina yi se de tazo ta gaishe ni ta tafi abunda ni kaina al'amarin nata yana daure min kai... ko umma zan sanarwa ta tambayeta oho..mutum sai karewa yakeyi babu wani dalili.. Juwairiya tadan jinjina kai.. Tace... ni kaina ramar da takeyi ta fara bani tsoro har fa baiwarta na kira na tambaye ta ko surayya bata cin abinci ne sosai amma se ta tabbatar da cewa tanacin abinci... Na kasa gane daga ina damuwar take har yanzu? Jalal ya jawo ta jikinsa yana zame dankwalin dake kanta.. Tabbas kin cika me kyakkyawar zuciya juwairiya.. duk abubuwan da surayya tayi miki a baya amma kin damu da ita haka? Juwairiya ta kwantar da kanta a kirjinsa..      Ni ban rike ta da komai ba amale sbd nasan kishi babu abunda baya haddasawa mutum bare mu mata.. Jalal ya sumbaci goshinta,shiyasa nake son ki sosai... juwairiya ta dago itama ta sumbaci goshinsa kafin tace.. nima haka Amalena... Yace kada ki damu dolene mu tuntubi surayya dan ceto rayuwar ta... duk da dai zan iya cewa abunda ta shukane take girbewa yanzu.. Juwairiya tayi saurin rufe masa baki tana girgiza masa kai.. Yayi dariya yana fadin.. to uwar hakuri.. Nidai ba kamar ki bane dole na fadi gsky abuna... ****** "Magaji ne ya kalli juwairiya da tsabar mamaki.. Ta gyada masa kai tana fadin kaji fa abunda daya faru kenan.. ashe wai har yayi aurensa wannan Mustaphan gashi yanzu ni kaina na kasa lallashin zainaba dan ta saka damuwa sosai a cikin ranta kasan yaudara babu dadi ko kadan.. Magaji ya gyada kai cikin jimami.. ni ma a jiya nayi aike can kasar kanon don a gano min meke faruwa dashi ashe shi gayen har yayi auren sa Allah sarki haka kaddarar su take.. Juwairiya ta gyara zamanta..tace Shine nake so dan Allah magaji ka taimaka min wajen saka zainaba ta rage wannan damuwar da ta jefa kan ta a ciki..kaga kaima yayanta baza so ta kamu da wata cutar ba ai ko?   Magaji ya jinjinar da kai dan kuwa shima ya tausayawa zainaba sosai.. Yace babu damuwa zan gwada na gani.. Juwairiya tace nagode sosai magaji.. Ya mike yana fadin.. Ai GIWAR AMALE  duk abunda kika ce nayi miki ya zama dole nayi miki shi ai. Juwairiya tayi dariya.. Ai kuwa godiya nake sosai.. ******* Tunda ga wannan lkcn magaji ya zage sosai wajen farantawa zainaba har mamakinsa takeyi..   kullum Shine duk safiya kafin ya shiga fada sai yayi (branching) a sashen ta sun gaisa.. Da yamma ma haka kafin ya tafi gida sai ya leka wajenta sun yi sallama..   Zainaba tun abun yana isar ta har dai ya zamo itama ta fara jiran zuwan nasa a kullum.. Kamar yau jiya har alkawari yayi mata akan zai zo su fita wajen masarauta tare suyi yawo amma taji shi shiru wannan lkcn abunda bai saba ba..   Ta kalli zabba'u tace.. Kije ki duba min a fada ko magaji yana can.. cike da damuwa tayi mgnr.. Zabba'u tace toh ranki ya dade..sannan ta fita da sauri.. Tana fitane sukaci karo da rabi da khadija su kuma zasu shiga sashen. Zabba'u ta gaishe su tayi gaba abunta.. Su kuwa suka karasa cikin sashen.. Suna shiga zainaba ta mike a tunanin ta ko magajin ne yazo.. Tana Ganin khadija ce sai taja tsaki.. Khadija da cikinta har ya fito sosai tace.. Ai dole ne kiyi min tsaki tunda naji lbrn kin fara mallake min yayana.. Zainaba ta waro ido.. Ni ? yaushe? Khadija ta kalli rabi sukayi dariya.. Ai duk masarautar nan bayi sun gama