🔥🔥 *_KUFAN WUTA_* 🔥🔥 Free page 01 *TAFIYA DA GWANI ME DADI* *ZAFAFANKU BIYAR sune suka sake dawo muku da wasu sababbin tsararru kuma zafafan labaransu guda biyar kamar yadda aka saba* RAYUWAR MACE rano NOOR ALB Mamuhghee MASARAUTA miss xoxo BAK'AR INUWA Billyn Abdul KUFAN WUTA Huguma Zaku samu gaba daya labaran akan naira 1k kacal 2_400 3_500 4_700 *Zaku saka kudin ta wannan account din* 1487616276 BILKISU IBRAHIM MUSA ACCESS BANK *SAI KU TURAWA WANNAN NUMBER SHAIDAR BIYANKU* 09032345899 *KATIN MTN KUMA* 09166221261 *_TEAM ZAFAFABIYAR_* _MUJE ZUWA_🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️ Dogon layi ne sosai kamar irin na kowacce unguwa ta masu matsakaicin qarfi,hagu da dama na layin gida jene a jere na masu matsakaiciyar rayuwa,wadanda basu cika mugun kyau ba,kamar yadda kuma basuyi lalacewa da rashin kyan gani ba,duk da cewa wani gidan yafi wani kyau,kamar yadda kowa da irin yadda ubangiji S W T ya tsara masa matakin rayuwar da zai wanzu a kai. Yawancin gidajen plate ne masu soraye,masu ginin benen daga cikinsu 'yan qalilan ne,haka nan gaban gidajen akwai kwata wadda tabi ta kowanne qofar gida,saidai kuma a rufe take da slap,duk da cewa zakaga daya biyu na wani gurbi da babu slap din,gurbin dake nuni da cewa cirewa yayi ko karyewa,ko kuma an tsigeshi ne bisa qarfi da da yaji,da kuma qiriniya irin ta yara,wanda bisa dukkan alamu ma slap din an hada taro da sisi ne daga mazauna layin an ginashi. Daga can tsakiyar qarshen layin,wanda zaka iya karya kwana ta shiga dakai wani layin daban,dandazon yarane a tsaye carko carko sunata hargowa,idan daga nesa ka taho,zaka iya hangen yadda qura take tashi a wajen,alamu dake nuna cewa fada ake sosai a wajen. Idan ka duba tsakiyar wajen sosai,yara ne guda biyu,wadanda gaba dayansu ba zasu zarta shekara goma ba gaba dayansu,'yar baqar dirarriyar yarinyar nata qoqarin kada abokiyar fadan nata,wadda idan kayi mata kallon farko ba zaka zaci zata iya dambe haka da abokiyar fadan nata ba,kasancewar bata kai wancar garin jiki ba,fara ce ba sol ba,kana iya hangen doguwar sumar kanta me santsi yadda ta debi qasa da yashi na wajen,sakamakon cirewar danwakalin kanta,baya ga hijabinta data ci damar dashi tun daga sanda za'a fara fadan. "Iman.....iman.....ga malam nan" wata yarinya ta qaraso wajen bayan taja birki tana haki,da alama daga wani sashen ta kwaso gudunta ta kuma tuqe a nan. Sarai iman din ta jita,saita qara himma da hanzarin ganin ta yar da rahama kafin malam din ya qaraso,ta tabbatar matuqar bata gama ba ya qaraso fadan yazo qarshe,hakanan kuma babu makawa itace me laifi a wajen malam din,koda kuwa ta fisu gaskiya. Saidai bata kai ga cimma burin nata ba taji tsawar malam din a kanta Dattijon mutum,wanda a qalla shekarunsa sun tasamma hamsin,sanye da fararen kaya qal,riga 'yar ciki da wando,sai babbar riga malum malum,kansa sanye da farin rawani,hannunsa dauke da buzu daya nade wani abu a ciki,daya hannun nasa kuma yana riqene da baqar leda "Ke hajaru,kinci gidanku!,saketa nace" Ya fada cikin kaushin murya idanunsa duka bisa yarinyar. Tunkude rahama hajar iman tayi,ta duqa tana kwasar takalmanta da dankwalinta da suka turbude cikin qasa,ranta a bace na rashin samun damar tumurmusa rahama da batayi ba,dai dai lokacin malam ya waiwaya ga yaran yana musu fada,tare da kora kowa zuwa gida,bayan ya bude ledar hannunsa ya fidda alewa ya rarraba musu. "Muje gida ke kuma,'yar qaniya" ya fada yana tasa qeyar iman zuwa gida,suna tafe yana mata sababi har suka isa qofar daya daga cikin gidajen dake jere a layin. Tun daga qofar gidan zaka karanci cewa gida ne na makaranta,ma'ana gidan da ake karantar da almajirai,saboda babbar rumfar kwanon da tabarmi dake malale saman simintin dake qasan rumfar kwanon,tun daga malalen simintin,tabarmin dake shimfide din zuwa qasar dake gaban gidan a share wajen yake fesss,kai kace lomar tuwo zata fadi ka duqa ka dauka abarka kaci saboda tsabar tsabta. Da hanzari almajiran dake zaune a wajen,wadanda basufi biyar ba suka miqe "Sannu da zuwa malam" duka suka furta,daya daga cikinsu ya matso yana niyyar karbar ledar hannun malam din,sai ya dakatar dashi "Yi zamanka habu....inasu haladu?" Ya jefa tambayar ga daya daga cikin mazauna wajen,wanda ya fisu girma da wayo "Basu dawo ba tukunna,amma nasan suna hanya" kai malam din ya jinjina "Shikenan,ku fara shirin sallar magariba,duk wanda ya dawo kada ya fita,inason ganinku gaba dayanku" "To malam" suka amsa masa cikin girmamawa,saiya juya ya saka kai zuwa soron gidan. Faffadan tsakar gida ne mayalwaci sosai,wanda ke dauke da bishiyar mangwaro da babu kamarta a unguwar,wata iriyar bishiya da Allah ya sanyawa albarka,me yawan fidda 'ya'ya masu dadin gaske da kusan kowa yake amfana da ita. Dakuna biyu ne daga hannun damanka wanda suke falle daya da kuma rumfa da uwar daki,sai wasu da suke kalloka kana shigowa gidan,suma rumfa da uwar daka ne gaba dayansu,baya ga wani babban dakin falle daya dake a soron gidan. Gab da soron gidan anan rijiyar gidan take,ma'abociyar ruwa me kyau da sanyi,wanda koda da rani ne nata qafewa,anan kusan duka 'yan unguwar ke diban ruwa idan aka shiga yanayi na rani wanda ake yawan samun qafewar rijiyoyi da kuma janyewar ruwan famfo,bandakinsu na daga can wani dan sakaye sai kitchen dake taqi kadan daga dakunansu. Yadda qofar gidan da sorayenshi suke qal haka cikin gidan yake,komai a killace cikin tsafta a kuma muhallinsa. Daga qofar kitchen din wata farar macace zaune saman kujera 'yar tsugono,sanye da wata jar atamfa data qara ma haskenta kyau,duka duka matar shekarunta na haihuwa zasuyi arba'in,saidai da alama ita din ma'abociyar tsafta ce da ado. Kwando ne a gabanta wanda ke cike da alayyahu tana tsinkewa,baya ga albasa data gama yankanta tuntuni,cikin sauri sauri take aikin,da alama bata saba kaiwa dare kamar haka bata gama abincin dare ba. Sau daya tak ta daga kai ta kalli iman wadda fa shigo tana gursheqen kuka,tabi takalmanta da ta riqo a hannu saboda tsinkewar da yayi,saita maida kanta taci gaba da aikinta,kamar ma batasan da wanzuwarta ba,abinda ya sake tunzura iman din,tayi zaman 'yan bori a waje tana aje takalman nata a gefe,tare da sake bude muryarta tana sakin kukanta. Ko dagawa ta sake kallon iman batayi ba,saboda irin wannan koke koken da rigimar ta banza da wofi ba yau ne farau ba a wajenta,kusan kowa na gidan yasan da zaman wannan,har zuwa sanda malam yayi sallama ya shigo,sai tayi qoqarin rage sautin kukan nata,ta hau zazzare idanu. Da malam din ya kalleta dariya ta bashi,amma saiya danne,ya maida kansa ga matarsa safiya da ake kira da inna,wanna tuni ta miqe tana masa sannu da zuwa,bayan ta ajjiye aikin da takeyi ta qaraso ta rusuna ta karbi ledar hannunsa. "Yanzu ke hajaru.....bakya jin fada kenan ko?" Malam din ya fada yana kama kunnensa da hannu daya "Sau nawa zan hanaki fada da yara?,.....ina cewa ko sati ba'ayi ba kukayi fada da asama'u....naja miki kunne,shine har kin manta?" Tsuru tsuru tayi tana raba idanu,tsoron yadda malam keta fiddo mata manyan idanunsa irin nata ya shigeta,takan jima har ma ta manta kafin malam yasa hannunsa ya daketa,duk ranar da ya daketa din kuwa lallai ba shakka ta qureshi ne.....kuma fa zata ji a jikinta "Daga yau bazan sake miki magana ba,amma zan saki a mari idan baki wasa ba" ya qarashe maganar yana sakin kunnen nasa. Inna da tuni ta koma bisa aikinta tana saurarensu,haushi sosai yake cikata kan yadda malam din bai iya zagewa ya daki iman sosai kamar yadda takeso,saida yakan gaya mata cewa,duka baya tarbiyya,kuma bashi ke gyara yaro ba,saidai ya batashi,nasiha da kuma nusarwa sune suka kamata. Sannu da gida yayi mata kamar yadda ya saba,yana tambayarta kowa lafiya,ta amsa masa da lpy qalau,wannan kusan dabi'arsa ce,mutum ne shi managarci,wanda yake matuqar kula da iyalinsa dama buqatunsu,bakin gwagwadon ikonsa,abinci abinsha da suttura duka bai yarda sunfi qarfin iyalinsa ba,komai qanqantar abu ya daukewa gidansa,saidai duk da haka bai hana inna sana'a ba,saboda sanin muhimmancinta ga diya mace. Gangarawa malam yayi ya daura alwala,ya maida rawaninsa yana shaidawa innar zai sake fita,bazai shigo ba sai an idar da sallar isha'i "A dawo lafiya,Allah ya tsare" tasan ya fadi hakanne don kada ta damu da rashin gamaabincinta akan kari,shi yasa ya fita ya bata sarari don ta samu ta kammala a nutse. Fitar malam din kamar dama jira hajar take ta sake bude baki da sabon babin kuka,abunda ya qule inna sosai,tayita qoqarin danne zuciyarta don kada ta kaiwa hajar din hannu,amma ko alamun sassauta kukan hajar batayi ba,abinda ya dinga tunzura inna kenan,taji babu makawa saita jibgi hajar din sannan zataji sassauci,don haka ta saki dambun data gama hadawa tana maidashi madambaci hawa na biyu,ta miqe a fusace. Malam na gyara hannunsa daga qofar fita daga gidan,yana magana da wani babban dalibinsa sahabi,ya daga kansa a hankali sanda ya fara jiyo muryoyinsu,duk kuwa da cewa basu kai ga qarasowa inda yake ba,amma kuma har zuciyarsa ta tafi inda suke. Su dinne kuwa,matasan yara su biyu ne tafe,suna jere da juna,dukkaninsu shekarunsu basu wuce sha bakwai ba,yanayin fuska da kuma yadda suke tafe cikin raha zai iya sawa mutum yace 'yan biyu ne,saidai kuma kamanni da sukayi matuqar shan bambam a tsakaninsu zaisa ka gane ba twins din bane. Matashin farko ya dara dan uwansa fari da haske da kuma tsaho kadan,wanda idan baka da lura ma babu lallai ka gane hakan,yana da zagayayyar fuska da madaidaicin hanci mai tudu,siraran labba masu kyau da kwantaccen gashin gira,duk da cewa akwai sauran shekaru masu tarin yawa a gabansa.....amma kuma sai gashi saje ya fara fito masa sosai,alamun dake nuni da cewa mutum ne me yawan gargasa,don sumar kansa ma kawai ta nuna alamun hakan. Wani irin idanu gareshi kamar na mai jin bacci,saidai idan kuma ya budesu sosai xaka fahimci manya ne suna da girmansu,duk da bai gama girmansa ba,amma kuma zaka fahimci shi din dogo ne,ya fito daga jinsin yaren da sukafi alaqa da fulani,yana sanye da riga t,shirt me kwala mai gajeran hannu,sai wani wandon jeans wanda ya danyi fari kadan,qila saboda yawan morarsa da yakeyi ne,saidai kana kallon jikinsa kasan gwani ne wajen tsafta,domin kuwa.....duk da wuni da yayi wajen aikinsa,hakan baisa koda karin gugarsa ya bace ba bare akai ga yin dauda,muhammad al'ameen kenan. Saurayi na biyu shima farine,don har yafi dan uwansa fari,hakanan shima ba baya bane wajen kyau duk da cewa shima shekarun nasa basu gama bayyana komai ba,abu gudan da ya sake bambanta su....yafi dan uwan nasa garin jiki,shi kuma shadda ce a jikinsa,duk da cewa ba wata ta azo a gani bace ba,amma shima fes yake,saidai hannunsa da yayi baqi,sabida aikin gyaran mota da yake koya a wani garage,umarul farouq kenan wanda ake kira da faruku. A ladabce dukkaninsu suka qarasa daura da malam,suna masa barka da yamma,fuskarsa fadade da fara'a,zuciyarsa kuma cike da alfahari dasu yake amsa musu da "Yawwa.....ya wajen aikin?" "Alhmdlh" suka amsa masa a kusan tare "To ma sha Allah" sai suka miqe suka nufi cikin gidan,wanda al'adarsu ce kowacce rana,idan suka dawo gida lokaci irin wannan,basa shiga dakinsu dake soron,wanda shi suke fara tararwa,har sai sun shiga sun yiwa innar sannu da gida sun shaida mata dawowarsu. A fusace inna ta ciri wayar radio dinta dake a gefanta,wadda ko awa biyu ba'ayi da kawota daga gyara ba,aikin da ya kacame mata yasa bata samu tashi ba bare ta miqa ta daki,sai tayi kan iman cikin fushi tana fadin "Bari na dakeki da kyau.....sai kiyi kukan me dalili" "don Allah innarmu" kalmar data ratsa kunnensa kenan,abinda ya sanyata tsaiwa cak daka dukan iman da tayi niyyar yi,ko da bata juya ba tasan waye,ba yau ta fara jin hakan daga bakinsa ba,matuqar yana gidan,matuqar kuma yana kusa baya yarda da adaketan,ya gwammace ya horata ta sassauqar hanya,amma baya qaunar a daga hannu a daketa. Kafin innar ta gama miqewa tsaye daga durquson dukan da tayi shirin mata....tuni har ita iman din ta miqe da hanzari,ta kuma falla da gudu tayi inda alameen din yake tsaye. Kafin ta iso ya duqa,ya kuma yiwa jikinsa garkuwa da hannyensa,saboda yasan tana zuwa din jikinsa zafa fada da shagwabar nan tata,abinda ya jima da yi mata shamaki da aikatashi,saboda yadda a kullum take qara girma,shekarunta suna daduwa. Ilai kuwa tana zuwa abinda ta shirya yi kenan,saidai ya sanya hannayensa ya riqe nata hannuwan,ta sakar masa kuka,cikin sigar lallashi ya fara magana "Ya isa haka.....ya isa,karki bari aga hawayenki mana" yana maganar ne tare da sanya gefan dankwalinta yana goge mata fuskarta,sannan ya miqe daha durquson da yayi ya kama hannunta suna takawa zuwa tsakar gidan. Tsaki yaji daga bayansa,ya kuma san ba kowa bane illa sadiqu,wanda ya tabbatar da cewa zuciyarsa yayi matuqar kaiwa nesa,da kuma kara da yayi masa yau,banda haka tabbas ya sani....da tuni ya jima da kai hannu jikin iman din,kamar yadda ya saba duk sanda wani abu irin haka ta faru. Yana riqe da hannunta har suka qarasa inda inna ke tsaye daura da qofar kitchen,ya russuna yana fadin "Barka da gida inna" yana kuma ajjiye mata daya daga cikin baqaqen ledoji guda biyun da ya shigo dasu "Barka kadai aminu,ya wajen aikin?" "Alhmdlh inna" "Ma sha Allah,Allah ya qara albarka" ta fada tana ajjiye kallonta kan Ledar da ya ajjiye ya tura gaban innar "Alhamdulillah inna" ya amsa mata,saidai hankalinsa yana kan iman,wadda har yanzu take kumburi "Me iman tayi inna?" Lamin ya maida dubansa ga innar bayan ya dauke idanunsa daga kan iman Sai da innan ta tabe bakinta sannan ta ja ledar ta fara budawa kafin ta bashi amsa,amsar da tasan koda ta bashin babu abinda zai sauya zani "Fada dai fada dai ita da yara,fadan da kuma kai da kanka sai da ka rabashi amma malam ya ganta da yaran bata haqura ba,ita ba za'a gaya mata ba taji kenan?". Kansa ya juyar ga iman,wadda ta sake tale baki tana shirin fara wani sabon kukan "Me yasa iman?,ina cewa ni da malam duka mun raba wannan fadan ko?" Cikin muryar dake nuni da cewa tana gab da sake sakin wani sabon kukan tace "To ba sune ba.....da na fito sai su fara tsokanata....bayan kuma ni ban kula su ba.....wai idona irin na mage" qaramin murmushin da ya sake qawata fuskarshi ya sake,yana kuma duban qwayar idanun da take magana a kai,tabbas qwayar idanun nata dama eye lashes dinta ba irin na kowa bane,wannan yasa yara da yawa suke tsokanarta,abinda ita kuma ta tsana kenan,yake kuma yawan hadata fada da yaran,tasha sanya kuka kan a cire mata idanun a sauya mata wasu,duk saboda yadda yaran suke tsokanarta,ko kallonta inna batayi,alameen dinne yake tsayawa ya lalace bata haquri da lallaminta,tare da qoqarin yi mata bayanin cewa ba ciwo bane. Cikin nutsuwa ya tattara hankalinsa a kanta "Sau nawa zaance ki daina damuwa uhmm?,dukanmu muna son ganinki haka,kuma ke me kyau ce,bakiga duka kin fisu kyau bane?ke ta dabance kinji?,ki daina damuwa da abinda zasu fada" murmushi ta saka kamar kowanne lokaci idan ya yarrasheta irin haka,sai ta gyada kai tana murmushi,abinda ya sanya dimple dinta na hagu da dama lobawa,sai shima ya biye mata wajen sakin murmushin "aminu.....an kira salla,ka tashi kayi buda baki ka rabu da wanann sakaryar" cewar inna,tana turo jug na ruwan sanyi data jefawa qanqara gabansa,waiwayowa yayi ya dauki ruwan kana ya miqe yana duban iman "Zanje sallah na dawo...." "Ina tsarabata?" Ta fada a shagwabe tana langwabe wuya tun kafin ya qarasa maganar da yakeyi,murmushi ya sakamar mata,shi kansa yana yaba rigima irin na iman,shi yasa babu wanda suke shiri dashi kaf gidan saishi kadai,sai kuma malam wani zubin "Zan taho miki da ita" ya amsa mata yana shirin daga qafarsa "Qaniyarki....ke me yasa kullum bakya hankali?" "Idan na iso wajen saina balla mata dan yatsa,laifinsa da yake biye mata" saddiqu daya gama daura alwalarsa a bakin famfo ya fada bayan ya zubda ruwan kuskure bakin da ya guntsa,yana warware dogon hannun rigarsa tare da jefawa iman din harara kamar idanunsa zasu zazzago qasa "Amma dai ina cewa ba da kai take ba ko?,to ba ruwanka" alamin ya fada yana watsawa saddiqun nashi idanuwan,sanda yazo gab da shi zai fice daga gidan,xuwa qofar gidan don miqawa malam kofin ruwan sanyi suyi buda bakin tare,kamar yadda suka saba,kusan dukansu suna azumin litinin da alhamis,hatta da iman qaramarsu ta fara,yau dinne kawai ya zamana shi da malam ne kawai suka samu damar yi,saddiqu yayi zazzabi na kwana biyu,bai jima da warwarewa ba,abinda ya hanashi yi kenan,ita kuma inna uzuri irin namu na mata,sai kuma iman wadda tun safe al'amin ya daure mata qarqashi kan cewa yau akwai rana,tasha ruwa abinta,ta bari sai ranar alhamis tayi,inna tayita mita har ta haqura ta sanya musu idanu,idan da sabo ta saba da wannan dabi'ar ta al'amin da iman,bama ita ba,duk wanda ya rayu dasu koda na 'yan kwanaki ne sai ya fuskanci haka. _ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha'awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki_ _CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA_ _GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_ +234 818 401 7452 *Tasted and trusted*👍🏽👍🏽https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b *FREE PAGE 02* _ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha'awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki_ _CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA_ _GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_ +234 818 401 7452 *Tasted and trusted*👍🏽👍🏽 _____________________________ Basu shigo gidan ba su duka sai bayan sallar isha'i,saboda suna tsayawa daukan karatu wajen malam cikin almajiransa,hannunsa riqe da baqar leda wadda taketa maiqo dauke da awara me zafi da tasha cabbage da yaji mai uban yawa. Dai dai lokacin da iman din ke zaune gefan tabarma tare da innarmu wadda ke lazumi bayan ta gama tata sallar,abincinta na gefe bata tabashi ba,innar tana ankare da ita amma bata kulata ba,iman din irin yaran nan ne da ko kadan basa qaunar abinci,wani lokaci har sai innar ta ajjiye madoki kusa da ita sannan zata ci abincin,wannan dalilin yasa bata da kumari ko kadan,kusan duka sa'anninta sun fita girman jiki. Tana jin sallamar alamin ta miqe daga shirin kwanciyar da takeyi,ya qaraso gefanta ya zauna yana ajjiye mata ledar awarar,fuskarta a wadace da murmushi ta janyo ledar ta fara budawa tana cewa "Na gode yaya alamin" shima murmushi kawai yayi ba tare daya amsa ba,suka bita da kallo sanda ta miqe zuwa kitchen,da alama plate din da zata juye awarar take nema. Kusan lokaci daya suka dauke idanunsu shi da inna,sai innar ta ajjiyr carbin hannunta gefan daddumarta tana cewa "Zauna aminu" sabule slippers din qafarsa yayi,ya zauna daga gefa,cikin yanayi na nutsuwa "Me yasà koda yaushe saidai ka yita biyewa shirmenta?,ta yaya ku da kuke nema ya kasance koda yaushe baka da aiki sai batar mata daa kudi?,yanzu meye laaifin daambu da bazata ci ba,saidai awara?" Murmushi ya saki kawai,sannan a nutse yace "Inna mu din mune dolen imaan,mu ya kamata ace munyi mata daman,idan bamuyi mata ba waye zaiyi mata,kuma bata roqan kowa a waje saimu da muke yayyenta,kuma ma amfanin neman kenan inna,iman ba wani abu take tambaya ba da ya wuce dan abun marmari" kai kawai innar ta raausayar,dama tasan zaa rina indai lamin ne,wannaan ba shine karo na farko da magana irin wannan ta ratsa tsakaninsu ba,ta rasa wacce irin qauna da kulawa ce wannan da yakewa imaan din,duk da cewa sun kyautata masa matuqa da gaske,kyautatawar da duniya ma ta shaida da hakan,amma kulawar da iman ke samu daga gareshi ta musamman ce. Koda ta matsa wajen ganin cewa ta hanashi,ko kuma ya rage tasan bata bakinta ne kawai,lamin din bazai sauya ba,a nata hasashen da ganin kamar ya kamata ya rage din,tunda ko babu komai akwai yayarsa dake aure a qauyensu,wadda wasu nauye nauye nata dana yaranta duka ya daukesu bisa wuyansa,kasancewarsa yaro jan gwarxo,mai himma qoqari da kuma neman na kansa,komai dadi komai wuya,kuma komai rintsi,kwata kwata baisan wata kalma ta lalaci,son jiki ko kuma qyuya da ganda ba,dukkan wani aiki da zai samar masa da kudi na halak yana tallafarsa,ya kuma karbeshi hannu bibbiyu yayi,babu girman kai babu ha'inci ko son jiki. "Shikenan,Allah yayi muku jagora,yasa albarka a nemanku" "Ameen inna...ameen" ya fada yana jin dadin addu'arta,uwa ce me yawan addu'a ga 'ya'yanta,kome qanqatar alkhairi idan sukayi,bakinta baya gajiyawa da yi musu addu'a dare da rana. Duk sanda tayi masa addu'ar sai yaji dadi qwarai da gaske qasan ransa,ya rasa mahaifiyarsa tun hankali bai fara riskarsa ba,sai gashi Allah ya musanya masa da wata makwafinta a sanda baiyi zato ko tsammani ba,a lokacin da ya dauke haso ya kuma debe tsammani daga samun dukkan wani tattali kulawa ko kuma jin dadi,cikin tausayi da kuma jin qai na ubangiji ya hadashi da wasu kwafin na iyayensa. Daga inda take zaune take binsu da kallo,sanda ya karbi awarar da kansa ya juye cikin farantin robar da iman din ta dauko,sannan ya zauna yana gutsutsura mata da daya da daya yana miqa mata tana ci suna hira,kallo daya xakayi musu ka tabbatar da cewa lallai akwai shaquwa me girma a tsakaninsu. Lumshe idanunta inna tayi,bahaushe yayi gaskiya da yake cewa "Da da da dukiya babu wanda yasan me morarsu sai Allah" ta Sauke idanunta tana tuna ranar farko da suka fara sanin lamin,ya kuma shigo rayuwarsu ya zama daya daga cikin iyalan gidan. Malam ibrahim khalili shine cikakken sunansa,haifaffen garin maiduguri,cikakken babarbare wanda ya fito daga gida na ilimi da karatu,asalin gidansu malam khalili gida ne na malamai,da suka gaji karatu tun daga kakanninsu,malam khalili yana daya daga cikin yara uku da suka gaji mahaifinsu,duk kuwa da cewa su biyu rak mahaifiyarsu ta haifa Allah yayi mata rasuwa. Khalili ya tashi da son karatu da kuma nema tuquru,wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya yabar maiduguri,ya shiga duniya neman karatun qur'ani dama na addini haiqan,daga gari zuwa gari,har ma wasu qasashen da muke maqwabtaka dasu. Sosai karatu ya daukewa khalili hankali,bai samu yin aure da wuri ba,har zuwa sanda ubangiji ya nufeshi da zuwa qasar niger. A canne ya hadu da fatima buzuwa,tana zuwa daukan karatu makarantar wani abokinsa,yarinya ce a sannan me qwazo da kuma hazaqa,don lokacin ma ta kusa kammala haddar qur'ani,tana izifi na hamsin da biyar,tun daga baqara take rubutawa a allo ta haddace sannan ta wanke a sake yi mata qari,ta samu tarbiyya me kyau da kuma kulawa,duk da cewa mahaifinta ya rasu,amma mahaifiyarta batayi sakaci da tarbiyyarta ba,saboda ita daya Allah ya basu. Lokaci daya soyayya da shaquwa ta shiga tsakaninsu,suka fahimci juna da kyau,manya suka shiga maganar aka tsaida maganar aure,ba dadewa suka angwance,ya kuma daukota ya taho da ita garin kano,inda anan ya bude tsangayarsa shima,yana karbar almajirai daga kowanne gari ko qasa. Almajirancin makarantar malam khalili ba kamar sauran almjirci bane da muke gani ayanzu,wada aka watsar da duk wani mutunci da kuma kimarta a yanzu,yara suke wahala da sunan neman ilimin alqur'ani me girma,wanda sam hakan bashi da tushe bare asali sam cikin addininmu. Dukka yaron da zai karba sai ya kasance makusancinsa ne ya kawoshi,zaa rubuta adreshinka da lambar wayar wanda ya kawoka,sunan gari dana qauyenka da kuma inda za'a iya samunka,sanna bai yarda a kawo masa yaro babu haka ziqau ba babu abinda zaici,abun kwanciya da kuma kayan baqatun yau da kullum,saboda shi din bai yarda da fita bara a makarantarsa ba,karatu aka kawo yaran shi sukeyi,yakan baka zabi idan ka soma hankali,kana da sha'awar karatun boko?,idan kana dashi zai shaidawa iyayenka ya sanyaka a makaranta,idan baka buqata kuma zaka kama sana'a ne,don bai yarda da zama babu sana'ar yi ba,saidai kowacce sana'a kake kana yinta ne bisa sanya idanunsa da kulawarsa,da kuma tabbatar da cewa sana'ar da kakeyi din bata sabawa addini da kuma al'ada ba. Wannan dalilin ya sanya makarantarsa ta kasance mai tsari,mutane da dama sukeso kawo yaransu karatu nan wajensa,saidai duk shekara akwai adadin da yake dauka,idan suka cika kuma baya sake dauka sai wata shekarar. Zamansa da fatima wani irin zama ne me matuqar dadi da kuma ban sha'awa,khalili wani irin mutum ne managarci,mai halaye da kuma dabi'u masu kyau,tsayyen akan harkar gidansa da kuma sauke nauyin iyalinsa,idan kaga fatima zakayi tsammanin tana auren wani me halin ne,saidai ko daya,tsabar kula da take samu ne da kuma tsaiwar mijinta wajen sauke nauyinta,babu abinda ta nema ta rasa,tana matuqar jin dadin xama dashi,kamar yadda shima yake yaba mata,yake kuma matuqar jin dadin xama daa ita,saaboda ita din macace ta gari,mai tarin biyayyawa mijinta,wadda tasan dai dai ta kuma san akasin hakan,bai taba cewa tayi ta musa ba,kamar yadda bai taba cewa ta bari taqi ji ba,Shi yasa shima yake qaunarta,da kuma qoqarin ganin ya hidimta mata iyakar iyawarsa,bata nema komai ta rasa ba cikin gidanta,cikin wannan yanayin,shekara biyu da aurensa Allah ya albarkaceta da samun haihuwar santalelen da namiji,aka sanya masa abubakar saddiq. Daga kan saddiq tayita haife haife suna mutuwa wato WABI,makusanta da wasu cikin dangi sukayita so malam khalili ya qara aure,amma yace sam baiga dalili ba,yanajin dadin zama da matarsa,bai nema komai ya rasa ba,idanma ta hahuwa ce,kana iya haifar yaro guda daya amma ya zame maka me albarka fiye da masu tarin yaran,indai yana da rabo a haihuwa zata qara,ita kanta a sannan ta bashi dama amma yace bazaiyi ba,Cikin ikon Allah kuma sai Allah ya basu haihuwar hajar iman,haihuwar da duka fidda rai da ita,zuwan iman a daidai wannan lokacin ya janyo mata soyayya mai tarin yawa,saboda tazo a sanda basu zata ba,ta kuma zo a dai dai lokacin da suke marmari da buqatar qaramin yaron cikin gidan. Shekarar iman daya a duniya da watanni biyar lamin ya shigo rayuwar cikin gidan a lokacin. Yadda jama'a keta yabawa malam khalili kan yadda makaranta da kuma dalibansa suke a tsare ya sanya malaman wasu tsangayun dake unguwarsu da kuma wasu unguwannin suka shiga adawa da kuma takun saqa dashi,suke kuma matuqar jin haushinsa,ganin cewa ya fita daban da sauran malaman tsangayu,babu bautarwa ko azabatarwa ga dalibansa,kamar yadda bai yadda ya zama cima zaune me matacciyar zuciya ba,sai abinda iyayen yara suka dauko suka bashi,aah,shima kamar kowa,duk sanda ya tashi dalibansa shima yana tafiya neman kudinsa,ya dawo kuma lokacin da aka kusa sake zama ci gaba da karatu,komai nasu na tafiya a tsare ne,kana ganin dalibansa da yadda yake tafi da komai dole ya baka sha'awa. Daren wata jumma'a ne,tana zaune tsakar gidanta daya kasance sai ita daya,sai hajar dake kwance a gefe saman wani abun shinfidarta me hade da katifa maras tudu,duk kuwa da cewa akwai motsin almajirai da hayaniyarsu daga qofar gida amma cikin gidan ba kowa,saboda babu wanda ke shigarwa malam gidansa gaba gadi don suna almajiransa,idan kaga yaro cikin gidan,to qaramine wanda shekarunsa basu wuce wanda shari'a ta wanzar da hani na shigarsa gidajen matan aure ba,tana da mai mata aike da maiyi mata wanki ana biyansa duk a cikinsu,bai yarda suyi mata aiki ba tare daya biyasu ba,saboda yace su din mutane ne suma kamar kowa. A hankali hayaniyar tasu ta fara raguwa,da alama an gama rabon abincin dare ne,wanda ake auna cikin abincin kowa a hada,manya a cikinsu su dafa a rabawa kowa,a wani gida da suke zaune wanda yake daura da gidan malam din,gida ne da wani bawan Allah ya bayar kyauta su dinga kwana,hankalinta bai wajen sosai,yana can ga tunanin abinda ya tsaida malam da din bai dawo yadda ya saba ba,shi da saddiqu da yayi masa rakiya. "Taho a hankali....riqeshi sadiqu" ta jiyo maganar malam din tun daga soro,abinda yasa ta ajjiye allon da take rubuta fasayakfika humullah ta maida hankalinta ga qofar shigowa gidan. Malam dinne da sadiqu da wani dan farin yaro da bata sanshi ba,ta miqe tana masa sannu da xuwa,ya amsa hankalinsa yana kan yaron "Maza dora ruwan zafi innar saddiqu" malam din ya fada yana tsugunnawa a gaban yaron,yana yage ragowar rigar jikinsa,da hanzarinta ta koma madafa,ta hada ragowar itacen data gama girki ta kunna ta dora masa ruwan,sannan ta dawo tsakar gidan,inda malam ke tsugunne gaban yaron yana masa sannu,sadiq na tsaye a saman kanshi yana kallonsu. Kujera 'yar tsuguno ta jawo ta zauna,idanunta akan yaron da yake cikin hali na galabaita ta yiwa malam sannu da zuwa "Yauwa binta" ya amsa da alamun rashi na a bace ne "Ki duba maganin zafi don Allah idan akwai,idan ruwan yayi zafi ki juye sadiqu ya tayashi gasa jikinsa,bari naje na dawo" daga haka malam din ya miqe ya fita. Duk yadda malam din yace tayi haka tayin,ya gasa jikinsa da kyau,sauran ta sakashi ya shiga bayi yayi wanka dashi,cikin kayan sadiqun ta zabo wasu ta bashi ya sanya,don xasuyi kai daya dashi,yana gamawa ta zuba masa abinci,ta koma ta dauki iman data tashi ta fara rigima ta fara bata nono,daga inda take din tana kallon yadda sadiqu ya sanyashi a gaba yana kallo,tun dazun shima zuciyarsa a karye take fuskarshi ta nuna hakan. Malam ne yayi sallama,ya qarasa gaban yaron yana duban yaron daya ambata da lamin,ya bashi paracetamol din daya shigo dashi da kuma ruwan tea me zafi a leda,yace idan ya gama yasha yasha maganin,sai saddiqu ya kaishi daki ya kwanta. https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu. *_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 *_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_* _____________________ *KUFAN WUTA*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_ *YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form din kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.* *_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_* +234 903 177 4742 _Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*03 https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *ZAFAFA BIYARRRRR* *_INGANCIN LABARAI_* *_FASAHA NUTSUWA DA IYA SARRAFA ALQALAMI_* *_TSARI DA TSANTSAGWARON HIKIMA_* *_SOYAYYA MAI RATSA ZUKATA DA NARKAR DA ZUCIYA_* *_JIGON LABARAI DA YASHA BAMBAM DA NA SAURA MAI SANYA ZUCIYA MAMAKI DA TUNANI_* *_YIN LINQAYA CIKIN DUNIYAR LABARI KAJI KAMAR DAKAI AKEYI DA GASKE NE_* *DUKA SAI CIKIN GAMAYYAR LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR* *_ADADE ANAYI SAI GASKIYA_* *_HIKIMA KASHIN KWANCE_* *ABOKAN HIRA NE GA WANDA KE CIKIN KADAICI!