💥 *AMANATA CE* 💥 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/OUD2pf7LpH1gw7 17/4/2024 💫LAFAZI WRITTER'S ASSOCIATION💫. {L A W A} ==Kyakkyawan lafazi acikin rubutu nadanfare dabin 'ka'idojin adabin hausa=== 💥AMANATA CE💥 << BY AYSHERTY>> Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, wanda shine yabani iko da daman fara rubuta wannan littafi.👏🥰 Ina miqa dunbin godiyata agareku masoyanaa,tare da fatan alkhairin da kukemin,Allah yasaka da alkhairi,Allah yabar zumunci, nagode maku.🫂 *I dedicated this book to u my AMRATY much love Allah yabar qaunaa🫂🌹* --------------------------------------------------- *....FREE PAGE...* PAGE 1_2 Tunda tatashi yau take acikin fargaba, sanin cewa yau zae dawo,domin baqaramin mugunta yake mataba, ita wallahi batasonma yadawo qasannan gwanda yayita zama can UKn, don tasan indae yadawo shikenan hutunta yaqare acikin gidannan,tsaki taja tana turo baki gaba,shi wannan miskilin dan rainin wayon sae masifar bala'i ba abinda ya iya sae sa mutane aiki da mugunta. SABIYYA! SABIYYA!! Zumbur tamiqe daga kwancen da take tana fadin na,am MAMII! ganinan tanadan daga muryanta,saeda tatashi tsaye nace wowww ma sha Allah domin duk wannan tunanin nata tana kwance cikin blancke ta rufe jikinta har wuya, kyakkyawace ajin farko,doguwace amma ba sosaiba dan kuwa ita baza,acemata gajeriyaba,farace sollll tanada shape mae kyau irin dae shape din da ake cewa 8,tanada dara dara idanu masu dauke da zara zaran eyelashes, tanada dogon hanci da kuma matsakaicin baki pink lips wanda yai daidai da zubin fiskarta, amma kana ganinta kaga shagwababbiya tagaban kwatance, kai tsayawa fadan kyan SABIYYA ma bata bakine nidae kawai nace ma sha Allah. Dasauri tayi palourn jin mamii naqara kiranta, ahankali take tafiya kamar bataso amma ita ahakan sauri take har tazo daedae kan sopa inda mami take,gani mamii, yade daughterna naganki wani so cool,baki tatura tace toh mami aikinsan dae yaya zae dawo, zae fara takuramun, murmushi mamin tayi tace hmmm keda yayan naki ai ba,a shiga tsakaninku idanma anshiga za,aji kunya, yanzunma muka gama waya yace kije ki gyara masa part insa anjima zai sauqa,diddira qafafu tafara tan cewa yanzu shi yayannan tun kafin yadawo zai fara sani aiki duk masu aikin gidannan? Allah ni bazan gyara masaba,bayan kona gyara cemin yake ba,abinda na iya?tafada tana kawo hawaye idonta, ya,isa SABIYYA kyaleahi bari nasa samira tagyara mishi inkuma bae masaba inyadawo yagyara abinshi, gyada kai tayi tana ficew daga palourn,wani part naga tashiga dayake gidan part ukune, part din gefen naga tashige,tana shiga ko sallama batayiba tawuce tayi cikin palour kai tsaye kan cushion dake falon tazauna 3seater tajuya baya,bata dadeba da kwanciya wata mata dattijuwa sosai tafito,kawai sae ganin mutum tayi salati tayi tace meye kuma wannan haka da za,a somin palour akwanta,sai ansamin datti,tun safe nake tsaye,saboda yau dan lelena zae dawo, wani irin kallo SABIYYA tayiwa matar tana turo qaramin bakinta na tsiwa tace tab wannan mugunne dan lele? Wallahi dakankima zaki koreshi baridae yadawo zamu ganii,mutun sae miskilancii, bude baki ANNA tayi tace ehh lallai SABUYA 😂 wallahi kamar agabansa akai, ni ficemin daganan karki batamin gurii,kinsansa badae tsaftaba,tabe baki tayi tace dama ko bakiceba tafiya zanyi, oho dai aje can aiwa AISHA rashin kunya badae ananba,ficewa sabiyya tayi kamar zata tashi sama. Page 3_4 Bangaren tsakiya tashige tana zuwa wata kyakkyawan mata na fitowa daga kitchen da alama aiki take,fadawa jikinta sabiyya tayi tana cewa wasshhh AMMIna nagaji,tureta tayi tana cewa matsa can!! aikin dana saki kenan ko sabiyya kuma dama bakije taro yayan nakuba? Baki taturo tace tohfa Ammi kince yaya kikewa abinci,kowa sae yawanice yaya yaya!!! Mutun sai mugunta kuma aitaimasa wahala, kumani Allah bazanje tarisaba,hakana naga ANNA wai sae gyara ake saboda ga gold zae dawo,walkahi shiyasa mamii take burgenii ita baruwanta dashi ko harkansama bata shiga tafi sonama tafada tana tana hawa stape.