dauka soyayya kukeyi da yaya magaji wai kullum ashe se yazo sashen ki...hakane?khadija ta kashe mata ido.. Zainaba taja tsaki,ai dama gulma bata yiwa yan masarautar nan kadan.. Khadija ta kalleta da gefen ido kafin tace.. Ai shikenan dama tunda babu abunda ke tsakanin ku dama wani sako ne ya aiko min na fada miki amma.... Ai zainaba bata san lkcn data riko khadija gaba daya ba tace.. Me ya fada miki dan Allah? Dama wlh neman sa nakeyi.. Duk yau bai zo ba.. Khadija ta kwashe da dariya..tace Toh taya kike so marar lafiya yazo nan din ?bacin yana can a kwance.. Zainaba hankalin ta duk ya tashi.. Ta mike babu shiri tace.. Dan Allah khadija kizo muje gidanku mu duba sa.. Khadija tace,lallai ni da wannan cikin? bazan iya wata tafiya ba gsky..kije ke kadai ai masoyinki ne ko? Zainaba taja tsaki ai dama ke ba mutumci bane ya ishe ki,bari naje samira tayi min rakiyar. Khadija tace,yarinya wlh gwara ni.. samirar da laulayin cikin zata miki rakiyar?bari ya turaki ya kamaki.. Zainaba taja tsaki tayi gaba abunta da sauri... "hansai ce ta kalli laure sun saka juwairiya a gaba wai su ala dole dubata sukeyi.. Ace anyi aure har ya kai wata uku kenan amma shiru babu wani lbr?   Juwairiya ta shagwabe fuska tace.. Umma na fada muku ni bani da komai wlh.. Laure tace baki da komai shine duk kika canza cikin yan kwanakin nan.. kece shan mangoro kullum fa sai Amale ya aiko jakadiya da rabin buhu kuma baifi kisha biyar ba.. sai dai mu dau sauran mu kai rumfar cab bayi a shanye shi. Hansai tace, gashi yanzu bakya cin abincin kirki se kin amayar dashi.. Laure tace,ranar ma du'bu cemin tayi kin aika hanne wai danwake kike son ci.. Juwairiya tayi wiki wiki da ido.. Toh umma dan kawai inason danwake shine inada wani ciki?    Sallamar gimbiya kilishi ce sukaji.. Duk suka mike dan gaishe ta.. Ta kallesu tace.. Me naji kuna fadane? Kun tsare min diyata da wasu tambayoyin ku.. Ina ruwanku idan ma cikin ne da ita? (Dan taji komai kafin ta shigo dama jakadiya ce takai mata lbrn kuma tabbas ta gano juwairiya ciki ne da ita,ba karamin murna tayi ba ).. juwairiya ta rufe fuskarta cike da kunyar kilishi.. Hansai da laure sukayi murmushin murna.. Kilishi tace,yanzu dai ina so kulawar ku a gareta ta linku dan yanzu muke bukatar kulawar ko? Ta kalli juwairiya..dake ta sunne kai.. Hansai tace,ai gimbiya kada ma ki damu da wannan dan ya zama dolen mune mu kula da diyarmu. Kilishi tayi murmushi tace toh mun gode sosai.. *********** Labari ne yaje wa SARKI JALAL har fa'da.. Dan dama kowa burinsa yaje yayi masa wannan albishir din ko zai samu wani abu daga wajen sa na tukwici... Wayyo zo kuga murna kamar yayi mai..!dadi sosai ya mamaye zuciyarsa.. Ya kasa ma yarda wai juwairiyar sa ce keda cikin sa a jikinta?.. Ya mike babu shiri yayi waje.. Ko Kafin ya karasa sashenta sai da yayi kyauta har babu adadi duk wanda ya hadu dashi se ya bashi wani daga jikinsa... Yana shiga sashen nata ya tarar da hanne a falon.. Tace masa ai uwar dakin nata na cikin uwar daki.. Ciki ya shige cike da murnarsa.. A lkcn juwairiya na tsaye ne tana daura zaninta.. Sai ji tayi kawai anyi sama da ita.. Jalal na dariya cike da farin ciki marar misaltuwa ya shiga juyawa da ita yana ta shi mata albarka.. Sosai take dariya itama tana rokon sa daya