* *ABOKAN TAFIYA GA WANDA KE CIKIN NISHADI* *WARWARAR MATSALA GAME NEMAN MAFITA* *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 *_TEAM ZAFAFABIYAR_* ______________________________ Ajjiye iman inna tayi sannan ta nufi daki,ta dauko babbar tabarmar malam din da yakan zauna a kai ta shimfida masa,sannan ta gabatar masa da abinci da ruwan wanke hannu,ta zauna nesa kadan dashi tana ci gaba da shayar da iman wadda ke rigima saboda bata qoshi ba,ta sakeyi masa sannu da xuwa "Yauwa sannu binta,ya hidima ya gida" "Alhmdlhi" ta fada tana dan murmushi,duk data saba da irin wannan kulawar tashi,amma duk sanda ya tambaya din hakan yana mata dadi,saboda tasan cewa mata da yawa ne suke neman hakan basu samu ba "Wannan yaron da kike gani sunansa lamin,na tsinceshi ne a can unguwar da naje nida saddiqu dubiyar abokina,abinda ya bani mamaki yaro qarami yashe gaban famfon tuqa tuqa,jikinsa duka tabo na duka,yasha ruwa yanata amansa,wadda ina tsammanin babu komai ne a cikinsa,yayimin kama da almajiri don haka na matsa kusa dashi,sai daya dan rage aman na tambayeshi sunansa da kuma inda yake,yamin bayani,ashe almajirin makarantar malam dan lami ne,sai na tuna kwanaki uku da suka wuce tabbas naji ana neman wasu cikin daliban,na tambayeshi me yakeyi to a nan,kansa tsaye ya shaida min guduwa yayi,na masa fada na kuma nemi dalilin da yasa yabar makarantarsu,shi baya jin tsoron wani abun kada ya sameshi,a yadda na fahimta tsoron malamin da makarantar yafi tsoro akan duk abinda zai sameshi,abun takaicin kudi malamin yake sanya musu duk ran laraba,kowa sai ya kawo wadan nan kudaden,idan kuma ba haka ba,zai ma yaro duka mai tsananin da zai gwammace koma ta yayane ya samo ya kawo masa,to shi kusan duk sati sai an dakeshi,saboda baya iya kawo komai,don yace bazai iya yadda sauran sukeyi ba,don cikinsu harda masu sata don kawai su kawo,lamarin ya dagamin hankali,na daukeshi na maidashi gaban malamin,duk da inajin tausayinsa,amma babu gatan da xanyi masa da ya wuce hakan,saidai abun mamaki abun takaici kuma abun haushi,sanda naje ga malamin,tunda ya tambayi waye ni ya fara yimin wani kallo,nasa ma'anar kallon,tunda sarai nasan waye malam dan lami,yana daga cikin masu adawa da tsarina,amma ni hakan bai dameni ba,burina da fatana shine kowa ya gyara,tun kafin nakai ga cewa komai ya soma dakawa lamin tsawa,tare da jifansa da miyagun sunaye da kuma kalamai,ya kuma fara hanqoran neman manya cikin dalibansa su dauke lamin su saka masa shi a mari,abinda bai jima da fita daga ciki ba,a nan na nuna masa nima ainihin xafina,na hana kowa yaxo wajen ya taba yaron,a nan malam dan lami ya tada husumar cewa dalibinsa ne,kuma babu wanda ya isa ya hanashi yi masa duk hukuncin da yaga dama,tunda a hannunsa aka danqashi,indai kuwa bazai hukunta laminu ba,saidai yabar masa makarantarsa,ya koreshi,ya kori yaron ba tare daya tsaya yaji meye zance ba,bai tsaya yaji me yaron shima zaice ba,bai kuma sanar da magabatansa ba bare susan ina yaronsu ya koma" "Na fuskanci tijara yake ji,don haka bance komai ba na tattaro al'aminu,na wuce dashi chemist saboda yanayin ciwuka da raunin dake jikinsa na tabon bulalai da duka da kuma mari daya dade a qafarsa ya zame masa ciwo. A hanya nake tambayarsa wayeshi da kuma qauyensu,ya shaidamin shi din dan birnin kudu ne,mahaifiyarsa ta jima da rasuwa tun yana qarami,yayarsa da ita ta riqeshi har zuwa sanda ya tasa,mijin yayar yace bazai iya daukar nauyinsa ba saboda shima bashi da komai,yayarsa bata da yadda zata riqeshi saboda shi da itan duka marayu ne,hakan ya sanya mijin yayar ya kawoshi bara,ya damqa shi a hannun malam dan lami,tunda kuma ya tafi bai waiwayoshi ba,duk da cewa bai wani jima a makarantar ba,azaba ba wacce bai gani a waie malamin ba,don kusan karatun ma dana tuntuba ba wani mai yawa bane,azabar da suke sha tafi karatun yawa,wanna dalilin ya sanya na yanke shawarar kawoshi makarantata yayi karatu,zuwa sanda zai warware kuma mu nemi ita 'yar uwar tasa ko mijinta mu gaya masa inda yake a yanzu". Kai inna ta gyada idanunta na kan lamin,zuciyarta cike da tausayinsa,tunda malam yake kawo almajirai bata taba ganin yaron da taji ya kwanta mata ba kamar lamin din,a dan awannin da yayi dasu wanda bai wuce awa daya da rabi ba,ta fuskanci nutsuwar dake tattare da yaron,komai nashi a hankali yakeyi cikin nutsuwa "Allah ya rufa asiri,ya gyara mana xukatanmu" shine abinda inna ta fada,suka kuma fara rayuwa da lamin din,wanda cikin kwanaki biyu ya sake da sadiqu,wani irin sabo sukayi sosai dashi,saika zaci sun dade tare. Tun farko dama aminu din bai soma kwana cikin almajirai ba,cikin dakin saddiqu suke kwana,hakanan hatta da suttura ta saddiqun yake sanyawa,kafin daga bisani malam ya bayar da kudi inna ta samo musu gwanjo masu kyau shida saddiq din,sosai sadiq ke murnar samun dan uwa,lokaci kadan lamin ya shiga jiki da zukatan su inna,saboda yarone haziqi,duk wani aiki da saddiq keyiwa inna da malam alamin din ya daukeshi,sai malam da inna na hanashi suna raba musu kowa ya dauki nasa. Kusan tare sukayi rainon iman da inna,idan inna tana aiki tofa iman tana hannunsa,yayita tiri tiri da ita kenan,tun tana masa qyuya har ya zamana duk cikin gidan babu wanda take yarda dashi Kamar yadda take yarda da alamin,wani lokaci idan aiki ya kacamema innan idan ya dauki iman sai tayi da gaske ta korashi makaranta sannan zai tafi,sannu a hankali sai sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu,baya son kukanta,baya son abinda zai taba iman din,da a daki iman din gwara a dakeshi,koda malam ya sanyasu makaranta sai ya zamana sai ya fara kai iman sannan shi zai wuce,koda kuwa shi xaya makara,kudin break dinsa kuwa badai yaci a cikinsa ba,komai ya gani shi zai kwasowa iman din ya kawo mata,idan kaga yadda yake matan sai ka rantse da Allah ciki daya suka fito. Kamanni ne kawai zasu tona asiri,saboda kowa a cikinsu kamanninsa daban,hasken fata ne kawai ya hadasu,tun iman na qarama ta fita daban,tana da kyan fuska qwarai da kuma yalwar suma,wadda ta gajeta daga wajen inna. 'yar lele iman take a wajen alamin tun tana da qananun shekaru,zai iya hana cikinsa ya bata,duk abinda tace tana so to matuqar yana dashi sai ya bata,idan babu kuwa zai nema mata,abinda yasa ya tashi kenan da zuciyar nema,zama da madaukin kanwa inji hausawa sukace shike kawo farin kai,tun saddiqu bashi da ra'ayi har zama da lamin ya sanya ya zama mai neman na kanshi kamar alamin din. Kusan duk kudin daya samu wajen nemansa fiye da rabinsa siyawa iman wannan ne siya mata wancan,tun bata isa ado ba yake mata siyayyar kayan kwalliya da qyale qyale,tun malam da inna na fada,har suka fahimci a jininsa yake kulawa da iman,bazai iya dainawa ba,dole suka haqura suka sanya masa idanu,saidai innan tayi masa fada da kuma dabarar ya dinga aje wani abu saboda yayarsa,wadda a yanzu shekaru ke sake jaa nauyi na dada hawa kanta,tana kuma da buqatar taimako ko yaya ne. Alamin shine kewa iman komai,itama duk abinda take da buqata alamin din take durafafa kanta tsaye,bata ko kallon sadiqu dan uwanta,saboda yana da zafi shi din,hakanan yanzu yanzu ba wani abu bane yakai mata bugu idan tayi ba dai dai ba,sabanin alamin.....wanda bashi da daukan zafi a kanta,hasalima yana tare duk wani abu da yasan xai bata ranta ko ya cutar da ita,idan tayi ba dai dai ba cikin ruwan sanyi zai nusasheta ya kuma gyara mata,tana kuma daukan maganarsa fiye data kowa cikin gidan. Dinki dashi lamin yafi qwarewa,ya iya dinkin mata kamar masifa,har zuwa yanzu da yake kan shekara ta kusan goma sha shida,wannan yasa iman dake da shekaru goma sha daya cikin rayuwarta tun a sannan ta zama abun kallo,indai tayi kwalliya kowa sai ya yaba,tana da kyau sannan kuma alamin din yana fitar da ita da dinkuna sai kace wata qatuwar budurwa,don idan kaga dinkunan da take sanyawa saika tambaya waye yayi mata,sau tari idan yayi dinkuna ya samu kudi sosai,yakan je kasuwa ba tare daya gayawa kowa ba,ya samo mata atamfa falle bibbiyu masu sauqin kudi ya mata skert da riguna tsala tsala,saboda bata iya daura zani ba har yanzu,abinda yake hadata da inna kenan,kullum fama take amma har yanzu iman din bata iya ba,koda yaushe saidai ayi mata riga da skert ko kuma doguwar riga. Idan kaga iman din saika dauka diyar wani ce,saboda bata rasa komai ba,kullum tsaf zaka ganta cikin suturu masu kyau. Amin Abubakar haifaffen garin birnin kudu ne dake jahar jigawa,bafulatani ne uwa da uba,abinda yasa ya gaji kyau kenan shima tun quruciyarsa,tun shekarunsa basu fara nuna ba,yaro ne da tun a halittarsa Alla ya masa baiwa masu tarin yawa,yana da nutsuwa qwarai da gaske wadda ta hade masa da miskilanci,miskilancin da tun zamanin quruciya ya sanya ba kasafai zaka ganshi cikin wasanni irin na yara ba,yafi ganewa yana zaune daga gefe yana kallonsu,idan abu ya burgeshi ya saki murmushi kawai. Kafin rasuwar mahaifiyarsa ya samu tarbiyya qwarai daga wajenta,wannan tasa ya zama wani na daban,idan yana wasu abubuwan saika dauka wani babba ne me shekaru. Yadda malam da kuma inna suka riqeshi abune da bazai manta dashi kafatanin rayuwarsa ba,sun masa wani gini sun kuma zame masa garkuwa kuma ginshiqi cikin rayuwarsu,ya fahimci daga inna sadiq da kuma malam dukkaninsu suna qaunar iman,suna dannewa ne saboda yanayi irin na tarbiyya,shi kuma baiga abinda zaiyi ya faranta musu ba fiye da kula da abinda sukeso,hakan yasa ya sanyawa kansa bawa iman din dukkan kulawa,sannu sannu kuma sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu. Wani lokaci har mantawa yakeyi,yakan kallo iman din a matsayin 'yar uwarsa ta jini,har sai idan wani abun ya gitta da zai sanya ya tuna cewa ba jininsa bace. _shimfida kenan......muje zuwa_ _ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha'awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki_ _CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA_ _GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER_ +234 818 401 7452 *Tasted and trusted*👍🏽👍🏽🔥🔥 *KUFAN WUTA*🔥🔥 NA *HUGUMA* Free page 04 *_MASOYA 'YAN QASAR NIJER,ZAKU TURA KATIN WAYA(AIRTEL/MOOV) TA WANNAN NUMBER_* +22795166177      Zaune take saman kujera 'yar tsugunno,sanye da uniform na makarantar primary din da take zuwa,tana ta qoqarin daura takalmin sandal a qafarta,komai nata tsaf kuma fes,karin guga ya kama uniform din jikinta sosai,shaidar cewa suna samun kulawa yadda ya kamata,hatta da takalmin sandal din qafarta qyalli yake,kamar yadda farar safarta take qal kamar baa sakata.        Wannan kusan duka aiki da horon lamin ne,idan baiyi mata da kansa ba,to ya riga ya koyar da ita,iman din akwai tsafta kamar yadda lamin din yake,bare ma kafin ta yiwa kanta wani abu sau daya yayi sau goma,wankinta da nashi duka suna wuyansa,kama daga uniform dinsu zuwa kayansu na zaman gida.        Lamin din na tsugunne gefan kitchen yana shirya mata abinci a wani dan qaramin kwando me kyau,wanda shi da ita sukaje ta zaba ya siya mata,tana ta masa surutu yana biye mata,wanda duka akan jarrabawar common interence da zata zana ne a yau,inna na daga cikin kitchen din tana zubawa shi yana shiryawa har ya gama,dai dai sanda ta gama sanya safa da kuma warin takalmi daya,dayanne ya gagara,don haka lamin din ya qarasa wajen ya tsugunna ya kama takalmin yana daura mata,sannan ta miqe tana diban takardunta sabon pencil biro har ma da cleaner dasu sharpener da lamin din ya siya mata.          Suka miqe suna yiwa inna sallama,saboda lamin din ne zai kanta har can inda zasu zana jarabawar da kansa,daidai lokacin malam ya shigo "A'ah,har kin gama shiryawa kenan,to ai Allah yasa motar bata tashi ta barki ba" malam ya fada yana danna wayarsa Tecno keypad dake hannunsa saboda yaga lokaci "Dama ba tare zamu tafi ba,ya lamin ne zai kaini" iman ta fada tana duban malam "A'ah,wanne irin sakarci ne wannan,ya ga motar makaranta zaki ce saidai laminu ya kaiki?,ki wuce ki shiga cikin 'yan uwanki dalibai ku tafi" "Ai malam kada ma ka bata bakinka,babu yadda bayi dasu ba,tun jiya nake sababi,amma dole ne naja bakina na tsuke,saboda shine yake goya mata baya,wai kada ta shiga cikinsu uniform dinta ya cukurkude......sai kace tafi kowa" jin inna ta sako baki ya sanya iman ta fara narai narai da ido kamar me shirin sanya kuka tana duban lamin din,so take ya sanya baki,kada su malam su hanashi ya rakata.        Zahiri ita tsoro takeji,saboda yadda taji wadanda suka gama primary wancan shekarar suke fadan wahalar jarabawar,duk da yadda lamin din ke qarfafa mata gwiwa tare da nuna mata cewa ba wani abu,suma sunyi fa,iya karatu tasan ta yishi,don a rana suna kwashe awanni masu yawa lamin din yana mata lesson,tana da matuqar qoqari da fahimta,saboda haka duk karatun da yake mata tana daukeshi,wannan dalilin ne yasa lamin din yaci burin tayi karatu mai zurfi,duk sa'ilin da suka zauna suna hira kuwa rabin maganarsa kenan,wannan abu yayi tasiri itama cikin ranta,bata da burin daya wuce ta ganta ta gama qaramar makaranta ta shiga jami'a,ta zama likita lawyer ko 'yar jarida,cikin ukun nan takeso ta zama daya. "Malam kasan wannan shine karonta na farko da zata fita wani waje tayi jarrabawa irin wannan,rakatan kuma zai qara mata qwarin gwiwa,tunda makarantar basu hana ba malam ka bari na kaita" da qyar lamin yasha kansa ya barsu suka fice.        A soron gidan ya dakata yana cewa "Bari na tada sadiq ya rakani,tafiya bibbiyu tafi dadi" "Yaaya,Allah bazaije ba koka tasheshi" iman ta fada tana jan tunga,sai ya waiwayo ya kalleta,taso bashi dariya yadda ta tsuke dan qaramin bakinta ta marairaice,ya fuskanci so ne batayi yaje din,don tabbas idan suka tafin tare bazai barta ta sake ba,duk kuskuren da tayi saiya taso mata da fada hantara ko kyara. "Ina zuwa dai" ya fada yana saka kansa cikin dakinsu.        Saidai duk yadda yaso tada sadiq din ya rakashi ya qiya,sai ya cusa kansa ma qasan filo yana cewa a dawo lafiya,Allah ya bada sa'a,dole ya fito daga dakin ya barshi.         Dadi iman din taji,ta dinga boye dariyarta har sai data fito ta dara,harara lamin din ya watsa mata da lumsassun idanunsa "Ni kikewa dariya saboda ya yarfani ko?" Sake qyalqyale masa tayi da dariyan "To ai yaa lamin kai kam baka iya harara ba,hararaka irin ta masu jin bacci ce" fara'ar fuskarta kadan ta ragu "Ya lamin,ni dakai me yasa dukanmu bamu da lafiyar ido?" Ta tambayeshi sanda suka kusa ficewa daga layin nasu tana dubansa,da alamun damuwa cikin muryarta.        Murmushi ya sake wansa iyakarsa saman lebansa,duk da qarancin shekarunsa amma yanayinsa kamar wani babban matashi,akwai wani iri kwarjini na daban dake fita saman fuskarsa.        Duk da cewa a shekara ta sha bakwai yake amma hankalinsa tabbas yafi na iman din nesa ba kusa ba,kasantuwarsa namiji ita kuma diya mace         Cikin harshen da yake ganin zata iya fahimta ya fara mata magana "Lafiya lau idanunmu suke ni dake,ba kina gani sosai ba?,ko akwai wani abu da bakya iya gani" saifa girgixa kai alamun a'ah "To kin gani ba.....nima ina gani sosai,har daga nan ina iya ganin wanda ke tsaye gaban rumfar malam dalha" ya fada yana nuna wajen da yatsa,abinda ya sanyata tada kai ta kalli wajen,kawai tazarar nisa a tsakaninsu,don haka abun ya bata mamaki,har ta fidda idanu,sannan ta waigo gareshi "Yaaya" kai ya jinjina mata,bata sake kokwanto ko tantama ba,saboda tasan halin lamin din tunda ta fara wayo,qarya itace abu na qarshe da baya kusantarta a rayuwarsa kaf,koda ya gaya mata waye a tsayen,da suka isko wajen saita ga shi dinne kuwa,abinda ya sanyata sakin dariya "Na yarda Allah yaya,lafiyarmu qalau" murmushi ya kuma saki a maimakon dariya "Na gaya miki dama,yanayin halitta ce,kowa da yadda Allah ya halicceshi,kamar yadda yayi wani dogo,wani gajere,wani fari wani baqi,wani me kyau wani akasin haka" "Wani me suma me kyau irin taka,wani kuma tashi irin ta yaya sadiqu ko?" Wannan karon dariya ta bashi,har haqoransa suka bayyana "Zaki bayani duk randa kika fada a gabansa,shima sumarsa me kyau ce sosai iman....,amma taki tafi tasa kyau sosai" murna ta cikata,tadanyi tsalle kadan "Don Allah yaya ba na fishi kyau ba?" "Neeeesa ba kusa ba" ya fada yana duban fuskar dake cike da quruciya,murmushi na fita daga kan tata fuskar "To amma me yasa yake cemin me idon mage,mummuna?" Ta tambayeshi tana tura baki,saiya sake sakin murmushi,indai yana tare da iman din bata bari fuskarsa da bakinsa su huta "Ki rabu dashi,kishi yake dake" ta saki qaramar dariya cikin nishadi,tana jin dadin zama da ya lamin fiye da kowa cikin gidansu,duk sanda zai bata amsa,yana bata amsa ne ta yadda zata dace da ra'ayinta da kuma abinda takeson ji,indai yana nan baya bari bacin rai ya zauna saman fuskarta,da irin wadan nan hirarrakin sannu a sannu har suka samu abun hawa,ya kaisu inda daliban shekarar daga makarantun wannan qaramar hukumar zasu zana jarrabawar.         Sai daya tabbatar da shigewarta exam hall din sannan ya juyo zuwa gida,a qafa ya zabi ya tako zuwa gidan,saboda kudin dake gareshi su isa kawosu gida shi da iman din zuwa la'asar idan an gama jarrabawar.         Yana gab da isowa qofar gidan nasu ya hangi yarinyar na tahowa,ubaida 'yar layinsu ce,ya fuskanci duk sanda xasu hadu da yarinyar saita dinga wani sinqe sinqe,idan sukayi clashing kuwa haka zata gaidashi cikin girmamawa,duk da cewa kwata kwata shekarun da ya bata basu wuce biyu ko daya ba,saidai yanayin garin jiki da kuma kwarjinin da yake dashi,zaka zaci cewa wani babban yayanta ne.        Yanzun ma yana kallonta tayi wuf ta shige soron wani gida ta buya,saidai taci gaba da leqensa har ya wuce ta sannan ta fito.        Yana da yawan gumi,don haka sanda ya isa dakinsu ya jiqe da zufa,ya samu sadiqu ya fito a wanka daga bandakin da ba'a dade da yi musu ba cikin dakin nasu,wanda suka hada kudi abinsu shi da saddiqun aka musu,saboda girma da sukaga sun fara,lamin ne ya kawo wannan shawarar,kuma ta kwantawa saddiq din,da yake dakin ma sha Allah yana da girma,don ya dauki katifunsu guda biyu bayan leda me kyau dake malale a dakin,da yake ba wanda yake shigar musu kuma wuni suke wajen sana'a ledar lafiya lau take,sai kujera guda daya doguwa da kuma kwabet ta katako mara tsaho amma kuma tana da fadi,anyi mata bangare biyu kowa da sashen kayansa,kusa da kujerar akwai wani dam teburin na katako da talabijin ta zaune,da receiver a kanta,wadda suka jona daga maqota,dama ba wani kallon arziqi suke ba,sunfi kallo sanda ake ball da wani waje,shima kusan sadiq ne me wannan nacin,lamin din yafi ga sauraren news a redio.        Suna hada ido ya harari sadiq din wanda yake daura tazugen gajeran wandonsa "Baka kyauta ba wallahi,abinda kake sam bai kamata ba" "Allah ya sani bazan iya irin rayuwarka ba,yarinya sai shegen fi'ili da shagwabar banza da wofi,kamar wata yayayya,ayita riritata,yarinyar da an kusa bude mata littafin ayyukanta nan da wasu shekaru kadan" sadiq din ya amsa masa yana zura riga a jikinsa,harararsa lamin ya sakeyi "Idan bamu kula da ita ba da waye ne zamu kula?,ita kadai ce fa a gabanmu?,kuma ma ina wani shagwaban yake?,kaidai matsala ce dakai kawai,kuma idan baka canza ba bazamu taba dai daitawa ba" daga haka yaja towel dinsa dake hannun kujerar ya shige bandaki,yana jiyo sadiq yanata qananun maganganun indai iman bata canza ba shima bazai canza ba.       Kansa kawai ya kada cikin takaici,dukkaninsu har yau sun kasa karantar iman,kamar shi daya shi da.malam ne suka fuskanceta,ba shakka tana da sakalci da shagwaba wani lokacin da gabunta irin na yaran da ake haifa daga qarshe,to amma fa tana da hankali da wata irin nutsuwa,haka kuma tana da fikira da saurin fahimtar abu,ko yaya ka zauna da ita zaka san cewa uwa ta gari ta taka muhimmiyar rawa wajen nutsuwarta da dabi'unta,yarinta kuwa har yanzu bata wuce lokacin ba,so dole sai an dinga mata uzuri ana nusasheta harta wuce lokacin.        Sanda ya fito lallausar sumarsa mai santsi da zaka zaci relaxer yake sanya mata tanata digar ruwa,zuwa sannan har sadiqu ya shiga cikin gida ya karbo musu abun karyawa,kunu ne me zafi sai qamshin lemon tsami yake,sai kuma fanke da qosai wanda ya tabbatar qosan nashi ne,saboda shi fanken bai dameshi ba,qosai ne koda ya huce zai cishi a haka yana jin dadinsa,koshi ko alala,sau tari sadiq na tsokanarsa da cewa "Wai lallai saika nuna kai cikakken bafullaci ne,qauna ce shadidiya tsakaninku dama da qosai" wani lokaci yayi dariya ya barshi,wani lokaci kuma ya rama.        "Yauwa,daga kan plocker dinka akwai saqo gashinan an bani,ka duba" sadiq ya fada yana qoqarin kai cup din kunun bakinsa,ajjiye towel din da yake goge kansa dashi yayi ya qarasa gaban locker din,wadda take dauke da tarkacen kayan shafa na maza,kai kace wani zabgegen saurayi ne,tarin turaruka ne kala daban daban,kama daga roll-on, sure,body spray,body mist masu sanyi,da turaruka na kaya  shaving cream,da body cream masu sauqin kudi,man wanki baki da mayukan gashi na maza,sai kuma man saka takalmi yin qyalli.          Hannu yakai ya dauki farar takardar da aka nannadeta four corners,ya ware a hankali,sannan ya zuba mata sleepy eyes dinsa da suke a lumshe,yana bin yadda aka zane takardar da zanen furanni da kuma tsuntsaye,sannan ya sauka ga saqonnin soyayyar dake rubuce a tsakiyar wani lafcecen heart (zaku iya tunawa da wasiqar soyayya da ake rubutawa zamanin quruciya?,ya kai zunzurutun zinaren mazirarin zuciyata?😂).         Maida wasiqar yayi sama a qasa yana lalubo sunan marubuciyar,sunan ubaida ya bayyana,saiya linke takardar,sannan ya waiwaya ya dubi sadiqu "Yaushe ka mayar dani dan iska ka fara karbo wadan nan abubuwa kana kawomin?,bari to na ajjiye na kaiwa malam,kada wataran ya kamaka ya zaci bakinmu daya,ko kuma ni nake aikenka" da hanzari sadiq ya tashi yana danne dariyarsa yasha gaban lamin dake zura jallabiyarsa ta barci "Kaga.....ni kada ka yimin sharri,ni ina ruwana?,ina zaune ta aiko qanwarta ta kawomin,kaga kenan bani na janyota ba ko bare kace" tsayawa yayi yana duban sadiq din,ya sanshi qwarai da rawar kai,saboda yawancin lokuta idan yaga ana tashi daga aiki lamin din ya biyo masa ya sakashi a gaba sunyo gida,suna isowa anyi magariba sunyi masallaci,saga can sun zauna karatu da malam,ana tashi hira cikin abokansu lamin din baya bari su zarce awa daya zai takura sadiq din kan su shiga gida,ko su zauna a dakinsu suyi wata hirar,ko suyi karatu,ko su kalli ball idan nepa sun agajesu da wuta,ko kuma su zauna tare da inna kafin malam ya shigo,yakan yi qorafin "Waikai.....sai kace wasu mata da Allah,kai ko dan 'yammatan nan da akeyi na layi bamu da,kana gani su buhari fa,yarinyar nan ta bayan layinmu har dan wasiqa suke aikawa junansu" kallonsa kawai lamin yakanyi "Shekararmu nawa ne?" "Sha bakwai mana,ni harda watanni ma" "Tabdijan,a shekara sha bakwan har mukai wannan matakin?,meka ajjiye?,me kake dashi?,wanne mataki ka taka a karatu?" "Mtseeww,ka gane mana,bafa wai aure zamuyi bafa,kawai irin dai soyayyar nan da kowa ke tabawa ce,ai abun kunya ne a yadda mukafi dukka samarin unguwar nan kyau amma ace mune bamu da budurwa" "Nidai a wajena ba abun kunya bane,amma tunda kai a wajenka haka yake,kaje Allah ya bada sa'a" daga haka ya maida hankalinsa ga qaramar tvn dake gabansa,wanda suke hasko wasan da ake bugawa ta gasar nahiyar turai,tsakanin Manchester da Barcelona.        Yana jin sadiqun yana mitar yanzu kallon qwallon ma sudanje gidan kallo suyi cikin mutane amma abu ya gagara,kowa yana can ma su suna cikin gida kamar mayu.         Shi sam irin wadan na shirmen na tashen girma Allah ya tsameshi,baya bashi sha'awa ko kadan,yadda yake gudanar da rayuwarsa yafi masa dadi,shi mamaki ma yake idan yaga sa'anninsu suna soyayya,tome zasuce a wadannan shekarun nasu?,dariya suke masa idan ya fadi hakan,sau tari sukance "Dama mune muke da kyau irin naka?,kai don bakasan yadda 'yar mata matan nan ke sonka ba,miskilancinka kawai yasa suke shakkar yi maka magana".         Hannu lamin ya sanya kan locker din tasa bayan ya gama wannan tunanin,ya ciro wani man fito da saje da qasumba da sadiq din ya siyo tun rannan,wurgi lamin yayi dashi saman kujera "Shi yasa dama ka siyo wannan saboda kayi sauri ka hada gemu kai dole gaka babba ko?" Yadda lamin yayi maganar cikin jin haushi ya sanya sadiq qyalqyalewa da dariya dole "To wai kai din da kaketa haka waliyyi ne kai?,girman nan fa yana tahowa na gaya maka gaskiya,don ko a yanzu haka habarka ta fara gemu,toni kuma saina zauna a haka a rainani?,ko kai rannan ina ganinka kanata matse matse?,waye yayi wankan asuba shekaran jiya?" Ya qarasa fada qasa qasa saboda kar a jiyosu.         Kafin sadiq ya ankara lamin ya kwada masa wani comb da yake taje sumarshi,a baki yaso ya sameshi Allah ya taqaita masa ya goce ya samu kafadarsa,sai yayi qofa yana sheqa dariya "Kaga kenan gwara ni,kiran girman kawai nake,kai kuwa ya fara samunka,idan ka gama shiryawa ina jiranka a wajen inna" saboda wajen sana'arsu zasu wuce,don suna hutu ne saboda sun kammala rubuta jarabawar qualifying,suna jiran wucewarsu S S3,bugu da qari ma kuma weekend ne.         Yana shiryawa maganar sadiq na dawo masa,a ranar ya faki idanun sadiq yayi wankansa ne baisan yana ganinsa ba,bayason sadiq din ya sani,saboda yana kunyar abinda zaice masa,duk da cewa daga shi har sadiq din ba jahilai bane,tun kafin zuwan wannan lokacin malam ya musu bayanin xuwan nasa,saidai shi abun naso yazo masa da wani yanayi na daban,yana jin cewa halittarsa ta dabance,don kusan bai taba ganin ko ji daga sadiq din ya shiga yanayi irin nasa ba.        A nutse ya shirya,kamar ko yaushe tsaf dashi,cikin wani yadi mai sanda sanda me sauqin kudi,yayi kyau,dai dai da matashi mai qananun shekaru.         A tsakar gida ya samu inna da sadiq din,ya miqe suna yiwa inna sallama,ta rakasu da kyakkyawar addu'a da kuma fatan alkhairi,ta bisu da kallo tana jin alfahari da 'ya'yan nata,wanda tsakanin sadiq din da lamin bata banbace wanda tafiso a cikinsu,tun bayan shigowar lamin din rayuwar gidan.       Tun qarfe uku ya katse dukkan ayyukansa bayan ya dauki uzuri waje ogansu ya koma daukar iman din.        Baifi jiran minti talatin yayi ba daliban daga makarantu daban daban suka fara fitowa,yana tsaye harde da hannayensa ya hangota,ya zuba mata idanu yana murmushi ganin yadda take waige waige,ya tabbatar da cewa shi take nema,yadan sake sakayewa kadan don ya gani ko zata iya ganoshi,saidai batayi wani nisan zango ba golden eyes dinta ya hango mata shi,saita taho da dan gudunta ma gauraye da quruciya tana dariya,tana zuwa ta daneshi.         A hankali yasa hannunsa yana zareta daga jikinsa,ita kuma tana sake maqaleshi tare da fadin "Ya lamin mun gama...." "Imaannn" ya ambaci sunanta yana dan dagewa kadan "Sakeni mana" turus tayi bayan ta sakeshi tana kallonsa,baki a tabe alamun shagwaba "Yaya me nayi maka?"ganin yadda fuskarta ta nuna rashin jin dadinta saiya duqa a gabanta yana duban golden eyes dinta "Iman.....daga yau kin girma fa,kin zama babba,ko baki gani bane?,kin zana jarabawar fita daga primary,zaki tafi secondary,duk wanda yaje secondry kuwa ya girma.....wadda ta girma kuma ba'ason tana taba maza kinji?" Saita tura baki gaba "Ni bana kula kowa Allah ya lamin,ko mazan ajimu ma Allah,kaine kawai,kuma kai ba yaya na bane?" Kansa ya gyada yana sake fidda murmushi "Yayanki ne,amma ko nidinma daga yau na hana kinji?saboda kin zama big girl" Kanta ta gyada,saidai da alama har cikin ranta bata gamsu ba,yana ankare da ita yadda tayi kicin kicin da rai,duk yadda yake janta da hira kan yadda taji jarabawar taqi sake masa ta bashi labari,bai gaji ba yaci gaba da janta da hirar har suka iso bakin titi don su tari abun hawa.         Dalibai ne birjik da masu daukarsu,daga gefansa wata 'yar matashiya ce riqe da hannun wata daliba,da alama qanwarta ce,tunda ya shiga wajen dauko iman ya lura da yadda taketa satar kalloshi,dauke kai yayi yanzun ma kamar dazu,ya sanya hannunsa cikin aljihunsa ya fito da baqin glass dinsa da yakan sanya lokaci lokaci.       Sanyawar da yayi saita sake haska kyanshi cikin farar fatarsa,ya miqa hannu yana tsayar musu da adaidaita sahu,gaba kadan dasu ta tsaya,ya taka ya tsaya yana masa bayani inda zai kaisu.        Yana shirin shiga yarinyar ta qaraso tana fadin inda zata itama "Shiga muje" mai adaidaitan ya fada mata jin hanya daya ce,abinda yasa fasa sanya qafafunsa,ya kuma dauke kwandon iman da ya zura a motar yaja baya yana cewa "Kuje kawai" binsa ta danyi da kallo "Dukkanmu qannenmu muka dauko,kowa gida kuma yakeson zuwa,kuma tunda yace muje ai hanya dayace ko?" Ta fada tana dan fara'a,kai ya gyada "Ga wasu 'yan uwanki can daga gaba,idan hanya daya zaku shikena sai ya cike dasu" yanayin fuskarta ya nuna bataso ba,amma haka ta saka qanwartata itama ta shiga.        "Yaya sun tafi fa,dama shiga kawai mukayi" sosai ya kalleta sannan ya amsa mata "Babu kyau hada maza da mata guri daya,nima bazanji dadi ba idan kika shiga keda wani" tadai jishi ne,amma bata fahimta abinda yake nufi ba.       