(nikam nace mutum da danshi ace ba,a tatasa) girgiza kai AMMI tayi tace Allah yashiryeki SABIYYA. Tana hawa saman tashige wani daki daga ganu dakintane,wowww ma sha Allah yayi kyau sisai,wata qofa tashiga da alama bathroom ne wanka tayi da sabulanta masu matuqar tsada da qamshi, tadauro towel tafito. Mai kawai tashafa tadu Wata hadaddiya black abaya tasaka tagyara kanta palour tafito tayi kwanciyarta akan three seater tadau wayarta tana dannawa. Sae wajen 4:30 naga anbude tangamemiyar gate din gidan ,sae ga wata dankareriyar jib tashigo wasu motoci biyu na biye da ita,kai tsaye a parking space sukaiwa motocinsu masauqi, dasauri drivern yafito ya bude back seat dib jib din,saeda akadau kusan 5mints kafi yaziro zara zaran qafafunshi,mae dauke da black cover shoe,candae yafito gaba daya,wowwwww ma sha Allah wannan kamar ba dan NIGERIA ba,kyakkywane aji farko shekarunsa bazasu wuce 35 dogone sosai,bashida haske sosai yanada faffadan qirji, bakinsa zagayayye madaidaicii,yanada hanci kamar anzana,ga saje gashin kansa baki wulik, ammafa idan akace kyau toh * KHUBAIB *yakai kai tsaye kina kallon KHUBAIB zaki gane cikakken bafilatanine gaba da baya, ragowan nasauran motanne suka fito gaba daya sukai compound en gidan kallonsu yayi daya bayan daya baega SABIYYA ba jinjina kai yayi aransa yana fadin hmmmm uwar tsiwa,zama ki fitone.😂 Wani saurayine yadaebi trollynsa yakai Part din Mamii,shikuwa yahuce bangarenshi ya watsa ruwa,kai tsaye part en AMMI ya nufa yana shiga ammi na fitowa daga kitchen da munna tatareshi a,a my SON ashe kun qaraso shiyasa naketajin hayaniyarsu juhaifa awaje kenan,ehh wallahi Ammi na sameku lafiya,lafiya kalau Alhamdulillah ya hanya?zauna mana, cikin palourn yaqaraso dan baema kula da itaba,ita kuwa tunda yashigo qamshinsa yatabbatar mata da shidinne, Ammi ce tace yauwa SABIYYA tashi kiyi saving nashi zanje sama daddynku yadawo abun yaquremin ban qarasaba tafada tana hayewa upstair, tura baki tayi tana sako sabbin kwallah tana diddira qafafu nata qunquni tayi dining, kallon saman yayi yaga Ammi ta wuce biyo bayan SABIYYA yayi ita batasanma ya biyotaba tanata qunquninta, tagama saving nasa,tajuyo zatayi mishi tsiwa kawai taji tayi karo da abu....... BY AYSHERTY....✍🏻 LAFAZI WRITTERS ASSOCIATION AMANATA CE (By Aysherty) Page 5_6 Dagowan dazatai sukayi ido hudu dashi, Dan Allah Yaya karkamin komi ohh kinsan me kikai kenan? kai tashiga girgizawa Dan ita batasa yajitaba,rabawa tayi ta gefenshi zata wuce fizgota yayi tafada qirjinshi kunnenta yamurde ihu tasa Dan jitai kamarma kunnen zaecire .wayyooo Ammiey dasauri yacikata yana turata yace out mara kunya. Dagudu tafita kai tsaye part en Anna tayi tana zuwa tagada jikin Anna tana kuka, toh kekuma keda wa haka zakizo ki nemi ki karyamin qasusuwa haka? cikin shagwaba tace koh ba yaaya bane? toh waye haka kuma Ina wannan mutumin mae kamada samudawa?cikin kuka tace shii. Anna tace toh daga dawowarsa har kin tsokano shi kenan zaku fara tallahn hali,cikin kuka tace bashineba ba.abinda nai masaba yakama dukana da belt kuma wallahi Anna da zafiii, tafada tana turo baki, duka ?Anna tafada cikin mamaki gyada kai tayi. Anna tace yoo banda shi shashashane inashi Ina dukan mata. hardasa su balt, kamar yasamu doki? ni wallahi har ya gundureni kwata kwata barni dashi shiga ciki ki kwanta. dasauri tashige bedroom en Anna ta haye gado ta lullube har wuya tana dariya Dan tasan zaesha masifa gurin Anna. Bayan yagama cin abincin Ammiey tasauko tareda daddy tace har kagama son? ehh Ammiey nagama, Ina sabiyyanfa batai saving naka bako? uhm bakomai Ammiey nama gama ai, Allah yashirya sabiyya Ammiey tagada. Barka dadare Abba,yafada tareda Dan rissinawa ga Abban wanda yake riqe da hannun Aaufaa barka dae son ya aikin? Alhamdulillah Abba, ma sha Allah, Allah yayi jagora AMIN Abba, yafada tareda barin part en. PAGE 7_8 WACECE SABIYYA!WANENE KHUBAIB! Alhaji Ahmad da Alhaji Mus,ab manyan yan kasuwane,tun suna yara kansu aahade yake suna tare da maihaifiyarsu FATIMA