sauke ta kasa.. Jalal ya sauke ta kan gado yana kamo hannayenta duka biyun ya rike gam.. Yace.. Giwata na gode kwarai da gaske.. Juwairiya ta lumshe masa ido tace.. Amale ai Allah ne abun godiya bani ba .. Jalal yaja lumfashi ya daga kansa sama yace.. Ya Allah na gode maka da wannan babbar kyautar da kayi mana,Allah kayi wa dan mu albarka ka kuma sauki matata lafiya.. Juwairiya na murmushi ta amsa da amin.. Jalal yace,wlh bakiji irin farin ciki da nake ciki bane yanzu.. Khadija zata haihu haka ma kema a cikin wannan shekarar zan zama baban yara biyu.... Juwairiya ta dan kamo hannunsa..tace Amale ka kuwa samu lkcn tambayar surayya meke damunta? Jalal ya girgiza mata kai abubuwa ne dayawa a kaina juwairiya.. Amma zan saka hamza ya dauko min me magani zuwa gobe se a duba ta.. Juwairiya taja lumfashi tace hakan ma yayi.. Jalal ya rungume ta yana fadin.. Na kagara naga dan'mu/yarmu ni dake Giwata.. Yadan rike habar sa🤔Ko dawa zayyi kama a cikin mu? juwairiya tayi dariya.. Da ni mana tunda a cikina yake.. Jalal ya dago fuskarta yace.. Ke yarinya SARAKI da babansa zayyi kamanni.. Juwairiya tace amma ai a cikin mamansa yake ko?😛 Jalal yadan turo baki... Wato ma zolaya ta kike ko? juwairiya ta make kafada ni na isa nayi wa baban SARAKI zolaya? Jalal ya mike yana fadin.. Toh bari naje wajen khadija tunda ita har addu'a takeyi danta/yarta yayi kama da ni.. Juwairiya tayi saurin mikewa tana fadin.. Nima ai na yarda.. Jalal ya kwashe da dariya yana sake rungume ta ciki da tsantsar farin ciki da nishadi... Team RUMFAR BAYI              *RUMFAR BAYI*           (A historical fiction) Na Afrah bhai Page 43 *KARSHE.........* ONELOVE😘 ********************       "Washe gari... Sai ga mai magani ta dira a cikin sashen sarki jalal.. Jalal ya saka jakadiya taje tayi masa kiran surayya da kuma juwairiya..    Ai kuwa sai gasu sun shigo.. Surayya gaba daya jikinta babu wani karfi duk tayi laushi.. Jalal ya kalleta yace,surayya tunda kin ki sanar dani meke damunki yanzu dole ne ki tsaya me magani ta duba mana ke dan mu san halin da kike ciki..bakya ganin duk yarda kika koma ne? Surayya ta shiga girgirza masa kai tana zubar da hawaye...tace Sarkina nasha fada maka babu abunda ya ke damuna kada ka damu dani duk laifin da nayi muku....am...kuka yaci karfin ta.. Juwairiya ta dafa ta..a sanyaye tace.. Ah ah surayya ki bari kawai a duba ki dan hankalin mu bazai taba kwanciya ba idan har bamu san meke damun ki ba...   Da kyal su juwairiya suka samu surayya ta yarda me magani ta duba ta..    A firgice me magani ta kalli jalal tana fadin.. Mai martaba ai guba ce a jinin ta.... GU'BA!!!!!! Jalal da juwairiya suka hada baki wajen fada cike da tsananin fargaba.. Ita kanta surayya sai da lumfashin ta ya dauke na wasu yan dakikai..     Mai magani ta saka surayya ta kwanta flat a kasa,sannan ta saka wasu allulori ta tsaka su a saman ciki ta  sake fitowa dasu.. Sai ga wani bakin jini ya fito bakikkirin dashi.. Ta sake kallon jalal tace, Guba ce me tattare da bakin asiri,kuma tabbas da baku kawo ni nan yau din nan ba ina tabbatar muku da cewa a cikin watan nan zata iya rasa rayuwar dan bakin asirin dake jikinta ya gama gurbata jinin dake jikinta.. Jalal tashin hankali sosai ya shiga.. Juwairiya ma duk ta rude ta kama hannun surayya dake kuka sosai tace.. Dan Allah surayya ki sanar damu meya same ki?waye yake son kashe ki? A ina kika ci wannan bakar Gubar? Surayya duk a rikice take jin abunda me maganin nan ta fada.. Ta rirrike  juwairiya tana wani irin matsanan cin kuka... Sannan ta sanar dasu duk abunda ya faru.. maganin neman haihuwa  ne da sukaje amsa a wajen wani malam can Sandamu,tunda tasha maganin ta rasa sukuni...   