Basu dade ba suka sake samun wani abun hawan,a hanya ya siya mata tarkacen alawoyi,abinda ya sanyata sakewa kenan,ta dinga bashi labarin jarrabawar,da kuma yadda ta amsa kowacce tambaya,don kusan duk abinda ya karanta mata shi taga ya fito. *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 *_TEAM ZAFAFABIYAR_*🔥🔥 *KUFAN WUTA*🔥🔥🔥 NA *HUGUMA* *ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 *LAST FREE PAGE* *_GA WADDA KE BUQATAN BIYAN KUDINTA,ZATA IYA TUNTUBARMU TA WANNAN NUMBERS DIN_* 09032345899 KO 09166221261 Tun bayan zana jarabawarta ya soma mata tanadin tafiya zuwa makarantar gaba ba tare da kowa ya sani ba,ya siya duk abubuwan da yasan zata iya buqata da kadan da kadan,zuwa lokacin ya fara canza yanayin kusancinsu,sabida girma daya fara zuwan mata,a sannan ta shiga shekara ta goma sha uku,duk wasu abubuwa daya kamata ace ta sani yana koyar da ita cikin dabara da kuma hirarsu,abubuwan da ya kamata diya ta sani a shekarun fara girmanta,bugu da qari innarta itama ba baya bace,sau da dama idan ya gaya mata wani abun takan ce inna ta gaya mata,saidai bata fiya daukarsa serious ba kamar idan shine ya gaya matan,tafi maida hankali idan shine ya fada mata da kansa. Cikin sa'a jarabawarsun ta fito,taci wata government school da basu da nisa da ita,ba bata lokaci malam ya fara mata shiryen shiryen komai,saidai ya tadda amin yaci rabin aikin,shuru malam yayi cikin mamaki tare da qara qaunar amin din har cikin jininsa,irin kulawa da iman ke samu a wajensa ko dan uwanta da suke ciki daya sadiq bata sameta ba. Bashi da abinda zaice masa banda godiya,godiyar da take saka amin din jin nauyi da kunya,saboda shikam har yanzu a nasa ganin bai sakawa su malam din da komai ba,don har kwanan gobe arziqinsu yakeci,sun sanyashi cikin iyalinsu,yana kwana ya tashi muhalli daya dasu,kuma har kwanan gobe malam din bai daina ciyar dashi da dauke masa wasu buqatu irin na uba da dansa ba. Duk da haka malam din ya kwakkwafeshi kan ya dinga adani da tanadi,ya daina qarar da duka nemansa akan iman din kadai,ya shaida masa yana taru,bai nutsu ba sai daya samu tabbacin hakan daga bakin sadiqu. Bangaren inna ma saidai addu'a da fatan Allah ya jiqan mahaifansa,amin din hannun kyauta gareshi,abun duniya bai rufe masa idanu ba sam,kulli yaumin baya taba shigowa hannunsa rabbana cikin gidan,wannan dabi'a tasa har sadiqu ya koyeta,hakan kuma bai sanya ya manta da yayarsa dake garinsu ba wadda tasha dawainiya dashi ba,duk sanda zaije ganinta yakan riqe wani abu me kauri yakai mata. Cikin nasara iman ta fara zuwa makarantar,yarinya ce mai hazaqa da kaifin basira,gefe daya kuma ga alamin,ya soke hirar dare saidai karatu,idan sun gama karatun ayi hirar kafin inna ta korata ta kwanta,cikin qanqanin lokaci tayi suna cikin makarantar. Sannu a hankali rayuwa keci gaba da tafiya musu cikin nasara,iman ta gama js 1 ta tafi js 2,har ta tafi zuwa js 3,a sannan tuni yammatanci ya fara zuwar mata,duk wani baiwa da surar kyau na 'ya mace ya fara bayyana a jikinta,wani irin sassanyan kyau wanda hatta da inna ya sanya take sake saka hankalinta da kulawarta akan diyartata,don ko ita duk da tashen kyau da tayi zamanin quruciya bata kai iman din ba,inda Allah ya taimaketa iman din nada wani irin nutsuwa da kuma kamun kai,bata da hargagi ko hayaniya,ko rawar kan yaran da suke tashen girma. Ta bangaren alamin ma ya sanya kulawarsa sosai akan iman din,bama shi ba harda sadiqun da suke ganin kamar bai damu da al'amuranta a baya ba,saboda lokacine na sabbabin qawaye,kuma lokacine da qananun samari da suma suke tashen girma suke iya shiga rayuwar yarinya,su sauya ta tare da koya mata dabi'u kala daban daban. A sannan Allah ya fara sanyawa nemansa albarka,don cikin shagon nasu da suke dinki a yanzu haka shima ya mallaki keke nasa ma qashin kansa,idan bashi da makaranta zama yake ya wuni yana dinkinsa,idan kuma yana da lectures sai ya bada haya wani ya hau,da kudin dinkinsa yake sponsoring karatunsa da komai na rayuwarsa,ya taimaki yayarsa da a yanxu babu abinda zatace dashi sai hamdala,hakanan daga inna har malam gajiyar alamin din sukeci sai godiya. Yana da tsari da kuma bin komai a sannu,bai dauki rayuwarsa da zafi ba,bai kuma dauki kansa a wani ba,komai nashi moderate yake yinsa tsaka tsaki,babu qarya a ciki,baya kallon wai collage yake,dole sai yayi abinda wane da wane sukeyi,idan ka ganshi baka isa ka aibatashi ba ko kai waye,yana da tsafta da sutura ta zamani bakin gwargwado,saidai duk abinda yasan zai zame masa wahala baya kawoshi cikin rayuwarsa,hatta da wayar hannunsa mai matsakaicin kudi ce,bai damu da sai ya riqe babba ba,tunda wannan din zatayi masa komai da babbar zatayi masa,yakanyi tunanin gwara ya sanya kudin cikin sana'ar dinkinsa,don a yanzu wani keken yakeso ya sake siya banda wanda yake dashi. Dukkan wani rufin asiri da kuma kyautatuwar rayuwa ya sameshi,iya shi da sadiqu a qananun shekarunsu sun tsayawa gidan,sun saukewa malam abubuwa da yawa su sukeyi,don hatta da harkar karatunsu,kama daga kudin registration da sauransu su sukewa kansu da kansu. **********Kamar yadda al'adar gidan ranar kowacce juma'a tuwon shinkafa akeyi miyar taushe,wannan juma'ar ma hakan take,gefin magariba IMAN ta gama komai,ta kuma killace gidan kamar yadda ta koya daga mahaifiyarta,saboda a yanzun da shekarunta suke goma sha biyar,dukkan wani aiki da ada yake wuyan innar yanzu ya dawo wuyanta,ta horu da wannan tun tana da shekara goma a duniya,don haka sam komai baya bata wuya a yanzu. Tsaye take gaban dogon madubin dake jingine,wanda ya kusa rabin qofar dakinta,gefe da gefansa sama da kuma qasansa an zagayeshi da katako mai kauri saboda ya bashi kariya,tare da samun damar tsaiwa sosai a muhallin da aka ajjiyeshi. Daure take da zanin data fito daga wanka dashi,sai tasa hannu ta zare dan qaramin hijabin da take xurawa duk sanda zata shiga wankan,take jiqaqqe gashinta daya kwanta har gadon bayanta ya bayyana,yasha ruwa sosai,saboda wankan tsarki da tayi na al'ada data gama. Sai data sanya qaramin towel ta sake goge gashin nata sarai,tadan fifitashi kadan yasha iska,sannan ta shafeshi da mai,ta kuma sanya cumb ta tajeshi,take ya dauki sheqi,cikarsa kuma ta bayyana,taja kujera ya qarama da takan zauna akai idan zatayi kwalliya,ta fara mulke jikinta da mayukanta da take amfani dasu. A nutse ta gama shafa manta,ta shafe fuskarta da powder,tana yi tana duba dan qaramin agogon dake manne a saman mudubin nata,wanda lamin ya siya mata,saboda tashi tafiya makaranta. Gaban akwatinta dake shaqe da kaya ta zauna tana duba kayan da zata sanya din,batason ta saka wadanda zasu dameta,saboda zafi da akeyi,uwa uba ma kuma ba jimawa zasuyi a jikinta ba zata cire ta saka na kwanciya barci. Garin daga kayan idanunta suka sauka kan wasu kaya baqaqe masu adon farin zare,da sauri ta sanya hannu ta daukosu tana waresu,sai yanzu ta tuna dasu,kayan da inna rabi ta bata(yar uwar innarta),kaya ne na buzaye masu kama da saqin fulani,saidai shi plain zani ne da kuma riga mai kama da buba,wadda iyakarta cinya,kala biyu ne kayan,akwai jajayensa,dukansu ta ajjiyesu da zummar zata saka kuma bata saka din ba,sai yanzu data binkito wajen ta gansu. Miqewa tayi ta fara gwada rigar,ta isa gaban madubi,tar kamanninta suka fito,baqaqe kayan sun kwanta saman farar fatarta sun qara mata wani irin kyau,sun kuma tafi da qirar jikinta,duk kuwa da cewa a sake suke,sai ta dan soma jujjuyawa kadan tana sin ta sake ganin yadda suka amsheta,tana qiyasta ranar da zata sakasu. Qwalla mata kiran da inna tayi ya dakatar da ita daga abinda takeyin,tana daga dakin ta amsa tana duba agogi,tasan ba shakka ta gota lokacin da take kaiwa su ya saddiqu abinci,don haka ta rarumi zanin kawai ta daura,ta yafa dankwalin kayan saman kanta. Innar bata tsakar gidan,tabbacin cewa daga rumfarta take mata wannan kiran,bata kai ga shiga rumfar innar ba ta jiyo muryarta tana fadin "Ki dauki abincinsu aminu ki miqa dakinsu,ashe tun yammaci ya dawo bashi da lafiya,bai qaraso ciki ba ya shige dakinsu ya kwanta abinsa,sai yanzu da abubakar ya shigo yake gayamin" har cikin ranta taji wani rashin dadi jin cewa baijin dadi,bai kuma gayawa kowa ba,bayan ita idan bata da lafiya bai barinta tayi jinya ita kadai,tun daga zamanin quruciya har yanzu data fara sanin ciwon kanta,sai ta amsawa innar da to,ta juya da sauri zuwa kitchen,ya debi kayan abincin data riga ta shirya musu,wanda dama ba kasafai take kai musu ba,sunfi shigowa su dauka da kansu,ta nufi soron tana takawa a hankali,cikin ranta tana fatan samun jikin nasa da sauqi. Tana dab da bakin qofar dakin nasu sadiq ya daga labulen ya fito "Ki zubamin a plate ya dan sha iska,yanzu zan dawo" ya fada yana sanya takalminsa,ta amsa da to kana tayi sallama ta saka kanta zuwa cikin dakin. Babu kowa a dakin,sai motsin ruwa daga toilet din nasu,ko ina fes yake,sai qamshin tsintsiyar turare da kuma turarukan da suke amfani dasu daya gauraye dakin,tanason dakin tun ainihi,saboda yafi kowanne daki dake gidan sanyi da kuma dadin zama,a zamanin quruciya,tasha shiga dakin ayita nemanta,har bacci yayi awon gaba da ita. Table din da tasan suna ajjiye karikicen kayan abincinsu ta qarasa kai ta dora a nutse,sannan ta bude fa fara zuba lafiyayyen tuwon farar shinkada,da miyar taushe wadda aka sakawa tantaqwashi,cikin mintuna qalilan qamshi ya bade dakin. Plate biyu ta zuba harda lamin din,saita koma saman doguwar kujerar dake dakin ta zauna,tana dakon ya fito tayi masa sannu,duk ranta babu dadi sosai,dama kusan sati guda suna sabani dashi,basa haduwa sam,inna ta gaya masa yana wasu dinkunan biki ne,shi yasa yake fita da wuri ya kuma dade bai dawo ba,ga kuma makaranta. Tana tausayin yadda yake nema tuquru,ya dauki sana'arsa da muhimmanci,fiye da yayanta sadiq,don shi wasu lokutan yakan zauna a gida yace bazai fita ba,musamman idan lectures suka hade masa ranar yasha wuya,amma bata taba ganin lamin din yana hutu ba,idan tayi magana sai ya saki murmushin dake qarawa idanunsa lumshewa yace "Babu wani hutu a nan duniya,namiji kuma da struggling aka sanshi". Yana da dabi'ar jimawa yana wanka,don haka sai ta tura hannunta cikin gashin kanta tana dan warashi saboda ya sake samun iska,a hankali har dankwalinta ya zame daga kanta,saita kamo gashin ta rabashi biyu ta fara kitsa kalba wai ko zaifi saurin shan iskan. Sai da ya sanya hannu ya sake sharce gashinsa da kyau,sannan ya kama murfin qofar bandakin ya murdata ya bude a hankali cikin rashin qwarin jiki. A hankali idanunsa suka fara sauka a kanta,tayi nisa da kitsa jelar kalbar,kayan jikinta sun haskata ainun,har suna canza mata yanayi zuwa ainihin bafulatanar niger kuma shuwa zam. Bin jelar da take kitsawar yayi da kallo,zuciyarsa ta wani buga,sai ya lumshe idanunsa kana ya budesu duka lokaci daya,maimakon dauke idanunsa da yayi niyyar yi daga kanta,haka sai ya gagara,ya maida idanun nasa yana ci gaba da kallonta "Anya ko zaka iya ci gaba?,zaka iya daurewa?,zaka iya cika alqawarin daka daukarwa kanka?" Jerin gwanon tambayoyin da ya jefawa kansa kenan,sai ya sake lumshe lumsassun idanuwansa da zazzabi ya sake sanyawa suka rusuna suka kuma janye,ya budesu lokaci guda yana qoqarin hadiye wani abu,kana yayi qoqarin jan qofar bandakin ya rufe,lokaci guda kuma yana takowa zuwa cikin dakin,yana qoqarin daure fuskarsa. Motsin nasa yaja hankalin iman,bata damu da rashin walwalar dake fuskarsa ba,saboda tasan cewa bashi da lafiya,qila shine abinda ya kawo qarancin walwalar. "Sannu ya amin" ta fada cikin nuna tsantsar kulawa "Yauwa" ya amsa mata a dan dake,saita sake zubawa fuskarsa idanu,yau kadai sai take ga ya canza mata,wani girma da kwarjini da tsahon rayuwarsu tare bata taba gani saman fuskarsa ba a yau take gani,kodon yaune ta fara yi masa kallon qurilla?,ko don yaune kadai ranar da zata iya tunawa ya hade mata rai haka? "Ina dankwalinki?,me yasa zaki bude kanki gaban abincinmu?,ko so kike ki haramta mana ci?" Yayi maganar still a dake,hannunta ta sanya ta baya ta janyo dankwalinta ta lulluba saman kanta,tun daga sanda ya horar da ita zama da dankwali,mawuyacine ka sameta babu shi,maimakon ya zauna sai ya nufi inda kayan shafarsa suke,ya janyo turaren da yake mulke singalalin hannayensa dasu ya fara shafawar,wannan dalilin yasa komai nashi qamshi yake,komai nasa kana iya ganeshi saboda qamshinsa na daban da yake yawan amfani dashi,abu guda daya cikin rayuwarsa da bai daukeshi da sauqi ba,yana kuma iya sanya ko nawa ne ya siyeshi wato TURARE. Bayan ya gama ya dauki na jikin ya fara fesawa,cikin lokaci qanqani sassanyan qamshinsa ya budade dakin,iman dake zaune ta lumshe idanunta tana zuqar qamshin har cikin zuciyarta,tana mutuwa da mayatar son wannan qamshin tun ba yau ba,tayi tayi ya siya mata ko ya san mata nashi amma ya gaya mata turaren maza ne,mata kuma basa sanya turare maza,dole ta haqura,take amfani da wanda ya zaba mata,har kawo yau. Bata ankara ba taga ya iso gaban flask din,ya bude flask din data zuba dan farfesun busashen kifi datayi musu da sauran kifin da malam ya siyo musu tun shekaran jiya waccar,basu iya cinyeshi ba saboda basu da yawa a gidan "Ka kawo na zuba maka ya amin" ta fada tana kai hannunta da sauri kan kwanukan,saidai cikin rashin sa'a sai hannayensu suka hadu waje guda,saboda ya kawo nasa hannun ne shima don ya zuba,itama takai nata. Da sauri ya janye nashi hannun,zuciyarsa na wani irin lugude cikin qirjinsa,karon farko itama a rayuwarta data ji wani shock har cikin jijiyoyinta,shuru ya ratsa na second guda,kafin ta rigashi sake maida hannunta tana yunqurin zuba masa,tare dayi masa sannu da jiki,ranta da zuciyarta yana bata cewa yau miskilanci ne ya hadu da ciwo hala,abinda ta jima bata gani ba tattare dashi. Idanunya ya sauka kan jelar kalbar datayi guda daya,wadda keya reto gefan kunnenta saboda tsahonta "Da sauqi alhmdlh" ya amsa yana janye idanunsa,tare da lalubar kansa,wai yau din me yake damunsa ne?,kamar yau ne ya fara ganin iman din. Sosai yayi qoqarin hana idanunsa sake maida idanunsa kanta,saboda ya tabbatar a yau din akwai wani sabon al'amari dake shigarsa wanda baisan dashi ba "Shikenan yaya?" Ta fada tana sake nannade jelar kalbar cikin yatsanta guda daya tana kuma kallonshi "Eh" ya amsa mata a taqaice "Allah ya qara lpy" ta fada tana juyawa zuwa hanyar fita,don ta karanci da gaske yau 'yan miskilancin ne a kusa,ta kuma fi kowa sanin halinsa idan suka motsa masa,idan ya sauko da kansa zai nemi inda take,ita kuma tayita qorafi kenan a sannan,saidai yayi murmushi kawai yace baisan sanda shi hakan ta faru ba. Baisan ita yabi da kallo ba sai da ta fita a dakin,idanunsa suka sauka kan labulen dake lilawa,saiya dauke idanunsa da sauri,ya zamo daga gefan katifarsu ya sauka qasa sosai yaja abincin gabansa,yanata qoqarin ganin yaci,saidai duk da hakan tunani ne fal ransa. Yana tuna maganar da sukayi da malam tun yana ajin farko a collage,malam din ya masa kyautar da har duniya ta nade bazai taba mantawa dashi ba,ya shaida masa ya bashi iman din halak malak,ya bashi ita a matsayin matar aure. Sosai alamin yaji girma da nauyin kyautar malam din,bazaice baya son iman ba,kamar yadda bazaice yanajin soyayyarta a ransa ba,soyayya irin ta aure ba,yana mata soyayya irin ta 'yan uwantaka,saidai shi kansa yasan cewa matsayi ya bata a zuciyarsa bana wasa ba,matsayin da take dashi a wajensa ba na nan kusa bane,saidai koma mene a sannan yana ganin tayi matuqar qanqanta ya tunkareta da maganar soyayya,tunda yaci mata buri da kuma tanadi nayin zuzzurfan karatu,ya karba hannu bibbiyu kuma ya samu zuciyarsa tayi na'am da hakan,saidai ya barma ransa akwai ajiyayyen lokaci da zai fara tunkarar iman din da dasa mata soyayyarsa ta hanyar data dace,ta hanyar da bata kaucewa shari'a tsari da kuma al'ada ba,saboda haka ya nemi alfarmar malam din bayan ya gabatar masa da qudurinsa,ya shaida masa babu komai,shidai fatansa Allah ya sake hada kansu,sai gashi a yau rana tsaka ya soma jin wani baqon lamari game da iman din,tun lokaci bai kai masa Target din da yayi ba. *1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_ *1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_ *1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_ *1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_ *1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_ Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 *_TEAM ZAFAFABIYAR_**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_* *_DUK WADDA TASA HANNUNTA TAYI MAN SHARING LITTAFI NA ZUWA WANI WAJE ALLAH YA BIMIN HAKKINA DON ISARSA DA BUWAYARSA_*🤲🏽🤲🏽🤲🏽🤲🏽 *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,ZAKI IYA TUNTUBARMU TA WANNAN NUMBERS DIN* 09032345899 Ko kuma 09166221261 06 Daki ta wuce kai tsaye don cire kayan,tana tafe tana hangen fuskarsa cikin idanuwanta,bata taba ganin wanda miskilanci yakewa kyau ba irinsa ba,ba tun yau ba,tun shekarunta basu kai haka ba tasan da wannan. Sake shanshana hannunta tayi karo na barkatai tana sheqar qamshinsa data dauko wajen saurin bude masa Flask din abincin,saita saki ajiyar zuciya,haka kawai yau din take jin zuwan nata dakinsu wani iri,cikin kasala ta qarasa cire kayan,sai ta zumbula doguwar rigarta kawai,ta dauki littafanta ta tafi dakin inna,saboda yau ta tabbatar babu zancan karatu,tunda amin din baya jin dadi. Sanda ta shiga dakin innar ta fita dubo amin din nata,babu jimawa ta dawo,tana ta mitar yadda ya dawo ya shiga daki ya kwanta da ciwo a jikinsa bai gayawa kowa ba,motsi kadan sai tambayo sadiqu jikin nasa,bata samu sukuni ba sai data tabbatar da sauqin. Wani abu daya tsayawa iman din a rai,yadda ta dinga juyi wajen bacci tana hango fuskar ya amin din,sai zuciyarta ta dinga raya mata kodai laifi tayi masa,qamshinsa daya nacewa hannunta ya dinga shiga hancinta,a ranar ta jima tana juyi kafin ta samu bacci yayi awon gaba da ita. Washegari abokansu na unguwa da wajen aiki daidaiku suka dinga zuwa dubashi,abinda zai baka tabbacin yana da kyakkyawar mu'amala da jama'a,dole inna tasa bayan ya dawo daga makaranta,da zata dora sanwar dare ta qara mudu,ta kammale komai kafin magariba kamar yadda ta saba,ta shiga bandaki tayi wanka saboda zafin da ake dan tabawa,sannan ta shirya ta dawo falo wajen inna sukayi sallar magariba. Tana saman abun salla tana dakon baqin da suka shiga dakinsu ya sadiq din su fita ta shiga ta dubashi,don da safe da zata wuce makaranta ta samu yana barci,data dawo tanata aiki ga kuma 'yan dubiya,abinda yasa wunin yau gaba daya bata ganshi ba kenan,duk sai takejin babu dadi,take kuma ji wani iri,kamar akwai nisa distance dake shirin shiga tsakaninsu kenan,ta lura tun daga sanda ta shiga js2 yayi bala'in sauyawa,ko wasa da dariya da zaman hira da suke ada yanzu babu kaso casa'in cikin dari,saidai kulawar da yake bata babu abinda ya sauya "Naji hayaniyar ta ragu,ki leqa kikai musu abincin,nasan halin amin,indai yana ciwo bason abinci yake ba" tsam ta miqe tana gyara yafen mayafinta data yi sallah dashi,sannan ta nufi kitchen ta debi abincin tayi soro. Da sallama ta cusa kai soron,wata baqauwar murya ce ta amsa mata,matasa ne guda biyu da zasuyi shekaru kusan daya dasu sadiq,daya na zaune saman daddumar da aka shimfida masa saman ledar dakin,dayan kuma na zaune gefan katifar sadiq. Dan daburcewa tayi kadan saboda yadda taga sun zuba mata ido,sam bata saba cudanya da maza ba,uwa uba kuma ta zaci lamin da sadiq ne kawai a cikin dakin,saita taras da akasin haka "Yana bandaki,yanzu zai fito" daya daga cikin samarin ya fada ganin yadda tayi turus,saita duqa a hankali ta ajjiye kwanukan,tana samun waje gefe daya ta tsugunna don jiranshi ya fito bayan ta gaidasu. Shuru yadan ratsa a tsakani,daya daga cikin samarin da tun dazu yake satar kallonta ya fara janta da hira,da qyar take amsa masa tambayoyin da yake mata,qasan ranta haushinsa na kamata,don me zai dameta da wata hira,bayan ita ba itace ta kawota ba?. Minti kusan takwas sannan ya bude toilet din ya fito,jikinsa da lema sosai,har jallabiyar daya sanya tana mannewa a jikinsa. Da ita ya fara hada idanu,kowannensu ya janye idanunsa daga na dan uwansa,wani nauyi yau daya taji idanun nasa sunyi mata,rashin fara'arsa ta kwanakin nan gaba ta sauyashi,ta sanya tana jinsa kamar wani baqo a wajenta. "Ya amin....barka da dare,ya jikin naka?" Sai daya gyada kai yana hadiye wani abu daya tsaya masa na haushi da takaicin junaid,saboda ya lura da irin kallon da yake binta dashi "Da sauqi alhmdlh..... I hope kinje makaranta?" Yayi mata tambayar dai dai sanda sadiqu ke shigowa da lemukan fanta masu sanyi a hannunsa,sai maltina ta gwangwani guda biyu,dama abinda yaje siyo musu kenan,da zummar idan ya dawo yaje ya dauko musu abincin "Naje yaya" "Ma sha Allahu,qanwar saddiq ce da alama?" Junaid ya tambaya idanunsa a kanta yana washe baki,bata amsa ba saiya gyada kai,ta maida idanunta tana kallon yadin mayafin dake jikinta kamar ba bata ba "Tubarakallah......kina aji nawa yanzu?" "Js 3" "Kune 'yan placement na bana ko?" Sai ta sake gyada masa kai kawai,don ta ankara da yadda ya lamin din yayi dif kamar baya dakin,hasalima man shafawarshi yake budewa zai shafa,saidai fuskarshi a dinke take tsaf "Muje ki lalubi cokula ki bani" sadiq yayi saurin fada sanda junaid ke qoqarin jefa mata tambayar,abinda ya sanyata miqewa sadiq yabi bayanta,duk da hakan sai da junaid din yace "Kaje ka dawo muyi magan.....ko mu fara da amin kafin ka iso" ya fada yana dariya dariya,daya dan saurayin yana tayashi,suna dan duban amin da suke zaton zai tanka,saidai baice dasu komai ba,hakanan yanayin fuskarsa na nan a dinke,abinda yasa ya musu kwarjini ya kasa maganar dashi,don dama tuni sun dade da sanin halinsu,tun suna 'yan qasa da shekara sha takwas,lamin din ba kowanne yayin magana da shirmen magana yake tankawa ba. Har sadiq ya dawo da spoon din ya zuba abincin suka fara ci yanayinsa bai koma dai dai ba,yanajin sanda junaid din ke neman izini daga wajenshi ko sadiq din ya gana da iman,domin yace shikam ta gama yi masa,yadda yaketa kodata da yabata yasa wani abu yayi masa tsaiwar mashi a wuya,ya dinga jin kamar ya kai masa naushi a fuska,abinda ya sanyashi miqewa ya fice zuwa qofar gidansu ya zauna saman dakali. Fayau yau qofar gidan yake,saboda kusan dukkan almajiran malam sun tafi ganin gida,sau biyu dama yake barinsu suje duk shekara ganin gida,su kuma dawo lokaci daya sanda ya sanya musu. Iskar zafi na kadawa sosai ta wajen,sai ya jingina bayansa da ginin qofar gidan,ya lumshe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya,saman harshensa yana jin wani daci daya tabbatar bayan na rashin lafiyar da yayi,harda mugun kishin iman din daya tsinci kansa a ciki. Baisan ya akayi haka ba,daga jiya zuwa yau gaba daya iman din ta birkita zuciyarsa,sonta ya taso masa da wani irin qarfi da a baya bai taba jin makamancinsa ba,daga jiya zuwa yau kuma da abokansu wajen mutum hudu ke taya iman din sai yaji ya kasa sukuni,shigowarta na qarshe da daddare kawo musu abinci ya sanya yayi mata kallon qurillar daya tabbatar da cewa eh tabbas ta girma ta kuma fara zama budurwa. Bai dauka cewa girma zai zowa iman din haka gadan gadan ba,duba da yanayin jikin fulani da take dashi,to ashe duk ganinta da yake cikim hijabi yasa yake wannan hasashen,girma da murjewa take ta ciki ba tare da an ankara ba,har ga Allah bazai iya fadan yadda ya dauki bashi itan da malam yayi da matuqar qima da daraja ba,saboda kima da mutuncinsu da yake gani,to amma ya sakawa ransa cewa bazai tunkari iman din da wata magana ta soyayya ba a yanzu,zaici gaba da bata kulawa ne kamar yadda suka saba a baya,har sai ta shiga ajin qarshe ko na kusa da qarshe na kammala secondary dinta. Tun ba'ayi nisa ba ya gane akwai gyaran daya kamata yayiwa tarayyarsu,kamar yadda suke kusa da juna koda yaushe din nan ya kamata ya janye,ta dinga kallonsa a matsayin yaya da gaske,don tun farkon girmansa ya fuskanci cewa yana da wata dabi'a a halittarsa a matsayinsa na da namiji na yawan sha'awa,inda Allah ya taimakeshi me yawan kamewa ne shi,banda hakan......yadda 'yammata ke mutuwar sonsa.....iya cikin matan dake kawo musu dinki kawai,banda na 'yan ajinsu a makaranta,gefe guda kuma ga 'yan unguwa da sauransu,wannan ya sanya ya sake janyewa iman din,abinda yaketa bata mamaki kenan da taraddadin shin me tayi masa ne?,duk da cewa qasan ransa shima baijin dadin hakan,saidai hakan shine dai dai,kuma zai sanya nutsuwa a zukatan malam da inna,koda basu nuna masa hakan saman fuskarsa ba. Tsakiyar tunaninsa yaji hayaniyarsu junaid suna fitowa,suka masa sallama ya amsa musu sama sama,ya bisu da kallo sanda sadiq ke taka musu zuwa bakin titi sunata hayaniyarsu irin ta samari,sai ya bisu da kallo har suka dan kaucewa ganinsa. Ba jimawa yaga dawowar sadiq din,ya qaraso inda yake zaune ya dafa kafadarsa "Tashi mu koma ciki,wajen na akwai sauro,ko gama warkewa bakayi ba kazo ka zauna ka baza masa jikinka yanata gutsira a banza" yunqurawa yayi ya miqe cikin qarfin hali yabi bayan sadiq din zuwa cikin dakin nasu. Sunwa wajen kaca kaca kamar yadda akasan yanayin cin abincin maza samari yake,yana jin sadiq din ya buda murya ya fara kwadawa iman din kira,yasan kuma cewa zaiyi tazo ta gyara wajen ta kwashe kwanukan,sai lamin din ya dakatar dashi "Dakata malam,kuturu ne kai da bazaka iya kai kwanuka ba?,ni idan na gama zan gyara wajen,daga yau ma banason ta sake kawo abinci indai akwai baqi a ciki,saidai idan kaine a ciki" waiwayowa yayi ya zubawa lamin din ido,ya karanci tsabar gaskiyarsa yake fada saman fuskarsa,sai ya saki murmushi ya dawo ya zauna gefan lamin din "Duk da cewa bani na kar zomon ba....amma zan baka shawara,kada ka tsaya kallon ruwa kwado yayi maka qafa,diya mace duk yadda kake raina girmanta tasha kan tunaninka,kana mata kallon kamar tayi qanqanta da soyayya,ka gwada mata bayani kaga idan bata dauke karatun ba gaba daya,ni na rasa abinda ma kake jira,an maka kyauta an kuma baka dama amma ka tsaya wani tsari naka?,ka saka kai kawai,Allah ya bada sa'a" sadiq ya qarashe yana dukan kafadar lamin. Yana cin abincin yana tattauna zancan shi da zuciyarsa,akwai kunya soyayya da yarinya tsakanin mahaifinta da mahaifiyarta,mutanen da yake musu kallon mahaifansa,abu daya ya yankewa ransa,zai fara bata kulawar data banbanta da irin wadda yake bata a baya,zai fara dafa zuciyarta da soyayya ba tare da ya furtata gareta ba,ta yadda da kanta zatayi dako ta kuma zaqu da ranar da zaya furta mata din,saiya saki wani murmushi wanda ya qawata fuskarsa data dan qara haske kadan sabida zazzabin da yasha. *********Kamar kowacce rana da bata da makaranta asabar ko lahadi,yauma haka ta tashi tayi dukkan wasu aiki na gidan,kama daga shara wanke wanke da kuma dora karin safe. Ta gama komai tas inna na daga rumfarta tana sallar walha,ta debo kayan data bata din zuwa bakin famfo nan tsakar gida,sannan ta koma kitchen tana goge duk inda ta bata din. A nutse yake takowa zuwa cikin gidan,sanye da jallabiyyarsa da yake amfani da ita yawancin lokuta idan ba fita zaiyi ba,hannunsa riqe da ledar da mlam ya bashi ya kawo cikin gidan bayan sun gama karatun da sukeyi duk safiya da wurwuri bayan an tashi almajirai. Kai tsaye ya isa rumfar inna da sallama,ya cire slipper dake qafarsa ya shiga. Tana zaune saman abun sallah tana jan carbi,fuskarta ta wadata da murmushi sanda ya tsuguna a gabanta yana gaisheta,cike da kulawa ta amsa masa tana sake tambayarsa qwarin jikinsa,duk da cewa ya warware "Alhamdulillah na warware ai inna,yau ma zan fita aiki in sha Allah" "Ma sha Allahu,Allah ya qara lafiya" "Ameen inna...ga wannan ledar,malam ne yace na kawo a dafa masa" "Tana kitchen ai,saika miqa mata,kace kada ta cika masa yaji da yawa" innar ta fada bayan ta bude taga meye a ciki,ya amsa da to ya miqe tsam da ledar ya nufi kitchen din. Ta bada hankalinta ga aikin da take sosai taga kamar inuwar mutum cikin kitchen din,abinda ya sanyata zabura kenan,ta waiwayo da sauri,har tsummar hannunta tana faduwa a qasa. Idanu suka hada dashi,yana tsaye jingine da jikin qofar,ya zuba mata idanu yana binta da kallo,gabanta yayi wani mugun faduwa,kamar karo na farko kenan data taba ganinsa,cikin sanyin jiki ta duqa don ta dauke tsummanta tare da cewa "Ya lamin.....ka bani tsoro" kusan a tare suka duqa din,shine ya samu nasarar dauke mata tsumman,suka dago a tare,idanunsu ya fada cikin na juna,yadan ja baya kadan saboda sunyi kusanci da yawa,ya miqa mata yana ci gaba da kallonta tare da cewa "Dama can matsoraciyar ce" idanunta ta janye daga nasa,saboda nauyin da taji zuciyarta nayi,qamshin turaren jikinsa yana busowa zuwa cikin kitchen din,kai bakace baiyi wanka ba,tsabar abotarsa da turare ne kawai,yayi wani fresh 'yar cutar da yayi kwana biyu,sai sumar kansa dake adan hautsine saboda bai gyara ta ba,daga sallah makaranta suka zauna kawai,hakan kuma sai ya qara masa kyau. "Yaaa banfa zata ba" ta fada da salon shagwabar data saba masa magana a baya,sautin muryarta yaji ya tabashi,ya kuma saukar masa da kasala,ya sauke boyayyar ajiyar zuciya,tare da dora ledar hannun nasa kan kantar da take gogewar "Barka da safiya yaya,ya jikin naka?" Ta furta tana kaucewa kallonsa,saboda wani yanayi da takeji duk sa'ar data kalleshin "Alhamdulillah,na warware.....gashi nan,malam yace adafa masa,inna tace karki cika yaji da yawa" a marairaice ta waiwayo "Yaaya,na gama komi fa,Allah saura wanke wanke,kwanciya nakeso nayi" yadda tayi masa maganar ya sake tafiya dashi,sai ya harde hannayensa a qirji ya zuba mata idanu harta gama,duk da bashi take kallo ba,amma tanajin idanunsa a kanta "Yanzu idan mijinki yace yanason ki dafa masa abu kamar haka hakan zaki ce?" Banbarakwai taji maganar tasa,fa waiwayo da sauri sai taga ita yake kallo,fuskarsa ta wadata da murmshi "Inna na miki haka ne saboda tanason ki gina gidanki da kulawa,ki shagwaba mijinki da soyayyar da zatasa ki tsaya masa a zuciya" wata irin kunya ce ta rarrafo ta rufeta,saboda yanayin yadda yake mata maganar kawai ta sanya taji kamar qasa ta tsage ta shige,wannan kuwa ya lamin dinta ne?,magana yake mata da wani irin sound da bata sanshi dashi b,wani irin kallo na daban da sexy eyes dinsa,gaba daya taji kaman ya zare mata laka,sai ta juya tana ci gaba da aikin a hankali,kunya na nuqurqusarta. Bata ankara ba har ya dauki kwanon dake kusa a ita ya juye kifin a ciki yana cewa "Tunda raguwa ce ke bari na tayaki" tare suka dawo tsakar gidan,tana wanke wanke,shi kuma yana gyara mata kifin,gaba daya sai ta jita cikin wata takura da bata taba jin irinta ba tsakaninta da lamin din,saboda duk wani motsi ko daga kai da zatayi saita samu tagomashin wani kallo da ta kasa farrasa na meye?,saidai yana sanya zuciyarta karyewa da kuma yin laushi. Ya sakankance sosai abinsa,yanata aikata mata da kallon da yake da tabbacin zai wuce kai tsaye zuwa cikin zuciyarta ne yayi masauki me kyau,koda bai furta komai a gareta ba,baya da fargaba saboda inna tace zata shiga tadan kwanta,malam kuwa yayi baqi a waje,wanda yasan yawanci idan sukazo sukan dauki awa biyu tare kafin su tafi,sadiq kuwa baida matsala dashi,shi ba baqonsa bane bare yaji kunyarsa. Kusan tare suka gama komai da ita,sannan ya wuce dakinsu bayan ya sanyata ta saka masa ruwan wanka. *HILTI UNISEX CHOCOLATE* *_chocolate ce ta musamman daga qasar TURKEY_* *_Maganin matsalarki hajiya keda mai gida cikin tsari babu yane yamen magunguna_* *Ki tuntubi wannan number don k'arin bayani* 0818401745207 *_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA KUMA BASU HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI AMIN._* __________________________________ _SAKINA VENDIBLES_ _SAKINA VENDIBLES_ _SAKINA VENDIBLES_ _(INDE HARKAR TURARUKA NE MASU KAMA JIKI DA GIDAH KAI HARDA TSUGUNNO. SAKINA VENDIBLES ITACE KAN GABA)_ _SUNA DA KAYA INGANTATTU MASU MATUKAR KYAU AKAN FARASHI MAI RAHUSA.)_ _KINASON ASAN KIN ISA MACE? WADDA ZAKUYI GOGAYYA DA MASU SAKA DESIGNER TURARE AMMA KI FUSU KAMSHI? DUK INDA KIKA GIFTA ASAN EH. KEDIN TABANCE , KIN ZARCE SAURAN MATA)_ _AKWAI KHUMRAH WHITE AND BLACK_ _KULACCAM BLACK (FOR HAIR( AND WHITE FOR BODY_ _WASU DAGA CIKIN KAYAYYAKIN MU SUN KUNSHI👇_ Turaren wuta list* Queens special Kajiji mix Kajiji whole Gabgab Brown Hawiii Special Halut Sandal balls Sandal strips Sandal flakes Dubai oud White Hawii Classy Dufr Black bange Black bange Musky Dorrot(Na tsuguno) Cous cous *_DA SAURAN SU DA YAWA_* *_Handles_* *Instagram* @sakina_vendibles *Facebook* @Sakina vendible *Tiktok* @Sakina vendibles_ Tsaye take gaban mudubin nata tana karanto addu'o'i,bayan ta gama shirinta tsaf na tafiya makaranta don zana jarabawar placement,kamar kullum,tayi kyau cikin uniform din da a kullum idan ta saka zaka dauka ta sanyashi ne da nufin gayu ko ado,saidai sam ba haka bane,qirarta ce,haka Allah ya yita,fatarta na daukar kowanne irin nau'in dressing. Lokaci daya gabanta ya dan fadi,ta kuma lumshe idanunta sanda ta jiyo muryar ya al'amin yana tambayar inna bata fito ba,wannan wani baqon yanayine da bata jima da tsintar kanta a ciki ba,a duk sanda zataji murya ko motsin ya al'amin din. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana wara idanunta da suka dauki mintuna a kulle sanda ta tsinci muryar inna tana kiranta,cikin yanayi na me kama da me alhini ko tsoron haduwa da ya al'amin din ta zura takalmanta half cover masu kyau,wanda al'ameen dinne ya siya mata,kamar yadda fiye da rabin komai nata da take amfani dashi na rayuwarta. Dashi suka fara hada idanu sanda ta fito tsakar gidan,saita sauke idanunta daga kanshi da hanzari saboda yanayin kallon da ya jefeta dashi,wanda shi kansa baisan yayi ba,tayi masa kyau sosai yau din,duk da ya saba ganinta amma yau din kamar an qara mata girma da shekaru,itama cikin ranta take tadinshi,yayi wani kyau cikin shadda light blue daketa qyalli,bisa alamu sabuwa ce kar,yau ya fara sanyata,hakan kuma baya rasa nasaba da daurin auren dan abokin malam din da zashi,wanda malam dinne ya wakiltashi yaje,saboda a jiya shi ya wuce Niger,can dangin inna da akayi mata rasuwa zai musu gaisuwa. Ko kadan bata zargi kanta kan yadda takejin sauyi da baqunta tattare da ya al'amin din ba,saboda ita kanta tana ganin kamar shima ya sauya,kallo da yanayin firarsu gaba daya ya canzata,bata saba jin nauyinsa ba idan suna hira a baya,tana hira dashi kamar yadda takeyi da ya sadiq,amma a yanzu tanajin akwai wani banbamci a tsakaninsa da ya sadiq din. Tana qoqarin gaidashi inna ta fara mata fada "Kinsan yana jiranki zaki shiga ki zauna....." "Innaaa.....bansan lokaci yayi bafa....girkin nan shi ya cinyemin lokaci" ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba,boyayyen murmushi ya kubce masa,abun ya zame mata cikin jininta,ta saba maganarta a haka,abinda ke sake daukan hankalinsa dangane da ita kenan,duk da yana qoqarin boyewa da kuma dannewa "kaima duk da kai aminu,da tafiyarka,tasan hanya ai,ta tafi da kanta" Baice komai ba,yadan saki sassanyan murmushin nan nasa,sannan ya matsa inda ta hada komai nata ya sanya hannu ya dauka yana fadin "Mun wuce inna,daga wajen daurin auren shago zan wuce" "Ba zaka dawo ka karba abin karin naka ba" sumarsa irinta buzaye daketa qyalli ya shafa da hannunsa "Ina da ayyuka da yawa ne inna.....akwai dinkin wata amarya da nake,nace mata tazo jibi ta karba,banaso tazo ban gama ba" kai inna ta gyada,ta sanshi da matuqar qoqari wajen cika alqawari,mutum ne shi kaifi daya,mai matuqar qoqarin ganin ya cika alqawari,sam bashi daga cikin jerin layin teloli "Haka ne,to Alla ya dafa ya tsare mana ku,sai kun dawo" "Ameen inna" suka amsa gaba dayansu,sannan ya sanya iman a gaba suka fice. Cikin jikinta take jin kunya nauyi da kuma wani irin yanayi,yayin da shi kuma tunaninsa yayi nisa game da yadda zai tafiyar da koma a tsakaninsu bisa tsari da tsafta,tafiyar sai tazo da sabon salo,saboda ba haka ya saba rakata zana jarrabawa ba,sau biyu tana satar kallonsa,ya ganta sarai,amma sai yayi kamar bai ganta din ba,har zuwa sanda sukayi tsaye a bakin titi suna jiran abun hawa,daga layin cikin layin da yake facing dinsu,wata mata dake sanye da uniform fari da ash,wanda hakan ke alamta ma'akaciyar jinya ce wato (nurse) take tunkaro bakin titin,dukkaninsu sun ganta,har zuwa sanda ta iso titin daga daya tsallaken ta tsaya "Kamar haka nakeson ganinki.....ina miki sha'awar karatun jinya,ina miki sha'awar ilimi me zurfi"muryar al'ameen wadda ta fara cika da amo na mazantaka a 'yan watannin nan ta ratsa kunnen iman din. A hankali ta daga kanta ta sanya dubanta ga matar,tun ba yau ba dama ta sani wannan shine burin al'amin din a kanta,ta dade da haddace hakan,kusan kowa a gidan ya sani,don haka sau tari idan suna irin wannan hirar ma babu me ce musu uffan,tsakaninsu ne "Kiyimin alqawarin zaki cikan wannan burin" cikin mamamki kalamansa ta daga idanu kamar zata klalleshi amma kuma ta kasa,saboda tuna yadda take ji,da kuma yadda idanuwansa ke mata nauyi yanzun a jiki da zuciya "Bake da kula kowanne irin saurayi,bake ba soyayya" lafazin nasa ya ratsa ta tsakiyar tunaninta ya katse mata shi shi wani sauti mai taushi kuma qasa qasa. Wata irin kunya ce ta dirarta mata,ire iren maganganunsa kenan da suke caza mata kai,da kuma sake sanyata jin kunya da nauyinsa,maganganun da a baya baya mata su,tadan sadda kanta qasa,qaramin murmushi yana qwace mata "Eh,wannan ce hanya daya da zaki taimaki cikar wannan buri nawa,ki bari,idan lokaci yayi,ni zan zaba miki ɗanɗasheshen miji da zai dace dake" qarasa rufeta kunyar tayi,sai ta kare fuskarta da hannunta tana cewa "Ni ban kula kowa ya al'ameen,kuma ma waye zai kulani nima?,dubeni fa?" Murmushi ne ya qwace masa sanda ya saka hannu yana tsayar musu da wata adaidaita sahu sannan ya bata amsa "Kina da kyau imani....ke kyakkyawa cw ta ajin qarshe ko farko zance,irin kyan dake jan hankalin kowannw namiji....wanda ke ba zaki gane hakan ba,amma a taqaice,ke sarauniya ce" wanda tun daga ranar ta samu sunan queen daga wajen al'amin,sunan da ya koma kirata dashi lokaci lokaci,musamman idan ya zamana babu malam ko inna a wajen,don ta sadiq dama ya maidashi kamar wani kakansa,ba wai kunya ko nauyinsa yakeji ba,yayin da sunan ya tsayewa iman,yake kuma matuqar yi mata dadi,zuciyarta nata mata saqe saqe akan al'amin din,me yasa ya canza?,me yasa yanzu yake tsaye mata a rai?. Cikin guntar karatun litattafan hausa data fara a boye ya samu amsoshi da dama,saidai kuma har yau bai furta mata ina sonki iman ba,to hakan meyake nufi?. *******. ******. ******** Tun dazun data zauna a wajen hankalinta yake rabi da rabi,daya a wajen,daya kuma ya karkata kan jinkirin shigowar al'amin gidan yau,sau biyu tana tura almajiran gidansu suna gano mata rumfar karatu ko yana wajen malam sai ace mata baya nan,tunda ta gama ayyukanta tayi alwalar magariba ta shimfida musu tabarma ita da inna a nan wajen sukayi sallah take saka ran shigowarsa,amma shuru kakeji,gashi har qarfe tara na dare na haramar yi,har sadiq ya shigo yaci abincinsa ya sake fita. Ta gwada kiransa ta wayar inna kuma sau uku ana ce mata a kashe wayar take,har inna dake jin radio ta rage sautinta tana jajjabin rashin shigowar tasa,wanda bata sauke ba sai ga sallamarsa. Wani boyayyar ajiyar zuciya da batasan daga inda ta taho ba iman din ta sauke,shi dinma koda ya shigo idanuwansa suna kanta,ta miqe a kunyace a kuma nutse tana gyara daurin dankwalinta tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa tana yunqurin karbar ledojin hannunsa "Yauwa Queen" ya furta qasa qasa yadda innar ba zata jiyo ba,saita saki murmushi tana dora kayan saman daddumar data tashi a kai,inda shi kuma ya qarasa yana zama a kai tare da yiwa inna barka da gida,ta miqe daga kwanciyar da take tana amsa masa tare da tambayarsa dadewar da yau yayi,har tana shirin tura sadiq ya dubosa. Murmushi yayi yana jin dadin yadda har kullum inna ke nuna masa qauna da soyayya irinbya da da uwa "Aiki ne yau ya riqeni inna,ban gama musu ba,kuma gobe zasu shigo da safe su karba,na katse ne na shiga kasuwa,shi yasa dinkin ya kaini har dare" jinjina kai inna tayi,tana sake jin qaunar al'ameen din cikin rai da zuciyarta,har kullum shi mutum ne dake sanya cika alqawari gaba da komai a rayuwarsa,ya tsani saba alqawari "Sannu da qoqari,Allah yayi jagora" "Ameen inna" . Iman na daga kitchen tana qoqarin hado masa abincinsa tare da dora masa ruwan wanka take jiyo hirar tasu,ta hada komai a nutse a kuma tsaftace kamar yadda inna ta horar da ita ta fito dashi zuwa inda yake zaunen. "Sannu da aiki autar inna" ya furta cikin kulawa,ta saki murmushi bayan ta duqa ta aje a gabansa "Kinga bar abincin nan,zo kiga.....siyayyarki ta tafiya nasreen memorial academy" sosai maganar tayi mata ba zata,makarantar da inna ta kusa dukanta a kanta,saboda yadda ta nace ta kafe tanason makarantar,ita kuma inna ta haneta da zancanta,saboda private school ce da duk term ake biyan kusan dubu goma sha biyar,innan kuma tasan matsawar alamin din yaji tofa sai ya kaita,shi yasa ta sanyata a daki ta ja mata kunne,koda ta sanarwa malam murmushi yayi "Bansan ko tabarar auta ke damu hajar ba,banda haka.....yaci ace wasu abubuwan zuwa yanzu tafara ragewa,yaron nan hidima da kuma bautar da yake mata ko ciki daya suka fito iyaka kenan,kinyi dai dai,taci gaba da zuwa ta gwamnatinta yadda ta saba,tunda ita takeyi tun tasowarta,kuma tana da basirar gane abubuwa,gashi lafiya lau komai ke tafiya" Laqwas jikinta yayi sanyi sanda yake fiddo siyayyar da yayi mata yake kuma shaida mata sati me zuwa zata fara zuwa,an gama koma,idanunta suka ciko rau rau da qwalla tana satar kallon inna,tana tsoron kada tace itace ta tusashi gaba ka dole sai ya kaita,ko kuma ita ta gaya masa zabinta. Ta bangaren innar ma jikinta sanyin yayi,wane irin yaro ne al'ameen din?,ta tabbatar yinin da yayi har dare a shago kudin wannan siyayyar ya hada ya kashewa iman din gaba daya,tabi kayan da ya zazzage din da kallo,litattafai ne tari guda, school bag,takalmi me kyau da 'yan makaranta,biruka da pencils,hatta da uniform din makarantar gashinan a dinke a goge sai sanyawa kawai. Fada sosai inna ta rufe iman dashi,wannan karon harda al'amin din,kan me yasa zai dinga biyewa iman din da duk abinda tace tana so,ita din 'yar wace da bazata ci gaba da zuwa makarantar gwamnati ba,kamar yadda saura suke zuwa?. Sosai yaji babu dadi saboda kukan da yaga iman din tanayi,saida inna ta soma sassauta fadan sannan ya mata magana cikin kwantar da kai,yana mata bayani zafa fahimta banbamcin karatun makarantun gwamnati da kuma da na kudi,tare da nuna mata shima yana sha'awar ya canza mata makaranta dama,bawai ita ta sakashi ba,ya dade yana wannan tanadin. Saida inna ta tabbatar ba iman ce ta tursasashi ba sannan ta fara saukowa,saidai duk da haka bata bar mita ba "Yanzu kai da kake da nauyin 'yar uwarka a ka,ga naka karatun,sanna kuma ka dauka duk wata lalurar iman ka rungume?" Murmushi kawai ya sake "Ba komai inna,Allah zaiyi,mudai aci gaba da yi mana addu'a.....sannan don Allah inna karki sake cewa komai sadiq yaji" ya fada da sauri,saboda jin muryar sadiq din dake shigowa da sukayi,kuma yaga reaction na fuskar iman,yasan sadiq din dan hada waje ne,maimakon ya gyara saidai ma ya bata,saidai duk da hakan daya shigo shima sai daya tofa albarkacin bakinsa,magana dai bata mutu har shigowar malam,shine ya yayyafawa abun ruwa,ya sanya albarka a ciki,ya kuma ja kunnen iman,sannan ya kebe da al'amin din bayan kowa ya tashi ya basu waje. "Yanzu kai malam al'ameen haka za'ayi dakai?" Cikin fargabar ko wani laifi ya yiwa malam ya daga kai ya dubeshi,malam din ya fahimci abinda ke yawo saman fuskarsa,sai ya saki murmushi "Kai da zaka zama magidanci nan gaba,haka zaka zauna sai abinda takeso zakayi mata?,shifa namiji kullum so ake ya zama tsayayye,yana da kyau a dinga bawa mata dama kan raayi da zabinsu,amma kuma bafa akan komai ba,qarqashinka zata zauna nan gaba kadan,to dole tun yanzu ka dinga azata akan tsari da tafarkin da kakeso ta kasance akai" cikin hikima malam din ya dinga nusasheshi,daga bisani kuma suka fada hira,wanda wannan ba sabon abu bane dama tsakaninsa da malam din ba,sunawa juna kallo da da mahaifi ne. Ya jima yana nazari kan maganganun malam,su suke ganin kamar yana biyar son ran iman dinne,wanda sam shi ba haka bane,duk abinda yakewa iman....tun kafin ya soma jinta da wani matsayi daban a cikin zuciyarsa kawo yau,yana mata ne saboda ta cancanta ta kuma dace yayi mata hakan,sau tari kuma zabu da ra'ayinsu ana samun arashi yana zuwa daya,iman din ta dabance cikin rai da rayuwarsa,duk da yana ganin abubuwa sosai tattare da ita,ita dinma kamar ta canza,amma nan gaba kadan zai qarasa bude mata komai,yana son yabi komai ne bisa tsari na hankali da dacewa,da wannan ya kwanta a ransa. *ZAFAFA BIYAR 2022* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKANFARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA_ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 YAN NIJAR 👇 +227 95 16 61 77 Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_*08 *_LITTAFIN KUDINE,ZAKI IYA TUNTUBAR WADAN NAN NUMBERS DIN DON SIYAN NAKI_* 09032345899 Ko kuma 09166221261 _______________________________ Misalin takwas da rabi na safiyar ranar litinin din,zaune take saman doguwae kujerar dake falon principal din nasreen memorial academy,tayi neat cikin shigar uniform din makarantar da shima ya karbeta fiye da makarantar data baro,idanunta sunyi narai narai tana kallon al'amin daya miqe yana sallama da principal din,bayan sun gama komai shi da sadiq sun damqata ga hannun hukumar makarantar,baqunta take ji sosai cikin wannan makarantar,tamkar yau ne rana ta farko data fara zuwa makaranta,al'ameen ya waiwayo a nutse ya sanya hannunsa a aljihun wandon lallausan yadin jikinsa da iya tsahon rigar ya tsaya a gwiwarsa,ya ciro 200 ya miqa mata "Idan ba zaki iya komawa gida ba ki jirani na dawo,sai na maidake" hannu tasa tana amsa "Zan iya yaaya" ta amsa mishi a tausashe,principal din yayi murmushi "Wannan qanwar taka da alama kana ji da ita" ua fada cikin salon barkwanci,sai al'amin ya waiwaya ya dubeshi sannan ya saki murmushi "Auta ce" "Oh....i see" ya sake sakin murmushi ya musu sallama yabu bayan sadiq suka fice. Tana zaune nan tana rarraba idanu,har principal din ya kira daya daga cikin masu goge goge dake aiki a makarantar,tayi masa kiran Assistant monitor din ss 1,ba jimawa ya dawo yace tana zuwa. Ba'a rufa minti biyar ba tayi sallama,cikin nutsatsiyar muryarta,tana sanye da uniform irin na iman din,iman din ta bita da kallo,tana da haske saidai baikai nata ba,tana da madaidaicin kyau,a qiyasce shekarunsu zasuyi daya da ita "Ga new student nan,ayi mata seat,sannan a shigar da sunanta cikin register" "Okay sir" ta amsa a ladabce,sannan ta waiwaya zuwa sashenbda iman ke zaune. Suna hada idanu ta sake mata murmushi,saita soma takawa zuwa inda take din tana dubanta,har yanzu kuma murmushin bai bar kan fuskarta ba,ta duqa ta dauki hand bag din iman din tana cewa "Taso muje" saita miqe tana dan jan rigarta tabi bayan yarinyar. Tare suka jera cikin yanayin baqunta,saita waiwayo ta sake sakar mata murmushi "Sunana munira hasan......nice assistant monitor na ss 1,monitor dinmu namiji ne.....kefa,meye sunanki?" "Hajar ibrahim khalil" "Yadda kike da kyau haka sunanki yake da dadi" munira ta fada tana sakin murmushi gami da kallon iman. Martanin murmushin iman din ta maida mata tana cewa "Na gode" sukaci gaba da takawa,maganar muniran na maimituwa a ranta,sai ta sanya hannu ta shafi fuskarta a fakaice,an jima ana fadin ita me kyau ce,saidai ita bata taba ganin kyan ba a karan kanta,hakanan bata taba baiwa maganar wani muhimmanci ba. Kai tsaye munira ta kutsa kai cikin ajin,wanda ya dauki shuru,kowa ya bada hankalinsa ga allon da malamin dake tsaye yaketa cikashi da rubutu daliban suna kwafa suna mayarwa zuwa ga litattafansu. Sallamarsu sai taja hankalin kowanne dalibi dama matashin malamin dake tsaye gaban allo,ta qarasa daura da malami tana cewa "Sir,sabuwar daliba ce inji principal,yace a saka sunanta cikin register" kai ya gyada gami da cewa "Okay"idanuwansa nakan fuskar iman,wadda ta fara jin wani iri,saboda yadda idanuwa sukayi mata caa na dalibai maza da mata,musamman ita da banda primary data yi da maza lokacin bata da wayo, junior dinta ajinau mata ne zalla,kasancewarta government school "What is your name?" Malamin ya jefa mata tambayar da harshen nasara,cikin sassanyar muryarta data sake janyo mata idanuwa ta amsa masa,sai ya jawo register din kusa dashi ya rubuta sunan,sannan ya bawa munira umarnin tayi mata wajen zama. Kai tsaye seat dinta ta matsa mata,saboda tsarin zaman duk seat daya mutum biyu yake dauka,da su biyu ne akai ita da qawarta,to bayan an shiga sabon term sai aka canzawa qawartata makaranta,hakan ya sanya take zaune ita daya,saboda ba da kowa ita din take jurar zaman ba. Ranar farko a makaranta ga duk sabon dalibi rana ce dake cike da baqunta da rashin sabo,kusan hakan taso faruwa ga iman,saidai kuma kirkin munira ya hana hakan faruwa,saboda janta data dinga yi da hira,koda aka fita break tare sukayi break din,aka dawo suka zauna a seat dinsu,tana ta bata labaruka da suka danganci makarantar da yadda take,har zuwa lokacin da aka kada bell an tashi kenan,iman din ta saba jakarta tana nufi qofa bayan ta yiwa munira sallama. A qafa ta fara takawa sabida tadan qara gaba inda babu cunkoson dalibai sosai,tana tsaka da tafiya taji muryar munira na kiranta,saita dakata ta kuma waiwayo suka hada ido,kowa ya sakarwa dan uwansa murmushi,ta dakaci muniran har ta qaraso inda take,suka jera sukaci gaba da tafiya tare,kafin daga bisani muniran tace "Ya na ganki kina takawa a qafa?" Waiwayawa iman tayi tadan dubeta cike da mamakin tambayar tata,to ame takeson ganinta?,kamar taji tambayar da ta yiwa kanta sai ta dora "Ko mai daukarki ne bazai samu zuwa ba?,ranar farko a makaranta kuwa ai bai kamata ya barki kiyi tracking ba". Sai yanzu ta fahimci zancanta,saita murmusa "Dama can motar haya nake hawa,saidai wataran idan hanya ta biyo da yaa al'ameen ta qofar makarantarmu ya jirayeni mu koma gida tare" kai munira tadan jinjina,tana cike da mamaki,saboda kallon farko data yiwa iman,ta mata duba ne na yaran da suka fito gidan hutu,sam kyan qira da dirin da Allah ya bata tayi zubin gidan yaku bayi ba,ta tsammaci zata ga wata shimfidediyar mota tazo daukarta ne,saita aje tunanin nata tana tambayar iman din unguwar da take. Sanda ta gaya mata idanu ta fiddo "Ai bamu da nisa da juna,abun hawa daya zamu hau,tunda nima yau shuru ba'azo daukata ba" ta fada tana saka hannu tana tsayar musu da adaidaita sahu,suka masa bayani suka shige,iman din na qoqarin neman ragi kan kudin da ya gaya musun,amma sai taga muniran bata damu da price din da ya fada ba,don haka itama sai tayi shuru kawai. Suna tafe muniran na jan iman da hira,a dan zamansu na awanni iman din ta fuskanci muniran kamar daga gidan masu dashi ta fito,koma ba haka ba to tabbas gidan data fito sunfi nasu wadata,tadan saki jiki kadan da ita tana biyewa hirar tata,har aka kawo inda muniran zata sauka,wanda daga nan zuwa gidansu iman baifi naira 20 ba kudin mota. Kudin da ya buqata munira ta ciro ta biya musu,iman zata doje tayi gaba abinta bata tsaya ma sauraren qorafinta ba,mai adaidaita yaja sukayi gaba,cikin ranta kafin su qarasa gida tana ta yaba kirkin muniran da karamcinta,azamansu na wasu taqaitattun awanni. A dan gajiye ta shiga gida,saboda akwai qaerin lokacin tashi kadan a wannan makarantar kan makarantar data baro. Da sallama ta kutsa tsakar gidan nasu qarfe biyu da rabi da minti biyar,inna dake duqe tana baza masarar data wanke don ta samu tasha iska akai niqa ta dago tana amsa sallamartata,idanunta akanta,ta sabule jakar bayanta ta zauna saman kujera 'yar tsuguno tana dan goge zufar goshinta tare da yiwa inna sannu da gida "Yauwa,an taso kenan?" Ta fada tana juyawa zuwa ga aikinta "Wlh inna,duk na gaji,makarantar tafi waccan nisa" "Ah to,aishi sa kai yafi bauta ciwo" tasan mita sarai inna zata dorar,don haka ta saki dariya kawai ta miqe tana daga jakarta "Amma inna karatun da ake mana a waccar makarantar baiko kama qafar rabin na wannan makarantar ba" "To Alla ya taimaka" ta amsa mata. Kamar zatayi gaba sai kuma ta dakata "Inna ya al'ameen bai dawo ba?" "Tunda ya fita dai bai shigo ba" saita daga hannunta duban fuskar siririn agogon silver dake hannunta tana duba lokaci,wanda yau ta fara sakashi,kuma al'ameen dinne ya siya mata saboda makarantar "Amma dai inna ba tuwo zakiyi ba" "Zanyi ko zakiyi?" Kai ta gyada cikin salo na zaquwa da son jin amsar innar "To zanyi inna" "Bashi bane maqiyar tuwo.....dambu nakeso wai nayi" sai fuskar iman din ta dan saki,don ita gaba ce tsakaninta da tuwo,tunda taji batun dambu kuwa,tasan saboda malam da al'ameen za'ayishi,don haka tayi damarar zagewa tayishi yayi kyau yayi dadi ko don al'ameen din,tana matuqar jin dadin yadda yake yaba mata idan tayi girki,da yadda yake nuna jin dadinsa,koma bayan sadiq dake kusheta,wani lokaci har sai malam ya shiga sannan zai qyaleta,duk da shima yana yine kawai saboda tsokana,bawai don bata iya din ba,don ta fannin girki inna ta yarda da ita dari.bisa dari,tun tana da shekara takwas innar ta fara shiga madafa da ita,tana da shekara sha biyu kuwa ta sakar mata girkin,saidai ta dinga tayata ko duba mata,zuwa yanzu kuwa da ake magana fa gama zama cikakkiyar qwararriya. Ruwa kawai ta watsa tadan tsakuri abincinta kamar yadda ta saba ta fito ta kama aikin,yau dama babu islamiyya,anyi bikin yaye wasu dalibai da suka sauke alqur'ani,don haka aka basu hutu,wanda ida an koma su iman dinne 'yan babban aji,duk da ita dama already tana biyo bayan duk inda aka biya matan da hadda wajen malam,wani lokaci kuma idan abubuwa sunwa malam din yawa al'ameen ya karba mata. Cikin karsashi da kuzari take aikinta,tana yi tana yiwa inna surutun makarantar,wanda ada al'ameen din ta tarawa labaran,saidai tasan ba lallai ta sake ta bashi labarin sosai ba,sabida kaifi da nauyi da idanuwansa a yanzu suke mata,ta rasa dawa kuma zata tattauna wannan,qawarta daya a unguwarsu,to itama takan jima basu hadu ba saboda yanayi na karatu da kuma tsarin tsaron fita a gidan kowannensu,saidai tanata timing da sanya lokacin da zata fita taje susha hira da ita. Ganin ta kammala hada komai,dambun ya hau wuta,kuma tsakar gidansu babu kowa,saita debo 'yan qananun brassier dinta da ta fara amfani dasu a boye ta zuba a botiki ta zauna daga bakin famfo,wanda yake daura da qofar shigowa ta fara wankesu. Ta jima tana ajiyarsu,tun wani lokaci da sukaje nijer,anty raheena 'yar uwar inna ta bata tace ta ajjiye zasuyi mata amfani,bata aminta da hakan ba sai sanda amfaninsu ya taso mata,ta rasa wanda zata gayawa tana buqatarsu. Babu irin wannan hirar tsakaninta da innarta tun farko,ya alameen din nata kuma koda wasa ba zata iya tunkararsa ta gaya masa tana so ba,sai ta tuna da ajiyarta, doon haka ta debo abunta ta fara amfani dasu hankalinta kwance,amma tanata boye boye,don sai irin haka gidan babu kowa take wankesu ta shanyasu a bayan qofar dakinta,ko idan ta shiga wanka. Tana wankesu tana dan rera karatun qur'ani da tausashiyar muryarta mai cike da sanyi nutsuwa da kuma tashen 'yammatantaka. Daidai lokacin da al'ameen wanda kansa ke ciwo ya shigo cikin gidan,tun daga soro yayi sallama kamar yadda ya saba,saidai muryarsa bata da wani qarfi me yawa saboda gajiya da kuma ciwon kai,wanda ya tabbatar stress ne na dinki. Sam bataji shigowarsa ba,kamar yadda shima ya ganta bagatatan a farkon qofa,don sam bai kawo samuwar wani mutum zaune a wajen ba. Saman fuskarta ya fara sauke ganinsa,ta langabe kanta gefe guda,qaramin bakinta me dauke sa jajayen labba yana motsawa a hankali,sautin karatunta yana fita da kadan da kadan,gefan da kanta ya karkatan jelar manyan kitso guda hudu dake kanta sun kwanto ta nan har saman qirjinta. Tayi masa kyau ainun,fuskarta da maqerin budurci ke aikinsa a kanta tayi wani fresh tare da annuri na daban,saiya lumshe idanunsa qirjinsa yana bugawa,wani abu mai sanyi da qarfi da girma ya tsaga qirjinsa ya sauka saman zuciyarsa,ya tabbatar wani feeling ne me cike da soyayya da kuma qauna ya saukar masa,sai ya bude idanun nasa yana saukesu zuwa ga abinda take wankewar. Idanu ya qurawa brasssier din nata yana mamakin yaushe ta fara amfani dasu,qaramin murmushi ya qwacewa fuskarsa,ya sani tunda can tana da yawan zama da hijabi cikin gidan,to amma kwanaki yaji yadda inna ke qorafin bata cirewa ko cikin daki tasha iska,wala'alla yana da nasaba da hakan?. A firgice ta dago sanda taji sallamar mutum saman kanta,a zabure ta miqe saboda ba zatan ganinsa,har tana fatali da ruwan wankin da abebaden dake ciki tayi dakinta da gudu,sai ya bita da kallo,dariya ta qwace masa,ya duqa a hankali ya kwashe mata abubuwanta da hannu daya ya maida ga botikin,sannan ya tako zuwa cikin gidan yana aake jaddada sallamarsa,inna dake can uwar daki ya fito zuwa rumfarta tana amsa sallamar,saiya taka a hankali zuwa rumfar innar yana cire takalman qafarsa,rabin hankalinsa na ga dakin iman din data turo qofar ya murmusa ya shiga rumfar innar. *_HILTI UNISEX CHOCOLATE STILL AVAILABLE, GRAB YOURS NOW,DAB TAKE DA QAREWA_*👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽 0818401745209 *Game buqatar biyan kudin zafafa biyar,zai iya tuntubarmu ta wannan number* 09032345899 Ko kuma 09166221261 __________________________________ "Tunda ta shigo ta fara tambaya da cigiyarka,nasan kuma labarine kawai cike taf da bakinta zata baka na makaranta" inna ta fada mishi bayan sun gaisa,tana ninke abun sallar data bari a wajen ta gashi ta shiga ciki,murmushi ya sake yana dan shafo kansa,yana funa dramer dinsu ta yanzu yanzu "Aiki take tayi ai inna,na dauka yau zata huta sabida gajiyar sabuwar makaranta" dan satar dubansa kadan inna tayu,duk sanda ya nuna wata kulawa kan iman din hakan namata dadi qwarai,kuma dama shi ba baqon abu bane a wajensa,tana da tabbaci da yaqinun diyarta qwaya daya tilo ta dace da mijin aure,namijin da yasan abinda yake,mai yawan tausaya mata da qaunar farincikinta "Diya macace al'aminu,gwara taci gaba da sabawa akan hakan,na gana nauyun iyalinta ne zai hau kanta,mace bata da wani hutu da ya wuce tayi abinda ya dace a matsayinta na mace,to daga baya saita huta din" dan nauyin innar yaji ya kamashi,saiya gyada kai sannan ya miqe yana yiwa inna sallama. Koda ya fito tsakar gidan babu ita har yanzu,hakanan babu motsinta,ya gifta inda ta tashin idanunsa nakan botikin wankinta,ya sake sakin murmushi ya wuce soro,ya saka key ya bude dakinsu ya shiga. Saman kujera ya zube yana furzar da iskar daya zuqota tun daga hunhunsa,hannunsa yana saman kansa yana shafa sumarsa daga gaba zuwa baya a hankali,yanajin yadda kansa ke sarawa,gefe guda kuma yana qarewa dakin nasu kallo,yasan hargitse kadan yana buqatar gyara,kwana biyu bashi da isashen lokaci da zai zauna ya gyara din,dinki yake na jama'a tuquru saboda gabatowar azumi,yanason ya samu isashen kudi a hannunsa da zai yiwa gidan siyayyar kayan azumi,ya yiwa iman kayan sallah sannan yaje ya gano yayarsa itama da nata kayan azumin dana sallah,inna tasha hanashi saboda sadiqu da malam duka suna tasu siyayyar,amma sam yaqi yarda,inda daga qarshe yace baya jin dadin hakan a ransa,sai yaga kamar innar ta warshi ne shi,wannan furucin yasa ta qyaleshi,bata sake magana ba. Ruwa ya fara diba ya shiga wanka ko zaiji dadin jikinsa,bayan ya fito ya murzawa qofar dakin nasu key,duk da yasan babu me shigo musu kai tsaye,ya sanya boxer da singlet ya koma ya kwanta saman doguwar kujerarsu yayi rub da ciki. Idanunsa ya runtse gam,tunanin iman na dawo masa,surorinta na bayyana cikin idanunsa,wani yanayi na mamayar ilahirin jikinsa,tsigar jikinsa na tashi,sai ya sake gyara kwanciyar tasa yayi rub da cikin da gaske,ya sake rufe idanunsa a hankali yana ci gaba da dulmiya cikin tunaninta,murmushi na qwace masa saman fuskarsa lokaci bayan lokaci,sai daga bisani yaso dakatar da kansa saboda ganin yadda tunanin ke neman qara ta'azzara ciwon kan nasa,don haka ya haqura da kwanciyar,ya miqe ya balli paracetamol biyu cikin magungunansa yasha,ya sanya jallabiya ya jawo qofar dakin nasu ya fito zuwa qofar gida. Yaci sa'a malam yana nan,an gama karatun yamma yana shirin sallamar yara,ya cire takalmansa yayi tattaki cikin girmamawa zuwa gaban malam din,yayin da shima malam ya bishi da kallo wanda ke nuna tsantsar kulawa. Gefansa ya zauna,bai kuma yi magana ba har ya gama sallamarsu "Al'ameenu.....lafiya kake kuwa?" Malam ya jefa masa tambaya,sai ya daga kansa cikin murmushi ya dubi malam,yana yabawa da jinjina qoqarin bayin Allahn,yadda suke iya hakaito damuwar daje tattare dashi,ta ciwo ce ko akasin hakan "Kaina ne yake dan min ciwo" "Subhanallahi.....matso nan" malam din ya fada,saiya matsa gabansa kadan,ya sanya hannu saman kansa ya kama masa shi da addu'o'i,ya matsa bayan ya gama yana masa godiya,wanda babu jimawa yaji ya fara sauka,daga bisani ma suka shiga tattaunawa,har zuwa sansa sadiqu ya dawo dava wajen aikinsa shima ya zauna nan wajensu yana cewa "Na biya ta wajen aikinku mu taho tare,saina taras waika taho" "Kaina ne ya fara ciwo,saina yanke na dawo gida na huta" cikin yanayin nuna alhini da damuwa yace "Subhanallah,sannu" "Yauwa,da sauqi ai,malam ya kamamin ya sauka" ya fada ganin yadda fuskarsa ta nuna damuwa "Kaine ma man,ka dinga kwanciya wasu kwanaki kana hutawa,kana stressing kanka da yawa wallahi" murmushi kawai ya sakar masa ba tare da yace komai ba,shi a karan kansa a jikinsa yakejin akan struggling bai fara komai ba,namijin duniya dan gwagwarmaya ne,abinda ya saba gayawa sadiqu kenan. Basu shiga gida ba anan suka yada jam'in sallar magariba su da sauran jama'ar dake salla a wajen duk sanda malam ke kusa,aka idar suka sake zama hira,irin zaman da ba kasafai lokaci ke basu damar yinta ba,saboda baqi da kuma yanayin aikinsu,daga bisani malam din yayi baqo,suka shiga tattaunawa,hirar sauta koma ysaka insa da sadiqu,sunaga qus qus dinsu saboda kada malam yaji,saboda hirar irin tasu ce,yana bashi labarin yarinyar datace tana sonshi,al'ameen din nata sukar abun,saboda shi sam yana qalubalantar mace tace tanason da namiji a irin wannan zamanin,daga qarshe malam ya tura daya daga cikin almajiransa su sanya a fito da abinci,wanda dama da wuya kaga anyi girki a gidan dai dai cikin masu gidan,saboda baqin da malam din kanyi lokaci zuwa lokaci,sadiqu yacewa yaron ya gayawa iman ta hado da nasu. Cikin gidan babu kowa sai ita,don haka inna ta tsaida yaron malam din,ta taya iman shirya abincin,yaron ha daukar mata wani ita kuma ya dauki wani suka fito dashi. Tunda ta doso wajen idanuwansa na kanta,cikin lullubin hijab har qasa,duba daya zaka yiwa hijabin kasan tsafta ta wadaceshi,don harda karin guga,idan kuma ta kusanto inda kake zaka iya jin qamshin body mist din da take amfani dasu,'yan 300 ne,saidai suna da sanyin qamshi,tana da maitar son qamshi da turare,don haka tun kafin ma takai haka ta iya zaben turare, training din al'ameen dince,tun daga tsafta zuwa son qamshi,girki ne kawai aikin inna. Har zuwa sanda ta fara isa gaban malam ta ajjiye musu nasu abincin bayan ta duqa ta gaidashi shi da baqonsa idanunsa na a kanta,girma da 'yammatancinta yana sake cika sosai,ta zama budurwan gaske,saita qaraso gabansu a hankali,daidai sanda baqon malam ya furta wata magana data dauke hankalin al'ameen daga wajen kwata kwata ta maidashi kan hirar su malam din. "kada dai ace hajarunka ce ta girma haka?" Murmushi malam din yayi "Itace mana" kai ya gyada "Ikon Allah,girman dan mutum babu wuya" "Ka kwana biyu baka ziyarcemu bane shi yasa" malam ya amsa masa gana wanke hannunsa cikin kwanan wanke hannu dake gabansa wanda inna ta hado dashi "Lallaifa an kwana biyu" sai yadanyi shuru kadan sannan yace da malam "Ni kuwa malam khalilu,da zaka amince ai da mun qulla wani alkhairi" daga kai malam yayi ya dubeshi sanda yake qoqarin bude kwanonin abincin "Ina saurarenka malam basiru" "Me zai hana yaron wajena ilyasu yazo yaga hajaru,bamusan me Allah zaiyi ba,kaga idan Allah ya daidaita tsakaninsu ai mu shikenan,kakarmu ta yanke saqa,tuwona mai na" Saura kadan maganar tayi tafiyar yaji da numfashin al'ameen,idanunsa suka fara laluben iman dake duqe a gabansu tana ajiye musu nasu abincin sabida bacewa ganinsa da take neman yi,zuciyarsa tayi wani bugawa tare da qara adadin gudunta. Ajjiye murfin hannunsa malam yayi yana duban baqon nasa "Zanfi kowa jin dadi matuqar hakan zata kasance,inama ina da wata diyar bayan hajaru da na baku,kuyimin aikin gafara,tuntuni na bayar da hajar,lokaci kawai muke jira a zartar da komai nan kusa in sha Allahu". Nannauyar ajiyar zuciya alameen din ya saki,yana share gumin dake goshinsa tare da duban tsakiyar blue din qwayar idanun iman din dake haske cikin dan hasken dake kewaye da wajen,kamar tasan ita yake kallo saita daga kai suka hada idanu,ta sakar masa da murmushi tana sadda kanta qasa cike da jin nauyi da kunyar abinda ya faru dazun,abinda ke alamta masa cewa bataji maganar dasu malam ke tattaunawa ba,nauyin numfashin ajiyar zuciyar da ya saukar ne ya sanyata daga kai suka hada ido da ita. Kusan baici wani abincin kirki ba ya tattara ya koma cikin gidan,dakinsu ya fara shiga saidai ya kasa zama,yanason yin magana da iman din,ba kasafai ya fiya son kebewa da ita ba saboda kare haqqin sharia sa kuma gujewa shaidan,amma dole ya zaqulo dalilin da zai sanya su zauna suyi magana da ita,don haka ya dauki sabuwar wayarsa daya siyo a dazun ya juya da niyyar fitowa,dai dai sanda sadiq ya shigo ya wuce cikin gidan ya barshi a dakin yana amsa waya. Dakin malam da ya gani a bude ya tabbata malam din ya shigo cikin gida,kuma idan ya shigo din inna na tare dashi,hakan ya sake bashi qwarin gwiwar isa ga rumfar inna. Cikin saa ya sameta zaune tsakiyar litattafanta,ta bajesu tanata qoqarin gwada assignment din da aka basu a yau din,wanda zasuyi zanen zuciya ne tare da fitar da kowanne chamber na cikinta. A hankali ta daga kanta tana amsa sallamar tashi,sai kuma ta maida kan nata ta duqar tsakanin qafafunta tana juya abun zanen dake hannunta,ya sake sakin murmushi,ya qarasa a hankali kan kujerar dake daura da ita ya zauna saman hannun kujerar,cikin lallausar muryarsa daya ragewa kaifin sauti yace "Hajar 'yammata" ji tayi tamkar zata lume a wajen,sautin muryarsa a yau din ya zama na da an cikin kunnuwanta,uwa nauyinsa da takeji ya ninku cikin ranta daga sanda yaga abinda taje wankewa dazun "Ina fatan kin kwashe wankinki,saboda banason kowa yazo ya gani" saita saki abun rubutun ta juyar da kanta ta sanyashi saman kujerar tana boye dariyarta cikin jin nauyi,ta tabbata zaiyita tsokanarta ne idan batace wani abu ba,don haka cikin siririyar muryarta tace "Don Allah ya alameen....don Allah" yasan me takeson fada,saiya saki qaramin murmushi me dan sauti kadan,ya zamo ya zauna sosai saman kujerar yana cewa "To shikenan....duk da dai an boyen.....shikenan dai,ungo wannan,sakamin a charge" a hankali ta juyo tana avoiding hada idanu dashi,tasa hannu biyu ta karba wayar da yake miqo matan "Laaaa yaya,taka ce?" Kai ya gyada mata tana juya wayar a hannunta "Tawa ce" saita narke kadan,duk da bata bari sun hada ido ba "Don Allah yaya yaushe zaka siyamin nima,kaga fa na shiga senior" ya santa qwarai da son waya,saidai a yanzu bashi a ra'ayin ta riqe qaya torching kwata kwata saboda wasu dalilai "Wannan bata ishemu ba?,abuna ai naki ne" "Yaaya,idan ka fita fa da abarka zaka dinga fita" "Zan dinga bar miki ita duk weekend kina danawa,shikenan?" Cikin murna tace "Yauwa yaya,na gode" "And....idan naga yanayin performance naki a wannan term din,zan siya miki qaramar keypad indai inna da malam sun bari" sosai ta nuna murnarta,ta tashi ta fara qoqarin saka masa a chargyn "Idan kin gama kizo zamuyi wata magana" ya fada yana saukowa tare da buda takaddan data fara zanen yana kallon zanen nata. Tana gama sanya chargyn waigowar da zatayi taga ita yake kallo bayan hannunsa na riqe da zanenta,wani weakness ya saukar mata,duk kuzarinta na daxu ya gudu,batasan wane irin power da magnet ne a idanun yayan nata ba,wanda a baya da babu su sai a yanzu "Zauna a nan" ya mata nuni da wajen da yake buqatar ta zauna din,inda zai zamana suna fuskantar juna ne,ta zauna ta lanqwashe qafafunta "Wa kikeso a zuciyarki?" Ya jefa mata tambayar kai tsaye,abinda ya sanyata daga kai ba tare da tako shirya ba ta dubeshi saboda jin saukar ba zata da tambayar tashi tayi mata,idanunsa cikin nata ya jinjina kai "Yes.....zuwa yanzu kin girma queen,ke din ba yarinya qarama bace kamar yadda kike kallon kanki,zuciyarki zata iya fadawa soyayya at any time.......wa kikejin kina so" sosai ya jefata cikin nazari,kafatanin rayuwarta batasan kowa ba bata saba da kowa ba sama dashi,bata taba kallon kowa ba taji wani abu na daban a kanshi ba sai shi,inda tasan soyayya ko alamominta,ba shakka zata iya cewa wala'alla shi takeso,amma yanzun batasan shaquwa ko ganin girma bane,duk bata sani ba. Maganarsa me nauyi ce,don haka ta girgiza masa kai kawai "Uhunnn..... talk to me mana,ki gaya min" sake girgiza kai tayi da qarfi,murmushi me qarfi na son qwace mata,wanda ya cakuda da kunya "Don Allah yaya,babu kowa fa" kamar yace "Harda ni?" Sai kuma ya danne wannan a ransa,ya saki nannauyar ajiyar zuciya,ya sake cooling muryarsa sosai "Bani aron hankalinki iman" sau daya ta daga kai ta kalleshi ta mayar qasa tana sake gada nutsuwarta kamar yadda ya buqata "Inaso ki bani dama guda daya tak a rayuwarki iman,ina da wani tanadi na musamman cikin rayuwarki" "To yaya" ta fada a sanyaye.