wato 《Anna》tun suna qanana mahaifinsu ya rasu,sun taso cikin kulawar mahaifiyarsu dan sunsamu tarbiyya.tunda mahaifinsu yarasu suka shiga cikin quncin rayuwa.sunsha Wahala mahaifiyar tassu tasha wahala duk dangin baban suka karbe kadarorinsa sukace nasune, bayanda suka iya sbd basuda qarfi sunaji suna gani bazasu iya komiba sbd lokacin suna yara sae qanwaru daya Amina, wannan dalilin yasa suka tashi da neman nakansu inda suka dinga samun nasarori suna habbaka kasuwancinsu bisa gaskiya amana atsajaninsu,bayan Ahmad yakai shekara 38 shikuma mus,ab 36 alokacin Anna ta matsa musu kan suyi aure anan dae aka samu Ahmad din yayi ya auri matarsa kykkyawa Hafsa《Mamii》suna yaya biyar KHUBAIB shine babba inda yagama karatun doctor dinshi a uk kuma yana aiki tsakanin qasashe yanada hospitals nashi nakanshi,ayanzun yanada shekara 35 sae mae binsa Umar,sae Maryam,khadeeja,sae autaa Mubeen. saeda KHUBAIB yashekara biyar sannan mus,ab yayi aure da matarshi shima kykkyawa AISHA 《Ammiey》 saeda tai shekara biyar bata haihuba, har suna tunanin ko na lafiyaba? sunje asibiti antabbatar musu suna lafiya kawai lokacine baeyiba anan yan uwanshi suka matsa mada yaqara aure,yace abarshi da matarshi lokacine.nandae KUBAIB yadawo hannun Ammiey itace komanshi, kwatsam itama tasama ciki murna kam ba,a magana, har ta haifi yarta mace aka samata sunan ANNA wato fatima suna kiranta SABIYYA,gata kam sabiyya nasamu amma duk gatan bai hana sun tsaya sun bata tarbiyyaba,inda ayanzu takeda shekara19 kuma tagama secondry highet institution zataje,saeda sabiyya tayi shekara 15 sannan Ammin taqara haifan namiji mae suna Aayaan,sae qaramarsu Aaufaa. sabiyya tataso cikin shagwaba da tsiwa ga tsojana shiyasama basa jituwa da yayannata KHUBAIB. CIGABAN LABARI 😊 Part ensu yanufa yaje suka gaisada mamii da daddy,sannan yawuce part dinshi yawatsa ruwa,jallabiyya yasa ashh color yafesa perfformance dinshi da yake using da dare,masallaci ya huce bayan anyi issah yashigo gidan, part din Anna yawuce tareda sallama amsawa tai ciki ciki,yadae mutuniyar naga kin wani hade rai kobakya murna dadawowana ne inkoma yafada tareda zama saman sofa,ehh kakoma tunda dae kai sallamammene MAE dukan mata bakada hali daga dawowa kasa wannan mitsitsiyar yarinyar kana duka da balt kamar an aikoka, tafada tana matsar qwalla.nikuma Anna wana duka daga dawowana? wannan yarinya SABUYA 😂 haba Anna kema kinsan halin SABIYYA da tsiwa da rashin kunya,nan yafada mata duk yanda akai,sakati tafara tana cewa yau naga shedaniyar yarinya wallahi ba halina kikayiba, bansaniba kocan dangin bafilatanar uwarki ki dauko wannan haliba, har da zuwa kikwantamin afaka.toh wallahi tun wuri fitomin daga dak....kaikuma zauna dan albarka inkawo maka ferfesun da naimaka na kaji mae romo romo,ina cikin dokin ganinka wannan mae kamada tsinken jiki ba auki tazo ta batamin shiri, kasan irin kudin da na kashe gurin hada maka wannan lafiyauyan ferfesun? tun safe ban zaunaba ina abu daya, murmushi kawai yayi yace toh Allah dae yasa kin iya girkin? galala tayi da baki tace hmmm lallai.amma banabi ta halinkuba kaida waccan fingin kawai tashige kitchen din flask din tadauko mishi dan qarami takawo mishi hade da ruwa masu sanyi,ta ajiye batace komaiba,sabiyya kuwa tunda taji maganar nama take abakin qofa tana leqowa tana ganin an ajiye masa tanannade riganta tazo da gudu tadauke flask din ta gudu sae part din mamiij tabar Anna da sakin baki😂, kuka Anna tafasheda tace nashiga uku ni pateee wannan wace irin aljanar yarinyace datasan irin kudin da na kashe gurin hada wannan ferfesun da saeta tausayamin tun safe ban tsugunaba Ina aikinshi.