Jalal  kam takaici duk ya ishe shi.. sbd neman haihuwa gashi nan  taje zata kashe kanta a banza.. Mai maganin tace.. Ni abunda ban gane ba a nan shine.. Shi me yasa malamin zai nemi ya kashe ki da bakar guda? Bacin da kudin ki kika je wajen sa neman taimako.. Juwairiya tace nima shine na gani ai.. Ta kalli jalal tace.. Amale dan Allah ka saka aje a dauko mana wannan malamin ya fadi dalilinsa na son kashe surayya da bakar guba.. Jalal ya kalli jakadiya yace.. Kije ki sanar dasu shamaki aje can sandamun a dauko min wannan bokan malamin!!!.. "Malam sandamu a gaban sarki Jalal da sauran(royal family)... Jalal ya kalli sarkin dorina dake tsaye yana ta bude hanci.. Yace.. idan har bai fada mana gsky ba akan dalilinsa na son kashe gimbiyar daura surayya.. toh na baka izinin lugwigwita shi a nan wajen..    Malam na Sandamu ya hau wiki wiki da ido tsoro ya shige sa sosai.. Hamza yace.. Kayi mgn malam!!!!ko kaga tsararrakin ka a nan ne? Malam ya zube kasa yana neman gafara yace.. Wlh tallahi babu ruwana a ciki.. Sarkin dorina ya kai masa duka mai shiga jiki.. Malam ya hau ihun azaba sannan yace.. Wallahi BAIWARTA ce,baiwarta ce wlh babu ruwana a ciki !!!!.. Jalal yace baiwarta ce? Gaba daya wajen suka cika da al'ajabi da kuma tsananin mamaki!.. Surayya da kyal take iya bude ido ta kalleshi.. UMAYMA ta gama cutar  da ita.. har abada ba zata taba yafe mata ba.. Yanzu dama kashe ta dake da niyyar yi? Lallai mutum abun yarda bane..     Turaki yace,me baiwar tayi? Malam yace,watarana ne tazo har wajena da makodan kudi sosai.. tace min.. zasu zo tare da uwar dakin ta akan tana neman haihuwa... Shine ta biyani akan tana so na taimaka mata mu cuce ta mu bata wannan Gubar a matsayin maganin daukar cikin..    Shine na ni kuma na hada ta da wanj bakin aljani shiyasa take ta fama da wannan ciwon ciki duk dare,aljanin ne yake zuwa yana lalata jinin ta da wannan gubar..       Gaba daya wajen aka hau sallalami... Nan suka tsare shi sai ya karya wannan asirin da yayi mata..   Malam yasha bugu kamar ba gobe sannan ya karya asirin dake jikin surayya..duk ya gama tsorata..   A Take surayya ta sume a wajen kilishi ta saka bayi suka dauke ta zuwa sashen ta.. """"""A cikin kankanin lkc labarin duk bazu a cikin masarautar... juwairiya kam ta tausayawa surayya sosai... Mutum ba abun yarda bane ashe dai cutar ta kawai umayma takeyi.. oh rayuwa kenan se ka rantse da Allah umayma tafi kowa san surayya... ALLAH dai ya tsare gaba.. Amin **************** """"A haka rayuwa taci gaba da tafiya a cikin masarautar ta daure... Dan A yanzu kam surayya ta murmure sosai jikinta ya dawo.. dan kuwa tana samun kulawa sosai daga wajen yan gidan.. Duk da dai da farko sun ji haushin ta sosai na bin malamai da takeyi.. Sai kuma daga baya suka gane dai cewa abunda ta shuka ne ta garbe yanzu duniya tayi mata hankali.. "Wasa wasa cikin juwairiya ya fara girma gashi yanzu har yayi wata shidda... Jalal kam na mugun son cikin nan dan kullum sai shiga sashen ta ya duba ta.. Duk kuma abunda da take so sai ya saka ayi mata shi.. khadija kam a watan nan ake saka ran haihuwar ta.. "Yau dai shirye shirye kawai akeyi a cikin masarautar dan yau ne daurin auren MAGAJI DA ZAINABA..     