[04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 10 *_Wannan littafin na kudi ne,game buqata zaki iya tuntubar wadan nan numbers din_* 09032345899 Ko kuma 09166221261 "Imannnn" ya danja sunan nata,ta amsa da na'am,har yanzu idanunta suna qasa "Bana so ki kula kowa,banason kiyi soyayya da kowa..... infact ma,na miki zabin mijin aure wanda zai dace dake in sha Allah.....kin yarda?" Kai fa gyada tana sake saukar da kan nata qasa "Kinyimin alqawari?" Saita sake jinjina masa kan,ya sauke numfashi mai nauyi daga qirjinsa yana furta "Alhamdulillah". Shuru yadan ratsa dakin,yana ci gaba da kallon zanen nata,saidai zuciyarsa ta rarrabu kashi kashi wajen tunani iri daban daban "Zanen nan yayi kyau,ina tunanin yadda kika iya zanen zuciya har haka.....soyayyarki zata kasance me kyau haka" da sauri ta daga kanta suka hada idanu,wadanne irin manya manya kalmomi ya al'ameen ke mata amfani dasu ne haka,gashi ya ritsata da idanu yana kallonta,sai ita ta janye nata idanun tana sake qunshe fuskarta waje daya,ya saki murmushin nasarar da yake hangowa,yana iya hasashen yadda yake samun ci gaba da kuma galabar narkar mata da zuciya kowacce rana idan ta bullo kafin ta fadi. Shi ya zauna ya tayata aikin gaba daya kasancewar science yayi shima,banda rashin zamowarsa dan wani shi din mutum ne me matuqar qwaqwalwa daya kamata ace ma zuwa yanzu yayi nisa a karatun likita da yake jarabar so,suna aikin yana dan janta da hira don ta saki jikinta,tadan sake amma ba kamar yadda suka saba ba,bai bar cikin gida ba saida inna ta fito daga wajen malam,sannan ya wuce dakinsu ya barta da tarin tunani cikin kwanyarta. ********WASHEGARI****** Bayan tasowarta daga makaranta wanda shima tare da munira suka taho,ta kuma sake biya mata kudin mota,bayan tayi wanka ta sauya kaya taci abincinta inna ta bata dakan garin kunu wanda akewa malam,tace takai bayan layinsu ta tsaya a daka ta taho dashi "Don Allah inna zan leqa gidansu bushira" bushiran ba boyayya bace a wajensu,nutsatsuyar yarinyace da suke taba qawance da iman,wanda tun quruciya itace kadai ta dauke halayyar iman din,duka sauran irinsu rahama abokan fadanta ne,banda yanzu da girma da hankali yazo ake gaisuwar mutunci a wuce wajen. Tana kaiwa mai dakan kudin ta zarce gidansu bushira,wanda gidajen dake tsakaninsu da gidan dakan bai wuce gida shida ba,tayi sa'a fa sameta a gida,dama kuma ba inda take zuwan,islamiyya ce,kuma makarantarsu daya,anyi musu hutun sauka sai wani satin xasu koma "Wata sabon gani" bushira dake cire lallen data yiwa yatsu hannunta ta fada tana tabe baki bayan sun shiga dakinta da suke kwana da qannenta,murmushi ima tayi suka shiga tsokanar juna da hirar duniya,kafin daga bisani iman din fa budewa bushira abinda ke tafe da ita. Shuru iman din tayi na kusan minti goma tana juya bayanan da bushira tayi mata,baya ta gama bata labarin komai,ta dauke hannunta daga kumatunta "Amma bushira,ta yaya yaya al'ameen zai soni,bayan yayana ne?" "Yayanki,ciki daya kuka fito?,ko yaya sadiqu ne?" Kai ta girgiza alamun a'ah "To kuwa kinga ya halatta kuso juna ku kuna qaunaci juna,dama kuma abinda yafi dacewa kenan,don kusan dama ke din rainonsa ce......kuma ko ke qarya kike kice baki sonshi munafuka" bushira ta qarashe maganar tana ɗakawa iman duka a cinya gami da sakin dariya wadda ta sanya uman din dole ta tayata "Ya al'ameen ya gama haduwa iman,idan ma bakiso wata ce zata daukeshi,yana cin list na sahun farko na kyawawan unguwan nan wanda babu na biyunsu,duk yadda zan gaya miki yadda 'yammatan unguwar nan ke sonshi da fatan ya sosu ba zaki gane ba,abu daya ya rage miki....ki jira sanda zaice kawai yana sonki ki karbi tayinsa hannu bibbiyu.....idan ma yayi nauyin baki ke ki furta kawai a wuce wajen" duka iman ta kaiwa bushira a gadon bayanta "An gaya miki bani da ajine,duk yadda muka taso tare dashi bazan bari ajina ya zuba ba" "Gaskiya ne tawan,kema a unguwar yayinki ake,kawai shakkar malam dasu ya al'ameen din ya hana a fara tareki ko sallama dake,amma ni kaina masu kamun qafa dani a kanki suna da yawa,harda masu motoci wallahi" miqewa iman tayi tana daure gashinta mai santsi da ya ware wanda dama babu wuya ya warware din,ta maida hijabinta saman kanta tana fadin "Su riqe motocinsu.....kinga na manta shaf da aiken daya fito dani ma" "Muje na taka miki" bushira ta fada itama tana janyo hijabinta suka yiwa ummansu sallama suka fito tare. *******SANNU SANNU****** Kwanaki ke shudewa sa iman cikin makarantar nasreen,zuwa sannan bata da wata qawa ko aminiya data wuce munira,shaquwa me qarfi ta fara shiga tsakaninsu,duk da banbancin halaye da kuma dabi'u dake a tsakaninsu,gami da sukunin rayuwa. Cikin sati uku ta fahimci wace munira,'ya mace guda daya tilo da mamanta ta haifa bayan yara maza qannenta guda hudu,tana ji da ita ainun,tana bata kulawa da gata,kusan mafi yawa daga cikin familyn su munira masu arziqi ne masu sukuni,saidai shi mahaifin muniran rufin asirin Allah gareshi,mamarsu muniran ta fishi kudi,hakan ya sanya komai na gidan take tafi dashi yadda takeso idan ma maigidan yayi wanda baiyi mata ba,tana ji da munira sosai,hakan yasa ta daukaki rayuwarta,tanason rayuwa me tsada sosai,hakanan takan kutsa kanta inda Allah bai kaita ba,gidajen 'yan uwan mamanta masu dashi ainun babu inda bata sani ba,wani lokaci idan ta shilla ta debi kayanta ta tafi daya daga cikin gidajen nasu,takan jima bata dawo nasu gidan ba,har ma sai kayi zaton 'yar gidan ce. Da yake fara ce hakan sai ya sake qawata fuskarta,ya kuma ja hankalin samari a kanta,tana da samari sosai,kuma dukkaninsu 'ya'yan manya ne,wayar hannunta kuwa a lokacin babbar iPhone ce,dukkan abinda take ta'ammali dashi,tun daga sutura zuwa cima masu tsada ne,komai zatayi saita siya me tsada,saboda mamanta ta tsaya mata,batason sam taga muniran tata ta shiga cikin danginta an raina ta,hakan ya sanya take kashe mata kudi tuquru. Saidai kuma muniran nada kirki daidai gwargwado,hakan shi yake taimakawa wajen boye da yawa daga halayyarta da basu dace ko kamata ba. Ba komai na halayenta iman ta sani ba,tunda iyakarsu makaranta,da an rabu shikenan,sai kuma washegari,iya abunda ta sani muniran tana da kirki da kuma yawan kyauta,duk da tana zillewa duk wani abu da zaisa muniran ta kashe mata kudinta,kamar tafiyarsu tare,da yawan lokuta zillewa take tayi tafiyarta saboda kada muniran tace zata biya mata kudin motar. *MONDAY MORNING* Cikin clean uniform dinta da suka dauki karin guga kyakkyawar matashiyar hajar Ibrahim Khalil ke takowa tana nufar ajinsu,kafadarta daya saqale da jakarta,daya hannun kuma dan madaidaicin flask din abinci ne a ciki. Kana duban fuskarta zaka karanci ranta a bace yake,saidai hakan wani kyau ya qara mata na musamman,sandin bacin ran nata makara datayi,aka kuma shanyasu a bakin gate har na wajen awa daya cikin rana,wanda wannan shine irin punishment din makarantar tasu. Kamar ance ta daga kanta saman varander dinsu,ta daga kyawawan blue eyes dinta,idanunta sauka ga malamin,sir arabi,malamin daya takurata tun zuwanta makarantar,da shegen kallo naci da kuma shishshigin shiga harkarta,shike daukarsu darasin turanci wato English,yammatan makarantar da yawa suna yinsa,saboda motar da yake hawa,kana kallonsa kasan ba talauci ko babu suka sanyashi koyarwar ba,saidai ita sam imani hakan bai dameta ko ya dadata da qasa ba,don sam jininsu ita bai hadu dashi ba,ya fiya jin kansa saboda yaga yana tashen samartaka,yana sanya shaddodi da hawa mota,ita sam a rayuwarta batason mutum me jin kansa ma,izza da fadin rai,shi yasa tako ina ya al'ameen yake burgeta. Yana da wani irin kwarjini gami da aji,uwa uba miskiline naqin qarawa idan baiso ba,hakan yasa baya daukar raini ko izgili,amma sam baida girman kai ko dagawa. Ta sauke nata idanun tana jan tsaki qasa qasa,gami da qare hade ranta gab da zata shiga cikin ajin nasu,sabida yadda yawanci lokaci irin wannan sanda tazo a makare mazan ajin ke binta da kallo,abinda ta tsana ita kuma kenan,don haka a dake ta shiga ajin. "keda mutumin naki ne?,na hangeshi tsaye upstair" munira ta fada tana danne dariyarta sanda iman ke zama kusa da ita,tana duba littafin subject din da akeyi "Shine mana,me shegen kallon tsiya,banason mutum me kallo" "Tsaurin idanu dai,kwata kwata baki dace irinsa bama,shi bai gani ba kedin kalar matar manya ce" waiwayowa iman tayi sanda take dora littafin saman table dinta "Kamar yaya?" Murmushi munira tayi tana ci gaba da copying note dinta "Kamar har yanzu bakisan baiwar kyan da Allah yayi miki ba,ai kyan kyau irin naki ki morewa babban gida,inda zaa jiqaki da kudi da mota,fita qasashen waje babu kama hannun yaro,shine kika mori kyanki,amma ba kowanne irin kalar namijine zaizo ya tsaya gabanki da sunan yana sonki ba" tsaki iman taja,saboda ta dauki maganar munira a matsayin shirme,ta bude littafinta ta fara kwafar note din da sauri da sauri don ta fuskanci ya kusa dawowa ya goge wanda ya fara. "Am telling you fa,kina ganin kamar wasa ce maganata?,to Allah koni da ban kama rabin qafarki a kyau ba,zakiga kalar mijin da zan zaba" "Don Allah ki shiru ki barni da bacin ran da yake damuna" dariya muniran ta saki tana ci gaba da rubutun,har zuwa sanda malamin ya kammala yayi musu explanation ya sallamesu. "Me ya hanaki zuwa makaranta Friday ne?" Iman ta tambayi munira tana maida littafinta jaka,sai data juya manya idanunta,da alama amsar da zata bayar amsa ce da take mata dadi cikin ranta sosai sannan tace "Kinsan biki muke na wata cousin dita,so ran Friday muka tafi garinmu acan zaa daura aure,kuma ina cikin wanda aka siyawa ticket zasubi flight,kinga ko bazan bari nayi missing ko damata ta wuceni ba,nayita neman number dinki na gaya maka,sai dana fara checking wayana naga ashe bamu taba exchanging numbers ba......ki bani number dinki saboda irin hakan,kinga nama canza sabuwar waya,ranar aka bani gift dinta" munira ta fada tana saka hannunta a aljuhun rigarta. Kallo daya zaka yiwa wayar kasan cewa bata qananun kudade bace,hakanan sabuwa ce fil sai sheqin sabunta take,munira tabi wayar da kallo sannan ta amsa mata "Nikam ai bani da waya,ta ya al'ameen nake ara duk weekends nayi game ko browsing" kallon mamaki qarara munira ta jefi iman dashi,harda dan ja baya "Kina ss 01 amma ace baki da phone iman, jokes apart please,wasa kikemin ko number dince ba zaki bani ba?" "Tunda baki yarda ba ai babu amfani na dage saina gamsar dake,duk yadda kika dauka hakane" "Am sorry my friend,Allah na dauka wasa kikemin....amma kuma,ba sani ba wallahi,da dana canza na baki dayar,sai qanina na bawa wanda yake bin me bina" idanu iman ta fidda "Ni shegiya kaza,ya al'ameen bazai bari ba,amma ina saka ran muna gama wannan term din zai siya min keypad sabuwa in sha Allah,yayi alqawarin idan nayi abun kai zai siyamin" dariya sosai munira ta saki tana kallon iman "See you don Allah,wani irin keypad?,to ko 'yan aikin gidanmu banjin akwai me keypad,don Allah karma ki fada wani yaji,sai ajinki ya zuba,mazancan da kike jawa aji saisu rainaki,su dauka qaramar yarinya ce ke". Rai sosai iman ta bata tana dubanta "To sai me?,ni ina farinciki da duk abinda nake dashi,kuma iya abinda yake ganin ya dace dani kenan,kuma ina farinciki da hakan" "Wait mana iman" munira tayi saurin dakatar da ita ganin kamar taji haushi "Nifa ba abinda nake nufi kenan ba,ki fahimceni.....ina nufin yanzu budurwa kamarki,ai ya kamata a sakar miki mara a siya miki waya me kyau saboda gudun raini daga wajen tsararrakinki.....na tabbatar yana da kudin da zai iya siya miki babbar waya,ko yaya ne kaima kayi dan abun xamanin nan da kowa yakeyi" duban munira kawai take,tabbas ya al'ameen idan tace tana so zai siya matan,amma a hakan ma babu lallai su malam su yarda ba,sai tayi shuru bata sake cewa komai ba,saboda isowar wata 'yar ajinsu da tata wayar,tazo munira ta tuttura mata pics da wasu videos,da kadan kadan sai ga masu wayar suna zuwa,sunata sending ma junansu abunda kowa keson sawa a wayarsa. Tana daga gefe tana kallonsu,kowacce wayar hannunta babbace,wata daga gidansu wata kuma saurayine ya siya mata,ba shakka tana bala'in son waya da maitarta,amma ba zata takura ya al'ameen din ya siya mata sama da wadda yace zai siya matan ba. [04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 11________________ *_Huuuuuum! Idan kaji hanci a sama yayin gittawar mata ƴan ƙwalisa ko shiga gidajensu kasan maganar ta ƙamshi ce_* *_Ina magana ne aka kayan ƙamshi ƴan gaske ba saka iska ta hure maka ba_* *_Ina mata ƴan ƙwalisa ma'abota so da ƙaunar ingantattun haɗin turaruka ƴan gaske? To kuzo maza ga dama a tafin hanunku cikin sauƙi da sauƙaƙawa._* *_Ana siyarda Turarukan Wuta na yan Maiduguri Set na amare. Ana bada sari kuma._* *_Sannan akwai kayan gyaran jiki. Akwai zumar qiba result cikin 1 week. Turaren daki, jiki, kaya, tsuguno, humra, colacca, turaren wanka, mopping scents, air freshener._* _Address Kano, Mariri Maiduguri Road. WhatsApp number 07068145252_. *Sai kunzo🤳🏻* ___________________________________ Tare suka jero da muniran bayan an tashi kamar yadda suka saba,suna tafe suna dan hira munira na tsokanarta "Nikam kullum aka tashi daga makaranta dalibai basa gajiya da kallonki iman?" Tsaki taja,itama abun yana damunta,don har ta yanke shawarar fara sanya niqabi "Sai suyita ai,kamar kai dayane mutum,su ba bil'adama bane 'yan uwanka" "Kin fita daban seriously,shi yasa kike shan kallo" munira ta fadi sanda take nufan wata mota ash jaye da hannun iman,dakatawa iman din tayi tana qoqarin kuma zame hanunta daga na munira "Ina kuma zaki kaini ga hanyar titi?" Waiwayowa tayi tana dubanta,fuskarta dauke da murnushin nan "Oops,sorry,na manta in gaya miki,me daukana ya dawo da daukata,dama shike maidani gida indai naje gidan uncle jibril,yawanci ina bin motar haya ne idan ina gidanmu" kai iman ta jinjina tana saita hanyarta zuwa titi "To sai gobe,Allah yabamu alkhairi" da sauri tasha gabanta "Ban gane ba,bayan ta hanyar unguwarku xamu wuce,ki shigo don Allah,yana da kirki,zai ajjiyeki unguwarku,cousin dina ne sadam,lokacin tashinmu lokacin ne shi kuma yake komawa gida cin abinci,shi yasa yaje biyowa ta nan ya daukeni mu wuce tare" kai iman ta jinjina "A'ah fa,zanbi adaidaita kamar yadda na saba" dambu taliya ta kada iman amma taqi,har sau da na cikin motar ya fara mata horn,dole ta haqura tace da ita "Shikenan,bani number wayar to" "Idan kin kira amma kice ni kike nema,don ya al'amin ko inna cikinsu wani zai daga,saboda numbers dinsu ne" dariya munira ta saki "Allah ya sawwaqe,yanzu inda saurayi kikayi haka zaki gaya masa kenan?" "Ke kika sani,ni bani da wani saurayi ma" da wani mamakin take duban iman din,saidai ta share ta soma karanto mata digit's din tana lodawa a wayar tare sa serving,sukayi sallama tana jajata mata Allah yasa ta samu mota da wuri,saboda sadam ya gaya mata ana wuyar abun hawa yau din,sakamakon taadar da man fetur yayi,da yawa wasu masu ababen hawan sun haqura sun ajjiye abun hawan nasu a gida. Ta samu tulin dalibai kuwa masu jiran abun hawa,haka nan tabi sahunsu itama,tana fatan su samu da wuri kodon ranar da ake dasawa. Kusan duk motar da zatazo ta wuce a cike take,wata kuma kafin ta qarasa inda ta tsaya wasu sun shige sun cikata,tana nan a tsaye tsayin wasu mintuna ta hangi kamar gilmawar motarsu munira,sai kuma taga ta tsaya taja da baya ta dawo dab da ita "Why not ki qyaleta....ba'a dole wajen taimako fa" sadam daya dan hada rai ya fadawa munira "Qawatace,banason ganinta tana sha ranar nan,kayi haquri minti daya" "Ok" ya amsa qasa qasa yana jona wayarsa a chargy,munira ta bude murfin motar ta fito ta nufi inda iman take. Da farko musu taso ta sake mata,sai da taga muniran taji haushi,sannan kuma me motar ya fara buga musu horn sannan ta bita,sanyin ac ya ratsata sanda jikinta ya shige motar,ta maida murfin ta rufe sanda munira ke mita "Haka kawai ki tsayar da kanki a wannan ranar babu gaira babu dalili,bayan ga abun hawa,ai tsaiwa a ranar nan sai dole" "Ina yini" tayi qoqarin gaida matuqin motar ba tare data amsa mitar da munira ke mata ba "Laf....lafiya qalau.... 'yammata" harshensa yadan sarqe,bayan idanunsa sun sauka a fuskar iman dake ciro jakar bayanta zuwa saman cinyarta ta glass din gaban motar,gabansa yadan fadi,ya zuba mata idanu na wasu sakanni ba tare daya iya dauke idonsa daga kanta ba,tunda yake bai taba ganin halittar mace da komai yaji.....ta kuma tafi da imaninsa irin wannan ba,wani irin kyau mai cika idanun me kallo,abinda yasa yadan daburce har ya qara mata da kalmar 'yammata kenan ba tare da ya sani ba,kalmar kuma data dan ja hankalin munira tabi sadam din da kallo,don tasan ba dabi'arsa bace hakan. Haka kawai ya samu kansa cikin rashin nutsuwar da yake da tabbacin ya fada kogin soyayyar iman ne farat daya,ya dinga satar kallonta lokaci bayan lokaci,har sai da iman din ta ankara,ta kuma tsargu,tare da tuhumar kanta na meye xata shiga motar wasu,koda rana zata kasheta?,sai ya basar,ya fara soko musu hira,yana kuma jan iman din din "Wanne layi zamu shiga?" Ya tambayi iman din kai tsaye,idanunsa na kanta ta cikin mirror "Ya isa,anan ma zan sauka" ta fada tana sake gyara jakarta "A'ah,ai da kin barmu mun cikasa ladanmu ko?" Ya fadi yana dan saki murmushi,munira ma ta saki nata tana gyada kai "Aikuwa dai" "A'ah na gode,babu nisa,zan qarasa da qafata" bai sake cewa komai ba ya fara qoqarin faka motar,sannan ya saka hannunsa a aljihun gaban motar ya budeshi,ya ciro wrapper din 'yan dari dari sababbi ya miqa munira "Bata,tasa kati a waya" "Ina taga waya,saidai tasha chocolate" munira ta fada cikin sigar zolayar iman tana miqa mata kudin. Kememe iman taqi amsar kudin,saima ta soma takawa tayi gaba abinta tana cewa sai gobe "Ni nasan ba zata karba ba,amma ka barni da ita,zan kai mata gobe" tace da sadam,saiya sauke ajiyar zuciya,cikin kasala ya tada motar "Ban taba ganin yarinyar data yimun ba irin qawarkin nan ba,ki shigemin gaba don Allah na mallaketa" dariya munira ta saki "Karka damu,indai zaka saki kudi duk ba zaya gagara ba" "Mayyar kudi,bansan ina zakikai son kudi ba muni" dariya ta sake "A'ah ya sadam,kudi fa abun sone,babu meson wahala ko talauci,ko aikin nan da kake yanzu ba kudin kake nema ba?". Murmushi yayi kawai,don yasan wajen magana badai a kada muniran ba,gaba daya shi yanzu hankalinsa ya tafi ga iman. Koda washegari taje mata da kudin makaranta cewa tayi ba zata karba ba wallahi,harda qarin handset daya siya ya dora mata akai,kusan fada sukayi da iman din akan hakan,ita ta dage saita karba,dan uwanta ne,kuma babu dadi maida hannun kyauta baya,yayin da iman din tace sam batasan wannan zance ba,kawai daga haduwa da mutum sai ta karbi abun hannunsa?,tace waye ya bata ma a gida?. Wani kallo muniran tayi mata "Au daman duk yammatan da samari ke musu kyauta nunawa suke a gida suce wanene ya basu?,kowacce boyewa take tayi amfani dasu abunta,ki karba kawai,don gaskiya bazan iya maida masa ba,don bansan bayanin da zanyi masa ba" "Ki riqe na baki kyauta tunda ba zaki iya mayarwa ba" "Bani ya bawa ba,amma zan ajjiyesu har zuwa randa zaki amsa" ta fada cikin bacin rai tana zuge handbag dinta ta jefasu ciki,zancan bikin qawayensu guda biyu dake matsowa da aka zauna yi shi ya raba gardamar,duk da haka muniran bata sauko ba. Koda aka tashi tun daga bakin gate ta lura da motar jiya ce tazo daukan muniran saita zame ta gudu,ta canza hanya ta shiga motar haya tayi gida,washegari ta dinga mita da qorafi iman din tace da ita "Kada ma ki soma batawa kanki rai,don Allah bazan sake shiga motar wani a gida baa sani ba" tasan da gaske take idan tayi magana,don haka bata sake cewa da ita komai ba,sai kumbure kumbure da take mata alamun tashi fushi,dariya ta saki "Kyayi ma ki sauko" amsar da iman din ta bata kenan. ********. ******. ******** A nutse ya ajjiye almakashinsa saman keken da yake kai,sannan ya miqe ya nufo inda iman ke zaune saman wani stool tana fuskantarsa. Ganin ya dosota saita dauke idanunta a hankali,ya saki qaramin murmushi da ya sake qawata fuskarsa,ya zauna saman wani keken dake daura da ita,ya dora qafarsa daya saman wata kujerar roba da babu kowa akai. Shagon nasu yanzu babu kowa sai wani dan matashi guda daya daketa faman dinki,da alama masu kayan suna hanya ne,koma bayan sanda ta shigo din da yake cike da matasan,sunata shirin fita wata ball ta abokinsu,shi dinne yace ba zashi ba,don ba wani abokinsa bane na kusa,saboda dama ba mutum ne shi me tara abokai da yawa ba. "Banfiyason zuwanki shagon nan ba,kina ganin dai yadda kullum yake cike da mutane" dan turo baki gaba tayi "To ya alameen,idan ka dawo gida inna ba zata bari muyi magana bafa.......kuma lokaci yana qurewa,bikin gaba daya saura uku" idanu ya zubawa lips din da take turowar,kamar ya kama ya tsotse haka yakeji,saiya dauke idanun nasa yana tattara kansa waje guda "Me yasa baki kirani a waya ba?" Saita fidda idanunta duka a kanshi "Ka manta ne,inna ta hanani taba wayarta,tace ina qarar mata da kati" "Haba da Allah haba,ya zaayi ace budurwa kamanki aron wayar inna kike?,ai kinfi qarfin haka,wani idan ya ganki zai zaci babbar iPhone ki manya manyan Huawei kike riqewa" ya fada da salon tsokana. Kallon da al'ameen ya jefeshi dashi yasanya shi jan bakinsa yayi shuru,kafataninsu sunsan halinsa baya daukar wargi,hatta da ogansu me shagon wani lokaci kamar shakkar al'ameen din yake saboda kwarjinin da Allah ya zuba masa,uwa uba kuma mutum ne shi mai tsaiwa akan gaskiya,idan kaga ya dage kan abu,to idan akayi zuzzurfan bincike shine me gaskiya "Bani mu gani" ya fada yana miqa mata hannu,sai tabi hannun nasa da kallo daya nannade hannun rigarsa zuwa gwiwar hannu saboda yaji dadin kallo,cike yake da gargasa da jijiyoyin da zasu shaidamaka cikin jikinsa a murde yake,kuma qaqqarfan namijin duniya ne. Kunya ta kamata sanda ta miqa masa yankin atamfofin guda biyu taga ya janye hannunsa yana jan hannun rigarsa yana rufe hannayen nasa,idanunsa kuma na bisa fuskarta,da alama yaga kallon data bishi dashi kenan. Murmushi ya saki sanda taja hijabinta ta kare fukarta,yana qoqari yaga ya gujewa duk wani abu da zai sanya taji wani abu tattare da ita,bayason ya raba mata hankali tun yanzu ko yayi cikakken wasa da hankalinta,saidai lokaci yana nan zuwa da zai mantar da ita kowa cikin duniya saishi kadai. Tana miqa masa ta sauka daga kan kujerar don ba zata iya ci gaba da zama ba "Qawata zata kawo dinki yaaya don Allah,kada kace aiki ya maka yawa" "Karta damu,indai ta wajenki ta biyo" "Saika dawo" ta fada tana masa sallama,bai amsa ba illa binta da yayi da kallo,kominta a nutse kuma a tsare Allah yayi mata shi,yana jin sara qiris ya fara tilastata sanya niqab,yana jin ciwo cikin qirjinsa da zuciyarsa duk sansa ta fita koda makaranta ne,yafi jin dadi da samun nutsuwa udan ya dawo gida ya sameta cikin gidan. Wani irin shauqinta yakeji yana fusgarsa har ta bacewa idanunsa,ya sauke ajiyar zuciya yana sauka dubansa ga qyallen atamfofin data bashi,ya daga kai a hankali ya dubi matashin daketa aikinsa "Yahaya......ka dubamin atamfar nan don Allah ka gaya min kudinsu gobe ko jibi" "An gama" ya fada yana miqewa tare da miqa hannu ya karbesu. *********. *******. ****** K'arfe hudu da minti ashirin da hudu wayar inna ta kada,iman data kai jug din data hadawa munira lemo kitchen ta dire da sauri ta dawo ta daga tana amsa kiran,munira ta tsammata,kuma ita dince,saita aje wayar tana jan babban hijabinta ta dora saman atamfar dake jikinta,wadda al'ameen ya zauna ya bata lokaci sosai ya tsara mata dinki na gani na fada "Inna zan leqa waje na shigo da ita" "Saikin dawo" inna dake zaune tana qoqarin gyara saitin radio dinta ta fada,tana son ta kamo freedom radio don jin shirin mu qyaqyata kafin biyar na yamma tayi. Slippers dinta ta zura ta tako zuwa soron gidansu. Gab da zata fita shi kuma yana qoqarin shigowa,saura kadan suyi gware,taja da baya tana yarfe hannu tare da yamutsa fuska,abinda ya taimaka qwarai wajen fitowar dimple dinta duk sanda ta motsa fuskarta,yayin da shi kuma yaja da baya yana qare mata kallo. Yana iya hangen yadda tayi wani kyau duk da cikin hijabi take,yana jin shi daya ne a duniya yake iya ganin kyanta koda cikin lullubi take,kuma a kanta kadai yake da wannan baiwar "Ina zakije?" "Qawata din nan da zata kawo maka dinki zan shigo da ita" "Koma ciki" saiya koma da baya ya qwalawa daya daga cikin almajiran gidan kira,yace ya duba layin,idan yaga wata baquwa tana neman gidan nan ya shigo da ita,ya dawo ya zarce dakinsu sannan tuni iman ta kona ciki,duk da taso ya barta taje da kanta ta shigo da ita,saidai ba zata iya yi masa musu ba. Ba jimawa saiga sallamar munira,iman ta fito da sauri,suka rungume juna cikin murna,kamar wadanda suka jima basuga junansu ba,kai tsaye suka fada dakin inna. Cikin girmamawa ta gaida inna,innan ta amsa mata,sannan ta miqe ta fice zuwa dakin malam da tun daxu dama takeson shiga ta gyara masa kayan sawarsa ta barsu su biyu cikin rumfarta. "Hajar ibrahim khalil" munira ta fadawa iman wadda keta qoqarin zuba mata lemo da abinci bayan ta qarewa falon nasu kallo "Munira sulaiman" "Yaudai gani a gidanku,naga randa zakizo nima namu gidan" hararta tayi cikin wasa "Aiba zuwana kikayi ba,kawo dinki ne ya kawoki ko?" "Eh duk da haka,inda hakanne ma ai da shagon zan tambaya nakai musu direct,da qyar mafa yaron da kika aika ya ganoni" ta fada tana daukan lemon takai bakinta "Nazo fita mukaci karo da ya al'ameen,shi yace na koma ya tura sa'idu" ajjiye lemon tayi "Yaudai zanga ya alameen da zancansa ya cika mana kunnuwa aka hanamu sakat,ya al'ameen din nan me shegen tsauri da takura,hala ku biyu inna ta haifa kawai" kai ta girgiza mata tana murmushi "Mu uku ne,kawai yaya sadiq" "Amma ban taba ji daga bakinki ba" zamanta fa gyara saman kujera "Barshi wannan,bamu cika shiri dashi ba" dan dariya muniran tayi suka ci gaba da casa hirarsu,har ta soma bata labarin bikin wata cousin dinta da zasu fara,wanda tsiran kwana ukune dana qawarsu amina,wadda ta kawo dinkin ankonta yanzun. Yadda taketa bawa iman labarin bikin da yadda aka tsara komai ya tabbatar mata tana matuqar ji da bikin,har ta zolayeta da haka "Keee,ba dole ba,kinsan manyan mutanen da zasu halacci bikin?,inda naji dadi ana ya gobe dinner din amina zaayi kamu,ran dinner din amina ranar event din gidansu ango za'ayi ba namu bane,so babu lallai naje,washegari ne zaa tashi bikin gadan gadan" "Wai ita aminan dinner zatayi?" "Eh mana,wannan atamfar ai ita zaa saka ranar" tabe baki iman tayi,saboda ita duk wata harkar dinner ba zuwa take ba,bata damu da ita ba,koda ta damu dinma tasan ba dabi'ar gidan bace,babu me barinta "To inajin babu ni a zuwan" "Saboda me?,ya al'ameen zai hanaki ko?" Dariya ta kubcewa iman "Au,sharri zaki masa?har kinyi tafsiri ma?" Itama tana dariyar ta amsa mata "Eh to ai nasan qarshen zancan kenan,nidai badon yayanki bane Allah cewa zanyi da wata a qasa,wannan tsanani da boyo haka?,barima dai ya shigo inga ya yake ya alamin din" maganarta saita dan shigi iman,duk da haka tana dariya ta miqe "Yama fa shigo gidan amma kin jishi shuru,bari na duba koya gama na masa magana" ta fada tana ficewa,ta manta bata dauki hijab din nata ba. *LITTAFIN NAN NA KUDI NE,KI TUNTUBI WADAN NAN NUMBERS DIN DON BIYAN KUDIN NAKI* 09032345899 KO KUMA 09166221261 [04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 12 _YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_ _THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_ _DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_ _KHUMRAHS_ _KULACCAMS_ _TURARUKAN WUTA_ _NA TSUGUNNO_ _NA KAYA_ _NA GIDAH_ _NA GASHI_ _NA WANKA_ _NA WANKI_ _NA MOPPING_ _AIR FRESHENER_ _CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_ _WARDROBE BALLS_ _SCENTED PEBBLES_ _ARABIAN OIL PERFUMES_ _HAIR SPRAY AND CREAM_ _DILKE AND HALWA SET_ _KABBASA_ _BURNERS_ _KASKO_ _TONGS_ _COAL IGNITERS_ _SKIN CARE PRODUCTs_ _OUR TURARE SAMPLE SETS_ _BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_ _KUJERAR TSUGUNNO_ _SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_ _MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_ _SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_ _instagram:yerwaincense_and_more_* _WhatsApp: 08095215215_ ____________________________________ Tun daga bakin qofar dakin nasu qamshin turarensa ke karakaina,ya cika soron gaba daya,taja numfashi sosai ta sheqi qamshin,tana matuqar son qamshin turarensa,har yau kuma bata taba jin kowa da irinsa ba,babu abinda yake kashewa kudi sosai wajen siyansa irin turare. Knocking tayi yace a shigo,ta tura qofar a hankali,idanunta suka sauka a kanshi,yana tsaye gaban mudubi yana ajjiye kwalbar turaren da ya gama fesawar yana qoqarin dora hula saman kanshi,yayi kyau cikin shadda ruwan makuba,dinkin zamani daya fidda samartaka sa zallar kyan da Allah ya bashi. Ta cikin madubin ya kafeta da idanu,abunda bataso,sai ta kauda da kanta tana cewa "Yaaya,ta iso tun dazu tana jiranka" "Ganinan fitowa,wani waje zani na tsaya ne na shirya gaba daya kar na saba alqawari" ya fada yana daura agogon hannunsa,saita gaza tafiya yaci gaba da satar kallonsa har ya fuskanci haka,ta basar da sauri,sabida wani iri takeji da ganin kwalliyar da yayi din "Yaa ina zaka da yammar nan" sai daya gama daura agogonsa tsaf sannan ya amsa "Akwai wani da muka hadu da yace nakai takarduna,wala'alla idan da rabo zan samu scholarship,tunda