😂😂 shikuwa gogan naku ido ya lumshe ya jingina jikin kujera....... Follow the AYSHERTY READERS HUB 😘♥ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VabieVQ5Ejy0dPcySR1h https://chat.whatsapp.com/HrLqaKJbOUD2pf7LpH1gw7 PAGE 9_10 Bata tsaya ko inaba sae part en mamii kallonta mami tayi tace kedawa Daughter wannan irin gudu haka da flask?mami daga gun Ammiey nake shine naga Yaya zae qwaceminn shine nagudo gurinki, nan tazuna tacinye abinta, Bayan Anna tagama koke kokenta takalleshi taga yama rufe ido tasaki baki tace yo aikai sallamammen ma baka damuba dagowa yayi ya kalleta yace badae ni kikayiwaba tace ehh fa yo wanake dashi in ban makaba? Toh kiqyaleni da ita,inkuma baki bataba insiyo miki wani,kwafa tayi tace kaidin kaidinne taci albarkacinka.murmushi yayi yace toh koh kefa da kya tsaya kina biyewa shirmenta? Yafada tareda ficewa a palourn, part dinshi yaje yakwanta. Nan suma su daddy da Abba sukazo sukaiwa Anna sallama kowa yanufi part enshiii. *Ban mance dakuba mutanen arziqi yan AMANATA CE FANS GROUP luv uhh oll 😘* *Kuma ban mance dakuba yan AYSHERTY READERS HUBB 😘😘 qaunarku ajinina take ALLAH yabar qauna nagode da fatan alkhairynku gareni masoyana* <<<>>>>>>> Tundaga ranan bata sake bari sun haduba indai tajishi guri toh zata san yanda zatai bazai gantaba, Yau yakama sunday da yamma suka shirya itada maryam driver yakaisu wani qaton super market zasuyi siyayya,dama ita SABIYYAn siyayyan kayan bikin ummi qawarta kawai tace zatai,ita kuma maryam driver zae kaita gidansu mamii, Bayan sungama siyayyanne tace kawai driver yakai maryam ita tahau ko napep ne taqarasa gida,haka kuwa sukai maryam tahau driver yaja suka tafi, tadade bakin titi ko kyallin napep babu dayake manyan gurarannanne bakasafai napep suka fiye shigowa gurinba, har tazo tagaji ga garin hadari yafara hada hadariu, nanfa jikinta yafara rawa dan tunda take bata taba kaiwa haka wajeba ita kadai, wani guy ne yafito daga gurin yazo zae shiga motanshi, iskane yataso sosai tarda qura, mayafintane yacire yabi iska saekan wannan guy din,saejin abu yayi mae qamshi kan fuskanshi, qoqarin motsawa take amma takasa sbd gaba daya jitake kamarma bakomi jikinta, durqusawa tayi tasaki kuka,tana fadin wayyooo Ammina, harya juya sae ganinta yayi duqushe tana kuka,dasauri yadawo tareda mayafinnata ya durqusa gabanta yace yadae babe,sorry ga mayafin naki karba tayi jiki na rawa tasa, sannan tamiqe ahankali tace nagode, murmushi yayi yace bakomai babe amma. Ina zaki haka naga kamar siyayya kikaiko? Ehh tabashi amsa ataqaice,ayya inba damuwa muje inyi dropping naki gida,dasauri tace a,a nagode, haba bae kiyarda dani kinga hadarinema agarin kar ruwa yasauko yataba wannan kykkyawan jikinnaki,gefe taqara matsawa tace a,a, zanje dakaina,hakadae yadunga mata naci har ta yarda dasauri yabude mata front seat tashiga,yasa mata lugagges dinta back seat, sannan yadawo driver seat yayiwa mitan key suka bar wajen, saeda suka hau road sannan yadan kalleta yace babe wani unguwa? Nan dae tafada mishi sukadau hanya, suna tafiya yana mata fira daga uhmm sae a,a shine answernta, har yakawota bakin gate din gidansu yayi perking, ahankali tadago takalleshi zatamai godiya taga ya kafeta da idi, turo baki tayi, murmushi yayi yace woww beautiful, rufe fiskarta tayi tana murmushi tace nagode sosai,, uhmm please zanso insan sunan wannan kykkyawan, sadda kanta qasa tayi kafin tace sunana SABIYYA woww nice name,nikum sunana Aaryan, please babe wallahi tunda naganki naji ina matuqar sonki,please kibani dama in gabatarda kaina gareki,murmushi tayi dan itama tunda taga guy din yay mata, amma sae tai shiru,,uhmmm please beauty please kibani numbernki inyasao sae inzo har gida muyi magana ko, qasa tasadda kanta tace ni banida waya ai,haba beauty kamarki ace bakifa waya wannan ta hannunkifa??? Daqyar dae yashawo kanta tayadda tabashi numbern,dakanshi yazagayo ya bude mata mota tafito sannan ya kwaso mata lugagges enta,yarakota har gate, suna qarasawa khubaib na fitowa zaije masjid ganinsa datai saida yayan cikinta suka hautsina, dakewa tayi amma kana ganinta kasan atsorace take,beauty waye wannan dan da yaganshi saeda gabanshi yafadi,yayane tafada ataqaice tareda karban kayan tai masa godiya tashige, shikuma yajuya yaiwa motanshi key yabar wajen..... PAGE 11_12 Tana shiga tayi part dinsutayiwa Ammi sannu da gida,sannan tanuna mata siyayyan tabata wa,enda