Juwairiya ce uwar biki dan kuwa duk ita aka bar wa duk wani shirye shirye na bikin.. hakan kuwa ba karamin bata wa jalal rai yayi ba dan shi kam yafi so a bar masa giwar sa ta huta... "An daura auren ne da karfe biyu na ranar asabar.. Dun'bim jama'ar kasar daura suka halarci daurin auren MAGAJI dan gidan WAZIRI da kuma gimbiya ZAINABA diyar mai martaba tsohon sarki Abdul-Jabbar.. "Amarya zainaba ba karamin  gyara tasha ba.. Dan tun sati daya kafin bikin me gyaran jiki tazo daga kasar borno ta shiga gyara ta a can sashen juwairiya.. dan nan ta dawo da zama ko su samira sai dai su leko su.. "Yau kuwa fulani ce ta aiko mata da kaya na alfarma data  saka ayi mata na musamman.. Gimbiya kilishi ma dai ba'a bar ta a baya ba dan kuwa sai data aikowa zainaba zinari me kyan gaske..   Samira itama da tsohon cikin ta,nafisa kuwa cikin ta karamine shiyasa duk  tafi su karfi a wajen hidimar da akeyi da ita da surayya.. Dan itama Surayya dai har a wannan lkcn shiru bata samu cikin ba,sai dai a yanzu ta bar wa Allah komai ta rungumi kaddarar ta..   Magaji ango ansha babbar riga sai washe baki akeyi... jalal ne babban abokinsa kuma babban yayar amarya,hidima kam a ranar ba a magana.. "Karfe shidda na yamma aka fara shirin kai amarya.. Khadija dama ita tana can gidansu tunda sune dangin ango da katoton cikin ta haihuwa yau ko gobe.. An kai amarya dakin ta lafiya a can kusa da gidan Waziri magaji yayi ginin gidansa babban gaske.. taro ya watse lafiya aka bar amarya da halinta..   Magaji kam yayi farin ciki sosai da kasancewa da zainabar sa dan kuwa a daren farkon su ba karamin faranta masa tayi ba.. Kwana biyu da auren su da zainaba.. Khadija ta sullubo yarta mai kama da ita sosai.. Jalal yayi murna sosai hakama sauran yan uwa.. Yarinya taci sunan kakar su jalal wato SHAFA'ATU ****************** Bayan wata uku.. "A yau juwairiya ta tashi da nakuda sosai.. Hansai da laure sukayi kiran jakadiya aka sanarwa sarki da kuma su gimbiya kilishi..     Addu'a sosai aka shiga yi mata dan ta haihu lafiya dan ba karamar wahala take sha ba. Surayya kam na gefen ta tana rike da hannunta tana tayi mata sannu.. Jalal kam ya kasa zaune ya kasa tsaye.. Turaki da hamza ne ke ta basa baki dan ya kwantar da hankalin sa.. Bayan wucewar awanni uku sai ga kukan jarirai ya cika sashen.. Nan aka hau murna bayi nata wakokinsu na nuna murna da farin ciki..   Hansai ta kalli laure duk sunyi zufa tace.. Allahu akbar.... Yan biyu ne kuma duka maza.....!!!!!!! Gu'da du'bu ta hau yi jakadiya kuwa tayi waje da gudun ta... Sai sashen Sarki jalal.. Yana ganinta ya mike tsaye da saurinsa... ya taro ta hankalinsa a tashe.. Ta shiga rangwada guda tana rangwado wa jalal kirari cike da tsantsar farin cikin ta.. "Ga toya matsafa,babban Bajimi Babban Bako,Ga magajin Rumfa! Ga........ Jalal yayi sauri tsayar da ita cike da kagara yaji da mai ta zo....dan kuwa hankalinsa ya kasa kwanciya ko kadan.....bai san halin da juwairiyar sa take ciki ba... Jakadiya taja lumfashi kafin tace Allah ya sauki GIWAR AMALE lafiya sumul.. ta haifa mana samari har biyu kyakkyawa kamar ka Sarkin mu..,Allah ya kawo mana TAGWAYEN SARAKAI..jinin JALALLUDEEN sarkin da ba kamar sa...! Murna sosai Jalal yayi... Ya rasa me zai ce sai godiya da yake ta zuba wa Allah... turaki da hamza ne suka zo suka rungume sa suna taya sa murna sosai suma.. Sati na zagayo wa akasha bikin sunar yan tagwaye.. ba karamin kudi jalal ya kashe ba.. Mai martaba tsohon sarki ne ya radawa yaran suna.. Hassan shi yaci sunan ABDULSAMAD na biyu... Shi hussaini kuwa yaci sunan kakansa ABDUL-JABBAR na biyu.. Sai dai gimbiya kilishi ta samo musu sunan banza kamar haka.. Hasssan wato abdulsamad zasu ringa kiran sa da YARIMA SARAKI.. Shi kuma hussaini Abdul-Jabbar SADAUKI zasu ringa kiransa dashi.. Bayan sati biyu itama samira santalo nata dan shima namiji ne,ranar suna yaci sunan JALALLUDEEN na biyu wato kawun sa sarki Amale kenan..   Nafisa kuwa sai da yan biyu sukayi kusan wata uku sannan ta haifo yarta mace wacce taci sunan kilishi wato MAIMUNA kenan..   Surayya baiwar Allah se dai ta zama uwar ya'ya dan kullum hanne sai ta kai mata yan biyu dan su dan debe mata kewa.. Hakan kuwa ba karamin dadi yakeyi mata ba,kullum sai tasha kukan bakin cikin yarda ta mayar da rayuwar ta a baya gashi yanzu ta cuci kanta... Jalal kuwa har tausayin ta ya fara ji dan kullum bata da mgn sai ta Sadauki da saraki.. ************ Bayan shekaru sha tara 19yrs.. "A cikin wadan nan shekarun  da suka gaba ta... juwairiya ta sake haihuwar yan matan ta har biyu.. akwai me sunan mahaifiyar ta wato ZARAH'U fatima kenan suna kiranta da BATOOL sai kuma JAHAWIR itace karama kuma autar su a ciki.. Zainaba da magaji nada yaran su biyu suma mace da namiji.. Akwai IBRAHIM KHALEEL da RASHIDA.. Samira ma ta sake haihuwar ZEENATU... nafisa kuwa yaranta uku yanzu itama maimuna,Ramla da halimatu.. Khadija ta sake haihuwar ABUBAKAR  da FADILA.. Masarautar daura kam ta cika da yara masu albarka da shiga rai.. "Juwairiya ce na hango ta kara girmanta tayi jiki ta kara haske ga wani irin kwarjini da ta kara.... Zaune take a sashenta..ta hakimce akan kilisar..   ta kalli hanne tace wai ina yarima saraki ya shiga ne?   Hanne ta buga uban tagumi tace.. Ai ranki ya dade ni na rasa me yarima saraki yake nema a cikin *RUMFAR BAYI*.... nan kullum fa sai ya matsa min akan wai shi sai ya shiga har ciki yaga irin tsarin wajen.... Nasha fada mishi Kanskanci ne ace dan Sarki kamar sa ya shiga RUMFAR BAYI  amma gaba daya ya kasa fahimta.. Juwairiya tayi murmushi tace,Saraki kenan yanzu... Yanzu dai jeki ki kira min shi sannan ki biya sashen khadija ki kira min su BATOOL da JAWAHIR suma tunda shi sarkin yawo Sadauki yabi babansa ziyara gidan magaji.. Hanne ta mike ta fice tana fadin toh ranki ya dade .... "Tana shiga sashen khadija ta iske yaran gaba daya yan matan sai wasa sukeyi amma banda JAWAHIR ta na can a zaune abunta tana kallonsu.. Hanne da rabi sukayi murmushi dan ba karamin burge su halayen jawahir yake ba kullum a natse zaka same ta..ga fara'a da son mutane sam bata da wata damuwa ba kamar Batool ba..   "YARIMA SARAKI  kuwa yana can kogin mai martaba a zaune tare da bawan sa Cigari suna shan iska abunsu.. Ya hakimce yana kallon yarda ruwa ke gudana a wajen ga iska me sanyi yana kadasa sai lumshe ido yakeyi..   Hanne ce ta shigo wajen da sallama.. Ta jinjina kai tana mamakin irin kasaita da girman kai na yarima saraki... Sam shi ko mgn ma wahala take masa in ba da babansa sarki  JALAL suke mgn ba toh da kyal ne kaji muryasa a wani waje.. Shiyasa take tausayawa cigari kullum sai dai suyi zaune babu uhm bare uhm uhm..    Kirari kawai ta shiga yi masa... Lafiya jinjirin wata sha kallo.. Lafiya sukukun bakaka.. Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Lafiya Gar'kami wandon karfe Lafiya Toron Giwa SARKIN GOBE.. Kai kawai ya jinjina mata kafin a kasalance yace.. Meke tafe dake inna hanne? Ta kalli Cigari daya tsare ta da ido.. Tace,dama GIMBIYA GIWAR AMALE  ce take son ganinka..   Ya mike cike da nutsuwa ya kalli Cigari yace muje.. Sukayi gaba aka bar hanne tana ta sakin murmushi.. "A falon ta ya iske ta saman kilisarta.. Ya zauna yana yankwashe kafafunsa.. juwairiya ta kurawa dan nata ido tabbas dolene ta gode wa Allah daya bata ya'ya nagari masu so da kaunarta..    "SARAKI inaso ka fada min miye dalilin ka na son shiga cikin RUMFAR BAYI? Ya dago suka hada ido da ita.. Yace umma..... Kawai so nake naga a inda mahaifiyata tayi Rayuwa a baya... Juwairiya tayi murmushi..tace Saraki kenan... Ya dan dukar da kai yace,ki bani izinin ki gobe na shiga cikin RUMFAR BAYI.. MUMA haka UMMA...! Sukaji muryar JAWAHIR da BATOOL  a bayansu.. Juwairiya tayi murmushi kawai kafin tace dasu... kada ku damu yarana gobe nayi muku alkawarin zamu shiga  cikin RUMFAR BAYI..daku Zamu canza DOKAR wannan masarautar.. Dan babu wani Kanskanci aciki.. dan kawai Jinin sarauta ya shiga muhallin Bayinsa..... Nayi rayuwa a cikin RUMFAR BAYI kuma tabbas yana da babban tahiri a kaina.. ******** "A Lkcn da jalal ya dawo tare da SADAUKI a sashen juwairiya suka sauka nan suka hade da yaran duka aka hau fira cike da kaunar juna.. Kafin saga bisani jalal ya janye matarsa sukayi sashen sa.. "Suna shiga ya jawo ta jikinsa ya Rungume ta yana fadin.. Maman yara nayi kewar ki dayawa.. Juwairiya tayi murmushi tace.. nima haka Amalena.. Ya shafa gefen fuskarta yace... a kullum bazan bar shi miki albarka ba dan kuwa nasha fada miki KE Din TA DABAN CE a cikin zuciyar JALALLUDEEN... Juwairiya tayi murmushin farin ciki tace.. Nagode sosai da soyayyarka ALLAH YA KUMA BARMU TARE har abada.. Jalal ya janyo ta jikinsa kafin ya amsa da.. AMEEEEN....GIWATA...                             Karshe... Tammat... A yau na kawo muku karshen littafin RUMFAR BAYI... "Idan nayi laifi ko wani sa'bo a rashin sani ina neman gafarar ka Allah... Godiya ta musamman ga... "Duk Fans din RUMFAR BAYI nagode sosai da Kaunar ku,na kuma gode da duk addu’o'in ku Allah yabar zumunci.. "Godiya ga dukkan RUMFAR BAYI whatsapp Groups.. "Godiya ga PHERTY NOVELS group. "Godiya ga FATIMERH XARAH didi i love you😘 "Godiya ga WATTPADIANS u guys r just d best.. "Godiya ga TASKAR MARUBUTA group. " godiya ga RASH KARDAM HAUSA NOVELS. "Godiya ga QUEEN MEEMI Fans.. AFRAH BHAI LOVE YOU ALL...😘😘 Watch out for my new novel inshaAllah...                         Coming Sooon.... And👇 Dnt forget to follow me on instagram @khadi_nana