suna da hanya" "Allah yasa a dace" tayi masa addu'ar da har cikin ranta haka yake "Ameen qanwata,na gode" tadanyi murmushi sannan ta miqe ta nufi hanyar waje. Cikin tattausar muryarsa yayi sallama cikin falon,munira ta daga kanta daga danna wayarta da takeyi tana amsa sallamar "Wow"bakinta ya motsa ta furta kalmar qasan zuciyarta,ta gyara zamanta sanda suke magana da iman "Karbomin fura wajen inna" ta amsa da to sannan ta miqe ta fita zuwa wajen innar,dakin ya danyo shuru,saiya qarasa kujerar dake daga bakin qofa ya zauna a hannun kujerar. Cikin fara'a gami da mutuntawa munira ta gaidashi,ya amsa kadaran kadaham,sanda iman din ta dawo da furar a cup ta miqa masa itama ta koma ta zauna. Sai daya fara kurbar furar a hankali cike da nutsuwa sannan yace "Muga kayan" saita dauka ledar ta aje masa a gabansa ta fidda kayan tana masa bayani,baice komai ba harta gama yana shan furarshi,sai data kammala dai dai sanda ya gama sha ya miqe da cup din a hannunsa "Imani....ki dauka ki aje wajenki,idan zan fita jibi ki tunamin" "To yaya" ta amsa masa sanda yake fita. "Wow....wow,wannan shine ya al'ameen?,badan wani abu ba da na saka kai wallahi" harara iman ta balla mata "Ba zaki yaudararmin yayana ba,saboda nasan baida kudin da zaki tsaidashi takara" dariya ta saki,tabbas abinda ke cikin zuciyarta kenan,saidai ba zata iya fitowa kai tsaye ta gayawa iman din ba,tako ina al'ameen yakai namiji,abu daya ya rageshi rashin 'ya'yan banki masu yawan gaske da zasu maisheshi wani,amma banda haka tabbas gawurtacce kuma isashen namiji ne. "Yanzu haka maganar ci gaba da karatunsa ce ta futar dashi" iman tadan bata labari "Allah sarki yayanmu,Allah ya bada sa'a" "Ameen" iman ta amsa mata,daga haka suka fada wata hirar. ********. *******Tana daga zaune gefan katifar dake shimfide dakin iman,bayan ta karbi dinkunanta da sukayi kyau sosai wanda al'ameen din yayi mata,wayarta na hannunta tana ta danne danne,da yake gwana ce qwarai ita din wajen danna waya,shi yasa babu inda ke mata wahalar shiga loko da saqo na kowacce irin waya "Kiyi sauri don Allah muje kada mu samu layi" munira tace da iman wadda ke shiryawa zasu wuce gidan qunshi,saboda gobe zaa fara bikin qawartasu "Na gama ai,hijabi kawai xan saka" ta fada tana ware gogaggen hijabinta me kyau "Kiwa Allah ki aje hijabin nan,wallahi wajen 'yan gayu ne sai kisa a dinga mana kallon tara saura kwata,ko kamar nawa mayafinne ki saka,tunda kinga dai babba ne,kuma bashi da shara shara" inan din ta buda baki zatayi magana munira ta dakatar da ita "Nasan yanzu zaki kawo karatun ya Alameen,goben ma kenan haka zakiyi?" Murmushi kawai iman tayi,don kamar ta shiga zuciyartata,maganar al'ameen din ya hanata saka mayafai zatayi mata,saita aje hijabin,ta bude ma'ajiyar kayanta,ta ciro daga cikin sabbin lafayar da yagana ta bata,wata 'yar uwar mahaifinta har guda biyar masu azabar kyau da tsada. "Kai kai kai,ke kinga kyan datayi miki kuwa,ma sha Alla,da ana musayar kyau Allah da tuni na karba naki na hadaki da nawa" munira ta fada cikin nuna santi da yabawa da kyan iman din tayi,wanda zahirin gaskiya gaskiya ta fada,wani kyau lafayan tayi mata,idan ka kalleta kamar ba zaka dauke ido ba,ita kanta dai data juya ta sake kallon kanta a madubi ta gasgata hakan. Tana tsaka da sanya halfshoe dinta da ya alameen ya siya mata 6k wanda ya dace da lafayar jikinta wayarta da ya alameen din ya bata tecno ta dauki tsuwwa,munira ta kalli sashen da wayar take,ta tuntsire da dariya tana cewa "Ana kiranki a rakani kashinki?' sai data manna mata harara sannan ta isa inda wayar take "A haka nakeson kayata" "Amma dai wallahi ba girmanki bane,dressing dinki sam bai kamaci wannan wayar ba" ta saba da jin wannan lafuzzan daga bakin muniran,don haka tayi banza da ita ta isa inda wayar take ta daga abunta. Sai data gama wayar ta dubi muniran "Su hamra ne,already wai suna wajen,har an fara yiwa wasu,mu kadane bama nan" "Nasan zaa rina dama,munyi delay da yawa" munira ta fada tana daukar ledar kayanta. Saida suka biya wajen inna,munira ta yiwa innan sallama da kuma godiya,ita kuma iman ta karbi kudin qunshin sannan suka fito suka wuce. AMARYAR KB BEAUTY PARLOR,katafaren wajen gyaran amare da uwayen gidaje,yammata harma da zawara,waje ne na alfarma wanda ya kasance iya kudinka iya shagalinka,wajene daya amsa sunansa,duk sanda kaje haka zakaga manyan hajiyoyi suna karakaina,suna dukkan wani nau'in gyaran jiki da kuma kayan magunguna na gyaran jiki da aka warewa waje na musamman a ciki. Amarya sakina itama iyayenta da danshinsu,hakanan wanda zata aura din shima ba baya bane,tun asali gidansu basu damu da karatun boko ba,kasuwanci sukafi bawa qarfi,don haka sanda miji ya fito mata ya kuma tabbatar musu zai siya mata dukkan wani certificate,basu wani jinkirta ba aka cireta daga karatun aka fara shirin auren nata. Tun daga shigarsu wajen iman tasan waje ne na matan da suka isa,dukkaninsu qawaye ne,saidai bata wani saba can dasu kamar yadda suka shaqu da munira ba,don haka bayan 'yan caftarsu ta qawaye da murnar shigowarsu,sai ta samu waje saman kujerun da aka tanada a wajen tayi zamanta,tana sauraren hirarrakin dake tashi a wajen,da kuma shige da ficen 'yan gayu mazansu da matansu. Hira suke irin ta matasan yammatan dakeji da tashen quruciya,dukkansu babu wadda ba daga babban gida ta fito ba,kusan ita daya ce ma kawai zaa ce iyayenta ba wasu masu kudi bane,saidai ita din ma shigarta fes take,kai bakace hakan ba. Abu daya ne idan ka lura dashi zaka gane banbamcinsu,manya manyan wayoyin dake hannun kowaccensu,da kuma irin kudaden dake jakarsu,kowacce ta fito da tata tana harkar gabanta. Mutum uku cikinsu saida samarinsu sukazo har qofar wajen suka basu kudin lallaen da gyaran gashi,kowanne cikin babbar mota,hakan kudin da suka basu sababbin ne a rafarsu. Kafin zuwan nasu suka saka gasa,duk wadda kudin da aka bata yafi na sauran yawa ita zaa fara yiwa,daga qarshe fahima ita ta cinye,dole ita aka saka za'a bari a fara yiwa. Ita dai nata idanu,sai wata matashiya dake kusa da ita wadda batafi sa'arsu ba da aka sawa lalle,tun dazu ake kiranta babu me daga mata,don haka iman din ta matsa kusa da ita "Bari na daga miki" "Yauwa na gode" ta fada a yagance tana murmushin jin dadin hakan da iman din tayi mata,ta riqe wayar da kafadarta ta fara amsa kiran,murya can qasa,wanda da alamu saurayinta ne ya kira,don sunyi doguwar waya sosai,har aka gama yiwa amarya sakina qunshinta da qawarta da sukazo tare,ango yazo daukarta,dukka suka tashi mata takiya,munira na cewa sai sunje sun gaisa. Ko alamar motsawa iman batayi ba,amma munira ta finciki hannunta,dole ta bisu. Yana jingine jikin fara qal din motarsu,wadda da alama sabuwa ce,su biyune shida wani matashin saurayin kamarsa,cikin fara'a da barkwanci irin na angwaye da qawayen amarya,tana tsaye daga gefe tana kallonsu,don ita komai ma sabo ne a wajenta,saboda wannan shine karonta na farko na bikin qawa a waje,ko cikin dangi ma ba kasafai take zuwa ba saboda nisa da suka dan mata,daga na uwa har na uban,sai dai daiku dake nan garin da suke. Kowa cikinsu ta fara gabatar masa da kanta da kuma sunanta,har aka gama,munira ta waiwayo "Matso mana iman" abinda yaja hankalin angon da abokin nasa kenan" Idanu abokin ya zuba mata sosai,ya furta "Subhanallah" har zuwa sanda ta iso idanunsa yana kanta "Itama cikin qawayenku take?" Saurayin me suna hashim ya tambaya bayan ta gama gaidasu "Eh....iman,ba kasafai ta fiya son shiga jama'a ba ai" "That's good" ya fada yana gyada kai,still ita yake kallo,abinda yasa ta takura kenan,taja da baya tana fadin "Bari naje kafin ku gama,kada azo kanmu babu kowa" "Wait iman....ki tsaya ki karba kudin liqi mana" kafada ta daga "A'ah,na gode sosai wallahi" daga hakata qara sauri tayi ciki tana mita cikin ranta,gaba daya batasan me yasa mazan yanzu suke da shegen kallo ba. Basu jima sosai ba suka dawo,sauran su uku kenan da suka rage ba'a yiwa ba "Haba iman.....haba da Allah,me yasa kike abu kamar baki waye bane,ke dan samarin nan ma na yayi da akeyi ki kasa yi,guy iya haduwa amma ki yarfashi ki taho,ke kinga yadda ya rude da zancanki bayan kin taho,Allah annabi a hadaki dashi?,at last dai dole muka bashi number dinki" idanunta ta zaro "Me yasa zaku bashi don Allah,me yasa zakuyimin haka?" Ta fada adan rude,dukkaninsu suka sanya dariya "Seriously da gaske nake,yanzu me zance da ya al'ameen idan yaga wani ya kirani?" "Waima.....wai.ya al'ameen,to meye a ciki?,shi kansa yasan kin isa a kirakin,waima idan bai bari an kirakin ba,jiqaki zaiyi yasha?,a yadda Allah ya halicceki iman saidai idan ba zaki dinga fita ba a gida zaki boye kanki" munira ta qarashe bayanan suka kuma goyi bayanta "Gaskiya kam,koni da za'a bani dama yaya na zan yiwa kamu" budurwar da ta taimaka mata dazu ta sanya baki a hirarsu,kowa ya sanya dariya. Ko a jikin munira ta qara gaba ta cire dan kwalinta don a fara yi mata gyaran gashi,yayin da iman ta dinga binta da harara tana gasa mata ita. Daidai sanda aka gama musu wayar muniran ta dauki tsuwwa,ta daga da hanzari "Ina zuwa.....Allah bazanyi missing ba,gani nan zuwa" shine abinda muniran ta fada tana maida wayarta jaka "Don Allah don annabi qawalli ki rakani kamun nan,ban zaci abun haka aka shiryashi ba sai yanzu da batula ta kirani,ba zamu jima ba in sha Allah zamu taho,kinga hanya daya zamuyi,gida zan koma zan debo kayana,sai gobe zan wuce gaba daya" da farko uzuri ta bata kan yamma tayi sosai,kafin suje ma magariba tayi,kuma malam yana fada idan tayi dare a waje,haka ya al'ameen,da qyar munira tasha kanta,tace zata rakata har gida ta yiwa inna bayani,zannan ta aminta,nan cikin kayan data amso dinki ta zabi daya daga ciki ta sauya,ta kuma biya aka mata lite makeup,tayi tayi iman ta dauki wani a ciki itama ta sauya tace aa,kayan jikinta sun isheta. Tun daga shigansu wajen iman ta tabbatar lallai bikine na manya,wadanda sukaci suka tada kai,wani mahaukacin gida ne mai dauki da tafkekiyar haraba,wanda ama qawata ta da decorations irin na biki,duk yawan jama'ar dake wajen ta daukesu tsaf,harda ragowar sararin da motocin gidan ke fake abinsu basusan anayi bama. Tunda suka shiga din iman ta samu seat ta zauna,daga inda take din tana iya hango yadda komai ke wakana,amarya tayi kyau iya kyau tare da angonta,sai gudanar da komai ake cikin fariya boko da kuma nuna wadata. A hankali ta daga kanta ta kalli yadda sama ta fara duhu,alamu suna nuna anyi kira sallar magariba zuwa yanzu,duk da bata iya jiyo kiran ba saboda tashin kidan daya karade wajen. Kome take kuma ko a ina take bata wasa da salla,haka aka tarbiyyantar da ita,don haka ta laluba wayarta ta fara kiran munira babu qaqqautawa,wanda sai a kira na biyar ta samu ta daga,tace mata gatanan zuwa,ba jimawa kuwa sai gata,da alamu biki yayi biki "Nifa zan wucw gida gaskiya,gashi har anyi sallah mu bamuyi ba" "Don Allah ki bani minti goma kacal,ummi ce zata bani saqo na tafi dashi" mahafiyace,ba zata iyace mata karsu jira ba,saita rausaya kai "Idan na koma gida malam ya koroni kyasan inda zakiyi dani,kaini wani wajen nayi sallah" dariya ta saki "Ba korokin da zaiyi,ya kori auta ai babu wannan maganar,muje na rakaki" tare suka jera da ita,saidai duk inda suka gifta sai an kalli iman din,yawanci kallo ne na baqunta da kuma tsarin surar da Allah yayi mata,wadda ta fita daban data sauran mata. Ganin yadda hanyar shiga gidan ke cike da mutane sai iman din ta dakata da bin munira "Gaskiya ki samarmin wani gurin inda zan kebe ni kadai nayi sallata,cikin gidan nan da alama a cike yake,kuma ni babu wanda na sani" tayi qoqarin nuna mata babu komai ta shiga amma tace a'ah,don haka ta jata can bayan gidan,inda garden din gidan yake,wanda ke wadace da grass carpet,da kuma famfunan da ake bawa lambun ruwa "Yauwa,yanzu naji daidai" iman din ta fada tana ware idanunta cikin wajen saboa yadda ya birgeta,wata iska ta daban wajen yake fitarwa,bugu da qari shuru yake kamar ba cikin gidan dake cike da hayaniyar biki yake ba "Ki kirani idan kin gama saimi wuce,ni hutun sallah nake" "Baki da matsala,amma dana gama zazu zamuyi gida" "In sha Allahu" ta fada tana juyawa da sauri zuwa ciki,iman ta bita da kallo,cikin ranta tana mamakin yadda muniran ke bala'in son alaqa da masu kudi,take kuma qaunar bikinsu,saita dage kafada,qila don ta taso taga haka danginsu yake. A hankali take takawa zuwa wajen wani famfo daketa zuba shi kadai yana aika ruwa zuwa sasannin shuke shuken dake fadin lambun,ta tsaya a gabansa cikin nutsuwa,ta waiga ta tabbatar babu kowa,sai ta fara ware lafayar dake jikinta don kada ta jiqe,ta ajjiyeta gefe,ta daura alwalar,sannan ta dauketa ta yafata a matsayin mayafi kawai ta tada sallarta,sai data idar sannan ta miqe,ta zameta daga kanta ta fara daura abarta a jikinta. Sau uku tana nadata tana jin batayi mata dai dai a jikinta ba,karo na hudu taja tsaki ta fara warewa da xummar sake daurawa "Kawo na tayaki tunda kin kasa" sautin muryar daya daki dodon kunnenta kenan wanda ya razanata,ta kuma rude gaba daya,ta damqe lafayar tata da hannayenta gaba daya,a kuma matuqar tsorace sannan a razane ta waiwaya don ganin waye?,daga ina kuma ya shigo ko ya fito?. *ZAFAFA BIYAR* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 YAN NIJAR 👇 +227 95 16 61 77 Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_*13 _YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_ _THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_ _DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_ _KHUMRAHS_ _KULACCAMS_ _TURARUKAN WUTA_ _NA TSUGUNNO_ _NA KAYA_ _NA GIDAH_ _NA GASHI_ _NA WANKA_ _NA WANKI_ _NA MOPPING_ _AIR FRESHENER_ _CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_ _WARDROBE BALLS_ _SCENTED PEBBLES_ _ARABIAN OIL PERFUMES_ _HAIR SPRAY AND CREAM_ _DILKE AND HALWA SET_ _KABBASA_ _BURNERS_ _KASKO_ _TONGS_ _COAL IGNITERS_ _SKIN CARE PRODUCTs_ _OUR TURARE SAMPLE SETS_ _BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_ _KUJERAR TSUGUNNO_ _SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_ _MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_ _SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_ _instagram:yerwaincense_and_more_* _WhatsApp: 08095215215_ ____________________________________ Matashin saurayi ne tsaye a bayanta,fari qal,wanda har wani yellow yake saboda haske,ma'abocin kyau na gaske,wanda fuskarsa ta cika da baqin gemu da kuma sumar kai,ba siriri bane kamar yadda yake ba mai qiba ba,jajayen lips dinsa dauke suke da murmushin da ya bayyana fararen haqoransa,yana sanye da wata muguwar shadda daketa faman zuba qyalli da maiqo,ruwan hanta wanda ta dace da fatarsa da kuma fitar da kyansa muraran,hannayensa na goye qirjinsa,wanda hakan ya bayyana muqullin motar dake soke cikin daya daga cikin 'yan yatsunsa. Tsoro ya sanya ta sake ja da baya ganin yadda yake ci gaba da kallonta,murmushi shimfide saman fuskarsa,cikin wata murya mai zaqi ya sake cewa "Gashi nadin yayi miki kyau sosai da sosai,saidai kuma kuma baki iya daurawa ba,halan mama ce ta daura miki kafin ki fito?" Rasa amsar bashi tayi sai idanu da take rarrabawa "Wannan auta ce da alama" ya sake fada yana komawa da baya a hankali ya zauna saman kujerar concrete dake wajen,har yanzu bai janye idanuwansa daga kanta ba,hakanan murmushin da yakeyi baibar kan fuskarsa ba "Iman.....iman" sautin muryar munira ya fara shigowa wajen,da alama ita take nema "Uhunnn.....da alama ke suke nema,abokan tafiyarki ne ko?" Ba tare daya jira amsarta ba ya dora "ki daura abarki,lemme close my eyes" ya fada yana lumshe qananun kyawawan idanunsa. Ta tabbatarwa kanta ba zata iya fita a haka ba,saboda al'ummar dake harabar wajen sun ninka shi a yawa,saita leqa a hankali,ta tabbatar da gaske idanunta a rufen suke,don haka cikin sauri ta fara daurawa. "Are you finished......an min izini na bude idanuna?" Ya fada a tausashe "Eh" ta amsa cikin sanyi,ya bude idanun nasa tarwai saman fuskarta "Wow.....wow I didn't realize yadda ta miki kyau kamar yanzu da nake kusa dake, please ke wanne yare ce?......i think kanuri ne suke amfani da ita ko?" Yadda yayi maganar har saman fuskarsa ya nuna da gaske so yake ya sani,don haka ta gyada kai "Eh sune" "It means ke din kanuri ne?" Kafin tace komai munira ta iskota "Canza waje kikayi kenan inata bul......" Maganarta fa maqale a maqoshi sanda idanunta suka sauka a kansa,saita rusuna da sauri cikin girmamawa "Yallabai barka da yamma" cikin wata dakiya wadda bada ita yanzu yanzu suke magana da iman ba yace "Barka" kafin wani a cikinsu ya sake magana wata muryar ta sake cika wajen da kiran sunan "Bassam.......bassam" "Hey guys.....wannan kiran fa?" Ya fada yana daga sautun muryarsa dake da zaqi,wanda har sai da iman tadan sake kallonshi. Mutum biyune suka qaraso wajen,dukkansu samari ne da kana musu kallo daya zakasan sunaji da jini da ajiki da kuma tashen samartaka,kowannensu kalar shigar dake jikinsa zata fallasa maka wadatar da yake ciki "Shege....baka da mutunci wallahi,na dauka da gasken kayi tafiyarka" daya daga cikinsu ya fada yana cika yana batsewa,tare da jifansa da harara,baki ya tabe kamar yadda mata kanyi "Gab nake da tafiyan ai,rabo yasa na ratso ta nan" yayi maganar kansa tsaye yana nuna iman da yatsan hannunsa,dukka suka waiwaya suna kallonta,abinda ya sanyata gaba daya taji ta tsargu ta kuma takura, "Rabon samun matar aure" kamar saukar tsawa iman taji maganar,wanne irin magana ce wannan yakeyi,bayan har yanzu basu zarce mintuna ashirin da fara ganin juna cikin rayuwarsu ba,batasanshi ba bai santa ba,har yanzu ko kalma daya tak bata furta gareshi ba,saita rutsashi da kallon mamaki,ganin haka shima ya tsareta da nasa kallon tare da murmushi mai qawatarwa "Yes,da gaske nake" ya tabbatar mata yana lumshe idanunsa tare da budesu a lokaci guda "Muni......qawarki ce?" Daya daga cikin wandanda suka shigo wajen ya tambaya,cikin murmushi tare da madaukakin farincikin da muniran keta qoqarin dannewa tace "Eh yaya ahlan,aminiyata ce......" "Zaku iya bamu waje mu tattauna?" Matashin da aka kira da bassam ya fada still bai iya dauke dubansa daga kan iman ba,sai ahalan din yaja da baya "Baka da matsala,but kada ka dade da yawa" "Alright" ya amsa a taqaice,dukkaninsu sai suka juya suka fara barin wajen,yayin da iman ta bisu da kallo cikin taraddadi,tamkar ta bisu amma ta gaza daga qafarta daga wajen. "Have a seat please" ta tsinci muryarsa yana tsaye daga bayanta kamar wani bodyguard da uban gidansa,ya tashi daga mazauninsa ya bata daman zama,bata da abun cewa illa qarasawa da tayi,a hankali ta zauna kamar yadda ya buqata,saidai bata wani saki jikinta ba kamar wadda ke dosane saman garwashin wuta. Qarasowa yayi a hankali,ya shimfida handkerchief a gabanta qasa saman grass carpet din yayi xaman dirshan,tazarar dake tsakaninsu ba me nisa bace,saidai bai kusantota da yawa ba,ya aza mata dukka idanunsa sannan ya fara magana da ita. "sunana bassam balarabe madaki....." Kai tadan daga kadan ta kalleshi,kamar tasan sunan,kamar tana dan jinsa cikin kafafen yada labarai "Nine da na uku a wajen mahaifina,da na farko a wajen mummy na,shekarata ashirin da da takwas,'yan kasuwane mu duk da muna karatun boko me zurfi,hasalima nine jagoran dukka kamfanonin madaki general enterprises,ban taba aure ba,saidai for now zan sanya damba,domin kuwa naga matar aure,sai kuma inda qarfina ya qare,ki daga kanki ki kalleni da kyau kiga nayi miki ko banyi miki ba,saboda ni din mutum ne kaifi daya,banason boye boye kuma ban iyasa ba....."shuru ne ya ratsa tsakani,bata ko motsa ba bare ta daga kai ta kalleshi,sai wani bugu da zuciyarta keta famanyi,saboda tsayin rayuwarta bata taba tsaiwa da wani da sunan saurayi ko soyayya ba saishi. Duk yadda yayi kan ta dubeshi ko tace wani abu taqi,har wayarta ta dauki tsuwwa,sunan inna ya bayyana,abinda ya sanyata miqewa zumbur kenan "Innata ke kira,tun daxu muka fito,kuma tacemin kada nakai dare a waje" tayi masa bayanin tana qoqarin bin bayan kiran inna daya katse. Wayar ya zubawa idanu har zuwa sanda kiran ya shiga,a dan rude takewa innar bayanin gata nan a hanya,bata saurareta ba sai fada da taketa tsula mata kamar xata rufeta da duka ta cikin wayar,dai dai sannan munira ta sake shigowa. "Kije xan rakota zamu fito" amsar daya hawa munira kenan,saidai kafin ya miqe iman har tabi bayan munira,cikin azama ya cimmata suka jero. Sai gaba daya ta duburce saboda yadda idanuwa suka dinga yawo a kansu,suka dinga jan hankalin mutane,ta lura sam ko a jikin bassam,sai hira da yake janta dashi cikin lanqwashashiyar murya,idanuwansa a kanta duk bayan sakan uku zuwa biyar,har suka qaraso parking lot na gidan. Milk color din wata jibgegiyar mota ya bude mata yana fadin "Bismillah" baya taja,idanunta na nuna alamu na tsoro "Xan qarasa titi nahau napep" waiwayawa yayi ya kallo munira "Ke baki gaya mata anguwarnan ba'a samun abun hawa na haya ba?" "Bata sani ba" munira ta amsa masa cikin wani salo na yauqi irin na 'yammatan da suke ji da kansu "Ok,muje na fitar dake titi a motar,amma bisa sharadi daya......idan ba'a samu abun hawa ba,zan kaiki unguwarku" a jikinta takeji zaa samu,don haka tace masa ta yarda,saiya gyada kai yana murmushi "Allah kasa nayi winning", ya fadi harda daga hannayensa sama,tadan dauke kai kadan yana son bata dariya ganin yadda ya haqiqance bilhaqqi. Wani sassanyan qamshi ke tashi cikin motar,ko ba'a gaya maka ba kasan turaren da yake amfani dashine ya hadu da qamshin freshener na mota da kuma sanyin ac ya bada wani yanayi me mugun dadi,tun daga waje dama zakasan motar sabuwa ce,cikin motar kuma shi xai qara tabbatar maka da hakan. Addu'ar bassam itace taci kuwa,don sun jima suna tsumayin samun abun hawa saidai babu shi,dole hakanan tana ji tana gani suka dauki hanya zuwa unguwarsu,zuciyarta ta dinga bugun uku uku,ranta cike fal da tsoro da kuma fargabar kada ta hadu da wani dan gida. Tunda suka soma tafiya yake janta da hira,cike da nuna tsantsar kulawa da wani salo dake nuna zallar shauqi,baiji kunya ko nauyin ganin idanuwan munira ba ya dinga fayyace mata zuciyarsa,kalamansa suka dinga yi mata nauyi aka,har kunya tasa ko cikakken motsi ta kasa,karo na farko da wani ya zauna yana shirya wasu manyan kalamai wai duk don saboda ita,ta yadda lallai kamar yadda ya gaya maya ne,shi din bashi da boye boye ko kuma rufa rufa,a haka har suka iso dab da layinsu,tasa ya ajjiyeta daga baya baya. Har tasa hannu zata buda murfin motar da hanzarinta,ya danna mata Lock "Ya zaki tafi ki barni haka?,babu gamsashshiyar amsa,sannan kuma babu madafa,so koke gobe ayi jana'izata?" "Me kake buqata?" "Phone number dinki" ya amsa mata kai tsaye,so take ya barta ta wuce don haka ta fara karanta masa yana serving,duk da haka bai barta ba har sai daya kira yaji ta shiga sannan yace "Thank God" ya furta yana fitowa shima da sauri dava motar,ya zagayo inda take ya bude mata cikin girmamawa. Waiwayowa tayi ganin ya fara take mata baya yana biye da ita kamar wani bodyguard,ta buda baki zatayi magana,ya ritsata da kallon nan nasa "Tattaki zan miki angel...."ya amsa mata tambayarta tun batakai ga yinta ba "A'ah,don Allah ka bari,wallahi na gode,zan qarasa,munira zata rakani" hannayensa ya sanya ya rufe fuskarsa kadan yana furzar da iska "Banso kika dakatar dani ba....but,ba yadda zanyi,abinda zuciyarki keso ya zama kamar umarni ne a gareni.....munira" ya kira sunan muniran da tayi mutuwar tsaye a gefe "Ki kulamin da ita,har ku isa gida banaso ku quda ya tabata.....deal" tunda ya fadi hakan tasan me yake nufi,ko banza yau za'ayi mata yayyafin kudi,tasan a zaune take wannan,haka suka jera da iman din zuwa cikin layinsu,bassam ya bita da idanu,yana jin kamar ya hadiyeta,wani wawan kamu soyayyarta tayi ma zuciyarsa,irin kamun da ba'a taba yi mata irinsa ba,bayajin zai iya haqura da yarinyar ba tare da ya mallaketa ba. *ZAFAFA BIYAR* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 YAN NIJAR 👇 +227 95 16 61 77 Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_*[04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 14 _YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_ _THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_ _DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_ _KHUMRAHS_ _KULACCAMS_ _TURARUKAN WUTA_ _NA TSUGUNNO_ _NA KAYA_ _NA GIDAH_ _NA GASHI_ _NA WANKA_ _NA WANKI_ _NA MOPPING_ _AIR FRESHENER_ _CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_ _WARDROBE BALLS_ _SCENTED PEBBLES_ _ARABIAN OIL PERFUMES_ _HAIR SPRAY AND CREAM_ _DILKE AND HALWA SET_ _KABBASA_ _BURNERS_ _KASKO_ _TONGS_ _COAL IGNITERS_ _SKIN CARE PRODUCTs_ _OUR TURARE SAMPLE SETS_ _BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_ _KUJERAR TSUGUNNO_ _SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_ _MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_ _SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_ _instagram:yerwaincense_and_more_* _WhatsApp: 08095215215_ _____________________________________ Cikin wani irin zumudi da zakwadi munira tayi hanzarin kamo iman suka jera "La'ilaha illallahu,wallahi kin cika 'yar baiwa iman.....dama ni jikina yana bani ke matar manya ce,da alama ke zaki zama tararuwar gidanku.....iman,kinsan kuwa waye bassam a karan kanshi kafin akai ga mahaifinsa?,kinsan yammatan dake layi da kai kawon kama qafa dashi?,bakya amfani da social medias ne,amma da basai na gaya miki waye bassam ba" hankalinta duka yayi gida,saidai tana saurara gami da fahimtar kowacce magana ta muniran ke magana akai "To sai akayi yaya?" "Don girman Allah kada kiyi mana baqulu da baqinciki,don wallahi bake kadai ba,hatta ni na warke,na kuma sake zama babbar yarinya,don Allah kada ki qauron baki,kada kice baki sonshi,saboda bassam irin mazan da kowacce mace ke buri da qauna ce" munira ta fada tana marairaicewa "Nifa tsaya kiji,na yiwa ya al'ameen alqawarin bazanyi soyayya da kowa ba" idanu munira ta fitar kafin ta maidasu "Kamar yaya?" "Eh,yace idan lokaci yayi zai fitarmin da miji" dariya ta saki sosai cikin nishadi "Dalla can,ashe ke baki da wayo,ya fadi hakane fa a sannan saboda qananun shekarunki,kada farinjinin da kike dashi maza suyi amfani da kya da kike dashi su yaudareki,amm kawo yanzu ai kinkai munxalin fara zance ma,tunda dukkanmu zance muke,ga wasu ma an fara aurarwa,koshi yaga bassam zai miki sha'awarsa,zai kuma so ya zama surukin gidanku" kai iman ta kada "Duk abinda ya al'ameen ya fada yana nufin abinda ya fada din" "Ikon Allah,nifa ban ganewa wannan dagiyar ta ya al'ameen ba,banda yayanki ne ai da sai nace ko kansa yakewa tanadi ne?" Waiwayawa kawai tayi ta kalli muniran,saita dauke taci gaba da tafiya batace komai ba,kunnuwanta na sauraren magiyar muniran kan kada ta tankwabar da soyayyar bassam kamar yadda ta yiwa dan uwata sadam "Ke kamar bakisan rayuwa ba iman,wasu har rubutu da maganin farinjinin samun mai kudi ake musu,ke kuma kin samu daga Allah amma zaki wofantar da damarki,ki godewa Allah wallahi,koda bakison sadam ko qawance kukayi wallahi saikin tserewa sa'a a cikin dangi da qawayenki,saikin wuce kallon raini,ke ba zakisan haka ba,amma ni naga abubuwa da dama kuma ina kan gani cikin dangin umma na,saboda mahaifina ba kowa bane,mahaifiyata tana auren mutumin da ba wani ba" wannan hirar ita ta kaisu ga qofar gidansu iman,wanda babu mutane sosai,sai dai daikun daliban malam da suka dawo daga gurare daban daban akayo gida kuma,wasu na cin abincinsu na dare wasu na hira,saboda yau din ba ranar karatu bace,uwa ba kuma alamu na nuna malam din baya kusa ma. Kallon da inna ta watsa mata sanda ta shiga shi ya sanyata ta shiga taitayinta,munira ta qaraso ta rusuna gaban inna "Don Allah inna kiyi haquri,wallahi gidan qanwar umma ta rakani,ummance kuma ta tsaidani zamu amshi saqo mu taho mata dashi,don Allah inna kiyi haquri,laifina ne" "Allah ya tsare gaba,amma ku kiyaye,kada ku bari ku dinga yin dare a waje,'ya'ya mata ne ku" "In sha Allahu inna,ayi haquri,na gode" munira ta fada tana miqewa,suka qarasa dakin iman din "Don Allah qawa na roqeki,nasan zai kiraki,koda baki sonshi ki tsaya ki saureshi a rabu lafiya" munira tace da iman cikin lallabawa sannan ya fito bayan sunyi sallama. Kayan jikinta ta fara cirewa ta sanya na zaman gida,sannan ta daura alwalar sallar isha'i,ta dawo dakinta ta tayar,data idar tayi zaune saman abun sallar,tana jin gajiya na nuqurqusarta,ta daga kai ta dubi agogo,bataji duriyar alameen ba,da alama bai dawo bane,da tuni ya nemeta. Idanunta suka sauka kan ledar da munira ta ajjiye mata me kayan takeaway na bikin data hadota dasu,ta janyo ta bude ta gani,su souvenir's ne kala kala harda na banza da rashin sanin ciwon kudi,sai kuma kayan ciye ciye. Jakarta ta zaro cikin kayan ta bude don ciro wayarta,hannunta ya sauka kan wasu abubuwa,ta zazzagesu da hanzarinta. Sabbin kudade ne fil a miqe,yan 200 bandir guda,idanu ta fiddo waje cikin tsoro da mamakin yadda akai kudin suka samu,sai kuma tayi tunanin na munira ne,tunda jakar na hannunta,don haka ta dauki wayarta ta cire lock din ta fara qaqarin nemanta,saita ga alamun tex,ta buda don duba daga ina yake. Ta zaci daga kamfanin mtn ne,don su kadai ke tura mata saqo,saidai a yau din akasin hakanne,don kuwa wata tsararriyar number ce dauke da wani zazzafan saqo,wanda ke cike da wasu shiryayyu kuma tsararrun kalamai dake nuna zallar shauqin soyayya da ma'abocin saqon ya tsinci kansa a ciki. Sau uku tana karanta saqon tana komawa farko,sai daga qarshe idanunta suka kai kan sunan bassam,ta maimaita sunan sannan ta goge saqon da sauri,zuciyarta na bugawa,ta fita ta kira munira "Kinyi mantuwar kudinki cikin jakata fa" "Ba nawa bane,naki ne,bassam yace a baki" kicin kicin tayi da ranta "Amma me yasa zayimin haka?,kinsan dai bana karbar kudin kowa ko?ko sadam da yake dan uwanki ban karbi kudinsa ba kin sani,bare wannan da bansan kowa nasa ba" "iman.....wai me yasa kike haka ne?,kinsan dai babu kyau maida hannun kyauta baya ko?,ya zaa dinga miki alkhairi kina qin karba?" "Na karba idan an gani a gida nace me?" "Dama ni bance ki nuna ba,idan kinsan za'ayimiki fada ki ajjiye abinki ki dinga zara kina amfani dashi" "Banaso munira,kizo kawai ki karba abinda ki maida masa" dariya taji ta qyalqyale dashi "Toni ina zan ganshi yanzu?,bayan kin fita daga motar naji yana waya,a taqaice dai a abuja zai kwana ba'a kano ba,sannan na riga da nayi masa alqawarin zame masa jagora wajen samunki,kinga idan kina tsoro ma kina iya bashi dama yazo gida yaga malam......hakan zaisa kuyi tarayyarku babu tsoro ko shakku,kiyi amfani da kudinki kawai malama,sai da safe" munira ta katse wayarta abunta ta barta da waya a hannu. Karar shigowar kira ya sanyata zabura,saura kadan wayar ta subuce a hannunta,tayi qoqarin saka wayar a silent sannan ta nutsu ta duba me kiran,idan har idanunta dai dai suke nuna mata number dazu ce data tura mata saqo,saita samu kanta da latsa ok,ta kara wayar a kunneta. Zazzaqar muryarsa ce ta fara dukan kunnenta,a hankali ta amsa masa sallamarsa "Kin tafi kin barni da kewarki,inajin kamar ba awannin da suka shude bane muka rabu,kamar wasu shekaru ne suka raba tsakaninmu....." Yayi maganar cikin salon iya jan hankalin diya mace,da kuma zallar qwarewa wajen sace zuciyar diya mace "Don Alla kice wani abu kafin zuciyata ta fashe imani......zuciyata ta kamu da mahaukacin sonki,wanda har ta fara hasashen yadda rayuwa zata kasance mata babu ke". Wata ajiyar zuciya cw ta subuce mata saboda nauyi da kalamansa suka fara yiwa zuciyarta "Me zance maka to?" Ta samu kanta da furtawa "Koda bakice komai ba ki saki jiki ki bani dama,don koda baki fada ba na samu labarin nine mutum na