za,akai dinki, Taawuce upstair tana zuwa ta dora wayanta kan mirrow tafada bathroom tayi wanka tafito tasa sleeping dress tafito tadauko Aaufaa takwantarda ita,itama tahau gado,Ammi ce taturo qofan tace kebazaki sauqo kici abinciba? A,a Ammi naqoshi wallahi,toh mae kikaci da kika qoshi kinsanfa banason wannan rashin cin abincinnaki common kinsakko kokuwa? Turo baki tayi tana kawo hawaye idonta ta sauqo tayi palourn wajen dinning tabufa taje spagetti kawai taci with soup tayi brush takoma,harta fara bacci wayanta yahau ringing tsaki tayi tajawo wayan,bakuwan number tagani bata dagaba har yakatse,can aka kuma kira dagawa tayi tai shiru, hello beauty taji sassanyar murya,shiru tayi saeda aka qara fadin hello are u on the line? Uhmm helloo kawai tace, murmushi yayi yace sunanan Aaryan kinganeni? Ohhina yini? Lafiya qalau beauty ya daren? Alhamdulillah...... pls atayani sharing *Aysherty ce* _LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ Alhamdulillah tace, yauwa ma sha Allah beauty koh kin fara baccine?uhmm ehh nakusan dae farawa, hmmm beautyna kinsan me? a,a yafada ahankalii, wallahi tun dazun dana gankii naji ina matuqar qaunarki, lokaci daya naji qaunarki azuciyata, please kibani dama inzo in ganki? Yafada yana marairaicewa, uhmm toh aini yanzu karatu zanyi,nayi qarama da aureni tafada cikin yar shagwabar da tasa yanayinshi canjawa, haba my beauty ai aure lokacine ko kin gana ko baki gamaba in lokacin yazo saikiga kinyi,kuma indae karatune nidakaina zan barki kici gaba da karatunki agidana.... Nan dae yadinga janta da fira mae adadii har suka gama wayan takwanta bayan tasanarda shi randa zaizo...... Washe garii da yamma.. Gate din gidan aka bude nan motar Khubaib ta shigo gidan kai tsaye parking lot ya wuce, breaf case inshi ya dauka ya wuce, ta garden yazagaya yazo daedae kujerun dake garden yahango SABIYYA kwance a qudundune,kamar zae huce saedae yatsaya ya qaraso inda take, kallonta yayi itama ta kalleshi yaga yanda take rawan sanyi ga bakinta duk abushe, alaman batada lafiya.tsugunawa yayi kee me kike anan dasauri takamo hannunsa jiyayi jikinta zafii rauu,yaya banida lafiya nakasa tashi,kaina ciwo zazzabi nakeyi,yunwa nakeji,,tafada cikin raki, hade fuska yayi dukda tabashi tausayi kuma yayi niyyar duk sanda suka hadu saeta gane kuranta, amma dayake miskiline yamaze yace toh mae yakawoki nan??? Itadae sae qoqarin shigewa jikinsa take domin baqaramin sanyi takejiba tundazu takasa tashi saboda jirin da takeji, kallonta yayi yadda ta cukuikuyeshi tana rawan sanyi,fuskanta na qirjinshi,, toh tashi muje ciki, kuka tasa mashi tace yayan bazan iyaba jiri nakeji,rasa yanda zae mata yayi kawai yasa hannu yadauketa sukai part din Ammi lokacin da yashiga Ammi na zaune itada Aayaan da Aaufaa sunata mata fira sama sama suna ganin anturo qofan Aayaan yace laaa yaya mae yasamu antyy Ammi anty,dasauri Ammi tataso tace son lafiya mae yasameta? Kaita dakinta nan yayi stair yakaita bedroom dinta yakwantar kan bed Ammi ce taqara tambayansa nan yamata bayanin kimai, Ohhj Allah yagyara halin sabiyya saeda tacemin kanta na ciwo zataje garden duba wasu takardu nace tabarshi akwai sanyi,ashe can din tatafi? Abba ne yashigo dakin yace yade son batada lafiya ne? Eh Abba nan Ammi tamasa bayani, toh kadubata kawai nizanje mutattauna kan tafiya makarantarta ukn gun yaya toh Abba, Amminma fita tayi taje kitchen dafa mata light abinda zatadanci. Bude lumsassun idanunta tayi tadorasu kan fuskanshi,shima ita yake kallo,sannan yamatso bakin bed din yadan hau yace meke damunki ? Fuska adaure,, turo baki tayi tana sakin sabbin kwallah tace,ni yaya karkamin allura please,, firgitattun idanunsa ya watsa mata wanda yasata sadda kai qasa dasauri tana turo baki hadeda shagwabe fuska, kallonda yayi matane yasata fadin tohh nii zazzabii nakeyi da ciwon kai ai,tafada tana hawaye, aikuwa yazama dole inmiki alkura kuka tasa mishi ni wallahi banasi tohh abanmin ciwona, bae kukataba qara tasa,wayyo yayaa zafiiii ahankali yada murza mata wajan sannan yakwantarda ita kan bed, yajuya yabar dakin tabishi da harara tana turo baki ahankali tace,wallahi yana sani yamin da zaf, ahankali kuma ba,a dadeba bacci yay awon gaba da ita. PAGE 13_14 Banayan Abba yaje sun hadu part din Anna tareda daddy duk suka tattauna kan tafiyar SABIYYA dan ita maryam tace ita a india takeso tayi karatunta gurin uncle dinta (Yayan mami) ita kuma sabiyya dama tun farko UKn takeso, saekuma gashi khubaib nacan,sae suka yanke shawaran tunda khubaib din zaeyi aure sae sutafi tare tayi karatunnata can.haka dae suka tattauna kan lamarin yayan nasu har dae sukai sallama kowa yayi part insa. Khubaib kuwa Part dinsa yaje ya watsa ruwa,bayan ya fitone yaga miss calls 3quater yasa da T-shartt sannan yadau wayan tsaki yadanja ganin mae kiran kamar ba dazu suka gama wayanba harta sake qira,call din yabi 2rings tadaga tan yanga hello babe ina kasaka wayan ne inata qira baka picking? Murmushi yadanyi yace haba babe dazufa muka gama waya kwata kwata sati nawane? Hmmm babe bazaka ganeba naqagu naga anyi aurennen wallahi, hmmm Banan kenan kamarma kin fini zumudi, hmm haba babe kasan fa yanda nakejinka araina, hmm dagaske?ehh mana babe aikaima kasani,,toh amma ko an daura ba,asatin zamu tafiba sbd zamu tafi da SABIYYA zaa dunga zuwa skul acan sin, DUMMMM haka gaban Banan yafadi sbd ita wallahi tunda taga SABIYYA taji ta tsaneta kwatakwata ko ganinta batasonyi, dan indae taganta ko tajita sae gabanta yafadi, yanaji kinyi shiru babe,,murmushin dole ta qaqalo tace uhmm bakomai ai qanwar muce,har ransa yaji dadin abinda banan din tafada, ahaka dae suka dan taba fira sannan suka kashe wayan, kwanciya yayi yana tunani wannan auran nasa shifa kwata kwata bai tabajin yanson banan ba hasalima bai tabajin komi akantaba, kawai zai auretane kodan maganan da ake yawan yimishi kan aurennan, amman badan yana soba,gashi kuma za,a hadasa da wannan yar rigimar,tsaki yaja hade da lumshe lulu eyes dinshi. *WACECE BANAN???* Banan yar shahararren mae kudice wadda akalla zatakai shekara 25,kyakkyawace ba laifi, yar gata agurin iyayenta,su biyu iyayensu suka haifa Banan, da Aayrah,yan gatane na gaban kwatance, ammafa yan duniyane bakadanba, basuda kamun kai ko kadan domin kuwa tsabagen gata da sangartar da suke samu indae kaga banan toh itace hotel wajan alhazai da masu kudi, itace gidan rawa, club, dasauran gurare irin wadannan wanda babu tarbiyya cikinsu, amma kwata kwata daddynsu bayason wannan dabi,ar mummyn tasuce take goya musu baya,tace ai baza,a takure mata yayaba abarsu su shaqata, ahaka yake haquri domin shima baya iya komai akansu,duk ammallakeshi. Tunda suka hadu da Khubaib lokacin yaje company siyan mota itama taje, tunda taganshi taji tana matuqar qaunarshi har zuciyanta, nan tafadawa mummyn tata itadai saeshi gaba daya ta susuce musu, dahaka ta dinga bibiyansa, har tagane shi likitane nan tasamo bayanansa, haka itada qawarta ishma da mummynta suka dunga bibiyansa har suka tsara plan din za,akai Banan din hospitals dinsu amatsayin batada lafiya emergency haka kuwa suka tsara, bayan tasa wani bakin kwalli idonta, qawarta ishma tataho mata dashi, wanda suna hada ido da khubaib zaejishi atarkonta, dariya sukayi ganin alamun samun nasara yazo,haka kuwa suka dauketa ranga ranga suka kaita,lokacin da suka kaita akai emergency da ita, nan suka nemi khubaib din yadubata daqyar suka samu yazo dan sunci sa,a ranan yashigo, nan yace su fita zae dubata yayi iya dubansa baiga wata matsalaba, ita kuma sae wani fizge fizge take, nan yafita zuwa office dinsa,dasauri tadau phone enshi ta kunna tayi sa,a babu password, nan taduna taga numbernsa, dasauri tadauko phone dinta tadau numbern, dasauri tafita ta,ajiye jin ana murda handle din qofan, takoma takwanta, marairaicewa tayi tana hawaye, please doctor kadubani tafada agalabaice, tausayi tabashi domin shi bayason ganin mace cikin wahala, kuka tasaka masa tana riqe handa dinshi, kallonta yaqarayi yaga yanda take wahala, ahankali yace juya zan miki injection