farko da zan fara bude zuciyarki,so inason ayimin alfarma a kuma bani dama,nayi dashe me kyau,wanda zai bada kyakkyawar yabanya......don Allah beauty" ya qarashe maganar cikin marairaicewa. Murmushi mara sauti ya subucewa fuskarta,ashe itama watace,ashe takai a gaya mata kalamai har haka anema soyayyarta,itama ashe takai,kalaman baqine ga kunnenta,saboda haka nan da nan ta sake ta bashi kunnuwanta,yayi amfani da wannan damar ya dinga mata hira me matuqar dadi,yana kodata gami da yabata takowanne fanni,tare da kuranta matsayin data samu cikin 'yan daqiqu,da kuma yadda zuciyarsa ta mato mata. Kiran sunanta da taji inna nayi daga tsakar gida ya dawo da ita daga nisan kiwon da tayi,cikin hanzari ta katse wayar,ta kuma kasheta gaba daya ta tura qasan filo,cikin yanayi rashin gaskiya ta kwasa ta yiwo waje da sauri ta tsaya kan inna "Gani inna" kallo ta bita dashi a nutse kafin daga bisani tace "Me kika shiga daki tun dazu kika zauna kinayi ko abincinki baki dauka ba?" "Sallah nake inna?" "Qara'insu kikeyi?" Da sauri ta girgiza kai "A'ah inna,isha'i ce kawai,gajiya tasa dana gama nadan kwanta,kinsan munsha zaman lalle" "Yayanki ya shigo,bakiji shigowarsa ba?" Tayi mamaki,don har ga Allah bataji shigowar tasa ba da gaske,karo na farko da irin hakan ta faru,don babu wani abu dake shagaltar da ita ta kasa jin shigowar al'ameen din "Banji ba inna,gyangyadi ya saceni" ta fada tana istigfarin qaryar data sharara "Dauki abincinsu kikai musu,daga nan ki cewa sadiqu yazo ina kiransa" "To inna" ta fada tana daukar babban farantin kayan abincinsu tayi dakin. Kamar ko yaushe sai data tsaya tayi sallama aka bata izini sannan ta cusa kai,dashi idanunta suka fara karo,hannunsa riqe da wayarsa yana kallon wasu styles na dogayen riguna daya dora a account dinsa na Instagram,wanda bai jima da budeshi ba bisa shawarar sadiqu. Sexy eyes dinsa da suka sake lumshewa saboda gajiya da yunwa ya buda a hankali ya sauke a kanta,ta qaraso a nutse ta ajjiye farantin "Sannu da zuwa yaya" "Yauwa queen.....ya gida?" "Lafiya lau yaya,ya aiki" "Alhmdlh,zubamin abincin" ya fada yana zamowa daga saman kujerar zuwa qasa,hankalinsa akan lallenta baqi da ja wanda yayi masifar zanuwa saman farar fatarta me haske sosai "qunshin yayi kyau sosai queen" ya samu kansa da fadi sanda take qoqarin zuba masa abincin,saita daga kai suka hada idanu,cikin jin nauyinsa tace "Na gode yaya" "Amma garin yaya kikayi dare haka?" Dan raurau tayi da fuskarta "Allah yaya munira na raka wajen event din cousin dinta,kuma ta yiwa inna bayani" "Ki kiyaye please,kinga ke Queen ce,bai kamata sarauniya guda a dinga ganinta a araha a waje ba har dare" murmushi ya sake subuce mata,ta gyada kai tana murza yatsun hannunta,daidai sannan sadiqu ya fito daga bandaki "Zubamin nima ina zuwa,abu me sanyi yau nake sha'awar sha" ya fadi yana nufar qofa "Inna tana kiranka ma" "Tom" ya qarashe amsa matan yana ficewa. Yana cin abincin yana satar kallonta,sake kyau da zama cikakkiyar budurwa take,hatta da fuskarta ta nuna hakan balle gangar jikinta,kamar ma so take ta haura shekarunta,tana dagowa suka hada ido,sa ya mata nuni da wata leda "Ga mayafinki can" cikin murna ta tashi ta dauko tana dubawa "An gode yaya,Allah ya qada budi,amma yaya kala biyu ne fa" "Wannan zai hau kowanne kaya cikin ankon,kiyi amfani dashi,daga baya saina sama miki dayan" kai ta gyada kawai,amma bataso hakan ba,saboda anyi duka qawayensu kala daya zasu saka. Tana maidashi cikin ledar sadiqu ya shigo da lemukan a hannunsa,ya miqa mata wasu "Ki dauki daya ki kaiwa inna sauran" ta karba tayi godiya sannan ta fice. A wajen inna abincinta ta karba tace zataci a daki,hankalinta da tunaninta duka ya koma kan wayarta,koda ta shiga dakin,kunna wayar shine abu na farko data fara yi,tana gama kunnuwa saqonni suka fara rigen rigen shigowa a jere kusan guda biyar,saita koma ta zauna,murmushi na subuce mata tana qoqarin budawa ta karanta. [04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 15 _YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_ _THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_ _DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_ _KHUMRAHS_ _KULACCAMS_ _TURARUKAN WUTA_ _NA TSUGUNNO_ _NA KAYA_ _NA GIDAH_ _NA GASHI_ _NA WANKA_ _NA WANKI_ _NA MOPPING_ _AIR FRESHENER_ _CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_ _WARDROBE BALLS_ _SCENTED PEBBLES_ _ARABIAN OIL PERFUMES_ _HAIR SPRAY AND CREAM_ _DILKE AND HALWA SET_ _KABBASA_ _BURNERS_ _KASKO_ _TONGS_ _COAL IGNITERS_ _SKIN CARE PRODUCTs_ _OUR TURARE SAMPLE SETS_ _BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_ _KUJERAR TSUGUNNO_ _SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_ _MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_ _SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_ _instagram:yerwaincense_and_more_* _WhatsApp: 08095215215_ _________________________________ Dukkan saqonnin nasa suna tafe da kalaman dake nuna rudun da ya shiga kan katsewar wayar da kuma jinta a kashe da yayi bayan ya sake kira,magiya yake mata kan ta taimakeshi ta buda wayar tata,ta daure tayi kiransa,murmushi ta kuma saki,yanzu kashe wayarta kawai ya sanyashi a damuwa?,wanne irin so ne wannan?,har ta dannan kiransa ta fasa ta katse,ta ajjiye wayar ta jawo abincinta tahau ci,saidai tana ci gefe guda kuma zuciya da qwaqwalwarta suna dawo mata da abubuwan da suka faru wunin yau,tun daga haduwarsu kawo yanzu,duk kyanta da yake fadi gani take ya fita,saita miqe ta isa gaban mudubi tana qarewa fuskarta kallo,kalamansa a kanta na dawowa kanta turyan turya,sai ta kuma sakin murmushi,ta juya ta dauki kwanon abincinta da kayan ciye ciyen bikin da muniran ta hadota dashi don ta kaiwa inna ko zata iya cin wani abun a ciki. ***********Washegari*******. Da saqonsa tayi karin kumallo,wasu irin shiryayyun kalamai dake dauke da dandasa dandasan kalaman zallar soyayya,dolenta murmushi ya subuce mata bayan ta kammala karantawa,yakansa ta shiga mamakin wai ita din me muhimmanci ce har haka?,itama ashe watace data cancanci samun qauna maqura?,tana wannan tunanin saiga kiransa,ta sake yin sauri wajen saka wayar a silent. Sai data katse ya qara kira sannan ta daga "Beauty.....girmanki ne,amma kuma so kike na haukace na kasa aiwatar da abinda ya kaini abuja?kinsan kuwa samun hadin kanki shine kawai abinda zai bani nutsuwar aiwatar da abinda naje yi din?" Murmushi ta saki a boye "Ni wacece da hakan zata faru da kai?" "Kina mamakine ko kina tantama?,lallai da alama har yanzu bakisan irin matsayin da kike dashi a wajena bane,kinsan tunanin kina da wani masoyin da ranki keso kadai daga jiya zuwa yau ya sanyani nayi zuru zuru,zakiyi mamakin yadda na koma,please beauty......kicemin ni kadai ne wanda ya fara yaqin neman soyayyarki,duk nasan mafarkine kawai nakeyi,amma mace kamarki lodi lodin maza nasan ke gware a kanta" yadda yake maganar cikin laushi da sanyi ya bata dariya,har batasan tace dashi "Kai kadai ne" ba,wani qaramin ihu ya saki,wanda yake nuna zallar farincikin da zuciyarsa ke ciki "Yes.....kice na sanar da mommy a daidai" idanu ta zaro "Me?" Ta tambayeshi cikin mamaki da fargaba "Eh, already labarinki yaje wajen mommy,tun a jiyan ban iya barci ba sai dana gaya mata komai dana sani game da ke,infact ma ita harta matsu taga beautyna,na gaya mata,ta qara haquri har na shawo kanki tukunna" "Bassam" ta kira sunanshi a karon farko "Nifa na yiwa yayana alqawarin bazanyi soyayya da kowa ba, already ma yace shine zai zabarmin miji" wani mummunan faduwa gabansa yayi,take ya rikice mata,har abun yayi matuqar bata mamaki,da gaske yake kan duk abinda ya fada,da gaske ne yadda yake kururuwar sonta "Please give me a chance beauty,ki bani dama....na miki alqawari indai na kasa sace zuciyarki da samun soyayyarki zan amshi sunan looser,zan kuma rabu daki,amma na tabbata yayanki baya nufin abinda ya fada" sai data ce ta bashi damar sannan taji salama da sukuni cikin muryarsa. Da hanzari tayi masa sallama tana katse wayar,ganin ya kusa cinye mata lokacin aikinta,ta cusa wayar qasan pillow,sannan ta janyo dankwalinta ta daure sassalkan gashinta ta futo tsakar gida,qirjinta cike fal da bitar kalamai da al'amuran da suke gudana tsakaninta da bassam,tun daga haduwarsu kawo yau. Tana tsaye a kitchen tana dama kunu,tayi nisa cikin tunaninta,a hankali ya qaraso bakin qofar kitchen din,idanunsa suka sauka a kanta "Assalamu alaikum" yayi sallama cikin tattausar muryarsa dake cike da wata irin nutsuwa ta halitta,ta waiwayo a hankali suka hada ido,sai ta saki murmushi tana dan motsawa kadan "Wa'alaikumussalam,ina kwana ya amin" "Lafiya qalau queen,ki tashi lpy?" "Lpy qalau....." "Ma sha Allah,na godewa Allah da queen ta tashi lpy" murmushi ta sake,sai taji kalamansa na mata kama dana bassam "Zan samu ruwan dumi?" Tunda taji haka tasan daga motsa jiki ya dawo,shi yasa suk safiya bata rabo da ruwan dumin saboda shi,matuqar tana kitchen din,tasan yana shigowa zai nema "Eh yaya" ta fada da sauri,tana juyawa zuwa inda ta ajjiye flask din ruwan zafi,ta fara zuba masa,idanunsa na biye da ita. Daidai yadda tasan zai iya sha ta zuba ta miqa masa,hannu biyu yasa ya karba "Na gode" murmushin da ya sake fidda dimple dinta tayi,tana jin kunya ta masa abu ya gode mata. Ta zaci fita zaiyi a kitchen din,amma sai taga yaci gaba jingina da qofar,yana kurban ruwan yana binta da kallo,yana monitoring duk wani motsinta,wutar qaunarta tana sake ruruwa cikin ransa,yana jin cewa lokaci kadan ya rage komai yazo qarshe,banda ma delay da ya samu naci gaban karatunsa yadda yaso,da tuni zuwa yanzu komai yayi nisa,saboda ya riga ya tsara ci gaba da karatun iman din a gidansa,hankalinsa sai yafi nutsuwa da hakan "Akwai wani abune yaya?" Ta tambayeshi cikin jin kunya da kuma nauyinsa,miskilin murmushinsan nan mai cike da nutsuwa da wata izza izza ya sake,ya tashi daga jinginar da yayi ya tako zuwa kitchen din,ya dora mata cup din kusa da ita "Babu komai.....kawai ina kallom queen dita yadda take qara girma kullum tana zama 'yar budurwa" "Kai yaaya" ta fada da sauri tana sunne fuska,shi kuma ya saki 'yar qaramar dariya mai sauti kadan,ya taka ya fita a kitchen din. Wunin ranar gaba daya bassam bai barta ta huta ba,kowanne motsi nashi sai ya gaya mata ga abinda yakeyi,duk wani schedules nasa daga safiya zuwa dare tsaf sai data sani,tamkar tare suke aiwatar da komai. Ko wajen kamun surayya haka tayita fama da saqonninsa,yayin da munira ta hanata sakat da zancansa,batasan ya akayi ba sai ji tayi qawayenta sun fara tsokanarta da MRS BASSAM,kowacce a cikinsu cewa take "Gaskiya ba qaramar sa'a kika taka ba,yaro ne matashin saurayi da jini ke zagayawa a jikinsa,yaro ne da kudi amma hausawa sukance abokin tafiyar manya, friend dina ne a insta,kije kiga yadda 'yammata ke rushing a kansa,daya daga cikin qawayensu ta fiddo wayarta,ta shiga account dinsa na Instagram ta buda mata hotunansa ta miqa mata. Ta jima riqe da wayar a hannunta tana bin duk wani abu nashi daya dora a can,ta yadda da duk abinda suka fada din,daga kan hotunansa dake kan shafin nasa zakasan ba qananun kudi yake riqewa ba,kowannw hoto sutturu na alfarma ne a jikinsa,rabu da matan social media da kyakkyawan namiji,tarin followers ne dashi jingim maza da mata,abun ba'a cewa komai,kowanne hoto nasa ko wata magana da zaiyi,zaka tadda tarin comments da likes rututu a qasanta,ta sake gyara zama tana bin wallafar tasa. Ba qarya bane,komai yaji tattare da bassam din,ta sauke ajiyar zuciya tana sakin murmushi sanda wata 'yar ajinsu da ba wani magana suke da ita can can ba ta shigo tana tsokanarta itama da mrs bassam "Ya hadu guy din,bazan boye miki ba,nayi iya qoqarin na sameshi,to amma nasan ni ba type dinsa bace,shi din sai kyawawa dama irinku,ina tayaki murna gaskiya iman" murmushi kawai iman din ta bita dashi tana sake maida idanunta kan fuskar bassam. Kwana biyu sukayi suna casar biki,tana zaune qawayenta nata liqi wa amarya,saboda tasan ita din bata da kudin da zatayi liqin,sai daga bisani ta bude jakarta dauko wayarta don duba lokaci,batason ta sake dare kamar na rannan idanunta suka sauka kan kudin da bassam din ya bata,bata taba komai ba a ciki banda kudin transport datayi musu ita da qawayenta,saita zari masu yawa a ciki,itama ta isa saman stage t fara liqawa ango da amarya,take taji kanta daidai da sauran qawayenta dake wajen,suka dauki ihun sai mrs bassam,abinka da zuciya da kuma aikin dan adamtaka,sai taji kata yana fasuwa a hankali,sannu sannu sai datayi liqi me yawa da ya sanya mc kama sunanta sannan ta sauka ta kona gurin zamanta,cin maganinta ya sanya samari da yawa dakeson kawo mata caffa suka kasa qarasowa inda take. ********Washegari********** Wunin sakina,ranar ne kuma za'a kaita,saidai dukkaninsu basuje ba sai yammaci,dukka qawayen suka hadu,cikin daya daga cikin lafayoyinta da bata taba sanyawa ba ta shirya kanta,duk tafisu tsada shi yasa ta zabi ta sanyata,milk color ce me haske,sai adon gold a jiki,takalmin qafarta me tsini ne kuma mai tsinin dunduniya,ta ciki wani lace ta sanya mara nauyi,wanda ya amin yayi mata dinkin straight skeet da riga me dogon hanu,ta tara gashinta tayi masa nadin alkaki ta qasan daurinta samfurin ture kaga tsiya. Fadin kyan da tayi a lokacin bata bakine,saika rantse da Allah daga gidan wasu hamshaqan ta fito,saboda kulawa da take samu gami da sutura me kyau,kowa kaffa kaffa da dama dama da ita yake cikin qawayenta,abinda ta lura dashi ya fara faruwa tun sanda munira ta shaida musu bassam shine masoyinta "Komai yaji,wanka iya wanka,amma wallahi kika fito da wayar hannunki sai naji kamar zan nutse" munira ta fada dai dai yadda iman dince kadai zata iya ji. Sauke wayar tayi tana duban munira,wanda dama ta dauko wayarne saboda jin qarar shigowar saqo,wanda kuma take da yaqinin ba daga kowa yake ba illa bassam _"Kinyi kyau iya kyau baby.......,yanzu na shigo gida daga tafiya,amman bazan iya daurewa ba.....sai nazo naga wannan kwalliyar beautyna"_ wannan shine saqon da taci karo dashi,wanda mamaki ya kamata kan ta ina ya hangi adonta. Maimakon ta bawa munira amsar maganarta saita buge da tambayarta "Ya akayi bassam yaga kwalliyata?" Idanu munira ta wara "Wallahi ban sani ba,shida baya nan yana abuja?" "Ya dawo gida yanzu,kuma yana zancan zuwa ya ganni ba tare daya nemi address ba,bari naga gudun ruwansa,ta ina zai lalubo ni?" Ta fada tana gyara zamanta gami da gyara rufin lafayarta. Murmushi munira ta saki "Har yanzu bakisan waye bassam ba,mai kudin da idan yaso zai iya sanin duk wani motsi naki,amma bari mu gani,da rabon muje gidan amarya a lafiyayyar mota" munira ta fada cikin murna,batabi ta murnar munira ba,don tasan babu lallai yazo din,tunda baisan ina suke ba,saita dan goce kadan ta jingina da kujerar dake daura da ita. A hankali zuciyarta da qwaqwalwarta suka shiga tunani,suka shiga hasko mata fuskokinsa data gani cikin hotunansa na ista cikin mabanbantan yanayi da shiga kala daban daban,tarin tulin 'yammata daketa commenting akai,da kuma qoqarin jan hankalinsa zuwa private chat,a hankali taji shauqin son ganin fuskar tasa na saukar mata,saita lumshe idanunta tana bitar lausasan kalamansa da suka zame mata abokai cikin kwanakin nan,dasu take kwana dasu take tashi,ta kuma hadasu da fuskarsa iya shiga da tsari na jikinsa,take taji komai yayi mata dari bisa dari,sai ta lumshe idanu tana sauraren hirarrakinsu,tare da kasa kunne taji xai kirata ko zai turo saqo ya nema address?.*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_* 16 Taji mamaki sosai sanda yake shaida mata yana qofar gidan,ta dubi munira duban tuhuma,ta daga hannayenta sama alamun ba ruwana. A matuqar darare fa shiga motar sanda ya bude mata da kansa ya mata izinin shigar,shima saboda idanuwan yammata dake qofar gidan ana shirye shiryen daukar amarya da sukayi musu caa kamar zasu cinyesu. Nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana shafar qirjinsa "Thank God,sai yau dana ganki sannan naji kamar an ciremin qaya, beauty,i really missed you" kunya ce tadan saukar mata,taja lafayanta ta sake boye fuskarta ta murmushi "I liked it baby,inason kunyar nan taki,amma dai ya kamata adan fara rageta,a nunamin soyayya ko?". Hira yake janta da ita sosai cikin wani salo da yasan yana tafi da zukatan 'yammata,ya hada mata abubuwan sha da ci duka cikin motar saman dan wani abu da ake janyowa me kama a table,saidai taqi taba komai saboda bata saba ba,ba zata iya cin komai a gabansa ba,uwa uba kuma a takure take jinta,ga kalamansa daya cikata dasu wadanda suka yiwa kanta nauyi,taketa jin kunyar yadda yake marairaice mata kamar zai kwanta aka ta soshi don Allah,yayi alqawarin zai mallaka mata komai. Abinda bai sani ba tuni ya fara barin burbushin wani abu a cikin zuciyarta,ya sanya zuciyarta ta fara narkewa da kadan da kadan,hakanan tanajin wani abu na tabata duk sanda ta kalleshi,ta kuma tabbata kowacce mace ma dole taji irin wannan,saboda dan gayu ne iya gayu,wanda gayun ga hade da kyau da kuma ilimi quruciya da kuma wadatar arziqi. Kafewa yayi kan shi zai kaita gidan amarya,bazai barta tahau motar kowa ba,nan kuwa ta samu qawayenta 'yan tayi,kowacce tace a motar itama zata,a haka suka dibi mutum hudu daga cikinsu suka wuce. Ko a hanya ma bai barta ba,hira yake mata qasa qasa cikin kalaman da zasu iya wafce ko sace zuciyar kwacce irin mace,idam yaji tayi shuru cikin murya me kama da rada zaice "Uhmmm baby......baby kice wani abu mana,don Allah karki haukatani" wani abun ko bataso saita amsa masa. Da suka isa ma hanata fita yayi yaci gaba da dasa mata dashe me wuyar cirewa,su sauran suka shige ciki,sai da yaga an ragu sannan ya mata tattaki har qofar gidan ta shiga,sannan ya daw jikin motarsa ya jingina yana jiranta. Tana shiga kamar dama jiranta sukeyi kowacce ta shiga ihu da kuma zolayarta "Ku keshan soyayyarku,amma nice nake sumewa" inji zee qawarsu "Gaskiya gaskiya kika bar wannan guy din kin tafka asara,keee.....me tsada be wallahi wannan,samun namijin da komai yaji a tare dashi kamarsa ai abune me wahalar gaske,tabdi,gaskiya kin shiga sahun mata masu sa'a a duniya" daga daga cikinsu ta sake fada "Banda zaman amana ake ai ni zanyi wufff dashi" batasan ta jefa mata harara ba sai da suka kwashe mata da dariya "Almura,ashe ya fara sace zuciyar da akaqi bawa kowa dama". Haka suka hadu sukayita yi mata cari. Duk yadda taso ya barta ta samu abun hawa na haya ta koma gida yaqi ji bare gani,duk ta gama tsurewa,yayi parking qofar wani babban store ya fita bayan yace tazo su shiga tare amma taqiya. A qalla kusa minti talatin ya barsu cikin motar ita da qawayen nata kafin ya dawo,siyayya yayi mata mai ubansun yawa data sanya iman din tsurewa,ya dubi su munira yace su shiga ciki su karbo sauran kayan duka nasu ne. Sai da suka fita ya fidda wasu qananun leda guda biyu,daya daya bude wani dan qaramin akwati ne me azabae kyau,zobe ne a ciki me bala'in kyau da daukar idanu ya miqa mata "Saka,so nake naga yadda zaiwa kyawawan hannuwanki kyau" ya fada yana murmshi,yadda ya tsareta da kallo ya sanya dole ta saka zoben,ko don ta tsira daga kallon da yake jifanta dashi "Ma sha Allah,da dama da nayi kissing wannan kyawawan yatsu,Allah ya mallakamin su" tsananin kunya ya hanata magana,sai kawai ta janye hannun nata ta boye cikin mayafi. Leda ta biyu still shima wani kwalin ne,wanda ke dauke da wata santaleliyar wayar hannu,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan cewa ba qaramar wayar bace,bawai a girma na jiki ba,a'ah,kudaden da aka zuba kafin a mallaketa. Miqa mata wayar yayi,ta janye hannunta taqi karba tana dubansa "Na siyeta ne saboda ke,an saita komai da komai nata,akwai layi a ciki,na siyeshi ne saboda ni kadai,nafison duk sanda na kiraki na sameki available" babu jan dogon bayani tace mishi ba zata karba ba,yaji babu dadi har saman fuskarsa,saidai a nata ganin haka shine daidai,don batasan inda zata sanya wayar ba. Wannan dalili yasa ta kasa musanta masa sanda ya bata gift na ledar daya loda mata siyayya,suna tafe munira na mata rakiya kamar kowanne lokaci,saidai jikinta asabule yake "Munira,nufar gidanmu fa kike da wadan nan kayan" "Na sani,ki tsaya ki gani mana" ta bata amsa babu alamun damuwa a tattare da ita. A bakin famfo suka samu inna tana tarar ruwa a buta,da alama bandaki zata zagaya,ta daga kai tana amsa sallamarsu,cike da ladabi kamar kullum munira ta gaida innar,ta amsa mata tana tambayarta mutanen gidan,ta soma gajiya da ganin yarinyar tare da iman,bata fiyason mu'amalar iman din da baqin fuskar qawaye ba,duk da dama silar bikin sakina ne ya kawota gidan. "Inna wai kaya ne da sakina ta bayar a rabawa tsakaninmu qawayenta da muka yi mata hidiman biki,shine nace ta ajjiye mana a wajenta,idan yaso in an tashi sai a raba,sai iman din ke tsoron kada ki fada,shine nace bari na roqeki don Allah" Idanu innar ta sauke kan ledar da muniran ke nuna mata,kowaccensu tayi shuru tana jiran jin amsar da innan zata bayar,kamar ba zatae komai ba sannan ta amsa "Ba damuwa,amma karsu jima,banason ajiyar abinda ba naka ba" "In sha Allahu inna" daga haka ta miqawa iman ledar,sukayi sallama ita ta juya ta fice. Cikin kwanakin gaba daya bassam ya sanya wuta wajen nema soyayyar iman din,ya kuma ci galaba da gagarumar nasarar da bai taba kawowa kansa zai samu ba,ita kanta iman din ta fada wani muguwar soyayya da bata taba tunanin zata fada ta ba,sannu a hankali ta dinga ganin kyan da bassam da kuma sauran jama'a ke kururutawa tata,ta kuma hango dacewar da sukayi da bassam din. Da kuma dacewarsa da zamantowarsa miji a gareta. Ta samu sakewa da dukka kaya da siyayyar bassam sanda taje maiduguri ta dawo,saita sanya dukka kayan cikin tsarabar da yagana tayi mata,a zuwan ita ta bata su,ta fidda fella fellan laces din ciki ta bawa al'ameen ya dinka mata. Haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi sanda ya bude laces din xai dinka,tailor ne shi da yasan aikinsa,ya kuma san kudin kaya masu tarin yawa,a idanu kawai akace ka yiwa lace din kudi kasan ba qarami bane bare aje ga ainihin kudinsa,kusan guda uku ne kuma dukka haka suke. Yagana 'yar kasuwa ce,tana kuma samu sosai da kasuwancinta,to amma kuma laces din sunyi tsada da yawa,saidai daga bisani ya gargadi kansa,yakuma share maganar cikin ransa,tunda ya riga ya aminta da wace iman din,rainonsa ce,ta kuma tsotsi tarbiyya daga inda suka tsotsa,wato wajen inna da malam,ya budesu yayi mata dinkuna masu kyau,da suka sanya ta dinga murna sanda ya kawo mata su,ta kuma ajjiyesu,batayi amfani dasu ba sai da bikin murjana,daya 'yar ajintasu. Ta fita sosai cikin qawayen nata,ta kuma fita daban,ta haska yadda ya kamata,ta dinga jin kanta yana fasuwa cikin qawayenta,saidai tayi qoqari matuqa wajen hana kanta jin izza ko girman kai. Kasancewar bassam ma'abocin tafiye tafiye ne,baya nan akayo bikin murjana,yaji babu dadi sosai,saboda yaso su kasance tare a lokacin,don har yanzu abu na gaba da yake buri da buqata shine ta gabatar dashi a gidansu,ya samu 'yancin zuwa ganinta kai tsaye a duk sanda yaso. Saidai ita a nata bangaren cike take da tsoro da kuma fargaba,tsoron yadda zatayi bayani wa malam inda ta sanshi,a inda suka hadu,da kuma yadda akai har suka saba babu wanda ya sani,ina zatace ta samu lasisi ko kuma umarnin sauraronsa,uwa uba kuma ta sani,burin ya ami tayi karatu,basuyi cewa zata gabatar da mijin aure a dai dai wannan gabar da take aji biyar a makarantar secondary ba. Duk da baizo ba amma tuni wayarsa ta samu baquncin hotunanta tsala tsala ta hannun jakadiyarsa munira,wanda suka sake haukatashi tare da susutashi,suka kuma sanyashi qara daura damara da cin burin kasancewa da iman din,da kuma maidata ta zama matarsa kuma mallakinsa,ko me zaya kashe kuwa. Tafiyar al'ameen zuwa jigawa garinsu ya sake qulla wani sabon kusanci da kuma shafin soyayya tsakanin iman da bassam,saboda wayarsa daya bar mata aro kafin ya dawo,ita kuma tayi amfani da wannan damar,ta bude account na Instagram WhatsApp da Twitter,yadda zata samu damar ganin bassam din yadda ranta yakeso. Ta kuwa kalleshin,babu wani hoto nasa data tsallake ba tare data masa kyakkyawan kallo uku ko sama da haka ba,gayu iya gayu,kudi iya kudi ta gansu,gefe guda kuma ga ilimi kamar yadda take da sha'awa,daya qyalla idanu ya sameta ta WhatsApp kuwa kamar zaiyi me saboda murna,hakan ya sanya ta sake zama mayyar waya,kullum tana manne da ita a daka,Allah Allah take ta gama abinda take ta dauki wayarta su kasance tare. Tuni inna ta fara lura da canje canjen dabi'u da kuma halaye tattare da iman din,abinda yasa ranar da amin ya dawo daga qauye,suna tsakar gida,inna na saman babbar tabarma,shi kuma yana kan kujera 'yar tsuguno yana bawa inna labarin ci gaban da qauyensu keta samu,iman din na saman tabarma daban,ta tattara hankalinta gaba daya saman wayar,abinda yaso jan hankalinsa kenan,duk da suna hira da inna,amma kusan bayan kowanne minti sai ya daga kai ya kalleta,yasan cewa ba haka suka saba da ita ba a lokaci irin wannan daya dawo daga tafiya,tana nuna kewarta sosai a kanshi,abinci na musamman take masa,ta hada da ruwan zafi na wanka takai masa,yana cin abincin tana damunsa da hirar abubuwan da suka faru bayan baya nan,shima kuma tana tambayarsa abubuwan daya gani da sauye sauye da aka samu. Miqewar da tayi yasa inna tace "Ina zuwa?" Fuska tadan ya mutsa kadan "Kwanciya zanyi inna,na gaji" idanu ta kafeta dashi "Me yake damunki ne kwana biyu da kika koyi kwanciyar wuri?" "Kawai inna,saboda makaranta ma,da shirye shiryen qualifying da mukeso mu fara" sam maganar bata shigeta ba bare al'amin,wanda ya maida kansa ga qaramar keypad din daya tafi da ita,yana serving station din da yake yawan sauraran labarai a cikinsu "Wannan wayar ke daukan hankalinki iman......" Maganar da taso tadan tsoratata,amma saita dake,saboda tasan halin innar da matuqar bin qwaqwaqwafi "Games ne da yawa na dauko inna,kuma inajin dadin yi" "Dole ki maida masa wayarsa,tunda tana neman canzaki" saita marairaice cikin tsoro da faduwar gaban kada a yanzu yanzu innar tace ta miqa masa abarsa tunda ya dawo,kafin kuwa ta gama tunanin nata abinda ta zata din ya afku,innar tace da ita "Bashi wayarsa maza,tunda Allah ya dawo dashi lpy alhmdlh,aikin mori abinda kika mora,dama kullum malam cikin fadan me yasa ya barta a hannunki yake" "Don Allah inna........" "Karki min magiya" "Zan karba gobe inna,ki qyaleta" al'ameen ya shiga maganar,saboda ko waye mutum komai qanqantarsa bazaiso irin wannan titsiyen ba,zuciyarsa kuma fes take kan iman din,baya shakka ko zargin zata aikata wani abu ba dai dai ba,ko kuma ya saba da tarbiyyan gidan,yadai bata uzuri kan cewa rashin sabo ne,da kuma daukin wayar tunda ta jima tana sonta. _________________________________ *mg's skincare* Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩 Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️ Shin kinafama da Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata? Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫 Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind Bridal kit:18k Beauty kit:11k Student package:7k Herbal whitening soap:3k Chat 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Facebook: mg's skincare Instagram:glow_with_mgs Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝 Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩 Then @mgs skincare gat you covered 💯 Now is time to glow😍 Pamper ur skin🦵 Shine like bride👰🏻‍♀ Glow🧖‍♀️ 💯 tested nd trusted🤝 Guarantee Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 0704688116617 _YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:_ _THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME_ _DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN💘🙏 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU_ _KHUMRAHS_ _KULACCAMS_ _TURARUKAN WUTA_ _NA TSUGUNNO_ _NA KAYA_ _NA GIDAH_ _NA GASHI_ _NA WANKA_ _NA WANKI_ _NA MOPPING_ _AIR FRESHENER_ _CURTAIN AND CHAIRS SPRAY_ _WARDROBE BALLS_ _SCENTED PEBBLES_ _ARABIAN OIL PERFUMES_ _HAIR SPRAY AND CREAM_ _DILKE AND HALWA SET_ _KABBASA_ _BURNERS_ _KASKO_ _TONGS_ _COAL IGNITERS_ _SKIN CARE PRODUCTs_ _OUR TURARE SAMPLE SETS_ _BRIDAL SET (SAITIN AMARE)_ _KUJERAR TSUGUNNO_ _SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA_ _MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE_ _SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED_ _instagram:yerwaincense_and_more_* _WhatsApp: 08095215215_ __________________________________ Washegari bai karba wayar ba kamar yadda yace din,saboda sabgoginsa na dinki da kuma neman samun damar ci gaba da karatunsa da yaketa fafutuka,saidai a ranar yanajin yadda inna ke mitar yadda iman din fa tashi a makare ta fara ayyukan gida,wanda saboda quracewar lokaci bata samu gama aikin ba,inda daga qarshe ta shirya ta wuce makarantar a makare,innan kuma ita ta qarasa sauran aikin da ya rage din. Washegari qarfe takwas saura minti biyar na safe ya fito a shirye zashi su hadu da mutumin daketa masa fafutukar ganin ya samu tallafin karatu,ya gaida inna dake dauraye flask din malam na kunu sannan ya tambayeta malam,tace yana qofar gida,ganin takalman iman na makaranta yasa ya tambayi inna iman dun bata wuce makarantar ba? "Ina zata wuce,ta zama abunda ta zama,babu abinda ta iya sai kasala da sakalcin banza" sai yaji a ransa indai waya ce take sanyata hakan bai kamata ya barta da ita ba,don ko a jiya da daddare yana jin bambamin sadiqu kamar zai bugeta kan yace fa.kiqo masa abinci ta shantake,dama kuma can sadiqun zafi gareshi,bai cika haquri ba,don haka sai ya qarasa rumfar inna da kansa. Sallamarsa da shigowarsa gaba daya yayita,tana zaune a qas tana saka farar safarta,ta daga kai tana murmushi gami da amsa sallamar tasa,gabanta yadan fadi da fari,saboda ganin da tayi ya danyi mata zubi da bassam saboda adon da yayi "Ina kwana yaya?" Maimakon ya amsa mata sai ya maida mata da tambaya yana dan tsuke fuska "Me kike har yanzu baki tafi makaranta ba?" "Yaya makara nayi wajwn tashi" "Kin fara wasa da karatunki ko?" Saita girgiza kai "Aah yaya,bacci ne......" "Is ok,idan na dawo zan karbi wayata,ki sakamin a charge idan sun kawo wuta tayi full" a sanyaye ta gyada kanta,sam batason ya karba wayar,saidai......wayarce ta shiga ranta ko kuma alaqarta da bassam ce bataso ta yanke?. Tare suka fita shi da ita,sai daya sanyata a abun hawa ta tafi sannan ya tari nasa yahau,kasancewar ba hanya daya zasuyi ba. Tun a makaranta ta turawa bassam saqon maida wayar,ta kuma goge duk wani account da wani abu daya shafeshi,kama daga hotunansa daga tuttura mata,da kuma saqonnin sms,sai data tabbatar bata bar komai akai ba sannan ta maida wayar tata jaka,saidai rabi da rabi na karatun ranar ba shigarta yake ba,tana can ga tunanin yadda zasuyi kewar juna ita da bassam din,ta saba chart dashi,kuma yafi.mata dadi akan kiran ways,a chart dinne take sakewa sosai ta gaya masa sirrikan zuciyarta. *********Goma da rabi na daren ranar,wanda tayi dai dai da kwanaki biyu da amsar wayar daga hannun iman din,har ya gama shirin kwanciya saboda sammakon da yakeson yi gobe zuwa shagon dinki don kammala dikunan wasu amare,sai kuma ya miqe ya jawo locker dinsa sake jikin katifarsa,ya dauko wayar ya sanyata a charge,saboda tunaqa da yayi zai turawa wani mutum photon wasu takardu nasa. Gefan katifar ya koma ya zauna yana jiran charge din yadan hau,saboda bashi da tabbacin akwai charge akai,ya bata mintina goma sannan ya koma gaban socket din ya zauna yakunna wayar,bayan ta daidaita ya shiga gallery dinsa ya fada laluben hotunan takardun,tunda already yana dasu,saidai sama ko qasa ya rasasu,ya dinga kaikawo bai gansu ba,har zai haqura ya sake sabbin dauka,duk da yasan ba zasuyi kyan wadancan ba,saboda wadancan din anyi scanning dinsu a computer,sai kuma ya tuna,ya wuce zuwa recycle bin na wayar. Tun daga farko ya fara cin karo da hotunan da baisansu ba,bai kuma waye mai su ba,sa'an nan baisan mutumin dake jikin hoton ba rututu masu yawan gaske. Sosai kansa ya daure,ya dinga bin hotunan da kallo daya bayan daya,mamaki na sake cikashi ta yadda hotunan suka shiga cikun wayarsa. Sannu a hankali ya gangaro kan hotunan iman,iman dinsu dai,cikin salo na gaye da kwalliya,hotunan da sukayi masifar kyau suka kuma fidda duk wani kyau da Allah ya bata,duk da cewa shigarta bata bayyanar da tsiraicinta ba,amma kyan da tayi cikun hoton,kyau ne da bai taba ganin tayi irinsa ba a zahiri. Gaba daya qwaqwalwarsa so tayi ta tsaya da aikin yin kowanne tunani bare ta bashi hint na abinda ke faruwa,saboda yadda ta dode gaba daya kamar bata taba wani tunani ba,sai ya koma ya zauna dirshan sanda kwanyarsa ta taimakeshi ta tuna masa cewa iman itace mutum ta qarshe da wayarsa ta jima a hannunta. Wani mummunan faduwa gaban al'ameen yayi,har yaji kamar an samu wani abu an buga masa akai,gudun zuciyarsa ya dadu sosai,sai ya sauka da sauri,ya koma binciken wayar,bakinsa cike da addu'o'i cikin rudewa. Duk inda ya shiga babu komai an share,manhajar WhatsApp itace abu na qarshe daya duba,ba tare da yana da wani yaqini na samun wani abu ko hujja ba. Ga mamakinsa yana shiga WhatsApp din ya bude sarai,da alamun account din da akayi amfani dashi shine har yanzu kan wayar ba'a shareshi ba. Suna da hoton dake kan number farko kuma qwaya daya dake kan account din gaba daya ya sanyashu furta "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" dukkan wata dakiya da jarumta tasa ta fara zagwanyewa lokacin da ya fara bin chart history din,yana karanta hirarrakin da akayi cikin inbox din,wani irin gudu zuciyarsa taci gaba dayi kamar zata faso qirjinsa ta fado waje,kunnuwansa sukayi dummm wanda ya dauka har tsakiyar kansa,a hankali cikin wani salon sanda feeling na daina gane abinda ke kewaye dashi ya fara kutsawa cikin jikinsa,yana aikawa kowanne sashe na jikinsa,a hankali ya daina gane komai da kowa sai zallar tashin hankalin daya tsinci kansa a ciki,tashin hankalin da yayi masa ba zata,tamkar zuwan ajali ga dan adam. A hankali sai wayar ta gagara riquwa a hannunsa,ya zameta a hankali ya saketa gefansa,ya koma ya zauna sosai yana son fahimtar da kansa abinda ke faruwa,kamar bashi da idanunsa ya gani ba,saidai kuma wani sashe na kwanyarsa na gaya masa,ba iman dinsa ba,ba iman dinsa bace,hala ta bada aron wayar itama ga wani,idan ma ita dince ko dai wasa take?. A sannan ji yayi babu abinda yake da buqata banda yaga iman a gabansa ya tambayeta abinda ke faruwa,yana da burin idan ta tashi amsa masa ta amsa da cewa wasa take,ba da gaske take ba. Ba tare da la'akari ko kuma duba da cewa dare ya fara yi ba ya miqe da hanzar ya nufi qofar fita,yana so ya sadu da ainihin cikin gidan. Garam sukayi karo da sadiq dake shirin shigowa da ledar balangun da ya tafi siyo musu,saboda dukkanins mutane ne masu son cin dadi a bakunansu,hakan bai basu matsala ba,saboda kowannensu neman kudi yake tuquru "Haba mana master......saurin me kake?,gani na dawo,wajen ne akwai layi,kasan ya iya gashi" ja baya yayi yana duban sadiqun da yake mulmula goshinsa,wanda shi sam bai ma damu da nasa goshin da ya buge ba,saboda rudanin da yake ciki,gaba daya ma ya manta wai sadiq din ya tafi siyo musu nama. Idanu sosai sadiqu ya zuba masa yana masa wani baqon kallo "Amin.....lafiya kuwa?,wani abu ya faru ne bayan na fita?" Qafafunsa dake a mace kamar lawashin da yasha rana ya fara janyewa da baya da baya,bayan hankalinsa a sannan yakai kan agogo,ya kuma tabbatar bazai iya shiga cikin gidan a yanzu ba,sabosa bai taba shiga din ba idan ba wani abu bane ya taso "Babu komai" ya amsa ma sadiqu yana zubewa gefan katifarsa,tare da yin hobbasa na ganin ya saisaita mood na fuskarshi "Koda naji" sadiqun ya fada yana cire takalmansa ya dorasu saman abinda suke dora takalma dake bakin qofar dakin sannan ya shigo,ya bude musu naman yana bawa amin din labarai kamar yadda suka saba duk dare kafin su kwanta. Idan yace yana gane abu daya da sadiqun ke fada to tabbas ya zabga qarya "Ya baka cine?,wai anya lafiya kake kuwa?" Kalmar da sadiqun yace dashi kenan yana rutsashi da ido,abinda yayi silar daya ringa miqa hannu ya a zaqular naman yana hadiyewa ba tare da ya tsaya cikakkiyar taunawa ba bare ya gane wanne irin taste gareshi,haka ya dinga tsaya masa a maqoshi kamar wanda ke cusa dan wake,abinda yayi sanadiyyar qwarewarsa kenan yahau tari,wanda ya sarqafeshi sosai,sai da yasha ruwan sanyin da sadiqu ya bashi sannan ya lafa,da wannan ya fake yaje ya kwanta,saboda qirjinsa da ya dauki zafi,sadiq yace may be ko ulcer dinsa ce ta motsa kuma. Tunda ya kwanta idanuwansa a rufe suke gam,ko qwaqwaran motsi baya qaunar yaji a kusa dashi bare magana ko surutu,lokaci bayan lokaci yana bude idanunsa ya sauke ga agogo,yana qididdigar mintunan da suke gabansu kafin wayewar gari. Zuciya da tunaninsa sunkai sun komo,ya kuma rasa a wanne bigire zai ajjiye tunani da zuciyarsa,karafkiya qaryata juna da sa'insa babu kalar wadda ba'a samu ba tsakanin sashe biyu na zuciyar dake qirjinsa,wata zuciyar na rinjayar da qaryar cewa ba iman bace,haka ba zata faru ba,yayin da wara zuciyar ke tabbatar masa da iman dince,saidai ta aikata komai ne bisa rashin sani,koma meye ya riga ya yankewa kansa hukunci kawo qarshen komai,koma meye zai faru ya faru,qirjinsa bashi da qarfin daukar zuciyar da zata rasa iman haka cikin sauqi,saima ya korewa kansa wannan tunanin da yake kallonsa a baqi kuma mummunar fata cikin rayuwarsa. Dai dai lokacin da iman din take can kwance saman tata katifar a zahiri,a badini kuma tayi matuqar yin nutso kuma me zurfi cikin kogin qaunar bassam,wanda ta ara masa daqiqa masu dama yana sake karanta mata yadda qaunarta ta tashi zuciyarsa a aiki,irin girma da kuma matsayin da take dashi,abinda ya sake sawa taji kanta ya fasu,alfahari da samun bassam da kuma soyayyarsa ta shigeta,ta bude masa tata soyayar sosai wadda ta narkar da ilahirin zuciyar bassam,ya kuma dauka mata alqawura masu matuqar nauyi a mizani,girma kima da kuma martaba cikin duniyar soyayya,wanda daga qarshe sukayi tarayya kan alqawari guda,duk rintsi.....duk wuya.....suna tare,babu gudu kuma babu ja da baya,dukkan wanda ya sauka daga kai ko kuma ya sauya,la'ana da kuma hukuncin cin amana yahau kansa. Wannan kusan itace hira mafi dadi da sukayi da bassam a wajenta tsahon tarayyarsu,domin kuwa ko bayan ya sauke wayar sun rabu kasa runtsawa tayi,murmushin dake kan fuskarta cikun duhun dakin yaqi barin fuskarta,hirarraki muryarsa da gwala gwalan kalamansa sukaqi barin qirji da zuciyarta,ta dinga tariyarsu tana jin wani dadi qauna da shauqi yana sake kamata,zuciyarta jaririyar zuciya ce,wadda ta fara soyayya ta zahiri a karon farko,don haka komai baqo ya kasance mata,sai daga bisani fa samu baccin yayi awon gaba da ita,cike da mafarkan bassam,wanda a ciki har ya zama miji a gareta. Kwata kwata baccin da yayi tsahon daren dukansa bai wuce na awanni uku ba,suma din a tsitstsinke,a kunnuwansa akayi kiran asubahi,yayi alwala suka fice masallaci tare da sadiqu,wanda hakan al'adarsu ce,kuma acan suke tadda malam. Miqewa sadiqu yayi ya dubeshi bayan an idar da sallar,wasuma har syn fara watsewa "Nikam yauma idan zaman azkar dinkan nan zakayi saidai mu hadu a gida,don wallahi jiya kwata kwata bacci bai isheni ba" ya fada yana miqa "Shikenan,saina taho" ya amsa masa yana sake maida kansa qasa,don bayason sadiq din ya fahimci bai samu bacci ba. Yana kallon sadiq ta qasan idanunsa har ya fice,hakanan yaji bazai iya komawa cikin gidan ba,ya kintata wani lokaci ne da zai cimma iman,duk da cewa yau tana da makaranta alhamis ce. Cikin wani nishadi da walwala take zuba kunu da awarar data soya cikin cup da plate don taci ya wuce makaranta,ta gama shirinta tsaf,kana duban fuakarta zakasan wani nishadi takeji,bassam ya raya darenta ya kuma qawata mata safiyarta da kyakkyawan saqon barka da safiya. Ta juyo zata fito kenan yayi sallama bakin qofar kitchen din,idanunsu suka shiga cikin na juna,sai ta hangi baqon yanayi tattare dashi,saidai bata kawo komai ba cikin ranta ta zarce da gaisheshi,ya amsa mata yana nazarinta "Akwai ruwan dumi?" Ya tambayeta yana jingina da qofar kitchen kamar yadda ya saba,tsaiwarsa kwnan duk sanda zai karba ruwan,duk da yawanci a gajiye yake shigowa dama saboda exercise da yakeyi,sabanin yau,da babu execise din da ya iya fita,saidai zuciyarsa a jigace take qwarai,wanda hakan yayi tasiri har zuwa gangar jikinsa,ya matsu ya kuma damu ya fidda abinda yake zuciyarsa da ransa komai da komai ma ya huta "Yaaya...gashi" ya tsinci muryarta tana masa magana,da alama tun daxu ta zuba ta miqa masa,sai ya karba ya fara kurba a hankali,bayan ya matsa mata hanya "Idan kin gama ki dauko litattafanki ina jiranki" har tadan dakata sai kuma ta amsa da to tayi gaba,kasancewar ta saba lokaci lokaci yakan rakata,koda ba har makaranta ba to xai kaita bakin titi,saidai a kwanakin nan abun yaja baya. *_LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR_* _BIYAR : DUBU DAYA (1k)_ _HUDU: 700_ _UKU: 500_ _BIYU: 400_ _DAYA: 300_ _AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA: _ *_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_* Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank Number shaidar biya👇🏼 *_09032345899_* *KATIN MTN*👇👇 09166221261 YAN NIJAR 👇 +227 95 16 61 77 Ga 'yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number ______________________ ZAFAFA BIYAR VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA) VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA. TWO PAGES DAILY INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE. *_TEAM ZAFAFABIYAR_*18 Jerawa yayi da ita kafada da kafada sanda suke takawa a hankali,idanunsa qur saman hanya,zuciyarsa na taraddadi da fargabar abubuwan da zayaji. Satar kallonsa ta sakeyi a karo na barkatai,ganin sun nufi hanyar makarantar tasu kai tsaye ba tare da ya tsaidan mata da abun hawa ba "Yaya,a qafa zumuje?,ka manta?,kawai dan nisa fa?,naga munbi ta layin nan" lokaci ya kalla a hankali kafin ya sauke hannunsa ya kuma sake rage speed na tafiyar,ya zaro wayar dake aljihun hagunsa ya miqawa iman idanunsa cikin nata "Karbi ki dubamin" cikin rashin fahimta ta miqa hannu ta karba wayar,ta kuma bude kamar yadda ya umarceta. Abinda ta gani din shi ya birkita kwanyarta cikin sakanni,duk da tasan da wanzuwarsa,amma bata tsammaci yaci gaba da wanzuwa cikin wayar ba,take rudewa suka bayyanar mata,saidai tayi qoqarin bawa kanta dakiya da qwarin gwiwa,tunda babu wani na sabo ko rashin tarbiyya kaf cikin charts dinsu,bugu da qari ma tana jin lokaci yayi da zata bayyanawa duniya bassam dinta "Waye wannan?" Amin ya fada yana kallon wayar kafin ya maida dubansa ga fuskar iman. Har cikin ranta taji tambayar kamar tazo mata a dai dai,don saboda dama ya amin dinne kawai take tunanin zatayi maganar dashi,ya kuma fuskanceta har ya kai zancan gaban malam,to saidai shima duk sanda ta yunqura zata yi masa maganar sai taji ya mata wani mugun kwarjini,amma yanzun komai zaizo da sauqi. Sunne kai tayi irin na alamun jin kunya "Saurayina ne ya amin"ta fada tana rufe fuskarta da tafin hannu. Hasbunallahu wa ni'imal wakil,ita yayi qoqarin zuqowa saga mafitar maganarsa zuwa saman harshensa,sannan yayi azamar dafe wata bishiya da tafiyarsu ta ratso dasu ta gefanta don neman agajin tsaiwa sa qafafunsa. Kasancewar sautin addu'ar tashi bai samu fitowa ba illa maqalewa da yayi saman harshensa.......wannan ya sanya sam batasan me yake faruwa ba,cikin wani irin tashin hankali yaci gaba da kallon iman duk da fuskarta a rufe take da hannunta "Iman......ina alqawarin da kika yimin ba zakiyi soyayya da kowa ba?,ina alqawarin da kika yimin na bani damar zabar miki miji na gari?" Yanayinta ya sauya kadan cikin boyayyar fuskarts,duk da bata kalli tasa fuskar ba amma ta fuskanci sauyun sauti sosai fiye dana dazu "Yaaya.....kayi haquri,na saba maka wannan alqawarin,amma shima ina da tabbacin irin mijin da kakeson zabarmin dinne,kuma zaka yaba da zabina yaya,ya shiga rayuwarta ne katsam" qara dafe bishiyar yayi da kyau saboda jin jiri na dibansa da yayi,babu sauran kwana kwana ko boye boye "Iman......nine mijin da na yi miki tanadi,ni ya amin dinki nine mijin dana zaba na kuma killace kaina saboda ke,iman.....ni amin nike sonki iman,zuciyata ta girma da sonki ta kuma rayu da sonki tsahon shekaru masu yawa". Kamar wadda aka jibgawa wani abu a saman kanta haka taji,ta yaye fuskarta da sauri da kuma hanzari don tana da buqatar tabbatarwa kanta ba shirin film akeyi a wajen ba,tana son ta gani da gaske ya amin ne?,kuma ba wasa yake mata ba?. Saidai kuma.....kallon farko ta karanci zallar gaskiyar dake fitowa tun daga zuciyarsas shimfide saman fuskarsa muraran,abinda ya sake firgitata,ta danyi baya kadan tana jin tashin hankali yana rufto mata,ta yaya haka zata faru?,ta yaya zaice wai da sonta ya rayu?,me yasa bai gaya mata tun da can ba sai a yanzu data riga tayi alqawari da wani,data riga tayi nisan kiwo cikin duniyar soyayyar wani?,ta yaya zata gane yaren da yakeson koya mata bayan bashi ta iya ba?,meye yake shirin faruwa?. "Ya ameen,da gaske kake?,nice fa iman dinka?"kai ya gyada mata yana kallon tsakiyar idanunta kai tsaye "Na sani,iman dita ce,shi yasa nake gaya mata halin da zuciyata take ciki,ina sonki iman......burina kuma na aureki,in fact,malam ya jima da bani ke!" Maganarsa ta qarshe saura kadannta wargaza kwanyarta "Me?!" Ta furta da wani sauti me kauri da amo "Eh,malam ya bani ke tuntuni" ya fada yana gyada mata kai tare da tabbatar mata. Kanta ta soma girgizawa,sam sam kwanyarta ba zata dauki wannan batun ba,wacce iriyar magana ce haka mara dadin saurare?,ta yaya zaizo mata da wannan maganar?,tsahon zamansu da rayuwar da sukayi a muhalli guda bai taba tunkararta da maganar ba sai yanzu?sai daidai wannan lokacin?. Ci gaba tayi da gigixa kanta tana koma da baya,kafin ta juya cikin wani irin hanzari ta nufi hanyar gida,ya miqe da sauri yabi bayanta yana qwala mata kira,saidai ko waiwayawa batayi ba bare ta saurareshi,har ya fara rufa mata baya,sai kuma ya tsaya cak bayan ya yiwa kansa birki ya kuma gayawa kansa gaskiya kan bai kamata ya bita ba din,jama'a suna kallonsu,sannan kuma gida zata shiga a hakan,shigarsu tare cikin wannan yanayin su duka biyun bai kamata ba,kuma yana biye da ita,sai ya dawo a hankali cikin wata kasala da mutuwar jiki ta gaske,ya duqa ya dauki jakarta data sulale a wajen ya soma takawa a hankali shima zuwa hanyar gidan,kwanyarsa na juyawa,tunaninsa yana hautsinewa,yaya iman ta dauki maganar?,me ya sanyata firgicewa haka?,wadan nan sune tambayoyin da ya dinga maimaitawa kansa su wanda bashi da amsoshinsu. A hanya komai kama kamar iman bai gani ba,hakan ya alamta masa ta jima da isa gida kenan?,wannan yasa daya dawo shima bai shiga gidan ba,dakinsu ya wuce kai tsaye,ya zame saman katifa yayi rub a ciki,bayajin akwai wani abu da zai iya tabukawa,saboa ya jin kamar qafafunsa ba zasu iya daukar gangar jikinsa ba. Yadda batasan a gida ya wuni ba itama shima baisan tana kwance cikin dakinsu ba,dukkaninsu wani irin yini sukayi mai wahala qunci da kuma takura,tunanin dake qirjin kowannensu ya nauyayar masa,wani irin yanayi mara dadi na zulumi da kuma fargaba,fargabar data kasance mai tarin banbamci a tsakanin iman da ameen. Sai magariba da ya shiga cikin gidan inna keta mamakin dama yana ciki?,saboda sadiqu nada aiki da yawa a ranar a garejinsu,abinda ya sanyashi fitar wuri sannan kuma har zuwa lokacin bai shigo ba "Banajin dadi ne inna,kuma banaso na gaya miki nasan zakiyita damuwa ne" amsar daya bata kenan "Ikon Allah,don iman bata jin dadine itama,nasan da dole zata bincikoka,nayi mamaki nima da banji motsinka ba ashe jikinne.....don Allah aminu ka daina zama da ciwo baka fada,babu kyau,a qalla ya kamata ko leqaka a dinga yi ko ana ganin yanayin jikin naka,baka zauna a daki kai kadai ba kamar babu kowa cikin gidan uhmmm" "In sha Allah inna,kiyi haquri" ta amsa masa sa babu komai,yanayin sanyi da yanayinsa ya koma saita azashi da cewa don bayajin dadin jikinsa ne,daga bakin qofar dakin iman din ya tsaya yayi mata sannu saboda wanzuwar inna a wajen kada taga ya wuce,ya jiyota can qasa sosai ta amsa masa,sai ya sake wucewa zuwa dakinsu. ********. ****. ******** Munira ce rike gam da hannun iman din sanda suke zagayawa zuwa bayan ajujuwansu,bata sakar mata hannu ba sai da suka dangana saman wani dan tudu wanda asalinsa tarin qasa ne saboda jimawa a wajen ya koma kamar dutse. "Tunda kika shigo na tabbatar ba lafiya ba,gashi jiya na dinga zura idanu an bani saqo na baki amma baki shigo ba" munira ta fada tana duban iman dake zaune ta rungume qafafuwanta a qirjinta. Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke,a.hankali ta fara magana cikin sautin da sai ka dauka wani babban ciwo tayi "Rayuwata na neman fadawa garari munira......na shiga rudani me zurfi daga jiya zuwa yau,irin wanda ban taba hasasowa ba" matse fuska munira tayi tare da sake tattara hankalinta waje daya "Rudanin me?,me ya faru?rabuwa kukayi da bassam?" Kai ta girgiza "Muna gab da rabuwarne wala'alla" "Karki gayamin wannan mummunar kalmar mana iman,kina haukane?,bassam din zaki bari ya subuce miki?" "Munira.....ya ameen ke sona" saita firfitar da idanu waje "Yayannaki da kuke ciki daya?,wanne irin hauka ne wannan?" "Ba ciki daya muke ba,riqonshi inna tayi,kuma almajirin malam ne,dalibinsa ne" sak munira ta tsaya tana kallon iman,tarin mamaki ne fal saman fuskarta,sai iman ta gyara zama ta gaya mata duk yadda akayi. Fuska munira ta yatsina "To don yana sonki shine me?,kawai saiki zauna a rabaki da wanda zuciyarki takeso?,wanda zai zama hutun rayuwa a gareki matuqar kika aureshi,karki manta,'yammatan wannan zamanin SHI SUKE BURI" Kai iman ta girgiza tana jin tashin hankali na sake ninkuwa cikin ranta "Munira.....bakisan halin malam ba,na tabbatar baya magana ta tashi,kuma wallahi wallahi indai ya ameen ya tabbata yana sona malam ya sake fahimtar hakan babu wanda ya isa ya hanashi bashi ni duk duniya" murmushi munira ta saki,sai ta matso kusa da iman din sosai "Kinga,ayi me baro baro kawai a wuce wajen......ki bude bakinki malama,karki cuci kanki,ki gayawa kowa kina son bassam,kuma shi kike da burin aura,ki gayawa ameen bassam kikeso kanki tsaye,idan kikace zaki tsaya kunya ko kara,to wallahi kina ji kina gani za'ayi babu ke,ni dama na dade ina zargin sonki yake,shi yasa ya tajura rahuwarki ya hanaki sakewa kamar kowacce diya,abu daya ne ya ciremin zargina da kika gayamin cewa yayanki ne.....amma Allah na tuba,me na sama yaci ballantana ya baiwa na qasa,ki duba surarki da kyau....banda ma yiwa kai kasada me zaisa yace yana sonki a irin wannan lokacin da arziqi ya qwala muku kira?,me yake dashi da zai riqeki iman?,ina cewa makarantar da zaici gaba ma kokawa suke shi da ita da fafutukar ganin ya sameta,idan kika auri bassam.....bashi kansa ba,hatta da abokansa dana kusa dashi.....danginsa na qauye rankatakaf sun huta,amma shikenan saboda ya dankwafe rayuwarki sai yace wai yana sonki saboda cuta da mugunta,yana da kyau yana da kwarjini na daukar hankali,amma magana ta domin Allah bashi da sinadarin riqe mace kamarki.......da dinki zaici da ke?,koda karatun da bashi da tabbacin samunsa?ke rabu da gaibu fa ki kama dahir,kuma shima matuqar yana sonki ai zaiso ci gabanki ne,bawai ya aureki ku dankwafe waje daya babu ci gaba ba" ire iren maganganun munira kenan data ci gaba dayi,kamar zata ari baki. Iman tana saurarenta tsaf,ita ba wannan bace damuwarta,babbar damuwarta soyayyar bassam da zuciyarta ta saba da ita,kuma batajin zata iya jurewa rasashi. "Gashi inji bassam......,jiya ya aiko yaranshi ya kawo min da daddare saboda ya kikkiraki jiyan bai jiki ba,ya damu sosai,shi kansa yaron nasa idan kinga motar da yake hawa ko......hmmmm" tayi zancan sanda take fidda waya sabuwa dal tana miqa mata. Wannan karon batayi musun karba ba,jiki a sanyaye ta amsa,saboda tana jin wannab shine lokaci mafi dacewa da su kasance tare da juna da bassam din. Nan da nan labari wayar ya karade cikin qawaye da classmates dinta,tanajin mazan ajin suna fadan kudin wayar,mamaki ya kamata,ta jujjuya wayar a hannunta tana mamaki yadda mutum zai iya narka kudi kamar haka ya siya waya qwaya daya jal.19 Cikin jiki zuciya ruhi da kuma idanu ya tabbatar akwai matsala,irin matsalar da duk sanda zuciyarsa ta gaya masa akwaita yana qoqarin qaryata kansa da tunaninsa,komai da komai din na iman ya canza kuma ace ya janye daga muhalli da bigiren da ya santa ada,duk dacewa ba mazaunin gida bane shi.....amma kuma gaba daya iman din ta yiwa idaniyarsa qaura,ya daina ganinta,walau da safe koda dare,tamkar wasan buya ta tsiro dashi a tsakaninsu a tsanake,yasha ganin wucewarta wuf a duk sanda ta karanci motsinsa a waje ki tahowarsa izuwa wajen. Iman din dake tiri tiri da dukkan wani abu da ya shafeshi a yanxu ba ita bace,iman din dako yaushe take shiga kokwanto da wasi wasi duk sanda wasu awanni suka shude bataji motsinsa ko gilmawarsa ba,dukka a yanzu sun kau,kwanaki biyar din da suka biyo bayan maganarsu bai sake sanyata a idanunsa ba,koda muryarta zai iya cewa baifi sau uku ya jiyota ba tsayin kwanakin. Wata iriyar rayuwa yake a kwanakin wadda shi kansa baxaice ga inda ta dosa ba,saboda rashin gane ainihin abinda iman ke nufi,ina tasa gaba?,meye alqiblarta?, Duka bai sani ba,tarin damuwar dake danqare cikin zuciyarsa ta bayyana cikin ayyukansa na yau da kullum,ada idan gana dinka riga goma a wuni daya,a yanzu biyu yake iyayi,sauran duka tunani ya cinyeshi. _wannan kenan_ K'arfe takwas na dare bayan kammala sallar isha'i ya shigo gidan,wanda direct daga masallaci gidan ya nufo,tunda dama can shi ba ma'abocin zaman majalissa bane,koda ya zauna din baya wuce minti goma zuwa ashirin zai sallama dasu ya wuto gida yaci gaba da sabgoginsa. Sanda yake sanyo kai cikin gidan tare da sallama a bakisa yaga kamar wani abu ya gifta wuf zuwa daki,inna ta daga idanunta tabi iman da kallo wadda ita dince tayi hakan,cikin mamaki tana amsa sallamar amin din,ta fuskanci wasu sauye sauye sosai game da alaqar ameen din da iman,yau dinne kuma idanunta suka ganeta real,zuciyarta tadan tsinke kadan,tana fatan kada ubangiji ya sanya wata matsala ce ta afku tsakaninsu komai qanqantarta,don basa fatan hakan,saboda ko a jiya sun jima ita da malam suna tattauna batu akan aminu da iman din "Barka da dare inna" amin ya fada cikin murmushin sannan me sanyi da akullum yake fuskantar innar dashi,fuskantar da da zai yiwa mahaifiyarsa cikin girmama a tarin ladabi. Cikin nata salon kulawar da kuma nuna qauna ta sakar masa fara'a "Yauwa aminullahi,sannu da qoqari,an samu shigowa?" Ta qarashe maganar tana tura masa kujerar tsuguno,sai ya zame ya zauna kan shimfidar abun sallar da iman ta tashi yanzu akai,ya zauna sosai akai ya tanqwashe qafafunsa yana gaidata kamar wanda ba tare suke gida daya ba. Cikin kulawa ta amsa masa,sai 'yar hira ta shigo kan wajen aikin nasu,aduk sanda wata matsala ko ci gaba suka sameshi kam aikinsa,da ita yake shawara,da ita yake tattaunawa,su kashe su binne,inna takanji matsalarsa dari yayarsa dake jigawa bataji guda daya ba. Duk wannan hirar fiye da rabin hankalin inna yana kan dakin iman,tana zuba idanu tare sa saka ran ganin fitowar iman,tana fara'a gamida nuna kulawa dayi masa sannu da zuwa,ta kuma debo abincinsa ta gabatar masa kamar yadda suka saba,sabanin haka shuru kakeji. Hankalin inna ya dan daga kan,ranta kuma sosu,ta kasa jurewa sai data daga murya cikin sauti mai qarfi ta qwalawa iman din kira. Kai tsaye kuwa kiran ya isa kunnuwan iman,wadda ke kwance rub da ciki kan katifarta,ta nutsa cikin duniyar chart da bassam,wanda har bata iya jin hirar dake gudana tsakanin inna da bassam dake zaune daga qofar dakinta. Da hanzari ta danna wayar qasan pillow,tunda dama babu wanda yasan da zaman wayar,koda yaushe kuma a silent take,ta tashi da wani irin reaction na rashin gaskiya ta fito waje tana gyara daurin dankwalinta. Tamkar batasan ya shigo gidan ba,tamkar ba dalilin shigowarsa yasa tabar tsakar gidan ba ta gaidashi,duba daya yayi mata yasan lallai mawuyacine abinda zuciyarsa keta gujewa ba shine ya afku ba,iman din dake marmarinsa a yau ita ke gaidashi babu wani doki babu komai,fara'a da ya santa da ita babu kaso casa'in cikin dari. Da wani mugun bin qwaqwafi inna ke karantarsu gaba dayansu,saita danne tace da iman "Wanne irin sakarcine wannan,ki wuce ki dauko masa abincinsa,kin kama kin wani qule daki?,haka kawai kin koyi nunqufurcin banza da wofi na zaman daka?,inacewa baki jima da fitowa ba?,me kika koma yi a ciki ko wutar nepa babu?" Gabanta ya fadi saboda tasan halin inna sarai,tana matuqar qoqari wajen kiyayewa duk wani abu da zaisa inna ta zargi akwai wata a qasa amma a banza,mutum ce ita me mugun kula da kuma tsantseni "Inna kayana na fito dasu na manta zan gyara na barsu a waje" ta fada cikin marairaicewa "Saiki wuce ki debo masa abincin" ta sake maimaitawa tana miqe qafafunta da sukeso su fara mata ciwo,dama kwana biyun daurewa kawai takeyi "Zan fara watsa ruwa,kamar nan da minti ashirin sai a kawomin" "To shikenan....,idan zaki hada masa ga kwadon xogale can ragowar na malam da yayi buda baki dashi saiki hada masa dashi" da to ta amsa tana nufar kitchen,saidai ranta a bace yake sosai,kawai saboda amin din innan ta sakata a gaba take mata fada,yadda innar ke nuna masa kula da tattalinsa koda yaushe ko ya sadiqu bata yi masa haka,abincinma sai an wani hada masa kulli yaumin kamar wani magidanci,rana dai daine zai shiga kitchen ya dauko da kansa yaci. Tunda take dashi bata taba ganin aibun hakan ba sai yau,sai yau da zuciyarta ta karkata zuwa wani hanya daban ba wadda a baya take kai ba. Kwata kwata bata qaunar su kebe da amin din baki daya,wannan shine babban dalilin da haduwarsu cikin gidan ma ta haramatata,saboda batason ya sake dauko.mata magana makamanciyar wadda yayi mata a rannan,shurunsa da rashin nemanta da baiyi ba shima a kwanakin ya sauqaqa mata dukkan wani tsoro da kuma zulumi nata,koda bata buda baki tayi magana ba tana kyautata zaton ya zuwa yanzu ya gane inda ta dosa. Tana hada abincin tana mita qasan ranta,fuskarta a hade,hakanan bakinta yana ta motsawa,tasan yayi hakkanne kawai don ya samu damar magana da ita,kuma batajin zata sake bashi wannan damar. Data gama hadawar saita koma daki dauko hijabinta,hasken wayarta dake alamta shigowat saqinnin bassam ya zaunar da ita,ta saki murmushi sanda ta fara bin saqonnin nasa,saita manta da aikin da zatayi ta shiga maida masa amsa. Ya jima tsaye gaban mudubi gana sharce kansa yana kuma duban fuskarsa,kwanyarsa na masa bitar tarin maganganun dake cunkushe daga zuciyarsa zuwa bakinsa,mamakin yadda komai yake qoqarin sauyawa cikin qanqanin lokaci yakeyi. Cikin jallabiyya ya shirya bayan ya feshe jikinsa da turarensa kamar yadda ya saba,hatta da boxer na ciki bai tsira ba,sai ya koma saman kujerar dakin ya zauna yana duba lokaci,tayi delay sosai,amma sai ya bata uzuri,kamar hadda hali da dabi'ansa yake,mutum ne shi mai yawan bada uzuri,zaiyi wuya karon farko ya kamaka da laifi,sai ya dora hannunsa saman sumarsa da har yanzu danshin ruwan dake jikinta bai bushe ba,yana shafata a hankali daga gaba zuwa baya,yana jin yadda damuwa ke sandar jiki da zuciyarsa. Wayarsa ya maida gefe ya ajjiye yana furzar sa zazzafar iska daga bakinsa sanda yayi kiran layinta yaji busy,wani abu ya tsaya masa a maqoshi ya kuma tokare masa maqogaro,a hankali yaci gaba da shafar sumarsa yana lallashin kansa da kansa,sai ya lumshe idanunsa yana sake fitar da iska mai tsaho wai ko zata rage masa nauyin da yakeji cikin qirjinsa. Kiran wayarsa da akayi shi ya dauke masa hankali,ya kuma zuqe yawan mintunan data dauka bata kawo masa abincin ba. "To ba damuwa,bari zan kira idan na duba" amsar da ya bayar kenan sanda yaji motsinta,da kuma sallamarta a bakin qofa cikin zazzaqar muryarta,ya bata izinin shigowa yana qoqarin sanya wayarsa a silent,wanda kafin ya gama ya daga kansa harta ajjiye abincin ta juya "Iman" ya qwala mata kira,ta waiwayo tana jin ba dadi a zuciyarta kan tsaidatan da yayi "Zo ki zauna......magana zamuyi" "Yanzu zan dawo" ta amsa masa a taqaice,saiya gyada kai lumsassun idanunsa suna zube saman fuskarta,yana ganin sauyi muraran daga iman dinsa zuwa wata iman din ta daban,ta juya da hanzarinta ta fice,cikin ranta tana jin saidai suyi maganar da wata amma ba ita iman din ba. Amma kuma tana saka qafarta a tsakar gida inna dake fitowa daga daki ambaci sunanta "Wai wanne irin baqin hali kika koyo imani?,wannan zobon da kika ajjiye ya gama hada sanyinsa babu mesha ba zaki kai masa ba,bawan Allah azumi yakai fa?" Kamar zata dora hannu aka ta zunduma ihu haka ta dauki jug din zobon ta nufi soron dashi,bata taba jin inama tana da qanne ba irin yau,da babu shakka saidai fa ta tura daya daga cikinsu ta samu ta dawo,domin har a jikinta tana jin bassam nacan yana jiranta,haka fa tura qofar dakin ranta a bace sallamarta a ciki,daidai sannan nepa suka kawo wuta,hasken farin qwan lantarkin dake dakin ya mamaye ko ina,ya kuma taimakawa ameen qwarai wajen ganin yanayin fuskar iman din. Can nesa ta samu ta zauna bayan ta dire masa jug din,kanta a qasa kamar wata surukarta tace gani. Baiko motsa ba sabda tayi maganar,sai kafeta da yayi da lumsassun idanunsa na wasu daqiqu,sannan ya miqe cikin nutsuwar nan tasa,ya taka a hankali ya rage tazarar dake tsakaninsu,a hankali ya zame saman carfet ya zauna saitinta,ta yadda zasu iya ganin juna yadda ya dace. Dakakkiyar muryarsan nan me cike da amo na mazantaka ta fara fita,yau din cikin wani irin yanayi na sany da laushi,duk da cewa dama can ita iman din wannan amon ta saba ji daga gareshi,bai fiya kausasa mata a magana ba "Iman.....a duniya idan akwai wanda zai fadi halayyata bayan inna da yayata to kece ta ukunsu,banajin ko sadiqu ya sanni yadda kika sanni" sai ya sanyi shuru yana sauke numfashi gami daci gaba da kallonta sannan ya dora "Kwanaki biyar da suka shude,munyi magana dake.....na bayyana miki komai,saidai kuma har yau na kasa karantar me wannan iman din take nufi?,ina ta fuskanta?,ina ta sa gaba?iman baki sona ne?,ko ya amin din naki bai miki ba?,idan banyi miki ba iman ki fito ki gaya min,saboda ni ba baqonki bane......"ga fada maganar cike da qwarim gwiwar samun akasin abinda zuciyarsa ke raya masa,saida amsar da iman din ta bashi tayi matuqa girgizashi,ta motsa masa zuciyarsa fiye da yadda ya zata ko kuma ya tsammata......amsar da bai taba kawowa koda cikin mafarkansa zai jita daga bakin iman din ba,bai taba zaton zata iya furtata ba "kayi haquri ya amin........bassam nakeso" ta amsa masa,tamkar dama jira take a bata wannan damar. Dukkan wata jijiya dake kai saqo jini da kuma iska a jikinsa zuwa muhallansu sai da ta tafi hutu na sakanni,kafin ya samu nasarar zuqo numfashinsa,bayan ya tabbatar numfashin ya koma saman qirjinsa yadda ya dace,sai ya fara kokwanton duniyar zahiri ce ko ta mafarki,saboda haka yayi qarfin halin motsawa kadan "Iman.....sake maimatawa naji". Yayi maganar sautin muryarsa na fidda wani amo wanda zai alamtawa mai sauraron da kunnensa da kuma qirjinsa ya cika da hikima cewa lallai akwai wani abu mai tsananin nauyi da yake shirin danne zuciyar da wannan sautin ya fito daga gangar jikinta......