kuka taqara samasa tana juyi,sitake kawai su hada ido ko haqanta ya cimma ruwa, hii you are wastinh my time,yafada yana kallonta tareda jan injection en juyowa tayi suka hada ido,wani irin faduwa gabansa yayi sakamakon haduwar qwayoyin idanuwansu guri daya, injection din da ba,aiba kenan, kawai sae gani tayi ya fice daga room din don wani iri yadingaji awannan lokacin daqyar ya iya kaiwa office dinshi yasa key, ita kuwa su isma suna ganin fitarshi awannan yanayin suka shiga dakin shewa sukasa suna dariya, nam suka tattare kayansu sukai gaba ganin haqansu ya cimma ruwa..... kwanciya yayi kan sopa dake office din ya lumshe idanuwansa dayakejin sun masa nauyi, gaba daya tunaninta yahanashi sukuni,, tunani yayi kawai yaje yasameta, romm din yakoma amma wayam bakowa. Gaba daya hankalinshi nakanta,ahaka lokacin tashinsa baeyiba kawai yatattare takardun yarufe office din yaja mitarsa yayi gida. PAGE 15_16 ..........Bayan sun koma gida dadare taqirashi ganin bakuwan number baeyi picking ba sae da aka qira sau uku, sannan yayi picking gabansane yafadii dummmm jin muryanta tana fadin yafe doctor, shiru yayi taqara cewa hello doctor i,m your patient some hours back, jiyay hannunsa yagara rawa jin itance, sannan yace where are you going all of you? hmmm bawannanba doctor ainama warke, at first tun lokacin danafara ganinka agurin Hameem motors.......nan tafada mishi irin son da take mishi,shima tsintan kanshi yayi da fada mata irin yanayin da yashiga tun farkon ganinta...... Alokacin da tamatsa mishi da zancen auren, yakai maganan wajansu Abba,sunyi farin ciki jin zaeyi aure, amma daga baya da akai bimciken wacece yarinyar fada sukayi masaa sosai,akan wace irin yarinyace wannan nan yace yaji yagani ita yakeso dasukai qoqarin hanashi, har cuta yayi kamar zae mutu,ganin hakan yasa sukace Allah yasa hakan ne yafi alkhairy,nan aka tura akai musu baiko aka tsaida ranan biki wata uku ayanzu bikin nasu saura sati biyu..... *muje zuwa* taku har kullum Aysherty.... 🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌🌌 *Yawan comment react dinku yawan typing* *Sannan kar amanta da sharing please* *By Ayherty* *PAGE 17_18 *CIGABAN LABARI* Bayan sun gama wayan tatashi dagudu tana kuka taje gurin mummy, tafada jikinta mummmy kinji wani rainin hankalii wai da wannan mae kamada aljanun zae tafi idan anyi auren,, whatttt !!! Mummy tafada cikin qarajii, meyake nufi da ita zae tafii, ehh haka yace wai karatu zatai, miqewa mummy tayi tace, ya isa daughter rabudashi kallonta Banan tayi tace inrabudashi fa kikace? Wallahi nasan bawani karatu iskanci dae, ya isah nace, zokiji kunnenta tamiqa mata tarada mata magana,qara tayi tace dagaske mummy, yes kedai kikwantarda hankalinki. Shikenan mum nagane, futa tayi ranta fess, nan tashirya tadau key din motorn ta tayi gidansi ishma domin tattauna yanda events din bikin zae kasance....... Lokacin da tafada mishi cewa yayi shifa inma za,ai wani ecent to iya dinner kawai za,ai rana daya, kuja tasa masa tace duk qawayena kowa abikinsa ana kece raini amma ni rana daya za,ai ganin zata daga mada hankali yasa yace taturo account dinta sufadi nawa suke buqata yatura musu, su suje suyi, shi badaban friends dinsa da zasuzoba, shi baiyi niyan yin kowani events ba. Haka rayuwa taci gaba da juyawa,kwanci tashi asarar mae rai!!! Yau yakama thursday iya yau zasu kawai zasuyi event dinsu coz khubaib yace yafison daurin auren friday, don sunday zaeyi resuming work, kuma bayason bidi,oeh a bikinsa,dan wadannan event dinma dazasuyi daqyar yayarda, da cewa yayima bazaejeba amma tunawa da yayi friend dinsama zasuje haja yahaqura, daqyar ta kalallameshi yayardan zaije. Tun safe suke shirye shirye, gidan har yacika da yan uwa, su Amina ma qanwar su daddy (anty meena) duk sunzo da yayanta, su uku, dangin babansuma wasu sunzo sunata borin kunya ganin yanzu suma sunada abin duniya. Yan uwan mamii kuwa ba,a magana dan bikin dan gatan famiky ake. Da dare around 8:30 duk sunci ado dan yau kamu zasuyi kuma a friends and family event center za,ai, sunata hidima Ango yasha wata dakakkiyar shadda skyblue yar ciki da babbar riga, yasa wata tsadaddiyar hula dark blue,yasa wani black covershoe, yadaura watch dinsa mae masifar kyau yafito shar dashi ga kannan nashi da face nashi sunsha gyara yanata qyalli kaii ma sha Allah kawai nace, motocine maqil qofar gidan anata daukan mutane zuwa friends and family event center gurin da za,ai Dinner. Daga wanka tafito tana tsane jikinta da towel, dan tun dazu tazo part din mamii dan kayansu yanacan itada maryam adakin maryam din, maryam tuni taqosa da jiranta, dan da cewatai kanta na ciwo bazataba, nan mami tace tayi zauniyarta, maryam kuwa taje tafadawa Ammi, nanfa Ammin tarufeta da fada kan cewa setaje, nandai tagama zumbure zumburenta tashiga wanka,da maryam tagaji dajiranta kuma da Ahsan dinta zata tafi amotarsa ( dan gidan uncle Jaid inda zataje karatu india suma aikine yamaidashi can). Tunda bikin yayan yatashi gaba daya takejin badadi, itadai tasan ba farin cikine batayiba amma tarasa dalilin faduwar gabanta,gashi za,a hadata da wannan matartasa, da kowa yasan duniyancinta. Daqyar dae tashafa mayujanta masu qamshi tayi dan light make-up dan uta bason tafiyan takeba, sannan tasa jewelries dinta na gold masu kyau, sannan tadau diguwan fitted gown dinta tasa dark blue, tayi dan simple steps akanta, tadauko takalminta dark blue maedan tsini tasa, sannan tayafa dan mayafinta blue maedan duhu kadan amma yanda dan haske, ga hannayenta sunsha lalle kaii ma sha Allah kawai nace danaga tafito, dakin mamii tashiga tayi sallama, wowww ma sha Allah daughterna kinyi kyau sosai, amma ya,akai kikai late haka dun kiwa yatafi? Sadda kanta qasa tayi tace shiryawa nai mamii, toh daughtena yanzu wazan samu yakaimin kee, kowa yatafi tunda dinner dib yana dayane, shiyasa kowa yatafin, toh mami nahau napep kawai, zaro ido mami tayi tace daughtena napep fa kikace rufamin asiri, kidau wannan wankan kicemin kyahau napep??🙊 uhmmm kawai sabiyya tace, Mamin ce tace bari inkira wannan miskilin muji in basu tafiba su ajiyeminke, dummm haka taji gabanta yaqara faduwa, mae yakeson faruwa danine tafada cikin ranta. Muryan mami ne takatseta daga tunanin datake jin tana cewa, kun tafine!? Bataji mae yaceba, mami taqara cewa bari daughtena tafito kuyimin dropping nata okay? Toh kawai yace, dan yasan rigina kawai za,a hadasada. Yauwa daughter maza kije suna parking space zasuyi dropping dinki zuwa waje,okay mami saena dawo, kidafamin hallop cius cous, dan yau anan zan kwana sannan tafice bata jira cewan maminba, murmushi mami tayi tace uhmm daughter rigima yau kuma nan za,a kwana kenan, nandai tacigaba da harkokinta da aiyukanta dan tace baza taje wajan shashancinnanba. Kar amanta da Comment, reac, share. PAGE 19_20 Gaba daya ranshi yagama baci, sabida jiran dasuke mata bayason jira kokadan,tafiya take amma kamar bazata takaba,daqyar taqaraso gurin moton, back seat yabude nan tahangoshi ciki gaba tabude zata shiga sanin cewa back seat na Amaryane,amma saetaga kaya aciki, rufewa tayi tashiga back din tarufe tazauna, wani irin sayi da qamshine ya ziyarci hancinta mae dankaran dadi, tazauna yanda kasan itace amaryan tsabar dacewan dasukai, harara ya dalla mata sannan yace ubanwa yahanaki bin mutanen da sae yanzu zaki batawa mutane lokaci!?? Dan bakinta na tsiwa taturo gaba tace toh badae mami ce tace kutsayani ba!? Kuma ni ai shiryawa nak.... Tsaki yaja yace shhhhh bansan jin komi, tura baki tayi takauda kanta gefe tana kallon window, nan wani friend dinshi jameel yajasu suka tafi tareda kunna musu kida. Kadan kadan yana tashi sukai gidan su isma don daukota. <<<<<<,Idan ran Banan yai dubu yabaci sbd jira tun dazu take kiranshi baya picking,shi baimasan tana kiranba wayan na silent, suna zuwa ana fito da ita itama tasha kyau ba kadanb tasa street gown pinck color mae uba tattara tayi kayu da anmata dauri dark pinck net din da tayafa kuma light ne sae hill shoe light pinck. da jakanta, tayi kyau ma sha Allah,